[8/5, 18:59] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Na fara da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW._ *1* *APRIL 20th 2021.* *American Hospital Dubai, 2:30pm.* _"hey don't move, we are us navy seals...God! Damn it...we have a tango in the north wing every week. stop! stop! stop!...great team work guys, yeah we will mark you for the assist on this one."_ sautin da ke fitowa kenan daga cikin ƙatuwar plasma ɗin da ke manne a bangon ofishin, cikin wani american film me suna Steel Brigade. dai-dai lokacin da sojojin suka kama mutumin da ke sanye da mask, dai-dai lokacin Yusuf da ke juyi akan kujerarsa yasa tafukan hannunsa duka biyu ya shafo fuskarsa tare da fitar da iska daga bakinsa. "ohh dammm it". "ai na faɗa maka sai sun kama shi". Kalid wanda har yanzu bai ɗauke idonsa daga kallon tv ɗin ba ya faɗa a sa'ilin da duka haƙoran gabansa ke bayyana a waje alamar yayi farin ciki da abinda ya faru. Yusuf ya ƙara juyawa akan kujerarsa zuwa gefe guda sannan yay guntun tsaki yace,"ko waye producer ɗin nan sam bai iya tsara film ba". "hhh to ai hakan shine dai-dai, kai kana kallon sojojin nan kasan bana banza ba ne...kuma gwara a kama shi tun a farko, wasan zai fi tafiya dai-dai". "kuma wataƙila ya suɓuce masu ba". "ta ya ya?, macece fa ai da kamar wuya ta iya ƙwacewa". "wannan ai ba mace ba ce". "bari su buɗe fuskar zaka gani, ai yanayin gudun kaɗai zaka fahimci macece, itama ba me kamar maza ba". shirun Kalid ɗin ya haɗe da sanda sautin maganar film ɗin ta ci gaba da tafiya, nan sukai shiru suna ci gaba da kallon. _"get the mask!!...there is no harmful in the air we already checked, expect for the thorpe's breath."_ ɗaya cikin sojojin yay maganar a tsawace inda a take ya fizge mask ɗin daga fuskar mutumin, kuma lokaci ɗaya zaton Khalid ya bayyana, hakan kuma ya wanzar da dariya a fuskarsa, nan ya juyo ya kalli Yusuf dake aikin jan gajeran tsaki babu ƙaƙƙautawa alamun ba hakan yaso ba. lokacin da Yusuf ya buɗi baki zai yi magana lokacin ƙofar ofishin tayi ƙara, aka turota a hankali inda wata matashiyar budurwa ta bayyana hannunta riƙe da wasu takardu, jikinta kuma sanye da unifom na ma'aikatan jinya. ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin ofishin tana ƙarasawa gaban tebirin da Yusuf ke zaune kan kujera yana juyawa gefe zuwa gefe a hankali. cike da girmamawa ta rissinar da kanta tare da aje fayel ɗin hannunta akan teburin tana tura su zuwa gaban Yusuf. "Ranka ya daɗe ga result ɗin da aka samu". ta faɗa sanda ta ke harɗe hannayenta zuwa baya. "ta farka ne?". Yusuf ɗin ya tambaya a sa'ilin da ya buɗe fayel ɗin yana dubawa. "ehh ranka ya daɗe ta farka wajen ƙarfe ɗaya da minti goma sha biyu, amma bata fi sakan huɗu ba ta koma, da alamu dai har yanzu da saura kamin ta dawo hayyacinta". shiru ya biyo bayan maganarta, idon Yusuf ta cikin farin gilishin da ya manna na bin rubutun da ke cikin fayel ɗin, karantarsu yake da fahimta, wucewar daƙiƙa 1,2 Yusuf ya ɗago kansa akan fayel ɗin, ya kai hannu ya shafo goshinsa sannan ya jinginar da kansa jikin kujera yana mai sauke gajeran numfashi. _"huuuuhh"._ hucin iska ta fita daga bakinsa. *"EXOGENOUS DEPRESSION".* ya faɗa cikin amon sauti na tausayawa haɗe da kulle murfin idonsa. furucin nasa kuma yasa Kalid maido da kallonsa gare shi. "tana cikin matakin biopolar kenan?". Yusuf ya jijjiga kansa tabbacin hakan ba tare da ya ce komai ba, na tsawon wasu sakanni ya ɗaga ido ya kalli Nurse ɗin yace,"kuma iyaka binciken da jami'an tsaro suka yi babu wani danginta a ƙasar nan?". "ƙwarai ranka ya daɗe sun bada tabbacin hakan...ni kaina lamarinta na ɗaure min kai". Kalid yace,"gaskiya da sake a wannan lamarin, su ƙara bincike domin idan ba zaman ƙasar nan take ba to wa ya kawota ya ajiyeta kuma ya tafi ya barta cikin wannan mawuyacin yanayin?". Yusuf ya ƙara fitar da iska daga bakinsa kamin yace da nurse din,"Ƙarƙashin kulawar wa ta ke?". "Ranka ya daɗe tana ƙarƙashin kulawar Dr Nameer, sai dai gaskiya tana fuskantar matsala". "wanne irin matsala?". "Dr Nameer yana da zafi, so kuma shi yace muddin babu wani nata ba zai bata wani kulawan da ya dace ba...infact yanzu ma yaƙi rubuta alluran da suka kamata ayi mata saboda wai ko ya rubuta bata da me saya mata". karo na babu adadi Yusuf ya ƙara girgiza kansa tausayi fal ransa, sannan ya ɗauki ƙaramar takarda yay signing a jiki ya miƙa mata tare da fayel ɗin. "kije Pharmacy Sumayya, ayi dukkan abinda ya dace akan matar nan, zan saka maki kuɗi a account, dan Allah ki kula da ita ni kuma nayi miki alƙawarin biyanki da kauri". ta rissina ta ɗauki fayel ɗin tana yi mishi godiya sannan tayi musu sallama ta fice daga ofishin. bayan fitarta da wucewar minti uku Yusuf ya miƙe yana kafa hular zanna bukar a gashin kansa, fuskarsa na bayyana ainihin damuwar da ke cikin ransa. "tashi mu tafi Kalid". "a'a ba kana da sauran aiki ba?". "ba zan iya komai ba Kalid, kaina ciwo yake. zan yiwa Dr Yusrah magana". Kalid ya miƙe tsaye shima, suka nufi ƙofa yana cewa da Yusuf. "Dr ka rage saka damuwar wani a ranka...". kuma bai ƙarasa maganar ba Yusuf ya tari nunfashinsa da cewa. "Kalid idan har matar nan tana da miji a raye to ya cika azzalumi, idan ma yana raye ne ko ya mutu to tabbas ƴaƴanta salwantattu ne, basa neman albarka kwata-kwata, basu san darajar uwa ba, domin ko kaffara ba zanyi maka ba ta dalilinsu ta shiga wannan bala'in rayuwar, kuma duk san da nayi tozali da wani ɗa nata sai nayi shari'a da shi". maganar yake cikin zafin rai kamar zai kaiwa bango duka. "tabbas ba zai wuce takaicin miji ko na ƴaƴanta ne ya zama silar wannan ciwon nata ba...amma ni abun mamakin ace tana cikin wannan mawuyacin halin kuma babu kowa nata a tare da ita". Kalid yay maganar a sanda suke sauka daga kan steps su na ƙarasowa cikin reception kamin su sa kai su fita gaba ɗaya daga asibitin. kuma har suka isa bakin mota cikinsu babu wanda ya sake magana. on their way to hotel wayar Yusuf tayi ƙara, ya kai hannu ya cirota daga aljuhunsa, ya ɗaga vedio call ɗin da ya shigo yana mai raba hankalinsa gida biyu, ɗaya ga tuƙin da yake, ɗaya kuma ga fuskar matarsa da ta bayyana a cikin wayar. "You Excellency what am i seeing on your face?, whats wrong?, are you oak?, wani abu ya faru ne?, what is the problem?". tarin tambayoyin da suka fito daga bakin Nuratu kenan zuwa ga mijinta, cikin kiɗima da bayyanuwar tashin hankali na farat ɗaya, dalilin damuwar da ta gani a tare da shi ta haddasa ma ta ruɗewa na neman fitar hayyaci. kallo ɗaya na yanayin da take ciki zaka yi kasan macece mai tsananin so da ƙaunar mijinta, gami da tausayinsa, wanda bata so ko da ƙuda ɗaya ya taɓa mata shi, kan kace kwabo hawaye sun fara reto akan kuncinta, cikin ƙanƙanen lokaci kuma ta fashe da kuka, kukan da ya haddasa wani duka a ƙirjin Yusuf. "Sweety". sai a yanzu laɓɓansa suka buɗe da kiran sunanta, ta ɗago kanta da ta duƙar tana kuka ta zuba idonta cikin nasa. sai kawai ya sakar ma ta wani kyakykyawan murmushi, irin murmushin nan da zai tsayar da kukan nata. amma me? kamar yanda ya riga ya sani ba zata yi shirun ba, hasalima kamar ya ƙara tunzurata ne, dan kawai ɗora hannu tayi akan fuskar ta ƙara fashewa da kuka, kuka sosai kamar ƙaramin yaro me neman shan nono, sautin muryarta na fita cikin kuka na shagwaɓa da damuwa take ƙara cewa. "ni ba irin wannan ba, bana son wannan ka jefar da shi. indai murmushin ƙarfin hali ne a tare da kai your Excellency bana ƙaunarsa, kuma ba shi zai sa na sami sassaucin raɗaɗin damuwar da na riska a tare da kai ba". tuƙin yake amma gaba ɗaya attension ɗinsa ya koma gareta, kyawawan idanuwanta na kan wuyansa tana bin wani dunƙulallan abu da ke wucewa ta maƙogoronsa, muryarta ta ƙara narkewa tana cewa. "please tell me what is the problem?, Did you do something that you did not succeed on it?". ta riga ta san waye mijinta, yawancin damuwarsa na ta'allaƙa ne akan rashin cimma nasararsa akan abu musamman ma ta ɓangaren aikinsa, amma da mamakinta sai taji yace,"keep calm Sweety". voice ɗinsa ya fito very cool. sai ta gwaɓe kamar ƙaramar yarinya tana cewa da shi. "to ni dai ka dawo gida idan Allah ya kaimu gobe. ka bar komai da kake yi ka dawo, otherwise i will keep on crying". "Sweety isn't a big deal faa, please don't bother your self kinji". "ni ban yarda da kai ba". sai kawai ya tsarate da wani kallo da ya sa ta saki wani murmushi da ya fito da annurin fuskarta, sannan kamar sai a yanzu ne ma ya lura da irin shigar da ke jikinta wanda yasan ta kira ne dan ta nuna masa, dan haka ya kanne mata ido guda ita kuma sai ta cije gefen leɓenta kaɗan. gaba ɗayansu sai murmushinsu mai ƙarfin sauti ya fito a tare. wucewar daƙiƙa 2 su na aikawa junansu saƙo ta irin kallon da suke ma juna kamin Nuratu ta ɗan cukule fuska tace da shi. "this time around idan ka dawo sai nayi shari'a da Kalid". yanda tayi maganar da gaskiyarta yasa shi yin murmushin da ya bayyanar da haƙoransa, Kalid da ke gefe yana charting ya saki dariya yana faɗin. "yi haƙuri Madam tuba nake". "i will not accept your apology tunda kai dai har yanzu ka kasa koyon yanda zaka kula da amanar da aka baka". "wani abu ya faru ranki ya daɗe?". ya tambayeta cike da zolaya da kuma son ƙara kunnata. "au kana ma tambayana ne me ya faru ko?, Allah dai ya dawo daku lafiya zaka min bayani daki-daki. lawyer nake, kasan abunda zan aikata da wanda ba zan aikata ba". *No 3. Shongo Housing Estate, Gombe State.* *17:00 pm.* gidaje guda 5 ne a duk girman estate ɗin, kuma a kallo ɗaya zaka yiwa gida me lamba na uku ka gane ba ɗaya yake da sauran gidajen ba, tun daga girmansa zuwa tsaruwar ginin da yanda aka fitar da fasalinsa. anyi tsarin ginin gidan da ado da kwalliya irin na gidan sarauta, idan har ba sani kayi ba zaka tsammaci wata babbar masarauta ce. duk jikin bango da zaka kalla birjik yake da ado na ƙawa cikin nau'i iri-iri don burge idon me kallo. daga cikin gidan, second part da ke kallonka a yayinda shigowa cikin haraban gidan, a cikin tamfatsetsen parlon na alfarma wanda yake shaƙe da kayan alatu na more rayuwa, me ɗauke da royal italian cushion. sautin waƙa ne ke tashi acikin wata mp3 da ke manne ajikin wani glass kamar drower. _Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday happy birthday, happy birthday to you._ waƙar na fitowa ne a cikin sautin kiɗa, yayin da ƴan mata da yaran da ke kewaye da shi ke tafi da hannayensu cikin murna da annashuwa, suma su na bin sautin waƙar fararan haƙoransu duk a waje. yana tsaye ne a gaban ƙaton cake ɗin da akai masa kwalliya da tsari me kyau an saka +1 ajiki, ga candle guda ɗaya a kunne a saman cake ɗin. irin yanda fuskarsa ke washewa da murmushi ba zaka taɓa ganewa hakan ba a kallo 1 zuwa biyu da zaka yi masa. lokacin da sisters ɗin nasa suka gama bin waƙar sai ya sunkuyo da kansa yayi blowing wutan candle ɗin sannan ya ɗago yayin da idanuwansa ke a lumshe yana yiwa kansa adu'a acikin ransa, for few seconds ya buɗe yana sauke ganinsa akan ɗaya daga cikin sisters ɗinsa wadda duk ta fi sauran matan haske da kuma dogon hanci. kyakykyawan murmushi suka sakarma junansu lokaci ɗaya. da ido yay mata alama ba tare da yay magana da baki ba, hakan yasa ta matso kusa ta riƙe hannunsa ya yanka cake ɗin, laɓɓansa na talewa da murmushi mai faɗi. ya yanko cake ɗin yana juyowa ga hannun damansa inda wata farar dattijuwa kyakykyawa ke tsaye sai murmushi ta ke, haƙoranta sunƙi rufuwa saboda irin farin cikin da take ciki, jikinta sanye da tsadadden less brown and black colour, tasha ɗauri kace budurwa me ji da tashen ƴan matanci. bakinta ya nufa da cake ɗin da ya yanko ya saka mata, ta karɓa tana faɗin. "Happy birthday Son. wish you long life and prosperity". "Use miyyete Maama, midon nana beldum joddaki emada eder duniyaru am". (Amin na gode Maama, ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata). ya faɗa yana yanko wani cake ɗin, sai da ya kalla duka sisters ɗin nasa su huɗu sannan ya sauke kallon ƙarshen nasa akan Zaituna, kallon da yay mata ne kawai ya fahimtar da ita mai yake nufi, dan haka ta matso kusa da Maama, ta buɗe baki itama ya saka mata cake ɗin a baki, ta karɓa tana faɗin. "Mi seyake be yaltugo nyandere danyeki ma Hamma am. Allah ɓeddane njamu be jutal balde barkante jo". (Barka da zagayowar ranar haihuwarka Yayana. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana masu albarka.) fuskarsa ta ƙara washewa da annuri, ƙwayar idonsa na haskawa da wani ƙyalli na farin ciki da son ahalinsa. sai ya dangwalo icing cake ɗin ya lakuta mata a hancinta da gefen kumatunta kamar ita ce birthday girl ɗin, yana faɗin. "Special thanks to you Sweetest". daga nan kuma ya dinga yankar cake ɗin yana sakawa sauran sisters ɗin nasa a baki, suma duk su na binsa da wishing. haka ya gama basu sannan suma kowacce ta yanko ta nufo bakinsa da shi, sai dai bai karɓi na kowa ba sai da ya fara amsar na Maama da Zaitoon tukunna. su na haka Kalil ya shigo aka ɗora da shi, gaba ɗaya shi sai ya koma ma kamar shi ne me birthday ɗin, dan gaban cake ɗin ya zauna yana ta ci. kuma zuwansa wurin sai ya sauya ƙaramin birthday partyn da Maama ta haɗa zuwa babba. cike da murna gami da so da qauna for one another suke ta abinsu, kowa jikinsa ya ɓaci da cream na jikin cake. *Ɓangaren Masu Aikin Gidan.* *17:40 pm.* "Fillo kar ki zauna don Allah". wata ƴar tsohuwa fara ƙal da ke zaune a gefen katifa tana cura fura ta faɗa. "Kaka am debbo ba zan jima fa yanzu zan dawo". ta faɗa tana zura hijab kalar c-green wanda ya ɗauki farar fuskarta matuƙa. ta zura siririyar ƙafarta cikin takalmi sannan ta nufi ƙofa tana faɗin,"sai na dawo Kaka". Can bayan gidan ta nufa, kasancewar yamma tayi hayaniya ta ɗan ɗauke ba kamar da safe ko rana ba, mafi akasari a irin wannan lokaci masu hidimar gidan sun tafi don hutawa kasantuwar ayyukan da suke sha tun sanyin safiya. da yake gate ɗin gidan biyu ne, kuma gate ɗin baya ta nan ma'aikatan gida ke shige da ficensu, shi kuwa main gate na masu gidan ne. a bakin bishiyar da Amir ya saba tsayuwa duk sanda yazo anan ta same shi yanzuma, ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya jingina da jikin bishiyan yana jiran isowarta. tun daga nesa da ya hangota ya kafeta da ido, kuma kamar kullum sai Fullo ta tsaya da tafiya tana ɗan turo baki gaba. ganin hakan yasa Amir ɗauke idonsa daga gareta yana fitar da siririyar dariya a fuskarsa. sannan yasa tafukan hannunsa ya rufe fuskar. bai san da ƙarasowarta wajen ba sai jin maganarta yay acikin kunnensa tace. "ja66ama". (barka da zuwa) tayi maganar a hankali. sai a yanzu ya buɗe fuskar ya juyo da fuskarsa zuwa gefen damansa inda ta ke a tsaye, bai ce mata komai ba sai wani sanyayyan murmushi da ya ɓalle masa a saman fuska. irin kallon da yake mata yasa taji nauyi ta rufe fuskarta tana ƙara faɗin. "awari jam?". (anzo lafiya?) nan ma shiru yay bai amsa mata ba, ita ma kuma bata jira ƙara cewarsa ba ta kuma ɗorawa da faɗin. "noi him6e sare?". (ya mutanen gidan?) Amir ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya tare da jan leɓensa na ƙasa zuwa cikin bakinsa ya tsotsa kaɗan. a shagwaɓe tace,"wai yau ba za'a min magana bane?". har yanzu murmushin da ke kan fuskarsa bai ɗauke ba yace,"mi tawi on jam?" (na sameki lafiya?) "lafiya lau". ta faɗi hakan tana ƙara yin ƙasa da fuskarta da alamar dai macece ita mai kunya sose. "Inna vi mi hofnuma". (Inna tana gaisheki) "mi ja6i". (ina amsawa) "shine kika barni na daɗe a tsaye haka ko?". ta ɗan cije leɓenta kaɗan tana kallonsa sannan tace,"kayi haƙuri. na tsaya ƙarasa aiki ne, kasan me Martaba baya gari, to kuma duk san da zai dawo Kaka ake bawa aikin fura, shi ne yau bamu gama da wuri ba sai yanzu. yanzu haka ma na taho na barta tana ƙarasa curawa ita ɗaya. da ta gama zamu tafi can masarautar mu kai". "Allah sarki Kaka...Allah dai ya kawo min arziƙin da zan zo na ɗauke ku nan bada jimawa ba". ta haɗe girarta alamun son ƙarin bayani akan abinda yace. sai ya ɗaga tasa girar yana cewa,"ehh mana, ai idan na aureki ba ke ɗaya zan ɗauka ba. har da Kaka zamu tafi...Halimatu indai na aureki to lokacin hutun Kaka ne yayi". wannan furucin na Amir zuciyarta taji ya ƙara burgeta, ta kuma ƙara yin amanna da shi. muryarta mai sanyin nan ta fito a hankali da cewa,"Allah ya buɗa ya bada arziƙi mai yalwa da albarka. ya kaimu lokacin". "ameen ƴar aljannah". ya faɗi hakan san da yake sunkuyowa daidai fuskarta. "yanzu bari na barki kije kici gaba da taya Kaka aiki, nasan yana da yawa. gobe in Allah ya kaimu na dawo". "tom shikenan Allah ya kaimu. ka gaida min da Inna idan ka koma". ya sunkuya ya ɗauko wata ƙaramar baƙar leda da ya aje a ƙasa ya miƙo mata. "ga wannan mangoro ne da bai nuna ba irin wanda kike so". tasa hannu biyu ta amsa cike da jin daɗi. "amma kam na gode. dama ranar nan Maijidda ke ce min ta ganshi a kasuwa da suka je, ina ta kwaɗayinsa tun ranar ashe da rabon zan sha". "nima na fito zan taho wajenki naga ni a bakin hanya, nace to ba zan zo haka ba hannu na dukan cinya ba, sai na siyawa farin cikina wani abun". yatsun hannunta na naɗe acikin ledar tayi murmushi da ƙara yi masa godiya. sai da ta juya ta nufa cikin gida sannan shima ya juya ya tafi. "Fullo! Fullo!!". muryar Maijidda da ke fitowa daga nasu ɓangaren ke ƙwala kiran sunan, sunan da kusan kowa ke kiran Halima da shi a cikin gidan idan ka ɗauke Kaka wadda ba ko da yaushe ta cika faɗa mata hakan ba, tafi kiranta da Halimatu. jin kiran ya sata dakatawa daga tafiyar da take tana yatsina fuska har lokacin da Maijidda ta ƙaraso wajenta. "na rasa me ya shiga kunnenki ya toshe miki ji akan cewar bana son irin wannan kiran sunan na mafarauta". Fullo ta faɗa tana ɗan hararta. "ke kuma gaki kullum a cikin ƙorafi". "nayi ɗin". ta faɗa tana sake ɓata rai. Maijidda ta taɓe baki tana cewa,"ke dai kika sani. daga ina kike? mene wannan?". ta jera mata tambayoyin tana ƙoƙarin amsar ledar hannunta. "daga inda kika aike ni Kaka". Maijidda tayi gajeriyar dariya bata ce komai ba. wanda tuni har ta buɗe ledar ta ɗauko mangwaron ta fara gatsa. hakan kuma yasa Fullo jan tsaki tayi gaba abinta, dan idan da abinda ta tsana a halin Maijidda shi ne cin abu ba tare da ta wanke ba, ita dai da ta ga abunda bakinta yake so ba ruwanta da tunanin wankewa zata afashi cikin baki. sun shigo tsakar gidansu suka ci karo da Masu aiki nata zubewa ƙasa su na aika gaisuwa da kirari. Fullo ta ɓata rai sosai ta kama hannun Maijidda ta dakatar da ita daga tafiyar da suke. "lafiya?". Maijidda ta tambayeta. "mu juya don Allah". "saboda me?". "ni wannan gaisuwar sarautar har ga Allah ba ƙaunarta nake ba. ko waye ma haka a ɓangarenmu oho". ta ƙarasa faɗa da jan tsakin ƙorafi tana ƙoƙarin juyawa. Maijidda ta fizge hannu tana cewa,"ai idan kinga na koma to tabbatarwa nayi ba wanda nake zato bane ya shigo wajen nan. haka kawai kiyi mana buƙulun ƴan silallan da zai bayar". "banza mayyar kuɗi, wallah idan ba kiyi wasa ba da wannan shegen son kuɗin naki za'a cuceki". Fullo ta faɗa tana barin mata wajen ta fice da sauri gudunma kar Kaka ta hango inuwarta ta ƙwala mata kira. tana fita ta nufi famfo ta wanke mangoro, ta dawo ta zauna kan wani ɗan tudu tana sha. kusan tsawon minti biyar tana zaune a wurin, kuma zaman na dole, duk gudun kar tayi gaisuwar da bata da niyya. a wajen Maijidda ta dawo ta sameta, ta zauna itama tana cewa,"kin gani, dubu biyu ce ya bawa kowa. kema ga naki na karɓo miki". kallo ɗaya ta yiwa kuɗin ta ɗauke kai, kuma tana juyawa gefe idonta ya sauka akansa, yana tafiya cikin takun isa, taƙama da cikar izza. duk tsayin zamanta a gidan bata taɓa ganin me kalar halittarsa ba, hakan yasa ƙananun laɓɓanta taɓewa kan ta dawo da kallonta ga Maijidda tace da ita. "waye wancan ɗin? tunda naga ke babu wanda ba ki sa ni ba acikin gidan nan saboda shegen shishshigi...cikin masarauta ma idan aka je yanda kike faɗar sunan jama'a kamar kece uwarsu". "kanki ake ji. yanzu amsar tambayarki zan baki ko na jira ki gama neman maganar?". Maijiddan ke maganar tana ta shan mangwaronta. "ki riƙe amsarki kar ki faɗa ai ba damuna yayi ba. dama naga ne ban taɓa ganin irin halittar bane acikin gidan nan tsawon zamana". "to sunansa Turaki". jin sunan da Maijidda ta ambata ya ƙwala ƙarar sautin wani abu acikin kanta, babu shiri ta miƙe a zabure tana gyara ɗaurin zani. "me kika ce?". "ba ki ji me nace bane hala? to nace Turaki ko". lokaci ɗaya idon Fullo ya manne a bayan Turaki da ke tafiya yana kusan kaiwa ga barin harabar ɓangaren masu aikin gaba ɗaya. a hankali kuma idonta ya rufe, cikin duhun idanunta na haska mata sunan Muhammad Turaki da ke jikin farar takardar nan da babu zanen komai ajikinta sai na sunansa. "tashi muje Maijidda". "zuwa ina?". "ina wannan baƙar ledar da na baki ranar bikin gimbiya Safiyya?". "tana ɗakin Yami". "je ki ɗaukota da sauri. ki sameni a bayan tanki cikin lambu, ki taho da ashana dalon Allah". _till we meet in the next page! Your Comment will make me to continue or stop._ *dont forget to vote, react and share to other groups please🙏* [8/6, 18:33] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya *3* *Dare, 20:45pm.* Ƙafafun Hajiya Madina suka shigo cikin ƙaton parlon, wanda ƙamshinsa ya haɗe da sanyin acn da ke hurawa ya haɗu ya bada wani sanyin ƙamshi me motsa zuciya. Jikinta sanye da ash abaya wadda taji adon stones ajiki, ƙyallin stones ɗin sai wurgawa suke ta cikin hasken fitilun parlon. Ganin Ƴaƴanta ya saka ta sakin murmushin da bata shirya masa ba, tana ƙaunar yaran fiye da yanda take son kanta, kowa yasan da hakan, abu ne ma da kamar tayi tambarinsa a goshinta. Tana tsaye daga bayansu tana ƙare musu kallo cike da so da ƙauna, su kuma hankalinsu ya tattara kan tab ɗin da ke kan cinyar Sameer su na kallon pixx ɗin da su kai ɗazu na birthday ɗin Turaki. Gyaran muryar da tayi ne ya ankarar da su zuwanta, suka ɗago a tare su na kallonta fuskokinsu na washewa da murmushi. Ta zauna a kujerar da ke fuskantarsu tana faɗin,"shi ne aka kasa jira nazo, wannan cin amanar har ina?". Tayi maganar da sigar wasa kamar wadda ke tare da ƙawayenta. Samha ta ɗauko tab ɗin ta nufo wurinta tana faɗin,"Maama kinga wanda aka maku ke da Hammah duk yafi kyau wallahi". ta zauna kusa da ita tana nuna mata hoton da aka ɗauka a sanda Turaki ke saka mata cake a baki. Allah ɗaya yasan me taji cikin zuciyarta a wannan lokacin, dan shi kansa murmushin da ya suɓuce a leɓenta bata san da zuwansa ba. Ta kai hannu ta shafa hoton, ƙwayar idanuwanta na haskawa da ƙyallin wata ƙauna da ke tsakanin Uwa da Ɗa wanda Ubangiji kaɗai ya san girmanta. "gaskiya munyi kyau, kamar ban haifi Hammah ba, kalle ni wata ƴar suwet a kusa da shi. Wannan idan sirikata ta gani ai sai tayi jealous idan bata san wacece ni ba". Ta faɗi hakan cike da raha, haƙoran makkan da ke bakinta guda biyu su na bayyana duka a waje. Taci gaba da scrolling har tazo kan wanda su kai gaba ɗayansu,"kai amma wannan ma yay kyau. 1 Family na Baffa kenan". San da tazo kan wanda Turaki yake shi kaɗai ta ƙara cewa,"wannan kam shima enlargement ɗinsa zan bada a ƙara min, Hammah yayi kyau sosai kamar wani magidanci". Sameer yace,"Maama wai duk sai kin cika bangon ɗakinki da parlonki da hoton Hammah ne?". "ƙila hakan ce zata kasance, dan sai dai idan bai yi sabon hoto shi ɗaya ba". Sai da suka zo ƙarshe a kallon hotunan sannan ta ƙara cewa,"gaskiya Hammah ya dawo ya fito min da matar aure, dan na ƙagu naga sirikata". nan dukansu suka haɗa baki wurin faɗin,"aiko dai Maama ya kamata ace Hammah yayi aure, sai tsofewa yake yi". Kallon da tayi musu ne yasa babu shiri suka gimtse bakinsu, saboda kalmar tsufa da suka jinginata da Turaki. "Hajjah nyamdu mae henyi". (Hajiya abinci ya kammala). Mai aikin da ta ƙaraso wurin a yanzu ta faɗa sanda take tsugunawa a gefen hannun kujerar da Hajiya Madina ke zaune. Ba tare da ta juyo ta dubeta tace,"usema be habdugo". (sunnu da ƙoƙari) "aha Hajiya Miyetti". (yauwa Hajiya na gode) Daga haka ta miƙe ta bar wajen cikin azama dan barin musu wajen. Hajiya Madina ta ɗauke tab ɗin daga kan cinyarta tana ajeta kusa da ita, sannan ta kalla ƴaƴan nata tace da su,"my bloved ones dinner is ready". Tare suka miƙa kaf ɗinsu suka nufa dining area, warm coolers na abinci ne zafafa masu kuɗin gaske, an jere akan dining table ɗin wajen kala shidda, kowanne cooler da kalan abinci da ke ɗauke acikinta, ta yanda kowa idan zai ci abincin zai ci favorite nasa ne. Zaytuna ta buɗe flask ɗin da ke ɗauke da Mandi rice ta zuba a plate ta miƙa shi gaban Hajiya Madina, sannan kowa ya shiga zuba nasa abincin. Tunda suka fara ci babu wanda yay magana sai ƙarar cokula da kake ji har su ka kammala, wanda Hajiya Madina ce ta fara gamawa, ta yagi tissue ta goge bakinta. "albishirinku". Ta faɗa tana jefa tissue ɗin cikin durstbin. "goro Maama". Suka faɗa bakunansu a haɗe. "this time Baffa yayi suprising namu, mo don dow lawol vartugo". (yana kan hanyarsa ta dawowa). "na jam kam?". (amma dai Lafiya ko?) "jam saliiman, mo vii mo yenwi Muhammad mako tan". (Lafiya lau. Kawai yace yana kewar ganin Muhammad ɗinsa ne) "daɗin biyu kenan, to Baba ma yiidama to Dada ma kam yiidima". (Idan Babanka baya sonka to Mamarka na sonka). Muryar Khalil da ke shigowa cikin parlon a yanzu ta amsa lokacin da shima yake jan kujerar dining zai zauna. Idon Hajiya Madina ya maƙale akansa tana cewa,"dume a tammi". (me kake nufi?) Khalil yay murmushi kamin yace,"banda nuna launiyar warin fata kawai Baffa sai ya dawo gida saboda mutum guda, hala mu dama ya manta ya haifemu?". Maganar yake cike da zolaya. Hajiya Madina tayi murmushi kaɗan tace,"me yasa baka yi zuciya kazo a na farkon ba?". Shima yana murmushin yace,"to yanzu dai ba sai ya dawo ba ya tarar Hamman baya nan. Dole dai ni zai gani ai". "Jealosy". Ta faɗa tana binsa da wani kallo. A rayuwar Hajiya Madina babu abin da take so irin ta ganta cikin ƴaƴanta, kuma kowanne cikin farin ciki da jin daɗi ba a cikin damuwa ba. Suna cikin tattaunawa akan batun gobarar da ta kama ɗazu wajen ɓangaren Lambun gidan, take basu labarin aima har an sallami me gadin wajen, saboda sakaki da yake akan aikinsa. Inda dukansu suka ce hakan yayi daidai, duba da ko lokacin da aka zo wajen bama ya cikin gida gaba ɗaya, baima san da kamawar wutar ba, balle yasan abin da ya haddasa kamawarta. Wata matashiyar budurwa baƙa ta faɗo parlon cikin sauri me kama da sassarfa, kayan jikinta kawai zaka kalla ka shaidi itama ƴar aikin gidan ce. Wayar hannunta na ringing a karo na uku da kiran wayar ya ƙara shigowa. Ta ƙaraso gaban kujerar Hajiya Madina da sauri ta durƙusa tana miƙa mata bakinta na faɗin. "kiyi haƙuri Hajiya, na ɗan matsa ne har kira na farko ya shigo ya yanke". Hajiya Madina ta bita da wani irin kallo, ƙwayar idonta na haskawa da ƙyallin ɓacin rai, ta karɓi wayar tana karawa a kunnenta. Kana iya jiyo sautin maganar da ke tashi ta ciki, sai dai baka iya jiyo abin da ake cewa, tsawon wucewar 120second ta miƙe daga kan kujerar da ta ke, Zaytuna taja mata kujerar baya sannan ta fito ta nufi ƙofa. Ba tayi magana ba har sai da ta sanyo ƙafarta waje, kan step na farko da zai shigo da kai cikin parlon, sannan muryarta ta fito da wani irin amon sauti. "Suite Eo5, 6th Floor Plot 1010 1st Avenue, By Shehu Shagari Way, Central Business District, Abuja". Abunda ta faɗa kenan ta kashe wayar, kuma tana kan hanyar kaiwa ga ɓangaren Baffa sai jiyo horn tayi a baya, tana juyowa taga motarsa ce ke shigowa. Hakan yasa ta dawo da baya domin tarbar mijinta, inda wani farin ciki da annuri ya mamayeta. *Dare, 20:45pm.* "wai ha jonta a nyamae nyamdu mae na?". (wai har yanzu ba ki ci abincin bane?) "mihari Kaka". (na ƙoshi Kaka) "nde nyamuda dume?". (da kika ci me?) "Kaka nabfa ƙoshi ne kawai". "bimi daga fajira wala ko metuda wukkugo nder reduma". (ce nake tun safe babu abinda kika ƙara sawa a cikinki). "Kaka minanata bana mi nyaman kodume". (Kaka kawai bana jin daɗin bakina ne). "To ko ananata beldum 6anduma?, nde an nyauma heftata'ke sae to guwallinima wakkati gotel.". (to ko ba kya jin daɗin jikinki?, Tunda ke ciwonki ba gane masa ake ba sai in ya kwantar da ke lokaci guda). "mi jamo Kaka. nane Amir waddiniyam mangoroje, daga mi nastai min njaride be Maijidda.". (ƙalau na ke Kaka, ɗazu Amir ya kawo min mangoro, tun kamin na shigo muka shanye da Maijidda). Kaka ta jinjina kai tace,"ni ai na iya fita a ban abin duniya na hana duk wanda ya gani na kawo maki saboda ina ƙaunarki". Fullo ta ƙyalƙyale da dariya bata ce komai ba. Kaka ta nemi wuri ta zauna tana gyaran man shanu, sallamar Maijidda ta ratsa cikin kunnuwansu san da take shigowa hannunta ɗauke da kwanukan abinci. Kaka da Fullo suka haɗa baki wurin amsa mata, ta ƙaraso kusa da Kaka ta aje kwanukan abincin. "a'a me muka samu haka?". Kaka ke tambaya tana buɗe murfin tasar abincin. "masa'Allah tuwon dawa har haka. Aina Yami ta samo si?". Maijidda tace,"tace na faɗa miki Jakadiya babba ce tace a kawo miki. Wai kici ki ƙara ƙarfi da ƙiba". Kaka tayi dariya tana faɗin,"to sikenan, godiya nake sosai. Dama kinga duk mun kasa cin shinkafar ɗazu". Rufe bakin Kaka kenan tambayar da Fullo tayi mata tayi wani wawan duka a cikin kanta, inda har sai da ta zabura taja da baya. "Kaka idan mutum ya tone asiri ko ya ƙone shi, wani abu yana samunsa ne?". "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yanzu wannan tambayar daga ina?, Fullo kullum faɗa miki nake bakinki ya dinga faɗar alkhairi ko yay shiru, yanzu tsakani da Allah kamarki ina ke ina magana akan asiri?, yanzu inda baƙuwan fuska wajen ba sai ya tsammaci wani abun daban ba. Dan shi ba zai dubi rashin hankalinki ba". "kai jama'a Kaka, ina batun rashin hankali anan, tambaya ne fa mabuɗin ilimi...amma shikenan tun ba ki amsa min zan tambayi Amir". "aikuwa tambayarki gare shi dai-dai yake da rabuwa da ke. Dan tsammani zai yi shi za ki asirce ko kuma kin yiwa wani ne. Kinga ni dai ki rabani da batun asiri, dama ya ya lafiyar kura? Ban gama fita daga tashin hankalin ɗazu ba za ki ƙara jefa ni cikin wani". Maijidda tace,"Kaka tashin hankali kuma?, me ya faru?". Kamin Kaka tayi magana Fillo ta amshe. "bafa wani abu bane. Akan wutar da ta tashi ɗazu ne wai shi ne take ta tsoro kar binciken da aka saka na gano musababbin tashin wutar ace ɓangaren masu aiki ne". Ta miƙe tana ɗaura ɗan kwalinta tana cigaba da cewa,"kuma na faɗa mata tunda dai tasan ba ita ta saka ba mene zai sa ta damu kanta". Maijidda tace,"to taya ma za'ace ɓangarenmu ne mu da ba zuwa wajen muke ba". Ta faɗa cikin dakiya, dan tunda akai zancen wutar jikinta ya fara ɓari, saboda ɗazu tana ji Yami na faɗin wai wutar sai da ta shiga har cikin lambu, ta kusa cinye rabin shuke-shuken ƴaƴan itatuwan da ke ciki. "to ma ace ma ɓangaren namu ne, dama ni na gaji da zaman gidan nan...kinga idan aka koremu ma koma rugarmu mu hankali kwance". Kaka ta ɗauko murfi zata ƙwala mata tayi saurin matsawa daga wurin tayi bakin ƙofa tana dariya. "Kaka bara muje gaida Hajjah Gana, kwana biyu ban leƙa ba kar ta shigo tana miki ciwon baki". "kar ki yi dare". Shi ne abinda tace da ita, sannan suka sa kai ita da Maijidda suka fita. Tun da suka fito Maijidda ke ta surutunta, Fullo dai bata ce mata komai ba. Har sai lokacin da Maijiddan ta ankare da inda suke nufa sannan tayi saurin dakatawa da tafiyan ta dubi Fillo tace. "wai ina zamu je?". "ina kika ga mun nufa?". "cikin gida". "to muci gaba da tafiya". Maijidda tayi shiru tana kallonta kamin tace,"idan kina wani abun kamar ba ke ba. Wanne ɗan aiki ne kika taɓa ganin yaje ɓangaren masu gida idan ba Hajiya ce ta buƙaci zuwansa ba...ko kuma kin bawa wani ajiya ne?". "babu wanda ya taɓa zuwa dan ko Kakata ma sau uku ta taɓa shiga. Ni kuma yau ina son shiga kuma tare da ke zamu je, dan ke ɗaya ce hanyar da nake da ita tiryan tiryan da zata kaini ɗakin Turaki". Ai shirunta sai ya haɗe da sauke hannunta da Maijidda tayi daga saman kafaɗarta. Tayi saurin juyawa a tsorace zata koma inda suka fito. Da azama kuwa Fillo tasha gabanta. "ke ban faɗa miki ba. ɗazu fa wutar da na haɗa asiri na ƙona". Ai kamin ta ƙifta ido ta buɗe Maijidda ta kwasa da gudu ta barta a wajen, dan ita har ga Allah ta fara tsorata da lamarin ƙawartata. _Please don't skip any page without commenting, react and vote. Becoz thats the only way you will show your love and appreciation towards me. It encourage me to do more🥰._ Don Allah share to other groups fisabilillah🙏 Youtube Channel-Nishadi Multimedia [8/6, 19:29] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *4* *E9611, Ibb Way. Maitama Phase 1 Abuja.* Ɗil 1,2,3,4,5, Adadin seconds ɗin da suka buga kenan ajikin agogon da ke manne a bangon ɗakin, tagogin windon ɗakin a buɗe suke, iska ta busa inda ta shigo ta cikin windon ta ɗaga labulen tagar zuwa sama. hasken rana ya ratso ta tsakanin labulen ya haska idon Turaki da ke tsaye a gaban madubi yana saka agogo a tsintsiyar hannunsa. Wannan hasken yasa shi kanne ido tare da ɗagowa ya kalla tagogin da iskar ke ta busowa zuwa ciki, na tsawon seconds ɗaya sannan ya maida kansa ƙasa yaci gaba da ɗaura agogon. haka kawai daren jiya da zai kwanta yaji ba ya buƙatar iskar bature, ko ta fanka ko ta Ac, dalilin da ya sa shi buɗe window kenan, kuma ko da ya tashi sai ya manta bai rufe ba har ya kunna Ac, wanda sai a yanzu ya fahimci dalilin da yasa Ac ɗin taƙi yin sanyi yanda ya kamata. ya gama taje sumar kansa ya miƙa hannu bakin gadon da hularsa ke ajiye zai ɗauka, yana ɗora hannu akai agogon ɗakin ya buga ƙara, sai ya ɗago kansa a kaikaice ya kai kallonsa ga inda agogon yake. Ƙarfe 9 na safe shi ne lokacin da ya buga, Mutumin da yazo cikin kansa a wannan lokacin shi ne Bello Ƙaraye, ko bai faɗa ba yasan yanzu yana can yana mita shi kaɗai na barinsa da yay yana jiransa. Sai kawai ya motsa leɓensa sannan ya ɗauki hular ya saka. Ya zauna a bakin gadon dan saka takalmi wayarsa ta shiga ƙara, ringtone ɗin i love you Maama ya karaɗe duka ɗakin. Ya miƙa hannu ya ɗauki wayar kuncinsa na murmusawa. bai picking call ɗin ba har sai da ya yanke tukunna yabi bayan kiran, bugu ɗaya aka ɗaga tare da yin sallama. Allah ɗaya yasan me yaji acikin zuciyarsa a wannan lokacin, bai amsa sallamar ba sai da ya lumshe idonsa tukunna. "Babana". Sautin muryar Hajiya Madina tayi amo a cikin kunnensa, Sunan da ta kirasa da shi ya fama masa wani ciwo da ke manne a zuciyarsa, ciwon da ba zai taɓa warkewa daga gare shi ba har san da numfashinsa zai tsaya, ya riga ya san da wannan, kuma kowa ma ya san da shi. Lokaci ɗaya yaji wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙogoronsa ya hana yawu wucewa, bai san lokacin da ya ɗaga wayarsa ya daki goshinsa da ita ba. Irin hucin da yake jerawa ya ankarar da Hajiya Madina situation ɗin da yake ƙoƙarin shiga, dan haka da sauri tayi ƙoƙarin dakatar da hakan ta hanyar kiran sunan da ita kaɗai ke kiransa da shi, kuma shi kaɗai ne sunan da za'a faɗa masa ya faranta ransa. "Me babban suna, be patient please". Lokacin da tayi furucin kwanciya yay a jikin gadon yana fuskantar P.O.P, yatsun hannunsa na hagun a saman karan hancinsa yana murzawa da ƙarfi, yayinda idanuwansa ke a kulle har yanzu basu bar raɗaɗi ba. "Ina kwana Maama". "Ka tashi lafiya?". "lafiya lau, ina fatan duk kuna lafiya?". "muna lafiya lau, Ya wurin aikin naka?". "Aiki mun gode Allah, yanzu nake shirin fita". "Glad to hear that, Allah ya taimaka ya bada sa'a da nasara". Daga kan dining ɗin da Hajiya Madina ke zaune, ta kai glass cup ɗin da ta ɗauka bakinta ta kurɓi lemun ciki na five alive, sannan ta ƙara cewa da Turaki. "When are you coming back home?". "Ina kan hanya zuwa wani satin Insha'Allahu, munyi magana da Baffa jiya". Jin yace mata sunyi magana shi da Baffa ta murmusa kuncinta kamin tace,"To shikenan Allah ya dawo min da kai lafiya". "amin ya Allah Maama". "ina fatan Baka da matsalar komai ko?". "Babu Maama". "to Allah yayi maka albarka...Make sure you eat your breakfast before going to office". Ya kai hannu ya shafo gefen fuskarsa inda gashin sajensa yake kamin ya amsa da,"insha'Allahu Maama". Taso su tattauna wani batu amma saboda wani dalili nata sai ta fasa, Basu yi sallama ba sai da tayi masa adu'a sosai tukunna. Kuma kiran nata na katsewa kiran Bello Ƙaraye ya shigo a lokacin, ya ɗaga da guntun murmushi a fuskarsa, sallamar da yay sai da Bello Ƙaraye yayi kamar ba zai amsa masa ba. "Ba zaka fito bane yau?". Turaki na dariya ƙasa-ƙasa yanda Bellon ba zai ji ba yace,"ehh kamar dai hakan". "naga dukkanin alama ai". Bello na faɗar hakan ya katse kiransa, bayan ya jawa Turaki tsaki na ɗan rainin hankali kawai. Gaba ɗaya Turaki bai yi niyyar yin break fast ba, amma saboda abin da Maama tace haka dole yaja ya tsaya da ya fito parlo. Ya nemi kujera ya zauna tare da janyo center table gabansa, dama already yasa wani ɗan aikensa yay masa order na chips tun 6, kuma da yaga zai yi late sai ya yanke shawaran idan yaje office yaci, to amma babu yanda zai yi tunda Maama tayi magana. Ya ɗauko chips ɗin zai kai baki sai ya dakata saboda Zaytuna da ta faɗo a ransa, duk da cewar tana cikin ransa a kowacce bugawar daƙiƙa. To amma dai a yanzun ba ya jin zai iya saka komai acikinsa idan har itama babu abunda taci. Wayarsa ya ɗauko ya kira lambarta, kira na farko bata ɗauka ba sai ana biyu shima sai da ya kusa yankewa. "Hellow Hammah nah". Ta kira sunan nasa cikin muryar bacci. Yatsun hannu basu isa sun ƙirga adadin farin cikin da ya shiga ba da jin muryarta. Ya sauke numfashi sannan yace. "ba za ki daina wannan malalacin baccin naki ba ko Zaytun?". "Hammah nah jiya bamu kwanta da wuri ba ne, ka san Boɗejo tazo...to ta tsaremu da wannan hirar tata mara ƙarewa bamu ankarewa ba sai gani mukai lokaci ya wuce". "yayi muku kyau ai, kuyi ta biye mata tana hanaku baccin kirki, bayan ita ta riga tayi nata tun yarinta". Zaytun tayi murmushi me ƙarfin sauti ba tare da tace komai ba, kasancewar ita ɗin ba mai yawan magana bace. Turaki ya ƙara cewa,"dama i just call to check on you, I hope all is well?". "komai lafiya Hammah nah". Yay ɗan jim before saying,"idan kinyi breakfast let me know...amma yanzu fa za ki tashi bana son zama da yunwa, ki kalla time ki gani ƙarfe nawa". Ba tare da ta duba komai ɗin ba tace,"Yanzu fa Safiyan yay Hammah". Tayi maganar a shagwaɓe. "shafo cikinki sai ki faɗa min yanda yake". Ta kai hannu kan stomach ɗinta sannan tace,"Hammah yana nan yanda ka san shi a shamule". "to kinga alamar yana buƙatar abinci kenan, i keep telling you babu namijin da zai ɗauke ki alhalin yasan cikinki da bayanki a haɗe suke, he will be thinking you can not bear him a child". Tabbas ya faɗi maganar ne to entertain her, kuma hakan ce ta kasance, dan sai da tayi dariya sosai har baccin da bai bar idonta ba ya saketa lokaci ɗaya, ta miƙe zaune akan gadon tana ɗora pillow akan cinyarta, fuskarta cike da annashuwa tace da shi. "ni da nake so ko da Allah bai azurtani da ƴaƴa da yawa ba, ya bani guda ɗaya tilo da zan saka masa sunan Hammah nah. Dan haka dole na tashi naje naci abinci ko da banyi niyya ba...ni Hammah idan ma kaga ana tallan maganin da ke ƙara tumbi ka sayo min kawai". Turaki yay siririyar dariya da cewar,"wasu na neman ragewa mu kuma muna neman na ƙari". Yay maganar yana mai duban agogon hannunsa sannan yace,"zan wuce office na kusa late". Daga haka su kai sallama cike da kewar juna. *After 10minutes, Growth Stack Software.* *Zone 5, 1st Floor Novare Central, Dalaba St, Wuse 900285, Abuja.* Motarsa ta shigo cikin company ta ƙarasa zuwa wurin da aka tanadarwa ma'aikata domin aje motoci. Tun kafin ya ƙarasa buɗe murfin motar wani tsoho ya ƙaraso wajen cikin sassarfa. "sannu da zuwa ranka ya daɗe". "yauwa Baba sannunmu". Ya faɗa yana fitowa daga motar ya rufe. Tsohon ya buɗe bayan motar ya ɗauki ƴar ƙaramar jakar laptop ɗinsa, sannan yay cikin office ɗin da ita. Shi kuma Turaki ya mara masa baya, tunda staffs ɗin wurin suka ganshi suke ta rissinawa su na gaida shi matsayinsa na Managing Director a ma'aikatar. Bai shiga office ɗinsa ba kai tsaye ya wuce zuwa ofishin Manager, ya ɗauki kusan 5minutes sannan ya fito ya wuce nasa office ɗin bayan Manager ya shaida masa ya tsayar musu da lokacin da zasu shiga meeting ɗin. Zamansa kenan akan kujerarsa sai ga Saktariyarsa ta shigo, ta aje record book ɗin da ke hannunta a saman table ɗinsa, ya janyo shi zuwa gabansa yay rubutu ajiki sannan ya ƙara miƙa mata. Ta ɗauka sannan tace da shi. "ranka ya daɗe PWC sun shigo tun aroud 8:30". Ya ɗago daga kan computernsa ya kalleta, yana mai ɗan ƙanƙance idonsa cikin yin nazari kafin yace da ita. "dama muna da Appointment ne da wasu this week?". "a'a ranka ya daɗe, nima dai nayi mamakin zuwansu..to amma da suka ce min daga ofishin Manager suke sai na tsammaci shi ya turo su wurinka". Ta faɗa tana buɗe wani file na daban da ke hannunta ta ciro wani envelop a ciki, sannan ta miƙa masa. "sun ce na baka wannan". Duk a cikin harshen turanci ta ke maganar. Ya miƙa hannu ya karɓi envelop ɗin ya buɗe, cikin seconds ɗin da ba su haura 10 ba ya gama karanta abin da ke jikin takardar. Bayan ya gama ya miƙa mata tare da cewa. "ki kai office ɗin Manager, zamu yi waya da shi yanzu". Ta rissina tare da karɓa sannan ta fita daga office ɗin. Don Allah share to other groups🙏 Youtube Channel-NISHADI MULTIMEDIA [8/7, 18:42] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *5* Fitarta da minti biyar akai knocking ɗin door, ba tare da ya ɗago kansa daga kan system ba yace,"yes come in". Muryar nasa ya fito a hankali yayin da hannunsa guda ke dunƙule a gefen bakinsa. Bello ƙaraye ya shigo cikin office ɗin ya zauna akan kujera, ya fuskanci Turaki da har yanzu bai ɗago ido ya kalle shi ba yace da shi. "sai yanzu ka ga damar fitowan?". Turaki na typing a Laptop yace,"kai ma dai kasan ba mata gare ni ba balle na sami me tashina da wuri". Bello Ƙaraye yay masa wani duba yace,"tun yaushe ake cewa kayi auren kaƙi. ni na rasa ruwan idon uban me ka tsaya yi da har yanzu ka rasa macen da tayi maka". Turaki yace,"Lokacina ne bai yi ba, ko kaga nayi girman da za'a dinga tarata da maganar aure ne?". Bello ya harare shi yace,"sannu motsin gado". Turaki yace,"Yauwa, don haka sai a barni na sarara". Bello ya ƙara cewa,"yanzu Asma'u ɗin ma bata yi maka ba?". "yes, she is not beautifull enough, and you know me well bana son abu mara kyau...idan kana sonta ka ƙara ata biyu na bar maka". Bello dake masa wani kallo yace,"Ba ka da hankali...let close the charpter kamin ka ɓata min rai. kuma bari na faɗa maka, ka daina discouraging mutum akan abunda kai bai yi maka ba alhalin shi yayi masa, Ishaq told me you were telling him to get rid of that girl after all kasan yayi magana da iyayen yarinyar nan...tsaya ma! just because you think the girl was too local shikenan sai akace ba za'a aureta ba?". Turaki yay guntun tsaki yace,"ka zo muyi magana akan aiki ne ko kuma zamu tsaya kan shirmen zancenka ne, da baku da aiki sai zancen soyayya, mace, aure". Har yay shiru sai kuma ya ƙara cewa,"to for what reason ma yana da degree har biyu zai je ya ɗauko yarinyar da she didn't even finish secondary school". "to kai ina ruwanka?, shi ai yasan da hakan yaje ya ɗauko ta ko". Turaki yay tsaki, Bello bai ce da shi komai ba ya fiddo laptop ɗinsa daga cikin jaka. Yay danne danne ya juyar da fuskar laptop ɗin yana nunawa Turaki. "Na sami number'n contractor ɗin, zanyi waya da shi zuwa dare". Turaki ya faɗa sanda ya gama karanta rubutun da ke jiki, sannan ya miƙe daga kujerarsa zuwa gaban wata drower da tarin takardu suke a cikinta. Bello Ƙaraye na binsa da kallo har ya taka steps, hannunsa ya kai cikin drower ɗin yana fito da wani file ƙunshe da takardu fal a ciki. Ya dawo kan kujerarsa yana duba takardun cikin file ɗin. Bayan yay musu ɗai-ɗai ya kwashi wanda zai amfani da su ya wuce cikin madaidaicn parlon cikin office ɗin, daga bisani Bello ya mara masa baya. Tsaye ya tarar da shi yana fuskantar gilashin windo, ya harɗe hannunsa guda ɗaya ta baya. Idanunsa na kafe ne akan glass ɗin kamar mai son ɗakko wani abu ajiki. Bello ya zauna kan kujera yana ƙarewa tsayuwar Turaki kallo, tsayuwar nan tasa mai cike da ƙasaita da taƙama, kana kallo zaka san an gaji sarauta cikin jini da asali. Sanyin Ac yasa idanuwan Turaki lumshewa, muryarsa a kausashe yace, "tunda naji ana talking of billions tunanina ya bani da akwai wata a ƙasa". Ya faɗa sannan ya juyo ya zauna kan kujerar da ke fuskartar Bello, ya shafo fuskarsa da duka tafukan hannunsa biyu kamin yace,"dole ne ma ba zamu yi aiki da wannan company ɗin ba". Bello ya dube shi da mamaki yace,"saboda me?". "yanzu Accounter suka fita shi da mutanen nan". "ta ina kai ka gansu?". "a bakin gate suka tsaya, shi kuma ya fita da mota ya ɗebe su". Ya faɗa ƙwayar idonsa na haskawa da dimbin ɓacin ran da ke ciki, ya ɗora ƙafafunsa kan table ɗin na tsakiyarsu, sannan ya koma ya jingina da kujerar da yake zaune. Idanunsa a kulle yake cewa,"rayuwa cike ta ke da marasa halacci, ko kaɗan bana son mutum mara gaskiya". "So now how are we going to tackle this problem?". Bellon ya faɗa shima in astonishing at what Turaki had said. "na san yanda zanyi tackiling ɗin abun, let's get out of the meeting first". *Gombe, Dukku.* *Alh. Ahmad Alfindiki Residence, 8:30am.* "Kaima ai ka sa ni, it's either na kwana gida ko kuma na wuce gidan Khalid, na tsani kwana a hotel if not necessary". Yusuf ke magana a wayan da ke maƙale a kunnensa, yasa key ya rufe motan sannan ya wuce ɓangaren Inna Wuro wato Kakarsu, har lokacin da ya shiga parlonta bai gama wayar ba. Inna Wuro na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun parlon ta kalli Yusuf da ya duƙa yana cire takalminsa, ta taɓe baki ta ɗauke kai taci gaba da kallon tv da ta ke. "yes kusan 2 weeks ma kenan, but i think i will be coming back next tomorrow by God willing. Becox akwai patient ɗin da nake da ita acan". Yaci gaba da wayar yana ƙarasowa ya zauna kan 1 seater. "alright i will you call before then insha'Allah". Inna Wuro dai da ke kallo hankalinta ya rabu gida biyu, tun shigowarsa ta ke jera ƙwafa. Ji ta ke kamar ta tashi ta fizge wayar ta rotsa ta a ƙasa, sai taga ta tsiyan shigo mata waje babu sallama. Ta lura ma gaba ɗaya yaran gidan sun maida ita ƴar iska, kowa ya tashi shigo mata waje sai ta kaɗo masa yake shigowa da sallama, sun fi gane su shigo kullum su na ɓaɓatu a waya kamar dan su bature ya ƙera wayar. Yusuf da ya gama wayar sai da yay typing message a wayarsa kana ya sakata a aljihu, sannan ya kai idonsa kan Kakarsu yace,"Ina Kwana". Ba tare da ta dube shi ba a fusa ce tace,"yana kwano". Yay ɗan murmushi ya ƙara cewa,"kin tashi lafiya?". "da baka ganni anan ba ai". Yace,"to Allah ya ƙara lafiya". Bata dai amsa mishi ba taci gaba da kallonta, kallon da gaba ɗaya ba fahimtarsa ta ke ba. Bakinsu kawai taƙe kallo tana yin dariya a inda ya kamata, ta kuma ja uban tsaki a inda akai mata ba daidai ba. Ta gefen ido ta ke ta kallon Yusuf, wanda ya sauko ƙasa ya takwashe ƙafafunsa, ba tace da shi ƙala ba sai da ya janyo flask gabansa sannan cikin hanzari ta dakatar shi. "me haka?, kwanon abincinka ko nawa da zaka wani janyo shi gabanka?, ko kuma Uwarka ta dafa ta kawo min ne da zaka nuna min iko da shi?, salon dai neman magana irin ta bawa...ina ce da ka shigo ko sallama baka min ba balle na sami arziƙin gaisuwa, saboda ka maida ni abar banza shine sai da ka gama waya da wanda ya fini tukunna zaka durfafi abincina...to baka isa ba, kuma ba'ai wannan halittar da zata taɓa min kwano ba, ka tashi ka koma ka zauna ko kuma ka bar min parlo tun bamu samu saɓani da kai ba. Ni bana son tashin hankali haka kawai". Yusuf ya miƙe ya koma kan kujerar ya zauna ba tare da yace mata komai ba, ta kalle shi kaɗan ta kwaɓe fuska kamin tace,"yafi maka dai". "amma dai ina ce bayan na gama wayar na gaishe ki". Yace da ita yana kallonta. "bata yi min bane". "wa?". "ita gaisuwar taka". "ohh to Allah huci zuciyarki". Ta amsa da amin. Yaci gaba da danna wayarsa, tsawon mintina kusan uku yaji maganar Inna Wuro na cewa. "aiko ka akayi ne?". Bai zaton da shi ta ke ba, dan farko ɗagowa yay yana dube duben ta inda zai ga mutum, sai da yaga ba kowa sannan yace. "ba wanda ya aiko ni". "to kuma zaman ma mene?, zuwa da sassafe haka, babu fa jimawa aka gama min gyaran wurin nan. bana son a ɓata min waje dan ni ba fiya son ƙazanta nagi ba...da ba za'a bar mutum ya huta ba dole sai anzo ɗaukar magana". Rufe bakinta kenan Aliyu ya shigo parlon, ta bishi da ido har sanda ya nemi three seater ya kwanta yana ɗora ƙafafunsa akan hannun kujeran. Haushi ya tuƙeta tace,"idan ka tashi Amadu ya gyaran wajen". Shi dai bai kulata ba ya ɗauko earpice a aljihu ya saka a kunne, Yusuf na kallonsa yana mamakinsa, shi dai a wannan zamanin bai ga namiji mara lissafi ba irin Aliyu, yana namiji tunda akai hutun ASUU shikenan ya zama kamar mace, kullum yana gida sai shegen aikin jin waƙoƙin banza, yaƙi sana'ar fari balle ta baƙi, idan anyi magana yace ai Babansa ya tara musu...kuma in ana faɗa masa gaskiya Ammi tace ba haka ba. Ya jijjiga kansa kawai yana jan ƙaramin tsaki na takaici. Aliyu yace da Inna Wuro,"naga mutanen ƙauye sun zo". Tace,"to su tsaya a iya ɓangaren ku bana son gayya". Yay gajeriyar dariya sannan yace,"ya za'ai su zauna a ɓangarenmu?". Tace,"nima ya za'ai su sauka a ɓangarena?, Ni dai magana ta Allah idan kaje ka faɗawa Uwarka kar a soma turo min kowa, dan wancan karan banji daɗin zuwansu ba. Banda Amadu ya gina masai babba da ban san yanda zanyi ba, abunda ban taɓa gani ba sai a lokacin kashi har bakin masaina. Ɗoyi kuwa iri-iri babu kalar da ban guntsa ba, inda ace Uwarku ce kaɗai a gidan nan ai da warin kashin yaran ƙauyen nan shi zai zama ajalina. To sai Allah yasa akwai Falmata, tazo da kanta wallahi ta wanke min banɗaki nan ta sanya masa turaren wuta". Aliyu yace,"itama Ammin ai zata yi miki, dan dai bata sa ni ba ne, kuma ai da sai ki faɗa mata". Ta kama baki tace,"to ina ma ta ke zuwa waje na balle na sanar mata. ni fa idan kaga mun haɗu da ita Amadu ne zai yi tafiya mu haɗu a wajen masa rakiya kamar kishiyoyi, amma ni ina nake da wani arziƙi a wajen Zainabu...kana dai kallo ko gaisuwar safe". Bai sake cewa da ita komai ba, don sam ba ya son abin da take yiwa mahaifiyarsu. Ta miƙe ta ɗauki flask ɗin abincin da aka kawo mata tun ɗazu bata ci ba ta wuce da shi kitchen, dan idan ta barshi Aliyu ma saka masa hannu zai yi, shi kuma ba jin magana yake ba. Fridge ta buɗe ta saka yanda ma ko da wani ya shigo kitchen ɗin ba zai gani ba, har ta nufi ƙofa zata fita sai ta tuna ta dawo ta sakawa fridge ɗin key dan lemon da yake ciki sauran guda uku, Amadu bai san ya ƙare ba kuma cikin Ƴaƴansa babu mai ɗaukowa a ɓangarensu ya kawo mata, basu iya kawo mata komai ba amma sun iya suzo su cinye mata duk abinda aka ajiye mata. Bata dawo parlo ba sai da tayi sallar walha, tana zuwa ta tarar da Yusrah ta shigo, ta bita da kallon sama da ƙasa ta ƙarasa bakin ƙofar ta jawo ta rufe tana faɗin,"kamin na huɗu ya shigo, ba dan ba dan ba sai nace Amadu gidan taron jama'a ya buɗe min". Ta murza key tana mitar,"kai da ɓangarenka amma ba za'a barka ka huta ba". Sannan ta saƙala key jikin abin maƙale labule tana cewa da su. "idan zaku fita ga key ɗin anan, idan zaku fita nace ba wai idan kunji knocking ba". Cikinsu babu wanda ya tankawa maganar da ta ke, dan haushi kamar ta rufe su da duka. ta kallesu su duka tace,"Amadu kuka share bani ba". Sannan ta juya ta koma ɗakinta. Yusrah ta zauna kan kujerar da Inna Wuro ta tashi, ta buɗe jakarta ta ɗauko office pins tare da madubi, ta shiga ɗaura ɗankwali. Tana ɗaurin ta ke cewa Yusuf. "Yaya ashe ka shigo. Ɗazu Ammi ke cewa ƙila har ka koma ba lallai ta ganka ba...idan ka gama abinda kake naji dai tana batun zuwa abuja yau". Ya ɗago da ido ya kalleta yace,"me zai kaita Abuja?". Time da ta ke gama ɗaura ɗankwalin tace masa,"biki mana...daughter ɗin ƙawar nan tata da aka haɗaku kaƙi, ita ce zata auri ɗan gwamnan jigawa". Ya maida idonsa kan wayarsa yace,"When will she come back?". Tace,"I don't know. but i heard her saying sati guda za'ai ana bikin". Karo na biyu ya ɗago ya sake kallonta. "kuma Daddy ya barta?". "kai dai Yaya babu ruwanka. Ka barta taje tai hidimanta ta dawo". Still yana kallonta yace,"ki shirya ku tafi tare". Tayi saurin kallonsa da cewa,"niii babu inda zanje. Haka kawai na bita Ammi ta dinga cusa ni cikin yaran nan masu shegen ji da kai su na min kallon raini". Ya ƙara cewa,"you mean ita ɗaya zata tafi?". "kamar dai hakan. Amma ƙila Nabla ta bita kasan ita amara ƙirjin biki ce". Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihu. Yana cikin saka takalminsa Inna Wuro ta dawo parlon, tayi kasaƙe tana kallon Yusra da ke yafa ɗan yalolon mayafinta a kafaɗa. "kuma fita za ki yi a hakan?". Inna Wuro ta tambayeta tana kuma ƙarewa shigar jikinta kallo. Yusra ta jefa cingom bakinta ta amsa mata."yesss mun koma school yau...na manta ma ban faɗa miki ba, ko da yake jiyan na shigo ai na tarar kinyi bacci, an kafe mana result na samu pass all". Inna Wuro tayi mata wani kallo, kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta juya ta dakatar da Yusuf da ke shirin fita tana ce masa. "wai kuwa kana kallon a yanda yarinyar nan zata fita shine ba zaka tsawatar mata ba, kana babba amma kai sam baka san abin da ya kamata ba, da kai da hoto duka ɗaya. Kalla fa gantalallan ɗinkin da ke jikinta, wuya duk a buɗe kusan rabin nono a waje, amma a haka ta ke ikirarin zata fita har makaranta salon ta jawa Amadu zagi". Sam Yusuf bai lura ma da kayan da ke jikin Yusra ba balle ɗinkin, sai bayan da ya gama saka takalmin ya kalleta, sai aukin zumɓura baki gaba ta ke yi tana ƙunƙuni, da gaskiyar Inna Wuro dole tace gantalallan ɗinki, shi a wurinsa ma wannan ɗinkin asarar kaya ne. "ke kar ki kuskura ki fita a haka". Ta ƙara kumbura kamar za tai kuka ta nuna kayan jikin nata. "fisabilillahi me wannan ɗinkin yay, ni gaskiya babu abunda zan sauya tunda ko Ammi ta ganni da su kuma bata ce komai ba". Inna Wuro tace,"yo wannan Uwar taki sanin ya kamata tayi da zata hanaki fita tsirara". Yusuf ya wurga ma ta wani mugun kallo. "yaushe na fara wasa da ke? Ki wuce ki sauya su babu inda za ki fita a haka". Yana rufe baki Aliyu ya miƙe daga kwancen da yake, shima yana mata wani banzan kallo irin na ba ya son raini yace,"Uban waye sa'anki anan da ana yi miki magana kina ke ba haka ba. Kin wuce kinyi abunda akace ko sai na saka miki ƙafa". Yusra ta fashe da kuka tana bige-bigen ƙafa a ƙasa, ta wuce Inna Wuro tana faɗin ba zata ƙara zuwa site ɗinta ba sai dai idan sauya mata suna akayi. Inna Wuro ta bita da cewa,"ai dama bani ke gayyato ki ba, ke kike kawo kanki". Ta dubi Yusuf tace,"yau zaka koma kano ɗin?". Yace,"may be". Ta taɓe baki tayi ciki abinta. "kai kasan abunda kace, ni dai nafi ƙarfin zagi da yaren bature. Na ɗauka yau ɗin zaka tafi na baka saƙo ka kaiwa Nuratu". Jin ta ambaci abar ƙaunarsa yay saurin cewa,"ki bada yau zan koma". Tace,"na fasa ai". Sannan ta dubi Aliyu tace,"kai kuma ɗan zaman kashe wando idan zaka tafi karka bar min tv a kunne ka kashe min". Yusuf na fitowa yay part ɗin Ammi mahaifiyarsa, har ya shiga parlon sai ya fito sakamakon murɗawa da cikinsa yay, ya koma part ɗin Hajiya Falmata da suke kira da Umma. Step sisters ɗinsa ya tarar a parlon su biyu, Salma da Kursum. Ya ƙarasa shiga ciki ya zauna kan kujera suka gaishe shi, Salma ta miƙe tana faɗin,"bari na kira Umman". Tare suka dawo da ita, Salma na gaba ita tana baya da waya kare a kunnenta tana bada sallahun da za'a taho mata da shi daga kano. "yanzu ka shigo?". Ya kalli Umman da tayi masa magana yace,"na ɗan jima ina wajen Inna Wuro". Tace da shi,"aiko ga breakfast ɗinka can ina ga ma yay sanyi". Ta kalli Kursum tace,"je kiyi warming abincin Yayanku". Within 3mints Kursum ta dawo ta janyo center table ta ɗora plate ɗin abincin a kai. Yana ci su na magana da Umma, tana sanar masa tafiyar Nameer da yay a ɗazu, ya samu aiki a wani company da ke can taraba state. Bayan ya sauke spoon daga bakinsa yace,"Nameer ɗin yace min Daddy bai yarda da zuwansa can ba". tace,"da ƙyar Alhaji Saleh yay conviecing ɗinsa ai, shi ne Nameer ɗin ya wuce yau da wuri". "to Allah ya taimaka ya bada sa'a". Umma ta amsa da amin. Sauri sauri Yusuf ke yi wajen cin abincin dan gaba ɗaya hankalinsa na can wurin Ammi, fatansa ma Allah sa Yusrah bata faɗa mata ya shigo ba. Yana gamawa ya miƙe yana yiwa Umma Sallama. Ta tambaye shi,"when zaka koma?". Yace,"may be da yamma ko kuma gobe". Umma tace,"Nuratu tayi min complain jiya da mu kai waya...". Tun Umma bata ƙarasa maganar ba yay murmushi tare da cewan,"tare zamu tafi insha'Allahu". Itama tayi murmushin tana cewa,"sai ka dinga haƙuri da rigimar Nuratu, musamman yanzu da ba ita kaɗai bace". Fitowarsa daga part ɗin Umma na Ammi ya wuce, a parlo ya tarar da ita su na magana ita da yaranta, ya ƙaraso ciki kansa a ƙasa gabansa sai faɗuwa yake. Ammi kam ko iskar da ta ɗebo shi ta kawo shi bata kalla ba, maid ɗin da ke riƙe da trolley ɗin Ammi ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa. Sai da ya bari Ammi ta gama magana da yaranta sannan ya gaisheta, tai banza da shi tamkar bata ji shi ba. ta zo fita ne ma ta tuna da ƙararsa da Yusrah ta kawo mata sannan ta dakata daga fitan, ta dawo tayi tsaye akansa. "idan ka wulaƙanta ni nayi maka shiru ba zan yarda ka dinga saka min yara kuka ba ka aje wannan a ɓangaren tunaninka...idan ba haka ba wallah ba zamu kwashe ta daɗi da kai ba, ba ruwanka da sabgar ƴaƴana ka fita a harkarsu". Ya ɗago ido ya kalleta ta ɗauke nata daga kallonsa, muryarsa a ƙasa yace,"ita Yusran me tace miki dama?, babu wanda ya duketa balle zagi, kayan da zata fita da su ne basu dace ba akace ta sauya shikenan sai ta ɓare baki...". Ammi ta wurga masa wani kallo tare da cewan,"ni rufe min baki, ina ruwanku da shigar da tayi, ina ce ai ba tsirara zata fita ba ko?...da ƴaƴan waccan Matar ne da kake kallonta da gashin ido ai ba zaka ce da su ƙala ba, sai nawa ƴaƴan da aka raina shi ne za'a bi a takura musu...to da gatansu tunda ban mutu ba saboda haka a bar takura musu, na faɗa maka. itama kuma Kakar taka ka faɗa mata...shima Aliyun zai shigo ya same ni". Ya girgiza kansa kawai, kamin yace,"kiyi haƙuri". Tana ƙoƙarin fita maganarsa ta tsaida ita,"Ammi dan Allah ki kwana ɗaya kawai". Tace,"tunda takarda aurena a hannunka ta ke me zai hana Yusuf". "dan Allah Ammi, wallah idan ki kai nisa da yawa gidan ba ya daɗi". Tayi murmushin takaici,"har yaushe asirin da ke kanka ya kunce daka fara sanin muhimmancina acikin gidan nan?...kaima ka zama mace ka iya makirci kenan, to ni ba zaka yaudaren ba, ko ɗazu baka san ina kallonka ka shigo ka fita ba ne saboda kana tsoron kada uwarka ta tsine maka...". Yusuf yay saurin katseta da cewan,"Ammi don Allah ki daina irin wannan maganar...". Itama bai ƙarasa ba ta katse shi da faɗin,"an riga an shanyeka ai duk gaskiyar da zan faɗa a iska zaka dinga jinta". Yay shiru bai ce komai ba, ta ƙara cewa,"ka tashi ka kaini airpot". Yay saurin miƙewa yana karɓan jakar hannunta suka fita tare. Tunda suka shigo motan babu wanda yay magana, har ga Allah Yusuf naso yay hira da mahaifiyar tasa amma yana tsoron ta balbale shi da faɗa, dan yanzu da abunda yake na faɗa da wanda ba na faɗa ba duka na faɗa yake zamar mata indai tsakaninta da shi ne. Tunda yazo ma yake son mata albishir da cikin Nuratu amma yana tsoron abunda hakan zai haifar, dan bata ƙi ma tai muguwar adu'a ba tunda ba son auren nasu ta ke ba, ita duk abunda ya shafi Falmata to shikenan ta ɗaura gaba da shi, yasan da ace Nuratu ba jinin Falmata bace Ammi zata ɗan rangwanta masa akan ƙin zaɓinta da yay. Maganarta ta kutsa cikin tunaninsa. "yarinyar da na so na haɗaku ce za'ai bikinta. Da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai ya haɗata da wanda ya fika. Ɗan governor ɗin Jigawa ne, yaron ance a ƙalla ya mallaki sama da miliyan 500. Shi ɗaya ne a wurin mahaifinsa, babarsa ita ɗaya ce for morethan 35years da suke tare da mijinta...ba irin Babanka ba da shekara 15 muka ɗauka tare yaje ya ɗauko min annoba". Yusuf yace,"Allah sanya albarka a auren nasu". Aciki ta amsa masa, yana kallon yanda ta ke hararsa ta cikin window, tunda yake da ita ba su taɓa fita tare ba ta shiga back seat ba sai yau, tunma bayan auren nasu dama bata yarda ta shiga motarsa, hanya ma bata so su haɗa da shi. "Ammi Nuratu ta kwan biyu bata da lafiya". Ya faɗa cikin kwantar da murya. Ammi ta dakata daga danna wayar da ta ke yi ta ɗago ta dube shi, kamar ba zata ce komai sai can kuma a hankali tace,"bata da ƴan'uwa ne?". Ya rumtse idonsa sosai kamin yace,"tana da su mana Ammi". "ohh tou kuma kazo kana faɗa min bata da lafiya, ai su zaka je ka sama bani ba da ban haɗa dangi da ita ba". Bai ƙara cewa komai ba yay shiru, Sani Abacha International Airport ya ajiyeta, bai baro wajen ba sai da jirginsu ya tashi tukunna. Yana kan hanya abokinsa Dr Huzaifa ya kira shi, saboda haka ya yanke hanya ya biyo ta shongo estate. Slowly yake driving ɗin, Idonsa na kallon left side yana kallon wani gini da ake ƙarasawa, idonsa ya sauka akan yashin da tifa ta juye yanzu ta bar wajen. Kamar wanda ya tuna wani abu sai ya waiga yana daɗa kallon wajen da ya bari, hoton wannan yarinyar ya haska a cikin idonsa a wancan lokacin da ya taɓa wucewa ta wajen. Tana zaune a gefen yashi ta ƙudundune tana rera kuka a hankali, ta riƙe siririyar doguwar ƙafarta tana kallon wajen da taji ciwo cike da tashin hankali. Gaba ɗaya ciwon ba wani babba bane, amma kace wadda akace ƙafartata ce ta ruɓe za'a yanke saboda kawai jinin da ya fito a wajen ɗan kaɗan. sai yaga kamar yanzu ne abun ya faru, dan bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba tunawa da yay da irin dramar da suka sha da ita akan kawai ta bari ya saka mata bandage akan ciwon da taji. _"jinina zai ƙare"._ Haka ta faɗa masa a lokacin da ya tsuguna gabanta yana tambayarta me ya faru, cikin muryar kuka, kuma duk da cewar muryar tata ɗauke ta ke da kukan da tasha, hakan bai hana daɗin muryarta fitowa ba. Ta runtse ido ma ta kasa kallon ciwon, ya koma mota ya ɗauko first aid amma ko da ya dawo sai ya tarar bata wurin, abun yay matuƙar bashi mamaki a sannan, dan zatonsa ma ko aljana ya gani ko kuma aljanu suka buɗe masa ido yau, saboda kyan yarinyar ma yafi kama da na aljanu. Kuma sai can zai bar wajen ya hangeta ta ɓoye a bayan bulo, ashe first aid box ɗin da ya ɗauko ne yasa ta guduwa. [8/8, 00:57] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *6* Yau ya kasance juma'a. Ƙofar gidan na Judge Dikko Habib cike yake da ɗumbin mutane masu zuwa karɓan sadaqa, yara da manya musamman ma magidanta marasa ƙarfi, haka gidan yake kasancewa a duk wata juma'a, zaka ga mutane babu masaka tsinke tun an idar da sallar asubahi sun bi layi su na jiran fitowar Mai gidan. Judge Dikko Habib babban alƙali ne wanda ake damawa da shi a manyan shari'ar da ta shafi cikin ƙasa da wajenta, kuma alƙalin da gwamnatin tarayya keji da shi. Dattijon ƙwarai mai halin dattako da nagarta, Yawancin zamansa a america yay, karatunsa ma tun daga secondry har matakin phd duka acan yayi. Matansa Biyu Hajiya Ramla da Hajiya Madina amma ainihin sunanta Aina'u, Ƴaƴansa 6, uku maza uku mata. Kuma kaf cikinsu babu wanda ke karatu a nigeria duka waje yake fitar da su. Turaki ne ma kawai yayi secondry a nigeria kamin ya fita US yay degree da masters ɗinsa acan. Idan yazo zai bawa kowa sadaqa zai ba shi kuɗi dubu uku, sai ma'aikatan gidan maza su bika da kwanon shinkafa, taliya guda biyu da kwalaban farin mai da manja. Judge Dikko ba ya taɓa barin wajen har sai ya tabbatar da kowa ya samu, duk kuwa da uban yawan da mutanen ke da, ba ya gajiyawa kuma ba ya ƙosawa, hakana duk nisan tafiyar da yayi duk irin muhimmancinta zai katse kome yake yi ya dawo alhamis dan kawai waɗannan mutanen da Allah ya ba shi ikon taimaka musu. Ya faɗa saveral times gani yake idan har ba shi ne da kansa ba to ba za'a riƙe amana kamar yanda ya bayar ba, saudiya kawai yake tafiya ya iya haƙura, shima kuma sai ya kira Muhammad Turaki a duk inda yake ya dawo ya tsaya akan ragamar abun, dan shi kaɗai yake ganin zai iya kwatankwacin abinda shi zai yi da kansa. Kuma a wannan juma'ar ne ma'aikatan gidan basa samun hutu ko kaɗan, dan tun daga safe har dare su na rabon abincin sadaqa. Ƙarfe goma da rabi Baffa ya dawo cikin gidan daga rabon sadaqar da ya fita, Khalil da ke ƙoƙarin shiga motarsa zai fita ya hange shi, hakan yasa ya rufe motar ya taho da sauri. Ya rissina a gaban mahaifin nasa cike da girmamawa yana faɗin,"Barka da dawowa Baffa". tare da miƙa hannu don karɓar jakar hannunsa, wadda yake zuba kuɗin sadaqa ya fita da ita. Baffan ya dube shi yace,"ba fita zaka yi ba?". "fitar ba wata mai muhimmanci bace". Ya faɗa yana ƙara miƙa hannu don amsar jakar. Baffan ya miƙa masa, shi kuma yana masa sannu tare da adu'ar Allah ya bada lada a irin ayyukan alkhairan da yake yi. Tare suka jera su na tafiya, su na entrance na shiga parlo Baffa yace da Khalil. "Muhammadu ya dawo ne?". "a'a bai dawo ba". "amma ɗazu sai naga motarsa". "ai dama ba da ita ya tafi ba, da GLK ya tafi". Baffa bai ce komai ba ya shiga katafaren parlonsa bayan Khalil ya buɗe masa ƙofa. Hajiya Madina coming down from stairs take welcoming nasa. Khalil ya miƙa mata jakar hannunsa tace ya wuce ya kai bedroom ɗin Baffa. Tana gyara dining area ta ke cewa Baffa, "yau ka dawo da wuri, hala ba'a taru ba yanda aka saba". "ba haka bane, jikina nake jinsa babu daɗi". "subhanallahi". Ta faɗa tana saurin barin abinda ta ke yi ta dawo kusa da shi ta zauna. Tana taɓa jikinsa looking worried tace,"i hope ba ciwonka ne zai tashi ba". Tai maganar tana ɓalle maɓallin gaban rigarsa. Sannan ta miƙe tana cewa,"let me reduce the AC". Kayan breakfast ta ɗauko ta dawo da shi gabansa ta aje saman wani medium glass table. His favorite dish kunun gyaɗa da awaran ƙwai, da kanta ta ke feeding nasa tana jera masa sannu, bayan ya gama ta ba shi drugs sannan ta buƙaci da ya tashi ya koma bedroom yace a'a ta barshi nan. Ƙasa ya sauko ya zauna kan tattausan carpet ɗin da ke malale, haɗuwar parlon da tsaruwarsa kace turakar sarki, ya kishingiɗa da tum tum ɗin da ke gefensa, in a state of misery yace. "ban san me ya riƙe yaron nan ba". Yay maganar yana sosa gashin gemunsa. Hajiya Madina ta sauke nunfashi kamin tace,"yace yana hanya ai...ka kwantar da hankalinka please ba wani abun damuwa ba ne. Duk yanda akai aiki ne yayi masa yawa". "to Allah yasa". Ya faɗa fuskarsa na nuni da damuwar da ke ransa, na rashin dawowar Turaki gida tun a ranar da ya dawo ya kirasa ya sanar masa ya dawo gida yana da buƙatar ganinsa. Suka ci gaba da magana akan rayuwa, a haka har ya fara samun relief na ciwon kan da ya fara gallabansa ɗazu. yay nisa yace,"yaran nan ba su tashi ba ne?". Hajiya Madina tace,"what is the time now?". Ta faɗa tana duban agogo tukunna ta ƙara cewa,"masu baccin dama Zaytuna da Nihal ne, Samha ta tashi yanzu...itama tana tunanin baka shigo ba ne thats why baka ganta ba, tunda time ɗin dawowanka bai yi ba". Yay murmushin manyace yace,"da asuba da naje gaida Boɗejo ina jinta ita da Zaytuna". Ya ƙarasa maganar yana ƴar ƙaramar dariya, yayinda Hajiya Madinan ke taya shi dan lamari indai aka ambaci Boɗejo a ciki to za'a dara. fararan haƙoransa a waje yake faɗa mata cewar,"da asubar nan fa ko lazimi bata gama ba take mitan Allah kaimu safiya ta bar gidan ita ba zata iya da gorin da ake yi mata ba". Hajiya Madina ma tayi dariya sosai, lokacin kuma hankalinsu ya karkata kan yaransu da ke shigowa parlon bakunansu ɗauke da sallama. Shigar jikinsu kaɗai zata shaida maka ƴaƴan wani ƙusan ne, ballanta azo ga kallon fatar jiki da zata tabbatar maka da hutu, jin daɗi da gata ya zauna. Baffa ne ke amsa sallamar tasu yana miƙewa zaune daga kishingiɗar da yay ajikin tumtum. Samha, Zaytuna da Nihal suka zube a gabansa, cike da tsantsar girmama da ladabi suka gaishe shi cikin taushin murya. ba sai an faɗa ba, irin zaman ma da su kai a gabansa shi zai baka tabbacin an gina tarbiyarsu bisa bigere na addini, duk da Judge Dikko ɗan boko ne hakan bai sa yay watsi da koyarwar addini da al'ada ta fulani ba ya ɗauki ɗabi'ar bature ya gina iyalinsa akai. Idanuwansa na bin kowacce da kallon so da ƙauna da ke tsakanin uba da ɗansa yake amsa musu cikin farin ciki da annashuwa. Adu'a yake jero musu iya adu'a su kuma su na amsawa da amin, Zaytuna wadda ke da idon hawaye tuni idanuwanta suka ciko da ƙwalla, haka ma muryarta tayi rauni wajen amsa albarkar da mahaifinsu ke saka musu. Da yake shi mutum ne me barkwanci a cikin iyalinsa ya kalla Nihal cike da zolaya yace,"Auta ya naga kinyi fari har kinfi Boɗejo, saura ƙiris ki koma Zabiya". Babu shiri Nihal tayi dariyar da duka haƙoranta suka bayyana a waje tana rufe bakinta da hannu. Baffa ya ƙara cewa,"ki sammawa Mamanki abinda kike shafawa ko ta ƙara yin kyau ta koma ƴan mata". Yay maganar cike da barkwanci. bata bar dariya ba tace,"Baffa ni babu abin da nake shafawa tsabagen hutu ne kawai". Yay murmushi, Hajiya Madina tace,"yo Allah na tuba ni wa zai ganni ma yace na ajiye maka waɗannan yaran...ni jikina ma ai yafi na wata budurwar, man bature kuwa ai sai dai mu barwa wasu danmu da namu farin Allah ya halitto mu". a cikin amon yanda tayi maganar zaka tsinci tsagoron kishi duk da cewar maganar anyita ne for raha becouse of ayi dariya. "Zaytuna naga hannun naki". Hajiya Madina tace tana duban inda Zaytuna ke zaune, gefen mahaifinta tamkar zata shige cikinsa. ta taso ta dawo kusa da ita tana nuna ma ta hannun. "ya fara sauƙi ai...da zafi har yanzu?". "ehh Maama yana zafi". "sannu, did you take your drugs?". Tace,"ehhh". "To Allah ya sauƙe". Baffa yace,"to wai ba za'a nemo wata ƴar aikin bane?, kuma ke har kina shirmen me da kika bari ruwan zafi ya taɓa ki". Hajiya Madina tace,"tsautsayi dai da ba ya wuce ranarsa, ita kasan kamar inji ba son zama take yi ba tai aiki ba ko masu aikin su na nan...amma idan yau Jamilar bata dawo ba sai nayi magana da Yami ta samo wata, ai dama sati ɗaya Jamilar tace zata yi". Sahma tace,"ai Maama a nemi wata kawai, dan bana tunanin Jamila zata dawo, naji Sha'awanatu na cewa kamar aurenta za'ai". "ai da hakanne zata faɗa, ko ta kira waya ta sanar". Baffa na riƙe da hannun Zaytuna yake cewa da ita,"please Babyn Baffa a daina shiga kitchen kinji, bana so wani abu ya dinga taɓa min lafiyarku". Sameer da suka shigo shi da Khalil yace,"to wai a yanke hannun mana". Zaytun tayi masa wani kallo tace,"sai kazo ka yanke ai". yace,"kar ki bari a barmu daga ni sai ke a gidan nan kiga aiki da cikawa". Baffa with full of smile on his face yace,"ƙyale shi haushi yake ji hannunki yafi na budurwarsa kyau, kuma nan gani nan bari...". tun bai ƙarasa ba Samha da Nihal da ita Zaytunan suka ƙarashe faɗin,"ɗumamen mayya ba". su kai maganar su na dariya. Sun ɗau tsawon lokaci su na hira kafin yaran su tashi su tafi, su na fita Baffa ya kamo hannun matarsa yana cewa,"haba ƴar shawalwalata ɓata fuskan kuma na menene?". Bai jira me zata ce ba yaci gaba,"kema dai ai kin san waɗannan idanun tsufan nawa kallon jaririya ma suke miki ba budurwa ba, me za'ai da wata ƴan mata ina da ke ƴar shila, kin fa riga kin rufe ƙofar tuntuni, to mene kuma wani batu zai sa ki ɓata fuska ummm Babyn Baby, please saki ran karki ɓatan kwalliyan da akayi mani nake kallo ina jin daɗi". ya ƙarasa maganar yana shafo fuskarta ita kuma tana ƙoƙarin danne murmushin jin daɗin da ke neman suɓuce mata, yanda yake yi mata kamar ƙaramar wata yarinya, har sai da yayi nasarar sakata yin murmushin da ya haɗe da dariya. "yauwa ko ke fa gimbiyata, sarauniya a fadar zuciyata, ina sonki fa, ina sonki da yawa wallahi...kai Allah dai ya ƙara miki kyau". Ya faɗa yana kamo dogon hancinta. sai kuma ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa,"wai yaushe zamu ƙara tafiya honey moon ne?". Hajiya Madina tace,"da gaske fa nayi zaton ko ka ƙyalla ka gano wata ƴar baturiyar ne". Yace,"waa nii rufani ki saya, at this age ace idona bai daina gane gane ba, ke ɗaya kin ishe ni. Soyayyarmu bata tsufa ba balle ta mutu". Yana nuna idanuwansa yace,"ai wannan idanuwan babu abunda suke gani sai ke, ke ɗaya tallin tal Aina'u ta Habibullahi". "to yanzu tashi mu koma ɗaki ka samu ka rama baccin asuba da baka koma ba...nima na samu na tafi guest parlo kasan yau ranar amsar kukan mata ne". Suka miƙe tsaye tare yana faɗin,"ai nayi zaton idan munje ɗakin soyayya zamu sha". tayi murmushi ta kama hannunsa. "to kai dai muje mana Your Excellency". Da haka suka haura stairs. **** "ni kuwa na godewa Allah, wai ko Allah Fillo ba za ki daina wannan kukan alluran haka ba". Kaka ce ke maganar tana daga cikin ɗaki tana gyara, dan yau tun before 7 ta tafi kai Fillo asibiti, dalilin ma da ya sa suka dawo da wuri saboda Amir ne ya kaisu, a can asibiti suka tarar da shi da wuri yaje ya kama musu layi, tun daren jiya ya kasa zaune ya kasa kwance saboda yanayin yanda ya tafi ya barta da jikinta. tun wancan ranar da Fillo ta ƙona asirin nan shikenan ta kwanta ciwo, har sati guda tana kwance jiki sai dai yay ta tsamari ba sauƙi. Sai ma yau ɗin da ta ɗanji daɗi. A yau ɗin ne Kaka ta ƙara ƙudurtar cewar Fillo bata da wani miji a wannan duniyar sai Amir, saboda samun namiji a wannan zamanin kamarsa babu shi, yau ta daɗa yabawa da hankalinsa, yana da duk wasu good qualities da ake buƙata a wurin ɗa namiji, ga uwa uba ilimin addini. ko sisinta bata kashe ba shi ya biya komai da akai bill, duk da ba kuɗi ne da shi ba, amma akwai zuciyar nema da kuma kyauta, babu yanda ba tayi ba akan ya karɓa ya ƙara amma yaƙi. dai-dai da ruwan sha wannan sai da ya siya mata na Faro da suka dawo, da kayan marmarinsa iya koƙarinsa. tana lure da shi banda tayi masa da gaske a ɗazun bai so tafiya ba. Fillo dai kukanta ta ke rerawa da ƙarfin sauti ba kaɗan ba, da Kaka ta gaji da halinta tayi mata banza. Har ta gama duk abinda take Fillo dai bata daina kuka ba, kukan da bana komai ba ne sai na allurar da akayi mata. allurar da taja akaita fushi da masoyin da ake ji da shi, dan har Amir ya ƙaraci zamansa a parlon nan ya tafi bata ko saurari duk kalar lallashin da yake yi mata ba. "kinga yau burabusko akayi...Allah sarki su Yami sun sha aiki". Maganar Kaka keyi tana ɗiban burabuskon a cikin kwano ta saka a baki. ta kalli Fillo tace,"tunda kina sonsa daure ki tashi kici". Fillo taja majinar hancinta tana ƙoƙarin tsaida kukan da takeyi tace,"miyar mene?". Kaka tace,"miyar ganye ce, kuma yayi daɗi sosai". Fillo ta koma ta kwanta,"ki aje min zanci anjima". ta faɗa sannan taci gaba da kukan kamar ƙanƙanuwar yarinya. "Allah ya shirya min ke...ni banga wani hankali a tare da ke ba da Amir ya gani ya nace miki". "ni daga yau ai babu ni babu shi, can yaje ya nemi wata ba dai ni Haliman Ammi ba, dan ba zanje gidan da za'a kassara rayuwata ba". Kaka ta taɓe baki,"to dama Fillo wa ya ɗauko shi ya kawo miki. Ke kika yayibo abinki". Kaka na sauraron radio akai sallama daga bakin ƙofa, ta amsa tana cewa a shigo. Zaytuna ta ɗaga labulen ɗakin da ya sha jiki ta shiga ta ƙara yin sallama. "jaɓɓama lale". Kaka ta faɗa a sanda ta ke bin Zaytuna da ido da rashin gane wacece. Ita kuma ta nemi wuri zata zauna a ƙasa Kakan tace,"ah haba dai ga darduma yi haƙuri ki shimfiɗa hannuna da maiƙo". Zaytuna ta karɓi darduman ta shimfiɗa ta zauna akai. Kaka tace,"sai dai ban gane wacece ba wallahi". Tai maganar fuskarta ɗauke da fara'a, tana so kuma ta gano a inda ta san kamannin da ke fuskar. "ehh ba lallai ki shaidani ba gaskiya. Daga cikin gida dai nake". Kaka ta washe baki tace,"ƙwarai kuwa ga kamannin Alhaji nan...sannu da zuwa, baƙuwar tamu ashe babbace...bari na kawo miki ruwa". Ta miƙe Zaytuna tace,"a'a wallah Inna ki barshi ai yanzu zan wuce". Kaka tace,"ai ko ba za ki sha ba saina kawo". Ta faɗa tana nufar inda kwandon wanke-wankensu yake ta ɗauko farantin roba, Allah ya taimaka akwai purewater wanda Amir ya siyo musu ɗazu mai sanyi kuwa, ta sako guda biyu ta ajiye agaban Zaytuna su na daɗa gaisawa. Zaytuna bata da niyyar shan ruwan saboda a ƙoshe ta ke, amma gudun kar Kaka taji babu daɗi dole ta ɗauka tasha, tasan tsohuwar zata iya ganin kamar ko ƙyanƙyami ne ya hanata sha. balle ita bata ma ga rashin tsabta a wajen ba, komai fes-fes wajen ɗal-ɗal an share, shi kansa ɗakin sai ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke yake, duk idon da ya ga wajen dai ba zai ce wurin ƙazamai bane. Ɓangaren masu aikin a haɗe yake, amma kuma kowa da gefen da yake. kan Kaka a ƙasa tace,"ranki ya daɗe Allah sa dai ba wata matsala bace". Zaytun tace,"a'a Inna lafiya lau, kawai dai na shigo ɓangaren naku ne ina gaidaku". "Allah sarki aikuwa mun gode". Zaytun ta miƙawa Kaka farar leda mai kauri irin ta store tace,"ga wannan, atamfofin marasa ɗinkin naki ne...akwai doguwar riga guda biyu sai a bawa yarinyar, banma san da ita ba ne sai da Maijidda ke gaya min...da yake Maijiddan kawai na sa ni sauran duk sai yanzu nake ganin fuskokinsu". Kaka tace,"Allah sarki, ai Maijidda ita ta jima a gidan nan, su kam ai duk sai daga baya suka zo...itama ta wurin nawa bayan rasuwar mahaifiyarta na ɗaukota". Lokaci ɗaya idon Zaytuna ya kawo ruwa, kewar tata mahaifiyar ya kamata, tayi saurin danne hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata, wannan ciwon da ke manne a zuciyarta ya taɓu. Muryarta so cool tace,"Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu". Kaka ta amsa da amin, ita kuma ta yunƙura ta miƙe, dubu biyu ta ciro a purse ɗin ta ajiyewa Kaka. "gashi ai adu'a wa iyayenmu". Kaka ta zabga godiya ta koma jero adu'oi kala-kala, ita kuma tana ta amsawa da amin cike da jin daɗi. Yayin da taji ƙaunar Kaka ta shiga ranta, dan ita a rayuwa babban abinda zaka yi mata a duk duniya ka burgeta shine kaiwa iyayenta adu'a, tabbas kai mata hakan zata girmamaka kuma zata mutuntaka. Kuma har gaban abadan ba zata taɓa mantawa da kai ba, kuma haka ta dinƙa maka alkhairi kenan. Har ta fita bata lura da Fillo da ke gefe ɗaya a rakuɓe ba, ta nannaɗe jiki da wani mayafin Kaka me kauri saboda sanyin da ta ke ji, fuskar nan tayi jajur tsabar ansha kuka an ƙoshi. ta haɗe rai babu annuri ko kaɗan. ƙememe tana ganin Zaytuna amma taƙi gaisheta kuma har haɗa ido sunyi, tana lura da yanda Kaka ke aikin jefa mata harara amma tayi fuska, shi yasa itama Kaka ɗin taita adu'a a ranta Allah yasa kar Zaytuna lura da ita balle ta bata kunya. Kaka da ta dawo daga rakiya tace da Fillo. "ke dai ki sauya hali dan gidan wani za ki je, kuma wannan halin naki dai ba halin zama uwa ta gari ba ne". Maijidda ta shigo, tayi wajenta tana yi mata dariya tare da tsokanarta akan kukan allura. Bata kulata ba tayi mata shiru, ita kuma ta miƙa mata ƴar ƙaramar waya ƙirar nokia irin ta da can wadda aka fara sakawa sunan rakani kashi, wayar duk ta jeme tasha kyauraye, banda Yami babu ma me iya riƙe wayar. "Amir ne ya kira yace na kawo miki. Wai ya kira ta Kaka a kashe". Kaka tace,"ai ita ta tsinka cajar garin shirmen banzanta". Fillo ta kalli wayar da ke kan cinyarta, sannan ta kalli Maijidda da jajayen idanuwanta da suka sha kuka suka ƙanƙance tace,"kin ɗauke min ita a jikina ko sai na ƙarasa kasheta". Sanin cewar zata aikata Maijidda tayi saurin ɗaukewa tana faɗin,"yanda Yami ke ji da wayar nan kika fasa aini za ki jawa faɗa". [8/8, 19:09] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *7* Acikin ɗan ƙaramin falon nasu, Fillo ce zaune ta takure daga jikin bango, jikinta gaba ɗaya a nannaɗe da babban mayafin da suke rufa da shi saboda sanyin da ta ke ji, kallo ɗaya za kai mata ta baka mugu mugun tausayi saboda yanda ta rame duk da cewar ita ɗin dama asali ba mai ƙiba ba bace, amma kana kallon ramarta a yanzu zaka san ta lalura ce. Fillo cikin tuƙewar wani kukan ta kifa kanta saman gwiwoyin ƙafarta, kukan da ya kusa yin rugu-rugu da zuciyar Amir da ke zaune yana fuskantarta daga ɗan nesa da ita, yana jin zuciyarsa na matsewa da wani irin zafi. Ya ɗauke ƙwayar idonsa daga kanta ya mayar kan magungunan da ya ɓallo a hannunsa, sai kawai ya janyo ledar magungunan kusa da shi ya zuba su a ciki ya ɗaure. Ya sauke numfashi very calmly yace da ita. "ba saboda na takura miki ba, saboda lafiyanki Halima...but kiyi shiru ki bar kukan na zubar kin fasa sha". zatonsa furucinsa zai yi tasirin da zai tsayar da kukan nata, amma sai yaji taci gaba da abunta kamar ba da ita yay maganar ba. Sai ya duƙar da kansa a cikin damuwar da shi kaɗai yasan me yake ji, Allah ma ya sani, da ace yana da iko da har abada Halimatunsa ba zata yi ciwo ba, haka kuma da ace da yanda zai yi ciwon nan ya bar kanta ya dawo kansa tabbas da yayi hakan ko da hakan zai zama ajalinsa, shi dai kawai ya ganta cikin ƙoshin lafiya da walwala. ya ƙara ɗago kansa ya kai kallonsa gareta, ganin har yanzu kamar ba zata daina ba yace da ita,"Halima kin san kuwa irin zafin da nake ji a zuciyata?, ki yiwa girman Allah ki daina wannan kukan wallahi ko kaɗan bana sonsa, yana taɓa zuciyata...indai magani ne nace ba za ki sha ina ce shikenan ko?". Fillo ta ɗago da kanta, idon nan ya ƙara yin loko yayi jawur, jijiyoyin kanta sun fito raɗau kamar idan kasa hannu zaka kamosu waje. Amir ya tsareta da idanu ita kuma tana saka hannu ta goge hawayen, amma da ike ita ɗin me ruwan hawaye ce tana gogewa wani na kuma sakkowa. Ita ɗaya tasan irin azabar da ta ke ji a gaba ɗaya jikinta, ita ɗaya tasan me ta ke gani a cikin barcinta tun daga waccan ranar zuwa yau. cikin muryarta da ta disashe da kuka tace,"ni nace maka waɗannan magungunan naku babu abunda za su yi min. ka daina asarar kuɗinka Amir, kawai a kira Malami yayi min adu'a". Amir dai dubanta yake da mamaki, ita ba aljanu ba amma kusan sati biyu kenan da ta ke ciwon nan ta kafe akan ita dai a kira Malami yay mata karatu, ba maganin asibiti bane maganin ciwon da ke damunta. kuma anyi anyi ta faɗa me ta ke ji tace ita babu komai zazzaɓi ne kawai. Asibiti kuma a duka test ɗin da suka mata sun ce ma babu maleria. Cikin kwantar da murya yace,"insha'Allahu kin daina shan maganin, amma ki bar kukan gaba ɗaya hakan kawai zai sa na kira Malam yay miki adu'a". Ta ɗan kafe shi da ido tana tunani cikin ranta, maganarsa da ta kutso cikin kanta ta katse abunda ta ke tunani. "amma tun da nima kusan Malamin ne nayi maki adu'an ko Halimatu nah?". Kai kawai ta gyaɗa masa, ta sani ɗin in har ba'a kira Amir Babban Malami ba to ba za'a kira shi ƙarami ba, Babansa Malami kai kafatanin gidansu ma, kwatancen gidansu ma idan za'ai gidan malamai ake cewa, kuma kusan shi ya gado mahaifinsa 100% cikin yara 28 da Allah ya ba shi. Ya taso ya matso kusa da ita, ya bar tazaran inches tsakaninsu. "me da me kike ji?". Ya tambayeta yana kai hannunsa ya taɓa goshinta. Sai ta rufe ido tana jan numfashi, so ta ke ta tambaye shi abin da Kaka taƙi amsa ma ta, ta tambaye shi makomar wanda ya ƙona asirin da ba nasa ba, kuma so ta ke ta yi musu bayanin ta ƙona asiri, ko ta samu ta waraka daga wannan masifar da ta jawa kanta. to amma ta ya?, ta ina zata fara?, da wanne irin bayani zata faɗa musu?, wacce fahimta zasu yi ma ta?, shin zama su yarda da ita ne?. Bama zata soma wannan katoɓarar ba, saboda idan Kaka ta fahimceta ba lallai Amir ya fahimta ba, kuma wataƙila idan wani yaji ta ɗaure kanta akan cewar ita ke da niyyar masa asirin. Ita dai ta sa ni ko meke damunta a halin da take ciki yanzu yana da nasaba da ƙona asirin da tayi, ba zata iya tantance irin mummunar halittar da ta ke gani cikin mafarkinta ba, ita tayi hakan bisa tausayi da kuma son taimakawa wanda ake son cutarwa, to amma kuma shikenan daga taimako?. Sai kawai ta rumtse idonta sosai, tabbas ba Muhammad Turaki kaɗai ba da akayi asirin saboda shi, tun daga kan wanda tunanin yin asirin yazo kansa, da mai zuwa ya amso asirin, da masu zuwa suyi aikin asirin, duka sun shiga uku, rubuce yake a tafin hannunta sai taci uwar uban duk wanda yay sanadin shigarta wannan mawuyacin halin. "ya kike jin ciwon kan?". Amir ya tambaya with a look of concern and sympathy. Ta haɗiye abun da ba zata kira shi da yawu ba, sannan ta buɗe ido ta kalle shi. "ina jin kan kamar ba nawa ba, kamar ma ba na mutane ba". Ya sauke numfashi kamin yace,"sannu". ita kuma ta gyaɗa masa kai kawai. Nan Amir ya kama kan nata ya shiga karanto adu'oi yana tofa mata, tsawon mintuna yana yin hakan kamin ya tsaya. Sannan ya miƙe ya ɗauko ruwan faro da yake siyo mata yanzu ya buɗe sabo ya tofa adu'ao aciki ya bata tasha, kana ya rufe ya aje mata sauran a kusa da ita. Fillo ta rufe idonta ta jinginar da kanta ajikin bango, her breathing slows down, abu kamar almara sai taji ciwon kan da ya addabeta tsawon sati biyu ya fara tafiya, har ma tana neman ta rasa shi gaba ɗaya. Hatta wannan nauyin da jikinta yay shima ya fara saki, to 10minutes sai taji komai yayi sauƙi kamar ba ita ba. Maijidda tayi sallama cikin ɗakin daidai da buɗe idon Fillo, ta ajiye ƙwaryar furar tana zama kusa da Fillon. "sannu". Tace da ita kamin ta juya gun Amir tace mishi,"sannu da zaman jinya Amir". Yay murmushi kaɗan sannan yace,"yauwa Kuluwa". Ya faɗa da zola dan bata son sunan, tace,"ni dai daga yau idan ka ƙara kirana da wannan sunan sai na rushe gwamnatin da ka kafa a zuciyar ƙawata". "yaushe kika yi wannan isar?". Yay tambayar yana kallon inda Fillo ta ke, wadda ta samu relief a yanzu, dan har idanuwanta sun yi tangarau, tana kallonsu ne kawai bata cewa komai. Maijidda tace,"ka dai bi a hankali kawai, ita masoyiyar taka ai tasan girman isar da nake da ita". "ah lallai ne mai girma Kuluwa". Suka yi gajeriyar dariya su duka. Amir yace da Fillo,"ya kike ji yanzu?". Idonta akan ledar magungunan da ke can bayansa tace,"idan ka tashi tafiya ka tafi da waccan ledar ka jefar a bola". ya waro ido waje yace,"haka likitan ya karanta mana dama?". ta ɓata rai tace,"koma me ya karanta ni dai a zubar da su kawai, ai naji sauƙin". Maijidda tace,"ai sai ki bari idan Kaka tazo kyayi mata wannan bayanin". Sai kawai Fillo tayi narai-narai da idanuwa, fuskar nan a marairaice tana duban Amir kaɗan tace,"dan Allah Amir...wallah idan Kaka tazo ba zata bari a zubar ba, ni kuma naji sauƙi". Tana yin shiru ya ɗauki ledar ya saka a aljihunsa yana faɗin,"yanda kika ce ranki ya daɗe". Wayarsa tayi ƙara ya ɗauka, ƙaramar waya ce ba wata babba ba, yayi shiru yana sauraron maganar cikin wayar kamin yace,"tom shikenan Bandirawo ina kan hanya insha'Allah". ya ƙara yin shiru for seconds kan yace,"ahh mai jiki da sauƙi, yanzu haka ma ina wurinta". "tom zata ji insha'Allah, mun gode". Ya katse wayar ba tare daya dubi Fillo ba yace,"Bandirawo ne, yana yi miki sannu da jiki". Tace,"ina amsawa". Sannan ya miƙe yana roƙonta akan ta daure taci abinci, gyaɗa kawai tayi, ta yunƙura itama zata miƙe dan yi masa rakiya yace a'a ta koma ta zauna. Zuciyarta na harbawa da soyayyarsa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, cikin sanyayyan muryarta da ciwo yaywa lahani tace,"na gode". Ƙwayar idonsa akanta da tsananin shauƙinta yace,"da me?". Still idonta kan yatsunta tace,"ni dai kawai na gode, Allah ya bada lada". Ya sauke numfashi yace,"amin". Sannan ya nufi ƙofa, ita kuma tana ce masa ya gaida su Inna. Bayan fitarsa Maijidda tace,"ke kam Fillo kin more da mijin aure, Amir mutumin kirki ne, ki ga fa tun da kika kwanta yake sunturi akanki". Fillo dai bata ce mata komai ba, don ita tunaninta ma na wani waje can na daban. Dogon tsakin da Fillo taja na takaici shi yasa Maijidda saurin kallonta da mamaki. "shi kuma tsakin fa?". Fillo tayi shiru tana jin wani ɗaci a cikin ranta, tunda tazo gidan nan bata taɓa shiga ɓangaren masu gida ba, kai hasali ba matar gidan ma bata taɓa ganinta ba balle ƴaƴanta, idan aka cire wadda tazo ranar nan ta kawo musu kwancen kaya, abunda kawai ta san bakin kowa na faɗa shine Uwar ɗakinmu Hajiya Madina. Amma haka kawai ta ke jin bata son mutanen gidan, dan ta ra'ayinta da tuni sun bar aiki sun koma wani wajen to dan Kaka taƙi ne. To dan me yasa ma ba zata ji zaman gidan ya fice akanta ba yanzu?, sanadin fa taimakon ɗansu ta shiga halin da ta shiga. sannan again tana kwance cikin wannan halin sun zo sun ɗauke mata Kaka sun mayar da ita aiki ɓangarensu, aikin da idan ta fita tun safe sai dare zata shigo, ta lura sam bata samun hutu da can ɗin. Akan me ma zuciyarta zata so matar gidan?, tuwo ne a idonta da ta kasa ganin girman tsufan Kaka da har suke loda mata uban aikin da zai gajiyar da ita. Ko da yake in aka ce baka da shi dama shikenan taka ƙararriya ce, talaka dai na ganin rayuwa. "salamu alaikum". Maijidda ce ta amsa sallamar da aka yi daga ƙofar ɗakin, Fillo kuwa a ciki ta amsa, sai bin ƙofar ɗakin da tayi da ido. Wata tsohuwar mata ta leƙo kai cikin ɗakin tana kiran sunan Kaka. Maijidda tace,"ki shigo bata nan". Ta shigo ɗakin tana faɗin,"bata nan?, ina lafiya dai ko?, kwana biyu banga gimlawarta ba acikin ɓangaren nan". "lafiya lau, ta koma cikin gida da aiki ne shiyasa". Maijidda ta bata amsa. Ta ƙara cewa,"Allah sarki shi yasa ashe, ni fa naga kwana biyu bana ganinta a wurin aiki. Kuma da yake ta saba leƙowa a gaisa ko da ba ranar aikinsu ba shi yasa ma nace bari na leƙo naga ko ba lafiya ba". Maijidda ta ƙara cewa,"lafiya lau, idan ta tafi ne bata shigowa sai dare". Matar tace,"to kwa sanar mata na nazo idan ta dawo, kuma kuce ina yi mata barka an samu ci gaba". "to insha'Allahu za'a faɗa mata". Yanzu ma dai Maijidda ce ta amsa, dan Fillo ma babu alamar zata yi magana. Matar har zata fita sai ta dawo tana cewa,"kinga na manta fa ashe Fillo babu lafiya, kusan ni ɗaya ce ban shigo dubata da jiki ba". Ta kalla Fillo da ke kumbure ta haɗe gira duka biyu tace,"ya sauƙin jikin naki Fillo?". Ba don taso amsawa ba tace,"naji sauƙi". tace,"to Allah ya ƙara lafiya...sai anjimaku". Da haka ta fice tana fita Fillo taja uban tsaki tace,"har ga Allah haushin komawar Kaka aiki cikin gida nake, gaba ɗaya an riƙeta da aiki ba'a barinta ta huta. su ko tausayinta ma basa ji, ko ba su da tsohuwa ne oho?, tun fa da ta fara aikin nan idan ta fita da safe bana ƙara ganinta sai wata safen, dan kamin ta shigo nayi bacci, jiya har kusan goma da rabi bata shigo ba...jiya da ta dawo ina ganinta tana miƙa tsabar gajiya, kawai don bana cikin hayyacina ne amma da sai naje gidan nace su sallamemu". Ta gama ƙorafinta cikin masifa, Maijidda dai bata ce ma ta komai ba, sai ma ƙwaryar furar da ta janyo tana sha. ruwan hawaye ya kawo idon Fillo, muryar in breaking tace,"ni ban san ba ko basu ga yanda Kaka ta tsufa ba ne...amma me suka ɗauki kansu?". Maijidda tace,"masu kuɗi mana. kuma dai ba za ki ce su na sahun masu kuɗi marasa kirki ba. za ki so kanki ta wannan ɓangaren in kika faɗi haka...ke dai ki yiwa Kaka adu'a kawai, banda ke sanin kanki ne ba zata juri wannan bautar ba tunda ta tsufa da yawa". Bata ce komai ba, Maijidda ta ƙara cewa,"ga furar kisha da sanyi". "aina kika samu ƙanƙara?". "Yami ta aike ni ɗazu na ganta shi ne na sayo, nasan za ki so". Fillo tayi shiru, idonta na kallon yatsun ƙafarta. "ni dai kici abinci kar naci amanar Amir". "ba zan iya ci ba Maijidda sai Kaka ta dawo". "haka za ki yini da yunwa kenan?". "zanci amma idan ta dawo". "Amma dai kin san sai dare ko?". Fillo tayi shiru, itama Maijiddan bata ƙara ce ma ta komai ba. For a while Fillo Let out a long sigh of despair, duka tafukan hannunta saman fuskarta tana ƙoƙarin danne kukan da ke neman cin ƙarfinta. "Maijidda tsawon yaushe idanuwana zasu ɗauka kamin Dada ta dawo gare su?". tausayin Fillo ya kama Maijidda matuƙa, bata iya cewa komai ba sai hannu da ta saka itama tana goge nata hawayen. **** Sakkowa yake daga stairs a hankali hannunsa riƙe da mug, three quarter ke jikinsa brown colour da white t-shir me coller dark blue. har yanzu ba'a cire masa bandage ɗin goshinsa ba. yana sakkowa parlon direct kitchen ya wuce, ya zuba sugar a cikin tea ɗin, sannan ya fito ya ƙarasa kujera ya zauna. Kaka wadda ya barota a kitchen ta fito da sauri, ta ƙaraso inda yake, da rissinawa ta ke faɗin. "sannu ya yallaɓai". Turaki ya amsa mata yana ɗan runtse ido saboda zafin ciwon dake kafaɗarsa. Kaka ta saka masa pillo daga bayansa sannan ya jingina da kujerar. "sai me kake da buƙata Yallaɓai?". Ƙafafun Kaka a ƙasa lokacin da ta ke tambayar tasa. ya ɗan rufe ido yana jin tausayin tsohuwar a ransa, tukunna ya buɗe yana kallonta ta wutsiyar ido yace,"babu komai, kije ki huta haka don Allah". tace,"to Allah ubangiji ya ƙara maka lafiya, ina bayan kitchen idan da buƙatar wani abu". Tana faɗin hakan ta miƙe zata bar wajen, har tayi tattaki zata nufa kitchen ta fita ta baya sai ya dakatar da ita, tsawon kwanaki shidan da tayi a wurinsa sai jiya ya san sunanta a bakin Maama. "Kaka". ta juyo idanuwanta a ƙasa, tun ranar da ya dawo ta dawo aiki ɓangaren, ita ta ke ta lura da shi da ciwonsa, yana ganin ƙoƙarin tsohuwar sosai, yana jin tausayinta matuƙa a cikin ransa, sai dai bai taɓa jin tausayinta da yawa haka ba sai a yau da yake kallon fuskarta me bayyane da damuwar da ke cikin ranta. kullum zuciyarsa na gaya masa tsohuwar kamar wannan bata samun hutun rayuwa, to ina ƴaƴanta?, waye a ƙarƙashin kulawarta da ta kasa samarwa kanta hutu a wannan shekarun nata?. Sai dai tambayar da ke zuciyarsa yanzu damuwar da ke fuskarta ta mene?, ya ƙara ɗaga ido ya kalleta, tana tsaye har yanzu bata motsa ba, ji yake kamar ya tambayeta menene matsalarta amma sai yaga wannan ba huruminsa ba ne. Saboda haka sai yace,"Kaka tun da yau na sami sauƙi kije kawai ki huta kema". Har yanzu kan Kaka a ƙasa tace,"to yallaɓai". ta faɗa tana sake juyawa ta nufi hanyar kitchen. Kamar bata fahimci me yake son ce mata ba. "Kaka ina nufin ki tafi ki huta sosai". tace,"Yallaɓai ai kar na tafi kuma wata buƙatar ta tashi". Kamin yayi magana sai ga Zaytuna ta shigo, ta wuce inda yake zaune tana kara masa waya a kunnensa, ya maida hankali ga wayar ita kuma tace da Kaka. "ki tafi ɗin kawai babu matsala, zan zauna da shi". da yake taji last conversation ɗinsu kamin shigowanta parlon gaba ɗaya. Kaka tace,"to Zaytuna na gode, Allah ya ƙara masa lafiya. Kya sanar da Hajiyar". "tom shikenan babu matsala". Da hakan Kaka ta bar wajen. daga ɓangaren Bello Ƙaraye da ke magana ta cikin wayar Turaki yace,"all this while ina ka bar wayanka, i have been calling tana ta ringing ba kai picking ba". Zaytuna ta sauke cup ɗin tea daga bakinsa, bayan ya haɗiye tea ɗin da ya kurɓa ya amsawa Bello da cewan,"Maama ce ta ɗauke wayan wai na samu na huta da kiran da ake mani, i though ma tayi switch off nata ashe kunne ta barta". Bello yace,"anyway, how are you feeling now?". Cikin sanyin jiki yace,"Alhamdulillah". Bello yace,"hope kana iya cin abinci yanzu ko?". Yace,"yanzu haka ma am taking tea". Bello ya ƙara cewa,"Good, batun drugs fa?". Yay tambaya cike da concern. Turaki yay ɗan jim yana tuna yanda Maama tayi ta fama da shi akan shan magani ɗazu da safe. jin shirunsa Bello yace,"i know, ba za'a sami matsala da kai ba a ko'ina sai a ɓangaren shan magani...you should have grow up by now gaskiya". Turaki yace,"ka kira ka gaya min magana ne na kashe wayana?". "yo tsakani da Allah ace ka girma amma kana gudun magani da Allura". "ina ce ciwon jikina yake ko?". "ai kuma da yake mun damu da kai...by the way zan shigo cikin satin nan". "Allah ya kawo ka". Bello yace,"ameen, Allah ya ƙara lafiya...and please ka dinga kulawa kaji" Turaki ya amsa mishi,"toh". Sallama Bello yyi masa ya katse wayar, ba'a ɗau lokaci ba Maama ta shigo parlon. [8/8, 19:41] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *8* Idanuwan Turaki da Zaytuna suka ware akan Maama da ta shigo fuska babu yabo babu fallasa, suka bita da kallo har ta zauna kan kujera ta harɗe ƙafafu tana girgiza su. Dukansu suka sauke numfashi mai nauyi dan sun san tunda suka kalla fuskarta a haka to lallai akwai damuwa. "ɗauki wayar nan ki kira min Bello". Muryan Hajiya Madina ta fito da wani irin amon sauti. Zaytuna ta ɗauki wayar Turaki da ke kan cinyarsa, tabi kiran Bello da suka gama waya da Turaki babu jimawa. ta miƙe ta isa ga kujerar da ta ke ta bata wayar, a kiran farko bai picking ba sai ana biyu, shima sai da ya kusa katsewa tukunna. Daga ɓangaren Bello yace,"Turaki ya dai?". Hajiya Madina ta numfasa tace,"Bello ba shi ba ne". Jin muryarta yay saurin gyara zama daga inda yake, ya gyara yanayin muryarsa, cike da ladabi ya gaisheta, ta amsa masa tare da tambayarsa ya aiki, yace mata aiki alhamdulillah. Shiru na ƴan sakanni ya biyo baya, Turaki dai kallonta kawai yake, kiran Bello da tayi na menene?, me zata ce da shi?, to me ya faru ma tukunna?, dan yanayin fuskarta kaɗai yana shaida cewar there most be something behind. "kana jina Bello?". ta faɗa tana yiwa Zaytuna nuni da dining area, inda a lokacin Zaytuna ta miƙe ta isa wurin dining ɗin, ta ɗauki cup ta tsiyaya watermelon juice aciki, ta ajiye jug ɗin sannan ta dawo ta miƙawa Maama. "ina jinki Maama". lemun da ke hannunta ta kurɓa kamin tace da shi,"application for annual leave, ina ce ka miƙa musu ko?". Yace,"ehh Maama na miƙa tun a washe garin ranar da yay accident ɗin". Tace,"good, how many months kasa?". yace,"munyi waya da shi yace na saka just 1 week". ta ɗago ido ta yiwa Turaki wani kallo na ashe baka da hankali, hakan kuma yasa yay saurin sauke idonsa ƙasa, duk da bai san akan mene kallon ba tunda ba jin abin da Bello yace yake ba, amma wannan kallon yasan ba a banza ba. Ta kalla goshinsa da ƙaton plaster ke manne a wajen, sannan ta tsurawa kafaɗarsa ido, tana hasko yanda wajen ke nannaɗe da bandage kwanaki biyar da suka wuce kamin jiya a kwance, ai har yanzu hannunsa na hagu baya moving sosai, amma shine saboda bai da cikakken saiti, yay wannan mummunan accident ɗin sannan yace wai hutun just 7days ya ɗauka, which means monday zai koma aiki. Tayi gajeren tsaki, ta lura Turaki nema yake ya kashe kansa a bautar company kawai, yafi damuwa da aikinsa akan lafiyarsa da rayuwarsa, to ita ba ƴar iskar uwa ba ce. Ko da yake shima Bello ba shi da hankalin ai, yana kallo har kusan fitar da rai su kai da Turaki, basu taɓa zaton zai farka ba saboda mugun ciwukan da ya ji, amma shine har yake biye masa da ɗaukan hutu na kwana bakwai kawai. Daga ɓangaren Bello so yake yay magana amma yana gudun faɗan da zai biyo baya, dan shima sai bayan da ya kai takardar yaga yayi rashin tunani. ta katse tunaninsa da cewan,"then write a resignation letter ka ƙara kaiwa". Turaki da Zaytuna duka a lokaci guda suka ɗago ido su na kallonta da mamaki tsantsa, hatta Bello daga inda yake bai san lokacin da ya miƙe daga zaune ba, yana daɗa tambayarta abunda tace. "ehh resignation letter nace, takardan barin aiki ba, And if you can't tell me sai na saka Khalil ya rubuta ya kai". Bello ya haɗiye wani yawu yace,"amma Maama hakan sai nake ganin will not be the best solution, we should just add him a days more off...idan ya dawo sai a san zaman da za'ai da Manager to let him know what is going on". a fusace tace,"kar ka rubuta ka bari zan rubuta sai na bawa wanda na isa da shi ya kawo, kuma ai dama ban kira na faɗa maka don neman shawaranka bane, umarni nake baka tunanina cewar na isa matsayin mahaifiyar amininka". In calm voice yace,"kiyi haƙuri Maama". Bata ko ba shi amsa ba ta kashe wayar, tana kallon yanda idanuwan Turaki suke kallonta kamar zasu fito waje, amma sai tayi kamar bata san yana yi ba, taci gaba da shafa wayarta har sanda ta nemo lambar Khalil ta kira shi, ringing biyu ya ɗaga. a taƙaice ta amsa sallamarsa ta ɗora da cewa. "You have Bello Ƙaraye's number right?, Anyway if you don't have i will send it to you now, call him and ask abunda na karanta masa, as early as tomorrow morning ka fara aiwatar da abin da nace before you leave to koma ina ne zaka je". Bai tsaya yin wani tambaya ba, haka itama bata jira cewarsa ba ta katse wayar ta ajiyeta gefenta. Ba tare da ta kalli Turaki ba tace,"mun gama magana da Baffa, shima ya amince da hakan, so i do not want to hear anything different... ina ce dama saboda kuɗi kake musu aikin ko?, to mahaifinka ya tara maka arziƙin da har jikokinka ba zasu yi talauci ba, no need of any job, ka zauna a gida kamar mace, kaci ka sha ka kwanta...bautar company ta ƙare, dan ba zan yarda kaci gaba da yi musu aiki ba su na neman hanyar da zasu kashe min kai saboda kawai kana da gaskiya, ba zan lamunta ba...i won't let anyone kill my son come what may!, aikin ai ba dole ba ne, ko da ace bamu da cin yau balle na gobe, rayuwarka da lafiyarka ta fiye min wannan tsinannan company ɗin". Ba shi da ta cewa a yanzu, dole ne zai yi shiru har zuwa sanda zata sakko ta huce before yay Comprehending nata. bai san reason ɗin da ya sa ta ke tunanin accident ɗinsa yana da alaƙa da wasu ke son ganin bayansa ba. "hannun da sauƙi?". Ta tambaye shi tana kallonsa with so much Sympathising na uwa. Ya amsa,"ehh sosai ma". "Allah ya ƙara maka lafiya...tsakanina da wanda ya nemi ya cutar da kai kuma Allah ya isa ban yafe ba, tunda ba wani ya haifa min kai ba". Shi dai bai ce komai ba, ta kalli dining ta kalli Nihal da ta shigo tace,"ki zubo pepper soup". ta wuce dining ta zubo ta kawo mata, ta karɓa sannan ta miƙe ta isa kujerar da Turaki yake, ta kalli mug ɗin da yake aje kan table ɗin gabansa tace,"yaushe kasha wannan?". Yace,"ina gama sha kina shigowa". bata ce komai ba ta ɗebo ppper soup acikin spoon ta kai bakinsa, ba son ci yake ba sam amma babu yanda ya iya haka yay ta karɓa har sai da ya cinye tas, tana tambayarsa ko zai ƙara yay saurin cewa,"a'a". kansa ya kwantar jikin kujerar ya lumshe ido, Hajiya Madina na waya da wani Asp akan Case ɗin accident da Turaki yayi har 2times, cikin idanuwan Turaki kuwa hoton yanda yay accident ɗin ke haska masa, abunda ya ɗaure masa kai, the samething da wancan, ko da yake gwara wancan yaga motar da ke binsa a baya wadda ya tabbatar da attacking nasa ta ke son yi, Amma wannan kam kawai ji yayi burki ya tsinke masa, kuma before he notice anything stearing ya ƙwace daga hannunsa, kamin ganinsa ya ɗauke gaba ɗaya yana tunawa da motarsa ce ɗaya akan titin sai farar motar da ta duki tashi ya ƙarasa gangarawa bakin bishiya, wanda sanadin buguwar kansa da glass kenan kuma sai farkawa yay ya gansa a hospital. Fatansa ɗaya Allah yasa motar da ta buge shi mutanen ciki basu sami matsala ba, saboda ba laifinsu ba ne, shi ne wajen yayi ƙoƙarin kama stearing ya shiga gaban motar ita kuma tayi saurin kaucewa. Amma Maama ta dage kan motar na sa ne ta hankaɗa shi. yamma liƙis Boɗejo ta shigo parlon, babu kowa, tayi tsaki ta nufi hanyar stairs tana mita. Akan wanne dalili ne ma su duka zasu yashe su wani haura sama after all sun san hawa saman wahala yake yi ma ta. Ƙofar bedroom nasa a buɗe yake, daga bakin ƙofar ta tsaya tana kallon ikon Allah, sai kace wani gwal ko tauraro, yana zaune kan gado sun wani baibaye shi, basu san da zuwanta ba sai da ta shiga ta zauna kan stool ɗin da ke fuskantarsa. tace,"wai baka ji sauƙi ba ne har yanzu?, mutum sai kace mace". murmushi yayi bai ce mata komai ba. ta ɗan harare shi tace,"ashe an kwance maka ƙaton rawanin?". Samha tace,"rawani kuma?". tace,"ehh ko za kice min ba haka bane, wadda ba zan faɗi ra'ayina ba sai dai nata". Samha tace,"yo ni wani abu nace Boɗejo, gyara ne fa kawai nake miki...idan wani yaji sai yay zaton rawanin sarauta kike nufi, alhalin ba haka bane...mene haɗin bandage da rawani fisabilillah?". Boɗejo tace,"to banga damar cewa bandage ɗin ba...ina ce ba da ke nake maganata ba". Samha bata ce komai ba, Turaki yace,"wai babu wani maganin da akeyi ne irin wannan ciwon ya warke kusa?". Boɗejo tace,"lokacin da muka sameka a asibiti rai a hannun Allah ban bada shawara ba ne?, kaje ka tambayi ita Madinar, sai da nace a kira Waziri ya saka maka hannu a gocewar ƙashin nan sai ce tayi inaa ita ba haka ba, gwara asibiti suyi hoto su gano matsalar, yo ni kuwa me zan ƙara cewa wanda ya wuce nayi shiru tunda bani na haifa ba". Turaki yay shiru, ta ƙara cewa,"ƙarafun da asibitin suka danneka da su ba suyi tasiri ba ne da kake neman wani magani na daban?". Yace,"sunyi mana, naji sauƙi fa kawai dai ba yanda ya kamata ba...kafaɗar ce bana iya motsata". tace,"ba sauƙin kenan, ni ai sai dai nace Allah baka lafiya, amma ba dai bada shawarar inda ya kamata akai ka a sama maka lafiya ba, ko kuma maganin da zaka sha...tunda ita Madinar ta ɗauki dukkan yardarta ta ɗora akan bature, yo bature ko gaibu". Zaytuna tace,"Boɗejo asibiti ai ba gaibu bane, yama fi saurin taimakawa lalura". Boɗejo tace,"to ko na asibitin ko na gidan duk wanda akayi ni dai fatana Allah ya ba shi lafiya". Sai kuma ta kalli Turaki tace,"yo kai me ka yiwa mutane suke neman rayuwarka?, gaka dai da kyan hali kuma ni ban san dalili ba, Muhammadu ka faɗa min gaskiya ko dai kana aikata wani mugun abun a ɓoye bamu sa ni ba?". Ya ɗago ido ya kalleta zai yi magana Hajiya Madina ta shigo ɗakin, a cikin wayar da ke kare a kunnenta cikin tsawa tace,"just do as i said! thats all, i don't want that your blabaring". ta ƙarasa bedside drower ta zauna tana dire wayar da ta katse a gefen Turaki, tasa hannu ta ɗan matsa kafaɗar Turakin, yay saurin rumtse ido tare da yin,"ashhhh". Ya faɗa cikin dauriyar zafin ciwon da yaji. "still dai?". ta tambaya. Shi kuma ya ɗaga ma ta kai. Hajiya Madina tace da Boɗejo,"babu wani mugun abu da yake aikatawa, gaskiyarsa ce tayi yawa, saboda yaƙi bada haɗin kai akan wani cuta da mutanen da ke son haɗa partnership da company nasu, bcox hakan zai jawa company ɗin asara babba. shine yasa suke so su kashe shi dan samun biyan buƙatarsu". Baki buɗe Boɗejo ke sauraronta, tana yin shiru tace,"yo ina dalili anan, wallahi sai ya bar musu aikinsu babu dole, dama kai ka ɗorawa kanka ba ce akayi dan kayi karatu dole kaci ribarsa ba, an tara an ajiye muku, ba ku kaɗai ba har ƴan gabanku, to mene kuma na cewar sai anyi aiki a ƙarƙashin wani?, ina su waye masu bibiyar rayuwar taka?". "Boɗejo ai zar...". Hajiya Madina ta dakar da shi daga abunda zai ce. tace da Boɗejo,"zasu shigo hannu ne tunda ƴan sanda na kan bincikensu". Boɗejon tace,"dole ma a binciko ko su waye, dan babu wanda zai yi kasadar shiga rayuwar jinin Sarki Sulaiman Dukko bai fuskanci tsatstsauran hukunci ba...ɗan babban alƙali kuma jikan sarki, a nemi aga bayanka sannan a zuba ido, hakan ba mai yiwuwa bane...aiki kuma ka barshi har gaban abadan". Hajiya Madina tace,"abun da nace nima kenan, to matsalar yana jin sauƙi abin da ya faɗawa uban akai za'a zauna". Baɗejo ta muskuta tace,"ina ce ai na isa ko?, to bari Dukkon ya dawo ya sameni...wallahi sai dai idan bana numfashi amma wannan aiki dai ba zaka koma shi ba, can suje su ƙarata da duk irin asaran da zasu yi, ai ma'aikatar bata ubanka bace balle asarar ta shafeka". Hajiya Madina ta jinjina da kai da jin daɗin hukuncin Boɗejon. sai dai jin sabon furucinta shi yay saurin dakatar da ita daga shafa masa magani da ta ke yi. "aure ma zaka yi, ka wartsake kaje ka nemo matar aure ka kawo mana, cikin ƙaramin lokaci ba da daɗewa ba, abun yayi yawa ace kamarka baka da aure, ga mata da yawa nan a dangi, Allah dai ya baka lafiya". Shirun Boɗejon ya haɗe da walƙiyar wani haske a idon Hajiya Madina, hoton abubuwa da dama suka bayyana acikin hasken. Ta san dai tayi ƙasa da idonta, amma bata san lokacin da murfin idonta ya rufe ya buɗe ba, wucewar sakan 1,2,3, wani abu da ita kaɗai ta barwa kanta sa ni ya dira a tsakiyar zuciyarta. Da daddare Baffa yana dawowa Boɗejo ta same shi da kanta a ɓangarensa, tace zuwa tayi ta faɗa masa Muhammadu ya bar zuwa aikin da yake yi acan Habuja, Baffa da yaso yayi ƙoƙarin fahimtar da ita akan hakan ma da ke faruwa da shi hanya ce ta matakin nasara a rayuwa, kuma ai mutanen ba zasu taɓa samun nasara ba tunda Allah na tare da mai gaskiya a ko yaushe. tace ita dai indai ta isa Muhammadu ya daina zuwa aikin can tunda ba aljanna ake rabawa a wurin aikin ba. **** *8:00am.* Fillo na zaune a uwar ɗaki da ƙur'ani a hannunta tana karatun suratul yasin, taji daɗin jikinta sosai tun aduar da Amir yay ma wancan ranar, da ya je gida haka ya jido mata ruwan adu'oi daga wurin mahaifinsa ya kawo mata, ruwan adu'ar da suka zama na shanta yanzu, shi yasa yanzu sumul ƙalau ta ke jinta kamar bata yi wani ciwo ba. ta rufe qur'anin da ta kai ƙarshen sura, ta tashi ta koma kan katifarsu ta kwanta, idonta na kallon rufin ɗakin. tasa hannu tana shafa kusa da ita wurin kwanciyar Kaka, ji kawai tayi ruwan hawaye ya cika idanuwanta ba tare da ta san da zuwansu ba. tun ƙarfe shida da rabi Kakan ta fita aiki cikin gida, ita ba wai fitar sassafen bace ke damunta, tunda a nan ɓangaren ma ƙarfe shida suke fita, to amma ai anan tana ganin gimlawarta da jin muryarta, amma can idan ta tafi sai dare zata ƙara ganinta. Yunƙurawa tayi ta tashi ta nufi jakar kayanta ta zuge zip ɗin, sai kawai ta zubawa kayan ido, bata san wanne zata saka ba dan yau Kaka ta manta bata ɗauko mata wanda zata saka ba. Kamar zata yi kuka ta shiga ɗebo kayan tana fito da su, kayan duk sun tsufa da yawa, kwana biyu Amir bai yi mata ɗinki ba kasancewar ba shi da kuɗi, kullum haƙuri yake bata. Atamfar ta ɗaya ce me kyan gani ta sallah ƙarama da ya ɗinka mata, kuma da so take sai babbar sallah zata kuma sakata. har tayi choosing wata atamfarta leda sai ta tuna da cewar Amir yace zai zo anjima shi da abokinsa. dan haka sai ta ajiyeta ta ɗauko me sabuntar full cotton ta saka. Ɗinkin riga da skirt ne, ya zauna ɗas ajikinta, rigar ta kwanta a shafaffen cikinta, breastcuff ɗinma yay dai-dai da breast ɗinta maidaidaita, ƙafar nan tata ƴar sirit acikin skirt ɗin. kayan ta maida ta ɗauki ɗankwalin ta fita, wurin Maijidda zata je tayi mata ɗauri irin wanda ta taɓa yi mata Amir yay ta santinsa. don ita ba iya ɗaurin ɗankwali tayi ba, tafi gane ta saka hula akanta. Tana fitowa su kai kiciɓis da Kaka ta dawo, da mamaki ta ke kallon Kakan, wadda kana gani kasan cikin ƙarfin hali take. Saurin riƙeta tayi suka shigo ciki, Kaka ta zauna ta riƙe kanta da taji yana sara mata sosai. "sannu Kaka, ni dama tun jiya nake cewa ba kya jin daɗi kika dage min ke lafiya kike". Fillo tayi maganar kukan da ke bakinta na shirin fitowa. Kaka tace,"ni ƙalau nake...ciwon kai ne kawai, kuma ina shan magani zai daina". Cikin sauri Fillo ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauko panadol da ruwan adu'a da take sha ta kawowa Kakan. Kaka ta karɓa tasha sannan ta kwanta ta rufe idonta kamar mai bacci. Fillo dai kallonta kawai take yi, tsoro da fargaba fal ranta, idan mutuwa tayi mata haka ya zata yi?, ina zata kama?, wa zai zama gatanta?, shikenan sai ta dawo ainihin maraniya ta gaske. Hannu tasa ta goge hawayen da ya sakko mata, ta kama hannun Kaka ta riƙe gam. Kusan minti goma Kaka ta farka daga baccin da ya fara ɗaukanta, ta kalli Fillo da ta rafka uban tagumi alamu na nuna hankalinta ma gaba ɗaya baya jikinta. Sau uku ta kira sunanta ba taji ba, sai da ta bubbugi kafaɗarta. "tunanin ne kike?". "kin farka?". Tamyaryoyin suka fito daga baku nan su a tare, Kaka ce ta fara amsa mata da cewar,"ehh na tashi amma yanzu zan koma". Ita kuma tace,"to ki koma dan Allah, ƙila isassan baccin da ba kya samu ne kwana biyu". Kaka dai kallonta ta ke yi, tunanin da inda zata fara yi mata bayani take, kamar da wuya ta yarda taje tayi aikin nan, ba don komai ba ganin a halin da take ciki, sannan babbar damuwarta ma ta ya za'a sami jituwa tsakanin Fillo da su Nihal?. Da ace Zaytuna ce kaɗai to ba zata ji wani fargaban aikata ba. "yau ba'a gama abinci da wuri ba, ko na tambayo miki Yami?". Kaka tace,"a'a naci zuwa anjima...yanzu tashi za kiyi kije kici gaba da aikin dana baro". Fillo ta buɗe baki tana duban Kaka da irin kallon mamaki. murya a kumbure tace,"ba ki da lafiyar ma ba za su yi miki uzuri ba Kaka, ni babu inda zanje na barki ke ɗaya a haka babu lafiya, suyi aikin da kansu ko kuma su nemi wata". Kaka ta kwantar da murya tace,"a'a Halima ba haka za'ai ba, kinga aikin nan ma fa ba wata wuya ne da shi ba, daɗewar ma da kika ga ina yi saboda mara lafiyar gidan ne, hatsari yayi me muni yana buƙatar kulawa, zama kawai za kiyi idan yana da buƙatar wani abu kiyi masa, idan dare yayi Hajiyar ta sami zama shikenan sai ki taso kiyi tahowarki...kina gani fa kula da shi kawai aka ƙara yawan albashina ya koma har dubu ɗari". Fillo ta daɗa ɓata fuska babu alamar zata amince da zuwan tace,"yau ya kula da kansa, gobe naje in Allah ya kaimu". Ta faɗa tana miƙewa ta fita ta wuce ɗakin Yami, babu kowa a falon su, tana ta sallama ba'a amsa ba. ba tayi mamakin jin shirun Yami ba, wataƙila tana can wurin aiki tana lura da masu yi, tun da ita da Kaka ne manya. Maijidda kuwa ta san ba zai wuce ta kaɗa yawonta ba, ta ɗaga labulen zata fito sai ga Yami ta dawo. kular abincin dake hannun Yami ta karɓo ta shigo ma ta da ita, gaisawa suka yi ta ke faɗa mata Kaka bata da lafiya. jin hakan Yami ko zama ba tai ba ta suka fito suka wuce, idanun Kaka na bisa ƙofa suka sameta. Yami tai mata sannu Fillo kuwa ta shige ɗaki dan ma kar Kaka ta ƙara tada maganar zuwanta cikin gida, tayi shiru a ɗakin tana tunanin dake sakata zubar da hawaye, kiran Yami yasa ta fito. Yami ce ta lallamata ta yarda da zuwan, kafin ta wuce sai da ta ƙara komawa ɓangaren Yami tace da Maijidda dan Allah ta kula da Kaka bata lafiya, yanzu zata dawo ba jimawa zata yi ba. A compound ta tsaya ta rasa entrance ɗin da zata nufa, ƙofofi ne suke kallonta na part har guda guɗu, ita bata san ina Kakan ke zuwa ba, ita bama ta taɓa shigowa nan ba, kuma bata ga kowa da zata tambaya ba, kuma ba zata iya zuwa wurin me gadi ta tambaye shi ba. Ta nan tsaye Khalil yazo ya wuceta, fitarsa kenan ya dawo saboda mantuwar da yayi. yafi minti biyar kafin ya kuma fitowa, ya ƙara wuceta. sai da zai shiga mota sannan hankalinsa ya ba shi kamar fa mutum ya gani tsaye har 2 times. [8/9, 19:25] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *9* Khalil ya kalli me gadi daya buɗe masa gate,"waccan fa?". ya tambaye shi yana Indicavit masa Fillo. Me gadin yace,"ehh tou Yallaɓai nima dai bayan fitowata daga banɗaki nan na ganta tsaye, ina ce ma cikin masu aiki". Khalil ya maida kallonsa ga Fillo, ba fuskarta yake kallo ba, side view ɗinta kawai yake iya gani, tsinin hancin nan ya fita ta gefe kamar allura. to ai kaf cikin masu aikin babu fara kamar wannan, infact bama sa gari dukansu, banda tsohuwar da ya gani jiya su Samha suka ce masa ita ke aiki yanzu kamin a sami wasu. to ko dai ba mutum bace?, banda haka ya za'ai bawa yazo cikin rana ya tsaya sama da minti biyar, kuma bai ganta da jakar kaya ba balle yace baƙuwa ce ta shigo, to wannan ƴar ƙauyen ma baƙuwar wa zai ce?, yana da tabbacin ba tasu bace, and cikin yaran gidan babu me yin ƙawance da wannan villager ɗin. ba tare da ya dubi me gadin ba yace,"baka ga lokacin da ta shigo ba ne?". "a'a ranka ya daɗe, bata nan ta shigo ba gaskiya, dan ko second ɗaya banyi da shiga ɗaki na ɗakko radio ba na fito, can kuma ina ɗaga kai na hangeta tsaye a wurin". mamaki ya kama Khalil, ya bar motar a buɗe ya nufi inda ta ke, me gadin ya mara masa baya. taji zuwan mutum wurin, taga kuma inuwarsu a ƙasa inda idonta yake kallo, amma sai tayi kamar bata san da zuwan kowa ba. ai yana kallonta ɗazu yazo ya wuceta yay shigewarsa ciki, ya ƙara fitowa ya wuceta ko sannu kamar bai san darajar ɗan adam ba. To yanzu da ya dawo ya tsaya gabanta me ya dawo da shi ko kuma me zai mata?, tukunna ma shirun da yay bai yi magana ba yana jiran cewarta ne?, ashe kuwa wannan ranar zata ƙare akansu. Shi kam Khalil tsayawa yayi yana ƙare mata kallo da yanda ta ke wasa da yatsun hannunta, yatsunta sirara dogwaye gwanin sha'awa, farcenta fari ƙal da shi. abunda zuciyarsa ta raya masa shine yarinyar kurma ce ko kuma makauniya, tunda ga shi dai ko yanzu da ya tabbatar tasan da tsayuwarsu a gabanta ko motsi bata yi ba, tana nan kamar wadda aka sassaƙa. yanayinta ne kaɗai zai nuna maka ba'a waye ta ke ba, amma kyawun surarta ba zaka taɓa cewa hakan ba. "lafiya dai?". Ya tambaya idonsa tarr akanta. Ta ɗago kyawawan idanuwanta farare ƙal da babu ko kwalli ta ɗan kalle shi, tukunna ta mayar da idonta ƙasa tace,"aiki nazo yi?". Da mamaki yace,"Wanne irin aiki?". Har yanzu idonta na ƙasa ta ba shi amsa da cewa,"ni dai haka aka ce nazo nayi aiki, Kakata ce ke yi, ita kuma yau bata lafiya". Khalil ya gyara tsayuwa tare da cewa,"kuma sai tace miki idan tazo aikin cikin rana ta ke nema ta tsaya?". ta girgiza kai tace,"a'a, ban san inda zan shiga nayi aikin ba ne". yana daɗa ma ta duban tsanaki, a cikin ƴan ƙauyen ma wannan lamba ɗaya ce. yay wani guntun tsaki yace,"shi kuma bakinki wari yake yi da ba za ki iya buɗe shi kiyi tambaya ba?". muryarta tayi sanyi yayin faɗin,"ai banga mutane ba ne". Yay mata wani kallon up and down na ban haushi sannan yace,"shi me gadin da kika gani dodo ne ko?". Fillo na ƙifta idanuwa ta ɗago zata dube shi taga har ya bar wajen, tabi bayan nasa da kallo, saurin tafiya yake amma ba zaka gane hakan ba a lokaci ɗaya. Tana jan yatsunta hannunta tace da me gadin,"Baba ina zan shiga?, ginin ne na gansa da yawa". "ko dan gaba in kika je wuri ki dinga tambaya, ai matambayi baya ɓata". Me gadin ya faɗa yana yi mata nuni da part ɗin Hajiya Madina. Cikin sanyin tafiyarta ta wuce, kawai tsayawa tayi a bakin ƙofar dan bata san ta yanda zata buɗe ba, bata taɓa ganin irin wannan ƙofar ba, inda ma ace handle ne irin wanda ta saba gani sai ta murɗa wataƙila ta buɗe, amma wannan ma ai ba ƙofa bace glass ne kawai. Kusan 2minutes tana tunanin ta yanda zata shiga, sai gani tayi an turo ƙofar daga ciki ta buɗe. ta kalli Sameer wanda ya fito bai lura da ita ba, ya saki ƙofan ta ƙarasa rufe kanta sannan ya fara taka steps zai sauka. Fillo dai kokawa ta kama yi da ƙofar, ta tura ciki taƙi shiga, ta kuma yi ƙoƙarin kama handle ɗin ta janyota nan ma ƙarfinta ya kasa. kamar zata yi kuka ta juya taga saura steps 2 ya ragewa Sameer ya gama sauka. Cikin saurin murya tace da shi. "don Allah kazo ka buɗe min". Ko da ya juyo ya ganta kamar ba zai dawo ba sai kuma ya dawo ɗin, ta wutsiyar ido ya ke kallonta. Maama me ƴan aiki, ko aina ta samo wannan kuma oho. Yasa hannu ya janyo glass ɗin da aka rubuta open daga jikin handle ɗinsa, yay ɗan murmushi saboda yanda yaga Fillo ta kafe hannunsa da ido da alama tana so ta koyi yacce zata buɗe ne saboda gaba. Ya bata hanyar shiga yana ce mata,"ki ke shiga ta back door, in ba haka ba ƙasusuwanki akan wannan ƙofar za su ɓalle". Gyaɗa masa kai kawai tayi tukunna ta shige ciki, ai bama sai ya faɗa mata ba, dan ta gama ayyanawa daga yau ba zata ƙara dawowa ba. Yau ɗin ma saboda bata so Kaka taji babu daɗi ne shi yasa banda haka tuni ta juya, ƙofa sai kace dutsen duniya, ai da taci gaba da gwada ƙarfinta wajen buɗewa kaf ɗinta zata kakkarye. Tana tsaye tana ƙarewa haɗuwar parlon kallo tare da saƙe-saƙe cikin ranta Samha ta fito daga wani room a cikin parlon, ganinta ƙatuwa yasa Fillo saurin durƙusawa tana gaisheta a tunaninta ita ce Hajiya Madina. Murya can ƙasa Samha ta amsa gaisuwatata ba tare da ta ko kalli inda ta ke ba, ta wuce ta zauna kan kujera tana ɗaukan remote ta sauya channel. Wani abu ya tuƙe a wuyan Fillo, kenan haka Hajiyan ke wulaƙanta mata Kaka?. tausayin Kakar ya kamata, cikin ranta tana adu'ar Allah ya horewa Amir dai suyi aurensu ko sa huta da wannan bautar a ƙasan wasu balle a dinga wulaƙanta su. "gadin ƙofa aka saka ki ne?". Samha ta tambayeta bayan wucewar daƙiƙu biyar. Fillo tace,"a'a Hajiya, ban san aikin da zanyi ba ne". Samha ta ɗago ido tana ƙare mata kallo, garin kwashe-kwashen Maama yau kuma me ƙanjamau ta ɗebo musu, halitta babu kyan gani jiki sam babu tsokar arziƙi, kai da gani kasan ba'aci an ƙoshi ba. baki ta taɓe sannan ta ƙara ce mata,"Maama bata karanta miki aikin da za ki ke yi ba?". Sai a sannan Fillo ta ɗago ido tana kallonta, ashe ɗazu kallon tsoro tayi mata, yarinya ce da girman jiki dalilin da yasa tayi zaton matar gidan ce. A hankali tace,"ba'a nuna min ba". ta faɗa tana tura baki gaba. Da hannu Samha tayi mata nuni, ita kuma ta shige sum sum kamar munafuka ta nufi kitchen ɗin, sai faman takure ƙafafuwanta ta ke yi saboda sanyin AC da yay yawa a tiles ɗin, ga shi takalminta ta barsu a can waje. Turaki na tsaye a bakin friedge, ya ɗauko maltina ya buɗe ya tsiyaya a cup, ta tsuguna tana gaishe shi, zaton ta ko me gidan ne, amma bai amsa mata ba kasancewar da earpod a kunnensa duka biyun, har ranta taji babu daɗi, a yau ta ƙara yarda da cewar talaka wulaƙantacce ne indai yana ƙasan me kuɗi. Turaki kam bai ma san da shigowanta ba, ganin ya juyo daga inda yake facing tayi saurin matsawa daga bakin ƙofa ta ba shi hanya, yay ficewarsa still bai lura da ita ba dan hankalinsa ba wajen yake ba. tafi ƙarfin minti biyar a tsaye daga gefe ɗaya, haɗuwa da tsaruwar kitchen ɗin kawai ta ke ƙarewa kallo, ita dai badan-badan ba sai ta rantse gidan ƴan yan kan kai ne nan, ko kuma tace ba'a duniyar take ba gaba ɗaya. Fitowa tayi daga kitchen ɗin dan sanin abunyi, bai zai yiwu Kaka na can kwance ba lafiya ba tazo ta tsaya anan babu aikin fari balle na baƙi. tana fitowa su kai kiciɓis da Hajiya Madina, tana kallonta ta shaida ita ne matar gidan, tayi saurin durƙusawa ƙasa ta gaisheta, Hajiya Madina ta amsa fuskarta da fara'a tana ce mata ta miƙe tsaye. Fillo ta miƙe kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya Madina tasa hannu ta ɗago fuskarta tana mata wani kallo, wani kwarjini yarinyar tayi mata, itama Fillon hakan ta ke a wurinta, shi yasa tun kallon farko bata bari sun ƙara haɗa ido ba. Allah ma ya sa ni Hajiya Madina ta girgiza da ganin yarinyar nan wanda ta rasa dalilin hakan, tsintar kanta tayi da jin wanzuwar sabon yanayi, babu shakka yarinyar zata zamar mata jigon wani abu, ta san da wannan. ta kawar da mamakin a gefe guda, Kafin ta buɗi baki tayi magana Fillo ta rigata. "Kaka Rabi ce ta turo ni na ƙarasa aiki, bata jin daɗin ne yasa ta tafi". Tayi maganar idanuwanta na kan tafin hannun Hajiya Madina da ke tallafe da haɓarta. Hajiya Madina ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tace,"masha'Allahu sannunki, ya sunanki?". "sunana Halima". "sannu Halima, Allah miki albarka...ke jikar Kaka Rabin ce?". Ta ɗaga kanta,"ehh jikarta ce, a wurinta nake da zama". "to sannunki kinji, amma jikin nata ba tsanani yayi can ba ko?". Ruwa ya kawo idon Fillo sanda tace,"ehh na dai baro ta zata yi bacci, tace kanta ke ciwo". Hajiya Madina tace,"to Allah ya bata lafiya...kin ƙarasa aikin?". ta girgiza kanta alamar a'a. "ai yanzu na shigo kuma ban san aikin da zanyi ba". Hajiya Madina ta sauke hannunta daga haɓarta, bata san me yasa zuciyarta ke wani irin zillo ba. ta kalla kujerar da Turaki ke zaune, bai ci komai ba ta sani, kuma ba zai ci girkin kowa ba idan ba nata ba, ƙannensa ma sai an kai ruwa rana yake iya cin abincinsu balle na wata ƴar aiki, ita kuma tana so ta fita cikin gaggawa, su na da meeting na friends ɗinsu da suka saba duk ƙarshen wata. "mu shiga kitchen ɗin". ta faɗawa Fillo. Tayi gaba ita kuma ta bita a baya. tayi mata nuni da wata drower tace,"buɗe ciki ki bani ƙwai guda 10". cikin sauri Fillo ta ɗauko ta kawo mata, ita kuma ta ɓare ledar indomie super pack guda biyu ta jefa acikin ruwan zafi, sannan tasa Fillo ta yanka albasa ta kuma yi greating taruhu. In few minutes Hajiya Madina ta gama soya indomie da ƙwai ta zuba a plate, sannan ta dafa tea da ya ji kayan haɗin Sahaz Special Spices(08024976578) lokaci ɗaya kitchen ɗin ya kaure da ƙamshin spices, Fillo sai shaƙe ƙamshin ta ke yi. Ita dai Fillo na tsaye a gefe tana kallon duk abinda ta ke yi, da kuma bin umarnin duk abinda ta sakata, tana yi mata bayanin abubuwan da zata yi, ba wani aiki ne me wuya ba, Kula da buƙatun Turaki ne kawai. "miƙo min wancan tray ɗin na tsakiyan". Hajiya Madina ta faɗa tana ma Fillo nuni da inda zata ɗauko tray ɗin. ta jere kayan break fast ɗin akai ta bawa Fillo tace ta wuce da shi kan dining. "Hajiya ina ne dining ɗin?". Allah ya taimaketa bata da ƙauyancin faɗin abu, Hajiya Madina tayi murmushi bata ce da ita komai ba. Sai da ta gama wanke hannunta a sink tukunna tace da ita,"muje na nuna miki...in kin kai akwai ɗaki idan kika fita ƙofar kitchen daga baya, sai ki zauna in yana buƙatar wani abu za ki ga kira ya shigo ta wayar ɗakin, landline ce, ɗagawa kawai zaki yi ba sai kin danna wani wuri ba...please kar ki yi delay wajen amsa kiransa, becouse bai da lafiya isashshe". Fillo ta biyota a baya suka fito, tayi mata nuni da dining area ta wuce taje ta aje akai. "if ya gama sai ki kwashe kayan ki wanke...kar ki ce za ki ɗora abinci, ba ya cin abincin kowa sai nawa". Tana faɗa mata hakan tace taje tace masa his breakfast is ready. da faɗin hakan ta haura upastairs cikin sauri. Fillo dai bata gane guntun turancin da Hajiya Madina tayi mata ba, tayi shiru tana nazari da son gano abinda tace ɗin amma ta kasa. Ta ɗaga kai ta kalli inda Turaki ke zaune kan kujera ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, cikin ranta tana mamakin isa da jin kai irin nasa, wato bama iyaka masu aiki yake walaƙantawa ba har da matarsa. komai da take rayawa cikin ranta ya katse lokacin da Zaytuna ta shigo parlon, ƙananun kaya ne a jikinta sunyi mata kyau sose, kamar balarabiya ta watso gashinta ta baya, ta saka head band akan gashin. Wurin Turaki ta wuce tana smiling ɗin da ke fiddo da asalin kyan fuskarta, ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa, ta kamo hannunsa guda ɗaya su kai shaking. "Hamma nah yau ka tashi da wuri haka". yasa yatsa ya lakuce mata hanci,"aka ce miki irinki ne ni, bacci babu sauƙi". Dariya tayi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa tace,"Hamma nah na fa rage, tunda ka dawo ai baka kalla na kai 10am ban tashi ba ko". Idonsa na manne kan news ɗin da ake a aljazeer ya ɗaga mata kai kawai. Conversation ɗin nasu shi ya warwarewa Fillo komai, kenan wannan shi ne Hammansu da Hajiya Madina ke ta faɗa mata ɗazu, ba me gidan ba kamar yanda ta zata. Kenan shine mara lafiyan da Kaka ke bata labari?, ta ƙara kallonsa da kyau tana jinjina wani lamari da ke cikin kanta. tana jin Zaytuna na tambayarsa,"Maama bata sakko ba?". "yes". Ya amsa mata before ya kalleta yace,"wa akai ma kwalliyan?". Ya tambaya da salon zolaya. Ta maƙale hannunsa tana cewa,"kai Hammah nah ni kam wa zanma kwalliya banda kai". leɓensa na talewa da murmushi yace,"ummm to kinyi kyau sosai...kinyi break fast?". Ta gyaɗa masa kai,"tare zamu yi da kai". Ya hurar da iska daga bakinsa,"to ai Maama bata sakko ba har yanzu, ni kuma bana so ki zauna da yunwa. ko muje kitchen ɗin mu dafa tare kinga mun hutar da ita?". ta ɗaga masa kai alamar ehhh, hannunsa na riƙe da nata suka miƙe tare, kai tsaye kitchen suka wuce, su na shiga ƙamshin egg ya shiga hancinsu, idonsu kuma ya kai kan wanke-wanken cikin sink, Zaytuna ta dube shi, shima ita ɗin yake kallo idonsa na haskawa da irin abinda nata ke haskawa. "but yaushe Maama ta sauko har tayi girki ban sa ni ba?". "may be bata san ka shigo ba, ko ka shiga ɗakinta?". "nop, time ɗin da na shigo bata tashi ba ai". Fitowa suka yi daga kitchen ɗin, Zaytuna ce ta kula da Fillo bayan da Turaki ya haye upstairs, ta kalleta da murmushi a fuskarta tace,"sannunki". Da yake Fillo ta shaidata ta duƙa har ƙasa ta gaisheta, Zaytuna ta amsa tana tambayarta lafiya tayi tsaye anan. "Kaka ce bata da lafiya shine na amsheta". "ohh kece jikartata dama?". ta gyaɗa kai,"eh ni ce". Zaytuna ta sakko daga step na farko da ta hau, ta dafa kafaɗar Fillo tana kallon fuskarta, haka kawai taji yarinyar ta burgeta. "sannunki, kina da kyau sosai...amma jikin Kakar da sauƙi ko?". "ehh na dai barta tana bacci". "Allah ya bata lafiya". Zaytuna ta faɗa tare da kai kallonta kan dining ɗin, tana buɗe plate tace,"ke kika girka?". "a'a Hajiya ce, babu jimawa ta hau sama. tana ta yi min bayanin wanda zai ci abincin to ban gane ba ne". Zaytuna na murmushi ta ƙara dafa shoulders ɗinta tace,"na Hammah ne, ba ki lura da shi ba ne a zaune?". Fillo tace,"nayi zaton Alhajin gidan ne". Zaytuna da Nihal wadda ta shigo yanzu taji abinda Fillo tace suka saki dariya tare. "Lallai kuwa Alhajin gidan, yau an maida Hammah tsoho...ke sai kace mara gani sosai ki kasa banbance dattijo da matashi". Nihal ke faɗa. zata hau upstairs ta ke cewa da Zaytuna. "Adda kije Baffa na kiranki". "oak, to kice da Hammah ya sakko ga breakfast ɗin nasa". Nihal ta haye upstairs ita kuma Zaytuna ta fita, suka bar Fillo tsaye a wurin. da jikin bango ta jingina har sanda Hajiya Madina suka sakko ita da Nihal da Turaki, da shirin fitarta ta sakko hakan yasa tayi mata adawo lafiya, babu jimawa Turaki ya dawo daga rakiyan da suka tafi yi mata. yana waya da Bello Ƙaraye ya shigo, ya zauna kan dining ɗin ba tare da ya taɓa abu guda na abincin ba. har sanda ya gama wayar Fillo dai na nan tsaye kamar soja, wasa kawai take da yatsun hannunta, hanakalin na can wurin Kaka, tana ta zullumin wannan bawan da har yanzu bata sami kallon fuskarsa ba ya samu ya sallameta tayi tafiyarta. Turaki na danna waya ya ɗago ido ya kalleta suka haɗa ido, tayi saurin ɗauke nata, shi kuma ya kalli kayan abincin sannan ya ƙara kallonta ta gefen ido. maganar Maama na dawo masa cikin kansa, wai ita tayi helping nata da greating taruhu da yankan albasa, to ta ya ma zai soma cin abicin da wannan yarinyar ta saka hannu?. wani ɓacin rai ya ziyarce shi, ai ko abincin restaurant ba kowanne yake ci ba, balle kuma na wannan abar. yau bai san me ya sami Maama ba, ita da ta ke haƙura da ko menene akan buƙatarsa kawai, amma yau akan wani meeting har tana haɗa dafuwar abincinsa da ƴar aiki. murya a tamke yace da Fillo,"ja kujera ki zauna". Ba dan tasan su biyu ne kawai ba da sai tayi zaton ko da wani yake, tunda babu wata alama da ta nuna da itan yake. kuma duk da hakan dai sai ta tsaya, domin tasan kujerar da yake magana tafi ƙarfin zamanta. Ita duk rayuwarta ma bata taɓa ganin irin kujerun ba ma. kusan 2minutes da maganar tasa ya ƙara ɗago ido yana mata wani duban yatsine, yay saurin kauda kansa a tsawace yace,"do you want me to repeat my self before you sit?". Saurin rufe ido tayi tare da ƙanƙame jikinta, sai rawar jiki ta ke yi kamar me jin sanyi. A rayuwarta ta tsani tsawa, bata sonta ko kaɗan, tsawa na firgitata, tsawa na sakawa ta kusa fita a hayyacinta, tsawa na sakawa ta tuna wani moment da bata son tuno shi a rayuwarta, tsawa na sawa har suma tayi, dalilin da yasa a ko yaushe ta ke guje duk abinda zai sa ayi mata tsawa. tafi minti uku kafin ta dawo normal, da ƙyar ta iya haɗiye yawun bakinta, a hankali ta buɗe ido ta sauke su akansa, irin kallon da yake yi mata gani ta ke kamar zai duke ta...idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta shiga ƙiftasu gudun kar su zubo, ta kama jan yatsun hannunta tana danasanin zuwanta, da wannan abun da yayi mata ai gwara ta yiwa Kaka gardamar ba zata zo ba. ta kalle shi suka haɗa ido, ta yi saurin ɗaukewa tana jin faɗuwar gaba. Muryarsa har cikin kanta ya ƙara cewa,"Do I look like someone who would talk to you and ignore?". Da ƙyar ta iya buɗe ido tana kallon yatsunta, shi wai bai san bata jin wannan yaren ba ne da yake ta ɗaga mata murya da shi. ita bata san ba ma ko abincin ma ba ya ci da kansa sai an ba shi, ƙilan shi yasa yake tayi mata wannan ihun, to ai ba laifinta bane laifin babarsa ne da bata yi mata wannan bayanin ba, kuma ma ya za'ai ace wannan ƙaton ba zai iya cin abinci da kansa ba, banda dai lalacewa. in cool voice da ke rawa tace masa,"kayi haƙuri ka daina ɗaga muryar, ni ban san me kake cewa ba shi yasa, bana jin wannan yaren". Yay ma ta wani uban kallo kafin yace,"na farkon ma ba ki ji ba?". tace,"wanne?". Ya galla mata harara bai ce komai ba, haka kawai taji tana tsoronsa, yanda taga ya jijjiga kai bata san me zai aikata ba, saboda haka hannunta na shaking taja kujeran ta zauna a ɗarare. "na zauna". ta faɗa tana kusan ƙwarewa. ta wutsiyar ido yake kallon hannunta da ke rawa akan plate, yana da tabbacin yarinyar nan bata da isashshiyar lafiya. Muryarsa a kausashe yace,"buɗe abincin kici". ta wani waro ido waje ta kalle shi, cikin sanyin jiki tace,"na ƙoshi". rufe bakinta ya haɗe da wani mugun kallo da ya watso mata, bata san lokacin da ta damƙe plate ɗin abincin ba. Turaki kuwa kallon ƙasusuwan jikinta kawai yake, ina alamar ƙoshi anan?, kamu ɗaya zai yi mata ta ɓalle gaba ɗayanta, idan kuwa yace zai yi mata kallon tsab sai ya ƙirge duka ƙashin jikin nata, kuma a hakan ta ke ikirarin ta ƙoshi. ya karkato kanta murya a ɗage yace,"kin ci abincin nan ko sai na miƙe kinga asalin tsayina?". babu shiri Fillo ta kai hannu cikin plate ɗin zata fara ci, ya dakatar da ita cikin tsawa da cewan,"ɗau spoon". [8/9, 19:47] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *10* wannan tsawar da Turaki ya sakar mata ita tasa ta rikicewa gaba ɗaya, she was completely out of her mind, spoon ɗin da ta ɗauka ya faɗi ƙasa ya bada sautin wata ƙara wadda sai da Turaki yasa hannu ya toshe kunuwansa. haushin hakan yasa shi damƙo hanunta cikin zafin nama, wanda bai san lokacin da yay hakan ba. ɓacin rai ne kawai, jin mugun riƙon da yayi mata sai kawai ta fashe da kuka tana ƙara rumtse idanuwanta da kyau, ta shiga girgiza kanta a hankali cikin zubar hawaye masu zafi. muryarta tayi can ƙasa, amma hakan bai hana lafuzan bakinta shiga kunnansa ba, thats why he focuse attention on something she is saying. "dan Allah kar kiyi mata komai". ya so yaji dukkan abunda tace sai dai hakan ya gagara, sai wanda kawai ya tsinta, kuma daga shi ɗin tayi shiru, bata sake cewa komai ba sai shashsheƙar kuka da ta ke yi. ya ƙura mata ido kawai yana dubanta da kyau da kuma mamakin fitar hayyacin da tayi a lokaci ɗaya, ba sai an faɗa masa ba da ganin yarinyar yasan bata da isashshiyar lafiya. lokacin da ta dawo cikin natsuwarta ta shiga buɗe idanuwanta a hankali ta sauke su akan hannunsa da har yanzu ke riƙe da nata gam. ƙirjinta banda up and down babu abinda yake, idonsa na kan dining table ɗin da alama wani abu yake tunawa, hakan yasa bai san da buɗe idanuwan nata ba sai jin maganarta yayi. "Hannuna". ta faɗa muryarta na fitowa a hankali. ya ɗago ido ya kalli hannunsu da ke haɗe, sai kawai yasha mur sannan ya kalleta yace,"ba ki da hankali da za ki sakarwa mutane cokali yayi wannan uwar ƙarar, kuma kukan na uban mene?". bata ce da shi komai ba tayi shiru, ƙoƙarin ta janye hannunta ta ke amma yaƙi sakinta, ta matse ido kaɗan ta buɗe tare da cewan,"ka matse min fata". sai a lokacin ya ankare ya sakar mata hannu, ta wutsiyar ido ya kalli yanda fatar wurin tayi jawur. ita dai tunda ya sakar mata hannun sai ta kama wajen tana shafawa a hankali saboda zafi, so take ta gama hucewa ta miƙe ta tafi inda tafi kauri, tafiyar da ba zata ƙara dawo da ita nan ba, wannan zuwan nata shine na farko kuma shine na ƙarshe ba za'a kuma wani ba. ta miƙe zata bar kujerar ya ɗaga kai ya kalleta, murya a tamke, fuska a ɗaure yace,"koma ki zauna, in kinga kin tashi a wurin nan to kin cinye wannan ƙazantar taki". ta kalli abincin ta kalle shi, ta ɗan haɗe fuska sannan tace,"Hajiya ce ta girka bani ba ai". yanda muryarta ta kumbura wajen faɗa sai ya zamana kamar da rashin kunya ta faɗa, hakan yasa yay saurin ɗagowa, da miƙewarsa tsaye da kai hannu fuskarta zai mareta duk bai san lokacin da yay ba. banda Allah ya taimaka tayi saurin yin ƙasa da fuskarta da sai ya sharara mata maruka. ya yiwa dining table ɗin wani mugun duka hannunsa na dunƙulewa akai. "saboda nace kici ƙazantarki shine za ki buɗe ba ki kice min Hajiya ce ta girka, what do yo mean by saying that?". ta ƙanƙame jikinta saboda ganin kamar zai saka ma ta hannu, ya hankaɗa kujerar baya ya fito yay tsaye gabanta, tana jin yanda hucin isakar hancinsa ke sauka a jikinta. kallonsa ta ke ta ƙasan ido, zata iya rantsewa wannan mutumin ko me jinnu ko kuma me ƙarancin lafiyar ƙwaƙwalwa. yana shirin kai hannu ya shaƙi wuyanta don ta fassara masa abinda ta ke nufi da maganarta, sai ga Zaytuna ta shigo parlon, tun daga bakin door da ta hangesa tayi saurin ƙarasowa ta riƙe hannunsa tana dubansa a rikice. "matsa baya". tace da Fillo wadda ke duƙe har lokacin, kuma jin hakan yasa tayi saurin matsawa da baya ta raɓe daga bango tana sauke numfashin kamar wacca tayi tseren gudu, zuciyarta cike fal da tsoronsa. Zaytuna ta juya ta ƙara kallonta sannan ta ƙara maido da kallonta kansa. "please Hamma nah sorry". idan da zata zauna zaman lissafi zata iya lissafa wucewar kusan rabin shakara rabon da taga ya shiga cikin wannan mood ɗin, mai sauya shi ya fita daga Turakinsa ya koma wata halittar ta daban. zata faɗa ko aina ne he is very simple Man, abu biyu ne kawai a duniya masu rikiɗar da shi, su saka ya fusata har ya aikata wani mummunan abun ba'a cikin hayyacinsa ba. sai dai mamakin da ta ke ta ya Fillo ta fama masa ciwon da ke zuciyarsa, ko kuma garin ya ta taɓa abunda zai iya aikata kisan kai akansa?. tana kallon Fillo tace,"me kika yi masa?". tana girgiza kanta tace,"ni ban masa komai ba. abinci yace sai na cinye kuma ni na ƙoshi". "an kira shi a waya ne?". "ni ban sa ni ba". Zaytuna tayi shiru, dole cikin biyun abunda ke haddasa masa ƙunci zuci ya faru. tasan ko menene baida alaƙa da mahaifiyarsu tunda Fillo bata san komai ba akai, amma duk yanda akai bisa kuskure ta taɓa Maama, shi kuma ɓangaren da baya ɗauka kenan. idon Fillo na kan Turaki, tsab zata iya lissafa adadin jijiyoyin da suka fito raɗau ajikinsa, tun daga kansa har hannayensa da wuyansa. fahimtar da tayi masa mutum ne shi da ba'a sanya mahaifiyarsa a cikin kowanne lamari saboda muhimmancinta. kuma ita sai a yanzu take ganin rashin kyautarwarta, bai kamata dan yace taci ƙazantarta ba ta buɗi baki tace ai Hajiyarsa ce ta dafa, kenan jagwalgwalon ba nata bane na uwarsa ne, matsayinsa na wanda tasan ya bata shekaru da yawa bai kamaci irin wannan maganar daga gareta ba. ko babu wannan ma yaci ace ta darajarta shi duk da jin kai da ta fahimci yana da shi, tunda ita da Kakarta a ƙarƙashinsu suke rayuwa sama da shekaru biyar, ba'a taɓa haɗasu da mara kyau sunci ba matsayin su na ƴan aiki, haka kuma ba'a basu makwanci mara kyau ba. idan ba zata manta ba me gidan da kansa na shiga ɓangarensu ya gaida tsofaffi, Hajiya Madina ce ma bata taɓa gani amma ta taɓa ji ance ta shiga sau ɗaya. kawai sai tayi ƙasa da idonta tana jan yatsun hannunta, maganar Kaka na dawowa cikin kunnenta na wani lokaci can baya da ta taɓa faɗa mata. "Halima dan Allah ki rage jin kai domin ke ba ɗiyar kowa bace, ki rage zafin zuciya, ki zama me haƙuri, ki zama mai sadda kai ga wanda duk kika san ya shiga ɓacin rai ta sanadiyarki, karki ce ba za ki bada haƙuri ba domin tsugunawa wada ba gajiyawa bane, ka zama me haƙuri ma da iya bada haƙuri wani babban arziƙi ne gare ka...bada haƙuri babu abinda zai rageki da shi sai dai ma ya ƙareki da abubuwa da dama...zai iya sawa aga mutumcinki, zai iya zama silar ɗaga darajarki". Fillo ta rufe ido ta haɗiye wani busashshen yawu, a hankali ta shiga sauke gwiwoyinta har ta kai su ƙasan tiles ɗin. muryarta ta fito da amon rashin jin daɗi tace,"dan Allah kayi haƙuri". hannunsa na cikin na Zaytuna ya damƙe da kyau, ya waigo yana mata wani irin kallo kamin yace,"cinye abincin nan shine zai wanke ki". itama sai ta ɗago ido ta kalle shi,"to idan na cinye zaka haƙura?". "kurma ce ke da ba kiji me nace ba". faɗin hakan yasa ta miƙe ta zauna kan kujerar, har yanzu hannunta bai bar rawa ba ta ɗauki spoon ta fara tura abincin bisa dole. kuma har lokacin su na tsaye shida Zaytuna idanunsu duk akanta, daga yanda ta ke ci yasan cin dole kawai takeyi, sai dai shi babu ruwansa ko zata amayar sai ta cinye. sai da tacinye tass tukunna ta ɗago da kanta ta kalle shi idonta na zubar da hawaye, yay saurin rumtse idonsa yana kauda kai gefe, idan da abinda ba ya son gani a rayuwarsa shine hawayen mace. yana jin zata miƙe ba tare da ya kalleta ba yace,"wa zai shanye miki tea ɗin?". jin hakan yasa tasa hannu ta ƙara goge wani hawayen, sannan ta kalli Zaytuna tace,"Anty na ƙoshi idan na kuma cin wani abu amai zanyi". Zaytuna tace da shi,"Hammah ai mata afuwa". ya wurgawa Zaytuna wani kallo sannan yace da Fillo,"kin zuba kinsha ko sai na barki da Allah akan zagar min Uwata da kika yi". tayi saurin girgiza masa kai. yace,"to zuba rabin kofi ki shanye". tana zuba tea ɗin tana hawaye haka ma har ta shanye bata bar kuka ba. sai a sannan yay ƙasa da murya yace,"aikin da aka kawoki shi kawai za ki dinga yi, duk ranar da kika ƙara gigin saka hannu a abinda zanci sai kin cinye shi ta hanci". yana faɗar hakan ya bar wurin, yana fiddo waya daga aljihunsa yay picking call ɗin Bello Ƙaraye. a bakin ƙofar parlo ya tsaya yana cewa,"bana part ɗina ina part ɗin Maama". da faɗin hakan ya katse wayar ya maida aljihu sannan ya nufi kujera ya zauna. Zaytuna ta wuce upstairs bayan tace da Fillo idan baƙo ya shigo ta kai masa ruwa da lemu. ta amsa da tou, sannan ta miƙe ta kwashe kwanukan abincin da aka tursasa mata ci ta kai su kitchen, ta dawo ta gyara wurin ta goge ya zama fess sai ƙyalli glass ɗin yake. a kitchen ma kusan duk wani abu da ake cin abinci a cikinsa sai da ta fito da shi ta wanke, wannan koyarwa Kaka ce gareta, kwanukansu kullum sai sun wanke su ba iyaka wanda suka ci abinci ba kaɗai. a hankali ta ke yin komai gudun kar ta fasa wani abun tunda komai tangaran ne. bayan ta gama gyara kitchen ɗin ta fito ta hau upstairs ta tambayi Zaytuna aina zata ɗauki lemun. Zaytuna tace,"ki buɗe friedge za ki gansu aciki, amma karki manta ki haɗa da cup". ta amsa da,"to Anty". sannann ta sakko ta koma kitchen ɗin, sai da ƙyar ta iya buɗe friedge ɗin saboda bata san yanda ake buɗe shi ba. drinks ne kala-kala aciki da ruwa na jarka, ta san dai ruwan amma lemun idan aka cire fanta bata taɓa ganin duk sauran ba musamman five alive na kwali. kawai sai ta ɗauka ƙaramin tray ta saka kowanne guda ɗaya tare da faro guda biyu. lokacin da ta iso wurinsu Turaki ya sauke hannun rigarsa na dama yana nunawa Bello yanda ciwon wurin yayi, babu wanda yasan da zuwanta wurin balle tsayuwar da tayi tana bin ciwon nasa da kallo ganin yacca yay rami, ita bata taɓa ganin ma irin ciwon da yay haka ba. cikin kaɗuwar ganin ciwon ta sauke idonta ƙasa kawai tayi tsaye a wurin, tafi ƙarfin minti uku kamin Bello ya ankare da ita yace,"bismillah mana". ya faɗa yana kallonta. ta ƙaraso ta aje tray ɗin saman table ɗin da ke tsakiya, sannan ta tsuguna ta gaida Bello cike da ladabi shima kuma ya amsa mata da fara'a. tana durƙushe Zaytuna ta iso itama hannunta ɗauke da bowls guda biyu, duka snacks ne aciki.l ta aje kusa da tray ɗin. idonta na kallon Bello tace,"Hammah Bello ina kwana". shima nasa na kanta yace,"lafiya lau Zaytun, ya kike ya hutu kuma?". ta amsa mishi da,"lafiya lau wallahi, ya office?". ya amsa da,"office babu daɗi, aminina ya gudu ya barni ni ɗaya". Turaki yace da shi,"sai ka jira Maaman ta dawo tunda ƙorafi ya kawo ka gidan". Bello yay murmushi bai ce da shi komai ba suka shiga taɓa hira shi da Zaytuna. idon Turaki ya kai kan Fillo da ke durƙushe a wurin har yanzu, wani haushi ya kama shi, tunda ake ƴan aiki a gidan nan ba'a taɓa bagidajiyar yarinya irin wannan ba, shi bai san ba ma ko hankali ne bata da shi kwata-kwata. "ke sai ance ki tashi ki tafi sannan za ki gurgura ƙafafunki ki tafi, ko kuwa kin zauna jin hirar da ba taki ba?". kanta a ƙasa yake, kuma hankalinta ba'a garesu yake ba dan hirar da suke ma bata ji, banda yanzu da maganar tasa ta shigeta, tasan da ita yake, ba tare da ta ɗago ba tace,"ina jira a bani umarnin tafiya ne". rai ɓace yace,"kiyi ta zama har a busa ƙaho". ile kuwa yaga ko motsawa bata yi ba, wani sabon haushi ya turnuƙe shi, duk yanda akai ko aji bata taɓa shiga ba. Fillo dai cikin ranta faɗi ta ke yi akan me zaisa ta tashi ba'ace taje ba salon ace tayi ba dai-dai ba, bata manta da wani lokaci ba lokacin da suka zauna a masarauta, Fulani ta bada aike a kaiwa Yarima Mansur, ita Kaka ta bawa ta kai, ta sameshi a wanjen shaƙatawa shi da abokinsa, data ajiye musu zata tafi ai cikin tsawa ya maido da ita da cewar uban wa ya bata izinin tafiya, akan haka har kusan horar da ita akayi, to dan dai Kaka na da matsayi ne a wurin Fulani. to ita kuwa yanzu me zai sa ta kuma maimaitawa, ai jini ba wasa bane, shi da Yarima Mansur duk abu guda ne, balle shi wannan ɗin da ta ke ganin yana da girman izza. "tashi kije kinji, ki zauna ɗakin baya inda abin buƙata za'a kiraki a waya". Zaytuna ta faɗa tana dubanta. Fillo ta tashi cikin sanyin jiki ta wuce, Zaytuna ma ta fita daga part ɗin zuwa nasu. Bello yana kallon Turaki yace,"Beb ɗin da ta tashi tana da hankali, itama ƴar'uwarku ce?". Turaki yay masa wani kallo,"me yasa baka da hankali ne Bello?". Bello yace,"tambaya fa nayi". Turaki yaja dogon tsaki yace,"baka iya bambamce ƴan aiki ne kai, ko kaga tayi kama da Baffa ne ko Maama". ganin yanda yasha murr Bello yace,"sorry maida wuƙar, ban zaci maid bace saboda surarta na kalla ba kayan jikinta ba". Turaki ya jefa masa wani banzan kallo,"kana nufin muma a rame muke kamarta?". "thats is not what i mean, kuma itama ai ba rama bace da ita, halittar jikinta ce a haka". ba tare da Turaki ya sake kallonsa ba yace,"wataran sai ka rasa idonka akan kallon mutane". Bello yay dariya sosai, daga haka kuma suka ɗora hirarsu ta abokai tare da ƙara tattaunawa akan batun aikinsa da Maama har yanzu ta dage akan ba zai koma ba. *Dubai, 12:00am.* Nuratu ce a ɗakin zaune kan kujera, gefenta tarin drugus ne sai ɓallo su take yi tana zuba su a hannu. ta miƙe ta ƙarasa friedge ta buɗe ta ɗakko ruwa mara sanyi ta buɗe, sannan ta ƙarasa wurin gado ta zauna a gefe. zuciyarta fal da tausayin matar da suka ɗauko a asobiti suna kulawa da ita, ta kai hannu ta ɗago kan matar daga pillon da take kwance. sai a sannan matar ta buɗe nauyayyun idanuwanta ta zuba su kan Nuratu tare da sakar mata murmushi. "sannu Mommi". Nuratu tace da ita tana sakar mata nata murmushin. kai kawai ta ɗaga mata alamar yauwa. matar da suke kira da Mommi ta buɗe baki Nuratu ta zuba mata maganin, sannan ta kurɓi ruwan da shima Nuratu ta bata, ta haɗa ta haɗiye maganin. lokacin Yusuf ya shigo ɗakin, ya ƙaraso ya zauna akan bedside drower, cike da girmamawa haɗe da ladabi ya gaisheta, yana tambayarta sauƙin jikin. kasancewar bata magana sai da ta amsa musu da kai. Yusuf yace,"Mommi yanzu ina ke miki ciwo?". ya tambaya da tsantsar kulawa, ta kalle shi ta sakar masa murmushi tare da girgiza kai alamar babu komai. ya ɗan lumshe idonsa sannan yace,"masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya". ta jinjina kai alamar ta gode, sannan ta kamo hannunsa ta riƙe cikin nata, tana shaking nasu alamar nuna godiya a gare shi mara iyaka. ya dubi Nuratu yace,"Mar'atussaliha ki shirya Mommi mu fita outing ta samu taga gari, zaman wuri ɗayan zai isheta haka". Nurata tace da shi,"tom ur excellency". har ya miƙe tsaye zai fita kukan da Mommi ta saka ya dakatar da shi, wannan fashewar kukan nata ya haifar musu da tashin hankali. inda ya koma ya zauna shi da Nuratu suna aika mata tambayar me ya faru. sai dai shiru bata ce komai ba illah hawayen dake daɗa sakko mata, kuka biyu takeyi, kukan baƙin ciki da farin ciki. abunda Yusuf da matarsa suke yi mata iyaka abunda Ƴaƴan cikinta zasu yi mata kenan. _su waye su?, aina suka tsintota?, ina ne nan wurin da ta ke sabuwar rayuwa?._ tambayoyin da suke yawo cikin kanta kenan tun daga ranar data farka a asibiti zuwa ranar da suka ɗaukota suka dawo da ita gidansu. so ta ke tasan amsar waɗannan tambayoyin sai dai ba ta da bakin da zata yi magana, haka kuma bata san ta yanda zata gwada musu ba har su fahimceta. tunawa da wani lokaci yasa ta ɗora hannu a kunnuwanta ta toshe. domin tana jin faruwar abunne kamar a yanzu da ta ke zaune. [8/12, 07:57] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *2* "Maijidda na kasa gane wajen". Fullo ta faɗa a sanda ta ke ƙarewa babban filin wurin kallo. Dukkan tunaninta da hasashenta ta ɗora shi a wurin na fiye da daƙiƙa biyar amma sam ta kasa ta fahimci inda akai haƙan ramin. Maijidda na tsaye itama ta ƙarasa bakin kujerun wajen(resting chairs) ta zauna. Ta ajiye digar da ke hannunta sannan itama tabi wajen da kallo cike da nazari da kuma son tunanowa. "wallah Fillo nima na kasa tunawa kin san an kwan biyu...amma wai ajiyar me ki kayi ne a wurin nan?". Fullo bata ce da ita komai ba, sai baki da ta zumɓura mata ta harareta kaɗan. ta zauna bakin tudun da ke wajen tare da naɗe ƙafafunta, kamar wadda ta shiga ajin makarantar allo. Yatsanta manuniya akan leɓanta na ƙasa tana ƙarewa faɗin wajen kallo, da kuma tsirran ciyayin da suka firfito a ƙasar wajen. Cikin zuciyarta tana ayyana ya za'ai ta manta wajen nan, bayan tasan tsawon watanni biyar da aka ɗauko bata ko zo wurin ba, hoton gun na haska mata acikin idonta a duk san da ta tuno, abu ne da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba amma ta kasa mantawa da shi a cikin ranta. Ita dai ta san ta kuɗuri aniyar tarwatsa alƙadarin waɗanda su kai aikin dama wanda ya saka su. Abunda ta ke son sani a yanzu shi ne waima waye Muhammad Turaki?, mene alaƙarsa da waɗanda suke neman ganin bayansa?, wanene shi a cikin gidan nan?, me yasa tsawon shekaru takwas da ta ɗauka tana rayuwa a cikin gidan nan bata taɓa ganin ko da gimlawar inuwarsa ce ba sai yau?, me yasa bata taɓa jin zancensa ba a inda ya dace a dinga ambatonsa?, me ya yiwa masu son kassara rayuwarsa?. Bata da dukkan amsar waɗannan tambayoyin, sai kawai ta lumshe ido tare da hura iska a bakinta kamin ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya. Bata manta da abunda ya faru ba a wajen, tsawon watanni biyar da suka wuce. Komai yana nan daki-daki a cikin kanta, fuskokin mutanen da su kai aikin ne kawai ba zata iya shaidawa ba, dan a lokacin bayansu da kayan jikinsu kawai ta gani kamar yanda taga Muhammad Turaki a yau, amma ko muryarsu taji a yanzu zata nuna su ta rantse da Allah cewar su ne. MUHAMMAD TURAKI, harufan sunan da manyan baƙi suka ƙara haskawa cikin idonta, sunan da yake a jikin wannan farar takardar da babu zanen komai acikinta sai na sunansa da jan fenti. Sunan da ta kasa karantawa a randa tayi arangama da layar, kuma haka tayi ta ajiyar takardar har sanda Amir ya shigo cikin rayuwarta, ya fara koya mata karatu har tazo ta iya haɗa harufan a wata takarda ta daban ta maimaita rubutun sunan, sannan ta iya karantawa. Ita dai bata san asiri ba, bata san ya ake yinsa ba, kuma bata san ya yake ba. amma zata iya rantsewa cewar aikin da waɗannan mutanen su kai asiri ne duk da bata ji sun ambaci wani abu da zai haska mata hakan ba, kuma babu tantanma asirin yana da alaƙa da sunan da ke rubuce ajikin wannan farar takardar da aka maida ita laya. Abu guda kawai ta san da shi, shine idan har ta manta wurin da akai haƙan aka binne, to ba zata manta maganganun mutanen ba a lokacin da suke aikinsu. Aikin da suka gudanar a sanda ƙafafu suka ɗauke a cikin wannan babban gidan da ba ya rabo da shiga da fice ako da yaushe, ranar da akai naɗin Yarima Abbas zuwa wani matsayi da bata san wane matsayi bane, taji dai labarin irin rikicin da aka sha akan naɗin a wajen Kaka da Yami. kuma zata iya cewa Allah ya nufeta da zuwa wajen ne saboda ta zama wata hanya ta tarwatsa mugun ƙudurin da ake shirinyi akan wani bawan Allah, tunda tsawon shekarun da ta ɗauka tana rayuwa cikin gidan bata taɓa zuwa wurin ba sai a ranar, lokacin kowa ya watse ana can masarauta ita kuma ta dawo dan ɗaukar ƙwaryar furar da ta dama zata bawa Amir. A lokacin bata san ta ya ma akai ta kai kanta wajen ba. Ita dai kawai ta ganta ne ta ɓullo ta cikin lambu, ta durƙusa ta ƙasan bishiyan ayaban ta fito, kuma tana fitowa ne taci karo da wasu mutane su uku su na kalle kalle dan tabbatar da babu kowa a wurin da alama basu da gaskiya. Bata kawo komai a ranta ba ta ɗau hanyar zata fito ta bar wajen sai kawai taji namijin cikinsu na cewa. _"nan wajen ne, tace daidai inda tafukan ƙafarsa za su taka kamin ya kai ga shiga cikin lambun"._ _maganar ta fito ne daga bakin bafaden da ke tare da wasu mata su biyu._ _"andai ƙi aji shawarata, amma ni gani nake yafi ace an binne acikin lambun gaban kujerar hutawan da yake zama...amma anan wurin zai iya ma tsallakewa ya wuce"._ _Ɗaya daga cikin matan ta faɗa._ _Ɗayar muryar ta amshe da faɗin,"ni sai da muka zo gudanar da aikinma sannan nake jin zuciyata ta cika da fargabar abin da zai biyo baya, sai nake ganin kamar ba zamu yi nasara ba asirinmu zai tonu"._ _Ɗayar matar da ke tsaye kusa da ita ta wurga mata harara tana faɗin,"to kuwa mugun tunaninki ya ƙare akanki ke ɗaya...wannan ma ai baƙin ciki kike mana, kina jin irin uban kuɗin da Shugaba tayi mana alƙawari amma shi ne kike wannan mugun fatan...mtswww gaskiya ba ki haɗu ba, to ni kam dai akan wannan ɗaruruwan kuɗin da naji babu kasadar da ba zanyi ba"._ _"zafa ki iya samun kuɗin kuma ki kasa jin daɗinsu. Tunda idan aka kama mu bamu da wani mataimaki sai Allah dan ko ita shugaba sanin kanku ba zata waiwayemu ba gudun kar nata asirin ya tonu...ni kam ina tsoro sosai wallahi jikina na bani wani abun zai faru, dan ba lallai muyi nasara ba sai da mu faɗi"._ _A ƙufele ɗayar ta kuma cewa,"to zabiya uwar zancen ai sai kije ki faɗawa Jakadiya ke ba za ki iya wannan aikin ba saboda ga abunda kike gudu...kinga sai ta musanya ki da wadda take ganin za tayi mata aikinta ba tare da ta ji wani ɗar ba...mutum da shegen son kuɗi amma sai uban tsoro"._ _Rufe bakinta kenan Bafaden ya washe haƙoransa da faɗin,"yo ta jewa Jakadiya da wannan zancen ai sai dai wata ba ita ba. Dan tun a wajen zata zama tarihi kamin ma maganar ta kai ga kunnen Shugaba. Da farko da aka kirawo ki aka tambayeki za ki iya ba ki ce ba za ki iya ba sai bayan da kika gama jin sirrinsu saboda rashin hankali. To wa kike tunanin zai barki da rai?"._ _"ni fa ba wani abu nace ba, hankalina ne kawai yau ɗin naji bai kwanta ba. Dan duk randa asirinmu ya tonu, ko ita Shugabar da muke taƙama da ita ba zata iya ƙwatarmu ba, ƙila ma ta juya mana baya"._ -Da Bafaden da ɗayar matar su kai tsaki a tare. "to idan kin shirya rasa ranki da kuma dubu ɗari biyar ɗin da za'a ba ki kina iya juyawa ki tafi, mu ki barmu muyi aikinmu...akan kuɗi da kika ganmu babu kasadar da ba zamu iya ɗauka ba"._ _su na rufe baki Bafaden ya durƙusa ya shiga haƙe ƙasar da ke wurin, wanda bai tsaya ba har sai da yayi rami mai ɗan zurfi tukunna. Sannan macen da bata da tsoron ta ɗauko gorar ruwa a cikin jakar da ke hannunta ta juye ruwan a cikin ramin. Sannan ta miƙa hannu ta karɓi wata baƙar leda a hannun ɗaya matar ta zira a cikin ramin. Duk abunda suke yi su na yinsa ne cikin saurari-sauri gudun kar azo a gansu._ _Kuma bayan sun maida ƙasar ne sun rufe suka tsaya su na tattaunawa, wanda yanzu da su ke maganar Fillo bata jiyo komai da suke cewa saɓanin maganganun da su kai a ɗazu duk ta ji su._ _Alokacin zuciyarta na faɗa mata ne ta tunkari inda suke dan su san wani fa ya gansu, amma ɗayan ɓari na zuciyarta na hanata aikata hakan gudun karta fito suyi mata illa, duk da bata ga fuskar ko guda acikinsu ba amma tasan ba mutane bane masu imani a zuciyarsu._ _Cikin gudu mai kama da sauri suka bar wajen, sai da ta tabbatar sun bar wajen sannan ta fito, sai dai ko da taje wurin juyin duniya ta kasa gane inda akai haƙan aka binne, dan babu wata alama ta ɓurɓushin ƙasa da zai nuna maka anyi haƙan ƙasa a wajen, wannan ya nuna mata sun ƙware a iya aikinsu, kuma ba yaune farau ba._ _Ta ɗau kusan minti guda tsaye a wurin tana tunanin abinyi sai kawai taji gabanta ya yanke ya faɗi, ƙirjinta kuma na bugawa sosai, zuciyarta na faɗa mata tayi hanzarin barin wajen tun wani bai zo ya ganta ba, dan idan akazo aka kamata ta ina zata fara bayani?, waye zai wanketa daga duk wani kalar zargi da za'a ɗora akanta?, gatanta Allah gatanta Kaka, bata mantawa da lokacin da ɗaya daga cikin yaran gidan yaci abinci yay ta amai, aka ce ai mai aikin da ta kai masa abinci ce ta saka masa wani abun, idan har yanzu tunaninta na jikinta, to ai ba zata manta ba tsawon shekara guda da akai abun har yau mai aikin tana cikin kurku a kulle akan laifin da ba'a da tabbacin ta aikata shi._ _Saboda haka bata san lokacin da siraran ƙafafunta masu kama da sillan kara suka bar wajen ba cikin sauri kamin daga bisani kuma ta haɗa da gudu, sai dai a lokacin da ta ke shirin barin harabar wajen gaba ɗaya taji tayi tuntuɓe da dutse, ta tsuguna domin ɗaukewa kawai sai tayi tozali da laya da kuma wata leda baƙa ɗaure a wurin, cikin kanta bata kawo tunanin komai ba tasa hannu ta ɗauki layar da ledar sannan ta janye dutsen daga wurin._ _A wannan lokacin kai tsaye ɓangarensu ta koma, ta zauna ita ɗaya dan kowa yana can masarauta anata hidimar bikin naɗi, ita kuma duk tsoron kar ta fito a ganta ita ɗaya a cikin gidan a fara yi mata tambayar tuhuma. A ranar ma haka dole ta kashe haɗuwarsu da Amir._ "wai tunanin me kike?". Maganar Maijidda ta dawo da ita cikin duniyar zahirin da ta bari tsawon daƙiƙu masu yawa. Kallonta kawai tayi ba tare da tace da ita komai ba. "Fullo kin san fa wurin nan ba wajen zuwanmu bane, ɓangaren masu gida ne. Amma kin kawo mu kin ajiye salon azo aganmu ace wani abun muke ƙullawa". "Maijidda wuta zamu cinnawa wajen nan". Maganar ta Fullo tasa Maijidda zaro ido waje tare da hanzarin miƙewa tsaye. Da yake ita sarkin tsoro ce tuni jikinta ya hau makyartata. Kuma bata kai ga ƙara magana ba, Fullo ta kai hannu ta ɗau ƙaramar galan ɗin petir ɗin da suka sato a cikin gida ta shiga yaryaɗawa a wurin. Sai da ta juye shi tas sannan muryarta ta fito a hankali da cewar,"Maijidda matsa baya". Cikin tsoro ba tare da mamakin abunda Fillo zata iya aikatawa ba tace,"ke wai me yasa ba kya iya kallo matsalar da zata faru a gaba, ke kawai abunda yazo cikin kanki shi kike yi. Yanzu mene amfaninki na cinnawa wajen nan wuta? salon kija mana barin gida". "ai kin san dai ni ba mahaukaciya ba ce ko, duk abunda kika ga nayi ina da dalili...dan haka matsa da baya". "wai na matsa da baya kike cewa, ke kuma fa?, kina kallo fa petir ɗin da kika zuba yana da yawa, kina kunna wutar nan fa tasowa sama zata yi". "ni dai kija da baya kawai nace". Sautin muryarta ya fito cikin amo na ɓacin rai. babu shiri Maijidda taja da baya tayi nesa da ita. Fullo kuwa tasa hannu a gefen zanin da bata iya ɗaurinsa ba har yanzu ta kunto layar da take ajiye da ita. tasa a tsakiyar tafin hannunta na dama tana ƙare ma ta kallo, kamin daga bisani ta shiga warware baƙi da jan zaren da aka naɗeta da su. Sau uku tana duba sunan da ke jikin layar, ranar farko da ta fara warwareta ta kasa karanta rubutun da ke jiki tun lokacin bata iya karatu ba, da rana ta biyu da karatun da Amir ke mata ya fara zama akanta ta ɗauko ta duba dan haddace yanda harufan jiki suke, da kuma rana ta uku da ta rubuta harufan a wata takarda ta daban tayi compairing rubutunta da na jikin layar dan tabbatar da tayi daidai, kuma a ranar ne ta iya karanta hurufan da ke jiki, harufan sunan MUHAMMAD TURAKI. To amma ga mamakinta sau ukun nan da ta buɗe bata taɓa cin karo da wani rubutun na daban ba bayan sunan Muhammad Turaki da yake jiki, sai yanzu da take ganin wani rubutun sunan na daban da akayi shi a ƙasan na turakin shi kuma da baƙar tawada amma ya fara disashewa hakan yasa ta kasa fahimtar kome aka rubuta. Kawai sai taji wani dunƙulallan yawu ya wuce ta maƙogwaronta, tun a ranar farko da layar nan taje hannunta wani ɓari na zuciyarta ke gaya mata Halimatu kar ki jawa kanki bala'i, irin wannan abun mutum idan ya gani kauda idonsa yake akansa, amma yau kece da ɗaukar takardar da babu makawa anyi ne dan asirin wani. Amma yau sam zuciyarta bata yi mata wannan gargaɗin ba, illama ƙwarin gwiwar da take bata akan tayi iya duk ƙoƙarin da zata yi kan ganin ta karya wannan asirin, dan zata iya rantsewa wanda ake abun akansa ba shi da alhakin kowa, don haka ta shirya yin jihadi akansa. Saboda haka kawai sai ta cure takardar wuri guda ta jefar, ta ɗauki baƙar ledar da ta bawa Maijidda ajiya gudun kar Kaka ta gani, itama ta jefar a wurin. Muryarta ta fito a fili tana faɗin,"har yanzu banda tabbacin asiri ne ku ka yi ko ba shi ne ba, to koma dai menene sai dai yaci ku ku ɗaya, ga abinku nan ya koma kanku". Tana faɗar hakan ta ƙyasta ashana ta jefa, nan da nan ko wuta ta kama da wajen. Garin tayi baya ta bige ƙafarta a jikin kujerar wurin har taji ciwo a babban yatsan ƙafarta. Amma ko tsayawa tabi ta kan ciwon ba tayi ba. Maijidda ko banda ambaton, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Babu abinda ta ke. Har sanda Fullo ta risko wajenta ta kama hannunta dan su bar wajen. "ni kam na shiga uku da ke Fullo, yanzu kin san iyakar inda wutar nan zata tsaya ne?, ba kya gudun abinda zai faru damu?". "idan an tambaya sai kice mune muka kunna kinji". Fullo ta faɗa tana ƙara jan hannunta dan su bar wajen. Duk rashin iya gudu na Maijidda sai gashi har tana kusan kerewa Fullo saboda ita numfashinta ya fara ƙoƙarin tsayawa. Kuma kan kace kobo hayaƙin wutar ya fallasu a cikin gidan, saboda wuta ce ta tashi ba kaɗan ba sakamakon fulawoyin da ke wajen, cikin mintunan daba za su haura biyar ba sai ga fire service sun zo. Irin tashin hankalin da wutar ta haddasa a zuƙatan al'umma Allah ɗaya yasan yawansa, an kewaye wajen anata salati, saboda irin tashin ƙarni da ke fita ta cikin wutar yana shiga cikin hanci ya haura saman ka, ya haddasa faɗuwar mutane da dama a wurin. wani irin wari ne da ba shi da daɗi, dan asthmatic ma bai iya tsayawa. Haka ambulance tayi ta shige da ficen ɗaukar mutane. A yayinda a wannan lokacin Fullo da Maijidda na can cikin uwar ɗakin Yami, hankalin Fullo kwance kamar ba ita tayi ba, Maijidda kuwa tayi tsilli-tsilli da idanu kamar ta fashe da kuka. Tana ta yiwa Fullo maganar amma kamar da dutse ta ke. Dan ita a wannan lokacin ma tunaninta na kan wani lamari na daban da take haskowa wanda take tunanin yafi wannan hatsari. Ƙarshe dai da Maijidda ta isheta da maganar da ba zata iya zaman jinta ta miƙe ta bar mata ɗakin. Ta wuce ɗakinsu ta ɗauki littafinta ta hau assignment ɗin da Amir ya bata, wanda kusan kwana huɗu kenan da bata amma batayi ba saboda shiririta. Don Allah share to other groups🙏 Youtube Channel-Nishaɗi Media. [8/12, 08:00] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *11* "Mommi dan Allah kiyi shiru". Nuratu ta faɗa idanuwanta na kawo ruwa, zuciyarta cike da tsananin tausayin matar. Yusuf yace,"Mommi hawayenki babban tashin hankali ne a wurinmu, dan Allah ki daina, ko menene kike tunawa zai zama tarihi da izinin Allah...and ina da yaƙinin 100% komai naki ya kusa daidaituwa duk da cewar bamu san me ya faru dake ba har kika zo ƙasar da babu wani naki acikinta, fatanmu Allah ya baki lafiya domin musan ta inda zamu fara". shima ɗin maganar yake cike da tausayinta. Mommi ta sake su daga rungumar da tayi musu, tasa hannu zata goge hawayenta Yusuf ya riƙe hannun nata tare da saka handky ɗinsa ya goge mata. ta sakar musu murmushi, irin murmushin da ake kira na ƙarfin hali, sannan ta jinjina musu kai na ƙara godiya a gare su tare da nuna jin daɗin kasancewarta tare da su. su biyun suka taimaka mata ta sauko daga kan bed, Yusuf ya fice ita kuma Nuratu tayi mata rakiya zuwa toilet. bata wani jima a wankan ba ta fito dafe da bango. Nuratu na ajiye mata kayan da zata saka tai saurin bari ta taho tayi mata jagoranci suka ƙaraso ta zauna kan wata kujera. Nuratu ce tayi mata komai, tun daga kan shafa cream har saka kayan. abaya ce white da adon stones masu ƙyalli. sai hijab ɗin peach ta ɗora mata akai wanda yake daidai ƙirjinta. kasancewar Mommi fara ce sosai sai kayan suka amsheta matuƙa, idan ba wanda ya sani ba sai ka iya rantsewa balarabiyar ƙasar ce dan tayi kama da su sak. "Mommi ending this week zamu wuce Saudia muyi Umarah for 1 week daga nan sai mu wuce naija, Excellency ya gama gudanar da aikin daya kawo shi, aikinsa zai koma can nigeria gaba ɗaya". Nuratun ta faɗa tana bata kubza a baki haɗe da black tea, Mommi taunar ta ke yi da ƙyar saboda jin wani nauyi a ƙirjinta kamar an ɗora dutse. magana Nuratu ke tayi amma hankalin Mommi gaba ɗaya ya bar jikinta, tunaninta ya tafi can wata duniya ta daban, ita ɗaya ta san me ta ke tunani, kuma ita ɗaya tasan me zai iya faruwa. halin da mahaifiyarta ke ciki shi tafi so ta sa ni kamin azo kan kowa da komai. ta rufe ido kaɗan ta buɗe ta ɗorasu kan Nuratu, sai tayi dauriyar maida ƙwallar data cika idonta sannan ta matso ta sumbaci Nuratu a goshi. Yusuf na parlo zaune da waya kare a kunnensa yana sauraron maganganun da Umma keyi masa. tsawon lokaci kafin ya numfasa yace,"Umma please don't let Ammi knows munyi waya dake". daga inda Umma ta ke ta galla harara kamar yana gabanta, tai shiru kamar ba zata ce komai ba, tana shirin yin magana ya rigata. "please Umma". tayi hanzarin katse shi,"tana part ɗinta ina part ɗina how will she know?, ko da yake aini ce aku sarkin surutu". yanda yaji muryata yasa shi sosa kai tare da cewan,"ba haka nake nufi ba Umma". dai-dai lokacin Nuratu ta ƙaraso wajen ta zauna saman cinyarsa tare da kwantar da kanta bisa kafaɗarsa, shi kuma ya zira ɗayan hannunsa acikin rigarta yana shafa cikinta, har zuciyarsa ji yake tamkar babynsa yake shafawa a zahiri. Nuratun ma ta ɗora nata hannun akan nasa suna shafa cikin tare. komai na ubangiji ne, kuma komai lokaci ne, shekararsu biyu da aure Nuratu bata taɓa ɓatan wata ba, maganganu har sun fara tashin ai bata haihuwa, ya kamata ya ƙara aure tun kamin ya mutu baiga ɗansa ba. cikin masu maganganun harda Ammi mahaifiyarsa, da yake dama ita ba ƙaunar auren ta ke ba, kasancewar Nuratu ƴar Yayar kishiyarta ce wato Umma. lokacin daya gama service ɗinsa ta aika shi har abuja yaje yayi kwanaki a gidan best friend ɗinta Hajiya Habiba don yaga yarinyarta. amma Yusuf na dawowa a lokacin ya tarar da Nuratu da tazo hutu shikenan sai yace shi fa ita yake so, duk yanda Ammi tayi yace shi Nuratu kaɗai zai aura, kuma da yake mahaifinsa ba mai takurawa ƴaƴa bane, abunda suke so shi yake so haka dole aka bi abinda Yusuf ke so. Ammi tayi kamar tai hauka a lokacin, ita baƙin cikinta akan me zaisa ya auri jinin kishiya banda yana so ya tozartata a idon duniya. to fa shikenan kuma sai ya jawo ta ɗauki fushin duniya ta ɗora akansa. dama can ana ƴar hakan saboda tana jin haushin shirinsa da Umman. sam Ammi bata son Nuratu, kuma Nuratu yarinya ce me hankali. dan ko sau ɗaya ma bata taɓa nunawa Yusuf rashin jin daɗin tsangamar da ta ke samu daga wurin mahaifiyarsa ba. hasali ma idan yana bata haƙuri sai dai tace masa its matter of time hakan zai zama kamar ba'ai ba. hatta wani lokaci da Ammin taje har gidansu Yusuf baya gari ta wanke Nuratu tass akan sun asirce mata ɗa, da kuma cewar Allah ya isanta da ta aure mata yaro alhalin tasan ita juya ce. Nuratu bata taɓa danasanin auren Yusuf ba sai a ranar, saboda wankin babban bargon da Ammi tai mata na maganganu marasa daɗi da tsayawa a rai. hakanne ma yasa bayan tafiyar Ammin ta kira Umma tace ita kam tasa Yusuf ya saketa bata iya ci gaba da zama da shi, tunda dai haihuwar nan ba itane zata bawa kanta ba. ta kwashe duk abinda Ammi tayi mata ta faɗawa Umman, silar inda faɗan gaba me tsanani ya shiga tsakaninsu kenan. Umma bata biyewa faɗan kishi na Ammi, amma akan wannan abin har sai da Daddy yace shi ba zai iya da jarabarsu ba sai ya maka su a kotu. dalilin samun sauƙi kenan shima kuma dan Umman tana bagararwa ne, amma da saboda Ammi ne har gaba da kotu sai dai akai su. maganar Umma ta katse su Yusuf daga abinda suke ƙoƙarin yi, sai lokacin Yusuf ya farga ya amsa kiran sunansa da tai. "ina Nuratu?". Umman ta tambaya da ɗaure muryarta. "ga ta nan". "to bata". ya cire wayar daga kunnensa ya ɗora akan kunnen Nuratu, ta wani narke tana shagwaɓewan Umman. "ba dai ki da wata matsala ko?". Umman ta tambaya da tsansatar kulawa. tayi kamar za tai kuka tace,"Umma ni so nake mu dawo, anan bana samun duk kayan kwaɗayin da nake son ci". Umma tace,"kai Nuratu". tace,"Allah Umma, nan fa babu irin su goruba, tsamin gaye, kuma fa har Farar ƙasa ma babu Umma, ga shi duk abunda naci ni ba sonsa nake ba sai ya dawo". ta ƙarashe maganar tana fashewa da kukan taɓara. daga inda Umma ta ke tai murmushi. "ai ke kika dage sai kin bisa, amma kiyi haƙuri kinji, haka ƙaramin ciki yake Nuratu. ai kun kusa dawowa, idan kun dawo ma nan gida za ki dawo ba zan barki ke ɗaya ba...yanzu dai zan san duk yanda za'ai na aiko miki abubuwan da kike so kamin dawowar taku, kiyi list sai ki turo min". "tom Ummana. ina su Kursum?". Umma tace,"suna bedroom ɗin su". "kice ina gaida su kuma nayi fishi tunda basa nemana...kuma ko ɗansu yazo ba zan basu shi ba". Umma tace,"ai kina da wayarsu ki kira su mana". sannan ta ɗaure murya tace,"ina Yusuhun?". lokaci ɗaya Nuratu ta nemi hawa bori ajikinsa akan Umma tace Yusuhu, dan ita bata son sunan ana ɓata masa suna ya koma na ƴan ƙauye. ita kuma Umman duk lokacin da Yusuf ya ɓata mata rai ko ya ya ne sunan da take faɗa masa kenan. "bana son iya shege Malama bawa mijinki". tana ɓata fuska tace,"don Allah Umma ki daina cewa Yusuhu idan wasu suka ji sai su ɗauka". Umma tace,"to sai kizo ki faɗawa ubansa ai yay masa sabon yanka". sai around uku na yamma tukunna suka fita outing, Mommi nata jin daɗin fitar tasu saboda yanda suke ta ma ta hira su biyun, kowa so yake ya nuna bajintarsa na ɗebe ma ta kewa tamkar wasu ƴaƴanta. basu suka dawo gida ba sai after isha'i. *Nigeria, Gombe, Dikko resident.* kan Fillo duƙe tana yankan farce suna magana da Kaka, wadda ke ta yabon Turaki saboda mutumcinsa. Fillo dai bata cewa komai, dan ita duk da halin kirkin daya nuna bata jin zai wani burgeta. saboda haushinsa ma ta ke ji gaba ɗaya, har ga Allah ta tsani mutum me ji da kai, wannan yasa tun a wancan ranar da ta fara zuwa aiki ɓangarensu taji ko kaɗan bata ƙaunar ma hanya ta ƙara haɗata da shi ko bisa kuskure. ita bata ma yi tsammanin yana da halin ƙwarai har haka ba da zai iya taimakawa wani, tayi mamakinsa sosai. sai daga baya taga ashe tayi masa bahaguwar fahimta ne, bata san da yaje duba Kaka da jiki ba sai daga baya, tun ranar farkon aikin nan nata daya kira waya a ɗakin baya da akace ta zauna, bata ɗaga ba saboda baccin daya fara ɗibarta. da kansa yazo ɗakin ya sameta tana bacci, yana shirin juyawa ne ta farka, ta tambaye shi akwai buqatar wani abu ne fuskarsa a tamke yace mata babu, sai kawai ya fice daga ɗakin. kuma babu jimawa ya ƙara dawowa ya tambayeta ina tsohuwar da ta samu anan, tace masa ai ko da tazo babu kowa a ɗakin. kamar bai yarda da abinda ta faɗa ba lokacin, saboda ɗan jim yayi kamin ya fice a ɗakin. sai bayan isha'i da ta koma ne ta tarar da uban cartons jere a falonsu, maltina, madarar gwangwani da ruwa da kayan marmari kala-kala, ga kaza gasashshiya, abun ya bata mamaki sosai, duk da zuciyarta ta raya mata ko Amir ne ya kawo, to amma iya ƙoƙarinsa dai tasan baida kuɗin wannan uban sayayyar. tana tambayar Kaka tace mata ai Zaytuna ce suka zo ita da Yayanta suka kawo mata, a lokacin bata kawo cewar Turakin ba ne dan haka kawai godiya tayi tana daɗa faɗawa Kaka kirki irin na Zaytuna da Hajiyarsu, Kakan itama na ƙara faɗar nata kirkin da ta san Zaytunan da shi a ɗan tsukukun zaman jinyar Turaki da tai. Sai da Fillo ta shiga ɗaki taga ledar drip da tarin magani akan katifarsu sannan tai saurin fitowa daga ɗakin, tsayawa tayi kawai tana kallon Kaka kafin ta iya buɗar baki tace,"Kaka wa akaiwa ƙarin ruwa?". Kakan tace,"ni ce, ai da suka zo dubani ɗinne sai shi Yayan Zaytunan ke cewa ina da buqatar asamin ruwa domin na samu ƙwarin jikina. yana zaune anan ya kira likita yazo ya dubani shine har ya biya kuɗin waɗannan magungunan, ina ji likitan yana lissafin kusan dubu takwas Halimatu...ai yaran nan sunyo halin iyayensu". a lokacin hannu Fillo tasa ta goge hawayenta bata ce wani abuba. kuma tun daga ranar kullum sai Turaki yazo ya duba jikin Kaka sati guda kenan. ita bata ma san shine Turakin da tai kasada akansa ba sai ranar da Hajiya Madina ta aikata ɓangarensa tace tai gyara. anan ne tana shiga taga lafcecen enlergment ɗinsa a jikin bangon bedroom ɗin wanda daka shiga shi zai fara maka maraba. kuma a sannan babu hoton abinda ya shiga haskawa a idonta sai na sunansa dake jikin wannan farar takardar da ta ƙona, kamar yanda akai rubutun manya ajikin hotonsa haka ma yake a jikin takarda. tarin tambayoyi da mamaki suka maƙale a kwanyar tunaninta. tambayoyin da ta ƙudurcewa ranta son sanin su nan kusa bada jimawa ba in har taci gaba da zuwa aiki, tunda Hajiya Madina tace ko da Kaka taji sauƙi ba zata dawo ba ita zata ci gaba da aikin. dan sosai Hajiya Madina ke sonta, tunda ko da akace za'a ƙaro wasu ƴan aikin tace a'a a barsu ita Halimatunta kawai ta isheta yanzu, inma zaa ƙaro to a ƙaro ɗaya saboda kar aikin yay mata yawa, kullum cikin yabonta take tace bata taɓa ganin yarinya me hankali da natsuwa ba irinta, hakan yasa ta ke jin daɗin aikin sosai. ko a ƴaƴanta ma da Samha ne kawai basa wani ɗasawa amma ko Khalil idan ya ganta ya dinga tsokanarta da Sojan Rana. kuma sau tari indai Hajiya Madina na parlo sai tace itama ta zauna ayi kallon tare da ita, Turaki ne ma ta fuskanci kamar baya so talaka ya raɓe shi, shi yasa fuskarsa kullum ɗaure ta ke akanta, ko da yake ba ita ɗaya ya kewa hakan ba har ƙannensa idan aka cire Zaytuna da Khalil. saurin da ta ke yanzu ta gama yankan farcen ta wuce don taji Hajiya Madina na faɗin yau zasu unguwa duka gida. Kaka ta katse shirunta da cewar,"kin kuwa ɗauki namanki?". ta ɗago tace,"aina?". Kaka tace,"a'a na aje miki nama cikin farar robar nan, da za ki wanke-wanke ba ki gani ba?". "ni banga komai aciki ba, ƙila Maijidda ta shigo ta wawashe shi...wa ya kawo miki nama dama?". Kaka ta dire wani hijabi da ta ke linkewa tace,"Yayan Zaytuna ne ya shigo jiya da daddare, ba ki jima da kwanciya ba lokacin...nace masa ai ma na gama warwarewa lafiya ta samu dan jibi ma zan dawo aiki shine yace a'a nai zamana na ƙara hutawa tunda akwai me taimaka min, koma da babu a nemo wata". Fillo ta miƙe ta ɗauko tsintsiya tana share wurin da ta ɓata tace,"an gode masa...yana ta abu na masu kirki alhalin ba haka yake ba". Kaka dai shiru tayi, ita kuma ta ɗauki hijabi tana ce mata. "zan tafi Kaka. yau babu kula da buƙatun ɗan gwal da wuri zan dawo dan naji Hajiya tace zasu je unguwa". Kaka tace,"sai kin dawo ki gaida Hajiyar". tana fitowa haraba sukai kiciɓis da Maijidda, Fillo ta tsaya tana kallon yanda ta ke jera hamma daga gani kaga wadda ta taso a bacci. Maijidda tace,"yauwa dama wajenki za ni". ta faɗa tana miƙa mata wayar hannunta tace,"Amir ne ke kira tun asuba". Fillo ta kallesu ita da wayar kafin tace,"kuma ai sai kice masa bama tare". Maijidda tayi hamma sannan tace,"ai yaƙi gane wannan bayanin, ni dai ungo idan kin gama kya kawo wallahi mugun bacci ke idona". ba tare da Fillo ta karɓa ba tayi gaba abinta da cewar,"sai ki faɗa masa kinzo ba ki sameni ba". Maijidda tabi bayanta da kallo tana faɗin,"ni ban iya ƙarya ba, Allah haka zan faɗa masa kince idan yazo ya sameki acan". a parlo ta samesu kaf ɗinsu, ita kam rayuwarsu na burgeta. ta durƙusa ta gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ajiye hisnul muslim ɗin dake hannunta a gefenta, sannan ta zare medical glass ɗin dake a idonta ta saka shi cikin box ɗinsa. ta kalli Fillo da fara'a tace,"Halimatu kin shigo?". kan Fillo a ƙasa tace,"ehh Hajiya, Kaka na gaishe ki". tace,"ina amsawa, jikin nata da sauƙi dai ko?". "ehh taji sauƙi ai, tama ce zata shigo gaida ki zuwa anjima". "a'a ita da ba ƙwarin jiki ba, zan shiga na dubata insha'Allahu...yanzu maza ki fito da break fast naga already Zaytuna ma ta kammala komai". ta amsa da,"tou". sannan ta miƙe ta wuce kitchen din bayan duk ta gaida yaran. a kitchen ta sami Zaytuna tana ɗauraye hannunta, ta ƙarasa tana yi mata sannu da aiki. Zaytuna tace,"yau kinyi late". Fillo tai ɗan murmushi tace,"na tsaya yima Kaka aiki ne zata yi baƙi". "oh Allah sarki, jikin nata dai da sauƙi ko". "ehh taji sauƙi sosai". "to Allah ya ƙara mata lafiya". "amin ya Allah". ta nufi drower ta taka kujera ta ɗauko babban tray, Zaytuna na goge hannu a towel tace,"na kammala komai fito da su kawai za ki...kiyi da jiki dan Allah zamu fita ne har da Baffa". "tom Adda". Zaytuna ta dakata daga fitar da zata yi ta tsaya tana kallonta, ta girgiza kai kawai sannan tace,"wannan jiki naki Fillo anya ba sai mun nemi magani ba, komai kike salalo salalo kamar mara jini ajiki". tana faɗar hakan ta juya zata fita ta bar Fillo da ƴar dariya. Turaki ya shigo kitchen ɗin ko maganar da Zaytuna ma ke yi bai tsaya sauraro ba. ya wuce kai tsaye wajen drink trolly ya ɗauki mug, Fillo na shirin ɗaukar tea flask ta ɗora akai muryarsa ta tsayar da ita, ita bata ma san da shigowarsa ba. yo ita me ta sani da wani wait ɗinsa da zai ce mata wani wait, mutumin da ba zai yi hausa zalla ba dole sai ya haɗa da yaren da ita bata iya shi ba, ko da yake taga duka haka suke, shi yasa wataran suke shanyata a tsaye idan suka faɗi abinda bata sani ba, banda late da Zaytuna ta saba faɗar mata shi har ta fahimci me hakan ke nufi to me ta sani bayansa. dan haka kawai sai ta kuma yunƙurin ɗaukar tea flask ɗin, Turaki da idonsa ke kan hannun Flask ɗin da zata kama yace,"Wae ankam a iri 6iddo toi kam a nanako volwanego?". (wai ke wacce irin yarinya ce da ba'a faɗar magana kiji ne?) kakkausar muryarsa a sama ya doka mata tsawar da ta saka ta ture flask ɗin ba tare da saninta ba, ya zamo zai faɗi ƙasa yay saurin isowa ya tare shi. kamar yasa hannu ya bibbigeta don haushi, shi haushinsa da yarinyar saurin rikicewarta akan abindai bai kai ya kawo ba. ga shi ya tsana yaga da anyi magana jikinta ya hau rawa, shi yasa ya cewa Maama su kaita asibiti a binciki lafiyarta. ta ɗauki tsawon 2mints jikinta na rawa kamin ta daidaita, ta buɗe idonta da ta rumtse gam ta sauke kan dogayen yatsun ƙafarsa, sannan ta sauke hannunta daga kare fuskarta da tayi. sai lokacin ta ɗago ido ta kalle shi, ita yakewa wani irin kallo da bata son gani a wannan ƙwayar idon nasa da bata kama da ta mutane. muryarta kamar zata yi kuka tace,"Wadu munyal mi anda be min a vondi on". (kayi haƙuri ban san da ni kake ba). ya zabga mata harara ya bar wajen, ya ƙarasa ya buɗe coolers ɗin da Zaytuna ta zuba kayan soye-soyen da tayi, ya zuba chips a plate sannan ya zuba tea a mug ya fice. Fillo tabi bayansa da ido kawai, ita bata tasa ta ke ba, burinta yanzu bai wuce ta sami damar ahiga ɗakinsa ba, ba tare da sanin kowa ba ta gudanar da abinda zata yi. shi yasa ta ƙagu suyi-suyi su fice. [8/12, 08:00] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *12* bayan ta gama jera komai a dining tazo ta tsuguna gaban Hajiya Madina. "Maama ko mai ya kammala". sunan da yaranta ke kiranta da shi itama da shi ta ke kiranta, Hajiya Madinar ta faɗa mata haka a watarana, sanda ta ke ce mata. "Fillo ban taɓa ƴar aikin da nake jinta tamkar ƴar cikina ba irinki, saboda haka daga yau Hajiya ya fita daga bakinki, ki dinga kirana da Maama kamar yanda kika ji ƴaƴana nace min kinji". Hajiya Madina ta shiga kallonta ta wutsiyar idonta ba tare da ta amsawa maganarta ba, Fillo kuma dai har yanzu tana nan durƙushe bata motsa ba, kuma tunaninta bai bata ko Hajiya Madinar bata ji ba ne, a'a tasan taji kawai dai a jininsu ne basa amsa maka nan ta ke sai sun ɗan ɗau lokaci. "oak tom, kije ki zuba naki kici". abinda Hajiya Madina tace da ita kenan. Fillo ta miƙe ta wuce, sannan suma suka nufa dining, by the time Turaki har ya gama nasa, yana zaune wajen yana aikin danna waya. suna cikin yin breakfast ɗin ne wayar Nihal tayi ƙara, ganin sunan dake yawo jikin screen ɗin wayar gabanta ya faɗi, jikinta na rawa ta kai hannu tana gyara zaman medical glass nata, ta cikinsa ta ke kallon Hajiya Madina wacce ta dakata da cin abincin tana yi mata wani duba ta ƙasan ido. duk ta dabarbarce, tsoronta Allah tsoronta kar tace ta miƙa mata wayar. saboda haka tayi saurin kai hannu tai mute na ringing ɗin, sai dai kamin ta ɗauke hannunta daga kan wayar sabon kira ya ƙara shigowa. babu shiri ta haɗiye wani dunƙulallan yawu tare da rufe ido. sai dai kamin ta buɗe maganar Hajiya Madina ta shiga cikin kunnuwanta. "give me the phone". kamar zata yi kuka ta ɗauki wayar hannu na rawa ta miƙa mata. Hajiya Madina ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta miƙawa Khalil, ya karɓa ya saka a aljihunsa. har suka kammala breakfast ɗin babu wani wanda yay motsi na hira ko kuma tsokanar juna kamar yanda suka saba da mahaifiyar tasu, saboda yanayin da ta tashi da shi yau sun kasa gane kanta, ga shi Nihal ta ƙara dagula musu ita. Samha ta ɗaga landline en dake gefensu ta kira wayar ɗakin ma'aikata. bugun da bai wuce 2 ba Fillo dake can ta ɗaga. "ke kizo mun kammala". abinda tace da Fillo kenan ta kashe wayar. wanda a ɓangarenta azamar tashin ta ke yi saboda tana lissafe ne da lokaci, su kan ɗauki 10-15minutes a dining, kuma buƙatarsu da zarar sun kammala da shi ai clearing wurin. tana shigowa parlon Hajiya Madina na shirin hawa upstairs, ta kalleta tace mata. "idan kin gama ki sameni a ɗaki". Fillo ta amsa da,"tou". sannan ta shiga gyara wajen. komai nata cikin sanyin jiki ta ke yinsa amma kuma nan da nan ta ke gama abu, tana gama wanke-wanke bata tsaya ɗora lunch ba tunda tasan basa nan kuma bai wuce suyo takeaway na dinner ba idan sun tashi dawowa. zata wuce ɗakin Hajiya Madina Khalil dake parlon a zaune shi ɗaya ya tsayar da ita. "sojan rana zo nan". ta tsaya daga hawa saman ta juyo da murmushi fuskarta, abunda ke burge shi da ita fara'arta da tsabtarta, bata da wannan cunkus ɗin irin na sauran ƴan aikin da suka yi a baya. har ta ƙaraso ta tsuguna a gefen kujerar da yake zaune bai bar kallonta ba, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Hamma Khalil gani". ta faɗi sunan nasa kamar yanda taji ƙannensa na faɗa masa. yace,"ai nai zaton ko kina ciwon baki ne". ya faɗa da salon zolaya. ta murmusa da cewan,"ciwon baki kuma?". yace,"ehh mana, da na kiraki ai ba ki amsa ba tahowa kawai kika yi". ta saki murmushi me faɗi da cewar,"Hamma Khalil to ai kaine kake faɗin sunan da ba nawa ba, shisa sai nayi zaton ko bada ni kake ba". shima murmusawar yay kafin yace,"yanzu ke tsakani da Allah duk wanda ya ganki ranar nan da kika yi ƙeƙam a tsakiyar rana me zai yi zato?, kinga kam dan na kiraki da sojan rana ai ba laifi ba ne". murmushi kawai tayi bata ce komai ba. "anyway, wanne class kike before ki taho aikatau?". furucin da yay yasa ta ɗagowa ta kalle shi kaɗan sannan ta mayar da kanta ƙasa. "bana zuwa makaranta ai". da mamaki ya kalleta,"gaba ɗaya ba ki taɓa zuwa makarantar boko ba?". ta ɗaga masa kai tabbacin hakan. ya girgiza kansa,"to islamiya fa?". ruwan hawaye ya cika idonta kafin tace,"nayi islamiya kamin Ummi ta rasu, kuma itama tana yi min a gida". yace,"wace Ummi?". sai da tasa hannu ta goge hawaye tukunna tace,"mahaifiyata". lokaci ɗaya tausayinta ya kama shi. "Allah ya jiƙanta". ta amsa da,"amin na gode, Allah yaja da ransu Baffa". shima ya amsa da,"amin na gode. amma kuma idan baki je makarantar boko ba taya akai ranar nan kika karanta saƙon da Maama ta bar miki?". taja yatsanta na tsakiya bata ce komai ba. ya katse shirun,"tambayarki nake". murya a hankali tace,"wanda zan aura ne ya fara koya min yanda zanyi karatu, kuma daga baya sai muka daina saboda ayyuka da suka yi masa yawa". kalmar wanda zan aura ta ba shi mamaki. to amma sai dai aure wa ƙaramar yarinya kamar wannan a wajen ƴan ƙauye ba wani abu bane, wataƙila da ace ba anan suke zaune ba yanzu haka tana da ƴaƴa. ya sauke numfashi yace,"yayi ƙoƙari shi wanda za ki aura ɗin...yanzu yaushe ne bikin?". tace,"ba'a tsayar ba tukunna amma dai da an kusa wani dalili yasa aka ɗaga". ta faɗi hakan idonta na kawo ruwa sosai, kuka ta ke sonyi a lokacin amma saboda Khalil ɗin ta hana kukan samun ƴancin fita daga bakinta, domin bata so ya gano wani ciwo da rayuwarta ke ɗauke da shi. ya ɗaga kafaɗarsa ya ajiye wayarsa sannan ya fuskantota gaba ɗaya. "to kin san menene?, mu a gidan nan idan mutum zai yi aiki dole sai yana karatu, kije ki tambayi duk wanda ya taɓa aiki anan, haka tsarin Baffa yake...and dalilin daya sa ma inaga Maama bata yi miki zancen ba kwana biyu aiki ya sha kanta ne, amma yanzu idan kinje ki tuna mata, akwai Malamin da yake zuwa yana yi muku karatu". ta ɗago ido tana kallonsa, kamar bata fahimci me yake son cewa ba. ya ɗaga mata gira,"ehh idan kinje ki cewa Maama ke ba ki yi karatu ba". ta gyaɗa kai kawai sannan ta miƙe zata wuce. Turaki ya shigo parlon a lokacin yana waya. ta gabansa ta wuce tana ji yana cewa,"me zan yi da yarinyar da bata waye ba, ka bar wannan batun she is not my type...infact ni babu aure ma a lissafin rayuwata". hannuwan Fillo suka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta buɗe, tayi sallama amma ba'a amsa ba. hakan yasa tasa kai zuwa ciki ƙafafuwanta na luntsumewa cikin tattausan carpet ɗin dake malale a duka ɗakin tun daga bakin ƙofa, kai kace cikin auduga kake sanya ƙafa saboda tsabagen taushi. tayi tsaye daga nan bakin ƙofar bayan ta maida ƙofar ta rufe, jikinta take takurewa saboda yanda sanyin ac ke ratsata. ta kusan minti uku tsaye sannan Hajiya Madina ta fito daga wata ƙofa da idan ba sani kai ba ba zaka ce ƙofa bace. da sauri ta durƙusa a ƙasa tana kama gefen zanenta ta riƙe. dalilin wani abu da yayi duka acikin kanta sanadin furucin da taji Hajiya Madina tayi acikin wayar da ta ɗauka yanzu da aka kira. "asiri fa kika ce Lubna, wa ya faɗa miki?". abinda Hajiya Madinan ta fara kenan cikin muryar razani, amma ita a wannan lokacin kalmar asirin ce ke ta maimaituwa acikin kwanyar kanta, lokaci guda kuma hankalinta ya gushe daga cikin ɗakin ta lula wani wurin can daban da tunanin abinda ya danganci asirin. "to shikenan Allah dai ya kyauta...ni ma kinga zamu je gidan Alhaji Babba ne akan lamarin Hammansu, sam yaƙi aure kuma ko zancen auren baya so ayi masa, mun rasa kuma dalilinsa dan ko jiya sun fi awa shi da Baffansa kan ya sanar masa da dalilinsa yace shi babu komai haka ɗaya, sannan babbar matsalar duk wannan nacin ibadar tasa yanzu ba yayi, sai kiga ko sallah ake yana zaune...to shine Boɗejo ke ganin abun kamar ba lafiya ba". Hajiya Madina ta faɗawa ƙawarta Lubna da suke wayar. daga ɓangaren Lubna ɗin tace,"subhanallah, gaskiya kam dai wannan labari ba lafiya ba a tashi a nemi magani, namiji har namiji kamar Turaki ace baya son aure, ai lamarin akwai duba...Allah dai ya kawo komai da sauƙi". Hajiya Madina tace,"amin ya Allah...shikenan sai mun ƙara yin waya, dan Allah karki manta da saƙon nan ki bayar akai musu". daga ɓangaren Lubna ta sake cewa wani abu sannan Hajiya Madina tace,"ina ta ƙoƙarin yin hakan. sai dai ina tsoro Lubna, ban san mutanen dake bibiyar rayuwarsa ba, haka ban san wanne irin shiri suke yi akansa ba, dalilin da yasa na dage akan cewar ya haƙura da kowanne irin aiki zamansa a gida shine kwanciyar hankalinmu, haka kuma shima a nasa ɓangaren wannan ne kaɗai tsaron da zai samu...wallahi ba ki ga munin last accident ɗin da yay ba, Lubna sai dana gama cire rai da shi tukunna ya farfaɗo...amma akan maganar wannan company ɗin da Baffa ke cewa zai buɗe musu wataƙila na yarda ya zama jagoran ciki amma in har bai ɗara daga state ɗin nan ba, amma muddin wani gari ko wata ƙasa ce can daban hakan ba zai yiwu ba". haka suka ci gama da tattaunawa tsawon mintuna kafin suyi sallama. ta ajiye wayar tana mai cewa da Fillo,"buɗe wancan closet ɗin ki ɗauko min wasu takardu daga sama". Fillo ta miƙe dan cika umarninta, tana ɗauko takardun tana mamakin irin jama'ar da Allah ya bawa Hajiya Madina, ko da yaushe acikin yin waya ta ke, inda take gani da itace gaskiya ba zata iya ba, domin idan kunnenta bai ciwo ba to bakinta zai yi. yanzu fa ta gama waya ko minti biyu ba'a ƙara ba amma har an kuma kiranta. "zan bar su a gida, akwai yarinya idan kazo zata baka". abinda ta ke cewa dana wayar kenan, kuma lokacin da Fillon ta ƙaraso ta durƙusa ta bata takardun. "alright sai ka zo". daga haka wayar tasu ta yanke, ta dubi Fillo tace da ita,"gobe za ki fara ɗaukar karatu a gidan nan, ba ke ɗaya bace akwai wata sabuwar ƴar aiki da za'a kawo anjima za kuci gaba da aiki tare. bana son fitina Halima, bana son kuskure, ki kula da hakan. karatun boko da arabiya zai ke yi muku. ki tsaya ki maida hankali, domin akwai aikin da nake so kiyi min, aiki ne na masu ilimin boko, idan kin mayar da hankali, idan har kinyi nasarar samunsa Halima za ki sha mamakin yarda zan mayar da ke, duniyarki zata sauya, za ki zama abar kwantance, bayanki zai zama tarihi, idan kuma akasin hakan, tabbas ina mai tausaya miki da asara mafi girma da za kiyi a rayuwarki". Fillo so ta ke ta ɗago ta kalleta amma ta kasa, jan yatsunta kawai ta ke. "ungo wannan". sai a sannan ta ɗago tasa hannu biyu ta karɓi takardun. "ki adana su, zuwa ƙarfe biyar na yamma akwai wani zaizo ya karɓa, baƙi ne dogo yana da ƙasumba...ba shi kawai nace kiyi, kije masa da fuskar mutumcinki Halima...nasan kin gane lissafina". Kan Fillo a ƙasa tace,"tom Hajiya". "bani lafayata fara". Fillo ta miƙe ta ɗauko ta kawo mata. ta cikin mudubi Hajiya Madina ke ta kallonta, zuciyarta na me jin so da tausayin yarinyar. bata bar kallonta ta cikin madubin ba tace,"zo ki saka min wannam fil ɗin". Fillo ta matso zuwa bayanta ta karɓi fil ɗin a hannunta sannan ta saka mata kamar yanda taga Zaytuna nayi mata a duk sanda ta saka lafaya. ita ta ɗaukar mata jakarta suka fito a ɗakin, suna saukowa ta ke faɗa mata,"akwai key ɗin ɗayan bedroom na Hammansu acikin drower na mirrow, idan mun fita kije ki gyara masa. dan Allah ki gyara me kyau, ki kaɗe duk wata ƙura". "tom Maama, sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya" har bakin mota tai mata rakiya, Khalil ne zai ja motar dama, ta shiga tana tambayarsu, "ina Hammanku da Nihal?". Sameer yace,"Hamma ba lallai yasan mun fito ba, amma naga Nihal tayi wajensa da nake fitowa". "kira min shi". Sameer ya ɗauki waya ya kira shi, sai dai kamin ta kai ga yin magana ma yace gashi nan fitowa. Fillo kuwa tana komawa key ta ɗauka ta fito ta wuce ɓangaren Turaki, ɓangarensa dake jikin na Baffa. tana shiga parlon taji maganarsa na tashi a parlon. tayi saɗaf ta ɓoye ta wajen wani corrido, dan har ga Allah ita ba so ta ke suke haɗuwa ba saboda bata son wannan tsawar da yake sakar mata, yana sakata tana tunawa da moment ɗin da ba son tunawa da shi ta ke ba. kuma har zuwa wannan lokacin tana ƙyale shi ne kawai saboda darajar mahafiyarsa, banda haka da tuni ta nuna masa tafi ƙarfin ya dinga zaburar da ita dan kawai tana aiki ƙarƙashin arziƙinsu. shi da Nihal ne wadda taji tana roƙonsa akan dan Allah ya bawa Maama haƙuri. maganar ta ke tana karyewa saboda kukan dake fita daga bakinta. ta leƙo taga Turakin na tsaye ne ya harɗe hannayensa ta baya yana fuskantar gabas, kansa a sama kamar me tunani. ita kuma Nihal gwiwoyinta na zube a ƙasa a gabansa. kafin ya juyo gareta yaci gaba da magana bayan shirun da tayi. "arziƙi da talauci duka na Allah ne, idan Allah ya baka arziƙi ba yana nufin kafi kowa bane acikin bayinsa, kuma ba wai an baka dama ba ne dan ka wulaƙanta wanda bai da shi ba, shima idan Allah yaso yana iya ba shi nasa rabon, ko kuma ya ƙwace daga hannun kai da kake wulaƙanta talaka ya bawa wanda ka raina...but kin san me nake so ki fahimta?". Nihal ta ɗago da kanta tana kallonsa, sannan ta girgiza kanta alamar a'a. shi kuma yaci gaba,"Mama uwa ce da yau ba zata so ace ƴarta ta shiga gidan da zata wahala ba, wannan haka yake ga kowacce uwa...burin iyaye ne ace ƴaƴansu sunyi aure sun zauna a inda zasu ji daɗi, dan haka Maama bata hana alaƙarki da shi ba ne saboda yana talaka ba...". tun bai kai ga ƙarasawa ba ta katse maganarsa,"Allah Hammah tace makusarsa a wajenta shine talaucinsa, banda haka babu abinda zai hana ta barina mu'amala da shi...kuma ni wallahi Hammah ina sonsa, shi kaɗai zuciyata ke da muradin aure". ya kai hannu ya shafo wuyansa yana mai lumshe ido ya buɗe. "ba za'a hanaki aurensa ba dan kawai yana talaka, idan har na gari ne to ba shi da wani aibu a idon Baffa...saboda haka ki kwantar da hankalinki, ta shi muje". ta miƙe ya kama hannunta suka fita. Fillo ta sauke ajiyar zuciya, duk yacce ta ke tunanin mutumin nan ba haka yake ba. shi ɗin me kyau ne, kuma ta fahimci yana da kyan zuciya. contact 08024976578 [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *13* Hakimi wato Alhaji Babba zaune akan royal chair ɗin da ke tamfatsetsen parlon da ya gaji da tsaruwa da kayan alatu, duk wani kayan jin daɗi na mo re rayuwa an zuba a wannan parlon, haka idan har kai farin shiga ne a zuwa gidan, to tabbas zaka iya rantsewa ba'a ƙasar nigeria kake ba. farin rawani ne akansa, kana masa kallo ɗaya zaka san jinin sarauta ya gama ratsa shi. kamar yanda tarihi ya gabatar, an kafa Masarautar Gombe a shekarar 1804 a lokacin jihadin Fulani wanda Buba Yero mabiyin Usman ɗan Fodio ne. Buba Yero ya mai da Gombe (Abba) hedikwatarsa ​​domin yaƙin da ake yi da matsugunan Jukun na Pindiga da Kalam, daga nan kuma yayi ta kai hare-hare har zuwa Adamawa da ke gefen kogin Benue. a lokacin sarki Alhaji Bukar Dukku shi ke riƙe da sarautar garin gombe, bayan rasuwarsa ne kuma babban ɗansa Hashim Bukar Dukko ya karɓi sauratar, wanda ya riƙe sarautar tsawon shekaru masu yawa. Sarki Hashim Bukar ya ajiye ƴaƴa a ƙalla guda takwas kuma dukansu maza, kuma duk su takwas ɗin sun fito ne daga tsatson mace guda ɗaya Sarauniya Falmata, wacca a lokacinsu ne aka kafa tarihin sarkin daya zauna da mace ɗaya tal a karagar mulkinsa har rayuwarsa ta ƙare ba tare daya mallaki ko da ƙwarƙwara ba. cikin ƴaƴa takwas daya bari sune Adam, Ishaq, Lateef, Harun, Ibrahim, Yusuf, Isma'il, Shu'aib. akaf cikin yaran babu wanda ya samu kulawa me girma da gata daga wurin mahaifinsa irin babban ɗansa Adam, kasancewar tunda Sarauniya Falmata ta haife shi sai da ta shafe shekaru shida kafin ta ƙara samun wani cikin, lokacin har sun yanke tsammani da samun wani rabon, kuma daga haihuwar Yarima Ishaq shikenan ta shiga jero haihuwar ƴaƴa har sai da ta jera 8 gaba ɗaya. duk da ƙarancin shekaru da Yarima Adam ke da shi a wancan lokacin, hakan bai gaza fahimtar cewar shi wanene ba, ya san daga tsatson daya fito, domin a ko da yaushe mahaifinsa na faɗa masa cewar gaba da bayansa shi ɗan sarauta ne dan ko mahaifiyarsa ma ƴar sarki ce. bayan tarin ƙauna, soyayya, gata da kulawa wadda Yarima Adam ya samu a wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, sai kuma na ɓangaren al'umma. waɗanda suke ƙasƙan da kansu a gare shi matsayinsa na ɗa ɗaya tilo a wurin Mai Martaba da suke jin basu da tamkarsa. hakan kuma ya haifar da aƙida ta girman kai da gadara a wurin Yarima Adam, har ta kai ga yana nuna ƙasƙanci ga na ƙasansa, hatta ga hadiman dake kewaye da Sarki kuwa. tun kamin ayi masa ƙanne ya haddace wani furuci dake fitowa daga bakin al'umma na kirarin da suke yi masa da Yarima Sarkin Gobe, kai ɗaya ne Yariman da akai babu irinsa, bayanka sarauta gabanka sarauta. amma tun daga lokacin da mahaifiyarsa ta ƙara haihuwa sai yaji salon wannan kirarin ya sauya, kuma bai gyaru ba har zuwa lokacin da ta tsaya da haihuwa, kirakiran ya tashi daga kansa shi ɗaya ya koma har ga sauran ƴan'uwansa. dalilin da yasa zuciyarsa tayi baƙi kenan akan ƴan'uwansa, dan yana ganin silarsu zai iya rasa wasu tarin nasarori daya rubuce su a tafin hannunsa. da tafiya tayi tafiya sai ya zamana sam Yarima Adam baya ko da raɓar inda ƴan'uwansa suke, tsakaninsa da su nisantar juna, basa samun fuska a wurinsa matsayinsa na babbansu. tun zuciyarsa na raya masa wani abu wai shi ƙiyayya har hakan ta tabbata akan ɗan'uwansa Yarima Lateef, wanda ya ƙwace duk wata fada da yake da ita a wurin mahaifinsu, wannan soyayyar da gata da dukkan komai da ya samu lokacin da yake shi ɗaya daga wurin mahaifinsa gaba ɗaya sai ta koma kan Yarima Lateef, hatta da soyayya da girmamawar da al'umma suke ba shi. kuma hakan ya samo wuri ne dalilin banbancin halayya, cikin kaf su takwas ɗin da Mai Martaba ya mallaka babu wanda ya ɗauko kyawun halayyarsa da ɗabi'unsa sai Yarima Lateef, shine yasan darajar mutane, saɓanin sauran da suke nuna ƙasƙsanci ga mutane, haka shine kaɗai mai sauƙin kai amma kaf sauran suna da mummunar ɗabi'a ta girman kai, kuma shi ɗaya ne mai son mutane da yi musu fara'a, gaba ɗaya Yarima Lateef kan manta da cewar shi ɗin jinin sarauta ne kasancewar ba'a gabansa take ba, amma ƴan'uwansa sarautar itace abar alfaharinsu da tunƙahonsu, a karan kansu sukan ji tamkar su mutstsuke juna saboda girman izza, kowannensu mulki da muƙami kawai yake wa hari a rayuwarsa amma banda Yarima Lateef. shakarun Yarima Lateef 24 a duniya mahaifinsa ya aura masa ƴar gidan wazirinsa me suna Rumana, itama kuma sai ta samu matsuguni na soyayya a wurin Mai Martaba ta dalilin ɗansa da take aure, dan tunda akayi auren Mai Martaba da Sarauniya Falmata suke kiranta da gimbiya. a wannan lokacin Yarima Lateef yayi auren biyayya ne kawai ba don yana son Rumana ba, sai bayan auren kuma ya gane cewar zaɓin mahaifinsa kyakykyawan zaɓi ne a gare shi, kuma dama abinda yasa baya son auren ganin cewar yayyansa Yarima Adam da Yarima Ishaq basu yi aure ba, sai yake ganin kamar babu dacewar ace shi ya riga su yin aure. wannan aure na Yarima Lateef shi ya ƙara janyo masa baƙin jini a wurin ƴan'uwansa musamman Yarima Adam. kuma auren nasa babu jimawa shima Yarima Adam ɗin ya bijiro da nasa inda ya kawo ƴar gidan gomnan garin gombe a matsayin wacce zai aura, bayan zugo shi da Jakadan Sarki yayi akan cewar muddin yana son kujerar mahaifinsa to yayi aure tun mahaifinsa na raye, idan kuwa ba haka ba wannan burin mulkin nasa da saurautar zasu ta shi a tutar babu ne, dan zai kasance abu me wahala a ba shi saurauta alhalin baida iyali. shi kuwa a sanda Jakada ke ba shi wannan shawarar ji yake da zai iya kashe Lateef ba tare da kowa ya sa ni ba da babu abunda zai hana shi, to tsoronsa ɗaya ne, ya riga ya sa ni abu ne me sauƙi Mai Martaba yasa shima a kashe shi ko kuma ya kashe shi da hannunsa. dan Mai Martaba kan mance da kowa da komai akan Yarima Lateef, kuma yasha tarasu ya faɗa musu cewar zai iya yin komai akan Lateef. kuma bayan rasuwar Sarki Hashim Bukar anyi tata ɓurza wajen naɗa magajinsa, don har sai da ta kai ta kawo duka Yaran sun fito da abunda yake zuciyoyinsu ƙiriƙiri, rigima ta ɓarkewa junansu kowa na ganin ya cancanci a basa wannan sarautar. majaifiyarsu Sarauniya Falmata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa akan babban yaƙin dake shirin ɓarkewa, Lateef shi ɗaya ne me ƙoƙarin ganin ya kwantar mata da hankali domin har sai da ta kai ga ya ɗauketa daga ƙasar ya fitar da ita da matarsa me jaririn yaro a lokacin, saboda komai zai iya faruwa hatta ga rasa rayuka kuwa. to amma dai yake Allah ya tsara cewar Lateef shi zai hau kujerar mulki, duk irin yanda Adam ya kai ruwa rana wajen ganin ya hana faruwar hakan shi da muqarrabansa amma Allah bai ba su iko ba. daga ƙarshe haka dole suka haƙura suka zubawa sarautar Lateef ido wadda yake gudanar da ita cikin gaskiya, tausayi gami da jin ƙan al'umma kamar yanda mahaifinsa ya aiwatar a lokacin nasa mulkin. Sarki Lateef ya gaji mahaifinsa ne wajen auren mace ɗaya tun auren da mahaifinsa yayi masa na Rumana, kuma lokacin da Sarauniya Rumana ta haifi ɗa na uku Allah ya yiwa Sarauniya Falmata rasuwa. bayan rasuwartata ne wannan ɗan guntun haɗin kan dake tsakanin ƴaƴanta wanda yake na dole a gare su saboda ganin idonta sai ya ƙarasa rugujewa, don tana rasuwa kowa ya kama gabansa, da yake dai shima Yarima Adam Allah ya rubuta dole zai riƙi sarauta haka ya zuba uban dukiya aka ba shi sarautar yankin Funakaye, yankin da Babban ɗansa ke mulka a yanzu tun bayan rasuwar Sarki Adam. sai a wannan lokacin Sarki Lateef ya samu lafiya, aka sarara da bi masa ta ƙarƙashin ƙasa, kwanciyar hankali ta samu a gare shi. Allah ya azurta Sarki Lateef da yara huɗu, babban ɗansa Abubakar wanda yaci sunan Kakansa Sarki na biyu a wancan zamanin,  suke kiransa da Yarima Babba, sai dai a yanzu Ƴaƴa da Jikoki na kiransa da Alhaji Babba, kuma a yanzu shi ne Hakimin Kaltungo. sai ɗansa na biyu da yaci sunan mahaifinsa Hashim suke kiransa da sarki na uku, kuma Hashim shine wanda ya gaji sarautar mahaifinsa Sarki Lateef tun bayan rasuwarsa. a lokacinsu ba'ai wannan tashin hankalin ba na nuna son mulki ga kowannensu, hasalima mahaifiyarsu Sarauniya Rumana ita ta bada zaɓin cewar shine zai maye gurbin mahaifinsu, kuma daga wannan maganartata babu wanda yaja balle a tsaya ja'inja aka tsaya akan abinda tace. sai ɗansu na uku Habib suke masa alkunya da Dikko, wanda yake babban alƙali a cikin ƙasa da wajenta, wanda gwamnatin tarayya ke ji da shi, kuma mahaifiyarsa ke alfahari da shi saboda gaskiyarsa. Falmata(Faɗima) itace autar Sarauniya Rumana(Boɗejo), wacca aka haifeta bayan rasuwar mahaifinsu daya tafi ya bar Rumana da cikinta. ya kuma bar wasiyyar cewar indai an haifi mace a saka mata sunan mahaifiyarsa Falmata, kuma kar a ɓoye mata suna a dinga kiranta da wannan sunan. hakan kuma akayi sai dai Ƴaƴa na sakayawa suce mata Inna Falmata, mahaifiyarta kuma tace mata Sarauniya. bayan biyo ɗan shirun da aka samu a falon na Hakimi wato Alhaji Babba, akan faɗan da yake ta yiwa Turaki na batun ƙin amincewarsa akan auren da iyayensa suke so yayi, yaci gaba da cewa. "to mu ba mutanen banza bane ya kamata kasan da hakan Turaki, babu yacca za'ai ace mu ƙyaleka akan ra'ayinka na cewar kai ba zaka yi aure ba, wannan ma zancen banza da wofi ne...idan ka manta to ka tuna su waye mu, saboda haka wallahi ƙaryarka ka bar mana abin kunya a tarihin sarautarmu...na san idan ta ra'ayin mahaifinka ne sai da ya zuba maka ido, to mu ba zamu zuba maka wannan idon ba kaji ni da kyau". A wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke, kansa a duƙe yake, yana zaune ne a gefen ƙafafun macen da duk duniya baida kamarta Hajiya Madina. itace ta kawo ƙararsa ba kowa ba, aure take so yayi ya riga yasan da wannan batun ba tun yau ba, ya sa ni shine burinta akansa. to amma me yasa?, me yasa a matsayinta na wadda ta isa da shi bata gindaya masa umarnin hakan kai tsaye ba sai dai ta kawo ƙararsa gaban wanda cin mutumci shine abin yinsa?. wani dunƙulallan abu yaji ya tsaya a maƙoshinsa, zuciyarsa ta katse da raya masa abubuwa a sanda Hakimi ya ƙara yin magana. "Turaki ko dai baka da lafiya ne?, idan kasan akwai wannan matsalar a tare da kai to ka faɗa tun wuri a maganceta, duk da cewar abu ne da kamar wuya namiji kamarka ace yana da matsala makamancin hakan". Boɗejo dake gefe tace,"ah tou dai nima shi na gani. wannan zance dai na batun ba shi lafiya ma ƙarya ne, ni nafi ga wani algungumin ne ya jefe mana shi, tunda dai kaga maitar ibadar nan da yake ma yanzu fa duk ya daina, kuma wallahi ko waye Allah ya isa bamu yafe ba...yanzu duk wani dogon zance ba shi bane, a tashi tsaye a nema masa magani kawai idan aka biye ta uwar tasa da uban nasa ba zasu yi masa wannan abin arziƙin ba". Turaki ya buɗe idanuwansa ya zube akanta, magana ta ke tana ƙara kambaba zancen asiri ne akansa. bai san lokacin da bakinsa ya buɗe ya katseta da faɗin,"Boɗejo ke kuma komai ya faru shikenan sai kice aikin asiri asiri". tayi masa wani kallo ɗaya sannan ta maida kallonta kan Hakimi tace,"me na faɗa maka Yarima Babba tun kamin ayi zaman wannan kotun?, ai sai dai idan ban faɗa ba amma yaron nan sai ya tanka, baka ga kallon da yake min bane kamar ma zai tashi ya rufeni da duka...haka fa ubansa ya koya masa kuma alhalin ni ba irin rainon da nayi muku ba kenan, wallahi duk irin son da yake ma yaransa bai kama ƙafar wanda Ubanku Allah ya jiƙan rai ya nuna muku ba, amma ku dai baku san wani abu wai shi raina na gaba ba, hasalima wallahi baku san babba na magana ku saka baki ba, amma su dai Ƴaƴan Dukko halinsu kenan Babba na magana su nuna bai kai ba...to alhamdulillahi daɗin abin Turaki bani na kawo ƙararka ba Uwarka ce gata nan a kusa da kai, kuma billahillazi da ace lokacin da nake sarauniya ne sai kasan na faɗa ka saka baki". Turaki yay ɗan guntun tsaki, ya ɗago kai ya kalli Hajiya Madina, suka yi ido huɗu da ita. a kallon da yay mata ya gano expression ɗin dake tare da ita. sai yayi saurin kai hannu wuyansa ya shafo shi, ɗabi'arsa ce hakan. yawanci Boɗejo kance wani ƙullin yake shafowa. ya sauke numfashi, muryarsa ta fito a hankali, cikin girmamawa da biyayya yace da Hajiya Madina. "Maama ba sai kin kai ƙarata wani wurin ba. kin isa da ni, kin isa ki bani umarni na bi ko ina so ko bana so, kin isa kija layi kice kar na shata na haƙura dan dole na, bin zaɓinki dole na, yacca kike so nayi haka zanyi muddin hakan zai faranta ranki...". bai ƙarasa ba amon muryarta ya fito da faɗin,"aurenka nake son gani Me babban suna, ina so kayi aure tun ina da rai Hammansu, ka sani ina sonka fiye da numfashina, babban burina a yanzu shine naga aurenka, naga matar da zaka aura, naga jikana, naga kalar rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankalin da zaka shimfiɗa da iyalinka...Hammansu wannan auren da baka so shine mutumcin mutum, kuma shine ƙarshen jin daɗin rayuwa...ita rayuwa nan guda ɗaya ce Hammansu, haka ran ɗan adam guda ɗaya ne. lokaci tafiya yake baya jira, so kai enjoying rayuwarka tun lokacin bai ƙure ba, ya zamana kazo baka mori dukkan jin daɗin rayuwar ba...babu wanda aka yiwa alƙawarin kaiwa gobe a wannan duniyar, tsari kawai muke da hange, kuma zata iya yiwuwa mu matu a lokacin da muke ta shirin tsare-tsaren gobenmu, and that will be the end of us, ni kuma ina so mu tafi ne a lokacin da muka bar masu tunamu a kowacce daƙiƙa. da zarar ance babu kai shikenan duk wasu memories daka bari suma sun tafi, amma ɗa fa?, shi ɗaya ne memory da zaka tafi ka bari a kasa mancewa da kai, hakan yasa nake so kayi aure tunda sauran lokaci, auren nan daga zuriya mai ƙarfi irin zuriyarmu, *SARAUTA*, ta yadda zaka bar bayanka, wannan kawai shine burina akanka Hammansu". idanuwan Turaki a ƙasan carpet suke, amma ƙwayar idonsa wasu yatsu ta ke hangowa sirara da suke karkarwa kamar waɗanda ake girgiza su. ya haɗiye wannan yawun dake saman harshensa zuwa cikinsa, sannan ya rufe idonsa ya buɗe a lokaci ɗaya. laɓensa na sama da na ƙasa suka tale, harufan bakinsa suka fito da faɗin. "Aure! zanyi aure Maama, zanyi yanda kike so, kuma insha'Allahu sai na cika miki dukkan burinki akaina, kuma insha'Allahu ba za'a wayi wata rana da za'ace kin rigani tafiya ba, ni nake so na rigaki tafiya Maama, ni nake so, bana so ki tafi ki barni, rayuwar zata yi min tsanani, zan daina jin daɗinta kwata-kwata, zan dinga jinta ne kamar ana min feshi da ruwan dalma, dan Allah Maamaaaa". maganar yake da kakkaryewar kowanne harafi, kuma maganar tasa ta katse gaba ɗaya a sanda yaja sunanta wajen faɗi. lokaci ɗaya ya nemi ya fita hayyacinsa. sautin kuka kawai yake ji acikin kansa, wannan sautin kukan na yarinta da na jarirai, saboda haka yay saurin saka duka hannayensa ya toshe kunnuwansa, tare da kifa goshinsa akan ƙafafun Hajiya Madina da ke zaune tana hawaye. har zuwa lokacin da ya daina jin ihun kukan acikin kunnensa sannan ya ɗauke hannunsa, ya shiga sauke numfarfashi, gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, kamar ma ya burkice ne, hannayensa masu rawa a yanzu suka damƙe zanin Hajiya Madina. a jikinta ta ke jin irin rawar da jikinsa yake yi, jikinsa na rawa amma ita a wannan lokacin tata zuciyar ce ta ke rawa, so take itama ta taya shi kukan, irin kukan da yake yi, so take ta taya shi ko yaya ne, ko da sau ɗaya ne. Zaytuna dake kusa da Boɗejo ta taso cikin kyarmar jiki, ta dawo gabansa ta durƙusa, sannan ta shige jikinsa gaba ɗaya itama nata kukan na ƙara ƙarfi, Turaki yay mata wata runguma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma na riƙe ne da zanin Hajiya Madina da yake jin kamar a lokacin ƙwace musu ita za'ayi. wani tausayi ya ratsa zuciyoyin duk wanda yake zaune a parlon banda zuciyar mutum ɗaya da ke ƙissima tarin abubuwa acikinta. lissafi take, lissafin yanda komai zai tafi, lissafin yanda komai zai warware, lissafin yanda baya ba zata taɓa gogewa ba, lissafin yanda komai zai tafi akan nata tsarin lissafin. **** Komai na ɗakin abin kallo ne, ko da ace baka san kuɗin kaya ba kallo ɗaya da za kai ma ɗakin da kayan da suke cikinsa zaka san cewa tabbas an narka dukiya wajen siyan kaya da kuma tsara ɗakin. ko da ace za'a ɗauki tsawon shekara 10 zuwa sama ba'ai renovating ɗakin ba, ba za'a gane cewar komai da yake ciki ya jima ba. lokacin da Fillo ta buɗe ɗakin zata gyara shi, tsayawa kawai tayi tana mamakin abinda za'a gyara, ina ƙurar da Hajiya Madina ta ke faɗi?, babu, infact irin ƙamshin dake tashi a ɗakin ko ɗakin da ake gyarawa kullum albarka, saboda haka ne tama rasa ta inda zata fara, gani ta ke sai dai ta ɓata ba dai ta gyara ba, dan komai tsaf tsaf, ɗakin yafi ƙarfin basirar gyaranta. amma a hakan dai ta gyara dole, tunda umarni aka bata, kuma sai bayan da ta gyara ne ta fahimci ashe da gasken yana biɗar gyaran. komai ya ƙara zama fes-fes, adon ɗakin dark blue and silver ne, kalar da ta burgeta kuma tasan ta dace da mamallakin ɗakin. a sanda ta gama gyara komai, sai ta shiga binciken abinda ta daɗe tana roƙon Allah yayi sanadiyar shigowarta ɗakin, wannan asirin da akace an saka shi a ɗakinsa, ba ɗakin da yake kwana ba, wannan ɗakin da zai koma da kwana bada jimawa ba, yes taga asirin, ta ganshi a inda taji sunce sun ajiye, ƙasan gadon, a mulmule yake kamar yanda taji sun faɗa, sam ba wari yake ba, wani irin daddaɗan ƙamshi yake yi, irin ƙamshin nan da ba zaka so ka daina shaƙarsa ba, irin ƙamshin nan dake motsa zuciya ta faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa. hasalima da ta ɗauko sai ƙamshinsa ya gauraye duka ɗakin, ya kore ƙamshin air freshner da turaren wutan da ta yiwa ɗakin. tunaninta guda ɗaya ne a lokacin asirin na menene?, to dama asiri yana ƙamshi?, ai tayi zaton asiri wari yake yi?, anya wani bai ganta ba a lokacin da ta laɓe yasa suka faɗi wannan maganar domin a ɗana mata tarkon ɓera?. ta tsorata da wannan tunanin, amma ko menene dai ba zata taɓa barin wannan dunƙulallan abin ya ƙara zama a ɗakin ba balle har Turaki ya kwana tare da shi. saboda haka cikin hanzari ta yunƙura ta miƙe zata fice, kwatsam idanuwanta suka sauka akan takardun da suka faɗo ɗazu da zata shiga ƙarƙashin gadon tace sai ta fito ta mayar da su. ta kama gefen zanenta ta ƙulle wannan abin da har yanzu zuciyarta taƙi yarda da cewar asiri ne, babu ko ɗigon tsoron zai iya cutar da ita, ta durƙusa ta kwashe takardun ta buɗe drower ta zuba su, sai dai cikin rashin sa'a wata takarda me duhu ta faɗo. daga tsayen da take kawai ta tsaya tana kallon takardar, baƙa ce, duk da duhunta hakan bai hana hoton abinda ke jikin takardar bayyana ba. dai-dai take gani ko kuwa gizo ne idanuwanta ke yi mata?, kalmar Tashin hankali dai tayi kaɗan wajen kwatance da halin da ta shiga a lokaci ɗaya. ƙafafuwanta suka tafi a hankali gwiwoyinta na zubewa a ƙasa gaban takardar, waɗannan siraran yatsun nata na rawa ta ɗauko takardar, sai bayan ta ɗauko ne taga ashe harda wata ƙaramar takarda anyi stapling ɗinta ajiki. ƙwayar idonta ta manne akan ƙaramar takardar dake ɗauke da sunan asibitin *As-Salam International Hospital*, Assalam ɗin kawai zuciyarta ta iya karanta mata banda international Hospital ɗin. *Nile Corniche, Athar an Nabi, Old Cairo, Cairo Governorate 4220501, Egypt.* kamar haka address ya biyo bayan sunan asibitin, bin kowanne rubutu ta ke da ido ba don zata iya karantawa ba, har tazo inda ta ke da ilimin karantawar, karatun da ta samu daga wajen Amir, *NAME* zuciyarta ta faɗa, sannan ta ƙara faɗar sunan da ya ke rubuce akan siririn dogon layin da aka zana dan rubuta sunan majinyaci, *MUHAMMAD TURAKI HABIB*. ƙasan sunan kuma wani dogon layin ne da aka rubuta *KIDNEY FAILURE*. A duk cikin tarin rubutukan da takardar ke ƙunshe da su, suna uku zuciyarta ta iya karantawa, As-Salam, Name da kuma Muhammad Turaki Habib. kuma ta ke zuciyartata tayi wani girgiza da karanta sunan nasa, ba kamar ranar farko ba da bata ji komai ba sanda ta karanta sunan nasa. sai kuma ta maida idonta ga haƙiƙanin hoton dake jikin baƙar takardar, ta taɓa riƙe irin takardar nan, wasu shekaru baya da suka wuce, kamar haka ne ba zata manta ba, likita ya basu takardar dake ɗauke da hoton ƙodar da akayi. _"tana ɗauke da ciwon ƙoda"._ ba zata manta ba haka likita yayi musu bayani a wancan lokacin. allon ƙirjinta ya girgiza lokaci ɗaya, me hakan ke nufi kenan?, shima wanda sunansa ke rubuce ajikin wannan takardar yana ɗauke da irin ciwon da ya kashe mata Adda?. bata san lokacin da ta shiga girgiza kai da sauri ba, ai bata manta ba ta faɗa a baya, anyi an gama, ba zata ƙara rasa wani mutum da ya samu gurbin motsi a zuciyarta ba, kuma wannan alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta. kuma shikenan sai ta shiga rera kuka, zaman durƙushen da bata tashi daga shi ba kenan har zuwa yanzu, tunda ta tuna irin baƙar wuyar da Addanta tasha kafin ta mutu, bayan sun gama sa rai da cewar ta sami lafiya, a wankin ƙoda na arba'in da huɗu(44) da akayi mata, ashe tsawon lokacin da ta ɗauka tana fama ciwon ajali ne. Hawayen dake bin idanunta ya gangaro ya sauka akan takardar dake riƙe a hannunta, wadda ta tsirawa ido babu ko ƙifce. _"Mutuwa zai yi shima"._ wani ɓangare na zuciyarta ya faɗa mata hakan. a lokacin idan ka ga Fillo zaka iya rantsewa hankalinta ya gushe gaba ɗaya daga jikinta, dalilin ambatar kalmar mutuwa da zuciyarta tayi mata, allon ƙirjinta ya ƙara yin wani duka a karo na babu adadi, wata tsawa ta ziyarci cikin kanta, tsawar da ta haɗe da kiran daya shigo ta cikin wayar ɗakin wadda ke manne ajikin bango. _Idan Ayyukan da suke gabana na ɗaya daga cikin abin da ke hana ni yin typing, to tabbas rashin comment ɗinku shi ne maƙasudin abin da ke saka na ɗauki tsawon lokaci banyi ba...ko da na zo yin typing ɗin ma sai naji banda wannan ƙwarin gwiwar, tunda ko nayi babu masu tarbarsa hannu biyu, saboda haka ku daina ganin laifina, har da na ku laifin...amma idan har kun gyara la shakka nima zan gyara...Ina baran adu'anku akan jarabawar da na kammala a yau don Allah._ [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _nace muku i love you ko na bar kayata?...kai aradu sai na faɗa ko me xaku yi sai dai kuyi😏, idan na faɗa sai na ruga da gudu yanda ba zaku iya kamani ba😝...nace ba *I LOVE YOU MY FANS* 🏃‍♀._ *15* tunda taga Turaki ne ke tunkarota tayi ƙasa da kanta, ta shiga wasa da hannunta, haka kawai kuma sai ta tsinci kanta da mugun faɗuwar gaba, saboda haka a hankali ta shiga karanto innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil. _laifin me ta aikata?._ shine tambayar dake yawo acikin ranta, dan ita dai ta sa ni tsawon lokacin da ta ɗauka a gidan nan bai taɓa ambatar sunanta ba, to amma yau kiran nata na menene?. tana cikin wannan saƙe-saƙen yazo ya wuce ta gefenta, ta ɗaga kai tabi bayansa da kallo tana ganinsa har ya shige part ɗin Boɗejo, sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya me nauyi. maganar Khalil da ta ƙaraji a gabanta ita tasa ta baro da kallonta daga entrance na boɗejo. "ina za ki?". Khalil ɗin ya tambayeta yana kallon hannunta dake karkarwa tana ƙara damƙe box na glass din, ya lura kamar tana so ta hana hannuwan nata karkarwa ne amma hakan ya gagara. tace,"Boɗejo ce ta aikeni ɗakinta zan ajiye mata idon baturenta". Khalil yay murmushi yace,"kema ta koya miki idon bature kenan...to amma me ya samu ƙafarki?". ta ɗan kallesa da mamaki amma sai ta kawar, bayan ta kalli ƙafartata tace da shi,"babu komai". sai kawai ya jinjina kansa yace,"to shikenan tunda babu komai je aiken". ya faɗa yana tsare ƙafafun nata da ido, sai ta tsaya bata tafin ba, ya ɗago ido yaga shi take kallo, da murmurshi ya ɗaga mata gira ɗaya yace,"ehen je ki mana". ya faɗa ba tare daya nuna mata so yake ya ƙureta ba. ta juya zata tafi sai kuma ta ƙara juyowa ta kalle shi, ya ɗauke kansa yana kallon sama as in idonsa ba'a kanta yake ba. tana fara tafiya taji yace,"babu komai?, to shi wannan jan ƙafar na menene?, ko wani laƙanin ne nima a sammin?". ba tare da ta juya ba ta girgiza masa kai bata ce komai ba, ta rumtse ido tana so ta ɗaga ƙafar ya ƙara cewa,"to jan ƙafa dai babu kyau, idan ma dai da kyau to kika ci gaba da janta ƙafarki faso zata yi ki rasa mijin aure, dan babu me kaiki gidansa kina yaga masa ledar ɗaki". bata san lokacin da ta saki dariya ba, ta ɗan waigo tana kallonsa tace,"Hammah Khalil kana da ban dariya". hannayensa a aljihu yace,"ke kuma kina da ban mamaki". tace,"mamaki kuma?". yace,"yes, banda haka ace mutum na ciwon ƙafa kuma yaƙi faɗa kuma a tambaya ya mu sa...to faɗa min, magani kike tsoro ko kuma allurar?". ita kam bata san taya akai ya lura da ita ba tun farko, duk yanda ta dinga ɓoyewa ashe sai an iya ganewa. fuskarta tayi narai-narai kamar me shirin kuka, yana lure da ita da hakan, ya fiddo da hannunsa daga aljihun sannan yace,"je ki kai aiken kizo mu wuce asibiti". ta ɗago ido ta kallesa sai dai bai bata damar magana ba ya ƙara cewa,"ina jiranki a mota". yana faɗin haka ya juya ya bar wajen, ita kuma ta juya ta ƙarasa part ɗin Boɗejon. Khalil ya kira Hajiya Madina a waya ya sanar mata zancen ciwon ƙafar na Fillo wanda itama bata san da shi don tunda suka dawo bata ganta ba. a parlon Boɗejo Fillo ta tarar da Turaki hakimce akan kujera ya zubawa tv dake kunne ido, kallo ɗaya zaka yi masa ka gane kallo kawai yake amma ba don yana fahimta ba, dan gaba ɗaya hankalinsa baya wurin. tunda tayi masa kallo ɗaya bata ƙara ba, a iyakar wannan kallon ta gane cewar yana ɗauke da damuwa, wata damuwa da yake so ya rabu da ita. dole ta gabansa zata wuce kafin taje bedroom ɗin Boɗejo, ta durƙusa a gabansa tace,"ina yini". bata sa ni ba ya amsa ko ba amsa ba, ta tashi ta bar wajen. tana ajiye glass ɗin ta fito, zata fice daga parlon taji muryarsa yace,"ban ruwa". sai kawai ta tsaya tana kallonsa da mamaki, anya kuwa da ita yake?, ba shine rannan yace ko ruwan goran da zai sha ba karta ƙara ɗora hannunta akai ba. "ba kiji bane?". maganarsa ta katseta daga tunaninta, ta ɗago suka haɗa ido da shi, tayi saurin ɗauke nata ta nufi hanyar kitchen, lucky kawai tayi amma ba don tasan nan ne kitchen ɗin ba, har ta shiga kitchen ɗin tana jin idonsa akanta. ta dawo ta ajiye masa ruwan akan table ɗin dake gabansa, har ya zuba ruwan ya sha bata miƙe daga tsugunawar da tayi ba, kamar wadda yace mata tayi ta zama karta ta shi. ƙwayar idonta ta jima akan yatsan ƙafarsa, sai can ta ɗan ɗago kai ta kalle shi, yasha ruwan amma still cup ɗin na riƙe a hannunsa, idonsa a rufe, haka kuma ya kwantar da kansa jikin kujera ya tusa ɗayan hannunsa cikin sumarsa yana yamutsawa. kawai sai taji tausayinsa na gaira babu dalili ya tsarga mata, ta jima tana kallonsa ba tare da saninsa ba sannan ta tashi ta fita daga parlon. zata shiga ɓangaren Hajiya Madina fitilar mota ta hasketa, tasa hannu ta kare tana kanne ido. sai sannan ta tuna ma da maganar Khalil na zasu asibiti, ita kam ai ko me za'ai ba zata je asibitin nan ba. ai dama ta gama ayyukanta, wurin Kaka zata gudu wadda ba zata takurawa ciwonta ba, dan haka da sauri ta ɗau hanya zata tafi sai ga Hajiya Madina ta fito. "au baku tafi ba?". Hajiya Madinan ta tambayeta tana tsareta da ido. tace,"ehh Maama yanzu dai zan tafi, dama nazo zan miki sallama ne". Hajiya Madina ta tsaya tana kallonta, kamin tai tambayar da zata mata sai ga Khalil ya ƙaraso wajen, yana zuwa yace,"ɗauko mayafinki". kamar zatai kuka tace da shi,"Hamma Khalil ai naji sauƙi". baice komai ba Hajiya Madina tace,"me ya samu ƙafar taki dama?". idanuwanta suka yi narai-narai tace,"gurɗewa nayi ɗazu da zan sauko daga bene". Hajiya Madina tace,"ki dinƙa kulawa Fillo, je ki shirya kuje ya kaiki asibiti, duk ƙanƙantar ciwo bama barinsa sai anga likita". ba don tana so ba sai dan ba yarda zata yi, saboda bata son yi mata musu. a mota ta sami Khalil na jiranta, ta buɗe baya ta shiga, nan ma sai shine ya buɗe mata don bata iya ba. ƙamshin cikin motar daya gauraye da sanyin ac ya bata da wani daɗi, ta buɗe ƙananun ƙofofin hancinta ta zuƙe ƙamshin tana jin wani sanyi a ranta. Khalil nata bin waƙar turancin dake tashi a motar, ita dai tayi shiru sai bin titi take yi da ido tana kallon hanya, rabon da ta fito har ta manta, kullum suna wuri ɗaya idan ba wani taro za'ai a masarauta ba shine har da su ma'aikatan ake tafiya, Maijidda ma ta fita yawo itace Yami ke yawan aikenta, ita kam Kaka da ta aiketa ma gwara taje da kanta. a harabar asibitin yayi parking, tayi ƙoƙarin ganin ta buɗe motar da kanta, ta fito sannan ya sakawa motar key. "idan munje ki faɗawa likitan harda ciwon baki na damunki". ya faɗa da sigar zolaya, tai ƴar dariya bata ce komai ba, tabi bayansa zuwa cikin asibitin. wani babban likita ne ya dubata, sai dai tasha kuka sosai saboda matsa ƙafar da akayi, sunan Kaka kuwa ta kira yafi sau biyar. a wani pharmacy Khalil ya tsaya ya siya magungunan da aka rubuta masu yawa harda allurai. tunda suka ɗauko hanyar dawowa Fillo ke jin kanta na wani mugun sara mata, Khalil na kallon duk wani motsinta ta cikin mirrow, sai cije fuska take yi hawaye na sauka a saman kuncinta, bai ce mata komai ba don duk tunaninsa ko har yanzu kukan allurar ne. ita kuwa kanta ke mata wani azababben ciwo, yayi mata nauyi kamar an ɗora dutse, ga shi sai take jin tsoron da bata san dalilinsa ba, ji take kamar ana tsoratata acikin kanta, kuma kamar kiranta ake ana tazo. tasa hannu ta damƙe zanin jikinta, daidai lokacin da Khalil yayi parking a compound. kusan tare suka fito daga motar, ya bata ledar drugs ɗin yana yi mata sannu. karɓa tayi tare da yi masa godiya sannan tayi masa sai da safe. ɓangarensu ta wuce bata wani biya ta yiwa Hajiya Madina sallama ba, tana tafe tana haɗa hanya saboda ganinta dake neman ɗaukewa gaba ɗaya, a yanzu ta manta da ciwon dake ƙafarta, ta ciwon kan kawai take yi. duk da uban hasken fitulu dake gauraye da harabar gidan amma ita wani duhu take gani na daban, ta damƙe kanta haka har ta kai ɗakinsu, kuma sai lokacin ne taji idonta ya washe, ta buɗi baki tai sallama cikin ɗakin. jin yanda tayi sallamar Kaka ta kafe ƙofar ɗakin da ido har ta shigo, tabi ta da ido har ta nemi wuri ta zauna tana jefar da ledan tulin drugs ɗin. sannan ta ƙara fashewa da wani kukan. Kaka ta katse lazimin da take yi tace,"ke Lafiya?". tayi shiru bata ce komai ba. Kaka ta ɗaga murya sosai,"kin san dai bana son shashanci ko Halimatu, menene ya faru?, wani kuskuren kika aikata?". ta ɗago tare da girgiza kanta alamar a'a. Kaka tace,"to menene?, wadda kuka baya yi mata wahala". bata yi magana da baki ba sai nuni ta yiwa Kaka da ƙafarta. Kaka ta kalli ƙafar da ta kumbura tace,"subhanallah garin ya?". da ƙyar ta buɗi baki tace,"nazo saukowa a bene na gurɗe". Kaka ta kawo hannu zata taɓa tayi ƙara tana janye ƙafa tana cewa,"Kaka akwai zafi fa...yanzu ma daga asibiti muke sun ƙara karyani shine kika ga ta kumbura haka, saura kaɗan na mutu Kaka". Kaka nayi mata wani kallo tace,"kice gata suka yi miki...to sannu sai ki daina kukan, ke idan ba'ai miki hakan ba kina zaton zuwa safiya za ki iya motsar kafar ne ma, Allahk dai ya sakawa Hajiya da alkhairi". sai sannan Kaka ta kai idonta kan ledar maganin da ta yasar can gefe, tace da ita,"ledar kuma ta mene?". tana shaƙar majina tace,"wai magani ne". Kaka tace,"wai kuma haka za ki ta shansa ba har sanda Allah zai kawo miki sauƙi". Fillo taiwa Kaka da maganin wani kallo ta wutsiyar ido, Kaka na ganin hakan ta miƙe ta ɗauka ledar tana faɗin,"jefar da magani a bola ai ba wahala yake miki ba, gwara na ɗauke nayi masa guri tun ba kisa anyi asarar kuɗi ba...dan na san kuɗi ne bana wasa ba aka kashe". Kaka ta shige cikin ɗaki da ledar maganin dan yi musu wajen ɓuya. kuma tana shiga aka saki wata uwar tsawa a tsakiyar kan Fillo, ta buɗa baki zata yi adu'a da ihu sai taji ta kasa, ta ya zata kwatanta?, wani irin ciwo take ji acikin kanta da ba zai kwatantu ba, ita ɗaya tasan azabar da take ji, ga gefen cikinta ma da takeji kamar ana caccaka mata allurai. kira kawai take ji acikin kanta, kira daga muryar da bata san ta ko waye ba, kuma muryar da bata taɓa ji ba. _"zo da nisa, maza zo da sauri"_. wannan kalmar ita ake ta faɗa mata, ta kai hannu ƙugunta ta damƙe wannan dunƙulallan asirin da ta ɗauko, kuma kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta miƙe ta fice daga ɗakin. lokacin da Kaka ta fito daga ɗaki sai tayi tunanin ko ta shiga banɗaki ne, hakan yasa bata nemeta ba, har ta girgiza kai tana faɗar Allah ya kyauta raki irin na Fillo, bata san ya za'ai ba idan tazo haihuwa. kuma sai bayan minti goma sai ga Maijidda ta shigo ɗakin neman Fillo, Kaka wadda har ta kwanta a lokacin tace mata,"yo aini nayi zaton wurinku ta nufa, ta shigo tana kukan ciwon ƙafa to nama zaci banɗaki taje, dana ji shiru kuma nace ƙila tayi wajenku". Maijidda ta zauna tace,"bata je ba Kaka". ta faɗa muryarta na nuna rashin jin daɗi. Kaka tace,"ƙila can cikin gidan ta koma, yanzu ai zaki ganta tunda ba can dai zata kwan ba, yanzu haka tayi mantuwar wani abu ne shi yasa ta koma". Maijidda dai tayi shiru bata ce komai sai ɓata rai ta ke, Kaka na kallonta dai bata tambayi ba'asi ba, saboda tasan kwanan zancen, akan dai Fillo ne da basa zama tare yanzu shine take ta yin wannan kumburin. shiru-shiru Fillo bata dawo ba sama da kusan rabin awa, Maijidda lokacin itama har ta fara hamma. ta fara masifar ita wannan aikin bata sonsa sam, zata sa Yami ta nemi wata yarinyar akai musu a ƙyale mata ƙawarta. Kaka tace,"to wai ke Maijidda iyaka akayi miki da shiga cikin gidan da ba za ki dinga binta ba ko me?, ba sai ma ku dinga yin aikin tare ba". Maijidda tace,"ni bana son shiga wurin da za'ake min gani gani Kaka, tunda sun san basu ɗaukeni aiki ba ina zuwa za'a fara min tambayar yanda Uwata ta haifeni". Kaka tace,"aiko dai kin yiwa Hajiya sharri dan ba haka halinta yake ba...zaman jira ne kuma sai kita zama karki yi bacci har sai ta dawo, waya san ma ko acan zata kwana tunda har ta kai wannan lokacin...to ni dai na kwanta sai da safe". Maijidda dai tai zaune jugum tana sauraron radion Kaka dake kunne, har lokacin da gidan radion suka tashi a aiki. daga ƙarshe dai data gaji da jira ta tabbatar Fillo ba dawowa zata yi ba ta tashi ta rufe ƙofar ɗakin sannan tabi Kaka ɗakin ta kwanta itama a inda Fillo ke kwanciya. ƙarfe sha biyu da minti goma sha biyar na dare a lokacin, motar Turaki akan hanyar da bai san ya akai ya biyo cikinta ba. hanyar tayi duhu dulum sai haushin karnuka dake tashi. gefe da gefen hanyar shukoki ne na masara da shinkafa da alama dai gonaki ne a wajen. ya rasa me yake damunsa gaba ɗaya, shi dai yana zaune yaji kawai yana so ya fito yasha iskar gari, kuma da har ya wuce Lambu sai ya koma ya ɗauki key ɗin motarsa ya fito. da farko gidan Mai Martaba yaso ya nufa, sai kuma zuciyarsa ta sauya masa ra'ayi, ya dinga bin titina yana sauka daga wannan zuwa wannan. tuƙin kawai ba dan ya san inda hankalinsa da tunaninsa yake ba, shine har ya shigo wannan layin da bai san ina motar ta kawosa ba, dan ba shi ya kawo kansa ba.. wuri ya samu yayi parking ya fito ya jingina da jikin motar yana fuskantar inda shukar shinkafar take, idonsa akan Shukar yake amma ba ita yake kallo ba, ba kuma tunani yake yi akanta ba, wucewar minti goma ya kalli agogon wayarsa yaga ƙarfe sha biyu da rabi a lokacin. sai kawai ya buɗe motar ya koma ciki, ya kuma nausawa cikin gonar ba tare da tsoron daren ba. driving ɗin yake with high speed kamar me shirin barin gari, ba ganin gabansa yake da kyau ba a lokacin duk da fitilar motar daya kunna. yasa hannu a rigar kujera zai ɗauki glasses ɗinsa sai ya tuna ɗazu da zai karanta jarida yasa Nihal ta ɗauko masa. yay guntun tsaki kawai, jin komai yake babu daɗi, cikin kansa kamar babu komai, kamar ma ba'a cikin duniyar yake ba. da hakan yasa hannu ya daki stearing da ƙarfi, horn ya kama nan wani Kare dake gefen wata bishiya ya tashi da gudu ya tsaya a tsakiyar hanya, ganin hakan yasa Turaki ƙara danna horn da ƙarfi, nan karen ya bar wajen da gudu. tsaki kawai yake jerawa, ya jera yafi ƙarfin ƙirgen yatsu, bai san meke damunsa ba, bai san meke masa daɗi ba, bai san me zaiyi ya samu salama ba. kawai sai ya tsinci idonsa da haska masa wasu shafuka acikin al-qur'ani, da haka kuma zuciyarsa ta fara karanta abunda ƙwayar idonsa ke haska masa. sannu a hankali yaji yana samun relief, nan ya kai hannu ya kunna alqur'ani, ƙira'ar Shuraim ta fara tashi acikin motar. ba tare da ya sani ba, haka kuma ba tare daya ankare ba yaji ya daki abu. gabansa ya faɗi, bakinsa ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, duhun idanunsa ya washe lokaci ɗaya, yayi mugun taka burki babu shiri ganin yana neman bi ta kan abinda ya buge wanda bai san mene ba a lokacin, ƙarar taka burgin ya bada wani ƙara ƙuuuu, tunaninsa ɗaya ne wata dabbar ya kaɗe. sai dai me zai faru?, a lokacin daya fito daga motar cikin hanzari sai kawai yaga mutum yashe a ƙasa cikin jini, macece, amma kamar ba mutum ba haka zuciyarsa ta faɗa masa. saboda haka kamin ya kai ga tsugunawa gaban wadda yake da tabbacin ta riga ta zama gawa sai daya kalli ko'ina da ina, yaga babu kowa kuma babu alamun kowa, sannan ya tsuguna yana mai jin fargabar kai hannu ya taɓata. bakinsa ɗauke da tarin adu'oi yasa hannu ya juyo da ita daga kifen da take, jini duk ya wanke mata fuskarta, babu ta yanda za'a ganeta. ya janye gashin kanta daya baje akan fuskar. ya ƙara furta innalillahi sannan ya kama hannunta wanda yake a damƙe kamar ta riƙe wani abu, ya taɓa yaji artery ɗin wurin na motsi. ya sauke ajiyar zuciya, ji yayi kamar yayi hamdala a lokacin. kansa ya ƙulle da tunanin ma me zai yi, kuma tana ina zai fara, kuma me ya kamata yayi. yana riƙe da hannun tsawon wucewar wasu daƙiƙu sannan ya miƙe da sassarfa ya buɗe bayan motarsa, ya kunna fitilar motar sannan ya dawo ya ɗauketa ya sakata a motar, yarinya ce ba wai babba ba, hannunta guda ɗaya ya sauka akan kafaɗarsa, ya ɗauke yana kallon hannun nata da yake a damƙe. ƙwayar idonsa ya tsaya cak a kanta, wacece?, me ta fito yi a irin wannan lokacin?, daga ina ta ke?. zuciyarsa ta ƙara ɗarsa masa anya kuwa mutum ce?, sai yayi saurin ɗauke idonsa daga kanta ya sauke ajiyar zuciya. ya rufe bayan ya dawo mazauninsa yana ƙara volume na karatun daya kunna. yana kunna motar ya ɗauki wayarsa ya kira lambar Hajiya Madina, dai-dai lokacin daya hau kan titi ta ɗaga wayar. muryarta tattare da tarin bacci ta kira sunansa tana mai mamakin kiran nasa a irin wannan lokacin ƙarfe ɗaya na dare. daga ɓangaren da take ta miƙe zaune akan gadonta cikin faɗuwar gaba ta kunna bedside lamp. "Hammansu". ta kira sunansa cikin wani amon sauti da bata san tana da shi ba. a wannan lokacin Turaki kamar zai yi kuka, ya juya baya ya kalli yarinyar sannan muryarsa dake ɗauke da tashin hankali yace,"Maama na kashe rai". "what?, ban ji da kyau ba Hammansu". tayi maganar a ɗage tana durowa daga saman gado babu shiri. "Maama ban san ya akai ta shigo gabana ba, its like kamar jefota akai". a rikice yay maganar kamar yanda yake a rikice. Hajiya Madina da ta faɗa toilet tana wanke fuska don ta wartsake daga mafarkin da take tunanin tayi tace,"kana ina Hammansu?". yace,"ban san inda nake ba Maama, ina dai kan wani titi. har yanzu banga wani wuri dana sa ni ba, banga asibiti ba ko ɗaya Maama...kamar da sauran ranta ina tsoron karta ƙarasa mutuwa". muryar Hajiya Madina a ɗage tace,"wai wacece ne? kuma me kake so ka faɗa min?". ya ƙara juyawa ya kalli bayansa sannan yace,"accident nayi Maama, kuma ban san wa na kaɗe ba". tace,"na shiga ukuna, to da yaushe ka fita daga gida ban sa ni ba?, daka fita ma ina zaka je me Babban suna?". ya kulle idonsa sannan yace,"Maama duk ba wannan ba, bana so ta mutu ta sanadina, bana cikin hankalina wallahi ban san lokacin dana kaɗeta ba, na kasa fita daga inda nake, kamar ma na bar garin gombe gaba ɗaya". Hajiya Madina ta zube a gefen gadon da ta ke ta fashe da kuka. wucewar daƙiƙa biyu ta sauke numfashi tace,"ka nemi wuri kayi parking, ka kunna datarka...zamu bi location ɗinka yanzun nan...kai ta biya innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zaka samu mafita kamin ƙarasowarmu insha'Allahu, take care kaji, kama kashe motarka kawai". yayi shiru bai ce komai ba. ta katse shirun da cewar,"Hammansu kana jina?". idanuwansa a rufe yace,"Maama idan ta mutu fa?". yay maganar da tsananin rauni. tace,"i beg you stop negative thinking, ba zata mutu ba da yardar Allah, gamu nan tahowawa". tana faɗar hakan ta kashe wayar, tabi layin Khalil da kira, kira na farko dana biyu duk bai ɗaga ba sai ana uku, cikin bacci ya kira sunanta. tunma bai ƙarasa faɗar sunan ba tace,"Khalil ta shi a barcin nan muna cikin tashin hankali, tayar da mota gani nan". Allah ya taimaka Khalil baida nauyin bacci, yana jin haka ko tambayar ba'asi bai jira yi ba ya diro ya zira jallabiyarsa ya fita. Hajiya Madina ma zani ta ɗaura akan kayan baccinta sannan ta zura hijabi ta fito da warikan takalma, sai salati ta ke yi. *Please Vote, Comment and Share* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *14* Fillo tasa hannu ta goge hawayen dake fuskarta, ta ɗaga kai tana bin wayar dake ringing da ido, tunani takeyi akan taje ta ɗaga ko karta ɗaga, ɗaya ɓari na zuciyarta ya rinjayeta akan taje ta ɗaga ɗin. saboda haka ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta a mace, bata ma ko iya ɗaga ƙafa sai janta take yi har ta ƙarasa inda wayar take manne a bango. ta kai hannu ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina ta kaɓe abinda ke jikin zaninta sannan tace,"Fillo". jin muryarta acikin wayar yasa Fillo saurin saita natsuwarta, sai da ta gyara muryarta sosai sannan ta amsa kiran. "Na'am Maama". Hajiya Madina tamkar tana kallonta ne a lokacin, don tana jin muryartata tunaninta ya bata kamar da wani abu, apple ne a hannunta a lokacin, amma cikin wani irin zullumi ta ajiye tana tambayar Fillo,"kuka kike yi?". Fillo ta haɗiye wani abu sannan ta ƙara gyara muryarta tukunna tace,"a'a Maama". Hajiya Madina tace,"but how comes naji muryarki some how?, wani abu ya faru ne?, ko ba kya jin daɗi?". ta jero tambayoyin ga Fillo muryarta na fita da sautin dake nuna damuwa da kulawa. kamar tana gabanta ta girgiza kanta tace,"a'a Maama lafiya lau". ta faɗa cike da mamakin yanda akai Hajiya Madinan ta gane kuka acikin sound ɗinta farat ɗaya, dan har sai da ta kai ga ta kalli wayar ko dai tana kallonta ne. Hajiya Madina ta ƙara cewa,"tiles ɗin nan yana da tsantsi sosai i forgot to tell you that, Allah yasa ba faɗuwa kika yi ba wajen yin mopping?". duk da cewar bata fahimci ɗan guntun turancin ba amma ƙarashen maganar ya fahimyar da ita dukkan maganar. tace,"a'a Maama nayi takatsantsan, har na gama ban zame ba". Hajiya Madina tace,"to yayi kyau, kin gama aikin?". tace,"ehh yanzu nake shirin rufe ɗakin". Hajiya Madina tace,"me amsar saƙon da na baki yazo yana ta jiranki, kije ki kai masa sannan ki ƙarasa aikin...muma mun kusa dawowa muna jira Boɗejo ta shirya ne tare zamu taho". tace,"tom Maama Allah ya dawo daku lafiya". da haka wayar tasu ta katse, Fillo tabi wayar da kallo tana jin son Hajiya Madina har cikin ranta, a iya ɗan zaman da tai ta gama karantar matar, zata rantse duk wanda ya faɗi aibun Hajiya Madina to ɗan hassadarta ne. macece da bata da ɗagawa ko kaɗan, bata tunƙaho da arziƙinsu, bata wulaƙanta talaka, bata da ƙasƙanci, kowa nata ne, kowa ganinsa ta ke ɗaya suke, kowa sonsa ta ke yi, mutumta duk wanda yake tare da ita takeyi babu tozarci. ƙasa ta duƙa ta tattara takardun ta mayar cikin file ɗin da suka faɗo, sannan ta mayar cikin wata drower daban da wadda suke ciki da. ta fita daga ɗakin jiki a saɓule, da ƙyar ma take yin tafiyar tamkar me ƙarancin jini a jiki, tana saukowa daga upstairs ɗinne cikin tsautsayi ta gurɗe ƙafa. bakinta ya furta bismillah kafin ƴar ƙarar da ta saki ta biyo baya. cikin jin zafi da raɗaɗi na lokaci guda ta riƙe ƙafar tana cije fuska. gurɗewar ba ƙarama bace, dalilin da yasa idanuwanta suka cika da tarin hawaye kenan, wani sabon kukan ya ƙaru akan wanda zuciyarta bata gama yinsa ba, sai da ta ɗauki kusan 4minutes sannan ta tashi ta sauko da ƙyar sai ɗingisa ƙafar takeyi, sai da ta kashe light na parlon tukunna ta bar side ɗin. a ƙofar ɗakin me gadi ta tarar da mutumin, baƙi ne kamar yanda Hajiya Madina ta sanar mata, yana da curar ƙasumba, fuskarsa kuma sam babu fara'a. me gadi dake jin radio ganinta yasa shi yin murmushi, ta rissina ta gaishe shi ya amsa mata yana tambayarta ya aiki, ta amsa masa da lafiya. sannan ta tsuguna a gaban mutumin da ko inda take bai kalla ba tun zuwanta, bata sani ba ko haka yake ko kuma ita yakewa hakan dan ta ɓata masa lokaci oho. "ina yini". ya kalleta ta wutsiyar ido, kamar ba zai amsa ba can kuma yace,"lafiya". ta fito da hannunta daga cikin hijab wanda ke ɗauke da file ta miƙa masa tace,"ga shi wannan tace a baka". sai da yayi mata wani kallo kafin ya warta, dan ba zata kira hakan da karɓa ba sai dai warcewar, hakan kuma ya ɓata mata rai, ta miƙe cikin ɗaurewar fuska. tafiyarta zata yi, ba zata ƙara ko da ɗigon minti anan ba, cewar ita ƴar aiki ce hakan ba yana nufin a dinga wulaƙantata ba. ta sani ita ba wata bace, ba ƴar wani bace, amma wallahi tafi ƙarfin wulaƙantawar kowanne kalar mahaluƙi, talauci ai ba hauka bane, dan haka yanda bata wulaƙanci haka ba zata yarda a wulaƙanta matsayinta ba ko da wasa, ita ƴar mutunci ce kuma da darajarta, aiki suke ake biyansu ba wai roƙo suke ba. saboda haka yanda ya warce bai karɓa da arziƙi ba, haka itama zata bar wajen ba tare da ta jira nasa saƙon ba inma yana da shi, ai dama ce akai kawai ta ba shi, to idan ma yana da wani abin faɗa sai ya jira Hajiyar ta dawo ya bata, amma ba dai ita Fillo ta jira saƙonsa ba. abunda bata sa ni ba a wannan lokacin shine, tun yunƙurawar da tayi zata tashi shi kuma ya bar wajen, saboda haka ko da ta kalli inda ya zauna taga babu shi bata yi wani mamaki ba, tayi tsammanin faruwar hakan. tace da me gadi,"Baba kayi haƙuri dan Allah ban miƙo maka abincinka ba, wallahi ina cikin aiki ne sai yanzu na samu sarari amma bari naje na kawo maka yanzu". Tsohon ya washe bakinsa da duk haƙoran da suka ɓaci da goro yace,"laa babu komai ƴar nan, karki damu". juyowar da zata yi kawai taga mutum tsaye a bayanta ya harɗe hannaye a ƙirji, da tsananin mamaki ta ke kallonsa from head to toe, baki buɗe ta kasa rufewa, what would she call the situation she got into ?, tasan dai gefe ɗaya farin ciki ne ya lulluɓeta, to amma ɗaya yanayin fa?. idan tace ba ta kewarsa tayi ƙarya, idan tace bata yi murnar ganinsa ba tayi ƙarya, idan tace bata son ganinsa ta yaudari kanta. cikin wani irin emotions da ta ke jin kanta tayi saurin saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta, murmushi kawai take yi, irin murmushkin nan me faɗi dake fallasa kyawun fuska, wani daɗi ne kawai ke ziyartarta, ji take yi tamkar an mata albishir da kujerar makka. tana son ganinsa, tana ta so ta kasance da shi amma babu dama, lokaci yayi mata ƙaranci tunda ta fara wannan aikin, rabon da ta saka shi a ido tafi sati uku, har Kaka ta gama ciwonta ta gama basu haɗu ba duk da cewar kullum sai yazo dubiya, sai dai idan ta koma Kaka ta bata sallahun saƙon gaisuwarsa daya bar mata. Allah ya sa ni sai yanzu da ta gansa take jin tamkar ta ɗauki shekaru bata gansa ba, kuma Allah ya sa ni a yanzu ji take yi kamar ta rungume shi don tsananin farin ciki, ta ya ya?, ta ya ya zata nuna masa irin jin daɗin da ta yi na ganinsa?. ta ramin yatsunta take hango fuskarsa da gaba ɗaya babu walwala, lokaci guda tasha jinin jikinta, wanne irin bayani zata yi masa ya fahimta?, ko me zata ce ba lallai ya gane ba, abu ɗaya kawai tasan yana ransa shine yanzu ta fifita aiki akansa. sai kawai jikinta yay sanyi, still hannunta na rufe da fuskarta tayi ƙasa da kanta tana jin kamar tayi kuka. bata yi aune ba taji faruwar al'amarin da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu ita da shi, hannunta ya ruƙo, wannan hannun nata da bai taɓa riƙewa ba tsawon lokacin da suka ɗauka tare, me zata yi yanzu?, zata sakar masa hannun ne ya sauke kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi ko kuwa zata hana hakan?, domin gani ta ke kamar ba zata iya haɗa ido da shi ba, kunyarsa ta ke ji sosai, kunyar riƙe ma ta hannu da yayi, tana ganin tamkar sun aikata wani babban alfasha ne. idanuwanta suka ciko da ruwa, ta shiga ƙiftasu a hankali, dai-dai lokacin kuma da ya sauke hannun nata daga kan fuskarta, kallonta yake har yanzu, ya kasa ko da ƙiftawa, ji yake kamar ya ɗauketa, ji yake kamar ya sureta ya kaita duniyar da babu kowa aciki daga shi sai ita. a ƙoƙarinta na zame hannunta daga nasa ta ɗago ido tana kallonsa, kamar ruwa ta ke gani anasa idon shima?, kamar yana so yay kuka ne?, kamar rauni ne take gani a ƙwayar idon nasa?, kenan shima yayi kewarta har irin haka?. shi kuwa kallon da take yi masa gani yake kamar tana masa kallon tuhuma ne, me yasa yazo nan?, me yasa ya biyota?, me yasa bai tambayi izininta ba?, ai tun kamin yazo ɗin sai daya shiryawa amsa waɗannan tambayoyin, ya kuma san zata yi masa rangwame ko da zata hukuntasa. ya rumtse idanuwansa tare da ƙara riƙe hannunta sosai yana murzawa sannan yace,"kiyi haƙuri, na kasa ci gaba da jurewa shi yasa na biyo ki". cikin sanyayyar murya tace,"hannuna". sai taji yace,"ba kuma zan iya sa ki ba Halimatu, wallahi ba zan iya ba. dan Allah ki barni". ba tare da ta ɗago kanta daga sunkuyen ba ta raba hannayen nasu, sannan tace,"me yasa to baka tambayeni ba kafin...". bata ƙarasa ba ya katseta,"naga zan mutu shi yasa, kuma bana so na mutu ban mallakeki ba, ba kuma na so na mutu ba muyi sallama ba...ina ta son ganinki, ina ta so nayi magana dake, amma wannan aikin yabi ya toshe kowacce ƙofa, ita kuma zuciyata sai zafi take tana kukan rashinki, shisa yau nace babu abinda zai min shamaki da ganinki ko da ace fadar sarkin gombe kike aiki yau sai na shigeta na ganki, daga nan kuma nima sai na nemi taimakon a ɗaukeni aikin muke yi tare ina rage miki, ta yanda zanke samun ganinki ko da yaushe...nazo da complete takarduna, please kiyi min iso ko Allah zai sa a dace". ta kalleshi tana murmushi, da gaske yake babu wasa a maganarsa neman aikin yazo. ta kalli takardun ta ƙara kallonsa tukunna tace,"ni babu takardun komai aka ɗauke ni". yace,"arziƙin Kaka kika ci shine dalili". ta juya idanu sannan tace,"ko da babu Kaka ni banga ana ɗaukan me wanke-wanke da shara da takardu ba". yace,"kuma dama na iya wanke-wanke sosai ba". ta saki dariya sosai tana ɗora bayan yatsunta akan bakinta. yana kallonta har yanzu fuskarsa bata gama saki ba yace,"dariya na baki?, Allah da gaske na iya wanke-wanke, kuma ki tambayi Inna kiji, idan na wanke kwano har ƙyalli yake ya dawo kamar sabo, kuma na tabbata na fiki iyawa...saboda haka nasan idan suka ɗaukeni a kwana ɗaya zasu bani ɗaki a gidan nan, wataƙila ma ke su kore ki, kuma dama haka nake so dan wallahi bana ƙaunar wannan aikin". tayi wani murmushin tace,"kaga ni kuma ina sonsa, tunda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri...yanzu haka ma Kaka ta kusa siya min ƙaramin fili da kuɗin da ake ajiyewa". ya ɗan kauda kai gefe sannan ya dawo yana ƙara fuskantarta. "sau nawa kike aikin ruwa?". ta juya idanu sannan tace,"ummm ya danganta, ina wanke kwanuka kuma zanyi girki idan Adda Zaytuna bata yi ba, sannan kuma in wanke banɗaki 6, shikenan". "shikenan!, wannan yawan aikin shi zaki kira da shikenan Halimatu?". ya maimaita kalmar da mamaki. ta ɗaga gira,"eh, ai babu wahala tunda ba ɗauda suke yi ba, nan da nan nake kammalawa na tafi ɗaki na huta...saboda haka ka bar damuwa watarana sai labari". yace,"balle ma kin kusa ki daina, very soon insha'Allahu...nayi mafarki na zama ɗangote". ta waro ido tana kallonsa, ya ɗaga kai yace,"da gaske, wai na koma Ɗangoten Gombe, na aureki mun bar ƙasar gaba ɗaya, muka ajiye Inna da Kaka a saudia mu kuma muka wuce London Honeymoon". tayi far da ido ta maimaita kalmar, "Honeymoon, kamar na taɓa jin wannan kalmar amma na manta aina". "zaki ma santa ne lokacin da mukayi aure, Allah Halimatu na aureki da Uwar kuɗina a yawon shaƙatawa kawai zamu ƙare rayuwarmu, wani banzan aikin gida duk ba za kike yi ba". tasa hannu cike da kunya ta rufe fuska,"ni fa yarinya ce nace ka daina faɗa min kalmar aure". yay mata harar wasa yace,"kin manta ɗazu kika zo duniyar...ai na tabbata a karatun aure babu wanda ba ki sani ba sai dai ki raina min wayo, sai kace ba aminiyar Maijidda ba". ta danne dariya tace,"me kake nufi da Maijiddan?". yace,"oho". haka sukai ta hira ba tare da sun san lokaci ya tafi ba, Fillo sam ta manta ma a inda suke, sai da mai gadi ya ankarar dasu. cike da kunyar mai gadin ta bar wajen dan idan ta biye ta Amir ba zasu tafi haka ba, yana faɗa mata wai yau subscription zai yi. bin ta yayi a baya yana ta murmushi, tsaye ya sameta a gate ɗin da zai shigar da kai ɓangaren ma'aikatan gidan, tana ta jan yatsun hannunta kamar yanda hakan yake sabonta ne. ya jingina da ƙofa yana kallonta yace,"wai kuɗi kike lissafawa a jan yatsun nan ko me?". idonta na ƙasa ta jinjina kai,"ehh kuɗin ɗangoten Gombe nake ƙirgawa". yay murmushi yace,"Allah ya amsa". itama tace,"amin". sannan ta kalli yanayin garin da magriba ta ƙarato tace,"muyi Sallama su Hajiya na kan hanya, kuma akwai sauran aiki gabana". yace,"aikin me?". tace,"Adda Samha ta bar min guga kuma tana da yawa, gata bata da sauƙi mafaɗaciya ce". "barkono ce ita?". tace,"kafi barkono in kaji ana faɗa". ya kalli agogonsa yaga har ƙarfe shida da minti goma, ya sauke numfashi sannan yace,"to sai yaushe?". daga yanda yay maganar sai yay mugun bata tausayi, itama ba dan tana so zasu yi sallamar ba, lokacin da bata fara aikin ba ai babu ruwanta da wani kallon lokaci, ko zasu kwana suna shan soyayyarsu babu mai katse su. "kawai zance banda lafiya kaga zan huta ranar". ya ɗan zaro ido waje yace,"a'a bana so kiyi ƙaryar ciwo, kawai dai zan ƙara dawowa". ya faɗa yana jan ɗan cif-cif ɗin gemunsa. "a'a ni kam ban yarda kazo ka ban kunya ba". ta faɗa tana kama gefen hijabinta. yace,"ohh kina jin kunyar kar suga saurayinki ba ɗan gayu ba kuma talaka ko?, alhalin ke me kyau ce". tayi saurin girgiza masa kai yanayin fuskarta na sauyawa,"ko kaɗan ba haka bane, dan Allah karka ƙara wannan tunanin Amir, ba zanji kunyar nunaka a koma ina ne ba wallahi, kai nake so ba gayunka ko kuɗinka ba, kuma so nake maka na tsakani da Allah". tayi naganar kamar zata yi kuka. "bance ki zubar min da hawayenki ba, kin san suna da tsada...na faɗa ne dan na zolaya, kiyi haƙuri". tai knodding kanta kawai, kamar ba zasu yi sallamar ba, sai da tayi da gaske tukunna sukai sallamar ta juya ta tafi, kuma tana cikin tafiyar ne ya dakatar da ita da tambayar me ya sami ƙafarta, dan a ɗazu bai lura ba sai yanzu. tace masa babu komai tsayuwar da sukai ne yasa ƙafar yin tsami, ba don ya yarda ba sai dan karya takura mata ya ƙyaleta. sai bayan isha'i mutanen gidan suka dawo, bata ma san sun dawo ba saboda lokacin tana ɗakin ƴan aiki zaune cike da kewar Kakarta, yanza basa yini tare ko kaɗan, da dare yayi sai safiya ta taho aiki. tayi zurfi cikin tunani taji wayar ɗakin na ƙara, tana ɗagawa taji muryar Zaytuna na cewa da ita,"kina ina ne?". tace,"laa Adda kun dawo, banji ƙarar mota ba". Zaytuna tace,"to kizo". ta ajiye wayar ta miƙe tana jan ƙafar dan sam bata so a gane ciwon dake ƙafarta. Boɗejo kawai ta samu a parlon, ta ƙarasa ta tsuguna ta gaisheta. sannan ta tashi zata hau upstairs, Boɗejo ta tsayar da ita. "kinga ke ƴar nan zo kai min idon baturen nan nawa ɗakin kwana na". Fillo ta rissina ta karɓa, Boɗejo ta kalleta tace,"ke kuma zuwan yaushe?". tace,"ban jima ba". "Allah sarki, to sannu Allah yayi miki albarka". Fillo tace,"amin". Boɗejo tace,"to ɗakin nawa kin sa ni ne?". Fillo ta girgiza kai alamar a'a. Boɗejo ta ɗora ƙafarta kan tumtum ɗin dake ƙasan carpet tace,"can ɓangaren ƙarshe nake kusa da su Turaki, nan suka wullani wallahi daga ni sai halina, kamar ba saurauniya ba ada". ta jefa wata choculate a baki ta ƙara cewa,"ai da mijina shine sarkin garin nan, to daya rasu ne kuma ɗana Habibu ya hau kan kujerar...kin ganni kamar ban haɗa jini da sarauta ba ko?, wallah bata dameni ba in faɗa miki ƴar nan, banda ma dai Allah ya ƙaddara da hakan ai bata faru ba, shi yasa ko ƴar izzar nan ma ta masu sarauta banda ita, sha'anina kawai nake ba zan iya takura kaina ba wallahi, ina dalili. me gidan nan aini ya biyo, idan kika gansa ba kyace Yarima ba, shi dai Habib ɗin dama da kin gansa kinga wanda sarauta ke yawo a jininsa, aishi wannan Yaron na gidan nan yayo, umm Turaki ba wallahi kam...sauran yaran Ibrahimu da Samir za ki gansu kamar ƴaƴan tsintuwa". Fillo dai murmushi take tayi, taji sosai tsohuwar ta burgeta. "ba kya magana ne?". Fillo ta girgiza kai tace,"a'a ina yi Hajiya". Boɗejo tace,"auyo ni fa nace ai da an banu...ba ki da magana dai ina ce ko?, dama ai ba kiyi kama da sauran ƴan aikin ba iyayen zuba kamar tsohuwar kanya, wallah na faɗa miki su nan suke zubewa su sakani gaba inta basu labarin masarauta wai suna so, ita surukar tawa tayi ta jin haushina, itama wannan ƴar Samha taita ɓata rai wai ita ba haka ƴan sarauta suke ba, to ni dai basu isheni kallo ba ma dan bana bi ta kansu, ina dalili ka takura kanka akan wata banzar aba sarauta". Fillo tayi murmushi me sauti still dai bata ce komai ba, haka kawai taji tana so ta ɗauki lokaci tare da tsohuwar suna hira. sai yanzu Boɗejo ta bata glass ɗin dake cikin box ɗinsa tace,"idan kinje sai kin kunna fitilar ɗakin dan ba lallai bane an kunna min, tunda me ta'adin Sameer baya nan can muka baro shi gidan Hakimi...akan mudubi kawai zaki ɗora min shi kinji ki riƙe da kyau kar ya fashe, na huɗu kenan da Habib yasa akayo min shi daga dubai, da yake acan ake duba min lafiyar idon". Fillo tace,"to Hajiya". Boɗejo tana kallonta sosai tace,"a'a wallahi sunana Rumana ko kuma kice min Boɗejo kamar yanda jikokina ke kirana. ina wani batun Hajiya anan salon dai a ƙarawa mutum jin kai, ai da Hajjah suke ce min, Mai Martaba na rasuwa na rufe ido nace ko Rumana ko wani sunan, to shine fa baturen yaron nan ɗan gidan sarki Habib ya saka min Boɗejo, da ike shi ne jikana na farko, kai izza acikin yaron nan kamar ba zai taka ƙasa ba". tana faɗar baturen yaro Fillo ta gane Yarima Abbas take nufi. "kema ɗakin kwanan masu aikin kike?". ta girgiza kanta,"a'a wurin Kakata nake". "can da nisa ne kenan?". "a'a Boɗejo nan ɓangaren ma'aikata, nan muke da zama". Boɗejo tace,"auyo ce min zaki tsaffin bayina ne ku, to ai shikenan dama ce nake nan kike kwana nace to kizo ɗakina mu kwan tare dan sosai na yaba da hankalinki wallahi". Samha ta faɗo ɗakin rai ɓace, tana jifan Fillo da wani irin kallo tace,"ke dan Uwarki ina aikin da na saka ki?". maimakon bata amsa sai kallo da Fillo ta bita da shi, cikin ranta tana maimaita dan uwarki, kalmar da ta jima bata ji an faɗa mata ba. "ba magana nake miki ba?". Fillo ta rufe ido tana jin zuciyarta na suya sannan ta buɗe tace,"Adda Samha ai nayi". "kika yi a gidan uban wa?. bance miki acikin trolly za ki jerasu ba, gobe da asuba zan bar ƙasar". sai taja tsaki tace,"ni ba'a taɓa bagidajiyar ƴar aiki ba sai akanki wallahi, to minti uku na baki kije ki kammala shiryan kaya tun ban nuna miki other side of me ba". a sanyaye Fillo tace,"kiyi haƙuri don Allah, zan gyara yanzu". ta faɗa tana barin parlon, guntun hawayen dake maƙale a idonta ya sauko, a rayuwar nan ko mene zaka yi mata kayi amma karka sako mahaifiyarta aciki, bata so, bata so ko kaɗan. kuma ɗazun sha'afa tayi gaba ɗaya, ta gama gugar sai ta zuba cikin wadrobe tana ta sauri saboda ƙafarta da ke mata zafi, amma tana ta alla alla kafin su dawo taje ta gyara. Boɗejo ta kalli Samha tace,"ki dai dinga bin duniya a hankali, ni wallahi duk kece me ɗaukan duniya da zafi su dai su Zaytuna basu ɗorawa kansu wannan masifar ba...yo Samha kuɗin ubanki ɗin me?, shi ya bawa kansa?, to in gaya miki nan da kika ganni kafin Babana ya zama wazirin Sarki kika ganmu sai kin tsartar da yawu, to amma yau fa?, matar wa na zama kuma yanzu uwar su wa na zama?, kuma wane irin matsayi na taka?...to wallah kaɗan daga cikin ikon Allah kiga ƴan aikin nan da kike narkawa uwar tsawa kullu yaumin sun lula sama ke kuma kina nan ƙasa". "wallahi ba amin ba, wannan ai mugun baki ne Boɗejo". Samhan ta faɗa tana wucewa ta haye sama. a bakin side ɗin su Turaki, Fillo tazo wucewa zuwa part ɗin Boɗejo, Khalil dake balcony a tsaye yana waya idonsa ya sauka akanta, ya lura da yanda take ta ɗingisa ƙafa tana tafiya da ƙyar. ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli adadin minutes ɗin, sannan yace,"please hold on 2minutes". daga haka ya aje wayar nan kan table ya fito. "Fillo". kiran sunan nata ya dakatar da ita daga tafiyar, muryar Kalil taji, amma ko da ta juyo maimakon ta gansa sai taga Turaki na tunkaro inda ta ke. *Please comment, Share and Vote pls.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _avoid any mistake plss🙏._ *16* *Shongom LGA, Gwandum, Yabayo village.* rubutun da map location ɗin ya zana kenan ajikin wayar dake riƙe a hannun Khalil. with high speed yake drving motar kamar zai tashi sama. adu'a yake cikin ransa Allah ya kaisu lafiya, idan ba haka ba za'a iya samun gagarumar matsala a wannan tuƙin nasa, saboda kukan mahaifiyarsa dake gigita hankalinsa da tunaninsa, da kuma tunanin halin da ɗan'uwansa, Yayansa mafi soyuwa a gare shi yake ciki. tunda suka taho kuka kawai takeyi, duk wata magana ta kwantar da hankali ya faɗeta amma taƙi tasiri a gareta, ya rasa me kuma zaiyi, yasan dai ba zata taɓa natsuwa ba har sai sun isa inda take da buri, to amma atleast yana so ta tsayar da wannan kukan nata ko dan ya samu yayi tuƙin nan lafiya. ya ƙara kallonta a karo na babu adadi yana jin zuciyarsa na tsinkewa, ya cine fuska ya wani daki stearing da mugun ƙarfi, kamar ya fasa ihu haka yake ji. shi amsar ma da yake so ya sani wai me ma ya fitar Hammansu a wannan salasainin daren?, shin ba ya shiga bedroom ɗinsa yayi masa gud night ba, ya tarar kuma lokacin har ya fara bacci. ya sauke numfashi yana barin kallonsa ga tuƙin da yake, a hankali yace da ita. "Maama dan zatin Allah kiyi shiru ki daina wannan kukan, wallahi yana ɗaga min hankali, stearing nan nema yake fa ya ƙwace a hannuna". tasa gefen hinabinta ta goge hawayent tana so ta tsayar da kukan. ta ɗago ta kalle shi idanuwanta duk sunyi jawur sun yi girma. cikin sanyin murya kuma a raunane tace da shi,"to ka kira min Baffan naku". ya rufe idonsa ya buɗe ya sauke agabansa, da zafin nama ya kaucewa bishiryar daya kusa duka. ya furta subhanalla sannan yace,"Maama na faɗa miki insha'Allahu babu wani abu da zai sami Hammah, shima nasan bige mutum ɗin da yay ne yasa ya rikice har yake faɗa miki bai san a inda yake ba...". ta katse shi da cewar,"ni dai idan ba zaka kira min Baffan ba to ka faɗa min, sai na sauka na nemi masu waya su ara min". yace,"to me za kice masa?". ta ɗan kalle shi yana mata abu kamar ba ɗanta ba, sai tayi shiru bata ce masa komai ba. shima shirun yayi, can ta ƙara cewar,"yanzu dai ba zanci arziƙin wayar taka ba Khalill?". buɗar bakinsa yace mata,"kina so ki rasa mijinki ne?". ta girgiza kai da sauri. "to ki haƙura da wannan kiran dan baida amfani, kin san dai Baffa ya fiki shiga tashin hankalin akan lamarin daya shafi ƴaƴansa, yanzu idan kika faɗa masa ya yanke jiki ya faɗi a inda yake fa?, kin san dai yanda ba kya kusa da shi ɗin nan anything can happen. so kiyi haƙuri har mu ƙarasa ai mun kusa zuwa, na kira mijin Inna Falmata yace ga police nan da ambulance zasu biyo mu a baya, dan Allah Maama kiyi haƙuri kita adu'a kawai kinji uwa ta gari". ta gyaɗa masa kai kawai tukunna tace,"to amma baka sauri ka ƙara speed". yace,"to Hajiya Maama yanzu kam za kiga mun isa...ai wurin ba wata tafiya me nisa bane". tana kallonsa tace,"Yabayo fa Khalil". yace,"can ɗin fa, yanzu za kiga munje Maamancy, situation ɗin da kike ciki ne fa yasa ki ganin nisa". ta kuma gyaɗa kai bata ce komai ba, taci gaba da tasbihin da take yi. a wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke ya kwantar da kansa jikin kujerar, abinda zai iya faruwa da shi dalilin accident ɗin nan ba shine damuwarsa ba, ran yarinyar kawai yake ji, baya so ta mutu, idan ta mutu bai san wanne hali iyayenta zasu shiga ba. ya buɗe idanuwansa a hankali ya sauke su akan titin da duhun dare yasa ba'a iya hangen komai. yaji wani abu da bai san menene shi ba ya tsarga masa. ya juya baya yana kallon yarinyar, har yanzu zuciyarsa faɗa masa take da gawa yake tare, ta riga ta mutu, irin jinin da ta zubar ba zai barta ta rayu ba. ya miƙa hannu ya ruƙo nata wanda yayi sanyi kamar ƙanƙanra, hakan ya wanzar da wani abu wai shi tsoro a zuciyar Turaki da bai taɓa ji ba tunda ya girma, babu wata shakka ta riga ta mutu yasan da wannan, shikenan haƙƙin rai ya hau kansa. idanunsa ya kulle ya bawa kujerar duka yana jin kamar ya saka kuka. me ya yiwa rayuwa ne da take neman tayi masa ɗaurin goro, yana ƙoƙarin buɗe nauyayyun idanuwansa yaji an buɗe ƙofar motar, mamakinsa ɗaya ne ta ya aka buɗe ƙofar bayan yasa lock?, wa ya buɗe?, yasan dai 10minutes bata isa ta kawo su Maama wurin nan ba, duk da he dont have comfirmation of where he is, amma yasan ko ina ne nan da nisa yake. kuma kafin yay wani yunƙurin juyo da kansa ga ƙofar sai yaji an daki wuyansa, duka bana wasa ba, irin dukan nan da zai yiwa jijiyar wuya lahani, ya rumtse ido saboda tsananin azabar daya ratsa dukka ilahirin jikinsa. tabbas no any doubt wani ne zai yi attacking nasa, but wanene wannan?, and how comes aka san da wanzuwarsa a wannan dajin?. Allah ya sa ni a situation ɗin nan da yake ciki ba shi da courage ɗin da zai iya encountering ko waye da faɗa don ganin ya ƙwaci kansa. inda ace ba'a irin wannan halin yake ciki ba, da ace baya cikin fargaba da taraddadin mutuwar wadda ya kaɗe, to zai yi fighting da koma waye dan ganin ba'a cutar da shi ba, zai ƙwaci kansa ta ƙarfi even if ace 1% chance yake da shi, and he most win saboda ba zai taɓa bari yayi failing ba wajen kuɓutar da rayuwarsa, not becouse of burin da yake so ya cimma a rayuwa ko kuma saboda baya son mutuwa da wuri, no!, its just becouse of his Mom, Maama na buƙatarsa a raye, idan ya mutu ya barta bai san ina zata saka kanta ba, ya riga ya sani her only hope and wish is su rayu tare da shi. but still bai karaya ba haka yasa hannuwansa biyu ya riƙe hannun wanda ke son shaƙe masa wuya, sai dai inaaa girman mutumin ya shallake tunaninsa, ko ace da kuzarinsa ba zai iya gwada jiki da shi ba. haka yana ji ƙaton mutumin ya shaƙesa da iyaka ƙarfin da numfashinsa zai ɗauke gaba ɗaya, kuma take yaji yana neman shaƙar iska ya rasa, saboda haka kawai sai ya sare ya sallama. yana jin mutumin na magana da wasu ta waje amma bai san me suke cewa ba, sama-sama yake jinsu. so yake yaji muryoyinsu, so yake yaji ko da kalma ɗaya ce tak ta abinda suke faɗa, ta yanda ko da Allah yasa yayi surviving zai iya samun hanyar da zai kama su. daƙiƙa 1,2,3 ta wuce mutanen suna magana, kuma har lokacin jibgegen mutumin na shaƙe da wuyan turaki da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya toshe masa baki da hanci, a taƙaice dai babu ta inda iska ke samun shiga lungs na Turaki. yana ji aka buɗe ƙofar baya, ya hangi siririn mutum ta cikin mirrow ya duƙa akan yarinyar, bai san waye ba dan baiga fuskarsa ba. har yanzu mutanen magana suke da junansu, kuma har yanzu ya kasa jin komai da suke cewa, ya rufe idonsa yana kokawa da cikinsa dake so ya fitar da iska. ƙirjinsa yake jin yana yi masa zafi, ji yake kamar zai mutu, fatansa ɗaya ne a lokacin, kar ya mutu a lokacin sai a hannun Maama, so yake ya mutu yana kallon fuskarta. wasu adadin sakanni suka wuce ta cikin kansa, a lokacin da ya gama saddaƙar da tafiyarsa lahira, a lokacin ne yaji words guda 22 sun shiga cikin kunnensa, kalmomin da suka fito daga bakin siririn mutumin dake riƙe da hannun yarinyar da ya kaɗe. _"yarinyar nan zata yi mana amfani, da sauran ranta. ni ko da ta mutu ma ina sonta a hakan, dole ne zan moreta saboda na kwaɗaitu da ita"._ furucin da mutumin yayi kenan, kuma furucin da ya sami nasarar shiga cikin kunnen Turaki har ya zarce zuwa cikin zuciyarsa ya dunƙule a waje ɗaya. ƙarfi da kuzarin da Turaki yake jin ya rasa na ƙwatar kansa shine yazo masa acikin giftawar sakan ɗaya, wasu manyan jijiyo suka bayyana a hannayensa da goshinsa, tamkar idonsa akan siririn mutumin yake, kuma kamar yasan abinda yake shirin aikatawa, dan haka kawai zura hannunsa yayi ta baya ya damƙi hannun mutumin wanda yake shirin ɗaukar yarinyar, sannan yasa ɗaya hannun nasa yana ƙoƙarin ya cire hannun ƙaton daga bakinsa. damƙar da Turaki ya yiwa siririn mutumin ta shiga ratsa jikinsa, mutumin ya ɗaga murya wajen cewa wanda ke riƙe da Turaki"gayen nan fa bai suma ba, ya riƙe min hannu kuma kamar ba zan iya ƙwacewa ba, bugawa shege bindiga akai". da maganar da yay, da ɗauko bindigar da ƙaton yayi, da samun nasarar da Turaki yay na cire hannun mutumin daga bakinsa, suka haɗe lokaci ɗaya da ƙarar jiniyar motar ƴan sanda dake tashi daga can nesa. babu shiri ƙaton mutumin ya saki Turaki ya falla da gudu zuwa motarsu, shima siririn ya fizge daga hannun Turaki ya falla zuwa motar, ashe basu biyu bane kawai, suna da yawa, kamin Turaki ya zuro ƙafarsa daga cikin motar ya fito tuni sun bar wajen sai tashin ƙurar motarsu. tsayawa yayi yana bin bayan motar da kallo, so yake yaga lambar motar ko zai samu wata shaida amma duhun dake cikin idonsa ya hana. can kuma tunaninsa ya dawo kan yarinyar, dan haka da sauri ya buɗe bayan motar, ganinta yasa shi sauke ajiyar zuciya. ya shiga tattaɓata yana jin kamar ko sunyi mata wani abu ne. ji yake ba zai iya cigaba da jira ba, barin wajen zai yi, idan shi ya cutu ba komai ba ne, amma baya so wani abu makamancin wanda sheɗanin can ke faɗa ya faru da yarinyar, dan haka cikin azama ya koma seat ɗin driver zai tashi motar, dai-dai nan kuma motar Khalil ta ƙaraso wajen, motar police na biye da su a baya, yayin da abulance ke bin bayan ta police ɗin. Khalil na yin parking Hajiya Madina ta fito daga cikin motar, ƙafarta ma ko takalman babu ta barsu a mota, a guje ta tsallaka side ɗin da motar Turaki take har tana bigewa da dutse, ko gabanta bata gani da kyau, burinta ɗaya ne a lokacin taga lafiyarsa, hawayen nata ma nema suke su tsaya da zuba saboda kamar sun ƙare. tunda ta fito daga motar ƙwayar idon Turaki ta tsaya cak akanta, kamar wanda aka sassaƙa haka ya kasa ko da motsawa, kallonta kawai yake, kallonta yake tana tahowa gare shi da irin tashin hankalin da bai taɓa ganinta aciki ba, da wannan tausayin na uwa shimfiɗe a fuskarta, da wannan tsoron na mahaifiyar da bata son rasa ɗanta acikin ƙwayar idonta, yana gani tayi tuntuɓen amma ya kasa motsin da zai fita ya tareta daga faɗuwar, alhalin kuma so yake ya fita ya rungumeta, amma ya kasa, ƙafafunsa sunyi nauyin da ba zai iya ɗagasu ba, sai kawai ya rufe ido wani hoto na can lokacin baya yana haska masa. Hajiya Madina na ƙarasowa ta buɗe motar hannunta sai karkarwa yake. "me babban suna". sunan da ta kirasa kenan a sanda ta buɗe motar ta gansa kamar gunki. kuma ganinsa a hakan sai idanuwanta suka haska mata hoton wani abu da ba zata iya jurar gani ba, haka ma zuciyarta ta ɗarsa mata faruwar wani lamari da ba zata iya ɗaukarsa ba. a hankali ta shiga sauke ƙafafuwanta har gwiwarta ta kai ƙasa, sai kawai ta kifa kanta akan ƙafafunsa ta fashe da wani gunjin kuka me taɓa zuciyar duk wani me sauraro, irin kukan da duk wani me rauni yaji shima sai yayi. sai a wannan lokacin ne Turaki ya iya motsa hannunsa ya kamata ya ɗagata, sannan ya fito daga cikin motar, ya kasa magana haka itama ta kasa, kuka takeyi shima hawayen yake, ya jata zuwa jikinsa yayi mata wata runguma, itama wata runguma tayi masa wadda take daban da tasa, har tsakiyar babban yatsansa yaji rungumartata, irin rungumar da rabon da tai masa ita tun yana yaro. likitocin dake cikin ambulance ɗin suka fito cikin hanzari, da gadonsu suka iso wajen motar Turaki, Khalil ne ya buɗe bayan motar, yayin da nurses suka janyo yarinyar suka ɗorata akan gadon suka yi ambulance da ita. cikin sanin makamar aikinsu wasu nurses ɗin suka shiga goge jinin da yake kan fuskarta, yayinda wasu daga cikinsu kuma suka shiga ƙoƙarin ganin sun saita numfashinta ganin cewar da ranta. duk aikin da suke gudanarwa akan idon Khalil dake tsaye hannayensa acikin aljihunsa, kuma tsananin mamaki ya wanzu a fuskarsa lokacin da suka gama goge fuskarta tayi tas, wa zai gani?, yana gani dai-dai kuwa?, ba yarinyar daya kai asibiti bace ɗazu, Fillo ce fa me aikinsu. sai kawai ya fuskanci wurin da Hajiya Madina da Turaki ke tsaye har yanzu, tana ta aikin tattaɓa shi da kallon ko'ina a jikinsa kamar wadda ta ɗauki tsawon lokaci bata gansa ba. Turaki yake kallo ba Maama ba, kallonsa yake yana recalling back wani moment da Fillo tace masa,"tsoronsa nake ji". haka ta faɗa masa jikinta na kyarma, sanda ya shigo kitchen zai ɗauki abu. tambayarta yayi kawai menene ya faru yaga kamar a tsorace ta ke, shine ta faɗa masa hakan, kuma ko da ya tambayeta me ta ke tsoro sai ta kalli ƙofar kitchen ɗin sannan tasa hannu ta goge hawayenta tukunna tace masa,"Hammah". "me yasa to?, yayi miki wani abunne?". tambayar da yayi mata kenan. amma amsar da ta ba shi ita ta ɗaure masa kai,"babu abinda yayi min amma yace zan cutu idan har ban bar inda yake da rayuwa ba, wai haka yaji zuciyarsa tana faɗa masa...kuma ni bana so mu daina wannan aikin saboda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri, kuma ni wallahi Hammah Khalil banda mugun nufi, bana cutar da kowa sai ƙoƙarin ganin na kare wanda za'a cutar". abunda ta faɗa masa kenan tana hawaye, bai ce mata komai ba a lokacin, kawai ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fice daga kitchen ɗin. kuma yana zuwa ɗakin Turaki ya maimaita masa abunda ta faɗa, Turaki bai mu sa masa ba, hasalima ce yayi masa. "Khalil haka jikina yake bani, haka zuciyata take faɗa min...kamar yanda nake jin Granny zata iya cutuwa idan muna rayuwa a wuri ɗaya, haka nake ji akan wannan yarinyar itama". Khalil ya sauke ajiyar zuciya sanda tunanin nasa ya katse, sukai magana da wani police sannan yayi tattaki ya ƙarasa wurin su Hajiya Madina. yana zuwa ya sanar mata cewar,"Maama DPO yace zamu wuce". ta haɗiye wani yawu sannan tace,"pack anything that is very important daga cikin motar nan ka kaisu cikin taka...sai a bar wannan anan, ko ta zama rabon wani ko kuma in Allah yayi azo a ɗauketa daga baya, tunda babu me drving ɗinta yanzu". Khalil na kallonta da tsananin tausayi yace,"wani police ɗin yay driving ɗinta, ko kuma ni na tuƙa, ku sai ku tafi tare da wani acikinsu". tana kama hannun Turaki ta riƙe tace,"a'a mu tafi dai taren, wani cikin nasu yaja wannan ɗin, sai ka faɗa musu key ɗin na jiki". da faɗin hakan taja hannun Turaki suka yi gaba, shi kuma Khalil ya shiga motar ya ɗauko wayarsa sannan yabi bayansu. hakan akayi, cikin police mutum ɗaya yay driving motar Turaki. sai da suka yi nisa a tafiya sannan Khalil yace,"Hammah kasan wa ka kaɗe?". Turaki bai ce komai ba, kuma sai a wannan furucin nasa Hajiya Madina tama tuna da wata halitta da aka buge, ta manta da wannan batun ta ɗanta kawai take, kuma tana ganinsa lafiya shikenan ta ƙara mancewa da batun gaya mata da yayi ya buge wani. tace da Khalil,"koma wacece fatanmu ta rayu, idan ta dawo hayyacinta sai ta faɗi inda take ko kuma akai sanarwa gidan radio". Khalil yace,"Maama ai wadda muke tare ce, Fillo ce". da maɗaukakin al'ajabi Turaki da Hajiya Madina suka waro ido a tare. tace,"wace kuma Fillo?". Khalil yace,"me aikinmu dai". Turaki dai bai ce komai ba, bai san ya zai kimanta yanda yaji maganar acikin kansa ba. Hajiya Madina tace,"me yasa kace itace Khalil?". ya sauke numfashi yace,"idan munje asibiti za ki gani Maama". *Taraba.* ɗan ƙaramin tsakar gidan share yake tass, sai simintin yay haske kamar sabo. daga ɓangaren yamma wata ƙaramar ƙofa ce ta langa-langa, inda yake nan ne kitchen. wata dattijuwar mata ta fito daga ɗaki wanda yake daga ɓarin yamma ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta shiga. ta sunkuya ta sauke tunkuyar daga kan gawayin da take girki da shi. tana saukewa sai ga ƙaramin yaro da bai wuce shekara bakwai ba yazo wajenta yana faɗin,"Yaya ki zuba min abincin kar mu makara". sunan da suke kiran mahaifiyar tasu da shi kenan Yaya. ta kalli yaron sannan tace,"to Yasir yanzu zan zuba maka, ai kaga sai yanzu na sauke". ta faɗa a sanda ta ke ƙoƙarin ciro farantan roba daga cikin kwandon wanke-wanke. ta shiga zuba farar shinkafa da mai da yajin a faranti daban-daban, tana ta jin labarin da Yasir ke bata na yacca ake duka a islamiyar tasu. bayan ta gama rabon abincin tace da shi,"kira su Maimuna su zo su ɗauka, wannan kuma riƙe namu ne ni da kai, ka riƙe da kyau". ya karɓi filas ɗin abincin ya wuce yana ƙwala kiran Maimuna da Hindu kuzo ku ɗau abinci inji Yaya. yana shiga ɗaki Yaran suma suka fito suka ɗauki nasu, anan tsakargidan suka shimfiɗa tabarma suka zauna suna ci, Yaya na faɗa musu idan suka ɓata wurin sai sun share. hakan yasa Hindu tace da Yayarta Maimuna,"ni dai kinga ban ɓata wurina ba ko". wani saurayi da bai fi 26 years ba yayi sallama gidan, dogo ne sosai kuma ɗan siriri kamar sandar kara, fuskarsa kewaye da saje wanda ya haɗe da gemunsa, ga kuma gashin bakinsa shima da yaywa fuskarsa kyau. yaran suka amsa sallamar tasa suna yi masa sunnu da zuwa, ya amsa musu sannan ya shiga ɗakin kishiyar mahaifiyarsa da sallama a bakinsa. ta gama cin abinci tana siɗe yatsu lokacin, ya zauna kan kujerar parlon da duk taji jiki. ta kalle shi da tausayi tace,"an dawo?". sai dai ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ehh Yaya sannu da gida". tace,"yauwa, ya wurin ɗinkin naku?". yace,"ɗinki babu daɗi Yaya, yanzu ma gudowa nayi saboda kaina da nake jin kamar zai fashe, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina kan ɗinkin ƴan bikin nan". tayi murmushi tace,"to ya za'ai, neman halal da wuya, wataran kuma za'aji daɗi da izinin Allah...amma dai ka kammala musu ɗinkin nasu ko?". Hamid yayi gajeriyar dariya yace,"yanzu ma da su muka gama rigima ai, Suhaila na cewa ba zata ƙara kawo min ɗinki ba balle ranta ya ɓaci, kuma dan nace idan tayi haka ta burgeni shine tayi fushi ta tafi, inaga da kuka ma ta wuce". Yaya ta miƙe tana cewa,"an dai ji kunya wallahi, budurwar taka ma sai kayi mata halinku na teloli". gajeriyar dariya kawai yayi baice komai ba, Yaya ta miƙe tace da shi,"ka ɗauko abincinka kaci ka koma ka ƙarasa aikin mutane, bana son saɓa alƙawari Abdulhamid". ta shiga ɗaki don shirya Yasir, shi kuma ya wuce kitchen ya ɗauko abincinsa. yana cin abincin ne ƙannensa da suka shirya zasu wuce makaranta suka zo suka ce da shi kuɗin makaranta. yana kallon Maimuna yace,"har lokacin biya ya yi?". ta ɗaga kai alamar eh tare da cewar,"shekaranjiya da jiya ma duk sai da aka fito da mu, bamu shiga aji ba". yace,"kuma dan shirme shine baku faɗa ba". tace,"Kawu ai ban sani ba ko baka da kuɗi". yayi mata wani kallo yace,"ina ruwanki da rashin kuɗina, karki ƙara yin irin haka". tace,"to Kawu". Yaya ta fito daga ɗaki tana cewa,"ba laifinta ba ne ni nace su bari ba yanzu ba". yasa hannu a aljihunsa yace,"a'a Yaya to ai zuwan nasu baida amfani kenan tunda ko sunje ba barinsu ake suyi karatun ba, kuma ni ai na sami kuɗi kwana biyun nan". tace,"to Allah ya ƙara horewa dai". ya ɗauki dubu uku ya bawa Maimuna ƴar shekara goma yace,"ungo ki bawa Malam Ado, kice na Yasir da Hindu ne, dan Allah suyi haƙuri su ɗaga ƙafa jibi insha'Allahu za'a bayar da naki". ta duƙa ta karɓa suna yi masa adu'a, sannan Yaya tayi musu adua suka tafi. fitarsu babu jimawa mai gidan Yayi sallama, sallamar da ta hassada faɗuwar gaba a zuciyarsu Hamid. "Shema'u! Shema'u". kiran da me gidan keta ƙwalawa kenan, Yaya ta miƙe jiki a sanyaye ta fita tana cewa,"sannu da zuwa". yay mata wani banzan kallo yana zuƙar tabar dake hannunsa sannan yace,"sai yanzu kika ji kiran nawa ko amsawar ce ba ki ga damar yi ba?". bai jira cewarta ba ya ɗora da faɗin,"mutuniyar banza da wofi kawai, to ki gama rashin mutuncinki wallah idan banga dama ba aljannah dai ba za ki shigeta ba, tunda a ƙasan ƙafata aljannar taki take, kuma har saina ɗaga miki za ki shiga...kuma indai don ta ni ne na rantse sai da ki zama ƴar kallo, kina ganin mata na tururuwar shiga ke kina daga gefe can". *Pls Vote, Comment and Share.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *17* Yaya dai tayi shiru bata tankawa maganarsa ba, idan ma tace zata basa haƙuri wani sabon cin mutuncinne zai biyo ba, to shirun shi yafi alkhairi, but down deep in to her heart zafi ta ke ji, wannan halin na mijinta bata so, ƙaddara dai ta riga fata, ta ɗauki aurenta da Hayyo matsayin wata jarabawa daga ubangiji, kuma tana roƙon Allah ya bata ikon cinyewa. ta mayar da tarin ƙwallar da ta cika idanunta. ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗago ta kallesa tace,"a ɗauko maka abinci?". Hayyo yayi mata wani kallon banza yace,"mayya kawai wadda kare ya cinye zuciyarta, indai haƙuri ne naga Halima ma, dan haka kema muna nan wannan kafirin haƙurin naki zai kaiki maƙurar da za ki bar gidan nan da ƙafafunki. yo guda nawa kuma akayi?, saki dai kike so saboda ki tafi da hujja to ni ba zan sakeki ba dan bana yinsa, musulmin ƙwarai ne ni sam bana son al'arashin ubangiji ya girgiza". Yaya ta girgiza kai kawai tana me cike da takaici, ita kanta ta sa ni haƙuri yayi kaɗan ya barka ka zauna da Hayyo, sai dai darajar ƴaƴa, tun bayan aurenta da shi daya sami biyan buƙatar kansa ya fito mata da asalin halinsa wanda yake ɓoyewa a lokacin aure, ta kuma san asalin waye shi wanda yake ɓoyewa idan yaje neman aure. tunda ta haihu ta bar zamansa ta koma zaman ƴaƴanta, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta a wurin uban da bai san darajar ƴaƴa ba sam, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta su gantale ba, gwara ko Hayyo zai kasheta ta zauna ta kula da su, ko da ace sai dinga gutsirar naman jikinta ne, zatai ta haƙuri tana jurewa har Allah ya raya mata yaranta ta aurar da su, daga lokacin sai ta tafi ta bar masa gidan, ta bar masa Yasir tunda shi namiji ne, kuma tasan zai sami kulawa a wurin Yayansa Abdulhamid. Hayyo ya zuƙi sigarin hannunsa ya feso mata hayaƙin yace,"a fito min da tabarma". ta juya cikin parlon tana sa hannu ta goge hawayenta. Hamid na zaune ya kasa ƙarasa cin abincinsa saboda baƙin cikin da takaicin rashin kyan hali na mahaifinsa, ya kalli Yaya da tsananin tausayi, ya sauke ajiyar zuciya yana tuno da tasu mahaifiyar, itama haka tasha fama, dan zai iya cewa ma har yanzu Yaya bata ɗanɗani baƙar kuɗar da tasa mahaifiyar tasha ba a wurin Babansa. adu'a yake kullum, kuma yasan adu'arsu ta karɓu, lokaci kawai zasu jira sai dai idan ba'a raye, but dole-dole za'a zo time ɗin da mahaifinsu most regret all his past, lokacin da Allah ya shirye shi kenan. ya miƙe tsaye jiki a saɓule ya karɓi tabarmar da Yaya ta ɗauko, yana kallon yanda hawaye ke bin kuncinta zuciyarsa na tsinkewa. muryarsa can ƙasa gudun kar Hayyo ya jiyo shi yace da ita. "Yaya dan Allah ki bar kuka, komai lokaci ne kuma komai yana zama tarihi...kin san abinda zai kuma biyo baya idan yaga kina wannan kukan". ya faɗa tare da goge mata hawayen. tace da shi,"na gode Hamid". yace,"abincin nasa na kitchen ko?". ta ɗaga masa kai,"ehh yana ciki, cikin wannan filas ɗin daka siyo mana da azumi". Abdulhamid ya fice hannunsa riƙe da tabarmar. Hayyo na jingine da jikin bango yana ta zuƙar tabarsa cikin ƙwarancewa da jin daɗi. Hamid ya shimfiɗa masa tabar, Hayyo ya zauna har lokacin bai ko kalli Hamid ba. "sannu da dawowa Abba". kamar yanda ya tsammata dama babu amsa, dan shi zai iya cewa rabon da magana ta haɗasu da mahafin nasa tun azumi wata biyu kenan, haka ɗaya babu siɗi ba saɗaɗa, ko ya gaishe shi baya amsawa, hakana duk maganar da zai yi masa ba zai tanka masa ba. dan haka ya miƙe jiki a saɓule ya nufa soro inda ɗakinsa yake, ya ɗauko ƴar ƙaramar radio sabuwa ya dawo ya durƙusa gaban Hayyo. ya kamo gidan radiyon daya san nan ne zaɓin Hayyo, ya ajiye a kusa da shi. lokacin kuwa ana labaran siyasa, cikin ran Hayyo yaji daɗi sosai, dan shi a rayuwarsa daka masa kyautar kuɗi ma gwara ka basa radiyo, tana saka shi nishaɗi musamman idan labaran siyasa ake. amma ba zai taɓa nunawa Hamid yaji daɗi ba balle ma har wata adua ko godiya ta shiga tsakaninsu. jiya da shekaranjiya da bai saurara shirye-shiryen da yake ji ba duk jinsa yayi kamar mara lafiya, saboda tsohuwar radiyonsa taɓaci tun ranar da akayi wani mamakon ruwan sama, ta shige cikin ruwan daya cika ɗakinsa dalilin zubar da yayi. kuma babu kuɗi hannunsa dalilin ma da har ya ɗau wannan kwanakin babu ita. kuma yasan Hamid ya siyo radiyon ne saboda shi, tunda akan ƴan ƙanan yaran ya sauke ɓacin ransa na lalacewar rediyon, dan duk sai daya bi ya zane yaran, ko yau da safe da zai fita yaga shatin wayar daya tsulawa Maimuna a fuska bai baje ba, amma bai ko bi ta kanta ba tunda ƴaƴa ne da basa gabansa, su rayu ko su mutu babu abinda yay masa zafi, haka suyi lafiya ko rashinta ko a gefen yatsansa. ai yasha faɗawa ƴaƴansa da ku da shegu ɗaya na ɗauke ku, shi yasa bana wani ganinku da ƙima. zai fi muku ma ku nemi wani uban ko kwa ɗanji daɗi, amma a hakan dai Hamid yace masa a hakan kuma muke ƙaunarka Abba, muke alfahari da kai, duk tsanani ba zamu taɓa barinka ba, kuma zamu yi duk iyakar ƙoƙarinmu wajen ganin mun faranta maka, wajen ganin bamu saɓa maka ba. zamu maka biyayya, kuma zamu tsare mutuncinka. acikin radiyon aka sako waƙar ɗan ƙwairo, Hayyo ya kama bin waƙar yana buɗe flask na abincin da Yaya ta aje masa. kamar wanda yaga kashi daya ga shinkafar, amma a haka ya cinyeta tas. da yamma Yaran suka dawo daga makaranta, tunda sukai sallama suka ga Abban nasu a tsakargida suka kama raɓe-raɓe jikin bango. suna mugun tsoronsa, sunfi sakewa idan babu shi a gidan, idanma fita yayi sukan manta da shi. wataran Maimuna ta cewa Yaya ita gwara ma ace bata da Baba akan dai ta nuna Abba ace shine Babanta. a lokacin Yaya taita mata faɗa da cewar kata ƙara jin wannan zancen a bakinta, amma duk da haka Maimuna a makaranta bata amfani da sunansa, sai dai sunan Yayansu, Maimuna Abdulhamid haka ta ke using. *VISION APARTMENTS, Zurich, Switzerland.* a tsaye take a gaban windon parlon, windon dake ɗauke da manya manya gilasai, kalarsa ta haɗe da yanayin yanda hasken garin yake a lokacin. lokacin yammaci ne, yanayin garin na nuna cewa ruwan sama bai jima da ɗaukewa ba. sanyin danshin ruwan na ratsowa ya shigowa cikin parlon, wanda ya gauraye da sanyin ac da kuma ƙamshin dake cikin parlon. hakan ya haɗu ya bada wani sanyayyan ƙamshi me daɗi, kalar komai na parlon ruwan toka ne. sanye take da baƙin wando wanda ya ɗameta, hannayenta dake ɗauke da bangles acikin aljihun wandon, riga ce me ƙaramin hannu milk daga ciki sai ta ɗora rigar sanyi me kauri akai, irin rigar sanyin nan me gashi a hularta. hular ta rufe kusan rabin fuskarta. fara ce sosai, me kyan fuska, hancinta har baka, idanuwanta manya. jelar gashinta ta zagayo ta gefen wuyanta ta sauka akan kafaɗarta, hakan zai shaida maka kitso ne guda ɗaya tal a gashin nata. kallon gilashin windon take tana ganin yacca sauran ruwan sama ke sauka akansa. sam ba haka taso ba, ba haka taso lamarin ya tafi ba, sai da ta rufe ido ta buɗe sannan tace. "ba haka muka tsara ba, ba shirin da muka yi ba kenan. abunda muka tsara shine Turaki zai mutu a wannan ranar kuma a wannan lokacin cikin wannan dajin, lissafin da mukayi kenan, mun lissafa tarihinsa zai shuɗe ne cikin ƙanƙanan lokaci, zamu goge hotonsa da sunansa da duk wani abu daya dangance shi daga wannan zuciyoyin guda biyu...to amma me yasa komai ya rushe?, lissafin da mukai ya hargitse?". da shi take magana, saurayin dake zaune akan kujera yana fuskantarta, fari ne shima, me kaurin jiki, me siririn saje. shekarunsa ba wasu masu yawa bane, ƙananun kaya ne jikinsa blue jeans and red t-shirt long slip, sai facing cap baƙa daya saka. tarin gashin girarsa ya kusa haɗewa, kallonta kawai yake tunda ta tsaya a gaban windon, har zuwa yanzu da take magana da shi. "kina nufin laifina ne kenan?". a zafafe ta juyo ta fuskance shi tana ɗage hular rigar sanyin ta koma baya ne. "ƙwarai laifinka ne, idan da ace ba lusaran mutane kaje ka samo ba me zai sa shirinmu ya ruguje?.". sai tayi shiru taja dogon tsaki sannan tace,"now what will happen next?". har yanzu bai ɗauke ƙwayar idonsa a kanta ba, sai daya miƙe tsaye sannan yace,"shi zai kawo kansa garemu next ba sai mun wahalar da kanmu ba". matashiyar budurwar tayi masa kallon baka da hankali sannan tace,"ta ya?". yay guntun murmushi yace,"rauninsa mana". tace,"like how?". ta faɗa fuskarta na nunawa da rashin fahimta. "Mahaifiyarsa, Maama, Hajiya Madina. ita zamu ɗauke, ita ɗaya zamu ɓatar Turaki yazo garemu da kansa, da ƙafafuwansa ba'a mota ba, da wannan damar zamu yi amfani wajen ganin mun cimma burinmu akansa, burinmu kuma mafarkinmu na ganin baya raye". kamar bata gamsu da hakan ba a yacca ya gani a fuskarta, hakan yasa yayo tattaki zuwa gabanta, ya zagayeta sannan ya tsaya a bayanta. "karki ji komai, babu wata matsala...wannan karan babu kuskure ina da yaƙinin hakan...wancan matsalar da aka samu yaran sun ce unexpected suka ji syring ɗin motar police, banda haka tuni sun gama da shi. kuma kinga muma bamu tsammaci hakan ba, ba ki karanta min da cewar hakan zai iya faruwa ba, da tunda wuri za'a aiwatar da komai...Hajiya Madina itace matsalarmu a komai shi yasa ya zama tilas dole mu fara ɗauketa daga kusa da shi". ta sauke numfashi tace,"kasan mene?, a rayuwa raunin Turaki mutum biyu ne, Hajiya Madina da kuma Zaytuna, saboda haka tunanina ya sauya. zamu fara gamawa da Zaytuna kafin zuwan komai...Zaytuna tana da saurin yarda, tana da saurin sakin jiki musamman ga talaka, dan haka na san ta inda zan ɓullowa lamarin...kaima bance ka tsaya da naka aikin ba". tana faɗar haka ta ɗauki wayarta da ke kan center table, ta nufi hanyar bedroom tana faɗar,"gobe zan bar ƙasar nan". "nima haka". shima saurayin ya faɗa yana me ɗaukar car key ya fice daga apartment ɗin. **** ƙafafun Turaki suka fito daga parlon, sanye yake da wata dakakkiyar shadda aqua colour da tayi bala'in yi masa kyau, ɗinkin boda ne da aikin sama. kansa babu hula sai dai sumar kan tasha gyara sai ƙyalli take yi. duk ya rame, ya fige, fuskarsa ta ɗanyi duhu, idonsa yayi jaa kuma ya faɗa ciki kamar mara lafiya, saboda kawai saka abu a ransa da yayi, yarinyar nan daya kaɗe wadda tsawon kwana uku sai jiya ta farfaɗo, tun ranar da accident ɗin ya faru baya iya cin abinci, rashin bacci da kuma rashin kwanciyar hankali duk sun dabaibaye shi. ya kalli agogon wrist ɗinsa yaga goma harda minti biyu. "Khalil". ya kira sunan Khalil wanda ke daga cikin parlo, ya amsa masa yana faɗin,"gani nan fa". Turaki ya ƙara magana da muryar ƙorafi,"kai indai za'a fita tare da kai sai ka ɓata lokaci". a time ɗin ne kuma Khalil ya fito, suka jera tare zuwa part ɗin Baffa, bakinsu ɗauke da sallama suka shiga parlon, Baffa yana zaune da mijin ƙanwarsa Falmata SS Ƙasim Kurfi. Khalil da Turaki suka zauna ƙasa suka gaishe su. Alhaji Ƙasim ya shiga tambayar Khalil wurin aikinsa. after few minutes Baffa ya dubi Turaki yace,"ya jikin yarinyar da ka bige?". kansa na ƙasa yace,"ban sa ni Baffa, amma dai jiya da daddare likitan yace ta farka after mun baro hospital ɗin". Baffa ya jinjina kai, kamar ba zai ce komai sai kuma yace,"amma dai you supposed to go and check on her, kai ne sanadin halin da take ciki, so alhakin kula da lafiyarta ya rataya a wuyanka na faɗa maka hakan tun ranar dana dawo, bai kamata a tambayeka jikinta ba kai tsaye kace baka sa ni ba...idan ni ne kai ko asibitin ba zan ke iya bari ba". Turaki yace,"dama can zan tafi yanzun". Baffa yace,"tou yayi, kuma idan kaje ka zauna da doctor ɗin nata kaji game da lafiyarta". ya amsa da,"to Baffa". suka tashi zasu tafi Baffa ya tsayar da su, yace da Khalil ya ƙarasa ya buɗe drower dake can wajen tv ya ɗauko masa envlope. few seconds ya ɗauko ya kawo, Baffa ya buɗe ya ciro sabbin dollers ya bawa Khalil, ya karɓa yana jiran cewar Baffan. already Turaki ya kai ƙofa, kiran sunansa da Baffa yayi ya dakata ya juyo, Baffan yace da shi,"kuyi changing nata before ku ƙarasa asibitin sai ka bawa Kakar Yarinya". Turaki yace,"to Baffa Allah ya ƙara wadata". da haka suka fice. bayan sun shiga ɓangaren Boɗejo sun gaisheta sannan suka wuce wajen Maama, a bedroom nata suka sameta, sun ɗan jima wurinta kafin su fito, itama ta bada nata saƙon dubiyar akaiwa Kaka. motar Khalil suka shiga, Turaki ne ke driving, yayin da Khalil ke kujerar gefensa yana karanta jarida, news update ɗin da aka saki akan ASUU strike, tsaki yake taja saboda takaici, yanata ƙorafi akan strike ɗin, gami da tausayawa ɗan talaka da baida yanda zai yi. ko jiya yana zaune Maama ta ɗauki nauyin karatun wasu yara su biyar zuwa turkey, maza uku mata biyu. tunda yake ta complain ɗinsa dai Turaki bai ce komai ba, hasalima tun shigowarsu motar bai yi magana ba, seems like hankalinsa ma baya cikin motar. Khalil ya ɗaga wayarsa da call ya shigo, yayi taking 3minutes yana wayar before ya gama. kuma sanda ya gama ɗin Turaki ya juyo ya kalle shi a lokacin da yake ƙoƙarin yin U-turn. "ina sketch ɗin ne?, jiya kace zaka nuna min muka manta gaba ɗaya". Khalil ya juya baya ya ɗauko takardar, yana nunawa Turaki yanda akayi zanen sabon company nasu da Baffa zai buɗe. yana kallon sketch din yana kuma driving a hakan. yanda akayi sketching ɗin bai yi masa ba sam, hakan yasa shi cewa. "wanne Arch ɗin ne yay wannan zanen?". Khalil yace,"Yahya Ƙosa". yace masa,"why zaka bawa daƙiƙi irin Ƙosa zanen abin arziƙi?, me Ƙosa ya iya?, kai baka ga irin haukan daya zuba ba ne a gidan Hakimi, har kwanan gobe Hakimi complain yake da wannan gidan". Khalil yace,"ni fa Hammah is not my fault, Baffa da kansa ya basa, nawa karɓa ne kawai. Baffa ma so yayi ana kawowa a bawa engineer na faɗawa Maama ai baka gani ba tukunna". Turaki yace,"ka yaga shi kawai dan ba za'ai amfani da shi ba, ji wani shirmen banza fa wai office na accounter a compound na Company...kuma a hakan degree holder yake ko?". Khalil yay dariya yace,"kafa san komai Hammah". tsaki Turaki yayi yace,"ka kira Lawan Shehu kai masa bayanin komai, shine zai yi mana aiki me kyau". sai da suka tsaya a banka sukai changing doller tukunna suka ɗauki hanyar Miyetti Hospital.  Khalil ne ya fara wucewa ward ɗin yayin daya bar Turaki a mota yana waya da Bello Ƙaraye, zai biyosa daga baya. kiran sallar da akeyi a masallaci ya fito da Turaki daga motar, yana waya da Zaytuna a lokacin bayan sun gama da Bello. cikin sauri yake tafiyar yana so ya fara zuwa ward ɗin da Fillo take sannan ya wuce masallaci dan baya son rasa jam'i. yana tafiya yana wayar bai gani ba yayi karo da mutum, wayarsa ta faɗi ita kuma jakar hannunta ta faɗi kayan ciki suka zube kasancewar jakar ba me zip bace. Turaki ya kalla wayarsa daya tabbata ta fashe, tukunna yabi tarkacen jakar da suka zube da kallo, kayan makeup ne duka, sannan ya ɗago ido yana kallon wadda suka yi karon. haƙuri yake niyyar bata, amma ganin yacca take faman cika tana batsewa sai ya ɗauke kansa ya fasa, laifinsa ne amma haƙuri dai ba zai bada shi ba. ganin baida niyyar bata haƙuri kuma baida niyyar tsugunawa ya kwashe mata kaya yasa a gadarance tace da shi,"are you blind da kake tafiya baka kallon gabanka?, kuma hala baka gaji arziƙi ba shi yasa baka san yanda ake bada haƙuri ba. to ka duƙa ka kwashe min kayana ka miƙon jakata". da wani irin ɗacin rai Turaki yake kallonta, imagine wadda yayi ƙanwa ta uku da ita take faɗa masa haka. yarinyar kyakkyawa ce, me hasken fata kamar madara, mai kyakkyawan jiki irin wanda yaji komai da ake buƙata a jikin ƴa mace. kallon farko ba sai ka ƙara na biyu ba zaka san macece da ta samu hutu, gata, da tarin ilimin boko. Kuma ba sai an faɗa maka ba, a maganarta da yanayinta zaka gane ƴar sarauta ce da mulki ya gama ratsa gaɓoɓin jikinta. Turaki ya ɗauƙe idonsa akanta yana me fesar da iska daga bakinsa, matsawar yaci gaba da tsayuwa anan komai zai iya faruwa, saboda haka ya taka da niyyar barin wajen ba tare daya tsaya ya ɗauki wayar ba, baida buƙatarta domin ba zai rasa komai ba tunda yana ajiya a goggle, welcome back na line nasa kawai zai yi. sai dai yana niyyar barin wajen kawai yaga fadawa sun kewaye shi ta ko'ina, one by one ya kalle su, sannan ya ƙara kallon yarinyar, bai san lokacin da wani murmushi ya suɓuce masa ba har sautinsa ya fito. yasa yatsansa ya sosa girarsa, kafin ya shafo wuyansa still da smiling akan leɓensa. a lokacin ne ɗaya daga cikin fadawan ke ce masa,"ka bawa gimbiya haƙuri sannan ka nemi yafiyarta, idan ba haka ba fushin Mai Martaba zai tabbata akanka, kuma zaka fuskanci hukunci daga masarautar kano". shirun bafaden ya haɗe da tayar da iƙama a masallaci, muryar Turaki ta fito da wani amo mai taushi zuwa ga Gimbiya Aisha yace,"zanje nayi sallah, ki jira na dawo zan duƙawa izzarki kamar yanda kike so, zanta baki haƙuri har sai kin ƙoshi". yana faɗin hakan ya wuce ya ɗauki hanyar masallacin cikin sauri, tafiyar da ba zaka ce sauri yake ba saboda nutsuwar da ta shimfiɗu acikinta. Gimbiya Aisha tabi bayansa da kallo tana jin wani malolon abu na tsaya mata a rai, _ta jira shi ya dawo._, haka ya faɗa mata fa, waye shi?, me yake ji da shi?, aina ya samo wannan isar?, ina ya sami ƙwarin gwiwar saka idonsa cikin nata bayan yaji wacece ita?. ta rufe ido tare da haɗiye wani busashshen yawu na takaici, for few minutes ta kalla fadawan dake yin kamar zasu yi mata sujjada ta basu umarnin tafiya. Fillo na kwance kan gado drip na shiga jikinta, drip na kusan huɗu kenan da aka saka mata a yau, daga safiya zuwa yamma. saman room ɗin kawai take kallo, dan su Kaka duk sun tayar da sallah, Maijidda kuma ta tafi raka Amir. hankalinta yana cikin ɗakin amma tunaninta yana waccan ranar da komai ya faru, komai ɗin da har yay sanadin kwanciyarta a asibiti. tunda akayi admiting nata sai jiya ta farka a kwana na uku, mutumin da idanuwanta suka fara gani a lokacin da ta farka likitan da yake dubata. kallo ɗaya tayi masa ta mayar da murfin idonta ta rufe. ƙoƙarinta a lokacin shine ta motsa amma sai taji ta kasa motsa ko da yatsa. Wani irin ciwo jikinta yake yi masa tamkar wadda aka kwan ana duka. da ƙyar ta ƙara iya buɗe idon, jin eyelids nata takeyi kamar an danne su da dutse. ta ƙara sauke idonta akan likitan da har lokacin yake kanta yana gudanar da aikinsa, bata gani da kyau amma gani takeyi kamar ta san fuskar, tana kallo ya ɗauko allura ya zuba acikin drip ɗin dake saƙale. da sauri ta daɗa rufe ido ta juya fuskarta gefe tana sauke numfashi sama-sama acikin tsoro, giftawar second ɗaya ta daɗa buɗewa ta tsaida ganinta a saman rufin ɗakin. ba rufin ɗakinsu bane, aina take?, a hankali ta zagaye room ɗin da idanunta tana so ta fahimci ina ne nan inda take, kuma waye shi wannan mutumin da ta fahimci daga ita sai shine acikin ɗakin. Sai a lokacin tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata. abinda ta fara fahimta shine nan asibiti ne kenan. but taya akayi tazo wajen?, lokaci ɗaya sai hoton fitowarta daga ɗakin Kaka ya haska mata acikin kanta da cikin idonta, a hankali ta mayar da idon ta rufe, nan take komai ya shiga haska mata daki-daki. tasan ta fito daga ɗakinsu, kuma kai tsaye gate ta nufa da ta fito daga ɓangaren nasu, ta miƙi wata doguwar hanya tana ta tafiya ba tare da sanin ina zata je ba, ita dai kawai acikin kanta tana jin ana ce mata ci gaba da tafiya. kuma sai da tazo bakin wani ruwa ta waiga taga ba gini gaba babu gini baya sannan ta fahimci ta baro cikin gida ta kuma baro kusa da gida. fargaba da tsoro suka nannaɗeta, me ya kawota nan ɗin kuma me tazo yi?, ta tsaya tana ta kallon ƙaton kogin, bata san me zata yi ba?, bata san me take kallo acikinsa ba?, a jikinta kawai take jin bata so ta koma gida, kuma zuciyarta na raya mata cewar bata yi sallar la'asar, magriba da isha'i ba, sai dai ba zata yi su ba, dan tun lokacin da ta ɗauke wannan abin daga ɗakin Turaki taji sallah ta fice a ranta. saboda haka sai ta nemi waje ta zauna a gefen kogin, ta zura ƙafafunta cikin ruwan, kamar mahaukaciya kuma sai ta kunce ɗankwalinta ta ajiye a gefe, gashin kanta dake tuje waje guda ya barbaje. har lokacin hankalinta da tunaninta na jikinta amma kamar bata san tana yin komai ba. a gefen wajen ta kwanta inda tayi matashi da ɗankwalinta, bacci take so tayi amma ba zata iya ba, kamar shikenan idanuwanta sun daina rufewa da sunan bacci, tana ji kamar shikenan ta gama rayuwa a Halimanta, kamar zata koma wata sabuwar rayuwar ne. tsawon lokaci taji kamar an mintsineta, hakan yasa ta miƙe zaune a zabure tana karkaɗa ƙafarta acikin ruwan kogin. cikin rawar hannu ta kwance gefen zaninta ta fiddo da wannan abin, ta tsaya tana kallon abun zuciyarta na cika da mamaki, lokacin data ɗaukosa yana da duhu amma yanzu taga yay haske. me kenan?, kafin ƙwaƙwalarta tayi lissafin komai iska ta kaɗa ta kore abin daga kan tafin hannunta ya faɗi ƙasa yana gangarawa gefe ɗaya, da farko tsayawa tayi tana kallon yanda iska ke daɗa kora shi zuwa gaba, daga bisani kuma sai ta tashi zata je ta ɗakkosa, sai dai tana zuwa dai-dai ciyayin da abin ya shige taga wuta ta kama a wajen, kuma ba'a ƙara ko sakan biyu ba hankalinta ya dawo jikinta baki ɗaya. dan haka take a lokacin wani tsananin tsoro ya kamata, ta dinga waige-waige a wajen, ina zata yi yanzu?, babu kowa a wurin nan daga ita sai bishiyoyi sai wannan ruwan. bata san sanda ta fashe da kuka ba, wutar dake ƙara ruruwa ta kusa kamo rigarta tai saurin matsawa daga wurin, kuka takeyi sosai, "Kaka". sunan da take ta ambata kenan, ita bata san ta inda zata bi ta koma gida ba, saboda haka ta zube a wajen tana daɗa fashewa da matsanancin kuka, tsoro na ƙara cikata. tana cikin hakan taji zuciyarta na biyo mata wasu ayoyi acikin alqur'ani da kuma wasu adu'oi dake cikin hisnul muslim, bakinta na karkarwa ta fara biyosu a fili. sai taji komai dake cikin kanta na washewa, haske na zuwar mata, mafita na zuwa cikin kanta. sai tayi zumbur ta miƙe, zuciyarta na faɗa mata ta bar wajen da sauri. tasa hannu ta toshe hancinta saboda warin hayaƙin, wani irin ɗoyi ne yake tashi aciki, tai azamar barin wajen da gudu amma sai taji ƙafarta guda ɗaya ta riƙe, sai sannan ta tuna da ciwon dake ƙafar. amma a hakan ta dinga jan ƙafar tana ɗaga waccan har ta bar wurin, kuma tana zuwa bakin wata ƙatuwar bishiya taji tushh abu ya fashe, bata tsaya ba taci gaba da tafiya, tsoro kuma na ƙara kamata, haka har ta shigo cikin wasu gonaki, ananne tsoro ya tsananta gareta saboda kukan karnuka dake tashi, bata san lokacin da ta kwasa a guje ba ta manta da ciwon dake ƙafarta duk da tana jin zafin ciwon na ratsata. ta fito kan hanya kawai taga fitilar mota na haskawa, da fari kamar ba zata tsaya ba sai ta tsaya tana miƙa hannu don tsayar da motar, dole zata tsaya ta nemi taimako in ba haka bata san ina zatai ba, haka kuma bata san meke cikin wannan dajin ba, komai zai iya faruwa da ita. tana ta ɗagawa motar hannu, so take tai magana amma ta kasa, ga motar ita take tunkarowa, a wannan lokacin kuwa kan Turaki na ƙasa yana ƙaro volume na karatun qur'anin daya kunna, lokacin har ya ƙaraso inda take ba tare daya san da mutum a gabansa ba, a time ɗinne ta fahimci ko waye na cikin motar baya ganin gabansa, saboda haka cikin hanzari ta ɗaga ƙafarta da tayi mugun nauyi zata janye daga wurin, sai dai inaaa, kafin tai wani yunƙuri Motar Turaki ta daki gwiwoyinta ta kifo kan motar tasa. ta san sanda kanta ya ƙwalu a jikin motar, ta san lokacin da ta silalo ta faɗo ƙasa, taga kuma lokacin da tayoyin motar ke ƙoƙarin bi ta kanta. take ta sallama da rayuwar, yau dai tasan babu abinda zai hanata bin Umminta, zata je su rayu tare harda Addarta, zata bisu shikenan sun bar Kaka ita ɗaya. tana kallon tayoyin motar na ƙara motsi suna tahowa zasu talitse kanta, sai dai daga nan, ji da gani da numfashinta duka suka ɗauke. bata san me ya faru ba bayan nan, sai yanzu data farka, ta farka ta ganta acikin ɗakin asibiti, kan gadon asibiti, that means wanda ya bugeta mutumin kirki ne kenan?, shi ya kawota asibitin ko ya?, idan ba shi bane to wa ya tsintota daga cikin wannan dajin ya kawota nan?, ina Kaka?, ina Maijidda?, ina Yami?, ina Amir?, shin wanne hali suke ciki?. shin sun samu labarin inda take?, ko kuma suna can suna nemanta?, wacce amsa zata basu a lokacin da kowannensu yay mata tambaya?. duk ba wannan bama, idan ta miƙe yanzu zata koma gida, ta san kuma amsar tarin tambayoyinsu, ba zata ɓoyewa Maijidda komai ba domin ita zata kawo solution. abun ɗaya ne kawai ke cikin kanta a yanzu itace sallah, sallolin da bata yi ba a wancan ranar na la'asar da magriba da isha. to kwana nawa kenan yanzu?, sallar kwanaki nawa ne akanta?, wa zai bata amsa?, don tasan ba lallai akan lokaci aka sameta ba balle ta iya ƙiyasta wasu kwanakin, kuma dole zata rama sallolin dake kanta. ta kulle ido ta motsa ƙafafuwanta zata yunƙura ta tashi zaune sai taji tamkar zasu karye saboda sandarewa da kuma azabar ciwon da suke yi mata. kawai sai ta fashe da kuka, kuka sosai, likitan daya gama aikinsa ya tsaya akanta, tana jin yanda kallonsa ke shiga jikinta. baice komai ba har sai da ta tsaya da kukan dan kanta ta buɗe idon tana kallonsa, murmushi taga ya sakar mata tare da ce mata. "sorry". muryarta na fitowa da sautin kuka tace,"dan Allah zanyi sallah". murmushi taga ya ƙarayi sannan yace,"za kiyi sallah amma ba yanzu ba, ki bari ko zuwa safiya ne". sai ta koma tana bin ko'ina na ɗakin da kallo, agogo take nema taga lokaci. tace da shi,"me yasa to ba zanyi ba yanzu?". yana kallonta yace,"saboda ba za ki iya ba...". tun bai ƙarasa maganar ba ta kalle shi da idanunta da suka kawo ruwa ta katsesa da faɗin,"zan iya, Allah zan iya". tai maganar tana son fashewa da kuka. Dr Yusuf yace mata,"to shikenan tashi ga banɗaki nan ki shiga, can kuma jakar kayanku ce sai ki ɗau hijab aciki ga abin sallah can". ta kalli inda yayi mata nuni, ta maimaita kalmar jakar kayanku acikin ranta, ta juyo ta kalle shi yana niyyar fita tace,"dan Allah wa ya kawoni nan?". yace,"police da kuma wanda ya buge ki". ta maimaita kalmar a ranta kan tace,"dama ya tsaya?". yace mata,"ehh yana da imani shisa". hawaye na ƙara sauko mata a sanyaye tace,"Kakata fa?". ya juyo ya kalleta sannan yace,"kin fasa yin sallar ne?". ta girgiza masa kai tare da cewa,"a'a zanyi". ta faɗa tana so ta tashi amma tana jin ba zata iya ba, komai yayi mata nauyi kamar an danneta, kawai sai ta saka kuka. Dr Yusuf ya dawo yana bata haƙuri da faɗin,"na faɗa miki ba za ki iya tashi ba, akan aikina fa nake, zuwa wayewar gari insha'Allah da kanki za ki tashi bama sai an taimaka miki ba". bata bar kukan ba tace,"to idan ban kai goben ba fa naje nace da Allah me?, ni dai dan Allah ka taimaka min na tashi na sauke nauyin da yake kaina". Yusuf dai da yaga zasu yi daru da ita kuma ba jin duk wani bayani da zaiyi zata yi ba kawai sai ya sakar mata allurar bacci. baccin da bata farka a shi ba kenan ba har sai washegari da wajen ƙarfe goma, lokacin su Kaka sunzo, tana buɗe ido akan Kaka ta sauke wacca ke zaune kan kujera ta rafka uban tagumi. Maijidda kuma na tsaye jikin bango kana kallon fuskarta zaka san tasha kuka ta gode Allah, itama duk ta faɗa saboda tashin hankalin da suka shiga. Yami ce kawai me ɗan ƙarfin hali da take ta tausar Kaka akan ta daure ta saka abu acikinta tunda likitan yace zata farka. kuma kwana biyu Kakan banda ruwa babu abinda take sha, shima idan tasha ɗacinsa take ji. "Yami ba zan iya sa komai acikina ba sai yarinyar nan ta farka, yau fa kwana huɗu kenan, faɗa mana suke tana raye, ni dai ina tantamar hakan, gwara kawai a faɗa min gaskiya a bar ɓoye-ɓoye aini musulma ce na yarda da mutuwa". Yami dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kallonta da ta maida kan Fillon, itama dai ta fara tantama akan maganar likitocin nan, ace kwana huɗu mutum bai farka ba kuma sannan ace yana raye?, to mene amfanin ɓoyewar?. sai kawai ta gyaɗa kai cikin ranta tana faɗin wataƙila kuma ba'a so a ɗora alhakin mutuwar tata ne akan Turaki shiyasa, tasan zasu iya komai tunda suna da uwar kuɗinsu. Fillo da take jinsu a lokacin ta kira sunan Kaka, wani farin ciki ya baibayesu suka yo kanta. Maijidda tayi mata wata runguma har sai da ƙashin bayan Fillo ya amsa. kuma a sannane Amir yazo, tunda ya shigo ya kafeta da ido, kallonsa take shima kallonta yake, zuciyoyinsu na saƙa abubuwa iri ɗaya dangane da junansu. kalmar da Amir ya fara faɗa mata shine,"za ki iya yin sallah?". kai kawai ta ɗaga masa, Yami ta kamata ta sakko a gadon ta kaita banɗaki. lokacin data fito Amir kawai ta gani har sannan yana tsaye idanuwansa duk sun faɗa ciki, kana kallonsa zai baka matuƙar tausayi. shi ya shimfiɗa mata sallaya, ya tayata saka hijabin, yace mata idan zata iya ramawa duk ta rama, idan ba zata iya ba tayi wasu ta bar wasu sai jimawa. tambayar da tayi masa shine,"kwana nawa yau?". "huɗu". amsar daya bata kenan. kuma tunda ta tayar da sallar bata tsaya ba sai data rama duka sallolin dake kanta, har lokacin Amir bai zauna ba yana tsaye. tana idarwa kuma sannu kawai yay mata, zai fice a ɗakin tabi bayansa da kallo tace,"ina zaka?". "tafiya zanyi". amsar daya bata kenan ya fice daga ɗakin bai jira cewarta ba, jikinta yayi matuƙar sanyi, su Kaka suka dawo ciki ta tambayi Maijidda suka ce ta tafi raka Amir. Yami ta zuba mata abinci ta ajiye a gabanta, har lokacin tana kan sallaryar ta miƙe ƙafafunta, da ƙyar tayi sallar, ƙarfin dauriya irin nata kawai. "na ƙoshi Yami". kalmar da ta faɗa kenan, kuma kafin Yami tace wani abu an turo ƙofar ɗakin an shigo, Dr Yusuf ne, suka amsa sallamarsa sannan ya umarci Fillo da ta koma kan gadon za'a ƙara saka mata drip. gadon ta koma ta kwanta, yay mata wasu tambayoyi dangane da yanda take ji tana basa amsa, acikin drip ɗin ya zuba duk alluran da za'ai mata. yana gama saka mata kuma yace da Kaka,"idan ya ƙare a bata abinci taci". da haka ya fita. sai yanzu su Kaka suka sami natsuwa, Yami ta zuba musu abinci suka shiga ciki, lokaci zuwa lokaci Maijidda na lura da ruwan daya kusa ƙarewa. bayan wani lokaci hankalinsu ya karkata ga turo ƙofar ɗakin da akayi, ganin wanda ya shigo da sauri Kaka ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa tare da amsar ledojin dake hannunsa. Khalil ya shigo yana ta kallon Fillo, mamakin da kowa yake akanta shine taya akai ta fita acikin wannan daren?, kuma me taje yi a wannan dajin?. shi dai abinda zuciyarsa ke raya masa shine Turaki ne ya ɗauketa zai je ya cutar da ita, Turaki ne yay komai, har yau haka zuciyarsa ke faɗa masa. *Plss Comment, Vote, and Share.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _🤔zato dai zunubi ko da ya kasance gaskiya, ku daina ɗaukar hakki babu kyau ni gaskiya nake faɗa muku, ahh tou🤣, yo kowa ya tashi sai ya wani kama cewa Hajiya Madina kaza-kaza, banda ma dai neman magana yaushe kuka taɓa ganin ta cutar da wani daban balle Turaki da ya gama nannaɗe zuciyarta😒...to a daina gaskiya ban so, duk wanda naji ya ƙara taɓata zan hau bori😭😭..._ *18* After long minutes sai ga Zaytuna itama ta shigo room ɗin, har lokacin Khalil yana nan bai tafi ba, yana zaune akan kujerar da Kaka ta ajiye masa. yana kallon Zaytuna da mamaki yace,"from where?". bayan duk ta gaida su Kaka tare da tambayarsu ya me jiki tace da shi,"bamu jima da shigowa garin ba, so muna sauka a airpot mu kai waya da Hamma yake ce min yana nan". Khalil ya ƙara tambayarta,"ya Granny ɗin?". tace,"tana lafiya, duk tana gaishe ku...da ta saka rigimarma sai mun zo tare tana so taga Hammah". yace,"Allah sarki Granny, insha'Allahu zan matsa masa akan muje, sai mu dawo a ranar tunda dai am sure ba zai kwana ba". Zaytuna ta cirewa Fillo drip nata da ya ƙare yanzu, itama tana tambayarta yanda take jin jikin tana faɗa mata komai da sauƙi ƙafarce dai har yanzu. after five minutes Zaytuna ta yiwa su Kaka sallama saboda kiran da Baffa yake yi mata, tare suka fita da Khalil wanda yake ta mamakin yacca akai har yanzu Turaki bai shigo ba. bayan fitarsu Maijidda ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"mene damuwar?". tace,"me kika gani?". Maijidda tace,"na san dai ba ki da lafiya amma yanayin fuskarki ya nuna akwai damuwa a ƙasan ranki". Fillo ta haɗiye yawu tukunna ta ɗago ta kalla Maijidda sannan tace,"me yake damun Amir?". Maijidda ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo gefen gadon kusa da ita ta zauna, ta kamo hannunta ta riƙe acikin nata tace,"me kika gani?". Fillo ta dake ta hana kuka ƙoƙarin fitowa tace,"sannu fa kawai yace min, ina amsawa yasa kai ya fice". "kinyi masa wani laifi ne?". ta girgiza kanta,"a'a ni banyi masa komai ba. kuma ko da ace ma nayi masa ba zai min haka ba tunma da ya ganni banda lafiya". Maijidda tace,"to kwantar da hankali ba abin da kika masa, kawai yana cikin damuwa ne akan lamarinki. yace ya kasa fahimtar me ke faruwa, yana ganin kamar mutanen ɓoye naso su shafeki ne tun a wancan ciwon da kika yi, amma wannan karon sai yaga kamar ma sun riga sun shigeki...baki gani ba wallahi yanda yake ta sadaƙa yana sauke miki alƙur'ani, anan fa yake kwana kullum ba ya tafiya, abinci sai Innarsa tayi da gaske". Fillo tai ɗan jim kafin tace,"to ai ni banda wasu aljanu, hasashensa ne dai kawai". Maijidda tace,"to aikuwa abin da kowa ke faɗa kenan". Fillo ta kalli su Kaka da suke can gefe su na maganarsu, hankalinsu ba ya kansu gaba ɗaya. murya can ƙasa tace,"Maijidda ina asirin da nace miki zan ɗauke a ɗakin Turaki?".  idanun Maijidda a waje take kallon Fillo da al'ajabi, ai dama tunda hakan ta faru ta fara tunanin da wuya idan ba karambaninta ne ya bata damar ɗauke asirin da ta gaya mata zata ɗauke ba. ita kam ta fara tsorata da lamarin ƙawarta, ta bakin Amir aljanu sun shigeta domin mutum dai ba zai yi abin da takeyi ba. Fillo taja hannun Maijidda da taji tayi shiru,"kina da matsala wallahi, shi yasa wani lokacin da faɗa miki abu gwara shiru". bata bawa Maijidda damar magana ba taci gaba,"na ɗauke asirin harma ya ƙone". "shima ke kika ƙona shi?". ta girgiza kanta,"aa wallahi ikon Allah kawai, ba ki gani ba kamar tashin bom haka yayi tushhh, kinji yanda yake ɗoyi kuwa Allah kika shaƙa kayan cikinki sai sun kusa zubowa...kuma kin san me?". ta faɗa tana muskutawa ta gyara zamanta akan gadon inda ta juyo ta fuskanci Maijiddan. "ina ga wannan asirin ne yake hana Turaki Sallah, ai dama na faɗa miki naji Maama na kokawa da hakan. kinga nima fa tun sanda na ɗauko shi naji bana sha'awar yin sallah kwata-kwata...bari dai mu bar asibiti zan baki labarin komai". ita dai Maijidda tsuru tayi tana zubawa sarautar Allah ido, ta ɗanja baya kamar tana tsoron Fillo ne. muryarta itama a can ƙasa tace,"wani lokacin idan muna magana sai naga kamar bake ba, shi yasa bakina ba ya rabo da ayatulkursiyu...to Allah dai ya ba ki lafiya ya rabaki da su lafiya. insha'Allah sai anyi galaba akansu...". bata ƙarasa ba Fillo ta kai mata duka a kafaɗa ita kuma tayi saurin kaucewa tana dariya. "Allah ki bar wannan zancen Maijidda bana so, ba wasa bane wannan, wani yaji ai sai ya ɗauka gaske. ƴar wulƙanci kawai". Maijidda har sannan fuskarta da dariya tace,"yo daga miki abin arziƙi, adu'a fa Haliman Amir?, ina ga ma wannan dalilin Allah ya duba ya aiko Malam Amir gareki, kinga ai sa dinga cin ƙwal uwarsu a hannunsa, dan ba raga musu zai yi ba da adu'a...waya sa ni ma yanzun ko ba ke bace". wannan maganar tasa Fillo zuro ƙafafunta zata sauko a gadon ta damƙeta, ita kuma tayi wajen su Yami tana ta dariya. Fillo tayi ƙwafa,"Allah kika ci gaba sai na bugo miki wannan ƙarfen". ta faɗa tana nuna ƙarfen da ake saƙale drip a jikinsa. Kaka dai idonta na kansu tun ɗazun, tana jin zuciyarta na washewa daga damuwar dake tare da ita, sai yanzu hankalinta ya dawo jikinta. ko babu komai tasan Fillo ta sami lafiya, abu ɗaya yayi saura, matsalar jinnu da suke tunani sun shafeta. Fillo ta rafka tagumi tana tunani Kaka ta miƙo mata abincin da bata ci ba ɗazu, ta ɗago tana ɗan yamutsa fuska, murya a narke da shagwaɓa tace,"Kaka na ƙoshi fa". Kaka tayi mata wani kallo tace,"karɓa kafin ranki ya ɓaci, kin farka za ki ɗora daga inda kika tsaya ko. wadda bata tausayin kanta kawai". Fillo na turo baki ta karɓi plate ɗin. "wallahi ki cinye shi kafin na dawo". Kaka ta faɗa tana kaiwa ƙofa. Yami ta miƙe tabi bayanta suka fita tare. a bakin ƙofar suka tarar da Turaki wanda jin za su fito yay saurin matsawa daga jikin windon da yake tsaye a wajen tun ɗazu. su na ƙoƙarin durƙusawa ƙasa su gaida shi ya dakatar da su. "dan Allah Kaka bana son kuke tsuguna min irin haka, ni fa jikanku ne, ku daina kallon wani matsayi da nake da shi, mutum nake kamar kowa". Yami tace,"ranka ya daɗe kallon matsayi ai ya zama dole kam. kai ɗin ne dai ka fita daban da sauran da suke da irin matsayinka. kuma muna godiya a gareka bisa kyautata da mutumtawa, Allah ya haɗaka da mace ta gari". Kaka ta matsa daga bakin ƙofar tana basa hanya. "ka shiga ciki yallaɓai bismilillah, ai tama farka tun ɗazu, jiki da sauƙi kam". idonsa na kan handle yace,"to masha'Allahu, Allah ya ƙara lafiya...ina dai daɗa bada haƙuri Kaka". Kaka dai bata kallonsa tace,"kai haba ranka ya daɗe wane mutum, aimu wannan tsautsayin abun farin ciki ne garemu. in banda haka ina ma za'a ganta?, da yanzu muna cikin tashin hankali". bai ce komai ba ya kama handle ɗin ya buɗe ƙofar, su Kaka kuma suka wuce bayan sun ce masa zasu je ɗaya ward ɗin ne zasu yo dubiyar wata Ƴar Ƙawarsu da aka yiwa aiki ta haihu ɗan yazo babu rai, yayi musu a dawo lafiya sannan suka wuce shi kuma ya shiga room ɗin. Maijidda nata fama da Fillo kan taci abinci amma taƙi, bai maida ƙofar ya rufe ba, kawai ya tsaya yana kallon Fillo kamar ɗazu da ya tsaya. yana kallonta ta window sanda suke abinsu ita da Maijidda. shi mamaki ta basa sosai bai yi tsammanin ma yarinyar na magana ba, da sakewa irin haka, zatonsa a tsorace take ko da yaushe irin yanda ya saba ganinta. idanunsa suka nuna masa irin ramewar da ta ƙarayi, ƙasusuwan jikinta tsab zasu lissafu, idonta ya faɗa yayi loko kamar yanda yaga nasa yayi da ya na duba madubi ɗazu. basu san ya shigo ba sai da Maijidda ta miƙe tana faɗin,"kiran Amir zanyi na faɗa masa kinƙi cin abincin, shi kya ji maganarsa tunda kinfi sonsa". ta harareta tace,"ku kuma da banji maganarku ba bana sonku kenan?". Maijidda ta ɗaga kafaɗarta,"alama ta nuna hakan". Fillo tayi shiru ta maida ƙafafunta kan gadon ta jingina da pillow, sai lokacin Turaki ya tura ƙofar ya rufe ya ƙarasa shigowa. dukansu suka kai idonsu bakin ƙofar, gaban Fillo ya faɗi, taji wani tsoro ya kamata. ta wutsiyar ido yake kallonta, kuma yaga wannan tsoron a idonta wanda bai gani ba a ɗazu da take tare da ƴar'uwarta. da sauri Maijidda ta aje abincin da ke hannunta ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa muryarsa bata fitowa sosai. ta miƙe ta ɗauki kujera daga gefen gadon Fillo ta kai masa, amma sai bai zauna ba. Fillo dai da bata san ma shi ya kaɗeta ba, dan ba'a faɗa mata ba. tana dai cike da mamakin waɗanne irin mutanene su, ita ba kowan komai ba garesu amma sai zuwa suke su na dubata, taji su Kaka sun ce jiya da yau ne kawai Hajiya Madina da Baffa da Boɗejo ba su zo ba, amma hatta Hakimi kansa sai da ya zo, kuma shima Mai Martaba sai da ya aiko iyalinsa suka zo. ƙwarai kirkinsu ya wuce tunanin mutum, kuma la shakka ba zasu taɓa faɗuwa a rayuwa ba sai dai cigaba. ba tayi zaton ma Turaki zai iya zuwa dubata ba tunda wanda bai sonka ba ya sonka, no matter what happen to you ba zai nuna tausayinsa akanka ba. zuro da ƙafafuwanta tayi daga kan gadon zata sauko ta gaishe shi, sai taji muryarsa kamar a saman kanta yace,"ki sauko kiyi me?". bata ɗago ta kalle shi ba tace,"zan gaishe ka ne". Idonsa har lokacin na kanta yace,"wa ya farlanta miki hakan?". Bata ce komai ba tayi shiru sai wasa da yatsun hannunta take ta duƙar da kai. shi kam kallonta kawai yake, ta wani natsu kamar wadda taga mutuwa, kamar ba ita ta gama surutu ɗazu ba harda dukan wata. ɗakin yay shiru Maijidda na daga gefe har yanzu a tsugune, ya maida kallonsa kan abincin da Maijiddan ta aje yace,"ki kawo mata abincin". Maijidda ta ɗauko plate ɗin da ke ɗauke da tuwon semovita da miyar agusi da naman ganda akai, ta miƙawa Fillo wacca tuni idonta ya cika da ruwa sai aikin ɓata fuska take. da mamakin Maijidda babu tirjiya balle musu Fillo tasa hannu ta karɓa, kallon abincin kawai take ba don tana jin zata iya ci ba. bakinta babu taste ɗin komai hakan ne yasa ba zata iya cin komai ba, kuma bata ma jin yunwar. wucewar daƙiƙa biyu Turaki yace mata,"wa kike jira yazo ya ci miki?". ba tsoronsa take ji ba, ita kawai yana yi mata kwarjini ne, ko bata kalle shi ba indai yana waje sai taji girman kwarjininsa ya cika wurin. ba don tana so ba ta gutsiri tuwon da spoon ta kai baki, ta tauna ta haɗiye da ƙyar kamar me tauna magani, tana yin spoon huɗu sai ga amai ya yunƙuro, Turaki yay saurin ɗauke idonsa daga kanta ya kauda kai gefe yana jin zuciyarsa na tashi, Maijidda ta kamata suka wuce toilet, duka ta amayar da ɗan guntun abin da taci, ta wanke baki suka fito har sannan yana tsaye sai dai yanayin fuskarsa ya sauya. sai sauke numfashi takeyi tana maida ƙwallar idonta, ta ƙasan ido take ta kallonsa, tana ce sannu yazo yi mata?, shi bai yi ba kuma bai tafi ba ya tsaya kamar wani sandar ba'are, Allah ya sani ji take kamar akanta yake a tsaye, da zata iya da ta buɗe baki tace masa ya tafi kawai. a bakin gadon ta zauna. kuma tana zama taji ya ƙara cewa,"ki ɗauka ki ƙara ci, sai ki ƙara zuwa kiyi wani aman, ki dawo ki ƙara ci kije ki amayar haka har ki cinye shi". wannan karon ba ita ta kalle shi ba Maijidda ce, tana masa kallo ɗaya ta ɗauke idonta ta koma can kan ɗaya gadon da ke cikin ɗakin, room ɗin 2patient ake admiting acikinsa amma ko da Baffa yazo sai ya biya kuɗin ɗaya gadon dalilin da yasa take zaune ita ɗaya kenan. jin an turo ƙofa Turaki ya kai idonsa wajen, Dr Yusuf ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. duk da cewar tun ɗazu da Turaki ya baro masallaci yana office ɗinsa hakan bai hana su daɗa yin musabaha ba. as usual fuskar nan tasa da murmushin da ba ya yankewa. "ya me jikin ranka ya daɗe?". Dr Yusuf ya tambayi Turaki. "gata nan maganin gardama ya rage ku bata before ku sallameta". Dr Yusuf yay ƴar dariya yace da Fillo,"ya kike jin jikin naki?". Tace,"naji sauƙi". yace,"to Allah ya ƙara lafiya. yanzu cin abinci yay miki saura shi ne za ki samu ƙwarin jikinki". tace,"to". ya juya ya karɓi file daga hannun nurse ɗin da ta shigo ɗakin yanzu, yay rubuce-rubuce sannan ya rufe ya bata. ya fuskanci Turaki yace,"insha'Allahu by wenesday zamu sallameta. komai normal babu wata matsala". Turaki ya kalleta ya kalli tuwon yaga ko rabin cinsa bata yi ba, yace da Dr Yusuf. "Allah ya kaimu. amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?, tunda bakinta nayi mata wahalar cin abincin". da murmushi a leɓen Dr Yusuf yace,"babu matsala sai ayi hakan. bari yanzu sai mu fara preparation ɗin shiga da ita ɗakin tiyata...sai dai kuma fa idan za'ai irin wannan aikin dole sai a ɗinke bakin mutum gaba ɗaya ya zamana mutum ya dawo ba ya magana, wurin da za'a yanka a cikin nasa shi ne zai koma yagar bakinsa, abinci da ruwa ne kawai za'a dinga zubawa a ciki". Turaki ya sosa girarsa sannan yaja kujerar da ke kusa da shi ya zauna. "ayi abinda ya dace kawai Dr". sai ya kalla agogon hannunsa yace,"nan da minti nawa za'a shiga tiyatar?". Dr Yusuf yace,"in the next 5minutes, office kawai zan shiga na fito, ita dai yanzu a shiryata". Turaki yace,"alright a fito lafiya". Dr Yusuf ya fita Nurse na biye da shi, wacca take ta dariya ƙasa-ƙasa da zancen da akai, ta lura sosai maganar ta tsorata Fillo. Maijidda ma na gefe a tsaye, itama dariya take ƙasa-ƙasa farkon da akayi zancen farka ciki, saboda yanda taga Fillo ta tsure tana raba idanuwa, amma daga baya da taga kamar maganar da gaske ne sai tayi jugum tana dai ta kallon Turaki ta gefen ido, tana kuma jin tausayin Fillo na tsarga mata. _"amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?"_ maganar ta Turaki ta daɗa maimaituwa acikin kanta. farko da ya faɗa bata razana ba, amma da ta shiga bin fuskokinsu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sai ta tsorata ainun, dan ko ɗigo babu na alamar wasa a yacca fuskokinsu ke nunawa, hakan ya tabbatar mata lallai da gaske suke, farke mata ciki za'ai sannan kuma a ɗinke bakinta ta daina magana har a abada. idan da abinda yafi tashin hankali wannan maganar tasa ta shiga ciki, hangota take babu bakin magana kuma cikinta a yage, ta haɗe murfin idanunta da suke neman zazzagowa ƙasa, dan tunda aka fara maganar suke a waje. jikinta rawa yake sosai, ƙatuwar malmalar tuwon take ta kallo, lissafi take yi, lissafin yanda za'ai ta cinye shi acikin miniti biyar kafin a shiga da ita tiyatar da suka ce. ta ɗago ido ta kalli Maijidda da ke kallonta, yanda take a tsorace haka Maijiddan ma. cikinsu biyun kowa ya kasa cewa komai, tsoron Fillo ɗaya ne! tace zata basa haƙuri ya sakar mata wannan uwar tsawar da bata so, dan taga kamar hakan yake jira, dalilin da ya sa bakinta mutuwa kenan. Maijidda tayi sum sum ta fice zuwa kiran su Kaka, tana fita Fillo ta sakko a kan gadon ta wuce toilet, Turaki ya bita da kallo har ta dawo. ta koma gefen gadon ta zauna, ta saka hannunta da ta wanke ta fara cin tuwon tana kai ƙatuwar lomar da ta fi ƙarfin bakinta. kana gani kasan tura tuwon kawai takeyi, bata ko tsayawa ta gama cinye na bakin zata ƙara saka wani, tunda take bata taɓa cin malmalar tuwo me girman wannan ba, kai abincin kansa bata cin da yawan hakan, shi yasa Yami kullum ke mata tsiyar taƙi ci tana ta bushewa. yana zaune yana shafa wayarsa amma indonsa sam ba akan wayar yake ba akanta yake, tun lomar farko da ta kai baki. ba ƙaramin ba shi dariya tayi ba ya danne yana cije leɓe murmushinsa na fita saboda dariyar ba zata dannu duka ba, yanda take ta tura abinci cikin sauri, har yunƙurin amai tayi amma tayi maza ta maida shi, ga jikinta ma gaba ɗaya rawa yake kamar mazari. cikin mintunan da ba zasu haura uku ba plate ɗin ya zama babu komai, ta cinye tas sai nishi take yi, ta sauko taje ta wanke hannu ta dawo. ta kalle shi taga ma hankalinsa bai kanta, wayarsa kawai yake dannawa, kamar tayi magana ta roƙe shi suyi haƙuri sai dai tayi shiru, ta kama yatsun hannunta sai jansu take kace tana lazimi. idanuwan nan da suke loko sai ƙifƙiftasu take. Turaki duk yana kallonta, har maganar da bakinta ke son yi yana kallon yanda ɗan ƙaramin leɓen ke motsawa. shi gani yake ma kamar ƙunƙuni take tana zaginsa. su na haka aka murɗa ƙofa, tana jin hakan gabanta yay mugun faɗuwa ta haye kan gadon gaba ɗaya a zabure, ta takure ƙafafuwanta tana shirin sakin kuka. muryarta na karkawa ta cewa Turaki,"tun ɗazu na cinye abincin dan Allah kuyi haƙuri". tana rufe bakinta sai taga ashe su Kaka ne ba Dr Yusuf ba kamar yanda ta tsammata. hakan yasa ta saki ajiyar zuciya tana bin Kaka da ido, taga fuskar Kakan a haɗe alamar ɓacin rai. "sannu fa me babban suna". Turaki ya tashi ya amsawa Kaka. "yauwa Kaka sannunku da dawowa. ya me jiki?". tace "da sauƙi...kayi zamanka mana". yace,"a'a Kaka dama ina niyyar tashi ai". tace,"ni dai da ka zauna wallahi, bana jin daɗi idan kana ƙin zaman nan saboda mu". ya kalli tsohuwar da jin tausayinta a ransa, sosai suke kama da Fillo kawai dan ita ta tsufa ne. ba ya son musu da babba saboda haka dole ya koma ya zauna. bayan ya zauna Kaka tace,"muna daɗa godiya fa me babban suna, babu abin da zamu ce sai Allah ya saka maka da gidan aljannah. kai da iyayenka kuna kulawa damu Allah ya biyaku da alkhairansa". yace,"amin Kaka na gode". ta sake cewa,"Maijidda ce taje take faɗa mana abin da ke faruwa na za'a shiga da ita tiyata, shi ne muka taho. nace ai hakan ma wani gata ne akai mata". Yami tace,"Allah yasa dai ayi a sa'a". ya sosa girarsa leɓensa na fitar da murmushi yace,"ehh likitan ne dama ya bada shawarar hakan". karaf Fillo tayi saurin cewa,"a'a ba shi bane kaine ka fara faɗa masa. ni dan girman Allah Kaka kuyi haƙuri indai abinci ne zanke ci". Kaka tayi mata banza, Yami tace,"to ai magana ta ƙare tunda har likitan ma yayi shirinsa. kiyi adu'a kawai Allah yasa ayi miki a sa'a, hakan ai gata akayi miki Fillo kinga yanzu cikinki ga dinƙa samun abincin kirki. magana kuwa kya dinƙa nuna abunda kike nufi da hannu". Yami na yin shiru Fillo ta fashe da kuka tana kifa kanta a gwiwarta, ta sani babu wanda zaiji tausayinta, kuma babu me jin kukanta tunda bata da uwa bata da uba a raye. Turaki ya ɗauke idonsa akanta, zai fita Kaka tace,"a'a me babban suna tunda dai sa hannunka ne a yin aikin nan to ka ɗan jira likitan yazo a ɗauketa a gabanka. mu ba jin maganarmu take ba,". Tana faɗin haka suka fice su duka suka bar Maijidda a tsaye, itama sai ta fara hawayen. bayan fitar su Kaka ya jawo kujera sosai gaban gadon sannan ya zauna, ya aje wayarsa akan gadon, sannan ya sarƙe yatsunsa wuri ɗaya. yace da ita,"haƙura za'ai da farka cikin ko kukan za ki ci gaba?". kalmar farka cikin ita ke ɗaga hankalinta, tayi saurin ɗagowa fuskarta tayi sharkaf. "dan girman Allah karka sa a farke min ciki, zan dinga cin abinci kullum, ai kana kallo na cinye na ɗazu. dan son da kake yiwa Maama da Adda Zaytuna kace ba za'ai min ba". mamaki yasa kawai ya tsareta da ido, ta ya akai tasan yana ƙaunar mutanen nan guda biyu?, ta ya tasan zai iya yin komai akansu?, wa ya faɗa mata ana roƙonsa da su ya aikata abin da bai niyya ba?. ya sauke numfashi sannan yace,"an fasa". a hankali tace,"na gode, Allah ya kareka daga sharrin maƙiyanka". ta faɗa tana goge hawaye da ɗankwalinta da ya zame. suka haɗa ido tayi saurin ɗauketa nata, ya kalli gashin kanta yace,"ɗaura ɗankwalin ki bani amsar tambayata". Ta ɗaura ya ƙara cewa,"to ki cire tsoron ki nutsu". ta haɗiye wani irin yawu tana saita nutsuwarta. taji yace,"ɗago idonki ki kalle ni". tayi yunƙurin yin hakan amma sai ta kasa, yaci gaba da kallon siraran hannunta da suke ta karkarwa, sai kawai ya miƙa hannunsa ya haɗe hannayenta biyu ya riƙesu cikin nasa guda ɗaya, sai dai da mamakinsa duk da hakan basu bar karkarwar da suke ba kamar ma ƙaruwa abin yayi, cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi wannan rawar da jikin nata yake yi bana lafiya ba ne. jin yanda ya riƙe hannuwan nata yasa ta kulle ido wani abu na wucewa ta maƙogoronta. kuma kafin ta buɗe idon taji yace,"me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?". ta buɗe ido ta sauke a saman sumarsa tana jin numfashinta na ƙoƙarin katsewa. **** Yusuf na zaune a office yana operating computer wayarsa tayi ringing, ya kai hannu ya ɗauki wayar, yana duba sunan me kiran yaga Inna Wuro, ya katse tukunna yabi bayan kiran. Inna Wuro na ɗaga kiran ta maka salati,"innalillahii wa'inna ilaihi raji'una. Yusuf kana ina?, kaiwa Allah kazo da sauri babu lafiya". tun salatin farko da ta ja ya miƙe daga kan kujerarsa, tana cewa babu lafiya bai jira komai ba ya kai bakin ƙofa, yabar office ɗin cikin sauri hankalinsa a tashe. daga parlon Inna Wuro ta soke wayarta a gefen zani bayan kiran wayarsu da Yusuf ya katse. ta kalli Nuratu wacce ta tattare carpet ta kwanta a ƙasan tiles, sai yamutsa fuska take yi hannnunta riƙe da tulun ƙasa ƙarami da aka zuba yashi acikinsa, acikinsa take tofa yawu. "ina dalili, gwara ya baro duk abunda yake yi yazo aiwa tufkar hanci, ba zan iya rainon wannan cikin nasa me shegiyar ƙazanta ba. ba ni nayi ciki ba dan haka ba zanyi wahalarsa ba, azo duk abi a dinga tofe min ɗaki da yawu yana ƙarni...yanzu fa fisabillahi ji wani abu, anyi shara kin ɗage min carpet salon dai ayi baƙo a tafi anayi da ni a duniya bana gyara wajena, alhalin ba haka nake ba, kai da gyara wani can da baku haɗa komai da shi ba yazo ya ɓata maka...kuma ni dai gaskiya nake faɗa miki kwanciyar ƙasar nan illa zata miki, inda rabon kin haifo ɗan da sanyi yayi ƙatutu a jikinsa ne ni ba abin da ya dameni ba ne". ta ɗau mayafinta da ke kan kujera ta fita daga parlon, ɗan ƙaramin durstbin na shara ta ɗauka a ƙofar parlon sannan ta wuce ta nufi can inda incilerator yake zata zubar da sharar sai mita take yi. "yanzu ni ba abin na faɗawa Amadu irin cin kashin da ƴaƴansa suke min ba yaga kamar ina tukura musu alhalin nazo ina cin arziƙinsa, Zainabu ta ƙullace ni tace zan haɗa ƴaƴa da ubansu. gwara nayi shiru na haƙura watarana sai labari, amma tsakani da Allah ni ba daɗin hakan nake ji ba, kawai dai dan babu yanda zanyi ne, amma cuta kam ana cutata". ganinta mai gadi ya taso da sauri. "Inna ina za ki haka da kanki?". Ta tsaya tana gyara mayafi tace,"ni ko wa nake da shi da zai min bacin na ƙarfafa jiki na yiwa kaina". ta ɗaga ƙaramin durstbin ɗin sharar tace masa,"kaga dai yanda kwandon nan ya cika ko?". ya ɗaga kai yace,"na gani". tace,"to billahi ina faɗa maka ko dattina ɗaya babu a ciki, bar ganin daga ɓangarena ya fito". Mai gadin yace,"to fa garin ya haka kuma Inna?". tace,"kar ka tsammaci aljanu ne, wallahi ko ɗaya basu da hakki, mutanene marasa tausayin tsoho. Ƴaƴan Amadu ne wallahi, haka suke zuwa su cika min ɗaki alhalin ubansu yayi musu nasu, to ba za su zauna a nasu ba dole dai sai anzo wajena an ɗauki magana. ni kuma bana biye musu kasanni da haƙuri, ban iya ɗaukar magana ba saboda bana son tashin hankali. kuma dai naga gidan na ubansu ne arziƙinsu nake ci shi yasa na iya zamana da su banda haka kullum sai anji kanmu...yanzu fa ka duba ka gani wannan sharar daga safiya zuwa yammacin nan aka tarata, da ci banza ci wofinsu aka mayar min da ɗaki kamar bola. yo ni kuwa me zanyi wanda ya wuci Allah ya isa". Mai gadi yace,"a'a dai Inna haƙuri za'a ci gaba da yi, banda dai Allah ya isan kinga ai jikoki ne". tace,"yo abunda ba ni na haifa ba balle bakina ya bisu su gantale, barni nayi kayata ni dai kam ai Allah ya isar min kawai. kai ai baka san wani abu ba ma, Allah ya isa ai sun saba da ita, dan jiya yaron nan Aliyu ce min yay wai babu wajen shigar tawa, daga nan na sallama nace Allah ya isa kam yanzu na fara har sai tawa ta sami shiga... yanzu ka duba ka gani banda dai rashin tausayi ina uwar me ƙaton gidan nan da kai shara, ko da yake rayuwa ce kowa yay na gari kansa...haka zanta haƙuri har dai Allah ya kawon mafita, ko kai haka iyalinka ke Uwarka?". Mai gadin yace,"a'a Inna". tace,"kaga inda arziƙi yake, banda gidan Amadu inda Ƴaƴan ba kyau matan ba kyau". Mai gadin ya karɓi basket ɗin yace,"kawo na zubar miki, ai ba kyaje wurin can da kanki ba yamma tayi". ta sakar masa tana faɗin,"kai da yake ai kasan darajar babba. na gode Allah yayi maka albarka ya raya maka iyali, yasa ka gama da duniya lafiya, Amadu na dawowa zansa shi yay maka kyauta wallahi. ni ko zamu koma kanon ma ai ba zan bari a tafi babu kai ba, wa zai so ya rabu da ɗan arziƙi irinka". nan ya barta tana ci gaba da surfa mita, ta zubawa gate ido tana ta Allah Allah motar Yusuf ta shigo. Mai gadin ya dawo ya bata basket ɗin ta wuce tana ta ƙara gode masa. tazo wucewa ta ɓangaren Ammi ta saki basket ɗin ya faɗi ƙasa, babu shiri ta saki salati tana ɗora hannu aka. "la'ila ha'illallahu Muhammadu Rasulillahi". Ammi ta dakata da shiga parlonta ta juyo tana kallonta. kamar ba za tayi magana ba, yanda taga Inna Wuro ta ɗora hannu aka yasa dole ta magantu har tana dawowa da baya don ganin lafiya. "me ya faru?". cewar Ammin tana bin wurin da kallo. Inna Wuro ta sunkuya ta ɗauki durstbin ɗin tace,"a'a babu ruwanki, yaushe rabon da magana ta haɗani da ke, tunda azumi ya fita kika ƙulla gaba da ni, sai yanzu ne da kika ga ina neman cutuwa sannan za ki kulani, to gaskiya matsa daga kusa da ni bana son munafurci...duk wanda yay na gari dai kansa, ni ɗin dai wallahi ba abar banza bace nafi ƙarfin wulaƙancin bawa tunda ni na haifin me ƙaton gidan nan". jin haka Ammi tayi tsaki a ƙasan ranta tayi wucewarta, dama tasan ba wani abin arziƙi ba ne, bai wuce abinta da ta saba. Inna Wuro ta bita da ido ta taɓe baki, bata ce komai ba ta wuce side ɗinta, cikin ranta sai masifa take yi Yusuf bai dawo ba har yanzu. tana shiga ta tarar da Kursum ta fito daga ɗakinta. tayi saurin ajiye durstbin ta cire mayafinta ta aje. tabi hannun Kursum da ido har tazo ta zauna, idonta akan bowl da Kursum ta ciko da alkaki tace. "babu masifar da ta wuce haihuwar ɓeraye wallahi. to ni Safiyya mene marabar ƴaƴan Amadu da ɓeraye?, ka ajiye aje a ɗauke babu neman izini. to ba zan iya ba, Allah ya dawo da shi lafiya, ko ya min gidana daban ko kuma ya katangeni a gefe ɗaya, ba zancen haɗa mana ƙofar shigowa ɗaya da ku...ban son fitina ban iyata ba, Allah kuma ya rabani da ita, ku kuma naga tashin hankali kuka fi so to can ya ƙare akan ku". tana cikin wannan sababin Nuratu ta miƙe tayi hanyar ɗakin Inna Wuro da sauri tana rufe bakinta da amai ke shirin zubowa. Inna Wuro ta koma da ba ya tayi wani zaman dirshen akan kujera, ta kama kanta ta riƙe tana girgiza shi. "wowowo, tashin hankali kala-kala a cikin gidan nan. tayi ta zabga amai babu ƙaƙƙautawa duk ta lalata min bandaƙi. to Yusuf ɗin yazo yau dai zamanki ya ƙare a ɓangarena, ya kwasheki ya mayar da ke gidanki ko dai yasan yacca zai yi da ke. banda ma dai kar yay min kallon mara mutunci ai kamin ya dawo zan kai miki kayanki waje". sai kuma tayi ta gumi,"wannan masifa duk ni na jawowa kaina da nace ki dawo wajena da zama, shegen shishshigi irin nawa dai...in nasan hakan kike laulayi wallahi da ban soma ba. gwara can Uwarsa ta riƙe ki, tunda ita ƙanwar Uwar taki tasa ƙafa ta bar gidan, ace aikin Umara har yanzu ba'a gama ba kusan sati uku...wa ma yasan inda ta kaɗa". *Vote, Comment, and Share.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *19* Yusuf na zuwa gida ko horn bai yi ba balle ya tsaya jiran wani abu shi buɗe gate, ya fito daga motar cikin sassarfa. yasan yana da patient, matarsa dake ɗauke da juna biyu mai wuyar laulayi, yau lafiya gobe babu lafiya, shi yasa duk hankalinsa ya tashi tunda yaji irin salatin da Inna Wuro ta zabga, duk wanda yaji wannan salatin ya san ba lafiya ba kamar yanda ta faɗa. jinsa yake kamar ya ɗauki kansa ya dire a parlon Inna Wuro, ƙaramar ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka yana zuwa turawa yayi ya shiga. mai gadi dake daga cikin ɗakinsa a zaune yay masa sannu da zuwa, a sama ya amsa masa ya wuce kamar zai tashi sama gabansa sai faɗuwa yake. hango Ammi yay zata shiga motarta, ya bita da kallo for some seconds, atleast dai zuciyarsa ta sami natsuwa ko ya ya ne, dan shi abunda yake hasashen ya faru daban ne, to kuma tunda yaga Ammi taci kwalliya kuma bai ga wani alamun tashin hankali tare da ita ba sai ya fara nutsuwa. but still dai gabansa bai daina faɗuwa ba, ba zai yi la'akari da yanayin Ammi ba akan ba wata matsala bace babba, komai ma zai iya faruwa ba tare data sa ni ba, idan ma ta sani zata iya yin banza taci gaba da sha'aninta, ranar nan ma haka tayi da akazo aka ce mata Nuratu ta faɗi, baki kawai ta taɓe ciki-ciki tace Allah bada lafiya, Ko da aka kwantar da Nuratun bata je asibitin ta dubata ba, zallar ƙi take nunawa aurensa da Nuratu babu ɓoye-ɓoye ga kowa. yana wannan saurin tafiyar ne dan ƙarasawa side ɗin Inna Wuro sai yaji wayarsa na ringing, yasa hannu a aljihu ya ɗauko. yana ganin sunan Ammi ƙirjinsa yay wani irin bugawa, da ƙyar ya iya ɗaga kiran a lokacin da yake dab da katsewa. kasa cewa komai yayi daya ɗaga wayar but still bai daina tafiyar ba, sai dai ya rage saurin tafiyar tasa, jin bakinsa yake kamar ba zai iya cewa komai ba. Ammi tace masa,"shawaran da zuciyar taka ta yanke maka kenan Yusuf?". mamaki ya kama Yusuf, taya akai ta gansa?, a hankali ya juyar da kansa gefe yana kallon inda take sai yaga bata wajen, ba abin yace mata ba shi bane tunda dai ta riga ta gansa ɗin. ya buɗe baki zai yi magana ta tari numfashinsa,"yau da safe baka shigo inda nake ka duba ni ba sannan ka dawo kana ganina amma kasa kai ka wuce saboda banda mutunci yanzu a idonka. idan Falmata ce ka isa kai mata haka?, ko sallah kaga tana yi a compound ɗin nan ai sai ka jira ta idar tasa maka albarka tukunna zaka wuce. to ni dai Allah ya isa rabani da akai da kai wallahi, ba'a san irin baƙar wuyar dana sha kafin haihuwarka da lokacin haihuwarka ba, ba yafewa zanyi ba. kuma kaje duk wanda zai saka maka albarka wallahi bata kai tawa ba, a banza a wofi, kai da ka san darajar uwa ma da baka fifita kishiyata akaina ba, shashashan banza marar hankali kawai, idan baka sani ba ka sani uwa tafi gaban wasa". muryar Yusuf a hankali kuma da ladabi yace,"kiyi haƙuri Ammi amma ba yanda kike tunani ba ne, yau da safe ko gidan nan banzo ba Allah". taja tsaki tace,"aikin banza. to ka juyo ka kaini unguwa in ka dawo kaje duk inda zaka je". yasa hannu ya shafa kansa tare da rufe idonsa bai ce komai ba kuma bai motsa daga inda yake ba. Ammi ta ƙara cewa,"baka ji me nace ba ne?". yace,"naji Ammi". tace,"ba zaka kainin ba ne?, ko kuma izinin uwar taka zaka fara zuwa ka nema?". ya ƙara sosa kansa yace,"ai Umman bata dawo ba Ammi". da a kusa da ita yay maganar da babu abinda zai hanata buge masa baki, cikin zafin rai tace,"zan zauna zaman jiranka ne ko ya?". yace,"Ammi dan Allah ki kira Aliyu, Inna Wuro ce ta kirani Nuratu babu lafiya zan ɗauketa mu wuce asibiti...". tun bai ƙarasa ba ta dakatar da shi,"ai nasan da Aliyun ban ce shi ba sai kai. Yusuf matarka ko mutuwa zata yi ba zaka je wurinta ba a yanzu sai ka kaini ka dawo, na faɗa maka in ba haka ba kuma zaka sha mamakina, zan maka abinda baka taɓa tsammani ba daga gareni". ƙasan zuciyar Yusuf yaji babu daɗi, bai san ya zai kimanta mata abinda yake ji ba, shi ta barsa yaje yaga kawai halin da Nuratu take sai ya fito ya kaita, hakan ne kaɗai zai basa natsuwar yin driving ɗin da take so, to amma yasan ko me za'ai ba zata yarda ba, kamar yanda ta faɗa ne ko mutuwa Nuratu zata yi, sannan kuma uwarsa ce, jayayya da ita ko bijire mata ya ɗaukowa kansa hanya ta taɓewa ne. dabara ta faɗo masa yace,"Ammi na bar motata a hospital". a fusace tace,"ko da motarka ma kazo ni ba zan shiga cikinta ba, ina da tawa a ita zaka kaini. motarka ai sai Falmata amma ba ni ba, kuma ni dai na faɗa maka ƙafarka ka ɗaga kayi cikin gida to ban yafe ba, idan kaga dama kai ta tsaiwa muna dragging muna ɓatawa junanmu lokaci". Yusuf ya kulle idonsa ya fesar da iska me zafi daga bakinsa, ya katse wayar yana kallon side ɗin Inna Wuro ya koma da baya ya nufa wurin motar. a cikin motar ya sameta a zaune, ya buɗe driver seat ya shiga, bai juya ya kalla back seat inda take ba yace,"Ammi ina yini, kuma ina zan kai ki?". Ammi tace,"gaisuwarka dai ka riƙe, inda zaka kaini kuma kowanne store ya kama, wurin dai da zan samu abinda na fita saya, dawowarmu kuma sai Allah yayi". tana yin shiru yay ma motar key, yay reverse har tayar motar na amsawa, wanda inda ace wajen da ƙasa sai ƙura ta tashi. suna fitowa daga cikin gidan kamar ance ta ɗago kai daga kallon wayarta taga motarsa. tace,"kace a hospital ka bar motar?". sai daya kulle ido sannan ya iya ƙaryar cewa,"dama nace da Mujahid ya kawo min ne". tai murmushi kawai tare da girgiza kai bata ce komai ba. store wurin huɗu suka je, ba dan tana rasa abunda zata saya a kowanne ba, sai dan kawai ta ɓata masa lokaci, dalilin da yasa ta dinƙa gutsira sayayyar kenan, har yamma tukunna suka ɗauko hanya. sai da suka shigo cikin anguwarsu sannan ta ƙara ce masa,"nace maka gida zamu wuce ne direct?, to kai reverse ka kaini gidan Kawun ka". shirunta ya haɗe ta kiran daya shigo a wayarsa, ya kalla sunan dake yawo akan screen ɗin, ganin sunan Inna Wuro ya kulle idonsa da yake jin yana masa zafi, zuciyarsa ta matse hankalinsa na ƙara tashi. minti goma sha biyar suka ɗauka kamin su iso cikin unguwar gargajiyan, da ƙyar motarsa ta shiga cikin layin, daga bayan gidan yay parking motar. yana kallon Ammi ta mirrow ta buɗe motar ta fita ba tare da tace masa ƙala ba, yaji kamar ya fashe da kuka. sai da ta kai ƙofar gidan tukunna ta sami yaro ta nuna masa mota tace yace da mai motar ya miƙo mata jakarta. a lokacin hannu kawai Yusuf ke jira ya ɗora akansa ya saki kuka, ya san da biyu ta manta jakar. jakar kawai ya bata ya juya ya koma mota, Yusuf tun yana kallon wucewar sakanni har ya koma yana kallon adadin mintuna, minti 1 zuwa 5 suka wuce har aka tafi goma Ammi bata fito ba, lokacin ne kuma ya ɗauko wayarsa da niyyar kiranta sai yaji anyi knocking glass, yana ɗaga kai yaga Kawunsu wanda yake Yaya ne a wurin Ammi me suna Malam Mudi. cikin sauri ya buɗe motar ya fito ya duƙa yana gaida Kawun kansa a ƙasa. "Yusuf gidan baƙonka ne daka ƙi shiga ka zauna a mota?". Yusuf yasa hannu ya sosa ƙeyarsa yana neman abinda zai ce, kan yay magana Kawun ya ƙara cewa,"ai Zainab ɗin ke cewa kai ka kawota kana waje, shiru shiru baka shigo ba shine nace to bari nazo naji ko munyi maka wani laifinne". Yusuf yace,"a'a wallahi Kawu babu komai, dama na ɗan tsaya ne muna waya da abokin aikina, shiyasa ban shiga ba amma dama yanzu nake niyya". tare suka jera suka nufa gidan, suna tafe suna tattaunawa akan wasu batutuwa har suka shiga gidan, da yake Malam Mudi mutum ne me sakin fuska. acikin gidan Umma Ladi taitawa Yusuf tsiya tana cewa ko dai sirikinta zai zama ne bata sani ba da ya maƙale a waje yaƙi shigowa, shi dai murmushi kawai yake har suka fito. da suka koma gida shi ya kwashi siyayyar da Ammi tayi ya kai part nata, sannan ya fito ya wuce na Inna Wuro, yana tafe yana duba agogo, daga lokacin da ta kirasa zuwa yanzu awa biyu kenan. hularsa ya ɗaga ya sharce gumin daya haɗo masa duk da cewar ba zafi akeyi ba, amma halin da yake ciki na rashin sanin a wanne hali Nuratu ke ciki yasa shi haɗa zufa. babu kowa a parlon lokacin da ya shiga, tsaye yayi kawai yana kallon trolly ɗin kayan Nuratu dake tsakiyar parlon a ajiye. mamakinsa ya tsaya akan Inna Wuro dake janyo ƙaramar trolley tana fitowa daga cikin ɗakinta tana maganganun ƙasa-ƙasa, har ta ƙaraso gabansa bai iya ɗauke idonsa daga kanta ba, amsar tambayar dake ransa kawai yake so ya samu tun kamin yayita. bata lura da shi ba saboda sababin da take tayi har sai da ta zo gabansa, shima warin asibitin da taji ne yasa tasan da tsayuwarsa a wurin. ta ɗago tai masa kallo ɗaya ta ɗauke kai. "ashe kazo, nai zaton ai ko ka zama tarihi da nake ta danna maka kira kana ƙin ɗauka. baka san ni ba wata tsiyar zance kayi min ba, idan ka manta na tuna maka ɗana me wannan ƙaton gidan ya tara abinda kai baka da shi, dan haka nafi ƙarfin roƙo a wurinka Yusuf". tasa ƙafa ta tura masa duka trollys ɗin gabansa tana cewa,"gasu nan, dama niyya nake na fita da su na ajiye su daga bakin ƙofa sai kuma Allah ya kawoka ka rage min aiki". Yusuf dai kallonta kawai yake yi, sai da tai shiru sannan yace,"kiran da kika min na mene?". jin yanda yay maganar ta ɗago ido ta kallesa ta taɓe baki sannan tace,"naga duk ka firgice kamar wanda ya tsarewa zaki. to ni dana kiraka ce ka ke me ya faru?, kasan dai haihuwa ba yanzu ba. gani nai nayi na Allah nayi na Annabi, to na gaji da rainon cikin da ba ni nayi ba, shi yasa na doka maka kira kazo kai awon gaba da ƙazamiyar matarka, ba zan iya da tofe-tofen yawu da amai ba, duk ta lalata min wuri da ƙarni. kai baka ji ba daka shigo?, ko da yake yanzu yarinyar can me aikin babarka tasa omo da turaren ƙamshi ta goge min ko'ina, wallahi da ba zaka iya shigowa ba daga bakin ƙofa zaka tsaya, amma matarka ai bata haɗu ba yasin, ciki sai kace akanki aka fara, sakan ɗaya biyu sai a tofar da yawu, can kuma sai dai kaji ana kyalayo amai". ta rufe ido ta dafe goshi tace,"wuwuwu abin dai ba kyan gani da kwatance". ran Yusuf idan yayi dubu ya ɓaci, idan da tasan muhimmancin aikin da tasa ya baro da bata masa haka ba. yaji kamar ya bige ta dan takaici, ya matsar da trolly ɗin gefe ya shige ɗakinta, yana shiga ya fito yana tambayarta ina Nuratun?. "yo ni ina nasan ma inda take, wannan dai fitsararriyar ƙanwar taka ita tazo ta ɗauketa bayan ta gama karta min rashin kunya...yo tsakani da Allah ina gani zan cutu kuma sai naƙi yin magana?, ƙarnin yawu da amai ne fa ke neman halaka ni. banda ma dai halin butulci irin na ɗan adam ina wani zai kallen ya gurza min baƙar magana, to akan Nuratu dai idan ba'a gode min ba ba za'a tsine min ba sai dai idan kuma son zuciya, wane zai iya ɗawainiyar da nai da ita, ce nake ita kanta ƙanwar Uwartata da aka kawowa ita guduwa tai ta barta ta wani fake da ta tafi umarah. haka nake hana idona bacci saboda yarinyar nan, tana bacci ina gefenta ina tofa mata duk kalar adu'ar da ta zo bakina gudun kar a haifi ɗa mara ƙafa, tunda naga alamar tana da mutanen ɓoye, Allah na tuba mene jinnu basa iya aikatawa sai dai Allah yay mana katangar ƙarfe da su kawai...ita dai waccen ƙanwar taka in kaje ka faɗa mata ɗibar albarkar da tai min taje dan kanta ni ba ramawa zanyi ba, kuma ba zanyi Allah ya isa ba tunda dai ina da hankali". Yusuf ya ɗauke idonsa daga kanta yaja trollys ɗin zai fice daga parlon kukan Inna Wuro ya dakatar da shi. ya juya yana kallonta da mamaki, kuka takeyi sosai tana faɗin,"wallahi karka daɗa karka raga ni ko zagin matarka banyi ba, kawai na gaji da ƙazantar ne na tofe-tofen yawu da amai shi yasa nace ta bar min wuri, kuma inda ace ta ban haƙuri ai zan haƙura, amma da yake butulu ce sai dai ta kalleni ta fashe da kuka duk dan wani ya ganta taja min masifa, nace to ta fita ta zauna daga bakin ƙofa idan kazo ba sai ka shigo min ciki ba tafiya kawai zaku yi, ashe taji haushi sai ta faki idona ta dannawa ƴar dabar gidan nan waya, ko minti ba'a ƙara ba sai gata kamar kububuwa ta faɗo parlon nan tana ta huci, da ace ban matsa baya ba da yanzu akan gawata kake tsaye, baka ga irin ɗiban albarkar da Yusra tai min ba, karka ji irin zagin da ta dinƙa surfa min Yusuf, harda kalar zagin da ban taɓa ji ba tunda uwata ta haifeni, wai akan matar Yayanta ba abinda ba zata iya ba, da zasu fita fa sai da ta bangaje ni, nai galantoyi zan kife a ƙasa bangon nan ya riƙeni, yo ka faɗa min ina zan manta da wannan cin mutuncin?, har da cewa fa idan an haifi yaron nan ba zan ɗauke shi ba sai dai kallo daga nesa, to dama ita ta haife shi?, matsalar ban iya haɗa husuma ba ne dana kai ƙararta gaban Amadu wallahi, amma duk da haka ka sanar mata inuwarta na ƙara gani a ɓangarena sai na buga mata duk abinda na raruma". Yusuf bai ce mata komai ba ya fice ya barta tana kukanta. sai da ƙyar Aliyu da ya shigo ya iya lallashinta tai shiru, amma har sannan bata bar maimaita maganar ba. Nuratu na kwance akan gado Yusra ta shigo ɗakin nasu, ta ajiye bowl ɗin dake hannunta akan dressing mirrow sannan ta isa gadon ta miƙar da Nuratu wadda duk jikinta yay weak, pillow ta saka mata ta jingina da shi, tukunna ta koma ta ɗauko bowl ɗin dake ɗauke da fruite salad da ta haɗa mata. "Anty please ki daure ki shanye wannan duka, kinga dai cikinki babu komai". Yusrah ta faɗa tana me cike da tausayinta. Nuratu ta karɓa tasa spoon ta fara sha, sai da ta kusa shanyewa tukunna ta ajiye, tunda ta tashi yau babu abinda ta iya ci, duk abinda tasa a baki baya zuwa cikinta yake dawowa, tayi amai yafi sau biyar, shi yasa Inna Wuro tace yau ba zata iya ba. Yusrah na waya da saurayinta da ta kalla ta ajiye bowl ɗin ta taso. "ina zuwa i will call you letter". ta faɗa tana aje wayar a gefen gadon. "Anty Nuratu ai babu abinda kika sha, gaskiya ni dai ki daure ki ƙarasa shanyewa". Nuratu kamar za tai kuka tace,"na ƙoshi Yusra". haka dai har sai da Yusra tasa ta ƙarasa shanyewa, a lokacinne Yusuf ya shigo, tana ganinsa kuma tasa kukan shagwaɓa, kamar wanda aka zarewa laka ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon. Yusra ta gaida shi ya amsa murya a ƙasa, ya janyo Nuratu jikinsa yana shafa kanta yana lallashinta. ba tare da ya kalli Yusra ba wace,"what did she eat?". Yusra tace,"yanzu ta gama shan fruite salad". ya sake cewa,"ki gasa kaza ki kawon yanzu". "tom Yaya". ta faɗa tana fita daga ɗakin. Nuratu kuka ta ƙara sawa tana faɗa masa,"Excellency ni na gaji da wannan cikin, plss remove it for me". bai iya cewa komai ba ya rufe idonsa ya ɗora haɓarsa akan gashinta, hannunsa na kan cikinta yake bata haƙuri. ji yake da damar da zai mayar da cikin jikinsa da ya maida, tunda ta sami cikin nan bata huta ba, kullum a cikin wahalar laulayi take, ga shi yanzu aka fara ba'aje ko'ina ba, cikin ko 4 months bai kai ba. "ki daina kukan nan please". ta ƙara narkewa a jikinsa tace,"ka kira min Umma". ya ɗauko wayarsa a aljihu ya kira Umman ta vedio call, idon Nuratu na kan wayar tana jiran ɗagawarta. daga can ɓangaren Umma na kitchen lokacin ta ɗaga kiran, kallo ɗaya taima Nuratu ta hangi tarin kukan da idonta yasha ayau. da tsananin tausayinta tace,"what's wrong Nuratu?". "Umma ki dawo dan Allah, ki dawo ki kaini a cire min wannan cikin bana sonsa, na haƙura da samun Bilal ɗin". Umma ta sauke numfashi tace,"a'a Nuratu ba'a faɗar haka, babbar ni'ima ce fa Allah yay miki da ya azurtaki da samun cikin nan, wasu na nan basu samu ba suna cikin damuwa. adu'a kawai za ki Allah ya yaye miki wahalar laulayi ya kuma sa ki haihu lafiya. kar na kuma jin kince ba kya son cikin nan kinji ko". Nuratu ta ɗaga mata kai alamar taji, tana kwance a jikin Yusuf har lokacin, ko kunyar Umman basa ji. Umma ta kalla Yusuf wanda hankalinsa baya wajen, ta ƙara cewa. "am coming back next tomorrow insha'Allah, zuwa yamma in Allah ya yarda na dawo gida, ki daina kukan ya isa haka...irin wannan wahalar Mamanki tasha fama da ita lokacin da tana da cikinki, kamar ba zata rai ba, me ciki dama sai tai haƙuri ta jure". sun jima suna wayar Umma na lallashinta da kwantar mata da hankali kafin su yi sallama. sai magriba Yusuf ya fito daga ɗakin su Yusra shi da matarsa, har lokacin Ammi bata san cewar suna ɓangarenta ba. yasa Yusra ta kai kayan Nuratu motarsa, ba zai iya barinta a gidan ba tunda Umma bata nan, Inna Wuro kuma ta gaji, Ammi kuma ba sauraronta zatai ba, sisters nasa kuma kowacce na busy da study nata ba zai yiwu ya takura musu ba. so is better ya tafi da ita can hotel ɗin da yake kwana su kwana for 2days ɗin da ya rage masa ya koma aiki kano, in yaso sai yasa wata nurse din ta ke lura da ita. hannunsa riƙe da nata sukai parlon Daddy, sai da zasu shiga ya saketa, shi ya fara shiga sannan itama ta shiga. Daddy na zaune akan carpet lokacin, Ammi na kan kujera suna hira da shi, Daddy ne ya amsa sallamar tasu Ammi kam har ta buɗi baki zata amsa ganin Nuratu yasa tai shiru ta amsa a ciki. daga baya suka tsuguna dukansu, bayan Yusuf ya gaida iyayen nasa Nuratu ma ta gaishe su, Daddy ne kawai ya amsa mata, jikinta taji yay sanyi tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata a lokaci ɗaya, har ga Allah bata son wannan ƙiyayyar ta uwar mijinta, kuma duk duniyarta idan aka cire mahaifiyarta aka cire Umma babu macen da take so irin Ammi, ko da ace ba ɗanta take aure ba tana son Ammi saboda tana ɗaya daga cikin mata da suke burgeta. Daddy ya kalle su yana smiling yace,"my daughter i hope there is no worries?". kan Nuratu a ƙasa a ladabce tace,"babu Daddy". yace,"to Allah yayi muku albarka, ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kuma rabaki da cikin jikinki lafiya". ita ta amsa a hankali Yusuf ya amsa da ƙarfi. Ammi dai tun amsa sallamarsu bata ce komai ba. Daddy ya ƙara cewa,"ina mara lafiyar da kace kuna ruƙo a wajenku?". Yusuf yace,"tana can gida muka barota, There was a widow's nurse who took care of her zuwa mu koma gida". Daddy yace,"but kana following situation ɗin da take ciki ko?". yace,"ehh Daddy, ko ɗazu ma munyi vedio call da ita, magana ce dai har yanzu bata yi amma she is getting better". Daddy yace,"masha'Allah, Allah ya bata lafiya, amma har yanzu baka sa cigiyar ƴan'uwanta ba ne?". Yusuf yay ɗan jim kamin yace,"ehh Daddy banyi hakan ba tukunna, saboda kaga ba mu san ma daga inda take ba, and if mukai mata zancen da ya shafi ƴan'uwanta da kuma inda ta fito, her mood was changing a lokaci ɗaya sai ta shiga state of frenzy, so thats the reason yasa muka daina mata maganar gaba ɗaya". Daddy yace,"Allah ya kyauta, Allah masanin gaibu, but there must be something about her gaskiya, kuma ko menene lokaci zaizo da zata biɗi komawa inda ta fito, kace da dukkan alama tana da ƴaƴa?, kaga kuwa ba zata ƙare rayuwarta haka bata nemi ta koma garesu ba, ku dai kuci gaba da bata kulawa da taimaka mata, Allah ya baku lada". a tare suka amsa da,"amin ya Allah Daddy". shiru ya gifta a parlon, Yusuf na taraddadin yanda zaima Ammi maganar tafiyarsu. da Daddy yaga shirun yay yawa ya katse abinda zuciyar kowa ke saƙawa yace,"or do you need anything?". Yusuf yace,"a'a Daddy, dama zamu tafi ne". yace,"ok ba anan zaka barta ba?". ya ɗan sosa ƙeyarsa da kunya yace,"ehhh Daddy". Daddy ya kaɗa kai yace,"alright to ku tashi haka dare nayi, amma dai ita da ka barna nan cikin ƴan uwanta ai yafi ka tafi da ita wani hotel". Yusuf yace,"da yake zamu je asibiti ne da safe". Daddy yace,"to yayi, Allah bada lafiya. ku tashi haka". Yusuf na kallon Ammi wadda ke zaune tana jinsu amma kamar ma hankalinta baya garesu, ta haɗe girar sama da ƙasa ta ɓata rai. yace,"Ammi zamu tafi". yana faɗar hakan Nuratu ta ɗago ido ta kalleta, yanda taga Ammi ta taɓe baki taji kamar an soka mata kibiya a ƙirji. Yusuf ya miƙe tsaye ita kuma ta rissinar da kai tana cewa,"mun gode Ammi da Daddy, Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana me amfani". daga haka suka fice daga parlon zuciyar kowannensu babu daɗi. **** "kin tabbata ba kya jin ciwon komai?". Yusuf dake tsaye a gaban gadon Fillo ya faɗa, yayinda wata nurse dake kusa da shi ke riƙe da file. Fillo tace,"bana jin ciwon komai Dr". ya jinjina kansa, ya karɓi file ɗin hannun nurse ɗin yay rubuce rubucensa. ya ƙara cewa,"gobe da safe insha'Allahu zamu sallameki, Allah ya ƙara lafiya". Fillo ta amsa da amin sannan ta ɗago ido ta kallesa, ƙwayar idonsu ta sarƙe ana juna, Yusuf yaji zuciyarsa ta girgiza, yasan akwai kamanni, amma bai taɓa zaton cewar akwai tsananin kamannin da suka kai irin haka ba bayan na wanda suke identical 2wins, a tare da wa zaisa kamannin yarinyar nan?, idon, fuskar, yanayin komai iri ɗaya ne, sai dai ya rasa iri ɗaya da na waye, tunaninsa da hasashensa ya gaza basa. yayinda a wannan lokacin zuciyar Fillo ke ƙara faɗa mata tabbas tasan wannan fuskar ta Yusuf, sai dai ta kasa tuna aina ne, aina ta taɓa ganinta?. _Comment ɗinku shine ƙwarin gwiwata, rashinsa shi yake sawa na hutar da kaina._ *dont forget to share, comment and vote.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *20* bayan sati ɗaya jikin Fillo ya ƙara yin sauƙi sosai, yarinyar har wani fresh tayi hasken fatarta ya ƙara fitowa saboda kwanciyar da tayi a asibiti me kyau, da kuma irin cimar da take ci me rai da lafiya. na musamman Hajiya Madina ke yin lafiyayyan girki a kai mata, girkin da zai ji ganyayyaki masu ƙara lafiyar jiki da kuma hanta acikinsa, tunda aka kwantar da ita duk wani abinci da zata kai baki da hanta take yin lomarsa, fruite salad kam da bata taɓa shansa ba sai da ya ginsheta. kuma tunda suka dawo bata ci gaba da zuwa aiki ba sai Kaka ce ke yi, Hajiya Madina tace ta ƙara samun hutawa na sati ɗaya sannan sai taci gaba, har wannan lokacin kuma bata san Turaki ne ya kaɗeta ba, duk zuwan da yake yi akai akai zatonta halin karamci ne kawai irin nasu. sa fiya ce yanzu dan ko takwas da rabi bata yi ba, Kaka na daga falo tana sauraren Shaik Ibrahim Daurawa a radio, Fillo kuma na ɗaki tana shiryawa. Kaka tace,"wai ba zaki fito ki wuce ba ne?, kullum sai kin ɓatawa bawan Allah lokaci Fillo, Allah raina yana ɓaci da wannan abin naki". daga inda Fillo take ta ɗan gwame fuska tace,"Kaka fuskar hijab ɗin ce fa ta yage shine nake ɗinkewa". Kaka tace,"uhm haka dai kike kullum da uzurin da zaki bayar, to ki bar ganin saurayinki ne Allah sai nace ya fara yi miki bulalar makara, wataƙila ki fi maida hankali akan karatun". dariya kawai Fillo tai bata ce komai ba, amma har hangowa take wai Amir zai daketa, tana sonsa dan haka ba zata ƙi tsayawa ba amma shi ɗin tasan ba zai taɓa iyawa ba, ko wani me gangancin yaga zai gwada sai iyakar inda ƙarfinsa ya ƙare. ta fito daga ɗakin sanye da hijab ruwan toka, hannunta kuma tana riƙe ne da qur'ani izu sittin ta rungume shi a ƙirjinta haɗe da dardumar sallah. "na tafi Kaka". Kaka ta ɗago ta kalleta tace,"Allah ya bada sa'a, amma ku gama da wuri kinga Hajiya Madina tace ki koma aikinki yau, kya gaida Amir ɗin kice ina daɗa masa godiya Allah ya jiƙan mahaifa". tace,"tom Kaka". da haka ta fice. daga can bakin gate wurin da ya saba zama ta gansa, a durƙushe a ƙasa da alama ya gaji da tsayuwa ne. bakinsa na motsi yana latsa counter dake saƙale a yatsansa, baƙin yadi ne a jikinsa mai taushi mara tsada wanda ya karɓi jikinsa sosai. ya kuma fito da kyawunsa na usulin bafulatani, sumar nan tasa kwantacciya ta fulani tai luff sai ƙyalli takeyi, da takalminsa da agogonsa dai-dai na me rufin asirin ubangiji. tunda ya ɗaga ido yaga Fillo na tahowa zuwa gare shi kyakkyawan murmushi ya ɓalle a saman fuskarsa, zuciyarsa na ƙara cika da tausayi da soyayyar Halimatunsa, ruhinsa na ƙara buƙatuwa da ƙwaɗaituwar ta zama mallakinsa. a lokacin da ta iso wurin ta sakar masa nata sanyayyan murmushi da yake motsa zuciyarsa. ta durƙusa a gabansa ta gaishesa. Ya amsa yana kasa ɗauke ido daga dogayen yatsunta da ta rufe fuskarta da su, murmushinsa na ƙara faɗaɗuwa. sai da yay gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace,"Barka da fitowa gimbiyar Amir, sarauniyar da ta kafa fadarta acikin zuciyar Amir, kazalika uwar ƴaƴan Amir". ta ƙara rufe fuskar da hijab ɗinta, wani daɗi na ratsata. Yay ƴar dariya yana jin tana ƙara burge shi saboda wannan kunyartata. yace,"duk da an hanani ganin fuskar hakan ba zai hana ni faɗin kinyi kyau sosai, matsalar guda ɗaya ce dai da bana so". ya ƙarasa maganar amon muryarsa na sauyawa, tai saurin buɗe fuskarta, so take ta kallesa amma ta kasa, ta sauke idanuwanta a ƙasa da rashin jin daɗi tana jan yatsunta tace,"wacce irin matsala ce?, mecece matsalar da baka so?, a shirye nake da gyara ko menene saboda kai?". ya murmusa kuncinsa sannan yace,"Kunya! itace matsalar kuma itace bana so, amma a iyaka tsakaninmu banda wani daban, sai dai na san ba zaki iya dainawa ba balle ki rage, tunda ba tun yau ba nake roƙon alfarmar a rageta ko ya ya ne saboda tana ƙwarata, amma kamar ma ba'a jin me nake cewa...ni kuma tsakani da Allah ina so ake a bani damar ganin cikin idanuwan gimbiya, ina sonsu, so me yawa ba kaɗan ba". Fillo na murnushi ta ƙara ƙoƙarin sake rufe fuskar sai taga ya haɗe hannayensa alamar roƙo yace,"dan Allah Fillo nah, ki tausayawa zuciyata, ki tausayawa idanuwana". haka dole ta haƙura da rufe fuskar, ba zata iya saka ƙwayar idonta a cikin nasa ba, amma ba zata hanasa ganin fuskarta ba, dan haka ta ɗago kai yanda zai kalleta sosai, amma bata iya barin idonta a buɗe ba ta kullesu. sai da Amir ya ɗauki kusan minti ɗaya yana kallon fuskarta ba tare da ita tai magana balle shi da ya shiga shauƙi. da yana da dama, da yana da yanda zaiyi da yau Fillo bata ƙara kwana a gidan nan ba, da yau Fillo a gidansa zata kwana, kusa da shi, kusanci sosai irin kusancin da zai ɗorata a saman ƙirjinsa ya dinƙa faɗa mata kalaman da zasu mantar da ita duk wani kalar ƙalubale da ta fuskanta a rayuwarta. "ina sonki, ina miki so me tsanani, ƙaunar da nake miki ba mai fasaltuwa bace, bana fatan na rasaki Halimatu, bana fatan Allah ya kawo abinda zai rabani da ke, ke ɗaya ce tal a ƙurya da wajen zuciyata. please ki so ni ko da kwatankwacin yanda nake sonki ne, domin idan babu ke tare da ni Allah babu makawa sai na zama gawa". tai saurin ɗago ido ta kalli raunanun idanunsa. "ina sonka ai kaima kasan da wannan, kuma ba zamu rabe ba insha'Allahu, matarka ce ni har a aljannah insha'Allahu". haka ta faɗa, kuma hakan ke maimaituwa a cikin ransa, maimaituwar kuma ke haifar da jin daɗi tare da shi. da taga kamar yau bai da niyyar suyi karatun muryarta a sanyaye tace,"yau ina da aiki a cikin gida". take annurin fuskarsa ya ɗauke, ya haɗe rai ɓacin rai na ziyartarsa. ya miƙe kawai ba tare da yace mata komai ba ya nufi inda suke zama suyi karatun, baya son wannan aikin nata ya tsane shi. ko wannan karatun da ya tsira yi mata, yayi hakanne dan ya daƙile mata zuwa aikin shi yasa ya saka da safe zasu ke yi, amma ashe na banzar yayi, kamar mayu sun liƙe ita zata ke musu aikin, yanda baya so tai aikin haka baya so Kaka tayi, to amma baida yanda zaiyi, shi ba me ƙarfi ba ne, idan ita ya nemi hanyar hanata bai isa ya hana Kaka tayi ba, to amma me yasa ba zasu nemi wata yarinyar da ta dinga yi musu ba?, su bar masa Fillonsa ta huta kamar a baya. Fillo ta ƙaraso jiki a sanyaye ta shimfiɗa masa dardumar, sannan ta shimfiɗa ɗankwalinta ita kuma ta zauna akai, har sanda ta zauna shi yana tsaye kamar ba zai zauna ba, ita dai bata ɗago ta iya kallonsa ba, saboda hawayen cikin idonta zasu sami nasarar zubowa, ko kaɗan bata son ganin ɓacin ransa, musamman ace itace sila. sai da ya zauna sannan tace da shi,"kayi haƙuri, dole ce tasa ba dan muna so ba mu kanmu. aikin nan shine rufin asirinmu, kana gani Kaka daɗa tsufa takeyi jikinta na ƙara saki, ba zata iya ɗawainiyar da tayi a baya ba, ni kuma da ta riƙe ni bayan banda kowa dole na taimaka mata a yanzu dana kawo ƙarfi, tana buƙatar taimakona. kuma yanzu idan banyi aikin nan mun sami kuɗin ba da me kake so Kaka ta kaini gidanka Amir?". ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta yace,"ni ke nake so ba abinda za'a kai ki da shi ba". ta girgiza kai tace,"a'a Amir, duk da bamu da komai, kuma ni ɗin ba kowan kowa bace, amma ina so na wuce gori a ko ina ne. kuma baya nan ina so ko bayan ran Kaka na kalli wani abin da zan gani naji daɗi, na san nima an tafi an bar min gado". yace,"shikenan, bismilillah". ya faɗa yana mata alamar ta fara karatun. tasan maganarta bai masa daɗi ba amma dole ta faɗa, kuma gaskiyar kenan. ba'a san gawar fari ba, kuma ba fata take ba, amma idan Kaka ta mutu, shi kuma ta aure shi shima ya faɗi ya mutu rabo bai samu a tsakaninsu ba, wa take da shi kuma me zata kama?, gwara tai duk kalar wahalar aiki tayi su sami kuɗin da Kaka ke fatan su samu ta cika burinta na siya mata fili, da kuma jarin da zata samu sana'ar yi. cikin zazzaƙar muryarta ta fara biyo masa haddar karatun da yake biya mata kullum, acikin ƙira'a me daɗin gaske, kuma tartilan tajwidan, kace wata balarabiya. haka tai ta biyawa har sai da ta kawo inda suka tsaya sannan tai shiru, ta buɗe ƙur'anin yay mata ƙari. yau ko tajweed ɗin bai biya mata ba ya miƙe yana mata sallama, muryarta a raunane tace,"tun yanzu?, kuma ba zamu yi tajweed ɗin ba? kayi haƙuri dan girman Allah". bai juyo ba daga tsayen da yake, hannayensa na aljihu idanuwansa a kulle. abinda ba tai zato ba abinda bata taɓa tsammata ba daga gare shi, magana ce ya faɗa guda ɗaya tal, amma magana ce me zafi, wadda take daidai da tsawon kalmomi fiye da dubu, zafinta ke dai-dai da sukar mashi a ƙahon zuci. bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, ƙafafuwanta na rawa suna neman su gaza ɗaukarta, kallonsa take amma wani Amir ɗin na daban take gani ba Amir ɗinta da ta sani ba. tasan dai ɓacin rai kan iya saka mutum yay komai amma batai zaton ɓacin rai zai iya sa Amir ya huda ƙirjinta da kibiya ba. zata jure komai ba, amma ba zata juri maganar ba, cin fuska baya ɗaya daga cikin abinda zata ɗauka, dole zata mayar masa, dole itama ta saka masa ɗacin da ya saka a tata zuciyar, ya kamata ace shima yasan wacece asalin Fillo, wannan Fillon da bata ɗaukar wulaƙanci daga ko waye, duk kuɗinka, mulkinka, matsayinka, muƙaminka, basu zasu hana ta rama abinda akai mata ba. ta tattaro sauran courage ɗin da take da shi, laɓɓanta suka tale da niyyar yin magana daidai lokacin shi kuma ya juyo ya fuskance ta. taja dogon nunfashi ta sauke, ta haɗiye wani abu da bata san menene shi ba, ta dunƙule hannunta da zuciyarta ke ingizata akan aikata abinda dole zai saka tayi da na sani. Amir kallonta kawai yake yana ganin yanda take haɗa zufa duk da iskar dake kaɗawa a wurin, ɓacin ran dake fuskarta na haɗewa da jin zafin abinda ya faɗa mata acikin zuciyarsa, yana jin tamkar wuta ce ke ruruwa a tare da shi, me zai ce yanzu?, ta ina zai fara?, me zai faɗa mata da zai goge tabon da dasa mata yanzu?. _"akwai abinda bai sani ba, tabbas akwai abinda bai sani ba a tare dake, ki faɗa masa hakan Fillo"._ abinda zuciyarta ke faɗa mata kenan, sai dai at the moment da ta ɗago kai suka haɗa ido sai komai nata ya ruguje, dukkan plan ɗinta na cin zarafinsa ya rushe, ta sauke idonta ƙasa tana jin ba zata iya komai ba, ba zata iya yiwa wannan mutumin komai ba, wannan mutumin dake gabanta ba ɗaya yake da kowa ba a duniyarta. ta duƙa ta ɗauƙi qur'anin da dardumar ta juya zata tafi, sai taji muryarsa a sanyaye ɗauke da sautin nadama da danasi yana cewa,"dan darajan Allah kiyi haƙuri ki yafe min, ba laifina ba ne, na kasa controlling zuciyata ne". Fillo taji wani dunƙulen abu ya tsaya a maƙoshinta ya hana yawu wucewa, halaccin da Amir yay mata ba zata manta da shi ba, amma bata jin ko me Amir zai faɗa mata ayanzu zata iya ci gaba da tsayuwa a wurin nan, bata jin akwai wani mahaluƙi a wannan duniyar da ya isa ya hana ƙafafuwanta takawa ta bar wajen nan, ba zata saurare shi ba, ba zata taɓa sauraronsa ba, kuma ba zata ƙara zuwa wurin nan ta tsaya ba wai saboda Amir, ko da ace kuwa gawar Amir ce. tana ɗaga ƙafarta taji yace,"ki tsaya ki fahimceni dan Allah". a ranta ta maimaita ta tsaya?, yana nufin ta tsaya su fuskanci juna ya bata haƙuri ta haƙura?, ai ba zata taɓa tsayawa ba balle ƙwayar idonsa ta karya alwashin data ɗauka. cikin ƙunar rai ta bar wajen, tana ji yana ƙwala kiran sunanta yana roƙonta, kuma wannan kiran sunan nata da roƙon da yake mata na dawo mata da rayuwar ta a baya, yana tuna mata wani lokacin a can baya, lokacin da ta haura katangar gidansu ta dire, cikin duhun dare ba da rana ba. har ta isa ga ƙofar shiga ɓangaren nasu Amir bai daina kiran sunanta ba, kuma duk da irin tazarar dake tsakaninsu bata bar jin kiran sunan nata ba a bakinsa, kiran sunan da take jinsa ba daga muryar Amir ba, daga wata murya ta daban, muryar Yayanta abin ƙaunarta Hamid, Hammah Hamid. ayanzu Kaka kawai take lissafawa wadda ta rage mata a cikin rayuwarta, amma duk ranar da Kaka ta faɗi ta mutu to tasan tana da Hamid, shi kaɗai take da shi ko da ace kuwa har lokacin Hayyo na raye. tun da Kaka taga ta shigo ɗakin a fusace tai shiru bata tanka mata ba, tana kallo ta wurgar da dardumar da ɗankwalin tai cikin ɗaki da qur'ani a hannunta, ko sallama ba tai ba. Kaka ko ta girgiza kai a fili tana faɗin,"Allah ya shiryaki, banda me ƙaunarki wane zai miki wannan gatan na ɗaukar ɗawainiyar yi miki karatu kullum, karatun ma na qur'ani, kuma ba biyansa kike ba, ya kashe uzurinsa da lafiya ko babu yazo ya koyar dake, shi ɗin ma dai da zai iya kenan, idan wani ne tuni bai rabu dake da wannan halin naki ba...kina asibiti yaron nan sai daya zama kamar marayan da bai da gata". Maijidda ta shigo bakinta ɗauke da sallama, Kaka ta amsa mata. a tunaninta ko Fillo bata dawo daga karatun da take ɗauka a wurin Amir ba ne shiyasa ma batai maganarta ba. ta zauna nan kusa da Kaka suna hira, Kaka tace,"ke ni fa tunda muka baro asibiti lissafin karɓar aikinmu ya kubce min, Yami bata ce miki komai ba?". Maijidda tace,"ku zaku karɓi na rana yau, amma naji kamar Yami na cewa ma yau ba za'ai girkin sadaqa anan ba, daga can masarauta za'a kawo". Kaka tace,"ohh ke haka ne fa, jiya Hajiya ta aiko a faɗa mana kinga na manta". suna hirar Maijidda na duba agogo tana kallon ƙofa da jiran shigowar Fillo, amma ganin har tara da rabi ta wuce bata shigo ba yasa tace da Kaka,"Fillo daga wurin karatun zata wuce aiki?". Kaka tace,"ai zatona faɗan ma dake akai da naga baki yi zancenta ba". Maijidda tace,"a'a ba muyi faɗa ba, me kika gani Kaka?". Kaka tace,"tun ɗazu fa ta dawo daga wurin karatun, tana shigowa ta shige ɗaka bata fito ba, Allah masanin fushin nata". Maijidda ta miƙe da azama tayi cikin ɗakin, tana shiga taga Fillo tsaye ta kifa kanta da bango, jikinta sai karkarwa yake yi. haka take ita, indai ranta ya ɓaci duk haƙuri da lallashin da za'a mata ba zasu yi tasiri ba sai tayi kuka ko kuma tayi masifa, idan ba haka ba ba zata huce ba, haka ba zata kwana a tsaye ne tana ta fizgar numfashi da karkarwar jiki, babu me iya controlling ɗinta. Maijidda ta kalli wayar hannunta dake ringing, tunaninta ko Dr Yusuf ne ya ƙara kira dan sau biyu yana yana kira a safiyar nan yana cewa ta haɗasa da Fillo tace masa bata dawo daga wurin karatu ba, to sai taga ma ba shi bane Amir ne. ta kalli Fillo ta kalli wayar, ya zatayi dole masifar dai akanta za'a juyeta ta sani, ai ba yau farau ba, tasan halin ƴar'uwarta, idan tana cikin irin wannan yanayin ko magana bata so ayi mata, ita kuma ba zata iya barinta haka ba tunda Kaka ba sauraronta za tai ba, in akai haka kuma Fillo da wartsakewa sai dai gobe. "Fillo wai menene?, wa ya ɓata miki rai?". Maijidda ta faɗa. Fillo tai shiru ba motsi balle amsa. ta ƙara cewa,"to kiyi haƙuri kinji, fushi fa na abokan sheɗan ne, ki zauna muyi kukan tare to, ni bana son ganinki a haka Allah". Maijiddan ta faɗa in breaking voice. nan ma dai babu amsa babu motsi. hakan yasa Maijidda ta dafata,"ni ce fa nake baki haƙuri Fillo, Hassanarki, Hussaina Hassanarki ce fa, ko kina so na mutu ma barki ke ɗaya?". Maijidda dai kamar me magana da gawa ko kuma gunki, ta yarfar da hannu kamar zatai kuka, ta ƙara kallon kiran Amir dake shigowa a karo na uku, ta dafa kafaɗar Fillo zata juyo da ita tana cewa,"kinga fa Amir ne ke ta kiranki, kar...". ai bata ƙarasa ba Fillo ta ɗago a harzuƙe cikin fusata tai wurgi da hannun Maijidda dake kan shoulders ɗinta, wayar Yami ta faɗi a ƙasa ta wargaje, ƙashin hannun Maijidda yay wata ƙara kamar an karya shi. a zafafe kuma cikin amon muryar da ya cika ɗakin Fillo ta ce mata,"dilla Malama ki rabu da ni, ki ƙyaleni, babu ruwanki da ni, ki matsa daga kusa da ni in ba haka ba duk abinda na miki ke kika jawa kanki". tana faɗin hakan kuma sai ta fashe da kuka, Maijidda cikin jin zafin hannunta ta matso ta rungume Fillo, sai suka durƙushe a ƙasan wajen, sosai Fillo ke kuka Maijidda kuma na tayata, Kaka dai na daga falo tana jinsu bata bi ta kansu ba. sai da aka ɗan ɗau lokaci sannan Fillo ta fara samun sauƙi cikin ranta, har daga ƙarshe ma ya zama ita ke lallashin Maijiddan. itama kuma a sannan sai taƙi yin shiru, taci gaba da zubar da hawayenta a kafaɗar Fillo. Fillo na shafa bayanta tace,"ke Hassana wai mene haka, ki daina mana". Maijidda tace,"to ai kece, na faɗa miki bana so kike bari Shaiɗan yana tasiri akanki akan fushi". Fillo tace,"to ba na daina ba, idan kuma ba zaki shirun ba sai mu ci gaba dan kin san dai ba zan zuba ido kina kuka ina zaune ina kallonki, zuciyata ba zata ɗauka ba". Maijidda tace,"nima ai baki saurareni ba a farko har ma kika ji min ciwo". ta faɗa muryarta na daɗa bayyana kukan da take yi. muryar Fillo ta karye tace,"to kiyi haƙuri, idan kuma ba zaki daina ba shikenan sai mu fasa auren miji ɗayan". sai a lokacin Maijidda ta ɗago suna gogewa junansu hawaye, Kaka na daga falo tace da su,"ke Maijidda kin san dake za'aje gidan sarki ko, ke kuma idan kinga dama ki fito kije kiyi musu aikinsu, in ba za ki ba kuma ki faɗa min sai na miƙe". Fillo tace,"to Hajiya Kaka gamu nan". sai da zasu fita sannan suka lura da aika-aikar da suka yiwa Yami, Maijidda tai salati tana rufe baki da faɗin na shiga uku. Fillo tace kin shiga uku ko mun shiga uku, yau akan akwalar wayar nan Yami ba sai ta cinyemu a ɗanyanmu ba. Kaka da ta jisu tace,"zan kuwa faɗa mata". hannu na rawa Fillo ta ɗau wayar tana haɗeta suka fito falo. "yanzu Yami sai tace mun cuceta mun datse hanyar da zasu ke gaisawa da bazawarinta".  Maijidda ce ta faɗa, Kaka tai dariya, Fillo dai duk ta tsure sai ɗaure kyauraye takeyi, fatan ta ɗaya tana ɗora batirin wayar ta tashi. bakinta faɗi yake,"kece me Jidda ki kai magana da ƙarfi, da Kaka bata ji ba ai sai mu ajiye a kusa da ita bata sani ba muyi ficewarmu, Yami ba zata ce komai ba ƙarƙari tace da Kaka Ƙawata to ya za'ai babu komai ai, da saninki ai ba zaki fasa ba". ta faɗi maganar tana kwaikwayon muryar Yami. su duka sukai dariya, kuma cikin sa'a tana saka batirin ta kunna sai ga wayar ta kama. a tare suka sauke ajiyar zuciya. lokacin kira ya shigo da sabuwar lamba, ta miƙawa Maijidda tana miƙewa. ita kuma tace da ita,"ki ɗaga Dr Yusuf ne, tun safe yake kira wai na haɗaku, yama dai ce na masa kwatancen gidan nan nayi masa, ƙila ko zuwa zai yi". Fillo ta harareta tace,"yazo yayi me?". tace,"haka nace miki zai zo?, ce fa nayi ƙila zuwa zai yi, ki ɗaga kiji koma menene daga bakinsa". ta aje wayar a cinyar Maijidda ta tashi sai Kaka tace,"babu kyau dai wulaƙata mutum, musamman wanda ya taimaka maka a rayuwa, ba masu gidan nan ne kaɗai suka taimaka miki ba, harda shi likitan, dan shima ya bada jininsa an zuba miki". Fillo na ɓata fuska tace,"to Kaka yanzu sai kiji yace ai wani magani ko wata allura ya kawo". Kaka tace,"to ki ɗaga mana kiji dai me zai ce tunda ya neme ki, in allurar ce tunda ba shi ne zai yi miki ba ai sai kin so za'ai, abu da kece Halimanki, tun kan ki shigo nan zaki jefar da ita, sai kace kwanciyar asibiti tasa kin manta wacece ke". ba dai haka Fillo taso ba, sai dai bata son jayayya da Kaka, ta karɓi wayar ta ɗaga, tana yin sallama Yusuf ya ɗauki muryarta. daga cikin motar da yake ya kwantar da kansa jikin kujera sannan ya amsa sallamar. Fillo tace,"ina kwana, ya kake?". maimakon ya amsa mata sai taji yace,"ai na shanyu har na bushe, daka ni kawai ya rage ayi". taso yin dariya amma sai ta maze tace,"kaman ya?". yace,"kamar yanda Sister ɗinki bata faɗa miki ba, na kirata nace zanzo na duba jikinki before na bar gari tace min to, ta ban address kuma nazo inata kiranta taƙi ɗagawa, at the end ma sai ta kashe wayar, nayi zuciya zan tafi kuma sai na tuna da saƙonki nace to lallai ko zan kwana anan ba zan tafi ba". bakin Fillo a gaba tace,"saƙon me?, kuma ai ba daidai tayi maka kwatancen gidanmu ba". yay murmushi yace,"tambaya har guda biyu a jere, duk ranar da kika zama lauya ai sai ki ɗaure mutum. to da fari dai address daidai aka ban, domin kuwa gani a ƙofar gate ɗin gidan Alƙali Dikko, kuma gate na ɓangaren ma'aikatan gidan, gani ina kallon me gadi baƙi ɗan lukuti kamarki. saƙo kuma sai kin fito kya gani". da ƙosawa tace,"na san saƙon allura ne kuma bana so kuma ma bama gidan mun tafi ƙauyenmu, sai ka tafi". cikin kwaikwayon muryarta Yusuf yace,"kuma ma ba allura kaɗai bace harda magani, kuma ma da wuƙar farke ciki, kuma ma me gadi yace min kuna nan ba kwa fita, kuma ma ba zan tafi ba har sai kin fito". a wannan karon dai sai da sautin ƙaramar dariyar Fillo ya fito, Yusuf ya gyara zamansa yana sosa kansa wanda yasha sabon aski yace,"kinga Malama ki fito kawai nai miki tiyatar nan a wuce wurin, ni ban haƙura ba har yanzu nafi gane ai miki bakinki acikinki sai a ɗinke wannan bakin tsiwar da Maijidda tace yana isarsu". tasa hannu ta rufe fuskarta cike da kunya, sai kuma tace da shi,"to ka shigo kawai me gadin ba zai hanaka ba, sai kace masa wajen Kaka kazo". Yusuf ya kalli gate ɗin sai kuma yace,"a'a dai ki fito ɗin kawai, ba jimawa zanyi ba akan hanya nake". tace,"tom". ita da Maijidda suka fita, hannayensu saƙale dana juna, hijab ɗin jikinsu iri ɗaya komai da komai. yana cikin motarsa fara BMW, sai da suka isa wurin sannan ya fito. jikinsa shadda ce ƴar ubanta dark blue, ta amshi farar fatarsa, tunda ya fito yake ƙarewa girman gidan kallo tare da jinjina kai, yasan wannan gidan ko filoti goma sha albarka, har ƙasa suka tsuguna suka gaishe shi. hannayensa harɗe a ƙirjinsa yace,"Hassana da Hussaina". su kai murmushi kawai basu ce komai ba. Fillo ta lura yana da magana, hakan yasa tace,"Kaka tana gaisheka, kuma muna da aiki a cikin gida". yace,"ina amsawa, nima yanzu zan tafi ai ba sai kin kore ni ba, saboda nan da minti 20 jirginmu zai tashi. kawai ji nayi ina so nazo naga mara lafiya ne". Fillo tace,"ai naji sauƙi". yace,"ehh naga alama ai, Allah ya daɗa lafiya". ta amsa da amin, sai kuma duk suka yi shiru. Yusuf yace,"ranar da zaku bar asibiti baki bari na baki amsar tambayarki ba kika gudu". ta ɗago ta kalle shi tace,"amsar me? aini ban tambayeka komai ba". yace,"ehh bakinki bai faɗa ba amma ƙwayar idonki ta faɗa...kina jin kamar kin taɓa sanin me wannan fuskar ƴan gayun ko". ya faɗa dan raha yana shafa fuskar tasa. bata ce komai yace,"ko ba haka bane?". tace,"nayi mamaki daka fahimta". sai yay murmushi yace,"zaki iya tuna watarana?, lokacin baki kai haka girma ba, time ɗin gidaje uku ne kawai a estate ɗin nan, kin fito yawo kika ji ciwo kika zauna kan yashi kina kuka, wani bawan Allah me tausayi yazo ya sameki yasa ki kai shiru da ƙyar, yace ki nuna masa gidanku ya kai ki kika ƙi kika ce Kakar ki zata dukeki saboda bata san kin fito ba, yace to ki tsaya ya ɗauƙo first aid a mota ya wanke miki ciwon kamin ya dawo kika ɓuya a bayan bulo, kuma ya durƙusa yana haɗa hydrogen kika felle da siraran ƙafafunki kika bar wajen, kina gudu kina waige saboda kar ya kamoki". Maijidda ta ƙyalƙyale da dariya, Fillo kuma kunya ta kamata tasa hannu ta rufe fuska tana murmushi, Yusuf ma murmushin yake. tace,"kuma baka manta kamannina ba har wannan lokacin?". yace,"to yaushe akai abin?, shekara ɗaya da rabi ne fa kawai. kuma ai ba wani girma kika ƙara ba da za'a kasa ganeki, kin dai ɗan ƙara wayo ne kawai, sai abinda ba'a rasa ba, amma ai nasan ko yanzu kika ji ciwo zaki tirje a tsakiyar layin nan ki ta kuka abinki ke ɗaya har sai kinga me allura zaki gudu". murmushi bai bar fuskar Fillo ba har lokacin, taji hirar na tafiya da ɓacin ran da Amir ya haifar mata. Maijidda tace,"gaskiya baka da mantuwa". yace,"ai duk randa zan wuce ta wurin nan ai sai na tuna, kin ga fa haka ta riƙe ƙafa tana kallon ciwon tana ta tsala kuka kyace yanke ƙafar akai, kuma abin takaici ciwon fa ɗan ƙaɗanne ba me yawa ba". ya faɗa yana kwaikwayon yanda takeyi a lokacin. ya basu dariya sosai, yana da fara'a da barkwanci, Maijidda tace,"wallahi na tuna lokacin, ai in faɗa maka ciwon nan anfi wata guda ana jinyarsa, haka take ko ya taga jini a jikinta sai ta hargitse". yace,"kice da idonta biyu aka kaita asibiti ran na da mun shiga uku, ƙila duk patients namu sai sunce a sallamesu dan babu me iyawa da kukanta". Fillo ta harari Maijidda tace,"sharrin Hassana ne fa". Yusuf yace,"zan yarda ai, kece fa". ya kalli agogo yace,"kun ce zaku yi aiki nima kuma zan tafi, bara na ƙyaleku kar na cika ku da surutu, ina da yawan hira da ƙannena, ina son sisters mata musamman kamarku, amma ku ɗin sai naji kuna burgeni sosai". suka ce,"mun gode". yace,"nima na gode, amma ya kamata dai aje ayiwa Kakata godiya na dubiyar dana zo nayi". Maijidda tace,"tom shikenan kayi mana kwatance, sai mu zo wataran". yace,"yaushe kenan". tace,"ehh tou sai mun sami damar fita idan kamar Yami ta aikemu gidan sarki". yace,"to ai kuma ƙila lokacin bana nan". Fillo ta sami kanta da tambayarsa,"ina zaka je?". yace,"ai a kano nake da zama, nan nake zaune ni da matata, nan garin kuma gidanmu ne da Inna Wuro ta samu tayi bake-bake acikinsa ta hanamu sakat, ta mayar da gidan kamar nata...saboda haka idan zaku zo ku tabbatar kun fesa turare kamar zai yi magana, kun kuma kai mata ƙunshin leda ko da babu komai aciki in ba haka ba kun shigesu da sababi". Maijidda tace,"Kakarku ce Inna Wuron?". yace,"ita ta haifi Dad namu amma ta zamar mana ciwon kai, kowa ya gaji da ita...nima dan dai ita ta raine ni banda haka tuni na ɗinke bakin maganarta". sukai dariya su duka, Fillo ta katse hirar da cewa,"tom bari mu tafi, mun gode sosai Allah ya kai ka gida lafiya". suka faɗa a tare suna niyyar wucewa. sai ya tsayar da su. "tsaya ki karɓi alluranki Malama, ki kaiwa ɗaya Kakar taku da kuke cewa Yami wadda kike ɗan tsoro ta dinga tsira miki". Fillo ta ɓata fuska tana kama hannun Maijidda dan su tafi. sai gani sukai ya fito da fararen ledoji guda biyu manya, Fillo na ganinsu ta gane irin ledar kantin da Zaytuna ke yin siyayya ce. ya miƙawa Maijidda yace,"ga shi duka na na mara lafiya ne amma kema idan kina so ana iya tsira miki ko guda ɗaya ce, tunda naga da amana a tsakaninku". Maijidda ta karɓi ledojin tana masa godiya, shi kuma ya zagaya ɓangaren driver seat ya buɗe motar, idonsa na kan fuskar Fillo da ta cukule, sai haɗe gira takeyi kamar zata yi kuka, tana ta harar Maijidda. ya shiga motar yana ta smiling, ya zuge glass na ɗayan kujeran me zaman banza ya leƙa da salon tsokana yace,"Auta ya dai? a saki ran please kar Kaka tace na taɓa mata Hussaina, kuma dan Allah banda kukan allura kinji, kinga kin girma". Fillo da ta gama kumbura tai tafiyarta ta bar Maijidda a baya, yana kallon Fillo har ta shige cikin gida, haka kawai yake jin yarinyar ta tsaya masa a rai. ya kuma kasa gane dalilin hakan, tun randa suka bar asibitin yaji kamar zuciyarsa ta shaƙu da yarinyar, kamar yana ya dinga ganinta kullum, kamar dai yana so ya fahimci wani abun amma ya gagara. sai daya tabbatar da shigarsu gidan sannan ya bar layin yana ji a ransa yana so ya ƙara kasancewa da yarinyar. *Please Vote, Comment, and Share.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *21* Maijidda ce ta wuce da ledar kayan, Fillo na faɗa mata karta soma ta ambaci sunanta idan Kaka ta nemi ba'asin karɓan kayan Dr Yusuf. ai tasan an hanasu shine yana miƙowa ta amshe. Maijidda na ɗan jin tsoro tace,"to ni ai nai zaton da gaske alluran ne shiyasa na karɓa". Fillo na dariya tace,"kinga ke dai kije kisha faɗanki ke ɗaya, ni na tafi aiki. da nasha faɗan Kaka gwara na sha na Hajiya Madina". tana faɗa ta ƙara saurin tafiyarta tana taiwa Maijidda dariya, ita kuma nata jin shakkar shiga da kayan, ji take kamar ta koma taga idan Dr Yusuf bai tafi ba ta basa kayansa, to amma tasan zuwa yanzu ya tafi kam, dan ko ɓata lokacin da suka yi a wurin duba kayan tasan yaje inda zai je. tun shigowarsu gate Fillo ta dage sai sun wuce inda ake zubar da bolar gidan sun zubar da maganun, wanda zatonsu abinda ya faɗa hakan yake. kuma sai da suka je zasu zubar ne suka tsaya suna kallon uban kayan da mamaki. leda ɗaya tulin kayan ƙwalama ne kamar hauka, madara, snacks da choculates da lemukan kwali, tarkace dai iri-iri. sai ɗayan ledan kuma kayan makeup ne aciki, shower gel manyan roba guda biyu wanda mutum sai yafi wata yana wanka da roba, sai lotions da su powder, duka dai dangin kayan kwalliya, kuma da gani kuɗi ne ba na wasa ba aka kashe wajen sayayyar. Fillo ta shiga parlon da sallama tana tafiya a hankali, kanta a ƙasa sai jan yatsun hannunta take yi, Hajiya Madina na zaune akan kujera, ƙafafunta duka biyu akan tum-tum, Sameer na zaune a gaban ƙafafun nata ya tankwashe ƙafa yana yanke mata farcen ƙafarta. sai Nihal dake ɗaya kujeran a zaune tana duba wata handout, daga dining area kuma Zaytuna ce a zaune tana danna waya. Fillo ta ƙarasa ta durƙusa a gefen kujera tana gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ɗauke idonta daga karanta story book ɗin da take yi ta kalli Fillo tana amsa gaisuwar tata. "Halimatu anji sauƙi kenan". tace,"ehh Maama na wartsake gaba ɗaya". "to masha'Allahu, Allah ƙara miki lafiya. kina da ƙwarin dai da zaki iya aiki ko?". Fillo tace,"ehh Maama". Hajiya Madina ta gyaɗa kanta, tai shiru for some seconds sannan tace. "to jiya an kawo miki ƴar'uwa da zaku ke aikin tare, ta kammala komai tun ɗazu, yanzu sai ki tashi kije lesson teacher ɗin ku yazo, idan kuka kammala ke sai kiyi aikin rana". wani daɗi ya mamaye Fillo, ko babu komai burinta na yin karatun boko zai cika, abunda mahaifinsu ya kasa yi musu yau wasu bayin Allah zasu mata shi. tunaninta ya tafi can wani lokaci baya, tana wannan tunanin taji Hajiya Madina na ƙara cewa,"dan Allah ku mayar da hankali kunji ko, abunda za'a muku a makaranta shi zai muku, kuɗi masu yawa aka biyasa, akwai percentage ɗin da za'a ke cirewa a cikin kuɗin aikinku, so idan kun mayar da hankali akan karatun kanku kuka taimaka, idan kuma kunƙi kunwa kanku asara babba". Fillo tace,"insha'Allahu Mama zamu mayar da hankali, insha'Allah ba zan baku kunya ba zanyi abinda kuke so nayi". Hajiya Madina ta jinjina kanta. a lokacin sabuwar maid ɗin da aka kawo ta iso wurin ta tsuguna kusa da inda Fillo take. tace,"Hajiya gani". Maama tace,"yauwa ga ƴar'uwar aikin naki nan. ki bata nata reading materials ɗin da Zaytuna ta baki ɗazu, sai kuyi maza ku wuce me karatun na can na jiranku, awa biyu zaku dinƙa yi, da zarar kun kammala ku yo cikin gida, a kama kai bana son shashashancin banza if not zan sallami yarinya". duka su biyun suka amsa da,"to". sannan Fillo tace,"aina zamu sami Malamin?". Nihal tace,"ku tashi muje let me escort you". ta faɗa tana gyara zaman glasses ɗinta, da gyara dogon wandon dake jikinta. "je ki ɗauko littafan naku". ta faɗa tana nuna Ɗausiyya ɗaya ƴar aikin. da ganinta tana da hanzari akan yin abu, dan cikin sauri ta ɗauko ta dawo, kuma kallo ɗaya zaka mata zaka san she is typical ƴar ƙauye, balle kuma ka kai ka ga kallon the way take abubuwanta, maganarta duka hi da ha ne, jiya ana kawota Hajiya Madina tasa Baba Jummai dake kawo mata ƴan aiki ta kaita saloon aka wanko dattin kanta, kuma suna dawowa tasa tai wanka me kyau da dettol da turaren ƙamshi. haka Hajiya Madina take, bata nuna ƙyama ko ƙyanƙyami ga duk yaran da ake kawo mata, karɓarsu take ta nuna musu hanyar gyara kawai. Nihal na gaba suna biye da ita a baya, zasu fita daga falon Zaytuna ta kira sunan Fillo, ta waigo tana kallonta bayan ta amsa kiran. ta mayarwa da Zaytuna murmushin da take yi mata. "i wish you all the best in your studies dear". abinda Zaytuna tace mata kenan, kuma kamar yanda bata fahimci me tace ba haka itama Zaytunan ta fahimci bata san abinda tace mata ba. Zaytuna ta ƙara mata wani murmushin tace,"ina yi miki fatan alkhairi a karatunki, Allah ya bada sa'a". kan Fillo na ƙasa tace,"amin ya Allah, na gode Adda". da haka tabi bayan su Nihal da suka riga suka fice. awa biyu suka ɗauka suna karatun kafin su gama, kuma sosai Fillo ta gane duk abinda aka koya musu ɗin, karatun ya mata daɗi fiye da yanda ta tsammata, ashe shima karatun boko haka yake da daɗi?, shi kansa teacher ɗin nasu sai da ya mata kyautar biro, har yana tambayarta ko ba yanzu ta fara ɗaukar darasi ba, dan ko da ya basu class work guda biyu ta faɗi a examples ɗin da ya ce su bayar, rubutun ta kuwa baka ce wacce ke koyo ba, Ɗausiyya ce yay ta fama da ita, to itama kuma da yake tana da kishi sai da tai ƙoƙarin iyawar. teacher ɗin nasu ba bahaushe bane, amma yana jin hausa sai dai bata kama bakinsa sosai ba. yay da hausa ya haɗe da turanci, su gane hausar da yake yi su bagarar da turancin nasa, idan ya faɗi wani abin da hausa Fillo har gimtse dariyar dake taho mata take yi. dan da ace ita da Maijidda ne ma sai sun saki kayarsu. suna komawa sallah kawai sukai sannan suka fito suka shiga kitchen, suna aikin Fillo na bitar karatunta, ɗan gutun turancin da brain ɗinta ta haddace sai maimaita shi take a zuciyarta, idan ta faɗesa a fili kuma sai taji maganarta wani banbarakwai sai tayi dariya, haka kawai Amir ya faɗo mata a lokacin, idan yay mata turanci sai yace ta faɗi abinda yace sai ta kasa, yace zata iya tace ita kunya take ji tasan ba zai yi daɗi a bakinta ba irin yanda yake daɗi a nasa bakin, sai kuma ta tuna abinda ya faru tsakaninsu a ɗazu, tai saurin watsi da tunaninsa tana jin zuciyarta na zafi. Zaytuna ce ta taya su Fried rice ɗin da basu iya ba, sun maida hankali sosai wajen ganin yanda ake yi, duk abinda ta ɗauko na vegetable zata faɗa musu sunansa da amfaninsa da kuma yacca ake sawa, babu jimawa suka kammala Fried rice ɗin. suna aikin Ɗausiyya ke tambayarta,"Anty kuma sai ku iya cin abinda muka saka hannu?". Zaytuna tai murmushi tace,"Hammah ne kawai baya cin abinda ƴan aiki suka dafa, amma mu kam muna cin duk abinda ƴar aiki ta dafa muddin ta kula da irin tsaftar da muke so, kema baki ga yau fes dake kika fito ba, kuma ina kallonki duk abinda kike yi cikin tsabta kike yinsa...yanzu ma kalle ki tsab, to tsabta ita ke sawa aci girkin mutum, duk daɗin girkin mutum idan baida tsabta sai dai yaci kayansa shi ɗaya". Zaytuna da Ɗausiyya suka ɗauka tray suka fita da shi, suka bar Fillo da ƙarasa haɗa kunun shinkafar da Samha tace tana so tasha. ta fasa madarar gwangwani ta ruwa kenan sai taji kamar mutum a bayanta, ta waigo ta ga Turaki ne tsaye hannayensa a aljihu yana kallon abinda take preparing, da alama ma ba shigowarsa kenan ba. sai ta nemi ta dirirce, ta durƙusa a gabansa da sauri tana gaishe shi, ita bata san me yasa ba amma duk sanda ta gansa sai ta tsorata. bai amsa mata ba ya wuce ya ɗauki cup ya dawo, tana nan durƙushen har lokacin, da wani irin voice tace da shi. "kana buƙatar wani abu ne?". ya kalleta amma ba ita yake kallo ba hannayenta yake kallo, yace. "tashi". ta miƙe tana ɗan matsawa daga kusa da shi. fuskarsa a ɗaure yace,"what is this?". ta so fahimtar abinda yace, amma hakan bai samu ba, jin tai shiru ya waigo ya dubeta, tana tsaye kamar gunki duk ta cika da tsoronsa, hannun nan sai karkarwa yake, shi kuma abin na basa takaici. yaja guntun tsaki ya ƙara cewa,"i am asking you, what is this that you are making?". yanda yay maganar murya a sama yasa ta fara ƙoƙarin hargitsewa, ta ƙanƙame hannayenta a jikinta tare da kulle idonta, shin har sai yaushe zai fara fahimtar wannan yaren ita kam bata jinsa, ita kuwa ko ba dan komai ba ai dole ta tsaya ta mayar da hankali akan wannan gatan da Hajiya Madina tai musu ta koyi turanci. ji take kamar tayi kuka, bata ko ƙaunar tana aiki a kitchen ya shigo, ko ba'a kitchen ba bata so tana aiki taga giftawarsa, ita haɗuwa ma da shi totally bata so. Turaki ya tsaya yana kallon ikon Allah, shi kam ba dan ba dan ba, da sai yace yarinyar nan bata sahun mutane sai dai wata halittar. karkawarwa take kamar wadda ruwan sanyi yaywa mugun duka, ko kuma wacce iskar fanka ke kaɗawa. sai ya ajiye cup ɗin hannunsa kawai ya rungume hannunsa a ƙirji, ya jingina da jikin drower ɗin yana ta kallon sarautar Allah, ba zai ƙara magana ba balle motsi har sai ta gaji dan kanta ta dawo cikin hayyacinta, sannan zai buɗi baki ya faɗa mata karta ƙara ganinsa ta tsorata tunda shi ba dodo ba ne. lokacin da ya tsareta da tambaya a asibiti ya haska acikin kansa da cikin idonsa, wannan lokacin da ya riƙe hannayenta dan hana su rawar da suke yi, amma still basu daina ba sai ma rawar hannun nata ya haɗe har da nasa, tambayarta yay kawai me ya kaita wannan wajen, amma yanda tabi ta ruɗe ta nemi ta firgice har sai da yasa ɗaya hannunsa ya riƙeta da kyau, dan kamar zata faɗo ne daga kan gadon. _"me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?"_ tambayar da yay mata kenan amma kamar ya tuhumeta ne akan me yasa tai kisan kai. sai da ya matse hannunta da ƙarfi sannan ta buɗe ido ta kalle shi hawaye na sakko mata tace masa,_"ina?"_ harara kawai ya galla mata a lokacin, kafin yace,_"wurin da kika je za ki kashe kanki"._ sai kawai ta shiga girgiza masa kai, cikin rawar murya tace,_"Allah ba kashe kaina naje yi ba, ai babu kyau mutum ya kashe kansa"._ taji yay shiru bai yi magana ba, sai ta buɗe idonta dake rufe ta sauke a kansa, ƙwayar idonta ta shiga nasa, taji wani abu da bata taɓa jinsa ba, taga ya ɗaga mata gira duka biyun yana cewa,_"ummm ina jinki, to wa kika je kashewa?"._, saura kaɗan yay dariya saboda yacca ta ƙara ruɗewa da tambayar tasa, har tana ja da baya wanda inda ba'a kan gadon take ba tsab zata arta da gudu. ƙoƙari take ta zare hannunta a cikin nasa tana girgiza kanta cikin tashin hankalin da ya rufeta farat ɗaya. hawaye ne sosai yake sakko mata a sanda take ce masa,_"Allah babu wanda naje kashewa, me yasa zan kashe wani, akan me?, ko cinnaka bana iya kashewa ka tambayi Kaka kaji, dan Allah kayi haƙuri kar ƴan sanda suji su kamani"._ tai shiru tana fashewa da kuka, har sannan bai ɗauke idonsa daga kanta ba, ganin kallon da yake mata yasa tace,_"na rantse da Allah babu wanda naje kashewa, nima gani na kawai nayi a wajen, ban san ya akayi naje ba, kuma ina ta neman hanyar gida na rasa"._ ya ƙara damƙe hannunta sannan yace,_"har lokacin da ya kaɗeki baki sani ba?"._ ba tare da ta kallesa ba tace,_"na sani, ina ta ɗaga masa hannu bai ganni ba kawai sai ya bige ni"._ numfashi ya sauke yace,_"to kin yafe masa ko kin barsa da Allah?"._ sai da ta ɗago ta ɗan kallesa tukunna tace,_"na yafe masa"._ ya ƙara sauke numfashi sannan yace,_"to aljanun naki da suka kai ki su nawa ne?, dama suna yawo dake ko ranar su ka fara?"_ a wannan lokacin kawai tsaida idonta tayi akan kafaɗunsa, ta girgiza masa kai tace,_"banda aljanu ai, ni banda aljanu, ko Malami za'a kira a tambaya"._ yace,_"wanne Malamin?"._ tace,_"Malamin Ruƙiyya"_. yana kallon yanda take kallon ƙirjinsa kamar me karantar wani abu a wajen, sai da ya kalli wajen yaga babu komai kawai dai ba zata iya kallonsa ba shine take kallon wajen. sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya saki hannayenta ya miƙe ya fita daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba. a yanzu da yake kallonta sai yake ganin kamar a wancan lokacin, har yanzu yana mamakin me ya kaita wajen, me taje yi?, abu ɗaya kawai zai yarda da shi tana da aljannu kuma su suka kaita, abunda kowa ya faɗa kenan. to ya yarda da wannan, amma wannan tsoron nata fa?, shi jininsa babu tsoro a cikinsa, saboda haka ya kamata wannan tsoron nata ya ragu tunda har jininsa na yawo a jikinta yanzu. ya rumtse ido yana tuna the first abunda likitoci suka faɗa sanda suka isa hospital, _"ta zubar da jini da yawa, jini take buƙata a halin yanzu, cikin gaggawa ba da ƙurewar lokaci ba"._ haka suka faɗa a sannan, kuma ba zai iya cewa ga wanda ya nuna masa hanyar laboratory ba, tsintar kansa kawai yayi a wurin, ba tare da kowa ya sa ni ba. abunda ya tsana a rayuwarsa shine ɓata lokaci da kuma dogon bayani, kuma abinda ya sani jininsa AB+ ne, to don me kuma sai an tsaya wani ɓata lokacin gwadawa?, dan haka dawowa kawai yayi ya kama hannun Zaytuna suka faɗa room ɗin da aka kwantar da Fillo. _"ki saka mata jinina, ko leda nawa ake buƙata, ko da za'a kwashe shi duka"._ kayan aiki a ajiye suke to jiran me za tai?, dan haka kwanciya kawai yay akan gado tayi jone-jonen da zata yi, nan take jininsa ya fara shiga jikin Fillo. daga fara shigar jinin bai kuma sanin me ya faru ba, farkawa kawai yayi yaga wani yayi replacing nasa akan gadon, Dr Yusuf, likitan da shima yay kyautar nasa jinin wa yarinyar. sai daga baya Zaytuna ke masa bayanin ai ance shima yana buƙatar ya huta ne dalilin da yasa aka cire nasa kenan, dama leda 1 da rabi ake buƙata, Dr Yusuf ya bada rabin. Turaki ya numfasa yay tattaki ya ƙarasa gaban Fillo dake tsaye har yanzu bata buɗe idonta ba, wataƙila tana jira ne taji ya fita daga kitchen ɗin sannan sai ta buɗe idon, ko kuma tana jira ne ya bata umarnin buɗewar, tunda ita bata da umarnin kanta sai na wani, ya lura da hakan tun farkon zuwanta. sai dai yana zuwa dab da ita taji gabanta yay mugun faɗuwa, allon ƙirjinta ya girgiza, taji kamar ta arta a guje. so take tasa hannu ta toshe hancinta saboda ƙamshin turarensa da ke shiga hancinta, ba saboda rashin daɗinsa ba, idan tace ƙamshinsa babu daɗi tayi ƙarya, wannan ƙamshin yana ɗaya daga cikin ƙamshin da zata iya cewa da wuya a samu ƙamshi me daɗi irinsa. sai dai da ace tana da iko, da ace tana da iko da Turaki da ta haramta masa sanya wannan turaren, da tasa ya bar ƙasar nan yaje wata ƙasar sun wanke duk wani sauran ƙamshi na irin turaren nan dake jikinsa, ba ta son ƙamshin ta tsane shi, ba don komai ba sai don an haɗa asiri da shi, wannan asirin da yay sanadin zuwanta cikin dajin da ta kusa mutuwa. ranar da Turaki ya tsareta da tambayar me ya kaita wancan wurin yana kama hannunta taji ƙamshin, ƙamshi ne da ba zata manta da shi ba, ta jima tana zuƙar ƙamshin a lokacin dan tabbatar daga inda yake fitowa, tunaninta ko asirinne ya kuma biyota, da ga baya ta ankara da cewa ba ƙamshin kowa ba ne sai nasa, that means ya tabbata kenan asirin nan nasan ne, kuma an haɗa asirin ne da turaren da yake sawa...saboda haka yanzu fatanta guda ɗaya ne, Allah ya bata wata dama da zata hana Turaki saka wannan turaren, ko kuma Allah ya ɓatar da turaren daga duniya gaba ɗaya. jin takalmin Turaki gaba ɗaya akan kafaɗunta tai firgit ta buɗe ido ta sauke kallonta akan ƙafafunsa dake cikin takalmin shigowa kitchen. ta haɗiye wani busashshen yawu sannan ta iya buɗe baki tace,"kayi haƙuri ban san me kake cewa ba". ya fito da hannayensa daga aljihu ya tamke fuska yace,"na miki kama da dodo?". da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yace,"to me yasa duk ranar da kika ganni kike rikicewa ki bi ki firgice, ko ina kama da aljaninki?". nanma ta girgiza kai cikin sauri tace,"a'a". yace,"to ina jinki tsoron na mene?". a hankali tana shirin yin kuka tace,"bana so a ɗaga min murya ko kuma a min tsawa". yace,"ni kuma haka nake miki ko?". bata ce komai ba tayi shiru. sai taji yay ƙasa da muryarsa yace,"mene wancan abun da kike haɗawa?". ta ɗaga ido ta kalli robar da take dama kunun tace,"kunun shinkafa ne, Adda Samha tace na dama mata". ya matsa daga gabanta ya ƙarasa wurin yana faɗin,"an gama?". tace,"a'a zan zuba madara ne". yace,"zo ki ƙarasa". sai tai ɗan jim bata motsa ba, ya juyo ya wurga mata wani kallo da niyyar ya doka mata tsawa sai kuma ya taushi zuciyarsa ya sauke murya ƙasa yace,"nace kizo ki ƙarasa ko". ta taho kamar me ciwon ƙafa, ta fasa madarar ta ɗaga gwangwanin tana zubawa hannunta nata rawa, madarar rabi ce ta shiga rabi duk ta zube a ƙasa, haka har ta juye gwangwani ɗaya sannan ta ƙara fasa wani, zata zuba sai taji ya kama hannunta ya karɓi madarar ya zuba da kansa ya jujjuya. yana gama juyawa ya tura mata cup ɗin da ya ɗauko gabanta, bai magana ba amma ta fahimci me yake nufi. sai tace,"zan zuba siga". ta faɗa tana nufar drowern dake sama, ya bita da kallo yana tunanin ta inda wannan ƴar a bar dake iyakar cikinsa zata iya ɗauko abu a wancan drowern dake luluƙin sama. ya lissafa yaga ko da abu zata taka sai ta ɗora me tsayi tukunna tsayinta zai kai, lissafin nasa ya ƙare a kallon siraran ƙafafunta dake yawo a cikin zani, babu makawa ta taka wani abun ta faɗo sai ƙashinta yay breaking in to pieces. ta ɗauko doguwan kujera zata taka ta hau sai ganinsa tayi ya ɗauko roban ya miƙo mata, tana so ta kalle shi amma tana tsoron idonsa, tasa hannu biyu ta karɓa ya wuce ya bar mata wajen. zata zuba sugar ɗin taji yace,"a little bit". sai ta dakata da zubawan. yana ganin hakan sai yace,"ɗan kaɗan". kaɗan ɗin ta zuba, kuma data zuba sai data ɗago ta kalle shi, ba tai magana ba amma kallon nata ya bayyana masa abinda take nufi, itama kuma shirun nasa ta gane cewar yayi. ta zuba kunun a cup ɗin da ya ijje mata sannan ta ɗauko ƙaramin plate ta ɗora cup ɗin akai ta ɗora spoon, ta ɗauka zata fitar masa da shi taji yace,"give me". da sauri ta miƙa masa ya karɓa dan ta gane me yace, bata manta karatun ɗazu ba da teacher nasu ya faɗa musu ma'anar give me da hausa. yana karɓa ya fice ya bar kitchen ɗin, da fitarsa ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, ta ɗauki tea flask ta juye kunun aciki ta ɗauka ta fita da shi, tana fatan Allah yasa Turaki baya falon a lokacin. samunsu tayi duk suna dining suna lunch, tace da Samha. "Adda Samha nan zan ajiye ko ɗakinki zan kai miki?". Samha bata kalleta ba tana wani shan ƙamshi tace,"ajiye anan". ta zagaya ta gefen da Nihal ke zaune ta aje, sannan tai tsaye ƙeƙam a wurin. tana jin idon Hajiya Madina akanta, duk sai take jin wani iri da kallon, ta ƙara yin ƙasa da kai. "Idan kin kawo abu kike tafiya bayan kin ajiye ba sai kin jira an miki izinin tafiya ba, kinji ko?". tace,"tom Maama". Hajiya Madina tace,"da sauran abincin a kitchen ko zaku ɗiba anan, ko kuma wani abun zaku dafa?". tace,"akwai saura Maama". tace mata,"to kije ku ci". har zata tafi Zaytuna ta kalli cup ɗin dake gaban Turaki, ya shanye rabin kunun ya bar saura. taga idan an barsa asararsa za'ai, kuma wannan na flask ɗin yanda suke da son kunun shinkafa ba zasu bar ko kaɗan ba, kuma tasan Fillon da ta haɗa bata rage ko kaɗan da zata sha ba, tasan abinda zata iya aikatawa. dan haka tace mata,"zo ki ɗauki wannan". Fillo ta zagayo gefen da take, ta ɗau cup ta riƙe. "ki shanye shi karki zubar". ta wuce ta koma kitchen ɗin, ta tarar Ɗausiyya ta zuba musu abincinsu a wani ƙaton roba, da dukkan alama Ɗausiyyan na da shegen ci, kuma bata saba cin abinci a ƙaramin kwano ba. ta ɗauki wani cup ɗin separately ta juye kunun da Turaki ya rage, bayan ta wanke cup ɗin ta maida shi ma'ajiyarsa tabi bayan Ɗausiyya suka fita. **** Boɗejo na zaune a tamfatsetsen falon na gidan Hakimi, wata maid nayi mata tausa. da sallama aka shigo falon, Boɗejo ta ɗauke kanta ga barin kallon tv ta koma kallon ƙofa. ganin masu shigowa ta buɗe baki cike da jin daɗi tace,"Ilham". ta faɗi sunan tana me cike da mamakin ganinta. Ilham da ƙawarta suka ƙaraso ciki, ita ta ƙarasa inda Boɗejo take ƙawartata kuma ta zauna akan kujera. "bari in samu ladan nima". Ilham ta faɗa sanda ta zauna a ƙasa tana cewa da maid ɗin ta tashi ta tafi zata ƙarasa ma Boɗejo tausar. "rai kan ga rai, ashe da rabon ƴar nan zan ƙara ganinki kamin na mutu". Ilham tace,"bar zancen mutuwa my Only Granny, yanzu ai zaki ke ganina akai-akai tunda dai Allah ya yarda an kammala karatun". Boɗejo da har yanzu daɗi bai saketa ba tace,"ai ko dai naji daɗin kammala karatun nan, haka kawai Hashimu ya wani kwasheki ya kai ki wata uwa can duniya kiyi karatu ke ɗaya, ai ranar nan sai dana masa tatas nace idan baya ƙaunarki ne ya faɗa mana sai muje mu ɗauko ki mu dawo dake, wannan wane irin karatu ne ace shekara biyar anata faman yinsa babu ƙarewa". Ilham tai murmushi tace,"to Boɗejo ba gashi har mun kammala ba". "haka ne dama komai ai lokaci ne, yanzu ai ba tausa zaki ba Ilham jikina zaki taho". Ilham ta bar matsa ƙafar da ta fara tayi jikinta suka rungume juna. duk su biyun suna masu jin daɗi. Ilham ƴar gidan Hashim ce mai martaba na yanzu ɗan Boɗejo, itace ƴarsa mace ta biyu wacce taci sunan Boɗejo Rumana, ta tafi america karatu inda ta karanci business administration, kuma tunda ta tafi bata dawo ba sai yanzu, shekara biyar cif. ba don babu halin dawowar ba sai dan kawai mahaifinta yafi so ta nutsu tai karatunta, ya kanje ya dubata akai-akai shi da mahaifiyarta wacce itace mata ta biyu a wurinsa. Boɗejo ko da yaushe acikin mitar karatun Ilham ɗin takeyi duk sanda taje wajen me martaban, har ta kance ko dai dan yaga an saka mata sunanta ne shiyasa baya ƙaunarta, da ƙyar yake samu ya lallasheta, idan yace ta shirya akaita taje ta ganota sai tace ita ba zata je ƙasar arna ba, dama saudiya ne to anan tafi kauri amma ita kam ba dai ta hau jirgi taje ƙasar arna ta kwasowa kanta zunubi ba. Aisha na gefe tana kallonsu da burgewa, ita bata taso ta sami kakanninta ko ɗaya ba duk sun mutu. shi yasa idan taga tsofaffi sai taji suna burgeta, dalilin da ya sa ta biyo Ilham kenan suka taho tare, amma yau tayi niyyar komawa kano saboda kar mahaifinta me martaba sarkin kano ya dawo bata nan, yana dira wanda zai so ya fara ganawa da shi itace, kasancewarta auta. Hajiya Atika matar Hakimi ta shigo ɗakin, itama tai mamakin ganin Ihlam tace,"yaushe kika dawo?". tace,"jiya da yamma, tun jiyan ma naso nazo naga Boɗejo Mami tace na bari dai zuwa yau". Hajiya Atika na murmushi tace,"lallai ne to sannun da zuwa, fatan an kammala karatu lafiya?". tace,"lafiya lau Hajiya, ai banma taho ba sai dana jira result ya fita. jiya ina dawowa Me Martaba yay min kyautar wannan gidajen guda biyu na estate ɗinsa". Hajiya Atika tace,"masha'Allahu, Allah yasa a amfana da karatun da akai, ita kuma ƙawar taki fa?". Ilham ta kalli Aisha sannan tace,"ai ba tare mukai karatun ba, tazo min sannu da zuwa ne, itama ta kusa kammalawa tana karantar AEE ne a Germany". Aisha ta gaida Hajiya da Boɗejo, suka amsa suna sanya musu albarka. Ilham tace,"Hajiya ita ɗin fa ƴar sarkin kano ce". Boɗejo tace,"ni fa ince, shiyasa da ta shigo taƙi gaisheni ta hakimce mana akan kujera, ashe izzar masu sarautan ce, to ni nan da kike gani na haka kamar ba kowa ba to sarauniya ce ada, kuma ni na haifi Baban wannan yarinyar, kinga na zama matar sarki uwar sarki, nan gaba kaɗan ma zan zama Kakar Sarki, dan sai an sami wani jikan nawa ya hau kujerar sarautar nan, dan haka ki sadda kanki ƙasa ki min biyayya ki kwashi albarka, ko me gidan nan Hakimi da kike ganinsa ɗana ne shine na fari, kinga kuwa indai girman izzar sarauta ne aini ke da ita bake ba yarinya". dukansu suka yi dariya. sai yanzu Hajiya Atika ta samu damar isar da saƙon Hakimi. "dama Hakimi ne yace na faɗa miki ko kema zaki je wajen taron nan na buɗe company ɗin su Turaki". Boɗejo tace,"shi Turakin ne zai buɗe kamfani ko kuma ɗana Dikko ya buɗe masa?". Hajiya Atika tace,"ehhh Alƙalin ne ya gina ya kuma mallaka masa shi da Khalil, kamfanin haɗa lemuka ne". Boɗejo tace,"ni dai ince, amma ina Turaki yaga kuɗin buɗe wani kamfani ai sai dai ɗan nawa. kuma tunda dai ya riga ya mallaka masa ba zani ba, babu wani taro da zanje ni kam, gwara naja mutuncina". Aisha da Ilham na kallonta, Hajiya tace,"to akwai wata matsala ne Boɗejo?". tace,"matsaltsalu ma kuwa, wa ya aikeni zuwa gurin da yake mallakin Turaki!, tun fa ranar da akai wannan zaman akan batun aurensa nace ko aikin asiri ke cinsa shikenan fa ya daina kulani, idan ya ganni ma ɗauke kai ya ke, jiya ma da suka zo gidan nan shi da ubansa kallon arziƙi bai min ba, yana ji Dikko na gaishe ni amma balagaggen yaron nan sai yasha mur ya kauda fuska gefe, to yanda ya ƙullace ni ɗin nan na sake naje kamfanin nasa ai sakawa zai yi a kore ni, kaɗan daga aikinsa, dama ya taɓa korata daga ɗakinsa daga zuwa in dubasa, kinga kuwa me zai kaini kamfani kuma, a'a ku ɗin dai kuje sai kun dawo, wannan ɗan ai halin wan Kakansa yayo, Sarki Adam ba, basu da kyau sam". Hajiya tace,"to Allah ya kyauta, bari na sanar ma Hakimin". Boɗejo tai shiru bata ce komai ba tana ta shafa kan Ilham, har Hajiya ta fita sai ta dawo tace,"Ilham ku ba zaku je ba?, su Hanifa tun ɗazu suka tafi. shi ma Me Martaban yanzu naji sunyi waya yana batun zasu tafi". kafin Ilham tace komai Boɗejo tace,"kinga Atika du Allah tafiyarki, yaushe yarinyar ta dawo ko hutawa bata yi ba ace ta wani kama shiga cikin hayaniya, ƙila ma taje taron buɗewar kuma a fara haɗa lemon aƙi sammata, tunda me kamfanin ba mutumci garesa ba, gwara taja mutumcinta da ajinta". Ilham tace,"Boɗejo ina son zuwa fa, dama haka nace ma Mami zan bi ku mu tafi, kuma fa idan banje ba Hammah Turaki ba zai ji daɗi ba tunda yasan na dawo, yaga duk ƴan'uwa sunje ni banje ba, sai yay zaton wani abu". tana rufe baki Boɗejo tace,"Allah ba zaki ba, babu wani taron buɗe kamfanin lemu da zaki je, ki zauna ki huta abinki. mene wani wani Hammah Turaki balle rashin jin daɗinsa, ya daɗe bai ji rashin jin daɗin ba, Turako ba Turaki ba". tunda Ilham taji ta rantse kawai sai ta haƙura, ita da Aisha suka durfafi dubulan da alkaki da aka kawo musu. suna ci Boɗejo na basu labarin sarautarsu ta da. *Comment, Vote and Share Please.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *22* After 4months, cikin ƙaton office ɗin da sanyin Ac ke ta busawa yana haɗewa da daddaɗan ƙamshin turaren dake jikinsa yana bada wani irin sanyayyan ƙamshi me motsa zuciya. Turaki ne zaune akan kujera dake ɗan juyawa da shi gefe zuwa gefe, one of his fingers on his lips, cikin yanayi na nazari akan wani lissafi nasa. numfashi ya sauke sannan ya shiga operating laptop ɗin dake kan table a gabansa, ya ɗau lokaci kafin ya ɗauƙi wayarsa a gefe yay calling numbern Khalil. in the next 3minutes sai ga Khalil ya shigo office ɗin, tun shigowansa Turaki ke kallonsa har sanda ya ƙaraso ya zauna kan kujera. "Director". Turaki ya faɗi sunan da yake kiran Khalil da shi a yanzu tun bayan mallakar wannan company ɗin da sukai. Khalil ɗin shima yana kallonsa ya amsa da nasa sunan da yake kiransa da shi na yanzu. "yes Manager". anan ne kuma Turaki ya ɓullo da wata magana wadda ta shafi aikin company ɗin nasu, sun ɗau tsawon lokaci suna tattaunawa akan issue ɗin, Khalil nata ƙara kawo dabaru da zasu daɗa ɗaga company ɗin nasu zuwa sama, dan sam basa saka kamfanin nasu a matsayin ƙarami saboda yana sabon buɗewa, so suke cikin ƙaramin lokaci ya kai wani babban mataki da ba kowanne company ke samu ba at once. a lokacin Turaki ya haɗa urgent meeting da staffs nasu, aka shiga aka ƙara tattaunawa kowa na bada POV nasa akan ganin kamfanin ya haɓɓaka. sai da suka ɗauki tsawon awa guda sannan suka gama. suna kammalawa kuma Turaki ya bar office ɗin, ya tafi airport ɗauko Bello Ƙaraye wanda ya dawo daga sudan yaje wani course. akan tinin barin Gombe international airport, cikin motar ƙirar Bugatti, motar da Mai Martaba ya bawa Turaki ita a ranar buɗe company ɗinsu, Bello ya kai hannu yay reducing volume na karatun qur'anin da suke saurare tun barowansu airport, can kuma sai ya kashe gaba ɗaya. yace,"Kana ciwon baki ne?". Turaki yayi masa shiru bai tanka masa ba, idonsa na manne akan titi. Bello yay tsaki,"duk inda ɗan rainin hankali yake daga kanka an rufe ƙofa. banda iskanci tun tahowarmu nake magana but you refuse to answer me, kuma tsabar miskilancinka ya kai intaha ina kallon bakinka yana motsi amma ba zaka faɗi abinda ke cikinka ba...i don't know what is exactly wrong with you, i saw some changes in you tun before na tafi, to ni ba ɗan iska bane da zan ta tambayarka kana min banza". Turaki yace,"ka bani damar magana ne balle na faɗa maka abinda ke cikin nawa?, tun fa da na ɗaukoka ka isheni da Bima Restaurant, sai kace baka taɓa cin abinci ba a duniyarka. tun saukar ka you din't even ask about my health, abinci abinci kawai shi ka sani, kai idan kana jin yunwa you see nothing balle ma ka lura da ramewar da mutum yay". yanda yay maganar a ƙufule Bello Ƙaraye ya bushe da dariyar ƙeta, shi dai tunda ya fito a jirgi ya kalla kamar idanun Turaki sun faɗa loko, to amma bai lura da muguwar ramewar da yay ba sai yanzu, yanwa yake ji sosai shi yasa idonsa ya rufe da ganin komai. yace,"to ka bani damar ganin ramar da kayi ne balle nace Muhammad Turaki baka da lafiya ne?, tunda fa da ka ɗaukoni fuskarka take a ɗaure, sannu wannan bata haɗani da kai ba, to ta ina zanga wata rama?, motsin bakinka kawai na lura da shi...anyway what is wrong with you?, did you go to the hospital?". Turaki yay masa wani kallo yace,"ciwon uban me nace maka ina yi da zanje asibiti?, ni lafiyata ƙalau". Bello yace,"ikon Allah, to naji lafiyarka lau. what is the problem?". Turaki yay masa shiru yana kallon titin gabansa, cikin ransa yana tunanin ta inda zai fara yi masa maganar, sarai ya san rainin hankalin Bello, yanzu sai ya faɗa masa kuma ya ɗauki maganar a gantale. ba zai nutsu ya fahimci naganar ba balle ya basa damar fayyace masa komai. Bello dai na gefe yana kallonsa, ganin baida niyyar cewa komai ya ɗaga kafaɗa ya maida hankalinsa kan wayarsa, ko mene idan tayi tsami zaiji, ba zai iya da wannan miskilancin ba, yunwar dake rarakar cikinsa ma ta ishe shi. shirunsu ya ratsa cikin motar, sai can Turaki yace,"just give me your full attention let's talk". yay maganar a hankali. Bello ya kallesa yaga Seriousness ɗin dake kan fuskarsa, sai ya kifa wayarsa a kan cinyarsa yace,"na baka duka attention ɗina, idan ma so kake na cirosa na miƙo maka gaba ɗaya sai nayi hakan". Turaki ya waigo yay masa kallo ɗaya ya ɗauke kai, ya dinga motsa bakinsa kamar bebe, shi yasan hali na rainin hankalin Bello shi yasa yake ta shakkar faɗa masa, he never take things seriously a lokacin da ya kamata. Bello ya katse tunaninsa,"mu tafi Restaurant ɗin kawai, ba zan iya isa gida banci komai ba". sai a sannan Turaki ya buɗe baki yayi maganar da tasa Bello ya zabura, har yana ƙoƙarin miƙewa akan kujera. da wani mugun shock Bello ke kallonsa yana ganin kamar ba Turakin da ya sani ba ne, wannan wani Turaki ne na daban da zai iya aikata abunda yake faɗa, amma nasa Turakin ko da ace giyar wake yasha ba zai iya aikata abinda wannan ya faɗa ba. "what! kace mene?, na kasa fahimtar me kake son cewa". Bello ya tambaya har sannan idanuwansa a waje. Turaki yace,"abunda kaji na faɗa". Bello Ƙaraye ya cire hular kansa yana goge wani uban gumi da ya fara keto masa, ya koma kamar wanda yaywa sarki ƙarya. "wait Turaki! wait!, abar zancen wasa dan wannan maganan naka ba magana bane da za'a ɗauka matsayin wasa...". bai ƙarasa abinda zai ce ba Turaki ya katse shi,"ni dama na taɓa faɗi maka abu a wasa ne? balle ka ɗau maganar nawa a shashance". Bello yace,"to idan ba wasa kake ba Hauka ka yi?, dan maganar da kayi bata masu hankali bace kuma ba magana bace da hankalina zai ɗauka...kasan kuwa me ka faɗa?, Turaki are you in your sense? yaushe lissafinka ya fara kwancewa?". danger ta tsayar da motarsu, fuskar Turaki a ɗaure ya juyo ya kalli Bello yace,"kaga Malam, ban faɗa maka personal issue na ba dan ka dinga min ihu aka ba, idan ka gane fine, idan ba gane ba just keep quite". Bello yace,"ba zanyi shirun ba". yay ɗan jim yana maimaita furucin Turankin acikin kansa, anya kuwa bai sha wani abu ba kafin ya ɗauko sa?. ya ɗaga kai ya ƙara kallon Turakin da tsananin mamakin da yaƙi barinsa, da ƙyar ya iya buɗe baki yace masa,"da sanin wa kuma da izinin wa akai hakan Muhammad?". Turaki yace,"da sanin kaina da izinin kaina ni ɗaya, sai kuma me?, sai akayi ya ya?". da wani mugun jin haushinsa Bello yace,"sai ka yi ba dai-dai ba, kuma tun wuri kaje ka warware kwaɓar da ka aikata kai ɗaya, karma akai gaba naji kana ambatar sunana". murya a sanyaye Turaki yace,"abinda nake ganin ya dace nayi shi nayi Bello, sakayyar da ya kamata nayi kenan Bello, kai kanka ka sani komai da lissafi nake yinsa, bana abunda bai dace ba ka sani. and na san babu wanda zaiyi suppprting nawa shi yasa nayi komai ni ɗaya, even if its you na tabbata hakan zaka aikata...ba zaka gane komai ba sai na maka cikakken bayani Bello, wannan hargagin naka duk ba shi bane, ka fara ɗaukar maganar da nai maka da mutunci sannan sai nai maka bayani dalla-dalla". "bayanin banza Turaki, wane bayani zaka min dalla-dalla da zan fahimce ka?, wait!  tunaninka ma kaina zai ɗauki maganar daka zo min da ita ne?, to ba ni kaɗai ba, babu me ɗaukar wannan zancen banzan naka, so tun wuri ma kwaɓar da kaje ka aikata kai ɗaya kaje ka warwareta kawai Malam". a fusace yayi maganar, shima kuma Turaki cikin fusata yace,"Bello Tukur Ƙaraye karka ƙara min ihu acikin mota, karka ƙara ɗaga min murya". shima Bello ya ƙara fusata yace,"Muhammad Turaki Habib ba zanyi ƙasa da muryata ba, kayi duk abinda kake ganin za kayi, ya za'ai ka aikata ba dai-dai ba kuma kace ba zanyi magana ba. tunda dama kasan ba zan goyi bayanka ba ai dole kaƙi yin shawara da ni kaje ka aikata abinda kake ganin ba zai zame maka matsala ba...ni har yanzu na kasa gane menene acikin kanka balle na fahimci kan zancen naka, anya baka sha wani abun ba?". Turaki yay masa banza, Bello ya dinga kallonsa da bala'in mamaki, ko a mafarki bai taɓa zaton Turaki zai iya aikata abinda ya faɗa ba balle kuma a zahiri. shi ya san waye Turaki, tun suna yara suke tare, ya san sarai abinda zai aikata da wanda ba zai aikata ba, and ya san ba zai taɓa aikata abu ba tare da ya nemi shawararsa ba ko kuma ya faɗa masa ba. Turaki baya gaban gansa sai da sanin mutum huɗu, dole Maama ce mutum ta farko da Turaki zai sanarwa abunda zai aikata, sannan shi ya biyo bayanta, sannan Baffa, sannan Zaytuna, dole mutum huɗun nan sai san abu kafin ya aiwatar da yinsa. amma this time around baya zaton cikin su huɗun akwai wanda yasan da wannan batun, sai a yanzu da shi ɗin ya sani, ya san abinda ba zai iya ƙaryatawa ba tunda yaga gaskiyar lamarin akan Fuskarsa da kuma furucinsa. wai har yana faɗa masa abunda ya dace shi nayi Bello?, tukunna ma! Bello ya sauke numfashi yace,"Maama ta sani?, ni ne daka mayar da ni banza yanzu kaje kai gaban kanka baka faɗa min ba?". har yanzu murayar Turaki da sanyi yace,"itama bata sani ba". Bello ya zaro ido,"what!". yace masa,"yes, bata san komai ba akai. kai ɗin ma na faɗa maka ne saboda na kasa riƙe abin ni kaɗai, ban san wane kalar asiri kayi min ba da bana iya riƙe sirrina sai na sanar maka". fuskarsa a tamke yayi maganar kamar yanda muryarsa ma take a tamke. Bello yay ƴar dariya yace,"Allah ka hauka ce ko kuma ka fara shaye-shaye, faɗa min waye ya baka gurguwan shawarar nan na fara shaye-shaye?". Turaki ya kallesa ta gefen ido yace,"Bello ni nake shaye-shaye?, ni kake cewa ina hauka? just saboda na fita hakkinka tunda na san bama ɓoyewa juna komai". Bello yace,"ai mahaukaci ma ba zai yi abinda kayi ba, sai me shaye-shayen dai, dan abinda ka aikata na ƴan ƙwaya ne, wanda yake cikin hankalinsa ba zai taɓa aikata haka ba wallahi...and imagine, ko kunya baka ji ba kake faɗa min wai Maama bata sani ba. so ko me zaka yi a haukace kake sai dai kaƙi yarda, kana buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa dole". Turaki yay parking motarsa, without looking at Bello yace,"fitar min a mota". yace,"inje ina?". Turaki yace,"kaje inda masu hankali suke". Bello yay dariya sosai, dariyar dake ƙara ƙular da Turaki, ya dinƙa jin wani tuƙwiƙwi a zuciyarsa. Bello yace,"dan Allah dan Annabi ka juyo ka fuskance ni muyi maganar gaskiya, ka faɗa min cewa ƙarya kake yi, becouse the only Turaki i know ba zai yi wannan haukar ba". Turaki ya kallesa yana jin kamar ya bubbuge shi, wani takaicin Bello ya ƙara cunkushe masa a heart. yaja tsaki kawai ya fice daga motar, Bello na kallonsa ya tsayar da me napep ya hau suka bar wajen. ya tafi ya barsa da tunani kala-kala acikin ransa, abunda Turaki yayi sam ba na mutane ba ne. sai kuma yay shiru yana dogon nazari, to ma...sai kuma ya sauke numfashi, da ya sani ya basa damar yi masa bayani dalla-dalla, ƙila ya fahimce shi ɗin, amma duk da haka idan shi ya fahimta ta ya iyaye zasu fahimce shi?, da wanne idon ma zai jewa Hakimi?. fitowa yayi daga motar ya koma driver seat yaja motar, yana ta kiran wayar Turaki amma bai picking ba, kuma yasan yana sane, kuma ko da ace ya bisa gida yanzu ba zai taɓa sauraronsa ba, so gwara ma ya bari sai gobe sa haɗu, saboda haka kawai sai ya wuce gida da motar tasa. **** Fillo na zaune cikin inuwa a filin ƙofar ɗakinsu na ƴan aiki, littafi ne a gabanta da biro a hannunta. bitar karatunsu take yi dan gobe lesson teacher ɗin nasu zai yi musu exams. Ɗausiyya ta ƙaraso wajen itama, ta zauna akan tabarmar kusa da Fillo, ta leƙa abinda take karantawar sannan tace,"yauwa du Allah ki ƙara min bayanin wannan, ni ɗazu duk ban gane ba, ya saka turanci da yawa a maganar tasa". Fillo ta aje littafin, ta falli takarda ta shiga yiwa Ɗausiyya bayani turyan turyan kamar itace teacher ɗin. suna cikin yin karatun ne suka ji wayar ɗakinsu na ringing, Ɗausiyya ta miƙe tana ƙorafin ba za'a barsu su dinƙa hutawa ba, yanzu sai ace suzo suyi aiki yen yen yen. Fillo ta bita da kallo tana faɗin,"ke kuma da samun wuri, dama me kika zo yi idan ba aikin ba". Ɗausiyya ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Zaytuna tace da ita,"ina Fillo?". tace,"tana waje tana karatu". tace mata,"kice tazo ta sameni". "tom Anty". ta faɗa tana ajiye wayar ta fito daga ɗakin. inda suke ta koma ta zauna ta ɗauki nata littafin tana sanarwa da Fillo saƙon. Fillo tace,"wacce Antyn?". tace mata,"Anty Zaytuna mana". Fillo ta miƙe tana faɗin,"au nai zaton Anty me dogon baki ce, wallah har gabana ya faɗi". Ɗausiyya tayi dariya tace,"idan itace ai ba zaki ga na dawo yanzu ba, da tuni tana nan tana surfa min zagi ni da iyayena kafin tace min kiranki take". Fillo ma tai dariya tace,"ba kya nan ai ɗazu aka ce mana shegu masu warin baki". Ɗausiyya tace,"sai kika mata shiru baki yi mata rashin kunya ba?". Fillo ta harareta tace,"ai tunda na faɗa miki sai kije ki mata tunda you are the boss". su kai dariya gaba ɗayansu Ɗausiyya na faɗin,"Anty Samha ta mu ta bala'i". kafin nan Fillo ta wuce kiran da ake mata. a ɗaki ta sami Zaytuna tana waya, ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran ta kammala, Zaytuna tayi mata alama da hannu cewar ta shigo ciki ta zauna. ta bar ƙofar a buɗe ta shigo daga ciki ta zauna akan carpet. Turaki yazo shiga ɗakin ganin Fillo sai ya fasa, ya tsaya yana kallon duk su biyun, babu wanda ya gansa kamar yanda basu ji alamar zuwansa wurin ba. yasa hannu ya janyo ƙofar a hankali yanda ba za tayi ƙara ba sannan ya wuce, duk dan kar suga giftawarsa. sanda Zaytuna ta kammala wayar ta dubi Fillo tace,"me kike yi yanzu?". Fillo tace,"babu komai, mun gama aiki, ina karatu ne dama kamin na tafi". Zaytuna tace,"to kinga dama kayan wadrobe ɗin nan zaki gyara min, Hammah na min yankan farce ya yanke ni, na kasa taɓa komai". Fillo tace,"sannu Addah". tace,"yauwa, na gode...idan kika gama ki ɗauki wancan ƙaraman trolly ɗin ki tafi da ita". Fillo ta kalli trolly ɗin da take nuna mata, small size ce kamar waccan da ta bata, tace,"tom Adda, na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙarawa Baffa da Maama lafiya". Zaytuna tace,"amin...na dai faɗa miki tun ranar nan, duk wasu tsaffin kaya da kika san kina da su ki bayar". Fillo tace,"na bayar Adda, wanda muke iri ɗaya da Maijidda kawai na bari". Zaytuna tai shiru for few seconds kamin tace,"tom shikenan, goben kuzo ke da Maijiddan, ina son ganinta". ta amsa,"insha'Allah Addah". Zaytuna ta shiga toilet, ita kuma Fillo ta fara gyaran da ta sakata. lokacin da Zaytuna ta kammala shiryawa zata fita wayarta tayi ringing, ganin sunan Happiness a jiki tayi saurin picking tana faɗin,"Hammah nah". daga inda yake ya amsa da,"na'am Zaytun". sai kuma tai shiru tana jin cewarsa. ta waigo ta kalli inda Fillo take kafin ta amsa masa da cewa,"to Hammah". ta ƙara yin shiru na few seconds sannan ta ƙara cewa,"to Hammah, nima zan fita ne yanzu sai na dawo". da haka wayar tasu ta katse. tana sa wayar a jaka tace da Fillo,"idan kin gama kar ki tafi kinji, ki kunna system sai ki ƙarasa kallon da kike yi ran nan". wani daɗi ya mamaye Fillo, tana masifar son film ɗin, tun wancan ranar da ta kawowa Zaytuna assignmnt ta tarar bata nan sai Turaki ne a ɗakin, ta juya da sauri zata koma taji ya kirata yace ta dawo, ta shigo ɗakin ta zauna tayi tsilli-tsilli kamar ɓeran da aka girgiza acikin ruwan buta. tun zaman da tai a wurin gaba ɗaya sai ya manta da ita, kallonsa kawai yake acikin system. time to time sai yayi dariya ko kuma yay tsaki, Fillo dai na durƙushe a wurin kamar me neman gafara, kuma tun tana jin tsoro har tsoron ya barta, sai dai taita kallonsa ta wutsiyar ido, tana ƙara jin sabon haushinsa, idan taji yay dariya sai ta tambayi kanta dama yana dariya?. tafi ƙarfin minti goma sha biyar duƙe a wajen, tun tana a takure har ta saki jiki itama ta shiga kallon da yake yi a system ɗin, sai da aka kirasa a waya sannan ya tashi ya fita, ya fita ya barta da ci gaba da kallon, daɗin kallo ya mantar da ita yammar da tai, ta miƙe ƙafafu har sai da cajin laptop ɗin ya ƙare, lokacin ana sallar magriba. kuma sanda ta miƙe zata fita daga ɗakin sai ga shi ya dawo, ya kalleta ya kalla room ɗin, ta dabarbarce tana sarƙe yatsunta, ƙirjinta yana ta bugawa. daga sama taji muryarsa yana tambayarta,"ina Zaytun?". kanta a ƙasa tace,"bata dawo ba". sai yay mata kallon tsab yace,"ke kuma me kike yi anan?". ta ɗago kai tai masa duban mamaki tana saurin ɗauke ido daga cikin nasa da ya kafeta da su, bata bar jan yatsunta ba tace,"kaine ai ka tsayar da ni, kace nazo kuma aka kiraka ka tafi". yay shiru bai ce komai ba, ya juya zai tafi muryata na ɗan rawa cike da tsoro tace,"na tafi?". yace,"a'a kiyi ta zama". daga haka ya wuce ya barta a wurin. ta bar ɗakin da kewar film ɗin da bata ƙarasa gani ba, kuma da ta koma ranar raba dare suka yi tana bawa Maijidda labarin film ɗin, bata ma san ya akai Zaytuna tasan ta kalli film ɗin ba. kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta tace da Zaytuna,"Adda ban iya kunna laptop ɗin ba". Zaytuna tace,"kina buɗewa zata kama, Turaki is the password". tace,"tom". sai ta ƙara ce mata,"zaki iya ɗin ko na kunna miki?". tace,"zan iya Adda, Adda Nihal ta taɓa gwada min". Zaytuna tayi murmushi tace,"ranar da kika sa ta dinƙa mana mitar ƙauyancin da kika mata?". kunya tasa Fillo rufe fuska. bayan fitar Zaytuna babu jimawa ta kammala gyaran wadrobe ɗin, ta ɗauki ƙaramar trolly ɗin ta buɗe taga sabbin kaya ne kamar wancan time ɗin da ta bata. abaya guda huɗu sai riga da skirt na material guda biyu da na atamfa guda ɗaya. duka kayan kamar sai da akayi measurement ɗinta, dan babu alamar ma kayan ragesu akayi. cike da farin ciki ta mayar ta zuge zip ɗin, wannan ma rabawa zasu yi ita da Maijidda kamar yanda suka raba wancan. maimakon taja trolly ɗin sai ta ɗauka ta ɗora akanta, ta fito ta rufe ɗakin farin ciki duk yaƙi barinta. zata sauka a stairs sai taji kamar mutum na sauke wahaltaccen numfashi a cikin ɗakin da yake gaba dana Zaytuna. sai taji ta kasa tafiya, ta tsinci kanta da komawa da baya har ta iso ƙofar ɗakin, ta tsaya tana ƙara tabbatar da abunda kunnuwanta ke jiyowa. bata manta da wani lokaci ba da suka zo gyara ita da Ɗausiyya, Nihal ta ke ce musu su gyara kowanne room dake upstairs banda wannan da yake da coffee door, shi ba'a buɗe shi totally. for sure daga room ɗin take jiyo sautin, to anya kuwa daidai ta ke ji acikin kunnuwanta?, ai ranar har suka gama zaryarsu anan basu ji wani abu makamancin haka ba, ta tsaya tana Contemplating ta buɗe ko ta tafi, abunda kunnenta ke jiyowa dai ba na wasa ba ne, ba irin abunda mutum zaiji bane ya ƙyale ya tafi. sai kawai zuciyarta ta tsaya akan ta buɗe ɗin, ta sauke trolly daga kanta. tasa hannu ta murɗa handle na ƙofar room ɗin, door ɗin ya buɗe yana bada wani sautin ƙara. tsabar mamaki da tsorata Fillo sai taji kamar ƙafafunta ba zasu ƙara ɗagawa ba, tabi wurin da Turaki yake a yashe a ƙasan tiles dafe da ƙirjinsa, numfashinsa na fita da ƙyar. ruwan hawaye na sauka ta gefen idonsa, kawai sai taji kanta yayi wani irin nauyi, hawayen nasa ya ɗimautata, kamar wannan ace yana hawaye?, me ke damunsa?. bata san lokacin da ƙafafunta suka kaita gabansa ba gwiwoyinta suka durƙushe a saitin da kansa yake, ta kallesa taga kamar ma a sume yake, gabanta ya faɗi saboda yacca idonsa ya tsaya a wuri ɗaya cak baya ko motsi. ta kai hannu ƙasan hancinsa taji yana numfashi, sannan ta sauke wata nauyyar ajiyar zuciya. tausayinsa yay bala'in kamata, taya zata iya barinsa taje ta sanar da halin da yake ciki?, idan ta tafi me zai iya faruwa before ta dawo?, me zata yi don taimaka masa a wannan lokacin?, a yanzu kamin wani yazo?, sai taji cikin kanta kamar babu komai, dukkan wata dabara tata ta yanke mata, bata san me zata yi ba. acikin wani yanayin dake da wuyar fassaruwa tasa tafin hannunta me taushi ta shafa fuskarsa, sannan ta duƙo da kanta saitin kunnensa muryarta da rauni tace masa,"baka da lafiya? sannu, ka daina hawayen, bari naje na kirawo Maama". ta faɗi hakan tana ƙoƙarin miƙewa, ta yunƙura zata miƙe sai taji ya ruƙo hannunta ya dawo da ita. ƙwayar idonta ta faɗa cikin nasa a sanda hawayen ciki suka sami nasarar gangarowa kan kumatunta. a sanyaye tace,"zanje na kira maka Maama ne". sai taga ya girgiza kansa a hankali cikin ƙarfin hali. ta sake cewa,"to kana da magani a kusa na ɗauko maka?, aina zan ɗauko?". nan ma kansa ya girgiza mata a hankali. cikin dauriyar abinda yake ji acikin zuciyarsa. sai ta samu kanta da ce masa,"to me zanyi maka? me kake so?". sai taji ya ƙara damƙe hannunta sosai, ya sauke kallonsa daga kanta ya tsayar ajikin bangon dake facing nasu. ta tsaya kawai tana kallon gefen fuskarsa, tana jin yanda ruwan hawayensa ke ɗiga a saman skirt ɗin jikinta, tana jin yana ɗauke kansa daga ƙasa yana ɗorawa a saman cinyarta, tana ji yana ƙara damƙe hannunta, tana jin yanda wani abu ke fita daga tafin hannunsa yana shiga cikin nata, tana jin wannan zafin da ta tabbatar yana ji a zuciyarsa yana taɓa tata zuciyar. ta rumtse ido for few seconds sannan ta buɗe, ta buɗe tana bin inda yake kallo har sanda ta sauke kallonta gaba ɗaya akan ƙaton enlargement ɗin dake manne a bango. tayi mugun zabura da hoton da ta gani, ta tsayar da ƙwayar idanuwanta cak akan hoton tana ƙarewa dattijuwar matar dake jikin hoton kallo, ba sai an faɗa ba matar balarabiya ce, kallon matar take tana hango tsananin kamanni na Turaki dana Zaytuna a tare da ita, tun daga murmushinta har dimple ɗinta daya lotsa ciki sosai babu abinda ya banbanta daga na Turaki dana Zaytuna. _but who is she?_, tambayar da taiwa kanta kenan, kuma kafin zuciyarta ta raya mata wata amsa sai ganin Turaki tai ya miƙe tsaye yana toshe duka kunnuwansa biyu yana doka goshinsa a jikin glass da ƙarfi. tayi azamar miƙewa tana ruƙo shi tana faɗin,"ka daina, zaka ji ma kanka ciwo". ta faɗa cikin tashin hankalin da ta rasa na menene, kuma rufe bakinta kenan jinin dake fita a goshinsa ya zuba akan ƙirjinta. ta kalla jinin dake ƙirjinta, ta kalla jinin dake fitowa a goshinsa, idonta a waje tace,"ka bari". ta faɗa da wani mugun ƙarfi tana sa hannu da iya ɗan ƙarfin da take da shi ta fizgo shi daga bakin glass ɗin da yake tsaye, sai gasa a gabanta, taja hannunsa ta zauna da shi a ƙasa tana kunce ɗankwalinta ta ɗaure masa goshin. "menene? ka daina kukan to dan Allah, ka faɗa min me kake so?, me zanyi maka?, ka jira anan karka ƙara tashi zanje na kira Maama". ta faɗa kukan dake bakinta na fitowa. kuma sanda ta yunƙura zata miƙe lokacin ya janyota jikinsa ya rungume tsam yana kama hannunta ya toshe kunnensa da su. muryarsa na fitowa cikin muryar namiji mai rauni da faɗin,"don Allahhhhh, ki taimaka min". *Comment naku shi ne ƙwarin gwiwata.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *23* ya ƙara maimaitawa,"help me pleaseeee". ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta. Fillo ta haɗiye yawun bakinta da ƙyar, ita bata taɓa jinta a jikin ɗa namiji ba ko da Yayanta Hamid. amma yau itace gaɓa ɗaya cikin jikin wani ƙaton ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da tasa ta jin kasala, kuma tana ta ƙoƙarin ta fita a jikin nasa ta kasa. sai tayi shiru kawai tana sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa, beat ɗin na fita da ƙarfin gaske, sai taji tana jin tsoro. muryarta a hankali tace,"taimakon me zanyi maka?". ta faɗa tana so ta raba jikin nata da nasa, lokaci ɗaya sai tsoronta ya ƙaru jin yacca jikinsa ya saki gaba ɗaya. ta fita daga jikin nasa a sanda ya tafi luu ya faɗi ƙasa, bata san lokacin da ta kurma uban ihu tana tallafo kansa da sauri. ta shiga girgiza shi tana cewa,"ka faɗa min taimakon me zan maka?, me kake so na maka?, Turaki ka tashi dan Allah". kuka take sosai tana cewa ya tashi, da dai ta tabbatar cewa ya suma sai ta miƙe a ruɗe ta fice daga ɗakin, har ta kai step na ƙarshe zata sauka daga stairs sai kuma ta fara tunanin idan ta tafi ta barsa shi ɗaya cikin wannan halin me zai iya faruwa da shi?. dan haka da sauri ta ƙara komawa har tana kusa zamewa, Allah ya taƙaita tsautsayi bata faɗo daga benen ba. yana nan a sumen har yanzu, tai kansa cikin kiɗima tana ƙara jijjigasa tana cewa,"ka tashi don Allah, ka tashi ka faɗa min duk abinda kake so zanyi, zan taimaka da ko menene ko da ace zan rasa raina ta sanadin hakan". duk wata dabara nata da tunaninta ya gushe a brain ɗinta, tayi dirshen a wajen tana ta kuka abinta, tsoronta Allah tsoronta ace mutuwa yayi, wa ya kashe shi?. sai kawai ta ƙara fashewa da kuka tana tallafo kansa zuwa kan cinyarta, tasa hannu ta share hawayenta tana ta maganganu ita ɗaya. "kar ka yi min haka dan Allah, kar ka mutu a sanda yake daga ni sai kai a wajen, za'a ce ni na kashe ka, wallahi haka zasu ce. kuma ni ban san komai ba, ban san me ya sameka ba, dan Allah dan Annabi ka farka karka mutu yanzu, ka farka ka faɗa min duk abinda kake so, ka faɗan duk kalan taimakon da zanyi maka, ni kuma nayi alƙawarin zan maka shi". ta ƙarasa maganar tana kifa goshinta akan nasa, sam sam bata san me ya kamata tayi a yanzu ba, abu ɗaya ta sani, shine ba zata taɓa fita ta barsa shi ɗaya a cikin wannan halin ba. can kawai sai taji zuciyarta na faɗa mata cewar ta kira waya, ta kira Maama ta sanar mata komai, to amma da wacce wayar?. ɗago da kanta tayi ta fara laluben aljihunsa dan ɗauko wayarsa, ta gama lalubenta bata ji komai ba sai wallet ɗinsa. tunaninta wayar ko tana cikin wallet ɗin ne, hakan yasa ta buɗe wallet ɗin da niyyar ɗaukowa, amma da mamakinta tana buɗewa taci karo da hoton mutum biyu, na Zaytuna da kuma Dattijuwar matar da ta gani a jikin wancan hoton. kanta ya ƙara ƙullewa ta rasa wanne irin tunani za tai akan lamarin dake yawo cikin ranta, yanzu ba lokacin buƙatar lallai sai ta san komai ba ne, yanzu lokaci ne na kuɓutar da Turaki da take ganin kamar rayuwarsa tana jingine da ita ne, warwarewar abunda bata sani ba shi yafi komai sauƙi a wajenta, idan ya farka zata zauna ta zana komai dake ƙulle cikin kanta a tsakiyar tafin hannunta, tukunna ta karance shi da zurfin tunaninta, idan lissafin nata yayi dai-dai, to ta tabbata daga nan zata warware komai a cikin sauƙi. cikin azama ta miƙe ta nufi hanyar fita sai Allah ya nufeta da ganin wayarsa akan locker, ta isa wajen ta ɗau wayar hannunta sai karkarwa yake. ba security a wayar, dan haka tana buɗewa kai tsaye lambar Maama ta laluba, bata ma san ta yanda akai ta iya wayar ba tunda ba taɓa riƙe waya tayi ba a rayuwarta, ko wayar Yami ma tsakaninta da ita in Amir ya kira Maijidda ta kawo mata tasa mata a kunne, amma ko ɗaga waya bata taɓa yi da kanta ba. scrolling kawai take a ɓangaren miscalls amma ta rasa lambar da ta dace ta kira, bata san wani Bello Ƙaraye ba, haka bata san lambobin biyun da babu suna a jiki na waye ba, fita tai daga ɓangaren call ta shiga contact, take taci karo da sunan My world, cikin sauri ta danna kiran ya tafi. daga can ɓangaren Hajiya Madina da ke zaune akan kujerar dake cikin ɗakinta. ƙafafunta a harɗe tana jin yanda zuciyarta ke matsewa, tana jin yacca zuciyarta ke faɗa mata kamar ba zata iya komai ba, tana jin yanda idanuwanta ke faɗa mata kamar ba ita ta haifi ƴaƴan dake zaune a gabanta ba, tana jin yacca ƙwaƙwalwarta ke faɗa mata rayuwar Turaki ita tafi cancanta da ta ingata sama da ta sauran, cikin kanta na lissafa mata kamar yanda take jin bata da kowa a duniyarta sai Turaki, haka shima Turaki ke jin ba shi da kowa a duniyarsa sai ita, ita ɗaya jallin jal. ƙwayar idonta ta wulƙita ta kalli Zaytuna, sannan ta kalli Nihal, tukunna ta sauka akan Samha, duka Yaran suna daga kan gadonta ne suna hira cike da soyayyar junansu. Samha kawai take iya gani a lokacin, kallon yarinyar take da irin kallon da ita kaɗai tasan ma'anarsa, ta kuma san manufarsa, ta kuma san lissafin da ƙwayar idonta ke yi akan yarinyar, ta kuma san ciwon da kallon nata ke hifarwa da ƙwayar idonta. da ace zata iya, tabbas da tace komai ɗin da take ji take gani ƙarya ne, to amma bata isa ba, bata isa ta kira abubuwan da tasan suna tafiya ba a matsayin ƙarya, ita gaskiya take bi, kuma gaskiyar ta sani, kuma gaskiyar zata bi. sanda ta rufe idonta tana sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ne wayarta dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗaga tana kallon screen ɗin da sunan THE BEST ke yawo ajiki. lokaci ɗaya taji duk wani ɗaci da ɓacin ranta ya gushe, tana jin wani ɓari na damuwar da take ciki ya yaye, fuskarta ta bayyana jin daɗin ganin kiran nasa, sai ta ɗaga tana faɗin. "Me Babban suna kana ina?, ina ta kiran wayanka baka ɗauka ba, na kira Bello yace bakwa tare, ina ka tafi?, Khalil yace baka je office ba yau, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, duk inda kake ka dawo gida yanzu kaji, ina nan na kasa samun nutsuwa tun kiran farko da nayi maka ban samu ba, yau na kiraka yafi sau goma kiran baka picking, tukunna dai kayi lunch?". maganar take muryarta na bayyana tsananin damuwar dake ƙunshe a cikin ranta, ba don komai sai dan rashin sanin halin da yake ciki tun safe da ya bar gida. haka take ita, indai ya fita a gida basa 1hour basu yi waya ba taji ya lafiyarsa, idan kuma yana gida to jiddan walahairan yana part ɗinta, suna tare ko a parlo ko kuma a bedroom ɗinta, sai dai idan ranar yana jin miskilancinsa har da ita to sai dai ita ta bisa part ɗinsu. ta kan tsokane shi da cewa,"Hamman'su kana juya ni kamar waina a tanda". Fillo da ke tsaye tana sauraren maganar Hajiya Madina, tausayin matar yay bala'in kamata, sai ta kasa yin ko da motsi, tai shiru ta kasa yin magana, tabi inda Turaki yake yashe kawai tana kallonsa, me yake faruwa da rayuwarsa ne?, me zata faɗawa Hajiya Madina yanzu?, ya zata yi idan taji a halin da ɗanta yake ciki?. sai ta tuno yacca Hajiya Madina ta shiga tsananin tashin hankali a wata rana da ya yanke da wuƙa yana yanka lemu, ta dinga kuka akan ɗan jinin da ya zuba daga jikinsa, ta tuna yanda Hajiya Madina ta koma bata iya nutsuwar minti ɗaya babu Turaki a kusa da ita a lokacin, ta tuna yacca duk bugawar sakan, duk wani motsi nasa sai tace,"menene me Babban suna?, me kake so?, me zan maka?, ciwon yana zafi?, sannu kaji, Allah ya baka lafiya". haka ta dinƙa ririta shi kamar jariri sabuwar haihuwa a lokacin. sai Fillo taji inaa ba zata taɓa iya kasassaɓar sanarwa da Hajiya Madina halin da Turaki yake ciki ba a yanzu, ba zata iya ba har ga Allah, bata son taga uwa ta shiga tashin hankali, balle kuma Uwa irin wannan da lokaci ɗaya take fita daga hayyacinta akan ɗan da ta ƙwallafa rai akansa duk kuwa da tana da wasu Ƴaƴan da Allah ya bata. Hajiya Madina ta rufe ido ta buɗe tana kallon agogo, ƙarfe biyar na yamma, yau watarana ce da ta kafa tarihi a tsakaninta da Turaki, rana ta farko da Turaki ya saɓa umarninta a iyaka tsayin rayuwarsa, to amma me yasa?. sai kawai ta rufe ido ta ƙara buɗewa tana sauke ganinta a daidai lokacin da agogo ya nuna biyar harda minti ɗaya, sai taji ranta ya ɓaci. kuma cikin nuna ɓacin ran tace,"baka taso a stubborn ba, kuma duk cikin ku shida kai nafi karewa daga duk abinda zai sa ka zama stubborn, amma me yasa sai daka girma?, kana so ka zama Stubborn kamar Khalil ko?. saboda nace duk sanda ka fita ya zama kuna tare da shi ko ina zaka je, ba wai ina nufin ka zama mara ji ba kamarsa, na sani da takurawa ace lallai duk inda zaka je sai da ƙaninka alhalin ka mallaki hankalin kanka, amma ka sani ni uwa ce da ba zan so wani abu ya cutar da ɗana ba, ya kamata ka tuna da akwai masu faraurar rayuwarka a kullum, dalilin da yasa nace duk sanda ka fita ya zam kana tare da Khalil ko Bello duk da nasan dabarata bata isa ta hana faruwar abunda Allah ya shirya ba. amma dai atleast kasancewarka tare da wani zai sa suke tsoron tunkararka. kuma sai da kayi min alƙawarin ba zaka saɓa umarnina ba akan hakan ba, Me Babban suna me yasa yau rana ta farko ka saɓa umarnina?, Khalil yace ko minti 2 baka yi a office ba ka fita, Bello yace kana ɗaukosa a airport kuka rabu. ina ka tafi tun bayan rabuwarku?, me yasa baka dawo gida kaci abincin rana ba?, me yasa kaƙi ɗaga wayata?, me yasa kake son haddasa ciwona ya tashi?, me yasa tun ɗazu ina maka magana kayi min shiru?, rashin maganar na menene?, lafiya?". tunani da lissafi dake a cikin kan Fillo ya tarwatse, gabanta yay dukan tara-tara, kallon Turaki take yi tana tuna irin tarin tasa soyayyar wa mahaifiyarsa, zuciyarta na faɗa mata taje ta same shi ta faɗa masa Maama ce, Maama na son yin magana da shi, zai farka idan yaji hakan, tabbas zai farka. ta isa gabansa tana jijjigasa a hankali daidai kunnensa tana faɗin,"ka tashi ga Maama". a zatonta ko jin hakan zai sa ya farka daga dogon suman da yayi, amma inaa kamar ma da gawa take magana. sai kawai wani kuka ya kubce mata. cikin kiɗima Hajiya Madina tace,"innalillaihi wa'inna ilaihi raji'un...". ko salatin bata ƙarasa ba Fillo tace,"Maama ki zo". ta faɗa tana kuka sosai. daga ɓangaren Hajiya Madina ta zabura ta miƙe daga kan kujera, cikin gigita da tsananin tashin hankali na farat ɗaya, me kunnenta yake ji ne?, kamar kukan wani take ji kuma kamar ana so ace mata tazo ga Turaki babu lafiya. "waye ke magana?, ina Muhammad ɗin?, ke wacece?". kukan Fillo ya ƙaru tace,"Maama ni ce, Hammah ɗin ya faɗi ya suma Maama kizo da sauri". wayar dake hannun Hajiya Madina ta nemi ta faɗi a ƙasa, Samha da idonta ya kai wurin tai saurin taro wayar sanda ta sauka daga saman gadon. ta taro wayar a lokacin da itama Hajiya Madina ke neman faɗuwa, Nihal tai saurin riƙota. Samha tace,"Lafiya Maama, menene?". Hajiya Madina ta kalleta ido a waje, a hankali ta kalli Nihal, sannan ta kai idonta ga Zaytuna wacce tayi tsaye ƙeƙam. sai kuma ta dawo da idonta ta sauke akan wayar tana kallon call ɗin dake tafiya, Hammah aka ce mata alhalin ga ƙannensa anan tare da ita. cikin neman fitar hayyaci tace,"to wace me magana a wayar?, wai Hammanku ya suma, to aina?, garin ya?". ta wurga tambayoyin ga Samha. duk su ukun suka maimaita,"Hammah ya suma?". Hajiya Madina ta ɗaga musu kai kawai hawaye na sintiri a saman fuskarta. "hello, dan Allah wake magana, ina me wayar yake dan Allah?". Nihal ta faɗa acikin wayar bayan ta amshi wayar daga hannun Samha. babu amsa sai kuka dake tashi kawai, Zaytuna ta silale a wajen, Nihal tayi kanta da sauri. Samha ta ɗau wayar ta kai kunne, dan tuni Hajiya Madina tayi mutuwar zaune, ta koma kamar me paralize idonta a wuri ɗaya kawai yake, jinta take kamar rayuwarta ta ƙare, kamar shikenan ta gama aiki. daga ɓangaren Fillo tace,"Hammah ne ya suma". Samha ta waiga taga sauran sisters ɗinta suna nan, ɗaya ta suma ɗaya na ƙoƙarin ganin ta sumen ta farfaɗo. to wace ke faɗin Hammah ya suma?. sai ta dakewa faɗuwar gaban da take ji tace,"to waye yake magana, kuma wanne Hammah ɗin?". Fillo na ƙara jijjiga Turaki tace,"ni ce Fillo, Hammah Turaki ne ya suma Maama, tun ɗazu yaƙi yay motsi kamar ya mutu". a matuƙar razane Samha ta miƙe tsaye tana faɗin,"what! mutuwa?, dan uwarki ke kina ina?, ta ya kika san abinda ya faru da Hamman'mu?". jin furucin Samha yasa jikin Fillo yin rawa a lokacin zuciyarta na faɗa mata shikenan tata kuma ta ƙare, ita dama ta sani ita za'a ɗorawa alhakin faruwar komai. "Fillo aina?, aina ya suma?". Hajiya Madina da ta amsa wayar take tambaya kuka na ƙwace mata. "Maama ɓangaren su Adda Zay...". bata ƙarasa ba taji alamun faɗuwar waya a ƙasa. kuma zata iya cewa rabin second ne ya kawosu, dan ganin su kawai tayi tsaye akanta. Hajiya Madina ta fizgo Fillo ta miƙe tsaye, ta zabga mata mari a fuska, marin da yasa jinta da ganinta suka ɗauke na wucin gadi. kamin ta dawo dai-dai ta ƙara ɗauketa da wasu marikan har uku. "uban wa ya buɗe room ɗin nan?". babu abinda Fillo ke ji a lokacin balle ta iya bada amsa. "ba magana nake miki ba, ban yi muku iyaka da wannan room ɗin ba?, bance duk sanda zaku yi aiki babu ruwanku da taɓa wannan ɗakin ba?, wa ya baki key ɗinsa?, me yasa baki hanasa shigowa ba?, kin buɗe baki kin yi min magana ko sai nasa ƴan sanda sun kamaki kin ƙare rayuwarki a bayan kanta?". Fillo na kuka tace,"wallahi Maama bani na buɗe ba, nazo wucewa ne...". bata barta ta ƙarasa maganar ba tasa bayan hannunta ta kifar da ita a ƙasa, Fillo ta zube a ƙasan tiles kanta na dukan bango, lokaci ɗaya taga giftawar wasu taurari acikin idanuwanta. abunda kawai zata ce ta ƙara ji shine Hajiya Madina ta mata gargaɗin cewa,"duk abunda ya sami ɗana, duk abunda ya sami lafiyar ɗana sai naga bayanki Fillo, tabbas sai kin ƙwammace ina ma baki zo duniyar nan ba". daga nan bata ƙara jin komai ba kamar yanda bata ƙara ganin komai ba na tsawon wucewar minti goma sha biyar. kuma sanda ta dawo hayyacinta daga buguwar kan da tayi, sai taga babu kowa a ɗakin sai ita ɗaya. tsawon minti biyar tana kuka, a hankali ta dinƙa kewaye ɗakin da kallo, babu komai acikinsa face shirgin takardu dake cikin locker, sai kuma gadon jarirai irin wanda ta taɓa gani a ɗakin Fulani, sanda Kaka ta zauna yiwa Gimbiya Zahra wankan jego. wanne abu ne acikin ɗakin da ya haddasa shigar Turaki situation ɗin da ta zo ta same shi aciki?, ina abunda yasa ba'a so a buɗe ɗakin?. ta kalli komai kuma bata ga komai ɗin da zai zama dalili ba. taimakonsa tayi, kuma taimakon take da niyyar yi masa, amma ga da abinda aka saka mata da shi, ya za'ai ta manta?, waye zai taushi zuciyarta akan abinda ta ƙudurce na ramuwa?, Amir ne kawai, kuma yanzu babu Amir a cikin rayuwarta, tsawon watanni huɗu sai taji tana kewar Amir a yau. sai ta runtse ido tana jin zafi a zuciyarta, ta miƙe tsaye da ƙyar tana dafa bango saboda hajijiyar da take ji, ko'ina na ɗakin take bi da kallo, so take taga illarsa, ba zata taɓa barin ɗakin nan ba sai taga illarsa da kuma dalili, wannan dalilin da ya haifar da komai. ta miƙe da ƙyar ta tafi tana jan ƙafarta dake yi mata zugi har ta ƙarasa gaban enlargement. kallon matar take yi da kyau cike da nazari da son gano wani abu amma ta kasa, abu ɗaya ta fahimta matar nan na da alaƙa me ƙarfi da Turaki, saboda tsananin kama, kamannin da suka zama kamar an tsaga kara, sai dai irin alaƙar da take tunani zuciyarta na faɗa mata cewa ba ita bace, wannan matar bata yi kama da wacce ta ajiye ɗa kamar Turaki ba, shekarunta kaɗanne, kuma ko da auren ƙauye aka mata baici ace ta haifi ɗa kamarsa ba balle har ta haife shi, ta haifi Zaytuna. ba ma wannan ba, idan ma tayi tunanin ita mahaifiyarsu ce to Hajiya Madina fa?. ta dafe kanta da take jin kamar zai fashe tana saurin dafa gadon jariran, bata buɗe idonta ba har sai da ta daina jin juwar, idonta ya sauka acikin gadon jariran, kan award frame dake kan bargon jariri, tasa hannu ta ɗauko tana kallon award frame ɗin, tayi concentrating akan hoton jiki da sunan jiki. *her Excellency RAMLA MUHAMMAD TURAKI*, sunan da yake rubuce a jiki kenan. wai wace wannan matar?, mene alaƙarta kuma da sunan Turaki?, *MATARSA!*, haka zuciyarta ta faɗa mata, kuma tabbas hakan yake, amma ina take?, mutuwa tayi?, rabuwa suka yi?, take anan zuciyarta ta warware mata dalilin da yasa ba'a son buɗe ɗakin, da kuma dalilin da yasa Turaki shiga critical condition. saboda wannan ɗakin na da alaƙa da ita shiyasa ba'a so a buɗesa, sannan ganin hotonta na fama ciwon da ta jiwa Turaki a zuciyarsa, wannan ciwon da tabonsa ya kasa goguwa daga garesa. wanne irin ciwo ne?, me tayi masa wanda ya kasa mantawa?. ta ƙara ƙulle idonta for 1minutes sannan ta buɗe tana ƙarewa gadon jariran kallon, ta tabbata wannan room ɗin shine silar komai, kamar yanda gadon jariran nan ke da alaƙar komai, kenan idan tunaninta ya bata dai-dai *ƊA* ne silar komai, jaririnsu!, to ina jaririn?, kuma itama uwar tana ina?, ta mutu ne?, ita ɗan da suka mutu?, kenan wannan shine ciwon dake manne a zuciyar Turaki?. sai kawai Fillo ta sauke numfashi tana hurar da iska a bakinta, ta koma ta isa gaban englargement din ta cirosa, sannan ta dawo ta ɗauko award frame ɗin ta fice da su daga ɗakin. *6hours pass, Miyyetti Hospital, Room 05.* cikin vip room ɗin, Turaki ne jingine a jikin pillow ɗin da aka saka masa a bayansa, goshinsa ɗaure da bandage, an naɗe wurin da ya ji ciwo da shi sanda yake dukan kansa ajikin glass. gefensa kuma wata farar tsohuwa ce kamar balarabiya a kan kujera, da siririn farin medical glass a idonta, tayi jugum tana ta kallon jikan nata. lokacin da aka kawo Turaki da Zaytuna asibiti, lokacin ta kira wayar Baffa take sanar masa tana ta kiran wayoyin yaran bata samu, har ta babarsu Hajiya Madina ma ta kira bata samu ba, shine Baffan ke faɗa mata halin da suke ciki na cewar suna asibiti, Zaytuna da Muhammad duk sun suma, kuma for morethan 15minutes ba wanda ya farfaɗo acikinsu. a lokacin Granny ta kira ɗanta tace a yanzu ba da ɓata lokaci ba tana son zuwa nigeria, kuma a awa biyar da minti hamsin da biyar sai gata ta a asibitin cikin tashin hankali tana ta kuka, sai dai ko lokacin da tazo ɗin duk sun farka, Zaytuna ma har ta miƙe, shine dai ke kwance saboda ciwon dake jikinsa. Granny ta numfasa tace,"Ramla dai ta cuci kanta, dan ba zance ta cucemu ba...so do you know what i want from you Muhammad?". Turaki ya haɗiye abu ya kalleta yana jiran cewarta. "Muhammad ka manta da Ramla, ka manta da ita da abinda ya shafeta, ka samawa kanka lafiya, ka samawa kanka kwanciyar hankalin daka rasa tun ranar da tasa ƙafa ta tafi ta barku...". Turaki ya katseta da faɗin,"Granny do you know what you are saying?". ta jijjiga masa kai,"i know Muhammad, i mean you should forget Ramla in your life, just like she forget you". sai ya kwantar da kansa yace,"Granny hannunka baya ruɓewa kace zaka yanke ka jefar". tace,"idan ta kama a yanke sai a datse shi a huta, komai ai kamawa take". kansa ƙasa yace,"but karki manta duk lalacewar uwa uwa ce, how can i forget her?, na fa manta da ita da abinda ya shafeta kike cewa?, how?, ki daina faɗar abinda ba zai yiwu ba Granny". yanayin yanda yayi maganar sai yay mugun bata tausayi. sai kuma ya rumtse idonsa zuciyarsa na tafarfasa,"even though I was six years old at the time. Granny har yanzu ina ganin hoton komai tar acikin kaina, ina kallon lokacin da tasa ƙafa tayi tafiyarta ta barmu ba tare da ta ko waiwayi kukan da nake ba, bata dubi kukan Zaytuna dake naɗe aciki showel ba, tayi tafiyarta ta barmu, as if ba daga jikinta muka fito ba, as if ba ita ta tsuguna ta haifemu ba, kamar ba da auren sunnah ta samar da mu ba, inda ace wutar ta cinyemu fa?, da ace mun mutu fa?, da Allah bai kawo Maama a lokacin ba fa?". lokaci ɗaya sai hawaye ya shiga sakko masa akan kuncinsa, cikin kunnensa yana jin sautin kukan Zaytuna da ta dinga tsalawa a lokacin, yana jiyo nasa sautin kukan dake fita da harufan sunan Mum. yana jin komai kamar yanzu yake faruwa, tana fa kallon yanda wuta ke ci a ɗakin, amma ta tankaɗasa ya koma ciki ta rufe ƙofar ta barsa daga shi sai jaririyar dake cikin gado kusa da inda wutar ke daɗa kamawa, tayi tafiyarta ko tausayinsu bata ji ba, me suka mata?, har yanzu tambayar da yake ta so yayi mata kenan, ya ganta ya tsuguna agabanta ya tambayeta zunubin da suka aikata mata, sannan sai ya roƙar musu yafiyarta, idan ta yafe musu sai ya bata labarin abinda yake ɓoyewa kowa, kowa banda Bello da Zaytuna. to aina zai ganta?, yaushe zata dawo?. *Please Comment and Share and Vote.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Please avoid any mistake._ *24* "nima da nake mahaifiyarta na manta da ita, na manta na taɓa haihuwar ƴa me kamarta ko sunanta, na jima da cireta a sahun ƴaƴana. saboda haka kaima ka manta cewar ita mahaifiyarka ce tunda har ta iya manta da cewar tana da ƴaƴa, ka riƙe wadda ubangiji ya dubeku ya tausaya muku ya baku ita ta maye gurbinta...Allah ne kaɗai yasan hikimarsa akan hakan, wataƙila ba zaku sami tarbiyya da soyayya daga wurin Ramla ba shiyasa ya ƙaddara faruwar wannan lamarin". jin maganan Granny ɗin yasa Turaki buɗe idanuwansa, ya buɗe su a daidai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa ɗakin. kallo ɗaya yayi mata yaji tsananin tausayinta ya kamasa, ya ƙara jin ƙaunar matar a ransa, haka ne, basu sami soyayyar mahaifiyarsu ba, kuma basu samu tarbiyya daga wurinta ba, amma Allah ya basu wacce tayi musu dukkan waɗannan gatan, wanda iyakacin abinda wadda ta haifesu zata musu kenan. hijab ɗin dake jikinta fuskarsa ma a karkace ta saka, ya bita da kallo har sanda ya sauke ƙwayar idonsa kan bayan hannunta. tabon ƙonuwar da tayi tsawon shekaru 25 har yanzu yanan bai ɓace gaba ɗaya ba, sai kawai yasa hannu ya goge hawayen da ya sakko masa a lokacin da bai sani ba, idan bai so Maama ba wa zai so?, idan bai ƙauna ce ta ba wa zai nunawa ƙauna?, idan bai kula da ita wa zai bawa kulawarsa?, wataran har yana jin yafi sonta fiye da wadda ta kawosa duniya, har yana jin tausayinta fiye da yanda yake tausayin Mum ɗinsa. Hajiya Madina ta ƙaraso bakin gadon, Granny na amsa sallamarta, jikinta duk a sanyaye taja kujera ta zauna, ta dubi Turaki da muryanta da yay ƙasa tace,"sannu me Babban suna". ya amsa da,"yauwa Maama, thank you so much for your care". ganin yanda ta ƙura masa ido sai ya sauke idonsa ƙasa, yana jin nauyinta na shigarsa, ya sani yayi mata laifi. laifi har guda biyu a rana ɗaya, ya saɓa umarninta na cewa duk inda zai ke tafiya yanzu suke tafiya tare da Khalil, sannan yazo yasa kansa a situation ɗin da ya shiga, saboda wannan condition ɗin da yake shiga ne a duk sanda ya shiga ɗakin mahaifiyarsa shi yasa ba'a so ya shige shi, yasa ma aka rufe ɗakin gaba ɗaya Baffa ya ɓoye key ɗin, ya gargaɗe shi da ko da wasa kar ya ƙara tunkarar ɗakin, tunda duk sanda ya shiga yana tunawa da komai da ya faru a ranar da Mum ta tafi ta barsu, sai ya dinƙa jin komai tamkar a lokacin yake faruwa, sai ya dinƙa ganin yacca wuta ta ke tashi da yanda ya dinga kuka Zaytuna ma tana yi, sai yake jin kukan a cikin kansa. hakan sai yasa yake jin wani irin raɗaɗi, ya dinƙa jin wani irin abu a tare da shi da ba zai iya kwatantasa ba a yayin da yaga hotonta. idan yana ganin hotonta sai yaji kamar ya cirota daga cikin hoton ta zama a zahirance, yay mata kallo na zahiri sai ya rungumeta ta yanda ɗumin jikinta zai ratsa shi, taci gaba da rayuwa tare da su ko da ace ba zata so su ba, shi dai kawai ya dinga ganinta yana jin daɗi, yake yi mata duk wata kalar biyayya, ya kuma nuna mata zallar soyayyarsa, irin wannan soyayyar da ta ke only between child and his mother. alƙawarinsa ne daga zarar da ya sami job ba zai dinga barinta tana zuwa office ba, ta gama yiwa gwamnati aiki, shi zai dinƙa biyanta da kuɗin da yafi wanda take samu ba tare da tayi aikin ko da rubutu a takarda ba, alƙawarinsa ne zai nema mata wacce zata dinga kasancewa tare da ita idan baya kusa da ita, zai nema mata yarinya kamilalliya kuma kimtsatstsiya, irin yarinyar da ta san darajar uwa, irin wacce tasan kalar soyayya da kulawar da ya dace a nunawa uwa, irin wacca yasan ko da a bayan idonsa ba shi da haufin ba zata bari ko da ƙuda ya taɓa mahaifiyarsa ba. ya ƙara ɗago kai yana kallon Hajiya Madina, wacca a yanzu tayi ƙasa da kanta tana goge hawaye. sai ya rumtse ido sosai yana jin wani ɗaci a zuciyarsa. a hankali yace,"dan Allah Maama ki daina kuka a gabana, bana so, yana ɗaga min hankali...kiyi haƙuri ji nayi kamar idan na shiga room ɗin Mum zan ganta, naji ne kamar tana kirana a lokacin, dalilin da yasa na buɗe kenan...kuma dana shiga sai ban ganta ba, ban ganta ba ko da inuwarta sai hotonta". ta ɗago tana daɗa goge hawayenta da cewar,"me Babban suna bana so naga wani abu ya sameka, bana so ko kaɗan. amma wannan hawayen ba naka bane, na Ramla ne, ina ji inama na san inda take naje na dawo da ita, ta dawo muci gaba da rayuwa tare. ta zauna tare da ƴaƴanta ko sa sami kwanciyar hankali, babban damuwata shine rashin sanin halin da take ciki". Granny tace,"shekarun aka faɗa muku kwana 25 kacal, idan zaku yarda da ni ku yarda kawai, ko da ace zaku samu labarin Ramla, ina jin sai dai ku sami labarin mutuwarta". Maama tayi shiru tasa handky tana ƙara goge hawayenta tace,"in Allah ya yarda tana raye, me Babban suna yace yana ji a jikinsa tana raye kuma in a safe place". Granny tace,"ke komai aka faɗa sai dai ki faɗi view ɗin wani me Babban suna, to ai sai kuyi ta zaman jiran ganin dawowarta, haka zaku zauna har zuwa busa ƙaho, zai fi muku ku haƙura da ita kawai". Turaki yace,"insha'Allahu zata dawo". ya faɗa da sautin murya mai matuƙar ban tausayi. Hajiya Madina ta kallesa tace,"da ma da kanka ka buɗe ɗakin?". sai ya ɗaga mata kai alamar ehh. lokaci ɗaya zuciyarta taji rashin daɗi, taji tana dana sanin abinda ta yiwa Fillo, taji tausayin yarinyar ya kamata, taji ta ƙara son yariyar a ranta, taji ta ƙara ƙwaɗayin auren yarinyar wa Turaki, her only beloved son Muhammad Turaki. "Me Babban suna nayi zaton Fillo ce ta buɗe zata yi aiki a ɗakin, da ta kirani nazo naga condition da kake ciki sai na yanke mata hukunci me tsauri, tana ta faɗa min bata da laifi ashe gaskiyarta take faɗa min ni kuma naƙi sauraronta. Allah na gode maka da ban yanke hukuncin da zanzo ina da na sani ba, niyyata muna komawa gida zan sallamesu ita da Kakarta, a zatona duk itace silar halin da ka shiga, ashe dai ƙoƙarin taimakon naka take da gaske". Maganar takeyi yana sauroronta, idanuwansa kuma na gane masa Fillo a lokacin, yana tuno yanda ta dinga roƙonsa akan ya daina jiwa kansa ciwo, da kuma yanda ya ƙanƙameta yana neman taimako daga gareta, da sanin cewar in ya faɗa mata abunda yake buƙata zata taimaka masa kamar yanda ta saba, kamar yanda ta saba taimakonsa ba tare da ta san cewar ya sani ba, wannan tight hug ɗin da ya mata ji yayi kamar idan ya faɗa mata Mum ɗinsa yake so ta dawo masa da ita, to zata ce masa ya buɗe idonsa gata ta kawo masa ita, amma sai lamarin ya kasance ba haka ba. sai ya lumshe idonsa yana daɗa hasko Fuskar Fillo, ta ya zata dawo masa da Mum idan ya faɗa mata?, ta ina zata fara kamar yanda bai san ta yanda ta fara wancan taimakon akansa ba?, sai ya matse idonsa yana jin wani abu da bai san menene ba yana tsarga masa. tsawon lokaci Granny da Maama suna jimanta rashin Ramla tare da su, Turaki duk yana jinsu har lokacin idonsa na a rufe, amma tunaninsa na can wani wuri na daban. akayi sallama a room ɗin, Hajiya Madina ta miƙe da sauri daga kan kujerarta tana yiwa Fulani matar me martaba barka da zuwa. cikin takun ƙasaita da girman izza ta ƙarasa shigowa ta nemi kujerar da aka nuna mata ta zauna. hular alkyabbar dake kanta ta ɗage tana duban Turaki kafin tace,"Allah ya ƙara lafiya". tai maganar kamar tana jin nauyin bakinta, kuma kamar bata so ba. ya ɗan rissina kansa cike da girmamawa ya amsa mata,"amin ya Allah, na gode Mami". Hajiya Madina ma tana rissinawa ta ƙara ce mata,"sannu da zuwa". sai da ta ɗauki minti ɗaya kan tace,"yauwa. ashe Muhammad bai ji daɗi ba, to Allah ya inganta lafiya, ina ganawa da baƙi Mai Martaba yake cewa mu shirya mu taho hospital... accident ya ƙara yi?". Hajiya Madina tace,"aa ba accident ba ne, rauni ne ya samu acikin gida, amma yazo da sauƙi ma tunda glass ɗin da ya fashe ne ya soke shi a goshi, but Drs ɗin ma sunce babu wata matsala, zuwa safiya zamu tafi gida". sai bayan wucewar sakanni goma sha biyar da maganar Maama sannan Fulani tace,"Allah kiyaye gaba. zamu koma". ta faɗa tana miƙewa, su kai sallama da Granny, Hajiya Madina kuma ta tafi yi mata rakiya. Turaki yabi bayansu da kallo, yana ji a ransa Hajiya Madina itace rayuwarsa. hoton wancan lokacin ya shiga haska masa, yana ɗan ƙarami bai san mene mutuwa ba amma yasan me wutar dake ci a cikin ɗakin zata iya haifar musu shi da ƙanwarsa, kasancewarsa yaro me bala'in wayo, kuma tun yana buga ƙofa yana faɗin,"Mum please come and open us". har ya gaji ya daina faɗa. ya shiga toilet da gudunsa ya ɗebo ruwa a ƙaramin cup yazo ya dinga watsawa labulen da ya kama da wuta amma wutar bata mutu ba. ya ɗauko abu ya taka yana leƙa cikin gadon da Zaytuna ke kwance yana so ya kamo hannunta ya ɗaukota su fita a ɗakin amma ya kasa, ƙarfinsa da tsayinsa ba zai kai ba. idan ya juya yaga wutar ta ƙara kama wani wajen sai tsoro ya daɗa kamasa, ya ƙara zuwa ya buga ƙofa in ya kira Mum yaji shiru sai ya dawo ya kuma taka abu a ƙoƙarinsa na ɗauko Zaytuna amma sai ya kasa, sai ya ƙara saka kuka yana ta kiran sunan Mum. daga ƙarshe kawai sai ya zauna a gefen gadon ya kifa kai da gwiwa yanata kuka, kuka mai ban tausayi, yana ta kallon hoton Mum acikin idonsa, yana ji a zuciyarsa babu daɗi, yaro ne shi amma ya san me ake nufi da laifi, dan haka ya dinƙa jin haushin kansa akan laifin da yayiwa Mum ba tare da ya sani ba, laifin da gashi har ya shafi ƙanwarsa da yake tsananin so. lokacin da ya saddaƙar shi da ƙanwarsa sun mutu, saboda hayaƙin da ya gauraye ɗakin da ba a iya ganin komai ta yanda wutar ta ƙara yawa saɓanin da kaɗan take ci tunda gefen labule ta kama, amma zuwa lokacin har ta kama katifa ƙauri yana tashi, ɗakin yayi duhu, shi kuma sai tari yake yi yana ta so yaja gadon Zaytuna amma ba zai iya ba. a lokacin ne kuma hayaƙin ya fallasu acikin gidan, mai gadi yaje ya sanarwa da Hajiya Madina cewa wuta ta kama a ɓangaren Hajiya Ramla, kuma ya ga ta fita tun ɗazu ita kaɗai babu yaran. jin wannan batu yasa Hajiya Madina barin ɓangarenta a rikice ta yo ɓangaren Hajiya Ramla, ta shigo ɓangaren tana taƙwala kiran Your Excellency, sai taci karo da wayarta a kan dining. wannan yasa Hajiya Madina ƙara hargitsewa ta haye sama da sauri, garin hawan ta zame ta faɗi, amma bata kula da faɗuwar ba ta tashi tana ɗingishi ta wuce direct zuwa ɗakin Hajiya Ramla, tana zuwa ta murɗa handle taji ƙofar a rufe, gashi tana gani daga ɗakin wutar ke ci, sai tabi ta rikice ta koma ƙasa ta kira me gadi tana daɗa tambayarsa ya tabbata yaga fitar Her Excellency, yace ya gani tun kusan minti biyar ma kenan, amma ba da yaran ta fita ba, kuma bama da mota ta fita ba. Hajiya Madina ta ɗora hannu aka tana salati, suka dawo saman ita da me gadi, kuma suna zuwa suka jiyo kukan Turaki yana buga ƙofa yana cewa,"Mum please come and open us, please Mum, the fire is coming closer to us". jiyo muryarsa yasa Hajiya Madina yin tangaltangal zata kife a ƙasa, tana duban me gadi tace,"my children are inside Malam Hamisu. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, taimaka min Malam Hamisu ƙofar a rufe take". ta faɗa tana fashewa da matsanancin kuka tana kama handle tana jijjiga door ɗin. Malam Hamisu ya murɗa handle ya tura ƙofar yana duddukanta amma taƙi buɗewa, sai daga baya tunanin ɗauko spare key ya zowa Hajiya Madina. ta kira me aikinta tace tayi gaggawar zuwa side ɗin Baffa ta ɗauko duka keys ɗin da ta gani acikin bedside drower, kuma cikin mintuna kaɗan sai gata ta kawo. Malam Hamisu ne ya iya buɗe ƙofar don ita ba zata iya ba saboda yanda jikinta ke rawa gaba ɗaya. jin an danno ƙofa da ƙarfi hakan yasa Turaki ya tsorata, ya buɗe bakinsa ya kira sunan Mum da ƙarfi yana ƙara fashewa da kuka, sai yaji muryar Hajiya Madina saɓanin wacce yayi tsammani. ba zai iya tuna abinda ta dinƙa faɗa ba amma ba zai manta yanda ta dinga lalubensu ba acikin hayaƙin har ta gansa, tana zuwa ta janyo shi zasu fita sai ya tirje yana ce mata,"Maama Jaishuna". tsananin firgicewa da rashin sanin inda kanta yake bama tasan me yake faɗa ba har suka fito daga ɗakin, tari ya sarƙe shi maganarsa ta maƙale, Hajiya Madina ta dinƙa jijjigasa har Allah yasa tarin ya tsaya. kuma sai a sannan ta gane me yake cewa, lokacin da ta rungume shi tana kuka sosai, ya tureta a jikinsa yana nuna mata ɗakin yana cewa Baby Jaishuna. ta na fuskantar abinda ya faɗa ta kunce goyon dake bayanta wanda ta manta ma da shi, ta koma ɗakin a sukwane tana kurma ihu tana zabga salati. within a minutes sai gata ta fito tana janye da gadon Babyn, don sai da ta fito ta ɗauko Zaytuna acikin bed ɗinta wacce a lokacin numfashin jaririyar ma ya ɗauke gaba ɗaya saboda uban hayaƙin da ta zuƙa. Malam Hamisu dake tsaye da yara a gabansa cikin ɗimauta yana dubanta ya ƙwala ƙara yana faɗin,"wuta a rigarki Hajiya". taji sanda ya faɗi cewar wuta a rigarta, amma ba zata iya cewa ga yacca akayi ta cire rigar tayi wurgi da ita ba, domin hankalinta gaba ɗaya baya jikinta, yayi kan jaririyar yarinyar da ta gama saddaqarwa ta rasu, ta saddaqar da sun rasata, kuma banda Malam Hamisu ya lura da wutar ya ankarar da ita da sai dai wutar ta babbake su, duk da cewar wutar ɗan kama jikin rigar tata yayi, to sai Allah dai ya taƙaita komai yazo da sauƙi. ganin Hajiya Madina ta rage daga ita sai rigar nono sai zanen jikinta, Malam Hamisu yaja yaran suka sauka zuwa ƙasa. itama ta sauko daga benen a ruɗe cikin tsananin tashin hankali tana salati tana kuka tana jijjiga Zaytuna. bayan mintuna biyar sai ga fire service sunzo, motar su tayi parking a compound tare da motar Baffa, ya fito shima a matuƙar razane yana kallon yanda hayaqi ke fitowa ta window. ya nufa me gadi da mugun tashin hankali yana tambayarsa ina iyalinsa, ganin Baffan yasa Turaki kamo hannun Khalil suka fito daga ɗakin me gadin da ya saka su aciki, a lokacin Khalil shekararsa biyu dan ko yayesa ma ba'ayi ba kasancewar baida cikakkiyar lafiya an haife shi a bakwaini. ganin yaran Baffa yayi kansu da gudu ya ɗauke su, idanuwansa a warwarje yake tambayarsu ina Madina da Ramla, Turaki na kuka ya girgiza masa kai alaman bai sani ba shima. sai Malam Hamisu ne yake sanar masa ai babu jimawa Hajiya Madina ta fita a mota tayi asibiti da Zaytuna. kuma ya kamata abi bayanta gudun kar a sami mummunan haɗari dan hankalinta ba'a jikinta yake ba. "Her Excellency fa?". Baffan ya tambaya da tsananin ruɗu bayan jin abinda Malam Hamisu ya faɗa masa. "ranka ya daɗe ita bata gidan, fitarta babu jimawa wutar ta tashi". Baffa yaja yaransa yana cewa da Malam Hamisu,"ka ji da fire service ɗin nan, zan bi bayan Madina". da faɗar haka ya shiga mota yaja suka bar gidan yabi bayan Hajiya Madina, yana driving ɗin yana bin hanya da kallo har ya iso asibiti, shima motarta ya gani a wajen asibitin sanda zai wuce, bai tunanin wannan asibitin tazo ba tunda ba shi suke zuwa ba. Samun Hajiya Madina yayi a ward ɗin tayi dirshen a ƙasa sai kuka take yi, tana ganinsa ta miƙe tayi kansa tana nuna masa emergency room ɗin da jaririyar ke ciki, gaba ɗaya ma ta kasa magana sai jan nunfashi take yi tana masa nuni da hannu. Jikin Baffa sai ya mutu zatonsa ko sun rasa yarinyar ne, ya nufi ƙofar emergency room ɗin yana leƙawa ta glass, likitoci ne kusan biyar akan yarinyar ana ƙoƙarin ganin an ceto ranta, duk da suna ganin da kamar wuya yarinyar ta rayu, wannan furucin nasu ne yasa tunda Hajiya Madina ta zube a ƙasa bata motsa ba tai dirshen tana ta kuka tana roƙon Allah. kuma cikin hukuncin ubangiji sai gashi numfashin yarinyar ya dawo bayan an shafe rabin awa akanta ana ta saka mata wasu machines, duk da likitan ya faɗa musu the Baby is now alive amma hankalin Hajiya Madina bai kwanta ba, har sai da suka shiga room ɗin da akai admitting Babyn taga idonta biyu an saka mata robat oxygen a hancinta sai wutsil wutsil take sannan ta dawo cikin nutsuwarta. tukunna hankalinta ya kwanta ta daina kukan da Baffa ya shafe rabin awa yana lallashinta bata ji ba, a sannan ne kuma zafin ciwon jikinta ya ratsata, tana dubawa taga ashe ta ƙone ne a bayan hannunta da kafaɗarta, sai kuma targaɗan da tayi a ƙafa garin hawa bene. Hajiya Madina tasha wuya sosai da ƙonewar da tayi, ba za'a kira ƙonewar da ƙarama ba dan round tayi babba, dan bayan sunyi 1week a asibiti na kwanciyar da akai da Zaytuna sai da suka ƙara 1week saboda caɓewar da ƙunuwar tata tayi, ashe ƙarfin hali take tayi. saboda tashin hankalin da suka ƙara shiga na ɓatan Hajiya Ramla, babu inda ba'a duba ba babu Hajiya Ramla, haka babu cigiyar da ba'ayi ba within that 2weeks amma babu amo babu labarinta, wannan ne ya ƙara firgitar da Hajiya Madina ta ƙara fita hayyacinta gaba ɗaya, ta mance ma da wani abu ciwo dake jikinta balle xafinsa, dan idan ma tace zata bi ta kan ciwon tausayin Zaytuna da Turaki ba zai barta ba. cikin wannan hali da suke ne na jimamin ɓatan Ramla kowa ya ƙara tabbatarwa da Alƙali Dikko yayi sa'ar mata a duniya, situation ɗin da Hajiya Madina ta shiga a silar ɓatan Hajiya Ramla ba zai faɗu ba, yanda kasan wacce uwarta ta mutu, abinci wannan bata ci sai an mata da gaske, kuka kuwa da ace ruwan hawaye na ƙarewa tuni nata ya jima da ƙarewa. Hajiya Madina macece ta gari, me kyawun zuciya, wacce babu algus a tare da halinta, wacce take zaune da kowa lafiya take kuma nuna kowa nata ne, bata ƙyamar kowa kuma bata munafurta kowa, dan sau tari akan cewa da Hajiya Ramla matsalar kishiyarki ɗaya ne, bata iya munafurci ba. ita kanta Hajiya Ramla tasan tayi sa'ar abokiyar zama, abunda kowa ke faɗa mata kenan tunda aka auro Madina, shi yasa suke zaune lafiya babu fitina, babu faɗa balle tashin hankali, kansu a haɗe kamar waɗanda suka fito ciki guda. tunda aka haifi Turaki Hajiya Madina ta mayar da shi kamar ɗan cikinta, idan ba sani kayi ba ba zaka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, an aurota dalilin rashin haihuwar Ramla, to kuma sai Allah ya nuna ikonsa ko da ta shigo gidan itama sai da ta shafe shekaru masu yawa bata ko yi ɓarin ciki ba, har Allah ya bawa Ramla ciki ta haifi 2wins maza, ranar suna yaran akasa musu sunansu Muhammad da Lateef, Muhammad shine aka saka masa sunan mahaifin Ramla suke kiransa da Turaki kamar yanda ake kiran mahaifin nata, shi kuma Lateef shine yaci sunan mahaifin Dikko zasu ke kiransa da Abi, to kuma a ranar sunan da daddare sai Lateef ɗin ya rasu. sai da Muhammad Turaki ya shekara huɗu ciff a duniya sannan Hajiya Madina ta haifi nata yaron wanda yaci sunan mahaifinta Ibrahim suke kiransa Khalil, shekararsa biyu shima Ramla ta ƙara haihuwar ƴa mace me suna Zaytuna. part ɗin kowacce daban amma baka ganinsu ba'a tare ba, in kuwa ka gansu separately to dare ne yayi za'a tafi makwanci, amma da zarar safiya tayi sun tafi breakfast side ɗin Baffa, har sanda wani acikinsu zai yi baƙo, ko kuma idan Hajiya Ramla zata tafi office, idan wannan tayi ba daidai ba ɗaya zata gyarawa ƴar'uwarta kuma su amshi gyaran cikin sauƙin kai. wucewar sati da watanni anata saka ran ganin ko Hajiya Ramla zata dawo amma shiru kake ji, da haka har aka shafe shekara guda, kuma a lokacinne aka sallama da cewar ta rasu. dalilin da yasa Hajiya Madina ƙara jan Turaki da Zaytuna a jikinta kenan saboda tausayin maraicin su na uwa, ta rungume su a ƙirjinta tamkar ita tayi naƙudarsu, babu ranar da bata kallonsu bata zubar da hawaye ba har suka girma, ƙarshe ma sai ya zamto tana nuna musu tsantsar so da kulawa fiye da waɗanda ta haifa a cikinta, son su take yi domin Allah ba da wata manufa ba. haka kuma kwata-kwata bata nufar yaran da sharri, abinda zai samesu sai ya ɗaga hankalinta wanda zai sami Khalil ko Samha bai ɗaga mata hankali ba ko kusa, don gani take tamkar in wani abu ya samesu lallai Allah xai tuhumeta domin amana ce da tayi alƙawarin ta ɗauka, ta ɗauki alƙawarin zata riƙe su kamar yanda Ramla zata riƙe su, kuma tayi alƙawarin ba zata kalle su da sunan ƴaƴan miji ko ƴaƴan kishiya ba sai ƴaƴan da ta haifa acikinta. bayan shekara goma a wata rana ta laraba sai ga message a wayar Baffa, saƙon da Hajiya Ramla ta turo musu kan cewar tana nan a raye bata mutu ba, kuma ko da xa'a ɗauki tsawon shekara 100 kar su taɓa sawa a ransu cewa ta mutu, tana nan a raye nesa da su sai dai ba zata taɓa dawowa gare su ba har abada. wannan saƙon ya girgiza kowa, kuma wannan saƙon shi ya haddasa jin haushi a zuciyar Zaytuna, take jin tana tsananin fushi da mahaifiyarta, tana jin yau ko da ace za'a kawo mata gawarta ba lallai ne ta dubeta ba. saɓanin Turaki da saƙon ya ƙara haddasa masa damuwa a ransa, lokacin shekarunsa goma sha shida, yana can europe wurin Kakarsa ta wurin uwa, kuma tun daga lokacin har kullum tunaninsa guda ɗaya ne, a wanne hali Mum take ciki?, ya lafiyarta take?, menene damuwarta?. abu ɗaya har kullum ransa ke basa akan barinta gidan shine, wataƙila tayi fushi da shine, tayi fushi da shi akan tana tunanin cewar shi ya haddasa kamawar wutar ɗakin, alhalin shi bai san da komai ba, bai ma san da cewa wutar ta kama ba sai da tayi magana, time ɗin da ta fito ɗaga toilet tayi wanka tana tsane jikinta da towel, shi kuma yana zaune akan gadonta yana homework ɗin da Hajiya Madina ta basa, sai ji yayi Mum ɗin na tambayarsa aina ya sami ashana har yayi mata ta'adi, ta tambayesa ɗin tana yowa wurin da labulen ya ɗan fara ci zata kashe wutar. yana iya tuna yacca taja tsaki a sanda ta kama labulen da sunan zata watsa ruwan dake hannunta, sai yaga kawai ta tangarar da jug ɗin ya faɗi ya fashe, ta wuce ta isa wadrobe ta ɗauki abaya ta zira ta fita ta barsu a daidai lokacin da wutar ta fara ci sosai, yaji tsoro ya sakko akan gadon yabi bayanta da gudu, sai kawai ta hankaɗosa ciki tana doka masa tsawa bayan ta ambaci ainihin sunansa da bata taɓa faɗa ba tunda ta haife shi, taja ƙofar ta rufe tasa key ta cire ta tafi da shi. wannan ɗalilin ya barwa kansa, kuma har kullum yana roƙon Allah ya haɗa fuskokinsu kamin ya kai ga kushewa ya roƙeta ta yafe musu, ya faɗa mata gaskiyar cewar bai san komai ba akan kamawar wutar. "Hammah Hakimi na magana a waya". maganar Zaytuna ta dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi. ya karɓi wayar yana karawa a kunnensa tare da yin sallama. sun ɗau lokaci suna waya Hakimi na tambayarsa yanayin lafiyar tasa, kafin daga bisani suyi sallama. washegari ƙarfe goma na safe akayi discharge nasu suka koma gida. kuma suna komawa inda ya fara dosa bayan sunyi lunch shine ɓangaren ma'aikata, dalilin ganin tun dawowarsu bai ga gimlawar Fillo ba, tun da suka dawo yake ta zuba ido ko zai ga ta wuce amma ko inuwarta bai gani ba, kuma yana ta sauraren yaji wani yayi zancenta har da Maama amma sai yaji ba wanda ya ambaci ko da sunanta. [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Please avoid any mistakes._ *25* "barka da shigowa ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya magajin me gida". adu'ar da ma'aikatan ke tayi masa kenan tunda ya shigo ɓangaren su. yasa hannu a aljihu ya ɗauko bandir na kuɗi ya bawa shugabar ma'aikatan wato Yami, ta duƙa har can ƙasa tasa hannu biyu ta karɓa suna ƙara yi masa adu'oi na fatan alkhairi. tun da ya nufi ɗakin Kaka aka je aka sanar mata, kamin ya ƙaraso tuni ta daɗa kimtsa wurin ta kunna turaren ƙamshi. Turaki yayi sallama a ƙofar ɗakin idonsa na mannewa akan yagalgalallan labulen ɗakin, Kaka ta taso da sauri tazo ta buɗe labulen tana faɗin,"Barka da zuwa ranka ya daɗe". ta yaye masa labulen shi kuma ya shiga, sai bayan ya zauna sun gaisa da Kaka sannan ya fara tunanin acutual abinda ya kawosa. tun bayan gaisawar su da Kaka ya kafe ƙofar ɗakinta da ido, ta yanda ba zaka taɓa fahimtar ga inda yake kallo ba, sama da mintina goma shiru bai ga alamar Fillo ko inuwar Fillo zata fito daga cikin ɗakin ba, kuma motsi kaɗan zai ji daga waje sai ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa bakin ƙofa yaga ko ita ce, but sai yaga babu kowa. ya sauke numfashi a daidai sanda zuciyarsa ke ayyana masa tasirantuwar wani abu, kuma lokacin ne Maijidda ta shigo ɗakin tana ta mita. ganinsa yasa tai saurin zube gwiwoyinta a ƙasa tana gaida shi. bai amsa mata da baki illa kansa kawai da ya ɗaga mata. ya miƙe ya yiwa Kaka sallama ya tafi, Kaka ta bawa Maijidda furar da ta dama ta bisa da ita. daga can ɗakin Hajiya Madina Fillo ce zaune a gabanta, kanta a ƙasa, idanuwanta sun cika da ruwan hawaye, tana jin kanta na mugun sara mata kamar zai faɗo ƙasa, maganganun Hajiya Madina nema suke su juyar mata da dukkan wani tunani nata, a yanda dukkan zancen Hajiya Madina suka ratsa jikinta bata jin zata iya ko da ɗaga ɗan yatsa guda a yanzu dai. Hajiya Madina da idanuwanta ke manne akan Fillo itama nata idanun na zubar da ruwan hawaye tace,"wannan shine dalilin da yasa nace miki ina so ki nutsu kiyi karatu, kuma wannan aikin shine wanda nake faɗa miki zaki yi min Fillo, tun a kallon farko da nayi miki zuciyata ta faɗa min zaki iya, hakan yasa na zaɓe ki, ina fatan kuma zaki warware komai cikin sauƙi ba tare da abunda nake gudu ya faru ba". a wannan karon da Hajiya Madina tayi magana, sai Fillo taji kamar tana neman ta tarwatse gaba ɗayanta ne. manyan idanuwanta suka maƙale a kan ƙafar Hajiya Madina dake cikin wani tsadaddan takalmi, so take ta haɗe dukkan maganganun Hajiya Madina wuri guda sannan ta watsar da su a gefe ɗaya, domin bata tunanin akwai ta yanda zata yarda cewar wannan jarumar matar dake gabanta ba itace mahaifiyar Turaki ba. amma dolenta a yau kuma a yanzu ta yarda da hakan, ta yarda da wannan macen ba ita bace asalin mahaifiya wacce ake kira uwa a wajen su Turaki ba. "ban san me zance miki ba Maama, abu ɗaya kawai da na san ya zama dole shine jinjinawa, dole zan jinjina miki, kamar yanda na jinjinawa masu farautar rayuwar Turaki". ta faɗi hakan tana me ɗagowa ta sanya idanuwanta cikin ƙwayar idon Hajiya Madina, sannan ta iya miƙewa jiki a saɓule tana jin kamar ba zata iya tafiya ba, ta bar ɗakin tana barin Hajiya Madina a cikin tsananin tashin hankalin da ba zai misaltu ba. a parlo ta tarar da Samha zata hau stairs wurin Maama, tana jinta tana yi mata magana tayi mata banza bata ko kalleta ba. ta baro side ɗin cike da mamaki da tunani kala-kala acikin ranta, kuma cike da tsoron ɗan'adam, ko waye shi kuma ko ya kuke da shi. a coumpound ta tarar da Ɗausiyya acan wajen bakin famfo tana wanki, ta ƙarasa wurinta tana ce mata. "idan teacher yazo ki faɗa masa bani da lafiya, ba zan iya karatu ba yau. please ki basa assignment ɗina kar yay zaton ko saboda shi naƙi zuwa". Ɗausiyya na kallonta tace,"tun jiya kike kuka Fillo, kuma na tambaye ki kince ciwon kai ne kawai, ni dai wallahi ban yarda dake ba. dan Allah ki faɗa min ko da wata damuwar, mun riga fa mun zama ɗaya". Fillo tace,"kawai bana jin daɗin jikina ne, zanje nasha magani jiyan ban sha ba dama. nasan Adda Zaytuna zata neme ni kice mata Kaka ce tayi kirana". tana faɗar haka ta juya zata bar wurin, lokacin ne motar Zaytuna tayi parking a compound ɗin tana fitowa daga cikin motar, ta ƙwala mata kita hakan yasa Fillo dakatawa da tafiyar ba don taso ba. taje wajen motar tana yiwa Zaytuna sannu da zuwa, Zaytuna ta tsaya tana kallonta da son karanto matsalar dake damunta. "what is the problem?". Fillo ta girgiza mata kai tana faɗin,"nothing Adda". yanayinta kaɗai shi zai ƙaryarta furucinta, Zaytuna tace,"ki ɗauko leda a backseat ki biyo ni da shi". ta faɗi hakan tana wucewa ta barta a wurin. ta ɗauko ledan kayan dake rinjayar ƙarfinta. ko da ta shiga part ɗin su Zaytuna bata sameta ba don haka ajiye kayan kawai tayi ta fito, don yanzu ita sam bata son abinda zai kaita wannan part ɗin ita ɗaya ba tare da wani ba, tun abunda ya faru a jiya take jin tsoron ƙara shigowarsa. haka ta sakko daga upstairs ɗin zuciyarta cike da tunani kala-kala. ta biyo ta corridor ɗin da zai fitar da kai ta baya, sai dai tana zuwa wajen ƙofa taja tayi turus tayi saurin laɓewa saboda abinda ta gani da kuma abinda take ji. tsabagen girgiza da Al'amarin bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tana saka hannu ta toshe bakinta gudun kar numfashinta dake neman tsarƙewa ya fallasata. ta rumtse ido da kyau cikin ranta tana ta adu'a Allah yasa kar a ganta, tayi shiru tana sauraron dukkan zantukan da ake yi, lokaci ɗaya ta ƙara girgiza taji kamar kunnenta ba daidai yake jiyo mata ba, cikin azama ta miƙe tabar wajen da sauri ta koma ta parlo ta bar side ɗin gaba ɗaya sai haki take yi. ta jima a compound zaune a wajen flowers tana ta mayar da numfashi, kafin ta iya miƙewa ta nufi part ɗin su Turaki, cikin sanɗa kamar wacce ke gudun wani ya ganta. tana shiga ta tarar da Khalil a parlo yana kallo, ta tsuguna ta gaida shi cikin rasa makamar abinda zata ce ya kawota. sai kuma taji Khalil ɗin yace,"ke Maama ta aiko?". da sauri ta ɗaga masa kai tace,"ehh". yace,"to kinga ba wani gyara ne me yawa ba, toilet kawai zaki wanke min kinji, yaron dake mana aiki ne bai da lafiya". ta miƙe tana cewa,"tom Hamma". Khalil ya bita da kallo har ta ɓacewa ganinsa, ganin yacca take tafiya kamar mara gaskiya. bata ɗauki lokaci ba ta kammala wankin toilet ɗin Khalil, tana gamawa kuma ta faɗa bedroom ɗin Turaki, da shigarta shima ta wanke nasa sannan ta kimtsa ɗakin gaba ɗaya, ta saka masa turare me ƙamshin gaske. kwalbar turaren dake kan dressing mirror ta ɗauka ta riƙe a hannunta, design na kwalbar yayi matuƙar burgeta, sai dai ƙamshin har yanzu bata ƙaunarsa, kamar wacca taga kashi haka take aikin yamutsa fuska still tana riƙe da kwalban, can kuma sai ta saki kwalban ya faɗi ya fashe, ya fashe a sanda take ƙara saka ƙasan takalminta ta murje kwalban sai ɓata rai take. ƙarar fashewar ya haɗe da rufe ƙofar ɗakin, ta ɗago kai da sauri tana kallon door ɗin sai ganin Turaki tayi ya jingina jikin ƙofar, ya rungume hannayensa a ƙirji yana kaɗa one leg. tsoro sai ya kamata ta dabarbarce tana ja da baya, duk ta rasa yacca zata yi da kuma abinda ya kamata tayi, taji kamar ta kurma ihu saboda yanda ya kafeta da ido yana kallonta fuskar nan a haɗe, alamar ya harzuƙa da ta'adin datayi masa. sai tai saurin duƙawa ta shiga tattara kwalban da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma tana toshe hancinta da shi, bata ankara ba kwalban ya shige mata cikin fata nan da nan jini ya fara zuba. cikin jin zafin ciwon ta furta,"wayyoo Kaka". ta faɗa tana yarfa hannu jinin na fallatsuwa a wani wurin. ganin yanda jinin ke fita sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin,"wayyo jinina, wayyo Kaka, wayyo jinina zai ƙare". Turaki da har lokacin yake tsaye yana kallonta yana kallon jinin dake zuba, yaja tsakin takaici ya bar bakin ƙofar ya ƙaraso ciki. akan bed ya ajiye wayoyinsa sannan ya shige toilet, after 10mints ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, ƙaramin dake hannunsa kuma yana goge sumar kansa da shi. ya kai idonsa wurin da ya barta yaga bata wajen, sai kwalban sai jinin da yaɓata wajen, ya ci gaba da goge kansa yana ƙarasawa bakin gadon ya zauna. ɗago da idonsa da zai yi ya ganta tsaye bakin ƙofa ta kama handle ta riƙe, sai aikin murɗa shi take yi duk tabi ta ruɗe, har lokacin kuma bata bar kukan ba haka kuma bata daina yarfar da hannun ba. da mamaki kawai ya tsaya yana dubanta, jinsa yake kamar ya tashi ya mammaketa don takaici. ta juyo da kanta a daidai lokacin da yake ƙoƙarin ɗauke kansa daga kanta, karaf suka haɗa ido, Turaki ya ƙara shan murr, ita kuma ganinsa babu riga yasa tayi saurin runtse ido tana ƙara fashewa da kuka. bayan Turaki ya saka kaya, ya dawo ya nemi waje ya zauna bakin gadon, ya ɗauki wayarsa yay dialling numbern Zaytuna. tana ɗagawa yace mata,"ki bada bandage a kawo min". yana faɗar hakan ya kashe. ya ajiye wayar sanda Fillo ta kira sunansa,"Hammah don Allah kayi haƙuri, jinina zai ƙare". tai maganar acikin kuka, ya galla mata harara ta ƙasan ido yana ƙara jin sabon takaicinta acikin ransa. jin ana knocking door ya taso yasa key ya buɗe ƙofar, ya karɓi box ɗin dake a hannun Ɗausiyya ya maida ƙofan ya rufe tare da ƙara sanya key sannan ya dawo ya zauna bakin gado. "zo nan". ya faɗa idonsa akanta. kamar ba zata zo ba sai kuma ta miƙe ta taho kamar me shirin faɗuwa, ganin cewar in taci gaba da tsayuwa a haka jininta duka zai tsiyaye. ta tsuguna a gabansa wurin da ya nuna mata, ta miƙa masa hannun ta runtse ido tana jan numfashi. ya kalli hannun ya kalleta sannan yace,"are you stupid?, kwalban ma da ya shiga ba zaki iya cirewa ba kika barsa a jikinki?, ke shashashan ina ce wai". cikin kuka tace,"to ai ba zan iya ba, jini ne yake fita". "jinine yake fita shine cire guntuwar kwalba ya gagareki?". ita dai bata ce masa komai ba banda kyarmar jiki da take yi, yaja dogon tsakin da yayi duka har cikin kunnenta, ya kamo hannun ya cire kwalbar sannan ya shiga treating mata ciwon, tunda yasa spirit ya goge jinin ta tsala uban ihu tana neman fincike hannun, hakan yasa ya riƙe hannun da kyau yanda ba zata ko iya ja ba balle ta iya fizga har ya ɗaure mata wajen da bandage sannan ya sakar mata hannun. zuwa lokacin tayi kuka ta gode Allah. muryarsa a tamke ba tare da ya duba irin zafin ciwon da take ji ba yace,"tashi ki gyaran waje, saura ki ƙara saka hannu tunda baki da hankali". ta miƙe sai sheƙar kuka takeyi ta ɗauko tsintsiya ta tattare wajen. tana kammalawa ta nufi ƙofa zata fita taji ya ƙara saka key ya kulle. "na gama ai". ta faɗa tana kallonsa a ɗarɗarce. ba tare daya kalleta ba yace,"kin san tsadar turaren da kika fasa?". da sauri ta girgiza kai tace,"a'a, amma don Allah kayi haƙuri bada sani na bane". ya ɗauke idonsa daga kan wayarsa ya ɗora akanta sannan yace,"balle ma da saninki kika fasa ɗin, dan haka abu ɗaya na san da shi sai kin biyani turarena, kuma a yanzun anan wajen ba sai anje ko'ina ba, if kika biyani sai ki sami damar fita daga room ɗin nan". maganarsa yasa ta ruɗe ta shiga ba shi haƙuri tana roƙonsa. tayi mugun basa tausayi amma ya ɗauke kansa kamar baya jinta. wucewar mintina biyar sai yaji shiru ɗakin, kukanta ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, tun before ya juyo da kansa ya kalli bakin ƙofar ya fara tunanin ta yanda akayi ta fita after yasa key, sai dai yana juyowa ɗin sai ya ganta ta ɓingilar da kanta ajikin ƙofa baccin kuka ya ɗauketa kamar jaririya. zai iya cewa bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba, banda yasan abubuwa da dama ba, to tabbas zai rantse wannan rigimammiyar yarinyar ba itace hatsabibiyar dake cusa kanta cikin haɗarin da ba nata ba. ya jima yana kallonta a hakan, matsawar ya barta ta ɗauki tsawon lokaci tana bacci a haka wuyanta sai yayi ciwo sosai saboda yanda ya barƙale, hakan yasa ya sakko a gadon yazo ya ɗauketa ya dawo ya kwantar da ita akan gadonsa, yaja blanket ya rufeta yana jin zuciyarsa na matsewa. for few minutes yana daga kishingiɗe ajikin pillow daga ɗayan side ɗin, tunani kawai yake yi kala-kala acikin ransa, daga bisani ya miƙe ya bar ɗakin, yana fitowa yaci karo da Bello na niyyar shigowa, ganin junansu yasa duk suka ɗaure fuska. Bello na ƙoƙarin ya ture shi ya shiga room ɗin, shima Turaki na ƙoƙarin ya turasa baya ya nuna masa hanyar da ta fi dacewa da shi. "Malami ban hanya". Bello ya faɗa cikin tamkewar fuska yana sa hannu ya ture Turaki gefe, ya murɗa handle ya shiga bed room ɗin. sai dai yana shiga ya fito da sauri yana dakatar da Turaki daga tafiyar da yake yi zai sauka daga benen. "Turaki me nake gani a ɗakinka?". a fusace Turaki ya juyo yace da shi,"uban wa ya kai ka shigar min ɗaki dama?". shima Bellon a fusace yace,"da sai da izininka nake shiga?, ko kuma dama Baffa ce yayi ɗakin naka ne kai ɗaya?...ba wannan ne a gabana ba Muhammad, faɗa min me na gani a ɗakinki?, warware min komai tun ban fara shakku akanka ba". Turaki yaja tsaki ya sauka a benen ba tare daya ce masa komai ba. Bello yayi ajiyar zuciya yana sa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Zaytuna. *Masarauta Kaltungo.* "nifa duk bayannan naki a banza nake jinsu, shekaru ba su zasu hanani cimma alwashin dana ɗauka ba Jakadiya, tunda har naga bayan Ramla to babu abinda zai hanani ganin bayan Madina, ki rubuta wannan ki ajiye, ko bayan raina zaki faɗa cewar ni Fulani nace duk wata mace da Dikko zai aura rayuwarta a hannuna take". furucin da Fulani tayi kenan a sanda idanuwanta ke sauka a ƙasa, tana jin zuciyarta na zafi da tafarfasa, tana jin yanda zuciyarta ke kuka, kukan da ta ɗauki tsawon shekaru masu yawa tana yi kuma har yanzu bata daina yinsa ba. ƙafarta kawai take kallo wadda tasha adon sarƙa na gwalagwalai da azurfa, kallon ƙafar tata take yi a zahirance, amma a baɗini ƙafar Alƙali Dikko take kallo, ƙafarsa take kallo tana tuno yanda ta riƙe ƙafafunsa a wancan lokacin tana roƙonsa akan kar ya rabu da ita ya aureta ko da bayan auren zaisa wuƙa ya kasheta, da kuma yadda ya fizge ƙafafunsa ya fita daga ɗakin ya barta ba tare da ya waigo ya kalleta ba, waigen kallon da bai ƙara yi mata ba har yau tsawon shekaru 37, duk da kasancewarta matar Yayansa Mai Martaba Hashim. ta rumtse idonta sosai tana jin zafi a zuciyarta, ganewa ne kawai mutane ba su yi ba, amma zafin so yafi ƙarfin kwatance, ita zata iya cewa zafin so yafi zafin wuta zafi da raɗaɗi, muddin wanda kake so bai bar tasirantuwa a zuciyarka ba. Allah ya sani har duniya ba zata taɓa daina son Alƙali Dikko ba duk da cewar akwai igiyar auren wani akanta, auren ma da har suke da rabon ƴa a tsakani, ƴa me shakaru 21 a duniya, son Alƙali Dikko ba daga gareta bane, so ne daga Allah. taja wani dogon numfashi ta sauke, a sannan ta buɗe ido ta sauke akan ƙaton tray ɗin dake gabanta. Jakadiya Haulat tace,"ranki ya daɗe ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi, Allah ya huci zuciyarki uwar gijiyata...yanzu kamata yayi kisha furar nan domin ki samu kiji sanyi a ranki, tun safe babu abinda kika sa a bakinki...batun Hajiya Madina da Ɗan Ramla tamkar tsoma allura ne acikin ruwa, kisa a ranki lokacin kawar da su daga rayuwar Alƙali Dikko yazo ƙarshe, zasu barshi kamar yanda Ramla ta barsa". Fulani tayi murmushin takaici me ciwo, sannan ta ɗago ido ta yiwa Jakadiya kallon tsab kafin nan tace,"ban taɓa yin wani shiri akan Madina ba, kasantuwar nasan Dikko ba sonta yake ba, zatona a lokacin Mai Martaba zai sawwaƙe min daga nan sai na maye gurbin Ramla, ashe duk lissafin da nayi akan hakan da ƙazamin tunani nayi shi...dukkan wani shirina ina yinsa ne akan ɗan Ramla, shirye-shiryen da nayi akan na tarwatsa yaron nan yafi ƙirgen yatsu, sai dai har yanzu na kasa ganewa Jakadiya, na kasa fahimta, na rasa dalilin da yasa cikin tarin ƙullin da nayi akan Turaki babu wanda yay tasiri, amsa ɗaya nake so daga bakinki ba daga bakin boka ba, haka kuma abu ɗaya nake so na sani daga wajenki ba daga wajen boka ba, meke warware aikin Malam?, menene ke warware duk wani ƙulli da nayi?, waye yake lalata min dukkan shirin da nayi?". sai kuma ta miƙe tsaye a fusace, ta ɗaga murya cikin tsawa tana nuna Jakadiya tace mata,"faɗa min gaskiya, kina aiwatar da aikin da na saka ki ko kuma cin amanata kike yi?". cike da tsoro da rawa jiki Jakadiya tace,"wallahi, wallahi Ranki ya daɗe ina sawa a aiwatar da duk abinda kika ce, wallahi kuma ko kaffara ba zanyi ba waɗanda na saka suyi ba zasu ci amanarmu ba, ni kaina ina matuƙar mamakin yanda komai ke warwarewa acikin sauƙi, sai dai ina tunanin ƙarfin adu...". ai tun Jakadiya bata ƙarasa ba Fulani ta ƙara ɗaga murya wajen dakatar da ita acikin tsananin fushi da ɓacin rai,"dakata munafuka, tabbas sai naga bayanki Jakadiya domin babu wanda yake cin amanata na ƙyale shi...karki ƙara buɗe baki kice zaki faɗa min zancen banzan da ba yarda zanyi da shi ba, ƙarya kike yi kice tasirin adu'a zai karya aikin asirin da nake ɓarnatar da kuɗi akai, aikin boka tumbutsu ne ba aikin wani galhonaho ba, bokan da yake aiki tamkar yankan wuƙa, kuma tunda har aikinsa yayi tasiri akan Ramla ƴar Turakin Taraba, bana tunanin aikinsa zai ƙi cin wani tsiyatattan halitta Turaki, don haka kamar yanda na ɗauki alwashin ganin bayan Madina da Turaki a wannan ƙarnin, haka kema sai naga bayanki Jakadiya tunda har kika ci amanta". Jakadiya ta zube gwiyoyinta a ƙasa ta shiga roƙon Fulani cikin tsananin ruɗewa, ana cikin haka Ilham ta turo ƙofar ɗakin ta shigo. cike da shagwaɓa ta faɗa jikin Fulani ta sakin kuka da cewar,"dan Allah Mami ki barni naje, Allah ba zan jima ba zan dawo...sau biyu kenan Hammah Turaki na ciwo bana zuwa na duba shi, kuma yana ta min complain ɗin hakan". Fulani ta tureta daga jikinta, ta fita rai a ɓace daga turakar tata. Ilham ta buta da kallo kafin daga bisani ta zube akan gado tana sakin kuka. tana cikin kukan wayarta ta shiga ringing, ta ɗau wayar tana kallon screen ɗin, ganin sunan Turaki na yawo a jiki yasa ta sakin wani kyakykyawan murmushi sannan ta ɗaga tana cewa hello cike da shagwaɓa. daga ɓangaren Turaki ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ba ki damu da lafiya ba right?". Ilham ta ƙara narkewa da muryar shagwaɓa tace,"Hammah yau zan zo insha'Allah". Turaki yace,"ba sai kin zo ba, ni gani na zo. ina ɓangaren Abbas...but ba zan jima ki hanzarta". *Comment, Share and Vote.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *27* Fillo ce zaune akan dakalin bayan ɗakinsu, daga yanda ta zabga tagumi kasan tunanin wani abu takeyi wanda ke damun ranta. ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jajir, idon kuma ya ƙara girma. Maijidda ta ƙaraso wajen tana faɗin,"na tsani wannan tagumin naki wallahi". Fillo ta ɗago ido tana kallonta, bata iya cewa komai ba saboda zafin da zuciyarta ke yi mata, tun ɗazu take so tayi kuka ko ta sami relief amma kukan yaƙi zuwa. "kwana nawa kina kuka?, zatonki kuka na maganin damuwa?, to idan baki sani ba kuka baida amfanin komai, damuwarki ya wuci ki kaita gaban Allah, akwai me yaye miki sama da shi ne?, amma sai kiyi ta faman kuka kuma ayi tambayar duniya kiƙi magana, da me kike so Kaka taji?, bafa isassan lafiya ke gareta ba. kuma ke har me kika nema kika rasa a duniyar nan da zaki ɗau damuwa kisawa ranki kina ƴar ƙaramarki, salon dai jawa kai matsala". Maijidda tayi shiru a sanda taji Fillo ta riƙe hannunta gam, tasan ba komai bane illa kukan da take so tayi, ta janyo Fillon jikinta ta kwanta a kafaɗarta, tuni kukan da Fillo ke jira tun ɗazu yazo mata, saida tayi me isarta tukunna ta yakice daga jikin Maijidda tana goge hawayenta. cikin muryar kukan da bai gama sakinta ba tace,"Maijidda ke kike ganin ban rasa komai ba tunda Kaka ta tsaya min, amma a zahirance ni nayi babban rashi tunda har na rasa uba, ba wai don ya mutu ba, yana raye amma na zama kamar banda uba a raye, tunda uwata ta haife ni ban sami soyayyar uba ba irin wacce ko wanne ɗan halak ke samu, ban sami gata ba irin wanda kowanne ɗan halak ke samu daga wurin mahaifi, ban samu tarbiya ba daga wajen ubana, ban sami ilimi ba daga garesa, ban sami kulawarsa ba, ban sami farin ciki daga wurinsa ba balle naji daɗi daga garesa, ya kirani da suna shegiya, ya kirani da ƴar zina alhalin akan shimfiɗar sunnah ya samar da ni...". muryarta ta harɗe tana kifa kanta akan cinyar Maijidda tana ƙara fashewa da sabon kuka. "Maijidda banyi dacen uba ba, ni kaɗai ce nayi rashin sa'ar uba, ta dalilin baƙin cikinsa har yau ban san inda Ummina take ba, bamu san ina ta tafi ba, ki tayani adu'ar duk inda take Allah yasa tana cikin kariyar ubangiji, jikina na bani Ummina bata rasu ba tana raye, amma Kaka wai sai tayi ta ce min Ummi ta mutu". kukanta ya ƙaru sosai, kuma daga ita har Maijiddan kukan suke yi. "Maijidda i wish ace ana sauyawa tuwo suna dana sauya Hayyo a matsayin ubana, i wish Hayyo is not my father, I wish I could take revenge for what Hayyo did to me and my mother. but i can't, i can't do that Maijidda, duk da lalacewarsa i still feel his love in my heart". da ƙyar kukan Fillo ya tsaya bayan da ta ɗau tsayin mintuna tana bawa zuciyarta haƙuri da kalar tata ƙaddarar. tana riƙe da hannun Maijidda tace,"ina key ɗin motar Turaki da na baki ajiya?". Maijidda tace,"yana ƙasan kayanmu. amma Fillo ba kya tsoron garin mayarwa a ganki". tana kallon wani side na daban tace,"idan ma an ganni there is no problem, and ba ma komawa ɗakinsa zanyi na ijje ba, Maama zan kaiwa". Maijidda tayi ajiyar zuciya tace,"gaskiya Hajiya Madina ta dabance, ni tunda kika ban labari na rasa ma abinda zance, nayi matuƙar girgiza da lamarin". Fillo tace,"ni kaina farko ban yarda ba sai da kunnuwana suka jiye min...kiji fa wai a tsinke burkin motar, wai sai ta kira shi tace yaje ya ɗaukota a anguwa motarta ta lalace, wai in ya taho sai me tirela ɗin yasha gabansa kawai yabi takansa". Fillo ta rumtse ido gam tana jin kanta kamar zai buga. "Maijidda wannan masifa har ina?, ace ka dinga harin jinin ɗan'uwanka?, me ya yi musu?, Allah da ƙyar ƙafafuna suka iya ɗaukata suka kai ɗakinsa, ke yanda na tafi a rikice ko a hannunsa naga key ɗin motar sai nayi kokawa da shi na ƙwace, ko kuma na faɗa masa komai kowa ya huta, saboda Hajiya Madina yasa kawai ban faɗa masa ba amma wallahi nayi niyya, to kawai dai ina tausayin halin da Maama zata shiga ne. kuma nayi rashin dabarar na faɗa mata ma tun a daren, dan da wuya in babu spare key da zai ce zai yi amfani da shi". Maijidda tace,"to Allah dai kar ya tsare shi daga dukkan shirinsu". "amin". Sabira wacca itama jika ce a wajen iya Hanne abokiyar aikin su Yami tazo wajen ta zauna. taci kwalliya daga yanda ta riƙe jakar hannunta kasan shirin fita tayi. tace da su Maijidda,"nan kuka yo ashe?". Maijidda tace,"ehh, nan ɗin yafi iska". Sabira tace,"duk yanda akayi ba'a sanar da me gidan nan wutar ɓangaren nan ta lalace ba, ji fa kwana huɗu muna cikin duhu da zafi". Maijidda tace,"ita kanta Hajiyan bata sani ba, kwana biyu basa zama. amma naji Yami tace sun faɗawa incharge zai bar mata saƙo". tace,"gwara haka, cikin daren nan duk sai ka kasa bacci wallah, ga zafi ga sauro". cike da tsokana Fillo na kallon Sabira tace,"uwar yawo sai ina aka dosa?". Sabira ta ƙara turo ture kaga tsiyanta gefe ta tauna cingom dake bakinta, bayan ta karkaɗa ƙafa tace,"ni zan so ma ki rakani, dan wannan shirin nawa da kika gani bana wasa ba ne". Fillo tayi ƴar dariya tace,"rufani ki saya, ke dai da yawonki amma ba dani ba, sai dai ko Maijidda gata nan itace uwar yawo irinki". Maijidda tace,"balle ma ba zuwan zanyi ba". Sabira tace,"ko zaki je ma ba zaki bini ba dan abinda zanje yi ba da irinki sanyi ƙalau ake zuwa ba, dan sai ki lalata min aiki. Fillon dai itace daidai da tafiyata". Fillo tace,"wai ina zaki haka, naga sai wani faman cika kike kina batsewa". Sabira tace,"ruwan masifa da bala'i zanje na juye". ta jijjiga kanta tana yin ƙwafa me ƙarfi,"ai na rantse yau idona idon kishiyar Anty Jummai sai na rotse mata kai". sai ta karkato tana facing su Fillo da kyau ta shiga basu labarin kishiyar Yayarta. "wai fa kawai dan Anty Jummai tana da haƙuri, kuma ita ƴar talakawa ce shikenan kullum sai cin kashin da kishiyar taga damar yi mata. tayi ta zaginta wai ƴar matsiyata kyace ita ubanta haifarsa akayi da kuɗin, ga shegen haɗa makircin tsiya tayi ta jawa Anty Jummai Faɗa a wurin me gidan, jiya Allah ne ya taƙaita bai saki Anty Jummai ba". Fillo da tausayawa tace,"kishiya dai kowacce kala ce bata da daɗi, Allah kai mana tsari da sharrin kishiya dan ni har ga Allah a duniyata inda abinda na tsana bai wuci kishiya ba wallahi". ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah,"ubangijina na roƙeka ba don nafi kowa ba Allah karka sa mijin da zan aura yay min kishiya, ko na shiga na tarar ko a shigo a tarar da ni". Maijidda tace,"ki dai roƙi Allah ya haɗaki da abokiyar zama ta gari shine kawai, ba wai batun kar a miki kishiya ba, in haka ne ina kike so akai sauran matan?". zuciyar Fillo na sosuwa tace,"mu bar zancen nan kawai, zan iya haɗiyar zuciya a wurin nan. kishiya fa! ni Fillo da kishiya?, to ta ina ma za'a fara zaman?, in ke ganin abinda nake so tare da wata?, Allah karka nunan wannan ranar. Maijidda cewa fa kike wai kishiya ta gari, ke a duniyar nan har akwai kishiya ta gari?, hmmm yarinya baki san wace kishiya ba, amma kishiya babu ta kirki, ba sai na faɗa miki ba tunda kin riga kin san tarihin gidanmu, kin san baƙar wuyar da na sha hannun kishiyar uwa...ke Allah ya tsinewa kishiya kowacce kala ce ma". Maijidda tace,"to Allah ya kyauta". Sabira ta miƙe tana faɗin,"bari naje, dan zuciyata azalzalata kawai take yi". Fillo tace,"je ki wallah ki ƙwatarwa Yayarki ƴanci, ki tsaya tsayin daka karki fito a gidan nan sai kin nunawa kowa Antynki na da gata, ke idan ta kama ma kiji wa Anty Jumman ciwo ki fito waje kina kururuwa, waye bai iya makirci ba ai sai in bai so ba, karki yarda ki taho sai an garƙame shegiya a cell, ke inta kama ma ki ɗau wuƙa ki saka a hannunta kafin akawo ɗauki, ana shigo kice gata can da wuƙa wai duk sai ta kasheku". da gaske Fillo ke ta maganarta, bayan tafiyar Sabira Maijidda tace mata,"yau ba zaki je aiki ba?". Fillo tace,"tun ranar dana fasawa Turaki turarensa nake shakkar komawa, so nake a bamu albashi tukunna sai na siyo masa tsiyarsa. shisa naiwa Maama ƙaryar banda lafiya". Maijidda tace,"to yau dai Dr Yusuf yace zai zo, ki tashi mu san abinda zamu yi masa". Fillo ta kalleta ta taɓe baki,"ni ba abinda zanyi tunda ba gayyatarsa nayi ba". sukai shiru for some seconds sannan Maijidda ta katse shirun da faɗin,"Fillo Amir fa?, ya kamata ko me yayi miki kiyi haƙuri ke kam, tsakanin harshe da haƙori ma an saɓa, kuma shi dama zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa ne. zatonki zaki samu masoyi kamar Amir?, karki zama butulu ki mance da irin halaccin da yay miki a rayuwa, ni dai dan Allah ko mene yayi miki kiyi haƙuri ki manta, tunda ni kinƙi ki faɗa min". Fillo tai guntun murmushi na takaici,"shi bai faɗa miki abinda yayi min ba?". Maijidda tace,"ni ba abinda yace min, kuma bana so na sani tunda har ke kika kasa faɗa min, abinda nake so kawai shine ku dawo daidai komai ya wuce..". Fillo tai saurin tarar numfashinta,"har gaban abadan, igiyar soyayyar da ke tsakanina da shi na datseta har mutuwa, kije ki faɗa masa hakan, in ma yana wani lissafin rayuwa tare da ni ne to ya daina deceiving kansa, domin ni Halima na barsa har gaban abadan, wallahi ko Amir ne kaɗai ya rage namiji a duniya ba zan auresa ba". sai kuma ta fashe da kuka,"idan har da gaske Amir sona yake tsakani da Allah ba zai taɓa goranta min ba, duk da banga laifinsa ba. laifin Hayyo ne da ya sheganta ni da bakinsa, in ace Hayyo bai kira ni ƴar Zina ba yau da Amir bai buɗi baki yace min ƴar gaba da fatiha ba...". furucinta na ƙarshe yasa Maijidda tayi zumbur ta miƙe,"kika ce me?, Amir ɗin ne ya faɗi haka?". cikin matsanancin kuka tace,"Allah shahida idan nayi masa ƙarya Allah kar ya ɗagani anan wurin, kije ki tambayesa. daga nace bana so naje gidansa babu kayan ɗaki gudun gori shi ne ya tashi ya juya min baya yana faɗa min wai kar na manta ni ƴar zina ce, saboda haka ko ba'a min gorin kayan ɗaki ba ana iya min gorin an haifeni without marriage. Maijidda wanda nake so da aure ya faɗa min haka tun ban auresa ba, just imagine anyi auren, waɗannan kalamai kike tunanin zai dinga gaya min?". Maijidda ta sauke numfashi da matuƙar mamakin ace Amir ne zai faɗi haka. ta rasa abin faɗa saboda tayi matuƙar girgiza, idonta kawai Amir ɗin yake hango mata, bata taɓa tsammanin zai iya faɗawa Fillo haka ba saboda bala'in son da yake yi mata. Fillo dai kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa, har sai da wayar hannun Maijidda tayi ƙara ta ɗaga suka gaisa da Dr Yusuf yace musu ga shi a waje, sannan Fillo ta goge hawayenta ta shi suka tafi bayan ta wanke fuskarta. *** A ɓangaren Bello, Turaki da Khalil. zaune suke a parlo bayan sun kammala breakfast, kowanne da takardu a gabansa da kuma biro, suna tattaunawa akan batun sabon company da Baffa yace za'a ƙara buɗewa. Khalil na kallon takardar dake gabansa yace,"anawa tunanin gaskiya gwara a buɗe na sarrafa kayan miya a maida su na gwangwani ko leda. tunda shine kamfanin mafi ƙaranci da muke da shi a nigeria, kuma ina ganin hakan za'a sami abinda ake so fiye da tsammani". Bello yace,"view ɗinka yayi kyau, sai dai yanzu mu fara kammalawa da wannan da Maama tace". Turaki ya kalli Bello tace,"me Maaman tace?". Bello ya duƙa yay rubutu jikin takardar gabansa tukunna yace,"Company ɗin dake Lagos da Baffa yace a siyar, tace ba za'a sayar da shi ba za'a maida shi na fulawa, Shine batun da nai muku jiya cewar zanje Hong Kong, saboda injinan da za'a siyo na yanda za'a sarrafa fulawan. but ina ganin tafiyan ba ni ɗaya zanje ba da kai zamu tafi Turaki, zanyi convincing Maama mu tafi tare. tunda tafiyan jirgi ne ba wai a mota ba, becouse kai ka fini sanin kaya masu kyau, idan ni ɗaya ne za'a iya haɗani da fake one". Turaki ya ɗan ciji leɓensa kaɗan sannan yace,"why not su turo da kayan kawai ba sai anje ba". Bello yace,"yanda ma fake one's ɗin zasu fi zuwa kenan. Maama already ta riga taga hotunan su, dan ko launching nasu ba'ayi ba, shisa tace naje ayi a gabana, so ta re da kai dai zamu tafi". Khalil yace,"shikenan Turaki Flour Mills ya tabbata kenan, dan nasan hakan za'a saka tunda Maama ce ta kawo idean". Bello da sigar tsokana yace,"ah haba dai sai kace shi ɗaya ne ɗa, ai sai dai a haɗa sunan mu duka". Turaki ya taɓe baki ya miƙe tsaye yana faɗin,"i don't think i will go with you, kayi tafiyanka kawai ko kuma kuje da Khalil. beside; Sameer ma na Hong Kong ɗin kana iya samunsa acan". Bello yace,"aiko dole sai kaje, ka zama cikin shiri kawai Malam, coux daga nan ma tictiket ɗinmu zanje amsa". ba tare da Turaki ya ƙara cewa komai ba ya fice daga parlon. direct part ɗin Boɗejo ya nufa, acan ya tarar da sisters nasa duka a zaune sun saka Boɗejo a tsakiya sai hira suke, sai bayan ya zauna kan kujera ya fahimci lissafi suke tayi, lissafin aurensa. Samha cikin zumuɗi da tsananin murna take faɗin,"ai Boɗejo babu zancen wani 1week, biki zamu fara from day 1 to day 10, kuma kowacce rana sai mun zubar da naira, sai doller tayi kuka ita kanta sai ta san ana bikin first born a gidannan". Nihal ta taso a kusa da Boɗejo ta dawo kusa da Turaki, ta kamo hannunsa tana cewa,"please Hammah ka sama mana Anty kaji, Allah mun ƙagu ayi bikinka, Allah duka burinmu na kan wannan ranar Hammah, I feel like your wedding day is the first wedding in the world". shima ya riƙe hannun nata yana kallon innocent face ɗinta yace,"to kun zaɓa min matar ne?". dai-dai nan Samha ta taso itama ta zauna gefensa,"ka yarda mu zaɓa maka Hammah?, akwai friends ena da friends Zaytuna da yawa da suke sonka, duk basa ƙasar nan, gasu kyawawa masu class, sai wacca muka ɗaukar maka". tana kallon Zaytuna tace,"ina wannan balarabiyar ƙawar tawa da mukai vedio call ranar nan?, kin tuna ta?, basu dace da Hammah ba don Allah?". bata jira cewan Zaytuna ba koma garesa tana ƙara cewa,"Hammah ka yarda muyi maka zaɓi?". ya kalleta sai kuma ya kalla Zaytuna wadda ke ta kallonsa da tarin murmushi. kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace,"kuyi adu'a Allah ya kawo ta gari, aure ai lokaci ne". Boɗejo tace,"a'a lokacinka fa yayi kai harma ya wuce tuni, dan dai kawai Uwarka da Ubanka sun zuba maka ido ne, sai abinda kake so za'ai, yo wannan gata ai ba gata bane. kai in baka san mutumcin mutum aure ba ai su sun sani, to ni dai ina gajiya sai na haɗaka da duk wadda naga dama, Allah na tuba ƴan mata gasu nan birjik a danki...kuma dai ma ni in faɗa maka yar gida muke so jinin sarauta ba bare ba, ah tou karma lokacin da hankalinka zai dawo jikinka kace zaka ɗauko wata can daban, ina ga Madina ce kawai ta shigo zuri'armu a bare". shi dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujerar. Nihal ta daɗa riƙe hannunsa sosai tana faɗin,"can't wai to see your wedding day Hammah, wayyo Allah wa ya ganni da Sister inlaw". ta faɗa cikin wani irin expression tana faɗawa jikinsa. ranar a part ɗin Boɗejo suka yi lunching, shi Turakin ma bai iya cin komai ba, yanayinsa kamar dai wanda bai cikin natsuwarsa. after la'asar ma da ya dawo daga masallaci part ɗin Boɗejo ya koma, lokacin da ya shiga bedroom nata tana waya da Inna Falmata. ganin shigowar tasa yasa tace,"to sai anjima Falmata, a dai ci gaba da aiki me kyau don Allah, kinga acikin sati huɗu yau munci kwana biyar, to shi haka lokaci yake sai dai idan ba'a saka shi ba, nan dai nan sai kiga yazo". daga haka ta kashe wayar ta ajiye a kusa da ita, ta kalli kan gadonta da Turaki ya kwanta, he don't know why yake jin jikinsa yayi sanyi, tunda Bello yace masa zasu yi tafiya tare yake jin wani feeling mara daɗi a tare da shi, and for the first time da yake jin kamar zai rasa rabin jikinsa, Boɗejo ta kai hannu ta taɓa ƙafarsa taji zafi like zazzaɓi ne ke shirin kamasa. tai salati tana faɗin,"baka da lafiya ne Turaki?". ba tare da ya buɗe idanuwansa ba yace,"lafiyata lau, kawai ina jin ba daɗin yanayina ne". Boɗejo tayi saurin tashi tsaye,"a'a baka jin daɗi ai yana nufin baka da lafiya, tun ɗazu dama na lura da yanayinka, to da yake kai ɗin me ƙauran baki ne ba zaka fito kace baka da lafiya ba sai dai ciwo yay ta cinka". dai-dai nan Ɗausiyya ta shigo ɗakin riƙe da ƙwaryar fura a hannunta. ta shigo da sallama ta nemi wuri ta ajiye, zata juya Boɗejo tace,"kinga garzaya da gudu ki kira min Zaytuna a, kice tazo da sauri Turaki babu lafiya. bance ki bari Uwassa taji ba balle tazo ta ɗaga min hankali da bala'ƴaƴƴan kukanta anan". in few minutes Zaytuna ta shigo ɗakin hankalinta a tashe, kai tsaye inda yake kwance ta wuce. kamar zata yi kuka ta taɓa jikinsa da yay zafi rau. "Hammah wake up mu tafi asibiti". ya buɗe idonsa da sukai jajir ya kalleta. ahankali yace,"ɗauko drugs ena". yana faɗa ta miƙe cikin sauri ta fita, bata jima ba ta dawo ɗakin jikinta sai rawa yake yi, tuni kuma hawayen dake cikin idonta ya sami nasarar gangarowa, bata ƙaunar wannan ciwon nasa na kidney ya tashi, idan ya tashi sai sun gama fidda rai da shi tukunna lafiya take samuwa. Boɗejo ta fito daga toilet a lokacin, tana kallon Zaytuna tace,"ciwon ne ko? ai tun jiya nake lure da shi tunda naga ƙwayar idonsa da kuma yacca ya ɗan kumbura ɗin nan, to kin sansa da ƙarfin halin jaraba, bai san cutar kansa yake ba". Zaytuna na hawaye tace,"inje in kira Maama?". da sauri Boɗejo ta girgiza kai,"a'a sam bakinki alaikum, da yardar ubangiji yana shan magani zai sami lafiya. ko kin manta itama bata da lafiya ne?, jiya likita da ya aunata yace jininta yayi mugun hawa sama, so kike tazo ta mace mana lokacinta bai yi ba, a'a bari tukunna dai a ɗaura aurensa ta gani tana raye". ta zauna kan kujera tana faɗar,"dan Allah kinga kwaɗa kira ɓangaren masu aikin nan wannan yarinyar Fulani tazo ta matsa min ƙafata, naga ta iya matsa ƙafa, kwanaki da tayi min kyace tausar inji irin wacca Hashim ke biyan uban kuɗaɗe ai min, ni tunda nazo ma ban ganta ba sai wannan baƙar nake ta gani tana suntiri, yanzu ma ita ta kawo min fura kuma ba zan iya sha ba gaskiya, da ganinta ba bafulatana bace irinmu. ni Allah yasa ma ba korar Fulani ɗin kuka yi ba, ni ƴa su aka koreta kuwa ba'a kyauta ba, yarinyar ga natsuwa ga hankali ga kyau da tarbiya, in kuwa an koreta to zama a dawo da ita gaskiya, dan ina son tausarta tayi masifar iyawa". Zaytuna tace,"tana nan ba'a koreta ba. bata jin daɗi ne". Boɗejo tace,"Allah sarki ashe shisa, ni wannan ƴa ma da ƙyar in ba sikila bace, Allah dai ya bata lafiya, anjima sai ki rakani wajensu na dubota, wannan yarinya ai tayi, idan nazo biki ga ladabin da take min ba wallahi, ba irin sauran ƴan aikin ba da sunzo sun waye sai su koma maka kallon ɗan banza, yanzu dai ban ruwa a kofi inyi masa tofi sai ki basa maganin ya sha, wannan ciwon nasa ba ƙaunarsa nake ba". Zaytuna ta ƙurawa Turaki ido sosai, wannan gajeran numfashin ke ɗaga hankalinta, fatanta ɗaya kar akai stage ɗin da kowa zaiji jiki ata dalilin ciwon. ta sauke numfashi sannan ta miƙe ta fita ta ɗauko faro ta dawo, a cup ta zuba ta miƙawa Boɗejo. zata ƙara fita Boɗejo tace,"tsaya ki basa ya sha, kin san ba sanin kan magungunan nayi ba". tace,"ya sami bacci ne, zanje na dawo". Boɗejo tace,"to alhamdulillah indai yay bacci ciwon ma ai da sauƙi". kusan awa ɗaya da rabi Boɗejo na tare da Turaki, yana ta bacci har zuwa lokacin, ita kuma tana gefensa cike da tausayinsa sosai. tana tayi masa adu'a iri iri, lokacin har ƙarfe shida da rabi na yamma tayi. lokacin Fillo ta tura ƙofar ɗakin ta shiga da sallama, Boɗejo ta amsa tana yi mata maraba. ta shigo ta tsuguna tana gaidata, idon Boɗejo akanta tace,"sannu, aiko ga shi nan duk kin ƙara zaftarewa, kina cin abinci kuwa ƴar nan?". kan Fillo a ƙasa tace,"ina ci". "to magani fa?". tace,"shima ina sha Boɗejo". "to Allah ya baki lafiya, kunje asibiti an yi miki tasa-tsai kuwa?". Fillo ta girgiza kanta alamar a'a. Boɗejo tace,"wannan ai sakaci ne, bara Allah ya kaimu gobe Khalil ya kaiki asibiti su gwadaki, amma wannan jiki naki ke kam ai yana buƙatar binciken likita". tace,"to Boɗejo na gode...dama Adda Zaytuna tace kina nemana". "ehh kinga da tausa zaki yi min irin wacca kika min ranar nan, to kuma sai take ce min baki da lafiya". Fillo tace,"ai naji sauƙi, zan iya yi miki". sosai Boɗejo ta tsaya tana kallonta da matuƙar tausayinta, tukunna tace,"a'a bari kya yi min gobe. yanzu dai ɗauko mopper ki goge ruwan nan kafin wannan marar lafiyar ya farka yaƙi sakkowa akan gadon". jin ance mara Lafiya Fillo ta ɗago kai ta kalli kan gadon, gabanta sai da yayi mugun faɗuwa ganin yacca fuskar Turaki ta kumbura kamar wanda yayi mummunan accident. Boɗejo ta ɗau mayafi tana faɗin,"bara naje in dawo, wurin Dikko zanje. in kin goge ki ɗan jira ina dawowa kar a barsa shi ɗaya, in kuma Zaytuna ta dawo shikenan. ni baccin nasa ma ya fara bani tsoro, Allah yasa dai lafiyar ce". tana Fita Fillo ta goge tiles ɗin, ta nemi wuri ta zauna tana ta kallonsa, numfashinsa da ƙyar yake fita, tausayinsa take ji har cikin ranta tana yi masa aduar samun lafiya. Turaki ya buɗe idonsa a hankali yana kallon ɗakin, Fillo ta taso da sauri tazo ta durƙusa a gaban gadon ta saitin da yake. "barka da tashi, Boɗejon ta fita amma tace yanzu zata dawo". ta faɗa tana kallon ƙasa, ta wutsiyar ido ta kalli yanda ya cije fuska ya miƙe zaune da ƙyar, Turaki ya dinga kallonta babu ƙiftawa, tun ranar da ta fasa masa turare rabon da ya ƙara ganinta, yau ɗin kuma kamar ta rame sosai. ta gefenta ya sakko daga kan gadon ya wuce toilet without saying anything to her, kanta na ƙasa har sanda ya fito a toilet yana goge ruwan fuskarsa da towel ɗin hannunsa. ya dawo ya zauna gefen gadon tare da kwantar da kansa a jikin gadon, Fillo dai har sannan tana tsugune a wurin sai jan yatsunta take yi. after some minutes ta miƙe tana ce masa,"zan kirawo Maama". ta faɗa tana juyawa zata fita. sai taji ya riƙo hannunta dake aikin karkarwa, duk sai ta dabarbarce ta juyo a tsorace, idonta na ƙasa ta kasa kallonsa, dan lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa. ya janyota ta zauna gefen gadon, tare da kamo ɗaya hannun nata ya riƙe sosai. can ƙasan maƙoshi taji yace,"kina so kiyi kwanan ɗakin daga ni sai ke?". da sauri ta girgiza masa kai tana son ƙwace hannunta daga nasa. bayan ya sauke nunfashi yace,"to saita natsuwarki, bana son wannan tsoron". ba ta ko sake yunƙurin motsi ba, haka shima yana riƙe da hannayenta har sai da yaji jikinta ya daina rawar sannan ya tallabi haɓarta ya ɗago da fuskarta yana kallonta. "me ya ramar da ke acikin 5days?". ta girgiza masa kai kawai bata yi magana ba. ya sake cewa,"in tambaye ki za ki faɗa min gaskiya?". tayi shiru bata ce komai ba, sai da ya ɗan ɗaga muryarsa sama tukunna ta ɗaga masa kai da sauri. yace,"faɗa min dalilin da yasa kika fasa min turare?". tuni ruwa ya kawo idonta tace,"ban sani ba ne, amma zan biyaka in ƙarshen wata yayi". yace,"gaskiya nace ki faɗa min ba ƙarya ba". tai saurin ɗago ido ta kallesa kaɗan, sai taga ya rufe nasa idon ya kauda gefe ɗaya yana girgiza mata kai. "ina fa kallonki sanda kika fasa, intentionally kika jefar da shi a ƙasa har kina toshe hanci, warin me kika ji yana yi?". kawai sai ta fashe da kuka tana cewa,"kayi haƙuri dan Allah zan biyaka nace". yace,"na haƙura kuma na yafe ba sai kin biyani ba, amma idan kin faɗa min reason ɗin da yasa kike toshe hanci akansa". bata san lokacin da ta saka ƙwayar idonta a nasa ba tace,"nawa ne turaren?". yace,"50k". jin ya faɗi kuɗin albashinsu gaba ɗaya tace,"warinsa ne bana so shisa". Turaki ya sauke dogon numfashi tare da sakin hannunta. kansa jingine da jikin gado ya kulle idonsa. Fillo dai nata kallon fuskar tasa, taji yace da ita,"bani ruwa zan sha magani". ta miƙe kamar wadda bata da ƙwarin jiki, ta isa ga inda taga ruwan ta ɗauko na cup ɗin dana jarkar, ta dawo ta ajiye a kan bedside. a hankali tace,"ga ruwan". ya buɗe idonsa tare da miƙewa zaune sosai. ya buɗe ledan magungunan da Zaytuna ta ajiye duka ya ciri iyakar wanda zai sha, Fillo nata kallon kwalayen maganin jikinta yay sanyi saboda hoton kidney da ta gani ajiki. ta ɗan kallesa kaɗan tace,"Adda Zaytuna tace baka ci abinci ba". shima ya kalleta kaɗan sannan yace,"nayi loosing appetite". tana jan yatsanta ɗaya tace,"ka daure kayi ko spoon biyu ne tukunna kasha maganin". idonsa a tsakiyar kanta yace,"akwai abincin anan ko sai kin ɗauko?". tace,"ga shi nan a flask". yace,"kaɗan za ki zuba". ta miƙe ta ɗauko flask ɗin da ta shigo da shi wanda Zaytuna ta bata. tana buɗe flask ɗin tace,"Adda Zaytuna ce ta dafa". hakan da ta faɗa sai yasa shi ɗan murmusa kuncinsa, tunaninta zai yi zaton ita ta girka yaƙi ci, bata san ma ko da ita ɗin ta dafa ba zaici. yana kallo ta zuba kaɗan ta miƙo masa. ya karɓa yayi spoon 3 ya ajiye. tace,"ka ƙara please, babu komai acikinka maganin ba zai maka aiki ba". idonta na kallon gefe tayi maganar, Turaki ya tsaya yana ta kallonta, kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa. ya ƙara spoon 5 akan wanda yaci tukunna ya ajiye, ta miƙo masa maganin ya sha sannan ta karɓi cup ɗin hannunsa ta ajiye. daga inda take a tsaye tace,"zanje in faɗawa Boɗejo ka tashi". ta faɗa tana shirin barin wajen, sai ta ƙara jin the same abin da yay ɗazu na kamo hannunta ya zaunar da ita gefensa. haka kawai Turaki ke ƙara jin jkinsa yayi sanyi sosai, still holding Fillo's hand har kusan 3minutes tukunna yay ajiyar zuciya ya saki hannun nata. ita dai ganin baya kallonta yasa ta sami damar kallonsa, da taga ya ɗan motsa kai sai tayi saurin ɗauke idonta. tana kallo within minutes ɗin da yasha magani kumburin jikinsa ya fara sacewa. Turaki ya duba agogon hannunsa, ya ɗauki wayarsa ya riƙe, wata ajiyar zuciyar ya sauke muryarsa a hankali yace,"you take care of yourself, zanyi tafiya but ba zan jima ba zan dawo, ba zan wuce 4days ba. if you need something meet Zaytuna, be carefull with anything that will put you in to trouble please". ita dai Fillo kanta na ƙasa idonta na kallon yatsunta, tana jin duk abinda yake cewa, tana jin maganar kamar da ita yake yi, sai dai tasan ba da itan yake ba, wataƙila kamar wancan ranar ne da yace thank you for saving my life tayi zaton da ita yake ashe waya yake yi. bata san dalili ba amma sai taji jikinta yayi matuƙar yin sanyi da jin zancen nasa, ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, sai taji ƙirjinta ya buga saboda yanayin yacca taga ƙwayar idonsa ta sauya. sai ta sami kanta da kasa ɗauke idonta daga ganinsa, tana kallo ya saki murmushin da ya tsaya a lips ɗinsa, kamar ita shima haka yake jan yatsun hannunsa. da taga ya ƙura mata ido sosai sai ta sauke kanta ƙasa ruwan hawaye na cika idonta without knowing the reason why. taji yace,"jibi zamu tafi, Hong kong zanje. ba za ki yi min adu'a ba?". duk da haka kanta na ƙasa tace,"da ni kake?". yace,"ni da waye a ɗakin?". tace,"to ai kaine mutum ba ya gane da shi kake magana". yace,"to da ke nake, adu'a nake so kiyi min naje lafiya na dawo lafiya sannan na dawo na tarar da ku lafiya". haka ɗaya sai taji wani iri da furucin nasa, yana maganar kamar wanda ke magana da matarsa, in same ku lafiya!, har da ita kenan?, to wace ita a cikin rayuwarsa?. sai yanzu taji wani bala'in tsoro ya kamata akan tafiyar tasa, voice ɗinta na fallasa kukan da take sonyi tace,"kai da wa zaku tafi?". Yace,"ni da Bello". tayi shiru kamar me dogon nazari kafin tace,"wannan abokinka ɗin me abin dariya?". ya ware idonsa tarr akanta yana mamakin maganartata yace,"ehh shi". tace,"daga kai sai shi zaku tafi?, zai iya kula da kai sosai?, ina nufin kamar yanda ba zai bari wani abu ya taɓaka ba?". tana tambayar taji tafin hannunsa akan haɓarta ya ɗago kanta, ya ɗago da fuskarta lokacin da hawayen cikin idonta ya sami nasarar gangarowa. ba tare da sani ba Turaki ya janyota jikinsa yana ƙarewa fuskarta kallo wacce hawaye ke ta sunturi akan kumatunta idanuwanta a kulle. ƙwacewa take sonyi amma ta kasa saboda wani irin kasala da taji yana neman rufeta dalilin jin kanta a kafaɗarsa tana shaƙar wani ƙamshi me bala'in daɗi. yay taking deep breath yana jin kamar yayi hugging ɗinta, he feels like he doesn't want to move away from her, yana jin kamar ya fasa tafiyar just becouse of her, sai dai he has to go, ko dan gudun kar a haɗa Bello da fake kaya. ƙirjin Fillo na bugawa tace,"zanje in kira Maama". A hankali yace,"to kukan me kike yi?, ko na fasa tafiyar?, ko na kira Bellon ki faɗa masa ya kula da ni?, kuma nima ai zan iya kula da kaina". gaba ɗaya sai take jin yacca yake mata magana kamar cikin mafarki ko kuma dai ba da ita bane wata ce daban irinta yakewa magana. bata san ta yanda bakinta ya buɗe ba ma har take iya magana haka duk da uban tsoronsa dake tare da ita, dan wani irin faɗuwan gaba da take ji. ta ɗan kallesa kaɗan ganin yana kallonta tayi saurin ɗauke idonta, taja yatsanta ɗaya tace,"ba zaka iya kula da kanka ba ai, amma shi naga yana sonka, kuma yana da mutunci, Maama zata basa amanarka...Allah ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allah yayi maka katanga kan katanga daga dukkan sharrin me sharri, Allah ya ɗoraka akan maƙiyanka, Allah ya tsareka da tsarewarsa ya kiyayeka da kiyayewarsa, ka kula sosai da kanka Maama zata ji daɗin hakan, kar ka yi wasa da shan magani". tunda ta fara maganar yake kallonta babu ko ƙifce, da wani kalar tunani da yake akanta. kamar ya buɗe komai a yanzu, but zuciyarsa na faɗa masa not now, this is not the right time da ya kamata ya buɗe komai. yana ji ta zame jikinta a hankali tana miƙewa tsaye, so take yi ta bar ɗakin amma kamar an riƙe mata ƙafa, kuma kamar tana jiran umarninsa ne. tayi dai tsaye ta kasa motsawa balle ta tafi. tsaye shima ya miƙe yana kulle idanuwansa, jikinsa duk babu ƙwari haka yake jinsa, bai taɓa jin zai yi tafiya yana fargabar tafiyar ba ko kuma yana tsoro, amma this time around da zai tafi yayi just 4days ji yake kamar wani mugun abu zai faru kafin dawowarsa, ko kuma wani mugun abu zai faru da shi. bayan ya zuba hannayensa cikin aljihu taji yace,"bana son yawan kuka. when am back you will help me find Mum". kallon da take yi masa bana mamaki bane tunda a yanzu ta riga tasan komai, kallo kawai take yi masa me cike da tausayawa, bata ankara ba sai ganinsa tayi tsaye a gabanta dab da ita, tayi wani ƴar guntuwa a gabansa dan da kaɗan ta wuce cikinsa, magana take so tayi masa amma bata san ta ina zata fara ba, hannunta nata karkarwa taji ya sunkuyo da kansa ya ɗora goshinsa akanta yana kama hannayen nata ya riƙe. muryarsa can ƙasa taji yace,"yauahe hannayenn zasu daina kakkarwa?". sai taji kamar numfashinta zai yi seezing, jin an turo ƙofar ɗakin ta firgita taja da baya, ganin Zaytuna duk sai ta rikice, so take ta fice daga ɗakin da gudu before Zaytuna ta ɗago daga sunkuyawar da tayi tana ajiye abu, amma ya riƙe hannunta ta yanda duk abinta ba zata iya ƙwacewa ba, Zaytuna ta ajiye aiken Boɗejo da ta shigo da shi ta fita. tana fita Fillo ta fashe da kuka tana ture hannunsa daga riƙon da yay mata. ƙarar shigowar text a wayarsa yasa ya saketa ya nufi wayar, ita kuma ta buɗe ƙofan ta falle da gudu. Turaki ya buɗe messge ɗin Zaytuna da ya shigo yana karantawa. _Boɗejo and Maama are coming._ yana gama karantawa ya juyo da kallonsa inda ya bar Fillo, sai gani yay babu ko ɓurɓushinta, yasa hannu ya shafo wuyansa yana smiling. *please vote, share and comment.* [8/27, 20:40] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *26* Ilham ta shigo parlon Yarima Abbas bakinta ɗauke da sallama da wani irin emotions a tare da ita. tun shigowarta kanta ke sunkuye a ƙasa kamar ta shiga fadar Me Martaba. ta ƙarasa gaban table ɗin dake tsakiyar su Yarima Abbas ta ajiye ƙaramin tray dake hannunta, bayan ta ajiye ta ɗago ido ta kalli ɓangaren da tasan anan ne zata yi tozali da Turaki, tunda from there hancinta ke jiyo mata ƙamshinsa, wannan ƙamshin turaren da ita ta basa kyautarsa har ya zama choice ɗinsa. idonsa da nata suka haɗu wuri ɗaya, kuma ba tare da ƙwayar idonsu ta fita ata junansu ba suka saki wani sanyayyan murmushi wa juna. wanda hakan ya wanzar da jin kunya a tare da ita, Turaki kuma da har sannan murmushin bai ɗauke masa ba yace,"zo nan". Yarima Abbas dake cike da jin girma na izza yace,"kafi kowa sanin bana son yara suke zuwar min sashina ko, amma duk sanda kazo sai ka dinƙa wani kiransu suna shigo min da dattin ƙafafu". ba tare da Turaki ya dube shi ba yace,"da wa kake?". rai ɓace Yarima Abbas yace,"yaushe wannan rainin hankalin zai bar jininka Turaki?". Turaki ya ɗauke idonsa akansa yay masa banza bai tanka masa ba. Ilham ta zauna akan hannun kujerar da Turaki yake, ya kamo hannunta ya riƙe yana cewa,"wai ni wannan Kunyar tawa da kike yi tun sanda kika dawo ta mene?". kanta na ƙasa tace,"kunya kuma Hammah?". yace,"ehh mana, kuma ni ban haihu ba, balle nace ɗana kike kamu". ta ke fuskanta yay turning zuwa na shagwaɓaɓɓu tana ɗan dukan ƙafa a ƙasa tace,"yanzu Hammah ka rasa da wa zaka haɗani sai ɗanka". murmushi kawai yayi yana shafa beard ɗinsa. idonsa akan tray ɗin da ta aje yace,"mene wannan?". tace,"your favorite, since morning na dafa idan zan tafi na kai maka...". sai ya katseta da cewan,"have you forgotten?". sai ta ɗan ɓata fuska tace,"ban manta ba, but ai naga ada ne". ya gyara zamansa yana faɗin,"ba da bane har yanzu Ilham. girkin Maama da Zaytun kawai". wani irin rashin jin daɗin ya ziyarci Ilham, fuskarta ta nuna hakan, Turaki ya kalleta yace,"fushi?". ta girgiza kanta da sauri,"a'a". yace,"to saki fuskan". ba tare da tayi hakan ba tace,"to har girkin matarka ma ba zaka ke ci ba Hammah?". yace,"dalilin da yasa zanyi aure na zauna a kusa da Maama kenan". tace,"amma Hammah akwai...". ya tari numfashinta da faɗin,"akwai mutuwa ko?, na san da hakan. ki tayani adu'ar na riga Maama mutuwa ba naga tata ba". Ilham tace,"to Allah ya ƙara mata lafiya ya kuma bata tsawancin kwana me albarka". ya amsa da,"amin lelen Boɗejo". ya sauke numfashi sannan yace,"ina gyalenki?". tace,"na barosa kan bed ɗin Mami saboda kace na hanzarta". hannunsa akan fuskarta yace,"je ki ɗauko ki dawo, ki faɗawa Mami zaki min rakiya". fuskarta ta washe da murmushi tana tambayarsa,"ina zamu je?". ya shafo wuyansa sannan ya bata amsa,"perfume zamu sayo". idonta ya ƙanƙance a sa'ilin da take kallonsa. "ƙarewa yayi?, in ɗauko maka nawa?". yace,"a'a wani zan sauya". idonta na ƙara ƙanƙancewa tace,"canjawa kuma?, perfume naka ɗin? your best choice ɗin?". ya ɗaga gira ɗaya,"yes, bana son ƙamshinsa yanzu". tayi knodding kanta sannan ta miƙe ta fita. Yarima Abbas ya rakata da harara, yayinda Turaki ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta har sanda ta fice, bai san dalilin da yasa yake tausayin yarinyar ba, ko dan ta kasance ita ɗaya a wurin mahaifiyarta ne?, ba hakan bane, hakan kuma ba zai zama dalili ba. yana son Ilham kamar yanda yake son Nihal, Samha da kuma Zaytun. yana ƙara sonta da burin faranta mata saboda yanda itama take sonsa tun yarintarta, ta ke masa kallon jininta fiye da yanda take kallon su Yarima Abbas. ya sauke numfashi yana jinginar da kansa jikin kujera tare da rufe idanuwansa, baya manta alkhairi a rayuwarsa ko da ace daga baya zaka saka masa da sharri, wannan alkhairin naka garesa zai mantar da shi girman sharrin da kayi masa. sai dai har yanzu ya kasa mantawa da sharrin da Mami tayi masa, tsawon shekaru da yawa har yau neman dalili yake na ƙala masa sharrin sata da Fulani Azima tayi. idan ya tuna cewa bayan da mahaifiyarsu ta tafi ta barsu, a cire Hajiya Madina a gefe, babu wata mace da ta nuna musu ƙauna tsurarta gami da tausayi tare da kyautatawa irin Fulani Azima. ta so shi shi da Zaytun kamar zata haɗiye su, tayi sa'insa da Mai Martaba duk akansu. ya faɗa rijiya Fulani ta bisa cikin rijiyar an ɗauko su tare, a matsayinta na matar Mai Martaba ta zubar da gwiwoyinta gaban mahaifinsa tana roƙonsa akan ya bata Turaki zata kula da shi fiye da yanda zata kula da ɗan cikinta har zuwa ranar da Ramla zata dawo. to amma sai dai me?, a lokacin da ya shaƙu da ita, ya saba da ita, ya shaƙu da ƴarta, yake ganin ta zamar masa uwa, sai Fulani ta rikiɗe ta koma kalar wata mace ta daban, mace me cike da tuggu da makirci, ta shiga muzguna masa tana goranta masa akan zaman da yake yi acikin masarautar alhalin ita ta rabosa da Hajiya Madina, ba wani ya ɗaukosa ya kawosa ba. ta ƙala masa sharrin satar gwal a lokacin da baiji ba bai gani ba, ta ƙara da faɗin ya satar mata kuɗaɗe, kuma ba tare da wani tunani ko bincike ba Mai Martaba ya yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata, hukuncin da Hajiya Madina tayi tsalle ta dire agaban Mai Martaba tace muddin aka ga an saka ɗanta a prison to wallahi sai dai idan bata numfashi. ta kuma fuskanci Baffa gaba da gaba tace ya sani, idan har matsayinsa na alƙali bai shigar da ƙarar Fulani akan ƙazafin da ta yiwa ɗanta ba, to la shakka babu kaffara sai ya rabu da ita, kuma ya rubuta ya ajiye, rabuwarsu ba yana nufin zata tafi ta bar masa Turaki da Zaytuna bane, a'a zata tafi da gaba ɗayansu ne ta kowanne hali, ko da zai dinƙa yankar naman jikinta yana goranta mata ba ita ta haife su ba. asalin samo gaba me ƙarfin gaske kenan da ta shiga tsakanin Hajiya Madina da Fulani, har tsawon shekaru masu yawa, har sai lokacin da Turaki ya kammala degree ɗinsa na biyu sannan gabar tasu ta ƙare, bayan Hajiya Madina ta tambayi Turaki ya faɗi kyautar da yake so tayi masa yace mata yana so ta daina gaba da Fulani, domin gaba abar ƙyama ce tunda Allah baya so, kuma ma'aikin Allah yace kar mutum ya rama sharri da sharri dan haka ta bar batun ɗaukar fansa da tace zata yi akan abinda Fulani tayi masa, ta yafe mata kamar yanda shima ya yafe mata. a duk sanda ya nemi abu a wurin Hajiya Madina take a wurin take yi masa ba tare da ɓata lokaci ba muddin bai fi ƙarfinta ba, amma a wannan roƙon da yay mata sai da ta ɗauki tsawon kwana biyu shi kansa bata shiga sabgarsa ba, wai sunan shawara take tayi da zuciyarta taga idan zata iya yafewa wanda ya ƙalawa ɗanta sharrin sata. daga baya kuma sai komai ya warware tunda suka ƙara tausarta shi da Khalil da Bello, daga nan kuma Hajiya Madina ta sauko ta ci gaba da bawa Fulani girmanta na matsayin da take da shi. yana zaune cikin tunanin abubuwan da suka faru a baya Ilham ta dawo, sai da ta taɓasa tukunna ya buɗe idonsa ya sauke akanta. tayi kyau acikin shigar da ta sauya na sky blue ɗin code less me shegen tsada, ya miƙe yana ɗaukar key ɗinsa ya kalli Abbas yace,"babban Yarima zan wuce". ba tare da Yarima Abbas ya ɗago daga operating laptop nasa ba yace,"ka gaida Maama da Zaytun". fitowarsu daga sashin Yarima Abbas suka ci karo da Fulani Azima ta fito daga turakarta kuyangu uku na biye da ita. haka kawai Turaki yaji gabansa ya faɗi da ganinta, lokaci ɗaya kuma ƙwaƙwalwarsa ta shiga karanto wasu ayoyi na kariya dake cikin alƙur'ani, ba wai yana nufinta da mugun abu bane, a'a haka kawai tun a ranar da taje asibiti dubasa yaji zuciyarsa ta kasa kwanciya da ita, kuma yana ta ƙoƙarin yakice abinda zuciyarsa ke raya masa akanta amma hakan yaci tura, in yayi ƙoƙarin watsarwa sai maganar Fillo ta dinƙa dawowa cikin kansa na batun asirin da tace ta ɗauke akansa. *ASIRI!* har yau kalmar nan tsaye take a cikin ransa. kenan inda Allah bai shigo da Fillo cikin rayuwarsa ba shikenan duk kalar asirin da yaji ta ɗauke akansa sai ya kama shi?. ya rufe ido ya buɗe yana kawar da wani tunani dake shiga sashen tunaninsa. Fulani Azima ta tsaya da tafiya tana kallon Turaki da Ilham dake tafiya, wai Turaki ne tare da ƴarta?. lokaci ɗaya zuciyarta tayi wani mugun matsewa. taji kanta ya sara mata, lallai bata ga ta zama ba, sai ta sake sabon shiri, dole ne ma ta koma wurin boka, zata faɗa masa ya sauya tsarin aikinsa, sannan kuma yayi mata duba akan duk shegen dake lalata mata aiki. a harzuƙe ta juya ta koma ta fasa zuwa inda ta nufa. cikin motar Turaki dake tafiya akan titin zuwa PERKY FRAGRANCE STORE, wayarsa dake hannun Ilham tayi ringing a karo na huɗu, kuma a karo na huɗun ta ƙara ce masa,"Hamma ya kamata kayi picking call ɗin nan". shima a karo na huɗun ya ƙara bata amsa da cewar,"picking ɗin ba ya da wani amfani". a karo na biyar da kiran ya ƙara shigowa Ilham ta tsaya tana kallon lambar da babu suna ajiki. kasancewar kiran ba huruminta bane dalilin da yasa tun farko bata bi ta kan lambar ba, sai a yanzu da idanuwanta ke kallon lambar cikin kanta kuma na karanto mata lamabar ƙawarta Gimbiya Aisha. har sanda kiran ya katse Ilham bata bar kallon lambar ba, haka ɗaya sai taji kamar an soketa da kibiya a ƙirjinta. kenan dama da gaske Aisha take yi mata. conversation ɗin su na last haɗuwarsu ya shiga yawo acikin kanta. ranar buɗe company ɗin su Turaki, ranar da Turaki yay kwalliyar da babu macen da zata kalle shi bata kwaɗaitu da ya zama mallakinta ba. kuma a sannan Aisha ke bata labarin ta taɓa ganinsa a asibiti sanda taje duba wata cousin sister ɗinta, taso tayi masa wulaƙanci irin wanda kare ba zai shinshina ba amma sai ya juya ya tafi ya barta da zummar zaije ya dawo ya bata haƙuri, ashe juyawa yayi ya tafi da zuciyarta. ya tafi da dukkan nutsuwarta da tunaninta, don haka a ranar buɗe company da ta ƙara ganinsa ba zata yi saken da zai suɓuce mata ba. a lokacin Ilham faɗa mata tayi kai tsaye cewar indai Hammah Turaki ne ba zai sota ba, hasalima ko kulata ba zai yi ba talkless of batun soyayya har ta kaisu ga aure. ta faɗa mata bai taɓa soyayya da wata mace ba. sai dai buɗar bakin Gimbiya Aisha ce mata tayi,"Ilham, ni kuma ki rubuta ki ajiye, zan sauke duk wani jin kai dake kansa, zai soni, zai nemi aurena, zai aure ni a sanda ya gama haukacewa akaina". Ilham tace mata,"asirce min ɗan'uwa zaki yi?". Gimbiya Aisha na murmushi tace,"bana fatan watarana tazo da zan aikata saɓon ubangiji Ilham, amma ki sani, zan haukata ɗan'uwanki ne kawai da salon soyayyata me zafi, irin wacca zai hanaku sakat har sai kunzo kun ɗaukar masa ni kun kai masa gidansa. da gaske nake miki Ilham ina son Brothernki sosai wallahi, kuma ina adu'ar Allah yasa ya zama mallakina, nasan kuma zan samu tunda dai har sarauta ce ta haɗu da sarauta". Ilham ta rumtse idonta sosai tana jin wani iri a ƙasan zuciyarta wanda ta rasa dalilin hakan. ta wutsiyar ido take kallon Turaki dake driving cikin ƙwarewa, yana bin karatun ƙur'anin da ya kunna. ta mayar da murfin idonta ta rufe tana jin a ranta kamar zata yi kuka. Turaki ya kai sanyayyan hannunsa ya taɓa goshinta, lokacin ta buɗe ido tana miƙewa zaune. yace da ita,"did anything happend?". ta girgiza masa kai,"ba komi Hammah". "kuma kika yi silent bayan na san wannan bakin baya rabo da labari". tai murmushi tukunna tace,"to ai naga kana bin karatu ne". Turaki ya kai hannu ya kashe karatun sannan yace,"ina jinki, bani labari". "wanne iri to?". yace,"irin fitinar da kika dinƙa yi da kina yarinya bayan na koma Europe wurin Granny". tasa hannu ta rufe fuska tana cewa,"to ai kasan wannan time en, kaga babu batun a baka labari". ya ɗan waigo ya kalleta yana cewa,"give me my phone". ta miƙa masa yay dialling numba ɗin Zaytuna ya kira. sai da kiran ya kusa katsewa sannan tai picking, bayan picking ɗin shiru yay baice da ita komai ba. sai itace tayi murmushi daga inda take tana duban Fillo dake bacci hankali kwance akan gado tace,"bata tashi ba". Turaki yace,"up to now?, lafiya kuwa?". Zaytuna tace,"lafiya lau, rashin bacci ne da bata yi ba jiya". "why is that?". tace,"naje wurin Kaka nace mata ko da zata ji shiru Fillo bata dawo ba zata kwana a wurina, saboda naga kaman bata jin daɗi tun ɗazu tana ta bacci...so Kakan sai take ce min ai jiya ma kwana tayi bata rumtsa ba tana ta kuka, kuma tayi tambayar meke damunta bata sanar mata ba, ta dai bar hakan a rigimarta kawai...dana dawo kuma naji jikinta da zafi, kukan da tayi ma zai iya sa mata zazzaɓi". Turaki took a deep breath with out saying anything, hakan yasa Zaytuna kwantar da murya tace,"i will prescribe some drugs sai ka taho da su saboda ciwon yatsanta. like da fever ma a jikinta". yace,"oak send it to me right now via message". sai kuma yace,"Bello fa?". Zaytuna tai dariyar da ya bayyana haƙoranta tace,"he left since, da ƙyar na taushe shi wai sai yaje wurin Maama anyi wacca za'ai". tsakin Turaki ya fita da ƙarfi yana cewa,"mahaukaci ne ai...don't pick up his calls again". Zaytuna na murmushi tace,"na hannun daman naka Hammah?". yace,"ehh shi". ya faɗa yana katse wayan. ya kashe kiran yana parking a ƙofar store ɗin da suka zo. suka fito a tare da Ilham wacce ya zagaya yana tambayarta dalilin sauyawan mood ɗinta alhalin ba a haka suka fito ba. **** a hankali Fillo ta buɗe idonta daga ɓaccin da ta tashi, ta sauke ƙwayar idonta akan gadon da ta san ba katifarsu bace ita da Kaka. tayi wani mugun zabura ta tashi zaune tai saurin durowa daga kan gadon, cikin ranta tana faɗar kalmar innalillahi. ta rasa ma da wanne irin tunani zata yi amfani wajen tuna komai. bakin ƙofar da ta san ta riƙe handle tana kuka kawai take bi da kallo, da yaushe tayi baccin?, kuma ya akayi tazo kan wannan gadon?. kawai sai ta duƙe a wurin ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, lokacin kuma taji kiran sallah ya shiga cikin kunnenta wanda ko ba'a faɗa ba tabbata na magriba ne. ta miƙe da sauri ta wuce ƙofa zata buɗe taji ƙofar a rufe, ta dawo a hargitse ta shiga duba keys acikin drowers bata gani ba, taji zuciyarta ta ƙuntata. shin Turaki wanne irin mutum ne shi mara uzuri da yafiya a rayuwarsa, akan kawai ta fasa turare zai kulleta a ɗakinsa ita ɗaya?. kawai sai maganarsa ta dawo mata sanda yace idan ta fita a ɗakin nan to biyansa turarensa tayi. kulle idanuwanta tayi tana jin hawaye na biyo kuncinto da tsananin jin haushi da takaicin kanta. me ma ya kaita?, har sai yaushe ne zata daina shiga hurumin da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba?, dan ana so a cutar da Turaki doesn't mean ana so acutar da Hammah Hamid ne. ina ruwanta da Turarensa ma da har zata fasa kawai saboda bata so?. bata taɓa jin taji haushin kanta a wani abu da ta aikata ba sai a yau. ta san turaren me tsada ne kamar yanda ya faɗa, to yanzu da wanne kuɗin zata biyasa?, shekaranjiya Kaka ta kwashe ƴan kuɗaɗenta ta bayar an siya tumakin da suke kiwo. kawai sai ta ƙara durƙushewa a gaban mudubi tana kuma sakin kuka, ko na misƙala zarratan Turaki baya da tausayi kuma baya da imani, sam baiyi gadon mahaifinsa ba, kuma bai yi gadon mahaifiyarsa ba kamar yanda taji labarinta a bakin Maama ɗazu. tana cikin wannan kukan ne taji an buɗe ƙofar, ko bata ta ɗago ba tasan shine, hakan yasa taƙi motsawa, saboda so take yi ta taushi zuciyarta gudun aikata abinda zata zo tana dana sani, dan tasa a ranta sai Turaki yasan ya kulleta a ɗaki. yau zata masa abinda zai sa ya koyi haƙuri da yafiya, in ba haka ba kuma ta barsa da sharrin waɗanda suke neman rayuwarsa, wannan ma kaɗai ya isa ya shiga hankalinsa. Turaki ya shigo ciki yana mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙara saka key, zaton Fillo bai saka key bane, hakan yasa ta miƙe da azama cikin dabarar data tsara cewar zata bige shi ta buɗe ƙofar ta fice da gudu, irin gudun da ba zai iya kamota ba. kuma ba zata ƙara yardar ma tazo ɓangarensu aiki ba sai dai in Ɗausiyya. Turaki ya tsaya yana kallonta da mamakin yanda ta wani taso a sukwane kamar wacca taga mugun abu, ya ɗan matsa zai bata hanya gudun karta bigesa daidai nan ɗakin ya gauraye da uban duhu sakamakon ɗauke wuta da akayi. babu shiri Fillo ta cakumo Turaki ba tare da sanin inda ta nufa ba tana kurma uban ihu tare da ƙanƙame shi. "wayyo Allah nah, na shiga uku, Kakata". ihun take yi tana ƙara ƙanƙameshi kafin kuma ta shiga roƙonsa,"dan Allah ka kunna fitilar, wallahi ba zan ƙara ba, na bi Allah na tuba insha'Allahu ba zan ƙara yi maka ta'adi ba, kuma zan biyaka turarenka amma kaima Allah ka kunna hasken bana son duhu". maganar take tana ƙara cikwikwiye shi, Turaki yasa hannu ɗaya ya riƙeta sosai ajikinsa, ya duƙa ya ajiye ledar hannunsa sannan yasa ɗayan hannun a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kunna tourch. idanuwanta a rumtse suke gam hakan yasa ba zata shaida hasken fitalar wayar ba, kuma har lokacin bata bar roƙonsa ba akan ya kunna fitilar tana ƙara shigewa jikinsa. ya leƙa fuskarta ya kalla yanda duk take a tsorace, sai haɗa uwar zufa take, ya girgiza kai kawai yana mamakin bala'in tsoro irin nata. yayi ajiyar zuciya a daidai lokacin da wutar ɗakin ta dawo, yay guntun tsaki na ɗan jinkirin da aka samu before a kunna generator. shi kansa baya son wannan ɗauke wutar duk da ba kasafe aka cika ɗaukewar ba, dalilin da yasa ya dami Baffa kenan akan kawai a haɗa transformer a gidan a huta. cikin sheƙar kuka Fillo ta ƙara cusa kanta cikin ƙirjinsa wanda tuni maɓallin wajen ya cire. karan hancinta na gogar fatar ƙirjinsa tace,"dan darajan Allah Turaki kayi haƙuri, idan na kuma yi maka ta'adi kayi min duk abinda kaga dama, ni ba da gangan na fasa maka turare ba suɓuce min yayi a hannu. kai ma Allah da ma'akinsa ka kunna hasken zan biyaka". "kinyi alƙawarin zaki biyani?". da sauri ta ɗaga kanta,"ehh zan biyaka amma ba irin naka ba". guntun murmushi ya sauka akan leɓensa yana bin tsakiyar kanta da ɗankwali ya zame da kallo. kansa ya ranƙwafo saitin kunnenta yace,"to ki sakeni sai na kunna hasken". da sauri ta girgiza masa kai,"a'a ka kunna a haka, idan na sakeka wani abun zai kamani". yace,"wanne abu ne zai kamaki?". Fillo taji kamar tasa masa duka, sai kawai ta daɗa sa kuka tana cewa,"ni dai ka kunna don Allah, duhu tsorata ni yake wallah". ya kai hannu kamar zai shafi gefen fuskarta sai kuma ya fasa yace,"to idan na kunna ta ina zaki sani bayan kin rumtse ido. ki buɗe idonki tuni aka dawo da light". jin hakan yasa a hankali ta shiga buɗe idonta, sai da ta tabbatar idan ta buɗe duka idonta zata ga haske sannan ta buɗe, ta buɗe idonta duka tana saukewa ajikinsa. take ta zabura ta sake shi tana fita a jikinsa tare da ja da baya, sai aikin rarraba idanuwa take yi. sai kuma tayi saurin dafe kanta da taji yayi mugun sara mata a lokaci ɗaya, jiri ya nemi ya ɗebeta ya yasar, Turaki daya lura da hakan yay saurin kamo hannunta ya janyota ta dawo gabansa, ƙarar bugun ƙirjinta tarr a kunnensa. yana riƙe da hannunta da take son ƙwacewa ya sunkuya ya ɗauki ledar, ya jata suka zagaya zuwa ɗaya side na gadon. cikin fargaba da tsoron matakin da zai ɗauka akanta na yadda tasa rigarsa ta cikwiwiye kamar an ƙwato a bakin jaki. idanuwanta sukai rau-rau tasa hannu tana ture nasa tana cewa,"kayi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba". bai ko kalleta ba fuskar nan a haɗe ya zaunar da ita a gefen gadon. sannan shima ya zauna kusa da ita yana janyo table gabansa, ya buɗe coolern abincin dake kai yaga dambu ne na cous-cous da yaji hanta acikinsa sai ƙamshi yake. daga buɗewa duka wajen ya baɗe da ƙamshi. ya juyo da kansa kaɗan ya kalleta tana ta matsar ido, ya tamke murya yace,"when did you wake up?". taja majinar hancinta cikin muryar kukan da bai barta ba tace,"kayi haƙuri dan Allah". Turaki ya daki gefen gadon yayo kanta gaba ɗaya yana sakar mata tsawa,"nace when did you wakeup?". da bala'in tsoro tasa hannu ta kare kanta jikinta sai kyarma yake yi, cikin rawar murya tace,"ban jima ba". bai ƙara bi ta kanta ba ya tashi ya fita, after few minutes sai gashi ya dawo riƙe da wani ledan daban. ya ajiye akan gadon ba tare da ya kalleta ba yace,"ci abinci". tsananin tsoron yanayinsa da ya rikiɗe bata tunanin zata yi masa musu, don haka da azama ta sauka a gefen gadon, hannu na rawa ta ɗauki plate ta buɗe coolern ta zuba abincin ta ajiye a gabanta. tunda ta zuba taji idanunsa akanta, hakan yasa ta kasa sakewa, kuma ta kasa ɗagowa ta kallesa balle ta nemi izininsa taje ta wanke hannu, shi kuwa ciwon hannunta kawai yake kallo da Zaytuna ta ƙara dressing. sai da ta ga ya yunƙura zai tashi sannan tayi saurin cewa,"zan wanke bakina". yay gaba abinsa bayan yace,"karki je ki wanke kici a haka". yana fita a ɗakin ta miƙe ta shiga toilet, bakinta ta wanke da macline sannan ta ƙara wanke toilet ɗin tukunna ta fito. har lokacin kuma hawaye bai bar sauka a fuskarta ba, ita tsoron da take yi kar Maama ta nemeta, duk da tasan zuwa yanzu Kaka na can tana jiran dawowarta. ba zata iya cewa ba zata ci abincin ba don tana jin yunwa sosai, ga shi kuma girkin ya burgeta, ƙamshinsa kawai taji tasan girkin Adda Zaytuna ne. tana cikin ci taji ƙarar buɗe ƙofa, tun da ta hangosa ta wutsiyar ido tayi mugun tsorata da sauri ta ajiye spoon ɗin ta kama jan yatsunta. ya dawo ya zauna a inda ya tashi, ya kalla plate ɗin abincin tukunna ya kalleta yaga yanda take ta raba idanu, yaja tsaki cike da takaici. zai ɗaga murya sai kuma yay controlling kansa, calmly yace,"du ka za ki cinye, ke kika zuba ai ba wani ya zuba miki ba...finish eating and take your drugs". ya faɗa yana jefata mata ledan magungunan. ta ɗan kallesa taga baya kallonta tace,"idan na cinye to zaka barni na tafi?". yace,"idan kin biyani abinda kika fasa min ba. ko an faɗa miki da kuɗin banza aka saya". tace,"insha'Allahu zan biyaka amma ba irin wancan ba, sai dai wani daban, Kaka bata da kuɗin wancan". yay mata shiru, tana ɓata rai tace,"kuma ni lafiyata lau ai". ta faɗa tana ture ledan maganin daga kusa da ita. sai da ta cinye abincin da ta zuba tass sannan ta miƙe ta wuce toilet ta wanko baki ta dawo, ta ɗauke plate ɗin ta ɗora akan table. kamar bada ita yake ba yace,"ba da kuɗin banza na sayo su ba, ɗauki kisha". ba don komai ba sai saboda gudun kar ya sakar mata tsawa ko kuma yay mata wannan kallon da bata so tayi saurin ɗaukan maganin tasha, tana sha tana hawaye, bata miƙe ba sai da taci kukanta duk yana jinta amma bai ko kalli inda take ba. bayan ta gama kukan ta zagayo ta gabansa ta zube duka gwiwanta biyu a ƙasa, ta haɗa hannayenta waje ɗaya alamar roƙo tace,"dan darajan Allah kayi haƙuri, kaga dare yayi Kaka na can tana jirana. kuma nasan Maama zata neme ni". ta faɗa sabon kuka na taho mata, amma sai ta danne shi. Turaki yaci gaba da kallon wayarsa, kamar ba zai yi magana ba can sai taji yace,"thank you for saving my life which you have done so many times. but i want to ask you something and please you tell me truth". furucinsa ya bata mamaki matuƙa, how does he knows that?, zuciyarta ta ambatar mata sunan Maijidda, ita kaɗai tasan wannan sirrin nasu. to amma!...sai ta ɗago kai don kallonsa ƙirjinta na bugawa, gani take kamar maganar da yay ba da ita da yayi ba, ganin waya ce kare a kunnensa yasa ta sauke dogon numfashi, hakan ya shaida mata ba da ita yake magana ba. cikin wayar da Turaki yake da Bello ta faki idonsa ta ƙarasa zaro key ɗin da ya leƙo ta aljihunsa ta yanda ba zai ji ba, ga mamakinta harta miƙe sai taji ya riƙe hannunta gam. ta rumtse ido kamar zata yi kuka, ganin za tai magana yay saurin ɗora yatsansa saman lips ɗinsa alamar tai shiru. hakan yasa tai gum tana bo ne fuska. bayan ya gama wayar ya dubeta, tai tsaye ta rufe idanuwanta gam ko motsi taƙi yi tunda ya riƙetan. tsoronta Allah tsoronta kar yaga key ɗin motarsa da ta ɗauke, dan a second fitarsa ta ɗauke tasa acikin rigarta. taji yace,"ni zan shanye sauran maganin?". ta buɗe ido ta ɗauki ledan da yay mata nuni da shi, cike da ƙaguwar ya sakar mata hannu. tace,"wa zan kaima?". yana sakin hannunta yace,"ki wuce da shi". tace,"ina?". yace,"duk inda kika ga dama". tana hararsa ta ƙasan ido tace,"ƙofan a rufe yake". ta faɗa tana yamutsa fuska. ya miƙe yaje ya buɗe ita kuma ta fice da gudu, wannan gudun nata kuma yasa shi sakin gajeran murmushi yana girgiza kansa. cikin sanɗa ta fita daga side ɗin nasu gaba ɗaya, ko tsayawa ba tayi ba a compound tayi ɓangarensu dan bama taso su haɗu da Maama a yanzu, sai safiya kuma. sai after take jin wani mugun ƙamshi me shegen daɗi na binta, ta dinƙa jan hanci tana so taji daga ina ne, sai da ta shinshina jikinta taji ƙamshin a jikinta yake. tsabar daɗin ƙamshin nunfashinta har kusan sarƙewa yayi, tana tafe tana lumshe ido har ta kusa zuwa ɗakin Yami. aina ta samo wannan ƙamshin to?, ƙamshin da zata iya ce duk duniya babu ƙamshin da ya kaisa daɗi. idanuwanta a lumshe ta ƙaraso ƙofar ɗakinsu, lokacin Maijidda ta fito daga ɗakin suka yi karo da juna. Maijidda ma taja hanci tana shaƙar ƙamshin tare da cewa,"kai Fillo wannan ƙamshin fa?". **** Boɗejo dake zaune kan kujera a babban parlon Mai Martaba tace,"ah tou ni ɗin dai na gama magana...idan kuma kun lalace ne to sai naji, amma batun auren Ilham da Ɗan'uwanta wancan kumburarren babu wanda ya isa ya hana sai dai ko bayan raina, sai in kuma ikon me sama". Mai Martaba ya sauke numfashi yace,"amma Hajjah...". da sauri ta katse shi,"Hashim kai kaɗai ne me shegen taurin kan da ba zaka tuba ka daina kirana da Hajja ba ko?, kasan Allah karka bari raina ya ɓaci akanka, ya nazo ina batun haɗa yara aure kana ce min ba haka ba yanzu kuma kana ƙara kirana da sunan da kasan bana so". cikin kwantar da murya Mai Martaba yace,"kiyi haƙuri". Boɗejo ta ƙara haɗe rai tace,"ka riƙe haƙurinka. muyi batun da ya kawoni wajenka, ba tun yau nake faɗa ba sai dai zan ƙara nanatawa ina so ku haɗa Muhammadu da Rumana aure, in kuma ban isa ba sai inji". Baffa ya ɗago kai ya kalleta yace,"balle ma kin isa Boɗejo, sai dai kawai ya kamata ayi duba a lamarin, tunda bamu san ba ko su yaran nan zasu so haɗa su auren da za'ai". Mai Martaba yace,"abinda nake so ki fahimta kenan Mama, zamanin yanzu ba ɗaya bane da na da, yanzu ba'a haɗa yara aure gudun abinda ka iya zuwa ya dawo a zamantakewar tasu muddin babu soyayyar junansu, amma kuwa idan aka tabbatar da yaran nan suna son junansu shikenan salamun alaikum mu kanmu ba ƙaramin farinciki zamu yi da hakan ba". Boɗejo ta tafa hannu tana salati kafin tace,"na shiga uku, Hashim yanzu al'adar tamu zaka rushe?, kai kasan a yanda akayi aurena da ubanku kuwa?, tabɗijam, to da kasan ta yanda aka laliƙa min ubanka na aura da baka zo min da wannan ƙabali da ba'adin ba...shashashan sarki kawai, kai idan akai hakan ma ba ƙarfafa zumunci akayi ba, amma kana batun wani idan basa son junansu, a'a to da ƙiyayyar junansu suke yi?, ko an faɗa muku su irin ƴan'uwan mahaifinku ne kafin su tuba, kai gaskiya Hashim kana da gurɓataccen tunani, wai idan basa son junansu!, maganar nan naka har ga Allah yayi min zafi, to karka ƙara wallahi, don ni dai kaf jinina babu me mugun hali, kowa son ɗan'uwansa yake yi...tsakani da Allah ina Turaki zai ce baya son Ilham ƴar'uwarsa?, kuma itama ta ina zata ce bata sonsa yarinyar da kullum zancenta akansa yake, babu fitowar rana da faɗuwarta da ba zata ambaci sunansa ba, dan ma dai waccan uwar tata me baƙin hali da mugun nufi na hanata zumunci da shi, to a gaskiya indai ana so aga dai-dai abi umarnina kawai, auren nan yinsa za'ai babu wani zaman tuntuɓe-tuntuɓe balle asa jinina ya hau". Mai Martaba zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"a'a dakata, dakata ba sai kace komai ba. ɗaga waya kawai ka kira min Hakimi yazo yanzun nan, ban sani ba ko haɗe kanku kuka yi kuke so ku nuna min kune kuka haifi yaran nan, ni banda wani hurumi da su, in haka ne kuwa sai in kama gabana na barku da halin bijirewa maganata". Baffa ya tausasa murya yace,"ba bijire miki zamu yi ba Boɗejo, zamani muke so ki duba. kuma muma fa bamu ce ba za'ayi hakan ba, ce muka yi a fara jin ta bakinsu tukunna, idan sun amince da junansu mu abin farinciki ne a wurinmu wallahi". Boɗejo ta jijjiga kai ta harɗe ƙafafu tace,"to bara kaji Dikko, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin Ubanku ba sai a ranar da aka kirani akai min zancen aurenmu da shi...ina zaune lafiya daga zuwa na gaida mahaifiyata zanyi kwana uku a wurinta sai Kakanku yasa Babana ya doka min kira wai inje fada ana nemana, kai kasan tashin hankalin da mahaifiyata ta shiga a dalilin wannan kiran kuwa?, saboda kiran fada bai cika zama alkhairi ba, ina zuwa ga Babana Waziri ga Mai Martaba ga Ubanku a zaune aka ce ga mijin da akayi min, kuma a gobe za'a ɗaura mana aure. yo da ike ni me biyayya ce ban bijire ba daga ni har shi uban naku, hasalima shi tausata yake yana cewa muyi haƙuri mubi umarnin iyaye zamu ga ribar hakan, to dana aure shi Dikko mutuwa nayi ko me?, gashi nan dai ku huɗu na haifa jeras tare da shi, idan bana sonsa zan bari a haife ku ne?. sai akan ƴaƴanku zaku ce ba haka ba, Turakin ma da wancan algungumar Azimar ta raine shi, Turaki fa har goya Ilham yayi, to banda dai rashin tsoron Allah irin naku ina ku ina cewa baya sonta? ku dai ku ke kyautata zato akan abu, ba wai kowa yake hasashe mara kyau ba. na tabbata babu abinda zai sa yarannan suƙi amincewa muddin kun nuna musu kuna so, banƙi ba shi ɗan naka ya iya botsarewa to amma shima na san na ƴan mintina ne tunda yana da ladabi, kana cewa haka kake so ba zai ja ba zaice ya amince, sai dai idan kuma a munafurce ni a hure musu kunne". daga Baffa har Mai Martaba babu wanda ya ƙara yin magana, Boɗejo ta tafa hannu wani bafade ya shigo parlon yana zubewa a ƙasa. tace,"maza kira min sarkin gida". fitarsa babu jimawa sai ga sarkin gida ya shigo, ya zube agaban Boɗejo tace,"ɗau waya ka kira min Hakimi". Sarkin gida ya kira wayar Hakimi da wayar Mai Martaba, bugu ɗaya biyu ya ɗaga. yay saurin miƙawa Boɗejo. ta karɓa tasa a kunne, bayan sun gama gaisawa tace,"kana jina?". a ladabce yace,"ina jinki ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai". tace,"amin, Allah yayi maka albarka...dama magana zanyi da kai". kamar yana gabanta saboda tsananin ladabi yace,"tom shikenan, ɗazu ance min kin fita, gidan Dikko zanzo ko fada?". tace,"a'a yi zamanka akan kujerarka. dama batu ne na aure nazo maka da shi, ina so a haɗa auren Turaki da Ilham, ba kuma na so ya wuce wata guda tunda da arziƙinmu, wata gudanma saboda zan gyara jikata ne banda haka cikin sati ɗaya za'ai komai a gama". Hakimi yace,"tom shikenan ranki ya daɗe, za'ayi yanda kika ce. Allah ya tabbatar da alkhairi". tace,"amin ya Allah". da haka suka yi sallama, da yake a handsfree ta saka duk conversation ɗinsu su Mai Martaba sunji. "da akwai wanda zai ja ne?". ta faɗa tana kallon su duka. a tare suka haɗa baki wajen faɗin,"a'a, Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi". tana nuna musu fushinta na gardarma da suka yi mata a farko tace,"kai Dikko ka kira min Falmata yanzu a waya". Baffa ya ɗau wayarsa ya kira Falmata ya miƙawa Boɗejo, sallamar Falmata kawai ta amsa tace da ita,"anjima za'a kawo Ilham gidanki, ki gyarata gyara na ban mamaki Falmata, gyaran da ba zai sa Turaki ƙara kallon wata mace da sunan sha'awa ba har mutuwarsa, irin gyaran da ba zai so Ilham ta matsa a kusa da shi ba". Inna Falmata ta amsa da,"tom ranki ya daɗe". Boɗejo ta dubi Mai Martaba bayan gama wayar tace,"sai kuma me?". ya rissinar da kansa yace,"ya kamata a sanar da Fulani Azima da kuma Madina". Boɗejo ta haɗe rai tace,"ashema ba so nake auren ya tabbata ba. gwara ma in Madina kace, amma wace wata Fulani Azima?...to maganar aure dai cikin sirri nayi ta, ko yaran ba zasu sani ba sai ranar ɗaurin aurensu, magana daga ni sai ku nayi ta, idan naji ta a wani waje kuma wallahi tallahi akwai Allah". tana gama faɗar hakan ta miƙe. "Dikko tashi muje gidanka zan wuce". *Comment, Share and Vote.* [8/28, 10:43] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *28* washegari da safe Fillo ta gama shiryawa kenan sai ga Yami ta faɗo ɗakin kamar an jefota. fuskarta a haɗe take kallon Fillo, ita kuma tana ganin hakan tasha jinin jikinta. Yami ta miƙa mata wayar hannunta tana faɗin,"ungo nan, idan ta kama ki tafi da ita can, abu ɗaya kawai na sani shine ki tabbatar kin ɗaga kiran Amir kunyi magana da shi, ki kuma basa damar zuwa idan ya buƙaci hakan". idon Fillo suka ƙanƙance tana kallon Yami da ta ɓata rai, ƙirjinta taji yana bugawa da sauri sauri domin bata tunanin zata iya bin umarnin Yami. Yami ta doka mata tsawa,"kin karɓa ko saina hamɓare ki". tuni jikinta ya hau kyarma tayi sauri ta karɓi wayar tana duƙawa a wurin ta fashe da kuka. Kaka tace,"to dama ni dai da naga ba kiyi magana ba yasa nayi shiru, zatona ko baki san komai ba". Yami tace,"ai ina sane, na zuba mata ido ne naga iyakar gudun ruwanta. sai naga rashin hankalin nata da gaske ne, to banda ma dai ɗan Adam butulu ne dan ubanki ina ke ina juyawa Amir baya, duk abinda Amir zai yi miki a rayuwa ai ke me iya shanyewa ce ba wai kiyi zuciya da shi ba, wane irin alkhairi ne yaron nan bai yi miki ba, wane kalar halacci ne bai yi miki ba, ke inda baya sonki da gaskiya har yace yaji ya gani ya aminta zai aureki sanda ake hure masa kunne da cewar ke ƴar gaba da fatiha ce. amma saboda toshewar basira irin taki har ki iya ɗaukar fushi da shi na tsawon wata da watanni, gaskiya kin bani kunya da mamaki". cike da takaici Yami ta ƙarasa maganar. Fillo dai kuka kawai take yi tana jin zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta, ita ake bawa laifi?. gaskiya ko Yami da Kaka zasu haɗu su kasheta bata jin zata iya yin abinda suke so akan Amir, in har dan ta ɗaga kiran Amir ne ko ta basa damar zuwa gwara ta mutu, dan ko kaɗan bata son jinsa balle ganinsa. Kaka tace da ita,"ni dai ban taɓa tunanin a ɗan guntun ililimin da kika samu daga wurin Amir ba, ilimin da wanda ya haifeki ya kasa baki shi, zaki iya butulcewa Amir ba, ko da kuwa me zai yi miki, irin faɗi tashin da yaron nan ya dinƙa yi a game da rayuwarki ta inganta da kuma lafiyarki yafi ƙarfin wulaƙanwa daga gareki. amma babu komai iya abinda kika yi ma kin zubar min da mutuncina a idon iyayensa, na kuma gode, domin babu wanda zai yarda cewar bani na saka ki ba". Fillo na kuka sosai ta ɗago ta kalli Kaka tace,"shikenan ko mene ya faru sai a ɗora min laifin?, me yasa ba za'a tambaye ni abinda yayi min ba?". Yami ta galla mata harara tace,"rufewa mutane baki, ba'a haƙuri ma'aikin Allah yay haƙuri?, ko kuma ba'a yafiya muke yiwa Allah laifi mu nemi yafiyarsa kuma ya yafe mana. to wallah tun muna shiri da juna ki sasanta tsakaninku a yau. nace masa yazo, dan haka ki tafi da wayar kwa haɗu da shi acan. mu ba mutanen banza bane da sai da aka tsayar da maganar aure tsakaninku sannan ki nuna mana ba haka ba, ƙarya kike yi kinyi kaɗan". Kaka tace,"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni". jin furucin Kaka yasa Fillo ta dinƙa kallonta babu ko ƙifce, ji take ina ma ta haɗiyi zuciya ta mutu, anya ma Amir bai asirce mata Kaka ba?, ko da yake babban asirin da zakai wa mutane akan suƙi ganin bad side of you shine ka zama mutum na ƙwarai a idon duniya. ta tashi ba tare da tace komai ba tai fuuu ta fice daga ɗakin tana ƙara sakin kuka. a ƙofar ɗakin taga Maijidda a tsaye tana hawaye, tai mata kallo ɗaya ta ɗauke kai tayi gaba abinta, Maijidda tabi bayanta tana kiranta, Fillo ta juyo a fusace tace da ita,"da kika iya zuwa kika faɗawa Yami na butulce masa why can't you ki faɗa mata shi irin wulaƙancin da yay min, why not ki faɗa mata ya kira ni da ƴar zina ko sa nuna masa kuskurensa, amma sai kika karesa kika bar laifin akaina ni ɗaya. babu komai, thank you for that, ko yanzu kin nuna min matsayina wurinki, kin nuna min ni ɗaya zan iya fighting akanki ba dai ke kiyi akaina ba". Maijidda ta riƙo hannunta tana so tayi mata magana amma Fillo cikin ƙunar ran da take ji ta fizge tayi gaba abinta. Maijidda nace mata,"wallahi ni bancewa Yami komai ba, ita ta fuskanta da kanta shine ta ɗauko wayar ta kawo miki amma wallahi ni ko ɗaga wayar Amir ban ƙara yi ba tunda kika faɗa min abinda yay miki". Fillo dai ko tsayawa bata yi ba balle ta tsaya sauraron abinda Maijidda ke faɗa, dan tuni ta toshe kunnenta daga jin abinda ma zata ce mata wanda bata ganin she can believe her. har ta shiga parlon Hajiya Madina bata daina zubar da hawaye ba, da tarin tunani fal cikin ranta a game da Amir da kuma Kamal, mutumin da ta fara haɗuwa da shi lokacin da ta gudo daga gida, kuma mutumin da yace ba zai iya auren ƴar gaba da Fatiha ba. ganin babu kowa a parlon kai tsaye kitchen ta wuce, tana shiga ta kunna tap ta wanke fuskarta acikin sink, jin motsi kamar an shigo kitchen ɗin tai saurin saita natsuwarta tana daɗa komar da hawayen dake ƙoƙarin sake sakkowa. "menene Fillo?". taji muryar Hajiya Madina a bayanta, hakan yasa ta juyo da sauri tana durƙusawa ta gaida ita. Hajiya Madina ta ƙarasa shigowa cikin kitchen ɗin, tace da ita ta miƙe. tana kallonta sosai tace,"kukan me kike?, wani abin aka yi miki?". Fillo ta girgiza kai,"a'a Maama, kaina ne ke ciwo". "kuma shine kike kuka haka, baki san zaki ƙarawa kanki ciwon ba ne?". tayi shiru bata ce komai ba. Hajiya Madina tasa hannu ta taɓa kan nata sai taji zafi rau. "subhanallah, kin sha magani?". ta girgiza kai tana so ta riƙe sabon kukan dake ƙoƙarin zuwa. "ya haka Fillo, banda abinki ba sai da lafiya ake yin komai ba, sai kisha magani kiyi kwanciyarki tunda ga Ɗausiyya. maza jeki bedroom ɗina akwai magani cikin drowern madubi, ki buɗe ki ɗauka sudrex ki sha. sai kije ki kwanta zuwa anjima". tace,"tom na gode Maama". sai tasa hannu a gefen zanenta ta ciro key na mota. Hajiya Madina tasa hannu ta karɓa tana faɗin,"thank you very much". kan Fillo a ƙasa tace,"kiyi haƙuri ranar ban sami damar faɗa miki ba, naga idan nace sai nazo na faɗa miki before muyi taking any action zasu cimma burinsu ne, thats why na tafi ɗakin Hamman kai tsaye". Hajiya Madina ta dinƙa kallon key ɗin babu ko kifta ido, cikin idonta haskowa take yi wai Turaki na driving ga babban mota yayo kansa kuma babu burkin da zai taka ya ƙwace, wanne kalar mummunan haɗari ne zai faru?, wataƙila shikenan rayuwar Turaki ta ƙare kenan kamar yanda suke so, ina alƙawarin kula da su data ɗauka?, tai saurin rumtse ido tana girgiza kanta da kawar da abinda ke cikin kanta. ta dafa shoulder ɗin Fillo ta ƙara ce mata,"na gode, ina miki godiya da ƙoƙarinki wajen ganin rayuwar ɗana ta kuɓuta, insha'Allahu a wannan shekarar da ke za'a yi aikin hajji, ƙafata ƙafarki zuwa saudiya Fillo". Fillo na kallon fingers ɗinta tace,"Na gode Maama Allah kuma ya amsa". sai taji kawai Hajiya Madina ta janyota jikinta tayi mata side hug, tana jin ruwan hawayen da ya fito daga idonta ya sauka akan kafaɗarta. muryarta da rauni tace,"yanzu ba don ace Allah ya nufeki da jinsu ba shikenan komai da suka shirya sai ya faru ko?". Fillo dai tayi shiru bata ce komai, illa iyaka tsananin tausayin Hajiya Madina dake acikin ranta. ta janye a jikin Maama tasa gefen mayafinta ta goge mata fuska tace,"please Maama stop crying, adu'a kawai zaki ci gaba da yi, Allah ya ƙara kare Hammah su kuma Allah ya shirye su". Maama tace,"insha'Allahu, je ki sha maganin. hope kinci abinci?". tace,"zanci yanzu sai na sha maganin". Maama tace,"akwai sauran breakfast a dining, ki ɗiba ki wuce da shi ɗakina sai kici acan, ki tabbata fa kinsha maganin". Fillo bata wuce ba ta sunkuyar da kanta tana wasa da gefen mayafinta, Hajiya Madina ta fahimci tana so tayi magana, hakan yasa ta kamo hannunta tace,"do you have something to say?". ta ɗaga kai tace,"ehh Maama, dama ce zanyi hope ba wanda ya san zaiyi tafiya?". da mamaki Hajiya Madina ke kallonta, ai tayi zaton daga ita sai Bello suka san da batun tafiyar Turaki Hong kong. kan tai magana Fillo tace,"dama naji yana waya da Hammah Bello ne akan tafiyar". Maama tace,"ehh babu wanda ya sa ni, na kuma hana Khalil yay maganan ma if muna tare. je ki sha maganin bana son ciwonki". Fillo ta fito a kitchen ɗin, Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, tana ƙara jin yarinyar na shiga can cikin ranta. a dining Fillo ta zuba chips da awara da souce, ta hau sama ta ɗauko maganin sannan ta dawo ta ɗauka abincin da wuce ɗakinsu, kamin ta fito Khalil da ta samu a parlo yana kallo yana ta tsokanarta da acici. kaɗan ta samu taci abincin saboda bakinta da take jin babu taste, tana shan magani ta kwanta a wurin, ko da teacher ɗinsu yazo ma bata samu ta iya zuwa ba, Ɗausiyya na tashinta tace ta faɗa masa bata da lafiya. bata tashi ba sai 12, shima ƙarar wayar ɗakinsu ce ta tasheta. daga ɓangaren Nihal tace da ita,"Fillo please if you are not doing anything zo ki taimaka min da gyara closet ena". Fillo tace,"toh". ta ajiye wayar ta shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fito ta wuce. tana shiga parlo ta tarar da Zaytuna zaune, sai taji gaba ɗaya ta kasa ɗaga ƙafarta saboda azaban kunyar Zaytuna ɗin. sim sim kanta a ƙasa ta ƙarasa shiga ta durƙusa har ƙasa ta gaida Zaytuna. Zaytuna dai data san komai kuma ta fahimci komai sai tayi murmushi sannan ta amsa gaisuwar. tace da ita,"sai yanzu kika shigo?". still kanta na ƙasa tace,"na shigo tun safe, Maama tace na kwanta saboda kaina dake ciwo". "ayyah Allah ya sauƙe, ko ayi allura?". cikin azama Fillo ta miƙe tayi upstairs bayan tace,"a'a na warke". Zaytuna ta rakata dariya, ta jima bata ga me tsoron Allura kamarta ba, duk zafin ciwo aka ambaci allura sai tai firgigita ta taashi wai ta warke, ko da ace ciwon cinta yake. a ɗakin Neehal tare suka gyara kayan closet ɗin, Nihal sai labari taketa bata, mostly duk akan school ne wanda hakan ke ƙarawa Fillo jin kwaɗayin tayi karatu sosai, har itama ta kai matakin university, dama Maama tayi mata alƙawarin indai lesson teacher ɗinsu ya bada good perfomance akanta to zata zana private waec, in yaso idan zata je malasia course na phd nata sai su tafi tare, wanda hakan ya ƙara mata ƙaunar Hajiya Madina. sosai Nihal ke burgeta saboda sauƙin kanta, ita da Khalil sune kaɗai suka yo halin mahaifiyarsu. after azhar Fillo na parlon Boɗejo tana yi mata tausa, Boɗejo sai labarai take yi mata kala-kala. kuma labarin sosai yake yi mata daɗi, wani wurin tayi dariya wani wurin kuma tai murmushi, wani wurin kuma ta jinjina irin tuggu da ke cikin gidan sarauta, cikin ranta tana godiya ga Allah da yasa bata da haɗi da sarauta. can sai taji Boɗejo tayi shiru, ta ɗago kai ta kalleta, sai taga hanyar bedroom ɗinta take kallo, Fillo ta waiga taga Turaki ne ya wuce, gabanta taji ya faɗi, da sauri ta juyo tana ci gaba da matsawa Boɗejo ƙafarta, fatanta ɗaya Allah ya kawo abunda zai tasar da ita daga wurin nan yanzu, kuma Allah yasa kar Boɗejo tace zata aiketa ɗakin nata, dan sam bata so ta haɗu da Turaki. Boɗejo tace,"ina faɗa miki to haka ake yi fa idan biki ya tashi, in kika ga yanda ake kashe kuɗi sai kiyi zaton ko ba'a san ciwonsu ba ne. to da yake al'adar gidan sarauta ce hakan, indai za'a yiwa Yarima aure ko kuma Gimbiya to zaki ga yarda ake ɓarin kuɗi kyace ba'a talauci a nigeria, musamman ma ace bikin sarauta da sarauta ce ta haɗu, to ina faɗa miki in aka tashi kai lefe hatta bayin gidan sai an yi musu sutturu an kuma basu kuɗaɗe. kinga lokacin bikina dangin Mamana sai da suka dinƙa cewa ko dai siyar da ni akayi. yanzu dai ai zaki ganewa idonki tunda muna tare, in bikin Ilham ya tashi uban kayan da zaki samu sai kinsha mamaki, har sai kin kyautar kema". tun farkon fara labarin Fillo batai magana ba, har Boɗejo ke cewa ko tana ciwon baki ne, amma haka kawai da taji ta ambaci sunan Ilham sai ta sami kanta da tambayar,"Boɗejo wacece Ilham?". Boɗejo tace,"kul Gimbiya za ki ce, ita ɗin ai ƴar me martaba ce, yanzu in a gaban fadawa kika faɗi sunanta haka gatsal ai kin shiga uku, ƙila ma Fulani tasa a ɗaureki...ita aka sakawa sunana ai shiyasa nake masifar sonta, baki taɓa ganinta ba?". tace,"ban ma taɓa jin sunanta ba". Boɗejo tace,"kika ce kuma shekararku biyu a masarauta kafin a ƴanta ku ayo nan da ku...ko da yake zai yiwu ɗin ki kasa saninta, tunda uban ita kaɗai ce baya so, tun tana ƙarama ya kaita can ƙasar arna bata dawo ba sai da ta shekara biyar". Fillo tai shiru ita dai ƙirjinta sai bugawa yake haka ɗaya babu gaira babu daɗi, wayar Yami dake soke a gefen zanenta tayi ƙara, tai banza da kiran har ya katse, lokaci ɗaya taji sabon ɗaci da ɓacin rai a zuciyarta. sanda kira na biyu ke ƙara shigowa sai taji kamar ta rotsa wayar, Boɗejo dai nata zuba labari tausar ƙafa yayi mata daɗi. can dai ta gaji tana kallon Fillo tace,"ki ɗaga wayarki mana, anata kira kin sha re, yanzu fa idan samuwa ce shikenan kin yiwa kanki. haba ƙila ma ba lafiya ba tunda kika ga kiran yayi yawa haka, kusan sau shida fa ina jin ma ko bakwai". Fillo ta ciro wayar hawaye na sakko mata, tabi sunan Amir dake jikin screen da kallo. maganar Kaka ta ɗazu ta haska acikin kanta,_"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni"._ ba don waɗannan maganganun da Kaka ta faɗa mata ba, da idan ta ƙara sauraron Amir a rayuwarta shegiya ta ke, ai me zuciya akewa gori ba mai dukiya ba. tana ɗaga wayar ba tare da ta amsa sallamarsa ba tace,"ba ta gate ɗin ɓangarenmu ba, main gate na gidan". tana faɗar hakan ta kashe wayar ta cillar tana ɓata fuska. ta yunƙura zata tashi tana cewa da Boɗejo,"zanje Yayana ne yazo yana ƙofar gida". Murmushi ya sauka a fuskar Boɗejo tace,"Allah sarki, to gaida shi dan Allah. ki buɗe friedge ki tafi masa da fura tana cikin gora, jiya Nihal ta dama min ita da daddare, akwai inibi ma duk ki haɗa masa da shi, ko kuma zaki shigo da shi ciki ne?, ko can ɓangarenku ɗin zai je?, a'a kinga ma kawai shigo da shi nan ɗin mu gaisa, yanda kike da mutumci ai dole a mutunta baƙonki". ta girgiza kai tace,"a'a Boɗejo sauri ma yake ai, ba zai shigo ba na sani". Boɗejo tace,"to ɗaukar masa abin sawa a baki ki kai masa, ba kyaje haka ba gaskiya hannu na dukan cinya". ba yanda Fillo ta iya haka dole ta ɗauka Furan da inibi saboda takurawan da Boɗejo tayi mata, amma tana fitowa ta bawa me gadi, dan da dai ta bawa Amir gwara ta zubar a kwata, hakan kuma babu kyau. ta jima tsaye bakin ƙofar gate ɗin kamin tasa ƙafa ta fita saboda bala'in zafin da zuciyarta keyi mata, dole ta fara controlling kanta kamin ta fita. daga can ƙarshen katangan gidan ta hangosa tsaye jingina akan machine, ta tsaya taƙi ƙarasawa wajen sai shi ya ƙaraso inda take. bata jin zata iya ɗaga ido ta kallesa hakan yasa yana kusantota ta rufe ido da hannunta tana ƙara yin ƙasa da kanta. Amir na ƙarasowa gabanta sai ya zube a gabanta yana sa dukkan gwiwoyinsa a ƙasa, ya haɗa hannayensa wuri guda alamar roƙo, cikin muryar dake bayyana dana sani da ɗumbin nadama yace,"dan darajar Allah da manzonsa kiyi haƙuri ki yafe min abinda nayi miki, nasan nayi kuskure kuma na karɓi hukuncin da kika min. amma horarwa ta isa haka, da nisanta ni da kanki da kike wallahi tallahi gwara kice na kwanta a akan titi mota tabi ta kaina, and am giving you full assuarance of zanyi hakan domin ba zan iya ci gaba da rayuwa babu ke a tare da ni ba...i know halina ba zai sa ki yafe min ba, but ki ji tausayin Uwar da ta mallaki ɗa guda ɗaya, wannan ɗan nata kuma ya kamu da son mace guda ɗaya, wanda son nata zai iya zama ajalinsa, ita kuma uwar bata so ta rasa ɗanta, ki kwatanta yanda wannan uwar dake son ɗanta zata ji in har ta rasa shi...kiyi haƙuri, kiyi haƙuri, dan Allah da Annabinsa Halima". kuka ya kubcewa Fillo, ta sauke hannunta daga fuskarta, ta buɗe idonta a hankali tana sauke su akan Amir, da tsananin mamaki ta ɗan ja da baya saboda ganinsa durƙushe a gabanta yana hawaye, kallonsa take sosai tana ganin yanda hawaye ke sauka kamar an kunna famfo. bata san sanda tace,"na fa yafe maka". ta faɗa tana turning around gudun kar wani ya gansu. Amir bai motsa ba still duka gwiwoyinsa na ƙasa yana hawayen so, jin zuciyarsa yake kamar zata faso ƙirjinsa, anya zai iya ci gaba da rayuwa babu Fillo?. tana kallon gefe tace,"ka tashi kar wani yazo ya ganka". acikin muryar da ta jiƙu a maye na so yace,"mene aciki dan wani yazo ya ganni durƙushe a gaban wacce nake ƙauna duk duniya bayan uwata?, ko ban miki laifi ba ni me zube gwiwoyina gabanki ne balle kuma na aikata laifi. Halimatuna ba zan taɓa miƙewa daga nan ba har sai kin dubi hawayena, ko da zaki shiga gida ki barni haka". Fillo ta ƙara waigawa ko'ina bata ga kowa ba, muryarta a ƙasa tace,"Amir na haƙura, in ban haƙura babu abinda zai fito da ni wajenka". ya ɗago da sauri yana kallonta, yana ganin yacca hawaye ke sunturi akan kumatunta, sai yaji zuciyarsa ta ƙuntata sosai, yaji wani mugun sonta ya ƙara kamasa, ji yake ina ma there is chance ɗin da zai iya hugging nata da yayi hakan, sai dai babu wannan damar, but he will use another chance yaga ya tsayar da zubar hawayen, to make sure ya goge wannan dattin baƙin cikin da ya haddasa mata. dan haka sai ya dinƙa jan gwiwoyinsa akan ƙasar wanjen har zuwa gabanta, yasa hannu ya riƙe siraran ƙafafunta da suka shige cikin tafin hannunsa, yace,"kiyi haƙuri don Allah, na tuba ba zan ƙara aikata kuskure makamancin haka ba". a hankali tace,"Amir na haƙura fa". ya girgiza kansa da cewar,"zubar hawayenki na shaida min baki haƙura ba, kuma baki yafe min ba, kiyi min rai ki daina bari hawayenki na zuba a ƙasa, wallahi tallahi ina jin kamar za'a zare raina ne". tasa hannu ta goge hawayenta tace,"na haƙura Allah kuwa". ya miƙe yana murmushi, suka haɗa ido tana jin kamar ba zata iya sakin nata murmushin ba, sai dai kuma ƙwayar idonsa da ta shiga cikin tata ta dagargaza alwashinta, taji ba zata iya yi masa komai ba, dan haka ta sakar masa sanyayyan smiling ɗin da sai da Amir ya nemi bango ya dafe. tai masa harar wasa tana faɗin,"duk ka wahalar da ni". ya kafeta da ido murmushin kan leɓensa yaƙi ɗaukewa, ya bar jikin bangon ya matso kusa da ita sosai har tana jiyo numfashinsa da bugawar zuciyarsa, yay ƙasa da murya sosai saitin kunnenta yace,"please can i hug you?, just a little, don't say no plsss". da sauri Fillo ta ɗago kanta ta kallesa, taga yanda idanuwansa suka sauya kala, tai saurin juya masa baya tana jin wani irin kunya na rufeta. ganin zata gudu yay saurin riƙo hannunta ya janyota yace,"in baki juyo ba da gaske zanyi hugging na...". ai bai ƙarasa ba ta juyo da sauri tana kulle idanuwanta. rufe idon nata kuma ya bawa Amir damar ƙare mata kallo tas, ji yake kamar ya ɗora lips ɗinsa a nata, kamar ya tsaga ƙirjinsa ya ɓoyeta aciki, kamar a barsa daga shi sai ita a wannan duniyar, he can't even imagine kalar soyayya da tarairayan da zai nuna mata idan suka yi aure. a hankali yace,"buɗe idonki ki faɗa min ni dake wa yafi wani wahala da har kike faɗin duk na wahalar da ke". cike da kunya ta buɗe ido tana tura baki gaba tace,"ka sakar min hannu a waje fa muke". ya ɗaga shoulders ɗinsa yace,"and so?, hannun matar fa da zan aura na riƙe shi kuma munafiki ina ruwansa?...kinga bar batun ma na sakar miki hannu dan ba zan iya ba, watanni bakwai ɗin dana ɗauka bana tare dake Allah ɗaya yasan baƙar wuyar dana sha, dube ni fa kiga yanda duk na fige na lalace, duk wanda ya ganni ya ga wanda yay jinya ba ƙarama ba, cin abinci da ƙyar bacci kuma sai ɓarawo. but you". ya faɗa yana sa ɗayan hannunsa ya ɗago fuskarta,"hankalinki kwance har da wani kumatu kinyi, kinyi haske abinki alamun baki da wata matsala balle damuwa. lallai yau na yarda ni ɗaya nake kiɗa da rawata, Allah sarki ni Amir ashe son maso wani nake yi". Fillo ta kauda fuska gefe tace,"ai kaima kasan abinda kayi min baka kyauta ba, da farko na rame sosai saboda jin ciwon abinda kayi min, amma da na cireka daga raina gaba ɗaya sai na sami salama, in yi baccina hankali kwance ba tunaninka balle na damu. kuma ni ka sakeni kar wani ya ganmu, this is not a privacy place". Amir ya ware idonsa sosai akanta yana kallonta da mamaki yace,"Halimatuna am i hearing well?, english fa naji kina yi". ta juya ƙwayar idonta tace,"da ka barni ai ba wulaƙanta nayi ba, yanzu haka lesson teacher na bai jima da tafiya ba". mood ɗin Amir ya sauya, yana niyyar fizgota jikinsa ta cije tana ƙwacewa daga hannunsa har sai daya saketa. ta bisa da kallon sauyawar mood ɗinsa tace,"lafiya?". without looking at her yace,"please and please, i beg you for the sake of Allah, let by gone be by gone. bana son tuna baya, karki ƙara cewa na tafi na barki, if not kuma Allah zan miki tafiya me gaba ɗaya, dan zanje na tunkuri mota gaba da gaba tabi ta kaina". tayi far da ido tana haɗe hannayenta a ƙirjinta tace,"tom ba zan ƙara ba insha'Allah. am sorry, ina Innah?". ya ɗan kalleta yay mata harar wasa, harar da tasa Fillo ƙyalƙyalewa da dariya sosai wanda duka haƙoranta na gaba sai da suka bayyana. cikin nishaɗin da take jin kanta aciki tace,"ɗan ƙara yi na gani". fuskarsa na washewa da dariya ya kai yatsansa zai ɗalli fuskarta tayi saurin kauda fuska still tana dariya. Amir yay ƙwafa yace,"zaki bayani, nima sai na rama kukan da kika sa na dinƙa yiwa Innah". ya sauke numfashi yace,"Innah na gaida ki, ƙila gobe tazo ko jibi, zasu zo da kayan sa ranarki. Halimatu nan da next 2months nake so na mallakeki matsayin matata. na sami aiki a wata makaranta yanzu haka ni ne Director a school en, last month ma na saya wancan machine ɗin da kike gani". tace,"wow congratulations". yanda ta faɗa kace wata baturiyar gaske, kawai sai ya waigo yana kallonta da burgewa da sha'awa. yace,"Halimatu yanda kike da kyau da burgewa haka komai naki yake, kinji ko in kika yi english kamar a bakinki aka yisa, ina irin americans ɗin nan na cikin tv masu news?, wallah fa kamar haka, taya hakan ya kasance?". ta basa labarin komai tare da cewan,"kuma Adda Zaytuna da Maama ma totally bama hausa da su yanzu, wurin da nayi mistake zasu gyara min". Amir yace,"masha'Allah, Allah sakama mutanen gidan nan da alkhairi, but". tace,"but what?". ta tambayesa ƙwayar idonsa na shaida mata kishin dake ransa, tai murmushi tace,"teacher ɗin ma fa inyamuri ne, duk ya zama jagwal, shi ko kallo ma bai da shi". ya lakuce mata kumatu yace,"time ɗin da zai kalle ki ai ba sani zaki yi ba. gwarama muyi auren ni naci gaba da koya miki". ta ware ido,"Maama ai tace zan zana waec na wuce UNI". ya fincikota gabansa yace,"UNI ɗin da zaki je ta wuce gidana". sai da suka kusa 1hour tsaye a wajen suna hira kafin hankalin Fillo ya dawo jikinta, don gaba ɗaya Amir yayi amfani da salon soyayyarsa ya kawar da duk wani fushi da take yi akansa, kuma ita kanta bata san sanda salon soyayyar ya ɗebeta ba ta manta da komai, har ta sake da shi suka koma kamar ba suyi faɗa ba. tana leƙen agogon hannunsa tace,"Amir time, tausa fa nake ma Boɗejo na taso. kuma haka nace yanzu zaka tafi, ni duk naji ma ina jin kunya dan wannan tsohuwar sai ta ɓaro ni". yay murmushi me sanyi yace,"shikenan ki koma ciki, amma zan dawo da daddare bayan kin koma aiki, ban gaji da ganinki ba gaskiya". su kai sallama zai tafi yace,"i love you so much Halee". tace,"thank you, bye bye. ka gaida Inna". ta faɗa tana juyawa don barin wajen. ai da sauri ya riƙo hannunta ya koma gabanta yana faɗin,"Allah sai kin faɗa". ta shagwaɓe fuska tana cewa,"zan faɗa but not now, not 2day". yace,"ai kinji na rantse". sai da ta kulle idonta tukunna ta iya cewa,"i love you too". ta faɗa Amir na jin wani mugun daɗi acikin ransa, ya kama hancinta ya ɗan ja sannan ya saki hannunta asking her me take so ya taho mata da shi anjima, tace duk abinda yaga ya dace da ita. ya juya ya tafi yana ɗaga mata hannu, itama cike da kunya take ɗaga nata. sai da ya hau machine ɗinsa ya tafi sannan ta nufi gate. daga Amir har Fillo cikinsu babu wanda ya lura da motar da tai parking daga can gefensu, tun fara hirarsu ba jimawa, haka yanzu ma da ta zo shiga gidan bata kula da motar ba, so tana zira ƙafarta cikin gate taji an mugun danna horn kamar za'a tashi duniya, ta juyo a tsorace tana kallon bayanta. ba tare da gama tantance motar waye ba ƙarar horn ya kuma shiga kunnenta tana jin kamar dodon kunnen zai mutu. ta ɗan yatsine fuska tana shigewarta tunda ba huruminta bane na me gadi ne, bata taɓa ganin kalar motar ba acikin gidan balle tace ta gidan ce. ta shige da saurinta, kiciɓis suka yi da mai gadi ya fito daga banɗaki riƙe da buta a hannunsa sai sauri yake yi. yace,"ƴar nan Allah sa ba Alhaji bane". Fillo tace,"wallah ban sani ba Baba, amma motan kamar bana gidan ba, ban dai sani ba". Me gadi ya fice da sauri, ganin ba motar gidan bace yasa shi ƙarasawa don ganin waye. Turaki ya gani aciki fuskarsa kamar an aiko masa mutuwa, ya tabbatar da AC kunne a motan amma yana ganin yacca zufa ta tsatstsafo a goshinsa. Me gadi ya rissina yana faɗin,"ranka ya daɗe ashe kaina, kayi haƙuri na shiga banɗaki ne. motar kuma ban shaida ta waye ba shisa, bari inje in buɗe". da ƙyar Turaki ya iya buɗe baki saboda yacca yake jin kansa kamar zai fashe yace,"ba gate zaka buɗe ba, yarinyar da ta shiga yanzu zaka kira, da sauri". cikin sauri me gadi ya koma, lokacin Fillo na dab da entrance na side ɗin Boɗejo taji me gadi na ƙwala mata jira. "ki zo da sauri yallaɓai ne ke kira". ita da yace yallaɓai sai tayi zaton ko Baffa yake nufi. don haka ta ɗago ƙafa tana cewa,"tom". shi kuma yana ƙara cewa,"yace kije da sauri". Fillo ta ƙara saurin tafiyarta har tana jin kaman za tayi tuntuɓe. tunda ta fito jajayen idon Turaki ke kanta har ta ƙaraso ta ɗayan glass ɗin, ya sauke glass ɗin ba tare da ya waiga ya kalli ko da inuwarta ba. dan a yacca zuciyarsa ke tafarfasa zai iya shaƙota ya shigo da ita ta cikin glass ɗin. Fillo ganinsa yasa gaba ɗaya ta tsure, da ƙyar ta tattaro yawun bakinta tace,"gani". ta faɗa kamar me koyon magana, bala'in tsoro na kamata saboda yanayinsa da ta gani, ita ko babu yanayinsa ma tana jin tsoronsa. "buɗe ki shigo". haka taji amon muryarsa tamkar saukar aradu aka. zata tsaya tunanin maganar tasa taga ya juyo a fusace ya zuba mata rikitattun idanuwansa da suka koma kamar na tiger. babu shiri ta nufi ƙofar baya zata buɗe a tsawace taji yace,"kika shiga nan babu abinda zai hanani ɓalla ƙasusuwanki na zubar a wajenan". take ruwan hawaye ya sakko mata ta dawo tana buɗe gaba ta shiga da tsananin ruɗewa, duk ta firgice ta gigice. ta rufo ƙofar motar tana kifa kai akan cinyarta ta fashe da kuka. Turaki ya dinƙa kallonta babu ko ƙifta ido, a hankali kuma ya mayar da ƙwayar idonsa kan hannun hagunta da Amir ya riƙe for morethan 2tyms, yaji zuciyarsa ta ƙara tamkewa, trying his best to be very calm gudun kar ya illata ƴar mutane, ya damƙo tsintsiyar hannunta dake rawa yana mata mugun riƙo kamar zai karya ƙashin wajen. ta ɗago da kanta a gigice tana kallonsa da tsananin jin zafin riƙon. cikin muryar kuka tace,"me nayi maka?". tambayartata yaji kamar ya tsinka mata marin da zai yi sanadiyar ɗaukewar jinta da ganinta gaba ɗaya, wataƙila hakan yasa tasan laifinta. acikin rishin kukan da take yi tace,"jiya fa kace ka haƙura, amma tunda baka haƙura ba i will give you half of the money now, ending month sai na cika maka sauran". shi dai kallonta kawai yake yi yana tunani iri iri cikin ransa, tana batun ta basa 25k now, aina ta samu 25k?, wanda ya tafi ne ya bata?, me tayi masa ya bata?. sai ya rumtse ido gam yana ƙara damƙe hannun da mugun ƙarfin da yafi na ɗazu har sai da ƙashinta yayi ƙara, idan ce masa akayi an ganta da wani ba zai taɓa yarda ba don ba tayi kama da wadda zata tsaya da namiji ba, amma with his own 2eyes ya ganta tsaye da namiji a inda babu kowa sai su kaɗai, ƙofar gidan da babu masu wucewa, sama da rabin awa suna hira cikin nishaɗi har tana wage masa all her 32teeths. which kind of purnishment did he supposed to give her?, shin ya ɗimautata da sanar da ita cewar akwai igiyoyin auren wani akanta guda uku reras?, ko kuma yayi mata abinda ba zata ƙara kallon wani namiji ba a rayuwarta?, balle harta bari ya riƙe mata hannu har tai masa dariya har ta barsa yaja hancinta. "wallah zan baka 25k daga baya zan cika maka sauran, amma kayi haƙuri ka sakar min hannu da zafi wallahi, ƙashina ma har ya ɓalle ina jin". tsabar ƙuluwa Turaki bai san lokacin da ya dunƙule hannunsa ya daki bakinta ba ya fashe, shi zata faɗawa ya sakar mata hannu bayan ita halalinsa ce?, and ta iya barin wani ƙaton banza can daban da ba muharraminta ba ya riƙe mata hannu ba tare da ta hanasa ba?. Fillo ta fashe da kuka sosai tana sa gefen mayafinta ta danne leɓenta da ya fashe. "ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?". kuka take sosai tayi maganar, idon Turaki manne akanta yana hasko tsayuwarsu da Amir, cikin jin zafi a heart ɗinsa ya kulle idonsa, yaja motar with high speed kamar duniya zata tashi, tayoyin motar suka bada sautin ƙuuuuu akan kwalta, wannan ƙarar ta haddasa tsoro na bala'i a zuciyar Fillo, kuma tsananin tsoron yasa farat ɗaya ta ɗago da kanta dake kan cinyarta, ganin yanda yake zabga mugun gudu akan titi tayi jikinsa a rikice ta riƙosa tana faɗin,"kayi a hankali dan Allah zamu yi accident fa, ka daina nufar bishiyan can". *Please vote, comment and share.* [8/28, 19:06] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *29* motar Turaki bata tsaya a ko'ina ba sai a compound na cikin company nasu, ƙarfe biyar na yamma a lokacin, and at that time an ma yi closing, bai san exact abin da ya shigo da shi ba, kawai ɓacin ransa ya kaisa. yay parking yana daɗa tabbatar da duka glasses na motar a rufe suke, ya kunna karatun qur'ani sannan ya buɗe lock. ya kalli Fillo da har lokacin kanta ke kife a gefen kafaɗarsa, tun san da ta ke roƙon yay driving nasu a hankali taga baida hankalin dainawa shikenan sai tayi shiru, kuma tsoron da takeji shi ya hanata ɗagowa a kafaɗar tasa. wucewar 20seconds yana kallonta, yana jin yanda numfashinta ke sauka a hankali, a tunaninsa duk bacci ne take yi, nan kuwa tsabagen zuciya ce tasa tai luff kamar wadda baccinta yay mugun nisa, wani irin zafi take ji a zuciyarta kamar ana rura wuta, in ace ta ɗago a ɗazu da tabbas babu abin da zai hana hannuwanta shaƙe Turaki, in yaso suyi accident ɗin da gasken gasken. kafaɗarsa ya janye nan take kanta ya ƙwalu da kujeran, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda suke, bata ko motsa ba har ya fice daga motar, tana kallo ya saka lock ya wuce ya barta, ita kuma ta rakasa da ido. tana ganin yacca ƴan tsirarrun staffs da basu wuce ba kowa na gaida shi, shi kuma yana ɗaga musu hannu. duk ƙoƙarin da tayi don ganin lock ɗin motar ya fita ta kasa, kenan rufeta yayi a motar ya tafi ya barta?, koma me zai faru da ita ya faru da ita?, to me yake nufi da ɗaukota ɗin?, ga shi ya kashe Ac balle ta samu sauƙin zafin gari da na zuciyarta da take ji. wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, sai ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka, kuka take sosai har tana jin kamar zata shiɗe, ga kanta na uban sara mata, ga zufa duk ta wanke mata jiki, sai da tayi me isarta tukunna ta ɗago tana goge hawayen, tana jan majinar hancinta ta ƙara trying buɗe motar amma taƙi buɗuwa. sai kawai ta jinginar da kanta jikin kujerar ƙirjinta sai bugawa yake, ta cikin glass ɗin ta fahimci magriba ta gabato saboda yanayin yacca garin ya lulluɓe, zuwa lokacin duk staffs sun ɗaɗe sai me gadi kawai da take iya hangowa ta cikin mirror. ta rufe idonta tana bin suratul Yusuf dake tashi cikin ƙira'ar Yousuf Kalo. Turaki kuwa tunda ya shiga office ɗinsa zama yay kawai ya rufe idonsa, yayi hakan ne kawai saboda temper ɗinsa yay cool, dan in yaci gaba da kasancewa tare da ita a yanda yake mugun jin haushin abin da tayi ba abin da zai hana sa illata ta. sai da ya ɗauki tsawon awa guda bai motsa a yanda yake ba, yana kallon kira daga different numbers na shigowa wayarsa amma babu ɗaya da yay picking. Fillo dai har sannan tana zaune sai wurga idanu kawai take yi, Allah ɗaya yasan yanda take ji a cikin ranta, taja Allah ya isa tafi kai ashirin, in ace da wani abu da zata iya fasa glass ɗin tuni ta fasa ta fita ta windown. tana cikin tunani a ranta sai taga Turaki ya fito daga wani building daban da inda ya shiga ɗazu, cikin sauri yake tafiya yana sauke hannun rigarsa da ye tattare, da alamu alwala yay zai wuce masallaci tunda ga ruwa nan a fusakarsa. bata ɗauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, bayan minti goma sai taji lock ɗin motar ya fita, kuma kamin ta kai ga buɗe murfin idonta taji ƙofar side ɗin da take ta buɗe. "out". taji muryarsa ta shiga kunnenta san da take buɗe idonta duka. kamar tayi banza da shi sai kuma taji tana tsoron yin hakan, Allah shahidi bata tsoron uban kowa a duniyar nan amma tana mugun shakkar Turaki. ta tattaro mayafinta tana ƙudundune jikinta sannan ta fito a cikin motar ta tsaya a gefensa, tana fitowa ya rufe yay gaba yana cewa da ita,"follow me". tabi bayansa tana ɗan kalle-kalle, sai yaba kyan company ɗin take yi, daga waje ma kenan ina kuma ga an shiga ciki. suka shiga cikin office ɗinsa sannan suka wuce cikin wani ƙaton parlo, inda anan ne yake Turaki ke hutawa. "kiyi sallah". abinda yace mata kenan ya wuceta ya zauna kan ƙaton farar cushion. Fullo ta kalla haɗuwar parlon ta ƙara kallo tana me jinjina uban yawan dukiyar da aka kashe wajen ginin company ɗin da kuma abinda aka zuba acikin office ɗin, wato kuɗi dai suna inda suke, talaka da baida su ne yake ganin kamar babu su kwata-kwata. kanta a ƙasa ta fuskanci kujerar da yake zaune, muryanta a hankali tace,"banda alwala". yanda tayi maganar kawai yasa shi ɗago da kansa yana kallonta, ko kurma yaji sautin murayar nata yasan da ɓacin rai aciki. sosai yake kallonta da son gano abin da yasa tayi uban hasken da yake gani ajikinta, ba haka yasan asalin hasken fatarta ba, to daga ina wannan mugun farin?. jin yay shiru ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, ta tsuke fuska da baki tana ƙara ɓata rai. shi kuma yay mata nuni da hannu yana mata nuni da toilet. bata motsa ba kawai ta tsaya, ita ba zata iya shiga toilet yana zaune a wurin nan ba, sai dai in su shekara a haka, in yaso daga baya ta rama sallolin. da kansa ya gane manufarta, hakan yasa ya miƙe ya fice bayan yace mata,"don't waste my time". yana fita ta shiga toilet ɗin, cikin toilet ɗin kansa mugun ƙamshi yake kamar ba'a shigarsa. tai alwalan ta fito, mayafinta ta yafa ta tayar da sallah akan darduman da ta gani. la'asar da magriba tayi a haɗe, bayan ta idar ta duƙar da kanta saboda mugun sarawar da taji yana yi, ga jikinta ya fara zafi alamun fever na son kamata. ita kanta ta san ma dole tayi zazzaɓi da ciwon kai ko saboda kukan da tasha a yau. minti 1,2,3 har minti ashirin suka wuce Turaki na zaune office yana jiran fitowarta amma shiru. cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi jira take ya koma yace mata ta fito, tsaki yaja ya tashi ya koma cikin parlon. zaune ya ganta har sannan akan darduman kaman me lazimi, to amma jin motsinsa bai sa ta ɗago ba, alhalin ya santa da shegen tsoro, ya tsaya yana kallonta yaga dai durƙushen kanta kamar ba na lafiya ba tukunna ya ƙarasa ciki ya zauna kan kujerar dake kusa da ita. yasa hannu ya ɗago kanta looking at her innocent face da yay ja, with the other hand ya taɓa forehead nata yaji zafi rau. ya rufe idonsa kaɗan ya buɗe yana ganin yacca hawaye ke suntiri akan kumatunta, kallon hawayen yake yana hango lokacin da yake zaune a gaban Hayyo yana faɗa masa cewar,"ehh kamar uba nake a wurinta amma ni ba mahaifinta ba ne, wannan yarinyar da kake gani ai ƴar zina ce, ƙwarai ƴar gaba da fatiha ce ranka ya daɗe, mahaifiyarta ma mahaukaciya ce, garin haukar nata ta gudu shekaru da yawa har yanzu bamu ganta ba, kuma har yanzu ni ban saketa ba. amma dai saboda a rufawa yarinyar asiri indai da gaske kake sonta ranka ya daɗe kawai ka biya sadakinta yanzu a take, batun sauran kayan al'ada da ake yi duk ba sai kayi mata ba, tunda dama ba faɗar addini bace, sadakin dai nata kawai ka kawo itama idan an bata babu hankalin riƙe su, tunda dama ni ne maɗaurin aurenta, babu wanda ya san danginsu tunda a titi na tsinci uwar naji tausayinta na aureta. ita kuma tsohuwar da kake cewa Yarinyar na hannunta gaskiya to ban ma san wace ba, ƙila ma ko irin tsaffin nan ne macuta". ya ƙara hasko lokacin da yasa hannu a aljihunsa dan ɗauko kuɗi, amma sai yaji babu komai. sai ya ƙara kallon Hayyo wanda ya gano tsananin kama ta Fullo a tare da shi, ya sauke numfashi yana me jin wani iri a ransa, zuciyarsa na ƙara ƙarfafa masa miƙa sadakin Fillo, ko da bai aureta saboda taimakon da tayi masa ba, tabbas ta cancanci a aureta saboda rashin dace na uban ƙwarai, dan ko kaffara ba zai yi ba Hayyo shi ne mahaifinta. to amma da me zai bayar da sadakin nata?, yay shiru yana tunani cikin ransa, ko kaɗan ba ya so ya miƙe daga kan tabarmar nan ba tare da ya mallaki yarinyar da ta dinƙa cusa kanta a haɗari ba saboda kawai ta cece shi, ba don so ko kuma wani abu daban ba, sai son kyakykyawar zuciyarta. yana iya tuna yacca ya dinga jin kallon da Hayyo keyi masa, yana tuna furucin da Hayyo yayi masa kan cewar,"ranka ya daɗe in har babu sadakin yarinyar nan kazo ayau, to ina mai tabbatar maka da cewar ba rabonka ba ce, domin kuwa tun tana ƙarama akwai wani tsoho da ya roƙi a bashi ita, to banda ma dai tasa ƙafa ta gudu da maganar da nake shaida maka yanzu tayi ƴaƴa kusan uku. dan haka kana tafiya zan yi masa magana ya bada sadakinta, in yaso tunda Allah yasa kai kasan inda take, sai kayi mana jagora muje mu taho da ita". "zan bayar da sadaki, amma sai naga shedu". haka yasan ya faɗa masa, kuma minti goma ba'a ƙara ba sai ga Hayyo ya dawo tare da mutum huɗu, ya shaida mutum ɗaya wanda Hayyo ya nuna masa yace shi ne limamin babban masallacin anguwarsu, saboda lokacin da ya shigo unguwar ya tsaya yayi sallah a masallaci, dalilin da yasa ya gane shi kenan, sai mutum ukun da bai sansu ba, amma daga tsufansu ya san ba mutanen banza bane. yana tuna sanda Liman ya buɗe baki ya tambayesa ina waliyansa, kuma a lokacin magana ɗaya ya faɗa wadda daga ita ba wanda ya ƙara cewa komai Liman yace ya miƙo sadakin. "ni maraya ne, bani da kowa sai Allah". hakan ya faɗa musu, kuma daga faɗar hakan babu wanda ya ƙara masa wata tambaya aka ce ya ajiye sadaki. still idonsa na kan Hayyo yace,"banda kuɗi yanzu". kuma tun bai rufe bakinsa ba Hayyo yace,"kana iya tashi ka tafi, yarinya dai ba rabonka ba ce". zuciyarsa ta faɗa masa cewar in har Fullo zata iya sadaukar da ranta da kuma lafiyarta akan ta kuɓutar da shi daga wani ƙulli, alhalin ba dangi iya bare na Baba, to ba ya jin shi zai kasa iya sadaukar da komai nasa don ganin ya mallaketa, mallakarta kaɗai shi ne sakayya mafi kyautatawa da zai yi mata. saboda haka take a wurin a ajiye key ɗin motarsa a gaban Liman yace,"na bayar da motata a matsayin sadakinta". ba zai taɓa mance yanda Hayyo ya dinƙa kallon maƙullin motar ba with so much expression, har ƙwayar idonsa irin ta Fullo na yin kamar zata faɗo waje. amma duk da haka sai da yasa aka shiga cikin gida aka kira masa wani saurayi, saurayin shima me kama da Fullo sak, idan bai manta ba sunan da Hayyo ya kira saurayin da shi ne,"Hamid". saurayin ya amsa masa da,"na'am Abba". sannan Hayyo ya ɗago kai ya kallesa yace ya zagaya baya, ya gano masa motar da ke wajen kuɗinta zai kai nawa. and abinda Hamid ya dawo ya sanarwa da Hayyo shi ne,"kuɗinta zai kai miliyan hamsin ko sama da haka". kuma ba tare da ƙara yin wani bincike ba Hayyo ya kalli ƙwayar idon Turaki yace masa,"kaje yarinya ta zama mallakinka, aure ya ɗauru". haka ya baro garin Taraba a train zuciyarsa cike da tarikan mamaki iri-iri a game da lamarin Fullo da mahafinta, duk da cewar yaso ya keɓe da Hamid to amma bai samu dama ba. Fillo ta buɗe idonta dake yi mata zafi tana kallonsa, idonsa a rufe yake, har sannan kuma bai saki kan nata ba. in cool voice nata tace da shi,"please ka daina taɓani any how babu kyau. kuma dan Allah ko kuɗin napep ne ka bani na koma gida, Maama da Boɗejo zasu neme ni, turarenka kuma zan biyaka insha'Allah". a sannan Turaki ya buɗe idonsa yana ɗauke hannayensa akanta. yana kallon gefe daban kamar zai yi magana sai ya fasa ya miƙe. ya nufi ƙofar fita yana cewa da ita,"biyo ni". ta tashi cikin sauri tabi bayansa. tunda suka hau titi take ta kallon hanya har suka iso asibitin Miyetti, fita yay a motar ya barta ita ɗaya ya shiga pharmacy ya sayo magunguna ya dawo, sannan suka ɗau hanyar gida. ko da suka ƙarasa gida Turaki yay parking sai Fillo ta kasa fitowa a motar, ta tsinci ƙafafunta da kasa yin motsi su fita daga motar. tana kallo ya fice ya barta a ciki, sai ta bisa da ido tana kallo ya wuce side ɗin Boɗejo, gaba ɗaya ta rasa me take ji a tare da ita, tasa hannu zata buɗe motar ta fita sai ga motar Samha tayi parking kusa da ta Turaki. da dukkan alama tun fitar safe da tayi sai yanzu ta dawo, Fullo tayi saurin maida ƙofar tana rufewa a hankali gudun karta ji ƙara, kasancewar tend glass ne amotar hakan yasa babu me hangota a ciki sai dai ita ta ga na waje. tayi ɗuff ta ɗauke wuta dan ji take kamar zasu iya jiyo numfashinta. Sameer taga ya fito daga driver seat sannan Samha ta fito ta ɗayan seat ɗin, ta zagayo ta side ɗin Sameer ta karɓi roban Maltina a hannun Sameer, sun ɗauka atleast 2minutes su.na magana kamin su saki murmushi, tukunna suka bar wajen su na wucewa cikin gida. Fullo taji ta wani girgiza, bata san wannan shirin nasu kuma na menene ba, bata ji su ba, bata san me suka ce ba. taja nunfashi ta ɗauka ledar maganin da Turaki ya saya ta fita daga motar, cikin saurin tafiyarta tayi side na Boɗejo cikin zuciyarta tana ta fatan kar Allah ya bawa Samha ikon ganin Turaki, haka kawai zuciyarta ke faɗa mata wannan roban malt ɗin ba malt bane kawai a ciki, haka kuma ba don kowa aka shigo da shi ba sai don Turaki, tafiya take tana harɗewa tana ƙara jin tsoron mutum acikin ranta, idan ba a film ba bata taɓa tunanin za'a iya samun siblings ɗin da zasu iya kashe ɗan uwansu a gaske ba, sai ga shi yanzu ta gani a zahiri, abin na faruwa a inda take rayuwa. maganar Hajiya Madina ta haska cikin kanta, lokacin da tace mata,_"ba halina ba ne, ba haka zuciyata take ba, tunda Allah ya halicceni banda mugun nufi akan kowa, zuciyata bata da tsatsa ko kaɗan, kullum roƙon Allah nake kar yasa na cuci wani a rayuwata, amma ban san a ina Samha da Sameer suka ɗauko wannan mugun halin ba, ban sa ni ba, dan ba halin mahaifinsu ba ne..."._ kasa ƙarasa maganar tayi a lokacin saboda kukan da ya ƙwace mata. kamar wadda tayi gudun famfalaki haka Fullo ta shiga parlon Boɗejo, gaba ɗaya ma sallamar ta mance da ita. babu kowa a parlo dan haka kai tsaye bedroom na Boɗejon ta wuce, ta san ba zai wuce can Turaki yayi ba, ta buɗe ƙofar tana shiga da sallama. Ilham da ke gefen Turaki a zaune ta amsa sallamar tana faɗin,"bismillah". gaba ɗaya Fillo sai taji ƙafafuwanta sunyi matuƙar sanyi, bata san dalili ba amma haka kawai taji gabanta ya faɗi da ganin Ilham da tayi da kuma yacca ta ganta zaune manne ajikin Turaki. zuciyarta taji na faɗa mata cewar kawai tayi reverse, amma sai taji ta kasa gaba ta kasa baya. Ilham na kallonta sosai tace,"ki shigo mana, ba aiki za ki yi ba?". kan Fullo a ƙasa tace,"ehh". Ilham tace,"to bismillah". Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, ta shigo ciki idonta a rufe tana jin kamar jiri ne ke neman ɗibarta ya zubar. Ilham na riƙe da hannun Turaki tace,"to Hammah ba sai mu tafi tare ba, tun fa da na dawo ban ƙara zuwa ko'ina ba, Mami sai tace wai a'a, kuma ni ko dubai ina so naje na sha iska, please Hammah zan bika". ya kama hancinta yaja ba tare da ya ce komai ba, wucewar 3seconds ya miƙe ya fita Ilham tabi bayansa, Fullo kuma da ke tsaye gefe guda ta bisu da kallo. su na fita ta jefar da ledar hannunta akan kujera, taji kamar tana so tayi kuka, amma ba zata yin ba saboda har yanzu kanta ciwo yake yi mata. ta rumtse idonta sosai, da ƙyar ta iya gyara abin da zata gyara a ɗakin cikin few minutes ta fice. tana fitowa parlon ta tadda Turaki zaune a kan kujera shi ɗaya, da remote hannunsa yana sauya channel. ta tsaya tana kalle-kalle ko zata ga Ilham, sai dai da dukkan alama bata nan. table ɗin gabansa tabi da kallo, fruites ne acikin plate sai roban malt a gefen plate ɗin. tayi tsaye daga inda take sai kallon roban take yi, kamar me son ganin wani abu aciki. tayiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai, bata san me yasa ba haka kawai taji tana mugun jin haushinsa for the first time. inda yake ta ƙarasa ta aje ledan maganin kusa da shi tana cewa,"ka manta a mota". sannan ta kai hannu kan table ɗin ta ɗauke roban malt ɗin zata bar wajen. yay saurin riƙo hannunta ya dawo da ita,"ɗauka ki tafi da su". ta waiga ta kalla ledan sannan ta kallesa, tace,"maganin da ka saya ne fa". shima ɗin yana kallonta yace,"nayi miki kama da mara lafiya?". Sai ya galla mata harara yace,"ɗauka ki wuce da shi". kamar zata yi kuka tace,"shi maganin dama haka kawai ake shansa?, kawai daka sami magani sai kace dole sai na sha. ka barni na wuce please Kaka na can na jirana". Ya janyota ta zaune kan kujerar kusa da shi. zai ƙwace roban malt ɗin ta damƙe da kyau. ya dinƙa kallonta da mamaki kafin ya iya buɗe baki yace mata,"aje". ta maƙe kafaɗa ba tare da tace komai ba. ya ƙara ware idonsa yana kallonta, ta rufe ido ta cije fuska tana son janyewa a kusa da shi ta tashi. jin ba zai saketa ba ta buɗe ido ta kallesa tace,"ni wannan nake son sha ba magani ba, don Allah ka bar min". bai san time ɗin da ya saki baki ba yana kallonta, in bai manta ba lokacin da aka kwantar da ita a asibiti uban malts ɗin da aka ajiye ai duk ƴan dubiya aka dinƙa bawa saboda bata sha, hasalima ko anyi forcing nata tasha sai tayi amansa, amma yanzu shi take ce ma malt take son sha. sai ya sassauta riƙon da yay mata yana ƙara tamke fuskarsa yace,"aje nace". ta kallesa taga yanda idonsa ya kaɗa yay jawur, sai kawai ta kifa goshinta akan ƙafarsa ta fashe da kuka. ya waiga yaga har yanzu Ilham bata fito a kitchen ba, dan haka da azama ya miƙe ya ɗau ledan drugs ɗin sannan ya kama hannun Fullo suka fice daga parlon, tana ta tirjewa yaƙi sakinta har sai da suka shiga ɗakinsa, ya wurgata kan gado yana saka key ajikin ƙofar, sai dai abin da ya matuƙar ba shi mamaki yana waigowa yaga ta buɗe roban malt ɗin tana zubar da shi a ƙasan tiles. *vote, comment and share.* [8/29, 12:57] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *30* Turaki ya harɗe hannayensa a ƙirji yana ta kallon yanda Fullo ke juye malt akan tiles, sai da ta juye tass tukunna ta turo ɗan ƙaramin bakinta da ya ƙurawa ido, yaga ta tashi without looking at inda yake tsaye ta wuce inda wani ƙofa yake ta buɗe, waje ne kamar balcony, mopper ta ɗauko ta dawo tukunna ta shiga toilet ta ɗebo ruwa ta goge wurin tas da turaren ƙamshi me daɗi. kamar yanda bai san me zai ce mata ba haka bai san abin da zai yi mata ba. duk tana jin yacca kallonsa ke shiga jikinta amma tayi kamar ta manta tare suka shigo ɗakin, in ace ba Turaki ba ne ba zata taɓa yarda ta ɗau tsayin sakanni ba balle mintuna tare da wani ƙato a ɗaki ɗaya, but shi ko da yaushe zuciyarta faɗa mata take yi he is a good person, he will not hurt you, sai dai ma ya kare mutuncinki da iyakar ƙarfinsa. kuma kamar yanda zuciyartata ta faɗa mata haka Hajiya Madina ta faɗa mata,_"me babban suna ba zai taɓa cutar da ke ba Fullo, ko kaffara ba zanyi ba akan hakan, saboda haka kar ki taɓa jin ɗarr dan kun kasancewa wuri ɗaya tare da shi"._ kuma in the same day ne bayan ta koma ɓangarensu, da Kaka ta ganta a firgice ta tambayeta lafiya?, ta faɗa mata cewar tana ɗakin Maama ne Turaki ya shigo, kuma ya hanata fita yace taci gaba da aikinta shi kuma ya kwanta kan kujera. abin da Kaka tace mata a lokacin shine,_"ba'a shaidar ɗan kuturu sai ya kwana 100 da yatsa, to amma ni zan shaidi Turaki, ba wuri ɗaya muke kwana mu tashi ba, ban san halinsa ba, amma zanyi rantsuwa kan cewar Turaki ba zai cuci ƴa mace ba, ko da ace kuwa zasu kwana wuri guda. kawai dai ki kula sosai Fullo"._ sai da ta gama mopping en sannan tayi bakin ƙofar wurin da har yanzu yake tsaye, tayi ƙasa da kanta sosai ƙirjinta sai bugawa yake yi, tana ta aikin jan yatsu shi kuma yay shiru kamar baya wurin. sai da ta gaji da tsayuwa tukunna tace masa,"dare yayi, Kaka tana jirana". tai maganar a sanyaye. ya sauke hannayensa ya zuba su cikin aljihu sannan yace mata,"kin gama shan malt ɗin?". da mamakinsa sai yaga ta ɗaga masa kai alamar eh, ya ƙara cewa,"ya isheki ko a ƙaro?". tace,"ya isheni". hannunta kawai ya kama suka koma zuwa ciki, har yanzu jikinta kwai zafi sosai. yay mata nuni da bakin gadon na alamar ta zauna, tace"don Allah". maganar ta katse dalilin haɗa idon da suka yi yana jifanta da wani wawan kallo. babu shiri ta zauna hawaye na biyo kuncinta, yaja stool ya zauna yana ce mata,"tare aka haife ku da kuka ne?". tai saurin girgiza kai, yace,"to yi min shiru, in kuma anan kike so ki kwana kar ki fasa". babu shiri tayi ɗif tana goge hawayenta da gyalenta. shiru ya gimla cikin wasu ƴan sakanni, tana ɗago ido ta kallesa taga yana ɓallo magani, bata san lokacin da tace,"ni kam na shiga uku". yaci gaba da ɓallan maganin sannan yace da ita,"bani ruwa". cikin azama ta miƙe ta nufi ƙofa zata fita, a dabararta na in ta fita ba zata dawo ba, amma tana zuwa taji yasa key a ƙofan, ta waigo tana ce masa,"ƙofan rufe yake". ba tare da ya kalli inda take ba yace,"not necessary sai kin fita, ga ruwa nan akan drower". taji kamar tai ihu, sai kace wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta wuce inda roban faro yake ta ɗauko tare da cup, ta kawo masa yace ta zuba a cup, ta zuba sannan ya kamo hannunta ya zuba maganin yace ta shanye. da ƙyar ta sha maganin tana sha tana hawaye, suma da guda ɗai-ɗai ta dinƙa sha, tana gama sha sai ga amai nan ya taho, ta miƙe da sauri tayi hanyar toilet taji yace,"idan kin gama aman sai ki kwanta anan". ya faɗa yana nuna mata gado da bakinsa, tare da miƙewa zai fice. kamar wacce aka dannawa pause haka ta tsaya tana sa hannu ta rufe bakinta, idanuwanta suka firfito waje dan ita ɗaya ta san me take ji, haka har sai da maganin ya koma, tana sauke numfashi tace,"na shanye". yay mata shiru ya fice ya barta, yin duniya ta buɗe ƙofan duk da cewar there is spare key amma ƙofan yaƙi buɗuwa, means ya bar key ta waje kenan, wucewar five minutes sai ga shi ya dawo da coolern abinci a hannunsa, tana kallo ya wuce sai dai at this time ta kasa attempting buɗe ƙofan, binsa tayi da ido kawai har ya zauna kan kujera. ya waigo da kansa yay mata kallo ɗaya, kuma take ta gane nufinsa a sanda suka haɗa ido, ta taho a hankali tazo ta zauna a ƙasa, ta ɗauko coolern dake kan table da plate ta zuba soyayyan taliya da vegetables ta zuba kaɗan, kuma kamar ance ɗago ta ɗago taga ya zabga mata wani nugun kallo, ba shiri ta ƙara abincin ya ɗanyi auki sannan ta fara ci. har ga Allah dama yunwa take ji, rabonta da abinci tun safe, hakan yasa ta zage tana cin abincin, ba ta ankare ba taga har ta cinye. son samu ace tayi ƙari to amma ba zata iya ba, Turaki dai idonsa na cikin glass yana operating laptop ɗin dake gabansa, tana ta kallonsa for almost 2minutes taji agogon ɗakin yayi ƙara, tana dubawa taga har 8:30. ta juyo tana ƙara kallonsa tace,"don Allah ka buɗen ƙofan na tafi, hakan babu kyau, Kaka tana can tana jirana". ya kalleta ya kalla coolern gabanta yace,"kin cinye?". ta girgiza masa kai,"na ƙoshi". yana ta kallon coolern yace,"buɗe na gani". ta buɗe yaga saura kaɗan bai fi spoon goma ba, ya galla mata harara yace,"juye ki ƙarasa cinye shi, wa kike tsammanin ya cinye sauran jagwalgwalonki?". ta marairaice tace,"cikina na ciwo". yace,"zo ɗau magani ki ƙara". sai ta rumtse ido sosai tana yin ƙasa da kanta, ta shiga afa abincin kamar me cin magani. kafin ta ɗago ta kallesa taga yanda idonsa ya sauya kala, haka ɗaya sai taji bala'in tausayinsa cikin ranta. kuka ta ke son yi amma bata so ta yi gudun kar ciwon kanta ya ƙaru, ga shi duk iyakar ƙoƙarinta ta kasa yi masa rashin mutuncin da ba zai ƙara sa shi shigo da ita ɗakinsa ba, infact kallonta ma ba lallai ya ƙara yi ba, to amma daga zaran tai attempt na yi masa wani abu sai wannan girman kwarjinin nasa ya tarwatsa duk plans nata. with breaking voice tace,"baka ci abincin ba, kuma ɗazu kace kana jin yunwa, ka cinye wannan ɗin". kai tsaye ya bata amsa da,"yara ne suka girka". yanda voice ɗinsa ya fita sai ta ƙara jin tausayinsa haka siddan. tace,"to haka zaka kwana da yunwa?". still ba tare da kallonta ba yace,"Maama tayi bacci". sai tai shiru tana kallonsa, taji ƙwalla ta cika idonta da tausayinsa, ta lura ba ya iya sakewa idan ba tare da Hajiya Madina ba, haka kuma magana ma baya iya yinta sai yana tare da Maama ko Zaytuna, da su kaɗai take ganinsa taga yana ta zuba magana har haƙoransa su dinƙa washewa da dariya, to randa kuma aka ce mahaifiyarsa ta dawo fa?, tunda ta fara aiki bata taɓa ji ko ganin yaci abincin da ba Maama ce ta girka ba in har a gida yake, ko office ya fita sai Maama tayi girki an bawa driver ya kai masa, to hana rantsuwa ita yasa ta taɓa dafa masa indomie ya kuma sha kunun da ta dama, wataran har Nihal ke tsokanarta da Fullo ƴar sa'a, Hammanmu yaci abincin hannunki. anan hawayen da suka cika idonta suka sami nasarar gangarowa, kewar tata mahaifiyar ya daɗa kamata, duk da Kaka na faɗa mata zuwa yanzu Ummi ta rasu, amma ita ajikinta ba ta jin hakanne, tana ganin kamin duniya ta tashi kamar zata ga Ummi, kamar zasu ƙara rayuwa tare da Ummi, kamar Ummi ta kusa dawowa gareta, amma sai zuwa yaushe zata ga Hammah Hamid?. wayar Turaki tayi ringing, bai ɗaga kiran ba sai da ya tsayar da duk abin da yake yi, daga yanda ya saita natsuwa zaka san da mutum me muhimmanci zai yi magana. ya ɗaga wayar yana rissinawa tamkar yana gabanta, yace,"kin tashi Maama?". daga ɓangaren Hajiya Madina tace,"na tashi me Babban suna". yace,"how are you feeling now?". tace,"feeling much better dear son. am sorry nayi bacci ban jira ka dawo ba, Zaytuna ta min allura ban san time da baccin ya ɗauke ni ba". Turaki ya sauke numfashi yana miƙewa tare da ce mata,"naji daɗin hakan ai, atleast kin samu kin huta. gani nan zuwa". tace,"i know you are tired, kayi kwanciyanka sai da safe tukunna. have you eaten your dinner?". yay shiru bai ce komai ba, tace,"na dafa maka tea, yana perlonku ka duba. ka tabbata kaci ka ƙoshi before you sleep". yace,"to Maama, thank you, Allah ya ƙara miki lafiya". tace,"yauwa bye bye, sleep tight. karka manta da adu'a". ya ajiye wayar yana kwantar da kansa jikin kujera. Fillo dai nata kallonsa tana jin wani tausayinsa na ratsata. gani tayi ya tashi ya fita yanayinsa na juyawa zuwa na marasa lafiya, kuma kamin ta yunƙura tabi bayansa sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da basket, ya wuce ya ajiye kan table ya shiga toilet ya fito. kaɗan ya zuba tea ɗin, soyayyan bread da ƙwai ne, slice biyu ya ɗauka yaci. zuwa lokacin bacci har ya fara ɗaukar Fullo, ta kifa kai a jikin gadon. a cikin baccin nata taji yana waya yana cewa,"haka fa, ai dalilin da yasa ma ba'a fiya son a tsaya ƙofar gidan ba kenan, both the two side, an ma fi samun wannan matsalar daga ta gate ɗin ma'aikatan gida. yes, ai kwanaki ma akwai baƙuwa da muka yi tana taɗi anan main gate so basu ankare ba sai jin abu tayi ya nannaɗe mata jiki, ana dubawa akaga ashe maciji ne. the same abin da ya faru da wata ƴar aiki ma, tana compound nasu ne ko tana bakin gate tana zance, na dai manta but itama ce akai abu kawai taji yana shiga cikin kayanta, ashe wani tsohon maciji ne yayi girmana, da ƙyar aka cire macijin nan a jikinta, ƙarshe ma mutuwa yarinyar tayi, shiyasa ai duk wanda ya san hakan yana kiyaye tsayuwa a compound ko bakin gate, don akwai ɓoyayyun macizai da yawa, shiga jikin mutum kawai suke kamar an aiko su, most especially masu tsayawa suyi zancen nan, suna tsaye sai dai suji maciji ya shige jikin...". ai bai ƙarasa ba Fillo ta kurma wani uban ihu tana haɗewa da salati, cikin second ɗaya ta tashi a ƙasa ta dire akan gado. ta cure a wuri ɗaya tana faɗin,"na shiga uku na lallace, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, maciji wayyo Allah na". faɗa take tana ƙara maimaitawa ataimaka mata maciji ne, maciji ya shige mata jiki, shi dai kawai yana zaune yana kallonta kamar tv, yay hanging wayar ƙaryar da yake yi, sai da ya tabbatar tsoron ya shigeta sosai ta yanda gobe ko uban Amir ne yazo ba zata sa ƙafa ta fita wajen ba, tukunna ya buɗe baki yace,"keee". ya faɗa da ɗan ƙarfi, wannan kiran sai ya ƙara tunzurata ta saki ƙara me uban ƙarfi tana dunƙulewa ta kai ƙarshen gadon ta cure wuri guda. "ka kore shi dan zatin Allah, wayyo gashi nan ya hau ƙafata, innalillahi Kaka kizo ki taimka min, Maciji ne ajikina gashi nan yana bina". tunda Fullo take bata taɓa tsorata irin yau ba, hawaye a fuskarta kam tamkar an kunna famfo, acikin blanket ɗin da ta rufe kanta da shi ta ɗan buɗe ido kaɗan sai taga duhu, nan ta ƙara sakin wani uban ƙaran da yafi wancan, ɗiff kuma sai tai shiru kamar ruwa ya cinyeta. wannan shirun nata sai Turaki yay zaton ko tsoronne yasa ta ɗauke wuta, saboda haka kawai ya ɗauke kansa akanta yaci gaba da aikinsa, computer yake kallo amma babu abin da ke haska masa acikin ido sai lokacin da Amir ya riƙe hannunta ya kuma ja hancinta. haka ɗaya kuma yaji ya kasa natsuwa, yaji kamar tsoro na so ya kamasa, yana typing a wayar hannunsa yana kallon kan gadon inda ta dunƙule, a ransa yaji kamar shirun nata ba lafiya ba, in bacci ne takeyi minutes ɗin da tai taking a haka tuni ta mirgina, in kuma tsoronne zuwa yanzu ai ya barta, sai yaji hankalinsa bai kwanta da hakan ba, ya ajiye wayarsa ya miƙe ya isa kan gadon yana dukan ƙafarta dake cikin blanket, shiru shiru bata motsa ba. sai yaji kamar zuciyarsa ta harba a lokaci ɗaya, ta-ke ya haye kan gadon ya yaye blanket ɗin, yana taɓata yaji jikinta ya saki ta tafi luu ta faɗa gefensa, tuni idonsa yayo waje yana furta innalillahi, kamin ya diro akan gadon ya shiga toilet ya ɗebo ruwa. tun bai haye kan gadon ba ya watsa mata ruwan a fuska sai gata ta farka a matuƙar firgice tana ƙwala kiran,"Umminaaaa". ta faɗa tare da fashewa da raunataccen kuka, irin kukan da duk wanda yaji sai ya taɓa zuciyarsa. tsakiyar gadon ya haye ya janyota jikinsa ya kewayeta da hannayensa duka biyun yana me rufe idonsa. wani abu da bai san menene ba yaji ya tsarga tun daga tsakiyar kansa har tsakiyar tafin ƙafarsa, sunan Ummina da ta ambata shi ya daki zuciyarsa, bai taɓa jin tausayinta ba sai ayau. "Ummina". ya ƙara jin sunan ya haska cikin kansa, kenan ta tsorata ainun, tsoron da ya kai gejin da har take ganin babu mai iya taimakonta sai Umminta, ta tsorata ta kira sunan Ummin da bata raye akan tazo ta taimaka mata. idonsa ya buɗe ya sauke a tsakiyar kanta, tunawa yake da san da Kaka ke shaida masa cewar,"marainiya ce Mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta ma haka". to amma har yau neman dalilin da yasa Kaka ta ɓoye masa cewar mahaifinta na raye yake, sai dai tunaninsa na bashi ko don saboda Hayyo baida kyan hali ne. sai yaji ruwa ya cika idonsa kamar zai yi kuka, bata da Ummi bata da Abba amma tana da shi, tana da shi har abadan abadina, kuma alƙawarinsa ne zai tsaya mata kamar Umminta, zai tsaya mata ba kamar Hayyo da ya sani ba, zai tsaya mata ne kamar nagartaccen uba. sai ya ƙara rungumeta a jikinsa yana jin yanda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso ƙirjinta saboda firgicin da ta ke aciki, numfashinta kuma na fita a wani fiffizga, tana ta kiran sunan Ummi a hankali. ya buɗe ba ki zai yi magana yafi sau uku duk sai yaji yama rasa me zai ce. can kuma a hankali ya kira sunanta dai-dai satin kunnenta,"Fulaniii". ya ambaci sunan kamar me koyon magana, haka kuma amon muryar kamar ba nasa ba. Fullo ta ƙara ƙanƙame shi tana daɗa tattarewa a jikinsa kamar zata shige jikinsa duka. he took a deep breath hugging her more, yasa hannu yana shafa sumar kanta a hankali ya kasa cewa komai. kusan 3minutes yana jin yanda heart ɗinta ke beating fast, a hankali yace"menene?, me ya tsorata ki?, kiyi shiru babu komai, am with you". ya furta cikin sigar rarrashi yana riƙe da hannunta guda. acikin fizgar numfashi tace,"Maciji ne". yace,"aina?". ta daɗa shigewa jikinsa sosai tace,"a ƙafata, ka kore shi please, gashi nan zai shige jikina". tai maganar duk a ruɗe tana daɗa ƙanƙamesa. ya sauke numfashin yana murza tafin hannunta murya can ƙasa yace,"babu wani maciji fa, buɗe idonki ki gani". ta girgiza kanta da ke kan cikinsa tace,"a'a akwai, kai ne ka faɗa". yace,"to aini waya nake yi". ta ƙara girgiza kanta, yayinda Turaki ke rufe idonsa yana jin wani iri a jikinsa. tace,"ai sanda ka faɗa shi ne sai na jisa a jikina". ba tare da ya buɗe idonsa ba yace,"to ai ya tafi, buɗe idon ki gani babu komai, na kore shi". tace,"to ka kunna light". yace,"a kunne yake". ta buɗe idonta a hankali hasken ɗakin na shigewa cikin idonta, sannan ta zare jikinta daga nasa tana jin yanda gabanta ke faɗuwa har sannan, hannuwanta sai kyarma suke yi. Turaki yay saurin sauka akan gadon ya buɗe ƙofa ya fita, for few minutes sai gashi ya dawo da cup a hannunsa ɗauke da ruwa aciki me sanyi. har sannan Fillo na takure akan gadon waje ɗaya sai raba idanuwa take yi, motsi kaɗan take jira ta kurma ihu, ya ƙaraso gaban gadon fuska babu yabo babu fallasa, ya miƙa mata cup ɗin, ta kallesa ta kalli transparent glass cup ɗin a hankali tace,"dan Allah...". bai barta ta ƙarasa ba yace,"amsa Malama ruwa ne". ta ɗaga hannuwanta da har lokacin kyarma suke yi ta karɓa tasha sannan ta miƙa masa ya ajiye. "sakko ki tafi to". da sauri ta ɗago ta kallesa tace,"inje ina?". yay mata wani mugun kallo kamin yace,"Kaka na can na jiranki". sai tayi narai-narai da idanu tana marairaice fuska ta leƙo da kanta ƙasa wai ta gani ko macijin yana nan har time ɗin. "ɗaure kanki". ta lalubo ɗankwalinta da yay can gefe ta ɗaure tujajjan gashinta. "oya to yafa mayafinki ki sakko ki wuce". tuni hawaye ya sakko mata muryarta na rawa tace,"wallahi ba zan iya sakkowa ba". looking at her yace,"saboda?". tace,"kamar na daina tafiya". wata dariya ta tahowa Turaki amma ya gimtse, babu me ganinta a wannan condition ɗin bai yi dariya ba. ya isa bakin ƙofa ya buɗe ba tare da ya kalleta ba raising his voice up yace,"zo ki fice". ta kallesa ta tuna zancen macijin da yay kawai sai ta fashe da kuka sose, ta shiga roƙonsa tana faɗin,"dan Allah don Annabi ka ƙyaleni anan, ba zan iya tafiya ba ƙafana ya daina aiki". sai kuma ta goge hawayen ta ɗago ta kallesa tace,"to ka ɗauko min wayan Yami a perlon Boɗejo sai na kira Kaka tazo ta ɗaukeni". ya haɗe rai ganin tana kallonsa yace,"Kakan ce zata zo ta ɗauke ki?, rashin imanin naki har ya kai haka?, and you even have the guts to send me right?, yaronki ne ni?". tace,"Allah baka haƙuri, kuma ni ba zan iya tafiya da ƙafata ba a yanzu, tsoro nake ji dan Allah ka barni sai da safe". ya zaro ido waje yace,"a ɗakin nawa?". ta gwame fuska tana jin komai babu daɗi a tare da ita tace,"to ni ya zanyi, idan na sakko fa majicin zai kuma bin ƙafata, dan Allah ka ƙyaleni anan sai ka tafi ɗakin Hammah Khalil". yace,"ke zo ki tafi can ɗin". tayi shiru bata ce komai ba, yanda tayi laƙwas tai mugun basa tausayi, yace,"to idan na barki anan ni aina zan kwanta?, kuma ai kince babu kyau". tana goge hawayen fuskarta tace,"ai nasan ba zaka yi min komai ba. kuma ai ga kujera can sai ka kwanta akai, amma ka kira Kaka ka faɗa mata". ya maida ƙofan ya rufe ya dawo ciki ya wuce kan kujera ya zauna. har sha ɗaya na dare yana kan computer, kuma a lokacin suka yi waya da Bello yake faɗa masa flight ɗin 8 zasu bi gobe in Allah ya kaimu. a wannan lokacin Turaki bai iya amsawa ba har Bello ya gaji da hello hello ya kashe wayar. zuciyarsa kawai yake ji tana bugawa, kamar yanda gabansa ya tsananta faɗuwa, me ke shirin faru da shi?, tunda yake bai taɓa jin irin haka a tare da shi ba. doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da kwanciya akan kujeran, ya rufe idonsa da zummar yin bacci amma sai ya kasa, wannan faɗuwar gaban nasa ya tsananta har ya kai stage ɗin da ba ya jin zai iya yin bacci sai dai in ɓarawon bacci ya ɗaukesa. tashi yay ya shiga toilet yayo alwala yay nafila raka'a huɗu, ya ɗan jima yana ta adu'a kamin ya tashi ya buɗe closet ya ɗauko pijams nasa ya saka. gaba ɗaya ya manta da wata Fillo a ɗakin sai yanzu da zai hau kan gado, yasa hannu ya dafe goshinsa, me ya sa me shi ne?, agogo ya kalla yaga har 12 tayi babu damar ya tasheta yace zai rakata. ƙaramin tsaki yay ya hau gadon ya kwata ta gefe, ita kuma tana daga tsakiya ta dunƙule rufe da blanket sai baccinta take, baccin da bata san lokacin da ya ɗauketa ba. wasa-wasa dai har ƙarfe ɗaya Turaki na kwance idonsa a lumshe ya kasa bacci, ya miƙe zaune yana kunna deemlight. ya matsa tare da ɗago Fillo dan gyara mata kwanciyarta, amma sai yaji cewar ba hakan ya kamata yay ba, ya rufe ido yana cije fuska sannan ya ɗagota gaba ɗaya ya kwantar da ita a jikinsa. dai-dai nan ya ƙara hasken light yana ƙarewa innocent face ɗinta kallo, hawaye duk ya bushe akan fuskar, ta tsuke fuskan kaman me shirin dambe, ga zufa da ta ke haɗawa kaman an watsa mata ruwa. shi jikinsa ba me son sanyi bane dalilin da yasa bai fiya zama da Ac ba kenan, amma haka dole ya sauka yaje ya kunna Ac sannan ya dawo again ya ɗagota zuwa jikinsa ya kwantar, da hannunsa ya dinga goge mata zufar kan fuskarta yana jin zuciyarsa na matsewa da zafi zafi. sai yay hugging ɗinta tightly a jikinsa kanta na mannewa a chest ɗinsa, wani irin baƙon al'amari yake ji tare da shi, gefen fuskarsa ya haɗe da tata fuskar, ya kamo hannunta a hankali ya riƙe cikin nasa. ya bayar da sadakinta amma yau sai yake jin like he can't believe cewa wannan jaririyar mallakinsa ce, halalinsa, his wife, his only wife da ya gama tsarin rayuwarsa cewar da mace ɗaya zai rayu, ba tare da sanin cewar itan bace, ba kuma tare da ya taɓa lissafin cewa zai rayu da irinta ba ma, is he dreaming?. sai yaji wani abu me kama da farin ciki a tare da shi, ya ɗago da fuskarsa akan tata yasa hannu ya shafi gefen fuskarta, yana jin kwantaccen sajenta na burge shi, ɗaya hannun kuma na cikin nata hannun yana murzawa. maganganun da ta faɗa masa a mota ɗazu suka haska acikin kansa,_"ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?"._ ya ɗora goshinsa kan nata yake cewa,"ban taɓa jin na tsani wani mutum ba balle kuma ke da kika taimake ni, kuma ta ya zan karya siririn hannun da nake kallo yana burgeni?, wannan bakin kuma ban san zai fashe ba Allah, but am so sorry, shikenan?". maganganun yake yi kamar tana jinsa. and for the very first time he felt her all over his blood, he felt as if his life depended on her, ajikinsa yake jin kamar she needed him at this time, kamar ya fasa yin tafiyar just becouse of her, duk wannan faɗuwar gaban da yake ji akan zai yi nisa da ita ne, abin da bai taɓa ji ba tsayin rayuwarsa ko da akan Maama da Zaytuna da ba ya so yay nesa da su. A hankali ya kai fuskarsa daidai tata yana daɗa ƙarewa ramammar fuskarta kallo, fuskar rigima, fuskar kasada, sai yay murmushi yana kai babban finger nasa kan lips ɗinta yana shafawa. Fillo dai kamar matacciya, baccinta kawai take yi. Turaki still holding her hands da ɗayan hannun kuma yana shafa lips ɗinta yake ta kallon lumsassun idanunta, zai iya rantsewa bai san time ɗin da wani fitinannan murmushi ya ƙwace masa a fuska ba, ya lumshe idanu tare da ƙoƙarin kai lips ɗinsa saman nata trying to kiss her sai kawai yaji zuciyarsa na faɗa masa,"not now, not today, but one day, in that special night, the night that will come not once, but for your entire life". ya rumtse idonsa sosai tare da jan wani wawiyan ajiyar zuciya ya sauke, ya ɗago kansa yana kwantar kansa a pillow, ita kuma ya daɗa gyara mata kwaciyarta ajikinsa tare da jan blanket ya rufesu, sai shafa gashin kanta yake yi, duk shafa ɗaya sai yaji zuciyarsa ta buga, haka har ɓarawon bacci ya ɗauke shi. sai gab da asuba Turaki ya farka, yana tashi yay alwala yay raka'atanil fajr sannan ya wuce masallaci saboda ya makara, ko da ya dawo masallaci side ɗin Maama ya wuce, ya shiga bedroom nata ya sameta ta idar da sallah tana lazimi, anan ya zauna har ta idar suka shafa aduan tare, lokacin 6 har tayi. gabanta ya zauna ta ɗora hannunta saman kansa, ta dinƙa jero adu'oi tana tofa masa tana hawaye, har sanda ta ɗauki kusan minti 7 a haka sannan ta ƙarashe da faɗin,"Allah ya kai mun ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare min kai, dan Allah ka riƙe ibadarka, kar kayi wasa da azkar da adu'a. Bello yace ƙilan zaku iya kaiwa har 7days, but bana jin hakan zai yiwu, in ya wuce 4days ɗin ko ka taho ko na biyoku, Allah ya tsareku". Turaki ya amsa da amin yana me ɗago da kansa, ganinta tana hawaye hankalinsa yay mugun tashi. "Maama lafiya?, menene?, in ba kya so naje na haƙura kawai, Bello zai iya komai shi ɗaya and beside zai sami Sameer acan". ta girgiza masa kai da cewar,"a'a ku tafi tare, Sameer ai ya dawo jiya, yace yaje room ɗinka time kayi bacci". Turaki ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya rungumo Maama shima hawayen na sakko masa, ya tsani tafiyar nan da zai yi sam baya son yaje, dan ba shi da yanda zai yi tunda Maama tace yaje ɗin, amma ji yake kamar in yafi wani abun zai faru, kamar tafiyar tasa zai sa ya rasa ɓarin jikinsa. Fullo dai da asuban bayan fitar Turaki masallaci ba daɗewa ta tashi, taga ita kaɗai ce a ɗakin, cikin ranta ta ƙara yabon kyan hali irin na Turaki, watakam bai ma iya kwana the same room da ita ba, ta sauko a gadon tana tafiya a hankali saɗaf saɗaf saboda har sannan tsoron daren jiya bai barta ba, abinda ta fara tunawa ma kenan da ta buɗe idonta, maciji a compound da kuma bakin gate, yo ita kuwa me zai sake tsayar da ita a wannan wurin, ai har mutuwa. a rufe taji ƙofan sanda taje buɗewa, ta ɓata fuska ta dawo ciki ta shiga toilet tayi alwala ta fito, tana idar da sallah ana ɗauke wuta, hakan yasa a sukwane ta koma kan gadon ta kwanta tana ƙudundunewa tana adu'a a fili, har bacci ya ɗauketa. Turaki ya turo ƙofan ɗakin ya shigo, darduman sallah kawai ya kalla ya shaida tayi sallah ta koma ta kwanta, a yanayin kwanciyar kuma yasan tsoron jiya dai har yanzu bai barta ba. kayansa ya cire ya shiga yay wanka, komai a hankali yake yinsa gudun kar ya tasheta, 7:30am ya gama shiryawa cikin ƙananun kaya da bai cika sasu ba, ya ɗauka brief case daidai nan Zaytuna ta shigo ɗakin. duk da ita tasan Fullo matar Turaki ce hakan bai hanata jin kunya ba da ta shigo ta tarar da shi yana kissing forehead ɗinta. sai ta tsaya ɗaga bakin ƙofan tace,"B Ƙaraye yazo". ta faɗa tana murmushi. ya ƙaraso gabanta ya kama kumatunta yace,"ki zage ki dinƙa faɗar sunansa Bello, dan shi gatsal yake faɗar Zaytun a gabana". tasa hannu ta rufe fuska tace,"ai ni ba ya faɗa a gabana". Turaki yay murmushi yay mata side hug yace,"ki kula min da kanku, mussaman waccen fitinanniyar, dan Allah kisa ido akanta sosai kin riga dai kin san bata ji, sanya kai a hatsari shi yafi komai sauƙi a wurinta. ki faɗawa Kaka zata dawo wajenki da zama for some days dan na riga na tsoratata ba lallai ne take iya zaryan zuwa side ɗinsu da nan ba. ki sa ido akan fitarta, bata son cin abinci, bata son shan magani, na baki amanarta na baki amanar Maama na kuma baki amanar kanki, just 4days zanyi in dawo". ya ƙarasa faɗa Zaytuna ta rungume shi. cikin kukan da take yi tace masa,"jiya nayi mafarki Mum ta dawo, ta dawo hannunta da ƙafarta duk ciwo". ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"ta kusa dawowa da izinin Allah, ina dawowa zamu nemota ni da Fulani". a sanyaye tace,"Hammah bana tunanin Mum na raye". yace,"yaro ma na riga babba mutuwa, so shekaru ba sune mutuwar mutum ba, gamu da Maama har yanzu a raye, kisa a ranki Mum ta kusa dawowa garemu da ranta da lafiyarta, zan faɗawa Fulani issue ɗin da zarar na dawo". kiran wayar Bello da ya shigo a karo na kusan huɗu yasa shi sakinta yana waiga yana daɗa kallon Fillo. ji yake kamar kar ya tafi, ya kama hannun Zaytun suka fita yana faɗa mata,"idan kinje wurin Kaka ki ɗauko cream ɗin da ta ke shafawa ki jefar, i don't think wanda kika saya ranar nan take shafawa". Zaytuna tace,"tayi haske sosai ko?, nayi zaton ma wanda na sayo mata ne so after na tambayeta tace min bata fara using da shi ba, tana shafa wani da aka kawo musu, Kaka ta hanata buɗe sabon wai almubazzaranci, but zanje ɗin sai na ɗauke". suka fito compound ɗin Bello dai na tsaye sai hararsa yake, Turaki ma ya hararesa ya ƙarasa wurin Maama, sallama dai kamar kar ai tafiyar, kuma kamar wannan ne karo na farko da zai fara tafiya, Nihal ma ta dage cewar ita dai zata bisa, yace sunyi late ai da tun jiya ta faɗa masa sai a anso tictiket har ita, Samha ma ta riƙesa tana faɗin kawai ba sai ya tafi ba ita bata so yana nisa da su, Hajiya Madina ta zabga mata harara tana me jin wani ɗaci da baƙin ciki na kasancewar Samha ƴarta. Ilham kam da ta kwana a gidan tana riƙe da hannun Boɗejo tana goge hawaye. Boɗejo tace,"ni wallahi duk kun saka jikina yayi sanyi, tafiya sai kace yau zai fara, ko saboda kawai ya jima bai yi nesa daku ba?. fisabilillahi irin wannan sallamar da kuke yi ai ta masu bankwana da juna ce, irin fa wannan sallamar akeyi idan mutum zai mutu. to ni dai gaskiya idan tafiyar nan bata zama dole ba ke Madina sai kisa shi ya haƙura". ta kalla Hajiya Madina taga tana goge hawaye tace,"ka ga wani ƙarin tsinkar da zuciya kuma". Turaki dai yana tsaye jikinsa duk yay sanyi, shima ji yake kamar idan ya tafi ba zai dawo ba, sai kallon side ɗinsu yake yi, kamar zai ga Fillo ta leƙo ta window, kamar zata leƙo suyi sallama. ya sauke ajiyar zuciya ya kira sunan Ilham, ta ɗago tana goge hawaye ta tafi zuwa gabansa, ya ɗauke hannunta daga fuskarta yana sa handky ɗinsa ya goge mata fuskar, a hankali yace,"kukan mene?". tace,"nace zan bika tun jiya". yay murmushi yace,"4days fa kawai zanyi na dawo". ya faɗa yana ɗago kai ya kalla Nihal yace,"auta zo". tazo itama nata hawayen na sauka a lokacin. yace,"ku shiga kuyi min rakiya to". Boɗejo tace,"kaga in ɗaukowa Ilham mayafinta ku tafi tare kawai, ni bana son kuka yana ɗaga min hankali". Khalil wanda zai driving nasu yace,"Allah babu da wadda zan tafi da ita, ina sauke su nima da inda zanje". Boɗejo na hararsa tace,"kana kama da mutanen kirki amma ba haka kake ba, in motar kai ka saya sai ka hanasu shiga ai". Khalil dai ya tubure babu me binsa, har sai da Hajiya Madina tasa baki, amma hakan bai sa ya yarda sun tafi da kowa ba. ƙarfe tara Fillo ta tashi, ta tashi a firgice tana bin ɗakin da kallo, ta sauko daga kan gadon da sauri tana rarrabawa idanuwa. har yanzu babu alamar ya shigo, to ta ya zata fita daga ɗakin alhalin yasa key?. tana ta ɓata rai ta shiga gyara ɗakin, tana gyaran gado taci karo da farar takarda a ninke, ta ɗauke ta aje kan side drower sai kuma taji tana buƙatar buɗewa, bata san ba ko yana da alaƙa da mugwayen mutanencen. ta zauna gefen gadon ta warware takardan, farkon abin da ya fara burgeta handwritting ɗin jiki, sai kuma zanen heart da peppern ke ɗauke da shi. sannan tabi rubutun da kallo tana karantawa acikin yaran fulatancin da aka rubuta. _Nisa tsakanin zuƙata biyu ba ya nufin shinge fa ce tuna kyakykyawar alaƙa da ke tsakani...ƙwarai akwai wanda yake ƙaunarki kwatankwacin yadda makaho ke buƙatar ido, fiye da yadda kurma ke buƙatar ji, fiye da yadda gurgu ke buƙatar ƙafa, Dai-dai da yadda mara lafiya ke buƙatar lafiya, cikin ƙanƙanen lokaci yana jin kin zama rayuwarsa gaba ɗaya, kula da kanki shi ne mafi abin da yafi so daga gareki kiyi masa a san da yay nisa da ke, amana!, amana!, amanar kanki a tafin hannunki daga gare shi._ haka siddan Ilham ta faɗo cikin zuciyarta a sanda ta gama karantawa, ba wai don ta santa ba ko tasan matsayinta, tana hasko hoton yanda ta same su jiya a ɗakin Boɗejo. ta taɓe baki ta miƙe tana jefar da takardar a ƙasa, tabi ta kanta ta wuce ta gyara kan table ɗin dake hargitse da takardunsa, tana gyaran ɗakin tana kumbura ba tare da sanin dalili ba, kuma har ta gama gyaran bata bi ta kan gadon da ta soma gyarawa ba, saboda haka ɗaya taji gyarasa baida wani amfani duk da ita ta kwanta akai. tana riƙe da kwanukan abinci a hannunta taji an turo ƙofar ɗakin an shigo, idonta ya manne akan Ilham dake shigowa kamar wacca ƙwai ya fashe mata a ciki, fuskarta duk hawaye, ta shigo ba ko sallama ta wuce ta gaban Fillo ta faɗa kan gado tana ɗauko pillow ta rungume a ƙirjinta. wani abu da Fullo bata san ko menene ba ya tokare mata a maƙoshi, tasa kai ta fice a ɗakin da sauri. *vote, comment and share.* [8/29, 20:48] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* ```DAGA MARUBUCIYAR``` 1-Sirrin Ɓoye 2-Al'amari 3-Hidaya Noor 4-Alhussain 5-Sanadin Talauci 6-Ƙaddarar So 7-Prince Khaleed Da sauran su..... *31* wani abu da Fillo ke ji akan Ilham ya tsaya mata a ƙirji kamar ƙurji, har ta baro upstairs ɗin wani irin ɗaci take ji a tare da ita da bata san dalilinsa ba. lokacin da ta fito compound zata wuce ɓangarensu ta tarar ana rage flowers ɗin gidan, wajen duk yay kaca-kaca, tausayin masu aikin cirewar da gyara wurin ya kamata, neman halal da wuya, kuma a haka namiji ke fita yasha wahala ya kawo macen da bata arziƙi ba tayi masa ɗiban albarka, ta girgiza kai tana me jin tausayin kowanne namiji acikin ranta amma banda Hayyo mahaifinta. sai da taje gab da shiga gate ɗin nasu kawai maganar macijin jiya ta dawo sabuwa acikin kanta, take kuma tsananin tsoro ya rufeta ganin wani reshe na flower da aka sare wada yay kama da jikin macijin, ba shiri ta kurma uban ihu tana duƙewa a wajen sai kururuwa take, da sauri masu aikin suka yo kanta suna tambayar lafiya, dai-dai nan Khalil ya ƙaraso wajen shima yana duƙawa gabanta da tambayar lafiya. cikin kukan da take tace,"maciji ne". with suprise kowa ya ƙara maimaita abinda tace,"maciji kuma?". ta ɗaga kanta jikinta sai rawa yake yi. nan da nan masu aikin suka shiga laluben wajen, Khalil kuma yace ta tashi sai ta girgiza masa kanta tace,"ba zan iya ba". yace,"kin gurɗe ne?". ta ƙara girgiza masa kai ba tare da tace komai ba. yana murmushi yace,"daure ki tashi babu komai anan, macijin ai ya tafi ga shi can sun kashe shi". tun ɗazu da ta duƙe sai a yanzu ta ɗago da kanta tana rarraba idanuwa, yacca take yi ɗin ba ƙaramin bawa Khalil dariya tayi ba. bai kasa riƙe dariyarsa ba ya saki yana ce mata,"tashi na raka ki". ya faɗa saboda yanda yaga duk ta firgice, firgicewar da ba zata iya tafiya ita ɗaya ba. ta miƙe da ƙyar sai ƙanƙame ƙafarta da jikinta takeyi, ya wuce gaba yana cewa,"muje". idonta ya sauka cikin compound ɗin nasu, maganar Turaki ta cewar ai wadda ma macijin ya maƙale mata mutuwa tayi, sai taji inaa ba zata taɓa iya shiga ɓangarensu ba, tana jin ma kamar sai dai Kaka ta dawo nan itama. ba shiri taja da baya tace da Khalil,"Hammah Khalil ba nan zani ba ɗakinmu zan wuce". tana tafe tana ɗage ƙafafu haka ya rakata har ƙofar ɗakinsu, zaune ta sami Ɗausiyya na gyaran zogale, ganin Fillo yasa Ɗausiyyan ƙyalƙyalewa da dariya tace,"matsoraciyar kawai". Fillo na hararta tace,"tsoro ai halal ne, kuma tsoron me kika kalla nayi". Ɗausiyya tace,"ai ina kallonki sanda kika zube, har nayo wajen naji ana batun maciji babu shiri nayo reverse". Fillo na ƙara harararta sanda take zama kan gadonsu tace,"ashe kema matsoraciyar ce". Ɗausiyya tayi dariya tukunna tace,"2days kina makarar shigowa". Fillo na kwanciya kan gadon tace,"wani lalataccen barci nake fama da shi 2days ɗin, in kuma kina da magani sammani". tai maganar tana jin jikinta a saɓule, yanayinta duk babu daɗi kamar wani abu na shirin faruwa mara kyau. Ɗausiyya tace,"aiko dai ki nemi magani. ɗazu da Hammah Babba zai wuce yana cewa da Adda Zaytuna wai in yaje can wurin da zai je zai sayo mata maganin daina bacci, da kina nan kema da kin faɗa masa tunda naga yana da kirki, kawai dai baida sakin fuska, jiya ma 2k ya ban". lokaci ɗaya Fillo taji allon ƙirjinta ya girgiza, Turaki ya tafi?, when is he coming back?, tare da Bello suka tafi, ta ya zai iya kula da kansa?, ya tafi da maganinsa?. tarin tambayoyin da suka zowa cikin kanta kenan a lokacin, ga shi babu ɗaya da take da amsarta, dan haka ido kawai ta lumshe kamar me bacci, tana jin Ɗausiyya nata magana amma bata jin zata iya buɗe baki ta amsa mata saboda faɗuwar gaban da take ji, wani irin yanayi da bata taɓa jin kanta aciki ba, like kamar dai something bad will happen soon. bayan kwana biyu aka kawo akwatin sa ranar auren Fillo daga gidan su Amir, Innarsa da wasu Anties nasa guda biyu na ɓangaren mahaifi su ne suka kawo, akwaiti guda ɗaya da atamfa 4 aciki sai less da zai kai 6k guda biyu, shadda ɗaya da material guda ɗaya, da fashion na yari da sarƙa guda biyu sai takalmi da jaka duk guda ɗaya, sai kuma hijabs har ƙasa guda biyar da 5k a haɗe, akasa ranar aure wata biyu masu zuwa. kaya dai masha'Allah sunyi kyau sosai gwanin san barka, kowa ya gani sai ya yaba, haka akaita zuwa ana gani ana tafiya da masha'Allah, su Yami kam baki har kunne jikarsu tayi goshi. sai dai fa duk wannan bidiri da akeyi Fillo bata ko ga tayar akwatin ba balle kayan da suke ciki, dan ƙememe tun ranar da Turaki ya tafi ta kasa zuwa ɓangarensu tsaboda bala'in tsoron da ke ranta, kayan sawarta ma sai Maijidda ce ta kawo mata tace musu wai jarabawa za'ai musu, kwana suke su na karatu ita da Ɗausiyya shisa. farko dai a tsorace take da zuwan, to amma da aka kawo kayan sai tsoro ya haɗe da kunya shisa ta kasa ko da zuwa, idan taje bata san taya zata fara haɗa ido da mutane ba, tasan kuma halin Maijidda zata sata a gaba ne da aikin zolaya, dama tun washe gari ma tazo tana mata lissafin abubuwan da zasu yi da biki, ita dai har ta ƙaraci surutunta bata ce mata ƙala ba, Maijidda ma da haushi ya cikata ta karɓi wayar Yami da ta zo amsa tai wucewarta da cewar bata ƙara zuwa, ita zata je tayi nata shirin ita ɗaya. tun ranar da aka kawo kayan Amir ke ta doka mata kira akan zai zo, tai masa godiyar kaya har yake tambayarta ko sunyi, tace masa sunyi tunda har Maijidda ta faɗa dan ita bata je ta gani ba. Amir dai juyin duniya yazo yaga Fillo sam taƙi, idan tayi kamar tace masa yazo sai taji inaa a dai yi auren tukunna, ai haka taji Turaki yace duk masu yin zance a gidan, shisa ga ƙannensa nan cikinsu babu wadda ke yin zance ashe dalilin kenan, Amir tun yana lallashi da roƙo da ƴar murya Fillo dai taƙi yarda da zuwansa, har yay fushi ma washe garin ranar gaba ɗaya bai kirata ba, kuma sai sauƙi yazo mata ranar Yami ta aiko Maijidda ta karɓar mata wayarta. kuma da Hajiya Madina tayi mata batun me yasa bata zuwa wurin Kaka sai tai mata ƙaryar ai tayi tafiya ne, sai dai fa a wannan kwanaki biyun Fillo tayi muguwar rama, tun daga kan fuskarta har jikinta, na farko tsoro ya hanata sukuni, na biyu kuma kewar Kaka duk ta addabeta. ɓangaren Amir dai da yaga ba zai iya da azabtuwar rashin ganin Fillo ba ya kwaso ƙafa yazo gidan, ya sanarwa me gadi cewar wurin Hajiya Madina yazo saboda ya sami damar shiga cikin gidan kai tsaye, ta yanda zai zaƙulo Fillo a duk inda take ya fito da ita, shi ba zai iya da rashin ganinta ba, yana ƙara kwana bai sata a idonsa ba tsab zai iya rasa ransa. Mai gadi ya sanar ma da Hajiya Madina, akayi masa iso zuwa parlon baƙi, taje ta same shi suka gaisa, zatonta ma ko masu buƙatar taimako ne amma sai taji yana mata bayanin wurin Halima yazo. kusan minti guda Hajiya Madina ta ɗauka tana kallonsa cike da nazarinsa, tare da kuma mamaki matuƙa akan batun wurin wacca yazo, ashe yanda take tunanin Fillo ba haka take ba?. tashi tai tana ce masa ya jira yanzu zata zo, aka kawo masa ruwa da snacks da kuma juice na pineapple, kayan dai na aje kan table ɗin dake gabansa yana kallonsu amma ya kasa ko taɓa ruwan, bini bini sai ya duba agogon hannunsa, shiru shiru Fillo bata fito ba wucewar mintina goma da tafiyar Hajiya Madina, a ransa sai ya fara tunanin kamar ko ba zata zo ba ne, kuma kamar Hajiyar ce ba zata barta ba, sai yaji ransa yay mugun ɓaci. ɓangaren Fullo kuwa su na can su na aikin suyar wainar shinkafa Baffa zai yi baƙi, suna faɗansu ita da Ɗausiyya kan ita Ɗausiyya na cika mai a suyar, ita kuma Fillo na zuba kaɗan, faɗan dai ya tashi akan kowacce ta sakawa ƴar uwarta ido, Zaytuna da Nihal kuma na gefe suna haɗa miyar agusi da ganda, suna jinsu suna yi musu dariya. Nihal ta waigo ɗauke da dariya a fuskarta tana kallon Ɗausiyya tace,"ke fa kece aikinki baya kyau, mai idan yay yawa a abinci baya daɗi Ɗausiyya kuma kin san dai akwai masu ulcer". Fillo na kallon Ɗausiyya tai dariya tace,"ah tou kin dai ji, in kuma man kike so ai sai ki bari in tazo ƙarshe ki soya taki da duka galand ɗin, lafiyarki ai ba lafiyar wani ba". Ɗausiyya ta galla mata harara ta ɗauki waina guda ɗaya acikin wacca Fillon ta soya ta wuce wurin Nihal tana faɗin,"Adda Nihal kalla fa ki gani, abu ƙamas ai sai taja mana magana ace muna da maƙon mai alhalin akwai wadatarsa". ta buɗe cikin wainar tana ƙara faɗin,"ji fa aba a bushe kamar ba'a saka komai ba, yanzu dan Allah cikin abokan Baffa wani ya kai bakinsa ai direta zai yi dan wannan dai ba zata ciyu ba Allah". Nihal na taɓa wainar tace,"gaskiya kuma fa haka ne, mutane da basa rasa abin faɗa sai su tafi suna cewa Baffa baya wadata gidansa da isassan man abinci". Ɗausiyya ta kalla yanda Fillo ta cika tai fam tace,"ah tou, dan haka ki zuba mai isashshe kiyi suya Malama, in yaso kyayi tsumulmularsa a gidanki babu ruwan koya, ƙarƙari kijawa mijinki magana wurin abokai da dangina a tafi ana yi da ke biki iya girki ba". tai ƙarashen maganar tana dariya. Fillo tace,"ko ba komai dai mijina yace ina da tattali, ke kuwa kullum sai kinsha masifa akan haukar almubazzaranci da kike masa". Zaytuna tai dariya sosai. Nihal da bata fiya shigowa kitchen ɗin ba tace,"haka kuke aikin dama kamar kaji?". har sannan dariya bai ɗauke akan fuskar Zaytuna ba tace,"kika biye su ba abinda zai hana bakinki yagewa, dan kamin barinki kitchen ɗinn sai kin ji wani complain ɗin na daban". dai-dai nan Hajiya Madina ta shigo, duk suka yi shiru, ta dubi Zaytuna da Nihal tace,"sannunku da aiki". suka amsa da yauwa, tace da su,"where is Samha?". Nihal tace,"na ga ƙawarta tazo ɗazu sun fita". Maama bata tace komai ba ta maida kallonta ga Fillo tace,"meet me in my room". ta faɗi hakan tana juyawa ta fita. Fillo ta miƙe tana wanke hannu a sink, taiwa Ɗausiyya gwalo tace,"kuma ai aiki me kyau in ba haka ba ran mutum ya ɓaci". ta faɗa tana mata gwalo sannan ta fice daga room ɗin. tun da ta shiga room ɗin Hajiya Madina taga yanayin fuskarta sai jikinta yay sanyi, ta ƙarasa shigowa ta zauna a ƙasa tana fuskantarta, duk lokacin da taga fuskar Maama ahaka tasan to da matsala,so farkon abinda yazo cikin kanta shine Turaki, 4days dama taji Zaytuna na faɗin zai yi, ga shi yau har kwana 5, lafiya?, meke faruwa?, ko kuma yana kan hanya?. rashin sanin amsa yasa ta ɗago kai da sauri ta kalli Hajiya Madina da ke ta kallonta ta kasa cewa komai. murya a hankali tace,"Maama lafiya?, Hamman har yau bai dawo ba". Hajiya Madina ta sauke numfashi tace,"zasu taho jiya sai Baffa ya tura su El-Salvador zasu yi signing wani contract da wani kamfanin fulawa acan, jibi insha'Allahu zasu sauka". Fillo tace,"Allah ya kaimu ya dawo da su lafiya". ta faɗa kanta na ƙasa. Hajiya Madina na studying nata tace,"kunyi da wani zai zo wurinki ne?". tambayar taji ta a wani iri, hakan yasa tai saurin ɗago kai tana kallon Maaman, kan tai magana Hajiya Madina ta jefa mata tambayar,"Amir yazo wajena yace min yana son ganinki. waye shi?, aina ku ka haɗu?, dama can ya sanki ne?, da yaushe kika fita har ya ganki ya biyo sawunki?". Fillo ta sadda kanta ƙasa tana wasa da fingers dinta tace,"wanda zan aura ne, amma wallahi ba muyi da shi cewar zai zo ba yau". with Astonishment Maama tace,"wanda za ki aura Fillo, asin how?". Fillo ta kwashe duk bayanin komai har kayan sa ranar da aka kawo ta faɗawa Hajiya Madina. ita dai kallonta kawai take tana ganin kamar yarinyar ƙarya take yi, ƙarama da ita haka age of 17 going to 18 ace za'ai mata aure?, tasan cewar su ƴan ƙauye ne da basu fiya bawa rayuwar ƴa mace muhimmanci akan yanda zamanin yanzu ke tafiya ba, amma bata taɓa tsammanin za'a iya aurar da yarinyar nan kusa ba kasancewarta me ƙaramin jiki sosai, in ba sani ma kayi ba zaka iya rantsewa ba 18 zata shiga ba. dalilin da yasa tun a ranar da yarinyar ta kwanta mata a rai ba tayi hanzarin shigar da tata buƙatar garesu ba kenan, kiwon Fillo da take yi tanadi ne take taiwa ɗanta Muhammad Turaki, ashe har wasu sun mata shigar sauri, wani ya riga ɗanta, wani daban zai mallaki kamilar yarinya me natsuwa da hankalin da irinta ke da wuyar samu, ba ɗanta Muhammad Turaki ba, wani daban can. yanzu wa zata ƙara kama masa?, har cikin ranta bata ji daɗin wannan batun ba sam, to amma ya zata yi, shirinta da lissafinta daban ne, hakama yanda ubangiji ya shirya lamarinsa daban, kuma na ubangiji shine dai-dai, kuma dama ita kullum adu'arta alkhairi take nema. dan haka yanzu adu'a ta rage mata akan Allah yaywa Turaki da Khalil zaɓin mace mafi alkhairi a gare su. ta sauke numfashi tana daɗa kallon Fillo tace,"amma Fillo me yasa baki faɗan ansa ranar aurenki ba na fara shiri?, ko haka kike so na kaiki?, ko kin manta nace ke ƴata ce?". ta faɗa cike da zolaya, Fillo kanta na ƙasa bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta kamata. Hajiya Madina ta miƙe ta isa wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu sabbin kaya irin na ƴan turkey, kayan da Baffa ya tahowa da Nihal ne tsaraba, ta ciro set biyu aciki ta bawa Fillo tace,"ungo kiyi maza kije ki shirya yana parlon baƙi yana jiranki tun ɗazu". Fillo ta kalla kayan sannan tace,"Maama zanje da waɗannan ma". ta girgiza mata kai tace,"daga wurin suyar waina fa kika taso, haka zaki je wajensa kina tsami?, salon ya raina min ƴar tawa tun yanzu...a'a je ki gyara jikinki shaf shaf kije ki samesa dan ya jima kusan 15minutes, in kin dawo kizo ki min list na abinda kike so na siya miki". Fillo ta amshi kayan tana ta zuba godiya ta fita, fuskarta kawai ta ɗauraye ta ɗauki turaren Ɗausiyya ta fesa, sosai tayi kyau acikin kayan kamar dama dan ita aka siyo. haka kawai sai take jin sam bata ƙaunar zuwa wurin Amir, alhalin tun randa aka kawo kayan sa rana ta ke ta so ta gansa, kwana 5 tasan tayi kewarsa sosai da soyayyarsa, tunda in sunyi waya ma faɗa suke, bata saka mayafin kayan ba tasa hijab saboda yanda ta jita uncormfortable a riga da wandon. ta tafi tana ta ɓata fuska, ji take kamar har yanzu bata huce daga haushin Amir ba, kamar ranar nan da ta kulasa ba ita bace, kamar yau idan taje zata yi masa wulanci ne wanda zai sa ba zai ƙara dawowa ba. sanda ta shigo parlon ya miƙe a zuciye zai tafi, ganinta kuma yasa ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya cike da farin cikin ganin nata. tun daga kan yatsun ƙafarta yake kallonta har zuwa kan fuskarta, last da yazo ta fita da mayafi bata yi masa kyau irin yau ba da take acikin hijab. ta tsaya daga bayan kujerar da yake tana cin magani bata ce masa komai ba. ya harɗe hannayensa a ƙirji yace,"nai zaton ai ba za'a barki ki fito ba dan naga wani iko ake nunawa da ke a gidan nan, ko basu san tawa bace?". tai masa shiru tana ƙara ɗaure fuska tana jin kamar ta juya ta koma. sai taji yay ƙasa da murya cikin amo na shauƙin so yace,"fushi ake dani har haka da ba za'a min ma smiling ɗin nan dake melting heart ena ba?, zunubin me na aikata wanda ban sa ni ba gimbiya?". sai kuma ya kama kunnensa yace,"am sorry, ba zan ƙara ba insha'Allah, kar a kuma yi min horon da zuciyata ba zata iya ɗauka ba this time around". ba tare da ta kalle shi ba tace,"tunda nace maka ka bari zan saka maka ranar zuwa ai sai ka bari ko, ba wai ka ɗauko ƙafa ka taho ba notice ba". yay murmushi yana zagayowa inda take tsaye, ji yake kamar ya rungumeta a duk sanda yake tare da ita. yace,"kiyi haƙuri nayi kuskure, kasa haƙuri nayi wallahi, 5days ɗin nan ji nai kaman an shekara 5". ta daɗa ɓata rai tace,"to ni aiki nake yi yanzu, Baffa ne zai yi baƙi anjima kaɗan muna aiki". ta faɗa tana ƙoƙarin barin wajen, zai riƙo hannunta tayi saurin janyewa tana cewa,"bafa kyau ka daina min irin haka, ni ban ma san yaushe ka lalace irin haka ba na taɓani". yay dariya sose yace,"tsabar ƙauna ce, amma ba zan ƙara ba daga yau, zan jure zuwa ranar da za a kai min ke...yanzu dai kafin ki tafi dan Allah kiyi min murmushi ko zan sami sauƙi". ta ƙara cin magani tace,"ba zaka samu ba kam, kaga tafiyata". ta faɗa tana wucewa sai ya daɗa dakatar da ita da cewa,"sorry na manta. Kaka tayi min magana akan siyar da filayenki guda biyu saboda hidimar biki da zata yi da su, to na faɗa mata cewar za'a bada takardu tace suna wurinki ke kika adana su, yanzu ya za'ai?, saboda an sami wanda zai siya da tsoka dan kowanne zai iya siyansa 1Ml". ta juyo ta kallesa tace,"Kakan tace maka za'a sayar min da fili saboda hidiman biki?". ya ɗaga kafaɗarsa,"yes, in kin koma zata daɗa miki bayanin hakan. ko na kira Yami sai kiji daga bakinta?". tace,"tabɗijam, ashe gwarama da Allah yasa na ɓoye takarduna, to aiko babu me sayar min da fili ko guda ballantana har filaye 2. ayi haƙuri kamin lokacin Allah zai bada yanda za'ayi duk wata hidima...ka gaida su Inna sai anjima". ta faɗi hakan tana ficewa daga parlon ta bar Amir da sakin baki yana binta da kallo fuskarsa na nuna damuwa da rashin jin daɗi. in ya lura kamar yanzu bata son auren nasu dan ƙarara yaga hakan a fuskarta, me ke shirin faruwa ne?, wani ne ya hure mata kunne a lokacin da sukai faɗa da shi?, waye shi?, aina yake?. sai yaji wani bala'in kishi ya tokare masa zuciya, a fusace yabi bayanta dan jin amsar tambayoyinsa sai dai yana fitowa compound ɗin ya tarar babu ita, haka ya bar gidan zuciyarsa na masa ƙunci. da daddare Fillo na kwance a ɗakinsu wajen 9 na dare, time ɗin sun gama karatu ita da Ɗausiyya, suna hirar duniya Fillo kuma cikin ranta tana ƙudurcewar gobe zata cire tsoro taje ɓangarensu, ta kuma bawa Kaka shawaran kar a sayar da fili ko ɗaya gwarama a sayar da dabbobinsu. wayar ɗakin tayi ƙara Ɗausiyya ta miƙe tana mita tai picking call ɗin. daga ɓangaren Zaytuna tace,"Ɗausiyya Fillo tayi bacci ne?". tace,"a'a". "to ce mata tazo da sauri please". tace,"tom Adda". ta ajiye wayar tana kallon Fillo da har ta rufa bacci ya fara ɗaukarta, tace,"kije Adda Zaytuna na kiranki". ta sakko daga kan gadon tana yamutse fuska saboda baccin dake cinta, veil ɗin da ke ɗaure akanta ta warware ta yafa ta fita. cike da tsoro ta fito compound, tana tafe tana dube-dube har ta ƙarasa sashen su  Zaytuna, ta buɗe ƙofar ɗakin Zaytuna ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ganin Zaytuna bata ɗakin ta tsaya gefe tana jan yatsun hannunta, bacci sai daɗa fusgarta yake, Zaytuna kuma na toilet tana wanka, jin sallamar fillo yasa ta ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin, wannan yasa Fillo neman kujera ta zauna tana ta jera hamma. wayar Zaytuna da ke kan gadonta tayi ringing har sau biyu, ana ukun ta leƙo a toilet ɗin tace da Fillo,"ɗaga please ko waye kice bana kusa". Fillo ta miƙe tana layin bacci taje ta ɗau wayan, dai-dai lokacin kiran ya katse, sai kuma ya ƙara shigowa, sai da zata yi picking tayi noticing vedio call ne, ta ɗaga murya wajen faɗawa Zaytuna cewar Vedio call ne. Zaytuna tace mata,"wanne suna ne jiki?". tace,"DH". tace,"just pick". Fullo ta gyara zaman gyalenta tai picking call ɗin tana kauda fuskarta daga kan screen ɗin wayar, call ɗin nayin connecting tace,"bata kusa, idan ta dawo zata kira". daga hotel ɗin da Turaki yake zauna kan gado ya lumshe idonsa sannan ya buɗe yace da ita,"ke kuma kina ina?". tace,"ina ɗakinta ita kuma ta fita". Turaki dai so yake ta haska fuskan nata gaba ɗaya amma taƙi, sai side face ɗinta da yake kallo, ita ba ta ɗauki muryarsa ba ma, ya san halinta zata iya tayi droping wayar ko kuma ta bar wayar a haka taƙi haska fuskan ba tare da ta ƙara cewa komi ba har sai Zaytuna ɗin tazo. ya miƙe daga kishingiɗen da yake ajikin pillow ya zauna sosai sannan yace,"bata ɗakinta ta fita, ke kuma kika shigo har kike ɗaga mata waya. what those that means?, stealing or snatching or what?". ai furucinsa na ƙarshe yasa Fillo bata san ma sanda ta haska screen ɗin wayar gaba ɗaya ba a fuskanta, ta cune tana ɗaga gira duka biyun sama tace,"banyi kama da ɓarauniya ba balle in tsaya ɓata lokacina kan snatching, kuma ai ita me wayan da kanta tace in an kira na ɗaga, if not ba zan taɓa picking ba ko za'a dawwama ana kira". tai maganar tana murguɗa ƙaramin bakinta, dan ko waye ya bata haushi ya ɓata mata rai, duk da ba'a son ranta ta faɗi hakan ba, stealing fa!, ya san mene ma'anar danganta wani da sata? Turaki yay murmushi sai kuma ya ɗaure fuska yace,"ni kike faɗawa haka?, sa'anki ne ni?". sai a lokacin ta ɗauki muryarsa, a tsorace ta murza idanuwanta tana ƙifƙifta su, ta shiga uku ita ce kalmar da ta ambata cikin ranta. sai taji ƙirjinta na duka a lokaci ɗaya, ta marairace fuska tana yin kamar zata yi kuka tace,"kayi haƙuri ban san kai bane". ya ƙara tamke murya yace,"ɗago kanki ki kalle ni". ya faɗa muryarsa a ɗage. ta ɗago kanta tana dab da fashewa da kukan dake ƙasan ranta, ta tsana, ta tsani wannan ɗaga muryar da yake mata. kuma a yau babu abinda zai hanata faɗa masa kar ya ƙara raising mata wannan voice ɗin nasa. so tayi itama ta ɗaga murya wajen faɗa masa ta yanda zai shaida gargaɗinta garesa, amma sai taji muryarta tayi sanyi tana ce masa,"bana so kake ɗaga murya haka dan Allah". Turaki ya shafo wuyansa yace,"are you commanding me?". Ta girgiza kai ba tare da tace komai ba tana sa hannu ta goge hawayen da ya sakko mata. sannan tace,"Adda Zaytuna ɗin wanka take yi, zan faɗa mata idan ta fito". ta faɗa tana ƙoƙarin kashe wayar yay saurin dakatar da ita, shin bata san tun randa ya taho ba ya rasa natsuwarsa saboda tunaninta, tunanin halin da take ciki, bata san tun ranar da ya taho ba yake jin fargaba akanta ba, kuma tun da ya sauka a kowanne bugar sakan na agogo so yake ya ganta, yaga motsinta, yaga yacca lafiyarta ke ciki, bata san a daren yau ya rufe ido yafi sau 5 ba amma ya kasa baccin duk saboda yana so ya ganta, ko ya samu hankalinsa ya kwanta, ko wannan faɗuwar gaban ta bar shi. ya tausasa muryarsa yace mata,"ce nayi ki ɗago ido ki kalle ni bawai ki kashe wayar ba". da ƙyar ta iya samun courage ta ɗaga ido ta kallesa tana jin ƙirjinta na ta duka, sai dai kallo ɗaya da tayi masa sai ta kasa ɗauke idon nata gaba ɗaya, wannan tsoron ganinsa ɗin da take ji sai taji ya yaye, taji tana so ta kalle shi tai ta kallonsa. kallonsa take yi ta kasa ɗauke idonta a kansa, zata iya cewa kamar ya rame, kamar yana cikin damuwa, kamar yana buƙatar wani abu. ya katse tunaninta da faɗin,"kina da matsala ne?". har yanzu idonta na kansa tace,"me ka gani?". yace,"me ya sami idonki?". ta lumshesu tukunna tace,"bacci nake ji". muryarsa na ƙara yin ƙasa yace,"bayan bacci fa?". tace,"ba komai". yace,"are you sure?". tace,"yes". ya ƙara kallonta sosai sannan yace,"daga tuesday zuwa yau faɗa min kalar fitinar da kika yi". ta waro ido waje taje,"fitina kuma?, ai ni bana fitina, da hankalina". ya murmusa kunci sosai yace,"kuka fa?". sai ta sami kanta da ba shi amsa kai tsaye da cewar,"ai dama kaine kake sa ni kukan, kuma baka nan". yace,"really?". tace,"yeah". leɓensa ya tale da murmushin da bai shiryawa ba yace,"magani fa?". ta cune fuska tace,"wannan ma ai kaine kake min dole, kuma da baka nan duk bana sha". yace,"abinci fa?". ta juya idonta tana jin baccin na ƙara zuwa tace,"ina ci mana". ta faɗa tana ɗan shagwaɓe fuska. Turaki yay shiru bai ƙara cewa komai ba, tsawon 30seconds kallon siraran yatsunta kawai yake da ta tallafe haɓarta da shi. sanda ya buɗe baki zai ƙara yin magana sai ta riga shi da cewar,"yaushe zaku dawo, Maama duk ta damu". yace,"ba yanzu ba sai next year". jin hakan bata san sanda ta ɗago ido ta kalle shi ba ta maimaita abinda yace,"next year kuma?". ya ɗaga mata gira,"yes, Maama zata zo idan tana son ganina, also Zaytun. ko bayan su akwai wanda ya damu da rashina ne?". tayi shiru bata ce komai ba duk da tana so tace wani abu ɗin. Turaki yace,"oya kashe wayan, dare yayi Kaka na can na jiranki". ta ɗan kalle shi tace,"to naga duk ka rame, baka da lafiya ne?, ko wani abu yana damunka?". yace,"lafiyata lau, ina dai kewar Mum ne". tace,"wacece haka?". ta tambaya as if bata san komai ba. yace,"Yayar Maama ce, ta daɗe da ɓata bamu ganta ba har yanzu, ki tayamu da adu'a Allah yasa mu ganta very soon. ko idan na dawo za ki taimaka min mu nemota?". yanayin yacca voice ɗinsa ya fito sai taji tausayinsa sosai, tace,"ka san inda za'a ganta ne?". yace,"a'a, kawai dai jikina na bani kamar ke za ki ga inda take". Tace,"sai dai na tayaku da adu'a, amma ni ban san aina zan ganta ba". yace,"adu'an ma mun gode. bye". da sauri tace,"da gaske sai next year?". ta tambaya tana tsare shi da ido. sai taga kamar yayi murmushi sannan ya ɗaga girarsa alamar ehh.  ta sake cewa,"to kana kula da kanka?". ya girgiza mata kai alamun a'a ba tare da yay magana ba. tai ajiyar zuciya kamar zata ce wani abu sai ta fasa, haka ɗaya take jin bata so ya yanke kiran, haka ɗaya take ji kamar idan ya kashe wayar shikenan ba zata ƙara ganinsa ba, hakama kamar ba zata ƙara jin voice ɗinsa ba. ya katse shirun nata da faɗin,"kin daina jin baccin?". ta ɗaga kanta,"ehh ya tafi. ba zaka jira Adda Zaytuna ɗin ta fito ba?". ya girgiza mata kai baice komai ba. tace,"tom shi abokinka ɗin da ku ka tafi tare fa?". yace,"ba shi wayar zanyi?". ta tura baki gaba tace,"ince masa me?, tambaya nayi ko yana kula da kai". Turaki na murmushin leɓe yace,"ai ba wanda ya biyasa kuɗin kula da ni. shima ta kansa yake". tace,"to magani fa?". yace,"haka kawai ake shan magani da ma?". Tace,"ai kai baka da lafiya". daga ita har shi ba wanda ya ƙara cewa komai, tana ta gyangyaɗi riƙe da waya yana kallonta, ƙarshe sai kashe wayar yayi ganin kaman tayi nisa a gyangyanɗin. Zaytuna na fitowa ta sameta akan gadon ta ɓingile tana bacci riƙe da waya a hannu, ta tasheta ta gyara kwanciyarta akan gadon. washe gari Fillo dai bayan sun gama aiki, leson teacher nasu ya tafi ta kama hannun Ɗausiyya tayi mata rakiya ɓangarensu. tana shiga ta faɗa jikin Kaka ta rungumeta cike da murna, Kaka tace,"ai ce nake kin koma can gaba ɗaya?". Kaka tayi maganar itama cike da jin murnar ganinta, kamar sun shekara basu ga juna ba. Maijidda ta kama hannunta ta jata zuwa cikin ɗaki tana cewa,"yarinya zo kiga kayanki. wallah sunyi kyau harda irin shaddar ƴar gidan Mamu aciki". Fillo dai tunda ta zauna gaban ƴar ƙaramar akwatin, kallon yacce Ɗausiyya da Maijidda ke aikin fito da kaya kawai takeyi. ita dai ji take kamar bata murna bata farin ciki da ganin kayan, kuma kamar tana farinciki ta dai rasa taƙamemen abinda take ji ɗin. har la'asar suna zaune, Maijidda da Zakiyya itama Jikar Yami da tazo hutu har Ɗausiyya suna ta tsara abubuwan da zasu yi lokacin biki. Zakiyya na cewa,"ke Fillo kike cewa ai kar a fara shiri yanzu, lallai baki san halin lokaci ba. to wallah yanzu za kiga wata biyun tayi, gwara duk abinda kika san zaki yi ki fara shi tun lokaci bai ƙure miki ba". Maijidda ta janyo Fillo jikinta ta raɗa mata abu a kunne tana dariya, Fillo tayi tsaki tana tureta. Maijidda suka tafa ita da Zakiyya suna tsokanar Fillo da cewar,"an matan Amir an kusa shiga sahun manya". Fillo dai babu wanda tanka. Yami ta shigo ta ƙwalawa Fillo kira ta fito, tazo ta durƙusa tana gaida Yamin, itama Yami na tsokanarta da cewar ai tayi zaton kunyar ba zata ƙara barinta shigowa ba har ai auren. kunya ta ƙara kama Fillo, Yami ta miƙa mata robar wani magani tace,"shanye wannan yanzu". ta karɓa ta shanye da ƙyar duk ba wani rashin daɗi ne da shi ba. sannan Yami ta ƙara ce mata,"kun gama jarabawar?". tace,"za dai mu fara Yami". tace,"to za ki ke samun shigowa kullum ko na haɗa miki magungunan ki tafi da su?". tai shiru bata ce komai ba tana kallon tulin wasu takarcen magani iri-iri, dama tun washe garin da aka kawo kayan Maijidda ta fesa mata labari wai Yami tasa a kawo mata magungunan da zasu gyarata tun daga sokoto da niger, ita dai haushi ne ya tuƙeta a lokacin saboda taƙi jinin taji ana cewa,"maganin mata ko kuma maganin gyara mace". Yami ta ware wasu ta zuba a leda tace,"gasu nan ki tafi da su, basu da ɗaci babu bauri babu komai, su zama sune ruwan shanki kinji ko. wannan kuma haɗin zuma ne itama kike sha akai-akai, dan Allah Fillo karki mana asarar kuɗinmu, in kin mayar da hankali kinyi amfani da su kanki kika taimaka". ita dai Kaka na daga gefe tana jinsu, bata ce komai ba har sai da Yami ta gama sannan tace,"da ki haɗa mata da wannan ruwan tsarkin ko, tunda naji Babuwan tace shima da wuri zata fara amfani da shi". Yami tace,"kinga kuwa na manta, shi da tace ma ya rage wata biyun zata fara amfani da shi". nan dai Yami ta haɗa mata duk abinda ya kamata ta kuma yi mata bayani. wajen biyar da rabi na yamma Hajiya Madina ta kira Fillo tace taje ta ɗauko mayafinta tazo ta rakata anguwa. wata sabuwar shadda da Maama ta ɗinka musu ita da Ɗausiyya ta saka, shaddan ash colour me duhu, an mata ɗinki me kyau ajiki kai ba kace ɗinkawa akayi dan a bawa ƴan aiki ba. tana zaune a parlo Hajiya Madina ta sauko daga stairs, waya ce riƙe a hannunta suna vedio call da Turaki, tana faɗa masa irin yacca kowa ke missing ɗinsa har Baffa, tana basa labarin Ilham ma jiya ta ke cewa zata biyo shi sai taji cewar baya Hong kong yanzu. irin yacca suke hirar kamar ba ɗa da uwa ba. Bello a gefensa yace,"Maama ni ba kuyi missing ɗina ba kenan, alhalin ni ke kulawa da shi". cike da tsokana Maaman tace,"Bello ke kuma wa acikin kayan miya, a'a Hammanmu dai shi muka sani, hatta ƴan aikin gidan nan sunyi kewarsa, yaushe rabon yay nisa damu irin haka, wlh gidan duk ba daɗi". ta miƙawa Fillo jakar hannunta tana cewa da Turaki,"tom zan fita ne, zanje wajen wannan matar da na faɗa maka nasa ta nema min marayun da za'a ke taimaka musu kullum, to shine zanje naga inda take da zama". Turaki yace,"ok to Allah ya taimaka ya bada lada, Nihal ce kusa da ke?". tace,"a'a su duk sun fice ai, ana bikin ƙawar Zaytuna sunje dinner party, ka san Baffanku ba so yake ba shisa nace suje mata da wuri su dawo da wuri, yafi ace basu je ba gaba ɗaya". Turaki ya sauke numfashi kaɗan yace,"Maama ke ɗaya kuma za ki fita?, ki bari mana gobe sa raka ki". tace,"ni da Fillo zamu je, bani ɗaya zan tafi ba me Babban suna". yace,"yauwa hakan yafi ai". sai kuma ya shafo wuyansa yace,"Maama please ko za ki bata ta kaiwa Salihu(me gadi), akwai saƙo dana bar masa, ina so naji ko yay concluding abin". ta miƙawa Fillo wayar tace,"kaiwa me gadi da sauri". Fillo ta miƙe tana ajiye jakar hannunta akan kujera, Hajiya Madina tace,"no tafi da jakar ai yanzu zan fito". Fillo dai tunda ta amsa wayar ta fito bata kalla screen ɗin ba, tafiyarta kawai take yi shi kuma yana ta kallon fuskarta da ta haska. ta kaiwa me gadi wayar ta dawo bakin mota tana jiran Maama, wucewar minti biyu sai ga me gadin ya dawo mata da wayar ta karɓa tana kallon screen ɗin, ganinsa yasa ta gaida shi. ya amsa yana ƙarewa kwalliyarta kallo duk da ba wani kwalliya tai ba, farar powder kawai ta sha sai lip balm. tace,"in mayarwa da Maama wayan?". yace,"no, i just want to say ki kula da kanki sosai kinji, hakama ki kula min da Maama, kar ki barta kuyi dare a inda zaku ɗin". ta amsa da,"to". he have alot to say to her but dole ya taƙaita, at last kawai ya tambayeta,"kina da wata matsala ne". ta girgiza masa kai alamar a'a. shi kuma ya kashe wayar, Fillo tabi wayar da kallo tana jin kamar wani abu a tare da ita na tafiya da katsewar wayar. ta tuna yanda yake kallonta yana tambayar kamar yana magana da matarsa. ko da suka je gidan Asabe Ƙuli, basu jima acan ba, kan hanyar su ta dawowa Hajiya Madina ta tsayar da driver a ƙofar wani store. a mota ta bar Fillo da Drivern bayan tace mata,"Fillo bari yanzu zan fito kinji. rigar jarirai kawai zan sayo inda muka je ɗin nan ne jikarta ta haihu". Fillo tace,"tom Maama sai kin dawo". har Hajiya Madina ta fita a motar sai kuma ta dawo ta miƙowa Fillo wayarta tace,"bana son zaman shiru riƙe wayan ko ƙur'ani kya karanta, ko kuma za ki biyoni ne?". Fillo ta girgiza kanta tace,"a'a Maama sai kin dawo ɗin". ta faɗa tana amsar wayar. game ɗin da take yawan ganin Maama nayi ita ta shiga, tana cikin yi sai ga kira ya shigo wayar, ganin sunan,"My Husband". na yawo jikin screen ɗin yasa ta fita daga motar tace da drivern bari ta shiga ta kaiwa Maama. sai da ta fito taji garin so silent, babu ma inuwar mutane dake giftawa, tana shiga ta bawa Hajiya Madina wayar ta fito. duk da tana hasko motarsu dake tsallake haka ta taho a ɗan tsorace ta tsallaka, sai dai sanda tazo bakin motar ta buɗe ƙofar motar zata shiga taji wani abu mai sanyi a wuyanta, sanyi irin na ƙarfen wuƙa. da sauri tayi yunƙurin juyawa bayanta jin numfashin mutum akanta, nan da nan taji numfashinta na seasn, sai kuma taji murya dai-dai kunnenta cikin raɗa da kakkausan amo ance,"wallahi kina ihu ko wani motsi sai na yanka maƙoshinki da kaifin wuƙar nan dake wuyanki". ai sai tayi ɗiff ta fasa yin ihun da tai niyya, idonta ya maƙale a driver seat sai taga drivern baya ciki, dan haka ayanzu bata da wani zaɓi da ya wuce umarnin da aka bata. tayi tsilli-tsilli da idanu tana jin yadda sanyin kaifin wuƙar ke wucewa har cikin zuciyarta. ta runtse ido sosai zuciyarta na tsananta bugawa, cikin kanta ya haska da kalmar mutuwa!, sai kuma gefen ƙwaƙwalwarta ya karanta mata ya ya Kaka zata ji labarin mutuwarta?, wanne hali Amir zai ji a sanda aka faɗa masa ta mutu?. tana ji mutumin yasa tsumma ya toshe bakinta sannan ya shiga janta har suka bar bakin motar, ita dai idonta wurgawa yake yana kallon ƙofar store ɗin da Hajiya Madina ke ciki, so ta ke ta hango fitowarta in yaso ta san ta yadda zata ƙwace bakinta ta ƙwala mata kira, sai dai har suka baro bakin motarsu aka zo da ita wajen da bata san ina ne ba, bata ga kowa a wurin ba ko da kuwa Maama. taji an buɗe motar da suke kusa da ita a yanzu an buɗe ƙofar baya. tana jin sanda wata murya daban da wacce ke riƙe da ita yace,"sakata aciki". duk wannan abin da ake har yanzu wuƙar na wuyanta motsi kaɗan suke jira tayi su fille kan. suka zirata acikin motar, tana kallon wanda ke front seat fuskarsa lulluɓe cikin bakin ƙyalle, wanda ke riƙe da ita yana shigowa ya rufo ƙofar, sannan ya ɗauke tsumman da ya rufe mata baki da shi, daidai da buɗewar bakinta zatai ihu, daidai kuma da juyowar na gaban ya danna mata wani tsumman da ya rufe hancinta da bakinta. take ta shaƙi ƙamshin wani abu a jikin tsumman, bata da ilimin sanin chloroform balle a yanzu da taji ƙamshinsa tayi ƙoƙarin ɗauke numfashinta, kuma wannan ƙamshin abin da ta shaƙa ya wuce har cikin kanta sai taji kamar zata mutu, ƙirjinta kamar ana rura wuta tana ci bal-bal, lokaci ɗaya kuma sai taji numfashinta ya sarƙe gaba ɗaya, ta kasa shaƙar iska, a hankali kuma sai jinta da ganinta suka ɗauke duka, nan take kuma tai laƙwas ta tafi luuu tana faɗawa jikin na kusa da ita. ba tare da ɓata lokaci ba motar ta bar wajen cikin speed ɗin da ba za'a taɓa zargan muggan mutanene acikinta ba. har sanda zasu wuce driver da ya dawo daga fitsarin da yaje ya bi motar da kallo, yana jin kamar bai yarda da motar ba har ta ɓacewa ganinsa. dai-dai nan kuma ya ɗaga kansa yana ganin me tahowa daga bayansa...                  *LULLUƁIN BIRI don catch fire.......* *comment, vote and share.* [8/30, 09:42] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* '''DAGA MARUBUCIYAR''' 1-Sirrin Ɓoye 2-Al'amari 3-Hidaya Noor 4-Alhussain 5-Sanadin Talauci 6-Ƙaddarar So 7-Prince Khaleed Da sauran su..... *32* ganin Hajiya Madina yasa drivern tafiya wurinta da sauri ya karɓi ledan kayan dake hannunta, a gaban mota ya aje manyan ledan kayan kusan guda 5, da gani kasan ba siyayya bace ta jarirai kamar yanda ta faɗa, siyayya ce ta musamman tayita don yin kyauta ga Fillo. drivern ya buɗe mata back seat ta shiga, sai dai tun kamin ya zagayo ɓangarensa har Hajiya Madina ta kula da rashin Fillo cikin motar. hakan yasa ta buɗe motar ta leƙo kanta tana faɗin,"Ɗan Usaini ina ƴata?, ina Halimatu taje?". Ɗan Usaini ya dakata da buɗe motar yace,"Hajiya ai taje kai miki waya ni kuma naje ɗan yin uzuri". Hajiya Madina tace,"ban gane nufinka ba". yace,"ruwa naje kamawa, to ban san ba gaskiya ko ta dawo na dai barta ta shiga ciki kai miki waya". lokaci ɗaya Hajiya Madina ta fito a motar gaba ɗaya,"ka daina cewa ta kai min waya. kai wayar tun yaushe ne?, kusan fa minti biyar kenan, tana bani ta fito". Ɗan Usaini na waige yace,"to ko ta zo ta tarar bana ciki sai ta koma, bari na duba cikin store ɗin". ya faɗa yana barin wajen, Hajiya Madina tabi bayansa. lokacin hankalinta duk bai tashi ba amma dai ta tsorata, ina Fillon zata je?, idan cikin store ɗin ta koma ai tana shigowa zasu yi clashing tunda tana daga bakin ƙofa tana biyan kuɗi. daga cikin store dai har wajensa babu Fillo, a wannan lokacin hankalin Hajiya Madina ya fara tashi, haka suka dinƙa zagayen arean wajen suna kiran sunanta suna dubawa amma ba ko alamarta. Ɗan Usaini na tare da me gadin store ɗin yace da Hajiya Madina,"ƙilan ko da ta shiga kai miki wayar makuwar hanyar fitowa tayi". Hajiya Madina dai tana tsaye ta kasa cewa komai, saboda yacca take jin numfashinta na neman yankewa, iska ce a wajen ke ta kaɗawa amma ita zata iya rantsewa hucin zafi take ji ajikinta, zata iya rantsewa kamar ji da ganinta ya ɗauke. ƴar mutane ta ɓta ata sanadinta?, me zata ce da Kakar yarinya?, me zata ce da wanda ke shirin aurenta?. lokaci ɗaya kanta yay wani mugun sarawa kawai sai ta fashe da kuka, staffs dake cikin store ɗin suka fito dai anata ƙara lalube, tsawon kusan minti 30 inuwar Fillo ma ba'a gani ba. da ƙyar Hajiya Madina ta iya picking call ɗin Baffa, ta faɗa masa halin da take ciki, sai dai kamin yace komai Hajiya Madina ta yanke jiki ta faɗi a lokacin, dalilin abinda taji Ɗan Usaini na faɗawa me gadin wajen. "to ni dai bana ce hakan ba ne, zargi kawai nake da hasashe. kaga bakin bishiyar can anan naga motar tayi parking, kuma wallahi tun lokacin da zan tafi fitsarin naji hankalina bai kwanta da motar ba, to kuma sanda nake dawowa sai naga motar na barin wajen, sai na bita da kallo har ta ɓacewa ganina, kasan Allah ba wai don saboda ɓatan yarinyar nan ba, jikina kawai naji bai aminta da motar ba, Ya Rahmanu dai yasa ba ƴan garkuwa bane suka yi gaba da yarinyar nan". da hanzari akai kan Hajiya Madina, da ƙyar aka iya kamata aka sakata a mota sai asibiti. Tunda suka isa asibitin aka karɓe ta aka shiga bata taimakon gaggawa saboda yanayin yadda ta ke a sume, su na tsaye cirko-cirko a ƙofar ɗakin aka shiga da ita suna jiran suji me likitan zaice in ya fito, ba'a fi mintina biyu ba ya fito yana ƙarasa zare gloves ɗin hannunsa a lokacin ne kuma Baffa ya iso wajan da hanzarinsa. ganinsa yasa Ɗan Usaini nufarsa, sai dai ko ta kansa Baffa bai bi ba yay wajen likita. "Likita ya jikin matata?" Baffa ke tambaya yana kallon likitan da yake goge hannunsa da hand sanitizer. ya kalla Baffa yace,"Patient ɗin ku jininta ya hau sosai, akwai abinda ya firgita ta lokaci ɗaya shiyasa BP ɗinta yayi high, wannan dalilin ya saka ta suma, but yanzu an saka mata drip kuma da izinin Allah da ta farka zata dawo dai-dai." Ɗakin Baffa ya shiga ya tarar da ita a kwance tana bacci, ya zauna gefenta ya kamo hannunta yana ta kallonta, tausayinta yayi matuƙar kama shi, ya sa ni fiye da hawan jini ma za'a iya faɗa indai akanta ne, saboda ita macece da bata iya saka abu a ranta ba, tana da saurin ruɗewa nan da nan musamman akan ƴaƴanta, haka ma akan wanda ta damu da shi, ta kan kasa juriya da dauriya. ya san tana matuƙar son Fillo, dan ko da yaushe suka zauna tana yawan masa labarin yarinyar, irin tarbiyar yarinyar da hankalinta da natsuwarta da kamun kanta, har ta kance masa ita ina ma ace yarinyar ta zama rabon wani acikin Khalil ko Turaki. kuma sau tari tana faɗa masa insha'Allahu zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wajen ganin yarinyar ta samu wadataccen ilimi domin itama rayuwarta ta inganta, yarinyar ba kalar yaran da za'a banzatar da rayuwarsu ba ne. Hajiya Madina bata farfaɗo ba sai bayan sallar isha'i, kuma tana farkawa idonta ya sauka akan Baffa dake waya da wani police yana shaida masa ɓatan Fillo, sai dai suna haɗa ido yay saurin sallama da police ɗin gudun kar taji a ƙara samun matsala. ta kama hannunsa tana faɗin,"Baffa yarinyar mutane, ƴar mutane ta ɓata a hannuna Baffa, me zance da iyayenta Baffa?, me zan faɗawa mijin da zata aura Baffa?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi wallahi banda masaniyar inda tayi, Baffa wallahi da nasan hakan zata faru ba zan fita da ita ba". daga yanayin yanda take maganar kasan bata cikin hayyacinta. sai kuma tayi shiru tana kallonsa kamin cikin sanyin murya tace,"Baffa an ganta ne?, Ɗan Usaini ya nuna motar mutanen?". ta faɗa tana sakin kuka me ban tausayi. Baffa Ya kama hannunta sosai, ya kwantar da murya yace,"Please stop crying, Insha'Allahu za'a ganta very soon, ba wai ɓata tayi kamar yanda muke tunani ba insha'Allah". tace,"Baffa ta ya?, Ɗan Usaini fa yace yaga motar da bai yarda da ita ba, kuma fa lokacin ne ta fito ta kawo min wayata, Baffa me kake tunanin ya faru?". Baffa ya ƙara sauke numfashi sannan yace,"ki bar wannan tunanin Madina. kuma insha'Allah cikin daren nan zamu ganta, nayi report mawa police and zasu fara aikin nemanta yanzu". sai ya ɗauko wayarsa yay dialling numbern Inspecter Sise, yana ɗagawa yace da shi,"ta farka, wanne irin bayani kuke buƙata daga wajenta?". Inspecter Sise yace,"ka bata wayar muyi magana". Baffa ya kalla Hajiya Madina sannan yace da Inspecter,"tana da saurin ruɗewa, please a san irin tambayar da za'ayi mata". tambayar kayan dake jikin Fillo da kuma yanayin yarinyar da kamanninta da yanda akayi ta fito duk su Inspecter ɗin yaywa Hajiya Madina, kuma duk ta ba shi amsa, sai dai daya tambayi hoto tace gaskiya bata tunanin yarinyar na da hoto ma. daga nan kuma inspecter ɗin ya ƙara cewa da Baffa zasu yi arresting Ɗan Usaini domin shima zai iya zama suspect nasu. motar police tazo asibitin cikin ƙanƙanen lokaci, aka sawa Ɗan Usaini handcuff aka wuce da shi, hankalinsa a tashe yana ta rantse-rantsen shi wallahi bai san komai ba akan ɓatanta, yaje kama ruwa lokacin, ai masa rai wallahi baida hannu. To har wajen dai sha ɗaya na dare babu wani batu na ganin Fillo ko alamun ganinta, tun Baffa yana ganin ɓatan kamar da wasa har ya dawo ya ɗauke shi da gaske, a sannan kuma shima hankalinsa ya fara tashi. Hajiya Madina dai har lokacin banda kuka da ambaton Allah babu abinda takeyi, ƙememe kuma taƙi yarda aje gida a tambaya ko ta koma, sai Khalil kawai ta yarda Baffa ya kira ya gargarɗe shi akan kar ya bar kowa yaji zancen, kawai dai ya san yanda zai shiga wajen Kaka su gaisa ya gani ko yarinyar ta koma, shima kuma letter ya kira ya sanar musu bata nan. a sanda waɗanda suka ɗauke Fillo suka fito daga cikin gari, lokacin ne kuma suka ƙara speed na motar, gudu na fitar hankali suka dinga shararawa akan titin da babu kowa, gudu na ganganci kamar basa son rayukansu. sai da suka yi tafiya a ƙalla ta awa guda sannan suka shigo cikin wata unguwa, daga nan kuma suka fara tafiya with normal speed gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sosai sannan suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi, haka suka dinga wuce gidaje da shaguna, sai da suka zo kan wani incomplete building tukunna sukai parking motar, ɗaya daga cikin su ya fita ya buɗe gate suka shiga da motar ciki. compound ɗin gidan ƙato ne, sai da suka je har entrance na shiga cikin gidan sannan sukai parking a wajen. na gaban motar shi ya fata fitowa yana cire face mask ɗin fuskarsa da ya dame shi, sannan wanda yay driving motar ya fito, sai ɗayan da ya rage a baya ya cicciɓo Fillo kamar wata jaririya, shima ya fito sannan suka nufi cikin gidan a tare da sauran. Babban parlo ne da ba'a gama ginasa ba but ansa tiles anyi filasta paint ne kawai ba'ayi ba sai ƙarashen wearing, suka wuce zuwa wani dogon corridor inda ananne zaka tarar da jerin ƙofafi na rooms, a ƙofa ta ukun ƙarshe suka tsaya, ogan nasu shi ya buɗe sannan wanda ke saɓe da Fillo a kafaɗa ya fara shiga, yana shiga ya kwantar da Fillo kan wani ƙaramin gado kamar gawa. Madaidaicin bedroom ne da shi kaɗai akai completing gininsa acikin ɗakunan dake gidan kusan guda 7. ogansu ya ƙaraso gadon ya zauna daga gefe, yasa hannu ya mammari fuskar Fillo don tabbatar da nauyin sumanta, sannan ya ɗago kansa ya kalla ɗaya daga cikin yaransa yay masa alama da yazo. mutumin da duk cikinsu shine ƙato yazo ya hau kan gadon riƙe da shimfiɗeɗiyar igiya a hannunsa, ya jirkitar da Fillo gefe ya ɗaure mata hannayenta ta bayanta, ya kuma haɗa ƙafafuwanta wuri ɗaya suma duka ya ɗaure, sannan ɗaya daga cikinsu ya miƙo masa masking tape ya nannaɗe bakinta da shi. Sai da suka tabbatar ko da ta farka babu ta yanda zata iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi tukunna duk suka fice daga ɗakin suka barta ita ɗaya suka rufe da key. Fillo dai bata farka ba sai da ana tada iƙama na sallar asuba, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin nauyi, ga warin wani abu a ƙofofin hancinta, gaba ɗaya wani irin ciwo jikinta keyi mata tamkar wadda aka ɗau kwanaki ana duka, ta rufe idonta ta rumtse sose sannan ta buɗe tana jin eyelid nata yay mata nauyi sosai, sai a sannan kuma ta fara bin ɗakin da kallo har ta sauke ganinta akan roof na ɗakin, sose take kallonsa da mamaki sannan ta ƙara juyar da ƙwayar idonta ta sauke akan ƙofar ɗakin, daga roof ɗin har ƙofar basa cikin irin waɗanda ta sani, ba ƙuma sa cikin inda tasan tana kwana. daga paint na ɗakin har kan gadon da take duk bata san su ba, to aina take?. tana ci gaba da bin ɗakin da kallo tana so ta tuna a inda take, da kuma yacca akayi tazo nan ɗin amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta cunkushe taƙi yin tunanin abinda take so. sai tayi ƙoƙarin motsawa don ta tashi amma sai taji ta kasa, ta ƙara yunƙurawa taji babu ta yanda za'ai ko da hannunta ya motsa balle ƙafarta, wannan ya tabbatar mata da cewar a ɗaɗɗaure ta ke gaba ɗayanta. sai sannan tayi ƙoƙarin buɗe bakinta tayi magana shima sai taji bakin a liƙe yake, ta hanci kawai ta ke numfashi banda baki. sai ta rufe idonta tana juyar da fuskarta ɗayan side ɗin sannan ta buɗe idon, nan ta ƙara tabbatar da bata san ina ne nan ɗin ba, take ta fara kokawa da numfashinta saboda tsoro, dai-dai lokacin kuma taji ana sallamewa daga sallah a masallaci, sallar da ta fahimci sallar asuba ce tunda raka'a biyu taji anyi, cikin kanta taji ƙwaƙwalwarta na biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kuma a hankali cikin ikon ubangiji tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata. sai ta rumtse idonta hoton komai na haska mata tarr tun daga ɗora wuƙa a maƙoshinta, da shigar da ita cikin mota, da kuma juyowa da akayi aka toshe mata hanci. take tayi ƙoƙarin ƙwalla razananniyar ƙara sai taji ashe fa bakinta a manne yake. to Ina ne nan ɗin?, waɗanda suka ɗaukota su waye?, me yasa suka yi mata irin wannan ɗaukowar?, nan ɗin da suka kawota me zasu yi mata?, me yasa suka ɗaɗɗaureta haka har da toshe baki?. tarin tambayoyin da ta yiwa kanta kenan, kuma take ƙwaƙwalwarta ta bata amsa da,_"you have been kidnapped"._ take kuma zuciyarta ta ƙara maimaita mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. ƙirjinta ya dinga bugawa hawaye nabin kuncinta, tashin hankalinta ɗaya shin wanne hali Kaka ta ke ciki yanzu?, Wanne hali Amir yake ciki?, wanne hali Maijidda da Yami suke ciki?, ya Hajiya Madina zata kasance idan ta dawo taga babu ita?. idan har kidnappers ne suka ɗauketa shin sunyi contacting da wani nata?, wa suka tuntuɓa?, adadin nawa suka nema kuɗin fansarta?, wa zai biya maƙudan da suka ambata?, sai brain ɗinta ta ƙara biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil. ta buɗe idanunta ruwayen hawayen ciki na samun damar gangarowa, kuma a sannan ta fahimci hasken dake ta wajen window da take gani gari ya fara wayewa kenan?. take kuma ta tuna da cewar fa bata yi sallar magriba da isha'i ba, ga asuba ma a kunnenta akayi amma bata yi ba. taja ƙafafuwanta da suka sandare tana so ta lanƙwasa su sai taji kamar zasu karye idan tayi hakan, saboda azabar ciwon da suke yi mata. babu ta yanda zata iya miƙewa ta tashi ko da zaune ne, balle kuma ta iya sauka daga kan gadon, dan haka kawai sai ta fashe da kuka sosai, can bayan wasu awanni taji muryar mutane  ƙasa-ƙasa a bakin ƙofar ɗakin. Ta juyo da fuskarta tana kallon ƙofar, tana kallo aka turo ƙofar mutane uku suka shigo, Ƙaton cikinsu shi ya fara shigowa tukunna wasu sirara suka biyo bayansa bayan ɗayan cikinsu ya maida ƙofa ya rufe. tana kallo su suka ƙaraso bakin gadon, Ƙaton ya jawo wata kujera ya zauna yana facing ɗinta, tana kallo yaywa ɗaya daga cikinsu alama wanda shine duk yafi siranta a cikinsu, ya zagayo daga bayansa ya hau kan gadon ya ɗagata ya zaunar da ita, sai a sannan ta sami damar ƙarewa inda take kallo da kyau da kuma mutanen dake tare da ita fuskokinsu duka a rufe. ƙatoton ya auna Fillo da bakin bindigar da take hannunsa yace,"zamu buɗe maka bakinka, idan har muka buɗe kayi wani yunƙuri na yin magana ko kuma ihu sai na fasa kanka da alburushi". Ya faɗa muryarsa da ƙarfi har tana amsawa a ɗakin, sai dai kana jin hausar tasa kasan riƙaƙƙen inyamuri ne. hawayen Fillo ya ƙaru akan fuskarta, tana jijjiga masa kai alamar taji me yace cike da tsanin tsoro gami da tashin hankali. Ƙaton ya kalli tsamurmurin dake kan Fillo tsaye yay masa alama da bakin bindigarsa. take tsamurmurin yasa hannu ya ɗaye masking tape dake manne da bakin Fillo, tsananin azaba yasa ta rumtse ido don ji tayi kamar ya haɗo da fatar bakin nata ne ta cire. so ta ke tasa hannu ta shafa wurin ko ta sosa amma babu dama, tunda basu kunce mata hannu ba, saboda haka sai ta rumtse idonta sosai tana jinginar da kanta da bango har sai da taji zafin ya lafa tukunna ta buɗe. ta buɗe ido ta sauke kan ƙaton mutumin dake latsa waya, rabin fuskarsa rufe take da hanky, tana kallo ya ɗaga hannunsa, ɗayan mutumin dake tsaye tun ɗazu a bayansa ya zagayo ya dire kwanon abinci a gabanta da pure water guda ɗaya. sai tabi kwanon abincin da kallo sannan ta ɗago ta kalli ƙaton dake saita da ita da bindiga, ya zare mata manyan idanuwansa yace,"buɗe kaci". tana ƙoƙarin danne kukanta tace,"dan Allah zan fara yin sallah tukunna". mutumin ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata, a tsawace yace,"kaga nayi kama da wanda ke yin Sallah?, to nan wurin da kake gani ba'a sallah, ko adu'a muka ji kayi sai mun ɓula kanka da alburushi. adu'a ɗaya muka yarda kayi shine a biya kuɗin fansarka, daga wannan bamu yarda da kowanne kalan adu'a daga bakinka ba, do you hear me well?". da sauri ta ɗaga kanta sai dai bata jin zata iya ta zama haka ba tare da sallah ba, don haka ta ƙara buɗe baki tace,"nayi muku alƙawarin wallahi ba zanyi wani motsi ba, ko adu'ar ficewata daga nan ma ba zanyi ba muddin ba zaku cutar da ni ba, amma don girman Allah ku barni nayi sallah, ko magriba da isha'i na jiya banyi ba". tana rufe baki mutumin ya buga mata bindigar hannunsa a bakinta yace,"only when you are out of here shine zaka je kayi ta sallolinka, but not in this place, sallah acikin wurin nan is prohibited from you". sai kawai ta fashe da kuka sose tare da faɗin,"to su waye ku?, Me nayi muku?, Me kuke so tare da ni?". ƙaton mutumin ya bushe da dariya yace,"mu kidnappers ne, kuma ba zamu sakeka ba har sai an biya kuɗin fansarka naira miliyan biyar, idan kuma ba'a biya ba zamu yi gunduwa-gunduwa da namanka sannan muka aikawa da iyayenka". cikin matsanancin kuka Fillo ta ambaci kalmar innalillahi a karo na babu adadi tun bayan farkawarta, suna batun miloyan biyar kafin a karɓeta. wa take da shi da zai biya waɗannan maƙudan kuɗin?, me Kaka zata ɗaga ta siyar a sami waɗannan kuɗin?, ta san babu me biyan waɗannan kuɗin a karɓeta kamar yanda babu abinda Kaka zata ɗaga ta siyar a sami wannan uban kuɗin. saboda haka sai kawai ta rumtse ido tana jin tana sallamawa da duniyar, ita kuma haka kalar ƙaddarar take?, fatanta guda ɗaya ko da ace ba zata fita anan tana roƙon Allah yasa kar mutanen su cutar da ita su rabata da mutuncinta, a hankali yanda ba zasu ji me tace ba ta furta,"Ya Allah ka fitar da ni daga gurin nan cikin amincinka da salamarka". Ƙaton mutumin ya ƙara sakar mata tsawa yana cewa,"buɗe abinci kaci". tana kuka cikin firgici da razanin da take ciki tace,"babu ta yanda zanci ai". sai a sannan ya tuna da cewar a ƙulle take, ya daɗa kallon wanda ke tsaye kanta ya bashi umarnin kunceta. cikin zafin nama tsamurmurin ya kunceta kamar zai wurgata ta faɗo ƙasa, sanda ya gama kunceta ɗin sai ta sauke ajiyar zuciya saboda relief da ta samu, ta kama hannun nata tana shafawa, jinin da ya daskare waje ɗaya na saki yana bin ko'ina, kamin a hankali taji dama-dama. ba ta so ya ƙara yi mata tsawa don haka ta ɗauka pure water ɗin ta kuskuren bakinta ta zubar da ruwan a jikinta, sannan ta janyo kwanon abincin ta buɗe, taliya ce jallof babu kyan gani, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta tashi, amma saboda babu yanda zata yi dole ta shiga cusawa a bakinta tana taunawa da ƙyar. ganin ta fara cin abincin suka tashi suka nufi ƙofa zasu fita, tai ƙarfin halin cewa,"bani da kowa sai Kakata, ku taimaka min dan Allah". suka mata shiru suka fice suna rufe ƙofar, sai kuma taji an ƙara buɗewa ƙaton mutumin ya leƙo yana faɗa mata,"if you dare try to make any sound, i swear I will fill your brain with this". ya faɗa yana mata nuni da bindigar hannunsa, kuma ta tabbata he means it. taji alamun an saka key a jikin ƙofar which means sun ƙulleta kenan, sai ta ture kwanon abincin dake gabanta, tabi ƙafarta da kallo tana noticing yanda ta kumbura sosai, ta jawo ƙafar da ƙyar tana shafata sannan tayi ƙokarin zuro ƙofar ta sauko daga kan gadon tana tsayawa akanta. da ƙyar taja ƙafarta bayan ta ɗauko pure water ɗin ta isa bakin wata ƙofa da ta gani acikin ɗakin, daban da wacce suka shkigo. ta kama handle ta buɗe ƙofar a hankali sai taga banɗaki ne, tai saurin faɗawa ciki tai tsarki sannan tayi alwala ta fito. ɗankwalinta tasa ta tattare ƙasan wajen, bata san ina ne gabas ba, kuma lokaci ɗaya maganar Amir ta haska mata sanda yake cewa shi addini ɗan sauƙi ne, idan ka tsinci kanka a garin da ba naka ba, kuma babu mutane a wajen da zaka yi sallah balle ka tambaya, to kana iya fuskantar ko'ina ne ka tada sallarka, don haka ta fuskanci inda take jin yafi kwanta mata ta tada sallarta da babban mayafin dake jikinta, sai da ta rama sallolin jiya dake kanta tukunna tayi asuba ta kuma yi sallar wadha ɗin da bata wuceta. Bayan ta idar bata yi saurin tashi a wurin ba sai da tayi dogayen adduoi sannan tai saurin miƙewa ta koma kan gadon gudun kar su dawo ɗakin su sameta. ta zauna da yaƙinin duk sanda suka kawo mata abinci zata yi amfani da ruwan wajen yin ibadarta. kuma zamanta kenan cikinta ya murɗa, tasan ba komai bane face yunwa, kuma take sai amai saboda tuntuni take jin zuciyarta na tashi saboda wannan farar taliyar da ta ci mara ɗanɗano. har yanzu tunaninta guda ɗaya ne, ta ina zasu fara neman wanda suke saka ran zasu biya kuɗin fansarta?, alhalin a wannan duniyar babu wanda ya san da su banda Allahn da ya halicce su. a can ɓangaren kuwa tunda gari ya waye ƴan sanda suka ƙara tsananta bincikensu, har sannan kuma ba'a sallami Hajiya Madina ba don ita tace gwara a barta a asibitin har sanda za'a ga Fillo sannan ta koma gida ta iya haɗa ido da Kaka, amma banda cikin critical situation ɗin nan da suke ciki. sai dai tunda ta farka ta tashi da zullumin ko zasu ji labarin cewar an ganta, amma police ɗin na daɗa faɗa musu shiru babu labarin yarinyar, sai dai sun sanar da Baffa cewa za su cigaba da bincike insha'Allah, kuma ganin har rana tayi still babu wani labari ya saka dole aka sanar da Kaka halin da ake ciki. ba Kaka kaɗai ba, hatta ƴaƴan Hajiya Madina sai a sannan suka san abinda ya faru banda Khalil da ya san komai tun a jiya. dan Baffa ce musu yayi sun ɗauki hanyar abuja a lokacin Maama na da seminar a gobe ƙarfe 8. Kaka dai mutuwar zaune tayi daga inda take, tabi Hajiya Madina da Baffa da Khalil da kallo, kamar dai bata fahimci zancen da suke mata ba, kamar ba dai-dai taji ba, kamar suna so suce Fillo ta ɓata tun daren jiya kuma har zuwa yammacin yau ba'a ganta ba, wannan mummunan labari ne, kuma bata tunanin waɗannan salihan bayin zasu iya zuwar mata da shi. Hajiya Madina ta fashe da kuka ganin yanda Kaka ta daskare, tana cewa,"ki yafe min Kaka, wallahi ban san hakan zata faru ba da ban fita da ita ba". Yami dake tsaye itama ta kasa motsi take kallon Maama da tausayawa tace,"ki daina kuka Hajiya, tsautsayi ne, kuma cikinmu babu wanda bai san ƙaddara ba me kyau ko mara kyau". sai sannan hawaye ya sauko a fuskar Kaka, dai-dai take ji da gaske faɗa mata suke jikarta ta ɓata, tayi inda ba'a san ta nufa ba, kuma yini guda babu ita babu labarinta. cikin muryar kuka tace,""Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya Rahimu ka bayyana mana yarinyar nan a duk inda take, ka dawo da ita garemu cikin amincinka". ta faɗa tana mayar da idonta kan Hajiya Madina tace,"ki daina kuka Hajiya, ba ki da laifi ko ɗaya, dama ubangiji tuni ya shirya faruwar hakan, ko ace bata dalilin fitarku ba, ni musulma ce nayi imani da ƙaddara, saboda haka ki daina ɗorawa kanki laifi, ki share hawayenki don Allah, adu'a kawai ya kamata muyi Allah ya tsareta a duk inda take ya kuma dawo da ita garemu cikin amincinsa". sannan Kaka ta ƙara maida dubanta ga Maijidda dake ta uban kuka, tace da ita,"ki kira Amir a waya ki sanar masa". Yami tace,"a sanar masa kuwa?". Kaka tace,"to ɓoyuwar ai babu amfani, gwara a faɗa masa ɗin sai su shigar da adu'a kafin tashin ɗalibai a makaranta". Yami tace,"haka ne kuma, tunda su gidan malamai ne ko saukar ƙur'ani a iya yi cikin ƙaramin lokaci". Maijidda ce ta kira Amir, kuma tun kamin ta sanar masa yasan babu lafiya tunda yaji muryarta tana kuka. kuma zata iya rantsewa da ta faɗa masa faɗuwa yayi a inda yake saboda yanda taji ya saki salati a gigice. ƙarar salatin da kowa sai da ya jiyo daga cikin wayar, wannan yasa Kaka ta ƙara ruɗewa hankalinta yayi ƙololuwar tashi. kowa dai a wajen yayi shiru, zuciyar kowa da abinda take saƙawa, daga ƙarshe dai Baffa yace su Zaytuna su kwaso kayan Kaka a taho da ita ɓangarensu, hakan kuma akayi suka ɗaukar mata abinda zata buƙata suka taho da ita wajensu ita da Maijidda da har yanzu ita ɗaya ce bata bar kukan fili ba. kuma ita kowa yafi jin tausayi bayan Kaka, tsabar kuka idonta sunyi luhu-luhu. ɓangaren Ameer kuwa har drip aka saka masa, dan lokacin da aka faɗa masa akan machine yake bai san ma sanda ya saki kan machine ba ya faɗa wani rami shi da machine ɗin, duk ya kurkurje yay rauni a duk jikinsa, ƙarshe sai wasu bayin Allah ne suka kaishi asibiti, a asibitin ya bayar da lambar Mahaifinsa aka kira nan da nan kuwa sai ga asibiti ya cika da mutane, abinka da me tarin ƴan'uwa. Innarsa na zuwa ya faɗa mata abinda ya faru, kuma take ta ƙaryata tace sai dai in ko yaranne a ƙuruciyarsu suke so su gwada shi da irin son da yakewa Fillo, sai dai itama ko da ta kira abinda Yami ta faɗa mata kenan, Amir dai nata kallonta with his all hope ace ƙaryar suke yi masa, gwada shi suke so suyi, kuma in har gwajin ne yasan yayi nasara, sai dai zai faɗa musu kar su ƙara yi masa irin wannan wasan gudun rasa rai wataran. sai dai tana ajiye wayar yaji tana faɗawa mahaifinsa halin da ake ciki, dan haka nan da nan brothers ɗinsa suka watse akayi gida dan fara karatu da adu'oi. faɗar dai tsananin tashin hankalin da Amir ke ciki ba zai misaltu ba, don lokaci ɗaya har ya faɗa kamar wanda ya jima yana jinya, Dr ma har yana cewa in ba'a kiyaye an nema masa abinda yake nema ba zuciyarsa zata iya taɓuwa. a daren wannan ranar dai Kamar yadda Fillo bata iya runtsawa ba, haka ma Hajiya Madina, Kaka, Maijidda da kuma Amir, dan Amir saura kaɗan ya rage ma ya bar asibiti a daren ya fita nemanta. Tashin hankali dai duk bai bar kowa ya runtsa ba, yaran Hajiya Madina kansu sun kasa bacci saboda halin da mahaifiyar su ke ciki, shi kansa Baffa har sannan yana kan matarsa yana bata baki. at the end dai Baffa yaga zaman kukan duk ba shi bane, dan haka yace kowa yay sallah ai adua, a haka suka raya wannan daren daga masu sallah sai masu karatun qur'ani sai masu tasbihi haka har asuba da tayi. bayan sunyi sallar asuba Anty Zulfa ƙanwar Hajiya Madina da tazo ita ta zauna tana jero Adduo'i kowa na amsawa, cikin adu'ar suna  roƙon Allah ya kare Fillo a duk inda take, ya kuma dawo da ita garesu cikin amincinsa, da ameen suka amsa har ta idar suka shafa, suka shafa aduar a daidai sanda Baffa ya turo ƙofa ya shigo. ya zauna akan kujera idon kowa akansa, ya numfasa sannan ya shiga yi musu bayanin abinda police suka ce game da report ɗin da aka shigar. yace,"ku kwantar da hankalinku dan Allah tunda dai har Police sun riga sun shiga maganar, kuma yanzu zasu ƙara bazama gurin nemanta". ya kalli Kaka yace,"na basu hotonta da shi saurayin nata ya bamu, kuma duk an baza shi a lunguna da saƙunan garin nan, an miƙa cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hoton nata". cikin kuka Hajiya Madina tace,"to amma me yasa zasu shigo da tunanin cewar Kidnappers ne suka ɗauketa. Baffa idan sune ai da tuni sun kira waya, mun kwana na biyu fa kenan Baffa, Kidnappers ba zasu yi shiru har haka ba. dan Allah Baffa a dai ƙara bincikawa ƙila wani wurin tayi, idan kuma kidnappers ɗinne a nemo su, su faɗa mana abinda suke so". ƙarfin kukanta ya katse maganar tata. to wasa-wasa dai har tsawon kwana uku lamarin Fillo shiru, Kidnappers ɗin da aketa tunani suma shiru basu kira ba, wannan ya ƙara ɗaga hankalin kowa, aka kuma bar tunanin cewa kidnapping Fillo akai, dan idan shine tuni sun kira waya, abin dai yafi kama da ɓata, Kaka na batun ita gwarama taga gawarta ta huta. adu'a kawai ake ta ko'ina, sadaƙa kuwa a gidan Alƙali Dikko babu dare babu rana. Amir kuwa yana can ba ci babu sha saboda tsananin damuwa, musamman idan ya zauna yana tuna moments ɗinsu shi da ita. lamari fa ya ƙara ta'azzara, dan tun ana lissafin kwanaki aka daina aka shiga sati, to abu kamar wasa daga sati ɗaya sai gashi an tafi sati na biyu har an shiga na uku. daga nan kowa ya saddaqar da cewar an rasa Fillo har a bada, kuma duk wannan bidiri da ake Turaki bai sani ba, da ya kira waya Zaytuna kawai shaida masa tayi sunyi tafiya ita da Kaka zasu yi wata guda. amma tun ranar da sukai waya da Maama yaji hankalinsa bai kwanta ba, tace masa kar ya damu ciwon kai ne ba wata matsala ba, ya zauna yay concentrating kan sabon project ɗin da Baffa yasa su. haka kuma dole ya haƙura ya maida hankalinsa kan aikin da Baffa yasa su, sai dai zuciyarsa ta kasa natsuwa, rabin tunaninsa na kan Fillo, so yake yaji ko da muryarta ne, amma babu hali, tunda har Zaytuna yasa ta tambayi Yami ko suna gaisawa da su kaka ta waya, Zaytuna tace masa Yamin tace itama wallahi duk ta rasa ta inda zata same su. kuma randa Fillo ta cika kwana 21 cif, ranar kidnappers ɗin suka kira wayar Yami suka shaida musu suna buƙatar naira miliyan 5 cas,idan kuma babu to su yanka musu ƴarsu su turo musu da namanta a kwali, suka kuma bada gargaɗin cewa in har suka sanar da wani batun hakan to ko da sun kawo kuɗi lallai sai sun yake ƙafafun yarinyar, aka kuma saka musu muryar Fillo dake ta kuka tana roƙon Kaka akan azo aceceta zata mutu. wannan batun yasa Kaka da Yami suka yi ɗiff ko Maijidda basu bari ta sani balle su Hajiya Madina da sun tsab zasu iya sanar da police. Kaka ta kira Amir a waya yazo, ita da Yami suka bincike ɗaki tsab suka kwaso takardun filayen Fillo da Abdulhamid, filaye guda huɗu da kuma takardar wata gona, ta bawa Amor tace dan girman Allah yay shiru aje a siyar duka ayau azo aje akai kuɗin nan. cikin sa'a kuwa Amir na zuwa gaba ɗaya abinda aka saya filayen da gonar miliyan ɗari huɗu da hamsin. dan haka ko da ya kawowa Kaka kuɗin sai aka ƙara ɗauka shanu guda uku akaje aka siyar har kuɗin yayi making yanda aka nema. kuma Amir shi ya ɗau kuɗin yaje ya kai inda Kidnappers ɗin suka buƙata, bai dawo gida ba sai wajen biyu na dare cike da tsoron dajin da yaje ya ajiye kuɗin, har ya kasa bacci saboda firgici. su Kaka kuwa ana can anata zabga adu'a, Kidnappers ɗin sunce da an kai kuɗin zasu saketa ta dawo gida a lokacin, amma har sallar asuba har wayewar gari babu ko da inuwar Fillo. hakan ya ƙara ɗaga hankalin su Kaka, suka kasa tsaye suka zaune ita da Yami, sai zagayen ɗaki suke yi, ana hakan wayar Yami dake ƙugu a soke tayi ƙara, da sauri jiki na rawa ta ɗauko ta kara a kunne, abinda ya doki kunnenta a lokacin shine Kukan Fillo. tace,"Fillo kina ina?". tace,"Yami sunce ba zasu sake ni ba, wai kuɗin yayi musu kaɗan sai an ƙaro. Yami karku ƙara musu ko biyar, ni na saddaƙar mutuwa zanyi, ki faɗawa Amir kar ya ƙara zuwa dan sun ce zasu karɓi kuɗin kuma su kashe shi, He has done so much for me that I can not repay him, bana son rasa shi Yami, kar ya ƙara zuwa dan Allah, gwara ya rayu ni na mutu, Yami ki kula min da Kaka bata da kowa sai ni sai Allah". ta faɗa tana kuka sosai, kuma me taɓa zuciya. ƙit kamin Yami tace wani abu an kashe wayar. Amir yazo gidan jikinsa duk a sanyaye don tuni Kaka ta kira ta shaida masa, ko da ya shigo ɗakin zubewa yayi daga bakin ƙofa, har tsawon minti biyar ya kasa cewa komai, sai da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yace,"Kaka ko dai mu sanarwa da su Hajiya?, tunda sunce a a shirye suke suyi duk abinda ya kamata". Kaka tai saurin girgiza kanta tace,"a'a Amir, ana faɗa musu zasu kai lamarin ga hukuma, su kuma mutane nan kaji abinda suka ce muddin hukuma ta sani sai sun kasheta". Amir ya haɗiye wani abu a maƙogoronsa da ƙyar sannan yace,"shikenan Kaka, zanje yanzu akwai wani filina acan ƙauyenmu zan siyar da shi, shima kuma gidan da zamu zauna zan siyar da shi. gaba ɗaya in Allah ya yarda za'a iya samun ko miliyan biyu ce, sai a haɗa a ƙara basu". daga yanayin yanda yake maganar in ka kalle shi sai kayi masa kuka, bakinsa duk ya bushe, gaba ɗayansa ya wani firgice ya zaftare saboda rama. Yami da Kaka suka haɗa baki wajen ce masa,"a'a karka sayar da komai Amir". ya miƙe kamar zai faɗi yace,"Kaka bamu da wata mafita da ta wuce wannan. gobe zan dawo in Allah ya yarda, kuma a gobe zasu saki Fillo da izinin Allah, fatana ku kwantar da hankalinku kuyi ta adua". Kaka tace,"to Amir a haɗa da sauran shanun can guda 5 da suka yi saura, akwai awaki ma guda 10 duk ka siyar sai a haɗa". da kansa kawai ya iya amsa mata sannan ya fice jiki duk a saɓule, yana tafe yana layi kamar wanda yasha ƙwaya, bacci ne fal a idonsa da wata azababbiyar yunwa da yake ji, amma baya jin cikin biyun ɗa zai iya samuwa, shi da cin abinci da bacci kuma sai Fillo ta dawo. kuma a safiyar ranar ne Turaki ya kira Khalil yake tambayarsa ga me da jikin Maama. dan shi har yanzu bai yarda da lafiyar da take ta faɗa dan bai ji a voice ɗinta ba, kuma taƙi yarda suyi vedio call. Khalil mutum ne shi da baida wani ɓoye-ɓoye, ko saƙon mutuwa ne kai tsaye yake sanar da shi, dan haka kai tsaye Khalil yace masa,"Hammah ai yau kusan 3weeks kenan ana cikin tashin hankali, zancen da nake maka yanzu haka Maama bata cikin hayyacinta, ta fita ita da ƴar aikin nan Fillo an sace ƴar, har yanzu shiru babu labarin yarinyar, shisa ka kasa jin Maama a yanda kake so". Turaki ya ɗauke wuta, ya daskare daga zaunen da yake, wayar ta silale daga hannunsa ta faɗo ƙasa, maganar Khalil ta shiga tariya acikin kansa. yarinyar ta ɓata, an saceta, 3weeks ba'a ganta ba, babu labarinta, ba'a san ina take ba. hannunsa ya dunƙule ya naushi kujerar da yake zaune, ya dinƙa karanto innalillahi wa'inna ilaihi raji'un har Bello yazo ya sa me shi a sanda idanuwansa suka kaɗa suka yi jawurr. *Vote, Comment & Share.* [8/30, 20:26] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* ```DAGA MARUBUCIYAR``` 1-Sirrin Ɓoye 2-Al'amari 3-Hidaya Noor 4-Alhussain 5-Sanadin Talauci 6-Ƙaddarar So 7-Prince Khaleed Da sauran su..... *33* *Switzerland* sanya take cikin rigar sanyi mai kauri sosai, dogon wando ne fari a jikinta sai p-cap red colour da ta saka, wanda shigar ya amsa farar fatar jikinta sosai. yanayin fuskarta kaɗai zai shaida maka cewar bata cikin walwala da annuri, haka kuma ƙwayar idonta na shaida rashin nutsuwar da take da ita a zuciyarta a kullum a ko da yaushe. a tsaye take daga jikin window tana leƙan waje, tana kallon yacca ruwan sama ke sauka, sanyin garin na ratsowa har cikin ɗakin yana shiga jikinta. ta sauke dogon numfashi tare da ɗaga gorar hollandia ɗin dake hannunta ta ƙara kurɓa, ta buɗe lumsassun idanuwanta a sanda take juyowa ta fuskanci kyakykyawan farin bafulatanin dake zaune kan kujera yana danna wayarsa, shima fuskarsa kaɗai ta isa ta shaida maka cewar zuciyarsa a ƙunci take. Samha ta ɗauki tsawon daƙiƙu biyar tana kallon Sameer kafin ta buɗe baki tayi magana, muryarta ta fito acikin rauni da kuma damuwa. "tsawon shekaru masu yawa, har kullum, har yanzu na kasa haƙuri da juriya akan yacca nake ganin mahaifiyata ta fifita wani daban akan ni da ta haifa, tafi son sa fiye da ni da ta haifa, tafi basa kulawa fiye da ni da ta haifa, tafi kyautata masa fiye da ni da ta haifa, tafi damuwa da damuwarsa fiye da ni da ta haifa, hankalinta yafi karkata 100% akan ƴaƴan da bana cikinta fiye da wanda ta haifa acikinta. ka faɗa min ta yanda za'ai nayi farin ciki duk da cewar ban taso a tagayyare ba, ban taso a cikin talauci ba, ban taso da rashin gata ba, ban taso na nemi abinda nake so na rasa ba, ban taso na rasa soyayyar mahaifi da ta mahaifiya ba, sai dai wannan soyayyar tasu ce tayi min kaɗan, ba kalar wannan soyayyar nake so daga wurin mahaifiyata ba, kalar waccan soyayyar da take nunawa Turaki da Zaytuna ita nake so, ita nake da buri ita nake da muradi, amma tsawon shekaru masu yawa na rasata, na kasa samunta duk ta yanda na so...shi yasa ya zama dole na kawo ƙarshen wannan bambanci da iyayenmu ke nunawa ko ta halin ƙaƙa, ko da ace asanadin hakan zan rasa raina". ta ƙarashe maganar muryarta na bayyana wani irin baƙin ɗaci dake tasowa daga ƙasan zuciyarta. shirun da tayi yasa Sameer ya ɗago da kai yana kallonta, tana tsaye hawaye na bin fuskarta, ba ta da alamar zata hana su zuba balle tasa hannu ta goge su. ya rufe idonsa for few seconds ya buɗe yana sauke numfashi tare da ajiye wayarsa a gefensa. "ke kaɗai ce dama kika rasa dukkan abinda kika lissafa?, ko kuma ke ɗaya ke cikin irin wannan ƙuncin?". kanta na ƙasa tana kallon ƙafarta dake cikin black socks tace,"bani ɗaya bace, ko Hammah Khalil da Nihal na san basa jin daɗin haka, deep down there heart na san suna jin zafi, domin babu ɗan da zai so yaga iyayensa na nuna banbanci tsakaninsa da ƴan'uwansa...so amma abinda nake so ka fahimta Sameer inda ace hankalin mahaifiyamu na kan mutum guda acikinmu da ta haifa, to da atleast zamu sami sassaucin raɗaɗin zuci, ba wai take nunawa kamar ba ita tayi naƙudarmu ba". cikin zafin nama tai wurgi da hollandia ɗin dake hannunta tasa ƙafa ta murje, tana huci take cewa,"wani sa'in zuciyata na faɗa min Turaki da Zaytuna asiri suka yiwa Maama, ba haka suka barta ba, don babu uwar dake cikin hayyacinta zata ke nuna irin son kai tsakanin ƴaƴanta da na kishiyarta, but what ever lokaci yayi, wallahi a wannan karan babu fashi da tsiya tsiya sai na aika da su lahira, zanbi ta irin waccan hanyar da suka bi, ko duk bokayen duniya zan bi saina sa an kawo min ƙarshen su Turaki". Sameer ya hura iska a bakinsa sannan yace,"bin boka is not the best solution dear tunda aikin asiri na karyewa, and ba zan bari ma mu aikata shirka ba. abu ɗaya kawai da yake nan waɗan nan mutanen su zamu ƙara bawa kwangilar...". ai tun bai ƙarasa ba ta duki table ta katse shi da cewar,"kuɗina ba zai ƙara zuwa hannun gantalallun can ba". sai kuma ta nemi kujera ta zauna ta dafe kai,"Sameer ni abinda ma yake ban mamaki, me yasa duk sanda mukai wani shiri sai kaga Turaki ya kuɓuta daga wannan shirin namu?, ka duba fa kaga last da muka sa aka datse burkin motarsa, tsakiyar dare fa muka bi, wa ya ganmu?, wa yaji plan ɗin mu?, amma sai ga shi da safe yana batun bai key na motarsa ba, kuma tun daga ranar har yau bai ƙara hawa wannan motar ba, anya Sameer?, ga shi ba wani muka sa akan aikin ba balle muce ya munafurce mu, da kanmu muka yi aikinmu, kai na kasa ganewa gaba ɗaya". Sameer shima ya kwantar da kansa kan kujera yace,"ni kaina nayi mamaki sosai a wannan time ɗin, musamman da naga up to now baya hawan motar. amma mutumin da yake kwana yana sallah har sai gari ya waye sannan ya rumtsa, mutumin da yake driving yana sauraron karatun alƙur'ani yana bi, mutumin da baya rabo da ambaton Allah a bakinsa, mutumin da common magana ɗaya yayi sai ya ambaci Allah, to ki faɗa min ta ya ba zai kuɓuta daga haɗarinmu ba?, taya ba zai kuɓuta daga sharrinmu ba?, ai muma wasa muke, iyakar kuɗin da muka ɓarnatar ya kamata zuwa yanzu ace mun haƙura kawai, mu fahimci cewar Turaki yafi ƙarfinmu dan yana tare da kulawar ubangijinsa". Samha tace,"idan kai ka haƙura ni dai ba zan haƙura ba, dole ne ma sai na ƙwaci soyayyar mahaifiyata, dole ne ma sai na ƙwatarma kaina hakki. ka duba kaga banda mota guda ɗaya da kuma fili guda ɗaya me Baffa ya taɓa mallaka mana?. amma Zaytuna motarta biyu, bayan fili har gida tana da shi, Turaki kuwa an handame duk wata kadara an basa, komai Baffa yay yunƙurin yi mana sai Maama tace shi ya kamata a bawa saboda shine Babba, ko kuma tace ai su basu da uwa sai kace mune muka sa uwar tasu ta gudu". Shiru ya ratsa kafin Sameer yace,"to yanzu what next kike ganin zamu yi?". tace,"akwai wani dodo anan ƙasar, na faɗa masa zan basa kwangilar kisan mutum biyu, yace min zan ba shi 20ML, nace masa 10ML zan ba shi, da ƙyar dai muka ƙarƙare a 15ML, dan haka zan sayar da motata ɗaya da kuma sabon filin da Maama ta bani, sai muga abin yi". Sameer yace,"hakan yayi". daga haka ta wuce ciki ta barshi anan parlo. *Gombe.* a cikin parlon na Kaka, tana zaune ta zabga tagumi tana jan carbi, sai Yami ma a gefe ta zabga nata uban tagumin, sai Maijidda dake kwance akan ledar ɗakin, ba bacci take yi ba idonta ne kawai a rufe. dukkansu kallo ɗaya zaka yiwa fuskokinsu ka shaida bala'in tashin hankalin da suke ciki, duk sun rame sosai. tun a daren jiya Amir ya ƙara kai kuɗin da kidnappers suka nema amma shiru har safiyar yau babu wani labari na dawowar Fillo, tun kiran da suka yi na cewar sun ɗauki kuɗin zasu yi abinda ya dace to basu ƙara kira ba, haka su Kaka suka yi kwanan zaune kamar yanda Amir yay daga can gidansu, amma shiru-shiru babu wani bayani. to haka yau ɗinma tun 11 na rana Hajiya Madina tayo musu aiken abinci amma sun kasa ci. dan a inda Ɗausiyya ta ajiye flask ɗin tun ɗazu yana nan a inda yake babu wanda ya taɓa shi. Yami ce tace,"Ƙawata ki ɗanci abincin nan ko loma biyu ce dan Allah". Kaka ma tace,"ke ya kamata kici tunda kina da matsalar ulcer". Kaka ta dubi Maijidda tace,"tashi ki zuba abincin nan kici". bata buɗe idonta ba hawayen daya taru aciki ya sauko tace,"ba zan iya ci ba Kaka". dai-dai nan suka ga an ɗaga laben ɗakin, da sauri suka waiga kusan a tare suna kallon ƙofar, da fatansu ace Fillo zasu gani, but sai saɓanin hakan, sai suka tsaya suna kallonsa sun kasa ɗauke idonsu akansa. kamar yadda shima ɗin bin su yake da kallo ɗaya bayan ɗaya. kallon su yake yana so ya hango maganar da Khalil ya faɗa masa a fuskokinsu, babu wanda yasan da dawowarsa hatta kuwa Maama, dan ko driver bai kira yaje ɗaukansa ba, daga airpot napep kawai ya nema ya hau ya taho. ta gate ɗin ma'aikatan gidan aka sauke shi, kuma yana shigowa straight ɗakin Kaka yayo bai ko bi ta kan ma'aikatan dake gaishe shi ba, dan wata magana ma da yaji suna yi ta Allah ya sanya alkhairi duk bai fahimta ba. Kaka ta ɗauke idonta akansa tana cewa,"bismillah me Babban suna". baya jin zai iya ɗaga ƙafafunsa daga wurin da yake ya shigar da ita cikin ɗakin, dan ya riga ya gama samun amsar tambayarsa a fuskarsu, ta tabbata matarsa ta ɓata, har tsayin lokaci ba'a ganta ba. kuma sai ka lura sosai zaka hango uban hakin da yake yi tamkar wanda ya taho a guje tun daga El-Salvador. Yami ta yunƙura ta miƙe ta ɗauko darduman sallah ta shimfiɗa tana cewa,"bismillah ga wuri". Turaki ya ziro daguwar ƙafarsa ciki yana takawa tamkar wanda bai da jini a jikinsa. ya zauna hoton Fillo na haska masa acikin idonsa, tunaninsa ya katse sanda Kaka tace,"ina yini, an sauka lafiya?". Yami ma ta gaishe shi sannan ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya maganar ba yace,"lafiya lau". sai kuma duk sauran maganar tasa ta katse ya kasa faɗin komai. sai da Yami tace,"muna godiya da kulawarku, Allah ya bada lada". shirunta ya haɗe da fashewar kukan Kaka. Turaki ya juyar da idonsa kanta yana ta kallonta kamar yaune ya fara ganinta. kuka sosai Kaka take kamin tace,"ni da gawarta ne ma na gani hankalina zai fi kwanciya, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". furucin nata na ƙarshe ya haɗe da rufewar idanun Turaki yana dukan ƙirjinsa, for few seconds yana jin kukan Kaka acikin kansa da kuma hasashen halin da take ciki. ya buɗe idon ya sauke a ƙasa murya a sarƙe yace,"ki daina faɗar gawa Kaka, ganin gawarta ba yanzu ba insha'Allah, za'a ganta very soon aci gaba da adu'a Allah ya bayyanata". yanda yake yin maganar sai yaji kamar me koyon magana dan bai ma san ta yanda ya haɗa kalmomin ba ya faɗa. Yami tace,"Allah ya amince". Turaki yasa hannu ya shafa fuskarsa tukunna ya yunƙura zai miƙe sai yaji Yami da Kaka na maimaita kusan magana mai shigen wacca yaji ɗazu da yana shigowa. "ashe kuma lokaci yazo to ubangiji Allah ya sanya alkhairi". ana cikin wannan halin suke faɗar kalmar Allah ya sanya alkhairi!, to ko dai duk tsananin tashin hankali ne yasa kowa ya fita a hayyacinsa har yake faɗar abinda bai kamata ba. sai da ya isa bakin ƙofa sannan ya juyo yana kallon Kaka yace,"kuma babu gidan wasu ƴan'uwa da zata iya zuwa can?". Kaka tace,"babu, duk inda ya kamaci ace an bincika duk an duba. dan shi wanda ma zai aureta da kansa yaje can dangin mahaifinta ya duba, kwanansa ma biyu acan ɗin, amma ko da ya dawo yace wallahi bata can". Kaka ta faɗa tana sake fashewa da kuka. Turaki ya dinga kallonta kafin ya fice daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba. ya wuce yana maimaiata kalmar wanda zata aura cikin ransa. daga nan kai tsaye ɗakin Maama ya wuce, lokacin da ya shiga zaune ya sameta a gefen gado ta zuba uban tagumi. har ya cire takalmansa ya shigo ya zauna kusa da ita bata sani ba, sai da ya janye hannun da tayi tagumi tukunna tai firgigit ta ɗago tana kallonsa. tana ɗago ido ta gansa sai ta fashe da kuka tare da kifa kanta a kafaɗarsa. ya rumtse idonsa sosai yana jin kukan nata na taɓa zuciyarsa tana ƙara matsewa da damuwar da take ciki, yasa hannu a kanta yana cewa,"innalillahi wa'inna ialihi raji'un, Maama whats wrong?, kukan me kike Maama?". ya faɗa dan yana so ya ƙara tabbatar da komai daga bakinta, amma da mamakinsa sai gani yay ta ɗago tana yi masa zancen da ya ɗaure masa kai matuƙa ya kuma rasa ina ta nufa. "Me Babban suna ka taɓa ce musu kana sonta ne?, ko kuma ita tace maka tana sonka ne da har ka amince musu?, yanzu shikenan ni ban isa ba, ban isa ai magana da ni akan abinda ya shafi rayuwar ɗana ba?, kuma a rasa a lokacin da zaa shirya bikinka sai lokacin da akaga ina cikin tashin hankali, me Fulani Azima ta shirya?". sai kukanta ya ƙaru sosai hakan yasa tayi shiru tana ƙara kwantar da kanta a kafaɗarsa. "Maama ban fahimci abinda kike son cewa ba, me ya faru?". sai ta ɗago da kanta ta kalle shi sosai, a ƙwayar idonsa ta gasgata cewa bai san duk abinda ke faruwa ba. saboda haka sai ta miƙe tsaye ta kamo hannunsa tace,"ka muje ka faɗawa Baffa da gatanka, kai ba maraya ba ne, dan haka ba irin wannan shirin kayi ba, ba irin wannan tanadin ka yiwa aurenka ba". bai iya cewa komai ba har suka fita daga ɗakinta suka bar part dinta suka nufa na Baffa still tana riƙe da hannunsa. suna shiga suka tarar da Baffa zaune a parlo yana kallon news ya ɗora hannunsa akan tumtum ɗin dake kusa da shi. Hajiya Madina ta nemi kujera ta zauna tana rufe fuskarta da duka hannunta biyu, Allah ɗaya yasan abinda take ji a zuciyarta, kuma ta lura in bata yi da gaske ba zuciyartata na gab da bugawa. Turaki ya kalleta ya kalli Baffa wanda ko juyowa bai yi ba ya kalli inda Maama take, dan haka abin sai ya ɗaure masa kai ya dinƙa kallon su 1 by 1, abinda zai iya rantsewa bai taɓa gani ba a tsakaninsu ba kenan tsawon rayuwarsa, fushi da junansu dai, shi ko irin wannan saɓanin da ake cewa ana samu tsakanin Mata da Miji ma bai taɓa gani ba ko da a fuskokinsu. to me yake faruwa ayau ɗin?, duk akan ɓatan yarinyar ne ko ya?, me Maama take son faɗa masa ne ɗazu da bai fahimta ba?. sai ya sauke ƙafafunsa ƙasa ya zauna daga gefen kujerar da Maama take, ya kai hannunsa ya ɗora akan yatsun ƙafarta yana jin wani abu na tsarga masa. tunaninsa ɗaya ne me ya saka masa Maama zubar da hawaye irin haka?. bai san lokacin da ya haɗe yatsunsa ba ya dunƙule, banda akan ƙafar Maama yake babu abinda zai hana shi nausar koma menene. sai da ya rufe idonsa ya buɗe tukunna ya buɗe baki yace,"Barka da Rana Baffa". a sannan ne Baffa ya gyara zamansa yana kallonsa yace,"yaushe ka sauka?". yana kallon mahaifin nasa da son gano abinda ke faruwa yace,"ban jima ba. na baro Bellon acan zai ƙarasa projects na jiya da kayi magana". tun ajiya da suka yi waya da Khalil yaso ya taho amma sai Baffa ya kirasa yace zai yi representing nasa a wani program da yake da shi da safe, dalilin da yasa ya zauna ɗin kenan, kuma ayau ɗin ko Bello bai san ya taho ba saboda daga can airpot yayi. Baffa yace,"an dawo lafiya?". yace,"lafiya lau". shi dai jikinsa duk a sanyaye yake, musamman da har yanzu yaji Maama na kuka kuma Baffa ko kallon inda take zaunen bai yi ba. baya so yayi saurin interfering shi yasa yay shiru, amma sai yaji ba zai iya jurar jin kukan Maama ba, hakan yasa idonsa a ƙasa yace. "Baffa da akwai wata matsala ne?". Baffan yace,"ita Babar taka bata faɗa maka ba ne?". Turaki ya ɗago ido ya kalli Hajiya Madina sannan ya kwantar da kansa gefen gwiwarta yace,"a'a, bamu zauna da ita ba tukunna". Baffa yace,"to gobe bayan an idar da sallar juma'a insha'Allahu za'a ɗaura maka aure, kai da ƴar uwarka Ilham, dan haka sai ka zama alert". da wani bala'in shock Turaki ke kallon Baffa, maganar na maimaituwa acikin kansa. bai san sanda ya furta,"aure kuma Baffa?, dama ana irin wannan auren?, Baffa aure ban shirya ba kuma bada yarinyar da nake so ba?". kamin Baffa yay magana Maama ta buɗe fuskarta da tayi shaɓe-shaɓe da hawaye tace,"kaji ai zancen da nake maka ba. yanzu tsakani da Allah idan har aka yi masa hakan an masa adalci kenan?, ina aka taɓa yiwa mutum aure ma bai san da zancen ba sai kace wani gantalalle, and beside ita kanta matar da aka lalaƙa masa bai ce yana sonta ba, haba Baffa ka dawo cikin hayyacinka mana, ɗanmu fa da gatansa taya za'a ce za'a masa irin wannan auren da ko mara gatan ma ba'a yiwa irinsa, abar ta batun ma ni a sanar da ni tunda dama ni ba kowa bace, amma dai at first ai ya kamata shi a sanar da shi in ya amince sannan, idan ma kuma dolen ake so ayi masa sai a sanar da shi tunda wuri ba wai sai a ƙurewar lokaci irin haka ba, kawai tsakani da Allah dan anga yaro yana da biyayya sai ake zaluntarsa duk ta inda aka so, wannan ba daidai bane wallahi, kuma Allah ko kotu muka je sai an ƙwatarwa ɗana hakkinsa". Baffa ya ɗago ido ya kalleta da kyau yace,"you are free to go there Madina, ki shigar da ƙara gaba da kotu kinji. abu ɗaya kawai nake so in sanar miki shine babu mahaluƙin da ya isa ya hana wannan auren. duk fitinar da zaki tayar wallahi sai dai ta ƙare miki ke ɗaya, wannan batu na aure magana ce ta mahaifiyata, saboda haka babu uban da ya isa ya hana, ɗa nawa ne ba na wani ba, kuma tun a jiya na faɗa miki muddin kika nemi ki ɗaga min hankalin ki tada fitina akan wannan batun, to tabbas zai yanke tsatstsauran hukunci akanki". Hajiya Madina ta ƙara fashewa da kuka sosai. Turaki dai na zaune kamar gunki sai kallon Baffa yake kamar yana kallon sabon mutum. sai da Hajiya Madina taci kukanta sosai tukunna ta ɗago tace,"muddin ina raye, muddin da lafiyata babu wanda ya isa yaywa ɗana auren dole, sai kace wata mace. abunda ko ada can ba'a yi ba, idan ma auren dolen ake so ayi masa a fara faɗa masa mana, ba wai aje a ɗauko ɗiyar matar da ba ƙaunarsa ta ke ba a haɗasa da ita". sai tai ta ɗauke idonta daga kan Baffa ta maida kan Turaki, tasa hannu ta ɗago fuskarsa daga saman cinyarta da ya kwantar, ta kalla cikin idonsa tana ganin yacca ƙwayar ta sauya kamar bata shi ba, taji wani bala'in tausayinsa ya kama shi, yana da mugun haƙuri kuma yana da tsananin biyayya ga iyaye ko da ace zai cutu, tana kallonsa tace,"kana da ni Hammah, ni mahaifiyarka ce da ba zan iya zuba ido naga ana cutarka ba, saboda haka ka faɗa min zaka iya auren Ilham ko ba zaka iya ba?, ka shiryawa wannan auren ko baka shirya masa ba?". Turaki ya haɗe murfin idonsa ya rufe yana jin wani abu na taso masa daga ƙasan zuciyarsa, dama har yanzu shi under 20years ne shi bai sani ba?, dan a ganinsa yaron ma da yake 20years ba za'ace zaa masa irin wannan auren ba, me yasa Baffa?, me yasa zai biyewa rikicin tsufan Boɗejo?, ofcourse baya san wannan auren, kuma ko da ace zai iya so ɗin kukan Maama kaɗai na iya sa shi ya ƙetare umarnin Baffa da bai taɓa ƙetarewa ba tunda aka haife shi, to amma sai dai Baffan ya karya shi da furucisa guda ɗaya, ya sagar da shi daga duk abinda yay niyyar yi. dan shi tanadin da yake Baffa na gama zancensa daga nan sai ya miƙe yaje ya sami Ilham ɗin yay mata cin zarafin da ko da gawarsa ba zata yarda a ɗaura mata aure ba, to sai dai a yanzu Baffa ya gama da shi tunda har yake batun zai ɗauki tsatstsauran mataki kan Maama, bijirewar tasa ba zata haifar da komai ba sai ɗa mara ido. dan haka zai amince ya auri yarinyar, amma ya tabbata da kanta zata bar gidan, dan ba zata taɓa samun fuskar zama da shi ba, ya sa ni ita ta amince tana sonsa tunda har aka yarda da auren, but she will regret. yanzu baida lokacin yi mata komai saboda ba abinda ke gabansa ba kenan, neman Fillo ne a gabansa yanzu. yasa hannu ya dafe kansa yana jin zafin dake kansa na ratsawa a jikinsa. ya buɗe ido ya kalli Hajiya Madina da har yanzu hannunta ke kan goshinsa tana kallonsa kamar ba zata ƙifta ba. ta ƙara ce masa,"karka cuci kanka, sai in har ka yarda za'ai auren nan, idan baka yarda ba yanzu ka miƙe in kai ƙara gaban Babban Alƙali, dan yau daga uban har ƴaƴan sai na maka su a kotu dan ba zan ci gaba da zuba ido ina kallo ana zaluntar min kai ba wallahi, ko zaka yi aure ba'a cikin shiri ba na yarda amma sai in wadda kake so". bata ma san sanda tai furucin daga uban har ƴaƴan ba. Turaki ya kalla mahaifinsa yace,"Baffa ni fa ba yaro ba ne". Baffa yay saurin ɗaga masa hannu yace,"sanin hakan yasa muka haɗa aurenka da ƴar'uwarka, ka shirya gobe after salatul juma'a za'a ɗaura aurenka. haka muka zauna muka yanke ni da mahaifiyata da ƴan'uwana, and that is our final decision, idan har kuma ka bijire min to tabbas zan sallamaka a cikin ƴaƴana sannan in sallami itama Babar taka dake ɗaure maka gindi". Hajiya Madina tayi hanzarin miƙewa daga kan kujera tace,"in har zan cika alƙawarin dana ɗauka na riƙe yaron nan bisa amana, to Alƙali Dikko dan ka sakeni ba zanji wani ɗar acikin raina ba. so barazanar sakinka ba ita zata sa in sauka akan bakana ba, aure in kaga anyi tabbas to da amincewar yarona". tana gama faɗar haka tace da Turaki,"Hammah ta shi muje, inga wanda ya isa yayi maka auren dole, ko da kai yaro ne ba'a isa ba balle kuma da hankalinka". cikin ɗaga murya Baffa yace,"Madina wai me yasa baki da mutumci ne, auren nan na faɗa miki mahaifiyata ce ta shirya shi, shine har kike so in ta ke umarninta?". Maama ta taɓe baki tace,"cikin ku huɗu da Allah ya bata kaf ɗinku wa aka yiwa auren dole?, kuma jikoki nawa gareta?, sauran ƴaƴan nata rasa ƴaƴa suka yi da ba zata yiwa ƴaƴansu ba sai nawa ɗan da aka sawa ido dan an gansa yafi kowa haƙuri, yafi kowa biyayya. to daɗin abinda ƙasa bata cika bakina ba balle a cuce shi...Me Babban suna ta shi ka ji, aure sai in bana numfashi, kaf ƴaƴana ba wanda aka isa aiwa auren dole". Turaki ya riƙe kansa da ke neman barazanar fashewa ya riƙo hannun Maama yace,"zan aureta Maama, zanyi auren na amince. adu'a kawai zaki yi min". ƙyam idonta ya tsaya akansa tana hango tsananin ƙarfin halin dake tare da shi wajen ganin ya furta hakan. ta maida kallonta kan Baffa tana kallonsa, ko a jikinsa, bai damu da halin da ɗansa zai shiga ba ma?. ta ɗauke kanta tace,"babu komai akwai Allah, idan ma saboda wata manufa aka haɗa auren nan Allah ya saka maka ya kareka daga sharrin mugun mutum...and ko banza ƴarsu ce zata wahala wallahi tunda babu sonta a zuciyar mijinta. kuma sai in dai bai ga wadda yake so ba, abu da Allah ya halasta masa auren mace huɗu, yana ganin wadda yake so zan ɗaura masa aure da ita wallahi kuma banga wanda ya isa ya hana faruwar hakan ba, in masa auren gatan da ko ƴaƴan masu mulkin ma ba'a yi musu". taja hannunsa,"tashi muje Allah yayi maka albarka ya baka ladan biyayya, idan ba me tarbiya ba waye ma zai yarda da wannan kalar cutarwar". ta mayar da kallonta kan Baffa tana cewa,"Allah ya bawa mutum ƴaƴa amma baida burin da ya wuci ya ƙuntata musu, duk wai ace mutum shi yana bin maganar manyansa, Allah na tuba yayye ba iyaye ba har sunsa na baƙantawa ɗan cikina, ita kanta yarinyar nasan ba kai tsaye akai komai ba sai da ubanta yaji ta bakinta, amma kai wai me biyayyar yayye ka yanke hukunci kanka tsaye, sai anyi magana ka dafe ƙirji kana nishi hawan jininka zai tashi, inga me zaman jinyarka yau". tana gama faɗar hakan ta kama hannun Turaki, kamar wani ƙaramin yaro haka ta ja shi suka fita daga parlon Baffa na bin bayanta da kallo, ko kaɗan bai mamakinta ba dan dama yasan za'a rina, in ace dai Turakin yana son yarinyar yasan babu abinda zata ce balle har ta tada jijiyar wuya haka, amma akan hakan yau ɗaya har tana faɗar wai yana ƙuntatawa ƴaƴansa, when akai haka?. acan parlonta ta tarar da duka yaranta zaune sunyi jungum-jungum, Khalil da Nihal da Zaytuna, Samha da Sameer basa nan dan basu dawo daga ƙasar da suka tafi ƙulla mugun nufinsu ba. ta shigo tana ta masifa, Khalil ma yay tsaki yace,"gaskiya, gaskiya abinda Boɗejo tayi bata kyautaba sam. wannan wane irin aure ne tsakani da Allah?". Nihal ma na turo baki tace,"yanzu dan Allah duk burin da muka ci akan auren Hammah sai azo mana da shi a irin haka?, shirin me muka yi tsakani da Allah, ni wallahi wannan tsohuwar dama ta mutu". Zaytuna dai ba tace komai ba illa kallon Turaki da take tayi ƙwayar idonsa kamar ba nasa ba. Nihal ta miƙe ta isa kusa da shi tana ɗora hannunta akan nasa tace,"Hammah kai kace kana son auren da har tai mana wannan shirmen?". bai ce komai ba, lokacin Hajiya Madina ta ƙaraso wajen riƙe da cup a hannunta da ruwan sanyi aciki, ta zauna tana tallafo kan Turaki ta bashi ruwan ya sha. bayan ya sha ta ajiye cup ɗin tana faɗin,"suje can suyi bikinsu su kaɗai, ni da ƴaƴana dai babu mai zuwa,  wanda ya fasa cewa ina baƙinciki ba ɗan halak ba ne. kuma kaima ana ɗaura auren kayo kwana ka dawo gida". Nihal na matsar ƙwalla tace,"yanzu Maama sai kace bamu da gata sai ayi bikin Hamman'mu a haka babu shagalin komai?, duk fa ina ta cewa friends ina idan Hammanmu zai yi aure kowa zan gayyace shi. shi Baffan dan tana babarsa kawai kuma sai ya wani kama biyewa rikicin tsufanta, ni taja ma wallahi har Ilham ɗin na tsaneta, ƙilan ma harda wannan munafukar Babar tata aka haɗa baki". Hajiya Madina tace,"kwantar da hankalinki Nihal, shi da yake da ikon auran mata har huɗu, Allah ya kaimu nan da ranar da zai hango zaɓin ransa. anan za'aga inda ake aure, lokacin zamu yi namu shagalin bikin akan matar so, kuma ko a yanzu ina da arziƙin da zan iya yin bikin da zaici uwar nasu acikin kwana biyu cal, sai dai ba zan ɓarnatar da dukiyata ba akan auren matar shige". ta kalli Khalil tace,"kaima uban ƴan ladabi da biyayya, ka sake nai kiciɓis da kai zaka je wurin ɗaurin aure gobe babu abinda zai hanani sa maka kafa na fyaɗeka a ƙasa, in taka ƙafar in karya banza". Nihal tace,"dama ni wallahi babu inda zanje dan ɓuya ma zanyi ko Baffa ya kira wayata Allah ba zan ɗaga ba. dan dana hau whatsapp naga Marfu'a(Yayar Ilham wadda itace ta farko a ƴaƴansa mata), ta ɗora invitation card na dinner da cocktail ranar saturday da sunday". Hajiya Madina da har yanzu ta ke a fusace tace,"sa ji uwar kunya kuwa, dan gobe ma zamu bar ƙasar ni da shi, sai su nemi uban da zai yi replacing angon, ai insha'Allahu duniya sai ta gane auren cusa kaine, ango ba so yake ba". tana kallon Zaytuna tace,"kema uwar rawar ladabi da biyayya, Allah sa inga kin shiga lamarin bikinsu kiga asalin ɓacin raina". ta faɗa tana maida hannunta kan goshin Turaki da take jin zafin kan na ratsa fatar hannunta, a lokacin Turaki ya buɗe idonsa yana kallonta muryarsa a raunane yace,"Maama da gaske ne kun fito da yarinyar nan ta ɓata?". ta ke Hajiya Madina ta fashe da kuka tace,"ko dan wannnan dalilin tashin hankalin da nake ji ai yaci ace a tsayar da maganar auren ɗana?. banda ma dai Baffan Baffa ne ai sai ya miƙe tsaye yace ko za'ai a bari aga yarinyar mutane dana fita ta ɓatar tukunna, amma har shine yana min tsawa yana cewa babu ruwan auren ɗansa da ɓatan yarinya. yanzu fisabillah me Kakar yarinyar nan zata ɗauke ni?, ba sai su koma min kallon matar banza ba azzaluma na ɓatar musu da ƴarsu nazo ina shagalin bikin ɗa, wallahi ni dai sanyin Baffanku ba komai bane fa ce cutarwa". ya rumtse idonsa ya buɗe tukunna ya ƙara cewa,"garin ya akayi ta ɓata?". nan ta kwashe labarin komai ta ba shi. "to su police ɗin suna cewa wai sun fi tunanin kidnappers, ka faɗa min Hammah idan kidnappers ne tuni basu kira waya ba, amma fa shiru shiru har zuwa yau babu wanda ya kira waya, ko'ina an duba babu ita kamar ɓacewar aljani, har yanzu dana sanin fita nake da yarinyar nan, dan Kakarta da wanda zata aura zasu ga kamar da gangan hakan ya faru, kasan zuciya bata da ƙashi". ta faɗa tana kuka sosai. Idonsa a lumshe yace,"ki daina kuka Maama, insha'Allah an kusa a ganta". dukansu suka amsa da amin. sannan ya miƙe yace,"zanje in kwanta, kaina yana ciwo sosai". tace,"tafi ɗakina, kuma ka cire damuwar komai a ranka. yanda kake da gatanka zakai auren gata nan da wani lokaci insha'Allah. Dikko ne yay sirika ba Madina ba". Turaki ya wuce ya hau upstairs yana jinsa kamar ba shi ba, yana jin komai kamar a mafarki. kuma kafin ya kwanta sai da ya kira Bello ya sanar masa, tsaban shock Bello ashar ya ɗura a lokacin, har bai san sanda yay formating document da yake haɗawa ba. kuma Turaki bai jira cewarsa ba ya kashe wayarsa. *Washe gari, Juma'a, Masarautar Kaltungo, Ƙarfe Ɗaya da rabi na rana.* ana idar da sallar juma'a a masallacin aka ɗaura auren Muhammad Habib Lateef da Rumana Hashim Lateef akan sadaki dubu ɗari uku. ɗaurin auren da ya samu halarta manya manyan ƙusoshin ƙasar nan, dan duk wanda yake da faɗa aji a ƙasar nigeria da wajenta sai da Mai Martaba ya gayyace shi ɗaurin auren, kuma cikinsu babu wanda ya turo wakilinsa duk da kansu suka zo. duk girman masallacin fada sai da mutane suka cika shi taf, ciki da wajensa babu masaka tsinke, ango dai yana tare da mahaifinsa dan babu abokinsa ko ɗaya, Bello ma da yace zai biyo jirgin safe Maama ce tayi sai taci ubansa matsawar yazo. ango dai kamar ba ango ba dan fuskarsa babu walwala, ga shi dai acikin mutane kuma inda ake ɗaura aurensa, amma hankalinsa gaba ɗaya na can kan Fillo, ina take? da kuma halin da take ciki. bayan gama ɗaurin aure aka tafi reception, inda ɗumbin jama'a suka ci sukai hani'an, dan babu wanda zai ce bai goge haƙori da naman kaza ba. ana dawowa daga reception kuma aka koma can gidan mai martaba, cikin masarauta kenan, duk ta yanda Turaki yaso ya zame ya zille ya tafi gida abin yaci tura, dan Baffa na riƙe da hannunsa sai nunawa jama'arsa shi yake cike da tsantsar farin cikin da ba zai misaltu ba, shi kansa Turakin sai da yaji tausayin mahaifinsa, bakin Baffa sam yaƙi rufuwa, da zarar sun gaisa da mutum zai nuna masa Turaki yace,"shine babban ɗan nawa, asa masa albarka". haka ya dinƙa yawo da shi yana nunawa jama'arsa da jama'ar mai martaba. Turaki kam ya koma kamar yaro, bai sami salama ba sai da suka dawo fada, dan iyakar wanda suka dawo fadan duk ƴan'uwa ne, yana jin wayarsa na ta buga ringing daga Maama sai dai babu ta yanda za'ai ya ɗauka. acikin fadar Mai Martaba ne zaune daga tsakiya akan royal chair, sai Hakimi a kusa da shi ta hannun dama, sai Baffa a kusa da shi ta hannun hagu, sannan Falmata a kusa da shi sai Boɗejo daga kusa da hakimi ta wani hakimci ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin alkyabba me ƙallin bala'i, sai ɗaukar idon jama'a take, bakinta yaƙi rufe haƙwaran makka ɗinta guda huɗu duk a waje. Mai Martaba ne ya fara doguwar nasiha ga amarya da ango akan zaman aure, bayan ya gama ya damƙa amanarta a hannun mijinta, ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da samun zuri'a ɗayyiba. bayan ya gama Hajiya Boɗejo ta ɗora da nata, tayi doguwar nasihar aure da babu wanda jikinsa bai amsa ba a wajen hatta Turaki, daga ƙarshe kuma sai ta fashe da kuka tana zuba musu adu'oi iri-iri. bayan ta gama Hakimi ma yay nasa, bayan ya gama Baffa yay musu tasa, sai a sanda yake yi musu nasihar ne kawai Turaki sai jin hawaye yayi ya sauko masa ba tare da sani ba, daga ƙarshe Inna Falmata ma tayi nata. bayannan kuma aka rarrabawa ƙur'ani da littafan adu'oi. daga nan kuma aka ɗauki amarya akayi cikin gida da ita ana batun gobe idan Allah ya kaimu za'a shiga sauran hidiman taron biki. Turaki na fitowa daga fada ya fice bai bari sun haɗu da Baffa ba, iyakar kyau dai yayi kyau kowa ya gansa yaga sabon ango amma sam babu wannan annurin na farin ciki a fuskarsa. Gimbiya Ilham kam tun sanda tai ƙoƙarin kama hannun Turaki taji yanda ya make hannunta taji jikinta yyi sanyi, musamman da ta kalla fuskarsa taga ya murtuke kamar wanda aka yowa aiken mutuwa, kace bai taɓa dariya ba a duniyarsa. Turaki na isa gida Hajiya Madina tasa key ta kulle side ɗinta dan bata ma so wasu ƴan bani ka iya ɗin suzo mata, ko kuma Baffa ya dawo yace zai shigo. hakan ko sai data faru, mutane suka dinga zuwa gidan suna juyawa, Mai Gadi na faɗa musu abinda Hajiya Madina tace masa na cewar basa nan, a same su acan masarautar. to haka dai ranar Hajiya Madina da yaranta suka yini cikin ɓacin rai, iyakar yin Baffa ya gana da matarsa da yaransa Hajiya ta toshe duk wannan ƙofar, sai haƙura yayi dole, dan ko a washe gari sai gidan Hakimi ya tafi yay breakfast dan shima irin Turaki ne bai iya cin abincin restaurant ba. kuma a ranar da daddare Boɗejo tazo ta tayar da wuta a gidan, kamar zata cinyesu saboda masifa akan Turaki sai yaje Dinner, har da cewa,"aini Madina ban san ke fitinanniya bace sai yanzu, ashe kin ma fi Fulani Azima haɗari, to wallahi dai akan auren jikana da jikata aniyarki ta koma miki". Maama dai ɗaga kai bata yi ta kalla Boɗejo ba balle ta tanka mata, har ta gama zazzaga masifarta da yaɓa magangunta. Boɗejo ta tasa ƙeyar Turaki a gaba tace,"wuce motar Nasiruddeen na waje suyi maka rakiya, in an hana ƙawayenka zuwa ai kana da ƴan'uwa". sannan ta juya kan su Zaytuna tace,"ku kuma ku wuce muje, haka kawai za'a tusa muku baƙin hali a zuciyarku, tsakani da Allah mene abin baƙin ciki a wannan aure banda ma dai zuciyar mutum ba ta da ƙashi. to kuyi gaba muje ba sai kunyi wata kwalliya ba, idan ban isa da wasu ba ku ai na isa da ku. ƙulla auren zumunci kuma yanzu na fara, kuma inga uban da zai sa Turaki ƙaro aure dan naji ana ƙishin ɗin haka, in ban ba'asa naje na bankawa ƴar mutane wuta ba". haka ta saka su a gaba har Khalil da su Samha da suka dawo a yau suka wuce suka tafi. wajen dinner dai iyakar haɗuwa ya haɗu, amarya da ango sun haska guri, amma ko kaɗan fuskar ango bata murmusa ba, MC ma da yay batun liƙi sai Khalil ne ya fito ya wakilce shi ya watsa bandir ɗin ƴan 500 har guda biyu. kuma fuskar ango kaɗai zaka kalla ka hasko tsantsar rashin son auren a tare da shi, Gimbiya Ilham kam da ƙyar ta iya controlling hawayenta ta dinƙa yaƙen ƙarya, saboda gaba ɗaya ta fahimci Turaki ba auren ne baya so kaɗai ba ita kanta ba sonta yake ba. bata tabbatr da hakan ba sai after an tashi daga dinner sunzo shigo mota yace,"ki bar cusa kanki gare ni, domin ni ba sonki nake ba, cusa min ke akayi. idan kuma wancan son kike tunani har kika iya amfani da shi kika sa aka ƙulla wannan auren to kinyi babban kuskure, domin ni son ƙanwa nake miki ba shirmen so irin naki ba. and again ki san da cewar baki da matsuguni a zuciyar Turaki dan already wata da ta fiki komai ta cike wannan gurbin". wannan maganganun nasa yasa tayi kuka ta gode Allah a wannan daren, kuma sai ta dasa zarginta akan Gimbiya Aisha. washe gari ma kamar ba zata je Cocktail party ba amma haka dole taje, shima kuma taga abinda yafi na jiya a wurin Turaki, don opalli ya nuna kowa ba auren so suka yi ba. ranar lahadi da za'a kaita tamkar ta shiɗe haka taji, tunanin ta inda zata fara zama da shi kawai take yi, Mai Martaba da Fulani Azima su suka kaita gidan anan Estate ɗin su Turaki, daga gidansa zuwa nasu babu nisa, gidan ya gaji da haɗuwa kamar a turai, bai san sanda Baffa ma ya gina gidan ba. shima Turaki Baffa da Maama ne suka masa rakiya, kuma banda cewar ɗanta za'a kai babu abinda zaisa taje. ko kula Baffa bata yi ba har suka je, yana ta janta da hira tai banza da shi sai Turaki da take kulawa, tana faɗa masa ya cire damuwa saboda yanda duk ya rame. acan gidan Amarya da Ango ma Hajiya Madina kallon inda Mai Martaba yake bata yi ba balle wata Fulani Azima, bata san ita Fulanin ba so take ba. haka suka gama yiwa ma'auratan nasiha da adu'a sannan suka baro su. kamar yanda sunnah ta koyar Turaki suka yi nafila tare da matarsa, bayan sun idar ya kama kanta yayi adu'a, sannan ya gabatar mata da abinci. ita taci dan shi bai iya cin komai ba, sai bayan da ta kammala ya tashi ya bar ɗakin ya wuce parlo ya zauna, tunda ya fito kuma yake ta tunanin Fillo, Allah kaɗai yasan me yake ji a zuciyarsa. ya jima zaune anan daga baya ya tuna fa cewar aure aka yi masa and amayar tana ɗaki, ko kaɗan baya ƙaunar ganin Ilham, kuma baya jin zai iya haɗa jiki da ita su kwana a shimfiɗa ɗaya, amma kuma ba shi da yanda zai yi, ba shi da wani hope, dole ne zai bi koyarwar addini, zai yi amfani da ilimin da yake da shi dan ganin bai kaucewa addininsa ba kuma bai ƙi yin koyi da sunnar ma'aiki ba a daren farko. babu zancen ya ƙauracewa shimfiɗarta a yau dan zai iya jefata a halaka, tunda addini ma ce yay ka ƙauracewa shimfiɗar mace a sanda tai maka laifi in har kayi wa'azi taƙi dainawa, Maganar kauracewa a shimfida sai idan har ta yi wani laifi ne , kuma kayi wa'azi taƙi dainawa, abinda musulunci yace kenan game da ƙauracewa shimfiɗar mace. dan haka a wannan dare dai Turaki ya mayar da Ilham cikakkiyar mace, ba dan ya so ba, kuma ba dan yana farin ciki ba, kuma ba dan yayi farin ciki ba da samun budurcinta ba. haka kuma rashin sonta bai sa ya zalunceta ba wajen kusantarta, ya tafiyar da ita a hankali ta yanda yasan ba zai ƙuntata mata ba, sai dai hakan ba shi ya hana Ilham kuka sosai ba a wannan daren. *Vote, Comment & Share.* [8/31, 00:32] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* _Shafin gaba ɗayansa sadaukarwa ne ga duk wani makarancin littafin *LULLUƁIN BIRI*, ina jin daɗin yanda kuke bibiyar littafin nan, alkhairin Allah ya isa gare ku._ *34* da asuba Turaki na dawowa daga sallan asuba kira na shigowa wayarsa, babu suna ajikin lambar dan haka ya tsaya yana kallonta da son ya fahimceta, ganin ba lambar da ya taɓa sani bace ya ɗaga. yana karawa a kunnensa Gimbiya Aisha ta kwaɗa sallama cikin dodon kunnensa da irin muryar da kana jinta kasan tasha uban kuka. banda koyawa ta addininsa da babu abinda zai sa shi amsawa, dan sarai ya shaida muryarta, kuma ko ba komai taji daɗin amsawar saboda muryarsa nan me daɗi, daɗin da take jin yafi na sarewa tsuma zuciya. daga kan gadon da ta ke tasa tissue ta ƙara goge idonta, with littile courage tace masa,"barka da asuba. ya amarci?". tsabagen mamaki ma bai san me zai ce mata ba, last kira da tayi masa Bello ne ya karɓi wayar ya keta mata rashin mutuncin da ko kare ba zai shinshina ba, kuma in ace Bello gaban fadawa yay hakan abu ne me kamar wuya idan ba'a fille masa kai ba, dan tsananin shock na irin maganganun da ya dinƙa yaɓa mata matsayinta na ƴar Sarki tsayawa tayi kamar statue, and a zaton Turaki ko ace shi ɗaya ya rage namiji a duniya Gimbiya Aisha ba zata ɗauke shi ba saboda abinda Bello yayi mata, amma shine yau take daɗa kiransa?. dama bata tsammaci zai amsa mata ba, saboda haka maganarta kawai taci gaba da yi. "ƙawata Ilham bata faɗa min zancen aurenku ba kwata-kwata, amma na gani a duniya, naga the best couples in the year of 2022, na jima banga perfect match couples irinku ba. duk da kai babu farin ciki a tare da fuskanka but hakan ba shi ya hana fiddo da ainihin kyawun surar da ubangiji yay maka ba, and wannan rashin bayyanar annuri da fara'a na fuskanka ya shaida min cewa auren dole ne akayi maka, kai baka so but ita tana so dan tata fuskar ta bayyana hakan 100%, but duk da haka fa duniya zata judging rashin walwalanka da a haka kake, amma to me da na riga na san fuskan da bai rabo da murmushi na san sam auren ba so yake ba. Anyway i congratulate you dear, Allah ya baku zaman lafiya. sai dai you have to know one thing, ni Aisha Sanusi M2 ni ce zan zama uwar ƴaƴanka, keep this in your mind". Turaki dai tun sanda ta fara maganar ya kunna TV yana sauraron karatun alƙur'anin da aka saka a channel ɗin saudi tv, abubuwan da ta faɗa ma ba komai yaji ba banda na ƙarshen. bai bari ta ƙara cewa komai ba ya datse kiran da ya haddasa masa ciwon kai. ya wurgar da wayar a gefensa yana daɗa jin ransa duk babu daɗi. yana gama bin azkar ɗin da yake sauraro ya jinginar da kansa da kujera, lokacin tuni gari ya waye har 6:30 ta kusa. idonsa a lumshe hoton Fillo nata haska masa, lokacin ne Gimbiya Ilham ta fito daga bedroom tana takowa da ƙyar har ta ƙaraso wajensa, abaya ne yello colour jikinta me bala'in kyau, ta ɗora hular chantly akan kwantacciyar sumar kanta, tayi kyau sose da light makeup ɗin da tayi sai zuba ƙamshi take yi, ta ɗauke hannunsa akan kujerar sannan ta zauna a kusa da shi ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hannun nasa kuma ta ɗora akan cinyarta. muryarta a sanyaye kuma a shagwaɓe tace,"Hammah fever na son kamani, kaina yana ciwo sosai, jikina ma duk ciwo yake yi". ta ƙarasa maganar yana jin saukar hawayen nata a kafaɗarsa, yana jin yanda ɗumin hawayen ya tsarga fatar jikinsa, yana kwatanto shi da zafin hawayen Fillo, wacce ya san a duk inda ta ke yanzu kuka take yi. bai ce da Gimbiya Ilham komai ba har wucewar daƙiƙa ɗaya, lokacin wayar dake kusa da shi tayi ringing, yana kallon new number ne ajiki yaƙi ɗauka. har sau biyu kiran na katsewa tunaninsa duk Gimbiya Aisha ce, sai kira na uku ya shigo da lambar Inna Falmata, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga yana yin sallama. daga can ɓangaren Boɗejo ta amsa sallamar tasa tana ɗorawa da faɗin,"ban kiraka da lambata ba saboda nasan ba ɗagawa zaka yi ba, ashe sabuwar lambar ma baka ɗagawa, sai ka ɗaga ta Falmata da yake kasan ta ƙanwar ubanka ce, ko ba komai halin girmama manyanka na burgeni, duk uban miskilancinka ka san manyanka". yaji kamar ya kashe wayar dan mugun haushinta yake ji, amma sai bai yi hakan ba. a daƙile yace,"ina kwana". tace,"lafiya lau, kun wayi gari lafiya?". yace,"lafiya lau". tace,"yauwa dama zan tambayeka ne ya ka sami Ilham ɗin?". ta faɗa tana yin ƙasa da murya. yace,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". tace,"ya salam, baka gane nufina ba ne?, ita yarinyar a ya ka sameta nake nufi?". ya ƙara cewa,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". Boɗejo taji kamar ta kai masa duka ta cikin wayar, dan in kusa gareta yake ma ba abinda zai hana faruwar hakan. cike da takaici ta ƙara yin ƙasa da murya tana faɗar,"ya zanyi tunda kai farin shiga ne, sai nayi opalli-opalli tukunna zaka gane. dama haka zancen ya zancen budurcinta?, ya ka same shi?, fatan dai ta kawo shi lafiya?". da ƙosawa yace,"gata ki tambayeta". ya faɗa yana direwa Ilham wayar akan cinyarta. ta buɗe idonta da ke rufe bacci na so ya ɗauketa, ta kalla wayar da call ke tafiya, da sauri ta ɗau wayar ta saka a kunne tana cewa,"Inna ina yini". Boɗejo tace,"Ilham ni ce, lafiya naji muryarka haka, kuka kika yi?, ko ba kya jin daɗi?, mene matsalar faɗa min, Turaki ne ya gaya miki magana babu daɗi?". Ilham tace,"a'a". ta faɗa tana sakin sabon kukan shagwaɓa. hankalin Boɗejo a tashe tace,"ni bana son kuka, ki buɗe baki ki min bayani, ko sai na zo?". cikin muryar kuka Ilham tace,"Boɗejo jikina duk ciwo yake min, zazzaɓi ne ajikina. kaina kamar zai cire, kizo dan Allah". Boɗejo tace,"bawa mara mutuncin wayar". Ilham ta kai hannu ta ɗora masa wayar a kunne, da masifa Boɗejo tace,"daga mugu sai kai Turaki, yanzu yarinyar babu lafiya shine dan tsabar zalunci baka wuce ka kaita asibiti ba?, haka kaga ubanka na yiwa Madina?. gaskiya ban yafe ba sai Allah yay mana sakayya tsakanina da kai. kuma dan uwarka Madina ka amsa min tambayar da nayi maka tun ɗazu, in kuma sai nazo har gidan kaga tsayina inji". Turaki yay guntun tsaki yace,"ni dai karki ƙara zagar min uwa. amsar tambayarki kuma ta kawo shikenan, karki ƙara kirana ki kira wayarta idan kina son magana da ita, ni ban haɗa komai da damuwa ba so ki barni inji da abinda ya damen". bai jira cewarta ba ya kashe wayar yana miƙewa ya bar wajen, Ilham tabi bayansa da kallo tana jin hawaye na sakko mata. yanzu shikenan irin wannan zaman zasu dinƙa yi da shi?, ana aure dan farin ciki amma tun ba'aje ko ina ba ta fara fuskantar ƙalubale, tana ji ana faɗar tun daga daren farko mace ke fara samun kula da tarairaya daga wajen mijinta amma ita nothing like that, ya sameta a virgin ɗinta amma kamar wadda ta zo masa a fafe, sai faman haɗe rai da kumbura yake ba, duk uban kukan da ta sha daren jiya sannu wannan bata samu ba, balle taimako daga garesa. and cikin ƙarfin hali ta gyara kanta duk da zafi da raɗaɗin da take ji amma hakan bai sa yaji tausayinta ba a sanda ta tabbatar da yaji uban zafin dake jikinta sanda take kwantar da kanta jikinsa, yanzu shikenan ita wannan soyayyar da take ta kwaɗayi a gidan aure ba zata samu ba kenan?, dama haka illar auren wanda baya sonka yake?. sai kawai ta kifa kanta a hannun kujerar ta fashe da kuka mai ban tausayi. daga can masarauta kuwa tuni ko'ina ya ɗauka da batun Gimbiya Ilham ta kai budurcinta gidan miji, kowa kuma sai ya shiga saka kyautukansa acikin wata ƙatuwar kwalla da ke dire a ƙofar turakar Fulani Azima, guɗa kawai kake ji na tashi da tafi ana son barka ana yabon Fulani Azima da tarbiyar da ta bayar. ƙarfe goma sai ga manyan motoci ƴan ubansu na jiniya a ƙofar gidan Turaki, mota guda biyu ɗauke da hadimai mata, suka fito suka isa inda wata baƙar mota ta ke cike da sassarfa. acikin motar ne aka shiga fito da manya manya coolers na abinci, wasu coolers ɗin abinci ne cikinsu irin na gidan saurata, sai wasu coolers ɗin kuma uban kayan gara ne kamar hauka. dan Gimbiya Ilham tsab zata shekara da su indai ba cin abinci aka dinƙa musu ba. haka suka dinƙa shiga da coolers ɗin suna fitowa suna kuma ɗibar wasu, sai da suka gama shigar da su tas sannan kuma sai ga ma'aikatan kamfanin Arewa culture Decoration suna shigowa ɗauke da kayan aiki a hannunsu suna nufar can baya inda ƙaton haraba yake wajen filoti guda, a wajen harda swimming pool irin tafkeken nan. suka baje kayan aikinsu kuma cikin ƙanƙanen lokaci suka shiga gyara wajen da decoration irin na gidan sarauta bango zuwa bango, haka ƙasan wajen ma duk an malale shi da uban carpet me taushi an baza uban tumtum sai ka rantse ko fadar mai martaba ake haɗawa. wata ƙawar Fulani Azima na zuwa taga irin yacca decoration ɗin ya haɗu sai tayi tsaye ta kasa motsi ta saki laɓɓa tana bin wajen da kallo cike da burgewa. "wow, la'ila ha'illahu, dan Allah aina aka samo waɗan nan masu iya aikin. kan uba ke kiga wuri kamar dama can a haka aka ƙera shi, na rantse da Allah wanda bai sani ba yazo wajen nan sai yace gidan sarauta ya shiga". sai tayi saurin zaro waya a jaka tana miƙawa ɗaya daga cikin ma'aikatan tana cewa,"ungo maza lafta min lambarku a wayata, ina zanyi saken wannan azababben decoration ɗin da bikin ƴata, habawaa ai dole jama'a suzo suyi kallo na kece raini ma, ta yanda gobe ba zasu ƙara ɗaukan gajigarin masu decoration na musu aikin wofi suna asarar kuɗi ba". ma'aikacin na murmushi yace,"Hajajju bari na karanto miki kawai". Hajja Balkisu tace,"yi da sauri, ai ni duk a tsume nake. yanda kasan in ɗauke wajen nan in tafi da shi". Ma'aikacin still da murmushi fuskarsa ya shiga karanto mata lambar yana rubutawa,"08067261323". tace,"me zan saka a sunan?". yace,"kawai rubuta Arewa Culture Decoration". daga cikin gida kuwa Gimbiya Ilham na zauna tana ta bin Hadiman dake kaiwa da komowa wajen kimtsa kayayyankin da suka shigo da shi. sai taji suna tafiya da zaman kaɗaicin da ta ke ciki, dan Turaki tuni ya fice daga gidan ko sallama ɓata haɗa su ba. can kuma sai taji parlon ya karaɗe da wata uwar guɗa kamar gidan zai tsage, ta rumtse idonta for the first time da hawayen farin ciki ya sakko mata tun kawota, ko ba komai tasan duk wannan abin da akeyi na murnar ta kai budurcinta gidan miji ne. Boɗejo ta fito daga bedroom ɗin da suka kwana riƙe da farin bedsheet ana haskawa mutane ɓacin da yay dan su shaida, ta bawa Jakadiya Hanne tana barin wajen da rawa. ta isa wurin Ilham ta rugumeta tana ƙara sakin wata uwar guɗa ta musamman, sai kuma kowa yayo kanta ana cewa,"barka Gimbiya, sannu Gimbiya, sannu sannu, Allah ya huce gajiya, ubangiji ya kawo albarkar ɗaki, sannu. Fulani Azima na cewa agaisheki, a gaisheki, ayi miki gaisuwa irin gaisuwar da babu mahaluƙin da ya taɓa samunta". daga nan Boɗejo da Inna Falmata suka kamata sukai cikin ɗaki da ita. bayan an yiwa Gimbiya Ilham gashin ruwan ɗumi mai kyau, sannan aka haɗa ruwan lalle da turare Boɗejo tayi mata wanka da shi, aka fito da ita sai zuba masifaffan ƙamshi take yi. duk wannan hidima dai da akeyi Boɗejo ƙwafa kawai take jerawa tana tunanin irin rashin mutumcin da zata yiwa Turaki tunda yasa ƙafa ya bar ɗanyan amarya ita ɗaya kamar mayya. kwalliya aka yiwa Ilham ta gani ta faɗa, tayi azaban kyau, aka fito da ita a lulluɓe da alkyabba fara tas me adon red ajiki, babu ta inda ake ganinta harta ƙafarta kuwa dake sanye cikin wani half conver na sarauta, akan cushion na babban parlon gidan aka zaunar da ita tayi zama irin na masu mulki, Mutum uku daga dangin mahaifiyarta suka zo suka ɗaga hular alkyabbar nata ana fasheta da turare me bala'in ƙamshin gaske, suna yi ana tafi ana busa shantu ana rera mata waƙa na son barka da kawo budurcinta lafiya lafiya, after sun gama bajakolin fesa turaren sai wasu bayi guda biyu suka zauna kusa da ita gefe da gefe suna mammatsa mata ƙafafunta. acan ɗaya ɓangaren kuwa Turaki na fita gida ya wuce, kaitsaye part ɗin Baffa ya nufa don zatonsa ko suna can suna breakfast, sai dai ko da yaje duk basa can Baffan ma bai tashi ba, dan haka ya taho side ɗin Maama, time duk sun zauna zasu yi break fast, kallo ɗaya Maama tayi masa tasan baici abinci ba, hakan yasa ta miƙe ta shiga kitchen ta dama masa kunun gyaɗa shap shap ta soya irish, duk da cewan akwai soyayyan irish ɗin amma tasan ba zai ci ba. sai after break fast ɗin ne Maama ta zaunar da Turaki a ɗaki tai masa nasiha sosai akan yanda zai zauna da matar da ba sonta yake ba, ta nusar da shi in har yay haƙuri ya kyautata mata to tabbas zai ga ribar hakan, tunda har yayi biyayya Allah ba zai barsa haka ba. tace,"Me Babban suna ko ni zan iya zaɓa maka Ilham matsayin wacce zaka aura, saboda yarinya ce me hankali da tarbiyya, ita kaɗai ta fita zakka acikin yaran Mai Martaba, to nasan dan ka aureta ba faɗuwa kayi ba ka sami uwar ƴaƴa ta gari. but ni ta yanda akazo da lamarin aurenne ya ɓata min rai, shiyasa duk naji na tsani auren wallahi, to amma ya zamu yi tunda ubangiji ya shirya faruwan hakan tuni. adu'ata Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina tsakaninku, ya kuma baku ikon fahimtar junanku ta yanda ɗaya ba zai cuci ɗaya ba". sannan ta ƙara cewa,"ka dai ji me nace maka ko?". ya ɗaga kansa kawai tabbacin yaji, dan bai jin zai iya magana. suna zaune da ita suna ta hira kiran Boɗejo ya shigo wayarsa, yana kallo yay banza da kiran, da ya ƙara shigowa ya kashe wayan gaba ɗaya yana jan tsaki tare da kwanciya kan gadon Maama. ita dai tana kallonsa amma ko kusa bata yi magana ba, saboda tasan irin ɗacin da yake ji a zuciyarsa, and beside ta lura kamar yana da wata damuwa acan ƙasan ransa, sai dai bai faɗa mata amma tasan duk runtsi zata sa ni. miƙewar Maama kenan zata shiga toilet taji an banko ƙofar ɗakin, kallon wajen da zatai taga Boɗejo a fusace ta shigo, ta bi Turaki dake gadon idonsa a rufe ta ƙarasa wajensa tana ta zazzaga masifa kamar zata bankawa ɗakin wuta. Hajiya Madina kam dama tana ganin itace ta shige toilet ta rufe ƙofa, haushin duk wanda ke da sanya hannu akan lamarin aurenan take. bata fito a toilet ɗin ba sai da taji Boɗejon ta fita, ta fito a ranta tana jin haushin irin zagin da Boɗejo ta dinƙa mata ita da Turaki, cikin ranta tana jin ina ma ace akwai ƙasar da babu wanda ya sa ni sai ita, da ba abinda zai hanata ɗauke Turaki a gobe ta kaishi can yaje ya huta na kwana biyu ko zuciyarsa tayi sanyi. acan gidan Turaki dai sabon biki ne ya tashi, dan yana zuwa ya tarar da danginsu da dangin Fulani Azima an cika gidan sai tashin busar algaita ta ko'ina, ta dole Boɗejo ta shirya shi har da cewa wallahi idan baiyi wasa ba sai tayi masa wankan da kanta. ya fito cikin dakakkiyar shadda fara da ta saje da alkyabbar Gimbiya Ilham, yayi azababben kyau har yafi na ranar ɗaurin aurensa. kamar dai wancan kwanakin haka yau fuskarsa duk babu walwala har akai taron aka gama, sai da Boɗejo ta tabbatar sun gama cika al'adarsu sannan hankalinta ya kwanta. jama'a sunci sun sha an bar arziƙin abinci a inda yake, bayan kammalawa Inna Falmata ita tayi jawabin godiya ga duk waɗanda suka zo da kuma tarin adu'oi wa ma'auratan, daga nan kuma sai aka shiga ɗaukar hutuna kamar hauka, kowa burinsa bai wuci yay short vedio yana hasko gidan ba ta yanda duniya zata gani ta shaida gidan arziƙi. ƙarfe biyar na yamma Turaki ya wuce police station kan sabon report da ya shigar tun a ranar da ya dawo, suka kuma tabbatar masa da cewar suna kan yin bincikensu, bai dawo gida ba sai 6 kuma ba gidansa ya wuce ba wurin Maama ya wuce, inda yaje ta tarar ta wuce wajen Kaka anzo ance tana can ta suma. *Kidnappers.* ga duk wanda ya san Fillo a yanzu zai iya rantsewa ba ita bace, saboda yanda ta fita a hayyacinta, abinka da mara ƙiba, kallo ɗaya zaka yi mata ka zubar mata da hawaye saboda yanda ta fige, idanuwan nan sun ƙara ɓurmawa ciki. zaune take akan ƙasan simitin wajen an ɗaure ƙafafunta da igiya, haka ma hannayenta an ɗaure su ta baya, yanda fuskarta tayi jawur da yanda jini ke fita daga bakinta kaɗai zasu shaida maka irin azababben dukan da ta sha a iyakar yau. ƙaton mutumin dake gabanta ya ƙara buga mata bindigar hannunsa a fuskarta, take bakinta ya ƙara fashewa kanta ya lanƙwashe. cikin burkitacciyar hausarsa yace,"muddin baka daina yi mana gardama ba, to wuya yanzu ka fara shanta. in bakayi wasa ba sai mun kaseka ayau ɗin nan". da ƙyar Fillo ta miƙar da wuyanta ta ɗago tana kallonsa da idanonta guda ɗaya da bata iya gani sosai da shi. kallonsa take yi tana hango ranar da suka tsareta suka ce ta bayar da lambar wanda za'a kira, lambar Amir kaɗai ta haddace a duniyarta kuma bata tunanin zata iya bayar da shi, saboda tsoronta kar ya cutu da jin halin da take ciki. sai da tayi da gaske tukunna ta iya haɗa lambar Yami ta bayar dan ba wani haddaceta tayi sosai ba, kuma sai da aka gwada lambar kusan sau uku duk ba correct ba sai ana huɗun Allah ya taimaketa kiran na shiga taji muryar Yami a sanda aka ɗaga, da wannan ta samu ta kuɓuta daga wahalar da suke bata. kuma tun a ranar da aka kawo kuɗin suka ƙirga suka ga harda ƙarin dubu ɗari biyar akai amma hakan bai yi musu ba suka ce fiye da wannan suke so, idan bata manta ba tana jin shi ƙaton na cewa,"wato iyaye naka suna sonka sose, tunda har gashi suna ƙara mana kuɗi akan wanda muka nema. wannan ya nuna mana sewan sun tara kudi da yawa, don haka ba zamu sake ka ba sai an cika mana kudi ya zama miliion goma". tunda taji ance ƙarin dubu ɗari biyar tasan Amir ne kaɗai zai yi hakan duk da bata san ta yanda akayi su Kaka ma suka sami wannan kuɗin ba. dan a ranar da suka kira waya aka sawa su Kaka muryarta tana cewa azo a ceceta, the first abinda Kaka ta faɗa mata shine,"ki daina kuka Fillo, kiyi ta adu'a kinji za ki kuɓuta, banda ƙarfin da zan kawo musu amma Amir zai zo ya tafi dake kinji". ta sa ni a irin son da Amir yake mata zai ƙara fiye da haka ma in har ace yana da shi, kuma tun a ranar ta ƙara jin Amir ya sami wani waje na daban a tare da ita, in ace da sonsa ya ragu da 85%, to a yanzu wannan son nasa zata ce ya ƙaru da morethan 1000%, saboda shi ɗin mai sonta ne kuma me ƙaunarta, dan haka a duniya bata da wani wanda ya fishi. dukan cikinta da akayi da ƙafa shi ya dawo da ita daga duniyar tunani. ta saki kukan da bata jin zata iya riƙe shi, ta shiga ambaton Allah a fili da kuma zuciyarta. ta buɗe bakinta wanda leɓenta suka riga suka zama ganda tace,"ku kasheni kawai, dan Allah ku kasheni ko na samu na huta. kunce sai an ƙara muku kuɗi an ƙara still kuna faɗin bai isheku ba, na faɗa muku bamu da wani gata sai Allah, dan Allah dan Annabi ku kasheni kawai". ƙaton ya jawo jakar kuɗi na biyun da Amir ya kuma kawowa naira miliyan biyu, sai dai basa tunanin da naira miliyan bakwai da rabi kacal zasu iya sakin yarinyar, sun jima suna kidnapping su yanke kuɗaɗe masu uban kauri, amma basu san me yasa akan wannan yarinyar ba suka buƙaci kuɗi kaɗan. cike da rashin imaninsa yasa ƙafa ya ta-ke ƙafarta yace,"ka san menene yaro?, ko iyaka motan gidanku da muka ƙwamusoka daga wajen da muka ganka ranar idan siyar da shi za'ai ya haura sama da miliyan asirin, saboda haka ku daina ce mana baku da shi. for the last time zamu kira waya ka faɗa a gida kace aciko mana miliyan uku, ana cikawa mu kuma munyi alƙawarin zamu sake ka". cikin tsananin azaba da wahalar da take ji tace,"ni Kakata kawai nake da ita a duniya, bayan ita banda kowa. wannan motar ba tamu bace ta gidan da nake aiki ce, dan Allah ku taimaka min, na tabbata Kakata duka gadonmu na wurin mahaifiyarmu ta siyar aka sami wannan kuɗin, a yanzu kuwa na san babu wani abu da zata ƙara ɗagawa ta siyar, kuyi min rai dan Allah". shirunta yay dai² da shigowar wani mutum dogo kamar sanda, ya ƙaraso gaban ƙaton mutumin yana miƙa masa waya yana cewa,"oga ka duba news ka gani". Ogan ya shiga kallon shafin facebook da yake nuna masa yana karanta bayanan dake jiki na ɓatan Fillo ƴar aiki a gidan Judge Alƙali Dikko, da kuma hotonta a ƙasa sanye da hijab. sai ya bushe da dariya yana sa ƙafa yayi fatali da kujerar dake kusa da shi, ya mayarwa da mutumin wayar yana faɗin,"ashe kamu muka yi me soka bamu sani ba, har muna ɓata lokacinmu wurin amsar 5million only". sai yay shiru yana ƙara sakin dariya yace,"Hardo kaje ka nema mana numban waya na gidan Alƙali, wannan yaro yana da taurin kan jaraba ba zai bamu wani number ba...kayi sauri ka kawo min in the next few minutes, yanzu ba miliyan 10 muke nema ba, miliyan 200 zamu karɓa". ya faɗa yana miƙewa daga kan kujerar yana ƙara sakin dariya cike da nishaɗi. sannan ya ƙara kallon ɗaya acikin yaran nasa yace,"Jibril, ka siyo kaza ka bashi yaci, domin ina sha'awan wannan yaro, ina so na huta da shi. a siyo masa kayan gina jiki a bashi yaci kafin nazo na biya buƙatana akansa, tun a ranar farko naji ina sha'awan budurci nasa, i know by that time uban Alkalai ya kawo mana 200Million namu, sai muna sakinsa yana tafiya". Kalmar Virginity yay wani duka a ƙwaƙalwar Fillo da yasa taji ta girgiza gaba ɗayanta, her virgin?, kamar dai bata fahimci maganar tasa ba da kyau, sai kuma taji wanda aka barta da shi na faɗin,"kash Oga banji daɗi ba kana riga ni shiga daɗin wannan kyakykyawan yarinyar, nima ina ta kwaɗayinta tuntuni, amma da zarar ka sha naka rabon daɗin nima zan sha nawa kafin a sallameta". yaja igiyar ƙafarta ya ƙara ɗaurewa da kyau yana cewa,"kai Budurci yana da daɗi, gaki da ganinki za ki daɗi ƴan mata". ƙwayar idon Fillo tun ɗazu ƙafe take a wuri ɗaya, tun bayan fitar wancan mutumin take so ta fahimci abinda ya faɗa kafin ya fita, kuma bata gane komai ba sai a yanzu, sai yanzu ta fahimci abinda yake nufi daga shi har wannan, suna maganar zasu amshi budurcinta ne kafin ta fita daga hannunsu. da sauri ta shiga jujjuya kanta da ke barazanar tarwatsewa, hawaye masu zafin gaske na daɗa biyo kuncinta, ta jinginar da kanta jikin bango tana jin ƙirjinta yay mata wani irin nauyi tamkar an ɗora dala da goron dutse akai, a hankali ta shiga ambaton sunan Allah tana fashewa da wani kuka me ƙarfin sauti cikin fitar hayyaci. ta jima tana kukan tana kiran sunan Allah, bata ma san time ɗin da mutumin da aka barta da ahi ba ya fita ba. zuwa yanzu ta san ruwan hawayenta sun ƙare, ƙazaman maganganun mutanen ke tayi mata yawo acikin kanta. ta sa ni shikenan tata kuma ta ƙare, dan haka ta sallama da rayuwar gaba ɗaya, kanta ta buga ajikin bango tana addu'ar,"Allah ka ɗauki raina kafin waɗannan azzaluman su cimma burinsu akaina, Allah ka ɗau raina ayanzu ko na huta da wannan bala'in". tsananin tausayin kanta ya lulluɓeta, babu ta yanda ta-ke tsammanin zata iya guduwa daga wajen nan, dan tayi attempting sau ɗaya suka kamata, shine tun daga ranar suka ɗaureta basu ƙara ƙunceta ba har zuwa yau, jini har ya gaji da daskarewa waje ɗaya a jikinta. idanuwanta a rufe taji kamar mutum na taɓata, a mutuƙar firgice ta buɗe ido tana sakin ihu cikin ƙaraji da bala'in tsoro, da sauri farin mutumin dake gabanta yasa hannunsa ya toshe bakinta. ta ƙwalolo ido waje tana kallonsa, ta san shi sosai kullum shine yake kawo mata abinci. a hankali taji yace,"ki shiru zan taimaka miki ne ki fita daga wajen nan, ki yarda da ni wallahi ba zan cuceki ba saboda haka karki yi ihu" ya sauke hannunsa a bakinta, cike da tsoro dan bata tunanin za ta yarda da shi. ya miƙa mata plate na abinci gabanta yace,"ki fara cin abincin tukunna". tace,"dan Allah karka yi min komai". yace,"wallahi tallahi banda niyyar cutar fa ce taimakonki, amma kici abincin ko kaɗanne kinji". tana ta kallonsa tace,"ba zan iya ci ba. dan Allah ka taimaka min". yace,"zan taimaka miki amma in har ba kiyi wani yunƙuri na tona min asiri ba". da sauri ta jijjaga kanta tana cewa,"zan bi duk ubarninka in har ba wanda zaka cuceni ba". yasa hannu ya kunce ɗaurin igiyar ƙafarta, sannan ya kunce ɗaurin na hannu, amma sai dai bai warware ba. yace,"kowa ya fita daga gidan nan, ni kaɗai ne amma zuwa nan da minti goma zuwa sha biyar Babban Oga zai iya zuwa saboda haka ba zan ce miki ki fita nan da wuri ba. kawai dai kiyi hankalin da ba zasu gane cewar wannan igiyar a kwance ta-ke ba, idan kika ta shi akwai ƙofa ta nan baya kusa da parlo da aka cire ki jiya, kibi ta nan ki fita. kina fita za ki hango wata ƙofa a wurin sai kiyi saurin buɗewa ki fita, za ki ganki cikin daji karki tsaya a kusa-kusa sai kin tabbatar kinyi nisa sosai da babu me iya riskar ki". yasa hannu a aljihu ya ɗauko ƙaramar waya yace,"ga wannan kina iya kira gida ki faɗi inda kike ko da za ki kasa gane hanya". tabi ƙaramar wayar hannun nasa da kallo kafin ta ɗago ido ta kallesa tana nazarinsa. yay mata murmushi yace,"ni dai har ga Allah iyakar abin zan miki kenan, ya rage naki kuma ki kuɓutar da kanki ko kuma ki zauna su cuceki tun kina ƙaramarki. dan wallahi ina mai tabbatar miki sai sun mayar dake yarinyarsu after sun gama talauta danginki, ƙarƙari ki kasa juriyar ɗaukarsu ki mutu su jefar da ke, dan Babban Oga bai da imani wallahi". yana gama faɗar hakan ya miƙe ya fitar ya barta, tabi bayansa da kallo kafin ta dawo da idonta kan wayar da ya bar mata. jin kamar motsi tayi saurin ɗaukar wayar ta tura acikin rigarta, Allah ya taimaketa kuwa tana sawa ana turo ƙofa a shigo. jere ta gansu duk kusan kansu ɗaya, zata iya cewa bata taɓa ganinsu ba duk da cewar fuskokinsu a rufe yake da mask irin wanda take gani a film, suka wuceta suka shiga ciki, in ta lura da kyau kamar harda mace, na ƙarshen ya duƙa gabanta ya mammari fuskarta yana wani makirin murmushi yace,"zamu huta sosai da kai". da faɗin hakan ya miƙe yabi bayan sauran. taji sabon hawaye ya taho mata, ta rumtse ido sosai tana rasa ma me take ji a ranta. dai-dai nan taji mutumin ɗazu ya dawo can ƙasa da muryarsa yana cewa,"you got the chance, zasu yi zaman meeting yanzu and atleast they will take up to 30minutes kamin su gama, babu wanda zai ji motsinki har ki fice, karki yi wasa da wannan chance ina daɗa jadadda maki if not wallahi a yau ko ba'a ɗau gawarki ba sai kin mugun raina kanki, dan kaf wannan mutane da kike gani sai sunyi amfani da ke". yay saurin ficewa gudun kar wani ya fito ya gansa tare da ita. *A dai-dai wannan lokacin.* wayar Hajiya Madina da ke riƙe a hannun Nihal tayi ringing, tai saurin miƙa mata sanda ta ke tambayarta,"waye?". tace,"ba suna a jiki". Hajiya Madina da jikinta yake a sanyaye ta karɓi wayar, dai-dai kuma da katsewar kiran, ta sauke numfashi jikinta duk a mace saboda halin da Kaka ke ciki, tun ɗazu suka zo asibiti amma har yanzu bata dawo hayyacinta ba, a sannan likita ya shigo ɗakin yana cewa,"Hajiya meet me in my office". da hanzari Hajiya Madina tabi bayansa, nan kiran lambar ɗazu ya ƙara shigowa, ta ɗaga tana yin sallama tana ci gaba da bin bayan likitan. daga can ɓangaren taji wata gwandareriyar murya na faɗin,"Hajiya mune kidnapper na ƴarku". tsabagen rikicewa sai wayar ta suɓuce daga hannunta tana tsaya daga bakin ƙofar tana haki kamar wadda tayi tsare, saura ƙiris wayar ta kai ƙasa Allah ya shigo da Turaki yay saurin riƙo wayar yana dubanta. "lafiya Maama?". da shi da kowa na ɗakin suka tambayeta a tare suna yowa kanta. tsabar gigita tama kasa cewa komai sai nunawa Turaki wayar ta ke da hannu. ya kalla screen ɗin wayar yana kallon yacca call ke tafiya, ya kara wayar a kunnensa yana cewa,"Salamu Alaikum". cikin ɗaga murya aka ce masa,"karku ƙara yi mana sallama ba ita muke buƙata ba". mamaki ya bayyana akan fuskar Turaki yace,"wake magana?". aka ce,"wanda suka yi garkuwa da yaro naku ne, kuna san yaron naku a raye ko kuma mu kashe shi mu aiko muku da namansa?". Turaki bai san lokacin da yaywa hannu Maama wata muguwar damƙa ba da yasata yin ƴar ƙara tana faɗin,"Me Babban suna zaka karya min hannu". bai ma san tana yi ba becouse he is totally getting out of control, ƙwaƙwalwarsa ta shiga faɗa masa anger ɗinka ba zai yi amfani yanzu ba, just relax and control your self. ya buɗe idonsa da ya rufe in just 10seconds, yaja leɓensa ciki ya cije da ƙarfi sannan a hankali ya sauke dogon numfashi, ƙwayar idonsa da ta sauya kala ta dawo yanda ta ke. ya ɗauko wayarsa a aljihu ya ɗauki lambar tasu, sannan ya bi bayan kiran nasu da suka katse. bugun farko suka ɗaga, cikin kwantar da murya Turaki yace,"muna jinku, me ku ke da buƙata?". mutumin yay dariya sosai yace,"kun tabbata za ku bayar da komai muka ce?, idan kun san baku shirya karɓan ƴarku ba karku sa mu ɓata bakinmu wajen yi muku bayani". Turaki ya ƙara rumtse ido yace,"duk abinda kuke so na tabbatar da zaku sa me shi". mutumin ya kuma dariya yace,"good. ga yaronku nan yana ta kuka kullum yana so yazo ya ganku, amma munce ba zamu sake shi ba sai an bayar da miliyan ɗari biyu tukunna mu barsa ya dawo gida da ƙafafunsa". zuciyar Turaki na bugawa fat-fat yace,"you got additional of 300million, zan baku miliyan ɗari biyar muddin baku taɓa lafiyarta ba wannan alƙawari ne, ta ya zaku karɓi kuɗin?, or throught bank za'a tura maku". mutumin yay dariya sosai yace,"zaka kawo mana kuɗin da hannunka". nan ya shiga korawa Turaki bayanin inda zai je ya kai kuɗin ya ajiye. Turaki ya tabbatar masa da cewar zai zo ɗin in the next few minutes amma su tabbatar ba su yiwa Fillo komai ba. mutumin na bushewa da wani dariyar yace,"ga yaronku kuyi magana dan ka tabbatar yana lafiya, idan kunji jishi yana kuka ba komai bane akayi masa, soro ne kawai da yake ciki". daga can inda mutumin ke zaune kan kujera ya ɗorawa Fillo wayar a kunnenta a tsawa ce yace,"yi magana da father naki". cikin matsanancin kuka tace,"Kaka". Turaki ya ƙara matse hannun Maama da har yanzu ke hannunsa, muryarsa a hankali yace,"Fulaniii". sai kuma ya fesar da iskar bakinsa me zafi yace,"kina jina?". a wahalce tace,"Turakii, dan Allah kazo ka cece ni, kashe ni zasu yi sun ce, wai zasu yi amfani da ni, ka faɗa musu Kaka bata da kuɗin da suke nema". ta faɗa cikin kukan da duk wanda yaji sai ya zubar mata da hawaye. Turaki ya tattaro jarumtarsa da yake jin tana neman barinsa yace,"kiyi shiru ki daina kukan kinji, zan zo in ɗauke ki yanzun nan. babu abinda suka isa suyi miki in har bakinki bai gushe da ambaton Allah ba, amma na faɗa miki ki daina kukan kinji Fulani". wannan jarumtar tasa ta maza yaji ta ƙwace, bai san sanda ya zube a gefen gadon Kaka ba, idonsa na cika da tarin hawaye, ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya magana ba, acikin zubar hawayen da babu wanda ya lura da shi a fuskarsa yace,"karki bari suyi miki komai kinji Fulani, i know who you are, i know you can protect your dignity, dan Allah karki bari suyi miki komai, dan Allah". yanda take sauke numfashi a wahalce kawai yake jiyowa, ya matse idonsa sosai yana jin zuciyarsa na wani mugun matsewa, yace ta sassauta kukan tace,"to zaka zo yanzu?". yace,"yes, i will come right now, just some minutes kinji". ƙit yaji wayar ta katse, ba tare da yabi ta kan kowa dake jiran cewarsa ba ya ratsa ta tsakiyar Maama da Yami ya fice daga room ɗin cikin sauri. yana shiga mota yay dialling number D.P.O yace masa,"ranka ya daɗe kun fara tracing numbern?". yace masa,"yes, before wayan naku ya katse har mun gano a inda suke, yanzu haka yara sun ɗau hanya. ka tsaya ka ɗauke ni a hanya". Turaki nasa hannu ya sha re zufar goshinsa yace,"please ka faɗa musu suyi a hankali kar suja su cutar min da ita". da haka ya katse wayar sannan ya kira wayar Khalil yace,"Bro i need five hundred million naira in cash right away, kaje Zenith Bank wurin Faisal, on my way to meet you there in the next 10minutes". acikin motar Turaki da yake sharara mahaukacin gudu akan hanyar zuwa ƙauyen pindiga, lokacin ƙarfe bakwai da rabi na dare har tayi, waya ce maƙale a kunnensa yana tabbatarwa da kidnappers ɗin cewa shi ɗaya ne ba tare da kowa ba kamar yanda babu wanda ya shaidawa maganar.. sai dai a dai-dai wannan lokacin da yake wayar da su, a dai-dai wannan lokacin Fillo ta samu damar zare igiyoyin jikinta ta miƙe tana bin hanya saɗaf saɗaf ta yanda babu me jin motsinta, kuma ta tabbata har ta fice babu wanda zai ganta kamar yanda mutumin nan ya faɗa mata. sai dai kuma me?, sanda ta ke zuwa gab da ƙofar zata fita, dai-dai jikin windown wani ɗaki, bala'in tsoron dake tare da ita sai ya koma zuwa tsantsar mamakin abinda kunnuwanta ke jiyo mata, muryar wanda ta ke ji da kuma sautin dariyarsa da abinda yake faɗa na saka jijiyoyin jikinta tsinkewa. ta ja ƙafarta a hankali ta isa jikin window tana leƙawa ta yanda ba za'a ganta ba, tana tsaye a wurin kunnuwanta na ci gaba da jiye mata abubuwan da yake faɗa, maganganun nasa da take jinsu tamkar ɗigar dalma ajikinta, in one time sai taji jikinta gaba ɗaya ya zama kamar na statue, ko hannunta ta kasa motsawa, ko idonta ta kasa ƙiftawa, zata iya rantsewa cewa zuciyarta kanta ta tsaya da aikin buga jini zuwa sassan jikinta. a sanda ƙyar idonta tayi tozali da shi ta siririyar ɓular, zaune tsakiyar mutanen wanda ya tabbatar mata shine Babban Oga da taji suna ta ambata, kuma yana ɗaya daga cikin mutanen da suka shigo ɗazu har tabi su da kallo. sai ta koma da baya ta lumshe idonta tana jin zuciyarta kamar ta zama ƙanƙara tana narkewa ruwan yana taruwa acikin idanunta, taji duk wani tsoro nata yana bin iskar wajen dake kaɗawa, taji kamar duk wani abu da yake cikin kanta yana farfashewa a ƙasan wajen da ta ke, taji duniya gaba ɗaya tayi mata zafi. sai ta ƙara matsawa da baya tana saka hannu ta goge hawayen da ya taru cikin idonta amma sai taji ƙamas babu komai, idonta a bushe yake kamar famfon da ya shekara guda babu ruwa, haka ma fuskarta. "Amir!". taji zuciyarta ta furta da wani irin amo kamar ba nata ba. "Amir ta ke gani anan, Amir ta ke ji yana faɗar shi zai fara keta haddinta kamin kowa, shi ta ke ji yana faɗar ya cika burinsa na shekara da shekaru ya gama handame musu komai, har yana faɗin bai zama lallai ma su barta da rai ba". gaba ɗaya sai taji jikinta ya ɗauki rawa kamar an jona mata electric shock, haka ma zuciyarta na harbawa fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito, numfashinta na fita da ƙyar tana jin kamar ana zare ranta. ta jingina kanta da bango tana kasa rufe idonta, komai da ta ke ji ta ke gani kamar mafarki ba gaske ba. ta ƙara dafe bangon wurin tana rumtse idonta tana girgiza kanta da ɗan sauran kuzarin da take jin tana da shi, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ta buɗe ido taga ba Amir ta gani ba, Allah yasa idan ta buɗe idon taga mafarki ne ta ke yi ba muryarsa ta ke ji ba acikin azzaluman mutanen da tasan babu makawa sai wutar Allah ta ci su. Ta shiga buɗe idonta a hankali tana mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙara tsananta. a lokacin ta ƙara jinsa yace,"ba zata san ni na tsara komai ba kuma na shirya ba har sai bayan na gama da rayuwarta. zanje yanzu dan ana kan hanyar kawo kuɗin fansarta...in ance ma nasan mutanen nan a shirye suka da yin komai akanta da tun farko ba'a ɗauki tsayin wannan lokacin ba, da ban tsaya na jira na gama haifar da tashin hankalin da bai da misaltuwa ba a wurin Kakarta, da a yanzu kuma bamu ambaci miliyan ɗari biyu ba, da 2billion naira zan ambata musu". Fillo ta buɗe baki tana ƙoƙarin furta kalmar innalillahi a fili amma sai taji ta kasa sarrafa harshenta, sai bakinta da ke rawa kawai, cikin fitar hayyaci ta juya da gudu ta buɗe ƙofar ta fice tana jin kamar numfashinta zai ɗauke. gudu take sosai acikin duhun daren, cikin jejin da take gani kamar ba'a duniya ba, ko gabanta bata iya gani sosai, sai da ta tabbatar tayi nisa sosai sannan ta duƙa tana haki a wajen da ta ke, wucewar daƙiƙa biyu ta ɗago ta ɗora daga inda ta tsaya, tun ƙafafunta na ɗaukarta har taji suna dab da dainawa, kuma a lokacin da ƙarfinta ya ƙare lokacin taji tayi karo da abu, karo da abu kamar mutum. tsoron da ya barta tun a ɗazu sai ya dawo sabo a sanda ta ɗago ido tana kallon halittar dake gabanta, da sauri taja da baya tana dafe kanta cikin ranta tana jin anya kuwa yau itace?, anya bata yi gamo ba?, anya zamanta a wajen can bai sa aljanu sun shiga jikinta sun rikita mata tunani ba?. sai ta juya tana kallon bayanta kan ta juyo ta ƙara kallon matar da ke gabanta wadda ta ke duk a firgice, firgicin da zata ce ya ninka nata, kuma mafaka take nema, inda zata tsira da ranta ta ke nema. sai taga matar ta ɗaga hannunta biyu tana haɗe tafun hannunta alamar roƙo, ruwan hawaye na bin idanunta, jini ya taru a ƙwayar idonta, a cikin rawar murya irin wadda ta sa ni taji tace mata,"dan Allah ki taimaka min zasu kashe ni, amma dan Allah kema karki cuce ni". ta faɗa acikin yaren fulatanci muryarta na shaida tsananin tsoro da kuma tashin hankali. hasken farin watan da ya hasko su ya haskawa Fillo sarƙar da aka ɗaure hannun matar da ita, ya kuma haska mata abayar dake jikinta wadda taci ubanta da mugun dauɗa sai wani kalar wari ke fita a jikinta,  yalwataccen gashin kanta a barbaje ɗauke da tsirarrun furfura duk ya tuttuje. Fillo ta tsayar da ƙwayar idonta akan dogwayen yatsun matar tana jin wani kalar hawaye me zafi da bata taɓa zubar da irinsa ba na bin kumatunta, kallon yatsun nata ta ke amma a yatsun wani hannun na daban, furucin da matar tayi na maimaituwa acikin kanta da irin sautin muryar da ta sani, ta rumtse idonta sosai tana jin ruwan hawayen dake ciki na ƙarasa sauka. bata san lokacin da ta faɗa jikin matar ba ta rungumeta tana fashewa da kuwa, kuma ƙarar harbin bindigar da suka jiyo ya cika dokar dajin yasa ta fizgi hannun matar sukai gefen wata bishi suka ɓuya, ba nata ƙirjin kaɗai ba, har na matar tana jin yanda yake bugawa kamar zai faso. a bakin bishiyar wajen suka duƙe Fillo ta kamo kan matar ta kwantar akan ƙirjinta tace,"Alhamdulillah, welcome back to the family". *please vote, comment and share.* [8/31, 00:32] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *35* Fillo na rungume da matar har bayan wucewar wasu daƙiƙu sannan ta zare jikinta anata, ta ƙara saka idonta akan fuskar matar don tabbatar da abinda ta gani ɗin kar taje ko idonta ke mata gizo. ai ko da ace bata taɓa ganin hotonta ba, tsananin kamannin da take da yaranta kaɗai ya shaida mata wannan itace matar da suka ɗauki shekaru ashirin da biyar basu ganta ba. ita ayanzu ma sai ta iya rantsewa hoton fuskar Turaki kawai ta-ke gani a fuskarta, ta kamo hannayenta tana daɗa kallo da suke sak da na Zaytuna tun daga kan tsayin yatsun har farcen, haka ma a sautin muryarta sai ka rantse kace Zaytuna ce tai magana, daga nan sai kuma ta sauke idonta akan sarƙar dake ɗaure da hannuwan nata. taji hawaye ya kusa sakko mata tsaboda tsananin tausayi, tayi attempting kunce sarƙar sai taga ba zata iya ba. ji tayi matar ta ƙara ce mata,"dan Allah karki cutar da ni kema". Fillo tai murmushin ƙarfin hali, taji tausayin kanta na bin iska yana tafiya, yayinda na matar ke biyo iska na lulluɓeta. tace,"ba zan cutar da ke ba Mum, adu'a nake so kiyi mu fita daga wurin nan lafiya". Hajiya Ramla ta dinƙa kallon Fillo tana jin kamar wani ya taɓa kiranta da wannan sunan Mum. Fillo tasa hannu a rigarta ta ɗauko wayar ɗazu, ta kunna sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"Mum za ki iya faɗin lambar Baffa ko ta Maama? sai mu kira su azo a tafi damu". Mum tace,"su waye hakan?". Fillo ta ɗago ido ta kalleta sannan tace,"lambar mijinki Alƙali Dikko ko ta abokiyar zamanki Hajiya Madina". Mum ta girgiza kanta tace,"ni ban san su ba ai, ban taɓa jin sunansu ba". sai kuma ta haɗe hannayenta tace,"idan kin san sune mutanen da suka saka ni a ɗakin duhu don Allah karki kira su, sun ce zasu yi tsafi da ni ne, kuma babu abinda nayi musu". Fillo tasa hannu ta goge hawayenta, babu makawa ƙwaƙwalwarta tayi formating abubuwa da yawa, kuma ba lallai ta tuna komai ba ayanzu ƙila sai ta gani da idonta. a lokacin suka ƙara jin harbin bindiga, cikin azama Fillo ta miƙe ta kamo hannunta a rikice tana cewa,"Mum zo mu gudu kar su kama mu". Hajiya Ramla ta miƙe da ƙyar suka nausa inda basu san ina zasu ɓulle ba suna ta zabga gudu, da sun gaji sai su tsaya su huta, sannan suci gaba da gudun, gaba ɗayansu a galabaice suke. *A dai-dai wannan lokacin.* Fulani Azima zaune a gaban boka dunƙus, idanuwanta na manne acikin ruwan ƙwaryar dake gabansa yana mata bayani, tana jin zuciyarta na tafarfasa saboda baƙin ciki. "to ban san dai abinda hakan ke nufi ba, amma kwata-kwata ko aljani ɗaya ya kasa nuna mana fuskar yarinyar, amma tabbas dai aljanu sun shaida ita ke lalata miki aiki". maganar ta ƙara ƙona ran Fulani Azima, ta ɗaga murya tana saka hannu ta toshe kunnenta tace,"wacece wannan?, wacece ita da har aljanu suka kasa gano min fuskarta?". sai kuma tayi ƙasa da murya tana kallon Boka tace,"ni dai na roƙe ka da Aljani Jambus ka nuna min fuskar yarinyar nan ko kuma sunanta, nayi maka alƙawarin ko menene zan bayar ko da kuwa kaina ne". Boka yay dariya yace,"haba Azima, yanda muke da ke ai kin fi ƙarfin haka a wajena. abinda nake so ki fahimta shine yarinyar nan tafi ƙarfinmu saboda tana tare da tsari a jikinta". sai yasa wani mifici ya rufe ƙwaryar sannan ya buɗe yace,"leƙo ki gani". ta leƙa kanta ta hango wata mace a tsaye doguwa siririya, amma baka ganin komai nata sai ɗan banzan duhu. yace,"to kinga ni babu ta yanda zamu ga fuskarta haka kuma sunanta ɓacewa yake akan aljanunmu". fuskar Fulani Azima na shaida mamaki matuƙa tace,"to saboda me boka?". sai yasa hannunsa acikin ruwan ya zuƙo hoton, daidai inda hannun Fillo yake yace,"ba lallai ke ki gani ba amma ni ina iya gani, wannan azurfar ta yatsanta azurfa ce ta tsari wadda ba zata taɓa barin wani aljani ya ganta ba balle har ya sami damar shigarta, bayan haka kuma ɗan autan aljanu ya faɗa min cewa yarinyar na kasancewa kullum cikin yin adu'oin tsari, bata minti ɗaya bata ambaci sunan Allah ba haka kuma bata min ɗaya bata ambaci adu'ar neman tsari ba. saboda haka babu yanda zamu yi da ita gaskiya, kuma shugaban Aljanu ya shaida mana muddin yarinyar na tare da Turaki babu abinda asirinmu ya isa yayi masa, domin ita ɗin kamar sila ce ta kariya a tare da shi". kan Fulani Azima yay matuƙar ɗaurewa, ta dinƙa hasaso tsayin yarinyar tana so ta kwatanta shi da na Ilham amma sam babu haɗi, tsayin Ilham bai ko kusan nata ba. to wacece wannan ɗin?, tabbas ya zamar mata dole taje gidan Alƙali Dikko da ƙafafunta, idan aljanu sun kasa ita ba zata gaza ba domin ba ta taɓa barin wani ya shiga gaban al'amarinta, dole sai taga bayansa ko waye. ta numfasa tace,"shikenan me girma boka, yanzu ya batun mu na janyo hankalin Alƙali Dikko kaina?". Bokan ya bushe da dariya yace,"kin haƙura kenan, ai nayi zaton har yanzu kina kan bakanki na cewar son gaskiya kike so Dikko yayi miki ba sai anyi amfani da asiri ba gudun lalacewa wataran". tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai tace,"mu bar tuna baya. yanzu dai a san abinyi akan Mai martaba, a kashe shi kawai na huta da aurensa da ke kaina. shi kuma Alƙali ayi aikin da za'a gama da rayuwarsa kawai, ina nufin ya saki kowa ya kamani ni ɗaya hatta kuwa da mahaifiyarsa. tashin farko abinda nake so shine Alƙali ya fita daga hayyacinsa yaywa Madina saki uku sannan duk ya kori ƴaƴansa, daga baya kuma sai ya dawo kaina ya mallaken ta yanda zamu yi rayuwa da shi har a bada. da wannan buƙatar ta biya sai a raba auren Ilham da Turaki, kuma ta yanda nake so mutuwar auren ta kasance Dikko yaje gidan da kansa ya umarci Turaki da ya saki Ilham". Boka ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yana ɗaga hannu sama yace,"buƙata taki ta biya Azima, duk yanda kika nema haka za'ai, kuma komai da kika nema zai faru tabbas, angama da wannan buƙata taki ki jira kwanaki biyu kacal". Fulani Azima ta saki wani murmushi na jin daɗi da kuma nasara, sannan ta miƙawa Jakadiya hannu. cikin rawar jiki Jakadiya tasa hannu cikin jaka ta ɗauko yari da sarƙa da zobe ta saka a tafin hannun Fulani Azima. har yanzu murmushi bai ɗauke a fuskar Fulani Azima ba ta ajiye sarƙar a gefen boka tace,"wannan kyauta ce na baka. kuɗinta kimanin miliyan goma ne, kyauta ce kawai ba kuɗin aikinka ba". Boka na murmushi yace,"godiya nake". tace,"sai muje ga lissafin abinda zan bayar akan aikin". ya ɗaga kansa sama yana kallon reshen bishiyoyi na tsawon daƙiƙa kafin ya sauke yace,"da farko za ki bayar da miliyan goma, sannan za ki kawowa jikokin Aljanu baƙin jaki guda biyar, sannan za ki haƙa kabari ki yanko mana zuciyar jariri fari wanda ana haihuwarsa ya mutu, sannan kuma muna buƙatar yatsa ɗaya na ita mahaifiyar Dikko". rufe bakinsa kenan sai suka ga jan ƙyalle ya faɗo gabansu ɗaure da wani dunƙulen abu. da tsananin mamaki yake kallon abin na tsawon daƙiƙa biyu kafin ya kai hannu ya ɗauko ƙyallen, ya ɗauko shi zaren da aka ƙulle shi na warwarewa. mamakin dake tare da shi bai gama sakinsa ba yaga baƙar kurciya ta faɗo kan hannunsa a ma ce, sabon mamaki tsantsa ya kama shi. ya ɗau kurciyar ya haɗe da wannan ƙyallan sannan ya juyo yana kallon Fulani Azima wadda idanuwanta ke a warwaje tana binsa da kallo. taji yace,"ya akai haka?". tace,"me ya faru?". yace,"me na faɗa miki shekaru ashirin da biyar da suka wuce kafin nayi miki aikin Ramla?". cikin saurin baki da rawar murya tace,"kace kar na kuskura inyi sakacin da asirin nan zai karye, domin duk ranar da ya karye ba zanji da daɗi ba". tana yin shiru yay wani guntun murmushi na tayata jimami sannan yace,"ban labarin yanda aka yi bayan barinta gida". jikinta na rawa tace,"lokacin da ta bar gida can ƙasar china ta nufa kamar yanda ka faɗa, bayan wata uku na bi sahunta zuwa dajin da kace anan aka jefa kurciyar domin na tabbatar da taje can ɗin. kuma ko da naje na ganta ɗin a gefen wata bishiya tana cin ganye, itama kuma ta ganni dan har ta dinƙa roƙona akan in taimaka mata bata san ta yanda akayi tazo wurin ba, ta bar Muhammad da Zaytun acikin ɗaki wuta tana ci bata san ba ko Madina ta kula kar yaran su cutu. sai nayi mata dariya nake faɗa mata cewar ni ce silar zuwanta wurin kuma ita da ƙara komawa wajen ƴaƴanta har abada. to muna cikin haka da ita ne sai ga wasu turawa sun zo, suna zuwa suke tambayata cewar nasan wannan mahaukaciyar ne?, da farko har zance musu a'a sai kuma nace ehh, sai ɗaya daga cikinsu yace min to suna da buƙatar siyanta idan zan siyar musu zasu yi tsafi da jininta, ni kuma jin hakan yasa ba tare da wani tunani ba na amince musu dan har inda suke da zama ma muka je tare suka min bayanin cewar zasu ajiyeta aɗakin tsafi tsawon shekara ashirin da shida cif kafin nan sai su zuƙe jinin jikinta suyi tsafin da zasu yi da shi, kuma tare da ni suka sakata a wani ƙaton ɗaki ko taga babu suka kulle suka ce za'a ke bata abinci ne kawai tana ci, don har sarƙoƙi suka saka suka ɗaureta saboda kar ɓacin rana yasa ta gudu, kaji abinda ya faru Boka, ko ɗaya ban saɓa ƙa'idar aikinka ba wallahi". Boka ya ƙara murmushi sannan yace,"Azima aikinki ya lalace, domin kuwa maganar da nake miki yanzu asirin da yake kan Ramla ya barta kuma ba da jimawa ba za ki karɓi sakamakonki saboda aljanin da yay wannan aikin ba me yafiya ba ne". Fulani Azima ta dafe ƙirji cikin bayyanuwar tashin hankali a tare da ita tace,"kamar ya Boka ban gane ba, me kake so kace min?, ta ya hakan zata faru?". yana ɗago matacciyar kurciyar da jan ƙyallen yace,"waɗannan sune asirin da ke kan Ramla, wannan kurciyar da kike ganinta tun ranar da ta ɗauki Ramla bata ƙara zuwa nan ba sai yanzu, wanda ke tabbatar da cewa Ramla ta baro inda ta ke ta dawo cikin garin nan, kuma mutuwar kurciyar nan shine zahirin cewa babu wani abu da ya sami Ramla". sai ya jefar da kurciyar sannan ya ɗauko ƙyallen yaci gaba da cewa,"wannan kuma shine ƙyallen da muka ƙulle ƙwaƙwalwar kifaye acikinsa saboda Ramla ta manta komai, dan haka faɗowar wannan da kuma warwarewarsa ya shaida mana Ramla ta dawo cikin tunaninta". ya jefar da ƙyallen ma sannan ya juya bayansa yana kallon akuyar dake tahowa tana kuka yace,"idan za ki iya tunawa wannan itace akuyar da kika kawo muka ɗaurewa baki saboda rufe bakin Ramla, tsawon wannan shekarun tana nan tare da ni bata taɓa kuka ba sai yau kuma ayanzu, hakan ke tabbatar da cewa bakin Ramla ya buɗe duk inda ta ke yanzu tana can tana magana". Fulani Azima ta ɗora hannu akanta tare da kurma ihu tace,"na shiga ukuna". Boka yace,"ba ki shiga uku ba tukunna sai kinga yanda reshe zai juye da mujiya". ya faɗa yana sa hannu ya daki ƙasar dake gabansa sannan yace,"kar hankalinki ya tashi sosai, ke ko garin da kike ba za ki bari ba, amma sai dai za ki kwanta baƙar jinyar da za ki ji gwara ace haukacewa kika yi ko kuma ɓatan kika yi da wannan ciwon da zai kamaki. domin za'a zo har kan gaɓar da hatta ƴarki ba zata iya zuwa kusa da ke ba". Fulani Azima ta fashe da kuka sosai tana cewa da boka yay mata rai. cikin wata razananniyar tsawa yace da ita,"Azima ta shi ki bar mana wuri". ya faɗa yana nuna mata hanya. suka miƙe tare ita da Jakadiya jikinsu sai rawa yake suka fita daga wajen tana ta uban kuka. suna fitowa tayi wani kukan kura ta shaƙi wuyan Jakadiya tana girgizata tana faɗin,"wallahi ba ki isa kin tona min asiri ba, ba zan kwanta cuta ba kibi ta bayan fage kije ki fallasa ni, zan kasheki sannan zan je in kashe Ramlar ma". haka ta dinƙa sambatun magana bata saki wuyan jakadiya ba har sai da ta tabbatar ta mutu tukunna ta jefar da ita a wayen, ta bar wajen kamar ana tankaɗata har ta fito daga cikin jejin, tana zuwa ta buɗe mota ta shiga Driver yaja su, sai da suka shigo cikin gari sannan tasa ɗankwalinta ta shaƙo wuyan driver shima tana faɗar,"ba zan barka a raye ba kaima ka tona min asiri, ba zan barka kaga ciwona baka tona min asiri". bata sake shi ba sai da ta tabbatar ya mutu, kuma kamin Fulani Azima tayi wani ƙoƙari na karɓar kan motar, motar ta gangara ta faɗa gefe, nan ta-ke glass ɗin motar ya tarwatse da yawa suka soki cikin kanta, ta kurma ihu tana neman ɗauki tana ƙoƙarin fitowa a motar, bata ankara ba ta kai fuskarta saitin wani glass da yay kamar kibiya ƙwayar idonta ɗaya ta soki glass nan take ruwan idon ya shiga tsiyayewa. *A dai-dai wannan lokacin.* *Yanda Abin ya kasance da kuma yanda abin ke faruwa.* sanda Turaki ya ƙaraso wurin da kidnappers suka buƙaci da ya ajiye kuɗin, yay parking motarsa ya fito ɗauke da dumin jakar kuɗin. ya tsallako side ɗin da suka ce yay tafiya me nisa sannan ya ajiye jakar a wajen, ya ɗauko wayar Maama dake aljihunsa ya ɗaga calling ɗinsu dake shigowa. daga can ɓangaren yaji ance,"kai ne kasa coffee yadi?". yace,"ehh ni ne". ya faɗa yana duddubawa ko zai ga ta inda mutumin yake. sai yaji mutumin na dariya yace,"ai ba zaka taɓa ganinmu ba ka bar wahalar da kanka da waige-waige, ka juya ka bar wajen ka koma bakin motarka ka jira yaronka zai zo ya sameka". jin haka yasa Turaki saurin juyawa ya bar wajen, for the next 5minutes sai ga mutumin yazo ya ɗauki jakar shi kaɗai, cikin sauri yake tafiya don barin wajen, a lokacin Turaki ya fito daga jikin wata rila da ya laɓe. yasa hannu a bayan wandonsa ya zaro bindigar da bai taɓa riƙeta ba sai a yau, ya saita ƙafafun mutumin ƙwayar idonsa na hasko masa yacca ake harbi acikin film, bai taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai a yau da ya shiga office ɗin DSP ya ɗauko ba tare da sanin kowa ba, kazalika bai taɓa riƙe bindiga ba balle har yay attempt na harbi, but today bindiga tazo hannunsa, and zai gwada amfani da ita ko da ace wannan itace dama ta ƙarshe da yake da ita a duniya. ya saita ƙafar mutumin ba don yana tunanin dai-dai ya saita ba, kuma babu ɓata lokaci kai tsaye ya saki bullet, kuma cikin sa'a bulle ɗin ya shige ƙafar mutumin, hakan kuma bai sa Turaki ya haƙura ba ƙara sakin bullet ɗin wanda a yanzu kai tsaye ya wuce zuwa kaɗar mutumin daidai sanda ƙafafunsa ke durƙushewa a ƙasa yana sakin jakar kuɗin ya riƙe kafarsa dake zubar da jini. abinka da wanda bai san kan lamarin ba kawai sai ya jefar da bindigar a wajen ya kwasa a guje ya ƙarasa gaban mutumin, ta baya ya damƙi kwalar rigarsa ya ɗago da kansa, ya zagayo ta gabansa yasa gwiwar ƙafarsa ya daki haɓarsa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwarsa suka haɗu waje ɗaya, ƙwayar idonsa ta firfito waje yana buɗe su da ƙyar saboda azabar harbin da ya shige shi ya kalli Turaki, cikin zafin nama Turaki yasa hannu ya fizge facemask ɗin dake fuskarsa. yana faman huci kamar mayunwaci za ki yace,"ina yarinyar ta ke?". ya faɗa cikin ɗaga murya sosai. sai kuma ya sassauta muryarsa yace,"zaka tsira da ranka, kuma zan kai ka asibiti sannan zan barka da wannan jakar kuɗin ka tafi safely, but first tell me ina yarinyar ta ke?". shirunsa ya haɗe da ƙarasowar ƴan sanda wajen, suna zuwa ɗaya daga cikin ƴan sanda yasa ƙafa ya daki gabansa atake ya ƙwalla wata razananniyar ƙara saboda yacca yaji kamar za'a zare masa rai, babu shiri ya ɗaga hannu yana yi musu nuni da katangar gidan dake can gabansu. Turaki is the first one da ya bar wajen a cikin gudu, wasu cikin ƴan sanda suka mara masa baya, yayinda wasu mutum biyu suka ɗauke wannan wanda Turaki ya harba sukai mota da shi. harbin farko da Turaki yayi su Amir sunji a lokacin suna laluben Fillo acikin gidan, kuma rashin tabbatar da cewar harbin bindigar suka ji da gaske yasa basu bi ta kai ba sai a harbi na biyu, anan hankalinsu ya tattaru wuri ɗaya saboda haka duk sai suka dakata da batun nemanta suka koma ta yanda zasu tsira. Amir yace,"duk yanda akayi shegun mutanen nan da police suka zo". wani me kama da shi yace,"tabbas kuwa, but har ta ya mu kayi sakacin hakan ya faru?". sai ya juya yana kallon mutumin da ya taimakawa Fillo yace,"hau katanga ka duba mana". yana hawa katangar ya ƴan sanda daga can nesa kamar cinnaku sun baibaye faɗin wajen, hakan yasa da ƙarfi yace musu,"police ne mota har guda uku". yana faɗar hakan ya dirge ta baya dan ba ya tunanin zai iya bari a rutsa har da shi. su kuma nan suka fara neman hanyar guduwa ta ƙofar baya da Fillo ta bi, sai dai cikin rashin sa'a suna buɗewar suga police tsaitsaye a wajen riƙe da bindigu, kuma babu wata-wata suka shiga sakar musu harbi ratata, harbin ya sami kusan mutum huɗu su kuma sauran suka koma ciki da gudu don tsira da ransu, sai dai ko a lokacin tuni wasu ƴan sandan ma sun cika gidan. "raise your hands up". su shidan da suka rage ba'a harba ba suka ɗaga hannayensu sama time ɗin da Dsp yay arresting ɗinsu. Turaki kuwa tun shigowarsu babu ta kan wanda yabi sai laluben inda zai ga Fillo, haka ya koma kamar wani zautacce ya shiga can ya fito ya faɗa can ya leƙa can, kaf babu inda bai duba acikin gidan nan bai ganta ba, sai ga shi ya faɗo parlon kamar an jefo shi yana zazzare ido ko zai ganta anan duk da perlon ya fara dubawa. jiri ya ɗebe shi ya tafi ya faɗa kan wata kujera dake wurin, yasa hannu ya dafe kansa da yake jin yana barazanar tsage masa, ya rumtse idonsa sosai yana rasa me ke masa daɗi a duniyarsa, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗago kai ya buɗe idonsa wacca ƙwayar ta kaɗa tayi jawurr ya sauke kallonsa akan Dsp yace,"yallaɓai banfa ganta ba, bata cikin gidan nan yallaɓai". muryarsa ta fito cikin bala'in rauni kamar zai yi kuka. Dsp na tsaye daga gefe yana kallonsa bai ce masa komai ba, har sai lokacin da wasu ƴan sanda guda uku zo, waɗanda sune aka saka su nemo Fillo a sanda suka shigo gidan. "yallaɓai babu wurin da bamu duba ba acikin gidan nan kaf babu yarinyar". Dsp ya kalli tawagar su Amir da suke tsaye hannaye a sama idanu duk sun raina fata, ya sakar musu wata uwar tsawa yace,"ku faɗa min ina ku ka ɓoye yarinyar?". da farko duk shiru suka yi sai da ya ƙara doka musu tsawar da tafi ta farko tukunna ɗaya acikinsu yana karkarwa yace,"mu ma bamu san inda ta ke ba". yana rufe baki yana jin saukar harbi a gwiwarsa, ba shiri ya saki ƙara ta azaba yana duƙe a wajen, tuni zufa ta shiga haɗo masa yana faɗin,"wallahi bamu san inda tayi ba ta gudu tun ɗazu, muna cikin nemanta ne ma ku ka zo". furucin nasa yasa Turaki miƙewa daga kan kujerar da yake a kiɗime yana faɗin,"what!, ta gudu?, baku san ina tayi ba?". ya furta yana jin kamar zuciyarsa zata buga. Dsp ya ƙara harbin ƙafar wanda yay maganar, azaba ta ƙara ratsa shi ya kuma ihu wajen faɗin,"dan Allah kayi haƙuri". Dsp ya ƙara sakar masa wani a hannu, a wannan karon ko motsawa bai yi ba don tsabar azaba, maganarsa ta fito a hankali yana cewa,"na rantse da Allah ta gudu tun ɗazu". Turaki yana shirin sauke ƙwayar idonsa kan mutumin kawai sai Allah ya kai idonsa kan Amir, yay saurin maida kallonsa kan Amir gaba ɗaya yana ƙare masa kallo da son tabbatar da abinda ƙwayar idonsa ke gani. cikin kansa ya haska da hoton lokacin da yake tsaye gaban Fillo har yana riƙe ma ta hannu har zuwa lokacin da ya juya ya bar wajen. "You!". Turaki ya faɗa in shock. sai kuma ya nufi wurin Amir gadan gadan kamar zakin dake cikin yunwa ya ga abinci. yana zuwa yasa hannu ya shaƙi wuyan Amir, ya dinga tura shi da baya har sai da ya kaisa bango ya gwara kansa a jiki. "waye kai?". Turaki ya tambaya . tun Amir bai basa amsa ba ya dunƙule hannunsa ya bawa fuskarsa wani mahaukacin naushi wanda yay sanadiyar ɗaukewar ji da ganin Amir na wucin gadin, hakama haƙorinsa ɗaya ya tsinke ya fara lilo. Amir ya ɗago kansa a galabaice sai dai tun bai gama buɗe idonsa ba Turaki ya ƙara sakar ma fuskarsa mugun naushin da yafi na farko, kan Amir yayi ƙasa jini na zuba ta hancinsa. Turaki ya ƙara yin kukan kura ya ɗago da fuskar tasa ya kuma naushin fuskarsa a gefen ido, take jini ya taru cikin idon Amir, haka ma jini ya shiga fita ta hanci ta baki. Amir yay yunƙurin ƙwatar kansa amma inaa lokaci ɗaya Turaki ya damƙi hannu da wani irin ƙarfin da bai san yana da shi ba barƙala hannun har sai da hannun Amir ya ɓalle. a taƙaice dai Turaki sai ya koma kamar mahaukaci wajen dukan Amir, ya koma tamkar zakin da ya shekara ba abinci ya kuma samu abinci a daidai lokacin da yake so, naushi yake ta kaiwa fuskar Amir hagu da dama cikin ƙaraji yana tambayarsa,"who are you?". sai da fuskar Amir ta kumbura tayi suntum babu kyan gani, ko'ina ya farfashe banda uban jini dake zuba ta gefen idonsa, tukunna Turaki ya bar fuskar tasa ya kai shi ƙasa yana tattaka ruwan cikinsa, yasa ƙafa ya dako shi ta can ya doko shi ta can, yay fatali da shi ta can, ya jefa shi ta can ya gwaru da bango, haka Turaki yayta ball da shi kamar wanda ya samu ball ɗin gaske. tun Amir na iya ihu har yazo ya daina, tun yana buɗe baki yana uban nishi da son yin magana har ya kasa, shi kansa so yake yace da Turaki who is he, dan wannan dukan da yake masa ko uwarsa ya kashe sai haka. da Dsp yaga dai Turaki na ƙoƙarin yin kisan kai yace da ƴan sanda dake tsaye,"ku dakatar da shi". amma me ƴan sanda uku akansa sun kasa ƙwace shi daga kan Amir, suma ɗin duk sai da ya watsa su gefe yana miƙewa cikin huci da cewar duk wanda ya ƙara zuwa kusa da shi sai ya haɗa da shi. bai ma san sanda yasa bayan hannu ya kwaɗe police ɗin dake ƙara yowa kansa ba, ya fizgo shi gabansa ya zare bindigar dake gaban wandonsa ya koma ya haye ruwan cikin Amir, ya cije fuska yana ɗaga bindigar ya bugawa Amir a kansa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwar Amir suka haɗe wuri guda yaji kamar kansa babu komai, tukunna Turaki ya saita ƙirjinsa da bindigar yana bala'in huci yace,"for the last time i will ask you, tell me who are you?, in ba haka ba wallahi sai na sakar maka harbi a zuciyarka". in ace da damar magana Amir zai yi, to amma ankai stage ɗin da yatansa ɗaya ma ba zai iya motsawa ba, balle kuma ya buɗe bakinsa da uban jini ya taru aciki yana tsiyayowa ta waje, shi da wannan mahaukacin dukan da Turaki ke yi masa ma da harbe shi ɗin yayi da ya huta, kuma baya jin ba zai mutu ba muddin Turaki ya ƙara dukansa, azzakarinsa kansa jini yake saboda Turaki ya daki wajen ya kuma ya daka yasa hannu ya kama ya murɗa, to ko da iyaka haka aka barsa ai yana jin sun gama ɗaukarwa Fillo fansa dan yasan ko ace ya tsira da ransa to tabbas a hoto zai tashi dan yana da yaƙinin Turaki ya gama kashe masa gaba, bai da burin da ya wuci a yanzu irin ya buɗe baki ya bawa Turaki haƙuri, kuma yaga Fillo ya nemi yafiyarta. Turaki na ƙoƙarin sakin bullet a ƙirjin Amir Dsp ya taho da sauri ya bige hannunsa bullet ɗin ya sauka a kafaɗar Amir, Amir ya saki wata gigitacciyar ƙarar da shi kaɗai yaji kayarsa babu wanda yaji, don hatta wurin fitar sautin muryarsa Turaki ya gama kashe shi. Dsp ya fizge Turaki daga kansa yay gefe da shi yana faɗin,"wa ya baka izinin yin harbi?, are you a police?, to ko mu ba'a bamu umarnin yin harbi kai tsaye ba". Turaki da duk ya gama ficewa a hayyacinsa yana ta uban huci yace,"yallaɓai na taɓa ganinsa a ƙofar gidanmu tare da ita, yafi ƙarfin rabin awa awajen kafin ya ƙyaleta ya tafi, and am sure shine ya ɓoyeta ma a yanzu, ka tambayesa inda ya ɓoyeta tun ban ƙarasa shi ba wallahi". Dsp ya dafa kafaɗarsa yana faɗin,"calm down mana, yanzu idan muka kashe shi waye zai faɗa mana inda ta ke?, to dole mu bi komai a hankali ba wai mu ɗauki mataki mai gaba ɗaya ba". Turaki ya dunƙule hannayensa duka biyun yaja da baya yana zaunawa kan kujera tare da fesar da zazzafar iska daga bakinsa. ya rumtse idonsa sosai yana ɗaga kansa sama, ba komai yake hangowa ba sai sanda Amir ke tare da Fillo, muryarsa na fita a hankali yace,"Fulani where are?, bana ce miki zan zo ba yanzu, why did you leave?". sai ya rumtse idonsa yana tunawa da maganar da ta faɗa masa,_"wai sai sunyi amfani da ni"._ bai san lokacin da daki hannun kujerar ba har sai da ƙashin hannunsa yayi ƙara. ya kifa kansa a hannun kujerar yana faɗin,"ina kika tafi?, Fulanii why?, why Fulani?, how do you think i will survive without you by my side?, please tell me where you are zan zo na ɗauke ki ko da ace daga na ganki zan mutu". ya faɗa a sanda wannan jarumtar tasa ta karye, raunaninsa ya wanzu, kukan dake can ƙasan zuciyarsa ya ɓalle, hawaye ya sauko masa ƙwayar idonsa na haska masa hotunan faruwar abubuwa kala-kala a tare da Fillo. "idan kika tafi da wa zanyi rayuwar farin cikin gidan aure irin wadda na tsara mana ni da ke kaɗai?, wa ye zai tayani nemo Mum idan ba kya nan?, dan Allah karki min nisan da ba zan saka miki da ceton rayuwata da kika dinƙa yi ba". sai kawai ya cije leɓensa na ƙasa ya kuma yin kukan kura yay kan Amir a fusace, da hanzari police suka ruƙo shi akai waje da shi. *A dai-dai wannan lokacin.* gudu suke sosai babu waige babu tsayawa har sai da suka ga cewar sun shigo cikin gari, kuma a lokacin ne Fillo ta faɗi tana kuka tace,"Mum ba zan iya ba na gaji". tausayin kansu ya kawo zubar sabon hawaye saman fuskar Hajiya Ramla, ta duƙa ta kamo Fillo tace,"ki daure mu ƙara yin gaba, kinga nan wajen ma ba kowa zasu iya kama mu anan". Fillo tace,"Mum ki barni ke ki tafi, su Adda Zaytuna suna can suna jiran dawowarki, Turaki kullum sai yayi kuka akan rashinki, dan Allah ki tafi Mum ƴaƴanki na buƙatar ganinki a raye". Hajiya Ramla ta dafe kanta da ta-ke jin wani abu na mata yawo aciki, so ta-ke ta ɗauki magangun yarinyar ta saka su a ɓangaren tunaninta ko Allah zai sa ta gane abinda ta-ke cewa. kuma kamar gimlawar Jinnu haka Hajiya Ramla taji maimacin furucin da Fillo tayi acikin kanta. ta dafe ɓarin kanta tana ta ambaton Allah har sanda taji wani abu na tafiya acikin kanta yana fitowa yana barin jikinta. lokacin kuma ta saki ƙara tana dafe kan sosai tana ƙara ambaton Allah. wucewar daƙiƙa biyu ta buɗe idonta ta sauke su a wurin da ta-ke, hankalinta da tunaninta da suka dawo dai-dai suka fara tambayar a ina ne nan ɗin?. magana ta farko da ta fara tunawa kamin gushewar hankalinta itace,_"ni Fulani Azima ni ce nayi miki asiri Ramla, saboda kin aure min farin cikina, dan haka kamar yanda na rasa Dikko kema kin rasa shi har abada domin asirin dake kanki har ki mutu ba zai barki ba, ƴaƴanki kuma zan saka su a tafin hannu dan suma sun shiga gonata tun da har ubansu yay kuskuren haifarsu da wata ba ni ba"._ wannan furucin na Azima shine furuci na ƙarshe da zata iya cewa ta tuna kafin hankalinta ya bar jikinta gaba ɗaya, ta rufe idonta tana tuna amintar dake tsakaninta da Fulani Azima tun suna Oxford University. sai kuma tayi hanzarin buɗe ido ta maida kallonta kan Fillo wacce wahala tasa tayi laƙwas sai nishi kawai ta-ke saukewa. ta kamo hannunta jikinta na karkarwa tace,"ina ne nan ɗin muke?, kuma ke wacece?, sannan ina Babana da Zaytuna?, aina zan gansu?". Fillo tace,"Mum suna gida ki tafi kije ki samesu, ni ƴar aikin gidan ce". tayi maganar da ƙyar tana jin ƴaƴan cikinta kamar zasu fito saboda masifar yunwa da ƙishiryawa. Hajiya Ramla ta ɗagota jikinta tana faɗin,"ta ya zan tafi na barki bayan kin taimake ni, ke ya akai kika tsinci kanki a wannan halin?". tambayar ta kawo zubar hawaye me zafi akan kuncin Fillo tace,"kidnappers ne suka ɗauke ni". Hajiya Ramla tace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yi haƙuri ki daure ki tashi muje kinje, kin san hanyar da zamu bi muje asibiti?, domin kina da buƙatar ganin likita ƴata". Kuka ya kubcewa Fillo tace,"Mum ai ba zan gane hanya ba, ban san nan ɗin ina bane dare yayi sosai". Hajiya Ramla tace,"kamar kin ban waya ɗazu ko?". kai kawai Fillo ta iya ɗagawa dan ƙarfinta ya ƙare bata jin akwai sauran yawu da ya rage a bakinta da zata yi magana. tasa hannu a rigarta ta zaro wayar Hajiya Ramla ta karɓa, ta danna 0 tana ƙoƙarin tuna lambar Baffa ko ta Maama amma sai taji ta kasa, tai ta trying taji ba zata iya rubuta duk wata lamba da taɓa sani ba". tace,"ƴata na mance lambar kowa da na sa ni, amma naji kina ta ce min Babana da Zaytuna banji kina min maganar Madina da Khalil ba, dan Allah suna ina?". Fillo ta kasa magana kwata-kwata. Hajiya Ramla ta yunƙura ta miƙe tare da kamo hannunta tace,"yi haƙuri ki daure mu bar wajen nan, idan muka isa titi Allah zai kawo mana mafita". Fillo ta ɗaga kanta kawai. "mu nufi gabas insha'Allahu sa'a ce zata fitar da mu". Fillo ta daure da ɗan sauran kuzarin da ta-ke da shi suka ci gaba da gudu, sanda suka fara hango titi dai-dai lokacin ne kuma mota ta shigo layin da wani mahaukacin gudu irin tuƙin ƴan wiwi, tsoro yasa su kasa kaucewa gaban motar, haka ma Aliyu dake driving rikicewa yasa shi rasa yanda zaiyi, ganin motar tayo kansu gadangadan babu ta yanda zasu kuɓuta Fillo ta ture Hajiya Ramla daga kusa da ita, dai-dai lokacin kuma Aliyu yabi ta kan Fillo ta gangara gefe ɗaya. cikin tsananin tashin hankali, ɗimauta da gigita Hajiya Ramla ta ƙwala ihu tana ɗora hannu akanta ta kurma salati, kafin tayi kan Fillo a guje tana ɗagota zuwa jikinta, ganin uban jinin dake zuba yasa ta fashewa da matsanancin kuka tana ƙara ambaton innalillahi. Aliyu ya fito daga mota a hargitse yana furta,"innalillahi wa'inna ilahi raji'un". Inna Wuro ma ta fito daga bayan motar ta taho da sauri tana faɗin,"shikenan ka shiga uku kai ɗaya Aliyu dan ban dani wallahi, yanzu ai kaga amfani jin maganata ni da kake ɗauka a watse, tuƙin mutuwar da nake hanaka kana maida ni gantalalla kana ƙara wani akai ga shi nan yau yaja maka masifa ka bige aljanu". tayo wajen da Aliyu ke tsaye ya rasa abinyi, jinin dake zuba jikin Fillo ya rikitar da shi tashin hankalinsa ɗaya kar ace ya kashe rai. ya zaro wayarsa a aljihu ya kira wayar Ammi, tana ɗagawa cikin dauriya da ƙarfin hali irin namiji yace,"Ammi ki fito na kaɗe wata yarinya, kuma kamar ta mutu Ammi". Hajiya Ramla kuwa sai kuka take yi tana jijjiga Fillo akan ta tashi, Inna Wuro ta ƙaraso wajen da Hajiya Ramla ke zube a ƙasa da Fillo akan cinyarta, ta tsaya daga ɗan baya tace,"bayin Allah aljanu kuyi haƙuri dan Allah, ni wallahi babu ruwana, saukata kenan daga saudiya ko awa ɗaya banyi ba, aka tura wannan gantalallan yaron yaje ɗauko ni, alhalin tuntuni na faɗawa ubansa ya daina aika shi taho da ni tunda baida hankali, to da yake dai nayi rashin sa'ar haihuwar ɗa me jin maganata sai ta ƴaƴansa, in gaya miki sarauniyar aljanu tun daga iya fat Aliyu yake fafara wannan tuƙin mutuwar da ni, ina ta roƙarsa Allah Annabi ya tsaya yaƙi tsayawa saurarena saima ƙara wani da yake yi, yanzun ma ina ta ce masa zai buge mutane yaƙi jina ashe da rabon manyan zai shafce, rashin jin maganata yasa ya buge ƴar sarkin aljanu dan ba tsautsayi bane yana sane, dan haka wallahi kuyi masa duk abunda kuga dama baida kirki ko kaɗan, ko ƙafarsa ce ma ku shanye ta yanda zai daina tuƙa motar, kuyi haƙuri aljanu ni dai banda laifin komai Aliyu ne ku kumbura masa ciki wallahi tunda ya kashe muku ƴarku". duk wannan maganar da take idonta rufe yake, sai yanzu ta ɗan buɗe ɗayan kaɗan tana kallon Mum, ita tsakaninta da Allah ta-ke maganarta aljanu suka bige, saboda yanda taga yalwataccen gashin Mum har kusa da ɗawawu, ga shi duk da uban dafewar da tayi hakan bai sa tsananin hasken fatar da ta-ke da shi ya dusashe duka ba, hakanne ya ƙara tsorata sosai ta-ke zaton aljanu ne musamman da taga dare ne yanzu, mai lafiya dai ba zai fito a yanda suke ɗin nan ba duka babu ɗankwali gasu a hargitse kamar sababbun kamu. ta durƙusa a ƙasa tana yin alamar roƙo tace,"me girma aljana kiyi haƙuri ki daina tunanin yanke hukunci da ni, ki sunkuci ƴarki ku ɓace kuyi nahiyarku dan Allah. idan kuma ba za ki haƙura ba wallahi na goyi da bayanki kici uban Aliyu dan ko kaɗan baida mutumci, ga gidansu can ubansu shine ɗana ni na haife shi da cikina, amma ba kiga yanda ake wulaƙanta ni ba a gidan, matansa biyu ɗaya me mutunci ɗaya watsatstsiya, amma duk su ɗin sai suka haifi gantalallun yara ba kiga yanda suke bani wahala ba wallahi har kuka sai kin yi min idan kinga a yanda nake zaune a gidan, ni kuma kamar mayya na kasa barin gidan saboda duk cikin yarana gidan Amadu ne kaɗai kullum ake shan shayi da ƙwai da naman ganda da safe, sauran gidajen ƴaƴan ko daga ɗumame sai koko babu ko sikari aciki, to ba zan mutu a wahala ba na dawo gidan Amadu ake ban kayan daɗi ana gani min azaba". Mum ta ɗago jajayen idonta tana kallon Inna Wuro, hakan yasa Inna Wuro zabura taga da baya tana faɗin,"wa'innahu min sulaimana wa'innahu bissimillahir Rahmanir Rahim". Mum na kuka sosai tace,"yanzu ba zaku taimaka min ba sai na rasa ƴata?". Inna Wuro na adu'a a bakinta tace,"ku kuwa kuna da taurin kai mutanen ɓoye, kawai kiyi siddabarunku ta tashi shine har sai anje asibiti salon dai aja kuɗin ɗana Amadu, kuma na faɗa miki indai Aliyu ne ku tafi da shi can nahiyar taku kawai kuci ubansa wallahi, ƴaƴan Amadu da yawa ba shi ɗaya ya haifa ba". Mum na kuka ta kalli Aliyu da duk yake a ruɗe, shima tsoron ya fara kama shi yana ganin kamar ta bakin Inna Wuro aljanun ne. adu'a kawai yake yana ƙara kiran wayar Mum da bata ɗagawa, Hajiya Ramla ta miƙe ta sunkuci Fillo da ƙyar zata goyata a lokacin ne Daddy da Ammi da me gadi suka iso wajen cike da tashin hankali. Aliyu yace,"ban san garin ya ba Daddy, nayi ƙoƙarin ƙwacewa na kasa". Daddy ya ɗago yayi masa wani kallo, sannan ya doka masa uwar tsawa yace,"dan uwarka baka da hankalin da zaka iya ɗaukarsu zuwa asibiti ne da har sai ka kira?, ko baka ga jinin dake zuba daga jikin yarinyar bane shashashan banza, comon zo karɓeta ku sata cikin mota". Aliyu ya taho cikin mutuwar jiki suka kama Fillo shi da me gadi suka saka a mota. cikin hanzari Daddy ya shiga driver seat sannan Ammi ma ta shiga gaban motar, Aliyu da Mum kuma sauka zauna da Fillo a baya, Daddy nata bawa Mum ɗin haƙuri, Ammi dai ta kasa cewa komai dan duk a ruɗe ta-ke. Daddy yace,"kiyi haƙuri Hajiya ki daina kukan kiyi mata adu'a, insha'Allahu matsalar ba babba bace". Inna Wuro ta ƙwanƙwasa glass tace da Daddy,"buɗen bus ina kwaso kayan jaririyar Yusuf da na yo mata tsarabarsu, da tsada na siyo dubu sha biyar duk guda ɗaya". Daddy yace,"kiyi haƙuri mu dawo tukunna kinga a condition ɗin da yarinyar nan ta-ke kar jininta ya ƙare". ta zabga salati tace,"Amadu yanzu har ƴar sarkin aljanu ta fini matsayi a wurinka, saboda kana tare da aljanu ba zaka iya jin maganata ba, to kaje ni dai ba abinda zance wallah sai dai Allah ya saka min". Daddy ya fito ya ɗauko jakar kayanta ya dire mata. ta kalli me gadi tace,"ɗaukar min muje, ni dai ba inda zan bisu, waye yake taimakar wasu aljanu, rabon ai su girgiza motar tasu akan titi ne suyi haɗari, in ko haka ta faru babu uban da zanyi jinya, suna gani aljanar da ta shiga jikin Yusuf akan son ɗaya daga cikinsu irin baƙar wuyar da suke ba shi. ɗazu ma ina bakin ka'aba har yana ce min wai in yi masa adu'a aga yarinyar nan da ta ɓata, kai baka ji ba kamar zai yi kuka da yana maganar, ni ko nace wallahi ba zan ba sai dai nayi adu'a Allah yasa su fita daga jikinka". Mum dai kuka kawai take yi har suka isa asibiti, suna isa Daddy ya kira Yusuf sai ga shi kuwa cikin hanzari ya ƙaraso, Allah yasa yana night duty, nan da nan aka shiga da Fillo Emergency room. *A dai-dai wannan lokacin.* Turaki na zaune acikin motar Dsp ya kifa kansa akan stearing, wayarsa dake aljihu ta shiga ringing cikin sauri yasa hannu ya ɗauko da dukkan fatansa daga gida ne za'a ce masa Fillo taje. sai dai ganin akasin lambar da yake tunani sai yaƙi ɗagawa ya aje lambar a gefe, kiran ya ƙara shigowa bayan katsewar na farko, cikin ransa yana tunanin me zai sa wannan me kiran ya kirawosa at this time. kamar ya sha re sai kuma ɗayan ɓarin zuciyarsa yace ya ɗaga, yana ɗagawa kuma daga ɓangaren Dr Yusuf yace da shi. "idan ba damuwa kuzo asibiti da gaggawa ga yarinyarku an kawo mana ita emergency, accident ɗin ma har yafi na da muni, jinin da ta ke buqata this time around yana da yawa, so please cikin gaggawa muna buƙatar kuzo". ai babu wani batun ƙarashen jin abinda Dr Yusuf ke faɗa ya wurgar da wayar akan kujerar me zaman banza, ya duba jikin motar yaga da key ajiki dan haka ƙofa kawai ya janyo ya rufe yaja motar a 360 yana jin kamar ya ɗauki motar ya dire a cikin asibitin. *Vote, share and comments.* [8/31, 00:51] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *36* Allah kaɗai ya kaisa lafiya zuwa Asibitin Miyetti saboda irin mahaukacin gudun da yake yi, yana isa asibitin direct office ɗin Dr Yusuf ya faɗa, yanda yake a matuƙar rikice haka shima Dr Yusuf ɗin yake. yana ta aikin sauke numfashin yake kallon Dr Yusuf idonsa tamkar zai faɗo yace,"tana ina Dr?, a wanne hali ta-ke ciki?". Dr Yusuf yaja dogon numfashi ya sauke, ya rufe idonsa for a while sannan ya buɗe ya sauke su akan Turaki yace,"an shiga da ita situation room, and she is in critical condition, wanda yake da kamar wuya...". "da kamar wuya me?". Turaki ya faɗa cikin ɗaga murya a sanda Dr Yusuf yay shiru da maganar da yake, ya zagayo ta gabansa a firgice yana daɗa cewa,"kaci gaba da min bayani Dr, da kamar wuya me?". Dr Yusuf ya kalli gefe guda tsananin damuwarsa da tashin hankalinsa na ƙara bayyanuwa yace,"da kamar wuya ta rayu". Turaki get in to a state of shocked, looking at Dr Yusuf with anxiety, like he did'nt understand what he said, ya buɗe baki zai yi magana Dr Yusuf ya dafa kafaɗarsa yace,"abinda yake nan shi nake sanar maka, bance ba zata rayu ba, but da kamar wuya tayi rai". cikin wani bala'in tashin hankalin da yafi na ɓarawon da aka kama Turaki ya damƙe hannun Dr, sai kuma a hankali kuma cikin mutuwar jiki yace,"Dan Allah Dr ta rayu, na roƙe ka dan Allah, ko menene kayi dan ta rayu ni kuma nayi maka alƙawarin duk abinda ka biɗa daga gare ni muddin bai fi ƙarfina ba zan baka, amma dan darajan Allah karka bari ta mutu". yanda yayi maganar dole yay mugu mugun baka tausayi. Dr Yusuf yace,"Allah ne kaɗai me rayawa da kashewa, zamu yi iya kar bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun ceto ranta, saboda gaskiya akwai matsala babba ma kuwa". Jikin Turaki ya ƙara mutuwa, yaji zuciyarsa na wani irin motsawa yana jin kamar ya mutu ya huta. yace,"wacce matsalace da har zata fi ƙarfin ku Dr?". Dr Yusuf yace,"a binciken da muka yi akwai abinda ya gigitata ya kuma ɗimautata da har yaja a lokaci ɗaya zuciyarta ta taɓu, kuma ta kai ga matakin ƙarshe na stage d, yana zama da wuya akai wannan matakin kaga an rayu sai dai kuma wani iko na ubangiji. yanzu fatan da zamu yi guda ɗaya shine in har Allah yasa ta farka to karta farka da tunanin wannan abin da ya girgizata ya haddasa taɓa zuciyarta a lokaci ɗaya, idan har hakan kuma ta kasance to tabbas farkarkawarta bugawar zuciyarta gaba ɗaya, daga nan kuma shikenan tata ta ƙare". ƙwayar idon Turaki ta kaɗai, yaja da baya ya tafi yana neman madafa saboda jinsa da yake yana neman yanke jiki ya faɗi, yay saurin dafe bango yana kifa kansa ajikin bangon yana jin jikinsa gaba ɗaya ya ɗau shaking. bai san me yake ji ba, bai san ta yanda zai kwantata yanda yake ji ba, haka bai san halin da yake ƙoƙarin shiga ba. Dr Yusuf yayo tattaki yazo kusa da shi ya tsaya tare da dafa kafaɗarsa yace,"yanzu taimako guda ɗaya ta-ke da buƙata a wurin mu shine jini...". tun bai ƙarasa bayaninsa ba Turaki ya damƙi hannunsa suka nufi hanyar fita, cikin gaggawa suka fito a tare suka nufa situation room ɗin da Fillo ta-ke. tana kwance kamar gawa, kallo ɗaya Turaki yayi mata ya kasa dauriyar riƙe hawayen dake cikin idonsa, kawai ya sake su suka sauko, kamar ba namiji ba, kamar ba jarumi ba, hawaye yake sosai kuma masu zafin gaske waɗanda yake jin zafinsu tamkar zasu ƙona fatarsa, gwargwadon irin zafin da yake ji a zuciyarsa wadda shima yake jin tana gab da taɓuwa. yasa hannu kamar ƙaramin yaro ya shiga goge hawayen sannan ya kwanta akan gadon da Dr Yusuf ya nuna masa, muryarsa ta fito da wani amon sauti da ba nasa ba yace,"in har da buƙata a kwashe duka jinina a saka mata". Dr Yusuf yay guntun murmushi ganin kamar Turaki ya zauce, yaji tausayinsa matuƙa kamar yanda shima yake tausayin kansa. kuma nan da nan akayi connecting jinin Turaki zuwa jikin Fillo. tun jonawar ya juyar da fuskarsa zuwa kan gadon da ta-ke, lokacin an samu gogge jinin duk da ya ɓata mata jiki, kallonta yake tayi yana mai matuƙar tausayinta a cikin ransa, yana kuma lissafin cewar da zarar ta farka komai na wahalarta yazo ƙarshe, zai zamar mata bango kuma jigo na madafarta. har tsawon awannin da jinin ya ɗauka yana fita daga jikinsa ya shiga jikinta bai ɗauke idonsa akanta ba. da ƙyar kuma ya yarda ya fito daga situation room ɗin yabi bayan nurse ɗin da tazo tai disconnecting abin shigar jinin daga jikinsa. yabi bayanta zuwa office din Dr Yusuf, ya same shi zaune akan kujerarsa ya riƙe kansa da duka hannu biyu, wanda kallo ɗaya zaka yi masa kasan cewar yana cikin matsananciyar damuwa. Turaki ya ƙaraso ciki jiki a saɓule jiri na ɗibarsa, ya nemi waje ya zauna sannan ya ɗauki maltina ɗin da nurse ta ajiye masa akan table ya fasa ya shanye. ya ɗora idonsa akan Dr Yusuf yana me cike da taraddin jin abinda zai fito daga bakinsa. Dr Yusuf ya furzar da iska daga bakinsa sannan yace,"zamu jira nan da 30mints muga abinda Allah zai yi". "insha'Allahu ma lafiya zata tashi". daga nan kowannensu sai ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran lambar da ya nema a contact list, daga ɓangaren Dr Yusuf matarsa Nuratu ta ɗaga kiran tana sallama acikin muryar bacci. ya kalla agogon hannunsa yaga ƙarfe biyu da rabi na dare a lokacin, a sanyaye yace da ita,"Farha har tayi bacci ne?". tace,"ban sa ni ba wallahi, na barta tare da Mommi na shigo ɗaki saboda kaina da ke ciwo, your Excellency ni dai gobe zuwa zanyi na nemo mata maganin kuka gaskiya". yay guntun murmushi yace,"ba wani magani da za'a bata, kowanne jariri ai yana kuka dama". Nuratu na noticing yanayin voice ɗin nasa tace,"ehh amma nata kukan yayi yawa". sannan ta daɗa cewa,"your excellency lafiya kuwa naji muryanka so sad?". yace,"lafiya lau". ba don ta yarda da cewarsa ba tace,"as early morning zaka dawo ko?". yace,"ehhh may be". tace,"Inna Wuro ma fa ta dawo, daga saukarta ta biyo ta nan wai anan zata kwana can gidan aljanu sun shiga, sai surutai ta-ke wai Aliyu ya kaɗe aljanu sun tafi da shi zasu ɗauki fansa, fatan ta Allah yasa kar su kashe shi tunda ya kashe ƴar sarkin aljanu, da gaske ne yay accident ɗin?". yace,"Allah ya gyara Inna Wuro, yanzu kina jina?, zan aiko driver ya ɗauke ku, sai ku shirya ku taho tare da Mommi". tace,"ni dama from your voice na gane babu lafiya, meke faruwa Dr?, kar dai da gaske Inna Wuro ta ke yi". jin duk tabi ta rikice yace,"relax, yarinyar bata mutu ba ai. akan maganar da nayi miki kwanaki ne". tace,"wai Dr nah kana ganin hakanne kuwa?". yace,"i pray so hakan ta faru, na gwada jinin yarinyar ɗaya yake da na Mommi, Swty sai dai kinzo xaki ga abinda nake faɗa miki, dan Allah kuyi da sauri ina so ku ƙaraso before yarinyar ta farka. kuma karku taho da Inna Wuro tazo ta ishi patients da zance, ki bar mata Farha itama kar taita kuka". daga haka ya katse wayar yana kallon Turaki dake yiwa Maama bayani. "ban san ya akai ba Maama, asibiti sun kira ni kawai, yanzu haka har an sanya mata jini likitan kuma yace zata farka nan da 30minutes". daga ɓangaren Hajiya Madina tayi magana sannan ya ƙara cewa,"ehh naga Dsp nata kirana amma ban ɗaga ba". tace,"tom gamu nan Me Babban suna, plss take care". yace,"Maama kizo da sauri dan Allah". ya kashe wayar ya saka a aljihu tare da miƙewa ya fita daga office ɗin ba tare da yace da Dr Yusuf komai ba. Fitar tasa babu jimawa Dr Yusuf ma ya biyo bayansa. inda ya same shi tsaye a bakin ƙofar room ɗin da Fillo ke ciki yana leƙenta ta cikin wani glass. daidai da ƙarasowar Daddy da Ammi wajen, Yusuf ya isa wajensu yana kallon Aliyu da ce masa,"Malami ka kwantar da hankalinka, kayi adu'a kawai Allah yasa ta farka". Aliyu ya sauke numfashi yana komawa da baya ya zauna kan kujera. Yusuf yace da su Daddy,"na fito ai tun ɗazu ban ganku ba". Ammi tace,"gida muka koma, da dukkan alama mutanen acikin tashin hankali suke, dan sai bayan zuwanmu da muka shigo cikin haske naga alamar hakan a tare da mahaifiyar yarinyar, ashe ko ɗankwali ma babu a jikinta, haka ma sarƙa ce ɗaure da hannunta. shine naga babu dacewar mu tsaya da ita a haka tunda mutane kowa na wucewa, dalilin da yasa muka koma gida kenan". Yusuf yace,"Ammi wannan matar fa ba mahaifiyar yarinyar bace, ni har na fara ɗaukar maganar Inna Wuro fa, saboda ita wannan yarinyar ta taɓa kwanciya a asibitin nan, tana da matsalar aljanu da suke yawan ɗaukarta su kaita wani wajen, shi yasa nafi tunanin nima ko aljanar tata ce ta fito a siffar mutane". Daddy yace,"a'a wannan matar mutum ce, kun riga kun san baiwar da Allah yay min, da naga aljani na san shine. ta bakin nata dai tace wasu mutanene suka sace su shine suka samu suka gudu". Yusuf ya sauke nunfashi yace,"ofcourse an kidnapping yarinyar in ban manta ba 1month kenan". Ammi ta nemi wuri kusa da Aliyu ta zauna, bayan ta dube shi da tausayawa ta kalli Yusuf tace,"ya jikin yarinyar?". yace"da sauƙi, nan da mintuna kaɗan ma zata farka". Daddy yace,"mun biya ta station sun kwance sarƙar hannun matar, da ƙyar suka yarda da mu akan hakan dan tunanin su ma wai ko me laifi ce ta gudu, to amma duk da haka sun haɗo mu da police ɗaya sannan sun shigar da report wai should incase. yanzu please kasa nurse ko kuma kai da kanka kayi ƙoƙarin mata treating hannunta, tsintsiyar hannun duk ya farfashe yay caɓa-caɓa da jini wallahi, abin tausayi". ya juya yana kallon Ammi yace,"tana ina?". tace,"gata can wajen corrido ɗin can tana sallah, naga hankalinta duk yaƙi kwanciya, ni tausayi ma ta-ke ban wallahi". Dr Yusuf ya kira wata nurse, yayi mata nuni da inda Mum ke zauna yace ta ɗau kayan aiki taje wajenta. ba ɓata lokaci Nurse ɗin kuwa tai treatment duk inda wani ciwo yake ajikin Mum, dauriya irin ta babba shi kaɗai ya hanata yin kuka, dan sosai take jin zafi da raɗaɗi, har aka gama ƙwayar idonta na kallon gefe ɗaya, sai bayan an gama tukunna ta ɗago tana kallon duka hannayen da aka ɗaure wajen bandage kaɗan ba mai yawa ba. a lokacin Turaki ya bar jikin ƙofar ya shiga kaiwa da komowa a wajen hannayensa sarƙe a bayansa, idonsa ya kai bayan Mum da har yanzu ke zaune bata tashi daga wurin da tayi sallah ba, adu'a kawai take akan Allah ya tashi kafaɗun Fillo, har ga Allah tana so ta nemi ahalinta a wannan lokacin to amma ba zata iya ba har sai Fillo ta farka, yarinyar ta taimaka mata a lokacin da take neman taimako. duk da bayanta yake kallo haka yayi tsaye sai kallonta yake ya kasa ko da motsi, ya kuma kasa ɗauke idonsa akanta, yana jin wani irin abu na shigarsa, yana jin kamar yana so yaga ko wace, gaba ɗaya bai san dai taƙamemen abinda yake ji a tare da shi ba. yay ajiyar zuciya ya juya ya koma bakin ƙofar, yaci gaba da kallon Fillo yana ta adu'a cikin ransa, bini-bini sai ya kalli agogo ya duba time, cikar lokacin da likita ya ɗiba kawai yake jira, da dukkan fatansa na in lokaci ya cika ta farka lafiya lau. sai dai haka ɗaya kuma yaji totally ya kasa samun nutsuwa, zuciyarsa na masa wani irin zillo, tunaninsa da hankalinsa ya rabu waje biyu, so yake yaci gaba da tsayuwa anan har sanda Fillo zata farka, haka kuma so yake ya bar wajen yaje wajen waccan matar da bai san wacece ba. ba tare da sani ba ya bar wajen ya nufa wurin da Mum ke zaune har yanzu, ya tsuguna ta gefenta daga ɗan bayanta, ba tare da sanin taƙaimemen abinda zai yi ba, idan ma magana zai mata shi bai san me zaice mata ba, zuciyarsa ce kawai ta kawo shi. ya buɗe bakinsa zai furta abinda bai san zai ce ba sai ga Ammi ta ƙaraso wajen, bai iya ce mata komai ba ya bita da kallo har ta zagaya ta gaban Mum ta tsuguna agabanta. Ammi tace,"kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki Hajiya, Ɗana ya tabbatar min da cewar ƴarki zata farka cikin amincewar ubangiji, kuma zata farka lafiya lau insha'Allah". a sannan Mum ta ɗago da kanta tace,"Allah ya amsa, amma Hajiya lokaci yaja da yawa, har yanzu fa shiru". tai maganar muryarta ɗauke da sautin damuwa. Ammi ta ƙara cewa,"adu'a zamu ci gaba da yi". Mum bata iya magana ba illa gyaɗa kanta kawai da tayi. bata san me take ji a tare da ita ba, amma dai tana jin zuciyarta na ƙara matsuwa da zullumin son kasancewa acikin ahalinta, ba abinda idanuwanta ke da muradi yanzu sama da su ga Babanta, taga ƴaƴanta tukunna ta sami kwanciyar hankali. Umma ta ƙaraso wajen, Ammi ta ɗauke kanta daga kallonta, Umma bata kula hakan ba tace,"Ammin Yara wannan itace mahaifiyar yarinyar da Aliyu ya buge ɗin?". Ammi ta kauda fuska gefe tace,"umm ita ce". ta faɗa tana miƙewa ta bar wajen, Umma ta zagaya ta ɗaya ɓarin ta zauna kusa da Mum, suka gaisa tana yi mata adua da sanar mata cewar itama mahaifiya ce wurin yaron da ya bigesu ɗin. Mum tace,"Allah sarki, mun gode sosai. kun tsaya mana baku bari mun wahala ba". Umma tace,"to ai hakan ya zama dole akan wanda yasan hakkin bawa". ta faɗa idonta na kan Turaki da har sannan yake tsugune daga can gefe, kamar wani mutum mutumi sai bin kowa yake da ido, shi abinda ya ɗaure masa kai tun zuwan Ammi wajen yaji tana batun mahaifiyar Fillo, shi yasa yaji kamar ƙafafunsa ma ba zasu iya ɗagawa ba dan haka kawai yaji jikinsa duk yay sanyi, kuma Allah Allah yake yaga fuskar matar. ganin tsananin kamar dake tsakanin Turaki da Mum wanda Ammi bata lura da hakan ba yasa Umma ce masa,"sannu fa, ya mai jiki?". Turaki yaji kamar ba da shi take ba, lura da hakan yasa Umma cewa,"da kai nake". ta faɗa tana murmushi. yana sauke idonsa a ƙasa yace,"Alhamdulillah". tace,"to Allah ya bada lafiya, dan Allah ina daɗa bayar da haƙuri a madadin yarona". shi dai bai iya cewa komai ba, ya zama kamar wani soko ko me neman gafara. kuma Umman na yin shiru ta hango Nuratu da Mommi na nufo su, har da Inna Wuro dake goye da Farha. itace a gaba ta taho tana cewa da Umma,"Falmata ni dai Amadu ya rantse yace min ba aljanu ba ne mutanene shisa ma na iya shigowa asibitin nan amma da a waje zan tsaya gaskiya, dan ban iya saka kaina a masifa, Aliyun ma ni da wurin ƴan sanda aka kaishi tunda ance har yanzu yarinyar bata farka ba, ko kawai ayi kotu da ɗan banza kowa kuma sai yay ta kansa kar aja kuɗin Amadu ya ƙare". Umma ta miƙe tana cewa,"sannu da zuwa Inna". tana rufe baki Nuratu da Mommi suka iso wajen, dai-dai kuma da miƙewar Turaki. yana tashi idonsa ya kai kan Mommi, ta ke idanuwansa suka firfito waje yana binta da kallo me ban mamaki da al'ajabi, me yake gani?, dama da gaske akwai fuska biyu a duniya?, wannan matar ai photocopy ɗin Fillo ce. Mommi da ta iso gabansa ta ɗaga masa hannu alamar sannu. mamaki na bala'i ya ƙara kama shi, bai san lokacin da ya kamo hannunta ba ya jata zuwa room ɗin da Fillo ke ciki. ganin hakan yasa kowa miƙewa yabi bayansu da kallo harta kuwa da Mum da taji su Umma na cewa,"ikon Allah wannan yaron na da lafiya kuwa". Nuratu tace,"ah wannan sai dai mahaukaci". ta faɗa tana bin bayansu da sauri. Inna Wuro tace,"ah tou haka duk zaku yi ta gamuwa da gamonku, ance aljanu ku ka kwaso kun dage mutanene, ni dai da naga ba zan iya ba ai ta kaina zanyi, wa zai zo ya wahala, haka kawai a shanyen ƙafa ko wuya banji ba ban gani ba". Umma ta dafa kafaɗar Mum dake bin bayan Nuratu da kallo tana jin shigar wani al'amari me girma a tare da ita. a hankali Umma tace,"am sorry to say, amma ɗanki bai da lafiyar ƙwaƙwalwa ko?". Mum ta juyo da kallonta gareta tace,"ɗana kuma?". ta tambaya da mamaki. Umma tace,"ehh fa, wanda ke zaune anan kusa da ke". kan Mum ya ƙara ƙullewa tace,"me kike son cewa ne?". ta tambaya tana jin ƙirjinta na bugawa. jin ƙarar saukar mari ya tattara hankalinsu kan su Turaki gaba ɗaya, Nuratu ce a gabansa tana huci tana faɗin,"baka da hankali ne?, ya daga ganin mahaifiyata zaka kama hannunta, ko an faɗa maka mu kafirai ne kamarka?, shashashan banza da wofi, to wallahi in baka bar asibitin nan cikin gaggawa ba sai nasa ƴan sanda sun zo sun tafi da kai yanzu". Turaki ya ɗago da fuskarsa yana dafe da kuncinsa, hoton fuskar tasa ya shiga cikin ƙwayar idon Hajiya Ramla da suka ƙaraso wajen da sassarfa. cikin zafin nama Turaki ya ɗaga hannu zai saukewa Nuratu zazzafan mari Hajiya Ramla ta zaro ido waje tana faɗin,"Babana". ta faɗa da ƙarfin sautin da yay amsa kuwa a wajen. Turaki yaji saukar muryar a cikin kunnensa, yaji shigar sunan acikin kansa da cikin zuciyarsa, daga jin muryar kasan muryar babbar macece, amma hakan ba shi zai hana shi gane mamallakiyar muryar ba, ba shi zai hana shi gane muryar kowa ce ba a duk inda ya jita, tsawon shekaru da yawa ba tare da suna tare ba, hakan ba zai hana shi gane muryar wadda ta kawo shi duniya ba, da wayonsa ta tafi dan haka a ko'ina kuma a kowanne hali yaji voice enta zai shaida. sai dai kafin komai dake cikin kansa ya gama wanzuwa sai ganin Hajiya Ramla yay a gabansa, ganin nata kuma ya firgita shi sau ɗaya yaja da baya, sai kuma ya dakata yana binta da kallo ƙwayar idonsa duk a waje. an ɗauki tsayin shekaru da yawa, sai dai duk tsayin shekaru da dogon zamanin da zata ɗauka ba tare da ƴaƴanta ba, hakan ba zai hana tana kallonsu ta shaidacewar su ɗin jininta ba ne, kamar yanda shima ba zai taɓa manta mahaifiyarsa ba, babu tantama wannan ɗanta ne, haka shima yake jin babu tantama wannan wadda ta kawosa duniya ce, ɗanta ne wanda ta tafi ta barsa a lokacin da yake shakaru shida a duniya, kamar yanda shima yake ganin uwassa wacce ta tafi ta barsa lokacin da yake da shekaru shida a duniya. sai kawai ta fashe da kuka, Turaki ma da yay mutuwar tsaye ya fashe da kukan farin ciki, ya taho da sauri ya rungumeta yana faɗin,"Mum, Mum are you really the one?, da gaske idona ba gizo suke yi min ba?, Mum ina kika tafi?, ina kika je Mum?, me yasa kika tafi kika barmu?, laifin me muka yi miki Mum?". maganarsa ta katse, kukan tsananin murna da farin cikinsa ya ƙaru. ya janye daga jikinta yana daɗa kallonta, daga shi har ita babu wanda zai iya kwatanta irin abinda yake ji a tare da shi. kallonta yake sosai da irin wannan tsananin so da tausayin da Allah ya halicce shi na daban a tsakanin uwa da ɗanta. Hajiya Ramla na hawaye ta kai hannunta ta kama fuskarsa, ɗayan kuma ta dungure masa kai fuskarta ɗauke da tarin murmushi, tace,"babu Alhamdulillah sai wannan tarin tambayoyin Babana". bai iya cewa komai ba, haƙoransa duka suka bayyana a waje kamar yanda nata ma suka bayyana, ya kuma rumgumeta sannan yace,"to Mum na faɗa Alhamdulillah...then you too should answer my questions". Hajiya Ramla ta ture shi daga jikinta tana cewa,"to ba zan amsa ba ɗin, in kuma ka zama Me girma Turakin Taraba sai in ji". ta faɗa da irin salo na wasa dake tsakanin uwa da ɗanta. ta kamo hannunsa tace,"where is Zaytun?". ya kasa ce mata komai, kawai sai ya ƙara rungumota yace,"to Mum aina kika ɓuya?, there are alot of questions but ki fara amsa min wannan". tace,"Babana muna gaban mutanene fa". ya zare jikinsa anata ya kama hannunta yaja ta zuwa wajen kujeru dake wajen ya zaunar da ita. shi kuma ya zube gwiwoyinsa a ƙasa tare da kwantar da kansa saman cinyarta yana kamo hannunta duk biyun ya riƙe su da kyau kamar wanda za'a ƙwaceta. daga ita har shi babu wanda ya iya cewa komai, hannunta a sumar kansa tana shafawa, shi murmushi ita murmushi, haƙoranta a waje nasa ma a waje. jinsa yake kamar ya buɗe cikinta ya koma ciki, haka itama ji take kamar ta tsaga ƙirjinta ta sanya shi a ciki, kowanne da maganar da yake son yi amma tsananin farin ciki da murnar da suke ciki ya ha rufe bakinsu. idon kowa dai tuni ya dawo kansu, aka bar batun Fillo da halin da take ciki, basu san tuni ta farka a lokacin su Dr Yusuf su kai kanta, kuma lokacin da zai shiga ɗin ne ya kama hannun Mommi ba tare da sanin kowa ba da hankalisu yay can kan su Turaki ba ya shiga da ita ciki ya tsayar da ita dai-dai saitin da idanuwan Fillo na buɗewa zasu sauka akanta. Hajiya Ramla tace,"Babana am asking you where is Zaytun?". ya ɗago da kansa ya kalleta kawai sai ya ƙara rungumeta. a lokacinne kuma wayarsa dake aljihu tayi ƙara, yace,"Mum ɗauko ki min picking ba zan iya sakinki ba". ta zaro wayar daga aljihunsa tana bin sunan dake yawo a jiki, kamin tace masa,"Beta Half". yace,"pick". tace,"my daughter inlaw right?". sai ya saketa ya karɓi wayan yana wani murmushin na daban, ya shafo kumatunta yace,"you will soon meet her". ya faɗa yana miƙewa tsaye still holding her hand ya juya yana kallon kowa dake kallonsu, idonsa ya sauka akan Inna Wuro da ta saki baki tana kallon film ɗin da zuciyarta ke raya mata shi take kallo. ya saki hannun Mum ya isa wurin da take, bakinsa gaba ɗaya yaƙi rufuwa, yana zuwa da sigar tsokana yace,"tsohuwa aron ɗan kwalin kanki". da sauri kuwa Inna Wuro ta kunto Farha da ke bayanta ta jefa masa zanin goyon tace,"komai ma ai sai a baku girmaku ne". ya karɓa ya juya bayan yace mata,"Thanku, zan baki tukwici after". ya isa wajen ya rufe fuskar Hajiya Ramla da zanin sannan ya zauna kusa da ita yace,"stay quite har inje in dawo kinji". tai masa knodding kanta kawai tana binsa da kallo da jin soyayyar nan ta ɗa na fizgarta. ya miƙe kenan sai ga Hajiya Madina ta iso wajen hankali a tashe, tana ganinsa ta yo kansa a rikice, za tai magana expression ɗin da take gani a fuskarsa yasa ta tsaya tana ƙare masa kallo. kafin ta ɗauke idonta daga kansa da mamaki tabi mutanen wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya, sannan ta ƙara kallonsa tace,"mene haka a fuskarka?, Fillon ta farka lafiya ne?". ya kamo hannunta yace,"insha'Allahu lafiya zata farka, yanzu just close your eyes i want to show you something". tace,"in rufe idona?, ka nuna min me?". ya zagaya ta bayanta yace,"suprise". sannan ya ɗora haɓarsa kan kafaɗarta yana fuskantar da ita wurin da Mum ke zaune yace,"gidan da kika gina a Ausburg nake so a matsayin tikwici". tace,"na ma baka Me Babban suna, amma ni dai barni in buɗe idona inga halin da yarinyar mutane ke ciki, ni ce silar condition ɗin da take ciki, so this is not time for joke, kaima ɗin mamakinka nake". ya saketa yana faɗin,"indai kika buɗe ban ce ba isn't a suprise, kuma sai na doka miki yaji". Hajiya Madina tai shiru ƙirjinta sai duka yake, Turaki ya ƙarasa wurin Hajiya Ramla ya ɗauke zanin daga saman fuskarta, sannan ya ɗora hannunsa a kafaɗarta ya kwantar da gefen fuskarsa a gefentata, Hajiya Ramla tabi Hajiya Madina da kallo tana jin wani irin shauƙi na kewar ahalinta da tayi, tana tuna irin rayuwar zaman lafiya, jin daɗi da kwanciyar hankalin da sukai da Madina. Hajiya Madina na yin kalar tausayi har sannan idonta a rufe tace,"Me babban suna kai ka taɓa saɓa umarnina, amma ni ba zan iya saɓa naka ba, but ai na san kana jin tausayina ko?, to mu jingine wasa gefe kaji ɗan albarka". muryarsa na fita da wani emotions yace,"gidan da ke Ausburg Maama". Tace,"naji nace maka, muna komawa gida zan baka takardun". yay murmushi me kama da dariya ganin duk yanda ta ƙosa yace,"promise?". Tace,"i do, har ma da key ɗin sabbin motocina guda biyu duk na baka". yace,"zanyi kyauta ne da su nima". tace,"tunda na riga na mallaka maka ikonka ne kai duk yanda kaso da su, can i open my eyes now?". yana dariyar jin daɗi ƙasa-ƙasa yace,"not now, untill i say". kawai sai yaga ta buɗe idon, Hajiya Madina ta buɗe idon da niyyar kai masa duka ganin yau yana neman mayar da ita wata yarinyarsa abinda basu taɓa yi ba, ƙwayar idonta ta sauka akansa sai kuma ta mayar da kallonta kan fuskar da take ganin kamar gizau a kusa da shi. in ace da abinda yafi mamaki tabbas ta shiga cikinsa, ta ƙara buɗe ido tana kallon Hajiya Ramla dake ta mata murmushi, ta ƙwala wata ƙara tace,"Your Excellency are you really the one?". ta faɗa bakinta na ƙin rufuwa tana ganin hakan kamar a mafarki. sai kawai tai sufa taje ta rungume Hajiya Ramla tana faɗin,"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah". ta faɗa tana ɗagowa daga jikinta ta shiga duddubuta wai ganin dai kamar ba dai-dai take gani ba. a lokacin ne kuma su Zaytuna suka ƙaraso wajen, abinda kowa ya gani yasa suka tsatstsaya da mamaki suna kallon Maama da tabi ta susuce saboda tsabagen murna. Maama ta waigo ta kalle su tace,"ubangiji yaji kukanmu ya amsa adu'armu ya dawo mana da Mum". ai kan kace me wannan asibiti ya karaɗe da ihun murna, duk suka tafi da gudu suka faɗa kan Hajiya Ramla suna ta ihu, wanda in ace a tsaye ta-ke sai sun kaita ƙasa. Zaytuna ce kawai ta tsaya taƙi zuwa wajen tana kaudar da fuskarta da gefe, dan ita bata ganin zata yi farinciki kamar yanda bata tunanin zata yafewa Mum. Ilham kuwa na tsaye daga gefen su tana ta kallon su cike da burgewa, musamman Turaki da ta kasa ɗauke idonta a kansa saboda yacca ta-ke ganin haƙoransa gaba ɗaya a waje, da irin tarin farin ciki da annurin da bata taɓa ganinsa ba aciki. a ɗazu hankalinta duk a tashe yake da bai dawo gida ba, haka da taji wurin kidnappers ya tafi hankalinta ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi, but a yanzu zata iya cewa kamar tana jin kanta ne a saman gajimare tana tafiya, ko ba komai tasan lokaci yayi da zata samu wannan gurbin da Turaki ke cewa ba zata same shi ba a zuciyarta, ta sani wuyarta mahaifiyarsa ta san ita matarsa ce, ita kanta bata san Mum ba dan ba'a haifeta ba lokacin, amma kallo ɗaya ta yiwa Mum ɗin tasan itace mahaifiyarsu da kowa ya taso a family yake jin labarin ɓatanta. a taƙaice dai Maama da iyalanta duk sai suka manta da batun wata Fillo saboda tsabagen farin cikin da suke a ciki. kuma haka suka zama ababen kallo a wajen dan tuni akai caa akansu ana kallon ikon Allah. gaba ɗaya sun cikwikwiye Hajiya Ramla sun kasa jin ma abinda ta-ke cewa na,"ina da patient kuyi a hankali". but inaa duk wannan batu da take yi babu wanda ya jita hatta Turaki dake manne a jikinta. kuma a lokacinne Kaka suka shigo ita da su Yami da Khalil waɗanda yaje ya ɗauko daga asibiti, sai dai me?, zuwan su wajen kawai suka ga Fillo a guje ta fito tana ƙwala kiran,"Kaka ga Ummina, Kaka Ummina ta dawo". *Vote, Comment, and Share.* [8/31, 01:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* _😂😂yau dai ina typing ina gyangyaɗi, so duk baragadar da ku ka ci karo da ita ku gyara da kanku kawai🤣🤣._ *37* gaba ɗaya Fillo sai ta rikice ta firgice ta nemi fita a hayyacinta, ba don komai ba sai dan tsananin murna da kuma mamakin ganin mahaifiyarta a lokacin da bata tsammata ba, tsabar farin ciki ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. ganin komai ta ke yi tamkar mafarki ko kuma ba daidai take gani ba, lokacin da ta farka da matsanancin ciwon kai ta tashi, amma buɗe idon da zata yi ƙwayar idanunta suka sauka akan Ummi dake zaune a gefenta ta kama hannunta ta riƙe tana hawaye. da farko tai zaton gizau idonta yay mata, dan haka tai saurin maida murfin idonta ta rufe sannan ta ƙara buɗewa, kuma a wannan buɗewar ne ta tabbatar da abinda ta gani ɗin gaskiya ne, Umminta ce a gabanta, wannan macen da tafi gwal, tafi zinare, tafi lu'u lu'u girma da daraja, wannan macen ce da bata da tamkarta a duniyarta, tauraruwar da ke haska duniyarta, mahaifiyarta ce mafi soyuwa a ranta, jarumar da tai fama da rainon cikinta tsawon watanni tara, jarumar macen da ta tsaya tsayin daka akan ibadarta da iliminta da kuma tarbiyarta, jarumar macen da ke sadaukar da farincikinta domin ƴaƴanta, jarumar dake ɓoye zafin ciwon rashin lafiyarta gudun tashin hankalin ƴaƴanta, jarumar uwar da ta kan iya haƙura da loma ɗaya na abinci da zata sa a bakinta ta rabarwa ƴaƴanta, tabbas itace, ba zata mantata ba ko da ace tana cikin ciwon hauka ne, har a naɗe duniya ba zata kasa gane ɗumin jikinta ba, ba zata manta wannan farar fuskar da bata iya bacci ba har sai ita tayi, abu ɗaya da ta san yake dahir shine uwa dabance, daban take da kowacce irin halitta a duniya, soyayyarta dabance da ta kowa, ƙaunarta ma haka, mahaifiyarta itace ranta itace jininta itace duniyarta. hawaye ta dinƙa ji yana bi ta gefen fuskarta, dama tasha faɗawa Kaka cewar Ummi bata mutu ba tana raye, kuma da izinin Allah zamu gana da ita, sai ga shi yau ta ganta, sai ga shi ta ganta a ranar da wani macuci, azzalumi ya dasa baƙin ciki a zuciyarta wanda ba zai taɓa gogewa ba, to mai ma zai ci gaba da zamar da wannan baƙin cikin alhalin ga mahaifiyarta ta dawo a sanda take tunanin babu me iya share mata hawayen baƙin cikin da Amir ya haifar mata?, ai babu wani sauran baƙin cikinsa kuma, ta san in ace bata sami ganin mahaifiyarta ayau ba, to tabbas baƙin cikin abinda Amir yayi mata shi zai zama ajalinta. zata iya cewa bata san lokacin da ta yunƙura ta miƙe zaune ba daga kwancen da take, jinta tayi kawai ajikin Ummi tayi mata wata tsatstsaurar runguma, Ummin ma ta kewayeta da dukkan hannayenta tana daɗa matseta a jikinta, Fillo taji saukar wannan ɗumin na daban wanda ajikin uwa kawai aka halicci yana ɗumama jikinta, tana jin wannan soyayyar mahaifiya ta daban tana ratsa jini da sassan jikinta, sai kawai suka fashe da kukan farin ciki a tare, babu wanda ya lallashi wani acikinsu har sai da suka yi me isar su tukunna. cikin muryar kuka tace,"Ummina ina sonki sosai". kuma abinda taji Ummin ta fara ce mata shine,"Auta wa ya kawoki nan garin?, me ya sa me ki haka?". ta tambayeta ɗin tana janyeta daga jikinta tana dubanta, tana yi mata kallo me cike da tausayi da kuma fargabar abinda bata fatan ya kasance a rayuwar ƴarta, domin tasan rashin uwa a tare da ƴaƴanta babu halin da baya jefa su, balle kuma su da basu yi sa'ar uba ba, wanda ko kallonsu ba yayi balle ya kula da rayuwarsu. a lokacin sai kawai ta faɗa ƙirjin Ummi tace,"Ummi kullum sai nayi kukan rashinki, Ummi ko me nake yi tare dake nake yinsa a zuciyata, Ummi duk sanda naga ƴa da mahaifiyarta sai nayi ta kuka in kasa ko da cin abinci. Ummina me yasa kika tafi inda ba zamu ganki ba?, me yasa baki ci gaba da wannan haƙurin naki ba?, me yasa kika bari takaicin ɗa namiji da baƙin cikinsa yasa kika nesanta kanki da ƴaƴanki da kowa naki?, Ummi kin san kuwa tsananin son da nake miki?, muna fa yi miki so me zafi, Ummi kin san buƙatar rayuwar ƴaƴa shine mahaifiyarsu, amma mu sai kika ƙaurace mana na tsawon shekaru da yawa, Ummi ba kiyi tunanin in ta gayyara ba?, ba ki yi tunanin...". bata ƙarasa ba Ummi tasa hannu ta rufe mata baki, hawaye na zubar mata tace,"tambayar da nayi miki daban, zancen da kike min daban". Fillo ta ƙara matseta tace,"kiyi haƙuri Ummina". tace,"ban san amsar tambayata". Fillo ta rumtse ido tace,"ai tun sanda kika tafi na dawo wurin Kaka. wannan halin da kika ganni a ciki kuma wanda zan aura ne sila". lokaci ɗaya jikin Ummin ya hau kyarma ta ɗago Fillo ajikinta tana bin ta da kallo tace,"ya zamo silar me?, me yay miki?, ina Kakan?". tace,"garkuwa yayi dani Ummi after all na basa dukkan yarda". ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, muryar Ummin ta fita a hankali da cewar,"ina fatan bai cuce ki ba?". bata iya amsawa da baki ba sai Kai da ta ɗaga kawai. anan taji Ummin ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, kafin ta furta,"Allah ya daɗa kare min ke, ya kareki daga sharrin duk wani abin ƙi. dan Allah kiyi haƙuri ƴata da abinda nayi muku, ban da bakin ce muku komai domin nasan ni ɗin me laifi ce, amma yanzu na dawo gareku sai mutuwa ce zata raba mu, ina roƙonku dan Allah ku yafe min, ki yafe min Autata". Fillo tace,"ni ba kiyi min komai ba Ummina". sai ta ɗago kai tana kallon Ummin tace,"Ummi to ya akai...". kuma karantar fuskarta kawai Ummin tayi ta bata amsa ba tare da ta ƙarasa ba. "Dr Yusuf, shi ya shigo da ni nan yay min nuni da ke, shine sabon ɗan da Allah ya bani wanda ya kula da ni shi da matarsa kusan shekara guda, ba ƙyama, ba hantara, sun ɗaukeni kamar mahaifiyarsu, duk da ni nayi musu laifi na ɓoye musu cewar ina magana tsawon lokacin da muka ɗauka, haka nayi ta wahalar da su da aikin rubutu a takarɗa kuma basu taɓa ƙosawa ba". maimakon kallon Ummi sai Fillo ta koma kallon Dr Yusuf, babu ko ƙyafta ido, kenan shisa watarana da yazo hira wajenta yace mata yana ganin me kama da ita sak, in ace zata yarda da ya kaita ta ganta, tave masa ba wani nan wasa yake yi, ashe Umminta ce ma, Umminta ya taimakawa har yake kyautata mata da irin halin karamcinsa. _"sun ɗauke ni kamar mahaifiyarsu"._ haka Ummin ta faɗa, ƙwarai yau ta ƙara tabbatar da cewa Dr Yusuf na musamman ne, kuma ya zama dole ta saka masa da taimakon mahaifiyarta da yayi, kamar yanda ta san cewa yafi ƙarfin duk wani abu da zata basa, haka bata san irin kyautar da zata yi masa ba domin nuna masa godiyarta, but zata tambaye shi kyautar da yake so tayi masa ko da ace za'a kai ga matakin da sai ta ɗaga zoben azurfarta ta siyar. Dr Yusuf ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa tana sauke idonta ƙasa tace,"Ubangiji Allah yay maka sakayya da gidan aljannah akan taimakawa Mahaifiyata da kayi, Allah ya rabaka da iyaye lafiya"...haka ta dinƙa jera masa adu'a kafin tace masa,"dan Allah Dr a wurin da ku ka tsinto ni ba kuga wata mata ba?". Dr Yusuf yace,"ai ba tsinto ki mukai ba, kawo ki akayi". ta ɗan dube shi da mamaki tace,"bai gudu ba?". yay murmushi kafin yace,"ƙanina ne yanzu haka yana waje tare da su Daddy nah, itama matar da kike magana tana waje, ƙila zuwa yanzu ma su Kaka sun iso dan anyi musu waya tuni". ai rufe bakinsa kenan t a saki hannun Ummi ta diro akan gadon tana ce da Ummi,"ba inwa Kaka albishir". bata jira cewarta ba ta fito da gudu daga ɗakin tana ƙwala wannan kiran sunan na,"Kaka ga Ummina". ba tare da ta lura da jama'ar da suke cike a wajen ba balle tabi ta kan dalilin da yasa akayi wannan dandazon. kuma cikin sa'a tana fitowar tayi karo da su Kaka na shigowa, idonta a rufe ta doka wani uban tsalle ta ɗafe Kaka tana ihun murna tana faɗa mata Ummi ce. Kaka lamarin sai ya nemi ya bata tsoro dan sai take ganin kamar ko Fillo ta samu matsala ne, ta tafi zata faɗi dalilin ɗafe jikinta da Fillo tayi sai taji an saurin riƙota ta gefe. Kaka ta fashe da kuka tana cewa da Fillo,"Fillo ashe dama Amir ne ya ɗauke ki, ashe yaron nan ba mutumin arziƙi ba ne, ashe Amir azzalumin bawa ne, ashe duk wannan kyawun halayyar tasa yardararmu yayi saboda cimma wata manufa tasa, ashe baƙin *BIRI* ne shi ya *LULLUƁE* kansa ta yanda ba zamu shaida mugun ƙudurinsa ba, Allah ya isa tsakaninmu da shi, ko yafiyarmu kaɗai ta ragewa Amir shiga aljannah ba zan yafe masa ba, sai Allah yay mana hisabi da shi, kuma insha'Allah sai yaga sakayya, sai ubangiji ya bi mana hakkin cutarmu da yayi tun anan duniya. yanzu muna kan hanya Khalil ya ɗauko mu ance an kawoki asibiti rai hannun Allah muka ji sanarwar an kama waɗanda sukai garkuwa da ke, wallahi tallahi ban shaida muryar matsiyacin ba sai Yami ce ta shaida, sai kuma da naji an ambaci sunansa, yanzu haka ance gobe za'a kai su kotu Hajiya Madina tace sai yayi zaman gidan yari". sai ta fashe da kuka sosai tana ƙara cewa,"yasa na siyar duk da wani abu da ku ka mallaka a wajen mahaifiyarku, sai da ya tsiyatamu tass Fillo, biyar ɗin kanmu bamu da ita a yanzu, yasa muka ɗauki dukkan yarda da amana muka ba shi?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, gaba ɗaya tsoron kowa nake yi Fillo, ta ya yanzu zaka iya tantance fuskar mugun mutum da ta mutumin kirki bayan mugwayen na amfani da fuskar mutanen ƙwarai?, Allah ya tawarwatsa rayuwar mutane irinsa a duk inda suke, adu'ata ɗaya Allah yasa bai lalata miki rayuwa ba". Fillo ta zame daga jikinta, tasa hannu ta goge hawayenta tace,"bai ida mugun nufinsa ba Allah yaɓullo min da hanyar guduwa, Kaka bana son kukanki dan Allah ki daina, ki manta da zaluncin da Amir yay mana ki barsa da Allah, indai duniya ce ga shi gata nan, yau ba ranar kukan baƙin ciki ba ce ranar kukan farin ciki ne, irin wannan hawayen nawa nake so kiyi ba irin wanda nayi a sanda na san cewar Amir Birin da ya lulluɓe kansa da mayafin da ba mai iya ɓata shi bane. Ummi ta dawo Kaka, Allah ya bayyana mana ita, dan haka ki kalla gabas ki yiwa jalla wa'azza godiya". Kaka bata bar kukan ba tace,"ke wai kina hauka ne, a ina kika ga wata Ummi?". Ummi dake riƙe da Kaka ta gefe ta kwanto a kafaɗarta tace,"gani Dada". "Halimatu". Kakan ta kira Ummi da mamaki matuƙa. "na'am Dada". sai Kaka ta rungumeta tana hawayen farin ciki itama,"Halimatu ina kika je?, dama kina raye Halimatu?, ƴata na yafe miki domin nasan ba komai ya saki barin gida ba sai baƙin cikin mugun miji, amma tsayin wannan lokaci ina kika shiga Halimatu har na ganki haka lafiya ƙalau?, kai Allah maji roƙon bayinsa". Ummi tace,"tashin farko Kawu Nasir ne ya bani goyon baya harma ya ɓoye ni a gidansa, daga nan labarin da yawa, amma waɗan can mutanen da kike gani ɗansu ne ya tsince a sanda na faɗa cikin wani hali, kusan shekara yanzu suke bani duk wata kalar kulawa". nan da nan kuma duka Families biyu sai suka manta da damuwar da ake ciki, a shiga babin farin ciki. dan kamar yanda su Hajiya Madina suka mance da lamarin su Fillo haka suma su Kaka suka manta da lamarinsu, dan suma waje suka samu suka zauna, Kaka sai kwarara adu'a take yi da godiya ga su Yusuf, tunda Ummi ta shiga faɗa mata irin alkhairan da suka yi mata. da ƙyar iyalan Dikko suka safafawa Hajiya Ramla suka bar jikinta, ta bisu da kallo tana cewa Hajiya Madina,"ranki ya daɗe yanzu duka waɗannan yaranmu ne?, har waɗannan samarin?". ta faɗa tana nuna Khalil da Sameer. Hajiya Madina tace,"ƙwarai kuwa". nan da nan ta shiga nuna mata su Nihal tana faɗa mata sunayensu, tai mata nuni da Ilham dake gefe ɗaya ta rakuɓe sai kallonsu take tana murmushi. tace,"ga inlaw ɗinmu can". Mum tace,"really?". Maama tace,"ga zahiri na kunya nan kina gani". ai nan da ko Mum ta buɗe mata hannu tace ta taho gareta, ta rungumeta da tsananin farinciki sai saka mata albarka take yi. kuma sai a lokacin Mama ta lura da rashin Zaytuna, sai ta miƙe tana dube dube dan dama tuni ta san da ƙullatar da Zaytuna tayi da Mum. ta ganta tsaye can gefe ta haɗe rai fuskarta a gefe ɗaya, ranta ya ɓaci sosai taji tama kasa magana, hakan ne yasa Hajiya Ramla fahimtar komai musamman da ta ɗaga ido ta kalli photocopy ɗinta, ba sai an faɗa mata ba ai tana kallonta tasan itace jaririyarta da ta tafi ta bari. Turaki ma ya dinƙa kallon Zaytuna yana tuna lokuta da dama da take ce masa,"ka daina damuwa da ita Hammah tunda ai itama bata damu da mu, ni fa Hammah Allah ko ace ta dawo inda take ba zan kalla ba balle na raɓeta". sai kawai ya miƙe ya nufi wajenta, yana jin Maama cikin muryar ɓacin rai tana cewa,"wannan ba itace tarbiyar da na baki ba Zaytuna, kuma ko ki ɗago ƙafa kizo mahaifiyarki tasa miki albarka ko kuma wallahi in ƙaraso nan inyi miki duk abinda zuciyata ta sani, dan ba ki isa ki lalata mana farin cikin da muke ciki ba". Tayi shiru a sanda Turaki yaje gaban Zaytuna ɗin ya kamo hannunta, har ta cije tana neman ƙwacewa, ban san me ya faɗa mata a kunne ba yasa ta biyo shi. suna zuwa gaban Mum Turaki ya zube duka gwiwoyinsa a ƙasa, yaja hannun Zaytuna da ta tsaya ƙiƙam itama ta zube nata gwiwoyin, dama wannan ranar ya daɗe yana jira, dama wannan lokacin yake ta jira, dan haka kawai sai ya haɗe hannayensa duka biyu alamun neman yafiya cikin amon sauti me mugun ban tausayi yace,"Mum dan Allah dan Annabi ki yafe mana, ki yafe min dan girman Allah, wallahi tallahi ban san ta yacca akayi wutar ta kama ba, da sanina ba zan haddasa gobara ba Mum kema kin san banda fitina, amma ina neman yafiyarka dan Allah Mum". yay maganar hawaye na sakko masa hoton komai na wancan lokacin na haska masa musamman a sanda yabi Mum ta hankaɗo shi ta rufe ƙofa ta tafi ta barsu. Hajiya Ramla ta fashe da kuka, kukan da ya tafi ya shiga kunnuwansu ya daki zuciyar Turaki da Zaytuna, suka yi saurin ɗago ido suna kallonta, a ɗazu zai faɗi duk wani saukar hawayenta da sunan hawayen farin ciki, amma wannan kukan da ta kasa riƙe ƙarfin sautinsa na shaida masa so take ta yishi iyakar gwargwado, ta yanda zata samu ta rage raɗaɗi da baƙin cikin wani abu dake ranta. to me ya kawo hakan?, shi da yayi mata laifi. kuma kafin ya gama karantar dattin baƙin cikin dake saman fuskarta sai yaga ta sauko daga kan kujerar, itama ta zube nata gwiwon a ƙasa ta rungumo su jikinta tsam. tana kukan sosai tana faɗin,"Babana babu abinda ka yi min, baka min laifin komai ba Babana. ni ce nayi muku laifi wanda har ba zan yafewa kaina ba sai in kun yafe min, dan Allah, dan Annabi Babana kai da Zaytuna ina baku haƙuri, ina roƙonku ku yafe min da nisanta daga gareku da nayi, sharrin shaiɗan ne". Zaytuna ta fashe da kuka tana shigewa jikin Mum ɗin sosai, cikin muryar kuka suka haɗe baki ita da Turaki suka ce,"Mum ke fa Uwa ce akan me za kike neman yafiyarmu bayan baki yi mana komai ba. to ma idan kinyi ɗin menene ai girmanki ne da cancantarki, balle ma har duniya ta naɗe ba za ki taɓa yi mana abinda zamu kallesa a matsayin kin mana laifi ba". furucin nasu sai ya zama kamar haɗin baki ko kuma tun can dama sun tsara hakan. sukai shiru suna barin jikinta, Turaki yasa hannunsa na hagu a gefen fuskarta ta ɓarin da yake, itama Zaytuna haka. suka ƙara haɗa baki da faɗin,"muna miki tsananin so, farin cikinki shi ne muce mun yafe ko?, to mun yafe miki Jarumar mata". sukai kissing nata a goshi suna jin wani irin shauƙi na daban da basu taɓa jinsa ba mara misaltuwa na bin jinin jikinsu. gaba ɗayansu kuma har Mum ɗin sai suka saki murmushi me faɗi, har haƙoransu duka na bayyana a waje. Hajiya Madina da su Neehal sai suka koma ƴan kallo, dukkansu sai murmushi suke yi, kuma har sannan Hajiya Madina bata bari Baffa ya sani ba saboda sanin irin fushin da yake da Hajiya Ramla, ta bari ne kawai sai dai ya gansu a gida. Zaytuna taƙi sakin mahaifiyartata tace,"Mum yau a jikinki nake so na kwana, yau ba zanyi bacci ba Mum zan zauna inta kallonki". suka riƙo hannunta ta miƙe ta koma kan kujerar ta zauna, sannan ne ta kalli Hajiya Madina da zolaya tace,"Madam kisa ƴaƴanki su sakeni in tafi wurin sabuwar ƴar da nayi". aiko karaf Neehal tace,"ki tafi ina Mum?". ta faɗa tana turo baki tai saurin zagayowa ta zauna kusa da ita tana kama hannunta da cewar,"ai mu daga yau kina manne wajenmu kuma". bata bar murmushi ba tace,"to zanje in duba patients ɗina, a ban izini dan Allah". Kusan duk a tare suka haɗa baki wajen faɗin,"patient kuma Mum?". tana kallon Hajiya Madina tace,"wata yarinya ce da ta taimaka min muka fito daga cikin jeji mota ta bigeta, tun ɗazu munfi 1hour amma shiru, tace min ƴar aikin gidanmu ce, dan tunda ta ganni ma take cewa muna kama da Zaytun". a lokacinne kuma sai ga Fillo nan tazo wajen kamar tasan zancenta akeyi, tana riƙe da hannun Ummi ta ƙaraso da kumburarriyar fuskarta da taƙi barin murmushi. ta saki hannun Ummi ta nufi wajen Hajiya Madina wacca ta buɗe mata hannu, ta shige jikin Hajiya Madina ita kuma tana rungumeta tare da faɗin,"hasken gidan Alƙali Dikko, haƙiƙa ke ɗin haske ce a tare damu Fillo". Fillo tace,"Maama nima ga Ummina na gani, ashe bata mutu ba". ta saketa tana faɗin,"haba dai". tabi Ummi da kallo kafin ta isa wajenta da sauri tana gaisheta suna yiwa juna barka da farin cikin da suka tsinci kansu a ranar yau. Turaki dai sai yabi Fillo da kallo, ba wai ya manta da ita bane, tun ɗazu hankalinsa na kanta, kawai dai ba zai iya barin Mum bane, amma Allah Allah yake yaga Dr Yusuf yazo wajen. ji yake kamar yaje ya sunkuceta ya ɗauketa ya kaita inda zai zama daga shi sai ita, silent place ɗin da ba za'aji sautin komai ba sai na dariyarta, dan tabbas zai ƙara yalwata wannan annurin da yake gani shimfiɗe a saman fuskarta. zai ajiyeta akan cinyarsa yayi mata godiya da irin salon da ba'a taɓa yiwa wani mahaluƙi shi ba duk girman matsayinsa da mulkinsa kuwa. Mum ta dubeta tace,"zo nan ƴata". Fillo ta isa wurinta zata tsuguna tace,"a'a zo nan". ta faɗa tana yi mata nuni da kusa da ita, yayinda take kallon Turaki tana cewa,"Babana matsa". Turaki ya matsa Fillo ta zauna, Mum na kama fuskarta tace,"how are you feeling now dear?, ina ke miki ciwo?". tace,"feeling much better Mum". ta faɗa da ƙyar saboda yacca take jin babban yatsan Turaki na ƙafarsa na yawo akan ƙafarta. ga shi yana matso da fuskarsa saitin kunnenta kamar baya ganin kowa da komai a wajen, ita al'amarunsa tun before ya tafi suka fara bata tsoro, kuma kawai sai ji tayi ya ratso da hannunsa ta baya ya matsa cikinta, ta ɗanyi zillo tana jin kamar ta fashe da kuka. a hankali ta yanda ko kaɗan Mum ba zata ji ba balle ta gane yace,"tanks immeasurably". ta ɗan kallesa kaɗan ta ɗauke idonta. a sannanne suka jiyo guɗa ta karaɗe cikin asibitin, Boɗejo ce ta taho sai rawa takeyi, take kuma wuri ya ƙara kacemewa da murna. Inna Wuro dai na gefe da sakakken baki cikin ranta tana faɗin ashe haka aljanu ma suke da haɗin kai. daga bige musu ƴa har sunyi cincirindo haka da wannan uban daren, sai dai babu hankali sam dan taga kamar murna suke yi. ta ratsa ta gefen su Kaka da suke tsatstsaye da ƴan gidan su Yusuf, ta tafi da sauri zuwa reception, ta sami wasu nurses su huɗu a zaune suna hira, tayi musu sallama suka gaida ita. tace,"ku ana can anata haska film kunan zaune da farin kaya kamar sabababbin gawa, a'a to ni dai da ku ka ganni kujerar zama nazo ɗauka. wata ƴar arziƙin tazo ta kai min kujera dan Allah in samu wajen zama tunda naga abin bana tsayuwa ba ne". Nurse ɗaya ta taso tana cewa,"Hajiya kawo Babyn". ɗayar kuma da mamaki tace,"film kuma Hajiya! a asibitin?". Inna Wuro ta gyara zaman mayafi tana riƙe Farha da kyau tace,"a'a babu zancen wani in kawo Baby, sunanta Farha ba Baby ba, kuma yanzu ina ni ina baki jaririya alhalin ban sanki ba?, inje ki cuceta in shiga uku, to wallah uwarta a kotu take yin aiki tsab sai ta iya sawa a ɗaure ni ba mutunci ne da ita ba, a hannuna ta san ƴarta haka kawai in baki ki yiwa ƴar allurar tetanus ki jamin jafa'i, yo banda ma tana can tana kallon Film ina zata bar min ita, ai basa bani ita nima kuma bana karɓa saboda sunan Zainabu Yusuf ya saka mata, ummm wai ko dai sunan uwarsa yasa bacin yasan Uwar ba mutumiyar ƙwarai bace, Allah yasa ma dai kar ƴar ta yo gadon hali, dan naga goshinta iri ɗaya da na Zainabun". Nurse ɗin tai murmushi kawai. Inna Wuro tace,"yanzu dai ɗaukar min kujerar muje, ko kuma sai an biya kuɗin ɗaukar ne?". Nurse ɗin tai ƴar dariya tace,"a'a Mama, kula daku ai aikinmu ne, muje". ta faɗa tana ɗaukar kujerar. Inna Wuro tace,"a'a in ma kince sai an biyaki ai sai a biyaki, albashin da ake baku dudu nawa yake, kuɗin fa abincin rana ɗaya ne da Amadu yake kashe mana, muje wallahi sai in sa ya baki wani abin ai ɗana yana da kuɗi, shisa ma kaf nabi Malaman duniya nace suke masa adu'a kar a sawa kuɗin ido su ƙare da wuri mu shiga uku mu gantale acin ɗumamen safe, shayi kuma ba madara balle isassan sikari". Nurse ɗin tayi gaba tana ƙunshe dariyarta, Inna Wuro na lura da hakan tace,"a'a wallahi dawo ki ajiye in ɗauka da kaina, sam bana haɗa hanya da ƴan banza irinku, shisa kaf ƴaƴan Amadu da Kursum ce bama shiri saboda irin wannan munafukar dariyar, sai inyi magana a wani ƙunshe dariya saboda ga taɓaɓɓa na magana ko?, to Allah ya isar min dan ba yafe miki zan ba, yanzu tsakani da Allah wani yazo wucewa ya gani ai sai yace min sannu, to sannu ina lafiya ƙalau ai zagi ne da cin mutumci, gaskiya ajiye kujerarki bana so na ɗauka da kaina, dama ku yaran asibitin nan duk ƴan banza ne sam baku da mutumci wallahi, kullum sai mutane sun kai ƙararku radiyo tsabar ba kwa so ku gama da duniya lafiya, to wallahi ni babu ruwana a lahira kuna kallo zan yi gaba in shige aljannah salin alin ku kam kuna baya ana ramawa talakawa abinda ku kayi musu". Nurse ɗin tace,"yi haƙuri Mama bada ke nake ba". Inna Wuro ta haɗe rai tayi mata wani kallo tace,"wato ke harda halin ƙarya irin na Aliyu kina da shi kenan, ina ganinki da idona kina ce min bada ni kike ba, to kawai na barwa Allah abar zancen bana son sabuwar fitina bacin wadda nake ciki". tasa ƙafa tayi fatali da kujerar, ta nemi wata ta ɗauka tayi gaba sai masifa take yi. sai da zata bar wajen kuma sai ta dawo murya ƙasa-ƙasa tace,"ba zaku zo kallon ba ne?, ai ko dai zaku yiwa kanku dan zaku rasa na ɗorarwa, kunga yanda jama'a suka cika wajen akayi maƙil da ƙyar ake numfashi, to dai za'ai babu ku wallahi indai baku zo ba dan faɗan aljanu da mutane ne, ɗana Aliyu ne ya kashe musu ƴarsu suka zo cin Uwassa Zainabu, ni dai du Allah kuzo ina gayyatarku kallo, ku taho da kujeru kuma ku sami na takawa dan anyiwa wajen rumfa nima sai na taka zan hango abinda ke faruwa, dan baku ga yacce suka zo da makamai suka yiwa wajen ƙawanya ba, ni yanzu so nake ma suce ba akan Aliyu zasu ɗau fansar ba akan Zainabu zasu ɗauka, ni dai da nayi sati ban bacci ba saboda tsabagen murna". jiyo tashin hayaniya ta tafi da sauri,"kai kai kai na tafi kar ayi babu ni, kar a shanye ƙafar Aliyu banga ta yanda akayi ba in kasa bada labari". Nurses ɗin na dariya suka biyo bayanta da sauri suma, ita dai sai jan kujera take tana ɗaga ƙafarta me ciwo da ƙyar, ɗayar nurse ɗin ta dage sai da Inna Wuro ta tsaya ta bata Farha, ta bata ita tana cewa,"ni da ace da jakar goyo ma sai ku ara min in sakata aciki kar inje tashin hankali yay tashin hankali nayi ta kaina in yasar musu da ƴa a wajen ban sani ba". suka gimtse dariyarsu Nurse Raliya tace,"zan riƙe miki ita Mama". tace,"aiko dai Allah rabaki da sharrin zaurawa ya haɗaki da saurayi me irin zuciyar ɗana Amadu, ya rabaki da sharrin samarin zamani masu munin hali irin na Aliyu". ta amsa da amin. tana tafe sai faman sauri take tana cewa nurses ɗin,"amma fa kuyi shiri ku riƙe takalmanku a hannu dan da zarar an fara sare-sare ta kaina zanyi in barku, dan ba zan tuna ma ni na gayyatoku ba, ku taho da sauri dai kar ayi a gama babu mu". kuma duk bakin room ɗin da Inna Wuro tazo wucewa sai ta leƙa tace,"jama'a ku fito ana faɗan aljanu da mutane ana can ana faman shanye ƙafafu, dan Allah ku fito jama'a ku taimaka mana kar a kashe jikana Aliyu, wayyo na Annabi ku taimaka jikana yana cikin masifa ya kashe ƴar aljanu, ku kawo mana ɗauki dan Allah, jama'a da yawa sun taru an rasa yanda za'ai da su kowa yabi su da kallo ana zazzare ido". jin wannan yasa mutane aka dinƙa fitowa ana ta faɗin subhanallah da innalillahi, dama tun ɗazu suna ɗan jiyo hayaniyar, kan kace me wannan wuri ya ƙara ɗinkewa da mutane kamar cinema, Inna Wuro ta rasa wajen ratsawa ta wuce sai ta tsaya daga gefe ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da tasa a lokaci ɗaya akayo kanta. kamin a rufeta tayi saurin jan kujerarta tabi ta gefe ta wuce ta samu wurin da zata bawa idonta hakkinsa, ta zauna tana ɗaga kai sai kalle-kalle take tana kiran,"ƙawayena masu farin kaya da na gayyato kuna ina?, gani anan tsakiya idan kun jini ku ɗaga hannu in zo in shigo da ku, ga sarauniyar aljanun nan duk an rungumeta ku hasko waya ku ɗaukarwa duniya". wani takaici ya turnuƙe Dr Yusuf, ya dinga kallonta yana jin kamar ya kai mata duka, Aliyu da ya dawo hayyacinsa ya ɓata rai yazo yana ce mata,"wai ke dan Allah mene haka?, jifa yanda kika tarowa mutane jama'a, ke ko ina akaje sai kin yarfa mutane, kinga tashi kawai mu tafi gida kamin ki gama ɓararwa da Daddy mutunci". ko kallonsa bata yi ba tasa hannu tana turesa gefe. "yo Aliyu tunda dai ba naka mutuncin zan ɓarar ba me kuma ya shafeka". ganin yaƙi matsawa ta zabga salati tana nuna masa can gefe da cewar,"mun shiga uku ga Zainabu can ta yanke jiki zata faɗi". Aliyu yay hanzarin matsawa yana wurga idanuwa, ta kallesa tai dariya tace,"ɗan ƙwal uba addababbe". ta buɗe idanuwa duka tana ƙara kallon su Hajiya Madina da su Kaka waɗanda a yanzu suka haɗe wuri ɗaya, waje ya zama kamar gidan biki, Hajiya Madina na rungume da Fillo tana cewa,"tabbas ke ɗin alkhairi ce, kin zama haske a cikin rayuwarmu tunda kika kusance mu, insha'Allahu nayi ɗamarar faranta miki Fillo har ƙarshen rayuwata". Daddy ya ƙaraso inda Inna Wuro take zaune tayi ƙyam da ido a waje ɗaya tana ta aikin kallon bidirin da har yanzu bata fahimci kansa ba ma. in zaka yanka wuyanta ba zata ce ga abu ɗaya da taji an faɗa ba tun ɗazu, balle tace maka ga akan ainihin abinda yasa ake wannan murna, ita dai abu ɗaya ta barwa kanta dukansu aljanu ne kuma uban Aliyu suka zo ci. Daddy ya rissina yace,"mu tafi gida Inna dare yayi sosai, ƙarfe uku har da rabi, alhamdulillah yarinyar ta samu sauƙi  dan Yusuf ma yace gida zasu wuce". ta kallesa tace,"to su kuma waɗancan da suka cunkushe waje ɗaya tafiya zamu yi mu barsu bamu gama kallonsu ba?". Daddy yace,"ai yanzu su ma zasu tafi". tace,"kai Amadu bana son halin Aliyu a tare da kai, ni kawai kayi tafiyarka ku ƙyaleni anan idan an gama na biyo motar haya, haka kawai yaran can da basu sami zuwa ba su rasa me basu labarin irin aratabun faɗan da aka sha, kai kasan halin ƴarka Yusra da gulma bata ƙi ta zageni tass ba akan ban kai musu rahota ba, ta dinƙa ɗaga min murya tana me amfanin zuwana wajen, to gwara ka barni in samu na kai musu, ni ƙafar Aliyun ma banga ta yanda aka shanyeta ba, yanzu dai ɗau wayarka kawai kayi musu hoto me motsi sai akaiwa sauran ƴan gidan da basu ga tashin hankalin da akai ba". Daddy yace,"wayata na barta can gida kinga a halin da aka taho ai". tayi shiru dai bata ce masa komai ba, dai-dai da ƙarasowar Nuratu wajen tace,"Inna Wuro ashe matar da muka riƙe a wajenmu babar yarinyar da Aliyu ya buge ce, shekaru da yawa basu haɗu ba sai yau Allah ya haɗa fuskokinsu". Inna Wuro ta daki ƙirji ta dafe, babu shiri ta miƙe da sauri tana cewa Daddy,"tarkata yanamu yanamu mu wuce Amadu, daga nan kai tsaye Kano zamu wuce wuce ko gida ba zamu koma ba, gwara muje wurin Malam Ahmad Sulaiman ya haɗo mana turaruka azo ake bankawa juna, ina dalili haka irin wannan ibtila'i na rainon Aljanu, to Allah yasa dai bata shiga jikin wannan ƴa Farha ba". Daddy dai yay shiru, tashin hankalinsa ɗaya ta botsare tace sai anyi kano a tsakiyar daren nan, dan aka ƙi zuwa shi abin zai zamewa tashin hankali  ta dinga kuka kenan tana ita ya biyata nononta da yasha kawai sai ta san nayi. Inna Wuro ta dinƙa bi tana cewa mutane ahalin Amadu Alfindiki kuna ina, mutane kuzo mu tafi gida ƙarfe uku ta dare tayi. Ammi tace mata,"Inna kiyi musu sallama, ki ɗan ƙara basu haƙuri sai mu wuce". ta daki cinya ta riƙe baki tace,"niiii, ba dani ba wallahi, akan me in bada haƙuri bani na kashe musu ƴa ba, ke dai da ya zamar miki dole da fitinannan ɗanki yaja miki masifa". har sai da suka je bakin mota sannan aka kula da babu wanda ke riƙe da Farha, Nuratu tace,"Inna wa kika bawa ita?". Inna Wuro ta fashe da kuka tana faɗin,"na shiga ukuna, wallahi ban san wanda ya amsheta ba, a hannuna fa take ƴar nan ban san garin ya ta bar hannun nawa ba, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, to aini sai yanzu ma na kula babu abu a hannuna, to dama abu ka ɗauka kamar baka ɗauka ba, Amadu kira Malam Ahmad ya buga mana istikara ko aga hannun wanda ta faɗa". tana yin shiru sai ga Yusuf nan ya fito ɗauke da Farha, ya wuce ta gabanta ko kallonta baiyi ba ya miƙawa Nuratu ita yace,"karki ƙara bawa tsohuwar can ƴata tunda ba'a kasuwa naje na siyota ba, ke ma kuma ba buɗe ido kika yi kika ga an ajiye miki ita kusa dake ba, sai da kika sha baƙar wuya kafin samunta". yay maganar ransa a ɓace. Inna Wuro na jinsa tace,"nima halina yaja min na shegen shishshigi da ƙwala kai a faranti, in ban damu da ɗaukar ƴarka ba ai baka zagar min iyaye har haka ba Yusuhu, iyayen da sun jima a ƙasa, tunda suka mutu babu uban da ya taɓa buɗe ƙazamin bakinsa yay musu irin wannan ƙazamin zagin sai kai Yusuhu, kamar bani na haifi ubanka ba?, amma babu komai Allah yana ji kuma yana gani, ranar gobe ya bi min hakkina. ƴarka kuma ni da ɗaukarta har abada, kai kallonta ma ba zan ƙarayi ba indai na cika ƴar halas, shegen banza kawai da yayo kama da dangin uwassa duk munana". tai gaba tana goge hawaye da gefen zani. "Amadu zo mu tafi kafin jinina ya hau". tafiyarsu ba jimawa su Hajiya Madina ma suka fito, da su da su Kaka aka kwashesu duka a sienna har biyu. cikin dare ne amma kace tsakar rana saboda yanda suke ta hanyaniya a mota. dan lokacin har an kira Granny a waya vedio call, itama duk wannan fushin da take yi sai ta manta da shi, tana ganin Mum ta fashe da kukan farin ciki, tana faɗin gobe-gobe zata taho, yanzu Adil zai je ya yanko mata ticket. taraddadin Hajiya Madina ɗaya ne su kuma Baffa ya lanƙwashe. kuma suna gab da isa gida Baffa ya kira wayar Hajiya Madina yake shaida mata cewar,"Fulani Azima tayi mummunan accident, su wuce masarauta kawai ba sai sun koma gida ba". *Vote, Comment and Share.* [8/31, 01:22] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *38* *Massachusetts General Hospital, Philippines.* acikin silent ward ɗin babu abinda kake ji yana tashi sai sautin kuka me ban tausayi. wata tsohuwa baƙa na sanye cikin les me tsada milk colour, ta baro inda take tsaye ta dawo kusa da Ilham ta zauna. ta janyota zuwa jikinta cikin sigar lallashi da ban haƙuri tace da ita,"Ilham wannan kukan naki da kika shafe kusan awa guda kina yinsa ba shine zai bawa Mahaifiyarki lafiya ba, saboda haka ki sha re hawayenki ki mata adu'a dan ita tafi buƙata a halin yanzu". maimakon Ilham ta daina kukan sai sabo ya ƙaru fiye da wanda take yi, kuma Kakar tata Hajiya Shema'u wacce take mahaifiya wurin Azima bata ƙara ce mata komai ba, sai bubbuga bayanta da take cike da matsanancin tausayin Ilham ɗin. a lokacinne kuma Ahlan ya iso wajen, ƙani ne a wurin Azima daga ita sai shi. ya zauna akan kujerar kusa da mahaifiyarsa, shima da ka kalla fuskarsa zaka hangi damuwa acikinta. yace da ita,"Umma me likitan ya ƙara cewa?". ta sauke numfashi ruwa na kawowa cikin idonta tace,"tou Me Martaba dai ya tafi wajensa tun bayan da suka fito da ita daga theater room ɗin, ban san yanzu kuma ya ake ciki ba". Ahlan ya sauke numfashi sannan yace,"nima jiya muna tare da jami'an tsaron da suke ta bincike akan accident ɗin nata, kuma har yanzu fa Umma babu labarin driver'n da suka fita tare. anje wurin iyalinsa su kansu sunce satin biyun nan cif ba su saka shi a idonsu ba nemansa suke, itama kuma jakadiyar tata fa har yau ba labarinta". da damuwa sosai Hajiya Shema'u tace,"to Allah masanin abinda ya faru, kuma ni gani nake idan lamari ne na ƴan garkuwa ai ita zasu ɗauke ba drivern ko Jakadiyar ba, kuma idan kidnappers ɗinne da tuni sun kira waya, amma koma mene dai mun barwa Allah, fatanmu Allah ya tashi kafaɗunta". sai kuma ta fashe da kuka sosai tana cewa,"da banyi niyyar faɗa muku ba saboda kar hankalinku ya tashi, sai dai faɗar ya zama dole ko don a tayata da adu'a. likita yace ta kamu da paralyse, ɓarin damanta ya mutu ya gama aiki Ahlan, idonta guda ɗaya ma shima ya mutu wai ruwan ciki ya tsiyaye gaba ɗaya, ƙafar hagun ma yanzu suna bayanin yanketa za'ai, Azima dai na cikin wani hali Ahlan, wannan yarinya sai dai Allah yay mata sakayya da wanda ya zama silar shigarta wannan hali". sosai take kuka sanda take maganar, wanda hakan ya ƙara tsawaita kukan Ilham. Ahlan a razane yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, paralyse Umma?, yanke ƙafa?, rasa ido ɗaya?, kai rayuwa kenan kowanne bawa da kalar ƙaddararsa, ita kuma Yaya ga ta yanda tata tazo mata. hasbunallahu wani'imal wakil". shima bai san lokacin da hawaye ya sakko masa ba, tausayin ƴar'uwar tasa yay matuƙar kama shi. Mai Martaba ya ƙaraso wajen jikinsa a mace, yana zuwa Ilham ta taso a jikin Hajiya Shema'u ta tafi ta faɗa jikinsa. ya rumtse idonsa sosai saboda tsananin tausayinta, ya kalli su Hajiya yace,"Dr yace kuna iya shiga wajenta". da sauri kuwa suka miƙe suka nufi wani dogon corridor hanyar da zai sadaka da room ɗin da aka kwantar da Fulani Azima. Mai Martaba ya zauna akan kujerar da suka tashi, ya kwantar da kan Ilham a cinyarsa, yay dauriya da dakiyar maganar da yake jin kamar da kuka a cikinta. yace,"kina so Maminki ta sami lafiya?". tai saurin ɗaga masa kai, yace,"to adu'a za ki mata ba kuka ba, indai kina kuka ba zata sami lafiya ba, kinga dai a halin da take ciki, halin da ko maƙiyinka ba zaka yi masa fatan ya shiga ba". ta ɗago daga cinyar tasa, yasa hannu yana goge mata hawaye, wani na kuma bin wanda yake gogewar. duk cikinsa ƴaƴa mata yafi son Ilham saboda sunan mahaifiyarsa da taci, ƙari da kuma da kyan halinta, dan duk cikin yaransa mata tafi kowa haƙuri da biyayya da nuna ita ɗin ba ƴar kowa bace. yana riƙe da hannunta ya nunfasa yace,"ya kamata ki koma gida haka Ilham, ba zai yiwu ki baro mijinki kizo ki tare anan ba, karki damu ko every weekend ne sai kizo kike ganinta kina komawa". tai saurin cewa,"Dad ni ba zan koma ba sai Mami taji sauƙi". yace,"a'a Ilham". cikin kuka sosai tace,"to Dad ai shima yayi min uzuri tunda yasan wacce bata da lafiya, ni dai ba zan koma ba, Allah Dad ba zan iya zama a ko'ina ba yanzu in ba kusa da Mami ba". Mai Martaba yay shiru bai ce komai ba, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗauko waya ya kira Turaki, yana ɗagawa daga ɓangaren Turaki cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya gaida shi. bayan sun gama gaisawa Mai Martaba yace da shi,"Muhammad babu damuwa dai ko idan Ilham ta zauna nan?". Turaki yace,"ba damuwa Dad". "ka tabbata Muhammad?, karka ce zaka yi kara ko kuma alkunya". yace,"ko ɗaya Dad, ai abinda ya zama dole shi ake dubawa". Mai Martaba yace,"to shikenan, Allah yayi muku albarka". daga haka suka yi sallama. su kai shiru daga Ilham har Mai martaba kowa yana jin ransa ba daɗi, in ace suna da iko kwana ɗaya tal ba za'a ƙara ba Fulani Azima zata warke, to amma lamarin ba nasu bane na ubangiji ne, sai dai su roƙe shi ya warkar da ita ba tare da tayi doguwar jinya ba. suna zaune kusan minti goma sai ga Sarauniya Mabruka wato matar Mai Martaba ta farko, ita da ƴaƴanta uku suna biye da ita tare da masu kula da su mutum uku. tun a washegarin ranar da Fulani Azima tai accident aka taho da ita Philippines domin ƙwararrun likitoci su dubata, dan Mai Martaba yana ganin kamar likitocin nigeria ba zasu iya ba, duk da cewar asibitin fada ma ba ƙanan likitoci bane acikinsa, kusan duk ɗinsu a ƙasar waje suka yi karatu, amma shi yafi ganin su taho nan ɗin. kuma families da dama sun so su biyo bayansu Mai Martaba yace a'a su ɗan dakata tukunna, ita kanta Ilham sai da aka kwana biyar sannan suka taho ita da su Hajiya Shema'u da Turaki, kuma shi ranar da yazo ranar ya koma bai zauna ba. kuma sai a yau da suka kwan 21days sannan mai martaba ya bar iyalinsa suka taho, don farko duk bai zaton za'aja haka ba, da zarar an mata aiki a ido shikenan zata dawo normal, to kuma likita sai yazo musu da bayanin duk da ya girgiza su. Sarauniya Mabruka ce ta fara sauka sauran biyun duk suna baya suma tare da nasu ƴaƴan. ta zauna kusa da Mai Martaba tana ɗago da Ilham daga jikinsa ta kwantar da ita a nata jikin, hadiman dake tare da ita suka watse suka tsaitsaya daga can gefe, Yarima Abbas da Yarima Lateef da Yarima Bilal suka zauna kusa da mahaifinsu ta ɗayan ɓarin. Sarauniya Mabruka tace da Mai Martaba,"ya jikin nata?". idonsa na tsaye ƙyam akan wata ƙofa cike da nazari a bisa faruwar accident ɗin ya bata amsa da cewar,"da sauƙi irin na malam bahaushe, zuwa anjima zasu ƙara shiga da ita theater za'aiwa ɗaya idon aiki, shima tana kukan bata gani da shi sosai, sai maƙogaronta da akai hoto akaga still akwai glasses na mota da suka farfashe mata aciki". "Allah ya sauƙe ya bata lafiya don nabiyyurrahmati". ta faɗa tana saka hannu ta goge hawayen da ya sauko mata. lamarin duk yasa jikinsu mutuwa, sosai suke tausayin Fulani Azima domin ita ɗin mutum ce a garesu, duk wanda zai buɗi baki ya faɗi aibutunta to sai dai idan maƙiyinta ko kuma wanda basa shiri. duk cikin su huɗun ita ɗaya ce babu ruwanta a yanda take nuna musu, ko irin kishin nan ma na rashin haihuwar ɗa namiji ita bata yi sam bata ɗaga hankalinta ba, hasalima kama nasu ƴaƴan take kamar nata, nan kuwa duk basu san tana bi musu ta ƙarƙashin ƙasa ba ne, fir'auna ce a zuciya Allah a fili. suka miƙe gaba ɗayansu suka wuce zuwa room ɗin da take, duk me cikakken imani kallo ɗaya zai yiwa Fulani Azima yaji saukar hawaye a fuskarsa, kwance take kan gadon kana kallon idonta na dama zaka san bata gani da shi kwatakwata, sai kallon kowa take yi da ɗayan shima kuma dusudusu take gani, ga karaya a hannayenta duka biyun banda ta ƙafarta guda ɗaya, kallon kowa kawai take tana hawaye masu zafi. ita so take ma tayi magana amma ta kasa, tun washegarin ranar da abun ya faru taso ta buɗi baki ta nemi yafiyar Hajiya Ramla a sanda suka je dubata, amma tayi tayi tai magana sam ta kasa, ga shi duk ta yanda taso tayi wata alama da zaisa a fahimci tana so tayi magana da Hajiya Ramla ta kasa, kuma daga yanda taga fuskokin familyn Dikko tasan ko kusa Hajiya Ramla bata tona mata asiri ba, akwai tabbas ɗin bata faɗawa kowa komai ba, wanda hakan ya ƙara haifar da danasani da kuma dama nadama a tare da ita, tana ji tana gani ko da bata mutu ba tata rayuwar dai ta ƙare, ita da matacce marabarsu numfashi kawai, babu abinda take biɗa a yanzu sama da ta kalli Hajiya Ramla a gabanta ta nemi yafiyarta, sannan taga Jakadiyya da Drivern da ta kashe suma tace su yafe mata, to amma ba zata samu duka wannan damar ba, haka zata tafi lahira da tarin zunubi da kuma hakkin waɗanda ta zalunta, shikenan ita kuma tayi biyu babu, babu nan duniyar babu can lahirar, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. sosai take kuka idonta guda ɗaya na hawaye, inama ace a dawo da baya, da tayi amfani da damarmakin da take da su ta gyara lahirarta, to sai dai hakan ba zai kasance ba, lokaci ya riga ya ƙure mata, yanda kowa ke ganin saukar hawayen nata babu wanda ya fahimci me take buƙata, sai tausayinta da kowa yaji yana roƙo mata lafiya a wurin Allah. Ilham ta ƙwace daga hannun Sauraniya Mabruka ta isa gadon ta faɗa jikinta ta fashewa da wani irin kuka, kukan da duk sai da ya saka kowa dake ɗakin hawaye babu shiri. *Dubai Quarters, Gombe State, Nigeria.* daga ɓangaren kudu, gida na tsakiya me lamba 20, flat house ne ɗan tsakiya me ɗauke da milk gate da abuja brown paint, sai flowers dake zagaye da ƙofar gidan, daga yanda wajensa yake da kyau zaka shaida cikinsa ma me kyau ne. daga cikin gidan Fillo ce a ɗakinta kwance akan madaidaicin gadonta, ba bacci takeyi ba idanuwanta a rufe suka kawai hawaye na bin gefen fuskarta. ta tashi zaune tana saukowa akan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah, tana cikin sallar Ummi ta shigo, ganin tana sallar yasa ta ce mata,"idan kin idar ki fito muci abinci". bayan Fillo ta idar ta kalli agogo taga har biyu saura, dan haka bata fita ba sai da ta saka uniform na islamiyarta tukunna, ta ajiye hijab ɗin da jakar akan gadonta ta fito cikin sauri. Kaka da Ummi na zaune a ƙasa kan carpet suna kallon tashar arewa 24 ana maimaicin kwana casa'in, ta zauna gefen Ummi sannan su kai bismillah suka fara cin abincin, bai fi spoon biyar Fillo tayi ba ta miƙe, Kaka da Ummi suka bita da ido har ta shiga ɗakinta. wucewar minti biyu sai gata ta dawo riƙe da jaka da hijab a hannu, ta zauna kan kujera tana kallo tv tana ji tana neman kasa riƙe hawayen dake yunƙurin zubo mata. sai bayan da su Ummi suka kammala cin abincin sannan Kaka na dubanta tace,"kinga, kinga Fillo ki kiyaye ni, na faɗa miki ki cire batun cutarwar da Amir yay miki a ranki amma kinƙi ji ko, haka kawai kina ƴar ƙarama dake kisawa kanki damuwa salon kija mana masifa, ke bama abin farin cikinki bane tunda har aka sami bayin Allahn da suka tsaya miki hukuma tabi miki hakkinki". take kuwa hawayen da take ta riƙewa suka zubo, ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, Ummi na kallon ƴartata da tausayawa tace,"Auta zo nan". ta taso ta dawo kan kujerar da Ummi take ta kwanta a jikinta. Ummi na shafa kanta tace,"kina so na koma inda ba xaki ƙara ganina ba?". da sauri ta girgiza kanta da cewar,"a'a Ummina". tace,"to ki daina kuka haka nan ya isa bana so, ki manta da duk abinda ya zama past ki focusing akan rayuwar gabanki, babu abinda zai fishsheki yanzu sama da ki mayar da hankali akan karatunki shine kawai gatanki har zuwa ranar da Allah zai kawo miki miji na gari kiyi aurenki". bata daina kukan ba tace,"Ummi har yanzu abin yana yi min ciwo sosai". Ummi tace,"sai ki godewa Allah da ya tona asirinsa tun bai aureki ya miki cuta me gaba ɗaya ba, ki kuma gode masa da ya kareki daga sharrinsa a iya zaman da ku kai da shi". tayi shiru bata ce komai ba, idonta na haska mata hoton jiya sanda suka je kotu ita da su Maama akan case ɗin Amir da aka ƙarke a jiyan, tana tsaye a bayan Mum taji Turaki ya kama hannunta ba tare da sanin kowa ba suka bar wajen, kuma duk ta yanda taso ta raba hannunsa da nata ta kasa har suka shiga wani ɗaki inda aka kai Amir shi da tawagarsa, kallo ɗaya tayi masa ta saurin ɗauke kanta gefe dan a duniya idan da mutumin da bata ƙaunar gani bai wuce shi ba. kuma tsabar rashin kunya irin da azzalumin bawa wai har yake zubewa a gaban ƙafafunta yana roƙonta Allah da Annabi akan ta yafe masa abinda yay mata, sannan ta roƙar masa alƙali ya sassauta masa hukuncin da aka yanke masa na zaman prison tsawon shekara goma sha biyar, har da wai in ya fito yayi mata alƙawari zai tuba ya koma mutumin arziƙi ya aureta. wannan maganar kuma ita tayi mata zafi bata san lokacin da ta ɗaga hannu ta wanke shi da maruka har biyu ba, Turaki kuma ya karɓi kulki a hannun police ya bata, ta dinga buga masa a fuska har sai da taga jini yana zuba ta hancinsa tukunna ta ƙyale shi tayi saurin fita daga ɗakin, in ba haka ba tsab zuciya zata iya sata ta rarumi duk abinda zai kai Amir Lahira ta buga masa. Kaka na kallon Ummi tace,"Halimatu kinga duk inda Hamid yake yana nan hankalinsa na kanki da tunanin halin da kike ciki, fushin fa da kike da mahaifinsa ba zai fa shafe shi ba tunda ba shi yay miki laifi ba". fuskar Ummi ta juye zuwa ɓacin rai tace,"Dada zan nemi Hamid amma ba yanzu ba, akwai lokacin da nake jira, dama in ace ma zan ƙara waiwayar gidan Hayyo to ace Auta na hannunsa ne, yanzu kuwa da bata wurinsa banga dalilin da zaisa in taka ƙafata a ƙofar gidansa saboda ina da wata ajiyar a gidansa ba, Hamid namiji ne baya buƙatata kamar yanda Auta ke buƙatata". Kaka tace,"bafa zance ake na ki dawo da shi hannunki ba, kije ya ganki yasan kina raye kuma kina cikin ƙoshin lafiya shine maganar da nake yi miki". Ummi tace,"ba yanzu ba Dada". Kaka ta gyaɗa kai tace,"ai shikenan ban san lissafin da kike yi ba. ni Allah yasa ma ta hanyar arziƙi Hayyo yayi kuɗin da aka ce  yayi". Ummi tace,"ni banma yarda da yaron da ya faɗa ba". Fillo tace,"Ummi da gaske ne fa, ai sanda ku ka tafi gidan Inna Azimi munje ni da su Badariyya, da muka shiga matan gidan suka ce ai kusan wata huɗu kenan da suka sayi gidan, masu gidan sunyi kuɗi sun tashi, to ni naso ma na tambayi inda suka koma kawai na fasa". Ummi dai bata ce komai ba tayi shiru, ita ai banda ma dai bata son musawa maganar mahaifiyarta ai bata ga me zai sa su ƙara komawa Taraba ba a rayuwarsu, tunda Allah baisa sunyi dacen dangi ba, ita bata yi dacen miji ba, ƴan'uwan Kaka kaf ba wani kula suke da ita ba, kamar ma ba ciki ɗaya suka fito ba ayanda suke nuna mata, kansu da matansu kawai suka sani, dalilin da ya dawo da Kaka nan gombe kenan ta samarwa kanta mafita na neman aiki a gidan sarki, daga nan kuma ta koma gidan Dikko ga kuma matsayin da Allah ya kawo su ayau. Maijidda ta shigo parlon bakinta ɗauke da sallama, su Kaka suka amsa mata ta nemi wuri ta zauna tana kallon Fillo dake jikin Ummi tana hararta da cewa,"Ummi dan Allah ki daina ɗora wannan ƙatuwar abar a jikinki". Ummi na murmushi tace,"autar guda?". Maijidda ta taso ta taho tazo itama ta ɗora kanta a kafaɗar Ummi tana cewa,"Ummi to nima ai autar ce". Fillo tasa hannu ta tureta tana faɗin,"dilla ɗaga min uwa, da wani ƙaton kanki anan zaki ce zaki kwanta jikinta salon kija kafaɗarta tayi ciwo". Maijidda ta harareta tana mayar da kanta wurin Kaka tace,"Kaka Yami tana gaisheki, wai ki bada wannan saƙon da za'a kawai Baba Huraira zata je gidan gobe". Kaka tace,"aiko gwara da Allah yasa ta tuna min, jeki ɗakina ɗauko wannan baƙar jakar tawa ta gado ki kawo min". Maijidda ta shiga ta ɗauko jakar ta dawo, Kaka ta ɗauko saƙon ta bata tana yi mata bayani. sannan ta ɗora da ce mata,"yauwa kuma ki faɗa mata jiya fa an karɓo kuɗaɗenmu na wajen matsiyacin yaron can, an karɓo miliyan shidan duka wallahi". Maijidda tace,"shege ai ni naso jefe ɗan iska akayi kowa ya huta da annoba". sai kuma cikin tsokana tace,"umm in iya bakina kar Fillo ta ƙullace ni". Fillo ta miƙe a jikin Ummi tana hararta tace,"banza kawai". ta faɗa tana tashi ta wuce ɗaki. Ummi tace da Maijidda,"kin fara zuwa yiwa su Hajiya Madina aikin?". tace,"ehh Ummi tun washe garin ma da ku ka taho ai". Kaka tace,"to Maijidda sai ki kula da Allah, na san ki kema hankali da natsuwa ba daga nan ba, dan haka ki iya zamanki da mutanen nan, ki zama me gaskiya da amana da kula da aikinki, kina ganin dai ta dalilin iya zama da su da Fillo tayi alkhairin da suka yi mana, bacin haka wa zai ɗauki gida sukutun guda ya bamu kyauta?, waye zai tsaya tsayin daka akan a karɓar mana hakkinmu wajen wancan azzalumin bawan?, aini babu abinda zance da Hajiya Madina sai dai ubangiji yayi mata sakayya da gidan aljannah, mutuncin matar nan ya wuce duk mutum yake zato wallahi". ƙarar wayar Kaka ta katse maganartata, ta ɗaga tasa a kunne ba tare da ta san waye me kiran ba dan bata iya karanta sunan ba. sai bayan kuma ta ɗaga ɗin ta ɗau muryar Dr Yusuf daga can ɓangarensa da yay sallama, bayan gama gaisawa ta tambayesa iyalin da mutanen gidan sannan yace ta bawa Ummi. Ummi na murmushi ta amsa sallamarsa tace,"Shikenan kuma sai ɗana ya manta da ni". Dr Yusuf ya sosa ƙeyarsa yace,"na isa na manta dake Mommi, wallahi kullum sai munyi kewarki, Mommi ban san me yasa kika ƙi yarda kici gaba da zama a wurinmu ba, ko mun miki laifi ne Mommi?". Ummi tace,"kul Yusuf naji ka ƙara ambatar kun min laifi, ni dai kawai abinda nake so ku sani shine har duniya ta naɗe ba zan manta daku ba da alkhairin da ku kai min,  ina nan zan ƙara zuwa na musamman in ƙara godiya, ina jikata Farha?". Dr Yusuf yace,"tana lafiya Mommi, jiya ma Nuratu ke cewa tana so tazo ta gaida ke, to kuma sai naji kamar Maijidda tace kun bar can gidan Alƙali". Ummi tace,"ehh wallahi, ai sun sallami Kaka daga aikin da sha tara ta arziƙi, sunce taje ta huta haka, wallah kam sun bamu gida anan Dubai Quaters, baka gida ba Yusuf so masha'Allah, dama nace sai munyi waya tukunna sai in sanar muku insha'Allahu, to ashe ma Maijidda ta rigani". yace,"masha'Allahu, Allah ya saka musu da alkhairi". "ameen Yusuf, dan Allah ka gaidar min da su Nuratu da Ammi da Umma, kai da kowa ma musamman Inna Wuro, gaisuwarta tafi ta kowa yawa". yace,"insha'Allah Ummi duk zasu ji, sai munzo gaisuwa". "to Allah ya kawo ku, ina nan ina zuba ido". daga haka suka yi sallama, Maijidda na murmushi tayi tafi tace,"mu dai abinmu sharr". ta faɗa tana kallon Fillo data fito cikin complete shirinta na tafiya makaranta, ta gimtse dariyarta Fillo ƙuma ta galla mata harara tana cewa da Ummi,"na fito Ummi". ta zauna Ummi ta dafa kanta tayi mata adu'a sosai, tana ƙara ce mata ta kula. Kaka da zolaya itama tace,"ke kuma sai da angon naki ya kashe wayar sannan za ki fito, wannan kiran dai ai nasan ba namu bane, naki ne ake wani wayance da Ummi ake nema". Fillo ta turo baki tace,"angon wata dai amma bani ba, me zanyi da wannan". ta faɗa da duk gaskiyarta. Ummi ta waro ido waje tace,"iye! Auta ɗan nawa kike cewa me zaki yi da shi?, ban da shi Auta kin isa yanzu ki ƙara saka ni a idonki?, ah lallai, wato babu ko kunya a gabana kike faɗin me zaki da ɗana, ba ki san nafi sonsa ba akanki". cike da shagwaɓa kamar zata yi kuka tace,"Ummi ni to ba zan auri me mata ba, dan Allah ku daina haɗa ni da shi". Ummi na ƴar dariya tace,"idan kin kwantar da hankalinki ma nima ba zan yarda ayiwa ƴata Nuratu kishiya ba, ah tou can ki yanka kije ki samo daidai dake ɗin, nima ɗana yafi ƙarfinki dan ba abinda zai yi da ƙwaila irinki". ta miƙe cike kunya tana barin kusa da Ummi tace,"ni bama yanzu ba ai, sai na zama barrister tukunna in zaɓa in dirje, by then Abba nah ya shiryu ya gane gaskiya sai yazo ya ɗaukemu, mu koma can inda muka fito sai mu bar tsohon ɗan naki anan da shi da gwalagwajin matar tasa". ta faɗa tana ƴar dariya, Ummi ta ɗau hula ta jefa mata. "kin ci ƙaniyarki naji kin ƙara kiran Nuratu da wannan sunan, ki kiyayeni wallahi". tana dariya sosai saboda yanda Ummin tayi tace,"nima to a faɗawa mijinta ya kiyayeni ya fita a sabgata, ya bar ganin ya taimakawa Ummina hakan ba zai sa ya kafa gwamnatinsa a zuciyata ba". sai kuma ta harari Maijidda tace,"ke kuma baƙar munafuka kici gaba da min abinda kike, Allah idan baki wasa ba naje na faɗawa Hamisu me gadi kince kin amince ya turo iyayen nasa. kuma wallah ki faɗawa Dr'n da yake wahalar dake kan yi masa campeign, Fillo ba zata auri me mata saboda haka ya kama gabansa". Maijidda tace,"wallah ba zan faɗa ba, insha'Allahu sai kin zama amaryar Dr". Fillo bata ce mata komai ba taiwa su Kaka sallama ta fita tana sai ta dawo. tun satin da suka dawo wannan sabon gidan da Hajiya Madina ta basu kyautarsa ta fara zuwa islamiyya wacca ƴaƴan maƙotansu suke zuwa, makaranta ce me kyau da tsada acan wajen gidan sarki, itama Hajiya Madina ce ta sakata dan har gida tazo ta sameta tana ƙara tambayarta,"Fillo ina sonki, ina tsananin sonki Fillo, gani nake har yanzu ban kyautata miki da rabin alkhairin da kika min ba, dan haka ki faɗa min me kike so na kuma yi miki yanzu?". Fillon na kukan farin ciki tace mata,"Maama ni makarantar Islamiyya nake so in koma, ina so na haddace alƙur'ani". kuma take a wurin Hajiya Madina ta kira Khalil ya gama yi mata komai a washegari kuma ta fara zuwa. yanzu haka kuma ana ma ta processing na zana private wa'ec ne, dan Hajiya Madina na gab da tafiya wani course kuma tana so idan zata tafi su tafi tare da ita kamar yanda tayi mata alƙawari. tana tsaye bakin titi tana jiran abin hawa wata jar mota tayi parking a gabanta, gabanta ya faɗi sanda aka zuge glass ɗin motar, ta ɗan ƙaƙalo murmushi tace,"Adda Samha ina yini". tace,"lafiya lau Fillo, makaranta zaki wuce?". tace,"ehh". "to shigo sai in ajeki a hanya". Fillo kamar ba zata shiga ba, saboda ita har ga Allah tana tsoron mutumin da ko da sau ɗaya ne ya taɓa cutar da wani a rayuwa, balle kuma wanda ya jima yana haddasa abubuwan za zai sa yaga bayan wani duk da Allah ba ya ba shi nasara, gani take tamkar su Samha ba akan Turaki bane kawai suke da wannan mugun hali, wataƙila sun cutar da mutane da yawa ma ba tun yanzu ba. ɗayan ɓari na zuciyarta yace mata,"ki kyautata musu zato a yanzu, ki ɗauki komai da ya faru a matsayin abinda ya jima da wucewa". Fillo ta sauke numfashi ta buɗe motar ta shiga, daga yanda ta kalla Samha na driving ɗin ta san tana cikin nishaɗi sosai. dan kamar ba wannan azababbiyar Samhan da ta sani ba a baya ba, kamar ba wannan Samhan da taji suna haɗa plan ɗin yanda zasu kashe ɗan'uwansu ba, ta saki baki sai labari take yi mata, hirar da ita dai bata cewa komai. Samha tai picking call ɗin Maama da ya shigo wayarta, daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"ina kika tafi kuma?". fuskar Samha na bayyana wani irin farin ciki da jin daɗin da bata taɓa jinta ba a ciki tace,"Maama yanzu zan dawo, naje siyo special gift ɗin da zan bawa Mum ne". ta jiyo fitar sautin murmushi a tare da Hajiya Madina wacce tace,"good, but ki dawo da wuri". tace,"tom Maama". sai kuma tace,"muna tare da Fillo ma yanzu haka, na ganta hanya zata wuce school na ɗauketa". da sauri Maama tace,"bani ita". Samha ta miƙawa Fillo wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina tace,"Fillo ƴata, Allah yayi miki albarka kinji, ubangiji yasa ki gama da duniya lafiya yarinyar nan, wallahi shigowarki rayuwarmu alkhairi ne. Fillo nayi amfani da shawarar da kika bani akan su Samha kuma naga nasara, domin kuwa Samha da kanta ma tazo tana faɗa min duk abinda suka aikata ita da Sameer, Allah yay miki albarka Fillo yanzu hankalina ya kwanta banda damuwar komai, ƴaƴana sun shiryu". Fillo dai murmushi take bata ce komai ba, daidai sanda suka zo gate na makarantar tasu, tace. "Maama mun kawo makaranta zan sauka". Hajiya Madina tace,"to shikenan, sai kin dawo Allah ya bada ilimi me albarka. a dage sosai kinji, gobe da safe ki shigo ina son ganinki, ko da yake ma zan aiko driver yazo ya ɗaukar min ke". daga haka sukai sallama, Fillo ta fita a motar, har ta bar wajen Samha ta kirata ta bata wani biro me kyau. ta karɓa tayi mata godiya sannan ta wuce, ta tafi tana me jin tausayin Samha a ranta, lallai rashin nunawa ɗa soyayya daga wurin uwa ba ƙaramin ƙalubale bane a rayuwarsa. banda hakan dama me zai kai su Samha ƙudurtar cewa sai sun kashe ɗan uwansu alhalin su babansu ba wata kujerar mulki garesa ba. ta tuna sanda ta zauna ta bawa Umminta labarin duk abinda ya faru ga me da taimakon da Hajiya Madina tace zata yi mata akan ta shiga jikin Samha ta dinga yawan bibiyar al'amuranta dan ta dinƙa jiyo mata plans ɗinsu akan Turaki. wannan dalilin yasa tace ta dage ta iya turanci saboda Samha bata fiya magana da hausa ba ko fulatanci sai dai english. kuma ba tare da dogon nazari ba kai tsaye abinda Ummi tace mata shine,"duk abinda yaranta suka aikata laifinta ne, domin babbar illar da zaka yiwa kanka shine ka nuna banbanci a tsakanin ƴaƴanka, ka nuna soyayyar wancan tafi ta wannan a gareka, ka kasa ɓoye musu yanda kake jin matsayin kowannensu a zuciyarka, tabbas idan zuciyar wani ta ɗauka ta wani ba zata ɗauka ba, nuna banbanci tsakanin ƴaƴa kan haifar da matsala sosai, domin zuciyar wasu zata yi ƙoƙarin ganin yanda za ai su kauda wanda ake so ko kuma su illata shi". Ummin tace mata,"dan haka yanzu shawara ɗaya da zaki bata tunda suma Allah yasa mahaifiyarsu ta dawo, to ta maida hankalinta kan waɗannan yaran masu raunin zuciya, karta ce zata fasa yiwa su Turakin abinda take musu dan hakan zai iya kawo gurɓataccen tunani a zuciyar mutane, ta mayar da kulawar yaranta equal to yanda take son su Turakin, shine kawai samun kwanciyar hankalinta". *Vote, Comment, and share.* [8/31, 01:25] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *39* *08:30am.* acikin bedroom ɗin na Baffa, Hajiya Ramla ce tsaye gaban mirror ita da shi, sanye take da shadda golden colour tasha azababben aiki ajiki, anyi mata ɗinki bubun sai ƙyallin stones take yi, tayi masifar kyau kamar balarabiyar usuli, ita da Baffan iri ɗaya sak. daren jiya tailor ya kawo musu ɗinkin su uku iri ɗaya, ita take taimakawa Baffa wajen shirin da yake yi, tana shirya shi ɗin suna hira cikin annashuwa da jin daɗi tare da alfaharin ƙara kasancewa da junansu. turare ta ɗauka ta fesshe shi da shi tuni kuwa ɗakin ya ɗauka da wani daddaɗan ƙamshi, Baffa ya rungumeta jikinsa yana faɗa mata irin son da yake mata da kuma kewarta da yay a sanda bata tare da su, albarka kawai yake zunduma mata kamar yawun bakinsa zai ƙare. wayarsa tayi ƙara ta zame daga jikinsa tai saurin isa kan gado ta ɗauko wayar, sai da tayi picking tukunna ta kara masa a kunne. daga can ɓangaren Boɗejo tayi sallama suka gaisa da Baffa, tana kuka ta-ke shaida masa halin da Fulani Azima ke ciki, shi kansa Baffa da ya dawo a jiya jikinsa yayi matuƙar sanyi ya kuma tsorata ainun da yanda ya sami Fulani Azima, ya ƙara jin tsoron Allah da kuma tsoron sharrin duniya, saboda yanda ta dawo kamar ƙwarangwal halittarta dai babu kyan gani a yanzu, har ƙwalla sai da yay musamman da ya fahimci tana so tayi magana da shi, to amma shi har ga Allah ba zai iya bata wannan damar ba saboda ba zai iya zaman kusa da ita ba dalilin mugun ɗoyin da take yi, mijinta kansa sai ta window yake ganinta balle kuma shi, yana ji ma ana batun dawo da ita gida saboda su kansu asibitin sunce ba zasu iya da ita ba. cikin sigar kwantar da hankali Baffa yace da Boɗejo,"kiyi haƙuri, adu'a zamu cigaba da mata Allah ya bata lafiya". ta ƙara sautin kukanta tana faɗin,"Dikko ni ƴarta nake tausayi, a jiya yarinyar nan Ilham tayi suma yafi biyar, ko abinci bata iya ci Dikko, aljanun da bamu santa da su ba sai tashi suke, yau baka ga yanda suka farfasa mata jiki ba". ta faɗa tana kuka sosai. Hajiya Ramla dake jiyo komai ta sauke numfashi tana jinjina al'amarin sakayya, ita dama tun can bata da niyyar tonawa Fulani Azima asiri akan abinda tayi mata, abunda zuciyarta ta yanke mata kawai shine zata barta da Allah sai kuma sun haɗu acan lahira, amma anan dai ba zata taɓa faɗar cewa ga wacca tai silar barinta gida ba, duk da cewar tunda ta dawo ta bada labari kowa ke cewa aikin asiri ne, to amma ko kusa bata yarda ta bar hakan a zuciyar mutane ba, duk da Hajiya Madina taso ta ɓaro komai ɗin dan har sunan Fulani Azima sai da ta ambata tana cewa wallahi sai taci ubanta zata kawo ƙarshen makircin matar, to da ƙyar dai ta tausheta ta bar maganar. Boɗejo na kukan sosai tace,"Dikko ka bawa Ramla wayar ina so nayi magana da ita". "tom shikenan, amma ki daina kukan hakan dan Allah". tace,"Dikko ina ni ina daina kuka kuwa yanzu, ai ni da barin hawaye har sai Azima ta mutu, amma indai zanke ganinta a wannan halin hankalina ba zai kwanta ba kamar yanda hawayena ba zasu tsaya ba, wallahi ma ni daka ganni na yafe mata duk wani kalar rashin kyautawa da tayi min". Baffa ya miƙawa Hajiya Ramla wayar, suka gaisa da Boɗejo, tai ƙasa da murya tana cewa. "kiyi haƙuri Ramla ƙarar ɗanki na kawo miki, wallahi yaron nan azzalumi ne baya tsoron Allah kwata-kwata, kinga dai ko maƙiyin Azima yana zuwa ya dubata amma shi tunda ya kawo matar tasa ya yasar anan bai ƙara waigowa ba, tace min ko kiranta a waya ma baya yi, idan ita kuma ta kira shi suna gaisawa ɗan banzan yaron nan zai kashe wayar baya ko tambayar lafiyarta balle ta uwar dake cikin wani hali, to dan Allah ki faɗa min wannan mijin aure ne, kuma wallahi ƙarya yake yi yace baya son Ilham, dan dai kin ɓata ne lokacin yarintarsa amma da ko ke sai kin aura masa Ilham, to ni dai yanzu abinda nake so daga gareki tunda kin isa da shi kisa yazo wajen matarsa ko da ba zai zo duba Azima ba dan wataƙila sharrin da tayi masa ne bai manta da shi ba, ba haka ake ba sam wallahi, ya kamata yazo ya kasance da ita ya kwantar mata da hankali da irin salon ma'aurata, to da yake dai shi ɗin baida addini shisa, kuma rashin hankali da tunani ke damunsa, duk da nasan Madina ce take zuga shi wallahi, kuma zan dawo ne zata gamu da fushina da bata taɓa gani ba". Hajiya Ramla ta tari numfashinta da cewa,"a'a Boɗejo Maamansa ai ba zata hanasa zuwa ba, ita kanta ina mai tabbatar miki da bata san da wannan rashin tunanin nasa ba da tuni ta tsawatar masa, amma zan faɗa mata insha'Allahu". Boɗejo tace,"to ai dama Madina ta gama hanadameki ke da ƴaƴan, sai yanda tayi da ku. ke yanzu Ramla baki da ikon sawa da hanawa ga ƴaƴanki dake kanki sai dai Madina?, ni ko a tarihi ina na taɓa jin wannan yardar dake tsakanin kiahiyoyi, ai tun a auren nan na san Madina ba haka ta bar mutane ba, to ni dai wallahi tallahi zan baɗawa idona toka, in mance da cewar Turaki jikana ne in maka shi a kotu, Allah sai nayi ƙararsa akan zaluntar Ilham da yake dan ubansa, ina na taɓa jin kalar wannan auren me cike tsantsar zalunci da rashin adalci, wato yana nufin ma bai damu da ita ba ya huta da ƙaya kenanan tunda yanzu bata kusa da shi". Hajiya Ramla ta kwantar da murya tace,"kiyi haƙuri Boɗejo zai zo insha'Allahu". "ke ni rufe min baki sokuwar uwa kawai wacce wata ta fita iko da abinda ta haifa". tai maganar a fusace tana kashe wayar cikin ɓacin rai, daga can ɓangarenta sai masifa take yi a asibitin muryarta ta karaɗe ko'ina, faɗawa me martaba take cewar yazo ya kaita kotu na ƙasar nan wallahi sai ta kai ƙarar Turaki akan wofuntar da matarsa da yay, sai taga ubansa Alƙali d ya tsaya masa. Baffa ya dubi Hajiya Ramla dake riƙe da waya tai shiru fuskarta na bayyana rashin jin daɗi, ya karɓi wayar daga hannunta wannan yasa tayi firgigita ta dawo daga gajeran tunanin da ta lula, ta sakar masa murmushin da bai fito daga can ƙasar zuciyarta ba, Allah ma ya sani ko kaɗan bata farin ciki da wannan auren tun a ranar da ta  san Ilham ƴar Fulani Azima ce, kuma in ace taso a ranar ko minti ɗaya Turaki ba zai ƙara ba da auren Ilham akansa, sai ta sa ya saketa, to amma babu yanda zata yi tunda har ubangiji ya riga ya shirya faruwar hakan, tsoronta ɗaya kar Ilham ta cutar mata da ɗanta tunda shi hali ana tsotsarsa a nono. muryar Baffa na bayyana ɓacin rai yace,"a zatona tunda har an riga anyi auren kuma yayi haƙuri shikenan komai ya wuce, ashe ƴan banza ya mayar damu, to wannan yaron sai na saɓa masa, naga alamun sai mun saka ƙafar wando ɗaya da shi, sai nayi fatali da wannan son da nake masa in har bai riƙi matarsa da kyau ba, shikenan sai ace ni ne ban isa da yarana ba, ita yarinyar ba biyayya tayi ba ta haƙura da zama da shi har take kyautata masa, ko dan ubansa an faɗa masa ita so takeyi, zai gamu da fushina tabbas, zai haɗu da ni". Hajiya Ramla ta sauke numfashi a sanyaye tace,"ai duk da kun aura masa wacce yake yaso da hakan bata faru ba, haka itama da kun bata wanda take so da hankalin ƴarku ya kwanta, da mijinta ya girmama halin da mahaifiyarta ke ciki. to amma ya zamu yi tunda me faruwa ta riga ta faru, wata matsalar dai muke ƙirƙirarta da kanmu yayinda ta zamar mana damuwa sai mu kirata da ƙaddara, kuma ma dai banda rashin adalci har ba'a ga biyayyar da Babana yayi ba ace za'asa ƙafar wando ɗaya da shi"... Baffa ya katseta da cewar,"wait! mu kenan bamu isa da ƴaƴanmu ba sai mu bari suke juyamu?, wato bamu isa muyi musu zaɓi su karɓe shi ba kenan?". tace,"a'a ai ƙarshen isa ai kun isa tunda har ya yarda aka ɗaura auren, ya kuma halarci ɗaurin aure har ya iya zama da matar, amma ko a musulunce ma auren dole dai bai halatta ba, ya kamata kuyi duba akan wannan, kun san irin cutuwar da zucoyiyin zasu yi kuwa?, ko baku taɓa cin karo da labarin auren dole yasa mata ta kashe miji ko kuma miji ya kashe mata?, duk abinda za'ai ake duba da yanda zamani ke tafiya ba yacca zamanin baya yake ba. kaga your Highness to tell you the truth, I personally do not like this marriage at all, kawai dan dai bani da yanda zanyi ne, bana son fitina sannan bana so yarona ya rasa kwanciyar hankalinsa, amma wallahi da sai Babana ya saki yarinyar nan, bana gudun maganar mutane, girgizar al'arshin ubangiji ne bana so". "wait your excellency, me Madina ta kimtsa miki a dawowarki?". ya faɗa yana dafa shoulders ɗinta. tai guntun murmushi tace,"ai ko Madina bata kimtsan komai ba, ba zan taɓa son auren nan ba, balle ma bata kimtsan ba, let me tell you this; i hate Fulani Azima with passion, hakama duk wani abu da ya shafeta, kamar yanda ƴarta ma ƙaunar ganinta bana yi balle kuma aurenta da ɗana, kawai dan banda yanda zanyi da abinda ku ka ƙadarta masa ne. but you keep in mind duk ranar da Babana sees his life choice no one will stop him from getting another marriage, ya zama dole a barsa ya auri zaɓinsa kamar yanda aka tilasta masa auren zaɓin wasu, yana da damar da zaiyi mata huɗu addini ya halatta masa hakan, so banga dalilin kuma da zai sa ace ita da ubanta ya zauna da mata huɗu ace ba zata zauna da kishiya ba, there is no such thing at all, Babana ba ƙaramin yaro ba ne". da tsananin mamaki Baffa ke kallonta, tunda yake da ita bata taɓa rufe ido irin haka tana faɗa masa magana ba dake fitowa daga can ƙasan ranta, tafi Madina haƙuri nesa ba kusa ba, ta kan haƙura da duk kalar zaluncin da akayi mata ta barwa Allah, ansha cutarta ba sau ɗaya ba sau biyu ba tace ta haƙura ta yafe, sometimes ma sai dai Madina ta tayar da jijiyoyin wuya a madadinta. amma yau duk abinda yake jin tana faɗa daga can ƙasan ranta yake fitowa, and she means duk abinda ta faɗa ɗin. ya buɗe baki yana so ya kawar da ɓacin ransa yace,"kin san kuwa Boɗejo ce ta shirya wannan auren?, kuma kin san ita tace bai isa ya ƙara wani auren ba sai in mutuwa Ilham tayi?". ta kama maɓallin rigarsa tana saka masa tace,"idan har kai zaka bi umarnin mahaifiyarka to shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar". ta faɗa sanda take gama ɓallewar, sannan ta nufi saman mirror ta ɗauko glasses ɗinsa ta saka masa. "yau dai ƙila gwamnati taci tararka dan ka makara da yawa". ta faɗa tana basa peck a goshi. shima yay mata peck a kumatun yana cewa,"yau ɗin rana ce ta musamman a wurina, dan haka office dole suyi min uzuri". ya faɗa yana kama hannunta su fito daga ɗakin, suka nufa downstairs, suna sauka daga steps Baffa yasa hannu ya rufe mata ido. tace,"ah Your Highness so kake in faɗi ne?". yace,"ta ina za ki faɗi bayan ina tare da ke, i want to suprise you with something shisa". tai murmushi bata ce komai ba har suka sakko gaba ɗaga daga benen, Hajiya Madina da iyalanta na ƙasan sunja line kowannensu fuskarsa na bayyana farin cikin dake tare da shi, Hajiya Madina ta saka irin shaddar dake jikinsu da akai musu ɗinki iri ɗaya. Turaki dake gaban layi ya matso ya rungume Hajiya Ramla, ƙamshin turarensa kawai taji itama tayi hugging nasa tana cewa,"Babana ya dai?, tunda na dawo kaƙi barina na huta, ko sai na mayar da kai ciki?, ko kuma sabon feeding zan fara ne?". daga kunnenta Turaki ya raɗa mata,"If all mothers were like you, planet earth would be filled with such great families. I pray that you find happiness in every second of your wonderful life. Happy Birthday to the best Mother in the world, i so much loves you Mum". ya faɗi hakan yana matseta sosai da jin wani irin shauƙi na ƙaunar mahaifiyarsa a tare da shi, nan da nan kuma duk sauran yaran suka yo kanta suna wishing ɗinta, sai da suka saketa sannan ta sami damar kallon Baffa da Hajiya Madina, sukai hugging each other suma suna mata prayers daga nan kuma ta ɗaga idonta ta kalla yanda sukai decorating parlon Baffa ya dawo kamar ba shi ba. wani farin ciki mara misaltuwa ya mamayeta tana jin wata iriyar soyayya ta daban akan families ɗin nata na bin dukkan sassa na jikinta. suka kama hannunta zuwa ƙaton center table ɗin da aka saka, an aje cakes kusan guda shida, kowanne an rubuta happy birthday to the special Mum, kallonta na ƙarshe ya sauka akan wanda akasa Happy Birthday your Excellency, tana kallo tasa hannu zata ɗauko suka tayata ɗaukowa suka kawo mata shi gabanta, da murmushin da ya kasa barin fuskarta tayi cutting cake ɗin tana cirowa ta kai bakin Hajiya Madina dake kusa da ita ta ɓarin hagu, Maama ta karɓa suna hugging each other da hawayen da ke sakko masu wanda basu san na menene shi ba. daga nan kuma kowa sai ya shiga bata gift ɗinsa, Turaki ne na ƙarshe a wanda ya ajiye mata passport har guda biyu, ɗaya na zuwa saudiyya ɗaya kuma na zuwa agentina inda zata je ta huta taji daɗinta. Hajiya Ramla ta dinƙa saka masa albarka da sambaɗa masa adu'a. suna cikin yin breakfast ne Hajiya Ramla ke sanarwa da Hajiya Madina saƙon Boɗejo akan ɗanta, Maama bata san lokacin da bakinta ya suɓuce ba tace da Mum,"kinga manta da wannan tsohuwar da Allah, fitinarta tayi yawa wallahi, duk tsufa ya rikitar da ita, ta barsa da abinda har yanzu bai gama isarsa ba mana, idan yaje shi zai bata lafiya ne ko menene ake so kuma da ba za'a bar yaro ya sarara ba saboda dai an liƙa masa ƴar gwal, to shima ai ɗan gwal ɗin ne tunda Uwayensa na ƙaunarsa". ta shiga zazzaga masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, har sai Baffa ya kira sunanta, a sannane ma ta tuna da batun zamansa a wajen ta manta tayi ɓarin zance irin haka akan babarsa. yanda ya kira sunan nata tasan ransa ne ya ɓaci matuƙa, taci gaba da cin abincinta da ta ƙoshi ba tare da ta kallesa ba tace,"Allah ya baka haƙuri ya huci zuciyarka, yi haƙuri na annabi sarkin masu biyayya". tukunna ta ajiye spoon ɗin ta miƙe tana kallon Turaki tace,"me babban suna duk sanda ta ka sami space sai kaje musu, ba qai ka matse kanka ba, sanda ka sami space nace, Allah ya baka ladan haƙuri da ladan biyayyar da kake yi". har tai gaba zata fice sai kuma ta dakata, dan tasan muddin ta tafi ba abinda zai hana Baffa zazzagewa Turaki kwandon bala'i, kuma Hajiya Ramla babu abinda zata ce, ƙila ma yasa shi tafiyar da bai shiryawa ba ayau ɗin. ta dawo ta koma dining ɗin ta tattara abincin gabansa tace,"tashi muje kaci acan, duk an bi an sa maka ido ka rame kana neman fita hayyacinka, ana aure ai ƙiba amma kai kai duk an tsabtareka". Turaki ya miƙe yabi bayanta suka fita, Hajiya Ramla tabi bayansu ta girgiza kai tana murmushi. after sun kammala break fast ɗin yaran duk suka miƙe suka fita, Mum ta dakatar da Khaleel ya koma ya zauna sannan tace da Baffa,"Khaleel yaga yarinya yana so, yana da buƙatar aje a nema masa aure". kunya ta kama Khaleel ya shiga sosa ƙeya, Beffa ya ɗan dube shi sannan ya dubi Hajiya Ramla yace,"ina ce ku keda ikon aurar da yaran ga waɗanda suke so, ai sai kuje ku nema masa ko". yana faɗin haka ya miƙe yana cewa da Khaleel,"ka ɗauƙo key zaka kaini Government house, da sauri fa 11 muke da meating". daga ɗakin Maama kuwa suna shiga ta dire masa abincinsa saman table tace,"ba inda zaka je wallahi, ai ba kai zaka bata lafiyar ba, in sunyi hankali sun dawo maka da matar shikenan, amma ba zaka bi sahunta ba wallahi ai ba mijin Hajiya bane kai". ta bisa da kallo tana cewa,"nace fa babu inda zaka je daka wani bi ka damu". ta wuce toilet ta barsa sai mita take yi. ya ɗauki wayarsa ya kira Bello, daga ɓangaren Bello yace,"sai yanzu kaga damar waiwayata". Turaki ya sauke numfashi yace,"ba wannan ba Bello, i want you to find a solution for me, kaina ya ƙulle wallahi, i don't know how to inform them about the other marriage, ban san kallon da zasu yi min ba ban kuma san ta yanda zasu ɗauki lamarin ba, and i want to be with my wife now". Bello ya shafa fuskarsa daga inda yake yana kwantar da kansa jikin kujerar office ɗin sannan yace,"explaining to them is not that difficult, yanda zasu ma yarda da zancen is the biggest tension, MT dole dai ka ja mana faɗan da ba zai ƙare ba at this age da muke da shi da muka wuce ai mana faɗa". yaja tsaki,"shikenan yanzu abinda kowa zai ce shine bamu da hankali, alhalin ni ban ma san sanda kaje kayi haukar taka ba, in ace ma kai ɗaya za'aiwa faɗan da sauƙi". Turaki yace,"now you have a suggestion for me, ko kuma magana zaka ci gaba da gaya min in kashe wayata". Bello yace,"gaka da masifa da gajen haƙuri, to haka kawai zan baka shawara ban gaya maka magana ba?, faɗan da zaka jawo min ni kuma fa?, mtswww where are you now?". "i am at home". yace,"are you coming to office?". "not sure". Bello ya sauke numfashi sannan yace,"I will come after I leave the office around six o'clock, kar ka fita kuma ka barni da zaman jiranka". muryar Turaki a sanyaye da kuma ban tausayi yace,"Baffa can break this marriage Bello, i am afraid that will happen, ko kawai inci gaba da barinsa cikin sirri?, ita kanta yarinyar ma fa matsala ce". cikin bada ƙwarin gwiwa Bello yace masa,"babu abinda zai raba aurenka insha'Allahu, ai da kyakykyawar niyya kayi, kuma rainonka akayi akan taimakawa, kuma karka manta kana da Maama, ita kaɗai in ka tuna kana da ita ya isa ka daina jin fargabar komai". Turaki ya furzar da iska daga bakinsa sannan yace,"thank you friend". Bello ya bushe da dariya yace,"ya da godiya tun ba'a sami mafita ba". Turaki zai yi magana Maama ta fito daga toilet, yaga ta nufa wadrobe ta buɗe ta ɗauko hijab ta tayar da sallah, ya bi kiran Bello da kallo da ke tafiya, he have alot to say amma dole ya haƙura ya kashe wayar ya bari sai sun haɗu anjiman. around 4 Turaki ya dawo yazo shiga da mota gate sai ganin Fillo yay ta fito daga cikin wata jar mota, kuma ta fito daga motar ta tsaya suna magana da na ciki ta window, yana kallon motar ya shaida ta Dr Yusuf ce, yaji kamar ya fito yaje ya bankawa motar wutar duk su ƙone. kusan 5minutes sannan Fillo ta bar wajen ta shige gida Dr Yusuf na ɗaga mata hannu ta glass ɗin da ya zuge. motarsa na barin wajen Turaki ya fito kamar kububuwa ya shiga gidan, yanda yake tafiya kamar zai tashi sama, yana zuwa ya sha gaban Fillo ransa a haɗe kamar hadari yace,"juya muje". tayi kamar bata jisa ba ta raɓa ta gefensa zata wuje ya wani fincikota ta dawo baya, idanuwansa a warwaje sun sauya kala ya ɗaga hannu ya wanketa da mari, babu shiri Fillo ta durƙushe a gabansa tana dafe kuncinta saboda wata hajijiya da taji tana neman ɗaukarta ta zubar. sai kuma kawai ta fashe da ku ka sosai tana jin zafi a ranta, ya dinƙa kallon yanda take durƙushe a gaban nasa tana kuka bilhaƙƙi, yaji kamar yasa ƙafa yay ball da ita saboda wani azababben kishinta dake sukar ƙirjinsa. Fillo ta miƙe a harzuƙe tana ɗaga hannu sama zata rama marin sai taga ko kusa hannunta ba zai kai fuskarsa ba, hakan yasa ta kuma fashewa da kuka tana damƙar kwalar rigarsa tana jijjiga shi. "ni me nayi maka?, Allah ba zan yarda ba sai na rama". ta faɗa tana dukansa da iyakar ƙarfinta a ƙirji sosai. ya kama tsintsiyar hannunta ya damƙe da kyau ya wancalar da hannunta daga jikinsa ta tafi zata faɗi Zaytuna da ta iso wajen tai saurin tarota ta faɗa jikinta. *Vote, Comment and share.* [9/2, 06:27] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *40* Zaytuna tayi matuƙar furgita da yanayin Turaki, hakan yasa ta riƙe Fillo da kyau ta jata su kai baya da shi saboda yacca yake faman uban huci kamar mayunwacin zaki. ta shiga kaɗa masa kai tana kallonsa tace,"Hammah dan Allah kawai ka kawo ƙarshen komai a yau ko zuciyarka ma ta huta, ita mene laifinta?, ita me ta sani?, bafa ta san komai ba". ta faɗa ita kanta tana jin tsoronsa saboda yanda taga jijiyoyin kansa duk sun fito raɗau. idonsa akan Fillo da ke ta kuka yana bin ta da wani irin mugun kallo na tsantsar jin haushi yace da Zaytuna,"saketa, ki saketa ko na haɗa har da ke". ya faɗa yana raising voice ɗinsa sama, har sai da Zaytuna tayi masa alama da yay ƙasa da murya kar cikin gida su jiyo, dan ita bata so a san lamarin ɓoyayyan auren nan acikin tashin hankalin da zai sa aƙi fahimta. ya ƙara sakar mata tsawa yana zare mata ido yace,"nace ki saketa ko?". taƙi sakin Fillon tace,"Hammah it is not her fault, me ta sani  agame da hakan balle ta kiyaye, you just go and inform Maam about everything shikenan kai da ita duk sai ku huta". yace,"tana haukar zan kawo ƙarshen komai, a hakan tana sauraron kowanne banza ya kulata, ita mahaukaciyar ina ce da bata san dai-dai da rashinsa ba?". kamar zata yi kuka ta ƙara cewa,"please Hammah...". da ya yayo kanta kamar tashin iska babu shiri ta saki Fillo tayi gefe ɗaya. me gadi yayo wajen da sauri yana bawa Turaki haƙuri duk da bai san meke faruwa ba amma da dukkan alama dai ba lafiyar. Turaki yay masa wani kallo shima yaja gefe, ya fizgi Fillo da ke ta tirjewa tana faɗin,"ni ka sakeni babu inda zan bika, me nai maka da zaka tsaneni, kuma Allah sai na rama marin da kayi min ai ba abin da na maka, Allah ni ka sakeni sai na rama". ganin yana ƙoƙarin duƙawa ya ɗauketa ba shiri ta saki jiki ta bisa suka fita. suna fita bakin gate ta gartsa masa cizo a hannu babu shiri ya saketa, ta falla a guje zata juya cikin zafin nama ya damƙota ya sunkuceta bai direta ba sai bakin ƙofa, bai ma san ashe a buɗe ya bar motar ba, yana zuwa ya buɗe front seat ya tankaɗata ciki yasa key ya rufe, dan yasan tsab zata iya guduwa before ya zagaya side ɗinsa. Fillo ta saki wata razananniyar ƙara tana ƙwala kiran Umminaaaa, ƙarar da ta fito tun daga cikin motar har waje, hakan ya ƙara ƙular da shi, yaji kamar ya buɗe ya fito da ita ya rufeta da duka, yay saurin zagayawa side ɗinsa ya buɗe ya shiga gudun karta cire lock ɗin, ya doka mata tsawa sosai da cewa. "za ki rufe min baki ko saina farfasa miki shi?". ta ɗago kanta daga jikin glass ɗin da ta kifa, ta waigo tana kallonsa da ƙwayar idonta da tayi jajir, numfarfashi kawai take saukewa kamar wacce tai tseren gudu, magana take so tayi masa but ta rasa ta yanda zata furta saboda neman shiɗewa da take yi, ta kasa cewa komai sai yarfar da ɗayan hannunta da take yi. ya ɗauke idonsa daga kanta yana kallon wurin da suka tsaya kwanaki ita da Amir, sannan ya mayar inda suka tsaya yanzu ita da Dr Yusuf, tukunna muryasa ta fito da wani irin amon sauti da ke shaida bala'in kishin da ke cinsa da kuma ɗacin ƙasan zuciyarsa yace,"ke akuyar ina ce da kowanne jaki zai dinƙa zuwa wurinki?, mutuncinki kika siyar ko me da ba za ki iya kame shi ba?, abinda ya faru da ke last bai isa kiyi hankali ba shine har kike ƙara sauraron wani namijin saboda baki da hankali, ke kinfi gane kiyita tallan kanki a titi ko?, ko ce miki akayi ƙofar gidan Alƙali matattarar ƴan iska ne da za ki dinƙa tara mana banzaye?". Fillo ta kasa jurewa azabar da take ji yana shigarta, ta miƙa hannu ta damƙo kafaɗarsa, wannan yasa maganarsa ta katse ya juyo yana kallonta, sai yaga tana ta kallonsa tana hawaye kamar an kunna famfo, yaga jikinta ya saki gaba ɗaya hannunta na barin jikinsa ya faɗi, yaga ta kwantar da kanta a jikin kujerar idanuwanta sun lumshe numfashinta na fita da ƙyar. sai yaji kamar tsoro ya kamasa, yay sauri kai hannunsa saman fuskarta, jin kamar bata motsi sai ya ruɗe ya shiga kiran sunanta yana girgiza fuskarta.  shiru bata amsa ba kuma kamar bata numfashi balle ta motsa, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi ya tattaro ƙafafunsa ya haye kan kujerar gaba ɗaya yana ƙoƙarin janyota jikinsa, can ƙasa yaji muryarta ta fita a wahalce da cewa,"hannuna". ta faɗa tana kama gaban rigarsa ta riƙe. yace,"what?". ta ƙara cewa,"hannuna". ta faɗa tana fizgar numfashi. a burkice yace,"hannunki?, me ya sami hannun naki?". bata iya ce masa komai ba sai rufe ido da tayi ta ɓingilar da kai a jikinsa. sai ya kamo hannunta da ke jikinsa ya duba yaga babu komai, ya kai hannu zai kamo ɗaya kawai sai ƙwayar idonsa ta sauka akan yatsunta a jikin ƙofa ya ɓame da su, bai san lokacin da ya furta,"innalillahi wa'inna ilaihi waji'un". a matuƙar gigice ba ya saketa daga jikinsa. da sauri ya buɗe murfin motar, daidai lokacin ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya ta wahala, gumi ya keto masa kamar yanda itama ta haɗa uwar zufa duk da ac ɗin cikin motar, ya kamo hannun yana duban yatsun, sunyi jazur jini ya tare a waje ɗaya, fatar da farcen sun haɗe sun laguɓe, siririn ƙashin wajen kamar ya karye, sai kawai ya rufe idanunsa yana kai yatsun ya saka su cikin bakinsa, ya cika bakin da iska ya hura musu iska, ɗumin iskar ya ratsa yatsun har ɓargon jikin Fillo. tayi wani zullo a jikinsa saboda tsananin azaba, ta saki sabon kuka tana cewa,"da zafiii". ta faɗa da ƙyar cikin mawuyacin hali. ya rugumeta sosai yana ɗora haɓarsa kan fuskarta yace,"am sorry Fulaniii, i didn't do it to you on purpose, please am very sorry". yaji yacca tai wata iriyar shaƙuwa, irin shaƙuwar da ke fitowa ba saboda ƙishirwa ba sai dan tsananin azabar da mutum ke ji, ya rumtse idonsa sosai yana cije leɓensa na ƙasa, yana jin kamar duk duniya ya rasa jin daɗinsa har mutuwa. wucewar sakanni 30 ya miƙa hannu ya ɗauko wayarsa ya kira Zaytuna, tana ɗagawa bai ko amsa sallamarta ba yace,"fito da sauri". Tsantsar damuwar da ta tsinta a muryarsa ita ta shaida mata babu lafiya, kuma ita tasa ta fitowa da gudu bada sauri ba, tana zuwa bakin motar ta leƙo tana cewa,"Hammah lafiya?". Ta tambaya da fargaba ganin tashin hankali shimfiɗe a fuskarsa. bai amsa mata ba ya fito daga motar ya zaga ya ɗauki Fillo ya shiga baya da ita, sannan ya iya cewa da Zaytuna,"mu wuce asibiti". ya faɗa muryarsa a sama kamar ita ke da laifin. akan hanya tana tambayarsa me ya faru amma bai iya ko amsa mata ba, sai jijjiga Fillo yake a hankali kamar yanda ake lallashin jaririn da ake son yay bacci, kuma har suka isa asibitin yatsun Fillo na cikin bakinsa kamar yanda take rungume tsam ajikinsa tamkar zai sakata cikin ƙirjinsa. ba asibitin su Dr Yusuf suka je ba, dan gani yake idonsa idon Dr Yusuf ba za'a kwashe ta daɗi ba, wani abokinsa ya kira Allah ya taimaka yana asibitin, allurar lidocane aka yi mata don kashe zafin wajen, aka haɗa mata da drugs na pain relive, duk tsoronta da allura amma ko kusa bata yi kuka ba saboda wahala ba zata barta yinsa ba, tana lafe jikin Turaki sai kallo da ido kawai, haka ma maganin da Zaytuna ta bata tasha sam bata iya musawa ba, ta zama kamar hoto sai kallon Turaki da duk ya hargitse take yi. ya sauketa daga jikinsa ya zauna da ita kan kujera ya fita cikin sauri, in few minutes sai gashi ya dawo da malt da madara peak kamar wanda likita yace masa tana da buƙatar jini. Zaytuna dai sai kallonsa take yi tana murmushi tana kuma tausayinsa, ganin yacca duk yake ta abu kamar ba Hammansu da ta sani ba, ko su suka ji ciwo ko rashin lafiya ba ya wannan rawar jikin akansu, akwai dai kulawa kamar me amma ba irin wacca take gani a yanzu ba. ta bisa da kallo har ya isa dispenser ya ciro cup ya haɗa malt ɗin da madara, ya durƙusa gaban Fillo ya kama hannunta ɗaya yana murzawa tare da kai cup ɗin bakinta, idonta ƙyam akansa da rashin makamar ma wanne irin tunani zata yi, ya kwantar da murya cikin sigar roƙo da lallashi yace,"please kisha kaɗan". ta girgiza masa kai idonta na tara ruwa, yay saurin saka handky ya matse hawayen yana cewa,"kukan ya tsaya haka please bana so, ciwon zai warke yanzu, aima ya kusa daina zafin ko?". sai kuma ya ƙara kai cup ɗin bakinta yana cewa,"please drink a little". yacca face ɗinsa tayi turning zuwa na ban tausayi da kuma magiyar da yake yi mata yasa ta buɗe bakin ta sha kaɗan. yana ganin ta kau da kai ya miƙawa Zaytuna cup ɗin ya ɗora hannayensa saman ƙafarta yace,"am sorry please forgive me, ba da niyya nai ba ban san hakan zai faru ba". ya miƙe ya fita ya dawo, lokacin Dr Anwar ya gama shafa mata wani magani a wajen, Turaki ya kasa tsayuwa waje ɗaya sai durƙusawa da ya ƙarayi agabanta yana riƙe hannun a hankali yace,"zafin yana raguwa?". tana kallonsa kawai wasu sabbin hawayen suka sauko mata, wannan ya ƙara rikita shi ya miƙe yana ɗagata ya rungumeta a gaban mutane da ke ta wucewa. "Fulanii bana sane, am sorry dan Allah". yanda taga duk ya gigice ɗin nan ya ruɗe ta tabbatar da ba ya sane ɗin, dan haka kawai sai tai masa knodding kanta a saman ƙirjinsa, tausayin kanta take matuƙa amma ji take kamar tafi tausayinsa saboda ganin kamar ma kuka yake so yayi koma yayi bata sa ni ba, so take ta zame daga jikinsa amma ya hana hakan, har sai da Zaytuna ta dawo daga pharmacy tukunna ya saketa ya duƙa ya sunkuceta kamar wata ƴar baby, tana ta kai masa duka kan ita ya sauketa amma yaƙi har suka zo mota. sai da suka shiga mota ta kallesa suka haɗa ido ta hararesa tana murguɗa masa baki tace,"ni nace maka bana son irin haka ba kyau". tun ɗazu sai yanzu ya ɗan sami relief jin muryarta da yay, murmushi ya sauka a leɓensa ya kai hannu zai shafo fuskarta ta ture hannun tana cewa,"nace ma ba kyau". a wannan karon kawai sai ya saki murmushi me gaba ɗaya yace,"to naji". cikin allurar da akayi mata dama har da ta bacci, so ko doguwan tafiya basu yi ba bacci ya ɗauketa, ya kwantar da ita sanda yake nunawa Zaytuna wani suya spot yana cewa ta tsaya a wajen. haka ya dinƙa tsayar da Zaytuna yana siyan kalolin nama a duk suya spot ɗin da ya gani, Fillo dai nata bacci bata san me ake ba, fruites ɗin ma da ya siya kamar me kafa tebur, a ƙarshe ya shiga wani store ya kwaso uban choculates kamar zai buɗe sabon kanti da su, gaban motar nan dai sai da ya cika maƙil da uban kaya kace mara lafiyan da ya shekara a asibiti za'a kaima. akan cinyarsa taita baccinta har suka iso gida,  yace da Zaytuna ta zagaya ta can bayan part ɗinsu tayi parking, lokacin yamma tayi ana gab da magriba garin yayi duhu, ya fito ɗauke da Fillo ya shiga ta ƙofar da babu me ganinsa ya shiga part ɗinsu, Bello ya tarar zaune a parlonsu ya ɗauke kansa kamar bai gansa ba yay bedroom ɗinsa, akan gadon ya kwantar da ita yaja blanket ya rufeta da shi yana yi mata peck a kumatu. Zaytuna kuma ta dinƙa shigo da uban kayan da ya siya tana ajiyewa, ta tsaya tana kallonsa yanda ya zube a gaban gadon gwiwoyinsa duk a ƙasa ya riƙo hannunta yana kallon fuskarta kamar zai haɗiyeta, ko me neman gafara ko wanda akace in ya tashi za'a saceta, ta sauke numfashi tana tunanin ta yanda za'a faɗi wannan aure dai, da kuma yacca za'a karɓe shi, sannan ta ankarar da shi cewa an fara kiran sallah a masallaci. kansa kawai ya gyaɗa mata alamar yaji, ita kuma tasa kai ta fita daga ɗakin haka kawai tana jin faɗuwar gaba da kuma tausayinsa. da ƙyar ya iya miƙewa yaje yayi alwala ya fito shap shap, ya ƙara zubewa a gaban gadon yana shafa fuskarta, ji yake kamar ya bari kawai yay sallarsa a gida ba sai yaje masallaci ba. ya kamo hannunta me ciwon wanda hakan yasa ta ɗan motsa amma bata tashi ba, sai ya dakata da motsin da yake yi, ya dinƙa kallon yatsun yanda suka koma, ta ƙara basa tausayi sosai yana jin kamar ya ciro zafin ya dawo da shi jikinsa, yana jiyo sautin ƙarar da ta ƙwala tana kiran sunan Ummi. jin ƙarar buɗe ƙofa yasa shi waigawa, ganin Bello yasa ya miƙe da sauri yana haɗe rai tare da ɗaukan key room yace da shi,"lafiya?". Bello ya kalli Fillo sannan ya kallesa yace,"uban me ka yiwa ƴar mutane?". Turaki yace da shi,"ina ruwan munafuki da abinda ya shafeni ni da matata". Bello yay dariya yace,"you find the solution right?". yace,"you don't have any access to worry about that, that's my personal issue, so get out". ya faɗa yana nuna masa ƙofa. Bello na kallonsa ido waje yace,"in fita daga ina?". Turaki ya kuma ɗaure fuska yace,"i don't want to waste my time masallaci zanje, dan Allah fita". ya faɗa yana tura Bello. a ƙufule Bello yace,"dilla Malami alwala zanyi ko baka ji ana kiran sallah ba ne". yace,"ba anan kaɗai ne akwai famfo ba, in ba zaka iya shiga other toilets ba sai ka bari kayi a masallacin, ko in kaje gidanku kayi". Bello na ƙunshe dariyarsa yace,"ban key ɗin zan rufe idan na gama". Turaki yay masa wani wawan kallo yace,"ka rufe ina in ka gama?". yace,"to ai naga kamar saurin da kake yi ne yasa ba zaka iya jirana nai alwalar ba". Turaki ya juya ya kalla Fillo na baccinta peacefully, yay ƙasa da muryarsa yana cewa da Bello,"kayi a hankali mana karta tashi, dan Allah dan Annabi kayi haƙuri kaje toilet ɗin Khaleel ko na Sameer kayi".  da rainin hankali Bello yace,"to ni anan naga damar yi dan haka ba inda zanje, mene za'a ɓoyen da za'a hanani alwala, shigowarka ai bai isa har ka aikata wani abu ba". Turaki ya rumtse ido yana jin kamar ya saka masa ƙafa yace,"kaiwa Allah ka bar ɗakin nan Bello, baka san zafin da nake ji a zuciyata ba kana kalle min matata kwance akan gadona, kai baka san haramun bane hakan?, Allah banda bana so ta tashi tuni nasa maka ƙarfi ka fita". Sai da Bello yaga ransa ya ɓaci sosai sannan ya juya ya fita, yana faɗin,"sannu me mata". Turaki ma yabi bayansa da sauri yasa key ya rufe ƙofar. yana kallon Bello tsaye ta ƙasan ido yace,"maye kawai". Bello yay ƙwafa yace,"ka buɗe ɗakin sai in nuna maka ƙarshen maita a gaban idonka". Turaki yaja tsaki yay gaba bayan yace masa,"mahaukaci, kuma ka bar min ƙofar ɗaki in ba haka ba na dawo na sameka Allah sai na ji maka ciwo". ana idar da sallah ko cikakken azkar bai yi ba ya baro masallacin, kuma tun bai shigo gida ba ya kira Zaytuna yace ta kira Ummi ta faɗa mata Fillo zata kwana a wurinta. Zaytuna da ɗan tsoro tace,"but Hammah kasan at any time Mum zata zo ɗakinka ko". yace,"zance mata zan kwana office saboda wani aiki". yana faɗar hakan ya kashe wayarsa yaci gaba da tafiya a gaggauce, a parking lot ya sami Bello ya fito zai tafi, bai ko tsaya ba ya wuce shi fuskar nan babu ko annuri kamar bai taɓa sanin Bello ba, Bello ya bisa da kallo yana dariya sosai. sai da yay me isarsa sannan ya ɗaga wayarsa ya kira Turaki, yana picking yace masa,"in tafi?". Yace,"ehh tafiyarka". daga yanda yake maganar a daƙile yasan haushinsa yake ji. yace,"baka buƙatar shawarar tawa kenan?". yace,"ehh bana buƙata". ya faɗi hakan yana kashe wayar. tun a masallaci hankalinsa ke kan Fullo, yana tafiya yana haɗa hanya saboda rashin ganin hanyar da kyau, hoton fuskarta kawai ke haska masa, a yanzu ma da zai buɗe ɗakin hannunsa duk rawa yake yi. yana buɗewa ya ganta tsaye a bakin ƙofar dama jira take yi a buɗe, ganin tana neman saka kai ta fice yay saurin tura ƙofar ya saka key ya kama hannunta ya kaita bakin toilet yace,"shiga ki alwala". ya faɗa yana tamke fuskarsa dan yaga kamar sai yayi hakan tukunna zasu dai-dai da ita. kuma bata musa ba ta shiga toilet ɗin jikinta sai kyarma yake, ba jimawa ta fito tana kyaɓe fuska kamar zata yi kuka tana yarfe hannun me ciwo, ya kamo hannun ya dinga hura mata iskar bakinsa me ɗumi har sai da ruwan wajen ya tsane tukunna ya ƙyaleta. ya riƙe hannunta yaje ya shimfiɗa mata darduma ya buɗe closet ɗinsa ya ciro sabon hijab da Granny taje saudiyya ta taho dasu ta raba musu tace suyi kyautarsa, shi kuma baida wanda zai bawa hakan yasa ta ajiyarsu suna nan kusan guda biyar. Fillo taƙi karɓar hijab ɗin har hannunsa ya ƙage, ya ƙara ɗago da hannun ya miƙa mata taƙi karɓa, shi dai ya san mayafinta na mota balle tace da shi zata yi. ita ko ta bisa da kallo da mamakin zuwan hijab cikin kayansa, zuciyarta taji tana neman dasa mata wani banzan tunani tayi saurin kawarwa, itama ta haɗe rai daidai da yanda ya haɗe nasa ta turo baki ta bar kusa da shi ta tafi kan dardumar tana kunce ɗankwalin kanta ta yafa. kawai sai ya tsaya yana kallonta da mamaki baki a buɗe yace,"a hakan za ki sallar?". ta ɗaga masa kai kawai, abinma sai ya kusa basa dariya, ya tafi yaje ya tsaya ta gabanta yana ƙare mata kallon mamaki da kyau, bilhaqqi da wannan guntun ɗankwalin zata yi sallar tunda gashi har kabbara tayi, mamakinsa bai ƙare ba kawai yaji ta fashe da kuka tana cewa,"to ni ba zanyi da wannan hijab ɗin ba". ya kalli hijab ɗin ya kalleta sannan yace,"ba'a sallah da irinsa ne?". ya tambaya da gaskiyarsa saboda irin me kwalliyar nan ne na saudiya. taja majinar hancinta tace,"ni kawai ba zanyi da shi ba". ya ƙara gyara zaman hannunsa a ƙirji yace,"saboda?". tace,"to ai ban san na waye ba". Yace,"aina kika ga na ɗauko?". ta ɗan kallesa tace,"to me ya kawo kayan mata cikin kayanka?". Yace,"sawa nake idan zan fita". bata kulasa ba kawai ta tsuguna ta ɗauki dardumar ta bar wajen ta sauya wuri, zata tayar kawai taji ya saka mata hijab ɗin yana gargaɗinta akan,"Allah kika yi gigin cirewa sai na ji miki ciwon da yafi na ɗazu". Ta kallesa tace,"da ma kana sane?". ya bar wajen yana faɗin,"ehh ina sane sai ki rama". tayi masa shiru ta tayar da sallar, saboda bata son lokaci ya ƙure mata shisa ma bata sa masa darun sai ya buɗe mata ƙofar ta fita ba. tana idarwa ta yasar da hijab ɗin a wajen ko adu'a bata tsaya yi ba ta nufi ƙofa, ta dinga murɗa handle taji ta kasa buɗewa, sai tayi ƙasa da murya ta shiga roƙonsa tana cewa,"dan darajan Allah kazo ka buɗe min, Maama ce fa ta kirani kuma ko wurinta banje ba, kaje ka ɓallo min yatsuna, kuma ni Allah bana so kake min irin haka, na faɗa maka bana so babu kyau kana kawo ni ɗakinka ka kulle, babu kyau kana taɓani, kuma ai yanzu kai ba yaro bane tunda ka yi aure ka daina irin haka". ya ɗaga ido yana kallon yanda ta rufe ido tana ta maganar kamar me shirin sa masa duka, yaci gaba da buɗe ledar kazar da ya ɗauko yace,"zan buɗe miki amma sai in kiyi duk abinda nace". tace,"ai nasan halinka". yace,"wane hali gare ni?". tace,"ai ko nayi ba zaka buɗe ba". yace,"ki ci gaba da saka ni magana kici gaba da zama anan, tunda nace miki zan buɗe ai zan buɗe, but in kinyi abinda nace". tana hararsa tace,"to rantse da Allah". kamar ƙaramin yaro yace,"Allah da gaske". tl Tace,"to me zan maka?". ta faɗa still tana tsaye bakin ƙofan, ya kalleta yana ɗan ƙunshe dariyarsa yace,"to anan zan saki aikin?". ta turo baki gaba ta taho kamar mara laka, har ta ƙaraso inda yake bai ɗauke idonsa akanta ba. ta tsaya ƙeƙam akansa yace,"hau saman kan nawa sai ki tsaya da kyau". ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"wai mene hakan?".  ya jawo ledan fruite ɗin yana yanka abarba yace,"abinda yay hakan shi yay hakan,  sai an tambayeki tare aka haife ku da Kuka kice ba haka ba". yaci gaba da yankan lemonsa yana kallonta ta gefen ido, ganin zata bar wajen yace,"dawo". ta tsaya ya ɗago yana mata nuni da gefen gadon yace,"zauna". kamar za tai masa musu sai kuma ta zauna tana aikin kumbure-kumbure. zai kama hannunta ta janye tana neman fashewa da kuka tace,"nace maka babu kyau, Allah zan faɗawa Mum". ya ɗaga gira ɗaya yace,"i will escourt you". ta langaɓar da kai cikin wata iriyar shagaɓar da bata san sanda tai ba tace,"Allah to sai in faɗawa Baffa". da sauri ya zaro ido waje yace,"kice masa me?". tace,"ince masa Turaki yana taɓani kuma har kulleni yake a ɗakinsa". Ganin da gaske take maganar yay saurin cewa,"Allah ya baki haƙuri". ya faɗa yana dawowa gabanta ya gutsuro kaza ya kai bakinta,"wannan za ki cinye sai in barki ki tafi". ta kallesa ta kalli gudar kazar sannan tace,"duka?". ya girgiza kansa,"a'a iyaka yanda likita yace kici". ya faɗa yana kama hannun ciwon da ƙara cewa,"wai sai kinci iyakar yanda fatar nan da ta loma zata ciko". ta kalli yatsunta da fatarsu ta shafe sannan ta kai hannun hagunta zata karɓa ya janye yace,"kafirai ke cin abinci da hannun hagu, kawai ki yarda in taimaka in baki tunda dai baki da hannun musulmai". ba yanda ta iya haka ta dinga amsar naman da ya gutsuro yana bata, tun tana kawar da kai tana ƙin karɓa har ta gaji ta dinƙa karɓa a dole tana ci, bai ƙyaleta ba sai da yaga taci da yawa sannan ya ɗauko madarar kwali ya bata itama sai da tasha rabi sannan ya yarda ya barta, ya bata ayaba da kankana suma tasha tana jin kamar zata yi amai saboda ƙoshi, ita dai kallonsa kawai take yi tana jin wani irin abu tare da ita. ya tattare komai ya kaisu gefe sannan ya ɗauko jakar uban choculates ɗin ya ɗauko ɗaya ya buɗe ya kai bakinta, ta kauda fuska tana yamutsa fuska tace,"na ƙoshi fa, zanyi amai". ya ɗauke yana faɗin,"ashe ba ki shirya fita a ɗakin nan ba". da sauri ta janyo hannunsa ta kai choculate ɗin bakinta ta gutsura sai ɓata fuska take yi, a haka sai da ta shanye guda ɗaya tass tukunna ya kafeta da ido yana kallonta da wani sihirtaccen murmushi. bata hanasa kamo hannunta me ciwon ba, ya tmbayeta,"yana zafin ko ya daina?". Tace,"yana zafi sosai dauriya kawai nake yi, kaine ina ta maka alama ka datse min hannu kaci gaba da masifarka, dan Allah ka mayar dani wajen likitan ya yanke min su na huta, kuma dan Allah ka rage masifa in ba haka ba wataran zaka iya ɓallani gaba ɗaya". ya shafo wuyansa yana wani irin murmushi da yake jin yana motsa ilahirin jikinsa da wani feelings na daban. sai taga ya sauke daga kan stool da yake zaune ya zauna gaban ƙafafunta, sannan ya ɗora kansa da hannunsa ɗaya kan ƙafafunta yace,"idan aka yanke kuma da wanne za kike wa mijinki ƙunshi yana kallo yana jin daɗi?, a barsu dai insha'Allahu zuwa safiya zasu daina zafin". ta ture kansa da ɗayan hannun tace,"ka ɗagani ba kyau". ya riƙe hannun ya mayar da kansa yana cewa,"naji, Allah kuma kika ƙara ce min ba kyau sai kin kwana a dakin nan yau". tai shiru tana sakin kukanta mara sauti, ya ɗago kansa haɓarsa kan gwiwarta yana kallonta sosai yace,"ai dama ranar nan kince min ni ke saki kuka, dan haka yi me isarki tunda yau Allah ya haɗa mu". da mamakinsa sai yaga ta saki kukan sosai, sai turesa daga jikinta take yi tana so ta tashi, shi kuma har ga Allah yau karo na farko kenan da yaji kukan nata na masa daɗi saɓanin da sai ya dinga jin kukan na haifar masa da jin zafi a zuciyarsa. har tsawon minti uku bai daina kallon yanda take da bakin kukan ba kamar yarinyar ƴar 3years, yasa wayarsa yana ta mata vedio, dan kansa dai yaji kukan ya fara taɓasa tukunna ya tashi ya kamota ya miƙar da ita. jikinsa ya janyota ya rungumeta yana lallashinta yana bata haƙuri, ita dai bata daina kukan ba kuma ba tai ƙoƙarin fita daga jikinsa ba. a ranta kuwa rayawa take yau babu abinda zai hanata faɗawa Maama irin wannan abinda yake mata. ya kai bakinsa saitin kunnenta ya kira sunanta, tana shagwaɓe murya tace,"ni Fullo sunana ba Fulani ba". Yace,"ba haka naga damar faɗa ba". Ya faɗa yana kai hannunsa saman sumar kanta. tasa ƙarfi tana ture shi tana faɗin,"dan darajan Allah ka ƙyaleni in fita, wallahi hakan da kake yi babu kyau, ni fa ba muharramarka bace, kuma idan wani ya shigo ɗakin fa?". yace,"zan bar ki ki wuce yanzu i promise, but you answer me first me yasa kika dinƙa taimakona?". ya faɗa yana janyeta daga jikinsa yana kallon cikin ƙwayar idonta, ta ƙanƙance ido tace,"taimako kuma?, wane irin taimako na maka ni kam?, ni ban taɓa maka taimakon komai ba, kaine ma ka taimaka min aka kulle Amir". ya matse tsintsiyar hannunta yana cewa,"kar na ƙara jin kin ambaci sunansa ko ba'a gabana ba". ya faɗa da sautin ɓacin rai da kuma kashedi me kyau. tace,"to ka sakeni in tafi". yace,"fara ban amsata tukunna, asirikan da kika dinga ɗaukewa akaina me yasa kika ɗauke su?, me yasa baki bari sun same ni ba?, kuma me yasa baki taɓa faɗawa kowa ba?". tai ƙasa da idonta tana so ta ƙaryata zancen nasa sai taji hannunsa a haɓarta ya ɗago fuskarta yana ɗagamata kai,"ehen am all ears, ba kuma na son ƙarya dan nasan komai". tayi narai-narai da idanu tace,"ni fa duk ban san me kake cewa ba, ni waye yace maka na ɗauke asiri akanka?". yace,"bakinki". ta waro ido waje tace,"da yaushe?". Yace,"ranar da kike bawa ƙawarki labari a asibiti, accident ɗinki na farko da na kaɗeki". tace,"da ma kaine ka kaɗe ni akace wani ne?". Kan yay magana ta tari numfashinsa da faɗin,"shima kana sane ka kaɗeni?". ya galla mata harara da cewar,"ehhh sai ki haɗa duka har marinki ki rama, yanzu amsa min tambayata". ta tankaɗe shi daga gabanta ta bar wajen da sauri, tana zuwa bakin ƙofa ya isa ya fizgota ya haɗeta da bango yana faɗin,"Allah you are going no where sai kin amsa min tun yaushe kika sanni?, kuma me yasa kika min asiri?". hakan yasa ta sakin kuka sosai, tana rantsuwar,"Allah ni ban taɓa saninka ba sai da na fara aiki a gidanku, sunanka kawai na sani ajikin takardar da akai maka asiri, amma wallahi bani nayi maka ba, banma san su waye ba jinsu nai kawai suna faɗa, kuma ma ai saboda idan na faɗa ba za'a yarda da ni ba shisa ban faɗawa kowa ba, ina tsoron kar ace ƙarya ne ni nayi maka, amma na rantse da zatin Allah bani ce nayi maka asiri ba". tai maganar idanuwanta a rufe, dalilin ba zai iya jin kukan ba ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"na yarda daina kukan cry cry Baby, kanki zai ciwo za ki zazzaɓi". tana fizgar numfashi da ƙarfi tace,"wallahi Allah bani bace kuma ban san su waye ba". ya ƙara yin ƙasa da murya very calmly yace,"ohh nace na yarda, na yarda ba ke kika min ba shikenan daina kukan haka, ko ba kya so na barki ki tafi?". da sauri ta girgiza kanta,"ina so". yace,"to inji kinyi shiru sai in barki ki tafi". ɗiff ta ɗauke wuta kamar ba ita ta cika ɗakin da kuka ba yanzu, ta lafe a chest ɗinsa tana jin yanda heart ɗinsa ke bugawa ba irin yanda ta san ainihin bugun zuciya ba, shima fuskarsa kwance akan gashinta ya lumshe ido, wayarsa na ta uban ringing bai ma san anai ba. har aka turo ƙofar ɗakin aka shigo daga shi har ita ba wanda yaji motsin buɗe ƙofar balle kuma motsin mutum. Hajiya Ramla tayi mutuwar tsaye daga inda take tana neman bango ta dafe, kafin dai tayi ƙarfin halin ɗaga ƙafarta da take jin kamar ta mutu ta dawo saitin inda zata ga fuskar wacce yake rungume da ita haka, bata san ba ko matar tasa ta dawo basu sani ba, sai dai tana zuwa ganin fuskar Fullo wacce idanuwanta ke lumshe yasa tayi saurin ja da baya tana dafe bango da furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. wannan dogon salatin da taja cikin razani shi ya dawo da Turaki cikin duniyarsa, ya buɗe ido a tsoroce jin muryar Mum akansa, ya kalleta ya juya ya kalla ƙofa sannan ya juyo ya kuma kallonta, sai kawai ya saki Fillo yana ja da baya, lokaci ɗaya sai ya dawo kamar wanda ya kashe ɗan sarki aka gurfanar da shi a gaban sarki. Mum ta bi ɗakin nasa da kallo sannan ta tsayar da kallonta akansa, ta tattaro yawun bakinta da ƙyar tace,"Babana, me nake gani haka?, kai ne da kanka tare da wadda ba matarka ba?". sai kawai ta ɗaga hannu ta wanke shi da marin da ya kai fuskarsa ƙasa, da kanta ta ɗago da shi ta ƙara wanke shi da wani sabon marin da ya kaisa ƙasa gaba ɗaya gwiyoyinsa suka zube a gabanta. Zaytuna tasa hannu ta rufe bakinta tana fashewa da kuka, tun ɗazu take kiransa a waya bai ɗaga ba, abinda take ta so ta faɗa masa kenan ga Mum nan. Fullo dai tuni ta durƙushe a wajen tana kuka sosai kamar ranta zai fita, cikin ƙunar rai da zafin zuciya ta rarumi lamp zata buga masa Zaytuna tayi saurin riƙe hannunta tana faɗin,"Mum ki tsaya kiji". tayi wancakali da ita gefe tai kansa tana kai masa ƙafa ta ko'ina. "mutumcin gidan namu zaka zubar mana?, dama abin da na haifarwa kaina kenan?, sheɗani na haifa dama ban sani ba?". yay saurin ɗagowa yana kallonta idonsa na hawaye yace,"Mum". bata barsa ya faɗi abin da zai faɗa ba tasa ƙafa ta daki gefen cikinsa. "kaico, kaico da haihuwar irinka, nayi dana sanin haihuwarka, me ma yasa na saka maka sunan da ba zan iya kiranka da shi kai tsaye ba na zazzageka, me yasa nake jin ba zan iya tsine maka ba kai tsaye, wallahi na tsani ganinka, kai ba ɗana bane, yau sai dai ko ni ko kai a gidan nan". ta ƙarashe maganar dai-dai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa a rikice, tayi fatali da kwalbar da taga Mum ta ɗauka zata rotsa masa, ta riƙeta da kyau tana cewa,"me idanunki suka gane miki your excellency da har ba za ki iya excusing ɗinsa ba". Mum na huci sosai kuka na zuwar mata tace,"kin san i spent morethan 5minutes a bakin ƙofar nan ina jiyo kukan yarinyar nan tana roƙonsa akan ya rabu da ita, amma ɗan banzan yaron nan yaƙi barinta ƙarshe da na buɗe ɗakin ajikinsa na ganta rungume da ita tana sauke numfashin wahala, bai ma san na shigo ba tsabar ya riƙa a iskanci, ki barni kawai na kashe shi Madina ba zamu zauna da gurɓatacce ba wallahi". Hajiya Madina taja da baya tana neman faɗuwa, tayi saurin dafe bango saboda daina gani da ta fara yi, ta shiga tashin hankali na farat ɗaya da take jin kamar zuciyarta na neman bugawa, batun hawan jini kuwa tasan tuni ya hau, tabi Fillo da ke kuka sosai da ido, sannan ta dawo da kallonta kan Turaki bata san lokacin da ta zube ba a gabansa, nan da nan hawaye ya shiga sauko mata. tana magana da ƙyar tace,"this is not the background i gave you, ba foundation ɗina bane wannan, dan Allah na roƙeka ka ƙaryata abin da idanuwa da kunnuwa suka ji, me babban suna me ya sameka?, me kaje ka sha da har ka nemi ka aikata abin da baka taɓa aikatawa ba tsawon shekaru talatin da biyar?, ina kaje aka baka wani abu kasha?, me yasa ɗazu baka ce min in barka kaje wurin matarka ba kana buƙatarta?, me ƙaramar yarinya kamila kamar Fillo tayi maka da zaka lalata mata rayuwa?, me babban suna me nai maka da zaka saka min da hakan?, so kake ka kashemu ko so kake kace mu mutu mu bar maka duniyar?, ashe da rabon kaine silar yanke farin cikin rayuwata?, ban yafe maka ba me babban suna, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, da ƙarin cewa,"ba tarbiyyata bace wannan me babban suna, ba haka na raineka ba, wannan sabon halin me muni daga ina?". Mum tace,"ki matsa daga gabansa kar na fallatso miki jini, ki matsa nace miki". ganin abin da take ƙoƙarin aikatawa Samha tai saurin doka tsalle ta dire a bayanta tana rirriƙeta. Zaytuna ta duƙe a wajen tana cewa,"Maama duk fa ba yanda kuke zato ba ne, dan Allah ku barsa yay muku bayani". a fusace Maama ta dunƙule hannu ta kai mata naushi ta baya tai mata wani mugun duka a hanci, tsananin zafi yasa tai shiru tana dafe hancin da take jin kamar ya cire. Turaki ya dinga kallon Maama dake ta kuka a gabansa, kuma irin mugun kallon da take masa in har ya bari ta miƙe akansa sai ta kaisa har lahira, ya ɗaga kai ya kalli Mum dake faman kokawa da Samha da Khaleel tana so ta ƙwace daga riƙon da sukai mata ta rotsa masa kwalbar hannunsa. ya rumtse ido sosai ya daki kansa da bango sannan ya buɗe baki yace,"Maama she is my wife, na bayar da sadakinta 5months da suka wuce, na damƙa sadakinta a hannun mahaifinta". "what?!!!". abin da Maama da Mum da Baffa da ke shigowa yanzu suka faɗa tare. Bello ma da ke zuwa yace,"ehh Maama ya aureta tun da daɗewa". *Vote, Comment and Share.* [9/3, 07:45] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *41* with confusion Baffa ke kallon Turaki, kuma tashin hankali da damuwar da ke tattare da Mum da Maama sai suka juye zuwa tsantsar mamaki. Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifta ido, so take ta tabbatar da idan a hayyacinsa yay wannan maganar, kamar dai ba ɗanta ba an sauya mata wani, kuma kamar dai yasha wani abu da ya juyar da tunaninsa. Mum ta jefar da kwalbar hannunta, ta mayar da ƙwayar idonta kan Bello wanda ganin zata kallesa ɗin yay saurin sauke idonsa ƙasa. Baffa yay ajiyar zuciya wadda babu wanda bai jita ba, muryarsa ta fito da amon da babu wanda bai sha jinin jikinsa ba acikinsu, ya juya zai bar ɗakin yace,"ku sameni a parlo". wannan sautin muryar tasa da kuma yacca ya juya ya fice ɗin Turaki ya tabbatar da ya gama shiga uku, Bello ma ya ɗora hannu aka ya furzar da wata iska daga bakinsa, ya san Baffa ya san ya faɗansa idan ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, yana da masifar son ƴaƴa shisa ma ba ya iya musu faɗa, but baya tolerating shits, ya san ba zai taɓa ɗaukar wannan kwaɓar da Turaki yajawa kansa ba, bayan wannan ɗan guntun jawabin da yay bai kuma san ta inda zai fara yin wani ba in aka tsaresu. Mum tazo ta wuce ta kusa da shi fuuu kamar zata tashi sama, kallo ɗaya zaka mata ka san a fusace take. Turaki yabi bayanta da ido kafin ya maida kallonsa kan Maama ya buɗe baki zai yi magana, tayi saurin ɗaga masa hannu,"dakata, kar ɗan ƙwaya ya sake yace zai min bayanin da kaina ba zai ɗauke shi ba". sai kuma ta miƙe tai bakin ƙofa tana ƙara faɗa masa,"kar in jini a cikin lamarinka". ta fice tana jin ita bama tasan actual tunanin da zatai akan maganar tasa ba, dan magana ce yay ba irin ta waɗanda ke cikin hankalinsu ba. kowa ya fita a ɗakin aka bar Turaki da Fillo kawai, ya miƙe yana jin kansa na sara masa, Bello ya dawo yay tsaya jikin ƙofar yana kallon abokin nasa da tausayi yace,"ka taso muje tun wutar da sanyi sanyinta before ta balbala ta ƙona mu". Turaki ya kallesa ya ɗauke ido, ya mayar da kallonsa kan Fillo da har yanzu take a wajen a duƙe kowa ma ya manta da ita, kukanta take tayi bata daina ba, ya tafi yana jin jikinsa kamar mara lafiya ya isa inda take, ya ɗagota tsaye yana faɗin,"please stop this crying its hurts me alot, from today ba zan ƙara saka ki hawaye ba, i promise". ya faɗa yana ƙoƙarin ɗora kanta a ƙirjinsa, sai ta hana hakan tana ɗago da kanta ta kallesa tace,"me kace musu?". Ya rufe ido ya buɗe yace,"ce musu nayi ke matata ce". ta kasa ɗauke idonta akansa saboda itama a shock take, and gani take kamar ya sha ƙwaya ne shisa yake wannan maganar da hankali ba zai ɗauka ba. "shi auren film ne dama?". yana kallonta yace,"ba film ba ne, namu ɗin ne dai ya zama kamar a film". ya faɗa yana matso da ita ta ƙwace daga riƙon da yay mata ta tankaɗa shi baya, cikin sheƙar sabon kuka tace,"leave me alone, Allah i hate you, ji a matsalar da ka jefa ni alhalin ni babu wanda ya taɓa riƙe hannuna ma, shikenan yanzu zaka ja Ummina ta yanka ni". tai maganar tana wani kukan sosai. da damuwa sosai yace da ita,"muje". taƙi tafiya, ransa a ɓace ya doka mata tsawa,"nace muje ko". jikinta ya fara kyarma ya kama hannunta suka fito, tafiya suke kamar marasa lafiya, ji yake kamar babu komai acikin kansa, kamar babu yawun da zai yi musu bayani, taƙaimaimai ma bai san ta ina zai fara ba. Bello dake daga gefensu yace da Fillo,"ki ɗaga ƙafa dan Allah, acikin matsala fa muke". suka haɗa ido da Turaki yace masa,"kaita innalillahi ni inata yin hasbunallahu". sai da Bello yay adu'a sosai tukunna ya iya saka ƙafarsa cikin parlon, ƙafafun Fillo suka fara shiga sannan na Turaki, idon Maama ya sauka akan hannunsa dake riƙe da nata wanda da alama forcing nata yay ta ƙasa ƙwacewa, lallai me babban suna ya riƙa da yawa. bai yi gigin nufar inda Mum da Maama suke ba, still hannunsa na riƙe dana Fillo ya wuce ta bayan kujerar da suke suka zagayo ta ɗaya side ɗin, Fillo tayi-tayi ta ƙwace hannunta ya hana hakan har suka zo tsakiya ya zauna sannan itama ta zauna, duk akan idon Baffa dake jinjina ƙarfin hali irin nasa, sai da suka zauna ya saki hannun nata tayi saurin matsawa ta bar kusa da shi. Baffa ya ajiye wayar dake hannunsa yana girgiza ƙafa, sai da yaywa Turaki kallon tsab ya tabbatar ba ƙwaya ce ke aiki a jikinsa ba sannan yace da shi,"maimaita abinda kace ɗazu". Turaki yace,"Baffa...". ganin zai masa dogon jawabi ya dakatar da shi wajen ɗaga masa hannu. "ce nayi ka maimaita abinda kace ba dogon turanci nace ka min ba". Turaki ya sauke numfashi ya sunkuyar da kansa yace,"na aureta tun 5months da suka wuce". yana yin shiru Baffa ya maida kallonsa kan Bello yace,"ehen?". yay saurin ɗaga masa kansa,"ehh Baffa da gaske ne ya aureta". Baffa ya sake cewa,"kai ka zama waliyin right?". da sauri ya girgiza kansa ganin irin kallon da Baffa ke watsa masa yace,"a'a wallahi Baffa, ban ma san yay auren ba sai after yake faɗa min, wallahi ban san yanda auren...". tsawar da Baffa ya sakar masa ta dakatar da shi,"shutup, waye marainin wayonka anan da zaka faɗa masa ba da kai akayi komai ba, marasa mutunci banza ƴan iska marasa hankali, waɗanda baku ɗauka iyayenku a bakin komai ba, wato har kuna da bakin ma da kuke maimaita min ko?, gaku kun balaga bari kuyi gaban kanku, to tunda ka aureta sai ka saketa yanzu dan ni ba zan yarda da wannan auren iskar ba, ba'a gidana ba, ba'a zuri'armu ba, ka saketa yanzu nace sannan ka min bayanin uban da yasa kayi gaban kanka". furucin Baffan na ƙarshe ya doka wata tsayawa acikin kan Turaki, bai san lokacin da ya ɗago yana kallon Baffa da wani bala'in tsoro ba, muryarsa na breaking yace,"saki kuma Baffa, dan Allah kar ka yanke min wannan tsatstsauran hukuncin ba zan iya ba". Baffa dai ya riƙe haɓa couldn't stop looking at him, dama saboda ya ƙara tabbatar da abinda yace shisa yace ya saketa ɗin, kenan da gaske yake ya aureta ɗin tunda ga tashin hankali nan ɓaro-ɓaro akan fuskarsa saboda yace ya saketa, ya dinga kallonsa  da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, yayi aure kuma har 5months duk ba wanda ya sa ni, to waye ya ɗaura masa auren?, kuma when hakan ta kasance?. "kayi aure Muhammad?, wa yay maka auren?". Turaki ya ƙara yin ƙasa da kansa yace,"Baffa ni ɗaya naje, dama ina da niyyar zan faɗa muku". ran Baffa ya ƙara ɓaci yana jijjiga kansa yace,"kana da niyyar faɗa mana bayan kayi gaban kanka?, ka ɗaurama kanka aure ba tare da saninmu ba Muhammad?, kayi aure babu ni ubanka da nake raye, babu ƴan uwana, ka shiryama kanka aure kai ɗaya, yaushe ka zama ɗan iska har haka?, yaushe ka mayar da ni mutumin banza ban sani ba?". sai kuma yay shiru ya mayar da kallonsa kan Hajiya Madina yace,"dama har haka ku ka mayar da ni mutumin banza da wofi?". kan ya ƙara magana ta tari nunfashinsa,"ya dai mayar da mu ƴan banza da wofi, ko idan da haɗin bakina akayi kaga na bari anyi wannan zaman?, to ni wiwin ma da ya fara sha ban sani ba balle sanda yaje ya ɗaura ma kansa aure, saboda haka kayi jan idonka akansa shi ɗaya, inma ɗauresa zaka yi duk kayi ba damuwata ba ce". sai kuma ta kalli Fillo tace,"kema ashe tantiriya ce ban sa ni ba...". kuma bata ƙarasa ba Turaki yay saurin katseta da cewa,"Maama bata san komai ba itama". da mamakin da yafi na da Maama ta saki baki tana kallonsa, sai ya juya yay facing Baffa yay kneeling murya a hankali yace "Kayi haƙuri Baffa, na san nayi kuskure amma ka yafe min dan Allah, wallahi ba zan ƙara maimaita makamancin haka ba, ba zan ƙara aiwatar da abu ba da saninku ba, dan darajan Allah kayi haƙuri ka bani damar da zan maka bayanin da zaka fahimce ni". Baffa yace da shi,"ai na kawo ƙarshen komai, sakinta kawai zaka yi dan wannan gantalallan auren ba'a zuri'armu ba". Turaki ya rumtse idonsa yana jin kamar ya kurma ihu, ya dinga roƙon Baffa akan yayi haƙuri ba zai iya sakinta ba,"dan Allah Baffa kuyi min duk abinda zaku yi min amma karku ce in saketa ba zan iya ba, dan Allah ku bani damar da zan muku bayani ku fahimta". Baffa ya jinjina kai yace,"zo nan Muhammad". bai iya miƙewa ba ya dinga jan gwiwoyinsa har ya kai gaban Baffan, Baffa ya miƙa masa waya yace,"ka kirasa kayi masa bayani, ƙila shi ya fahimceka, dan ni ban da ta cewa dan lamarinka yafi ƙarfin tunanina". Turaki ya karɓi wayar hannunsa na rawa, tun bai kai ƙwayar idonsa kan screen ɗin ba ya san wa Baffa yake nufi da ya kira, yana kallo kuma yaga sunan Hakimi ne akai calling kawai zai yi, sai yaji kamar ya fashe da kuka sanin cewa in har Hakimi ya san wannan maganar tasa kuma ƙare, ina shi ina kiran wannan azababben mutumin ya faɗa masa laifin da yayi da bakinsa, he can't even imagine yanda Hakimin ma zai yi fata-fata da shi, abu mafi sauƙi ne a wurinsa yasa a ɗaure shi bayan ya raba auren, saboda haka sai yay switching wayar off ya riƙeta a hannunsa, ko giyar wake ya sha babu abinda zai sa yay ma Hakimi bayani da kansa, ba ma ya fatan maganar taje kunnensa, inma zata je gwara ace taje masa a sabon aure zai yi, ƙaramin laifi ma yana ɗaure mutum na tsawon shekaru balle wannan da shi kansa ya san bai kyauta ba, dan lamarin aure ba abinda wasa ba ne. Baffa ya ɗaga masa murya yace,"kana ɓata min lokaci Malami, ka kirasa kayi masa bayani da kanka nace, idan kuma ka bari na ɗau mataki da kaina zaka sha mugun mamakina, sai kayi zaton bani na haifeka ba Muhammad". Turaki ya kallesa hankalinsa a mugun tashe,  ya marairaice yana haɗa hannayensa yace,"don girman Allah Baffa ba sai an faɗawa Hakimi ba dan Allah Baffa, i beg you kayi min hukuncin duk da zaka yi min amma karka faɗa masa". sai kuma ya juya wurin da Maama take yace,"dan Allah dan Annabi Maama kuyi haƙuri, idan nayi muku bayani Allah zaku fahimce ni, nima ban san nayi kuskure ba sai daga baya, kuma na rasa ta yanda zan maku bayani ne shisa aka ɗauka tsawon wannan lokacin". Maama ta kawar da kanta gefe ɗaya bata ko kallesa ba, ita aurar Fillo fa ba shi yay mata ciwo ba, ofcourse yayi ba daidai ba, but da auren ya ƙare akan Fillo abin yayi mata daɗi, takaicinta ɗaya da aurensa zai ƙare a unprepared marriage, shikenan mafarkinta akan aurensa duk sai ya tashi a banza?, bacin irin ƙwallafa rai da cin burin da tayi da aurensa mussaman da ta gama saka Fillo acikin lissafin ƙarin auren nasa?, wancan an yisa ba shiri wannan ma kuma sai azo mata da wani zance na daban da hankali ya kasa ɗauka. "Maama please". ya ƙara kiran sunanta dan ya san ita ɗaya yake da ita a wurin nan, roƙon Mum won't favour him shisa ma yake tsoron kallonta. tausayinsa ya kama Maama sosai amma sai ta kawar ta dake ta kalli Baffa tace,"ka yiwa tufkar hanci kawai, ka kira Hakimin da kanka ka faɗa masa komai, mu ba iyayen banza ba ne da zai ja mana magana a bakin duniya, inma sallamarsa zaka yi ka sallame shi ya tattara komatsansa ya wuce ya bar mana gida, dan ni ba zan ci gaba da zama da ɗan wiwi ba, rashin sanin darajar iyaye har ina haka?, ai cin mutumci da rashin sanin darajar tamu yayi yawa". ya miƙe daga gaban Baffa ya nufi Mum, tana kallon ya taho ta dakatar da shi,"karka sake kazo inda nake, banda hurumi da kai. su ma ɗin da suka gaza ɗaukar mataki akanka har yanzu lokacinka suke da, ni kuwa ka iso gabana banga abinda zai hanani shaƙeka ba". sai kuma ta mayar da kallonta kan Baffa cikin ƙunar rai tace,"kai har yarda kake da shi akan ya auri yarinya?, ta ina zai soma ɗaurama kansa aure babu iyaye, shege ne shi?, ko kuma shi uban yarinyar ba ƙwaƙwalwa akansa?, ai kawai ka zartar masa da hukuncin haikewa ƴar mutane da ya nemi yayi, ka bugasa a jarida ka yaɗawa duniya, ba wai ka tsaya sauraron zantukan kare kai daga bakinsa ba, mu zai rainama wayo saboda a rabu da shi shine zai ce ya aureta, ko ya taɓa ganin anyi haka a film da zai ce zai kwatanta?, to ka zartar masa da hukuncin da ake ma ƴan iska kawai, ka mance ɗanka ne kayi alƙalanci dai-dai da yanda kuke ma masu ɓata ƴaƴan mutane, batun ya aureta ma bai taso ba ƙarya yake yi kare kansa zai yi". hankalin Turaki ya ƙara tashi matuƙa, ya zube yana dafe kansa sosai yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi tallahi na aureta, na rantse da Allah na aureta, idan ban mallaketa ba babu abinda zai sa ki samemu a yanda kika ganmu Mum, mahaifinta ma shaida ne shi ya karɓi sadakinta...kuma wallahi ni banyi auren nan domin rashin sanin darajanku ba ko kuma ci muku mutumci ba, wallahi na amince an ɗaura auren ne saboda tausayinta, saboda ban da yanda zan yi a lokacin". ya ɗaga kai ya kalli Baffa yace,"Baffa tayi min taimakon da ba kowa zai iya yi min ba shisa na aureta saboda ina ganin hakan shi ne mafi cancantar sakayyar da zanyi mata". "Taimako?". Baffa ya tambayesa. ya ɗaga kansa,"ehh Baffa, kuma ka tambayeta kaji". Baffa ya kalli inda Fillo take kamar yanda Hajiya Madina ta buɗe ido tana kallonta, kar dai ta faɗa masa duk shirin da su Samha suke yi akansa, kuma tunaninta bai kai ga nisa ba taji Fillo na cewa Baffa,"ni bai aureni ba Baffa, bai ma san a inda Abbana yake ba, kuma banyi masa taimakon komai ba". Turaki ya saki baki yana kallonta da mamaki, sai kuma yace,"ehh Baffa bata san na aureta ba amma ƙarya take yi wallahi tace bata taimakan ba, taimakon da tayi min ko wanda muka fito ciki ɗaya ba lallai ya iya yi min ba, ku a bata ƙur'ani ta rantse da shi bata saka kanta a haɗari ba saboda ceto ni daga hallaka ni da aka nemi yi, wallahi Baffa asirin da akayi min ta dinga bi tana ɗaukewa". Mum ta riga Maama da Baffa furta kalmar asiri, Fillo ta ɗago kanta a rikice tana kallon Baffa tana girgiza masa kai,"Baffa ba haka bane, ni ban san abin da yake faɗa ba". kwarjin da ke tare da Baffa yasa bata san sanda ta fashe da kuka ba tace,"wallahi Allah bani nayi masa ba, waɗanda ma suka binne asirin ban sansu ba, jinsu nayi kawai suna faɗa, ni kuma nasan bai yi musu komai ba shisa na dinga lalata musu aiki". Baffa ya kalli Hajiya Madina yace,"kira min Kakar yarinyar nan". abin da take shirin yi kenan dama, dan ta fara tunanin anya ba aljanu a jikin Fillo, ta ɗauka waya ta kira Kaka wadda taji ta ruɗe jin tace suzo yanzu cikin gaggawa. Mum ta dinƙa kallon Fillo cike da nazari, muryarta kaɗai ta isa ta shaida maka abinda ta faɗa gaskiya ne balle kuma ka kalli fuskarta da gaskiyar ta fito ɓaro ɓaro, to waye zai ma Babanta asiri?, akan wanne dalili?, lokaci ɗaya kuma cikin kanta da zuciyarta suka haska mata sunan Fulani Azima, take ta furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wanda yaja idon kowa kanta. kawai sai ta fashe da kuka tana jin wani zafi da tashin hankali, me sukai ma Azima haka a rayuwa?, cutarwar da tayi mata bai isheta ba sai da ta biyo ta kan ɗanta?. kukan nata kuma shi yasa Fillo hargitsewa ta fashe da kuka sosai tana girgiza kanta tana cewa,"wallahi Allah Mum bani nayi masa ba na rantse da Allah". Baffa yace da ita,"in har ba ke bace me yasa baki sanar ba?". tace,"Baffa ai nasan idan na faɗa ba lallai a yarda dani ba, kuma wataƙila ma ace ni nayi masa kuma wallahi bani bace". Hajiya Madina ta sauke numfashi, calmly tace da ita,"nutsu Fillo ki juyo ki fuskance ni". tana fizgar numfashi ta juyo ta fuskanceta kanta a ƙasa tana cewa,"wallahi Maama bani bace, wasu ne su uku, kuma ban sansu ba". Hajiya Madina tace,"kuma kin tabbatar asirin ne?". tai saurin ɗaga kanta,"ehh Maama haka suka ce, Allah ne shaidata". "amma me yasa baki taɓa faɗa min ba?". tace,"Maama ban san ta yanda za'a yarda da ni ba, kuma da naga duk na kwashe waɗanda naji sun faɗa shisa ban faɗa miki ba, kuma bana so ku shiga damuwa ma". Mum ta fashe da kuka sosai tace,"idan na yafe na wa ba zan yafe na Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji da ko waye yake da hannu akan lamarin nan, me yarona yayi mata tsakani da Allah?". Maama na kallon Baffa tace,"kai kam har wanne kalar zunubi ka aikata da ake bibiyarmu da asiri?". zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"wait Baffa, ya kamata mu fara sauraran maganar da yarinyar nan tayi, ni na san wacece ita fiye da tunaninka, tunda ta faɗi hakan tabbas haka ɗinne, beside ka duba ƙarancin shekarunta ta ina zata iya haɗa ƙarya irin haka farat ɗaya?, kai fa alƙali ne kayi nazari akan furucin nata mana". ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"yi min bayanin komai kinji, karki ji tsoro". Fillo ta shiga basu labari tiryan-tiryan tun daga ranar farko har zuwa rana ta ƙarshe da tayi wannan accident ɗin da Turaki ya bugeta, al'amarin yay matuƙar girgiza su, suka dinga salati suna maimaitawa, Mum dai kuka kawai take yi magana ma ta kasa, banda Hajiya Madina dake ta aikin tsinuwa tana jan muguwar adu'a akan duk wanda ma ya san da zancen za'ai asirin ba iya wanda yay ba. Ummi dai kallon ƴarta kawai take yi da mamakin da yaƙi barinta da kuma tsoron kar ace aljanu ke aiki a jikinta, dan jefa kai a irin wannan haɗarin sai mutanen ɓoyen. Mum ta sauko daga kan kujera ta rungumeta tana yi mata godiya da saka mata albarka, haka ma Maama, sun ma rasa kalar godiyar da zasu yi mata, kamar zasu haɗiyeta saboda son yarinyar da suka ji ya shigesu, matsayin da take da shi a zuciyar Hajiya Madina ya nunku a sa'i guda. Baffa dai yay shiru saboda abin ya ɗimauta shi sosai, abinda yaji yana faruwa a film da kuma wata nahiyar yau shi ne akan ɗansa har ma da matarsa. Turaki ganin yacca idon Baffa ke kansa yace,"kayi haƙuri Baffa, da na zauna nayi nazari shine naga babu da abinda ya dace na saka mata da shi sama dana aureta, kuma ni banje wurin mahaifinta da niyyar aurenta ba a lokacin, tausayi ne yasa na amince aka ɗaura auren babu shiri, kuma Baffa ina tsoron kar da kuce min baku amince ba shisa ban faɗa muku ba nayi gaban kan nawa, amma dan Allah dan Annabi kayi haƙuri ka yafe min". Baffa yace,"to wa yay maka waliccin auren?". yace,"ba kowa Baffa, ni da naje wurin Baban nata izinin auren naje nema shi ne yace sai dai na aureta a lokacin in ba haka ba zai bawa wani ita". Baffa yace,"kai kuma ba zaka iya rayuwa babu ita ba?". ya girgiza kansa da sauri yace,"a'a Baffa, kawai naji ina da son ta zama mallakina a sanda na san waye mahaifinta". Baffa ya girgiza kansa,"har yanzu labarin film kake ban Muhammad, waye zai ɗau ƴarsa ya aura maka babu waliyi kamar dai wani mahaukaci irinka?". yace,"idan baka yarda ba zan iya kai ka wurin limamin masallacin da ya ɗaura so you can believe me". Baffa yace,"why not wajen mahaifinta daka ce ka damƙawa sadakin?, ko kuma da limamin ku ka haɗa bakin ƙarya?". Turaki ya kalla Fillo da yake jin kukanta na taɓa zuciyarsa yay ƙasa da murya sannan yace,"saboda yana da son zuciya ba lallai ya faɗi gaskiya ba idan akaje wurinsa, mugu ne zai iya cewa ma bai san da maganar ba". Baffa yace,"kamar yanda kaima baka da gaskiya ba, becoux i cant believe cewan kaje kaima kanka aure ba tare da saninmu ba kawai saboda zuciyarka na ganin abinda ya dace kayi kenan, da ta taimaka maka kana so ka saka mata ba akwai hanyoyin kyautatawa da yawa ba? dole lallai sai ka aureta sannan zaka biyata da abinda tayi maka?". Turaki yay girgiza kansa yace,"kayi haƙuri Baffa, gani nayi ko duka dukiyarmu aka bata ba'a biyata ba". sannan yay saurin ɗauko wayarsa ya shiga file manager ya lalubo record ɗin da yayi yace,"kuma Baffa zaka yarda da ni in kaji wannan". su Maama sukai shiru suna sauraron Hayyo dake cewa,"ni idan har ka tafi ba zan yarda da cewa iyayenka zaka je ka kawo ba, ka ajiye sadakinta kawai shi ne nasan da gaske aurenta kazo nema, duk da ba ƴata bace amma zanyi abinda uba na gari ya dace yayi a matsayina na wanda yaga an haifeta a titi na taimaka musu ita da uwarta, in kuma ba sadakinta a yanzu ina mai tabbatar maka kana barin wurin nan zan aurawa Malam Mudi ita tunda nasan inda take, sai muje da hukuma aje wurin tsohuwar da ta saceta mu karɓota". haka suka dinƙa sauraron maganganun Hayyo har zuwa sanda Liman yace da Turaki ya ajiye sadaki, ya jiye maƙullin motarsa bayan ya shaida musu cewa shi maraya ne baida iyaye, Hayyo kuma yace ya ba shi ita sai su haɗu can su zama shege da shegiya su haifi ƴaƴan sunnah. Baffa ya dinƙa kallon wayar Turakin kamar Hayyo yake gani acikin wayar, Kaka ta zabga salati tana faɗin,"wallahi tallahi wannan muryar Hayyo ce gata nan tarrr, yanzu lalacewar tasa har ta kai ya sheganta yarsa?, kai jama'a wannan duniya ina zaki damu?, ina azzalumai suke so suje da ɗumbin alhaki?, me ya sami Hayyo ni ƴar nan?, ni da nake uwar matarsa ma yana cewa bai sanni ba?, to wallahi tallahi Fillo ƴarsa ce ta sunnah ma kuwa, mutuwar zuciya ce kawai irin tasa da yake cewa a titi ya tsinto su, amma ai Allah yana ji yana gani". Ummi na kuka sosai tace,"akwai Allah, akwai ranar hisabi, ko da na yafe zaluncin da Hayyo yayi min a zaman aurenmu ba zan yafe sheganta min ƴa da yayi ba, ba zan yafe masa ba sai Allah ya saka min". Fillo tai jikin Ummi tana kuka sosai da jin maganganun Hayyo da suke yi mata zafi, kukan da duk ya taɓa zuƙatan wajen. Kaka na kuka tace,"waye kuwa zai so haɗa jini da Hayyo banda ƙaddara". Baffa yace,"shi waye shi ɗin ne?". Kaka tace,"Hayyo ai sheɗani ne, ba zaka tabbatar da hakan ba sai ka aura masa ƴarka, matansa sunfi goma kuma duka babu wacca ya saka, kowacce gajiya take tayi da muguntarsa ta bar masa gidansa, da zarar ya sami abinda yake so a wajen mace shikenan kuma ta zama abar banza a wurinsa tun balle ki sami ciki saboda baya son ƴaƴa, ba ya aje abinci a gidansa kuma baya bari a fita a nema kuma baya yarda masu taimakawa su kawo masa". ta numfasa ta ƙara cewa,"kaga wannan". ta faɗa tana nuna masa Ummi, tace,"maraicin uba ne yasa tayi zaman gidan Hayyo, har ta haifi wannan ƴa bai daina dukanta ba, saboda kawai ta haihu har sau biyu kuma taƙi tayi zuciya ta bar masa gida, ita kuma ƴaƴanta kawai take tausayi duk da tana da ɗan banzan haƙuri, akan dalilin barinta gidan ma abinci aka aika mata daga gidan wata ƙawata yana zuwa ya haɗa da ita da wadda ta kawo abinci da wannan ƴa yay musu duka, sannan yay mata zagi na ƙare dangi irin zagin da ko dabba ba aiwa shi ba, mahaifinta dake ƙasa kansa na san sai yayi baƙin cikin wannan aure saboda kiran sunansa da yay yana zaga, kuma wallah banda wannan yaro yay jihadi ya aureta ina me maka rantsuwa da Allah siyar da ita zai yi, dan manyan ƴaƴansa mata 3 wallahi tallahi duk siyar da su yay, bafa siya irin ta abayar da sadaki ba, a'a! a taya ɗan mutum a ɗau kuɗi a bashi ya ɗauko yarinyar ya bayar a tafi da ita, kuma da bakinsa zai faɗa yace ya siyar da wance shi baida hurumin rayuwa da ƴaƴa". kowa ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zuciyar Baffa na tafarfasa yace,"siyar da ƴaƴa kamar ba ɗan mutum me daraja ba, ƙwarai ya zama dole hukuma ta kama shi". Kaka tace,"waye hukuma zata kama?,  Hayyon?, yo iyaye nawa ne sukai ƙararsa kuma da anje station yake fitowa, ai lamarin Hayyo sai dai a barwa ubangiji kawai". Baffa yace,"lamarinsa bana ƙyalewa ba ne, kafin ya bar duniya dole ya gane kurensa, hukuma wacca ta san aikinta ita zata kamasa a wannan karon, ba irin hukumar cin hanci ba". Kaka ta girgiza kanta kawai dan tasan hukuma ta kama Hayyo ba abu ne me yiwuwa ba, yo a cikin mugun halayen Hayyo wanne ta faɗa babba aciki?, ai bata faɗi komai ba dan wani abun dole sai an sirrinta. Baffa ya katse shirunta da faɗin,"gobe insha'Allahu zamu je tare da ku". tace,"to ai ya tashi daga gidan da muka sani, ance yayi kuɗi sun bar unguwar ne ma ko garin Allah masani". Mum tace,"indai ɗan garin ne sai aje gidan iyayensa, a kama mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole zai kawo kansa". Ummi tayi wani murmushi me ciwo, Kaka ma haka sannan tayi ƙarfin halin cewa,"ai babu wanda ya san iyayen Hayyo balle danginsa, duk iyayen da yake amfani dasu wajen neman aure na bogi ne, hayarsu yake yowa, kuma wallahi duk binciken mutum ba zai san ba iyayensa ba ne, hmmm Hayyo fa sai Allah, wanda ya sansa kawai shi ya sansa". su Hajiya Madina suka shiga jijjiga kai tare da jinjina lamarin, tausayin Ummi ya kama su da ita kanta Fillon. Baffa na kallon Turaki yace,"you did the right thing my son, auren yarinyar nan da kayi jihadi ne babba, and i am proud of you for that tun da har kai tunanin tsamota daga hannun azzalumin uba, kana da lada a wurin Allah insha'Allah, Allah yayi maka albarka, don't worry komai ya wuce, ina shaida maka naji daɗi ƙwarai da gaske da ya zamana mugun halin mahaifinta ka fara dubawa, ko ni me iya aura maka itace a sanda naji halinsa, but hakan ba yana nufin next time ka ƙara yin gaban kanka ba tare da ka sanar damu abu ba". Turaki yace,"insha'Allahu Baffa i won't repeat such a mistake again". yaji muryar Baffan yana sa ke cewa "na yarda da aurenku na kuma saka masa albarka, idan mahaifiyarta da kakarta sun amince kana iya tarewa da ita a yau, i will call Hakimi and inform him, and i will try all my best to make Boɗejo to understand so that ba za'a sami matsala ba...fatana ɗaya ka zama adali a tsakanin matan da ubangiji ya ƙaɗarta maka aurensu, Allah yay ma rayuwar aurenku albarka". Wani irin Relaxation breath Turaki ya saki tare da faɗin Alhamdulillah ƙasa-ƙasa kafin ya ɗaga murya yace da Baffa,"thank you Father, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ya bani ikon faranta maku iyaka ƙarshen rayuwata". sai ya kusa bawa Baffa dariya, kamar ba shi bane ya firgice a ɗazu ba, tun balle da yace ya saketa. Baffa ya kalla Kaka yace,"to Kaka ban san ku a yanda zaku ɗauki wannan auren ba, kun yarda da auren ƴarku da yay babu saninku ko baku yarda ba?". Kaka tace,"wanne irin rashin yarda Alhaji, wa zai ƙi haɗa jini da nagartattun mutane irinku ai sai dai idan bai samu ba, kuma wa zai ƙi yarda ya aurawa ƴarsa mutum kamar me babban suna, yaro me hankali da sanin yakamata, ai ni sai dai nace Allah ya albarkaci auren kuma mun gode sosai dan ka yiwa wannan ƴa babban taimako a lokacin da ya dace dan inda baka yarda ka amince da auren ba Hayyo siyar da ita zai yi wallahi, babu wani wanda yaywa alƙawarin aurenta". Mum na kallon Ummi tace,"Maman Fillo baki ce komai ba?". Ummi ta kalli Fillo dake jikinta tana kuka tace,"to ai ni gani nake yaronku yafi ƙarfin auren wannan ƴa, abun kamar kwata-kwata babu haɗi, ina shi ina auta?, but ba zanƙi ba dan nasan ƴata hannun na gari zata shiga insha'Allah, kawai dai akwai abunda nake dubawa ne". Ummi tana kallon Turaki tace,"amma me Babban suna zaka iya zama da ita?, kasan tausayi daban so daban, karka ƙwari kanka kace zaka zauna da ita saboda ta taimaka maka, shi aure dan so da ƙauna ake yinsa, in akace za'ayi aure dan taimakon juna kawai ba lallai aji daɗin zaman ba, anfi so ayisa in har da so da ƙauna ta yanda duk za'aji daɗin zamantakewar har ƙarshen rayuwa". Turaki ya shafo wuyansa bai ce komai ba, Mum tace,"kayi magana, dan ba zai yiwu mu baka ƴa ba alhalin baka shaida mana kana sonta ba, dan haka in har ka san ma baka sonta to a miƙo maka takarda kawai". da sauri ba tare da shiri ba yace,"ina sonta Mum". Hajiya Madina tace,"a ina ɗin?, ina son yake?". ya ƙara shafo wuyansa cike da kunya yace,"Allah ina sonta Maama". Hajiya Madina ta miƙe ta kamo hannun Fillo dake ta aikin kuka, tana dubansa take cewa,"ina buƙatar lefen ƴata nan da 3days kafin na fara tunanin ko zan baka ita". sai yanzu hankalin Fillo ya dawo jikinta, ta waiga ta dubi Turaki sannan ta kalli Maama tace,"Maama ai ni bana sonsa, ba zan iya aurensa ba". Mum ta kalleta tayi murmushi, ganin ba wanda ya saurareta ta fashe da sabon kuka tana cewa,"Allah Maama ni bana sonsa, ba zan iya aurensa ba dan Allah kice ya sakeni, ni taimakonsa da nayi saboda Allah nai, dan Allah ya sakeni". Ummi ta buga mata tsawa,"kul kar na ƙara jin furucin nan daga bakinki". Hajiya Madina tace,"a'a yi mata a hankali, da gaskiyarya ai, dan shi yana so kuma shikenan ita ba za'aji ta bakinta ba?". ta kalli Turaki tace da shi,"ka zo ka nemi yarda ƴata da amincewarta akanka, kwana biyu na baka, idan ba kai nasara ba za ayi duk abinda take so". tana faɗar hakan taja hannun Fillo suka fita, wacca ke ta faɗa mata ita dai asa ya saketa yanzu ba zata zauna da shi ba. bayan fitarsu Baffa yay adu'a aka watse, ya rage daga shi sai Turaki, on serious note Baffa ke kallonsa kamin yace,"kenan ita Fillo itace uwar gida?" kansa a ƙasa yace,"ehh Baffa". ya numfasa ya sake cewa,"to ya zaman nasu zai kasance?, haɗe su zaka yi ko ya?". yay ɗan jim kamin yace,"yanda kace Baffa". "ahh wannan kuma ai kai zaka yi making decision, sai dai in shawara ta kama sai in baka". yace,"tom Baffa ka bani shawarar". "ka bari sai mun zanta da hakimi tukunna, now you can leave, sai da safe". *Vote, comment and share.* [9/3, 18:03] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *42* Jar mota ƙirar rangerover ta sauka daga kan titin ta gangara gefe tayi parking a gaban tebur ɗin masu sayar da fruites. matashin saurayin dake daga cikin motar ya zuge glass yay wa me siyar da pineapple sallama, mutumin ya amsa yana barin wajensa ya ƙaraso gun motar. zuwan nasa yasa Hamid miƙa masa hannu suka gaisa, me pineapple ɗin yace da shi,"ta nawa za'a zuba yallaɓai?". Hamid yace,"sako guda goma, kar a yanka kowacce". mutumin ya juya yaje ya zubo pineapple ɗin a cikin leda har guda biyar ya dawo, Hamid ya buɗe masa booth ya saka a ciki, kwata-kwata ba ita yay niyyar siya ba kawai dan mutumin ya rigada ya saka rai ne. mutumin ya dawo yana goge hannunsa da durster yace,"ranka ya daɗe an gama sakawa". Hamid ya juya bayan motar ya kalla mahaifinsa daga kishingiɗe kamar me bacci amma ya san ba bacci yake ba, sannan ya juyo ya ƙara cewa da me pineapple ɗin,"bamu apple". cikin sauri yaje ya dawo. Hamid yace,"nawa ne kuɗin?". yace,"ka bada dubu takwas". Hamid yasa hannu a aljihu ya ɗauko ya basa, yana shirin barin waje ya tsayar da shi da cewan,"yauwa kaga dan Allah tambaya nake dama". mutumin yace,"to Allah yasa na sani". Hamid yace,"gidan Alƙali Dukko nake nema". mutumin yace,"ohh gidan uban marayu zaka ce". sannan ya shiga yiwa Hamid kwatance yanda zai gane, Hamid yay masa godiya sannan yaja motar ya bar wajen bayan ya ɗau apple ɗaya ya miƙawa Mahaifin nasa yana roƙonsa akan ya daure yaci ko ya ne. tafiya kaɗan ta kawo su ƙofar gidan Alƙali Dukko, dai-dai lokacin da motar Maama ta shiga gidan, Hamid ya fito yana ƙarewa girman gidan kallo sannan ya ƙarasa yay knocking gate. me gadi ya buɗe ƙofar ya fito suka shiga gaisawa da Hamid, bayan sun gama gaisawa Hamid ke tambayarsa dan Allah ko akwai Hajiya Rabi anan gidan. Me gadi yace,"a'a wallah babu Rabi, wani yay maka kwatance da nan ɗinne?". Hamid yace,"ehh tou, daga can gidan sarki aka kwatanto mana nan ɗin, da tana aiki acan sai akace ta dawo nan gidan". Me gadi yace,"ohh ai nan ɗin main gate ne na gidan, da yake ɓangaren ma'aikatan gidan daban, daka zagaya ta baya zaka ga gate ɗin irin wannan ne". Hamid yay masa godiya sannan ya koma mota, yana zagawa ɗaya gate ɗin ya faɗawa me gadin sunan Kaka na ainihi shima yace gaskiya bai san wannan sunan ba, sai dai bari ya kira masa shugabar ma'aikatan. ba jimawa Yami tazo wajen, tana kallon Hamid tace,"kar dai jikanmu ne kai". ta faɗa saboda tsananin kama da Fullo da ta gani a fuskarsa kamar an tsaga kara. yace,"ehh to indai wadda nake nema ɗin ita kike nufi to ni jikanta ne". Yami na murmushi tace,"Allah sarki, ai da yake ma ta kwana biyu da tashi daga nan ɗin, amma bari sai muje yanzu na raka ka gidan da suka koma dake ba anan unguwar ba ne". Hamid ya jira Yami ta koma ta sanyo mayafi sannan suka tafi, ita bata ma lura da wanda ke bayan motar ba saboda tana nufar shiga baya Hamid yace da ita ta dawo gaba. sunyi tafiya me nisa kamin su isa gidansu Fullo, motar tasu ta shigo layin a sanda Fullo ke fita daga layin tana sanye da uniform da kuma niƙab zata wuce islamiya. ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka bata tsaya knocking ba, Yami ta shiga dan sanarwa da Kaka, a parlo ta sami Kaka ita ɗaya tana kallo, suna gaisawa tace da ita,"taso ƙawata, taso taso". Kaka na bin ta da kallo tace,"lafiya dai Ƙawata?". Yami tace,"lafiya lau Ƙawata, ke dai fito da sauri kiga abin mamaki abin farin ciki". cikin azama Kaka ta miƙe akan kujerar ta ɗauka hijab ɗin Ummi dake kan kujera tabi bayan Yami da sauri hankalinta duk ba'a kwance ba dan taga Yami a hargitse take. Fitowarsu bakin gate Kaka tayi saurin dafe ƙirji asanda tayi tozali da Hamid jingine a jikin mota. "me idanuna suke gane min?". wani farin ciki da jin daɗi suka mamaye Hamid ya baro jikin motar yana zuwa ya rungume Kaka. ta ɗan ture shi a jikinta tana faɗin,"Hamid kaine ka zama mutum haka?, dama zan ƙara sanyaka a idanuwa na?, Hamid dama kana raye baka taɓa nemana ba?". Hamid ya sauke numfashi yace,"kiyi haƙuri Kaka Allah ne bai nufa ba, amma wallahi kina raina, ta ya zan manta dake bayan kece silar zuwan mahaifiyata duniya". Kaka ta share hawayen farin ciki tana bin motar da kallo kamin tace,"to ya akai kazo nan Hamid?, kar dai wani abu ne ya faru mara daɗi?, wannan motar kuma ta waye?". Hamid yace,"Kaka ai ban manta da kina aiki a gidan sarki ba, na faɗa miki tsawon shekarun nan Allah ne kawai bai nufa ba sai yanzun". tace,"dan dai kaga bana tare da abu me muhimmanci a wurinka ne shisa ka kasa nemana". yaga tana kallonsa tana ƙara bin motar da kallo yace,"mota ta ce, ba zai yiwu mu shiga daga cikin gidan ba ne?". Kaka na kallonsa tace,"zai yiwu mana Hamid, ai shiga cikin gida ma dole, gidanku fa kazo taho muje". ta faɗa tana juyawa ya dakatar da ita,"Kaka mota ba zata shiga ciki ba ne?". tace,"to sai dai ka duba tunda mu ba mota garemu ba, tun zuwanmu dai ta wannan ƴar ƙofa muke shiga". ya ƙarasa ya duba yaga gate din ba me zugewa ba ne, hakan yasa yace mata,"Kaka to bari na fito da shi". tace,"waye?". yay ɗan jimm damuwa na bayyana a fuskarsa sannan yace,"tare da Abba muke, ba zai iya tafiya ba sai na taimaka masa". idanun Kaka a waje tace,"kana nufin Babanka Hayyo?". ya ɗaga mata kai,"ehh Kaka". da mamaki sosai tace,"to me ya sami ƙafar tasa da ba zai iya takawa ba, ko wani mulkakken ya zama?". ya sauke numfashi yace,"jarabawar ubangiji". Kaka ta taɓe baki tace,"Alhaki dai yake bibiyarsa". bai ce komai ba ya ƙarasa mota ya buɗe booth ya ɗauko wheelchair sannan ya buɗe bayan ya taimakawa Hayyo ya fito ya ɗorasa akan kujerar, tun fito da shi Kaka tayi masa kallo ɗaya taji mugun tsoro ya kamata kamin bala'in tausayinsa ya biyo baya, indai gani take yi da kyau ya rame kamar me cutar ƙanjamau, mutumin da yake jayent son kowa ƙin wanda ya rasa, mutumin da bama a gane girmansa ko ada amma yanzu girma ya bayyana ajikinsa sosai kace me shekaru ɗari. Hamid ya turo shi suka ƙaraso inda Kaka ke tsaye cike da tsoron duniya, hoton abubuwan da suka faru a baya suna ta haska mata a ido, ita dai banda Hamid ya faɗa mata yace Abbansa sai ta rantse tace ƙarya ne ba shi bane, dan gaba ɗaya ya fita daga kamanninsa tsabar wahala, kamar ba wannan ƙaƙƙarfan namijin da ke zage dukkan ƙarfinsa ya zane mata ƴarta ba. ta girgiza kai tana ƙara jin tsoro na al'amarin sakayyar wanda aka zalunta, a hankali tace da shi,"Hayyo". ya ɗago da wuyansa da ƙyar wanda ya laƙwashe. ya kalleta ya buɗe baki yace,"nannnnaaammm Daddddda". ya faɗa cikin ƙinƙinar da sai kayi da gaske zaka gane, kuma cikin murya kamar ta masu koyon magana. kawai sai Kaka ta fashe da kuka sosai tana ambaton,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". ta ƙara kallonsa tace,"Hayyo kai ne ka koma haka?". ta tambayesa tana tuna zaƙin maganarsa ada, wanda daɗin amon muryarsa na ɗaya daga cikin abin da yake jan hankalin mata garesa, dan ƙarya ne Hayyo yayi magana kana wajen baka ce kaji daɗin muryarsa ba. hawaye ya sakko a idonsa yace,"Kakkkkaaa dddddaaa Allllahhhh kikkki yaaafeeee miiiimmmmnn, dddda Allllahhhh kiiii neeemmmooo minnn Haliiimaaaattttuu". sai da aka ɗauki cikakken minti ɗaya da ƴan kai sannan ya iya faɗar kalmar da za'a faɗeta cikin sakanni biyu, yana maganar bakinsa na rawa, haƙoransa na daddatsewa akan harshensa. Hamid yasa handky yana goge masa uban yawun da ya dalala ajikinsa ya ɓata gaban babbar rigarsa kamar an sheƙa masa ruwa. ƙafafunsa suka shiga rawa akan wheelchair ɗin ya kamo hannun Hamid yana faɗa masa,"zaazzzzzannnn saukkkkkaaaa innnneeee miiii yaaaaaffiyyarrrr Dddddaaaada". kaman yanda Kaka ke hawaye haka ma Yami, saboda ƙarya ne ace kaga halin da Hayyo ke ciki baka zubar da hawaye ba. Hamid na kallon Kaka yace,"wai yana so zai sauko ya nemi yafiyarki". tace,"Hayyo ba sai ka sauko ba na yafe maka, ni baka min komai ba dama". ta dubi Hamid tace,"mu shiga". tai gaba suka biyo bayanta, Yami ta tura ƙofar. suna nufar entrance na parlon gidan Ummi ta fito, Kaka ta fara gani wadda ke aikin goge hawaye, bama ta lura da sauran ba, tai saurin ƙarasowa wajenta tana faɗin,"lafiya Dada?, na fito naga ba kya parlon me ya faru?". Kaka bata iya magana ba dan har yanzu a girgiza take, kuma kamin tayi mata nuni da su Hayyo, Ummi taji hannayen mutum a ƙafafunta da ɗigar ruwan hawaye. ta kai idonta kan Hamid dake zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta, ba fuskarsa ta kalla ba, saman kansa kawai ta kalla ta shaida ɗanta, sai taji wani abu ya tsarga mata, ta kulle ido tana jin taruwar ruwan hawaye aciki. "Hamid". ta kira sunansa da amon sautin da ya tafi ya taɓa har zuciyar Hayyo. "me kake nema a ƙafafuna Hamid?, laifin me kayi min?, tashi tsaye na ganka ɗana". Hamid ya miƙe yana hawaye, Ummi ta rungumosa jikinta suna kuka tare, wucewar daƙiƙa biyu Hamid ya zare jikinsa daga nata yana bin mahaifiyar tasa da kallo, wadda yaga ta ƙara kyau da girma kamar ba ita ba. "ya akai kazo nan Hamid?, wa ya faɗa maka inda muke?". tambayoyin da tai masa kenan, kuma kamin ya bata amsa idonta ya sauka akan halittar da duk lalacewar da tayi ba zata kasa ganeta ba a kallo ɗaya, tai saurin ɗauke ƙwayar idonta daga kan mutumin da take jin ta tsane shi tsana mafi muni. Hamid ya buɗe baki zai yi magana tayi saurin ɗaga masa hannu cikin fusata, ta kulle idonta tana huci na tsawon daƙiƙa ɗaya, ta buɗe su a sanda ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jawur, wannan damuwar da take tare da ita na tsawon shekaru ta taso tun daga can ƙuryar zuciyarta ta mamaye saman fuskarta. da tsananin ɓacin rai a muryarta tace da Hamid,"tunanina duk sanda zan ganka zan zama ina me farin ciki ne". ta faɗa tana ƙara ɗaga muryarta da faɗin,"me yasa kazo min da wannan abin cikin gida?, to idan baka sani ba ka sani, bana so kuma bana ƙaunar sake haɗa ido da azzalumin mahaifinka har in bar duniya, dan haka tun ina shaida kai ɗana ne ka fitar da shi daga gidan nan". tai maganar cikin zafin rai tana yi masa nuni da gate, Hamid ya dubi mahaifinsa da tausayi wanda ke ta kokawa da wheelchair yana so ya sauko, ya koma ya kalla Ummi yace,"dan Allah Ummi...". bata barsa ya ƙarasa ba ta doka masa tsawa. "Hamid ka fita da shi na faɗa maka, ka fita da shi tun ina iya kallonka ina shaida kai ɗana ne, Hamid ina me rantse maka in baka fitar da wannan matsiyacin mutumin daga gidan nan ba zan tsine maka". Kaka tayi saurin shiga maganarta da cewa,"kul, kul Halimatu, shi me yayi miki da zaki nemi ki sauke fushinki akansa". Ummi tace,"wallahi tallahi in har don inci gaba da kallon wannan azzalumin mutumin a inda nake ne to gwara in yafe Hamid muddin bai fitar da shi daga gidan nan ba, na tsani mutumin nan na tsani ganinsa, inata roƙon Allah kar ya ƙara haɗani ko da ace da inuwarsa ne shine Hamid saboda ba ya ƙaunata zai ɗauko shi ya kawo shi inda nake salon zuciyata ta buga". Yami tace,"kiyi haƙuri Ummin Fillo, ki tsaya ki saurare shi har yanzu shi ɗin mijinki ne, kuma kar ki manta shi uban ƴaƴanki ne, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, to kuma ina laifin wanda ya gane kurensa yazo neman yafiyarka". ta girgiza da kanta cike da takaici da ƙunar rai,"Yami baki san waye wannan mutumin ba, wannan da kike ganinsa azzalumi ne, mugu ne, macuci, dan Allah ku fitar da shi daga gidan nan tun ban faɗi na mutu ba". sai kawai ta fashe da kuka me cin rai, tana jin wani abu me ɗaci na taso mata, tana jin kamar ta shiga ciki ta rarumo duk abinda ta gani tazo taita rotsawa Hayyo. faɗowar Hayyo daga kan wheelchair yasa hankalinsu ya kai kansa, Hamid ya tafi da sauri ya ɗaga kujerar da ta danne shi, jikin Hayyo duk karkarwa yake, yana jan jikinsa a ƙasa yana so ya ƙarasa gaban Ummi, Hamid ya fara hawaye ya ɗagosa ya mayar da shi kan kujerar, sannan ya turasa ya kaisa gaban Ummi. gwanin ban tausayi hawaye ke sauka akan fuskar Hayyo ya haɗe hannayensa alamar roƙo, bala'in nadama da danasani shimfiɗe a fuskarsa, cikin ƙinƙina mesa zuciyar mutum ta tsinke yace,"dan darajan Allah ki yafe min Halima, ki tausayawa halin da nake ji, ke kaɗai kika rage ki yafe min acikin waɗanda suke raye, kuma muddin ba ki yafe min ba nasan ba zan gama da duniya lafiya ba, domin nasan na aikata miki abubuwan da Allah ba zai barni ba, dan Allah ki yafen ko na samu sassaucin bala'in da nake ji a tare da ni". Ummi na kallonsa da tsantsar tsana tace,"kai yanzu Hayyo har kana da idon da zaka kalleni ka buɗi baki kace in yafe maka?, yaushe kasan Allah da yau kake roƙon wani da shi?, to bari kaji na faɗa maka, banda idon da zan dubi halin da kake ciki in tausaya maka balle na yafe maka, ka cire batun yafiya tsakanina da kai dan ko da ace yafiyata ta rage maka shiga aljannah Hayyo ba zan yafe maka ba". Kaka, Yami da Hamid su kai ta roƙon Ummi akan ta yafe masa, amma sam taƙi, ƙarshe ma sai ciki ta shiga ta ɗauko mayafi ta fito tana kallon kowa tace,"in har ba zaku ɓadda shi daga inda nake ba to ni zan bar muku gidan". sannan ta kalli Hamid tace,"kai kuma ko a mafarki ka ganni karka nuna ni a matsayin mahaifiyarka, tunda kaima baka tausayina". tana zuwa bakin gate Fillo na turo ƙofa ta shigo, niƙab ɗinta a hannu tana yamutsa fuska alamun ta gaji, farat ɗaya hankalinta ya tashi ganin Umminta na kuka, gabanta ya faɗi tana tunanin me zaisa mahaifiyarta kuka a yanzu kuma?, ai tayi zaton zubar hawayenta ya ƙare kuma tunda har ta rabu da Hayyo. sai ta ƙanƙance ido tana bin kowa da kallo, ta tsayar da idonta bayan Hamid da bata ga fuskarsa ba, zuciyarta bata gama tunanin ko waye ba ya juyo, ta ware ido tana faɗin,"Hammah". ta faɗa murmushi na ƙwacewa a fuskarta, harta ɗaga ƙafa zata wuce wurinsa sai kuma idonta ya sauka akan mahaifinta dake kallonta yana murmushi da hawaye, alamun na yaji daɗin ganinta, lokaci ɗaya ta haɗe rai ta ɗauke idonta daga kansa. ta kalla Ummi dake ƙoƙarin raɓata ta wuce, ta kama hannunta zasu fita maganar Hamid ta tsayar da ita. ta juyo tana kallonsa tace,"Hamma dana ganka sai naji farinciki ya kamani, amma da naga wannan masifar a tare da kai sai naji kamar in haɗiyi zuciya in mutu, saboda na san ba komai ya samin Ummina kukan da ta jima bata yi ba, dan haka gwara mu bar muku nan ɗin dan ba zamu ƙara zama da masifar da zata hanamu farinciki da jin daɗin rayuwa ba". tana rufe bakinta Hamid ya ɗauketa da mari, kuma bai sauke hannunsa ba Ummi ta zabga masa marin shima. "ƙarya tayi ba masifar bane shi da har zaka ɗaga hannu ka marar min yarinya, to wallahi ka kiyayeni kar kaja ɓacin rai yasa bakina ya zama silar lalacewarka a duniya, kuma na fasa tafiyar kaje ka gangaro shi kuzo ku fita a gidan nan tunda ba uban wani ya gina mana ba". maganar Hayyo ta shiga kunnen Fillo a sanda yake cewa,"dan Allah dan Annabi ƴata ki yafe min, ki tausayawa halin da nake ciki, wallahi na san alhakinku ke bibiyata shisa na faɗa cikin wannan mawuyacin halin". Ummi tace,"ai baka ga komai ba, kaɗan ma ka gani, kuma insha'Allahu nan gaba maganar ma sai ta gagareka, da izinin Allah sai kowa ya gujeka ya barka kai ɗaya a halin da yafi wannan muni". Hayyo ya kulle idonsa yana ƙara roƙon su Ummi su yafe masa, tasa tazo ƙarshe su taimaka masa kar ya tafi lahira da alhakinsu, Fillo na kallonsa cikin ƙunci tana tuna voice ɗinsa da taji a wayar Turaki tace,"mu yafe maka kake cewa?, ka manta san da kake saka Ummina a ɗaki ka kulle kayi ta dukanta?, ko kuma ka manta san da kake bin ta har waje ka duketa a gaban mutane kana zaginta?, ko manta yacca ka azabtar damu da yunwa kayi?, ko kuma ka manta sheganta ni da kayi da har kake kirana da ƴarka?, to idan ka manta duk waɗannan abubuwan mu ba zamu manta ba, kuma tsakaninmu da sai Allah, da yardar Allah ba zaka mutu ba sai kaga shiga matsanancin halin da yafi wannan". a tsawace Kaka tace da ita,"kul ɗinki Fillo, kar ki ƙara wani furuci anan, wannan lamarin tsakanin iyayenki ne, duk lalacewar uba uba ne shi, uba ba abin wasa bane ki san da wannan, kamar yanda kike ganin mahaifiyarki da mutunci ya zama dole shima ki gansa a mutunci muddin kina son gamawa da duniya lafiya, ke ba dan shi ba ai da baki zo wannan duniyar ba, ki iya bakinki akansa kafin duniya tayi watangaririya da ke". Fillo tasa kuka tana faɗawa jikin Ummi tace,"ni wannan ba Babana bane, shi da ya sheganta ni a duniya ta ya za'ai ya zama ubana, mutumin da ya kasa bani ilimi da tarbiyya shi ne zai zama mahaifina?, ni dai ba Babana ba ne kuma ba zan taɓa yafe masa abunda yay mana ba". tarin da Hayyo ya fara babu qaqaautawa yasa Fillo haɗiye sauran maganganunta tayi kansa da sauri, Kaka tace da Hamid ya tura shi su shiga daga ciki, Ummi na tsaye tana jin zuciyarta nayi mata wani iri tabi bayansu da kallo. cikin ƙanƙanan lokaci dai Hayyo ya fita a hayyacinsa, tari kawai yake yana a basa ruwa ya sha, Fillo ta ɓare jarkan faro jikinta sai rawa yake yi ta zuba a kofi ta tallafi kansa ta basa ya sha, Kaka ta ɗauka lambar Dr Yusuf ta kirasa a waya yace gashi nan zuwa nan bada jimawa ba. cikin mintunan da basu wuce biyar ba Hayyo yasha ruwa yafi roba huɗu, da yasha zai kuma cewa a ƙara masa, kuma duk Fillo ce take basa, idan ta kai kofin bakinsa sai ya haɗa harda hannunta ya kama tukunna yake shan ruwan, hawayenta kuwa dake zuba ajikinsa jinsu yake kamar wuta, in ace ya san haka Ƴaƴa suke da tausayi da jin ƙai da bai wulaƙanta ƴaƴan da Allah yabasa ba balle ya wofuntar da su, bai san Ƴaƴa rahama bane sai da ya shiga wannan halin, lokacin da babu macen da zata kula da shi, haka kuma babu ƴaƴan da zasu zauna su basa kulawa, in ace babu Hamid bai san kuma ya zai yi ba, wataƙila da tuni ya mutu ya ruɓe ba tare da kowa ya sani ba. sai a yanzu da tasa tazo ƙarshe yaji sonsu da ƙaunarsu matuƙa na bin jinin jikinsa, sai yanzu yake jin ina ma ace ba ya zata dawo da ya kyautatawa iyalinsa, babu abinda yake buƙata a yanzu irin ubangiji ya basa aron lokaci, sannan ya ara masa lafiya ko ta ɗan kaɗan ɗin lokaci ne dan ya faranta ran iyalinsa, ya gyara halinsa, ya gyara lahirarsa, to amma ya san ƙarshensa yazo, ba zai ƙara samun wata dama ba a wannan duniyar balle kuma lokaci. yana ta kallon Fillo yana kuka sosai yace,"na karɓi sadakin aurenki tuntuni, na san da cewa hakkinki ne, dole na baki hakkinki, amma saboda son zuciya nawa ban nemeki ba balle na baki, sai na gina kaina da kuɗin motar da na siyar, ban ko fara morarsu ba Allah ya jarabceni da shiga wannan mawuyacin halin, dan Allah ki yafe min kar in mutu da hakkinki akaina". ya faɗa yana kuka sosai.  "na san ƙwarai na zalunceku, ba'a taɓa mugun mutum irina ba da ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, ban baku ilimi ba balle na baku tarbiya, hasalima duk naƙi karɓarku a matsayin ƴaƴan da na haifa, alhakinku kaɗai ba zai barni in ƙare da duniya lafiya ba, dan Allah ku yafe min ko na sami sassuaci a ƙabarina, kuce kun yafe min ko naga da kyau a ranar gobe". ya kamo hannun Hamid yace,"haƙiƙa banda tamkarka ɗana, Allah ubangiji yay maka albarka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin, ya baka masu kayatata maka fiye da yanda ka kyatata min, fiye da yanda ka dinga kare martabata da mutuncina, na san ba zan ƙara wani lokaci me tsayi ba, idan na mutu ka ɗauk Atm ɗin da na baka ajiya kaje ka ciro miliyan hamsin ka bawa ƴata, hakkinta ne". ya faɗa yana shafa fuskar Fillo, sannan yace,"ka nemi adalin alƙalin da zai raba maku gadonku babu zalunci, duk wata kadara da na mallaka taka ce Hamid na bar maka, na rubuta hakan a takarda ta nan cikin kayana, abinda kayi min ba zan taɓa iya biyanka ba Hamid, na gode, na gode, na gode Hamid, baka taɓa fushi da ni ba, baka taɓa guduna ba saboda mugun halina, matana da ƴaƴana sun guje ni amma kai ɗaya namiji da Allah ya bani kana liƙe da ni, kana faɗa min gaskiya a lokacin da nake da dama amma naƙi saurarenka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya, dan Allah yayin da babu ni ka zama uba a wurin ƴan'uwanka, kar ka bari zumuncinku ya yanke, kayi musu gatan da ni banyi musu ba, ka zama na gari Hamid, ka zama na gari, mutum ba ya danasanin zama mutumin ƙwarai har mutuwarsa, amma idan ka zama mutumin da wasu suke kuka da shi zaka yi danasani a sanda kazo mutuwa har bayan mutuwarka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya". Hamid ya kasa cewa komai yana dai riƙe da hannunsa yana hawaye, Hayyo na shaƙuwa ya kalla Fillo yace,"zan ƙara ruwan me sunan Umminta". Fullo ta ɗago kansa ta kuma basa ruwan yasha, a lokacin sai da ya shanye jarkan guda, yana kallon Fillo yana murmushin ƙarfin hali yace,"ki tayani roƙon yafiyar mahaifiyarki, ki faɗa mata ina sonta, ina sonta fiye da yadda baki zai furta, dan Allah ta yafe min ko na na samu naga haske a ƙabarina". yana faɗar hakan kansa ya langwaɓne gefe yana shaƙuwa sosai, ya dafe ƙirjinsa yana jin tsananin azaba na ratsa shi, magana yake so yayi amma shaƙuwa sam ta hana shi, can kuma sai ga jini yana fita daga bakinsa kamar zubar yawu, ya damƙo hannun Fullo da Hamid yace,"tawa tazo ƙarshe, ba zan ƙara ko da minti uku ba, mutuwa zanyi ƴaƴana, bana so na tafi na barku amma ban isa na hana mutuwa ta ɗaukeni ba, ba'a son raina zan rabu da ku ba sai don mutuwa ta zama dole a gareni ko ba yanzu ba,  idan na mutu ku nema min gafarar Allah, karku gushe face kuna me nemar min gafararsa a ko da yaushe, haƙiƙa ni ɗin me laifi ne a gare shi, mutuwa zanyi babu makawa, iyayena sun rasu tun ina saurayi, baƙin cikina ya zama ajalinsu, ku nemi dangina a ƙauyen Ngurore-Jabu under local government ɗin Karim-Lamiɗo, Wurkum district gidan Hakimin Wurkum, nanne gidanmu, anan ahlina suke, Allah yayi muku albarka, dan Allah kuce da mahaifiyarku ta yafe min, la'ila ha'illahu muhammadurrasulillahi sallahu alaihi wassalam". ɗif kamar ɗaukewar wuta haka numfashin Hayyo ya ɗauke, hannunsa ya saki ya faɗi daga riƙon da yaywa yaransa, Kaka ta fashe da kuka tace,"shikenan, Hayyo Allah ya jiƙanka yay maka rahama yasa can tafi nan". Fullo ta ƙwala wata ƙara tana jijjiga shi,"Abba nah, Abba don Allah ka tashi, Abba kar ka mutu, Abba kar ka tafi ka barmu muna buƙatarka, wallahi mun yafe maka duk abinda kayi mana, dan Allah ka tashi Abba nah, muna sonka a yanda kake Abba ka tashi please". Hamid dai kukansa a hankali yake yi, shi ɗaya yasan me yake ji a zuciyarsa, Kaka ta tashi ta fita dan kiran Ummi idan bata yi nisa ba, tana fitowa ƙofar parlo ta tarar da ita a tsaye tana goge hawaye da mayafinta, ta kalleta tace,"ya mutu ai". wasu sabbin hawaye suka ƙara zubowa a fuskar Ummi, Kaka ma ta goge nata tace,"ki shigo ciki asan abin yi kafin dare yayi, anan za'ai jana'izarsa ko sai mun koma can?, in sai mun koma can dole sai gobe za'a kai shi tunda kinga daren yayi, in kuma nan ɗin ne to na shiga masallacin can na faɗa in yaso ko bayan magriba sai a kaishi". kukan da Ummi ke ta riƙewa ya kubce mata, ta fashe da kuka sosai ta shiga parlon da gudu ta tafi kan gawar Hayyo, wanda take kallonsa kamar zata yi masa magana ya amsa mata, ta kifa kanta a ƙirjinsa tana riƙe hannunsa, kukan da bata taɓa yi ba a duniyarta yazo mata, da ƙyar muryarta ta samu ta fito acikin kukan tana cewa,"na yafe maka, Allah ya yafe maka, Allah yasa ka huta, ubangiji ya lulluɓeka da rahamarsa". lokaci ɗaya parlo ya karaɗe da kukan uwa da ƴaƴanta, zuciyoyin da su kaɗai suka san me suke ji, duk rashin kyan halin mutum yayin da akace babu shi mutuwa ta ɗauke shi sai mutuwarsa ta taɓa zuciya musamman makusantansa, ji suke yi inama zasu iya dawo da shi suci gaba da rayuwa tare da shi a yanda yake. kukan da Fullo da Hamid ke yi ya ƙara tsinkar da zuciyar Ummi, kuka sosai babu me iya lallashin wani, lokacin kuma Dr Yusuf ya shigo parlon, da Yami ya fara cin karo, yana kallonta jiki a sanyaye yace,"lafiya Yami?, waye babu lafiya?, ba dai jikin Ummi bane ya tashi?". tana goge hawaye tace da shi,"a'a ba ita bace, wanda ma aka kira ɗin kazo ka duba shi Allah ya karɓi abinsa". ya kalla wurin da su Ummi suka kewaye gawar sannan ya kalla Yami yace,"ban gane ba Yami?, waye mutu?". tace,"Baban Fullo ne yazo, kuma ashe ajali ne ya kawo shi". Yusuf ya isa wajen da sauri, sai dai yana zuwa fuskar da ya gani ita ta matuƙar basa mamaki har ya razana yaja da baya, ya kalla Ummi ya kalla su Hamid yace,"waye wannan ɗin?". babu wanda ya iya basa amsa acikinsu, ya dinƙa kallon Fullo dake aikin girgiza Hayyo tana faɗin dan Allah Abba ka tashi, ka tashi mun yafe maka kar ka mutu yanzu. Yusuf ya zube a wajen hoton gawar Hayyo da hoton Kawunsa Muhammad da ya sani na haska masa a ido. a fili ya furta,"Kawu Muhammad". sai kuma yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Ammi, har ta ƙare ringing bata ɗaga ba sai da ya kira lambar Aliyu yace ya kai mata. murya a daƙile tace da shi,"ya akai?". yace,"Ammi Kawu Muhammad". tace,"me ya sami Kawu Muhammad ɗin?, ganinsa kayi?". kamar yana gabanta yace,"Ammi ya mutu". a matuƙar razane ta miƙe jiki na kyarma tace,"ya mutu?, aina ka gansa da zaka ce ya mutu?, yaushe rabonka da shi ma har da zaka ce ya mutu?, wa ma ya san inda yake?". yace,"to ban sani ba Ammi ko idona ne yake gane min ba dai-dai ba, amma tabbas gani ga gawar Kawu Muhammad, zan tura address kizo yanzu ki gani ko shi ɗinne, amma na tabbata gawar Kawu Muhammad ne a gabana". Ammi ta jefar da wayar Aliyu tayi cikin ɗaki da sauri ta ɗauko mayafi tace da shi,"muje muje Aliyu, duba wayarka Yusuf zai turo da address". cikin mintunan da basu haura ashirin ba sai ga su Ammi sun ƙaraso gidan, ta shigo parlon duk a rikice tayi kan gawar da aka lulluɓeta a yanzu, ta kalla Ummi da su Fullo da babu abin da ke tashi a parlon sai gunjin kukansu, ta kai hannunta na kyarma ta ɗaga zanin da aka rufe shi da shi, tana kallon fuskarsa ta saki zanin ta zabura taja da baya tana ambaton ƙalu innalillahi... sai kuma ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"ashe rabon ba zamu ƙara ganawa ba sai bayan ka mutu zanga gawarka Yaya". ta kalli Ummi tace,"mijinki ne da gaske?". Ummi da mamaki take kallonta ta ɗaga mata kai kawai, Ammi tace,"Yayana ne uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya, tunda ya zama ajalin iyayenmu shikenan kuma ya kama gabansa bai ƙara waiwayon kowa ba, rabona da shi tun Yusuf bai fi shekara goma sha ɗaya ba, yazo gidana sau ɗaya lokacin ko sauraronsa banyi ba". tayi shiru tana bin gawar da kallo tana kuka sosai, "Allah ya jiƙanka Yaya yasa ka huta, Allah ya yafe maka zunubanka, ya haskakaka ƙabarinka, Allah ya sadaka da manzon Allah SAW". nan da nan kuma sai ta ɗauki waya ta shiga kiran ƴan'uwanta waɗanda suke uba ɗaya, dama su biyu ne a wurin mahaifiyarsu daga shi sai ita, duk da irin fushin da aka ɗauka da Hayyo hasalima wasu sun manta da shi, amma kan kace mene wannan waɗanda ke zaune anan Gombe har sun zazzo. saboda manyan yayyansa da ke can taraba dole aka fasa kaisa a ranar akace a bari sai gobe, a washegari da safe kuwa ƙarfe takwas na safe gida ya cika maƙil da ƴan'uwan Hayyo maza da mata, lokacin har anyi masa wanka jira ake babban wansu yazo ai masa sallah. lokacin da aka ɗauko gawar Hayyo za'a fita da ita a lokacinne mutane da dama da basu sami damar kuka ba suka saki nasu, saboda bala'in tausayin Fullo wacce ke ta kuka tana kiran a bar mata Abbanta dan Allah, sai da ƙyar Ammi ta iya ruƙota Hajiya Madina ta ƙwace hannunta daga kan makarar da ta yiwa mugun riƙo, sannan ne aka samu aka fita da gawar Hayyo daga parlon, kuma lokacinne Fullo ta yanke jiki ta faɗi bayan ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da ta amsakuwa a gidan gaba ɗaya. aljanun da ba'a santa da su ba suka tashi.... *Vote, Comment and Share.* [9/3, 19:37] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *43* *Taraba Satate, Wurkum district, Late Alhaji Aminu Barkinɗo Residence.* tafkeken gida ne me irin ginin gidan sarauta, sai dai ginin irin na zamanin da ne bana yanzu ba, but an ɗan sabunta shi ba kamar yanda yake ainihinsa ba. ƙofar gidan na marigayi tsohon Hakimin Wurkum danƙare yake da jama'a kace ɗaurin auren wani babban mutum ake ko kuma za'a ƙara yin naɗin sarauta ne. daga cikin rumfar tempol ɗin da akayi, Maudo ne zaune akan kujera yasha rawani yana amsar ta'aziyya daga bakunan mutane da dama, shi ne Babban ɗa a wurin marigayi Alhaji Aminu Barkinɗo, kuma shine wanda ya zauna a hannun mahaifiyar Hayyo a lokacin da ta na raye, domin shi tasa mahaifiyar ta rasu, kuma tun bayan rasuwar mahaifin nasu ya maye gurbin kujerar tasa har zuwa wannan ƙarni da muke ciki. daga cikin gidan, ɗumbin mutane ne ƴan gaisuwa ke ta hada-hadar shige da fice a ƙaton tsarkargidan da yay kusan filoti biyu, kana kallon yanda aka kakkasa ɓangare ɓangare zaka san family house ne. wata farar tsohuwa tukuf ta fito daga wani ɗaki tana dogara sanda, sai da suka ƙaraso tsakiyan tsakar gidan sannan ta tsaya tana kallon mai yi mata hidima wadda ke biye da ita a baya tun fitowarta, hannunta riƙe da ƙwaryar fura babba, ita ɗaya ta rage acikin matan Alhaji Aminu Barkinɗo, cikin su uku da ya aura ita ɗaya tayi tsawo rai haka. cikin yaren fulatanci tace da Hadimar,"ki nemo Gaji ki basa furan ya kaiwa Dottijo, tun ɗazu ya aiko Manga kuma ba'a samu an kai masa ba, kuma ƙila zai sha tare da baƙi ne, yi maza du Allah". Hadimar ta wuce da sauri tabi dogon soron da zai kai ka wani babban fili kafin ka fita zuwa waje. Dada ta waiga tana kallon masu fitowa daga ɓangaren Hakimi, ta ƙwala kiran,"Munyoɗo". sai da ta kira sau biyu tukunna wata farar dattijuwa ta fito da sauri tana amsawa, tazo gabanta ta rissina tana faɗin,"Dada gani, lafiya kika fito ke ɗaya?, kuma kin tsaya ai a rana, me kike da buƙata?, ina Petel din?". tayi maganar tana kamata ta matsar da ita daga cikin ranar. ta kalleta ta cikin glass ɗinta tace,"ina wannan shike, amnn mata na wurin Hayyo?". Munyoɗo tace,"wacce daga ciki Dada?". Dada ta ɗan ɓata fuska da muryar ƙorafi tace,"wannan yaro dai Allah ya jiƙan shi kawai, du yaje ya haɗo mata da yawa in ka tashi neman ɗaya sai kayi ta faman kwatance". tayi tsaki sai kuma tace,"wasu sun ƙara zuwa ne?". Munyoɗo tace,"ai Dada jiya duk sun gama zuwa, su bakwai ne yanzu sauran huɗun ance sun rasu, suna babban parlo yanzu haka". Dada ta girgiza kai alamar Allah ya kyauta sannan tace,"to wannan Balarabiyar za ki kirawo min". Munyoɗo tace,"tom Dada bari na duba". ta faɗa tana juyawa ta nufi ɓangaren da yake nanne na mahaifiyar Hayyo, ta shiga babban parlon da ya tara ƴan zaman makoki, ta dinƙa wuce su har ta ƙetara inda Ammi da Ummi suke zaune tace da Ummi,"Dada tana kiranki". Ummi ta amsa da to tana yunƙurawa ta miƙe, Ammi ma ta miƙe tana faɗin,"kin san Allah na sha'afa gaba ɗaya Dada tana nemana". tare suka fito gaba ɗaya, suka tadda har an ajiyewa Dada kujera ta zauna akai, suna zuwa ta ɗaga sandar hannunta ta bugawa Ammi, Ammi ta kauce tana faɗin,"kiyi haƙuri baƙi ne suka tsayar da ni". Dada ta harareta ta cikin glass bata ce mata komai ba, ta mayar da dubanta ga Ummi da ke tsugune a gabanta tace mata,"kije ki sako mayafinki mu wuce asibiti, ance tun shekaranjiya baki koma wurin yarinyar nan ba, ban sani ba ko isashshen hankali ne baki da shi". Ummi ta miƙe cikin sanyi jiki ta wuce, Dada ta kalla Ammi tace,"kije ɓangaren Giɗaɗo kice da matarsa ta bayar da ferfesun kaji da nace ayi, na santa da ɗan banzan cin yajin jaraba, idan ta san yayi yaji da yawa to ta zubar da shi ba mayu ne zasu sha ba, ta ɗora sabo na mara lafiya ne". har Ammi ta wuce sai kuma ta ƙara tsayar da ita,"kice da Belɗo ya fito da mota zai kai ni asibiti, yace da Safara'u taje ta haɗa min kayana a kawo min yau can ina kwana". tana tafiya sai ga wata hadima daga bangaren Modibbo ta fito, tayo wurin Dada da sauri tana zubewa tare da cewa,"Allah juttin balɗe ma, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Dada, da akwai abunda kike buƙata ne ayi miki cikin gaggawa?". Dada ta dubeta tace,"a'a bana buƙatar komai". Hadimar bata tashi ba ta cire takalmanta ta zauna akai ta shiga matsa ƙafafun Dada. lokacin maƙwabtansu suka shigo, da girmamawa matar ta tsuguna tana gaida Dada tare da ƙara yi mata ta'aziyya, Dadan ta amsa tana yi mata godiya sosai. matar tace mata tare da mijinta suke, Dada tace taje ta shigo da shi,ba jimawa sai gasu tare, suka gaisa da Dada wadda ke ta sanya masa albarka. "Dada wajen kuma da zafin rana da kin koma daga ciki". tace da shi,"zanje dubo yaron Hayyo ne, zafin mutuwar uban ya taɓata shi yana can asibiti kwance rai hannun Allah, Belɗo nake jira yanzu zai fito". daga nan suka yi mata sallama suka wuce. a ƙofar gida sanda su Ummi suka fito zasu tafi motar su Hajiya Ramla tayi parking, tun ranar ɗaya da suka zo suka koma sai yau suka dawo, Ummi ta ƙarasa wajensu tana yi musu barka da zuwa, su kuma suna ƙara yi mata ta'aziyya, Ummi tayi musu godiya sosai da sosai akan irin kyatatawarsu gare su. Hajiya Madina da damuwa a tare da ita tace da Ummi,"to ya jikin Fillon?". Ummi tace,"Alhamdulillahi da sauƙi, yanzu ma can zamu je, wataƙila ma dai zuwa dare su sallamota". Hajiya Madina ta kalla Hajiya Ramla tace,"to ko ni na bisu ne?". Hajiya Ramla tace,"ah ki dai bari mu shiga muyi gaisuwan, idan muka fito tafiya sai mu biya ta can ɗin ko". Hajiya Madina tace,"to shikenan". sai kuma tace da Ummi,"Me Babban suna yana nan ɗin ko yana can asibitin?". Ummi tace mata,"acan asibitin yake kwana ai, ya hana kansa natsuwa kwata-kwata, jiya ma nayi ta fama da shi kan ya dawo gida ya huta yace min to, sai bayan su Lamiɗo sun dawo suke ce min yana can ɗin dai bai tafi ba, dan Allah Hajiya ku wuce da shi yau ɗin ya samu yaje ya huta shima". Hajiya Madina tayi ɗan jimm kamin tace,"to bari dai muga yanda za'ai, sai kun dawo". Ummi ta kira wani cikin jikokin gidan tace yaywa su Hajiya Ramla iso zuwa wajen Dadda wadda itace matar Maudo babban yayan su Hayyo hakimin yanzu kenan. direct Taraba State Specialist Hospital motar su Dada ta nufa, a reception su Ummi suka tadda Kaka ita da ƙannan Hayyo da suke uba ɗaya su biyar, tare suka wuce ward ɗin da aka kwantar da Fullo, suna tafe Dada nata ƙorafin asibitin basu iya aikin komai ba, ace mutum kwanansa biyu yau amma shiru jiki babu sauƙin arziƙi, to ita dai idan jikarta bata sami lafiya yau ba to gobe ƙasar waje za'a fitar da ita ƙwararrun likita su dubata. Belɗo dai sai bata haƙuri yake yana tayi shiru kar likitocin suji, in suka ji ba zasu ji daɗi ba, tayi masa banza bata saurare shi ba har suka iso room ɗin da Fullo ke kwance. Ummi ta dakata daga ƙofar room ɗin bata shiga ba saboda nauyin sirikinta da take ji, tunda taga su Kaka a reception ta san shine zaune a wurinta. Turaki ya miƙe cikin sauri daga gefen gadon a sanda su Dada suka shiga room ɗin, ba shi yake cutar ba amma kallo ɗaya zaka masa ka hango bala'in ramar da yayi, ga damuwa kamar a lakuta a fuskarsa, ya matsa daga gefen gadon yana yi musu sannu da zuwa. Dada ta kallesa ta girgiza kai saboda tausayinsa tace,"sannu namijin ƙwarai, Allah ya baka ladan kulawa da matarka, ka kwantar da hankalinka zata sami lafiya insha'Allahu". ya kalli Fullo da ke ta bacci sannan yay ƙasa da kansa kamar zai yi kuka yace,"Allah ya amince". Kaka na kallonsa tace,"Me Babban suna ko zaka je gida kai wanka ka samu ka ɗan huta, rabonka da abinci ma tunda jiya da rana, dan Allah kaje kaci tunda likitan yace gobe da safe zasu sallame mu". da damuwa tsantsa a muryarsa yace,"Kaka ina so naga ta farka ne tukunna". Kaka ta gyaɗa kanta tace,"to Allah ya farkar da ita cikin ƙoshin lafiya". Dada ta zauna kan kujera tana fuskantar Fullo cike da jin tausayin yarinyar, sai adu'a take tayi mata a sanda ta kama hannunta ta riƙe, ta zaro wani diamond ring daga yatsanta ta saka ma Fullo, kuma sai ya zama kamar dama na Fillon ne, yay cif a yatsan nata. kamar zata yi kuka ta dubi Kaka tace,"se yaushe ne zai farka ni kam?". Kaka ta kalli Turaki shi kuma ya kalli agogon hannunsa sannan yace,"nan da awa ɗaya insha'Allahu". Dada ta dubi Hadimar da ke ta shigo da kayan abinci tana ajiyewa tace,"Uwar wannan yarinya shina waje ko?". Hadimar tace,"ehh ranki ya daɗe". ta gyaɗa kai tare da jan tsaki tace,"sam matar Hayyo uwar banza ce, kije kice da ita ta shigo ta yiwa ƴarta adu'a, ni ban sani ba ko ƙaunar ƴar ne bata yi". sai kuma ta hau bambami yi take kamar zata haɗiye kowa, da yake mafaɗaciya ta kata'i, sai da ƙyar Belɗo ya tausheta tayi shiru yace in bata so Fillo ta tashi to taci gaba da ɗaga murya sannan aka samu ta rufe baki. Turaki ya kalla ƙofar ɗakin da Adda Asma ke shigowa, idonsa ya sauka akan gyalen Ummi da ya leƙo ta jikin ƙofar, ya juya ya ɗauki wayarsa a kan drower ya fita cikin sanyi jiki kamar mara laka, ya sani in har yana cikin ɗakin Ummi ba zata taɓa shigowa ba, tun zuwansu asibitin sau ɗaya ta iya zama a ɗakin shima duk a takure kuma saboda shi, irin iyayen nanne masu bala'in jin kunyar sirikansu. tana ganin fitowarsa ta matsa gefe, ya durƙusa har ƙasa ya gaida ita, sai ta kasa amsawa ta bisa da kallo tana tsananin jin tausayinsa, kwana uku rak amma ya dawo kamar shine mara lafiyar da aka kwantar, idon nan yay jawur ya ƙanƙance tsabar ba ya samun bacci. ya katse shirun nata da cewa,"Ummi ki shiga daga ciki". tace,"a'a da ka koma kawai, ai ina jin ma yanzu zamu wuce". yace,"a'a Ummi ki shiga". sai ta ƙara kallonsa tace,"ya kamata ka huta haka". yay shiru bai iya cewa komai ba, kowa nata ce masa ya huta ya huta, ta ina zai iya hutawa alhalin Fulaninsa na cikin wannan halin. Ummi tace,"baka ce komai ba". yace,"tom Ummi". ya amsa ba dan yana jin zai iya aiwatar da abinda tace ɗin ba. Ummi na shiga room ɗin likita yazo, Turaki ya tsaya daga jikin window yana sauraron bayanin da Dr ɗin ke yi. "kar ku damu allurar bacci ce muka yi mata domin ta samu ta huta yanda ya kamata, ta yacca ba za'a samu damuwa ba idan ta farka, saboda gaskiya tana buƙatar hutu shisa ku ka kalla an ɗau tsayin wannan kwanakin bata farka ba, amma insha'Allah in the next 50minutes zata farka kuma lafiya lau da izinin Allah". duk suka amsa da amin, shi kuma ya ƙara da cewa,"sai dai akwai abinda ya kamata a kula da shi, kamar yanda na faɗa muku tunda farko ta samu heart failure, dan haka ya zama dole a kiyaye duk wani abu da zai iya zama damuwa a gareta, ai ƙoƙarin kiyaye ɓacin ranta sosai, ko stressing kanta da yawa kar ake bari tana yi, zan ƙara nanata muku duk wani abu da zai zamar mata damuwa ko ya sanyata ɓacin rai ko ya haifar mata da fushi to ya zama dole a kiyaye shi in har kuna sonta da ranta". da sauri Dada tace,"insha'Allahu za'a kiyaye hakan, baza ma mu bari ranta ya ɓaci ba balle kuma damuwa, ai ƴar gata ce gaba da baya, fatanmu dai Allah ya tashi kafaɗunta lafiya lafiya". Dr ya dubi ƴan dubiyan da ke ta shigowa ɗakin, da kuma hayaniyar waɗanda yake ji daga waje, ya sauke numfashi yace,"amm ya kamata a bata space dan wannan hayaniyar ma zata iya zamar mata matsala, da za'ai haƙuri ma ƴan dubiyan su dakata har zuwa ta farka". Dada ta ama masa"to shikenan yanzu kowa zai wuce kam". ya ɗauko wata takarda acikin file ɗinsa ya miƙawa Bobbo wanda ya dawo daga pharmacy siyo magunguna, Bobbo ya karɓa ya karanta sannan ya miƙawa Lamiɗo shi kuma yabi bayan likitan zuwa office ɗinsa. asibiti dai sai ya zama kamar gidan biki, dan cikin lokaci ɗaya ya ɗinke da ƴan dubiya waɗanda suke zuwa gaisuwa a shaida musu ƴar Hayyo na kwance a asibiti to duk sai suyo asibitin, kace wata ƴar ƙusan ce ke kwance dan manyan mutane ma sai zuwa dubata suke, a shiga a fita a shiga a fita haka aka dinƙa yi. irin karramammun mutanen da ke wajen in akace maka ƴan'uwan Hayyo ne sai mutum ya ƙaryata, zaka sha mamaki matuƙa in akace mutum me wannan gatan ne ya tsiyatar da rayuwarsa a iska. ba'a sami sasaucin mutane a asibitin ba sai ƙarfe sha ɗaya da rabi, shima kuma saboda Dada ta koma gida ne, dan tana ta waya tana cewa a bar mutane su daina zuwa haka, Dottijo yace mata ai duk wanda aka hana sai yace a'a sai yazo ya nan asibitin yay mata ta'aziyya, sannan Dada taga tafiyar tata is the solution saboda Dr na ta complain akan hayaniyar da ake samu. ƙarfe sha biyu dai-dai Fillo ta farka, motsin hannunta dake cikin na Turaki shi ya ankarar da shi, take yaja wani wawan ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin Alhamdulillah. Fillo ta shiga buɗe idanuwanta a hankali ta sauke su akan Turaki da ya ƙura mata ido yana sakar mata murmushi me haɗe da damuwa. tana jan numfashi a hankali tace,"ruwa". da ƙyar ya iya sakin hannunta yaje ya ɓare carton ɗin faro ya ɗauko ɗaya ya dawo, ya zuba a cup sannan ya ɗagota ya bata tasha, sai da ta shanye tass sannan ya ajiye cup ɗin. ya sanya mata pillow daga bayanta ya jinginar da ita, ita kuma ta shiga bin ɗakin da kallo, daki daki kuma abinda ya faru da ita ya dinƙa dawo mata. abinda zata iya tunawa shine Abbanta ya mutu, kuma har an kwana anyi masa wanka za'a fita da shi ai masa sallah a kaishi, to tunda aka fitar da gawar ba zata ce ta ƙara sanin inda kanta yake ba sai a yanzu da ta farka ta ganta a asibiti. Turaki ya dinƙa kallonta yana jin kamar zai yi kuka, duk ta zabge tai wani muguwar rama, ƙasusuwanta kamar sayi magana, haka idonta yayo waje ya ƙara ƙwalele kace idon aljanu. ya kama karan hancinsa yana rumtse idonsa, hoton wancan ranar ya dinƙa haska masa, sanda aljanun Fillo suka tashi ta dinƙa bige bige, tun ana iya samu a riƙeta a danneta har ta kai ga hakan ya gagari kowa, sai ƙyaleta akayi tana ta murginawa akan duwatsun compound tana ta ife-ife, ƙarar ihu kuwa har na bakin titi zai iya cewa yaji, kuma sanda aka kira wani malamin ruƙiyya yazo me mamakon a sami sauƙi sai gida ya kacame da masu aljanu, ƙannan Hayyo da Yayyansa da jikoki wancan ta faɗi waccan ta kwasa da gudu waccan ta shaƙe na kusa da ita, haka akaita fama da su, ƙarshe sai da aka tara Malaman Ruƙiyya har biyar a gidan sannan aka sami lafiya, ashe aljanun nasu duk na gado ne na kan Kakarsu wadda ta haifi mahaifin su Hayyo da kuma wadda ta haifi mahaifin su Hayyo, ita kuma Fillo har da waɗanda ta samu acikin dajin nan sanda da ta ɗauke asirin ɗakin Turaki. tasha buƙar wuya sosai dan duk jikinta sai da ya farfashe, fuskarta tai ta jini saboda burgimar da tayi akan duwatsu compound ɗinsu. wan mahaifin su Hayyo da suke kira da Dottijo shi ya kira waya yace idan an kaishi to a tattaro a dawo nan gida aci gaba da zaman adu'a kuma, aka shaida masa halin da ake ciki na tashe-tashen aljanun, yace to suyi gaggawar tahowa nan ɗin saboda a samu ai masu magani tunda dama akwai babban malamin da suke da shi acan wanda ke kula da matsalar tasu tunma mahaifiyar tasu na da rai. aiko dai Fillo tasha baƙar wuya, dan Malamin da yay mata ruƙiyya azababbe ne, bai ƙyale Fillo ba a wannan ranar sai da ya ƙona aljanun da suka shigeta na asirin da ta ɗauke, na gadon ne kawai masu shegen taurin kan bala'i da suka ƙi fita, suka ce su ai suna tare da ita ne saboda bata kariya, yinin ranar curr akanta akai ta fama, kuma sai ya zamana in an samu na waɗancan sun lafa da sun jiyo ihunta sai su ƙara tashi, ƙarshe ita sai ɗauketa akayi aka kaita can gidan Malamin, duk wanda yaga halin da take ciki kuwa sai yayi mata hawaye. kuma hankula sai suka ƙara tashi a sanda aljanun nata suka lafa, dan tun ana tsammanin baccin wahala take har abin yazo yafi ƙarfin wannan tunanin, cikin gaggawa aka tafi da ita asibiti lokacin Ummi har ta saddaqar itama ta rasu, bama ita ɗaya ba da dama sun zaci ta mutu, sai da likita ya fito yake shaida musu tana raye tayi dogon suma ne sai dai ba'a san ranar farkawarta ba. sai da Dottijo yayi magana sannan aka ragu a asibitin dan da kowa ya tare acan, yace a bar Kaka da su Adda Asma su zauna tare da ita, sai hadiman ɓangaren Jagarɗo su biyar da suke tare, aka barsu su goma suke kwana a wajenta, sai Turaki da yaƙi tafiya ya kafa ya tsare ko su Kakan baya bari su kwana a ɗakin sai shi, ya kwana da ita ya yini da ita baya ko matsawa daga kusa da ita. Fillo ta ɗago ido ta kalli Turaki, cikin raunin murya dake ƙoƙarin ɓallewa da kuka tace,"da gaske mutuwa ta rabani da Abbana?". Turaki bai iya ce mata komai ya ƙara damƙe hannunta a nasa, nan da nan sai ga hawaye nan zirrr kamar an kunna famfo, ba shiri Turaki ya bar kan kujerar da yake ya hayo gefen gadon ya tattarota jikinsa gaba ɗaya ya shiga lallashinta, ya dinƙa shafa bayanta tamkar jaririya yana faɗa mata kalamai tausasa na kwantar da hankali da sa natsuwa a zuciya, haka har ta daina kukan sannan ta zame daga jikinsa tace,"ina Ummi na?". yace,"Ummi taje gida ita da su Kaka yanzu zata dawo". tai ƙoƙarin zame hannunta daga nasa ya hana hakan, with much concern yace,"me kike so yanzu?". zata fara sabon kuka tace,"Abbana nake so, sai da ya fara sonmu shine mutuwa tazo ta ɗauke mana shi, kuma ni ina so na rayu tare da shi, ina so na sami wannan gata da kulawa da soyayya na mahaifi da ban samu ba, ina so nima na kyautata masa na sami lada, dan Allah kace ta dawo min da Abbana ina sonsa sosai bana so na rasa shi yanzu, albarkar da ya saka min sanda zai mutu bata isheni ba, tayi min kaɗan". idanuwan Turaki suka kawo ruwa calmly yace da ita,"kin tabbatar kina son Abba?". tayi saurin ɗaga masa kai, yace,"to indai kina sonsa ki nuna masa hakan ta hanyar yi masa adu'a ko da yaushe, itace abar da yafi buƙata daga gareki ba kuka ba, kuma ta hakan zai yarda da cewar kina sonsa, sai yay ta saka miki albarka daga can". ya ɗago haɓarta yana kallon cikin idonta yace,"Fulani nah wanda ya mutu ba ya dawowa, Abba ya tafi tafiyar da ba zai ƙara dawowa garemu ba sai dai muje mu same shi a aljannah a yayinda muma muka zama tarihi, dan haka ki daina kuka kinji Fulani nah, idan Abba ya tafi kina da ni, ni zan maye miki gurbin Abbanki, zan ba ki wannan gatan da kike buƙata, zan ba ki kwatankwacin irin wannan kulawar da kike biɗa, uba dabanne ba zance zan ba ki soyayya irin tasa ba, amma zan ba ki soyayya irin wacca ba za ki yi maraici ba". Fillo ta janye hannunsa daga haɓarta ta faɗa jikinsa ta kewaye shi da duka hannayenta, tayi ta kukanta a hankali a hankali yana jin hawayenta na sauka a bayansa masu ɗumi, hawayen da yake jin zafinsu kamar garwashi, bai hanata ba har sai da tayi me isarta tukunna ya janyeta yana tambayarta me take son ci. kanta na ƙasa tace,"bakina babu daɗi". "daurewa za kiyi, kinga cikinki babu komai, idan ba ki ci abinci ba Ummi zata shiga damuwa". ya sauka akan gadon yaje ya buɗe duka coolers na abincin kusan guda goma yace,"look here". ta ɗago ido tana kallon coolers ɗin abincin da mamaki, kamar abincin da sarki ya biɗi a kawo masa, kowanne kuma babu na yarwa, yaga idonta ya manne akan cooler ɗin ferfesun kayan ciki, sai yabi duk ya rufe sauran sannan ya ɗauko plate ya zuba kayan cikin da yaji ganyen zogala aciki, yazo ya ajiye akan table ya rufe. ya dawo bakin gadon ya kamo hannayenta yace,"muje ki wanke baki". tana kallon babban yatsanta tace,"ya akayi naji wancan ciwon?". ya ɗan rufe idonsa yaja numfashi sannan yace,"kin manta?". ta ɗaga masa kai, yace,"ok to zo muje mu dawo sai in tuna miki". yay helping ɗinta ta sauko akan gadon suka wuce toilet, shi ya shiga ciki ya tatsa macline ajikin sabon tooth brush sannan ya fito ita kuma ta shiga, after 4minutes ta fito tana yamutsa fuska saboda jikinta da take jin duk gaɓɓanta na mata ciwo, yana kallon fuskarta ya san alwala tayi, ganin ƙafar ma janta take yi yace,"ko in ɗauke ki?". tayi saurin girgiza masa kai alaman a'a,dan haka ya kama hannunta suka tafi a hankali har kan gadon, babu yanda bata yi ba akan ya barta taci ferfesun da kanta san yaƙi, shi ya dinƙa bata har sai da ta cinye shi akan dagewar da yay tukunna ya aje plate ɗin. kusan duk abin da aka ajiye a wurin nan sai da ya dinƙa ɗiba yana bata ko da 1 spoon tayi sai ya haƙura, ya ɓalle murfin hollandia shima ya zuba a cup, ta dinƙa sha da kaɗan kaɗan. yana cikin bata ne wayarsa ta shiga ringing, ƙwayar idon Fillo ta sauka akan sunan me kiran, ta ɗago ta kallesa sau ɗaya, ta kauda fuska daga cup ɗin da yake kawowa bakinta, bata san me yasa ba ta tsinci zuciyarta na yi mata wani irin zafi, kawai sai ta koma ta kwanta ta juya masa ba ya tana zura duka yatsunta a baki tare da rumtse idonta. ya aje cup ɗin hankalinsa tashe ya shiga tambayarta menene, ya kai hannu zai shafa fuskarta ta ma-ke hannun tana janyo top ɗin rigarsa da ke aje a gefen gadon ta rufe fuskarta, ya dinƙa kallonta a ruɗe yana jin kamar bai san yanda zai yi ya lallasheta ba. a karo na uku wayarsa ta kuma yin ringing, yaja gajeran tsaki ya ɗaga wayan ransa babu daɗi, yay shiru ba tare da yace komai ba, sallamar ma a ciki ya amsa. daga ɓangaren Ilham tace da shi,"Hammah mun dawo". tayi maganar da sauti me bala'in ban tausayi. jin yay shiru ta sake cewa,"Hammah". sai da ya taushi zuciyarsa sannan yace,"kun dawo lafiya?". tace,"lafiya lau". yace,"ya me jikin?". ta fashe da kuka tace,"ba sauƙi, har gwanda ma Mami ta mutu akan halin da take ciki". yace,"Allah bada lafiya, ina abu ne yanzu". yana faɗar hakan ya katse kiran ya mayar da hankalinsa kan Fillo, duk yabi ya rikice da sheƙar kukanta da yake ji na fita a hankali, yay ƙoƙarin ɗagota taƙi bari sai da ya shiga roƙonta kamar ƙaramin yaro sannan ta yarda ta miƙe zaune. yaga uban hawaye duk sun wanke mata fuska, ya zare yatsun nata daga bakinta, daidai da kukan da ta ɓoye ya samu ƴancin fitowa, hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi ya rungumeta yana cewa,"da kin san irin azabar da nake ji da zubar hawayenki, da kin tausaya min kin ƙara taimakona a karo na biyu, na roƙe ki dan Allah dan Annabi ki daina kar hakan yaywa zuciyarki da ke cikin ƙirjina illa". ta janye a jikinsa ta kallesa tace,"dan Allah". yace,"dan Allah what?, me kike so nayi miki? faɗi duk abunda kike so Fulani nah am ready to do it". tayi ƙoƙarin dakatar da kukan tace,"ka sakeni dan Allah". sai ya ƙame ƙam kamar wanda aka dannawa remote, ya zareta daga jikinsa, kallonta kawai yake da wani irin yanayi da shi ɗaya ya san me yake ji, in har da tasan wannan kalmar ta saki abin da take haifar masa da ba zata dinƙa faɗarta ba, to amma bai san ta yanda zai yi ya fahimtar da ita hakan ba, kuma yanzu lallaɓata yake ita da lafiyarta shiyasa ba zai yi amfani da fushinsa wurin nuna mata cewar ba ya so ba. ta ƙara cewa,"in kana ƙaunar Allah da Annabi ka sakeni, ni ba zan iya zama da kai ba". ta faɗa tana kuka sosai. ya sauke doguwar ajiyar zuciya yana furzar da iska daga baki sannan yace,"idan ban sake ki ba za ki mutu?". ta ɗago kumburarrun idanuwanta tace,"ni ban sani ba amma dai zan cutu". idanuwansa cikin nata kamar yanda nata ke cikin nasa ya kama hannunta ya ɗora a saitin zuciyarsa yace,"to ni muddin na sake ki wallahi mutuwa zanyi, so please kar ki ƙara faɗin haka i beg you". ta dinƙa masa kuka Turaki ya rasa inda zai tsoma ransa, ƙiris shima yake jira yasa kukan, ga kiran wayar Boɗejo sai shigowa yake yi, yay banza da kiran yaƙi ɗagawa. sai da kiran Baffa ya shigo sannan yay picking, kuma yana ɗagawa abinda Baffa yace da shi yasa shi damƙar hannun Fillo ba shiri. Baffa ya kashe wayarsa ransa a ɓace, Boɗejo na tsaye akansa sai zazzaga bala'i take yi. Turaki yay calling lambar Maama, ko da ta ɗaga daga muryarsa ta shaida ɓacin ran danke danƙare a xuciyarsa, tace,"lafiya me babban suna?, ba damuwa naji a muryarka ba illa zallar ɓacin rai, mene ya faru?, kai da wa?". ya rumtse ido yace,"Maama Baffa ne ya kirani". "yace maka me?". kamar zai yi kuka yace,"wai na koma yanzu Ilham ta dawo, Maama...". bai ƙarasa ba tace da shi,"baka ce masa mahaifin matarka ne ya rasu ba?". yace,"Maama to ba ya sani ba, ina jiyo muryar Boɗejo nata hayagaga". tayi tsakin takaici tace,"kayi haƙuri me babban suna, kashe wayar ga shi yana kirana, i will call you letter". Turaki ya kashe wayar yana kallon Fillo da ke ta kokawa da shi tun ɗazu tana so ta sauka daga kan gadon shi kuma ya hanata. "da me kike so naji wai?". ta kifa kanta a ƙirjinsa tana ƙara faɗin,"dan Allah ka sakeni ni bana sonka". yace,"naji, yanzu dai ki yi shirun zan yi abin da kike so". tayi shirun tana ɗagowa ta kallesa tace,"yanzu ai nake so, ni ka sakeni yanzu sai kayi tafiyarka can ɗin". yace,"ehh zanyi amma idan kin yarda kin bini munje gida tare, zan miki abin da kike so a daren yau, gobe da safe sai na dawo da ke". yana faɗar hakan tasa hannunta da iya ɗan ƙarfinta ta ture shi ta fita daga ɗakin, a ƙofar ɗakin ta sami Kaka zaune akan kujera ta faɗa jikinta tana fashewa da sabon kuka. *Vote, Comment and Share.* [9/4, 13:21] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *44* duk ta yanda aka so a lallashi Fillo tayi shiru akan kukan da takeyi taƙi ta daina, ta ƙara bawa kowa matuƙar tausayi, kukan nata ya dinƙa taɓa zuciyoyi, Adda Asma ta kwantar da ita jikinta anata ƙara bata haƙuri. lokacin Hamid ya shiga office ɗin Dr ya karɓo takardar sallama, dama a daren za'a sallamesu su wuce da safe to kuma ganin jikin nata yayi sauƙi sai suka ga is better su wuce kawai, bai fi 10minutes ba a office ɗin Dr ba suka fito tare da Bobbo da ya shiga office ɗin daga baya. Hadimai suka dinƙa fito da kaya daga room ɗin da akayi addmiting nata suna kaiwa motar Bobbo, sai a yanzu da suka zo tafiya Fillo ta sami damar ganin sabbin fuskokin da bata taɓa saninsu ba a rayuwata, but tana kallon Gaji da Adda Hassana gabanta ya faɗi, saboda kamannin da suke yi sosai da Abbanta, shi kawai ya fisu haske ne dan kamar Umminta yake, in ba sani kayi ba za kai tsammanin larabawa ne ba fulani ba, su Adda Asma kuma duk kana kallonsu ka san jininsa ne, abinda ya bata mamaki kowa sai nan da nan yake da ita kamar wata gwal. Turaki dai na tsaye yana ta kallonta ya kasa ɗauke idonsa akanta, zuwa lokacin yayi recieving kiran Baffa yafi sau biyar duk akan ya taho, kowanne kira kuma ya ɗaga sai yaji Boɗejo na zazzaga masifa da bala'i, banda ma dai Baffa ɗin ke kira da babu abinda zaisa ya ɗaga, daga ƙarshe ma sai ya fara ignoring call ɗin. Adda Samira ce ta fahimci yana so ya keɓe da matarsa hakan yasa taja su Adda Juwaira da su Kaka suka bar wajen, kamar ƙiris yake jira kuwa suna barin wajen yana saurin isa gaban Fillo da hazari ganin tana ƙoƙarin tashi ta bar wajen. ya kama hannunta ya maidota kan kujerar ta zauna, kawai sai ta ƙara fashe masa da kuka ita lallai ya saketa yanzu ba sai anje gida ba, ya dinƙa bata haƙuri da lallashi amma kamar yana tunzurata, ransa ya kai ƙololuwar ɓaci ya sakar mata uwar tsawa da tasa babu shiri ta faɗo jikinsa tana ƙanƙame shi, jikinta banda kyarma babu abinda yake yi. "ban san irin illar da zan yi miki indai kika ƙara ambatar min kalmar saki". sai kuma ya kwantar da murya gwanin ban tausayi yace,"wannan Kukan naki ba komai bane illa damuwa, muyi avoiding duk kalar wani abu da zai saka ki a damuwa muddin muna sonki da rai, haka Dr yace, bana so na rasaki Fulani nah ina so na rayu da ke, ki taimaka min, wannan kukan naki na faɗa miki baida amfani, in har za'a bawa Abba damar magana da yayi yace ki bar yi masa wannan kukan kiyi masa adu'a, so please ba kuka ba just pray for him". tayi ɗif tare da lafewa a jikinsa kamar ba ita ba, shashsheƙar kukan ma a hankali take yi yanda ba zai ji ba, ya kai bakinsa saitin kunnenta a hankali yace,"za ki bi ni mu tafi tare?". ta girgiza kanta da sauri alamar a'a, sai kawai ya rufe idanunsa tare da miƙewa ya kama hannunta itama ta miƙe. tana taka ƙafarta tace da shi,"zafi ƙafata". yace,"to in ɗauke ki?". ta girgiza kanta da sauri. ya riƙe hannunta suka koma office ɗin Dr, sai da Dr ya tabbatar masa ciwon ƙafartata babu damuwa ya kuma gamsu sannan ya kamo hannunta suka fito. su Kaka har sun tafi lokacin, tana wurga idanu a compound ɗin tace masa,"ina su Kaka?". yace,"sun wuce". ya faɗa yana nufar inda motarsa take, ita dai binsa kawai ta-ke yana riƙe da hannunta har lokacin, sai kallon baƙon asibitin ta-ke yi tunda ba nan aka saba kaita ba, suna zuwa bakin motar sai ga wani mutumi nan ya ƙaraso wurin da gudu-gudunsa. ya rissina yana cewa da Turaki,"ance in zo in tafi da ku ne". Turaki na kallonsa yace,"a'a ga motata ai, kaje kawai". mutumin ya ƙara rissinawa yana cewa,"umarnin Dada ne yallaɓai, Dottijo ma ya ƙara da nasa akai". Turaki ya kalla Fillo da ke ta kallon mutumin da rashin sanin sunayen da yake ambata. yace da shi,"kaje kawai babu damuwa". "tom shikenan ranka shi daɗe, A iso lafiya". ya juya ya bar wajen. Turaki ya buɗe front seat Fillo ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ɓangarensa, ya tada motar suka bar asibitin yana driving kamar baya so, ya maƙale hannunta a nasa kamar wanda za'a ƙwaceta ko wadda zata gudu. ita dai kanta na jingine da jikin kujerar, tana ta kallonsa ta gefen ido tana ganin yanda yake cije fuska yana matse goshinsa tare da dafe kai, har stearing ya kusa ƙwace masa, hakan yasa ya gangara gefe yay parking, ya kifa goshinsa akan stearing, Fillo dai sai kallonsa ta-ke yi, bayan wucewar daƙiƙa biyu tace da shi,"baka da lafiya?". yay shiru bai ce mata komai ba, har sai da ya ɗauki minti biyar a haka yaji ya ɗan sami relief tukunna ya ɗago, ɗagowar tasa tayi dai-dai da shigowar kiran Maama, yay picking yana magana da ƙyar. tace da shi,"me Babban suna na rasa yanda zanyi da Baffanku, kayi haƙuri kawai mu koma tare tunda Fullon taji sauƙi kaji, kasan dai yanda lamarin Boɗejo yake sai haƙuri". yace,"tom Maama". tace,"ba ku taho a asibitin bane?, su Kaka sun dawo tun ɗazu anata tambayar ko lafiya ku baku taho ba, ka san akwai ƴan uwan Babanta daba ƙasar nan suke ba suna so su ganta kafin su koma". yace,"ina kan hanya Maama". tace,"bana son damuwa Me Babban suna, karka zo min da ita ka jefar da ita tun a hanya kaji". ya amsa da,"as you wish". yaci gaba da driving ɗin, Fillo dai tsoro ya cikata duba da kamar ba'a hayyacinsa yake tuƙin ba, can yaji muryarta cikin ƙarfin hali ta ƙara tambayar,"baka da lafiya?". yay mata wani kallo yace,"kina da damuwa da lafiyar tawa ne?". idanuwanta suka yi narai-narai, ta kauda fuska gefe tana kallon titi tana jin zuciyarta nayi mata zafi, ita bata taɓa sonsa ba a rayuwarta, kuma bata taɓa jin zata so shi, abin da tayi masa taimakonsa kawai tayi, so how comes za'a ce shine mijinta?, me yasa ƙaddara zata yi mata haka?, ta ina zata fara zama da shi irin wannan zaman da taji su Ummi na faɗa wai zama na har abada?, taji ƙwalla ta cika idonta, wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙoshinta, in ace shima yana sonta wataƙila ta iya haƙurin zama da shi ɗin, but shima ba sonta yake ba, ya aureta ne saboda ya taimaketa da kuma tausayinta, sannan kuma ya aureta alhalin ya san ba zai iya zama da ita kaɗai ba?, shin ta ina zata fara zama da shi da bata sonsa da kuma kishiyar da bata ƙauna. ta rumtse idonta sosai cikin ranta tana adu'ar Allah ya ɗauki ranta kafin zuwan lokacin da za'ace an kaita gidansa. lokaci ɗaya hawaye ya shiga zubo mata, wataƙila da Abbanta yana raye da ya tsaya mata har sai an raba auren tunda bata so, ta kulle idonta tana jin wani bala'in zafi da ɗaci a ƙasan ranta, kishiya! ita Fillo da kishiya!, kuma kishiyar ma ƴar sarki yacce zata ji daɗin taka ta!, zata iya ɗaukar bull shits ɗinta kuwa?. kawai sai ta cije leɓenta na ƙasa, for some seconds ta buɗe ido a sanda motar ke ƙoƙarin dukan bishiya, da ƙarfi tace da shi,"kayi a hankali zaka ka bugi bishiya". yay saurin juya kan motar yana kaucewa bishiyar da ya kusa daka ba tare da ya sani ba, duk sai yaji dama ya bar wancan mutumin ya tafi da su, dan shi kansa ya san ba'a hayyacinsa yake ba, banda bala'in ciwo da kansa yake masa yana jin ƙirjinsa ma kamar zai bar jikinsa, ga idonsa ma ba sosai yake gani ba saboda azababben baccin dake cikinsu, ya ɗauka wayarsa zai kira Hamid yazo ya tafi da su sai kuma ya fasa, yaci gaba da lallaɓawa yana jan motar a hankali. sanda suka sauka akan titi ya shiga street ɗin da zai kai su gidan Barkinɗo, daga saman kansa yaji tana tambayar,"wai ina zaka kaini?, dan Allah ka kaini gida, ni ba wurin Maama zanje ba". bai ko waiga ya kalli inda take ba balle ya amsa mata. ta ɗauke idonta daga kansa taci gaba da kallon hanyar da bata sa ni ba, da irin ginin gidajen da zata ce in ba a tv ba bata taɓa gani ba, hanyar sam bata yi mata kama hanyar da ta taɓa bi ba, tunaninta ɗaya ne ta yanda zata buɗe murfin motar ta faɗa waje. sunyi tafiya me nisa a street ɗin sannan ya samu wuri yay parking, idonsa na manne da gabansa yace,"fita". Fillo ta ɗauke idonta daga kan symbol ɗin da take karantawa ta juyo tana kallonsa, kamar ba shine taji yayi maganar ba kuma sai taji ya cire mata tantama da ƙara maimaitawa. "fita". tace,"ai ban san ina ne nan ɗin ba, ba zan iya gane hanya ba". shirunta yayi daidai da doka mata tsawa yana ƙara cewa,"i said get out of my car". babu shiri ta buɗe motar jikinta na kyarma, ta fita ta tsaya tana riƙe da murfin motar, "dan Allah kayi haƙuri idan ka saukeni anan wallah ba zan iya zuwa gida ba, ban san ta nan hanyar ba". yana jinta dai bai tanka mata ba, ya ɗauko wayarsa ya danna kira a lambar Hamid, yana ɗagawa yace da shi,"kaine ka shiga mota yanzu?". Hamid yace,"ehh". yace da shi,"ƙaraso ka ɗauki wannan yarinyar, tana wajen symbol ɗin da akai addressing da sunan Hakimi". Abdulhamid yace,"ok tom gani nan". sai da ya hango motar Hamid ta taho tukunna ya figi tasa ya bar wajen, Fillo tayi saurin sa hannu ta kare idonta gudun kar ƙurar da ya baɗeta da ita ta afka mata a ido. Hamid yazo ya ɗauketa kuma har suka ƙarasa gidan bata iya ce masa komai ba, sai magana yake yi mata tayi shiru bata amsa masa ba, tambayoyi ne fal a bakinta amma jin bakin nata take yayi mata nauyi. tunda ta fito a mota kuma sai ta zama ƴar kallo, idonta kamar zai faɗo waje saboda kallon gidan da ake nufa da ita da kuma mutanen dake ta tururuwa akanta, suka shiga gidan tana jin muryoyi da dama na faɗin,"ga ƴar gidan Hayyon, masha'Allahu ta sami lafiya". sai kuma taji wata dattijuwa na cewa,"ɗauko ruwan tofin nan a bata Malam yace tana shigowa ta fara shansa". idanuwanta suka sauka akan Ummi da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin Hajjah mahaifiyar Hayyo, ta ƙwace daga hannun mutanen da ke riƙe da ita ta tafi wurinta ta faɗa jikinta, Ummin ta kama hannunta suka wuce ɗakin Dada, kuma zuwan nasu ne ta samu duk amsar tarin tambayoyin dake cikin kanta tun kafin tayi tambayar a bata amsarsu. mutuwar iyaye bata daɗi, kuma ba'a farin ciki da mutuwarsu duk lalacewarsu, but a ɓangaren Fillo abu ɗaya da zata iya buɗar baki tace shine mutuwar mahaifinta tayi mata rana, domin ta dalilin mutuwarsa yau gasu cikin jin daɗin da basu taɓa hangar cewar zasu ji shi ba har su mutu, gatan da basu san suna da shi ba yau gasu acikinsa. sai nan da nan ake da ita da Hamid da sauran sisters ɗinta kamar wasu gwala-gwalai, tarairaya kace ƴaƴan wasu shegen ƙusan, motsi kaɗan a tambayesu me suke so. cikin satin mutuwar kafin ayi adu'ar bakwai haka aka dinƙa ɗaukarsu ana zagawa da su cikin dangi, babu inda ba'a kai su ba adai familyn mahaifinta da suke nan cikin taraba state, waɗanda basa ƙasar ne kawai ba'a kaisu wajensu ba amma suma sunyi vedio call da su. a hankali ta dinƙa jin damuwar mutuwar na tafiya tana barinta, sai in sun zauna ita da Hamid ne sai suyi ta tambayar junansu wai me yasa Abba ya tsiyatar da kansa haka har yayi irin wannan rayuwar ƙasƙancin bayan yana da gatansa, amsar da basu da ita har kullum kenan. *After 55days.* *Saudiyya, Jeddah, Sanabile, House no 08.* *13:00pm.* Rauda ta fito daga cikin bedroom ɗin hannunta riƙe da biro da jotter, yayinda Fillo ke biye da ita a ba ya nata hannun riƙe da laptop. suka ƙaraso parlo Raudha na cewa,"yanzu to ya kika ga lissafin?, tunda dinner ce kawai ai hakan yayi ko? sai dai ban san ba ko after an kai ki akwai abinda za'ayi". Fillo bata ce da ita komai ba ta zagaya ta side ɗin da Dada take ta zauna kusa da ita, taci gaba da operating laptop ɗin tana duba wata university acan Europe, dan tun bayan sati ɗaya da rasuwan Abbanta ta zana private waec tare da su Raudha da Amatullahi sauran jikokin gidan, aka kuma ce kowanne ya nemo university ɗin da yake so ya tafi, so ita taso ta zauna anan nigeria but due to haukar Asuu da ta sani yasa ta fasa cikewa ta-ke bincike akan Uni ɗin da Raudha tace su tafi can kawai, yanzu lissafin karatunta kawai take yi ba lissafin wani aure ba kamar yanda taga an mayar da hankali akai tun bayan adu'ar arba'in. Dada da ke shan tea ta ɗago kai ta kalla Fillo, ta girgiza kai tana yamutsa fuska kamar wacca taga kashi tace,"tirrrr, tirrr, tirrr da wannan mugun hali naki irin na Hayyo". Fillo kamar zata yi kuka ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"kai dan Allah Dada, Abba nah fa ya mutu ki daina min irin haka, duk in kin ambaci sunansa fa sai ya tashi a ƙabarinsa". Dada ta watsa mata wani kallo na ki shiga hankalinki da ni sannan tace,"an faɗa ko ba halin nasa ba ne, wani yace kar ya zama mutumin ƙwarai?, to in faɗa miki har duniya ta naɗe Hayyo dai bai da halin kirkin da za'a shaide shi da shi gwara ma ki daina nunawa duniya shi ubanki ne, ko kuma kike bari ana ambatarsa akai-akai ko ake masa adu'ar samun rahamar ubangiji. banda iskanci ke kenan ba ki da aiki sai faman ɓata fuska ki yita turowa mutane laɓɓa gaba kamar ganda, to wallahi ki kiyayeni tun ban ɓata miki ba, ana tausaya miki saboda rashin mahaifi amma kina yiwa mutane iya shegen da kika ga dama, to ni ubanki zanci ba kowanne iskanci nake ɗauka ba". ta gama faɗan tana harar Fillo kamar idanuwanta zasu zazzago, sannan ta juya kan Raudha tace,"ina jinki kin gama lissafin abin da na saka ki?, kuma kin duba shagon da yafi kowanne anan Jeddah ɗin?, ba sanin kan shagunansu nayi ba inda dai Riyadh ne can nafi zama". gaban Raudha ya faɗi, nan da nan ta shiga zare idanu kafin tace,"kiyi haƙuri Dada wallah na mance, amma zanyi yanzu". da muryar faɗa Dada tace,"in saka ki aikin tun yammacin jiya kice min ba kiyi ba?, to uban me kike rubutawa yanzu?". "Dada ai kin san can dangin mijin Fillo sun ce za'ai events kafin ta tare, shine dama nake lissafin abubuwan da zamu yi, ƙanwar mijin tana ta yo waya ta tambaya ko mun gama shirya abubuwan da muke so kuma duk banyi ba, ita kuma inata tambayarta taƙi ce min komai kiyi mata magana dan Allah". ta faɗa duk a ɗarɗarce saboda irin kallon da Dada ke bin ta da shi da makafin idanuwanta. Dada ta gyaɗa kai ta juyo ta fuskanci Fillo tace,"ke ɗauko min sanda ta". sanin hali yasa Fillo miƙewa babu shiri ta wuce ɗakin Dada, in few seconds sai gata ta dawo tana miƙawa Dada sandar daga baya-baya. Dada ta karɓa ta saita kafaɗar Raudha ta muƙa mata, tuni zafin dukan ya ratsa Raudha idonta ya ciko da ruwa. Dada ta fara mata masifa,"uwaki da ubaki ke da lissafin bikin, wato har wani shirin bikinta kuke yi saboda ba kwa ƙaunarta ko?, saboda ubanta ya mutu shikenan sai ace bata da me tsaya mata?, to tana da ni Kakarta, ni ce nan gatanta, dan haka banga wanda zai ɗaukar min jika ya kaita inda ba'a ƙaunarta ba. ko za kice baki da labarin Kakar yaron bata sonta?, har tana faɗin wai ya sakar min jika, to dama ko bata sa shi ya saketa ba ai mu zamu buƙaci ya saketa tunda dama jikar tamu ba sonsa take yi ba, ni inama na taɓa jin anyi gantalallen aure irin wannan Allah dai ya gafartawa Hayyo, to in har ba so ake rai ya dinƙa ɓaci ba kar in ƙara ji an tada maganar auren nan". taja dogon tsakin da duk su Fillo sai da suka toshe kunne, ta doka sandarta akan table ɗin dake gabanta, fuskarta na bayyana tsurar ɓacin rai ta hau ruwan bala'i kamar zata haɗiye gidan. "wace ita da zata ce jikanta yafi ƙarfin jikata ba zai zauna da ita matsayin matarsa ba?, to me take ji da shi, kuɗi ko mulki ko kuwa sarauta?, idan tana ɗagowar cewa suna da Gombe a hannunsu to muma haka muke da Taraba a tafin hannunmu tun daga sama har ƙasa. ita wai ƴar wofi har wani kashedi take turo min kar in sake jikata ta tare a gidan jikanta saboda yana aurar ƴar sarki, to idan ban sa an ƙwace sarautar tasu ba Allah ya tsine, babu ƙulla ƙullar da ba zan iya yi ba akan a tsigesu a kujerar sarautar nasu sai inga ta tsiya, yo banda ma dai ƙaddara ina jikata ina jikanta?, ai wallah sam babu haɗi, jikata tafi ƙarfin wannan mummunan jikan nata, wani dogon banza ma da shi kamar basamude, ai Fillo matar larabawa ce ba matar mutumin da zuwansa saudia ma bai fi ƙirgen yatsu ba, yaron ma da bai ma san darajar mace ba, tun sadakar uku bai ƙara waiwayanta ba shi ga shi ɗan iska, iya haka ma ai ya shaida maka wannan yaro baida ilimin addini sam, mu kam kaf zuri'ar Barkinɗo babu wanda yake jahili babu kuma wanda ke auran jahili, babu ta inda aka barmu daga addinin har bokon, saboda haka can ta kwaɗa jikan nata ta cinye itace a yunwa ce, mtswww daga jin ma yanda take hayagaga akan sarautar tasu kasan ci akai aka rage musu". tai shiru tana faman huci sai girgiza ƙafa ɗaya akan ɗaya take yi, ta kuma jan tsaki ta kurɓi tea sai kuma ta zubar da shi acikin wata ƙatunwan silver me kama da sink. ta kama haɓa tana jijjiga kai na irin takaicin nan ya isheta, ta ɗora manyan idanuwanta akan Fillo tana faɗin,"to ni dai ban yafewa ubanki ba da yasa aka raina mu haka, banda yaja mana raini har ina wannan figaggiyar tsohuwar ta samu zarrar yo min aiken in raba jikata da jikanta dan yafi ƙarfinta, jikarta ƴar sarki ce tafi ƙarfin ta haɗa kishi da jikata ƴar aiki a gidan Alƙali yake ko uban me oho?, har ƙara faɗa take yi mu kuka da kanmu in har muka bari akayi tariyar auren nan". tai shiru tana cizon yatsa kafin ta shiga nuna kanta,"har ni ake yowa wannan baƙin aiken rashin mutumcin ban ɗau matakin komai ba?, ni ƴar sarkin taraba, uwar gwamnan taraba, uwar hakimin wurkum, Kakar soja, uwar macen da tafi kowacce mace kuɗi a nahiyar africa, yo ni kam yaushe nayi wannan saken?, dama har haka tsufan ya lalatar da ni?, ko da yake duk Hayyo ne yaja min ba kowa ba kuma yaje shi da Allah". cikin ɓacin rai ta ƙara buga sandarta akan table har saida glass ɗin ya tsage. "to billahillazi idan ban sa jikan nata yayi fatali da gimbiyar waje ba ya zauna da Fillo kaɗai ba shegiya nake, Hassana sunana na fita fitina da rigima wallahi, taje ta binciki tarihi taji ba'a taɓan ƴaƴa da jikoki a zauna lafiya". tahi ƙwafa tare da miƙewa,"na rantse Allah ne ya rufawa Hayyo asiri bamu ƙara gamuwa ba da wallahi tallahi babu abin da zai hanani kai ƙararsa gaban alƙali, haka kawai yaja anai mana kallon ƙanan mutane har ana ci mana mutuncin da kare ba zai shinshina ba, akan jikarmu zata tare a gidan aurenta a kira waya ana mana gargaɗi, kashhh, amma babu komai idona idonta sai ta san tayi min aiken baƙaƙen maganganu, sai ta san tasa shegiyar matar tasa ta kira jikata ta zazzageta, zan nuna mata na fita ɗanyen kai, kowa ai shegen kansa ne, jikan nata da ta-ke ta haƙilo akansa zan nuna mata mune rayuwarsa, ba dai ance yana matuƙar ƙaunar Fillon ba, to aradu sai ya sakar min jika sai dai ya mutu, in ya mutu ita ke da asara bamu ba". zata bar wajen ta kalla Fillo taga tana kuka, ai ko ta ɗaga sandarta ta dinƙa bugun Fillo da ita tana faɗin,"saboda nace sai ya sake ki shine kike kuka, ke ko ace ma Kakar tasa bata kira taci mutuncinmu ba kya yarda ki koma wurinsa ne yanda yay fatali dake ɗin nan ya manta da aurenki da ke kansa, to kuwa sai dai ki bi ubanki amma wannan aure sai ya mutu a yau-yau ɗin nan, dan ba zan yarda kije inda za ake miki kallon raini da ƙasƙanci ba duk da cewar ubanki yaja miki, kiyi kukan jini ba na ruwa ba, indai jikan wannan figaggiyar tsohuwar ne na rabaku bake ba shi, ya sakar min ke ki samu mijin aure anan kafin mu koma, babu abinda za kiyi da ɗansu, in ma saboda taimakon da suka yi miki ne gantalallar uwarki ta kasa cewa komai to ai kema kin masa taimakon da yafi nasu, ni na gode Allah ma da bai mayar da ke saura ba". tayi hanyar ɗakinta sai jaraba take yi, ta buɗe ƙofa zata shiga ta waigo ta kalla Raudha tace,"ɗau waya ki kira min Jagarɗo". sai kuma ta fasa shiga ɗakin ta dawo ta zauna, ranta ɓace take ta kallon Fillo da take kuka, banda tana tausayin karta ɓaɓɓallata da sai ta ƙara mummuƙa mata sandar ko ta shiga hankalinta. Raudha ta miƙo mata wayar tana cewa,"ga shi Dada". ta karɓa ta kara a kunne tare da saka glass ɗinta kamar ganinsa zata yi, bayan sun gaisa tace da shi,"kana jina?". daga ɓangaren Jagarɗo yace,"ina ji Dada". tace,"to ka saka Kakinka na sojoji ku ɗauki hanyar gombe yanzun nan, ka shiga har cikin gidan Alƙali wa yake oho, ka kamo ɗansa da yake auren Fillo kasa masa ankwa sannan ka basa biro da takarda kace ya sakar min jikata, in yaƙi kayi gidan gyara hali da shi da figaggiyar Kakarsa da ta yo min aiken rashin mutunci". Jagarɗo yace,"amma Dada inaga wannan fa sakin nan ba masalaha bane, kar a maida yarinyar nan bazawara tun tana ƙaramarta". ta fusata tace,"a mayar ai bata zama sauran wani ba, ya saketa yau ɗin nan in ba haka ba ai tashin hankalin da ba'a taɓa yi ba". tana faɗin haka ta kashe wayarta, ta kalli Fillo ta doka mata tsawa tace,"ɗago da kanki ki bani lambar mijin naki". Fillo ta ɗago kanta, hawaye duk ya wanke mata fuska, cikin muryar kuka tace,"ban san lambarsa ba". Dada taja tsaki tace da Raudha,"kira min AbdulHamid a waya". ko sallamar Hamid ɗin bata amsa ba sanda ya ɗaga wayar, tace da shi,"ka turo min da lambar mijin Fillo yanzu yanzu". sanin wace Dada yasa ko tambayar ba'asi bai yi ba, haka kuma bai jinkirta ba wajen turawar, dan duka 2 numbers ɗin ya tura mata, gudun ma kar ta ƙara kira ta zazzage shi tace ya tura mata ta ƙarya. Fillo ta miƙe tayi bed room ɗinsu tana jin zuciyarta kamar zata fito, har sau biyu kiran wayar Turaki na shiga bai ɗaga ba sai ana uku, lokacin suna tare da Bello a office, ganin lambar saudia ce yasa bai hanzarin picking ba dan bai san ko waye ke kiran ba. yana ɗagawa yayi sallama Dada ta amsa kamar abin arziƙi, daga can ɓangarensa ya kurɓi ruwa sannan yace,"wake magana?". Dada tana kalla Raudha tace,"munafuka mene ma sunan shi?". baki na rawa Raudha tace,"kamar Turaki naji suna faɗa". Dada tai gyaran murya sannan tace,"Turaki ne?". yace,"ehh ni ne". tace,"yauwa to suna Hassana Kakar Fillo ta wurin uba, Fillo uwar gidanka da bata tare ba har yanzu ka shaida?". Turaki ya gyara zamansa yana rissinar da kai kaman a gabanta yake yace,"Allah sarki Dada ina yini". tace,"lafiya". Turaki ya shafo wuyansa yana jin nauyi da rashin dacewar abin da yayi, tun ranar sadakar uku da ya baro Taraba bai ƙara waiwayar garin ba balle ta kan Fillo da ya san ya baro acan, ya sani tana da hakki akansa amma fushin da yayi da ita baya jin zai iya ƙara nemanta sai idan ita ta neme shi, shi ba lusarin namiji bane da zai bari son ƙanƙanuwar yarinya yake walagigi da shi, dalilin da yasa ya banzatar da ita da lamarinta kenan, kuma ya ɗau alwashin indai ba gajiya akai aka kawo masa ita ba shi dai da kansa ba zai nemeta ba, Maama tayi fama da shi har ta haƙura ta zuba masa ido, shi yanzu yaji ma da bala'in Boɗejo na kullum kullum, da fitinar da Ilham ta tsira ba dare babu rana, ta wanni fannin ma sai yaga barin Fillon acan shi yafi akan ya ɗaukota ya kawota nan ɗin, dan bai san abunda Boɗejo da Ilham zasu aikata ba. yace,"Dada dama...". tayi saurin katse shi da cewa,"riƙe dama ɗin ka, zatonka biko na zo?, a'a ko ɗaya wallahi ajinmu da girmanmu ya wuce nan, kiranka nayi dama in sanar maka da cewa Kakarka ta kira waya tayi mana kowanne irin kalar rashin mutunci, tace muddin Fillo bata rabu da kai ba to mu kuka da kanmu da duk abinda zai biyo baya, tace babu batun tarewarta a gidanka in ba haka ba zata cinnawa gida bom, tace ba zai yiwu daga auren ƴar sarki a ɗauko ƴar aiki ace za'a haɗata da ita a matsayin kishiya ba, itama kuma matar taka tace ba zata zauna da kishiya ba Fillo ta nemarwa kanta mafita tun bata yi mata lahani ba, to shiyasa na kiraka in faɗa maka cewa ka sakar min jika saki uku rasss domin tafi ƙarfinka ta kuma fi ƙarfin zaman gidanka ba wai dan muna tsoro ko kuma muna gudun abunda zai je ya dawo ba, a'a wallahi fin ƙarfinka tayi in ma faɗa maka gaskiya, akan me zata zauna a gidan daƙiƙi da daƙiƙiya alhalin ita da iliminta, to dan haka idan da kana tunanin cewa bata da gata shiyasa ka maki giya kaje aka maku kalar wannan watsatstsen auren to yanzu ka sani da gatanta, mutuwar ubanta ta bankaɗo mata daraja da ƙima da mutuncin da take da shi, ita ba salwantacciya bace da za'a kaita gidan da wata figaggiyar tsohuwa can zata ke kallonta banza a wofi, gwarama in saboda matarka ce nace Fillo ta daka shegiya daidai gwargwadon ikonta dan babu matsoraci a zuri'armu. in taƙaita dai, Turaki kake ko waye yanzu da muke wayar nan ka rubuta takardar saki uku rerass ka yo min aikenta, idan kuma kaƙi sakar min jika aradun Allah zan sa a ɗaure kaff zuri'arku, dan bani da kyau, mutunci ba isata yayi ba". Turaki ya rumtse idonsa sosai, farar ɗaya ciwon kai ya kama shi, ya rasa me zaice da Dada, idonsa ya dinƙa haska masa irin jalalar da Boɗejo ta dinƙa yiwa Maama da Mum akan auren nan da zancen tarewar Fillo da akai, cin mutunci babu kalar wanda bata yi musu ba, har da cewa zata sa Baffa ya sakesu su kama gabansu, tana faɗin wai Ilham ba zata zauna da kishiya ba itama ai ita ɗaya ta zauna, in ace dai wata Turaki ya aura to in goma zai yi babu abinda ya dameta, amma akan Ilham zata iya cinnawa kowa wuta a ƙone, sai taga ta inda wata shegiyar ƴar aiki zata raba miji da Ilham, banda ma dai ana so a bar masu abin kunya ace za'a haɗa ƴar sarki da ƴar aiki, to ba'a isa ba, yanzu dai baida sukuni ta hanasa sakat, bini bini ta kira shi tace ya saki ƴar aikin da yaje ya aura a titi babu waliyi. ya furzar da iska daga bakinsa yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, in da yasan haka auren yake me zai kaishi yin auren duka biyun. Bello nata tambayarsa me ke faruwa bai iya ce masa komai ba, har sai da Dada taji shirun yayi yawa sannan tace da shi,"baka ce komai ba, sai fa ka sakar min jikata, kaima ai ba ƙaunarta kake yi ba munafiki algungumi, kayi zaton gata ne bata da shi kaje ka maki giyarka ka aureta ta yanda zaka wulaƙantata, har da wani cewa tausayinta da taimakonta yasa ka aureta, a gidan uwar wa kake tausayin nata, yaushe rabon da ka waiwayeta?, ai dama duk me hankalin da yaji kalar wannan auren ya san na cin mutunci ne, to aradun Allah ko ka sakar min jikata ko babbar kotun duniya ta rabani da kai". a hankali Turaki yace,"kiyi haƙuri dan Allah Dada...". ta ɗaga murya wajen saurin katse shi da cewa,"kai bafa sulhu na kiraka muyi ba, in sulhun zan nema in kira waccan jarababbar Kakar taka mana, to ka daina bani haƙuri dan babu shi a tsakaninmu kuma ba zanyi ba, ka sakar min jikata kawai, yanda ake jinka ɗan gwal kai da matarka itama haka take ƴar gwal ba daga sama ta faɗo ba". ya ƙara cewa,"Dan Allah Dada...". Dada tayi ɗiff ta kashe wayarta, ta jefar da ita a ƙasa tai ɗakinta, Raudha tabi bayanta da kallo cike da takaici, yaushe aka siya mata wayar amma tana neman ta kashe mata ita. *Gombe, 11:00am.* a sanda suka gama wayar da Dada, Turaki ya baro office ɗinsa yana jin kansa duk ya cunkushe. Bello dake driving ɗin yace da shi,"karka sakawa kanka damuwa, komai zai warware insha'Allah". Turaki ya kallesa da jajayen idonsa cikin ƙaraji yace,"fisabillahi saboda mace sai in rasa kwanciyar hankalina, ta ko'ina ji nake babu daɗi, haba dan Allah". Bello ya sauke numfashi yace,"ba mace bace rashin kwanciyar hankalinka MT, kai ne ka jawa kanka matsalar duk da kake ciki, yanda kayi gaban kanka a auren nan dole ka fuskanci ƙalubale, in ace da izinin iyayenka kayi komai wallahi wannan matsalar ba zaka shigeta ba". "shiyasa nayi deciding rabuwa da ita ai tunda itama bata sona, but Maama da Mum sun hana, to ni zan haɗa har ita Ilham ɗin na sakesu, ba zan iya da wannan damuwar ba". ya faɗa daidai da sanda suka ƙaraso bakin gate, Bello ya bushe da dariya, kafin yayi magana tuni Turaki ya fice daga motar ya shige gida. yana shiga yayi kiciɓis da Boɗejo a compound tana ta masifa akan bai bi ta kan Ilham da bata da lafiya ba, ta tsayar da shi bai ko bi ta kanta ba yay wucewarsa side ɗin Hajiya Madina, kai tsaye upstais ya haye, yana zuwa yay knocking door, daga ciki Hajiya Madina ta ɗaga ido ta kalla bakin ƙofa kafin tace,"come in". ya murɗa handle ɗin ya shiga gabansa na faɗuwa, yana saka ƙafa suka haɗa ido, ba shiri ta ɗaure fuska kamar bata san shi ba, ta ɗaga masa hannu da cewa,"get back". ya marairaice,"please Maama i want to talk to you, dan Allah kiyi haƙuri akan laifin da ban san nayi miki ba". ta ɗauke idonta daga kansa tace,"nace ka fita ko". ya ƙarasa shigowa yana ƙoƙarin zube gwiwoyinsa a ƙasa, ganin hakan yasa ta miƙe zata bar masa ɗakin ba shiri ya rigata fita, ya fita yana riƙe kansa da yake jin kamar zai bar jikinsa. part ɗin Hajiya Ramla ya wuce, tana ganinsa ta ajiye cup ɗin dake hannunta tana tambayarsa,"Babana lafiya?". ta tambaya duk da tasan yana cikin matsala, amma yau ɗin tana ganin ba irin yanda ta saba ganinsa aciki ba, damuwar ta girmama. ya zauna akan kujera yana daɗa riƙe kansa ba tare da ya ce mata komai ba, ta baro dining area da sauri tazo ta zauna a kusa da shi, ta dafa kafaɗarsa tana cewa,"what is wrong with you Babana?, kai da Boɗejo ne?". ya ɗago ido kamar zai yi kuka yace,"Maama ce". "me ya haɗaka da Maaman?". ya kwantar da kansa a kafaɗarta yace,"almost 1week fa Mum ko gaisuwana bata amsawa, ban san laifin da nayi mata ba wallahi, and taƙi bani damar ma da zan bata haƙuri, na mata sending apology through text message and letter duk tayi ignoring ɗina, kuma ina so nayi magana da ita Mum". Hajiya Ramla na kallonsa da tsananin tausayi tace,"and duk ina ina hakan ta faru?". ya kama hannunta cikin sanyin murya yace,"kinyi busy da yawa a office Mum, kuma kinga Baffa ya hanani zaman gidan nan". ta sauke numfashi tace,"tashi muje". yace,"Mum ko munje fa ba zata saurareni ba, korana take yi". ta kama hannunsa kawai suka fita zuwa side ɗin Hajiya Madina, suna shiga parlo tana saukowa daga upstairs, taiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai ta wuce kan kujera ta zauna, yabi bayan Mum suka ƙarasa ya zauna kusa da ƙafafun Hajiya Madina. Hajiya Ramla tace,"ina bayar da haƙuri a madadinsa Madam". Hajiya Madina ta kalleta tace,"bai faɗa miki laifinsa ba?". yay karaf yace,"ki faɗa min Maama zan gyara". nan da nan ta fara masifa tana cewa da Hajiya Ramla,"yaron nan saboda baida mutunci yana so ya mayar damu ƙanan mutane yaje dubai ince idan sun tashi dawowa ya taho da trollys amma ya kawo min guda goma sha biyu kacal, ba wannan ba ma!, nace ya haɗo lefe but sai ya turawa Zaytuna 1ML wai ta siya abin da taga ya dace, wato gamu faqararru da miliyan ɗaya zamu haɗa lefe ko?, in tambayeka ma! zatonka Fillo ƴar aiki daka sani a baya zaka kaiwa lefe da zaka kashe 1ML kacal?, to in haka ƙwaƙwalwarka ke faɗa maka ta yaudareka, Fillo ƴar aiki daban Fillon da zaka kaiwa lefe daban, in ka manta ka tuna gidan da kaje kayi gaisuwar mahaifinta, ka tuna irin mutanen da ka samu, ka san da cewa kenan tafi ƙarfin naira miliyan ɗayanka, Fillon yanzu ƴar gata ce gaba da baya kuma ƴar gidan manyan mutane, beside wallahi ko da ace Fillo ta nan a yanda ka santa tun farko baka isa ka kawo min lefenta na miliyan ɗaya na karɓa ba, kai ka san da cewa taimakonka da tayi tafi ƙarfin dukka arziƙin ubanka har da naka. to make it short, kaje ka sami ubanka Alƙali Dikko ka tambayesa lefen nawa suka haɗawa ƴarsu daga nan sai kayi abin da ka san zai ɗaga mutuncinmu ba wanda zai ja mutuncinmu ya zube ba, dan mu ba marowata ba ne". kansa a ƙasa yace,"Maama kiyi haƙuri amma wallahi bani na tura kuɗin ba, time ɗin account ɗina ya sami matsala kuma kaina ya ɗau caji da damuwar Boɗejo shine nasa Bello ya tura mata, kuma wallahi sai da nayi masa magana yace ai hakan ya isa wai almubazzaranci babu kyau". Hajiya Madina ta zare ido tana doka masa tsawa tace,"rufe min baki shashasha, shi Bellon da zai haɗa nasa lefen da 1ML ya haɗa da har ya mayar da kai ɗan iska, me yasa baka tuna masa check ɗin da na basa yaje ya haɗa nasa lefen ba?, ko kuma baka faɗa masa gidan da kaje ka sami Fillo a yanzu ba?, to wallahi wallahi ba zan kai iyaka akwatu sha biyu ba, kuma ba zan kai lefen miliyan ɗaya ba, tashi ka bar min parlo". ya ɗago ya kalleta kamar zai yi kuka, ya marairace yana roƙonta akan tayi haƙuri. tace,"fitar min a parlo tun ina ganinka da gashin ido, ai ba iyakarta kenan ba, nace kaje ka gano lafiyar matarka kaƙi zuwa yau kwana hamsin da wani abu, wanne kallo kake so mutanen nan suyi mana?, amma na lura da hakan bai dame ka ba saboda kana tare da zaɓin ubanka acikin gidanka ko?, kai kasan maganganu marasa daɗin da Boɗejo tazo ta yiwa mahaifiyarka yanzu kuwa?, kuma duk akan Ilham, me ta-ke nufi da mu?, auren nan muma da muke iyayenka muka haƙura da yanda kaje kayi gaban kanka balle ita, ta bar yarinya ta tare a ɗakinta amma ta hana kowa kwanciyar hankali, ba'a zama da kishiya ita uwar yarinyar ta zauna da kishiyoyi, haba dan Allah tun yaushe ake abu ɗaya, abu mitsitsi yaƙi ci yaƙi cinyewa, comon tariyar da za'ai lokaci ɗaya a wuce wurin ta hana rawar gaban hantsi, tabi tasa mahaifinka ya takura maka saboda kai baka da uwar da zata baka umarni ko me?, but shikenan zan yiwa tufkar hanci, idan ta san wata ai bata san wata ba, yanda ɗanta yake bin umarninta haka kaima zaka bi umarnin taka mahaifiyar, ai uwa bata fi uwa ba". ɓacin ranta na ƙara tsananta ta waiga gefenta ta ɗauko jotter, ta falli takarda ta jefa masa da biro tace,"umarni nake baka ba ja'inja nace muyi ba, ka saki Ilham saki ɗaya". yay saurin ɗago kai yana kallonta,"Maama in saketa kuma?". ya kulle ido yana jan ajiyar zuciya,"Maama itama fa Fulani Kakarta tace sai na saketa". ta buga masa tsawa tace,"ba batun Fillo nake yi ba yanzu, ka fara sakar musu ƴa tukunna". sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"umarninki ne a matsayinki na wacce ta ɗau cikinsa wata tara ta kuma haife shi da wuya bata sauƙi ba, kamar yanda itama take jin ta ɗauki cikin wata tara ta haife bata sauƙi ba, idan ta cije ki fita cijewa, kin sa ya saki Ilham kuma ba zai saki Fillo ba". ta ƙara maida kallonta kan Turaki tace,"nace ka sakar musu ƴa ko". babu shiri ya shiga rubutu, _Ni Muhammad Habib Dikko na saki Rumana Hashim saki ɗaya._ ya gama rubutun daidai da faɗowar Boɗejo parlon, kuma daidai da shigowar kiran Dada a wayar Hajiya Ramla.... *Comment, share and vote.* [9/4, 18:52] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *45* Boɗejo ta ƙara ɗaure fuska a sanda take isowa kan Turaki ta tsaya. "mara mutuncin banza da wofi, kai har nawa kake da zaka raina ni?, har ni ina maka magana ka yi banza da ni ka ƙaro gaba wato ga ƙatuwar shashasha na yi maka magana ko?, ko da yake babu komai, ba ni karaina ba ubanka ka raina". ta gyara zaman gyalenta tana saka hannu ta ɗago kansa sama,"wallahi bari kaji na faɗa maka kayi kaɗan kace zaka wulaƙanta min Ilham, sanin kanka ne kaf jikokina na fi ƙaunarta, ba'a haifeka ba ba'a haifi uwar da zata haifeka ba, ɗan iskan banza yaushe kaciyarka ta girma har da kake jin kafi ƙarfin kabi umarnina da na ubanka. kai ka sa ni dai Ilham tafi ƙarfin wulaƙancinka, domin kuwa ta fika gata, ita ɗaya a wajen uwarta bata taso ta san wata aba damuwa ba, saboda haka baka isa kace zaka haɗata da kishiya ba, kishiyar ma mara aji ƙasƙantacciya wadda tayi aiki a gidanku, haba dai cin mutunci haka har ina!, a wanne garin mahaukatan ma ka taɓa jin an yiwa mace kishiya alhalin ko shekara bata rufa ba, ka tambayi uwarka kaji shekarun da ta rufa bata taɓa ɓatan wata ba kafin ayi mata kishiya, duk da dai na san cewa ba kowa ke zugaka ba illa waɗannan munfukan marasa yafiya da haƙuri". ta faɗa tana nuna Hajiya Ramla da Hajiya Madina da baki tana bin su da harara. "kuskure uban waye ba ya yinsa, haka laifi uban waye ba ya yinsa, ku waye ya san adadin laifin da ku ka yiwa ubangiji kuma ku ka roƙe shi ya yafe muku. dan uwar yarinya tayi masa laifi ai ba yana nufin yarinyar ce da kanta tayi masa ba, ku wa yasan kalar mutanen ma da ku ka yiwa sharrin da yafi wanda tayi masa, kuma naga dai anyi shekara da shekaru da yin abun, kuma ke Madina bace kika yi kun yafe ba, amma saboda dai zuciyarki baƙa ce sai yanzu za ki wani fa-ke da abunda aka riga aka manta da shi, saboda dama kina baƙin ciki da gatan da Allah ya yiwa Ilham wanda ƴaƴanki basu samu ba, to kuwa sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu domin gata da mulki da jin daɗi da ilimi da tarbiyya Ilham ta yiwa ƴaƴanki zarra, har a naɗe duniya kuma ba zasu samu abunda ta samu ba". ta maida hankalinta kan Turaki,"mara imani wanda bai da tausayi, yarinya bata da lafiya amma ka iya tsallaketa kasa ƙafa ka bar gidan saboda ga ka baƙin mugu azzalumi, to idan ba ka sa ni ba ka sa ni, akan Ilham ina iya ɓatawa da uban kowa, in nace uban kowa har da nata uban kuwa, ka ga kenan naka uban ba komai ba ne a idona. saboda haka yanzu tun muna ta lafiya lafiya ban ja abinda zai hana kowa kwanciyar hankali ba to ka miƙe ka wuce muje ka kaita asibiti, shege ɗan banza ka samu ka ɗirkawa yarinya ciki shi ne za ka watsar da ita, to miƙe mu tafi, alhakin kulawa da ita ai akanka ya ke yanzu ba'a kan iyayenta ba". shi dai kansa har lokacin na ƙasa yana ta kallon rubutun sakin da yay, ya rasa gaba ɗaya me ma yake ji a tare da shi, tsabar bala'in ciwon da kansa ke yi masa ji yake kamar zai bar jikinsa. sai da Boɗejo ta kai bakin ƙofa tukunna ta waigo tana ƙara cewa,"wai kuwa ba zaka taso ba?, ka san Allah in har wani mummunan abu ya sami Ilham sai nasa an ɗaureka". tayi ƙwafa tana bin su Hajiya Madina da wani kallo na ban haushi tace,"algungumai duk ku biyun da ba ku da aiki sai saka yaro agaba kuna kimtsa masa yanda zai bijirewa umarnin ubansa, yau zan gani sai dai ko ni ko ku acikin gidan nan muddin ba'ai abunda nake so ba, dan ya zama dole yau a saki waccan yarinyar, domin a yanzu dai Ilham ba zata zauna da ita ba har sai ta haife abinda ke cikinta, zan nuna muku na isa zan kuma nuna muku kaf a ƙasana ku ke, munafukai biyu masu son raba zumuncin ƴan'uwa, abokan sheɗ...". ba ta ƙarasa ba Turaki ya dakatar da ita a fusace,"ya ishe ki Boɗejo, zan lamunci duk kalar rashin mutunci amma banda cin zarafin iyayena a gaban idona. haba don Allah don Annabi, duk kin bi kin hana kowa kwanciyar hankali akan wata banza yarinya can, idan tafi ƙarfin a wulaƙantata me yasa kika na ce aka aurawa wanda ba ya sonta ba kuma zai taɓa sonta ba". bai san lokacin da ɓacin rai ya kaisa ɗaga ɗan yatsa ya na nuna ta da shi ba. "kina cin darajar kin kawo mahaifina duniya ne shiyasa nake ɗaga miki ƙafa akan irin cin kashin da kike yiwa Maama da Mum, darajarsa kike ci nake yi miki duk kalar wata biyayya da girmamawa, banda haka wallahi da comon inuwarsu aka ce ki yiwa kallon banza ba za kiyi ba, da tun na farko da kika yi ba za ki so ki ƙara na biyu ba. saboda haka yau ta zama rana ta ƙarshe da za ki ƙara ɗaga muryarki akansu in ba haka ba zanyi abunda ban taɓa yi ba". kai da ganin yanda yake maganar ka san ya fusata, kamar ma zai kaiwa Boɗejo hannu, Hajiya Madina ta kallesa ta sauke idonta ƙasa leɓenta na talewa da murmushi, alamun taji daɗin abinda yayi. Hajiya Ramla tayi saurin miƙewa tana sauke hannunsa da yake nuna Boɗejo da shi,"me haka Babana?, kar fushi yasa ka aikata ba daidai ba, yi haƙuri komai yay farko ai zai yi ƙarshe...". yana kallon Bodejo da ta saki baki tana kallonsa da tsananin mamaki ta taho gare shi yace,"ai komai ɗin ma yazo ƙarshe, ba zan iya ci gaba da ɗauka ba". ya faɗa yana barin kusa da Mum ya ƙarasa gaban Boɗejo kafin ta iso gare shi, ya miƙa mata farar takardar da ke hannunsa yana cewa,"na gaji, na gaji da masifarki da neman tashin hankalinki, gaba ɗaya kin hana kowa sakat, to ina buƙatar Mum da Maama da Baffa su sami nutsuwa hankalinsu ya kwanta su huta da fitinarki, nima kuma ina da buƙatar nawa hankalin ya kwanta, ba cikakkiyar lafiya gare ni ba so ba za ki kwantar da ni ba". ya manna mata takardar ajikinta. "ga shi nan ki samawa kowa lafiya". Boɗejo tayi mutuwar tsaye ta kasa ko motsi, bin sa kawai ta-ke da ido, taji ƙirjinta na bugawa kafin ta iya ɗaukar takardar tana duddubawa, tayi masa kallon tsab sannan tace,"wannan kuma na menene?". bai ce da ita komai ba ya nemi kujera ya zauna yana dafe kansa, Khalil ya shigo a lokacin tayi saurin dakatar da shi daga hawa upstairs da yake shirin yi. "zo, zo nan Khalil". ya dawo ya tsaya gabanta, ta miƙa masa takardar hannu na rawa,"duba min mene aka rubuta a ciki". ya warware takardar, kalmar NI da ya fara cin karo da ita tasa shi ɗago ido ya kalli Mum sannan ya kalli Maama sannan ya juya bayansa ya kalla Turaki. Boɗejo ta doke shi,"na ce ka karanto min abunda aka rubuta ba wai ka bi su da idanu ba, saninsu ne baka yi ba ko me". ya sauke gwaron numfashi yana murza idonsa da kyau sannan ya shiga karanto ma ta abinda ke jiki tiryan tiryan. Boɗejo ta lailayo wata uwar ashar ta yarfa a sanda ya gama karantawa, ta fizgi takardar da ga hannunsa ta isa gaban Turaki ta wurga masa. "kai ka isa, ka isa ka saki Ilham, to bilahillazi samun kwanciyar hankalinka da na iyayenka shi ne ka mayar da auren nan". Maama ta miƙe zata bar wajen tayi saurin dakatar da ita cikin hargowa,"tsaya baƙar munafuka, gidan uwar wa za ki je da kika miƙe sim sim za ki tafi?, ai na san ba kowa yasa yayi sakin nan ba sai ke algunguma, wallahi ban san Dukko annoba ya kawo cikin gidansa ba sai yanzu, Madina!, baƙin kaidin ki har ya kai haka Madina?, to kuwa tunda kika sa ya saki Ilham, sai kin sa ya saki ɗayar ko kuma ke ma in sa a sake ki". Hajiya Madina taji wani abu ya taso mata, tayi saurin haɗiye shi da ambaton Allah. Boɗejo ta miƙo mata takardar tana faɗin,"yanda kika sa ya saketa haka za ki sa ya mayar da ita, ungo nan ba shi". Maama na kallonta tace,"na san ina da babban matsayin da zan iya sawa ya saketa, amma ban yi hakan ba tun farko, ki daina alƙanta sakin jikarki da ni, ba ni na saka shi ba, wadda take ganin ta isa da shi kaf duniya itace ta ba shi wannan umarnin ba ni ba, kuma saboda gujewa fushin ubangijinsa da kuma taɓewar duniya yasa ya bi wannan umarnin". Boɗejo ta bi Mum da kallo kafin tayi ƙarfin halin ce ma ta,"Ramla kika sa ya saki Ilham?". Mum ta kawar da kanta gefe tana jan yatsunta tace,"kiyi haƙuri, amma abin da nake ganin ya dace shi na sa shi ya aiwatar, hakan shi kaɗai zai sa hankalin kowa ya kwanta, da ga mu har ke har kuma ita yarinyar". mayafin Boɗejo ya zame ya faɗi. "haka kike Ramla?". ta tambaya da tsananin mamakin Mum ɗin, wanda take tantamar da ƙyar idan ita ce tasa Turaki yayi wannan sakin. Mum ta fuskanceta tace,"ba zance haka nake ba ko ba haka nake ba, amma idan hakan bai yi miki daɗi ba Allah ya huci zuciyarki. naga masalaha ake ta nema tuntuni, wanda kuma ta hakanne kaɗai za'a samar da ita. kiyi haƙuri da abinda zan faɗa, ina son farin cikin ɗana, ina so ya sami kwanciyar hankali da nutsuwar da ya rasa tun daga ranar da ya auri Ilham...". "dakata! me kike so ki faɗa min?, so kike kice an aura masa annoba da har kike faɗar ya rasa kwanciyar hankali. to cikin ku biyun kar wadda ta ƙara ambatar min kalmar tashin hankali anan, tashin hankali na can wurin shegiyar yarinyar da yaje ya aura a titi, kuma tunda kika sa ya saki Ilham, to ya zama dole kisa shi ya saki waccan yarinyar da ban yarda da asalinta ba, ba zan taɓa yarda a kawo mana gurɓatacce cikin zuria'armu ba ku san da wannan, dan haka ba shi umarni ya saketa". Mum ta rufe ido ta buɗe sannan tace,"ina son rayuwar ɗana, ban shirya rasa shi a yanzu ba, kamar yanda nake tsananin son farin cikinsa, hakan yasa ba zan taɓa raba shi da abunda yake farin cikinsa ba. idan kika ce lallai sai ya saketa hakan zai zama barazana ga rayuwarsa, domin kuwa uwar gidansa itace rayuwarsa, rabuwa da ita dai-dai yake da rasa ransa, saboda haka ni ba zan sa ya saketa ba, dan Allah kiyi haƙuri a bar min yaro ya huta haka, kamar yanda ɗanki yake so ya rabu da ke lafiya haka shima yake so ya rabu da ni lafiya, sam ba zai iya ƙetare umarnina ba". Boɗejo ta nemi kujera ta zauna tana salati, ta dafe kai tana girgiza shi,"yau naga abinda ban taɓa gani da ji ba a tarihin rayuwata, ni yau ake bijirewa umarnina, ni yau ake ja-inja da ni. Ramla da Madina me ku ka taka?, me Azima tayi muku da ku ka tsani ƴarta haka?, zumuncin da ubangiji yace a yi shi ku ke so ku rushe yau?...babu komai bari Dukkon ya shigo". ta miƙa hannu ta ɗauko jakarta da ta tangarar a ƙasa ta ɗauko wayarta, da ƙyar ta iya lalubo lambar Baffa dan ta san duk wanda tasa ya nemo mata ayanzu ba zai nemo ba. ringing biyu ya ɗaga, ta amsa sallamar tana cewa da shi,"kana ina?". "ina gida". "kana cikin gidan naka ka barni da matanka suke min rashin mutunci suna gaggaya min maganganun da suka ga dama?, Dukko kana so ka gama da duniya lafiya kuwa?, to ka bar duk wani abu da kake kazo ɓangaren Mandina yanzu dan babu lafiya". tana faɗar hakan ta kashe wayarta, idonta akan Turaki da har yanzu yake dafe da kansa, danasanin aurensa duka biyun fal cikin ransa. mintunan da basu wuce biyar ba Baffa ya shiga parlon Hajiya Madina, tun daga baƙin ƙofa yake kallon Hajiya Madina da Kuma Hajiya Ramla waɗanda ke tsaye sun kasa zama, ya ƙaraso ciki da sauri wajen mahaifiyarsa ya zauna a ƙasa yana cewa,"ranki ya daɗe gani, lafiya dai?". "ina kuwa lafiya Dukko". ta faɗa tana ɗauke ido daga kansa ta mayar kansu Hajiya Madina tace,"waɗannan marasa mutuncin matan naka sun sa yaron nan ya saki Ilham". with shock Baffa ya ɗago yana kallon Maama, Boɗejo tai saurin cewa da shi,"a'a ai ba ita ce tasa yay sakin ba, gata nan ita ta saka shi ya saki matarsa saboda bata tsoron Allah bata gudun girgizar al'arshin ubangiji". ran Baffa a ɓace ya miƙe yana kallon Hajiya Ramla. "kika sa ya saki Ilham?, a bisa wanne dalili Ramla?, wace ke?". Mum tayi murmushin takaici tace,"wace ni kake tambaya Dukko?, har ka manta shekaru 33 ba ya da na tsuguna na haifa maka yaron cikin tsananin wahala?, tunda ka manta bari na tuna maka, ni ce wannan matar da ta ɗauki cikinsa tsawon wata tara, na raini cikin da wuya bata daɗi ba, na kuma haife shi acikin mawuyacin halin da kai kanka kake tunanin ba lallai na rayu ba, na shayar da shi tsawon shekaru biyu, na ci kashinsa na sha fitsarinsa, ka tuna wacece ni ko kuma dai still na tuna maka?, to ni ce mahaifiyarsa, ni ce wannan uwar da ubangiji ya faɗeta sau uku kafin ya faɗi uba sau ɗaya tal. ka san kuwa da cewar ni ɗin bata wasa ba ce, ina da ikon sawa ina kuma da ikon hanawa ko ana so ko ba'a so muddin ana so a gama da duniya lafiya, so banga dalilin da zai sa abi a takura rayuwar yarona ba, yayi biyayyar amma hakan duk bai yi muku ba, ya kuke so yayi da ransa?, so kuke sai ya faɗi ya mutu tukunna?, tunda har yay biyayya ya auri zaɓinku ku barsa ya auri zaɓinsa mana, amma son rai duk ya hanaku kuyi masa adalci, to ni nasa ya saki amaryarsa zai kuma tare da uwar gidansa kamar yanda zuciyarsa take so, kamar yanda hakanne zai zama farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa". ta ƙara kallon Baffa da kyau tace,"dan Allah ka samawa yaron nan lafiya haka nan, iyakar biyayya yai maka, wadda tun da ka haife shi yake yi maka har kawo yau bai taɓa bijirewa umarninka ba". Baffa ya ɗaga muryarsa,"shutup Ramla". ya juya yana kallon Turaki yace,"ban goyi bayan ka rabu da kowacce acikin su ba, amma ka mayar da matarka yanzu anan, idan ba haka ba nayi mugun saɓa maka". still kan Turaki na ƙasa bai ɗago ba, Mum tace,"wallahi tallahi sai dai idan bana numfashi amma ba zai mayar da ita a yanzu ba, yanda kake bin umarnin mahaifiyarka saboda ka gama da duniya lafiya, shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar saboda ya gama da duniya lafiya, yanda kake gudun fushin taka mahaifiyar haka shima, yanda kake so ka haɗu da ubangijinka lafiya shima haka yake so, haba Alƙali ka bar yaro ya huta mana ko so kake sai kasa masa ciwon zuciya duk saboda kai baka so ka ɓatawa taka mahaifiyar". ta mayar da idonta kan Turaki da tsananin tausayinsa tace,"Babana ta shi kaje". ya miƙe jiki ba ƙwari zai wuce Baffa yace,"daga yau na haramta maka shigowa gidana, kar in sake ganin ƙafarka a ƙofar gidan idan kuma ba haka zaka sha mamakin abin da zan maka, fitaaa a gabana". ya ƙarasa maganar a tsawace wadda har sai da ta tsorata su Maama. Turaki yay saurin ɗago kai yana dubansa, zai yi magana Mum ta tari numfashinsa da cewa,"je ka Babana, Allah yayi maka albarka". Turaki ya fice yana jan ƙafafunsa da yake jin kamar ba zasu ɗauke shi ba. yana fita Hajiya Ramla ta dubi Boejo tace,"ina ƙara baki haƙuri, Allah ya huci zuciyarki". Sannan ta kalli Baffa tace da shi,"kayi haƙuri your highness". bai ko kalleta ba ya durƙusa gaban mahaifiyarsa yana bata haƙuri tare da lallashi. Hajiya Madina ta ɗauki wayarta ta bar wajen ranta fess, tayi upstairs tana danna kiran lambar Ummi, tana yin picking bayan sun gaisa take shaida mata cewa,"Ummin Fillo insha'Allahu ranar litinin zamu kawo lefe". Ummi ta amsa da,"Allah ya kaimu". daga haka suka yi sallama. ɓangaren Turaki kuwa yana zuwa compound kiran wayar Dada ya shigo wayarsa, kamar ba zai yi picking ba sai kuma ya ɗaga, abinda ya tsammata shi ɗin ne ya faru, dan yana sakawa a dodon kunnensa ya ji tana da masifa tana cewa,"ka sakar min jika ko kuwa?, ka san Allah kar ka bari in muku ɗanyen kai". muryarsa ta fito kamar ta mara lafiya da cewa,"Dada in tana kusa ki bani ita sai na faɗa mata". a harzuƙe tace,"ka faɗa mata me?". yace,"shi abunda kika ce". tace,"wai sakin?". yace,"ehh". tace,"haba yaro aini ba ƴar yau ba ce, kaje ka tambayi tarihina na fi son komai za'ai ayisa da hujja, dan haka furtawa da baki kaɗai ba zai gamsar da ni ba, ba kuma shi tabbatarwa da jama'a kayi ba, saki a rubuce nake so kayi shi cikin farar takarda ka yo min aikensa". a hankali yace,"shikenan Dada, ina kan hanya yanzu zuwa gida, idan naje zan rubuta insha'Allahu". tace,"ya dai fi, a sakar min jika dan bazan kawota gidan da za'a ke ma ta kallon banza ba" ta kashe wayarta tana ta jaraba akan Fillo dake kwance kan gado tana aikin kuka tun ɗazu. Ilham na kwance a ɗaki hadimanta na matsa mata ƙafa Turaki ya shigo kamar an hankaɗo shi, ɗaya bayan ɗaya hadiman suka miƙe suka fita da azama. yay tsaye bakin ƙofa yana kallon Ilham wacce ganinsa yasa ta ɗauke idonta gefe tamkar bata ga shigowar tasa ba, shiru ya ratsa ɗakin na ƴan sakanni sannan muryarsa na shaida ɓacin rai yace da ita,"ki fito waje ki same ni". har yay bakin ƙofa zai fita sai yaga kamar bata ji me yace ba, hakan yasa ya maimaita mata amma da mamakinsa sai yaji tace,"in fito in yi maka me?". yay ƙyam yana ta kallonta from head to toe da son gano wani abu, sai dai hakan ya gagara, ba ya son wata sabuwar damuwar dan haka bai ƙara cewa da ita komai ba ya juya zai fita sai yaji tana cewa,"na faɗa maka zan kuma ƙara nanata maka Turaki, ba damuwata ba ne ka auro duk wacca ka ga dama, but ka san da abu guda ɗaya shine ba zan zauna da kishiya a cikin gida ɗaya ba, in har kuma ka aikata wannan kuskuren to ina mai tabbatar maka da cewa kayi bankwana da zaman lafiya da kwanciyar hankali kenan, sonka da nake ba shi yake nufin ka ɗebo duk yayin da ka ga dama ka watsa min ba, wallahi! wallahi! wallahi! muddin wata tare acikin gidan nan sai dai ko ni ko kuma ita". sai kuma tayi shiru tana fashewa da kuka tana miƙewa zaune ta kifa kanta da gwiwa, sosai take kuka tana faɗin,"me nayi maka a rayuwa kayi min wannan tsanar, ka rasa da me zaka ƙuntata min sai da kishiya, kishiyar ma aure ko wata biyar ba'ai da yi ba, waɗanna kalar maganganu kake tsammanin kunnuwana zasu dinƙa ji daga bakin mutane, kamata, tsakani da Allah kayi min adalci kenan?, kai ko tausayina ma baka ji, ina cikin tashin hankali na irin mawuyacin halin da mahaifiyata ke ciki, kai baka zauna ka rarrasheni ba kuma kace wai ka auri wata tun kafin ni, wanna kalar rainin hankali ne wannan?, to wallahi duk wacce ta shigo gidan nan sai naga bayanta ka rubuta ka ajiye". Turaki yay murmushin takaici ya fice ya bar ɗakin, ba tare da yace da ita ƙala ba, bedroom ɗinsa ya wuce kai tsaye, yana shiga yay kiran lambar Bello. Bello na ɗagawa yace da shi,"kai MT you should have call me ka faɗa min bama baman da suke tashi a gida, kawai kasa na ɗau ƙafa na tafi zance Boss yace kar in ƙara zuwar masa gida in ba haka ba sai ya ɓalla ni, Boɗejo kuwa kamar zata bankawa motata wuta, to ni dai yace in ƙara jadadda maka inuwarka ma kar ya sake gani. you thank God kana da gidanka har da mata, ni yanzu fisabilillah ta ya zan jure rashin ganin Zaytun har tsawon lokacin da zai sauko daga dokin fushinsa?, MT please ban shawara dan wallah jin zuciyata nake kamar ana ɗinketa da zare da allura, AC ce fa a motata amma uban gumi kawai nake haɗawa". a sanda Turaki ke ɗaura towel a ƙugunsa yace,"kana jina?". Bello yace,"yo MT ko ban da kunnen jinka ai ya zama dole ma na aro na saurareka, balle kuma akwai, ma za ka faɗi duk wata kalar shawara da kake ganin zata zama way out". Turaki ya cika bakinsa da iska ya fesar yana kama ƙugu sannan yace da Bello,"plss kar ka min hauka, i want ask you something and be serious ka bani amsa, ta ya ake gane mace na da ciki?". Bello ya lailayo wata ashar yace,"dan ubanka dama har haka kayi babban aiki?, shege wooo kace baka sonta?, to da kake tambayata ya ake gane mace na da ciki waka taɓa gani na yiwa?, ni ba ɗan iska ba MT karka ƙara min wannan tambayar, ka ɗauketa kuje asibiti ka tambayi waɗanda suka karanci abun, ka ban shawarar kawai da na tambayeka ta ya zanke ganin Zaytun?". Turaki yaja tsaki da cewa,"useless". sannan ya kashe wayar. ya ƙara lalubo lambar Dr Hasheer, sai da kiran ya yanke sannan Dr Hasheer ya kira shi, bayan sun gaisa yake ce masa. "Dr kana gida please?". Dr Hasheer yace da shi,"ehh lafiya dai?". Turaki yace,"in ba damuwa don Allah ka leƙo gidana". Dr Hasheer yace,"ok babu damuwa, on my way right now". ya dire wayar yana shiga toilet ya sakarwa kansa shower, bai jima ba aciki ya fito yazo ya tayar da sallar azahar don ba ya jin zai iya fita masallaci, duk da already ma an riga an idar. idarwarsa kenan Dr Hasheer ya kira shi yake shaida masa yana ƙofar gida, yace da shi alright ga shi nan fitowa. jallabiya ya zura ya sauka ya fita ya shigo da Dr Hasheer, suka ɗan zanta a parlo na ƴan mituna sannan Dr Hasheer ya ba shi urine container. sanda ya shiga ɗakin Ilham tana toilet, har zai tsaya jiranta kuma sai kawai ya isa bakin toilet ɗin yay knocking. ta kashe shower ɗin tana tambayar waye, yace,"ni ne, are you coming out now?". tai masa shiru bata yi magana ba har tsawon minti uku, bai ji ta amsa mishi ba kuma bai ji ta kunna shower ɗin ba. ransa ya ɓaci kawai ya murɗa handle ɗin ya faɗa ciki, ya ɗaure fuska ya haɗe girar sama da ƙasa ya miƙa mata robar,"yi fitsari ki ban". "ban gane ba". ta faɗa tana kallonsa nata ran itama a ɓace tana ɗaure tata fuskar. da yay mata jan ido ya sakar mata tsawa bata san lokacin da ta miƙa hannu ta karɓa roban ba, zuciyarta kamar zata fito waje dan baƙin ciki ta durƙusa tayi fitsarin ta miƙa masa. ya karɓa yana ƙare mata kallo tsab a naked ɗin da take don gano wasu alamomi da Dr Hasheer ya faɗa masa, ya watsa mata banzan kallo sanda zai fice, ko ƙofar bai rufe ba ya bar ɗakin kamar iskar guguwa. Dr Hasheer ya miƙe ganin ya fito, Turaki ya bashi container ɗin da yake riƙe da ita kamar ya riƙe kashi, yace,"please Dr kar ya wuce yau". Dr Hasheer yace,"you just give me 1hour, shima saboda ba hospital zan wuce direct ba, amma da zarar mun kammala gwajin i will call you and tell you the result". Turaki ya basa hannu su kai shaking yana faɗin,"thank you so much". su kayi sallama ya wuce shi kuma ya haura upstairs ɗakinsa. yana shiga ya buɗe locker ya ɗauko jotter da biro ya hau kan gado ya zauna, ba ya son tashin hankali ba kuma ya son abunda zai zama silar rugujewar farin ciki a tsakanin iyayensa, dan haka dole yayi abun da yake ganin ya dace, kowa da kowa ma ya huta. but a sanda ya ɗora biron akan takardar sai yaji ya kasa rubuta abunda yake ganin zai zama mafita ta ƙarshe, yaji zuciyarsa tayi wani irin matsewa, ya jinginar da kansa jikin gadon yana tunani tsawon wucewar daƙiƙu masu yawa. daga bisani ya ɗauko wayarsa ya kira wayar Mum, ko da ta ɗaga ta tambaye shi lafiya sai yaji ya kasa faɗa mata abunda yake shirin yankewa, hakan yasa yace mata ya kira ta ne kawai. tace da shi,"Babana karka sake ka sawa kanka damuwa kaji ko, ba komai ya sa Baffa faɗa maka haka ba illa ɓacin rai, kayi haƙuri ka ba shi space zuwa wani lokaci. Allah yayi maka albarka". bayan sunyi sallama ya kira lambar Hajiya Madina, tana ɗagawa ko amsa sallamar tasa bata yi ba balle taji abunda zai ce mata tace da shi,"ya akai?". ya kira sunanta kamar yaron dake buƙatar shan nono. tace,"ka ga me babban suna, in kace zaka biyewa wannan uban naka da shima tsufa ya fara rikitar da shi to zaka dawwamar da kanka acikin damuwa ne, don haka ka rabu da shi ka ba shi space zuwa ranar da zai nemeka da kansa, kai ɗin ai na dabanne mahaifinka ba ya iya fushi da kai mai tsawo, naji fitinanniyar Kakarka na cewa zasu zo su ɗauki kayarsu yanzu, to da zarar sun zo sun ɗauketa ka rufe gidanka ka huta abinka, ko office karka dinƙa zuwa har matarka ta tare, kaji ni ko?". ya sauke numfashi yace,"tom Maama". tace,"yauwa Allah yayi maka albarka, zamu kai lefe monday in Allah ya kaimu, zasu fara biki ranar wednesday but Ummi bata faɗa min ranar da zasu gama ba, sun ce sai Dada ta dawo ita zata yanke wannan". magana take tayi ta hana shi faɗar abunda yake so yace, har ta gama sannan tayi masa sallama. ya kasa sauke wayar daga kunnensa sai sulalewa tayi daga hannunsa. ya maida hannunsa kan takardar da har yanzu ke hannunsa, ya shiga rubutu a sanda yake jin zuciyarsa na bala'in matsewa, yana rubutun muryar Fillo na amsa kuwa a cikin kansa, kamar yanda hotonta ke haska masa acikin idanuwansa tun daga ranar da ya fara ganinta har zuwa ranar ƙarshe na rabon da ya sanyata a idonsa. ya rumtse idonsa gam a sanda ya kammala rubutun, kuma ba tare da ya iya buɗe idonsa ba ya nannaɗe takarda ya ɗaga ƙasan pillownsa ya saka. yaja wata doguwar a jiyar zuciya yana kwanciya ko zai sami sassaucin abin da yake ji a ƙasan ransa. *Vote, Comment and share.* [9/5, 12:01] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *46* *Taraba.* acikin gidan babu abin da kake ji yana tashi sai hayaniyar mutane masu hadadar biki. Inna Kareema ta fito daga sashin Kawu Abdullahi hannunta ɗauke da ƙatuwar cooler na abinci, tana nufar sashin Jagarɗo suka yi kiciɓis da baƙuwar da ke shigowa. ta tsaya da tafiyar fuskarta na washewa da tsurar fara'a, ta ajiye kular a ƙasa tana faɗin,"maraba maraba da mutanen Abuja, wato ku sai yau ku ke tafe?". ta faɗa tana ƙarasawa ta tarota tare da amsar ƙatuwar jakar hannunta. Dattijuwar baƙa me suna Yaya Sahura ta ce,"yo ke Kareema ai wannan biki da sai an gama za ku ganmu". Inna Kareema ta ce,"kai haba dai, lafiya?". Yaya Sahura tace,"ƙalau, ai mu zatonmu litinin ta sama aka ce za'a kawo lefe, taron biki kuma a fara shi ranar laraba, sai daren jiya da Lamiɗo ya kira waya yake cewa da Baban Yara ai bai ga gimlawarmu ba, shi ne yaufa babu shiri muka bugo sammako". Inna Kareema ta ɗauki kular abinci suka ci gaba da tafiya tana faɗa ma ta,"to ai kin san auren a yanda yazo, shi Dottijo ma ce ya yi mene na cewa sai anyi wani taron biki tun da dai ɗaurin aure an jima da yinsa, akai yarinya ɗakinta kawai, to kuma kin san lamarin Dada. ita taron ma ce tayi sai anyi sati guda ta yanda Kakar mijin zata gane su ne ƴan iska, da ƙyar Dottijo ya shawo kanta yanzu dai za'a yi shi kwana biyu, to jiya anyi Kamu, yau zamu yi al'adarmu ta fulani da kika sa ni, sai gobe kuma a kaita gidanta". Yaya Sahura tana dariya suka wuce suna ci gaba da tattaunawar su. "hmmm ai da yake Kakar mijin duk ita taso ta ɓata lamarin, karki ga irin tataɓarzar da aka sha kamin Dada ta yarda amma da tsaye tayi tace ko zai mutu sai ya sakar ma ta jika, da ƙyar su Dottijo dai suka shawo kanta ta haƙura". a parlon Hajjah suka ya da zango in da babu kowa, Yaya Sahura ta zaro ido waje tana faɗin,"wannan uban akwatunan fa kamar za'a buɗe sabon kanti, kar dai kice min su ne lefen?". Inna Kareema ta wuce ta ajiye kular hannunta tana faɗin,"hhh aiko dai abin da kowa ke faɗa kenan, Fillo dai ai abun nata sai son barka, ƴa tayi goshi dan kaf jikokin gidan nan albarka, banda haka da yanzu Dada taja ma ta tayi asarar wannan abun arziƙin". "masha'Allahu, kiga akwatuna kamar ba'a rashin kuɗi a ƙasar nan, kalla fa yacca aka ɗaure su da ribom kyace lefen da ake kaiwa gidan sarki ko gidan shugaban ƙasa". Yaya Sahura ta faɗa tana tattaɓa akwatunan da aka jere su waje ɗaya ɗaiɗai har guda ashirin da takwas. Inna Kareema ta wuce ta rufe ƙofa, ta dawo tana cewa,"ai buɗe su duk ki gani, gwala-gwalai ne aciki har takwas. lefen nan dai in faɗa miki tun ranar farko ba'a ƙara buɗe su ba kin san ba zuciyar kowa ke da kyau ba, masu ɗan hali ba'a gane musu, zan rantse miki kaf kayan ciki babu na ƙasar nan. kin gansu nan kuma Dada ta ce ko kwalli ba za'a taɓa ba". su kai dariya tare, sannan su ka shiga buɗe akwatunan na gani na faɗa, Yaya Sahura sai saka albarka take tana yabawa. daga can ɗakin Dada kuwa waya ce maƙale a kunnenta, magana take yi cikin faɗa tana cewa,"ka ga Arɗo ni bana son wannan magana, su kwashe kayansu kawai, duk wani kaya da suka zuba a kwashe su akai musu gidan su ba ma neman taimakon kowa don muna da shi, haka kawai salon yarinya ta tare azo ana goranta ma ta ana cewa ai kayan ɗakin nata ma iyayen miji ne suka yi ma ta, a'a sam ku kwashe musu kayansu ku jera na ku". da ga cikin wayar Arɗo yace,"to Dada wallahi duk mun rasa yanda zamu yi da su fa, ita mahaifiyar yaron ta ce gudunmawarta ne, Fillo ai ƴace a wurinta...". tayi hanzarin katse shi a yayin da ta kulle ido tana girgiza kai,"Arɗo akwai ka da shegen taurin kai, ka faɗa musu gudunmawa bama so ta bawa ƴarta, ni jikata bata buƙata". Arɗo yace,"tom shikenan Dada yanda kika ce". ta sa ke cewa,"yanzu an kammala kawo kayan gaba ɗaya?". yace,"a'a da yake bedroom ɗin guda huɗu ne mu kuma order ɗin biyu aka yo, to amma yanzu Saifullahi ya kira wani abokinsa da ke can ƙasar turkey ya taho da su zuwa gobe idan zai dawo". Dada tace,"to shikenan ya yi, ina fatan kun faɗa masa kaya masu kyau da tsada ake buƙata ko?". ya ce,"an sanar masa Dada". "kuyi maganar kuɗi da shi sai ka kira Maudo ka faɗa masa, akwai wasu kayan ƙyale-ƙyale ma da Amatullahi ta nuna min jiya kuma bamu taho da su ba daga can saudia ɗin, zan sa ta turo maka a waya sai ya duba yaga idan akwai acan ƙasar sai a taho ma ta da su". ya amsa da,"to Dada, sai ta turo yanzu". tace,"to naji, Giɗaɗo ma sun taho yanzu da sauran kaya. don Allah ku yiwa ƴar nan jere na kece raini, irin jeren da zai hana wannan figaggiyar tsohuwar kwanciyar hankali. ni ban so ma ya haɗe musu gida ba wallahi, na so ya raba su dan sam bana son abin da zai ɗagawa jikata hankali, ina tsoron haɗe su gida ɗayan nan kar suje su ke cutarta tun da ita Allah bai yi ta da baki ba, shashasha ce banda kuka babu uwar abin da ta iya". Arɗo yana murmushi ya ce,"Dada ai ko hakan ma kamar ya raba musu gidanne, kowacce da part ɗinta kuma da tazara sosai tsakanin part ɗin na su". ta taɓe baki bata ce da shi komai ba ta kashe wayar tana ajiyewa a gefenta ta dubi Safara'u ta ce,"ke jiya da ku ka je gidan su angon kun gani da gaske bai da lafiyar ko kuwa iskanci ne da rainin hankali kawai za'ayi mana saboda kar yazo bikin?" Safara'u ta ce,"ƙwarai kuwa Dada, dan har sai da muka je asibitin ma sannan aka sallame shi lokacin, ba shi da lafiya sosai gaskiya ance yana fama da ciwon ƙoda ne". Dada ta taɓe baki ta ce,"Allah ya kawo sauƙi, rashin lafiyarsa dai ba ita zata hanamu shagulgulan biki ba". ta waiga ta kalli Amatullahi da ke charting ta ce,"abun jiya da kika nuna min ki turawa Arɗo yanzu". sannan ta kalla hadimarta da ke matsa ma ta ƙafa tace,"ki leƙa ɓangaren Gaji ki kirawo min Fullo, idan ba'ai wasa ba tana can tana ɗan banzan halin nata, dan yau ko ganinta banyi ba tun safe, ina kyatata zaton ma ko abinci ba ta ci ba". tana rufe baki Maijidda ta shigo ɗakin, ta wuce tana ajiye kayan hannunta, Dadan ta dubeta tana cewa,"yauwa ke ina wannan ƴa take?". Maijidda ta turo baki tana ɓata rai tace,"tana can". tazo wucewa Dada ta rarumi sandarta ta buga ma ta. "can ina?, dan ubanki ko sheɗan ya san can ne da zan tambayeki kice min wani can... sai yanzu ma na gane mugun halin da Fullo ta kwaso wajenki ta koya, ai Hausawa basu yi ƙarya ba da suka ce abokin ɓarawo ɓarawo ne, haka ma zama da maɗaukin kanwa...sam sam ba kiyi halin ƙwarai irin na kakarki ba, dole na raba ƙawancenku dan ba za'a kaita gidan miji ba kije ki lalata mata aure". Maijidda ta sosa wurin da ta duketa saboda zafi ta ce,"tana sashin Kawu Musbahu ɗakin Adda Amina". zata fita Dada ta dawo da ita,"ke zo nan". ta dawo tana rakuɓewa wuri ɗaya kamar mara gaskiya, Dada ta kalleta tsab sannan ta ce,"me aka yi miki da ma?". Maijidda ta fara hawaye tana cewa,"tun jiya take ta kuka kuma duk na tambayeta abin da aka yi ma ta taƙi faɗa min, ina ta rarrashinta ma taƙi yin shiru, zazzaɓi ya rufeta na bata magani ma taƙi tasha". "wacece da ma?". tace,"Hussainata mana". Dada ta miƙe tana dogara sandarta ta fita a fusace, ta shiga parlon Amina mutane na ta gaida ita babu wanda ta amsawa ta wuce kai tsaye cikin ɗakinta. tana shiga ta sami Fullo kwance akan gado tayi ruff da ciki, ta taƙarƙare ta buga ma ta sandarta a baya, babu shiri Fullo ta miƙe a tsure tana dafe wajen, idonta na fara zubar da hawayen da suka tsagaita ma ta, sosai zafin dukan ya shigeta dan ƙashin bayanta har sai da ya amsa. Dada ta dinƙa kallon idanuwanta da suka yi jawur, sun kumbura tsabagen uban kukan da take sha a ƴan kwanakin nan, fuskarta kanta tayi jaa ko tausayin kanta bata ji. ran Dada a matuƙar ɓace ta ce,"ke wai dan uwar ubanki tare da kuka aka haife ku ko kuma an haifeki ne dan ki yi ta kuka a duniya?". ta nemi wuri ta zauna tana ta faɗa. "ƴar banzar yarinya mara tawakkali, idan ba za ki iya jurar rashin uban naki ba ki sha fiya-fiya ki bi shi mana, idan kuma auren ne ba kya so ki buɗe baki ki faɗa mana, ko an gaya miki mu muna kai zuri'armu gidan wanda basa so ne. nan na tayar da jijiyoyin wuya akan sai an sake ki saboda ina so na ƙwatar miki ƴancinki, iyayen yaron nan suka zo su kai ta bani haƙuri naƙi na haƙura har sai dai aka kai ƙarata gaban mahaifina tukunna, shi ma ɗin saboda ban iya ƙetarewa maganarsa ne amma da sai na dage akan bakana saboda ko kaɗan ni bana jurar naga za'a wulaƙanta min jinina, da kika san ba za ki iya zama da shi ba tun ranar da suka kawo lefe ba sai ki faɗa ba ace su juya da abinsu, to wallahi tallahi ki shiga hankalinki da ni tun banyi mugun saɓa miki ba, dan tsab sai in baɗawa idona toka nasa Jagarɗo ya kai ki barikinsu ya ƙulleki, ni bana son halin ƴan iska saboda haka ki kiyaye ni". Fullo ta ɗaga idanuwanta da take jin sun ma ta nauyi ta kalla Dada ta ce,"banda lafiya ne". Dada ta zabga ma ta uwar harara ta ce,"da ba ki da lafiya kuma sai aka ce kuka ne zai yi miki magani ko?, mtswww". ta miƙe ta fita ta bar ɗakin tana ta faɗa, a parlon ta sami Ammi cikin mutane tana raba musu Dakkere(abinci ne na fulani), ta kirata tazo tace ma ta. "ɗanki ya wuce ko yana nan?". Ammi ta ce,"wanne a ciki?". ta harare ta ce,"mutanen ƙwarai ake nema ba ƴan wiwi ba, likitan nake tambayarki ba wannan mara kunyar ba". ta ce,"yana nan, amma ina jin kamar shi ya wuce kai Maudo airpot ɗazu". "to ina waccan yarinyar ƙanwarsa, me aikin asibitin?". "sun je gidan Fatima anjima kaɗan zasu dawo". Dada ta ɗanyi tsaki tace,"ma za kirawota ta dawo ta zo ta duba jikin yarinyar nan, tayi mata allura yanda zazzaɓin zai fi saurin sauka kinga ajima akwai taro, ba'a tara jama'a babu amarya ba, ko kuma an gayyota jama'a kuma su zo ace musu ba taro". Ammi tace,"bata da lafiya ne?". "yo gata can dai tana neman kashe kanta ai, ciwo yana cin ta babu wanda ta faɗawa saboda shegen nurƙufanci da miskilanci da baƙin hali irin na Hayyo". Ammi ta ɗauki waya ta shiga kiran lambar Yusrah, tana ɗagawa ta ce da ita ta dawo yanzu sai ta koma. Dada ta sa aka kira ma ta Ummi, tana zuwa Dada ta ɗaga sandarta ta rafka ma ta a ƙafa. Ummi ta ɗan ja da baya tana bata haƙuri tun bata ji laifinta ba. "ki shiga ciki kiji damuwar ƴarki tun da ke dai soluwar uwa ce". ta faɗa tana bin Ummi da harara. Fullo dai na zaune tun da su Dada suka fita, tana riƙe da farar takardar da Turaki ya bata ranar da suka je dubo shi a asibiti bai da lafiya, kallon takardar ta-ke tana juyata gudun hawayenta na ƙaruwa. ta jinginar da kanta jikin bango idanuwanta a rumtse tana ƙoƙarin danne kukan dake neman cin ƙarfinta, babu abin da ke haskawa cikin ƙwayar idanuwanta sai rubutun da ke cikin takardar, kawai sai ta kasa riƙe kukan ta sake shi ya fito da ƙarfi a sanda Ummi ke shigowa ɗakin. hankalin Ummi tashe ta yo kan gadon tana tambayarta lafiya, bata ma san ta shigo ba sai a yanzun, da sauri ta cusa takardar a cikin rigarta. Ummi ta kwantota kafaɗarta tana lallashinta da ban haƙuri. zatonta duk kukan ba na komai ba ne sai irin kukan da wasu amare ke yi idan zasu bar gida. Fullo ta samu ta rarrashi zuciyarta da ƙyar saboda bata so Ummi ta san abun da yake faruwa, bata san irin damuwar da zata shiga ba in har taga takardar sakin da ke hannunta, ba lallai ta iya ɗaukar wannan ƙaddarar ba, zata ga kamar itama bata yi dacen samun miji ba ne kamar yanda ita ma bata yi sa'ar miji ba a sanda ta auri mahaifinta, dalilin da yasa ta ɓoye kenan kuma ba ta tunanin za ta faɗa, ai tun da har ana zaman idda a gidan miji zata yarda su kai ta, ranar da ta gama iddarta acan sai ta sanarwa da kowa abun da ya faru, amma ba a yanzu ba da ba ta san wanne irin hali Ummi zata shiga ba akan hakan. Yusrah ta shigo tayi ma ta allura, aka kuma ɗebo uban magunguna a first aid da aka ɗauko a ɗakin Innah aka bata. Ummi ce da kanta ta bata abinci taci, sai da taci da dama sannan ta ƙyaleta. "ki daina kukan haka nan kinji Auta ta, bari naje ana ta baƙi daga ɓangarenmu, idan kika ji daɗin jikinki sai ki zo ku gaisa da su Yaya Murja". tana kallon Ummin ta ce,"wace ita?". "da babarta da Kaka ubansu ɗaya, su na can sun zazzo ma fa da yawansu, sai tambayarki suke yi, nayi zaton kuna can gidan Asma'u shiyasa ai". ta gyaɗa kanta kawai, Ummi ta fita daidai da shigowar su Maijidda, waɗanda suka shigo suna ta masifa akan ɗinkin da tela yayi musu ba daidai ba. AmaturRahman na faɗin,"na rantse da Allah in ace ba yau zamu sa kayan nan ba sai ya biyani zan baro shagonsa, ɗan iska me kama da ɗan daudu". Maijidda tayi watsi da nata akan gado ta ce,"ai ni idan kinga na saka waɗannan kayan to sauya ni aka yi, gwara idan na koma gida na dinƙa saka su idan zanyi aiki amma ba'a bikin Hussaina tah ba, ban da rainin hankali ɗinki sai kace ance masa tsofaffi ne zasu saka". Amatullah ma ta shigo ta jefar da ledar hannunta, Raudha ma haka, duk in ka kalla fuskokinsu ka san ransu babu daɗi. Raudha tayi tsaye jikin wadrobe tana fuskantar Fullo, ta harɗe hannaye tana cewa,"kin ga yanda fuskarki ta kumbura kuwa?". ta rufe idonta kawai ta kwanta tana juya musu baya, Amatullah ta ce,"ai ɗa zu Hammah Hamid ce yay idan ya dawo ya tarar ba ta daina ba sai ya zaneta babu ruwansa da matar aure ce". Raudha ta sauke numfashe ta ce,"i never see such a kind person me shegen kuka ma irinta, da muna saudia zatona ko dan Dada ta ce sai an saketa ne, da muka dawo kuma na kasa fahimtar auren ne bata so ko kuma kukan barin gida ne". "kin taɓa ganin amaryar da take kuka irin haka dan zata bar gida?, ita dai barta dan ta ga ƴar auta ce shagwaɓa tayi mata yawa shiyasa". AmaturRahman ta faɗa tana wucewa toilet. Raudha ta zauna kusa da Fullo tana kamo hannunta ta riƙe, ta ɗau wayarta tana kiran lambar me makeup da zata zo ta yiwa amarya anjima da za su yi Fulani Day, bayan sun gama wayar suka ci gaba da maganarsu ta abubuwan da zasu yi anjima. ƙarfe uku na rana aka fara shirya amarya, wata cousin ɗin su da ta zo daga benue tana ta complain akan rashin zuwan ango da aka ce ba zai zo ba, har sai da aka ce mata ai baida lafiya tukunna ta sarara ta hutar da yawun bakinta daga masifa. ita dai Fullo duk babu walwala, ƙwayar idonta na manne a cikin mudubi kai kace kanta take kallo, nan kuwa hoton ranar da suka je asibiti ne kawai ke haska mata. ta tuno sanda suka shiga room ɗin da Turaki ke kwance an saƙala masa oxygen, ga wasu abubuwa da akayi masa connecting, kallo ɗaya dai zaka yi masa idonka ya cika da ƙwalla haka kuma kaji tsoron Allah ya kama ka. ita da ta gansa ma sai da tayi mugun tsorata saboda kumburar da ya yi kamar an hura shi, a yacca yake ma zaka ce gawa ce, har yanzu ta kasa kwatanta abin da taji a lokacin da ta gansa da kuma abin da take ji zuwa yanzu. kawai sai ta rufe idonta tana hasko lokacin da ta gyara masa zaman hannunsa akan gadon a sanda ya buƙaci hakan, lokacin da taji ta kasa rabuwa da hannun nasa ta riƙe tayi masa irin riƙon da bata taɓa yiwa hannun wani mahaluƙi ba, har yanzu tana jin sautin muryarta a kunnuwanta da suka dinƙa fita da amo na tsananin tausayi suna jera masa kalmar sannu tamkar yawun bakinta zai ƙare, kuma a sanda take ji a jikinta kamar yana buƙatar wani abu daga gareta sai taji ya riƙo ɗaya hannunta ya zura ma ta farar takarda, wannan farar takardar da ke ɗauke da baƙin rubutu me ɗacin ɗanɗano, rubutun da take ji gwara a soketa da mashi akan abata karatunsa kuma a alaƙantata da shi, rubutun da taji ya tsayar da wani dunƙule abu a maƙoshinta ya hana ko da yawu wucewa, ita dai ta san ko kaɗan bata son Turaki, daidai da bugawar sakan na agogo ba ta taɓa jin wani abu me kama da sonsa a cikin zuciyarta ba, tausayinsa kawai take ji wanda shi ma daga Allah ne, amma ta rasa dalilin da yasa ta damu da sakin da ya yi mata, ta rasa reason ɗin da yasa take jin kamar ta mutu akan wannan sakin. ƙwayar idonta ta ƙara haska mata san da ta ɗauki tsayin daƙiƙu uku tana kallon takardar kafin ta iya ɗauke idonta daga kai ta sauke su akansa da yake kallonta da wani rauni da zata iya cewa ta gani acikin ƙwayar idonsa, ta san lokacin da idonta ya manne acikin ƙwayar idonsa, amma ba zata ce ga sanda hawaye masu azababben zafi suka shiga sauko ma ta ba, ta san dai ta ɗau tsayin lokaci tana kallonsa har sai da shi ya ɗauke nasa idon akanta ya kauda fuskarsa gefe, kauda fuskar da yasa taji kamar an tsikareta, tayi saurin miƙewa tana sakin hannunsa da ta riƙe ta fita da ga room ɗin tana danne kukan da yake cinta, kukan da har yau kowa ya rasa na menene har da ita kuwa, kuma kukan da har yau yaƙi tsagaita ma ta. hawaye su ka sauka akan foundation ɗin da me makeup ke blending ma ta, me kwalliyar taja tsakin ƙorafi tana matsawa da baya da cewar,"haba ke kuwa don Allah, haka fa jiya ma kika yi mana ki kasa akai ta westing time. idan ba za ki iya daina kukan ba kice a fasa yi miki mana ki daina wahalar da ni, ni wallah ban taɓa ganin amarya me masifaffan kuka ma irinki ba". tai maganar da muryar ɓacin rai. kowa sai ya hayayyaƙowa Fullo akan kukan da take yi sam bai dace ba, ran kowa ya ɓaci aka fara fita daga ɗakin ana barinta, Maijidda da tsananin tausayinta ta kamata suka shiga toilet ta wanke ma ta fuskar sannan suka dawo, me kwalliyar taƙi tasowa, duk da kuɗi za'a biyata masu yawa bata jin za tayi ta yin aikin wahala haka, har sai da Ammi ta shigo tayi magana tukunna ta miƙe tana jaddadawa Fillo akan kar ta ƙara ɓata ma ta aiki. sharp sharp akayi kwalliyar da tayi bala'in haska Fillo, ta dawo tamkar ba ita ba, aka fito da ita cikin shigar fulani kamar ka saceta ka gudu, Maijidda ta dinga roƙonta akan ta daure tayi murmushi ta kore damuwar fuskarta kar tayi musu irin ta jiya, duk ta yanda ta so ta yi hakan ta kasa, har sai da suka shiga parlon Maudo taji Dada na ba da labarin. "ehh mana, ai ni ban taɓa ganin ƴar banza mata ba irin wannan tsohuwar, ke ni da naje asibitin ma ban san sanda na tofar da yawu ba da na ganta, kin ganta kuwa a fige kamar figaggiyar kazar da bata kama abinci ba, naji haushin kaina ma da na zauna waje ɗaya ina ta masifa banje munyi ido huɗu da ita ba tun farko ta raina kanta, muna haɗa ido na zabga ma ta harar da ta fi tata, tana ta maganganunta ni dai na kirawo likita nace masa ga sabuwar mara lafiya nan". ba ta san lokacin da siririyar dariya ta suɓuce ma ta ba, kuma cikin sa'a Nuratu ta ɗauketa hoto a lokacin, hasken camerar yasa ta ɗago ido karaf camera woman ma ta ƙyasta ma ta, sai kawai taji abun ya burgeta hakan ya bayyanar da dukka kyawawan fararen haƙoranta, suka fito cikin wani salo na burgewa da ɗaukar hankali, idanuwanta su ka yi wa ta lumshewa suka buɗe ta kalli me hoton da irin kallon da ke tsuma zuciyar duk wani lafiyayyan namiji. tafin da aka fara ana waƙa irin ta su ta fulani sai taji a lokaci ɗaya yana tafiya da damuwar da take ciki, yana tafiya da wannan tarin hawayen da ke cikin ƙwayar idonta yana musanya shi da murmushi me faɗi. *Gombe.* "ka yi wankan?". Bello ƙaraye ya tambayi Turaki lokacin da ya sakko daga upstairs. Turaki bai ce da shi komai ba ya wuce dining, da ga yacca yake tafiya zaka san bai gama warwarewa ba, har yanzu jikin nasa da saura, duk ya bi ya rame, Bello ya taso shi ma ya isa dining ɗin yaja kujera ya zauna. "me za ka ci na zuba maka?". ba tare da Turaki ya kalle shi ba yace,"mene aciki?". Bello yana nuna masa flask na abincin guda biyu yace,"nan fried suppagetti ce, nan kuma tuwan shinkafa miyan agusi". Turaki ya sauke numfashi yana kwantar da kansa jikin kujerar dining ɗin ya ce,"couscous na ke so da miyan hanta". Bello yay ta kallonsa before yace,"akwai data a wayarka?". Turaki yay masa wani kallo, kallon da ya shaidawa Bello abin da yake nufi, hakan yasa shi cewa,"to ni dai duk da ba'a ji da ni a gidanmu irin yanda ake ji da kai, na rantse da Allah ban taɓa shiga kitchen da sunan girki ba sai dai in shiga in kwasa, to tsakani da Allah ta ina zan san yanda ake dafa wani couscous balle miyar hanta, yunwar dare dai ta taɓa sawa na dafa ƙonanniyar taliya, idan kuma za ka ci irinta yanzu in shiga kitchen ɗin". Turaki ya harare shi tare da jan tsaki. Bello yace,"to ai shiyasa nace ka ban wayarka sai in yi dowloading vedio, ina ce ai kuna da komai ko?". jin Turakin bai tanka masa ba yace,"yanzu dai tun da babu wanda kake so ɗin ka daure kaci tuwon shi ma ai ɗan uwan miyar hantar ne, kafin a kira Maama a faɗa mata, kaga tun safe baka ƙara cin komai ba kuma Dr ya hanaka zama da yunwa". Turaki ya ture plate ɗin da ya ajiye masa a gabansa, Bello ya ɗaure fuska yana cewa,"ban da ma dai girma irin na rashin lafiya me zai sa in zauna ina biyewa ƙaton gardi irinka ina yin nan nan da kai kawai saboda baka da lafiya, ehh tou sai kuma girma irin ta ƴan'uwantaka, kuma itama gaskiya na ga zaka cutar da ni sai a koma abota irin ta haɗuwar gate rabuwar bakin gate". yay tsaki,"haka kawai mutum Allah yay masa gata ya ba shi mace ya ta shi ya korata gidan iyayensu, Allah ma ya rufa maka asiri da wata billahi da ka ɗanɗana kuɗarka, ka bar ganin ina tare da kai ba komai zan iya yi maka ba kamar yanda matarka zata yi maka, banda ma rashin tunani da rashin shawara irin naka, da ka san Baffa yayi maka gate da gidansa ai da ka dawo sai kace ka mayar da ita, da tuni yanzu kana gaban Maama ana tarairayarka kamar ƙwai, abincin ma a baki ake baka ni kuwa duk abinka wallahi sai dai kaci da kanka ko kuma mu koma asibiti aci gaba da zaman jinya". Turaki ya kalle shi da takaici ya ce,"Bello when za ka zama me cikakken hankali?". Bello yana kai lomar tuwa ya ce,"ka siyo min kawai maganin jiran lokaci". Turaki zai yi magana akayi sallama a parlon, Bello ya kai idonsa kan Hamid, yay masa bismilla da ya ƙaraso, ya iso wajen nasu suna ta cewa ya zauna yana ce musu a'a. yana kallon Turaki ya ce,"akwai room guda ɗaya da babu key ɗin sa". Turaki ya rufe ido ya shafo wuyansa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce,"wanne room ne?". Hamid yace,"wanda ke downstairs". Turaki ya sosa girarsa sannan ya ce,"bari na dubo maka". ya ta shi ya shiga bedroom ɗin Ilham da ke nan ƙasa, ya buɗe drowern madubi ya ɗauko makullayen da suke ciki duka, ya dafe kansa da yaji yana mugun sara masa, kafin ya fito ya bawa Hamid ya ce su gwada dan bai san wanne ba ne aciki. Hamid ya fita bayan yay musu sallama, Bello ya kalli Turaki da damuwa ke fito masa ɓaro ɓaro me haɗe da tsoro ya ce,"Dr ya kawo maka result ɗin ne?". Turaki ya ce,"bai kawo ba, ya dawo ranar kuma sai ya tarar mun tafi hospital, but ya kira ni ɗazu ya ce she is not pregnant, ni dama na san zance ne irin na Boɗejo kawai, da na kusanceta ai ban bari sperm ya zuba a ciki ba". Bello ya tallafe haɓa yana dubansa ya ce,"ɗan ƙara min haske mana MT, kaga ni ma na kusa shiga da ga ciki and bana so na fara tara ƴaƴa da yawa, anyway before kace min ɗan iska, ni dai tsakani da Allah ban ga abin ƙi ba a tare da yarinyar nan Ilham ba da har ka yi kuskuren sakinta MT, Mace irin cikakkun matan da ake so da suka haɗa komai, waccan kam ta zo sai kama sha wahalar raino kamin jikinta ya ginu". Turaki ya cika bakinsa da iska sannan ya ce,"a wurina sakinta da nayi ba shi ne kuskure ba, babban kuskure a wajena shi ne da bana iya sirrinta abuna dole sai na faɗa maka". Bello ya ƙyalƙyale da dariya bai ce komai ba, for few seconds sannan ya ce,"yanzu ma ai na san akwai abin da ka ke so ka faɗa min tun ranar nan amma ka kasa, kuma na tabbatar ba dai-dai ka aikata ba shiyasa ka ke shakkar faɗa min, yanzu dai ina jinka me ka ƙara zuwa ka aikata da babu shawara balle zurfin tunani, dan na lura da kai tun da masu jeren kayan nan suka zo ka bi ka rikice kamar mara gaskiya". Turaki ya dafe kansa, sai da ƙyar ya iya faɗawa Bello abin da yake ransa, furucin farko Bello ya ce da shi,"totally MT baka da hankaliii, what are you telling me?, kai wai mistake ɗin farko ba ya zamar maka izina sai ka aikata da yawa?, har yanzu fa baka fita da ga matsalar da kake ciki ba shi ne zaka ƙara saka kanka a wata?, ko kuma ɓacin ran iyayen ne ba ya damunka?". ya daki dining table ɗin da hannunsa yana nuna shi da yatsa ya ce,"sam sam babu hankali a tare da kai, abubuwan da kake aikatawa masu lafiyar ƙwaƙwalwa basa yinsa". Turaki ya ture yatsan nasa yana cewa,"karka ƙara nuna ni kuma karka ƙara ce min banda hankali, damuwata nake faɗa maka matsayinka na aminina, mafita na ce ka tayani nema ba wai ka tsaya faɗa min baƙaƙen maganganu ba". ran Bello a ɓace ya miƙe tsaye,"an faɗa baka da hankalin, ka yi abun da za'ai maka kallon me hankalin ne?, har yaushe ka zauna ka zartar da wannan hukuncin akan yarinyar da gaba ɗaya ba ta cancanci haka da ga gareka ba?, kai da ba zaka zauna ka yi shawara da mutum ba sai bayan ka aikata abun da zai zame maka damuwa, kai ko da wani ma ya ce ka saketa ma ai sai ka zazzage shi, amma saboda toshewar basira irin taka yarinyar da banda taimakon Allah da kuma taimakonta da yanzu ka zama tarihi ko kuma da yanzu kana nan acikin lalurar da aka kasa maganceta, asiri fa!, asiri fa ta dinga ɗaukewa akanka MT, akwai wanda zai iya sa kansa a haɗari ne just becouse to save some'ones life irinta, sunanka fa kawai ta sa ni ba kai ba kuma tayi helping ɗinka har kake raye zuwa yanzu kuma cikin ƙoshin lafiya". takaici yasa Bello yin shiru yana rasa ma a wanne sahu zai saka Turaki, sai ya ƙyasta yatsunsa biyu ya ce da shi,"to bari kaji na faɗa maka, fushin Baffa akanka ba komai ba ne akan fushin Mum da zaka gamu da shi, sarai dai ka san da cewa tana son yarinyar nan. kuma in ƙara faɗa maka abu ɗaya, ba zan waiwayeka ba a sanda ka faɗa cikin cakwakiya ta biyu, ban san ka aikata ba kuma ba kai shawara da ni ba a sanda zaka aikata ba, dan haka karka kuskura ka neme ni". yana gama faɗar hakan ya fice, Turaki ya bi bayansa da kallo kafin ya tashi ya wuce ɗakinsa. babu abin da yake so yanzu irin yaje gidan su, amma Baffa ya ajiye ƙaton soja a bakin gate ya ce duk ranar da yaga wata fuska ko da mai kama da tasa ne a kama shi a ɗaure. washegari da safe yana kwance a ɗaki aka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakinsa, motsin ƙofar yasa shi buɗe ido yana kai dubansa ga me shigowar, ganin Maama yasa shi miƙewa zaune da sauri, ta iso wajensa tana jin tausayinsa na ratsata, ta zauna a kusa da shi ta dafa shoulders ɗinsa ta ce,"ya ƙarfin jikin naka". ya ce,"da sauƙi sosai". ta bi shi da kallo sosai tana lura da yanayin jikin nasa, babu kumburin ko kaɗan duk ya sace, ramar ce dai kawai da tayi masa yawa. ta sauke numfashi ta ce,"Bello ya ce min ba ya gari shiyasa na taho, ina drugs ɗin naka?". yana kallonta ya ce,"ƙarya yake yi, fushi yake da ni shi ne ya tafi". Maama ta girgiza kai tana murmushi ta ce,"Allah dai ya kyauta muku, anjima ne za ku shirya ai". ta miƙe tana isa table ɗin da yake tsakiya ta ɗauko magungunansa ta dawo ta zauna, ta ɓallo ta zuba masa a baki. "ka sha ka ƙara jin ƙwarin jikinka, anjima akwai dinner. su ma suna kan hanya sun taho kawo Fillo, amma ba nan ɗin zasu kawota ba direct, za su sauka a wurinmu after an dawo da ga dinner sai mu kawo maka ita, hakan ai ya yi ko? baka da lafiya ban zauna nayi shawara da kai ba me babban suna". shi dai bai iya cewa komai ba, Samha ta shigo ta dire basket na kayan abinci, ta zuba a plate kamar yanda Maama ta umarceta. kamar wani ƙaramin yaro haka Maama ta dinƙa feeding nasa, bayan ya gama ci ta cika masa bathtube da ruwan zafi ya shiga yay wanka, sanda ya fito ba ta ɗakin, bayan ya gama shiryawa zai fita sai gata ta dawo. "ai ba fita zakayi ba, koma ka kwanta ka huta. alfarma ɗaya nake so a wurinka me babban suna, ka cire damuwa don Allah, ka ɗauko rigar walwala da farin ciki ka saka, yau babbar rana ce a wurinka, ranar da ta ke zaɓinka". ya ce,"Maama Baffa...". ta dakatar shi tana faɗin,"sau nawa zan faɗa maka in dai batun Baffanku ne ka ajiye shi a gefe, kai fa kujera ne a wurinsa kana zaune zai neme ka, duk wannan hawa saman da ya yi na ɗan lokaci ne, tsohuwarsa na hucewa zai huce, space kawai yake buƙata, kai ma kuma da ma kana buƙatar space ɗinsu, mu kanmu da ka gani ba ya kula mu, jiya ma ya bar mana gidan ya kaɗa inda bamu sa ni ba". Turaki ya ja ajiyar zuciyar zai yi magana ta ƙara katse shi,"Bello zai zo maka da kayan da zaka saka anjima, Khalil zai riga ku zuwa can wajen dinner ɗin". ya gyaɗa kansa kawai kamar yaro bai ce komai ba har ta fi ce. *Taraba* tun safe da Fullo ta tashi tana yin sallar asuba ta shiga toilet ta rufe kanta, a ƙasan tiles ta zauna tana ta kuka ta damƙe takardar sakinta a hannunta, so take ta yi musu bayani amma ta rasa ta inda zata fara. Sai da Ummi ta shigo sannan da ƙyar ta buɗe toilet ɗin ta shiga ta fito da ita, ta bi su Maijidda da duk suke kwance kan gado suna ta baccin gajiya, dan ba su tashi a event ba sai 11 na dare, kuma suka dawo gida suka ƙara ɗorawa da wani ba su suka kwanta ba sai 3, shiyasa sallar asuba ma duk da ƙyar suka yi. Ummi ta zaunar da ita akan darduma ta ɗauko Alqur'ani ta bata ta ce,"kiyi ta karantawa za ki ji sauƙin koma me ke damunki. tun da dai ni da nake mahaifiyarki ma ban isa ki faɗa min matsalar da ke damunkin ba, to ga maganin kowacce kalar damuwa nan ki ta karatu, ƙarfe sha ɗaya naji Dada na batun jirginku zai tashi". Fullo dai kallonta kawai take yi, har Ummi zata fita sai kuma ta ƙara cewa da ita,"in ma kina tsoron faruwar wani abu ne a auren naku ki yi ta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah zai sanya komai ya zamo mafi alkhairi a gare ki, ni dai har zuciyata bana jin komai a game da tarewar nan taki ba, kullum adu'a nake ina faɗawa ubangiji, kuma na gamsu da son da yaron nan yace yana yi miki". Ummi ta fita ta barta, ita kuma ta buɗe suratul Yusuf ta shiga karantawa, kamar almara sai ta fara jin duk wata damuwa da fargaba da komai yana tafiya yana barinta. ƙarfe takwas Ummi ta dawo ɗakin, hannunta riƙe da tray wanda ke ɗauke da kayan breakfast, ta ajiye a gaban Fillo, ita kuma ta aje alqur'anin hannunta ta miƙe ta shiga toilet ta wanko bakinta ta dawo, tare suka yi breakfast ɗin ita da Ummi, su na ci Ummi na yi ma ta ƴan nasihohi akan sabuwar rayuwar da zata tsinci kanta, da maganganu tausasa da duk suka sanya sauran damuwar da ke tare da ita barinta. ƙarfe tara Ammi ta shigo ɗakin nasu tare da me makeup, ta tarar su Maijidda da Amatullah sun sa Fillo a gaba sai tsokanarta su ke, saboda ta daina kukan da ta ke yi sai su ke cewa ashe dama so take yi akaita gidan miji shiyasa ta ishe su da kuka, yau kuwa ga idonta nan ƙyam sai ƙyallin farin ciki da yake yi, ita dai tana zaune babu wanda ta tankawa. Me makeup ɗin ma sai da ta tsokaneta, Ammi na kallonsu duka ta ce,"to bara ta bar muku ɗakin sai inga wa zaku takurawa". ta kamo hannun Fillo suka bar ɗakin suka wuce sashin Lamiɗo ɗakin matarsa Diyam, anan aka zaunar da Fillo don shiryata, simple makeup aka yi ma ta amma tayi masifar kyau, gyaran jikin da akayi ma ta na 4days sai ka rantse an ɗauki watanni ana yi, sai faman shining take yi kamar fatar kifi, fatarta ta zama kamar madara tsabar kyau. riga da skirt na material me tsada cikin lefen da akayi ma ta na gida, sai aka ɗora ma ta alkyabba me mugun kyau red colour. Dadda ta shigo ɗakin, ta shigo tana faɗin,"kaiii Diyam ɓangarenki ai gaba ɗaya ya karaɗe da ƙamshin amarya". ta ƙarasa tana buɗe fuskar Fillo ta ce,"Masha Allah, Tubarkallah. Lallai Muhammad Turaki ya yi da ce da kyakykyawar ƴar mu, ai danasani na ƙayyade masa sabon sadaki". zuciyar Fillo ta buga, tasa hannu ta dafe takardar sakin da ke maƙale acikin brezier ɗinta. Dadda ta ce da ita,"ungo sha wannan". Fillo tasa hannu ta karɓa tana yatsine fuska, zata yi gardamar da ta saba Dadda ta ce,"ke wannan ba magani ba ne ruwan tofi ne Dottijo ya bayar a kawo miki, ma za yi bismillah ki kafa baki ki sha". tayi bismillah a fili ta kafa baki, ba ta sauke ba sai da ta shanye tass da ma tana jin ƙishirwa. "ko ke fa, adu'armu itace Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka ya albarkaci rayuwar aurenku, Allah ya baku zuri'a ɗayyiba, ya kauda fitina tsakaninku ya haɗa kanku ke da abokiyar zamanki". kowa da ke ɗakin ya amsa da,"ameen". a lokacin Dada ta shigo, itama ta bata wani ruwan tofin adu'ar ta sha, sannan ta ba ta wani magani na su da kuma wani turare da ta fesheta da shi lungu da saƙo, ta kuma bata wata ƙaramar kwalba itama da ke ɗauke da turare aciki ta ce,"karki yarda taje hannun kowa har ki shiga ɗakinki, ki shafa turaren ciki a lokacin da zai shigo ɗakin, karki yi wasa da duk abin da muka faɗa miki da kuma abubuwan da muka ba ki, so muke kiyi zarra, ki zama tauraruwar da ke haska cikin gidan mijinki". Dadda da Adda Asma su ka kamata a tare suka fita da ita, ɗakin Hajjah aka wuce da ita inda nan Ummi ta ke da zama yanzu ita da su Kaka da sauran ƴan'uwanta, ana shigo da ita Ummi kawai sai ta fashe da kuka, aka ƙaraso da Fillo gabanta ta durƙusa. Ummi ta zura hannunta cikin alkyabbar ta kamo hannunta ta riƙe anata, sai a lokacin Fillo ma ta saki nata kuka da bai zo ba tun ɗazu. "Yanzu kin zama matar aure, kin bar ƙarkashinmu kin koma ƙarkashin wani bawan Allah wanda Allah ya zaɓa miki matsayin mijinki, haka zalika aljannarki ta koma ƙarƙashin mijinki, bauta za kiyi, bautar da za ki saka a ranki cewa ba Muhammad Turaki za ki bautawa ba Allahnki za ki bautawa, biyayyar mijinki a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addininki, in dai har za ki yi ma mijinki biyayya to za ki shiga aljannah, faɗar Allah ce ba tamu ba, ki kula da abincin mijinki ki kula da shimfiɗarsa, karki wasa da tsafta, ki zama me haƙuri, karki ko yi rashin juriya da kawar da kai, in har kin riƙe waɗannan abubuwan riƙo me kyau to kuwa za ki kama mijinki a tafin hannunki, kina da kyau ki ƙara da wanka ƴata, Allah ya yi miki albarka Halima, biyayyar da ki ka yi min Allah yasa kema naki ƴaƴan da za ki haifa su yi miki. Allah ya sa wannan aure da ki ka yi anyi kenan sai mutuwa ce zata raba ku, Allah ya yi riƙo da hannayenki ƴata, Allah ya dasa tsananin tausayinki da ƙaunarki a zuciyar mijinki, Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakanin ke da abokiyar zamanki, don Allah ki zama me haƙuri a gidan aurenki kinji, da auren so da auren ƙiyayya duk sai anyi haƙuri sosai ake jin daɗin zamansa, ki girmama iyayen mijinki wannan zai ƙara ba ki fada a zuciyar mijinki, kar ki zamto me yi masa jayayya da ƙorafi hakan zai sa mijinki yaji kin fita a ransa, ki kula da duk haƙƙoƙin mijinki, ki dage da ibadah da kuma yawaita adu'ar tsari da zaman lafiya tsakanin ke da mijinki da abokiyar zamanki, kin san ba ki da lafiya dan haka ki nesanta idanuwanki da kunnuwanki da dukkan abinda zai zamar miki damuwa balle ki jawa zuciyarki matsala, sannan abu na ƙarshe da zan jaddada miki shi ne ki zama busy akan yawaita karatun ƙur'ani, wannan zai hana zuciyarki samun lokacin biyewa zugar shaidan, Allah ubangiji yayi miki albarka, ya baku zaman lafiya ya kauda fitina a tsakaninku, na yafe miki dukkan abin da kika yi min". rabuwa dai tsakanin mahaifiya da ƴarta sai ya zama abu me wahala, dan ƙam Fillo ta riƙe Umminta tana kuka me taɓa zuciya, kuma da yake itama Ummin tana da raunin zuciya sai su ke ta kukan tare, sai da ƙyar aka samu aka cire Fillo daga jikinta. suka fito aka wuce da ita part ɗin Maudo, shi da Dottijo ne zaune a parlonsa, anan aka zaunar da ita kowa ya fita ya rage daga ita sai su, Maudo ya ɗora hannunsa akanta ya dinƙa kwaranyo adu'a yana tofa ma ta, ya gama nasa Dottijo ma ya yi ma ta, sannan suka shiga yi ma ta faɗa da nasiha me ratsa zuciya, kukanta sai ya ƙaru, kuma lokacin kewar mahaifinta ta kamata, sun jima su na ma ta nasihohi kafin a fito da ita. ko ƙafar gida ba'a fito da ita ba anan ƙaton tsargidan akayi parking da motar Maudo me shegen tsada a gabanta aka shigar da ita, ana ta busa algaita da sarewa kamar wata ƴar sarki, Dadda da Inna Baraka yayyan Hayyo sai wata cousin ɗin Ummi me suna Innah Hajar su ne suka shiga motar amarya, sauran motocin kuma da mutane shida kacal suka bi bayansu, motar amarya tayi airpot sauran biyun kuma suƙa ɗauki hanyar Gombe. a gidan Alƙali aka yada zango, dan su da kansu suka turo motar ɗauko amarya a airpot, su Dadda sun sami tarba me kyau a wajen su Hajiya Madina, sun ga mutunci da karamci tsurarsa, lokacin da su Dadda zasu damƙa Fillo a hannun Mum sai ta girgiza kai tana yi musu nuni da Hajiya Madina ta ce,"ai ga mahaifiyar tasa can". Inna Hajar ta miƙa hannun Fullo akan ƙafafun Hajiya Madina tana faɗa ma ta ga amanar ƴarsu, Maama na murmushi me faɗi da jin daɗi take shaida musu sun karɓa, kuma insha'Allahu ɗan su ba zai bayar da kunya ba, Fillo sai ta rinƙa jin kamar ayau ne ta fara shigowa gidan Alƙali, kuma kamar ayau ne ta fara sanin su Maama dan duk sai take jin su sababbi a wurinta, a cikin hular alkyabbar da ta rufe mata ido banda kuka babu abin da take yi, ƙwayar idonta baƙin rubutun da ke ɗauke da adadin sakin da Turaki ya yi ma ta kawai ta ke haskowa, tana jin muryarsa na ƙara karanta ma ta a kunnenta. sai wajen ƙarfe uku sannan ƴan taraba waɗanda Dada ta zaɓa zasu zo Dinner suka zazzo, ciki kuwa har da ita kanta, tasha wanka na kece raini kamar ba tsohuwa ba, less ɗin jikinta kansa abin kallo ka ƙara kalla ne. sai ƙarfe takwas na dare tukunna aka fara shirin tafiya Dinner, faɗar haɗuwar da amarya tayi ma ɓata lokaci ne, alƙalami ma ba zai iya ba, ta yi kyau iyakar kyan da ƙaryar baki ya ce zai iya faɗa, wata arniyar doguwar riga ce da Maama tasa Samha tayo order ɗin ta daga europe aka taho da ita, kana kallo kasan kuɗi aka sa ba kaɗan ba aka saya rigar, shigar pink aka yi ma ta wanda hasken fatarta yayi bala'in ɗaukar colour ɗin, abin ba'a cewa komai sai dai masha'Allah. sabuwar mota fil wacca Mum ta bawa Turaki a ita zaa ɗauketa, Raudha da Maijidda su kai ma ta rakiya har bakin motar da Bello ne ke zaune a driver seat, aka buɗe mata bayan motar ta shiga, san da zamanta ya daidaitu lokacin balaƴaƴƴan ƙamshin turaren da ta san shi kaɗai yake amfani da shi taji ya doki hancinta, ta yi saurin ɗago kai tana kallonsa, ta gan shi yana kallon gefe guda da alama ma bai san da shigowarta cikin motar ba, Fuskar nan kamar an aiko masa da mutuwa, ya fito sak a asalin Turakin da ta fara sani a rayuwarta, sai dai duk da wannan ɗaure fuskar da ya yi hakan bai hana fito da azababben kyan da ya yi ba acikin arniyar suite ɗin da yasa, black da ratsin pink colour irin na jikinta. tuna cewar ita fa ba matarsa ba ce yasa tayi saurin ɗauke idonta akansa, tana me tuna haramcin hakan, idanuwanta suka ciko da ruwan hawaye suna ƙoƙarin zuba, sai dai ba ta basu damar hakan ba dan sam bata so yaga weakness ɗinta a yau balle ya alƙanta hakan da zafin sakin da yay ma ta. ta kafe ƙunshin hannunta da kallo tana jin ƙaguwar su tafi aje ayi ayi a gama taron ta daina ganinsa a kusa da ita. da ga Bello dake driving har su kowa zuciyarsa a cunkushe take, Maijidda ce kawai da bata san damuwar komai ba take jin zuciyarta wasai sai kallon titi takeyi, Bello kuwa bini-bini sai ya daki stearing yana jan dogon tsaki. can da tafiya tayi nisa Fillo taji kallon dake jikinta ya yi yawa ta ɗago ido, karaf ƙwayar idonsu ta tsarƙe ata juna, tasha murr fiye da yanda ya haɗe tasa fuskar, kwatakwata ba ta san lokacin da bakinta ya suɓuce da faɗin,"kana da buƙatar ƙara sanin addini da kyau, domin na lura sam baka san yanda shari'ar musulunci ke tafiya ba". tayi maganar a ƙasa yanda su Bello da ke gaba ba zasu ji ba. Turaki ya dinƙa kallonta da mamaki tsantsa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce da ita,"kin fini buƙatar komawa makaranta ke da kika kasa ba da takardar sallamar da aka ba ki". ya faɗa daidai da isowar motarsu event center, suka yi parking a bakin ƙofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota, Bello bai ko waiga ya kalli Turaki ba balle yay masa magana, ya fita ya tsaya jikin motar sai jera uban tsaki yake yi. sai da duk mutane suka gama shiga cikin hall sannan aka zo aka fito da Turaki da Fullo, Bello ya yi gefe abinsa kamar bai da wata alaƙa da Turaki, aka zagayo da Fillo side ɗin da Turaki yake nan da nan sai ruwan camera akansu, ƙememe suka ƙi riƙe hannun juna duk da ɓata ran da Anty Rahinatu(ƙanwar Mum) ta nuna musu, suka jera kamar ƴan ƙauyen ƙayayau. su Amatullah da suka zama ƙawayen Fillo su ne suka fara shiga a layi na hannun dama da ga nan sai iyayen gayyar a tsakiya, sannan abokan ango da Turaki bai sa a inda Bello ya kawoso su ba suka ja nasu layin a gefen hagu, abin dai gwanin burgewa, ba zaka taɓa kallon fuskar Turaki da Fillo ba kayi zaton ransu a ɓace yake, ko damuwa, hakan yasa duk hoton da aka ɗauke su sai sunyi kyau, ita dai tayi ƴar ƙarama a kusa da shi dan ita kanta sai nauyi take ji. su na ɗora ƙafafunsu akan step na shiga hall ɗin MC ya fara sanar da shigowarsu, kowa ya miƙe tsaye kamar an ce wasu masu mulkin nigeria ne za su shigo. ƙafafun Turaki da na Fillo suka shiga hall ɗin a tare, abokai kuma na take musu baya, cameras suka shiga ɗaukan su ta kowanne angle, me video coverage na ɗauka tun da ga kan takalmansu har zuwa kan fuskarsu. taro dai ya tafi a bisa tsari kamar yanda iyayen ango suka so ya kasance, yanda Bello ya zo ya yi baiograph haka AmaturRahman tazo tayi biograph na Fillo, anci an sha an bar abinci, biki dai kamar da ma an jima ana shirya masa dan sosai sisters ɗin Fillo suka dinƙa rawa, tashin kiɗa a wajenan kace bayyanar dujal, su dai waɗanda ake abin dominsu suna tsaye ƙyam kamar gumaka, gwara Fillon ma na ɗan murmusawa mussaman da ta ga cousin sisters ɗin suna ta shan rawa abin su, ruwan kuɗin liƙi kamar ba'a talauci a nigeria. Dada da Hajiya Madina kuwa watsa kuɗi kawai suke yi kamar babu talakan da ke buƙatarsu a duniya, har hannayensu sai da suka fara ciwo, rawa kuwa ba ka ce da jikinsu su ke yi ba, Dada sanda ta suɓuce zata faɗi akai saurin tarota, amma a haka taci gaba,  ita kanta Maama har sai da Khalil yaji haushi yazo ya janyeta, tazo tana rawa ta manta gaban ƴaƴa take da abokan ƴaƴa. sai a ƙarshen taro Fillo ta yanka cake ɗin da Turaki ko kallonsa bai yi ba, kuma babu wanda ya lura da hakan banda Bello da ke kallonsa yana jin kamar ya rufe shi da duka, Hajiya Sajida Yayar Hajiya Ramla ita ta rufe taro da adu'a sannan aka tashi. lokacin da aka tashi ƙarfe goma sha biyu, direct daga nan aka wuce da Fillo gidan mijinta. su na zuwa Dadda tasa tayi wanka sharp sharp aka ƙara shiryata cikin wani ɗinkin atamfa na riga da zani, aka ɗora ma ta sabuwar alkyabba ba irin wacca aka zo da ita ba fara ƙal me arnen kyau, a gurguje suka ƙara yi mata nasiha daga bisani kuma suka yi ma ta sallama suka tafi, tare da shaida ma ta zasu zo gobe kafin su wuce in dai Dada bata hana su zuwa ba. Adda Asma ta kalli su Raudha da suka wani maƙale mata ta ce,"sai ku tashi mu tafi ko". kusan duk a tare suka miƙe su na rataya jakunkunansu, Fullo ta kamo hannun Maijidda, ta ɗage hular alkyabbar da aka rufeta da ita, ta kallesu duk su biyar ɗin, Amatullah, Amaturrahman, Raudha, Maijidda, Khairat, da kumburarrun idanunta cikin sanyin murya ta ce,"yanzu tafiya za ku yi ku barni ni kaɗai?, ku zauna tare da ni don Allah". Khairat ta ce,"mu barki ke ɗaya ko mu barki ke da angonki?, gulmammiya rabonki da azababben kukanki tun jiya da kika ji za'a kawo ki gidan miji yau". Raudha ta ce,"bar ƴar ƙaniya za ta wani marairaice mana ba". Maijidda ta ce,"rabu da su zanke zuwa ina ganinki kinji Hussainata". Dadda ta sake ƙwala musu kira dan haka suka fice da sauri su na ƙara yi ma ta sallama da yi ma ta tsiya. tana jiyo takun su a sanda suka sauka daga bene, ta jiyo ƙarar rufe ƙofar parlon ƙasa, sai kuma ta dinƙa jiyo hayaniyarsu a compound suna shiga mota an buɗe musu gate sun fita. ƙarar zuge gate ya haɗe da bayyanar wani bala'in tsoro a ƙirjinta, tayi saurin tashi ta isa window ta leƙa, karaf idonta ya sauka akan Turaki da yake fitowa daga mota, tana kallo ya ɗau wata hanyar ta daban ba nata part ɗin ba, sai kawai taji saukar sabbin hawaye a saman kuncinta masu zafi kamar zasu ƙona fatarta, ta ƙara komawa ɗaya windown ta hangesa ya buɗe part ɗin da yake na Ilham ya shige, tana kallo ya zuge glass door na entrance din parlon, sai taji kamar ya haɗa da zuciyarta wajen rufewa ya datse. a hankali ta sulale a wajen tana rushewa da kukan da zata ce bata taɓa yin irinsa ba, yanzu ita ɗaya zata kwana a wannan ƙaton wajen?, tabi tangamemen bedroom ɗin da kallo, tsoro na masifa ya ƙara kamata, me yasa ma tayi wannan haukar na bari a kawota cikin gidan nan alhalin ba zaman aure zata yi ba zaman iddah zata yi?, ta jima zaune tana ta uban kuka har kusan ƙarfe biyu sannan ta miƙe ta shiga toilet tayi alwala tazo tayi sallah, sai bayan ta idar take jin wani irin loneliness da kuma wani irin tsoro na daban, tayi saurin barin kan dardumar ta haye kan gado ta ƙudundune a waje ɗaya, ƙarshe ɓarawon bacci ne ya ɗauketa. *Comment, Share and Vote.* [9/5, 19:08] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *47* kirayen sallar asuba ya farkar da Fillo da ga bacci, ta buɗe idanuwanta a hankali, tana miƙewa zaune aka ɗauke wuta, babu shiri ta koma ta ƙara dunƙelewa, har sai da taji masallaci na sallamewa da ga sallah tukunna ta ƙara buɗe fuskarta tana leƙowa, farko duhu ta gani sai kuma ta ga haske ya gauraye ɗakin. da ƙyar ta iya sakkowa kamar me tsoron taka tiles ɗin, alwalar ma kanta ɗaiɗai ta yi saboda tsoron toilet ɗin, ta fito ta isa kan dardumar da ta bari a shimfiɗe tun sallar daren da tayi. zata tayar da sallah taji kamar an buɗe gate, jikin windo ɗin ta isa ta ɗa ga labulen tana hangen bakin gate da mai gadi ke mayar da ƙofa ya rufe, kafin idonta ya manne akan Turaki da yake tafiya zuwa in da taga ya nufa jiya wanda ta tabbatar nan ne part ɗin Ilham, dubai jallabiya ce a jikinsa dark blue, sai carbi da yake hannunsa yana ja, a yanzu ma da ya zuge glass door sai taji kamar ya datse da zuciyarta, idonta ya ciko da ruwan hawaye sai dai ba ta basu damar zubowa ba, a hankali ta din ga bin tazarar da ke tsakanin part ɗin na su, cikin kanta tana jin kamar ƙwaƙwalwarta na couting ma ta nisan interval ɗin da ke tsakanin part ɗin na su, tazara ce sosai amma sai take ganin kamar tazarar daidai take da tazarar yatsun hannunta. jikinta taji gaba ɗaya ya saɓule, ta koma kan sallayar ta tayar da sallah, ta jima tana jero adu'oi a san da ta idar, haka kawai taji zuciyarta na raya ma ta kamar Turaki zai mayar da aurensu, ta yi saurin girgiza kanta, it can never be possible ta san da hakan, yanda ya ke da muguwar zuciya ta sani ko da wuri ɗaya zasu ke kwana su na tashi ba zai taɓa mai da auren ba, kuma itama ba ta jin ko da ya mayar da auren za ta yar da ta zauna da shi, ai yanzun ma zama kawai take yi da zarar ta gama iddah zata bar masa gidansa, bari kuwa na har gaban abada. ka sa ta shi ta yi ta koma kan gadon, kawai sai ta kwanta nan kan darduma jikinta tana jin duk yana yi ma ta ciwo, hawayen da take ta danne zubarsu taji sun gangaro, muryar Ummi kawai take son ji, ita kawai take son gani. cikin kanta taji na karanta ma ta yanzu ita ɗaya zata yi ta zama haka kamar mayya?, to ai ko wannan bedroom ɗin ya yi ma ta girma da zama ita ɗaya balle wawakeken part ɗin na ta da taji ana ta faɗarsa tun a jiya da su Arɗo su ka dawo daga jere, anya kuwa zata iya ci gaba da wannan zaman da zuciyarta ta tsara ma ta?, ba zata falllasa komai ba kuwa?, kamar fa hauka ne take yi hakan!, ita abin da ba ta so shi ne ƴar ƙaramarta da ita ace wai tana zaman iddah a gidansu, to wanne irin kallo za'a koma yi ma ta?, wanne kalar tunani za su koma yiwa silar rabuwar auren?. sai kawai taji kuka ya taho ma ta sosai, tasa hannu ta toshe bakin kamar akwai wanda ya ke kusa da ita ba ta so ya ji, ita dai ba zata iya wannan zaman ba, gwara ta yi tafiyarta kawai, ko kuma ta kira Ummi ta faɗa ma ta a kawo Sumayya ta tayata zama, Sumayya ƙanwarta ƴar matar Hayyo da har ya mutu da ita ɗaya ce ba su rabu ba, ko kuma ta cewa Maijidda ta dawo nan ɗin?, to ai in har ta faɗawa Maijidda kamar ta kai takardar sakinta ne gaban Dada. da waɗannan lissafin tunanin bacci ya ɗauketa, ƙarfe takwas yunwa ta farkar da ita, hasken ranar da ya ratso ta windon ɗakin yasa hankalinta kwanciya, tsoron ya bar jikinta. tana ta shi ta gyara kan gado, sannan ta shiga toilet tayi wanka, ta daɗe a toilet ɗin kafin ta fito, ɗaya da ga cikin lotions da aka jere ma ta akan dressing mirror ta ɗauka ta shafa, ta shafa farar powder tasa lip balm, sannan ta saka abaya baƙa, ramar da ta yi sai ta ƙara yin kyau sosai acikin kayan. tana sakkowa downstairs sai ta shiga laluben ƙofar kitchen, ƙofofi uku duk sai da ta buɗe, kuma dukansu bedroom ne sai 1 parlo wanda yake shi ne a middle, cikin sanyin jiki ta rufo ƙofar, kenan ita babu kitchen a part ɗin ta?, haɗe musu yay kenan su yi shairing guda ɗaya?, kenan duk wannan uban kayan kitchen ɗin da taga an siya su na can an haɗe su tare da na Ilham?, abun da ake nufi har in zata ci abinci sai taje part ɗin Ilham sannan zata dafa?, ashe kuwa an so yunwa ta kasheta,  dan wallahi in har dan sai taje part ɗin Ilham ne zata dafa abin da zata ci, to gwara tayi ta zama a haka har yunwar ta gaji da damƙarta ta kasheta. bakinta ya suɓuce da tsakin da ba ta san dalilin yinsa ba, ta koma upstairs ta buɗe jakar da Dadda ta ce an ajiye ma ta kuɗi, ta zaro 10k, hijab ta ɗauka ta sa ta fito ta sa mu mai gadi, ta durƙusa har ƙasa ta gaisar da shi yana amsawa da fara'a tare da saka ma ta albarka. sai taji nauyinsa, ba ta jin zata iya aikensa dan ya haifeta, idan bai girmi Abbanta ba tabbas za su yi sa'anni, ta yi shiru tana juya kuɗin a hannunta har sai da ya katse shirun na ta da cewa,"da akwai abunda ki ke buƙata ne?". ta ce,"Baba don Allah ko za'a sami almajiri a waje?". ya ce,"aike ne?". ta ce,"ehh Baba". ta faɗa kanta na ƙasa. kamar kuwa yanda zuciyarta ke raya ma ta taji ya ce,"ai kin san layin namu babu almajirai, sai dai ki kawo bari naje na siyo". ta na girgiza kai ta ce,"a'a Baba ka bar shi ba zan iya baka aike ba gaskiya". yay murmushi yana jin har ransa ta burgesa, da kuma yabawa da tarbiyarta da hankalinta, ya tuno san da Ilham tana nan, a rana ba'a aike shi ba a aike shi sau uku, kuma a gadarance da nuna isar mulki. "kawo ƴata babu komai ai sai aje a siyo miki, ai ba aikena kika yi ba, a matsayina na uba zan fita siyo miki abun da ƴata take buƙata saboda kare darajar aurenta". ta ɗago ido tana kallonsa, taji tausayinsa sosai a cikin ranta, ta miƙa masa kuɗin ta ce,"na gode Baba. da ma golden morn za'a siyo min babban ledan, sai madara na gwangwani babba, sai sugar rabin kwano, sai cornflask kwali biyu. za su isa kuɗin ko Baba?". zai ƙirga kuɗin ta ce,"dubu goma ne ban san yanda kuɗin na su yake ba". ya ce,"ehh tou nima gaskiya ban san yanda kuɗin yake ba, amma yanda za'a yi, bara idan naje in akwai ciko sai na karɓo miki lambar akawunt ɗinsa sai ki tura masa tunda da ma mun saba da shi, nima na kan yiwa iyali cefane acan". tayi ɗan jimm kafin ta ce,"bara dai na ƙaro in ya zama da sauran canji ko ma sun kai shikenan". ta faɗa masa hakan tunawa da tayi bata da waya balle wani account. 5k ta ƙaro, ta ba shi ta ce ya yi har na mota, dan indai ba'a tafiyarta ba tasan layin nan nasu kaf babu wani kanti. da ga fitowarta ta farko, da komawar da tayi ta ƙara fitowa duk a idon Turaki da ke tsaye a balcony na sama, hannunsa riƙe da mug da alama tea yake sha, ya bita da kallo san da ta koma ciki yana ji zuciyarsa na ƙirga masa girman laifin da ta aikata. sai bayan ta shiga kuma kawai sai idonta ya sauka acan dining area, adon wurin ya yi bala'in burgeta hakan yasa ta tafi, tana zuwa ta tarar da manyan warmcoolers na abinci guda huɗu da babban tea flask, tana kallonsu ta shaida su, coolers ɗin kitchen ɗin Maama ne da sai Baffa yana nan kawai ake amfani da su. ta buɗe ƙaramin coolern taga irish ne da miyar hanta da soyayyan ƙwai, ƙamshin ya ziyarci hancinta har sai da ta lumshe ido, ai ko bata jin yunwa sai taci balle kuma uwar yunwa na ƙwazafarta a ciki, mamakinta ɗaya ne da yaushe aka kawo abincin?, zuciyarta ta faɗa mata tana can tana bacci. ta ɗauko plate ta fara zuba abinci sai taji ana knocking, adu'arta ɗaya ne a lokacin Allah yasa su Dadda ne suka zo, ta miƙe da sauri taje ta buɗe door sannan ta zuge glass, idanuwanta suka sauka akan Bello da ke tsaye hannunsa ɗaya a aljihu ɗaya kuma yana maƙale da waya a kunnensa. taja da ba ya tana ba shi hanya tare da yi masa sannu da zuwa, ya shigo yayin da yake amsawa, ya wuce ya zauna kan kujera ita kuma ta durƙusa har ƙasa ta gaida shi, ya amsa ya ɗan kallonta da son fahimtar wani abu, sai dai ya gagara fahimtar komai ɗin. tana tsugune tana jan yatsun hannunta har wucewar daƙiƙa biyu sannan ya kalleta ya girgiza kai ya ce,"MT bai ta shi ba ne?". tai ɗan jimm tana nazari, kamar ta ce bai tashi ba kamar kuma ta ce masa ya fita, a wannan shirun na ta Bello ya samu amsar tambayarsa, tausayin yarinya ya kama shi, a irin hallacin da tayi masa sam sam ba ta kamaci wani abu wulaƙanci a wurin Turaki ba balle tozarci, dan babu tozararci irin sakin da ya yi mata tana ƙarama da ita, ya miƙe yana cewa da ita,"idan ya dawo kice masa nazo, ina ta kiran wayarsa bata shiga ya yi ƙoƙarin kirana". ta amsa da,"toh". sannan ta ce,"ba ka sha ruwa ba, ga tea zan kawo maka". bai kalleta ba amma yanda voice ɗin ta ya fito ya tabbatar ruwan hawaye sun cika idanuwanta, kuma so ta ke ta zubar da su, ya sauke numfashi ya koma ya zauna tare da cewa,"oak kawo min tea kawai, kisa nescafe idan ba takurawa". ba wai yana yin yunwa ba ne, a'a kawai ba zai iya ƙin tayan da tayi masa ba, dan sosai shi dai yake bala'in tausayinta. ta wuce cikin sauri ta ɗau mug anan kan ƙaton family dining table, ta cika shi da ruwan tea sannan ta ɗauki plate ɗin da ta zuba irish da miyar hanta taje ta kai masa, shi ya tayata janyo center table gabansa dan yaga kamar mug da plate ɗin da ke hannunta suna neman rinjiyar waɗannan sillan karan hannayen nata, kar yaje ata dalilinsa ƙashin ƴar mutane ya karye. ta na kallon carpet ta ce masa,"nescafe ɗin ne dai babu sai na bayar an siyo, kuma mai gadi ya fita bai dawo ba". da mamaki Bello ya ce,"sai an siyo?". ta ɗaga masa kai kawai tana sa hannu ta goge hawayenta. yay ta kallonta da mugun tausayinta ya ce,"kuma kin duba ko'ina a kitchen ɗin babu?". ta yi shiru, sai taji ya ƙara cewa,"tsaya tukunna!, faɗa min gaskiya kar ki ɓoye min komai, ke ɗaya kika kwana a nan ko?". da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yay guntun murmushi na takaici ya ce,"kar ki rufawa MT asiri, ɗan banza ne bai da hankali ko kaɗan, tunaninsa ba irin na mutane ba ne, gwara ma ki fayyace min komai dan ko kin ɓoye min shi ba zai ɓoye min ba. ki faɗan gaskiyar amsar tambayar da nayi miki". hawaye su ka ƙara zubo ma ta bata ce da shi komai ba, a wannan hawayen ya karanto duk wata amsar tambaya da yake son yi ma ta. ya sosa girarsa yana tunanin ta yacca zai shawo kan wannan lamarin, tun jiya yake tunanin ta yan da zai yi convincing Turaki akan ya mayar da aurensu, shikenan su zauna lafiya salin alin babu wanda ya san anyi, to amma ya san shegiyar gardama da rashin ɗaukar shawara irin tasa ba lallai ya amince ba, shi abun da yake gudu ma kar silar zaman nata a gidan azo a aikata kwaɓa, yay guntun tsoki ya ƙara trying lambar Turaki amma bai samu ba. ya ce da ita,"ƙofar tsakiyar nan anan kitchen ya ke, ki kawo min nescafe ɗin". sai ta juya tana kallon ƙofar da ta buɗe ta shiga ɗazu har tafi ƙarfin minti uku tsaye a ciki, ta ƙara juyo da kanta gare shi ta ce,"babu ai kitchen ɗazu duk na duba". yay gajeran murmushi ya ce,"ai na zaki dinƙa girki idan babu kitchen?, ko kin taɓa ganin gida babu kitchen?". ta ce,"a'a ƙila haɗe mana yayi da ita, anjima na ke son zuwa part ɗin nata". Bello ya kaɗa kai,"kina uwar gidan zai tafi bangaren wata yayi kitchen?, to ba haka ba ne, kowaccenku da nata kitchen ɗin, duba in da na faɗa miki". ba ta iya jayayya da Babba ba, amma ita ta san babu wani kitchen, ta tashi taje ta buɗe parlon, yana ta kallonta a san da ta shiga ta tsaya daga bakin ƙofar, yay smiling ya ce ta buɗe ƙofar ciki, ta ƙarasa shiga ciki ta isa wa ta ƙofa da ta gani ta buɗe, jimawa kaɗan sai gata ta dawo riƙe da ƙaton gwangwani na nescafe, ta ajiye masa ta koma dining ta zauna, yana shan ruwan tea ɗin yana ɗan janta da hira sama-sama, har da tsokanarta wai an bata award na amaryar da tafi kowacce amarya kyau tun da aka fara aure a nigeria. ita dai murmushi kawai take yi, kuma sai taji hirar tasa na yi mata daɗi musamman da yana bata labarin yarintarsu, irin yanda suke faɗa akai akai kamar ƴan tsaki, da yacca Baffa ke cin ƙaniyarsu, har ya ce yana basu purnishment ɗin yin dariya da haƙori ɗaya ko su ciji hancinsu in ba haka ba a dafa su a bawa mage ta cinye, sai suyi ta kuka suna bada haƙori in Baffa yaƙi haƙura sai su ɓuya a lambu, sun sha kwana acan yafi a ƙirga saboda basa son faɗan Baffa da dukansa ko kaɗan. sai ta sami kanta da yin dariya sosai, sai da ya ɗeba mata kewa tukunna yay mata sallama ya tafi, bayan tafiyar tasa duk sai taji babu daɗi, ta dawo ta koma upstairs tai kwanta zuciyarta cike da son ganinta a gida, yanzu ta san su Dadda sun ɗau hanya, tana ta so ta yi waya da Umminta taji muryarta, tun da ta tashi take mugun kewarta. ban da tunane tunane babu abin da takeyi har ƙarfe goma, sai lokacin ta tuna da aiken da ta bawa Baba, hakan yasa tayi saurin saukowa ta fita, tana fitowar kuwa ta tarar da Baba me gadi yana isowa entrance na ɓangarenta, ta tafi da sauri dan karɓar masa kayan, sai dai kamin ta ƙarasa Turaki ya rigata, ta ƙaraso wajen Baban a sanda Turaki ke miƙa masa hannu alama na ya ba shi kayan ba tare da ya ce masa komai ba. Fillo ta haɗe rai kamar ba ita ba, ko kallon in da inuwarsa take bata yi balle kuma shi kansa, tana yiwa Baba sannu da zuwa ta miƙa hannu za ta karɓi kayan taji saukar muryar Turaki a tsakiyar kanta. "idan har kayan nan suka je hannunta, to ka nemi wani gidan ka ci gaba da aikinka". ta dakata da karɓar ledar tana kallon hannun Baba da ke aikin karkarwa, taji mugun tausayinsa ya kamata, tana kallo ya kalleta fuskarsa nayi ma ta nuni da tayi haƙuri ta rufa masa asiri, ta gyaɗa kanta kawai shi kuma ya bawa Turaki ledojin, ya karɓa ya juya ya bar wajen, itama zata bar wajen Baban ya ce,"Hajiya ga canjin ki". ta waigo tana yi masa murmushi ta ce,"ka riƙe Baba". ya waro ido waje yana cewa,"dubu biyar ce fa Hajiya". ta ce,"babu komai Baba". ta faɗa tana barin wajen tare da goge ƙwallar idonta, shi kuma ya bita da kallo yana ta zazzaga ma ta adu'a yana sa ma ta albarka. kai tsaye parking lot ta nufa in da take hango Turaki a wajen motarsa ya buɗe ya shiga ƙafarsa ɗaya a waje, ya ajiye ledar kayan da ya karɓa, ɗaya a ƙasa ɗaya a saman murfin booth, ta ƙarasa wajen motar cikin sanɗa ta durƙusa ta kwashi kayanta, ta yi saurin barin wajen kamar za ta kifa ƙasa, fatanta ɗaya ta isa har ƙofar part ɗin ta bai fito da ga cikin motar ba, abin da ba ta sa ni ba shi ne, tana ɗaukar kayan ta juya shi kuma ya fito daga cikin motar, mamakin ƙarfin hali irin na ta shi ya tsayar da shi kawai yana bin bayanta da kallo, ya kasa yi mata magana balle ya cimmata ya karɓe, shi kallon ma da yake yi ma ta tun jiya kamar da akwai abin da takala. ya jijjiga kansa, koma me take ji da shi zai saitata ne within wani ɗan lokaci. bayan sallar azahar tana zaune kan darduma ta zabga uban tagumi sai taji kamar hayaniya a compound, ta miƙe da azama ta leƙa ta window sai taga su Adda Asma'u ne, ai kuwa babu shiri ta wancakalar da hijab ɗin jikinta ta fice da sassarfa me kama da gudu, saura kaɗan ta zame a steps, ta sauko parlon a san da ta ga ana ta shigo da manyan kuloli na abinci ana wucewa da su kitchen, taji Inna Hajar na cewa da masu shigar da kayan,"kar ku saka su da ga in da babu iska kayan gara ne". ta yi tsallen murna da farin ciki ta faɗa jikin Raudha, duk su ma sauran sai suka maƙalƙaleta anata Allah sarki ƴar marainiya, sai kuma aka ɓige da yi ma ta tsiya ana tsokanarta amaryar ƙamshi, har ta fara kumatu, ta harari Maijidda da ke ta kallonta tana murmushi. ta zame da ga wajensu san da Adda Asma da Dadda ke shigowa, ta tafi da sauri ta faɗa jikin Dadda, sai ga hawaye kamar da ma jiran ganinta su ke. Adda Asma ta ce,"yau naga tsiya, to in dai kuka za ki yi kam sai mu juya". ta yi saurin goge hawayen tana faɗin,"ku yi haƙuri Adda Asma na daina". ƙememe Adda Asma ta hana su Raudha zuwa bedroom ɗin Fillo, kamar ta san gulma ce zata kaisu, ta ce wallah duk wanda ya kuskura yaje ma ta ɗaki sai ta ɓata masa. ita dai Fillo ba ta ce komai ba, daɗi duk ya isheta saboda ganin ƴan uwanta, ji take kamar kar lokacin tafiyarsu ya yi, Dadda tasa su Raudha suka shiga kitchen ɗinta su ka ƙara gyara ma ta shi da cikin store, su kuma suka haura sama zuwa bedroom ɗinta, wasu kayan da aka zazzo ma ta da shi aka ƙara kimtsa ma ta su, da aiken Dada da ta bayar a ƙawo ma ta, sannan su ukun duk suka zauna suka ƙara yi ma ta ƴan nasihohi da ba'a taɓa daina yiwa ƴa mace in har an aurar da ita. a parlo suka zauna akai ta hira har akai sallar magriba tukunna suka yi haramar tafiya, Fillo ta riƙe Maijidda akan lallai ba zata tafi ba, ta rakosu compound tana ta kuka irin na jiya. bata ƙara jin kewarsu ba sai da magriba ta yi, lokacin ne kuma ta fara jin yunwa ta shiga kitchen, ta buɗe freezer taga babban botiki na miya da su ka zo ma ta da shi ɗazu, ta ɗauko flask ɗin da Inna Hajar ta faɗa ma ta akwai ferfesun kifi a ciki, ta zuba kaɗan ba da yawa ba, ta buɗe oven ta ɗauko gasassan biredi, sai dai ko da ta zauna sai taji kasa ci, dole haka tasa hijab ta fita ta kaiwa Baba me gadi. tana zaune a parlo har akayi sallar isha'i, a lokacin tsoro ya fara kamata, tayi azamar barin parlon ta koma upstairs ta kulle ɗaki, ta dunƙule akan gado tare da toshe kunnuwa dan sam ko ƙarar AC bata son ji, kamar dai yanda ta kwana jiya ita ɗaya haka yauma ta kwana ita ɗaya, cike da tsoro fal kamar zuciyarta zata bar ƙirjinta. *Masarauta Kaltungo.* wani mugun ɗoyi ne ke tashi a cikin turakar ta Fulani Azima, tana can da ga kusurwar ɗakin an kwantar da ita akan gado, ba ma lallai ka lura mutum ba ne idan ka shigo, halittarta tayi mugun muni kamar ba wannan macen ƴar gayu da ƙwalisa ba, me ji da mulkinta da kuma girman izzarta. idanuwan da suka firfito waje kamar na ƙwarangwal sai kallon Ilham take yi wacce ke durƙushe da ga can bakin ƙofa, tayi tagumi tayi nisa acikin tunani, taji bala'in tausayin yar tata ya kamata, ta sa ni alhakin mutane da dama da ta ɗauka ba lallai ya bar ɗiyarta taji daɗin zaman gidan aure ba, ko me ya faru da ita ta san ita ta janyo ma ta, ga shi ba ta da bakin maganar da zata nemi yafiyar mutanen da ta cuta su yafe ma ta ko ta samu sauƙin wahalar da take ciki, ƴarta ma ta samu hutu. ta san babban alhakin wanda ke bibiyarta ita ce Hajiya Ramla, domin ita ta yiwa cutarwa mafi munin zalunci, kuma yanzu a cikin tsoro take matuƙa ma kuwa, domin hausawa sun ce ka guji shirun wanda ka zalunta, shirun da Hajiya Ramla tayi har yanzu yana matuƙar ɗaga hankalinta, yana tsoratata, gani take kamar shirun nata shi ke ƙara shigarta wannan matsanancin halin da take ciki, kuma kamar tana shirya ma ta wani abu ne da zai ƙara jefata halin da yafi wannan da take ciki, domin ta san babu wanda zai san kayi masa cutarwa irin wannan ya ƙyaleka, ko da ace ya yafe maka to dole zai tona maka asiri, amma ita babu ɗaya cikin biyun. a kullum babu abin da take kira face mutuwa, ta gaji da wannan wahalar da take sha, jikinta ya fara addababben ƙaiƙayin da shi kaɗai taƙi jin ya tasar mata, ta ɗago hannunta guda ɗaya da ya shanye ya koma tamkar ba'a taɓa halittar tsoka ba ajikinsa, karkarwa kawai yake yi yama ƙi kaiwa inda take so ta sosa ɗin. ta fara rera kuka a hankali, kukan babu daɗin ji, shi ba na mutane ba kuma shi bana dabbobi ba. Ilham ta ɗago ido tana kallonta, ta miƙe tana jin duk duniyar ta isheta, ta sani mahaifiya ta wuce duk inda ake zato, babu me so ya rabu da mahaifiyarsa a kowanne irin hali kuwa, amma ita dai a yanzu zata ce gwara mahaifiyarta ta mutu, ba wai zata ce ta gaji da zaman jinyarta ba ne, but cutuwar da take yi a zamanta tare da ita shi tagaji da shi, a kullum ba tayi amai ba tayi sama da sau biyar. ta ɗauki facemask ta saka sannan ta ɗauki sandar share yana, ta isa gaban gadon tasa sandar tana sosa mata jikinta da ita, saboda ba'a saka hannu wajen sosa ma ta gudun kamuwa da cutar da likitoci suka faɗa, sun tabbatar da cewa duk ranar ruwan ƙurjin ya taɓa jikin wani to shi ma yana iya kamuwa da wanannan cuta ta ƙuraje wadda har yanzu suke bincike akan su. wahaltaccen amai ya tahowa Ilham babu shiri ta jefar da sanda ta fita a ɗakin da gudu ta shiga toilet, amai sosai tayi kamar wacca zata amayar da kayan cikinta, ban da haki babu abin da take yi idanuwanta duk sun yo waje saboda galabaita. ta wanko bakinta ta fito ta tsaya a ƙofar wajen tana sauke numfashi, wucewar daƙiƙa ta fita ta zagayo ta window inda me martaba yake tsayawa duk sanda zai ga Fulani Azima, a yanzu ban da shi da ƴarta babu wanda yake iya zuwa wurinta hatta kuwa da mahaifiyarta, suma ɗin da suke zuwo roƙar ma ta mutuwa suke yi a wajen ubangiji kamar yanda take roƙawa kanta itama. cikin muryar me rauni Ilham ta ce,"Mami don Allah kiyi haƙuri, zan je inci abinci sai in dawo, banda ƙarfi a jikina yanzu duk abin da naci ya dawo". ta faɗa tana kuka. Fulani Azima ta bi ta da kallo hawaye na biyo gefen fuskarta, kullum roƙon Allah take yi ya bata aron dama ko da na lokaci ɗaya ne tayi magana da bakinta ta sawa Ilham albarka ta kuma yi ma ta godiya. su kai ta kallon junansu duk su na tausayin kowannensu, Ilham ta share hawayenta ta bar wajen ta tafi ɓangaren Boɗejo, in da ta dawo da zama gaba ɗaya tun ranar da aka yi sakin Ilham, ta ɗau fushi da Baffa da Hakimi ta ce duk Me martaba shi ya fi son ta da ƙaunarta, kwanciyar Turaki a asibiti ma sai da ta taushi zuciyarta ta iya zuwa, shi ma dan taji ance ya na can rai a hannun Allah. ta shiga parlon da sallama, kana ganin yanda take tafiya kasan damuwa tayi ma ta ƙatutu, ta zauna kusa da Boɗejo wacca ke shan kayan marmari da aka ajiye ma ta a faranti, ta cire hand gloves ɗin da ke hannunta ta wanke acikin ruwan da wata baiwa ta kawo yanzu. sannan ta shiga cin fruites ɗin da Boɗejo ta dawo da shi gabanta. "Sannu Ilham Allah ya yi miki albarka ya ba ki ladan ɗawainiya da mahaifiyarki, ita kuma ya kawo ma ta hanyar hutu, wannan ciwo na ta gwara mutuwa da jinyarsa, shiyasa akace kullum ka roƙo Allah ya rabaka da doguwar jinya". cewar Boɗejo. hawaye na bin kumatun Ilham ta ce,"amin". sannan ta karɓi plate ɗin alkubus da miyar taushe da Boɗejon ta miƙo ma ta. tana ci tana zubar hawaye na tsananin tausayin mahaifiyarta. **** bayan sati ɗaya Fillo ce zaune a parlo tana kallo, tv ɗin da tun da ta tare sai jiya da Bello ya shigo ya sa aka haɗa ma ta ita. kuma sai yanzu ta fara jin daɗin zaman tun da tana ɗebe ma ta kewa, jiya ma tana kallon tayi bacci ba ta sani ba sai wajen 12 ta farka ta kashe tv ɗin ta haye sama, tsoron ma da take ji ya fara raguwa, da zarar ta kunna karatun qur'ani shikenan sai tayi baccinta lafiya lau. cikin sati ɗayan nan banda zaman kaɗaici babu abin da ta ke yi, kewar Umminta da Kaka kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, kullum sai taji kamar ta fita ta roƙi me gadi ya ara ma ta wayarsa, sai kuma ta tuna idan ta karɓo babu lambar wanda ta riƙe akanta, lambar Yami ma ta mance balle ta ce zata kira Maijidda ta kawo ma ta lambar Kaka, ita kanta Maijiddar kewarta take yi. babu wani wanda yake leƙo ma ta, ko da ga gidansu Turaki kuwa, tayi tsammanin ganin su Maama ma amma shiru ba su babu su Zaytun, hatta shi Turaki rabonta da ganin inuwarsa ma tun washegari, sau tari tana jin dawowarsa da daddare in an zuge gate ba ta ko leƙan windon balle ta kalli takaici, dan Allah ɗaya ya san adadin haushinsa da take ji a yanzu, kwatakwata bata ƙaunar ma wani abu da zai haɗata da shi, lokaci kawai take jira ta bar masa gidansa. kullum iyakarta da ga sallah sai bacci sai cin abinci haka take fama, fatar nan tata kam ta ƙara yin fresh saboda hutu, kuma duk ta gaji da hakan, sai uwar rama da take yi saboda damuwa da ta sakawa ranta da kuma rashin cin wadataccen abinci. ta ɗau remote ta sauya tasha zuwa africa tv, daidai lokacin da aka hasko marigayi Shaik Albani Zariya yana amsa tambayar wata mata da ta aiko akan bambancin iddah da kuma Takaba, hakan yasa ta dire remote ta tattara hankalinta gaba ɗaya tana sauraron bayaninsa. _"Takaba shi ne zaman da mace za tayi na tsawon wata 4 da kwana 10 bayan mutuwar mijinta. Ita kuma Iddah ita ce zaman da mace za ta yi idan mijinta ya saketa har sai ta yi jinin al'ada sau 3. Iddah mace za ta iya yin kwalliya da sauransu, amma ba zata iya yin maganar aure da wani ba har ta fita daga iddar. Ita kuma takaba mace ba zata iya yin kwalliya ba amma za ta iya yin tsafta, banda sanya duk kayan da suke ɗauke da ado na kwalliya. Amma dukkanninsu idan mace tana da ciki to dole ne idan aka haife cikin nan to iddar ko takabar ta yanke, Idan ma aka saketa yau kuma ta haihu Yau to iddar ta ƙare. Idan ma mijinta ya mutu a yau kuma ta haihu anjima to ta gama takaba. sai dai kuma idan akayi aure miji bai tare da mace ba, ko ya tare da ita amma bai taɓa kusantarta ba, to ba zata yi masa iddah ba duk tsayin lokacin kuwa da suka ɗauka tare, da zarar ya bayyana sakin tana iya yin aurenta ko da ace a daidai wannan gaɓar wani ya zo ya bayyana cewar zai aureta to ana iya ɗaura aurensu anan take insha'Allahu...wannan shi ne taƙaitaccen ba yani a game da tambayar da kika yi, wallahu ta'Ala a'alam"._ gama bayanin nasa yay haɗe da taruwar ruwan hawaye a idon Fillo, a hankali kuma sai taji hawayen su na sakkowa saman kuncinta, ta rumtse ido tare da cije leɓenta na ƙasa ta kifa kanta akan cinyarta, haka ɗaya ba tare da sanin dalili ba taji tana so tayi kuka, irin kukan da zata yi ya isheta, taji zuciyarta na matsewa da wani irin zafi tamkar ana hura wuta, ciwon kan da ta kwana biyu ba ta yi ba ta ziyarce ta, ta kasa danne kukan da ke neman ƴancin fita a bakinta kawai sai ta sake shi, ta miƙe da sauri ta haye upstairs tana jin wani irin wahaltaccen yanayi a tare da ita, tana shiga ɗaki ta faɗa kan gado ruff da ciki, kuka sosai take yi ta rasa ta ɓangaren da zata lallashi kanta. sai da ta kusa rabin awa tana kukan sannan ta daina, ai kuwa kanta yayi ma ta wani uban nauyi kamar zai faɗo, ta miƙe ta shiga toilet ta yi wanka a daddafe ta fito, ta buɗe wadrobe ta ɗauko doguwar riga ta atamfa ta saka, ta taka stool ta ɗaga ƙasan trolly ta ɗauko takardar sakin, ta zura hijab ɗinta tare da buɗe drower ta ɗebi kuɗi ta saka a jaka, abu biyun nan su kawai take buƙatar tafiya da su, takardar sakinta da zata zama shaida da kuma kuɗin da za su kaita Taraba. ta zauna bakin gado zuciyarta na karanto ma ta kuskurenta, ita ai duk ɗan guntun ilimin da take da shi ce take sai tayi masa iddah shiyasa har ta yarda ta zo gidansa, ashe yanzu ita kwata-kwata ma ba ta da wata alaƙa da shi, zaman haukarta na rashin iliminta kawai take yi. abun da ta kasa ganewa shi ne; me yasa ta damu da sakin nan?, me ya sa take jin kamar rabuwa da cikin gidan nan tamkar rabuwa da wani ɓangare ne na jikinta?, abu ɗaya kawai ta san yana rubuce a tafin hannunta, babu wani abu da zai hanata barin gidan nan ayau tun da har ba ta da wata alaƙa da shi, za ta tafi tabarsa nisan tafiya kuwa ta har mutuwa. sabbin hawaye suka shiga sauko ma ta, taji kamar hayaniya da ga downstairs, bata ta shi ba taci gaba da zamanta tana tunanin ta yanda za'ai ta tafi, ita ba sanin hanya tayi ba, ita ba lambar wayar kowa ba, ba ta taɓa sanin ina ne tasha ba balle ta kai kanta, anya ba zata nemi taimakon Baba me gadi ba?, dan ba zata iya zuwa gidan su Turaki ba. zuciyarta ta yarje ma ta hakan, dan haka ta miƙe tana ƙara goge hawayen fuskarta ta fita da ga ɗakin tana jin wani baƙin ɗaci a zuciyarta, tana fara sakkowa da ga steps ta hangi Nihal da wasu yara da za su yi sa'anni da ita, kuma kallo ɗaya ta yi musu ta tuna maganar Bello da yayi mata jiya cewar za'a kawo ma ta ƴan aiki, tai saurin komawa yanda ba za su jita ba, ta cire hijab ɗin jikinta ta ajiye tai saurin shiga toilet ta wanke fuskarta da sabulu, tana fitowa taga Nihal a tsaye tana ƙarewa ɗakin kallo. tayi ƙarfin halin ƙaƙalo murmushi kamar yanda Nihal ɗin ke yi ma ta. cike da zolaya Nihal ta ce da ita,"kai Antynmu ai sai muyi zaton ko honey moon ku ka wuce babu sallama, 1week ba ku leƙa mu ba". Fillo tai murmushin yaƙe ta tsuguna tana gaida ita. Nihal ta ce,"kar ki ban kunya don Allah tashi mana, ni ya kamata na tsuguna miki yanzu ai ba ke ba, matar babbar Yaya". Fillo taja yatsun hannunta ta ce,"Adda Nihal ina Maama da Mum?". ta ce,"su na kan hanyar zuwa ai, ashe ba ki da lafiya shi Hammah kwata-kwata bai faɗa ba sai yau. ya sauƙin jikin naki?". Fillo ta ɗago tana kallonta sai kuma ta ce,"naji sauƙi ai". Nihal ta ce,"kinga yanda ki ka rame kuwa". buɗar bakin Fillo zata yi magana suka ji shigowar mutum, Nihal ta gaida Turaki tana yi masa sannu da zuwa, bai ko amsa ma ta ba yayi ma ta nuni da hanyar fita ta zo ta wuce tana ɓata fuska, tun da Baffa yay masa gate da gida shikenan ya sauya musu ko magana ba yay musu up to now, sai kace su ne suka hana shi zuwa gidan. sai da Nihal ta fita tukunna Fillo ta ɗago ta yi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, yana tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata ido, kamar me son karanto wani abu a tare da ita, jin idonsa a kanta yasa ta haɗe gira sama da ƙasa ta juya masa baya. wucewar daƙiƙa biyu wayarsa da ke aljihu ta shiga ringing, ya sa hannu ya ɗauko yana picking tare da cewa Hajiya Madina,"Maama ba ta fito ba ne idan ta fito zan kira ki". muryar Hajiya Madina na bayyana damuwar rashin lafiyar da yace musu Fillo na yi ta ce,"to da ta fito ka kirani kaji ko?, nima gamu nan muna kan hanyar dawowa na tsaya her excellency ne za ta shiga office ta fito, ka dai ce kunje hospital ko?". ya shafo wuyansa ya ce,"ehh Maama ta ji ma fa sauƙi, na faɗa miki ma zatona ko Baffa ya dawo ne shiyasa bamu zo ba". ba ta ce da shi komai ba ta kashe wayar tana shaida Mum batun rashin lafiyar. "da me babban suna mu ka gama waya, ashe rashin zuwan na su ba ta da lafiya ne, ni dama dai ince cin amarci ai ba zai hana su zuwa su gaisar da mu ba muna kusa da su. yanzu kawai mu tafi gidan na su ko? duk da naji yace ai jikin da sauƙi". Mum ta ce,"ni kam ba zan iya zuwa gidan su ba, tun da taji sauƙi shikenan, ki kwantar da hankalinki please". Maama ta ce,"ni kam gaskiya sai naje na dubo su hankalina zai kwanta, sati guda ban saka me babban suna a idona ba". Fillo na murguɗe murguɗe da harare harare ta nufi hanyar toilet za ta shiga, yay amfani da sautin muryarsa wajen buga mata tsawa akan ta tsaya, duk ta yanda taso ta dake ta nuna rashin firgitarta sai da ta tsorata ta ƙame a wuri ɗaya jikinta na kyarma. ya ƙarasa shigowa ciki ya ja stool ya zauna akai, ya saita kira akan lambar Maama, sannan ya ɗago yana kallonta yaga har yanzu rawar jiki kawai take kamar me jin sanyi tama ƙi buɗe idanuwanta, hawaye na sauka a kuncinta. yay tsaki na ban haushi da takaici, ya miƙa hannunsa ya fizgota sai gata ta wancakalo bakin gado kamar sandar da aka janyo, abunka da mara ƙiba sam sam. "buɗe idonki". yanda yayi amfani da sautin muryarsa abin ya bata tsoro, kuma da ta buɗe ido ta kalle shi tsoron sai ya ƙaru fiye da misali, dan rikiɗewa ya ke yana komawa kamar ba mutum ba. muryarta na breaking ta ce,"tafiya zan yi". ya danna kiran Maama ya jefa mata wayar a jiki, niyyarta ta miƙe wayar ta tarwatse a ƙasa, amma sai taji Maama na magana, sannan ne ta ɗauka tana magana ta yanda Maama ba zata fahimci kukan da take yi ba a muryarta. *comment, share and vote.* [9/5, 19:45] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *48* "Daughter nah". Hajiya Madina ta kirata da sabon sunan da ta raɗa ma ta tun a ranar da aka kawo musu ita. "na'am Maama". with much care Maama ta ce mata,"ya jikin naki?, da sauƙi ko kuwa?, kina shan magani?, yanzu ya kike ji?, mene yake ya damunki?". waɗannann tarin tambayoyin yasa ta kallon Turaki ta gefen ido, idonsa na kan ɗaya wayar da ke hannunsa, fuskarsa kamar baƙin hadarin da ya haɗo, ta rufe ido ta ce,"Maama lafiyata lau, shi ne kawai yace miki ban da lafiya". ta faɗa kamar zata sa kuka. furucin nata yasa Hajiya Madina murmushi, ko ba komai ta san da gaske jikin nata da sauƙi kamar yan da yace, ta furta alhamdullahi sannan ta ƙara cewa,"kina cin abinci sosai ko?". ta ce,"ina ci". "to Allah ya ba ki lafiya Daughter, Allah ya sa kaffara, ki daure ki dinƙa shan magani kinji, becx bana so na ji wani abu yana taɓa min ke, zan zo anjima na duba ku, Allah ya yi muku albarka". a hankali Fillo ta ce,"Maama Ummina fa?". ta faɗa muryarta na ɓallewa da kuka. zaton Hajiya Madina ko tana so ta ganta hakan yasa tace mata,"za ki je kiga Ummin ki very soon, ni da kaina ma zan kai ki". kamar ta faɗawa Maama komai sai kuma tayi shiru, ita tambayar da tayi saboda Maama ta ce zata haɗa su a waya ne, in yaso sai tace da Ummi azo a ɗauketa dan ba ta fatan ta ƙara kwana acikin gidan da ba zaman aure take yi ba. ta sauke wayar da ga kunnenta bayan Hajiya Madina ta kashe, ta waiga tana kallon Turaki ta ce,"ka ba ni lambar Kaka ko Ummi please". maganar tata sai ya zama tamkar da dutse tayi, yay banza da ita ban da ma waya da ya kara a kunnensa yana amsa sallama, bata ɗauke idonta akansa ba taci gaba da kallonsa, hotunan kasadar da ta dinƙa yi wurin ceto rayuwarsa yana haska mata a ido, sai a yanzu ne ta yarda da cewa ɗan adam butulu ne, ita ba wai don ya saketa ba, a'a irin wulaƙanci ma da yake mata na nuna da ita da banza da wofi ɗaya, kuma ƙila duk yana mata haka ne saboda sanin mahaifinta da yay, da ma sai da ta faɗawa Ummi cewa wallahi bai aureta ba saboda abubuwan da ya faɗa sai don ya wulaƙantata, a lokacin Ummin ba ta yarda da ita ba hasalima faɗa suka haɗu suka dinƙa yi ma ta ita da Kaka, but yanzu ta san dole za su yarda da abin da ta ce, kuma ko ba komai ta san Turaki zai ga ishara akan aurenta da yay ba don komai ba sai domin ya tozartata. maganar da yake yi a cikin wayar ta shiga kunnenta. "no ba haka ba ne Faruq, bana fatan na ƙara maimaita kuskure, this time around ba zan yi gaban kaina ba, ba zan ƙara yiwa kaina aure ba sai da sanin iyayena, kai ba ma aure ba kawai, dukka wani abu na rayuwata, gaban kaina da nayi banji da daɗi ba, ni ɗaya na san halin da na shiga, but da na rabu da kowacce yanzu komai ya zamar min normal, ina cikin farin ciki da kwanciyar hankali". _na rabu da kowacce._ kalmar ta maimaitu a cikin kan Fillo, kenan har Ilham ma ya rabu da ita?, ita kuma me tayi masa?, wai wanne irin mutum ne shi ɗin?, kenan shi ma yana sahun mazan da basa mutunta aure, burinsu su aura su saka?. ta yiwa kanta tambayar da zuciyarta ke ba ta amsa, tunaninta ya tsaya cak san da taji yana cewa,"sunanta Aisha ƴar sarkin kano ce, insha'Allahu gobe nake so naje na gana da iyayenta, zan fara neman izininsu before na kai maganar gaban su Baffa, ita ba ni da matsala da ita becx ita ta fara cewa tana so na, so pray for me kar na sami matsala da Baffa, dan nima ina son yarinyar sosai...". cak maganarsa ta katse dalilin ƙarar fashewar abu da yaji, yay saurin ɗago ido yana kallon wurin da Fillo ke tsaye tana ƙoƙarin saka hijab, sai kuma idonsa ya kai kan wayarsa da ta tawarwatse a ƙasa, ta yi ragaga tamkar tayar mota ce ta bi ta kanta. bai san lokacin da ya miƙe ba yana bin ƙasan tiles ɗin da kallo, yana kallon kowanne pieces na glass ɗin wayar da ya barbaje. Muhimman abubuwansa da suke kan wayar!, hakan ya gimla a zuciyarsa, lokaci ɗaya ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, ya dunƙule hannu ya ɗago kansa a fusace yana kallonta wacce ke shirin ficewa, da zafin nama ya janyo hijab ɗin nata ya dawo da ita gabansa yana cewa,"are you mad?". ya ɗaga hannu sama a zafafe zai sauke mata kyawawan mari tayi saurin yin ƙasa da fuskarta, take jinkinta ya ɗauki rawa saboda yacce take jin hucinsa na cika ɗakin. babu shiri taja da ba ya tana rarraba ido, sai da ta kai jikin bango tukunna ta sami damar ɗago da kai tana kallonsa, tayi mugun tsorata da yanda ƙwayar idonsa ta sauya kala, da yanda taga kamar yana huruwa yana sacewa, tsananin tsoron abun da zai iya aikata ma ta yasa ta ɓallewa da kuka tana faɗin,"to ai bana sa ne". ta faɗi hakan dan ba ta tunanin kalmar haƙuri za ta iya fitowa da ga bakinta zuwa gare shi. Turaki ya rumtse idonsa gam for few minutes yana so ya taushi zuciyarsa, ya buɗe ido yana furzar da iska daga bakinsa, ya watsa mata wani mugun kallon da ya ƙara hargitsata, cikin ɗagowar murya ya ce,"zo ki ɗauko ki ban". hakan bai sa ta ko motsa da ga in da take ba, illa ma haɗe rai da tayi tana juyar da kanta gefe guda, Turaki ya daɗa fusata yay taku ɗaya ya isa gabanta, ya shaƙi wuyanta ya manna kanta da bango. ya zaro mata idanuwansa waje ya ce,"ke wacce kalar halitta ce ne da babu ƙwalƙwalwa a jikinki?". ya faɗa da wani amon sauti da ba nasa ba, zai iya rantsewa tun da yake ba'a taɓa ɓata masa rai ba irin yau, fashewar wayar ba shi ne damuwarsa ba, crucial documents na office da yay saving a phone storage, jiya ya gama ɓata lokaci wajen saving wani document na contract ɗin da suka karɓa, Bello kawai yake jira ya zo ya tura masa, yanzu shikenan ta jiƙa masa aiki, kwana yayi yana typing bai ko runtsa ba, haka ya dinƙa aikin babu daɗi saboda ya baro laptop ɗinsa a office. ya cije leɓensa na ƙasa yasa ƙafa zai fyaɗeta ta kife a ƙasa sai kuma ya fasa, ya buga mata tsawa da cewa,"wuce ki ɗauko ki ban". tuntuni ta daina tsoronsa, sai dai ta rasa dalilin da yasa ta kasa daina jin tsoron tsawarsa ba, tana tafe yana bin ta a baya. ta durƙusa sai kyarmar jiki takeyi ta ɗauko wayar ta ba shi, yasa handky ya karɓa gudun kar glass ya soke shi, ta yi tsaye tana zumɓura baki, ta ƙara jin saukar tsawar muryarsa da cewa,"tattaro glass ɗin". zata wuce ɗauko tsintsiya ya fincikota. "hannu za ki saka". ta kallesa taga babu alamar imani tare da shi hakan ya sa ba shiri ta durƙusa ta shiga tattara kwalban, idonsa ƙyam akan hannunta da ke zubar da jini dan tun a ɗauko wayar kwalabar ta soketa. sai da ta gama tattarawa ya wurga ma ta ɗayan handky ɗin, ta ɗauka ta zuba glass ɗin a ciki ta miƙo masa, ya karɓa yana nunata da yatsa cikin kakkausar muryar da ke shaida kashedi me girma ya ce,"kar ki kuskura, kar kiyi saken da zan dawo cikin gidana na sameki, in har kuwa na dawo na tadda ke ki tabbatar da cewa alƙiyamarki ta tsaya, dan sai kin ƙwammace ba ki taɓa sanin zuri'ar Alƙali ba balle kuma ni, and ki san da cewa sai kin biya ni wayata". yana faɗar haka ya fice fuuu ya bar ɗakin, ta bi bayansa da kallo kafin ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, babu abin da take ji a zuciyarta sama da danasanin saninsa, sai da ta daɗe a haka sannan ta miƙe tunawa da kashedin da yayi mata, ta ɗauki jakarta ta fita daga ɗakin tana jin zuciyarta kamar zata buga, jiri ne ma yake neman zubar da ita dan da ƙyar idanuwanta suke kallon gabanta, tana sakkowa da ga benen ta faɗi kanta ya ƙumu da ƙarfen benen, cikin ƙarfin hali ta tashi tana daddafa bango ta iso har ƙofa ta buɗe. daidai da zuge glass ɗin ƙofar da Hajiya Madina tayi, karaf idonta ya fara sauka akan hannun Fillo da ke zubar da jini, ta zaro ido waje tana ambaton,"subhanallahi". sai kuma ta kalli Fillon taga tana hawaye ga shi kamar ba ta cikin hayyacinta, tai saurin kamota ganin tana neman faɗuwa. "Daughter lafiya?, wannan jinin fa da ga ina?" Fillo ba ta iya ba ta amsa ba, haka ba ta iya kallonta ba, Hajiya Madina ta riƙeta suka yo waje tana cewa da Nihal,"ko ma ki tayar da mota". sannan ta ƙara cewa da Fillo,"ina me babban sunan?". sai a sannan ta iya buɗe baki tace,"ya fita". san da motar Maama ta fita da ga gidan Baba me gadi ya girgiza kansa cike da tausayin Fillo, yarinya ƙarama ana neman a ɗora ma ta hawan jini, tun ranar da aka kawota ya fuskanci ba auren soyayya akayi ba, dan shi dai bai taɓa ganin Turakin ya shiga part ɗin ba sai ɗazu da ya fito a fusace kamar macijin da aka dannewa kai. direct asibiti mafi kusa suka wuce, tun tahowarsu Maama da Nihal ke jera ma ta sannu, su na zuwa cikin gaggawa Dr yay ma ta treatment ɗin wajen, ya cicciro pieces na glass yafi biyar a tafin hannunta, aikuwa tasha azaba dan jini kamar ana tatsarsa hannun duk ya caɓe, akai ma ta allurai, Nihal taje pharmacy ta karɓo maganunguna, lokacin da ta dawo an naɗe hannun Fillon da uban bandage. daga fitowarsu zuwa yanzu kuwa Maama ta kira wayar Turaki yafi sau bakwai duk ba ta shiga, kuma duka lines ɗin nasa, hankalinta duk a tashe yake da ciwon Fillon, ta kira wayar Mum ta tambaya ko Turaki ya zo gida ta ce ma ta a'a, Bello ma yace ba sa tare. kan hanyarsu ta dawowa Maama ta matsa mata da tambaya akan yacca akayi taji ciwon, ta kasa haɗa ƙaryar da zata faɗawa Maama ɗin, tai shiru ita dai sai rera kuka takeyi a hankali, har sai da taji ɓacin rai a muryar Maama tukunna ta ce,"wayarsa na fasa masa ban sani ba". Maama na kallonta ido buɗe ta ce,"fasa waya kuma sai kiji ciwo haka?". tayi shiru tana daɗa yin ƙasa da kanta, Maama ta dinƙa kallonta tana so ta nazarci yanayinta, uwar ramar kaɗai da yarinyar tayi ya isa ya shaida maka hankalinta ba'a kwance yake ba sam, dole akwai wata matsalar a ƙasa, dole da akwai abin da yake faruwa wanda basu san da shi ba, tun da me gadi yace ma ta Turaki ya fita babu jimawa ta san akwai matsalar da ke faruwa musamman da taga Fillo a wannan yanayin, babu tantama saɓani suka samu duba da yanda duk Fillon take a tsorace. _me ce matsalar?._ tambayar da ta yiwa kanta kenan, sai dai babu amsarta. hakan ya sa ta kamo hannun Fillo tana kallonta ta ce,"ɗago ki kalle ni a matsayin Umminki wacce ba za ki taɓa iya ɓoyewa damuwarki ba". idanuwanta suka kawo sabon ruwa sanda ƙwayar idonta ke shiga cikin ta Maaman, tausayin Maaman shi ya fara kamata ganin duk ta damu, kafin girma da kwarjinin Maaman su mamayeta gaba ɗaya, ba zata iya yi ma ta ƙarya ba sam saboda ta kare kanta ko kuma ta kare shi, ta sauke kanta ƙasa muryarya a hankali ta ce,"da wayar ta fashe ne shi ne ransa ya ɓaci yace sai na kwashe glass ɗin da hannuna". da tsananin mamaki Maama ta ce,"me babban sunan da kansa?, ya ce ki kwashe glass da hannunki?, cikin hankalinsa yake kuwa?". wannan furucin kaɗai ya shaidawa Fillo ran Maama ya ɓaci sosai. Maaman tai shiru ba ta ƙara magana ba sai faman jijjiga kai da takeyi, idanunta na kan waya tana ƙara trying lamar Turaki, cikin sa'a kuwa yanzu ta shiga sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, ta ƙara kira nan ma bai ɗaga ba, sai da ta kira har sau uku sannan ta haƙura ta jefa wayar a jaka, cikin zuciyarta sai jinjina abin da Turaki ya aikata takeyi, ko da yake da ma ba'a sanin wani mugun halin namijin sai bayan ya yi aure. Fillo dai idonta na kan hanya, tunaninta ɗaya ta yanda zata faɗawa Hajiya Madina a sauketa a hanya, ta ga motar ta tsaya bakin wani islamic chemist, Maama ta buɗe ta fita ba tare da tace da su komai ba, ta bi ta da kallo ta glass har ta shiga kantin. a lokacin ta buɗi baki ta cewa da Nihal,"Adda don Allah ina ne hanyar tashar barin gari?". Nihal ta waigo tana kallonta ta ce,"me za kiyi acan?". tai shiru ba ta ce komai ba, lokacin Maama ta buɗe motar ta shigo, sanda ta rufo ƙofa Nihal ta ce ma ta,"Maama wai tambayar tashar da za'a bar gari take yi". Maama ta waiga taita kallon Fillo, wacce idonta ke kan hannun ciwon nata, tana nufin gidan su zata tafi kenan?, ta san ba komai bane ke damunta fa ce yarinta, bata ce komai ba tayi ƙwafa me ƙarfin gaske tana ɓallo maganin da ta siyo a islamic chemist ta bawa Fillo. Nihal ta kashe sautin waƙar da ke tashi, saboda ta san idan ran Maama ya ɓaci ba ta son jin komai na shiga cikin kunnenta. bayan doguwar tafiya Fillo taji motar ta tsaya, ta ɗago kanta tana kallon gate ɗin gidan, gabanta taji ya faɗi hakan yasa babu shiri ta juya tana kallon gefen da Maama take tace,"Maama yace na bar masa gida". "ki bar masa gida?". ta ɗaga kanta tabbacin hakan. "saboda kawai kin fasa masa shegiya waya ya buɗi baki ya ce ki bar masa gida?". sai kuma ta bar kallon Fillo ta koma kan Nihal ta ce,"shiga ciki ki gano min ko ya dawo". a tsure Fillo ta ce,"Maama ai...". kuka ya kubce ma ta ta kasa cewa komai. Maama na kallonta ta ce,"ai me?". ta buɗe baki tana jin kamar yawun bakinta yayi kaɗan su yi maganar da zata yi, tace,"he divorce me". da wani mugun shock Maama ta ce,"what?, divorce!, ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ya sake ki fa kika ce?". tayi maganar tana jin kanta na mugun sara ma ta, tai saurin dafe shi tana rumtse ido ta jinginar da kanta jikin kujera. Fillo ta fashe da kuka, Nihal ta shigo motar tana cewa,"bai dawo ba Maam...". maganartata ta tsinke jiyo numfashin Maama na fita da ƙyar, a ruɗe ta ce,"innalillahi, Maama". ta faɗa tana fitowa ta zagayo ta buɗe side ɗin da take, "Maama". ta faɗa tana kamota. Hajiya Madina na dafe da ƙirjinta da ƙyar ta iya cewa,"mu je gida da sauri". tun kamin su ƙarasa gidan Nihal ta kira Mum a waya ta sanar ma ta cewa BP ɗin Maama ya tashi, kafin su ƙaraso tana tsaye a compoud hankalinta a tashe sai safa da marwa takeyi. ko parking Nihal ba ta ƙarasa ba Mum ta buɗe, ita ta kama Hajiya Madina suka wuce, ko lura da Fillo ma bata yi ba, sai bayan ta kai Hajiya Madina bedroom ne ma taji tana ce mata,"ina amanar da mu ka karɓa?" Mum ta ce,"wacce amana?". Maama na magana da ƙyar ta ce,"Fullo". sai kuma muryarta ta karye tana cewa,"your excellency me babban suna ya cuce mu, sati ɗaya da aure ya saki yarinyar mutane". Mum ta zabga wani salati tana waro ido waje ta kalli Nihal da Fillo da ke shigowa ɗakin. sannan kuma ta juya tana ƙara kallon Maama wacca taga kamar ba'a hayyacinta tayi maganar ba, ta ce,"wai saki kamar ya ya dai Madam?, saki na aure? ko wanne kalar saki ban gane ba?". cikin ƙarfin hali na irin zafin da Maama ke ji a ƙirjinta ta ce,"divorce dai da kika sa ni, kawai saboda ta fasa masa waya bata sani ba, ki duba hannunta ma ki gani ciwon da yaji mata". farat ɗaya ran Mum ya kai ƙololuwar ɓacin da bai taɓa yi ba, ta ce,"ba shi da hankali ko kuwa shaye-shaye ya fara bamu sani ba?". ta kalli Nihal tace,"kirawo min shi dan ubansa". sannan ta kalli Fullo tace,"laifin me kika yi masa da har zai sake ki?". ta zube gwiwoyinta a ƙasa tace,"ai dama tuntuni na ya sake ni". Maama ba ta san lokacin da ta miƙe zaune ba tayi warkewar lokaci ɗaya, Mum ta nemi wuri ta zauna, a tare suka jefa mata tambayar,"wacce tuntunin Fullo?". "tun before na tare, na kasa faɗawa kowa ne...". kuka yaci ƙarfinta tayi shiru tana rumtse ido. Maama ta saki baki kamar yanda Mum tayi duk suka kasa cewa komai, wucewar daƙiƙu muryar Nihal ta kutsa cikin shirun na su da cewa,"Mum bai ɗaga ba". ba tare da tace ma ta komai ba ta miƙa ma ta hannu Nihal ta ɗora ma ta wayar, ta lalubo lambar Bello ta kira, bugu uku ya ɗaga, a fusace tace da shi,"da kai da shi kunci kutumar ubanku, kuna ina?". tayi tambayar a tsawace. zagin da tsawar suka daki kan Bello yayi zillo akan kujerar da yake, ya haɗiye yawu da ƙyar ya ce,"Mum". tai saurin katse shi,"zanci ubanka idan ka ƙara kiran sunana, na ce kuna ina?". cikin ƙinƙina Bello yace,"ni ina office shi kuma ban san inda yake ba". "ƙarya kake yi munafiki". yace,"wallahi Mum rabona da shi tun last week, ko haɗuwa bama yi a office". tayi shiru kafin tace,"to ka kira kirasa ka faɗa masa minti ashirin na ba shi yazo ya sameni". ta katse wayar, Nihal tayi saurin karɓa ganin tana ƙoƙarin jefar da ita a ƙasa. bayan minti biyu kiran Bello ya shigo, ganin Mum bata da niyyar ɗagawa Nihal ta ɗaga yace ma ta,"ki faɗawa Mum wallahi ina ta kiransa bai yi picking ba for morethan 4times, kuma ni ban san inda yake ba". Nihal ta faɗawa Mum, sai tace ta kira ma ta Khalil, yana ɗagawa Mum ta ce da shi,"ka kira min ɗan banzan Hamma'nku ka faɗa masa tun banyi masa baki ba ya sameni a gida cikin gaggawa". ba tare da jiran cewarsa ba ta kashe wayar. ɗaki dai yay shiru tamkar babu wata halitta acikinsa, ran kowa a cunkushe, zuciyoyin kowa da abunda take saƙawa. minti goma minti ashirin suka wuce, rabin awa ma haka, aka cika awa guda ma, duk su na zazzaune jungum jugum, Hajiya Madina ma ta kasa shan magungunan da aka ajiye mata. can suka ji buɗewar ƙofa an shigo, Zaytuna ta shigo tana ajiye jakarta, ta cire labcourt ɗin jikinta tana zazzare idanu wajen kallon kowa kafin ta buɗi baki tace,"Mum, Maama lafiya?". babu wanda ya kalleta balle ya amsa ma ta, sai tayi tsuru-tsuru ta kalli Nihal suka yi magana da ido ta nuna ma ta Fillo dake durƙushe a ƙasa. sai taja bakinta tayi shiru ta fasa sanar da saƙon Turaki da ya faɗa ma ta cewa tace da Mum yaje kano ne after magrib zai dawo, wayar da take kira ba ta ɗaguwa. shirun da yay yawa yasa Mum miƙewa ta fita, aka bar Maama da Fillo har sai da akayi sallar la'asar tukunna tace da ita ta tashi tayi sallah. gida dai sai yay ɗiff kamar gidan mutuwa, ran iyaye babu daɗi yara kuma duk sun shiga damuwa saboda yanayin da iyayensu suke ciki, bayan sallar magriba Hajiya Madina tana lazimi Turaki ya tura ƙofar ɗakinta, haka kawai yaji gabansa ya faɗi duk da bai san abun da ke faruwa ba, Hajiya Madina ta waigo dan ganin mai shigowa, tana ganinsa ta miƙe ba tare da ta shirya ba ta fuskance shi. murya a sama ta nuna masa hanyar fita ta ce,"fita, fitar min da ga ɗaki kafin na sa ƙafa na takeka in take banza". muryarta ta fita da tsananin ɓacin rai. yay tsuru tsuru ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga hannu ta wanka masa wari, ta shiga nuna shi da yatsa tana faman huci tace masa,"daga ranar yau zuwa ranar da za'a busa ƙaho babu ni babu kai, in har ka ƙara shiga sabgata tabbas hukuma ce zata rabani da kai, ma za juya ka bar min ɗaki". ganin ba zai fita ba ta rarumo ƙaramar kujerar da take zama zata buga masa, babu shiri ya juya cikin sauri ya fi ce. yana zuwa part ɗin Mum ya tarar da ita zaune a parlo ta zabga uban tagumi, zuciyarsa ta shiga lugude, ya tafi kamar munafiki ya tsuguna a gefen ƙafarta, bai san dai laifin da yay ba amma saƙon da Khalil ya ba shi ya san akwai laifin da ya aikata. muryarsa a hankali ya ce,"Mum lafiya?". ya tambayeta yana ƙoƙarin cire hannun da tayi tagumin da shi, sai dai tun kan ya kai ga taɓata ta make shi da mugun zafi. "matsa da ga kusa da ni". ta faɗa tana sauke masa rikitattun idanuwanta da ke nuna zallar ɓacin rai, nan da nan hankalinsa ya tashi ya shiga tambayar laifin da yayi. "wallahi tallahi idan har baka matsa daga kusa da ni ba ko me na ɗauka sai na buga maka in yaso ka mutu in huta da baƙin ciki da takaicin rashin dacen haihuwarka da nayi". ya buɗe baki ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana kallonta zai ƙara yin magana a mugun tsawace ta dakatar da shi,"na rantse da Allah ka ƙara min magana a wurin nan sai na fiddo maka da nonona ka biya ni wanda ka sha, banza mara mutunci shashasha butulu kawai wada bai saka halacci da halacci sai dai ya saka halacci da sharri, daga ranar yau ina me tabbatar maka da babu ni babu kai har abada kuwa". ta sauke yatsanta da ga kansa, ta ɗau wayar da ke kusa da ita ta kira Khalil, cikin mintina kaɗan sai ga shi ya shigo, tai masa nuni da kujera ya zauna a ɗarɗarce, ta ɗauki takarda da biron da ke kusa da ita ta wurgawa Turaki wanda ke dafe da kansa yana ta amabaton kalmar innalillahi a zuciya da fili, magana yake so yayi amma babu dama saboda rantsuwar da Mum tayi. "mu ba matsiyata ba ne, kai tsiya ta yiwa ƙatutu, Allah ya hore mana yay mana arziƙin da zamu iya siye duk abin da ka mallaka har kake taƙama da shi, ka rubuta kuɗin matsiyaciyar wayar da kashe hannun ƴar mutane saboda ita, ko nawa ne za'a biyaka dan kai ne faqararre". ta ƙyasta yatsunta biyu ta ce,"kuma ka sa ni, duk illar da hannun ƴar mutane yayi wallahi sai mun shiga kotu da kai". ganin zai yi magana ta kuma doka masa tsawa,"kuɗinka nace ka rubuta". yay taking deep breeth yana kulle idanuwansa yay rubutu ajikin takardar, da ido Mum taiwa Khalil nuni da ya karɓa, ya karɓa yana kallon abun da ya rubuta, Galaxy fold Z2 1.3ML tare da kuɗin gyara 700k. ya kalli Mum zai ma ta magana ta ce,"tura masa kayansa". Khalil ya ɗau wayarsa in few minutes ya turawa Turaki kuɗin, seconds kaɗan sai ga ƙarar shigowar alert a wayar Turaki. "Mum sun shiga". Khaleel ɗin ya faɗa yana dubanta. ba tare da ta kalle shi ba tace,"ka kira min Madam". ya tashi ya fita, babu jimawa sai ga Hajiya Madina ta shigo fuskarta sam babu annuri babu walwala, ta tsaya cak da ga baya tana cewa da Mum,"ya za'ai ki kirani alhalin wannan ɗan banzan yaron yana zaune anan, ko kaɗan yanzu bana son ganinsa, zan dawo in sameki after ya fita". ta faɗa tana juyawa Mum ta dakatar da ita da cewa,"so nake ki zame min shaida dalilin da yasa na kiraki kenan". hakan yasa Maama dawowa tazo ta nemi kujera ta zauna, ta juyar da fuska yacca ko kaɗan ba zata fuskanci Turaki ba. Mum tace,"ko bayan raina ban amince ba wannan ɗan banzan yaron yay aure, ina so ki zamar min shaida". da sauri Turaki ya ɗago ido yana dubanta, me ya yi zafi shi ba wuta ba?, laifin me ya yi har haka?, yaji duniyar gaba ɗaya tayi masa zafi kansa na neman tarwatsewa, da ƙyar ya iya tattaro yawun bakinsa ya ce,"Mum me yayi zafi haka?, wanne irin laifi na aikata muku?, idan abin da naiwa ƴarku ne na roƙeku don Allah kuyi haƙuri ni kaina na san nayi kus....". maganar tasa ta yanke lokacin da yaji saukar jotter da biro a fuskarsa. ya kalla Maama da ke kallonsa da tsananin ɓacin rai tace da shi,"ka rubuto min sauran sakinta shi ne zaka tabbatar min da kai isashshe ne, dan ba zan karɓi saki ɗaya ba domin kuwa Fillo ta gama aurenka har a naɗe duniya". ya kulle ido yana sauke numfashi, sannan ya buɗe yace,"Maama ce muku tayi na saketa?". "ba ka saketa ɗin ba ne?". ya shiga girgiza kansa yana faɗin,"ni ban saketa ba Maama, idan ma haka ta faɗa muku to ƙarya take yi". Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifce, kafin tace,"kai ko dai kayi hauka ne?, ko kuma shaye-shaye ka ke yi a ɓoye?". ya ce,"Allah ni Maama ban san da wani batun saki ba a tsakaninmu, sai dai idan ita take buƙatar hakan shiyasa ta faɗa". Mum na ta kallonsa ta kasa cewa komai dan kallon typical mahaukaci take yi masa, Hajiya Madina ta kira Zaytuna a waya ta ce taje part ɗinta ta ta zo mata da Fillo. wucewar minti uku sai gasu tare, Fillo ta rakuɓe waje ɗaya tana rarraba idanu akan carpet, Turaki ya dinƙa kallonta yana ganin yanda fuskarta tayi jawur, da kuma uban bandage ɗin da ke hannunta. Mum tace da ita,"karki ji tsoronsa ki saɓa shari'ar musulunci, faɗi ya sakeki ko bai sakeki ba?". cikin dusashewar muryar kuka ta ce,"ya sakeni". Maama ta ɗauki remote a kusa da ita ta jefawa Turaki sai ga shi a goshinsa, ya dafe wajen da lokaci ɗaya yayi malolo yana,"shhhh, Maama ni wallahi ban saketa ba ƙarya take yi". Fullo ta ɗago ido ta kalle shi ta ce,"wallahi fa kake cewa?". yanda tayi maganar dariya ta kusa fito masa amma sai ya dake ya zabga mata uwar harara ta yanda su Maama ba su lura ba, itama ta murguɗa masa baki tare da ɗauke idonta akansa ta kalli Mum tace,"tun a ranar da muka je asibiti duba shi ya sakeni, ni kuma na kasa faɗawa kowa,  shi ne yau yace in dai ban bar masa gida ba sai na ƙwammace da ban taɓa saninsa ba har ma da ku". ya kalli su Mum da duk idanuwansu ke kansa, da sauri ya ce,"Allah ban saketa ba". sai kuma ya juya ya kalli Fullon ya ce,"ni da bakina na furta miki hakan?". ta harare shi tana fito da ɗayan hannunta da ga hijabi ta miƙawa Maama takardar hannunta. ganin takardar idanuwansa suka fito waje da sauri ya kai hannu zai ƙwace a harzuƙe Mum tasa masa ƙafa ta hamɓarar da shi gefe. ya ɗago daga kifewar da yay yana ɗora hannu aka yana ambaton innalillahi da ƙarfi har sai da kowa ya kalle shi. sanda Maama ta gama karanta takardar sai ta kalli Mum, ta miƙa ma ta Mum ta kau da kai tana girgiza kanta alamar ba zata karɓa ba. Maama ta ce ma ta,"dan Allah ki karɓa your excellency, zuciyata zata fashe". Mum ta juyo da sauri ta karɓa, ta kifar da takardar a cinyarta da ƙyar ta yarda da roƙon Maama ta karanta. ta kalli Fullo a sanda ta gama karantawar tace,"yaushe ya baki wannan takardar?". ta tsagaita kukanta ta ce,"ranar da muka je asibiti duba shi". Mum ta ƙara cewa,"ruwan hawayenki ya wanke wajen adadin sakin, nawa ya rubuta?". furucin Mum ɗin yasa idanuwan Turaki suka ƙawalalo waje fiye da ɗazu, ƙirjinsa ya ce taratsatsa. Fullo ta buɗe baki wani sabon kukan na tahowa tace,"ai ban karanta ba". Mum ta miƙa mata takardar tana cewa,"to karɓi". Fullo ta karɓi takardar zata cusa a hijab Mum tace,"karantawa za ki yi ai, idan ba ki karanta ba sakin ai bai tabbata akanki ba, ki karanta sai ki nuna masa kuskurensa ki ɗau duk kalar matakin da kika ga ya dace da shi". tana gama faɗa ta miƙe ta bar wajen, Maama ma ta fi ce, Zaytun ta haye Uptairs tabi bayan Mum, aka bar Fillo da Turaki kawai, ta ɗago kumburarrun idanuwanta ta kalle shi taga fuskarsa kamar baƙin hadari, hawaye na sakko mata ta ɗora ido akan takardar, sai taji fargabar yau tafi ta ko yaushe, bata san me yasa ba ko kaɗan bata ƙaunar adadin sakin da yay mata, sai dai kuma a sanda ta shiga karanta rubutun da ke ji sai taga saɓanin abin da zuciyarta ta faɗa mata tun ranar da ya bata takardar, idanuwanta suka karanta abin da yake daban da wanda take ta haskowa yana rubuce a jikin takardar. wannan wani rubutu ne na daban, rubutun da ko kusa bai da alaƙa da abin da sakin da ta gama yankewa kanta anyi mata, rubutu ne take kallonsa da handwriting ɗin da ya burgeta, haka kuma taji kalaman da ke jiki na tafiya su na haɗewa da jinin jikinta, taji tana sha'awar da a karanta ma ta su a kunnenta. ta karanta sau ɗaya ta kuma gane ma'anar but haka kawai sai taji tana ƙara buƙatar ta ƙara karantawa. _my life depends only on you, i love you Fulani Nah, i love you up to the square of infinity, i promise you that i will take care of you morethan i will take care of my self, trust me when i say i can't do without you,  Fulani Nah love me even just a bit._ ta rufe ido a sanda ta gama karantawa, taji bugun zuciyarta na sauyawa zuwa wani yanayi da bata taɓa riskar kanta a ciki ba a dai ga me da Turaki, ta sauke numfashi ta buɗe idon tana sauke akan Turaki. tuni ya miƙe tsaye hannayensa na zube cikin aljihu, ta bi shi da kallo sanda ya wuce ta gabanta, sai da yaje bakin ƙofa sannan ya dakata ya juyo yana kallonta rai a haɗe murya a tamke ya ce,"kin taso ko kuwa". ta ɗauke idonta da ga kansa ta mayar gefe, ya ƙara cewa,"ba za ki taso ba". ta kumbura baki ta ce,"ai kace kar na koma maka gida". Turaki ya saki baki yana kallonta, zai sake magana sai ga Mum nan ta sakko, tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta ta isa kujera ta ɗauki wayarta, har ta juya sai kuma ta waigo ta kalli Fillo dake zaune ta ce,"tashi ki bi mijinki". Fullo ta miƙe ta bi bayansa lokacin har ya kai bakin mota, ta buɗe baya ta shiga, ya kalleta ta mirrow ya ce,"do i look like your driver?". ta hankaɗo laɓɓa gaba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana shafa bandage ɗin hannunta, tsawar duniya ta dawo gaba tayi biris da shi kamar ba wannan Turakin da take tsoro ba, yay ƙwafa yaja motar suka bar gidan, sai da suka kusa zuwa gida sannan ya tsaya ya fito ya zagaya ya buɗe side ɗin take, yasa hannu ya yo waje da ita ya mayar da murfin ya rufe tukunna ya koma side ɗinsa ya figi motarsa ya barta a wajen. tana kallo ya wuce gidansu da alama ba gidan ya nufa ba yanzu, ta juya ta kalla nisan da suka yo daga gidansu, sannan ta kalli kusancin da take da shi da na su gidan. har ta juya zata koma can gidan sai taji yo haushin karnuka babu shiri ta tattare riga ta falla gida a guje, ta dinƙa buga gate babu ƙaƙƙautawa tsoro fal ranta, Baba me gadi kuwa na can toilet ya fito da sauri yazo ya buɗe yana cewa,"kai jama'a waye haka?". yana buɗewa Fullo ta sunkuya ta ƙasan hannunsa ta shige da gudu, ya leƙo yana kallon waje bai ga komai ba, ya rufe ƙofar, yana juyowa yaga tuni har ta shige part ɗinta, ya buɗe hannu alamun ko lafiya?. ƙarfe sha ɗaya Fillo taji ƙarar zuge gate, ta miƙe da sauri ta leƙa ta window taga Turaki ya fito a mota, ta ga sun tsaya da me gadi su na magana, idan ta fuskanta kamar Baban na labarta masa yanda ta shigo ɗazu ne, kuma da mamakinta sai taga ya wuce part ɗin Ilham as usual. ta saki labulen windon ta koma kan gado ta kwanta da tunanin abubuwa kala-kala acikin ranta. *Vote, share and comment.* [9/6, 23:45] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *49* washegari da la'asar Turaki na zaune a falonsa Bello ya shigo, kallo ɗaya Turaki ya yi masa ya mayar kan computer ɗin da yake dannawa, Bello ya ƙaraso gabansa ya ɗaga robar faro ɗin da yake hannunsa ya tuttule masa ruwan ciki akansa. "Bello what kind of rubbish be this?". "ɗan iska ma nan ya ganka ya ƙyale MT, yanzu na ƙara sarawa girman rainin hankalinka, kuma ban yafe ba zagin da ka ja min, akan kujera nake amma sai da na miƙe babu shiri tsabagen shigar zagin nan, har yau a jijjige nake da shi, sai kace kayi abu ni da banyi ba ni ke kwana aciki". Bello ya faɗa yana zama kan kujera, Turaki ya dinƙa kallonsa da wani kallo kafin yay tsaki ya miƙe ya cire rigar jikinsa da ta jiƙe. "tukunna ma ni ban gane maka ba har yanzu, ni ka rainawa hankali ko kuma su Mum ɗin ka mayar marainan wayonka?, sarai dai da iliminka ka san yarinyar nan ba ta da iddah akanka amma ka barta tana zama acikin gidanka". Turaki bai tanka masa ba ya ci gaba da aikinsa, sai can Bello ya fara masa ƴar murya,"haba Aminina kar muyi haka da kai mana, faɗa min gaskiya don Allah. gudun ɓacin ran su Maama yasa ka ƙaryata sakin da kace min kayi ko kuma ni ɗin dai ka mayar sauna?". "munafiki kawai". Turaki ya ce da shi yana hararsa. Bello yay dariya sosai ya ce,"naji ka kirani da koma menene, ka san Allah idan baka faɗa min gaskiya ba to zanje na faɗawa su Maama gaskiyar abin da na sa ni, dan ni dai kace min ka saketa". ya faɗa yana miƙewa. da sauri Turaki ya ce da shi,"kai wai mara hankalin ina ne, yanzu sai kaje ka faɗa musu hakan?". Bello ya ɗaga kafaɗa,"ofcourse, zan zuba maka ido ka ci gaba da zaman haramun da yarinya saboda kana gudun ɓacin ran iyaye, ai gwara a faɗa musu kawai su san gaskiyar abin da ke faruwa, yarinya ta tafi gidansu ta sami wani mijin tayi aurenta, kai kuma ai maka duk hukuncin da ya dace da kai. ko nufinka ka mayar da ita ne baka faɗa min ba?". Turaki na daɗa ɓata rai ya ce,"ni dama ban saketa ba, ko da nace maka na saketa to wallahi tallahi ban saketa ba". dariya ta zo wa Bello ya ce,"yau har da su rantse min?". "saboda ka ƙyale ni na huta, kamar yanda ka barni na huta da takurarka na 7days". Bello ya jijjiga kai,"amma kai dai anyi mugun ɗan rainin hankali, da ma saboda na ƙyaleka na 2days yasa kace min haka saboda ka san zanyi fushi?". Turaki yay masa banza, sai kuma Bello ya ƙara cewa,"to kuma na ga har yanzu baka bar nan part ɗin ba?, ko kewar ta nan ɗin kake yi tunda ita ka ɗanɗana ka ji?, ko kuma ita ma baka saketa ba hankalin mutane ka raina?". Turaki ya dire abin da yake ya dafe kansa, wucewar wasu sakanni tukunna ya buɗe ido ya zuba akan Bello ya ce,"in kana ƙaunar Allah da Annabi ka ƙyale ni, saboda fa wannan shegen sa idon naka yasa na barka a yanda itama waccan yarinyar ta ɗauka". Bello ya gimtse dariyarsa ya ce,"tun da kace Allah da Annabi an wuce wurin. mu koma kan aiki, ɗa zu mun yi waya da financial sectary na IBTC company, ina wancan document ɗin da ka haɗa?,". "shi na ke haɗawa yanzu?". "what! ba jiya ka ce ka yi completing nasa ba?, yau fa ya kamata ace mun yi printing an kaiwa Baffa". "to ya zan yi, after na gama wayar ta lalace, kano ma na kai gyaran a jiya, na so na tsaya na taho da ita Khalil ya damen da kira akan in taho gida ya ga kamar ba lafiya, but mun yi da shi me gyaran za'a kawo yau, ni kuma ganin ba su kawo tun safe ba naga gwara in haɗa wani kawai". "wai wayar da ka siya last week ne ta lalace ko wanne?". "ita ce". "kaii! da ma ba original ba ce cutarmu suka yi, but tawa fa normal take, me ya sami taka ɗin da ma?" Turaki ya ɗan kalle shi sannan ya ce,"fasata ta yi, gaba ɗaya ta tarwatsata ta koma fanko". "ban gane ba, da ma ka haihu ne da har yara su ka fara yi maka babban ta'adi haka?". "nop ban haihun ba dai tukunna, fitowa tayi da ga cikin ta fasa sai ta koma". ya kalli Bello da kyau ya ce,"ka daina tambayar rainin hankali Bello, wataran sai ka haɗu da wanda zai rufeka da duka". ya maida hankalinsa ga abin da yake yi, Bello dai sai cika shi da tambayoyin rainin wayo yake yi amma sam yaƙi responding nasa, da ya gaji kawai ya miƙe ya tattara komatsansa ya fice ya bar masa part ɗin gaba ɗaya. part ɗin Fillo ya koma, lokacin tana kitchen su na aiki da yaran da aka aiko mata yau da safe, jiyo motsin shigowa parlon yasa tai saurin wanke hannu a sink ta fito, ganinsa ta yi zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan table ɗin, yatsansa ɗaya cikin baki ya kafawa laptop ɗin ido da alama nazarin wani abu yake yi, kafin ta ɗauke ido akansa taga ya miƙe da kayansa a hannu ya wuce upstairs, ta bi shi da kallo tana hararsa, sannan ta juyo ta mayar da idonta wurin da ya tashi tana faman ɓata fuska, haka kawai ya zo ya ɓata ma ta wuri, ya ɗauko table daga in da yake amma mayarwa ta gagara. ta wuce tana ƙunƙuni ta ɗauke table ɗin ta mayar da shi ainihin in da yake, sai maganganunta take yi ita ɗaya har Bello ya shiga ma bata sa ni ba, sai da ta baro wajen zata koma kitchen sannan ta lura da shi. tai murmushi tana gaida shi, ya amsa ma ta yana tambayarta ya lafiyarta, ta ce,"Alhamdulillah". yana kallon bandage na hannunta ya ce,"subhanallah ciwo kika ji haka?". ta ce,"ehh jiya ne na yanke, amma da sauƙi". ya ce,"ya salam to Allah ya sauƙe". "amin na gode". sai kuma ta ce,"ka zauna mana". ya ce,"nop ina sauri ne, MT fa yana nan ko yana ɗaya part ɗin?". ta ce,"na ga ya hau sama". Bello ya fito da flash da ga aljihunsa ya ce,"please ki ba shi wannan". tana tsaye da ga in da take tace,"ka hau ka same shi mana". ya ce,"no anata min waya daga office ne, ki ba shi yanzu please kice masa yay calling ɗi na". ta wuce taje ta amsa, shi kuma yay ma ta sallama ya tafi. kamar ta hau saman taje ta kai masa sai ta fasa tai wucewarta kitchen suka ci gaba da aikinsu, haka kawai yau ta tashi da kwaɗayin dambun gero, sanda ta shiga kitchen taga hannu ɗaya gareta har ƙwalla sai da tayi, kuma sai Allah ya taimaketa yaran suka zo a lokacin, nan da nan kuwa suka shiga kitchen ɗin tare. kuma sai da suka kamma dambun kawai taji gaba ɗaya bata son cinsa, tun safe da ta tashi take jin mararta na murɗa mata kaɗan kaɗan, yanzu kuma ciwon ya ƙaru sosai, ta san ba komai ba ne illa period ɗinta, haka yake yi mata da ma, da zarar yazo kuma duk sai ya cika mata ciki taji bata son cin komai, fatanta ɗaya ne kar tayi wahalallan ciwon da ta saba. ta kalli ɗaya cikin yara me suna Sakina ta ce ma ta,"kinga ɗauko wancan flask ɗin ki cika shi sai ki kaiwa Baba me gadi, idan kuma ba zaku iya cinyewa ba ki bawa Baban kice dan Allah ko da wanda zai bawa". ɗayar me suna Hannatu ta ce,"Anty ke ba za ki ci ba?". Fillo tai mata wani kallo ta ce,"na ce miki sunana Halima, bana son wani Anty. na ƙoshi naji ya fita a raina". ta juya ta fita, Sakina da Hannatu suka shiga gulman wai ciki ne da ita, su na cikin ƙusƙus ɗin su sai gata ta dawo, ta ce da su,"yauwa yanda ma za'ayi, dan Allah ku kaiwa Kakata, ai kun san ɓangaren masu aiki ko?". Hannatu ta ce,"anan gidan?". ta ce,"no can gidan su me gidan nan". Sakina tace,"ehh mun sani, kwananmu biyu ma a can". haka kawai taji wani daɗi tace,"kun san Yami?". suka haɗa baki wajen cewa,"ai a wajenta ma muka kwana". "yauwa to ita zaku kaiwa, kuce ina gaisheta kuma don Allah ta sa Maijidda ta zo". ta faɗi hakan ta fita a gaggauce saboda ciwon marar da ya fara tsananta ma ta. tana hawa upstairs taji karatun qur'ani na tashi a room ɗin da ke kusa da nata, ta yi wucewarta ɗakinta sai faman yamutsa fuska take tana danne mararta. har ta kwanta akan gado sai ta tuna da saƙon Bello, hakan yasa ta miƙe ta fito cikin ƙarfin hali ta wuce ɗakinsa, ta tura ƙofar tana sallama aciki-ciki, shi kuwa kamar bai ji sallamar ba dan bata ji ya amsa ba. ganinsa babu riga yasa tai saurin rufe idonta, ta shiga ciki tana lalube kamar makauniya har ta isa inda taji kamar mudubi ta taɓa, ta ɗora flash ɗin da Bello ya bata akai sannan tai saurin ficewa ta bar ɗakin. around 5 kiran wayar Maama ya shigo wayar Turaki, lokacin ya rufe laptop kenan, ya ɗaga da ga can ɓangaren Maaman ta ce masa,"ka na office ko gida?". "ina gida Maama". ta ce,"jiya Daughter ta manta magungunanta sai yanzu nake ganinsu, ka zo yanzun nan ka amsar ma ta dont waste time, ya hannun na ta?". ya ce,"da sauƙi". ba tare da tace masa komai ba ta kashe wayar, ba'a son ransa ba haka ya shirya, ba ya son wani faɗan dan haka bai tsaya ɓata lokaci ba, kuma ko da ya karɓo direct gidan su Bello ya wuce, Umma ya gani zaune a falo tana yiwa ƴan jikokinta karatun ƙur'ani, ya durƙusa ya gaishe da ita, tayi ta saka masa albarka kuwa tana jadadda masa akan ya gaida iyali. ya ce,"Umma Bello ya dawo ne?, na kira wayarsa ban samu ba". ta ce masa,"yana ciki bai jima da shigowa ba ma". ya wuce ɗakin Bello, kuma yana zuwa ya tarar da shi kwance rungume da pillow yana waya, Turaki yaja dogon tsaki na takaici, ya jefa masa flash ya juya ya fice ba tare da yace masa komai ba. bai koma gida ba sai bayan sallar magrib, yana shigowa parlo Sakina da Hannatu suka yi saurin durƙusawa su ka gaida shi, bai amsa musu ba illa bin parlon da yayi da kallo, ganin babu Fillo sai ya haye upstairs ɗin, yana buɗe ɗakinta ya ganta shame-shame a ƙasa sai murƙususu take yi, ya wuce ya dire ledar drugs ɗin akan stool, har ya juya zai fita sai kuma shashsheƙar kukan da ke fita a hankali ya dakatar da shi. dawowa yayi ya durƙusa a gabanta, ya tsayar da ƙwayar idonsa akan fuskarta da hawaye ke ta zuba, ga uban gumi ta haɗa kamar an watsa ma ta ruwa, ga wani irin nishi kamar me naƙuda, sai ka kasa kunnenka sosai tukunna zaka ji kiran sunan Kaka da Ummi da take yi a wahalce. ya ɗan taɓa hannunta yana cewa,"ke". ta damƙo hannunsa ba tare da ta sani ba ta murgina tare fashewa da kuka sosai. "wayyo Allah nah, wayyo Ummi nah, wayyo zan mutu". yasa hannu ya taɓa jikinta yaji zafi rau, sai kawai yaji ta ɗan ba shi tausayi, ya kamota zai ɗagota daga kannanaɗewar da takeyi kamar miciji tace,"a'a". muryarsa a hankali ya ce,"me yake damunki?". sai a sannan ta iya buɗe idonta a wahale tana kallonsa a disashe saboda ruwan hawayen da ya cika ma ta ido. shi kuma ganin tana kallonsa ya tamke fuska yana haɗe gira sama da ƙasa ya ce,"me?". ta mayar da idon ta rufe tare da kamo hannunsa ta ɗora akan cikinta, ya kalli cikin ya ƙara cewa,"me ya sami cikin?". cikin kuka ta ce,"don Allah ka kira min Kaka mutuwa zanyi, ko kuma ka kaini asibiti su cire min cikina don Allah". yay shiru for some minutes sannan ya ce,"me kika ci?". tai shiru ta kasa ce masa komai sai burgima take yi tana kuka sosai. ya miƙa yaje ya ɗauko ledar drugs ɗin da ya shigo da su, ya fita ya ɗauko ruwa a ɗakinsa ya dawo, ya durƙusa yana ce ma ta,"tashi ki sha magani". ta girgiza ma sa kai, ya ɗaga murya sosai,"na ce ki tashi ko". ta ce,"Kaka ta hanani shan magani". haushi ya kama shi ya miƙe zai fita karaf idonsa ya sauka akan tiles inda take kwance, wajen duk ya ɓaci da jini, yay saurin rufe ido yana girgiza kansa, lokaci ɗaya amai ya taso masa babu shiri yay hanzarin ficewa, amai sosai ya yi da ya shiga toilet, bayan ya fito ya tsaya yana tunani, yana jin zuciyarsa duk babu daɗi. Yay ta so ya tuna sunan abin da ya gani a ƙasa, ya dai san Nihal ma na irin haka wanda har suma take yi ita, sai kawai ya ɗauki wayarsa yay dialling lambar Zaytuna, tana ɗagawa ko sallamar bai amsa ba ya ce,"mene ma sunan wannan abun da kuke yi every month?". taji yay tambayar kamar a rikice, ba ta fuskance shi ba sai daga ba ya sannan tace,"oh menstruation". yay ɗan jim sannan ya ce,"wanne irin magani ake sha?". ta ce,"zan maka text ɗin su yanzu". yay ɗan guntun tsaki ya ce,"babu a gida?". ta ce,"akwai". ya ce,"to ki kawo yanzu, idan ana allura ma ki taho da ita". ya koma bakin gado ya zauna ya kulle idonsa yanata girgiza kansa, yana da ƙyanƙyami sosai fiye da tunani, ko Zaytuna da yake cin abincinta idan tana period ko ruwan hannunta ba ya sha, har yanzu zuciyarsa ba ta bar tashi ba, so kawai yake ya ƙara yin wani aman ko zai ji daɗi, kansa har wani ciwo yake yi. yana nan zaune yana ta aikin jera tsaki kamar aikin farilla, wayarsa ta yi ringing, yana ɗagawa bai ko jira abin da Zaytuna zata ce masa ba ya ce,"ki sameta a ɗakinta". "Hammah ai ban san ɗakin nata ba, ban taɓa shigowa ba". a daƙile ya ce,"zan kashe fitilar ɗakina". ta ce,"tom". Sanda Zaytuna ta shiga ɗakin, samu tayi ta kyala amai yafi guda huɗu duk wuri daban daban, sai dukan tiles take yi tana ambaton innalillahi, tana faɗin azo a taimaka ma ta, ta kira sunan Kaka ta kira na Yami. Zaytuna ta ƙarasa da sauri, ta ɗauki jarkar ruwan da ke wajen ta buɗe ta tuttula a cup ta bata magani ta sha, sannan tayi ma ta allura, tsabar wahala ma bata san wa ke kanta ba, a hankali a hankali kuma taji ciwon yana ɗan sauƙi. sai lokacin da iya buɗe ido ta kalli Zaytuna ta ce,"Adda". ta amsa mata tana cewa,"sannu". Zaytuna ta riƙeta ta kaita toilet ta ce ta daure ko ba tayi wanka ba ta ɗauraye jikinta, haka tayi wanka a daddafe ta fito, zata kuma kwanciya a ƙasan tiles ɗin Zaytuna ta hanata, ta buɗe wadrobe ta ɗauko ma ta riga ne ɗan kauri iyaka gwiwa ta bata, sannan ta kwanta akan gado, tana kwanciya baccin wahala ya ɗauketa. Zaytuna da kanta ta gyara wajen tas, har kayan da ta cire ta wanke su a machine, ta kunna turaren wuta sannan ta kira Turaki a waya tace masa zata tafi, toh kawai yace ma ta, before ya kashe wayar tayi saurin ce masa,"kar ta sha ruwan sanyi, da abu me zaƙi, da cocumber". bai ko ce mata ƙala ba ya kashe wayar kawai. tafiyar Zaytuna babu jimawa ya fito a ɗakinsa ya tafi ɗakin Fillo, fitila ya kunna ya hangeta kan gado, yanayin yacca tayi kwanciyar kaɗai zai shaida maka kwanciya ce ta wahala, dan hatta yanda numfashinta ke fita ma ba ta daɗi ba ne, hasken fitilar yasa ta yin juyi tana sa hannu ta kare idonta duk cikin baccin, lura da hakan ya sa ya kashe light ɗin ɗakin ya kunna ta wayarsa, ya mayar da ƙofa ya rufe sannan ya ƙarasa ciki, a bakin gadon ya zauna ya kai hannu ya taɓa wuyanta da kanta yaji still jikinta da zafi. wayarsa ya ɗauko ya kira Zaytuna, ta ɗaga tana sallama da alama ma ta fara bacci, yace da ita,"zazzaɓin bai sauka ba fa". ta ce,"da ma akwai zazzaɓi ne Hammah?". bai amsa ma ta ba kawai yaja tsaki ya kashe wayar, ya haska torch ɗin wayarsa ya ɗauko ledar maganin ɗazu yaga bata sha ba, ya zazzage ledar ya ɓallo adadin yacca zata sha, ya zuba ruwa a cup sannan ya ɗago Fillo zuwa jikinsa, ba tare da yay magana ba ko ya tasheta ya kafa cup ɗin a bakinta ya zuba ruwa sannan ya tusa mata drugs ɗin duka, ya ƙara zuba ruwa tare da toshe hancinta, take drugs da ruwan suka wuce maƙogoronta. tsabagen baccin na cin sosai buɗe ido kawai tayi ta mayar ta rufe tana gyara kanta a ƙirjinsa, ajiye cup ɗin ruwan yay tare da mayar da ita ya kwantar, yasa hannunsa ciki nata mara ciwon ya haɗe da nasa, yay ta kallonta wucewar wasu ɗaƙiƙu tukunna ya buɗe blanket ya rufeta, yana me kamo ɗayan hannun da.ke da ciwo, ya kalli ciwon ya kalli fuskarta, ya tuna jiya haɗe da yin ɗan guntun tsakin da shi ɗaya ya san dalilin yinsa. ya ƙara ɗaukar waya ya kira Zaytuna, sai da ya kira sau uku sannan ta ɗaga, lokacin bacci yaci ƙarfinta sosai, dan kamar zata yi kuka ta ambaci sunansa. ya ce,"wannan ciwon nata when suka ce za'a kunce?". ta ce,"Hammah ai ba da ni aka je hospital ɗin ba". sai ya hauta da faɗa yana cewa,"kuma ke ba ki san yanda za'ai masa ba za ki ce wani ba da ke aka je ba. mene amfanin karatun da kika yi?, ko haka kike yiwa patients ɗin da su ke asibiti?". faɗan ya fara hawan mata kai ta tari numfashinsa,"a bar shi ya ƙara kwana biyu tukunna". yaja tsaki yace,"ki fita ki bawa me gadi first aid". yana faɗa ya kashe waya ba tare da yace komai ba, ya fita daga ɗakin cikin sauri, zuwansa gidan yay daidai ya isowar Zaytuna bakin gate ɗin sai tangaɗin bacci take yi. kusan fizgar firstaid ɗin yay daga hannun nata ya juya ya tafi bai ko tanka mata ba, abun da bata taɓa yi masa ba kawai ta harari bayansa ta koma sai masifa takeyi. yana komawa ya tarar Fillo har ta tashi ta shiga toilet, zama yay bakin gadon yana jiran fitowarta, can sai ga ta ta fito tana jan ƙafa ɗaya, ya bita da kallo ta ƙasan ido, ita kuma ganinsa sai tai saurin juyawa zata koma toilet ɗin saboda rigar da ke jikinta, ƙafafunta tun daga gwiwa duk a waje, ga shi babu brazier a jikinta kuma ana hango shatin breast ɗinta. muryarsa a sama yace,"wallahi kika koma sai naji miki ciwon da yafi na jiya". cak ta tsaya ta manne a jikin bangon tana sakin kuka, ya taso ransa a ɓace ya figeta suka wuce, yana kallonta fuska ɗaure ya ce,"ban hannunki". za ta tsaya gardama ya bige hannunta daga kan fuskarta da take goge hawaye, ya kamo me ciwon ya shiga warware bandage ɗin, ya jawo stool ya zauna ya shiga ƙara dressing ciwon. tana kallonsa murya gwanin ban tausayi ta ce,"don Allah ka kira min Ummi". shiru kamar bai ji me ta ce ba, ta ƙara maimaita masa ya ce,"kin gyaro wayar ne?". tana kallon saman kansa da ke duƙe tace,"wacca wayar?". ya ce,"wadda kika fasa". a shagwaɓe ta ce,"to ai bana sa ne". Ya ce,"to sai ki jira sai randa kika gyara". kukan da ya tsaya mata ya dawo, ta dinga roƙonsa akan ya kira mata Ummi ko Kaka, bai ko bi ta kanta ba yana gama naɗa bandage ɗin ya ɗauki first aid ɗin yay ficewarsa. around biyu na dare Fillo ta kasa bacci saboda tsoro, duk yanda ta so ta dake tai bacci ta kasa, sai tayi ta jin kamar ana motsi a ɗakin, a imagination ɗinta ma kamar kukan wani abun take ji, ta buɗe ido a hankali ta diro akan gadon tana tafiya saɗaf saɗaf sai adu'a takeyi ta fita daga ɗakin, da gudu kuwa ta kwasa ta ƙarasa ɗakin Turaki, tana shiga ta tura ƙofa ta jingina da ƙofa tana sauke a jiyar zuciya. motsinta ya sa Turaki buɗe ido ya ƙaro hasken bedside lamp, ta kusa ba shi tsoro ganin gashin kanta duk a barbaje, takaici ya cika shi ya buga mata tsawa lokaci ɗaya kamar wadda aka ɗauko sai gata a bakin gadon tana kyarmar jiki. "don Allah ka yi haƙuri, wallah tsoro nake ji ɗakin sai kuka ake yi a cikinsa". ta faɗa a cikin muryar kuka me tattare da rauni, har ya ƙara haɗe rai zai korata sai kuma ya tuna matsalar da ke tare da ita ta aljanu, saboda haka ya fasa ya kamo hannunta ya zaunar da ita a bakin gadon kusa da shi. calmly ya ce,"idan ba ki daina kukan ba sai na kore ki". ɗiff tayi shiru tana ƙanƙame jikinta. tausayinta ya kama shi sosai, ya sauko yace ta haye kan gadon, ta kalle shi zata yi magana sai ta fasa ganin irin kallon da yake watsa mata, tai saurin hayewa ta ƙudundune a tsakiya, yace,"matsa can". ta matsa inda ya nuna mata, sannan shi ma ya hau ya kwanta bayan ya kunna karatun alƙur'ani. yana kwanciya yaji ta kamo hannunsa ta riƙe, ya ce,"what?". ta ce,"don Allah ka barni a haka". "to yi bacci kar in ƙara jin motsinki". ta ce,"to". har tsawon wani lokaci yaji alamun dai ta kasa baccin, kawai tayi shiru ne kamar tana baccin, zai zare hannunsa a nata tayi mugun firgita ta ƙwalla ƙara tana yowa kansa gaba ɗaya. yay saurin tattarota jikinsa ya kewayeta da duka hannunsa yana cewa,"shhhh ba ihu ba adu'a za kiyi kinji". ya ƙara maimaitawa,"kin ji". ta fizgi numfashi ta ce,"wani abu ne yake bin jikina yana kuka". ya ɗora hannunsa a gashin kanta yace,"ta ina kike jinsa?". a hankali ta ce,"a ƙafata". ya miƙa hannu ya daɗa ƙaro hasken lamp, ya ɗaga blanket ɗin yana bin ƙafarta da kallo, yau da yaga duka ƙafarta a zahiri sai yaji ya tsorata da irin sirantarta, ya sauke numfashi yana tunanin anya ba sai ya kaita anyi ma ta general check up ba kuwa?, shi idan ma ana ƙara nama a jikin mutum tsab zai kashe ko nawa ne a saka mata, sirantar tayi yawa sosai. ya sunyo da kansa yana kallon fuskartata, ta rumtse idanuwanta gam kamar ko ance ta buɗe ba zata buɗe ba. a hankali in a cool voice ya ce,"za ki ci abinci?". ta ce,"a'a". ya hurar da iska a bakinsa ya ce,"cikin ya daina ciwon?". ta ɗaga masa kawai. ya ƙara cewa,"me kike so yanzu?". ta ce,"babu komai". "har yanzu kina jin motsin abun?". ta girgiza ma sa kai kawai tana ƙara ƙanƙame shi. a kunnenta ya ce,"ki yita ayatul kursiyyu". ta ce,"ina yi". "to yi bacci". ta knodding kanta kawai. ya girgiza kansa yana jin tsananin tausayinta, a hankali yaji ta sauke numfashi hakan ya shaida masa tayi bacci, sai ya kwantar da ita kusa da shi sosai, duk yanda ya so ya zare hannunsa daga riƙon da tayi masa ya rasa yanda zai yi, saboda ba ya so yay ƙwaƙwƙwaran motsin da zata farka. kuma baccin da bai iya yi ba kenan, yay tayi ma ta karatu a cikin kunneta, har aka kira sallar asuba, sai lokacin ya zareta daga jikinsa ya rufeta gaba ɗaya ya shiga toilet yay alwala, sai da ya yi raka'atanul fajr sannan ya wuce masallaci bayan yasa key ya rufeta a ɗakin. [9/7, 00:10] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *50* sai ƙarfe goma sha ɗaya Turaki ya farka da ga baccin bayan asuba da ya kwanta, lokacin da ya tashi bai ga Fullo a ɗakin ba, bai yi mamaki ba ya san da ma tsoro ya kawota, ba don haka ba ya san ba zata taɓa zuwa ba. yana kunna wayarsa ya ci karo da messege ɗin Sectery nasa, da yake tuna masa appointment din da yake da shi da wani company na lemu by 3pm. saukowa yayi akan gadon ya shiga toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin shigar manyan kaya na kufta black colour da tayi masa masifar kyau. yana cikin fesa turare yaji cikinsa yayi ƙugi sosai alamar yunwa, dan daren jiya ma bai ci komai ba, yay gajeran tsaki na ƙorafi da takaici, ga shi da aure amma bai da matar da zata dafa masa abincin da zai ci, shin wai sai yaushe zai san yayi aure ne?, when zai fara jin wannan daɗin da ake cewa akwai shi a gidan aure?, wannan farin cikin sai yaushe?, ga shi ta bakin Bello da gaske rainon Fillo zai yi, rainon da baya jin cewar zai iya, ya ƙara yin tsaki yana dire perfume da ke hannunsa, yanzu ba abin yaje gida ba da sunan zai ci abinci a fara yi masa tambayar ƙwaƙwaf. jakar laptop ɗinsa ya ɗauka ya fita a room ɗin, daidai bakin ƙofar room ɗin Fillo ya tsaya, ƙofar a buɗe take, ya tsaya yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga, a ƙarshe zuciyarsa ta yanke masa yay tafiyarsa kawai, tun da har ta iya barin ɗakin nasa taji sauƙi kenan. yana saukowa parlo ƴan aiki suka fito da sauri daga kitchen, suka durƙusa suka gaida shi, hannu ya ɗaga musu ba tare da ya amsa da fatar baki ba, har ya kai bakin ƙofa idonsa ya sauka akan dining, flask ne guda biyu a ajiye sai na tea flask, ya kalli Sakina da ba ta koma kitchen ɗin ba ya ce,"ta sakko ne?". kanta a ƙasa ta ce,"a'a ranka ya daɗe bata sakko ba kwatakwata". yay ɗan jimm sai kuma ya ce,"ita tace kuke yin girki?". ta ce,"a'a ranka ya daɗe, mun ga dai hakan na cikin aikin mu ne". ƙaramin tsaki kawai yayi ya zuge glass ya fi ce, Sakina ta bi shi da kallo tana riƙe haɓa da jinjina kai. Hannatu na ganinta ta ce,"lafiya?, me kika guntso?". "uhmm ke wannan me gidan bai da sauƙi ko kaɗan, babu ma alamar mutunci a tare da shi, ni da ma tun ranar farko naji bai yi min ba sam, gaskiya matarsa na haƙuri da shi, irin mazan nan masu shegen girman kai da izza, fuska gaba ɗaya babu annuri". Hannatu ta ce,"wani abu kika gani hala". tayi maganar da irin suffa ta ƙwanƙwararrun munafukai. "ke kin ji yacca yake tambayar wa ya saka mu yin girki, kamar fa zai kawo min duka, babu wani irin taushi girmamawa ta ɗan adam acikin muryarsa". sai kuma ta taɓe baki,"ni da ma na faɗa miki tun ranar da muka zo na san ba zaman lafiya ake a gidan nan ba, ba ki ga ita kanta kamar ba ta da miji ba, sai dai ta sauko tayi kallo taci abinci ita ɗaya ta koma, tabɗijam ni kuwa dai duk kuɗin namiji wallahi ba zan yarda da rashin mutuncinsa ba, ke ni ba zan ma yarda da wani auren dole ba, ba zan iya namiji ya takani ba gaskiya". "ke ma dai Sakina ai da ma da gani ba auren soyayya akai ba, ni itace ma ta ke bani tausayi tun da naji ance tayi aiki a gidansu, wataƙila ƙarfi aka nuna musu aka aura ma ta shi dan anga ba su da hali, ni tausayi ma take bani kina kallonta kin san bata jin daɗin zaman, ko da yake babu komai zamu ɗaurata a hanya, naga ba ta da girman kai za ta sake da mu, zamu ba ta shawarwarin da zata saita mishi zama". Sakina ta nufi cooker gas tana faɗin,"ke yanzu dai buɗe firinjin nan ki ɗauko mana kazar nan da naji ta ɗan fara yami, mu gyara muci abarmu in ba haka ba a banza za'a barta ta lalace, naga matar gidan ba wani wayewa tayi da cin kayan daɗi ba, duk gata nan a ƙanjame ai. Allah na tuba ni ina da wannan uban kayan daɗin ma me zai sa in damu da takaicin ɗa namiji, ai ɗaukarka zanyi in bawa banza ajiyarka, kai ita ma dai wallahi anyi lusara, ko da yake wasu sun ɗaukaki soyayyar namiji fiye da jin daɗi, kuma kin san Allah duk yanda akayi ganinta ƙashi da rai yasa yake ma ta wulaƙanci, babu gaba babu baya kyace me cutar S, kai Allah dai mun gode maka, kuma banza da ita ma kawai ta jefa shi a kwandon shawara ta bawa jikinta ingantattun kayan da zasu farfaɗo da ita, ba dai gidan jin daɗi da hutu ta zo ba, wallah wata guda yay ma ta yawa ta murmure". Hannatu tai ƴar dariya tana fito da gasashshiyar kaza a freezer,"Sakina ko dai ko dai, kawai...". bata ƙarasa ba Sakina ta juyo tana yi ma ta wani kallo,"ko me?, ni da wannan miskilin mijin?, ba dariya ba murmushi babu fara'a?, azaba!, Allah ya kiyaye wallahi, ai ranar farko zan bakawa gidan nan wuta dan ba zan iya da mugun halinsa ba, dukanta fa yake yi". Hannatu ta riƙe baki,"kai don manzon Allah?". "mtswww ke sai shegiyar gulma ba kya sa ido a abu, jiya baki ganta tana kuka ba?, to da daddare ma lokacin da ya shigo na hau saman ina jinsa a ɗakinta yana zazzaga mata masifa ita kuma sai kuka takeyi, ke Allah yasa ma ba sakinta yay ba dan naga yau gaba ɗaya fa ba ta sakko ba". Hannatu tayi dariya,"wallahi yana sakinta zan shiga daga ciki, wa ye zai so rabuwa da wannan gidan da aka aje daula, aljannar duniya, ita ma ɗin dai shashasha ce kawai, ni fa yana burge ni sosai saboda yana da kyau kamar ka sace shi ka gudu, kuma da yardar Allah sai ya zama rabona". ta faɗa tana jujjuyawa,"kalle ni fa da kyau, kissar ƴan aiki zanyi kawai a wuce wurin". buɗar bakin Sakina za ta yi magana suka ji sallama a parlo, da sauri suka fita a tare, ganin Yami yasa suka ƙarasa da sauri su na yi ma ta sannu da zuwa, Yami na yi musu fara'a ta amsa musu, ta zauna akan kujera tana tambayarsu ya aiki. "ina matar gidan fa?". Yami ta tambaye su. Sakina ta yi saurin cewa,"bari a hau a kirawota yau ba ta sakko ba gaba ɗaya, ƙila ba ta tashi ba". Maijidda ta cire hijab ɗinta ta ajiye tana cewa,"ƙyale ta bari na hau na sakko da ita". ta faɗa tana nufar upstairs, kuma duk da haka Sakina sai da ta bi ta saboda taje ta yo munafurci. “Aa lafiya dai?” Maijidda ta tambaya lokacin da take ɗora ƙafafunta akan steps. Sakina ta ɗan sosa gefen fuskarta ta ce,“Aa da ma wai...”. dakatar da ita Maijidda ta yi kana ta ce,“Aa Kika ce bata sakko ba ko, na ce miki to zan je na gani ko lafiya, ina ga ai babu kuma buƙatar sai kin biyo baya na ko kuwa?. Kije kiyi aikin gaban ki”. Haka kawai ta tsinci kanta da fad’a mata wad’annan maganganun ba tare da sanin dalili ba. but still sai da Sakina ta bi ta ɗin bayan ta haye, kuma tana hawa ɗakin Turaki ta buɗe a hankali ta shiga, tai tsaye daga bakin ƙofa tana yi masa kallon tsab, ganin kan gadon ba'a gyare ba yasa ta riƙe baki tana jijjiga kai, ko me ta saƙa a ranta oho, da sauri kuma ta fito tana barin wajen ta nu fi ɗakin Fillo. Maijidda kuwa tana isa ta ga ƙofar d’akin Fillo a bud’e, bata yi mamaki ba sanin cewar Turakin baya nan, kai tsaye ta saka kanta ciki d’auke da sallama. Bata ji alamun za'a amsa ma ta ba don haka kawai ta kutsa kanta ciki, a karo na biyu ta ƙara yin sallama saboda son ta samu izini kamar yadda Manzon Allah (SAW) yay mana umarni da mu yi. Sai da tayi sallama uku babu amsa hakan ya sa ta ƙarasa ciki tana kuma ƙara yin sallama, rufe bakinta ke da wuya sai ta jiyo kamar shesshek’ar kuka, hakan ya bata damar yin sauri ta isa bakin gadon tana fad’in,“hasbunallah wa ni’imal wakil, na shiga uku ni Hauwa, Ke! Meye ka faruwa meye damuwan?, Wani ya mutu bani da labari ne?.”. kawai sai itama ta fashe da kukan, da ma itama gwanar hawaye kamar Fillon, ganin hakan Kuwa ya ba ma Fillo damar ‘kara fashewa da wani matsanancin kuka cike da shagwab’a da iya shege gami da zallar wawta. Sakina dai na laɓe bakin ƙofa ta kasa kai da kunne, ta rufe baki tana fito da idanu waje. Maijidda tayi saurin kai hannu ta janyo Fillo jikinta, da tsantsar kulawa da damuwa irin ta ƴan'uwantaka take fad’in,“wai don Allah me aka yi maki?, don Allah ki sanar da ni meye wai ni don Allah?”. Da k’yar Fullo ta bud’e baki ta fara magana, leb’en sama da na k’asa su na had’uwa su na faman luguden kuka,“wai wai ni fisabilillah haka kawai..”. Maijidda ta zabura tana k’ara fad’in, “wai Ke me?, don Allah ki min bayani inji?, kin san kuwa duk yanda gabana ke faɗuwa?". “to wai ba Turaki ba ne haka kawai shi kullum ya gagara ya fahimce ni sam, sai yay ta faman ji da kansa, kullum sai yay ta ƙin kula ni yana share ni, ko kallona ma ba yayi, sai dai fa yay ta hararata, kuma idan nayi magana sai yay ta min tsawa yana ɗaga hannu zai mareni, ni sai yay ta min abu kamar ba mijina ba, da ma sai da na faɗa muku ba ya so na, ni kawai gida zan koma, ki kira min Ummi a waya please". kukanta ya ƙaru a san da take ƙarasa maganar. damuwa ta bayyana fal a fuskar Maijidda, cikin sanyin jiki da murya ta ce da ita,"kuma kina yi masa biyayya?, kina sauke duk hakkinsa da ke kanki?, kuma ba laifi kika yi masa ba?". tasa hannu tana goge hawayenta ta ce,"ai ni bana kula shi ma". Maijidda ta ware ido,"ba kya me?, kwatakwata ba kya kula shi kike nu fi ko kuwa da ku ka yi faɗan ne?, ni ban gane rashin kulawar ba". "ni kawai ba na kula shi ai baya so na?". Maijidda ta raɗa ma ta abu a kunne, Fillo ta ɗago daga jikinta tana faman ɓata rai,"ni nace miki komai ma bana kula shi, sai jiya ma na fara ganinsa a gidan, ni dan Allah ki kira min Ummi a waya azo a tafi da ni". "Allah me girma da ɗaukaka, yau ina ganin iya shege, da ma Fillo har haka kika kai ba kiyi hankali ba?, mijin naki za ki ce sai jiya kika gansa bayan sati guda da aure?, kuna cikin gida ɗayan?, to wa kika barwa shi?, ɗaya matar tasa ko kuma ƴan aikin?". kuka ya ƙara zuwar ma ta,"to ai shi ne baya zuwa inda nake, kuma da yazo sai ya fara min tsawa alhalin ya san bana so". Maijidda ta ce,"tabɗijam, to wallah sai yau na tabbatar da ke ɗin nan dai ba ki da wayo sam, a iya ɗauke asiri kawai kika fi wayo. yarinya Allah ya tausaya miki ya ba ki miji kamar Turaki, mijin kece raini, mijin wuce sa'a, amma ki gantalar da shi da lamarinsa saboda shegen taurin kai da miskilanci irin naki. to ai ni dai a iya nasiha da faɗan da naji an miki ba'a ce sai ya zo inda kike tukunna za ki saurare shi ba, kuma ba'a ce lallai sai ya zo inda kike ba sannan kema za ki je inda yake, yo to da ma wanne miji ne zai kula matarsa alhalin ita ba ta kula shi?, da kike batun ma ba ya sonki, ai ko jikina duka kunnuwa ba zan yarda da wannan zancen ba, dan idan ba ya sonki babu abin da zai sa ya aureki, don billahi irin waɗannan mazan masu aji da ilimi ya ratsasu ta ko'ina ba sa auren macen da basa so, haba Fillo ki yiwa bawan Allahn nan adalci mana, wannan mutumin dai zuciyarsa babu mugun nufi ballantana kice saboda ya wulaƙantaki ya aureki, kuma da ma akan mene ba zai ke shareki ba, shariya ma ai dole dan wallah me iyawa da halinki sai me kai zuciya nesa, in wani ɗan wiwin ma kika aura Allah da tuni kin sha kutufo, to da yake ma kin samu wuri ne shiyasa kike abin da kika ga da ma. kuma idan gidan za ki tafi da gaske ai haɗa kaya za kiyi kibi hanya ba sai kin kira waya anzo an tafi da ke ba". sai kuma ta kwantar da murya ta shiga ba wa Fillo shawarwari masu kyau a matsayinta na aminiya kuma ƴar'uwa, tare da ƴan nasihohi wanda ta san idan har ta ɗauka tayi amfani da su ba zata yi danasani ba. kusan minti biyar sannan ta miƙe tana cewa,"wanko fuskarki tare da Yami muke, saura idan munje kiyi wawtar gaya mata abin da kika faɗa min, dan naga kamar hankali ya bar jikinki, wallahi kici uban faɗa in ta kama ma a haɗa miki har da duka, ki ce mata kawai ba ki da lafiya, in ya so ma ai tsammanin ciki kika ɗauka da wuri haka". ta ƙarashe maganar cike da tsokana tana ƴar dariya, Fillo ta harareta ta nufi toilet, ita dai dariya take tana ƙara faɗin,"Allah kina cewa ba ki da lafiya abin da za'a fara tunani kenan, nan kuwa ba'a san ko shimfiɗa baku taɓa haɗawa ba, balle ayi me kankat". su na sakkowa da ga step Maijidda na ƙara faɗin,"ni dai gaskiya nake faɗa miki kuma shawara nake baki, ki ajiye shegen taurin kanki da tsinannan miskilanci a gefe ki kama mijinki, billahillazi tsiwa da rashin mutunci ba naki ba ne a gidan nan, ki nutsu ki yiwa kanki karatun ta natsu, in kuwa ba haka ba na rantse da Allah sai kin yi kukan da yaci uwar wanda kike yi, sarai kin san dai ba ke ɗaya ba ce, matarsa na dawowa zai jefa ki a kwandon shara, ya mance da ke da batunki, ba kowanne kalar iskanci namiji ke ɗauka ba a wajen mace komin son da yake yi ma ta kuwa, yanda kishiyarki take wayayyiya sai ki zama ke da bola ɗaya acikin gidan nan in kika yi wasa. ke idan ma ita ba ta dawo ba ga ƴan aiki nan an ajiye miki cikakkakun ƴan mata masu buɗaɗɗan ido, inda rabon sun ƙwace miki miji sun barki da sakakken baki ne ke kika jiyo, dan wallahi ni ban wani yarda da ƴan aikin nan ba, son samu ma duk ki saita musu hanya kiyi aikinki ke ɗaya, mene abin wahala anan, haka kawai ƴan aikin yanzu da suke ƙwace maka miji". ita dai Fillo jinta kawai take bata ce mta komai ba, tun sakkowarsu Yami ke bin su da kallo har suka ƙaraso suka zauna kan kujera, Fillo ta sauko ta gaishe da Yami, ita dai Yami sai kallonta take yi cike da nazari da son gano wani abu, kuma cikin hikima ta iyaye manya ta fahimci abin da yake faruwa ba tare da ko ta tambayi Fillo ɗin ba, ai kuwa nan da nan Yami ta shiga yi ma ta nasiha sosai, da ƙara koya ma ta dabarun riƙe miji gam a tafin hannu, ita dai Fillo ji kawai take yi, don ba ta tunanin zata aiki ko da abu guda indai akan Turaki ne. lokaci ɗaya Fillo ta sake, su Yami su ka ɗebe ma ta kewar da take ciki, hira sosai kamar sun shekara ba su haɗu ba, tana ta zumuɗin za ta ji muryar Ummi ta tambayi Yami wayarta tace ai ta lalace, ɗoki da murnar da take ciki duk sai taji sun gushe, har la'asar su Yami su na nan ba su tafi ba. su na cikin kallo Turaki ya shigo, ita ta fara kai kallonta kansa, haka kawai sai taji gabanta ya faɗi, tayi saurin ɗauke idonta a kansa ganin wani kallo da ya yi ma ta fuskarsa a tamke. ya shigo ya zo ya gaida Yami, suka gaisa sosai tana sanya masa albarka tare da yi musu adu'a sannan ya wuce sama. bayan tafiyarsa Yami ta kalli Fillo ta ce da ita,"ban ji kin yi masa sannu da zuwa ba, ba ki tashi kin karɓi jakar hannunsa ba, duk lafiya?". ta turo baki gaba tana faman ɓata fuska, ai kuwa Yami ta shiga yi ma ta faɗa sosai kamar zata duketa. "ta shi ki bi bayan mijinki". murya a kumbure ta ce,"ai sai kun tafi zanje Yami". tai maganar alamarta na shaida ko sun tafi ɗin ba zuwa zata yi ba. Yami ta taso mata da faɗan da yafi na ɗazu, ba shiri ta miƙe kamar zata yi kuka ta wuce sama fuuu, tana hawa ta shige ɗakinta, sai kuma taji kamar Yami zata hawo saman, hakan yasa tai saurin fitowa ta wuce ɗakinsa. ta buɗe ƙofar ta shiga babu ko sallama, ta nemi bakin ƙofa ta maƙale tana jan yatsu sai kace munafuka, Turaki ya buɗe idanuwansa da ke rufe ya bi ta da kallo, ƙwayar idonsa kawai za ka kalla kasan akwai abin da ke damunsa, akwai abin da yake buƙata sosai, ta ɗago ido karaf suka haɗa ido da shi, sai ta saurin juya masa baya, ya miƙe zaune da ga kishingiɗen da yake ya ce,"is there anything?". ta juyo tana turo ba ki gaba cike da zallar yarinta tace masa,"Yami ce ta ce na biyo bayan ka". babu shiri murmushi me kama da dariya ya suɓuce a leɓensa, sai ya tallafi haɓa yana kallonta kawai, ganin hakan yasa ta ɗan duki ƙafafu a ƙasa ta ce,"ce tayi ka kira min Ummi a waya". sai ya ɓata fuska ya mayar da kansa jikin pillow yace,"ba ki faɗa mata kin tarwatsa wayar ba?". kamar zata yi kuka ta ce,"ai na faɗa maka bana sa ne". "to sai ki jira sai kin gyaro sai kiyi kiran". kawai sai ta saka kuka tana faɗin,"to wayan naka ai ba guda ɗaya ba ne, dan Allah ka bani in kira Ummina, yau kwanana 9 banji muryarta ba fa". ya galla mata harara, banda tana kuka tsab sai tayi dariya saboda yacca idanunsa suka yi a hararar, ta ƙara dukan ƙafafu a ƙasa da shagwaɓa sosai tace,"don Allah ka ba ni kaji, to ni ka bani lambar sai inje wajen Baba me gadi ya ara min tasa". ya kasa ɗauke ido akanta, sai yaji tana cewa,"kuma kai fa kace za ka zame min kamar Abba nah". sai ya sauke numfashi ya ce,"zo ki ɗauka". ta taho kamar wadda ta yiwa ƙasa laifi, tana zuwa bakin gadon taga duka wayoyi biyun akan bedside locker har ma da keypad, tana kallon wacca ta fasa ta gane ta, kenan an gyara ma shi ne yake ta yi mata ciwon baki, ta ɗan waigo kaɗan ta kalle shi taga hankalinsa bai kanta, sai ta kai hannu zata ɗauki wayar, caraf taji ya riƙo hannunta ya janyota jikinsa ya zaunar da ita kan ƙafafunsa da ke tankwashe. "da kika fasa ai ba ki iya ba da haƙuri ba, shi ne saboda rashin kunya yanzu an gyara za ki zo ki ɗauka, to ba ni sai kije can wajen me gadi ya ara miki". ta shiga kokawar ƙwace hannunta tana faɗin,"to ai kaine kace in zo in ɗauka". "ehh ai ƙarshen rashin kunyarki zan gani kuma na gani, ba ni wayata ba zan bayar ba, kije shi me gadin ya ara miki tunda dama wajensa kike zuwa aron abu". ta ce,"to ka ban lambar". kawai ya fizge wayarsa sannan ya ɗauketa daga kan ƙafar tasa ya dire a ƙasa, yasa wayoyinsa a aljihu yay shigewarsa toilet, after 3 minutes ya fito yana goge hannu da ƙaramin towel, mamaki yasa shi tsayawa yana kallon Fillo da ke durƙushe ta kifa kai akan gadon tana kuka bilhaƙƙi, yau rana ɗaya da ya tambayi kansa shin hawaye basa ƙarewa ne?, ko da yake in su na ƙarewa ai da tuni ya sami salama da wannan kukan, ya girgiza kai ya koma toilet ya mayar da towel ɗin sannan ya fito. ya dawo ya koma kan gadon yay kwanciyarsa ya juya ma ta baya, taji yana waya yana cewa,"oak gani nan, ki ajiye ki wuce, na bawa Samha saƙonki". ta ɗago kanta lokacin da yake sakkowa akan gadon yana barin ɗakin, ta bi bayansa da kallo, after few minutes sai ga shi ya dawo ɗauke da basket ɗin abinci, ya wuce ya ɗora akan table, sannan ya zauna akan kujera ya shiga zuba abincin da ke cikin flask, duk tana kallonsa yadda yake yi tamkar bai san da halittarta a ɗakin ba, ita kuma tana yi ana yana shareta shi yake daɗa tunzurata, hakan na ɓata ranta, har ya kammala cin abincin bayan ya tsarga masa ya taso ya dawo kan gadon, yay kwanciyarsa kamar mai bacci. can yaji ta riƙo hannunsa, ya juyo yana kallonta, ta kifa goshinta akan hannun nasa, hawayen idonta ya sauka akan fatarsa, ɗumin hawayen ya wuce ta cikin jijiyoyinsa har zuwa ƙirjinsa, tausayinta ya wanzu a zuciyarsa, gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, Allah ma ya sa ni yana tsananin tausayinta, basarwa kawai yake yi, ko shi da yake namiji ba ya jin zai iya ɗaukar 2days bai ji muryar Mum da Maama ba, balle har akai ga kwanaki tara, ai sai rashin lafiya ta kama shi. but sai ya ƙara ɗauke kansa akanta, ya tamke murya ya doka mata tsawa yace ta fitar masa a ɗaki, ta miƙe jiki a sanyaye kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki ta fita, kai tsaye ƙasa ta koma wajen su Yami fuskarta duk caɓe caɓe da hawaye, sai da taje ta tarar su har sun wuce, sai ta dawo ta koma ɗaki ta rufo ƙofa, ta hau gado taci gaba da kukan gado. sai bayan fitarta Turaki yaji gaba ɗaya bai kyauta da abin da yay mata ba, ko babu komai mahaifiyarta take ta roƙon ya kira mata, duk sai yaji ransa babu daɗi, kasa daurewa yayi ya ta shi ya bi bayanta, a dunƙule ya ganta a tsakiyar gado, ya girgiza kai ya ƙarasa ya hau kan gadon gaba ɗaya. ya ɗagota zuwa jikinsa ya kewaye yana ɗora haɓarsa a saman kanta, yasa hannu yana goge mata hawayen fuskarta, ya shiga hura mata iska a kunne yana faɗin,"cry cry Baby what the cry for umm?". cikin kukan ta ce,"ba kai ba ne". ya ce,"OMG! laifin me nayi da har ya sa kike kuka?". tana motsi a jikinsa kamar zata shige jikinsa gaba ɗaya ta ce,"ba kai bane sai kake yi min tsawa bayan ka san bana so". yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace,"to ai kece Fulani nah ba kya ji, duk yanda na so nai controlling anger na akanki sai kinja na ɗaga miki murya, phone ɗina fa kika fasa min da abubuwa masu muhimmanci a cikinta, but shikenan daga yau insha'Allah ba zan ƙara ba in dai tsawa ce". ya faɗa yana ɗago kanta daga ƙirjinsa ya ɗora goshinsa akan nata, ya hura iska a idonta suka lumshe yace,"shikenan?". kamar jiran tambayar takeyi ta girgiza masa kai da sauri tana cewa,"a'a". ya buɗe ido yana kallonta da shirin jin abin da yake tsammani, but sai yaji saɓanin haka. "ka bani haƙurin kukan da kake ta saka ni to, har ma da ciwon da kaji min". ba shiri ya tsura mata ido yana kallonta, sai yau ya ƙara ganin yarinyartarta ta fito sosai, ya ƙara tabbatar da muguwar rigimammiya ce, bakinsa yaƙi rufuwa da murshin da yake me haɗe da mamakin halin rigimarta. tana buɗe ido suka sarƙe a nasa, sai kawai ta tsuke fuska ta kai masa duka a ƙirji tana mayar da kanta ta kwantar, ya shafo gashinta yana cewa,"ni ne zan baki haƙuri ko da wani daban kike?". "kai ne mana, ai kaine kaji min ciwo, kuma kake min tsawa, kuma kake sa ni kuka, kuma kake share ni". ya ƙara ɗago kanta yana kallonta ya ce,"duk ni ɗaya!, to yanzu tsakani da Allah ba ki ji kunyar cewa in baki haƙuri?, ke fa kika fasa min waya me tsada, ni bance ki ban haƙuri ba sai ke". ta zumɓura baki ta ce,"to ai kaine ka janyo na fasa ban sa ni ba". "ni kuma?". ta ɗaga masa kai kawai. "to da nayi mene na janyo?, sharri kika fara?". sai kawai ta ƙura masa ido, kukan da ya tsaya ya dawo sabo, ya kwanto kanta jikinsa yana faɗin,"subhanallah!, ni kam naga ta kaina, Fulani wai me yasa kuka ba ya miki wahala?, wallahi Allah bana son hawayenki its hurts me alots amma kinƙi ganewa. kin ga ni dai yanzu mu bar ma zancen in dai kuka za kiyi, kin min laifi na miki laifi kowa ya rama anyi 1-1, yanzu dai mu shirya don ranar yau ba zata wuce ba sai anyi sulhu". ta kamo gaban rigarsa ta riƙe har sai da maɓallin ya cire, a hankali tace,"ni ba zan shirya da kai ba sai ka bani haƙuri". ya shafo wuyansa ya ce,"ya zanyi, bada haƙuri ai ba zai sa na ragu da komai ba, kiyi haƙuri". ta ɗauke hannunsa daga bayanta ta ɗago tana kallonsa, a shagwaɓe ta ce,"ba'a haka ba". sai ya lanƙwasar da kai yana kwaikwayon shagwaɓarta ya ce,"to a ya ya?". "ka kama kunnenka sai ka sakko ƙasa ka tsuguna". ganin bai da niyyar yi yasa ta juya masa baya tana faɗin,"to kayi tafiyanka kawai". ta faɗa tana sakin kuka kaɗan. wannan kukan ya sa shi saukowa ƙasa ya durƙusa, ya kama kunnensa da hannu ɗaya sannan ya kamo ɗayan hannunta ya ce,"to look at me mana". ko da ta juyo ta gan shi sai ya kusa bata dariya ganinsa ya koma kamar ɗan yaro. ya sarƙe yatsunsu wuri ɗaya wanda hakan yasa ta jin wani abu ya tsarga ma ta, shi kuma ya lumshe ido ya buɗe sannan ya ce,"we should ask for forgiveness if we make a mistake, I made a mistake and i am asking for your forgiveness, and i know you will forgive me, please am sorry for all my wrong deed, am so sorry Fulani Nah, promise you not to repeat such a mistakes insha'llah". kamar ya ƙara tunzurata sai hawaye sha, ya dafe kansa yana faɗin,"ya Allah! what again Fulani nah?, Is there anything else you want me to do after this?, ko kalar ba da haƙurin ne bai yi miki ba na sauya?". ya faɗa duk a ruɗe dan Allah shaidarsa ko kaɗan ba ya son irin wannan kukan nata, yana taɓa zuciyarsa, kawai dai dan babu yacca zai yi ne ma yake dakewa ya nuna kamar bai damu da ita da lamarinta ba, amma can ƙasan zuciyarsa shi ɗaya ya san me yake ji. cikin kuka sosai kamar zata shiɗe ta ce,"don Allah...". sai kuma tayi shiru ta kasa ƙarasawa. yay saurin komawa kan gadon ya riƙe hannayenta duka biyu cikin nasa ya ce,"don Allah what?, say it please, i am ready to do whatever you want". sai ta faɗa jikinsa tayi masa tight hug ta ce,"don Allah kar ka auro Aisha, bana sonta kar ka aureta don Allah, kace baka sonta, i will do whatever you say, but for Godsake don't marry her". he took a deep breath closing his eyes ya ce,"wacece Aisha?". "wadda kace zaka faɗawa Baffa zaka aureta". "when did i say that?". "ranar da ka ji min ciwo, kana faɗawa abokinka zaka aureta wai kana sonta, har na fasa maka waya bana sane, kuma ni bana sonta don Allah karka aureta". ya cika bakinsa da iska ya fesar, ashe plan ɗinsa yayi, ya shiga shafa gadon bayanta da gashin kanta in a romantic way ya ce,"the crying is enough, kinga ba ki da lafiya". tana sassauta kukan ta ce,"to ka fasa auren nata?". ya ce,"ba zan iya fasa aurenta ba". "saboda me?". ta faɗa tare da fashewa da sabon kuka tana zamewa daga jikinsa. "saboda tana so na, ni kuma ina so na auri wacca take so na, kuma tunda tana so na idan na aureta zanji daɗi, zata ke yi min duk abin da nake so, zata kiyaye ɓacin raina, ba zata barni da yunwa ba, zata ke yi min soyayya me daɗi. to kuma kinga yanzu ke ɗaya ce matata, ke kuma ba kya so na balle duk kiyi min wancan abubuwan...". bai ƙarasa ba ta katse shi,"who told you i don't love you?". "ke fa kika faɗa a gaban su Baffa ranar da nace na aureki, kuma ma fa har kika dage sai na sakeki, to ni bana so in takura miki shiyasa zan aureta saboda ina so in zauna da wacca take so na". sai kawai ta ƙara faɗawa jikinsa ta ƙanƙame shi tana faɗin,"Allah ina sonka, kuma zan ke yi maka koma menene, but don Allah kar ka auro ta". ya janyeta ajikinsa yana faɗin,"ba zan iya ba fa, Aisha tana so na sosai, ba zan iya butulce mata ba, kiyi haƙuri". lokaci ɗaya tari ya sarƙe Fillo, ta dafe ƙirjinta da take jin yana yi mata mugun zafi kamar ana hura wuta, ta damƙe hannunsa ƙam jikinta sai shaking yake yi, hawaye tamkar an buɗe famfo, abu kamar wasa kan gadon sai ya ɗauki rawa kamar yanda jikinta yake yi, sai juyi take yi da kanta tana sosa ƙirjinta da yake yi ma ta wani mugun zafi. Turaki ya ruɗe ya kamota, yanda yaga tana yi da ƙirji da yacca numfashinta ke neman yankewa sai ya tuna da maganar doctor na heart failure ɗin ta, hankalinsa ya tashi ya shiga ambaton innalillahi yana kiran sunanta, ya kasa janyota jikinsa saboda yacca ta sarƙafe, ta riƙe hannayensa sosai ta tsayar da ƙwayar idonta akansa, hoton yacca za su dinƙa shairing ɗinsa su uku ne kawai take hangowa cikin idon nasa, kamar ba zata iya jurar ganin faruwar hakan ba, kamar gwara ta mutu, kamar gwara ya rabu da ita kawai. "Fulani nah, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". maganar yake yi a kiɗime, ya sauko akan gadon ya bar ɗakin, ɗakinsa ya nufa cikin hanzari ya ɗauka drugs ɗinta da ya siya ya ajiye su safe gudun ɓacin rana, ya ɓallo ya buɗe bakinta ya zuba ma ta, sannan ya shiga tayata shafa ƙirjinta da take ta cewa zafi. a hankali taji ta fara samun relief, sai ta kai hannunta gefen fuskarsa ta kama tana faɗin,"Allah ina sonka, i am saying this from the bottom of my heart". ya shiga ɗaga ma ta kai yana faɗin,"yes i know, na fasa auren Aisha, ba zan aureta ba na yarda kina so na, kuma za ki min ko me nake so". ta sa babban yatsanta a gefen bakinsa ta ce,"i love you much, but ai kai baka so na, ka daina so na, kana sa ni kuka da yawa". yana murmushi ya kamo hannunta ya ɗora a ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa ya ce,"i wish i had the chance to open my heart to you, you would have seen that you are the only one inside without anyone else, kece fa zaɓin Muhammad Turaki, kuma zaɓin Hajiya Madina, kuma zaɓin Hajiya Ramla". sai ya tattaro ta jikinsa ya rungume tsam,"Fulani nah i promise to you insha'Allah zan saka ki murmushi more than yadda na saka ki kuka, ki kwantar da hankalinki babu wata Aisha da zan auro, wasa nake yi, i say it just to see your reaction". sai ta janye a jikinsa tana tsayawa da kallonsa as if she have never seen him before, har yaushe ya gane tana kishinsa da ya nemi yay wasa da rayuwarta haka?, duk yacca ta ke ɓoyewa da ma sai da hakan ya bayyana ta wani ɓangaren bata sani ba, sai ta tura baki gaba zata kau da fuska yay saurin saka hannu ya tare hakan, ya marairace yana kama kunnensa ɗaya kamar a ɗazu ya ce,"am so sorry ƴar lelen gidan su Zaytun, ki ce kin haƙura kar Hajiyoyin gidan Alƙali su ƙara min tsinin goshi da remote". daga ita har shi murmushi suke son yi but kowanne sai ya cije, ta kai yatsanta kan goshinsa tana shafa ƙullutun wajen da bai baje ba har yanzu, sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya, wanda hakan shi ma ya sa shi dariya, yana kama hancinta yaja. "kayi sabon ido a goshi". yasa haƙori ya ciji hancinta,"zan rama ne akanki". Sai kuma ya kwanta itama ya kwantar da ita a jikinsa yace,"shikenan mun shirya?, an daina kukan?, an daina min tsiwa an daina share ni?, an mayar da aurena?". ba tayi magana ba kawai ta ɗaga masa gira, yace,"thank you". ya faɗa yana shafa sajenta ita kuma tana so ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. bakinsa a saitin kunnenta yace,"to sai yaushe kuma". a hankali ta ce,"what?". ta faɗa yana jin saukar ɗumin iskar bakinta akan ƙirjinsa, wanda ya nemi ya haifar masa da kasala, jin yay shiru ta ƙara tambayarsa, sai ya sosa gefen fuskarsa yana faɗin,"just forget, not now". ya mirgina yana riƙe da ita a jiki yace,"ke yanzu da na baki takarda kawai sai kika ɗauketa as divorce paper?". kunya ta kamata ta ce,"to ai na ɗauka idan aka bawa mace farar takarda sakinta aka yi". yana wasa da hancinta ya ce,"tunda kin ɗauka ai sai ki sauke...oya bani labarin kukan da ki kai tayi, duk da na san rabi kukan shagwaɓa ne, to sauran rabin na mene?, na son Turaki da kishinsa ko na mene?". tasa tafin hannu ta rufe masa baki da ido, sannan ta ce,"i want sleep". ya sauke hannun da yake kan idonsa sannan ya ɗora nasa hannun akan nata da ke bakinsa yace,"its after 4 babu kyau baccin yamma". ta shagwaɓe tana cewa,"ɗan kaɗan zanyi". bai ce komai ba ya ɗora kanta a ƙirjinsa, take kuma bacci ya ɗauketa, da kukanta da baccinta suna ba shi mamaki, abu ne da duk basa yi mata wahala, ita dai shekarun ne kawai da ita but komai da take yi na ƴan 4-5years ne. ya kamo hannun da ke da ciwo zai warware bandage ɗin sai yaji ta motsa, hakan yasa ya ƙyale yaci gaba da looking at her innocent cute face. [9/7, 00:35] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *51* sai da aka fara kiran sallar magriba tukunna Turaki ya iya zame Fillo daga jikinsa, sanin cewa ba sallah zata yi ba kawai yaja blanket ya rufeta, yay kissing forehead nata sannan ya fita, yana zuwa ɗakinsa yay alwala ya wuce masallaci. a masallaci ya zauna har sai da akayi sallar isha'i tukunna ya dawo, for the first dawowarsa gida bai wuce ɗakinsa ba kai tsaye, bedroom ɗin Fillo ya wuce, yana shiga ya tarar har yanzu bacci take yi, ya girgiza kansa yana mamakin irin baccinta. durƙusawa yayi a gaban gadon yana yaye blanket ɗin ya kamo hannunta, ɗayan kuma yana shafa fuskarta sai kallonta yake yana murmushi, fuskar baccin nata kaɗai ya isa ya shaida maka rigimammiya ce, haɗe gefen fuskarsa da tata yayi, ya lumshe idonsa for some minutes ya buɗe, yasa hannu yana jan hancinta yace,"Fulani nah baccin ya isa haka". ta buɗe idonta a hankali, cikin baccin da yake cinta ta dube shi ta mayar da murfin idon ta rufe tana juya masa baya. murmushi yay ya miƙe tare da hawa gadon ya cicciɓeta ya fita da ita zuwa ɗakinsa. direta yay a ƙasa yana kama hannayenta ya ɗaga sama, sak irin yacca akewa ƙanan yara idan za'a tashe su, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta kalle shi tana sakin kukan shagwaɓa,"ni fa bacci nake ji". ya rumgumeta yana kwaikwayon muryarta shi ma yace,"ni kuma i want you to wake up, kin barni ni ɗaya i feel lonely, ki tashi ko rigima ce muyi". haka yay ta damunta har sai da ta wartsake tukunna ya ƙyaleta, ya kama hannunta suka isa wajen gado, ya zauna a gefe yana ƙoƙarin ɗorata a saman cinyarsa sai taƙi, taƙi zaman becose she is not feeling comportable saboda period ɗin da take ciki, tana jin ma kamar tayi staining. "mene amfanin ƙafafun nawa idan ba ki zauna akai ba?". ta ɗan kauda fuska tace,"ɗaki zanje". yaja hannunta har sai da ta juyo ta kalle shi yace,"nan ba ɗaki ba ne?". "to ai toilet zan shiga". ya miƙe tsaye yana faɗin,"nan ma ai akwai toilet ɗin, muje let me escort you". ya faɗa yana kama hannunta zuwa toilet, sai ta maƙale a bayansa taƙi shiga, ya janyota zuwa gabansa yana kallonta, ta kifa kai akan cikinsa tana cewa,"ni toilet ɗina ba wannan ba, ina so zanyi wanka". ya ce,"nan ma ai ana wankan". tasa taɓara,"ni ba wannan ba to, nawa zanje please leave me". ta faɗa tana ta maƙalewa a bayansa, bai kulata ba ya buɗe toilet ɗin suka shiga ciki duk da faman tirjewan da take yi, tana kallo ya kunna ruwa a bathtube har sai da ya cika sannan ya dawo da idonsa kanta, su na haɗa ido ta ɓoye fuska a bayansa, ya juyo da fuskartata yana cewa,"kiyi wankan anan". sai ta shiga dukan ƙafafu a ƙasa cike da kukan shagwaɓar da ke neman juyewa zuwa na gaske tace,"to ai..". ya katse maganartata ta hanyar ɗora yatsansa saman lips ɗinta,"ba na son musu, kiyi anan nace". tayi narai-narai da idanu hawaye na sakko mata tace,"to ai zan ɗauko abu ne". bai kulata ba ya janyo towel ya bata,"ko kiyi da kanki ko nayi miki". ta saurin karɓa ba tare da ta yarda ta kalle shi ba. "zan ɗauko miki ko me kike buƙata". ya faɗa yana sakin hannunta, yana ganin yacca take ɓata fuska, bai tsaya sauraronta ba ya fita ya rufe mata ƙofar. tana ta faman ɓata rai tayi wankan, idonta duk ya taru da ruwan hawaye ƙiris yake jira ya zuba, ita fa kawai saboda ya kira mata Umminta ta yarda suka shirya, shi ne zai wani kawota toilet ɗinsa yace tayi wanka. sai bayan ta gama wanka ne sannan ta ɗaga towel ɗin zata ɗaura, sai ta gan shi ɗan ƙarami sai kace ɗan kwali kwatan yadi, idonta ya haska mata tana fita da wannan ɗan ƙaramin abun shi kuma yana ɗakin a zaune, sai kawai ta turo baki gaba tana kifa kai da bango ta saka kuka. sai da tayi me isarta tukunna ta ɗaga ido tana ƙarewa toilet ɗin kallo, daga jikin hanger ta kalli wani towel ɗin da alama ma sabo ne, bathtube ɗin ta taka ta ɗauko shi, ta sauke ajiyar zuciya dan ya fi wancan da ya bata abin arziƙi, kuma sai da ta ɗaura taga shima bai yi ma ta ba, taji kamar ta kurma ihu acikin toilet ɗin, sai kuma tsoro ya kamata babu shiri ta nufi ƙofa ta buɗe ta fita kanta a ƙasa. Turaki na zaune saman gado yana facing toilet ɗin, da ma jiran fitowarta yake tun ɗa zu, Nihal na ƙasa tana jiransa yaƙi fita. tun da Fillo ta ɗago ido tai masa kallo ɗaya sai ta maƙale a inda take, taƙi yarda ma ta kalle shi, ta rumtse ido tana yunƙurin juyawa ta koma toilet ɗin taji yace,"ki na komawa zan sa nepa su ɗauke wutarsu, ni kuma na fita na bar miki gidan". babu shiri ta dakata, ta rumtse ido sosai tana baro ƙofar toilet ɗin cikin tafiya me kama da sauri, dan duk ya saka ma mata tsoro, sai da ta kusa zuwa kusa da shi sannan ta tsaya ta rasa ya zata yi, ita ba zata iya zuwa wurinsa a haka ba, ta ɗaga kai ta kalli ƙofa tana tunanin fita, tsoronta ɗaya ne kar ta fita a ɗauke wutar da gaske. shi dai kallonta kawai yake yi from head to toe, towel ɗin jikinta ko rabin cinyarta bai kai ba, siraran santala santalan fararen cinyoyinta duk a waje, breast ɗinta masu cika tsayayyu sun taso ta saman ɗaurin towel ɗin, ashe duk sirantarta ce take ɓoyesu a cikin kaya, but tana da su masha'Allah daidai misali, ya lumshe idanunsa yana sauke doguwar ajiyar zuciya, lokaci ɗaya hankalinsa ya nemi ya tashi, yasa hannu ya shafa fuskarsa yana kawar da abun da ke neman hargitsa lissafinsa. muryarsa ta fito a hankali sosai yace,"zo ki zauna". ya faɗa yana mata nuni da kusa da shi, sai taƙi yarda ta kalle shi balle ma ta zauna kamar yanda yace, gaba ɗaya sai yaji yana neman ya kasa jurewa, hakan yasa shi miƙewa ya nufeta. da sauri kuwa ta juya zata koma toilet ɗin ai ko yay saurin ruƙo hannunta, riƙo ta ɗin da yay towel ɗin jikinta ya kunce ya kusa zamewa, babu shiri ta tafi zata sunkuya but sai ya hanata hakan ya kama bakin towel ɗin ya ɗaure mata da kansa, ta fashe masa da kuka tana janyewa,"ni ɗakina zan tafi". bai saurari abin da take faɗa ba ya haɗeta da jikinsa yana hugging ɗinta very tight, ya ware duka five fingers ɗinsa a gadon bayanta, gently yake shafa very soft skin ɗinta, lokaci ɗaya yaji yanayin jikinsa na sauyawa gaba ɗaya, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa yana neman lips ɗinta ya haɗe da na shi ya tsotsa, kamar wanda aka tsikara kuma sai ya fasa ya ɗago kansa yana girgizawa, ya buɗe idanuwansa da suka fara rinewa yana kallon yacca duk jikinta ya ɗauki rawa sai kuka take yi masa a hankali. ya sarƙe yatsunsu wuri ɗaya yana ɗora goshinsa a nata goshin, murya a kasalance yace,"sorry". ta gyaɗa kanta kawai tana ce masa,"ni ɗakina zan tafi". ba tare da ya buɗe idonsa ba yace,"bana so ki tafi, ki zauna anan yau muna tare". sai ta buɗe ido tana kallonsa, yanayin yanda yake maganar kamar ba muryarsa ba. bata san lokacin da bakinta ya suɓuce da tambayarsa,"menene?". a sannan ya buɗe lumsassun idonsa ya kaɗa ma ta kai,"nothing". ya faɗa yana sauke numfashi,"me za kiyi a ɗakin naki?, ko can zamu koma?, ni bana son zama ni ɗaya". tana ƙifta idanu ta ce,"tsoro kake ji?". ya ɗaga mata kai alamar ehh tare da cewa,"da kika shiga wanka naji kamar za'a kama ni". sai ta turo baki gaba ta ce,"ba wani nan". ya matsa hannunta ya ce,"me kike nufi?". ba ta ce da shi komai ba sai kare ƙirjinta take yi da ɗayan hannunta. yana riƙe da hannunta suka isa bakin mirrow, ya zaunar da ita akan stool, ita dai sai kallonsa take ta cikin mirrow ɗin yanda yanayinsa ya koma kamar na mara lafiya, ya ɗauko lotion ɗin da yake shafawa ya ajiye mata, baya tunanin zai iya aikin shafa mata dan za'a iya samun matsala, ba yanzu yake so komai ya kasance ba, zai ci gaba da daurewa zuwa lokacin da ya ɗaukarwa kansa. ta ga ya bar wajen ya isa gado ya ɗauko babban kwalban humra ya jiye a saman mirriow ɗin, tafin hannunsa a saman haɓarta ya juyo da fuskarta yana ma ta nuni da kan gado ya ce,"your dress". sai kawai ta bi kayan da ido kafin ta gyaɗa masa kai, ba tare da ce komai ba, kuma ba tare da ta kalle shi ba. tana kallonsa ya fice daga ɗakin jiki a saɓule kamar mara lafiya ko wanda aka yo aiken mutuwa, duk sai taji kamar yana neman bata tausayi, ko me akayi masa oho?. sai da ya fita sannan ta iya ɗaukar man ta shafa, tana mita ƙasa-ƙasa ta ɗauki humrar ta shafa, kawai yaje ya ɗauko mata sabuwa alhalin ga buɗaɗɗu nan har guda uku a ajiye, tana gama shafawa ta wuce kan gado, tunaninta ɗaya pant da pad, kuma da mamakinta tana ɗaga kayan sai ga pad ɗin haɗe da sabon pant, wata uwar kunya ta lulluɓeta, yaushe ma ya san tana period ɗin?. tana murguɗa baki ta shiga toilet ta saka, garin ɗauko brezier ɗinta ta zame ta faɗa cikin bathtube ɗin ta jiƙe, ta rumtse ido kawai ta fito bayan ta shanya, cikin sauri ta ɗauki kayan ta saka gudun kar ya dawo. tana saka rigar taji kamar ta kurma ihu, ya san kuwa kayan da ya ɗauko mata?, ita kam bata jin zata iya saka kayan nan alhalin yana nan, duk rigar tayi transparent, kuma iyakar gwiwarta fa, hannun ma irin na vest, kuma ma ko ya haɗo mata da brezier, sai kawai ta doki ƙafafu a ƙasa da ƙarfi kamar tiles ɗin sun mata laifi. ƙofa ta nufa zata fita sai dai tana zuwa taji ƙofar a rufe ya saka key ta waje, ta cije leɓen ƙasa ta juya ta koma toilet ɗin, ta ɗauko brezier ɗin sai dai ba zata saku ba don sosai ta jiƙe. fitowa tayi tana hawaye, gado ta nufa ta durƙushe a wajen ta kifa kai tana kuka, can jimawa taji an buɗe ƙofar, bata ko ɗago ba dan ita haushinsa take ji, shi ma kuma da ya shigo ɗin kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, ya wuce ya ajiye basket ɗin abincin dake hannunsa, ya fito da cooler ɗin ciki ya ajiye akan table. bakin gadon ya dawo ya zauna, ya ɗagota ya ɗaurata saman cinyarsa tare da zagayeta da hannayensa ya ce,"kukan na menene?, me Fulanin Turaki ke so?". ta ɗago da kanta, tana matse idanu tamkar baby ƴar 2years ta ce,"ni ɗakina zan tafi". ɗan murmushi yayi yace,"naji to za ki koma can ɗin but tare zamu tafi ko?". tai saurin girgiza masa kai, ya ƙara cewa,"why?". "to ai kaima ga naka, kowa ya zauna a nasa ai". ya buɗe ido yana kallonta sosai kafin ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana shaƙar ƙamshin humrar da ke fita a jikinta. da wani irin murya yace,"to ni yau tsoro nake ji, ba zan iya kwana ni ɗaya ba, in kin yarda na bi ki ɗakinki, na yarda ko a ƙasa ne zan yi shimfiɗa, but please karki tafi ki barni ni ɗaya bana so wani abun yazo ya kamani, ba zan iya ƙwatar kaina ba". Fillo ta dinƙa kallonsa kafin ta ce,"kai ne ɗin kake jin tsoro?". ba tare da ya ɗago kansa dake kafaɗarta ba ya ɗaga mata kai kawai. sai kawai ta tsinci kanta da kama hannunsa ta ce,"to amma jiyan nan ai kaine ka kori abun da yake biyo ni". "to ai jiya kika ce, yau indai yazo to sai dai ya cinyemu dukanmu, kuma da ma jiyan ma ai ƙarfin hali nayi na zama jarumi saboda bana so wani abu ya taɓa ki". tayi shiru ba ta ce masa komai ba, ya ɗago kansa ya kalleta ya ce,"shikenan ma kawai, zan tafi gidan su Bello". ta kalle shi suka haɗa ido ta girgiza masa kai da sauri, sai kuma ta sauke idonta ƙasa tana jan yatsunta. "ai dare yayi yanzu". hannu yasa ya ɗago haɓarta ya ce,"look in to my eyes". sam taƙi sai ma ido da ta daɗa rumtsewa. idanuwansa na neman lumshewa ya zura hannunsa cikin rigarta, tana jin hannunsa a ciki tayi saurin buɗe ido ta zabura zata miƙe ya riƙeta, flat tommy ɗinta ya shiga shafawa yana faɗin,"na san wannan shafaffan cikin na buƙatar abinci ko?". magana yake yi duk yay wani collapse. ta ɗaga rigar ta fito da hannunsa tana cewa,"ni ka bari". yay knooding ma ta kansa, ɗaukarta yay zuwa kan kujera ya ajiyeta, ya buɗe cooler ɗin abincin, nan da nan ɗakin ya karaɗe da ƙamshin ƙwai. ta bisa da kallo a sanda yake ɗauko plate ya zuba soyayyar doya da ƙwai da kuma miyar souse, bayan ya gama zubawa ya juyo ya fuskanceta, da hannunsa ya ɗauki doyan ya kai bakinta. "wa ye ya dafa abincin?". taji bakinta ya suɓece da yi masa tambayar. "Zaytun nasa ta kawo mana, i know ba ki da lafiya, and ba ki iya girki ba, so na roƙeta alfarmar take dafa abinci tana kawo mana before na kai ki catering school ki koya". ta tsuke fuska tana kallonsa ta ce,"ni ce ban iya girki ba?, wancan ranar da na dafa indomie ai kace na iya dafawa". ya ce,"amma ai bance yayi daɗi ba ko?". ta turo baki gaba ta kauda fuska gefe,"Allah na iya girki nima, kuma ka tambayi Maama kaji, Baffa ma da yaci wainar masar da nayi sai da yace yayi daɗi Allah yay min albarka, Adda Zaytuna ma indai zata yi baƙo in tana asibiti tana sawa nayi mata, kuma ka tambayi abokinka ɗin kaji, kuma ma ka tambayi Kaka kaji tun ina ƴar ƙarama nake yin girki". ya dinƙa kallon bakinta yana murmushi, har tayi shiru bai yi magana ba, jin shirunsa yasa ta juyowa tana kallonsa ta ce,"Allah na iya girki". ya rufe ido ya buɗe ya ce,"ai tun kina ƙarama kika ce". tai saurin cewa,"a'a nufina tun ina ƴar ƙarama nake yi, ko time ɗin ma da muna masarauta ina yi". "ohhh yanzu kenan ke babba ce?". kamar jiran tambayar take yi ta ɗaga masa kai, murmushinsa me sauti ya fito yana cewa,"to ni ban ga girman ba, you are still a Baby in my eyes, dan haka ni ba zan ci abinci ƴar ƙarama ba babu daɗi, rabi ya dahu rabi bai dahu ba, ko yay ta ƙauri, ko a cika gishiri". su ka haɗa ido ta haɗe gira waje ɗaya ta murguɗa masa baki, yasa yatsa ya ɗalle bakin nata. "oya ba rigima na ce ba, abincin za'a ci, buɗe bakin". saboda yunwar da take ji ta buɗe bakin tana karɓa, sai da ya gama bata sannan ya matso kusa da ita sosai, ya ce shi ma ta ba shi hannunsa ya gaji zai karye, yay ta narke ma ta yana koma ma ta ƙaramin yaro, da taƙi ya ta shi zai bar wajen yana cewa ya fasa kira ma ta Ummi ɗin, babu shiri ta ɗauka plate ta kamo hannunsa ya dawo ya zauna ta shiga ba shi, kuma yaƙi yarda ta ba shi da spoon dole sai hannu ta saka, duk kaiwa ɗaya sai ya cije hannun nata, har ta gama ba shi bata yarda sun haɗa ido ba kanta na ƙasa, sai dai tana ta murmushin da ta rasa dalilinsa. duk yanda Fillo ta cije ta noƙe akan ba zata bi shi toilet ba sai da yaja ta suka tafi tare, da kansa yay mata brush, sannan shi ma yay nasa, su ka fito yana ɗauke da ita rungume ajikinsa, ita kuma tayi laƙwas ta lafe a jikin nasa kamar mage, ya wuce yay switching light off sannan ya kunna deem light, tukunna ya wuce kan gadon, ita dai duk sai kunyarsa take ji. ko a kan gadon ma a jikinsa ya kwantar da ita, murya can ƙasa ya ce,"Fulani nah". ta ce,"uhmm". ya shafo gashin kanta da yake jin laushinsa da santsinsa na shiga jikinsa ya ce,"mu bari sai Allah ya kaimu gobe sai a kira Ummi ko?". ta girgiza kai da sauri,"a'a yanzu dai". "to ai dare yayi, kar tayi tsammanin wani abu ne ya faru". kamar zata yi kuka ta ce,"ni dai don Allah yanzu". ya sauke numfashi ya ɗauko wayarsa ya bata, ta miƙe daga jikinsa tana cewa,"remove the password". looking at her eyes da suka koma sexy ya ce,"your name". ta tsaya kallonsa kafin ta ce,"Halima?". ya girgiza kai,"no, the other one". "Fullo?". nan ma girgiza ma ta kai yay, ta shagwaɓe ta ce,"to which one?". daidai kunnenta ya ce,"cry cry Baby". fuska a tsuke zata yi magana yasa hannu ya rufe bakin, ita kuma taƙi saka sunan da ya faɗa, ai ta san bata kai wannan matsayin ba, dan haka sai ta saka sunayensa duka biyun bai yi ba, ta sa na Mum da na Maama duk bai yi ba, tasa na Zaytun shi ma bai yi ba, da ga ƙarshe kawai tasa yanda ya faɗa ma ta ɗin shi ma ta ga bai yi ba, tana sa Fulani Nah taga ya buɗe, kuma da tsantsar mamaki sai taga hotonta akan wallpeper, hoton da ba ta san da shi ba, kuma ba ta san lokacin da ya ɗauke shi ba, dan bacci take yi ya ɗauka, mutum dai in yana bacci muni yake yi amma ita kanta ta san tayi kyau, sai kawai fuskarta ta washe da murmushin da ya bayyana haƙoranta. ta kalle shi ta ga idanuwansa a rufe kamar ya yi bacci, a hankali ta ce,"ai ban san lambar Ummin ba". ya buɗe idonsa da bacci ya fara fizgarsa ya ce,"Ummi nah". yana faɗa ya mayar da idonsa ya rufe, kamar kuwa yanda ya faɗa ɗin gaban Ummi sai da ya faɗi da taga shigowar kiran, ta ɗaga wayar tana karawa a kunnenta cike da jin nauyi na sirikinta da kuma fargabar abin da zata ji, duk da cewa duk bayan kwana biyu yana kiranta su gaisa, but ba'a irin wannan lokacin ba, ta ƙara duba agogo taga ƙarfe goma har da ƴan mintuna. "Ummina". "na'am Autata". Ummin ta amsa tana sauke numfashi, sai yanzu taji ta samu natsuwa. da murna sosai haɗe da farin cikin jin muryar mahaifiyartata ta ce,"Ummi nayi kewar ki sosai". "ni ma haka Autata, ya kuke?, ina fatan duk kuna lafiya?". sai kawai Fillo ta saka kuka tana faɗa ma ta ita dai tana so ta ganta, haka Ummin tai ta fama da ita tana lallashinta, sun jima su na wayar, dan hira sosai suka yi, har Kaka ma sai da suka gaisa da ita, tace akai wa Dada su gaisa, Ummi ta ce ai tayi bacci yanzu. "Ummi to yaushe za ki zo?". ta ce,"yau kwananki nawa Autata?, ko 2weeks fa ba ki yi ba, ki bari sai an kwana biyu zan zo in ganku kinji, hope babu wata matsala ko?". ta girgiza kanta kamar tana ganinta ta ce,"to Ummi ba za ki dawo nan ɗin ba?". ta ce ma ta,"su Dada sun hana, muna nan sun riƙe mu ni da Dadana, an bar mana ɓangaren Kakarki, ba ki ga ba an gyara mana shi sosai yayi kyau, har ƙaton enlargement ma akayi mana aka kafe a parlon, da hotona da na Abbanku da naki da na Hamid, duka aka haɗa yayi kyau sosai". Fillo ta sauke numfashi tana jin soyayyar Umminta da kuma kewar Abbanta ta ce,"Ummi ina zuwa zan ɗauke shi Allah". Ummi ta ce,"ba zan bari ki ɗaukar min nawa ba, sai dai ki roƙi Hamid ya ba ki nasa, shi ma ya saka a ɗakinsu". da haka suka ci gaba da wayar har sai wajen sha ɗaya saura sannan suka yi sallama, sukai sallamar cike da kewar junansu. ta riƙe wayar a hannunta tana ta kallon hotonta, so take alallai sai ta tuna ranar da yay hoton, iyakar fuskarta ne kawai da wuyan balle idan taga kayan jikin nata ta iya tuna ranar. but kan gadon yay mata kama da ɗakinsa na can gida, its like kamar ma ranar da ta kwana a ɗakinsa ne. a hankali ta juyar da kanta tana kallonsa, zatonta ko bai bacci ba, sai taga yana sauke numfashi alamu ma ya jima da yin baccin. hannu ta miƙa ta ajiye wayar a inda taga ya ɗauko, sannan ta kwanta tana barin tazarar 4inches a tsakaninsu, taji ta kasa rufe ido tayi bacci, taji kamar tana buƙatar wani abu daga gare shi, ganin da alama yay nisa a baccin ta sami damar ƙarewa kyakykyawar fuskarsa kallo, tana jin wani abu me kama da sonsa tsantsa na taɓa zuciyarta. laɓɓanta suka tale da wani kyakykyawan murmushi, abu ɗaya ta sani yanzu shi ne tana sonsa, idan tace ba haka ba tayi ƙarya, and ta yaudari kanta, but ba zata iya cewa ga rana ko kuma lokacin da ta fara sonsa ba, idan har ma ta faɗi hakan to tayi ƙarya. kallon fuskarsa kawai take yi tana jin tamkar kar ta daina, tamkar yay ta baccin ita kuma tai ta kallonsa babu ƙifcen ido, ta tuna wata rana, ranar da ta fara tambayar Maijidda, _kin san wani Turaki a gidan nan?._, kuma amsar da Maijiddan ta fara ba ta ita ce,_ wani kyakkyawa ne ajin farko, in kyawun kowa na fasaltuwa nasa ba zai fasaltu ba, don ko kyau da kansa yay ƙaryar yace zai iya faɗin kyan Turaki._ amsar da Maijiddan ta bata kenan, kuma haka kawai sai taji haushin maganar a yanzu, wanda ta san ba komai ba ne face kishi, sai ta yamutsa fuska tana ɓata ranta, haka kawai duk ya bari kowa ya gama kalle kyansa ita an bar mata saura. ta rufe ido tana so ta sami sassaucin zafin da taji zuciyarta nayi ma ta, kafin ta buɗe ƙwayar idonta ta sauka akan gashin kansa, baƙi wuluk da shi, kwantacce kamar na larabawa, cikin ɗan hasken ɗakin sai sheƙi yake yi, sai taji tana sha'awar ta taɓa taji kalar sulɓinsa, ta ɗaga hannunta a hankali zata taɓa sai ta fasa, gudun kar taje ta taɓa ya buɗe ido ya kamata. ta mayar da kallonta kan pink lips ɗinsa, ƴan daidai da su masu ɗaukar hankali, a iya kallon kawai ta shaida masu taushi ne. ta rufe ido ta kai yatsanta ta taɓo lips ɗin a hankali, tana taɓawa tayi saurin ɗaukewa tana rufe fuskarta kamar wadda ya kamata tana taɓawar. sai da ta ɗauki kusan 3mints idonta a rufe, tana jin kamar ta kuma taɓawa taita shafawa lips ɗin, tana buɗe idon kallonta na sauka akan ƙirjinsa da ya wadatu da kwantacciyar gargasa me kyan naɗewa. sai taji tana buƙatar ta taɓata itama, tayi nisa a kallon chest ɗinsa, ba tayi aune ba taji muryarsa yana faɗin,"you want to hug me right?". ba ta san lokacin da ta waro idanu waje ba, ta kalle shi tai saurin kulle ido tana ɓoye fuska ajikin pillo, yay murmushi yasa hannu ya matso da ita kusa da shi a kunnenta ya ce,"stop being shy, hug me the way you want, i am all yours". ta tura baki tana jin kamar tayi kuka tsabagen kunya, ya sa hannunta a bayansa but ta kasa rungume shi ɗin duk da tana so tayi hakan, sai kawai ya ƙara matso da ita sosai ya ɗora kansa saman shoulder ɗinta, in a cool voice yace,"lets sleep". ta ce,"ai bana jin baccin". "but yo want to touch this right?". ya faɗa yana kamo hannunta ya ɗora akan ƙirjinsa, da sauri ta rumtse idonta jin wani abu ya ratso tun daga babban yatsanta har tsakiyar kanta. "oya ki ta shafawa baccin zai zo, or should i bring cumb kiyi masa kitso?". zata juya masa baya ya hana hakan, sai ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, har yay bacci bata yi ba, sai da yay nisa sosai sannan ta shiga wasa da gashin ƙirjin nasa tana kuma shafa lips ɗinsa. *After 3Days.* ƙarfe shida da rabi a lokacin, Fullo ta sauko daga upstairs, english wears ne a jikinta, riga white sai skirt baby pink, sai hular chantaly itama pink colour, tayi kyau sosai acikin shigar. ta dubi parlon taga an gyara shi sai ƙyalli yake yi, duk da cewar da ma ba wai da datti yake ba, but ko ya wuri dai ya samu gyara kyau yake ƙara yi. wucewa tayi ta kunna burner ta zuba turaren wuta, nan da nan kuwa parlon ya karaɗe da ƙamshi, ta kunna tv tasa karatun ƙur'ani sannan ta wuce kitchen, tana tafiya kamar ba zata taka ba. yau da kanta take so tayi girki, kullum sai dai yasa Zaytuna ta dafa ta kawo musu, ta san akwai gajiyawa kawai dan ma dai ya haɗu da ƙanwa me biyayya ne, and kamar yanda ba zai iya cin abincin ƴan aiki ba haka ita bata tunanin zata barsa ci, ba ma ta fatan Allah ya kawo ranar da zai ci abincinsu. a kitchen ɗin ta sami Hannatu na feraye dankali, ta amsa gaisuwar da take yi ma ta da murmushi. "har kun tashi da wuri haka?, sannunku da aiki". Hannatu ta amsa ma ta da yauwa tana barin ferayar ta miƙe,"Anty akwai wani abu ne?". Fillo tayi ma ta wani kallo ta ce,"ni kam wai ba zaku bar faɗa min wannan sunan ba?. Hannatu ta ce,"ai Anty sai dai kiyi haƙuri gaskiya, amma ba zamu iya faɗin sunanki ba gatsal, ai in muka yi haka munyi rashin kunya, ke fa uwar ɗakin mu ce". ta gyaɗa kanta kawai ba tare da tace komai ba, Hannatu ta ce,"jiya na zo ɗakin naki da daddare na tarar kin rufe ƙofa, kin manta ba ki faɗi abin da za'a dafa da safe ba, sai Sakina ta ce taji kamar kince a soya dankali da ƙwai". ta ce,"in dai zaku ci dankalin ku dafa kawai, amma karku sa da mu". Hannatu ta dinƙa kallonta, so take ta fahimci wani abu, don kwana biyun nan ma sai gulma suke na rashin saukowar da bata yi, shi ma kuma me gidan baya fita, in sun ga ya sauko to masallaci zai wuce, har Sakina na cewa ta rasa uwar da suke yi a saman sai su wani koma kamar matattu, in banda ranar nan ma da akai baƙi taga sun sauko, har Fillon ta yini a ƙasa, sai shi da yake saukowa daukar abincin da ake kawo masa ya koma, wanda hakan ke ƙona musu rai, ba su san me ake nufi da su ba, ba su taɓa yin girki sun ci ba sai dai su dafa suci au kaɗai. Tunanin Hannatu ya tsaya cak sanda taga Fullo ta fito daga store hannunta ɗauke creat na ƙwai, ta tafi da sauri zata karɓa Fillo ta hanata tana faɗin,"bar shi Hannatu, kici gaba da aikinki". ta ce,"ai Anty da kin bari munyi aikinmu, ke da ba ki jima da tashi daga rashin lafiya ba". Fillo tayi murmushi kawai bata ce ma ta komai ba, ta ajiye ƙwan ta koma ta ɗauko semovita, shi ma ta ajiye sannan ta nufi friedge ta buɗe ta ɗauko ingrediant ɗin da zata yi amfani da su, butter, shredded coconut, youghurt, lemon juice syrup da almond seed. su ma duk ta ajiye su wuri ɗaya kana ta buɗe drower ta ɗauko baking powder, sugar da veg oil. semolina Cake take so tayi, wanda larabawa suke cewa Basboussa, tana sonsa sosai, dan lokacin da suka je umara yawancin kullum sai taci, hakan ne ma yasa ta zage ta koya a wajen kukun da ke dafa musu abinci, kuma yau tana so tayi shi ko don Turaki yaci yaji daɗi, ya san ta iya girkin ƴan gayu itama, so take ya koma cin girkinta kawai, ta yanda ko gida yaje ba zai ci ba sai ya dawo zai ci na ta, ita bata son yake cin abin hannun kowa, nata kawai. duk ingredient ɗin ta haɗe wuri ɗaya, tasa mixer tai mixing sosai, ta ɗauko pan ta shafa butter ta juye kwaɓin kana ta yaryaɗa pealed almond seed, ta kunna oven tayi heating na ta for 1minutes sannan ta saka aciki in 180 degree. tana nata aikin Hannatu da Sakina suna yin na su, sai dai su na hira tare, musamman da taji su na hirar ƙauyen su Maijidda, ta dinƙa tambayarsa wasu wurare da ta sa ni lokacin da suka je suka kwana biyu acan. 30minutes na cika ta ciro Basboussa ɗin, ta nemi flask da zai riƙe zafinsa, tana tuna yanda Zaytun ke yi idan zata saka kayan baking acikin flask sai ta saka tissue saboda kar gumi ya jiƙa sama da ƙasansa. ta dafa herbal tea shi ma sai tashin ƙamshi yake yi, in 45minutes ta kammala haɗa break fast ɗin da take ganin idan Turaki yaci sai kunnensa ya kusa tsinkewa, har hango shi take yi tana murmushi, suka gama aikin kusan a tare da su Sakina, lokacin har 8 ta kusa, su ma ta basu Basboussa ɗin sukai ta godiya, sannan ta saka wani a ƙaramin bowl ta bawa Hannatu tace ta haɗa a breakfast ɗin Baba me gadi ta kai masa. babban tray ta ɗauka ta jera breakfast ɗin su ta wuce da shi upstairs, dan ba ma ta so su zauna cin abinci a parlo su Sakina su shigo, ita yanzu duk ji take yi da ma ba'a kawo ma ta su ba, da ma can ɗin da take yin murnar zuwansu zaman kaɗaici ne yasa, har da Bello ya tambayeta a kawo su tace masa ehh. akan table ta ajiye, ta kunna turaren wuta a ɗakin, ta ƙarasa bakin window ta haɗe cuttons da suka rabu hasken ya ratso ta ciki yana haske fuskar Turaki, ɗakin sai ya koma deep. bakin gadon ta zauna tana kallonsa, da alamu ko motsawa bai yi ba tun da ta fita, dan yacca ta fita ta bar shi haka yake, sai taji tausayinsa ya kamata, cikin kwana ukun nan raba dare yake yana aiki a computer, jiya ma ƙarfe goma na dare Bello da Khaleel suka zo suka ɗauke shi suka je company, sun sami matsala da wani companny na lemu da suka haɗa partnership da su, su na neman su yi musu asarar over 10millions, ga shi basu sanar da Baffa ba gaban kansu kawai suka yi, dan ya hana su haɗa hannun jari, ita ba ta san ma lokacin da ya dawo gidan ba, duk da har 12 tana zaune tana kallo a laptop ɗinsa da ya tafi ya bar ma ta. fasa tashinsa tayi, ta fita ta koma kitchen, ta buɗe drower ta ɗauko ƙaton plastic bucket, ta buɗe shi ta ɗebi garin ciki. garin kunu ne na haɗin su alkama da gyaɗa da sauransu, wanda yake gyara jiki yasa kumari, shekaranjiya da Nuratu matar Dr Yusuf suka zo ta kawo ma ta shi, ta ce ta dinƙa damawa tana sha safe da yamma, kuma babu ranar fashi, ta gargaɗeta akan karta kuskura tayi wasa da shansa yana da amfani sosai ajikinta, dan akwai wasu sinadarai ma da aka ƙara ma ta akai. tai murmushi da tuna tsiyar da suka dinƙa yi ma ta, wai in taci gaba da zama haka ƴar duma dumar amaryarsa na dawowa zai mance da ita, sai kuma suka shiga faɗa mata abubuwan da taji duk sunwa kanta girma, Nuratu har da cewa tace ya siya ma ta waya domin akwai zafafan abubuwan da zata ke turo ma ta ta whatsapp, yanda take da kishiya dole ne sai ta miƙe tsaye, ta cire kunya ta jefar a gefe, ta buɗe idonta ta waye ta zama ƴar gari, ita dai duk bata ce musu komai banda ma kunya da ita rinƙa ji. tana gama damawa ta juye shi a flask, ta ɗebi iyaka wanda zata sha a silver cup me ɗan girma, dan sosai take jin daɗinsa musamman in yaji uban madara. yanzun ma madarar ta zabga masa kamar tayi magana, ta wuce ta ajiye shi akan ƙaramin dining ɗin dake nan kitchen. tana cikin wanke hannu a sink taji kitchen ɗin ya karaɗe da ƙamshin Turaki, ta lumshe ido ta zuƙi ƙamshin tana aduar Allah ya dawwamar da ita da wannan ƙamshin, ba tare da ta juya ba taci gaba da wanke hannunta, sai wani daɗi take ji yana ratsata, so take ta juyo ta kalle shi but tana jin nauyi, ta ɗauki kitchen towel tana tsane ruwan hannunta. jinsa tayi ya rungumeta ta baya yana sarƙe yatsunsa a saman shamulallan cikinta da yake kamar silifa. Ya ɗora haɓarsa saman kafaɗarta yace,"good morning". ta sauke idonta akan hannunsa da ke kan cikin nata ta ce,"morning". murmushi ya yi me sauti, ya juyo da ita yana kallonta, ya shafo fuskarta ya cire hular kanta, hannunsa cikin gashin kanta yana yamutsawa ya ce,"you look so take away". tayi murmushi ta ce,"thank you but a little". sannan ta bisa da kallo, three quarter ne ajikinsa pink sai t-shirt white, kamar ya san shigar da tayi itama, yana yi ma ta kyau sosai idan ya saka kayan, yama fi kyau a cikinsu fiye da manyan kaya idan ya saka, duk kwana ukun nan da yake zaune a gida su yake sakawa. ya hure ma ta ido da iskar bakinsa, tasa hannu tana rufe fuska saboda kunya, ya ɗauke hannun yana tambayarta,"what are you prepairing for me?". ta ɗan kalle shi tayi ƙasa da kanta ta ce,"only you?". ya lukuce hancinta,"to na gyara, for us". ta buɗe hannu ta ɗaga kafaɗa ta ce,"i dind't cook anything, am waiting for you to wakeup". "then...". "then you cook for us, me i don't know how to cook". ya ce,"really?". ta kalle shi ta ce,"you forget what you said?". ta ƙwace hannunta ta wuce dining ta zauna, yana murmushi ya bi bayanta, akan table na dining ɗin ya zauna yana kallonta, ya kamo hannunta guda yace,"so now what should i eat? i am feeling hungry". ya faɗa murya a marairaice. ta juya ƙwayar idonta tare da buɗe hannu alamar ita ma bata sa ni ba. sai kuma ta ce,"kuma Maama ta ce yau kar Adda Zaytuna ta kawo abinci gidan nan". ta faɗa da sigar tsokana, hakan yasa shi yin ƴar ƙaramar dariya. ta kalle shi ta ce,"ohh you did'nt agree?". sai ya kasa ɗauke idonta a kanta yana murmushi kawai, yana jin wani shauƙinta na shigarsa, komai nata da abunda take yi abun burgewa ne, ita kuma ta gyaɗa kai tana ƙara cewa,"shikenan zaka kalla in Adda Zaytuna za ta kawo abinci ko ba zata kawo ba". ya maida hannunsa saman gashinta ya ce,"then we all stay hungry". ta kalle shi ta ce,"ai ni ina da abincina". ta faɗa tana janyo cup ɗin kunnun ta ƙara juyawa. "what is this?". ya tambaya yana karɓar cup ɗin hannunta. ta buɗe hannun alamun ba ta sa ni ba, ya dinga kallon kunun yana yatsine fuska, kamar abun amai, ganin yacca yake yi da fuska ta miƙa hannu tana faɗin,"give me, da ma Anty Nuratu tace ni ɗaya banda kai". ya janye yana cewa,"to mene wannan ɗin data ba ki za ki sha?, kalla fa ba kyan gani". ta marairaice tana cewa,"ni to ka ban kar ka haramta min, kunu ne fa". ya ƙara kallon kunnun yana kanne ido kamar wanda ke kallon kashi ya ce,"wannan ne kunu?, haka ake dama kunu da ma?". ta shiga kokawar karɓa tana cewa,"ni dai ka ban kar ka haramta min, a haka nake son shan abuna, kai da ba zaka sha ba daɗi ya barka, kuma ko wataran ba zan sammaka ba". ya riƙe duka hannayen nata biyu acikin nasa guda ɗaya, ya dinƙa kallon kunun, for some seconds ya ɗauke idonsa akai ya kalleta yace,"da gaske shan wannan abun za ki yi?". kai kawai ta ɗaga masa tana tura baki gaba,"please ka ba ni kar ya huce". why not ba zai sha abin da zata sha ba duk kuwa lalacewarsa?, in har zata sha wannan ƙazantar da yake gani shi ma zai sha ko da after ya sha zai yi amai. sai ya kai cup ɗin bakinsa, tayi saurin riƙo hannunsa tana cewa,"is too hot, use spoon". ya riƙe hannunta da take ƙoƙarin riƙe shi, ai kuwa yana sha yay saurin dire cup ɗin saboda ƙona masa harshe da yay, ya diro daga kan table ɗin yana rumtse ido tare da zuƙar iska a cikin bakinsa yana,"sshhhhh". Fillo ta rikice tana ce masa,"sorry". sai tayi saurin buɗe fridge ta ɗauko ruwan sanyi ta zuba a cup, ta kai cup ɗin bakinsa kamar za tai kuka sai sannu take jera masa. ya karɓi cup ɗin ya ajiye ya janyota jikinsa, cikin sauri ya haɗe bakinsu, kai tsaye harshenta ya lalubo ya zuƙo ya naɗe da nasa, kafin ya fara kissing ɗinta with passion, ya zura hannunsa cikin rigarta yana shafa flat tommy nata gently, karo na farko kenan a tsakaninsu, tuni kuwa jikinta ya ɗauki rawa ta fara ture shi, duk ta tsorata da yanda yake yi mata, sai da ya ɗauki kusan five minutes minutes a hakan sannan ya sakar mata baki yana sauke numfashi, Fillo ta ja da baya tana faman zare idanu kamar wacce tayi ƙarya aka kamata. Turaki ya kalleta yaga yacca take aikin raba idanuwa, ƙirjinta na up and down, su ka haɗa ido ya sakar ma ta wani makirin murmushi yana tambayarta,"its sweet?". sai kawai ta fashe da kuka ta juya ta fice daga kitchen ɗin tana faman doka ƙafafu a ƙasa, ya ɗauki cup ɗin kunun ya bi bayanta yana murmushi. [9/7, 00:51] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *52* samun ta yay a ɗaki ta kifa kai akan gado, da murmushi ya ƙarasa ya ɗagota, murmushinsa ya ƙaru a san da suka haɗa ido, ko ba komai ya ɗanɗana ma ta, kuma yacca ƙwayar idanunta suka sauya ya shaida masa zata buƙaci zumar nan ba da jimawa ba. ya ɗora hannunsa a chest ɗinta yana cewa,"me ya janyo wannan nishin?". "ni bana son abin da ka min". ta faɗa tana turo laɓɓa gaba. "me yasa ba kya so?, ko bakin nawa babu daɗi?". ya faɗa yana ɗan cizonta a kunne. sai ta ƙara jin kunya, ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, karatun da Nuratu tayi mata na yawo a cikin kanta, duk sai yanzu take jin maganganun su na yi mata nauyi. haɓarsa ya ɗora a saman kafaɗarta, ya kai hannunsa saman cikinta yana faɗin,"how many days wancan abun yake yi ya tafi?". ta ɗago kai tana kallon inda idonsa ke tsaye a wajen, ba ta ga komai ba hakan yasa ta dawo da kallonta gare shi ta ce,"wanne abu?". yasa bakinsa a kunnenta ya hura iska, hakan ya haifar mata da sake jin kasala, ta lumshe idanuwanta tana jin abun da bata san ko menene ba na tsikararta, a hankali ya ce,"your menstrual blood". ba ta ce komai ba tayi ƙasa da kanta, ya ɗago fuskarta aiko ta kulle ido, sai ya mintsineta a ciki da sauri kuwa ta buɗe idon tana kallonsa. "stop ignoring, answer me". "7days". ta faɗa tana kama gaban rigarsa. sai ya sauke numfashi ya kamata suka miƙe suka koma kan kujera. "ga abincin ki". ya faɗa yana ɗebowa da cokali ya kai bakinta. sai ta tura hannun da yake riƙe da kofin gefe ɗaya, tasa hannu a gefen bakinsa tana faɗin,"na gani". ya ɗan buɗe bakin sannan ya zaro harshen nasa waje, tasa yatsanta akai kafin ta fara hura iska akansa, ɗumin iskar bakin nata na ratsa shi. "ya daina zafin?". gira kawai ya ɗaga ma ta ba tare da yay magana ba, ta shiga tsakanin cinyarsa tana cewa,"ai sai da na faɗi maka da zafi". "but ai daɗin wannan yasa zafin ya gudu". ya faɗa yana nuna ɗan ƙaramin bakinta da ta tsuke. kunun ya shiga bata da kansa, wayarsa dake aljihu tayi ringing ya ɗauko, ya ɗaga kiran Khaleel yana amsa sallamar da yay masa. Khaleel yace masa,"Hammah naga har yanzu baka shigo office, by 11 fa visitors ɗin nan za su zo". Turaki ya sosa girarsa ya shafo fuskar Fillo yace,"Fulani nah kina so na fita?". ta buɗe ido tare da girgiza masa kai. ya ce da Khaleel,"tunda Bello yana nan ba sai na fito ba". Khaleel yace,"but Hammah there are some issues fa da ya kamata a tattauna da kai". "in dai Bello yana nan ka san kamar ina nan ne ko". Bello da ke jinsa ya karɓi wayar hannun Khaleel yana cewa da shi,"MT wanne irin iskanci ne wannan wai, duk ka tattara komai ka bar min kai ga me aure, to ni ɗan iska na zama kake nufi?, kasan irin baƙar wuyar da nake sha kuwa?, kullum sai nayi ciwon jiki, but Allah ya kai mu next month idan na bari wata ya ƙare banyi aure ba shege nake, sai in ga da wanda zaka yi". Turaki yay wata dariyar ƙeta yace,"kayi a this month shi ne zan san kai zuciya". Bello yay tsaki,"don Allah ka fito Malami, ka san dai kai ɗaya zaka iya duba wannan algorithsm ɗin ko?". jin yay masa shiru ya ƙara cewa,"zan kira Baffa na faɗa masa ba ka zuwa office kwatakwata". "idan ka fasa". sai kuma su ka koma serious akan zancen na su. Ya jingina kansa da kujerar yana murza hannun Fillo, idanunsa a rufe yana sauraren report ɗin da Bello ke karanta masa. ƙwaƙwalwarsa na jin komai daki-daki yana ajiye su cikin memory ɗinsa, lissafin komai yake yi acikin ƙwayar idonsa tamkar shi yaƙe karantawa, har sai da Bello yay shiru sannan ya buɗe idonsa ya ce. "me na faɗa muku before ayi accepting contract ɗin nan?, babu irin bayanin da banyi muku ba amma ku ka kasa fahimta. sai da na faɗa muku kar muyi trusting mutanen nan mu ɗauki maƙudan kuɗi haka mu ba su, amma Khalil na faɗin within 2 months za su biya mu namu percentage ɗin, yanzu ai ga shi nan  just in a month budget ɗin mu ya rushe, idan ka lissafa gaba ɗaya bai fi mu tashi da 25%, now who knows asarar da za'a ƙara yi nan gaba?, ina tsoron Baffa ya san da wannan issue ɗin wlh". Bello ya sauke nunfashi ya ce,"ka san me zai faru MT?, kawai a mayar contract ɗin nan ya zama rabin shekara. in ba haka ba wallahi asarar da zamu yi ba ƙaɗan ba ce". Turaki ya girgiza kansa,"kai ma kasan ba za su yarda ba, an riga an rubuta komai har nayi signing, if ace kun yarda da lissafin da nayi ba zan yi saurin signing ba". yay shiru yana rasa irin tunanin da zai yi. "yanzu me kake ganin za'ayi?". "we should wait till tomorrow". Sun ɗau kusan minti goma suna tattaunawa kafin Turaki ya kashe wayar. "Turaki menene?". Fillo ta tambaya bayan ya ajiye wayar, ganin yayi looking so worried. yaja hancinta har sai da tayi ƙara yace,"Turaki ba, shi ne sunana a bakinki ko?". "to ai haka ne sunan naka". ta ƙara cewa,"har yanzu ba'ai settling matsalan ba?". ya shafo fuskarta,"an kusa insha'Allah". "to kaje office ɗin ma na". "kin fi office buƙatata". tace,"to kar Bello ya faɗawa Baffa fa". "rabu da shi ba zai iya faɗa ba, ko ya faɗa zan cewa Baffa ke kika hanani fita". ta ɗago da idonta ta kalle shi, tsinin hancinsa ya sauka a gefen nata sannan numfashinsu suka haɗe waje ɗaya. ya sa hancinsa yayi grazing akan nata, sai taji da ma su tsaya a haka, a hankali yace da ita,"yunwa nake ji". "to ai Adda Zaytuna ba ta kawo ba". "na kirata ba ta da lafiya, and idan na cewa Maama akawo abinci za tayi ta min tambaya ne har taga ko kamar muna faɗa ne". "Allah sarki, shikenan yau baka da cin abinci". sai ya marairaice ya kamo hannayenta ya ce,"ba zan iya zama da yunwa ba". "to ai ƴan aiki yanzu sun cinye abincin". yay mata wani kallo,"ni zan ci abincin ƴan aiki?, oya miƙe kije ki sama min abin da zanci". tana ƙunshe dariya ta ce,"sai ka roƙe ni, ka ce don Allah Fulani nah". ya lanƙwasar da kansa, ya karkata kansa dab da kunnenta, ya sauke muryasa can ƙasa sosai yace. "Dan Allah Fulani Nah". sai kuma ya ɗauka cup ɗin da ta gama shan kunu ya miƙa mata yana faɗin,"wa yidi, sadaƙa, iya ko gaya ne ba miya, iya ko ɗan ƙanzo ne, iya ko ɗan ya ya ne, iya nayi barar ban samu ba, don Allah iya ki taimaka". Fillo ta ƙyalƙyale da dariya, tana jin daɗi da nishaɗi na ratsata, tana jin daɗin na mamaye kowanne lungu da saƙo na cikin kanta, ta zame daga jikinsa tana faɗin,"close your eyes, kar ka buɗe har sai na dawo". yay knodding ma ta kansa kawai a yayin da ya rufe, yana rufewa ta miƙe taje ta ɗauko breakfast ɗin da ta haɗa ta ajiye, ta zuba iyakar wanda ta san zai ci sannan tace ya buɗe idon, da ma tuni ƙamshi ya doki hancinsa tun kamin ya buɗe, ya sauke idonsa akan plate ɗin da ke ɗauke da cake ɗin, ya kalleta with suprise on his face yace,"wow who makes this delicious?". "am the one, kana ta bacci naje kitchen". ta faɗa tana saka fork ta gutsura ta kai bakinsa, aroma ɗin na sauka akan harshensa ya lumshe ido, kafin ya buɗe tasa masa mug ɗin dake ɗauke da herbal tea a bakinsa, ya kurɓa ya kuma lumshe ido saboda tsabar daɗi. bai san da gaske yake jin yunwar ba sai a yanzu da yaji wannan abin me ɗan banzan daɗi, ko da yake ta ce ma ta yana jin yunwa, yana so ne ta fara shiga kitchen yau dan ya hutar da Zaytuna, ashe already ma ta haɗa masa lafiyayyan breakfast ɗin da bai yi tsammani ba. sai ganinsa tayi ya sauko ƙasa ya tankwashe ƙafafu yana faɗin,"zan iya faɗowa daga kan kujeran". "saboda?". "ni dai dawo nan". ta sauko akan kujerar ta zauna kamar yanda ya zauna, ta dinƙa ba shi yana karɓa kamar ƙanƙanen yaro, yana ta zuba mata santi ita kuma sai dariya take yi, har da ɗauko pillow tayi masa kariya wai kar ya faɗa gefe, sai faɗa mata yake yi wai tunda yake bai taɓa cin wani abu me daɗin wannan ba, ko wanda Zaytuna ke girkawa ma babu daɗi, ita ba ta saka sugar yaji kuma taste ɗinsa ma kaman abincin ƴan koyo, zai bata shawara idan sun tashi aure ta zo ta koya. Fillo ta dinƙa dariya tana cewa sai ta faɗawa Zaytun ɗin. duk da ita ta ƙoshi sai da ya ƙara bata ita ma taci, wai wancan ba abinci taci ba ai, ya kama complain ɗin an kawo mata jagwalgwalo ita kuma saboda kwaɗayi ta kama ci. da rana suna zaune su na kallon pixx na ranar dinner kiran Mum ya shigo wayarsa, yana ɗagawa bayan sun gaisa tace masa,"gobe idan Allah ya kaimu zamu je taraba, Yaya Naja tayi accident zamu je dubata, so sai ku shirya har da ku zamu tafi, but ita Halima zata zauna tare da mu ne, zamu yi 7days acan". kaman wanda yaji mugun abu ya zabura wajen tambayarta,"Mum har ita za'a yi 7days ɗin?". Mum ta ce,"bayanin da nayi ne baka gane ba ko me?, nace maka har kai zamu tafi but zaka dawo ita zaka barmu tare da ita, nima ina so na shiga wurin families so duk zamu je da ita taga ƴan'uwa". yanayin Fuskar Turaki ya sauya, sam bai ji daɗin hakan ba, yay shiru kamar ba zai amsa ba sai kuma yace,"to Mum, by what time zaku tafi ɗin?". ta ce,"da sassafe mana, za'a fita da ita india ne aikin ƙashi za'ai ma ta, so ina so na samesu kafin tafiyan na su". "to Mum, mu zamu bi flight ne". ta ce,"duk yanda kayi. and ku shirya anjima kuje ku duba Boɗejo, bata ji daɗi ba ashe har kwana biyu". ya ce,"gobe kafin mu tafi ba sai muje". "anjima nace Babana, ko so kake ka jawo mana magana, da ma kowa yaje tana faɗa masa mun san bata da lafiya amma bamu je dubata ba, alhalin ba'a sanar mana ba, ka san Baffanku ba ya nan. to bana son fitina ka shirya kuje anjima mu ma yanzu can zamu wuce, ina nan ina fama da Madam, itama wai sai dai a bari sai gobe". ya amsa ma ta da to sannan suka yi sallama. ya kalli Fillo wacca ta fara lumshe ido akan cinyarsa yace,"Fulani nah ba kya gajiya da bacci ne?". ta ce,"naji kana waya ne". "to tashi muyi hira, bana son wannan yawan baccin idan ina nan, if na fita sai kiyi ta baccinki". ta miƙe zaune ya sarƙe yatsunsu yana cewa,"after la'asar zamu je duba Boɗejo, wai bata da lafiya". ta ce,"Allah sarki, me yake damunta?". "ban sani ba nima, kin san jikin tsufa". ta ce,"to Allah ya bata lafiya". kwanto ta yayi jikinsa yana janye wani silin gashi da ya hau saman leɓenta yana ƙoƙarin shiga bakinta. ta buɗe lumsassun idanuwanta da bacci ya fara cika su ta kalle shi, ƙwayar idonsa ya maƙale akan plumpy lips ɗinta, ya ɗora yatsansa a saman lips ɗin ya shafa, numfashin bakinsa da ya fito ya haɗe da tambayar da ya jefa ma ta. "wanne irin alawa kike sha?". "da ina shan kowanne". "yanzu fa?". "guda ɗaya nake so, ibon". "ɗan naira goman?". "yes ɗan goman, flavour ɗinta yana min daɗi sosai". "kaman flavours ɗin ta yana da yawa ko?". ta ɗaga kanta,"diffrent flavours, but na fi son pink one ɗin me ƙamshin strawberry". "tana sa ƙamshin baki ne?". ta buɗe hannayenta alamun itama bata sa ni ba, sai yay murmushi me faɗi bai ce komai ba, sai ta gyara zaman kanta a cinyarsa ta fuskance shi, ta kalli yanda yatsansa ɗaya ke nannaɗo jelar gashinta wanda ta fahimci yana son taɓa gashinta. tace,"kayi shiru?, ko alawan bai da daɗi?, ko in daina sha?". sai tayi shiru tana jin babu daɗi, zuciyarta na faɗa ma ta ko teste ɗin bakinta yaji babu daɗi shiyasa yay ma ta wannan tambayar, lura da sauyawan mood ɗin nata yasa shi tambayarta,"what?". tasa hannu ta rufe idonta sannan tace,"ya sa bakina babu daɗi ne?". "me ɗin?". ya tambaya. "alawan mana, na sha yanzu da safe ai". yay murmushi, ya lura jikinta har yay sanyi, sai ya ɗago da fuskarta yana sunkuyo da tasa halfway da lips ɗinta, sai yaga ta rufe ido gaba ɗaya, cikin sexy voice ɗinsa yace,"ni ba teste ɗin ibon nake so ba, teste ɗin ki kawai nake so, ina so duk sanda nayi kissing ɗinki to teste only you not ibon". idanunta a rufe tayi murmushi kawai, nan moment ɗin nasu yaci gaba da yi musu daɗi, musamman a ɓangaren Fillo, hirarsa yake ma ta me cike da tarin tambayoyi kala-kala, da suka haɗa duk detail na rayuwarta, tun daga yarinta har girmanta, abin da yake ɓata mata rai da wanda ke sakata a farin ciki, films ɗin da take so da wanda bata so, her favorite food and drinks, wuraren da ta taɓa zuwa a rayuwarta, da kuma places ɗin da take da mafarkin zuwa, ta yanda akai ta fara taimakonsa and so on. ita kanta ba zata iya tuna rana na ƙarshe da tayi magana mai yawan ta yau ba, ko murmushi tayi sai ya tambayi dalilin yinsa kuma sai ta ba shi amsa in ba haka ba yay ta ma ta cakulkuli. ƙarshen tambayoyin suka tsaya akansa, tana tambayarsa yaushe ya fara sonta?. sai yasa hannu ya rufe bakinta da cewa,"turn ɗinki ba yanzu ba, sai watarana, har yanzu ban gama nawa tambayan ba". tayi murmushi tana kama hannunsa ta ɗora saman chest ɗinta, ta ce da shi,"to a bar sauran tambayan sai zuwa gobe, yanzu ka ban labarin ƙiriniyan da ka yi da kana yaro". yay guntuwar dariya, ya fara bata labarin sokancin da yay sanda yana ƙarami, but daga lokacin da ya haɗu da best friend ɗinsa Bello shikenan ya zama sai adu'a. yana faɗa ma ta lokacin yana ɗan ƙarami ba shi da ƙarfi, wani class mate ɗinsa ya kama shi zai zane shi after an tashi a school, ya kasa ƙwatar kansa sai Bello ne ya zo ya tare masa, da ma akwai shi da siyan faɗan da ba nasa ba, har kuɗi yake bayarwa ya siya faɗa, akan siyan faɗa har abincinsa break ɗinsa yana bayarwa. shikenan daga ranar su ka ƙulla abota da Bello, kuma daga ranar shi ma ya zama me ƙarfi ya ko yi faɗa da ƙiriniya, sai da ta kai ta kawo ya koma kamar wanda ke aiki da battery, kuma duk saboda zama da Bello, Maama tayi ta tofa masa lahaula. duk friday Bello a gidansu yake yini, kuma shi Bello babu abinda ya iya sai shegiyar fitina da dambe, sai suje can field Bello yay ta koya masa yanda zai ƙwaci kansa in wani yafi ƙarfinsa, har ranar ya gwada masa yanda zai shaƙe wuyan mutum, Bello ya shaƙe masa wuya har sai da numfashinsa ya kusa ɗaukewa, kuma kamar wani Malaminsa ko Babansa Bello yace yaje yay ta practical, tun da yana da ƙanne yay ta gwadawa akansu, ai kuwa da daddare ya shaƙi wuyan Khalil zai yi assignment ɗin da Bello ya ba shi, Baffa kuwa ya tarfa shi yay masa ɗan banzan duka ya kulle shi a store, aciki ma ya kwana dan sai da safe Maama ta sato key ta buɗe shi, kuma a washe garin da suka haɗu a islamiyya ya faɗawa Bello, sai yace zai koya masa yanda ake ɓalle ƙofa in an kulle mutum, ko kuma da an kaishi ɗaki za'a kulle ya fice a sukwance tun kafin a rufe, har haura katanga duk tsayinta sai da Bello ya koya masa, da yacca zai ɗauko key ɗin mota ya fice daga gidan, har yana ba shi labarin wai shi a gidansu sai da ya fasa glass ɗin mota har biyu, Abbansa yazo dukansa ya ɗafe wuyansa yaƙi sakinsa. watarana sun tashi a school yasa driver ya wuce da shi gidan su Bello, ya koya masa duk kalar yanda zai tseratar da kansa, wata rana kuwa yaywa Granny laifi zata kullesa a ɗakinta yay sufa yabi ta ƙarƙashinta, garin kamo shi ta zame ta faɗi, Anty Sa'adah ta kama shi ta murɗe masa kunne har sai da ya saki fitsari a wando. yay shiru yace,"kin san Bello har cewa yay inyi kashi a fo sai in dangwala in rubuta sunana ajikin bangon ɗakin Baffa, in dai yake ni to baya so na...ai ko in faɗa miki ina yin haka washegari Baffa ya kaini Europe wurin Granny". Fillo ta dinƙa dariya har da riƙe ciki, shi ma ya shiga tayata dariyar kamar yanda take yi. ta kama hannunsa ta ɗora a saman ƙirjinta tana rufe ido, yayinda dariyarta ke juyewa zuwa sanyayyan murmushi, a yanzu ta ƙara yarda cewa Turaki yana sonta har cikin zuciyarsa, kuma ba ta tunanin akwai abinda zai canja hakan, tana ganin zallar soyayyarta fal a cikin idanunsa a duk sanda ya kalleta, duk da har yanzu da bakinsa zuwa kunnenta dai bai furta ma ta kalmar i love you ba tun bacin wadda ta gani a takarda. acikin kwanaki ukun nan kacal tana cikin wata duniya ne ta daban me cike tarin kulawarsa da tarairayarsa, ta daina jin tsoronsa dan ya bi ya kulle duk wata hanyar tsoronsa a gareta, ta saba da shi yanzu fiye da tunanin kanta ma, ta saba da hirarsa da yake cikin yi ma ta ko da yana cikin aiki ne, kamar yanda ta saba da jikinsa, dan duk wani motsi nasa cikin taɓata yake yi, ko akan laptop yake to hannunsa ɗaya na cikin nata, ko kuma ya ɗorata ajikinsa yay aikin a haka, haka in bacci ne tana manne a jikinsa. kuma yanzu duk ta san abubuwan da yake so da wanda baya so, dan a kwanaki ukun nan duk ya lissafa ma ta halinsa, ya faɗa ko mai da yake so ta dinƙa yi masa, kuma sai a yanzu ta fahimci ashe shi mutum ne me sauƙin kai in har ka fahimce shi. bayan sallar la'asar Fillo na zaune ita ɗaya a ɗaƙin Turaki, wayarsa ce riƙe a hannunta tana game, ta ajiye wayar tana ɓata fuska, Tunda Turaki ya fita masallaci bai dawo ba, wai Baffa yayi baƙi daga ƙauye sun zo ba su sameshi ba, shi ne yace yaje ya kula da su, gaba ɗaya bai fi minti goma sha biyar da fitar ba, amma duk sai take jin babu daɗi, ta san dai akwai ƴan aiki amma gidan duk sai taji yay ma ta girma, ba ta san ta saba da shi ba har haka ba, ji tai tana kewarsa sosai kamar tun safe ya fita ya barta, abu ɗaya kawai ta sani ba zata ji daidai ba har sai ya dawo. tun ɗazu tayi wanka but ta kasa shiryawa, so take sai yazo yayi mata choosing kayan da zata saka, cikin kwana ukun nan duk shi ke zaɓa ma ta kayan da take sawa, and ta lura ya fi son ƙanan kaya, amma yanzu fita za su yi, ba ta san waɗanda zai so ta saka ba a yayin da fitarsu za ta zama karo na farko. ta ɗau wayar tana jin kamar ta kira shi, sai dai bata so ta dame shi, duk da bai faɗa mata ba tasan shi ma hankalinsa na kanta. miƙewa tayi ta koma ɗakinta, ta buɗe wadrobe ta watso da duka kayan ciki, ta kama ƙugu ta tsaya tana ƙare musu kallo. ta ɗauki wata blue ɗin atamfa, tsaye tayi a gaban full body mirrow tana kara atamfar a jikinta tana kallon kanta, ta ƙara haske sosai alamun jin daɗi na ratsata, kuma idan tasa atamfar ma zata yi ma ta kyau sosai, sai tasa hannunta a kumatunta tana taɓawa, sai taga kamar ƙashin wajen ya fara komawa nama yana son cika wajen. a lokacin taji ƙarar buɗe ƙofa, tana juyawa idanuwanta suka sauka akan Turaki da ke gyara zaman hula a saman lallausan gashin kansa, fuskarsa ɗauke da wannan murmushin da yake tafiyar da tunaninta, baƙin boyel ne acikinsa ɗinki boda, yayi kyau sosai, sai taji kamar ta ɗauke shi ta kaishi can ƙuryar zuciyarta ta adana, ta yanda babu wani da zai dinƙa ganinsa, sai ita ɗaya tallin tal. Turaki ya gama gyara zaman hular tasa, ya ɗago ya kalleta, ya furta ya Ilahi a sanda ya lura da ƙwayar idonta. ya ƙaraso ciki da sauri, ya tsaya a dab da ita yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa biyu. "Fulani nah me ya faru?, me ya same ki?, me ya taɓa ki?". yayi tambayar duk a lokaci ɗaya, me shirin kaɗan kawai sai ta sa masa kukan shagwaɓa, cikin sheshsheƙar kuka tace,"ba kai ba ne ka tafi ka barni ni ɗaya, gidan duk babu daɗi yay min girma". "shhh...". yasa hannu yana goge ma ta hawayen a hankali, ita kuma tana ƙara narkewa da shagwaɓe masa. duk sai yaji zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya san tunda ya sabar ma ta da zama tare da shi yanzu dole ba zata ji daɗin zama ba idan ba ya nan. "i'm sorry Fulani Nah, ban san zan jima har haka ba da ban fita ba sai in aika Sameer kawai, sai da naje naga ashe wai wata gona za'a ba su, kuma ba su faɗa min ba har sai da na dawo gida na duba takardar gonar a cikin takardun Baffa, ina ta sauri but kin san lamari irin haka dole yana ɗaukan lokaci". ya faɗa yana sa hannunsa a bayanta yana zagaye ɗan ƙaramin ƙugunta da shi, sannan a hankali ya ƙara raɗa ma ta,"am sorry, kin haƙura?". har sai da ya tabbatar zuciyarta ta nutsu sannan ya a hankali laɓɓansa su ka sauka akan cheeks ɗinta. sannan ya shiga tambayarta me yasa bata shirya ba, Mum na ta yi masa waya tun ɗa zu, idan ba su je yau ba za'a sami matsala. ta ce,"ni ban san kayan da zan saka ba ai". a lokacin taji sautin murmushinsa kafin ya saketa, closet yaje ya zuge ya buɗe ɓangaren da abayas suke jere a jikin hanger, ya ɗauko wata orange colour da tasha uban adon stones a jiki. "na ɗi son abaya akan atamfa ko less". ya faɗa yana ajiyewa akan gadon sannan ya kamo hannunta ya kaita gaban dressing mirro ya zaunar da ita kan stool, da kansa ya ɗauka body lotion ya shafa ma ta, ita dai kallonsa kawai take ta cikin madubin, kamar ba asalin Turakin da ta sani ba, ya ɗauka powder ya rambaɗa ma ta, taita dariya, ganin zai mayar da ita dodanniya tai saurin karɓar form ɗin ta gyara powdern. ba ta yarda ya saka mata brezier ba kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi, ta karɓa ta shiga toiler ta saka da kanta, tana fitowa ta tarar baya nan, sai ta ɗauki rigar ta saka, abayar ta ƙara haska fatar jikinta da tayi fresh, tayi rolling mayafinta, sai ta zama kamar balarabiya, kamar ba wannan Fillon da ke yawo cikin tsumman kaya ba shekarun baya da suka wuce, wannan wata Fillo ce ta daban, wacce ake rainonta cikin so da kulawa, wacca ake nuna ma ta babu wata tamkarta, wacca ta shigo cikin sahun masu ji da ado da ƙwalisa. ta ɗauko ƙaramar jaka kalar kayan, duk sai taji ta ƙosa Turaki ya dawo ya ganta, tana tsaye tana ta kallon kanta a madubi, tana tunanin duk ranar da akace ta ƙara kumari kuma ya zata dawo kenan saboda tsabar kyau?, sai ta tuna irin wankan da Raudha ke yi a saudiya idan zasu fita, tafiya tayi ta ɗauko wani box ta buɗe ta ɗauko glass ta saka. tana shirin fita yay daidai ta buɗewar Turaki ya sanyo kai, turus yay ya tsaya yana kallonta tun daga sama har ƙasa, laɓɓanta suka tsuke fuskarta na bayyanta murmushin jin daɗi. tana jiran kalman yabawa su fito daga bakinsa sai taji yace,"ina za ki a hakan?". ya faɗa annurin fuskarsa na ɗaukewa, bai bari tayi magana ba ya wuceta ya shiga ciki, binsa tayi da kallo taga ya ɗauko hijabi, babu shiri ta juya zata fita yay saurin damƙo hannunta. "babu abin da za ki fita a haka, da igiyoyin nawa uku reras akanki za ki fita a haka saboda an faɗa miki bana kishinki?". "to mene a wannan shigar?". "abubuwa da yawa kuwa da zasu ja hankalin wani ɗan banzan a kanki, ko ba kiga yanda kika yi kyau ba ne?". ta juya idanu tare da yin fari tana cewa,"ai baka ce nayi kyan ba". ya ce,"idan nace zan tsaya faɗa miki yacca kika yi kyau ba zamu samu damar fitar nan ba, dan duk lokacin za su tafi ne ba tare da na gama fayyace miki irin kyan da kika yi ba. oya ta ina zan zan cire wannan pin ɗin?". ta marairaice da cewa,"please ka bar ni a haka, wa ye ma zai ganni to bayan a mota zamu je?". sai kuma ta ɓata rai tana cewa,"wai ma ba gidan su me wancan part ɗin za mu ba?". ya kalleta yaga yanda ta wani ci kunu tamkar ba ita ba, yace,"can zamu sai aka yi ƙaƙa?, sai aka ce a gidan su babu maza ko babu masu idanu?". ta ɗan murguɗa baki,"sai ba zan dankama hijab naje gidansu ba tayi tunanin ni ƴar ƙauye ce wadda bata waye ba, ka sa aita gulmana idan mun baro gidan". "su waye za su yi gulman naki?". "ko ba tayi ita da muƙarrabanta ba za tayi ita da zuciyarta, don Allah ka barni in je a haka kar ta raina ni". dariya ta ba shi, but sai ya gimtse yana ɓata nasa ran shi ma, ta durƙusa tayi pleading hannayenta tana yi masa magiyar ita ya barta ta tafi a haka, a ƙarshe dole ya haƙura ya barta, sai dai bai yarda tasa glass ɗin ba ya zare shi yay jifa da shi, ya kama hannunta su ka koma ɗakinsa ya ɗauko facemask ya saka ma ta. "kuma saura idan munje in ga kin wage baki kina dariya ko murmushi...". tun bai ƙarasa faɗar abin da zai ce ba tace,"yanda zata ji daɗin cewa zaman ƙunci nake yi da kai ba, ni dai kawai babu ruwanka da ni ka bini da ido kawai". ya buɗe baki da mamaki fal yana cewa,"when?, where?, how?, duk a yaushe kika yi baki har kike magana haka?". ta turo baki gaba, ta ƙwace hannunta ta ɗauko baƙin glass ɗinsa ta saka masa,"yana yi maka kyau sosai idan ka saka, amma ni ɗaya zaka ke sakawa, promise". ya karyar da wuya,"i promise you". hannunsa ta riƙe suka fita, tunda suka hau saman titi kuma duk sai ta koma masa kamar ba wannan ƴar Babyn ba sarkin daru da rigima, wacce ta ke hawar masa bori ya zauna zaman lallashi, wannan wa ta Fulani ta daban ya ɗauko, me faɗa kamar yaƙi, da kuma ba da instructions. ta dage tana faɗa masa in sunje gidan bata yarda ya kalli kowa ba, bata yarda yay magana sama da sau biyar ba, bata yarda ya amsa gaisuwar kowa ba, bata yarda ya cire glass aga hasken idonsa ba. shi ma ya tamke murya yace,"duk da wa kike?". "da Muhammad Turaki". ya saki hannunta ya ɗalli bakinta, ta ɗauke idonta da ga barin kallon titi ta juyo ta kalle shi. "to ba sunanka ba ne?". "a bakin mutane ba, amma ban da naki". "to ni haka zan faɗa". yay murmushi,"wai to duk wannan cin maganin na mene?, ba fa a haka muka fito ba, ko nayi laifi bisa kuskure ne?". tayi narai narai da idanu ta ce,"ni kawai bana son zuwa gidan". "me yasa?". "bana so muje wannan matar ta ganka, na san dole zata kalle ka, na san dole sai taji wani abu akanka". tai maganar kamar zata yi kuka. yay shiru bai ce komai ba, sai da suka yi nisa a tafi sannan ta ƙara cewa,"kuma na san kaima zaka kalleta ko?". nan ma dai bai ce ma ta komai ba, hakan yasa kawai ta kifa kanta a saman gwiwarta tana jin wani bala'in zafi a zuciyarta, idan ta san haka ne da tun farko tace bata da lafiya ba zata iya zuwa ba. *_bari nayi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyata da nuna jin daɗi gare ku masoyana, tank you so much lovlies for keeping up with this story, ga shi dai muna ta tafiya amma ko kaɗan baku ƙosa da ni ba, duk da inata ƙoƙarin ganin na yanke labarin an gama shi kwatakwata. Anyway don Allah kuci gaba da bani ƙwarin gwiwa ta hanyar yin warm comments ɗinku da ku ka saba, haɗe da yin voting, mun kusa hattamawa insha'Allah._* *_ina son duk wani makarancin littafin nan tamkar yanda nake son ƴan group ɗina na Halima Hz palace, muaahh to all of you😘😘._* [9/7, 01:03] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *53* *Azima Tahir Lukman.* ashekarun baya masu yawa da suka shuɗe, Azima Tahir Lukman wata matashiyar budurwa ce, wacce ke matuƙar ji da kanta a ɓangaren kyau, ilimi da kuma dukiya ta mahaifiyarta wadda ta kasance ƴar siyasa. kyau irin na Azima ke tasirantuwa a zuciyoyin maza da dama, daga masu kuɗin har talakawa, a inda ta ware manyan masu kuɗi da masu mulki waɗanda su ne take ganin su kaɗai ne suka isa su mallaketa. kuma a kaf mazan da tayi mu'amala da su babu guda ɗaya aciki da zuciyarta ke jin tana so ko kuma zata iya aurensa, no; zata mu'amalanceka ne kawai domin kuɗin da suke aljihunka, da zarar ta gama da kai shikenan, saboda ta mallaki kuɗi a wurin irin alahazawan da ke zuwa wurinta ta kashe rai ba ɗaya ba, ba biyu ba. zuciyar Azima ta so mutum guda tallin tal ne a rayuwarta, wato Alƙali Habib Dikko, shi kaɗai zuciyarta ta so tsakani da Allah, wanda har take jin she can go to the extend akan taga ta mallake shi, alhalin kuma yana matsayin saurayi ne na aminiyarta da ta san cewa an saka musu rana. Ramla Muhammad Turaki itace babbar aminiyarta da suka yi university tare anan london, duk wanda yasan Azima ya san Ramla, haka duk wanda ya san Ramla yasan Azima, su kwana tare su tashi tare, su ci abinci tare su yi yawo tare, haka zalika ba sa taɓa aiwatar da abu sai da shawarar juna. Azima ta samu Ramla ne tare da Dikko, tare ta gansu, wanda shi ma kuma ya aminta da ita sosai, musamman da yaga Ramla ta ɗauki duk wata yarda da amana ta bawa Azima. sai dai daga lokacin da Dikko ya fara shirin kai lefen Ramla, a lokacin Azima ta fara kunno wutar gobarar da zata lalata lamarin auren, ta fara ɓata Ramla a wurinsa, abubuwa iri iri da zai sa yaji ya tsani Ramla babu wanda ba ta faɗa masa ba, tun baya yarda har ya zo ya fara yarda da ita, saboda sauyin da yake gani a tare da Ramla a lokacin da bata ba shi attension ɗinta, sakamakon final exams da za su fara. hatta vedion tsiraici na lesbian Azima ta ɗauka ta bayar anyi editing ɗinsa da fuskar Ramla ta bawa Dikko, daga wannan lokacin kuma yaji ya tsani Ramla kwatakwata, ita kuwa Ramla a lokacin bata kawo komai a ranta ba dangane da watsi da lamarinta da Dikko yay, ta ta'allaƙa hakan ne da space ya bata saboda ta samu tayi karatun exams sosai. sai dai kuma a lokacin da Azima take tunanin tayi nasara, a lokacin Allah ya toni asirinta a ranar wata laraba, inda wanda yay ma ta editing vedion tsiraicin Ramla yaje ya sami Dikko ya faɗa masa gaskiyar komai, a lokacin soyayya ta riga tayi nisa tsakanin Dikko da Azima, dan saura ƙiris su shigar da iyaye cikin maganar, dan Azima ta gama tsara yacca zata shimfiɗar rayuwar aurenta da shi. kuma duk wannan lamari da ke faruwa Ramla bata da labarin komai, yacca Azima ba ta bari ta fahimci wani abu ta ɓangarenta ba, haka shi ma Dikko bai taɓa tunkarar Ramla da irin abubuwan da Azima tayi akanta ba har kawo iyau da take matarsa, uwar gidansa, kuma uwar ƴaƴansa, wucewar shekaru sama da 20. lissafi ɗaya Azima tayi a bayan da Dikko ya juya ma ta bayansa, shi ne ba zata taɓa yin nisa daga gare shi ba, zata bi wata hanyar da zata kusance shi har ta wanke laifinta, kuma har ya yafe ma ta yace zai aureta kamar dai yanda taci burin hakan. dalilin da yasa ta shiga rayuwar Mai Martaba Hashim Latif kenan, saboda ta lissafa cewa ta wannan hanyar kaɗai zata iya samun damar kusantar Dikko, ta hakan ne ba zasu yi nisa da junansu ba, ta hakanne zata samu damar wanke laifinta gare shi, in ya so a sanda yace ya yafe mata sai tayi duk iyakar ƙoƙarin da zata yi ta raba aurenta da Mai Martaba domin ta mallaki Dikko, amma sai dai me!, lissafin da hasashenta duk sai ya tarwatse ya bi iskar da ta kaɗa tun a ranar da ta sanya ƙafafunta acikin gidan mai martaba. kuma daga lokacin da ta fahimci cewa ba zata taɓa samun Dikko ba, daga lokacin ta ɗauki alwashin ƙuntata rayuwar duk macen da ke rayuwa tare da Dikko hatta kuwa da ƴaƴan da zai haifa ba tare da ita ba. shigowarta cikin rayuwar Mai Martaba ta gane asalin menene mulki da kuma daɗin da yake cikinsa, wannan yasa ta dasa cin burika da yawa a rayuwarta, lokacin shaiɗan ya fara buga ma ta sabuwar ganga acikin kanta, akan aikata mugwayen abubuwan da ba zasu ɓulle ma ta ba, ya dinƙa rinjayar zuciyarta da cewa tayi duk fafutukar da zata yi wajen ganin ta mallaki kaso 70 cikin tarin dukiyar Mai Martaba kafin ta barshi. shiyasa daga lokacin da ta haifi Ilham, sai tabi duk wata hanya da zai sa Mai Martaba ya koma ganin ƴarta kawai a matsayin ita kaɗai ce ƴar da ya mallaka, wannan dalilin yasa ta kama fufutukar bin bokaye  kenan, wanda ya zama mafi muhimmanci a wajenta. kuma tayi nasara akan hakan, domin kuwa cikin ƴaƴa goma da Mai Martaba ya mallaka Ilham kaɗai idanuwansa ke iya gani a matsayin wacca ya haifa da cikinsa, wanda hakan ya janyo rabuwar kawuna a tsakanin sauran ƴaƴan da ita Ilham ɗin, domin ya mayar da ita tamkar ɗa namiji, duk wani abu nasa da ya mallaka yana rubuta shi da nata sunan, har ya kan yawan buɗar baki yace _na so ace Ilham Namiji ce, da ta gaji wannan kujerar tawa tun ina raye._ sai dai babu wanda ya taɓa gane Azima na ɗauke da wani mummunan ƙudiri, kasantuwarta mace mai dabara, macen da ta ke lulluɓe da mayafai guda biyu, ciki baƙi waje fari, sai dai ba ta taɓa barin wani mahaluƙi ya ganta da wannan baƙin lulluɓin sai dai farin da ta yafa daga waye. _"har yanzu mun kasa gano taƙaimemen ciwon da ke tare da ita. duk wasu injina da ya kamata muyi amfani da su sun gaza yin aiki wajen gano cutar da ke tare da ita"._ maganar da ɗaya daga cikin likitocin ke yi kenan acikin ofishinsa, acikin asibitin masarautar kaltungo, Mai Martaba ya miƙe cikin mutuwar jiki suka fito tare da Dr ɗin. a sanda suka fito ya tsaya daga can nesa yana kallon matar tasa ta silin hanyar da ta buɗe ta ƙofar ɗakin da take kwace. kallo ɗaya zaka yi mata tun daga nesa kaji zuciyarka ta motsa saboda tausayin mawuyacin halin da take ciki a yanzu, ka kuma ƙara jin tsoron ruɗin duniya, a yayin da zuciyarka za ta tuna ubangiji da dukkan irin ikon da yake zartarwa akan rayuwar kowanne bawa. kwance take an ɗaureta ajikin gadon ɗakin asibitin da ke cikin masarautar saboda yawan girgiza da take yi yanzu, idanunta a tsaye suke sun ƙafe akan windon ɗakin da ta nan ne kowa ke iya samun damar ganinta, har kuwa da ƴarta guda ɗaya da ayanzu ita ma bata iya zama tare da ita saboda bala'in ɗoyin da take yi wanda kowa ke cutuwa da shi, hatta kashi idan tayi sai ta jima cikin su kafin azo a kula da ita. gaba ɗaya ta gama lalacewa, ta koma ita da ƙwarangwal babu maraba, a halin da ake ciki yanzu, dukkan wani ɓangare na zuciyarta ya riga ya gama dagargajewa a ƙirjinta, tana jin ƙirjinta ne kamar Allah bai taɓa halittar komai a cikinsa ba, zuwa yanzu duniya gaba ɗaya ta gama yi mata zafi, babu abin da take fata sama da mutuwa, sai yanzu ta gane ka zalunci mutum Allah ya baka damar neman yafiyarsa, ko ka saɓawa Allah ka nemi gafararsa tun kafin ya damƙe ka, wata rahama ce babba daga ubangiji, atleast ka iya samun sassauci na daga bala'in da zaka shiga. halin da take ciki a yanzu ta tabbata babu wani abu na awo a duniyar nan da za'a auna ya fitar da kalmar da zata fassara shi, a yanzu ta afka ne cikin wani rami na nadama, nadamar da ta ke kira da mara amfani. ta kuma sa ni har ta mutu Allah ba zai bata damar yin magana ba, balle ta samu ta fayyace mugun abubuwan da ta aikata, balle har ta nemi yafiyar waɗanda ta cuta. ta sa ni wannan kaɗanne daga cikin hukucin da Allah zai yi mata. _(Ya Allah ka kiyashe mu daga sharrin zuciya, ka rabamu da aikata aikin danasani.)_ Hajiya Ramla ta zo tayi tsaye a bakin windon ɗakin Fulani Azima, kallon junansu suke yi, idon Fulani Azima sai hawaye yake zubarwa kamar an kunna famfo, tana ta girgiza kan gadon da take, da alama so take yi ta sauko, kuma so take yi tai magana da Hajiya Ramla, so take yi a bata aron dama ko da guda ɗaya ce, ko da ta minti ɗaya ce. in har Hajiya Ramla tace bata ji tausayinta ba tayi ƙarya, abu ɗaya ne kawai ta san da shi, shi ne ko akwai sama da abin da yafi tausayi ba zata taɓa yafewa Azima ba ko da ace zata shiga halin da yafi wannan muni. ta sauke numfashi tana ƙara kallon Fulani Azima wacca har yanzu idonta ke maƙale akanta tana jijjiga gadon. sai ta saka facemask ta fesa turare sannan ta fuskanci gaba ɗaya windon, tace da ita,"na san kina ta so ki buɗi baki ki nemi yafiyar abin da kika yi min ni da ɗana, kamar yanda kike so ki buɗe baki ki faɗi mugwayen abubuwan da kika aikata. ban da masaniyar ko Allah zai baki aron wannan damar, but ki sani ko da bayan raina kika sami damar magana, karki tsammaci za ki ambaci sunana da roƙon na yafe miki, karki saka sunana acikin waɗanda zasu yafe miki, Azima ba zan taɓa yafe miki abin da kika min ni da Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji ni da ke, sai Allah yayi mana hisabi. but just keep in mind da bakina dai ba zan taɓa faɗar abin da kika aikata ba, idan Allah ya nufeki da yin magana kafin mutuwarki kya bada labarin zaluncin da kika aikata, duk da bana fatan Allah ya baki aron wannan damar, gwara ki tafi da tarin alhakin mutane ta yanda za ki ɗanɗani abinda kika shuka tun a ƙabari kafin ranar tsayuwa a gaban ubangiji, Azima insha'Allahu har mutuwarki babu me yafe miki abin da kika masa domin ke ɗin azzaluma ce". tana gama faɗar haka ta bar bakin windon tana kuka. hango tahowarta yasa Zaytuna fitowa daga mota tazo ta kama hannunta. Hajiya Madina ta kalleta ta girgiza kai tace,"your excellency". Mum ta ɗaga kai ta kalleta, sai Maama tasa tissue tana goge ma ta hawaye. "don Allah ki daina zubar da hawayenki ga wacca bata kamaci a zubar ma ta da hawaye ba, duk da irin tsananin halin da take ciki, masu imani ake yiwa kuka ba azzalumai irin Azima ba". sai kuma ta numfasa ta ƙara cewa,"in dai ina raye Allah har Azima ta mutu ba za ki ƙara zuwa inda take ba, balle ki dinga zubar da hawaye haka a banza, ba gwara ki tara mana hawayen ba idan abin farin ciki ya same mu ki yi". "na daina ma daga yau, ba zan ƙara ɓarnatar da hawayena ba akanta". "better!, ki godewa Allah da ya saka miki tun daga nan duniya". da sauri Hajiya Ramla ta ɗago tana dubanta da mamaki. Hajiya Madina tayi murmushin da ya tsaya a iyakar leɓenta sannan tace,"ban da masaniyar wanda yay miki asiri kika bar gida, but haka ɗaya nake jin zuciyata ta kasa aminta da Azima, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya amma ni dai ita nake zargi, shiyasa ko kaɗan bana tausaya ma ta, wallah in har itace silar asirinki da na me babban suna da yardar ubangiji sai tayi mutuwar wulaƙanci". tayi shiru tana rufe idonta na sakanni sannan ta buɗe, sai kuma ta juya topic ɗin da cewa,"yanzu me babban suna suka shigo, ba ki gansu ba gwanin sha'awa sunyi kyau sosai, sai naji kamar ni ɗaya nai sa'ar haihuwar ɗa me kyau da kuma dacen balarabiyar sirika". Hajiya Ramla tayi murmushi. "ai ce nake ba za su zo ba, dan ɗan naki yayo halin kafiyarki". "yanzun ma na faɗa musu sannu ce kawai ta kawo su, da zarar sunyi ma ta sannu ko ta amsa ko bata amsa ba suyi tasowarsu su tafi". Hajiya Ramla ta girgiza kanta,"da ba ki ce musu haka ba ai". "hakanne ma yasa na hanasu zuwa wurinki nace su wuce wurin Boɗejon kai tsaye, kana tausayin me tausayinka ne, haka kana mutunta me ganin mutuncinka". ƙafafun Turaki suka shiga cikin parlon kafin na Babyn roba su bi bayansa, ya kama hannun Fillo da ke rakuɓe a bayansa suka shiga ciki. su ka zauna da ga ɗan nesa inda Boɗejo tasa wata hadimarta tayi musu nuni, tun da akace ma ta su ne ta sunkuyar da kanta, har suka zauna kuma ko ɗago kai bata yi ta kalle su ba don bata tunanin iyayensa ma sun isheta kallo balle shi kansa da wata sillan karan matarsa. Fillo ta kalleta taga tamkar bata san da shigowarsu ba, sai taji wani abu me kama da tsoro ya kamata, ta kalli Turaki suka haɗa ido, cikin bin umarnin da yay ma ta da ido ta buɗi baki ta ce,"Boɗejo ina yini, ya sauƙin jiki?, Allah ya ƙara miki lafiya yasa kaffara". ta haɗe duka maganarta a lokaci ɗaya, dan ta san abu ne me kamar wuya Boɗejo ta amsa ma ta, ile kuwa kamar yanda tayi tsammanin uffan ba ta ce ma ta ba. Turaki ya kama hannunta ya riƙe wanda yake jin yana rawa a jikinsa. ransa ya ɓaci sosai, daraja ɗaya Boɗejo zata ci haifar Baffa da tayi, ya rumtse idonsa ya buɗe, ya danne abin da yake ji yana taso masa a zuciya ya ce,"tsohuwa ashe ba kiji daɗi ba, na san ba komai bane sai kewata ko?, to ai gani na zo kuma naga sai wani ciccin magani kike yi, ko ba'a maraba da ganin nawa?". ya faɗa cike da tsokana dake tsakaninsa da Kakar tasa. ta ɗago tayi masa wani kallo me cike da ban haushi ta ce,"munafiki, mara mutunci, wanda ya kunyata ni akan kucakar ƴar aiki, wanda ya fifita mace akan bin umarnin mahaifinsa, kai har kana tunanin muryarka ma ina ƙaunar ji ne, ai tuni na sallamaka acikin jikokina, saboda haka ka bar bin wata hanyar shishshige min, ranar da Amaryarka ta koma ɗakinta wataƙila ma iya shiryawa in akwai rabon hakan". yay murmushi me faɗi har da sauti yace,"ashe zamu shirya ɗin dai, yanzu dai ya jikin naki kin ji sauƙi ko ya?". ta galla masa harara,"ina ruwanka da lafiyata, ka ga tun kamin raina yay mugun ɓaci tashi ka fita ka bar min waje, idan ba haka ba na ƙwala ihu yanzu na ƙalawa wannan ƴar banzar yarinyar sharrin da babu wanda zai iya ƙwatarta duk duniyar nan". fuskar Turaki ta washe da murmushi ya ce,"yo ba tana da Allah ba, shi ai zai ƙwaceta, yanzu dai ban gaji da ganinki ba kya bari in gama kallonki tukunna sai ki kora ni, ke kawai daga yi miki kishiya duk sai bi ki zama fitinanniya, wannan kishin naki yayi yawa". ta jijjiga kanta ba tare da tace da shi ƙala ba. Fillo ta miƙe ta ɗauki manyan ledojin da suka shigo da su guda biyu, taje gaban Boɗejo ta tsuguna ta ajiye, muryarta ta fito very cool da cewa,"ga wannan ba yawa, Allah ya ƙara miki lafiya". ta numfasa, ta ɗora hannunta akan ƙafar Boɗejo, cikin taushin murya tace,"don Allah kiyi haƙuri, Allah ya huci zuciyarki, da ni da shi duk bamu da laifi, zanen ƙaddarar mu ne ya zo a haka, tun kafin zuwanmu duniya ubangiji ya rubuta cewar zamu kasance a inuwa guda ɗaya, Allah ya rubuta hakan a lauhul mahfuz, dan haka ni ko shi ko wani babu wanda ya isa ya sauya abin da Allah ya rubuta zai faru, illa kawai mu roƙe shi ya juyar da abinda zuciyoyin mu basa so su zama alkhairi a gare mu, ya kuma saka mana haƙuri da dangana mu karɓi lamarin a yanda yazo mana". tayi ƙoƙarin ɓoye kukan dake shirin ƙwace ma ta. "don Allah don Annabi kiyi haƙuri ki daina fushi da kowa, duk mun san munyi miki laifi, babu wanda yaƙi bin umarninki, babu wanda zai so abin da ba kya so, kawai dai babu yanda zamu yi da lamarin da Allah ya shirya dole zai faru ne. don Allah Boɗejo ki daina fushi da Maama da Mum, haka ki daina fushi da mijinmu". ta ƙarashe maganar su na haɗa ido, sai Boɗejo taji wani abu da bata san menene shi ba ya tsarga mata akan Fillo, abu ɗaya ta sa ni kamar yarinyar tana da wani girma na kwarjini wanda ba zaka san da hakan ba zai ka kalli ƙwayar idanuwanta, haka kuma akwai hikimar zance a bakinta wanda samun hakan shima babbar baiwa ce. duk sai taji ta kasa yi ma ta cin mutuncin da tayi niyyar yi ma ta a duk ranar da tayi tozali da ita, alwashi ne da ta ɗauka, so tayi duk ranar da suka yi ido huɗu sai ta yiwa Fillo abin da zai sa ta bar gidan Turaki da ƙafafunta, tayi tafiyar da ba zata taɓa dawowa gare shi ba. idanuwan Fillo suka manne akan mirrow ɗin da ke fuskantarta, murmushi ya suɓuce a saman leɓenta wanda ita kaɗai ta san tayi shi, hatta Turaki dake kallonta ba zai ce tayi ba. Boɗejo ta haɗe rai tana ɗauke hannun Fillo akan ƙafarta ta ce,"Malama ta shi ki bar kusa da ni, kuma ki ɗau tsiyarki, ki kai can ƙauye inda ake yunwa, amma ba nan inda aka fi ƙarfinsa ba". Fillo ta marairaice murya ta ce,"tuba nake ranki ya daɗe, ina barin kusa da ke ne kawai idan har an dubi girman laifin da na aikata an yafe min ba, hakan kaɗai zai sa in sami sukuni da salama. Kaka bata fushi da jikokinta, ko da tayi hutu ne ta ɗauka saboda ta huta da rashin jinsu, ranki ya daɗe namu hutun ya isa haka a tausaya mana". mamaki ya hana Boɗejo cewa komai, ƙaramar yarinya kamar wannan ta iya zaro zancen tsari irin haka, zancen da tana da tabbacin ba har zuciyarta take yi ba, tsabar kissa ne kawai. "ka taso ka dawo nan". muryar Fullon ta fito ta wuce kai tsaye zuwa cikin kunnuwan Turaki, ya rufe bakinsa da ya buɗe yana kallonta tun ɗazu, ta sakar masa wani kyakykyawan murmushi da ya sa shi tasowa babu shiri, sannan nata murmushin ya ƙaru a sanda ta kuma yin tozali da madubin. ya zauna kusa da ita, ya kama hannunta guda yana murzawa, tare da kai hannu ya ɗauki apple dake cikin plate, ya gatsa sannan ya kai bakin Boɗejo ya ce,"Uwar gidana". ta mangare hannun nasa, ta taso masa cikin masifa har sai da Fillo ta ƙanƙame shi saboda tsorata ba tare da ta san tayi hakan ba. shi kuma yay saurin kewayeta da hannunsa yana cewa da Boɗejo,"yi a hankali tsohuwa Baby bata son hayaniya". sai ya ɗan narkar da murya yace,"kin ga kin tsorata min ita ko, haba don Allah Boɗejo wannan wanne irin fushi ne haka da ba'a hucewa, ce nake tun da har yarinyar nan ta riga ta tare shikenan komai ya wuce". ya faɗa yana shafa bayan Fillo, ita kuwa tun da idonta ya ƙara ƙyallawa ya sauka akan mirror ɗin ɗazu sai ta ƙara shigewa jikinsa tana sakin makirin nishin firgici. Boɗejo kuwa zazzaga masifa da zagege da baƙaƙen maganganu kawai take yi, tana ta zagin kafatanin ahalin Fillo, da Hajiya Madina, ran Turaki ya ɓaci sosai yay ƙasa da kansa, ya kasa ko da motsi ƙwaƙwƙwara. tun shigowar su Turaki parlon Ilham ita ma ta shigo ta ɗayar ƙofar, ganinsu yasa tayi turus a wajen, tayi tsaye ba tare da sun san tana wurin ba, ji take yi kamar ta juya, amma sai taji ta ka sa ɗaga ko da ƙaramin yatsanta, jan ƙafarta ma take so tayi but shi ma ta kasa, ji take yi kamar an daskarar da ita ne a wurin. kuma a lokacin da Fillo ta faɗa jikin Turaki sai ji tayi kaman an kunna gobarar wuta a ƙirjinta. duk sai taji ta rasa me yake yi ma ta daɗi acikin ranta, tun da ta baro gidansa bata ƙara ganinsa ba sai a yau, yau ɗin da take ganin kamar an sauya shi, ya ƙara kyau ya ƙara kumari, annurin fuskarsa ya fita daban da asalin yanda ta san shi. sai taji masifar son shi da kishinsa ya ƙara bin sassan jikinta, yau shi ne gabanta da wata mace da ba ita ba, macen da ta san ta fita asali, kyau, nasaba, ilimi kai komai na rayuwa ta san ta fi Fillo. a gaban idonta yake ririta ƙwailar da ta san bata da uban komai bacin kyau irin na ƴaƴan aljanu, har yake rungumeta a jikinsa alhalin ya san a cikin gidan su yake. duk sai taji duniyar ta ƙara yi mata zafi, taji kaman ta samu wuƙa taje ta ɓurmawa Fillo, gwara ta kasheta kawai ko ta samu ta sami sauƙin raɗaɗin ciwon son Turaki da kishinsa da ke neman hallaka ta. tana ganin sun miƙe za su tafi zuciyarta ta yanke shawarar zuwa ta bangaje Fillo, ta hankaɗata daidai saitin in da idanuwanta ke hango ma ta garwashin wutar da aka ajiye wanda akewa Boɗejo gashin ƙafa da shi. without second tought ta baro bakin ƙofar ta taho gadan gadan kamar wacca ake tunkuɗowa. idon Fillo ya ƙara sauka akanta ta cikin mudubin, kamar tasan abin da Ilham ɗin ke shirin yi, tana ganin ta kusa zuwa in da take, da gangan tai saurin wuntsilawa gefe zata faɗi aikuwa a kiɗime Turaki ya tarota yana faɗin Subhanallah. "Fulani Nah yi a hankali, am sorry kinji, hankalina na kan wannan tsohuwar ne". ta ɗage ƙafa tana cije fuska tace,"ka daina bani haƙuri ba kai ba ne". sai ta dafa shoulders ɗinsa ta ɗago tana duban Ilham dake gefe ɗaya tana faman huci tace,"ina yini, ya mai jiki, Allah ya sawwaƙa ya tashi kafaɗunta. kiyi haƙuri ban san za ki wuce ba da ban tsaya a hanya ba". Ilham taja dogon tsaki na baƙin ciki da takaici, ta bar wajen tana jin zuciyarta kamar zata ƙone. Turaki ya bi bayanta da mugun kallo, ya dunƙule hannu yana ɗauke idonsa akanta. "ita ta bige ki?". Fullo ta kalle shi tayi narai-narai da idanu kamar zata yi kuka ta ce,"don't bother your self, mu tafi kawai kaga ran Boɗejo a ɓace yake". sai ya tallafota jikinsa ya juya ya fuskaci Boɗejo, muryarsa na shaida zallar ɓacin rai yace,"wurinki muka zo ba wajenta ba, a da nake da hurumi da ita amma a yanzu ban da wata alaƙa da ita, ki ja mata kunne karta ƙara gigin illata min Mata ko da kuwa bisa kuskure ne, dan ba zan ɗauka a hakan ba. ina da sauƙin kai but akan wannan jaririyar da ke jikina ina iya rufe ido na manta duk girman alaƙar dake tsakanina da ko wanene in ci zarafinsa, wannan jaririyar tafi min duk wani mutum a duniyar nan bayan mutum uku, domin ta sadaukar da ranta da lafiyarta akaina tun kafin ta san waye ni, ta cusa kanta a haɗarin da ko wanda yake sona ba zai iya ba, saboda haka nake mutuntata, nake martabata, nake darajtata fiye da ƙima, fiye da lissafi duk wani me tunani. zan ɓata da ko waye matuƙar ya nemi ya cutar min da jaririyata, if not zan manta da alaƙa in nuna the bad side of me, hakan kuma babu wanda zai yiwa daɗi". a hasale Boɗejo tace,"to ai ka rufe mu da duka ni da ita shi ne kawai,  mene wani gargaɗinka, gargaɗin banza da zai bi ta iska, ai rama ma ta kawai zaka yi, wato ga Ramla an taɓa ko Zaytuna dole ka nuna baka da mutumci". ya rufe ido yana ƙara dunƙule hannunsa, Fullo ta riƙe shi ganin kamar yana ƙoƙarin aikata abin da ba zaiwa kowa daɗi ba. ya buɗe ido yana kallon Boɗejo yana ta huci yace,"kamar yanda Baffa ba zai iya haɗaki da Mum ba, haka ma ni, amma ki sa ni, gwara a taɓa Zaytun akan a taɓa wannan, saboda haka me kiyayewa ya kiyaye, wanda ba zai iya kiyayewa ba kuma ya shiga sata gonar Muhammad Turaki". yana gama faɗar hakan ya duƙa ya ɗauki Fillo suka fice, tana ta cewa ya sauketa amma yaƙi, hadimai da dakaran gidan sai kallonsu suke yi har suka shiga mota. ɓangaren Ilham kuwa su na fita ta kalli Boɗejo tana nuna kanta ta ce,"ni yarinyar nan zata haɗawa sharri, ko fa taɓata fa banyi ba Boɗejo, amma ki ga irin maganganun da Hammah yake faɗa, to wallahi ko ban da niyyar komawa gidansa sai na koma, zata gane tayi da ni". ta miƙe tana barin falon haɗe da yin ƙwafa me girma wacca ita ɗaya ta san ma'anarta. a hanya Turaki ya tsaya ya sayi kaza da takeaway na mandi rice. tun da suka taho daga shi har Fillo babu wanda yay magana a motar har suka koma gida. yana yin parking Fillo ta buɗe ƙofa ta fice tai tafiyarta, shi ma kuma ko da ya shiga part ɗin bai bi ta kanta ba ɗakinsa ya wuce, ya sakar ma kansa shower sannan ya kwanta akan gado ya runtse idonsa, tunaninsa guda ɗaya ne, Anya zai dawo da Ilham cikin gidan nan?. ya daɗe kwance yana lissafi acikin kansa, kafin ya buɗe ido ya sauko akan gadon ya fita, ɗakin Fillo ya shiga, zaune ya ganta akan gado tayi shiru kanta jingina da gadon, ya tsaya yana kallonta kafin ya ƙarasa bakin gadon, yana zuwa ya ɗaukota ya fito da ita zuwa ɗakinsa. [9/7, 01:16] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *54* akan kujera ya zaunar da ita, idanuwan Fillo suka manne akan hannun Turaki da suke cikin plate ɗin abincin da yayo takeaway, abincin da ta san ya siya ne saboda ita, ba don shi yaci ba. ya ɗebo ya kai bakinta, har yanzu ɓacin ran da ke saman fuskarsa bai gushe ba, idanuwansu ya sarƙe ana juna, ta kaudar da hannun nasa da ke nufar bakinta. "ban ji daɗin yanda ka yiwa Boɗejo ba". ya rufe idonsa bai ce komai ba. "don Allah kar ka ƙara, ko babu komai ita ce fa ta haifi Baffa, tana da girman da bai kamaci ai faɗa ma ta kowacce irin magana ba saboda ɓacin rai". still idonsa na rufe ya ce,"ba don hukuncin ubangiji ba, sannan ba don ke da taimakonki ba, da yanzu bana raye, ko kuma da ban kawo yanzu da lafiyar da zan yi tafiya ba, da yanzu wataƙila ina kwance marabata da matacce numfashi kawai, kuma wataƙila da har yanzu ban ga mahaifiyata ba. saboda haka girmanki da nake gani yafi gaban tunani, kina da girman da ba zan iya ganin an ci mutunciki na ƙyale ba". ta buɗe baki zata yi magana ya ɗora yatsansa a leɓenta,"shhhh bana son magana, ki ci abinci". ta kalli abincin ta ce,"bana ci". "saboda me?". "saboda kaima ba zaka ci ba, me yasa zaka tsaya siyan abinci bayan na iya dafawa, and beside da ka siyo bafa ci zaka yi ba, so kake ka kwana da yunwa?, ban iya rashin adalci ba kuma ba zan fara ba daga yau, Ummi ta jaddada min sau babu adadi cewar kar na taɓa barinka da yunwa". kafin yay magana ta miƙe, ta kamo nasa hannun shi ma ya miƙe. "muje kitchen na dafa mana abin da zamu ci". ya dakatar da ita,"kin gaji ba za ki iya girki ba, kuma kinga akwai ciwo a ƙafarki". "ni ban gaji ba". ta faɗa tana saƙalo hannunta guda a wuyansa sannan ta ƙara cewa,"idan ƙafan na ciwo ai sai ka ɗauke ni". murmushi yay tare da ɗaukarta su ka fita a ɗakin,  su na saukowa downstairs kitchen ya nufa, sai da suka shiga ya ajiyeta, ya kama ƙugu yana cewa,"zan ga yanda ake aiki da gurguwar ƙafa". tayi murmushi me sauti tare da jan gemunsa ta ce,"to ai da ka ɗauko ni na warke". ya buɗe ido yana kallonta,"ƙatoto da ni kika yiwa wayo?". ita ma ta kama nata ƙugun ta ɗaga kai sama ta juya idanu, sannan ta ce,"me zamu ci?". "duk abin da aka girka da waɗannan siraran hannun zan ci". ta dafa kafaɗarsa ta ce,"ummm Maama ta taɓa cewa kana son soyayyan indomie, so yau zan ci abin da kake so ni kuma bana sonsa, but na san daga yau zan fara so, in dafa ko?". ya ɗaga ma ta gira yana jin wani daɗi a zuciyarsa, ta wuce ta ɗora tukunya a gas, ya bi ta yana faɗin zai tayata, ta dakatar da shi,"no ba yanzu ba, zaka fara girki but not today not now, but one day. for now just sit and watch". kujeran dining ɗin dake kitchen ya ɗauko ya zauna gefe daga in da cooker gas yake, kafin ta gama yankan albasa idonsa duk ya cika da ruwan hawaye saboda yajin albasar, tuni kuma suka zubo, sai ƙyafta idanu yake, Fillo duk na kallonsa tana ƴar dariya, tace,"me aka maka kake kuka?". ta tambaya tana dariya ƙasa-ƙasa. "ni kike yiwa dariya?". ya miƙe zai bar kitchen ɗin ta maido shi ya zauna tana faɗin,"sorry, idan ka fita ina jin tsoro". ya ƙanƙace idanu yana kallonta cikin tarin ruwan da ya cika idonsa,"Fulani Nah idona yaji". "ni dai ka zauna haka, ina gama yankawa zai daina ai". ta faɗa tana narkar da murya, haka ya zauna babu yacca ya so, har sai da ta gama yankan albasa tukunna ta wanke masa fuska a sink. wayarsa tayi ringing yana dubawa yaga Sameer ne, yay picking Sameer na faɗa masa ga shi ya kawo masa ticket ɗin. ya kalli Fillo ya ce,"Fulani Nah zan amso saƙo wajen Sameer". tayi shiru kamar bata ji shi ba har sai da ya ƙara kiran sunanta. ta ɗan ɓata rai ta ce masa,"to ya shigo parlo ya jiraka mana, idan mun kammala sai mu same shi, ni ba zan iya jira idan ka fita ba, kafin ka dawo dodon kitchen ɗin ya cinye ni". yay murmushi yana girgiza kansa,"my drama queen". sannan yace da Sameer ya shigo ya jira shi a parlo ga shi nan fitowa. wucewar minti goma ta kammala suyar indomie ɗin, sannan ta haɗa pineapple juice, tana sane take ta delay dan ita bata cika son Sameer ba, musamman ma idan tana tuna ƙullin da suka dinƙa yi akan su kashe Turaki. "na gaji ka zo ka wanke min hannu". ta faɗa a sanda ta nufa sink ta tsaya. ya taso ya tsaya ta bayanta,  ya kama hannayen da suka shige cikin nasa, ya zuba morning fresh ya wanke ma ta. ta ɗauka abincin da tasa a plate shi kuma ta ba shi jug da cup ya riƙe suka fita, Sameer yana zaune yana jan tsaki kaɗan kaɗan saboda ya fara gajiya, ta ajiye plate ɗin akan table tana gaida shi, ya bawa Turaki ticket ɗin yana faɗa masa ba'a samu flight ɗin 8 ba kamar yanda ya ce, sai na 9 aka samu. kaɗan Sameer yaci indomie ɗin, shi ma saboda Fillo ta takura ne, bayan tafiyarsa suka koma kitchen suka ɗauki na su sannan su ka wuce upstairs. kamar yanda ya zamar musu jiki yanzu, kuma kowannen su ya saba da hakan, ba wanda ke iya cin abinci shi ɗaya, sai dai su yi feeding junansu, yanzu ma tare suka ci abinci. su na ci Turaki na zuba santi, ita kuma sai taji tamkar bata taɓa ƙin cin indomie da ƙwai ba saboda yacca take enjoying feeding ɗin nasa. bayan sun gama ci Fillo ta fita a ɗakin ta wuce nata, shi ma toilet ya shiga bayan fitarta, yay wanka sannan yay alawala ya fito ya wuce masallaci, bai dawo gidan ba sai da akayi sallar isha'i. ɗakinsa ya wuce direct, shigarsa ya tarar bata nan hakan yasa ya fita ya koma nata ɗakin, nan ɗin ma bata nan, ya murɗa handle ɗin toilet nan ma bata ciki, sai yaji faɗuwar gaba ta kama shi, cikin sauri ya fito sai gata tana hayowa upstairs ɗin. doguwar ajiyar ya sauke, ya harɗe hannayensa a ƙirji, idonsa akanta yana duban wata riga da take ninkewa. "ina kika je?". "yaushe ka dawo?". ya fizgota jikinsa,"answer me first". "kayan da zan bayar na ɗauƙa na kaiwa su Sakina". "su waye hakan?". "ƴan aiki mana". "me yasa ba ki faɗa min ba?". "to ai masallaci ka tafi". ya mintsini gefen cikinta da faɗin,"kuma daga kai musu kaya sai kika zauna hira". "ummm ina son hira da su sosai, da yake ƴan ƙauyen su Yami ne, ina son ƙauyen na su yana da daɗi shiyasa idan naji su na hira sai nayi ta tambayarsu wuraren da na sa ni". ya karɓi rigar hannun na ta,"ita wannan ɗin ya ba ki ba su ba?". "tayi musu kaɗan, waɗancan ɗin ma duk sai an buɗa musu". murmushinsa me sauti ya fito, yaja hancinta yana cewa,"ke ma kin kusa yin ƙiba ai". ya riƙe hannunta su ka wuce room ɗinsa, toilet su ka wuce ta wanke masa gashin kansa da yace yana yi masa ƙaiƙayi. su ka fito tana tsane masa kan da towel, ya zauna kan stool tana cakuɗa yatsunta acikin gashin tana sosa masa bayan ta shafa wani oil. ta cikin madubi da take kallonsa ta ce,"bacci?". ta tambaya ganin yanda idanuwansa suka sauya yana faman lumshe su. ya girgiza ma ta kai yana ƙara luma hannunta cikin sumar. "to ni idan ma baccin ne ka kore shi, ka fa ce zaka ban labari yau me daɗi". ya miƙe daga kan stool ɗin yana juyowa ya fuskanceta, numfashinsa ya shiga busawa akan furskarta. cikin kasalar da yake jin tana neman lulluɓe shi gaba ɗaya ya ɗaga hijab ɗin dake jikinta ya cire, ya dinƙa kallonta musamman breast ɗinta da suka bayyana sosai a cikin sleeping dress ɗin. sai duk taji nauyi da kunya sun kamata, ta taka zata bar wajen ya janyota, ya ɗaura kanta a ƙirjinsa ya zagayeta da duka hannayensa, yana jin wani abu na fizgarsa akanta. Fillo ta rufe ido ta buɗa hanci tana shaƙar daɗin ƙamshin jikinsa. taji ya warware gashinta da tayi parking, kafin a hankali taji ya kira sunanta da amon sautin da ya zama kamar ba nasa ba. "Fulani Nah". ta ce "ummm". ya nutsa yatsunsa cikin gashin kanta yana barbaza shi a fuskarta tare da kissing forehead ɗinta, sannan cikin taushin muryarsa yace,"I always want you very close to me Fulani Nah". maganar ta shiga jikinta sosai, tayi shiru tare da ƙara lafewa a ƙirjinsa, tare da zura hannu cikin rigarsa ta kama wasa da gashin ƙirjinsa, tana jin yacca bugun zuciyarsa ke duka acikin kunnenta. "say something Fulani Nah". ya faɗa yana yawo da yatsansa acikin kunnenta. bata iya magana ba sai kewaye shi da tayi da hannayenta. hakan ya ba shi damar ɗago da fuskarta, ya ɗora goshinsa akan na ta iskar bakinsa ta fito ta sauka akan lips ɗin ta. "say you love me Fulani". ta haɗiye yawu da ƙyar cikin mutuwar jiki tace,"i love you Turaki". murmushi ya suɓuce akan leɓansa, a hankali yace,"Turaki ko?". ta ɗaga masa kai tana daɗa mannewa ajikinsa. buɗe lumsassun idawunsa yay, ita ma ta buɗe nata, ƙwayar idonsu ta sarƙe wuri ɗaya yana jin yanda jikinta duk ya mutu, sai ya ɗanyi murmushi yace,"can i?". ta ce,"what?". ya ce,"kiss your sweet lips". ta ɗaga kanta kawai bata ce komai ba, sai ya ƙara sunkuyar da kansa a hankali ya ɗaura lips ɗinsa saman na ta. lokaci ɗaya taji tana neman barin jikinsa zata faɗi ƙasa, sai ya koma ya zauna kan stool ɗin yana zaunar da ita saman cinyarsa, ya shiga tsotsar lips ɗin tamkar wanda ya sami alawar da ba ya so ta ƙare. yana yi yana murza tafin hannunta, sai da yay kissing ɗinta sosai to his satisfaction tukunna ya ƙyaleta, ya saketa a sanda duk su biyun su ke mayar da numfashi, Fillo ta kalle shi da idanuwanta da kamar ba zasu buɗe ba, dan duk jikinta taji ya fara sauyawa, ta ɗan bugi ƙafafu a ƙasa kafin ta juya ta bar masa wajen, ya bi bayanta da wani irin kallo me cike da tarin feelings akanta, ya sauke numfashi yana jin yanda yanayin jikinsa ke daɗa sauyawa. sai ya miƙe ya bi bayanta cikin mutuwar jiki, tana shirin hawa gadon ta kwanta taji ya rungumota ta baya, ya shiga yawo da hannunsa a jikinta gently,"Fulani Nah this smell makes me body weak". ya faɗa yana yawo da hancinsa a wuyanta yana shinshina humrar jikinta. tuni jikin Fillo ya ɗauki rawa sosai, ta ɗan fara kuka tana faɗin,"Turaki let me". cikin muryarsa da ta sauya gaba ɗaya yace,"nooo". ya faɗa tana jin yanda ƙirjinsa ke bugawa a bayanta sosai, ta juyo a hankali tana facing ɗinsa, hannayensa na karkarawa ya tallabi fuskarta ya ce,"please Fulani Nah let's make a love this night". hawaye ya sauko a kuncinta ta ce,"what kind of love?". yasa hannu yana sauke hannun rigar ya ce,"allow me to show you". tayi saurin tura hannunsa tana faɗin,"no, i don't want". "please Fulani Nah, please don't stop me kinji, promise you i won't go deep, please let us enjoy". ya faɗa a sanda ya fara aika ma ta da wasu saƙonni, duk sai taji ya bata tausayi ganin ya koma kamar ba shi ba, kamar wanda bai da lafiya yake buƙatar taimakon gaggawa. tuni ya fara tafiyar da ita cikin salonsa da ta fara jin ƙafafunta na neman gaza ɗaukarta, abubuwan da taji su na neman su rabata da duniyar da take ciki, wasu saƙonni da taji su na nema suyi raga-raga da tunaninta. ta ji shi lokacin da jikinsa ya fara kyarma sosai kamar me jin sanyi, taji kuma lokacin da hannayensa duka biyu suka shiga cikin rigarta suna tafiya zuwa ƙirjinta, kuma taji san da yace,"can...?". ba ta bari ya ƙarasa ba ta ɗaga masa kai da cewar,"yes, we can". abin da bata sani ba shi ne lokacin da ya cire rigar jikinta yay wulli da ita, da lokacin da ya ɗauketa suka hau saman gadon. abu ɗaya da ta san da shi shine tana mugun enjoying hot romancing ɗin da yake da ita, wanda ke dab da mantar da ita a duniyar da take. yanda ya fita a hayyacinsa haka ita ma, bata dawo cikin hayyacinta ba sai da taji yana neman wuce gona da iri, hakan yasa ta fashe da kuka sosai tana ture shi, ganin yaƙi yana ƙara maƙaleta ta tuna masa da period ɗin da take. hakan ne ya sa Turaki dawowa cikin duniyarsa, yaja dogon numfashi ya sauke yana bawa katifar naushi, ya rumtse ido gam tare da rugumeta yana sauke ajiyar zuciya. da ƙyar ya iya buɗe baki yace da ita,"i am sorry Fulani Nah, i am out of mind". ƙirjinta sai bugawa yake sosai a jikinsa, ta jima tana kuka yana aikin lallashinta, da ƙyar tayi shiru sannan ta fara ƙoƙarin raba jikinta da nasa, ya hana hakan yana faɗin,"ba abin da zan ƙara yi miki, lets sleep together ok". ta ƙyar da suɗin goshi ta yarda amma da tuburewa tayi ita ɗakinta zata koma, don gaba ɗaya a tsorace take da shi, yay ta begging ɗinta, yana lallashi da ban haƙuri tukunna ta yarda tayi bacci ajikinsa. washe gari da safe kafin ta farka har ya haɗa ma ta kayan da zata tafi da su acikin trolly, sannan ya dawo ya tasheta, ko da ta farka ƙin yarda tayi ta kalle shi, ta sauko akan gadon kawai ta wuce toilet kamar dai tana fushi da shi. da ta fito yana zaune a bakin gado, ta fita daga ɗakin ba tare da ta kalli in da yake ba.  shi ma ɗin kuma bai bi ta ba balle ya takura ma ta, kuma yanda kowa ke da zuciya za su iya yin faɗa, sai ya miƙe ya shiga toilet yay wanka yazo yana shiryawa, dan Mum tuni ta kirasa ta faɗa masa sun ɗauki hanya. yana zaune yana saka takalmi Fillo ta dawo ɗakin, tunaninsa duk shiryawa ta tafi yi sai ganinta yay ta dawo ɗauke da tray, ta wuce ta dire akan table sannan ta ƙara fita. ɗaki ta koma don shiryawa, tuni ya fiddo ma ta kayan da zata saka, su na ajiye akan gadon, yau ma abaya ya ƙara ɗaukota ma ta blue colour kalar boyel ɗin da taga ya saka, da murmushi a fuskarta ta ɗauka ta saka sannan ta zauna duba iyakar kayan da ya haɗa ma ta, sai kace mace babu abin da bai saka ma ta acikin trolly ɗin ba, which he knows she will need. sai da ta gama shiryawa tsaf sannan ta fita ta koma ɗakin nasa sai zuba ƙamshi take yi, samu tayi har ya zuba tea a cup, yau ƙin yarda tayi yay feeding ɗinta, ƙarshe ma bata zauna kusa da shi ba, ta ɗauki soyayyan bread da ƙwai ta koma ɗaya kujerar, shi ko yaƙi bi ta kanta. ba su jima wajen yin breakfast ɗin ba saboda lokaci da ke neman ƙurewa, sannan ya kira Bello a waya ya sanar masa zai biyo ta office sai ya wuce ya kai su airpot, haka suka fito dai a gidan babu wanda ya kula wani. cikin lokacin da bai kai awa ɗaya ba suka sauka a airpot na Taraba state, su na sauka Drivern gidan su Hajiya Ramla yazo ya ɗauke su. gidan na su babban family house ne, parlon Granny cike maƙil da ƴaƴanta da jikokinta, kuma kamar zaman anyi shi ne domin tarbar su, su na shigowa aka yi kansu ana yi musu oyoyo kowa sai murnar ganinsu yake, Granny na faɗin a matsa a bawa kishiyarta hanya ta iso, Fillo sai so take yi ta ƙwace hannunta daga riƙon da yay ma ta amma yaƙi har sai da suka shigo tsakiyar parlon tukunna. Kowa sai zuwa yake yana rungumeta, da ma kowa ita ke ta so ya gani musamman waɗanda ba su sami zuwa dinner ɗin su ba, kuma kowa sai yaba kyanta yake yi kamar za su cinyeta, ana faɗin Turaki yay dace da tsaleliyar mata, ita dai sai murmushi kawai take yi, musamman yacca taga kowa na farin cikin ganinta, tamkar ita ma da ma can a family ɗin take. a kusa da Granny ta zauna wacca ta kama hannunta ta riƙe, tana yiwa wata tsohuwa bayanin ai yana da wata matar amma sun rabu, da alama tsohuwar ƙanwarta ce don sun ɗan yanayi. Tsohuwar tace,"yo wannan Tuzurun ma ai mata huɗu ya kamata a haɗa masa, sa'anninsa su na nan kowanne da yara amma shi sai yanzu yake aure, al'adar bature duk ta ɓata mana yara suyi ta zama suƙi aure". Fillo ta ɗaga ido yanda ba za'a lura da ita ba, ta sauke su akan Turaki da ke can cousin sisters ɗinsa sun baibaye shi, tayi dariya tana kallon yanda ya riƙe wata ƴar Baby yana cewa da Mamanta ta karɓi kayarta kar tayi masa fitsari ko kashi, ta karɓeta tana faɗin taga yacca zai yi ranar da aka haifa masa tasa, ba kashi ko fitsari ba tumbuɗi kaɗai ya ishe shi, Allah na tuba kwana nawa suka rage. kuma kamar ya san Fillo na kallonsa a lokacin, sai ya ɗago karaf suka haɗa ido, ya langwaɓar da kai ta sakar masa murmushi, shi ma yay murmushin yana kanne ma ta ido ɗaya, yau duk sai yanzu tayi masa murmushi, dan tun tashinta take faman cin magani, shi kuma bai takura ma ta ba dan ya san abin da yay ma ta ne jiya. gida dai sai ya koma kamar gidan biki, don har wata walima suka haɗa wai ta murnar zuwan Mum, wacca tun bayan dawowarta bata sami zuwa ba, Fillo kam sosai taji daɗin zuwanta, kuma nan da nan duk sai ta sake sosai, irin Family ɗin nan ne masu saurin sabo, kuma masu sauƙin kai da mutunta wanda ya shigo cikin su. da yamma su na zaune a bedroom ɗin Granny wata me suna Nilfat ta shigo, ta kalli Granny tace,"duk kinga balarabiya kin maƙale mata". Granny tayi ma ta daƙuwa tana cewa,"ungo nan". Nilfat ta ce,"na gode, ai ba zan bari muyi faɗa ba, dan lallaɓaki nake na bi ki europe nima naje na samo irin wannan sulɓin fatar taki da bata tsufa". ta wuce wajen Fillo tana cewa,"ki je inji mijinki". Hajjah Yayar Granny ta ce,"kije kice masa ba zata zo ba, ashe shi ma irin Ahmad ne bai da kunya". "yaran yanzu ne fa, ai sai adu'a kawai, amma kunya ina suka ganta". cewar Granny. "to Hajjah tafiya fa zai yi, ai sallama za su yi ba wani abu yace zai yi mata ba". Nilfat ɗin ta ƙara faɗa. Hajjah ta ce,"kije kice masa yay tafiyarsa, dole ne sai sunyi sallamar, kaji min mara kunyar yaro, ko wani abu zai bata". Nilfat tayi ƙofa tana faɗin,"ni dai ban taɓa ganin inda akayi irin haka ba gaskiya, ya zai tafi ba tare da yay sallama da matarsa ba, wallah idan ni ce sai ince ta fasa zama, in ɗau kayata mu tafi, yo in ma ba sallamar zai yi ba ina laifi anan dan miji ya nemi matarsa". Fillo dai na kusa da Granny kanta a ƙasa, har ga Allah so take taje ta gan shi, tun ɗa zu rabonta da shi wai sun fita shi da wani Baffayo ɗan gidan Anty Hajar. Mum ta shigo a lokacin, ta zauna tana cewa,"wai Babana zai tafi, jirgin ƙarfe bakwai zai bi, daga masallaci zai wuce". sai ta kalli Fillo tace,"je kuyi sallama". sai ta kasa sakkowa, duk kunya ta kamata, ga shi ita ba waya ba balle tayi masa text tace ya tafi kawai, sai da Mum ta ƙara yi ma ta magana sannan ta sauko akan gadon ta ɗauki mayafinta ta fita. a compound ta tsaya tana kalle kallen inda zata gansa, Fareeda na zance daga can wajen flowers ta ƙwala ma ta kira,"Antee". Fillo ta ɗaga kai da murmushi tana kallonta. ta ƙarasa wajen na su, Farida tace,"ga wanda zan aura". "masha'Allah". Fillo ta faɗa kafin su shiga gaisawa da Modi. Farida ta ce,"mijinki ba?". Fillo ta ɗaga ma ta kai. "yana ɗakin Baffayo". "ina ne ɗakin?". "ki zagaya ta wurin shukokin nan, ɗaki na tsakiya me bishiyar ayaba a gabansa". Fillo tabi hanyar da Farida ta nuna ma ta, tun daga ƙofar ɗakin ta san Turaki na ciki saboda ƙamshin turarensa da duk ya cika wajen, ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Baffayo ne ya amsa sallamar, Turaki kuma ya ɗaga kai yana kallonta, Baffayo ya fita a ɗakin, ita kuma ta zagaya ta zauna akan kujerar da Turaki yake, ta shige jikinsa kamar yanda ya buɗe ma ta hannu. "yau ni kike gudu ko?". ta ɗago kai tana kallonsa ta ce,"kaima ai mantawa kayi da ni ka tafi wani wajen". yaja hancinta,"munje gidan wani Kakanmu ne, ƙanin me sunana, da naje suna ta tambayarki nace za ku zo ke da Mum". "to me ka siyo min?". "ɗa zu ba gani nayi kin saka fura agaba kina sha ba, ko irin ma ki tuna da mijinki a kusa". "to a gaban su Mum ɗin zance kazo ka sha?". "ni ma shiyasa ai da naje Alhaji ya ban abin daɗi ban iya cewa zan ragewa Matata ba". tai murmushi da kiran sunansa,"Turaki". ya ce,"na'am Halima". ta ɗan bugi kafaɗarsa,"sunan fa Ummi ne". yasa hannu ya rufe bakinsa,"Allah na tuba ka yafe ni". sai kuma ya kama kumatunta yana cewa,"to ni ma ai sunan Abba ne kike faɗa". "to ai dai ba ainihin sunansa na faɗa ba, Turaki na ce". "ehh haka ne afiruwa". ta turo baki gaba,"mene afiruwa?". "ɗan siririn mutum da za ki gansa kamar lamba ɗaya, kin san one bata da kauri kwatakwata". ta shiga kai masa dukan wasa, shi kuma yasa hannu yana karewa yana dariya har sai da ya kama hannayenta ya riƙe. "ai indai ƙiba ce zan yi". yace,"ni ma na san da wannan, aikina kawai zanyi". sai kuma ya kalli agogon hannunsa ya ce,"za ki sa nayi late, jirgi ya tashi babu ni, tun ɗazu na aika ki zo kika ƙi, da nayi tafiyata ai". "da ni kuma yau banyi bacci ba nayi ta kuka, saboda duk yau nayi kewarka ban ganka sosai ba". "ehh ba ke bace naga yau duk kina ta shareni, kawai saboda na saka kinji daɗi jiya". ba shiri tasa hannu ta rufe fuska, ya ɗauke hannun yana faɗin,"idan kika tashi dawowa ki dawo da babban shiri". "shirin me?". ya goga hancinsa da nata yana jan haɓarta,"sai kin dawo ɗin dai, ke dai kawai kici tuwon dawar Innah kiyi ƙarfi". ta cuno baki tana faɗin,"ni dai sai ka faɗa min shirin me?". "shirin karatu". "wanne karatu?". "karatun manya". "wanne karatun manya kuma?, ni ban sansa ba ai". ya ɗora hannunsa saman cinyarsa ya tallabi haɓarsa yana kallonta ya ce,"karatun da zai mayar da ke cikakkiyar matar aure". ta ɗan murguɗa baki bata ce komai ba. ya lanƙwasa yatsanta ya ce,"ni dai kici tuwon dawa da yawa kiyi ƙarfi, don karatun ba na wasa ba ne, Mum tace 7days za kuyi, ni kuma 7days yay min yawa, dan haka ki dame ta ku taho jibi". tai lamo da kanta a kafaɗarsa tana cewa,"kamar ma kar na koma ai, family ɗin ku suna da kirki sosai". "ni ma haka suke ta ce min wai nayi sa'ar mata me hankali da mutunci, anyway yanzu dai faɗa min when zaku dawo?". ta ce,"to ka zauna anan mana kaima". "kije ki faɗawa Mum hakan". suka miƙa yana manneta a jikinsa,"7days yayi yawa Fulani Nah, ki faɗawa Mum hakan". ta ce,"7days yayi kaɗan Turaki, ina so zanje inga Ummi nah, kaga babu nisa daga nan". bai ƙara cewa komai ba ya kama hannunta suka fita, lokacin Baffayo har ya tayar da mota, yay ma ta side hug yace,"please don't stress your self wajen yin aikace-aikace da zuwa gaishe gaishe, dan gidan nan da kike ganinsu aiki suke kamar injina. fita indai ba'a mota ba ne kice da Mum ba kya jin daɗi". ta gyaɗa masa kai kawai tana jin babu daɗi, sam bata so ya tafi. ganin hawaye a fuskarta yasa shi cewa,"ko in faɗawa Mum ba kya son zama?". ta girgiza kanta alamar a'a tana riƙe hannunsa. sai yaji ta ba shi tausayi sosai. "daina kukan Fulani Nah bana son hawayenki". ya faɗa yana share ma ta hawayen. sai ya ɗaga waya yana kiran babbar ƴar gidan Inna me su na Hamida, tana zuwa ya ce da ita,"ki kula min da ita kinji, less hayaniya a inda zata zauna please, tana son bacci ki kula da haka, sai an bata abinci tukunna take ci if not zata zauna da yunwa, bata da cikakkiyar lafiya, so duk wanda zai zauna kusa da ita ki tabbatar is not addicted to ɓatawa mutum rai". tace,"insha'Allahu za'a kula me sunan tsoho". yay murmushi yana maida kallonsa ga Fillo, wacce ta maƙale hannunsa tana hawaye, ya sunkuya yana ɗora kumatunsa kan leɓenta yace,"ummm 1 peck". abin da bata taɓa yi masa ba, kuma shi ma bai tsammaci zata yi ɗin ba, tai masa peck a kumatu tare da kissing ɗinsa a goshi tana faɗin,"i will miss you". "i will miss you too, take care...bye bye". ta ɗaga masa hannu tana faɗin,"bye". ya sauke ajiyar zuciya,"ba ki min adu'a ba". tasa hannu akan ido irin yacca yara ke kuka tace,"Allah ya kai ka lafiya, Allah ya tsare hanya, Allah ya kare ka da kariyarsa". ya amsa da,"amin, thank you so much". kafin ya iya sakin hannunta ya wuce mota, ita kuma taji wani kuka ya taho ma ta but sai ta danne shi saboda Hamida, su na shiga ciki ta wuce ɗakin Hamida ta kwanta akan gado. wajen ƙarfe goma na dare sun kwanta ita da Hamida sai ga Nilfat ta shigo ɗakin, ta kunna fitila ɗakin ya gauraye da haske, Fillo ta buɗe idonta don ba baccin take yi ba. "au ashe baccin naku ma bai yi nisa ba, mijinki ne ya kira waya". ta ƙaraso tana bawa Fillo wayar, sai taji wani daɗi ya ratsata, tun ɗa zu take ta tunaninsa, ta kasa ko baccin har Hamida tazo ta kwanta tayi nata, infact jinta take kamar mara lafiya, ta karɓi wayar tana kallon Nilfat da zata fita tace,"ki tsaya ki karɓi wayar". ta ce,"wala, ba tawa bace ai ta Baffayo ce, yace da safe ya karɓa". ta fita tana rufe musu ƙofar, daidai da shigowar kiran Turaki wayar. tana ɗagawa ta saka kukan shagwaɓa,"tun ɗa zu sai yanzu ku ka je?". "am sorry Fulani Nah, na dawo ne na tarar Maama babu lafiya, yanzu muka dawowa ma daga asibiti". "subhanallah, me yake damunta?". "Bp ɗin ta ne, but da sauƙi, ko in kai mata wayar?". ya tambaya jin ta damu sosai. ta ɗaga kai kamar yana ganinta,"ehh". yana zuwa ɗakin ya tarar Maama tayi bacci, Fillo tace da safe ya faɗa ma ta tana yi mata sannu sosai. ya ce,"insha'Allah, tun ɗazu na kira Mum amma sai na kasa cewa ta baki. ba kiyi bacci ba ko tashinki aka yi?". "ai na kasa yi". "why?". tayi shiru ta kasa cewa komai. ya ƙara cewa,"why?, tell me". "i am missing your warm body that makes me fall asleep". taji murmushinsa me sauti ya fito. "sorry Fulani Nah, just close your eyes and go to sleep, I will come to your dreams, then you sleep like you used to". a shagwaɓe ta ce,"promise?". ya ce,"insha'Allah". ba su jima su na wayar ba yace ta kwanta zai je Baffa na kiransa. ta sauke numfashi tare da ce masa,"don't forget to Perform Ablution and recite Al'qur'an before you sleep". ya ce,"i will not forget, good nite". sam bata so wayar tasu ta ƙare, ta danne kukan kewarsa gudun karta ɗaga hankalinsa ta ce,"good nite, sweet dreams, please you take good care of your self". "insha'Allah". da ƙyar dai suka iya yin sallama, Fillo ta tashi ta kashe fitilar sannan ta dawo ta kwanta tayi lamo, ba don tana jin zata iya baccin ba, zuciyarta ta cika fal tare da tunaninka kala-kala, har ɓarawon bacci ya ɗauketa. [9/7, 01:30] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *55* kiran sallar farko a kunnen Fillo, tana buɗe ido ta ganta a inda saɓanin Mafarkinta ya nuna ma ta. ta ɓata fuska tana jin kamar tayi kuka, wayar Baffayo da ke gefen pillow ta ɗauko, adu'arta ɗaya Allah yasa babu pin a jiki, cikin sa'a kuma tana dubawa taga babu, don haka da sauri ta shiga message tayi typing text kamar haka. _I don’t just miss you, i miss the warmth in your breath, depth in your eyes, the touch of your fingers, and feeling your hands on my waist. I miss you truly and deeply._ after ta gama rubutawan kuma sai ta kasa sending, ta tsaya tana tunani, kunyar turawar takeyi, ta zuro ƙafafunta ƙasa daga kan gadon kamar wacca zata yi kuka, har sai da Hamida ta buɗe ido ta tambayeta,"Asiraawo lafiya?". "yi haƙuri na tashe ki, ji nayi kamar wani abu na bina ne, ashe zaren jikin rigata ne". Hamida tayi murmushi kawai tare da komawa ta kwanta, don ita kanta ta fahimci tana cikin kewar mijinta ne, duk da tana da nauyin bacci but tana jinta sai faman juyi take. Fillo ta tura text ɗin sannan ta wuce toilet ta yo alwala ta fito, har ta idda sallar asuba bata ga reply ɗin Turaki ba kamar yanda tayi tsammani. duk sai taji babu daɗi, may be ko text ɗin ne bai yi masa ba, ko kuma abin da ta tura ɗin ne bai dace ba, duk sai taji ta kasa komawa baccin da yake so ya ɗauketa. da safe wajen ƙarfe tara after sun gama breakfast, taji su na waya shi da Mum har take tambayarsa jikin Maama, tai ta jin kamar tace da Mum ta bata wayar, kewar muryarsa take yi kamar ta shekara dubu ɗari bata ji ba. kuma bayan sun gama wayar da Mum a tunaninta ko zai kirata a wayar Baffayo sai taga har ƙarfe tara bai kira ba, sai taji kamar ta fara fushi da shi, but haka ta ƙara ɗaukar wayar ta ƙara tura masa text. _The thought of you makes me smile, but the distance we share makes my heart ache. I am missing everything about you. I wish you were here Turaki._ ta tura da yaƙinin cewa a wannan lokacin zai dawo ma ta da reply tunda dai tasan yanzu wayarsa na hannunsa, but sai ta ƙara jin shiru, idonta ya ciko da ruwan ƙwalla ta ƙara tura masa text. _kuma ba zan dawo gidan ba._ tana turawa ta ɗauki wayar ta fita ta kaiwa Baffayo, har ya tambayeta ta gama ne tace masa ehh ko ya kira ma ba sai ya kawo ma ta ba. ta koma ciki ta shirya kamar yanda Mum ta umarceta don za su fara zagayen gaishe-gaishen ƴan uwa. to acikin kwana biyu dai Fillo sai taji tamkar an sakata a kurkuku, mugun bala'in kewar Turaki take yi, har wata rama tayi ka rantse bata da lafiya, duk dare in zata kwanta sai tayi hawaye, ta riga ta saba da kwanciya a jikinsa, wannan ƙamshin jikin nasa, wannan ɗumin jikin nasa da ɗumin iskar bakinsa me ƙamshin min, wannan cairing ɗin nasa da soyayyarsa. tun ranar da suka zo bata ƙara jin muryarsa ba, yau da safe ya kira Baffayo ya kawo mata waya amma da ta karɓa sai ta kashe kiran, yay ta kira taƙi ɗagawa ita alallai tayi zuciya tun da ranar nan duk yana kallon messges ɗinta bai yi ma ta reply ba. wasa wasa dai sai taga ina ba zata iya yin har 7days ba, gida kawai take so ta koma, wurin Turakinta, tana missing late-night talk ɗin su, tana kewar precious smile ɗin sa, she want nothing except his presence around her, being away from him in this 4days she feels like being caged for a lifetime in misery. a daddafe ta iya kwana biyar ɗin da suka yi, tuni ta fara cutar ƙarya me zafi ta yanda dole su tarkata su koma gida, hakan kuwa akayi, da Mum taga jikinta yay worst sosai musamman da taga kamar har da iskokinta dole suka ɗauko hanya a ranar. sai ga su ƙarfe biyar na yamma sun sauka, don jirgi su ka biyo saboda Granny tace ba lallai Fillon ta iya jurar zaman mota ba, kuma su na dira a gombe taji ta warware daga cutar da ta fara kamata. Zaytuna ce tazo ta ɗauke su a airport, duk tunaninta gidanta za'a wuce da ita but sai taga sun yi gidan su Turaki, ba haka ta so ba sam, yacca ta so ta koma gida ko da ace bata same shi yana nan ba, to da ya dawo ya zama yay tozali da ita. san da taga Maama sai da gabanta ya faɗi, ashe ciwo take yi sosai dan duk ta rame, ta faɗa kamar ba ita ba. sai taji ta kasa riƙe hawayen tausayinta a lokacin da Maama ta rungumeta tana yi musu sannu da zuwa tana sanya ma ta albarka. yinin ranar gaba ɗaya tana tare da Maama, da ta motsa Hajiya Madina zata ce Daughter me kike so?, menene?, ko jikin ne mu tafi asibiti?. haka ita ma ana ta ɓangaren, motsi kaɗan Hajiya Madina zata yi ta fara tmbayarta Maama me za'ayi miki?, akwai abin da kike so?, a ranar gaba ɗaya sai take jin Hajiya Madina acan cikin zuciyarta, taji tamkar tana tare da Umminta ne. bayan isha'i su na zaune duk ɗin su a dining za su ci abinci, Hajiya Madina ta ce ita bata jin daɗin bakinta ta ƙoshi, babu yanda Hajiya Ramla ba ta yi da ita ba but ta kasaci kwata-kwata, ciwon kan da taji ma yana damunta sosai sai ta miƙe ta koma ɗakinta, Fillo ta ɗauki flask ta bi ta. "Daughter ya ba ki zauna cin abincin ba?". Fillo ta ƙaraso ciki ta ajiye abincin, sannan ta kamo hannun Hajiya Madina ta ce,"don Allah Maama ki sauko kici ko kaɗan ne". haka ta dinƙa roƙonta har sai da Maama ta sauko, da kanta ta riƙa ba ta abincin tana ci, ba ƙaramin daɗin hakan taji ba, kuma Fillo ta ƙara samun wani gurbi acikin zuciyarta, ta ƙara yin farin ciki da jin alfahari a game da dacen mata da Me Babban suna yayi. and sosai taji daɗin hirar da Fillo take yi ma ta, sai wajen ƙarfe 9 sai ga Turaki ya shigo ɗakin, kallo ɗaya Fillo tayi masa ta ɗauke kanta, ya shigo ya zauna a gefen Maama yana kama hannunta ya riƙe. "my happiness ya sauƙin jikin?". Hajiya Madina ta kalle shi cike da so da ƙauna ta ce,"na ji sauƙi me babban suna, ya office?". "masha'Allah, Allah ya ƙara miki lafiya, Zaytun ta ce min Bp ɗin ya koma normal". "ai na faɗa maka na ji sauƙi, ɗa zu ma da kayi ta kira bacci na sa mu". ya sauke numfashi ya ce,"insha'Allahu za ki rabu da ciwon nan Maama, ciwon nan yana takura ni da yawa". "to Allah yasa, amma ka san girma ya riga ya kama mu, lafiyar sai a hankali, sai dai ai tayi mana adu'a ciwo ya dinƙa zuwa da sauƙi". sai kuma ta lura da yanda Turaki ya ƙurawa Fillo ido, ita kuma kanta yana ƙasa tana matsa mata ƙafarta ta ɗaure fuska. sai tayi murmushi tace,"Daugher ina fatan dai baku da wata matsala ko?". Fillo tace,"ehh Maama babu". "to Allah yayi maku albarka, ubangiji ya wanzar da zaman lafiya na har abada a tsakaninku, Allah ya kauda mugun ido akanku". a tare suka amsa da amin. sai ta kamo hannayensu duk ta haɗe a waje ɗaya tana cewa da Turaki,"me babban suna ina roƙonka da kar Fillo ta rasa farin ciki ko da na sakan ɗaya daga wurinka, amana na baka ita, ka kula min da ita don Allah kaji, tayi min taimakon da ba zan taɓa iya biyanta ba, thats why nake so ka raineta da zallar soyayyarka, ka mayar da ita tamkar jaririya". ya shafo wuyansa bai iya cewa komai ba. sai ta dubi Fillo ma tace mata,"Daughter ɗago ki kalle ni karki ji kunyata". Fillo ta kasa har sai da Hajiya Madina tasa hannu a haɓarta ta ɗago fuskarta ta ce,"yaushe za'a haifa min jika?, a yanzu banda burin da ya wuce naga jikana Daughter, so nake na ga ina wasa da jikokina, ina fatan za ki samar min su da wuri". kunya ta kama Fillo sosai. "Allah dai ya kawo mana na gari masu albarka". cewar Hajiya Madina. cike da zolaya kuma ta ƙara cewa,"kyawawa nake so ki haifa min masu kama da ke fa, kar ki yarda su yi kama da Me Babban suna, shi wani lokacin kamar bai da kyau". duk suka yi dariya ba tare da sun ce komai ba. ta ƙara cewa,"Allah Daughter duk ranar da Me Babban suna yayi miki laifi ki zo ki faɗa min wallahi sai na rama miki, kinga haka...". Fillo ta ɗaga ido taga yacca ta kama kunnen Turaki. "to haka zan murɗe shi wallahi har sai yaji a jikinsa". Fillo tayi ƴar dariya shi kuma ya wurga mata harara fuska a cukule. kafin nan tace da su,"to ku tashi ku tafi ko, dare yana ƙara yi". Fillo tayi saurin cewa,"Maama don Allah zan kwana anan". ta faɗa a marairaice. Maama tace a'a ta tashi tabi mijinta su tafi, har ƙwalla sai da tayi da suka baro wajenta, sai da suka biya ta wajen Mum suka yi ma ta sallama kafin su tafi. a compound juyin duniya Fillo taƙi yarda Turaki ya kama hannunta, bata yarda ma sun jera ba ganin babu idon kowa, tayi gefe yay gefe, suka shiga mota ma taƙi kallonsa, sai faman ɓata rai take yi tana cin magana. da tsokana ya ce,"kika ce ba za ki dawo gidan ba". ta kalle shi sosai kafin ta ce,"da kayi ignoring message ɗin nawa hakan ai bai sa na damu ba". tun yana tsokanarta har ya rabu da ita saboda ganin ta ɗauka zafi, a lallai fushi take da shi kan ƙin responding messages na ta. ya koma sai dai ya kalleta yay murmushi ya shafo wuyansa, shi ba abin da ma yake so irin ta kula shi suyi rigima, tayi kuka ko tayi masa tsiwarta. motar tayi shiru ba abin da kake ji yana tashi sai busawar ac da kuma sautin waƙar i miss you ta Beverley craven. _here in a silence i wait, there is nothing else i can do, it feels like my heart gonna break, and all i can think of is you, and how my aching arms long to hold you, and show you how much i care, but i'm couting the hours without you, and i don't know how much i can bear, becox i miss you morethan word can say, all i need you here in my life always, yeah i miss you, till you are back with me._ waƙar ta dinga bin gaɓoɓin jikin Fillo tana ratsata, ta kalle shi ta wutsiyar ido taga ya wani sha murr kaman ba shi ke tsokanarta ɗa zu ba fuskarsa a washe da annuri, wanda ta tabbatar na jin daɗin ganinta ne. sai ta ɗan murguɗa baki kamar yana kallonta kafin ta kai hannu ta kashe waƙar, tana ɗauke hannu yana ƙara kunnawa, zata ƙara kashewa taji muryarsa a tamke yace,"ranki zai ɓaci". "to bana son jin waƙar ni". yay mata wani kallo yace,"motarki ko tawa?". ta haɗe gira tace,"ba yanzu aka gama baka amanta ba, aka ce kayi min duk abin da nake so". murmushi ya suɓuce a leɓensa, ya tuna alƙawarin da yaywa Maama na kula da Fillo tun ba'a ranar yau ba, ya tuna girman alƙawari, sai ya kai hannu ya kashe waƙar. sai ya koma yi da kansa, Fillo taji waƙar tafi daɗi sosai a bakinsa, sai ka rantse shi ya raira, ta lumshe ido tana ta sauraronsa, har su ka zo gida bata sa ni ba sai da ya danna horn da ƙarfi sannan ta buɗe ido. "a sauka a miƙo kuɗin mota". ya faɗa a sanda take ƙoƙarin buɗe ƙofa zata fita. ta juyo ta ɗan kalle shi tace,"in doller or in naira?". "in doller". ta gyaɗa kai kafin tace,"to driver you wait for me". Turaki ya buɗe baki galala, zai kamota tayi saurin ficewa tana dariya, shi ma ya fito ya bi bayanta da sauri don ba ya so ta riga sa hawa upstairs becx akwai suprising ɗinta da yake so yayi. a parlo ya sameta su na gaisawa da su Sakina, waɗanda suke kallo a parlo, su na yi mata sannu da zuwa, ita kuma tana ba su haƙurin tafiyar da tayi bata sanar musu ba. bai ko amsa gaisuwar da su Hannatu su ke masa ba ya kama hannun Fillo su ka ɗauki hanyar upstairs, a steps na uku da su ka taka yasa hannu ya rufe ma ta ido. ta san duk neman hanyar su shirya ne don haka sai taƙi kula shi har sanda taji ya buɗe ƙofar ɗaki sun shiga. ƙafafunta suka lume cikin marbles, da sanyin ac'n da ke ratsawa ta ko'ina acikin ɗakin, kafin daddaɗan ƙamshin nan nasa dake motsa zuciyarta ya shiga hancinta, taji san da ya maida ƙofar ya rufe, kafin ya sauke hannunsa a hankali daga idonta ya mayar kan ɗan ƙaramin ƙugunta, tare da ɗora haɓarsa a saman ƙafaɗarta. "suprise". hakan ya faɗa before ta shiga buɗe idanunta a hankali. ba ta san lokacin da ta buɗe idanuwanta duka ba, laɓɓanta suka tale kafin bakinta ya buɗe, fuskarta kuma ta bayyana wani irin farin ciki da jin daɗi. ƙananun bulbs ɗin dake haskawa zuwa different colours of light su suka fara shiga idonta, kafin baloons ɗin da akai design da heart shape ta ɗauki hankalinta, zuciyarta kuma taji ta motsa da zafin ƙauna a lokacin da ta ɗora ido akan flowers ɗin da aka baza akan gado. gaba ɗaya sai ta kasa magana balle motsi saboda yacca abin ya burgeta, sai ta fara bin kowacce kusurwa ta ɗakin da kallo, ta san ɗakin, wan nan ɗakin ne da suke rayuwa ita da Turaki a cikinsa, kuma wan nan lafiyayyan gadon me ɗauke da flowers, gadon su ne me ɗauke da katifar nan me bala'in taushi da suke kwanciya akai manne da juna, but ta ya akayi yau ya sauya?, azababben decoration ɗin da aka yi masa ya mayar da shi tamkar ba wannan ɗakin da suke yini acikinsa ba. _me hakan yake nufi?._ tambayar da zuciyarta tayi kenan, kuma sai taji hannayen Turaki sun kama fuskarta sun karkartar da ita zuwa gaban body mirrow dake gefe ɗaya, ƙwayar idonta ta tsaya cak akan ballon numbers ɗin da aka jera me ɗauke da 1 and 9 making 19, a hankali kuma idonta ya sauka akan ƙaton cake ɗin dake kewaye da candles. muryar Turaki tayi whispering acikin kunnenta da faɗin,"Happy Birthday to you Fulani Nah". she was just astonished, ta juyo ta fuskance shi tana faɗin,"my birthday?". ya jijjaga ma ta kai alamar ehh. with great joy tace,"but how do you know Turaki?, i don't think there is anyone who knows my birthday date". ya ce,"har Ummi?". tayi ɗan shiru tsananin farin cikinta na kasa ɓoyuwa ta ɗaga masa kai. ya daɗa kama ƙugunta yace,"to Ummi ce ta faɗa min, tace ta haifeki a ranar da Yayarta ta rasu shiyasa ba zata manta da date ɗin ba, you are 19years older now, Kaka ce take lissafi ba daidai ba". ta juya ta ƙara kallon yanda aka ƙawata kyan ɗakin. "and all this becouse of my day?". "yes! domin farin cikinki kawai". ya faɗa yana sumbatar kumatunta. hawaye su ka saukowa Fillo ta juyo tayi masa wani irin tight hug. ruwan hawayen ya ɗiga a bayan Turaki, ɗuminsa ya wanzu acikin fatarsa, yasa nasa hannun wurin kewayeta yana shafa gashin kanta, ya ce,"why the Cry Fulani Nah?, i did everything just to make you happy not to make you cry, please stop crying let us celebrate the day". ta ƙara fashewa da kuka tana ƙara rungume shi. "you totally suprised me!, am so blessed and honored to have you, thank so much you for making my birthday so special. You made me feel like a princess and gave me the best gift anyone could ever receive. You are my best friend and I love you more than anything in this world! Thank you for making my day special with your love, care and amazing surprises. i am so lucky to have a wonderful husband like you". ta sake shi tana haɗe goshinsu wuri ɗaya,"Allah yaja da ran mahaifanka, Allah yasa ka rabu da su lafiya, Allah ya ba ni ikon faranta maka nima". ji tayi ya ɗagata sama yana hajijiya da ita yayin da suke rera waƙa tare, waƙar da ita bata iya ba sai in yayi sai ta kama, a haka ya dinƙa zagaye da ita acikin ɗakin har sai da ta fashe duk baloons ɗin da aka ɗaura. kafin ya sauketa ya kama hannunta suka ƙarasa gaban cake, ya zauna a kan ƙaramin carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen, sannan ya zaunar da ita akan ƙafafunsa da ya tankwashe. tare suka yi cutting cake ɗin, ta ciro ta kai bakinsa, har ya buɗe bakin sai ta fasa saka masa ta janye tana ƴar dariya, tasa a bakinta tana faɗin ba zai ci ba. ta ƙara yanko wani zata kai bakinta sai ya juyar da hannun ya saka a nasa, sai da ya fara taunawa sannan ya kai bakinsa nata ya ɗaga ma ta gira. tayi ƙasa da idonta sannan ta buɗe bakin, yasa bakinsa cikin nata ya zuba mata taunannan cake ɗin, a lokaci ɗaya tayi differenciating tsakanin daɗin yawunsa da cream na cake din. ta lumshe ido tana taunawa a hankali, yayin da Turaki ke yawo da hannunsa cikin rigarta, ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana faɗin,"Maama tace tana son ganin jikokinta, tana so tayi wasa da su". ya murza tafin hannunta ya ƙara cewa,"yaushe za mu samar ma ta su?". Fillo tayi murmushi tare da ɓoye fuskarta a saman sumarsa. ya mayar da hannunsa fuskarta ya shafo sajenta,"ki amsa min don in san lokacin da zan ƙara ganin farin cikinta ya ƙaru". "ni ma ban sa ni ba". ta faɗa in a cool voice. yay murmushi tare da ɗago fuskarta yana kallonta. "if you are ready we will get them today". tayi saurin girgiza masa kai,"not today". "then when?". tayi shiru ba tare da amsa masa ba. sai ya sauke numfashi yace,"ba kya tunanin nayi haƙuri da yawa kuma ina kan yi?". ta marairaice murya cike da tsoron da ya fara kamata tace,"ai kai mai haƙuri ne, ka ƙara yi". bai yi magana ba ya ɗauko wani card ya bata, ta karɓa ta buɗe ta shiga karanta abin da ke ciki. _On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a wife like you is indeed a gift.. Happy Birthday Fulanin Turaki, wishing you a long life and prosperity._ wani sanyayyan murmushi ya suɓuce ma ta, ta kai laɓɓanta saman goshinsa tayi kissing, ta ce,"tanx, really appericiate". martanin murnushin ya mayar mata, sannan suka saka cake ɗin a gaba suka yi masa cin yunwa. mutumin da baya shan choculate sai ga shi yay damalmala bakinsa da choculate wajen sha. bayan sun gama cin cake da shan choculate suka miƙe daga wajen, kwatakwata Turaki bai bari ta fahimci rashin jin daɗin da yake ciki ba. suka shiga toilet tare don yin brush, Fillo tace masa tana so tayi wanka, ya fita ya barta aciki, ɗakinta yaje ya ɗauko ma ta kayan da zata saka. after 10minutes Fillo ta fito daga wankan, sai dai lokaci ɗaya ƙirjinta yay wani mugun bugawa ganin Turaki duƙe a ƙasa ya riƙe cikinsa yana wani irin nishi. siraran ƙafarta suka jata cikin sauri ta ƙarasa gabansa, ta tsuguna tare da ɗora hannunta saman sumar kansa sannan ta kira sunansa. sai dai a wannan lokacin baya jin zai iya amsa mata balle ya iya ɗagowa ya kalleta, duk jikinsa rawa yake yi tamkar me jin sanyi, after all ɗakin lulluɓe yake da ɗumi me daɗi. cikinsa ne ke yi masa ciwo sosai, irin ciwon cikin da bai taɓa yi ba, wani irin ciwon ciki ne da yake jikin tamkar numfashinsa zai tsaya cak. yanayin nasa yay bala'in gigita Fillo, tuni idonta ya kawo ruwa ganin yacca yake shuri da ƙafafunsa a ƙasa, gaba ɗaya jikinta sai ya ɗauki rawa kwatankwacin yanda nasa ke yi. duk sai ta nemi dabara da wani tunani acikin kanta ta rasa, ta kasa magana ma ballanta ta tambaye shi me yake damunsa, and bata san me zata yi masa ba. cikin karkarwar hannu ta ɗago kansa daga duƙen da yake, hawayenta ya ɗiga a saman fuskarsa, ya buɗe idanuwansa da suka sauya kala ya dubeta. ta fashe da kuka tana tambayarsa me ya faru da shi?. da ƙyar ya iya buɗe baki yace ma ta,"cikina Fulani". a hargitse ta ce,"ciwo yake ma?". kansa kawai ya iya ɗaga ma ta. "ko cake ɗin da muka ci ne?". nan ma bai iya cewa da ita komai ba, ta tashi a rikice taje ta buɗe drower ta kwaso drugs ɗinsa, sannan ta fita da gudu ta sauka ƙasa ta ɗauko ruwa ta dawo. lokacin da ta dawo ya kwanta a ƙasa yana murƙusus, ta dawo ta ɗago shi da ƙyar, jikinsa duk ya jiƙe da gumi, kuka kawai take yi a lokacin ta kasa cewa komai. "buɗe bakinka kasha magani". ta faɗa cikin muryar da ta dusashe da kuka. sai ya buɗe idanuwansa ya dubeta a cikin gigitar ciwo da neman fitar hayyaci, ya manna kansa a cikinta gami da cusa fuskarsa a ƙirjinta. ƙamshin turaren da tayi wanka da shi ya ƙara motsa ciwon nasa, sai ya damƙo hannunta cikin kyarmar jiki ya ɗora a mararsa ya danna. lokaci ɗaya taji ya kanainayeta ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da taji tamkar zai ɓalla ƙasusuwanta, ƙanƙamar da ta hanata motsi ko kaɗan. hankalin Fillo ya ƙara tashi, cikin firgici ta buɗe baki, murya na rawa ta fara ce masa,"ga maganinka na ɗauko, don Allah ka tashi ka sha, i don't want to lose you". Wani irin rumtse idanu Turaki yayi saboda azaban murɗawar da mararsa ta ƙara yi, ya daɗa ƙanƙameta tare da ƙara danna hannunta a saman mararsa. Fillo ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin,"in kira Maama?, ban iya driving ba in kira Adda Zaytun?, ko Bello zan kirawo?, in je in faɗawa Baba me gadi?". tai maganar duk a gigice tana ƙoƙarin zare shi a jikinta taje ta ɗauko wayarsa. sai ya kai hannunsa zuwa wuyanta, ya sunkuyo da kanta yana ɗago da fuskarsa daga saman boobs ɗinta da ya cusa. muryarsa a shaƙe tamkar ba tasa ba yace,"Don't call any body Fulani". "no i have to, you are in critical condition, you have to see a doctor, let me call Ya Yusuf". ta miƙe taje ta ɗauko wayarsa, already akwai finger print ɗinta akai, hannunta banda kyarma ba abin da yake, tama rasa yanda za'ai tayi operating wayar. taji ya kamo hannunta yana repeating mata cewa kar ta kira kowa. "don't call any body Fulani, i don't need to see doctor, you can take care of me, the medicine is with you". "to me zan maka?". "i just need you Fulani, i need you very badly, please let me have you today". ta ƙanƙame hannunsa, hakan ya ba shi tabbacin bata gane nufinsa ba, yana numfashi sosai yace,"ina so in kusance ki, ina so muyi mu'amala ta auratayya, don Allah kar ki hanani kusantarki a yau, idan ba haka ba zan mutu, surely you will lose me". "to hakan shi zai sa ka sami lafiya?". idanuwansa a lumshe ya ɗaga mata kansa. Fillo ta rumtse ido sosai sabon hawaye na sakko mata, tare da jan wani irin gwauron numfashi, kana cikin tsananin harbawar da zuciyarta ke yi ta daɗa sunkuyo da kanta, ta haɗe fuskarta da tasa. numfashinsu ya gauraya, wani dunƙulen yawu ya wuce ta maƙogoronta da ƙyar, cikin bala'in harbawan da zuciyarta ke yi ta ɗaura lips ɗinta saman na shi a hankali. a hankali ta shiga shan lips ɗinsa kamar yanda ya koyar da ita. numfashin Fillo ya fara rawa saboda tsoro da ke cikin ranta, tayi ƙoƙarin zare bakinta don dakatarta da abin da takeyi, but sai taji ya ƙanƙameta tabbacin ba ya so ta katse. bata ankare ba sai ganinsa tayi ya miƙe zaune still bai raba bakinsu ba, a yanzu kuma shi ya shiga shan lips ɗin nata cikin salon da ya fara aika saƙo cikin ƙwaƙwalwarta. ta fara kuka a hankali tana so ta zare bakinta, ya damƙeta da kyau yana girgiza mata kai,"a'a Fulani". san da yay pressing lips ɗinsa on her boobs zuciyarta ta ambaci sunan Allah. tunaninta ya tsaya cak, taji yawun bakinta ya bushe kamar bushewar famfo, sannan taji kamar tana neman ta suma. "Please Fulani Nah...". haka taji kamar ya faɗa, but sai ta gaza fahimtar komai balle tayi komai ɗin da yake so. wucewar daƙiƙa ɗaya taji yana neman ɗauke bakinsa, da sauri tasa hannayenta a gaban rigarsa ta dawo da shi. jikinsa na rawa kamar mazari ya ɗauketa idanuwansu duk a rufe, amma a haka ya ƙarasa gado ya kwantar da ita yana zare towel ɗin jikinta a zafafe yayi wurgi da shi. tuni kukanta ya ƙaru, but bata tunanin a yanzu zata iya hana shi duk yanda ya so yayi da ita, domin ita kanta ta fara jin daɗin yanayin na su, abin da yake buƙata ita ma shi take buƙata a yanzu. Fillo ta lumshe idanu jin skin ɗinsa ya haɗu da nata, haɗuwar da tasa Turaki ƙara burkicewa, gently ya shiga shafa jikinta ya fara yi mata wani salo, wannan salon nasa shi ɗaya, salon da taji yana neman ɗaukarta ya kaita saman gajimare. a san da taji hannayensa a waji waje da bai taɓa zuwa ba, a lokacin numfashinta ya fara katsewa, tasirin abin da yake aiwatarwa na bin kowacce jijiya ta jikinta. wani abu yake yi mata da bata taɓa experiencing ba tun da ta zo duniya. cikin wata iriyar murya taji yana faɗin,"help me, Fulani help me please". a wannan lokacin kuka sosai Fillo ke yi, so take ta hanasa zuwa inda yake ta rawar ɗarin ya shiga amma sai taji ta kasa, roƙo da magiya kawai take yi akan ya ƙyaleta amma sam Turaki bai san tana yi ba. daga lokacin da taji ya fara adu'ar saduwa da iyali, daga lokacin firgicinta ya ƙaru, ta daina ji ta daina gane komai, domin abin da yake shirin yi ya shallake tunaninta, ba irin wannan abun da yay mata bane wancan ranar, duk yadda ta tsammaci abun ya wuce tunaninta, motsi wannan ta kasa balle ta samu ƙarfin ture shi, sunan Ummi da Kaka da Maama da Mum da shi kansa ɗin kawai take aikin kira akan su zo su ceceta. and cikin abin da bai fi ƙiftawar ido ba Turaki ya rabata da virgin ɗinta, ƙofar da sai da ya sha baƙar wahala kafin ya shigeta, lamarin da yay kacakaca da duk wani lissafi da tunanin Fillo. abu ɗaya ne ta san da shi, wanannan daren, wannan abun da ya faru, abubuwa ne da za su kasance a cikin ƙwaƙwalwarta, ɓangaren tunaninta, wurin da ba za su taɓa gogewa ba har abada. [9/7, 01:48] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *56* agogon dake manne a bangon ɗakin, tsintsiyar jikinsa ta kaɗa cikin sautin dake ba da ƙarar ɗil, ɗil, ɗil. sakanni 1,2,3 su ka wuce kafin ya shiga bugawar daƙiƙu 1,2,3 har zuwa biyar. sautin ƙarar ya shiga cikin kunnuwan Turaki kaɗai, kuma a wannan lokacin komai ya lafa, komai banda sautin kukan Fulani da ke tashi. dogayen gashin idon Turaki su ka ɗaga, kafin murfin idanuwansa su ka buɗe, ya waiga ya kalli Fillo, ya rungumota tsam a ƙirjinsa, numfashi kawai yake saukewa tamkar wanda yay tseren gudu tun daga china, magana yake so yayi but sam ya kasa, ji yake tamkar yau ne rana ta farko, kamar today is the first day he knows the virginity of a woman in his life, sai ya lumshe idonsa, abu ɗaya ne yake da akwai, daɗin wannan ya fi wancan. yana jin yanda hawayenta ke sauka a jikinsa, sautin kukanta na fita ɗauke da tsabar wahala, hawayen da suka wanzar da wani bala'in tausayinta a ransa, ya ɗago hannu da ƙyar zai goge mata hawayen sai yaji ta ture hannun a zuciye. ya buɗe idonsa ya kalleta sai yaga idonta a rufe yake, sai uban hawaye dake silalowa ta gefen idonta kamar an kunna famfo, da ma ya lafiyar kura balle an taɓota, yay wani irin murmushi da zai iya cewa bai taɓa yin irinsa ba, ƙara tsamketa yay a jikinsa har sanda baccin wahala ya ɗauketa. kissing lips dinta yay kafin ya zare ta daga jikinsa, ya sauka akan gadon yaje ya kunna fitila don ba ya jin lamp ɗin dake kusa da gadon iyaka haskenta zai wadatar da shi wajen kallonta. ya kalli agogo yaga ƙarfe ɗaya da rabi, dawowa yay ya zauna, yay tagumi yana kallon fuskar Fillo da tayi jawur kamar jini zai fito, dogayen gashin idonsa suka ƙifta a hankali, ya kamo hannunta ya riƙe yana kallon fuskarta da tayi looking so innocent. hawaye duk ya bushe a fuskar, wani irin azababben sonta da ƙaunarta yaji suna fuzgarsa, ya san yana sonta tun a lokacin da bai san ya kamu ba, but a yanzu sai yake jin tamkar wani sabon son nata aka dasa a zuciyarsa, gaba ɗaya ta gama mallake zuciyarsa a yau, he was in a state of indescribable joy. ya san yayi farin ciki da yawa a rayuwarsa, iyaka adadin farin cikin da ba zai ƙirgu ba, but bai taɓa tunanin cewa akwai wani farin ciki a duniya na daban ba kamar wanda yake ji a yanzu, sai yanzu ya shaida farin cikin duniya daban, haka ma farin cikin aure tare da wadda kake so daban. kallonta yake yi tamkar yau ya fara ganinta, sai ƙyalli take yi, she looks so gorgeous and affectionate. ya ɗora yatsansa saman lips ɗinta da ta turo gaba ta taɓe su, yay murmushi, in ban da bacci take yi ya san dole ma sai tayi masa tsiwa. ƙarfe uku da rabi hannun Fillo ya miƙe ya sauka akan cinyar Turaki, ta buɗe idanuwanta da suka yi mata mugun nauyi, ƙwayar idonta ta sauka akan fuskarsa. a san da su ka haɗa ido sai tayi saurin runtse ido ta juyar da kanta gefe. sabon kuka ne yake so ya ƙwace mata, so take ta motsa ta miƙe amma bata jin zata iya, every part of her body feels as if it is not her own, she is feeling pain everywhere, she wished ace bata yarda ta amince masa ba, kawai sai ta sa ki wani marayan kuka tana jin yacca take zugi ke ziyartar ƙasanta. sautin kukan nata ya tafi ya zarce har cikin ƙuryar zuciyar Turaki ya matse zuciyarsa, zuciyar tayi rawa, da sauri ya ɗagota ya rungumeta yana shafa bayanta, shi kansa ya san dole tayi kuka, ya san bai yi mata ta sauƙi ba, bai ma san ta inda zai soma lallashinta ba, jinsa yake kamar babu wasu kalamai akan harshensa. jin yanda hawayenta ke sauka akan fatarsa yasa ya dagota daga kafaɗarsa, sai kawai yasa harshensa yana goge ma ta hawayen, muryarsa na karyewa yake faɗin,"i am sorry wifey, you must pass this stage kafin kika zama cikakkiyar mace". yaji ta ɗora hannunta akan ƙirjinsa, kafin muryarta ta fito cikin rauni tana faɗin,"mutuwa zan yi". da sauri ya shiga girgiza mata kai yana faɗin,"not now, you will not die Wifiey, please don't say it again". ta ƙara cewa,"jikina duk ciwo, ba zan iya motsawa ba". ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka sosai, from the way tayi maganar za kasan a cikin ciwo take. "zai daina ciwon yanzu insha'Allah, my only wish is you stop crying". lallashinta kawai Turaki ke yi amma kamar yana tunzurata, Kukanta har cikin ransa yake ji, duk tausayinta ya lulluɓe shi, ji yake ina ma da damar da zai maida ciwon jikinsa. duk ya rasa yanda zai yi mata, cikin kansa ya zama babu komai balle yay tunanin wata dabara, kamar bai san wa ni abu da zai yi mata taji sauƙin ciwon ba, ranar da ya kusancin Ilham tashi yay ya barta balle ya iya tuna wani abu guda ɗaya da yaga ta yiwa kanta ko kuma shi ɗin yay mata. kuma kamar zai yi kukan shi ma, ya ɗauko wayarsa ya danna kiran lambar Zaytuna, har sau biyu bata ɗaga ba. sai ya kira ta Bello, sai da kiran ya kusa katsewa sannan ya ɗaga, kuma sai bayan Bello ya ɗaga tukunna ya fara tunanin me zai faɗa masa?, yace masa me?. yay guntun tsaki, yana jin Bello na ta hello hello MT lafiya a wannan daren, amma bai iya ce masa komai ba, sai kawai yay cilli da wayar ba tare da ya kashe ba. sai a yanzu yaji ƙwaƙwalwarsa na karanta masa abin da ya kamata yayi, ya kwantar da ita cikin sauri ya shiga toilet ya kunna ruwan zafi, ya fito a daidai lokacin da kiran Bello ya shigo wayarsa, ya ɗauki Fillo sanna ya ɗau wayar ya kara a kunnensa. ko abin da Bello ke cewa bai tsaya saurare ba yace masa,"after warm water then what?". Bello yace,"Allah ya saka min kawai". sannan ya kashe wayar bayan yaja dogon tsaki, Turaki na shirin ajiye wayar sai ga text ɗin Bello ya shigo. _sodium bicarbonate, salt and veniger._ yana karantawa ya mayar da Fillo ya kwantar, a wannan uban daren ya fita yaje part ɗin Ilham, dan acan ne yaga veniger da bakin soda, daga kitchen ɗinta ma ya ɗauko gishiri. yana dawowa ƙarar text na ƙara shigowa. _just use salt and veniger is oak._ ya jefar da robar baking soda ɗin sannan ya shiga toilet ya kashe ruwan da ya kunna yake ta zuba, ya zuba abin da zai zuba ya sirka ruwan sannan ya fito. yana kama blanket zai ɗaga ta damƙe tana girgiza masa kai,"please". ya rufe ido ya buɗe,"babu abin da zan ƙara miki Angel". sannan ta iya sakin blanket ɗin ya ɗauketa, yana sakata acikin ruwan ta fashe masa ta wani irin kuka tana riƙe shi, sai yaji kamar ya fito da ita, but he has no other choice. "sorry Angel, i know it is painful but that will only make you feel better". azabar duniya ta ishi Fillo, ta ƙara damƙo shi zata fito ya daɗa mayar da ita, kuka take sosai tana faɗin zata mutu, a sitz bath ɗin nan dai gaba ɗaya ta ruɗa Turaki ta gama gigita shi. kuma duk uwar masifar da ta dinƙa masa akan ita ya fita ya ƙyaleta bata son ganinsa amma yaƙi fita, har sai da ya tabbatar ta ga su tukunna ya cirota yay mata wanka da kansa, anayi tana kai masa duka, bayan an gama sannan ya naɗota a towel kamar new born Baby ya fito da ita. yana ɗorata saman gadon ta zabga masa harara,"ƙafana ba zai kuma iya tafiya ba". ya zauna tare da kamo hannunta, zata ƙwace ya hana hakan, kissing forhead ɗinta yay kafin yace. "Allah ya yi miki albarka, Allah yay miki sakayya da Aljannatul firdaus, na gode da kika kula min da kanki, yanda kika saka ni cikin farin ciki, ina roƙon ubangiji ya bani ikon faranta miki har ƙarshen rayuwata, insha'Allahu ba zan taɓa cutar da ke ba, wannan alƙawarina ne". sai ya saketa yace,"kina jin ciwo a jikinki?". ta ɗaga masa kai,"ai duk ka ɓalla ni". "ban ɓallaki ba Hottie, yanzu ma zan ke baki abincin da zai sa kiyi ƙiba ba za ki ɓalle ba". ta ɗaura kanta saman shoulder ɗinsa tace,"zafi nake ji". ya ce,"ai na?". sai tayi shiru, ya sauke numfashi yana shafo gefen fuskarta. "zai daina, zai daina zafin kafin safiya". sai kuma ya kira sunanta,"Fulani Nah". ta amsa,"ummm". ya ce,"I don’t have all of the words to express how much you mean to me. I can only say that you are the center of my life and everything else revolves around our love for each other.  I will keep caring, adoring and loving you forever, during the easy times and the challenges we will face. I love you so much Angel". ya shiga shafa fuskarta yana faɗin,"you deserve a gift from me in return of what you gave me". "Bacci nake ji". ta faɗa da tsantsar shagwaɓar da ta motsa zuciyarsa, cikin murya me ban tausayi. bargon ya ɗaga ya shigar da su ciki, da farko taƙi kwanciya a jikinsa saboda tsoronsa da take yi, kuma da ya shiga kalallameta sai ta lumshe ido ta lafe a ƙirjinsa lokaci ɗaya bacci ya ɗauketa. shi kuma baccin da bai yi ba kenan har akayi kiran asuba, ya ƙura mata ido sai kallonta yake yi kamar tv. ya zareta daga jikinsa a hankali ya tafi masallaci, har ya dawo bata ko motsa ba, yana taɓa jikinta yaji zafi rau kamar garwashi, yaji hankalinsa yay mugun tashi saboda zafin jikin nata ya wuce tunani. tarkacen magungunsa dake watse a ƙasa ya kalla, ya duba kaf ciki babu pracetamol, sai can ya tuna akwai acikin maganinta da ke ɗaki, yana zuwa ya tarar babu, sai ya dawo ya ƙara taɓa jikin nata yaji ba wani sauyi. ya ɗau waya ya kira Zaytuna bata ɗaga ba, sai ya kira ta Samha, tana ɗagawa yace,"kaiwa Zaytun". jin muryarsa a rikice ta ce,"Hammah lafiya?". ya buga mata tsawa,"nace ki kaiwa Zaytun". da sauri ta diro akan gadon ta fita zuwa ɗakin Zaytuna, lokacin ta idar da sallah kenan. ta karɓi wayar hannun Samha da ke yi mata alama da ido, ganin sunan Turaki ajikin screen ɗin taji mamakin kiran nasa a wannan lokacin ya kamata, ta haɗiye guntun yawu kafin tace,"hello Hammah...". ai tun bata ƙarasa ya yarfa mata zagi yana yi mata masifa akan ƙin ɗaga waya. baiwar Allah cikin sanyin murya tace,"na shiga uku, Hammah yau ni ɗin?, Allah ya baka haƙuri". yaja tsaki, ba abin tayi magana ba ya ƙara yarfo mata wani zagin, don haka tayi shiru tana jiran cewarsa. daki-daki taji yana karanto mata sunayen drugs ɗin da ta san nasa ne, daga ƙarshe taji yace,"wanne me zazzaɓi zai sha aciki?". ta ce,"babu pracetamol ne?". daga tambaya sai cibi ya zama ƙari, ya taso mata kamar zai rufeta da duka ta cikin wayar,"in akwai zan kiraki ne". ta ɓata rai tana jin kamar ta kashe wayar. "ibuprofen ko pracetamol zaka bata". "duk babu anan, ki kawo min yanzu". ta waro ido waje tace,"Hammah asuba ne fa". yay tsaki,"kaiwa Sameer ki faɗa masa ya kawon yanzu, kar ya taho a ƙafa". yana gama faɗa ya kashe wayar. ba'ai 5minutes ba sai ga Sameer ya zo, yana fita ko gaisuwarsa bai amsa ba ya warci ledar maganin ya dawo. ya ɗago Fillo ya zaunar da ita, ta buɗe ido a hankali ta kalle shi, zata sa kuka yay saurin cewa,"sorry Angel, sallah za ki yi". jin ya ambaci sallah ta buɗe ido gaba ɗaya, taƙi yarda yay helping ɗinta sai da kanta taje toilet, duk taku ɗaya idan tayi sai zuciyarsa ta matse, yau rana ta farko da yaji kamar yay ihu saboda rashin samun damar maido da ciwon wani jikinka. yana kallo ta fito tana dafe bango, ba zai iya jurar ganin yanda take takawa da ƙyar ba, kawai ya miƙe yaje ya ɗaukota, ya kunce towel ɗin ya saka mata jallabiyarsa, ya buɗe wadrobe ya ɗauko hiram ya yafa mata sannan ta tayar da sallah. after ta idar ta kalle shi kaɗan tace,"ina so in kwanta". ya taso ya ɗaukota ya dawo da ita kan gadon, sai da ƙyar ta buɗe baki ya zuba mata maganin ta sha, tun da ta sha kuma sai ta fara kukan ita Ummi ya kai ta wurin Kaka, tana jin zafi sosai ya kai ta su yi mata magani, acikin kukan kuma bacci ya ɗauketa. ƙarfe goma sha ɗaya Fillo ta buɗe idonta a hankali, daki-daki ta dinƙa tuna abin da ya shiga tsakaninsu a daren da ya wuce, har yanzu a cikin kanta tana jin haskawar furucinsa na please help da ya ambata yafi sau a ƙirga, bin ɗakin ta dinga yi da kallo kafin ta iya miƙewa zaune. karaf idonta ya fara sauka akan wani card da ya ɗauki hankalinta, ta ɗauko tana karanta rubutun da ke ciki, ɗauke da handwriting ɗin mutum ɗayan nan a duniyarta. _i am proud of you wifey, very proud of you Angel, you are a precious girft to me from God, i love you so much Angel...Allah ya bamu ƴaƴa ma su albarka. Barka da tashi._ bata san lokacin da wani murmushi ya suɓuce ma ta ba, ta kai hannu zata taɓa cikinta idonta ya sauka akan kwalin waya dake kan blanket ɗin, Samsung W21, kamar ta so ta san wayar, sai ta tuna shekaranjiya ne su Nilfat ke browing suka ganta, ana lissafin kuɗin wayar 1.4something ML, ta ɗauka kwalin tana shafawa. a lokacin ta ankare da farar takarda dake saman pillow daga gefen kanta, ta kai hannu ta ɗauko haɗe da maƙullan mota guda biyu da suke ajiki. tana riƙe su a hannunta zuciyarta ta karanta ma ta,_another suprise, a huge suprise._ a sannan idonta ya kai kan wani gajeran rubutu ajikin ƙaramar papper,_Gratification of what you gave me last night._ cike da zumuɗi ta buɗe takardar, doguwa ce ɗauke da dogon rubutu acikinta, takardar shaidar mallakar gida ce da ke ƙasar Ausburg ɗauke da sunanta a jiki, *Halima Muhammad Barkindo.*, ta ɗauki keys ɗin guda biyu tana juya su a hannunta. bata san lokacin da ta ƙwala ƙarar murna ba, daidai da shigowar Turaki ɗakin, ta kalle shi ta yunƙura zata miƙe sai taji ba zata iya ba, lokaci ɗaya hawayen tsananin farin ciki suka zubo mata. ta buɗe hannayenta tana kallonsa tattare da so da ƙauna, sunan da bata taɓa ji ya shiga cikin kanta ba, sunan da bata taɓa alkintawa ba a mind ɗinta, sai a lokacin taji wanzuwarsa acikin zuciyarta da ma ruhinta. "come to me Jannaty...". tray ɗin hannunsa ya ajiye kan table ya taho gareta, a gabanta ya duƙa ya shiga jikinta kamar yanda ta buƙata, ta kewaye shi tana masa wata special runguma, ta ce,"thank you so much for the gifts, thank you Jannaty, love you more, i'm very proud of you, you made my world so beautiful, Ya Rahman ya saka maka da gidan Aljannah". ta faɗa tana ɗora bakinta a wuyansa tayi kissing ɗinsa. "Jannaty...". ta kira sunan nasa bakinta yaƙi rufuwa. yaja hancinta ya ce,"yau ba Turakin?". sai tace,"Turaki ina so zan ga motan". "bakinki kawai ne ya iya faɗin sunan Turaki". ya kamo hannunta ta tsaya akan ƙafafunta da ƙyar, kafin ya ɗauketa suka fita, a downstairs su ka wuce su Sakina dake zaune a parlon su na kallo. a sanda Fillo taga motoci biyun, a lokacin ta nemi ciwon da ke jikinta ta rasa, ta doka uban tsalle ta maƙale wuyansa cike da tsananin murna. godiya kawai take zabga masa tare da jero tarin adu'oi, ta nemi wannan kunyar tasa da take ji tun a daren jiya ta rasa. "Maama tayi min kyautar su, ni kuma naga babu wanda ya dace da su sama da ke. ina sonki da yawa Angel". sai da ta shiga duk mota biyun kafin ya ɗauketa su ka koma ciki, yana faɗa mata idan taji sauƙi zai fara koya ma ta driving. ya sauketa a kan kujera, ta shaƙi iskar bakinsa da ta fita a lokacin, ta marairaice murya tare da faɗin. "you have your breakfast without me?". ya kalli yanda tayi narai-narai da fuska kaman zata yi kuka. "ban yi breakfast ba Angel". "but naji bakinka na ƙamshin mint leave and coffee". ya ɗaga mata gira tare da miƙewa yaje ya ɗauko tray ɗin da ya shigo da shi ɗa zu. "kurɓa ɗaya nayi, and am sorry for that". "wa ya haɗa wannan?". "ni ne". "ummm". "da gaske fa, i make this coffee for you, Zaytun na kira ta faɗa min yanda zan yi. tana ta min dariya da tambayar ƙwaƙwaf". da kansa yay feeding ɗinta har ta ƙoshi, sai bayan nanne ya kira sunanta da Mrs Turaki. abin da ya faru daren jiya ya dawo ma ta sabo, kunya ta lulluɓeta, ta yi saurin saka hannu ta rufe fuskarta. "wallah you are so sweet Angel, you finished me yesterday night, shiyasa zan koma kiranki da Hottie, ƴar ƙarama da ke kin zautar da ni". ba shiri ta ƙara ɓoye fuskarta a jikinsa. da daddare su na zaune, kan Fillo na saman cinyarsa, yayin da wayarta ke riƙe a hannunta, tun ɗa zu take ta danne danne taƙi rabuwa da wayar, abinka da ɗan ƙauye yayi agogo, magana ma in yay sai ta ɗau lokaci kafin ta ba shi amsa. "ba sabanban". tayi murmushi kafin tace,"su Ummi su na gaisheka, Dada tace in ce ka gaida Boɗejo". "yaushe ku ka yi waya?". "ɗazun da kaje masallaci. Ummi na tayani godiya". kallon da yay ma ta yasa tayi saurin rufe ido, ya kama hannun yana faɗin,"Don Allah Hottie, ɗan kaɗan fa". tai saurin barin jikinsa ta ajiye wayarta ta dunƙule a waje ɗaya. "ni a'a, har yanzu ina jin zafi". Daga wannan ranar, sabuwar rayuwa ta *MH*(Muhammad & Halima) ta fara,  sabuwar shaƙuwa, sabuwar soyayya, tarairayar juna da kulawa. zuwansu ƙasar Ausburg ba ƙaramin daɗi yayi mu su ba, Fillo an waye an kile, mo re soyayya kawai suke yanda su ke so, kullum su na kan hanyar yawon shaƙatawa, a fita tun safe a yini a bakin beech. wata irin soyayya Turaki yake nuna mata me ban sha'awa, yayin da ita ma anata ɓangaren bata ƙyale ba, don tuni Nuratu ta ɗorata a layin manya, ƙoƙari take yi sosai wurin ganin ta faranta ran Turaki, wajen ganin ta mantar shi kowacce mace a rayuwarsa, wajen ganin ta zama ita ɗaya a duniyarsa, gaba ɗaya rayuwar Fillo ta sauya acikin irin kulawar mijinta da tarairayarsa, this week su ne a wannan ƙasar another week su ne a wata ƙasar, acikin wata guda sun manta ma da nigeria gaba ɗaya. su ci abinci tare, su yi wanka tare, su yi bacci tare, shi kansa aikin gida tare su ke yi, su shiga kitchen tare su yi girkin su a tare, don ba sa tsayawa wani bin order, goggling girki take da irin kayan abincin ƙasar su sarrafa abinsu, kuma in suka dafa kamar ma sun fi ƴan ƙasar iyawa. a kullum idan suna tare sai su ke ganin tamkar lokaci a tsaye yake cak, tamkar babu kowa a duniyar nan sai su biyu kacal, rayuwa su ke yi acikin kwanciyar hankali da natsuwa. wajen ƙarfe bakwai na safiya a ƙasar Australia, Fillo na tsaye ne gaban mirror tana tattare jelar gashinta ta tufke acikin ribom, tana sanye ne da ƙaramar riga armless milk  colour da tayi matching da skin ɗinta, sai short skirt da ash color da ko gwiwarta bai kai ba. kayan sawarta kenan a kullum tun da su ka baro nigeria, don su ne choice ɗin Turaki, ba ya son wata atamfa da danginsu, shiyasa ko da za su taho ko ɗankwali bai bari ta ɗauko ba banda kayan dake jikinta, sai da su ka sauka a ƙasar tukunna yaje ya rakito ma ta uban ƙanan kaya kamar wanda zai buɗe store. tasa hannu a bayanta ta barƙala yay ƴar ƙara, a gajiye take gaba ɗaya, daren jiya su ka dawo daga saudia, bata taɓa jin rashin jin daɗin zaman jirgin ba sai a jiya. madubin ya haska ma ta fuskar Turaki da ke tsaye a bayanta, wanda yasa hannu ya zare ribon ɗinta gashinta, ya baje a kafaɗarta. "na fi son ganin gashinki a haka". ya faɗa yana rungumeta ta bayan tare da ɗora fuskarsa akan gashin yana goga hancinsa akai. "kullum ƙara kyau kike yi, tell me the secret". ya faɗa yana kama hannunta, ya shiga tracing jan lallen da akayi mata da suka je india. "hannun ya ƙara kyau da ya fara ƙiba yanzu". sai ya ƙara cewa,"na ga twins ɗina suna ƙara cika". ya faɗa yana zura hannunsa cikin rigarsa ya shiga shafa breast ɗinta. ta lumshe ido kawai kamar me jin bacci, jinta take yi kamar bata da lafiya. ganin yanda tayi wani collapse ya juyo da ita yana cewa,"what happened to my Angel?". da narkakkiyar shagwaɓa tace,"yaushe zamu koma gida, na gaji da zaman nan ɗin, yawon ma na gaji da shi, i want to see Mum, Maama, Ummi, Kaka, Dada, Adda Zaytun, Hammah Hamid, and Boɗejo, i am missing them alot". ya rufe ido kafin yace,"not now". ta riƙo hannunsa kamar zata yi kuka ta ce,"haba my soul, mu tafi gobe please, Allah na gaji da cin abincin ƙasarar nan, duk komai na ci babu daɗi, ina so inje in ci tuwon Kaka". "haba Hottie we just spend only 3months fa, ai bamu gama honeymoon ɗin ba, ki bari mu cika 5months ɗin da Bello ya ban takardar hutu da ƙyar". tayi shiru bata ce komai ba. zai ɗauketa ta hana shi tana faman yamutsa fuska, ya waro ido yana cewa,"why?, wani abu na damunki ne yau?, duk naga kin yi wani iri kamar mara lafiya, tell me ina ne yake miki ciwo?". ta wuce ta barshi bayan tace,"idan ka ɗauke ni zan iya yin amai". ya bi bayanta da kallo, har sanda ta kwanta kan gado kamar wata mage, duk sai yaji tausayinta ya kama shi, may be har yanzu stress ɗin jiya bai rabu da ita ba. ta buɗe lumsassun idanuwanta ta kalle shi kaɗan tace,"i want to sleep". ta faɗa tana mayar da idonta ta rufe. ya cire bluetooth ɗin dake maƙale a kunnensa ya ajiye akan mirror, tun da tace she want sleep tana nufin yazo ta kwanta a jikinsa, dan in dai ba dole ba bata taɓa iya bacci in ba ajikinsa. ya hau gadon tare da kwantar da ita a jikinsa, a hankali yake shafa bayanta. _tauraruwa ɗawisu, a Mata ni banga kamarki ba Fulani Nah. ke ce gaba domin kin ba su rata, tauraruwa ke ce me haska Mata, ko ince autar Mata don kina da gata, ba mai taɓaki in bar shi, me sonki dole in so shi...ehh ki yi ta farin ciki wurina kenan, in ga kina ta dariya shikenan, komai kike so zana zam yi miki sannan, abin da ba ki so in daina wannan, sannu sha yabo kece abar yabawa, Allah ya tsareki Mata ta kirki, Fulanin Turaki._ cikin golden voice ɗinsa yake rera mata waƙar a kunnenta, waƙar da a lokaci ɗaya ta kore baccin da take ji ɗin, wannan waƙar ta M Sharif da zata ce ita ɗaya ya iya a waƙar hausa, ita ma ɗin ya iya ne just becouse of her. a kullum bai rera mata ita ba yay sama da sau biyar, su na aiki yana rerawa, in tafiya suke a mota, balle kuma ta lafe a jikinsa. hatta bishiyar da su ke zama a ƙasanta in sun je beech za ta iya cewa ta haddace baitin. Turaki yay ta ƙoƙarin da zai hanata baccin, don so yake yi ta tashi su yi excercise, ba ya so ta koyi lalaci tun da wuri haka, and ya fara ganin alamu 3days ɗin da suka wuce. tana kuka kaɗan tace,"don Allah Jannaty ka barni in huta, shiru nake so ko da banyi baccin ba". "idan kuma kika yi baccin fa?". "zan so hakan, domin shi kaɗai ne abin da nake buƙata a yanzu". "ki bari sai da daddare, yanzu kina kwanciya za ki cika ɗakin nan da minshari sai kace rago na kuka, duk ki cika min kunne ina tsorata". babu shiri ta miƙe a jikinsa, ta sauka akan gadon tare da ɗaukar pillow, sai da taje bakin ƙofa sannan ta tsaya ta saita kansa ta jefa masa pillown. "kai ne kake minshari ba ni ba, ɗakin nan ma shaida ne. ka sha zamanka kai ɗaya, bye". yana dariya ya taso, ganin hakan tayi saurin jan ƙofar ta rufe tasa key, bata ko cire key ɗin a jiki ba gudun kar ma ya buɗe da spare, ta nufi ɗayan bedroom ɗin, don tana so ta huta ne sosai a yanzu, duk jikinta take jin ba ƙwari balle daɗi, ga zuciyarta da ke ta tashi, burinta tayi amai kawai ko ta huta, amma aman yaƙi zuwa. *BAYAN WATA ƊAYA.* *Nigeria.* [9/7, 02:02] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *57* *ƙarfe tara na safe.* tun daga ƙofar gidan zaka shaida ana wani babban taro a gidan, taro irin na bikin aure. motoci ne iri-iri daban danƙare daga wajen gidan, a yayin da gate ɗin gidan yake a wangale gaba ɗayansa, wasu mutanen na shiga ciki wasu kuma na fita. Khaleel ne tsaye a bakin gate, wanda yake ango a yanzu, waya ce kare a kunnensa yana faɗa akan abin da ban san menene ba. Sameer ya iso wajen a lokacin yana cewa da shi,"Hammah yace kaje gida ka same shi". sai a yanzu na fahimci da wanda yake faɗan a wayar, amaryarsa ce suke rigima akan irin ɗan ƙaramin lamarin nan da ba'a rasa shi tsakanin kowanne ango da amaryarsa. "to ba zan bayar ba, in za ki haƙura ki haƙura". daga cikin wayar ɓangaren Rashida ta ce,"haka kace?, to zaka san kayi da ƴar halak, wallahi sai in ce ma ba za'a kawo ni gidan naka ba". ita ma tayi maganar a fusace kamar yanda shi ma yayi. "hakan zai sa ki burge ni". ya faɗa yana kashe wayar ya jefa cikin aljihu, ransa a ɓace ya nufi mota ya shiga. daga cikin gidan, idan ka shigo compound, zaka kutsa ne ta cikin tarin jama'ar da ke ta hayaniya su na kaiwa da komowa wajen aikace-aikace, wasu na wucewa da manyan kuloli na abinci, yayin da wasu ke tsaye akan babban kaskon da ake suyar nama a cikinsa. idan ka lura da part huɗun da ke jere, za ka fahimci a ɓangare na uku daga ɓangaren dama, wanda shi ne ɓangaren Hajiya Ramla, anan ne taron mutanen yafi yawa, don ga takalman jama'a nan birjik daga wajen ƙofar parlon. a yayin da ka shiga cikin parlon, zaka tarar da manyan mata masu ji da kansu, waɗanda suka sha ilimin boko, boko ta ratsa su ta ko'ina, waɗanda mafiya yawan su ma'aikata ne a ƙarƙashin federal government. wasu na zaune akan kujera yayin da wasu ke zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale duka parlon da shi, kowa na hira da abokin zamansa, hayaniyar dai tayi yawa wacca ta kai ga har ba'a iya jiyo sautin muryar wata dattijuwa da ta shigo ciki tana kiran sunan Hajiya Ramla. a lokacin ne kuma Hajiya Ramla ke sakkowa daga saman bene tare da ɗaya daga cikin amaren da ake aurarwa wato Samha. magana suke yi yayin sakkowar ta su inda Samha ke ta ƙorafin hayaniyar. "na nemi Nihal na rasa, ki lalubo min ita acikin taron jama'ar nan don Allah, ta zo driver ya kaita su karɓo mana ɗinkin mu. kina kallo ma Fillo bata sami saka ankon ɗaurin auren nan ba, haka Babana ya zo ya sakani a gaba yana ta kumbure-kumbure, ni ban san ya akai ku ka kaiwa ɗan shiriritar tela ba". Samha ta amshe da cewa,"ai wallahi jiya na so da ni aka je da sai nayi masa rashin mutunci. ni yanzu Nihal ma aina zan ganta, da ƙyar ma idan bata ƙwace tayi gidan Hammah ba fa". a lokacin ne dattijiuwar da ta shigo tana laluben Hajiya Ramla ta ƙaraso wajen. Hajiya Ramla tace da ita,"sannun ku da aiki Maga". "yauwa Hajiya, wai da ma masu yankan nama ne suka ce Baffa ya kira waya yace a ƙara yanka raƙumi da raguna guda uku, sai akai raƙumin gidan Hakimi". "sun yanka ne?". "a'a da ma nace bari na zo na fara shaida miki". "to kinga garzaya ki faɗawa Madina, ki dubata a ɓangarenta ko ɓangaren yaran nan". "to shikenan, batun funkason can fa ya za'ai da shi?". "ai da kun gama ku kai gidan Babana, ɓangaren Fillo za ku kai, nata ne aka yi mata saboda baƙin da ke can". "to shikenan". Maga ta juya ta fita a parlon, yayin da Hajiya Ramla ta ƙarasa wurin mutanen da ke zazzaune a parlon, waɗanda mafi yawan su abokan aikinta ne. "sannunku fa". ta faɗa a sanda take zama akan ɗaya daga cikin kujerun, kusa da wata aminiyarta Hajiya Shamsiyya. "yo ke uwar amarya haka ake sai ki shige ɗaka ki barmu zazzaune anan". murmushi ya ƙwace a fuskar Hajiya Ramla tace,"haƙuri zaku yi, ƴar taku ce ta sakani gaba tana kuka". ta faɗa a lokacin da take bawa wata tsohuwa umarnin inda zata ajiye kulolin soyayyan naman da ta shigo da su. sannan ta ƙwalla kiran Ɗausiyya da sabuwar ƴar aikin da suka yi bayan auran Fillo, me su na Maraƙisiyya, cikin sauri sai ga su sun zo sun durƙusa a gabanta. "ku ɗauko farantai ku fara rabon naman nan, kowanne plate ku zuba yanka goma sha biyar". sai kuma ta kalli tsohuwar tace,"Yaya kun kai ɓangaren Madina kuwa?". "ehh Hajiya yanzu Yami ta tafi kaiwa". "to masha'Allah, sannunku da aiki". sannan ta ƙara cewa da ita,"Yaya don Allah ce da Madina ta bayar da maƙullin store, sai a samu waɗanda za su ɗebo lemuka aciki, a ɗebo katan arba'in, akai katan sha biyar gidan Babana, sai a bar sauran anan". cikin sauri tsohuwar ta miƙe ta fita, sai da ta fara zuwa ta duba wajen aikin suyar ta su sannan ta wuce ɓangaren Hajiya Madina. nan ɓangaren ma cike yake da mutane waɗanda mafi yawansu ƴan'uwa ne, duk sai ka kalla fuskokin su zaka shaida ashe Hajiya Madina ƴar dangi ce, saboda kusan duk kamannin su ɗaya. "Hajiya tana sama ne?". tsohuwar ta tambaya a sanda ta shiga parlon. "kamar dai ta shiga kitchen". wata acikin mutanen dake zaune akan kujera ta faɗa. "ta fito ta koma sama fa, yanzu suka wuce ita da Zaytuna". Tsohuwar ta miƙe cikin hanzari ta hau upstairs, ta tsaya a ƙofar ɗakin Hajiya Madina domin jiran iso bayan tayi sallama. a sanda babu wanda ma ya jita saboda akwai ƴar hayaniya acikin ɗakin. Hajiya Madina na tsaye a gaban madubi tana ɗaura sarƙa a wuyanta, a lokaci ɗaya kuma tana bayani ga Maga. "kinga ba wani nama da za'a kai gidan Hakimi, shi ya siyo mana, ko a gidansa ake taron, mu da aurar da ƴaƴa shi da karɓe nama. wani lokacin ma dai Baffa ya fiya neman suna, ya mayar da Hakimi kamar wani ubansa, to kice su yanka a haɗe gaba ɗaya da na gida, in Baffan ya dawo ace masa mantawa aka yi". Maga ta miƙe tana ƴar dariya ta fita, Yaya ta shigo ita ma, ta durƙusa tana cewa,"Hajiya wai ki bayar da maƙullin store za'a ɗebo lemuka". "Zaytuna duba drower ɗin nan ki miƙo mata maƙulli". sai kuma ta dubi Yayan ta ƙara cewa,"don Allah da an ɗebo a rufe saboda jiya sai da akayi mana ta'adi". Umman Nadiya ta shigo ɗakin a lokacin. "ke Madina da ma Turaki aure ya ƙara?". Hajiya Madina ta kalli fuskarta a cikin madubi tare da yin murmushin takaici sannan ta ce,"wa ya guntsa miki wannan maganar?, to ba sabon aure yayi ba tsohuwar matarsa ya mayar, ita ma kuma don fitinanniyar Kakarsa ta ƙara tayar da rigima ne, yauwa biyayya ya ƙara yi a karo na babu adadi, don Allah a bar ɗana ya huta a daina yawan zancensa ana faɗar masa da gaba, haba tun jiya da akace an ɗaura aure da shi ake ta ƙwala kiran sunansa acikin gidan nan kamar wanda yay sata, to idan ma auran ya ƙara zunubi ya aikata ko me?, ina ruwan wani?, ko ba mata huɗu aka halasta masa ba?, haba mutane da shegen gulma da tsugudidi". Umman Nadiya tace,"to jarababba Allah ya ba ki haƙuri, ni tambaya nayi ba wani abu ba". Hajiya Madina dai bata ƙara tanka mata ba, ta haɗe rai ta juya kan Zaytuna tana yi mata faɗan kukan da take tayi tun jiya da aka ɗaura aure. "ni dai ina ga sai na haɗa miki da duka tukunna, haba kuka yaƙi ci yaƙi cinyewa abu tun jiya, to ki shiga hankalinki da ni". Umman Nadiya tace,"to ai dole tayi kuka, ita kaɗai ce fa acikin su zata yi nesa". "yo nesa abu da ba ƙasar zata bari ba, Allah na tuba ina nan ina Abuja, shi ma ɗan banzan Bellon da ya biyewa Baffa ya mayar da shi can abujan, ai sai da na faɗa masa ya dage ya barsa su ci gaba da aikinsu anan. ban ma san munafikin dai da ya bayar da shawarar buɗe wani kamfani ba tare da saninmu ba, ko da yake yanzu ai mu ƴan banza ne a wurin Baffa, duk ya mayar mu ƴan wofi, wannan fitinanniyar tsohuwa duk ta bi ta hargitsa mana zama, Allah ya shiryeta kawai, yanzu tun da dai an mayar da auren sai ta bar hankalin kowa ya kwanta". ta kamo kunnen Nihal da ke shigowa ta murɗe,"ke, ke, ke, ki kiyaye ni fa". "Maama wallahi Hammah ɗin ne fa ya koro ni, wai daga nace ba za'a bawa masu jeran kayan Ilham abinci ba". "mtsww Allah ya sauƙa, to Mum ɗin ku tace ki wuce ki karɓo mana kayanmu tun ranki bai ɓaci ba". "ehh yanzu zan tafi, Maama to sauran kuɗin ai za ki cika min". "nawa ne?". ta ɓoye ƴar dariyarta tana leƙo jakar Hajiya Madina dake saman gado ta ce,"jiya na ƙara kai ɗinki na set uku, su zan saka ranar da za'a kai amare, balance ɗin dai har na ku yace 35k za'a bayar". "idan kuma babu naki fa?". "20k". ta zauna bakin gadon ta ɗauko jakarta, ta ƙirgo kuɗi 20k ta miƙawa Nihal ta ce,"ga namu ɗin, naki kuma bari nayi miki kwatancen ɓangaren Baffa ko kuma na ba ki lambarsa kawai, sa 08065....". kowa a ɗakin yasa dariya hatta Zaytun da ke kuka tun ɗazu, Nihal ta fara shagwaɓa tana zama kusa da Hajiya Madina ta shiga yi mata kirari da kalallameta. Umman Nadiya ta ce,"gaskiya ya kamata dai a bawa Auta kuɗi ta karɓo nata ɗinkin ita ma, ba wani sai taje gun Baffa". Hajiya Madina ta ce,"wannan ƴar fa da kike gani tun da biki ya taho ta fara fashin kuɗi, daga shekaranjiya zuwa jiya kawai tayi min fashin kuɗi sun kai kusan 100k. tsabar rashin sanin darajar kuɗi jiya makeup ɗin 20k akayi mata, ɗaurin aure kawai ba wani event ba. her Excellency kuwa ce tayi sai jiya ta ankare da ATM ɗinta, ta manta shaf ta bawa Nihal tun ranar da aka je jeran kayan ɗakin Samha, ƙarshe dai ta talauta ta babu ko sisi a account ɗin nata, to ni dai na bata shawara nace ta makata a kotun alƙali Dikko kawai, ina dalili yarinya duk ta bi ta yashe mu". "Allah Maama kina da kuɗi, to ki ban 5k sai Mum ta cika min 10k ɗin". "yo Nihal ko da Kakar ki Boɗejo uwar masifa kike tafe ai biyar ba zan ba ki ba, don haka ki tashi ki kama gabanki kawai, kije can wajen Uwaki ta ba ki". Zaytuna ta ce,"ke yarinyar nan wai me kike yi da kuɗi?, Maama ɗa zu ma fa tasa Hammah Bello ya turo mata 20k, ina jinta kuma again tana bin Khaleel tana yi masa ƴar murya". Nihal ta tura baki gaba ta ce,"daga yau ba zan ƙara tambayar mijinki kuɗi ba balle ki zo kina min tonon silili, kina terere da ni mijinki ya ban dubu ashirin. shi ma Hammah Khaleel ɗin da ya ban sai da ya faɗawa duniya ya bani, shiyasa zan mayar masa da kayansa, to wai ma idan baku bani ba waye zai ban? Hammah ne kaɗai a gidan nan zaka tambayrsa kuɗi ya baka kai tsaye babu ƙurewar tambayoyi". Hajiya Madina tace,"ba kya tambayar na hankali ne shiyasa, tambayar ƴan fashi kike yi, ban san ba kuma ko jari za ki kafa da kuɗaɗen mu". "Maama to ki ban don Allah, haba Maaman Hamman'mu, Maama me haƙorin maka guda biyu, Maama ƙawar Boɗejo, Maama ta hannun dama na". Hajiya Madina tayi dariya ta make hannunta dake kan haɓarta,"zan ci gidanku Nihal, naga alama kin mayar da ni Kakarki". sai kuma ta ɗauko kuɗi a jaka ta bata ta ce,"ga 5k nan daga haka ba zan ƙara ko ficika ba". Nihal ta rungumeta tana yi mata kiss,"Allah ya bar min ke uwar marayu har ma da masu uba, i love you so much. Allah yaja mana da ranki". lokacin Samha ta shigo ɗakin, bayanta wasu yara ne su uku ke biye da ita, Hajiya Madina ta bita da kallo, cikin sigar tsokana ta ce,"don Allah Umman Nadiya kin taɓa ganin amarya mara kunya irin wannan?". ta nuna Samha da ta wuce wadrobe ta buɗe tana ɗebo kaya. "ina irin ƴar ƙwallar nan da ake yi ta ranar ɗaurin aure, to in faɗa miki yarinyar nan dai bata yi ba, jiya Zaytuna na kuka ita tana wage haƙora talatin da biyu a waje, duk sai ta bani kunya...". Samha ta katse maganar Hajiya Madina da cewa,"kai Maama, ni yaushe akayi hakan, Allah ma nafi Adda kuka". "yo camera ai ba zata yi ƙarya ba, za'a kawo bidiyo ko bayan raina Umman Nadiya za kice na faɗa". Samha tayi murmushi ta ce,"Maama ina tawa atamfar?". "ki ka bani ajiya?". "Maama daga wurin Mum ɗin fa nake tace Adda ta taho da kayan nan". Zaytuna ta ce,"nawa kawai na ɗauko na bar miki naki acan, kiyi sauri kije ki duba in ba haka ba a ɗauke, kin san ɗakin Mum wasarairai take da shi, na nemi sarƙata sama ko ƙasa na rasa". cikin sauri Samha ta fita bayan ta ce da yaran su biyota da kayan da ta ba su. Nihal ta matsar da bakinta kusa da kunnen Hajiya Madina tace,"Maama gulma zan miki, kin san me Hammah yaywa Fillo kuwa?". Hajiya Madina tayi saurin mayar da hankalinta gareta. sai kuma Nihal ɗin ta tashi da sauri tana cewa,"kai ba ruwana, ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba". ta faɗa tana saurin ficewa ta bar ɗakin. Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, kafin ta mayar da hankalinta kan maganar da Mama Bilki ke yi mata. "Zaytuna za'a fara kaiwa kenan?". "ehh ita za'a kai gobe, jibi akai Samha sai gata mu karɓo amaryar Khaleel, ita anan zata zauna tare da mu, wancan matar ta me Babban sunan kuma yau za su kawota". Tana faɗa ta miƙe ta fita ta bar ɗakin, don hankalinta bai kwanta ba da maganar da Nihal ta fara yi mata, duk yanda akayi an sami wani misunderstanding tsakanin Turakin da Fillo, dan ta lura tun jiya da aka mayar da aurensa ya zama wani kalar masifaffe, da asuba ma tana jin Khaleel na complain ɗin faɗan da ya kama yi musu na babu gaira babu dalili, to tsoronta kar ya sauke fushinsa akan baiwar Allah, ita da ba ita tasa aka mayar da auren ba, wacca ita ta ma fi shi takaicin mayar da auren, don ta lura da hakan a tare da Fillo, kawai don dai yarinyar na da haƙuri yasa bata nuna ba, sai ka ɗauka ma ko bata san ciwon kanta ba shiyasa take ta hidimarta ko a gefen yatsarta. fatan ta ɗaya Allah yasa ba Boɗejo ba ce taje ta kunna musu wuta a gida. ko kuma halin jiya ya maimaita musu, don ance jiya ma kafin ɗaurin aure kusan rufe Fillo da duka yayi. **** "yauwa bayan kin auna fulawanki sai ki zuba butter, ki kwaɓa yeast ɗin da ruwan ɗumi kuma da shi za ki kwaɓin gaba ɗaya. yauwa to miƙo min gishirin can, if you like you can add sugar". bayanin da Nuratu ke yiwa Fillo kenan a kitchen ɗinta, a yayin da take koya mata yanda ake alkubus, tun san da suka dawo suka zo gidan taci taji daɗinsa tace zata koyi irin nata. Fillo ta ɗauko roban sugar da gishirin kamar yanda Nuratun tace, ta ajiye tana ci gaba da kallon yanda take yin kwaɓin da kuma sauraron bayanin da take yi mata. wucewar wasu mintuna Nuratu ta kalli Fillo jin tayi shiru, ta girgiza kanta kawai tare da jin tausayinta, kafin tace mata,"kin san mene?, wallahi tallahi cutar kanki za kiyi muddin za ki ɗauki damuwa kisa a ranki har haka, ke wa ya faɗa miki yanzu ana nuna damuwa da kishiya?, kina ƴar ƙaramarki haka?, amma...". ranta a ɓace ta ɗauki tukunyar da ta rufe ta bar kitchen ɗin. Fillo ta bi bayanta da kallo kafin ita ma ta bar kitchen ɗin, parlo ta wuce ta zauna, ta ɗauko Farha da ke cikin keken wasanta, tana cikin yi mata wasa Yusuf ya shigo, bayan sun gaisa ya ke ce mata. "jiya sai nake jin zancen an mayar da auren abokiyar zaman ki". wata ƙwallar ciwo ta tararwa Fillo a ido kafin tace,"ehh Yaya". "to Allah ya baku zaman lafiya, ayi ta haƙuri kin ji ko". "insha'Allahu Yaya, na gode". sai ya ƙara cewa,"amma ba ki da wata matsala ko?". "babu Yaya". "to masha'Allahu, kar fa kice za ki sakawa ranki damuwa kinji ko, kinga ba isassar lafiya gare ki ba. ya zancen karatun ki kuma?". tasa hannu ta goge hawayen da yay nasarar gangaro ma ta kafin tace,"lokacin da muna Ausburg har ya nema min addimission acan, to kuma da muka dawo sai yake cewa wai na haƙura kawai, to ban san me dai yake nufi ba, gaba ɗaya zan haƙura da karatun ko kuma wancan admission ɗin zan haƙura da shi". Yusuf ya sauke numfashi yay ɗan jim kafin yace,"ki ba shi lokaci tukunna, zuwa gaba sai kiji koma menene dai, amma karatun naki yana da muhimmanci sosai". ya miƙe daga kan kujerar da yake zai wuce ɗaki Farha tasa kuka, ya dawo ya karɓeta ya tafi da ita. wayar Fillo dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗauka ta kara a kunne tare da amsa sallamar Maijidda. "ke na zo kuma na tarar ba kya nan". "ehh wallahi naje gidan Yaya Yusuf ne". "lallai ma ke ɗin nan, kuma kika ce na zo na raka ki ƙunshi, kin san za ki fita za kisa na zo, ko don kawai dai kin raina min hankali, wannan ai rashin mutunci ne". "Allah ya ba ki haƙuri maida wuƙar, ba jimawa zan yi ba yanzu ma fa nake shirin tahowa. sanin halin ɓata lokacinki yasa nace bari kawai in je in dawo, don Allah ki zauna yanzu gani nan a hanya". "sai kin dawo, idan da mota kika fita ki yiwa Allah ki samo min mangoro a hanya". "to uwar biyu". Maijidda tayi dariya sosai tare da cewa,"rufa min asiri maza su kaini ba mata ba, uban wa na aura da har zan zama uwar biyu, ke ɗin dai". su kai Sallama Fillo na miƙewa ta nufi ɗakin Nuratu, samunta tayi tana haɗa wasu magunguna a leda da dukkan alama maganin mata ne. Fillo ta zauna bakin gadon tana cewa,"Anty tafiya fa zan yi...". kuma bata ƙarasa ba ƙarar wayarta ya katseta, ganin sunan Maama yasa tayi saurin ɗagawa. daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"Daughter lafiya ba ki shigo ba?". "Maama naje gidan Yaya Yusuf ne". "zuwa yaushe za ki dawo?, ko acan za'a yi miki ƙunshin?". "a'a wallahi Maama, wadda muka yi zata zo ɗin da safe ta kirani an yi musu rasuwa, wai da zata turo sister ɗinta but tana faɗa min bata ƙwarai sosai kamarta ba, shi ne nace ta bar shi kawai". "ok to ki taho yanzu, nasa a kira wacca ta yiwa amare tazo tayi miki, bana so ki ƙara zama haka babu lallai, da ɗaurin aure an ga ba kiyi ba mutane sai su fara zaton ko baƙin cikin damuwar kishiyarki yasa". "to Maama yanzu zan taho". "to shikenan sai kin dawo, yauwa kar ki manta ki taho min da ajiyar nan da na ba ki, ga dai Nihal nan zata ja da duk alamu ɗinkinki na gobe ma babu". Fillo tayi ƴar dariya. Maama ta ƙara cewa,"ga baƙi nan an ƙara yi, su na ta tambayar uwar gidan Turaki, idan kin zo duk zan miki bayaninsu, ƴan uwana ne na Kano, babu wanda ya taɓa zuwar min sai yanzu da bikin ƴaƴansu ya tashi". bayan sun yi sallama Nuratu tace,"to ke ko anan ma ba sai ki godewa Allah ba, iyayen miji na sonki miji na sonki, danginsa su na sonki to kuma dan me na damuwar don ya mayar da matarsa?, auren nan fa biyayya ce kawai zai yi ba wai don baya sonki ba, ko a haka matsayinki da nata ai ba ɗaya ba, matar so kike, ita kuma matar shige". "Anty Nuratu wallahi ni abin da nake tsoro raini da wulaƙanci". ta faɗa cikin rauni da muryan ban tausayi. Nuratu tayi guntun murmushi me sauti. "me zai sa ta raina ki?, a wanne dalili Fillo?, wurinki fa daban wurinta daban, ko za ku shekara dubu a gidan nan sai kun so za ku haɗu da juna. kinga look, ni fa ko a yanda na ɗauka ma sai ka yi abin da za'a rainaka ɗin tukunna ake samun damar rainaka, as far as kin kiyaye waɗan nan abubuwan wallah ko da me kishiya ke ji bata isa ta raina ki ba. na farko karki kuskuren saka mata Ido a lamarinta, kar ki ke kai ƙaranta, saurin faɗa da ita shi ne babban abin da ke janyo raini, da kuma ɗaukar zuga, in har kishiya ta fuskanci kina ɗaukar zugar mutane to billahi ta gama rainaki, haka zalika kar ki yi gigin dinga shiga kowanne lamarinta ko da ita da kanta ke cusa ki aciki, baya baya dai...". Fillo ta tari numfashinta,"Anty Nuratu to ni ina ma nake da lokacin waɗannan abubuwan akanta. ina miki batu ne na tana ganin ita ƴar sarki ce, ta fini ilimi, ta kuma fini wayewa, kuma tana da aikin yi, sannan zata dinƙa min kallon cewar ni ba kowa bace face ƴar aikin da aka tausayawa aka auro, Anty Nuratu dole ta raina ni". "to ai ƴar aikin ta fita tun da har tausayin ma yasa aka iya auro ki, ita da ba'aji tausayin nata an aurota ɗin ba fa sai cusata da aka yi?,  mtsww kin ga don Allah ni kar ki bayar da ni, ko wayewar ma ai bata fiki ba, wayewar shiga jami'a kawai ta fiki, amma ban da ta gidan miji, ko kin manta tsawon watanni da kika shafe a ƙasashe da dama kina durzar amarci ke da mijinki, ita ta sami wannan damar ne?, bata samu ba kuma ba zata samu ba". sai kuma ta miƙa mata ledar da ta gama zuba kaya aciki,"ga waɗan nan ɗin, ai duk nayi miki bayanin yanda za kiyi amfani da su". "to na gode sosai, Anty Nuratu sai garin kunun, don Allah a ƙara yi min, naji daɗinsa sosai wallahi, sometimes idan na kalli kaina sai inga kamar ba ni ba, ji fa kumatun da na tara". ta faɗa tana ƴar dariya me kama da ta ƙarfin hali. "wai ke zatonki kunu ne kaɗai ya saka ki wannan ƙibar, to har da Babyn mu". "hmm ni fa banda wani ciki. haka jiya Ammi ma da naje sai adu'a take wai Allah ya raba lafiya, ni dai nayi murmushi kawai. kafin mu taho test nawa aka yi duk ba ciki ba ne, ni kam ma ba yanzu zan haihu ba sai kamar nan da 2years lokacin na ƙara girma". "yanda za'aji daɗin cewa ke juya ce kenan, ki ma daina wannan kuskuren tunanin, yanda kike da kishiyar nan in har ta rigaki haihuwa sai kin fuskanci ƙalubale, gwarama ki roƙi Allah ya ba ki, in ya so kya huta daga baya". har bakin mota Nuratu ta rakata, ita kuma sai godiya take yi mata. "ki daure dai ta bakin Abban Farha ki ƙara zuwa asibiti su duba, don bani da tantama kin ɗauki ciki". Fillo tayi murmushi me ciwo,"idan cikin ne zai bayyana kansa Anty Nuratu. kin san fa nace masa muje asibitin wallahi ko tanka min bai yi ba, da na ƙara magana ma ce yay bai shirya tara ƴaƴa yanzu ba". tausayinta ya kama Nuratu, ta kawar da zancen dan ta lura kamar akwai damuwar da take ciki, kamar dai yanzu tana zaman haƙuri ne da Turaki kawai. "kin ji bikin Raudha an mayar da shi Adamawa ko?". "haka Ummi ta faɗa min jiya da muka yi waya". "ni ban so hakan ba wallahi, kawai dan ba yanda aka iya da Maudo ne. yaushe za ki tafi to?". Fillo tayi murmushi me ciwo tace,"ai babu ni a batun zuwa kam dan yace ba zanje ba, kuma wallahi ba zan ƙara yi masa maganar ba, na lura tun da zai mayar da auren nan ya ɗauko wata bura'uba ya ɗorawa kansa, kuma sai dai komai ya ƙare akansa shi ɗaya ni ba saurarsa zan yi ba, ban iya haɗa hanya da damuwa". Nuratu tace,"Allah dai ya kyauta, yanzu kam sai kin ta haƙuri, yan da za ki sami mijinki a ke ta ɗaya ba haka za ki same shi ba a ku biyu ba. shawarata kiyi ta adu'a Allah ya kauda fitina tsakanin duk ku ukun, abin da bai da kyau Allah ya mayar maku da shi me kyau. sannan don Allah ba ruwanki da wata fitina, imma daga ɓangarenki ko nata, ki kama mutuncinki ki riƙe, kar ki sake wani hargagi ko cin mutuncin ko fashe fashe da duk danginsu a same su daga gareki, wannan duk kishin marasa ilimi ne. kuma jiya na faɗa miki yau zan ƙara maimaita miki, babu ruwanki da shisshigewa ko tusa kai a wurinta wai ko dan ku zauna lafiya a'a sam, idan har taga kin ja ajinki da mutuncinki za ki ga tana jin shakkarki, idan ma tana tare da tsiya ne to zata sha jinin jikinta. sai kuma shawarar da zan ƙara ba ki, kafin ya amince kici gaba da karatu to ki fara business, kin san ance darajarka jakarka ko aljihunka, to ki kama kasuwanci kamu me kyau, ta yanda hankalinki zai karkata ɗungurungum akansa, ta yanda za ki zama baki da lissafin wata kishiya da takaicin miji sai na kuɗinki, wallah kasuwanci wani babban abu ne na siyawa kai mutunci wasu matan ne kawai basa ganewa, kuma kar ki yarda ki kama kasuwanci da kuɗinsa, ki kira Dada ki faɗa mata kina buƙatar kuɗi ko kuma kice a buɗe miki shago. Sannan ko da wasa kar ki sake mijinku ya fara samun tashin hankali ta ɓangaren ki, in ba haka duk san da wani laifi ya afku ko da ba ke bace zai ce ai kece uwar rigima, abu guda biyu ne zuwa uku naki, sanin darajar kai da sanin yadda za ki sarrafa ragamar miji, ki zama kece limamiyar ba wannan limamiyar da ke jan ragamar limancin layu biyu ba. Kissa da kisisina kamar ki lashi takashinsa amma shi ma ina jan kunnenki, mutunciki kar ki sake kiyi wasarairai da shi, domin shi ne limamin rayuwa". Fillo tasa tissue ta goge hawayenta, kuka ya kubce mata ta ce,"ni kaina na san sai nayi haƙuri yanzu Anty, Turaki ya sauya min fiye da tunani. wallahi Anty da yazo min da batun zai mayar da auren nan sam ban nuna masa ina ƙin dawowarta ba balle kuma na ɗaga masa hankali. amma jiya kafin su tafi ɗaurin aure kar ki ga yan da ya taso min da faɗa, har da zagi fa Anty, kuma wallahi ba wani abu nayi masa ba, cewa kawai nayi zan koma can gidansu sai an gama biki na dawo, wai buɗar bakinsa ce yay tunda ina baƙin ciki da zuwan wata ai dole nace zan bar gida, to babu in da zanje in zauna in kula da ƴan uwanta da suke zaryar shiga da fitar yi mata jere, idan suka buƙaci wani abu wa nake nufin zai ba su, ko shi zai baro wajen aikinsa ne ya kawo musu. to kar inyi kuskuren wulaƙanta masa Mata, don ƴar'uwarsa ce, kuma samun zaman lafiya tsakanina da shi na mutunta ƴan'uwansa, Anty kamar fa zai duke ni, duk yadda na so da kar a fahimci ina cikin damuwa sai da Maama ta fahimta, da na dawo da daddare sai ce min yayi wai naje na kai ƙararsa ina so in shiga tsakaninsa da iyayensa, to wallahi zai yi min abin da ban taɓa zato ba, zamana da shi babu dole..." kuka ya ƙara kubcewa Fillo sosai,"kuma wallahi tallahi Anty ban kai ƙararsa ba, na san dai nayi iyaka ƙoƙarin da za'a fahimci bana cikin damuwa amma na gaza, shi ne har Maama ta gane ta tsare ni da tambayoyi, kuma ita ma ban ce mata ga dalili ba haka nace mata bana jin daɗi ne, kuma da ta san da ma ban da lafiya bata ƙara tayar da zance ba, amma shi ne har yake ikirarin wai sai ya rabu da ni in har na nuna bana son ƴar'uwarsa ko kuma na ƙara kai ƙararsa wurin Maama. tsakani da Allah Anty ko anan idan tazo ya nuna mata ta fini matsayi ba sai yaja min wulaƙanci daga wurinta ba, yanzu nan ƙunshi nace za'a yi min sai ce yay ba da yawunsa ba". Nuratu taji tausayinta sosai, ta dinƙa bata haƙuri da lallashinta, tare da yi mata nasihohi da kuma wasu shawarwarin da zata ji daɗinsu muddin tayi amfani da su. kafin nan suka yi sallama taja motarta. [9/7, 02:17] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *58* dawowar Fillo gida ta tarar ana ta kai komo wajen shiga da kayayyaki ɓangaren Ilham, tun jiya ake wannan zaryar, ƴan'uwan mahaifiyarta ne kusan duk ɗin su, sai Boɗejo da Inna Falmata. sai dai bata san ba ko yau har da su tunda dai bikin ba ɗaya ba ne, duk da dai taga Boɗejo na nuna kamar bata da hurumi da auren su Zaytuna da Khaleel da Samha, kamar su ma ba jikokinta ba ne. ɗauke kai tayi daga barin kallon part ɗin Ilham ɗin, tayi wucewarta part ɗinta bayan ta tambayi Baba me gadi ko an kawo masa abinci, da shigarta kuma ta rufe su Sakina da faɗa akan rashin kaiwa Baba abinci da suke yi da wuri. ta kalli Maijidda da ke zaune a parlon ta haɗe rai, ta ce da ita,"yi haƙuri don Allah, sammako nayi gidan Yaya Yusuf, za su je taraba ne na bayar da saƙo akaiwa Ummi". Maijidda tace,"ba dai bikin Raudha ba". "shi ne ya taho wallah, next week in Allah ya kaimu". "kin ga da an kammala na su Adda Zaytun sai ki bi su ku tafi tare kawai". Fillo tayi murmushi me ciwo ta ce,"ni ma haka nace. ki hau sama ki jira ni bari na ajiye waɗannan kayan". ta faɗa tana wucewa kitchen, friedge ta buɗe ta zuba fruites ɗin da ta siyo, kusan kwana uku da ƙarewar na su amma Turaki bai kawo wani ba. fitowarta daga kitchen ɗin ta tarar da baƙi a parlon, fuskar farko da ta kalla ta shaida ƴan'uwan Ilham ne, don su na kama sosai da Fulani Azima. ta ƙarasa wajen su ta durƙusa har ƙasa, cikin ladabi ta shiga gaishe su, kuma ba tare da ta miƙe ta koma kan kujerar ba tayi zamanta akan carpet ɗin don bata tunanin zata iya zama kan kujera alhalin su na kai, hakan kamar da rashin ɗa'a. su uku ne manyan matan, kowacce sai da ta gama yi mata kallo a yatsine sannan suka haɗa baki wajen amsa gaisuwartata. Antyn Kano ta dubi Fillo da kyau kafin ta mayar da dubanta ga Mama Asabe ta ce,"wannan ce kishiyar Ilham ɗin?". Mama Asabe tace,"ina jin ita ce ko?". sai kuma kusan a tare suka jefawa Fillo tambayar,"kece matar nan ɓangaren ko kuma ƴar aiki ce?". kafin Fillo tayi magana Hajiya Zaliha ta amshe da cewa,"ita ce mana". "yanzu wannan ita ce wacce aka liƙawa Turakin da ma?, ai ce nake yi waccan da aka ce an ba shi a bushe take ko". Mama Asabe tayi maganar. Hajiya Zaliha ta taɓe baki ta ce,"yo ai dama saboda su taimakawa ƴar'su ta zama mutum kuma su ci arziƙi, shiyasa suka bi ta ƙarƙashin ƙasa suka kori Ilham aka liƙa masa ita, amma banda haka Turaki ai yafi ƙarfin tsummar ƴar aiki, ko da yake banga laifin iyayenta ba dan sun yi ƙoƙarin haɗa iri da mai dukiya kamar Turaki ba. hausawa suka ce bangon sukari a jingina da kai a lasa, yanzu ba gashi sun mayar da ƴar'su ta zama mutum ba, dama ai ƙwaɗayin dukiyar tasa ake ba wai saboda Allah suka nuna su na sonsa ba, yo ke daga jin labarin ɗauke asiri ai kin san ƙarya ne ma". Mama Asabe ta ce,"to ai ni a wata ruwayar ma ji nayi ance bata da asali, ance uwar na haifarta ta jefar da ita ta gudu, an ce ma bata san uban nata ba sai da zai mutu yazo neman gafarar uwar. to duk dai kin san harkar ta a haɗu a rufawa kai asiri ne shiyasa aka ɓoye gaskiyar zancen, amma dai tabbas an ce shegiya ce". Antyn Kano ta gyara zama tana duban Fillo, ta kama haɓa ta riƙe cikin izgili ta ce,"shegiya kuma?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe abun har haka yayi muni, yanzu tsakani da Allah ina gamin haɗi tsakanin tsarkakke da gurɓatacce, shege ai sai ɗan uwansa shege, gaskiya wallahi an zalunci yaron nan, ko da yake aikin asiri babu abin da ba yayi. to ni su Mai Martaba ma mene na haɗa Ilham kishi da ƴar gaba da fatiha?. kai talaka dai akwai zubarwa da kai mutunci, da zarar an ce an rasa cin na yau da na gobe shikenan sai kiga an faɗa harkar karuwanci kuma. Allah dai ya kyauta yasa kar a haifi iri". tun a zancen farko zuciyar Fillo ta buga da ƙarfin gaske, ranta ya ɓaci sosai. a yanzu da Antyn Kano tayi magana ta ɗago da kanta tana kallon su, lokaci ɗaya idanuwanta suka cika taf da ƙwalla. Mama Asabe ta sake cewa,"um to mu yi dai abin da ya kawo mu". ta kai dubanta ga Fillo ta ce,"ga shi ba sanin sunanki muka yi ba, to ma dai in aka kira ki da shegiya ai ba'ai lefi ba sunan yanka ne irin naku na haihuwar kan titi. allura muka zo ki bamu idan kina da ita za'a cire sartse". a lokacin zazzafar ƙwallar da ke cikin kurmin idanun Fillo su ka gangaro saman kumatunta, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, jin zuciyarta take yi kamar zata yi bindiga. she can't stay any more ana cin mutuncinta da na iyayenta. in ba haka ba za'a iya kaiwa gaɓar da wataƙila zaman aurenta ya ƙare yau a gidan nan. taji yo maganarsu su na ƙara faɗin,"ai Ilham ma tafi ƙarfin kishi da wannan wallahi, ta maishe da shegiya ƴar aiki kawai". cikin raɗaɗin zuciya Fillo ta miƙe zata bar wajen. Hajiya Zaliha ta dakatar da ita da faɗin,"ke figaggiyar kaza dama ba ki da tarbiyya, ina allurar da muka ce ki ba mu?, saboda kin mayar mu ƴan iska za ka kaɗa kai ki wuce ba ki ko tanka mana ba". Fillo ta runtse idanuwanta, ji take yi kamar ta tanka musu, kamar ta faɗa musu maganar da har mutuwa ba za su manta da ita ba, ta ci musu mutunci irin wanda ba za su ƙara sha'awar zuwa gidan nan ba har a tashi duniya, duk kuwa da cewar sun ajiye ƴa acikinsa. but ɗayan ɓarin zuciyarta sai ya haneta hakan, ba halinta ba ne, ba tarbiyar da aka bata ba kenan, tayi banza da su da maganar da suke yi ta haye sama tana goge hawaye. ba ta shiga ɗakinta ba sai da ta daidaita nutsuwarta tukunna, gudun kar Maijidda ta fahimci abin da ya faru. ko da ta shiga ba ta kalli in da Maijidda ke zaune ba tayi saurin shiga toilet ta wanko fuskarta, tana fitowa sai ga Hannatu ta shigo ɗakin, ta durƙusa tana faɗin,"Anty baƙi a ƙasa sun ce ki ba su allura". ta dafa kafaɗar Hannatu suka fita, su na tsaye ta wuce kitchen ta fito, ta tsaya tare da musu kallon banza kafin ta buɗi ba ki ta ce,"ban da zubar da mutunci ina ku ina aron abu?, anyway matar so bata da kayan faci a ɓangarenta balle tayi ajiyar wata allura". tana faɗar hakan ta haye sama abin ta, fiye da haka ta so ta faɗa musu, to gudun tashin hankali yasa ta rabu da su kawai. ko da ta koma ɗaki bata bari Maijidda ta fahimci komai ba, ta zauna suka cigaba da hira. "kin san Allah da tafiyata zan yi. ni kin san ba son ƴan aikin nan nake ba balle in zauna muyi hira da su. yanzu dai ina zamu je ƙunshin?". "to ai ma Maama tace wadda ta yiwa su Adda Zaytuna ita ce zata yi min, yanzu wurin saloon kawai zan je, mu bari sai da yamma ma je ko?". Maijidda tace,"a'a kin san halin lalle da cin lokaci, mu fara zuwa saloon ɗin tukunna". "to shikenan. bari naje na faɗa masa. kin san nace miki ina son zuwa gidan Yaya Yusuf, shi ne fa yau na buga musu sammako". ta yaye mayafin jikinta ta ajiye sannan ta fito ta nufi ɗakin Turaki, yana zaune kan kujera yana operating laptop, hannunsa riƙe da ƙaramin glass cup yana kurɓan coffee. yaji shigowartata amma bai ko ɗago ya kalli wurin da take ba, sai dai yayi mamakin ganinta ɗin, dan rabonta da ɗakinsa tun ranar da ya faɗa mata cewar zai dawo da Ilham, yau kusan kwana tara kenan. ko abinci idan ta gama a parlo take barinsa, ta ci nata ta bar masa nasa, ruwansa ne yaci ruwansa ne kar ya ci, yacca ya lura ma kamar girkin ma ba yi take ba sai dai ƴan aiki su yi, shiyasa shi ma baya shigowa sai yaci abinci a gidan su ko gidan su Bello. a ciki ya amsa sallamar da yaji tayi, ta ƙasan idonsa yake kallonta, tana tsaye daga jikin madubi ta maƙale, fuska sam babu annuri. yacca take fushi da shi haka shi ma yake fushi da ita, ranar da ya faɗa mata zai mayar da aure ta ƙona masa rai, yanda ta nuna ko kishinsa ba ta yi, irin ma ba sonsa take ba, kawai da ya faɗa mata ta kalle shi da fara'arta tace Allah ya sanya alkhairi, daga nan taci gaba da harkokin gabanta tamkar ba wadda kishiyarta zata dawo ba, shi kuma wannan nuna rashin kishin nasa ya ba shi haushi har ya ɗauki fushi da ita, kuma ganin bata bi ta kan fushin nasa ba ya ƙara hawa sama. ita kam tun da tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, ba komai take tunawa ba sai ranar da ya sameta a ɗaki tana kuka. ba kamar yacca ya tsammaci kukan nata ba, kuka take yi akan ciwon mara da ya matsa mata kwana biyu, amma buɗar bakinsa a lokacin ce mata yay,"ya fi miki ki koyawa zuciyarki haƙuri da son zama da kishiya akan wannan kukan da kike yi mara amfani, domin kuwa dawo da matata babu fashi, Allah ya halasta min na zauna da irinki har guda huɗu, balle kuma matar da na fara zama da ita kafin ke, ki san da wannan". idonsa kawai ta kalla a lokacin ta san ya faɗa mata hakanne saboda kawai ya ƙuntata mata. ita sai a yanzu ta yarda da batun sauyawar da maza suke yi idan zasu ƙara aure, duk da bata ga yana wani rawar ƙafa ba amma ya sauya fiye da tunaninta, magana wannan bata haɗa su acikin gidan, kuma ba nata laifin bane, nasa ne, don ita ko kaɗan bata ma bari kishinta ya fito ƙarara ba yacca zai gane, tun tana ɗora hakan akan tilasta masa ɗin da akayi har ta daina, ta fahimci zallar bura'uba ce kawai irin ta ɗa namiji, don sosai ya tsiri wa su halaye da bata sansa da su ba, ko zata narke tana masa magana baya tanka mata, ban da jiya da yaci zarafinta. "Jannaty..." ta kira sunansa a hankali, taji ta gaza ƙarashe abin da zata faɗa saboda kukan baƙin ciki da ya taso mata. Turaki yay banza da ita kamar bai ji kiran da tayi masa ba, sai dai still bai bar kallonta ta ƙasan ido ba, yana duban kumbararrun idanuwanta, ga wanda bai sani ba zai ce ciwon ido take yi, but to him da yasan kayarsa ya san uban kuka taci ta ƙoshi har ta godewa Allah. sai ya ɗauke kansa ya sauke ajiyar zuciya, kamar ba zai bi ta kanta ba, sai kuma ya ɗan ji tausayinta a ransa, ya maido da dubansa gareta sannan yace,"ke ba kya gajiya da kuka ne, kin shigo min ɗaki kin min tsaye sai wani faman cin magani kike kina faman ɗaga hanci". Ya ida maganar yana yi mata kallon sama da ƙasa. Cikin sanyin murya ta ce masa,"don Allah kayi haƙuri ka bar ni in yi lallen". ya tamke murya ya ce,"na ce ba za'ai ba". "to ya zan yi da Maama fa?, ita fa ta ban umarni akan in je ayi min". yay ɗan jim kafin ya ce,"fita ne daga gidan nan zuwa gidan mu ba za kiyi shi ba, idan me lallan zata zo nan tayi miki ta zo, idan ba zata zo ba ki haƙura". ta haɗiye ƙullun abu a maƙogoronta na takaici, ta sunkuyar da kanta ta ƙara cewa,"don Allah ka bar ni in koma gidan ku in zauna har a gama biki, don Allah don Annabi". ɗago kansa yay ya bita da kallo, duk tayi sanyi sosai kamar mara lafiya. nazartar yanayinta ya shiga yi, so yake ya gano dalilinta na dagewa akan sai ta koma gidan su har an gama biki sannan ta dawo. yaga ta ƙara kawar da kai gefe tana goge hawaye. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce,"matsayina na mijinki wanda aljannar ki ke ƙarƙashin ƙafata, ina me ba ki umarnin ko nan da parlo kar ki bari ayau, har sai an kawo abokiyar zamanki tukunna". yay maganar cikin muryar ba da umarni. ta dube shi a sanyaye,"yan zu ba zan iya cin alfarmar Maama ba?". tayi maganar cikin wani irin rauni. yan da bai tanka mata ba haka itama bata ƙata cewa komai ba ta fita. tana fita ya ɗauki waya ya kira Maama yace mata wai sun fita ita da shi sai zuwa yamma za su dawo, a faɗawa me ƙunshin sai gobe ayi. ƙarfe bakwai na dare aka kawo Ilham, sai da aka fara kaita gidan su Turaki sannan aka yo da ita gidanta. lokacin da Fillo ta jiyo guɗa sai da zuciyarta tayi wani mugun matsewa, yunwa take ji a lokacin ta ɗauko abinci zata ci, amma lokaci ɗaya taji ta ƙoshi, bata buƙatar komai a wannan lokacin sama da tayi kuka. ɓangaren Ilham kuwa tana can tana shan mugwayen shawarwari, an cika mata kai fal da abubuwan da muddin ta ɗauke su ba zata jima ba Turaki zai ƙara saita mata hanya. wajen ƙarfe takwas da rabi na dare, Fillo ce a ɗakinta tana shirin kwanciya bacci, wayarta tayi ƙara, waƙar da ke tashi wajen ringing ɗin ya shaida mata Turaki ne, hakan yasa bata ko matsa daga inda take ba balle taje ta ɗauka. har sau biyu kiran na shigowa ya katse bata ɗauka ba, tana gama shiryawa ta haye kan gado ta kwanta, ta dunƙule a waje ɗaya, idanuwanta na ta hasko mata yacca Turaki zai kwana tare da wata yau ba ita ba. tayi nisa cikin wata duniya ta daban Turaki ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya kunna fitila ya bita da kallo, ƙarasawa yayi gaban dressing mirror da ya hangi wayarta akai, ya ɗauka ya kunna, sai yaga a silent take, hakan ya tabbatar masa da cewa ba da gangan taƙi ɗaga kiran nasa ba. ajiye wayar yayi ya shiga taɓa ƙafarta, tana jinsa amma tayi masa banza, ta rufe idonta kamar me baccin gaske. zama yay a gefen gadon kafin yasa hannu ya yaye blanket ɗin da ta rufa da shi, ya rumtsa idonsa a lokacin da idanuwansa suka sauka akan cikakkun breast ɗin ta da ya kwan biyu bai haɗu da su ba. Fillo ta buɗe ido a lokacin ta zabga masa harara tare da faɗin,"lafiya?". ta faɗa murya a sama kamar ba ita ba. ba tare da ya kalleta ba ya miƙe tsaye, ya zuba hannayensa cikin aljihu sannan yace da ita,"ki sauko ƙasa ki same ni, ina so zan yi magana da ku". taja blanket ɗin ta gyara kwanciyarta kamar bata ji me yace ba. ya juyo yana kallonta,"ba magana nayi miki ba kika koma ki kwanta?, me kike ji da shi ne yanzu?". ta ƙara jan blanket ɗin ta rufe har kanta, yana tsaye yana ta kallonta yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ransa, ya fi ƙarfin minti uku a tsaye Fillo bata ko motsa ba balle yasa ran ma zata tashi ne, ya jijjiga kansa ya fita ransa a mugun ɓace. yana sauka ya tarar Ilham ta shigo a lokacin, tana tafiyar yauƙi ta wuce ta zauna kan kujera, sai kallon parlon take yi tana taɓe baki kamar wacca taga kashi, mamaki take yi sosai har cikin ranta, bata taɓa zaton kaya masu shegen kyau da tsada ba ne aka zubawa Fillo. kusan zata ce kuɗi daidai ne da nata, kuma in har ba son zuciya ba colour ɗin funitures ɗin Fillo sun fi nata kyau sosai ma. sai da aka kwashi kusan mintuna goma kafin Fillo ta sauko, sanye take da hijab har ƙasa, fuskarta wasai kamar bata da damuwar komai, sai ma bacci da ya fara nuna alamarsa a fuskartata. tun da ta taho Ilham ke kallonta idanuwanta kamar za su faɗo ƙasa, zuciyarta tayi mugun bugawa da wani masifar kishi, ta haɗiye yawu da ƙyar a maƙoshinta, dama har haka Fillo ke da azababben kyau bata sani ba?, a yau dai ba zata so zuciyarta ba kam Fillo ta ci uwar ubanta a kyau, kyan nata har tsoro ya bata, yarinyar ta koma kamar ba ita ba, ta ƙara fresh da kyau me matuƙar ɗaukan hankali, sai ƙyalli take yi, ga shi kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana ɗauke da ciki, bata san lokacin da wani uban gumi ya wanke mata wuya ba, ta damƙe hannunta a jikin kujerar tana ji kamar ta tashi ta bar parlon. Fillo ta wuce ta kashe tv, sarai ta san Turaki kallon news ɗin yake yi, ya bita da kallo, tun ɗazu yake a hasale da ita, ya lura ta ɗauki salon rashin mutunci, dole zai taka mata burki tun kafin akai ga nisa, don ba zai ɗauki wannan banzan halin ba, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai ɗauke idonsa akanta ba, so yake ya karanci ma'anar murmushin da yaga tana yi tun da ta sakko. "i'm sorry Jannaty, haɗewa nayi da shaf'i da wutri shiyasa na ɗan ɓata lokaci, i hope hakan bai ɓata maka rai ba". tayi maganar tana kallon Ilham ta ƙasan ido, wacca ta cika tayi fam tana kallon yacca Fillo ta wani maƙale a kusa da Turaki. Turaki ya sauke numfashi ya dube su gaba ɗayan su, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga yi musu nasiha akan zamantakewar su, ya faɗa musu yacca yake so zaman su ya kasance, ya faɗa musu abubuwan da yake so su kiyaye gudun ɓacin ransa da na su. daga ƙarshe kuma ya tsara yadda kwanakin kowacen su zai kasance, sannan ya ba su damar jin ta bakinsu, Fillo na wasa da yatsun hannunta ta ce,"duk yanda ka yanke Jannaty ni kam yayi min". ya kalli Ilham, wacca ke kallonsa fuskarta na bayyana rashin amincewarta akan hakan, sai da ya ɗaga mata gira ya ce,"ehen, ko kina ciwon baki ne?". ta kawar da kai gefe guda tana cin nagani ta ce,"da dai ka ƙara, kwana biyu sai kace a zamanin da, ko gidan ƙawata kwana huɗu ake yi musu su da suka fi mu jimawa ma kenan". Turaki yay mata mugun kallo kafin ya ce,"to kwana biyun na yanke ba zan ƙara ba, nan gidana ne ba gidan ƙawarki ba ne". ya danne ɓacin ran da ke ingizo shi, ya ci gaba da yi musu nasiha sosai, irin nasihar da kowaccen su sai da taji a zuciyarta, bayan nan yay musu adu'ar zaman lafiya, kafin nan ya rufe taron na su da adu'a. cikin ƙarfin hali Fillo ta danne bala'in abin da ke taso mata ta ce,"Allah ya amsa dukkan adu'oin da kayi mana ranka ya daɗe, insha'Allahu ta ɓangarena ba zaka taɓa samun wata matsala ba, zan kiyaye dukkan abin da baka so, haka zan yi ƙoƙarin aikata duk wani abu da kake so domin farin cikinka, na yi maka alƙawarin hakan muddin numfashina". sai kuma ta kalli Ilham tace,"abokiyar zamana ina yi miki barka da dawowa, ina fatan zamu haɗe kanmu mu zauna lafiya kamar yanda mijinmu ke so, ni dai ta ɓangarena ba ki da damuwa na ɗauke ki tamkar ƴaruwa ta jini. bismillah gaisuwar musulunci". ta faɗi hakan tana miƙawa Ilham hannu don su gaisa, but sai Ilham ɗin taƙi miƙa mata nata, ta yi mata kallon sama da ƙasa tare da jefa mata wani irin wulaƙantaccen kallo. ɗan runtse idanun Fillo tayi tare da yin murmushin takaicin da babu wanda zai fahimta, bata san cewa ita ma ba har zuciyarta ba, yanda bata so ta haɗa hannu da ita haka ita ma, don ko ace ma ta amince su gaisa ɗin cikin dabararta zata aiwatar da abin da zai hana hakan, ai ba don Turaki a wajen ba kallo bata isheta ba. Ilham ta miƙe a zafafe zata fita ta bar parlon Turaki ya dakatar da ita. "ta wurinki zan fara samun matsala kenan ko?". Fillo ta miƙe ta ce,"zan wuce ɗaki, Allah ya bamu alkhairi ya tashe mu lafiya, sai da asuba ranka ya daɗe". tana faɗa ta wuce upstairs cikin natsuwa, Ilham ma ta bar parlon kamar wacca iska ke tunkuɗawa. tun da Fillo ta koma ɗaki taji bacci ya ƙara ƙauracewa idanuwanta, ta gaza danne abin da take ji a zuciyarta don ta samu ta saita kanta, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe take, bata taɓa zaton zafin kishinta ya kai har haka ba sai yanzu, tayi saurin faɗawa toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah. salloli tayi ta jerowa, gani take kamar idan tayi kuskuren sallamewa zata iya yiwa kanta rauni. bayan ta idar tayi zamanta akan dardumar tana tasbihi, lokaci zuwa lokaci sai ta sharce ƙwallar da ke sakko mata.. zuciyarta zafi take yi mata sosai, hatta kanta jinsa take yi tamkar zai rabe gida biyu, gaba ɗaya jin duniyar take babu daɗi sam, wataƙila in ace yau ba zata yi kwanan gidan nan ba da zata iya samun sassaucin raɗaɗin da take ji a zuciyarta. a can ɓangaren Turaki kuwa tun komawarsa ya tarar Ilham ta rufe ƙofa, bai ko bi ta kanta ba ya wuce ɗakinsa, sai dai tun da ya koma zuciyarsa ta gaza yi masa daɗi, tazara!, irin tazarar nan da bai taɓa zaton zata kasance tsakaninsa da Fillo ba, ko da sukai shariyar juna ya kan shiga duk dare yaga sleeping beauty face ɗinta. ya zata ji yau zata kwana a ɓangarenta ita ɗaya ba tare da motsinsa a sashin nata ba?, sai yay shiru kawai tare da rufe idonsa, haka kawai ya ji ya damu sosai akan halin da yasan babu makawa tana cikinsa yanzu. ya san yay mata rashin kyautawa, bai kamata ya shareta ba har ya canja mata ya zamar mata wani kalar mutum na daban da bai raineta akan hakan ba. tabbas tana buƙatar rarrashinsa ko ya ne, tana buƙatar kulawarsa da rarrashinsa a wannan daren ko zata samu bacci, don kamar yanda ya san kayarsa ne daren yau ba lallai ne ta iya bacci ba. wajen sha biyu saura aka turo ƙofar ɗakin a hankali, tun bata ɗago kai ba ƙamshin turarensa ya daki hancinta. ta ɗago domin ganin shigowar ko ta lafiya ce, kallo ɗaya tayi masa ta watsar. kallo ɗayan da tayi masa ya fuskanci tayi kuka ne har ta godewa Allah, don idanuwanta sun yi mugun kumbura, sai kawai ya tsinci kansa da matsanancin tausayinta a ransa. ƙarasa shiga yay, ya zauna a gefen dardumar, ya dinƙa kallonta yana ganin yacca taƙi ɗago ido ta kallesa, kenan bata ko ƙaunar ganinsa a yanzu?. kafin ya buɗe baki yay magana yaga ta miƙe, taja dardumar ta jefar da rabin ƙafarsa da ke kai, ta ninke sannan taje ta kashe fitilar ɗakin ta haye saman gado. ji tayi ya biyota kan gadon, tayi saurin miƙewa zaune tana cewa da shi,"ka tashi ka fitar min a ɗaki". ta faɗa murya a karye, yayin da hawaye ke sakkowa saman kuncinta, hawayen da yake jin su har cikin ransa tamkar ana hura huta a zuciyarsa. ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa, sai taji ta kasa ƙwacewa, kawai ta kifa kai akan gwiyarta, tayi kewarsa har bata san iyaka adadinta ba. Cikin kwantar da murya ya soma magana yana faɗin,"na san ban kyauta miki ba akan canjawar da nayi miki, tsawon kwanaki tara kenan ina ƙuntata miki, ba zan hana ki jin haushina ba, amma ki yi haƙuri don Allah, ni ma nawa ranne babbu daɗi, tilasta min da aka yi akan mayar da auren nan duk shi ya dagula min lissafi ". tsabar tuƙuƙi da ɗacin dake tasowa a ƙarƙashin zuciyarta, tun da ya fara magana har ya kai ƙarshe bata ko kulasa ba, haka bata ɗago kai ta kalle shi ba, sai ma zame hannunta da tayi a nasa. Turaki ya gyara zamansa, ya matsa kusa da ita ta yadda numfashinsu yake gauraya da na juna, ya riƙo hannayenta duka acikin nasa yana murza lallausan tafin hannun nata, ya kifa goshinsa saman kanta yana sauke numfashi. baya jin a duniya akwai wata mace da zata kama zuciyarsa kamar ƙaramar yarinyar nan, kullum cikin adu'a yake yi Allah kar yasa sai ya rigata mutuwa. cikin hikima da iya tsara zance na miji ya shiga bata baki, yayi amfani da duk wasu kalamai da za su kwantar mata da hankali da shigar da nutsuwa cikin zuciyarta, har sai da yaga alamar hucewa a saman fuskarta. but hakan duk bai sa Fillo ta samu sauƙin zafin kishin da take ji ba, abu ɗaya kawai ta sani mijinta yana mata tsananin so, kuma yana sonta fiye da ɗayar matarsa. da kansa ya sauƙa ƙasa ya dafo mata indomie, ya zo ya sakata a gaba taci da ƙyar saboda lallamar da yake yi mata. tamkar ɗacin magani haka ta dinƙa cin indomie ɗin, but babu yanda ta iya sosai take buƙatar abinci, dan zata iya cewa rabonta da wani abu a ciki tun kunun gyaɗar da ta sha a gidan Yusuf. sai da ta kwanta sannan Turaki ya bar ɗakin, tana jin fitarsa ta ƙara fashewa da kuka, ba wai don tana so ba sai dan bata ma san lokacin da yake zuwar mata ba ɗin. washe gari da sassafe kuwa sai ga text ɗinsa akan ta shirya ta tafi gidan na su.  tsabar farin ciki da jin daɗi bata san lokacin data tura masa da reply ɗin thank you ba. lokacin da ta fito zata tafi yana hangota ta balcony, fuskarta ta gaza ɓoye jin daɗin da take ji, yay murmushi kawai tare da juyawa ya koma ciki domin ya sanarwa da Ilham ita ma ta shirya ta tafi, tun da kusan yaune yinin bikin gidan. da rana taro yay taro, cikin taron mutanen da ake ta ɗaukar hoto Fillo ta yanke jiki ta faɗi. cikin tsananin tashin hankali Hajiya Madina da Hajiya Ramla suka sureta aka yi asibiti. zuwan su babu jimawa sai ga Turaki shi ma ya ƙaraso, cikin matsananciyar damuwar da ta kasa ɓoye kanta ba. ya zauna kusa da Maama, ta dafa kafaɗarsa tace,"ka kwantar da hankalinka insha'Allahu ba wata matsala ba ce babba". Mum ta kalle shi rai a ɓace tace,"na jima da fahimtar kana ƙuntatawa yarinyar nan. to wallahi kaji na rantse maka muddin silar ɓacin ranka take kwance anan sai ranka yayi mugun ɓaci". wucewar mintuna ashirin su na zaune jungum jugum sai ga likita nan ya fito, ya buƙaci cewar wani acikin su ya biyo shi. Hajiya Madina tace da Turaki ya tashi yaje, ya shiga office ɗin Dr jikinsa a matuƙar sanyaye, duba da yayin da yake gani akan fuskar likitan. "Bismillah zauna". ya faɗa yana yi masa nuni da kan kujera. Dr ya ɗauko file ya buɗe, ya dubi Turaki ta cikin glass ɗinsa sannan ya ce,"Halima Borkinɗo right". Turaki yay saurin jijjiga masa kai,"yes". Dr ya sauke numfashi, ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce,"kun san cewa ta kamu da heart failure?". "mun sa ni Dr". "to amma ya akayi ku ka yi sakacin da har damuwa tayi mata yawa haka?, tana fa ƙoƙarin barin matakin farko da take ciki ne ta shiga na gaba". Turaki ya sauke doguwar ajiyar zuciya bai iya cewa komai ba. haushin kansa yayi matuƙar kama shi. "anyway ga wannan drugs ayi gaggawar siya mata, gudun samun matsala babba. and a kiyaye sosai da duk abin da zai haifar mata da damuwa kar a kai stage ɗin da Babynta zai cutu". idanuwan Turaki suka ƙanƙance yace,"Baby?". ya tambaya da mamaki sosai. Dr ya jinjina masa kai,"ƙwarai Baby, ko ba ku san tana da ciki ba ne?". bakin Turaki ya buɗe, duka haƙoransa suka yo waje,"i din't get you clearly Dr, wanne irin ciki wai?". Dr ya faɗaɗa murmushin sa, yana kallon Turaki yace,"zauna da kyau kar ka faɗi". sai ya ɗebo sauran takardun da ke cikin file ɗinsa ya zubewa Turaki a gabansa ya ce,"ashe kamata yayi in fara yi maka congratulations, so you are expecting a baby in the next five months Insha'Allah, a test ɗin da aka yi mata ya nuna mana cikinta yana cikin wata na huɗu ne, but how comes duk baku yi noticing ba?" Turaki ya kasa amsa tambayar Dr, sai ɗaga hannu sama da yay yana godewa ubangiji. ya daɗe a hakan kafin ya mayar da hankalinsa kan doctor ɗin yace,"thank you very much, ga wannan kasa mai a mota". ya ajiye masa kuɗi saman table ɗinsa, hakan kuma yayi wa Dr daɗi sosai, nan da nan ya shiga bawa Turaki shawarwari akan yacca za su kula da cikin. Turaki duk ya ƙosa ya miƙe akan kujerar, hannu ya miƙawa Dr ɗin su kai shaking, tukunna ya fita a office ɗin bakinsa sam yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki. kai tsaye room ɗin da Fillo ke kwance ya wuce, a ciki ya sami Maama da Mum, lokacin ta farka tana zaune, sun sakata da tambayar me take son ci, ita kuma duk ta narke tana faɗawa Mum wai Mangoro take so me warin gawasa. kallo ɗaya Mum ta yiwa Turaki ta zunguri Maama suka fita suka bar ɗakin, su na fita ya rungume Fillo da farin cikin da ba zai iya misaltuwa ba. ta ture shi daga jikinta tana turo baki gaba tare da ɓata fuska. "ni ka matsa daga kusa da ni". yay murmushi me sauti yana zura hannunsa cikin rigarta, cikinta ya shiga shafawa yana faɗin,"ta ya zan barki alhalin akwai ajiyata anan?. congratulations very soon za ki zama Mother". ta yi masa wani kallon mamaki, ya ɗaga mata gira duka biyu,"am serious Angel". sai ta kulle idonta tana jin wani daɗi na tsarga mata, ta kai hannayenta duka biyu ta dafa cikin tare da hannunsa da yake kai. "Allah ka azurta ni da zuri'a ɗayyiba". ta faɗa hawayen farin ciki na sakko mata, Turaki yay kissing ɗinta a goshi tare da faɗin,"amin summa amin uwar ƴaƴana, i love you so much". lokacin da suka fito su Maama har sun wuce, duk kunyar da yake ji, bai iya haƙuri ba sai da ya ɗaga waya ya kira su Maama ya sanar musu. bayan sun gama wayar ya kira Bello, yana ɗagawa yace da shi,"Bello ai na zan sami Mangoro me warin gawasa?". Bello ya ce,"yanzu na mayar da farantin tallan gida, ya ƙare tass da yake yau anyi ciniki". Turaki yay tsaki,"kai dai kana da matsala". "to MT haka kawai sai ka kama wani kirana kana tambayana in da zaka samu mangoro, hanyar kasuwa ne baka sa ni ba ko me?. ni don Allah kace a bani matata yau wallahi duk na gaji a matse nake". Turaki yaja dogon tsaki ya kashe wayar, ya kamo hannu Fillo dake dafe da ciki yace,"sorry Angel, duk in da mangoro yake zamu samo shi yanzun nan, ki tayani bawa Baby haƙuri". sai ya kuma ya fara ce mata,"yanzu idan namiji ne wanna suna zamu saka masa?". "ai kai kake da wannan alhakin". "to in dai namiji ne sunan Abba zamu saka, idan kuma macece zamu sa sunan Maama, in kuma twins ne duka maza zamu sa sunan Abba da Baffa, idan twins ne duka mata sai mu sa Maama da Ummi". "Mum kuma fa?". "ita ma zamu saka nata idan kin ƙara haifar wasu twins ɗin". "wai haka Doctor ɗin yace maka twins ne?". "hakan nake fata Angel". sai ta marairaice fuska, idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta damƙe hannunsa ta ce,"Jannaty ina tsoron haihuwa, an ce akwai wahala". tausayinta ya kama shi,"kar ki damu Angel insha'Allah ke kalar taki haihuwar zata banbanta da ta su, cikin sauƙi zata zo miki". "Allah yasa. amma Jannaty ka dinƙa yi min adu'a kullum na haihu da raina da lafiyata, ina so na raini yarana da kaina domin in ba su ilimi ingatacce tare da ba su kyakykyawar tarbiyya, ba na so na mutu a lokacin dana san ƴaƴana za su buƙace ni". sai kawai ya gangara motar gefe yay parking, yacca jikinta yay sanyi haka ma nasa, ya juyo ya kalleta yaga tana zubar da hawaye, ya janyota ya rungumeta. ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"Jannaty bana so su tashi acikin maraicina, ina so su ma suji wannan daɗin na uwa". lokaci ɗaya Turaki yaji idonsa ya ciko da ruwan hawaye, yana shafa bayanta yace,"mene kuma na zancen mutuwa Angel?, don Allah ki daina, da izinin ubangiji da ranki da lafiyarki za ki haihu, kuma insha'Allahu ubangiji zai ba ki aron tsawon ran da har auran ƴaƴanki za ki gani". ita dai bata iya cewa komai ba, kuma har suka ƙarasa gida jikinsu duk yay sanyi. Fillo kuwa tana shiga bedroom ɗin Mum ta rufe fuskar ta, saboda haɗa ido da su da tayi, don samun su tayi zaune su ma duk cikin farin ciki, kuma ganinta kowa ya shiga mata adu'ar Allah ya raba lafiya. Zaytuna da Samha sai tsokanarta suke yi wai ta zama uwar biyu. tun daga wannan ranar kuma Fillo sai ta koma rayuwar gidan su Turaki, don ƙememe Maama taƙi barinta ta koma can gidanta tace sai cikin yayi ƙwari, duk ranar kwananta nan Turaki yake zuwa sai su tare a ɗakinsa na gidan. sosai Fillo ke jin daɗin yanda Mum da Maama ke tarairayarta, musamman a wajen Hajiya Madina, don rainon cikin take yi cikin kulawa ta musamman daga wurin Kakarsa Hajiya Madina. macen da kullum cikin siyan kayan jarirai take yi, hatta gadon Baby tana zuwa saudiyya ta taho da shi, motsin Fillo kaɗan ta tambayeta me take so. Rayuwa ta cigaba da tafiya, a yayinda wasu abubuwan rayuwar kan sauya, lokaci yana tafiya a kullum kuma a ko da yaushe. wani lokacin cikin farin ciki wani lokacin baƙin ciki. A duk lokacin da agogo zai motsa, lokaci ne yake wucewa, lakacin da baza a sake maimaita irinsa ba, lokacin da ba zai taɓa dawowa ba. Sau da yawa ɗan Adam ya kan ƙagauta akan lokaci ya zo masa, musamman idan ya ƙosa akan cin burin wani abu da ya saka a ransa, sai ya gaza fahimtar irin saurin da lokacin yake yi, har sanda zai ankare da zuwan wannan abin da ya saka a ransa, anan ne zai ga tamkar ansa  igiya ne ana janyo wannan lokacin. hakan take a ɓangaren Fillo, tun daga ranar da likita ya ƙayyade musu watanni biyar a matsayin watannin da zata ɗiba kafin ta haife abinda ke cikinta, daga wannan ranar ta ƙosa da zuwan lokacin, zuwan ranar, sai ta koma ko da yaushe cikin kallon kaɗawar agogo take, cikin lissafa kwanakin kalanda, cikin haddar kwanakin da muke shiga muna maimaita su, cikin lissafi da hasashen irin soyayya, kulawa, ilimi tare tarbiyar da zata bawa abin da ta haifa. sau tari mu kan yiwa kanmu lissafin tanadin abubuwa, sai dai abubuwa sukan zan zo mana ne a yacca ubangiji ya tsara mana ba yacca muka tsarawa kanmu ba. wani lokacin ɗan Adam kan iya ƙirga sautin fitar numfashinsa, ba tare da ya san lokacin da numfashin nasa zai daina fita ba, fitar da ba zai ƙara samun damar ƙirga shi ba. buri wani abu ne da kowanne ɗan Adam ke cin sa, sai dai ba duka burin ɗan Adam ne ke cika ba, kuma sau tari cin buri na katsewa ɗan Adam ne a lokacin da numfashinsa ya daina fita. Rayuwa babbar nasiha ce ga kowanne ɗan Adam, akan ya gane cewa ba komai ba ne yake da tabbas ba a rayuwa, idan aka cire lokaci, lokaci ne kawai yake da tabbas, sai dai ɗan Adam ba shi da tabbas ɗin zai kai kowanne lokaci na bugawar agogo, ko tabbas ɗin lokacin da yake ta lissafawa rayuwarsa. ubangiji ya riga ya ƙayyadewa kowanne bawa iyakacin lokacin da zai ɗiba a duniya, numfashin wani zai daina fita ne a bugawar sakan, yayin da numfashin wani zai daina fita ne a bugawar minti, kowanne bawa na tafiya ne kawai akan lokacin rayuwarsa. a rayuwa ba ko da yaushe ne ɗan Adam yake yin murmushi ko dariya ba, ba kowa ne yake samun damar rayuwa tare da wanda yake so ba, ba kowa ne yake samun rayuwa a irin yacca yake so ba, babu wani bawa da ke samun ɗorewar farin ciki a rayuwarsa, fa ce wataran sai yayi kuka. *MUTUWA*, ita ce tabbatacciya, kuma ita ce abar dake kan kowanne rai, wacca bata da wani banbanci a tsakanin me kuɗi da talaka, babba ko yaro, me mulki ko mara mulki, ita ce wacca bata barin wani don wani yaji daɗi. sau tari ɗan Adam kan zauna yay ta tunanin yaushe ne zai mutu?, kuma ai na?, taya zai mutu ɗin?, mene zai iya zama ajalin nasa?, sai dai waɗannan tambayoyi babu wani mahaluƙi da yake da amsar su, mutuwar ce kawai take zuwa da kanta, walau ɗan Adam ya shirya mata walau bai shirya ba, ko ana so ko ba'a so, da zarar ta zo tafiya kawai ake yi, ta datse wannan numfashin da bawa yake fitar da shi, acikin jin daɗi wa ko akasin hakan. mutuwa ita ce kaɗai abar da ke iya yanke ƙaunar da ke tsakanin uwa da ɗanta, ko miji da matarsa, ko masoyi da masoyiyarsa, ko aboki da abokinsa. ta kan zo ne bagatatan ba tare da ta sanar ba, sau tari mu kan kasance tare da mutum, kuma a yayin da aka sami giftawar wani lokaci bayan rabuwar mu sai muji ance wane ya rasu, ko kuma wane ya mutu, a lokacin ne zamu yi tunanin me ya sami mutum?, taya za'ai ace ya mutu bayan muna tare a ɗa zu muna hira cikin wasa da dariya?, to ita mutuwa haka take, ta kan ɗauki bawa ne da lafiya ko ba lafiya, kuma a lokacin da wani ke kan hanyarsa ta zuwa duniya, a lokacin mutuwa ke ɗaukar wani ta raba shi da wannan duniyar duk son da yake yi mata kuwa, hakana duk son da ake yi masa. in ace mutuwa zata bar wani don wani yaji daɗi, da tabbas bata raba ɗa da mahaifiyarsa ba a lokacin da yake zuwa duniya ba, wata uwar kan samun damar ganin yaronta kafin mutuwar ta ɗauketa, yayin da wata yaron na fito ita kuma zata yi sallama da duniyar. a lokacin da aka ce mutuwa ta raba mu da wani mutum da yake sashi na jikin mu, ruɗewa da tsananin shiga tashin hankali tare da fitar hayyaci kansa mu gaza yarda da cewar an mutu ɗin, anyi tafiyar da babu dawowa, har ta kai ga ba ma gama yarda da cewar tabbas mun rasa wannan da muke jinsa wani ɓangare na jikin mu, har sai lokacin da aka ɗauki gawarsa acikin makara, aka tafi da ita zuwa maƙabarta, aka kama gangar jikin aka zura acikin ramin ƙabari, har a jera tukwane akan gawar, da ƙasar da za'a zuba akan tukwanen, sannan a shafe hasken farin likkafanin dake lulluɓe da gawar. a sannan ne zamu yarda da tabbas an tafi, an yi tafiyar da ba za'a sake dawowa ba, tafiyar da ba zaka ƙara ganin mutum ba sai a lahira, har ko da yaushe fatan guda ɗaya ne, mu mutu muna masu aikata alkhairi, mu zama masu cikawa da imani, mu zamto mun mutu ana yabon mu. a lokacin da kumburarrun ƙafafuwanta ke sakkowa daga matattakalar benen a hankali, a lokacin take jin wani baƙon yanayi yana ziyartarta, a lokacin take jin wani abu da bata saba jinsa ba, wani irin yanayi ne take jinta a ciki, wanda ya ke zarcewa har can ƙasan zuciyarta, ya motsa zuciyar tare da abin da ke cikinta. sai a lokacin da ta isa parking lot, tasa key ta buɗe motar, sannan ne ta fahimci kamar kewa ce take kamata, kamar dai zata yi kewar wani abu me muhimmanci a rayuwarta. sai dai abu guda ɗaya take so ta sani, menene dalilin da yasa take jin jikinta yayi sanyi sosai?, irin wannan sanyi da bai taɓa ji ba. wayar da ke riƙe a hannunta tayi ringing, duk irin farin cikin da take shiga a sanda taci karo da kira daga gare shi, yau sai taji wani mix feeling ya kamata, taji kamar tana tausayin shi me kiran ba ita kanta ba da take zama da ƙyar tashi da ƙyar. ta ɗaga kiran ta kara a kunne cikin jin sanyin jikin da ya ƙaru a gareta. "uwar ƴaƴana ina kewar ki, kullum idan bana tare da ke sai in ji ina kewarki kamar zan mutu, na kasa yin aiki yau gaba ɗaya, tun da na shigo office na zauna nayi jugum, sai nake jin kamar ban taɓa kewar ki ba sai yanzu ne zan fara, gabana yana faɗuwa, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, yau jina nake tamkar maraya, kuka zan yi Fulani Nah, ina jin kamar zan yi kuka irin wanda ƙanan yara ke yi, Fulani Nah in taho gare ki yanzu?, in zo in kwanta akan ƙijinki in dinga jiyo sautin bugawar zuciyarki a yayinda kike lallashina?, jikinki kawai nake buƙata ayanzu Fulani Nah, ina ji daga yau ba zan ƙara matsawa daga kusa da ke ba, zan daina fita aiki saboda ke, kina lafiya Fulanin Turaki?". maganganun da suka fito daga bakinsa kenan, kuma maganganun da suka haddasa wata muguwar faɗuwar gaba a ƙirjin Fillo. bata san lokacin data shiga motar ta zauna ba. "ki shirya yanzu kije wurin Maama, yanzu zan taho, ba zan iya zaman office ɗin ba, ina so yau mu yini tare, hira nake so muyi sosai, ɗa zu ta kira ni tace min faten tsaki take sha'awar ta sha". Fillo ta dafe goshinta,"Laaa ƙwara da Allah yasa ka yi wannan zancen, kamar na sani na dafa mata shi tun ɗa zu, kuma kaga har na fito zan tafi na kai mata ashe na barsa ban ɗauko ba". "ki bata ta ci da yawa Fulani Nah, duk yawansa kisa ta ta cinye shi kin ji, tana sonsa, shi ne favorite ɗinta, ta ce me kifi take son ci, in few minutes zan iso gare ku, ki kula min da kan ku, zan siyo miki mangoro, Maama kuma zan siyo mata gwanda". "tom Jannaty sai ka dawo, nima yau kewarka da nake yi ta banbanta da ta ko yaushe". "Fulani Nah saura 20days mu zama Mum and Dad ko?". "insha'Allahu Jannaty". "Allah yasa ki haihu da ranki da lafiyarki". bayan gama wayar ta su Fillo to koma ciki, tana shiga kitchen ɗin ta kira lambar Hajiya Madina. daga ɓangaren Hajiya Madina ta ce,"Daughter yanzu nake shirin kiranki, ina ta jin kewarki na damu na, idan babu abin da kike yi ki taho yanzu, in Me Babban suna ya dawo sai ku tafi tare". Fillo ta ce,"Maama faten tsakin me nama nayi, kina so ko nayi miki me kifin?". fuskar Hajiya Madina ta washe da murmushin jin daɗi, duk duniya tana bala'in son souls ɗin nan guda biyu, Turaki da Fillo. "kar ki wahalar da kanki, ba sai kin ƙara ɗora wani ba, zanci wanda jikana ya ci". "to Maama idan na zo ba zan dawo ba, yau ba'a ɓangarena yake ba". "to shikenan. ki hanzarta ki zo Daughter, ina so zan yi wasa da jikana, ina so yau nayi ta kallon fuskar ki". Fillo na murmushi ta kalli cikin da ke jikinta, haka Hajiya Madina take yi, aikinta yanzu bai wuce tasa Fillo a gaba ba tayi ta magana da cikin tamkar a gaske, in anyi dariya sai tace ai ita tana jinsa su ne basa ji, kuma idan ya fito zai ba su labari ne. haka ɗaya yau zuciyar Fillo taji tana so ta yafewa wannan mutumin da ta manta a rayuwarta, kamar ta yafewa Amir, sai ta rumtse idonta ta hura iska a bakinta ta fita daga kitchen ɗin. tana tayar da mota kiran Ummi ya shigo wayarta. "Auta kina lafiya?". "lafiya lau Ummi". "masha'Allah, ina zaune naji ina kewar ki". "wallahi nima Ummi jira nake naje gidan su sai muyi vedio call da ke, yau kawai ina ta kewarki sosai fiye da da. Ummi na yi mafarkin Abba ma, yace in gaida ke, sai naji kamar na bi shi Ummi". [9/7, 02:37] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *59* idan mu ka duba fuskar rayuwa, zamu ga gaba ɗaya tana tafiya ne based on yanda Allah (SWT) ya tsara mana. rayuwar mu na tafiya ne daidai da yanda ubangiji ya rubuta mana tun kafin zuwan mu duniya. duk hasashenmu, duk lissafin mu, duk yanda muke so, duk yanda muka tsara, duk yacca muke tunani, duk yanda ba ma so, duk yanda muke gudu, duk yanda muka yanke, to haƙiƙa yanda ubangiji ya rubuta mana hakan ne zai kasance, kuma na ubangiji shi ne daidai. sau tari idan muka duba fuskar rayuwa, zamu ga duniya tana yiwa wanda ya jima yana aikata laifi talala, zai ta aikatawa yay ta aikatawa, kafin ya ankare sai ya farga lokacin tuba ya ƙure masa, wani Allah zai iya nufar sa da tuba kafin mutuwa, wani kuma ba zai sami wannan damar ba, haka zai wuce lahira da tarin ɗumbin zunubi. haka sau tari zamu ga rayuwa ta rufta da wanda zai aikata laifi sau ɗaya tal a rayuwarsa, nan da nan sai ya fuskanci hukunci abin da muke tunanin me aikata babban kuskuren shi ya kamata ya karɓa. haka zalika idan mu ka ƙara duba fuskar rayuwa, abin da duk mu ka sani shi ne asiri gaskiya ne, tun da har yaci shugaban mu fiyayyan halitta Annabi Muhammadu (SAW), kuma tasirin adu'a ya warka da shi, har aka gano wanda yay wannan sihirin. sai dai abun da yake da akwai a tamu rayuwar, ba ko da yaushe Allah ya ke tona asirin waɗanda suka zalunci wasu bayin Allahn ba, sai dai ubangiji yay wa bawansa sakayya kawai. idan mu ka ɗauki ɓangaren masu aikin asiri ga wani wanda bai ji ba bai gani ba saboda son zuciya da tsantsar zalunci. zamu ga a yayin da suka yi asiri sun yi nasara, sai dai ƙarfin adu'a kan karya wannan asirin na su komin tsayin shekarun da za'a ɗauka, yayin da wasu za su sami waraka suci gaba da rayuwar su ta yau da kullum, yayin da wasu kuma warakar zata zama ajalin su. sai dai fa abin da yake da akwai ko da asirin ya karye to bai zama tilas dole ba a san wanda yay wannan asirin har kuwa duniya ta naɗe, duk da cewa a yanzu ubangiji ya daina barin wannan ladan gabar, sanda za'a barka kayi ta yawo da hakkin mutane har ka mutu sai anje ƙiyama tukunna. a'a! a wannan rayuwar da muke ciki ta yanzu, tun a duniya Allah yake wulaƙanta mutum, rayuwa tayi kacakaca da shi, tayi masa ɗaurin goro, wataƙila ma ya faɗa tsananin wuyar da ta fi ta wanda ya jefa a ciki, har sai ma ubangiji ya so ka da rahmarsa sannan zai baka damar roƙon yafiyar wanda ka zalunta, idan kuwa aka yi rashin dace ubangiji bai baka damar fallasa kanka ba, balle har ka nemi yafiya, to lallai wata shari'ar sai dai a yi ta kuma a lahira. a lokacin da motar tata tayi parking a compound ɗin gidan, ta fito daga ciki riƙe da babban flask na abinci a cikin basket, ta jingina da jikin motar domin numfasawa, saboda yanayin nauyin cikin jikinta. Auwal ɗan me gadin gidan ya ƙaraso wajenta cikin sauri, bayan sun gaisa ya karɓi flask ɗin domin taimaka mata, bata hana shi ba saboda ita ma tana buƙatar ataimaka mata ɗin, duk da flask ɗin ba wai nauyi ne da shi ba, kawai dai ko ƙaƙa abu yake yana yi mata nauyi a yanzu. part ɗin Mum tana fara nufa, a parlo ta sameta tana kallon news da ake yi, ta zauna suka shiga gaisawa Mum na tambayarta yanayin jikin nata. a lokacin da Fillo ke kallon Hajiya Ramla tace,"Mum lafiya dai ko?". tayi tambayar duba da yanayin Mum ɗin da ta gani, fuskarta da damuwa sannan ga jikinta kamar a sanyaye. "babu komai Daughter, kawai yanayin garin ne na yau". tana faɗin hakan kuma sai ta ɗauki wayarta ta kira lambar Hajiya Madina, har kiran ya katse bata ɗauka ba. sai ta miƙe tana cewa da Fillo,"na bar ki anan ko zamu je tare?". "ina Mum?". "wajen Maaman ku. naga tun safe ban ji ɗuriyarta ba, ƙafana na ciwo ban sami damar leƙawa ɓangaren nata ba, ina ta kiran wayarta kuma bata ɗaga ba". Fillo tace,"ai ba mu jima da gama waya da ita ba Mum, ita ma ta kira ni ai". Hajiya Ramla ta sauke numfashi, tayi gaba yayin da Fillo ta bi bayanta. shigar su parlon Hajiya Madina kiran Turaki ya shigo wayar Fillo, tana ɗaga yace da ita. "Fulani Nah kin ƙarasa gidan?". "na je Jannaty, lafiya naji ka kamar a damuwa". "babu komai. yau ɗin ne kawai nake jinta duk babu daɗi, ina Maaman?". "yanzu ai na shigo ɓangaren nata, ban hau saman ba". "kowa a gidan yana lafiya?". "Jannaty wai...". "just answer me". "kowa lafiya lau, Mum ma muna tare da ita". ya sauke numfashin da ta jiyo har cikin dodon kunnenta. "ina kan hanya ne go slow ya tsare ni. amma insha'Allah yanzu babu jimawa zan ƙaraso gida". san da ta shiga ɗakin Hajiya Madina ta tarar da Hajiya Ramla na taɓa jikinta, a yayin da take yin magana da Nihal tana tambayarta,"kuma bata ce miki bata jin daɗi ba?". "a'a Mum, ba ma fa ta jima da kwamciyar ba ai, lafiyarta lau". "to masha'Allah, idan ta tashi ki ce ta kira ni a waya. zan je saboda baƙin Haɗeja da za su zo". "tom Mum". Hajiya Ramla ta fita, Fillo ta ƙaraso ciki ta zauna a gefen gadon da Hajiya Madina ke kwance tana bacci. ita ma tasa hannu ta taɓa ƙafar Maaman sai taji babu zafi kamar yanda kowa ke tunanin ko zazzaɓi ne ya sata yin baccin rana haka. "Allah yasa ba ciwon kai ba ne". Fillo ta faɗa tana cire mayafin jikinta ta ajiye, tare da naɗe ƙafarta ɗaya ta ɗora akan gadon gaba ɗaya. Nihal da ke kan kujera tana aikin project a system tace,"lafiyarta fa lau, ko 10minutes bata yi ba da kwanciya, tace idan kin zo ki tashe ta". "ta fita aiki ne yau?". "a'a haka kawai ta tashi da gyaran part ɗin Baffa yau, nace yau dai soyayya ake ji". Fillo tayi dariya tana faɗin,"amma dai kin tayata?". "ina zuwa ma ce tayi in bar mata ɓangaren miji ita ɗaya take so ta sami ladan". shiru ya gimla na kusan mintuna biyar, Fillo ta miƙe taje ta ɗauko basket ɗin abincin, a ƙasa ta zauna ta buɗe ta zuba iyakar wanda zata ci a plate, Nihal ta taso ta zo ta zauna su ka shiga ci a tare. "gaskiya yayi masifar daɗi, no wonder Maama tace ba zata ci komai ba sai kin kawo mata, bari na tasheta yasin tun zafin flask bai jiƙa shi ba". "no barta tayi baccinta please, abu da an kusa la'asar, lokacin sallah nayi za ki ga ta tashi". bayan wucewar mintuna goma hannayen Turaki su ka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, ƙafafuwansa suka shigo cikin ɗakin yayin da sanyin Ac ke ratsa shi. ƙwayar idonsa bata sauka akan kowa ba sai Maama da ke kwance kan gado tana bacci. A lokaci guda yaji jikinsa yayi wani irin sakayau tamkar an zare masa lakar jikinsa, abun da bai yi tsammani ba sai yaji yawun bakinsa ya bushe, Me ke shirin faruwa ne?. ya saki handle ƙofar da yake riƙe da shi, ya kasa ɗaga ƙafarsa yana jin wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa, wani irin abu mai nauyin gaske, yana jin yanayin bugawar zuciyarsa na sauyawa, yana jin faɗuwar gabansa na ƙaruwa. ya san da cewa don mutum yayi bacci ba wani abu ba ne, dan bacci wani abu ne da ɗan adam ke yinsa a kowanne dare, to amma ba zai iya cewa ga ranar da Maama tayi bacci ba da rana, iyakar tsayin rayuwarsa zai iya faɗin hakan, ko da ace kuwa tana cikin halin jinya ne, baccin rana ba ya daga cikin al'amarin rayuwarta. to amma yau ɗaya, rana guda, rana ta farko kawai sai ta kwanta irin haka?, ƙarfe ɗaya da rabi na rana, har tayi irin baccin da bata ji buɗewar ƙofar tasa ba, kuma a lokacin da ya san tana zama tayi lazimin sallar azahar?. kawai sai ya ji wani abu ya motsa a ƙasan zuciyarsa, yaji kamar rauni na shirin kama shi, sai dai kamar ko da yaushe a rayuwarsa, yayi ƙoƙarin tattaro dukkan nutsuwarsa da dauriyarsa tare da dakiyarsa, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe. "me ya sami Maama?". ya jefa tambayar ga Fillo da Nihal yana tsaye a gefe guda. "bacci take yi, aiki tayi ta gaji". "aiki!?, ina ma su aikin?". "part ɗin Baffa ne fa Hammah, ka san bata barin ƴan aiki su je can". "gajiya bata sakata baccin rana, tasha magungunanta?". "lafiyarta fa ƙalau Hammah, kawai muna zaune muna hira tace bari ta kwanta kafin ta gaban goshinta ta ƙaraso". ya shiga girgiza kansa, ƙafafunsa na ɗagawa da ƙyar, haka ɗaya Maama ba zata yi baccin rana ba, no matter what bata baccin rana, bai yarda da wannan baccin nata ba. "kar ka damu lafiyarta fa ƙalau, ban da yanayin ciwon kai da sai ka tashe ta". kunnuwan Turaki su ka tsinci muryar Fillo a cikin iskar ɗakin. ta karɓi ledojin da ke hannunsa tana ƙara faɗin,"Allah lafiyarta lau, amma idan kana ganin a tasheta ɗin to". "a ƙyaleta?". ya gyaɗa kansa kawai, sannan a hankali ya tafi zuwa gadon, da tafukan hannunsa guda biyu ya kama kan Maama ya gyara mata kwanciyar. ya zauna akan bedside drower yana kallon fuskarta, kamar tayi haske?, kamar kuma ta ƙara yin kyau?, sai yasa hannunsa a saman goshinta ya goge guntun gumin da yake ganin kamar idanuwansa na haska masa. wucewar minti ɗaya!, biyu, uku har zuwa biyar, zuciyarsa ta kasa samun natsuwa da baccinta, saboda haka sai ya kai hannunsa gefen filon, ya shiga dukan filon a hankali yana faɗin,"Maama, Maama, Maama". ya kira sunan sama da sau goma amma shiru bata buɗa idanunta ba. a yanda ya sani, duk tsananin baccin da Maamansa ke yi kiran suna ɗaya ne ya farkar da ita, balle ma ita bata da irin nauyin baccin nan, hasalima ko baccin take aka murɗa ƙofa aka shigo sai ta farka, ko kuma idan taji motsi. dan haka zai iya cewa bai san lokacin da ya miƙe daga kan drower ɗin ba. kuma maimakon zama a bakin gadon kamar yanda yayi niyya sai ya tsinci gwiwoyinsa da zubewa a ƙasa, kafin yaji wani nauyi ya ziyarci hannunsa, irin nauyin da sai da ƙyar ya iya ɗaga shi ya taɓata. "Maama". hannunsa ya sauka akan jikinta da yay sanyi, a yanzu da ya taɓata bai ga ta farka ba, haka bai ji ta motsa ba, sai yaji adadin faɗuwar gabansa ya ninku da kusan kaso tamanin da biyar. sai kawai ya tsinci kansa da shiga tashinta kamar ƙaramin yaro, babu abinda yake da buƙata a yanzu irin ta tashi, ta buɗe idonta, ta kalli cikin ƙwayar idonsa kamar yanda zai kalli tata, ta faɗa masa wannan maganar da tace zasu yi idan ya dawo, bai taɓa jin ya damu da baccinta ba irin yau, bai taɓa jin baccin wani ya tsorata shi ba irin yau, bai yarda da wannan baccin ba, bai yarda da shi ba sam. girgiza ƙafafunta kawai yake yi yana kiran,"Maama, Maama, Maama ki tashi na dawo, kin ce Papaya ta ƙare na taho miki da ita ga shi na siyo, ga takardar scaning ɗin jikokin naki ma na karɓo, su biyu ne kamar yanda kika gansu a mafarki. kuma mun yi magana da Baffan yace za'a buɗe makarantar islamiyar, idan ya so sai a haɗeta da boko, kuɗin da kika ce na kai gidan marayun na kai ga receipt ɗin, amma sun ce na faɗa miki akwai yara guda goma sha biyar da aka kwantar a asibiti, to sai naje asibitin na biya bill ɗin da ake buƙata, waɗan nan yaran ma da aka kai su sudan, sun kira ɗazu sun ce na faɗa miki result ɗinsu yayi kyau, gobe za su sauka a ƙasar nan, sun ce na faɗa miki suna sauka wurin ki za su fara zuwa, suna ta cewa ayi miki godiya su da iyayen su. gwandar a markaɗa ko yanka miki za'a yi?". gaba ɗaya a wani ruɗe yake maganar, kamar dai wanda ya susuce, ya juyo ya kalli Fullo da Nihal waɗanda ke tsaye a bayansa. "Nihal ɗauko wuƙa ki yanka mata gwandar". sai kuma yace da Fillo,"Halima taci faten?". a karo na farko da ya taɓa ambatar ainihin sunan Fillo. "a'a naga tana bacci shiyasa ban tasheta ba". "sauri ki zubo mata Halima, yanzu zan tasheta". kusan a tare Fullo da Nihal suka juya jiki duk a sanyaye, hannayen Fillo na karkarwa ta buɗe flask ɗinta zuba faten tsakin da yawa, kafin ta yunƙura ta miƙe daga duƙen da take Turaki yazo ya karɓa, karɓar tasa tayi daidai da shigowar Nihal daga ɗauko wuƙar, ta ɓara ƙwallon gwadar ta yi masa wata iriyar rabawa, cikin sauri ta isa ta ajiye plate ɗin akan table ɗin da Turaki ya ɗauko ya ajiye a gaban gadon. har yanzu baya jin mazaunansa za su iya zama akan wani abu, don haka ko a yanzu ma gwiwoyinsa ƙara zubewa suka a gabanta, kafin yasa hannu ya juyo da kwanciyartata saitinsa, ya kalli fuskarta, ya kalli murfin idonta da yake a rufe, sannan ya kai ɗaya hannunsa ya kamo tsintsiyar hannunta guda ɗaya ya riƙe, tare da kai ɗaya hannun nasa ƙasan hancinta. jijiya bata motsi!, haka ma numfashin baya fita!, sai ya ƙara maida hannunsa wuyanta, nan ma beat ɗin dake wurin ba ya harbawa. ya san akwai suma kuma ya san akwai mutuwa, kamar yanda ya san banbancin kowanne, sai dai ba ya jin zai iya ɗaukar abin da yake ganin gaskiya ya ɗora Maama a wannan matakin, ba zai iya ba, ba kuma ya jin zai iya. don haka sai ƙafafunsa duka biyun suka tankwashe, yayinda da dukkan hannayensa ke riƙe da nata, a sanda kuma ƙwayar idonsa ta kasa ƙiftawa akan fuskarta. "ba ki taɓa yin bacci me nauyi ba irin na yau Maama, ba ki taɓa ba. tun ina ƙarami ba kya iya baccin rana kawai saboda mu, balle ma har ki sami damar yin me nauyi, amma yau zan bar ki ki huta, ki yi baccinki yanda ya kamata, na san kin gaji ne, zan zauna tare da ke har sai kin farka". a lokacin da yay shiru da maganar, a lokacin yaji tarin ruwan hawaye sun cika ƙwayar idonsa, zubowa suke so suyi ya sani, amma ba zai ba su damar hakan ba har sai abun da yake gudu akan farin cikinsa ya tabbata. shigowar Hajiya Ramla ɗakin yasa shi juyawa ya dubeta, sai ya ganta gaba ɗaya a rikice, cikin irin rikicewar nan da bai taɓa ganinta aciki ba. "Madam, Maaman yara, kar muyi haka da ke, kar kiyi mana irin wannan baccin, tashi haka don haka don Allah Madam". zantukan da Hajiya Ramla ke yi kenan a sanda ta sami zama a gefen Hajiya Madina, sai ta ɗagota zuwa jikinta, sai taji gaba ɗaya jikinta ya saki, jikin Hajiya Madina ya zame daga nata ya koma makwancinsa. ƙafafun Fillo suka tsuguna a kusa da Turaki, ta dafa kafaɗunsa hannuwanta na rawa, sai taji ɗan cikinta ya motsa a lokacin da ya riƙo nata hannun, ya juyo ya kalleta, suka haɗa ido tana ganin abun da bata taɓa gani ba acikin idonsa, ruwan hawaye!, ruwan hawayen da su ka sanya zuciyarta bugawa. lokacin da Hajiya Ramla ta tabbatar da baccin Hajiya Madina ba na farkawa ba ne, lokacin tayi ƙarfin hali da dakiyar kallon Nihal, wacce ke tsaye ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi, idanuwanta duk biyu a waje. "Mum Maama bacci take yi ko me?, suma tayi?, zata farka?, ana ta tashinta taƙi ta tashi". "idan baka saba aiki ba kayi to duk jikinka sai ya mutu, ina tunanin gajiya ce tasata wannan baccin me nauyi, ba sai mun tasheta bamu barta ta huta sosai". sai ta juya ta kalli Turaki, ta ƙara juyowa ta kalli Nihal ta ce,"ina wayata?". "Mum gata nan a hannun ki ai". tsabar ruɗewa ta manta ma da wayar na hannunta, ta shiga contact ta danna kiran lambar Family Doctor ɗin su. yana ɗaga tace da shi,"don Allah ka iso gida yanzu". bayan ta ajiye wayar Nihal ta ce da ita,"Mum wa kika kira?". "Dr Ibrahim ne". sai a sannan Turaki ya ɗago ya kalli Mum, mene na buƙatar likita kuma a wannan lokacin?, idan ya zo me zai yi?. su ka haɗa ido da Mum ɗin, tace da shi,"da yake tace min tana ciwon kai ɗazu, gwara ya zo ya dubata wataƙila BP ɗin ne ya hau ba mu sani ba". ta fita a riki ce, tana sauka ƙasa taci karo da Sameer da Khaleel, sai suka tsaya kallon juna. "da ma ba ku fita ba?". Khaleel yace,"dawowa muka yi, lafiya Mum muka ganki a haka?". "a'a babu komai, ko zaku koma kuga idan Baffa ya dawo?". Sameer ya ce,"yanzu ya kira mu, yace ya kira wayoyin kowa bai samu ba". "to ku tsaya anan ku kira min shi a waya". ta faɗa tana juyawa ta koma saman, Khaleel ya bi bayanta da kallo zuciyarsa cike da nazari da zurfin tunani. a san da Dr Khamis ya ƙaraso, idanuwan kowa na kansa a lokacin da yake wasu dube-dube a fuskar Hajiya Madina, da kuma gwaje-gwajen da yake yi. ban da Turaki da idonsa ke kan Maama kawai, yana jin wani bala'in ruɗani na shigarsa. cikin ƴan mintuna kaɗan Dr Khamis ya gama bincikensa, a sannan ne kuma idanuwan Turaki su ka koma kan likitan, yana kallonsa ya matsa kusa da Mum da Khaleel, wanda yake tsaye cikin ƙarfin hali. ya san dai likitan bayani yake yiwa su Mum, domin yaga bakinsa na motsawa, laɓɓansa na motsawa da harufan da riga ya san ma'anar su. kuma cikin sakanni uku sai ga Hajiya Ramla ta dawo kusa da Hajiya Madina, ta kamo hannayenta ta riƙe acikin nata, kafin a hankali laɓɓanta su tale da furta kalmar,"innalillahi ra'inna ilaihi raji'un, gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma". furucin da ya haddasa motsawar zuciyar Turaki sannan ƙarfin bugunta ya ƙaru a lokaci ɗaya. idanuwansa suna kallo Mum ta ɗauki zani ta rufe Hajiya Madina da shi, ta rufeta har fuskarta, ta lulluɓeta da wannan zanin da ta ɗauko a jiya tace musu ta siyo shi ne saboda goyon jikanta. ba zai manta da wannan lulluɓin ba, ba zai manta da shi ba har a bada. sai kawai ya kifa fuskarsa akan ƙirjin gawar, hannunsa na dama kuma ya shige cikin sanyayyan nata hannun na dama. "Maama, Maama, don Allah ba yanzu ba Maama". yay maganar da wata karyayyar murya, a san da yay wannan furucin, a sannan ne hawayen da suka taru acikin idonsa suka sami nasarar gangarowa saman kumatunsa. idanuwansa suka runtse, hoton rayuwarsu na tsawon shekaru 27 na haska masa daki-daki, a lokaci ɗaya kuma duk wani sauti na muryarta na amsakuwa acikin kunnensa da cikin kansa, sautin muryar da ya tabbatar ba zai ƙara jinsa ba. ya riga ya sani, faɗar ubangiji ce kullu nafsin zaa’iƙatul maut, Allah ya faɗi hakan har sau biyu a littafinsa me girma, duk wani bawa mutuwa tana kansa, duk wani me rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, yaro ko yarinya, babba ko ƙarami, sabo ko tsoho. ya sani Mutuwa dole ce, ya san mutuwa akan kowa ta ke, ka aikata sharri ko akasin haka zaka mutu, kana kan aikata daidai ne ko akasin haka, baka san a wani hali za'a ɗauki ranka ba, za mu mutu a yau, ko gobe  ko jibi, ko anjima ko yanzu, sai dai dukkanin mu babu wanda yasan a wanne hali zata riske shi, kai dai bawa baka sani ba! baki sani ba! ya sani yin mutuwa ko ambatonta bai da daɗi, amma dole ne sai mun mutu, dole za mu koma ga wanda ya halicce mu, wajibi ne mu amsa kiran ubangijin mu mai son mu, mai ƙaunar mu, mai jiran tuban mu a ko yaushe, dole ne zamu bar duniyar da aka ara mana, haka dole zamu tafi mu bar duk abin da muke so, haka dole zamu kwanta a ƙabari. kana tsaka da jin daɗin rayuwa mutuwa na iya zuwar maka, wani tazo mishi fuj’an, wani ta zo mishi idan yay fama da rashin lafiya, wani tari kawai zai yi, wani atishawa kawai zai yi, kuma da zarar ya furta Alhmadulillah sai Kaga a wannan lokacin an ɗauki ransa, wani yana sallah za'a zare masa rai, wani daga bacci shikenan za'a zare ran, sai dai ya farka ya gansa a ƙabari, gidan da yake na gaskiya, gidan kowa. duk irin son mu da duniya wallahil azim sai mun barta, duk irin so da ƙaunar da muke yiwa juna wallahil azim mutuwa sai ta raba mu, Ya Qadeer kai mana kyakkyawan ƙarshe, Ya Rabbi kasa mu dace duniya da lahira Ya'ilahi! Ya Hayyu Ya ƙayyum, kasa mu mutu muna matsayin mutanen kirki, ba waɗanda zamu mutu duniya da mutanen cikinta na tirr da mu ba, ya Rahmanu kasa kar mu mutu da hakkin kowanne bawa akan mu, don mun san cewa baka yafe hakkin wani akan wani, ya jama'atul musulim mu yafi juna!, mu yafewa junan mu!, kar mu dinga ƙullar junanmu domin ba mu san lokacin da zamu yi tafiya me gaba ɗaya ba. "ta mutu". Khalil yay ƙarfin halin furtawa sauran ƴan uwansa da kowannen su ke tsaye yana so ya fahimci abin da ke faruwa. "Kamar ya ya wai? Mecece mutuwa kuma?". Sameer yay tambayar a rikice. "da ma haka ake mutuwar?, ɗa zu fa muka gama hira da ita ko awa ɗaya ba'a yi ba, haba this is insane, wallahi Dr ɗin nan ƙarya yake, ya za'ai ma Maama ta mutu, me tayi?, laifin me ta aikata?, don Allah Mum a kira wani likitan ya dubata, don Allah a kira wani likitan ya zo ya tasheta". idan ace ba kallon fuskar Nihal suke yi ba, za su rantse da Allah cewa ba ita tayi wannan maganar ba, don kwatakwata muryar ba tayi kama da tata ba, ta fito ne cikin wani amon sauti na ƙololuwar tashin hankali, tana rawa tamkar iska na kaɗata. haka rayuwar take dama, hanya ɗaya ce da ita, ko kabi tafarkin gaskiya ko ka kauce duk dai ƙarshe waje guda kowa yake nufa, alkhairi ko sharrin da kayi kafin ka ƙarasa, shi zai zama shimfiɗa mai kyau ko mai muni a yayin da ka isa, sai dai fatan dacewa kawai. "ka kira Baffan ku ka sanar da shi, sai ka kira min Samha da Zaytun, amma ban ce ka faɗa musu ba". Mum tayi furucin ga Khaleel, wanda yake tsaye har yanzu hawaye sun gaza sauko masa. a wannan lokacin kuwa Nihal na kan gawar Hajiya Madina, tana girgizata akan sai ta tashi, tana roƙon su akan su kira likita me hankali ya tashi mahaifiyarta, ai hirar da suka kwana jiya su na yi baya nufin wasiyya ta bar mata, ita dai azo a tashi Maama, don tace mata a ƙarshen watan nan zata fara yi mata order ɗin kayan kitchen ɗinta. a wannan lokacin kuma Turaki ya iya ɗago da kansa, ya kalli Nihal ɗin sannan ya kuma kallon fuskar gawar, sannan ya ƙara kallon zanin da aka rufe gawar hannun Fullo ke damƙe da shi, sannan ya kai ƙwayar idonsa kan Mum da ke zaune kanta a ƙasa, hawaye na saukowa suna zuba akan kayan da ke jikinta, sannan ya kalli Sameer da ke duƙe ya rufe fuskarsa da dukkan tafukan hannunsa da alama kukansa yake so ya tsayar tukunna ya ɗago ya ƙaryata mutuwar, sannan ya kalli Khalil wanda ke jingine a jikin wadrobe waya riƙe a hannunsa ya ƙurawa gawar ido, gashin idonsa ba ya ko ƙiftawa. a wannan lokacin ne kuma hankalinsa ya fara gaya masa wataƙila zai sauya ma'anar rabuwa ta mutuwa a yau, don baya tunanin akwai abin da zai raba shi da gawar nan da yake riƙe da hannunta, Maamansa ba, babu me raba shi da ita. *BAYAN AWA BIYU.* a cikin wannan awannin, labarin rasuwar Hajiya Madina ya karaɗe cikin garin gombe, da sauran ƴan'uwa da suke na kusa da na nesa. lokaci guda tarin al'umma suka shiga ɓulɓulowa su na sauka a gidan Alƙali Dikko domin yin ta'aziyya, mutuwar da ta taɓa manya da ƙanan yara. cikin gidan ya ɗauki shiru, a zazzaune ake wasu na kukan fili yayin da wasu ke kukan zuciya, domin tabbas anyi rashi, an yi rashin mace mai tsanani son mutane da kyautata musu, mai kirki da sauƙin kai, macen da ke da tsananin kyautatawa marayu, macen da ba'a faɗa da ita acikin mutane in har ba ƴaƴanta aka taɓa mata ba, macen da a tsawon rayuwarta babu wanda ya taɓa buɗa baki yayi kuka da ita, ya kuma ya faɗi aibunta. a wannan lokaci ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawansa, shi kaɗai ya san adadin alhinin da ke cikin zuciyoyin ahalin gidan Alƙali Dikko, musamman yaran, waɗanda suka ruɗe da koke-koke, banda Samha da ke ta aikin suma tana farfaɗowa ta ƙara komawa. "an gama yi mata wankan, ku faɗa musu za'a shigo da gawar ciki su yi mata adu'a". "ina Hajiya Ramlan take?". "yanzu ta tashi, Samha ce jini ya yanke mata, ana tunanin ko ɓari tayi". a lokacin wani tsoho ya leƙo parlon yace,"to ina yaran su ke ne?". "Baba Musa gasu nan fa, ku shigo da ita ɗin". ya juya fuskarsa daga waje yana kallon mutanen dake tsaye yace,"sai kun ɗago makarar da kyau fa, yawwa kai ɗan karkata ta can". mutanen maza su huɗu suka shigo parlon da gawar, da yake acan part ɗin nata wasu Kakanninta mata da su Boɗejo suka yi mata wanka. su ka ƙarasa da gawar suka ajiyeta a tsakiyar yaran da ke zaune a ƙasan carpet, wacca Zaytuna ce kawai babu sai Samha da aka yi asibiti da ita yanzu. Baffa ya ƙaraso wajen ya zauna shima, zaman nasa babu wuya kira ya shigo wayarsa, daga can ɓangaren Zaytuna da ke ta kuka tace,"Baffa don Allah kar akaita sai na zo, ya tafi ya nema mana ticket yanzu zamu taso Baffa". "Zaytun kiyi haƙuri kinji ko, ki tayi mata adu'a kawai, idan aka ce za'a jira ku lokaci zai ƙure, kinga magariba na gabatowa". bayan gama wayar ya ɗaga kai yana cewa da Yayar Hajiya Madina,"Asiya kirawo Ramla don Allah, tazo su yi sallamar ƙarshe". "Baffa don Allah ku bar mana ita a haka ba sai an kaita wani wajen ba, mu zauna da ita a haka don Allah". Yayan Hajiya Madina Baba Nafi'u yace,"tun ɗa zu kake ta surutai Sameer, ya isa haka, kai musulmi ne ya kamata ka yarda da wannan mutuwar, batun a bar muku ita babu shi domin binne gawa wajibi ne". "don Allah Baba ku bar ta ko zuwa da safe ne, ƙila fa baccin ne yay mata nauyi da yawa, ko kuma shi likitan ne bai bincika da kyau ba, amma ɗazu mu ka gama hira da ita wallahi, wallahi lafiyarta ƙalau bacci kawai tayi tace idan Saamirawo(sirika Fillo) tazo to a tasheta". Nihal ke maganar duk a gigice. Baba Nafi'u ya ƙara cewa,"ku yi haƙuri kin ji Nihal, duk wani abu da ya ke faruwa tsarin ubangiji ne, namu tawwakali ne da addu'a, don haka ku yiwa mahaifiyarku adu'a". Baffa ya numfasa a hankali ya shiga kiran sunan yaran nasa da sirikan nasa ɗaya bayan ɗaya. "Khalil, Samir, Nihal, Halima, Ilham". sannan ya kalli Turaki daga ƙarshe yace,"Muhammad ku daure zuciyoyin ku, kuyi tawwakali ga Allah, wannan ita ce mutuwar, haka take, haka kowa yake haƙura da ita, haka take riskar kowanne bawa ba sai an shirya mata ba, mu ma nan duk jiranta muke yi. yanzu lokaci na tafiya, mutane na can a waje su na jiran a fita da ita, na san abin da kowannenku yake ji, na san raɗaɗin da zuciyarku ke yi muku. ku yi mata adu'a, wannan kukan da ku ke yi da musawar da ku ke yi ba gata bane a wurinta, zallar soyayyar da za ku nuna mata shi ne kuyi mata adu'a, wannan jinkirin kaita ɗin da ake ba alkhairi bane agareta". Maganar ta Baffa ta doki kunnuwan kowannen su, furucin da yay akan soyayya, sai kawai suka ji su na shuɗawa zuwa duniyar baya, wani lokaci me tsayi da ya shuɗe, kamar haka ne, kamar wannan lokacin su na zaune da ita take faɗa musu... _"ku nuna min soyayyar ku ko bayan raina Ƴaƴana, ina nufin kar kuyi kuka da rashina, adu'a za ku yawaita yi min"._ Turaki ya matsa kusa da makarar, Baffa ya kalle shi, zuwa yanzu idanuwansa ƙamas babu alamun danshi na hawaye, haka fuskarsa tayi fayau babu wani abu da zaka tsinta a ciki illa tsananin tashin hankalin da yake ciki. haka shi ma Khaleel, wanda tun ɗa zu sai ayanzu da ya ɗora hannunsa akan makarar sannan hawaye yay nasarar gangaro masa, sai dai yay saurin saka gefen rigarsa ya goge. hannun Turaki ya shiga cikin maƙarar, ya tallafo kan gawar, yasa ɗaya hannun ya yaye linkafanin ya tsayar da shi daidai wuyanta, inda fuskarta kawai suke iya gani, fuskar da suke gani tamkar zata yi musu magana. muryarsa ta fito cikin sanyi, ya shiga jero tarin adu'oin da ya san su na cikin kansa, yi yake yi yana ƙara maimaitawa, har tsawon lokacin da bai san ya ɗauka ba me tsayi, har sai da Baba Nafi'u yasa hannu ya dafa kafaɗarsa yace,"ya isa haka Turaki". shi kaɗai ne ya iya yi masa magana domin ko Baffa ba zai iya ba a wannan lokacin, shi kansa ya kifa kansa yana hawaye kamar yanda Hajiya Ramla da ƴaƴan suke yi. "ke kam taki tayi kyau Madina, tabbas ke ɗin ƴar aljannah ce, ki yafe min Madina, don Allah don Annabi ki yafe min". muryar Boɗejo suka ji ta amsa acikin ɗakin, a sanda take isowa wajen, kuma kukan da yaci ƙarfin ya hanata ƙarasa abun da zata faɗa. har aka yi sallar jana'iza Turaki da Khalil basa cikin hayyacinsu sosai, a tsaye kawai suke, hannayensu sarƙe dana juna, yayin da idanunsu ke kafe akan makarar da ke ɗauke da gawar dake gabansu. da ga bayan su kuma tarin ɗumbin jama'ar da ba zasu ƙirgu ba ne, don jama'ar gari yara da manya sun halarci jana'izar. ƙarfe shida na yamma aka kai Hajiya Madina ƙabarinta, inda ɗumin jama'ar da suka fi ƙarfin ƙirga suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya. acikin shirun da ya ratsa maƙabarta, babu sautin muryar da kake ji na tashi sai na manyan mutanen dake cewa. "yauwa bismillah ku biyo ta nan". "yauwa jama'a a ɗan gyara". "ku riƙeta sosai". "to ku miƙota nan". "yauwa to ku ajiyeta nan, masha'Allahu!". mutanen da suka ratso ɗauke da gawar ta cikin tarin ƙaburburan dake jere a cikin maƙabartar. suka ajiye makarar a bakin ƙasar da aka tone, kusa da ramin da yake gida matabacci, kuma gida na ƙarshe ga kowanne bawa, gidan da ke jiran duk wani mai rai, gidan da yake iri ɗaya da na me kuɗi da na talaka. Turaki da Khalil na tsaye kusa da juna, tsayinsu kusan ɗaya, zuciyar kowanne na tunani kala-kala a game da mutuwar da ta riske su a yau. abun da basu taɓa zato ba, abun ba su taɓa kawo shi nan kusa ba. "Bismillah". Muryar limamin masallacin unguwar ta janyo Turaki da Khalil daga dogon tunanin da ƙwaƙwalwar su ta faɗa, suka juyo a tare suka kalle shi, sannan suka kalli gawar dake gabansu, wadda aka fito da ita daga cikin makara, a lokaci ɗaya suka tsinci kansu da tarin ruwan hawayen da ya bar idon su tun ɗazu. a hankali Turaki ya durƙusa daidai kan gawar ya tallafo kan, Khalil da Samir da Baffa da Wan Hajiya Madina da Liman suka tallafi sauran jikin, sannan suka haɗu wajen zura gawar a cikin ramin ƙabarin. lokacin da suka zura gawar acikin rabin ƙabarin, zuciyar kowannen bawa dake wurin ta matse da ƙarfin imanin dake ƙaruwar a ƙirjinsa, tabbas duk wanda bai yarda da Ubangiji ba yayi asara, asara mai girma kuwa, haka duk wanda bai tuba ba kafin mutuwa tabbas yay babbar asara. idanuwan Turaki suka tsaya cak akan farin likkafanin, yana kallon yacca ake mayar da ƙasar da aka haƙe ana rufe gawar gawar da ke ciki, har sai da hasken likƙafinin ya dusashe, yayin da tukwane da tudun jar ƙasa suka shafe shi gaba ɗaya. daga wannan lokacin kuma ƙwaƙwalwarsa bata ƙara wani tunani ba, komai da ke cikin kansa ya zame yabar shi. abin da zai ce yana iya jiyowa a duniyar da yake jinsa kamar ba'a cikinta ba, tarin adu'oin dake fitowa daga bakin liman, kafin a hankali kuma ya fara jin sautin wani abu na shiga kunnensa, sautin takun ƙafafu su na juyawa su na barin wajen. sai ya kalli nasa ƙafafun, sai yake ganin tamkar ba zai iya ɗaga su ba, tamkar sun ƙame anan kenan har sanda tasa mutuwar zata zo ta riske shi. yaji an riƙo hannunsa, da ƙyar ya iya ɗauke idonsa akan ƙabarin, ya juya ya kalli Baffa da Khalil, kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali ya fara tafiya da baya, a haka ya dinƙa tafiya da baya har ya bar cikin maƙwabartar, yana tafiya yana barin Hajiya Madina, yana kusantar gidan da zai koma a yau rana ta farko ya riske bata cikinsa, rana ta farko da zai koma bai ji muryarta ba na kiransa da wannan sunan da ita kaɗai ta raɗa masa, kuma ita ɗaya take kiransa da shi, Me Babban Suna!. yaji wani uban gumi ya keto masa, ya wanke masa dukkan ilahirin jikinsa, a hankali kuma ƙwaƙwalwarsa ta karanto masa kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. shikenan sun yi tazara, tazarar da ba zasu ƙara kusantar junansu ba. a lokacin da suka koma gida, tsakanin Khaleel da Turaki sai aka rasa wanda ya riga wani shiga ɗakin Hajiya Madina, an dai gansu sun shigo sun tsallake tarin mutanen dake zazzaune. a cikin ɗakin na Hajiya Madina, Khalil na zaune a ƙasa, idonsa na manne akan gadon inda tayi baccin ƙarshe a duniyarta, yau rana ta farko da ya shigo ɗakin bai ganta ba kuma ko da ya zauna zaman jiranta ba zata shigo ba, shikenan ta tafi tafiya ta har abada, sun zama marayu, yanzu ba su da uwa, wannan jigon na jin daɗin duniya. a hankali yaji hawaye na sauka akan kumtunsa, masu ɗumi da yawan da yaji kamar an buɗe bakin famfo, kukan da bai yi ba tun a ɗazu shi ya taho a yanzu, kawai sai ya ajiye dukkan dauriyarsa, yay ƙasa da kansa, ya runtse idonsa da yake ganin hoton mahaifiyar tasa na haska masa, don haka saiya shiga rero kuka babu ƙaƙƙautawa, kuka tamkar ƙaramin yaro. a wannan lokacin kuwa Turaki ya kifa kansa akan gadon, ƙamshin Maamansa na fitowa daga kan gadon na ziyartar hancinsa, yayin da yake damƙe da wannan ƙaton zanin da take cewa zanin goyon jikanta ne. _"kwana ashirin da biyu ya rage Edd ɗin nata ya cika ko?, to Allah ya raba su lafiya. kaga Me Babban suna waɗan su gadaje na jarirai na gani da suka fi wanda na siyo kyau, mu sauya shi ko?"._ maganartata ta haska acikin kansa, shekaran jiya suka raba rana su na hira da ita, kuma yawancin hirar duk akan jikokin da taƙe ta burin ganin zuwan su ne, har daga ƙarshe ma take ce masa. _"to ni ina ta lissafina ma, wa ya sani ko ba lallai ba ne na kai wannan lokacin, Allah dai ya san adadin shekarun da ya ɗiba mana a rayuwa, ni dai idan na tafi ku yafe ni Me Babban Suna ko da nayi muku laifi bisa kuskure"._ sai kawai yaji ya rasa dukkan dauriyarsa, ya manta shekarunsa, yana tunawa cewar shi fa ɗan Maamansa ne, kuma Maaman ta rasu a yau, bai san lokacin da wani matsanancin kuka ya kubce masa ba, ya shiga rero shi tamkar yaro sai dai gaba ɗaya babu sauti, illa tarin ruwan hawayensa da ke sauka su na jiƙa bedsheet ɗin. har aka tura ƙofar ɗakin aka shigo tsakanin Turaki da Khalil babu wanda ya sani balle ya ɗago. Fillo ta ƙarasa ta zauna akan gadon, tana zama kuma Turaki ya ɗago kansa ya ɗora akan ƙafafunta, ya damƙe cinyoyinta yana wani irin girgiza. sai taji sabon kuka yazo mata, tunawa da tayi Nihal na can an rirriƙeta sai surutai take yi. saboda haka sai ta nutsa yatsunta acikin kansa tana motsa yatsun. *BAYAN SATI BIYU.* [9/7, 03:10] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *60* *Jarabawa daga Mahaliccin mu.* Rayuwa tana cike da nasara da kuma faɗuwa, kuma akwai lokutan da gwaje-gwajen da ake yi mana kamar ba za su ƙare ba. A cikin Alkur’ani me girma, akwai ayoyi da dama da Allah ya yi magana a kan hanyoyi daban-daban da za a gwada mu, amma kuma ya ba mu ƙunshin kulawa da zai taimaka mana mu bibiyi waɗannan lokutan masu wahala a gare mu. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:“Babu wata musiba da za ta samu musulmi face Allah ya kankare masa wani abu daga cikin zunuban shi, ko da kuwa tsinuwar ƙaya ce”. (Bukhari Wa Muslim). haƙiƙa jarabawa ba azaba ba ce daga Allah, tana daga cikin rahamarsa marar iyaka. Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, babu makawa kowannen mu yana fuskantar jarabawa a rayuwarsa. Rayuwa ba gadon wardi bane ga kowa, Akwai mutanen da ke fama da talauci, akwai masu fama da lafiyarsu, sannan akwai masu fama da danginsu, akwai masu fama da mutuwa a jere a jere. Jarabawar ubangiji ta bambanta ga ɗaiɗaikun mutane daban-daban, an yi su ne bisa la'akari da irin ƙarfinmu da rauninmu. Abubuwan da suka zama kamar gwaji a gare ni, wataƙila ba za su dame ku ba, nima akasin hakan. tambayar gama gari da kowa ke yi a lokacin da ya shiga wani hali shi ne; me ya sa Allah ya sa na shiga cikin wannan halin? Me ya sa ba zan iya zama mai farin ciki a ko yaushe ba?, Menene na yi don cancantar wannan jarabawar? Me yasa Allah ya jarraba ni?. kuma rashin sanin amsar waɗan nan tambayoyi wani lokacin yana iya nisanta mutum daga imaninsa. jarrabawa na iya haifar da mummunan tunani mai tayar da hankali wajen mutum ya aikata saɓo, kamar faɗin Allah ba ya so na!. ko ma mafi muni mutum yace Allah ba ya yi mini adalci(astagfrullah). Amma Allah shi ne Al-Adl, Mai adalci, kuma shi ne Ar-Rahman, Mai jin ƙai, wanda ba ya ya nufin cutarwa ga bayinsa, face yana son alheri a gare mu. Akwai hikima a yanayin da ya ke sa mu a ciki, duk abin da muke buƙata mu yi shi ne haƙuri. Akwai dalilai da yawa a cikin Alqur’ani da hadisi da suke taimaka mana wajen amsa tambayar dalilin da ya sa ake jarraba mu. An halicce mu ne domin mu bautawa Allah, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ake jarabtar mu. tabbas an halicce mu ne domin mu bautawa Allah, kuma dukkanmu mun yi alƙawarin yin haka kafin a aiko mu a duniyar. Jarabawa hanya ce a gare mu don cika wannan alƙawarin. jarrabawa ita ce hanyar da Allah ya ke bambanta mu, domin tana taimakawa wajen bayyanar da imani da rashin imani. Allah yana jarrabar mu, ya tsarkakemu ya kuma wanke mana zunubai. jarabawa gwaji ce ta maye gurbin wani mummunan bala'in, tabbas da munsan musibun da Allah yake kare mu, da ba za mu taɓa rasa sallah ba, kuma ba za mu taɓa son ɗauke goshin mu daga sujjada ba. Gwaje-gwajen da ke ɓata mana rai na iya zama nau'i na kariya daga wani abu mafi muni da wataƙila ya same mu. Allah yana so ya tsarkake mu, daga soyayyarsa da rahamarsa, domin mu samu ba Aljanna kaɗai ba, har ma da mafi girman darajar Annabawa da salihai. Gwaje-gwaje su na fallasa kurakuran mu da kasawarmu, kuma sanin hakan yana ba mu damar mai da hankali da himma wajen gyara waɗannan ɓangarori na halayenmu. Allah yana jarrabar wanda yake so. Annabi(SAW) yana cewa: "Duk lokacin da Allah ya nufi mutum da alheri, sai ya sanya shi cikin tsanani".[Bukhari]. me yasa?, domin idan bawan ya amsa jarabawarsa da haƙuri, da gamsuwa da hukuncin ubangiji, hakan yana kusantar da bawa zuwa ga Allah, Kuma Allah yana son masu haƙuri. Ibn Al-Qayyim (rahimahullah) ya ce idan aka yi mana jarrabawa, muna fuskantar zaɓi guda biyu; muyi haƙuri ba rashin haƙuri ba. muke sauraren Alqur'ani da yawaita ambaton Allah saboda wadatar zuci, domin karanta alƙur'ani yana ba da wadar zuciya, addu'a don neman taimakon Allah, da ƙarfinsa, da samun sauƙi daga jarrabawa. mu tunatar da kanmu jarrabawar da Annabawa suka yi, sun ba mu kyawawan misalai na juriya. mu tuna cewa kowanne mutum guda ana gwada shi ta hanyoyi daban-daban. mu tuna babu wani abu a cikin wannan rayuwar da ke dawwama, don haka jarrabawar za ta ƙare insha Allah. domin ko acikin alƙur'ani Allah yace,"Lallai ne tare da kowane wahala akwai sauƙi". ubangiji ba ya ɗaurawa wani rai face abin da zai iya ɗauka, Allah ya amince da mu, don haka mu ma muna buƙatar mu amince da iyawarmu ta cin jarabawa. Allah yasa mu da ce!. ƙarfe goma na safe a lokacin, Ilham ta fito daga ɓangarenta tare da wata yarinya da ba zata wuce shekara 8 ba. yarinyar ƙanwar Fulani Azima ce, aka bata ita kafin akaita makaranta, kasancewa yarinyar ta gama primary a halin yanzu. yarinyar na riƙe ne da jakar Ilham, tabi bayanta zuwa baƙar motar da taga ta shiga, sabuwar motar da me martaba ya bata kyautarta. a san da suka iso bakin gate domin fita, a sannan ne Fillo ke baro wajen Baba Me gadi da turtsetsen cikinta, da lokacin haihuwarsa kawai ake jira. Ilham ta zuge glass su na gaisawa da Fillo, da siririyar dariya a fuskarta tace da ita,"kin ga kuwa yacca kika koma?, Allah each and every day cikin nan kumbura ki yake ƙara yi". Fillo na kallonta tace,"ban da sharri dai". "Allah babu zancen sharri, jiya da muka ci dinner ba ki kumbura haka ba". Fillo tayi murmushi ta ce,"in ace ana mayar da cikin jikin wani ai ke zan mayarwa, ke ma ki ɗanɗana, ko da yake kwana nawa ne Allah na tuba, ina daga balcony zan ke hango ki a field kina aikin patrol". Ilham tayi dariya sosai tare da cewa,"Allah dai ya raba lafiya, ni ban ma fidda ran ba za ki haihu ba a yau". sai kuma ta nunfasa ta ce,"zan je gida ne, an yi min waya jikin Mami ya ƙara tashi". jikin Fillo yay sanyi tana me tunawa da halin da suka riski Fulani Azima a shekaranjiya da suka je dubata. cikin sanyin murya tace,"Allah ubangiji ya bata lafiya, ko in je in shiryo mu tafi tare?". "a'a ke da kike fama da kan ki, na faɗa miki bana fidda ran ba za ki haihu ba a yau, ƙila ma sai dai ai min waya ace Baby ya sauka. ɗa zu da asuba ai ina tayi miki dariya ta window". Fillo ma tayi dariyar ta ce,"hmmm aikin mijinki ne, haka kawai duk ya jigatar da ni da safa da marwa, ke kinji yanda ƙafafuna ke ciwo kuwa. ai ana kaiwa gobe sai dai kuga na kai kaina asibiti sun yanka ni sun ciro muku yaran ku". "da kanki ma za ki haihu insha'Allah, bari na tafi sai na dawo". "to a dawo lafiya, ki yiwa Mamin sannu don Allah". motar Ilham ta bar compound ɗin gidan, ita kuma Fillo ta shige part ɗin ta. a ɗaki ta sami Turaki zaune yana rubutu a takarda, tun safe yake aikin rubuce rubucen office, tayi wurgi da hijab ɗin jikinta akan gado, kafin ta nemi waje ta zauna ta miƙe ƙafafu. "Jannaty please come and massage my legs, Allah ciwo suke min sosai". ya ɗago ya ɗora idanuwansa akanta, matuƙar tausayinta ya kama shi, in ace yana da ikon da zai fito mata da Babies ɗin nan babu abin da zai yi masa shamaki da hakan, ya ƙagu ta haihu haka ko don ta huta. ya tattara takardun a gefe tukunna ya taso, kafin ya zauna a gabanta ta dakatar da shi da faɗin,"sorry ba ni riyon kayan su Maama". ya ce,"me kuma za kiyi da shi?". tayi masa wani kallo kafin tace,"kaji min mutum, me ake yi da gyara?, yau tun tashina ban gyara musu ba". sai yay zamansa kawai, ta ɓata rai tana faɗin,"zan yi maka kuka". ta faɗa a shagwaɓe. ya ɗago ido ya kalleta, sarai ya san zata aikata hakan, don haka ya miƙe yaje ya ɗauko ƙaton riyon da ke ɗauke da uban kayan Babies a ciki, ya ajiye zai zauna ta ƙara dakatar da shi. "diary ɗi na". ya rufe ido tare da karyar da kai, zai yi magana tayi kalar tausayi tana haɗa hannayenta ta ce,"yi haƙuri Baban Ƴan biyu, ai don Allah nace". sai da ya lakuce mata kumatu kafin ya fita ya bar ɗakinsa zuwa nata ɗakin, san da ya dawo tana waya da Boɗejo wacca ta kira tana tambayar lafiyar jikin nata. ya zauna kawai ya shiga matsa mata ƙafafun, yana tsokanarta da lukutar gombe, bayan sun gama wayar da Boɗejo ta harare shi tare da fizgar diary ɗin tace,"ka duba min sirrina ko?". "oho ke kika sani, ni me zan duba acikin diary ɗin da ake ɓoyewa kamar ana ƙulla munafurci a cikinsa, to ta ina ma zan iya gane watsaltsalun rubutun lukutar Gombe?, rubutun da ba iyawa aka yi ba". dariya tasa Fillo dakatawa daga rubutun data fara,"oho dai duk abin mutum ba zai ga me ke ciki ba, ah tou! sirinmu ne ni da ƴaƴana" "sirri ko munafurci?, yara tun basu zo duniya ba an fara koya musu hali mara kyau, ni dai gaskiya nake faɗa miki ki sauya hali, wannan ba halin zama mother ba ne". ta ƙara yin dariya,"magana ce bata isheka ba sarkin ƴan sa ido, sirrin uwa da ƴaƴa ne dai ba zaka gani ba". ta faɗa tana yi masa gwalo, sai ya sakar mata ƙafa suka shiga kokawa akan sai ya karɓi diary ɗin, ta ƙwalla ƙara babu shiri ya ƙyaleta yana aikin zaro ido da jera mata tambayoyi a hargitse. "menene ya faru Angel?, na bige miki wani wajen ne?". ta kashe masa ido ɗaya da cewa,"kasan idan baka daina takura min ba zan kaiwa Ilham jinginar ka, ka kwana dubu saba'in baka ganni ba". "Allah ya baki haƙuri yallaɓiya ranki shi daɗe me girma uwar gida, da ki hora ni da rashin ganinki ai gwara ki zane min ɗuwawu na kasa zama, rashin ganinki ai azaba ne a gare ni". "idan na mutu fa?". sai ya ɗago yana kallon fuskarta da ta ƙara kyau yace,"ban hana ki yi min zancen mutuwa akan ki ba". "Allah ya baka haƙuri ranka ya daɗe". ta faɗa da murmushi a fuskarta. bayan ta gama gyaran kayan Babies ɗin take ba shi labarin irin satar kayan da akayi ranar zaman sadaƙar bakwai ɗin Hajiya Madina. "Daddyn Maama ka san me?, ina sabon less ɗin da na ɗauki zaninsa nace za'a ɗinkawa little Maama riga da shi?, to wallahi har da shi aka ɗauke, daga in ɗauko in ajiye kan gadon Mum in shiga toilet, ai kuwa na jera Allah ya isa babu adadi, saboda les ɗin nan Maama na sonsa". yace,"Allah ya kyauta, rashin tsoron Allah ne duk yake saka sata a gidan mutuwa, Allah ya shirya masu yi kawai". ta amsa da amin kafin ya kamata ta yunƙura su miƙe tare, toilet suka shiga domin yin wanka, acikin banɗakin sai da aka ɓata tsawon awa guda ana shan soyayya, sannan suka fito suna dariya, ita tana faɗin idan ya ɗauketa a yanda take yanzu ƙasusuwansa duk sai sun ɓalle, yayin da shi kuma ke faɗin ya sani, hannun lukutar gombe tsaf zai ɓalla shi ya ɓalle gaba ɗayansa.. kamar kullum yauma suka shirya kansu, ita ta saka wata ƙatuwar bubu da ta ɗauka acikin kayan Maama, kuma rigar sai tayi mata kyau sosai, saboda girman cikin jikinta sai awon yayi daidai da ita. "amma dai ba zaka jima ba ko?". amon muryarta ya fito a lokacin da take ɓalle masa maɓallin rigarsa. ya ce,"No yanzu zan dawo babu jimawa, takardun nan kawai zan kaiwa Khaleel, don't be lonely, am always with you, ina cikin nan". ya faɗa yana pointing saitin zuciyarta. tayi wani kalar murmushi tana kamo fuskarsa cikin tafukan hannunta biyu ta ce,"ina sonka mijina, ina ƙaunarka". "ni ma ina yi miki tsananin so matata, Allah yayi miki albarka, yasa ki haihu da ranki da lafiyarki". "amin amin Daddyn little Maama". furuncin nata ya saka shi yin murmushi me faɗi, tare da duƙawa ya ɗage rigar jikinta ya yiwa cikin kiss, sannan ya ɗago suka yi kissing juna. da ƙyar ya iya sakinta yaje yana tattara takardun cikin sauri, ita kuma tana bashi labarin cewa,"Jannaty ka san me?". ba tare da ya juyo ba yace,"ban san may ba sai dai june". murmushin tayi sannan yace,"to ka san june?, tunda nake a rayuwarta ban taɓa hango kaina a matsayin uwa ba, ban taɓa tunanin zan ɗauki ciki ba balle har akai lokacin da zan haife shi". sai tayi shiru, yace,"ehen ina jinki lukutar Gombe". murmushi ya kasa ɗaukewa a saman fuskarta, tana kallon bayansa ta ƙara cewa,"sai ga shi Allah ya ƙadarta min ganin samun cikin, har zuwa watan haihuwarsa, zan haife ƴaƴa biyun da nagartaccen mijina ya bani su, na ƙagu in haife su Jannaty, ina tsananin son su fiye da kaina". cikin sigar zolaya yace,"har ni kin fi son su akaina?". ta ɗan taɓe baki tana kallonsa, da irin wasan da ke tsakanin mata da miji tace,"waye kai?". ya ƙaraso ya zauna kusa da ita ya mintsinin leɓenta, ya ɗora hannunsa a saman nata dake kan cikin. "yau kin ji sun juya?". ta ɗaga masa rigar tana faɗin,"kalla fa yanda suke ta ƙiriniya, duk sai duka suke kai min ta ko'ina, suma ai sun gaji da zaman". Turaki bai iya cewa komai ba illa shiru da yayi yana ta kallon cikin dake motsi, yana jinjinawa girman ƙudirar ubangiji. gaba ɗaya sai yake jin tamkar yasa hannu ya buɗe cikin ya ɗauko yaran, Fillo kuwa kallon cikin kawai take yi a gefe guda zuciyarta na saƙe-saƙen yacca rayuwar zata juya, yanda komai zai koma saɓanin tunanin su da hasashen su, yacca komai zai faru anan gaba kaɗan, nan da ɗan lokaci kaɗan ba me yawa ba, hakan take taji a jikinta. "ba fa na so yarana su yi kama da mijin lukutar gombe saboda bana so su yi muni, ka daina kalle min su". ya rungumota jikinsa yana cewa,"wallah ki roƙi Allah su yi kama da ni kiga yanda za'a dinƙa miki layi a ƙofar gida, in kuwa su kai kama da ke to kin shige su, ƙila sai dai mu ke kulle su a store". bayan fitarsa ta zauna a gefen gado, ta rufe idanuwanta a hankali, yayin da hannayenta ke ɗore akan ƙaton cikinta, ita ɗaya ke ta saƙawa wai yanzu halitta ce a cikin cikinta, halittar da ya girma kuma zai fito nan ba da jimawa ba, shikenan da zarar sun fito ita ma ta samu nata babies ɗin, irin wanda take gani daga nesa don bata iya ɗaukar jariri, za su fito a matsayin nata, yayin da zata amsa wannan sunan mafi daraja na Uwa, ƴaƴan su ita da Turaki, Ƴaƴan su ikon su. sai taji ƙwalla na neman taruwa a cikin idonta, ƙwallar da take ta zallar farin ciki da wani bala'in jin daɗin da ba zai misaltu ba. ta lumshe idanunta, ƙwaƙwalwarta na haska mata hoton yaran acikin kanta, ana jibi Hajiya Madina zata rasu ana scaning sai taji tamkar ta ɗauko su a wannan lokacin, babies ɗin su na kwance a cikinta gwanin sha'awa, ga sunan clearly a jikin screen cikin hoton black and white,  kansu a haɗe su na ta watsal-watsal yayin da hannun kowanne ke gefen bakinsa, idanunsu a buɗe tarr tamkar kayi musu magana su amsa maka. kawai sai ta fara hasko yanda kammanin babies ɗin zai kasance, bata san ya Allah ya tsara halittar kamannin nasu ba, wataƙila su yi kama da su, wataƙila kuma su ɗauko kamannin su daban, sai dai a son samunta duk su ɗauko kamannin Turaki, ta yan da zata dinƙa kallonsa a fuskarsu idan baya gida, ba ya ga hakama idan suka ɗauko kamanninsa zasu fi kyau, irin wannan kyan da sai ta dinga tofe su da adu'a a kaɗawar kowanne sakan na agogo. tashi tayi akan gadon, ta isa gaban dressing mirror ta ɗauko diary ɗinta, sannan ta duƙa ta ɗauki riyon kayan babies, ta fita a ɗakin Turaki ta isa zuwa nata. wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu set ɗin kayan sanyi da Hajiya Ramla tayo mata aiken su a jiya, sannan ta fita ta nufi ɗakin kusa da na Turaki, ɗakin da suka ware domin yaran su, ɗakin da Turaki ya rufe mata ido ya shigar da ita sannan ya buɗe yana nuna mata yana faɗin for our coming kids. ɗakin tamkar already dama yara na rayuwa acikinsa, domin anyi decorating ɗinsa da duk wasu kayan wasan yara, komai na cikinsa pink and white, kayayyakin da almost siyayyar Marigayiya Hajiya Madina ne, sai ta isa gaban gadajen guda biyu, a wannan lokacin babu abin da ƙwayar idonta ta haska mata irin hoton yaran a zahiri, ta gama ba su nono ta zo ta kwantar da su tana yi musu wasa, idan zata yi aiki sai ta saka musu karatun alƙur'ani kafin ta fita. yayin da suka girma su fara kiranta da Ummi, mahaifin su kuma su kira shi da Abie, ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata lokacin da zata fara shirya su cikin kayan makaranta, ta ba su lunch box na abincin su, sannan tayi driving ɗin su zuwa makaranta, yayin da suka dawo ta zauna domin yi musu home work ɗin da aka ba su, idan weekend ya zo sai su dinƙa yada zango a field su na yin wasa tare da ita, ko kuma suke shiga cikin swimming fool. ita dai ta riga ta gama tsara yacca rayuwar jin daɗi zata kasance tsakaninta da ƴaƴanta, ba zata zamto ɗaya daga cikin irin uwayen nan da basa jan yaran su a jiki ba,  ita zata zam yaranta na liƙe da ita ne ko da yaushe, ta dinƙa jin damuwar su suma su na jin tata, zasu zama manyan aminanta kamar yanda zata zame musu. sai taji kamar zuciyarta ta ƙara girma da tsiron wata sabuwar ƙauna ta daban, ƙaunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan ƙaunar ta ɗa da uwa, irin ƙaunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri na son tabbatar da abinda kake so, Allah shahidi, shi zai yi mata shaidar irin son da take yiwa yaran, tana ƙaunar su fiye da ranta, a yanzu su ne rayuwarta, in har babu su tabbas babu ita. har ƙarfe uku tana ɗakin yaran a zaune, sallolinta duk anan tayi, abinci ma da aka kawo mata anan taci, ko ƙwalli ɗaya bata bari ya zuba ba gudun karta ɓata musu ɗaki. zuwa lokacin kuwa sun yi waya da Turaki yafi sau goma, bini-bini sai ya kirata yace ga shi nan yana hanya, kuma taji gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake tun san da tace masa tana jin mararta na ciwo sosai, kamar dai zata fara labour. cikin mintunan da ba zasu wuce biyar ba bayan wayar su ta ƙarshe sai ga Turaki ya dawo, yana shiga ɗakin yaran ya ganta zaune akan darduma tana goge hoton enlargement ɗinsu ita da shi, fuskarta ta washe da murmushi, wani murmushi da Turaki zai iya cewa bai taɓa ganinsa a saman fuskarta ba. "welcome back". ya ƙarasa ya zauna a gabanta yana tankwashe ƙafafunsa, ya ƙura mata ido sosai yana ganin yanda take cije fuska, tana so ta ɓoye masa zafin ciwon da ke cinta, tana so ta ɗauko ƙarfin hali domin ta nuna masa babu komai, babu wani abu da yake damunta, babu wata matsala, duk saboda hankalinsa ya kwanta. "kin ci abinci?". "na ci, me ka taho min da shi?". ya matso da ledar da ya shigo kusa da ita yana buɗewa. "irin naman da kike so". ai ko nan da nan ta warci ledar, ta miƙa masa enlargement ɗin tace,"maƙala musu wannan, an manta jiya ba'a saka shi ba, mp3 ɗin su na karatun alƙur'anin ka bar shi a ɗakinka, ka ɗauko sai a ɗora musu a saman wancan table ɗin, ungo wannan diary ɗin sa min shi cikin wadrobe ɗin su, kasa shi ƙasan kayan Aayan". duk maganar tayi ne a lokacin da ta fara cin naman, Turaki ya miƙe yayi duk abin da tace, san da ya kammala har ta gama cin naman, ya shiga tsokanarta da kura, kasancewar naman yana da yawa sosai. sai da suka ƙara kimtsa ɗakin sosai sannan suka zauna a tsakiyar gadajen biyu, suka shiga hira, wata iriyar hira suke yi mai ratsa jiki, hira da zasu ce ba su taɓa irinta ba a tsawon zaman su, hirar da ta yiwa kowannensu daɗi matuƙa. kan Fillo na saman ƙirjinsa yayin da yake shafa gashin kanta, duk hirar da suke yi muryarta na fitowa ne tana ratsa dukkan ɗakin a hankali, cikin wani amo na rauni da ya gaza ɓoye dauriyar ciwon da ke cinta. ana sallar magriba ciwon naƙuda me tsanani ya ɓallewa Fillo, lokacin tayo alwala kenan ta fito daga banɗaki, tayi saurin dafa bango tare da duƙawa a wajen tana dafe bayanta, a lokacin wata azaba ta tsarga jikinta, sai taji numfashinta kamar ya tsaya cak a maƙogoronta, taji kamar duk wani ɓurɓushi na halittar jikinta yana barinta gaba ɗaya. ta rumtse ido na tsawon mintuna tana ambaton Allah cikin wata rarrauniyar murya, wani sabon bala'in zafi taji ya fara bin dukkan jijiyoyinta, sai taji ina ma ta kwasa a guje ta bar cikin ɗakin ta fita waje ko zafa sami sauƙi acan, sai dai ko yatsanta guda ta kasa motsawa, ji take yi tamkar an saka ƙaton dutse an danneta. muryarta tun tana fita da ƙarfi har ta zo ta daina fita, lokacin Turaki ya shigo ɗakin kamar an hankaɗosa, dama tun san da zai tafi masallaci yaji hankalinsa bai kwanta ba, yaji gaba ɗaya ba ya so ya tafi masallacin gwara yay sallarsa anan, amma sai ta hana shi, ta tilasta masa akan sai ya tafi masallaci ya sami jam'i. cikin tsananin tashin hankali ya ƙaraso in da take, cikin bala'in ruɗu na farat ɗaya yace,"kin gani ko, sai dai na faɗa miki ba zan fita ba". "ka kaini a cire min su Jannaty, ba zan iya ƙara kwana a haka ba, don Allah ka taimaka min, zan mutu...".. Sauran harufan suka katse sakamakon wani sabon ciwon da ya murɗa mata, taji kamar an saka kibiya an soketa a tsakiyar cikinta da mararta. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Fulani Nah daure mu fita". ta kalle shi cikin hasken da zata ce a matsayin mutum uku take ganinsa, ta tattaro dukkan sauran ƙarfinta da ya rage mata ta daure, ya kamata ta yunƙura ta miƙe tana dafa kafaɗarsa, zafin ciwon da ya ƙaru yasa duhu ya wanzu a cikin idonta, ta daina ganin komai, tabbas bata iya ganin komai harta mijinta da yake riƙe da ita, sai dai kunnenta na iya jiyo mata sautin muryarsa dake fita cikin tsananin tashin hankali. Allah ya taimaka musu a bedroom ɗin ƙasa ne, da basu san ta yanda za'ai su sauko daga saman ba. Turaki yaji tayi masa wata muguwar damƙar da zai rantse ba ita ba ce, domin ba ƙarfinta ba ne, bata da wannan ƙarfin ya sani. "ka ɗauko riyon Babies mu wuce asibiti". "ba zan iya tafiya na barki ba a haka". "zan iya Jannaty, zan iya daurewa, zan daure har ka dawo". nan da nan Turaki ya haye sama ya tattaro duk wasu abubuwa da za'a buƙata a asibiti, ya kira Ilham a waya ta taho part ɗin, tana shigowa parlon ta tarar da Fillo durƙushe a ƙasa tana ambaton Ya salamu, Ya Salamu ka kawo min da sauƙi, idan na kasa ubangiji ka bani dauriyar da zan iya. tayi kanta da sauri, Turaki ya sauko ya dire kayan hannunsa. "kira yaran nan su kai mota sai ki zo mu kamata". hankalin Ilham a tashe ta shiga ƙwalawa su Sakina kira, bata ma iya yi musu magana da baki ba sai nuni da tayi musu da hannu. fitowarsu compound Boɗejo ta iso gidan ita ma duk a ruɗe, tana ganin yanda suke tafiya da Fillon a hankali ta ɗaga murya wajen ce musu,"kai ai zuwa zaka yi ka kawo motar nan kusa, sai mun hanzarta kar ta haihu a mota". tsabar ruɗewa Turaki ya manta da tunanin hakan, don haka ya sakarwa Ilham ita ya wuce cikin sassarfa yana haɗawa da gudu. asibiti mafi kusa suka isa, su na zuwa aka karɓe su saboda ganin yacca Fillo ta gama galabaita cikin mintunan da gaba ɗaya ba zasu kai rabin awa ba, ƙari kuma da uban kuɗin da suka ji an sakar musu duk da cewa dama asibitin private ne. wucewar wasu mintuna da ba zasu wuce goma ba Dr ya fito yana shaida musu cewar ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai ayi mata CS. "in har zata haihu lafiya ku yi mata koma menene, ina da buƙatar matata don Allah". furucin ya fito daga bakin Turaki murya a kakkarye. Dr ya ba su takardar da za su yi signing akai, Turaki yay signing ɗin a san da hannunsa da jikinsa duka ke rawa. kafin Dr Yusuf ma ya karɓa yay sigining a ɓangaren signature na mahaifinta. cikin wasu ƙalilan ɗin mintuna aka shiga preparation ɗin yiwa Fillo tiyata. lokacin duk ƴan gidan su Turaki sun iso asibitin, da Ammi mahaifiyar Yusuf, da wasu ƙannen Hayyo mutum biyu da suke anan garin gombe Safna da Alawiyya. duk ɗinsu su na zaune a ƙofar labour room ɗin da aka shiga da ita tun ɗazu, kowa yay jugum jiki duk a sanyaye, babu wanda zaka kalla kaga kwanciyar hankali a tare da shi, mahaifiyarta sai kiran waya take yi ana faɗa mata ko tiyatar ma ba'a shiga ba har yanzu. Turaki kuwa zama da tsayuwarma sun gagare shi sai zarya yake tayi, time to time sai yasa hannu ya sharce zufar da ke saman goshinsa. motsin buɗe ƙofar labour ɗin da aka yi yasa duk suka tattara hankalin su gun, Dr ya fito cikin sauri ya nufi side ɗin operation thiater, a san da nurses biyu ke turo gadon da Fillo ke kwance akai, tana sanye cikin uniform ɗin da ake sawa na CS, nurses ɗin suka tsayar da gadon a san da suka ƙaraso saitin family ɗin nata. Mum ta fara duba tace,"Mum kun zo?". kallo ɗaya zaka yi mata ƙwalla ta cika idanunka, duk suka taso suka iso wajenta, ɗayan hannunta da babu canular shi ta dinƙa miƙa musu su na gaisawa tana amsa tarin adu'oin da suke tayi mata. tana duban Ammi ta ce,"Ammi Ummi bata zo ba?". "bata zo ba Fillo, muna dai tayin waya da ita, tana ta yi miki adu'a, tace kar ki yawaita raki kiyi ta adu'a". "Ammi ina ta daurewa amma na kasa yin nishin da suka ce, kamar dai ko ba zan haihu ɗin ba ne". "za ki haihu kar ki damu, insha'Allahu ƴaƴanki za su fito". "Allah yasa Ammi. don Allah a ki kira min Ummina". ta furta hakan ƙwayar idonta na mannewa akan fuskar Turaki da yake tsaye yana kallonta ya kasa tahowa wajenta. bayan sun gama wayar da Ummi, nurses ɗin su ka cigaba da tura gadon, suka tsayar da shi a gaban Turaki. duk sun kasa ɗauke ido daga na juna, ita da take cikin ciwo ita ce me ƙarfin halin yi masa murmushi, don a wannan lokacin Turaki baya iya jin ko murmushin menene zai iya yi, ko da ace kuwa haihuwar tayi, har sai ya ga ta koma asalin Fulaninsa da ya sani, ba wannan Fulanin da yake gani ba me ƙarfin hali. ta miƙa masa hannunta ya kama ya riƙe, ya zubar da gwiwoyinsa a gaban gadon yana ce mata,"sannu Fulani Nah, sannu ƴar aljannah". sai fuskarta ta juye zuwa tsantsar damuwa tace da shi,"kayi haƙuri Jannaty ba zan iya ba, nayi duk iya ƙoƙarina amma na kasa, Dr ɗin yace ƙugun maza gare ni ba zan iya haihuwa da kaina ba sai dai suyi min aiki". Turaki ya kasa ce mata komai, ya kifa goshinsa a gefen hannunta, ta ɗago ɗayan hannun dake da canular da ƙyar ta ɗora a kansa. "Ka kwantar da hankalinka don Allah Jannaty, babu abun da zai faru kaji?, lafiya lau za'ayi aikin nan da izinin ubangiji, kuma lafiya lau za'a fito maka da ni da ƴaƴanka". Turaki ya ɗago kansa ya kalleta, a san da yake amsawa da Allahumma amin. Fillo ta dinƙa kallonsa tamkar yaune ta soma ganinsa, mamaki take yi sosai, bata taɓa yi masa murmushi ba yaƙi mayar mata da martanin hakan, haka zalika bai taɓa kallon fuskarta ba, ba tare da tasa fuskar ta washe da kyakykyawan murmushi ba, a yau kuma a wannan lokacin fuskarsa na looking so hard, babu wani emotion da za ta ce ta tsinta a ciki, zatonta ranar yau ita ce ranar da yake ta jira, wan nan lokacin shi ne yake tsimayin jiransa saboda ƴaƴansa guda biyu za su fito duniya, don haka a wannan lokacin ya kamata ace taga yana farin ciki ko ya ya ne. amma tun a gida data fara ce masa ciwo, yay ɗan guntun murmushi yana tsokanarta da Lukutar gombe zata haihu zata sace a koma gidan jiya, zata dawo kamar muciya da zani. ta san tayi dariya a lokacin da yay wannan maganar, but ita a lokacin data tsokane shi da cewa haka aka gani a muciya da zanin aka nace sai da aka ɗauka, bata ga wani kuzari na martanin dariya daga gare shi ba, kawai dai ya miƙe ya ɗauko jarkar rubutu ya bata ta tasha cikin mutuwar jiki. ta lumshe idonta ta buɗe kafin tace,"ƙarfe nawa Jannaty?". zai iya cewa da ƙyar ya iya karantar agogon kafin yace mata,"takwas da rabi Fulani nah". ta sauke numfashi ta ce,"sun ce sai ƙarfe tara da rabi zamu shiga, da za su bani dama da na kalli gabas nayi adu'a". sai kuma tace,"ka ci abinci Jannaty?". bai iya magana ba illa girgiza mata kai da yay. "me yasa to?, kana so Aayan ya taso ya fika ƙiba ko?, mutane suke tsokanarka su na cewa ɗanka yafi ka ƙiba". sai ya daɗa riƙe hannunta kamar wanda za'a ƙwace masa ita yace,"ta ya zan iya saka wani abu a cikina alhalin kina cikin mawuyacin hali?". "Jannaty na faɗa maka ka kwantar da hankalin ka, lafiya lau za'ayi komai babu abin da zai faru". "zan ci abinci amma sai an fito da ke, wataƙila ma yau ba zan ci irin abincin da za kici ba, wan da zanci zai fi wanda zaki ci daɗi, ko don saboda nayi ƙiba a daina yi min gori". tayi murmushi,"to me zaka ci?". sai ya kai hannunsa ɗaya saman breast ɗinta ya taɓa yace,"madaran yarana zan sha, mu uku za kiyi feeding yau". "baka da damuwa guda ɗaya ma za'a bar maka, sai suyi shairing guda ɗaya". ta ƙara cewa,"ka yi min waƙar da kake yi min Jannaty". ya girgiza mata kai,"ban da waƙa sai dai adu'a". "to kayi min karatu cikin ƙira'arka me daɗi". a hankali kuma ya shiga biyo mata suratul shu'araa. har san da yazo kan aya ta ashirin da takwas,_wa'izaa maridhtu fahuwa yashfeeeen_. sai ta ji wani abu na bi ta ƙasan zuciyarta, ta kira sunansa da irin amon sautin da zai ce bai taɓa jinta da shi ba, ya kalleta idanuwansu suka sarƙe waje ɗaya, ya haɗiye wani abu da bai san menene ba kafin yace,"menene Fulani Nah?, me kike so?, ciwon yana raguwa?". ta mayar da murfin idon ta rufe ta ce,"hold me Jannaty, i want to talk to you". ta faɗi hakan tare da buɗe idanuwanta. "Jannaty duk da halin da nake ciki ina yi maka murmushi, please kayi min wannan kyakykyawan murmushin naka atleast ko da sau ɗaya ne, ko da bai yi faɗi da yawa ba, ka daure kayi min ko ya ya ne". shirunta ya haɗe da bayyanar haƙoran Turaki duka a waje, maimakon murmushin da tace tana so sai kawai ya sakar mata dariyarsa me daɗin sauti, dariyar da har ita ma sai da tayi irin tasa ɗin, dariyar da ta ratsa jijiyoyin Turaki ta zarce har cikin zuciyarsa ta huda wani waje. ta buɗe baki a hankali tace,"ko kai fa Baban biyu, please you take good care of our kids, ko babu ni na san kai uba ne na gari, na san yaranmu ba za su yi kukan maraici ba, kayi musu dukkan gatan da uba yake yiwa ƴaƴansa, ka ba su wadataccen ilimi, kaja su a jikinka ta yanda zaka dinƙa jin damuwar kowannen su, ka kula da tarbiyar su, tarbiyar su da iliminsu!, tarbiyarsu da ilimin su don Allah Jannaty". furucin nata yasa yaji kamar zai yi kuka, ya ƙanƙameta yana faɗin,"bana son magana irin wannan, you promise me that we will be together forever, so why talking like this?". "Allah ya baka haƙuri ba zan ƙara ba daga yau, ka yafe min". taja hancinsa laɓɓanta na motsa da murmushin ƙarfin hali tace,"i love you Turakin Fulani". sai kawai ya miƙe tsaye, ya manta da nurses ɗin da ke tsaye a gefe, ya manta da su Mum da ke tsaye su na kallonsu, ya manta da mutanen dake giftawa, yasa hannu ya ɗagota, ya haɗe bakinsa da nata yana kissing har tsawon minti biyu, kafin daga baya ya shiga kissing ko'ina na fuskarta sannan ya rungumeta tare da furta,"i love you morethan you do Fulanin Turaki". a lokacin ne kuma Dr ya bawa nurses umarnin cewa su wuce da ita ɗakin tiyatar. sai taji hannun Turaki na zamewa daga cikin nata, muryarsa na fito a mugun karye, yana yi mata adu'ar Allah yasa ayi cikin sa'a, Allah yasa ta fito lafiya. sai kawai ta rumtse idanuwanta gam, tana jin nurses ɗin na tura gadon nata suna barin wajen, tana jin kamar tana so tace musu su ƙyaleta ba sai an ciro yaran ba. Turaki yabi ta da kallo yana ganin yacca hawaye ke sauka ta gefen idonta, hawaye na farko da zai cewa ya gani a tare da ita tun a ɗazu da ta fara naƙudar. "don Allah kar kuyi min allurar bacci, ku yi min idona a buɗe, ina son ganin a yacca za'a fito min da Babies ɗina". ta faɗa idanunta na kallon likitocin da ke kanta tare da nurses, a lokaci ɗaya sai taji tausayin bawan Allahn da rayuwarsa take tamkar a nannaɗe da tata, Turakinta! Mijinta!, uban ƴaƴanta, wanda ta san a duk lokacin da tata rayuwar ta ƙare, lokacin da ta zama bata cikin rayuwarsa, to tabbas bata san ya duniyarsa zata kasance ba. sannan tausayin ƴaƴan da zasu fito daga cikinta yay mugun matse zuciyarta, bata san ya rayuwarsu zata kasance ba a yayin da babu ita, bata san ya tasu ƙaddarar rayuwar zata zama ba, bata san irin jarabawowin da za su fuskanta ba, duk da ta san babbar jarabawa a gare su shi ne na rashinta, za su taso ba tare da uwar da ta kawo su duniya ba, za su ta so ba tare da sun san wannan ɗumin jikin na uwa ba, za su taso babu wannan kulawa da soyayyar da yake a wurin uwa ba kaɗai. "bismillahir-Rahmanirrahim, bring the knife". haka taji likitan da ke tsaye akanta ya faɗa, kuma bayan wannan zata iya cewa jinta ya ɗauke na ɗan wani lokaci kafin ya dawo. a san da aka fara aikin, idanun Fillo a jiƙe suke sharkaf da hawaye, hawayen da ya hanata ganin komai sosai. a wannan lokacin dukkan tunaninta ya gama hargitsiwa da kowanne motsin dake faruwa a cikin ɗakin tiyatar, tana jin yacca sautin zuciyarta ke bugawa da ƙarfi acikin kunnenta. lokaci ɗaya taji sautin wata ƙara ta fita a jikinta, sautin da ta tabbatar na yanka ne, cikinta ake yankawa!, sai taji zafin ciwon da take ta daurewa ya ƙaru, zafinsa na ƙaruwa sosai da sosai, zafin da har ta kai ga kasa tantance cikinta ake yankawa ko kuma ruhinta ake zarewa. hawaye ya bi ta gefen fuskarta, ta ji kamar ta ɗago tasa hannu ta danne wajen da aka yanka ko zata sami sassauci, sai dai babu abin da zata iya, bata da ƙarfin motsi ko kaɗan, tamkar matacciya take. tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a cikin ɗakin tiyatar sai fafutukar da likitoci ke yi wajen ciro yaran daga cikin mahaifiyar su. kunnuwan Fillo sun ji lokacin da aka ciro Baby na farko, Babyn da taji Dr na cewa da nurses su yi ƙoƙarin su wajen ganin yayi kuka, sai taji wani farin ciki ya ratsata, farin cikin da taji tamkar an yi mata bushara da gidan aljannah. so take taga yaron da aka ciro, don haka cikin ƙarfin hali da dauriya ta karkata kanta gefe domin kallon jaririn da cibiyarsa kaɗai take iya hangowa, kuma a san da nurse ɗin ke juyowa zuwa sashinta, lokacin sabuwar azaba ta ƙara ratsata, tayi saurin rumtse ido tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. ambaton nata ya haɗe tare da kukan Baby na biyu da aka ciro, kukan da ya cika ɗakin gaba ɗaya, kukan da zata ce kamar ta tsinci sunan da take ta muradin ta haife su taji sun kirata da shi, Ummina!. a san da Babyn yay shiru sai taji jikinta ya tsaya a lokaci ɗaya, yay sanyi ƙalau, numfashinta mai nauyi na cigaba da fita, yayin da zuciyarta ke bugawa a hankali, hakan yasa ta fahimci cewa hargitsin azabar ciwon da take sha yazo ƙarshe, ƴaƴa biyun da ke cikinta an fito da su duniya, ta zama uwa, dukkan fatanta da burinta ya gama cika, atleast ta samu masu yi mata adu'a a kowacce daƙiƙa a yayin da komai ya riga ya kai ƙarshe. ta riga ta san abin da yake cikinta tuntuni, macece da na namiji ne ba sai an faɗa mata ba a yanzu. tana jin yacca motsin yaran da ake ta aikin gyarawa ke mutsutsu acikin kunnenta, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da son su da ƙaunar su, sannan a hankali ta fara jin komai na zamewa daga cikin kanta yana barin ƙwaƙwalwarta, cikin ranta tana adu'ar,_"Ya Rahman if you decide to take my soul at this time, i beg you Allah to give my husband and my childrens the strength to bear it, Allah kaji tausayin ƴaƴana, ka tausayawa maraicin su ka basu tamkar Hajiya Madina a matsayin wacca zata kula da su"._ da ga wannan furucin dake cikin ranta, sai kuma bakinta ya shiga maimaito kalmar shahadar da taji tana wanzuwa acikin kanta, hakan yasa idanuwan likitocin da ke ɗakin ya manne akanta, akan murfin idonta da ke barin kan twins ɗin da ake nuna mata amma ta kasa kallon su. kuma wucewar sakanni biyar komai ya zama ya ƙare, komai ɗin dake rayuwar Fillo, shikenan wa'adin da ubangiji ya ɗiba mata ya cika, alƙalaminta ya riga ya bushe, ubangiji yayi hukuncinsa. bayan wasu mintuna Turaki da ke tsugune a ƙofar ɗakin tiyatar yaji an buɗe ƙofar, bai motsa ba dan bai san ta yanda zai motsa ba, yana so dai ya buɗe idonsa yaga abin da ke wanzuwa, so yake ya buɗe ido ko ya samu zuciyarsa ta daina bugawar da take yi. acikin wata fargaba da ke tare da shi yaji an ɗora hannu akan kafaɗar sa, sai ya ɗan buɗe ido kaɗan yana kallon nurses guda biyun da ke tsaye akansa tare da likita, ba zai ce ga lokacin da ya miƙe ba, ya dai tsince shi ne tsaye akan ƙafafunsa yana kallon jariran dake hannun nurses ɗin, bai san me yake ji a zuciyarsa ba, amma dai ya san bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa hannu ya fara karɓar namijin, sakanni uku yana kallon yaron me kama da shi sak kafin ya miƙa shi ga Dr Yusuf da ke tsaye a kusa da shi, sannan ya daɗa karɓar macen da ita ce ƙarama, kuma a lokacin da ya ɗora idonsa akanta a lokacin Doctor ɗin yace da shi,"I am very sorry to tell you that your wife is no more, Allah yayi mata cikawa, ina yi maka ta'aziyya Allah yaji ƙanta da rahamarsa". a maimakon rufewar da idanun Turaki ke shirin yi sai yaji sun maƙale akan jaririyar da ke kuka a hankali, jaririyar da yake hasko fuskar mahaifiyarta a fuskarta. sai kawai yaji furucin likitan na maimaituwa acikin kansa,_"your wife is no more"._ sai yaji kalaman likitan suna ƙara tafiya a hankali, yayin da yake ji suna barin cikin kunnensa har zuwa cikin kansa da zuciyarsa in da suka samu masauki, don ya kasa gane ta yadda zai karɓe su balle har su yi ma'ana a cikin ƙwaƙwalwarsa. Fulani ta mutu?, yana nufin Fulaninsa ta mutu, Fulani ta mutu!, Fulanin da suka yini tare yau, to ta ya zai yarda da hakan?. sai kawai ya kutsa ta tsakiyar mutanen da ke gabansa ya faɗa cikin tiyata room ɗin still yana riƙe da jaririyar, yana shiga ya hangota an rufeta, rufewa tana nufin lulluɓewa har fuska, irin lulluɓewar da ya gani akan Maamansa sati biyu da suka wuce, irin lulluɓewar da yasan mamaci kawai ake yiwa, irin lulluɓin nan da ake yiwa gawa kaɗai. Turaki ya tsaya cak tamkar mutum mutumi, idonsa na kallon gawar, yaji guiwoyinsa sun yi sanyi ƙalau, irin sanyin da suka kasa cigaba da ɗaukarsa, don haka sai ya nemi bango ya dafe gudun kar ya faɗi jaririyar da ke hannunsa ta cutu, haka ya dinƙa jan ƙafa yana dafe da bangon har ya ƙarasa gaban gawar, a lokacin ƙafafunsa suka kasa ci gaba da ɗaukarsa ya zube a wajen, ya damƙi mayafin da aka lulluɓeta da shi, a hankali ya shiga adu'ar. "Allah ba yanzu ba, Allah ko don waɗannan jariran, zuwansu duniyar kenan Allah, Allah ka sauya musu wannan ƙaddara ya zama ka ɗauke ni ba mahaifiyar su ba, sun yi kaɗan da irin wannan jarabawar, Allah don Allah ka dawo da Fulani ka ɗauke ni,  Allah kar kasa Fulani ta tafi ta barmu, Allah ka tausaya mana ba zamu iya ɗauka ba,Allah ka tausaya mana don masoyinka fiyayyan halitta, Allah don son da kake yiwa Annabi Muhammadu SAW". sai ya kalli jaririyar da kukanta ya fara yawa yace,"Allah'n mu ka tausaya mana, don Allah Allah ka juya wannan ƙaddarar, ka ganta Allah tana buƙatar nonon mahaifiyarta a halin yanzu, idan kace ka ɗauketa bata da me bata abincinta, Allah ko ba don ni ba, don jariran nan Allah ka tausaya mana, Allah jarabawar tayi mana girma, a sauya mana, a dawo da Fulani a ɗauƙe ni Allah". sai yayi ƙarfin halin miƙewa ya hau kan gadon ya zauna, zama sosai har da miƙe ƙafa, ya ɗaga mayafin da aka rufeta da shi ya buɗe fuskarta, da farko daskarewa yayi a yanda yake, sai kuma yayi blinking idonsa, saboda ganin kamar likitocin sun yi makuwar saƙon da suka faɗa masa, domin wannan ba fuskar gawa ba ce, wannan fuskar ta me bacci ce, gata nan fess da ita, ta ƙara yin wani irin kyawun da bata taɓa yi masa ba, fuskarta ta ƙara yin doguwa, hakama hancinta kamar ba nata ba, ya ƙara yin tsaho sosai, fuskarta sai annuri take. a sanda ya lura da rashin motsin bugawar zuciya a ƙirjin matarsa, a sannan ya kamo hannunta ya ƙanƙame a ƙirjinsa ya haɗa da jaririyar, yana jin irin yanda zuciyarsa ke huci tana huda ƙirjinsa tana neman fashewa. shi musulmin ƙwarai ne ya san mutuwa, ya yarda da ita, so dole yay accepting jarabawarsa, dole ya yarda da ƙaddadararsa, yanzu ya tabbatar da likitocin ba ƙarya suka yi masa ba, ta mutu, ta tafi in da Maama ta tafi, ta tafi in da ba'a dawowa. sai kawai ya kwantar kansa akan ƙirjin gawar tare da rufe idonsa, yana jin wani irin bala'in kaɗaici ya lulluɓe shi, yana jin mugun tausayin kansa, yana jin tamkar shi ɗaya ne ɗan Adam ɗin da yay ragowa yanzu a duniya, sai yaji ina ma shi ma tasa zuciyar ta daina motsawa tamkar ta Fulaninsa, shi ma ya koma gawar ko ya daina jin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa, yana jin kamar ya zama gawar ya bi bayan matarsa masoyiyarsa, ya bi bayan macen da ta dinƙa kasada da ranta domin ceto rayuwarsa. a haka yay kissing ƙirjinta, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban kuka, domin a yanzu ya kasa yin kukan, alhalin kuma kukan yake so ya yi. wacewar mintuna ashirin da biyar, a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, acikin parlon na Hajiya Ramla, gawar da aka rufe na shimfiɗe akan carpet, in da a hankali sautin wasu muryoyi ke fita da kuka wajen sanar da mutuwar da akayi. a wannan lokacin Hajiya Ramla da Baffa da Boɗejo da Ilham na kan Turaki, wanda ya sume tun a dawowar su, tun a lokacin da suka dawo gida yake tsammanin zai ga Fulaninsa ta fito da ƙafafunta, amma sai yaga an fito daga mota wasu na ɗauke da gawarta, a lokacin ya san kallonta kawai yake yi, sai kuma yaji kukan jariran da ke hannunsa na tashi, kukan da ya ƙara haddasa bugun zuciyarsa, kukan da ya kaishi ƙololuwar tashin hankalin da har bai san lokacin da yanke jiki ya faɗi ba, ya san dai tare da yaran ya faɗi, amma bai san wanne hali shi da su suka shiga bayan faɗuwar tasa ba. don haka tun bayan faɗuwar tasa tsawon minti goma kenan a yanzu, ƙoƙari ake tayi wajen ganin ya dawo hayyacinsa, kuma da taimakon Dr Yusuf ya farfaɗo, sai dai kana kallonsa kasan baya cikin hayyacinsa, idonsa na tsaye ne a waje ɗaya ƙyam ya zama kamar gunki, cikin ransa ji yake ina ma bai farfaɗo ba shi ma ya mutu, har cikin zuciyarsa ji yake ina ma yabi bayan Fulaninsa da Maama, duk da cewa baya so ya rabu da yaransa, to amma bai san ta yanda zai fara rayuwa tare da yaran ba alhalin mahaifiyarsu bata raye, yana tsananin tausayin su, don haka a yanzu babu abin da yake so illa ya mutu shi ma, baya so yaci gaba da rayuwar sam. kamar daga sama mutanen parlon suka jiyo muryarsa na faɗin,"Wannan wacce irin jarabawa ce ubangiji yake yi min?, laifin me na aikata da za'a jarabce ni irin haka?...". Baffa yay saurin saka hannu ya rufe masa bakinsa. "kar ka yi saɓo Muhammad, kar ruɗani yasa ka fita daga imaninka, kayi haƙuri, ka yi tawakkali ka roƙi Allah ya baka dangana, kayi haƙuri komai muƙaddari ne, ka roƙi Alah ya baka ikon cinye jarabawarka". Turaki ya shiga sauke numfarfashi, ya shiga jan mazaunansa har ya ƙarasa gaban gawar da yake gani, ya ɗaga mayafin ya ruƙo hannunta. "Fulani Nah! don darajan Allah da Annabinsa ki tashi, na yarda ki tashi ni sai na tafi, ko kuma mu tafi tare, ba zan iya rainon yaranmu ba ni ɗaya, ban san me zan ce musu ba idan suka tambaye ni ke". sai kuma ya kifa kansa kan gawar yana ambaton,"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". faɗa yake yana ƙara maimaitawa, yana girgiza gawar, gani yake tamkar idan yana hakan zata farfaɗo, kamar zata dawo duniyar su ci gaba da rayuwar su tare, su raini ƴaƴan da Allah yaba su ciki kyakykyawar kula da tarbiya, idan yaji yaran sun yi kuka sai ya shiga girgiza kansa yana faɗin Allah ka sassauta min, Allah tayi min tsauri, Allah kaji tausayina. duk sai ya koma kamar wani taɓaɓɓe, sai maganganun kawai yake yi, idan aka ce yay haƙuri yay ƙoƙarin cin jarabawarsa sai yace ba zai iya ba, tayi masa tsauri, da farko an ɗauke masa Maama, mutuwarta bata gama sakinsa ba an ɗauke masa Mata, sannan an bar shi da marayu, marayun da ko nonon uwarsu ba su samu damar sha ba, to ta ina zai iya ɗauka?, ta ya ma zai iya cinyewa? haka akaita rarrashinsa amma inaaaa, a lokacin da ya rasa Maama ganin yake idan aka cire Mum to duk wata mutuwa da zata zo masa zai ɗauketa, zai iya ɗauka, but a yanzu da ya rasa matarsa, uwar ƴaƴansa sai yaga abun ba haka ba ne, da wuya, da zafi, ba zai iya da wannan jarabtar ba me tsayawa a zuciya. a wannan dare dai waɗanda suka sami yin bacci ƙailan ne, hatta Ilham sai ɓarawon bacci ne ya ɗauketa, domin sosai mutuwar ta taɓata, a ɗan sabon da suka yi Fillo ta shiga ranta, don tun bayan da Allah ya ganar da ita ta koma yiwa Fillo kallon ƙanwa ta jini ba wai kishiya ba. Hajiya Ramla kuwa na kan ɗanta, idan tayi rarrashin tayi rarrashin sai taji tana taya shi kukan da ya kasa yi. haka suka kwana ba su runtsa ba, yana riƙe da hannun gawar, yayin da jariran ke jikinsa su na bacci, waɗanda aka rarrasa da ƙyar suka daina kuka har baccin ya ɗauke su, waɗanda har gari ya waye ana tunanin wanda zai shayar da su. washegari ƙarfe goma na safe an gama haɗa gawar Fillo, gawar tana tsakiyar parlon na Hajiya Ramla cikin sutturarta, cikin wannan farin ƙyallan da ke jiran duk wani mai rai, mahaifiyarta da Yayanta da Kaka da Dada su na gaban gawar su na kuka, musamman Ummi wacca ake ta cewa su yi sallama, tayi mata adu'a domin wannan ita ce sallama ta ƙarshe da za su yi. "Allah ya jiƙanki Halimatu, Allah ya yafe miki kurakuranki, Allah ya baki Aljannatul firdausi, Allah ya karɓi shahadarki, Allah ya karɓi ruhinki cikin daraja, Allah yasa Manzon Allah ya karɓi baƙuncinki, Allah yasa mutuwa ta zamto hutu a gareki, Allah ya lulluɓeki da rahamarsa da gafarsa, haƙiƙa ba ki yi min komai ba, na yafe miki duniya da lahira, abin da kika bari Allah ya kula miki da su, Allah ya basu haƙuri da juriyar rashinki. sai mun taho muma". aka shigo da Turaki, ya zauna shi ma agaban gawar, yana jin sautuka na shiga kunnensa, sai dai a lokacin babu abin da ƙwaƙwalwarsa ke iya ganewa, har yanzu ya kasa karɓar mutuwar matarsa, ganin komai yake yi tamkar shirin wasa, tamkar shirin film aka haɗa don kawai a girgiza shi, don kawai a gwada irin ƙarfin soyayyar da yake yiwa Fulaninsa. "Muhammad ka yi mata adu'a, kuyi sallama Muhammad kaji". tun daren jiya, tun lokacin da labarin mutuwar matarsa ta riske shi, da zaman kwanan da yay agaban gawar, zuwa wayewar garin yau da ya ƙara tabbatar da ya rasata, sai a yanzu da ake cewa yay mata adu'a suyi sallama ya ji idonsa ya cika, saɓanin jiya da yake a bushe, har yana jin kamar ba zai taɓa zubar da ruwa ba, amma a yanzu tarin ruwan da ya cika a idonsa ba ya jin zai iya dakatar da su, saboda haka sai kawai ya kifa kansa akan ƙirjin gawar, hawayen ya ƙwace, kukan ya kubce, ya shiga rero kuka tamkar ƙaramin yaro, yana kukan jikinsa na girgizawa kamar yanda zuciyarsa ke yi. adu'ar da ake ta cewa yayi ya kasa yi, sai da ƙyar aka iya raba shi da jikin gawar, aka miƙar da shi aka riƙe shi, yana kallo aka ɗauki gawar aka fita da ita, da sauri ya bi bayan su, ya tarar da su suna saka gawar a cikin makara. abinda ya saka shi ƙara rikicewa, sai ya tsinci kansa da yiwa Allah godiya da ƴaƴansa ba su tsinci ganin wannan lokacin ba. ƙarfe sha ɗaya dai-dai aka yiwa Fillo sallah, a cikin ƙaton compound ɗin gidan Alƙali Dikko, bayan gama sallar gawar aka ɗauƙi makarar aka fita da ita daga gidan, Turaki na sahun gaba, ƙafafunsa ke jansa ba shi ne yake tafiyar da su ba, yayin da hannunsa guda ɗaya yake cikin na Bello ya riƙe shi da kyau, saboda gudun faɗuwarsa. a lokacin da aka isa maƙabartar, Hamid da su Yusuf da Baffa su ne suka fito da gawar daga cikin makara, Bello ya kama hannun Turaki ya kama kan gawar sannan aka sata a cikin ramin ƙabarinta, yana kallo ana fuskantar da fuskarta zuwa ɓarin gabas, yana kallo aka ɗauko fasassun tukwane aka jejjera a saman gawar, kafin daga bisani yaga ana zuba ƙasa ana toshe ko'ina, yana jin muryoyin da ba zai iya tantacewa ba na faɗin a toshe kowacce ƙofa, yana kallo bayan an gama rufe gawar ruf da ƙasa aka yayyafa ruwa a samanta, sannan aka ɗauko allon shaida aka dasa a wajen kan, allon da yake iya karantawa, komai yana faruwa kamar dai sati biyu da suka wuce. sunan da ke jikin Allon ɓaro ɓaro, sunan matarsa, sunan abar ƙaunarsa, wannan Fulanin tasa, wannan Fulanin da yake jin ba zai iya rayuwa ba a duk san da babu ita a tare da shi, yau shi ne a gaban ƙabarinta, da shi aka kawota, yana kallo aka sakata cikin rami bai iya hanawa ba, bai iya buɗar baki yace a'a ba, bai iya motsawa ba balle ya riƙe gawar. *Marigayiya Halima Muhammad Barkinɗo(Fulani), Allah ya jiƙanki da rahamarsa, 03/10/2022.* kamar hakan allon ke ɗauke da rubutun cikin manyan baƙi, ji yake kamar ya fincike allon ya jefar. a hankali ya dawo da tunaninsa ɓangaren da yaji ana doguwar adu'a, sai ya fara kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, kowa a tsugune yake ya ɗaga hannunsa, sannan Dr Yusuf da Hakim da Khaleel idanuwan suna hawaye, sai Baffa da Daddy(Baban su Dr Yusuf) fuskarsu fayau, sai ya mayar da kallonsa kan ƙabarin, shi ma ya ɗaga nasa hannun, ya shigo jero tarin adu'a wa ruhin matarsa, yi yake yi yana maimaitawa, har zuwa lokacin da yaji takun tafiya alamu na ƙafafu sun fara barin wajen. yana ji mutanen da ke kusa da shi suna tashi, kuma kafin kowa ya tafi sai an zo an dafa kafaɗarsa ance masa,"Allah ya jiƙanta, Allah ya bada haƙuri". da haka da haka sai da ya tsinci babu kowa a kusa da shi, sai shi kaɗai da yake zaune yana kallon ƙabarin ya kasa sauke hannunsa, har sai da Bello ya zo ya dafa shi yace,"kayi haƙuri ka tashi mu tafi". sai yaji Khaleel ma na ce masa,"Hammah kayi haƙuri". kawai sai ya saki kuka me ƙarfin sauti, ya kai hannunsa ya ɗora akan ƙabarin, a hankali yace,"insha'Allahu zan yi duk abin da kika ce, zan kula da yaranmu, zan ba su tarbiyya, zan saka su a makarantar da kika faɗa, ba zan bari su yi kuka ba, ba zan sa suyi kuka ba, ba zan bari su shiga cikin ƙunci ba, ba zan bar su suyi maraici ba, zan riƙe amanar da kika bar min, nayi miki alƙawari, zan kuma cika miki shi tabbas. don Allah ki yafe min da duk laifin da nayi miki, don Allah Fulani Nah, ki ce ina gaida Maama". Bello da Khalil suka kama shi ya miƙe. suka riƙe shi suka fara tafiya domin barin cikin maƙabartar, sai da suka zo bakin ƙofar fita ya juyo yana daɗa hango kabarin, yana faɗin,"zan dinga zuwa kullum ina gaishe ki, zan dinga zuwa kullum ina yi miki adu'a, idan Aayan ya girma zan dinƙa kawo miki shi kina saka masa albarka, na gode Fulani Nah, sai anjima kinji ƴar aljannah". komawar su gida suka tarar da ɗumin dandazon jama'a acikin rumfunan tanfol ɗin da aka yi kusan guda biyar, kai tsaye cikin gidan ya wuce bai tsaya a waje ba, yana shiga ya fara karɓar gaisuwar ta'aziyya daga mutane, ba wani ganin su yake yi ba, don ba ya gani da kyau. ya ratsa ta cikin falon Mum ya haye sama, daga ƙofar ɗakin nata ya tsaya yana kallon Nihal da Ilham da ke goye da marayun jariransa, sai ya shiga ciki ya kunto yaran daga bayansu da kansa, ya fito ya bar ɗakin, ya kuma ratsa mutanen dake parlon ƙasa ya fice daga sashin gaba ɗaya. kai tsaye ɓangarensa ya nufa, ya buɗe ɗakinsa ya shiga, ya zauna akan gado tare da jinginar da kansa jikin gadon, ya kwantar da macen a ƙirjinsa, namijin kuma ya ɗora shi a kan ƙafafunsa. "your mum is no longer with us, she is gone and she is never coming back, death have separated us, she wants us to pray often for her, tun kafin ta haife ku tace Allah yaywa rayuwarku albarka, kuma na san ta biku, Allah ya raya min ku. Allah ya bamu haƙurin rashin da muka yi, ina yi mana ta'aziyya". ya faɗa ya ƙara maimaitawa kamar yaran suna fahimtar me yake cewa, kafin a hankali ya rufe idonsa. in da a wannan lokacin Ilham ta shigo hannunta riƙe da tea flask, jikinta duk a sanyaye sai idanuwanta da suka yi jawur. ta ƙarasa ta zauna a bedside drower tana kallonsa, tana kallon yanda hawaye ke fitowa daga idonsa yana bin kumatunsa, yayin da bakinsa ke motsi yana furta abun da bata san menene ba. ta jima kafin ta iya saka hannu ta taɓo shi tayi masa magana, ya buɗe idonsa ya kalleta bai ce komai ba, Baby ɗin dake saman ƙirjinsa ta motsa, yay saurin gyara zama yana ɗagota daga ƙirjinta ya kalleta. "sorry little...". sai ya rasa da sunan da zai kirata, da Aina'u(Hajiya Madina) ko kuma Halima(mahaifiyarta)? cikin wata murya me mugun rauni ya ce,"yanzu baza ki iya samun ruwan nono ba?". ya jefa tambayar ga Ilham, kafin ta ba shi amsa sai ya ƙara cewa,"ki taimaka musu don Allah, tun jiya babu abin da suka ci, Mum tace min sun ƙi shan madarar, na san su na jin yunwa, don basu da bakin magana ne kawai amma da sun faɗa". kuka ya taho mata tace,"idan akwai yacca za'ai nonon ya zuba sai ayi, duk nayi nayi su kama nonon ko zai zuba sun ƙi. amma ɗazu da ku ka tafi kaita Fauziyya ta ba su sun sha". "wacece Fauziyya?". "ƙanwar Bello". sai ya ɗago da sauri ya kalleta yace,"don Allah kirawota tazo ta ƙara ba su, kinga Maama ta tashi, bana so tayi kuka". cikin sauri Ilham ta tashi ta fita, tana fita ya ɗauke Aayan daga kan ƙafarsa ya kwantar akan gadon, ya sauko yana jijjiga Maama a saman kafaɗarsa. idanunsa na ƙara cika da ruwan hawaye, ya tuna jiya kamar yanzu ya na tare da mahaifiyar su, yana hasko san da Fillo ta ɗauko kayan da ke jikin yaran a yanzu, yana tuna sunan lukutar gombe, yana tuna irin dariya me faɗin da take yi a duk sanda ya faɗa mata hakan, yana tuna ranar da tayi fushi da shi ta kalle shi ta murguɗa masa baki, har tana cewa ko ta haihu yaranta da sunanta za su bearing ba nasa ba, sai dai ace Muhammad Halima da Aina'u Halima, duk ba zasu saka Turaki ba, tana faɗin ai ita ta haifa, shi kuma yana faɗin ai dai shi ya bayar. yanzu bata raye, komai nata ya zama tarihi, ta tafi ta barshi da memories masu matse zuciya, yaji hawaye masu zafi sun sauko masa, tashin hankalinsa ɗaya ne, damuwarsa ɗaya ce, tunaninsa ɗaya ne, nonon wa yaran zasu dinƙa sha?. *BAYAN SHEKARA GOMA SHA SHIDA.* [9/7, 03:37] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *GAMJI WRITER'S ASSOCIATION*    _Home of exceptional writers._ *61* Da gudu ta fito daga cikin ɗakin, isowarta falo suka yi karo da Inna Wuro ta faɗi a ƙasa, ita ma medical glass ɗin idonta ya faɗi, nan da nan ta shiga kokawar ɗauko shi daga ƙasan. idanun sai ƙiftawa suke yi kamar an tsokane su, sai da ta saka glass ɗin sannan suka daina ƙiftawar, kuma kallo ɗaya zaka yiwa ƙwayar idon nata ta cikin glasses ɗin ka san ba lafiyayyu ba ne. yanda jikinta ke rawa zaka ce ko bata da lafiya ne, nan kuwa zallar rashin gaskiya ne a tare da ita. ta kalli Inna Wuro ta gefen ido, dariya ta taho mata tayi saurin sa hannu ta toshe bakinta. "huhuhu, la'ila ha'ilallahu, waiwaiwai. to ni dai sai dai in ce Allah ya isa kawai". ta buɗe baki zata yi magana Inna Wuro tayi saurin ɗaga mata hannu tana girgiza kai. "a'a fa ni ba sai kin ce min komai ba, ai na riga na kaiwa Allah ƙara, zai yi min sakayya da kansa, cuta ce dai kin gama yi min ita". Aliyu ya shigo a lokacin, Inna Wuro ta ɗaga kai ta dube shi tana aikin rumtse ido, ta yarfar da hannu ta ce,"gwara da Allah ya shigo da kai Aliyu, hanzarta ɗauko mota ka kawo bakin ƙofar ɗakin nan nawa, gidan sarkin ɗori zamu tafi tun ban gama shiga uku ba, ta ɓalla min duk ƙafafun nawa biyu, kai baka ji irin azabar da ke ratsa ni ba. waiwaiwai, huhuhu Allah dai ya saka min". Aliyu ya kai dubansa ga Maama wacca ke tsaye tana gyara zaman glass ɗin idonta, fuskarta ɗauke da siririn murmushin ƙeta, a yayin da dogwayen lashes ɗin sama da na ƙasa suka haɗe, kafin ta buɗe su kyawawan chocolate eye balls ɗinta masu ɗauke da ruwa su bayyana. suna haɗa ido da ita tayi ƙasa da kanta tana haɗe pink lips nata, still tana ƙunshe dariyarta. sim sim ta bar bayan Inna Wuro ta nufi hanyar fita Aliyu ya dakatar da ita, ta tsaya tana rumtse idanu kafin ta juyo ta kalle shi. cikin siririyar muryarta me bala'in zaƙi tace,"Uncle ba na sane fa". sai ya kalli Inna Wuro da har yanzu take dirshen a ƙasa, sai matsa ƙafafu take yi a lallai sun karye. "Inna to kinji bata sane". "to dama tsoron Allah take yi da zata faɗa maka gaskiya, ni dai tun da ta riga ta cuceni kaje ka ɗauko mota kawai mu tafi gidan sarkin ɗori tun ban koma amfani da sanda ba, dan ƙarshe dai asibiti su yanke ƙafafun, ni kuwa ina zan so naga ana tura ni a keken guragu". tayi shiru tana girgiza kai alamun takaici ya isheta."sam yarinyar nan bata da mutunci wallahi, ka duba fa Aliyu ka gani an fi ƙarfin awa guda da watsar da ni da tayi a ƙasan tiles ɗin nan, amma kalmar haƙuri ta gagara fitowa daga bakinta. alhalin tun duku dukun safiya aka baro gidan uba aka taho gidan ɗana cin arziƙi, to da yake ma dai ɗan Adam butulu ne, amma babu komai akwai Allah ai". Maama tace,"kiyi haƙuri Inna Wuro". "a'a wallahi ba zai yiwu ki cuce ni ba ki bani haƙuri, ke dai je ki kawai da mugun halinki". Maama ta fice daga ɗakin tana dariya. Aliyu yazo ya kama Inna Wuro don ɗagata, ta miƙe tana faɗin,"ba abin nace zan bawa Zainabu shawara ba tace zata ƙullace ni, ko kuma ta zage ni, amma da sai in ce ku kai yarinyar nan gidan ruƙiya zance na domin Allah kenan". Aliyu yay guntun tsoki,"zancenki kenan aljanu". "to kaji ba, ina kuma ga uwarka na faɗawa. yanzu in ace jikar Falmata ce wallahi kaina tsaye zanje in bata shawarar nan. yanzu kai Aliyu ban da kai ma dai halin uwarka ka yo na rashin son gaskiya tsakani da Allah ai ka san wannan ƴa dai tana da iskokai". yay mata wani kallo yana nufar kujera ya zauna,"babu wani zancen gaskiya tun da ba gani kika yi ta tayar ba". "to Aliyu har sai ta tayar za'a san tana da aljanu, ina batun watsota da suke yi a guje fa?, Kullum fa haka zaka ganta fuuuu kamar guguwa, haba a duba lamarin nan dai. ni ko da kaji na faɗi haka ba wai sonta ne bana yi ba wallahi". Aliyu ya ɗauki remote yana dannawa yace,"to ba wasu aljanu, kije ki duba ɓarna tayi miki". yana yin shiru tai hanyar ɗakinta cikin hanzari tana maganganu. kuma tana shiga ɗakin ta tarar da plastic bucket ɗinta yashe a tsakiyar ɗakin, murfinsa a tsakiyar gado yayin da aka yashe rabin dubulan da alkakin da ke cikin botikin. ta ɗora hannu a saman ka kafin ta zube a gefen gado ta zabga salati. "Jikar Zainabu ko masifa, to wallahi ba zai yiwu ba dole ma ƴar nan ta bar gidan nan yanzu babu ɓata lokaci, tun da dai gida Ɗana ya gina shi ba Zainabu ba, ina dalili jarabar sata har cikin ɗakina". Aliyu na tsaye bakin ƙofa ta kalle shi tace,"ashe kasan hali shiyasa kace in zo in duba dukiyata, to kuwa dai ban yafe ba ka faɗawa Zainabu da shi uban yarinyar". bai kulata ba ya sauke wayar kunnensa ya nufi gadon don tashin Farha, wacca ke ta bacci bama ta san wainar da ake toyawa ba. yasa hannu ya shiga tashinta, ta buɗe ido a hankali, ganinsa yasa ta miƙe zaune babu shiri tana murza idanuwa. Inna Wuro da ke gyara bokitinta tana lissafa dubulan da alkakin da ke ciki tace,"da yake kai ne ai kaga ta tashi, ni kuwa da nake ƴar iska idan na tasheta ai sai dai ta yarfo min zagi. ba abin na bawa iyayenta shawara ba su ƙullace ni, amma wannan ƴa ai da gani ta narki ruwan mahaifa, ya kamata kuma a fita da ita ƙasar waje su fasa kanta su kwashe shi, shi Yusufun da ike karatun likitancin banza da wofi yay ai ya kasa gane ƴarsa ta kwankwaɗi ruwan mahaifa". Farha ta sakko akan gadon tana ƙunƙuni ta fita daga ɗakin. direct part ɗin Ammi ta wuce, tana shiga parlo ta tarar da Ammi na cewa da Maama. "wa ya faɗa miki ana taɓa kayan Inna Wuro, salon dai kija min jarfa. yanzu idan ta fara mita ta dinƙa yi kenan har sai an biyata kayanta, duk abin da kika ga tsohuwar nan ta ajiye a lissafe kayanta yake". Maama ta turo ɗan ƙaramin bakinta, ta warware mayafin jikinta tana fito da uban dublan da alkakin da ta kwaso, ta buɗe leda tana zubawa aciki tana faɗin,"Ammi to ba ita bace nace ta bani sai ta ɗau guda ɗaya tal ta ban, ni kuwa tana fita na ɗauki rabona". Ammi ta girgiza kanta,"to ai kuwa sai kiyi ki zuba a ledar ki ɓoye kafin ta biyo bayanki, don wallahi tazo wajen nan sai dai ku yi asararsa". cikin sauri kuwa ta juye shi cikin leda ta saka a jaka. kuma kamar jira sai ga Inna Wuro ta faɗo ɗakin tana faɗin,"to ina Zainabun?". su ka haɗa ido da Ammi da ke kan kujera tana danna remote wurin sauya channel. Inna Wuro ta banka ma ta harara kafin tace,"ban ce fa lallai sai kin gaishe ni ba. saƙon Amadu nazo isar miki, yace wannan aljanar jikar taki ta tattara komatsanta ta bar masa gida kafin ya dawo, idan kuma kika yi kuskuren da yazo ya sameta acikin gidansa to sai dai kotu ta raba shi da iyayenta, saboda shi dai bakin uwa bai bishi ba da za'azo har gida aci mutuncin uwassa". Ammi tace,"ai dama ba kwana zata yi ba, anjima kaɗan za'a zo a ɗauketa". "to shi yafi dai, yauwa ta bar gidan nan tun ba'a ƙure haƙurin ɗana ba, yo me ma na haɗa da ita da zata zo ɓangare na tayi min sata?, da ike ma dai ina da bala'in haƙuri shiyasa, don ma ban faɗa miki ba ne Zainabu, amma ƴar nan ƙafafuna biyu duk ta karya min, ban da Allah ya kawo Aliyu akan lokaci da ban san wa zai jona ni ba in samu in miƙe, amma dai na dai barwa Allah kawai". Ammi tace,"kiyi haƙuri Inna". "yo haƙuri ai dole tunda ni ba fitinanniya ba ce, kawai dai kija mata kunne kar ta ƙara zuwa gidan nan tunda batta da gado". Ammi tace,"to". "yauwa to sai anjima, zamu je wurin sarkin ɗori da Aliyu ne". "Allah ya sauƙe". "to amin Zainabu, na gode. amma ke ma dai sai kin rinƙa kulawa, in ba haka ba wataran tsaf zata jeho ki daga saman bene, tun naga aljanunta masu wurgi ne". zata fita a ɗakin Maama ta buɗe baki, cikin ƴar ƙaramar muryarta tace,"a dawo lafiya Inna, Allah ya bada lafiya". "amin in ma ba har zuci kika faɗa ba. ƴar banza da wofi me suffar ƴaƴan aljanu, kina fama da ƙaramar murya sai kace kukan mage, Allah ɗaya ma yasan manufar da yasa yayo ki a makauniya, sanyin tafiyar da aka ba ki ai ba'a banza ba, idan kin cuceni kin tsira kika cuci wani kafin kiyi taku biyu ai ya danƙo ki yaci ubanki. Allah dai ya jiƙan Uwarki ya gafarta mata, amma wannan halin dai ba nata ba ne sam". ta fita tana ta zazzaga masifa, Maama da Farha kuwa sai dariya suke yi, bayan fitarta sai ga Ayan ya shigo, ya zauna kan kujera, bayan sun gaisa da Ammi take ce masa,"ni ai fushi nake da kai, yaushe rabon da kazo ka gaida ni?". yana murmushinsa me kyau yace,"Ammi tare da Abie muke zuwa office shiyasa, kuma yau ɗin mun makara wajen zuwa gun Ummi ne shiyasa ban shigo ba a lokacin". sai ya kalli Maama yace,"ki taso mu tafi". Ammi tace,"da wuri haka?, ba zai bar min ku sai dare ba?". "Ammi zamu je dubo Maman su Antynmu ne". Ammi tace,"Allah sarki wannan mata dai tana shan wuya, Allah ya kawo mata sauƙi". "amin". Ammi ta rako su har bakin gate, Farha kuwa sai da ta raka su har bakin motarsu, har sai da suka gaisa da Turaki sannan ta juya ta koma gida, suna yiwa juna bye bye ita da Maama. "Abie kun gaisar min da Ummin?". Maama ta tambayi mahaifin nata a lokacin da motar su ke hawa kan titi. Turaki ya dubeta ta cikin mirror yace,"mun faɗa mata Maama". sai kuma yace,"Maama ko dai muje asibiti?". ta bar abinda take yi ta kai dubanta gare shi tace,"saboda me Abie?". yay ɗan jim kafin yace,"ina ga kamar ayi miki aiki a maƙogoronki, Maama muryarki tayi ƙanƙanta da yawa, wanda ya saba da ke ne fa kaɗai yake iya jin me kike cewa farat ɗaya". tayi knodding kanta tare da cewa,"Abie idan hakan yana damunka ayi min duk abin da kake so". ya numfasa kafin yace,"ba komai zamu ci gaba da zuwa gaban ka'aba muna roƙon Allah". tafiyar tasu tayi nisa acikin motar, yayin da suke hira jefi jefi, har sanda Turaki ya tambaye su,"ina da ina zan kai ku?". da yake duk friday haka yake kai su gidan ƴan uwa da abokan arziƙi ziyara, ko kuma wani lokacin su yini shi da Ayan a maƙabarta wajen Fullo da Maama, sai in yamma yayi yaje gidan su Yusuf wajen Ammi ya ɗauko Maama da suke sauketa acan tun safe. Ayan yace,"Abie muje gidan Anty Maijidda, kwana biyu bamu je ba, kuma last zuwa da muka yi mun barota bata da lafiya". Turaki ya amsa masa da to, sai da suka fara tsayawa a hanya suka yiwa ƴaƴan Maijidda siyayya kafin suka ɗauki hanyar gidanta. Turaki ya ba su kuɗi masu yawa su kaiwa Maijidda kamar yanda ya saba duk sanda ya kawo su. sai da yaran suka shafe kusan rabin awa kafin su fito tare da Maijidda wacca ta rako su. hangota yasa Turaki fitowa daga mota, ya ƙarasa ƙofar gidan suka shiga gaisawa da ita, tana ta yi masa godiya akan irin aiken da yake bayarwa akawo mata ita da yara. Maama na kama hannunsa ta riƙe yake tambayar Maijidda yaranta, ganin yau bai ga ko muutum guda ya rako su Ayan ba, da kuma ɗan ƙaramin ɗanta da ya zama kamar abokinsa, kasancewarsa irin yaran nanne masu saurin sabo. Maijidda tace,"wallahi kaga wata tahfeez aka buɗe a bayan layin nan, shine aka kaisu can". "har friday suke zuwa kenan?". Turaki ya tambaya. tace,"ehh juma'a zuwa lahadi, tun safe sai yamma". "masha'Allahu, Allah ya bada ilimi me albarka". ta amsa da,"amin amin". "to bari mu wuce, a gaida min da abokina". tayi ƴar dariya tana faɗin,"Musaddiq sarkin magana, zai ji insha'Allahu, da sun samu hutu ai zan kawo muku su, sai su yini". sai ta saka hannu tana share ƙwallar fuskarta tace,"Allah ya jiƙan Fillo". Turaki da Ƴaƴansa jiki a sanyaye suka amsa da,"amin ya Rahman". tukunna suka yi mata sallama suka wuce, inda suka ɗauki hanyar gidan Me Martaba domin zuwa duba Fulani Azima, wacca har yanzu ta nan kwance rai a hannun Allah, gaba ɗaya halittarta ta sauya ta koma tamkar ta ƙadangare, sai ka rantse da Allah ba mutum ba ce tun asali, wasu gashi sun tsatstsafo mata a jiki, idanunta sun yo waje ƙwayar kamar zata faɗo ƙasa, bakin da hancin sun shafe a waje ɗaya, kai abun dai babu kyan gani da kwatance. ga duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata ya zubar mata da hawaye idan bai san abun da ta shuka ba, wanda kuwa yasan me ta aikata muddin ya ganta sai jikinsa ya mutu gaba ɗaga, tsoron Allah ya ƙara shigarka, kaji gaba ɗaya duniyar ta fita a ranka, balle kuma kaji kana son sha'awa ko mallakar abun da ke cikinta. Maama da ke kallon bakin titi tace da Turaki,"Abie don Allah zan bayar da sadaƙa". Turaki yay parking a gefen hanya, ya zaro ɗari biyar a aljihunsa ya miƙa mata ta karɓa sannan ta buɗe mota ta fita. "na gode Abie". ƴar tafiya kaɗan tayi daga inda motar tasu ta tsaya, ta tsuguna agaban almajirin ta saka masa kuɗin acikin robarsa tare da faɗin,"Baba kayi adu'a Allah ya kai ladan ƙabarin mahaifiyata". tsohon ya shiga kwaranyo mata adu'a iya adu'a, daga mahaifiyartata har ita kanta da sauran ahalinta. ta ɗaga glass ɗinta tasa tissue ta goge hawayen da ya cika mata ido, kafin ta yunƙura ta miƙe jiki a sanyaye ta bar wajen nasa. tana cikin tafiya tayi karo da mutum, ba wai don bata ganin gabanta ba, sai don hankalinta da ya bar jikinta a lokacin. ta sunkuya ta lalubo gilashinta ta saka, sannan ta kalli mutumin da ta tsorata da ganin nasa, tayi saurin matsawa gefe tana ce masa,"kayi haƙuri don Allah". muryartata ƴar ƙarama kuma ƴar siririya me zaƙi ta fito ta shiga kunnen Amir ta ratsa jikinsa, ya kasa ƙifta idonsa akanta, kallon mamaki kawai yake yiwa yarinyar gabansa, wacca gaba ɗaya yasan bata kai shekara sha bakwai ba. abun da ya sani shi ne ya san wannan halittar, sai dai bai yi tsammanin zai sake ganinta a haka ba duba da tsawon shekarun da aka ɗauka, ya sani Fillo na da ƙaramin jikin da ba lallai shekarunta masu yawa su nuna a jikinta ba. to amma duk da haka abin da matuƙar mamaki ace ita ce a gabansa haka, babu wani alamar girma a tare da ita, after all shekaru goma sha bakwai ɗin da ya ɗauko bai ganta ba. jikin Maama na rawa ta daɗa ce masa,"zan wuce". Amir yay ajiyar zuciya bayan ƙare mata kallon tsab da yayi, tabbas wannan ba asalin Fillon da ya sani ba ce, wannan me kama da ita ce sak babu wani banbanci, sai dai in ace banbancin halayya, me hakan ke nufi kenan?, wata ce photocopy of her ko kuma ƴarta ce?. lokaci ɗaga matacciyar zuciyarsa da babu tsoron Allah acikinta taji ta kwaɗaitu da yarinyar, yaji sha'awarta ta ratsa duk wani ɓargo na jikinsa, take kuma ya fara tunanin ta yacca za'ai ya shiga rayuwarta a irin matsayin da ya saba shiga rayuwar sauran ƴan mata?, ya shiga rayuwarta kamar dai yanda ya shiga rayuwar me kama da ita. _(hmm Allah ya kyauta, ya kuma kiyashe mu daga sharrin zuciya, dama haka abun yake, ance wasu ko zasu je lahira su dawo halinsu ba zai taɓa canjawa ba, sai dai muyi adu'ar Allah ya tsare daga sharrin mugwayen mutane.)_ sai ya sauke idonsa akansa yana kallon jikinsa, wannan sam ba wancan Amir ɗin ba ne me ji da tashen ado da ƙwalisa a zamanin baya, wannan wani Amir ɗin ne na daban, wanda halittarsa ta sauya tun yana cikin prison, ya dafe ya zama mugun baƙi, yay wata muguwar rama kamar me cutar S, ya haɗa uwar ƙasumba a fuska kamar dodo, haka kansa ma ya tara uban gashi kamar mahaukaci, duk yayi duƙunduƙun kayan jikinsa duk a yayyage, ga uban ɗoyi da ke tashi a jikinsa kana ji kasan kwanan bola yake yi. warin jikin nasa ya doki hancin Maama, take ta duƙa a ƙasa saboda aman da ya taho mata, ta shiga kyalaya amai kamar hanjin cikinta zasu fito. Amir ya duƙa a gaban nata shi ma, zuciyarsa na harbawa kaɗan kaɗan, abu ɗaya yake tunani wanda yake jin har in ya rasa zai iya shiga wani hali, halin da yafi wanda yake ciki muni, muddin bai samu ya kusantu da yarinyar ba zai iya rasa lafiyar jikinsa. don haka zuciyarsa na ingiza shi ya kai hannu zai taɓa Maama tayi saurin miƙewa tana ja da baya. "mene haka?, na fa baka haƙuri". ya miƙe yana lashe leɓe, a hankali yace,"Ki tsaya na taɓa jikinki don Allah ko ya ya ne, idan na taɓa zan haƙura na barki ki tafi". Maama ta shiga girgiza masa kai tana ja da baya, yanzu kam ya gama tabbatarwa ba Fillon da ya sani bace, kuma ko da ace ita ɗin ce ma ba zata taɓa gane shi ba, don kwatakwata ya fita a Amir ɗin da mutane suka sansa, shiyasa har yanzu ma Ƴan sanda suka kasa kama shi bayan wani laifin da ya ƙara aikatawa lokacin da ya fito a prison. "sau ɗaya yarinya, sau ɗaya kawai za ki barni in taɓa ƙirjinki, ki tausaya min wallahi a bola nake kwana". yayi maganar da kana ji kasan ƙwaƙwalwarsa ta fara taɓuwa, lokaci kaɗan ya rage ya fara hauka tuburan. san da Maama ta kai ƙarshe ajikin wani ƙarfe, lokacin Ayan da Turaki suka iso waje, tana ganinsu ta ƙwala kiran Abie, Ayan yasa hannu ya juyo da Amir, da yake irin tsayin mahaifinsa yayo sai ya zamana tsayinsa yay daidai da na Amir ɗin. cikin zafin nama Ayan yasa hannu ya wanke fuskar Amir da zazzafan mari, ya damƙi ƙwalarsa yana jijjiga shi har sai da ya kai Amir jikin ƙarfen da ke bayansu ya buga kansa a jiki. "kai ba mahaukaci ba ne zuciyata ta faɗa min hakan, ubangiji yayi min baiwar gane mutane a kowanne hali suke ciki. sai na kasheka tun da ka yi yunƙurin taɓa min ƙanwata". ya faɗa yana ta buga kan Amir ajikin ƙarfen, Turaki kuwa na gefe rungume da ƴarsa a jiki zuciyarsa sai zafi take yi masa, idan har yace zai kai hannu ya taɓa Amir to bai san me zai ya faruwa ba, don wataƙila kafin ƴan sanda su iso wajen ya kashe shi. ɓangaren Amir kuwa abu guda ɗaya ya sani, ba zai taɓa iya ƙwatar kansa ba a hannun Ayan, bai da wannan ƙarfin ko kaɗan, hatta ruƙon da yaron yay masa ji yake kamar an jona masa electricity. zuwan police wajen suka ƙwace Ayan da ga kan Amir wanda yake ƙoƙarin kaiwa ƙasa. banda haki babu abin da Ayan ke yi, idonsa yay jawur kamar bana ƙaramin yaro ba, police suka kama hannun Amir suka saka masa ankwa, sai a yanzu idonsa ya kai kan Turaki, yaji gabansa yay mugun faɗuwa, ya wurga ido ya ƙara kallon Ayan, jini ba banza ba, don lokaci guda ya tuna da mugun dukan da ya sha lokacin da suka yi kidnapping Fillo. don haka tsananin tsoro ya kama shi, ya tabbatar yanzu idan Turaki ya gane waye shi to sai dai waninsa, dan haka gwara yabi ƴan sandan, duk runtsi zai fito ya sani. police su ka kama Amir suka saka shi a mota suka tafi. bayan su Turaki sun dawo daga dubiyar Fulani Azima, direct gidan ya wuce da yaransa, in da anan suke cin abincin dare duk friday. ana jin tsayuwar motarsu Boɗejo tace,"to ga kajin nan sun iso". Mum na zaune kan kujera, da jaririyar Nihal a hannunta ta gama yi mata wankan yamma, tayi murmushi da jin furucin Boɗejon. Turaki ya shigo tare da yaransa, waɗanda sai da suka fara zuwa ɓangaren Baffa suka gaida shi. jikokin gidan duk suka yi wajensa su na yi masa sannu da zuwa, ya ɗauki ƴar gidan Zaytuna me suna Aisha. Maama tayi jikin Boɗejo tana cewa,"nayi kewar tsohuwa". Boɗejo tace,"kinga ni kuwa yau ba wanda nayi kewa a cikinku, ko babu komai bakina da na Kakarku luff babu rabon faɗa". "ai kuwa tun da kika faɗi haka ba zan ba ki abin da na taho da shi ba". Boɗejo da a yanzu ta ƙara zama tsohuwa tukuff ta janyo Maama jikinta tana faɗin,"haba ƙawata ƴar mutunci yi haƙuri, ai yanda bana iya fita inci ni ɗaya ban rage miki ba haka kema na sa ni". Maama ta dubi Turaki da ya zauna akan kujera su na gaisawa da Mum, tace,"Abie ka ɗauko min leda ta?". ya kalli gefensa yay mata nuni da ledar, sannan ta miƙe taje ta ɗauko, tazo ta zauna ta buɗe ta ɗauko dublan ɗin ciki tana bawa Boɗejo, wacca ke tambayar aina suka siyo shi, ita kuma tana bata labarin yacca ta kwaso shi a ɗakin Inna Wuro. da daddare bayan sun gama cin abincin dare, suka fara haramar tafiya gida. Mum ta juye musu sauran teba da miyar gandar da akayi a flask tace su tafarwa da Ilham. ko da suka koma gida Turaki ajiye su yay ya ƙara fita, ya tafi siyo magungunan da likita ya rubutawa Ilham, wacca likitoci suka yi iyaka bincikensu akan rashin haihuwarta, suka tabbatar da cewa da wuya idan ta haihu sai in kuma wani iko na ubangiji. tana zaune a parlo tana kallo su Ayan suka shiga, tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kanta taci gaba da kallon film ɗin da ake yi a mbc action. ganin bata kula su ba Ayan yace,"Anty daga wurin Maminki mu ke". furucin nata yasa ta mayar da hankalinta gare shi tana jin cewarsa. "ya ku ka ƙara samun yanayin jikin nata?". Ayan yace,"ba sauƙi, sai tsanani da ya ƙara. yau da muka je jini yana ta zuba ta duburarta, sai botiki aka tara mata ma a wajen, ta ƙara motsewa babu kyan gani". Ilham ta saka kuka sosai tana kifa kanta akan ƙafafunta, tsawon minti biyar tana kuka kafin ta ɗago tare da ɗaukar wayarta ta shiga kiran lambar Turaki, sau kusan sau biyar kiran yaƙi shiga, ana ta faɗa mata not recherble. ta kalli agogo taga ƙarfe tara da rabi a lokacin, ta miƙe ta wuce ɗaki, ba jimawa sai gata ta sakko sanye da hijab. ta kalli yaran tace,"idan Babanku ya dawo kuce masa na tafi wurin Mami. ku faɗa masa ina ta kiran wayarsa taƙi shiga". su ka amsa mata,"to, a dawo lafiya". "Allah yasa". ta faɗa tana nufar ƙofar fita, maganar Maama ta dakatar da ita,"Anty ko za ki tafi da tebar?". ta kalleta tace,"Mum ce tayi?". "ehh". "Maama ba zan iya ci ba, ku cinye idan kuna so. akwai pancake a kitchen na ajiye muku, ba kwa buƙatar wani abu?". suka haɗa baki wajen faɗin,"ba ma buƙatar komai Anty". ta kalli Ayan tace,"saura ka sakata kuka". yay ƴar dariya yace,"Anty wai haka kawai nake sakata kukan?, sai fa tayi min ba daidai ba". tayi murmushin ƙarfin hali kawai ta fice ba tare da ta ƙara ce musu komai ba. sai wajen goma Turaki ya dawo gida, yana shigowa parlo ya tarar da Ayan akan Maama yana zazzaga mata masifa. "dilla Malama bani abu na, na rantse da Allah daga yau ma kika ƙara taɓa min kaya sai na faffasa miki baki, kin dai ji na faɗa miki". ya faɗa yana sakin ƙwafa me ƙarfi, sai kuma ya saka hannu ya dungure mata kai glass ɗin idonta ya faɗi, a rikice ta durƙusa tana neman glass ɗin. ta lalubo shi da ƙyar ta saka, ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana hura hanci tace,"kuma wallahi idan Abi ya dawo sai na faɗa masa". tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta wuce, ya fincikota yana faɗin,"ɗauko min kayana ki bani". ta fizge tana faɗin,"ba zan ɗauko ba ɗin". a zuciye Ayan ya ɗaga hannu zai mareta muryar Turaki ta dakatar da shi. "Ayan!". ya kira sunansa da ƙarfin sauti wanda hakan yasa Ayan ɗin nutsuwa. "me ta taɓa maka da ma?, kai da baka da haƙuri, na faɗa maka bana son wannan zafin zuciyar taka, idan ƙanwarka bata taɓa abinka ba na wa kake so ta taɓa?". Ayan na faman huci yace,"to Abie ita ce komai ta ɗaukar min sai ta lalata, kalla fa yanda ta fasa min sabon earpod ɗina, kuma shekaranjiya da Uncle Bello yazo ya ban shi". yay maganar yana nunawa Turaki. "kuma shi ne saboda rashin tunanin akan abun duniya zaka ɗaga hannu kace zaka mareta?, ranar da bana raye a haka zaka kula da ita?". Ayan yay shiru bai ce komai ba, ya kumbura yayi fam yana tunanin abin da zai yiwa Maama ya huce. "garin ya kika fasa masa abun sa?". "Abie ba na sane Allah, nazo sakkowa daga upstairs na zame shi ne ya faɗi daga kunnena". Turaki ya jefawa Ayan key ɗin motarsa yace,"ka je mota ka ɗauko nawa". yana rufe baki Maama ta ce,"Abie ni fa?, Farha ta karɓi nawa aro kuma ba zan iya cewa ta ba ni ba". "ki bari zan siyo miki wani Maama". washe gari da safe wajen ƙarfe takwas hayaniyar yaran nasa ta tashe shi daga bacci, ya tashi ya shiga toilet yay wanka, bayan ya fito yazo ya tsaya jikin window yana hango su. a field suke su na buga basket ball, Ayan na ta yawo da ball ɗin yana dariya, ita ma Maama na ta yawo wajen ganin ta kare ball ɗin daga shiga cikin raga, sai dariya take yi tana cije leɓenta, motsi kaɗan sai ta gyara zaman glass ta karyar da wuya alamun ta fara gajiya. duhun garin kuma ya fara hanata gani sosai duk da medical glass ɗin da ke sanye a idon nata. ta durƙusa tana nishi, Ayan ya jefa mata ball ɗin ta ƙwalu a saman kanta, ya kwasa da gudu yana faɗin,"idan kin isa ki biyo ni ki rama ƴar makauniya". haka yake yi mata sau tari, sai suna waje suna wasa sai ya tsokane ta ya gudu in dai yasan akwai hadari. zafin ƙwala ball ɗin yasa Maama miƙewa ta ɗauka ball ɗin, ta ƙanƙance ido ta cikin glasses ɗin sannan ta saita Ayan da ya juyo yana yi mata gwalo, ta ɗaga ball ɗin ta jefa masa, ai ko cikin sa'a sai ga ball ɗin a fuskarsa, ta buga tsalle tare da ihu tana faɗin,"wooo ai dai na rama". shi kuma ya dafe goshi yana faɗin,"yasin sai na faɗawa Abie ciwon idon ƙarya kike yi, ya daina asarar kuɗinsa a siyan glass kina gani tarr". lokacin kuma hadari ya ƙara ɗinkewa, lokaci ɗaya garin yay baƙiƙƙirin, sai ya zamto Maama bata iya ganin komai hatta da gabanta, hankalinta ya tashi ta ɗaga hannu ta shiga laluben gabanta tana kiran Ayan. "Ayan please ka zo, kar ruwan ya sauko, bana gani fa". tana rufe bakinta taji ana yi mata cakulkuli ta baya, tai saurin juyowa don kama shi, sai dariyarsa ta jiyo yana ƙara yi mata cakulkuli ta bayanta da ya ƙara zagayawa. "yarinyar ki bar min agogon da Ummi ta bar miki sai in taimaka in yi miki jagora". "to ai tace nawa ne ni ɗaya". "to shikenan sai ki taho da kanki". taji yayi shiru babu motsinsa, taita ƙwala masa kira yana gefenta a tsaye yay mata shiru, sai kawai ta fashe da kuka tana ta ƙwala masa kira. Turaki dake hango su yana murmushi, ya faɗa tunanin wani moment na su shi da Fillo. kamar haka suna tare a field ɗin suna yin wasan ƴar burin burin, ya ɓace mata tana ta kiran sunansa yay shiru yaƙi amsawa, kuma a sanda ta kunce ɗaurin idon taga bata gansa ba sai ta saka kuka. kamar dai yanda Maama ke yi a yanzu, sai ya tuna yacca ya dinƙa jin sautin kukan nata na dukan zuciyarsa a lokacin, amma duk da haka bai fito daga ɓoye mata ɗin da yay ba sai da ta shiga parlo. ta hau upstairs ta gama lalubensa a can baya nan sai ta dawo ƙasa, shi kuma a lokacin ya shigo parlon, suna haɗa ido da ita ya kwashe da dariya sosai ganin yacca hawaye duk ya ɓata mata fuska. kuma ganin nasa yasa ta ɗauki pillon kujera ta biyo shi, suka shiga zagayen kujerun parlon tana faɗin,"Allah ni ka tsaya in ƙwala maka". ya tsaya daga bayan babbar kujera yana haki yace,"saboda me to?, wannan ai mugunta ce, kawai sai ki kama ƙwala min pillow bayan kin san da zafi". "ni dai sai na ƙwala maka". ta faɗa tana turo bakinta gaba cikin shagwaɓa, tare da dukan ƙafafu a ƙasa hawaye na sakkowa ta ido ɗaya. sai ya kama ƙugunsa yana kwaikwayon yacca take yi da idanu, hakan ya daɗa tuzurata ta sa kukan shagwaɓa sosai. cikin dabara ta dinƙa matsawa zata zagaya ta bayan kujerar da yake tsaye, fahimtar hakan yasa shi barin wajen da gudu dariyarsa na ƙaruwa sosai. "to wai me nayi miki za ki ƙwala min abu?". ta ɗage gira duka biyu ta ce,"ba kai ba ne ka gudu ka barni ka saka ina ta nemanka ban ganka ba". "to sai ki bari naki turn ɗin yazo sai ki rama, amma ni dai ba za ki ƙwala min wannan pilon me zafi ba". "ni dai Allah sai na ƙwala maka ko kuma ka ban haƙuri". "tabɗijam sannu sara me baƙar takashi, kawai sai in kama ba ki haƙuri kina ƴar ƙarama da ke, bayan in da nayi haihuwar ƙauye da nayi jika da ke". abin da ya faɗa yasa ta cije leɓe tana tunanin abun da zata yi masa, bata ankara ba taji ya ƙwalo mata pillow a saman ka. ai kuwa sai ta ƙara fyallawa da gudu zata kamo shi, suka ci gaba da zagaye parlon cikin guje gujen su, shi yana ƙyalƙyala dariya ita tana cewa Allah sai ta rama, har sai da ta koma roƙonsa da Allah ya tsaya ta rama. sai ya tsaya yana haki yace,"to naji za ki rama, amma kar kiyi min da zafi". "ehh naji a hankali zan maka". ta faɗa tana jijjiga ƙafa ɗaya. sai ya sake yin dariya yace,"habawa yarinya ni za ki yiwa wayo". yana faɗar hakan iska tayi blowing laluben parlon ya rufe masa fuska, kafin ya buɗe tayi tsalle ta dira akansa, ta cukwikwiye shi suka faɗa kan kujera tana ƙwaƙwƙwala masa pilon, sai da ƙyar ya iya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa. "sai ance kin iya mugunta kice ke ba haka ba". "ai har sai ka ban haƙuri zan ƙyaleka". "ni fa ba zan bawa ƴar ƙaramar yarinya haƙuri ba". suka shiga kokayawa har sai da tayi nasarar gantsara masa cizo a kunne, zafin cizon ya ratsa shi ya ƙwala ƙara yana faɗi,"i am sorry". ta ƙara kai masa cizo a hanci tana cewa,"ba haka ba, sai kace don Allah". ai kuwa ya ƙwalla ƙara da ƙarfi yace,"Don Allah kiyi haƙuri Fulani Nah, haba Fulanin Turaki ƴar albarka". "waye yay nasara?". "kece Anty Fulani". ta ɗaga shi tana dariya sai haki take yi, tana tafa hannu tana cewa,"yau na zama Anty Fulani". sai kuma ta faɗa saman ƙirjinsa ta tura hannu cikin rigarsa tana yawo da shi akan ƙirjinsa. cikin muryarta mai sanyi da ratsa dukkan jijiyoyin jiki tace,"Jannaty idan muna wasa karka ƙara ɓace min irin haka, tsoro yana kama ni, bana so in ji bana tare da kai". ta faɗa tana kifa kyawawan idanuwanta cikin nasa, idanun da suke ɗauke da guntun ruwan hawayen kukan da tayi. "ba zan ƙara ba insha'Allahu Fulani nah, am sorry kin ji, i will always be with you". sai ya rumtse idonsa yana tunawa da kyakykyawan murmushin da ta sakar masa a lokacin, ya tuna yacca ta shigar da jikinta jikinsa ta ƙanƙame shi tare da faɗa masa kalmomin da a duniyarsa yafi so yaji sun fito daga bakinta. "i love you Jannaty, ina yi maka son da har bar san irinsa ba Jannaty, Allah ya barmu tare har abada". lokaci ɗaya yaji idanunsa sun cika da ruwa, ya dafe saitin zuciyarsa da yaji tana yi masa zafi. ya tuna bayan rasuwar Fulani sai da yay watanni kafin ya dawo cikin hankalinsa, hatta deppression sai da ya kama shi, ban da ma Allah yasa ta bar masa yaran nan da tuni zuciyarsa ta buga shima ya mutu. a hankali ya furta,"I have missed you, I am always missing you Fulani Nah, i am missing you like crazy". Muryarsa ta fito kamar zai fashe da kuka, duk da cewar hawaye tuni sun sauka saman kuncinsa masu zafi. muryar yaransa da ya jiyo su na nufowa ɗakinsa yasa yay saurin saka handky ya goge hawayen. suka shigo ɗakin su na zama kan kujera, ya juyo yana kallon su, yaji wani sanyi ya ratsa ƙasan zuciyarsa, a yanzu kaf duniya baya tunanin akwai wani abu da yake ƙauna sama da yaransa, sama da su biyun nan, babu shi. ya taka ya ƙarasa ya zauna a tsakiyar su, yaran suka sarƙafo da hannayensu ta wuyansa. "good morning Abie". sai Maama ta miƙe ta tsaya a gaban su. "this way! good morning Mr Sir". ta kwatanta gaisuwar a irin yanda suka taɓa ganin wani vedion Fillo da Turaki ya nuna musu, lokacin suna honeymoon a Ausburg, hakan yasa suka ƙyalƙyale da dariya dukansu, har sai da Turaki yaji damuwar dake ƙasan ransa na bin iska. lokaci ɗaya dariyarsu ta mutu a san da suka jiyo sautin muryar Fillo ya karaɗe cikin ɗakin, ta cikin audio record ɗin da ta taɓa yi tana karatun alƙur'ani. Maama tasa hannu a laptop ɗin ta kashe, ta juyo tana kallon mahaifinta da ya tusa hannunsa cikin sumar kansa, Ayan kuma na hawaye, sai kawai ita ma hawayen ya sakko mata, ta kifa kanta akan laptop ɗin da hoton Fullo ya bayyana akan screen ɗin. muryarta ta fito gwanin ban tausayi da cewa,"Allah ya jiƙanki Ummina". Ayan ma yace,"Allah ya gafarta miki Ummi". Turaki yace,"Allah yasa kina aljannah Halima". ya faɗi sunan nata da zai ce karo na biyu kenan da ya taɓa kiranta da shi. "Abie when zamu je taraba mu gaisar da Granny?". Ayan ya tambaya yana kallon mahaifin nasa. "yaushe hutun ku zai ƙare?". Maama tayi karaf ta ce,"2weeks reamaning". ya sauke numfashi kafin yace,"ku haɗa kayan ku sai mu wuce in Allah ya kaimu gobe". "photocopy of me". Turaki ya jiyo sautin muryar Maama na faɗin hakan, ya ɗaga kansa yana kallonta, ta kafa hoton Fullo a gaba tana kallo. "Abie ka taso muyi break fast". cewar Ayan da ke tsaye bakin ƙofa. "takeaway zamu yo ko mu tafi wurin Mum? tunda Anty bata nan". Maama tayi saurin tashi tana cewa,"Abie mun dafa ni da Ayan, tun saven o'clock muka gama, mun dafa maka favorite naka kunun shinkafa da ƙosan bread". da sauri Turaki ya miƙe cikin tsananin farin ciki, yana ta sakawa yaran nasa albarka, daga bisani suka fita cikin farin ciki zuwa downstairs domin yin breakfast. _Sauran rayuwar Turaki da Yaransa, Da rayuwar Amir, da Rayuwar Fulani Azima duka na barwa tunanin ku._ *THE END* *Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!* _*A yau fri 07/10/2022 muka kawo ƙarshen labarin LULLUƁIN BIRI, Alkhairan da na rubuta Allah ya haɗa mu a ladan, kurakuran da suke ciki Allah ya yafe min tare da ku da ku ka karanta.*_ _*Godiya mai tarin yawa da masoyan rubutuna a duk inda suke, waɗanda na sani da waɗanda ban sa ni ba, Musamman waɗanda Allah yake bawa ikon bibiyata a ko da yaushe, it really means a lot to me, Allah ya bar ƙauna tsakanina da ku, Allah ya faranta muku duniya da lahira.*_ _sannan ina me ƙara baku haƙuri da ta'aziyya akan rashin Maama da Fulani da muka yi. Babu yanda muka iya, adadin yanda ubangiji ya ɗibawa rayuwar bawa dole idan lokaci ya cika sai an tafi, duk soyayyar da muke yiwa mutum bamu kai yacca ubangiji ke son bawansa ba, illa iyaka mu bi mu mutum da kyakykyawar adu'a._ _hakana waɗanda ba su ji daɗin yacca asirin Fulani Azuma bai tonu ba, ina so ku tuna ko a rayuwarmu ba ko da yaushe asirin macuci ke tonuwa ba, wata shari'ar sai dai a lahira!_ _Sai mun sake haɗuwa da ku a sabon littafina in Allah ya kai mu da rai da lafiya._ _masu tambayar sunan sabon book ku dakace ni a status ɗina don har yanzu ban gama yanke sunan labarin ba, sai dai abu ɗaya da na sani zai zo ne ana kuɗi kan naira ₦500, kuma wataƙila a Arewabooks kawai zan ɗora shi amma dai ban gama deciding ba, kawai dai waɗanda basu da account a ArewaBooks kuyi ƙoƙarin mallaka sai kuyi following ena acan._ _Nagoode! Nagoode!! Nagoode!!_ Taku har kullum. *Halimahz* _(Anyway)_ _kuyi min dropping ra'ayinku game da labarin nan ta wannan number 07018098175 , insha'Allahu idan na sami lokaci zanke dubawa a hankali ina baku amsa._ _Allah ya sadamu da alkhairinsa, a yafe ni don Allah, sai an ajiman ku._ *Tarin godiya tare da jinjina ga:-* 1-Muhammad Kareem 2-Abbas Haruna 3-Mu'az 4-Nazifi Yareema 5-Abubakar Saleh 6-Abubakar Saraki 7-Anty Nice 8-Maryam Jam'are 9-Mum Sayyeed & Noor 10-Ummu Abdallah 11-Anty Bilqees 12-Ummu Adnan 13-Gamji Book Store 14-Halimahz Palace 15-Ummu Nabil 16-Nana Halima 17-Fatima S Haruna T/fulani 18-Ramat Novels facebook 19-Masarautar Billyn Abdul 20-Taskar Littafan Hausa 21-Nuraddeen Light 22-Surayyahms 23-SisNah 24-Matan Buri Fans 25-Ummu Nabil Novel groups 26-Basheer S Basheer 27-Surajo Salman _Kuna da adadin yawan da idan na tsaya lissafo ku sai mun ɗauki sabon chapter, amma ku sani kowannenku na raina, kuma kowanneku bani da bakin godiya gare shi sai dai adu'ar samun Aljannah._ *For gyara ko shawara am available ta number na da ke sama.*