11/12/2021 脿 11:27 - Les messages et les appels sont chiffr茅s de bout en bout. Aucun tiers, pas m锚me WhatsApp, ne peut les lire ou les 茅couter. Appuyez pour en savoir plus. 01/01/2022 脿 11:29 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *87-62-53-02* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai *Sajida & Samira*._ *Lu'u lu'u*& *Wata kokowar* *Ga kad'an daga abinda labarin ya k'unsa* *1* *K'ASAR TEXANDA* *09/07/2000* Shekara ta 2000 (dubu biyu) ita ce shekarar da wasu suka dinga farfagandan cewa za'a tashi duniya, sai dai lamarin Ubangiji ya fi da haka, dan a lokacin da ake taradaddin za'a bar duniyar, a lokacin ne kuma wasu ke zuwa duniyar, wasu kuma a lokacin suke bayyanuwa a duniyar ma, daga ciki kuwa akwai bayyanar cikin *haske marar iyaka* ga Juman. *MASARAUTAR KHAZIRA* A hankali ta bud'e idonta akan rufin d'akin mai kalar sararin samaniya, lumshe su ta sake yi sannan ta sake bud'ewa dai a kan rufin, cikin nauyin jiki ta juyar da kan ta b'angaren da take da tabbacin nan sarkin na ta ke kwantawa, kasancewar ta mace ta farko a gareshi saidai akwai k'wark'warori da yake zuwa garesu duk sanda ya so. Wayam ta ga inda yake kwancin wanda hakan ya tabbatar mata da lallai ya kai wa wata baiwar ziyara. A sanyaye ta mik'e zaune akan gadon tana mayar da dogon gashinta baya, dafe goshinta tayi a hankali ta shiga tariyar mafarkinta, ko kuma tace mafarkanta dan yanzu kam abun har ya fara zama mata jiki, wata hud'u kenan da take yawaita wad'anan mafarkan, indai har zata rintse idonta da sunan bacci, to tabbas zatai mafarkin wannan yarinyar mai abun al'ajabi. D'aga kan ta tayi tana huro iska tare da mik'ewa tsaye, wasu sauk'akk'in takalmi ta saka dake gefen gadon, hannu ta zura ta d'auki doguwar rigar baccinta fara tas mai zubi da alkyabba ta saka ta nufi hanyar fita, a falo na farko babu kowa babu komai sai kayan d'akin da suka k'awatashi, tana bud'e d'aya k'ofar dogarin dake tsaye yayi saurin sunkuyar da kan shi k'asa, ba yabo ba fallasa ta kalleshi tace "Ka je b'angaren hadimai ka kira min *Habbee*." Sake sunkuyawa yayi yace "Angama sarauniya ta." Falon na farko ta dawo ta zauna k'afa d'aya kan d'aya tana jiran isowar Jakadiyar ta ta da tafi aminta da ita, bugu da k'ari suna sirri su kashe su binne a tare. Jim kad'an sai ga dogarin ya k'wank'wasa k'ofar tare da bud'ewa a hankali, tsaye yayi gaban k'ofar ya rusuna yace "Sarauniya ta, Jakadiya Habbee ta amsa kiranki, tana neman izinin k'arasowa gareki?" Da hannu ta masa alamar za ta iya shigowa batare data kalleshi ba, juyawa yayi rike da doguwar sandar shi, sakan (second) k'alilan dattijuwar ta shigo da girmamawa da kuma rusuna kan ta k'asa, saida ta zauna k'asa gabanta tace "Uwar-gijiyata, fatan tsawon rai da lafiya d'orarriya, na zo da hanzarina domin son sanin abinda ke damun sarauniyata da har ya hanata bacci a tsohon daren nan." Sauke k'afarta tayi daga kan d'ayar sannan ta d'ora gwiwar hannayenta a kan cinyoyinta ta tallabe hab'a, kallon Jakadiyar tayi cike da damuwa da alhini tace "Jakadiya." Da sauri ta amsa da "Na'am ranki shi dad'e." A sanyaye tace "Ina shiga damuwa sosai akan mafarkin nan nawa, gashi malaman gidan abun bauta ma sun kasa fassara min mafarki na, shi ne dalilin da yasa na kiraki dan ki bani shawara, me ye abun yi?" Sunkuyar da kai ta sake yi ba tare da sun had'a ido ba tace "Uwar-gijiyata indai har yanzu kina mafarkin nan, to fa abun yi shi ne mu nemi sanin fassararsa, ina ga zaifi ki je ki ga babban malamin gurin bauta kai tsaye." Kallonta tayi ta sauke numfashi tace "Hakan zai fi ko?" Jinjina kai tayi tace "Hakan shi ne mafita ranki shi dad'e." Yatsina fuska tayi tace "To amma fa Jakadiya kinsan babban malami yana da kusanci da sarkina, duk tattaunawar da zamuyi dole sarki zai san komai, ni kuma ina tsoron kar mafarkina ya zama na sharri." Girgiza kai Jakadiya Habbee tayi tace "Babu abinda zai faru uwar-gijiyata, mafarkinki alkairi ne." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan, da sassafe zamu je mu gan shi." Cikeda girmamawa ta amsa mata da "To ranki shi dad'e, ni zan koma, a kwana lafiya." Da ido kawai ta amsa mata kafin ita ma ta mik'e tana turo d'an k'aramin bakinta ta koma makwancinta, kuma har lokacin sarki Musail bai dawo ba. Washe garin ranar litinin 10/07/2000 sarauniya Juman ta isa wurin bautar dake nesa da masarautar Khazira dan had'uwa da babban malamin fadar wato *Dhurani*, tsaye yake a gabanta hannayrnshi akan had'e kusa da cikinshi yana kallonta, yayin da take zaune akan kujerar katako doguwa kan ta k'asa, dan yana da matuk'ar girma a k'asar ta yanda wasu abubuwan shi ke ba wa sarki Musail shawararsu kafin ya gabatar, cikin kulawa a harshen slovaque yace "Sarauniya ta, me ye mafarkin na ki?" Ba tare data d'ago kan ta ba ta shiga girgiza kai tana bud'a baki kamar za tayi magana kuma damuwa da tsoro na hanata, a sanyaye ta d'aga kai ta kalleshi tana yatsina fuska tace "Babban malami, mafarkin nan yana damuna, kuma kullum kusan kala d'aya ne, yarinya da bata fi shekara biyar ba a duniya, amma sai na ganta a kan kujerar mulki cikin shiga irin ta sarakai, abun al'ajabi shi ne, idonta da kuma haskenta mai matuk'ar d'aukar ido, wannan hasken ya isa ya haskaka garin nan da kewayensa, kayan jikinta ma ban tab'a ganin wani gawurtaccen sarkin daya tab'a saka ko da kwatankwacin irinsu ba, suna da d'aukar hankali da k'yalk'yali tamkar madubi." Sake kafeshi tayi da ido tace "Babban malami, wasu lokuta a saman ruwa nake ganinta tana tafiya, kuma kullum k'ok'arin bani hannu take tana fad'a min wai na kawo hannuna ta cece ni, na...na rasa gane... Wannan abun, na rok'eka kayi wani abu a kai ba tare da sarki ya ji." Tunda ta fara magana Dhurani ya tsura mata ido yana kallo, tabbas wani yanayi ya shiga da asalinsa b'acin rai ne musababbin sa da tashin hankali, da sauri ya juya ya shige wata k'ofa dake cikin wurin bautar ya rufo, gaban wani teburi ya k'arasa ya bud'a wani k'aton littafi dake gabanshi, dama yana ajiyar wurin saboda jiran wannan ranar, sake karanta wurin yayi a k'alla ya maimaita ya fi sau goma kafin ya rufe. D'aga kan shi yayi ya kalli rufin d'akin goshinshi na tsatsafo gumi, lumshe ido yayi yana tunanin mafita akan bala'in dake shirin tunkarosu, da sauri ya bud'a ido skamakon jin wata shawara da zuciyarshi ta yanke mishi, sauke kan shi yayi k'asa ya sauke nannauyen numfashi ya juyo hannunsa rik'e da littafin yana murmushin mugunta ya fito. Sarauniya Juman da tunda ta ga ya bar ta nan ta shiga tashin hankali da jin cewa lallai mafarkinta ba alkairi bane kamar yanda tayi zato, mik'ewa tayi ta juya a sanyaye zata bar wuri dan Habbee na bakin k'ofa tana jiranta, fitowarshi tasa ta juyawa sai kuma ta tsaya, sake nuna mata wuri yayi inda ta tashi yace "Zauna sarauniyata." Komawa tayi ta zauna tana kallon shi a raunane tace "Babban malami lafiya ko?" Murmushi yayi yace "Lafiya lau, karki damu." Kujerar dake gefenta ya zauna yana kallonta yace "Ita wannan yarinya da kike gani a mafarkinki, *'yar da zaki haifa ce* wato *Zafeera*, ma'ana haske marar yankewa." Mamaki ne fal a kan fuskarta inda ta shiga jujjuya kan ta, da k'yar ta kalleshi tace "Zafeera? 'Yar da zan haifa? To amma ai..." Da saurita kalleshi kuma tace "Yaushe?" Wani murmushi yayi yace "Ai fara mafarkinta da kikayi alamu ne na cikinta na jikinki." Dafe mararta tayi mamaki bai bar fuskarta ba ta sake fad'in "Amma kuma ban ga wani alamu na samun ciki ba, a k'alla wata hud'u dana fara mafarkin nan, idan har haka alamu ne na samun cikin ta, to fa ina ganin jini a kowane wata, ta ya haka zata kasance? Bayan cikina na farko ban ga haka ba." D'aga mata hannu yayi a hankali cike da izza ya mik'e tsaye ya fuskanceta yace "Sarauniya Juman, kakan kakana ya kasance zab'abb'e ne ga abun bauta *Ghira*, shi d'in ya kasance d'an baiwar da ba'a tab'a samun kamar sa ba bayan shud'add'un wasu shekaru, mu malam gurin bauta mun yi amanna cewa k'arni bayan k'arni lokaci bayan lokaci abun bauta Ghira yana bijiro da wani zab'abb'e a cikin bayinsa, kakana ya fad'a min sanda kakansa ke gargarar mutuwa ya ambaci wata zab'abb'iya da zata zo mana bayan wani k'arnin, kin ga nan?" Ya fad'a yana mik'a mata k'aton littafin nan sannan ya ci gaba da fad'in "Ya suffanta mana alamun bayyanarta, zata kasance 'yar baiwa da kowane motsinta zai ba wa mai hankali mamaki, idonta masu matuk'ar ban tsoro da birgewa ne ga ma'abota kallonsu, sannan ki sani wannan 'ya da zaki haifa zata zama mafari ga sabon canjin k'asar Texanda baki d'ayanta. Dan haka 'yar ki ta samu sunanta tun kafin ki haife ta, *Zafeera*, ko kuma ki kirata da *LU'U LU'U*." D'auke idonta tayi daga kan littafin ta kalleshi a matuk'ar tsorace tace "Amma babban malamin, me ye manufar ganinta cikin kaya kamar na sarauta?" Juya mata baya yayi dan baya son fad'a mata gaskiya sannan yace "Alamu ne na ita ce abun bauta Ghira ya zab'a a cikin zab'abb'un sa, sannan zata zama mai daraja a cikin al'umma." Numfashi ta sauke ta ci gaba da kallonshi tace "To kuma me yasa take mik'o min hannu tana fad'a min zata taimake ni?" Da sauri ya juyo a hassale yace "Sarauniyata ya isa haka, kada ki tsananta tambaya a cikin lamarin ubangiji, ki je gida sannan ki yi shagali tare da farin ciki na zab'arku a cikin masu daraja." Lumshe ido tayi a sanyaye ta mik'e tare da aje masa littafin akan kujerar ta juya tana mai d'an rik'e k'asan rigarta saboda jan k'asa da take yi, a sanyaye har saida ta kai bakin k'ofar ta saki 'yar rariyar dake rufe mata fuska a matsayinta na matar sarki, Habbee da dogaran suna ganinta suka sunkuya suna mata barka da fitowa, a sanyaye ta k'arasa bakin dawakai guda biyun da aka k'awatasu da abun zama aka musu rumfa, shiga tayi ta zauna sai Habbee data zauna daga baya akan wani siddi dake bayan dawakan sannan suka bar wurin. *MASARAUTAR GIOBARH* Da sauri ya ja ya tsaya a in da yake sakamakon ganin sarkin da yayi tare da iyalinshi, sunkuyar da kai yayi sosai tare da had'e hannaye alamar girmamawa yace "A gafarce ni ranka shi dad'e." A mugun dak'ile cikin yatsina fuska ba tare da ya kalli dogarin ba ya ci gaba da ciyar da uwar gidan ta shi wacce ke kwance bata motsi. Matashiyar matar da ke gefenshi a tsaye rik'e da faranti ce ta kalli dogarin cikin harshen galloi tace" Lafiya? " Sunkuyar da kai yayi alamar risinawa sannan yace" Ranki shi dad'e, dama boka *Kasur* ne ya zo kuma ya tabbatar mana lallai sarkina ya ke son gani yanzu." A sanyaye matar ta kalli sarki *Wudar* saidai ba tace komai ba, d'an satar kallonta yayi kafin ya sauke numfashi ya sake maida hankalinshi kan uwar gidan shi ya sake mik'a mata lomar abinci, cikin rawar kai kamar wacce lantarki ya kama ta bud'a bakinta ta karb'a har rabi na zubewa, tissue ya d'auka ya goge mata baki sannan ya mik'awa matar nan farantin abinci. Mik'ewa yayi tsaye ya juya ya kalli dogarin yace "Yana ina?" A ladabce yace "Yana masaukin bak'i shugaaba na." Numfashi ya kuma saukewa sannan ya juya ya kalli matar nan yace "Ki kula da 'yar uwarki *Joyran*, ina dawowa." Da wani kallo mai wuyar fassara ta raka bayanshi tare da sakin murmushi, saida ta ga fitarsu 脿 d'akin ta kalli matar da ke kwance. Babban farantin ta ajiye a kan wani dogon desk kafin ta zauna kan gadon gefen matar, fuskar alhini ta nuna sosai idonta tap da k'walla ta rik'o hannunta da ko motsashi ba tayi, cikin muryar jimami tana kallon k'wayar idonta tace "Sarauniyata, kuma 'yar uwata *Kossam*, hak'ik'a ina matuk'ar jin rad'ad'in wannan ciwon naki, ina ma a ce ina da maganin cutarki? Tabbas da na sadaukar da duk abinda na mallaka dan samun lafiyarki,' yar uwata ki ci gaba da hak'uri kin ji, wannan ciwon jarabawa ce a gareki, ki tuna wani abu d'aya yayata, da a ce yau wanda ya zama sanadiyar shigarki halin nan yana duniya, na tabbata da zai fi kowa shiga damuwa na halin da kike ciki." Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da k'ara jimk'e hannunta tace" Kossam, hakan da nake ba dan bana k'aunarki bane, saboda ceton rayuwata nake haka, amma ina baki tabbacin komai ya kusa zuwa k'arshe." Muskutawa tayi kafin ta mik'e tsaye tana goge 'yar k'wallar da suka tarar mata, kallon Kossam tayi tana fad'ad'a murmushi tare da fad'in" Yar uwata, ni zan koma b'angare na, sai na dawo baki abincin ranarki." Tana fad'a ta juya da saurinta ta bar d'akin inda doguwar rigarta ke jan k'asa sosai. Hadimar da ta gani 脿 k'ofar d'akin ya saka ta k'are mata kallo, cikin wurga mata harara tace" Kossam ta ci abinci yanzu, idan za ta ci anjima 脿 kirani na bata." Da girmamawa ta amsa mata da" Angma ranki shi dad'e." Cikin sauri ta k'arasa fita tayi b'angarenta, hadimar kuma da kallo ta bita sannan ta murgud'a baki ta bud'a d'akin ta shiga tana fad'in" Sarauta, kamar mu d'in musakai ne da ba zamu iya bata abincin ba dole sai ita." *Masaukin bak'i* Bayan sarki Wudar ya zauna akan babban kujera ne ya tambayi bokan na shi me ke tafe da shi? Da sauri ya mik'e tsaye cike da zumud'in son sanar da shi abinda ke tafe da shi ya fara da fad'in" Shugaba na, labari nake tafe da shi wanda zai sa ka farin ciki, labari ne da nake da tabbacin zaka min kyautar da baka tab'a kwatanta yi ma wani ita ba." Cike da k'asaita da izza irin ta mulki sarki Wudar ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana k'arewa boka Kusar kallo, kamar mai ciwon baki ya d'aga labb'an shi yace" Ina jinka." Wangale baki yayi yana dariya yace" Sarki na, ka tuna zab'abb'iyar da mu ka maka bayani zata zo a zamanin mulkinka?" A zabure sarki wudar ya sauke k'afa d'aya yana zaro ido yace" Taya kake tsammanin daidai da sakan d'aya zan iya mantawa da lamarin yarinyar da ku kuka bani tabbacin ita ce ci gabana ? Kai fa ka fad'a min inhar na sameta to ni zan dama mulkin da ya fi na *Alexandre* ma, kana ganin akwai wani mutum da baya son ci gaban rayuwarsa ne ? Ko kuma zan zauna na zama shashashan sarkin da ba zai so dawwama a mulki ba ?" Sunkuyar da kai yayi yace" Ran sarkina ya dad'e, ba haka nake nufi ba, ina son maka tuni ne saboda abinda na zo da shi." Gyara zamanshi yayi yana hura hanci tare da fad'in" Je ga gundarin magana." Rusunawa yayi alamar girmamawa da kuma amsa buk'atar sarkin, d'aga kanshi yayi ya kalli fuskar sarki Wudar saidai bai had'a ido da shi ba saboda kwarjini, cikin nutsuwa ya fara fad'in" Sarkina, yarinyar da muka tabbata zata zo 脿 tarihi, kuma muka samu yak'ini ita ce silar duk wani ci gaba na ka da na 'yan k'asar nan, yarinyar da kyawunta zai wadaci masarautarka da kewayenta, yarinyar da haskenta zai mamaye gaba d'aya k'asar Texanda, yarinyar da shek'inta tamkar na *Lu'u lu'u*, tana kusantoka, dan bincikenmu ya nuna mana da taimakawar abun bauta cewa ba shakka cikinta ya bayyana, za'a haifeta yayin da zamuyi murnar cika shekara ta dubu biyu, sannan mu fara lissafin lokacin da tarihin garinmu ya fara canzawa izuwa shekara ta dubu biyu da d'aya." Da sauri sarki Wudar ya tashi tsaye yace" A wacce k'asa za'a haifeta? Wacece mahaifiyar *' yar baiwata*?" Rarraba ido ya fara yi tare da fad'in" E to, sarkina saidai akwai wasu yan matsaloli da muka gano a game da hakan." A tsawace rai b'ace yace" Ban damu ba, ban damu da kowace irin matsala ba, abinda na sani kawai shi ne zan kashe duk wanda yayi k'ok'arin shiga tsakanina da cikar burina, dan haka ina jinka?" Jiki a sanyaye yace" Shugabana, yarinyar za'a haifeta a masarautar sarki *Musail*, sarauniya *Zeyfi* ita ce mahaifiyar yar baiwarka." Wata arniyar dariya sarki Wudar ya bushe da ita tare da fad'in" Lallai boka Kusar baka da hankali, shin ka manta tsakani na da sarki Musail ne? Gaba ce marar iyaka, kuma a yanzu na samu damar da zan d'auki fansa a kan shi, duk da na sani hakan ba k'aramin jan aiki bane, amma akan cikar burina babu abinda zan yarda ya gagareni, zan auri 'yarsa a gaban idonsa idan bai kawo min tangard'a ba, idan kuma yayi taurin kai to zanyi shirin yak'i da shi, zan kashe shi da hannuna sannan na mayar da matarshi baiwata ma'ana surukata,' yarsa kuma zata zama matata a zahirance, a bad'ini kuma ita d'in *nasara* ce ga k'asata. " Tsawon lokaci sarki Wudar da boka Kusar suka d'auka suna tattauna kafin daga bisani su rabu zuciyar sarki Wudar na sake narkewa da mutuwar son zab'abb'iyarshi. *31/12/2000* *12:01* Yayin da milyoyin duniyoyi suke murnar tsallake shekarar fargaban za'a tashi duniya, a kowace k'asa an kacame da murnar shiga sabuwar shekara, a daidai lokacin Zafeera ta kutso duniyar ba tare da sanin wacece ita ba bare tasan manyan k'alubalen dake jiranta, a zahirance kam soyayya tsagwaronta ake nuna mata, saidai hatta mahaifiyarta da mahaifinta suna da na su nufin dake k'unshe 脿 cikin zuk'atansu 脿 game da ita, haka ma yayarta wacce aka haifa kafin ita mai sunan *Zafreen*, kama daga fadawan dake cikin gidan zuwa masarautun dake kewayensu babu wanda baisan da labarinta ba, saidai kad'an ne ke da kyakyawan k'udiri 脿 kan ta. *Babban* tashin hankalin da aka fuskanta a lokacin bai wuce b'atan yarinyar da aka haifa ba awa d'aya data wuce ba, an nemi Zafeera an rasata k'asa ko sama, hankalin kowa a masarautar ya tashi musamman ma na sarki Musail wanda babu wanda yasan asalin sahihiyar nuna damuwarshi akan yarinyar sai jakadiyarshi da kuma malamin fada Dhurani. A wannan rana a masarautar Khazira kowa baccin tsaye yayi, dan kuwa gida gida sarki yasa ana duba masa yarinyar shi tare da hadimansa guda biyu da aka nema a lokacin aka rasa, wannan yasa ya ta'allak'a b'atan yarsa da su, kuma yayi alk'awarin kashesu idan ya samesu. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:29 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *2* Abu kamar wasa sai ga k'aramar magana ta koma babba, dan kuwa fad'in k'asar Khazira da kewayenta an bincike amma babu Zafeera, a k'ank'anin lokaci sai b'atanta ya zaga duka masarautar da kewayenta, hankali ya tashi kuma ya d'ugunzuma musamman malami Dhurani da sarki Musail. *Egypt* Da bala'in k'arfi ya buga teburin cin abincin yana mik'ewa tsaye, a harzuk'e ya kalli dattijon dake bayanshi, ba tare da duba girma ko shekarunshi ba ya ci kwalarsa yana mai fad'in "Ina take? Ina suka kai ta? Su wa suka saceta?" Cikin jin rad'ad'i da fafutukar k'watar kanshi ya shiga fad'in "Yallab'ai ka min rai, ban da masaniya akan komai ni ma, labari na samu daga d'an lek'en asirinmu dake masarautar Khazira." Sakinshi yayi da k'arfi yana sake fad'in "To su waye suka d'auke yarinyar dana jima ina jiran zuwanta? Su waye su?" Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba yallab'ai, kuma shi ma ya fad'a mana wasu fadawa biyu ne ake zargi da saceta, saboda su ne aka nema aka rasa a yayin da aka rasa 'yar." Juyawa yayi da bala'in sauri yayi ciki yana fad'in "Ka samo min masaniya akan su, ba zan tab'a barin *lu'u lu'u* na a juji ba." Rusunawa yayi yace "To ranka shi dad'e." Saida ya ga b'acewarsa ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya juya ya fita a tank'amemen falon. *Bayan wasu shekaru* Sarki Musail ya sake zama mugu a gun jama'arsa, ba za'a ce yana mulkin kama-karya ba, sai dai ko ya ya mu'amula ta had'aku zaka ji ba dad'i, zalinci ne tsagwaro a cikin mulkinsa. Kamar yanda ya zamar masa jiki yanzu ma barasar shi yake ta d'irka, babban dakarenshi na gefe a tsaye yana kallon irin tanb'elen da yake, da k'arfi aka bud'o k'ofar wanda hakan yasa dogarin saurin d'ora hannunshi akan takobinshi yana sake had'e fuska, ganin Zafreen yasa shi d'auke hannu a takobin tare da d'an rusuna mata, a wulak'ance ta wurga masa harara tare da nufa wajen mahaifinta. Tana isa kusanshi ta tsaya duk da tana kallon bayanshi ne, cike da rashin kunya da tijara tace "Baa, wai me yasa kake neman lalata sunan masarautar nan ne akan wata b'atacciyar yarinya? Ka manta da ita mana tunda ta mutu." A sangarce ya juyo ya Kalle ta cikin halin maye, duk da yana namiji kuma dattijo amma kyakyawa, cikin layi yace "Ke...sha-sha-sha ce, kuma..mahaukaciya, ba za...ki gane...ba." Da mamaki da kuma rashin jin dad'i tace "Baa ni ce mahaukaciya? 脌 kan wannan abar?" D'an tsaki kawai yayi tare da tureta gefe ya zauna kan kujera mai kyan gaske, a hassale ta bi bayanshi ita ma cikin shigarta ta riga da wando k'anana, sai yalwataccen gashinta data d'aure tamau a kai wanda ya fito da kyakyawar fuskarta, cike da tsiwa ta shiga fad'in "Baa wai me yasa kuke min haka? Kai da Maa gaba d'aya ba kwa kulani, babu ruwanku da damuwata bare matsalata, shin Zafeera ita kad'ai ce kuka haifa?" D'aga kanshi yayi ya kalleta cikin muryar maye yace "Ba zaki gane ba gimbiya, da namiji ce ke da kin fahimci abinda nake ji." Da sauri ta matsa kusanshi ta dafa kafad'arshi tace "Baa, ka fad'a min matsalar ka zan fahimta, ni ma kamar namiji ce tunda zan iya yin komai da namiji zaiyi." Wani malalacin murmushi yayi yace "Ke yarinya ce gimbiya, ki je d'akinki ki kwanta kawai." Durk'usawa tayi tace "A'a Baa, ka fad'a min ni zan maka maganin matsalar ka, na gaji da ganinku kai da Maa kullum cikin tunanin yarinyar data jima da mutuwa." Cike da damuwa 脿 fuskarshi yace "Ba zaki iya ba gimbiya Zafreen, ki b'ace min daga nan." Mik'ewa tayi tsaye cikin sauri ta nufi in da dogarin nan yake, duk girmansa na jiki da kuma shekaru bai hanata saka k'afa ta hanb'areshi ba, sakamakon zuwan abun a bazata sai ya samu kanshi da fad'uwa k'asa, da sauri sarki Musail ya mik'e tsaye cikin layi kamar zai fad'i yace "Ke... Wai !" Sai kuma yayi shiru saboda wuk'ar dogarin data d'auka a jikinshi ta d'orata a mak'ogwaron dogarin, hankali tashe dogarin ya zare ido dan yasan tsaf Zafreen zata huda wuyanshi, dan kuwa halin mahaifinta babu wanda ta rage bata kwasa ba na mugunta. Juyowa tayi ta kalli mahaifin na ta tace "Na fad'a ma ka zan iya, ni ma namiji ce kuma zan ma ka anfanin da namiji ba zai maka ba." D'aga mata hannu yayi ya k'yafato ta alamar ta zo, maida kallon ta tayi ga dogarin ta aje masa wuk'ar sannan ta nufeshi, kafad'arta ya dafa yana kallon fuskarta yace" Kin tabbata zaki iya?" Jinjina kai tayi tace" Ka fad'i abinda kake so, ni kuma zan maka." D'auke hannunshi yayi 脿 kafad'arta yace" Zafeera nake son gani a gabana, zaki iya kawo min ita?" Mamaki ne ya bayyana a fuskarta tace" Mutanen gari suna cewa tun a ranar da aka saceta aka kasheta, ina ji 脿 jikina ta mutu." Girgiza kai yayi yace" Bata mutu ba, ina jin haka a jikina." Da wani mamakin tace" To amma tana ina? Na ga babu inda fadawanka basu zagaya ba a birni da k'auyukan k'asar nan, kuma yanzu haka an saka sanarwa ga duk wanda ya kawota zai tafi da arzik'in da har jikokinshi ba zasu k'arar da shi ba." Gyara tsayuwa tayi tace" Ka na ganin idan har tana raye wani zai kasa kawota ne ko dan kud'in nan." Wani kallo ya mata sai kuma yayi k'aramin tsaki yace" Zafreen wannan aikin na maza, ki je ki kwanta ki barni zan ci gaba da nemanta da kai na." Da sauri tace" A'a Baa zanyi, zan je nemanta ni da kai na, zan tafi kaji Baa." Wani kallo ya mata yace" Ta ina zaki fara?" Turo k'aramin bakinta tayi tace" Baa na fad'a ma ka ina son aikin d'an sanda, zan je inda dayawa daga cikin abokanai na suke karb'ar horonsu, hakan zai taimaka min sosai wajen samota." Dafa kanta yayi yana lumshe ido alamun bacci a idonshi sosai sannan yace "Kin tabbatar?" Waina idonta tayi tace " Baa, ya kake neman nuna kasawata ne tun ban shiga aikin ba?" D'an murmushin yak'e ya mata kawai ya juya zai shiga kusurwar da zata sadashi da d'akin baccinshi, saida yayi daf da shiga ta bishi da kallo tace "Amma ta ya zan ganeta bayan ko fuskarta ban gani ba da tana jaririya?" Cak ya tsaya tare da juyawa ya kalleta, 脿 sanyaye yace "Ki samu babban malami Dhurani, zai fad'a miki komai a kan ta." Nunota yayi da yatsa alamar gargad'i yace "Amma ki tabbatar kinyi nasara, idan kuma kika min wasa da hankali..." K'wafa yayi ya juya zai shige ta sake fad'in "Baa wai me yasa ka damu da ita haka sosai? Ni baku so na ne?" Wani murmushi yayi a tausashe wanda ya sake bayyanar da kyawun fuskarshi sannan yace "Idan Zafeera bata shigo hannunmu ba, daga ni har ke mun kad'e, dan babu makawa sai ta ga bayanmu." Da wani mad'aukakin mamaki ta ci gaba da kallonshi tace "Kuma a haka kake son ganinta? Me zai hana ba zamu kasheta ba kafin ita ta kashemu?" Da sauri sarki Musail da amintaccen dogarinshi suka zuba mata ido, kamar ba zai daina kallon ta ba sai kawai ya girgiza kai ya shige ciki, dogarin ma da sauri ya k'arasa gaban teburin ya kwashi k'aramar wayar hannun sarkin da kuma kwalbar barasarshi shi ma ya shiga d'akin kai tsaye. Ita kam 脿 fusace ta fita tana jin lallai in ta had'u da ita kasheta ma zatayi kawai saidai ta kawo mishi gawarta, dan ba zata yarda yarinyar ta rabata da komai nata ba. Sanda cikinta ya bayyana haka gaba d'aya gari ake magana a kan ta, iyayeensu suke nuna mata soyayya fiye da ita, an haifeta ta b'ata amma a ce bata tsira ba? Sam ba zai yiwu ba. *Washe gari* Zafreen ta gama duk shirinta ta nufi wajen malami Dhurani, bayanan daya bata dai kamar yanda ya fad'awa mahaifiyarta ne a sanda cikinta ya bayyana, dan haka ta dawo rai b'ace na jin cewa akan wane dalili ne k'anwarta ta zama zab'abb'iyar ba ita ba? Tana d'akin mai cike da tarin tsari da kyau tana had'a kayanta dan tafiya, k'wank'wasa k'ofar d'akin aka yi saidai kafin ta bayar da izini aka shigo, juyawa tayi dan ganin wanene haka? Kyakyawar mahaifiyarta ce ta shigo ita d'aya babu rakiyar bayinta ko sabuwar jakadiyarta, tsurawa juna ido sukayi saida ta tsaya daf da ita, kwalliya da adon dake jikin sarauniyar Khazira wato *Juman* zaka rantse ba ta haifi Zafreen ba, dan irin masu kula da kansu ne fiye da kima. Cike da nuna damuwa da alhini 脿 fuskar ta cikin tausashiyar murya tace "Gimbiya Zafreen, me kike shirin aikatawa haka? Me yasa zaki biyewa mahaifinki wanda kullum a maye yake? Ina zaki je neman 'yar uwarki...?" Cikin daka tsawa Zafreen tace "Ba yar uwata ba ce, ita d'in' yarku ce da kuke matuk'ar so, wacce ba kwa kula kowa da komai saboda b'atanta, wato dan ita tana zab'abb'iya ko? To zan nemo muku farin cikinku." Sake marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace "Zafreen ba haka bane, ke ma fa 'yarmu ce kuma muna sonki." A hassale tace "K'arya ne, da kuna so na dana gani a zahiri." Juyawa tayi ta rufe zip d'in jakarta, kallon hadimarta tayi dake tsaye bakin k'ofa ta mata alama da ido, d'aukar jakar tayi ta fita da sauri, ita ma zata wuce sarauniya Juman ta rik'o hannunta tace "Zafreen ki saurareni, ba zan bari ki tafi, yanzu ina zaki je? Ta ina zaki fara? Ba zaki tab'a samun ta ba." A wulak'ance ta shiga yatsina baki tana fad'in "Makarantar horar da sababbin d'alibai zan nufa, zan karb'i horon zama 'yar sanda sannan na nemi taimakon abokaina, zamu sameta kinji ko." Fizge hannunta tayi da k'arfi wanda yasa mayafin dake kan sarauniya Juman fad'uwa daga kafad'arta, kallon juna sukayi ido cikin ido sannan ta juya zata fita, cak kuma ta tsaya tare da juyowa a hankali, da mamaki ta dinga kallon wuyan sarauniyar kamar zata had'e ta. Da sauri ta kai hannunta ta d'aga doguwar sark'ar gwal d'in dake wuyan sarauniyar, 'yar k'aramar sark'ar dake wuyanta mai bak'in zare da wani k'aramin zagaye kamar ziro, cike da al'ajabi Zafreen tace "Maa, wannan sark'ar ai jabu ce, ina ta asalin?" Wani masifaffen murd'awa cikin sarauniya yayi inda ta zaro idonta kamar zasu fad'o, a take ta tambayi kan ta "Ya akayi ta gane?" Dan ko sarki Musail bai tab'a lura da hakan ba, duk dai ma yanzu ya zama bugagge kullum a shaye yake. B'oyayyen numfashi ta sauke tana tunanin abinda zata fad'a mata, dan bata so asirinta ya tonu a yanzun, kafin ta ce wani abu Zafreen ta sake fad'in" Maa dake nake magana fa, ina sark'arki mai daraja take?" Cikin inda inda tace" Am.. Zafreen, waccen sark'ar ta b'ata shekarar da mukayi tafi da mahaifinki wanda aka mana fashi a hanya, kinsan kuma sark'a ce mai darajar gaske, b'atanta 脿 wuyana zai tashi hankalin 'yan k'asar nan, shiyasa da taimakon malami Dhurani aka had'a min wannan d'in." Marairaicewa tayi kamar zatayi hawaye tace" Na rok'eki 'yata karki bari sarki ko wani ya ji labarin nan, karki fad'awa kowa kinji." Sam fuskar Zafreen bai nuna alamun gamsuwa da maganar mahaifiyar ta ta ba, sai kawai ta girgiza kai ta juya ta fice 脿 d'akin, da kallo ta bita saida ta ga b'acewarta kad'ai ta sauke ajiyar zuciya. *Alhamdulillah* _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *87-62-53-02* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai *Samira*._ 01/01/2022 脿 11:30 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *3* *29/12/2020* *Larhjadin* Da gudu ta fito daga motar ta tunkari dattijuwar dake tsaye da alama jiranta take, ihu ta saki tana fad'in "Mommaaaaa." Da fara'a matar ta tunkareta, amma sarautar Allah kawai sa茂 ta rusuna dake nuna girmamawa ga matashiyar, cak yarinyar ta tsaya ta had'e fuska cikin shagwab'a tace "Momma, ya kike abu haka kamar zaki rusuna min?" Cikin dubara da wayancewa ta saki murmushi tana mai dafa kafad'arta tace "Haba dai *princezna* (gimbiya), abu ne naji na taka k'afata." Dariya budurwar tayi ta rumgume maman na ta tana fad'in "Momma na nayi kewarki." "Ni ma haka." Ta fad'a tana lumshe ido wani dad'i na ratsata sakamakon had'a jikinta da tayi da sanyin idaniyar ta ta, sun jima haka kafin su raba jikinsu, kallonta dattijuwar ta dinga yi daga k'asa har sama. Dogon wando ne matsatse bak'i sai farar riga mai k'ananan hannu, takalminta flat ne masu d'amara fara, k'aramar jaka ce a kafad'arta bak'a sai hular dake kanta ta sanyi, baya ga haka babu wani abu mai kama da kwalliya ko ado a tare da ita bayan wata siririyar sark'a dake wuyanta mai kalar d'anyan gwal sai wani zagaye kamar ziro. Kyab'e fuska matar tayi tace "Gimbiya ta, ya naga kin k'ara ramewa? Dubeki fa." Dariya tayi data bayyanar da 'yan hak'oranta na gaba kamar na b'era tace "Momma kin manta karatu na ne? Ina shekarata ta k'arshe ne, shiyasa na dage nake so na ga na fito a major ta foresti猫re." Girgiza kai matar tayi tace "K'iriniya irin ta ki sai nema gimbiya." K'yalk'yakewa tayi da dariya ta dafa kafad'arta tana fad'in "Gimbiya gibimya kullum, wai ni Momma ko dai mijinki sarki ne ban sani ba?" Yanda tayi maganar cikin zolaya yasa matar yin dariya ita ma sannan tace "Maza ki samesu ku wuce, bana so ki k'ara ja min maganar da zan je bayar da hak'uri." Turo baki tayi tace "Momma dama kin gaji dani?" Dogo kuma siririn hancinta ta kama ta ja sosai tare da juyawa da ita suka nufi motar dake tsaye k'ofar gida, cikin kukan sangarta take fad'in "Momma ba zaki barni na ga Papa ba? Please." Dungure mata kai tayi tace " Ban hanaki yi min yaren da ba namu ba?" Da yatsunta tayi alamar sakata a bakinta tare da cewa "Nayi shiru, ni na tafi, sai na dawo, ki gaida Papa." Duk tayi maganar ne tana hawa matakalar motar k'waya uku sannan ta juyo, da mamaki maman tace "Amma ba kin zo ne dan muyi magana ba?" Dariya tayi tace "Momma zan fad'a miki." "Yaushe kuma?" Ta fad'a da jimami, dariya ta sake yi tace "Momma zan kiraki idan na koma." Girgiza kai kawai tayi ba tace komai ba, juyawa tayi zata k'arasa shiga sa茂 kuma ta juyo ta kalli maman na ta, ganin Maman na ta tayi ta sake irin sunkuyawar d'azu tace "Sauka lafiya princezna." Sam bata yi tunanin komai ba har motar ta su ta fara tafiya, kujerarta dake baya ta wuce ta zauna tare da cire hularta, hakan ya bayyanar da kanta wanda gashi ya fara tohowa, dan dukansu yan matan dake motar kowace kan ta k'wal kwabo ne sakamakon aikin da suke da burin yi. Wata budurwa ce tace "Hankalinmu zai kwanta yanzu tunda an kawoki gidanku kin ga Momma." Wani kallo ta watsa mata lokaci d'aya ta d'auke kan ta, tab'e baki budurwar tayi ta d'auke kanta ita ma, tafiya suka yi mai nisan gaske kafin suka isa nesa da garin, wani babban k'ofa wacce aka rubuta sunan makarantar *Skola skoli novych smestnancov* (makarantar horar da sababbin ma'aikata) da yaren slovaque suka tsaya tare da yin oda, jim kad'an aka bud'e musu suka shiga. Makaranta ce amma kamar gari guda, zaka tabbatar da girmanta ne kawai idan ka ga b'angarorin dake ciki, duk wani mai sha'awar karatun aikin saka kaki to nan yake ziyarta, kuma wanda ke karb'ar horon aikin soja ba zai san da zaman mai karantar horon police ba har sai in k'arshen sati ne da ake basu damar fitowa farfajiya har ma mai buk'ata ya fita waje. Yanzu ma a b'angaren masu karantar ilimin *eaux et for锚ts* (gandun daji/ruwa da daji) motar ta aje su suka dinga shiga ciki, kowace na ta d'akin ta nufa mai d'auke da gado guda hud'u. Kan gadonta ta zauna dan tasan yanzu wanka zasu fara dashi, ita kuma ba zata tsaya bin layi ko kuma zaman jira babu kaya a jikinta ba. D'aya daga cikinsu ce ta shiga wanka sai biyun da suka cire kayansu suka d'aura towel, d'aya daga ciki ne ta kalleta tace " *Ayam*, wai me yasa kullum Mommanki take rusuna miki kamar wata shugabarta? Ko al'adarku ce haka?" D'aga kai tayi ta kalli *Deeyam* d'in tare da gyara zamanta, saidai ba tace komai ba face k'ura mata ido, a zuciyarta kuma tunani take ita kanta ta fara ankara da haka, sau da dama idan ta lura tayi magana sai Momma ta kawo mata uzirinta. Ganin ba tayi magana ba kawai yasa Deeyam share zancen tare da kallon gashin Ayam d'in tace "Amma Ayam ba kya tsoron hukumar makaranta ta ganki kin ajiye gashin nan? Za fa su iya korarki dan kin taka musu doka kuma da gangan." Mik'ewa tayi tsaye tana sauke numfashi, hannu biyu tasa ta tattaro gashin kan na ta ta had'e wuri d'aya sannan ta kalleta tace "Kinga fa jibi ne shagalin k'arin haihuwata, nayi niyya 脿 wannan shekarar ba zan yi bikin k'arin shekarar nan da sulb'eb'en kai ba, dan haka in zaki iya ki je ki fad'a musu na tara gashi." Dariya Deeyam tayi tace "Amma dai zaki mana babban shagali a wannan shekarar ko?" Kanne mata ido tayi tace "Dole mana, shekarar mu ta k'arshe ce fa." *Giobarh* Kalar fatarshi kawai zata nuna maka lallai shi d'in daga gidan hutu yake, duk da yana da duhun fata amma kuma bak'inshi mai birgewa ne da d'aukar ido, tsiri-tsirin gashin kansa dake ta k'yalli yayi wara-wara alamar ana b'ata lokaci sosai wajen gyarashi. Leb'enshi na k'asa ya lashe yana kallon abokin na shi da k'ananan idonshi masu zurfi, kyakyawan abokin na shi kam dariya ya saki tare da k'ok'arin gimtseta 脿 harshensu na Gallois yana fad'in "Haba abokina, ka bari a rage maka sumar nan mana, taya kake tunanin zuwa wannan wajen a haka kuma da sunan kai malami ne?" A mugun hassale ya mik'e daga kujerar yana sake murtuke fuska, kallon mutumin dake tsaye gefensu yayi rik'e da jakar kayan aikinshi, a dak'ile yace masa" Fita a nan." Da sauri ya sunkuya ya juya zai fita, abokin ne yayi saurin fad'in" Kaga, jirani 脿 waje." Wata harara ya zabga masa ya nunashi da yatsa yace" *Haman* ka daina min haka bana so." Shima fuska a had'e yace" Na k'i na daina maka hakan *Umad*, me kake nufi ne wai?" Kawar da kansa yayi yace" Kai zan tambaya ai me kake?" A hankali Haman ya matsa kusan Umad d'in murya a sanyaye yace" Umad ka saurare ni, kaga fa gobe ne tafiyarka, kuma in da zaka je da abinda zaka je yi abune mai matuk'ar mahimmanci, to me yasa ba zakayi duk abinda kasan zai kusanta ka da lamarin nan ba?" Had'e hannaye yayi ya rumgumesu a k'irji ya sake gimtse fuska a dak'ile yace" Me kake nufi?" Jinjina kai yayi yace" Yawwa! Ka gane ko? Duk da kai d'in malamin bogi ne, amma ai ba kowa ya sani ba, kenan dole kayi kama da malamin horaswa, daga gobe fa kakin babban major na gandun daji zaka fara sakawa a jikinka, to kana ganin ya kamata a ce ka je a haka?" Shiru d'akin ya fara d'auka na wasu dak'ik'u, a tausashe ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalli Haman cikin yatsina fuska yace" Na sani Haman, amma ka fahimci wani abu, ni ba zama bane zai kai ni, da na je wurin nan abinda ya kaini kawai zanyi na juyo, ban damu da wata shiga ta ba." Cike da gamsuwa Haman yace" Na fahimceka, amma ni ina so ka tuna da nagartar aikinka." D'an k'ura mishi ido yayi na wasu dak'ik'u sai kuma ya jinjina kai alamar gamsuwa, hannu ya mik'a mishi sukayi musabaha tare da d'orawa da fad'in" Ka cika alk'awarinka Haman, duk rintsi babu wanda zai san komai akan aikina da kuma shirina, na rok'eka." Jinjina kai yayi yana murmushi yace" Baka da matsala da wannan d'an uwa, fatan nasara." Hararanshi yayi yace" Ka jira har lokacin shiga na jirgi yayi mana." 'Yar dariya yayi yace" To ai kace sammako zakayi, ni kuma ban iya tashin safe ba, kaga kenan saidai muyi waya idan ka sauka." Dukanshi yayi 脿 kafad'a yace" Baka isa ba ai yaro, kai zaka kaini har filin jirgi, ragon maza kawa." Shafa yalwatacciyar sumarshi yayi yace" Ni ma zan zama jarumi, da fari na saka rai a lokacin da mai martabanmu ya so auro mana zab'abb'iya, to amma da naga an kasa cimma burin sai kawai ni ma na cire rai tare da sauyawar tsarukan k'asar nan." Girgiza kai Umad yayi bai ce komai ba ya koma kan kujerar ya zauna, ganin haka ya sa Haman lek'awa ya kira mai askin dan ya rage wa Umad tsirakun daya tara a kai." *Larhjadin* Da sauri suke ta fitowa daga ajin suna tunkarar sale a manger (wajen cin abinci) dan minti sha biyar malamin ya basu. Ayam kam ba abincin ne ya dameta sai son tayi waya da Momma ta, hakan yasa ta nufi hanyar fita daga b'angaren na su, inda a nan ke da mai wannan alhakin. Sauri take sosai tana k'ara gyara zaman jakarta a bayanta, kusa da k'ofar zata fita wasu 'yan matan ma suka shigo, kaucewa tayi suka fara wucewa da d'ai-d'aya, amma Zafreen dake k'arshe sai ta shiga kallon Ayam tana yamutsa fuska tana jin gabanta na fad'uwa. Ayam ma kallonta ta shiga yi da idonta wanda basu da d'igon bak'i ko d'aya, daga kalar farin data mamaye girman idon, sai k'wayar mai d'auke da launin shud'i mai hasken sararin samaniya, 'yar k'aramar k'wayar kuma wani irin ratsin fari ne mai kama da zaiba, ga shi kuma launin shuud'in har wani tsage-tsage gareshi, daga can cikin k'aramar k'wayar kuma sai ka rantse ruwa ne kake kallo wanda zasu iya tafiya da kai. Da sauri Zafreen tayi k'asa da idonta tana jan tsaki, a ranta kuma cewa tayi "Mayya kawai." Ayam kam da sauri take dama rab'ata tayi zata wuce, dan gaba d'aya kallon Zafreen d'in yasa ta jin jikinta yayi wani iri har tsigar jikinta na tashi. Wajen ta wuce kuma kawai kafad'arsu ta gogi juna, zata fita a wurin Zafreen ta cabko hannunta ta dawo da ita baya, cike da wulak'anci da jin izza 脿 yarenta na slovaque tace "Wacece ke da har zaki rab'ani ki wuce?" Gyara tsayuwa Ayam tayi a hankali tasa hannunta ta b'amb'are na Zafreen dake jikinta, a tausashe kuma a ladabce itama 脿 harshen slovaque tace "Ni ba kowa bace, amma d'aliba ce nima a makarantar nan, kamar dai ke." Ta k'arashe tana nuna Zafreen, cikin jin haushi Zafreen ta nuna kanta tace "Kinsan wacece ni kuwa?" Wani dogon tsaki Ayam taja tare da fad'in "Shirme kawai, amsar tambayar nan fa na baki yanzun nan, akan me zan tsaya b'ata lokaci na a kan ki?" Yatsina fuska tayi cike da wata irin gadara da izza ta sake niyyar fita a k'ofar, tare gabanta Zafreen tayi tana fad'in "Ke kin isa ki fad'a min magana sannan ki wuce, k'arya kike." Kallon k'awayenta tayi dake gefe suna kallonsu tace "Ku fad'a mata wacece ni, ku fad'a mata ni ke da gaba d'aya k'asar nan da kewayenta, idan har na so yanzun nan zata bar makarantar nan." D'aga gira Ayam tayi ta turo d'an bakinta k'arami ta juya ta kalli k'awayen ita ma, wata doguwa a cikinsu ce tayi saurin fad'in" Ke kinsan wacece Zafreen kuwa? To ita ce gimbiyar Khazira, 'ya d'aya a gurin sarkinmu Musail." Babu alamar damuwa ko wata shakka Ayam ta tab'e baki tace" Da gaske? To ni kuma sunana Ayam,' ya ga... " Mai kula da shiga da ficen d'aliban ne ya katsesu ta hanyar fad'in" Kai ku fita a nan, kunsan minti goma na baku ku shiga ku ga k'awar ta ku." Da sauri k'awayen suka ce" Gimbiya zo muje, ki rabu da ita zamu had'u wani lokacin." Ido cikin ido suka kalli juna amma a take Zafreen tayi k'asa da na ta tana kallon fararen takalmi k'afa ciki masu kamar soso kuma kamar roba dake k'afar Ayam d'in, cike da shak'iyanci Ayam tace" Ki kula malama, wannan fa makarantar gwamnati ce, kuma shekara ta dubu biyu da ashirin muke, babu k'arancin 'yancin a zamanin nan, bugu da k'ari ni d'in haifaffar Larhjadin ce, esxuze moi." Baki bud'e suka bita da kallo har ta tsaya kusan mutumin dake zaune cikin case d'in shi, magana ta mishi hakan yasa shi mik'o mata wayar tafi-da gidanka ta shiga danna lambar gidan na su, dan ba kowane lokaci ake basu damar anfani da wayoyinsu ba. Rai b'ace kamar zata mutu ta juya suka fita tana fad'in "Na fasa ganin shi d'in ma." Da sauri suka rufa mata baya d'ayar na fad'in "Gimbiyarmu, kar ranki ya b'ace kinji, k'aramar alhaki ce wannan, zaki iya sa wa 脿 koreta ai." Cak ta tsaya sai kuma ta kalli wacce tayi maganar, ita kuma sunkuyar da kan ta tayi k'asa da tunanin ta fad'i ba daidai ba. Murmushi ta saki tace "Kin kawo shawara mai kyau *Laika"*, ban wayata?" Ta fad'a tana tara mata hannu, mik'a mata tayi ta karb'a ta shiga danna wasu lambobi sannan tayi gaba suka nufi na su b'angaren tana amsa waya. *Ayam* kam na ta buga wayar amma shiru ba'a d'aga ba, d'an tsakin rashin jin dad'i tayi tace" Watak'ila Momma na mak'ota." Aje wayar tayi ta kalli mai kula da k'ofar tace" Shin-shiy (nagode)." Da kallo mamaki ya bita 脿 zuciyarshi yana fad'in" Me yasa take son raina min hankali yarinyar nan, kullum da kalar yaren da take min." Zata shiga cikin sauri shi ma zai shiga a hanzarce, kafad'unsu ne suka had'u, amma Ayam dake wata pigigiya ce saida ta nemi fad'uwa a k'asa, cikin takaici da rashin sanin yaren da ita kanta tayi tace" Tirr! Yau jakuna nake ta had'uwa da su." Gyara jakarta tayi sai a lokacin ta d'aga kai ta kalli dogon mutumin, mummunan fad'uwa gabanta yayi sakamakon tsoron daya bata, ba wai hallitarsa ke da ban tsoron ba, had'add'iyar fuskar shi da babu annuri a cikinta, fararen idonshi k'anana daya zazzaro ya k'ura mata, girarenshi duka biyun daya bala'in d'agesu sukayi sama daga k'arshensu, ga kuma matsatsen bak'ar rigar dake jikinshi data fito da k'irarshi. D'an bakinta ta bud'e har hak'oranta suka fito ta shiga zazzare ido, gyara tsayuwarta tayi tare da sunkuyar da kanta, ko Momma da Papanta bata tab'a had'a ido dasu ba haka, duk yanda take son su kalleta itama kuma ta kalli cikin idonsu abun ya gagara, da sun had'a ido suke d'auke na su, haka ma daga k'awayen abokai da sauran mutane, hakan ya dameta har wata rana ta tambayi Deeyam me yasa bata had'a ido na tsayin sakan uku da ita? Sa茂 tace mata "Ji nake kamar ina kallon babban teku, hakan ya sa naji kamar zan fad'a ciki." Sake d'aga kanta tayi ta kalleshi, tar-tar suka sake had'a ido da shi yana mata mugun kallon nan kamar zai taka wuyanta ya yankata, mitsitsika idonta tayi ta motsa bakinta ta aro jarumta cike da tsiwa da tijara tace" Malam baka gani ne? Ina kake kallo da zaka kawo min hari haka?" Yanda yake kallonta babu rusunawa da kuma sak'onnin dake cikin kallon yasa ta juyawa da gudun tsiya ta shige ciki tana k'yalk'yala dariya kuma tana fad'in" Sai ka ce wani dorinar ruwa wacce kullum fuskarta a murtuke." Da kallo ya bi bayanta, yanda take gudu tana dariya hannayenta rik'e da jakarta, kayan makarantar ne jikinta, riga mai hannaye iya damtse mai ratsin shud'i, sa茂 farin wando shi ma da ratsin shud'i amma iya gwiwa yake, rigar ma tsayinta ya sauko kan cinyoyi kuma botira gareta a gaba har k'asa, sai hula fara dake kanta wacce a saninshi dai yasan ba doka bace sakawa. Takaici mai sunan takaici, haushi iya haushi had'e da jin d'aci a mak'oshinshi, ga kuma azababbiyar tsanar yarinyar da yaji har zuciyarshi, ba dan komai ba sai yaren da tayi magana dashi na Italy, shekararsa shida a garin yana karatunsa, dan haka babu abinda za'a fad'a ya gaza ganewa. Wata zazzafar iska ya huro ya shiga d'aga k'afar sa wanda kana gani zaka san ranshi a b'ace yake zuciyarshi kuma tafasa take, cikin ranshi ban da tsaki da k'wafa babu abinda yake, cikin jin haushi da masifa yake ayyana "Busassar banza, kafin na gama abinda ya kawoni sai na tabbatar ba kya iya banbance tsakanin ruwa da yawu, banza mai idon mayu." Kai tsaye ofishin babban jami'in ya shiga ya gabatar masa da kan shi, tarba ya samu kafin ya had'a shi da k'aramin mataimakinshi ya rakashi zuwa masaukin malaman ga masu buk'ata. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:30 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *4* Bayan fitar Umad aka kira wayarshi, ganin mai kiran yasa hankalinshi ya tashi da sauri ya d'aga kiran yana fad'in "Hello yallab'ai." Daga can b'angaren wazirin sarki Musail yace "Yallab'ai Jacob, ya aiki?" "Lafiya lau yallab'ai." Wazirin ne yace "Kaga na kiraka ko?" Amsawa yayi da fad'in "E yallab'ai, fatan dai lafiya?" Wani d'an murmushi yayi yace "Lafiya lau, gimbiya ce ta kirani yanzu take fad'a min sun samu matsala da wata 'yar talakawa, ta fad'a min yarinyar ta ci mutumcinta sosai." Mik'ewa yayi tsaye yace "A nan makarantar? Wacece wannan?" A gadarance yace "Sunanta Ayam." Zaro ido yayi dan har jikinshi saida ya amsa sunan, ba kasancewarta wacce gwamnati ta tsaya ma ba, shi kawai yarinyar tsoro take bashi, shiyasa ko kallon fuskarta baya son yi, yarinyar da zata maka yare kuma ta nuna bata son wane yare tayi ba. A ladabce yace "Yallab'ai ya kake so a yi yanzu?" Kai tsaye ya furta "A koreta ko da kuwa k'arshen shekararta ce wannan, hakan zai zama izina ga yan baya." Da sauri ya cire hular kansa yace "Me?" Da mamaki waziri yace "E, ko da matsala ne?" A gigice yace "Yallab'ai *Khatar* akwai babbar matsala ma, dan yarinyar nan da kuke gani gwamnati ce ke d'aukar nauyin karatunta, yallab'ai Ayam bana jin ko a k'asar England za'a iya korarta a makaranta bare 脿 nan k'asar." Cike da tsiwa waziri Khatar yace "To shine me? Waye ubanta a k'asar nan?" Girgiza kai yayi cike da tausayin kanshi dan har wata zufa ke tsatsafo masa yace "Yallab'ai Khatar ba 'yar kowa bace, hasalima mahaifinta ba wani hamshak'i bane, amma kuma tasirin yarinyar yafi na democrad'iya." Wawan tsaki ya ja tare da fad'in "Kenan yanzu babu abinda zaka iya yi?" A sanyaye yace "Gaskiya yallab'ai akan yarinyar nan zan iya rasa aikina had'e da tukuicin shiga babbar matsala, dan kad'an daga cikin ikon da gwamnati ta ba wa yarinyar nan, akwai lamunce mata ta ziyarci iyayenta duk sanda ta so, dan ma yarinyar na da lissafi ne take daidaita kanta da sauran d'aliban." A tsawace Khatar yace" Shiru malam, ni ba wannan na tambayeka ba." Cikin rarrashi yace" Kayi hak'uri yallab'ai, na maka alk'awarin zan ja mata kunne ta fita harkar gimbiya Zafreen." K'it! Ya kashe wayar hakan ya ba colonel d'in damar sauke numfashi mai nauyin gaske shi ma ya aje wayar. K'aramin Sajan (sergent) d'inshi ya kira yace" Kira min Ayam *Utais*, izuwa yanzu suna aji tare da malam *Pedro*." Sara masa yayi ya amsa da" To yallab'ai." Sannan ya fice. Mintuna k'alilan suka shigo tare da ita, fita yayi bayan ya mata iso ta samu wuri ta zauna tana kallon major d'in, saida ya rufe musu k'ofar kafin ya kalli fuskarta saidai ba cikin idonta ba yana wani inda-inda yace "Am... Ayam Utais, dama nasa...a kirani ne naji dalilin samun sab'aninki da gimbiya Zafreen?" K'uri ta masa da idonta hakan yasa shi mik'ewa tsaye yana dariyar rashin gaskiya kamar wacce tace kwab'e kayanka na zaneka, cikin duburburcewa ya ke fad'in "A'a, kin gane ko? Ba komai ma ba sa茂 kin fad'a ba, abinda nake so dake kawai ki rabu da ita, karki sake shiga sabgarta dan ke karatu ne ya kawoki nan, kin kusa kammala zangonki dan haka ki maida hankali kinji." Turo baki tayi gaba kawai ta jinjina kai alamar gamsuwa tare da mik'ewa zata fita, da sauri yace" Kina ji Ayam." Tsayawa tayi ta juyo tana saurarenshi, d'orawa yayi da fad'in" Gobe mai horar daku malam Pedro zai koma k'asarshi, dan haka gobe da safe zaku ci gaba daga inda kuka tsaya tare da sabon mai horarswa." A sanyaye ta maimaita" Sabon mai horaswa?" "E." Ya fad'a yana komawa ya zauna, jinjina kai tayi ta fita a ofishin tana tab'e baki da maimaita sabon mai horaswa? Waye shi? Kuma da wane salo zai zo shi kuma? Ko shi ma irinsu malam *Elinio* ne da ya gama latse 'yan mata kafin ya koma k'asarsa Brazil? *Suna* zazzaune wajen cin abinci da dare Ayam ta kalli k'awayen na ta su uku tace "Kunsan me? D'azu colonel yake fad'a min wai gobe za'a kawo mana sabon mai horaswa." Duk k'ura mata ido sukayi sai Deeyam da tace "Sabon mai horaswa kuma? Gobe gobe kuma? To me ya samu Pedro d'in?" Saida ta zura cokalin robar a bakinta tace "Yana nan, babu abinda ya sameshi, da alama wani aiki ya samu daya fi wannan." Jinjina kai sukayi kafin Ayam ta sake fad'in "Kunsan ni me nake so, ina tsoron kar a kawo mana irin malam Elinio, yana mana darasi yana tsaremu da ido yana kallar mana d'uwawu." Dariya Deeyam tayi tace "To ya zamuyi idan ma irinsa ne? Mu dai na mu bijire masa ne kawai." Kallon Deeyam d'in tayi tace "Ni kuma ba haka nake so ba, kunsan me zamuyi?" Girgiza kai sukayi inda d'aya a cikinsu tace "Sai kin fad'a." Cikin rad'a tace "Mu kai ziyara b'angaren malaman, ta haka zamu san wane iri ne shi dan mu d'auki matakin kare kanmu." Zaro ido sukayi sai Deeyam da tace "Ta ya ya haka zai faru? Ko kin manta ba'a barin d'alibai zuwa b'angaren da malamai suke, haka su ma malaman basa zuwa inda d'alibai suke?" Waina idonta tayi sannan ta k'urawa Deeyam su tana kallonta, kawar da kanta tayi murya k'asa k'asa tace "Ki daina kallona haka Ayam, na rantse miki saida gabana ya fad'i." Tab'e baki Ayam tayi ta d'auke idonta tace "To na d'auke, ni dai yanzu ku bar min komai a hannuna kawai, ku dai ku shirya zan tasheku a tsakiyar dare." Tana gama fad'a ta mik'e tare da juyawa ta bar wurin, da kallo suka bita da fari kafin d'aya 脿 cikinsu tace "Kamar kullum, yau ma mu zamu d'auke mata farantin abincinta." Deeyam dake cin abinci ce tace "Tunda kinsan da haka, me ye na bitar shi kuma?" Wata a ciki ma murmushi tayi tace "Lokuta da dama Ayam tayi abu sai ka d'auka wata sarauniya ce." Dariya suka yi gaba d'ayansu haka har suka kammala suka mik'e suma da farantan a hannayensu suna ajewa wurin da aka keb'e dan ajesu kamar sauran d'alibai. *01:43* Tana daddab'a Deeyam ta bud'a ido tace mata "Tashi mu tafi." Tashi tayi zaune tana murza ido tace "Ayam, ina kuma zamu je?" Cikin rad'a tace "Tashi mu tafi kedai." Sake bud'a idonta tayi ta kalli saura k'awayen dake bayan Ayam dukansu cikin kayan baccinsu, a hankali ta sulala ta sauka akan gadon. Cikin sand'a suka dinga fita a d'akin har sukayi sa'ar haurawa ta wani corridor ba tare da tsoron su fad'i ba, ai kuwa a sauk'ake sai gasu a b'angaren malam kamar wasu b'arayi, jerawa sukayi suka dinga hawa matakalar har suka iso wajen d'akunan, kallon juna sukayi Deeyam tace "Ina d'akin?" Nuna musu Ayam tayi tace "Wannan d'akin ne ai babu kowa." K'arasawa sukayi suka sake tsayawa cirko cirko, kallon su Ayam tayi tace "Yanzu Sabrine ke ki fara shiga." Waro ido tayi tace "Me yasa ni zan shiga." Cikin rad'a Ayam tace "To ai kin fi mu kyau da dirin halitta mai kyau." Harara ta wurga mata tace "Na k'i to, babu ruwana ni." Juyawa Ayam tayi ta kalli Deeyam tace "To ke ki shiga, tunda kina da abubuwan d'aukar hankali." Cikin fad'a Deeyam tace "To wai ke da kika jagorancemu me zai hana ki shiga?" Wata dariya tayi ta kalli kanta tace "Haba dai, dubeni fa, aini bana da fasalin d'aukar hankalin namiji, ba kowane namiji nake birgewa ba saboda nayi rama dayawa." Tab'e baki Sabrine tayi tace "To saidai mu koma kam, amma babu inda zanje." Deeyam ma had'e hannaye tayi tace "Ni ma haka." D'ayar ce ta kallesu tace "To mu koma kunji, bana son wani ya ganmu za'a hukuntamu." Cikin rad'a Ayam tace "Yanzu ku d'an aikin nan ne zai gagaremu? Kun manta irin tijarar da muka zuba a baya ne?" Deeyam ce tace "Bamu manta ba, amma dai yau kam ni dai babu ruwana, inda matsalar take shine rashin sanin waye malamin, ni bansan me yasa kika damu da son sanin wane iri ne shi." Gyara tsayuwa Ayam tayi da kyau ta kallesu tace "Ku fad'a min zaku shiga ko a'a?" "A'a." Sabrine ta fad'a tana juya baya, jinjina kai tayi tace "Shikenan, ni zan shiga ciki, amma ku jirani a nan." Murmushi Deeyam tayi tace "Fatan nasara." Harara Ayam ta jefa mata tana gyara hularta tace "Matsalarku ce." Kallon k'ofar d'akin tayi tana sauke numfashi, wani yanayi na tsoro da fad'uwar gaba take ji wanda bata tab'a ji ba, hatta da jinin jikinta ji take ya k'ara gudun tafiyarshi. Cije leb'enta tayi na k'asa sannan ta kai hannu ta k'wank'wasa k'ofar d'akin, amma sai ta ji shiru babu ko alamar motsi, sake kwank'wasawa tayi nan ma shiru, a karo na uku ta sake kwank'wasawa tana jan gajeran tsaki. Deeyam ce tace "Ayam, tunda kika ji shiru ki zo mu je kawai, watak'ila baya nan." Sabrine ce ta karb'e da fad'in "Ko kuma ma bai zo ba." Juyowa tayi ta kalli Sabrine da tayi maganar tace "Hakane?" D'aga mata gira tayi alamar e, jinjina kai tayi tace "Bari mu gani to." Cikin sand'a ta kama hannun k'ofar ta murd'a a hankali, jin ta bud'e yasa suka kalli juna, maida kallonta tayi ga k'ofar ta tura a hankali tana shiga cikin d'akin. Tattausan k'amshin turaren 112 ne ya fara mata maraba, sai kuma siririn hasken daya gauraye d'akin, komai na d'akin a gyare kuma a killace yake sannan a tsaftace, babu alamun da suka nuna akwai mutum a d'akin, hakan yasa ta bayan k'arewa d'akin kallo ta jawo k'ofar da niyyar rufewa. Cak! Ta dakata sakamakon tsikayar wani k'aramin hoto a gefen gadon ajiye, sakin hannun k'ofar tayi ta k'arasa da sauri ta d'auki hoton, k'urawa dattijuwar matar ido tayi mai cikar kamala da haiba, tana cikin shiga ta alfarma kamar wata sarauniya. Samun kanta tayi da sakin murmushi sanadiyar k'aunar matar data ji, a hankali a asalin harshenta na slovaque tace "Watak'ila ya manta da hoton ne?" Sai kuma ta tambayi kan ta "To amma wa ya zauna a d'akin?" Rashin sanin amsar yasa kawai ta d'aga kafad'a alamar ko oho, juyawa tayi ta fara tafiya hannunta rik'e da hoton. Tana daf da hita aka bud'e k'ofar k'aramar ban d'akin dake cikin d'akin, da sauri kuma a mugun tsorace ta kalli inda ta ji k'arar, a wani bala'in tsoracen wanda bata san sanda ya ziyarceta ba ta saki hoton wanda ke lullub'e da kwalba ya fad'i k'asa. K'arar glass d'in da kuma ihunta a tare suka gudana, sai kuma tayi saurin yin gum da bakinta kamar wacce aka tusawa k'wallon goriba a bakin. Idonta masu abun al'ajabi ta zuba masa tana kallo ba tare da rusunawa ko jin d'ar a yanda ta ganshi ba, a hankali take yi tana k'yabta idonta tana kuma sauke numfashi kamar wacce aka b'atawa rai, a zahirinta kamar jira take yace kul tace cas, amma a bad'ini kuma gabanta ci gaba yake da fad'uwa, ganinshi d'aure da towel d'in nan kalar shud'i ba k'aramin gigita mata lissafi yayi ba, dogo ne sosai mai k'ira da zubin jarumai, duk da ba wata murd'add'iyar sura ce da shi mai jan hankali ba, amma dai yana da fasali mai kyau wanda zai iya juyar da k'irarshi a duk ta yanda ya so. Duk da bak'i ne amma kuma bak'inshi mai kyau ne da k'yalli kamar na macen dake samun gyara a kai a kai. A hankali cikin b'acin rai da mamakin abinda ya kawota d'akinshi ya tsura mata ido, yana d'ora ido 脿 kan ta saida launin idonshi suka canza tsabar haushi da takaici, sai yake bala'in jin kamar ya k'urma ihu dan ya samu sassaucin abinda ya tokare masa zuciya. Ba ma wannan ba, wai a kan wane dalili ne shi kam yake had'uwa da wannan mai zubin aljanun ruwan, ga ta dai 脿 cikin kayan bacci wando iya gwiwa da riga mai k'ananan hannu, gaba d'ayanta fa ba zata gagareshi ya dunk'uleta a hannu d'aya ya jefata a hudar hancinshi sannan ya fyatota. Kallon hoton dake k'asa yayi, da sauri ya tako ya tsaya gabanta tare da durk'usawa yana kallon hoton, a mugun fusace ganin yanda hton ya fashe ya sa ya d'ago ya k'ura mata ido. Ayam da tunda ya fara takowar nan da sauri gabanta ya shiga dakan uku, kasa motsawa tayi sai bakinta data warwareshi daga kumburewar da ta mishi, hannayenta ta d'ora kan mararta ta dafe tana fatan kar fitsari ya taho mata. Umad kam cikin fitar hayyaci ya d'aga hannunshi ya wanketa da mari, a k'ufule ba tare daya bata damar gama fahimtar rad'ad'in ba ya nuna mata k'ofa da yatsa cikin hard'add'iya kuma nagartacciyar muryarshi da harshenshi da ya fi k'warewa a yaren Gallois yace "Fita a nan, kuma karki bari mu sake had'uwa, *b'arauniya* kawai." Da sauri ta d'aga idonta dake kallon k'asa ta kalleshi jin sunan daya bata. Shi ma sai lokacin ya fahimci wani abu a tare da ita, ya mareta marin da yake da tabbacin ya ratsata sosai, to amma" Me yasa bata yi ihu ba? Kuma bata fad'i ba duk da rashin nauyinta." Abinda ya tambayi kanshi kenan, sam kamar ma ba ita ya mara ba a fuska. A gaggauce ya kawar da tunanin ya maida hankalinshi ga Ayam data rumgume hannaye a k'irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k'wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab'a sanin ta iya ba tace "... *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:31 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *5* Ayam data rumgume hannaye a k'irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k'wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab'a sanin ta iya ba tace "Af Allan, ond byddwch yn mynd ar ol ar fy ol (zan fita, amma ka koreni a mutumce)." Baisan sanda mamaki ya sake bayyana a fuskarshi ba, gyara tsayuwa yayi da kyau dan ya Fahim I shekarar da zaiyi kisan kan shi ce ta kama, nuna ta ya sake yi a dake yace" Ke, ke mahaukaciyar ina ce?" Ba tare data rusuna idonta ba ta sake muskutawa ita m'a sannan tace" Sanin mahaukaciyar ina ce ni ba zai anfaneka da komai ba, kawai ka janye kalmar nan ta b'arauniya daka fad'a min." Hannayenshi bibbiyu ya rabka a k'ugunshi ya dafe jajayen idonshi a kan ta, ba alamar wasa a tare dashi yace" Ke 'yar garin nan ce?" K'urawa fuskarsa ido tayi ba tace komai ba, ganin bata da niyyar magana sa茂 ranshi ya sake b'aci, a harzuk'e ya cabki hannunta da nufin fitar da ita, da k'arfi ta fincike hannunta tana mai kallon inda ya rik'e, wani abu ta ji kamar wutar lantarki tana janta. Kallonta ya shiga yi shi ma da tunanin ko dai abinda ya ji ita ma ta ji? Tsaki ya buga kawai ya juya ya sake shigewa ban d'akin zuciyarshi kamar zata fashe. Ayam ma na ganin haka ta ja k'afarta data mata nauyi ta fita ita ma, a bakin k'ofar ta samu su Deeyam suna jiranta, da zumud'i Sabrine tace "Ya dai? Me ya faru 脿 ciki?" Shiru tayi sa茂 sauka a matakalar data shiga yi, Deeyam ce tace "Ya muka ji kinyi ihu? Ko dai d'an hannu ne shi ma?" Babu wacce ta amsa ma har suka koma ta inda suka fito suka koma d'akinsu suka kwanta, amma Ayam sai tayi zaune akan gado ta zabga tagumi tana sake kallon wuyan hannunta daya rik'e. *A* wajen Umad ma saida ya ji an rufe d'akin ya fito, wajen hoton ya k'arasa ya durk'usa ya shiga tattare glass d'in, a kwandon shara ya zuba sannan ya d'auki hoton yana kallo, cikin yarenshi yace " *Majka* (uwata), kiyi hak'uri ba laifina bane, waccen mahaukaciyar ce da ban san me ta zo nema ba." Ba tare daya saka kaya a jikinshi ba shi ma ya zauna kan gadon yana ta kallon hoton nan, so yake yayita zazzaga masifa ko ya ji sauk'i, amma dake mutum ne ba mai hayaniya ba sa茂 kawai yake ta tsaki shi kad'ai. Sai dai ya k'agu gari ya waye ya bincika ya ji wacece wai ita d'in? Da wannan tunanin har bacci ya d'aukeshi bayan ya tofe jikinshi da addu'o'in tsari. *Washe gari* Zazzaune suke a cikin aji kowa na mazauninshi zaman mutum d'aya, sunyi shiru kuma sun nutsu suna sauraren jawabain ban kwanan da malam Pedro ke musu, yana gamawa yayi murmushi a harshen fransanci yace "To d'alibai, ni zan tafi yanzu, sai mun sake had'uwa da ku, ina muku fatan nasara." A tare dukansu suka amsa da "Za mu yi kewarka malam." Dariya yayi wanda hakan yasa Ayam juyawa ta kalli Deeyam cikin rad'a tace "Malam Pedro na dariya dama?" Dariya Deeyam tayi a kan idon malamin, harara ya galla musu yace "Hirata kuke ko?" Da sauri Ayam ta girgiza kai alamar a'a, shi ma girgiza kan yayi yace "Na sanki fa Ayam, da ni d'in nan ragon namiji ne da kin jima da sani hauka." Girgiza kai ya sake yi yace "To d'alibai, ni zan tafi na bawa sabon malamin ku dama ya shigo dan ya gabatar muku da kanshi." Hannu ya d'aga musu ya nufi hanyar fita, su ma hannun suka shiga d'aga mi shi, tun bai k'arasa fita ba Ayam ta mik'e ta tsaya a inda ya tsaya shi ma, irin tsayuwarshi tayi da yanda yake cije fuska ta tsuke baki ta fara magana kamar yanda yake alama tana kwaikwayonshi tana fad'in "To ni zan tafi, wani aiki ne ya taso da ake neman agazawarmu, amma ban ji dad'in rabuwa da ku ba musamman da shekara ta kusa k'arewa, amma duk da haka..." Mik'ewar da duk sukayi d'aliban suna gaishe da malamin daya shigo yasa Ayam k'amewa tare da bud'e baki irin" Na shiga uku." Cikin sand'a kamar wacce k'wai ya fashe ma a cikita shiga takawa har ta zauna teburinta, tana jin takon takalmin malamin suna bada sauti d'a茂 bayan d'aya, saida ya tsaya tsakiyarsu sannan ya musu izinin zama. Shiru ajin ya d'auka bayan sun zauna, shi yana k'are musu kallo su ma suna k'are mishi kallo suna fahimtar wane iri ne shi ? Zaiyi dad'in sha'ani ko kuma d'aurarrar fuska ce dashi kamar malam Pedro. Ba tare daya juyar da kanshi ba iya idonshi kawai ya zuba mata, fuskar nan tamau da ita ba alamar annuri cikin dakusashiyar murya mai firgitarwa yace "Ya sunanki?" Kamar sauran d'aliban ita ma d'aga kai tayi ta kalleshi dan son sanin da wa yake, idon da suka had'a yasa gabanta tsinkewa ya fad'i tare da kad'awar kayan cikinta, 脿 take kawai ta tausayawa kanta, marairaicewa tayi tana matse k'afafunta daga sama, wuwulk'ita idonta ta shiga yi cikin daburcewa da sark'ewar murya tace "A.. Yam." Wannan karan d'auke idonshi yayi daga kanta ya sake fad'in "Sunanki?" 'Yar k'walla kawai ta ji ta zo mata a kan kunci, a sanyaye ta sake maimaita "Ayam." Takowa ya fara yi zuwa gabanta, da sauri ta sauke idonta tana kallon teburin, saida ya tsaya daf da teburin 脿 mugun kausashe yace "Ayam, baki da sunan uba ne?" D'aga ido tayi da sauri ta zuba cikin na shi idon, hawaye taji kan kuncinta suna kwaranya, sosai maganar ta mata zafi, amma saita shanye tunda malaminta ne a aji, kanta sadde k'asa tace "Ayam Utais." Cikin tsananin bala'in haushinta da yake ji 脿 tsawace ya buga teburin da take zaune 脿 kai da hannu cikin d'aga muryar data sa ajin amsawa baki d'aya yace "Ayam Utais, ba'a koya miki tarbiyyar mik'ewa tsaye yayin magana da malami ba?" Tunda ya buga tebur d'in yan matan ajin wasu sukayi ihu wasu kuma suka k'ame, kamar dai Ayam da ita ma k'amewar tayi amma fa kuma idonta cikin na shi. Abu d'aya ya zo masa a daidai lokacin, maganarshi da babban malamin shi a sanda yake son sanin alamomin da zai ganeta, a yanzun da abun nan ya faru sai ya tuna sanda malamin yace _"Had'uwarku ta farko ba zata bada k'ayatarwa ba, saidai 脿 wurinka da zaka aje hankali, kowane motsinta zai baka al'ajabi, a zahiri mace ce kamar kowace mace, tana jin tsoron abinda zai tsorata kowace mace, saidai ba komai ke tsorata ba, akwai b'oyayyar jarumta a tare da ita, abinda ya cancanci ya bata tsoro ba shi ke tsorata ba kai tsaye, wanda kuma kai zai iya kayar maka da gaba, sa茂 kaga ita abin ado ne a gareta, saidai fa duk da haka mace ce mai birgewa, saboda tana da abinda duk wani namiji yake tsananin so ga 'ya mace."_ A lokacin tambayar daya masa ita ce _" Menene shi abun?"_ Murmusawa malamin yayi sannan yace _" Rauni, tana da rauni, dan bata iya kare kanta ga duk wani abun cutarwa."_ Ajiyar zuciya Umad ya sauke ya mik'e daga rusunawar da yayi 脿 ranshi yana fad'in" Ba ita ba ce, wannan ba zata tab'a zama Zafeera da ake fad'a ba." Sake kafeta yayi da ido yace "Jiya da dare me ya kaiki d'akina?" Zaro ido tayi tana kallon shi kamar taga bak'uwar hallita, sororo tayi ta rasa bakin magana, kallonta ya sake yi yace "Cire hular kanki, ki zama daidai da sauran d'aliban." Tsura masa ido tayi a ranta tana tunanin watak'ila fa son takura mata yake saboda yanda suka fara had'uwa, to amma ita ma zata ji dashi a haka, a hankali tasa hannu ta cire hular ta kan ta. D'an zaro ido yayi yace" What?" Jinjina kai yayi a dak'ile yace" Kin kad'e." A sanyaye ta turo baki gaba tace "Sorry sir." Juyawa yayi ya kalleta yana rumgume hannaye da mamakin yanda ta gagara mik'ewa tsaye sannan ta masa magana, ita wacece? Sauran d'aliban ya kalla yana sauke hannayenshi daga k'irji yace "D'alibai, sunana Umad Wudar, sabon mai koyar da ku, ina fata zaku bani had'in kai mu k'arasa zangon shekarar nan daku lafiya, ina so ku d'auke ni a matsayin malaminku mai sauk'in kai a aji, amma a wajen aji zamu iya zama abokai, hakan zai k'ara mana fahimtar juna kuma ku ji a ranku daidai na ke daku, kun fahimta." A tare cikin d'aga sauti suka ce" E malam." Jinjina kai yayi ya nuna d'alibin farko yace" Ku gabatar min da kan ku." D'ai bayan d'aya suka dinga mik'ewa suna fad'in sunan su, saida aka kawo kan Ayam ta mik'e ta fara fad'in" Ay..." Da hannu ya mata alamar zauna tare da fad'in" Me ye abun dad'i a sunan naki da zan ji shi sau biyu? " Idonta tar a cikin na shi tace" Sorry sir." Girgiza kai yayi tare da jan tsaki ya kalli Deeyam dake bayan ta yace" Uhum!" Mik'ewa tayi ta fad'i sunanta, har zata zauna yace" Ana koyar daku turanci ne a nan?" Girgiza kai tayi tace" A'a malam." Kallon Ayam yayi ya yatsina fuska a zuciyarshi yace" Gidan uban wa ta iya sorryn?" Haka aka gama gabatarwa ya shiga darasinshi ba tare da b'ata lokaci ba, awa uku suka d'auka ba hutu ba shan iska, gashi in suka had'a ido da ita sai ya galla mata harara, ita kuma haka kawai taji kamar ta samu abokin wasanta, ta k'i d'auke idonta daga kan shi sai binshi da kallo take. Saida ya dubi agogon dake tsintsiyar hannunshi sannan yace" D'alibai ina ga anan zamu dakata, shin da mai tambaya a darasinmu? Ko kuma wanda bai gane wani abu ba?" Girgiza kai sukayi dan magana ta gaskiya sun fahimci darasin shi sala-sala, dan haka da ya ga babu mai tambaya ya juya da niyyar tattara nashi ya nashi. K'afa d'aya kan d'aya ta d'ora ta rumgume hannaye a k'irji tace" Sir ina da tambaya?" Wani iska ya feso ba tare daya juyo ba dan yasan ita ce, saida ya sauke nufarfashi ya saita nutsuwarsa ya had'e b'acin ranshi sannan ya juyo a dak'ile yace" Uhum." Duk da ba ita yake kallo ba sai yaji gabansa fad'uwa yake kamar mai jin tsoron tambayar da zatayi, cikin siriryar muryarta tace" Sir, indai har dorinar ruwa kakkausan jiki ne da ita ta yanda alburushi baya mata illa, kenan wane irin makami ne zai iya cutar da ita kai tsaye?" Kallonta yayi wannan karan kallo irin na k'urilla, kamar sub'utar baki yace da ita" Bomb." Da mamaki a fuskarta tace" To amma yallab'ai ai mu ba'a yarje mana aiki da bomb ba." Wani tsakin ya kuma ja ya juya zai d'auki jakarshi ta sake fad'in" Yallab'ai tambaya ta gaba?" A hassale ya juyo yace" Ina jinki." Cike da son danne dariyarta tace" Ka fad'a mana zakanya tafi zaki iya farauta, me yasa to duk da shi ne namiji kuma sarki?" Tsurawa fuskarta ido yayi dan ya fahimci ba shashashan tambayoyi take yi ba, cikin d'an saita muryarsa yace" Saboda shi zaki baya son jin rauni a jikinshi, sannan yana da son hutu kamar yanda yake da jin izza ksancewarsa sarki." Jinjina kai tayi sannan ta sake fad'in" To amma kuma me yasa zaki baya mu'amula da zakanyar da bata kusa cimmasa a shekaru ba?" Tarr! Ya kalli k'wayar idonta mai kama data mage a cikin dare, sauran d'aliban ya kalla sannan ya kalleta yace" A nan ajin nasan babu wacce ko wanda bai balaga ba ko?" Ihu suka saka tare da fad'in" E yallab'ai." Jinjina kai yayi fuskarshi ba alamar fara'a sannan ya sake kallonta yace" Zaki ai sarki ne, jarumtarsa da yarda da kanshi yasa baya tarayya da wacce yasan ba zata iya d'aukarsa ba." Cike da gadara ya juya ya d'auki jakarsa inda ajin ya kaure da ihu da maganganu, saida ya fita a ajin Ayam ta mik'e tsaye akan teburin tayi wata irin k'ara tare da tintserewa da dariya tace" Yan mata wai kun yarda?" Duk yan matan ajin suka amsa mata da" A'a." Wata ihu ta sake yi tace" Ni ma ban yarda ba, abinda na yarda da shi shine mace rijiya ce, kowace irin guga aka zura mana zamu karb'a kuma mu bada ruwa." Caraf a kunnen Umad da bai k'arasa fita ba, juyowa yayi ya kalleta, samun kanshi yayi da sauke idonshi kan 'yan tsiraun nonuwanta dake cikin rigar kayan makarantar, yan firit da su ta yanda zai iya had'esu duka biyu a tafin hannunshi kuma ba lallai su cika masa hannu ba, a hakan ma dan yana tunanin ta saka bras wacce zata k'ara mata aukinsu, girgiza kai kawai ya sake yi yana jan tsaki yace "Baki san me zaki yake nufi ba." Keb'antaccen gurin cin abincin malamai ya nufa, bayan ya gabatar da abinda yake da buk'ata sai kuma ya kasa ci ya tsaya amsa waya, Haman ne ya tambaye shi "To ya sabon aikin na ka?" Girgza kai yayi yace "Ba dad'i." Dariya yayi daga b'angrenshi yace "To amma ka fara abinda ya kai ka ne? Akwai wani abu daka fara samu?" Shiru yayi tare da sauke ajiyar zuciya, jin bai amsa mishi ba yasa Haman sake fad'in "Lafiya ko Umad?" Shafa sumar kanshi yayi wacce har yanzu yake takaicin rabashi da ita da akayi sannan yace "Tana jaririya fa ta b'ata, kuma babu wani wanda yasan wani abu a kan ta, ta ina zan ma fara nemanta a Larhjadin? " Dogon tsaki ya ja wanda hakan kamar d'abi'arsa ce kafin yace "Ya binciken da na saka ka? Ka samu wani abu ne ?" Cike dta karsashi yace "E yallab'ai, yanzu haka ma zan je wajen wani ne dan samun wasu bayanai." Jinjina kai yayi yana shafa sajenshi yace "Duk yanda ake ciki ka sanar min." Bai jira amsawarshi ba ya datse kiran ya aje wayar gefe, cike da k'yank'yami ya fara cin abincin, duk da tsabtarshi da kyau da kuma dad'i, amma shi dai bai masa ba ko kad'an,haka ya d'an tsakura ya mik'e ya bar wajen. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:31 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *6* Fitowarsa tayi daidai da k'arasowar su Zafreen zasu je b'angaren su Ayam dan ganawa da wata k'awarsu, zasu wuce shi ma zai wuce kawai Zafreen ta k'ura masa ido, baki da hanci ta saki tana binshi da kallo, cike da birgewa ta juya saboda har yayi gaba ba tare da sanin me take ba tace "Wow! Amma malamin nan ya had'u." Laika ce tayi saurin kallonta tace "Gimbiya Zafreen, kina nufin ya birgeki ne?" Juyawa tayi ta kalli Laika tace "Sosai ma, idan har zan iya yin aure to shi ne mijina." Murmushi ta saki ta kalli k'wayar idon Laika tace "Ina zuwa." Kafin Laika tayi wata magana har Zafreen ta tafi da sauri tana fad'in "Malam, malam ji mana." Tabbatarwa da yayi da shi ake yasa shi dakatawa ya juya, a tsanake ya shiga k'are mata kallo, tabbas kyakyawa ce data amsa sunan kyakyawa, komai na ta yayi kuma y had'u, bata da makusar da duk namiji mai son more rayuwa ba zai so samunta ba. Kayan jikinta sun nuna mishi a wani b'angaren take nata karatun, ga kuma wani yankakkan gashi dake kan ta mai kalar ruwan d'orowa wanda haka kalar idonta ma suke. Iya fatar jikinta ta nuna masa ita ma yar hutu, ko 'yar hamshak'in mai kud'i, ko 'yar mai iko ko kuma sarauta, tana k'arasowa ya sake gyara tsayuwarsa. Saida ta zo daf da shi sai kuma sai ta ji wani kwarjininshi ya kamata, kanta sadde a k'asa ta shiga doka murmushi, cikin sanyayyar murya tace "Malam barka." Fuskar nan a had'e ya amsa da "Uhum." Duburburcewa tayi ta shiga rausayawa kamar zata taka rawa, kame-kame ta fara tace "Am.. Dama dai... Ni sunana Zafreen Musail, gimbiya Zafreen Musail." Tsura mata ido, da fari dai ya d'auka mai hankali da ilimi ce, ashe ba haka bane. In banda abinda me ye abun birgewa a cikin nuna kai waye kai tsaye? Saidai yayi farin ciki da haka, dan tabbas idan bai samu 'yar uwar ta Zafeera ba, to kan ta zai *d'auki fansa*, dama ya fi son d'aukar fansar ne ta hanyar Zafeera saboda ita yaga an fi cin buri a kan ta, amma wannan ma zai iya maleji da ita madadin yayi biyu-babu. Wani d'an siririn murmushin mugunta ya sakar mata a dak'ile yace "Barka princezna, haka kuke fad'a a yarenku na slovaque ko?" K'ara washe baki tayi kamar zata fad'a masa tace "E yallab'ai, ka iya yarenmu kenan?" Shu'umin kallo ya mata yace "E, yanayi ne yasa na iya." Sake fad'ad'a murmushi tayi tace "Am...Yallab'ai, zan iya rok'on wata alfarma?" Da ido ya mata alamar "Ina jinki." Mamaki ne ya kamata ganin wannan ma yana neman ya fi ta shan k'amshi, basarwa kawai tayi tace "Zamu iya zama abokai?" Yatsina fuska yayi kamar ya ga abun k'yama yace "Hakan ai ya sab'awa dokar kowace makaranta." Tab'e baki tayi tace "Karka damu yallab'ai, indai ka amince wannan ba matsala bane, mahaifina shi ne sarkin Khazira, duk wata masarauta a k'asar nan a k'ark'ashin ta mu masarautar take, dan haka zan iya yin komai da nake so." Sake b'ata rai yayi yana mai jin wani takaici fiye ma da wanda ya ji yayin had'uwarshi da waccen tamatsirin, dan gaba d'aya wannan magana take ta alfahari da d'agawa wacce babu tunani a cikinta. Girgiza kai yayi ya d'an juya zai bar mata gurin, da sauri tace "Yallab'ai ya haka kuma? Baka ban amsa ba." Juyowa yayi a kasalance ya kalleta, lumshe ido yayi yace mata "Kiyi hak'uri." Juyawa ya sake yi yai tafiyarshi ya bar ta nan tsaye, haushi ne ya kamata ganin yanda ya cizgata a gaban mutane, fuska a kumbure ta juyo ita ma rai b'ace ta nufi wajen su Laika dake tsaye suna kallon komai daya faru. Tana isowa ganin yanda take cika tana batsewa yasa a cikinsu babu wacce ta tambayeta lafiya? Dan zata iya juyewa a kan su, a tsiyace take tafiyar kamar zata tashi sama inda suma suke biyarta a haka. Daf da bakin k'ofar shiga su Ayam su kuma zasu fita rakata kiran Momma, a rashin sani Sabrine da Zafreen suka bangaji juna, da k'arfi Sabrine tace "Aouch!" Zafreen kuma a mugun tsawace tace "Ke!" Kafin kuma kowa ya ankara Zafreen ta kwad'awa Sabrine wani wawan mari, ihun da tayi a firgice yasa Ayam waro ido ta sauke akan Zafreen d'in, a karo na biyu Zafreen ta sake d'aga hanu zata mari Sabine tana fad'in "Ke har wace..." Cak maganar ta tsaya mata, dan bata san lokacin da Ayam ta rik'e hannun na ta ba kuma har da nasarar marinta a fuska. Dafe kuncinta tayi tana kallon Ayam dake dafe da kafad'ar Sabrine tana fad'in "Kiyi hak'uri kinji, ke ma ai kina da gata." Kamata tayi zasu wuce ka rantse da Allah bata san me tayi ba, duk k'awayen kuma sun yi mutuwar tsaye saboda ganin girman lamarin, musamman ma Laika ta fi kowa tsorata, a sukwane Zafreen ta shak'i wuyan rigarta cike da masifa tana fad'in "Ke kin..." Yanda Ayam d'in ta zuba mata ido ta kalleta sai abun ya gigita Zafreen, yanda idonta masu launin nan mai ban tsoro suka samu sirkin launin ja na b'acin rai, sai kawai ta ji gabanta yayi wata mummunar fad'uwa, kamar wacce mai fad'a a ji ya bata umarni sai ta shiga zame hannunta a jikin rigar Ayam d'in, hakan ya ba su Ayam d'in damar k'arasa ficewa a wurin. Da kallo suka bisu har da ita Zafreen d'in data sake dafe kunci tana murzawa a hankali, ta ji zafi sosai na marin nan, yau ma sai suka fasa shiga kamar dai jiya suka juya da sauri suka bi bayan Zafreen dake tafiya har da gudu gudu. *Shigarsa* ke da wuya d'akinshi ya bud'e taga kenan ya hangi Zafreen zata mari Sabine a karo na biyu Ayam ta rik'e hannun kuma ta mareta, duk da b'angaren malamai da b'angaren su Ayam d'in ba wai yana kallon juna bane, kamar kusan a jere ma suke saidai akwai ginin babban ofishi a tsakaninsu (zauran malamai). Yanda ya ga wannan abu da tuna had'uwarshi da Zafreen d'in sai ya ji gabanshi ya fad'i, a yanayin da bai saba da shi ba ma'ana tsoro yace " Wai *wacece ita*?" D'ora hannunshi yyi a kai yace "Tsarki ya tabbata ga Allah." Maganar gaskiya ko shi da ke namiji ba zai iya marin Zafreen ba, dan tana da kwarjini da izza wacce kana gani kasan ta samo asali ne daga gidan sarauta, musamman ma ita da mahaifiyarta Juman 'ya ce ga sarkin Egypt (Ya akayi ka sani? 馃), sannan mahaifinta ma sarki d'an sarki kuma jikan sarki. *Ayam* kam suna fita Deeyam a mugun tsorace ta rik'o hannun Ayam tace "Ayam kinsan me kika aikata kuwa? Ita ce fa naji ana rad'e-rad'in gimbiya ce." Saida ya zage hannunta daga na Deeyam tana karbar wayar da mai kula dasu ya mik'o mata ta d'ora a kunne tace "Then." Da mad'aukakin mamaki Deeyam tace "Ayam ba wasa nake ba fa, gaskiya nake fad'a miki." Cikin muryar kuka Sabrine da marin ya gama gigitata tace "Gaskiya Ayam da baki mareta a kai na ba, zaki iya shiga matsala." Ko kulasu ba tayi ba sai ma saka lambobi da tayi suka ji tace "Yes Momma na, barka." Jim tayi alamar tana saurare daga gurinta kafin tace "Momma ina Pah?" Kyab'e fiska tayi tace "To gaskiya ni dai ki fad'a masa ba zan hak'ura sai ya zo gobe ya kawo min kyautar k'ara shekarata." Yanda Momma ta amsa mata yasa Ayam yin jim, sau da dama tana mamakin wasu abubuwa da iyayen na ta ke yi mata, da zaran zata fara tunanin haka kuma sai suyi gaggawar katseta, yanzun ma dai yanda ta bata amsa da dole ma ya amsa kiran sarauniyarshi ba shi ya d'auki hankalinta ba kamar yanda ta ji k'amshin gaskiya da kuma b'ari na tsoro a muryarta. A daddafe ba tare da karsashin da suka fara magana ba ta yanke kiran ta aje wayar, dafe gaban goshinta tayi zata tsunduma tunanin me hakan ke nufi ? Kawai Deeyam data damu sosai cikin d'aga murya tace "Ayam, hanklinmu a tashe amma ke waya ma kik..." Wani bahagon kallo Ayam ta mata tare da nunata da yatsa manuniya, cikin sanyayyar murya kuma a tausashe tace "Karki sake d'aga min murya, ni ba 'yarki bace." Jakarta ta d'auka wacce ta aje akan tebur d'in da wayar tangarahon ke kai, ko rataya ta batayi a bayanta ba ta juya a sukwane ita ma ta bar wurin a dole suka bi bayanta cike da zulumi da jinjina isa irin ta Ayam. *Egypt* Cikin girmamawa yaron na shi ya kalleshi cikin d'ard'ar d'in ta yanda zai karb'i abinda ya zo masa da shi yace "Shugaba na, sak'o ne daga Giobarh daga sarki Wudar, ka min izinin karanta maka abinda takardar ta k'unsa?" Duk da ya ji shi sarai amma ka rantse bai ji me yace ba, ci gaba yayi da wasarshi da wani k'aramin k'wallo na kwalba mai kamar *Dutsen Diamond*, matar dake zaune gefenshi cikin fararen kaya na yadi da kambunta a kai mai kalar gwal ce ta kalleshi a tausashe tace " *Bukhatir*, ka saurari abinda ya zo maka dashi mana, ka lamunce masa ya karanta maka me takardar tak'unsa, daga sarkin Giobarh fa sak'on ya zo." Ita ma banza ya mata sai ma 'yar wak'ar daya shiga rerawa yana fad'in "Lu'u lu'u ki dawo gareni, lu'u lu'u ki dawo gareni, idan babu ke a rayuwata, ji nake kamar ma na mutu." A mugum hassale matar ta mik'e tana daka tsawa da fad'in "Ina! Ba zai yiwu ba, Bukhatir ka fara wuce gona da iri fa, wannan wace irin rayuwa ce ? Me kake neman ka mayar da kan ka ne ? Lu'u lu'un banza da..." Tassssss! Ya d'auke fuskarta da mari, tuni bafaden dake tsaye ya rintse ido dan yasan dama haka zai faru, shi yasan yanda Bukhatir ke masifar son wannan lu'u lu'u, dan haka shi ma yake kaffa-kaffa indai abinda ya shafeta ne. Tunda ta sunkuya ta dafe kunci kasa d'agowa tayi, a nutse kuma a ikonce tsabar yana ji da kansa da burin mallakar masarautar Egypt ya nunata da yatsa ya mata alamar ta fita a nan, d'auke hannunta tayi daga kunci ta kalleshi da ido sun mata jajir, cikin shashek'a tace "Ni ka mara saboda na zagi wata ban..." Tauuuuu! Ya sake d'auketa da wani marin kuma, yanzu kam a hassale kuma a gigice cikin d'aga murya yace "Ki b'ace min da gani *Zeyfi*, kuma kar ki sake gigin tab'a kimar lu'u lu'uta, idan kuma kika sake to a bakin aurenki." Zaro ido tayi baki bud'e, ai da gudu ta fita a d'akin rigarta na jan k'asa, saida ya ga ficewarta yaja wawan tsaki, kallon bafaden yayi yace" Me ye? Me yace? " Jiki na kakkarwa ya shiga warware takardar, saida ya bud'e ya fara karantawa kamar haka _" Mai girma Bukhatir, wannan takardar d'amba ce ta neman sulhu tsakanina da kai, bisa tabbatarwa da mukayi mu da kai abu d'aya muke nema, zai fi idan muka had'a k'arfi da k'arfe wajen cimma burinmu, dukanmu manufa d'aya garemu a kanta, manufar kuwa ita ce *d'aukar fansa* ga sarki Musail, zanyi farin ciki idan ka had'a hannu da ni, hakan kuma zai zama k'aruwarka, idan ka amince da buk'atata ka turo min da sak'on gayyata zuwa fadarka, sak'o daga sarki Wudar."_ Zaune yayi ya tsunduma tunani, ya d'an jima haka kafin ya kalli bafaden yace "Me kake tunani game da hakan?" Cikin ladabi yace "Shugaba, a gani na wannan wata dama ce ta cimma abinda muka jima muna nema, duk da abu d'aya muke nema da su, amma ba kamar yanda sarki Wudar yake tunanin manufar d'aya bace." Jinjina kai Bukhatir yayi yace "Gaskiya ne, idan har muka had'a hannu da shi muka sameta, a dalilinta zan hau k'aragar mulkin kakan Zafeera ma'ana mahaifin mahaifiyarta Juman, idan haka ta kasance kuwa zan zama mai sa'a a doron duniya." Jinjina kai bafaden yayi tare da fd'in "Hakane shugaba na." Wani k'ataccen murmushi ya saki ya gyara zamanshi k'afa d'aya kan d'aya yana wasa da yatsunshi yace "Tun ina k'arami nake son hawa kujerar mulkin nan, saidai sarautar a hannun yayan mahaifina take, hakan yasa shi ke mulkar gaba d'aya k'asar nan, hatta da mahaifina da suka fito ciki d'aya shi ma duk'ar da kai yake a gabansa, sannu sannu sai na fara karkata hankali na kan 'yarsa k'waya d'aya tak, murmushin da take min na d'auka na so, ashe ita tana can tana soyayyarta da wani ba ni ba, hummmm! To me ya kamata na yi? Sai na zauna na zama d'an kallo kenan?" Wani malalacin murmushi yayi tare da girgiza kan shi sannan ya mik'e ha shige uwar d'aka yana fad'in" Ka tura masa da takardar gayyata." Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya fice zuciyarshi cike da farin ciki dan bai yi tsammanin zai amince ba. *Masarautar Khazira* Zaune suke akan babban teburin cin abinci kamar na bak'i, suna had'a ido ya sakar mata murmushi yace" Sarauniyata." Had'e fuska tayi ta kawar da kan ta, murmushin gefen labb'a yayi yana kallon farantin gabanshi da babu komai a ciki yace" Kina hushi dani saboda na fad'a miki ni na kashe mijin da da zai aureki, to me yasa kike tunanin zan k'yaleshi? Ba rabonsa bace ke, ki manta kawai." Girgiza kai tayi cike da takaici tace" Baka da tausayi Musail, bayan shi mutane nawa ka kashe? Yanzu ma gashi saboda son zuciyarka 'yata data rage min ina kallo ina jin dad'i, ka turata neman wata wacce ba zata tab'a samunta ba har abada." Cikin d'aga murya tace" Idan ta mutu ita ma sai na yi me kenan?" D'aga kai yayi ya kalleta a sanyaye yace" To sai me? Ni ba mijinki bane? Ai zan iya sake baki wasu 'ya'yan idan kina so." A hassale ta mik'e tsaye tace" Tirrr! Har abada ba zan bari ka sake rab'ar jikina ba, kuma ka sani burinka akan y'ata ba zai tab'a cika ba." Da mamaki ya kalleta yace" Me kike nufi Juman?" Cike da gadara tace" Ina nufin yata da kuka yi yunk'urin kashewa kai da Dhurani, na san komai da kuka shirya a kan ta, ba zaku tab'a nasara ba ka ji da kyau." Tsaye ya mik'e yana mata wani kallo yace" Juman, ko dai ke kika tseratar da yarki?" Ba tare da tsoro ba tace" K'warai, ni na kub'utar da ita, ka samota mana idan ka isa." Juyawa tayi zata bar gurin ya daka mata wata irin tsawa yace" Jumaaaaaaann." Dakatawa tayi ta juyo tana kallonshi, a sukwane ya nufota da babbar rigarshi, kallonshi ta dinga yi har saida ya zo kan ta, bai tsaya komai ba ya gaura mata mari, kafin ta ankara ya shak'i wuyanta da hannu d'aya, duk da shi ya shak'eta amma kuma idonshi sun bala'in yin jajir dasu duk sun fito tsabar takaici da b'acin rai, cikin fitar hayyaci ba tare da duba yanda take d'aukar numfashi ba kamar zata mutu yace "Sai na kasheki, sai na kashe ki Juman, ba zaki tab'a zama silar gurguncewar rayuwata ba kuma na k'yaleki." Hadimai biyun da suka taho da kwanukan abinci ne suka tsorata ganin wannan lamari, juyawa sukayi zasu fita inda babban bafaden sarki Musail *Adah* yayo kansu da gudu, hannayen sarkin ya rik'e yana bashi baki da yayi hak'uri ya sakeg'ta zata mutu. Hadiman da suka fita ne suka had'e da waziri Khatar zai shigo ciki shi ma, ai a tare suka sake dawowa da hanzari bayan sun fad'a masa, yana zuwa shi ma kamawa yayi suka shiga k'ok'arin b'amb'areta, da k'yar sukayi nasarar k'watarta a hannunshi duk ta galabaita dan k'iris ya rage ta suma, cikin hargagi sarki Musail yake nunata da hannu yana fad'in "Ba soyayyar da kika tabbatar ina miki fiye da komai bace ta sa kika min haka ? Ai dai tak'amarki ina sonki dan haka babu abinda zai faru ko? To ki ji da kyau Juman sai na hukuntaki, ke baki san waye ni ba shiyasa, amma da sannu zaki sani tunda kika tab'oni, kuma bak'ar 'yarki zan kamota abisa taimakawar bayina, a gaban idonki zan yanka wuyanta, dan ba zan bari yar dana haifa ba ta kasheni sannan ta rabani da mulkina ba." Adah ya kalla yace" Kai Adah, ka mata jagora zuwa kurkukun k'asa na *Sabah*." Maida kallonshi yayi gareta har yanzu da numfashinta take fafutuka yace" Zaki d'and'ani uk'ubata Juman." Gefenta sarkin yak'i Adah ya tsaya hakan yasa ta kallonshi sannan ta kalli sarki Musail tayi dariyar mugunta tace" Uk'ubarka wacce ce ban sha ba ? Kai dabba ne ba d'an adam ba, kuma 'yata tafi k'arfinka banza kawai." Kan ta ya sake yi da azama waziri dake ta rarraba ido tsakaninsu yana son fahimtar inda suka dosa ya shiga tsakaninsu, cikin d'aga murya sarki Musail yace" Ka fitar min da ita a nan, kuma na tsawon kwana uku ban yarda a d'iga mata ko da tafi d'aya na ruwa ba bare abinci, wannan umarni na ne." Fashewa tayi da dariya tace" K'arshenka ya zo Musail, na ga hakan nan ba da jimawa ba, ka tabbatar min da mafarkina zai zama gaskiya dalilin uk'ubar nan da kake neman sakani a ciki, tabbas 'yata zata zo a dalilin haka, wannan shi ne ma'anar hannun da take mik'a min a cikin kowane mafarkina." Cikin ladabi Adah ya mata nuni da k'ofa, juyawa tayi da sauri ta shiga takawa tana fad'in" Ku zuba ido ku gani, da sannu sabon tsari zai zo a k'asar Khazira, 'yata zata canza komai ko da hakan na nufin ta cire kawunanku ne, mak'ask'anta kawai." A dakonce waziri ya kalli sarki Musail da mamaki yace" Sarki na ka tabbata hukuncin nan ne ya kamaceta?" A hassale yace" To da me ya kamata nayi?" Dogon tsaki yayi ya nufi hanyar fita yana fad'in" Ka nemo min babban malami a duk inda yake." Sunkuyawa yayi yace" Angama shugaba na." Saida ya shige sannan ya d'aga kan shi, jiki a mace yana ta tunanin abinda ya faru yanzun ya fita isar da sak'on sarkin. *Wannan littafi na kud'i ne, ku garzayo ku biya na ku dan jin yanda zata kaya, dan an kusa rufe free page, dan neman k'arin bayani tuntub'i lambar dake sama, zan ga masoyan k'warai da masoyan baka馃槀.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:32 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *7* Ta b'angaren wurin kwanan hadimai da bayin gidan suka bi suka wuce, yanda hadiman suka yi tsuru suna kallo cikin jimami ana wucewa da sarauniyarsu yasa duk suka ji ba dad'i, a sanyaye take wucewa har saida suka kusa shiga ta wata kusurwa, d'aga kanta tayi dake k'asa ta kalli wani d'aya daga cikin fadawan gidan, wani k'ayataccen murmushi ta sakar masa ta juya harshenta zuwa larabcin parsi tace "Ko ta halin yaya kayi k'okari ku had'u da ita, ka sanar mata ta fad'a musu su ninka kulawarsu da saka ido a kan ta, dan komai ya kusa fitowa fili." Sake fad'ad'a murmushi tayi ta d'ora hannunta akan shi kasancewar matashi ne tace "Ka kula da kan ka." Duk da hawayen dake taho mishi saida ya rusuna mata yana jinjina kai alamar karb'ar sak'onta, wucewa sukayi haka hadiman wasu ke kuka wasu kuma jimamin ne kawai a fuskarsu, a haka aka shiga da ita wata hanya dake sadar da mutum zuwa k'asa, tafiya sukayi mai nisa a cikin wurin da zaka rantse a wata duniyar kake ko kuma wani ramin b'era ne, banda jan fitilun da suka haska gurin da zai kasance mai duhun gaske. A hankali suka fara isowa kurkukun inda d'akunan suke a laye kowane mutum d'aya ne a ciki, k'ofofin bak'in k'arfe ne da manyan kwad'on da ake datse k'ofar, daga sama kawai ake k'aramar tagar da iya fuska zata iya lek'awa ta ga na ciki. A b'angaren dama ya bud'e mata wani d'aki ta shiga sannan ya mayar ya rufe, babu komai a d'akin banda shafaffen simiti, baya ga haka babu komai a d'akin dan ko wuta babu kuma ba wata taga bayan wacce ke jikin k'ofar, ko haske iya na fitilun dake corridor wurin ne ke d'an haskaka sauran d'akunan. A hankali ta sulale ta zauna a wurin tana fashewa da kuka, kukan ba wai na canjin daya risketa bane a take, na yanda 'yarta da kuma marik'anta zasu kasance, tasan dole su sake jajdadda nemanta, suna samunta kuma kasheta zasuyi, wannan tunanin yasa ta yin kuka kamar zata shid'e. *Giobarh* Suna had'uwa da mutumin ya mik'o masa k'aramar farar takarda a nad'e, karb'a Haman yayi ya bud'a takardar ya karanta sannan ya kalleshi yace "Ka tabbata?" Jinjina kai yayi yace "Na tabbata yallab'ai." Shi ma jinjina kan yayi ya fito da dunk'ulen kud'i ya bashi yace "Nagode." Da sauri ya karb'a yana fad'in "Ni ma nagode yallab'ai, idan buk'atar wani abun ta taso ka nemeni kawai." Jinjina kai Haman yayi amma bai ce komai ba, lafiyayyar motarshi ya shiga cikin salo da k'warewa ya tayar ya bar gurin, tafiya yayi mai nisan gaske kafin ya isa ga lambun da aka bashi kwatancen. Fitowa yayi a motar ya tunkari shiga ciki, k'ofar da akayi da siraren k'arafu na ya tura ya shiga yana ta kalle kalle da son hango mutum, saida ya kai tsakiyar lambun ya ji motsi ta gefensa, waiwayawa yayi hakan yasa shi ganin mutum tsaye ya d'ana bindigarsa a kan shi yayi shirin kare kansa. Gyara tsayuwa Haman yayi ya fuskanci mutumin ya d'aga hannayenshi sama yace "Kwantar da hankalinki, ban zo nan dan na cutar da kai ba, ni ba mugu bane." Saida ya sake saitashi da bakin bindigar yace "Ta ya zan yarda da kai? Waye kai ? Kuma me ya kawoka sansani na?" Hannu d'aya Haman yasa aljihu ya fito da bajon shi ya nuna masa yace "Ni sunana Haman Bahar, jami'in bincike ne na farin kaya, na rok'eka ka tsaya muyi magana." Kallon tuhuma ya masa yzce "Na kasa yarda ba cutar da ni za ka yi ba." Cikin ankarewa Haman ya zura hannunshi bayan rigarshi a k'ugunshi ya ciro bindigarshi mai lasisi ya jefa a k'asa kusan k'afafun mutumin yace "Wannan shi ne, na rok'eka ka saurare ni, na zo ne muyi magana akan b'atan yar sarki Musail, an tabbatar mana da kai ne bafaden da kasan jakadiyar sarauniya Juman, dan ku ne masu gadin bakin k'ofar shiga masarautar kai da mijin ta mai sunan Utais." Sak'e yayi tare da sauke bindigar yayi k'asa da ita, ba tare daya daina tsareshi da ido ba yace" Me kake son sani daga gareni?" Gyara tsayuwa ya sake yi yana sakin numfashi yace" Kai ne mutumin da ka san mutanen nan guda biyu, sannan daga majiya mai k'arfi kai ma nemanka akayi aka rasa shekara d'aya da b'atan gimbiya Zafeera, dalilin b'acewarka nale son sani, da kuma inda zan samu Habbee da Utais." Wani d'an murmushi yayi tare da juyawa yana tafiya yace" Tambayarka ta d'aya kam zan amsa, amma ta biyun ka manta da ita." Da sauri ya bi bayanshi tare da sunkuyawa ya d'auki bindigarshi ya mayar a mazauninta yana fad'in" Me yasa ka ce haka?" Bai amsa mishi ba har saida suka shiga wani falo, wuri ya nunawa Haman ya zauna yana k'arewa d'akin kallo, tsaye yayi a kan shi yace" Shayi zan kawo maka ko ruwa?" Girgiza kai yayi yace" Ko d'aya, nagode." D'aga kafad'a yayi irin oho d'in nan sannan ya zauna kujerar dake fuskantar Haman d'in, k'urawa juna ido sukayi kafin yace" Ina jinka." Gyara zama Haman yayi yace" Me yasa ka bar masarautar Khazira?" Cikin sakin fuska yace" Dalili ne mai k'arfi, umarta ta akayi da na bar k'asar, ba ni ne bari dan ina so ba." Da mamaki yace" Waye ya umarceka?" Ba tare da kwalo kwalo ba yace" Sarauniya Juman ce." Wani sabon mamakin ne ya kama shi yace" Sarauniya Juman kuma? Amma me yasa?" Gyara zama yayi ya sauke ajiyar zuciya yace" A duk masarautar ni kad'ai na iya yaren k'asar Azarbhaijan, hakan yasa ni da su Habbee muke hira a tsakaninmu dan su 'yan k'asar ne." Da matsanancin mamaki Haman yace" Akan haka ta umarceka kayi nesa da masarauta?" Jinjina kai yayi alamar e, ba tare daya shanye mamakin ba yace" In hakane kuwa kar ka ce min sarauniya na da hannu a b'atan yarta?" Wata yar dariya yayi sannan yace "Ka canka daidai." Girgiza kai Haman yayi yace "Amma ta ya ta iya jurewa haka? Me yasa ma tayi hakan?" Cikin rashin sani yace "Wannan ne kuma ban sani ba, abinda na sani kawai shi ne ta kub'utar da 'yarta." Jinjina kai Haman yayi yace "Na ji wannan, yanzu zaka taimaka min ka fad'a min inda zan samu su Habbee?" Girgiza kai yayi yace "Kamar yanda na fad'a maka ka manta da tambayar nan, dan ni ma ban sani ba." Murmushi Haman yayi yace "Kaga, ka daure ka fad'a min, idan ma wani abu kake so ni ka fad'a min zan baka, binciken nan yana da mahimlanci a gareni." Mik'ewa yayi tsaye yace "Na fad'a maka ni ban san inda suke ba, sak'o kawai nake isar wa da sarauniya." Shi ma tashi yayi tsaye yana sauke numfashi yace "Amma ta ya kake isar mata da sak'on?" Ajiyar zuciya mutumin ya sauke kafin yace "Kana neman k'ureni ka sa na karya alk'awarin dana d'auka." Cikin rarrashi Haman yace "Kai kanka nasan za kayi farin ciki a ce yau farin cikin sarauniyarka ya dawo ta dalilinka, gimbiya Zafeera yarinya ce da muka fuskanci girman lamarinta, dalilin hakan rayuwarta ta shiga cikin had'ari mai girman gaske, muna son sani wani abu a kan ta dan bata kariya ne daga masu son cutar da ita." Jim yayi yana kallon Haman na tsawon dak'ik'u, muskutawa yayi yace" Na yarda da kai yallab'ai, ba dan komai ba sai dan abinda ka fad'a gaskiya ne cewa rayuwar gimbiya Zafeera na cikin had'ari." Numfashi ya sauke kafin yace" Zaka samu cikakkun bayanai inda suke a wajen wata tsohuwa dake k'auyen Larhjadin. " Cike da zumudi Haman yace" Me ye sunan tsohuwar? A wane gari ne?" A nutse yace" Ruman, k'auyen *Tankara*." (Mai Dambu ta mu ina godiya da wannan kyautar, Allah bar zumunci) Hannu ya mik'a masa cike da jin dad'i yace "Nagode sosai,na ji dad'in had'uwa da kai." Jinjina kai yayi shi ma yace "Ni ma haka, fatan nasara." Murmushi yayi sannan suka saki hannun juna ya fita a lambun gaba d'aya, a hanyarshi ta zuwa k'auyen Tankara ya kira lambar Umad, dan yayi niyya yau zuwa gobe sai ya samo bakin zaren nan, dan sun jima suna doguwar tafiya saboda yarinyar nan, abinda ya fi basu wahala kuwa shi ne kafin su samu wanda zai iya basu bayanai a kan ta, da k'yar suka samu wata baiwa da sarki Musail ya ma ciki, amma saiya koreta saboda a lokacin yana cikin tashin hankalin neman Zafeera, ita kuma haushin yanda ya koreta bai sakata a layin k'wark'wararsa ba ma bare ta zama matarsa yasa ta fad'a musu bafaden da taji suna wani yare da su Habbee. *Umad* na tsaka da jinjina k'arfin halin Ayam na marin da ta wa Zafreen ya ji k'arar wayarsa, da sauri ya d'aga ya d'ora a kunne amma bai ce komai ba, Haman da yasan komai ne ya fara fad'in "Kana ji?" "Umm." Ya fad'a a k'asan mak'oshi, d'orawa da "Na samu mutumin nan Umad, ya ban adreshin d'aya mutumin kuma na sameshi." A zabure ya tashi tsaye yace "To ya kukayi? Me ya ce?" A tsanake yace "Ya fad'a min komai, yanzu haka zan je k'auyen Tankara ne." Da mamaki Umad yace "Tankara kuma?" "E." Ya fad'a kai tsaye, da alamar tambaya yace "To amma me yasa?" Kamar yan1 gabanshi ya shiga girgiza kai yana fad'in "Umad lamarin nan fa ya wuce yanda kake tunaninshi, wai ma kasan da sarauniya Juman ita ce ta sa aka d'auke yarinyar dan ta kub'utar da ita?" Da mad'aukakin mamaki Umad ya shiga zagayen d'akin hannunshi akan k'ugunshi yace "Idan na fahimceka sarauniya Juman ita ta umarci jakadiyarta Habbee da mijinta da su gudu da yarinyar, haka kake nufi?" Jinjina kai yayi yace "Tabbas kuwa hakane." Wani shak'iyin murmushi Umad yayi sannan yace "Hummm! Sannu sannu dai, komai ya kusa fitowa fili." Zura hannunshi yayi aljihu yana takawa a hankali yace "Shikenan Haman, ka ci gaba da bincika mana komai a tsanake, Allah ya kiyaye ka." Murmushi yayi yace "Nagode, sai na kiraka." Lumshe matsakaitan idonshi yayi alamar to kamar suna kallon juna. *Khazira* Hankali tashe babban malamin ya iso fada, sai ga sarki Musail na ta kewayar d'akin ya cire babbar rigarshi ya aje sai zufa yake, cikin tsawa da hargagi ya kalli malamin yace "Babban malami ta ci amanata, Juman ta ha'ince ni, shin soyayyar dana nuna mata ce ta gagara? Ko kuma butulci ne irin na mace?" Jim ya d'anyi kamar zai ba wani damar fad'an wani abu, sai kuma yay saurin fad'in "Yanzu me ye abun yi baban malami? Ya zanyi na samota ta dawo gareni? Ina so na kamata da hannaye na, Dhurani bana so na mutu yanzu." Ya k'arashe maganar yana d'aga murya, cikin rarraba ido Dhurani yace "Sarki na, wannan ai abu ne mai sauk'i, mu takura gimbiyar mu har sai ta fad'a mana." Khatar ne yayi saurin fad'in "Da zata fad'a ai da ta fad'a, shekaru ashrin fa muka d'auka muna bilinbituwar nemanta, a gaban idonta muke yi da me ta tab'a taimaka mana?" Sarkin yak'i Adah ne ya d'an jinjina kai duk da ba'a buk'ace shi ba yace "Gaskiya ne, amma ko bata fad'a da bakinta ba mu zamu nemota." Kallonshi sarki Musail yayi yace "Adah bana son wasa, wane irin nema ne baku mata ba ? Tun kana da k'ruciya kake yawon nemanta, sai yanzu ne zaka ganta?" Sunkuyar da kai yayi yace "Sarki na, sa'ilin da zamu kai sarauniya kurkukun sabah sun yi wani yare ita da d'aya daga cikin bayinka, bana tamtama cewa maganar da sukayi ta shafi gimbiya Zafeera." Da saurin bala'i sarki Musail ya tunkareshi yace "Wanene shi? Me suka tattauna?" Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba ya shugabana, dan kafin ta masa magana saida ta canza harshe." A bala'in tsawace yace "Waye shi a gidan nan, je ka kawo min shi nan." Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya juya cikin takon k'arfi yaf fita a falon, bai d'auki lokaci ba ya dawo waccen bafaden na bayanshi, gefe sarki yak'i Adah ya tsaya shi kuma ya zube har k'asa yana gaishesu, saidai a zahirinshi da bad'ini hankalinsa a tashe yake, ba ka da abun zargi ma ka ji tsoron amsa kiran sarki Musail bare kuma shi da yake ji a jikinshi asirinsa ne ya tonu. Cikin daka tsawa sarkin yak'i Adah yace "Kai k'ask'antaccen bawa, sarki yana so ya ji abinda kuka tattauna tsakaninka da sarauniya Juman?" D'aga kai yayi ya kali sarkin yak'i jikinshi na makyarkyata, kame-kame ya fara ya rasa me zai ce da shi, a sukwane sarki Musail yayi kan shi, kafin ka ce me ya saka k'afa ya hankad'ashi ya fadi kwance, kafin ya tashi yasa k'afar ya take masa k'irji, cikin k'araji yana zazzaro ido yace "Zaka fad'a min ko sai na kasheka a banza? Ka sani duk wanda yace zai shiga tsakani na da cikar burina kamar wanda zai taimakawa mak'iyana kyautar takobi ne dan yak'ata, dan haka ba zan bar shi a raye ba, yanzu fad'a min me ta fad'a maka?" Cikin tashin hankali da tsananin tsoro yace" Sarki na, shugaba na ka min rai karka kasheni, ta ce ko ta halin yaya na isar da sak'onta, na fad'a mata ta ninka saka ido akan gimbiya." A tsawace ya sake fad'in" Wacece? Kuma a ina take?" Cikin rawar jiki yace" Wata tsohuwa ce, a k'auyen Tankara." "Me sunanta?" Dhurani ya tambaya daga gefenshi, cikin rawar leb'e yace "Ruman, Ruman ne." K'atuwar takobin dake k'ugun sarkin yak'i Adah ya jawo, kafin kowa ya ankara kawai ya sokawa bafaden nan ita a tsakiyar ak'ogwaronsa ta hudashi zuwa wuya, wani huci ya shiga saukewa ya mik'awa Adah wuk'ar yana fad'in "Duk wanda ya yi k'ok'arin hanani kasheta to shi ma kasheshi zan yi, sarkin yak'i." Da sauri Adah ya amsa yana rusunawa, juya baya yayi yace "Ka d'ebi wasu daga cikin mayak'anka ku nufi Tankara, idan tana nan ku taho da ita, idan kuma hakan ya gagara ku sanar da ni, ni zan je har inda take sannan na kasheta da hannu na." Amsawa yayi da "Angama Ranka shi dad'e." Kafin ya kama hannayen gawar nan ya jashi k'iiiii har ya fice da shi a falon. *Larhjadin* Ba wani yammaci bane sosai, amma dake makarantar akwai wadatar shuke shuke sai tayi luf sai iska mai sanyi dake kad'awa, duka d'aliban mata suna tsatsaye bakin mota inda dreban ke jiransu, suna cikin shiga ta kakin ma'aikatan gandun daji, riga da wando kalar shud'i da babu kwalliya, saidai daga yanayin d'inkin da wasu ado da akayi ga rigar zai shaida maka masu tsaron k'asarsu ne, bak'ak'en huluna ne a kan su sun daidaita musu zama cikin k'warewa, ga kuma takalminsu bak'ak'e k'afa ciki sai k'yalli suke sun d'auresu tamau da d'amara. Gyara tsayuwarta tayi tana murgud'a baki tace "Wai malamin nan bai san lokutan karatu dana hutu bane? Ya zai shanya mu a nan?" Sergent d'in colonel ne ya tsaya gabansu cikin d'aga murya yace "Ayam Utais, yallab'ai canal (colonel) na san ganinki yanzu a ofishinshi." Waina idonta tayi ta kalli Deeyam da ita ma ke kallonta tace "Wai ni sai yaushe ne canal d'in nan zai barni na huta?" Murmushi Deeyam tayi tana rik'e d'amarar k'ugunta a hannu tace "Ranar da ke ma kika barshi ya huta, ba ke kullum 'yar masifa ba ce." Turo baki tayi gaba alamar rashin jin dad'i sannan ta nufi hanyar tafiya tana fad'in "Sai na je kuma yayi ta sadda kai k'asa kamar ya ga gyatumarshi." Yanda aka mata d'inkin daidai da zubin hallitarta yasa kayan suka karb'eta da kyau, duk da bata da wasu mazaunai na a zo a gani, amma dake ta d'aure da zanzaro sai hakan ya basu damar juyawa. Motocin data gani da suka amsa sunansu masu bala'in kyau da kuma shek'i yasa ta k'ura musu ido a ranta ta ayyana "Ko dai bak'i a ka yi?" Suna kai wa bakin ofishin ya ja ya tsaya ya nuna matata shiga, kallon shi tayi t tab'e baki sannan ta kama hannun k'ofar ta murd'a, k'afa d'aya ta fara zurawa ta shiga a matuk'ar nutsuwa da kuma wani irin kwarjini da izza, tana k'arasa shiga kamar dai mutanen ciki ita ma sai ta zuba idonta tana k'are musu kallo. Canal dake kujerarshi ya had'e hannaye wuri d'aya sai rarraba ido yake, amma tana shigowa ya mayar da hannayenshi k'asan teburin ya koma kallon takardun gabanshi kamar wanda ya ga aljana. Waziri Khatar kuma na kujerar dake fuskantar ta canal d'in fuskarshi a matuk'ar had'e yanda zta gigita mai kallonta, ga shigar da yayi ta alfarma ita kad'ai zata sa ka rusuna mishi ka d'auka sarkin ne da kanshi. Sai Zafreen dake tsaye bayan wazirin ta rumgume hannayenta ta k'urawa Aya d'in ido. Sai kuma wanda zata iya cewa shi bata san me ya kawoshi nan ba, dan in wannan yana zaune ne saboda marin da ta wa Zafreen, to shi kuma fa? Yallab'ai Umad kenan, gashi dai cikin kakinshi a shirye tsaf, amma kuma ya barsu suna jiranshi har yanzu gashi za'a zo a nemi b'ata mata rai. Yanda ta tsaya gaban tebur d'in yasa canal d'aga kai ya kalleta, suna had'a ido kawai sai ya ga kamar hararanshi ma take, da sauri ya mayar da kanshi ga d'aya daga cikin fadawa biyun da Khatar ya shigo da su yace "Rufe k'ofa." A ladabce bafaden ya rufe k'ofar a lokacin ta juya ta kallesu sannan kuma tasan da zamansu, maida kallonta tayi ga canal d'in tace "Yallab'ai ka ce kana son gani na." D'aga kai yayi ya kalli fuskarta, amma abinda Umad dake zaune yana tsare kowa da ido ya lura da shi shine yanda yake ta yawo da idon na shi ya kasa tsayar dasu a kan fuskarta bare ya kalli idonta, hakan yasa shi dasa alamar tambaya aka wannan lamari. Cikin taushin murya yace "Ayam, me ye dalilin da yasa kika mari gimbiya Zafreen? Shin ban fad'a miki ki fita a sabgarta ba?" Gyara tsayuwarta tayi ta juya ta kalli Zafreen d'in, sai kuma ta kalli waziri daya cika fam yana jiran fashewa, tab'e baki tayi ta kalli canal tace "Tun ranar ai na fita a harkarta, ita ce ta sake shiga hurumi na." Wata irin tsawa ya daka mata tare da buga tebur din ya mik'e tsaye yana fad'in "Ke d'in banza, wacece ke da zaki ja da ita? Kinsan matsayinta a makarantar nan kuwa? To ko yanzu ta so z..." A hassale ta kalleshi gaba da gaba ta zazzaro idon ta wanda launin shud'i yayi wani kore-kore ga mai kallonsu, cikin tsiwa da fad'a tace "Waye kai da zaka min tsawa? Uba na ne kai ? Na sanka ne? Ka zo d'aukar mata fansa ne? To ina jira kayi yanda zakayi da ni." Sake k'ura masa ido tayi ta nunashi da yatsa manuniya tace "Malam murya k'asa, ni ba kowa bace amma haka kawai nake jin na tsani a d'aga min murya, kuma a jinina nake jin kamar ina da izzar da zan hukunta duk wanda ya min hakan cikin d'anyan kai." Juyawa tayi ga canal, tuni ya gyara zamanshi yana ta k'yak'yabta ido, tabbas da yana da addinin musulunci a lokacin daya shiga karanto addu'ar tsari da shed'anu, sam bai yarda da Ayam dan lamarinta tsoro yake bashi, shi fa babu kamar ma yanda jikinshi ke d'aukar b'ari idan ya hangeta kawai, har ya kan tambayi kan shi k'awayenta da sauran mutane basa jin hakane ? Sai kuma ya ba kanshi amsa watak'ila dan sun saba da ita ne shiyasa, dan sun fad'a mishi tun suna yara suke tare tun a makarantar *Ansawwd* (ma'ana *inganci*). A sanyaye kamar ba ita ba tayi kalar tausayi tace "Canal yarinyar nan fa marin k'awata tayi, kuma ka sani kai ma bana son a tab'a min k'awayena, to me yasa zan k'yaleta?" Cikin sub'utar baki yace "Gaskiya ne, na sani Ayam, yanzu kiyi hak'uri ki je na jiranki zaku tafi jeji." Wani k'ayataccen murmushi ta saki tace "Shukran." Sakin baki yayi a ranshi yace "Yau ma wani yaren?" Juyawa tayi cikin takon k'arfi da salo ta fita a ofishin babu wanda yayi yunk'urin hanata, Umad dake zaune mik'ewa yayi ya sarawa canal d'in sannan yace "Yallab'ai da izininka zan tafi." Da hannu ya nuna masa k'ofa alamar ya tafi d'aya hannunshi kuma na share gumi da yayi, saida Umad ya fita Zafreen ta girgiza kan ta ta dawo hayyacinta, rarako idonta tayi tace "Kutumar can, wacece ita?" Khatar daya kasa anfanuwa tunda ta shiga kora masa bayani ko k'yabtawa bai yi sai yanzu, cikin fitar hayyaci da rashin sanin me ya fad'a yace "Ta musamman." "Me?" Zafreen ta fad'a a tsiwace, kamar mari ta gaura masa haka ya zabura ya juya ya kalli canal, cikin masifa ya shiga fad'in "Dama haka kake mata kashedin? Wai wannan wace yarinya c da kai kan ka ke tsoron had'a ido da ita? Me ta taka a k'asar? Dan gwamnati ta d'auki nauyin karatun ta ba shi ke nufin zata taka kowa ba, ka fad'a min wacece ita?" Tsura masa ido canal yayi yace "Wacece ita?" "E, wacece ita?" Ya fad'a a zafafe, numfashi ya sauke sannan yace " *Abinda idonka ya nuna maka*, ita d'in ita ce, bayan haka bansan komai ba." Tsaki Khatar ya ja tare da juyawa ya kalli Zafreen yace "Zo muje gimbiya." Da sauri suka fice a ofishin canal na kallonsu, saida suka fita har da bayinsu shi ma ya ja tsakin yace "Aikin banza, naga ma kai ka fini firgita da lamarinta tunda suman tsaye ka yi, can kuje ku k'arata da matsalarku da ita ni ku daina sakani, tunaninta kad'ai hawan jini yake tayar min." *Ayam* kam na fitowa ta kawo daf da motocin da Khatar ya zo ta tsinkayi muryar Umad yace" Ke." Yi tayi kamar bata ji ba ta ci gaba da tafiya, sake fad'in yayi" Ke." Nan ma ko waiwaye bare hasa ran zata tsaya, saida ya bushi iska ya daddage yayi ta maza yace" Ayam." Cak ta tsaya tare da juyowa tana murmushi tace" Na'am yallab'ai." Gyara tsayuwarta tayi saida ya k'araso yana d'an cije leb'e da mamakin kenan ta ji banza ne ta masa? Tsareta yayi da ido kamar mai son gano wani abu a fuskarta sannan yace" Me yasa kika wa babban mutum fitsara? Dama rashin kunyarki ta kai haka? Sannan me yasa kika mareta?" Ajiyar zuciya ta sauke irin ka dameni d'in nan sannan ita ma ta zuba idonta a na shi a yaren Italy tace"... *Saura k'iris a rufe free page, hanzarta ki biya na ki, farashin mai sauk'i ne.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:32 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *8* Cikin yaren Italy tace "E tu? Il figlio verde o uno dei loro cortigiani (kai kuma fa? D'an korensu ko d'aya daga cikin fadawansu?" Zaro ido yayi a tsawace cikin b'acin rai yace "Silenzio! Omicidio cosa ci dirai, pazzo (shiru ! Ki dinga sanin me zaki fad'a mana, mahaukaciya)." Cike da shak'ihanci ta gyra tsayuwa tace "Kai ma ka dinga sanin sunan da zaki dinga kirana dashi malam." Girgiza kai yayi irin na takaicin nan yace "Nonsense (shashanci)." Murmushi tayi tace "I'm not talking about nonsense, I'm telling you so i can do what you don't expect (ba ina magana bane akan shashashanci, ina fada ne dan zan iya yin abinda baka tsammani)." Da mad'aukakin mamaki yace "How do you change language like this? Who are you (ta ya kike iya canza yare haka? Wacece ke)?" Sunkuyar da kan ta tayi tana murmushi tace "Tu me prend juste comme tu me vois, je ne sais m锚me pas, c'est juste moi (Ka d'auke ni a yanda ka ganni kawai, ni kai na ban sani ba, ni ce kawai)." Juyawa tayi a sanyaye zata tafi ya bita da kallo, gyara tsayuwa yayi har ga Allah jiri yake ji na son kwasarshi ya jefar a k'asa, yarinya kamar aljana ko wata matsafiya, da sauri ya girgiza kan shi ya kawar da abinda zuciyarshi ke sak'a mishi a kan ta, takawa ya shiga yi da k'arfi k'arfi har ya isa garesu inda suke tsatsaye. Ganinshi ya taho yasa d'aliban duk suka dinga shiga cikin motar wasu ta k'ofar gaba wasu ta baya, Ayam ma na daf da shiga ta ji an ce "Gimbiya ta." Da farin ciki ta kalli inda ta ji sautin kuma ta gane sautin waye, da gudu ta sauko a matakalar ta nufeshi tana fad'in "Pah." Tana zuwa ta bud'e hannaye zata fad'a jikinshi kawai ya rusuna kamar yayi ruku'i, hakan ya k'ara saka Umad ghara tsayuwarshi yana kallonsu. Marairaicewa tayi ta turo baki tace "Pahhh? Me yasa?" D'agowa yayi yana dariya yace "Tuba nake, ai ba laifi nayi ba dan na kira gimbiya ta da gimbiya." K'arasawa tayi ta bud'e hannayenta ta rumgume shi tsam tana sauke ajiyar zuciya, bai yarda ya rik'e jikinta ba, dan wanda tayi ma suna d'aukan hakan wata alfarma ce garesu, su suka raini yarinyar tun tana k'arama, sun sha al'ajabi da mamaki a game da abinda ya shafeta, har wasu lokuta sukan shiga yanayi na tsoro da fargaban ko dai ba mutum bace, lallai sun yarda rashinta a msarautar nan shi ne yafi alkairi. Hannunshi dake b'oye a bayanshi ya fito da shi cikin murmushi yace "Gimbiya ga kyautar ki." D'agowa tayi ta kalleshi tasa hannu biyu ta karb'a tana dariya tace "Amma Pah ai gobe ne ranar, me yasa ka kawo min kyauta yau?" Da fara'a a fuskarshi yace "Maman ki ta fad'a min kin je bana nan, kuma kin kira kika tambaye ni, shiyasa na kawo kai na kafin ki sake nema na." Fad'ad'a murmushinta tayita sake rumgume shi tace "Thank you Pah, I'm so proud of you." Kallonta yayi a ladabce yace "Na sha fad'a miki bana gane kowane yare bayan na slovaque da azharbaijan, ban fahimci me kika fad'a ba." Had'e murmushinta tayi tace "Pah, dama ina so na tambaye ka, wai me yasa sai na dinga yin yaren da ni kaina ban sani ba? Na lura hakan ya fara tsorata mutane game da ni." Girgiza kai yayi yace " Ban sani ba, bansan komai akan haka ba, ina ga baiwarki ce haka." Cike da gamsuwa ta saki fuskarta tace" Pah, ce wa nayi nagode sosai, kuma ina matuk'ar alfahari da kai." Kan shi ya rusuna dake nuna ya ji dad'in abinda ta fad'a a matsayinta na shugabarshi, kamar katari sai kuwa ya had'a ido da Umad dake tsaye yana kallonsu idonshi cikin bak'in glass, duk da basa kallon juna ido cikin ido, amma sai Utais ya k'ureshida ido, lura da inda yake kallo yasa Ayam juyawa, da sauri ta kalli Utais tace "Pah, ni zan tafi, zamu fita ana jira na." Hannu ta d'ora a kafad'arshi ta sumbaci kumcinshi tace "Pah zan kiraka, kar fa kayi nisa da gida." Bai kula da abinda ta fad'a ba dan hankalinshi ya tafi kan Umad, saida ta juya zata tafi yace "Waye shi?" Juyowa tayi ta kalleshi ta kuma juyawa ta kalli Umad, gimtse fuska tayi tana jin haushin yanda ya tsaya musu haka kamar mai son ganin me zasuyi, kallon Utais tayi tace "Sabon mai horar da mu ne Pah, kar ka damu ka je kawai." Jinjina kai yayi ya gyara tsayuwarshi ya bita da kallo, saida ta shiga motar rik'e da kwalin kyautarta sannan Umad ya shiga ta d'aya k'ofar, tayar da motar akayi hakan yasa Utais ya shiga d'aga mata hannu ita ma daga ciki tana d'aga masa hannu kamar zasu rabu, saida sukayi nisa sosai har sun kusa fita a makarantar ya daina d'aga musu hannun, numfashi ya sauke a hankali ya furta "Wanene shi? Ya aka yi ya min kama da wanda na sani da jimawa?" D'aga kafad'a yayi ya shiga takawa shi ma dan dama idan ka zo ganin wani baka shiga da abun hawanka idan ba kai d'in wani bane, bare kuma shi da bus ya hau ya zo nan d'in kuma ita zata sake maida shi inda ya fito. Tunda motar ta fita a harabar makarantar d'aliban suka kwashi rera wak'ar da suka saba yi a irin wannan lokacin, amma Ayam hankalinta ya karkata kan mahaifinta, zuwan nan da yayi ya sata jin wani abu daban, bai tab'a zuwa a irin wannan lokacin ba, yanda ya sunkuya mata ga da ga kuma ya jadadda mata da dan ya kira gimbiyarsa da gimbiya me ye a ciki ? Ajiyar zuciya ta sauke ta sake k'amk'ame kwalin kyautar daya bata, Umad na zaune a kujerarshi a baya yana k'arewa yanayinta kallo daga cikin glass, wata zuciyar ce tace masa "Akan me zaka mayar da hankalinka kan wannan yarinyar? Ka duk'ufa neman abinda ya kawoka mana." D'auke kan shi yayi haka har suka isa jejin mai abun al'ajabi da tsoratarwa, fitowa sukayi suka kama layi a jere, gabansu ya tsaya hannayenshi goye a bayanshi cikin d'aga sauti yace" Shin a cikinku akwai mai sha'awar ganin wata dabba ne a zahiri?" Bakwai a ciki ne suka amsa da" E yallab'ai." Hannun damansa ya kalla ta farkon ya tambaya da" Me kike son gani?" Cikin d'aga murya ba tare da idonta ko gangar jikinta ya motsa ba tace" Alfadari yallab'ai." Kallonta yayi yace" Me yasa?" Tana yanda take tace" Ina so na tabbatarwa kai na lallai ana samar da shi ne ta hanyar had'a jaki da kuma doki suyi barbara." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa ya kalli ta gaba ita ma ya tambaye ta, da haka duk suka fad'i kalar dabbar da suke son gani a rayuwarsu har aka zo kan Sabrine dake kusan Ayam tace" Dorina yallab'ai." Kallonta yayi ita ma yace" Me yasa?" Tana kallon gabanta tace" Saboda jiya ka fad'a mana tana da kakkausar fata, ina so na tab'a na ji." 馃槀 Takawa yayi a hankali ya tsaya gaban Ayam, haka kawai ya ji zuciyarshi na kakkarwa da jin d'ar d'in tambayarta, dan bai san me zata fad'a ba ita, karta fad'a musu abinda zai kashesu ma, k'wayar idonta yake kallo daga cikin gilashin nan sannan yace" Ke fa?" Kamar sauran ita ma muryarta a sama tace" Zaki yallab'ai." Tsamm! Ya ji tsigar jikinsa ta tashi wani yam yam yam, sauran kam duk kallonta sukayi baki bud'e, dreba kan shi dake cikin mota zaune saida ya lek'o ta taga, jinjina kai yayi a ranshi yace" Na sani dama ita ce, me ma yasa na lek'o? Aljana kawai." Sake had'e rai yayi yace" Me yasa?" Ba alamar wasa ita ma tace" Haka kawai yallab'ai, burina ne tun ina k'arama." A hankali ya janye gilashin daga idanunshi ya kalleta ido da ido ko hakan zai bata damar canza ra'ayi, d'an sakin fuskarsa yayi sannan yace" Zakin gaske kike son gani ? Ko kuma na teddy?" A lokacin kallon fuskarshi tayi ta saki murmushi tace" Na gasken yallab'ai." Muskutawa yayi yana kallonta ta k'asan ido yace" Me yake birgeki a game da zaki?" Sakin hannayenta tayi tare da gyara tsayuwarta ta shiga kallonshi tana dariya tace" Ka gane yallab'ai, wannan tafiyar tashi ta k'asaita, wannan yalwataccen gashin daya masa k'awanya, idonsa masu d'aukar hankali, ni kawai ina so na ganshi a zahiri sannan na shafa bayansa, sannan ina so na ga faffad'ar k'afarsa wacce ke iya illata sauran dabbobin da duk ta daka sau d'aya." Wani basaraken murmushi ta saki ta tafa hannayenta tace" Kai gaskiya zaki yayi, ina son ganinshi a zahiri idan da yiwuwa ma mu zama abokai." Mayar da gilashinshi yayi a d'an hassale yace" Ina wasa da ke ne da zaki zauna yi min wannan bayanin?" Cike da fara'a tace" A'a yallab'ai, amma ai a wajen aji ne." Da mamaki yace" Kamar ya?" Kallonshi cike da yanayin yarinta tace" Yallab'ai ai jiya kai ka fad'a a aji ne muke d'alibi da malami, amma a wajen aji ka ce zamu zama kamar abokai." D'aga girarsa yayi ya juya zai shiga cikin jejin yana fad'in" To to d'alibai a motsa..." Ayam ce tace" Yallab'ai." Juyowa yayi ya kalleta, kamar wata sakara ta saki baki tace" Dama ka tambaye mu ne ba dan ka cika mana burin mu ba?" Fuskantarta yayi yana sake cire gilashin yace" Me kike nufi? Zakin kin d'auka abun wasa ne?" Turo baki tayi gaba tace" Na sani yallab'ai." "Dan haka ki manta da son ganinshi kawai." Ya fad'a yana juyawa zai bar wurin, a sanyaye tace "Ba zan iya ba, zan had'u da shi ko ta halin yaya." A gadarance ya juyo yace "Kin tabbatar?" Jinjina kai tayi tace "Na tabbata." Wani shak'iyin murmushi yayi yace "Shikenan zan nuna miki zaki, amma ki sani idan kika firgita ko kika suma a wurin nan, to tabbas ke zan mik'a mishi a matsayin abinda zai yi kumallo da shi, kin yarda?" Murmushi tayi ita ma tace "Na yarda yallab'ai, amma fa idan ban tsorata ba?" Zuba mata ido yayi yana kallo kamar ba zai ce komai ba kafin ya gyara tsayuwarshi yace "Zan miki kyautar da zata baki mamaki da zaran na tabbatar da gaskiya a kan ki." Shiru tayi ta k'ura masa ido kamar zata yi tunanin maganar sa, shi ma abinda ya fahimta kenan kamar zatayi tunani kawai yayi saurin fad'in "Jira ni." Waya ya ciro daga ajihunshi suna kallo yayi nesa da su yana amsa waya, bai fi minti uku zuwa hud'u ba ya dawo garesu ya tsaya, cikin karsashi ya shiga nuna musu yana fad'in "D'alibai, ku nutsu sosai sannan ku kula, bindigogin dake jikin d'amararku ba sa d'auke da alburusai na kisa sai na kashe jikin kowace irin dabba, shi ma zaku harba ne idan kun shiga had'ari, sannan ina so ku maida hankalinku kan bishiyoyin wajen, sannan ku yi taka tsantsan d kuma lura da inda zaku saka k'afarku, dan a jejin nan an fara samun b'ata garin dake shigowa wasu suna kashe dabbobi masu wuyar samu, wasu kuma suna karya itace suna shiga da su cikin gari, dan haka ku kula sosai ku tuna da shekararku ce ta k'arshe wannan." Sara masa sukayi da buga k'afafunsu suka amsa da" To yallab'ai." Da k'arfi sosai yace" Kun gane?" " E yallab'ai." Suka sake fad'i a tare, jinjina kai yayi yace" Ku yi gaba zan zo a bayanku, zan fara nunawa shed'aniyar nan abinda ta nema, kuma bana son saka rayuwar d'aya a cikinku had'ari." Da k'arfi ya sake fad'in" Kun gane." "E yallab'ai." Suka amsa da shi, sake jinjina kai yayi yace "To to ku motsa, kuyi aiki cikin had'in kai." Rarrabuwa suka fara yi suna gudu wasu su biyu wasu uku duk suka famtsama zuwa cikin jeji, juyowar da zaiyi ya ga ashe shi take kallo, kallo mai ma'anar "Ina jin kunyar ka fa malam." Yatsina fuska tayi tace "Na fad'a maka ka kiyaye kirana da kowane suna." Cire giashin yayi yana murtuke fuska yace "An fad'a, me zakiyi ? Wai ma ke ya akayi kika raina ni?" Kawar da kan ta tayi tana wuwulasu tace "Ni ba mace ba ce, kawai ina ga fa so na kake shiyasa kake tunanin haka." Wani irin yatsina fuska yayi ya ja baya yace "Ke? Me? So? Da ke kuma?" Girgiza kai yayi yana ci gaba da yatsina fuskar nan yace "Allah ya sawak'e min wahala." Da sauri ta kalleshi da mamaki a fuskarta tace "Allah ka ce? Waye shi?" Ba alamar damuwa da tambayar data masa ya gyara tsayuwarshi yana d'auke kan shi daga kan ta yace "Allah shi ne wanda ya hallice ni, ya hallice ki kuma y..." Da sauri ta katseshi da fad'in "Shi ya hallici sama d k'asa? Da duk wannan tsirren dake cikin jejin nan? Shi ne ya k'agi tekunan da suke ambaliya a doron k'asa?" Da mamakin tambayarta yace "E hakane." Gyad'a kai tayi ta tafa hannunta tace "Dama na ce, na sani akwai wani dake juya duniyar nan wanda buwaya da izzarshi ta fi gaban wasa, amma ba wani banzan abun bauta Ghira ba wanda ko jini babu a jikinshi bare ya anfani wani." Kallon Umad tayi irin kallon tsanake ta sauke numfashi tace "Wane addini ne wannan? Ya ake a shiga? Ina so ni ma na zama d'aya daga cikin mabiyansa, na fi son ubangijin da zan bautawa ya zama mai jin buk'atuna, zan so ubangijin da zan bautawa ya zama shi ne ya samar da ni ba wai wanda kakanninmu suka samar ba, zan so ubangiji na ya kasance a tare da ni a ko yaushe ba wai sai na sha wahalar d'aukarsa a cikin jakata ba, kuma ina so ubangiji ya zama mai amsa rok'ona a sanda na rok'eshi, kuma wanda ba ya gajiya da amsa buk'ata ta bare ya min gori wata rana, wannan ubangijin nake da buk'ata, shiyasa ban tab'a bautawa kowa ba." Gyara tsayuwa Umad yayi sai ma ya rasa bakin magana, kallonta kawai yake ita kuma tana ganin haka ta kyab'e baki tace" Haka dayawa ke ta fad'a, wai ina tsoratasu, wasu ma sun daina kulani saboda launin ido na da kuma wasu abubuwan, kai ma idan ka tsorata zan saka a layin ragwayen maza." A karon farko da murmushi ya sub'uce masa a gabanta, sosai yayi murmushi har hak'oransa na bayyana a fili, ganin haka sai ita ma ta saki murmushin tace" Karka damu malam, ba zan yarda kowa ya ji major Umad matsoraci bane." Iskan daya fara kad'awa mai k'arfi had'e da k'ura da kuma k'arar jirgi a sama yasa Umad d'aga kan shi, ita ma d'aga kan tayi sama suna kallon jirgin helicopter d'in, da kai ya mata alama yace" Muje." Zaro ido tayi tace" Kai ka kira jirgi? Ina zamu je?" Kallon shegantaka ya mata yace" Ba zaki kike son gani ba?" Jinjina kai tayi alamar e, saka gilashin shi yayi a ido hakan ha k'ara fito masa da kyawusa, hannun hagu ya mik'a mata yace" Muje to." A hankali ta d'aga siririn hannunta na dama ta d'ora akan tafin hannun Umad, da k'arfi ya jimk'e hannuta sakamakon shock d'in da ya ji irin na ranar, sai ya bar hakan a matsayin dan bai cika tab'a jikin mace ba tunda ai ita bata ji komai ba a ganinshi. Fuskarta ya kalla da kyau yana sake nanato kalaman malaminshi akan yarinyar daya fito nema, musamman inda yake fad'in _"Akwai b'oyayyar jarumta a tare da ita, abinda ya cancanci ya bata tsoro ba shi ke tsorata ta ba, wanda kuma kai zai iya kayar maka da gaba, sai ka ga ita abin ado ne a gareta..._" Tabbas ya fara jin wani abu a kan yarinyar nan, inba haka ba ta ya zata amince da shi haka a sauk'ak'e, lallai da ita xe wacce yake nema sai yace mata "Jarumtarki ta ban haushi, amma kuma raunin da kika nuna na yarda da ni ya birgeni." Jan ta yayi suka nufi inda jirgin ya tsaya, suna isa k'ofar dama a bud'e take, taimaka mata yayi ta fara shiga sannan ya shiga shi ma, d'amara suka d'aura a k'ugunsu, tashin jirgin aka fara su kuma suka fara k'ok'arin saka abun sauraron magana a kunnayensu saboda basj damar jin maganar juna ba tare da k'arar iskan ta kawo cikas ba. Zura kan ta tayi ta d'aya k'ofar tana hangen k'asa ta taga, murmushi ta shiga saki ita kad'ai musamman yanda ta ga bishiyu na kad'awa su kuma suna k'ara haurawa sama. Kafad'arta ya daddab'a tana juyowa yace "Kin tab'a shiga jirgi ne?" Girgiza kai tayi tace "Ban tab'a tsayawa gani ga shi ba sai yau." Girarshi d'aya ya d'aga sama da mamakin kuma shi ne babu tsoro a tare da ita? Tafiya suka yi mai nisa saidai duk a cikin dajin suke, saida suka kai inda aka saka allon sanarwa dan daga nan zuwa inda mutum zai k'ara a cikin had'ari zai yi shi, dan dabbobi ne iri iri masu cutarwa a wurin. Jami'in tuk'in jirgin ne yace wa Umad "Yallab'ai a shirya sauka mun iso." Kallonta Umad yayi yace "Kin shirya?" "E yallab'ai." Ta fad'a da karsashinta, jinjina kai yayi sannan ya ba matuk'in umarnin sauka, saida ya tabbatar sun tsaya sannan ta ga ya zura hannu a k'asan kujerar da yake zaune ya d'auko bindiga, wacce ke k'ugunshi ta aiki ya aje ya duba alburansan waccen ya d'auka, d'anata yayi ya saita mata komai tana kallonshi baki sake, yanda yake wasa da bindigar sai ta ji ya birgeta, kallonta yayi yana shirin fita yace "Mu je." Shi ne ya fara fita, za ta diro shi kuma daidai ya juya tare da rik'o k'ugunta da duka hannayenshi bayan ya soka bindigarshi a k'ugu, cak ta ji ya d'agata ya sauko da ita, kunya ce ta rufeta dan hakan bai tab'a faruwa da ita ba, kaa had'a ido tayi da shi haka shi ma sai ya ji kamar yayi gaggawa a lamarin. Bindigar ya ciro sannan ya kalleta da kulawa ya shiga mata kurmanci wanda dama dole suke koya saboda irin haka, dan wata dabbar sauti zata ji ta farmake ka wata kuwa sautin tafiyarka ma, jinjina kai Ayam tayi dan ta fahimci abinda ya fad'a mata wato ta biyoshi a baya a hankali sannan ta kula. Cikin sand'a suke tafiya Umad na gaba tana binshi a baya sai kalle kalle suke, k'wari da k'ananan dabbobi kam suna ta had'uwa dasu wanda ba sa cutarwa, suna cikin tafiyarsu a hankali cikin ciyayi koraye ya mata alama da hannu cewa ta tsaya. Tsayawa kam ta yi tana lek'awa ta ga me ya gani, a wuyanta ta ji motsi daf da hular kan ta, da sauri ta zura hannu da niyyar d'an sosawa, tudun abun da ta ji mai tabbatar mata da k'waro ne yasa bata ankara ba kuma bata shirya ba ta kwamtsa k'ara iya k'arfinta. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:33 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *9* Da fari kam zabura Umad yayi dan abun bai yi tsammaninshi ba, bugu da k'ari kuma k'arar a cikin kunnenshi na hagu ta sauka, amma yana ankara a cikin salo da k'warewa yayi azamar had'ata da bangon da suke tsaye kusanshi, hannu d'aya yasa ya rufe mata baki d'aya hannun dake rik'e da bindiga kuma ya zagaye k'ugunta da shi, duk da idonshi cikin gilashi suke amma yanda tayi shiru dole suka k'urawa juna ido, d'an motsa wuyanta tayi tana lumshe ido, a hankali ya d'auke hannunshi daga bakinta ya mayar kan wuyanta, yana jin ya tab'a abu yayi k'ok'arin cireshi a jikinta, gam ya ji alamar k'waron mai kakkausan k'afafu ne da tsini hakan yasa ya mak'ale mata a dogon wuyanta. Yatsu biyu yasa still idonshi cikin na ta duk da ita ba wani ganin na shi take sosai ba, tana dai hangen kamar ita yake kallo kuma kamar ba ita yake kallo ba, cire k'waron yayi tamkar fara ce ta lak'e mata a jiki. Wani numfashi ta sauke a take idonta suka kawo ruwa dan koma dai menene tabbas ya cijeta, lumshe ido tayi ta sauke kan ta k'asa, k'waron ya nuna mata cikin masifa yace "Dubi, k'waron da zai iya wucewa ta hudar hncinki, shi ne fa ya hau jikinki kika shaidawa duka jejin nan cewa mun shigo, amma a haka kike cika mana baki ke zaki kike son gani." Kallon k'waron tayi bak'i wulik da shi kamar suffar gizo kuma kamar hankaka, marairaiccewa tayi tace" Sorry." A tsawace yace"Shet up, kika sake min maganar zaki wallahi sai na fasa bakinki da hannun bindigar nan." Turo baki tayi gaba alamar rashin jin dad'i, kafin ta shirya yin wani abun Umad ya fizgi hannunta da k'arfi suka juya dan komawa inda suka fito yana fad'in" Dole muyi gaggawar barin nan, dan hankalin kowace dabba yanzu ya tashi da tunanin an shigo farautarsu, dan haka su ma zasuyi k'ok'arin farautar rayuwarmu, ni kuma ban shirya rasa raina tare da ke ba." Bin shi take kamar zata fad'i k'asa dan sosai yake jan ta, ba tace komai ba face biyarsa da take kawai, sunyi kusa da inda allon sanarwar nan yake na a kula akwai had'ari a nan daga cikin ciyayin suka ji motsi, cak ya tsaya tare da sakin hannunta, d'ora hannunshi yayi a kan k'irjinta da niyyar mayar da ita baya, dan ya fi ta tsayi sosai a iya d'agawar da ya ma hannunshi dole kan k'irjin zai sauka. Da k'arfin tsiya ta buge hannunshi tare da saka hannayenta ta rufe nonuwanta tana fad'in "Me ye haka?" Kan shi kawai ya juyo ya kalleta ya kuma kalli k'irjin, dan shi sam bai ma san me ya tab'a ba bare ka tabbatar da niyyarshi, juya kanshi yayi ya sakar mata tsaki yana girgiza kai yace "Allah tsare ni, b'erayen?" Cike da masifa ta shiga gatsina baki tana fad'in "B'erayen, amma a hka suka birgekahar kake k'ok'arin yi min..." Kallon daya mata yasa tayi shiru tana sinne kai, matsowa yayi daf da ita yace "Nake k'ok'arin yi miki me?" Yanda ta sake soke kai k'asa yasa shi sakin murmushi a ran shi yana jin kanshi na huruwa sama na farin cikin ya tsorata ta ta k'i fad'an abinda tayi niyya, juyawa yayi yana sake maida hankalinshi kan sautin nan da yake ji, a bazata ya ji muryarta tace" Zaka min rashin d'a'a mana." Lumshe ido yayi tare da juyowa, da yatsu biyu ya mata kurmanci ya nuna mata" Ki maida hankali, akwai abinda ke tahowa ta nan." Jinjina kai tayi fuskarta fal tsoron abinda ya fad'a d'in, yanda yake sand'a ita ma haka take yi tare da ciro bindigarta ta kashe jiki ta rik'e da kyau, sautin k'ara kusanto su yake, kamar numfashi had'e da gurnani, abinda ya sani kawai shi ne idan ma dabba ce to babba ce daga yanda k'ananan tsirrai ke motsawa, duk da ba'a jin sautin tafiya, amma sai dukansu jikinsu ya basu lallai fa kamar ana sauke takon k'akk'arfar k'afa a zuk'atansu. Kamar almara ko a mafarki sai ga k'osasshen zaki ya b'ullo daga sark'ak'iyar itacen da duwarwatsu, tuni Umad ya zaro ido dan wallahi a take ji yayi wannan zakin shi ne wanda aljanar nan ta fasalta, dan ba k'arami bane wajen girma haka ma a shekaru, dan fuskarsa ta nuna haka, lalubo hannun Ayam yayi da ta lek'a ta kafad'arshi, tana ganin zaki ta saki fara'a cikin jin dad'i tace "Oh my God, lion." Da azama ya juya ya fuskanceta ya d'ora yatsarshi a labb'anshi yace "Shiiiiiii." Juyawa yayi ya kalli zakik dake tafe a tak'ama da gadara, ga dukkan alamu ihunta ne ya fargar da shi cewa an shigo komarshi, ko kuma dai shawagi ne ya ke amma ba farauta ba. Had'e yawu yayi ya laluba a hankali ya cire gilashinshi ya soka a gaban rigarshi mai mab'allai, sake damk'o hannunta yayi da niyyar su ratsa ta b'angaren hagunsu su zagaye zakin su fita dan su tsira da ransu, sai dai suna fara takawa kamar sunanshi ne suka kira sai kuwa ya juyo ta bangaren da suke. K'amewa Umad yayi ya rintse ido yana furta "Hasbunallah wani'imal wakil." Haba wa? Ai sai zakin nan yayi wata kukan kura, gudu cikin k'arfi da salo ya yo kan su, Umad na ganin haka ya ja hannun Ayam da gudu, tsaf ta kubce hannunta daga na shi ta tsaya tare da juyowa ta fuskanci zakin. Umad dya tsaya ya ga me ya tsayar da ita yana ganin zakin nan ya nufo kan ta cikin gurnani bakinshi a bud'e, bai san me ya aikata haka ba, a kan wani dalili ya ji zai iya fansar rayuwarta, shi dai ji yayi kawai ba zai iya bari komai ya sameta ba, dan haka yayi gaggawar tureta gefe ya tsaya inda take, bindigarshi ya saitawa zakin ya rik'e da kyau yana jiran ya ga me zai faru. Zakin nan na zuwa bai b'ata lokaci ba wajen nuna izzarshi, wani irin tsalle ya daka sama sai kuwa a jikin Umad bayan ya saki duka faratunshi, tare suka fad'i inda bindigar ma tayi ta kan ta, wata irin mirginawa zakin yayi y ske mik'ewa tsaye, Umad ma duk da bala'in dukan nan da yaji bai hanashi jarumtar tashi ba. Sake shirin kai farmaki yayi a karo na biyu, saidai ina gaba da gabanta, tuni Ayam ta shiga tsakanin Umad da zakin nan kan gwiwarta tana d'aga masa hannaye alamar sun yi saranda sun mik'a wuya, ai Umad yanda kasan idonshi zasu fad'o k'asa haka yayi dan al'ajabi, kallon zakin yake irin yanda ya tsaya cak suna kallon juna ita da shi. Juyawa yayi ya hangi bindigarshi, gyara zamanshi yayi zai rarrafa ya d'auka Ayam tayi saurin juyawa ta kalleshi, da hannu ta masa alama a hankali tace "Shiiiiiii!" Da mamaki bakinsa a sake yace "Kuuuutt! Ni d'in?" K'uro idonta tayi sosai ta d'ora yatsa a labb'anta cikin rad'a tace "Kayi shiru mana, na maka alk'awari ba zan fad'awa kowa kana tsoronshi ba." Juyawa tayi ta kalli zakin, a hankali ya dinga takowa har saida ya tsaya gabanta, lumshe ido tayi dan ita kan ga zuciyarta rawa take tana jin me ye a jikinta da yasa zakin ya daina hargagin son halakasu? Me ma yasa tayi tunanin shiga tsakaninshi da Umad ne? Gashin da ta ji na tab'a jikinta yasa ta bud'a ido, cike da d'ard'ar da tsoro ta kai hannunta na hagu ta shafa gashin nan, sai kuwa zakin nan ya sake kwantar da kan shi a jikinshi, dariya ce ta sub'uce mata ta juya ta kalli Umad tana fad'in "Yallab'ai ka gani, na tab'a shi yau, burina ya cika." Sake juyawa tayi ga zakin ta ci gaba da shafa shi har zuwa bayanshi, kallon idon juna suke ita da zakin. Umad kam mik'ewa yayi tsaye ya d'auki bindigarshi, zai saka a k'ugunshi ya ji Ayam tace "Sunana Ayam, kai fa?" K'ura mata ido yayi har ta kalleshi ta nunawa zakin tace "Malami na ne, sunan Umad." Da sauri Umad ya k'arasa ya gareta ya finciko hannunta yana fadin "Tashi muje na maida ke inda na d'auko ki, rayuwa cikin mutane bata kamace k..." Wata zaburowa zakin yayi ganin yanda ya finciki Ayam, tuni suka ankara Ayam ta dakatar da shi da hannu Umad kuma ya k'urawa zakin ido, sake durk'usawa tayi kan gwiwanta ta marairaice tace" Zan tafi ka ji, abokina ne shi kar ka cutar da shi, zan dawo wani lokacin." Mik'ewa tayi bayan ta sake shafa gashin nan na shi ta bi bayan Umad, sauri take kamar yanda shi ma yake yi hankalinsa a matuk'ar bala'in tashe, idan kai na bindiga ya fashe to tabbas na shi zaiyi kowane lokaci, gashi wata zuciyar na ta fad'a masa ita ce, amma sai ya kawar da zancen saboda tunanin ta ya zai sameta a b'agas haka? Sannan yanda aka suffanta kyawunta wannan ko kama k'afarta ba tayi ba, da ma dai kyawunta ya kai na Zafreen zai iya yarda. To amma kuma wasu halaye da d'abi'unta abun tsoro yake son fara bashi, sai kuma yanzu ya fara gasgata canal Jacob da yaga ko fuskarta baya kalla. Sautin dariyarta da yaji ne yasa shi juyowa a hankali, wani k'arami kuma mai kalar shud'i da yellow d'in tsuntsu ne ya gani a tafin hannunta tana wasa da shi kamar tana masa cakulkuli, da azama ya dawo gareta ya d'auki tsuntsun ya d'aga hannunshi sama ya tashi, a karan farko daya tab'a ta da niyya kenan, hannayeshi biyu ya sa ya tallabi fuskarta suka kalli juna. Muryarsa na rawa kamar wanda ya kid'ime yace "Ke! Kalle ni da kyau, ki wa Allahn daya hallice ki karki haukata ni, ki fad'a min gaskiya Ayam, who the hel are you?" Yanda ya matse kumatunta yasa bakinta kumburowa, cikin shagwab'a ta kalli idonshi ita ma tace "Ni ce, Ayam... Utais." Cikin jin haushi ya saketa ya juya yace "Merde." Murmushi tayi ta bi bayanshi saboda ya ci gaba da tafiyarshi, k'asa ta shiga kallo tana tafe tana rausayarta, tsautsayi yasa idonta sauka akan wata k'atuwar wahainiya kore shar da ita, bud'e hannayenta tayi ta sunkuya kamar zata rumgumeta tace "Wow! Wahainiya." Da sauri ya juyo ai kuwa da gudu ya arta ya damk'ota dan tayi niyyar bin bayan wahainiyar, yana nasarar cabkar k'ugunta ya cirata sama ya labta a wuyanshi, cikin takon k'arfi da sassarfa ya shiga takawa har saida ya isa gaban helicopter dake tsaye yana jiransu, yana k'arasawa matuk'in ya fito yana tambayarsa lafiya? Dan ya d'auka ko ta samu rauni ne, da hannu ya masa alamar ya tashi jirgin kawai, yana zuwa jefata yayi ciki shi ma ya shiga ya zauna. Jingina yayi a kujerar ya lumshe ido, a sanyaye ya shiga sauke numfashi wani bayan wani, saida suka daidaita a sama sun fara nisa ya bud'e idonshi, d'an juyawa yayi ya kalleta jin shiru, gabanshi ne ya fad'i sakamakon had'a idon da sukayi, ta masa k'uri da ido ta fito da 'yan hak'oranta kawai tana kallonshi. D'auke kan shi yayi a kan ta ya d'ora hannunshi kan cikinshi, a hankali ya fara b'alle mab'allen rigarshi saida ya ciresu tas, singlet d' in shi kuma jini ne ya fara b'ata ta sakamakon faratun zakin nan da suka tab'a shi. Tana ganin haka ta sake zaro ido tace "Wayyo Allah, jini kake zubarwa." A tsawace yace "Shiru dallah." Gum ta ja bakinta ba ta sake cewa uffan ba, amma kuma idonta akan shi suke, duk wani motsinshi biye take da shi, yana k'ok'arin cire rigarshi ta kakin shi suka sake had'a ido, cike da takaici yace "Wai malama mi ye na k'ura min ido? Ki kalli gabanki mana." Ba tare data d'auke idonta a kan shi ba tace "Tambayoyi gareni, ina tunanin ko ba zaka iya amsa min su bane." A hassale yace "To kuma da kika san haka me yasa zaki zuba min wannan idanun na ki masu kama da *dutsen lu'u lu'u*." Wata kyakyawar dariya tayi tare da cire hular kan ta gajeran gashinta daya fara tsirowa ya bayyana tace "Da gaske?" Girgiza mata kai yayi ya k'arasa cire rigarshi, zaro ido tayi tana kallon k'wanjinshi, da gayya ya sake juyawa ya kalleta, cike da gatsali yace "Daina kallo na, ko na birgeki ne?" Da sauri ta kau da kan ta tace "God forbid, me zan ci da kai ni kuma?" Kallonta yayi galala yace "Amma wace gulma ta kai ki d'akina daren jiya?" K'yak'yabta ido tayi tace "Kawai na je tantancewa ne." K'ala bai ce mata ba sai ma mayar da rigarsa da yayi, haka har saida suka sauka inda suka rabu da sauran d'aliban, tuni sun samesu a wurin duk suna jiransu, tuni su Deeyam suka kewayeta suna tambayar ta ko ta ga zaki ? Da farin ciki ta shiga labarta musu har suka shiga mota dan komawa su ma suna fad'a masa abinda ya faru ta b'angarensu. *Tankara* A sauk'ak'e Haman yayi nasarar samun gidan Ruman, bayan sun gaisa kuma ya fad'a mata shi jami'i ne, cikin rashin fahimta da tsoro tace "To amma yallab'ai me kake nema daga gareni? Me na yi?" A ladabce yace "Baba ina neman wata mata da miji ne, kuma an tabbatar min da kina da alak'a da su." Da mamaki tace "Su wa kenan? Kuma wa ya fad'a maka haka?" Murmushi yayi yace "Habbee da Utais." A take jikinta ya d'auki kyarma tsabar tsoro da fargaba, neman sunkuyewa tayi daga tsayen da take, cikin in'ina da tashin hankali tace "Kai kuwa wa ya fad'a maka na san su? Su waye ma su d'in?" Dariya yayi wacce ta fitoda kyanshi ya mik'e tsaye, cike da isa yace "Baba gashi kin fara d'orani a mizani, tambayarki ta farko ita ta nuna lallai kin san su, tambayarki ta biyu kuma ta nuna ba gaskiya kika fad'a ba." Gyara tsayuwa yayi yace "Shin Baba zaki iya fad'a min inda zan same su? Ko kuma sai na..." Bindigar k'ugunshi ya fito da ita yana shafawa, hakan ya k'ara rud'ar da ita sai ta rikice ta fashe da kuka, durk'ushewa tayi k'asa tana rok'onshi "Ka yi hak'uri zan fad'a maka, amma ka min alk'awarin ba zaka cutar da 'yata ba." Da tsananin mamaki yace "Wacece' yar ta ki? Habbee?" Jinjina kai tayi alamar e, jinjina kai yayi yana murmushin mugunta a fan shi yace "Lallai gimbiya Juman, wato kafin ta b'atar da 'yarta saida ta bi ta goge duk wani sawu da za'a bi dan kamata." Kallonta yayi yace "Ina jinki fad'a min? Babu abinda zai same ta." Mik'ewa tayi tana share hawaye tace "Larhjadin, bayan kasuwar *Buffar*, gida mai lamba 115." Dad'in daya kama shi ne yasa shi rumgume tsohuwar ya sumbaci kuncinta, ko ba komai zai samu hutu da nutsuwa idan ya kammala aikin nan, sakinta yayi ya juya cikin sauri ya fita yana fad'in "Nagode Baba." Wayarshi ya ciro a aljihu ya kira lambar Umad, sai dai bai sameshi ba dan lokacin suna jeji, duk da haka bai hak'ura saida yayi ta jarabawa, a k'arshe dai wani masauki ya samu mai kyau ya kama d'aki dan ya jira wayewar garin gobe tunda har magriba ta wuce. *Larhjadin* Keb'entacciyar asibitin makarantar Umad ya kai kan shi sakamakon yakushin da zakin nan ya masa, cikin k'warewa da nagartattun kayan aiki aka dubashi tare da yi masa allurar kashe duk wani dafi, kuma dama sam baya jin ciwon yakushin kamar yanda yake jin bala'in ciwo a jikinshi inda zakin nan ya daka masa k'afafunshi, lallai ya yarda k'afafun zaki zasu iya kashe mutum ma. *09:30* Ayam ta shigo d'akin da aka kwantar da shi, dan bata san me ke faruwa ba saida Sabrine suka fad'a mata, su ma dan sun tafi karb'an magani ne na zazzab'i, kayan bacci ne a jikinta amma ta d'ora rigar sanyi a kai wacce zaka d'auka ta mata yawa ne, amma haka tsari da zubin rigar yake. Saida ta je ta tsaya gaban gadon kdonshi rufe alamar bacci yake, rumgume hannayenta tayi tana kallonshi, ta jima tsaye tana k'are masa kallo tana doka murmushi, daga bisani kuma hannunta ta d'ora akan hannunshi dake kan k'irjinshi. Kamar wacce ta daddab'ashi a take yaji wani yanayi a cikin baccinshi, tsam ya bud'e idonshi ya sauke akan fuskarta, da sauri ta d'auke hannunta tace "Am.. Sannu, ya jikinka?" Muskutawa yayi ya tashi zaune da kyau yana kallon fuskarta, ba tare da yanayin wasa ba yace da ita "Me ya kawoki nan?" Kamar marar gaskiya tace "Na zo duba jikinka." Kallon tuhuma ya mata yace "Kin zo duba jikina ne amma kuma kike shafani haka?" Baki bud'e tace "Lahhh! Ni fa kawai dubaka na zo na yi." "Saboda kinsan dalilinki nake kwance a nan kenan?" Ya fad'a yana tsareta da ido. Kawar da kan ta tayi ta turo baki a ran ta tace "Masifaffe." Wani irin kallo ya mata kamar ya karanta me ta fad'a a fuskarta yace "Me kika fad'a?" Da sauri ta kalleshi tace "Yallab'ai na ce ba, ni kam me yasa ka cika masifa dayawa ne? Ko sau d'aya ka jaraba yin wuni d'aya tak ba tare da b'acin rai ko had'e fuska ba mana, murmushi zai maka kyau sosai." A hankali ya juyar da kan shi kan d'an teburin masu jinya inda ya d'ora bindigarsa, d'ora hannunsa yayi a kan bindigar ya kalleta cike da gadara yace" Zaki bar nan ko sai na fasa miki baki?" Zaro ido tayi sai kuma tayi dariya tace" Yallab'ai haushi na kake ji ne saboda na nuna maka zaki?" Gyara zama yayi yace" Ke! Ke ce ma kika nuna min shi kenan?" D'auke kan ta tayi daga gareshi tace" Kusan haka mana, ai na ga kai kuna had'uwa da shi gasar tsere kuka fara." Me Umad zaiyi ba k'yalk'yalewa da dariya ba, sai ga shi da rik'e ciki yana dariya har da hawaye a gefen idonshi, kallonshi take har ta kai ta tab'e baki ta juya zata fita dan bata son dariya mai yawa, cikin k'yak'yala dariya yace" Ina kuma zaki je?" Cikin sangarta tace" Ba korata kayi ba." Jingina kan shi yayi a gadon yana tsagaita dariyar yace" Ban tab'a dariya irin haka ba tunda na ke Ayam, haka ma babu wanda ya tab'a kwantar da ni a gadon asibiti sai zakinki." Murmushi tayi tace" Ba wani nan, jarumatarka ce ta kawo ka gadon asibiti." Da sauri kuma sai tace" Wai ma me ye dalilin da yasa ka tari zakin nan ne? Kana tsoron kar ya illata ni ne?" K'wayar idonta ya kalla yace" Ji nayi ba zan bari wani abu ya sameki ba, hakan zai sa na d'auki kaina a matsayin mai laifi na har abada." Dariya tayi tace" Shiny shiy." Kallon daya mata na alamar tambaya yasa ta cewa" Nagode to." Juyawa tayi zata tafi tace" Saida safe." "Karb'i." Ya fad'a yana mik'o mata wayarshi, karb'a tayi ta kalla da alamar tambaya, cikin sakin fuska yace "Ta mutu ne, ki saka min caji a d'akinku, likitan ya ce dole a nan zan kwana, kuma abin cajina yana d'aki." A ladabce ta amsa ta juya zata fita, muryarshi ta sake ji yace "Nawa ne kwanan watan haihuwarki?" Juyowa tayi tana murmushi tace "Yanzu haka 12:00 nake jira tayi na cika shekarata ashirin." Murmushi ya mata yace "Wace shekara?" Kai tsaye tace "Dubu biyu da biyu." K'ura mata ido yayi sai ya rasa bakin magana har ta fita, saida ta fice ya fad'a a fan shi "Anya kuwa ba ita bace?" *To fa yar uwa, ga wasar na d'aukar zafi gashi mun kusa zuwa k'arshen free page, dan haka ki hanzarta ki biya na ki dan samun damar kwamushe na ki karatun a nutse.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:33 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *10* Ko da ta saka wayar sai bata ga tayi alamar ta d'auka ba, ta jima zaune tana son ta ga wayar ta nuna mata tana d'aukar cajin, Deeyam da suke zaune kan gado suna jiran 12:00 ta yi ne tace mata "Dan Allah ki rabu da wayar nan ki zo, mu ji me kike shiryawa?" Cike da damuwa tace "Wayar nan ce ta k'i d'auka fa." Sabrine ce tace "Ki kunnata mana ta yiwu ta d'auka." Jinjina kai tayi ta danna wayar dan kunnawa, Deeyam ce tace "E lallai, irin wannan damuwa haka, da alama fa akwai k'amshin wani abu tsakaninki da malam Umad." Ganin wayar ta kama kuma lallai ta fara d'aukar cajin yasa ta mik'ewa ta nufosu tana tab'e baki tace "Kinji wani banzan tunani kuma, malamin na wa?" Tsaki tayi ta zauna tana fad'in "Ba zan iya had'a hanya da mai saka uniform ba, dama dai shi d'in joker ne ko kuma mai aikin gidan zoo, zai fi armashi." Bushewa sukayi da dariya sai Deeyam da tace "Ke kuma ki rasa wanda kike son yin rayuwa da shi sai wanda bai kai komai ba." Sabrine ce tace "Ba ma wannan ba, me yasa take son auren irin mutumin nan?" Zuba mata ido sukayi, numfashi ta sauke sannan ta kalkesu dukansu tana murmushi tace "Saboda ina so na rayuwa kusa da dabbobi, ina son ganinsu a kewaye da ni." Gyara zama tayi tace "Ba wannan ba, yanzu me kuka shirya min ne na ga kuna ta b'oyo d'azu har da korata a d'akin nan." Da sauri dukansu suka ce "Ba komai." Da kallon tuhuma ta bisu tace "Kun tabbata?" "E." Suka fad'a a tare, tab'e baki tayi ta mik'e ta nufi gadonta ta kwanta tana fad'in "Da 12:00 tayi ku tasheni." "Ba ma sai kin fad'a ba." Cewar Deeyam, dan suna son bata mamaki kamar yanda ita ma take basu idan irin wannan ranar ta zo musu, Ayam k'awa ce da kowa zai yi fatan samu, zata tsaya maka idan buk'atar hakan ta tashi, idan kana da kad'aicin yan uwa ita ta kan maye maka wannan gurbin, idan kuma maraici kake fama da shi zata mantar da kai shi, duk abinda take da tana baka ba tare d tunanin yawanshi ko darajarshi ba, haka kuma zata iya tare maka duk bala'in dake neman tunkaroka iya k'arfinta, kamar dai yanda tayi a kan Sabrine tsakaninta da Zafreen. *12:57* ta d'an fara juya kan ta tana motsawa kamar zata farka, sam mafarkin da take yi bata jin dad'inshi, yatsina fuska take yi duk da a cikin bacci take, a can k'asan mak'oshi cikin bacci take fad'in "Ku daina, ku daina azabtar da ita, ku daina." 12:00 a daidai kunnenta suka taru su uku suka d'aga murya wajen fad'in "Barka da zagayowar ranar haihuwa." A mugun zabure ta tashi zaune da k'arfi tana zazzaro ido a tsorace, Deeyam ce tace "Ke mu ne fa." Kallonta tayi kamar bak'uwar hallita a hankali ta fara saisaita nutsuwarta, shafa kan ta tayi ta sauke ajiyar zuciya tace "Oh, thanks." Wani k'aton cake suka aje mata gabanta suka fara tafawa suna mata wak'ar murnar k'ara shekara, bushe wutar tayi sannan ta yanka cake d'in, a bkin Deeyam ta fara sakawa sannan ta saka a bakin Sabrine da d'ai k'awar ta su, dukansu ma yankawa sukayi suka saka mata a baki sannan suka dangwala suka shafa mata a fuska, daga haka suka haukace inda suka dinga d'ibar cake din suna shafawa junansu suna ta dariya suna tsalle akan gadon cikin nishad'i, dan iya daren garesu kawai da zasu iya yin wannan farin cikin, idan ba haka ba babu lokaci zuwa wayewar garin. Wata babbar kwalba Deeyam ta d'auko ta lemu mai tsadar gaske sai ka ce barasa, saida ta girgizashi sannan ta bud'e duk ya pallatsar musu a jiki, kowa kofin tangaran ya mik'a ta zuba mi shi, suna tsaka da sha suka ji vibration na waya, a tare suka juya hakan yasa Sabrine cewa "Tun d'azu fa ake kiran wayar nan." Deeyam yace tace "Watak'ila kiran ujila ne, ko wani abu mai mahimmanci." Lek'a wayar Ayam tayi ta ga lambar an rubuta sunan *Ffrind* (aboki) da yaren Gallois, d'auke kanta tayi tace "Ku manta kawai, abokinsa ne." Mantawar sukayi kamar yanda ta ce, saidai tuni aka sake kiran hakan ya katse musu shagalinsu, Deeyam ce tace "Ayam me zai hana ki kashe wayar nan, idan ba haka fa ba zamu huta ba." D'an k'aramin tsaki tayi tace "Haba, malam ka kira sau d'aya ka ji ba'a d'aga ba kayi na biyu har da na uku, me zai hana ka shafawa mutane lafiya?" Sabrine ce tayi saurin fad'in "A'a fa Deeyam, ni ina ga da d'agawa mukayi ko kuma dai ta je ta kai masa wayar, ki tuna fa akwai ujila a rayuwa, muka sani matarshi ce ko kuma mahaifiya ko mahaifi." Cike da gatse Ayam tace "Ke ki je mana tunda ke ce matarsa d'in." Murmushi tayi tace "Babu inda zan je in fad'a miki, ke zaki je tunda ke ya bawa wayarsa." Deeyam ma cewa tayi "Gaskiya ne, ki je ki kai masa to." Tsaki tayi ta kalli jikinta sai kuma ta kallesu, sauka tayi daga kan gadon ta d'auki wayar ta nufi hanyar fita, Deeyam ce tace "Akwai sanyi fa a waje, ki saka rigar sanyi mana." "An k'i."Ta fad'a kai tsaye tana ficewa a d'akin, da kallo suka bi d'an k'ugunta da baya juyawa saidai dake tana da k'ira ba zaka gane komai ba. Likitar dake daf da k'ofar shigowa ma'ana sai ka bi ta kan ta zaka wuce tana ganin Ayam ta murje idonta daga baccin dake son d'aukarta daga zaune, ba alamar girmamawa tace "Ke ina zaki je yanzu a daren nan?" Kallonta Ayam tayi tace "Zan je gurin yallab'ai ne." "Me zaki je yi?" Ta fad'a a gatsalce, gyara tsayuwa tayi tace "Dama kina zaune a nan ne dan tambayar abinda zai shigar da kowa nan?" Mik'ewa tayi tsaye cikin hassala tace "Ke bana son shashanci banza, ya zama dole na san me zai shigar da ke ciki, idan ba haka ba kuma ki koma." Matsowa tayi ta tsaya gabanta cikin gadara ta rumgume hannayenta, zuba mata ido tayi kamar zata had'iyeta tace "Kika ce saidai na koma?" Haka kawai tsigar jikinta ta tashi ta ji ta kasa jurar kallonta, samun kan ta tayi da rusuna kan ta tace "Kinyi sa'a yau bana jin bala'i, da..." Kasa k'arasawa tayi sai kawai ta kalli k'irjin Ayam tace "Shiga kawai." Sama da k'asa Ayam ta galla mata harara ta wuce, tana shiga zaune ta sameshi yana kurb'an coffee a farin kofin tangaran. Bud'a k'ofar da tayi ce ta ja hankalinshi zuwa kan ta, yanda ya so yi mata kallo d'aya sai abun ya ci tura ya kuma gagara, bai d'auke idonshi daga kan samb'ala samb'alan cinyoyinta ba wanda suke a cikin fari kuma gajeran wando iya cinyoyinta, haka ma rigarta fara ce mai siraran hannaye, kan ta kuma yanzu babu komai a kai face launin gashinta mai kalar maroon da d'an ratsin yellow yellow. Gabanshi ta tsaya cike da shak'iyanci sakamakon lura da kallon da yake mata tace "Wato na maka kyau ko? Saboda ka ganni a hakane? Ai dama ni d'in kyakyawa ce." Cikin jin kunya da takaicin kan shi ya duk'ar da kai yana fad'in "Me ya kawoki kuma? Ko dai kin gagara bacci ne a dalili na?" Yatsina fuska tayi tace "Tabb'! Akan me ni kuwa zaka dameni?" Ziiii! D'in da wayarsa dake hannunta tayi yasa ta mik'o masa tace "Uhum ka gani, wannan abokin na ka ne ya addabi mutane, a gakiya mutumin nan da ina da wani iko a hannu na dana sa an d'aure min shi, haba mutum sai takurar tsiya." Duk tana maganar shi kuma yana kallon bakinta ne, saida ta dasa aya ya karb'i wayar ya duba sunan, kallonta yayi yace" Nagode to zaki iya tafiya, amma ki sani zan tuna miki wata rana." Da mamaki tace" Me zaka tuna min?" Girgiza kai yayi alamar ba komai, sannan ya lumshe mata ido ya bud'e alamar tafi, baki ta bud'e da matsanancin mamaki tace" Kai! Ni zaka kora da ido? Na rantse babu inda zan je sai ka min magana da baki, kaji ka kamar wani sarkin gaba d'aya k'asar Texanda." Wani malalacin murmushi yayi yace" Kenan dole sai nayi magana da baki?" D'aga kafad'a tayi tace" Haka kawai na ji bai min ba da ka min magana da ido." Girgiza kai yayi saboda fara hawa masa kai da tayi ya nuna mata k'ofa yace" To ta fi." Zura dogayen k'afafunta ta fara yi ta masa bye bye tace" Saida safe." Saida ta kai daf da k'ofa zata fita yana k'are mata kallo yace" Barka da zagayowar ranar haihuwarki." Juyowa tayi da fara'arta tace" Merci beaucoup." Juyawa tayi ta fita a d'akin saidai kafin ta rufe kofar ta sake kallon shi, murmushi ta sakar masa tace" Halinka ya had'u yallab'ai, kai mutumin kirki ne." Rufe k'ofar tayi ta fice shi kuma bai san sanda ya saki k'ayataccen murmushi ba har saida ya ji an sake kiran wayar, yana d'agawa cikin jin haushi Haman yace" Haba Umad, me ye haka dan Allah? Ya zanyi ta kiranka akan abu muhimmin amma baka d'aga min waya? Tun yamma fa nake kira." Cikin rashin jin dad'in rashin kyautawa yace" Kayi hak'uri Haman, wallahi na samu wani d'an had'ari ne sakamakon shigarmu jeji, amma da sauk'i yanzu." Cikin kulawa har ya manta da b'acin ranshi yace" Subhanallah, me ya sameka Umad? Kana ina yanzu?" Girgiza kai yayi ya aje kofin hannunshi yace" Ba komai karka damu, na ji sauk'i yanzu ai, fad'a min ya ake ciki daga wajenka?" Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace" Umad munyi nasara da yardar Allah, adreshin unguwa da lambar gidan da gimbiya Zafeera take duk yana k'wak'walwata." Da k'arfi ya sauka daga kan gadon yace" Da gaske Haman? Ka samu? Ina take?" Cikin farin ciki yace" E na samu, kuma abun farin cikin tana cikin garin da kai ma yanzu kake kamar dai yanda kayi hasashe tun farko." Cike da k'aguwa da zumudi da farin ciki yace" Da gaske Haman? A ina take? Ban adreshin?" Murmushi yayi yace" Na yi tunanin haka dama, na so zuwa garin yau amma na ga zanyi dare." A k'age yace" Haman ba wannan na tambayeka ba, ina ne adreshin da zan sameta? Zan yi sammako na je na had'u da su." Dariya Haman yayi yace "Bayan kassuwar Buffar, gida mai lamba 115, amma Umad..." Bai barshi ya k'arasa ba yace "Nagode Haman, zan kiraka zuwa safe." K'it! Ya yanke kiran ya shiga tattara komai na shi dake wurin ya fita a d'akin, likitar na masa magana amma ko kulata bai yi ba saida ya bar asibitin kwana kwanan. *01/01/2021* Tun gari bai gama wayewa ba d'aliban suka duk'ufa wajen gudu a filin makarantar, sun yi har sun fara gajiya amma yallab'ai Umad babu shi babu dalilinshi, cikin hakane Zafreen da tawagarta suka biyo ta filin zasu wuce. Da gangan Zafreen ta bi ta inda Ayam ke gudu, Ayam kam na ganinta a cikin gudunta ta nemi kauce mata, amma dake neman fitina take da d'aukar fansa sai kawai ta tareta gadan gadan ta bankad'eta. Fad'uwa ta nemi yi hakan yasa tayi baya tana tangal tangal, amma ikon Allah sai Ayam ta jawo hannun Zafreen hakan yasa suka fad'i tare k'asa. A tare suka saki k'ara inda Zafreen ke kan Ayam d'aro-d'aro, da sauri su Laika suka kamo Zafreen ta mik'e tsaye, Ayam ma mik'ewa tayi tana kallon Zafreen d'in, hannunta na dama ta d'ora kan sark'arta tana k'ok'arin mayar da ita cikin rigarta dake riga biyu ce jikinta, d'aya ta sanyi mai zip a gaba sai k'aramar daga ciki. A mugun razane kuma a kid'ime cikin tashin hankalin da Zafreen bata tab'a tsammanin fuskanta na ta ga wannan sark'a a wuyan Ayam wacce sark'a ce da ba ko ina ake samunta ba sai a wajen maccen data kasance mata a gurin sarkin Khazira, tabbas ana na bogi amma ta gasken kana ganinta zaka fahimceta, dan dutsen da aka k'era sark'ar da shi daga k'asan ruwa ake samunshi, had'akar lu'u lu'u da murjani ke samar da da dutsen sark'ar, hakan yasa Zafreen jin mugun jiri na neman kayar da ita ya tima a k'asa. Kamar wacce aka tsoratar ko aka firgita ta juya tana fad'in "Ina! Hakan ba zai faru ba, ina!!!!" Da gudu ta juya ta nufi hanyar da ake zuwa dan amsa kiran waya, su Laika ma da gudu suka bita suna kiranta, Ayam kam tab'e baki tayi ta gyara sark'arta ta juya a tsanake dan komawa b'angarensu dan ta gaji kam, tunda bai zo ba kuma shi ya sani. Zafreen na zuwa a gigice ta shiga danna kiran lambar mahaifinta, tan fara kururuwa kam aka d'aga, a matuk'ar rud'e ta shiga fad'in "Pah, pah na ganta, na rantse da abun bauta Ghira na ganta, na ganta sanye da sark'ar Mah, na ganta da ido na." Cikin fitar hayyacin daya ninka na Zafreen sarki Musail ya amsa da "A ina? Ina kika ganta?" Saida ta shiga yarfa hannaye tace "A makaranta ne, yanzu haka tana wajen motsa jiki, gudu take, Pah ita ce na rantse." Kamar zai fasa mata dodon kunne yace "Gamu nan zuwa, yanzu zamu zo Larhjadin d'in, waziri da Adah tun jiya suna nan dama, sun samu wasu bayanai akan ta." Da sauri tace "Pah indai suna nan su ma ai sun isa, ba sai ka zo ba Pah zamu kawo maka ita." Jim ya d'anyi sannan yace "Shikenan 'yata, na yarda dake." Aje wayar ta yi ta juya ta kalli su Laika tace "Ina so na had'u da ita yanzu." Jinjina kai sukayi suka nufi inda suka barta, amma da basu sameta nan ba sai kawai Laika ta ce su tafi dan su ma lokacin na su darasin yayi, idan sun fito sun had'u da ita. *A k'ofar* gidansu Ayam gari ya k'arasa wayewa Umad, safiya na yi ya danna k'ararrawar sanarwar dake jikin k'ofar, daga ciki ya ji an ce "Ana zuwa." Gyara tsayuwa yayi ya k'urawa k'ofar ido yana tunanin fuskar mahaifiyar ce ko ta 'yar zai fara arba da ita dan mace ce tayi magana. Gaba d'aya k'ofar Habbee ta wangale ta sauke idonta cikin na Umad da shi ma ya saka na shi a cikin na ta, ganin bak'uwar fuska ce sai ta saki murmushi tace "Yaro da me zan taimaka maka?" Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace "... *Yar uwa kin biya na ki ne? To ki hanzarta dan jin me zai faru, ga Umad k'ofar gidansu Ayam yana neman Zafeera dan d'aukar fansa, ga sarki da mutanenshi ma daf da ita, shin wanene ma Umad d'in nan wai? Sai kin biya na ki zaki san haka.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:34 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *11* Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace "Mahma, na zo muyi magana da ke, zan iya shigowa ciki?" Had'e fara'arta tayi tace "Magana da ni kuma? A kan me?" D'an d'aga idonshi yayi zuwa saman kanta dake ya fita tsayi ya hangi d'akin, a take kuma ya kalleta yace "Mahma, mai gidan baya ciki ne?" Murmushi tayi tace "Shi ka ke nema?" D'aga kai yayi alamar e tare da fad'in "E mahma." Kaucewa tayi a hanyar tace "Shigo ciki, ya d'an fita zai siyo mana gasasshen bredi ne, yana shigowa yanzu." K'afafunshi ya shiga zurawa cikin d'akin yana bin bayanta, amma idonshi akan gaba d'aya d'akin yake, komai kallo yake yana so ya ga ko zai ga hoto kafin ma ya ga zahirin, saidai babu komai daya shafi mutum, muryar Habbee ce ta katse shi daga wulk'itawar da yake ta ma idon shi tace "Me zan kawo maka?" Murmushi yayi yacce "Coffee." Jinjina kai tayi ta juya ciki, da kallo ya bita kafin ya sake maida idonshi kan komai dake d'akin, yana cikin kallon aka sake danna k'ararrawar k'ofa, da azama ya mik'e da tunanin Utais ne, Habbee kuma har ta fito dan ta bud'e k'ofar, juyawa yayi ya kalleta yace "Karki damu zan bud'e." Murmushi tayi tace "Nagode." K'arasawa yayi bakin k'ofar ya kama hannun zai murd'a sai kuma ya lek'a ta yar hudar da aka yi don tsaro ne dama, mutumin daya gani ne yasa shi zaro ido, duk da kayan jikinshi ba na masarauta bane amma ya san shi farin sani, da sauri ya shiga waigawa neman inda zai b'oye, a k'arshe wani labule ya d'aga ya shiga saboda jin an banko k'ofar da k'arfin da yasa Habbee daga madafa fad'in "Waye wai?" Umad na kallo ta labulen nan har suka shigo tsakiyar d'akin, tunaninshi bai wuce son sanin abinda ya kawosu ba, tsakiyar falon suka shiga suna ta waige waige alamar su ma wani abun suke nema, d'aya daga cikinsu ne ya kalli Habbee dake ta tsatsaresu da ido yace "Ina mijinki yake?" Cikin fad'a fad'a tace "Me zaku masa? Su waye ku? Me kuke nema a nan?" K'akk'arfan ne ya d'aga hannunshi sosai ya d'auke fuskarta da mari, a gigice ta dafe kunci tana fashewa da k'ara har ta fad'i k'asa, a tsorace ta kalleshi sanda ya d'ora yatsarshi akan labb'anshi yace "Shiiiiii!" Hannu yasa ya d'aga rigarshi ya ciro bindiga ya d'ora mata a kai yace "Ina yake?" Daidai shigowar Utais kenan rik'e da takardar dake nad'e da bredi, sakin kayan yayi suka zube ya ruga a guje yana kiran "Kai! Su waye ku? Me ta muk..." Bai gama fad'a ba d'ayan ya zuba masa k'ulli a ciki, duk'uwa yayi yana dafe cikinshi kamar zai mutu, tarin lafiyayyar gashin kan shi ya kaa da k'arfi ya jawoshi k'iii saida suka kawoshi daf da inda Habbee take zaune suka jefar, dukansu suka nunawa bindiga wanda yafi kaushin a cikinsu yace "Ina take?" Kallonsu sukayi a tare Utais ne yace "Wacece?" Wani wawan naushi ya zuba mishi a baki yace "Karo na k'arshe kenan da zaka nemi raina mana hankali, dan haka daga yanzu zuwa sanda zamu bar nan kasan me zaka fad'a mana." Habbee fashewa tayi da kuka tace "Na rok'eku ku rabu da shi, ku daina dukansa hakanan." A tsawace d'ayansu yace "Shiru." Sake nuna Utais yayi da bakin bindiga yace "Tana ina?" Lumshe ido Utais yayi ya had'e wasu yawu masu d'aci, bud'e idon yayi ya kallesu yace "Saidai ku kashe ni, amma na yi alk'awarin ba zan fad'a ba, ba zan tab'a cin amanar sarauniyata ba." Jinjina kai d'ayan yayi ya d'an ja baya kad'an ya d'ana bindigar ya saita akan Habbee yana fad'in "Idan kai a shirye ka ke ka mutu, ban sani ba ko ka shirya rasa matarka ma? Zan k'idaya uku ka ceci matarka." Da sauri ya kallesu a rud'e yace "A'a na rok'eku, kar ku tab'a ni ku min ko ma menene, kar ku cutar da ita." Cikin kuka Habbee tace "A'a ka barsu, na yarda su kashe ni indai akan alk'awarin da muka d'aukawa sarauniya ne." A tsawace yace mata "Shiru, kina da buk'atar kasancewa a raye, ko kin manta kina da mahaifiyar da rayuwarta ta dogara a ta ki ne? Ita kan ta gimbiya ta fi buk'atarki fiye da ni." A hassale mutumin ya daka musu tsawa ya saka yatsarshi zai danna kunamar bindigar a kan Habbee yana fad'in" Ku mana shir..." Bai gama fad'a ba alburushi ya tashi kan shi sai fad'uwarshi kawai suka gani da kua sautin alburushin, k'ara Habbee tayi a take Utais ya jawota jikinshi suka duk'e, d'ayan kam da wani irin sauri ya kalli inda harbin ya fito, saidai tuni Umad ya kawo daf da shi, bai ankara ba kawai ya buga mi shi hannun bindigar a hanci ya b'arke da jini, a take kuma ya rik'e hannunshi mai bindigar ya karya wuyan hannun hakan yasa shi sakin k'ara, su Habbee na kallon ikon Allah sai gani sukayi ya kama wuyansa gaba d'aya ya murd'e ba tare daya barsu sun shaida wanda yayi ajalinsu ba ya turasu kiyama. A matuk'ar tsorace suka shiga kallonshi sai Utais da yayi k'arfin halin tashi tsaye yana kallonsa, nunashi yayi da yatsa jikinshi har b'ari b'ari yake yace "Kai ne? Me ka ke yi anan?" Gyara tsayuwarshi yayi tare da soka bindigarshi a mazauninta ya kalli Habbee yace "Mahma, ki gafarce ni kar ki fahimce ni ba daidai ba." A tare kuma ya kallesu yace "Kun ga, ya zamar muku dole ku fad'i sirrin da kuke b'oyewa tsawon shekara ashirin, ko ku fad'a ko kar ku fad'a kun sani da dole zata zama shugaba, dan haka ban ga anfanin b'oyewar ba har yanzu." Jiki a d'arare Habbee tace "Waye kai? Ya akayi kasan da maganar nan? Ko dai kai ma kana cikin masu nemanta?" Fuskarshi a d'aure yace "Sanin waye ni ba shi ne a yanzu ba, ina so na san wacece gimbiya Zafeera?" Girgiza kai Habbee tayi sai Utais da yace "Kai kuma a cikin wace tawagar masarautar ka ke?" Wani kallo ya musu ya zura hannu ya fito da bindigar yana sake saisaita ta, wani shak'iyin murmushi yayi yace "Kar ku d'auka na taimake ku daga hannunsu ne, gani na yi basa buk'atarta tunda har zasu juri jin jayayya a kan ta, shiyasa na k'ara musu gudu." Tsakiyar goshin Utais ua d'ora bindigar dan yasan mace ta fi rauni sannan ya kalli Habbee fuska a tamke ba alamar wasa yace" Zaki fad'a ko sai kin ga gawar mijinki?" D'aga hannaye tayi tana girgiza kai tace" A'a, a'a na rok'eka kar ka kashe shi zan fad'a, zan fad'a maka." " A'a Habbee, kar ki..." Dungura masa bindigar yayi yace" Zan fasa kanka na sake jin bakinka." Jiki na rawa Habbee ta nufi inda Umad ya b'uya d'azun a bayan labule, bud'a labulen tayi ta wareshi gaba d'aya, Umad na kallonta ya ga ta tura wurin ka rantse bango ne, amma sai gani yayi wurin yayi baya alamar dai mashiga ce, juyowa tayi ta kalleshi tace "Zo ta nan." Kallon Utais yayi ya sake kallonta, nuna Utais yayi alamar ya fara wucewa, gaba Utais yayi sannan ya bishi baya ba tare daya d'auke bindigar ba, saida suka shiga dakin Habbee ta kunna hasken daya gauraye wurin. Dauuuu! Hotonta da hasken d'akin suka daki idonshi a tare, zazzago idonshi yayi kamar zasu fad'o k'asa yana sake k'urawa sosai, gab d'aya jikinshi ya ji ya d'auki wata irin tafiyar tsutsa yayam yayam, sauke bindigar yayi daga kan Utais ba tare daya sani ba, baki da hanci da ido duk bud'e yana kallonta. Ganin kamar baya hayyacinshi yasa Utais kallonshi yace "E ita ce, nasan abinda kake tunani kenan, ni ma ko da na ganka jiya na ji ban yarda da kai ba, sannan ina ji kamar na san fuskarka, sai dai na rasa inda na sanka." A hankali Umad ya taka ya k'arasa gaban tabkeken hoton da aka manna a bango na takarda, rigar sanyi ne jikinta kalar bleue mai haske da dogon wando, gashinta mai yawan gaske da yasha gyara kalar maroon ya kwanta a gadon bayanta, d'aya hannunta a mik'e har yana gugar cinyarta d'ayan kuma ta rik'e damtsenta da shi ta kalli hoton. Ba wai kyau ta yi a hoton ba da yasa ya k'ura mata ido, kawai mamaki da al'ajabin yanda dai ta kasance ita, *Ayam*, ita ce zab'abb'iyar nan? Ita ce lu'u lu'un da ake ta haurigiyar nema? "Waye kai?" Habbee ta fad'a daga bayanshi, ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya d'auke ido a kan ta ba yace "Tun ina shekara ashirin nake neman hanyar da zan bi na d'auki fansa a kan sarki Musail." Juyowa yayi ya kallesu yace "Yau kuma gashi Allah ya kawo ranar, burina a kan Ayam mai girma ne, da kua nasan ita ce na fara had'uwa da ita ranata ta farko dana fara zuwa makarantar nan da nayi awon gaba da ita, ina tabbatar muku da saidai ku samu labarin b'atanta a karo na biyu." Zaro ido sukayi da sauri Habbee ta durk'ushe k'asa tana kuka tace" Mun rok'eka dan soyayyarka da iyayenka kar ka kasheta, bata san komai ba ita bta da laifi, me yasa zaka d'auki fansa a kan ta madadin mahaifinta daya cutar da kai?" Da sauri ya kalleta yace" Kasheta kuma? Na fad'a muku zan kasheta ne? Ai na nemeta ne dan na fi kowa bata kulawar data dace, rad'ad'in rashinta kawai nake so mahaifinta ya ji." Gyara tsayuwa yayi yace" Kunga babu lokacin b'atawa a nan, ko ba komai mak'otan nan sun ji hatsaniyar data faru, a kowane lokaci yan sanda zasu iya zuwa nan." Dafe k'ugu yayi da hannaye biyu yace" Aurenta zaku bani yanzu ni kuma na karb'a, idan kuma kun fi so mu bi ta d'aya hanyar shikenen, sai na koma makaranta na sameta." Kallon kallo suka shiga yi wa junansu, mamakin lamarin shi da kula abinda ya zo musu da shi yasa suka kasa aiwatar da komai, d'aga kafad'a yayi yace" Shikenan tunda baku son ceto rayuwarta, amma ku sani a halin da ake ciki yanzu mahaifinta ya rufe sarauniya Juman a kurkukun Sabah, sannan sarki Wudar na garin Giobarh ma ya baza dakarunsa dan nemo masa ita, wad'annan ma biyu ne daga cikin su, haka ma mai Bukhatir wanda yake kamar d'a ga sarkin Misra shi ma nemanta yake ido bud'e yana son aurenta, kuma wannan a shirye yake ya kashe iyayensa ma saboda ita." Rab'asu yayi zai wuce da sauri Utais ya rik'e hannunshi yace" Mun amince, amma a bisa sharad'i d'aya." Kallonshi yayi ya jefa masa tambayar me ye sharad'in? Cike da kalar tausayi yace" Ka bamu tabbacin ba cutar da ita zakayi ba, ka rantse da abinda kake bautawa babu abinda zaka mata." Murmushin gefen labb'a yayi yace" Na fad'a muku ba zan bari wani ba ma ya cutar da ita bare kuma ni, kawai ina so ne ta wa sarki Musail nisa yana ji yana gani har k'addarar mutuwarsa ta gilma ta hannunta kamar yanda ake farfagandan fad'a." Jinjina kai Utais yayi yace" Shikenan mun amince, yanzu ya za'ayi ta zo nan dan mu shawo kan ta?" Yar dariya yayi yace" Ni musulmi ne, kula zan aureta ne kamar yanda addini ne ya shar'anta min, zaka zama waliyinta yayin da zan wakilci kai na." Kallon juna suka yi da Habbee sannan suka jinjina kai, zaune yayi akan shafafffen tiles d'in dake d'akin da babu komai ya nuna musu su zauna su ma, laluba aljijunsa yayi sai kuma ya kallesu yace" Kuyi hak'uri fa babu kud'i hannu na, makullin motar da ya zo asalin masaukinshi ya d'auka ya aje gabansu yace "Wannan makullin motata ce Ferrari, na bata ita a matsayin sadaki." D'aukar makullin Utais yayi yana tsura masa ido, da sauri Umad yace "Karka damu fa, da zaran na d'auketa daga nan zan bata har da takardun motar, yanzu ka damk'a min amanarta ni kua na karb'a." Kamar wasa Utais ya mik'awa Umad auren Ayam daga nan wurin da taimakawarshi, suna gamawa Umad ya kalleshi yace "Cin ta, shan ta, suturarta, kula da lafiyarta, addininta, zamar mata abokin hira, iliminta, duk nayi alk'awarin kiyayewa iya k'arfina, haka ma sauke nauyin saduwa." Mik'ewa yayi yana fad'in "Insha'Allah ni zan zama uban jikan sarki Musail." Mik'ewa sukayi su ma Habbee ta sake fad'in "Wai waye kai?" Wani siririn murmushi ya saki ya juya ya kallesu yace "Umad, d'a ga sarki *Wudar*, *yariman Giobarh*." Gaba d'aya cikinsu ya yamutsa suka shiga k'arewa kansu kallo, ganin babu wanda ya ce wani abu ciki alamar girgizar daya basu yasa shi cewa "Hankalinku ba zai d'auka ba dama, gaskiya ne mahaifina ma nemanta yake, amma manufar shi daban a kan ta, tawa ma manufar daban a kan ta, mace mai daraja Musail ya d'auke mana bayan ya rabani da d'an uwana da na fi so a duniya, shiyasa ni ma na d'auke masa 'yarsa mai daraja, abun farin ciki kuma shi ne daya yarda ita ce zata zama silar mutuwarshi, hakan zai bani damar jijjiga rayuwarshi na yi wasa da ita kamar biri da mai wasa da shi." D'aga musu hannu yayi har ya kai k'ofa zai fita sai kuma ya juyo ya tarawa Utais hannu yace" Ara min makullin nan na mayar da kai na makaranta wajen amaryata." Baki wangale jiki a sake Utais ya mik'a masa makullin sun rasa ta cewa, fita yayi daga d'akin yana fad'in" Ku gaggauta barin nan garin kafin yan sand su nemeku da tuhumar kashe mutanen nan biyu." Daga haka ya fice a gidan mutane kam har sun fara taruwa a na hangen benen na su, suna dawowa daga doguwar sumar nan suka zabura suna kallon junansu, a gigice Habbee ta shiga fad'in" Me ka aikata haka? Me yasa ka amince masa? Yanzu idan fa ya kasheta?" Rik'ota yayi yace" Kinga ki nutsu, da fari mu bar nan kamar yanda ya fad'a, idan ba haka ba kuma za'a kama mu." Da sauri suka fita a d'akin suka nufi d'akin baccinsu dan d'aukar abubuwansu masu mahimmanci. *To yar uwa kin dai gani, ga Umad zai koma makaranta da auren Ayam a kan shi, shin zai sameta a makarantar kuwa? Ya akayi ma mutanen nan suka zo daidai da zuwan Umad? Wa ya sanar da su har suka yi kok'arin riganshi zuwa? Ya Ayam zata yi idan ta ji wai Umad ya aureta? Ya ma zasu rayu tukuna a cikin abokan gaban nan? Idan kika biya na ki ne kawai zaki samu damar sanin wad'annan abubuwan, ki hanzarta ki biya na ki.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:34 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *12* *Ayam* na komawa b'angarensu d'akin baccinsu ta shiga, kayanta ya cire tz d'aura towel ta shiga wanka, sa'ilin da ruwan ke sauka kan ta ta samu damar rufe ido, a lokacin tunanin mafarkinta ya dawo mata wanda su Deeyam su ka katse mata shi a daren jiya, haka kuma ta had'e abun ta ba tare data yarda kowa ya ji ba, d'an gashinta daya had'e da juna ta shiga murzawa tana mayar da shi bayanta tana gumtsar ruwa a bakinta tana tofowa, idonta a rufe suke k'am ta shiga fad'a a ran ta "Me mafarkin ke nufi? Ko dai mafarki ne kamar kowane? To amma me yasa matar ba tayi kama da wanda na tab'a sani ba?" Da sauri ta bud'a idonta sakamakon jin motsi a d'akin, amma sai ta share ta ci gaba da wankanta kawai, dan tunaninta su Deeyam ne. A tsanake ta k'arasa wankanta ta d'auro towel, hannun k'ofar ban d'akin ta kama dan bud'ewa, tana zuro k'afa d'aya ta fito ta k'arasa fito da k'afar d'aya tana fad'in "Ke! Me ya kawoki n..." Wani duka aka mata a kai ba tare da imani ko tausayawa ba, ko shurawa ba tayi ba ta fad'i gure a sume inda kan ta ya b'alle da jini a k'eyarta, cike da jin dad'i da farin cikin zata cika burinta a kan ga Zafreen ta kece da dariya ta mik'e tsaye tana kallon k'akk'arfan matashin da suka saka ya musu wannan aikin, wanda saida suka jadadda mishi ya mata dukan da zata suma. Tafa mi shi tayi da murna tace "Aikinka na kyau, nagode sosai." Laika dake gefenta ne tace "Gaskiya ne, ni ma ki min godiya." A wulak'ance ta kalleta tace "A kan wane dalili?" Shiru Laika tayi saida Zafreen ta juya bayanta ta maida hankali ga Ayam dake yashe kwance, bata ankara ba Laika ta d'auki hoton dake aje gefen gadon Sabrine na ita da danginta, sai kuwa ta fasawa Zafreen shi a kai har saida madubin ya mutu a kan ta, take ita ma ta zube bayan ta dafe kanta tana k'ok'arin juyawa ta kalli Laika. Kallon juna sukayi Laika ta ciro wata k'aramar waya a cikin rigar mamanta ta danna wasu lambobi ta d'ora a kunne, a tak'aice tace "Angama." Tana aje wayar sai kuwa wata irin kara ta gauraye makarantar an danna na'urar dake nuni da idan wani had'ari ya samu musamman ma gobara, ai kuwa tuni hatsaniya ta kaure a makarantar dan kuwa sauran munafukan da ke tare da su Laika ne sukayi nasarar tashin zanga zanga a ciki, sai gashi sun fara farfasa abubuwa har da motocin malamai da ofisoshinsu. Makaranta ta hautsine, duk jami'an sun yi iya k'ok'arinsu amma abun da gaske fin k'arfinsu aka yi, ana cikin hatsaniyar nan aka fitar da Ay da Zafreen ta bayan makaranta inda jirgi ya d'aukesu, Laika ma da tawagarta sulalewa sukayi suka bar makarantar, inda suka bar wanda basu ji basu gani ba a hannun jami'an makarantar suna son hukuntasu da laifin tayar da tarzoma. Tunda ya doso ya ga wannan hayaniya da tashin hankali jikinshi ya bashi babu lafiya, yana fitowa daga dalleliyar ferrarin nan da gudu ya nufi inda yake tunanin samunta, bai damu da kowa ba da kuma abinda kowa zai fad'a. Yana zuwa b'angarensu yayi sa'ar kicib'is da su Sabrine sun fito da gudu zasu fita, hannun Deeyam ya rik'o da sauri yace "Tana ina?" Girgiza kai tayi tace "Mu ma ita muke nema, mun shiga d'aki amma bamu sameta ba." "Shiiit!" Ya fad'a yana sake zubawa a guje ya juyo ya sake tambayar "Ina d'akin?" Nuna masa tayi da hannu, bai jira komai ba ya bangaji k'ofar ta bud'e ya shige, turus ya tsaya kallon d'akin, da gudu ya k'arasa gaban tagar daya gani bud'e ya lek'a, tabbas ko ma su wanene ta nan suka fita da ita, ga alamu nan ya nuna har da sawayen takalmi. Dafe gaban goshinshi yayi yace "Ya Allah! Su waye kuma yanzu?" Wayarshi ya ciro da sauri ya shiga daddanawa ya d'ora a kunne, jim kad'an Haman ya d'aga, cikin tashin hankali ya nufi hanyar fita a d'akin yana fad'in "Haman kana ina? Akwai matsala fa." Shi ma hankali tashe yace "Matsala kuma? Me ya faru?" Da azama yace "Kai dai ka fad'a min inda ka ke zan zo na sameka." Da sauri shi ma yace "Ina nan masauki na dana fad'a maka." K'itt! Ya yanke kiran ya shiga takawa da sauri har ya k'arasa ga motarshi ya shiga ya sake barin harabar makarantar. *Egypt* Babban masaukin daya tanada dan wannan ranar yasa aka sauke mishi su, ya kashe kud'i masu azababben yawa dan kawai ya k'awata mata wannan gida, Zafreen ce ta fara bud'a idonta a hankali da suka mata nauyi har suka d'an fara kumbura, a hankali ta zura hannunta ta dafe k'eyarta saboda tuna abinda ya faru, a sanyaye ta furta "Wash!" Muskutawa tayi ta tashi zaune sai kuma ta zabura da k'arfi saboda ganin Ayam kusanta kwance ita ma, juyawa tayi dan son ganin ko akwai wani kusansu, sai kawai ta ga kan ta a madubin drower da Bukhatir ya shak'ewa Ayam kaya da ita, saboda a bazata ta ga kanta sai ta saki yar k'arar data saka Ayam motsawa ita ma, tana bud'a ido ta sauke akan kwalliyar rufin d'akin wacce aka yi kamar da gwal aka yi ta. Ganin Zafreen yasa ta yunk'ura da sauri ta tashi zaune, za ta yi magana sai kuma ta dafe kan ta da ta ji yana mata ciwo sosai, d'an kallon kanta tayi sai ta ga daga ita har Zafreen an nad'e musu kai da bandeji fari, kallon Zafreen tayi tace "Ina ne kika kawo ni nan? Ke ba fa na son iskanci kin ji ko, ki fita a harkata kafin na sake b'ata miki rai." K'wafa tayi ta mik'e tsaye tana k'arewa kanta kallo ta madubin, towel d'in jikinta shi ne dai har yanzu, Zafreen ma mik'ewa tayi tace "Ke kinsan wacece ni? To ni ma ina son sanin inda nake." Tsaki Ayam tayi ta nufi inda ta ga k'ofa da niyyar fita, kafin ta isa bakin k'ofar aka bud'o aka shigo, kallon kallo suka shiga yi da k' akk'arfan matashin dake cikin shiga ta alfarma, had'e fuska Ayam tayi ta dafe k'ugu tace" Wannan wane irin rashin mutumci ne? Ina ne nan kuka kawomu?" Wani sanyayyar murmushi ya saki ya bud'e hannayenshi zai rumgume ta, da sauri ta ja baya tace" A'a, kai mahaukaci ina ne? Waye kai?" Ba tare daya d'auke murmushin dake kan fuskarshi ba yace" *Pr茅cieux*, embrasse moi, tu sais combien da temps je passe a attendre ce jour (mai daraja, rumgume ni mana, kinsan lokacin dana d'auka ina jiran wannan ranar)?" Nunashi tayi da yatsa tace" Zan wanka maka mari idan ka kuskura ka tab'a ni." Murmushi ya kuma saki ya juya ya kalli wasu matasa guda biyu dake gefenshi ya nuna musu Zafreen yace" Ku d'auke wannan daga nan ku kai ta b'angaren bak'i, wannan b'angaren na gimbiya ta Zafeera ne." A wani yatsine ta kalleshi inda Zafreen tace" Ni kuma me yasa kuka kawoni nan? Waye kai ma?" Gyara tsayuwarshi yayi yace" Sunana Bukhatir, mai jiran gado a Egypt." Zafreen ce ta d'ora da" To ni kuma me na ke a nan? Ku maida ni makaranta mana, kasan ka mu su waye?" A wulak'ance ya kalli Zafreen yace" Na sani, kuma a dalilin yawan fad'a da kike yi ne ya kawoki nan?" Hanya ya nuna mata hanya yayi ba yanda ta iya dole ta shige gaba suka bi bayanta, kallon Ayam yayi yace" Ma pr茅cieux, zan turo hadiman da zasu kula min da ke yanzu, wannan shigar bata dace ki ba." Juyawa yayi zai fita Ayam tayi kukan kura ta shak'o rigarshi dam a hannayenta tana kallon fuskarshi tace" Babu inda zaka je sai ka mayar dani inda ka d'auke ni." Cikin matsanancin shauk'inta ya lumshe ido ya fara zura hannunshi akan cinyarta yana neman zurawa a cikin towel d'in, ido lumshe yace" Gashi kin kawo min kan ki, Zaf... Eera." Da sauri ta ske shi ta ja baya tana hararenshi, wani shakiyin murmushi yayi ya juya ya fita, da sauri ta kama k'ofar zata bud'e sai ta ji a rufe take gam, tsaki tayi ta shiga zagaya d'akin tana sln sanin a ina take? Me ta zo yi a nan? Su waye kuma take tare da su? Bud'e k'ofar da aka yi yasa ta saurin juyawa, matasan mata ne su biyu da kayansu iri d'aya a jiki, da girmamawa suka rusuna suna gaisheta, cikin fad'a ta nufesu tana musu yarensu tace "Wai ku su waye? A ina nake nan ne?" Nuna musu k'ofa tayi tace "Maza ku bud'e min k'ofar nan." Rusunawa sukayi a ladabce cike da tsoron kar su mata ba daidai ba ransu ne zai b'ace daga gurin mai gidan na su, d'aya daga ciki ce jikinta na rawa tace "Ranki shi dad'e yallab'ai ne ya umarcemu da mu tayaki shirya kan ki." A tsawace Ayam tace "Ranki shi dad'en banza, wane banzan shiri ne zaku tayani? Mu saka ce ni aka fad'a muku? Ko dama can fil azal ku kuke min wanka ne? Mtsssss!" Rikicewa sukayi suka rasa yanda zasuyi, cikin hushi ta nufi k'ofar ta sake kamawa zata bud'e, amma sai ta ji ta gam ta k'i bud'ewa, a tsawace ta kallesu tace" Zaku bud'e min ne wai ko sai na bajeku a nan?" Da sauri suka fara riga rigan bud'e mata k'ofar, d'aya a ciki ce ta d'ora hannu a k'ofar tare da danne wani mab'alli dake k'asan hannun k'ofar, bud'ewa tayi ta kauce mata a hanyar, ai kam ficewa tayi da sauri tana k'arewa tabkeken falon kallo, tsaye tayi ta shiga bin ko ina da kallo dan gaskiya d'akin ya birgeta sosai, tab'e baki tayi ta ci gaba da tafiyarta ta nufi inda take ganin nan ne mafitar. Zata bud'e k'ofar kenan aka bud'e daga waje, cak ta tsaya ta zubawa mai shigowa ido, saidai sab'anin d'azu da fuskarshi ke d'auke da fara'a da annashuwa, yanzu kam fuskar a had'e take tam, yanda ta lura yana ta kallon bayanta ne yasa ta d'an juyawa, matasan matan nan ta gani duk sun zube k'asa kawunansu sadde jikinsu sai b'ari yake. Juyawa tayi ta kalleshi sai kawai ta ja tsaki ta kula juyawa ta kallesu tace "Ku mik'e tsaye kunji, me ye na wani rusunawa har k'asa gaban mutum d'an uwanku." D'aya a ciki ce tayi k'arfin halin d'aga kan ta ta kalketa sai kula ta sunkuyar, muryar Bukhatir ce ta sa ta juyo sanda yake fad'in "Me na fad'a muku a kan ta?" Jiki na kyarma d'ayar tace "Yallab'ai mun yi iya k'ok'arinmu amma ta k'i..." Kashe fuskarta yayi da marin daya sakaya girgiza kamar zata fad'i kwance, a mugun hassale ya nunasu da yatsa yace "Ba k'ok'ari ba, abinda yasa na d'auko ku shi ne dan..." Gauuuu! Ayam ma ta d'auke fuskar Bukhatir da mari, a wani irin razane matan da kuma dattijon ne dake bayansu suka kalleta, dan su kam yanda suke girmama Bukhatir ko sarkin Egypt basa girmamawa haka, idonshi da suka kad'a sukayi jajajir ya d'aga ya kalleta, ido cikin ido suka kalli juna babu mai alamar rusunawa. Tunanin hanyar da zai fara hukunta ta yake, tunanin kalar muguntar da zai mata yake, hasaso hukuncin da zai mata yake wanda zaiyi sanadiyar ta fara kakkarwa sanda ta ji sautin muryarshi, amma ikon Allah sai ya ji ya kasa aiwatar da komai, sai ya ji wani tausayinta a zuciyarshi ya malayeshi sanda suka had'a ido, sai kawai ya d'auke hannunshi daga kuncin yana murmushin takaici, dan ko iyayenshi ba zai tuna ranar da suka tab'a marinshi ba, ba dan kar ya zama mak'aryaci ba sai yace tun na k'uruciya wanda bai san anyi ba ma. Sake kallon fuskarta yayi yana lashe leb'enshi kafin yace "Idan har kina son barin nan sai ki fara bin duk wani umarnin da zan gindaya miki." A zabure tace "Kai a wa da zan bi umarnin ka?" Sunkuyar da kai yayi k'asa yana murmushi kafin ya kalleta yace "Mijin da zai aureki." Da wani mamaki tace "What!" Ba tare daya daina murmushin ba yace "Ba zaki gane komai ba a yanzu, ki fara shiga ciki ki shirya dan ki samu ki suturta min jikinki, idan kin fito zamuyi magana dake." Rumgume hannaye tayi tace "Kafin nan ka fara amsa min wad'annan tambayoyin nawa." Girgiza kai yayi yace "Zafeera mahimmanci gareki a wajena, idan na mayar dake sarauniyata ko fuskarki bana so kowa ya gani, ta ya zan yarda ki tsaya a haka wasu na kalleki? Kin san wacece ke kuwa? Kin san girma da matsayin darajar da kike da shi? Allah ya karramaki dan haka zan tayaki karrama kan ki." Cikin jin haushi tace" Tukuna ma wane banzan suna kake kirana da shi ne?" Murmushi yayi mai kama da dariya ya juya zai fita yana fadin" Ki fara shiryawa sannan, zan amsa duk wata tambayarki." Da wata matsiyaciyar harara ta bi bayanshi har ya b'acewa ganinta, juyawa tayi a masifance tace wa matan" Sai ku tashi mu tafi ko? Zaku tsaya k'aton gardi na dukanku kamar ubanku, wahe shi ma tukuna?" Yanda tayi tambayar tana rik'e k'ugu yasa d'aya a ciki tace" Kamar d'a yake ga sarkin k'asar nan." Yamutsa fuska tayi tace" Kama ne ma yake ba d'an sarkin bane, to wace k'asar ce wannan?" D'ayar ce ta amsa da" Egypt." Da mamaki ta kallesu tace" Egypt? Kuna nufin nan a Egypt nake?" Jinjina kai sukayi hakan yasa ta ita ma ta jinjina kai ta k'arasa bakin kofar d'akin, bud'e mata sukayi ta shige suka bi bayanta. *Khazira* A kausashe ya buga teburin yana kallon Adah da kan shi ke k'asa kamar zai fasa d'akin yace "Ta ya ya haka zai faru? Sai da na ce zan je da kai na kuka tabbatar min da zaku iya, yanzu me kuka aikata kenan?" Cikin girmamawa Adah yace "Ka gafarce ni sarki, mun tarar da hatsaniya ne a makarantar, ga dukkan alama wasu abokan gabar ne suka fara ganota shiyasa suka tayar da zanga zangar, da haka kuma sukayi nasarar d'auke mana gimbiyoyinmu." Da wani sabon mamakin yace "Me? Gimbiyoyi kuma?" Cike da d'ar d'ar yace "E shugabana, gimbiya Zafreen da gimbiya Zafeera sun b'ata a cikin tarzomar nan." Da bala'in k'arfi sarki Musail ya cire kambun dake kan shi na tsantsar gwal daya sa aka k'era masa dan alfahari ya jefar a k'asa, a fusace ya juya b'angaren da Dhurani yake ya kalleshi, sai kuma ya tattare rigarshi dake jan k'asa ya tunkari hanyar fita, rufa masa baya sukayi inda waziri Khatar ke fadin "Sarki na, ka nutsu mu bi komai a hankali, na tabbata sarki Wudar ne ya d'aukesu, dan shi ke da burin son d'aukar fansa a kanmu." Dakatawa yayi ya juya ya kalli Khatar da yayi maganar, jinjina kai yayi yace "In kuwa hakane sarki Wudar ya jaza ma k'asar sa yak'in duniya na uku, dan babu abinda zai hanani shiga masarautarsa sannan nayi fata-fata da su." Dhurani ne yace "A'a sarkina, ba da haka zamu fara ba, kafin mu farmake su buna buk'atar samun tabbaci suna hannunshi, daga bisani koma menene sai ya biyo baya." Adah ne yace "Hakane shugabana, dan na tabbata kamar yanda muke tsananin buk'atar gimbiya Zafeera, haka shi ma sarki Wudar, ba kuma zai kamata bane dan ya kasheta." Cikin hassala yace "To yanzu ya zamuyi? Me ye mafita? A yanzu na fi buk'atar Zafeera a kan Zafreen d'in." Adah ne yace "Wannan mai sauk'i ne shugaba na, zanyi magana da d'aya daga cikin masu lek'en asirinmu dake sintiri a cikin fadarsa." Nunashi yayi da yatsa yace "Ka tabbatar nan da zuwa yammacin yau ka samo min masaniyar komai." "Angama yallab'ai." Ya fad'a yana rusuna masa, saida suka ga ficewarsa kafin su ma duk suka bar wurin babu wani mai farin ciki da yanayin da yake ciki, dan su kansu sun fi buk'atar a samu Zafeera a kuma k'ara mata gudu zuwa lahira, dan su canjin da aka ce zata kawo shi ne yafi tsaya musu a rai, a ganinsu zata rabasu da addinansu ne, muk'amarsu da martabarsu, hakan kuma ba zasu bari ya faru ba mundun ran su. Bai zame ko ina ba sai kurkukun sabah, tsabar a rikice yake bafade d'aya ne ya take masa baya zuwa can, hannunshi rik'e da doguwar rigarshi cikin sauri har suka isa can, mai tsaron d'akin da take ne yayi saurin bud'ewa sarki Musail ya shige. Tana zaune rakub'e a jikin bangon ta had'a kai da gwiwa, idonta a rufe suke ruf dan ko ta bud'e babu abinda take gani face dishi-dishi da jiri, har saida ya isa gabanta ya durk'usa irin tsugunnon maza ya finciki gashin ta sakamakon gyalenta daya sauka a kan kafad'unta, da k'arfi ya d'ago kan ta har saida ta saki yar k'ara saboda zafin da ta ji, da k'yar ta d'aga idonta ta kalleshi. Cikin gadara da cika baki ya mata murmushi yace "To ya kike sarauniyata?" Kamar wacce ke cikin maye tayi luuu da idonta ta saki wani murmushi ita ma tace "Yan...da kake, haka na ke." Tura kanta yayi da k'arfi har saida ta bugu ga bango ya fashe da dariya yace "K'arya kike sarauniyata, ni ina lafiya kuma ina cikin farin ciki." Cikin layi tace "Kai ma ba gaskiya ka fad'a ba sarkina, hankalinka a tashe yake kamar yanda muryarka ke b'arin tsoro saboda ka fara jiyo k'amshin mutuwarka." Da sauri ya mik'e tsaye yana lumshe idonshi dan gaskiya ta fad'a kam hankalinshi a tashe yake, cike da k'arfin hali ya kalleta yana nunata da yatsa yace" Ki zuba ido ki gani Juman, gobe warhaka ke da 'yarki duk zaku mutu, wannan alk'awari na ne." Malalacin murmushi tayi ba tace komai ba har saida ya fita a wurin, a zahirinta kam bata nuna damuwa ko tsoron abinda ya fad'a ba, amma k'asan zuciyarta cike take da tsoro da alhini da zulumin abinda zai iya aikatawa. *Larhjadin* Ko da Umad ya isa ya samu Haman a masaukinshi fad'a masa abinda ya faru a makaranta yayi, saidai haka kawai ha k'i yarda ya fad'a masa batun auren nan, dan dama yayi ne saboda yasa hankalinsu Habbee ya kwanta su ji nutsuwar zuci su tabbatar tana hannu na gari, duk da dai yasan ba lallai sun yarda da shi ba musamman da suka san waye, amma dai yanzu a tunaninsu tana tare da shi kuma ba zai bari a cutar da ita ba kamar yanda ya fad'a musu, dan haka a sanin da yake da shi yasan aurenshi da Ayam zai cika k'aida ne idan da amincewar iyayenta mahaifa tunda suna raye, shaidu da kuma sadaki. Cikin tashin hankali Haman yace "Me? Yanzu kana nufin ta sake b'ata kenan?" Jinjina kai yayi ya kalleshi yace "Hakan alamu suke nunawa, amma a yanzu zamu iya cewa mun san inda take." Cike da k'aguwa yace "A ina kenan?" Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Zan koma gida yanzun nan, ta hakane zan san inda take." Da mamaki Haman yace "Kana nufin zaka koma masarauta kenan?" Jinjina masa kai yayi alamar e, cikin d'ar d'ar yace "Bana tunanin sarkinmu ya sameta, me zai hana ka fara saka ido akan Bukhatir?" Da wani mamaki Umad ya kalleshi ya d'aga labb'enshi da k'yar yace "Bamu tab'a maganar Bukhatir da kai ba, ya akayi ka san shi?" Zaro ido yayi alamar firgici, a take kuma ya had'e komai ya saki murmushi yace "Haba dai, ka manta ka min maganar sa? Daga gareka na ji batunsa ai." Cike da son waskewa ya d'an zagaya ya matsa daf da shi ya dafa kafad'arshi ganin kamar bai yarda da abinda ya fad'a ba yace "Ka gane ko, ina ga zai fi ka fara ta can d'in, zuwa gobe sai mu koma tare." Wani arnan kallo Umad ya masa sai kawai ya jinjina kai alamar to sannan yace "Shikenan." Sallama sukayi inda Umad na d'aukar hanya masaukin daya fara sauka ya k'arasa ya had'a kayanshi, dan yayi niyya yau ba sai gobe ba zai d'ora da neman Ayam, dan sai yake gani kamar Haman ya manta shi ne wajen rashin yarda da kafuwa, duk aminci da yardar dake tsakaninku ba zai saka shi d'auke ido a kan ka ba, bare al'amari na wacce yake da tabbacin za'a iya sadaukar da bilyoyin kud'i don samunta. Yana gama shiryawa saida ya fito ya d'auki hanyar zuwa filin jirgi sannan ya kira canal Jacob dan sanar da shi aikinshi ya k'are, dama hanya aka masa a gwamnatacce dan cika aikinshi, to tunda ya tabbatar da wacce yake nema ai shikenan. *Bayan awa shida (Giobarh*: yana sauka a k'aton jirgin emirates d'in motoci guda hud'u ne suka zo dan d'aukarsa, sanda suka shiga rusuna masa d'aya daga ciki ya karb'i jakarsa mamaki ya shiga yi na samun tabbacin abinda yake zargi, dan ko mahaifinshi sarki bai fad'a ma zai zo ba, amma ga tarba ta musamman daga masarautarshi. Limozine d'in da aka bud'e mishi ya shiga ya zauna suka mayar da k'ofar aka rufe suka d'auki hanya, gudu ake sosai dan tafiya ce mai nisan gaske daga filin jirgin zuwa fadar ta su, a d'an lokacin nan kuma tangale hab'arshi yayi yana kallon titi a zahiri a bad'ini kuma tunanin komai daya faru kuma yake faruwa yake, da wannan suka share awa d'aya a hanya kafin motocin su tsaya a k'ofar gidan suna oda. Masu gadi biyu ne suka shiga jan k'ofar suna bud'eta tsabar girmanta da kuma nauyin da take da shi, danna hancin motocin sukayi a cikin farfajiyar wanda shi kan shi filin gidan wata k'asar ce daban data gaji da kyau da had'uwa. *K'arshen free page, idan kina da buk'ata garzaya ki biya naki, sai kun zo masoyan asali.* *Masoya na da suka biya kud'insu dan wannan littafi ina son sanar da ku zaku min alfarma d'aya, zan dinga sakar muku sabon shafi ne sau biyar a rana, saidai bai tsayar da ranakun ba gaskiya, kamar yanda a kowace rana ogana zai iya shigowa gari, hakan kuma na raunana rubutu na na kasa samun kai na, fatan zaku fahimce ni.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:35 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *13* A k'ofar babban b'angaren motocin suka tsaya, da sauri suka firfito suka jeru suna jiran fitowarshi inda d'aya a ciki ya bud'e mishi k'ofa, k'afarsa d'aya ya fara zurowa mai sanye da takalmi kalar maroon k'irar turkey amma ba k'afa ciki ba, karasa fita yayi gaba d'aya cikin sauri ya tunkari shiga ciki suka rufa masa baya, saida suka kai daf da falon suka tsaya sai biyu da suka bi shi zuwa ciki, tunkarar matakalar da yayi yasa shi d'aga musu hannu alamar su dakata kafin ya shiga takawa da sassarfa kamar zai yi gudu. D'aki na biyu a jerin corridor ya k'wank'wasa, bai jira izini ba ya bud'e ya shige dan yasan wacce ke d'akin ba zata iya bashi izinin ba, cak ya tsaya yana kallon sanyin idaniyar tashi, wani annuri ne ya ziyarci fuskarshi sanda ya d'ora idonshi akan kyakyawar fuskar dattijantakarta, a hankali kuma har sanyayyan murmushi ya bayyana a fuskar shi ba tare da sanin shi duk dan shauk'in ganin *mahaifiyarsa*. Bai yi k'asa a gwiwa ba tunda yasan ba zata iya motsa ko da k'afarta ba yasa shi saurin k'arasawa gareta, saida ya zagaya b'angaren hagunta sannan ya durk'usa kan gwiwarshi d'aya, hannunshi na hagu yasa yana shafa gashin kan ta yana mayar mata da shi baya, tattausan murmushi yake sakar mata hannun dayan shi kuma ya sak'alashi cikin na ta, a sanyaye ya furta "Fy Mam (mahaifiya ta, a yaren Gallois)." Farin cikin ganin mahaifiyarshi da kuma tsananin tausayin halin da take ciki yasa shi jin wata k'walla na taruwa masa a gefen idon shi, cike da k'arfin halin son kawar da ita yace " Fy Mam kina lafiya ko?" Idonta dake rufe ya kalla wanda yasan ba dan bacci take ba da ta amsa masa da ido, k'urawa fuskarta ido yayi cikin muryar jimami da alhini ya sake fad'in "Komai ya kusa zuwa k'arshe fy Mam, na samota dana tafi, kuma zan tabbatar na kawo miki ita har nan, bansan ko nayi kuskure ba, amma dai dole ne sarki Musail ya d'and'ani hukunci, dole ya ji rad'ad'in rashinta yayin da zai hangeta a cikin gidan nan, amma kuma babu yanda zai yi, ko ta zama ajalinsa, ko ta zama silar rugujewar duk wani iko na shi, wannan bai dameni ba, zafi da tashin hankalin da zai shiga na rashinta ma kawai ya isheni." Sake damk'ar hannunta yayi tare da sako hawayen daya gagara tsayar da su cikin k'unar zuci yace" Sai na d'aukar miki fansa fy Mam, a dalilinshi ne kike kwance ba kya motsa ko da yatsanki, a sanadiyarshi ne mahaifina ya rasa duk wani farin cikinshi, a sanadin shi ne na rasa d'an uwa na..." D'ora goshin shi yayi a hannunta yana zubar da hawaye, wannan d'umi hawayen dake sauka hannunta ne ya farkar da ita, saidai ido kawai ta zuba masa tana kallon sumar kan shi, saida ya ci kuka mai isarshi ya d'ago kan shi ya zuba idonshi a fuskarta, suna had'a ido ya saki murmushi yana share k'wallan shi yace "Fy Mam, kin tashi ne?" Ido kawai ta zuba mishi ba tace k'ala ba, murmushi shi dai kawai yake sakar mata, hannunshi na cikin na ta yana ta mammatsawa, banko k'ofar d'akin da aka yi aka shigo yasa shi d'aga idonshi ya kalli k'ofar, kan farin gemun mahaifinshi ya fara sauke idonshi kafin gaba d'aya farar fuskarsa, wani bayyanannan murmushi ya saki ya mik'e tsaye da hanzari ya tunkareshi, shi ma sarki Wudar da farin cikin ganin gudaliyarsa kuma magajinshi yasa shi bud'e hannayenshi yana fad'in "Fyddai (d'ana)." Da fara'a shi ma ya rumgumi mahaifin na sa yace "Fy nhd (mahaifina)." Sosai suka rumgume juna kowa na shak'ar k'amshin junansu, cike da so da k'auna sarki Wudar ya d'an bubbuga bayanshi hakan yasa suka d'ago suka kalli junansu, da farin cikin sake had'uwa da sukayi Wudar yace "Yaro na ya kake?" Da fara'a ya sunkuyar da kai yace "Ina lafiya mahaifina, kamar yanda kake gani." Jinjina kai yayi yace "Ya akayi ka zo baka sanar dani ba? Baka so na san da zuwanka ne?" Kallon fuskarshi yayi yace "Amma yanzu ya akayi ka sani?" Da fara'a ya amsa masa da "Abokinka ne ya sanar da ni, Haman." D'an girgiza kai yayi tare da k'yabta idonshi alamar sam bai ji dad'i ba, nuna masa mahaifiyarshi yayi yace "Ka ga jikin na ta ko? Har hanzu Umad k'ok'ari nake akan rashin lafiyar mahaifiyarka, izuwa yanzu abun ya daina bani mamaki sai ma tsoro." Jinjina kai yyi yace "Mam ta kusa samun lafiya Ba, insha'Allah." Da mamaki sarki Wudar ya kalleshi yace "Me ka fad'a a k'arshen?" Girgiza kai yayi alamar ba komai, sai kuma ya sunkuyar da kai yace "Ka gafarce ni mahaifi na, ni zan je b'angare na." Da alamar mamaki a fuskar sarki Wudar ya kalleshi yace "Sosai nake mamakin sababbin halayanka Umad, wai me yake damunka ne?" Kallon fuskar mahaifin na shi yayi, irin kallon nan na tsaneke kallo na basira, a take kuma ya d'auke idonshi ya mayar k'asa yace "Sarki na, zan sanar da kai komai da zaran mun zauna." Bubbuga kafad'arshi yayi ya jinjina kai alamar gamsuwa, cikin nutsuwa yace "Ka huta da kyau, zuwa dare zamuyi tafiya." D'an kallonshi yayi da mamaki sai kuma ya sunkuyar da kai yace "To Ba." Da ido ya masa izini da zai iya tafiya, a ladabce ya rab'ashi ya fita a d'akin, hadiman dake bakin k'ofar ne suka rusuna masa alamar gaisuwa, bai kula da su ba sai wucewa inda zai sadashi da na shi b'angaren. A kasalance ya k'arasa had'add'en b'angaren shi, cike da gajiyar tafiya ya shige b'alle mab'allansa amma kuma idonshi a lumshe yana tunanin _"Ina take? Shin zai iya samunta a cikin gidan nan kuwa?"_ Ajiyar zuciya ya sauke ya bud'e idonshi tare da jefa rigarshi kan gado ya nufi ban d'akin shi yana tunanin tabbas idan suka zauna zai fad'awa mahaifinshi ya fa jima da canza addininshi. Tunda ya fita sarki Wudar ma ya k'arasa kusa da uwar d'akinshi, sunkuyawa yayi ya sumbaci goshinta ya kalli fuskarta yace "Ina son ki, anjima zanyi tafiya ki min addu'a, zan je cinikayyar lu'u lu'uta, ba zan dawo gidan nan ba sai da ita." Sake sumbatarta yayi sannan ya fita a d'akin cikin rakiyar hadiman shi biyu dake take masa baya. *Egypt* Irin yanda ta ga suna d'aukaka lamarinta da kuma yi mata komai daban yasa ta jefawa kan ta tambayar *wacece ita*? Dan yanda ta ga hatta da ruwan wankanta kalarsu daban, wata irin kalar pink mai duhu ga kuma wasu furannin flowers da aka zuba a ciki, uw uba k'amshin da ruwan ke fitarwa, yanda suka tsaya a kan ta bayan ta fito suka dinga shiryata kamar yar tsana, wata doguwar riga kalar ja suka wacce kamar da tattausan leshe aka d'inka ta har jan k'asa take, kamar yanda ta nuna bata so haka suka barta da fuskarta babu kwalliya, saidai farar hodar ruwan da aka shafa mata wacce ta dace da kalar fatarta, jan bakin da suka shafa mata a leb'enta kalar ja, duk da gashinta gajere sosai haka suka shafe mata shk da mayuka suka mishi gyara mai kyau sannan suka d'ora mata kambu mai kalar ruwan zaiba kuma kamar hasken lu'u lu'u, hakan sai yasa ta fito kamar wata sarauniya tayi kyau kamar ba gobe, bandejin kanta kam wani sabo suka nad'a mata kafin su shiga take masa baya su fito. Ta siririn corridor suka bi da ita, ko da suka kai bakin k'ofar b'angaren na shi suka tsaya, d'aya a cikinsu ce ta bud'e mata k'ofa alamar ta shiga, kallonsu tayi kafin ta tattare rigarta ta shiga takawa a hankali, kamar yar k'auye haka ta shiga k'arewa babban falon kallo, amma abun mamaki duk kyau da had'uwarshi bai kai na falon da waccen garjejen k'aton ya ce falonta ne ba a cewarta fa, tana cikin juyowa ta inda kujerun zama na alfarma kirar Italy suke kawai ta zabura tare da sakin yar k'ara tace "Ahhhhhh!" Sai kuma tayi shiru ta sake tsura musu ido, da d'an hanzari Bukhatir ya k'araso gareta yana fad'ad'a murmushi yace "Kwantar da hankalinki gimbiya." Wani kerere ta shig binshi da kallo tana had'e fuska da kula yatsina ta, k'ofar dake fuskantar ta aka bud'e, Zafreen ce ta shigo ita ma ta shirya sai dai babbanci na nesa ne tsakanin shigar Ayam da ta Zafreen d'in, sauk'akk'an riga ce doguwa kalar fara wacce ta saukar mata har k'asa, gashinta a sake yake da kuma bandeji a kan ta saidai alamu sun nuna ita ma an canza mata wani ne. A wani gadarance Ayam ta d'auke kai daga kallon Zafreen ta kalli Bukhatir dake gefenta ta dafe k'ugu tace "Malam fad'a min me nake yi a nan? Waye kai kuma me yasa ka kawo ni nan? Sannan wannan kayan bana son su a sama min k'ananu." Shi dai da fara'a a fuskarshi ya nuna mata maza da matan dake gefensu duk sun mik'e tsaye yace "Muje ki gaisa da mutanenki tukuna." Lumshe ido tayi mai nuni da ka fara kaini bango kafin ta tunkaresu da tafiyar sauri, tana zuwa gabansu ta tsaya tana kare musu kallo, daga bayanta Bukhatir ya nuna mata wani dattijo yace "Gimbiya Zafeera, wannan shi ne sarkin gida, ma'ana duk masu aikin gidan nan a k'ark'ashin saka idonsa suke." Cikin girmamawa dattijon ya rusuna yana mata wani yare da ba larabci parsi da Bukhatir ke yi ba, amsawa tayi a mutumce a kuma ladabce kamar ba yau suka fara had'uwa ba. D'an kawar da kan ta da zatayi ta kula duk mutanen har da Zafreen da Bukhatir sun zuba mata ido, nuna mata d'ayar yayi yace "Wannan kuma ita ce shugar mata, daga yanzu kuma zata zama mai kula da ke." Ita ma a wani harshen ta gaisheta, ba tare da tayi tunanin komai ba ta amsa mata a mutumce, har yanzu ma kallonta suka ci gaba da yi, Bukhatir kuma da musamman yasa aka samo masa mabanbanta yare dan ya tabbatar da abinda Laika ta fad'a masa na cewa canza yare kawai take sakin baki yayi yana kallonta, haka saida suka gaisa da kowa su kan su ma'aikatan a tsorace suka k'arasa gaisawa da ita, dan bakinta da yanayinta bai nuna koyen yaren tayi ba, kowane amsashi take da k'warewa a harshenta. Kallonsu yayi yace "Zaku iya tafiya zan nemeku." Wani kallo ta watsa masa wanda yana had'a ido da ita yasa shi jin fad'uwar gaba, a wulak'ance tace "Da kasan suna jin yarenka me yasa baka basu izinin yi min ba?" D'auke idonshi yayi daga cikin na ta ya shiga kame-kame yana fad'in "A... A... Am... Dama, ni ma ban sani ba." Sama da k'asa ga kalleshi ta yatsina fuska tace "Mak'aryaci." Da mamaki ya waro ido ya kalleta sai kula ya jinjina kai ya maida kallonshi ga Zafreen yace "Kin shirya ne? Dan. Dreba na jiranki zai mayar dake inda kike so." Da zumud'i Zafreen tace "E, amma ita fa?" Had'e fuska yayi yace "Babu ruwanki da ita, ki je kawai." Gyara tsayuw tayi ta rumgume hannaye tace "Ba zai yiwu ba, na wa mahaifina alk'awarin zan koma tare da ita." Takawa yayi cike da izza ya tsaya gabanta yace "Zafeera ta zo kenan babu komawa, idan zaki je ki je, idan ba zaki je ba sai tare da ita, to ki sani zan sama miki d'aya daga cikin ma'aikata ki aura sai ki zauna a nan da lasisi." Cike da fad'a tace "Kai har ka isa ma, ba zan je ba kuma tare da ita zan bar nan." Girgiza kai yayi yace "Kar ki ce zaki kawo min wasa a nan, a halin da ake ciki yanzu na fara jin rayuwata ta fara d'aukar saiti daga zuwanta yau, na rantse miki da Allahn da nake bautawa ko ubanki ya zo nan ba zai rabani da ita ba." Gyara tsayuwa tayi tace "Lallai kana son tak'aloma kan ka yak'i da dakarun Khazira, ka sani sarkina ba zai barka ba, dan buk'atar da yake wa Zafeera ta take wacce kake mata ta shanye, dan haka ina mai baka shawara da ka gaggauta sakin yarinyar can mu tafi kafin mutuwarka ta riskeka." Da sauri ta k'arasa gabansu cike da masifa ita ma tace" Wai ku tsaya malamai, su waye ku? A kan wa kuke magana? Me kuka shirin aikata min ne da kuke jayayya haka kuma a kai na?" Da lalama Bukhatir ya juyo gareta yana fad'in" Kin ga kwan..." Da k'arfi Zafreen tace" Ba wani hankali da zata kwantar, kinga ke *k'anwata ce*, uwar mu d'aya kuma ubanmu d'aya, iyayenmu nemanki suke kamar zasu yi hauka." A hassale Bukhatir y kalleta yace" Amma ai ke neman kasheta kike, ni kuma kareta nake son yi daga sharrinku." Hannaye ta d'aga musu tace" Ya isa, ya ksa haka." Kallon Bukhatir tayi ido cikin ido ta tsareshi da su tace" Fad'a min, wacece ni? Ni d'in nan wacece?" Janye idonshi yayi daga cikin na ta yana sunkuyar da kai yace" Zafeera, gaskiya ta fad'a, ke yar uwarta ce." D'aga mi shi hannu ta sake yi alamar yayi shiru, dafe kan ta tayi ta nuna kanta tana kallonshi tace" Ka ga da ni da wannan bamu da wata alak'a ta jini, makarantarmu ce kawai d'aya, ina ga fa kuskure kuka yi kuka d'auko ni a zuwan wacce kuke nema." A hankali Zafreen ta tako gabanta ta rik'o sark'ar dake wuyanta ta nuna mata tace" Kinga wannan sark'ar, a duk duniya zaki sameta ga wacce ta kasance mata ce a gurin sarkin Khazira, hakan kamar al'adace da aka gada iyaye da kakanni, wannan dake wuyanki mahaifiyarmu ce ta baki ita." Yanda take kallonsu galala yasa Zafreen fad'in" Ki yarda dani Zafeera, idan kin amince ki biyoni mu je tare, zaki gani da idonki kuma zaki ji daga bakin mahaifiyarmu." Girgiza kai tayi da taji yana mata wani nauyi yana kuma d'aukar zafi sannu sannu tace" Ku taimaka ku had'ani da iyaye na, na rok'eku." Cikin rarrashi Bukhatir yace" Shikenan na ji, yanzu ki kwantar da hankalinki kinji, zan kawo miki su kafin nan ki saki ranki, nan gidanki ne kiyi abinda kike so, kin ji?" Jinjina kai tayi alamar to, Zafreen ta kalla kamar wata bak'uwar hallita a gurinta, wai yar uwarta? To ko dai bugun da aka musu a kai Zafreen ta samu matsalar k'walwa, ko kuma dai garin mahaukata aka kawota. Da sauri ta kalli Bukhatir da ta ji waya na kururuwa a aljihunsa, yana ciro wayar ya duba mai kira ya kallesu ya musu nuni da yana zuwa, d'ora wayar yayi a kunne ya d'anyi nesa da su. Kallon juna suka dinga yi har saida ya dawo kusansu ya kalli Zafreen yace "Tafiyarki ta fasu yau, sai zuwa gobe da safe." Da sauri tace "Saboda me? Ni bana so na kwana a nan, gidanmu zan je ni ma,tare da k'anwata." Ta k'arashe tana kallon Ayam da ita ma ta kalleta da mamaki. Ba alamar wasa yace mata "Saboda zamu karb'i manyan bak'i ne, daga yanzu zuwa lokacin da zasu iso an rufe shiga da fita." Da mamaki ta yatsina fuska tace "Su waye wannan?" Saida ya nufi hanyar fita yace "Sarkin Giobarh." Da kallo suka bishi saida ya fita Ayam ta kalleta tace "K'anwarki?" Dariyar baki da hankali ta mata ta juya ita ma ta bar d'akin duk da kuwa ta ji Zafreen na fad'in "E k'anwata ce ke, kuma nan gaba kad'an zaki san da haka, ki jira ki gani har nan mahaifina zai zo ya d'aukeki." Ganin ta fice bata kulata ba yasa ta jan tsaki ta bita da harara tace "Shegiyar banza, gidan uban wa ta iya yarukan nan?" Sake wurga mata harara tayi ta k'ofar data fita tace "Sai na kasheki zan huta, indai har na kwana a nan to a nan zan kasheki saodai su d'auki gawarki." Buga k'afarta tayi alamar jin haushi ta juya ita ma zuwa inda ta fito tace "Banza." *04:30* Tuni gidan ya kaure da hayaniya sakamakon dirowar bak'i daga masarautar Giobarh, sarki da kan shi tare da d'anshi mai jiran gado, mota takwas ta sauke inda fadawa da hadimai da ma'aikata suka shiga take musu gaba da baya da kuma gefe gefensu, inda suka had'e da mutanen Bukhatir wanda yayi iya k'ok'arin sa duk da bai karb'i sarautar ba, amma dake Ayam na hannunshi ya fara jiyo k'amshinta sai kawai ya tara jama'a shi ma aka musu maraba har zuwa babban falon. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:35 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *14* Akan babban teburin cin abincin mai d'aukar mutane goma sha biyu, Bukhatir ne zaune akan kujerar tsakiya dake iya fuskantar kowa, a tunaninshi sarki Wudar zai zauna a nan, amma sai gani yayi ya ja kujerar kusa da shi ya zauna, Umad kuma ya zauna kan kujerar da ke fuskantar Bukhatir d'in. Haka kawai had'uwarsu ta farko ya ji ya tsani matashin, wani cin magani da yake da wani jiji da kai shi dole ga d'an sarki, hakan sam bai masa ba. Mutane shida ne a wurin gaba har da mataimakin sarki da kuma na hannun daman shi, inda fadawanshi masu tsaronsa suke bayanshi d'an nesa kad'an tsaye, shi ma Bukhatir dattijon nan ne a bayanshi tsaye. Mata biyu ne ke zuba musu had'add'e kuma lafiyayyen abincin da aka girka dan su, sarki Wudar ne ya kalli Bukhatir cikin rad'a dan dama a kusa suke yace "Me zai hana ka gabatar mana da ita?" Wani shak'iyin murmushi Bukhatir yayi yace "Yallab'ai ina fata dai ba ka zo da tunanin zaka tafi da ita bane ko?" Da sauri Wudar ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kanshi, numfashi ya sauke yana tunanin me Bukhatir ke nufi kuma? Ko ya manta da yarjejeniyarsu ne? D'aga kan shi yayi ya kalleshi cikin sassauta murya yace" Ka fad'a min adadin farashinka? Zan biya ko nawa ne." Wata dariya Bukhatir ya tintsere da ita ba tare da sanin yayi ba, ganin kowa ya maida hankali a kan shi har da Umad daya kalleshi cikin jin haushi yasa ya tsagaita, kallon sarkin yayi a cikin rad'a shi ma yace" Yallab'ai, me yasa kayi tunanin tana da farashi a gurina? Ai ni ma na karb'i gayyatarka ne dan na tambayeka farashinka, dan bana so ka d'auka ni ma ci amana ne, ka taimaka min wajen samota kuma na juya maka baya." Irin kallon nan mai saka fad'uwar gaba sarki Wudar ya masa, fuskarsa a tamke yace" Bukhatir kasane zaka dinga fad'a min, idan ba haka ba yayan mahaifinka zai san duk abinda kake shiryawa a kan shi, haka zalika zai samu labarin bayyanar jikarshi a k'asarsa." Wata harara harara Bukhatir ya wurga masa sai kuma ya shiga rarraba ido yana tunanin lallai fa komai nasa zai lalace idan har Emir ya san da batutuwan nan. Iska ya huro tare da jan plate d'in abincin gabanshi ya kalli sarki Wudar yace" Na yarda zaku gana, amma ba zaka tafi da ita ba, daga baya zamuyi magana akan wanda ya dace ta zauna tare da shi." Kafin sarki Wudar yace wani abu Bukhatir ya kalli dattijon dake bayanshi, da ido kawai ya masa alama, amsawa yayi da girmamawa ya nufi wani sashe na daban. Umad dai na zaune yana kallon komai a tsanake yana kuma d'ora komai a kan ma'auni, yasan mahaifinshi na neman Zafeera, amma yasan dan ya d'auki fansa ne a kanta kamar dai shi, amma bai san dalilin da yasa yake zafafawa ba sosai haka, duk da dai yanzun ba wai ya fahimci akan me suke magana ba, amma yana ji a jikinshi batun ba zai wuce na son had'uwarshi da Zafeera ba, tunda har a bincikenshi sunan Bukhatir ma ya fito a cikin masu son samunta kuma su mallaketa, to baya raba d'ayan biyun cewa zasu had'a k'arfi da k'arfe ne dan ganin sun samota sannan su muzgunawa mahaifinta, dalilin da yasa Bukhatir kuma yake son kassara sarki Musail d'in wannan ne kam bai sani ba sai nan gaba. K'wasss! Sautin takalmin k'afarta ya isar musu da sak'on zuwanta farfajiyar, wanda dama yake a k'age da son ganin zab'abb'iya, da ma wanda sam bai da niyyar kallon b'angaren kamar Umad saida suka samu kan su da juya kusan a tare. Take yanayin fuskarshi ya canza daga had'ewar nan zuwa wani sassauk'an murmushin da baisan sanda ya kubto ya taho masa ba, inda zuciyarsa ta shiga masa wani irin sanyayyan duka tana sanar da shi ta iso, jikinsa kuma gaba d'aya wani karsashi had'e da kasala ya ji suna saukar masa, a tausashe ya juyo da kanshi yanda babu wanda ya fahimta, murmushi ya sake yi bayananne tare da shafa sumar kan shi, a hankali a kan labb'anshi ya furta " *Zakanya*." Tun daga k'asa har sama sarki Wudar yake k'are mata kallo, bakinshi bud'e kamar zaka fad'a a guje, kallo d'aya zaka masa kasan tabbas yana cike da farin cikin daya shekara da shekaru bai samu kan sa a ciki ba, wani b'oyayyan murmushi ne ke fita a fuskarshi mai kama da lallausan dariya. Ta b'angaren Bukhatir ma haka yake, duk da shi d'in ya ganta ba kamar sarki da sauran jama'ar ba, amma dai haka ya kafeta da ido har saida ta k'araso dattijon nan ya ja mata kujera ta zauna. Tsarguwa ta fara yi dan kallon da mutanen wurin ke mata tana ji kam a shari'ance ma ya wuce k'a'ida duk da bata da madogara mai kyau, saidai bata nuna hakan ba sakamakon ganin yallab'ai Umad, tsura masa ido tayi tana kallo amma shi kan shi a k'asa, kamar ta k'wala masa kira tace "Yallab'ai." Sai kuma muryar Bukhatir ta katseta sanda yake nunawa sarki Wudar ita yace "Yallab'ai ga Zafeera." Wani mahaukaciya kuma siririyar dariya sarki Wudar ya dinga yi yana kallonta kamar marar gaskiya yana fad'in "Ehehehehe... Hahahahaha... Ehemmm, na gan ta, na gan ta Bukhatir, fiye ma da yanda ake fad'a." Kallon Zafeera Bukhatir yayi ya nuna mata sarki yace "Ma pr茅cieux, ga yallab'ai sarki Wudar, ga kuma d'an sa, wad'annan mak'arrabansa ne sun zo ganinki." Wanda ya nuna yace mata d'an sarkin ta bi da kallo galala, amma har yanzu idon shi na kallon farantin gabanshi, cikin larabcin parsi tace "Dama d'an sarki ne?" Baki wangale sarki yace "E, d'ana ne." D'agowa yayi ya kalli mahaifin na shi, d'an tsakin jin haushi yayi a ranshi yana ayyana kar mahaifinshi la ya zama sakarai a gabanta fa, dan ya ga yanda suke k'arewa da canal Jacob. Juyawa tayi ta kalleshi cikin hatsari suka had'a ido, k'yabta ido tayi sau d'aya sau biyu sau uku, shi kam dan ya fahimci me take fad'a sai ya shiga yin zooming fuskarta yana kallon idon na ta da gashinsu yayi mata wani zar-zar-zar, ganin bai fahimci komai ba sai kawai ya d'auke idonshi ya d'auki cokalin gabanshi. Cikin jin haushi Ayam ma ta d'auki cokalin gabanta duk da babu komai a cikin farantin ta, turo baki tayi a dole ita ta ji haushin ya k'i kulata ta shiga caccakar farantin na ta, kamar sub'utar baki a harshen italien tace "Wai me ya kawoku nan?" Dukansu zuba mata ido sukayi, saidai babu wanda ya fahimci me ta fad'a sai Umad, shi ma yana kallonta da ya ga kowa ita yake kallo sai kawai ya d'auke kan shi, kamar wanda baya son yin maganar a harshen data masa magana shi ma yace "Kar ki nuna musu kin sanni, kiyi harkan gabanki kawai." Wani irin kallo ta masa irin mamakin nan a zuciyarta tace "Kutttt!" A zahiri kuma farantin ta ta dinga kallo da ake zuba mata abinci amma cokalin a hannunta tana t daddaga shi a teburin wanda hakan yasa duk mutanen suke kallonta, ita ma mayar mi shi tayi da fad'in "Ashe kai d'an sarki ne, shi ne ka je makarantarmu a matsayin malami." Shiru yayi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya kalli fuskar Bukhatir kamar irin da shi yake magana yace "Kasancewata d'an sarki matsayi ne da Allah yake son gani na a haka, zamana malami kuma aiki na ne da nake so." Kallonshi tayi tare da dakatar da bubbuga cokalin cikin masifa tace "Ama kuma shi ne baka tab'a fad'a mana ba, kenan zuba ido ne kayi kana jira mu maka rashin kunya ka hukunta mu?" Kallonta yayi saidai kafin yace wani abu tayi saurin fad'in "Ni ba wannan ba, wannan k'aton garjejen basamuden daya kawoni nan ya aje, bana son ganinshi kuma bana son zama a nan, ka yi wani abu a kai yallab'ai Umad, sato ni sukayi." D'an satar kallon Bukhatir yayi da a daidai lokacin ya tsura masa ido, ido cikin ido suka dinga kallon juna da shi kafin Umad yace mata" Ki zama cikin shiri, zan bar nan tare dake." Murmushi tayi ta fara tsakurar abincin, zata kai lomar farko suka had'a ido da Wudar banda murmushi da kallonta ba abinda yake, murmushin yak'e ta masa ta kai lomar bakinta tana taunawa, sautin wasu takalmin suka ji daga bayansu da kuma alamar mai tafiyar ranshi a b'ace yake, dan yanda k'arar ke fita da k'arfi da kuma sauri zai tabbatar maka da haka, Bukhatir da kujerarshi ke fuskantar k'ofar da kuma sauran mutanen Wudar kawai suka kalleta, cike da gatsali da raini ta tsaya tsakanin kujerar Bukhatir da sarki Wudar hannunta d'aya rik'e da rigarshi data sauka k'asa sosai, cikin d'aga murya tace "Wai ni ka fad'a min zaman me na ke a nan? Na je na fita banzayen masu gadin can sun hanani, me kake nufi da ni?" Fadawan dake bayan sarki Wudar ne suka zaburo sukayi kanta d'ayan na fad'in "Murya k'asa yarinya a gaban sarki kike." Juyawa tayi ta wani kalkesu a wulak'ance kuma a gatsine, sake juyawa tayi ta k'arewa mutanen kan teburin kallo, sake juyawa tayi ta kalli fadawan tace "To ai ni nan ban ga wanda ya d'auki kalar kama da bawan gidan mu ba ma bare kuma sarki." A tsawace Bukhatir ya buga tebur d'in ya nuna mata k'ofa yace "Bar nan kafin na lalata miki fuska." Tsaki ta masa ta harareshi sama da k'asa kafin ta juya da k'arfi zata koma, saidai had'ewar da idonta sukayi dana Umad yasa ta tsaya cak da mamaki ta kalleshi, a hankali ta k'arasa gabanshi tana k'ak'aro murmushi a fuska tace" Yallab'ai, kai ne?" Da sauri ta k'arasa ta ja kujerar kusa da shi ga zuba tagumi tana kallonshi bakinta har kunne tace" Amma ya akayi ka zo nan? Kai ma kasan wannan mutumin ne?" Kallonta kawai ya tsaya yi da mamaki bai ce komai ba, murmushi ta kuma saki ta kalli Ayam tace" Yasan dalilin zuwan mu nan ne?" Sai kuma ta kalleshi tace" Yallab'ai, kayi wani abu kai, mutanen nan sato mu sukayi bamu san su ba, ina tsoron kar su siyar da mu fa." Sarki Wudar da baya jin yarensu ne ya kalli Zafreen fuska a murtuke yace" Idan ma kina son d'ana ne to ya fi k'arfinki." Kallonshi Ayam tayi ta tab'e baki ta ture plate d'inta ta juya dan barin wurin, sarki Wudar ma ture plate d'inshi yayi yace" Cin abinci ya k'are." Kallonshi Umad yayi yace" Hakan na nufin zamu tafi kenan?" Sauran ma duk mik'ewa sukayi sai Bukhatir da yace" Ina ganin hakane, na ji dad'in ziyararku." Sarki Wudar ne ya kalli Bukhatir yace" Mu yi magana ko?" Jinjina kai yayi ya nuna masa wata hanyar yace" Muje ta nan." Su biyu suka nufi hanyar duk sauran na kallonsu, saida suka shige ciki su kuma suka nufi hanyar fita, Zafreen da haushi ya gama kamata ganin bai kulata yasa ta mik'ewa tsaye tace" Yallab'ai." Kallonta yayi a wulak'ance cikin jin haushin abinda ta fad'a gaba d'aya a kan su har da mahaifinshi, yanda ya zuba mata ido yasa ta fad'in" Wai me yasa kake shareni haka? Na rok'eka kayi wani abu da zan bar nan." Cikin abokan tafiyarsu ne ya nunawa Umad hanya yace" Yarima mu je." Zaro ido tayi ta kalli Umad da kyau tace" Yallab'ai, dama kai d'an sarki ne?" Girgiza kan shi yayi ya rab'ata ya wuce suka fita, amma abun mamaki sai ta bishi a baya tana fad'in" Yallab'ai kar ka barmu a nan, ban yarda da mutumin nan ba, kar ya cutar da mu." Bakin motocinsu suka tsaya Umad hannunshi rik'e da waya yana dannawa. Yanda ta tsaya masa k'ik'am yasa ya d'ago kai ya kalketa, gyara tsayuwarshi yayi ya soka wayar aljihu, nuna mata hanyar da suka fito yayi yace "Muje muyi magana." "Tom." Ta fad'a da fara'a a fuskarta, har zasu shiga falon da suka fito sai kuma ya kalleta yace "Ina ne suka ajiye ku?" Turo baki tayi tace "Ni ga b'angaren da yasa aka aje ni can." Ta nuna b'angaren dake fuskantar wannan d'in, sai kuma ta nuna b'angaren dake manne da wannan wanda yafi kowane girma tace "Amma ita anan suka ajeta." Gyara tsayuwarshi yayi ya shiga kallon ko ina na gidan, mai gadi a bakin k'ofa, wani dattijo dake bawa flowers ruwa saboda yamma tayi sosai, sai masu tsaron k'ofar b'angaren da Ayam d'in take su biyu, sai kuwa mutanen da suka zo tare da su, kallon Zafreen yayi yace "Ki je ki canza shigarki, zan d'aukeki a nan." Da sauri ta jinjina kai cikin farin ciki ta nufi hanyar b'angaren da take, tun kafin ta shige ya k'araso kusan abokan tafiyarsu ya mik'awa d'aya a cikin dreban hannu yace "Makullin mota." Mik'a masa yayi ya karb'a sannan ya kalli dreban yace "Shiga ciki." Kamar yanda ya ce haka yayi ya shiga bayan motar ya zauna, shi ma shiga yayi bayan ya zauna ya kalli dreban, fuska a had'z alamar bayar da umarni yace "Ban rigarka." Da mamaki ya kalleshi har saida yayi sub'utar baki yace "Rigata kuma yallab'ai?" "E, ko ba zaka bayar ba?" Da sauri ya girgiza kai ya shiga b'alle rigar dake nuna aikinsa ya mik'a masa, karb'a yayi ya sakata a cikin rigarshi ya daidaita mata zama, fita yayi a motar sai kuma ya zura hannu ya ciro hular dreban dake kan shi. Da sauri ya koma falon da suka fito, saida ya waiwaya inda ya ga mahaifinshi sun nufa, ganin babu kowa yasa shi yin sassarfa ya bud'e k'ofar da aka shigo da ita d'azu, ya d'auka ko wani d'aki ne amma sai ya ga corridor ne, babu kowa a k'ofar shiga dan haka ya shige ciki, ya d'auka yanda babu kowa a k'ofar haka ma a ciki, amma sai ya samu d'aya daga cikin matan nan zaune tana kallo, a zahiri kallon ba wai wani dad'i yake mata ba, dan da alamar gyangyad'i ma take, amma kuma aikin da aka sata na kula da Ayam yasa dole ta kasance a ankare. Da sauri ta mik'e tsaye tace "Yallab'ai ya dai? Kana buk'atar wani abu ne?" Dakewa yayi ba alamar rashin gaskiya tare da shi yace "E, ban d'aki." A ladabce tace "Yallab'ai ban d'akik bak'i ta can wajen ne." Ta fad'a tana nuna masa k'ofa alamar sai ya fita, fuska a gimtse yace "Ban da lokacin da zan koma baya, ke baki san ujila bane." "To to shikenan, ga hanyar can yallab'ai." Ta nuna masa d'akin tsakiya, hanya ya kama zai shiga sai kuma cikin ladabi tace "Yallab'ai." A gadarance ya juyo gareta, sake tausasa murya tayi tace "Ka bi sannu, domin madame na ciki, tana da masifa sosai, ka taimake ni kar kayi abinda zata hassala ta ja min uk'uba." Da ido ya mata alaar ba komai sannan ya sa kai d'akin, kan shi tsaye ya tura k'ofar, amma d'akin duhu kuma babu motsi, gefenshi ya kalla sai kuma yayi sa'a da makunnin, kunnawa yayi amma bai ga kowa ba a iya dubawarshi, k'arasawa yayi gaban ban d'akin ya d'an k'wank'wasa saboda jin k'arar ruwa, babu wanda ya amsa shi sai ya gyara tsayuwa ya d'an jira, ganin fa bai da lokacin jira yasa shi sake k'wank'wasa murya a tausashe yace "Jiranki fa na ke." Shiru ya ji babu wanda ya amsa mi shi, haushi ne yasa shi jan tsaki ya tura k'ofar yana zuba idonshi ta ko ina, sam babu alamar mutum a ciki, dafe goshi yayi ya furta "Ina kuma take?" Rufe ban d'akin yayi ya juyo ya fito matar nan na mi shi barka da fitowa, bai kulata ba dan hankalinshi ba kan ta yake ba ya fice, wajen motocinsu ha nufa yana zuwa kuma sarki Wudar sun fito shi da Bukhatir daidai kuma da dawowar Zafreen ta saka kayanta wanda ta zo da su. Fuska a had'e Umad ya bud'a motar ya shiga tare da mik'awa dreban daya kasa fita saboda singlet ce ta rage mi shi makulli, turus Zafreen ta tsaya tana kallonsu dan gaba d'aya kuzari ta rasa ta tunkararshi bare tasan a wacce a ke ciki. Tana tsaye tana kallo suka gama sallamarsu duk suka shiga motocin suka d'auki hanyar barin gidan, Umad da ranshi ya gama b'aci tuni ya yanke shawarar zai raka mahaifinshi zuwa filin jirgi, daga nan zai san yanda zaiyi ya sulale musu ya dawo, dan yayi alk'awarin sai ya koma tare da ita, ba zai barta nan ba ko da zai shekara d'ari ne ko kuma hakan na nufin rasa rayuwarsa. Sarki Wudar ma ya tafi amma fa yayi niyyar sai ya had'awa Bukhatir wata mak'ark'ashiyar da zata dawo da Ayam hannunshi, dan ba zai yarda ya rasata ba bayan shekarun daya kwashe na jiranta. Suna isa filin jirgin dama an basu izinin tashi saboda an san da zuwansu, har farfajiyar jiragen aka bawa motocin izinin k'arasawa saboda sarki Wudar, duk firfita sukayi suka rufe motocin, sun fara takawa kenan sun bada baya suka ji an d'an bubbuga boot, Umad da dreba da sarki ne suka juyo, ganin ba komai sai suka juya suka ci gaba da tafiya, bubbugawa suka sake ji da k'arfi har da tagomashin ihu ana kiran "Kaiiiii! Taimako?" Umad na d'aukar muryar ya dawo da gudu yayi azamar d'aga boot d'in, da wani irin k'arfi Ayam ta tashi zaune ta sauke kakk'arfan numfashi, kallonshi tayi idonta duk sun rikid'a tace "Da na mutu fa, kai akwai takura a cikin nan." Tattare rigar tayi ta zuro k'afafunta ta diro daga motar, Umad kam a bad'ini farin ciki ne ya kama shi, to amma mamakin yanda akayi ta shigo nan sai ya hana shi shak'at, da sauri sarki da sauran mutane suka k'araso, sarki Wudar da farin ciki a fuskarshi yace "Zafeera, ke ce dama? Ya akayi kika zo nan?" Murmushi ta sakar masa ta tafa hannayenta tace "... *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:36 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *15* Murmushi ta sakar masa ta tafa hannayenta tace "Ni ce, ai guduwa na yi, na rok'eku ku tafi da ni, idan na bar nan daga can zan koma garina ni ma, kai tsaye ma gidanmu zan wuce dan mutanen can sun tsorata ni da haukansu." Da fara'a sarki Wudar ya amsa mata da "Haba ai ba sai kin rok'emu ba, mu da masarautarmu ai duk mallakinki ne." Nuna mata hanya yayi yace "Muje ko?" Kallon wani bafaden shi yayi cikin rad'a yace "Ka tabbatar bata samu matsalar hawa jirgi ba." Jinjina kai yayi ya juya zuwa gurin masu ruwa da tsakin na kampanin, su kuma tuni suka shiga jirgin har da Ayam d'in wacce har zata zauna kusa da Umad sarki Wudar ya nuna mata kusanshi yace "Zauna nan." Cike da girmamawa ta zauna kamar yanda ya ce dan ita a uba take kallonshi tunda mahaifin malaminta ne, sun d'auki a k'alla minti sha biyar kafin jirginsu ya d'aga zuwa k'asar Giobarh. Kamar wacce ke son fakar idon mutane tayi sata haka Ayam ke son fakar idon sarki ta ma Umad magana, bakinta cike yake da kalamai inda zuciyarta ke tumbatse da tambayoyi kala kala, shi kan shi Umad a k'alla zata jefa masa tambayar data bawa guda biyar baya, dan haka ta matsu, ta k'agu ko jirgin nan ya sauka su keb'e ta fara bayani. Har ga Allah sai ta fara bashi dariya saboda yanda ta tsaresa da ido bakinta kam mm-mm-mm kawai yake, hnnayenta dake kan hannun kujerar sai bubbugasu take tana d'an jijjiga k'afafunta, daya kalleta yake d'auke kan shi dan ya sani ne da magana a bakin nan da take ta turo masa. Adadin awoyin da suka d'auka gurin tafiya yanzu ma suka b'ata illa sab'anin sakanni kawai, Ayam ta ga ikon Allah ganin idonta sanda aka shiga yi musu tarba ta musamman ana murnar dawowarsu ka d'auka shekara sukayi basa nan. Ita yanda ta ga ana t sunkuyawa Umad shi ya fi bata mamaki, suna shiga katafaren falon ta kuma bud'a idonta tana lumshe su a hankali, saida suka kai tsakiyarsa suka tsaya, a k'alla hadimai maza da mata sama da goma ne suka ding rusunawa suna gaishesu, babban abun mamakin yand sarki Wudar ke ta nunata yana fad'in Zafeera ce, kai ita wannan suna ma k'ona mata rai yake, wani wai Zafeera a ganinta fa. Wani dattijuwa ya nuna mata yace "Wannan ce zata zama mai kula dake daga yanzu, duk abinda kike da buk'ata kai tsaye ki fad'a mata zata sanar min." Da mamaki Ayam ta d'aga labb'a tace "Amma kum..." Nuna mata wata kyakyawar matashiya yayi wacce shigarta ta banbanta data sauran da alama itama babba ce a gidan yace "Wannan Joyran kenan, k'anwar matata ce, sakamakon rashin lafiyar dake damun uwar d'akina wacce muka rasa gabanta yasa yanzun alhakin kula da cikin gidan nan yake wuyanta." Kallon fuskarta Ayam ta sake yi, a kallon nan d'aya tak ta ji sam matar bata kwanta mata a rai ba, uwa uba kwalliyar dake fuskarta ta wayayyi, kayanta kua duk da na sarauta ne manya amma rigar ta fito da maman ta sosai. Joyran ma haka ta k'ura mata ido cike da zababbiyar tsana da kishi had'e da takaici da jin kamar ta shak'o wuyanta, tsabar ta rasa jurar halin da take ciki yasa ta gagara b'oyewa har saida tabi Ayam da mugun kallo sannan ta d'auke kan ta ta mayar kan sarki Wudar, wani fitinannen kallo ta masa ta shiga masa signa da ido alamar tana son magana da shi ya kuma biyota. Da kai ya fara amsa mata ta hanyar gyad'ashi kad'an yanda babu wanda ya gane, sai kuma ya lumshe ido alamar tabbatarwa, tana samun amsarta ta juya a fusace ta bar falon zuwa b'angaren daya zama na ta yanzun. Sarki Wudar ne ya kalli dattijuwar nan yace "Ki rakata d'akin kusa da na sarauniyata, ki mata duk abinda ta buk'ata." Sunkuyawa tayi tace "To shugabana." Matsawa tayi kusa da Ayam ta nuna lata hanyar da zasu bi tace "Muje ranki shi dad'e." Satar kallon Umad tayi da gaba d'aya yayi kamar baya wurin yake ta danna wayarshi, kallon sarki tayi a shagwab'e ta nuna Umad da yatsa tace "Yallab'ai, ka had'a ni da wannan mana ya rakani, na ga ya na jin yaren da na iya." Dakatawa yayi daga danna wayar amma bai kalleta ba, sarki Wudar kam jiki na b'ari na ta fad'i buk'atar ta ya nuna Umad yace "Yarima na, ka je sai ka rakata ka ji ko, idan da wani abu da take buk'ata sai ka fad'awa jakadiyarta." Kallon fuskar mahaifinshi yayi irin kallon me kake nufi kuma? Ni ma fa masu hidima ne da ni, ha kuma zan zauna yi ma wata rakiya. Maida kallonshi yayi gareta, har yanzu dai abu d'aya yake gani tareda ita wato zance, sake kallon sarkin yayi ya jinjina kai alamar to, a wani gadarance cikin takon sanyi ya shiga takawa kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki, haka suka shiga taka matakalar har suka haye sama yana gaba tana baya, d'aki na farko suka wuce haka ma na biyu inda mahaifiyarshi take, na uku ya bud'e ya kauce a hanya alamar ta shige. Hannu biyu ta sa ta tura k'ugunshi zuwa cikin d'akin, kamar zai fad'i haka yayi yana kallonta da mamaki, shiga tayi ta ja k'ofar ta rufe da sauri ta k'arasa gabanshi, takalmin k'afarta ta cire da hannunta masu tsini sannan ta dafe k'ugu suna ci gaba da kallon juna tace "Uhum! Tel me, me yake faruwa?" Wani shashantar da zancen yayi ya mayar da wayarshi aljihu, juyawa yayi ya k'arasa gaban gadon dake lafiye da shinfid'a ya zauna, kallonta yayi yace "Ban gane ba?" Da sauri ta matsa gabanshi ta zauna k'asa ta tank'washe k'afafu ta rik'e k'afarshi d'aya tana ta mitsikawa tace "Ka ga na fa gane ka, tambayoyi na a kan ka masu yawa ne, yanzu ka fara amsa min wannan?" Jinjina kai yayi yana siririn murmushi yace "Zana duka tambayoyin, zan amsa miki su d'aya bayan d'aya." Sakin k'afarshi tayi ta dinga nuni da yatsunta tana lissafi tace "Na d'aya... Ba kayi mamakin ganina a gidan nan ba, shiyasa ban ji ka tambaye ni me kike yi a nan ba ko me ya kawoki nan? Na biyu kai ma me ya kai ku can a wannan lokacin? Shi mutumin nan waye shi? Me yake nema a gareni daya saceni? Sannan me yasa ka ce kar na nuna musu na san ka." Gyara zamanshi yayi ya sauke numfashi yana kallon fuskarta yace" Me yasa kika tambaye ni duka wannan? Me yasa shi baki tambaye sa ?" Yatsina fuska tayi tace" To ai na tambaye shi amma shi da yarinyar nan suka dinga fad'a min wasu maganganu na daban." Kafeta yayi da ido yace" Me suka fad'a miki?" Cikin turo baki tace" Wai ni yar uwarta wannan ita mai shegen girman kan ce, wai k'anwarta." Mik'ewa yayi tsaye ya d'an shiga takawa d'aya biyu sannan ya juyo ya kalleta ita ma ta juya ta kalleshi yace" Gaskiya suka fad'a miki, yayarki ce." Zunbur ta mik'e tsaye tace" Me? Kamar ya? Ka kuwa san me kake fad'a?" Girgiza kai tayi tace" Ta ya ya?" Kallonta yayi cike da tausayin yanayin da zata samu kan ta yace "Ki samu kiyi wanka ki ci wani abu sai ki huta, zuwa dare zamuyi magana." Matsawa tayi kusanshi ta girgiza kai tace "Ba zan iya ba yallab'ai, ka daure ka fad'a min ko na samu sassauci, ina so na san dalilin da yasa aka kawoni nan, kuma ina so na ga iyayena." Tsare fuskarta yayi da ido yace "Ayam." Zuba masa ido tayi ita ma tace "Na'am." A sanyaye yace "Kiyi abinda na ce, bana so idon mutane ya dawo kan mu yanzu." Dantse leb'enta tayi da hak'ora dan yanda ya mata magana yanzun ba zata iya musawa ba, sunkuyar da kai tayi dan gabanta fad'uwa yake, tunaninta bai wuce son sanin wane irin garari ne ke neman tunkaro rayuwarta haka? Me ye b'oye a cikin rayuwarta haka da ake neman bankad'o mata shi yanzu? Ko kuma dai sab'ani aka samu wata ake nema ba ita ba? Rashin sanin ko d'aya daga cikin amsoshin nan yasa ta jin k'walla taf a cikin idonta. Lumshe ido Umad yayi ya sake bud'ewa a kan ta, dan ba komai ya zo masa ba sai tunanin ta yanda zai fara fad'a mata wacece ita, da kuma alak'arsu ta yanzun, a hankali ya tako gabanta ya saka yatsa d'aya ya tallabo hab'arta, suna had'a ido hawayen suka gangaro kan kumatunta har saida suka sauka kan yatsarshi. Cike da rashin jin dad'i yace "Ohh! Haba dai zakanya, kuka kuma? Kiyi hak'uri kinji, na miki alk'awarin fad'a miki komai anjima, yanzu babu lokaci ne, ki daina kukan nan bana so." Kamar k'ara zugata ne yake sai kawai ta fashe da kukan da ita kan ta a rayuwarta bata tab'a irinsa ba idan ka cire na farin ciki da tayi sanda gwamnatin Khazira ta d'auki nauyin karatunta a sanda iyayenta suka nemi gazawa, ba tare da sanin me tayi ba, cike da son samun wanda zai rarrasheta, cike da kwad'ayin a lallab'ata ta fad'a k'irjinshi tana ci gaba da kukan. Gam gam ya rintse idonshi sakamakon irin jijjigar da jikinshi ya d'auka, ya san ba da wata manufa ko niyya tayi ba face hakan su ba komai bane, saidai shi yanzu yana da ak'ida, yana da madogara da kuma k'akk'arfar shari'ar dake saitashi ga daidai da barin daidai, sa'a d'aya ita ce akwai igiyarshi a kan ta, amma dake abun sabo ne gareshi sai ya gagara komai, jinta yake har cikin b'argon jikinshi da jininshi, jin ta yake can k'asan k'asan zuciyarshi kamar tare aka haifesu, sai yake tuhumar ko dai jikinta ne ke da wannan tasirin. Jin bata samu abinda take nema ba sai kawai ta jaye jikinta daga na shi cike da kunya kanta sadde ta juya mas baya, bakin gadon ta zauna tana share fuskarta ta k'i d'aga kai bare ta kalleshi. Shi kan shi sai yaji wata kunya ta kama shi daya kasa d'an daddab'a bayanta ko ya ya dan ta ji sanyi, a kunyace ya juya shi ma ya fice a d'akin. Tana ganin ya fita ta fad'a kan gadon ta sake rushewa da wani kukan tana sake fad'in "Wai me yake shirin faruwa ne da ni?" Umad na fita kai tsaye b'angaren Joyran ya nufa inda ya ga mahaifinsa yayi, bai samu kowa a b'angaren ba haka ma a falon, tsaye yayi a tsakiyar falon yana dubawa, a ranshi ya tambayi kan shi "Ina kuma suka nufa?" Hannu d'aya yasa ya shafi sumarshi ya d'aga kafad'a alamar ohon nan sannan ya juya zai fita, ya fara takawa kenan ya ji sautin Joyran ta kwamtsa k'ara da "Ahhhhh." Dakatawa yayi ya juya ya kalli k'ofar da ya ji sautin, da d'an sauri ya fara takawa dan ya ga ko lafiya, sai kuma ganin mahaifinshi yayi ya fito daga d'akin Joyran a bayanshi ta rik'e babbar rigarshi tana share hawaye. Wani irin mummunan bak'on yanayi ne ya ziyarceshi sanadiyar abinda zuciyarsa ta hasko masa lokaci d'aya, gagara komai yayi sai zuba musu ido suna ta kame-kame, daga bisani kuma sai mahaifinshi ya juya gareta a hassale ya fincike rigarshi ya nunata da yatsa yace "Na gama magana Joy, ko kina so ko ba kya so yanda na fad'a haka za'a yi, dan ba zan yarda ki zubar min mutumci ba, kowa laifina zai gani a ce da saka hannu na a faruwar komai." Juyowa yayi dan fita har ya zo daf da Umad zai rab'ashi ya wuce, da kallo Umad ya bishi yace" Sarki na, meyake faruwa ne?" Wani huci ya dinga saukewa yana hararen Joyran data k'araso garesu, cikin shashek'ar kuka tace" Umad, mahai..." Da sauri ya katseta da fad'in" Ciki ne da ita, ni kuma ba zan yarda wannan labarin ya fito ba." Da matsanancin mamaki ya kalli sarki yace" Ciki?" Kallon Joyran yayi data shiga k'yabta ido, a razane yace" Ta ya ya? Goggo wa ye ya miki ciki kuma ba..." Da sauri sarki Wudar yace" Waziri ne, dama soyayya suke amma rashin lafiyar mahaifiyarka ta sa ta k'i aminta da maganar auren." Wani iska Umad ya huro daga bakinshi ya dafe goshi, shiru kamar ba zai ce komai ba, ya d'an jima haka suma kuma jiran abinda zai fad'a suke, can ya d'ago ya kalleta yace" Amma gwoggo m yasa zaki yarda da haka kamar wata k'aramar yarinya, yanzu gashi ya kike so muyi?" Sarki Wudar ne yace" Abinda nake fad'a mata kenan, na ce a zubar ta dage ita ba za'a zubar ba." Zaro ido yayi ya kalli mahaifinshi yace" Sarkina zubarwa kuma? Gaskiya ni ma ban goyi da bayan haka ba, kar a zubar mahaifina." A d'an hassale yace" To yanzu ya kuke so a yi? Ba fa zan yarda a haifa min shegen nan ba." Da wani kallo Joyran ta d'aga kai ta kalleshi, da k'yar ta had'iye abinda ya tokare mata ta sunkuyar da kai, a nutse Umad ya kalli mahaifin na sa yace" Abba na ka je kawai, zamuyi magana da ita, kar ka damu da abinda mutane zasu fad'a, zan ji da komai." Kallon Joyran sarki yayi irin kallon garhad'i kafin ya juya a hassale ya fita, ajiyar zuciya Umad ya sauke ya kalli agogon hannunshi, kallonta yayi da sauri yace" Goggo zan je amma zan dawo, ki kwantar da hankalinki kinji." Jinjina kai tayi alamar to, da sauri ya juya ya fita dan sallolin dake kan shi yae san saukewa wanda suka riskeshi a hanya. *12:36* daga d'akin mahaifiyarshi cikin sand'a ya shigo nan ba tare da ya bari kowa ya gan shi ba, a hankali ya bud'a k'ofar ya shiga ya mayar ya rufe, yana juyawa das ya sameta zaune tsakiyar gadon, fad'uwa gabanshi yayi dan yanda ta zubawa k'ofar ido da kuma yanda take zaune ya nuna fa tun da ya fita ya barta haka take, a hankali ya k'araso yana kallon fuskarta da idonta da sukayi jajir suka d'an kumbura, jiki a mace ya zaune gefenta yana ci gaba da kallonta ita ma kuma haka. Cikin tattausan murya yace "Me yasa da aka kawo miki abinci kika kori mai aikin?" "Saboda ba shi nake da buk'ata ba." Kallonta yayi yace "Me kike da buk'ata yanzu?" D'auke kai tayi daga gareshi tace "Iyaye na, ina so na gansu, ka mayar dani wajensu ni har karatun ma na fasa." Girgiza kai yayi yana murmushi ya jawo wayarsa a gaban aljijunshi, tana kallo ya dinga danna wasu lambaobi, ko da ya danna ok ya mik'o mata wayar yace "Kiyi magana da su, hakan zai sa hankalinki ya kwanta." Da sauri ta karb'i wayar ta d'ora a kunne jin tana k'ara, ana d'auka cikin muryar kuka da sangarta tace "Hello!" Cikin zumud'i da karsashi Habbee ta amsa da "Gimbiyata, gimbiya kina lafiya?" Mik'ewa tayi tsaye tace "Mah ban da lafiya, gaba d'aya bana jin dad'i, so nake na ganku." Cikin ladabi Habbeetace "Kiyi hak'uri kinji gimbiya, zamu had'u nan kusa, ki kwantar da hankali ki saki jikinki da mutumin nan, mutumin kirki ne, na tabbata zai kula dake yanda ya kamata." Juyowa tayi ta kalli Umad sannan tace "Mah, ni ban yarda da kowa ba, maganar gaskiya ma a tsorace nake, wasu abubuwa ke ta faruwa a nan kuma babu wanda yake min bayanin komai." Daga b'angaren Habbee ta numfasa tace "... *Kuyi hak'uri da wannan yan uwa, akwai gobe Insha'Allah* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:36 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *16* Daga b'angaren Habbee ta numfasa tace "Gimbiyata, ki gafarce mu, tabbas kan ki zai d'aure idan kika ji b'oyayyan sirrin dake tattare da ke, watak'ila ma ki kasa yarda damu, amma dai gaskiya ce wacce kowa ya san ta ban da ke kawai, fatana kawai idan kinji gaskiyar nan kar mu zaba ababen zarginki bare ki hukunta mu." Rud'un data shiga ne yasa sai ta ji kamar bata fahimtar, sai kuma tayi k'arfin halin saurin fad'in" Dakata Mah, wai ke ma ya kike neman kin d'aure min kai ne ? So kike ki tabbatar min akwai alamar gaskiya a zantuttukan mutanen nan kenan?" Numfashi ta sauke har saida ta ji sautinshi a kunnenta kafin tace" Hakane ranki shi dad'e." K'ank'ance idonta tayi tana karkad'a yatsanta tace" Kenan gaske da yarinyar nan tace ni yar uwar ta ce? Kuma mahaifinmu shi ne..." Da k'arfi tace" Kai... Ina ba zai yiwu ba, kuna yanzu Mah?" Saida Habbee ta kalli lafiyayyen d'aki da suke sannan tace" Wani waje ne mai sirri ne, ya ce kar mu fad'a saboda tsaronmu na wuyansa." A harzuk'e tace" Ina kuke mah? Ina son ganinku yanzu." A ladabce Habbee tace" Kar ki damu gimbiyata, zamu had'u nan kusa." D'auke wayar tayi a kunnenta ta mik'a masa tarz da fad'in" Ina son ganinsu yanzu, ya za'ayi?" Mik'ewa yayi tsaye yana huro iska ya kalli fuskarta, saida ya mayar da wayar aljihunsa a nutse yace" Ki gane Ayam, rayuwarki na cikin gagarumin had'arin da ubangiji ne kad'ai yasan iyakarsa, ba wai wani banza bane ke neman rayuwarki, masarautu ne suke wawarki, yayin da wasu daga gefe ma suka nemanki ruwan a jallo, dayawansu a shirye suke da su biya bilyoyin kud'i dominki, wasu alkairi ne a zuk'atansua game da ke, wasu kuma akasin haka, na d'auki alhakin kula da ke ne dan na ga na hana masu nemanki cin nasara a kan ki, ki bani dama ki kuma kwantar da hankalinki, hakan zai bani damar ceto rayuwarki." A sanyaye kuma a ladabce cikin sigar tausayi tace" Wane irin had'ari ne na ke ciki haka?" Kai tsaye yace mata" Had'ari ne da ya kai matakin kisa, kamar yanda na fad'a miki kowa da manufar sa ta son samunki, wasu na nemanki ne kawai dan su kasheki." Tsoro k'arara ya bayyana a tare da ita ta zazzaro ido ta ji kayan cikinta na neman yamutsawa, ckkin muryar d'ar-d'ar tace" Me na aikata musu haka da suke son kashe ni?" Da hannu ya mata alamar ta zauna kan gadon, zaunawa tayi tana rarraba ido dan tsorl ya gama kamata, a cikin aljihunsa ya ciro takarda, zaune yayi kusanta ya warware takardar ya mik'a mata yace" Karanta." Karb'a tayi ta fara karanta takardar dake nuni a cikin littafi aka cirota ko kuma an buga irinta ne, ba wani dogon bayani bane a takardar face zanannun zanen da aka tsara kuma aka wassafasu a cikin tsari ta hanyar fad'in _" A wace shekara ce? A wane wata? Wace rana ce wannan? Babu wanda zai sani a cikinmu, saidai alamun bincikenan malaman babbar fadar k'asar Texanda dake birnin Khazira ya tabbatar da za ta zo, za'a haifeta ne kawai dan zuwa da sabon tsari sannan ta wanzar da adalci, zuwanta shi zai kawo k'arshen duk wani azzalumi ko da sarkin dake mulki ne, zatayi mulki na ban mamaki da ba'a tab'a kwatanta irinshi a k'asar ba, zata kafa tarihi da dubbanin shekaru zasu shud'e ana magana a kai, tambayar a nan ita ce, *talakawan gari ne zasu haifo wannan biwar? Ko kuma cikin msu kud'i ne da iko ? Ko kuma dai wannan lu'u lu'u zata fito ne daga masarautar khazira*?"_ Da mamaki ta kalleshi dan abun bai wani d'ad'ata a k'asa ba tace" Me wannan ke nufi? Jaridar yaushe ce? Ko kuma labarin film ne, kana so na fito jarumar?" Wani murmushi ya saki dan sosai ta bashi dariya, gyara zamanshi yayi yace"Kin fahimci me labarin ke magana a kai?" Jinjina kai tayi ta yatsina fuska tace" Kusan haka." Shi ma jinjina kan yayi yace" Ayam wannan rubutun wani babban mutum ne yayi shi, wannan mutumin shi ma yana da baiwa irin ta wannan da akayi magana za'a haifa, sanadin baiwar da Allah ya masa gaba d'aya masarautar khazira aka shiga girmamashi, sanda ya sanar da abinda zai faru gaba ba kowa ya yarda ba, saidai kuma an zuba ido ana jiran tsammanin a ga ta inda wannan zab'abb'iyar zata sake fitowa." Gyara zama ya sake yi ya sauke numfashi yace" Shekara ta dubu biyu daidai wata na hud'u sarauniyar khazira ta samu ciki, tun samun cikin na ta sai wasu alamomi suka dinga bayyana mata a mafarkinta, bayan ta sanar da babban malamin fadar k'asar wanda yake jika ne ga waccen zab'abb'en, sai ya sanar da ita ai tana d'auke da cikin wannan 'yar baiwar ce, sai gashi kam bayan wata shida ta haifi yarta mace wacce aka lak'abawa sunan *Zafeera* tun kafin ma a haifeta, wanda Zafeera yake nufin haske marar yankewa, a wajen wasu haihuwarta zai kawo k'arshen matsaloli da dama musamman na mulkin zalinci da sarki ke yi a wannan lokacin, amma a wajen wasu bayhanarta sharri ne da kusantowar rugujewarsu, hakan yasa a daren da aka haifeta, tun bata bud'i ido ta kalli mahaifiyarta ba sai aka nemeta aka rasa." Cike da jimami da rashin jin dad'i Ayam tace" Ayyah, to amma ya mahaifiyarta tayi? Gaskiya akwai tashin hankali." Siririn murmushi yayi yace "Ba kamar yanda kikayi hasashe bane." Gyara zama tayi tace "Ban gane ba?" Kallon fuskarta yayi yace "Mahaifiyar da kan ta ne ta b'atar da 'yarta ta hanyar damk'a amanarta ga amintacciyar jakadiyarta da kuma mijinta." Waro ido tayi tace "Toh? Amma gaskiya tayi k'ok'ari, kuma hakan ya k'ara tabbatar min da soyayyar uwa daban take." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa sai kuma yayi shiru, ita ma d'an shiru tayi na dak'ik'u sai kuma ta kalleshi tace "To amma mahaifinta fa? Ban ji ka ambace shi ba." Ajiyar zuciya ya sauke ya tsura mata ido yace "Ba da sanin mahaifin yarinyar ta bada ita ba." "Me ya sa to?" Ta tambaya tana tsareshi da ido, mik'ewa yayi tsaye ya juyo ya fuskanceta yace "Akwai wani al'amari ne a tare da shi mahaifin na ta, amma yanzu ba zan sanar da ke ba kai tsaye." Mik'ewa tayi ita ma tace "Me yasa to?" D'auke idon shi yayi a cikin na ta yace "Ki tambayi wani abun daban ba wannan ba, lokaci ne zai fahimtar dake waye shi d'in." Girgiza kai tayi ta gyara tsayuwa tace "To amma me yasa ka bani wannan labarin? Kana da wata alak'a ne da masarautar Khazira ?" Kallonta yayi sosai cikin tattausan murya yace "Bana da wata alak'a da ita, ai kin gani ni ga masarautar mu nan, amma fa ke kina da alak'a da wannan masarautar." Ya fad'a yana nunata da yatsa, zaro ido tayi tsabar mamaki sai kuma ta k'ank'ance su tana kallonshi kamar bata gane me yace ba, a hankalce ta shiga d'ora duka kalamanshi a mizani kafin daga bisani ta kalleshi tace" Wace irin alak'a? Na rok'eka Umad kar ka ce min labarin daka bani ina da nasaba da shi." Hannayenshi biyu ya zuba cikin aljijun rigarshi ta sanyi bak'a mai hula sannan ya kalleta yana sauke numfashi, jinjina mata kai yayi sosai sannan ya d'ora da fad'in" Tabbas, labarin dana baki ta ko ina kina da nasaba da shi, Ayam ke ce wannan yarinyar baiwar, ke ce lu'u lu'un Khazira, Ayam ke ce *Zafeera*." Zuba masa ido tayi, jiri ne ta ji ya fara d'ibarta, da d'an sauri ta shiga sauke numfashi tana girgiza kai tana so tayi magana, saidai tashin hankali da halin ba zatar data shiga ya fi knarfin d'aukar hankalinta, kafin ta ankara jirin nan ya kwasheta ya zubar a k'asa, dan dama tana tattare da matsananciyar yunwa ga baccin data kasa samu tayi. Da azama ya sunkuya yana girgiza ta da kiran sunanta, d'ora yatsanshi yayi daidai hudar hancinta ya saurari sautin fitar numfashinta, tabbatarwa da yayi tana numfashi yasa shi saurin d'aukarta cak ya shinfid'e kan gadon, zaune yayi daf da ita yana kallon fuskarta cike da tausayinta, hannunta ya kama ya dinga shafa tafin hannunta yana murzawa da sauri sauri, a hankali kam sai ta fara d'an motsa idonta amma kuma bata bud'esu ba. Sunkuyar da kan shi yayi kamar zai sumbaceta ya kira sunanta "Ayam." Jujjuya kan ta ta fara yi tana yatsina fuska tace "Na'am, Mahh... Mah." Sakin tafin hannunta yayi ya shiga murza tafin k'afarta, sannu sannu ta fara bud'e ido har ta bud'esu tas a kan rufin d'akin, da sauri kuma sai ta kalleshi suna had'a ido ta yunk'ura zata tashi, luuuuuu da ta ji tayi d'akin ya juya mata yasa ta komawa ta kwanta, kamar zata fashe da kuka tace "Yallab'ai kira min iyaye na, ina so 'a gansu yanzu, na rok'eka ka taimaka." Mik'ewa yayi tsaye yana had'e fuska yace "Ki kwanta ki huta yanzu, zan sa a kawo miki abinci ki ci, da safe zamuyi koma menene." Fashewa tayi da kuka marar sauti ta dafe goshinta tace "Me yasa ba zaka fahimce ni ba yallab'ai, abinda kuka zo mi da shi safiya zuwa daren nan ya girmi tunani na, ko a tatsuniya ban tab'a kawo hakan zai faru ba, ta ya lokaci d'aya zaku nuna min wad'anda suka reneni ba su ne iyayen da suka haifeni ba? Ta ya kuke so na yarda da ku haka?" Sauke numfashi yayi yace" Na fad'a miki iya abinda zan iya yanzu, zuwa safe zamu ci gaba da tattaunawa." Yana fad'a ya fice a d'akin inda ta bishi da kallo, kasa kukan tayi mai sauti sai marar sauti hannunta kuma dafe da kan ta saboda yanda yake juya mata. Ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba wata matashiyar jakadiya ta shigo d'auke da faranti a hannunta shak'e da kayan abinci, ajewa tayi cikin ladabi tace "Ranki shi dad'e ga abinci inji yarima na, da wani abu da kike da buk'ata?" Mik'a mata hannu tayi tace "Kamani na tashi." Da sauri ta kamata tayi zaune, a raunane tace "Bani ruwa." Sunkuyawa tayi a ladabce tace "Amma ranki shi dad'e yallab'ai Umad ya ce ki fara da ruwan d'umin nan, hakan zai ba wa hanjinki damar warwarewa." Jinjina kai kawai tayi almar to, tana kallo ta had'a mata tea da zuma kad'an a ciki ta mik'o mata ta karb'a, a hankali ta dinga kurb'awa tana sha, saida ta shanye tas ta mik'a mata kofin ta ajiye. Bangon d'akin ta kalla inda agogo ya nuna mata k'arfe 01:15, sake mik'a mata hannu tayi tace "Taimaka min na sauka, ina so zan shiga ban d'aki." Da taimakonta ta shiga ban d'aki, da fari fitsarin dake mararta ta so tsiyayewa, sai kuma ta cire kayanta ta shiga baho ta dinga tsala wankanta tana k'arewa ban d'akin kallo, had'uwarta da tsabtarta duka sun birgeta, ga rigar wanka kala uku a jere haka ma towel, mayukan wanke baki da shampoo had'a da turaren baki da na ruwa, sam sai ta manta ma da dare ne ta dinga anfani da komai kamar wata gasar zata tafi, sai da ta ji agogo tayi alamar k'arfe biyu ta buga yasa ta fitowa sanye da rigar wankan data sauko sosai a hannayenta rigar kuma har ta kusa sauka a k'afafunta. Tana fitowa ta samu matashiyar nan durk'ushe da alama ita take jira, da mamaki tace "Wai dama kina nan baki tafi ba?" Da ladabi tace "Ban tafi ba ranki shi dad'e, ina jiran umarninki ne ko kuma idan da wani abu da kike da buk'ata." Numfashi ta sauke ta k'araso gaban gadon ta zauna tace "To yanzu zuba min abinci na ci sai ki tafi ki kwanta ke ma, dare yayi fa sosai." "To ranki shi dad'e." Ta fad'a tana mik'ewa, saida ta gama had'a mata lafiyayyen abincin ta ajiye mata gabanta har da ruwa da lemu, kallonta tayi tace "Ki je kawai, da safe kya zo ki d'auke kwanukan." Jinjina kai tayi ta fita tana mata saida safe, a ladabce kuma a hankalce ta shiga tsakurar abincin tana yi tana nazarin duk abinda ya faru daga safe zuwa daren nan, sai ta ji kamar tayi dariya saboda a almara take ganin abun, sai kuma ta kyab'e fuska ta matso k'walla saboda jin kamar zuciyarta na son yarda da abinda suke fad'a mata. Tana kammala cin abincin ta koma ban d'aki ta wanke bakinta ta dawo, ruwa tasha kad'an sannan tayi zaune, ta jima zaune kafin ta gyara ta kwanta ta ja zanin rufa lallausa ta rufe jikinta ko rigar wankan bata cire ba. *Egypt* Kamar da wasa mai kula da ita ta tabbatar da bata d'akin, fargaba da firgici sai ya hanata fad'a masa ta shiga neman hanyar da zata sanar masa. Yana tsaye tare da Zafreen ta dafe k'ugu ta matsa ya mayar da ita gidansu ko ta jaza masa bala'i, cike da jin haushinta yace "Kiyi duk abinda zakiyi, ba zan mayar da ke d'in ba sai gari ya waye." Juyawa yayi ya shige ciki kai tsaye d'akin da Ayam ta ke ya nufa, bai samu kowa a d'akin ba amma dake har da mai kula da ita su biyun sai kawai ya fito da tunanin ko sun shiga zagayawa da iga ne a gidan, yana fitowa suka had'a da d'aya daga ciki ta dawo, da mamaki ya k'are lata kallo yace "Ina gimbiya take?" Da ladabi tace "Tana ciki yallab'ai, ita ce ta aikeni na samo mata wannan." Ta fad'a tana nuna furanni masu kyau, da mamaki yace "Amma kuma bata ciki, me ta ce miki zatayi da su?" Girgiza kai tayi tace "Gaskiya ban sani ba ni ma yallab'ai." Tureta yayi gefe ya fita a b'angaren ya shiga zagayawa duka gkdan amma shiru, b'angaren ya sake dawowa sai kuma ya ci karo da d'aya mai tsaronta sai gumi take ido sun mata jajir, cikin daka tsawa yace "Ina gimbiya ta?" Cikin i'ina da tsoro ta shiga masa nuni da hannu tace "Yallab'ai ni ma, wallahi ban san inda ta shiga ba." Da matsanancin mamaki yace "Baki san inda ta shiga ba? Kika ce bako san inda ta shiga ba?" Gaba d'aya ya tashi hankalin gidan ta hanyar sa wa a bincike ko ina, ta b'angare d'aya kuma waya yake amsawa daga waje yana bada masaniya daga masu taimakonshi, dattijon nan dake tare da shi yana gefe tsaye ya kalleshi yace" Yallab'ai. " A hassale yace" Me ye?" A ladabce yace" Ina ga fa kamar sarki Wudar raina mana wayo sukayi." Zazzaro masa ido yayi yace" Kamar ya?" A sanyaye yace" Ina tunanin su suka d'auke ta." Jim yayi yana sake rarako idonshi waje ya jinjina kai yace" Kuma fa haka zai yiwu." Jinjina kai yayi yana murmushi yace" Lallai sarki Wudar ya nemi tashin hankali da ni, kuma zai ga abinda ya fi k'arfinshi." Kallon dattijon nan yayi yace" Zuwa wayewar gari zai samu sak'o daga sarkin Khazira. " *Yan uwa kuyi hak'uri da wannan dan Allah* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:36 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *17* Kamar wasa sai kam Bukhatir ya shirya cikin shigar alfarma da take nuna ya fa yi niyyar zama mai mulkin k'asar Egypt na gaba, motoci aka shirya inda ya umarci Zafreen da ta shirya zasu tafi, ba kuma Zafreen kad'ai ba har da matarshi Zeyfi, ita kan ta tayi mamaki dan ba zata iya tuna lokacin da sukayi tafiya tare ba, duk da yanzu ma bai fad'a mata inda suka nufa ba, amma hakan ma ya mata dad'i tunda dai ga ta ga shi, dan kwana biyu kenan ko gidan da take bai kwana saboda zumud'in Zafeera wacce ta ke ganin ta shigar mata hanci a duk'unk'une, tana sunan matarshi ne kawai, amma gangar jikinsa da zuciyarsa sun haukace aka wata wacce bai ko tab'a ganinta ba bayan jiya. Haka kam akayi inda suka d'auki hanya zuwa babban birnin Texanda, *awa takwas* suka d'auka a hanya kafin suka isa masarautar. Sanda sukayi oda daga k'aramar tagar dake jikin k'ofar mai gadi lek'o, ganin bak'in motoci yasa shi bud'e k'aramar k'ofa ya fito, motar dake gaba ya lek'a ta madubi yace "Yallab'ai daga ina?" Dreban dake tuk'a motar da Zafreen take ciki ne yace "Daga Egypt tare muke da gimbiyarku." Idonshi ya sauke a kujerun bayan motar, ganin Zafreen ta wurga masa wani kallo yasa shi saurin rusunawa yace "Ranki shi dad'e." Da sauri ya juya ya koma ciki ya rufe k'ofar k'arama sannan ya shiga fafutar bud'e k'atuwar k'ofar mai taya wacce turawa ne kawai yake, saida ya bud'esu gaba d'aya sannan hancin motocin suka durfafa ciki, duk tak'ama da ji da kan Bukhatir saida ya tabbatar lallai sarki Musail yana murza mulki a daular nan, irin dukiyar daya zuba wajen k'era gidan nan, shuke shuken dake wurin ka rantse lambuna ne ta ko ina, manya manyan b'angarori ne guda uku, na tsakiyar kuma shi ke shaidawa mai kallo a nan sarki Musail yake rayuwarsa. Kamar yanda sauran motocin ke bin motar dake gaba har saida suka tsaya daf da b'angaren tsakiya, ganin fuskarta daga cikin farin gilashin motar yasa wasu masu tsoron k'ofar su biyu d'aya a cikinsu ya taho da sauri ya bud'e mata ta fito, juyawa tayi ta kalli Bukhatir da matarshi da suka fito su ma, kallon bafaden nan Zafreen tayi tace "Ina mahaifina yake?" Da ladabi yace "Shugaba na yana fada." Juyawa tayi ta kalli Bukhatir tace "Pah yana fada, zaku same shi a can ne ko zaku jira?" Wani kallo ya mata yace "Ai mu masaukin bak'i ne ya dace da mu, dan maganar data kawomu babba ce." Harara ta galla masa sama da k'asa ta kalli bafaden nan tace "Ka kaisu masaukin bak'i." Rusunawa yayi yace "Angama ranki shi dad'e." B'angaren dake hagun su ya nufa yana kallonsu alamar su tafi, da kallo Bukhatir ya bita sanda take shigewa ciki da mamakin yanda ta bayar da umarnin a rakasu masaukin bak'i. Jinjina kai yayi ya kalli Zeyfi ya rik'o hannunta, da sauri Zeyfi ta kalleshi tana sakin murmushi dan hakan ya mata dad'i sosai, gana son mijinta so mai tsanani kuma tana kishinsa, saidai tana tsoronsa da kuma shakkun halayensa, dan tun ranar daya wanka mata mari a kan Zafeera bai sake ko kallon fuskarta ba, ita kamba tasan ya zatayi da Bukhatir ba, wasu lokuta har mamakin irin biyayyar da take masa take, gashi dai tana so ta haihu da shi, amma gaba da gaba ya fad'a mata bata isa ta fara haihuwa ba har sai Zafeera ta zo ta fara haihuwa sannan ita ta biyo baya, tabbas ta ga illar auren tushe, watak'ila da mai son ta ta aura da bata ganin wannan k'ask'ancin, amma dake mahaifinta kwad'ayi yasa shi aura masa ita wulak'anci kawai take gani ta ko ina. Zafreen na shiga duk hadimai suka kama jikinsu, d'akinta ta shiga da sauri sauri ta shiga cire kayanta inda hadimar ta shiga ban d'aki dan had'a mata ruwan wanka, tana kammalawa ta fito ita kuma ta shiga d'aure da k'aramin towel tace "Ki kawo min madara mai sanyi." "To shugaba ta." Ta fad'a tana ficewa a d'akin, bata wani jima a wurin wankan ba ta fito dan dama ta shirya a can, madarar data samu ajiye ta d'auka tana kurb'awa tana kallon kan ta a madubi, dafe k'ugu tayi tana shan madarar tana ayyana _"Ashe dama ita ce Zafeera? Tana da abun al'ajabi yarinyar? Shi yasa ta iya d'aga hannu ta mare ni a fuska? Ai kam zatayi nadama, zan samota sannan na hukunta ta, zata san ni ce gaba da ita ko a haihuwa ma."_ K'wafa tayi mai k'arfin gaske tare da aje madarar ta shiga shiryawa a tsanake, cikin shigarta ta alfarma na kayan sarauta ta shirya inda ta fito fes da ita ta gama kyau, fitowa tayi daga d'akin tana ta k'amshi abun ta, jakadiyar da suka had'e da ita yasa ta tambayar "Ke ina Mah?" Da sauri ta d'aga kai ta kalleta tana rarraba ido da tunanin ta inda zata fara fad'a mata, sunkuyar da kai tayi tace "Ranki shi dad'e sarauniyata bata nan." Yatsina fuska tayi tace "Ina kuma ta tafi?" Kad'an ta ja baya dan tsoron mari take idan ta bata amsar, girgiza kai tayi dan kare lafiyarta tace "Ni ma ban sani ba gimbiya." Tsawa ta daka mata tace "Kamar ya baki sani ba? A gidan nan fitar Mah tana b'oyuwa ne ko dan yan rakiyar da Pah yake had'ata da su, zaki fad'a min ko sai na wulak'antaki?" Jiki na b'ari ta durk'ushe k'asa tace "Ranki shi dad'e ai sarauniya ta kwana biyu a gidan kurkuku na sabah." Da k'arfi tace "Me? Kurkuku?" Da sauri ta taka zata bar wurin sai kuma ta juyo ta kalleta tace "Akan me wai?" Shiru tayi hakan yasa Zafreen fita da sauri kamar zata tashi sama, b'angaren damansu ta shiga inda anan fadar take, sosai ke da banbanci tsakanin babban b'angaren da kuma nan d'in, inda kujerarshi take cikin sauk'i Zafreen ta hangeshi, fadawan kuma duk suna zazzaune suma a kan kujeru cikin shigarsu ta alfarma. Tunda suka ji an bud'e an shigo babu neman izini suka maida hankulansu kan k'ofar, ganinta yasa kowa mamaki har sarki Musail da waziri Khatar suka mik'e dan suna tsaka da maganar inda ta shiga ne ita ma, da sassarfa sarki Musail ya sauko a matakalar ta fari da ta biyu har zuwa ta uku wacce ita ce ta k'arshen dake sadashi da kujerar mulkinshi, bud'a hannayenshi yayi da farin cikin ganinta yace "Gimbiya Zafreen, yaushe kika shigo? Ina kika shigo haka?" Ja baya tayi cikin d'aga murya tace "Pah, me Mah tayi haka da zafi daka zab'i kulleta a kurkukun sabah? Kurkukun da kake rufe manyan masu laifin daka kama ko kuma kake son horar da mutum dan nuna masa ikonka." Sauke hannayenshi yayi ya dogara sandar shi a k'asa ya k'ura mata ido, shiru yayi bai da niyyar amsata, cikin jin haushi ta sake maimaita" Pah, mahaifiyata fa ka rufe a kurkuku, ina so nasan me tayi haka? Ka daina son ta ne?" D'auke idonshi yayi a kanta yace" Zafreen, shin ba ke kika bamu bayani akan sark'ar nan ba?" Gyara tsayuwa tayi tace" E." D'orawa yayi da" Me yasa bakiyi tunanin hanyar da suka samu sark'ar ba? Kin tab'a jin mahaifiyarki tayi k'orafi akan b'atan sark'arta ne?" Tsareshi tayi da ido tace" A'a, hasalima bamu san da b'atan sark'ar ba, daren da zan bar nan na fahimci bata tare da sark'ar." Buga sandarshi yayi k'asa sosai tare da d'aga sauti yace" To wannan dalilin ne yasa na rufeta, Juman ta ha'inceni ta yaudare ni, shiyasa na kawar da duk son da nake mata na hukunta ta." Da mamaki tace" Kana nufin Mah da hannunta a b'atan Zafeera kenan?" Shiru ya mata ya juya ya shiga takawa a tsanake har ya koma kan kujerarshi ya zauna, waziri Khatar daya kalla yasa shi gyara tsayuwarshi ya kalleta yace" Gimbiyata, an samu sarauniya Juman da laifi dumu dumu na b'atan Zafeera, dan da bakinta ta fad'i hakan saboda ta kub'utar da ita." Dafe k'ugunta d'aya tayi ta cije leb'enta na k'asa tana girgiza kai, ta d'auki sakanni a haka kafin ta kalli sarki tace" Mahaifi na, yanzu haka tare muke da wanda ya sace ni ya kuma sace maka Zafeera." Da k'arfi ya mik'e akan kujerar yace" Me? Wanene shi? Yana ina? Me ya kawosa nan?" Lumshe ido tayi ta motsa baki alamar tambayoyin sun hau mata kai ba kuma zata iya amsawa ba, a hankalce tace" Yana masaukin bak'i." Cikin zumud'i yace" Kenan suna can tare da Zafeera?" " A'a." Tana fad'a ta juya tana fad'in" Zan je na ga Mah, Adah ka rakani." Da kallo Adah dake kusa da sarki ya rakata yana jin takaicin iya shegen yarinyar nan, amma sarki Musail na kallonshi bai da zab'in daya wuce bin bayanta da sauri suka fita. Suna fita sarki Musail ma ya kalli waziri yace" Wanene wannan? Me yasa ya zo nan bayan yasan zan iya halaka shi?" Dhurani dake kan kujera kusa da waziri ne yace" Ka gafarce ni sarki na, ina ga ka fara had'uwa da shi, watak'ila akwai dalilinshi na zuwa nan." Da kallon tuhuma ya bishi yace" Kana nufin ko da magana ya zo na zauna na saurare shi? Bayan kuma ina zarginsa da nesanta ni da Zafeera." Waziri ma cewa yayi" Hakane sarki na, mu fara sauraranshi mu ji, ta haka zamu san inda Zafeera take." Jinjina kai yayi ya kalli Dhurani yace" Muje tare." Mik'ewa Dhurani yayi ya bi shi suka fita inda waziri ya ji haushin hakan, ya so aje da shi ya ji me ya kawosu me kuma za'a tattauna, hakan yasa shi jan tsaki ya fara safa da marwa dan ba zai iya zama ba har sai ya jie aka tattauna. *Giobarh* Duk da ta jima bata kwanta ba amma sai ga shi k'arfe 07:00 tana bugawa ta farka saboda sabon tashi, saida ta bud'a idon ta ne ta fahimci inda ta kwana, a gajiye kuma a kasalance ta yaye rufar ta sauka a gadon, gaban madubi ta k'arasa tayi tsaye tana kallon kanta da tunanin me zatayi ? Gudu zata fara da shi? Ko kuma gyaran makwancin data tashi? A sanyaye ta fad'a ban d'aki ta fara da wanke bakinta da fitsari sannan ta fito, gurin kaya ta fara dubawa dan ta ga ko zata samu k'ananan kaya na motsa jiki, saidai duka kaya ne manya a ciki irin wanda ta gani jikin matar nan ta jiya (Joyran). Rufewa tayi ta koma kusa da tagar gurin, bud'ewa labulen tayi hakan yasa hasken safiyar shigowa d'akin, ta madubin ta dinga kallon tarin shukokin wanda suka mata kyau take kuma ayyana lallai zasuyi k'amshi gurin kuma zai yi sanyi. Da sauri ta saki labulen ta nufi k'ofa dan fita ta shak'i wannan daddad'an oxygen d'in, tana bud'e k'ofar ta fara takawa, fitowarta tayi daidai da bud'a d'akin sarauniya Kossam da wata hadimar tayi d'auke da farantin abincinta, a ladabce ta gaishe da Ayam d'in ta amsa, fuskarta a sake tace "Dama da mutum ne a nan?" Da girmamawa tace "E ranki shi dad'e, ai d'akin sarauniya ne." D'aga girarta tayi sama tace "Oh ! Zan iya shiga ciki?" A ldabce tace "E to ranki shi dad'e zaki iya." Hannu ta kai ta bud'e k'ofar ita ce a gaba hadimar na bayanta, ganin matar kwance yasa Ayam kallon hadimar tace "Bata da lafiya ne?" "E, ai ta jima kwance a haka." Ta fad'a sanda take aje farantin hannunta, da tausayi Ayam ta kalli Kossam da idonta ke rufe tace "Me yake damunta ne?" Girgiza kai tayi tace "A gaskiya ban sani ba, shekara uku da fara aikina a nan, nima a haka na sameta." Da mamaki ta waro ido tace "Shekara uku? To ita shekara nawa ta d'auka a haka?" Cike da jimami tace "A yanda na ji suna fad'a shekara ashirin kenan." Da k'arfi tace "What? Oh my God." Ta fad'a tana k'arasawa ga Kossam, zaune tayi bakin gadon ta rik'o hannunta, kamar ta tsikareta da allura sai kawai ta tsam ta bud'a idonta ta zuba akan Ayam d'in, wani tattausan murmushi Ayam ta sauke ta kalli hadimar tace "Ta farka, tana magana ne?" Girgiza kai tayi tace "A'a ranki shi dad'e." Kallon Kossam ta sake yi, sanyayyan murmushi ta sakar mata a karo na biyu ta sake jimk'e hannunta, cikin taushin murya tace "Kina ji a ranki kamar ki ce wacece ni ko?" K'urawa fuskarta ido tayi tana son ta ga ko zata amsa lata da ido, sai kawai ta ji ta d'an jimk'i hannunta, kallon hannayen na su tayi sai kula ta sake kallonta tace "Kin gaji da kwanciyar nan haka ko?" Sake jimk'e hannunta tayi, da sauri ta sake kallon hannayen na su, k'ura mata ido tayi tace "Kina so kiyi magana ne?" Sake damk'e hannunta tayi, jinjina kai Ayam tayi tce "Zaki yi magana, zaki samu lafiya nan kusa ke ma." Mik'ewa tayi tsaye ta kalli hadimar tace "Taimaka min mu gyara mata jikinta ta ci abinci." Zaro ido tayi hadimar tace "A'a ranki shi dad'e, ai babu mai alhakin bata ko da ruwa ne sai mai girma Joyran." A yatsine ta kalleta zatayi magana sai kuma ta ji Kossam ta sake rik'e hannunga gam a cikin na ta kamar za'a rabasu, kallonta tayi da mamaki ta kalli hannayen na su, nazartarta tayi sosai ta shiga karantar yanayinta, sai kawai ta kalli hadimar tace "Wacece haka kuma?" Tausasa murya tayi tace "K'anwar sarauniya ce, ita ke kula da ita tsawon lokaci." Mik'ewa tayi daga rank'wafawar tace "Kuma dole sai ita ce zata iya kula da ita, babu wani wanda zai iya saka hannunsa da sunan taimako?" A tsawace tace "Malama kama min ita." Da sauri ta matsa suka kamata ta dinga nunawa Ayam d'in yanda suke taimaka mata, har baki saida ta wanke mata da mai ta tsefe mata kai sannan tace ma hadimar "Samo mata kayan sakawa." Da sauri hadimar dake mamakin iko na wannan yarinya ita ma tace "Ai kayanta suna d'aya d'akin, mai girma Joyran ce tasa aka mayar da su can." A dak'ile fuska a had'e Ayam tace "Ai cewa na yi ki d'auko min, ba wai ki fad'a min inda suke ba." Da sauri ta juya ta fita ta shiga d'akin da aka sauke Ayam d'in, ita kuma abincin ta d'auka ta fara ba wa Kossam wacce k'arara zaka fahimci fuskarta bata cikin yanayin nan na dumkum data saba. Duk da ta ji an bud'e k'ofar bai sa ta juyo ba dan tunanin ta hadimar ce, amma sai ji tayi an ce "Uban wa ya baki damar bata abinci?" A gadarance kamar wacce ta tashi da ciwon wuya haka ta juyo ta kalli Joyran wacce tashin hankali ya bayyana a gareta k'arara, d'auke kan ta tayi ka rantse bata san da mutum a wurin ba tace "Kin ci sa'a d'aya an ce yar uwar madam ce ke, ba dan haka ba da na ce *uban ki*." Kossam kan ta saida mamaki ya bayyana a fuskarta, uwa uba kuma hadimar nan data shigo d'auke da kayan da Ayam d'in ta buk'ata, haka ma Joyran kusan jiri ta ji zai d'ebeta, yanda ta zazzaro ido ta k'ura mata su kamar wacce ke kallon gawa na motsi, sam mantawa tayi da a inda take me kuma take yi saida ta tsinkayi muryar Ayam a kunnenta tana fad'in "Ki daure ki k'ara kad'an madam, please." Da sauri ta zabura kamar wacce aka mara ta k'arasa shigowa d'akin, cikin tashin hankali da neman bala'i ta bige farantin abincin tana fad'in "Ke har kin isa? Wacece ke da zak..." D'aga mata hannu Ayam tayi ta d'ora yatsa a labb'anta tace "Shiiiii!" Kallon fuskar Joyran d'in tayi tace "Haka kawai na tsani tsawa, na tsani a d'aga min murya musamman a k'ok'on kai na, na rlk'oki kar ki jawowa kan ki mummunar safiya ta hanyar tak'alata rikici, ina so na kafa kyakyawan tarihi a gidan nan kafin na barshi." Juyawa tayi ta kalli hadimar tace "Kawo kayan ki taimaka min a saka mata." A tsorace cikeda girmama lamarinta hadimar ta k'araso jikinta har rawa yake ta aje kayan kan gado, a tsawace Joy ta kalli hadimar tace "Ke! Idan baki bar nan ba sai na tozartaki." Da kallo Ayam ta bi hadimar data fita a rikice ta rasa me zatayi, zagayawa tayi ta d'auki kayan ta warware ta tako zata koma inda take, cikin jin haushi Joy ta fizge kayan ta jefar a k'asa tace "Fita a nan malama, sannan ki ji da kyau." Tayi maganar tana nuna Ayam da yatsa, d'orawa tayi da "Daga yau sai yau karko sake shigowa d'akin nan bare ki k'araso gareta, babu ruwanki da abinda ya shafeta, idan kuma kika sake to ki sani ki ma zaki tsinci kanki a mugun hali." A take, a bazata, kamar saukar aradu Ayam ta rulgume hannaye tana fad'in "Kamar yanda kika jefata kenan?" Wani mummunan fad'uwa ne gabanta yayi ta rarako ido ta kalleta, take wani gumi ya shiga tsatsafo mata a goshinta zuwa wuya, tsatsareta tayi da ido ta sake gyara tsyuwarta tace "Ko kuma zaki jefani fiye da halin da kika sakata ne duk tsawon shekarun nan?" Kame kame ta fara tana jujjuya kai tace "Ke ke..me kike...fad'a ne wai haka ? Baki da hankali da alama." Tana fad'a ta rab'ata zata fita a d'akin, ta kai daf da k'ofa kuma sarki Musail ya shigo daidai da Ayam tace "Ina da hankali, amma ki sani a cikin haukana zan bankad'o sirrin da kika jima kina b'oyewa ta hanyar wasar kura da rayuwar mutuniyar kirki." Rud'ewa Joy tayi ta kalli sarki Musail dake binsu da kallon tuhuma yana son sanin me ke faruwa, fashewa tayi da kukan makirci tana fad'in" Wannan ma ai tozartani kike yi, yar uwata ce fa, ya kike tunanin da hannu na a cikin rashin lafiyarta?" Shigowa yayi yana kallon Ayam yace" Gimbiya Zafeera, me yake faruwa ne? Tana neman b'ata miki rai ne?" Kallonshi Joy tayi da mamaki wato bai ma damu da damuwarta ba bare kukan da take, figaggiyar ma yake tambayar ko ana neman b'ata mata rai ne? Ayam kam murmushin yak'e tayi tace" A'a ranka shi dad'e, ba komai muna magana ne." Kallon Joy yayi yace" Ki koma b'angaren ki, sannan ki kiyaye b'acin ranta, dan zan iya yin komai a kan ta." Kallon shi Joy tayi ta k'ara kallonshi sau ba adadi, sai kawai ta juya ta fita dan bata san me zata fad'a ba, tana fita kuma Umad na shigowa har ma yana gaisheta amma sai ya fahimci bata cikin hayyacinta, yana shigowa ciki ya zuba idonshi akan ta, duk da rigar bata fito da jikinta ba face k'afafunta da kuma fuska sai tafukan hannu, amma sai ya ji ya tsani tsayuwarta haka kuma a gaban mahaifinshi. Bai kula da sarki Wudar dake tsaye ba haka mahaifiyarshi da idonta ke kan shi, fuskarsa a had'e ya kalleta yace "Malama ki je d'akinki ana kai miki kaya yanzu." Abun al'ajabi da mamaki daya kusan saka sarki Wudar suman tsaye shi ne yanda Ayam ta jinjina kai alamar to ta kuma kama hanya ta fice, sai ya ji ya fara kokonto ko dai ba ita bace, dan wacce aka fad'a fa komai matsayinka ita ce zata baka umarni kuma kayi jikinka na b'ari, hasalima ita waccen idonta kawai sun isa su saka mai aurenta durk'usawa kan gwiwoyinshi ya tambayi me take da buk'ata. To amma kuma wannan ya d'anshi ya bata umarni haka ta bi? Duk da dai yasan waye Umad wajen tsare gida shi ma akwai izza da shan k'amshi inda a msarauta yake, to amma ai ta ta izzar ta dame ta shi ta shanye dan ita harda baiwa a lamarinta, uwa uba kuma sarautarta ta fi tashi k'arfi. (Idan har ta zama yanda kuke fad'a ai bata dace da zama matar kowa ba kenan, dole ta auri kan ta) *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:37 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *18* Saida ta fita ne Umad ya kula da yanda ya ga mahaifiyarshi, da sauri ya zagaya b'angaren ta ya rik'o hannunta yace "Mahaifiyata kin tashi lafiya?" Zuba mata ido yayi amma kuma yana fahimtar amsar da take bashi ta tafukan hannayensu, shafa kan ta yayi da ya ga an gyara mata shi yau sannan yayi murmushi ya mik'e yace "Mah ina zuwa?" Yana fad'a ya nufi fita a d'akin sai ya ji sarki Wudar ya rik'o hannunshi, juyowa yayi suka kalli juna, a tausashe sarkin yace "Kasan wacece ita da kake bata umarni haka?" Wani malalacin murmushi yayi yace "Na sani Pa." Yana fad'a ya zage hannunshi a hankali ya fice a d'akin, kayan daya tanadar mata ya ba wa d'aya daga cikin hadiman gidan ta kai mata a d'akinta, inda shi kuma yana fitowa daga b'angaren sa ya ci karo da amininshi Haman ya zo gidan. Had'e fuska Umad yayi sosai ya tako kamar mai tsorontaka k'asar ya tsaya gaban Haman d'in dake jingine a motarshi, Haman kam dake k'are masa kallo ya san akwai abinda had'e fuskar nan ke nufi, amma sai ya dake ya mik'o masa hannu yana murmushi yace "Barka aboki." Hannun Haman d'in ya bi da kallo kafin ya kalli fuskarshi, kawar da kai yayi sannan ya mik'a masa hannun yana d'an jinjina kai, gyara tsayuwa Haman yayi yace "Wai me yake damunka ne?" A dak'ile yace "Me ka gani?" Da yar raha yace "Na ga kayi wani iri ne ai, kamar ba kayi farin cikin gani na ba, da wata matsala ne?" Tsakiyar k'wayar idon Haman d'in ya kalla fuskar nan a murtuke yace "Haman, bayan ni da kai bana jin akwai wani da yasan inda Zafeera take, ya akayi a sanda nake can kuma sai ga mutanen Baba na?" Sunkuyar da kai yayi yana k'yakyabta ido da sauri kuma ya d'aga kai yace "Kamar ya? Zargi na kake Umad? Na d'auka kafi kowa sanin ba mu kad'ai muke nemanta a lokacin ba." Jinjina kai yayi yace "Hakane, amma kuma mu kad'ai muka san gakamaimai inda take a lokacin." Gyara tsayuwarshi yayi ya d'an sassauta had'ewar da ya ma fuskarshi yce "Haman, kasan aikinmu aikin sirri ne, kuma zamu kai ga gaci ne ta hanyar Zafeera, a duniya babu wanda ya san sirri na sama da kai, kar ka yarda na fara d'ora alamomin tambaya a kan ka, hakan zai ruguza maka yardar daka samu a wuri na." Juyawa yayi zai nufi babban b'angaren yace" Muje ka ci abinci, sarki zaiyi farin ciki da ganinka." Da kallo Haman ya rakashi har ya shige ciki ya dain ganinshi, wani sakaran murmushi ya saki akn labb'anshi ya furta" Zamu gani Umad, zamu gani." Da sauri ya shiga taka matakalar ya shiga b'angaren shi ma, sai kuma ya samu Umad da sarki Wudar da kuma Joy zaune wajen cin abinci ana zuba musu, k'arasawa yayi a ladabce ya gaishe da sarki sannan ya masa izinin zama kusa da shi, yana zama kuma sautin tkalmin Ayam suka sanar da su zuwanta. Sarki Wudar da Haman da kuma Joy ne suka bi ta da kallo, rigar yadin dake jikinta mai santsi da kauri da k'yalli-k'yalli zai nuna maka yadin babba ne, saidai d'inki ne simple babu kwalliya, rigar har kasa ta sauka ta bak'in yadin sai hannayen da suka matseta sosai har zuwa gwiwar hannunta, daga k'irjinta ma zuwa ciki ya matseta sosai sai k'ugun da aka fito mata da tsarin surarshi sai tayi kyau sosai. K'arasowa tayi ta ja kujera kusa da Umad ta zauna, tana neman cire takalmin k'afarta, dan gaskiya bata saba saka wannan takalmin ba ko can dama, wasu lokuta tana sakawa ne idan zata tafi wani shagali ko kuma wani shagalin makaranta, duk da shi ma kad'an ne a aikinta ta saka riga da wandonta mai yagewa a gwiwa ko cinya ta saka takalminta k'afa ciki ta d'auresu tamau da zariyarsu, shiyasa yanzun sai k'afafunta suka fara ciwo saboda sakawar da tayi jiya da kuma yanzu. Da kallo ita ma ta bisu d'aya bayan d'aya kafin ta dire a kan sarki Wudar tace "Barkanku." Da wani irin alfaharin jin kasancewa gashi ga Zafeera ya jinjina kai ya saki murmushi yace "Barka gimbiya ta." D'an yak'e kawai ta masa ta maida hankalinta kan farantin ta, a hankali ta saci kallon Umad da shi ma lokacin yake kallonta, amma suna had'a ido yayi gaggawar d'auke na sa ya wani yatsina fuska irin ko menene d'in nan? D'auke kan ta tayi ita ma ta kalli Haman, da fara'a a fuskarta tace "Amma kai balarabe ne?" Da sauri ya aje kofin daya d'auka mai ruwa zai sha ya tsura mata ido, cikin zaro ido yace "Wacece ke kuma? Me yasa kika ce haka?" Murmushi tayi tace "Alamunka ne ya nuna, kuma da alama larabcin parsi kake, idan ba parsi ba to Ourdu." D'ora yatsanshi yayi a goshi yana rarraba ido, zufa zufa yake jin tana neman wankeshi daga zaune, to ta ya ma ta sani lokaci d'aya haka? Ko fa Umad bai san asalin waye shi ba, ya ita take neman saka shi a uku haka? Sarki Wudar kam wani farin ciki ne ya lullub'eshi har ya kalli Haman yace "Ita ce fa, Zafeera." Tsoron da Umad ya gani a tare da Haman d'in a lokacin sai ya sake jefa masa shakku a kan shi, tar tar yake kallonsa yana kuma karantarsa, cikin i'ina ya kalli Ayam yace "Ke ce dama? Sannu ko, ai mun jima muna nemanki." Murmushi kawai ta masa ta d'ibi abincin ta kai bakinta, sam ta k'i yarda ta kalli inda Joy take, saidai tar take kallonta ta k'asan ido, tana kuma ji a jikinta irin mugun kallon da take bin ta da shi, gyara zamanta tayi ta kyab'e fuska kamar yarinya ta kalli sarki Wudar tace "Am yallab'ai, zan iya tambayar wani abu?" Da fara'a yace "Zaki iya mana gimbiya, ai ki saki ranki kiyi duk abinda kike so, nan gidanki ne kuma masarautarki." Gyara zamanta tayi tace "Yallab'ai dama ina so ne nasan dalilin zama na a nan? Ina so na koma gida saboda ina karatu a can." 'Yar dariya yayi yace "Karki damu gimbiya, ki d'an bani lokaci kad'an, zaki san me yasa kike zaune a nan." Bud'a baki tayi a hankali tace "Amma..." Sai kuma ta jinjina kai kawai tace "Shikenan." Sake kallonshi tayi tace "Yallab'ai me yasa madam take gida kwance madadin asibiti?" Muskutawa yayi hana ci gaba da cin abincinshi yace "Bana jin akwai asibitin da ban fita da Kossam ba, amma magana d'aya ce ba'a san dalilin ciwonta ba, da fari tana magana, amma a k'arshe sai ta zo ta daina, boka ya fad'a mana sammu ne kawai aka mata, amma kuma shi ma ya kasa karya wannan sihirin." Tarrr! Ta sauke idonta cikin na Joy da ita ma take kallonta kamar zata fasa ihu, girgiza kai kawai tayi tace" Zata samu sauk'i ita ma, amma da taimakonka." "Kamar ya?" Ya tambaya yana tsare ta da ido haka ma Umad dake neman gasgata mafarkinshi da kuma abinda malamin nan ya fad'a masa cewa _"Ban san gaibu ba, amma a d'an ilimin da Allah ya bani zan iya karambanin fassara mafarkinka Umad, a ganina kar ka cutar da ita saboda kana jin haushin mahaifinta kuma kana son d'aukar fansa a kan sa, a gani na zai fi kyau idan ka sameta ka kyauta ta mata, alamu sun nuna zata iya zama silar warkewar mahaifiyarki, dan ni kai na abinda na fahimta a ciwon mahaifiyarka da sihiri a ciki, kuma ko shakka babu a kullum ana sake sabinta mata wani mugun k'ulli, saidai Allah ya barwa kansa sani, shin wanda ta had'a jini da shi ne ko kuma daga nesa, abu d'aya da zan fad'a maka shi ne, da na kusanta ne ake samun nasarar cutar da ita."_ Gaba d'aya ya tattara hankalinshi kan ta yana so ya ji me zata fad'a, a tsanake cikin ladabi tace" Ina nufin ka canza mata masu kula da ita, sannan ka kafa dokar hana shiga d'akinta idan ba kai ko d'anta ba, sannan duk abinda za'a mata anfani da shi misali ruwa ko abinci, to a tabbatar an duba lafiyar abinda zata ci sannan wanda aka yarda da shi ne zai bata." K'uri sarki ya mata yace" Gimbiya Zafeera, kina magana kamar kina so ki nuna kin gano wani abu ko kuma kina son fad'an wani abu ko?" Sanyayyan murmushi tayi ta girgza kai tace" Babu abinda na sani yallab'ai, saidai lokaci d'aya na fahimci ana ciyar da madam gubar da a kullum take dad'a kassara mata gabb'an jikinta, imma a ruwa ko a abinci." Tare Umad da sarki suka kalli Joy, rarraba ido ta shiga yi tana kallonsu tace" A'a, ya kuke kallo na kuma? Wannan yarinyar fa na kula munafuka ce, tunda ta zo gidan nan take min wani gani gani, ta ya kuke tunanin zan cutar da yar uwata? Ita kad'ai fa ta rage min a duniyar nan." Ta k'arashe maganar tana fashewa da kuka, Umad da ya ji tuni zuciyarshi ta fara d'arsa masa shakkunta ne a mugun dak'ile yace" Goggo kin ji mun ce wani abu ne ? Kallonki fa kawai mukayi, miye na tsarguwa kuma?" Dakatawa tayi da kukan ta kalleshi tace" Ni ba tsarguwa na yi, kula nayi kamar kun yarda da abinda da ta fad'a." Sarki Wudar ne ya tab'e baki yace" Idan ma aka samu da hannunki a rashin lafiyar matata babu abinda zai hanani hukunta ki." Da mad'aukakin mamaki ta kalleshi tace" Wudar, dama zaka iya hukunta ni?" Da mamaki Umad ya kalleta jin ta ambace shi da sunanshi wanda bai tab'a jin haka ba, Haman da ke neman haukacewa daga zaune shi ma tsatsaresu kawai yake da ido yana neman dalilin da zai tashe shi a wurin nan kafin yarinyar nan ta masa *bankad'a*, dan ya kula daga cikin dalilin da yasa kowa ke nemanta akwai son fallasa abinda ke b'oye, tunda gashi har ta zak'ulo sirrin daya b'oye shekara da shekaru. Sarki Wudar kam ranshi b'ace yace "Ko waye a duniyar nan zan hukunta shi indai akan matata ce uwar d'ana k'wallin k'wal a duniya." Malaacin murmushi tayi ta kalli Ayam sama da k'asa tace "Har wannan ma zaka iya hukuntata akan Kossam?" Wani abu Umad ya ji ya soki zuciyarshi da yasa shi wurga mata wani kakkausan kallo, Ayam kam mik'ewa tayi tsaye ta kalleta ta kalli sarki Wudar tace "Me kike nufi da abinda kika fad'a?" A wulak'ance Joy ta gyara zamanta tace "Ina nufin..." Tsawar da sarki ya daka mata tasa ta yin shiru ta kalleshi tana hararenshi, kallon su Umad yayi da Ayam yace "Ku jira a waje kun ji." A hassale Umad ya mik'e ya fita Haman da Ayam kuma su'a bayanshi, suna fita Haman kam bai yarda ya tsaya dan shi ma a tsorace yake, motarshi ya shiga ya tayar ya bar gidan, Umad na tsaye yana hangenshi har ya fita a gidan, bayanshi Ayam ta tsaya tace" Me nake yi a masarautarku?" A hankali ya juyo ya kalleta, kawae da kai yayi a gadarance yace "A yanzu dai kam ban sani ba ni ma, tabbas mahaifina ma yana cikin masu nemanki, sai dai bansan me ye manufarsa a kan ki ba, mu jira lokaci kad'an kamar yanda ya fad'a mu ga me zai bayyana mana." Da mamaki a fuskarta tace "Ko da manufarsa zata iya saka rayuwata a had'ari kana nufin mu zuba ido har sai zai aiwatar zamu sani?" Jinjina kai yayi ya juya mata baya yace "Kusan haka?" Cikin jin haushi ta koma ta gabanshi ta fuskance shi bakinta d'auke da masifa da niyyar tace "Wai kai wanene? Me kake ji da shi? Kai bana son iskanci ka ji ko, ka d'auke ni a nan ka mayar da ni garina." Amma kuma yana saka k'ananan idonshi masu sirkin ja a cikin na ta sai kawai ta sunkuyar da kan ta muryarta a tausashe sosai tace "Kana yi kamar baka damu da rayuwata ba yallab'ai, idan hakane to ka maidani garinmu." Wata dariyar rainin hankali ya mata yace "Damuwa da rayuwarki? Oho na gane! Wato so kike nima kamar sauran marasa aikin yi, na dinga binki sau da k'afa ina washe miki baki, ina nuna miki babu kowa sai ke ko? To ba zai yiwu ba, ni ba sakarai bane." Da sauri ta kalli fuskarshi tace "Sakarci? Hakan wai shi ne sakarci? Yanzu idan da ni k'anwarka ce zaka yarda kana kallo mutanen da ban sani ba suna neman juya min rayuwata? Ko kuma da soyayua muke da kai zaka yarda a rabamu ne? Da kuma ni matarka ce fa a ce z..." A mugun tsawace yace "Shiru malama." Zabura tayi tare da rintse ido gam ta k'ame wuri d'aya, k'urawa fuskarta ido yayi yanayin firgicin data nuna sai ya ji kamar yayi ta kallonta, sanyayyan murmushi ya saki a b'oye a zahiri kuma ya had'e fuska yace "Abinda na fad'a miki jiya ma baki yarda da ni ba, ya kike so na yi kenan?" A take ta bud'a idonta tace "Ka kaini wajen iyaye na to." A shek'e ya kalleta yace "Wane daga ciki?" Kallonshi tayi da fari da mamakin tambayar, sai kuma ta kawar da kai tace "Iyayena, wanda suka raine ni har na girma." Shi ma kawar da kan yayi yace "Suna cikin tsaro a inda suke, rayuwarsu na cikin had'ari, ba zan iya nuna miki su ba." Da mamaki tace "Me ya sa rayuwarsu a had'arin? Me suka aikata?" Kallon fuskarta yayi ya saki murmushi mai ciwo, kamo sark'ar wuyanta yayi yace "Ina kika samu wannan?" Kallon hannunshi tayi dake rik'e da sark'ar tace "Iyaye na suka bani." "Tun yaushe?" Ya tambaya yana tsareta da ido, ba alamar tabbaci a tare da ita tace "Ban sani ba nima, na ganta a wuyana ko da nayi wayo." Murmushi yayi yace "Wannan sark'ar a ranar da aka haifeki aka saka miki ita, Ayam karki dameni da son ganin marik'anki a yanzu, duk tambayoyin da kike da muradin yi musu kina da amsoshinsu idan kika aje hankalinki, ki nutsu ki fara tariyar alak'arki da su, dan su basu d'aukeki a 'yar da suka haifa ba sai yar da sarauniyarsu ta haifa, ma'ana gimbiyarsu." Matsawa yayi daf da ita ya saki sark'ar yace" Kina son ganin abun mamaki a rayuwa?" Idonta ta zuba cikin na shi tace" Ina son abubuwan mamaki a rayuwa, idan ban k'aru da ilimi ba na kan samu alfanu a tare da hakan." Jinjina kai yayi yace" Idan kowa yayi bacci zan tasheki sai mu je wani wuri." Da mamaki tace" Me yasa sai kowa yayi bacci? Me yasa baka son kulani a gaban mutane?" Juyawa yayi yana fad'in" Saboda tsaro ne." Da kallo ta bishi har ya shiga wani b'angaren da take tunanin na shi ne. A ciki kuma suna fita a hassale sarki Wudar ya rik'o hannun Joy yace" Me kike so ki tabbatar a haka? Me ye na k'ok'arin fad'a musu abinda ba yanzu na ke da niyyar fallasa shi ba." Jujjuya masa baki tayi ta fizge hannunta tace" Wannan kuma kai ka jiyo, amma ka sani inhar zaka dinga nuna ban da mahimmanci yanzu a gareka to abinda zai dinga faruwa kenan." Nunata yayi kamar zai tsone mata ido yace" Ki sani ke baki isa ki lalata min shirina akan Zafeera ba, kina gani akan idonki zan aureta kuma babu yanda zakiyi." Rai b'ace tace" To ko ka shirya hujojjin da zasu kareka daga zargi da jifan mutane, dan tabbas zasu san meye alak'ata da kai, sannan su san bayani a game da sabon yarimansu dake hanyar shigow duniyar." Tab'e baki yayi yace" Ki sani zaki burmawa cikinki wuk'a ne, na farko ke ce zaune a gidana, na biyu babu wanda ya tab'a gani na a b'angaren ki musamman da dare, na uku kowa dake gidan nan ya shaida irin shigar da kike yi, sannan ki tuna wani abu! Gimbiya Zafeera ta fara bayyana mana wani abun wanda shi ma zai iya sake jefaki bakin al'ummata." Yana fad'a ya juya ya bi ta k'ofar da zat sadashi da fadarshi dan gudanar da mulkinshi. *Khazira* Sarki Musail na shigowa suka had'a ido da Bukhatir, cak ya tsaya ya furta "Bukhatir?" Mik'ewa Bukhatir yayi yana murmushin munafurci yace "Ranka shi dad'e, barka da shigowa." Takawa sarki Musail yayi yana k'arasa shiga ciki yana fad'in "Bukhatir, me ya kawoka gida na? Me kake yi a nan? Dama kai ne bak'on da ya zo?" Dhurani ne ya kalli sarki Musail yace "Shugaba me yake faruwa? Ka san shi ne dama?" Kallon Dhurani kawai yayi bai ce komai ba ya sake matsawa kusa da Bikhatir, a kausashe yace "Me ya kawoka nan Bukhatir?" A ladabce dan ya samu abinda ya ke so ya sunkuyar da kai yace "... *Kuyi hak'uri da wannan, na so ya fi haka wallahi.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:37 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *19* A ladabce dan san ya samu abinda ya ke so ya sunkuyar da kai yace "Sarki na, mhe zai hana ka zauna sai mu tattauna." A wulak'ance sarki Musail ya nuna kan shi yace "Da wa? Da ni? Ai har abada, ka manta rabuwarmu da kai ne?" Murmushi Bikhatir yayi ya sake yin k'asa da kan shi yan tuna rabuwarsu ta k'arshe wacce basu sake had'uwar ba sai yau kuma yanzu, shekarun da suka gabata a baya gaba da gaba kuma ido cikin ido Bukhatir ya kalli sarki Musail yace _" Na yarda kayi nasara a kai na a kan ta, ban damu ba ko dan kana da mulki a hannunka ne kayi nasara a kai na, amma ka sani daga yanzu ni da kai gaba ce a tsakaninmu dan ka rabani da matar da nake da burin ta zama ta wa, shi kan shi wanda take so a matsayin abokin gaba na dinga kallonshi, kuma a kowace wucewar rana neman hanyar da zan kassarashi nake, na yi farin cikin mutuwarsa fiye da tunaninka, amma yanzu mutuwarka ita ce abar harina."_ Sanyayyar murmushi ya kuma sako dan sai yanzu kalaman suka bashi dariya ma, sarki Musail ma murmushin yayi yace" Da alama ka tuna, dan haka ka gaggauta barin nan kafin na sa a cire maka kai, komata ka shigo." Dhurani ne ya sunkuya daf da kunnenshi yace" Ina ga fa zai fi mu saurare shi, haka kawai ba zai zo ba idan babi dalili mai k'arfi." Kallon shi yayi yace" Malami ina so ka sani duk wani abu da zai min barazana da rayuwata babu ni babu shi, ka fi kowa sanin haka." Kallonsu Bukhatir yayi yace" A gafarce ni ranka shi dad'e, maganar dake tafe da ni mai mahimmanci ce, magana ce akan gimbiya Zafeera, na san zaka so jin inda take? Tare da kuma wa take?" Girgiza kai sarki yayi yace" Ta ya zan iya yarda da kai?" Nuna masa k'ofa yayi yace" Gimbiya Zafreen, ai ta dawo cikin k'oshin lafiya, ko bata fad'a maka tare suke da yar uwarta a can ba a hannu na?" Shiru sarki Musail yayi yana kallon fuskar Bukhatir, ya jima haka alamar yana ta tunani kafin ya jinjina kai ya taka a tsanake, wata k'ofa wacce wanda mai kallo zai yi tunanin ban d'aki ce ya bud'e ya nunawa Bukhatir yace" Akwai buk'atar muyi sirri?" Da girmamawa yace" Me zai hana." Bin bayanshi yayi da ido sarki Musail ya ma Dhurani signar ya biyoshi, shi ma wucewa yayi a k'arshe suka bar Zeyfi tsaye dan sauran abokan tafiyar sjna farfajiyar gidan, ganin haka ita ma sai ta koma ta zauna tana gyara lullub'inta ta maida hankalinta ga kallo b'angare d'aya kuma tana tunanin ko me ya sa ya zo nan da ita kuma? A ciki kuwa zazzaune sukayi suna ta kallon juna kafin sarki Musail yace "Ina jinka? Me yasa ka sace min yarana duka biyun?" Murmusawa yayi ya sauke numfashi yace "Ba na sacesu bane dan na cutar da su." Da sauri sarki Musail yace "To me ka musu?" Numfasawa yayi sosai ya d'an muskuta yace "A makarantar da su gimbiya suke akwai wasu makusanta na, daga bakinsu na samu labarin lallai ana bibiyarsu, da fari ban d'auki abun da mahimmanci ba saboda abunda ke tsakanin mu, amma a ranar da wata yar ajin su gimbiya Zafreen ta fad'a min ana shirin d'aukesu, sai na yi gaggawar tayar da hatsaniya dan na d'aukesu ba tare da hankalin kowa ya kai cewa su ne kawai aka rasa ba, sai dai kash ! Sarki Wudar yana da matuk'ar wayo da kuma mutane sosai, duk tsaron da nake ganin na ba wa gimbiyoyinmu saida ya d'auke mafi mahimmanci da tsadar." Nisawa sarki Musail yayi yana kallonshi yace "Kenan yanzu gimbiya Zafeera tana hannun Wudar?" Jinjina kai yayi yace "Shakka babu." "Ta ina ya bi ya d'auketa a cikin gidan da kake ikrarin ka bata tsaro?" Ya fad'a yana watsa mishi wani kallo, ba tare da alamar tsoro ko firgita ba yace "Na yi iya k'okari na wajen killacesu, saidai ko ma ta ya ya suka d'auketa a gidan nan na fi tunanin sa'ilin da sarki Wudar ya buk'aci mu keb'e ne ni da shi, to a lokacin mutanenshi suka d'auketa, ko kuma wannan d'an na shi." Jinjina kai sarki Musail yayi yace" Shikenan, zai gane yana tare da kadarata ma fi tsada da daraja a duniya." Da sauri Bukhatir ya kalleshi yace" Yawwa sarki na, ina so kayi iya k'ok'arinka wajen..." Shiru yayi ya had'e maganarsa sakamakon kallon da sarki Musail d'in ya masa, sunkuyar da kan shi yayi yace" A gafarce ni." Wani malalacin murmushi sarki Musail yayi yace" Har yanzu ban ji zuciyata ta gama yarda da kai ba Bukhatir, kai ma nasan kana son ganin bayana, ka samu Zafeera kuma ka rabu da ita ta sauk'i haka, da wuya gaskiya." A ladabce yace" Ka yarda dani sarki na, babu hannu na a b'atanta, hasalima sanda sarki Wudar ya zo ya so yi min tayin gimbiya Zafeera da duk abinda ya mallaka, amma na nuna mana darajarta ta wuce haka." Wata yar dariya yayi yatsare shi da ido yace" Amma me ya kai shi gidanka a ranar data kasance tana gidanka?" Kura masa ido yayi yace" Iyeh?" Wani kallon firgitarwa Dhurani ya masa yace" Aka ce me ya kai shi gidanka a wannan lokacin? Wata k'ulalliya xe a tsakaninku ?" Girgiza kai yayi yace" Kamar yanda na fad'a maka yana da mutane da dama da suke masa lek'en asiri, kar ka k'aryatani idan har na fad'a maka a masarautar nan ma yana da yan sa ido, dan ta hakane ya samu cikakken labarinta." Kallonshi yayi kamar zai hango gaskiya a fuskarshi sai kuma yace" Na yarda da abinda ka fad'a yanzun, amma Bukhatir..." Ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya d'ora da" Alamu sun nuna a matse kake da son ganin an samo gimbiya Zafeera, shin idan aka yi hakan me ye tukuicinka kai?" Gaba d'aya gabansa ya yanke ya fad'i ya shiga tunanin abinda zai fad'a masa, amma yanda ya tsareshi da ido yasa dole ya sunkuyar da kai yace "Farin ciki ma ya wadace ni idan har d'iyar yar uwata ta fito a hannunshi cikin k'oshin lafiya." Dariya sarki Musail ya bushe da ita kamar wani mahaukaci ya dinga gaggab'awa, da k'yar ya tsagaita kuma kamar ba shi ba ya kalli Bukhatir fuska a hade yace "Shikenan, zamu gani." Juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya ba tare daya juyo ba yace "Ba dan kar ka fita kana fad'in ban iya tarban bak'i ba, da ko ruwa ba zan ba ka ba Bukhatir dan nasan manufarka a kai na, amma karamci na ya isa insa a wadataku da abinci ko dan labarin daka siyar min." Da mamaki Bukhatir ya kalli k'eyarsa cike da takaicin wulak'ancinshi, wato ya ma d'auki abinda ya fad'a masa a matsayin labari har kuma ya siya? Sarki Musail ne ya katse masa shirunsa sanda ya juyo a hankali ya kalleshi yace" Ya suke? Suna cikin k'oshin lafiya?" Wani kallo Bukhatir ya mishi yana ji kamar ya mik'e ya shak'eshi, wallahi da yana da sarauta a lokacin babu abinda zai hanashi d'urawa Musail ashar saidai duk su k'one a nan, iyayen Juman fa yake tambayarshi, shi bai san komai ba dangane da yanda aurensu ya kasanxe da Juman, amma dai tabbas ya fahimci akwai barazana a ciki wacce ita ce ke d'awainiya da iyayenta har yanzu, tunda ya d'auketa daga garesu shekara ashirin da bakwai har yau bata tab'a taka k'asar Egypt ba ko da sunan taro bare da niyyar ganin mahaifanta, hakazalika su ma basu tab'a yunk'urin kawo mata ziyara ba, tsufa ya cimmu su sosai amma damuwarta ita ce ta k'ata tsofar da su, dan wasu lokuta har k'aura sukeyi daga masarauta su ware kansu gefen gari su hana kowa zuwa inda suke. Amma dan rashin mutumci shi ne yake tambayar wai suna lafiya? Da k'yar ya d'aga labb'anshi yace "Suna lafiya, sai dai ba sa cikin farin ciki." Tab'e baki Musail yayi yace "Hakane zai kasance dama, kuma kai ma nasan ba ka farin cikin, amma ka sake jaddada musu su sake yin nesa da ita, dan halin da take ciki yanzu idan suka ji zuciyoyinsu bugawa zasuyi su mutu a take." Yar harara Bukhatir ya wurga ma k'eyarsa sannan ya jinjina kai alamar to, ficewa yayi Dhurani na bin bayanshi shi kuma ya bi su da kallo da son sanin me kuma ke faruwa da Juman d'in? Tana ina ma? Me yake damunta? Shin tana farin ciki da auran waccen dabban ne ko kuma a'a? Girgiza kai yayi cike da rashin jin dad'i ya d'auke kan shi daga k'ofar yana d'an jan tsaki, mik'ewa yayi ya fito ya dawo falon ya samu Zeyfi zaune tana kallo, haushi ya ji ta bashi da kallon fuskarta, gefenta ya zauna yana sake murtuke fuska, ita kuma cikin ladabi ta kalleshi tace "Lafiya ko? Me kuka tattauna haka? Naga kamar ranka b'ace?" Ture hannunta yayi data dafa na shi hannun yace "Ba komai malama, zaki iya yi min shiru." A sanyaye tana had'e kukan dake taho mata a mak'osho tace "Me zai hana?" D'ora kan ta tayi bisa kafad'arshi taake cukukuiye hannunshi tana siraro yar k'walla, cikin jin haushi ya kalleta dan har k'asan zuciyarshi yake jin tsanar yarinyar, baya sonta bai kuma tab'a son ta ba, ita kawai zab'in mahaifinsa ce ba yanda ya iya, amma shi kad'ai yasan irin dakon kayan da yake a game da ita, zama da wanda baka so babban k'unci ne da zai iya baibaye maka rayuwarka har abada, indai yana kusa da ita to baya farin ciki bare murmushi, ita kuma ga ta da na ci da jaraba a ganinshi, shiyasa in zaiyi wata bai nemeta idan ta kai kanta gareshi sai ya kirata da jarababbiya mayya. Yanzu ma ya so tureta daga jikinshi, amma daya tuna sarki Musail ya ce zai wadatasu da abinci saiya k'yaleta, ammafa sai tsaki yake yana ta had'e fuska kamar kashi nea jikinshi, yayin da ita kuma take jin wata nutsuwa na sauka a zuciyarta na ganin bai turetaa jikinshi ba, sai ta ssamu kan ta da sake shige masa tana sauke ajiyar zuciya. *Giobarh* *Da yamma* sarki Wudar na zaune a lambun cikin masarautar tare da fadawa biyu dake nesa da shi yana jin dad'in yanayin, wazirinsa ne ya shigo bayan mai tsaron k'ofar ya masa izinin shiga, da sauri kamar zai tashi sama ya k'araso, zube gwiwoyinshi yayi k'asa yana mik'awa sarki Wudar takardar hannunshi yace "Shugaba na, gashi, akwai matsala fa babba." Rai b'ace ya kalleshi ya karb'i takardar yace "Waziri ba na fad'a hutu nake buk'ata ba kar wanda ya dameni?" A kid'ime yace "Ka gafarce ni yallab'ai, wannan takardar ta fito ne daga sarki Musail, hankalina ne a tashe shiyasa." Da sauri ya shiga warware takardar ya k'ura ido dan karantawa, firgitattun kalamai ne kamar haka _"Daga yanzu zuwa wayewar garin gobe ina buk'atar ganin 'yata gimbiya Zafeera dake hannunka, watsar da buk'atata kuma yana nufin yak'i kake nema da ni, kuma a shirye nake da fuskantarka dan ina da adadin dakarun da zasu iya k'wato min babbar kadarata."_ A razane ya kalli wazirin yana jin zufa zata keto masa, jefar da takardar yayi ya tunkari hanyar fita, da sauri wazirin mmaa ya bi bayanshi yana mai son jin hukuncin da sarki Wudar d'in zai yanke, dan in har ya zab'i yak'i da sarki Musail to fa shi dai kam babu hannunsa, magana ta gaskiya ma zai tattara iyalinsa su bar k'asar har su gama sai ya dawo, dan ya sani ne ba zasu iya da sarki Musail ba, alfaharinshi kad'ai ya isa ya saka shi d'auko wasu rundunoni daga mak'wabtan masarautu dan su yak'esu su kuma yi kaca-kaca da su. *Ayam* na d'akinta zaune duk ta matsu dare yayi ta ga abun bazatar nan ta ji an banko k'ofar an fad'o, da sauri ta mik'e tsaye tana gyara rigarta, da ladabi tace "Barka yallab'ai." Murmusawa yayi tare da saita nutsuuwarshi wuri d'aya sannan yace "Barka gimbiya Zafeera." Kallon idonshi tayi tace "Yallab'ai, zan fi jin dad'i idan ka kirani da Ayam." Murmushi yayi ya rik'o hannunta cikin na shi, fad'uwar da gabanta yayi ne yasa ta saurin saka idonta akan fuskarshi, kakkausan kallo ne ta masa dake nuni da me hakan ke nufi? D'an motsa hannunta tayi alamar tana so ta k'wace, amma sai ta ji kam ya rik'eta sosai, jan ta yayi zuwa bakin gadon suka zauna, sam ta k'i d'auke idonta a kan fuskarshi yayin da shi kuma ya kasa kallonta saboda kallon da take masa, idonshi na kallon cinyoyinta duk da cikin riga suke ya shiga fad'in "Gimbiyata, ina so ne na fad'a miki wani abu, sai dai ina jin tsoro." Mutsu-mutsu ta dinga yi da hannunta saida ta k'wace kafin ta d'an kawar da kan ta tace "Ina jinka yallab'ai, fad'a min ko menene." Gyara zamanshi yayi ta hanyar matse mata wuri, da sauri ta ja baya ta sake jefa masa kallon bansan iskanci tare da yatsina fuska tace "A'a yallab'ai, wai me ye hakane?" Fuskarshi d'auke da murmushi yace "Kina ji ko? Ban san ko wani ya fad'a miki tarihinki ba..." Da sauri ta jinjina kao tana sake matsawa baya tace "E e, an fad'a min, amma ban yarda ba, watak'ila kai zaka fad'a min gaskiya." Tsurawa fuskarta ido yayi yace "Kinsan komai game da ahalinki kenan?" Girgiza kai tayi tace "Ta ya zan san komai a game da su? Bayan ko kamanninsu ban sani ba." A nutse ya sake kallonta yace "Kinsan bayanin b'atanki?" A shashance tace "E, yallab'ai Umad ne ya fad'a min wai mahaifiyata ce ta bayar da ni dan ta kareni." Da alamar tambaya a fuskarshi yace "Umad? Dama kun yi magana da shi ne?" Tuna kalaman Umad da tayi cewa saboda tsaro yake nesa nesa da ita yasa ta saurin fad'in "A'a ai d'azu ne da ka ce mu jira a waje, mun fara maganar sai kuma na nuna masa ban fahimci komai ba kawai." Jinkina kai yayi alamar gamsuwa yace "Kin tabbatar ya fad'a miki mahaifiyarki ta ceci rayuwarki daga masu son cutar dake ne?" A gatsine tace "Haka ya fad'a, amma ni ina ganin me ye dalilin da zai sa a rabu da ni tun jinjira? Shin masu son cutar da ni d'in suna tare da ni ne a lokacin da take ganin rayuwa a cikinsu zai sa ni cikin had'ari?" "Tabbas." Ya fad'a yana kallonta, da mamaki ita ma ta kalleshi tace "Kamar ya?" Fuskantarta yayi da kyau yace "Gimbiya Zafeera, a lokacin masu son kasheki dayawa ne, saidai wanda ya fi su had'ari kuma babban cikinsu shi ne, sarki Musail, wato *mahaifinki*." Irin kallon nan na galala ta masa kamar wacce bata hayyacinta, duk da labarin sabin iyayenta ba wai ta yarda ba ne, amma dai sai ta ji abinda ya alak'anta mahaifinta da shi ya mata ciwo yana kuma neman zautar da ita, zunbur ta mik'e tsaye tace" No! No! No... No...Hakan ba zai faru ba." Cikin d'aga murya tana nunashi da yatsa tace" Yallab'ai ku gaggauta dakatar da labarin k'anzan kuregen nan na ku, kuna neman ku haukata da wannan banzayen labaran, kun manta ni d'in yarinya ce? Shekaru na ba zasu d'auki wannan k'arairayin na ku ba, please yallab'ai ku daina na rok'eku." Had'e hannaye tayi alamar rok'o tace" Na rok'eka ka mayar da ni garinmu, ka taimaka ka kaini wajen iyayena ina son ganinsu." Mik'ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace"... *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:37 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *20* Mik'ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace "Kwantar da hankalinki gimbiya, ki ban lokaci kad'an zan tabbatar miki da haka." Girgiza kai tayi kamar zata fashe da kuka tace "Yallab'ai ni kawai ina so na koma rayuwata ta baya, wannan labaran da kuke bani zasu iya saka zuciyata tarwatsewa, ta ya mahaifin daya kawoni duniya kamar yanda kuka fad'a kuma zai nemi kasheni?" A nutse yana tsare fuskarta da ido yace "Saboda ci gaban mulkinshi ne, gimbiya Zafeera tarihin magabata ya nuna ke ce zaki kawo sauyi a k'asar nan baki d'aya, ba kuma zaki kawo wannan sauyin ba har sai mahaifinki baya kan karagar mulkinshi, to da haka ki fad'a min ta ya zai barki bayan ya tabbatar zaki kawo k'arshen mulkinsa?" Dafe kanta tayi da hannu wasu hawaye masu zafi suka zubo kan kumatunta, cikin nutsuwa da sanyayyar murya tace" Da a ce zan kasance yar wannan sarkin da gaske kamar yanda kuke fad'a min, tabbas da na hak'ura da kawo sauyin nan dan kawar da duk wata hatsaniya tsakanin 'ya da ubanta, da zan yi k'ok'ari na ga ran mahaifin nan bai b'ace ba bare har na taimakawa son zuciyarsa wajen yunk'urin kasheni." Murmushi yayi yace" Haka kike gani, shiyasa na ce ki bani d'an lokaci dan tabbatar miki." D'auke hannunta tayi ta kalleshi a marairaice tace" Yallab'ai zaka iya barina ni kad'ai?" Cike da tabbaci yace" Me zai hana gimbiyata? Na barki lafiya." Juyawa yayi ya fita inda ta bishi da kallo har ya fice, a hankali ta lumshe idonta wasu hawayen suka sake gangaro mata, bud'e idonta tayi ta k'arasa gaban tagar ta bud'e labule, inuwar yammacin da shukokin da suka k'awata gidan yasa ta jin son kad'aicewa da kuma samun kyakyawan yanayin nan, sakin labulen tayi da sauri ta shiga takawa ta fita a d'akin. Kallon fadawa da hadiman take ganin duk wanda suka had'e sai ya sunkuya ya gaisheta a yarensu na Gallois, har ta fita farfajiyar suna gaisheta, zagayawa tayi ta b'angaren hagunta ta k'arasa kusa da shukokin, wani dogon numfashi ta ja idonta a rufe sannan ta sauke numfashin tana mai bud'e idonta akan koreyan shukokin, sanyin mai d'auke da ni'imtacciyar iska sosai ya mata dad'i, rumgume hannayenta tayi tana sake sauke numfashi. Sannu sannu ta fara shiga duniyar tunani har tayi nisa, a haka kuma tana takawa zuwa ga shukokin, saida ta d'aga k'afarta ta tsallake d'an dakalin da aka zagaye shukokin, shiga tayi ciki tana taka k'ananun ciyayin a rashin sani har ta taka mab'allin pampon dake ba wa shukokin ruwa a duk sanda lokacin ba su ruwan yayi, tana takawa sai kuwa tsinin takalminta ya dannu wasu k'ananun k'arafu na suka bud'e suka shiga feshin ruwa suna juyawa ta ko ina. Zuwan abun bazata da kuma yanda ruwan ke fita kamar ruwan panpo na sama yasa ta zabura ta waro idonta, da sauri ta kalli k'asa dan tasan tabbas ita ce ta taka, tana ganin wurin ta sunkuya da niyyar kashewa, sai kawai ta ji daga bayanta wani bafaden yace "Ranki shi dad'e ki barshi zan kula da komai." Mik'ewa tayi ta fito ta shiga takawa da sauri tana tattaro rigarta tana matse dan har ta jik'e da ruwa, lokaci d'aya kuma tana mayar da gashinta baya tana matseshi shi ma. Duk abinda ke faruwa tsaf a idonshi yana hangenta daga sashinta ta saman bene, da fari kam dariya ce ta kubce mishi, amma ganin zata koma inda ta fito tana matse kaya sai ya k'urawa duk wani namiji dake wurin ido yana son ya tabbatar da inda idonsu suke kallo, shin sun tsareta da ido sakamakon jik'ewar kayanta suna k'are mata kallo? Ko kuma dai hankalinsu na kan aikinsu kamar yanda suka saba? Saida ya ga shigewarta kad'ai sai kawai ya ji wata nutsuwa ta d'an sauko masa, ko ba komai yasan dai zata canza kayan jikinta. A wani ikonce ya d'auke kan shi daga gurin yana had'e fuska ya mayar kan k'aramar na'urar dake hannunshi yana ta binciken abinda yake k'ara son tabbatarwa, dan shakkun da yake da akan Haman da wanda Ayam ta k'ara masa a kai yasa ya ji bai yarda da kowa ba hatta ita kan ta hukumar ta su bincike kan miyagun laifuka da hana ta'addanci. Ko da ta koma d'aki wanka tayi gaba d'aya sai ta canza kayanta, yanzu kam riga da wando ne saidai basu da maraba da irin kayan yan Pakistan, dan har da mayafinsu su ma wanda ta rasa wa ya siyo mata kayan nan haka masu rufe jiki? K'arshe dai mayafin a kafad'unta ta daidaita ta d'orashi sannan ta fito a d'akin dan zaman haka kurum isarta yake, gashi ita ko gudu na tayi bare sauran motsa jiki. Masu gadin dake tsaron k'ofar d'akin sarauniya wanda yau ne aka sakasu saboda alfarmar data nema gurin sarki Wudar d'in ta kalla tace "Zan iya shiga ciki?" Jinjina kai d'aya yayi yace "Bayan shugabanmu sarki Wudar da yarima Umad, ke ce ta ukun da aka yarje mana mu barki ki shiga ciki, sai kuma jakadiyarta mai kula da ita." D'an murmushi tayi a hankali suka bud'e mata k'ofar ta shiga, yanda dai take da tabbacin zata sameta haka ta samu, kwance amma kuma idonta bud'e alamar ba bacci take ba, murmushi ta d'ora a fuskarta tana k'arasawa kusa da ita d fad'in "Sannu da hutawa madam." Zaune tayi bakin gadon daf da ita ta kamo hannunta kamar yanda tayi da safe ta rik'e jim, tsurawa fuskarta ido tayi tace "Kina da buk'atar wani abu ne?" Kamar d'azu da safe sai kawai ta damk'e hannunta alamar e, jim Ayam tayi alamar tunani sannan tace "Abinci?" Sarauniya Kossam k'ura mata ido tayi bata damk'e hannunta ba alamar a'a kenan, d'orawa tayi da fad'in "Ruwa?" Shi ma dai shiru tayi, d'orawa tayi da "Zaki shiga toilet?" Ganin dai ba amsa sai tayi saurin fad'in "Kin gaji da kwanciyar?" Matsa hannunta tayi alamar e, murmushi ta fad'ad'a tace "Na gane, bara na samu wanda zai taimaka min sai mu fitar da ke waje." Mik'ewa tayi tace "Ina zuwa." Fita tayi a d'akin sai kuma tayi katarin had'ewa da wata hadimar, dakatawa tayi tace "Na ce ba, ina za'a samu kujera irin ta masu jinya?" Jim tayi alamar tunani sai kuma tace "Ina jin akwai a d'akin ajiye kaya, da ana d'ora sarauniya a kai idan za'a kaita d'akin gashi." Jinjina kai tayi tace "Ok, ki kawo min." Jinjina kai ita ma tayi a ladabce dan dukansu an nuna musu mahimmancinta sannan tace "To ranki shi dad'e." Juyawa tayi zata koma ciki tace "Idan kin d'auko ki kawo min d'akin madam." Da mamaki tace "Madam?" Cikin fara'a tace "E, d'akin sarauniya ba." Jinjina kai tayi ta wuce da sauri dan cika umarninta, komawa tayi d'akin ta shiga kiciniyar kamata, da k'yar ta tasheta tayi zaune ta gyara mata lullub'in kan ta na kayan da tasa aka d'auko da safe aka saka mata. Tana dawowa da kujerar masu tsaron k'ofar suka hanata shiga, k'wank'wasa d'akin sukayi Ayam ta lek'o, da kanta ta fad'a musu ita ta nemeta su kuma barta ta shiga dan ta kama mata sarauniya Kossam, suna shiga ciki suka kamata suka ciccib'a suka d'ora kan kujerar, robar ruwan dake aje Ayam ta d'auka ta d'ora kan cinyar sarauniyar sannan ta shiga turata a hankali suka fito. Duk inda suka wuce sai an kallesu da mamaki, suna kaiwa k'ofar fita sarki Wudar da masu take masa baya zasu shigo ciki, da mamaki ya tsaya yana kallonta yace "Gimbiya ya haka?" Kyab'e fuska tayi tace "Ta ce ta gaji da kwancin ne wuri d'aya, shiyasa zan fita da ita waje ta sha iska ita ma." Da mamaki sarki Wudar ya juya ya kalli waairi shi ma ya kalleshi sannan ya kalleta yace "Amma ta ya ya ta fad'a miki haka ? Ita da ba magana take ba." Sanyayyan murmushi tayi tace "Yallab'ai, tsawon shekaru kusan ashirin da bakwai mace na kwance babu lafiya, dan bata magana sai ku kasa fito da wata hanyar da zaku iya magana da iga dan jin damuwarta? Hakan sam bai yi ma'ana." Bata jira me zai ce ba kawai ta turata tare da rab'asu ta wuce suka fita, cikin dubara suka sauka a matakar k'waya d'aya dake akwai, suka sauka tayi kwana da ita inda ta nufa d'azu data fito. A hankali saruniya Kossam ta lumshe idonta k'am, wani dogon numfashi ta ja a hancinta tare da sanyayyan k'amshin shukokin sannan ta fesoshi ta bakinta, har yanzu kuma idonta a rufe suke tana sauraren wannan danddad'an yanayin data jima bata ji irinshi ba, hatta da d'an ta Umad mai tsananin bata kulawar sai dai ya bud'e mata taga ko ya sa a bud'e da tunanin ta ga hasken rana ita ma dan k'warin ido, ko kuma ta shk'i wani iska na daban mai cike da yalwa da babu takura a ciki, amma yau ga shi wata daga zuwanta jiya yau ta fito da ita ta shak'i sabon iska mai tattare da nagartaccen oxygen. Bud'e idonta tayi a hankali ta sauke akan shukokin duk da duhu ya fara yi, saida Ayam ta kai ta daf da wurin sannan ta dakata, zagayawa tayi ta durk'usa gabanta tana kallon wani bayyanannen farin ciki dake fuskarta tare da nuna jin dad'in fitowar ta waje, ita ma murmushi ta mata tace "Yanayin ya miki dad'i ko madam?" Lumshe ido tayi alamar e, sake fad'ad'a murmushinta tayi tace "Da zan zauna a gidan nan da kullum na dinga fito da ke kema kina ca'za iskar shak'arki." Wani kallo sarauniya Kossam ta mata mai d'auke da alamar tambaya, fahimtar haka yasa Ayam fad'in "Ina son barin nan madam." Tsareta da ido tayi tana son tayi magana mai tsayi da ita sai dai babu baki, mik'ewa tayi tsaye ta dafa hannunta tace "Bari na d'an barki ki huta kad'an." B'angaren ta nufa zata koma amma lura da wani b'angare da bata san na waye ba? Kuma baya da kyalkyali kamar sauran yasa ta nufa can b'angaren, dan ko dogari babu ko d'aya a bakin k'ofar, tayi sa'a kuma k'ofar a bud'e take, tana kwank'wasa ta ji shiru sai kuma k'ofar ta d'an bud'e, a hankali ta tura ta shiga. Falon shiru hatta da hasken fitila ma ba mai haske bane sosai, tana cikin k'arewa d'akin kallo ganin wani sassauk'an tsari dake gareshi mai birgewa, ba zato ba tsammani ta a daidai k'aramin teburin tsakiyar da taga laptop ajiye ta ji tayi tuntub'e, tuntub'e kam ba k'arami ba dan abu ne ta ji tayi karo da shi kamar mutum, hakan kuma yasa ta tafiya gaba d'ayanta ta gaba har saida ta ji ta tsallake binda ke gaban na ta sannan ta fad'i, amma kuma ikon Allah sai ta ji bata kai k'asa ba an rik'eta, kuma ko shakka ba tayi cewa mutum ne ya rik'eta. Umad dake zaune kan sallaya gama sallarshi kenan yana tasbishi da hailala da takbiri ya ji an k'wank'wasa d'akin, da ya ji an shigo kula sai ya fara tunanin kalar tijarar da zai saukewa ko ma wane/ce hadima ce suka shigo masa d'aki bai bayar da izini ba, kafin ya ankara shi ma ya ji an tokareshi a k'ugu da k'afa sai kuma ji da yayi ana neman tausheshi daga zaune, dan haka ya fahimci ko ma wanene bai san da shi ba, da sauri ya tare mai neman fad'o masa ko dan kar su kassara dukansu. A cikin siririn hasken suka had'a idonsu, tsaf irin rik'on nan ne ya mata na d'aukar jarirai, k'afafunta a mik'e har rigarta ta d'an 'dage zuwa gwiwanta, hannun na hagu kam a k' amk'ame yake kan kafad'ar Umad duk ta zaro ido saboda tsorata da tayi. A hankali ya sauke wani tattausan numfashi ya d'an lumshe idonshi sakamakon b'oyayyan k'amshin turaranta da baya tashi sosai sai ga wanda suka samu kusanci irin haka, dan kuwa rexona ne mai sanyayyan k'amshi da dad'i. Lura da tayi har wani k'ara tallabota yake yi a jikinshi kamar zai rumgumeta yasa ta d'an muskutawa ta kyabta idonta tace "Yallab'ai." Wani luuuu yayi da idonshi da sukayi mi shi wani ruwa ruwa ya k'ara k'ank'ancesu, kamar wanda baya hayyacinshi sai ya knara kusanto da fuskarshi kusan ta ta, da sauri ta d'auke hannuta a kafad'arshi ta shiga yunk'urin tashi zaune. A d'an zabure ya janye hannayenshi daga kumkuminta ya ja baya yana mik'ewa tsaye gaba d'aya, sai kuma ya had'e fuskarshi iya had'ewa ba alamar wasa, ita ma mik'ewa tayi tsaye tana gyara rigarta cikin raha take fad'in "Sannu yallab'ai, ka gafarce ni ban kula da kai bane sam, ashe dama nan ne sashinka?" Kawar da kan shi yayi tare da zaunawa kan kujerar ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya, a d'an kaikaice ya kalleta fuska a gimtse yace "Me ya kawoki nan?" Kallon salayyar daya tashi tayi, a nutse ta kalleshi ta saki murmushi, sosai shigarshi ta birgeta ya had'e cikin doguwar riga kalar ruwan toka da kuma wata k'aramar hula a kan shi kalar kayan, girgiza kai kawai tayi tace "Ba komai." Takawa tayi zata wuce ta tsakanin k'afafunshi da k'aramin tebur d'in, saida ta wuce sai kuma ta juyo ta kalleshi tace "Yallab'ai, wai me yasa baka sakani a addinin nan na ka ba? Akwai wani sharad'i ne na shiga? Ko kuma dai saida tarin dukiya? Ka fad'a min na ji idan zan iya mana." Kallonta yayi duba da ta zo da maganar da yake son yi mata tuni a kan ta, dan abun farin ciki da alfaharinshi ne a dalilinshi wani ya karb'i addinin musulunci, nuna mata gefenshi yayi alamar ta zauna, da zumud'i ta zauna tana kallon fuskarshi, a nutse cike da dattako da shan k'amshi na jinin sarauta daya gama ratsa duka sassan jikinshi ya kalleta kamar wata wacce ke bashi haushi, da k'yar ya d'aga labb'an yace "Da gaske kina son shiga?" Jinjina kai tayi tace "E, ina so sosai." A hankali ya d'an jinjina kai sannan yace "Akwai sharad'i, sharad'in kuma shi ne ki tabbatar da zuciyarki kike so ba wani ne ya tilastaki ko kuma wani dalili na daban, sannan addinin musulunci addini ne da bai yarda da ka shiga yau kuma anjima ka ce zaka fita ba saboda wani dalilin, saboda haka ma har aka tanadi hukunci mai tsaurin gaske akan duk wanda yayi ridda, ma'ana ya bar addininsa da gangan." Cike da tabbaci tace "Na yarda da sharad'in yallab'ai, ba zan tab'a fita ba, kuma da gaba d'aya zuciyata zan shiga." Jinjina kai yayi ya numfasa yace "Shikenan zaki shiga ke ma, amma fa idan kin shiga akwai abubuwa dayawada zaki koyesu daga gareni, kinga kenan babu maganar tafiya gida." Tsam ta kalleshi da mamaki tace "Kamar ya? Hakan na nufin zan ta zama a nan kenan?" Hararanta yayi yace "Ke kuma baki son haka ko?" Turo baki tayi gaba tace "E gaskiya, na fi so na koma gidanmu ni ma." Murya k'asan mak'oshi yace "Kuma kina da dalilin zama a nan?" Tab'e baki tayi tace "Ni dai yanzu fad'a min yanda anyi na shiga addinin nan." A nutse yace "Ki fad'i abinda duk na fad'a." Jinjina kai tayi ta k'urawa labb'ansa ido, a tsanake ya shiga furta mata kalmar shahada tana maimatawa har suka kai k'arshe, kallonta yayi da sanyayyan murmushi a fuskarta yace "Alhamdulillah, yanzu ke ma kin zama kamar ni, ma'ana kin musulunta." Da farin ciki ta bud'e hannaye da niyyar ta rumgume shi alamar nuna farin cikinta na zamowar silar shigarta addinin, sai kawai ya d'aga mata hannu fuska a had'e yace "Dakata, hakan da kike shirin aikatawa yanzu haramun ne a addinin ki, duk namijin da tsakaninki da shi akwai yiwuwar aure, to hakan laifi ne dan shed'an zai iya shiga tsakaninku." Da alamar tambaya tace "The devil?" Jinjina mata kai yayi yace "Yes." Mak'ale kafad'a tayi tace "Ok, i got it." Gyara zama tayi tace "To yallab'ai yanzu ya zan..." Sai kuma ta zaro ido ta mik'e da sauri tace "Ohh! Na manta na bar madam a waje." Juyawa tayi da gudu ta fita a d'akin inda ya bita da kallo da tambayar "Wace madam kuma?" Mik'ewa yayi da d'an sauri ya bita dan ganin wacece kuma a wane hali ta barota d'in, hangensu a gefen flower yasa shi k'arasawa da sauri, yana zuwa da mamaki ya durk'usa ganin mahaifiyarshi sai murmushi take saki yace "Mah, ya akayi kika fito?" Idonta ta d'aga ta kalli Ayam data mik'e tsaye ta had'e hannaye kamar wata mai tsaron lafiyarsu, d'aga kan shi yayi shi ma ya kalleta sannan ya kalli mahaifiyar ta shi yace "Mah, kin ji dad'in hakan ne?" Wani abu da Ayam ta lura da shi shi ne d'anta Umad da ido take amsa mishi magana sab'anin ita, da ido ta ga ta amsa mi shi alamar e, murmushi ya saki ya jinjina kai sannan ya juya ya kalli Ayam a sanyaye yace "Nagode da kulawarki a kan mahaifiyata." Girgiza kai tayi tace "Kamar mahaifiyata take ni ma, nauyi ne a kai na." Kallon da suka bita da shi yasa ta jin ta tsargu, musamman ma sarauniya Kossam da ko k'yabtawa ba tayi, hakan yasa ta d'an rusuna tace "Zan barku, idan zaka tafi ka kirani sai na mayar da ita ciki." Da sauri ta shige b'angaren nan tana jin gabanta na bugawa haka kawai, b'angare d'aya kuma zuciyarta na son kulawa da matar. Tana b'ace ma ganinsu sarauniya Kossam ta kalleshi tana murmushi, da ido ta masa alamar" Yarinyar." Sannan ta d'aga yatsunta biyu da k'yar a mugun wahalce tayi alamar" Kirki." Ma'ana" Yarinyar kirki ce." Sannan ta nunashi da yatsa ta kuma nuna hanyar da Ayam ta bi sannan ta nuna yatsarta mai d'auke da zobenta na aure. Wani irin k'walalo ido Umad yayi ya k'ura mata, a d'an rud'e yace" Mah! Kina nufin fa...?" Sai kuma ya girgiza kai yana d'an k'ank'ance idonshi, nufinta fa ya *aureta*, ya auri Ayam take nufi? To ta ya zai fara fad'a mata ya aureta dan ya kareta? A ladabce ya mik'e tsaye ya koma bayanta kawai ya kama hannayen keken kujerar ya dinga turata zuwa ciki ba tare da yace komai ba, dan kai tsaye ba zai ce komai ba har sai ya ga abinda Allah ya yi. *01:20* Juye juye take a cikin baccinta tana mai fatan ta farka daga mafarkin da take na matar dake ta mata magiyar ta taimaketa, kamar daga sama ta ji an daddab'ata, a zabure ta farka tana zuba idonta akan wanda ke gabanta, ba dan fuskarshi a bud'e take ba da ba zata ganeshi ba, da mamaki tace "Yalab'ai, kai ne yanzu?" D'ora yatsa yayi a labb'anshi yace "Shiiiii!" Jefa mata kayan hannunshi yayi yace "Saka wannan muje." Da kallo ta bishi ganin ya nufi taga madadin k'ofa, zura k'afafu yayi alamar dai dirawa zai yi ta nan kuma ta nan d'in ya shigo, da sauri ta sauka daga kan gadon ta warware kayan, cikin dubara ta saka ba tare da d'ar d'ar ba dan ya juya mata baya ne, tana sakawa ta kalli kanta ta madubi, sak shigarshi da ta ta iri d'aya ce, bak'ak'en kaya na sanyi masu hula da bak'ak'en takalmi, matsawa tayi kusa da shi tace "Na shirya." Juyowa yayi ya kalleta, murmushi ne ya kubce mi shi ganin kayan na shi sun mata yawa amla kuma sun mata kyau, tana kallo ya sauka daga tagar amma bata ji alamar an dira ba, hannu ya zuro mata ta mik'a masa ta haura ita ma, saida ta lek'a ne ta fahimci ashe tsani ya d'ora a wurin, takawa sukayi har suka sauka tana nan kafin suka shiga ta shukoki suna sand'a har suka isa bakin babbar k'ofa. *Ki hanzarta ki biya na ki idan baki biya ba, domin samun na ki tuntub'i wannan lambar 94-98-56-52* _Masu buk'atar ci gaban *BADAK'ALA* ku aje hankalinku, tabbs akwai labari kuma shi ma da gaske ya faru, saidai ina so ne na ga adadin mabiya *lu'u lu'u* dan bana so na rikita kai na sannan na shiga hakk'in wanda suka biya kud'insu._ *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:37 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *21* Mai gadin dama yana d'akinshi, dan haka suka lallab'a inda Umad ya bud'e k'ofar suka fita a gidan, wani kyakyawan babur suka tarar a k'ofar, cikin salo da k'warewa Umad ya hau tare da saka hular kwano sannan ya mik'o mata ita ma, karb'a tayi ta saka kafin ta hau suka d'auki hanya. A k'alla tafiyar minti talatin suka samu inda Umad kuma ya dakata a wata garage dake rufe, tana tsaye tana kallo ya bud'e k'ofar ya fito da mota k'irar benz bak'a wulik, saida ya koma ya rufe garage d'in sannan ta shiga suka kuma d'aukar hanya, awa d'aya suka share a motar nan suka isa wani k'arami kuma k'ayataccen gidan da ba zaka tab'a tsammanin wani daya tara kud'i sama da pan ko euro ko kuma dolar milyan biyar ba, dan k'arami ne sosai daidai da k'aramin ma'aikacin da buk'atar gida ba zata gaza samunsa ba. Saidai a cikin gidan tsofaffi biyun ke rayuwa ko d'an aike babu, tsofaffi biyun sukan ware lokaci zuwa lokaci dan su keb'e kansu su samu lokacin farin ciki a tsakaninsu da kuma walwala ba tare da d'awainiyar al'umma ba, dan sarautar k'asar Egypt ba k'aramar sarauta ba ce kamar kowace, hatta da tsarin tafiyar da mulkin daban yake da na kowace masarauta kamar yanda tsarin shigarsu da yarensu yake daban. Sau d'aya Umad ya buga k'ofar suka gane waye a k'ofa, tsohon ne ya k'araso cike da dattako da haiba ya bud'e, murmushi ne ya bayyana a fuskarshi sanda suka had'a ido da Umad, kaucewa yayi a hanyar alamar ya wuce sai ya rufe k'ofa, da fara'a Umad da kuma girmamawa yace "Barka." Kamar dai kowane sarki ko jinin sarauta shi ma da ido ya amsa mi shi tare da d'an murmushin gefen labb'a, kallon fuskarshi Umad ya sake yi yace "Ba ni kad'ai bane, na zo muku da wata kyauta ne ta musamman." Idonshi kawai ya d'aga zuwa bayan Umad d'in dan ganin menene, a hankali Umad ya rab'a gefe dan ya bashi damar ganin wacce ke bayanshi. Suna had'a ido wani yanayi na musamman ya ziyarcesu a tare, sanyayye kuma k'akk'arfan fad'uwar gaba suka samu a tare, sai dai kuma wata irin alak'a mai k'arfin gaske da suka ji ta k'ullu a tsakaninsu lokaci d'aya. Ayam kasa d'auke idonta tayi ta saki baki tana kallon tsohon kamar zatayi magana, sai take jin kamar fuskarshi ta mata kama da fuskar matar da take gani a mafarkinta, dan a duk sanda tayi mafarkin matar tana tashi ta kan kasa hasasho yanayin fuskarta, amma yanzu tana ganin tsohon saita ji kamar fuskar ce. Daga can k'asar zuciyarta take jin wata narkakkiyar k'aunar tsohon da bata tab'a jin tana ma wani mahaluki a duniya ba, hakan yasa ta alak'anta ko ma menene a tsakaninsu to tabbas alak'ar mai k'arfi ce wacce ta isa ta sa su gauraya su zama dunk'ulallen abu. A hankali ta tako ta shigo d'akin idonta akan na tsohon nan, yanda shi ma yake kallonta zai tabbatar maka abu iri d'aya suke ji a jikinsu da zuk'atansu, wasu k'walla ta gani a idon tsohon sun taru suna neman zubowa, cikin wata irin muryar kuka mai tattare da shauk'i tsohon nan ya bud'i bakinshi yace "Idan har abinda nake ji a yanzu gaskiya ne, hakan na nufin yau ni ne a gaban jikanyata? 'yar da' yata ta haifa?" Ayam kam tuni k'walla suka zubo mata suka shiga wanke mata fuska wanda ita kanta bata san dalili ba tace "Ban san asalin me nake ji ba sanda na gan ka, amma dai ina jin daban a kan ka, waye kai ? Me ye alak'ata da gidan nan? Me yasa nake jin haka dana ganka?" Wani lafiyayyan murmushi ya saki ya kamo hannayenta duka biyun zuwa ciki, bin shi ta dinga yi har saida suka shiga tsakiyar falon, dan yanayin ginin gidan sak irin zubin k'irar yan Turkey aka mi shi, tsohuwar data samu zaune a kan kujera ta kwanta baya sosai jikinta lullub'e da tattausan bargo ne ya nemi haukatata. Sak fuskarta take gani a tsohuwar, abu kawai daya banbanta su shi ne ita yarinya ce ita kuma tsohuwa, ita ma mik'ewa tayi da sauri tana sake k'urawa fuskarta ido, irin dai abunda suka ji a farko haka yanzu ma suka ji, da sauri ta k'araso tana kallon mai gidan na ta tace "Habibi, kamar akwai wani abu tsakaninmu da wannan ko?" Jinjina mata kai yayi sannan ya juya ya kalli Umad dake bayansu a tsaye, a hankali tsohuwar ta kai hannunta wuyan Ayam ta kama sark'ar nan tana kallo, fashewa tayi da kuka ba tare data saki sark'ar ba tace" Wannan sark'ar ba zan manta ranar da waccen azzulumin ya sakawa 'yarmu ita a wuya ba bayan ya mana barazana da rayukanmu." Da k'arfi ta jawo Ayam suka rumgume juna tsam, Ayam da bata gama fahimtar me ke faruwa ba ita ma kukanta shiga rerawa, Umad kam wuri ya samu ya zauna k'afa d'aya kan d'aya yana kallonsu, sai tsohon ne ya rabasu ya ce su zauna, zaune tsohuwar tayi daf da Ayam ta rik'e hannunta gam kamar za'a rabasu, shi tsohon gefenta ya zauna suka sakata tsakiya. Kallonsu tayi dukansu tana ziraro wasu hawaye tace" Alamu sai k'ara nuna min suke Habbee da Utais ba iyayena bane na gaskiya, sai dai kuma bana so abinda ak fad'a akan mahaifina na gaskiyar ya tabbata, da haka ya faru zan so na yi ta zama a cikin rayuwar nan mai kama da mafarki." A tare tsofaffin suka d'ora hannunsu a kan ta da niyyar shafawa, amma da suka ji a tare suka d'ora sai tsohon ya janye na shi ya bar na tsohuwar, cike da kulawa da k'auna tace" Ayam hak'uri zakiyi, haka shi ne jarabawarki kin ji." Kallonta tayi tace" Ku su waye?" Ajiyar zuciya tsohuwar ta sauke ta nuna kan ta tace" Ni sunana *Bilkis* sarauniyar Egypt, wannan kuma *Abdallah* sarkin k'asar Egypt, mu iyaye ne ga mahaifiyarki wacce tayi nak'udarki wato Juman, gimbiyar Egypt sarauniya kuma a Khazira." Juyawa tayi ta kalli tsohon ta rik'o hannunshi tana kuka tace" Da gaske ku d'in ku kuka haifi mahaifiyata? Da gaske ne sarauniyar Khazira ta haifeni kuma ta bayar dani ga jakdiyarta?" Jinjina kai yayi yace" Tabbas gaskiya ne, duk da bamu had'u da mahaifiyarki mukayi magana baki da baki ba, amma dai abinda aka fad'a miki gaskiya, mahaifiyarki tayi hakane dan kub'utar da ke." Cikin matsancin kuka tace" To amma ce wa suke harda mahaifina ma cikin masu son kasheni, taya haka zai yiwu?" Sarauniya Bilkis ce tace" Zai yiwu, musamman ga mutum irin Musail mai son kansa da zuciyarsa, babu abinda ba zai iya aikatawa ba dan ganin mulkinsa ya ci gaba da wanzuwa a doron k'asa." Kallon tsohuwar tayi tace" Kenan gaskiya ne yana son kasheni? Idan har shi ya haifeni da cikinsae yasa zai nemi kasheni?" Ta k'arashe tana kallon duka dattawan, a nutse sarki Abdallah ya jawo kan ga ya d'ora a k'irjinshi ya shiga shafa kanta, a tausashe ya shiga fad'in" Shin yanzu lokacin da kike buk'atar sanin wannan ne? Me zai hana ki maida hankali kan mahaifiyarki wacce a yanzu take kurkuku a d'aure saboda ke." Da sauri ta d'ago ta kalleshi tace" Mahaifiya ta? Habb... Sarauniya?" Jinjina mata kai yayi yace" Ita." A rikice ta mik'e tsaye tace" Tana ina yanzu? Me yasa take d'aure a kurkuku ? Wane laifi ta aikata?" Mik'ewa Abdallah yayi ya kama hannayenta yace "Kwantar da hankalinki, babu laifin data aikata wanda ta cancanci wannan hukuncin, dama can shi ba adalin sarki bane, shiyasa yake ganin yaudara ce tayi data kub'utar dake daga sharrinsa." Sororo ta kalleshi tace "A tak'aice dai mahaifina ba mutumin kirki bane? To mahaifiyata fa? Ya zanyi ta kub'uta?" Girgiza kai Abdallah yayi sai kuma yayi murmushi yana kallon fuskarta yace "Duk da kowa ya yarda ke ce mai kawo sauyi a k'asar, amma bamu san ta ina kuma yaushe ne hakan zai faru ba, da fari dai mu zuba ido mu jira mu ga e lokaci zai mana, daga nan sai mu san abun yi." Cikin fashewa da kuka tace "To amma a ce ba zamu iya cetota ba har sai abinda lokaci yayi da mu?" Umad dake zaune yana ta kallonsu kamar ya samu wani kyakyawan film ne ya katseta da fad'in "Saboda shi lokaci ya fi komai adalci a rayuwa, shi ya fi yin sakamako mai kyau sannan ya hukunta kowa." Cike da tausayin kan ta ta koma kujerar ta zauna, a hankali ta d'ora kan ta a cinyar Bilkis tana shashek'ar kuka, shafa gashinta ta dinga yi tana fad'in" Kiyi hak'uri kinji, tsawon shekaru muka d'auka muna hak'uri mu ma, amma a yanzu zamu iya cewa komai ya kusa zuwa k'arshe." Kamo hannun Bilkis tayi ta rumgume shi a k'irjinta tace" Ku ma wai kun yarda ni yar baiwa ce? Wannan wace irin baiwa da zata saka kowa mararin halaka ka?" Gyara zama Umad yayi ya kalli fuskarta yace" A duniya kowane d'an adam da kalar baiwar da ubangiji yake hallitarsa da ita, Allah shi ne yafi sanin daidai da kuma ba daidai ba, wani mutumin a zahirinsa k'ansk'antacce ne kuma fak'iri, amma a bad'ini ubangiji kan iya aje baiwar da babu mahalukin da ya ma ita sai shi, ko a cikin littafi mai tsarki akwai ayoyi da dama da suke fad'akar da mu girmama d'an adam ko baka san shi ba, haka ma a hadisai ingantattu akwai irin haka, k'aramin misali da zan baki shi ne akwai wani sahabin Manzon Allah (S.W.A) da Allah ya hallice da siraran k'wabri, sai wata rana yana nufo majalisar fiyayyen hallita, sai sahabai suka dinga masa dariya suna nuna k'wabrinsa, a take fiyayyen hallita ya fad'a musu cewa wannan k'wabrin da suke gani sirara kuma k'anana, sun fi *dutsen* uhud nauyi a sikeli wajen Allah, dan haka su daina raina hallitar ubangiji." D'orawa yayi da fad'in" Haka kuma akwai wani sahabin Manzon Allah (S.W.A) da Allah ya jarabce shi da shan giya, kullum ya zo majalisin annabi ya kan zo ne a buge cikin maye, hakan yasa kullum sai annabi ya sa an mishi bulala, wata rana sai sahabbai suka dinga aibatashi suna masa fad'an akan me zai sa ba zai daina ba? Suna ta aibata shi sai annabi ya dakatar da su ta hanyar fad'a mu su ya zasu taimakawa shed'an a kan d'an uwansu, su mi shi addu'a mana Allah ya shirye shi, dan shi wannan da suke gani yana son Allah manzonsa." Gyara zama yayi yace" Kinga kenan zunubin da yake aikatawa bai hana ubangiji ya wadace shi da baiwar son shi da kuma manzon sa ba, dan samun wannan soyayyar ma babbar baiwa ce wace ba kowa Allah ya yake ba wa ita ba." A nutse ya ci gaba da fad'in" Ayam manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa ya fad'a mana, a cikin mutane akwai wanda da zai rantse ya ce za'ayi ruwa, to girma da darajarshi ya isa ubangiji ya tsallakar da rantsuwarshi ta hanyar kautar da shi daga yin kaffara, shiyasa babu kyau raina hallitar Allah kowace iri ce." Gyara zamanshi yayi sosai yana kallonta sanda take tashi zaune ta nutsu sosai tana saurarenshi yace "Ayam na yarda kina da baiwa ke ma, sai dai baiwarki ni a wajena a zahirance take, babbar baiwarki bata wuce canjin yare da ubangiji ya yassare miki kina yi ba, ke kan ki wani yaren baki san wane iri bane ko na wace k'asar ba, amma haka koke samun kan ki da shi a bakinki, inda aka samu matsala kuma shi ne da manyan dattab'ai suka shiga cikin lamarin baiwarki, hakan yasa aka dinga farfagandin zuwanki har maganar baiwarki ta fara zama kamar kasuwanci, da haka kuma sai mutane suka dinga yayatawa masu k'arawa na k'arawa masu ragewa suna ragewa, har aka tunbatsa baiwarki ta kai matakin da wasu suke ganin kamar zasu mayar dake waliyiyarsu, daga cikin masu nemanki dana tattauna da su burinsu kawai su had'a hannu da ke wajen hab'aka nauyin aljihunsu, ma'ana su mayar dake bokanya dan su dinga samun na kashewa." Wani dogon numfashi ya sauke ya dafe goshinshi yayi shiru alamar doguwar maganar nan tasa kan shi fara juyawa, Abdallah ne ya saki murmushi ya d'ora da fad'in" A wajensu babban malami Dhurani ma kusan haka take, malamin fada ne da mahaifinki ke matuk'ar yarda da maganar sa, saidai zan iya ce miki shi ne k'ashin bayan dake ingiza mahaifinki wajen ganin sun kasheki, dan kuwa ya san ko ba dad'e ko ba jima dole zalincinsu zai zo k'arshe, hakan yasa yake d'aya daga cikin masu son kasheki." Ajiyar zuciya sarauniya Bilkis ta sauke tace "Yarinyata, kinga tashi muje ciki ki huta, wannan labaran zasu iya tarwatsa miki tunaninki." Kallon sarauniyar Umad yayi yace "Ku tayata farin ciki, d'azun nan ta karb'i addinin musulunci ita ma." Da farin ciki suka kalleshi tare inda sarauniya ta jawota jikinta tace "Kai amma na taya ki murna, hakan yayi kyau sosai." Umad ma murmushin yayi yace "Saidai ku fara d'orata kan abubuwa muhimman dya kamata ta fara sani, dan lokaci bai bani damar sanar da ita ko da wankan daya hau kan ta ba." Mik'ewa sarauniyar tayi ta kama Ayam suka mik'e tace "Karka damu kanka da wannan, yanzun nan zan taimaka mata tayi komai." Kamata tayi suka nufi d'aki suka bar su nan zaune, suna shiga ta saketa ta nufi ban d'aki ta d'auko farin towel ta kawo mata tace "Cire kayanki zakiyi wanka ne." Cike da kasala tace "A wannan daren?" Murmusawa tayi amma ba tace komai ba sai kallonta har ta cire kayan ta d'aura wannan towel d'in, hannunta ta kama suka shiga ban d'akin, wata kujerar roba mai kyau ta nuna mata ta zauna sannan ta aje mata k'aramin bokiti da ruwa a ciki masu tsarki da tsarkakewa, sakata tayi ta cire towel d'in sannan ta ce ta d'aura niyya a zuciyarta zatayi wanka na tsarki na shiga addinin musulunci sannan ta fara da kama ruwa daga k'ugunta zuwa, a haka ta taimaka mata tayi wankan tsarki sannan ta d'aure jikinta da towel suka fito. *Suna* shiga ciki Umad ya sake gyara zama ya sauke numfashi ya kalli sarki Abdallah, cikin nutsuwa da son fahimtar da shi yace "Ranka shi dad'e, akwai wani abun da ban fad'a maka ba, ban san ta ya zaka fahimce ni ba." Murmushi ya masa irin na babba da yaro yana d'an girgiza kai a tsanake yace "Yarima Umad, karka damu kan ka, ka fad'i abinda kake son fad'a, ai yanzu mun zama d'aya." Sunkuyar da kai yayi k'asa yace "Magana ta gaskiya an d'aura mana aure da ita, amma fa..." Kallon sarki Abdallah yayi dan ya karanci yanayin daya shiga jin hakan, amma sai ya ga fara'a ce a fuskarshi da kuma mamakin dake nuna yana son jin yaushe haka ta faru? Sake sunkuyar da kai yayi alamar jin kunya yace" Ita kan ta bata sani ba, na yi hakane dan na tabbatar da zamanta a tare dani, dan na rasa wanda zan iya yarda da shi game da lamarinta bayan su Utais, su kuma a kowane lokaci za'a iya farmakarsu har da ita kan ta." Da tsantsar farin ciki sarki Abdallah ya dafa kafad'arshi yace" Masha'Allah Umad, ka yi aiki mai kyau gaskiya, hakan ya tabbatar min zaka iya yin komai akan jinkar nan ta wa." Da mamaki kad'an a fuskarshi yace" Amma yaushe haka ta faru?" Da kunya ya amsa da "A ranar dana samu had'uwa da su Utais, shi ha ba ni aurenta kuma na karb'a, bayan su da kai yanzu dana fad'a babu wanda ya sani." Jinjina kai ya sake yi yace "Hakan yayi kyau gaskiya, saidai wani hanzari ba gudu ba." Wani azababben fad'uwa ya ji gabanshi yayi da bai san dalili ba, hakan ya bashi damar k'ure sarki Abdallah da ido yana jiran ya ji me zai ce, cikin dattako sarkin ya d'ora da "Ina ga me zai hana ka fad'a mata? Dan gudun samun wata matsalar." Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sakayau a zuciyarshi kafin ya jinjina kai yace "Insha'Allah zan fad'a mata, amma ba yanzu ba, ina jiran lokacin daya dace ne." Jinjina kai yayi yace "Shikenan, amma dai ka kula, kar ka tsaya jiran lokaci kuma wani abun ya b'ullo." Murmusawa yayi a zuciyarshi yace "Hakan ma ba zai faru ba." A zahiri kuma bai ce komai ba. *Man d'umi* ta bata ta shafe jikinta da shi kafin ta mayar da kayanta suka fito, zaune suka samesu suna shan shayi suna ta murmushi alamar hira suke kuma tana musu dad'i, zaune sukayi inda Ayam ta kalli Umad cikin muryar data disashe tace "Yallab'ai yaushe zaka tafi gida? Dare fa yayi sosai, ko nan zaka kwana ne?" Kallonta sukayi dukansu inda sarki Abdallah ke sakin murmushi, cike da raha da nishad'in daya jima bai samu irinsa ba yace "Ai d'aki zamu ware muku na musamman ke da shi." Zaro ido tayi sai kuma ta kawar da kan ta ta tab'e baki tace" Ka daina fad'in haka." Dariya suka saka inda sarauniya Bilkis ta jawo kanta ta d'ora a cinya tace" Rabu da shi kinji, kwanta ki huta." Sarki Abdallah ne yace" Wane hutu kuma bayan yanzu zasu koma." Da sauri Ayam ta mik'e zaune tace" Me? Yanzu kuma? Ni gaskiya babu inda zan tafi, na zo kenan kawai shi ya tafi." Satar kallonta yayi ta gefe ido lokaci d'aya kuma ya d'auke kan shi, sarki Abdallah ne yace" Kin fa san duk sanda zai zo nan to ya kan faki ido ne, jimawar ta su a nan zai karkato da hankalin mutane da dama, kuma kinsan ba kowa ya san muna nan ba." Jinjina kai tayi tace" Hakane, amma ina so na zauna da ita." A nutse yace" Zaku zauna idan da rai, amma mu yi addu'ar komai ya daidaita tukuna." Jinjina kai tayi kamar zata fashe da kuka ta kalli fuskar Ayam ta shafi kumatunta tace" Allah ya miki albarka, ki kula da kanki kinji ko." Ita ma kamar za tayi kukan ta jinjina kai alamar to, mik'ewa tayi a kasalance ganin shi ma Umad ya mik'e, rumgume juna sukyi da sarauniya sosai har da matso k'walla, da k'yar suka rabu sannan ta juya ta rumgume sarki Abdallah, daddab'a bayanta yayi yace "Ki kula da kanki." Jinjina kai tayi ta d'ago daga jikinshi ta kalli fuskarshi, dariya tayi ta jawo farin gemunsa tace "Ina son wannan." D'an dungure mata kai yayi yace "Ja'ira, gemun na wa?" Dariya tayi ta d'an mak'ale a jikin sarauniya tace "To ai yayi fari ne sosai." Dariya suka saka gaba d'aya sai Umad daya murmusa yana girgiza kai dan shi ma abun ya birgeshi sosai, kallonta sarki Abdallah yayi yace "Kin san shekaru nawa ne a kai na kuwa?" Da yar harara ta kalleshi tace "Zasu fi d'ari ne?" Jawo hannunta sarki yayi hakan yasa ta tahowa kamar zata fad'a masa, sai kuma ya turata a k'irjin Umad yana fad'in "Kaga rabani da ita ku tafi kafin gari ya waye mu ku." Tsit sukayi suna kallon juna saboda tana fad'owa sai ya d'auka ko zata fad'i ne sai ya rik'e k'ugunta gam da hannunshi, jim sukayi suna kallon juna sai kuma ta d'an shiga k'ok'arin zamewa, da sauri ya saketa tare da juyawa yace" Saida safenku." Bai k'ara juyowa ba bare wani ya masa magana har saida ya fita, jiki a sanyaye ta bi bayanshi tana d'aga musu hannu, yana shiga motar ita ma ta bud'e ta shiga, saida suka ga tafiyarsu sun hau titi kafin suka rufe k'ofar suka koma ciki. Ta yanda akayi suka zo nan ta haka suka koma gidan, saidai suna isa asuba tayi fadawa har sun tashi kowa ya fara shirin tsayawa kan aikinshi, wanda da musulmai ne da sallah suke a lokacin, ganin mutane na ta shawagi yasa Ayam rik'e hannunshi gam a matuk'ar tsorace tace "Babu ta yanda zaka barni na shiga ni kad'ai, kawai mu tafi tare ka rakani." K'ok'arin k'watar hannunshi yayi yana fad'in "Sakeni malama, sallah zan yi." "Nima ai sallar zanyi, muje idan ma kasheni za'ayi a kashemu tare." Tayi maganar tana jan shi zuwa ciki, ba yanda ya iya haka ya dinga binta har suka taka matakalar d'aya ta tura k'ofar suka shiga dan masu tsoron k'ofar basu iso ba, falon shiru babu motsi kuma babu haske, hakan yasa shi zame hannunshi ya nuna mata hanyar yace "To wuce." Kallonshi tayi sai kula ta juya zata tafi, juyawa yayi shi ma zai fita suka ji muryar sarki Wudar yace "Daga ina kuke yarima?" Cak ya tsaya ya rufe ido alamar sam bai so haka ba, ita ma da sauri ta kalli inda ta ji sautin, zaune ya ke ya saka tv gaba saidai bata san kallo yake ba ko kuma akasin haka, gyara tsayuwarta tayi tana kallon Umad daya juyo a hankali ya kalleshi shi ma. Sosa k'eyarshi yayi cikin rashin gaskiya yace "Am.. Pah, dama..." Da sauri Ayam tace "Yallab'ai ai kasan ni d'in dama na saba tashi a cikin bacci, wasu lokuta ma doguwar tafiya nake yi ba'a sani na ba, yanzu ma haka ce ta faru sai dai nayi sa'a ban yi nisa ba na had'u da d'anka, shi ne ya dawo dani." Kallon Umad tayi ta yatsina fuska tace" Wannan baiwar ita tafi bani wahala kam, ina tsoron wata rana na b'ata a haka." Juyawa tayi zata haura sama tace" Saida safenku, nagodz d'an yallab'ai." Da kallo sarki Wudar ya bi ta har ta fara hawa saman, a kunyace Umad ya kalli mahaifin na shi yace" Sorry..." Bai k'arasa fad'an abinda ya ke son fad'a ba ya tsaya cak, da sauri ya rab'a mahaifin na shi tare da k'arasawa gaban tvn, d'aukar remonte d'in yayi ya k'ara sauti, sunan da aka ambata wato *Ayam Utais* yasa ita kanta Ayam dake neman hayewa gaba d'aya ta dakata ta juyo ga tvn. Da sauri ta shiga saukowa ta dawo suka k'urawa tvn ido, sanarwa ce ta b'atanta daga gwamnati, inda aka nuna canal Jacob da su Deeyam duk suna bayar da shaidar abinda suka sani, ba wannan ne ya d'aga musu hankali ba kamar kud'in da aka fad'a gwamnati ta sa zata bawa duk wanda ya kawo ko da labarin inda take. Cikin rad'a Ayal ta matsa daf da Umad tace "Amma ai baka fad'a min gwamnati ma nema na take ba?" Shi ma cikin rad'ar yace "Ni la bansan daga ina aka samu wannan kusurwar ba, ko me ye tasu manufar su kuma?" Cikin rad'a tace "Ka binciko to, dan sam bana son rigima da gwamnati, saboda na tsani dokokinsu da kuma kurkuku." Juyowa sarki Wudar yayi ya kallesu yace "Me kuke tattaunawa?" A tare da alamar rashin gaskiya suka amsa da "Ba komai." Jinjina kai yayi ya sauke numfashi ya kalli Ayam yace "Ba lallai mu wayi safiyar nan lafiya ba, dan jiya mahaifinki ya mana barazana kan cewa zai yak'emu." Da mamaki suka kalli juna ita da Umad kafin ta kalleshi tace "Akan wane dalili?" Kallon Umad yayi sannan ya kalleta yace "Saboda ke." D'an k'ura masa ido tayi hankali tashe tace "To me ye abun yi?" Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske sannan yace "Kasa bacci na yi daren yau, shiyasa kuka sameni a nan ina ta tunanin mafita, mafita kuma d'aya ce zata sa ki kub'uta daga hannun mahaifinki, sannan ki samu dalilinki na zama a nan cikin aminci." Girgiza kai tayi tace "Me ce ce wannan mafitar? Ka fad'a min ni kuma a shirye na ke inhar zata hana jinin mutanen. Da basu ji ba basu gani ba zuba." Tsakiyar idonta ya kalla tare da kawar da duk wani fargaba da tsoro sannan yace "Mafitar ita ce *ki aure ni*." Wani irin zaro ido tayi ta ja baya tana kallonshi a gurgunce, girgiza kai ta fara yi alamar sam ba zata iya ba, kai sam ba zata iya ba. Umad kam wani bahagon numfashi ne ya taho masa da babu gaira babu dalili, wanda ya tabbatar da yana tsaka da cin wani abu ne da ya sark'e, a wani bala'in'en kallo ya dinga watsawa mahaifin na shi, wani abu yake d'an ji kad'an hak yana neman taso masa daga zuciyarsa a game da mahaifin na shi mai kama da jin haushi haushi da takaici takaici, sai yayi kamar zai yi magana sai kuma ya dakata, tabbas a razane yake kuma hankalinshi a mugun tashe yake, sai ya rasa dalilin samun kan shi a wannan yanayin da yayi a lokacin, shin kishin mahaifiyarsa ne yasa shi jin haka? Ko kuma dai martabar aurensa dake kan ta ne yasa ji haka a kan maganar? Kallon Ayam yayi yana son jin me zai fito daga bakinta, yanda tayi sororo ta sauke idonta k'asa tana ta wainasu ya tabbatar masa da tunani take. Da sauri ta d'aga kan ta ta kalli sarki Wudar ita ma da shi ma yake kallonta, cikin raunatacciyar murya tace "... *Mai son samun na ta ta min magana akan wannan lambar 94-98-56-52*. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:38 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *22* Da sauri ta d'aga kanta ta kalli sarki Wudar ita ma da shi ma yake kallonta, cikin raunatacciyar murya tace "Ina so na had'u da mahaifina yallab'ai." A tsorace suka kalleta sai sarki Wudar da yayi saurin fad'in "Me kika fad'a? Kinsan me kike nufi kuwa?" Jinjina kai tayi tace "E, na sani yallab'ai, ina so na ga fuskar mahaifina." Girgiza mata kai yayi yace "Saboda me? Gimbiya Zafeera kasheki zai yi idan kika fuskance shi." Jinjina kai ta sake yi tace "Na sani, amma kafin ya kasheni ina so na kalli fuskarshi, ina so nayi musayar numfashi da mahaifina, komai lalacewarsa shi dai ya kawoni duniya, kai kan ka da kake neman aure na a yanzu zan iya amincewa ne idan mahaifina zai saka min albarka." Da mad'aukakin mamaki ya kuma kallonta irin duba na tsanake, Umad dake kallonta hankali tashe ne ya matsa daf da ita ya kalleta yace" Hakan fa ba zai yiwu ba, akwai had'ari sosai." Mak'ale kafad'a tayi tace" Ba wani had'ari, kuma ma me ye asararku dan ya kasheni?" Rumgume hannaye tayi ba alamar wasa tace" Ina so na je." Numfashi sarki Wudar ya sauke yace" Kin tabbata idan har na sadaki da shi zaki amince da buk'ata ta?" Tsurawa fuskarshi ido tayi na sakanni sai kuma ta d'aga kai tace" Na yi alk'awari." A mugun tsorace ba tare da sanin yayi ba ya damk'i wuyan hannunta da bala'in k'arfi saida tace" Aouch!" Kallonshi tayi a tsorace ita ma cikin siririyar murya tace" Yallab'ai you hut me." Rintse idonshi yayi ya cije leb'en k'asa, a hankali ya shiga sauke numfashi yana daidaita nutsuwarsa tare da sassauta rik'on daya mata har ya saki hannunta gaba d'aya, bud'a idonshi yayi a sauke a kan ta, da k'yar ya k'ak'aro maganar yace" Kuskure kike aikatawa, karki aikata haka Ayam." Cikin rad'a tace" Me yasa? Da matsala ne?" Kawar da kan shi yayi yace" Babba ma kuwa." K'ura masa ido tayi tace" Wace iri yallab'ai." Sarki Wudar ne ya katsesu da fad'in" Tunda kin min alk'awarin haka ki shirya, zuwa wayewar gari zan sa a rakaki zuwa fadarki tamkar sarauniyar k'asar nan." Da farin cikin zata had'u da mahaifiyarta ta saki murmushi, ita har zuciyarta a uba take kallon tsohon nan, musamman ma daya tara farin gemun nan kamar na kakanta, uwa uba kuma mahaifin malaminta ne yallab'ai, sai kawai ta bud'e hannaye tsabar jin dad'i ta nufi sarki Wudar zata rumgume shi. Tana daf da kai wa Umad ya daka wani k'arajin ta hanyar fad'in "What?" Cak ta tsaya ta juya ta kalleshi inda sarki Wudar ma ya d'aga hannaye zai rumgume ta da farin ciki sai kuma ya kalli d'an na sa, a duburburce ya canza harshe zuwa yaren Italy yace "Ki gaggauta barin nan malama." Turo baki tayi tana kallonshi ita bata ji dad'i ba, bubbuga k'afafu tayi k'asa ta juya ta shiga haurawa sama. Da gudu, satar kallonta yayi ya d'an dafe saitin zuciyarshi yana sauke numfashi mai nauyin gaske, idonshi ne suka k'yallara suka had'u dana mahaifinshi, ganin wani tuhumammen kallo da yake masa yasa shi juyawa da sauri ya fice a falon yana godiya ga Allah da basu had'a jikin nan ba, a gaskiya rasa nutsuwarsa yake wasu lokuta, gashi bai san e ke damunsa ba da yake jin haushi haushin mahaifins1 wasu lokuta a game da ita, shin niyyarsa ce a kan ta ba mai kyau ba? Ko kuma dai kishinta ne yake? Saidai tashin hankali shi ne da ta ce zata had'u da mahaifinta kuma mahaifinshi ya amince da haka, me kuma zai faru a gaba? Me hakan zai janyo musu ko kuma zai janyo mi shi? Da wannan tunanin ya k'arasa b'angaren shi gaba d'aya jikinshi ba k'wari, da haka yayi alwala yayi sallah ya zauna kan sallayar yana jiran ya ji me zai faru. *Khazira* Kamar ba mahaifiya wacce ta haifeta ba, haka ta tsaya gabanta tana girgiza kai da murmushi d'auke a fuskarta tace "Mah, me yasa kika aikata haka? Ni dama na zargeki tun a waccen ranar, to me ye ribarki a yin hakan?" Girgiza kai sarauniya Juman tayi cike da takaici tace "Kaico Zafreen, hak'ik'a ubangiji yayi gaskiya da ya ce yana fitar da rayayye a jikin matacce, sannan ya fitar da matacce a jikin rayayye, ko da yake zan iya cewa sak halin mahaifinki kika d'auka, amma ina bak'in ciki da haka, dan na so a ce kin d'auko ko da kad'an daga halina ne, ki sani kuma wannan banzan halin na ki shi zai nesantaki da burinki." A wani wulak'ance ta kalleta tace" Me kike nufi Mah? Kin kuwa san girma da cin muradin burina? Shin kin ma san me ye barin na wa?" Ita ma a gadarance ta kalleta tana gyara zamanta tace" Me ye burin na ki daya wuce ki gaji mahaifinki, duk fafutukar da kike Zafreen kina yi ne saboda idan ya mutu ki hau kujerar mulkinsa." Cikin jin haushi ta kalleta tana mai d'aga murya tace" Kinsan da haka kuma shi ne kike min fatan rashin cikar burina, a kan me? Me yasa kike nuna min banbanci ne tsakani na da waccen banzar yarinyar da kika haifa?" D'auke idonta tayi a kanta tace" Ni ban nuna banbanci tsakaninku ba, saidai nasan na yi abinda kowace uwa zata iya yi ne, sannan abinda na mata ko kece a halin da take ciki zan mata." Tsugune tayi irin na mazan nan ta had'e hannayenta tana murmushin mugunta tace" Kinsan wani Mah? Na fita neman yarinyar nan ne dan na kasheta, sanda na fara had'uwa da ita da nasan ita ce, hak'ik'a dana fara canza mata kamanni, a ranar data mari fuskata kuma da ina da sanin ita ce, tabbas dana shak'e wuyanta har sai na tabbatar ta daina numfashi." Wani shu'umin kallo ta mata tace" Kinsan me zan aikata yanzu da nasan wacece ita?" Murmushin gefen labb'a tayi tace" Idan har muka sake had'uwa da ita saina kasheta ko ta wane hali, ba zan tab'a bari ta zama silar dakushewar rayuwata ba, na rantse miki sai na kasheta." Malalacin kallo ta mata tace" Na so a ce kan iyalina a had'e yake tamkar tsintsiya, ba zan hanaki yunk'urin d'aukar matakin da kike ganin shi zai kaiki ga cimma ga ci, amma ki sani zakiyi dana sani wata rana, yar uwar ki kuma ba zaki iya kasheta ba, dan rayuwarta ba a hannunki take ba." Mik'ewa tayi ta harareta tace" Ni kuma na miki alk'awarin zan nuna miki gawarta ganin idonki, sannan idan har burina ya cika, ke da masu bin addini irin na ki duk sai na hukuntak..." Bata bari ta dire maganarta ba saboda haushi duk da bata da kuzari haka tayi azamar mik'ewa ta d'auke fuskarta da lafiyayyen mari. A gigice ta kalli mahaifiyar ta ta tana rarako idonta hannunta dafe da kunci, rai a b'ace sosai sarauniya Juman ta nuna mata k'ofar fita tace "Fita ki bani wuri tun kafin na sab'a miki kamanni." Mugun kallo ta wurga mata ka d'auka ita ma yanka mata tapi zatayi, a hassale sosai ita ma ta juya zata fita tana yin k'wafa, ta fita kenan mai tsaron k'ofar ya rufe Juman ta matsa kusan k'ofar tace "Ki ji da kyau, ki rik'e abinda zan fad'a miki yanzu da mahimmanci, ki rubuta ki ajiye Zafreen, addini na zai mamaye k'asar nan, dan ina ji a jikina a duk inda yar uwarki take tana cikin hasken rayuwa mai cike da saitin shari'a." Tana gama fad'a ta juya ta koma inda take zaune, ita ma a hassale ta wuce inda Adah ma ya dinga binta da sauri har suka bar kurkukun. *A* wajen sarki Musail ma dako yake hakan yasa ko rintsawa bai yi ba kamar dai sarki Wudar, ya kasa ya tsare yana son gari ya waye ya gae sarki Wudar d'in zaiyi, idan har ya turo masa yarinyar sa to ya zab'i zaman lafiya kenan, idan kuma rana ta fito babu labarinta hakan na nufin ya zab'i tashin hankalin da salwantar da rayuka, kuma shi tun jiya ya shirya ma hakan haka ma dakarunsa. *Giobarh* Kayan daya tura aka kai mata su ta saka, riga ce doguwa kalar bleue mai haske, bata da wata kwalliya ta zo a gani, sai dai daga k'asa tana da kwalliya kamar bakin lesh, haka dattijuwar jakadiyar ta nad'a mata d'an kwalin gwanin sha'awa, hakan yasa tayi kyau da ita duk da ba kwalliya tayi ba. Fitowa sukayi zasu wuce amma ta nemi izinin shiga d'akin sarauniya Kossam dan ta mata sallama, dan ita kad'ai tasan me take shiryawa a zuciyarta, indai har ta tafi kam ba zata dawo ba har sai ta gyara tsakaninta da mahaifinta. A hankali ta shiga d'akin tana mai zuba idonta akan gadon, k'arasawa tayi kamar kullum ta zauna kusa da ita, rik'o hannunta tayi tana mai fad'ad'a murmushin fuskarta cikin sanyin murya tace "Madam, ni zan tafi gidan mahaifina, ban sani ba ko zan dawo, amma dai nasan zanyi kewarki, kuma wata rana zan zo na ganki." Hannunta dake cikin na ta ta sumbata tare da sakin hannun ta mik'e tsaye, sake sunkuyawa tayi ta sumbaci goshinta sannan ta kalli idonta tace" Na barka lafiya, ina rok'on ubangijina ya dubi lamarinki ya ci gaba da tsareki, Allah ya baki lafiya." Juyawa tayi ta fita ba tare data juyo ba dan tausayin matar yasa yar k'walla taruwa a idonta, sarauniya Kossam ma k'ura mata ido tayi tana son tace" Tsaya." Saidai ya gagara hakan, tana ficewa a d'akin ta lumshe ido sai taji kamar zatayi kuka saboda tafiyar yarinyar da ko sunanta bata ji ba har yanzu. Tana saukowa daga matak'alar daidai Joyran tana tsaye, ko kallonta ba tayi ba ta nemi wucewa ta barta, cikin jin haushi ta shak'o wuyan rigarta ta nunata da yatsa tace "Ke ce kika bada izinin a hanani shiga wajen yar uwata?" Da k'arfi ta fizge rigarta ta kalleta sama da k'asa tace "Ba ni ba ce halinki ne." Zata rab'ata ta wuce ta sake rik'o wuyan rigarta, cikin jin haushi Ayam ta buge hannunta da k'arfi tare da turata baya tana jan dogon tsaki, da sauri Joyran ta dafe mararta tare da fad'in "Kai kai kai!" A hankalce ta bita da kallo ta kuma kalli marar data dafe, sarki Wudar dake tahowa kusansu cikin shigarshi ta alfarma ganin abinda ke faruwa yasa shi saurin k'arasowa, babu wacce ta kula da shi sai ma wani malalacin murmushi da ta saki ta gyara tsayuwa tana k'are mata kallo tace "Ya kamata kisan wani abu, dan kin kassara rayuwar uwar gidan nan ba hakan ke nufin zaki samu nasarar maye gurbinta ba, haka zalika ko da kin samu ciki da wanda kike ganin makusancin gidan nan ne, ba zaki samu abinda kike da buk'ata ba, dan sarauniya ta kusa samun lafiya da izinin Ubangiji." Hanyar fita ta nufa haka shi ma sarki Wudar ya bita ba tare daya kula da Joyran d'in ba, cikin takonsu d'aya bayan d'aya sarki Wudar ya kalleta yace" A ina kika san tana da ciki?" Da sauri ta kalleshi a zuciyarta tace" Kenan dai gaske tana da cikin?" A zahiri kuma dakewa tayi tace" Yallab'ai ba fa iya gandun daji na ke da burin karanta ba." Jinjina kai yayi ya saki murmushi har suka fita, motoci ta samu a laye da tarin dogarai duk suna jiranta dan su rakata, kallonshi tayi tace" Yallab'ai wannan tawagar fa?" Da fara'a yace" Karki damu kan ki gimbiya, zasu rakaki ne har masarautarki." Cikin damuwa tace" Amma ai sun yi yawa." Girgiza kai yayi yana murmushi yace" Ba zaki gane ba, amma idan kika isa masarautar Khazira zaki fahimci girman matsayinki." D'an juyawa tayi ta sake kallon dogaran sannan ta kalli b'angaren Umad, a sanyaye ta kalli sarki Wudar cikin ladabi tace" Yallab'ai zan iya zuwa muyi ban kwana da yallab'ai d'anka?" Jim ya d'anyi ya kalli b'angaren na Umad shi ma, sai kuma ya jinjina kai ya mata alama da sandarshi fara tas wacce aka lullube da wani yadi sak kayan jikinshi yace" Zaki iya, amma karki jima, kinsan ana jiranki." Da fara'a ta nufi b'angaren Umad da farin cikinta, tsaye tayi k'ofar falon tana k'wank'wasawa a hankali, saidai shiru babu motsi bare a amsa mata, gyara tsayuwa tayi ta ci gaba da bubbugawa, amma da ta ji shiru dai sai tayi tunanin ko kamar jiya ne yana sallah, a hankali ta tura k'ofar tana fad'in "Yalkab'ai." Mayar da k'ofar tayi ta rufe ta shiga takawa a hankali, d'akin d'uf sai duhu hakan yasa ta shiga waige waige, d'an motsi ta ji daga gefenta haka kuma da alamar hasken wuta a d'akin, sakin jikinta tayi alamar ta ji dad'in haka, da d'an sauri ta nufi shiga d'akin tana zuwa ta tura k'ofar tana sake fad'in "Yallab'ai ni zan..." Cak ta tsaya tare da zuba idon ta akan abinda take gani, yawo ta dinga yi da idonta tana k'arewa k'aramin d'akin kallo wanda gaba d'aya bangon aka zagaye shi da hotuna birjik, a sanyaye kamar wacce k'wai ya fashe ma ta dinga d'aga k'afarta tana k'arasa shiga ciki, jinin jikinta ta ji yana tsintsinkewa, gabanta kuma na ta fad'uwa kamar zai kayar da ita. Tsaye tayi a tsakiyar wani allo dake shak'e da hotunan mutane wasu an musu alamar an gama da su, wasu kuma an rubuta harafi a kai ko kuma lamba, wasu mutanen kuma jan zare aka mak'ala aka ja zuwa wata fuskar alamar akwai alak'a a tsakanin ababen zargin. Babban abinda ya d'aga hankalinta ta ji numfashinta na neman tsayawa bai wuce ganin hoton mahaifinta da tayi ba da kuma na ta hoton a ciki, haka kuma akwai hoton wannan mutumin data gani tare da wacce ake fad'in yar uwarta ce (Khatar). Me kenan hakan ke nufi? Me hakan ke nufi? Me yallab'ai Umad ke shiryawa? Waye shi? Kafin ta samu amsar hakan ya shigo kunnensa manne da yawa alamar yana amsawa, da sauri ta juya ta zuba masa ido kamar yanda shi ma yana ganinta ya mata k'uri ya ajz wayar, hawayen da tayi k'ok'arin rik'ewa ne suka gangaro mata, cikin dagiya da kafiya ta share hawayen ta gyara tsayuwarta tace "Who are you? What are you looking for me? What about my father?" Sai kawai ta fashe da kuka ta matso kusanshi tace "Dama duk abinda ke faruwa shirinka ne? Ni da mahaifina da yar uwata duk muna cikin tsarinka ne?" Girgiza kai tayi tana rage sautin kukan ta tace "Nayi nadamar saninka, ka daga yanzu na daina yarda da duk abinda kuke fad'a akan mahaifina, dama ina da kokonto akan haka, ta ya uba zai so kashe 'yarsa, amma yanzu na fahimci komai, dalilin da yasa kake son na ci gaba da zama a nan ba wani dalili kenan." Rab'ashi tayi zata fkta sai kuma ta kalli fuskarshi tace" Zan je na ga mahaifina, i hate you." Da gudu ta fita a d'akin hakan yasa shi rasa me zai yi ma, to shi bai ga abin duk wannan rigimar ba, me take nufi to? Daga ganin wannan abun sai ta masa wata fasaara ta daban ? Da sauri ya bi byanta ya fita a b'angaren na shi, sai dai yana fita tana shiga mota wani dogari ya rufe aka tayar, da kallo kawai ya bi motar dan mahaifinshi na tsaye ba zai yarda yayi wani yunkuri da zai janyo masa zargi ba. *Kuyi hak'uri da wannan, wallahi na fita ne da k'anwata da zatayi aure, ku min uziri.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:38 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *23* Saida suka d'auki hanya aka shaidawa sarki Musail Ayam tana hanyar zuwa, irin farin cikin daya tsinci kanshi baya misaltuwa, dan ganinshi kawai yake ya kasheta kuma ya ci gaba da mulkinshi a nutse. A cikin k'ank'anin lokaci ya sa aka k'awata masarautar nan aka dinga shiga da fita ana shirin tarbanta kafin ta k'araso, duk da bai fad'a ba iya masarauta ne kawai, amma sai ga shi maganar har ta fita wajen masarauta mutanen gari sun fara d'auka suna yayatawa, kafin ka ce kwabo sai ga dayawa daga cikin talakawa sun fara cika k'ofar masarautar suna son ayi komai a gabansu. Mutanen sun kasu uku ne, wasu so suke su ga yanda take kawai, shin ta kai irin kurantata da ake? Ko kula dai ba akwai nak'asu ta wani wajen? Wasu kuma har zuciyarsu suke son ganinta dan su saka mata albarka na sabon canjin da ake fad'a ita zata kawo shi, inda kaso na k'arshen kuma su yan kashe kwarkwatar idon su ne kawai, su ga da gaske ne ko kuma k'arya ce? Tunda ta ji labarin wai Zafeera na hanyar zuwa, ta fito farfajiyar gidan ta ga an kacame sai kaye-kaye ake hankalinta ya rub'anya tashi, tambayarta bata wuce "Me yasa aka fi fifita Zafeera akan ta ba? Mutanen gari basu san ko kamanninta ba, amma daga cewa zata zo shi ne suke wani k'warya k'wayan biki? To ita me ye makomarta kenan?" A zafafe ta juya zata koma ciki dan d'aukar wayarta ta kira wanda zai bata shawara, tana shiga falon sarki Musail ya fito cikin wani shiri da ita dai bata tab'a ganinshi haka ba, k'are mata kallo yayi cikin had'e kyakyawar fuskarshi yace" Ya ke kuma baki shirya ba? Baki san k'anwarki zata zo bane?" Yamutsa fuska tayi tace" Sai me dan zata zo? Me ya dameni ni kuma?" Tsaki ta ja zata wuce abinta yace" Zafreen." Nunata yayi da yatsa yace" Ya kamata kisan ni mahaifinki ne, ba komai ne ya fito bakinki zaki fad'a min ba, ki kiyaye gaba." Turo baki tayi gaba zata had'eshi ta wuce rai b'ace gana gunguni, saida ya ga b'acewarta ya shiga dogara sandarshi wacce tsabar alfahari yasa aka sarrafa mi shi iga da narkakken gwal, cikin takon k'asaita kamar wani d'an agwagwa ya dinga takawa yana k'arewa gyara da shirin da ake ga ma gidan. *Giobarh* Suna fita a gidan da sauri ya koma ciki yana danna kiran lambar Haman, cikin sa'a bugu d'aya ya d'aga, duk da hankalinshi tashe yake ta yanda gaba d'aya baya da nutsuwa, amma haka ya tattaro nutsuwarshi a dak'ile da yan tsirarun kalmomi yace "Hukumarmu tana da hannu a cikin sanarwar da ake a gidan telebijin ne?" Cikin rashin tabbas Haman yace "Bana jin suna da hannu a ciki, saidai suna son sanin abinda ke faruwa." Cikin d'aurarriyar murya k'asan mak'oshi yace "Su kwantar da hankalinsu, yanzu haka tana daf da isa wajen mahaifinta." Da k'arfi Haman yace "Me? Kana nufin wai Khazira?" "E." Ya fad'a a take kuma ya kashe wayar, da kallo Haman ya bi wayar ya mik'e tsaye ya fara safa da marwa, rarako ido yayi yana tunanin inhar tana wannan babbar fada shi kam ta ya zai iya samun cikar buri sa ko kuma ya ce alk'awarin daya d'auka, ganin tunanin ba zai fisheshi ba yasa shi d'aga wayar ya danna wasu lambobi ya kira, bata jima tana kururuwa ba aka d'aga, shi ma hankali tashe ta yanda ya gagara b'oyewa a harshen larabcin parsi yace "Kinsan kuwa me ke faruwa ta wajen can? Ina ga kawai ki hak'ura da buk'atar nan ta ki, dan yanzu haka Zafeera tana hanyar zuwa Khazira dan had'uwa da sarki Musail, kinga kenan ba sai kin tiasta ni aurenta ba dan kasheta zai yi shi." Ita ma mik'ewa tayi daga inda take tace" Ka tabbata?" " Na tabbata man." Ya fad'a cike da tabbaci, cikin saurin maganarta dake samo asali lokaci zuwa lokaci tace" Kana ji d'an uwa na, ba zamuyi sake da wannan al'amarin ba, tsakanin 'ya da uba fa sai Allah, ba lallai sarki Musail ya kasheta ba kamar yanda kowa ke hasashe, ka ci gaba da saka ido akan su dan Allah, idan har shi bai yi wani yunk'uri ba kai sai kayi." Iska ya furzo yace" Yar uwata, kinsan abinda da kike nema na da shi akwai hatsari sosai, idan fa akayi rashin sa'a zan iya rasa rai na bayan na rasa abokina da kuma yardarsa." D'an tsaki tayi tace" Ka manta da Umad dan Allah, kai dai kayi komai da taka tsantsan kawai, babu abinda zai faru da kai, kuma kar ka manta ni ma a had'arin nake, amma a k'arshe idan mukayi nasara rayuwarmu ce zaga gyaru ni da kai." Jinjina kai yayi yace" Shikenan, zan ci gaba da jarabawa, ki kula da kan ki." Asanyaye ita ma tace" Ka kula da kanka kai ma." Da haka ya kashe wayar yana ajeta gefenshi ya dafe k'ugu yana tunanin lamarin shi kam, yana yi ne dai amma a tsorace yake musamman ma Umad shi ya fi d'aga masa hankali, idan har ya fahimci manufarshi wallahi kai tsaye zai iya harbeshi da bakin bindiga ba tare da ya ji ta bakinsa ba bare ya masa uzuri. *Wajen* Umad kuma suna gama wayar jalabiyar jikinsa ya canza ya fito rik'e da makullin motarshi, cikin hanzari ya nufi inda ake aje motocin ya shiga motarshi ya bar gidan. Tafiyar awa uku yayi kafin ya isa bakin ruwa (Beach), kai tsaye d'akin da aka k'erashi da nagartaccen katako, yana k'wank'wasawa d'aya yayi jim bai sake ba, yan sakanni aka bud'e k'ofar, da fara'a Habbee ta matsa gefe dan ya shigo tana fad'in "Sannu da zuwa yallab'ai." Ba tare daya kalli fuskarta ba yace "Yana ciki ne?" "E." Ta fad'a tana sake kaucewa a hanyar, shigewa yayi ciki amma yayi tsai yana duba ta inda zai ga Utais d'in, Habbee data rufe k'ofar kallonshi tayi tace "Yallab'ai me za'a kawo..." Bai bari ta dire ba yace "Yana ina ne? Ki masa magana." A tsanake ta kalleshi tace "Yallab'ai kamar da matsala ko?" Waina idonshi yayi alamar ya k'agu ba wannan yake son ji ba, jinjina kai tayi ta nufi d'akin baccin na su, tana kama hannun k'ofar zata bud'e Utais na fitowa daga ciki, juyowa tayi tana fad'in "Yawwa, dama yallab'ai ne ya zo." Da fara'a ya k'araso kusa da inda Umad d'in ke tsaye, d'an rusunawa yayi alamar girmamawa yace "Barka da zuwa yallab'ai, zauna mana." Ba tare daya amsa gaisuwar ba ko kuma tayin zaman daya mi shi ya kalleshi yace "Ayam ta tafi Khazira, na yi k'ok'arin hanata amma bata hanu ba, jikina yana bani akwai matsala babba, shiyasa nake so na ji daga gareku ta ya zan shiga masarautar nan ba tare da na samu matsala ba? Sannan na fad'a muku zaku bar nan yau d'in nan." Kallon fuskarshi Habbee tayi da tsoro taf a fuskarta tace" Me kuma yake shirin faruwa da gimbiyarmu? Ya akayi ta yi wannan kuskuren?" Cikin nutsuwa Utais ya kalleshi shi ma yace" Gaskiya bansan ta wata hanya da zaka iya shiga ba tare da ka samu matsala ba, dan ko masu fitar da sirrin masarauta wad'anda aka sani ne kuma suke ciki shekaru da dama." Dafe k'ugu yayi yana nazari sai kuma ya jinjina kai yace" Ku shirya zan wuce da ku na aje ku sai na wuce." A d'an d'arare Utais yace" Zuwa ina kuma yallab'ai?" Saida ya juya zai fita yace" Zaku tafi Egypt tare da sarki Abdallah, nan ne zaku fi samun tsaro da kulawa, ina jiranku a waje." Kallon juna sukayi saidai babu mai bakin magana, juyawa sukayi suka shiga d'akinsu dan tattara abinda zasu iya su wuce, dan wannan karan ma ai da sauk'i tunda shi zai tafi da su, waccen had'uwar ta su ta farko da saida ya gama tsoratasu da maganar yan sanda suka fita a gidan, suna hanyarsu ta zuwa wani wurin kawai mota ta tarbi gabansu aka ce su shiga, shi ne aka kawosu nan ba tare da sanin ina suke ba saida ya zo suka ganshi kad'ai hankalinsu ya kwanta. *Khazira* Da k'yar mutanen dake k'ofar gidan suka gusa aka shigo da motocin, Ayam da ke cike da zulumin abinda ta gani a d'akin Umad sai ta manta da komai tana kallon mutanen suna ta rububi da tururuwar lek'a a cikin motar kamar dai wacce ta aikata wani laifi yan jarida na son jin ta bakinta, motocin na shigewa masu gadin suka gaggauta mayar da k'ofar suka rufe, hakan yasa wurin k'ara kaurewa da hayaniya da cecekucen mutane. Daidai k'ofar shiga b'angaren suka paka motar da take ciki, daga ciki da take zaune ta kalli k'ofar, dattawa ne a k'alla su bakwai cikin shiga ta alfarma, k'arewa fuskokinsu kallo take ta ga ko zata ga mahaifinta a ciki, bata ganshi ba sai Khatar data gani wanda ba zata manta fuskarshi ba, bud'e k'ofar motar da akayi yasa ta dawowa daga hangen data tafi. A hankali ta zuro k'afarta mai d'auke da farin takalmi k'irar shelar na mata, yanda suka ma siririyar k'afarta kyau abun sha'awa, kafin ta zuro d'ayar dattawan nan suka juya suna kallon mai fitowa, ita ma bin bayansu tayi da kallo. Take ta ji gabanta ya tsananta fad'uwa ganin mahaifin na ta, hular kansa da sandar hannunshi, ga wata kabceciyar sark'a a wuyanshi, hannunshi dake rik'e da sandar ya mak'ala wata agogo ga zabuna kuma kaf kayan nan duk narkakken gwal ne dan nuna alfahari da k'arfin mulkinshi, kyakyawar fuskarshi take kallo, shin gyara da kulawa ne yasa yake d'an matashi? Ko kuma dai matashin ne a gaske? Dan fuskarshi babu farin gashi ko d'aya, idonshi manya masu kyau da d'aukar hankali zagaye suke cikin bak'in kwalli daya masa rau a ido, shauk'i da kuma soyayyarshi da ta ji a lokaci d'aya yasa ta k'arasa fita a motar da sauri. Tsaye tayi tana ta had'iyar kukan dake son kubce mata tana kallonshi har ya tsaya a kan matakalar, a hankali ya sauko k'afarsa kan matakalar ta farko, sannan ya sauko d'ayar ma a matakala ta biyu har ta d'aya inda sukayi kusa sosai, a hankali ta lumshe ido take kuma hawayen suka biyo kumatunta. Tabbas gana jin soyayyar su Utais da kuma shak'uwa na wad'anda ta fara bud'a ido ta gani a duniya, amma soyayyar wad'anda take gani yanzu sai take sake gasgata abinda ake alak'anta ta da su d'in, kallon farko data musu take jin wata bayyanannar soyayyarsu a zuciyarta, sai ta kasance mai son zama da duka iyayen na ta dan ta ji me ke faruwa a cikin rayuwar ta? Tana son tasan asalin gaskiyar komai? Dan har yanzu kanta a kulle yake game da wasu abubuwan, musamman da aka ce mahaifinta ya rufe mahaifiyarta saboda ita, to saboda me? *Wani* murmushin mugunta ya saki wanda ya sake bayyana kyawunsa, saida ya shanye komai dake zuciyarsa da fuskarsa a lokacin ya bud'e hannayensa da fara'a akan fuskarshi yace "Gimbiyata, ashe dama zan ganki ido da ido?" Kamar wani ne ya ingizata sai kawai ta fad'a jikinshi ta fashe da matsanancin kuka tana fad'in "Pahhhh!" Duk da idonshi k'amas suke ba alamar hawaye, amma haka ya k'ak'aro kukan makirci ya dinga kukan k'arya yana sake k'amk'ameta a jikinshi yana daddab'ata da fad'in " 'Yata, nayi kewarki sosai, na kasance cikin jiranki a kowace safiya, kowace fitowar rana kowane dare, nayi kewarki sosai." Ita ma k'amk'ame shi tayi tace "Ban sani ba Pah, bansan komai ba, Pahhhh!" Raba jikinshi yayi da na ta a zahirance wani mugun kallo ya mata, amma sam Ayam bata d'auki haka a matsayin wata manufa marar kyau a zuciya ba, d'an juyawa yayi ya nunawa dattawan fadarshi ita yace "Ga 'yata, ku gaisheta." Dukansu sai gani tayi sun rusuna kawunansu k'asa wasu na mata kirari da mai girma yar mai girma, wasu kuma suna gaisheta a ladabce musamman ma Khatar da baya fatan ta gane shi, da mamaki take kallonsu ta d'auka ai ita ce zata gaishesu da girmamawa saboda girmansu, tana cike da wannan mamakin ta ga ya sake nuni da hannunshi yace "Ki karb'i gaisuwa daga wajen jama'arki, shekaru suka d'auka suna bauta ga sunanki." Juyawa tayi inda yake mata nunin, take ta bud'e baki ta sake shi da alamar mamaki tana zazzaro ido, kafatanin fadawan gidan ne da hadimai da dogarai sama da guda d'ari suka jeru a bayanta kayansu kala d'aya duk sun k'ame sun rattab'e hannaye kamar wasu gunkaye, a tare duk suka rusuna kamar sunyi ruku'i suka fad'a a tare da "Barka da zuwa gimbiyarmu." Ganin babu wani yunk'uri da tayi yasea sarki Musail janyota jikinshi ya kwantar da kanta a k'irjinshi, a kunne ya rad'a mata "Ki musu murmushi, sannan ki d'aga musu hannu." Murmushin yak'e ta musu ta d'an d'aga hannu ta musu bye bye tace "H...hhi." Ta gefen ido ya wurga mata wata harara jin yanda muryarta ke rawa, jinjina kai yayi ya kalli fadawan yace "Gimbiyar Khazira mai girma Zafeera ta saka muku albarka, ku je ku ci gaba da ayukanku." Tare suka sake rusunawa suka ce "Godiya muke shugabanmu." Juyowa yayi da ita a hankali tana ga jikinshi har yanzu suka nufi ciki, had'a ido ta sake yi da Khatar hakan yasa ta nunashi da siririyar yatsarta tace "Kai ne?" Da sauri ya rank'wafa yace "Ni ne ranki shi dad'e, tuba na ke, ki gafarce ki abisa abinda ya faru." Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli k'ofar shiga falon da mahaifin na ta ke neman shiga da ita, k'arewa komai kallo take tana ganin ikon Allah, lallai anyi almubazzaranci wajen kera masarutar nan, dan kud'in da aka kashe abun har ya wuce d'aukar tunanin mai hankali, sai kuma yanzu ta yarda da abinda sarki Wudar ya fad'a ce wa idan ta zo msarautarta zata gani. A babban gurin cin abincin suka zauna, duk da ta d'anyi kalle kalle a masarautar Giobarh da gidan Bukhatir, amma kam wannan gidan ya dame wad'ancen dole ta saki ido tana kallo, har aka kawo abinci aka zuba a plate na alfarma masu tsada da k'yalli bata sani ba tana ta kallon komai da take ganin kamar da gwal aka yi shi, dan ko kujerun d'aukar ido suke kuma kalarsu kalar ruwan gwal ne, shiyasa take ta tamtama da tunanin ko gaske ne ko kuma zubin ne aka musu na gwal. Muryarshi ta tsinta yana fad'in "Ki ci abinci gimbiya." Da sauri ta kalleshi sannan ta kalli sauran kujerun guda goma cas amma su biyu ne kawai, d'an kallonshi tayi a sanyaye tace "Pah! Ina Mahh?" Fuskarshi ta ga ta fara canzawa sai kuma ya wayance yace "Ki ci abinci, zaki ganta." Kallonshi tayi da tunanin kenan har yanzu tana rufe? In kam hakane dole tayi wani abu a kai, ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace "To yar uwata fa?" Murmushin yak'e ya mata yace "Tana shiryawa ne, zata zo yanzu." Jinjina kai tayi ta fara cin abinci sannu sannu, tana ci tana k'iyasta kud'in da aka kashe wurin dafa abinci da kuma dad'inshi, cikin k'agauta ya sake fad'in "Ki yi sauri ki ci abinci, bayinki na jiranki zasu rakaki sashenki kiyi wanka, talakawan gari suna waje suna jiran jin wani abu daga bakinki." Kallonshi tayi da mamakin jin furucinshi kamar na wanda baya taula kalamansa, jinjina kai kawai ta sake yi alamar to, shi kuma kallon fuskarta yayi sanda ta kalli plate d'in gabanta, harara ya sakar mata yana k'aramar k'wafa a ranshi yake ayyana" Babu ta yanda za'a yi ki zo cikin sauk'i, na tabbata wata k'ulalliyar suka k'ula miki ki zo ki min, kafin ki aiwatar zan kasheki ni kuma, mutuwarki kuma zata zama kamar had'ari babu wanda zai tuhume ni." Sam mantawa yayi da maganar zuci yake har saida ya furta" Tsinanniya kawai, ki mutu ko na huta." Da sauri ta d'ago jin yayi magana amma ba ta ji me yace ba tace" Pah magana kake?" Da sauri ya girgiza kai yace" A'a karki damu, idan kin kammala ki je kiyi wanka ana jiranki." Lura da tayi kamar a matse yake da tayi wankan yasa ta cire hannunta a abincin ta ja kujerar ta baya tace" Zamu iya tafiya?" Hadiman dake gefensu ya kalla yace" Ku rakata zuwa b'angaren ta,ku tabbatar kun kula min da yarinya." Rusunawa sukayi sosai su ukun kafin su rufa mata baya d'aya a gaba, wata duniyar aljannar suka kai ta a matsayin masaukinta, nan ma lokaci ta b'ata tana k'arewa sashin kallo, d'aya daga cikin hadiman ne tace" Bari na duba ruwan da aka had'a mi idan bai huce ba." Zata shiga ban d'akin Ayam tayi saurin cewa" Baki ji ba." Tsayawa tayi ta amsa, a nutse tace" Karki saka min ruwan mai zafi." Jinjina kai tayi tace" To bari sai a canza." Ban d'akin ta shiga inda d'aya daga ciki ta mik'owa Ayam babban towel sai k'amshi yake, tana shirin kallabin data yana a kai suka ji ihun wacce ke ban d'akin nan, da gudu suka shiga su ukun dan ganin ko lafiya, ai kam daf da bahon ruwan suka ganta hannunta d'aya a cikin ruwan wutar lantarki sai janta take. Hankali tashe Ayam tace "Ku samo mana busashen abu." Da gudu suka fito ita kuma tana kallonta sai kakkarwa take, saidai ina kafin su dawo har rai yayi halin sa. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:38 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *24* Tsoro matuk'a ya kamata ganin abinda y faru daga zuwanta, da an samu akasi kenan da ita ce zata mutu? Shin wane irin had'ari ne wannan a daidai wannan lokacin? Shin me yasa sai... Kafin ta sake tambayar kan ta ta ji sarki Musail ya shigo a rud'e yana nuna tashin hankalin k'arya, rumgumota yayi jikinshi yana duddubata yana fad'in "Gimbiya Zafeera kina lafiya? Ba abinda ya sameki dai ko?" A raunane tace "A'a pah babu komai, saidai ita...matar ta mutu." Ta fad'a tana fashewa da kuka, shafa bayanta yayi ya sauke ajiyar zuciya yana feso iskan rashin jin dad'i, likitar agajin gaggawa dake cikin gidan ne suka fito da gawar a gadon arasa lafiya suka fita da ita, hakan uasa Ayam sake fashewa da kuka, shi kuma sai daddab'ata yake alamar tayi shiru. Suna fita da gawar Zafreen na shigowa da saurinta ta kalli sarki Musail tace "Pah lafiya? Me ya faru?" Girgiza kai yayi yace "Wani had'ari ne ya faru, sai dai abun ya zo da sauk'i tunda wata baiwa ce ta mutu ba 'yata ba." Kallonshi Ayam tayi haka ma Zafreen Ayam ta kalla tana mai had'e fuska, cikin nuna kulawa Ayam tace "Pah ita ma fa mutum ce, kenan da ya zakuyi idan ni ce?" D'an tsaki yayi daya nuna maganar ta haushi ta bashi yace "Karki damu da wannan, ki je kiyi wanka ki shirya." Sakinta yayi ya juya zai fita tayi saurin fad'in "Pah, idan so samu ne ina so na ga Mah d'ita yanzu, a zan iya wankan nan ba a yanzu dan na tsorata." Wani kallo ya mata tare da sakin murmushi yace "Tsoro? Ke d'in zab'abb'iyar Khazira?" Fashewa yayi da dariya wanda hakan ya zama jikinshi sakamakon yawan ta'ammali da giya, kallonshi ta dinga yi sai ta ji tsoronshi na samun muhalli a zuciyarta yana zaunawa, saida ya ga dama dan kanshi ya tsagaita ya nunata da yatsa yace" Ke ce zaki bayar da tsoro abisa tsarin, amma ba dai ke kiji tsoro ba." Shafa kuncinta yayi yace" Ki samu ko huta, zaki ga Mah d'inki anjima." Da kallo ta bishi har ya fice a d'akin, a wulak'ance Zafreen ta k'yasta mata yatsunta tace" Malama ji nan." A hankali ta kalleta da idonta da suka d'auki launin ja mai duhu kad'an, matsawa tayi daf da ita a gadarance tace" Kina farin ciki ne saboda kin zo babbar masarautar Khazira? Hummmmm! To kar ma ki fara yarinya, dan farin cikinki nan gaba kad'an zai koma ciki." Ba tare da hayaniya ba Ayam ta sake kallonta tace" Me kike nufi?" Murmushin gefen labb'a tayi tace" Ina nufin ni ce babbar 'ya a msarautar nan, hakan na nufin ni ce magajiyar duka fada da kuma kujerar mulkin, dan haka ki gaggauta barin nan sannan ki manta kina da ahali a nan d'in, idan kuma ba haka ba nadama ce zata biyo baya." K'asaitaccen murmushi Ayam ta sauke ta rumgume hannayenta a k'irji ta gyara tsayuwarta tace" Da alama ke kuma abinda ya sha miki kai kenan, to ki sani ni ban ma san da wannan masarautar ba sai kwana biyu zuwa uku da suka wuce, infact har yanzu ban ji na gama yarda da cewa ku d'in ahalina bane, har yanzu zuciyata raya min take tatsuniya ake rad'a min a kunnuwana, sarauniya Juman ce kad'ai na ke son had'uwa da ita ta kuma tabbatar min, idan har ta tabbatar min da bakinta shi ne zan yarda da sauki burutsunku." D'auke hannayenta tayi daga k'irji tace" Shawara d'aya yar uwa, ki rage soyayyar nan da kike wa mulki, dan idan har kika sameshi alamu sun nuna giyarshi zata fi haukataki." Sama da k'asa ta harareta tare da jan dogon tsaki ta fita a d'akin tana fad'in" Matsalarki ce kuma wannan." Da kallo kawai ta bita a zuciyarta tana fad'in" Ke ma zata zama ta ki nan gaba kad'an." Fita tayi a d'akin ita ma ta koma falo ta zauna jiran tsammani. Ta jima zaune ita ba kallo ba ita ba bacci ba har saida aka k'wank'wasa k'ofar d'akin, da sauri dan dama ta k'agu da zaman tace" Shigo." Bud'ewa akayi aka shigo, cikin ladabi hadimar ta sunkuya tace" Ranki shi dad'e, sarkina ne ya umarceni da na rakaki zuwa sama dan ganawa da mutanen gari." Da mamaki tace" Sama kuma?" Yar fara'a tayi tace" A saman bene nake nufi." Mik'ewa tayi tana fad'in" Oho." Fita sukayi suka bi ta matakala, suna kan tafiya a hawa na uku suka had'u da d'aya daga cikin dogaran gidan, rab'ewa sukayi dan hanyar ba wata mai fad'i bace, kamar Ayam ji tayi ya damk'a mata abu a cikin hannunta, abun mamakin kuma bai kalleta bai sai rusunawa da yayi saboda sanin matsayinta ya gaisheta kai tsaye kuma ya wuce abin shi. Ganin hadimar tayi gaba bata kula bda komai ba yasa Ayam bud'a tafin hannunta, k'aramar waya ce mai kyau fara sol da ita mai murfi k'irar Samsung, da mamaki take kallon wayar ta sake juyawa ta kalli mutumin har ya sauka, "Waye shi?" Shi ne abinda ta tambayi kanta ta bi bayan hadimar nan kawai tana sake jimk'e wayar a hannu. A saman fili ne da shi ma aka k'axatashi dan shan iska, wata k'ofa ta bud'e ta d'auka wani wurin zasu shiga, sai gani tayi kawai ashe titi ne zaka iya hange, kamar jira suke dama sai kawai ta ji ihun da saida ta zabura ta rike hannun hadimar nan, d'aruruwan mutane da suka taru dan ita, da mai kyakyawar niyya da mai akasin haka dukansu, gashi sai ihu suke suna d'aga mata hannu alamar jin dad'in ganinta. Cikin girmamawa hadimar tace "Duk dan ke suke nan ranki shi dad'e, shekaru wasun su suka kwashe suna fatan bayyanarki, dayawa sun ci buri akan dawowarki da sa ran sabon tsarin da zaki kawo musu, daga cikin talakawan nan akwai wad'anda suke sadakar abincinsu dan abun bauta ya kareki a duk inda kike sannan ya dawo musu dake lafiya." Da mamaki Ayam ta kalleta tace" Mutanen da sukayi sadakar abinci saboda ni, kuma shi ne za'a bani izinin ganinsu daga nesa?" Gyara tsayuwa tayi ta had'e fuska wanda ita kanta bata cika sanin tana kama jikin nan ba tace" Muje ki kaini ta inda zan gansu ga da ga." Kallonta hadimar tayi da niyyar yi mata gardama, sai kuma ta sake rusunawa jikinta na b'ari tace" Ranki shi dad'e izinin da mai martaba ya bani kenan, idan na sab'a masa zai iya hukunta ni." Saida ta gama saurarenta tas tace" Ki kaini na ce." Jinjina kai tayi jiki na kyarma ta rufe wannan k'ofar ta juya bayanta, ita a Ayam juyawa tayi sai ta ga ta bud'e wata k'ofar, rab'ewa tayi tace" Muje tanan ranki shi dad'e." Wucewa Ayam ta fara yi suka sauka a matakalar, suna kai wa k'asa ta sake bud'e wata k'ofar, suna bi ta siririn corridor sai ga su ga al'ummar nan, caaaa sukayi kanta kowa k'ok'arin rumgumarta yake, sa'a d'aya dogarai dake wurin suka dinga taresu suna maidasu baya. Hannaye ta dinga d'aga musu fuskarta d'auke da murmushi wasu kuma har hannun na ta suke rik'ewa, cikin hakane wani tsoho sosai daya tsufa ya shafi tafin hannunta sai kuma ya sumbaci hannun na shi, fashewa yayi da dariya yana murna da fad'in "Na gode abun bauta, ko yanzu ka d'auki rai na ban da bakin ciki dan jikina da na ta ya had'u." Da mamaki jin furucinshi ta kalleshi, sai ta fahimci dayawa dake tab'ata abinda suke yi kenan, a rikice kuma a mugun rud'e ta kallesu ta ja baya cikin murya mai fitar da amon tashin hankali tace" Me kuke yi ne haka? Ya haka kuma?" Girgiza kai tayi cike da damuwa hawaye na gangaro mata cikin kasalalliyar murya tace "Kun sani jin kunya ganin yanda kuke min abu kamar wata waliyiya, me nake aikatawa daya sha bambam da ku? Me na muku? Wacece ni? Me yasa bakuyi tunanin ni ma mutum ce kamar ku ba? Me ya hanaku fahimtar ni ma ina da irin buk'atocinku na rayuwa, kama daga cin abinci a lokacin buk'atarsa, shan ruwa yayin buk'atarsu, wanka da bacci duka ni ma iya ni, hakazalika idan abincin da na ci ya kai wani mataki na kan buk'aci shiga ban d'aki dan na fesar da marar kyau da kuma anfani a jikina." Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tasa hannu ta share hawayenta ta ci gaba da fad'in" Ni ba kowa bace, ya kamata a dakatar da wannan farfagadan da wasu suke son su mulkeku da shi, duk da bansan me ce ce asalin baiwar wad'anda suka gabace ni ba, amma dai nasan an zuzuta abun, dan haka daga yau bana son sake ganin kuna min irin wannan da sunan girmama baiwata ko dan ni zab'abb'iya ce, ni ma mace da namiji suka haifeni sannan aka raine ni kamar yanda aka reneku." D'ag musu hannu tayi zata juya ta koma wani namiji ya d'aga muryarsa yace" Hakan na nufin ke ba zab'abb'iya ba ce kenan?" Juyowa tayi sai kawai ta sauke ido akan shi, cike da fad'uwar gaba ba tare da tunanin zata iya hangoshi a cikin mutanen nan ba yayi saurin sunkuyar da kan shi k'asa, murmushi ta saki tace" E hakane, ni ba zab'abb'iya ba ce, tunda ni dai ban ga wani abu a jikina ko a cikin rayuwata ba daya sha bambam da na ku." Wannan tsohon daya tab'a hannunta ne yace" To amma gimbiya ya maganar canjin da zaki kawo mana? Dan na b'ata shekaru da dama ina ciyar da abinci dan kawai ki bayyana ko 'ya'ya zasu samu rayuwa mai kyau fiye da ta wa, duk da ba k'arfin ciyarwar gareni ba." Da mamaki ta kalli tsohon ta gyara tsayuwa tace" Baba yayanka nawa?" Kai tsaye ya bata amsa da" Bakwai, maza hud'u mata uku, amma duka matan na gidan aurensu." Kafeshi tayi da ido tace" Dukansu sunyi karatu?" A ladabce yace" K'aramar 'yata ita ce aka haifa shekara biyu bayan haihuwarki, daga lokacin da aka haifeki dukda kinyi b'atan dabo, hakan bai sa na cire rai da samun canji ba, daga lokacin na daina biyan kud'in karatunsu na ce su zauna gida suna kama min sana'ata, dan canji ya kusa zuwa da zasu samu rayuwa mai kyau." Had'e fuska tayi ta girgiza kai tana ji kamar ta wanka masa mari, saida ta feso zafin dake balbali a zuciyarta kafin ta sake jimk'e wayar nan dake hannunta ta kalli tsohon tace" A hakane kuma kake nema musu canjin rayuwa? Shin ko kasan da ace zan tattara takardun wad'anda sukayi makaranta ne sannan na basu aiki, kasan da 'yayanka babu wanda zai shiga ciki?" Cikin jin haushi da fad'a ta kalli dukan mutanen tace" Ire irenshi na wa ke akwai a nan? Wace irin rayuwar jahilci da mutuwar zuciya kukayi a baya? Saboda kawai an ce an haifi zab'abb'iya, shin cikinku akwai wanda zai iya nuna min wani canji guda d'aya tak wanda cikin wanda suka gabaceni suka kawo muku wanda ya tallafi rayuwarku da ta yayanku?" Kallon tsohon tayi ta d'ora da fad'in" Me aka tab'a canza muku kafin zuwana ni?" Wulwula ido yayi sai kuma ya girgiza kai yace" E to, zab'abb'e daya gabata wanda daga gareshi muka samu labarin zuwanki, a lokacin muna da k'arancin ruwa, kuma mun kawo kukanmu so ba adadi a wajen sarkinmu, to a lokacin shi ne ya mana rinjiyoyin ruwa wanda a yanzu malaman fada suka mayar da su panpunan zamani." Jinjina kai tayi tace" Na ji kun samu ruwa kyauta, bayan shi fa?" Wata dattijuwa dake gefe ne tace" Wa ya fad'a miki gimbiyarmu? Ai bayan rasuwarshi da wasu shekaru sai iyalenshi suka fara karb'ar kud'in jama'a idan zasu d'ebi ruwa, yanzu haka yara ne birjik a duk gurin birtsatsen nan suna karb'ar kud'i ana d'iban ruwa." Wani murmushi tayi tana girgiza kanta kafin tace" Anfani kawai suke da ku suna cika aljihunansu, amma daga yanzu ba zaku sake biyan kud'in ruwa ba, ni zan yi magana da sarkinku wato mahaifina, ku kwantar da hankul..." Ihun da suka saka da k'arfinsu da tapi na murnar abinda ta fad'a yasa ta dafe kunnuwanta da ta ji ihun har cikin dodon kunnuwanta, addu'a suka dinga mata da fatan alkairi da kirari sanda ta juya tare da rakiyar hadimar nan dogarai kuma suna rik'e mutanen saida suka ga shigewarta an rufe k'ofar kad'ai hayaniyar ta lafa wasu suka fara barin wurin ma. Suna cikin taka matakalar wayar dake hannunta tayi vibration, da sauri ta duba ta ga lamba ce babu suna, tab'e baki tayi ta bud'e ta kara a kunne, muryar sarki Wudar ce ta ji cikin shauk'i yace "Gimbiyata, fatan kin sauka lafiya?" Da mamakin jin muryarshi d tunanin kenan shi ya turo mata da wayar? Ganin hadimar nan ta juyo tana kallonta yasa ta mata alama da hannu tace "Ki je kawai ina zuwa." Saida ta ga ta juya ta tafi ta sauke ajiyar zuciya tace "Yallab'ai barka." Cike da jin k'uruciya da rashin kunya sarki Wudar yace "Ba yallab'ai ba, ki kirani da mijinki." Rintse ido tayi ta yatsina fuska kamar ta ga ba-haya tace "Yallab'ai?" Amsa mata yayi da "E mana, ba kin min alk'awarin aure ba, alk'awari kuma a wurinmu tamkar d'aura auren ne." S'an safe gaban goshinta tayi tace "Yallab'ai kana lafiya? Ya d'anka?" Wani abu ya ji a zuciyarshi saboda tambayar d'anshi da tayi, amma sai ya share yace "Ina lafiya, ke fa?" Jinjina kai tayi tace "Ina lafiya, nagode." D'oraw yayi da "Kin tabbatar kina lafiya? Babu wani abu daya faru?" Amsawa tayi da "E yallab'ai." Jinjina kai yayi yace "Shikenan, yanzu ya maganar alk'awarinmu?" A tak'aice cikin jin ya fara hawa mata kai tace "Zamuyi magana, zan sake kira anjima." D'if ta yanke kiran tana jan tsaki a zuciyarta tace "Kaga jaraba, me zanyi da kai ni kuma tsofai tsofai da kai." K'arasawa tayi ta shige ita ma ta samu hadimar bakin k'ofa tana jiranta, tana zuwa ta kalleta tace "Ki kaini wajen sarki." Da sauri ta kalketa jin wai ki kaini wajen sarki, rusunawa kawai tayi ta nufi hanyar da zata sadasu da shi d'in gabanta na fad'uwa dan bata san me zai mata ba idan har baya buk'atar ganin kowa ta kuma rakata gareshi d'in. Saida suka jira a bakin k'ofar wani dogari ya musu iso, jim kad'an ya dawo ya ba wa Ayam d'in umarnin shiga abisa yarjewar sarkin, tana zura k'afarta akan wani mahaukacin tattausan carpet ta lumshe ido, wani irin sanyi ne ya ratsata tare da ni'imtaccen k'amshi ga wani irin shup shup da d'akin yayi, tana k'arasa shiga ta wara ido tana kallon ko ina, a take idonta suka hasko mata hoton mutanen da ta gani yanzu, wanda dayawa daga ciki kana kallonsu zaka san talauci ya musu katutu, amma dubi irin daular dake cikin gidan sarautar nan, ka rantse da Allah arzikin duk duniya aka tara a cikin gidan. Jin bata ce komai ba sai kalle kalle take yasa sarki Musail gyara zamanshi yace "Ina jinki gimbiya." Da sauri ta dawo da hankalinta kan shi tana motsa bakinta a hankali tace "Amm..Pah, dama ina so ne zamuyi magana." D'ora k'afa d'aya kan d'aya yayi ya d'auki kofin glas d'in gefenshi da abun sha a ciki kalar ja ya kurba sannan yace "Ina jinki, zauna." Inda ya nuna mata ta zauna ta kalla sannan ta kalli kofin daya aje gefenshi, kai tsaye dai bata ce barasa bace, amma dai ta d'an ji tana shakku duba da kwalbar data gani zungureriya a ajiye, a hankali ta k'arasa ga kujerun na alfarma royal da kula k'irar Italy, zaunawa tayi kamar akan k'aya sannan ta kalleshi, ganin ya sakar mata murmushi ya sa ita ma ta saki murmushin. Da fara'a ya sake fad'in "Fad'i mana gimbiya ta, ina jinki." A nutse cike da kunya ta fara alama da hannunta tana fad'in "Pah dama magana ce akan mutanen da suka zo gani na, sun zo da buk..." D'aga mata hannu yayi yace "Gimbiya Zafeera, su ba mutane ne kamar kowane ba, talakawa zaki ce idan kina so na gane, ki dinga banbantawa." Baki sake ta kalleshi sai kuma ta jinjina kai tace "To Pah, dama shi ne suka fad'a min ruwa ma da suke sha su talakawa siya suke, bayan kuma d'aya daga cikin magabata ne suka samar musu da su dan su sha kyauta, amma yanzu wasu ne suka mayar da hakan kasuwanci." Irin kallon daya tsareta da shi yasa ta sunkuyar da kai, a dak'ile yace" Yanzu da kike fad'in duk wannan, me kike so na yi a kai?" Cikin rawa da jikinta ya fara na tsoronshi da kwarjini yasa ta d'an muskuta tace" E to...ina ganin...idan.." Sake d'aga mata hannu yayi yace" Dakat Zafeera, wa ya kitso miki duk wannan tsirfar da kika zo yanzu kike kora min? Yaushe kika zo nan d'in da har kika fara fahimtar matsalolin mutanen garin nan? Me kika sani? Me kike tunanin zakiyi?" Yunk'urawa yayi ya mik'e tsaye tare da nunata yace "Kina ji ko, ba neman matsala bace ta kawoki nan, kin zo had'uwa dani ahalinki ne ba had'uwa da k'orafe k'orafen jama'ar gari ba." Komawa yayi ya zauna tare da nuna mata k'ofa yace "Zaki iya tafiya." Kamar zata fashe da kuka ta ske kallonshi tace "Pahh...ka ce zan had'u da Mah, kuma na ga har yanzu..." Cikin jin haushi da tsawa yace "Kai! Wai me yasa kike da shan kai ne? Dama haka kike? Haka banzayen bayin nan suka raineki ko? Ki wuce ki bani wuri idan nasa an fito da ita zan sa a kiraki." Mik'ewa tayi tsaye ta kalleshi, ita bat1 gusa ba ita bata sauke idonta ba, k'ura masa ido tayi tana kallo kamar mai son tsaorata shi. Wani d'ar d'ar ya fara ji zuciyarshi na yi har da harbawar da baisan dalili ba, sai ga sarki Musail a gaban 'yarsa yana ta sissine kai, yana so dole ya kalleta ido cikin ido ya daka mata tsawa ta bashi waje, saboda ya nuna mata iko da izzarshi, amma kuma wani tasiri dake cikin idonta da suka ninka na shi kwarjini yasa dole yake kakkawar da na shi kamar mai jin kunyarta, gaba d'aya sai ya duburburce ya rasae zaiyi. Ayam ma data fahimci haka sai ta ji ba dad'i ganin yanda mahaifinta ke mata, gyara tsayuwarta tayi tare da d'auke idonta daga kan shi, sanyaya murya tayi a nutse cikin ladabi tace "Ina so a fito min da sarauniya Juman, na zo ne dama saboda ita kuma idan na tabbatar da abinda nake son tabbatarwa zan bar nan da ita, ba sarautarku ta kawoni nan ba, saidai akwai abu d'aya da bana yarda da shi shi ne, *rashin adalci*." Juyawa tayi a tsanake ta dinga takunta har ta fita a falon na shi, yanda ya idonshi suka kakkafe ya bita da kallo kamar ya ga gawa, rufo k'ofar da akayi ne ya dawo da shi hayyacinshi, a zabure ya lalubo wayarshi dake kan d'aya k'aramin teburin gefenshi ya danna wasu lambobin, ana d'agawa sarki Musail yace "... *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:38 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *25* Waziri Khatar na d'agawa sarki Musail yace "Ka bayar da umarni a fito da Juman, a fito da ita yanzu yanzu." Hankali tashe Khatar yace "Yallab'ai ka tabbatar? Wani abu ne ya faru?" Cikin fad'a yace "Idan ban tabbatar ba na kiraka, na ce ka fito da ita yanzun nan." Da sauri ya amsa da "To yallab'ai, yanzu kuwa." Aje wayar yayi yana sake rarako idonshi yana tuna abinda ya faru tsakaninshi da Ayam, girgiza kai yayi yace "Kai ina! Hakan ma ba zai faru ba, ba zan tab'a yarda da wannan ba." Tana komawa d'akinta ta samu hadiman nan suna jera mata kaya da aka siyo mata daidai ita, falo ta zauna zuciyarta cunkushe saboda rashin jin dad'in abinda ya faru tsakaninta da mahaifinta, ta jima zaune ita kad'ai tana tunanin nan kafin hadiman su fito suka durk'usa gabanta d'aya tace "Gimbiya an gama shirya kayan, ko da wani abu da kike da buk'ata?" Girgiza kai tayi tace "Ba komai, nagode, zaku iya tafiya." Kallon juna sukayi da mamakin jin ta musu godiya, wanda da Zafreen ce saidai ta bisu da tsaki ta musu alama da hannu su fita, mik'ewa sukayi suna fad'in sun barta lafiya kafin suka nufi fita. Kallonsu tayi suna daf da ficewa tace" Ya maganar wacce ta rasu? Anyi jana'izarta?" A ladabce ta k'arshen tace mata" Yallab'ai sarki ya sa a kai gawarta ga iyayenta." Da d'an mamaki tace" Ina kenan?" D'aya a ciki ne tace" Nan baya kad'an, mafi aksari iyayenmu sunyi aiki a nan kafin su daina mu kuma mu ka d'ora, to mai akwai babban filin da aka gina musu suke rayuwa anan." Da alamar tambaya tace" Kenan a gidan nan babu wanda ya je jana'izarta?" A hankali wata ta girgiza kai tace" Gaskiya sarki bai bamu wannan izinin ba." Jinjina kai tayi tace" Shikenan, d'aya a cikinku sai ta rakani na je." Zaro ido sukayi suka kalli junansu, wacce ta rakata d'azun ce tace" Ranki shi dad'e ki rufa mana asiri." Fuskarta ba alamar wasa tace" Asirinku a rufe yake, zaman lafiyarku d'aya shi ne muje d'aya a cikinku ta rakani." D'aya a ciki kamar zatayi kuka tace" Ranki shi dad'e idan har ya zama dole ki tafi dole mu dukanmu zamu rakaki, sarki ya umarcemu mu kasance tare da ke a ko ina." Mik'ewa tayi tsaye tace" To ai sai mu tafi." Wacce suka tafi tare ce ta sake fad'in" Duk da haka akwai dogarai da aka ware dan rakiyarki." Murmushi tayi ta girgiza kai tace" Ko ma menene dai mu tafi." Ita ma kan ta murmishin tayi kafin suka shiga take mata baya har suka fita falo. A falon suka had'e da Zafreen ta fito ita ma da masu take mata baya alamar fita zatayi, a wulak'ance ta bisu da kallo kafin ta tambayi hadiman da cewa "Ku kuma ina zaku tafi?" Cikin ladabi d'ayar tace "Zamu raka gimbiya ne babban gida." Yatsina fuska tayi tace "What? Babban gida kuma? Me zatayi a can?" Girgiza kai Ayam tayi tana murmushi tace "Aunty gimbiya ni na ce su rakani, zan je ta'aziyar d'aya daga cikin hadiman da aka rasa da sfiyar nan." Wani malalacin murmushi tayi tace "Ke kuma kalar zubar mana da mutumcin da zakiyi kenan? Me ya had'aki da talakawan nan? Me zaki je ki musu har inda suke rayuwa?" Girgiza kai Ayam tayi tana mamakinta tace "Ko na fad'a miki ba zaki fahimta ba, amma a tak'aice su ma mutane kamar mu, dan bamu fi su da komai ba." Tana gama fad'a ta nufi hanyar fita ba tare data sake ji daga Zafreen d'in ba wacce ta bita da kallon mamakin furucinta da kuma jin haushi. Yanda ta buk'ata haka ya faru, ta isa babban gidan wanda ke da babban filin tsakar gida sai d'akuna a jejere ba adadi, mutuwar da akayi kuma ita tasa kowa na gidan ke waje wasu zaune wasu tsaye suna kallon gawar da aka shinfid'e iyayen yarinyar suna kanta suna kuka da fad'in shikenan sun rasata. Kusa da su Ayam ta zauna ita ma ta share 'yar k'wallarta kafin ta shiga jera musu ban hak'uri da fad'in yanda abun ya faru, sosai hakan ya faranta ran iyayen da ma duk wanda suke cikin gidan, dan ko shekara talatin ka b'ata kana ma sarki bauta yau ka mutu ko jaje ba zai yi wa wanda abun ya shafa ba. Saida aka d'auki gawar dan kai ta gidan kad'ai Ayam ta bar wurin tare da abokatafiyar, suna shiga masarautar daf da k'ofar shiga falon wata hadimar ta ha'de dasu, a ladabce ta sunkuya tace "Ran gimbiya ya dad'e, mai martaba ne ya ce ki zo sarauniya ta iso." Da sauri ta kalleta tace "Ta iso? Tana ina? Muje." Da sauri ta shiga ciki suka rufi bayanta, rasa hanyar da zata nufa tayi hakan yasa hadimar nan fad'in "Nan ne gimbiya." Da sauri kamar zata tashi sama ta bita suka shiga haura matakalar da gudu gudu, saida suka kai k'ofar d'akin sai kuma ta tsaya turus, bud'ewa aka yi hadimar ta kalleta tace "Shiga ranki shi dad'e." Kallon k'ofar tayi dake bud'e kad'an, a hankali ta fara d'aga k'afarta tana shiga ciki idonta tsaye wuri d'aya, jin an rufo k'ofar daga baya yasa ta saurin juyawa hakan ya tabbatar mata lallai an rufe k'ofar, sake juyowa tayi gabanta tana mai baza idonta tana son ganin ta inda zata fito. Sauti tashin muryoyi taji daga wata mashigar,a hankali ta fara takawa zuwa ciki wanda labule ne ya musu shamaki, tana zuwa ta d'aga labulen sai kuwa mutanen suka bayyana, hadimai ne uku da jakadiyarta sai sarauniya Juman tsakiyar su suna caje mata kai bayan tayi wanka tsabar wahalat data shawo a gidan kurkukun nan. Jin shigowar mutum yasa su ma suka juya, suna ganin Ayam suka kama jikinsu suna mata barka da zuwa, mik'ewa Juman tayi a sanyaye ta juyo gaba d'aya ta zuba mata ido, ido cikin ido suka kalli juna yayin da a tarz sak'on ya isa ga zuciyoyinsu cewa lallai alak'ar mai k'arfi ce wacce ta isa su kira junansu da mai haihuwa da wacce aka haifa. Ayam data kasa motsawa Juman ce ta shiga d'agowa a hankali tana tunkarota tana k'ara gyara k'aramin towel d'in dake kafad'arta duk gashinta ya kwanta a kai, saida ta tsaya gabanta suka kallon juna, cikin sanyayyar murya Juman tace "Kamar jaririyar 'yata dana kalla sau d'aya tak a rayuwa?" Kamar ambaliyar ruwa haka hawaye suka fito daga kurmin idon Ayam suna sauka a kumatunta, cikin muryar kuka ita ma a tausashe tace "Ba zan iya tuna kamannin fuskar ba, dan ban tab'a ganinta ko a mafarki na ba, saidai duk da haka hakk'in haihuwa ne ya jawoni zuwa nan dan tabbatarwa da kai na mahaifiyata na neman taimako na." Sark'ar wuyanta ta jawo ta nuna mata tace "Da gaske ke ce kika saka min wannan a wuyana tun ina k'arama?" Jinjina mata kai tayi ita ma tana kukan tace "Tabbas ni na d'aura miki ita da hannu na a lokacin dana haifeki." A hankali tace "To amma me yasa?" D'an murmushi ta k'ak'aro tace "Saboda ta zama tsaro a gareki, sannan shaidar da zan iya ganeki ko a cikin dubu, sannan hujjar da zan iya nuna miki cewa ni na haifeki." Fashewa tayi da kuka mai ban tausayi ta saki sark'ar daga hannunta tace "Me yasa kika rabani da ke a lokacin da na fi buk'atarki? Me yasa kika zab'i kiyi nesa da ni a sanda zamanmu a tare shi ya fi komai mahimmanci?" Da sauri Juman ta saki towel d'in take rik'ewa hakan ya bayyanar da wuyanta dan d'aurin k'irji ne jikinta na farin towel babba, rumgumeta tayi tsam a jikinta suka fashz da wani sabon kukan, cikin magiya take fad'in" Kiyi hak'uri 'yata, ban yi haka dan bana sonki ba, da banyi abinda nayi ba da yanzu ba kya raye, idan kuma kin rayu to da kin sha wahalar da ni kuma ba zan juri ganin kina shan ta ba, shiyasa nayi nesa dake dan ki rayu cikin aminci, sannan ki zama mai kyawun d'abi'a da ba irin na mahaifinki da 'yar uwarki ba." K'am k'am Ayam ta rik'eta tana sauke ajiyar zuciya da fad'in" Na fahimta Mah, na fahimceki Mah na." D'agota tayi daga jikinta ta kalli fuskarta ta hanyar d'aga hab'arta tace" Kin yafe min kenan?" Langab'e kai tayi tace" Ban rik'eki ba Mah, ina sonki sosai." Ta fad'a tana sake komawa jikinta, ita ma matseta ta sake yi tana murmushi, daga bayansu jakadiyar sarauniya Juman ce tace" Ranki shi dad'e na fito miki da kayan da kika buk'ata." Cikin shagwab'a da sangarta Ayam ta bud'a ido ta kalli jakadiyar tace" Babu mai rabani da Mah ta, anjima ta saka." Dariya jakadiyar tayi haka ma Juman data d'agota daga jikinta tace" Sai yaushe kenan? Nayi ta zama a haka?" Rik'o hannayenta Ayam tayi tana mamatsawa musamman ruwan zafi' da tayi wanka da su yasa duk fatarta tayi taushi saboda rashin samun lafiyayyar shinfid'a a kurkukun nan, cikin shagwab'a tace" Mah, zaki zauna tare da ni ko? Akwai abubuwa dayawa da nake son tambayarki, ina rok'onki ki zauna tare da ni kuma ki amsa min, dan babu mai fad'a min gaskiya har yanzu." Jawo hannunta tayi ta zaunar da ita bakin gado sannan ita ma ta zauna, kallon jakadiyar tayi tace "Ku je jakadiya, zan nemeki anjima, yanzu lokacin 'yata ne." Rusunawa sukayi tace "To sarauniyata, mun barku lafiya." Dukansu suka fita kafin sarauniya Juman ta maida hankalinta kan Ayam tana murmushi tace "Ya kika rayu ba tare da ni ba?" A take tace "Cikin aminci, k'auna da soyayya." Jinjina kai tayi tace "Kin tabbatar kin rayu babu barazanar talauci?" Girgiza kai tayi tace "Babu Mah, sun ciyar dani da dad'i da ba dad'i, sun d'auki nauyin karatu na har zuwa sanda gwamnati ta d'auke musu nauyin, sun tufatar da ni iya iyawarsu." Jinjina kai ta sake yi tana k'asaitaccen murmushi kafin tace "Game da lafiyarki fa? Babu abinda ke damunki?" Girgiza kai tayi kafin tace "Babu Mah, idan da akwai ciwon dake damuna bai wuce yawan mafarkai ba tun ina k'arama, shi ma yanzu kuma na fahimci wa nake gani a mafarki na." Cikin zolaya ta lak'aci hancinta tace "Wa kike gani haka? Ko dai sirikin na wa ne?" Dariya tayi tana rufe fuskarta da tafin hannu tace "Lahhh! Mah ki daina." Dariya tayi ita ma kafin tace "To fad'a min wa kike gani?" Bud'e fuskarta tayi ta d'ago tace "Ke ce Mah, ke nake gani kullum kina neman taimako na, bansan me hakan ke nufi ba?" Numfasawa tayi ta rik'e hannunta gam suka kalli juna, a sanyaye tace "Ayam..." Da mamaki ta kalleta da sauri kuma tace "Ya akayi kika san sunan dana tashi ina amsawa? Tunda na baro Larhjadin yallab'ai Umad ne kad'ai ke kirana da sunan." Dariya tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tace "Saboda ni na fad'awa Habbee ta rad'a miki sunan *Ayam*, sunan dake birgeni kenan tun da jimawa, na so sakawa yar uwarki Zafreen, amma sai mahaifinku ya zab'a mata sunan Zafreen." Dafa kafad'arta tayi tace "Mafarkin da kika kasance kina yi ni na fara yin shi na tsawon lokaci, amma ina haihuwarki komai ya wuce." K'asa tayi da kan ta tana sakin murmushi tace "Umad? Umad?" Sai kuma ta kalli Ayam tace "Ta ya kika san Umad? D'a ga sarki Wudar." Da mamaki ta kalleta tace "Ya akayi kika san shi Mah?" Sosai tayi murmushi kafin ta kalleta tace "Yanzu dai ki bari na saka kaya, daga baya zamuyi magana bayan na ci abinci." Kyab'e fuska tayi ta ware hannayenta ta rumgumo Juman d'in tare da fad'in "Mah bana so kiyi nesa da ni ko na sakan d'aya, please ki zauna tare da ni." D'ago hab'arta tayi tace "Wai tsaya ban tambayeki ba, ta ya kika iya yaren slovaque? Su Habbee ne suka koya miki?" Girgiza kai tayi a harshen larabcin parsi tace "Ko d'aya Mah, kawai dai na iya ne saboda ni yar garin nan ce asali." Da mamaki ta waro idonta tace "Hada yaren k'asar haihuwata ma kin iya?" A harshen faransanci tace "Oui m猫re (e mahaifiya ta)." D'aga hannaye tayi ta dafe kanta tace "Tsaya tsaya! Wai me ye haka? Ta ya kike yaren nan a bakinki?" Zaune tayi da kyau tace "Ki je ki kammala duk uzurinki, sai muyi magana daga yanzu har wata safiyar." Kallon tuhuma sa kuma tsoro ta mata tace "Kin tabbatar?" Jinjina mata kai tayi tace "Na tabbata." Mik'ewa tayi ta nufi wajen kayan da aka fito mata da su ta shiga k'ok'arin sakawa, Ayam duk na zaune tana kallo ta shirya a tsanake babu mai cewa komai, saidai jefi jefi sukan kalli junansu suyi murmushi, kowa na jin zuciyarsa na masa wani iri game da d'an uwansa. Har ta gama shiryawa ta nufi wajen zaman mutum biyu gaban teburin da aka jere mata abinci mai rai da lafiya, kallon Ayam tayi ta mata alama da hannu ta taso, mik'ewa tayi ta nufeta ta zauna kusa da ita, zuba abincin tayi sannan ta kalleta tace "Mu ci." Da fara'a ta tsoma hannunta ba cokali ba ta d'ebo loma ta nufi bakin Juman, da fara'a ita ma ta bud'e bakin ta saka mata, ita ma d'iba tayi ta saka mata hakan yasa su sakin murmushi. Cikin farin ciki da jin dad'i da annashuwa suka dinga ciyar da junansu amma ba hira suke ba sai k'orafin da suke wa junansu na sun k'oshi, amma a haka Juman zata sake jefa mata loma a baki, sai ita ma tace sai ta rama haka har suka cinye wanda suka zuba a farantinsu. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:39 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *26* Suna kammalawa basu bi ta kan kwanukan ko gyara wurin ba suka koma kan gadon nan, tsakiyarshi suka haye suka tank'washe k'afafunsu hannayensu sark'e dana juna suna kallon juna, cikin nutsuwa da fara'a sarauniya Juman tace "Yanzu fad'a min, me kike son sani?" Cikin nutsuwa tace "Mah, ina so nasan *wacece* ni?" D'an murmushi tayi tace "Wacece ke kike tambaya Ayam?" Jinjina kai tayi tace "E Mah, ina so na sani." Jinjina kai tayi ita ma ta nisa sannan tace "Ayam, ke 'yata ce dana haifa a ciki na, kafin haihuwarki kuma malam Dhurani ya fad'a min ke mai baiwa ce da zaki zo bayan magabatan da suka shud'e masu irin baiwarki, na raini cikinki har na tsawon wata tara cike da kulawa da nuna miki k'auna, haka kuma mahaifinki na d'aya daga cikin wanda suka tayani kulawa da ke, haka muka ci gaba da rainonki har sanda cikinki ya isa haihuwa, saidai duk tattali da burin da muka ci na haihuwarki, haka ina ji ina gani sanda na haifeki ko wankan farko ba'a miki ba na mik'aki a hannun jakadiyata ta tafi dake." Da mamaki fal a fuskar Ayam tace"Me yasa Mah? Gashi dai a labarinki na fahimci Pah ma yana so na, amma kuma sai ake cewa wai yana son kasheni?" Numfashi ta sauke a hankali tace "Ayam, lokacin da cikinki ya kai wata shida, wata ranar alhamis da ba zan tab'a mantawa ba jakadiyar sarki ta zo min da wata magana, lokacin da sarki mahaifinki yayi bak'i ta je sanar dashi, anan ta ji wata tattaunawarshi da malam Dhurani suna maganar cewa ke d'in da zaran an haifeki to su gaggauta kasheki, idan ya so sai su samu wata jaririyar su damk'a min a matsayin wacce na haifa, jin wannan labarin ya tayar min da hankali sosai, saidai ban k'aryata jakadiya ba saboda tsufanta da kuma wasu alamomin da suka dinga bayyana min a game da sarkin, wasu lokuta ya kan furta zancen zuci a gaba ya fad'i wata mummunar kalma a kanki, wasu lokuta kuma idan ya sha giyarsa cikin dare na nemi taimakonsa kan wani abu sai ya dinga fad'in *banzan cikina* yana surutai, hakan yasa na ci gaba da saka ido akan shi ina masa kallon biri yana min kallon ayaba." Nisawa tayi sannan ta d'ora da" Tunda na fara nak'udarki sarki Musail yake tsaye a kai na shi da malam Dhurani da wazirinsa Khatar, da k'yar ya fita ya bar likitar gidan nan da jakadiyarsa suka dinga taimaka min, k'arfe 11:59 na ji kukanki bayan k'akk'arfan nishin da nayi, wanda kukanki ya dira a kunnuwana tare da sautin bugawar agogo k'arfe 12:00 ta buga na sabuwar shekara, babban abinda ya firgita ni a lokacin shine yanda mahaifinki ya banko k'ofar d'akin yana son a dole a bashi ke ya rik'e, hakan ya k'ara tabbatar min da abinda nake zargi ya kuma tsorata ni sosai." Kallonta tayi ido cikin ido ta sake jinjina hannayen Ayam d'in dake hannayenta tace" Ayam, b'atanki ba shiryayyen abu bane kamar yanda kowa ke zato, a daidai wannan lokacin na rok'i jakadiyata Habbee data gudu dake zuwa wani wuri mai nisa, sannan na umarceta data nemi taimakon mijinta akan hakan, saida na kori jakadiyar sarki na c ta had'a min ruwa, lokacin likitar ma ta bar d'akin sannan na lallab'a Habbee, da k'yar ta amince dan abun bazata ya zo mata, bayan ta amince ne na samu damar mik'a mata ke bayan na sumbaceki, har zata bi ta wannan k'ofar da kike gani..." Ta fad'a tare da nuna mata drower ta litattafai sannan ta d'ora da fad'in" K'ofar sirri ce a bayan nan d'in, wacce a d'akin sarki da iyalensa ake samunta saboda kaucewa farmakin magauta na bazata, to ta wannan hanyar Habbee ta fita dake a wannan daren bayan na d'aura miki wannan sark'ar wacce sarkin k'asar Khazira ne kawai ke d'aurawa wacce ya aura, sannan na bata kud'in da zasu kula da kansu har su kula da ke kanki ma, wannan ita ce Ayam d'in da kike son sanin wacece." A tare suka sauke numfashi inda Ayam idonta ke fitar da ruwa masu d'umi muryarta na rawa tace" Mah, kenan dai da gaske mahaifina yana neman rayuwata? To amma me yasa?" Sakin hannunta d'aya tayi ta share mata hawayen da suka zubo tace" Kiyi hak'uri Ayam, haka ta ki k'addarar take, hak'ik'a a yanda komai ya fito mana mahaifinki yana son kasheni, kuma ba komai ya kawo hakan ba sai dan ci gaba da kasancewa a kujerar mulkinsa wacce babu komai a ciki sai tarin zalinci da tauye hakk'in jama'a." Marairaicewa tayi tace" To amma Mah ke ma kin yarda ina da wata baiwa wacce har mahaifina zai so kasheni saboda ita?" Girgiza kai tayi tace "Ba zan ce komai ba a yanzu, saboda ban girma dake ba bare na fahimci me ce ce baiwarki, amma dai nasan akan haka mahaifinki ke neman rayuwarki." Kyab'e fuska tayi tace "To amma Mah, me yasa ba yar uwata bace aka haifa da baiwar nan? Tunda ita kuka fara haihuwa ko." Murmusawa tayi tace "Saboda ke ce ubangiji yake son gani a haka." A marairaice ta sake fad'in "Mah, su waye mutanen nan da suka fara fad'a min wacece ni?" Da mamaki ita ma tace "Su wa kenan?" Jim tayi alamar tana tunani sai kuma tace "Yawwa Bukhatir, sunansa Bukhatir a k'asar Egypt." Mamaki ne ya sake bayyana a fuskarta ta k'ank'ance idonta tace "Bukhatir ya had'u dake kenan?" Jinjina kai tayi tace "E, wata safiya ce dana fito daga wanka saboda jin motsin da na ji, daga nan ban san me ya sake faruwa da ni ba tun buguna da akayi a kai sai bud'ar ido da nayi na ganni a gidansa." A hankali ta dinga gyad'a kanta alamar jinjina abun da kuma gamsuwa kafin tace" Tabbas zai iya aikata komai, fatana kawai Allah ya kareki daga sharrinsa." "Waye shi Mah?" Ta fad'a a sanyaye, d'an yak'e ta mata kafin tace "Ayam Bukhatir d'an uwana ne, mahaifina shi ne gaba da mahaifinsa, ni kad'ai ce 'yar da suka haifa mace bayan shekarun da suka share a tare babu haihuwa, mahaifin Bukhatir mutumin kirki ne wanda mulkin yayansa baya gabansa, saidai Bukhatir tun yana k'arami yake sha'awar mulki, sanda suka haifeni sai ya yarda lallai idan na girma zan iya hawa kujerar mahaifina, saboda kuwa mu a wajenmu mace ma tana yin mulki sai idan bata buk'ata, bayan wani lokaci Bukhatir ya zo min da tayin soyayyarsa, amma ban karb'a ba saboda bai min ba, bana sha'awar mulki kuma bana son mai tsananin son mulki." Da mamaki Ayam tace" To Mah e yasa ya saceni ya kaini gidansa? Guduwa fa na yi bai sani ba, sanda na fahimci babu hankalin kowa a kai na na wa hadiman daya had'ani da su dabara na shige boot d'in motar bak'in da suka zo masa a lokacin." Girgiza kai tayi tace" A gaskiya ban sani ba, ban san dalilin da yasa ya saceki ba,saidai nasan lokacin da mahaifinki ya nemi aurena sun samu matsala har sukayi musayar yawu, watak'ila ko akan hakan yake son rama wani abu da aka masa." A hankali tace" To amma Mah, idan har kunyi soyayya irin haka da mahaifina, me yasa ya manta da komai ya jefaki a magark'ama saboda ni?" Dariya Juman tayi har saida hak'oranta sirara masu kama dana Ayam d'in suka bayyana, girgiza kai tayi tace" Ayam kenan, yarinya ce ke har yanzu." Da mamaki tace" Kamar ya Mah, ni fa na girma." Ta fad'a tana kumburo baki, dariya ta sake yi tace" Ayam ba haka abun yake ba, a shekara ta 1985 sarakunan gargajiya sunyi taro na musamman dan sake hab'aka zumunci da kawar da bambamce bambamce a tsakanin k'asashen, sarkin Egypt wato mahaifina, da sarkin Khazira wato mahaifinki, da kuma sauran sarakuna daga ciki har da sarki Wudar na Giobarh, duka sun hallara a wannan babban taron wanda mahaifina shi ne mai alhakin sauke bak'in, ma'ana a k'asarmu aka gudanar da taron, kwana uku aka d'auka ana wasanni kala daban daban, a na ci a na sha cikin farin ciki da annashuwa, b'angare d'aya kuma sarakuna na gudanar da abinda ya kawosu." Numfasawa tayi ta d'an gyara k'afarta data tank'washe sannan ta ci gaba da fad'in" A kwana ukun da akayi na kamu da soyayyar wani d'an baiwa, kinsan me yasa na kirashi da d'an baiwa? Saboda shine zakin daya fara sace zuciyata, da kallo d'aya ya birgeni ya kuma shiga zuciyata, lokacin da nake jin dad'in satar kallonsa ina tunanin hanyar da zan fad'a masa abinda ke zuciyata kafin su bar k'asar, sai ya turo da k'aramin k'aninsa mai shekara shida a duniya ya fad'a min wai shi ma yan so na." Damk'e hannun Ayam tayi sosai tana jijjigawa cike da farin ciki tace" Kin kuwa san irin farin cikin da na kwana ina yi a ranar? Na ji kamar duniya aka bani da komai dake cikinta, saidai kash! Ban tab'a tunanin wannan bak'in taro ne a gareni ba saida Musail ya shigo rayuwata, ki gafarceni idan kin ji ba dad'i Ayam saboda soyayyar d'a da uba, amma dai tabbas ban ji dad'i ba." A sanyaye Ayam tace" Me ya faru Mah?" Girgiza mata kai tayi tace" A'a Ayam, bana so daga had'uwarmu na zauna na yi ta fad'a miki mugayen halayen mutanen dake zagaye da ke." Rik'o hannunta tayi tace" Please Mah, ki daure ki fad'a min komai, na fad'a miki mutanen da ban sani ba suna kawo min farmaki ta hanyar rikita min k'wak'walwa, ina so na san komai daga gareki, hakan shi ne zai cire min kokonto na akan kowa da komai." Girgiza kai tayi tana sako da hawaye a idonta tace" Ba zan iya fad'a miki wannan ba Ayam, ki gafarce ni." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa tace" To shikenan na ji, amma ki fad'a min waye wanda kika so a zuciyarki? Sannan ki fad'a min me ya hana aurenku?" Murmushi tayi tace" Ayam ai idan na fad'a miki abinda ya hana aurenmu an gudu ba'a tsira ba kenan, dan abinda ya hana auren na mu shi ne abinda bana son fad'a miki." Jinjina kai ta sake yi tace" To na ji, waye shi?" Saida ta saki sanyayyan murmushi tace" Sunansa *Urab*, babban d'an sarki Wudar." Zazzaro ido tayi tace" Sarki Wudar Mah?" Jinjina kai tayi tace" E, d'an sarki Wudar." Da mamaki a fuskarta tace" Hakan na nufin yaya ne ga yallab'ai Umad? Dama 'ya'yan sarki biyu ne?" Gyad'a mata kai tayi tace" E, su biyu, Umad d'in ai shine k'aramin k'aninsa da nake fad'a miki." Juyar da kanta tayi gefe a ladabce tace" Kenan yallab'ai Umad sosai ya sanni ba sanin shanun talla ba? Kenan tabbas saboda ni ya je makarantar nan? Kuma mahaifinsa ya san wacece ni, amma kuma duk da haka yake cewa yana son..." Shirun da tayi yasa Juman saurin fad'in" Yake son me? Kin had'u dasu dukansu? Ta ya ya?" Girgiza kai tayi dan bata san me hakan zai janyo ba kafin tace" Ba komai Mah, na zauna tare da su na kwana biyu." Tsaf ta kwashe abinda ya faru ta fad'a mata, sai daga bisani kuma ta kalleta a tsanake tace" Mah, to ina shi yayan yallab'ai d'in yake? Ko gidansu dana zauna ban ji ko da labarinshi ba." Kallonta tayi sosai ita ma a tsanake tace" Ya rasu shekara ashirin da hud'u da suka gabata." Dafe k'irji tayi tamkar mahaifinta aka ce ya mutu tace" Me?" Jinjina mata kai tayi alamar e, girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace "Amma ta ya Mah?" Girgiza mata kai tayi tace "Kinga yanzu dai manta da wannan, bana so ki sa kanki a damuwa, yanzu bani labari game dake?" "Kamar me kenan Mah?" Ta fad'a kamar mai rad'a, jan hancinta tayi tace "Kamar k'awayenki, samarinki, karatunki, matsayin addininki a gareki." Bushewa tayi da dariya tace "Mah, a b'angaren karatu na dai kam zan iya miki albishir da ce wa tun dana fara daga ajin farko zuwa inda nake yanzu, indai za'ayi jarabawa to ni ke zuwa farko, k'ok'ari na ma yasa har idon gwamnati ya zo kai na suka dinga d'aukar nauyina." Rausayawa tayi ta ci gaba da fad'in" Kawaye kuma ni kam ban da tsayayya, duk k'awayen makaranta ne, da zaran mun rabu to shikenan ni da su sai ko kan hanya idan an had'u." Cikin jin kunya tace" samari kuma...ban tab'a yi ba Mah, ko na wasa." Jin tayi shiru yasa Juman fad'in" To addininki fa? Me ye matsayinsa a gunki?" Waina idonta tayi tace"... *In shaa Allah sai litinin kuma* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:39 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *27* Waina idonta tayi tace "Mah, babu wani addini da nake cikinshi a baya, dan abinda su Mah (Habbee) ke bautawa ina ganin hakan kamar b'atan basira, a gani na ba ta yanda zan sassak'a ice da hannu na sannan na ce gareshi zan nemi biyan buk'atoci na, a k'arshe ma sai ta kai da kud'i kad'an zaka iya siyanshi a kasuwar sabah sannan ka kai cikin gidanka, sai nake ganin hakan gaskiya bai dace da mutum mai hankali da tunani ba, duk da ban rayu da su rayuwa mai tsayi ba saboda makarantar kwana dana dinga yi, amma dai a haka suna min fad'an na samawa rayuwata madogara, dan rayuwa babu addini tamkar rayuwa ne babu alk'ibla, amma kullum sai na fad'a musu zan yi idan har na samu addinin daya dace, dan kullum a jikina da kuma hangena nake samun yak'ini tabbas akwai wani buwayi gagara misali wanda ya cancanci dukanin mai rai da numfashi yayi bautarsa gareshi, and...a k'arshe dai na samu ta dalilin yallab'ai Umad, yana bautawa ubangijin daya dace, gareshi ni ma na karb'a, saidai yanayi yasa babu abinda ya koyar dani game da addinin, amma kakata ta koyar dani wankan tsarki, sannan ta fara min bayani akan rukunan musulunci guda biyar." Cike da farin ciki marar misaltuwa Juman ta rumgumota tace" Wow! Masha Allah, a gaskiya na ji dad'in haka sosai, sai kuma yanzu na fahimci kuskuren da na yi saboda rufewar da ido na sukayi na son ganin na ceci rayuwar ki, sam na manta da madogararki, na manta nayi tunani akan jigon rayuwarki, zan nemi gafarar ubangiji na kuskure na, sannan daga yanzu zan fara d'oraki daga inda kika tsaya." Cikin jin dad'i ita ma tace" Nagode Mah." Da sauri kuma tace" Dakata, dakata, na ji kin ce kakarki? Wace kakarki kenan?" K'urawa fuskarta ido tayi tace" Mahaifiyarki, sarauniyar Egypt." Zaro ido tayi tace" Ina kika had'u da su Ayam? Iyaye na fa kika ce?" Jinjina kai tayi tace" Yallab'ai Umad ne ya kai ni wajensu." Da mamaki tace" Umad? Wai me yake nema ne?" Girgiza kai tayi tace" Ban sani ba ni ma Mah, amma ni yanzu babu ruwana da shi, dan yau da zan taho na shiga d'akinshi sai na samu wasu abubuwa da ke nuni da kamar wani ne ke shirya mana wani abu, ko kuma dai ana aiki a kan mu." Jim tayi tana tunani kafi' daga bisani tace" To ko dai shi ma..." Sai kuma tayi shiru, da sauri Ayam tace" Shi ma me? Mah ki fad'a min idan kinsan wani abu a kan shi." Girgiza kai tayi idonta na kallon k'asa tace" Um um! Ba lallai abinda nake tunani ba ya zama gaskiya." Cikin zumud'i tace" Duk da haka Mah fad'a min." Kallonta tayi tace" Kin gane ko? Zuciyata ce na ji ta raya min wasu abubuwa a game da yawan maganarsa da na ji kinyi, uwa uba kuma kika ce ya had'aki da iyayena, ina tunanin to ko dai shi ma ya shiga aiki irin na yayansa Urab ne?" Kallon tuhuma Ayam ta mata tace" Mah, tambayarki fa nayi kuma ke ma kin tambayeni, wane aiki kenan?" Cikin rashin tabbas tace" Jami'in sirri ne, a waccen lokacin jami'in sirri ne dake binciken manyan laifuka na k'asa." Jim tayi alamar tunani sai kuma ta jinjina kai tace" Lallai biri yayi kama da mutum, hakan na iya faruwa." Da mamaki Juman tace "Amma kum..." Bata gama fad'a ba aka bud'e k'ofar aka shigo, Juman na jin haka ta tabbatar da sarki ne, Ayam kuma juyawa tayi da sauri, tana ganinshi ta shiga k'ok'arin sauka daga kan gadon, da fara'a ya k'araso yana fad'in "Kaga 'ya da uwarta, ana tattaunawa?" Murmushi Ayam tayi a ladabce ta juya ta kalli Juman data had'e fuska tace "Mah zan fita, sai anjima." Da kai ta amsa mata alamar to, sannan ta mayar da dubanta k'asa tana sake cije fuska. Saida ya ga fitar Ayam ya haura kan gado tare da fizgo gashin Juman cikin b'acin rai yace "Me kuke tattaunawa da ita haka tsawon awa d'aya? Gulma ki ke koya mata? Ko wani abu ki ke fad'a ma ta game da ni dan ta bijire min?" Cike da bushewar zuciya ta fizge gashinta tana fad'in "E d'in, sai me? Tsoro ka ke ji ne kar ta san wani abu a kan ka?" Hab'arta ya rik'o ya matse yace "Ki saurare ni da kyau, ko ki fad'a ma ta ko kar ki fad'a dai mutuwa za ta yi, dan haka ki shirya ganin gawarta gabanki." Murmushin mugunta tayi tace "Ka jaraba ka gani mana, me ye na fad'a min idan ka yarda za ka iya kasheta d'in, ka je ka jaraba ka gani." Jinjina kai ya yi yace "Shikenan za ki gani." Ita ma jinjina kai tayi tace "Za ka gani mana in shaa Allah." Sakinta ya yi ya sauka daga kan gadon ya juya zai fita sai kuma ya tsaya cak ya juyo yace "In shaa Allah? Ki sani na hane ki da yin duk wani abu daya danganci addininki, daga yanzu kuma bana so na sake ji." Da sauri ta sauko daga kan gadon tace "Saboda me? Ka fara jiyo k'amshin sub'utar mulkinka daga hannunka ne?" Bushewa tayi da dariya tace "To ka ji wani abu da ba ka sani ba, ita kan ta wannan addinin take bautawa, kuma ina mai tabbatar ma ka lokaci kad'an ya rage ka fara ganin sahu sahun masallata a farfajiyar gidan ka." D'aga murya ya yi yace "Ba zai yiwu ba, sam haka ba za ta faru ba Juman, idan kuma haka ta faru sai dai in bayan ba rai na." A hankali ta d'auke kan ta ta furta "Ai dama haka aka fad'a ma ka, komai zai faru ne bayan ba ranka d'in." Da azama ya yi kan ta yana d'ga sandarshi da niyyar maketa, sai kuma wata zuciya ta horeshi tare da tuna mi shi Ayam, da k'arfi ya sauke hannunshi ya juya ya bud'e k'ofar da k'arfi ya fita kamar zai tashi sama. Tana ganin fitar shi ita ma tab'e baki tayi ta gyara zaman mayafinta da kyau sannan ta fita, jakadiyar ta da hadima d'aya za su rakata tace "Ku barshi kawai, wajen 'yata zan tafi." A ladabce suka amsa ma ta ita kuma ta wuce, dake ta san b'angaren sai gashi ta iso a sauk'ak'e, zaune ta samu Ayam kamar mai lissafin kud'i sai nuni take da hannaye, zaune tayi tana murmushi tace "Me ki ke yi haka?" Murmushi tayi ita ma tace "Ba komai Mah, sannu da zuwa." Numfashi ta sauke kafin tace "Yawwa sannu." A tsanake ta kalleta tace "Yawwa Mah! Ina so ki d'ora min karatun nan daga inda kakata ta tsaya min." Jim tayi tana kallon fuskarta tace "Ayam, ya ki ka ga iyaye na? Suna cikin k'oshin lafiya?" Cike da tabbaci tace "Mah suna cikin k'oshin lafiya, saidai na tabbata suna kewarki, zai fi kyau ki ware rana ki had'u da su ko da sau d'aya ne kafin waninku ya bar duniya." Jinjina kai tayi tace "Zan yi k'ok'arin haka In shaa Allah, ganinki ya haifar min da k'warin gwiwa." Da fara'a tace "Ni kuma idan za ki tafi wajensu to zan tafi tare da ke." Dariya tayi tace "To shikena', yanzu mu fara karatunmu ko, dan ya kamata ki san mahaliccinki da kuma yanda zaki bauta masa." Daga haka suka shiga karatu ta dinga sanar da ita abinda ya kamata ta fara sani a farko. *Giobarh* Tunda suka had'u bai ce masa komai ba, yanda ya zuba masa ido tuni ya gigita tunaninshi yasa jikinshi kwasar b'ari da tunanin ya gama gano manufarshi, coffee da yasa aka kawo musu ya kasa kurb'ashi saboda baya da nutsuwa. Ganin dai shirun ba zai fishesu ba yasa shi muskutawa yace "Umad ina saurarenka, me yake faruwa ne wai dan Allah?" Ba tare daya daina binsa da kallon nan ba hannunshi tallabe da hab'arshi yace "Wani sabon aiki za mu shiga." Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Haba Umad, yanzu abinda zaka fad'a kenan amma ka min shiru duk ka d'aga min hankali, ina jinka to me ye aikin?" Gyara zamansa yayi ya d'auke hannunshi daga hab'ar ya sauke numfashi, cikin nutsuwa yasa hannu yana juya kofin dake d'auke da coffee yace "Na fad'a ma ka Ayam tana masarautar nan, kuma kafi kowa sanin had'arin hakan, shiyasa ni da kai zamu je fadar da nufin masu neman aurenta." Da k'arfi ya zaro ido yana kallonshi yace "Me?" Zuba masa ido yayi amma bai ce komai ba, Haman kam firfita ya fara yi da hannunshi saboda gumin da yake ji, sai ya ke ganin kawai yasa da shirinshi akan Ayam d'in, yasan niyyarshi shi ma ta son aureta dan ya samar da farin ciki ga yar uwarsa. Umad kuma daya gama karantar yanayinsa kuma dama tun ranar da Ayam ta fad'i abin nan akan Haman d'in ya samu shakku a kan sa, daga ranar ya fara saka ido da bincike a kan shi, yanzu haka dai zai iya cewa Haman a tafin hannunshi ya ke tsaf, kallon duk wani motsinshi yake. Gyara zama yayi ya d'an sassauta had'ewar da ya ma fuskarshi yace "Haman na gama shirya komai, kai zaka shiga gidan a zuwan d'an kwamishin kud'i, saboda na samu labari sarki Musail na son k'ulla wata hark'alla da shi, kafin su had'u mu za mu gabatar da kanmu a zuwan masu neman auren d'aya daga cikin 'ya'yansa." Da mamaki Haman yace" Dakata Umad, idan har sarki Musail na son had'uwa da kwamishinan kud'i, me zai sa mu yi kasadar zuwa gidansa kuma? Asirinmu zai tonu kuma rayuka zasu b'ace." Wani malalacin murmushi yayi yace" Tuni ai sarki mahaifina yayi magana da kwamishinan kud'in, ba matsala game da hakan tunda kai ne zaka je a matsayin d'ansa." A kid'ime yace" Me yasa sai ni to?" Kai tsaye yace" Saboda ni akwai abinda zai kaini gidan." Murmushi Haman yayi yace" Idan na fahimta za ka shiga gidan nan ta hanyar d'ana tarko da ni, kana so ka samu damar yin abinda kake so a cikin gidan ta dalilin d'auke ma kowa hankali da sunan neman auren d'aya daga cikin yaranshi, hakane?" Jinjina masa kai yayi yace" Hakane, dan haka ka shirya zuwa dare jirginmu zai sauka a Khazira." Zaro ido yayi yace" Zuwa dare? Da wuri haka?" Mik'ewa yayi ya d'auki wayoyinsu guda biyu babba da k'arama da makullin mota yana fad'in" Me za'a jira kuma? Ka shirya kawai." Da kallo kawai Haman ya bishi har ya shige motarshi ya bar wajen parking d'in. *Yana* isa gida kamar yanda ya saba b'angaren mahaifiyarshi ya fara nufa dan duba halin da take ciki, yana zuwa ya samu Joyran bakin k'ofar d'akin na ta tana ta rok'on masu gadin su barta ta shiga, tana ganin Umad ta gyara tsayuwarta ta shiga rera kukan k'arya tana fad'in "Yawwa d'an yar uwata, ka duba ka ga tsarin nan da aka yi, yar uwata data rage min a hanani ganinta, tunda yarinyar nan ta zo gidan nan ban sake saka yar uwata a ido ba, ka rok'esu su barni na shiga na ganta ko hankalina ya kwanta." Saida ya d'auke kai daga gareta ya had'e fuska sosai muryarsa ba alamar wasa sannan" Doka ce, daga ni sai mahaifina zamu ganta, idan na fitar da ita shan iska zaki iya hangota daga nesa." Yana gama fad'a mai tsaron ya bud'e k'ofa ya shige ya barta baki bud'e tana mamaki, dan kawai ta gama gane ta kare mata, sarki Wudae ya daina kulata, yanzu Umad d'in ma mai mata biyayya shia ya daina, duk a dalilin yarinyar nan? Juyawa tayi a fusace ta bar k'ofar d'akin da tunanin sake b'ullo da wata hanyar dan ba zata hak'ura ba. *Egypt* D'an dakatawa yayi daga danna na'urar da yake ya zubawa k'ofar ido, ganin Zeyfi ta shigo yasa ya d'auke kan shi ya mayar kan na'urar ya ci gaba da dannawa Tana shigowa ta mayar da k'ofar ta rufe, hannu d'aya ta sa ta dafe bango d'aya hannun kuma ta sa a mad'aurin rigar dai dai k'ugunta ta warware k'ullin, cike da salon jan hankali ta cire rigar ta zubar da ita k'asa, hakan ya rage mata daga bras sai pant kalar ja da suka kamata suka mat kyau. Duk da ba kallonta yake ba, amma ganin abinda take ta wutsiyar ido sai ya sa ya d'aga kai ya kalleta, wasu mayatattun yawu ya had'e kafin ya sake d'auke kan shi, hak'ik'a kam shi namiji ne mai buk'ata, kuma a yanzun daya gan ta a haka ta tayar masa da duk wata tsohuwar sha'awarsa daya jima bai sauke ba sakamakon rashin samun kwanciyar hankali, saidai a yanzun ma baya jin zai iya samun nutsuwar da har zai yi hak'urin ya gamsu, dan labari ya samu wai Zafeera tana wajen sarki Musail, shi da ya zuba kunnuwa yana jiran ya ji yak'i tsakanin sarki Musail da sarki Wudar, a cikin wannan tartsatsin shi kuma zai zagaya ya d'auketa ba tare da shan wata wahala ba, sai kawai ya ji wai tana can kuma babu abinda ya faru. Ganin bai kulata ba yasa ta shiga takawa cikin kwarkwasa da kissa tana karairaya tana kashe masa ido, har saida ta hau kan gadon tana rarrafawa, k'afafunshi dake mik'e ta shiga shafawa tana sumbatarsu cike da k'warewa da son kai shi bango dan ya karb'i tayinta, d'aga jajayen idonshi yayi ya sauke kan ta, cikin dakusashiyar murya yace "Kk...e, la..fiya?" Bata tanka masa ba saida ta zo daf da k'ugunshi ta dinga zura hannu a cikin bargon daya d'an rufa zuwa k'ugun na shi, dake gajeran wando ne jikinshi mai roba hakan ya taimaka mata wajen zura hannunta ciki, tana tab'o kayan arzikin ya d'an zabura yana fad'in "Ke wai lafiyarki k'alau, me ye haka?" D'ago narkakkun idonta tayi cikin muryar d'aukar hankali tace "Idan baka so ka dakatar mana." Aje na'urar yayi yasa hannayenshi da k'arfi ya fincikota, kamar wanda zai cinyeta sai kuma ya cabki leb'enta ya had'a da na shi ya shiga tsutsa da sauri sauri, dake abinda take so ne sai kawai ta shiga biye masa suka dinga yamutsa junansu, sunyi nisa sosai suna neman gangarewa kawai k'aramar wayarshi tayi kururuwa. Da sauri ya d'ago dan wannan kiran sarki Abdallah kad'ai ke da wannan k'arar, hakan kuma ya tabbatar masa da ya zo kenan? Zunbur ya sauka daga kanta daga shirin neman hanyar da yake wawuro wandonsa ya maida ya d'auki wayar, saida ya nutsu ya saita kanshi ya tabbatar ba za'a gane komai ba kafin ya d'aga ya rangad'a sallama tare da d'orawa da fad'in "Allah ya ja zamaninka mai martaba." Zeyfi data tashi zaune kallonshi take ranta b'ace tana fatan wayar nan kar ta nesanta ta da shi, sai kuwa ji tayi yace "To mai martaba, gani nan zuwa in shaa Allah." Da sauri ya shiga gaggautawa yayi wanka ya fito yana shiryawa Zeyfi ta sauko daga ka gadon ta d'auko doguwar rigarta ta bacci ta saka, k'arasawa tayi kusa da shi tace "Ina kuma zaka je mijina?" Cikin b'acin rai da jin haushi yace "Ban gane ina zan je ba? Ina zamanki ne a gidan nan? Kuma ina kunnuwanki suka je lokacin da nake wayar da baki isa ki gane da wa nake yi ba?" Kwalbar turarenshi ya d'auka ya feshe jikinshi sannan ya d'auki k'aramar hula bak'a mai kyalli ya saka, juyawa yayi zai fita ta sake fad'in" Wai ina zaka tafi cikin daren nan?" Nunata yayi da yatsa yace" Idan kika sake min magana sai na dalla miki mari." K'wafa yayi ya juya ya zura wasu silipas ya bud'e d'akin ya fice, wani wawan tsaki ta ja ta cije yatsarta cike da takaici kafin ta bar d'akin. Yana fita k'ofar gidan ya samu bak'ar mota reng rover a pake, dreban motar ne ya fito ya bud'e ma Bukhatir d'in k'ofar baya ya shiga sannan ya mayar ya rufe ya tsaya bakin mota dan ya jirasu. Wani irin zama ne yayi a cikin motar na ladabi da girmamawa, ya kasa d'aga kan shi bare ya had'a ido da sarki Abdallah, a haka suka gaisa ya masa sannu da zuwa da tambayar "Ranka shi dad'e ai bansan kana hanya ba, da na d'aukoka da kai na daga airport." Murmusawa yayi cike da dattijantaka yace "Kar ka damu Bukhatir, da ina so a san zan dawo, da na kiraka a waya." Da giramawa ya fad'i "Hakane ranka shi dad'e, Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana." "Ameen." Sarki Abdallah ya fad'a yana jinjina kai a hankali, shiru motar ta d'an d'auka na wani lokaci kafin sarki Abdallah yace "Bukhatir, ka san me yasa na ta so da kai na na zo yanzu?" Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba mai martaba, sai dai na shiga zulumi da tunanin me ya hana sarkina zaunawa a d'akinshi na alfarma ya jira na d'an lokaci ni na sameshi." Jinjina kai sarki Abdallah yayi yace "Hakane, abu ne mai mahimmanci da ya shafi rayuwata, shiyasa na kasa hak'ura gari ya waye." Numfasawa yayi a hankali yace "Bukhatir, ka san da na had'u da 'yar' yata wato d'iyar Juman Zafeera?" Da sauri ya d'ago kai ya zuba idonshi cikin na shi, amma da sauri ya sadda kan shi yana mai jin gabanshi na tsananta fad'uwa, hatta da jikinshi saida ya ji ya fara kyarma zai d'auki rawa, yanda ya kasa furta komai yasa sarki Abdallah d'ora da fad'in" Na had'u da ita, kuma na yi farin cikin haka, saidai akwai wata babbar matsala." Da k'yar ya bud'i bakinshi yace" Sarkina wace irin matsala kuma?" Jim sarki Abdallah yayi sai kuma yace" Kamar yanda ka sani ne daga haihuwarta zuwa yanzu ta rayu cikin had'ari, amma ubangiji yana kareta daga sharri duk wani mai sharri, ban tab'a jin d'ar a lokacin da aka rasata ba, amma a yanzu ina jin zuciyata ta kasa samun sukuni saboda inda ta kai kanta." A ladabce Bukhatir yace" Ina ta kai kanta haka ranka shi dad'e?" Shiru sarki Abdallah yayi kamar ba zai yi magana ba, can ya numfasa yace" Wajen mahaifinta, sarki Musail." Da sauri ya kalli sarki Abdallah duk da dai yasan da maganar, amma dan kar ya saka mishi wani shakku yasa shi fad'in" Wajen sarki Musail? Kasheta fa yake son yi?" Jinjina kai yayi yace" Sanin haka yasa hankali na ya kasa kwanciya." Shi ma jinjina kai yayi tare da tunanin bari ya fad'a masa shawarar da shi kan shi ya yanke a kan ta d'in, kallonshi yayi a hankali yace" Sarki na, kwanciyar hankalinka shi ne kwanciyar hankalin duk wani dake k'asar nan, ka kwantar da hankali, ni na ma ka alk'awarin zuwa safe zan samo maka labarin yanda take ciki, daga haka kuma sai mu san abun yi, dan gaskiya zamanta a can akwai had'ari." A tsanake ya kalleshi yace" Ka tabbata zaka iya yi min haka Bukhatir?" Jinjina kai yayi yace" In shaa Allah sarki, wannan alk'awari na ne a gareka." Jinjina kai yayi a hankali yace" Shikenan Bukhatir, na yarda da kai, ina jira na ji daga gareka." Da haka suka rabu ya fito a motar su kuma su ka bar unguwar yana mai jin ya fara samun nutsuwa a zuciyarshi. _Ga duk wanda bai siyi *lu'u lu'u* ba ya hanzarta ya siya dan fara samun *Badak'ala* nan kusa_ *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:40 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *28* Yana shiga ciki d'akinshi ya wuce kai tsaye, ganin Zeyfi bata nan yasa ya mayar da k'ofar ya rufe, dan daya sameta korar kare zai mata dan ya samu damar yin abinda ya dace, da sauri ya cire hular kanshi ya d'auki na'urar nan ya shiga rubuta sak'o ga d'aya d'an lek'en asirin shi dake gidan sarki Musail. Bai aje na'urar ba bai kuma rintsa ba kamar yanda bai yi wani abu da zai anfane shi ba, haka ya d'auki sama da awa d'aya yana jiran ganin dawowar amsar tambayarshi, sak'on na dawowa yayi gaggawar bud'ewa ya duba, ya d'an shiga tashin hankali daga bayanan da mutumin ya bashi, saidai kuma ya ji a ranshi su ma bayanan wasu makamai ne da zai iya sake tunzura sarakunan biyu su kaure da yak'i, dan haka ya jinjina kai yana fatan wayewar gari tare da d'an kishingid'awa kafin gari ya waye. *Zaune* yake gaban sarki Abdallah kan kujera ya sadda kanshi sosai ya nutsu, cikin ladabi da girmamawa yace "Ranka shi dad'e, kamar yanda na maka alk'awari zan samo maka bayani akan halin da take ciki." Jinjina kai sarki Abdallah yayi yace "Na'am, an samu wani abu ne?" Jinjina kai yayi yace "E ranka shi dad'e, an fad'a min tana cikin k'oshin lafiya tare da mahaifiyarta, sai dai kuma a safiyar da ta zo wani abu ya faru wanda a zahirance ya yi kama da tsautsayi." Da mamaki sosai sarki Abdallah yace "Mahaifiyarta kuma? Kana nufin Juman?" Gyad'a kai yayi yace "E yallab'ai." Da sauri yace "To ta ya? Yaushe Musail ya fito da ita daga kurkuku?" Cikin ladabi yace "Jiya ne yallab'ai bayan zuwan ita Zafeera." Jinjina kai sarki Abdallah yayi yana murmushi a zuciyarshi yana ayyana "Kenan shi ma kwarjininta zai iya tasiri a kan shi?" Kallon Bukhatir yayi yace "Me ya faru to?" Cikin nutsuwa yace "A cikin d'akin da aka sauketa ne za ta shiga ban d'aki tayi wanka, kafin shigarta sai d'aya daga hadiman daya had'ata da su ta fara shiga dan tabbatar da auna ruwan kamar yanda Zafeera ta buk'ata, a tak'aice dai mai martaba sai gawar matar aka fito da ita, wai wutar lantarki ce ta ja ta har ta rasa ranta." Lumshe ido yayi a hankali yace" Subhanallah, Subhanallah, lallai wannan kam tsautsayi ne a zahiri, amma a bad'ini da wata manufa a kai." Sake kallon Bukhatir d'in yayi dake fad'in" Hakane ranka shi dad'e, shiyasa nake so na bayar da wata shawara idan har zai yiwu." Cike da kulawa yace" Me kuwa zai hana Bukhatir? Fad'a mana na ji, kar fa ka manta kai d'an d'an uwana ne, kuma a yanzu dai a yanda komai ke bayyana kai ne magajin wannan kujerar ta wa." Da sauri Bukhatir ya d'aga kai ya kalleshi ba tare daya b'oye sha'awarshi ta son mulki ba yace" Na'am ranka shi dad'e?" Jinjina kai yayi yace" Hakane, kar ka manta da mahaifinka yana raye akwai yiwuwar shi zai gajeni, to baya raye yanzu, ni kuma bana da d'a namiji, macen kuma tana gidan mijinta, ka ga kenan kai ne magaji na na gobe." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonshi, wani sanyin dad'i ne ya ratsa zuciyarshi, farin ciki ya mamayeshi ta yanda yake ji kamar ya zumduma ihu, sarki Abdallah ne ya katse masa shauk'insa da fad'in" Ina jinka Bukhatir, me ye shawarar ta ka?" Cikin farin ciki da jin dad'i yace" Ranka shi dad'e, a gani na rayuwar Zafeera ta na cikin had'ari, bai kamata mu sake yin shiru ba a karo na biyu, sarauniya Juman 'yarka ce, amma azzalumin sarkin nan ya rabaka da ita ba dan ya fi k'arfinka ba, a gani na yanzu Zafeera ba yarinya ce da ya kamata mu sa ido ita ma har ya ga bayanta ba, a gani na me zai hana mu tunkareshi a wannan karon, ko ba komai zamu karya alk'adarinshi na jin cewa ya fi k'arfinmu." Tunda ya fara magana yake saurarenshi yana jinjina kai, saida ya dasa aya ya sauke numfashi sannan yace" Na ji abinda ka fad'a Bukhatir, amma ka bani lokaci zan yi shawara, abinda na yanke a kai zan nemeka." Rusunawa yayi yace" Godiya nake ranka shi dad'e, sai na ji daga gareka." Jinjina kai kawai yayi bai ce komai ba, mik'ewa yayi a ladabce yace" Na barka lafiya sarki na, a huta lafiya." Sake jinjina kai yayi yana kallo har ya fita daga falon bak'in na shi, a take ya tsunduma kogin tunani akan shawarar Bukhatir d'in. *Khazira* A wajen su Ayam lokaci mai tsayi suka d'auka suna karatu, Juman ce kad'ai ta tsagaita saboda lokacin sallah zuhur, tana duba agogo ta kalli Ayam tace "Yanzu tashi mu yi sallah, ba laifi mun sha karatu, fatana dai idan mu ka idar ki fad'a min ko da rabin abinda na sanar da ke ne." Jinjina kai tayi tana murmushi sannan suka mik'e, ban d'akin Ayam d'in suka shiga tare, tsayawa Juman tayi bakin k'ofa tace "Ki fara d'aura alwalar na gani komai yayi daidai." Da "To." Ta amsa ta cire kallabinta data yana ta fara da wanke hannayenta da bismillah, a tsanake take kallonta tana gabatar da komai yanda ta koyar da ita, amma abun mamaki sai ga shi Ayam tayi komai yanda ta koya mata, za ma ka rantse da Allah ita ce ke koya mata, saboda yanda take wanke komai da kyau har zuwa inda aka ce d'in, ba wannan ya fi bata mamaki ba saida ta ga ta idar ta mik'e tsaye ta karanta addu'ar da ake karantawa bayan idar da alwalar ta d'aga hannu ta furta. _"Ashhadu an la'ilaha illallah-wahdahu la sharika lahu-wa ashhadu anna Muhammad rasulillah."_ _"Allahuma-ja'alni mina-tawwabina-waja'alni minalmutad'ahirina."_ _"Subhanaka-lahuma wa bi hamdika, ashhadu an la'ilaha illa anta, astagfiruka wa atubu ilaikh."_ Tana juyowa suka had'a ido ta mata murmushi tace" Mah na yi komai daidai?" Da farin ciki tace" Ayam, ai daidan ma mak'ura ki ka yi, ta ya ki ka iya rik'e komai da na fad'a miki lokaci guda haka?" Numfashi ta sauke tace" Mah, idan har akwai wata baiwa dana yarda ina da ita, to wannan ce ubangiji ya bani, a iya sani na ba'a tab'a maimaita min abu sau biyu ba." Dariya tayi ta jin dad'i sannan tace" Na ji dad'in haka, saboda haka ma zan had'aki da malami ku fara karatu daga daren yau, kafin nan da d'an lokaci ke ma ki fara koyarwa." Dariya tayi ita har hak'oranta suka fito waje kafin ta nufi wajen gado ita kuma ta k'arasa shiga ban d'akin dan yin alwalar ita ma. Tana idar da alwalar ta fito ta samu Ayam zaune tana jiranta, ganinta yasa ta mik'e tana gyara kallabinta, kallonta tayi da kyau tace "Mu je d'akina sai na baki hijab ki saka, kafin jibi ke ma zan sa a kawo miki." Da "To." Ta amsa suka fita a d'akin na Ayam suka nufi d'akin Juman d'in, hanyar da Juman ta biyo d'azu suka sake bi ta nan, a daidai corridorn da ba'a cika bi ba suka samu hadimai guda biyu suna sallah duk sun yane kawunansu da kallabin, yanda basuyi tsammanin zuwan wani ba a lokacin yasa da k'arfi suka juyo a tare sun ma manta da sallah suke. Da sauri Juman ta musu alama da hannu tace "Ku ci gaba." Durk'usawa sukayi k'asa kawunansu sadde suna sauke ajiyar zuciya, ko ba komai sun san zasu tsira da rayukansu, tunda ita kan ta a b'oye take sallah a sanin da suka mata. Da mamaki Ayam tace "Ku kuma me ye haka? Kuna ganawa da wanda ya hallici ita kanta uwae gijiyar ta ku, shi ne zaku wani tsaya rusuna mata?" Murmushi Juman tayi jin abinda Ayam d'in ta fad'a tace "Ba wai gaisheni suka tsaya yi ba, sun tsorata ne saboda basu san wa ke tahowa ba." Da sabon mamaki tace "Kamar ya? Tsoro kuma a cikin bautawa ubangiji?" Jinjina kai tayi ta kama hannunta suka nufi d'aki tana fad'in "Saboda a nan ba'a barin musulmi yayi ibadarsa yanda ya dace." Cak ta tsaya tare da d'an murza hannunta dake cikin hannun Juman har tayi nasarar raba hannayensu, idonta ne suka d'auki launi ja tsabar b'acin rai da takaici tace "Mah, idan sarki ba musulmi bane, me zai sa ya hana talakawanshi 'yancinsu? Wannan ai tauye' yanci ne ko a dokar k'asar nan, bare kuma a addinance." Girgiza kai tayi tace "A gaskiya Mah ba zan juri ganin haka ba, yanda kowane mai ji yana da addini yake bautarsa babu takura, ban ga dalilin da zai sa musulmi ma yayi bauta da takura ba, dan haka duka wani mai kad'aita Allah dake cikin gidan nan ya fito zamuyi sallah tare." Juyawa tayi da sauri ta kalli hadiman tace" Duk wanda kuka san addininmu d'aya da shi ku tara mana su a farfajiya." Da sauri Juman tace" A'a Ayam, kar ki fara da abinda zai saka rayuwarki a had'ari." Murmushi tayi tana kallonta tace" Mah, tun fa cikina na gudan tsoka nake cikin had'ari, bana jin kiramin had'ari a yanzu zai iya tsorata ni, dan da shi na girma." Bin bayan hadiman tayi da suka fita haka Juman ta bi bayanta jiki a mace tana mai k'arfafa zuciyarta cewa ba zata barta ita kad'ai ba. Tsaye tayi farfajiyar ita da Juman yayin da hadiman maza da mata suka dinga b'ullowa daga kusurwa daban daban, cikin k'ank'anin lokaci sai ga hadimai gabanta guda goma sha takwas, kallonsu tayi da kyau tace "Dukanku kuna da alwala?" Da "E ranki shi dad'e." Suka amsa mata, jinjina kai tayi ta kalli wasu dogarai biyu maza tace "Ku samo mana babban carpet." Da gudu suka juya suka nufi wani b'angare, jim kad'an suka dawo sun d'auko babban carpet guda sun tallabo, suna zuwa suka bud'eshi aka shinfid'a a nan, duba taron mutanen tayi da suke kallon ikon Allah har yanzu suna tambayar kawunansu me zai faru tace" A cikinku wa zai ja mu sallah azahar?" Kowa zaro ido yayi suka shiga kallon kallo, hakan yasa babu wanda yayi jarumtar nuna kanshi saboda tsoron me zai biyo baya, numfashi ta sauke ta kalli mazan dake gefe d'aya tace" Dukanku babu mai jarumtar da zai iya ne? Ko kuma mahaliccin na ku ne baku iya ganawa da shi ba?" Shiru wurin ya d'auka sai kawuna da suka sadda k'asa, d'orawa tayi da" In dai har taron maza kamar ku za'a rasa wanda zai jagoranci dayawa zuwa ga ubangijin talikai, to ina ganin dukaninmu babu anfanin rayuwarmu, dan ni dai a wuri mutuwa da kima ya fi rayuwa da tsor." Shiru tayi na dak'ik'u, jim kad'an kam wani matashi d'aya daga cikin masu bawa shukoki ruwa ya d'aga hannu yace" Ni zanyi jagorancin gimbiya, ko da hakan zai sa na rasa raina." Da jin dad'i sosai ta kalleshi tace" Addininmu bai yarda mu jefa rayuwarmu had'ari ba, amma wajen kare mutumci, addininmu, dukiyarmu, iyalinmu, addini ya bamu dama mu yi komai, dan haka mu daina b'oye addininmu alhalin wanda basa da addinin ma suke bayyana na su." Ai kam gaba ya shiga inda dukan hadiman suka shiga daidaita sahunsu, mazan na gaba sai kuma tazarar da aka saka tsakaninsu da mata ta kusan k'afa shida zuwa bakwai, sallah suka fara a nutse inda duka matan kalluban kansu ne suka yane kansu da shi. Sannu sannu hadimai da sauran dogaran gidan suka fara taruwa kallonsu, al'ajabi suke na ganin sabon abun, dan wasu basu tab'a gani ba ko da a b'oyen, saidai babu wanda yake jin zai iya tambayar wye silar wannan taro, dan kuwa kowa yasan bak'uwarsu ce, tunda haka bata tab'a faruwa ba har sarauniyarsu bata da wannan k'arfin halin. Raka'arsu ta k'arshe ce sarki Musail ya fito daga k'ofarda zata sadashi da fadarshi, ganin wannan taro yasa shi tsayawa yana kallonsu, hankalinshi tashe yake kallonsu yana zazzare ido, bubbuga sandarshi ya dinga yi ya rasa me ma zai fad'a, musamman jin yanda gidan yayi shiru, su kuma masu sallar suka duk'ar da kawunansu ka rantse basa numfashi tsabar girmamawa, lallai ya tabbatar wanda suke bauta a gareshi na da mahimmanci a garesu, suna girmamashi kuma suna jin kunyarshi tare da k'ask'antar da kansu zuwa gareshi. Juyawa yayi ya kalli sarki yak'i Adah dake bayanshi yace "Ka taho min da gimbiya Zafeera idan sun gama." Da sauri ya juya ya nufi shiga fadar, da mamaki Adah ya kalleshi yace "Idan ma ta gama ya ce? Lallai yarinyar nan barazana ce barinta a raye." Gyara tsayuwarshi yayi dan ya jirata kamar yanda ya ce, ya kai minti biyar a tsaye kafin ya ga sun fara tashi suna barin wuri ya k'arasa, a ladabce ya tsaya kusa da ita yace "Ranki shi dad'e gimbiya, mai martaba sarki na yana son ganinki yanzu yanzu?" Jinjina kai tayi ta mik'e a hankali hakan yasa Juman ma mik'ewa da sauri ta rik'e hannunta, kallon Adah tayi tace "Lafiya Adah?" Da girmamawa yace "Lafiya lau ranki shi dad'e." Kallon Ayam tayi fuskarta cike da damuwa tace "Ina jin tsoro Ayam, ina tsoron ko ya ga abinda ya faru yanzun." Murmushi tayi cikin nutsuwa tace "Mah, ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru da yardar Allah." Zage hannayenta tayi ta saka takalminta sannan ta ma Adah alama da ido su tafi, wucewa yayi gaba ita kuma ta bi bayanshi har zuwa fadar, har lokacin kuma bata daina kalle kalle ba dan har yanzu tsarin ginin masarautar na bata mamaki yanda aka k'erashi. Suna shiga fadar ta d'ora idonta akan sarki Musail dake zaune kan wata tamfatsetsiyar kujera ta alfarma hannunshi d'auke da sandarshi d'aya hannun kuma ya dafe hannun kujerar. Dhurani ne kawai a zaune sai Khatar a gefenshi shi ma zaune, cikin nutsuwa ta k'arasa tsakiyar kujerun nesa da sarki Musail a ladabce tace "Pah, an ce kana son gani na?" Cikin sanyi da taushi yace "Gimbiya Zafeera wa ya baki izinin tara min talakawan cen a cikin gida har ku dinga min wani surkulle?" Da fara'a a fuskarta tace "Pah, ba talakawan gari ba ne, dukansu hadiman cikin gidan nan ne." Had'e fuska yayi yace "E na gani, tambayarki na yi wa ya baku izini?" Da fara'a dai a fuskarta tace "Pah, ai domin ganawar bawa da ubangijinsa babu buk'atar neman izinin wani, da zaren yanayi ya bayyana ga bawa na lokacin ganawa da ubangijinsa, babu wani mahaluki da ya isa ya masa shamaki da hakan, indai ba mala'ikan d'aukar rai ne ya ziyarcesa ba." Cikin fushi da d'aga murya yace" Shiru! Kina so ki ce min akwai wani ubangiji ne bayan abun bauta Ghira?" A take ta amsa da" Akwai, wanda ya hallici talakawanka, ya hallice ni kuma ya hallice ka, abun bauta Ghira ba komai bane kamar yanda ba kowa bane face marar anfanin da ba zai anfani ko da kiyashi ba." Dhurani dake gefe yna ta hararenta jin an tab'o huruminshi yasa shi mak'ale murya yace" Gimbiya Zafeera, shi wannan abun bauta Ghira da ki ke magana a kan shi, shi ne fa yayi komai da kike gani, da izininsa komai ke faruwa, da kuma amincewarsa ke kanki kike raye a yanzu." Wata malalaciyar dariya ta saki ta kalleshi da kyau tace" Sai kuma gashi a gidan dana rayu babu sassak'en gunkinshi, to kenan ta ya har ya rayar da ni?" I'ina ya fara yana rarraba ido yace" E..to..ai buwayarshi..." D'aga mishi hannu tayi fuskarta a had'e sosai tace" Dakata, buwaya da kake magana a kai ta Allah mad'aukakin sarki ce, da kuma wannan buwayar zan buwayeku har sai mutanen garin nan sun gane gaskiya sannan sun fara bauta ga addinin daya cancanta, da sannu zan fayyace musu ku d'in hadimai ne kawai ga k'irkirarren abun bauta dan cika tunbinanku da kuma aljihanku." Nunashi tayi da yatsa ta d'aga girarya d'aya sama tace" Daga k'arshe kuma, kar ka kuma saka min baki yayin da nake magana da mahaifina." Juyawa tayi kan saeki Musail da ya ji gabanshi ya fad'i na shakkun abinda zai fad'a mata, Khatar kam da sauri yayi k'asa da kanshi yana satar kallonta, dan shi kam haka kawai take tsoratashi tun had'uwarsu a Larhjadin. Cike da k'arfin hali sarki Musail yace "Kinga Zafeera, ba'a son sake ganin wannan taron da kika min yanzu a cikin gida na, idan ba haka ba kuma zaki tilastani na d'auki mataki a kanki." Sakin murmushi tayi tace "Shikenan Pah ba za'a sake ba, amma tunda ka ce a cikin gidanka ne baka so, ka ware mana waje na musamman da zamu dinga yin ibadarmu hankali kwance, ko kuma mu koma babban gida dukanmu." Cikin b'acin rai kamar zai cijeta yace "Ke kina lafiya kuwa? Ina fad'a kina fad'a?" Yar dariya tayi ta girgiza kai tace "Pah, ba kana fad'a nake fad'a ba, sai bayan ka fad'a nake fad'a." Had'e dariyar tayi ta saka murmushi a fuskar sannan tace "Zan iya tafiya Pah?" Wani huci ya shiga saukewa kafi ya d'aga hannu ya mata alamar ta fita kawai, dariya tayi irin ko a jikinta nan tace "Nagode." Saida ta kalli Khatar da kanshi ke k'asa kafin ta saki murmushi ta fice a fadar, cikin farin ciki da jin babu abinda zai faru ta samu Juman tsaye tana jiranta inda ta barta, kama hannunta tayi suka nufi b'angaren Juman d'in tana tambayarta "Me ya faru a ciki? Ya gani ko?" Ba alamar damuwa tarz da ita tace "Ya gani, kuma babu abinda ya fad'a, zamu ci gaba da taimakon Allah." *Tana* fita Dhurani ya sauke numfashi ya kalli Adah daya rik'e hab'a, sarki Musail kuma saukowa yayi daga kujerarshi yana fad'in "Ina! Ta ya haka zata dinga faruwa? Ya zanyi yanzu?" Dhurani ne ya kalleshi yace "Ai matakin kawar da ita kawai zamu d'auka ranka shi dad'e, dan in ba haka ba labarin nan ya kusa tabbata a kan mu." Cikin k'araji sarki Musail yace "Amma ai tun zuwanta na shirya hakan dan mutuwarta ta zama kamar had'ari, da zuwa yanzu jana'izarta muke gabatarwa." Khatar ne ya d'aga kai ya kalli saeki Musail d'in yace "Sarki na, ku bar min komai a hannu na, ni zanyi wannan aikin." A haukace Musail ya kalleshi yace "Kai da ta shigo nan kanka ke k'asa, ta ya ne zaka kashe mana ita?" D'an murmisawa yayi yace "Mai martaba, ai *wata kokowar* (wanda bai siya ba ya siya ba, mai nemanshi ya tuntube ni, akwai cakwakiya) bata buk'atar jarumta, tunani take da buk'ata." Dhurani ne yace "Hakane kuma, ina ga a bashi dama ranka shi dad'e." Jinjina kai yayi yace "Shikenan, sai ka jaraba mu gani me zaka iya." Shi ma jinjina kai yayi yace "Nagode ranka shi dad'e, daga yanzu zuwa daren yau zaku ji kukan hadiman da suke tare da ita." Daga haka su ma zaman na su ya k'are dan abinda ke damunsu kenan, sun zauna ne da niyyar tattauna maganar ruwa da ta zo mishi da ita, amma bala'in da ta zo da shi ya girmi waccen sai ma ya mantar da su gaba d'ayansu. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:40 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *29* Kamar jiranshi ake ya koma b'angaren shi Adah ya mik'o masa wayarshi yace "Yallab'ai ana kiranka a waya." Kallonshi yayi kafin ya sa hannu ya karb'a ya duba lambar da babu suna, k'arasawa yayi cikin falon ya nemi guri ya zauna tare da aje wayar gefenshi har ta tsinke, a tsanake Adah ya kalleshi yace "Ranka shi dad'e, na ga har kiran ya tsinke baka d'aga ba?" Yatsin fuska yayi yace "Bak'uwar lamba ce." Cikin ladabi Adah yace "Hakane ranka shi dad'e, amma akwai yiwuwar wani mai mahimmanci ne, duba da lambarka ce ta manyan mutanenka." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce wani abu sai kiran ya gajeren sak'o ya shigo wayar, kallon Adah yayi yace "Duba ka gae aka ce." D'auka yayi ya duba kamar yanda ya ce, da sauri ya kalleshi yace "Yallab'ai, *Abraham Joshua* ne fa, komishinan kud'i da kake shirin yanda zaku tattauna da shi." Da sauri ya zura hannu ya karbi wayar yana k'ok'arin maida kiran yana fad'in "Ka tabbata? Abraham Joshua?" Kiran da ya sake shigowa yasa sarki Musail kallon wayar, jim yayi bai d'aga ba na yan dak'ik'u, daga bisani kuma sai ya d'aga, Adah na gefe yana kallonshi jin yanda suke gaisawa kamar sun san juna dama, bayan gaisuwar ne Abraham ya d'ora da "Ranka shi dad'e sarki na, dama wata muhimmiyar magana ce ta sa na kiraka." A tsanake shi ma ya amsa da "Muhimmiyar magana kuma? To ina jinka, Allah yasa dai lafiya?" Da fara'a yace "Ah lafiya lau, dama d'an waje na ne ya ke fad'a min ya ga d'aya daga cikin 'ya'yanka kuma ya na so." Shiru yayi daga haka na dak'ik'u sannan ya d'ora da "To na amince masa ya nemi aurenta a wajenka, saidai ya cika sauri dayawa, da na fad'a masa zamu je tare nan da kwana biyu bayan na dawo daga tafiya, sai ya nuna bai yarda da hakan ba, 'ya'yan manya a kowane lokaci farautarsu a ke, dan haka ya ce shi zai fara zuwa a yau, ni sai na zo daga bayan." Numfasawa yayi sosai sannan yace" Fatan dai ba muyi gaggawa ba ranka shi dad'e?" K'urawa Adah ido yayi yana kallo tare da shiga kogin tunani, hark'allar da yake son k'ullawa da kwamishinan kud'in ta isa ta sa ya amince masa, dan haka ya d'an murmusa yace" Ok, wannan ai ba matsala ba ne, ya zo kawai, nan ma kamar gidan su ne." Numfashi ya sauke kusan sau uku kafin yace" Amma...wace a cikin gimbiyoyin na wa?" A hankali yace" E to...ina jin dai kamar k'aramar." Jim sarki Musail yayi sai kuma ya tab'e baki a ranshi yake fad'in" Idan ta zama gawa kafin nan sai a maida auren kan gimbiya Zafreen." A zahiri kuma murmushi yayi ya amsa da ba komai kawai sai sun zo, har da tagomashin fad'in" Zan tura dreba ya je ya d'aukoshi." Da sauri Abraham yace" Yallab'ai sai dai ba shi kad'ai ya taho ba, tare yake da mai tsaron lafiyarsa." Jinjina kai Musail yayi yace" Wannan ba damuwa bane, ko su na wa zasu zo akwai masaukinsu." Suna Ida wayar ya kalli Adah yace" Ka kula da komai Adah, ka tura dreba ya d'aukosu a filin jirgi, sannan ka sa a shirya musu tarba ta musamman, dan neman aure zasu zo." Da sauri Adah ya kalleshi cikin ladabi yace" Ranka shi dad'e a gafarce ni, amma neman auren wa daga cikinsu?" Ba tare daya kalleshi ba yace" Zafeera." Da mamaki yace" Zafeera kuma? Ranka shi dad'e wacce muke shirin turata wata duniyar, me ye hikimar yin hakan?" Wani lallausan murmushi yayi yace " Ka zuba ido kawai ka sha kallo." Rusunawa yayi ya jinjina kai tare da fad'in" Na barka lafiya sarkina." *Suna* zaune d'akin Juman hadimai biyu suka shigo da farantan abinci, Ayam dake duba zoben da Juman ta nuna mata na azurfa wanda ta ce Urab ya bata shi, ajeshi tayi kan k'aramin teburin, suna zuwa su ma suka aje kwanukan akan teburin, a tsanake Juman ta kallesu tace "Me aka dafa yau?" Cikin ladabi d'ayar ta shiga bud'e mata kwanukan dan ta gani da idonta, murfin kwanan ta aje a k'asan zoben, hakan yasa Ayam data gani tace "Mik'o min zoben nan?" D'aukowa hadimar tayi ta mik'o mata, karb'a tayi saidai sub'utar hannu yasa zoben sub'ucewa ya fad'a cikin farfesun kifin da ke kusa, da sauri Ayam ta furta "Oh Allah." Da sauri hadimar ta d'auki cokali tana fad'in "Oh! Sannu gimbiya, bai fallatsar miki ba?" Girgiza kai tayi tace "A'a, ki gaggauta ki ciro shi." Cokalin ta sa ta d'auko zoben nan na azurfa, abun mamaki ya canja kala yayi bak'i sid'ik, sam Ayam bata fahimci me sauyin zoben ke nufi ba, amma Juman da ta san komai tuni ta mik'e tsaye tana dafe da k'irjinta tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Kallonta Ayam tayi tace "Mah, me ya faru? An ciro shi ai." Hankali tashe tace "Ayam baki gani bane? Guba ce a abincin nan." Zabura tayi ita ma ta mik'e tsaye tace "Guba kuma? Ta ya mah?" Nuna mata zoben tayi da hannun hadimar har ya fara rawa tsabar kad'uwa tace "Dubi zoben mana ki gani, ya canza kala." Kallon zoben tayi sannan ta kalli hadiman tace "Ta ya haka ta faru? Wani ne ke sonkashe min uwata?" Girgiza kai sukayi a tare alamar a'a suna neman fashewa da kuka, cikin tsawa Juman tace "Yanzu da ku za'a had'a baki a nemi kashe min 'yata? Me ta muku? Wa ya saka ku? Me aka baku da ni ba zan iya baku ba?" Kallonta Ayam tayi a nutse tace "Mah, kwantar da hankalinki." Kallon hadiman tayi tace "Ku d'auke abincin ku fita da shi, ku fad'a musu Allah ya fi su." Cikin rud'u Juman ta fashe da kuka tace "A'a Ayam, dole mu san..." Matsawa tayi kusanta ta rumgumeta tace "Shiiii! Ya isa Mah, ki nutsu kin ji, ki bar min komai a hannu na." Jinjina kai tayi tana sauke numfashi ta bi hadiman da kallo da su har ga Allah basu san ta ya haka ta faru ba. D'agowa tayi daga jikin Ayam tace "Bari na je da kai na na samo mana ko da kayan marmari ne, daga yanzu ba zamu sake yarda da kowa ba." Jinjina kai tayi alamar to, zaune tayi bakin gadon inda Juman ta fita a d'akin dan samo musu abin ci. *Giobarh* Tana kwance kan doguwar kujera da wayarta tana amsawa, cike da kissa take farfar da ido tana fad'in" Haka ni ma na yi kewarka waziri na, yanzu ka fad'a min yaushe zamu had'u?" Daga wajen wanda ta kira waziri ya amsa da" Ina so mu had'u Joy, sai dai dole mu dinga taka tsantsan, kinsan fa abubuwa sun fara canjawa, musamman yanzu da shegiyar yarinyar nan ta bayyana garemu." Yar dariya tayi tace" Da alama tsoronta ya gama tasiri a zuciyarka, ai ban sanka da tsoro da sarewa ba, k'aramar yarinya ce fa? Ubanta ma ya ya iya da mu bare kuma ita?" Jinjina kai yayi daga inda yake yace" Hakane, amma kinsan ita daban ce, a gaskiya bana iya d'aga idanu na a gaban yarinyar nan, kwarjininta ya fi na ubanta Musail, kamar...wata zakanya haka nake ji idan na ganta." Tsaki tayi ta tashi zaune tana fad'in" Ya isa haka malam, ya kake so ka nuna min ka fara sarewa da lamarin, kana so kace kenan mu hak'ura da burinmu?" A sanyaye yace" Ko bamu hak'ura ba Joy do'e dai mu bi a hankali." A hassale tace" Ba zamu bi d'in ba, zamu tafi da gudu dan cika burinmu, ta jima ba tayi abinda za tayi ba, kar ka manta shekara ashirin da shida mun aikata abinda har yanzu babu uban daya ganemu bare ya d'aga canzan, kuma idan akwai wanda za'a zarga a ciki sarki Musail ne." Numfasawa yayi yace" Na san da wannan, matsalata da ke garaje, Joy hanyar da muka bi muka aiwatar da waccen tsarin, idan kika bi a hankali wannan ma haka zamuyi." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan na ji, yanzu ya zamuyi da kai?" A hankali ya amsa mata da "A game da me fa? Halan kud'i kike so?" Yatsina fuska tayi tace "E mana, kai ma kasan ai zan buk'aci kud'i, tunda Wudar ya juya min baya saboda banzar yarinyar nan." Numfashi ya sauke yace "Shinkenan na ji, zan turo miki anjima, dan nasan wajenku yanzu dare ne." A sangarce ta amsa da "Hakane, shikenan sai na ji ka." Aje wayar tayi a gefe ta koma ta kwanta ta lumshe ido tana tunanin abubuwan da suka aikata masu yawan gaske ita da waziri Khatar d'in, wanda ba komai ya jawo haka ba sai soyayya, asali a makaranta suka fara soyayya a babbar jami'ar Khazira, a k'arshe sai iyayenshi suka zab'a mishi mata yayi aure, dan dama shi da ita soyayyar shan minti ce aka buga, duk da auren da yayi su kan ziyarci juna su kuma sha soyayyarsu, tsawon lokaci kuma bayan irin kitimurmurar da suka k'ulla ne na son cikar burinsu sai ta koma Giobarh wajen yayarta tana kula da ita. Yanda ta ji an d'ora hannu a k'irjinta yasa ta zabura ta tashi zaune tan kiran "Kai! Waye..." Sarki Wudar ne tsaye gabanta cikin saussauk'ar shigarshi ta kayan bacci, hular dake kan shi kuma ta tabbatar mata akwai abinda yake so gareta shiyasa ya shigo ta b'arauniyar hanya zuwa wajenta, had'e fuska tayi ta kauda kai daga gareshi ba tace komai ba. Murmushi yayi tare da zaa gefenta ya jawota jikinshi yana sumbatar kumatunta yace "Oh my madam, me ya faru ne haka ake had'e min fuska kuma?" Tureshi tayi da k'arfi cikin masifa tace "Me ma ya faru kake tambaya ta? To ban sani ba, ka ga tashi ka fita daga d'akin nan." Sake jawota yayi cikin dubara ya zura hannunshi kan mamanta dake babu bras a cikin rigar bacci, farin gemunshi ya fara shafa mata a kafad'a, inda bakinshi ke kan kunnenta yana rad'a mata" Haba sarauniyata, me yasa za ki fad'i haka? Ni ne fa, sarkinki." K'ok'arin kubcewar da tayi yasa shi sake k'amk'ameta a jikinshi, mayar da hannunshi yayi kan mararta ya shafa, tauri da kuma d'umin da take ji a wurin da neman mai tallafa mata a lokacin yasa ta lumshe ido ta sauke numfashi. Cikin dakusashiyar murya ta furta "Me yasa ka dinga wulak'antani a kan ta?" A hankli ya shiga sauke numfashi a cikin kunnenta ya rufe ido shi ma, a zuciyarshi ya amsa mata da "Saboda ta fiki komai a wajena, da ita zan kai matakin da babu wanda ya zata a duniya." A zahiri kuma cikin taushin murya yace "Kiyi hak'uri kin ji, ai yanzu bata nan." Cikin fad'a tace "Amma ai na ji labarin kun yi alk'awarin aure da ita, ko ka d'auka ban san me ake ba ne a gidan?" Jim yayi da tunanin a sanda sukayi maganar nan wa ya ji? Sai kawai ya share dan yasan kad'an daga aikin gidan masarauta kenan, cikin gurnani na abinda ke damunshi wanda shi ya kawoshi nan ya sake zura hannu yana shafa mamanta yace" Rabu da kowa kinji, ki kwantar da hankali yanzu, kinsan fa ba ke kad'ai ba ce ko?" D'ago kanshi yayi yace" Yanzu tashi mu je ciki ki ga wani abu." Matsawa tayi daga gefenshi tace" Ka ga malam, ni ba yarinya ba ce da zaka min wani banzan wayo kamar wata yar talla, na san me ya kawoka wajena kuma ban da buk'ata ni." D'auke kai tayi daga gareshi tace" Sai ka je can figaggiyar Zafeera ta ke ko wa? Ta sauke maka abinda yake damunka." Mik'ewa tayi tsaye d'auki wayarta sannan ta kalleshi ta sake fad'in" Ko kuma ka je nakasashiyar matarka ta biya maka buk'atar, amma ni ma daga yanzu na san ciwon kai na." Tana gama fad'a ta juya da sauri ta shige d'akin baccinta ta rufe da makulli, da kallo ya bita har ta rufe k'ofar, tab'e baki yayi ya mik'e yana d'an girgiza kan shi, to in banda abun Joyran ma ta ya sarki zaki fad'a masa haka? Gidan nan da ke cike da bayi da hadimai. D'akinshi ya koma inda ya samu d'aya daga cikin masu tsaron k'ofar shi ya kirashi zuwa ciki, bayan sun zauna ya nutsu ne yake fad'a masa "A cikin hadiman gidan nan wacece ka yarda da tsaftarta da kuma rik'on sirrin ta?" Sadde kai ya sake yi cikin girmamawa yace "Wajen tsafta kam ba za'a rasa ba ranka shi dad'e, a ge da rik'on sirri dai ne bamu da tabbas, amma zamu iya d'orata a hanya mu da kanmu." Jinjina kai sarki Wudar yayi yace "Wa ya fad'a maka amana koyawa mutum ita ake? Ai da ita ake haihuwar mutum." K'ara sadda kai bafaden yayi a zuciyarshi yace "Amma ni a zaman da na yi da abokina na fahimci addininshi ne ya koya masa zama hakan, ko ba'a haifeka da ita ba indai kana wannan addinin, to ya zama wajibinka ka koyawa kanka ita, rashin samun amana kuma a wajen mutum mai wannan addinin, to tabbas ka tabbata gurb'atacce a cikinsu." A zahiri kuma cewa yayi" Hakane ranka shi dad'e, amma girmanka ya isa ya samar da mai amana da rik'on sirri." Jinjina kai yayi amma bai xe komai ba, kusan minti biyu a haka kafin yace" Ka je ka zo min da ita nan." Da sauri ya mik'e yace" An gama sarki na." Fita yayi da sauri dan cika umarninshi, sarki Wudar kuma mik'ewa yayi ya koma d'akinshi dan zaman jiran wacce za'a kawo masa. A k'alla minti ashirin ya d'auka kafin suka dawo tare da wata budurwa, har k'ofar d'akin ya k'wank'wasa ya basu izinin shiga, shiga sukayi a tare ind ya d'ora ido akan matashiyar, bata da laifi kam kyakyawa yar duma duma, jikinta ma babu alamar k'azanta ko datti, saidai alamu sun nuna a tsorace take, dan gaba d'ay cikin d'ar d'ar take ta k'ame ta k'i sakin jikinta. Kallon bafaden yayi ya masa alama da zai iya tafiya, jinjina kai yayi ya tashi zai fita yace "Na barku lafiya." Yana kaiwa bakin k'ofar ya bud'e Umad kuma na tsaye bakin k'ofar, d sauri ya sake zubewa k'asa yana fad'in "D'an sarki jikan sarki, barka da warhaka shugaba na, barka, barka." Wani kallo Umad ya masa hakan yasa ya rab'ashi ya wuce sum sum sum, cikin takon isa ya shigo d'akin yana kallon mahaifin na shi da kuma yarinyar nan. Wangale baki sarki Wudar yayi ya fara kame kame ya rasa abin fad'a, har saida Umad d'in ya tsaya gabanshi ya kalli yarinyar yace "Je ki." Da sauri jikinta na rawa ta kama hanya ta fice a d'akin, ganin haka yasa Wudar matsawa kusanshi ya dafa kafad'arshi yace "D'ana, ka gane ko? Wannan d'in ai...ita.." A nutse ya k'urawa fuskarshi ido yana kallo yace " *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:40 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *30* A nutse ya k'urawa fuskarshi ido yana kallo yace "Ita d'in 'yar wasu ce, kuma addininta bai lamunce mata aikata abinda ka so aikatawa da ita yanzu ba, dan ba siyota kayi a kasuwar bayi ba, amma zaka iya neman aurenta hannun iyayenta, dan a gaskiya bana buk'atar wani k'anin wanda aka samu ba ta hanyar aure ba." Waro ido yayi yana kallon Umad d'in dake sake k'are masa kallo, a ladabce ya sanyaye yace" Ni zan tafi, lokacin tashin jirginmu ya kusa, sai na dawo." Juyawa yayi zai tafi sai kuma ya dakata, ganin kallon da yake masa ne yasa shi fad'in" Mahaifina ka kwantar da hankalinka, babu wanda zai ji maganar nan daga bakina, na san me yake faruwa tsawon lokaci, hakan yasa ban cika son zaman gidan nan, kuma ban ga laifinka duba da halin da mahaifiyata take ciki, takaici d'aya ne kawai yanda ka kasa samun halak d'inka kake bibiyar haram, haram d'in ma wacce ta k'azanta." A ladabce ya girgiza masa kai yana sadda kanshi yace" Dan Allah Babana kar ka tilasta mata ta zubar da cikin nan, dan kuskure ne akan kuskure." Juyawa yayi a ladabce ya fice a d'akin ba tare da Wudar ya ce komai ba, dan sosai maganganun suka dakeshi, saboda bai tab'a tsammani ba kuma abun ya zo masa a bazata, hakan ya hanashi tambayar ina Umad d'in ma zai je? Dan kunya ta gama lullub'eshi baya jin zai sake d'aga ido ya kalleshi. *Khazira* Ka rantse da Allah mahaifinta kuma sarki Musail bai gargad'eta kan sallah nan ba, domin kuwa la'asar ma a farfajiyar suka yi ta kamar yanda suka yi sallah zuhur. Suna cikin sallahr nan motar su Umad ta shigo gidan, saidai madadin k'ayatuwar gidan ta d'auki hankalinsu, sai ya zamana sallah ce ta d'auki hankalinsu duba da abu ne da ake yi a b'oye. Saida suka fito daga motar wani bafade ya d'auko jakarsu k'waya d'aya tak ya nufi ciki da ita, girgiza kai Umad yayi dan yasan wannan kam na daga cikin aikin Ayam. Bin bayan bafaden sukayi kamar yanda sarki Musail d'in ya umarta a saukesu a babban falo na babban b'angare dan su fara cin abinci, sannan a nan ne zai had'u da Ayam d'in. Suna kammalawa suka nufi shig ciki sai Juman ta kalleta tace "Ke je ina zuwa." Da alamar tambaya tace "Ina zuwa Mah?" A sanyaye tace "Zan ga mahaifinki ne." Jinjina kai tayi ta shige ciki, tana shiga falon suka had'a ido da wata jakadiya, sam bata kula da tsiyarta ba ta taka matakalar ta shiga hayewa sama da sauri. Sam bata gansu a zaunen nan ba, amma shi tun shigowarta yake kallonta, saidai yanzu kuma da take hawa matakalar sai ya ji gabanshi ya tsiri fad'uwa haka kawai, yanda take hawa da gudu gudu haka zuciyarshi ke harbawa tana dokawa, jikinshi ke bashi kamar da wani abu, hankalinshi ya kasa kwanciya duk da bai ga wani abun zargi ba. Yanda jinin jikinshi ke tsinkewa yana wani d'add'aurewa yasa shi d'an mik'ewa tsaye, kalonshi Haman yayi yace "Ya dai? Ina zaka je kuma?" Girgiza kai kawai yayi tare da d'an takawa yana ci gaba da kallonta har ta haye na d'aya ta shiga taka na biyun wanda daga shi zai sadata da d'akin Juman, bata ankara ba, kamar a mafarki, ba zato ba tammani kawai ta ji k'afarta tayi wani k'iiiiiiii, takalminta da a plate ne masu d'amara, tiles d'in kuma irin mai shegen walk'iyar nan ne da sulb'i, hakan yasa duk isa da izzar Zafreen kan ga bata cika anfani da takalmi masu tsini ba, idan ka ga ta sakasu sai ta sauko k'asa. Abun ne ya had'u yayi yawa, hakan yasa ta kasa rik'e kanta yanda bata da wata dabara daya wuce ta rintse idonta ta anbaci "Ahhhhhhh." A k'asan zuciyarta kuma Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un take furtawa, saidai firgicin ya hanata fito da shi, dan ba kad'an ba silb'in nan ya ja ta. Bata yi k'asa a gwiwa ba wajen fara mirginowa daga kan matakalar, da wani irin sauri ya ma matakalar hawa biyu a na uku ya had'e da ita tana neman k'arasa durkowo, cak yasa hannayenshi da wata irin zummar cimmawa ya d'auketa cak a jikinshi. Tabbatarwa da tayi ba'a k'asa take ba, sannan ta ji a jikin mutum take bayan wuntsilawar data fara yi, ga kuma k'amshin daya daki hancinta wanda a jikin mutum d'aya ta san shi, da kuma yanda shi ma ya wani k'amk'ameta sai kawai ita ma tayi luf a jikinshi ta sake rik'eshi sosai, idonta kuma har yanzu suna rintse, inda ta shiga sauke numfashi tana fad'in "Oh Allah, Oh Allah na, Alhamdulillah." K'am k'am ya ci gaba da mak'ale mata kamar wata wacce za'a k'wace masa, shi ma idonshi a lik'e suke inda gabb'an jikinshi ke karb'an sak'onnin da zuciyarshi ke wadatuwa da su, sai ya ke jin kamar wata masoyiyar daya jima bai had'u da ita ba ne, sai ya ji kamar namijin da aka tura yak'i ne ya dawo da ranshi ya kuma samu iyalinshi lafiya, wata irin kewar wacce yake rumgume da ita ya ji tana lullub'eshi, bugu da k'ari ga wani yanayi da wani shauk'i da ya d'ebeshi kamar ya daure ya sumbaceta. Yanda siririyar muryarta ta karad'e gidan sanda tayi wannan ihun yasa duk wanda ke b'angaren saida ya ji kuma ya fito har da Zafreen dake kwance a d'akinta tana danna waya. Haka ma duk da ihun a kad'an ya shiga dodon kunnenta, amma abunka ga mahaifiya sai Juman ta juya tare da furta "Ayam." Da gudu ta fice a fadar ba tare data fad'i me take son fad'a ba, sarki Musail daya shiga kid'imar abinda ta fad'a masa na batun gubar da aka zuba musu shi ma da wani irin sauri ya sauko daga kujerarshi ya bi bayanta kamar zai ruga shi ma, hakan uasa fadawan duk suka rufa masa baya Khatar da Dhurani suna mai fatan a ce ta mutu daga ihun nan da suka ji. Shigowarsu a hargitse yasa su saurin dawowa hayyacinsu, raba jikinsu sukayi da sauri suka kalli juna kamar an firgitasu, Ayam ce hakan ya firgita ta har tace "Kai ne? Yallab'ai?" Da sauri Juman ta matso kusanta tana duba jikinta tace "Me ya sameki Ayam? Ihunki na ji?" Da sauri sarki Musail yayi kanta yana d'aga hannunshi alamar zai dafa kanta yace "Me ya sameki? Kina lafiya ko?" D'aga kai tayi alamar e sannan tace "Lafiya ta lau Pah." Juman ce ta sake fad'in "Me ya faru to? Wani ne ya miki wani abu?" Girgiza kai tayi alamar a'a tana satar kallon Umad, hakan ne ya b'ata ran sarki Musail yace "Ana magana kuna ji kunyi shiru, a cikinku babu wanda zai fad'a mana me ya faru ne?" D'aya daga cikin hadiman dake kawo abinci ne tace "Ranka sho dad'e muna kawowa bak'i abinci, shi ne muka ji ijunta daga sama, kafin mu farga silb'i ya jata ta fad'o daga..." Hankalinshi a matuk'ar tashe yace "Daga saman nan?" Ya fad'a yana nuna saman, a sanyaye hadimar ta jinjina kai, sake kallon Ayam yayi ya fara takawa zai tunkareta, kamar kuma an tsikareshi saiya dakata tare da basarwa, a wani gadarance ya kalli Umad dake kallonshi yana son tabbatar da abinda idonshi ke hango masa a game da sarki Musail d'in. Cikin k'asaita ba tare daya d'auke ido daga gareshi ba yace "Waye kai?" Fuskarshi babu alamar rusunawa, idonshi tsaf suke kallon cikin na sarki Musail wanda ba kowa ke haka ba, fuskarshi babu alamar ladabi ko zai girmamashi, a gadarance ya furta "Umad." K'ank'ance ido sarki Musail yayi yace "Ba sunanka na tambaya ba, waye kai na ce?" Da sauri Haman dake gefe a tsaye tun sanda Ayam ke burususuwa tana fad'owa ya mik'e ya matso, cikin ladabi da girmamawa sam ya ma manta da tsarin da suke a kai yace "Yallab'ai, shi ne ai abo...mai tsaron lafiya ta." D'auke kai yayi ya kalli Haman d'in yana yatsina fuska, kallo ya k'are mishi sai ya ga indai ba wani abu ba kuma, a zahiri dai kam sam Umad bai yi kama da wanda zai zama abinda Haman d'in ke fad'a ba, duba da wasu b'oyayyu da kuma bayyanannun yanayi dake tattare da Umad. Da sauri sauri Zafreen ta fito daga d'akinta hannunta rik'e da waya, tana zuwa ta tsaya cak tana kallonsu tace "Pah, me yake faruwa a nan?" Kafin ya bata amsa kuma ta kai kallonta kan Umad, da wani irin zumud'i ta nufeshi bata tsaya komai ba ta fad'a jikinshi ta kwanta tayi luf da dariya a fuskarta tana fad'in "Yallab'ai, kai ne a nan ma?" D'agowa tayi daga jikinshi ta kalli fuskarshi yanda yayi sororo da al'ajabin dama arharta har ta kai haka? Cikin farin ciki tace "Yallab'ai ni ka biyo ko? Na sani da ma kai ma kana so na." Zura hannunta tayi cikin na shi hannun ta mak'ale masa kamar za'a rabasu, Juman kallonta take da mamakin irin yanda ta ballagazar da kanta haka, kamar ba wannan mai izzar da d'agawa ba? Gashi babu kunyar kowa haka take tsaye da kayan jikinta, farin wando na jeans iya cinyoyinta da riga kalar pink mai siraran hannaye, duk da kyanta ya bayyana da kyakyawar surarta, amma dai babu kimarta a idon masu kallonta haka kuma darajarta. Tunda ta fad'a jikinshi Ayam ta ji fad'uwar gaba tare da jin wani haushi ya taso mata da takaici, har saida ta kasa b'oyewa ta ja d'an k'aramin tsaki ta d'auke kai daga kallonsu tana yatsina fuska, haka kawai abun ya b'ata mata rai har tana jin da zata samu damar keb'ewa da shi a yanzu data tuhumeshi akan me da ta rumgume shi bai tureta ba? Bata sake kallonsu ba saida ta ji Musail yace "Ina kika san shi?" Cikin zumud'i da rashin kunya tace "Pah ai a makarantar da na je a nan yake koyawa." Wani kallo Dhurani ya masa yace "Idan kuma malami ne kai, ta ya ka zama mai bashi tsaro?" Wani kallo ya wurgawa Dhurani da alamar b'acin rai yace "Aikin gwamnati na ke, duk wanda ya tari gabana zan yi." K'ura masa ido Juman tayi ta kasa d'aukewa har saida murmushi ya sub'uce mata, sak kallon yayanshi take masa Urab, hakan yasa har ya fahimta ya d'an karkata idonshi ya kalleta, cike da kunya da girmamawa ya rusuna idonshi tare da kanshi a ladabce yace "Barka sarauniyata." Sake murtuke fuska sarki Musail yayi ganin sai matarshi ya sakar ma fuska amma shi ya maidashi kamar wani sakarai ma, jinjina kai yayi a b'oye sannan ya kalli Haman yace "Sannu da zuwa." Rusunawa yayi ace "Barka yallab'ai." Muryar Juman ce ta dawo dasu da ta kalli Umad tace "Sannu ko?" Jinjina kai yayi a ladabce yace "Sannu ranki shi dad'e." Yatsina fuska sarki Musail yayi yace "Mu je mu ci abinci." A sanyaye Ayam ta mak'ale kafad'a tace "Ni dai na k'oshi." Juman ma sama da k'asa ta kalleshi tace "Ni ma haka." Hannun Ayam ta kama zasu bar wuri ta kalli Umad tace "A ci lafiya." Hanyar masaukin Ayam suka nufa inda sarki Musail ya bisu da kallo, a ciki yayi k'wafa alamar zku sani sannan ya nufi wajen cin abincin ba wai dan yana buk'ata ba sai dan bak'inshi. Rankayawa sukayi kan teburin Umad na ta k'ok'arin b'amb'are hannunshi cikin na Zafreen amma ta rik'e gam, har saida suka isa duk suka zazzauna, tsaye ya so yi dan sake k'ara fahimtar komai na gida da takon kowa, amma sai Zafreen ta zaunar da shi da k'arfi har saida Musail ya kalleta yace "Ke!" Sai kuma ya d'auke kai yana girgiza kan shi, haka aka zuzzuba abincin kowa ya fara ci. Cokalansu kad'ai ke k'ara a wurin, cikin siririyar murya Zafreen ta kalli sarki Musail tace "Pah, kasan na jima ina fad'a maka ban samu wanda ya dace dani ba a garin nan?" Zuba mata ido yayi shi dai bai ce komai ba, d'orawa tayi da "To yanzu na samu, wannan ne." Ta k'arashe tana nuna Umad da ka rantse baya jin yaren ta, duk da dai d'in gaskiya bai cika jin yaren slovaque ba, amma dai yana ji jefi jefi saboda yanayin aikinshi da shige shige da kuma sa kai. Haman a dake ji jefi jefi da Khatar da kuma Adah duk kallonta sukayi dan Dhurani tafiyarshi yayi bai tsaya ba, sarki Musail ma kallonta yake yi kamar ya wanka mata mari, haushin hakan yasa bai ce k'ala ba sai Haman daya kalla a nutse yace "Me ye sunanka?" A ladabce ya amsa da "Ranka shi dad'e sunana Haman." Jinjina kai yayi irin na dattawa yace "Haman Abraham Joshua kenan?" Gyad'a kai yayi alamar e, lumshe ido yayi alamar gamsuwa, a tsanake ya sake furta "Me ye aikinka? Kuma a ina ka fara sanin Zafeera? Me kuma ya sa kake son aurenta?" Cikin d'ar d'ar Haman yace "Yallab'ai na kammala karatu na, inda nake da burin mahaifina ya sama min aiki a babbar ma'aikata, Zafeera kuma mun fara had'uwa ne a Giobarh, saidai ban mata magana ba a saida na fara sanin wacece ita, ina kuma so ne na aureta dan ina sonta." Wani hamshak'in murmushi sarki Musail ya saki yace" Bayan son da kake mata, sai kuma wane dalili?" A hankali ya karkata ya saci kallon Umad da shi ma ke kallonsu ko abincin baya ci, sai kuma ya kalli sarki Musail yace" Saboda yar babban gida ce, ita ce ta dace ni." Sauk'akk'en murmushi ya saki ya d'an fara tsakurar abincin yana fad'in" Mu ci abinci yanzu, nan da awa biyu zan had'aku da ita dan ku tattauna, idan kun fahimci junanku mahaifinka na zuwa nan ranar d'aura muku aure za'a saka." Wani k'ayataccen murmushi Umad ya saki a ranshi ya ayyana" Lallai ma, ku gama duk shirin ku, na wa ne zai yi aiki a k'arshe." Haka suka ci gaba da cin abincin da tattaunawa tsakanin Haman d'in da sarki Musail, bayan su babu wanda ya saka musu baki banda Zafreen dake ta k'ok'arin d'aukar hankalin Umad d'in tana ta washe masa baki. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:41 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *31* Wajen Ayam kuma d'aki suke ita da Juman inda ta tambayeta a tsanake "Mah, a game da lamarin ruwan garin nan, yau nayi magana da wasu daga cikin talakawa sun fad'a min komai, ya zanyi na taimakesu akan haka?" A tsanake ita ma tace "Ayam ai maganar ruwan nan kasuwanci ya shiga cikinshi, duk da gwamnati na iya yin ta, bana jin zaki iya wani abu tunda baki da abu biyu." Da alamar tambaya ta kalleta tace "Kamar ya Mah?" Numfashi ta sauke tace "Na d'aya baki da kud'i, na biyu baki da iko." Da mamaki tace "Idan ina da su kenan zan iya taimakon al'umma?" Jinjina kai tayi tace "Tabbas, idan kina da kud'i zaki iya taimaka musu, idan kina da iko zaki mallaki dayawa daga cikin masu fad'a a ji." Shiru tayi tare da fad'awa kogin tunani, sai ta ga bata da wad'annan abubuwan, da sauri ta rik'o hannun Juman tace "Mah, ke fa? Ai kina da iko saboda ke ce sarauniyar k'asar nan, kuma nasan kina da kud'i ma." Murmushi tayi ta girgiza kai tace "Bana da ko d'aya yanzu Ayam, sanda mahaifinki ya jefani kurkuku ya datse min asusun bankina, gaba d'aya masarautar nan yanzu ba zan iya saka baki a abinda ya shafeta ba." Da mamaki a fuskarta tace "Saboda me Mah? Na d'auka yanzu ai kin fito." Sake fad'ad'a murmushi tayi tace "Ayam kenan, kafin ya fito da ni saida aka fad'a min na wucen gadi ne." Cike da alhini a fuskarta tace "Mah...na kasa yarda Pah duk yake wad'annan abubuwan, har yanzu bana jin wani iri a jikina idan na ganshi." Lak'ace hancinta tayi tace "Saboda yana mahaifinki ne mana, soyayyar dake tsakaninku ba zata bari tsoro yayi tasiri a kan ki ba." Ajiyar zuciya ta sauke bata sake cewa komai ba, haka ita ma Juman ba tayi magana ba, saidai dukansu da abinda suke tattaunawa a zuk'atansu. *08:30* Na dare ta fito cikin wasu had'add'un kaya na masarauta wanda suke jan k'asa har da babban mayafin da aka d'ora mata a kai amma ya sauka a baya, karo na farko a rayuwarta da aka shafa mata jan baki kalar leb'enta pink, bayan yau kam bata tab'a sakawa ba, tana dai shafa man leb'e amma ba jan baki ba. Sanyayyan k'amshinta ne ya fara sanar da su tana zuwa, suna juyawa a tare da sauri Haman ya mik'e tsaye dan sak sarauniyar Khazira idonsa suka gane masa, hakan yasa shi saurin mik'ewa da girmmawa yana neman gaisheta. A b'oye Umad ya ja rigarsa ya d'an motsa labb'ansa yanda ba kowa zai gane ba yace "Kula fa, kar ka kwafsa." D'an gyara tsayuwarshi yayi ya saisaita kanshi ya dakata daga hard'ewar da yake shirin yi ya rusuna mata, da k'ayataccen murmushi ta k'araso a nutse zauna tare da nuna masa zai iya zama, zaune sukayi a tare inda ta d'an k'yallara idonta ta kalli Umad. D'auke kai tayi ta kalli hadiman da suka rakota, a nutse kamar wata sarauniya ta furta "Zaku iya tafiya." Saida suka rusuna kafin suka nufi hanyar fita, saida ta ji sun rufe k'ofar sannan ta kalli Umad dake tsaye bayan Haman k'ik'am, sauke k'arar data d'ora kan d'aya tayi ta gyara zamnta cikin yanayinta data saba tace "Me ye haka yallab'ai? Duk wannan shirin na miye? Me ye wani neman aure na da kuma mai tsaro?" Haman kam mik'ewa yayi ya koma kusa da Umad yace "Zai miki bayani, duk shirin sa ne wannan." Kamar a rashin sani ta mik'e tsaye tare da wurgawa Umad wata harara, takawa tayi har zuwa inda suke tsaye, da yatsa ta shiga masa k'wak'waran kashedin "Ka ga yallab'ai bana so, bana son wannan bibiyar da kake min, idan har gaske ne rayuwata na cikin had'ari, to ka barni na mutu bai dameka, amma ka sani idan har wani abu ya samu mahaifina a zuwan nan na ku, wallahi Allah sai ka gane kurenka." Jujjuya d'an k'aramin bakinta tayi ta juya ta barsu tsaye baki sake da mamaki, bugo k'ofar da tayi bayan fitarta ne yasa Umad sakin wani lallausan murmushi yana girgiza, wai shi ta kalla duk da matsayinshi a gareta, da kuma matsayin da Allah ya masa kasancewarsa mai jiran gado, bata duba kasantuwarshi na malaminta ba ta kalleshi ta nunashi da yatsa sannan ta ce wai *zai gane kurensa*. Shafa sumar kanshi yayi ya zauna kan kujera yana furta "Zakanya, ni ne zan gane kure na?" Jinjina kai yayi yace "Zan gani." Da sauri Haman ma ya zauna yana fad'in "Ka ga Umad dan Allah ka fad'a min me ye shirin ka? Ni wannan shirun da ka min ina bin uamrninka bana son shi wallahi." Kallonshi yayi fuska a had'e yace "Zan fad'a maka, ka k'ara hak'uri kawai." Jinjina kai yayi yace "Shikenan zan jira." Tana komawa d'aki ta samu Juman ta shiga fad'a tana fad'in "Mah ni wannan kayan sun isheni, cirewa zanyi." Dariya tayi tace "Zaki fara sabawa da zaran kin zama sarauniya." Kallonta tayi kamar zatayi kuka tace "Haba Mah, ki daina fad'a mana." Jinjina mata kai tayi tace "Na ga wannan ranar Ayam, na ga haka a mafarkina, saidai nasan ba lallai mafarki ya zama gaske ba." K'ala ba tace ba saida ta cire kayan nan ta d'auki wata sassauk'ar riga a cikin wanda aka kawo mata ta bacci ta saka, warware gajeran gashinta tayi wanda har yanzu yake tohowa ta sakeshi dan ya sha iska, kan gadon ta kwanta ta kalli Juman tace" Mah, yau na farko a rayuwata ina so na kwana tare da ke kaina a kan k'irjinki." Dariya tayi tace" Baki da matsala gimbiyata, ni ma zan so hka duba da yau zan yi bacci a nutse hankalina kwance." Da mamaki tace" Saboda me Mah?" Cikin rad'a da fara'a a fuskarta tace" Saboda Umad na gidan nan, ganinshi ya bani k'arfin gwiwa, duba da shekarun dana fara had'uwa da shi da kuma yanzu." Girgiza kai tayi ta buga hannunta akan cinya alamar" Haba mana Mah." K'yalk'yalewa tayi da dariya tace" Da gaske nake fad'a miki." Turo baki tayi tace" Ni da yanzu mana fad'a masa ya daina bibiyata, ni sam ban wani yarda da shi ba." Kallon tuhuma ta mata tace" To da kike jin haka a game da shi, me ya hana ki fad'awa mahaifinki?" Jim tayi sai kuma ta d'aga kafad'a alamar bata sani ba, matsawa Juman tayi kusanta ta ja dogon hancinta tace" Ko dai ko dai? Ko dai akwai abinda k'aramar yarinyata ke b'oye min ne?" Rik'e hannun Juman d'in tayi data ja mata hanci da shi tana k'yalk'yala dariya tace" Mahhhh...hancina fa, ni ba wani abu da nake b'oye miki, d'azu ma ba'a gabanki na saka kaya ba?" Janye hannunta tayi daga hancinta sai kuma ta shiga mata cakulkuli tana fad'in" Ban yarda ja'irar yarinya, fad'a min me kike ji a kan shi? Da alama idan baki zama sarauniyar Khazira ba zaki zama sarauniyar Giobarh." Cikin farin ciki suka dinga wasarsu har Juman ita ma ta canja kayanta suka kwanta, daga kwance ma duk abubuwan da zasu anfaneta a cikin addininta ta dinga sanar da ita, k'aramar wayar da Ayam har ta manta ta ta ce sak'o ya shigo, d'auka Juman tayi ta mik'o mata tace "Wayarki." Karb'a tayi tana duba wayar dan har ta manta wace kala ce ma, bud'e murfin tayi ta duba sak'o gajere kamar haka _"Ki ji magana ta, bayan d'akinki da na mahaifiyarki ki kwana a ko ina ki ke so, idan kuma kina son kasancewa cikin tsaro, to ki kwana a k'ark'ashin kulawar Umad."_ Tashi tayi zaune tana sake karanta sak'on, me hakan ke nufi kuma? Wa ye ya turo mata sak'o haka? Gashi dai lambar ma a rufe take, tsaki tayi kawai ta rufe wayar ta aje gefe ta koma ta kwanta. Cike da kulawa Juman ta kalleta tace" Lafiya? Me ya faru?" Ba yabo ba fallasa ta amsa da" Ba komai." D'ora mata tayi daga inda suka tsaya ta ci gaba da fad'in" A duk wani hadisi daya tabbata kuma ya zo daga iyalai ko sahaban manzo (S. W. A) babu wanda ya nuna Annabi Muhammad yayi wankan tsarki wanda ba cikakke ba, ma'ana wankan da bashi da alwala, amma magaba sun inganta wanka da baya da alwala ma, wasu daga ciki sun ce ko da a cikin kogin ruwa ka tsumbula da niyyar wankan janaba to yayi, haka ma idan a buta ne ka d'aga ka kwarara a kan ka shi ma yayi..." Numfashin da Ayam ke saukewa ne yasa ta satar kallonta, ai kam idonta a rufe alamar bacci, da alama kuma ta fara jin dad'inshi saboda yanda ta turo baki hannunta akan cikin Juman, murmusawa tayi ta d'an muskuta kwanciyarta sannan ta gyara hannunta ta fara shafa gashin Ayam d'in. Irin dad'in da take ji marar misaltuwa na ratsata sanadiyar kasancewa tare da 'yarta, hakan yasa murmushi ke shinfid'e akan fuskarta idonta a lumshe tana d'an rera wak'a a can k'asan zuciyarta ta farin ciki da godiya ga Allah, sannu sannu ita ma har baccin ya d'auketa mai dad'in gaske data jima ba tayi irinsa ba. Yanda ya ji shiru daga d'akin yasa shi shigowa cikin sand'a, ganin dukansu bacci suke yasa ya ci gaba da takawa saida ya zagaya inda Ayam ke kwance, a hankali savoda baya so su farka ya sunkuya tare da d'an d'ora hannayenshi a kan gadon ya tokaresu, matsawa ya dinga yi saida ya kai kanshi kusa da na ta, cike da shauk'i da so da k'auna ya d'ora labb'anshi ya sumbaci kanta, a hankali ya d'ora hannunshi akan gashinta ya shafa wasu k'walla na cika masa ido. Motsawar da Ayam ta d'an yi ce tasa ya zabura ya mik'e tsaye ya rarraba ido cikin rashin gaskiya, kamar zata bud'a ido sai kuma ta sake yin ram da cikin Juman ta ci gaba da shek'a baccinta. A hankali ya zagaya ta b'angaren Juman yasa hannu ya daddab'ata, a tarz suka bud'a ido suka kalleshi kafin su raba jikinsu dana juna, cikin had'e fuska sarki Musail yace "Ke me kike a nan? Ba ga d'akinki can ba?" Turo baki tayi gaba tace "Pahh, nan nake so na kwana, kai ma ka zo ka kwanta a nan." Murmusawa yayi yace "Zafeera, ki je d'akinki ki kwanta kinji, na zo ganin mahaifiyarki ne tunda na ga ita bata san ta je inda nake ba." Cikin magagin baccin daya kasa sakinta ta kalli Juman sannan ta rarrafa ta sauka daga kan gadon, ganin kamar tana had'a hanya yasa shi saurin kama hannunta ya rumgumota a jikinshi, saitin kunnenta ya rad'a mata" Ki tabbatar baki je d'akinki ba a daren nan." D'aga kanta tayi t kalleshi da mamaki da kuma fad'aw tunani, amma kafin ta ankara ta turata k'ofar d'akin ya rufe ya barta tsaye da zulumi. Ganin gidan shiru ga fitilu duk an kashe yasa ta saurin d'aga k'afa ta nemi haurawa sama, dakatawa tayi sai kawai ta bi ta wata kusurwar duk da bata san ina zata kai ta ba, cikin tsoro tsoro take tafiya tana sand'a, duk k'ofar data wuce saita kalla da mamakin yawan d'akunan dake cikin gidan, jin ana bud'e wata k'ofar daga bayanta da makulli yasa ta saurin ruguwa cikin sand'a, d'akin dake k'arshen kusurwar kawai ta bud'a ta kuma yi sa'a a bud'e yake, dan tsoronta bata san wa ye zai fito ba, kuma sak'on nan da kuma abinda mahaifinta ya fad'a mata ya tsorata ta sosai, ga ka duhun cikin gidan wanda sai d'an siririn hasken jar fitila kawai. Tana shiga d'akin ta mayar da k'ofar da sauri ta rufe tare da juyawa ta dafe k'irji dan ta sauke numfarfashi, sai dai bala'in data gani ne ya yi barazanar tafiya da numfashinta, kakkafewa idonta sukayi inda ta ja numfashi amma bata samu damar saukeshi ba, ga hannunta akan k'irji ta tsaya k'am kamar gawa. Fitowarshi kenan daga wanka ya gama goge jikinshi, wandonshi ya d'auka 3 quater zai saka, hakan yasa shi zame towel d'in dake d'aure a k'ugunshi, amma da ya ji an shigo d'akin kamar ba lafiya ba sai ya dakata ya juya da k'arfi rai b'ace da tunanin wane marar tunanin ne, ganinta yasa komai na shi ya tsaya ya rasa abun yi, musamman daya fahimci kamar ta fita hayyacinta sakamakon mugun ganin da ta yi. 馃槍 A saib'ance ya sunkuya ya d'auki towel d'in ya d'aura yana jan tsaki da fad'in "Ko ma menene ke kika ja." Wani tsakin ya kuma saki tunawa haka ma waccen ranar ta bankad'o mata kai d'aki, saidai anyi sa'a ranar yana cikin ban d'aki ne. Sake juyawa yayi ya kalleta ya ga tana nan yanda take, girgiza kai yayi ya fara takawa zuwa gareta, yana tsayawa gabanta ya k'yasta mata hannu yace "Ya dai? Kin ga wani abu ne?" K'arfin halin irin na ta yasa ta d'aga baki za tayi magana, sai ta ji babu abinda zai iya fitowa sai kurmanci, hakan yasa ta daddagewa ta d'aga bakinta ta kwamtsa k'ara, da wani irin sauri ya sa hannu ya rufe mata baki tare da jawota jikinshi ya had'e gam, tana jin haka sai kuma numfashinta ya b'ace b'at ta sume a jikinta, hakan yasa jikinta ya saki kamar wata matatta. _Domin samun *lu'u lu'u* da kuma *Badak'ala*, ki biya naira d'ari biyu kacal ko kuma 400f cfa, dan samun na ki tuntub'i wannan lambar 94-98-56-52._ *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:41 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *32* Girgiza kai Umad yayi ya huro iska daga bakinshi, d'ago kanta yayi ta hanyar jawo gashinta ya kalli fuskarta, da gaske suma tayi daga ganinshi haka? Ko kuma dai dama a kid'ime ta zo? K'ofar da aka k'wank'wasa ne yasa shi kallon k'ofar a tsorace duk da hakan ba d'abi'arsa bace, duburburcewa yayi ya fara tunanin inda zai sakata, dan ganinta a d'akinshi a wannan yanayin zai iya zama barazana ga shirinshi, da sauri ya jata zuwa drower dake gefen ban d'akin ya bud'e, cak ya d'auketa ya sakata a ciki zaune dangalgal akan k'ugunta saboda babu kaya a wurin, mayarwa yayi ya rufe daidai da bud'o k'ofar an shigo, cikin rashin gaskiya ya kalli k'ofar yana d'an k'ank'ance idonshi. "Zafreen." Abinda ya ambata kenan a zuciyarshi, k'aramin tsaki ya ja na takaicin halayyarta, yanda take takowa gabanshi cikin rigar bacci iya cinyoyinta, hakan yasa shi ya fad'a tunanin to me take nufi? Saida ta zo gabanshi ta tsaya ta d'ora hannunta akan wuyanshi, cike da saloda k'warewa tace "Yal'ab'ai, ba kayi bacci ba?" D'ora hannun d'aya tayi hakan yasa ta sarkayeshi da hannayenta ta yanda ba zai iya zame mata ba, kanne masa ido d'aya tayi tace "Kasan wani abu? Na zo ne na tayaka hira, nasan zaka buk'aci hakan." Zuba idonshi yayi cikin na ta tare da saka hannayenshi biyu ya d'auke hannayenta daga wuyanshi, had'e fuska ya sake yi murya a dak'ile yace "Ki daina tab'ani, saboda ni muharraminki ne." D'aga gira tayi tace "Me ye haka kuma?" Juyawa yayi kan gadon ya d'auki rigarshi singlet bak'a yana fad'in "Ba zaki gane ba, amma addini na na da tsari, ba komai ya lamunce min aikatawa ba." Da alamar tambaya tace "Addininka? Wane addini kenan?" Saida ya fara saka rigarshi yace "Addinin musulunci." Yana sakawa ya juyo ya kalleta yace "Zaki iya tafiya, dare yayi, bai kamata kasancewarki nan ba." Lab'e baki tayi tace "Me ya hanashi kamatan?" Nunata yayi a hassale yace "Saboda ke ba matata ba ce." Zaro ido tayi cikin sangarta tace "Dama kana da mata?" A hassale ya tunkareta ranshi b'ace ya figi hannunta, bud'e k'ofar yayi ya wurgata waje sannan ya kalleta yace "Baki san ko ni waye ba, ki yi nesa da ni har zuwa lokacin da zan bar nan, idan kuma baki kiyaye ba..." Da hannunshi yayi alama a wuyanshi cewa lallai fa zai yankata, hakan ya tsorata ta ta zaro ido sai kuma ta juya ganin shi ma ya rufe k'ofar da k'arfi, yana juyowa da niyyar tunkarar drower nan ya bud'e, sai kawai Ayam ta sa k'afa ta banko k'ofar ta bude tana sauke nannauyen numfashi sakamakon zafin daya addabeta a ciki kamar dai ranar data shiga boot, saidai tana so ta fito kuma ta hak'ura dan ta ji muryar yar uwarta, babban dalilin da yasa kuma ta k'i fitowa shi ne, tana so ta ji hirarsu shin akwai wani abu tsakaninsu? ko kuma dai ba komai, shin wani abu zai iya faruwa a tsakanin su? Ko kuma mutanen kirki ne. Jin babu abinda ya faru ta ji kuma ya rufe k'ofa yasa ta fitowa da k'arfi dan samun numfashi mai kyau. Kallo yake binta da shi a lokacin da ta sauko gaba d'ayan ta tana rintse ido dan k'afafunta sun rik'e sosai. Wani kallo ta masa sama da k'asa kafin ta kyab'e bakinta da siga irin na raini ta fara d'ingisa k'afarta da niyar rab'ashi ta wuce dan har ga Allah ba zata iya ko da minti biyar a d'akin nan ba, dan wata matsananciyar kunyarshi ma take ji, halin data sameshi sai take jin ba zata k'ara had'a ido da shi ba har abada, gwara ta tafi kawai ko wacce zata faru ta faru. Idonsa ya lumshe yana jin yanda kansa ke sarawa haka kuma tashin hankali dake jikinsa na k'ara hauhawa da neman agaji, gaba d'aya yarinyar ta gama raina shi ta yadda baya tunanin akwai wani da ya masa rainin nan, shigo masa a haka da ta yi ta wani sume masa dan raini da wulakanci ko? K'ofar ta kama da niyyar bud'ewa ta fita dan ta tabbata ko ya ya ne yanzun yar uwarta ta yi nisa da k'ofar, sai dai bata kai ga aikata hakan ba ta ji ya damk'i hannunta na hagu sannan ya juyota a cikin yan sekwanin da basu kai biyu ba haka kuma ya mata janyowar da sai da ta daki k'irjinsa da goshinta kafin ta d'ago tana zazzaro ido cike da tsoro tana kallonsa. Tsayinsa ya d'an rage gaba d'ayanta ya d'auketa a hannayensa ya nufi gadonshi da ita , inda duk takunsa d'aya sai yayi yak'i da zuciyarsa kan ya yi ne ko kar ya yi? Anya a yanzu ya kai wajen da zai yi? Idan ya yi me zai faru? Me zata d'auki lamarin? Idan bai yi ba me kenan? Yana wannan tunanin har ya direta a saman gadon da ta zabura tana kallonsa wuk'i wuk' i idonta na firfitowa tamkar wace aka matsewa mak'ogwaro ta kusan mutuwa sai kuma aka saketa. Duhun daya mamaye d'akin ne ya sakata saurin fad'in "Mais tu fait quoi comme 莽a? (Amma me kake yi haka)." Ba amsa, ba alamun ma an jita hakan ya sa ta rarafo tana lalube da nufin sauka ta tafi dan ta kula yau ban da tataccen wulak'anci baya jin komai, wani shashareta da yake, ga cin magani uwa jaraba ya had'e fuska, sam ba zata lamunta ba musamman a daren nan. Numfashinta da nasa da suka had'e waje d'aya ne ya sakata d'an zabura tana son ja baya, sai dai bai bata damar ja bayan ba ya k'ara janyota jikinsa sosai ta yadda ta fahimci kamar a yadda ta shigo ta tardo shi ne ya koma, wato ba wani suturar arziki a jikinsa sai shi sai gyafton towel d' insa, hakan ya sa gaba d'aya jikinta ya d'auki rawa ta bud'i baki da niyyar kuma yi masa maganar me yake haka ne?, Sai kawai jin wani lalausan abu ta yi ya rufe nata bakin da d'umi d'umi da santsi santsi sai k'amshi maclean da ya k'ara yi mata bismillah. A hankali take jan numfashi sakamakon jin bayan nan harshenta ya laluma ya shiga tsotsa da d'an saurin da ya sakata saurarawa dan gaba d'aya ta rikice, a hankali ya idasa hayewa saman gadon yana ta tare duk wani k'aramin motsinta dan kar ta hana masa samun abinda yake son samu cikin ruwan sanyi har ya idasa lik'e mata kafin ya saka hannunsa cikin rigarta ya shiga lalubarta, hakan ya sa ta ja wani irin numfashi da sauri tana rik'ewa ta kuma k'wace bakinta da ihu tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'une! dama kana cikin musulmai masu aikata mugayen laifuka a doron k'asa? Dama haka ka ke? Wallahi na d'auka kai mutumin kirki ne, wayyo Allah na! wayyo Allah na dan Allah ka bari ni ba yar iska bace ban tab'a yi ba!" Jikinsa gaba d'aya k'ara d'aukan rawa yake hakan ya sa da gaggawa ya had'e bakinsu yana lumshe idannuwansa sannan yayi anfani da k'arfin da ba d'aya ba ya idasa saka hannun nasa cikin rigar ta ta gaba d'aya, wato ya damk'i abinda bata so a damk'ar. Gaba d'aya ta shid'e dan tsoro, gaba d'aya take kokowa da numfashinta, sai dai bai bata damar cirewar ba dan ma kar ta masa wani hayaniyar da k'abli da ba'adinta ita malama. Rigar ya ida cirewa gaba d'aya yana mai cire bakinsa a cikin nata, ihu ta so fasawa ya rufe mata bakin yana k'ara lalubarta domin ba ganin juna suke da kyau ba duba da duhun da d'akin ya d'auka. Da k'arfi tace "Kunna wuta, ka kunna wuta na ce." Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace "Ki kuma sume min?" A kid'ime cikin fitar hayyaci tace "Ba abinda zai sumar da ni, ka kunna ko zaka dawo hayacinka ka daina tab'a ni, so kake Allah ya k'ona ka ne? Mah ta fad'a min hakan haramun ne Allah baya so." Ajiyar zuciya ya sauke gaba d'aya ya rufeta yana k'ok'arin cire wandon dake jikinta, rik'ewa tayi da hannayenta ita ma gam, hakan yasa suka d'an fara gardama ita ta ja shi ma ya ja, da k'yar ya b'amb'are hannunta na dama sai kawai ya zura cikin bakinshi yana tsutsar yatsunta, lumshe ido tayi tana jin wani tsigar jikinta na neman tashi, sai take jin ba zata iya warto hannun ta fito da shi ba. Ba tare data ankara ba cikin dubara ya cire pant d'inta gaba d'aya domin ya kula idan har ya ci gaba da kwatanta mata shine a ruwa tsundum. K'afafunta ya ware gaba d'aya da d'an k'arfi kafin ya dire leb'ensa a wajen da sai da cikinta ya juya tsabar firgici da tsoro da mamaki, wani d'an ihu ta saki a lokacin da ya tsotsa ya kuma tsotsa sai kawai ta fashe da kuka tana fad'in "Wayyo! Wayyo k'aik'ayi a kaina, Inna lillahi wayyo shed'an, wayyo shed'an ka yi nesa da ni, zuciyata ki daina kaini, wayo ka kula ka dawo hayyacinka kar ka min haka, wayo wayo." Ta k'arashe tana fashewa da kuka da jujjuya kanta akan pillow data d'ora kanta, hauka hauka, hankali hankali, ta fara jin abun na ratsata, sai ta ji kamar zata shafa sumar kanshi, amma kuma sai ta taushi zuciyarta kar ta zo tayi abun kunya. Yanda ta ji yana mata wata arniyar tsutsa a wurin yasa ta ji kai! Yunk'urawa tayi da k'arfi ta nemi zillewa, sai dai kamar yasan me za ta yi kawai ya mata makulli da hannayenshi a k'ugunta ram, jin ba zata iya tashi ba dole tallabo kanshi a rikice duk da ba ganin juna suke ba tace "Yallab'ai, yallab'ai Umad, ni ce, ni ce Ayam ka kalle ni ka ji, ka fad'a min me ka sha dan Allah? Ka ga fa kai..." Yan tamilon nonuwanta ya kuma cabkowa yana murzawa, rintse ido tayi tana sako waqu sabbin hawaye daga kurmin idonta. Ba tare data tab'a ko da mafarkin zuwan wannan rana ba, a bazata abun ya zo mata, bak'on al'amari ne da bata tab'a tsammanin riskarshi ba bare ma ta kamanta yanda zai zo mata, hakan kuma baya rasa nasaba da dogon burinta na son ganin ta zurfafa karatu har ta kai matakin general a fanninta, ba ma wannan lamarin dake shirin samunta ba a yanzun, ko saurayi na wasa ita bata tab'a yi ba, shin bata da kyau irin wanda maza suke so ne? Ko kuma fasalin surarta ne bai musu ba? Babu wanda ya tab'a tayata a rayuwa ko da wasa, hasalima ko irin yan iskan nan babu wanda ya tab'a mata kallon rashin d'a'a. Cak ya dakatar mata da tunanin ta sanda ta ji kakkauran wani abu na d'an shiga gabanta yana kuma dakatawa, gam take rik'e da hannayenshi tana ta son ta zille sama ko ta k'waci kanta, saidai rashin aukinta da nauyi yasa yayi ram da k'ugunta ko motsawa ba tayi a hannunshi. Tabbatarwa kansa da yayi ba zai shiga a sauk'i bane yasa shi had'a goshinsu waje d'aya yana huro da iskar bakinshi kan fuskarta, duk da cikin duhu ne a haka yake jin tabbas hawaye take sosai ko dan yanda take shashek'a da d'an rera kukan a sanyaye, k'urawa fuskarta ido yayi cikin dak'ilalliyar murya k'asan mak'oshi yace "Ki gafarce ni." Kamar jira take sai kuwa tayi saurin fad'in "Shikenan ba komai, na maka alk'awarin ba zan fad'a ma kowa ba, d'agani to?" Abun daya shiga ta gabanta a lokacin yasa ta damk'i damatsenshi ta yunk'ura kamar zata tashi sama ta hanyar bank'aro k'irjinta tace "Ahhh..." Tafin hannunshi yasa ya rufe bakinta hakan ya hanata bud'a baki tayi ihu a wannan daren, gam gam ta sake lik'e idonta ta fara jujjuya kanta tana turmutsashi a cikin pillow, dakatawa tayi da kukan sai bakinta dake furta "Hasbunallah wani'imal wakil, hasbunallah wani'imal wakil..." Abinda Juman ta fad'a mata kenan bayan sallhnsu ta la'asar, gashi a yanzun ta mata rana dan tana karantawa tana jin dad'i a bakinta. Kad'an ya so horata dan a yanda idonshi ke gane masa ba wasu kayan k'ishi ne a jikinta ba, ikon Allah sai ga 'yar firit ta rik'e masa wuta tana ta shayar da shi mamaki, yan mitsil d'in nonuwan nan na ta yake kuma matsa yana lindawa uwa zai mayar mata su ciki, duk da k'aramtarsu amma dake su ya fara mu'amula da su sai ya ji su ne na musamman a wajenshi. Duk da ba shiryawa ranar sukayi ba dukkansu, amma dai ya gamsu iya gamsuwa, hakan kuma baya rasa nasaba da anfani da zallar kayan marmari, shiyasa ta dinga ambaliya tun daga lokacin daya fara tab'a ta, gashi girman hallitarshi daidai ta ta hallitar, kirip yayi a ciki suka dinga gogayya da junansu, fata d'aya yanzu gareshi ta ci gaba da zama a haka ko sun ji dad'in kasancewa a inuwa d'aya, dan daga yanzu zuwa wayewar gari baya jin zai d'aga ma duk wanda ke son cutar da ita k'afa, kai idan ta kama ya kikkirta rashin mutumci ya buga k'irjinshi ido rufe sannan ya ce *matata* ce zai aikata hakan, dan abinda ya faru yanzun kima, martaba, daraja duk suka k'ara dad'a mata a wajenshi. Don yayi matuk'ar mamakin yanda ya sameta a cikakkiyar budurwarta, hakan fa na nufin ba yar soyayyar mintin nan, ba soyayyar shan ice cream, bare a ce ka kai kanka inda za'a keta haddinka, hakan babbar nasara ce, duba da yanda zamani ya koma yanzu, musamman ita da yaushe ne ma ta shiga addinin da bai yard da hakan ba, amma a haka ta kare mutumcinta ta tseratar da shi wanda gashi yau zai janyo mata komai, dan halin da akz ciki yanzu zai sake zama garkuwarta, sannan ya mallaka mata komai daya mallaka, hakazalika zata zama *sarauniyar* Giobarh wata rana, idan kuma ita ma irinshi ce bata da sha'awar sarauta, sai su koma a gidanshi da ma'aikatarshi ta mallaka masa sannan su yi rayuwarsu a sake cikin farin ciki. *Ki biya na ki dan karatu a nutse, domin tabbatar da haka ki tuntub'i wannan lambar 94-98-56-52* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:41 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *33* Tunda ya gama ya kwanta gefenta ya rumgumeta tsam a jikinshi, a hankalce yake sauraren numfashinta dake sauka a kan k'irjinshi mai d'umin gaske, irin yanda take ta shashek'ar kuka, ga jikinta da yake jin yana d'an sake d'aukar zafi, wanda idan ba zuzutan lamarin yake ba zai iya cewa har rawar d'ari yake jin jikin na ta na yi, hakan yasa shi sake matseta a jikinshi gam tausayinta na k'ara ratsashi, irin yanda ta jure bata masa hargagi ba, ba tayi ihu ba sai fawwalawa Allah komai, dan tunda ta ji an shiga ta tabbatar ya ratsata kawai ta saki jikinta sai hawaye da take. Hannu ya zura ya k'ara jayo zanin rufar ya rufeta ruf, hannun ya kuma sa wa yana shafa gashinta daya warwatse yana maida mata shi baya, haka suka ci gaba da zama saida ya ji komai na sa a yanzun ya zama daidai, numfashinshi ya fara fita sannu sannu, gumin daya had'a ya tsane a jikinshi sannan ya sake mannata a jikinshi, cikin tausashiyar murya ya furta "Sannu kin ji, sannu, kina jin zafi ne?" Saida ta sauke wasu numfarfashi a gaggauce sannan ta d'aga masa kai alamar e, sake d'an matseta yayi yace "Zai daina kinji, kiyi hak'uri." Cikin muryar kuka da har ta disashe abunda ba'a saba ba tace "Yanzu...ne ka ga...ya dace...ka ban ha...k'uri?" Murmusawa yayi yace "Ki yi hak'uri na ce, nan gaba idan zan yi zan fara baki hak'uri." Kiciniyar tashi ta fara daga jikinshi, amma yanda ta ji ya rik'e gam yasa ta saki wani marayan kuka tana fad'in "Ka yi hak'uri yal'ab'ai, dan Allah karka sake min abun nan da ka yi da zafi sosai..." Rufe mata baki yayi da tafin hannu yace "Ba yanzu nake nufi ba, sai..." Yanda take zillewa yasa bai gama fad'a sai kuma yayi saurin fad'in "Wai dakata, me ma ya shigo dake d'akina a wannan daren?" Fashewa tayi da kuka ta ja zanin rufar ta rufe fuskarta, da sauri ya sauka daga gadon yana fad'in "Shikenan fa, bari na taimaka miki." Da sauri ya nufi wajen mab'allin wutar ya kunna, hasken daya had'e d'akin yasa Ayam saurin sake rintse idonta ta dunk'ule cikin zanin, k'arasowa yayi ya jaye darar da niyyar tallabota, rik'e zanin tayi gam cikin masifa tace" Bana so." Sakin zanin yayi ya tab'e baki ya juya ya shige ban d'aki, tana jin k'arar ruwa alamar fitowarshi ba yanzu ba ta bud'e fuskarta, abinda ta tambayi kanta shi ne" Ta ya ma zan had'a ido da kai? Mugu azzalumi, sai na sa Pah na ya cire min kan ka." Zura k'afafunta tayi k'asa tana rintse ido, jikinta baya mata wani ciwo dan ta saba da motsa jiki, saidai Allah na gani k'asan nan na ta bala'i zugi yake mata kamar ta kama ruwa da barkono, zafi rau wurin ga wani curewa da yayi kamar an k'ulleshi. Yunk'urwa tayi ta mik'e tsaye kan k'afafunta, juyawa tayi ta lalubi rigarta doguwa da pant d'inta daya jefo k'asa, da sauri ta zura rigar pant d'in kuma tattareshi a hannunta ta rik'e, takawa ta fara yi cikin sand'a har ta bar d'akin ta nufi na mahaifiyarta dan ita take da buk'ata a yanzu a halin da take ciki. *Tun* fitarta kuma sarki Musail ya fara k'ok'arin cire rigar jikinshi, saukowa tayi daga kan gadon tana fad'in "Kar ma ka fara, ka daina kusanta ta tunda dai kai ba Allah ne a gabanka ba." Fizgota yayi ya had'a da jikinshi ya tallabo hab'arta yana kallon k'wayar idonta yace "Ke zaki hanani abinda na yi niyya ne ? Kar fa ki manta ke matata ce." Tureshi tayi a jikinta tana fad'in "Ban maka musu ba, amma aure na da kai ya kusa k'arewa." Da azama ya tunkareta daga shirin ficewar da take ya sake figo siririn hannunta, a hassale ta juyo har tana fad'awa k'irjinshi, gam gam ya matseta a jikinshi cikin b'acin rai da rad'a kamar a kunne yace" Me yasa ba ki da tunani ne ? Ta ya za ki barta cikin wannan had'arin? Me yasa bata bar nan d'in na kamar yanda..." Yanda take ta gilma idonta akan fuskarshi ne yasa shi d'auke idonshi yace" Share kawai." Da mamaki murya a tausashe tace" Me kake magana a kai? Wacece wai?" Gashinta ya fizga da k'arfi ya d'aga kanta sama suna sake kallon juna da kyau, had'a bakinshi yayi da na ta ya shiga tsutsa da sauri sauri tare da d'aukarta yana neman direta kan gado, bille bille ta fara tana neman ya sauketa. *A* lokacin ne Ayam ta saki ihun nan na farkon ganin Umad kafin kuma ta suma, dukansu sun ji hakan yasa Musail sakin Juman ba tare daya shirya ba, dan a zuciyarshi ya ji kamar an yakushe shi da k'arfi, a sukwane ya fita a d'akin saidai bai san ina zai nufa ba, kusan dai a falon nan babu inda bai duba ba amma babu ita, kuma fadawan dake bakin k'ofa sun tabbatar masa ba fita tayi ba, har d'akin Ayam d'in saida ya shiga bata nan, sai kawai ya koma d'akin Juman cikin fad'a yana fad'in "Kin gani ko? Tana ina yanzu? Me ya sameta?" Kamar wacce ke kallon bak'on abu haka ta kallehi tace "Wai wacece ka ke nuna damuwa a kan..." A tsawace hankali tashe yace "Ban sani ba, 'yata na ke miki magna a kai Juman, me ya sameta?" K'wafa yayi ya juya zai fita tayi saurin rik'o hannunshi, cak ya tsaya ya juyo yna kallonta, kamar zata fashe da kuka ta marairaice tace "Me ya sameta? Wani abu ka shirya a kan ta dama? Shi ya sa tana baccinta a jikina ka korata daga d'akin nan? Musail me ya sa ? Me yasa zaka kashe min yata?" Fizge hannunshi yayi yace "Ni ban kasheta ba, sake ni." Tare k'ofar tayi da sauri tace "Babu inda zaka je Musail, 'yata fa, wallahi Allah sai ka nemo min yata." A harzuk'e dan ya fi ta shiga tashin hankali yace "Kuma daga nan ne zan nemo miki ita d'in?" Fashewa tayi da kuka ta sulale a bakin k'ofar kamar ranta zai fita, sunkuyawa yayi yace "Juman, ki kauce a hanyar nan na je na duba na ga halin da 'yata take ciki, idan muna nan kuma wani mummunan abu ya faru da ita fa?" Da sauri ta tashi tsaye ranta b'ace ta fara kai masa bugu a k'irji tana cewa "Kar ka sake kiranta da 'yarka, yata ce ni kad'ai Musail, duk abinda ke faruwa ai kai ne mai alhakin k'ullashi." Rik'e hannayenta yayi duka biyun ya mannata a k'irjinshi ya tallabe kanta ta baya yana kiran "Shiiiiiiiiii! Ya isa haka, ya isa haka na ji." Bata daina fad'in "Bai isa d'in ba, mugu azzalumi, kana so ka kashe 'yarka ta cikinka da hannunka, wallahi Allah sai ya mana hisabi, ba zan tab'a yafe maka abubuwan da ka min ba, ka rabani da iyayena, ka rabani da masoyi na sannan ka rabani da yata ma yanzu? Me ya rage min yanzu da baka d'aukeshi ba? Fad'a min me ya rage? Rayuwata? To ka d'auka gani gabanka..." Had'a bakinshi yayi da na ta a zafafe yana tsutsa tare da yakice rigarta ta k'arfi da yaji ya nufi gado da ita, a hassale ya jefata ya kuma bi kanta ya taushe, da sauri sauri da kuma alamar k'eta ya bud'e k'afafunta yana son ankarar da ita ta dawo hayyacinta. K'in yarda tayi da hakan ta hanyar kokowa da shi tana ta bille bille da dukansshi tana fad'in "Ka d'agani, ka d'agani na ce Musail, Allah ya isa tsakani na da kai, mugu azzalumi, kuma da yardar Allah zaka ga k'arshenka." Cikin fitar hayyaci duk da yau ya shigo d'akin na ta ba'a bige ba, amma haka ya ware iya k'wanjinshi ya auna mata mari a fuska, bala'in daya ratsata ta hanyar d'aukewar jin ta da ganinta yasa tayi gum da baki ta dakata daga shure shuren. Ban da" Suuuuuuiiiuuiuuuuu!" Ba abinda take ji a kunnenta, gashi dai idonta na kallonshi amma a zahirin gaskiya ba ganinshi take ba, a tsawace cikin b'acin rai yace" Ke wacece irin macece wai? Me yasa kike min haka Juman? Dan kin jima da gane rauni na a kan ki ne? Sau na wa ina k'ok'arin zama na k'warai a duniyar nan ? Amma ke d'in nan ke kika dakusar da ni, k'iyayya hauka ce? Dan ba kya so na sai a ka ce ke min komai da ranki yake so? Me ye haka wai Juman? Yanzu akan wanene dalili ne zaki hanani fita na ga halin da 'yarmu take ciki? Me yasa ba zaki bani damar aikata aiki k'waya d'aya tak na gari ba kafin mutuwa ta?" D'agata yayi ya zauna gefenta yana dafe kanshi dake matsanancin ciwo kamar ana buga masa guduma, cikin sanyin murya yake fad'in" Bana son haka Juman, bana so ina muzguna miki, amma dayawancin lokuta ke kika kai ni bango, ban san me ya sa ba?" Jiki a mace ta tashi zaune tana gyara rigarta, gefen fuskarta ta tab'a inda take jin kamar ya kumbura, cikin kuka mai raunin gaske tace" Baka so na Musail, da kana so na da baka min abubuwan da ka min ba, baka so na ni da Zafeera, Zafreen kad'ai kake so ita data d'auko hallayarka." A marairaice ya kalleta yace" Juman ina sonku mana, ku fa na wa ne, me yasa ba zaki karanta ko da kad'an daga wani abun alkairi dana aikata a rayuwata ba? Tabbas na san na yi laifuka masu yawa, amma ki...." Sai kuma ya dafe kanshi ya sunkuyar da shi k'asa yana rintse ido, kallonshi tayi sai kuma ta tab'e baki ta kawar da kanta. Shi ya kasa cewa komai saboda bala'in da kansa ke mishi, ita kuma ta k'i magana saboda haushinsa da takaici, saida suka d'auki minti ashiri da biyar a haka babu mai k'wak'waran motsi, a hankali ya d'aga kanshi sama yna jan dogon numfashi kafin ya kalleta yace "Juman, na tabbata da zan yi fitar rai a gabanki ba zaki taimaka min da komai ba bare ki damu." Jinjina kai yayi ya mik'e tsaye yace "Nagode Juman." Kallonshi tayi da sauri jin yayi magana da wata murya, ganin ya juya zai fita yasa ta saurin fad'in "Godiya a kan me?" Malalacin murmushi ya mata yace "A kan haifa min ababen soyuwata." Yana fad'a ne ya juya zai fita sai kuma aka k'wank'wasa k'ofar, da sauri ya k'arasa tare da bud'ewa, Ayam ce ta shigo a wani mugun yanayi a d'imauce, da sauri ya rik'o damatsen hannayenta cike da kulawa yace "Zafeera, lafiya? Me y sameki?" Murmushi ta k'ak'aro mai kama da kuka tana k'ara cukuikuiye pant d'inta, da gudu Juman ta k'araso ta rik'ota ita ma tana k'are mata kallo, hankali a matuk'ar tashe ta lumshe ido dan ita har ta ga abinda shi bai gani ba ta furta" Illa lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil." Bud'e ido tayi ta kalleta ta matso hawaye da k'arfi tace" Ayam garin ya ya hka ta faru? Wa ye?" Pik'i pik'i tayi da ido ta dukar da kanta tana duba jikinta, to me ta gani a nan ita kuma? Me take ma nufi da tambayarta? Jawota tayi zuwa cikin d'akin saida ta kai ta har bakin gado ta zaunar da ita, a lokacin ne Musail ya iya lura da yanda Ayam d'in take shi ma musamman ma tafiyarta. Da sauri ya dafe kanshi ya k'arasa gaban gadon gefen Ayam din shi a ya zauna, rintse ido yayi sosai yana sake matse kan shi dake sarawa sosai. Durk'usawa Juman tayi ta kama hannuwanta suna kallon juna tace "Ayam fad'a mana me ya faru da ke?" Hawaye ne suka fara bin fuskarta kafin tace "Kiyi hak'uri Mah, ba laifina ba ne ni ma, tsautsayi ne." Jan majina tayi sai Musail daya d'ago da sauri ya dubeta da kulawa yace "Waye Zafeera? A gidan nan ya ke?" Fashewa tayi da kuka tana kallonshi ba tace komai ba, dafa kafad'arta yayi yace "Ki daure ki fad'a mana kinji, mu iyayenki ne, zamu bi miki hakk'inki ta ko wace hanya." Jinjina kai Juman tayi tace "Hakane Ayam, ki fad'a mana kinji?" Girgiza kai tayi cikin kuka tace "A'a Pah, ku barshi kawai na yafe mishi, bana so wani abu marar kyau ya faru tsakaninku, shi ma daga babbar masarauta yake, nasan ba halinsa b..." D'aga mata hannu sarki Musail yayi alamar tayi shiru, dan har ya gane shaid'anin da yayi aika aikar nan, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauka dan dama tashin hankalin bai wuce ya ji waninsa ne ya karb'e budurcinta ba shi ba (Musail d'in nan fa akwai ayar tambaya kan shi). Kama hannun Juman yayi suka nufi k'ofa, cikin rad'a yana kallonta yace "Karki d'aga hankalinki a kan wannan, ki dai taimaka mata ta ji dad'in jikinta." Da mad'aukakin mamaki tace "Me? Kana so ka ce min babu wani matakin da zaka d'auka?" K'asa k'asa yace "Babu, ki yi abinda na ce." Cikin d'aga murya tace "Ka fad'i haka mana, saboda dama ba damuwarka ba ce ita d'in, to amma ka sani tana da uwa, ni ma kuma ina da iyaye sannan suna da iko a hannu, wallahi ko zan mutu saina k'watar mata 'yancinta." Zai yi magana sai kuma ya kalli inda Ayam ke zaune, ganin ta k'ura musu ido ya sa shi jan hannunta suka fita a d'akin, bakin k'ofar suka tsaya inda yace" Wai ke me ya sa baki da hankali ne? Ni ne nan mahaifinta, kuma haka na ce kiyi dole ki yi." A hassale ta fashe da kuka tace" Musail ka kuwa san me kake magana a kai? 'yarmu fa alamu sun nuna gyad'e aka mata kuma a cikin gidan nan, me yasa zamuyi shiru ba zamu nemi mai laifin sannan mu hukuntasu?" Girgiza kai yayi ya ja tsaki kawai ya wuce ya barta nan tsaye, share hawayenta tayi ta bud'e k'ofar ta shiga ciki, bata yarda ta kalli Ayam ba ta wuce ban d'aki dan had'a mata ruwan da zata ji dad'in jikinta. Ayam ma daga zaunen hawaye take yi na abinda ya sameta, da kuma abinda ta gani daga iyayen na ta, rashin jituwar yayi yawa haka, wanda ta san kuma k'iyayyar da mahaifiyarta ke wa mahaifinta ita ce silar komai, a yanzu kam bata ganin akwai wani abu da zatayi da zata siyawa mahaifinta wannan soyayyar da shekaru ashirin da shida suka kasa siya masa, tunda bata san yanayin zamansu ba ta b'angaren kyautatawa. *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:41 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *34* Fitowa tayi daga ban d'akin ta kama wuyan hannunta ba tare data mata magana ba, zafin da ta ji a hannun na ta yasa ta dafa wuyanta, kallonta tayi kamar zata fashe da wani kukan tace "Ayam kin ji fa jikinki zafi, me yasa wai ba zaki fad'a mana wanda ya miki wannan abun ba? Ayam har fa cikin gidan mahaifinki haka ta faru." A sanyaye sosai cike da kasala tace "Mahhhh! Karki damu kanki mana, ba abinda kike tunani ba ne." Da kallon mamaki tace "Haba Ayam, ni fa na haifeki da cikina, kallo d'aya na miki nasan wani abu ya faru dake." Cike da gajiyawa ta d'ora kanta a kafad'ar Juman tace "Mah zaune na ke so na yi." Janta tayi zuwa ban d'akin tana fad'in "A'a ba zama zakiyi ba, mu je kiyi wanka." Shagwab'ewa tayi tace "Amma kuma Mah sanyi nake ji." Ba fara'a a fuskarta tace "Haka zaki hak'ura." Suna shiga ban d'akin ta nuna mata bahon wankan tace "Cire kayanki ki zauna a ciki." Cikin dubara ta fara aje pant d'inta da har lokacin yake mak'ale a hannunta gam, a sanyaye ta shiga zame rigar jikinta har ta cireta gaba d'aya, k'arasawa tayi ta d'an taka tudun wajen da bai kai tudun matakala ba sannan ta fara zura k'afarta ta dama. Da sauri ta cire tana furta "Washhhh!" Juyawa tayi ta kalli Mah data matso kusanta ta kamata, kakkare jikinta ta fara yi tana fad'in "Mah dama baki fita ba? Please ki fita ki barni, ni fa ba yarinya ba ce." Ba ta kula da abinda ta ce ba sai kallon k'fafunta da take tace "Shiga ki zauna min." Cikin d'ari d'ari ta sake zura k'afafun har ta fara k'ok'arin zaunawa a ciki, tana zaunawa ta ji wani fitsari na neman kubto mata saboda zafin da ta ji na ruwan, a firgice ta mik'e tsaye tana shirin yin magana Juman tace "Bana son wasa Ayam, zauna min a ciki." Cikin kuka tace "Mah zafi wallahi, k'onewa zan yi." Harara ta dalla mata da Ayam d'in bata tab'a tunanin zata iya yin ta ba sannan tace "Zaki zauna ko sai na jefaki da k'arfi?" Da sauri ta rintse ido ta fara sunkuyawa a hankali har ta zauna ciki tsumdum, bakin bahon ta rik'e gam gam idonta a rufe duk da haka tana jin suna cika da hawaye, kasa zama tayi wuri d'aya haka ta dinga motsawa tana ta yan dabaru saboda rad'ad'i take ji sosai, sannu sannu kawai ta fara ji zafin ruwan na raguwa saida ta ji ta zauna daidai ba tare data motsa ba. Lura da haka yasa Juman a dak'ile ta mik'o mata farin towel tace "Tashi ki d'aura wannan." Karb'a tayi ta mik'e tsaye ta d'aura sannan ta fito, wata k'aramar buta mai ruwan gold ta k'arfe ta nuna mata tace "Sake kama min ruwa a nan." A sangarce ta kalleta tace "Again?" Ba alamar wasa tace "Yeah, zuwa safe kuma da kaina zan kaiki asibiti a tabbatar min da lafiyarki." Numfashi ta sauke ita dai ta duk'a dan kama ruwan, wani sabulu ta mik'o mata na ruwa na kuma tsarki tace "Ki wanke da wannan." Karb'a tayi ta matsa sabulun a hannunta sannan ta shiga wanke gabanta da kyau, tana idawa ta mik'e ganin Juman ta fita tana fad'in "Sai kiyi wankan tsarki." *Sarki Musail* na fita daga d'akin kai tsaye b'angaren masaukin bak'in ya nufa, yana zuwa daidai k'ofar d'akin ya k'wank'wasa. Umad da fitowarsa kenan ya d'ora idonshi akan gadon, ganin bata nan ne ya firgita ya fara neman riga dan sakawa ya fita, yana tsaka da neman rigar sakawa ya ji an k'wank'wasa k'ofar, da sauri ya juya ya kalla sai kuma ya taka da niyyar zuwa ya bud'e da tunanin ko ita ce ta dawo, dalilin mantuwa ko dai ta canza shawara? Yana bud'ewa tsakninshi da mahaliccinsa ne saida ya ji fad'uwar gaba ganin sarki Musail a tsaye, sarki sarakuna mai ji da isa da k'asaita. D'auke idonshi yayi ya mayar da duban k'asa, lura da ba tafiya zaiyi yanzu ba yasa shi rab'ewa, yanda hannayenshi ke baya duka ya goyasu cikin gadara ya fara takowa cikin d'akin, saida ya shigo Umad ya maida k'ofar ya rufe sannan ya juya yana k'arasa saka rigar dake hannunshi. A ladabce cikin girmamawa ya kalli k'eyarsa yace "Yal'ab'ai lafiya?" A hankali ya juyo ya sauke dubanshi akan Umad d'in, ba alamar wasa a tare da shi kamar yanda yanayinshi yayi daidai da wanda zai iya firgita mutum ya bud'a bakinsa da k'yar yace " *Sadakin 'yata na zo karb'a*." Murd'awa kayan cikinsa sukayi tare da hautsinawar da tasa ya dafe k'irji, a baibai ya kalli sarki Musail d'in yana neman k'arin bayani yace "Yallab'ai?" A sanyaye ya dawo da hannayenshi gaba ya had'esu ya kuma tsatsareshi da ido sannan yace "Sadakin 'yata na ce, ka manta da ka yi alk'awarin mallaka mata makullan motar da ka fi so wato Ferrari? Amma kuma har yanzu kana murzata ka manta da ba taka ba ce." Numfashi ya sauke kafin ya gyara tsayuwarsa yace "Na ga ka mori sadakinka, shiyasa na zo karb'an sadakin da kai na, dan nasan kai ma ka sani aurenka da *Ayam* ba nagartacce ba ne saboda dalili d'aya tak." Yanayin da yake kallo kamar na tsoro yasa sarki Musail yin murmushi ya sake gyara tsayiwa a gadarance yace" Dalilin shi ne a lokacin da Juman ta ba wa Habbee yarinyar nan, basuyi yarjejeniya kan ce wa idan sun samu mijin da ya dace su aura mata ba, sai gashi su sun aurar da ita babu amincewar iyayenta alhalin kuma mu na raye, dan haka a shari'ar musulunci ma auren nan bai yi ba." Yar dariya ya k'yalk'yala tare da fad'in" Amma ka kwantar da hankalinka, na yarda da kai ai, shiyasa ma ban kwance auren ba tun a inda aka d'aurashi ba." Da matsanancin mamaki Umad ya ji kanshi na neman yin bindiga yace" Yallab'ai, ta ya ka yi duk kasan wannan? Ka samu su Habbee ne?" Bushewa yayi da wata dariya ya waro ido yana kallonshi yace" Samun su kuma? Bayan ka b'oyesu a fadar suriki na?" Girgiza kai yayi yace" Umad! Umad! Umad, idan har zan fad'a maka abinda na sani a yanzun, to tabbas kan ka zai fashe." Cikin k'asaita ya maida hannayenshi bayanshi ya goyasu sannan ya kalli Umad fuska a had'e yace" Kafin 'yata ta farka daga bacci ina son damk'ar sadakinta a hannu na, ko kuma rai yayi mugun b'aci, dan zan iya yin komai a kan ta." Tako d'ai d'ai ya fita a d'akin ya bar Umad da jimami, zulumi, tunani da kuma firgici mai d'auke da tsantsar mamaki, sai ma ya rasa ta inda zai fara tunanin? Ta ya haka ya faru? Ko dai tubka ya ke ta gaba ana warwara ta baya? Anya kuwa su Habbee babu alamar tambaya a kan su? Ko dai shi ma sarki Musail d'in akwai wani abu da yake b'oyewa? Da k'yar ya k'arasa bakin gadon ya zauna, sai gashi madadin raka'a biyu daya saba yi kafin kwanciya bai tsaya yin ta ba, bai kuma d'auki na'urarsa ya fara binciken wasu abubuwa ba, sai kawai ya dinga tunani da k'walwarshi dan sai ya ji na'urar ma bai yarda da ita ba. *Washe gari* da k'yar ta tashi tayi sallah, a haka ma dan Juman ta bata magani tasha na rage rad'ad'i da zazzab'i, tana idar da sallah ta koma ta kwanta ta ja lallausan bargo ta rufe, da kallo Juman ta bita sannan ta girgiza kai, duba agogon d'akin tayi sannan ta mik'e daga kan sallayar, wayar fax d'in dake d'akin gefen gado ta d'auka, a nutse ta shiga jera lambar wayar likitarta sannan ta aika mata kira, saida wayar tayi k'ara kamar zata tsinke sannan ta ji an d'aga, cikin girmamawa da mutumtawa suka gaisa da juna kafin ta fad'a mata tana buk'atar ganinta gida, a ladabce ta amsa mata da "Shikenan ranki shi dad'e, in sha Allah zan shigo nan da wasu mintuna." Jinjina kai tayi ita ma tace "Nagode, sai kin zo." Aje k'aramar carbin hannunta tayi mai duwatsun irge talatin da uku sannan ta cire hijabinta mai riga ta nufi ban d'aki, wanka tayi kafin ta fito ta shirya a sauk'akakk'en shiri ba kwalliya a fuska, tana kammalawa ta fita a d'akin tare da sakawa k'ofar makulli dan sam bata yarda da gidan nan ba, cire makullin tayi ta tafi da shi zuwa madafa. Shigarta yasa duk ma'aikata kama jikinsu suka dinga gaisheta, amsawa tayi a lokaci d'aya kafin ta nufi duk inda tasan zata samu abinda take da buk'ata, wata hadimar ce tace "Ranki shi dad'e me kike da buk'ata? Ki bari sai a had'a miki." Girgiza kai tayi tana yatsina fuska tace "A'a ku barshi, yanzu ni bansan da wa zan yarda ba a gidan nan, tunda har a cikin nan za'a kai min abinda aka saka guba, wato na ci da ni da 'yata ba?" Sake girgiza kai tayi ta shiga d'aukar k'wan da take son soyawa, duk jinin jikinsu suka sha suka ci gaba da aikinsu, mai dafa abincin mai martaba na kari daban, masu shara da goge madafar daban, masu dafa abincin bak'i ma daban. *Bacci* ya fara d'aukarta daga ta cikin ban d'aki wani da bak'ak'en kaya da rufaffiyar fuska ya hauro ta siririyar tagar dake ciki, a daidai bahon wankan ya saukar da k'afafunshi dan kar ya fad'a ciki gaba d'aya, saida ya tabbatar ya tsaya da kyau sannan ya tsallaka bahon ya sauko, a hankali ya bud'e k'ofar ya shigo d'akin, ganin Ayam dunk'ule tana bacci ya lallab'a saida ya je daf da ita, hannunshi mai d'auke da safa bak'a da wani k'aramin abu kamar reza mai kaifin gaske ya ciro, sake matsawa yayi kusa da ita sosai ya d'ora a gefen wuyanta da niyyar ya mata mummunan yankan rago. Saidai k'ofar da aka tab'a kamar za'a shigo ne yasa ya yanki wuyanta ba daidai ba, ganin jini ya b'allo daga wuyanta ita kuma ta farka a razane tana dafe wuya tare da furta "Auch!" Da gudu ya juya zuwa ban d'akin inda Ayam ta zuro k'fafu da niyyar sauka ta bishi, sai kuma ta ji rad'ad'in wuyanta na k'aruwa, hannu ta kai ta murza wurin lemar da ta ji yasa ta dubi hannun na ta, zaro ido tayi ganin jini ne ya wanke hannunta, da sauri ta mik'e tana sake rik'e wurin gam ta tunkari k'ofar da kai tsaye ta ji ana bubbugawa. Murd'a k'ofar ita ma tayi amma sai ta ji a rufe, jijjiga k'ofar ta dinga yi da hannu d'aya inda d'ayan ke kan wuyanta sai neman shure shure take, a gigice sarki Musail dake bakin k'ofar yace "Wai Juman ba zaki bud'e k'ofar ba ne?" Daga bayanshi Juman dake tahowa d'auke da farantin abincinta ta furta "Gani nan mana sarki na." Ta k'arashe a aladabce saboda gilmawar hadimai ta ko ina da kuma masu kula da gidan, juyawa yayi da sauri ya kalleta da mamaki, saida ta zo daf da shi cikin rad'a yace "Ina Zafeera?" Wani wawan kallo ta masa sanda take k'ok'arin zura makullin ta hudar k'ofar tace "Tana ciki." Cikin rad'a ya sake cewa "Me yasa kika barta ita kad'ai?" K'ofar data bud'e ta kuma murd'a lokaci d'aya yasa ta zuro kai tana fad'in "Saboda ba jaririyar da zan goya ba ce a baya n..." Turus ta ja ta tsaya sanda idonta suka gane mata Ayam durk'ushe cikin jini sai kawai ta saki farantin ta druk'ushe tana kiran "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ayam me ya same ki?" Da k'arfi ya shigo shi ma ganin wannan yasa ya sunkuya yana fad'in "Zafeera? Zafeera? Lafi..." Sai kawai ya k'arasa kusan gadon ya fara waige waige, k'ofar ban d'akin dake bud'e ya shige yana ganin taga a bud'e ya juyo da sauri, cikin hargagi ya kalli Juman da daidai shigowar likitarta yace "Ku bata kulawar da ta dace, karki kuskura ki k'ara yin nesa da ita." Ficewa yayi daga d'akin ba tare daya kula da komai ba, likitar na duba yankan wuyan Ayam d'in ta kalli Juman hankali tashe tace "Sarauniyata, ya kamata mu kaita asibiti, tana zubar da jini dayawa da buk'atar a ma ta d'inki." Mik'ewa Juman tayi tace "To me mu ke jira? Mu tafi mana." Kamata sukayi suka fita da ita, cikin kid'ima Juman ta kalli wani bafade tace "Ka kira mana dreba ya kai mu asibitin cikin gida." Da sauri bafaden yayi abinda ta umarceshi, kafin su fita k'ofar falon har drzba ya paka mota, shiga sukayi inda ya kewaye shukokin nan sannan ya zagaya ta bayan gidan tafiya ce mai d'an tsayi idan a k'afa ne, yana aje su daga cikin asibitin ma kujerar marasa lafiya aka fito da ita aka d'orata suka shige cikin asibitin da tsarin gininta yayi kamar wani k'aramin gida mai kyau. Suna shiga kai tsaye bloc aka wuce da ita dan kula da lafiyarta. Tunda ya shiga fadarshi ya ja baki yayi shiru yana jin maganganun fadawan na tashi sama sama, bai ce komai ba sai zuba musu ido, bai kuma nuna yana cikin tashin hankali ba, saidai yana lura da yanayin kowa da kuma son ganin wanda yake zargi d'in ya shigo. A hargitse ya shigo fadar yana kama babbar rigarshi, da sauri sarki Musail ya gyara zamanshi ya tsura mishi ido, kujerarshi ta kusa da sarki Musail d'in ya ja ya zauna yana kallonshi bayan ya rusuna masa. A d'an daburce Khatar ya kuma kallonshi sannan ya kalli Dhurani a b'angare d'ayan kusa da sarkin sannan yace "Ranka shi dad'e, yanzu nake samun mummunan labari a cikin gida." Rik'e hab'a sarki Musail yayi a dak'ile yace "Wane irin labari kuma waziri?" A sanyaye yace "Ranka shi dad'e, gimbiya Zafeera ce aka farmaketa a d'akin sarauniya, yanzu haka sun tafi asibitin cikin gida." A kasalance sarki Musail yace "Kenan bata mutu ba yanzu ma? Wai wane irin mutane ake ba wa aikin nan ne?" Kaf fadar suka dinga kallo kallo sai Dhurani daya kalli sauran fadawan da basa cikin tsarinsu yace "Zaku iya jira a waje, da alama mai martaba na cikin alhini." Jiki a sab'ule cike da takaici suka mik'e suka fita, wanda ya rage Khatar ne da shi Dhurani sai kuma Adah, da sauri Khatar ya kalleshi yace "Sarki na, da alama akwai mai ruguza mana tsarinmu, jiya cikin dare mutanenmu sun ziyarci d'akin gimbiya Zafeera, amma basu sameta gaba d'aya, saidai ko ma waye ya kai mata farmakin nan yanzu, bana jin d'aya ne daga cikin mutanenmu, dan har yanzu babu wanda ya tuntub'e ni da maganar." Da mamaki Dhurani yace" To wa ye kenan ya yi?" Girgiza kai Khatar yayi yace" Ban sani ba gaskiya, sai dai nan gaba zamu sani." A k'ufule sarki Musail ya kalleshi yana ji ya shak'i wuyanshi sannan bakinshi ya furta" Kai Khatar 'yar ta wa kake so ka kashe? Yata ta ciki na? Shin me ta tsare maka a rayuwa?" Amma sai ya dake yace" To wane irin hwanb'asawa kake game da lamarin? Ba dan ka ce na bar maka a hannunka ba, da yanzu na shak'e wuyanta." Da sauri Khatar yace" A' a yallab'ai, ai shi yasa na ce zan yi komai, kar ka d'auki matakin nan da hannunka, ina k'ok'ari a kai." Cikin d'aga murya yace" Wane k'ok'ari ka ke?" Cikin ladabi yace" Yallab'ai ai jiya mun yi k'ok'arin ciyar da su guba a abinci, amma sai wani abu ya faru suka tsallake wannan tarkon..." D'aga masa hannu yayi tarz da duk'ar da kanshi k'asa, k'afarshi dake sanye cikin takalmi masu kyau da k'yalli ya dinga buga k'afar d'aya bayan d'aya, wani huci ya fara jerawa yana saukewa, jikinshi rawa ya fara d'auka tsabar takaici da k'uluwa, d'aga kanshi yayi da sauri ya mik'e tsaye da wani irin sauri ya kama hanya ya fita tsabar haushi har k'afafunshi na hard'ewa. Da kallo suka bishi har da Adah ma daya bi bayanshi da sauri yana hararen Khatar, kallon junansu sukayi Khatar yace "Me ya faru kuma?" Girgiza kai Dhurani yayi yace "Ba na ce ba, ban dai fahimci komai ba, duba da ko halin da aka fad'a masa 'yarsa na ciki bai damu ba." Cikin rad'a Khatar yace "Ko dai bai ji dad'i ba ne da na fad'a masa." Harara Dhurani ya wurgawa k'ofar kafin ya kalli Khatar yace "Rabu da shi." *Sarki Musail* na fita daga nan cikin sauri ya shiga takawa zuwa asibitin, da girmamawa Adah yace "Ranka shi dad'e, ka bari a d'auko mota." A hassale yace "Ni rago ne ? Na ce ba zan iya tafiya can d'in ba?" Wucewa yayi kamar zai tashi sama Adah na bin shi, daf da k'ofar shiga Umad ya zagayo ta bayan asibitin shi maa kid'ime suka kacame, turus sukayi suna kallon juna sai kuma suka fara k'ok'arin shigewa. Karo sukayi da juna hakan uasa Umad dakatawa Musail ya wuce sannan ya shige shi ma da gudu, inda suka ga Juman tsaye suka tsaya a tare suka had'a baki wajen fad'in "Ya jikin ta?" "Ya jikin ta?" Kallon juna sukayi sai kuma suka kalli Juman da ta ja majina tace "Ban sani ba ni ma, tana ciki har yanzu basu fito ba." Lumshe ido yayi ya jingina a bango ya rumgume hannayenshi, k'ok'arin dakatar da zuciyarshi kawai yake akan abinda take raya masa, sam baya so ya fara d'aukan mataki sai ya ji halin da take ciki, indai har aka fito masa da gawarta yanzu, to shakka babu Zafreen ma za ta bi yar uwarta ba da jimawa ba, dan a dalilinta zai bayyana waye shi a duniya. Tsantsar tashin hankalin shi ne rasa dalilin da yasa za ta yi haka, saboda sarauta ne? Ko kuma dai son zuciyarta? Ko kuma wani ya sakata? Girgiza kai ya fara yi a hankali idonshi a rufe yana jinjina lamarin. Takon takalmin da suka ji a bayansu an shigo ne yasa su juyawa shi ma a nutse ya bud'e ido, zuba mata su yayi tun daga k'asan takalminta masu tsinin gaske bak'ak'e, zuwa dogon wandon jikinta daya kamata bak'i, sai rigar mai siraren hannaye ita m bak'a da gashinta data d'aure, dan kyau kam akwai shi, saidai kyan d'an maciji ne. Sarki Musail ma kallonta yake da mamakin abinda ya kawota, idan har ta san me ya faru shi ne zata shigo haka? Ba wani alamar abun ya dameta a matsayin Zafeera na yar uwarta, girgiza kai shi ma ya d'auke kanshi daga kallonta, tana zuwa ta ja birki ta tsaya ta kalli Juman a shek'e tace "Mah, ta mutu ne?" Wannan tambayar da tayi ita tasa kowa dake wurin kallonta, gyara tsayuwarsa yayi ya dafe k'ugu d'aya irin zai kirta rashin mutumcin nan yana kallon k'wayar idonta yace "... *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *35* Gyara tsayuwarsa yayi ya dafe k'ugu d'aya irin zai kirta rashin mutumci nan yana kallon k'wayar idonta yace "Ki zo kin ji ta mutu ne dalilin yankan da kika mata?" Wur wur ta kalleshi tana wurga ido zuwa fa Juman da sarki Musail, k'are masa kallo tayi ta rik'e wayarta da kyau tace "Me kake fad'a ne haka?" Rai b'ace ya girgiza kai tare da tab'a ta ya koma d'aya b'angaren ya tsaya, dan in takura kanshi wajen yin magana, to shakka babu kasheta zaiyi da marin da ba lallai ta rayu ba, idan kuma ta rayu ba zata rasa kamuwa da matsalar ji ba. Juman dake ta kallon Zafreen d'in ce ta girgiza kai tace "Akane Zafreen? Yar uwarki ce fa." Wani mugun kallo ta mata kafin ta d'auke kan ta zuwa ga k'ofar da aka bud'e, a hankali aka turo gadon da take kwance a kai an mata allurar bacci da kashe zafin jiki kafin aka mat d'inki a wurin. Duk rufa sukayi kan su har aka fito da ita gaba d'aya, kallonsu likitar tayi tace "Ba ta cikin had'ari yanzu, idan ta samu hutu zata wartsake." Dafe k'irji Juman tayi tace "Alhamdulillah." Turata aka yi zuwa d'akin hutu inda Juman ta bi bayansu, saida suka shige d'akin Zafreen ma ta juya a fusace ta bar wurin takalminta na k'ara, ita ma tana ficewa sai suka kalli juna Umad da Musail, kallo irin gwada gwa, hannu ya zura aljihu ya ciro makullin motar da ko ina yana tare da shi, mik'a masa yayi yasa hannu ya karb'a ba wanda yayi magana Musail d'in ya bar asibitin shi ma Adah ya rufa masa baya, suna fita b'angaren shi yayi yana bayar da umarnin "Adah ka kira min Khatar a b'angarena yanzu yanzu." Rusunawa yayi yace "To ranka shi dad'e." Ya fad'a yana ratse hanyar da suke bi a tare. *Suna* fita Umad ma kiran sarki Abdallah yayi ya fad'a masa halin d ake ciki, cikin tashin hankali sarki Abdallah yace "Ya take yanzu Umad? Tana ina?" A sanyaye yace "Tana lafiya yanzu, ga ta can d'akin hutu." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah, na ji dad'in haka." A dak'ile Umad yace "Sai dai kuma akwai matsala." Nutsuwa yayi sosai yace "Wace irin matsala Umad? Me ya faru?" A nutse ya sanar da shi abubuwan da suka faru daga zuwanshi, madadin mamaki da wasu tambayoyin sai kawai ya ji yana murmushi mai sauti yace "Umad, Umad, shi ne ka tare da amaryata ba sanarwa ko? To gobe zan shigo Khazira, shigowa ta farko bayan aurar da 'yata, kuma a fadar Musail zan sauka dan a shirye na ke da shi, sannanba ni kad'ai ba har da sarauniyata, dan ita zata raka maka amaryarka d'akinta." Yar dariyar da bai zata ba ce ta kubce masa yana girgiza kai, shiru da dukansu sukayi ne yasa a tare suka d'auke wayar daga kunnensu. *A* wajen Musail kuma yana tsaye a falonshi yana safa da marwa Adah ya dawo tare da Khatar, suna shigowa ya kalli Khatar saida ya zo daf da shi ya tsaya, rusunawa yayi yace "Sarki na ka ce in zo?" Dafa kafad'arshi yayi tare da zagayashi cikin tako d'ai d'ai yana fad'in "Khatar kasan wani abu kuwa? Na jima ina taraka, na dad'e ina rik'eka a zuciyata, amma alamu kullum nuna min su ke ni d'in nan dai ni ne zan ga bayanka." A rikice ya juya ya kalleshi cike da neman k'arin bayani yace "Ranka shi dad'e, ban gane ba? Me kake fad'a ne haka?" Murmushi ya sakar masa tare da zagayowa gabanshi ya kalli fuskarshi yace "Kar ka damu, zaka fahimta yanzu." Ba tare daya d'auke hannun daga kafad'a ba yace "Khatar, nasan abubuwa da dama da kuka aikata min kai da Dhurani, tabbas ni mugu ne kuma azzalumi, amma ba shashasha ba, lalacewata bata kai matakin da zan so kashe 'yata ta cikina ba saboda son mulki, hasalima yarinyar da kuke ganin kamar ina k'in ta ne, tsananin azababbiyar soyayya na ke mata, soyayyar da ko mahaifiyarta bana jin tana mata ita." Wani mugun kallo ya masa yace" Shi ne ka yi k'ok'arin kasheta? Kuma ma harda matata? Matar da na fi so a rayuwata?" Girgiza masa kai yayi yace" Ka yi kuskure, ka yi kuskure Khatar." Hannu ya mik'awa Adah shi kuma ya ciro wuk'ar dake k'ugunshi ya mik'o masa, yana damk'e wuk'ar a hannu bai yi wata wata ba wajen rumgumo shi jikinshi ya burma masa wuk'ar nan a ciki, k'arar daha bud'a baki zai yi sai kuma Adah ya koma ta bayanshi ya murd'e masa wuya tsaf, daga haka suka gama da Khatar aka rufe babinshi. Za a iya cewa mutuwar kare Khatar yayi, dan uamrni ya ba wa Adah a jefar da gawarsa nesa da nan inda kafin a gano shi ya kashe shi lokaci ya ja. Fita yayi ya bar Adah na k'oknarin d'aukar Khatar dan cika umarninshi, Musail na fita asibitin ya sake komawa, lokacin da Adah ya fito da gawar Khatar yana son sakashi a bayan mota a daidai lokacin Umad zai koma b'angarensu dan fita shi da Haman, abinda ya gani yasa shi ciro wayarsa ya d'auki hoto a matsayin shaida sannan ya sa ido a kanshi har saida ya shiga motar ya tuk'a, yana fita a gidan Umad ma ya karb'i makullin wata k'aramar mota a hannu dreban gidan ya bi sawunsa. A cikin asibiti kuma Juman ya samu zaune a kujera ta rabka tagumi tana kallon Ayam da ke bacci har ta k'ara fad'awa dama kuma ba kauri ba, dan tun jiya da ta zo gidan nan ba ta ci abinci ta k'oshi ba, bala'in gida da tashin hankali ya fi k'arfin tunaninta, gashi a kwana d'aya tak an hari rayuwarta sau uku kenan, ta ya mutum zai rayu a haka? Zulumi da fargaban kowane lokaci za'a iya farautarka sannan a kasheka, ai musiba ce babba kuwa, dan haka da ta ji sauk'in nan kawai d'auketa zatayi ta koma gaban iyayenta ita kanta zata fi samun nutsuwa. Bakin gadon ya zauna yana kallon fuskar Ayam d'in, sauke numfashi yayi mai nauyi tare da laluba aljihunsa ya ciro makullin nan, mik'a wa Juman yayi yace "Idan ta dawo hayyacinta ki bata shi, mallakinta ne izuwa yanzu kuma ta cancance shi." A shashance ta karb'a tace "Na miye wannan d'in?" Tab'e baki yayi yace "Ba ke kin tseratar da ita ba? Wace kariya kika bata bayan haka? Kawai kin had'a da mutanen da kike ganin kin san su ne a matsayin bayinki, hatta yanda zaki ji lafiyarta sai dai a baki labari daga bakin mutum hud'u, ni kuma kai tsaye nake samun labarin lafiyarta." Mik'ewa yayi tsaye yana kallonta yace" Juman, ni ba wawan uba ba ne, ki daina min kallon da ki ke min, ya isa haka." Cikin d'aga murya tace" Ba zan daina maka ba har sai ranar da na tabbatar baka neman 'yata da sharri, me yasa wai ba zaka hak'ura da burinka na son kasheta ba? Ka barta ta rayu ni kuma na maka alk'awarin d'auketa daga nan tayi nesa da kai da sarautarka." Gyara tsayuwa yayi da kyau cikin isa da fitar da kowane harafi yace" Kin d'auka sanarwar da aka dinga yi daga gwamnati saboda mahimmancinta a gare su ne ? Ko kad'an, ni ne na yi haka dan na jawota gare ni, daga yanzu kuma ni ne zan dinga kareta har sanda numfashi zai bar gangar jikina." Juyawa yayi zai zauna kan kujerar dake gefen gadon na zaman mutum uku, rik'e hannunshi tayi tace" Kamar ya zaka kareta da kan ka? Ba kai kake son kasheta ba?" Tsaki yayi ya bige hannunta tare da zaunawa kan kujerar yana sake kallon fuskar Ayam, komawa tayi ta zauna ita ma tana kallonshi sai tunanin abinda ya fad'a take yi, sai dai sam zuciyarta ta kasa yarda da abinda ya fad'a, dan ita a ganinta abubuwan da ke faruwa har yanzu bai d'auki mataki d'aya ba a kai. *Giobarh* Abun al'ajabi ne tashin sarauniya Kossam da k'afafunta a safiyar yau, abun kamar al'amara, ba taimakon kowa ba kuma sanin kowa haka aka wa yi gari aka ganta da k'afafunta kamar yanda take a da shekaru da suka wuce, kowa kallonta yake kamar ya ga sabuwar hallita har sanda sarki Wudar ya zo inda ta ke da mamakin da ya fi na kowa. Ido cikin ido suke kallon juna amma mamaki ya hanashi magana, d'an murmusawa tayi a ladabce tace "Mamaki ko? Ba abun mamaki ba ne." D'an jujjuyawa ta fara kamar tana neman wani kafin ta kalleshi tace "Ina yarinyar nan?" K'asan k'afafunta ya kalla ya dai tabbatar ita ce sannan ya kalli fuskarta, da mamaki yace "Wai...ya haka? Kossam, ya haka ta faru?" Murmushi tayi mai tsadar gaske tace "Wannan yarinyar ce, a duk inda take yanzun na tabbatar suna tare da Umad, na ga hakan a mafarki na kuma na gasgata." A kid'ime ya zaro ido yace "Me? Umad? Da Zafeera?" Da mamaki da kuma fara'a ta kalli fuskarshi tace "Zafeera? Ita ce dama? Sunanta kenan?" Hankali a tashe yace "E, amma me ya had'ata da Umad kuma?" Girgiza kai tayi tace "Ban sani ba, amma dai akwai wani abu dake faruwa a tsakaninsu." Da k'arfi cikin rud'u yace "Baki sani ba?" Cike da izgili ta d'aga kafad'a alamar e ta juya zata fita tace "E, ban sani ba, amma yanzu zan sani tunda na samu lafiya." Fita tayi daga falon ta tunkari b'angaren Joyran, a hankalce take tafiyar tana kallon k'afafunta da mamakin yanda farat d'aya ta tashi yau, haka kawai a mafarkinta ta ga wannan yarinyar da kuma Umad, hak'ik'a tun ranar da yarinyar ta hana kowa shiga wurinta sai amintattunta, tun ranar Joyran bata sake shiga d'akinta ba, abincin da take bata da abinda take shafa mata a jiki duk ta daina, tun daga ranar ta fara jin canji a jikinta, daren jiya kuma bakinta ne ta ji yana tirsasata tayi magana, haka kawai ta fara d'aga harshenta da a baya kamar shi ne aka danne aka hana mata magana da shi, amma sai ta ji ya saki har ta fara furta sunan d'anta Urab da kuma Umad. Tsakiyar dare tana bacci sanda mafarkin nan ya zo mata tana ganin hoton fuskar yarinyar da kuma d'anta a gefenta, yanayinta ya nuna kamar shagwab'a take dan tayi takwaf takwaf da fuska ne, amma bata tantance ba kawai ta ji ta zumduma ihu da ya sa ta tashi daga baccinta a firgice, mantawa tayi da larurarta kawai ta mik'e tsaye tana zazzare ido, saida ta hangi kanta a madubi ne sannan ta kula ita ce fa a tsaye, tsaye kan k'afafunta yau? Sai kawai ta shiga takawa tana godiya ga abun bautarsu tana mai son sake ganin yarinyar nan da har yanzu bata san ko da harafin farko na sunanta ba. Joyran na tsaye tana ta kai da kawo da wayarta a hannu tana fad'awa k'awarta cewa "Ki taimaka min k'awata ki je ki samu mutumin nan ya min wani sabon aikin, nan da India ai ba wata tafiya ba ce, kuma zan d'auki nauyin komai na tafiyar ta ki, kin ga na rantse miki ina cikin tashin hankali." Jim tayi alamar gana sauraren abinda ake fad'a daga can, da sauri ta d'auka da fad'in" Ba zaki gane ba k'awata, komai fa nema yake ya lalace a nan, kinga dai kwana uku kenan ban ba ta abinci ba bare na saka maganin, gaba d'aya yarinyar nan ta lalata komai, yanzu haka Wudar d'in ya juya min baya, jiya ya shigo yana son na bashi had'in kai, na d'auka zai sake dawowa saboda ba zai iua hak'ura da ni ba, amma kuma har yanzu bai waiwaye ni ba, gashi Khatar ma da ya ce zai turo min kud'i har yanzu shi ma bai turo ba." Marairaicewa tayi tace" K'awata, idan har lamarin nan ya lalace na rantse miki barin garin nan zan yi, tattarawa zan yi na koma can gurin Khatar, dan cikinsa ne a jikina." Daga bayanta ta ji an ce" Ki bar nan ki je ina 'yar uwa?" Da k'arfi ta juyo tana zazzago idonta dan tabbas tasan murya da jimawa, ganin Kossam tsaye gabanta ta k'are mata kallo tas, sai kawai ta saki wayar ta fad'i k'asa da k'arfin tsiya tace" Kossam? Ke ce a kan k'afarki? Ta ya ya? Bayan bokan nan ya fad'a mana haka zai faru ne kawai idan sauyi ya zo." Saida taa gama fad'a sai kuma ta fahimci me ta aikata, wata dariya Kossam ta dinga shek'awa kafin ta girgiza kai tace" Haka ya fad'a? Da alama kun jima baku had'u ba ko? Tunda bai fad'a miki sauyin ya zo ba." Rarraba ido ta fara yi tare da k'ak'aro murmushi tace "Amm..yaya...ba fa abinda...nake nufi ba kenan, kawai dai..." Shiru tayi ba tace komai ba, da fara'a a fuskar Kossam tace "Na fahimta, yanzu dai barin garin nan ba shi ne mafita ba, ki zauna tare da ni, zan ji dad'i sosai." Juyawa tayi zata fita sai kuma ta tsaya ta kalleta, a dak'ile tace "Cikin jikinki, me yasa kika so d'orawa mijina da farko? Amma yanzu kuma daga bakinki na ji asalin na wa ye." Girgiza kai tayi cike da takaici tace "Ban tab'a tsammanin haka daga gareki ba, Joyran kin ci amanata kuma kin zalince ni, amma..." Jinjina kai tayi ta cije leb'e tare da juyawa ta fice a falon, tana ganin fitarta ta d'ora hannu a kai ta durk'ushe ta fashe da kuka tana fad'in "Na shiga uku ni Joyran, me na aikata haka? Ya zan yi yanzu?" Kamar an tsikareta sai kuma ta zabura ta mik'e tana rarumar wayarta a k'asa ta shige d'akin baccinta dan had'a kayanta, dan ba zata k'ara awa d'aya gidan nan ba sai ta barshi, matsala d'aya shi ne isashen kud'i da bata da a hannu, amma duk da haka zata harhad'a kan kud'ad'enta da kuma siyar da kadarorinta in ya so ta kama gabanta. *Egypt* A falon na alfarma mai d'auke da mafiya dattijai suka gama tattaunawa, sun jima suna hirar data shafi ci gaban talakawa akan tallafin da masarautar zata bayar na ilimin yara k'anana. Bayan sun kammala duk da ya gaji sosai yana kuma buk'atar hutu, amma haka ya sa aka shigo masa da Bukhatir, zaune yayi d'aya daga kujerun wanda suka tashi a ladabce, cikin girmamawa yace "Ranka shi dad'e ka ce ka na son gani na, ina fata dai lafiya?" A sanyaye ya sauke numfashi yace "Bukhatir, na kiraka ne dama akan tafiyar da nake so na yi gobe." D'an kallonsa yayi sai kuma ya sadda kanshi yace "Tafiya kuma sarki na? Zuwa ina?" A hankali ya furta "Khazira." Da sauri wannan karan ya d'ago ya kalleshi yace "Khazira?" Jinjina kai yayi a hankali yace "E." Sunkuyar da kai yayi yace "Amma yallab'ai komai lafiya? Tafiya Khazira haka kai tsaye?" Jim yayi yana sauke numfarfashi kafin daga bisani yace "Lafiya ba lafiya ba, zan je ne dan gudanar da shagalin bikin jikata." Da wani mamaki ya d'aga kai ya kalleshi yace "Jika kuma? Zafreen ta samu mijin aure ne?" D'an murmushi yayi a hankali yace "Ba Zafreen ba ce, Zafeera, ko kuma na ce Ayam." A gigice ya d'aga kanshi ya kalleshi, cikin fitar hayyaci da mantawa yace "Zafeera ce za ta yi aure? Ina raye?" Da kallon tuhuma sarki Abdallah ya kalleshi d kuma mamaki yace "Kamar ya kana raye? Kana son ta ne?" K'iri k'iri ya masa da ido yana kallo ba rusunawa, sai ya ke ji kamar ya hau sa da duka ma, yanda shi ma ya ga yana kallonshi yasa sarki Abdallah fad'in "Lafiya dai Bukhatir?" Da sauri ya sauke kanshi k'asa yana girgizawa yace "A'a, a'a ba komai." Jinjina kai yayi yana murmushi yace "Shikenan, ka je ka shirya tare da iyalinka za mu tafi, sannan a can gida ma (gidan iyayen Bikhatir) ka sanar da su, zamu tafi a jirgin safe in sha Allah." Nauyayyen numfashi ya sauke yana jinjina kai amma bai ce komai ba, dan abun ya fi k'arfin yace komai, irin yanda aka shammace shi haka sai ya ji kamar zai mutu. *Alhamdulillahn* 01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *36* Sai daf da yamma ta farka daga nauyayyen baccin, idonta ta fara saukewa akan Juman dake kusa da ita tana kallon d'inkin da aka mata a gefen wuyanta, cike da kulawa Juman tace "Ayam, kin farka?" D'an rufe idonta tayi sannan ta bud'e kafin ta muskuta tana son tashi zaune, dage d'aya gefen na ta taji an rik'eta an rumgumata a k'irji da niyyar taimaka mata, k'amshin turaren ya fara kai mata a hanci, hakan yasa ta zabura ta d'aga kai ta kalleshi, iskan bakinshi ne ya fara dukan hancinta yanda iskar hancinsu ya daki na juna. K'ok'arin janyexa tayi daga jikinshi da mamakin wane rashin kunya ne kuma haka? Sai sarki Musail daya mik'e a lokacin zai fita ya kalleta yace "Bari ya taimaka miki, jikinki ba k'wari." Yatsina fuska tayi ta d'an sake satar kallonshi, kawar da kai tayi tana kallon Musail ta d'aga bakinta da k'yar tace "Pah, ba na son...ganin sa a nan, please ka ce ma sa ya tafi." A take suka kalli juna Umad da Musail, da ido ya masa alamar ya tafi kawai, Juman kuma da mamaki tace "Me yasa Ayam? Ya zo taimaka miki ne fa." K'ofar d'akin aka bud'e aka shigo, kallon Haman d'in sukayi da ya shigo yanzu har da ita kanta Ayam, k'arasa zame jikinta tayi daga na shi tana kallon Haman tace "Ai ga mijin da zan aura nan, me zai hana shi ya taimaka min madadin mai kula da shi?" Wani kallo ya watso mata daga tsayen da yake ba tare daya mik'e daga rank'wafawar da yayi ba wajen taimaka mata, sai kuma ya kalli Haman d'in dake ci gaba da takowa a hankali amma alamun tuhumar kansa sun bayyana a tare da shi, kallonshi yayi ya mik'e tsaye da kyau tare da zuba hannayenshi a aljihu. Cikin kulawa Haman ya kalleta yace "Ya jikin na ki? Da sauki?" Ayam ma kallon Haman d'in take dan haka kawai take jin haushin Umad da son ganin ta k'untata masa, amma da fari tana buk'atar ta samu lafiya kafin nan, k'wafa tayi a zuciyarta ta mik'awa Haman hannu tace "Dan Allah taimaka min, ina so zan shiga bayi." Ba tare da tunanin komai ba ko ran wani zai sosu ge da hakan, duba da tsarin da suke kai shi da Umad, da kuma yanda ya dinga jadadda masa shirin su kar kuma ya yarda ya kwafsa, sai kawai yayi azamar rik'o hannunta sannan ya matso daf da gadon. Daga cikin aljihun ya nemi damk'e hannunshi ganin yanda gaban idonshi ya rarumi hannunta, wasu d'atattun yawu daya had'e yasa Musail waro ido da kyau ganin yanda mak'wallaton dake wuyanshi ya wani yi sama da k'arfi sannan yayi k'asa, a hankali ya taka zuwa kusan Umad d'in ya dafa kafad'arshi yana murmushin mugunta. Suna kallo har ta sauko da k'afafunta ta saka takalminta suka nufi hanyar ban d'akin dake cikin d'akin, bud'e mata k'ofar yayi ta shiga sannan ya tsaya yana jiran fitowarta. A wani hassale a kuma dak'ile Umad dake hango ta ya ma zai tsaya kuma a k'ofar? Sai ya jira ta fito ko me? Uzirin na ta zai saurara? Cike da takaici yace "Zo ko?" Saida ya gyad'a sannan ya tako ya dawo gabansu ya tsaya, Musail da har lokacin bai d'auke hannunshi a kafad'ar Umad bane ya kalleshi cike da son k'ular da shi yace "Gaskiya dokin k'arfe, da ba buk'atar b'oye b'oyen ai." Da mamakin dake neman kasheta Juman tace "Wai me yake faruwa ne? Umad...?" Kallonta Musail yayi yace "Kin tuna shi kenan? Na d'auka ba zaki ganeshi ba, saidai na manta akwai kamannin Urab a fuskarshi." Girgiza kai yayi da dariya irin na "Haba yara." Sannan ya d'auke hannunshi a kafad'ar Umad ya kama hanyar fita, da kallo duk suka bi shi kuma kowa da abinda ke ranshi, Juman mamakin yanda ta ji yayi wasu maganganu yanzun take, ba ma yanzu na ita fa tun daren jiya duk ya sauya mata, wasu abubuwa yake yida suke sakata cikin rud'ani suna kulle mata kai, kamar ya san da faruwar komai? Kamar kuma yana hankalce da komai? To in hakane kenan me ye sunansu? Me suka aikata su? Me kuma zai aikata musu tunda ya san gaskiyar? Haman kuma maganarshi a cikin tsoro ta antayashi, dan shi ma dai tunaninshi kenan, idan har ya sani wane mataki zai d'auka a kan shi? Me zai iya yi masa? A matsayinsa na wanda ya taimaka ana so a raina masa hankali, gashi shi kuma ko shirin bai gama sani ba, dan sai Umad na son wani abun ne kawai zai ce masa yi min kaza, amma har yanzu bai san dalilin zuwansu gidan nan ba da dalilin da yasa ya ce ya nemi auren Ayam, wacce a yanzu dai ya gama fahimta shirin shi na farko ba zaiyi tasiri na dan ita kanta Ayam d'in tsoronta yake ji, ama shiri na biyu na zai kasa aiwatarwa ba tunda ba shi kad'ai ke farautar wannan matakin ba. A wajen Umad kuma kallon tsana ya bishi da shi da jin cewa lallai shi ya *kashe masa d'an uwa*, sannan a dalilin *mahaifiyar shi* ta fad'i sumammiya, wanda daga wannan ne suka rasa lafiyarta, sannan shi ne yayi dalilin mutuwar *mutumin* daya taimaka masa har ya samu masaniya akan inda zai samu Zafeera, haka kuma yanzun yake farautar rayuwar su Habbee dan ya kashesu, uwa uba kuma yake farautar masa mata, ita ma so yake ya hallakata. Dan haka ba zai yiwu ba, tabbas ya zo gdan nan ne saboda Ayam, amma da niyyar ya k'ara samun wasu sirri da hujja da zasu nuna sarki Musail azzalumi ne sannan makashi, ba kuma zai bar nan ba har sai ya tabbatar an zartar masa da hukuncin da ya dace, ba zai tab'a bari burinshi da wahalarsa ta shekara da shekaru su tafi a banza ba. Dalilinsa na shiga aikin hukumar sirri shi ne dan ya gano abinda ya faru a k'asar Egypt shekaru ashirin da shida, yana so ya san asalin abinda ya kawo wannan hatsaniyar, ya kuma samu da haka ya dinga bibiyar lamarin, hatta Ayam ya shiga rayuwarta ne a dalilin yayanshi. Sai dai a kowane lokaci sarki Musail yana sake tabbatar masa shi mai laifi ne da baya son a tonaasa asirinsa, dan a lokacin daya gano wani muhimmin anfani da waziri Khatar zai masa, sai kawai d'azu ya ga gawarshi akan titi wanda Adah ya jefar, bayan ya bar wurin ne ya zo ya su a ya kuma tabbatar, dan haka yanzu makaminsa d'aya daya rage shi ne *Adah*. Kowane sarki, kowane mai iko, kowane mai mulki yana da na hannun dama, kuma na hannun daman sarki Musail shi ne Adah, dan haka Adah ne harinsa na gaba kuma zai yi nasara wannan karan da yardar Allah. Murd'a k'ofar da Ayam ta yi ta sa suka kalli k'ofar, da sauri Haman ya d'aga k'afarshi da niyyar k'arasawa ya kamata duba da yanda ta ke tafiyar sannu sannu tana ciccije fuska, saidai kafin ya d'ora k'afar a k'asa Umad ya sha gabanshi tare da nufa inda ta ke, ya na zuwa bai tsaya komai ba ya rik'o hannunta sannan ya fara takawa da ita a hankali. Cak ta tsaya tana kiciniyar yakice hannunta, jin ya rik'eta sosai yasa ta sake k'ok'arin kubcewa tana fad'in "L芒che moi ma main (sake min hannu na)." Kallonta yayi, duk da fuskarshi a had'e take kuma ranshi a b'ace, amma dai sai ya ji ba buk'atar ya had'e mata fuska yayin da zai mata magana, dan haka a sanyaye ya furta "Ko mu je ki taka da kanki, ko kuma na taka miki k'afafun, wane ki ke so?" Kamar jiranshi take sai kuwa ta d'aga murya har da lik'e ido tsabar masifa tace "Ba na so d'in, na ce ba na so, dole ne malam? Sake ni zan tafi da kai na." Sunkuyawa ya yi kamar zai gyara d'amarar takalminshi, kafin ta ankara sai ji tayi ya kwashi k'afafunta ya yi sama da ita, wutsil wutsil ta fara da k'afafun tana fad'in "Mahhh! Mah ki na gani fa? Ki masa magana mana ya sauke ni." Saida ya kawota kan gadon ya dire sannan ya rik'e k'ugu yana kallon fuskarta, wata masifa da ya ga tana neman koya daga jiya zuwa yau, rigimar da take neman d'orawa kanta, jinjina kai ya yi ba tare da ya d'auke idonshi daga kan ta ba. Juman da abun ya d'aure mata kai ta rasa me za ta yi tunani a kai, ga wanda ya zo maganar aurenta, amma kuma ga wanda ke matse mata waje, kallonsu kawai take kamar bak'in fuska a gabanta. Cikin takaici ta kalli Haman da shi ma mamakin yanda Umad d'in ke mata yake, cike da masifa Ayam ta nuna shi da hannu tace "Wai a haka ne za ka aure ni? Kana ganin abinda ya ke min amma ba za ka d'auki mataki ba." A fusace ta d'auke kai daga kallonshi ta furta "Banza kawai." A tare suka zaro ido, Haman kam sai ya ji ta muzantashi, amma ya zai yi tunda yar Musail ce, Umad kam shafa sajenshi yayi sannan ya kuma tsareta da ido yace "Me za ki ci?" Harara ta wurga masa tace "Ban sani ba." Wani shak'iyin murmushi ya saki ya juyo ya kalli Juman kamar gunki da kuma Haman da ya d'an had'e fuska yace "Ku d'an ba mu guri sarauniyata, zan sa ta yi magana." Jinjina kai Juman tayi tace "Shikenan." Kallon Ayam tayi tace "Kar ki yi taurin kai kin ji, ki fad'a ma sa abinda ki ke so." Da sauri ta kalleta tace "Mah, Mah kar ki fita, jira ni to..." Ta yi maganar ta na sauko k'afafunta za ta fita ita ma, hannu ya sa ya dangwarar da ita ta koma zaune, a hassae ta kalleshi za ta yi magana, amma ganin ba ita ya ke kallo ba sai ta yi shiru tana hararanshi. Ya na ganin fitarsu ya juyo kan ta tare da zaunawa gefenta, fuska a had'e yace "Me za ki ci?" Kallonshi tayi idonta taf da k'walla tace "U...mad, ka san dai idan na maka Allah ya isa za ta bi ka ko?" Zuba idonshi yayi cikin na ta kamar zai yi dariya, sai kuma ya gyar zamanshi da kyau saboda hango irin abinda zai mata yanzun, cike da isa yace "Na sani, amma ba zan bari ki yi ba, idan ma kin yi babu abinda za ta min." Da alamar tambaya tace "Haka ka ce?" Da ido ya mata alamar um! Rumgume hannaye ta yi a k'irji tace "Shikenan ka je na bar ka da..." Shak'o rigarta ya yi da k'arfi hakan yasa ta kawo masa karo goshinsu ya had'e, kafin ta san dalilin da ya sa ya yi haka sai kuma ta ji d'umi a cikin bakinta, dan idonta rufewa sukayi sanda goshinsu ya kauru. Tsutsar da aka mata a baki ne ya tabbatar mata da lallai fa bakinshi ne a na ta bakin, hannayenta biyu ta d'ora a k'irjinshi sannan ta sa k'arfi dan ta tureshi, gam ta ji ya sake nane mata ya lik'e, zaro ido tayi ta fara tureshi da k'arfi tana "Um..umum..umm..." Irin tsutsar da ya ke mata kamar ta gayya dan sai ya yi kamar zai cire hak'orinta, sai kuma ya cabki harshenta ya na lalubar mata dadashi, saida ta ji leb'enta na zafi alamar azaba ta saki jikinta gaba d'aya ta bud'e idonta da ta lumshe, sharrr hawaye suka sauko a kuncinta, bud'e idonshi yayi da suka rikid'e suka zama ja sai rufewa suke k'arfi da yaji, ido cikin ido suka had'a ido hakan yasa ta kuma lumshe idonta ta masa alamar ka yi hak'uri yallab'ai. Samun kanshi yayi da saisaita tsutsar da ya ke mata, a hankali a hankali ya fara mata yanzu har saida ita kan ta ta fara jin tasirin abun a jikinta yanda ta sakar masa bakin ta daina k'ok'arin k'wacewa, sannan ta lumshe idonta ruf tana sauke numfashi daga k'asan mak'oshinta. Lis ya mata wanda hakan duk ya galabaitar da su, yana sakin bakinta mik'ewa yayi ya shiga takawa da mugun sauri zai bar d'akin har had'a k'afa yake, ita ma idonta a rufe ta jingina a gadon dan haka bata san ya fita ba, numfashi take saukewa sannu sannu har ta jawo pillow ta rumgume tayi shiru. Wurin ranar asibiti su ka yi shitare da Juman da sarki Musail dake yawan lek'owa, sallah kad'ai take sauka daga gadon tayi ta koma ta zauna, abinda kuma Juman ba ta sani ba shi ne, sarki Musail da kanshi ya shiga madafa ya bayar da umarnin a dafa musu abinci sannan jakadiyarsa ta tsaya kan girkin, tare da alk'awarin idan aka samu matsala tabbas zai ganawa mutum azaba, amma sanda aka kawo abincin dukansu d'ari d'ari suke da abincin, saida ya d'auki cokali ya sa a bakinshi ya ci ta tabbatar ya had'e sannan kad'ai ta zuba ta fara ci, saida ta cinye da tsawon minti biyar kafin ta zuba ta ba wa Ayam. Dariya yayi kawai yana girgiza kan shi sannan ya fice, sai yamma sosai aka sallameta inda suka koma masarauta a mota. *Da dare* A d'akin Ayam Juman ta kwanta bayan Ayam d'in ta yi wanka ta saka kayan bacci masu laushi, lafiya lau suka kwanta kuma gida ya yi shiru alamar ko wa ya kwanta dan ya huta ma ran shi. *03:00* wata mummunar k'arar fashewar tukunyar gas ta sa duka mutanen gida farkawa a kid'ime, kuma daga d'akin abinci wannan abu ya fara, saidai a lokacin da turmutsutsun mutane ya fara cika gidan, sai kuma wutar ke dad'a yad'uwa a sauran sassa daban, a cikin haka kuma aka ji wata k'ara mai kama da jiniyar motar asibiti ta karad'e gidan wacce ke nuna lallai wasu sun karya tsaron gidan sun hauro ciki, sai kowa ya k'ara rikicewa ana ta neman mafaka inda mazan suka shiga neman makamai dan kare kansu da iyalensu da kuma sarkinsu. Wad'anda ke cikin falon k'arar harbin bindiga suka ji daga waje alamar fa yak'i ne ke faruwa, kafin ka ce me an fara turo k'ofar falon, duk matan ihu suka saka suna b'uya mazan kuma suka sake rik'e makamansu a hannu suna jiran kar ta kwana. Ana bud'e k'ofar aka shiga harba bindogogi ana ba da wuta ba kakk'autawa, sai ga mutanen nan ne dake rufe da fuskokinsu da bak'ak'en kaya sun shigo sun fi su ashirin. Da azama suka shiga falon tre da da tsayawa waje d'aya, wanda ke gabansu da ya nuna shi ne shugaban tafiyar ne yace "Ku duba mana ko ina dan mu samota, ku yi aiki da jiki." Da azama suka shiga sassarfa suna fad'awa duk wani wuri da suka san d'aki ne, jim kad'an suke dawowa suna sanar da shi babu kowa a d'akin, hakan yasa ya kalli matan da suka rakub'e dan duk sun harbe mazan yace" Ke zo nan." Jiki na rawa wacce ya kira ta rarrafo ta durk'ushe gabanshi, cikin kakkausan murya yace" Ina Gimbiya Zafeera?" Jiki na kakkarwa tace" Ban...ban...sani...ba" Wani mahaukacin mari ya wanka mata a tsawace yace "Za ki fad'a min ko sai na kasheki?" Ya fad'a yana nunata da bakin bindiga, fashewa tayi da kuka jiki na sake b'ari ta nuna masa kusurwar tace "Ta can ne." Juyawa yayi ya kalli yaran da suka dawo masa yace "Mu je." Tunkarar k'ofar suka yi duk da bindigoginsu a hannu, daga gefensu d'aya daga cikin yaran Umad yayi kukan kura ya naushe shi a baki, lokaci d'aya ya kama hannunshi mai bindigar ya murd'e tare da d'ora hannunshi daidai kunamar bindigar, kafin ya ankara ya saki alburushi ga d'aya mutumin dake gefen wannan, Haman da shi ma suka fito tare yana rik'e da bindigarshi da azama ya tashi kan yaran biyu hakan ya rage sai shugaban na su. Umad ya saitashi da bakin bindiga kenan sai kuma wasu yaran suka fito wad'anda suka bazu neman Ayam, hakan yasa shi da Haman suka b'uya a k'asan matakalar da zata kai ka d'akin Juman, wuta suka dinga ba wa junansu aka dinga ba ta kashi, cikin taimakon ubangiji duk suka kashe yaran inda shugaban ya k'arasa shigewa wajensu Ayam. Fitowa sukayi daga malafarsu suna kallon juna Umad yace "Ka gane, wad'annan mata ka tsaya tare da su, zan je na ji da wan...ahhhhhhh." K'ara ya saki sakamakon harbinsa da wani ya yi a bayanshi ga kafad'a, da wani irin salo da k'warewa Haman ya saita kan mutumin ya tasheshi a aiki. Da sauri ya kalli Umad daya rufe ido hannunshi na jini yace" Umad, kana lafiya?" Matse bakinshi yayi sosai ya daure duk da rad'ad'in da yake ji ya bud'a ido ya kalleshi yace" Lafiya lau na ke, zan je na duba kar ya cutar da ita." Cike da damuwa Haman yace" Ba za ka iya ba Umad, ka bari ni na je." A hassale Umad ya kalleshi yace"... *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *37* A hassale yace "Zan iya mana, zan iya, zan iya." Da gudu ya juya ya nufi hanyar d'akin na ta, Haman kuma k'arasawa yayi kusa da hadiman nan da suka lab'e bayan kujeru. Daga waje kuma har yanzu sara da suka ake da harbi tsakanin dakarun sarki Musail da maharan nan, inda cikin k'warewa duk su ka yi nasarar kashe maharan sannan rabin su suka tunkari b'angaren sarki Musail, wasun su kuma suka shigo falon dan ba wa sarki da iyalinshi kariya. Kasancewar Adah wanda ya san sarki Musail farin sani ne, sai ga shi cikin tawagar wad'anda suka shiga falon da kiyyar kare iyalinshi, yanda Haman ya saitasu da bakin bindiga yasa Adah saurin d'aga hannayenshi yace "Kar ka yi harbi, mu ne." D'auke bindigar yayi sannan ya matso kusa da su yana fad'in "Wannan harin fa? Daga ina haka?" Da sauri Adah yace "Ba wannan lokacin, dole mu gaggauta ba wa iyalin mai martaba kariya kafin su cimma su." Sama ya tunkara zai hau tare da mabiyanshi sai Haman yace "Ina ga suna d'akin gimbiya Zafeera." Juyowa Adah yayi ya kalleshi sai kuma ya kalli wani yace "Ku biyu ku je d'akin gimbiya Zafreen, ku tabbatar babu abinda ya sameta, akwa mab'oya ta sirri a d'akin, ku yi k'ok'arin dubata a ko ina." Da gudu gudu suka nufi inda ya fad'a musu suna kuma rik'e makamansu a hannu, shi kuma tare da wasu suka nufi d'akin Ayam d'in dan ba ta kariya. *Umad* na isa k'ofar d'akin ya tsaya tare da duba bindigarshi dan ganin alburushi na wa ya rage masa, k'waya biyu ne dan haka ya mayar ya sake d'anata, lumshe ido yayi yana jin yanda rad'ad'in nan ke ratsashi, bud'e ido yayi tare da jan dogon numfashi sannan ya sauke, a hankali cikin sand'a ya sake kawowa daf da k'ofar, d'an lek'awa yayi dan ganin k'ofar d'akin a bud'e take, saidai babu abinda ya gani, k'arar fad'uwar abu da ya ji tare da k'arar Ayam yasa yayi kukan kura tare da mantawa da komai ya danna kanshi cikin d'akin yana mai saita daidai kan mutum da bindigar. Cak ya tsaya saboda ganin wata rufaffiyar fuskar da aka nad'e da rawani, wannan mutumin da ya shigo d'akin na jikin shi ga dukkan alama kuma ya kashe shi ta hanyar murd'e masa wuya. Sakin mutumin yayi hakan yasa shi fad'uwa k'asa ba rai bare ya motsa, fad'uwar da ya yi tasa Ayam ta saki kwalbar turaren data d'auka dan kare kansu daga sharrin mutumin nan, amma kafin ta kai ga haka kawai ta ga wannan mutumin da fararen kaya ya fito daga wata k'ofar ta cikin d'akin da bata san da ita ba kawai ya damk'i mutumin nan, wanda da ita ce a k'alla zasu d'auki awa d'aya suna gabza fad'a, ita bata yarda ya kayar da ita ba, shi ma kuma bai fad'i ba saboda girmanshi. Da sauri Umad ya tunkari inda take tsaye ya d'an shiga k'are mata kallo sannan ya kalleta yace "Ba abinda ya same ki?" Girgiza kai tayi alamar e, sannan ta kalli Juman dake kusa da gado tana kallon mutumin dake gabanta, kallo ne take masa zuciyarta na bugawa sosai, jinin jikinta kanshi tsitsinkewa yake, kallon sani take masa ba kuma sanin shanun talla ba, farin sani mai sunan farin sani dake nuna kasan ciki da waje na mutumin, yanda take sororo a tsaye ta kasa gusawa har saida Ayam ta dafata cike da kulawa tace "Mah! Kina lafiya?" Kallon Ayam tayi kamar wacce ta farfad'o daga doguwar suma, sai kawai ta girgiza mata kai alamar ba komai. A hanzarce mutumin ya taka zai bar d'akin da sauri Umad ya rik'o hannunshi, hakan yasa mutumin juyowa ya kalli hannun Umad dake rik'e da na shi hannun, a hankali ya d'aga jajayen idonshi manya ya kalleshi, murya a dak'ile Umad yace "Wa ye kai?" Maida kallonshi yayi ga k'ofa ba tare d ya ce komai ba, shiru yayi bai amsa ba haka kuma ba alamar zai amsa d'in, saidai da alama yana jiran ya sake masa hannu ne. Sannu sannu Ayam ta fara takowa kusansu saida ta zagaya inda fuskar mutumin ke kallon k'ofa, d'aga kanta tayi kad'an dan ya d'an fita tsayi, ido cikin ido suka dinga kallon juna wanda su kad'ai ne suka fito daga fuskarshi. Irin yanda ta tsareshi da idon nan sai ya samu gabanshi da fad'uwa, kwarjini da tasirin baiwar dake cikin idonta, sun dame na shi sun shanye duk da kuwa shi ya *haifeta*. Waro idonta ta yi a sanyaye sosai cikin murya kamar ta rad'a tace " *Pah*, Abba na, kai ne?" Sai kuma ta k'ank'ance idonta ta ziraro da hawaye tace "Na sani dama, na sani babu ta yanda za ayi a ce mahaifina ne ke son kashe ni, Pah, yau gashi ka nunawa duniya kai masoyina ne, ka nunawa kowa da ke da tarihina zaka iya fansar rayuwata da na ka ran..." Fad'awa tayi kirjinshi tana sake fashewa da kuka, da sauri Juman ta d'ago k'afarta ta nufosu, tana zuwa gabanshi ta tsaya ta sa hannu ta jaye rufin fuskar nan yayi k'asan hab'arshi, da sauri ta rufe bakinta da tafin hannu tsabar mamaki ta zaro ido, kyarma jikinta ya d'auka tana ci gaba da kallon fuskar Musail dake kallonta shi ma idonshi taf da hawaye yana shafa bayan Ayam dake rusa kuka. Da k'yar bakinta ya iua fuska "Kai ne? Mu...s..." Sai kuma ta d'ora hannunta a kan ta tare da ture d'an kwalin kan na ta, hakan ya bayyanar da dogon gashinta bak'i k'irin ya sauka a gadon bayanta, ganin yanda jikinta ke rawa kamar ba zata iya tsayaw da kanta ba sai kawai ya jawota ita ma ta fad'o k'irjinshi ya rik'eta tsam tsam. Umad kallonsu yake bakinshi d'auke da manyan tambayoyi, saidai ba damar furta ko kalma d'aya a yanzun. Kamar wanda aka tsikara Ayam ta d'ago ta kalli fuskar sarki Musail tace "Pah, yar uwata? Ta na ina?" Da sauri shi ma ya dawo hankalinshi ya d'aga Juman daga jikinshi, da azamaya tunkari k'ofa zai fita sai kuma su Adah da tawagarsa suka shigo, duk tsayawa sukayi suna kallonsu, da ido Adah ya musu alama tuni suka zagayesu, cikin dakakkiyar murya Adah yace "Ranka shi dad'e babu abinda ya sameku?" Girgiza kai sarki Musail yayi yace "Lafiya lau muke a nan, ina Zafreen?" Adah ne yace "Na tura dakaru d'akinta, za su kula da ita." Jiniyar motar kwana kwana da ta asibiti da suka ji ne yasa sarki Musail nufa hanyar fita, tareshi Adah yayi yace "A'a sarki na, har yanzu bamu tabbatar da tsabtace gidan nan daga mahara ba, ka jira anan tukuna." Wani jan kallo ya masa yace "Ba ka da hankali, ka san me ye nauyin al'umma kuwa?" Da sauri ya fice a d'akin yana fad'in "Ka zauna nan ka kula min da iyalina." Fita yayi hakan yasa Umad da wasu daga cikin dakarun suka bi bayanshi, Adah kuma nuna wa su Ayam gado yayi yace "Ku zauna." Hannun Juman ta kama da kufin su zauna kamar yanda ya ce, amma sai Juman ta fizge da sauri ta fita a d'akin, da gudu gudu Ayam ta bi ta bayanta haka shi ma Adah ya bisu da sauri tare da dakaru ukun da suka rage tare da shi. Yanda suka samu mutanen dake falon ne yasa suka dakata a nan, lokacin da jami'an kwana kwanan suke shiga da gudu da kayan aikinsu na kashe wuta, lokacin dogaran nan suka fito daga d'akin Zafreen suka tsaya gaban sarki Musail suka ce "Yallab'ai gimbiya Zafreen bata d'akinta." Cikin tashin hankali Musail yace "Kamar ya? Ta na ina?" Girgiza kai d'aya a ciki yayi yace "Ba mu sani ba yallab'ai." A tsawace sosai yace "Maza ku nemo min 'yata, ku nemota duk inda take." Da sauri aka sake bazuwa dan neman Zafreen, inda masu aikin kwana kwana da ke ta aikin kashe wutar nan, motocin asibiti ma da suka zo suna ta shiga da gadon majinyata dan duba ko akwai wanda ya jikkata. Kan kujera Ayam ta zaunar da Juman da ta ga kamar akwai abinda ke damunta saboda yanda take kallon Musail da shi bai ma kula ba, ita ma zaunen tayi ta buga tagumi tana kallon shige da ficen jama'a. Haka suka karad'e gidan wajen neman Zafreen amma babu ita babu dalilinta, da suka sake fad'a masa haka kamar zai yi hauka ya ciro wayarsa zai kira lambarta, cak Umad ya rik'e hannunshi, suna had'a ido ya girgiza masa kai a tausashe yace "Tana nan zuwa, za ta zo, yanzun nan." Da mamaki a fuskar Musail yace "Kamar ya? Ya aka yi ka sani? Ta na ina?" Wani d'an murmushi yayi ya d'auke kan shi yace "Idan ta zo zaka ji." Jim yayi yana kallon sai kuma ya d'auke kai shi ma ya kalli Adah yace "Adah, duk inda Dhurani ya ke ka kawo min shi gabana yanzu yanzun nan." Da sauri Adah ya amsa da "Angama ranka shi dad'e." Duka dakarun suka bi bayanshi hakan yasa falon ya rage daga Musail sai Juman da Ayal sai kuma Umad, amma klwa ya fita wanda yasan ya ji ciwo yana gaban motar asibiti, wasu da aka harba kuma wanda harbin bai zo da ajali ba tuni an d'aukesu zuwa asibiti dan ceton gaggawa. Cikin nutsuwa Umad ya shiga takawa zuwa d'akin baccinshi dan ya samu damar yin sallah subah da lokacinta ya yi, kamar jiran tafiyarshi suke Musail ma ya fita a falon ya nufi b'angaren shi. Ganin su kawai suka rage Ayam ta kalli Juman ta dafata tace "Mah, me yake damunki ne?" Kallon Ayam tayi ta k'ura mata ido, ta jima tana tunani tana kallon fuskarta sai kuma ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi, girgiza kai tayi tace "Ba komai." Jinjina kai Ayam tayi tace "Kin tabbata?" Sake jinjina mata kai tayi alamar e, ita ma jinjina kai tayi tace "Mu je muyi sallah, na ga hasken alfijir ya keto." Jinjina kai Juman tayi kawai ta mik'e, tsoro da fargaban ko har yanzu wani abun zai iya faruwa ya sa Juman ta ce su d'aura alwala a ban d'akin dake falon kusa da gurin cin abinci, a nan sukayi alwalar suka fito, Ayam da kanta ta shiga d'akin Juman ta d'auko musu duk abun buk'ata wajen sallah. Suna kabbara sallarsu motocin jami'an tsaro suka danno cikin gidan su ma, abun ka ga abinda ya shafi mulki da kud'i, sai gidan ya k'ara hautsinewa da hayaniya, inda yan kwana kwanan sukayi nasarar kashe gobarar ba tare da ta yi k'amarin da ta bar madafar ba, saidai d'akunan dake kusa da ita sun fara d'aukar bak'in hayak'i wasu kuma silling d'insu har ya fara kamawa da wutar, cikin sa'a dai babu wanda ya ji rauni daga wutar sai jakadiyar sarki da aka d'auka ranga ranga sakamakon hayak'in daya daketa saboda asim dake gareta. Suna daf d gama sallar Musail ya shigo tare da sipetan (Inspector) jami'in tsaron da ke son yi ma kowa tambayoyi yanda hakan ta faru, inda sauran jami'an ke ta duba gawawwakin mutane suna d'aukarsu hoto da binciken k'wak'waf. *Umad* ma na idar da sallah wayarshi k'arama ya rik'e ga hannu yana kallo, tunane tunane kala daban daban ne suka ziyartarshi a lokacin, yana so ya kira wayar tangarahon dake falo da kowane d'aki dan yayi magana da Mah d'inshi, jiya ta kasheshi da al'ajabi kafin bacci ya d'auke shi, sanda aka kirashi ya ga sarki Wudar ne, amma yana d'agawa ya ji muryar da tun yana shekara shida rabonshi da ita, saida ya jiri ya jefashi kan gado ya fita a hayyacinshi, sai ga shi yana zubar da hawaye abinda ya jima bai yi ba, ita kuma shi kuka aka rasa mai rarrashin wani. Da k'yar Kossam ta rarrashe shi sannan ta tambaye shi inda yake, k'in fad'a mata yayi da fari sai dai kawai ya tabbatar mata yana lafiya, saida ta yi ikrarin zata nemeshi sannan ta je inda ya ke kad'ai ya fad'a mata yana Khazira, abinda ta fad'a masa a lokacin ta kuma kashe waya shi ne yasa shi shiga wani yanayi na daban, sai ya rasame zai yi a lokacin, gashi daya maida kira sai aka k'i d'agawa har ta tsinke. Yana so ya ji da gaske mahaifiyarshi zata iya aikata abinda ta fad'a cewa " *To ni ma zan zo Khazira gobe da safe, za mu had'u da kai sannan mu je masarautar Musail, zan nema ma ka auren 'yarsa Zafeera yarinyar da ta kula da ni, kuma a dalilinta na samu sauk'i yau, na gani a mafarki na Umad, aurenka da ita alkairi ne.*" Abinda ta fad'a kenan ta kashe wayar, ganin tunanin ba zai gyarashi sai ya kai hannunshi zai aika kiran, jin jiniyar motocin jami'an tsaro da ya yi yasa ya mik'e daga kan sallayar ya soka wayar aljihun wandonshi ya fita a d'akin da sauri. Yana k'arasowa falon daidai da zuwan Haman, haka ma sarki Musail ya zauna kan kujera haka ma sipetan yan sandan, su Ayam ma suna sallame sallarsu suka gyara zama, kan kujera Juman ta zauna amma Ayam sai ta gyara zama a k'asa. Jami'in ne ya kallesu a harshen slovaque yace "Ina tayaku jimami sarauniyata." D'an lumshe ido tayi ta gyad'a kai alamar ta amsa, d'orawa yayi da fad'a musu sunanshi da kuma aikinshi sannan ya ci gaba da fad'in "Me zaku iya cewa game da wannan abun da ya faru?" A tare kuma a sanyaye suka girgiza kai alamar ba komai, gyara zamanshi yayi dan su fahimce shi da kyau yace "Am sarauniyata, ina nufin..." D'aga masa hannu Musail yayi fuskarsa a had'e yace "Jami'i, ka dakatar da tambayoyinka har sanda mai laifin ya k'araso, su basu san komai ba game da abinda ya faru." A ladabce jami'in ya kalleshi yace "Ranka shi dad'e, muna so mu tattara bayanan da zamu samu wata makama ne, bincike muke so mu yi game da al'amarin nan, duba da cikin maharan duka dakarun masarauta sun kashesu, guda biyu ne muka samu a raye kuma mugun rauni ne a jikinsu, wanda kafin mu iya ji daga bakinsu zai d'aukemu kwana uku." Shirun da Musail yayi ya tabbatarwa jami'in ya yarje masa kenan ya ci gaba, sake gyara zamanshi yayi cikin kujerar ya juya ya kalli wata jami'a dake sanye da kayan aikinta hannunta rik'e da alk'alami da takarda yace" Ki d'auki duka bayanansu." Jinjina kai tayi tare da kafa alk'alaminta akan takardar tana kallon Juman da Ayam, a tsanake ya fara tambayarsu inda kowace tambaya da wacce ke amsa mi shi ita. Umad na ganin haka ya nufi d'akin Zafreen, yana tura k'ofar ya shiga babu kowa a d'akin sai hasken fitila, d'akin shiru kuma a gyara tsaf babu wani abu da ya same shi, da hanzari ya nufi wajen drowerta ya bud'e, bincikawa ya fara yi yana d'add'aga kayan yana dubawa ko zai samu wata makamar. A k'ank'anin lokaci ya hautsina d'akin da bincikenshi, har k'ark'ashin gado saida ya lek'a amma babu abinda ya samu, mik'ewa yayi ya rik'e k'ugu yana kallon d'akin, tsaki yayi zai fita na jin haushin bai samu komai ba, har zai fita sai kawai wani abu ya zo masa a rai, lokacin daya taka kujerar dake gaban madubi ya lek'a sama, daya sauko ya manta ya rik'e drower sosai ta yanda indai aje ne take to tabbas za ta motsa, amma sai ya tuna batayi motsi ba alamar a kafe take. Da sauri ya dawo tare da dubawa, sai kuma hasashenshi ya bashi daidai, komawa yayo b'angaren shi na hagu ya tura kwabar zuwa dama, jin bata motsa ba yasa ya koma b'angaren dama ya tura zuwa hagu, sai gashi kamar k'ofa mai taya drower ta motsa k'ofa kuma ta bayyana. Murd'a k'ofar yayi ya shiga d'akin mai duhu, wayarshi ya ciro ya kunna fitila da taimakonta ya kunne hasken wurin, hanya ce doguwa da zata kai ka har zuwa fita a bayan garin, wanda kowane d'aki na sarki da iyalansa akwai hakan. A hankali ya fara takawa da san tabbatar tana ta fita ko kuma ta k'ofar gida, ya taka d'aya biyu kenan ya ji k'afarshi ta taka wani wuri kamar dai wanda ya rizga, cak ya tsaya ya maida dubansa k'asa d'aga k'afarsa yayi yana sake kallon wurin da aka d'an rufe da babban carpet, jaye carpet d'in yayi sai gashi tilles d'in da aka jera a wurin d'aya an d'orashi ne kawai. Yana d'aga tilles d'in fari mai fad'i sai ga takardu sun bayyana da k'aramar wayar salula. D'aukar takardun yayi ya fara dubawa, abinda ke ciki y so zautar da tunaninshi, dan haka yayi gaggawar maidawa ya aje sannan ya fito daga d'akin ba tare daya gyara komai a yanda yake ba. Yana zuwa falon ya samesu yanda ya barsu, saidai a yanzun Dhurani na tsaye kan k'afafunshi yana fuskantar Musail, sai kuma Adah na bayan Musail d'in a tsaye, jiki a sab'ule ya k'arasa ya zauna kusa da Juman inda Haman ya ke, muryar Musail ya ji yana fad'in "Nagode jami'i, zaku iya tafiya." Jinjina kai jami'in yayi ya mik'e tare da juyawa suka fita, suna fita Zafreen na bud'o k'ofar d'akinta ta fito rai b'ace, ta fito ne da niyyar yin rashin mutunci ta ji wa ya shigar mata d'aki, dan ta wannan k'ofarf sirrin ta fita sannan ta dawo ta nan, amma ganinsu zaune babu mai magana yasa ta ja tsaki. Tsakin da tayi shi ya dawo da hankalinsu kan ta har suka d'aga kai suka kalleta, ta juya zata koma Musail yace "Zo nan." Tsayawa tayi amma kuma bata juyo ba, a tsawace abinda bai tab'a mata ba yace "Na ce ki zo nan." Sakin k'ofar tayi ta turo baki ta shiga takowa da takalminta k'afa ciki, saida ta zo tsakiya ta tsaya tana yatsina fuska tace "Ga ni, me ye?" A hankali Juman ta kalleta wacce tayi lak'was ta sare da lamarin Musail tace "Zafreen, mahaifinki ne fa, haka ya dace ki amsa masa kiran da ya miki?" Juyowa tayi ta kalleta a wulak'ance tace "Ban saka da ke ba, ki bari na ji me zai fad'a min mana." Rai b'ace Ayam dake zaune k'asan carpet ta mik'e tace "Ke Zafreen, ya kamata kisane zai dinga fitowa daga bakinki, wannan iyayenmu ne, idan ke ba zaki girmama su ba to kar ki raina su a gabana." A hassale kamar dama jira take ta matso kusan Ayam tana fad'in "Me za ki yi? Idan na musu rashin kunyar me za ki yi?" A hassale ita ma tace "Zan yi abinda ba ki yi tsammani ba ne, kuma ki jaraba ki gani." Waina idonta tayi ta ja tsaki tace "Ohh! Wai ni ban san ya aka yi kuka kub'uta ba, sai yaushe ne wai?" Da mamaki Musail yace "Sai yaushe me?" Daga zaune ba tare daya d'aga kai ya kalli kowa ba yace "Sai yaushe ne wai za ku mutu?" Da sauri duk suka kalleshi sai Juman data dafe k'irji tace "Me?" Sannan ya d'aga kan shi ya kalleta yace "Abinda take nufi kenan, sai yaushe ne za ku mutu ta gaji masarautar nan, ita da kuma *mahaifiyarta*." Ido Juman ta zaro haka ma Musail, Adah da kuma Haman da Ayam, da sauri Musail ya mik'e tsaye yana kuma zazzaro ido yace "Me ka ke fad'a ne haka? Kan ka d'aya kuwa?" Gyara zama Umad yayi yana kallon Musail a shek'e cikin isa da k'asaita yace "... *Domin samun lu'u lu'u ko badak'ala tuntub'i wannan lambar 94-98-56-52* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:42 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *38* Gyara zama Umad yayi yana kallon Musail a shek'e cikin isa da k'asaita yace "Ina nufin mahaifiyarta, yallab'ai duk abinda ya faru jiya zuwa yau, yarinyar nan ce Zafreen, kuma ta yi hakane da taimakon wasu da suke da burin ganin bayanka, daga ciki akwai Bukhatir, wannan malamin da kuma tsohuwar hadimarka *Nanna*." Juman dake tsaye kallonshi tayi da mamaki amma kuma ta kasa cewa komai, cikin jin haushi Zafreen ta matso kusan Umad ta nuna shi da yatsa tace" Dama kai ne ka shiga d'akina ka min bincike? Akan wane dalili? Baka da wannan damar malam." Galala ya kalleta tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yace" Ba yau na ke bincike a kan ki Zafreen, tunda na fara aiki na ke bincike akan duk wani dake zagaye da Ayam, sannan na kan dasa ayar tambaya akan duk wani dake da kusanci da ita, na nesa ko na kusa, musamman ma ke da kika sake tabbatar min da zargina ta hanyar shiga makarantar da ta ke." Kamar wacce kanta zai yi bindiga Juman ta dafe kai ta kalli Musail tace" Ban fahimci komai ba, Zafreen dama ba 'yata ba ce?" Wuru wuru ya fara yi da ido yana sinne kai k'asa, a gadarance Umad ya kalleta yace" Sarauniya dan Allah zauna, ni zan fad'a miki komai, dan na gaji da wannan nuk'u nuk'un." Da sauri ta zauna tana zuba masa ido dan abinda take son ji kenan, gyara zamanshi yayi a mutumce ba tare daya kalleta ba yace" Sarauniya, duk abinda zan fad'a miki abinda na ji ne daga bakin wacce abun ya faru da ita, ma'ana tsohuwar hadimarku Nanna Kapoor, ta fad'a min awa d'aya da rabi ne bayan kin haihu ita ma ta fara nak'uda, allurar da aka miki ta bacci ta sa baki samu damar ganin abinda kika haifa ba wanda bai zo a raye ba, a wannan tsakanin ita kuma ta haife abinda ke cikinta wanda sarki Musail shi ne musababbin shi, k'arfin mulkinshi ya nuna mata tare da mata alk'awarin kud'ad'e masu yawa idan har ta ba shi yarinyar da ta haifa, amma sai tayi taurin kai saboda soyayyar d'a da uwa, to fa hakan ne yasa aka koreta a wulak'ance sannan ya raba da yarinyar wacce aka baki a matsayin yar da kika haifa." Kallon fuskarta yayi cike da ladabi yace" Amma magana ta gaskiya ke namiji ma kika haifa ba mace ba." Yanda ta saki baki ta saki ido tana kallonshi, hawaye kawai ke malala a idonta, juyawa tayi ta kalli Musail tace" Da gaske ne abinda ya fad'a?" Lak'was jikinsa yayi tare da komawa ya zauna kan kujera kanshi k'asa yace" Hakane, gaskiya ne abinda ya fad'a." Fashewa tayi da kuka tace" To amma me yasa? Me yasa ka rabata da 'yar da ta sha wahala ta haifa? Ka san rad'ad'in da uwa take ji idan ta rasa abinda ta haifa?" A sanyaye Umad ya kalleta yace" Saboda soyayyarki ne sarauniya, a duk mutanen da na zanta da su abu d'aya suke fad'a min, sarki yana son sarauniyarsa fiye da komai." Cikin k'unar zuci da tsana Zafreen ta fara kuka tana kallon Musail tace" Kai mugu ne azzalumi, ka rabani da mahaifiyata saboda farin cikin matarka, kun banzatar da ni kun wulak'antani saboda son zuciyarku, ba zan tab'a yafe muku ba." K'ank'ance ido Musail yayi yana kallonta yace" Kenan saboda haka kike son kasheni?" A harzuk'e kamar zata kai masa duka tace" Ba ma kai kad'ai ba, har da su duka iyalinka, dukanku na so kashewa, kuma sai hakan ya tabbata." A hassale Musail ma ya mik'e tsaye yace" Saboda me za ki had'a da su, ni ne na miki laifi, me yasa su zasu fuskanci hukuncin?" Cikin fitar hayyaci tace" Saboda dalilinsu ka wulak'anta mahaifiyata, a da ina ganin kulawarka, amma daga ranar da aka haifi wannan..." Ta fad'a tana nuna Ayam sannan ta d'ora da" Sai ka canza min, na d'auka kana son samunta ne dan ka cutar da ita, shiyasa har na yi yunk'urin taimaka maka, amma kwanaki kad'an da suka wuce na fahimci ba gaskiya ba ne, hasalima na gano kai ne ka ke bata kariya da kulawa." Kallon tuhuma da neman k'arin bayani ya mata, hakan yasa ta yin murmushin yak'e tace" E, na gano komai ai, ka tuna *Ahmad*?" Rarraba ido yayi yana kallon k'asa, wata dariyar ta kuma yi tana fad'in" E mana, Ahmad ba, wanda yake isar da sak'onka a wajen su Habbee, na ganshi kuma ya fad'a min komai dake faruwa." Dafe k'irji Juman tayi ta mik'e tsaye tace" Me kike fad'a haka Zafreen? Me ya sako su Habbee a cikin wannan maganar?" Wani kallo ta mata tace" Saboda ba ke kad'ai su ke wa aiki ba, har da shi ma Musail d'in." Da sauri Juman ta kalleshi tace" Da gaske hakane?" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace" Hakane Juman, lokacin da aka nemi Zafeera aka rasa hankali ya tashi matuk'a, dan yanda na shirya bata kariya ban shirya da b'atanta ba, sai nayi tunanin masu nemanta ne suka sameta, a kwana biyu tak aka nemo min inda su Habbee suke da yarinyata, dan na bata kariyae data dace haka na sa Adah ya kashe abokan tafiyarsa su uku sannan ya dawo min da labarin Ayam tana cikin k'oshin lafiya, daga lokacin na canza musu gari daga k'auye zuwa Larhjadin, wanda mak'iya da dama tunaninsu bai basu wanda suka sace Ayam za ta zauna gari kusa da Khazira ba, da wannan na samu nasarar saka ido a kan duk wani motsin Ayam, sannan na ke sa wa ana k'ara bincika min haka lokaci zuwa lokaci." Wasu hawaye Juman ta sako masu zafin gaske tace " *Abban Ayam* kasan da haka me ya sa baka tab'a fad'a min ba ko sau d'aya? Me ya sa baka fad'a min kai ma so ka ke ka ceci rayuwar 'yarmu ba?" Girgiza mata kai yayi yana matso yar k'wallar data taru a kurmin idonshi yace "Ta ya zan fad'a miki a lokacin ki yarda Juman? Ba kya saurarata sannan kin tsaneni, bugu da k'ari kina kallona a matsayin wanda ke son kashe 'yarmu." Numfashi ya sauke a nutse yana kallon k'asa yace "Bayan Dhurani ya sanar da ke fassarar mafarkinki, ni ma ya had'u da ni ya sanar da ni, saidai ya k'ara da fad'in wannan yarinyar da za'a haifa za ta zama tashin hankalina ce, ita ce mafarin rugujewata da kawo k'arshen mulkina, sannan ya fad'a min tabbas ita ce za ta zama silar mutuwa sannan ta kawo k'arshen mulkin zalincina, na ji ba dad'i sosai a lokacin sannan na shiga firgici na abubuwan daya fad'a min, sannu sannu na fara shiga damuwa na abinda ya fad'a min, haka na fara rasa nutsuwata saboda tunanin mutuwata, wata rana da yamma sai kawai na je fadar abun bauta Ghira dan na samu mafita a wajen Dhurani, a wannan lokacin ne na san komai na kuma fahimci komai, na samu malami Dhurani da waziri Khatar da biyu daga cikin fadawa na suna tattaunawa a kai na, kasancewata sarki ya sa masu gadin k'ofar kai tsaye suka bud'e min, shiyasa ba su tunanin wani zai iya shigo musu ba tare da izininsu ba, abinda na ji ya gigita ni, na shiga tsananin firgicin da ya fi wanda na zo da shi." Numfasawa yayi sosai sannan ya d'ago ya kalli Juman dake ta shashek'ar kuka Ayam na durkushe gabanta tana rarrashi yace" A nan na ji duk shirin da suke na ganin bayana ne, suna shirin kashe ni dan su maye kujerar mulki na, sannan su d'auki fansa akan laifin da ni ban san ya faru ba sai a tarihi, amma sai gashi da taimakonsu suna tunzurani ina aikata abinda al'ummata zasu k'i ni su kuma kirani da azzalumin sarki, juyawa na yi a wannan lokacin na koma saboda kaina daya fara sarawa, saboda abinda na ji malam Dhurani ya fad'a, cewa ya fad'a min k'arya akan yar cikina da za'a haifa, tabbas baiwarta gaskiya ce, saidai batu na zata kasheni ta ruguza mulkina k'arya ne, shirinshi ne kawai saboda yana so na kasheta da hannu na dan kar ta kawo masa targand'a a cikin lamuransu, na jima da jimamin wannan lamarin a rayuwata, daga baya kuma bayan tattaunawa da zuciyata da kuma shawarar da amintacce na wato Adah ya bani, sai muka fara buga wasar daidai da na su, inda a zahiri na ke nuna musu na tsani Zafeera kuma kasheta shine burin rayuwata, amma a bad'ini ina kulawa da matata da kuma abinda yake cikinta, wanda wasu lokuta da gangan na ke fad'in magana marar dad'i duk dan tunanin abinda zai je ya dawo." Sosai Juman ke kuka haka ma Ayam data girgiza kanta tana hawaye tace" Ban tab'a yarda ba har zuciyata cewa wai mahaifina zai kashe ni, duk da ban san shi ba kuma ban tab'a ganinshi ba, amma dai na ji a zuciyata ban gamsu ba, ashe duk makirci ne, kuma aka yi sa'a ya mamaye duniya har kowa ya yarda da hakan." Yanda jikin Dhurani ke rawa ne yasa shi yin zaune k'asa d'abas kamar an hankad'ashi, zufa yake sosai yana ta zazzare ido, cikin magiya da rawar murya yace" Ran...ranka shi...dad'e, ka min...rai, na tuna." Girgiza kai Musail yayi yace" Ba na kiraka nan dan na yafe maka ba ne, dole ka fuskanci mutuwa Dhurani, zunubinka babba ne." Kallon Zafreen yayi yace" Abinda ya faru tsakani na da Nanna ba abu bane da kowa ya sani, ta ya kika san labarin mahaifiyarki?" Kafin ta yi magana Umad dake k'are mata kallo a lalace yace" Dhurani ne, gashi nan gabanka, shi ne ya busawa labarin rai, saboda yayi anfani da ita ta yanda zata zama barazana a gareka, kuma yayi nasarar samun haka tunda har yanzu burinta bai wuce ta kasheku ba sannan ta maye abinda take ganin na ta ne." A hankali Musail ya kuma kallon Dhurani yana jinjina kai, murmushin yak'e yayi yace" Kun k'irk'iri labari, sannan kun aiwatar da wasan, ku kuka samar wa da kowane jarumi rawar da zai taka, sannan a bayan fage ku kuke taka taku rawar." Cikin takaici da hargagi Juman ta nunashi da yatsa tace" Amma Dhurani Allah ya isa tsakani na da kai, ba zan tab'a yafe maka ba bak'in munafiki, dama abinda ka shirya mana kenan? Ka tunzura mijina da labarinka na k'arya hakan yasa na dinga jin haushinsa ina wasan b'uya tsakani na da shi." Jan majina tayi ta kalli Musail tace" Indai har abubuwan da suka faru sa saninka, kenan ka san da zuwana a lokacin da kuke tattaunawa kan yanda zaku kashe Zafeera bayan na haifeta?" A hankali ya gyad'a mata kai alamar e tare da fad'in" Ina sane na tura jakadiya ta turo min ke, saida na tabbatar na ji takon tafiyarku sannan na fara magana tsakanina da Dhurani, na kusan kinji saboda yanda kika canza min daga lokacin, saidai ban san me kike shiryawa ba har sai ranar da na ji daga su Habbee cewa ke kika saka su." A hankali Umad ya kalli Musail d'in yace" Shiyasa ka san komai kenan? Hatta da aurena da... Ayam?" K'uri kowa ya masa da ido yana kallo kamar wanda ya fad'i wani mugun abu ban da Musail kawai, shi ma Umad bai yarda ya kalli kowa ba sai dakewa da yayi ya buga fuska, a sauk'ak'e Musail ya jinjina masa kai alamar e, sannan ya gyara zamansa ya kalli Adah, nuna masa Dhurani yayi yace "Ka kai min shi kurkukun Sabah." Da sauri Dhurani ya mik'e yana fad'in "Ba zai yiwu na Musail, akan me zaka k'ask'anta ni haka? Ka sani wasa kake da wuta kuma zata k'ona ka." A hassale ya kalleshi yace "Na yarda Dhurani, amma dole ka fuskanci k'ask'anci a rayuwarka kafin ka mutu." Cikin fitar hayyaci ya fara fizge fizge saboda rik'eshi da Adah yayi yana fad'in "Musail sai na kasheka, sai na kasheka zan ji sauk'i a cikin zuciyata, kamar yanda babanka ya kashe min kakana, dole kai ma ka mutu mutuwar wulak'anci." Da kallo suka bishi har Adah da wasu dogaran suka d'auki suka fice da shi, da mamaki Ayam ta kalli Musail tace" Pah, me yake magana a kai ne wai? Wacz d'aukar fansa?" A tsaanake ya kalleta yace" Mahaifina ya kashe kakansa lokacin da kakanshi Allah ya masa baiwa kwatankwacin ta ki wacce ake alfahari da hakan, saidai kakan na shi yayi anfani da haka ta hanya marar kyau, a wasu k'auyukan talakawa na fama da matsalar ruwa, mahaifina ya rok'i alfarmarsa ya bayar da wani filinsa da bincike ya tabbatar za'a samu ruwan da gaba d'aya gari zai sha ya wadatu, amma ya k'i a lokacin, saida mahaifina ya siyi filin da manyan kud'ad'en da suka wuce k'a'ida, sun yi hakan a sirrance kamar yanda mahaifina ya buk'ata, sannan ya aje takardun filin na k'warai a hannunshi bayan sun saka hannu, hakan yasa har yanzu mutane ke ganin kamar kakan Dhurani shi ne ya zamar musu silar samuwan wannan ruwan, inda suka girmamashi suka d'aukakashi ya zama waliyinsu, hakan da ya faru shi ne mafarin matsalar da ta sa mahaifina ya kashe shi, saboda mahaifina yana da adalci ba kamar ni ba da zalinci ya fi yawa a mulkina." Numfasawa yayi sannan ya cigaba da fad'in" Lokacin da mutane suke girmama suke zuwa da matsalarsu dan ya magance musu, lokacin ne k'anwar mahaifina ita ma ta je dan ya mata addu'a a gaban bak'in gunkin da suke bautawa dan ta samu miji tayi aure, saboda tun bayan mutuwar mijinta tana zaune gida babu aure, saidai madadin ya mata addu'a sai ya mata fyad'e, sannan ya tsorata da fad'in idan ta fad'a abun bauta zai la'anceta ba kuma zata ga biyan buk'ata ba, k'anwar mahaifina ba lusarar mace ba ce, dan haka ta tureshi daga jikinta sannan ta tabbatar masa zata fad'a dan mahaifina ya k'watar mata 'yancinta, jin haka sai ya tsorata ya kamata ya kuma shak'e wuyanta, bai saketa ba saida ya ga ta daina shurawa kad'ai alamar ranta ya bar gangar jikinta, da taimakon yaronsa na hannun damansa suka binneta a gonar wani manomi, saidai da ubangiji ya tashi kawo k'arshenshi, a sauk'ak'e aka tono gawarta saboda mammalakin gonar da ya ga abinda bai tab'a gani ba kuma ba shi yayi ba, bayan an tonone aka ga gawarta wacce lokacin hankalin masarauta ya tashi ana ta nemanta, wannan dalilin ne ya hassala mahaifina ya sa jami'ai a cikin lamarin, to fa shine da aka gano gaskiyar maganar ta hanyar amintaccen yaronsa kawai mahaifina ya cire masa kai ba tare daya jira hukuma ta d'auki matakin daya dace a kan shi ba." Jiki na kakkarwa Juman ta kalleshi tace" Ba wannan ba, maganar aure... Ayam da Umad...me hakan yake nufi?" Gyara zama ya kuma yi wanda Ayam ta kalli Umad ba ko k'yabtawa tana jira ta ji me mahifinta zai fad'a, cikin nutsuwa Musail yace" Tun daga sanda ya fara shigowa rayuwarki na samu labari daga gurin masu bibiyarki ba dare ba rana, da kallon fuskarshi a allon wayata da aka turo min na san ko wanene saboda kama da yake da sarauniyar Giobarh da kuma yayanshi Urab wanda na kasa yayin neman auren mahaifiyarki, bayanan da suka biyo bayan hoton su suka tabbatar min da kokonto na, bincike na sa aka min sosai a kan ka har saida na san abubuwa uku game da kai masu mahimmancin da ba kowa ya sani a ge da kai ba, na farko shi ne musulunta da ka yi iyayenka basu sani ba, na biyu kuma shi ne aikin sirri da kake da hukunmar binciken miyagun laifuka, na uku kuma shi ne k'udirinka akan Ayam, da haka nasan ranar da ka je gidan su Habbee ka kuma nemi aurenta a wajensu." Da sauri Ayam tace" Pah ban gane ba? Ya nemi aurena kamar ya?" Jinjina mata kai yayi yace" Hakane, ya nemi aurenki a wajensu, duk da ba amincewarki a ciki, amma ni na yarda da shi saboda mutumin kirki ne, zai kula da ke Ayam." Kallon Umad tayi d kanshi ke sadde yana wasa da yatsun hannunshi, a sanyaye ta furta" Ta ya haka ma zata faru? Bayan babu soyayya a tsakaninmu." Murmusawa Musail yayi yace" Zaku saba Ayam, da sannu za ki so shi, amma dai ba zan miki dole ki zauna da shi ba, dan na fi kowa sanin illar haka, akwai zuciyar da kyautatawa bata sa ta tausasa." Had'a ido sukayi da Juman da sauri tayi k'asa da na ta tana mai jin kunyarshi, muryar Zafreen suka ji dake tsaye tace" Duk wannan ba shi zai sa na saurara ba, ka rabani da wacce ta haife ni, sannan ita ma ta rabani da wanda na ke so." Ta k'arashe tana duban Ayam da ita ma ta kalleta a lokacin haka a Juman, da mamaki Juman tace" Wa ye kike sl da ta rabaki da shi haka?" Nuna Umad tayi tace" Wannan ne." Kallon Umad sukayi da yayi kamar bai san suna yi ba, Juman ce tace" Amma ai ita ma bata sani ba, ki bi komai a hankali mana Zaf..." D'aga mata hannu tayi tace" Kinga ni ba da ke nake ba, hak'uri na hak'ura da shi dole, tunda na ji ya rabata da budurcinta daren shekaran jiya, amma ku sani wallahi ba zan rasa abunda nake so ba ni kad'ai, dole dukkanmu mu rasa wani abu da muke so." Mik'ewa Juman tayi tana kallonta tace" Kamar ya? Me kike nufi?" Tab'e baki tayi tace" Ina nufin dole na kashe yarinyar nan sannan na kashe shi shi ma.." Ta k'arashe da nuna Musail, da sauri Ayam ta mik'e tsaye tana fad'in" Idan ina raye ba zaki kashe mahaifina ba, idan kuma ni zaki kasheni saboda Umad ne, to ki d'aukeshi na bar miki, ni ba wani damuna yayi ba..." Ta k'arashe maganar da kallon gefen da Umad yake, duk da kansa a k'asa yake amma saida ya dakata da matsa hannayenshi da yake yana taune leb'ensa yana nanata kalmar *ba damuna yayi ba*. A hankali Musail ya mik'e tsaye ya tako zuwa gaban Zafreen ya kalleta yace "... *Ki garzayo ki biya na ki.* *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:43 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *39* A hankali Musail ya mik'e tsaye ya tako zuwa gaban Zafreen ya kalleta yace "Na d'auka na raineki da kulawa, ki kashe ni ba damuwa, amma 'yata ki rabu da ita ta rayu cikin farin ciki." Tsakiyar idonsa ta kalla tace "Ni ba' yar ka ba ce? Idan ka san ba ka so na me ya sa ka yi cikina?" D'auke idonshi yayi daga kanta yace "Ina so na ji daga bakinki, shin da hannunki a wannan harin ko babu?" A hassale tace "Da hannu na a ciki, kuma da taimakon wad'anda ba ka tsammani na zartar da hakan, d'ayan ka kama shi yanzu sai kuma ni da ke gabanka, amma na biyun ina tabbatar maka zai ga bayankkkka..." Duk da ta kai k'arshen kalmar amma marin daya mata ya gigita ta sosai, k'ara ta saki ta da durk'ushewa tana dafe kunci, da sauri Ayam da ta fi kusa da ita ta sunkuya ta kamata sannan ta kalli Musail dake huci tace" Pah, ka yi hak'uri mana." Tallabo fuskar Zafreen tayi dan ta ga ko bata ji ciwo ba, da k'arfi ta fizge fuskarta ta mik'e a hassale ta kalleshi sannan tace" Ko za ka kasheni ba zan canza k'udiri na a kan ka ba, mugu." Juyawa tayi da sauri zata koma d'akinta sai kuma ta tsaya cak sakamakon fadawan da suka shigo da gudu gudu suka jeru a bakin k'ofar, daga ganin dakarun zaka fahimci daga masarautar da suke, Juman da ta fi kowa gane su wanene tuni ta mik'e tsaye tana zazzaro ido tana kallonsu. Babban dogarin cikinsu ne ya fara shigowa hannunshi rik'e da bindiga dan bada tsaro, a bayanshi tsofaffin suka shigo, cikin nutsuwa da shan k'amshi suke takon, saidai fuskarsu ta nuna alamun tashin hankali da jimami, rik'e suke da hannun juna cikin shiga ta alfarma, fararen kaya masu ado kamar ba gobe, inda Bilkees ke sanye da wani babban lullub'i har yana jan k'asa. Saman fuskokin da suka sauke dubansu yasa fuskarsu ta canza daga alhinin nan zuwa murmushi dake bayyanar da tsantsar farin ciki da kuma annuri. Umad da Haman da shi dai tunda ake tattaunawar nan bai ce uffan ba ne suka mik'e a tare saboda girmamawa, Juman na had'a ido da iyayenta wani dad'i ya lullub'eta, da gudu ba tare da jin ta manyanta ba ta isa garesu, tana zuwa ta sake k'urawa fuskokinsu ido, ba ta jira komai ba ta fad'a jikin mahaifiyarta wacce ita ma k'walla suka fara gangaro mata. Cikin kuka mai tsananin gaske Juman ta furta "Mah, na yi kewarku sosai." Cikin kuka ita ma ta amsa da "Ni ma haka Juman, kin girma sosai." K'am k'am suke mak'ale da juna hakan yasa sarki Abdallah rumgume su gaba d'aya yace "Ni ne ba kwa k'auna kenan?" D'an d'agowa sukayi suna had'a ido ta fad'a jikinshi tana sake fashewa da wani kukan, daddab'ata ya dinga yi yana share k'walar farin ciki shi ma yana fad'in "Shikenan 'yata, ya isa haka, kukan ya isa haka." Da sauri Ayam ma ta matso ta rumgume Bilkees, sun jima haka kafin ta d'ago tana murmushi saboda abinda sarki Abdallah ke fad'i cewa "Mik'o min matata nan na rumgume." Fad'awa tayi jikinshi tayi luf abinta kamar za ta yi bacci. Musail da ya gama tsurewa a tsaye kallonsu kawai yake, mamakin yanda suka musu dirar mikiyar nan ya ke, wad'anda basu tab'a zuwa ba su ne yau suka zo? Zuwan ma kuma da wasu irin dakaru kamar ma su jiran ya k'i, ga shi sun musu wani irin zuwa da sassafe haka, gashi tashin hankalin da suka kwana dashi har yanzu gidan a hargitse yake, hadimai sun bazu ta ko ina ana ta gyaran gidan saboda kamewar da yayi, wannan hayaniyar ce ma da nisa a cikin abinda suke tattaunawa ya hanasu jin shigowar motocinsu sai kawai dirowar dakarun nan. A hankali ya shiga takawa k'afafunsu na neman bijire masa haka dai ya kai kanshi gabansu ya tsaya, a ladabce abinda bai tab'a yi ba, hasalima bai gansu ba bare yayi sai gashi ya rusuna yana fad'in "Barkanku da zuwa masarautar Khazira." Sarauniya Bilkees da sarki Abdallah tare suka kalli juna, sai kuma Juman data kallesu ita ma tana mamakin abinda yayi, cike da dauriya sarki Abdallah ya gyad'a kai yana murmushi sannan yace "Muna godiya da wannan karamcin." D'an juyawa yayi ya kalli babban bafadenshi ya masa alama da ido, juyawa yayi ya umarci sauran dakarun da su fice, suna fita kuma Bukhatir ya shigo tare da Zeyfi su ma cikin shiga ta daraja, sannan mahaifiyarshi ta biyo bayansu da sauran yan uwa a k'alla goma. Ido da Zafreen ta d'ora akan Bukhatir yasa ta waro ido tana kallonshi, satar kallon mutanen dake wajen tayi sannan ta kuma kallonshi bakinta d'auke da tambayoyi bila adadin. Farin cikin daya kacame iyalin a lokacin na murnar ganin juna bayan shekaru masu tsayi, shi ya d'auke hankalinsu har Zafreen ta matsa kusa da Bukhatir daga bayanshi cikin rad'a tace "Me ka ke yi nan a daidai wannan lokacin? Baka san abubuwa sun lalace ba ne?" Saida ya saci kallon mutanen ya ga babu mai kallonshi sannan yace "Na sani, amma dole ce ta sa na zo, sarki ya umarce ni ba yanda zan yi." Tsaki tayi cikin jin haushi tace "Kashh!" Juyawa tayi ta nufi d'akinta ranta a b'ace sosai, da kallo Musail ya bita tare da k'ank'ance idonshi sannan ya saci kallon Bukhatir, k'wafa yayi a sanyaye tare da murmushin mugunta wanda shi kad'ai yasan ma'anarsa. Da tsantsar farin ciki Juman ta kuma kallonsu da kyau tace "Mah, ya aka yi kuka zo nan haka ba sanarwa? Ya kuma na ganku gaba d'aya?" Yar dariya tayi ta kalli Ayam dake gefenta ta dafa kanta tace "Shagalin bikin jikata muka zo." Da sauri suka shiga kallon kallo, duba da su ma akwai magana a bakinsu yasa Musail fad'in "Ranka shi dad'e, ina ga mu je b'angarena mu zauna, dan nan ana gyarawa, wata yar hatsaniya ce ta faru da tsakiyar dare." Cike da dattako sarki Abdallah yace "Mun samu labarin komai da ya faru, shiyasa ma muka taho da wuri haka dan tabbatar da kuna cikin k'oshin lafiya." Galala Musail ya kalleshi sanda yayi magana yana mamakin furucin shi, hakan na nufin shi ma yana da nashi d'an lek'en asirin a cikin fadarsa? Adah ne ya fara wucewa gaba sannan Musail suka fita a falon, cikin nutsuwa da kallon juna har suka shiga falon na shi, wanda babu wanda bai kalleshi ba saboda had'uwarsa da tsaruwa, wuri suka samu duk suka zauna, inda Ayam ke zaune tsakanin sarki Abdallah da sarauniya Bilkees akan kujera mai zaman mutum uku. Juman kuma na zauna kujerar mutum biyu ita da Musail sai Adah dake tsaye a bayansu, sai Umad da Haman da Bukhatir suna k'asa kan carpet da sauran yan uwan Bukhatir maza da mata. Juman dake kallon iyayen na ta ne ta fara cewa "Pah, ya aka yi kuka san abinda ke faruwa?" Kallonta Ayam tayi tace "Ba wannan ba Mah, ya aka yi suka kan da maganar auren da ake fad'a a kai na?" Hararanta Juman tayi tace "Kin manta kin bani labarin Umad ya kaiki wajensu? To ta ya ba zasu sani ba." Turo baki tayi ta d'ora kanta a kafad'ar sarki Abdallah, a tausashe ya saki murmushi cikin kamala ya fara magana a nutse "Na samu labarin abinda ke faruwa ne a tv a labarai safiya, ai abinda ya faru ya fi k'arfin yan jaridu da gwamnati suyi shiru, maganar aurenki kuma ai tun ranar da ku ka je ya fad'a mana." Jinjina kai duk sukayi sai Ayam data turo baki ta sake langab'ewa jikin sarki tace" Grand Pah, ni dai ku fad'a masa ban yarda ba, kawai ya auri yar uwata Zafreen, dan ita ce take son shi ba ni ba." Yar dariya sarki yayi tare da maida hankalinshi kan Juman dake fad'in" Baki isa ba yarinya, tunda mahaifinki ma ya amince to an wuce wajen." Yanda Bukhatir ke ta rarraba ido yana kallonsu ne yasa sarki Abdallah fad'in" Yawwa Bukhatir, ka san dalilin da ya sa tafiyar nan na ce sai da kai?" A ladabce ya kalleshi cike da son b'oye damuwarsa yace" A'a ranka shi dad'e." A nutse yace" Na kiraka ne saboda ina so ka ganewa idonka, sannan ka rarrashi zuciyarka tayi hak'uri da abinda take so, sannan ka tuna da mahallicinka wanda shi ya k'addara faruwar hakan." D'agowa yayi ya kalleshi da kyau yana son k'arin bayani, a hankali sarki Abdallah ya jinjina masa kai alamar e sannan yace" Na san komai Bukhatir, na san dayawa daga abinda ka ke b'oyewa, tsananin son Ayam da ka ke da burin ganin ka mallaketa, idan da Allah ya rubuta matarka ce tabbas da mun yi farin ciki da haka, saidai Allah bai rubuta za ta zama ta ka ba, ka yi hak'uri da hakan ka d'aukeshi a matsayin k'addararka." Nunfasawa yayi sannan yace" Sai kuma soyayyar da ka ke wa kujerata, Bukhatir kai ne magajin wannan kujerar tun fil'azal, duba da ban da magaji ko magajiya, ina so in shaida maka daga yanzu da nake maganar nan na bar maka sarautar k'asar Egypt, ka zama sarki daga yau nad'aka kawai ya rage, saidai kafin hakan ta kasance sai ka min wani alk'awari guda d'aya a gaban duka mutanen dake wajen nan." Sadda kai Bukhatir yayi yana jin gaba d'aya tunaninsa ya tsaya cak, ya rasa da wanne zai ji, shin zai yi bak'in ciki da rashin Ayam ne? Ko kuma murnar samun wannan kujera da duk abinda yake dan ita yake yi? Duba da dama yana son samun Ayam dan ya yi alfahari da shi ya samu zab'abb'iyar, sannan ya buga k'irji a gaban sarki Musail yayin da zai nunashi da yatsa yace ya auri 'yarsa da yake burin kashewa, sannan ya bata matakkan tsaro su zuba ido har su ga lokacin da' yar zata kassara uban. Mamakin kalaman sarki Abdallah yasa Juman kallonshi da mamaki tace "Pah, wai dama Bukhatir Ayam yake so?" D'an murmushi kawai yayi bai ce komai ba, maida hankalinshi yayi ga Bukhatir yace "Ba ka ce komai ba Bukhatir?" Sake d'aga kanshi yayi a sanyaye yace "Nagode ranka shi dad'e, wannan karamci a gareni, Allah dad'a girma da lafiya." A hankali Umad ya kalli sarki Abdallah yace "Ranka shi dad'e, kafin ya d'auki wannan alk'awarin zan so sanin wani abu daga gareshi." Lumshe masa ido yayi dake nuna ba damuwa, kallon ju'a sukayi wanda hakan yasa Bukhatir had'e fuska yana jin tsanar Umad d'in har k'asan zuciyarshi, Umad kam ko a jikinshi duk da mugun kallon da yake masa, cike da dagiya da rashin tsoro yace" Bayan duk abubuwan da ka yi zamu iya cewa an yafe maka, amma laifin da yanzun kuka aikata babba ne, wanda yayi sanadiyar jikkatar wasu mutanen, tambayar a nan ita ce, shin ka yi hakane dan ka taimaki Zafreen ta cimma burinta? Ko kuma dai yarjejeniya ce a tsakaninku ta kowa zai cika burinsa dalilin hakan?" Kallon Umad duka mutanen wurin sukeyi sai Bukhatir dake neman rikicewa a zaunen nan da yake, wuk'il wuk'il yake da ido yana son satar kallon mutanen wurin amma ya kasa, cike da borin kunya yace" Me kake fad'a ne haka? Ban san akan me kake magana ba." Wani murmushin rainin hankali Umad yayi ya d'auke kansa bai ce uffan ba, sarki Musail ne ya kalleshi yace" Umad, me kake son fad'a ne?" Kallon Musail d'in yayi yace" Yallab'ai, kwana biyun da mukayi a nan na saka ido akan Zafreen sosai, hakan yasa na gano wata alak'a data k'ullu tsakaninsu su biyun nan, farmakin da aka kai wa Ayam a d'akinta wanda aka yanketa ma Zafreen ce ta yi, sannan harin da aka kawo yau ma, Dhurani da Zafreen da kuma shi Bukhatir ne suka d'auki nauyin maharan." Babu wanda bai kalli Bukhatir da mamaki da kuma jijjiga ba, inda mahaifiyarshi ta rabka salati tana fashewa da kuka, dafe k'irjinta tayi tana fad'in" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Bukhatir wace riba za ka ci a cikin aikata hakan?" Wuru wuru ya fara da ido yace" Nifa ban san akan me yake magana ba, ta ya ma zan iya aikata dan Allah?" Shiru falon ya d'auka sai kallonshi kawai suke, a saib'ance Umad ya kalli Haman dake gefenshi, kallon da ya masa yasa gaba d'aya Haman ya ji fitsari na neman kubto masa ya zubo, hakan yasa ya bi Umad da kallo irin na ka taimake ni, idan ka san wani abu kar kayi magana a nan ka jira mu bar nan sannan. A hankali Umad ya girgiza kan shi sannan ya kalli Zeyfi ita ma a daidai lokacin shi take kallo saboda yanda ta kula yana kallon Haman, suna had'a ido tayi k'asa da na ta tana jujjuya jakarta dake gabanta, sai kuma ya juya ya kalli Haman yace "Da ka fad'a ita d'in yayarka ce ai, ba wani abu ba ne dan kana son taimakon 'yar uwar ka, ni kaina duk abinda na ke saboda d'an uwa na nake yi." Kallonsu aka fara yi suma har Bukhatir da ya kalli Umad yace "Waye d'an uwan na ta?" Banza Umad ya masa dan shi ma haushinsa yake ji saboda soyayyar da yake ma Ayam, maida kallonshi yayi ga Zeyfi yace "Ke me ye had'inki da wannan?" Cikin turo baki gaba tana sissine kai tace "D'an uwa na ne." Da sauri ya kalli Haman sannan ya kalli mahaifiyarshi yace "Mah, dama tana da d'an uwa da ban sani ba?" Tab'e baki mahaifiyarshi tayi tace "Ban sani ba nima sai yanzu, ai ba ni na had'a aurenka da ita ba, mahifinka ne kuma baya raye." Da mamaki yace "Amma ai Pah ya fad'a min kafin ya rasu cewa na rik'eta amana ni kad'aita gareta tunda iyayenta suka rasu." A sanyaye Zeyfi tace "Ya fad'a maka hakane saboda haka d'in ne, Haman tun yana yaro ya bar gida saboda basa shiri da mahaifinmu, kullum cikin fad'a suke akan sab'anin ra'ayi, dan haka wata rana ya ce zai bar gida su manta da shi, cikin hushi mahaifinmu ya ce ya fi ruwa gudu, sannan shi ma ya sa a ranshi kamar bai tab'a haihuwar d'a namiji ba, wannan dalilin yasa nake ni kad'aita, saidai ni ban yada zumuncin dake tsakani na da d'an uwana ba, muna had'uwa a kai a kai sannan muna waya ma, saidai mahaifinmu ne sam ya k'i hak'ura, amma mahaifiyarmu ma sukan gaisa da shi ta waya, har ta rasu tana binsa da addu'ar alkairi, sab'anin mahaifinmu da ya rasu yana hushi da shi." Musail ne ya kalli Umad da kulawa yace" ka yi maganar d'an uwanka, Umad fansa kake son d'auka har yanzu?" D'aga ido yayi ya kalleshi yace" A gaskiya yallab'ai na shiga aikin bincike ne saboda kawai na samu hujjar da zan gurfanar da kai a gaban kotu na kashe min d'an uwana, amma yanzu...da na fara sabawa da Ayam kafin na san wacece ita, bana jin zan iya yin wani abu na k'i ko wanda zai cutar da kai, sai dai kawai ina so 'a san dalilin da ya sa ka kashe min d'an uwana, shin saboda ka auri matar da take son sa ne?" Girgiza kai Musail yayi yace" Umad ba ni na kashe maka d' an uwa ba, hasalima ban da hannu a cikin kashe shi, kawai tarkon mak'iya na fad'a kuma sun yi nasara." Da mamaki duk suke kallon kafin sarki Abdallah yace" Kana so ka ce duk hatsaniyar da aka tayar a ranar baka da hannu a ciki?" Girgiza kai yayi ya kalli Umad yace" Ka tuna labarin dana fara baku d'azu? Sanda na je fada wajen Dhurani, to ai bayan maganar Zafeera na samu suna tabttaunawa kan yanda suka tsara wannan farmakin, lokacin da na buk'aci auren Juman ban samu ba na shiga cikin damuwa da b'acin rai, hakan yasa na shawarci Dhurani da Khatar, nan suka zugani suna nuna min bai kamata na nemi wani abu na rasa ba, sai Khatar ya ce na bar komai a hannunsa zai d'auki mataki, ba tare da sanin abinda zai aikata ba kawai na bashi umarnin yayi duk abinda zai sa Juman ta zama ta wa, to a nan ne suka tashi hatsaniya wanda a cikin wannan hatsaniyar suka yi nasarar kashe Urab, kuma a yanda na ji suna fad'a a ranar Khatar ya y hakan ne saboda cika burin wata masoyiyarshi." Shiru ya yi inda Umad ya kalleshi yace" Masoyiyarshi kuma? Wa kenan?" Kallon Umad d'in dake nuni zai fad'i abu marar dad'i sannan yace" Ban san cikakken labarin ba, amma idan ka samu k'anwar mahaifiyarka za ta sanar da kai komai." Zaro ido yayi yace" Joyran?" Jinjina masa kai yayi yana kallonshi shi ma, wuri wuri ya fara da ido yana rarrabasu, ba zai ce k'arya ba ce kai tsaye tunda har ua gane tana neman da mahaifinsa, saidai me ye ribarta a cikin aikata hakan? Ta yi ne dan ta samu mahaifinshi? Ko kuma dan ta mulki gidan kamar yanda ta yi kafin zuwan Ayam ta samarwa gidan 'yanci? Zunbur ya mik'e yana laluba wayarsa a aljihu, da sauri ya fice a falon ya barsu da bin shi da kallo, saida ya b'ace ma ganinsu sarki Abdallah ya kalli Bukhatir yace "Zamu dakatar da nad'aka matsayin sarki har sai mun tabbatar da baka da laifi." Ajiyar zuciya Musail ya sauke ya kalli sarki yace "Yallab'ai, ina rok'onku da ku yafe min abisa abubuwan da suka faru, sannan zan so ku huta yanzu, zuwa dare zamu tattauna akan wata magana mai mahimmanci." Kallon Juman yayi dake gefenshi sannan yace "Abinda ya shafi tsakani na da ita, da kuma tsakani na da Ayam." A sanyaye sarki Abdallah ya gyad'a sannan yace "Ba damuwa komai ya wuce, saidai zuwan nan na mu kamar yanda na fad'a shagalin bikin Ayam ne ya kawo mu, dan haka za'a fara shagalin nan daga gobe, dole k'asar nan ta shaida ana bikin 'yar gata, ya ga sarki Musail sannan jikanya ga sarkin Egypt." Murmushi Musail yayi yace" Duk yanda kuka yi d'aya ne, Allah nuna mana." Da mamaki sarauniya Bilkees tace" Wai ko dai ka musulunta ne kai ma?" Sunkuyar da kai yayi irin a gaban surukan nan ya shafa kanshi kawai bai ce komai ba, mahaifiyar Bukhatir ce ta d'ora da basu hak'uri akan abinda Bukhatir d'in yayi sannan ta nema masa afuwa da fad'in shi kad'ai ne babba daya rage musu, kar su rabasu da shi, hannu bibbiyu sarki Musail da Abdallah suka karb'i k'orafinta kafin zaman na su ya k'are. Masaukin bak'i aka kai su sai sarki Abdallah da aka keb'e musu wuri na musaman sannan aka shiga had'a musu girki na musamman da karin kumallo. *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:43 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *40* Umad a fita daga nan d'akinshi ya nufa, iya abinda zai buk'ata kawai ya d'auka na daga kud'i da passeport d'inshi da kuma babbar wayarsa, fitowa yayi ya sa dreban gidan ya kai shi filin jirgi, yana shiga ciki dan samun izinin tafiya sai ga Joyran na jan k'aramar jakarta da sauri, da mamaki ya kuma dubawa da kyau dan ya tabbatar ita ce ya gani? Ko kula dai tsabar son had'uwa da ita yanzun ne yasa yake ma wasu matan kallonta? Har ta d'an gitta ta gabanshi ta wuce sai k'amshin turarenta mai k'arfin gaske ya shaida masa tabbas ita ce dai wacce zaka tafi yanzu dominta, to amma me ya kawota nan? Kafin ya samu amsar ya taho sukwane yace "Aunty." Bata juyo ba saboda tunanin wa zai kirata da haka a nan d'in, saida ya matsa daf da ita yace "Aunty Joy." Da sauri ta juyo saboda d'aukar muryarshi da kuma tabbatarwa da ita dai a ke, suna had'a ido duk da hular dake kanta (hana sallah) da bak'in gilashi k'ato data saka saida ta ji gabanta ya fad'i har ta furta a k'asan mak'oshi "Umad kuma?" Bai yi mamakin ganinta a wannan lokacin ba, saidai mamakin da ya ke shi ne hala bata san gogan na ta ya bar duniya ba? Da mamaki da kuma rawar murya tace "Amm..Umad, me...kuma ka ke y...a nan? Ina nufin me ya kawo ka nan?" Murmushi ya sakar mata tare da sunkuyawa yace "Ina kwana auntyna." Wani murmushi ta saki wanda kai tsaye daga zuciyarta ya fito sakamakon ganin ya gaisheta kamar yanda yake yi a da, kafin zuwa shed'aniyar nan ta lalata mata komai, damtsenshi ta dafa tace "Lafiya lau Umad, baka amsa min tambayata." Kallon k'wayar idonta yayi sannan yace "Aunty mun zo shak'atawa ne tare da abokaina, yanzu ma wani malaminmu ne ya zai zo saboda zamuyi yawan bud'a ido da shi, shiyasa na zo nan." Dariya tayi tace "Masha Allah, Umad kai dai baka son zama wuri d'aya." Wani malalacin murmushi ya mata bai ce komai na, rik'o jakarta yayi yana kallon fuskarta yace "Aunty ke fa? Me ya kawoki Khazira?" Cikin kame kame tace "Uhmm..ka gane, ni ma dai na zo had'uwa da wata k'awata ne da mukayi karatu tare, tayi aure kuma ban samu na zo ba saboda hidimar kula da aunty (Kossam), shine yanzu na zo na mata murna." Jinjina kai yayi yace "Yayi kyau hakan, amma kafin nan aunty mu je na kaiki masaukinmu, dan kinga bai kamata ki d'ora mata nauyi ba ko?" Da sauri tace "A'a a'a Umad, ai mun yi da ita zan sauka a gidanta, ka ga ba zata ji dad'i ba, kuma m ai zata turo drebanta ne ya d'aukeni." Cewa yayi "Duk da haka aunty na, mu je mu jira dreban, idan ya zo sai ya saukemu a masaukin." Yanda yayi gaba da jakarta yasa bata da wani zab'i sai bin bayanshi, gasu tsaye mutane na ta barin wajen amma su suna nan, tana son sanin ta yanda zata ribace shi ya bar wajen sannan ta shige taxi, amma ya gagara hakan, hatta ruwa da ta ce ya kawo mata da jakar ta ta ya tafi ya siyo ya dawo, k'arshe dai kallonta yayi yace "Aunty na, anya kuwa dreban nan zai zo?" Dariyar yak'e tayi tace "To gashi dai shiru, amma zai zo, zai zo na sani." Girgiza kai yayi tare da tare taxi yace "Ba zai zo aunty, idan har tana ganinki da daraja ba zata yarda ta kasa turo mai d'aukarki kafin saukar jirginki ba, ni kuma ba zan tafi na bar nan ba na bar ki a tsaye." Tura jakarta yayi a boot ya bud'e mata gidan baya yace "Shiga aunty." Kamar zata fashe da kuka ta kalleshi amma haka ta shiga a dole saboda tana jin nauyin yi masa gardama, shiga tayi ta zauna ya rufe sannan ya shiga mazaunin gaba dreban taxi ya ja su zuwa titin da Umad d'in ya fad'a. Da k'aramar wayarshi yake ta latse latse har suka yi nisa, Joy kam daga baya kamar zata fashe saboda takaici, k'eyarshi kawai take zabgawa harara kamar ta kashe shi, ga haushin da uwarshi ta k'unsa mata yau d'in, kawai ta sa hadimai na ta mata wani shirye shirye, data tambayeta ko lafiya ta ce zatayi tafiya ne, data tambaya zuwa ina sai cewa tayi "Bai dameki ba." Haka shi ma Wudar shirin ya gama tsaf ya ce ai tare zasu tafi, duk da ya yi tambayar har ya gaji cewa ta fad'a masa ina za ta je, sai kawai ta ce wajen d'anta Umad, yin me? Yana ina? Duk ta k'i amsa mi shi, hakan yasa yanzu dai kafin ta baro gidan ta baro hadimai na ta loda kayayyaki a moto wanda duk mai hankali ya gani zaka san neman aure ne za'a je yi, sai dai na wa? Kuma a ina? Bata sani ba, cikin wannan hada hadar ta kutso kai ta badd'a kama ta fita abinta. Akan babban titin dake bayan filin jirgi motoci na police guda biyu suka tari gabansu, dole ta sa dreban tsayawa da tunanin laifin me ya yi kuma? Wace dokar ya taka ne haka mai girma a cikin tuk'i? Jami'ai hud'u ne suka fito daga motocin, sai jami'a mace d'aya data fito, cike da izza Umad ya fita ya bjd'e murfin da Joy ke zaune tana kallon me ke faruwa, amma sam hankalinta bai tashi na saboda bata ga abinda tayi ba. Suna k'arasowa dukansu suka sara masa da girmamawa, da mamaki Joy ta kalli jami'an sannan ta kalli Umad da tunanin wa ye shi kuma a gwamnatance, hannunta Umad ya kamo sanda jami'ar ta k'araso ya karb'i ankwan hannunta, ba zato ba tammani ya mata awarwaro da ankwar nan a hannayenta, mamaki ne ya hanata katab'us sai kallonshi tana fad'in "Kai Umad, lafiya? Me na yi kuma? Me ye haka wai? Ka manta ko ni wacece?" K'ala bai ce mata ba sai jan hannayenta da yayi saida ya sadata da motocin jami'ai ya dannata baya ta zauna sannan ya mayar ya rufe, gilashi ya ciro bak'i daga aljihunshi ya manna a idonshi, juyawa yayi zai shiga mazaunin mai zaman banza ya ji tana jijjiga tana fad'in "Kaiiiii! Umad, ka kunce min abar nan, me na maka ne wai?" Shiga motar yayi ya ja wata raga dake tsakanin kujerar baya da kujerun gaba saboda baya da buk'atar hayaniyarta, saidai yana jin yanda take ta bubbuga motar tana hargagi, bai kulata ba saidai yana kallon wani jami'i da ya d'auko jakar Joy d'in a bayan taxin nan sannan ya biya mai taxin suka taho, tayar da motocin suka yi har da jiniya irin ta yan sanda sannan suka nufi babbar headquarter jami'an bincike na k'asa. D'akin bincike suka ajiye ta, kalle kalle ta shiga yi tana ta jujjuyawa, d'akin studio ce ta musamman, dan iya maganarka kawai zaka ji sai wanda ke kusanka, amma ko iska bata shigowa daga waje bare ta fita, lullub'e yake da bak'in yadi mai kaurin gaske, sai wata faffad'ar taga wacce ita daga ciki kanta take gani ma'ana madubi, saidai daga waje jami'ai ne na musamman da na'urori a gabansu, inda daga nan suke iya sauraren duk abinda ke faruwa ko zai faru a ciki. Kujera biyu ce wacce take zaune a kai sai wacce ke fuskantarta, inda k'akk'arfan teburin dakz gabanta aka d'aure hannayenta da ankwa mai d'an tsayi wacce ta fi wacce aka saka mata da farko. Cikin hargagi ta fizgi hannayenta tana kwaroroton fad'in "Wai babu kowa a nan ne? Me na yi ne? Akan wane dalili zaku kawo ni nan ku a je? Ina buk'atar ku kira min lauyana." Shirun da yayi yawa babu mai kulata ne yasa ta sake fizgar hannayenta har saida kujerar da take zaune ta motsa tare da fad'in "Banzaye kawai, sai kun yi nadamar ajiye ni a nan da ku ka y...." Cak maganarta ta tsaya saboda k'ofar da aka bud'e aka shigo, Umad ne fuska kici kicin saidai akan bak'ak'en kayanshi ya d'ora wata bak'ar jacket mai d'an ratsin fari sai daga baya an rubuta Police da manyan harufa. A gadarance ya k'arasa ya ja kujerar sannan ya ciro k'aramar bindiga daga k'ugunshi ya ajiye, zaune yayi ya rumgume hannaye ya jingina a kujera yana zuba mata idonshi da ba wani girma ne da su ba sai tarin kwarjini kamar na damisa, murya a dak'ile kamar saukan aradu yace "Magana ce za mu yi ba wasa ba, kuma duk abinda zai fito daga bakinki ya zama gaskiya, idan ba haka ba zan manta da wacece ke a gare ni na d'auki tsatsauran mataki a kan ki." D'ora hannayenshi yayi a kan teburin ya d'ag girarshi ta hagu sama yace "Kin fahimta?" A hassale tace "Kai wane irin d'a ne? Ni fa k'anwar mahaifiyarka ce, Umad me na yi da za ka kawo ni nan?" Had'e yawu yayi tare da sake tsura mata ido yace "Khatar ya fad'a mana kina da alak'a da harin da aka kai masarautar Egypt shekarun da suka wuce, me zaki ce a kai?" Zazzaro ido tayi na mamakin ya kuma wannan maganar ta fito? Khatar? Ya aka yi Umad kuma ya san shi? Duburburcewa tayi ta kalleshi tace "Ka ga Umad ba zan yi magana ba, ina son ganin lauya na sannan." Wani jan kallo ya mata da yasa ta sadda kanta k'asa cikin dakakkiyar murya yace "Tunda kika ga na zo da ke nan kai tsaye, kuma na d'auko miki gundarin zancen a take, ke kinsan ba wasa ba ce ta kawoni, Joyran..." Ya kira sunanta ya nunata da yatsa kafin yace "Ki bani amsar tambayata kafin na turo jami'ar da za ta bincika min ke yanda ya kamata." D'aga hannayenta tayi dake d'aure tace "Shikenan na ji, zan fad'a ma ka Umad, amma..." Marairaicewa tayi tace "Kar ka bari kowa ya ji maganar nan Umad, ka ji?" Jajayen idonshi kawai ya zuba mata yana kallo, cikin shashek'ar kuka na munafurci ta fara fad'in "Tabbas da taimako na a cikin kai harin nan, sai dai ba da makami ba ko wata hanya ta daban, mun kasance muna soyayya ni da Khatar tun a makaranta, sanda yaya Kossam ke d'aukar nauyin karatuna da duk wasu buk'atuna, sai na fara jin kishi a kan ta ina jin haushin me yasa ba ni ba ce a matsayinta? Wata rana na zo hutu Giobarh sai mahaifinka ya umarci da mu shirya za'a yi taro a k'asar Egypt, mun tafi cikin farin ciki tare da ku da kuma yaya Kossam, a Egypt sai muka had'u da Khatar shi ma ya aje a lokacin ba'a masa wazirin sarkin Khazira ba, duk sanda k'afa ta d'auke ni da shi muna tare muna soyayyarmu, a nan ne har na samu damar fad'a masa abinda na ke ji a zuciyata game da yar uwata, tambayar da ya min ita ce *"Me ki ke so a yi kenan?"* "Sai na fad'a masa ina so na zama sarauniyar Giobarh, na zama mai fad'a a ji a masarautar, da fari ya nuna min kishinsa saboda mun yi alk'awarin aure da shi, amma washe gari sai ya zo min da maganar wai zai cika min buri na, da na matsa masa me zai yi ne sai ya ce min *"Sarki Musail ne ya nuna sha'awarsa ga 'yar sarkin Egypt, saidai ita ta nuna bata son shi d'an yar uwarki (Urab) take so, kuma sarki Musail ya bani wuk'a da nama na yi duk abinda ya dace dan ganin ya sameta, dan haka zan jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya."* " Na tambayeshi ban gane me ya ke nufi ba, sai ya ce min *"Yau da dare zan sa a kashe min d'an yar uwarki, hakan zai sa sarkina ya samu Juman, daga baya zamu bar duk shaidar da zata nuna sarki Musail ne yasa a yi wannan aika aika, kinga kenan mun haddasa gaba mai tsanani tsakanin masarautar Giobarh da masarautar Khazira, hakan zai sa sarki Wudar ya nemi d'aukar fansa ko ta ya ya, idan aka yi nasarar cin Giobarh da yak'i, a k'arshe za'a kafa sabuwar daula a Giobarh kuma ke zaki zama sarauniyarta, idan kuma aka yi nasara akan Khazira..."* "Da sauri na tambayeshi to me zai faru? Sai ya ce *" Zan zama sarkin Khazira, ke kuma sarauniyar gaba d'aya Bussam, ya kika gani ?*" " Na ji dad'i sosai har cikin zuciyata, hakan yasa na yi dogon tunani a lokacin sannan na bashi ta wa shawarar na ce *"Madadin ka sa a kashe Umad shi kad'ai, me zai hana ku d'auki hayar mahara da dama su kawo hari aasarautar nan yau cikin dare?*" "Tambaya ta ya yie ye anfanin yin haka? Sai na ce masa *" Idan fa aka yi rashin sa'a aka kama wad'anda kuka turo, to shakka babu zaka kwana a ciki, dan gidan nan yanzu baibaye yake da hadimai da dogarai saboda yawan safakunan dake ciki, amma idan mutanen dayawa kuma kan mai uwa dawabi aka yi, to kai tsaye ba za'a zargi wani sarki ba, dukansu zasu dinga wa juna kallon kallo ne, a cikin hatsaniyar kuma sai a kashe Urab, ni kuma nasan mutuwar Urab daidai take da mutuwar Kossam, dan tana matuk'ar son yaron, kaga ni kuma ta wannan hanyar zan k'arasa kassara rayuwarta.*" " Haka muka kwana da shirinmu, kuma mun yi nasarar aiwatar da abinda muka tsara, a hakane aka kashe Urab kisan wulak'anci, wanda sanadiyar haka mahaifiyarka ta yanki jiki ta fad'i, ba'a iya aiwatar da komai ba dan masarutu da dama sun rasa mutanensu a lokacin ko da kuwa hadimi ne, ni kuma daga lokacin sai..." Fashewa tayi da kuka na gaske ta sunkuyar da kanta, wani wawan buga teburin yayi da yasa ta zabura kamar zata tashi tsaye, wanda hakan yasa fitsarin da take ji ya banko a guje ya taho mata daga zaunen da take, kwararararan da ya ji abu na zuba a k'asa yasa ya d'an yi jim yana saurarawa, a hankali ya tura kujerar da yake zaune baya sannan ya d'an lek'a, da sauri ya kalleta ya girgiza kai yace "Ina jinki." Yamutsa fuska tayi ta matse k'afafunta kanta k'asa saida ta gama tsiyaye fitsarin tas sannan ta d'ago a hankali ta kalleshi, a kausashe ya kuma fad'in "Ina saurarenki." Cikin sanyayyar murya tace "Wajen boka na kai yaya Kossam a India, nan ne aka bani maganin da kullum nake saka mata a abinci sannan nake shafa mata a jiki duk kwana uku, da wannan ne ta kasa anfanuwa tun daga waccen ranar sai jiya data tashi kamar a mafarki, kuma na samu abinda nake so, sai dai sarki Wudar bai aureni ba haka ma Khatar, sannan duk yanda na so na kashe mahaifiyar abun ya gagara, dan wani boka ma fad'a min yayi idan na matsa ni ce zan rasa raina, dan ita kam mutuwarta ba yanzu ba, amma dai ni da mahaifinka mun zama abu d'aya, a shekarun nan da aka d'auka ni da shi kamar mata da miji ne, saidai ban tab'a yarda shi ko Khatar da ke kawo min ziyara lokaci lokaci ba na d'auki cikin d'aya daga cikinsu, saboda ba wannan bane a gaba na, saida na fara gajiya da k'aryar da Khatar ke yi min a kullum cewa zai aure ni, sannan na dakata da d'aukar allura har na samu ciki da shi, sai kuma na yi k'ok'arin d'orawa Wudar saboda ina so abinda zan haifa ya zama magajin wannan masarautar, dan na fahimci Khatar ba zai tab'a zama fiye da waziri a masarautar Khazira ba, wannan shi ne abinda ya faru Umad, tunda na fad'a maka ka yafe min ka ji, kar ka hukunta ni dayawa." K'asa da sama ya harareta ya ture kujerar ya mik'e tsaye, bindigar ya d'auka ya sa a k'ugunshi yace" Mak'iyi na nesa ba wuya ka shawo kansa, amma mak'iyi na kusa ya fi kowane illa, shi mak'iyi zai iya dawowa masoyinka wata rana, amma mai maka hassada har abada baya tab'a canjawa, a haka za ki k'are Joyran, babu nan kuma babu can, doka ce za ta d'auki matakin daya dace a kan ki ba ni ba, dan waccen harin da kuka sa aka kai, yayi sanadiyar rayuka da dama, daga ciki kuwa har da yayana da nake matuk'ar so, sannan har da mahaifin shugaban hukumar nan ta mu, d'aya ne a cikin manyan bak'in da suka halarci taron." Juyawa yayi ya fice a wurin duk da yanda take k'wala masa kira tana ya yafe mata kar su d'aureta, ba za ta iya rayuwa a d'aure ba wa ye wa ye, haka yana fitowa jami'an dake nan wanda duk suka ji tattaunawarsu suka dinga sara masa wasu kuma na bashi hannu, shugabar hukumar kan shi hannu ya bashi suka gaisa bayan ya share k'walarshi yace "Nagode Umad, yau ta dalilinka na gano wanda suka kashe min mahaifina, atisayen *lu'u lu'u* ya zo k'arshe." Murmusawa yayi yana mai danne k'unar dake cikin zuciyarshi na rasa yayanshi yace "Nagode yallab'ai, ina neman wata alfarma?" Da fara'a dattijon yace "Ba komai, fad'i buk'atarka." Kan shi tsaye yace "Ina so zan d'auki hutu." Dariya yayi ya bubbuga kafad'arshi yace "Ai ko baka nema ba, abu ne da muka tanada maka tun kafin zuwan ranar nan." Jinjina kai yayi yace "Nagode yallab'ai." Girgiza kai yayi yace "Ba komai Umad....am...yarima Umad, zuwa dare zaga ka takardar izinin hutunka a e-mail d'inka." Jinjina kai yayi sannan ya ciro bindigarshi ya aje akan d'an teburin dake kusa, da mamaki dattijon yace "Baka buk'atarta daga yanzu kenan?" Murmushi yayi yace "Hutu zan yi yallab'ai, da kuma cin...amarci, ba karan batta ba." Bushewa duk wurin sukayi da dariya har wasu na tsokanarsa dama yana da aure ne, abu d'aya ya fad'a musu shi ne "Ina gayyatarku dukanku wajen shagalin biki na a fadar Khazira." Daga haka ya juya ya fita a gaba d'aya headquarters duk da yana jin tsiyar da wasu ke masa wai hala yar sarki ya kwashe? Wasu kuma suna fad'in ko dai ma *lu'u lu'un* atisayen na su ya d'auke kacokam. 馃グ *Mu sha kodumo, In Shaa Allah gobe za ku ji ni shiru saboda zamu yi tafiya amma ta wuni d'aya zuwa Katsina, ina baran addu'arku guy's.* *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:43 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *41* Babban teburin falon b'angaren sarauniya Juman aka zauna cin abinci, wanda sarauniyar ta sa aka gayyaci kowa zuwa nan, bayan cokula babu abinda ka ke jin k'ararshi, saidai kallon juna da ake kawai da ido, wani kallon mai ma'anoni da fassara, wani kallon kuma na katari ne kawai ido su sark'e da juna. Gyaran murya sarki Musail yayi ya aje cokalin hannunshi mai yatsu sannan ya had'e tafukan hannayen ya kalli sarki Abdallah da ke kujerar dake fuskantar ta Musail, duk da suna da d'an nisa haka ya d'aga muryarshi amma a tausashe yace "Ranka shi dad'e, ina ga tunda gaba d'ayanmu mun taru, me zai hana na fad'i abinda ya ke raina?" Cike da karammawa ya lumshe ido shi ma ya aje cokalin hannunshi yace "Me kuwa zai hana, bismillah fad'i." Ayam ya kalla dake kujerar daf da shi wacce take kallonshi tana tsakurar abincin saboda kallon da Umad ke mata wanda ke kurar dake fuskantar ta, murmushi ya sakar mata yace "Da ma ina so ne na mik'a mulkin Khazira ga me abun, ma'ana Ayam." Waro ido tayi tace "Kyu (Me)?" Da mamaki suka kalleta na sabon yaren da tayi inda Umad ya rumgume hannaye a ranshi ya furta "Wata sabuwa." Da sauri ta kalli inda sarki Abdallah yake tace "Grand Pah, ka ji me Pah ya ke fad'i? Gaskiya ni a'a." A sanyaye Juman ta kalli sarki Musail tace "Abban Ayam, ina ganin me zai hana idan ma mulkin zaka bayar ka ba wa mai buk'ata Zafreen, tunda ita ma ai 'yarka ce kuma babba." Kallonta yayi a tausashe yace "A gaskiya bana so na sake aikata wani kuskuren, Zafreen hali na gareta babu abinda ta rage, talakawan Khazira sun sha wahala a a hannuna, bana so na sake saka su uku." Marairaicewa Ayam tayi tace "Gaskiya ne Mah, ni kinga bana son wannan hayaniyar, idan so samu na ne na samu wani keb'antaccen daji mai d'auke da nau'in kowace dabba, na zauna tare da su na rayu da su cikin farin ciki." Wata basarakiyar dariya sarki Abdallah da Musail sukayi, haka ma sauran mutanen saida suka dara, inda Bukhatir ya narke ido yana kallon Ayam kamar ya sumbaci bakinta sanda take maganar, Juman ma cikin dariya ta kalleta tace" Ke burinki kenan a duniya? Rayuwa da dabbobi?" A hankali ta jinjina kai alamar e, maida kallonta tayi niyyar yi ga plate, sai kawai a tsautsayi suka had'a ido da Umad dake kallonta yana sakin b'oyayyan murmushi, suna had'a ido ta d'auke kai ta d'auki cokalinta, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli sarki Abdallah yana d'aukar na shi cokalin shi ma a ladabce yace "Yallab'ai, ai ita d'in sarauniyar jeji ce, ina ga dalilinta kenan na shiga karatun gandun daji, kuma da alama wannan foresti猫re d'in za ta zama sarauniyar dabbobi." Da fara'a sarki Abdallah yace "Da gaske Umad?" Jinjina masa kai yayi yace "Baka gani ba sanda suke hira da zaki, abun kamar al'amara." Waro ido tayi ta bud'e baki tace "Kai kai kai, ni d'in? Yaushe?" Kallon Juman tayi da ke k'yalk'yala dariya tace "Hakane ko Mah?" A nutse Musail yace "Ayam, maganar gaskiya nake fad'a miki, ki shirya zama sarauniyar Khazira." Turo baki tayi gaba tace "Pah, a gaskiya ban shirya ma hakan ba, sannan ka ga ina so na kammala karatu na, burina shine na zama major, sannan ni ban san komai a harkar siyasa ko sarauta ba, i can't take this risk Father." Sarki Abdallah ne ya kalleta yace "Pourquoi pas ma cher?" Yatsina fuska tayi tace "Haka kawai ba zan iya ba." Kallon sarki Musail yayi ya d'an masa hira da ido irin ta su ta manya, jinjina kai yayi irin na fahimta sannan ya ci gaba da cin abincinshi. Suna tsaka da cin abincin wani bafade ya shigo tare da sunkuyawa alamar girmamawa yace" Sarki na, bak'i daga Giobarh sun iso." Zaro ido Umad yayi ya kalli bafaden yace" Giobarh?" Da mamaki Musail ya kalli bafaden shi ma yace" Giobarh? Su wa ye haka?" A ladabce yace" Sarki Wudar ne da kuma sarauniyarsa." D'an zaro ido Musail yayi yace" Manyan bak'i haka? M yake shirin faruwa kuma?" Kallon bafaden yayi yace" Shikenan, ka musu iso." Sunkuyawa yayi sannan ya juya ya fita, Musail kuma mik'ewa yayi yana kallon Umad da yake kallon k'ofa yace" Ina fata ba maganar d'aukar fansa ba ne?" Kallon Musail d'in yayi sai kuma ya mik'e tsaye shi ma yace" Ba wannan yallab'ai." Hadimai ne suka fara shigowa mata d'auke da manyan kwando na roba mai kyau tamkar wanda aka sak'a da kaba, an musu kwalliya lullub'e da yadi mai k'yalli. Layawa sukayi su goma duk rik'e da kayayyaki a hannunsu, a nutse sarauniya Kossam da sarki Wudar suka shigo, kayansu kusan kala d'aya ne har kalarsu ne, kalar shud'in ta musu kyau ga ratsin fari da k'yalli k'yalli, inda duka rigunan na su ke jan k'asa musamman ma gyalen Kossam. Duk mik'ewa mutanen teburin sukayi suka tunkaresu a nutse, cike da girmama juna da karramawa suka dinga gaisawa, suma a ladabce suka sunkuya suna gaishe da sarki Abdallah wanda suka ganeshi sosai duk da dai shekaru sun ja sosai. Ayam dake bayan Musail tana hangen Kossam, sai yanzu ne take tuna lallai fuskar matar nan ce a hoton data gani d'akin Umad zuwanshi makarantarsu, dan yanzu fuskarta ta fi fitowa da kyau saboda an sha gyaran jiki da na kai, duk da ba kwalliya a fuskarta amma dai hoda da man leb'en data shafa kalar leb'en na ta sun sa ta k'ara kyau. Ta shagala da kallonta sosai ta ji murya kamar daga sama an ce "Zo nan 'yata, gujajjiya daga mahaifiyarta." Dariya mutanen d'akin sukayi sai ita data zabura ta sake kallon matar, hannun Kossam d'in ta kalla data mik'o mata, a hankali ta mik'a mata hannun sannan ta taka zuwa gareta, kallon juna sukayi sai kuma Ayam ta sunkuyar da kanta k'asa cike da kunya tace "Mah..." Hancinta Kossam ta ja tace "Shine dan kinga bana iya magana a lokacin kika gudu kika barni." D'aga kai tayi ta kalli k'wayar idonta, cikin dubara Kossam ta janye na ta idon saboda gagara da tayi wajen kallon idon Ayam d'in, d'an giggilma idon tayi tana kallon gefe gefe, lura da haka yasa Ayam sauke idonta k'asa tace" Ki yi hak'uri Mah...gani yanzu." Kallon fuskarta tayi da murmushi a fuskarta tace" Ba zaki sake guduwa ba?" Girgiza kai tayi tace" A'a Mah, can ma na gudu ne saboda ina so zan ga iyayena." Kyab'e fuska Kossam tayi tace" Dan haka zaki sake min nisa? Nasan haka zai faru, shiyasa na zo da shirina dan na wa tubkar hanci." D'an d'aga ido tayi ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kai, a nutse ta tallabo hab'arta ta zubawa fuskarta ido, cikin sanyayyar murya tace" Zafeera, za ki zama 'yata ta hanyar auren d'ana Umad?" K'uri ta zuba mata ido tare da jin dokawar k'irjinta, kasa cewa komai tayi sannu sannu har ta samu ta sunkuyar da kanta k'asa, yanda falon yayi shiru Juman kuma ta d'aga labb'anta za ta yi magana sarki Abdallah ya mata alama da ido tayi shiru, hakan yasa d'akin ya d'auki shiru na wasu mintoci, kamar an tsikani Ayam ta d'aga kanta tana murmushi tace "Mah, na yi farin ciki da kika samu lafiya, zan iya zama 'yarki mana...ko ma na ce na za...ma." Ta k'arashe tana kallon inda Umad ke tsaye wanda ya zuba mata ido yana kallo, da fara'a sarauniya Kossam tace "Da gaske za ki zama 'yata? Sirikata?" Da ido ta mata alamar e, hakan yasa Kossam fad'ad'a murmushinta ta kalli hadiman dake bayansu, mik'a musu hannu tayi d'aya daga cikinsu ta bata kwandon hannunta, tallabo kwandon tayi daga k'asa sannan ta juyo ta kalli Ayam, Musail da Juman dake bayan Ayam su ma ta kalla tace "Ina neman izininku da ku ba wa d'ana Umad auren 'yarku Zafeera?" Musail da Juman kallon juna sukayi, a k'ayace Musail ya saki murmushi Juman kuma ta b'oye dariyarta, sarki Abdallah ma haka tare da kusan wanda ke wajen. Da mamaki suke kallonsu ta ya suke musu dariya daga wannan maganar, da sauri Umad ya matso kusan Kossam cikin rad'a d yarensu na Gallois yace mata "Mahh...kiyi shiru mana, ki zo zamuyi magana a wane." Kallonshi tayi ta kyab'e fuska kamar zatayi kuka tace "Me na yi da suke min dariya? Sai ka ce na nema maka auren matarka?" Bai san sanda ya tintsere da dariya shi kan shi, abar da ya jima bai yi ba sai gashi yana k'yak'yatawa sosai duk da k'ok'arinshi na son rik'eta, cije leb'en k'asa tayi ta sake yin takwaf takwaf da fuska, da sauri ta mik'awa Ayam kwandon dake hannunta ta d'aga hannaye za ta daki Umad, da gudu cike da nishad'i ya lab'e bayan Wudar ya ruk'umk'umeshi yana fad'in "Pah ka gani fa, yanzu hakane ya dace mu yi farin cikin samun lafiyar Mah?" Ita kam k'ok'arin sai ta dakeshi take tana cewa "Ja'iri kawai, ta ya kai ma za ka dinga min dariya daga magana, me na fad'a ba daidai ba? Zaka zo nan ko sai na..." Cikin sa'a ta rik'o wuyan rigarshi ta jawoshi gabanta, fad'awa yayi jikinta yana ci gaba da k'yalk'yala dariya yace "Yi hak'uri Mah, zan fad'a miki wani abu to." Duk da Juman na jin kunyarta dan k'iris ya rage su zama surukanta, amma gashi 'yarta ta zama surukarsu, cikin ladabi tunda suna sama da ita tace "Yar uwa, ki rabu da shi haka mana, dole ne fa a miki dariya saboda abinda kika zo d shi." Dakatawa tayi ta kallet tace "To me ya sa za' a min dariyar?" Cikin danne dariya saboda yanda tayi maganar tace "To ai matarsa ce kike nema masa aurenta, kinga kuwa dole mu yi dariya." Zaro ido tayi ta kalli Ayam ta kalli Juman, sannu sannu sai ta dinga juyawa tana kallon mutanen wurin dake ta sakin murmushi ban da Bukhatir kawai. Da mamaki tace "Amma...." Bata fad'a ba ta dakata saboda wata damk'a da Wudar ya ma hannunta da k'arfin gaske, da sauri ta juya ta kalleshi. Gaba d'aya fuskarshi da yanayinshi ya nuna ya shiga wani hali ne na tashin hankali da kid'ima, yanda ya kakkafe idonshi kan fuskar Juman da ta yi maganar, ga kuma d'aya hannunshi dake kan saitin zuciyarshi baki bud'e kamar zai yi magana amma kuma maganar ta mak'ale. Gyara tsayuwarta tayi cikin rad'a ta dafa d'aya hannunshi daya rik'e na ta tace "Sarki na, lafiya? Me ya ke damunka ne?" D'aga baki ya sake yi da kyau yana so sai yayi magana, amma sai ya fara sauke wani irin numfashi kamar yana fizgoshi ne da k'arfi saboda barazanar barinshi da yake, idonshi da ya kafe kan Juman ne suka d'an motsa da k'arfi sai kuma suka rufe ruf, gagggaf jikinshi ya d'auki rawa haka yasa k'afafunshi ma suka kasa d'aukarsa, luuuuu ya tafi zai fad'i Umad yayi caraf ya tallabeshi. Saidai dake gaba d'aya ya saki jikinshi sai Umad d'in ya d'an motsa kamar zai fad'i shi ma, da azama Haman ya kama mi shi suka rik'eshi da kyau, hankali tashe suka rufa a kanshi wasu na firfita d'aya a cikin k'annan Bukhatir ta kawo ruwa aka shafa masa, shiru bai dawo hannaycinsa ba kuma Umad ya saurari harbawar jijiyar wuyarshi, kawai dai rud'u ne da tashin hankali ya ziyarce shi lokaci d'aya. Musail ne yace "Ku kaishi d'aki ku kwantar, bari a kira likitan cikin gida sai ya dubashi." Cire masa kambun kanshi Kossam tayi sannan su Umad suka ja shi zuwa d'akin Umad d'in da ya sauka. Inda Musail ya kira babban likitan ya kuma ce yana zuwa yanzu. Kossam dake tsaye juyowa tayi kan Juman da mamakin da har yanzu bai barta ba tace "Yar uwa, garin ya haka ta faru? Yarinyar da nake mafarkin ta zama sirikata, sai ku ku tabbatar min da mafarkin." Kama hannunta Juman tayi tace "Muje ciki sai na fad'a miki komai." Zasu wuce Juman ta sake juyowa ta kalli hadiman gidan tace "Dan Allah ku samawa kowa masaukin da ya dace da shi, sannan kayan nan babbar tsaraba ce daga surukanmu, dan haka ku adana su waje mai kyau, anjima zan zo na duba." Ciki suka shige hadiman kuma suka shiga yin abinda ta umarcesu, Ayam kuma mik'awa wata hadimar kwandon hannunta tayi sannan ta kama hannun sarauniya Bilkees suka nufi hanyar d'akinta, juyowa tayi ta kalli k'annan Bukhatir tace" Ku zo mu je." Bin bayansu sukayi su ma suka yada zango a d'akinta. *Wudar* ma cikin gaggawa likita ya zo ya duba shi, jininshi ne yayi mugun hawa sosai hakan yasa aka masa allurar bacci mai nauyin gaske, Umad da Haman barinshi sukayi a d'akin, inda Umad ke cike da mamakin abinda ya jawo wa mahaifinshi shiga wannan halin, shin soyayyar da ya ke wa Ayam ce ta kai wannan matakin? Ko kuma dai ya shirya wani gagarumin abu ne ga auren d'an daya rage masa? hakan yasa jin yayi auren ya jefashi a wannan halin? Ko kuma dai alhakin mahaifiyarsa ne Allah zai fara cire mata hakk'inta dalilin Ayam? *A gurguje* A al'adar k'asashen dama idan har an amince da neman izinin auren, to a cikin kayayyakin da iyayen miji ke kawowa har da kayan gyaran jiki, dan haka Juman bata tsaya b'ata lokaci ba wajen duba kayan nan ta d'auki duk abun buk'ata wanda ya shafi dukhan, dilka, madara, zuma, kurkum, haska amarya, man ja mai kyau. Hankali kwance a nutse suka sakata tsakiya ana ta darjewa a nutse, jakadiyar Juman da ita kanta Juman d'in, ga kuma Kossam da ta aje surukantaka a gefe tana shafawa Ayam d'in dilka da kan ta, ga kuma sarauniya Bilkees dake zaune tana taimaka musu da wasu abubuwa. Awa d'aya suka d'auka kafik daga bisani tayi wanda da zallar sabulu na zuma da madara, tana fitowa Bilkees ta bata madarar da aka dama da kauri da sanyi kad'an ta shanye tas, mai ta shafa wanda shi ma duk cikin kayan da aka sako ne sannan ta saka sassauk'an riga ta gabatar da sallah la'asar, bayan ida sallarta ne Kossam ke tambayarta abinda ta yi, nan Juman da Bilkees suka fayyace mata komai game da addinin har saida ta ji sha'awar shi ga ita ma. Ko da duhu ya fara shigowa masarautar Khazira ta d'auki harami ta kuma canza kala, dan kuwa ma'aikata daga kampani na musamman a wajen tsara wajen taro aka d'auko suka k'awata gidan, walwali mai d'aukar ido da kayan ado da alatu ta ko ina aka zagaye gidan kamar ba shi safiyar yau yayi gobara ba, shiga da fita kawai hadimai ke yi suna ta harkoki na k'ayata wajen bak'i da abubuwan ci da shi, haka ma babban tureburin da amarya da ango za su zauna. A d'aki kuma masu kwalliya na musamman aka kawo wanda kafin su shiga saida aka cajesu da akwatin kwalliyarsu, mai gyaran kai tana aikinta cike da k'warewa, haka mai wankin k'afafu da yanke farce, sannan aka mata gyaran farce na hannu aka shafa mata verni kalar fari da ba'a cika shaida an saka ba. Duk da har yanzu gashinta bai yi tsayi ba, amma da aka mishi wani irin gyara mai murd'ewa sai wanda zai ganta a lokacin ya d'auka tsayin gashin ne yasa aka mummurd'eshi hakanan, gashi an bar mata shi a yanda yake kalarshi ta asali maroon da tsili tsilin yellow yellow. Saida aka d'auki minti talatin ana gyara mata girarta da girar idonta, yanda ake so su tsaya cak ba tare da sun rabe da juna ba sannan su mik'e kuma su lank'wasa, daga haka aka ci gaba da mata saukakk'an kwalliya wacce ita kanta ta zuba ido take so ta ga yanda fuskarta za ta yi da kwalliya abar da bata tab'a yi ba. *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:44 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *42* Wani mahaukacin yadi ne aka mishi babbar riga da yar ciki kalar bleue daya k'ona, bak'ak'en takalmi ya saka da hula bak'a kamar d'inkin da aka ma rigar, haka ma agogon hannunshi ta fata bak'a ce, yayi kyau matuk'a ya kuma gama had'uwa. Haka ma Haman matsayinshi na babban amininshi ya shirya cikin farin yadi, shi ma tsaf ya fito abun shi gwanin sha'awa, yana mak'ala agogon hannunshi fara k'irar Gucci Umad kuma na fesa turare Rexona mai sanyayyan k'amshi ya kalli Haman kamar mai tuhumarshi yace "Haman, matata ka ke so ko?" Da wani irin sauri Haman ya kalleshi yana rarako ido kamar zai had'iyeshi da su, tabbas da abinci yake ci da ya sark'e, ganin ya dakata daga d'aura agogon yasa Umad aje turaren hannunshi ya kama hannun Haman d'in ya fara d'aura masa agogon, d'aga idonshi yayi cike da miskilanci da kayar da gaba ya zuba a fuskar Haman da ya gama rud'ewa yace "Na san shirinku kai da yayarka, ta so ka auri matata saboda mijinta ya hak'ura da ita dan ita ma ta samu daraja a gunsa, k'ok'arinta mai kyau ne, saidai niyyar ce mummuna, hakan yasa na muku uzuri kai da ita d'in, komai ya wuce." Kanne masa ido d'aya yayi yace" Ka birgeni kai ma, saboda ni da kai duka manufar mu d'aya ce ta tunkarar Zafeera, wato *soyayyar d'an uwa*." Yana gama mak'ala masa ya bubbuga kafad'ar Haman d'in sannan yace" Mu je, lokaci ya yi." Da kallo ya bi Umad d'in sanda ya juya zai fita, jin bai biyoshi a baya ba yasa ya juyo yana kallonshi, murmushi ya sakar masa yace" Come on! Mu je mana." Da k'yar ya d'aga kansa ya jinjina alamar to, jiki a sab'ule ya fara takawa har saida ya kai kusa da Umad, sai kuma ya had'e fuska yana kallonshi yace" Amma dai fatana shi ne a ce babu soyayyarta a zuciyarka, Haman kishinta na ke fiye da yanda ka ke tunani." Ya d'aga k'afa zai fita Haman yayi saurin rik'o hannunshi yace "Umad, ba haka ba ne, ka fahimta mana, ni dama ban tab'a jin son ta a zuciyata ba, kawai ina yi ne saboda yar uwata." Wani murmushi ya sakar masa marar manufa sannan ya fice a d'akin ba tare da ya sake bi ta kan Haman d'in ba, d'akinshi ya shiga inda aka kwantar da mahaifinshi, kwance yake idonshi a rufe yana bacci har yanzu, tsaye yayi bayan ya rufe k'ofar yana kallon mahaifin na shi, a raunane ya girgiza kai yana tambayar kan shi "Wannan wace irin jarabawa ce?" *Lu'u lu'u*? Kowa ita ya ke son samu, kuma dan duniya kawai, babu mai son ta a yanda take sai dan d'aukakar da zai samu ta dalilinta, yanzu ga son zuciya ya d'ora kowa a muk'amin daya dace da shi, mahaifinshi wanda ya haifeshi yana kwance da ciwon son matar da ya ke aure, bugu da k'ari matar nan ta gama haramta ga mahaifinshi saboda abinda ya shiga tsakaninsu. Ina ma kafin ya musulunta ne lokacin bai samu ak'ida ba, da yana iya jarumatar sadaukarwa mahaifinshi ita, sai ya ga me zai faru bayan haka, amma yanzu ko mutuwa ya yi mahaifinshi ba zai tab'a aurenta ba. A hankali y k'arasa kusa da shi ya zauna bakin gadon, rik'o hannunshi yayi na dama mai d'auke da zobuna na alfarma biyu ma su d'auke da dutsin gwal d'aya kuma lu'u lu'u, murza hannun ya shiga yi sanyaye kamar zai fashe da kuka y furta "Abba na." Yanda yake har yanzu haka yake ba wani canji, dan haka ya sake furta "Abba na...bud'e idonka ka ganni, ni ne Umad d'in ka." Duk da bai bud'e idonshi ba amma sai na'urar dake gefen gadon mai daidaita bugun zuciyarshi da numfashin shi ta d'an fara k'ara tin! Tin! Tin. Da sauri ya kalli na'urar sannan ya sake kallon Wudar da k'wayar idonshi ke motsawa duk da idon rufe suke, alamar yana so ya bud'e idon, sake matsawa Umad yayi daf d shi a sanyaye ya sake cewa "Abba..." Sannu a hankali sai kuwa ya bud'a idonshi tare da kiran sunan "Umad..." Cikin wata murya mai gurguri dake nuna jikkatuwa ya yi maganar, da azama Umad ya sake maida hankalinshi akan mahaifinshi ya amsa da "Na'am, ina jin ka Abba na, bud'e ido ka gani ni ne." K'ara bud'a idon Wudar yayi ya sauke a kan Umad ya rik'e tafin hannunshi gam wanda ke cikin hannunshi, shi ma Umad taimaka masa ya yi ya sake had'e hannayen na su da kyau, cike da kulawa da buk'atuwa Wudar ya saka idonshi cikin na Umad yace" Zafeera...Zafeera Umad." Kamar saukar mari haka ya ji maganar da saida ta sa shi rufe idonshi, daidaita nutsuwarshi yayi a hankali ya bud'e idon ya kalleshi, a sanyaye a kuma ladabce yace" Baa, Ayam tana nan lafiya." Cike da damuwa ya nemi tashi zaune yana fad'in" Ka kai ni wajenta Umad, ina so mu yi magana da ita ka ji, ka kai ni wajenta." Mayar da shi yayi kwance yace" Shiiiii! Ka nutsu Abba na, za ta zo, Ayam za ta zo." Kallonshi yayi cike da gigin tsufa yace" Umad, da gaske wai ka aureta?" Zuba masa ido yayi na d'an lokaci da tunanin amsar da zai ba shi, nauyayyen numfashi ya sauke har iskan bakinshi na fitowa kafin ya d'aga bakinshi da k'yar yace" E Abba, na aureta." Da sauri ya zabura ya tashi zaune yana fad'in" Umad kana da hankali? Baka san cewa ni nake so na aureta ba, yanzu matar ta w..." Zunbur raba hannayensu tare da mik'ewa da sauri tsaye ya bashi baya, dafe k'ugu yayi yana feso huci daga bakinshi. Fahimta da ya yi kamar ya fara hassalashi kuma ya san waye shi yasa ya marairaice yace" D'ana, yanzu ba za ka saurare ni ba? Ba za ka zauna na fad'a maka damuwata ba?" Juyowa yayi ya kalleshi ya ma rasa me zai ce masa, ba tare da ya ce komai ba kawai ya juya ya fita a d'akin duk da kuwa yana ci gaba da masa magana, saida ya rufe k'ofar ya kuma sauke wani wawan numfashi sannan ya ja tsaki ya kalli k'ofar d'akin, girgiza kai kawai yayi ya kama gabanshi. *Filin taron* A d'an k'ank'anin lokaci filin ya cika da manyan bak'in da dole zaka san bikin na manya ne, jama'a ne ta ko ina ka kalla, kama daga bak'in da aka gayyata, wasu a tsaye suke yayin da hadimai da kuma ma'aikatan da aka d'aukosu dan rabawa bak'i abun sha da abinci suke ta kai da kawowa, wasu kuma na b'angaren da kujerun zama suke suna zaune, duk wanda ka kalla yana cikin shiga ta alfarma, ko dai jinin sarauta ne ko kuma wani babban ma'aikacin gwamnati. Juman da mahaifiyar Bukhatir da kuma Kossam ne suka fito da Ayam, tana tsakiyarsu cikin doguwar riga kalar ruwan gwal ta tattausan yadi, babban mayafi suka rufe mata kan ta da shi sannan suka saka mata k'ananun abun da suka rik'e mata shi, sannan aka saka mata wani k'aramin kambu a kan ta wanda ya dace da kalar kayanta, sosai fuskarta ta yi kyau ta fito shar shar da ita. A tsanake suka rakata kan kujerar da aka tanada domin su suka zaunar da ita, daidai lokacin Umad shi ma ya shigo falon, Kossam ce ta masa alama da ya zo, a hankali kuma a gadarance ya shiga takowa saida ya zo ya tsaya, kamashi tayi ya zauna kan kujerar shi ma, kallonsu sukayi suka saki murmushi, Kossam wata yar k'walla ta share tare da fad'in "Kun yi matuk'ar kyau sosai, Allah kareku daga sharrin mutane." Da sauri Umad ya d'aga idonshi ya kalleta jin ta ambaci Allah a bakinta, wani murmushin ta kuma sakar masa ta lumshe ido alamar "Kar ka damu." Hannu Juman ta kai kan farantinbsilbar dake hannun adimarta ta d'auki farantin silbar mai d'auke da had'in madara da zuma ta kafawa Ayam a bakinta, yatsina fuska tayi ta d'ora bakinta ta d'an kurb'a sai kuma ta janye bakin, zaro mata ido tayi tace" Shanyewa za ki yi." Turo baki tayi ta sake kai bakin tana sha, saida ta shanye tas sannan ta d'auke mata kofin daga bakinta, mayar da kofin tayi ta aje kan farantin sannan ta d'auki wata dunk'ulalliyar madara wacce had'i ne na musamman ake ba wa amarya a wannan lokacin, shi ma a baki ta saka mata ta b'antara ta taune sannan ta cinye sauran ragowar, shi ma dai tana cinyewa yar k'aramar tasa ta d'auke mai d'auke da zuma a ciki farar saka ta saka k'aramin cokali ta dinga ba ta har sau uku sannan ta aje. Gyara tsayuwarta tayi ta fuskancesu gaba d'aya, akan farantin ta d'auki wata k'aramar kwalbar turare ta mik'awa Umad tace "Sai ka fesa mata." Karb'a yayi ya bud'e murfin ya fesa mata a jiki, lumshe ido dukansu sukayi saboda tasirin turaren, sai dukansu suka daure ta hanyar bud'e idonsu kamar babu wani abu da ya faru. Aje kwalbar ta yi sannan ta d'auki zoben azurfa ta mik'awa Ayam tace" Ki saka mishi a yatsar data miki." A sanyaye ta amsa tana kallonshi shi ma kuma kallonta yake, hannunshi na hagu ya mik'a mata wanda yake sanye da wani zoben a yatsar kusa da k'arama, kallon yatsun na shi tayi da kyau, a hankali ta kai yatsunta biyu ta cire mi shi wannan zoben sannan ta saka mishi na hannunta, kallonta yayi sosai murya kasa k'asa yace "Wannan fa mai daraja ne." Ba tare data boye muryarta ba ta amsa mishi a yaren Italy tace "Shi ma mai darajar ne." Tana gama fad'a ta kalli iyayensu da suma ke kallonsu suna murmushi duk da basu ji me ta ce ba ita, amma zoben na shi d ta saka a yatsarta babba ya k'ara basu sha'awa da dariya, wanda shi ma kuma hakan ya masa dad'i. Da haka Juman ta dinga gabatar da al'adarta har ta ida sannan suka ba wa bak'i damar zaunawa a mazaunansu dan su ci abinci, sosai d'akin taron yayi shiru dayawa saboda kowa mai ji da kan sa ne, bayan k'arar cokula da takalmin hadimai dake yawon raba abinci da kowane teburi babu wata hayaniyar, sai magana k'asa k'asa kawai da hirar mutane ke tashi. Ganin hankalin mutane baya kansu yasa Ayam yunk'urawa tare da fad'in "Ya Allah." Ta mik'e, takawa tayi zata sauka daga matakalar d'aya yace "Ina za ki je?" Juyowa tayi ta turo bakinta gaba tana jujjuyashi tace "To ai ban san an d'ora dokar hana d'aya daga cikinmu tashi a nan ba." Tana fad'a ta juya ta ci gaba da tafiyar ba tare da ta ji daga gareshi ba, da kallo ya bita yana murmushin gefen labb'a, tafin hannunshi yasa ya kama gemunshi dake ta k'yalli yana wasa da shi a ranshi ya ayyana" Rigima ko? To ai na bayar da hak'uri, kuma ma ai halalina ne." Wani murmushin ya kuma saki ya bi d'an k'ugunta da kallo, cije leb'en k'asa yayi ya d'an kawar da idonshi kad'an daga kanta yana tuno yar gajeruwar had'uwarsu da ita. Sake maida idonshi yayi kan ta dan baya jin zai iya kawar da gani gareta na sakan biyu, saidai abinda ya gani yasa ya zaro ido har ya furta "Iyeeeh!" Bai ankara da ya mik'e tsaye ba saida ya ji ya d'aga kafarsa ya taka k'asa, da sauri ya shiga takawa da gaggawa ya isa gareta, yana zuwa yay karaf ya karb'e kofin kwalbar mai shak'e da ice cream dan bak'in wanda take daf da kai wa bakinta da d'an cokalin k'arami. Da sauri ta kalleshi suna had'a ido ta kyab'e fuska tace "Sha zan yi fa, kai ma ka d'auki na ka mana." Hannunta ya rik'e gam a cikin na shi ya d'ora kofin kan wani tebur sannan ya jata zuwa wani corridor da babu kowa sai masu wucewa. Neman fizgewa take saida ya kai ta inda yake da buk'ata kad'ai ya dakata tare da mannata da bangon, saida ya mata runfa da k'irjinshi kamar zai fad'a mata sannan ya k'urawa fuskarta ido, hakan ya haifar da kusanci sosai a tsakaninsu ta yanda numfashinsu ke gauraya, k'asa ta sauke idonta tana wasa da hannayenta wanda bai ko bata damar had'esu wuri d'aya ba, cikin narkakkiyar murya a sanyaye yace "Kar ki sha sanyi kin ji...*Sajeeda*." D'aga idonta tayi ta kalleshi sai kuma tayi saurin sadda kanta k'asa, a hankali yasa yatsanshi ya tallabo hab'arta ya tilasta mata kallon fuskarshi, k'asa tayi da idonta sosai yanda sam bata kallonshi, daf da fuskarta ya sake matsawa yace" Me ye?" A hankali ta girgiza kai cikin gargadar murya kamar zata b'alle da kuka tace" Ka...wai dai...na ji..ka kira...fassarar suna na ne da yarenku." Mamaki ne ya bayyana a fuskarshi yace" Kenan kinsan Ayam yana nufin Sajeeda ne?" A hankali cikin dubara ta d'aga kai tare da fad'in" E." Gyara tsayuwarshi yayi sosai ya sake babbaketa ta yanda ba zata motsa ba yace" Kenan ni ma kinsan fassarar na wa sunan?" Shiru tayi bata amsa mishi ba sai k'ok'arin kawar da kanta da take, sake cewa yayi" Uhum! Ina jinki." Kallon k'wayar idon shi tayi da sauri tace" *Faruk* mana, na sani ai." Murmusawa yayi tare da sake tallabo hab'arta yace" To e ye na hassalar? Ki bani amsa mana da girmamawa." Cikin fad'a ta ture hannunshi tace" Ni ka matsa zan wuce." Har zata rab'ashi ta wuce ya rik'o hannunta hakan yasa ta tsaya cak, juyawa tayi suka kalli juna, cike da sigar tsokana yace" Ba kya tsoron abinda zan miki idan aka ware mana d'aki ne?" Da mamaki ta kalleshi tace" Ware mana d'aki kuma? Haka ka ke tunani?" Gyara tsayuwarta tayi tace" Yallab'ai, ka ga dai ai ina jin kunyarka ko? Kuma ina ganin kimarka da darajarka, to me yasa ba ka ji kunyar abinda ka yi ba?" Cike da danne dariyarshi duba da yanda take maganar yace" Amma ai na baki hak'uri ko? Kuma na ce zan dinga fara bayar da hak'urin kafin na yi yanzu." Hawayen data rik'e tun sanda ya matse mata wuri ne ta ji sun taho mata masu zafin gaske, nunashi tayi da yatsa tace" Dama can da nufi ka yi na farko? To ka sani ni ma n san 'yancin kai na kuma zan k'waci.'yancina." Yatsar da take nunashi da ita ya jawo da k'arfi hakan yasa ta fad'o jikinshi bata shirya ba, matseta yayi a jikinshi sosai ya kuma had'ata da bangon nan, k'ure fuskarta yayi da kallo har ya had'a hancinsu wuri d'aya, cikin taushin murya numfashinsu na gauraya yace "... *Nagode sosai yan uwa da uzurinku gare ni, Alhamdulillah mun gama sabga lafiya.* *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:45 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� _*LU'U LU'U*_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hak'ik'a Allah abun godiya, bayan share wata uku na dogon nazari da samun gamssashen hutu, hazik'ar ta sake dawo mu ku da wani sabon nagartacce kuma zak'wak'urin labari mai taken *LU'U LU'U*, kai dai daga jin lu'u lu'u kasan akwai magana a ciki, rubutun littafin zai zo muku daga alk'alamin marubuciyar nan dai da kuka sani mai *Badak'ala*, *Jihadi* da kuma *Matar mutum*,ma'ana dai ta ku *Samira Harouna* (Meeranku馃榿, Yasin ta ku ce), nasan kunsan labaran kuma kunsan me suka k'unsa, Dan haka zan ce ku garzaya da gudu Dan ku samu rabon karanta n'a ku Lu'u lu'u._ _Farashin mai sauk'i ne masoya, ga duk mai son ta samu n'a ta zata biya naira 200 kacal, ga Yan k'asa ta Niger kuma abar alfahari na zaku biya 400f cfa kawai, soyayya Dan Allah tana saka komai, k'awaye na ku zo mu tafi tare da ku, Dan ba zan Bari a barni a baya ba._ _Yan Niger zaku tura katin Airtel ko Moov akan wannan lambar, *94-98-56-52* sai ku tura shaidarku ta wannan lambar *88-35-50-01*._ Yan Nigeria kuma zaku tura ta wannan asusun *3120244299* Amina Maikudi Abdullahi First bank. ko kuma Recharge card na Mtn Akan lamba 080-38-85-69-44. _Masoya Yan mutan Niger sai mun ji daga gareku, mutanenku ne dai._ _Bismillahir rahamanir rahim_ *43* Cikin taushin murya numfashinsu na gauraya yace "Za ki hak'ura ne ko kuwa?" Sake sunkuyar da kanta tayi tace "Um um." Hannunshi d'aya da ya katangeta ya d'auke yayi saman wuyanta da shi, sannu sannu ya fara kai hannun k'asan rigarta har ya shigar da shi ciki yana k'ok'arin tab'a k'irjinta d'ora tayi ram da shi ta rik'e tana kallonshi kamar ya bata tsoro. Gimtse murmushin da ya so saki yayi sannan ya d'aga girarsa d'aya wanda hakan ke k'ara masa kyau, cikin had'e fuska yace "Me ye?" Kamar doluwa tayi da fuskarta ta hanyar kyab'eta tace "Kai zan tambaya ai, me ye haka?" Sannu a hankali ya matsar da fuskarshi saitin wuyanta har ya kai bakinshi kan fatar wuyan na ta, d'ora labb'anshi yayi tare da bud'esu yanda lemar labb'anshi ya dira kan fatar ta ta wacce ta d'auki d'umi na gyaran da ta sha, luf ya lumshe idonshi ya fizgi wani numfashi ya sauke shi da k'arfi, sai kuma ya sake rufe idon sosai ya fara tsutsar wuyanta sannu a hankali yana shak'ar wani daddad'a kuma sanyayyen k'amshi dake fitowa a sirrince daga jikinta. Yanda ta rik'e hannunshi haka ta kasa sakin hannun, gaba d'aya komai na ta ya tsaya saboda bak'on al'amarin da ya zo mata da shi, tunda suka samu kusancin nan sosai sai ta ja dogon numfashi ya kuma mata gardama wajen dawo da shi ta sauke, tattausan labb'anshi da suka tab'a fatarta yasa ta jin wani irin ni'imtaccen d'umin daya samo asali daga yawun bakinshi, duk da jikinta na fitar da wani sassauk'an d'umi, amma da ta ji na bakinshi sai ta ji kamar ita a cikin k'ank'ara take. Lumshe idonta tayi ba tare data san tayi ba ma sai ita ka ta langab'ar da kanta ta d'ora kan na shi kan dake tsakanin wuyanta, gimtse bakinta tayi saboda jin k'arfi da yaji tana son fito da wani sanyayyan numfashi mai kama da kuka, ga bak'on abun da take ji gaba d'aya illahirin jikinta, kamar ana mata tafiyar tsutsa sai wani yam yam ake mata, ga wani zut zut da take ji a k'asanta kamar tana neman wani abu ido rufe. Sumbatar wuyanta ya ci gaba da yi har saida ya zo daf da bakinta, sai ya d'ora labb'anshi kamar za tsotsa sai kuma ya d'an dakata, yayi haka kamar sau uku sai kawai ya had'e bakinshi da na ta wuri d'aya ya fara tsutsa a hankali. Shiru ta masa bata hanashi ba haka kuma bata kama masa ba, sannu sannu jikinta ya fara mutuwa har ta saki hannunshi dake sama kusan wuyanta daf da k'irjinta har yanzu, yana jin ta saki hannun ya fara yin k'asa da shi har ya kawo kan mamanta da suke cikin bras wacce bata da ciko. Tana jin haka kamar wacce ta farfad'o daga doguwar suma ta bud'e idonta ta zabura, da k'arfi ta d'auke kanta dake had'e da na shi ta sake rik'o hannunshi daya gama shiga cikin rigarta yake rik'e da mamanta, da sauri ya bud'a idonshi shi ma ya sauke kan wuyanta tare da d'auke labb'anshi dake sumbatarta, a hankali ya fara shirin ciro hannun na shi amma kuma sai ya ji ta rik'e hannun na shi sosai, d'agowa yayi a hankali ya kalli fuskarta da idonshi da suka fara kad'awa yace "Hannu na malama." Saida ta d'an wurga masa harara ta k'asan ido sannan ta turo baki kamar zata tsinkashi kafin ta sassauta rik'on data masa, wani murmushi ya saki a gefen labb'a sannan ya zaro hannu daga rigarta, gyara tsayuwarshi yayi ta hanyar d'an bata baya kad'an saboda asirinshi daya fara tonuwa, yana so yace mata "To tafi." Amma kuma sai bakinshi ya masa nauyi ya kasa furtawa, dan haka kawai shi ya fara d'aga k'afarsa da d'an sauri ya bar gurin kamar wanda yayi k'aro da wani mugun gani. *Bayan kwana hud'u* Duka ranakun nan da suka gabata irin shagalin da aka gudanar shi ake sake maimaitawa, sai dai na yau ya fi na jiya bambamcin mutane da kuma k'ayatuwar wurin had'e da canja wata al'adar na gudanar da shagalin bikin amare. Yau ma suna zaune kan wasu sababbin kujerun da aka kawata musu, inda Umad ya shirya cikin doguwar riga har k'asa da wandonta, saidai sak d'inkin irin na tubawa ne, inda rigar ke d'auke da kwalliya a gabanta har zuwa tsagar dake tsakiyarta, da kuma gefe gefe inda shi ma aka tsaga sai hula mai sunan dara bak'a wacce ta dace da kayan. Saida ta duba ta ga kowa hankalin shi na kan abincin da aka cika gabanshi da shi sannan ta zura hannunta a hankali zata tsakuri cake d'in dake gabansu wanda ta ji yawunta sai tsinkewa suke saboda ganinshi, ta lak'ato zata kai bakinta ya rik'e hannun hakan yasa suka kalli juna, cikin rad'a tace masa "D'and'anawa fa zan yi, yawuna gudu suke." Wani kallo ya mata mai kama da tsokana sannan ya jaye hannunta ya kai yatsun bakinshi ya lashe cake d'in na hannunta, lumshe ido yayi yace "Ummm! Ya yi dad'i gaskiya." Bud'e ido yayi ya kalleta yana murmushi yace "Me yasa kika cika kwad'ayi ne wai? Kullum rigimata da ke bata wuce hanaki ciye ciyen nan ba." K'ura masa ido tayi tana auna kalar rashin mutumcin da yake tata mata kwanakin nan, kullul cikin bibiyarta da tsokanarta yake, duk ya bi ya addabeta ya takurata, da gangan zai kai ta mak'ura idan ta bar wurin kuma ya bi bayanta ya mitseta son ranshi, dan jiya ma har zip d'in rigarta ya cire yana k'ok'arin kai bakinshi a inda bata so ya kuma kai wa na biyu ta raba kanta da shi, dan haka yau ba zata tashi ba kuma ba zata yarda ya kai ta mak'urar ba ma. Jaye hannunta tayi daga na shi ta kawar da kanta kawai, murmushi ya mata shi ma ya d'auke kan na shi, yanda yake matseta a bango yana masa dad'i musamman idan ranta ya b'ace ta fara masa wani yaren da bai sani ba, hakan na masa dad'i matuk'a idan ta juyar da harshenta, dan dama tana canza yare ne idan ranta ya b'ace ko ta shiga halin d'imuwa ko kuma mamaki, yanzun abinda ya fahimta game da ita shi ne babu kalar yaren da baya zuwa mata, sai ta furta abinda zuciyarta ta raya mata sai kuma ta koma wulwula ido tana so ta ji wai me ta fad'a ma. Babu abinda ya fi birgeshi kamar idan ya titseyeta ya tambayeta me ta ce? Sai ta gyara kalamanta ta fad'a masa wata fassarar daban cike da girmamawa. Cikin ma'aikatan dake raba abinci ne wani ya zo wucewa da faranti a hannunshi, d'aga masa hannu tayi ya k'araso a ladabce tare da gaisheta yana sunkuyawa, hannu ta kai zata d'auki farantin dake d'auke da wani d'an gassashen nama da parsil an masa ado da shi. Da sauri Umad yace "A'a, me ki ke yi haka?" Kallonshi tayi ranta na neman harzuk'a tace "Yunwa fa nake ji, sai na mutu ne." Kallon ma'aikacin yayi yace "Je ka." Da sauri ya bar wurin dan dukansu kowa d'an sarki ne, babu wanda zai bashi umarni ya kasa bi, tana ganin haka ta sake juyowa ta kalleshi, cike da tausar kanta na wani haushi haushi da take ji wanda da ba haka take ba cikin harshen Arabic tace "Wallahi idan ka cika damu na yanka ka zan yi, haba." Mik'ewa tayi da sauri ta sauka daga kan damdamalin ta nufi hanyar madafa, saida ya ga shigewarta ciki sannan ya saci kallon mutanen wurin ya mik'e shi ma ya bi bayanta. Haman da komai ke faruwa kan idonshi wani guntun tsaki ya ja sannan ya kawar da kan shi cike da k'una da takaicin kasancewar Umad ne mijin Ayam ba shi ba, asara goma da casa'in ce ta same shi, ba ga mulkin ba haka kuma ba ga Ayam d'in ba, shiyasa har yanzu k'udirinshi bai canza ba na burin mallakarta, kuma ko yanzu ya samu dama zai yi yanda zai sameta, tunda dukansu babu wanda ya fahicme shi bare a agaza masa, dan haka inhar ya samu damar aiwatar da wani abun to zai yi. *Ayam* na shiga madafar suka sha kicib'is da Zafreen ta fito tana b'oye abu a bayanta, kallon tsaf Ayam a mata take kuma ta fahimci bata d gaskiya, girgiza kai tayi irin ko a jikina sannan ta rab'ata ta wuce, dan tunda abun nan ya faru ko sannu bata had'asu, mamaki ma Ayam take abinda ya zaunar da Zafreen d'in, dan ita gani take da ita ce da ta koma gaban mahaifiyarta, duk da nan ne ya dace ta zauna wato gidan mahaifinta. Da sauri Zafreen ta k'arasa fita tana b'oye kwalbar gubar dake hannunta wacce ta so zubawa a abinci kowa ma ya ci ya mutu, amma sai ta ji ana shigowa ashe kuma babbar mak'iyarta ce, tana daf da kai wa k'ofar suka had'u da Umad. Babban abinda ya b'ata mata rai ko ya ke had'ata da shi bai wuce yanda yake shareta d'in nan ba, saika rantse d Allah idan ya ganta to makaho ma zai ganta, sam yi yake kamar bai ga mutum ba ta yanda zai iya shiga ta jikinta ma ya wuce tsabar sharewa, k'wafa kawai tayi tana ayyana komai ya kusa zuwa k'arshe, saidai dukkanmu mu rasaka Umad. K'arasa shiga yayi kamar dai bai ganta ba, kuma ya ganta kawai baya son raini ne bare ta kawo masa wargi, k'arasawa yayi kusan Ayam daya samu tana yanka gasashen bredi mai rid'i, jingina yayi kan dask d'in da ta aje ketch up da mayonnaise yana kallonta yace "Me zakiyi haka?" Ba tare data kalleshi ba tace "Ci zan yi, yunwa nake ji sosai, kuma na rasa dalilin da yasa kake hanani cika cikana." Murmusawa yayi yace "Ni ba hanaki nake ba, kawai dai ina kishin na ga kina tauna abu ne da bakin nan na ki a gaban wasu mazan." Kallonshi tayi tace "Amma kai za ka iya cin komai kenan a gaban wasu matan?" Da sauri shi ma ya kalleta yana hango wani abu a k'wayar idonta, sake murmushi yayi ya d'auke kanshi yace "Idan kina so sai na daina." Murgud'a baki tayi tare da yanka bredin a tsakuyarshi, ajewa tayi kan pate sannan ta d'auki kecth up da mayonnaise d'in nan ta had'ase wuri d'aya ta motse, duk yana kallonta hannayenshi hard'e a k'irji yace "Yaushe ne wai zamu tare gidanmu?" Ba tare data kulashi ba tace "Randa kake so mana yallab'ai." A take yace "Gobe ya min, gobe, kin shirya?" D'an kallonshi tayi na dak'ik'u sannan tace "Ba damuwa, ai dai ka shirya ko?" Jinjina kai yayi tare da kallonta yace "Ina so na baki mamaki zuwan goben, ki shirya da kyau." Kallonshi tayi sanda take shafa had'in nan a cikin bredi tace "Bayan wanda ka bani?" Sai kuma ta girgiza kai ta ci gaba da abinda take, sauke hannayenshi yayi ya matso kusanta ya zura hannunshi ta k'ugunta ya zagayo da shi, kwance yayi a gadon bayanta ya d'ora hab'arshi a kafad'arta yace "Wannan ai na musamman ne." Dakatawa tayi da abinda take tace "Yallab'ai wai me yasa ka zama wani iri ne? Dan Allah ka dinga jin kunya ka ji." Da k'arfi ya juyowata gabanshi hakan yasa ta shiga wuk'il wuk'il da ido saboda yanda ya juyota kamar b'era a kwano, had'ata yayi da teburin dake bayanta suna kallon juna yace" Bana da kunya kike nufi?" Da sauri ta girgiza kai tace" A'a ba haka nake nufi ba fa." Sake matseta yayi sosai yana matsa kanshi sosai kusanta kamar zai had'e bakinsu, baya ta dinga jan kanta tare da saka bredin nan a tsakiyarsu tace" Please yallab'ai, yunwa nake ji fa." K'ura mata ido yayi yace" Kwanan nan kin cika son ci dayawa ko?" Galala ta kalleshi tace" Amma ai da ba haka nake ba ko?" Da alamar tuhuma yace" To me ya kawo haka yanzun?" Sinne kanta tayi tace" To ai ni ban saba da zama wuri d'aya bane, nan kuma kullum zaune nake ban aikin komai, gashi da na ce zan motsa jiki sai Mah ta hana ta ce wai ni mace ce ba zan dinga bud'e jikina ba." Tuunda ta fara magana yake k'are mata kallo kamar yana neman wani abu a jikinta, saida ta dasa aya ya kalli idonta yace"... *Alhamdulillah* 01/01/2022 脿 11:45 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *44* Saida ta dasa aya ya kalli idonta yace "Wani abu ne ya ke damunki to?" Kyab'e baki tayi a sanyaye tace "Ni ma ban sani ba." Jinjina kai yayi ya d'an ja baya kad'an yace "To ci." Da sauri ta gyara tsayuwarta ta kai sandwich d'in nan data had'a baki ta gutsira, lumshe ido tayi tana taunawa tana jin dad'inshi a bakinta har kwanyar kanta, kallonta yake shi kuma ya gyara tsayiwarshi kamar ya samu tv. Tana tsaka da ci ko rabi bata ci ba wata hadimar ta shigo ciki, da girmamawa ta sunkuyawa tace "Uwar gijiyata, mai martaba sarki na son ganinki yanzu." Kallon sandwich d'inta tayi sannan ta kalli Umad, ajewa tayi ranta a jagule sannan ta nufi hanyar fit, da kallo ya bita har ta fita sannan shi ma ya bi bayansu. Tana zuwa ta samesu duk tsatsaye, da mamakin yanda suke tsaye wurin da kuma cika d'akin taron da ya sake yi da mutane wanda ke nuni yanzun kamar jama'ar gari ne kuma duk gasu tsaye ta k'arasa ta tsaya tsakiyarsu, gashi duk hankalin mutane ya dawo kansu yanzu, kallon Juman tayi tace "Mah, lafiya ?" Lumshe mata ido tayi alamar lafiya lau, Umad ma na fitowa kai tsaye wajen grp d'inshi na aika ya nufa inda Haman ma na tare da su har kuma shugaban su da sauran abokanan aikin, shi ma dawo da hankalinshi yayi kansu saodai idonshi na kan Ayam, duk wani motsinta a idonshi yake wakana. Sarki Musail ne ya d'anyi gaba kad'an sannan ya d'aga murya yace "Jam'ar Khazira d kewayenta, yau babbar rana ce a gareni da ku baki d'aya, rana da kuka jima kuna tsammanin zuwanta, ranar da wasunku suka shafe shekaru suna mafarkin tambayar yaushe za ta zo? To ga ta ta zo yau, yau rana ce da ni sarki Musail zan yi murabus daga kujerata, sannan na d'ora wacce ta fi cancanta, wacce ku ka dinga tsumayin ganin ranar da zata karb'i mulki daga hannu na, Zafeera." Ya fad'a yana juyowa inda take tsaye sai zazzaro ido take kamar ta had'iyi kunama, sake maida hankalinshi yayi kan mutane yace" Har cikin ziciyata na yarda da sabon tsarin da za ta gina muku, tun kafin na haifi abuta na san da zata kawo haske a k'asar nan, dan haka ina mai baku shawara da ku mata mubaya'a ku bita a cikin tsarin mulkinta, dan wainar da zata toya sai da ku zata toyata, idan har kun amince da haka sai ku fad'a mu ji." Cikin d'aga murya maza da matan suka amsa tare da d'aga hannunsu suka ce" Mun amince, mun amince." Murmusawa yayi ya juyo ya kalli Ayam ya kamo hannunta, irin tsoron dake fuskarta yasa shi d'an rusunawa cikin rad'a yace" Ke fa yanzu sarauniya ce, wannan fuskar tsoron na ki za ta sa talakawanki su rainaki, sannan su miki kallon wacce ba jaruma ba." A marairaice tace" Amma Pah ai dama ni ba jaruma ba ce ko?" Girgiza kai yayi tare da lumshe ido yace" Ba dai 'yata ba, da ba daga tsatsona kika fito ba, sai na yarda idan kin fad'i haka, now smile." Kallon mutanen tayi ta saki murmushi mai kama da kuka, kama hannunta yayi ya d'aga sama alamar ta karb'i mubaya'ar da suka mata, hakan yasa d'akin taro ya kwashi wani irin ihu mai k'arfi da hayaniyar mutane tare da tapawarsu. Har su Musail d'in da su Juman Abdallah duka dake nan tare da ita tapi suke mata suna murmushi, hadimai biyun dake tsaye gefe da wani abu kan faranti ne suka matso kusa, juyo da ita Musail yayi suka fuskanci juna yace "Gwiwarki d'aya k'asa dan karb'an kambunki." Idonta taf da hawaye tace "Pah kar ka d'ora min nauyin jama'a, bana da sha'awar hakan." Cike da k'auna ya shafa kumatunta yace "In Shaa Allah, da izinin Allah subhanahu wata'ala za ki iya Ayam." Tar tar ta kalli k'wayar idonshi cikin na ta, kamar sub'utar baki ba tare da tasan bakinta zai fad'a ba tace "To Pah *mijina* fa? Ya zan yi da aurenshi da ke kaina?" Juyawa yayi ya kalli Umad, wani murmushin shak'iyanci Musail d'in yayi, yaron na birgeshi sosai saboda shu'umi ne, wato har ya gama kassara masa yarinyar sa dai ta ciki da ta waje ? Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya kalleta yace" Kar ki damu da shi, ya amince da hakan." Sake langab'ewa tayi zatayi magana sai ya had'e fuska dole ta k'yale, a sannu sannu ta durk'usa yanda gaba d'aya rigarta ta rufe komai na ta ko k'afafunta ba'a gani, duka gwiwan ta durk'usa ta sunkuyar da kanta, hakan da tayi yasa Musail cire kambun dake kan shi na gwal ya d'ora mata kan babban mayafinta dake saman kai har yana jan k'asa, jin kambun ya hau kanta mutane kuma sun sake kaurewa da tapi da fad'in "Jinjina, sai kin yi sarauniya Zafeera, abun bauta ya tsareki." Sharrrr ! Hawaye suka wanke mata fuska, tallabota yayi ta mik'e ya d'ago fuskarta, girgiza mata kai yayi ganin tana hawaye yace "Bana so fa." Maida kallonshi yayi ga hadiman nan biyu da suka matso, bud'e kyalen sukayi mai k'yalli kalar ruwan zaiba, hakan ya bayyanar da wata kyakyawar sark'a mai kalar ruwan zaiba ita ma sai wani dutsi a tsakiyarta ja mai suffar kan zaki, d'auka yayi ya nufi wuyanta yana fad'in "Yanzu za ki zama sarauniyar Khazira, daga yanzu nauyinsu ya bar kai na zai koma kan..." Sautin k'akk'arfan numfashin Musail ne kawai ya ratsa wurin amma ba'a ji k'arar harbi ba, Ayam dake daf da shi jinin jikinshi ne ya fallatsa zuwa fuskarta da jikinta baki d'aya, kafin ta fahimci me ya faru? Sai ihu da hayanyar mutane ce ta gauraye wurin. Tartsatsin ihun Juman ne ya sa ta firgita ta juya ta kalleta sabda yanda tayi ihun ta fashe da kuka, hakan yasa a rikice ta kalli inda mahaifinta ke tsaye, saidai ina kwance ta ganshi sai neman rai yake amma yana k'i ya ma sa, sai numfashi yake sama sama yana had'iyar abu a mak'oshi, a hankali a hankali kuma idonshi sai suka fara lumshewa, labb'anshi ta kalla da yake furta "La'ilaha illallah, Muhammad rasulillah sallalahu alaihi wa'sallam." D'ago hannu yayi yana son rik'o hannun Ayam saidai take rai yayi halinshi, duka tana kallon komai dake faruwa, a gaban idonta har ya cika da kalmar shahada, sark'ar da yake shirin saka mata ta kalla wacce ya saketa ta fad'i k'asa. Tunda suka ga abinda ya faru Haman da tawagarsu suka bazama da azama tare da sanar da hadiman sarakunan uku cewa su shiga ko ina su duba, Haman da wasu daga cikin yan tawagarsu da gudu suka haura ta inda harbin ya fito, saidai suna zuwa suka samu d'aya daga cikin fadawan sarki Musail kwance shi ma cikin jini an harbeshi, kuma ga dukkan alama shi ne yayi harbin dan kar ya tona asiri shi ma aka kashe shi. Sanda mutane ke ta hayaniya wasu na son fita daga wurin wasu kuma suna lek'a abinda ke faruwa, lokacin Ayam ta dawo daga d'imuwar da tayi na wasu sakanni. Da iya k'arfinta cikin siririyar muryar da Allah ya hore mata ta kwamtsa k'ara tare da dafe kunnuwanta ta durk'ushe a wurin, hannayenta bibbiyu ta kai kan gawar Musail ta fara jijjigawa da iya k'arfinta, da sauri su Bilkees da mahaifiyar Bukhatir suka rik'eta suna k'ok'arin jayeta daga nan, wani harbin bindigar suka ji hakan ya tilasta ma kowa tsayawa cak a inda yake yana zazzaro ido. Zafreen ce rik'e da bindiga da alama a kid'ime take kuma ta sha wani abun, dan idonta sunyi jajir sai layi suke, kan Ayam ta nuna da bakin bindigar nan tace "Kar wanda ya motsa a inda yake, idan ba haka ba sai na harbeta." Cak kowa ya k'ara tsayawa har da Umad dake durk'ushe kan gawar Musail, cike da kulawa yake kallonta yana son hango ta yanda zai farmaketa ba tare da kowa ya ji rauni ba, sake jinjina bindigar tayi tace" Na ce kowa ya tsaya, kar wanda yayi yunk'urin wani abu, idan ba haka ba zan kasheta." Matsowa ta dinga yi sannu sannu tana yi tana kallon gabanta da bayanta, saida ta matsa har daf da Umad sannan tace" Ka ciro min kambun dake kanta." Da mamaki ya kalleta hakan yasa a tswace tace" Na ce ka ciro min kambun, ko kuma in tashi kanta da bindigar nan." Cikin rud'ewa Juman tace" Kin ga Zafreen, ita f..." A tsawace tace" Shiru, shiru malama." Umad ta sake kallo tace" Maza ka yi abinda na ce." A hankali ya fara takawa ya nufi Ayam data tsaya kan k'afafunta amma hawaye na mata ambaliya, hannunshi ya kai ya d'auko kambun dake kanta wanda ya mata kyau sannan ya mik'o ma Zafreen d'in, karb'a tayi da sauri kamar zata had'a da hannunshi sannan ta saka a kanta, kecewa tayi da dariya sannan ta sake cewa "D'auko sark'ar ka saka min." Cike da taka tsantsan ya sunkuya ya d'auki sark'ar sannan ya mik'o mata, sake nuna Ayam tayi da bindigar tace "Ka saka min na ce." Gyara sark'ar yayi sannan ya saka mata a wuya, zai ja baya ya bata wuri saboda ganin Haman sun dawo daga neman maharbin nan, da ido ya mishi alamar su nutsu sannan suyi koma da baya su yi wata dabarar da zata sa kowa ba zai jikkatu ba, yana cikin masa magana da ido kawai ya ji Zafreen ta shak'o wuyan rigarshi cikin halin maye tace "Na ce ina sonka...ina son ka ama..babu wanda ya kulani, to na ji kuje ku rayu kai da ita, amma ka ga yanzu ni ce mai mulki, ni ce saraunyar Khazira yanzu, hatta...da mahaifinka ma..a k'ark'ashina yake yanzu, dan haka..." Ba tare da tunanin komai ba ta d'ora labb'anta a na shi labb'an, kafin ya ankara har ta tsotsi bakinshi sannan ta raba bakinsu tana mashi wani mayataccen kallo tace" Ina son..." Bindigar ta d'ora a cikinshi da niyyar ta harbeshi Ayam da ita duk su rasa, yana jin ta d'ora bindiga a cikinshi yayi sauri cikin dabarar fad'a ya juyar da hannunta zuwa cikinta, kafin ta ankara da ina bakin bindigar yake ta danna kunamar, hakan yasa ta tashi kanta da bindigar, take ta k'walalo ido ta jimk'e rigarshi sosai, sannu sannu ta fara sulalewa sai gata k'asa kwance cikin jini. Jaye jikinshi yayi hakan ya sake haifar da turmutsutsu, a nan ma dai yau saida aka kira ambulance da suka tafi da gawawwakin, saidai ko ba komai yanda Musail ya cika da kalmar shahada haka gawarshi ta samu mutuntawa har da zubar hawayen talaka, inda aka kaisu mutuwa kafin gari ya waye a kaisu gidansu na gaskiya, mutane kuma suna ta cecekucen waye ya kashe sarki Musail? Wanda ba'a gano hakan ba, saidai ko ma waye an tabbatar ba zai wuce da hannun Zafreen d'in ba. Juman da Ayam sun gigice musamman Ayam da ke d'auke da jinin mahaifinta a jikinta, Juman kalamai d'aya take ta fad'a a bakinta har yanzu shi ne "Mah ko gafararsa ban rok'a ba, ban nemi yafiyarsa ba akan abubuwan da na masa, ya sadaukar da rayuwarsa a kai na da 'yata, ya zauna da mak'iyanshi da murmushi a fuskarshi, na nuna masa k'iyayye ya had'e ya shanye Mah, ya zanyi yanzu? Ya zanyi Mah? Ina son mijina, wallahi ina son mijina." Ayam kuma wuri d'aya kawai take kallo sai in ta k'yabta da k'yar, hakan yasa Bilkees ta kalli Umad tace" Ka je da ita d'akinta, ka kwantar mata da hankali, ni zan zauna da Juman a nan." Jinjina kai yayi sannan ya kama hannun Ayam bata ma san yayi ba har suka je d'akinta, zaunar da ita yayi bakin gado ya shiga ban d'aki, ruwan wankan ya had'a sannan ya fito ya kamata, saida ya tsayar da ita tsakiyar ban d'akin yace" Ki yi wanka ga ruwa nan, idan kin kammala ki d'aura alwala." Shiru kamar bata san yanayi ba, dan haka ya juyo ya fito daga ban d'akin ya rage kayan jikinshi sannan ya koma. Duk da ta fahimci singlet da dogon wandonshi ne a jikinshi, amma sam hankalinta ba nan yake ba, musamman bandejin dake nad'e tun daga kafad'arshi zuwa hannu wanda Haman ya cire mishi harsashin da aka harbe shi ranar nan, duk d tana jin kamar ta tambayeshi, amma ina gaba d'aya komai na ta ne ya tsaya. Gabanta ya tsaya k'ik'am ya fara zare mata zip d'in riga, da a hayyacinta take ba zata tsaya ba a yanda suke d'in nan, amma sai gashi ya rabata da komai ya rage daga pant d'inta sai bras farara k'ar da su, jawota yayi jikinshi kamar ya rumgumeta sannan ya b'alle mata bras, tana jin haka wasu hawaye masu zafi suka taho mata har suka sauka kan kafad'arshi. Cire mata yayi sannan ya sunkuya ya zage mata pant d'in, shi kanshi sai yake jin wani nauyi nauyi, watak'ila dan ko waccen ranar bai wani ganta sosai ba ne, yana ajiye kayan ya jata zuwa k'asan shower ya sakar mata ruwa masu d'umi. Wanka ya mata da sabulu tas sannan ya d'aura mata towel suka fito har yanzu tana nan kamar gunki, kan gadon ya zaunar da ita sannan ya d'auko man da ya gani ya zo ya fara shafa mata, jefi jefi ya kan kalli fuskarta, amma yanda idon nan nata masu abun al'ajabi suka yi ja sai yake jin tsoron kallonsu, gashi shi take kallo bata ko k'yabtawa sai an d'auki lokaci. *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:46 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *45* Tattausan kayan bacci ya d'auko mata dogon wando da rigarshi mai k'ananan hannaye farare tas masu tambarin sunan Rundahao, saida ya zaunar da ita yana k'ok'arin kwantar da ita sai ta dage ta k'i kwantawa, zaune yayi yana fuskantarta, ita ma shi ta kalla a lokacin suka had'a ido, a tausashe yace "Saki abinda yake ranki Sajeeda, bari hakan a zuciya zai haifar miki da damuwa." D'aga mata gira yayi yace "Yi kuka, yi kuka ki k'oshi Sajeeda." Kamar ya bata lasisin sai kuwa ta fashe da kuka iya k'arfinta, take ya lumshe ido saboda ji yayi kamar ta karci zuciyarshi da k'arfe. Jawota yayi jikinshi ya kwantar yana shafa bayanta alamar rarrashi, saidai bai ce mata k'ala ba ya bata damar kokawa dan rashin hakan zai zamar mata matsala. Saida ta ci kuka mai isarta daga nan har bacci ya d'auketa tana ta ajiyar zuci, gyara mata kwanciya yayi ya rufeta da abun rufa sannan ya koma ban d'aki yayi wanka shi ma ya d'auro alwala ya dawo, sallaya ya shinfid'a sannan ya kabbara sallah yayi raka'a takwas sannan ya sallame, mik'ewa yayi ya sulale ya fice kai tsaye d'akinshi ya nufa. Wudar ya samu idonshi rufe alamar bacci yake, saidai duk da ba wani tsaye yayi ya dubashi ba ya dai fahimci ba wani sauke numfashi yake ba, sharewa kawai yayi dan abinda ya fito da shi ba na wasa bane, mahaifinshi kuma yana ganin idan ma yayi gigin tashinshi zai kuma cakula masa lissafi ne da maganar matarshi. Dan haka ya rab'ashi ya wuce zuwa wajen da kayanshi suke ya canza sannan ya d'auki k'aramar bindigarshi ya saka a k'ugu sannan ya fita a d'akin a hankali. Tunda ya duk'ufa a cikin gidan nan daga inda aka yi harbi har zuwa gawar wanda aka samu, dagewa yayi da taimakon su Haman da sauran tawagarshi har saida suka gano bakin zaren, daf da asuba ya dawo gidan ya shiga d'akinshi dan canza kayanshi, abinda ya fara tsaya masa a zuciya shi ne yanda ya bar mahaifinshi haka ma yanzu ya same shi, sai hakan ya d'an jefa masa shakku, tunda dai ai mai bacci ya d'an motsawa ko da cikin baccin ne har kwanciyarshi ta canza, bare kuma shi da ba lafiya ce da shi ba. Da sauri ya k'araso gare shi ya kai hannunshi kan fuskarshi ya tab'a, sanyi k'alau ya ji kamar komai baya tafiya, da sauri ya sunkuya ya sake kai hannunshi kan wuyan shi ya tab'a, a rikice ya d'ago hannunshi ya rik'e wuyan hannun yana sauraren harbawar jijiyarshi, a kid'ime ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Pah! Pah ka tashi ! Pah kar ka min haka kai ma dan Allah, ka tashi." Cakumar rigarshi yayi ya rumgume ya tusa kanshi ay k'irjinshi yan hawaye, mutuwa dole ce ga duka mai rai, saidai ya ji zafin ta mahaifinshi daya kasance ya tafi ba tare da ak'ida ba, sannan ya tafi da ciwon son matar da yake aure, sam hakan bai masa dad'i ba. Masarautar Khazira dai sai ta sake rikicewa saboda mutuwar sarakunan nan guda biyu a lokaci d'aya, haka aka wayi safiyar gidan a kid'ime a kuma gigice ana ta shirin kawar dasu zuwa gidansu na gaskiya. Shaf ya manta da Ayam dake d'akinta, ya manta ita kanta a wani hali take na d'imuwa da kewa, sanda yake rumgume da Kossam dake kuka ne kawai abun ya zo masa a rai, da sauri ya d'an janyeta a jikinshi a ladabce ya mik'e da sauri ya nufi d'akinta. A k'ofar shiga sukayi kicib'is da ita ta fito, sanye take cikin wani irin shiri na ban mamaki, sak ta fito a sarauniyarta ta k'asar Khazira, hatta da kambun da mahaifinta ya saka mata da sark'ar da ya so saka mata saida ta sako sannan ta fito, fuskarta kuma a tamke take ba alamar fara'a bare tayi wasa da wani. Cak ya tsaya yana kallonta bakinshi da ya masa nauyi ya d'aga yace "Ay...ina zaki je? Ya haka?" Ba alamar fara'a tare da ita fuska a gimtse tace "Zan je ga kujerar da mahaifina ya bari, ba zan zauna na yi ta kukan rashinsa ba, zan d'auki mataki akan wad'anda suka kasheshi." Hanya ta kama zata rab'ashi ta wuce ya rik'o hannunta, juyowa tayi suka had'a ido a d'an kausashe tace "Sake ni." Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya saki hannunta, juyawa tayi zata wuce a tsanake yace "Mahaifina ya rasu." Cak ta tsaya ta juyo ta kalleshi, sai ta ji ba dad'i sosai, a hankali ta tattare rigarta dake jan k'asa ta dawo gabanshi ta tsaya, kallon juna suke kalar zasu had'e kansu, a ladabce ta furta "Kai...ma ka yi rashin mahaifi? Yanzu mun zama...marayu kenan?" Kuka ne ya k'wace mata da sauri ta fad'a jikinshi ta fashe da kuka, daddab'ata ya dinga yi yana fad'in "Shiiiii! Ki daina kuka kinji, In Shaa Allah Ayam ba zan bari ki yi maraici ba matuk'ar ina raye, ban sani ba dai ko ni..." Bata sanda ta d'ago ta d'ora yatsarta a kan labb'anshi ba tace "A'a..." Sai kuma tayi shiru ta sunkuyar da kanta, binta yayi da kallo yace "Uhum?" Cike da kunya tace "Ba zamu zama marayu ba, muna da iyayenmu masu k'aunarmu." D'aga idonta tayi a hankali ta kalli k'wayar idonshi tace "Kuma ni ina da kai, sannan kana da...ni kai ma." Rintse idonshi yayi gam ya cakumi bakinta ya shiga tsutsa a zafafe saboda bai tsammani jin abinda ta fad'a ba yanzu, saida ya tsotse man data shafa a bakinta tas sannan ya saketa suna kallon juna. Rufe idonta tayi ta sunkuyar da kai, amma sai ta ji idonshi na ta yawo a jikinta, da sauri ta wuceshi ta nufi hanyar fita har da d'an gudunta ta bar wurin. Saida ya ga b'acewarta sannan ya girgiza kai yana murmushi ya bi bayanta dan ana shirin tafiyar jana'izar sakaranan na su ne ya kubto ya taho. Dayawa sun so a tafi da Wudar zuwa kasarshi inda shi ma zai samu gatan da kowane sarki ke samu idan ya rasu, amma sai Umad ya ce tunda har ya mutu a nan to anan ubangijinsa ke son a binneshi, ba buk'atar sai an canza masa k'asa. Saida rana ta hantse sosai aka yi bisar gawawwakin, inda Sarki Musail ya samu tagomashin da duk wani musulmi dake wurin ya sallaci gawarsa, sab'anin Wudar da d'aukarsa kawai aka yi zuwa makwancinsa. Bayan an dawo daga bisarsu ana ta hada hadar karb'an ta'aziyya, Kossam kuma da hadimanta sun yi shirin komawa Giobarh dan tayi takaba a d'akinta, gaba d'aya cikin gidan shela ta karad'e kunnen kowa cewa sarauniyar Khazira na son ganin kowa da kowa a filin taro. Duk wanda ya ji haka yayi mamaki, saidai haka suka mik'e suna tunkarar filin taron dake d'aukar dubannin jama'a, hatta wad'anda ke kurkuku saida ta sa aka fito mata da su daga ciki har da Dhurani. Ba iya talakawan garin ba ne kad'ai, har da manyan mutanen da suka halarci jana'iza sun zo su ji me zata fad'a, haka ma akwai wasu sarakunan na wasu garuruwan da masu garin wasu k'auyuka da dagatawansu, hakimai, malamai da dai sauransu. K'us k'us k'us kawai ke tashi ana yi ana kallon kallo ana jiran fitowar ta, dayawa sun zo ne dan su ji me za ta fad'a haka me mahimmanci da sai yanzu za ta fad'eshi bayan mahaifinta yanzu aka kaudashi? Shin sabon tsarin da suke tunanin zata kawo musu ne za ta fara da gaggawa haka? Ko kuma dai game da rasuwar mahaifinta ne ? Da gudu gudu fadawan suka fara shigowa suka layu a ind zata fito ta tsaya sun k'ame sos1i sun kuma cije ba wasa, hakan yasa kowa yayi shiru ya kuma nutsu aka zu a ido kan k'ofar da suka shigo. K'was ! K'was! Sautin takalminta masu tsini suka shaidawa kowa shigowarta, girman kujerarta da d'aukakar da Allah ya bata yasa kowa dake nan hatta da Juman dake tsaye tana hawaye a jikin Bilkees, da ita kan ta Bilkees da Kossam sai da suka rusuna tare da masu rusunawa, wani irin kwarjini ne Allah ya bata, musamman yau data fito fuskar nan a had'e, dole duk wani dake k'aqa da ita ya bata girman da Allah ne ya mallaka mata. Tsaye tayi inda fadawan suka gyara tsayuwarsu su ma kamar yanda take fuskantar mutane, kowa da kowa taje kallo kafin ta d'an gyara muryarta a nutse ta had'e tafukan hannayenta tace "Gaisuwa a gareku." Amsawa sukayi da "Gaisuwa sarauniyar mu." Yanda suka amsa kamar gurin zai tsage biyu, yanda ta sake nutsuwa tana kallonsu yasa su ma suka yi shiru suka maida hankalinsu kan ga. A nutse cikin dattako da k'arfin hali tace " Jama'ar Khazira, na san kowa na cike da son jin dalilin da ya sa na tara wannan taron yanzu da gaggawa, ba komai yasa na kira taron nan ba sai wasu abubuwa da ke kan faru." Gyara tsayuwa tayi ta kallesu da sigar mamaki tace" Shin mutanen Khazira zuciyarku ta mutu ne da har wasunku suke bacci da mafarkin ni Zafeera zan zo na canza muku rayuwarku? Wacece ni? Me kuka d'auke ni? Ni ma mutum ce kamar ku, me yasa da aka zauna aka fad'a muku tatsuniya a kai na kuma kuka yarda? Ba kowa ba ce ni kuma ban ga wata tsiya da zan iya tsinana muku ba, labarin zuwana duniya ya isa kunnen masu ci da ceto ne a cikin kowane irin addini tare da tasirantuwa kan son d'aukar fansa, hakan yasa aka k'ullawa iyayena mak'ark'ashiyar da su kansu suka yarda zasu haifi zab'abb'iya, ku ji da kyau, ni nan na fad'a babu wani zab'abb'e bayan fiyayyen hallita wanda ba'a haifa ba ba kuma za'a haifi kamar sa ba." A sanyaye muryarta na rawa tace" Duk wasu abubuwa da nake yi ko ake gani a tare dani ba komai ba ne fa ce k'udurcewa da kukayi a ranku lallai ni d'in zab'abb'uyarku ce, idan har akwai wani abu da zan iya cewa ubangiji ya min da ba kowa ya ma ba, ba zai wuce canza yare da na ke yi ba musamman idan raina ya b'ace ko kuma na shiga mamaki, bayan wannan babu wani abu daya zama daban da na ku yan uwa na, da wannan nake kira gareku a matsayinku na mutane masu daraja, ku mik'e tsaye ku saka yayanku su yi karatu, ta hakane ci gaban da kuke tsammanin zan kawo muku ni kad'ai, bilyoyin matasa irina zamu kawo muku shi, ku kashe Zafeera a zuk'atanku, ku manta da wata Zafeera a shafin zuk'atanku, ku dage sannan ku maida tunaninku ya zama yanda zaku kawo ci gaba da hannayenku a k'asarku, jiran wani ya kawo maka ci gaba shi ke mayar da kowace k'asa baya, amma idan kai mai k'asar kayi tunanin ciyar da k'asar ka gaba, to za ka cimma nasara." Gyara tsayuwa ta sake yi tace" Jiya zuwa yau ne kawai 'ake sarauniyar Khazira, kafin mahaifina ya bani mulkin nan na fad'a masa bana sha'awarsa, dan na fi buk'atar siyasa akan sarauta, a yanzun ina sarauniya ne kawai dan na fad'a muku ku tsaya da k'afafunku sannan ku tsayar da shugaban da kuka ga ya cancanta ya mulkeku, amma ni Ayam...zan ajiye mulkin nan sannan na tafi tare da *mijina* dan na masa bauta a gidan aurenmu, ina fata ba zaku fahimce ni ba daidai ba? Sannan ba zaku kirani marar adalci ba, na sani ta ko ina wani babban matsayi ne ke bibiyata, amma dai mulkin Khazira ya fi k'arfin iyawar Ayam, duba da yanda mahaifina ya rayu a tsakanin makirai, wanda hakan yasa ban rayu tare da su ba sannan aka dinga farfagandin cewa mahaifina yana son kashe ni, sannan ni ce zan zama silar mutuwarsa..." Hawaye ne suka sauko a kumatunta ta d'an sunkuyar da kai, jima kad'an ta d'ago ta share hawayen tace" Na yarda a wannan karan, na yarda ni ce zan zama silar rasuwarsa, tunda gashi duk ni na jawo komai...." Fashewa tayi da kuka ta sunkuyar da kanta, a hankali ta d'auke kambun da yake kanta ta d'ora akan farantin da wata hadimar ta matso tana fad'in" Ba zan iya rik'e wannan ba, gashi nan a ba wa wanda ya cancanta." Yanda abun ya daki zuciyar kowa yasa talakawa wasu suka fara kuka suna fad'in" Hugabarmu kar kiyi saurin d'aukar wannan matakin, zamu so ki mulke mu kamar yanda marigayi yayi mahaifinki, zamu zama masu biyayya a gare ki." Girgiza kai tayi a sanyaye tace" Idan har akwai wani abu da zan iya yi muku a yanzu bai wuce na baku shawara kan ku samu madogara, ku samu ak'idar data dace da ku, nufina ku shiga addinin musulunci, dan shi ne zai haska muku rayuwarku har ku kai ga gacin da kuke da buk'atar kai wa." Wasu ne suka amsa da" Addinin musulunci?" Jinjina kai tayi tace" Addini na, addinin mahaifiyata, addinin mahaifina kuma addinin mijina, duk da mahaifina yana addinin musulunci, bai samu damar janyo ra'ayinku ba saboda magauta, amma ni ina mai baku shawara da in kun ji zaku iya ku shiga, dan addini na ba addini bane da ke tilasta wanda baya ra'ayi shi ga, sharad'in shi dai ne idan ka shiga baka fita, idan kuma ka fita bisa bayar da mashirmancin dalili to hukuncin kisa na hawa kan mutum." Cire sark'ar nan tayi ta mik'awa wata hadimar, sake had'e hannayenta tayi za ta musu sallama, sai kanta ya sara da k'arfi sosai, d'an lumshe idonta tayi sai kuma ta bud'e ta kallesu da kyau, a sanyaye sosai yanda ba kowa ya ji me ta ce ba tace" Na barku lafiya." Bud'e ido tayi sosai ta taka k'afata ta kuma juya da niyyar barin wurin, mugun jiri ne ya kwasheta sai kuwa ta sulale tayi k'asa ta fad'i, musulman ciki ne suka furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Inda hadiman dake kusa da ita suka rufa a kan ta, da gudu Juman da Kossam du sukayi kanta. *Umad* dama bai halarci taron ba yana d'akinshi yana kallon komai ta na'ura saboda tunda ya ji maganar taron hankalinshi bai kwanta ba, dan haka ya dasa na'urar d'auka yake kallo ta computer, ganin haka kuma shi dai bai ga alamar harbi ba haka kuma ba alamar wani abu daya faru. Da mugun saurin da bai san yana da shi ba ya mik'e da gudu ya fito a d'akin ya nufo d'akin taron, yana zuwa ya ratsasu ya wuce ya tallabeta ya mik'e, da sauri su Juman duk suka rufa masa baya suka bi bayanshi har saida ya kai ta d'akin Juman din ya sauke a kan gado, da azama ya kalli Juman yace "A kira likita." Zaune tayi kusan Ayam d'in tace "Ina zuwa." Ruwa ta kai hannu ta d'auka dake gefen gadon cikin jug na tangaran fari k'ar da shi ta zuba a hannunta sannan ta shafa mata a fuska, a hankali ta fara motsawa har ta bud'a idonta, ajiyar zuciya suka sauke inda Juman ta d'an bud'a idon Ayam d'in, jim tayi tana kallo sannan ta kawo hannunta ta kalli tafin hannunta. Murmushi ta saki hakan yasa Ayam kallonta Umad ma haka, cike da jin kunya yace "Mah, me ya sameta ne? Ko farmaki ne aka kawo mata ?" Mik'ewa Juman tayi tsaye ta zagaya bayanshi tana murmushi tace "Farmaki ne." Hankali tashe yace "To amma daga ina haka?" Gimtse bakinta tayi ta matsa kusan Kossam da ita ma ta zabge sakamakon mutuwar na ta mijin, cikin kunne ta rad'a mata magana hakan yasa suka saki murmushi duk da halin alhinin da suke ciki, matsawa Kossam tayi kusanshi ta kama kunnenshi ta murd'e tace" Ja'irin yaro ashe abinda ka zo ka yi kenan? To farmakin daka kai mata waccen daren ne ya bayyana kan shi." Juman da Bilkees duk k'yalkyalewa sukayi da dariya, shi kuma sam bai fahimci inda suka dosa ba dan haka ya kallesu da mamaki yace"... *Ku yi hak'uri da wannan, sannan kuyi hak'uri da ji na shiru kwana biyu, matar yayana ta haihu shiyasa.* *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:46 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *46* Shi kuma sam bai fahimci inda suka dosa ba dan haka ya kallesu da mamaki yace "Kamar ya Mah?" Dungure masa kai tayi tace "Shak'iyi, ciki ne da ita to." Wani irin zaro ido Ayam tayi ta wangale bakinta gaba d'aya ta rarraba idanunta akan su, shi ma da sauri ya kalleta yana wulk'ita ido da mamaki, sosa k'eya ya fara cikin sand'a ya sulale ya bar d'akin, Ayam ma sauka tayi daga gadon tana kallon k'eyarshi tace "Yallab'ai tsaya, dakata mana, wallahi ka zo..." Ficewa sukayi daga d'akin kuma dukansu kama gabansu sukayi dan kunya ce ta gaske ta rufe su. Har k'ofar falon suka rakaso zasu tafi, ban kwana sukayi cike da taya juna jimami kafin su nufi motocinsu, tare da Umad suka jera suna tafe inda take tambayar shi "Yaushe za ku taho?" A ladabce yace "In Shaa Allah Mah zamu shigo." Jinjina kai tayi tacce "Ka ga dai yanzu tana buk'atar kulawarka, ka kula da ita ka ji ko?" Jinjina kai yayi yace "Shikenan Mah." *A kwana uku* matan da suka rasa mazajensu takaba suke irin ta addinin musulunci, inda yayansu da masoya kuma suke cike da jimami har yanzu, Umad ma ya koma Giobarh karb'ar tashi ta'aziyar inda suka tattauna da sarki Abdallah lallai lallai zai dawo nan da kwana kad'an dan ya d'auki matarsa. Kwana biyun da yayi bata ganin gilmawarshi sai ta fara fahimta ashe ya mata illa a tsanake, bata tab'a yarda tana jin wani abu a game da shi ba sai kwanan nan, hakan yasa kullum cikin tuna ranakun hidimar bikinsu take, irin yanda yake matse mata wuri, da yanda komai sai ya tab'a jikinta, sai hakan ya zama abokin nishad'inta, uwa uba kuma idan ta dafa cikinta ta furta "Ciki ne da ki? Kuma wai na Umad?" Sai ta saki murmishi mai sauti ta rasa dad'i take ji da hakan ko kuma akasin haka, a yanzu dai bata wani laulayi inba yawan cin abinci ba, duk da mutuwar nan da aka yi bata wasa da cin abinci, idan ta ji cikinta na buk'ata ko kuma ita ce tayi sha'awa ta kan umarci hadimai su wadata gabanta da kayan alatu. *Bayan kwana uku* Lomar farko kenan ta kai bakinta wayarta ta d'auki kururuwa, saida ta kuma kai loma ta biyu baki sannan ta karb'i wayar da hadimar ke mik'o mata, dannawa tayi ta d'auka sannan ta kara a kunnenta a sanyaye cike da sangarta tace "Hello." A tausashe Umad ya amsa da "Hello! Ya kike?" Turo baki tayi tace "Lafiya lau, ya hak'uri?" "Alhamdulillah." Ya fad'a kafin ya d'ora da "Me kike ci?" Hannunta ta kalla dake cikin plate d'in da aka had'a mata kwad'on salade da cocomber sannan tace "Salade." Numfasawa yayi yace "Yana sa ki ci sosai ko?" Kyab'e fuska tayi tace "Um." Murmushi yayi yace "Zai daina, yanzu fad'a min yaushe zaki zo?" Zaro ido tayi tace "Ina?" A hankali ya furta "Gidan ki mana, gidana." Girgiza kai tayi tace "Um um! Na zo ka dinga min wannan abun ko?" Gimtse dariyarshi yayi yace "Wane abu kuma na ke miki?" Shagwab'ewa tayi tace "Ka yi ta tsutsar min baki kana tab'ani ko ina." Da mamaki yace "Ba kya so dama?" Da sauri tace "E." Jinjina kai yayi kamar yana gabanta yace "Shikenan to na daina daga yau." Ita ma kamar tana gabanshi tace "Ka yi alk'awari?" A take yace "Na yi." Jinjina kai tayi tace "Shikenan zan zo." "Yaushe kenan?" Ya fad'a yana gyara zamanshi da yin yar mik'a, a sanyaye tace "Idan na fad'awa Mah." Lumshe ido yayi yana d'an taune leb'enshi cikin wani irin salo yace "Ina... son...ki Aya...m, sai kin zo." Daga haka ya kashe wayar ita kuma ta bi wayar da kallo, murmushi ta tsinci kanta da saki na jin dad'in abinda ya fad'a, aje wayar tayi sannan ta ci gaba da cin salade d'inta hankali kwance. Saida ta kammala sannan ta mik'e a nauyaye tana jin wata kasala ta nufi d'akin Juman, da sallama a bakinta ta shiga inda Bilkees ta amsa mata dake zaune da carbi a hannunta tana ja. K'arasawa tayi ta zauna ta d'ora kanta a kafad'ar Bilkees, hannunta tasa ta rik'o hannun Juman tana murzawa a hankali tan kallon fuskar Juman d'in, tana tsananin tausayin mahaifiyarta sosai, irin yanda suka rayu da mahaifinta da rad'ad'in da take fama da shi yanzun na rabuwarsu kwatsam, sai abun ya nemi cireta a hayyacinta gaba d'aya, sa'a d'aya da mahaifiyarta ta kasance a tare da ita a daidai wannan lokacin, sannan ta zama jajirtatta mai d'ebe mata kewa da k'arfafa mata gwiwa da dad'ad'an kalamai, sannan take tunasar da ita mahaliccinta ne ya so hakan, sannan da tuna mata ita ma zata riskeshi inda ya je, sai komai ya zo mata da sauk'i har wani lokacin idan ta fara hawaye take gaggawar dakatar da su saita maye gurbinsu da ambaton Allah da yi wa mamacin addu'ar dacewa a sabon gidansa. Muryar Bilkees ce ta dakatar da tunanin sanda take fad'in "Ki shirya jirgin asubar yau zai tashi tare da ke, zaki koma kusa da mijinki." Da sauri ta d'aga kanta ta kalli Bilkees d'in, fuskarta data nuna tsufanta take kallo irin ta had'eta ba alamar wasa, turo baki tayi ta maida kanta saman kafad'ar tace "Ni ba gobe ba gaskiya Kaka." Kallonta tayi tace "Kamar ya? Saboda me?" Turo baki tayi tace "To ai shi ma ya ce sai sanda na ke so zan tafi." Da sauri Juman ta d'ago kanta ta kalleta, fizge hannunta tayi dake cikin na ta ranta a b'ace muryarta har hard'ewa take tace "Maza tashi ki bar nan, kuma ki tabbatar kin fara shirin tafiya wajen mijinki da asubar nan." D'auke kanta tayi daga kanta tana fad'in "Bai zama izina gareki ba ki rumgumi mijinki kafin mutuwa ta rabaku." Sai kawai ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da hijab, da sauri Ayam ta gyara zamanta ta dafa kafad'arta tace "Mah kiyi hak'uri dan Allah ki daina kukan, zan tafi to, na tashi ma kin gani ko ? Zan shirya yanzu kuma zan tafi d asubar." Mik'ewa tayi ta kalli Bilkees dake kallonsu ta rasa wacce zata rarrasa tace "Kaka ki ce tayi shiru to, na tafi ai kin gani ko." Da hannu Bilkees ta mata alamar ta tafi, hakan yasa ta juya da sauri ta bar d'akin zuwa na ta, dukanqu saida suka ci kuka har ita kanta Ayam d'in kafin ta fara tattara duk wani abu da ta san zata iya buk'ata a zamanta na dindindin. *Tana* zaune kan sallaya ta idar da sallah isha'i ya kirata a waya, a kasalance ta mik'e ta d'auki wayar dake kan gado sannan ta zauna bakin gado ta d'ora a kunne ta fara da sallama, amsawa yayi a nutse tare da fad'in "Kin wuni lafiya?" A sanyaye ta amsa da "Lafiya lau, ina wuni." A tausashe ya amsa da "Lafiya lau, ya na ji muryarki haka?" A shagwab'e tace "Ba komai." Cike da salo yace "Um um, ban yarda ba, fad'a min me ke faruwa?" Kamar zata fashe da kuka tace "Na fad'a maka ba komai, kawai da safe zan zo nan." D'an zaro ido yayi yace "Ina nan?" A kumbure tace "Wajenka mana." Da mamaki yace "Ayam...kina buk'ata ta a kusa da ke ne?" Langabe kai tayi tana tunanin ta fad'a masa tilasta ta aka yi? Ko kuma ta fad'a masa asalin abinda take ji? Kamar sub'utar baki tace "E." Da sauri sai kuma tace "A'a a'a." Yar dariya yayi yana girgiza kai kafin a sanyaye yace "Ayam, bai kamata ki taho ba tare da kin k'arashe aikin dana fara ba." Da mamaki a fuskarta tace "Aiki kuma? Wane aiki?" Ajiyar zuciya ya fara saukewa sannan yace "Da taimakon ubangiji mun yi sa'ar bin dindigin wanda yayi harbin nan bayan an kashe shi shima, da aka bi dindigin wayar mutumin kira na k'arshe daya amsa Bukhatir ne ya kirasa, yanzu haka Bukhatir na hannun hukumarmu kuma ya amsa laifinsa, wanda ya tabbatar mana shida margayiya Zafreen ne suka d'auki nauyin makashin da mak'odan kud'ad'e, gudun kar ya tona musu asiri kuma sai Bukhatir d'in ya kashe shi, dan haka ki k'arasa wannan aikin kafin ki taho." Numfashi ta sauke tace" Amma ai ka ce kun kama shi, ita kuma yanzu bata raye, me kuma ya rage da zan yi ni?" A sauk'ak'e yace" Akwai." Ita ma a tausahe yace" Me kenan?" Cikin nutsuwa yace" Dhurani, wanda shi ne wanda ya taimaka musu wajen gudanar da shirin, sannan shi ya gabatar musu da maharbin sannan ya samarwa da Bukhatir bindigar da bata da lasisi, sannan ki tabbatar kin tsayar da sarkin da zai mulki Khazira, dan barin Khazira ba sarki tamkar barin k'asar Texanda ne babu shugaban k'asa." Jim tayi kamar bata jin shi, gaba d'aya jikinta yayi sanyi, a sanyaye tana fito da siraran hawaye tace" U...mad, ina so na kwanta a jikinka,... Damuwa ta min yawa." Saida ta share hawayen tace" Please ka bani izinin zuwa da safe gareka, ina neman sassauci." Lumshe ido yayi y cije leb'enshi kamar zai yi kuka, aradun Allah mugun abun take taso mishi daga k'asa, wani irin tartsatsi take saka shi yana ji, dama a d'ane yake tun sanda ake shgalin nan saboda yawan tab'ata da yake, yanzu kuma da tayi maganar ta wata irin sigar d'aukar hankali, shi ma kuma ya d'auki maganar da wata sigar d'aukar hankalin, sai abun yake neman fin k'arfin sa. Shiru yayi ya kasa cewa komai, haka ita ma sai shashek'a da take yi a hankali a hankali, tabbatarwa da tayi ba zai yi magana ba yasa tace "Wa zan d'ora a matsayin sarki? Ni bansan wanda zai iya yin adalci ba, ka zab'a min ?" Da k'arfin bala'i ya fizgo maganar ta hanyar fad'in "A..da...h." A sanyaye baki bud'e ta amsa da "Adah? Sarkin yak'i?" Jinjina mata kai yayi kamar yana gabanta, sai kuma yace "E, mahaifinki bai da amintacce sama da shi, mai halacci ne da kuma amana." Jinjina kai tayi tace "Shikenan, zan gabatar da shi a matsayin sarki Khazira, sarkin k'asar Texanda." A hankali yace "Ya yi kyau." A ladabce tace "Yallab'ai, zan iya neman wata alfarma?" Jinjina kai yayi sannan yace "Uhum! Komai na wa na ki ne." Murmushi tayi kafin tace "Mah, ina so idan mah ta gama takaba ta dawo Giobarh kusa da ni? Ba na so na sake nesa da ita, ina so ta zauna tare da ni." D'an murmushi ya k'ak'aro yace "Buk'atarki ta karb'u, ni ma kuma zan baki mamaki idan kika zo safiyar gobe." D fara'a tace "Wane irin mamaki?" Cikin zolaya yace "Ke wata yarinya, idan na fad'a miki bai zama abun mamaki ba kenan?" Turo baki tayi tace "Na ji to, amma ni ba yarinya ba ce, tunda ni ma na kusa zama uwa." Tana fad'a ta kashe wayar ta aje tana k'yalk'yala dariya, shi ma dariya ya dinga tintsirawa yana girgiza kai ya aje wayar, mik'ewa yayi ya d'auki flask d'in tea ya zuba a kofi sannan ya matsa lemun tsami a ciki ya shanye ya kwanta ruf d ciki dan samun saukin abinda ke damunshi. *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:46 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *47* Mi'kewa tayi da azama ta fita a d'akin, bafaden dake k'ofar shiga d'akinta ta kalla tace "A sanar da taron gaggawa ga duka masu ruwa da tsaki na masarautar nan, sannan a had'a min kan yan jarida." Da girmamawa ya sunkuya yana karb'ar umarnin na ta, wucewa yayi ita ma ta nufi masaukin sarki Abdallah, tana zuwa kai tsaye suka barta ta shiga, ta sameshi zaune a kishingid'e yana danna carbi, zaune tayi tana fad'in" Barka da hutawa yallab'ai.". Murmushi ya sakar mata yace" Gimbiyata, ke ce warhaka?" Jinjina kai tayi ta kalleshi tace" Yallab'ai, mun yi magana da yallab'ai Umad yanzu, kuma ya sanar da ni wasu abubuwa, shi ne nake neman shawararka a kai?" Wani k'ayataccen murmushi ya saki yace" Ki zartar kawai, nasan komai da ya fad'a miki, kiyi abinda ya fad'a ba matsala." Da mamaki tace" Yallab'ai, wai komai yana sanar da kai ne?" Jinjina mata kai yayi a hankali yace" Ya kan sanar dani wani abun dan ya nemi shawarata, yaron kirki ne, shiyasa na fi kowa farin cikin kasancewarshi mijinki." Cikin zolaya ya d'an harareta yace" Duk da dai ma na fahimci kin fara son shi, amma dai ina kan bakana ni ma akan son ki." Dariya tayi ta mik'e tsye tana cewa" Ni ban ce ina son shi ba, haka kawai za'a lak'a min." Fita tayi a d'akin ya bita da kallo yana dariya, girgiza kai yayi yace" Allah ya daidaita tsakaninku, Allah wanzar da farin ciki a cikin rayuwarku." Tana fita wani bafaden ta sa ya nemo mata Adah wanda jimamin mutuwar sarki yasa ko fadar ya daina zuwa yana zaune gida, da girmamawa ya amsa kiranta ya zo, gaba tayi sannan tace" Ka jagoranci ne zuwa ga Dhurani." Da ladabi yace" An gama ranki shi dad'e." Da azama ya shiga gabanta fadawa biyu a bayanta suna take mata baya, a haka sukayi tafiya mai tazara zuwa kurkukun sabah, kallon wurin ta dinga yi saboda yanda ta ga wurin kuma dama bata tab'a zuwa ba sai yau d'in. Har saida suka isa inda Dhurani yake, yana ganinsu shi ma ya taso daga zaunen da yake ya tsaya suna kallon juna, tabe baki tayi tace "Wasu mutanen ba sa da sa'a a rayuwarsu, kamar dai kai d'in nan, da kana da sa'a da kayi nadama aka abinda ka aikata, amma sam babu wannan har yanzu a tsarin rayuwarka, hakan yasa ni Ayam Musail na yanke maka hukuncin d'aurin rai da rai a gidan kurkukun sabah, zaka dawwama a nan ba mataimaki, ba abokin hira ga kuma aiki mai tsanani, sannan ba'a baka damar ganawa da iyalinka ba ko da k'arshen shekara ne." Juyawa tayi zata wuce sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace" Mutuwarka ba zata zama da sauk'i ba, zan iya sa wa a cire min kan ka a yanzun nan, amma hakan zai zama sauk'i da hutu a gareka, ni kuma ba haka nake da buk'ata ba." Wani malalacin murmushi tayi tace" Ka ji dad'in sabuwar rayuwarka." Cikin b'acin rai Dhurani yace" Ke shashasha dak'ik'iya, kin d'auka zan tabbata a nan ne kamar yanda kike zato? To ba zan jima a nan ba, idan na so gobe goben nan zan bar nan, kuma ki zuba ido ki gani, ke ma saina ga bayanki kamar yanda na ga na mahaifinki." Kallon Adah tayi wani kallo dake nuni da sak'o ta aika masa, da sauri Adah ya zaro ido yana mamakin yanda ta bashi umarni kamar yanda mahaifinta ke yi lokuta da dama, wanda hakan har ya zama zaurace tsakaninsu, lallai *jini ya fi ruwa kauri*, da sauri ya kalli mai tsaron k'ofar yace "A bud'e." Da sauri bafaden ya bud'e k'ofar hakan yasa Ayam sunkuyawa kad'an ta shiga ciki, saida ta tsaya gaban Dhurani suna kallon juna, siriri kuma dogon hannunta ta d'aga ta wanka masa marin daya saka shi jin d'ummm! Hadiman da suke tare da ita a lokacin da Adah duk saida mamaki ya kamasu da kuma tsoro, duk girman Dhurani amma ta mareshi har saida ya d'an rank'wafa, rai b'ace tace "Ka sani da ina tare da iyayena tun a waccen lokacin, da baka yi abinda ka yi ba, amma da kayi abinda kayi ina mai maka albishir cewa zan fara nuna baiwata a kan ka, da izinin Allah marin nan da na maka sai ka fara zab'a da ma kasheka na yi da marin nan, ina kuma jiran ganin matakin da zaka d'auka saboda hakan, wawa dadk'ik'i." Tana fad'a ta juyo a hassale ta fice a kurkukun su Adah suka bi bayanta da sauri, suna fitowa daga wurin ake shaida mata an taru ita kawai ake jira. Tana shiga babban falon ta samu yan jarida zazzaune, masu micro da cam茅ra da k'aramin littafi da biro duk kowa jiran d'aukar labari yake, ga kuma dattawa kuma masu fad'a aji na Khazira zazzaune suma a kujeru na alfarma. Shigowarta yasa kowa ya mik'e ya gaisheta kamar yanda ake ma sarakuna, duk da ta aje mulkin amma dai har yanzu a matsayin sarauniya suke kallonta, amsa musu tayi ita ma da martabawa ta d'an adam sannan ta zauna kan kujerar da aka ware dan ita, a bayanta Adah ya tsaya yana zazzare ido ga duk wani da zai iya kawo wargi gareta. Cikin nutsuwa da k'warewa tace "Ba zan tsawaita abinda zan fad'a ba saboda nasan kowa na uzurin gabanshi na datse masa, abinda ya sa na taraku ba komai ba ne sai wata shawara dana yanke, ba kula ni kad'ai na yanketa ba, saida na shawarci magabata na, zan bar garin nan yau, shiyasa na ga bai dace na tafi ba tare dana bar sarki a bayana ba, dan haka zai iya haifar da wani tsurmutsutsun, abisa haka na yanke hukunci d'ora *Adah* a matsayin sarki *Khaizra*, sarkin da zai mulki gaba d'aya k'asar *Texanda*." Gyara zama tayi sannan ta had'e fuska tace" Idan kula akwai wanda bai amince ba ya d'aga hannunsa." Tuni yan jarida suka fara watsawa dan wasu kai tsaye suke fitar da labarin, Adah dake tsaye bayanta kallonta yayi ba ko k'yabtawa, sai kawai ya fashe da kuka ya durk'usa a bayanta tana kuka, dayawa daga cikin datawan Khazira hakan ya musu dad'i, dan haka mafi yawansu suka saki murmushin daya bayyanar da soyayyarsu ga Ayam abisa shawarar data yanke, wanda kula bai musu dad'i ba basu iya d'aga ko da idonsu ba bare su ce uffan, dan idonta na firgitasu kamar yanda suke firgita sauran marasa gaskiyar. Haka ma a labarai duk wanda ya ga hakan dayawa ya musu dad'i, dayawa kuma bai musu ba wannan kuma abu ne da dama dole a same shi, ba kowa zai ce yana son ka ba, saidai iyalin Adah hakan ya musu dad'i fiye da kima, inda suke hango kansu a matsayin masu mulki Khazira a yau? Lallai duniya sabuwa. Ayam dake shirin mik'ewa kan kujerar ta ji Adah yace "Alhamdulillah, Allah idan har mulkin nan alkairi a gareni Allah ka tabbatar, idan kuma sharri ne gareni ya Allah ka karb'i rayuwata yanzu yanzun nan kafin na zalinci wani saboda ikona." Hakan ya mata dad'i har ta sunkuya kusa da shi tace "Hakan na nufin ka musulunta kai ma?" Jinjina mata kai yayi yace "Tare da yallab'ai sarki muka musulunta, kuma na musuluntar da iyalina ma." Murmushi tayi tace "Allah abun godiya, ka nemi taimakon Allah wajen tafiyar da mulkin nan abisa gaskiya da amana, sannan ka yi k'ok'arin sauke hakk'in talakawanka, sannan ka d'orasu akan turban data dace." Dafa kafad'arshi tayi tace "Allah ya tayaka rik'o, ina maka fatan alkairi." Jinjina kai yayi yace "Nagode ranki shi dad'e, kin min hallaci a rayuwa, duk da ina jin dad'in kasancewata sarkin yak'i na mahaifinki, amma dai kin d'aukaka darajata a cikin dubunnai, da yardar Allah ba zan manta da haka ba, kuma zaku ci gaba da kasancewa a cikin martabarku kamar yanda kuke a yanzu, zan nuna muku nima d'an halak ne." Fad'ad'a murmushinta tayi sannan ta mik'e da sauri ta d'agawa yan jaridu da dattawan hannu sannan ta fita a falon, kai tsaye d'akinta ta koma inda garin Khazira ya d'auki haramar sabon labarai. Tunda abun nan ya faru basu had'u da Juman ba, har ta kwanta bacci cike da kewar mijinta. *Tsaf* ta gama shirinta cikin sassauk'an rigar abaya bleue da kallabinta ta yane kanta, dake asuba ce ba hayaniya sosai a gidan, d'akin Juman ta shiga da sallama a bakinta, kan sallaya ta sameta ta rabka tagumi tana jan carbi, har k'asa ta duk'a ta gaisheta kafin tace "Mah ni zan tafi." D'auke tagumin tayi ta kalleta a nutse sannan tace "Allah ya tsare, Allah kiyaye hanya." A ladabce tace "Ameen Mah." Jim ya biyu baya na wasu sakanni sai kuma Ayam ta kalleta tace "Mah, dan Allah karki saka damuwa a ranki dayawa, kinga hakan fa zai iya haddasa miki hawan jini, Mah ! Kin ga dai ke kad'ai gareni yanzu, dan Allah kar ki dinga kuka kinji, ki dinga masa addu'a." Majina Juman ta ja sannan ta jinjina kai alamar to tace "Na ji, zan kiyaye." K'ura mata ido tayi tana kallo kamar bata gamsu ba, a hankali Juman ta kamo hannunta ta rik'e gam sannan tace "Ayam, ki bi mijinki sau da k'afa, ki zama mai ladabi da biyayya a gareshi, ki yi iya bakin ranki wajen kyautata masa, ki zama mace ta gari a wajen mijinki, ki zama yar aljanna a gun mijinki, ki daure sannan ki dage ki zama macen da duk sanda mijinta ya kalleta zai yi murmushi, shawarar da zan iya baki kenan a matsayina na uwa gareki, sannan abu mai mahimmanci da zaki kula da shi Ayam shi ne gyaran jikinki, tsaftar jikinki, kar kiyi wasa da haka, duk abinda kika ga na miki a kwanakin nan ba abun wasa bane, dan haka ki kula sosai sannan ki zama mai gyaran jikinki dan ki zama tauraruwa a wajen mijinki." K'wayar idonta ta kalla tace" Kin fahimta?" Jinjina kai tayi tace" Na ji Mah, kuma In shaa Allah zan yi aiki da abinda kika fad'a min." Jinjina kai tayi ita ma tace" Tashi ki je, Allah ya tsare." Jinjina kai ta sake yi ta mik'e a sanyaye ta fita a d'akin, haka ta shiga har wajen Bilkees da Abdallah sukayi ban kwana sosai har da kukanta sannan suka tafi dreba ya jata zuwa filin jirgi. *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:46 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *48* Awa biyu da rabi suka kwashe a sararin samaniya, babban filin jirgi suka sauka inda mutane mabambamta ke saukowa daga jirgin cikin nutsuwa, da k'yar take d'auke da jakarta tana saukowa a matakalar, yanda ta mata nauyi ji take kamar ta saketa ta fad'i, ta gaji matuk'a abu d'aya kawai take hangowa kanta, tayi wanka ta sha madara mai sanyi sai ta kwanta akan gado ta d'ora kanta a k'irjin yallab'ai tayi bacci isashe. Haka ta sauko har suka fito daga zagayen da aka killace dan saukar jirgin, tana dosowa inda kowa ke jiran wanda ya zo d'auka suka had'a ido, ya hakimce gaban wata mahaukaciyar Ferrari jajir da ita ya had'e hannayenta, kamar yanda fuskarshi ke gimtse haka ita ma bata samu walwala ba da yanayin ganin fuskar ta shi, dan haka ta ci gaba da takowa sannu sannu tana jan akwati mai tayar har saida ta kusa k'arasowa kusanshi sannan ya gyara tsayuwarshi. Ta k'asan ido ta k'are masa kallo cikin shigar k'ananan kayan, kamar dai kullum ya yi kyau sosai, hannun da ya kai ya d'auki akwatin ta bi da kallo, take kuma ta raka bayanshi da kallo dan juyawa kawai ya yi, matse baki tayi tana d'an aika masa sassauk'ar harara, cak ya tsaya a hankali ya juyo ya kalleta. Da sauri ta kawar da idonta da tunanin ko ya ga sanda ta harareshi ne, cikin d'aurarriyar murya yace "Me ki ka saka a jakar nan ne haka? Ta yi nauyi dayawa." Kallonshi tayi sai kuma ta turo baki tace "Kayana ne fa kawai." Fuska a gimtse yace "Amma dai har da kayan masarufi a ciki ko? Dan na ga kin fiye taune taune yanzun." Kyab'e fuska tayi irin gaf take da fashewa da kuka tace "Amma ai ba haka na ke ci ba kawai, dalili ne ya kawo hakan." Da alamar tuhuma yace "Wane dalili ne zai saka ki cinyewa mutane abincinsu na shekara a kwana d'aya?" Zaro ido tayi ta bud'e baki galala, sai kuma ta fara dira k'afafunta tana kukan shagwab'a tace "Da nasan abinda za ka min kenan da ban zo ba, da ma nasan ba wani kulawa dani za ka yi ba, amma Mah ta matsa sai na zo." Murmusawa yayi ta gefen labb'a yana girgiza kan shi, a hankali ya dawo daf da ita ya kama hannunta, hakan yasa kukanta tsayawa tsaf ta kalle shi, janta yayi har suka tsaya daf da motar, gidan gaba ya bud'e mata da hannunshi wanda ya aje jakar k'asa ta shiga sannan ya rufe, d'aukar jakar yayi ya zagaya baya ya saka a cikin boot sannan ya zagayo ya zauna mazauninshi. Saida suka d'auki doguwar hanyar nan kafin ya kalleta yana rik'o hannunta a cikin na shi, kallonshi tayi sai kuma ta yi kasa da kanta, a tausashe ya furta "Ya hanya?" Jinjina kai tayi sannan tace "Lafiya lau." Murmushi yayi yace "Kina lafiya ke ma?" Cike daa kunya tace "Lafiya k'alau na ke." A hankali ya zame hannunshi a cikin na ta, kamar bazata sai kawai ya d'ora hannunshi kan cikinta, sannu sannu ya dinga saukar da hannu har ya kai shi k'asan cikinta ma'ana kan mararta dake shafe, zazzaro ido tayi sai dai bata kalleshi ba sai wani abu da take ji a gaba d'aya illahirin jikinta kamar yana amsawa. Cikin sanyayyar murya yace "Yana cikin k'oshin lafiya?" Rarraba ido ta shiga yi kamar wacce aka kama da kayan mutane, shiru tayi tana jiran ta ji ya d'auke hannunshi daga mararta, amma sai ta ji ma shafawa yake kuma kamar yana jin dad'in haka, dan tuk'i yake da hannu d'aya a nutse yana sakin murmushi, nefi jefi kuma sai ya dinga kallon hannun na shi yana sake shafa mararta yana kallon fuskarta. Jin ba za ta ce komai ba yasa shi fad'in "Ya su Mah da kuma matata?" Da sauri ta kalleshi gabanta ya wani buga da k'arfin data rasa dalilin haka da kuma saurin da bata d'auka tana da shi ba tace "Matarka?" Da sauri ya kalleta shi ma saboda yanda tayi ta kuma wani d'an zabura, da mamaki yace "Me ye?" Wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta girgiza kai alamar ba komai, sannan ya maida hankalinshi ga tuk'i yace "Matata sarauniyar Egypt." Wata sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin kanta da abinda ta ji sanda ya ambaci matarshi, kasa amsa mishi tayi har suka isa gidan. Tarba ta musamman ta samu daga hadimai da kuma yan uwan Kossam da shi kanshi Wudar wanda suka gama makoki, amma dakon jiran matar Umad wanda tsammaninsu ya raja'a kan shi zai zama sarki yasa suka tsaya dan tarbanta, sannan kuma 'ya ga sarkin Khazira sannan sarauniyar Khazira ta kwana d'aya. Yanda suka dinga nan nan da ita kuma kowa fuskarshi a sake sai ta ji dad'i matuk'a har take ji a zuciyarta lallai tayi sa'ar dangin miji. Tunda ya mik'a ta hannunsu ya fita bata sake ganinshi ba, har lokacin da aka kira wata dattijuwa da aka gabatar mata da ita a matsayin k'anwar mahaifin Umad, ta jima a waje kafin ta dawo ta umarci kowa dake d'akin da su fita zata shirya Ayam. Daga ita sai yayarsu Kossam da kuma jakadiyar sarki suka rage a d'akin, a tsanake suka fara tub'eta dan ta fara wanka, yayar Kossam ce ta rakata ban d'aki, ruwa ne na musamman da aka ma jik'e jik'e na musamman da kula had'i turaruka na musamman aka shiga zuba mata a jiki ba tare da an saka mata sabulu ba bare soso. Saida ta tsane jikinta d sabon towel sannan yayar Kossam ta bata madarar turare ta shafe jikinta da shi, suna fitowa ta zauna kan kujera gaban madubi, a nutse suka shiga mata gyaran gashinta wanda yanzun ya taso sosai har yana sauka fiye da wuyanta, sannu sannu suka shiryata tsaf a cikin kaya irin wanda sarauniyar Giobarh kawai ke sakawa, ita kanta data ga kayan sai Kossam ta zo mata a lokacin dan ita ke saka irinsu. *Umad* dake tsaye gaban madubi yana kallon kan shi bayan ya gala shiri, tunaninta yake a d'aid'aice, a hankali yake tambayar kan shi "Ko ta ci ta k'oshi? D'ana saka ta cin abinci yake." Sai kuma ya k'ank'ance ido yace "Ko ya za ta ji idan ta ji maganar nan? Ta gudu daga wani mulkin..." Sai kuma ya yi shiru, sake k'urawa kansa ido yayi, lallai duniya ba ta da tabbas, kwanaki k'alilan mahaifinshi ne ke saka irin kayan nan, masu ado da kwalliya sannan masu zubi biyu, amma yau gashi an saka shi sakasu ba dan ranshi na so ba saidan tagomashin da aka hasasho mishi. Dan Ayam na zuwa aka nemi ganinshi, yana isa fadar ya samu duka dattawan masarautar ne, zaunar da shi sukayi suka fad'a masa taka dokar garin ne barin kujerar nan na kwana uku babu mai mulkinta, dan haka shi ya cancanci hawa kujerar, nuna musu yayi sam ba wannan magana, bai da sha'awar mulki a tsarin shi, kasancewarshi mai aikin da yake so a cibiyar CBT ma ya da kuma kasantuwarshi d'an tsohon sarki ya isa, amma suka nuna su fa a shirye suke da su masa biyayya, sannan sun shirya karb'ar addininshi dan su samu alk'iblar data dace da duka wani mutum mai rai da numfashi, da ya ci gaba da tirjewa ne wazirin tsohon sarki kasantuwarshi mutumin kirki ya sa shi yi masa rad'a a kunne, nan ya tunatar da shi irin tagomashin da hakan zai haifar, sannan ya bashi tsoro da nusar da shi cewa idan fa wani ya hau kujerar ba lallai mutane su karb'i addinin musulunci ba, kenan ko dan wannan babbar falalar ya karb'a dan ya kawo gyara a k'asarshi. Da wannan ne yanzu haka yake tsaye kan k'afafunshi ya yi shiri irin na sarki inda zai je ya gurfana a gaban wani tsoho sannan ya saka mishi kambun da zai tabbatar lallai ya zama sarki, sannan a bashi sandar dake nuni lallai sarkin k'asaita ne. Su hud'u suka shigo d'auke da wani kwando a hannunsu mai d'auke da furanni a ciki farare, mik'ar da ita sukayi suka sakata a tsakiya, biyu na gabanta biyu a bayan ga kuma sauran dangin dake gefe da gefenta, hannu k'anwar mahaifin Wudar ta kai a saman kanta ta jawo wani sange shara shara ta rufe mata fuskarta, hakan yasa ko k'ure mata kallo kaya ba zaka ganeta ba, ita kanta dishi dishi take gani ba dan suna mata jagora ba ga kuma furannin da suke zubawa a wuraren da take d'ora k'afarta. Suna fita a d'akin suka tsaya, a tausashe ta ji an ce "Barka da fitowa ranki shi dad'e." Da sauri ta d'ago kanta saboda ta fahimci muryar da ta ji, muryar da ita ta fara ji a duniya a kunnenta kafin ta mahaifiyarta, muryar da ta jima tana d'aukin ganin mai dauke da muryar, hannu ta kai da sauri zata yaye labulen yayar Kossam ta rik'e hannunta tace "Ba gimbiya kike ba yanzu, ke sarauniyar Giobarh ce." D'auke hannayenta tayi ta saukesu k'asa, a sanyaye ta kalli matar tace "Wannan fa uwata ce, ta ya za'a hanani ganinta saboda Allah ya bani wani matsayi? Ba zan iya ba, zan d'aga na ga fuskarta dana jima ina mararin gani ko da hakan sab'awa dokarku ne." Da sauri ta d'aga mayafin fuskarta ta fito suka had'a ido da Habbee, wani murmushi ta saki mai kama da kuka wanda yasa Habbee sunkuyar da kanta kamar zata durk'ushe tace" Ki gafarceni uwar gijiyata, ka da ki zubar da hawaye ta dalili na." Da k'arfi Ayam ta jawota jikinta suka rumgume juna, kuka ta saki sosai tana fad'in" Na sha wahala tun bayan rabuwarmu da ku, an caza min kai na sosai Mah, an wujijjigani da labaran gaskiya wanda a gareni k'arya ne da farko kafin na yarda da su, Mah ! Me yasa ko sau d'aya baku fad'a min ba? Me yasa ba ku sake zuwa gareni ba? Me yasa Mah? Ina Aba?" Habbee dai a d'arare take neman yakicewa daga jikinta, a sanyaye tace" Ki yi hak'uri sarauniyata, idan kina da buk'ata zan sanar da ke komai daya fara tun daga haihuwarki." Jinjina kai tayi ta d'ago ta kalleta tace" Ina Aba?" Nuna mata hanya tayi tace" Yana fada wajen nad'in sarauta." Yayar Kossam ce tace" Mu je sarauniya Ayam, can muka nufa yanzu." Jinjina kai tayi da zumud'i ta sauko da mayafinta wanda ke nuni da matar sarki ta fi k'arfin ganin idon kowane mutan gari suka nufi fadar data cika tamk'am da dattawa da masu ruwa da tsaki. *A yi hak'uri ba yawa, saboda hidima ne.* *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:46 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *49* Suna isa fadar ba ta iya gane komai ba, sai dai tana d'aukin ganin marik'inta Utais, amma sam bata samu damar ganinshi ba har saida suka sadata da damdamalin da Umad yake tsaye cikin wata shiga ta alfarma, kayan sun masa kyau sun kuma mayar da shi babban mutum, duk da dishi dishi take gani amma a haka ta iya gane shi ne tsaye a gabanta, har kuma ta hangi yana sakar mata lallausan murmushi. Dattijon daya tsaya gabansu tare da kambu a hannunshi yasa suka kalleshi a tare, a hankali Umad ya rusuna gwiwarshi d'aya a k'asa hakan ya ba dattijon damar saka mishi kambun a kan shi, sannan ya mik'o hannunshi na hagu ya saka masa zoben azurfa mai kyau da girma, wata k'aramar takobi ya mik'a masa ya karb'a da hannu biyu, take wurin ya kaure da hayaniya da shewar shikenan ya zama sarki. A hankali ya mik'e tsaye yana sunkuyar da kanshi, wasu zafafan k'walla ne suka d'aso masa a kumatu, a sanyaye a k'asan zuciyarshi ya furta "Shikenan, shikenan nauyi ya hau kaina, madadin matata k'waya da'aya tak, yanzu nauyin dubbanin al'umma ne a kai, Allah ka ga zuciyata, na rok'eka ka bani ikon rik'e nauyin nan da adalci a tsakanin mutane na, Allah ka jib'anci lamurana dana mutane na baki d'ayanmu, Allah ka dafa min komai ya zama mai sauk'i a gareni..." Taffin da aka saka sanda aka saka ma Ayam wani kyakyawan zobe a hannunta da kuma kambun da bai kai girman na shi ba ya dawo dashi daga addu'ar da yake, kallonta yayi ita ma sai kallon zoben take tana jin wani nauyi na hawa kanta, fuskantarta yayi da kyau ya rik'o damatsunta ya juyota gareshi suna kallon juna. A hankali yanda ko na kusa da su bai ji me ya fad'a ba yace "Ki yi hak'uri Ayam." Lumshe ido tayi tace "Me yasa baka fad'a min hakan ko da a waya ba?" A raunane yace "Ban sani ba ni ma Ayam, sai yau d'in nan da kika zo gareni, kiyi hak'uri." D'an murmushi tayi tace "Ka daina bani hak'uri." Kallon zoben hannunta ta sake yi sannan ta kalleshi tace "Hakan na nufin na zama matar sarki yallab'ai Umad? Hakan ya tabbatar min da ni ma nauyi ya hau kai na kenan?" Jinjina kai yayi a nutse yanda ba kowa ya fahimci hakan ba yace "Hakane, da fatan zaki tayani d'aukar nauyin nan Ayam? Ina rokonki da ki kasance a gefena, hakan zai k'aramin k'arfin gwiwar aiwatar da mulkina a tsanake, ki zama mai tausaya min, hakan zai sa na zama mai tausayawa al'ummata, ki agaje ni Ayam, hakan zai saka ni farin ciki har na zama mai fara'a ga mutane na, ki tattaleni ki zama mai sama min nutsuwa a sanda kaina ya d'au zafi saboda girman nauyin dake kai na, hakan zai sa na zama adalin sarki ga jama'ata, na rok'eki." Ya fad'a yana had'a hannayenshi biyu alamar rok'o, da sauri ta rik'e hannayentshi duka biyun tana fad'in" Zan yi, zan yi sarki na, shugabana, farin cikina, kima da darajata, duk kai ne silar dana samesu, zan yi maka komai daka buk'ata, In shaa Allah, fatana Allah ya bani ikon rik'e wannan nauye nauyen, sannan ka zama mai kawar da kai daga kuraraina, ka zama mai tausasa min yayin da na b'ata maka, ka zama mai jink'ai na a sanda na kasa, ka zama adalin sarki a gareni yayin yanke min hukunci, ka zama uba ga wannan marainiyar, ka zama mai sassauci ga laifukana, hakan zai bani azamar kyautata maka." Da fara'a a fuskarshi ya amsa da" Zan yi, zan yi sarauniyata, In shaa Allah." Da murmushi a fuskarta ita ma tace" Na ji dad'i, kuma In Shaa Allah kamar yanda na kasance mata ta farko a gareka, zan k'ok'arta wajen ganin na zama makarantar farko mai inganci a gareka." D'an girgiza mata kai yayi cikin rad'a sosai yace" Matata ta farko, kuma matata ta k'arshe In Shaa Allah." Girgiza kai tayi ita ma tace" Bayan Mah ta fad'a min addinin islam ya yarjewa maza musulmi auren mace biyu, uku, hud'u, idan ba zaku iya adalci bane aka umarce ku da d'aya ko kuma abinda damarku ta mallaka." Janye hannunshi d'aya yayi daga na ta ya lak'aci hancinta yace" To ai saboda ba zan iya adalcin bane nake son k'are rayuwata da ke, ba zan iya had'aki da wata ba sarauniyata, sarauniyar zuciyata." Kallonshi tayi tar tana gimtse dariyarta tace" Ba wani nan, bayan ma d'aukar fansa ce ta had'ani da kai." Dariya ce ta sub'uce masa bai yi zato ba, jawota yayi jikinshi suka rumgume juna cike da shauk'in juna, hakan yasa fadar d'aukar tafi da hayaniya ana mai jin dad'in ganin haka. A wannan wunin basu samu tsagaitawa ba bare su huta, bak'i ta ko ina suka dinga halartar walimar da aka shirya ta zuwan sarauniya da kuma nad'in sarautar, sai gashi hatta da sarakunan wasu k'asar suna zuwa dan tayasu murna da addu'ar alkairi. Ayam ta gaji iya gajiya, gashi duk abinda zata kai bakinta sai da taka tsantsan saboda komai za ta yi sai a ce ita fa yanzu sarauniya ce, bata ma bud'e fuskar ba saboda tsaro bare kuma ta samu damar cika cikinta, gashi tana da buk'atar ta ci ta k'oshi iya iyawarta, amma an k'i bata damar haka. Ta galabaita sosai tana cikin jin haushin yanda aka kasa barinta shak'at jakadiyar sabon sarki ta shigo falon ta sanar da jakadiyarta mai martaba na son ganin sarauniya yanzu yanzu. Da sauri ta mik'e ta bi bayan jakadiyar da tunanin tana shiga ta fashe da kuka tace yunwa zata kasheta, saidai suna shiga nan ma wasu bak'in ne, tawagar ma'aikatarsu ne suka yi tattaki dan tayashi murna da ita kanta, dan haka ya kirata dan su gaisa. Ganinsu duk sai ya sage mata gwiwa ta k'arasa a nutse ta zauna, gaisawa sukayi sosai da girmamata saboda d'aukakar da Allah ya mata, dan in za'a bi salsala ne to gaba da baya ita d'in ba abar banzatarwa ba ce, ba dan tak'i karb'a ba da shi kanshi Umad zai zama k'asa da ita ne saboda kujerarta ke gaba da tashi. Addu'o'i suka musu kafin su mik'e da niyyar zuwa wajen da sauran bak'in suke, da kallo ta bisu har suka fice ta ga an rufo k'ofar, mik'ewa tayi tsaye ta jaye rufin fuskarta hakan yasa kwalliyarta bayyana, kallonta yayi yana murmushi zai fad'a mata kalma mai dad'i, sai gani yayi ta zube k'asa tayi zaman yan bori ta fashe da kuka iya k'arfinta tana dafe cikinta da fad'in "Wayyo! Mah ke! Mahhh ! Shikenan mutuwa zan yi ni wallahi." Da sauri ya zaburo ya zo gareta ya durk'usa yana rik'o hannunta yace "Me ya faru ne sarauniyata? Me ya sa ki kuka?" Tsit tayi ta kalleshi ta turo baki kamar zata tsinkashi tace "To ba yunwa nake ji ba, tunda na zo ban ci na k'oshi ba, komai zai yi sai a wani ce sarauniya sarauniya, ni na gaji ba zan iya ba gaskiya, kawai ka ban abinci na ci na k'oshi." Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi, a sanyaye ya furta "Yunwa ce matsalar?" D'aga kai tayi tace "E." Shafa kuncinta yayi yace "To kwantar da hankalinki, matar sarki ai ta fi k'arfin yunwa ta kasheta sai dai k'oshi." Hannunshi daya d'ora kan kuncinta ta kamo da hannu biyu, lumshe ido tayi ta saka yatsunshi biyu a cikin bakinta, wani d'ummmm ! Ya ji ni'imtaccen d'umi ba mai cutarwa ba, bai san sanda ya furta" Ahhhhhhhhh." Zaman dirshen yayi saboda kxantar da kanta tayi kan damtsenshi tana ci gaba da tsutsa ka rantse loli pop ce take tsutsa, da wani k'arfi k'arfi ya jawo hannunta d'aya ya d'ora kan kuncinshi yan shafawa, a hankali a hankali wasar dake tsakaninsu ta canza zuwa wani salo na daban, rana ta biyu kenan a garesu, had'uwarsu ta biyu kenan a rayuwa, hakan ya k'ara jigatasu musamman Ayam da tunda ta fahimci wani irin girma da mijinta ke d'auke da shi ta tsorata ta kuma zabura zata mik'e, amma haka ya danneta da hannu d'aya har saida yayi nasarar ida nufinshi a kan ta. Sai ga Ayam mai kukan yunwa ta koma na wahala, dan abun ne ya mata yawa, ga rashin k'oshi ga kuma azabar daya gana mata, amma haka ta daure ta k'i nunawa a fuska sai dai ta yamutsa fuska kawai, har saida ya sa aka kawo masa abinci mai rai da lafiya ya kawo mata har d'akin baccinshi kan gado, da hannunshi ya dinga bata tana amsa a kunyace, shi kuma ya k'ura mata ido yana kallo k'aunarta na sake huda zuciyarshi, shi kad'ai yasa me yake ji akan baiwar Allahr nan, shi kad'ai yasan irin abun da yake ji idan yana tarawa da ita, shi kad'ai yasan irin gamsuwar da yake samu a tare da ita, idan har zai iya bud'a bakinshi yayi magana sai yace " *Lallai abinda aka gani a hasashe kenan, shiyasa maza suke haukacewa a kan ta, watak'ila irin albarkar dake tattare a jikinta kenan, shiyasa kowa ke son ta zama tashi, sai kuma Allah ya wanke ya bani.*" Ta so yin bacci da ta k'oshi amma ya hanata saboda yamma tayi sosai, dole ta hak'ura ta zauna a b'angaren na shi shi kuma yana tare da ita, duk masu son ganinshi dole suka hak'ura saboda da an fana musu yana tare da sarauniya dole ka yi shiru. Sai bayan magriba kad'ai ta samu damar ganawa da Utais, tayi kukan rabuwa da sukayi kai tsaye, sannan ta nuna bata jin dad'in duk'a matan nan da suke, haka kuma ta k'uduri niyya a ranta zata nemi sarki alfarmar ya ware musu gidansu na daban ba kusa da ita ba, dan bata so tana ganinsu suna sunkuya mata, dan ita a uwayenta take kallonsu, su kuma har yanzu girmamata suke ba kuma zasu daina ba. *Rayuwa* kenan, sai gashi komai na tafiya daidai, duk da anyi rashi amma dake hukuncin ubangiji ne manta abinda ya wuce, sai suma basu yarda mutuwar iyayensu ta hanasu rayuwa ba, Umad na tafiyar da mulkinsa yanda ya dace, da taimakon dattawan zaurenshi da kuma fasihar matarshi, wacce a zahirin gaskiya baiwarta ke dad'a fitowa fili a yanzun ana gani, indai har zata bashi shawarar yayi kaza, to In Shaa Allah za'a ga da kyau ko da wajen yanke hukunci ne a tsakanin talakawan gari. Sannu sannu sai wani abun mamaki ya dinga bayyana, inda sunan Umad da masarautarshi ke bunk'asa a dalilinta, sai mulkinshi ya fara zama na al'ajabi da d'aukar misali ga sauran masu mulki da sarakuna, ta ko ina maganarsa ake ana bayar da misali da shi, hatta da harkar kasuwanci da Ayam ta bayar da shawara aka kuma rairaye matasa aka sama musu sana'oni, sai gashi Giobarh tafara karb'ar bak'in mutane suna zuwa ci rani a garin. *Bayan wata bakwai* Kallon shugaban yan kasuwan yake yana bayaninshi a tsanake da ladabi, saida ya kai aya kafin ya numfasa ya d'an muskuta, buk'atar da ya zo da ita yana son neman shawara dan yasan matakin da zai d'auka, saidai babban mai bashi shawarar ya barota ta koma bacci saboda sammakon da tayi ta je asibitin cikin gidan ta yi awo, idan ya tasheta yanzu rigima ce ta bugawa a jarida zata saka mishi, idan kuma ya yanke hukunci ba zai samu nutsuwa ba, dan shi kanshi yanzu yake yarda da abinda aka canfa a kanta, har wani lokacin ya kan takura zuciyarshi ta k'aryata abinda ake fad'a d'in, dan a matsayin shi na sarki baya so a ce ya yarda da irin wannan abun ta yanda zai kawo masa cikas a tafiyar mulkinsa, hakan zai sa wata rana ya ji lallai lallai sai da ita ne zai ciyar da mulkinsa gaba, kamar dai yanda mahaifinshi da Bukhatir suka canfa, amma da ya tuntub'i malaminshi sai ya nuna masa ba komai, indai har shawarar ta ta mai kyau ce kuma tana kawo ci gaba, saidai kar ya zama kullum zai shawarce ta kan lamuran mulki saboda wasu dalilai, dan haka yanzun ba kullum yake tuntub'arta kan abu ba. Hohoho! Ina masoya kuma makaranta litattafan hausa novel? Yau ma ga jarumar ta ku ta dawo a cikin sabon littafin ta mai taken *MALLAKINA CE*, *MALLAKINA CE* littafine da ya k'unshi wata irin cakwakiyar soyayya, sark'ak'iya da kuma ban al'ajabi gami da barkwanci, zai fad'akar ya nishad'antar da masu karatu, albarkacin sabuwar shekara da za'a shiga, littafin zai fara zuwa muku *15/01/22*, domin samun na ki da wuri ki/ka hanzarta biya dan karatu cikin salama, ka da ki bari a baki labari maza hanzar ta ki nemi naki akan farashi mai rahusa. Ga mutanenmu na Niger zaku biya katin dala dari Cfa zaku tura akan lamba kamar haka *94-98-56-52*, ga mtanen mu na Nigeria kuma zaku tura Naira 300 ta wannan account d'in 0594148516 lubabatu shehu Gt bank, bayan kun tura sai ku tura shaidar biyanku ta wannan lambar *94-98-56-52* Mun gode sai kun zo. *Alhamdulillah.* 01/01/2022 脿 11:47 - Mom Khalid: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LU'U LU'U* 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *NA* _SAMIRA HAROUNA_ _SADAUKARWA GA_ *'YA'YA NA* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ *Fin* *Fin* *Fin* *50* Kiran da ya shigo wayarsa wacce ba k'ara take ba saidai vibration yasa shi duba wayar, duk da jininshi har gudu ya k'ara saboda son ya kai hannu ya d'auki kiran, amma dake jikin har ya fara sabawa da tsaiko da jan aji irin na sarakai, sai ya zura hannu a hankali ya d'auki wayar, hakan ma wai dan daga shi sai shugaban yan kasuwan ne, da yana tare da babban amintaccen bafadansa ne da shi zai d'auko ya mik'o masa. Danna ok yayi ya kara a kunne yyi shiru, a k'asan zuciyarshi ya tambayeta "Me ki ke so sarauniyata?" A zahiri kuma sai yayi shiru saida ta furta "Sarkina." Lumshe ido yayi sannan cikin nutsuwa ba tare da wanda ke kusanshi ya ji ba yace "Sarauniyata." A shagwab'e ta furta "Ka dawo dan Allah, bana jin dad'i." Tsai yayi da idonshi zuciyarshi na dokawa da k'arfi yace "Me kike ji? Cikin ne?" Kamar za ta yi kuka tace "Bayana ke ciwo, ji nake kamar zai rabe biyu." Kallon shugaban yan kasuwan yayi ya taso daga cikin kujerar yana shirin mik'ewa yace "Ka gafarce ni, iyalina ce ba lafiya." Bai jira amsarshi ba kawai ya fice a falon na shi na karb'ar bak'i hannunshi rik'e da wayar bai kashe ba, ta k'ofar sirri da shi kad'ai ke bi ta nan ya shiga wanda yana bud'e k'ofar ta sadashi da k'aramin falonta, da sauri ya ratsa ta tsakiyar kujerun alfarmar dake zube ya bud'e wata k'ofar, turus ya tsaya sai kuma ya tafi a sukwane gareta yana jefar da wayar hannunshi. Juyowa Ayam tayi ta kalleshi wacce ta sauko daga kan gado tana matse fuska, b'ata rai tayi tana mai rashin jin dad'in ganinshi saboda abinda ta ji a jikinta, ita dai tana baccinta kawai ta ji wani lema mai d'umi na fitowa a k'asanta, tana tashi zaune ta ji abun na dad'a k'aruwa, a k'ank'anin lokaci sai ga ta tayi jagaf a cikin wannan abu da ita take ganin fitsari ne. Zagayowa yayi inda take ya rik'eta yana k'are mata kallo ganin sai tattare doguwar rigarta take marar nauyi, kallonshi tayi a marairaice tace "Sorry...na kasa rik'e kai na, tahowa kawai ya..." Wani zul ta sake ji ruwan nan sun b'allo mata, hakan ya sa ta ja baki tayi gum ta damk'i hannunshi, k'asan data kalla shi ma ya bi da kallo, ganin ba zata iya da abun kunyar nan ba yasa ta durk'ushe tace "Dan Allah ka kira min Mah, ka ce ta zo da sauri wallahi fitowa yake." Zaro ido yayi yace "Yaron? Yaron ne ke fitowa ? Amma fa wata bakwai ne." Yarfa hannunta tayi tace "Ni ban sani ba, kawai ka kira min Mah ni dai." "To to." Ya fad'a yana laluba wayarshi, dan tazara ce mai tsayi tsakaninsu da Mah d'in, hango wayar da yayi a k'asa ya hanzarta d'auka ya saka lambar Mah d'in ya kirata. Ko da Kossam ta zo saida kunya ta kamata, dan matsayinta na babba wacce ta yi haihuwar nan ta san ko menene, hakan na nufin haihuwa ta matso saidai ba lallai yanzu yanzu ba, hakan yasa ta umarceta ta shiga ta gyara jikinta, saidai kafin ta fito daga ban d'aki har ta sake b'acewa, hakan yasa ta ma kanta dubara wajen yin k'unzugun data tabbatar zai tare mata wannan ruwan, ko da ta saka kaya sai ta ji tsaf yanzu, yana zuba saidai baya b'ata mata jiki, tana fitowa ta samu Umad ne a tsaye amma Kossam bata nan, rumgumota yayi jikinshi yace "Kin d'aga min hankali sarauniya ta, na d'auka zaki haifa min yaro bakwaini ne." Cikin fara'a tace "To ai hakan na nufin zan haifi bakwaini ne." Murmushi ya sakar mata yace "Ba zaki yarda ba kema, e yasa to?" Kallonshi tayi tace "Saboda ni ce ke yi." Dariya yayi yace "Allah baki hak'uri Hajiata, tunda magana ce aka fad'a min." Tureshi tayi kad'an a jikinta tace "Ni dai ka tafi ka bani wuri." "Korata ki ke?" Ya fad'a yana k'ura mata ido, girgiza kai tayi tace "A'a, bana dai jin dad'in yanayi na kawai." Rumgume ta yayi sosai yace "Ni wannan bai dameni ba, ke kawai nake so Ayam, ke kawai." Cikin harshen Italy tace "To ai ni bana jin dad'i, salon ka min kishiya kuma ka fad'a mata ni k'azama ce ko?" Yar dariya yayi yace "Dan Allah kar ki fara hassala ki fara canza min yare." A harshen Gallois tace "To idan baka so ka tafiyarka." Raba jikinshi da na ta yayi yace "Idan na k'i fa?" A yaren fulatanci tace "Minkam miwala emi boya on (Sai na kwana ina kuka)." Tsura mata ido yayi da mamaki, d'an shafa k'eyarshi yayi ya sake jawo kugunta tsam ya matse sannan yace "Matar sarki me kika fad'a ne haka?" Matse bakinta tayi sosai ta d'aga kafad'a alamar "Uhum!" Marairaicewa yayi yace "Na rok'eki ki fad'a min abinda kika fad'a?" A harshen hausar da zuwa mata kawai yayi tace "Cewa na yi zan kwana ina kuka." Zaro ido yayi jin ta k'ara b'atar da shi, amma sai wata dubara ta zo masa, jayeta yayi daga jikinshi ya d'an had'e fuska yace "Yanzu ni kika aikawa wannan ashariyar?" It ma kamar yanda ya zaro ido d'azun haka tayi tace "Lahhh! Wallahi ba haka na fad'a ba, cewa na yi fa zan kwana ina kuka." Murmusawa yayi ya jayeta daga jikinshi yace "To na tafi." Gimtse bkinta tayi ta bishi da kallo, tana so ya zauna kusa da ita saidai gaskiya ruwan nan da take ta bulbulowa sun saka ta jin tsantsenin kanta, bare har ta zauna da shi a irin wannan yanayin. *Khazira* Kamar yanda ya zaa sabonshi shiga wuraren da jama'a ke taruwa dan ya ji matsalolinsu da kuma ganin yanda abubuwa ke tafiya, yau ma a shirye yake cikin sassauk'an yadinshi an masa d'inkin riga yar shara, sai wata hula daya saka a kan shi ga bak'in gilashi da kuma face mask daya saka, hakan yasa kowa harkar gabansa yake babu wanda ya kula da shi. Rab'ashi tayi ta wuce ba tare data kula da shi ba, hakan yasa shi juyawa ya bita da kallo, kallo irin na zuciya ta ga abinda take so, da sauri ya juya gaba d'ayansa sannan ya fara bin ta a nutse a nutse, alamu sun nuna masa ko dai 'yar sarki, ko wacce ta shafi sarauta, duk da abaya ce a jikinga, amma hadiman dake take mata baya suna rik'e da ledojin ke nuni ta shafi masarauta kai tsaye. Tunda ya bi bayanta shi ma escorts d'in shi suka bi shi a baya ba tare da yanda kowa ke ganewa ba, dan ba ma a layin da yake bi suke bi ba kasancewar kasuwa ce babba. Daidai motocinsu biyu suka tsaya, da sauri wani bafaden ya bud'e mata k'ofa tunda ya ga ta taho, hadiman kuma suka k'arasa gaban d'aya motar, ganin duk sun shiga da hanzari an tayar da motocin yasa shi juyowa inda escot d'in na shi suke, suna had'a ido da wani ya masa alama da hannu ya d'auko mota, dan in da ido ya masa ba zai gane ba dukansu bak'ak'en gilashi ne a fuskarsu. Cikin hanzari kam aka kawo motocin guda uku da babur biyu da matuk'ansu suka bi bayan motocinsu, doguwar tafiya sukayi har saida suka ga an dunfari shiga wani makeken gida, suna kallo mai gadi ya bud'e musu suka shiga su kuma suka tsaya, a hankali ya furta "Yar sabon sarki ce kenan?" Babban escot d'in shi ne ya juyo a ladabce yace "Ba masaniya yallab'ai, saidai idan kana so za'a bincika." Girgiza kai yayi sanda yake d'aure d'amarar wandonshi dan har ya canza kaya a cikin motar sannan yace "Ba buk'ata, zan sani da kai na." Yana fad'a ya bud'e k'ofar ya fito, duk fitowa sukayi sai ya dakatar da su yace "Yak'in neman aurena zan tafi, ba buk'atarku a nan." Da d'an sauri ya d'aga k'afarshi ya tunkari shiga, mai gadi na shirin rufe k'ofar ya ganshi, saidai yanda ya fito cikin shirinshi na wanda aka sani yasa shi kwasar gaisuwa a mutumce sannan ya bashi hanya ya wuce har yana lek'awa ya ga to ina jami'ai da masu tsaro, yana ganinsu a k'ofar gidan ya jinjina kai ya koma ya zauna. Har hadiman sun kwashi kayan data siyo sun shige da su, ita ma bakin wata flower ta tsaya tana amsa waya, hakan yasa daga bayanta ta ji an ce "Barka da warhaka." Mamaki ne ya fara rufeta saboda yanda aka mata magana ta jima bata ji haka ba, a hankali ta juyo ta kalleshi, wata fad'uwa gabanta yayi saboda wanda ta gani tsaye a gabanta, wannan kyakyawan matashin mai jini a jika, wanda ya shiga sahun jerin mutane mafi d'aukaka a harkar mulki, matashin daya shiga sahun manyan mutanen da ake zana sunansu, matashin da ya shiga d'aya daga cikin matasan da sukayi mulki da k'ananan shekarunsu, *Abdul Basid' Murphy* shugaban k'asar Texanda, wanda ya lashe k'uri'ar al'umma ba da kud'i ko kyautar cin hanci ba, sai dan cancantarshi da kuma zak'wak'urancinshi ga k'asarshi. Ba tare data sani ba ta aje wayar tace "Yallab'ai?" Murmushi ya sakar mata yace "Yallab'iya." Yar dariya ce ta nemi kubce mata sai kuma ta gimtse ta kawar da kanta, jim kad'an ta juyo ta kalleshi tace "Yallab'ai lafiya ko?" Kafeta yayi da ido yace "Lafiya ba lafiya ba, na zo kama wata mai laifi ne." Da mamaki tace "A gidan nan ?" Jinjina mata kai yayi alamar e, ita ma jinjina kan tayi tace "Bismillah to, wuce ciki." Gyara tsayuwa yayi ya kalleta da kyau yace "Yallab'iya, wajenki na zo." Nuna kanta tayi tace "Wajena kuma? Wani abu ne ya faru?" A tsanake yace "Ba abinda ya faru a yanzu dai, amma gaba kad'an zamu gane da yiwuwar faruwar wani abun." Nuna masa hanyar shiga falon tayi tace "Bismillah to." " *Ina son ki*." Kalmar daya fad'a kenan kamar saukar mari a kunci, da wani razanannen firgici ta kalleshi ta a zazzaro ido, a zuciyarta kuma tana maimaita kalmar ina son ki, me ya d'auketa to? Me ya gani a tare da ita? Wace manufa ce ta kawoshi gareta ? Yasan ma wacece ita? A hassale ta juya da niyyar barin wurin yayi gaggawar tare gabanta yace "Baki ce komai ba?" Kallonshi tayi fuskarta a had'e sosai tace "Me kake so na ce? Me zan fad'a maka? Kasan ko ni wacece? A budurwa ka d'auke ni? Da zaka tareni da wannan maganar kai tsaye." Wayar hannunta ta d'ago masa tare da danna madanni hoton Ayam ya bayyana akan screen d'in, nuna masa tayi tace "Ka ga wannan? To 'yata ce, yanzu haka ita ma tsohon ciki ne da ita, dan haka ka ja jikinka malam, ina girmamaka sannan ina mutumta alak'ar dake tsakaninka da tsohon sarki *mijina* mai mutuwa." Tunda ta fara magana yake kallonta, tana dasa aya madadin ta ji yace" Dan Allah ki gafarce ni, wallahi na d'auka budurwa ce a yanda na ganki." Amma sai ya saki murmushi ya kuma furta" Ina son ki, kuma ina so na aureki, ba zan takuraki ba idan baki amince ba, aa dai zan tabbatar na shiga rayuwarki na addabeki har sai kin fad'a cewa kin amince zaki aureni." Galala tayi da baki sai ta rasa me zata fad'a masa kuma, tana kallo har ya kama hanya ya fita a gidan, nuna kanta tayi a hankali tace" Ni? Ni wai yake so? Ni Juman? Ina ! Da 'yar tawa zan wani tsaya na yi aure, babba ma ba zan kula ba bare wannan da in ba tsarana bane a shekaru, to bai wuce shekaru d'aya ko biyu ne ya bani fa." Murgud'a baki tayi ta juya ta shige ciki tana bambami a zuciyarta da harare harare tana ji ya gama kunyata ta ai da wannan kalmar daya zo mata da ita. ************** Irin tsangwamar da matan dake magark'amar suka d'ora mata shi yayi sanadiyar zubewar cikinta wanda saida ta jikkata sosai saboda cikin ya kai wata hud'u, ta jima kwance a asibiti k'ark'ashin kulawar jami'an tsaro, yanzu kuma data samu sauk'i ta koma magark'ama sai ta canza sosai, kullum tana d'akinta ita ka'dai, idan kuma an fito da su ne to zaka ganta a rakub'e, da haka take cike da takaicin rashin nasararta a rayuwa da kuma nadamar abinda tayi wanda take ji a yanzu daa batayi ba. ************* Babbar magark'amar dake jahar Khazira aka kai shi, wacce ke tsakiyar babban tekun Gafil, saidai shi sab'anin Joyran ne dake nadama, shi kam kullum yana cikin kula duk wanda ya kulashi, yana cikin fad'a da mutane, wata rana ya doke wata rana kuma a dokeshi, Zafeera kuma ta k'i barin tunaninshi, har yanzu da ita yake kwana yake tashi, yayin da zuciyarshi ke k'ara k'ek'ashewa da tsanar Umad da farautar dama ko ya take ya kassara rayuwarshi, da haka shi ma yake tashi rayuwar a gidan da yake fad'in baya da iko a cikinshi, madadin rayuwa a matsayin sarki, yanzu yana rayuwa a matsayin mai laifi kuma duk ta dalilin Umad ne. ************** Tunda ta mareshi a fuska ya rasa lafiyar sa, kumburi ga dinga yi tana kumewa, kunnenshi kuma ya fara masa azababben ciwo, idan dare yayi baya iya bacci ko kad'an, sannu sannu abun ya fara k'amari har saida aka fara dubashi a asibitin masarauta, da aka kasa a nan asibitin aka turashi babbar asibiti, da abun ya ci tura kawai sarki Adah yace a dawo da shi a aje a kurkuku ya k'arasa girbe abinda ya shuka, dan a jikinshi ya ji kawai ba zai warke ba saboda wacce ta mareshi da kuma abinda ta fada bayan tayi marin. Izuwa yanzu kunnenshi ruwa yake fitarwa, ga kumburin nan da idan ka ga rabin fuskarshi zaka d'auka wani abun aka saka masa, duk ya gigice ya fita a hayyacinshi, a haka yake rayuwar wacce a kullum mutuwa yake fata ta zo ta d'aukeshi amma Allah bai kawo k'arshen kwanan na sa ba. *Giobarh* Adah da kanshi ya sanar da ita ai fa shugaban k'asa ne yake son mah d'in ta da aure, shi ma kuma yayi auren rasuwa matarsa tayi, d'ansu d'aya mai shekara uku a duniya, tana jin haka tace tasan me za ta yi, ai kam tsaf ta kwashe ta fad'awa su Bilkees, nan fa suka saka Juman gaba da umarninsu da shawawari, daga k'arshe dai ta amince amma fa ta rantse sai bayan Ayam ta haihu za'a d'aura mata aure, haka kawai ba zata tafi gidan miji ba ta bar yarta data haihu ba gyara, alhalin ranar da suka had'u da shi ma ta tafi siyo kayan gyaran da take tanadi ne ta ma 'yarta. 馃槀Zo ka ga Ayam ta yi sabon uba, tun yanzu yake ganin tab'ara, gashi shi ma mutum ne mai barkwanci sosai da kuma son d'an wanda kake so, hakan yasa yake biye mata a waya su sha hira har da tsare tsaren bikinsu suke, wata rana kuma har ya dinga tsokanarta da cewa yaushe za ta haihu wai? Ko tana so tai ta ganinshi a tuzuru ne ? Haihuwarta ta masa shamaki d zama ango. *Sati d'aya* cir ta kwashe tana zubar da wannan ruwan zak'i, a ranar da suka tsaya tana murna bata jin komai yanzu zata shirya ta tafi turakar mijinta, sai dai ina nak'uda ce gangariya ta sakota a gaba, da gaggawa Kossam da jakadiya da likitarsu mace suka rufu a kanta, cikin ikon Allaah saida ta kwashe awa uku tana nak'uda kafin Allah ya amince d'anta ya sanyo kai zuwa duniya. Masha Allah masarautun biyu babu wanda bai shaida an yi sabon magaji ba, sai gashi hatta da gwamnati ta san da haihuwar Ayam saboda ita ake jira ta haihu dama sannan shugaban k'asar ya angwace, tunda aka dinga ganin hoton yaron akan bpnshi na WhatsApp da Instagram da sauransu yan jaridu suka bibiyi labarin, daga nan suka shiga yayatawa su ma suna fatan alkairi. A satin nan d'aya da ya gabata haka Juman data zo take gyara yarta take mata wanka na musamman, saida Ayam ta ji a jikinta a iya hakama aka tsaya taji dad'in jikinta kuma zata birge mai gidanta. Ranar suna an ci an sha an tara bak'i bila adadi, anyi murna sosai da shagalin wannan rana kafin daga bisani yaro ya ci sunan *Abdul Waheed*, yaro mai shiga rai wanda yayi kama da Musail, hakan yasa yayi kyau gashi b'ul bul kamar ba d'an wata bakwai ba. *Bayan wata takwas* Zaune take a kan kujerar dake d'akin tana wayarta, yar dariya tayi a nutse tace "Abba na, gaskiya idan Mah ta haihu sai na biku har can, kun wani tafiyarku Atlanta kunyi zamanku." Dariya yayi shi ma yace "Karki damu 'yata ta kaina, ai jirgi na tanada da zai d'auko min ke da kuma abokina (Abdul Waheed)." Dariyar jin dad'i tayi tace "Yawwa Abbana, kuma ka ga..." Kafin ta kai k'arshe aka bud'o k'ofar d'akin na ta, sanin ko waye yasa tace "Abba zan sake kira ka bani Mah, yanzu gaba d'aya shareni take bata son muna magana." Dariya yayi shi ma yace "Kunya take ji saboda tana da ciki." Murmushi tayi tare da aje wayar ta juyo ta kalli mai shigowar, jallabiya ce jikinshi bak'a da hula a kan shi, sai Abdul Waheed dake d'auke a kafad'arshi cikin kayanshi na kanti masu kyau, tubarkallah ba zaka ce d'an wata bakwai ba ne, a haka ma dan sanda zai yi hak'ori yayi amai da zaho ne duk suka ramar da shi, amma yanzu har ya maido jikinshi gashi har ya fara tatata. Yana zuwa d'oro mata shi yayi a k'afafu ya kai hannunshi cikin rigarta ya ciro nononta, yaron na gani kam yayi ram da shi ya fara tsutsa, rufe ido tayi tana jin zafin tsutsar da yake saboda nonuwan sun cika mak'il sai zuba suke. Zaune yayi daf da ita a hannun kujerar ya k'urawa yaron ido dake tsutsar nonon idonshi rufe, kallonta yayi yace "Uwar yaron nan baki da tausayi wani lokacin, tun safe da kika kai min yaron nan ban kuma ganinki ba, ke wai ba kya tunaninshi ne?" Turo baki tayi tace "To ai ina so ne ya ga yanda kake gudanar da mulkinka dan yayi koyi da kai." A hassale yace "Sai kuma na ce miki ina buk'atar haka ni? Ko ya koya ai kya bari har yayi wayo ko?" Marairaicewa tayi tace "Shikenan ka yi ta min fad'a saboda na yi abinda ya dace, ai dai ranar da aka nad'aka mulkin nan kayi alk'awarin ba zaka hassala a kai na ba, amma shi ne...har da min tsawa yanzu." Hawayen k'arya ta fara sharewa hakan yasa ya jawo kanta a k'irjinshi yana fad'in" Shikenan to yi hak'uri, gani nayi yanzu ba kya kula wannan yaron, jiya ma fa Mah ta fad'a min wuni yayi wurinta bai sha nono ba, me yasa zaki k'i bashi abincinshi yasha ya k'oshi?" D'aga kanta tayi ta kalleshi sai ta mak'ale masa ido d'aya, da alamar raha yace" Akwai magana kenan?" D'aga gira tayi alamar e, jinjina kai yayi yace" To gama bashi yasha sai muje ki ga wani abun mamaki, amma tukuici na shine ki fad'a min me ke faruwa." Jinjina kai tayi tace" Na yarda." *Bayan minti arba'in* Hannayenta take ta lalubawa kamar makauniya saboda rufe mata ido da yayi da wani farin k'yalle, a hankali ya kwance mata d'aurin na fuska, a hankali ta fara bud'a idonta har ta saukesu fes a kan wani ni'iltaccen lambu, bayan korayen itatuwan data sauke idonta babbar zakanyar nan ce ta biyu ta zuba idonta a kan ta, wani farin ciki ne ya lullub'eta har ta furta "Wow!" Bud'a ido tayi sosai tana kallon gurin, a b'angarenta ne ya killace wani gurin aka nomashi da shuke shuke irin na jeji, sannan aka zuba nau'in dabbobi, zakanya, biri, barewa, rak'umin daji, dorina, aku, d'awisu da sauransu, nau'in tsintsaye kala kala masu kyawun gaske. Juyowa tayi ta kalleshi tace "Yallab'ai..." Juyawa tayi ta kalli zakanyar nan tace "A ina ka samota?" Dariya kawai yake saboda ganin farin cikin da take, rumgumeshi tayi sosai ta sumbaci wuyanshi tace "Nagode sosai mijina, ina alfahari da kai." Cikin kunne ya rad'a mata "A bani tukuicina." D'agowa tayi daga jkinshi suna kallon juna, hannunshi na dama ta kama a hankali har ta d'ora a kan mararta, sannan ta kalli k'wayar idonsa tace "Abdul Waheed, zai samu k'ane ko k'anwa." Da mamaki ya kalleta yace "Da gaske? Kina nufin ciki ne da ke? Amma..." Dariya ce ta kubce masa ya kalli cikin na ta ya kuma kallonta yace "Amma kuma shi ne kike farin ciki? Duk da kinsan Abdul Waheed bai ko shekara ba, sannan kin sha wahala wajen haihuwarsa." Langab'e kai tayi tace "To me ye a ciki? Ba na ka bane? Wahalarka ce ? Zan iya mijina, zan iya da yardar Allah, ko da shi ma ina haihuwarsa zan sake d'aukar wani, na yi maka alk'awarin ba zan gaza ba ko da bautarka ce zata kasheni." Wata wawuyar rumguma ya mata tare da bata wani zazzafan sumba mai haukata k'walwa da gaggar jiki... 馃グ馃 *Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka nuna min k'arshen littafin nan lafiya, kamar jiya ne aka fara gashi yau an kawo k'arshen sa da amincewarka, Allah nagode maka, Allah ka k'ara mana lafiya da aron rai.* _Hak'ik'a VIP grps kun nuna min k'auna, kun bi ni a novel d'ina na kyauta sannan kuka bi ni a novel d'ina na kud'i, kun min hallaci kuma kun nuna ku d'in masoya ne ba masoyan baka ba, hakan yasa a kullum nake kiranku da *yan amana*, ku d'in na daban ne a zuciyar Samira, Allah ya bar k'auna a tsakaninmu. Yanzu ma ga wani sabo nan na kud'i, na san zaku fara mamaki dalilin da yasa na ke son fara na kud'i? Dailin shi ne ina jin dad'in ganin wanda suke ikrarin suna tare da ni na kuma ga sun saka kud'insu sun siya saboda ni, hakan kuma na zama alkairi a gare ni, ina mai muku albishir da labarin *MALLAKINA CE* zai baku mamaki da sakaku nishad'i, dan na tabbatar zai fi *JIHADI* citta haka kuma zai fi *MATAR MUTUM* zak'i da saka walwala, abinda na ke so daku kawai shi ne ku biya kud'inku ku samu labarin, sannan alfarmar da zaku min ta biyu ita xe ku tayani tallata labarin dan k'ara samun masoyan asali._ *D'AND'ANO* A nutse kamar yanda ma fi aksarin masu sunan *Abbakar Sadiq* suke kasancewa ya shigo falon da sallama, cikin haiba da k'asaita ya dunfareta, tunda ta ji bai jira an amsa sallamar ba, bai kuma kalli kowa dake falon ba sai ita ya tabbatar mata da wata a k'asa, amma sai ta nutsu tana kallon dogayen k'afafunshi masu d'auke da zara zaren yatsu har saida yayi daf da ita ya rage kad'an yayi saura k'afarshi ta tab'a k'afarta da ke mik'e. Da wani irin sauri ta tank'washe k'afafunta ta ja baya sannan ta mik'e tare da sakin littafinta dake kan cinyarta tana karatu, rusunawa yayi tare da kai hannu da niyyar cakumar gashinta data bari a waje ba d'an kwali, sai muryar mahaifinshi wanda tun shigowarshi yana shirin amsa sallamarshi amma ya ga ba wannan ne a gabanshi ba sai ya dakata yana kallo ya ga me zai yi. A razane yace "Kai! Lafiyarka k'alau kuwa?" Da sauri ya janye hannunshi tare da d'agowa ya juya, sam bai yi tsammanin mahaifin na d'akin ba, ashe ba shi kad'ai ba ma har da mahaifiyarshi na zaune da kuma Goggon shi, cikin rashin jin dad'i ya dawo baya ya tsaya kusa da mahaifin na shi dake zaune kan kujera, kakkafeshi da ido Abba yayi yace "Da me ka yi niyyar yi Sadiq?" Murmushi ya saki ya girgiza kai, tsaf Umma dake kallonshi ta fahimci da matsala, wato murmushin nan ne mai kama da kuka da yake yi idan ranshi ya b'ace, shi kuma gashi miskilin tsiya bai cika nuna damuwarshi ba, mutum ne mai koyi da fad'ar Manzon Allah (S.A.W), yana had'e fushinshi ko da kuwa zai iya d'aukar mataki, Abba kuma da bai fahimta ba d'orawa yayi da "Ban yarda da wannan girgiza kan ba, za ka fad'a min ko kuwa?" D'aga kanshi yayi ya kalli mahaifin na shi, ba tare daya d'auke murmushin nan a fuskarshi ba yana kallon fuskarshi a ladabce yace "Abba, yarinyar can nake so na koyawa hankali, ina so na ji me ye tsakani na da ita da ke b'ata min suna? Me take nufi da ni da take min haka? Me kuma take nufi da abinda ta fad'a?" Da sauri Abba ya kalli *Sajeeda* dake tsaye da rigarta t-chirt da zanen atamfa, ta d'auki littafinta ta ri'ke tana kallonsu ita ma sai zare ido take. Mahaifiyarta da tun da ta ga ta wuntsila ta tashi tasan bata da gaskiya, harara ta cilla mata tace" Me kika masa?" D'aga hannu tayi sama dake nuni tsakaninta da Allah sannan tace" Wallahi Mama ni ban sani ba, duk wunin yau ma fa ni ban gan shi ba." Wani kallo ya watso mata, a tausashe kallon yake kuma a nutse, sai dai daga k'wayar idon na shi zaka fahimci kakkausan kallon, yar k'wafa yayi sannan ya maida kallonshi ga Abba dake fad'in" Me tai maka kuma yanzu?" Cikin sanyin murya yace" Abba har makaranta yarinyar nan ta samu *Zalika* ta fad'a mata wai ni da ita soyayya muke, kuma wai idan bata fita a harkata ba sai ta babbakata da ranta..." Nunata yayi da hannu yace" Yanzu Abba sai da ita zan yi soyayya? Ta rasa abinda zata had'ani da shi sai da kanta? Abba...Abba, wallahi na rantse da Allah idan yarinyar nan bata fita a shirgi na ba zan sauke mata kafad'a, bana so ta daina daga yau." Wata k'wafar ya kuma yi a sanyaye sannan ya mik'e ya fita a d'akin, da kallo duk suka rakashi inda Bintu ta bi Sajeeda da kallo, kallo ne na takaici da jin haushin taurin kan yarinyar, ta sha nuna mata ta fita a harkarshi, amma bata san me yasa bata ji ba? Umma kam ko kallon Sajeeda ma ba tayi ba sai mik'ewa da tayi ta bi bayan Sadiq, dan ita ta fi kowa sanin halin d'anta. Abba ma juyowa yayi daga kallon daya bi shi da shi na mamakin yanda ya kora gargad'inshi amma a tsanake ba tare da hargagi ba, cikin taushin murya da ruwan sanyi ya aika mata sak'o mai razanarwa. Kallon sauran yaran yayi dake karatunsu amma kunnuwansu da hankalinsu kaf yana ga abinda ke faruwa, inda Khausar sam bata ji dad'i ba, ta yi fatan ina ma Abba bayanan Yaya Sadiq d'in ya shak'i wuyan yarinyar can, tsawar da Abba ya daka musu cewa "Ku tashi ku koma ciki." Ita ta dawo da ita daga tunanin da take, da sauri duk suka mik'e suna kwasar litattafansu, saida suka shige Sajeeda ma ta juya zata shiga na ta d'akin yace "Zo nan." A hankali ta shiga takowa har ta zo kusa da shi, tsugunawa tayi a raunane kamar za tayi kuka tace "Abba gani." Gyara zamanshi yayi sosai ya matsa kusanta yana kallon fuskarta yace "Sajeeda 'yata, kinsan dai ni mahaifinki ne ko?" Jinjina kai tayi alamar e tare da amsawa cikin shagwab' a tace "E Abba." Jinjina kai yayi shi ma sannan yace "Ina so ki fad'a min me yasa kika samu budurwar yayanki kika fad'a mata cewa kuna soyayya? Me yasa kika yi haka?" D'agowa tayi ta kalleshi, sai kuma ta sunkuyar da kanta k'asa ta fashe da kuka marar sauti, dafa kanta yayi yace "Na d'auka ni da ke abokai ne, na d'auka bama b'oyewa juna komai? Yaushe muka fara haka da ke?" Girgiza kai ta dinga yi amma ba tayi magana ba saboda kukan dake tik'ak'arta, a sanyaye ya sake fad'in "Kinga Sajeeda, ki daure ki fad'a min abinda ya faru, kinga dai bana so ya tab'a lafiyarki a gidan nan, kin san fa bana so hakk'in maraya ya kamani." Cikin matsanancin kuka da shashek'a ta k'arasa yin zaune ta fara fad'in "Abba...ka ga dai ban tab'a fad'a ma kowa ba sai kai, bana so ka fad'a ma kowa kai ma, ya zama sirri a tsakaninmu." Jinjina kai yayi yace "In shaa Allah babu wanda zai ji, fad'a min ina jinki?" Saida ta ja majina ta fara fad'in "Abba ni ma bansan me yasa ba, ban san ko yaushe hakan ya fara faruwa dani ba, haka kawai dai na ke jin na tsani Yaya Sadiq ya dinga danganta kansa da wata 'ya mace, haka kawai nake jin ba dad'i idan yana firar wata ya mace a gabana, raina ya kan b'aci matuk'a idan yana alak'anta kansa da wata mace, wani irin abu nake ji a zuciyata a game da shi, Abba sai na ke ji idan zai nemi aure sai dubu, to zan lalata auren sau dubu saidai ni da shi duk mu zauna a haka ba tare da aure..." Da sauri Abba yace" Shiiiiiiii!" Girgiza mata kaibya dinga yi yana fad'in" Ko kusa kar na k'ara jin kin fad'i haka da bakinki, kar ki sake fad'in haka kin ji ko, me yasa kike tunanin zaku mutu babu aure?" Kallonshi tayi tana share hawaye tace" Saboda baya so na, ya tsane ni Abba, ban san me na masa ba? Ban kuma san hikimar dake cikin abinda nake ji a game da shi ba?" Kafad'arta ya dinga bubbugawa yace" Daina kuka haka ya isa, share hawayeki kin ji, In Shaa Allah indai Sadiq ne matsalar, to ni nan uban Sadiq *Aminu* na miki alk'awarin d'aura miki aure da shi." _____________ Sadiq dake ta fafutukar bud'e d'akinshi ya shiga rai b'ace yake fad'in" Na tsaneta, na tsaneki, me yasa ba zaki fahimci haka ba? Mayya kawai aljana bai bak'in hali." Umma dake sauraronsa girgiza kai tayi a tausashe tace"... *Kun ji salon labarin ? Me kuka fahimta game da d'an tsakuren nan?* *Bissalam*馃槏 *Alhamdulillah.*