*_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _1_ *Thanks to Almighty Allah for giving me ability and power to start the other part of the book _SHARIK~HAYATI_, many thanks to my follwers, fans and Family i luv u all❣️* Kwance Ummi ta sameta ta rufo da blanket, jin motsi yasa tayi saurin goge hawayen idanta ta tashi ta zauna, Ummi ta zauna gefenta cike da damuwa ta ce "U haven't eat dear" dan turo baki tayi ta ce "Na koshi Ummi" shiru Ummi tayi tana kallanta ganin yadda ta kara mungun rama akan da, ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To me zakici?" Tayi saurin girgiza kai ta ce "Banasan abinci kuma" Ummi ta ce "Me zakici to idan ba abinci ba, or do u need tea?" Ta girgiza kai, Ummi ta ce "Conflask?" Ta kara girgiza kai ta ce "Awara nakeso" Ummi ta ce "To bari na bawa Saudatu ta samo maki, tashi muje kasa" dan noke kafada tayi kamar zatai kuka ta ce "Ummi bacci nakesan yi" Ummi ta kamo hannunta ta ce "Sai kiyi a kasan ai, zakuyi sallama da Mummy ne, beside that ma banasan kina zama ke kadai" dan kwalinta Ummi ta daura mata sannan ta kama hannunta suka fito a dakin. Very slowly ta dinga bin Umminta har suka sauko a steps din, Mummy dake kallansu ta ce "Lafiya dai?" Ummi ta ce "Wai Awara zata ci" gefen Mummy Rafi'ah ta zauna ta ce "Mummy tafiya zakiyi?" Mummy ta kamo hannunta ta ce "Insha Allah, ina jiran driver ne, but kullum zan dinga zuwa kallanki harki samu sauki sosai, abinda nakeso dake shine ki daina kukan nan, idan Allah ya rubuta abu zai faru babu mahalukin daya isa canzashi, shi kuma Yusuf ki watsar da kashin sa, ki saki jikinki ki daina damuwa dashi, banda hauka irin naki ma mutum yaci amanarki haka amma ki zauna kina kuka akansa" share hawayen idanta tayi tana kallan Mummy ta ce "Ni bana san shi kuma, i hate seeing him, ko mai kamarsa banasan na gani, what is making me to cry is..." Fashewa tayi da kuka ta kasa karasawa, Mummy ta bata side hug ta ce "Dan ya barki da ciki a kanki aka fara? Ke dai ki kula da kanki ki haife abinda yake jikinkin ki kawai, ina guje masa ran da zai zo yana blaming abinda kika haifa dan dansa ne, wallahi babu me rabani dashi duk duniyar nan, saina wulakantashi kamar yadda yayi mana, sai na sa shi kuka da kunci na har abada, kuma d'a ba nasa bane, kece uwarsa kece ubansa" ita dai Rafi'ah sai share hawayen idanta take, bayan haka ta zame akan sofa ta kwanta akan carpet ta rufe idanta tana addu'a, wani zafi da takaici take ji deep down her, ba dan ba dan ba da tayi addu'a Allah yasa cikin ya bare itama ta hutawa rayuwarta. Bayan 10 minutes Saudatu ta shigo da warmer a hannunta, Ummi dake zaune suna hira da Mummy ta ce "Kin samu?" Saudatu ta ce "Ehh na samu" Ummi ta daga Rafi'ah ta ce "Dear, ga Awaran an kawo maki" a hankali ta bude idanuwanta tana kallan Ummi ta ce "I'm sleepy" Ummi ta ce "I know, try and eat ko kadan ma, tin safe bakici komai ba" gyara zama tayi ta jingina da jikin kujera sannan ta bude warmer din, fork Saudatu ta mike mata ta fara cin Awaran, daga Ummi har Mummy kallanta suke, kai kace tayi sati bataci komai ba, na bakinta baya karewa take saka wani, su kam hakan yayi musu dadi, indai zataci ai komai zaizo da sauki, kusan rabin warmer din ta cinye sannan ta rufe ta ajiye a gefenta ta ce "Anjima zanci wannan" Ummi ta danyi murmushi tana kallanta ta ce "Ba wanda zai ta6a" daga haka ta kwanta ta limshe ido, nan da nan bacci me nauyi ya dauketa. Ba jimawa driver yazo daukar Mummy, a hanyarsu zuwa gida yake fada mata Jawad ya dawo, with surprise Mummy ta ce "Har sunyi landing?" ya ce "Wallahi Hajiya, kafin naje daukoshi wani abokinshi ya kawo shi gida" Mummy ta ce "Inaga dai sanda ya kirani yayi rabin tafiyar". Anty Amina ce zaune a parlorn Ummanta tana shan exotic, lokaci~lokaci takan kalli Anty Rahama dake ta trying number Anty Khadija amma yaki shiga, Anty Amina tayi murmushi ta ce "Maman Leemah wai menene damuwarki akan Khadija ne? Naga randa abin ya faru munyi magana da ita tace sun bar kasar" Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce "Duk tasu?" Anty Amina ta ce "Ehh mana, ni lokacin kaina ya dau caji ban gaya miki ba, ga zaman dole na asibiti" Anty Rahama ta ce "Amma tace tayi aure a Kaduna da mijin ta wuce kenan?" Anty Amina tayi dariya ta ce "Kema kinsan ba zata harshi ba ai, mijin da aka zautarwa hankali ya bar matarsa da manyan 'ya'yansa ya aureta ta ina zata barshi, ai suna caan ko wacce kasa Allah masani, amma dai ni banga abin tada hankali dan baki sameta a waya ba, ina dai burinmu ya cika, shikenan sai mu barta ta sha iska" Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce "Hakane kuma, Allah ya raka taki gona" daga haka suka tafa Anty Amina ta ce "Atooh, haushinama yarinyar da tai ciki, koba komai zasu danganta d'an da Yusuf" Anty Rahama ta mata wani kallo ta ce "Taab ai kuwa wannan yayar uwartan ba yarda zatai ba, lokacinfa da mukaje da Yah Muhammad gidan Yusuf wuka ta dauka tana nemansa daki daki wai saita kashe shi, nasan dai ko zafin haushine ya sata haka baxa dai ta bari ya kar6i abinda Rafi'ah zata haifa ba, ke nifa mamaki abin ya bani, banyi tinanin wannan figigiyar zata daukar ciki da wuri ba, gaki nan zabgegiya dake shekara kusan 5 ba labari" nan da nan Anty Amina ta hade fuska ta ce "Dan Allah kimin cikin nan idan zaki iya, ba dai Allah ke bayar ba, nayi maganin harna gaji babu labari, kema naga a shekaru 22 da kikai gidan mijinki 'ya dya kawai kika haifa" Anty Rahama ta ce "Amma dai na haifi dayar ko, to dan Allah kema kiyi zuciya ki haifo ko nakashashshe ne" Anty Amina ta mike ta ce "Sai dai ke ki haifo, gashi mun fara gani kin haifo mai cuta" cushion Anty Rahama ta cilla mata cikin 6acin rai ta ce "Ki shiga hankalinki Amina, karki kara kiramin Ikleemah da mai cuta" fitowa Umma tayi a daki taja Anty Rahama tana bata hakuri suka shiga ciki, bayan nan ta fito ta rarrashi Anty Amina ma, wai ai sai ace basu da hadin kai, kuma abin kunya ne suyi fada a junansu, ita dai Anty Amina baki kawai ta ta6e taci gaba da shan exotic dinta. Fuskarsa dauke da murmushi ya shigo parlorn, Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "Mutanen Cyprus" ya dan shafa tulin gashin dake kansa ya ce "Ina yini Mummy" ta ce "Lafiya kalau, have a seat, ashe harka dawo?" ya ce "Ehh kusan awana 1 ma, fatan na sameku lafiya?" Ta ce "Alhamdulilah" mikewa yayi yana kallanta ya ce "Zan answer call ne" ta ce "Alright no problem" daga haka ya fita a parlorn, part din Maminsa ya shige hade da sallama, Abi na zaune a gefen Mami sai Ikram dake kan carpet a zaune, Jawad ya danyi kasa da kansa ya ce "Ashe ka dawo, na dauka zaka kirani na dauko ka" Abi ya ce "U don't have to worry son, kai da ka dawo a tafiya, Sadeeq ya daukoni" kan kujera Jawad ya zauna yana kallan TV, Abi ya kalli Mami data dan hade fuska ya ce "To meyasa bakije yau ba?" Ta juyo tana kallansa ta ce "Naga dai an sallameta har sun koma gida, gidanma kullum zan dinga zuwa kenan?" Abi ya sauke ajiyar zuciya ya ce "U have to go, asibiti da ban gida da ban, don't make me repeat my self kije kawai ki duba ta" tashi yayi ya fita a parlorn Mami ta bishi da wani irin kallo. Jawad dake kallanta ya ce "What's going on Mami?" Dan karamin tsaki taja ta ce "Ina kana da labarin auran Rafi'ah wanda akayi bayan kwana biyu da tafiyarka" ba karamin bugawa zuciyarsa tayi ba, ya daga mata kai yana kallanta, Mami ta ta6e baki sannan ta ce "She's divorced" with shock ya juyo yana kallanta ya ce "Divorced" ta ce "Saki ba, ya saketa saki daya" innalillahi Jawad ya dinga furtawa yana kallan mahaifiyarsa, Mami ta ta6e baki ta ce "Wallahi sakin wulakanci, daya bata takardar ya bar gidan shida matarsa, har yau ba'a san inda yake ba, ya tafi ya barta da karamin ciki, inka ganta kamar ka hureta ta fadi, ni cewa nayi ma da zubar da cikin sukai, yarinyar dako 18 bata cuka ba, sanda naje sunanta Ikram dina tafi shekara 1" kasa daina kallan Mami yayi, lokaci daya yaji komai nasa ya tsaya musamman data ambaci ciki, Mami ta gyara zamanta ta ce "Ni gani nake saboda cutarta ya gujeta, yanzu a zamanin nan yaushe zaka auri mata mai ciwan zuciya, duk wata fa sai sun kar6i magani ga uban tsada, shi kuwa inaga yayi na Allah yace ya gaji, ba dan ubanta nada dukiya ba inaga gidan da zasu zauna ma sai ya gagaresu" Tashi Jawad yayi ya shige daki, yana rufo kofar idanuwansa suka cika da hawaye, bai bari sun zuba ba saima murmushi da yayi ya dauki key din motarsa dake kan mirror din dakin, jin an bude dakin yayi saurin juyawa, Mami ta ce "Ya muna magana zaka tashi ka barni ba excuse" ya ce "Na tina akwai inda zanje ne" ta ce "Ina?" Ya dan shafa kansa yana kallanta ya ce "Wajen aiki, akwai papers din da zan kai musu wanda na taho dasu" Mami ta ta6e baki ta zauna bakin gado ta ce "Haka dai kullum aiki aiki, idan dai kayi aure barin wannan kotun zakayi ka nemi wata" a hankali ya ce "Ohk, saina dawo" daga haka ya fita a dakin. Driving kawai yake amma gaba daya tinaninsa ya tafi wajen Rafi'ah, minti 10 ya kaishi kofar gidan, yayi parking a waje sannan ya fito walking gently ya tura gate din, ganinsa yasa Mustapha ya kara bude kofar yana masa sannu da zuwa, daga masa hannu yayi ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din yaji kofar a bude, ya shiga parlorn da sallama, Saudatu dake jera dinner akan dinning ta ce "Ina wuni" ya ce "Lafiya kalau, Ummi na nan?" Ta ce "Ehh bari in mata magana" upstairs ta nufa ta kwankwasa dakin Ummi, bayan an bata izini ta bude dakin ta shiga da sallama, Rafi'ah na kwance akan gado Ummi na rarrashinta, dan wani saban kuka ta kafa musu tinda ta tashi a bacci, Ummi ta kalli Saudatu dake tsaye gefe ta ce "Kin gama abincin ne?" Ta ce "Ehh na gama, kinyi bako ne a kasa" Ummi ta ce "Bako kuma at this time? Babbane?" Saudatu ta girgiza kai ta ce "Ehh babbane, dogo dan fari haka, yana da gashi me yawa a kansa" sosai zuciyar Rafi'ah ya buga, dan tinaninta ko Yusuf ne, ta ruko hannun Ummi kamar zatai kuka ta ce "Dan Allah karkije Ummi" Ummi ta ce "Why Rafi'ah, bari na gani ko waye" daga haka ta zame hannunta ta nufi kofa ta fita, saukowa akan gadon Rafi'ah tayi tana kallan Saudatu ta ce "Fari ne?" Saudatu dake tsaye tana kallanta ta ce "A'a amma dai ba za'a ce masa baki ba" ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta kwanta, dan tasan Yusuf yana daya daga cikin mutanen da za'a kira su asalin farare, a hankali Saudatu ta ce "Allah ya baki lafiya" daga haka ta fice a dakin. Tana saukowa ta sami Jawad da Ummi suna gaisawa yana mata jajen abinda ya faru, Ummi ta danyi murmushi ta ce "Toya zamuyi, haka Allah ya tsara mana, da munsan haka zai faru ko auran baza ai ba, to amma Allah shi yake tsara komai a duk lokacin daya so" Jawad da kansa ke kasa ya ce "Hakane" Ummi ta ce "Bari na turo ta ku gaisa" daga haka ta mike ta wuce upstairs, kwance ta sameta tayi shiru ta kurawa window ido, Ummi ta kamo hannunta ta ce "Daughter" kifta idanta ta danyi sannan ta kalli Ummi ta ce "Who was d visitor Mum?" Ummi ta ce "Ahmad ne, kije ku gaisa" tsayawa tayi tana kallanta bata dai ce komai ba, Ummi ta ce "I mean Jawad" a hankali ta ce "Ohh" daga haka ta mike, hijab Ummi ta dauko mata tasa sannan ta ce "U wash ur face, duk idanki ya kumbura" a hankali ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta goge idanta with clean towel sannan ta fito, daga haka ta fita a dakin ta wuce downstairs, tin tana sakkowa yake kallanta ko kiftawa babu, ita dai kanta na kasa ta karaso parlorn da sallama, zama tayi akan carpet ta ce "Ina yini" ya ce "Fine, how are u then?" Silently ta ce "Same" Jawad yayi shiru yana kallanta, dago kanta tayi suka hada ido tayi saurin dauke kanta, a hankali taji muryarshi ya ce "Ya karfin jiki?" Ta goge hawayen idanta ta ce "Alhamdulilah" tinda ta rife bakinta hawaye suka dinga sakko mata tana sharewa da hijab dinta, Jawad ya danyi kasa da murya ya ce "Destiny, kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa, so u don't have to cry, one day one time u will laugh" fashewa tayi da kuka ta ce "I will never laugh again Ya Jawad, to laugh for what? Kasan zafin da nake ji deep down me, ni kadai nasan abinda nake ji, so nobody should tell me i will laugh one day" daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta, kallanta ya dinga yi daga inda yake zaune, jiin ta sausauta kukan da take ya ce "May be shi din ba alkhairi bane a tattare dake, Allah ya raba ku ne saboda ki samu wanda ya fishi alkhairi, just erase all ur bond together with him, ki manta dashi a rayuwanki, so don't cry for him pls" ta share idanta ba tare data kalleshi ba ta ce "I have to cry Yayah, he divorced me without any reason, ya azabtar dani a gidanshi ban gayawa kowa ba, after all ya tafi ya barni da cikinshi..." sarkewa muryarta tayi, hakan yasa tayi shiru tana kuka kasa kasa, Jawad ya ce "No, u don't have to, ai shi d'a na kowa ne, i can take care of the unborn child and still after his birth, so u forget about that man i beg u" a hankali kawai ta daga masa kai, ya ce "Promise u won't cry again" ta ce "Yes" ya ce "Yes what?" Ta ce "I can't make a promise to u, nasan sai nayi, saboda yin kukan kadai zai yi preventing dina from heart attack, inajin dadi idan nayi" Jawad ya limshe idanuwansa ya ce "To kiyi kadan" dagowa tayi tana kallansa, yana bude idanuwansa tayi saurin sunkuyar da kanta, ya ce "I think i have to go, kiyiwa Ummi sallama, Allah ya kara maki lafiya" silently ta ce "Ameen, nagode" daga haka ya mike ya fita a parlorn ta bishi da kallo, yana fita compound aka bude gate, motar Sadeeq ta shigo compound din, sosai Mami ta hade rai tana dalla masa harara, yayi karfin halin ya karasa parking lot din yana kallanta ya ce "Dama na gama abinda nake ne shine..." Wucewa tayi ta barshi nan wajen a tsaye, ya juyo yana kallan Sadeeq da fitowanshi a motar kenan ya ce "Till u come back" daga haka ya nufi hanyar gate Sadeeq ya bishi da kallo. _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _2_ Shiru Rafi'ah tayi ganin Mami ta shigo parlorn, ta mike a hankali tana goge hawayen idanta ta ce "Sannu da zuwa" Mami ta zauna kan kujera kamar bazata amsa ba, sai kuma ta ce "Sannu, ya karfin jiki?" silently ta ce "Naji sauki" Mami ta dago kai tana kallanta ta ce "A hakan?" Rafi'ah ta daga mata kai, sai kuma ta ta6e baki ta ce "Aike da jin sauki sai kin haife wannan jarabar ta cikinki, bayan haka kin samu me auranki, shine zaki ce kin fara samun sauki, dan mace ta zamu zama agidan miji ma wani falala ne, kinga idan kika kara fitowa ai ciwo ya koma baya" kara goge hawayen idanta tayi ta dan turo baki ta ce "Niba aure kuma zan sake yi ba" daga haka ta nufi upstairs, Mami ta mike ta ce "To kya gaisheta daman jikinki nazo dubawa" daga haka ta mike ta fice a parlorn Rafi'ah ta bita da harara. Very gentle ta dinga taka steps din harta gama hawa, ta shige dakinta ta rufo kofa, har zata kwanta aka bude kofar dakin, Abdul ya karaso yana kallanta ya ce "Sannu" ta ce "Thank u" ya ce "We just came back with Abba, na siyo maki grapes da Apple and shawarma" dan murmushi kawai tayi dan ita yanzu ta tsani komai idan ba dan~wake ba, kwanciya tayi tana kallansa ta ce "So much thanks bro, nagode" gyara mata blanket din jikinta yayi ya ce "Allah ya baki lafiya" ta ce "Ameen" ganin ta limshe ido yasa ya mike ya fita a dakin ya jawo mata kofa a hankali. Ammi ce zaune a parlornta Sameer na gefenta a zaune, gaba daya jikinsa yayi sanyi jin abinda dan~uwansa ya aikata, shida yake murna zai dawo gida yaga 'yan uwansa cikin farin ciki amma kuma yaji abunda ko a mafarki bazai yarda ba, Ammi ta dan goge hawayen idanta ta ce "Yarinyar nan ta sha wahala Muhammad, idan ka ganta gaba daya ta rame" Sameer ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce "Allah ya kyauta, kenan bai gayawa kowa inda zaije ba" Ammi ta ce "Ba wanda ya sani, wadanda ya kamata su sani su suka daukeshi suka tafi dashi, nasan Yusuf dina bazai iya butulci da wulakanta mace haka ba, wallahi Sameer akwai abinda yake faruwa" kamo hannunta Sameer yayi ya ce "Stop crying pls mother, in sha Allah wata rana zai dawo, na miki alkawarin zan kula da yarinyar da kuma abinda zata haifa" Ammi ta kara share hawayen idanta ta ce "Allah ya baka iko, zamuyi ta addu'a Allah ya bayyana shi" a hankali ya ce "Ameen, yanzu dare yayi kuma na dawo da ciwan kai, gobe insha Allah zanje na dubata" Ammi ta ce "Allah ya kaimu goben" ya ce "Ameen, amma dan Allah ki daina kuka". Karfe 12 na dare Jawad ya dawo gida, bayan yayi parking sai daya tabbatar gate man ya rufe gate sannan ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din kofar yaji a kulle, ya ciro wayarsa a pocket dinsa yayi dialing phone din Sadeeq, bugu biyu ya dauka hade da sallama, Jawad ya ce "Open the door for me, na parlorn Abi" da to kawai ya amsa sannan yayi hanging call din, few minutes Sadeeq ya bude masa kofar, ya shigo sannan Sadeeq ya rufe kofar ya koma dakinsa, har zai shige dakinsa Abi ya bude kofar part din Mami ya ce "Who's that?" Jawad ya juyo a hankali ya ce "It's me" Abi ya ce "Ya sai yanzu zaka dawomin gida Ahmad, is exactly past 12 now" kafin yayi magana Mami ta fito tana masa wani kallo ta ce "Gashi nan saiya gaya maka gidan ubanwa yaje daya kai dare haka bai dawo ba, tin bayan isha dana je gidansu yarinyar nan na samu shi yana fita, daga nan ko gidan uwarsa wa ya tafi ban sani ba" Abi dake kallansa ya ce "Where have u been Ahmad? Kaje gidan su Fatima ne" a hankali ya ce "Ehh, but i left there since 8, naje wajen Aliyu ne baya nan, shine naje asibiti wajen Umar anyi admitting dinsa ne, anan na zauna sai yanzu" Abi ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ya koma ciki, Mami dake tsaye tana kallansa ta ce "Kai ko tsoro bakyaji a tattaraka ubanka yana dan siyasa" a hankali ya ce "Ba abinda zai faru by God grace Mami" ta wurga masa harara ta ce "Aini gara kayi auranka ka barmin gida, idan yaso ka kai karfe 1 baka koma ba, wacce ka aura ne dai sai dai tayi hakuri" dan murmushi yayi yana kallanta ya ce "Sai da safe" daga haka ya shiga dakinsa ta bishi da harara. Washegari ya kama Monday, da safe Ummi ta gama hada komai da taimakon Saudatu, bayan ta shirya ta shiga dakin Rafi'ah ta sameta a kwance tana bacci, rufo kofar tayi ta koma dakinta, Abba dake zaune yana rubutu ya ce "Haka zaki fita ki barta at this condition kenan?" Dagowa tayi tana kallansa ta ce "I'm not staying long, 2 hours lectures kawai zan musu, sai meeting daza muyi, amma idan kace na zauna ba damuwa" Abba ya ajiye pen din hannunsa ya ce "No, idan kinga dai ba matsala kije kawai, amma kinsan tana bukatar me kula da ita ko?" Ummi ta ce "I knew, amma ga Saudatu ai, komai takeso zata bata" Abba ya ce "Ohk, Allah ya kiyaye" ta ce "Ameen, 2 days per week kawai nake da lectures din" ya ce "Alright, a dawo lafiya" Ummi ta nufi kofar fita ta ce "Allah yasa" daga haka ta fita a dakin, bayan ta sauko kasa ta zauna akan kujera tayi kiran Saudatu, cike da ladabi yarinyar ta karaso ta zauna a kan carpet ta ce "Gani Ummi" Ummi ta ce "Zan je aiki ne, idan Rafi'ah ta tashi ki bata tea first, after then akwai dan wake cikin warmer idan zata ci, kuma karta taita kwanciyar nan dan Allah, idan kin gama abinda kike zaki iya zama da ita" Saudatu tayi kasa da kanta tana murmushi ta ce "To Ummi insha Allah, a dawo lafiya" Ummi ta ce "Allah yasa" daga haka ta mike ta fita a parlorn. Karfe 10 Rafi'ah ta tashi, ta dinga bin dakin da kallo kafin ta mike a hankali ta zauna, yau kam Alhamdulilah jikinta ba zafi sosai, kuma batajin ciwo a ko ina, mikewa tayi ta dauki towel ta shiga toilet, kusan 15 minutes tayi taking a ciki kafin ta fito da towel daure a kirjinta ta zauna gaban mirror, Yusuf kawai ta tuna a lokacin, dan mostly idan ta fito a wanka shi yake tsayawa a bayanta ya taje mata kai ya taya ta shiryawa, jin kirjinta na bugawa yasa ta limshe idanta tana addu'a, bayan minti 2 ta bude idanta sannan ta shafe jikinta ta mike ta bar wajen, doguwar riga na atampa ta saka sannan ta daura dankwalinta ta shafa white powder sai lip gloss, sosai tayi mungun kyau duk da ramar da tayi, ta jawo phone dinta dake kan gado ta kira Mummy, sosai sukai waya, kuma jin muryarta yasa hankalin Mummy ya kara kwanciya, bayan sunyi sallama ta ajiye phone din sannan ta fara gyara gadon. Tana cikin gyaran Saudatu ta bude kofar, ta danyi murmushi ganinta ta ce "Anty Rafi'ah bari na gyara miki" Rafi'ah ta girgiza kai ta ce "A'a Saudat bari nayi kawai" Saudatu ta danyi shiru tana kallanta, sai kuma ta ce "Bari na kawo miki tea" ta ce "No, zan sakko kasa yanzu, Abbana ya fita ne?" Saudatu ta girgiza kai ta ce "Gaskiya banga fitan shi ba, amma Ummi ta fita" ta ce "Ehh jiya tacemin zata koma aiki yau" fita Saudatu tayi a dakin tana murmushi, ita kanta dadi taji ganin Rafi'ah a haka, ta wuce kitchen ta fara hada mata dan~waken kamar yadda taga Ummi nayi, Bayan Rafi'ah ta gama gyara dakin ta shiga dakin Abbanta da sallama, ya dago yana kallanta ya ce "Mother" ta danyi murmushi ta zauna gefenshi ta ce "Abbana" murmushi yayi shima yana kallanta ya ce "Alhamdulilah, jiki ya fara sauki" ta ce "Good morning" ya ce "Morning, how are u dear" a hankali ta ce "Banajin komai yanzu Abba, thanks for the care" hannunta ya kama suna shaking, tayi saurin sunkuyar da kanta tana murmushi, Abba ya ce "Allah ya kara miki lafiya" a hankali ta ce "Ameen" sannan ta mike tana kallan warmers din dake gefensa ta ce "Abba u haven't eat" ya ce "Yanzu zan gama naci Mamana" daga haka ta danyi murmushi ta fita a dakin ya bita da kallo cike da tausayi. Tana sauka downstairs ta samu Saudatu ta hada mata komai, ta zauna akan carpet ta ce "Sannu da kokari" Saudatu ta ce "Haba dai Anty Rafi'ah, ai indai ke zanyiwa abu zan iya yini inayi ba tare dana gaji ba" Rafi'ah na murmushi ta ce "To banaso kina kirana da Anty, just Rafi'ah pls" Saudatu ta ce "Wallahi bazan iya ba" ta ce "Zaki iya, kin ta6a ganin inda ka cewa wadda ka girma Anty?" Ta ce "Ehh mana, nidai koma menene bazan fasa fada ba, ya karfin jiki?" Ta ce "Yau kam Alhamdulilah, kawai inajin weakness ne" Saudatu ta danyi murmushi ta ce "Dama haka zakiji saboda cikin dake jikinki" Rafi'ah ta dan kalleta ta ce "How do you know that? taya kika san hakan" ta ce "Nima nayi kuma naji" Rafi'ah ta dan zaro ido tana kallanta ta ce "Kin ta6a aure?" Ta ce "Ehh, tin ina shekara 13 aka min aure a garinmu, inaga shekarana 14 da watanni na samu ciki, ina da tsohon ciki Allah yayi wa mijina rasuwa, a ranar daya rasu ranar nima na haihu amma dan yazo ba rai, ni kuma tawa kaddarar kenan" Rafi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallanta ta ce "Subhanallah, Allah ya jikansu" Saudatu ta ce "Ameen, amma tin daga lokacin ban sake aure ba, naci gaba da karatuna na islamiyya har nayi sauka, shine wata kawar mahaifiyata ta samar min aiki anan, nidai shekaruna 19 a duniya, amma wallahi ban ta6a haduwa da mutanen kirki irinku ba, Umminku, Abbanku, kema da Abdul ba wanda ya ta6a min abinda zanji ba dadi, Allah ya saka da alkhairi ya biya ku da gidan Allah" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "Ameen". Suna zaune suna dan hira aka danna bell, Saudatu ta gyara hijabinta zata bude kofa Rafi'ah ta ce "Wait Saudat, ki fara tambayar waye" Saudatu ta ce "Waye?" Sameer ya ce "Nine" jin muryar namiji yasa ta mike ta dauka hijab dinta akan kujera ta saka sannan Saudatu ta bude kofar, Sameer dake tsaye yayi folding hannayensa ya shigo parlorn yana kallan Rafi'ah ya zauna, itama zama tayi kasa ta ce "Sannu da zuwa" ya ce "Yauwa sannu" Saudatu ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya kalau, ya mai jiki?" Ta ce "Alhamdulilah" daga haka ta wuce kitchen ta kawo masa drinks da cup sai table water, Rafi'ah dai na kallanta harta ajiye ta bar wajen, a hankali ta dan kalleshi ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya kalau, ya karfin jiki?" Ta ce "Da sauki sosai" ya ce "Allah ya kara sauki" shiru duk sukayi na kusan minti 5, Sameer yayi breaking silent din ta hanyar cewa "Allah ya baki lafiya, jiya da daddare nayi landing, Mother told me all what happened, Allah yasa haka shine mafi alkhairi" a hankali ta ce "Ameen, nagode" ya ce "God knows best Fatima, shi yasan dalilin daya sa hakan ta faru, but i think hakan ya faru ne saboda shi din ba alkhairi bane a tattare dake, may be u will find someone better than Yusuf, so forget all what happened, i'm there for u, insha Allah i will take care of the Baby before and after his birth" Sameer ya karashe maganar yana kallanta, kin dagowa tayi ta kalleshi jin abinda yace is very similar to Jawda's speech, Sameer ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya raba lafiya" a hankali ta ce "Ameen, nagode" mikewa yayi yana kallanta ya ce "I'm going" ba tare data kalleshi ba ta ce "Ko in kawo maka tea?" Ya ce "No, i'm going with this" daga haka ya dauki Fanta daya ya rike a hannu ya ce "Ammi tace sunyi waya da Ummi wai bata nan ko" ta ce "Yes she's out" ya ce "Ohk, i will come back ltr" ta ce "Till u come, Allah ya kiyaye" daga haka ta tura kofar bayan ya fita, hijabin jikinta ta cire ta dauko dan~wakenta akan dinning taci gaba da ci tana kallan TV. _08103810398_ *I appreciate all ur calls and messages, nagode sosai da sosai i'm more than healthy now 🤗* *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _3_ Da yamma Rafi'ah na zaune a parlor tayi pillow da cinyar Ummi aka danna bell, Ummi ta dan kalleta ta ce "Open the door Rafi'ah" mikewa tayi a hankali tasa Himar dinta sannan ta bude kofar, murmushi ta danyi ganin Ammi a tsaye, Khairiyya ta rungumeta calmly ta ce "I missed u Anty" a hankali Rafi'ah ta ce "I missed u namesake" daga haka ta matsa gefe Ammi ta shigo. With smile Ummi ta cire glasses din idanta ta ce "Sannu da zuwa Hajiya" Ammi ta zauna akan sofa tana kallan Rafi'ah dake tsaye ta ce "Sannu, jiki ya fara sauki ko" Ummi ta ce "Sosai wallahi sai godiyar Allah" sake hannun Rafi'ah Khairiyya tayi ta ce "Ina yini Ummi" ta ce "Lafiya kalau Khairi, how are u?" Khairiyya ta ce "Fine Ummi", zama duk sukayi a kan carpet, Ammi ta kalli Ummi ta ce "Amma ta rage aman ko?" Ummi ta ce "Ehh, yau dai tinda ta tashi ba tai ba jikinma da sauki sosai" Ammi ta ce "Allah ya kara mata lafiya, ya kuma bata hakurin jurewa" Ummi ta ce "Ameen". Cikin few Minutes Saudatu ta jerawa Ammi abinci da abinsha, duk cikinsu ba wanda ya ci, Khairiyya ce kawai ta sha Mango juice, bayan sun dan jima Ammi ta kara musu sannu suka wuce, sosai itama taji dadin ganin jikin Rafi'ah. A haka rayuwar Rafi'ah ta dinga tafiya wata rana ta tashi garau wata rana taita amai harda zazza6i, duk bayan kwana biyu Jawad ya kanzo ya dubata, ba laifi yanzu tayi sabo dashi ba kadan ba, tin tana kin gaya masa abinda takesan ci harta fara fada masa, wata rana ma a waya zata kirashi, idan kuwa ta kira ko me yake sai ya bari ya kawo mata abinda ta bukata, kullum kara kwantar mata da hankali yake yana nuna mata misalai kala kala wanda suka faru kuma a yanzu komai ya zama tarihi. A yanzu a gidansa yake kwana, abinci kawai yake zuwa yaci idan yaga dama shima, dan mostly idan yaje gaishesu baya wani cin abinci, Mami kuwa komawarsa gidansa ba karamin dadi ya mata ba, hankalinta kwance ya fiye mata yazo ya gaisheta ya tafi, kayan Babies yake saya sosai yana tarasu cikin wani akwati, sai da yaga ya cika sannan ya daina sayan kayan, gaba daya unisex ya saya saboda baisan me zata haifa ba. Bangaren Sameer ma baiyi kasa a gwiwa ba, yakan zo ya duba Rafi'ah time to time, shima duk abinda yasan tana so saiya kawo mata, ita dai kawai kulashi take amma harga Allah batasan zuwan sa gidan, bata so ta sake sakin jiki da dangin Yusuf, yawanci Jawad yana haduwa da Sameer a gidan, idan ya tambayi Rafi'ah sai tace wani dan uwan Yusuf ne, ba wani shiri suke da Sameer ba, ko gaisuwa randa bata kansu basa yi. Rafi'ah kuwa tin sanda cikinta ya girma take zama da hijab, idan ta cire hijabi to tana tare da Ummi ne ko Mummy ko kuma Saudat, amma ko Abba ne yazo yini zatai tana yawo da hijab a jikinta, musamman da cikin ya shiga wata 8, kullum fadansu da Ummi ta tashi tayi aiki, dan tinda ta daina laulayi Ummi ta raba musu aikin gida ita da Saudat, wani lokacin harda kuka take karasawa sabida gajiya, ga ciwan baya da yake daminta sosai, amma hakan baisa Ummi ta daga mata kafa ba, gaba daya ta kara ramewa tayi fari akan da. kwanciya tayi akan gado tana sauke ajiyar zuciya, toilet dinta ta gama wankewa shine ta mike ta dan huta, tana jin an bude kofar dakinta ta juya tana kallan me shigowa, Ummi ce ta shigo da shirinta na zuwa aiki, ta zauna gefen Rafi'ah dake kwance ta ce "Kin sharemin parlorn?" Girgiza kai tayi kamar zatai kuka ta ce "Banyi ba, wallahi na gaji Ummi" Ummi ta mike tana kallanta ya ce "U don't have to, ki tashi kije ki gyara parlorn nan, sannan kuyi abinci idan kinga dama kuma ki gudu ki barta tayi ita kadai, idan kin huta kuma ki wanke inner~wears dinki da kika jera min su a toilet dan bazan wanke ba" hawayen idanta ta share bata ce komai ba, Ummi ta nufi kofar fita ta ce "Sai na dawo" tana fita Rafi'ah ta jawo phone dinta ta kira Mummy, bayan ta daga tayi sallama, da kyar ta amsa tana danne kukan dake cinta, Mummy da hankalinta ya fara tashi ta ce "Lafiya Fatima? Meya faru ne?" Cikin muryar kuka ta ce "Kinga Ummi bata daina sani aiki ba, kuma bayana ciwo yake bazan iya ba wallahi" daga haka ta fashe da kuka, Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To kiyi shiru ki daina kuka, kiyi abinda zaki iya sauran ki bar mata shi, zanzo yau da yamma, ban san meyasa Zainab ke haka ba wallahi, aiki ai kina yi amma wallahi baza kiyi abinda yafi karfin kuba, dama caan ba lafiya ba balle kuma ga larura, zanzo da yamma idan ta dawo" to kawai tace tayi hanging call din, da kyar ta mike ta zauna, ta kurawa kananun kafafuwanta ido ganin yadda suka kumbura, ta zira su kasa gently ta sauko akan gadon sannan ta dauki hijab dinta ta saka, koda ta sakko kasa kwanciya tayi akan kujera, sai sauke numfashi take daki daki, tana nan zaune Saudatu ta fito a kitchen tana murmushi ta ce "Anty Rafi'ah lafiya dai?" Ta ce "Ehh, hutawa nake" daga haka ta turo baki ta gyara kwanciya akan kujera ta limshe ido, bacci ne me shegen nauyi ya dauke ta, sai karfe 12 ta tashi, tana kallon agogo tayi sauri ta dauko tsintsiya sannan ta dawo ta fara share parlorn, tana gamawa kuwa batai mopping ba Ummi ta shigo tayi parking, Rafi'ah ta kalli Saudatu dake dariya kasa kasa ta ce "Dan Allah kice mata banda lafiya har amai nayi, zanje na kwanta" daga haka ta wuce sama da sauri. ```1 month ltr``` Tsaye suke duk tasu a kofar room din da Rafi'ah ke ciki, kana ganinsu kasan suna cikin babban tashin hankali, musamman Ummi data kasa controlling tears dinta, tausayin Rafi'ah kawai take idan ta tuno azabar haihuwa, Mummy dai na jingine da pillers din wajen ta limshe idanuwanta, banda salatin Rafi'ah da kiran Ummi da take ba abinda su ke jiyowa, Abba dai na tsaye yana ta addu'a sai kaiwa yake yana kawowa a area din wajen, bayan few minutes Dr Hisham ya fito a room din, Ummi ta mike da sauri tana kallansa ta ce "How is she Dr?" Ya ce "Alhamdulilah kenan, amma gaskiya ba zata iya haihuwa da kanta ba, zamuyi mata CS but sai mijinta yayi signing" Ummi ta share hawayen idanta ta zauna, Abba ya ce "Let me sign Dr" Dr Hisham ya girgiza kai yana kallan Abba ya ce "U can't sign both yallaboi, mijinta zai fara signing sai kuma kai" a fusace Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "Wane irin miji kake magana bayan ga mahaifinta nan, shekara nawa ana kawota asibitin nan kunfi kowa sanin danginta, mijin da shekara daya ba'a san inda yake ba, idan baza kuyi abinda ya dace ba mu kaita wani asibiti mana" sauke idansa Dr Hisham yayi ya ce "Kiyi hakuri Madam, rules din aiki ne ba wai nina fada ba" daga haka ya kalli Abba ya ce "Muje sai kayi signing din" daga haka Abba yabi bayansa zuwa office, cikin 20 minutes aka gama komai aka shiryata, ko magana bata iya yi sai kallon Ummi da take hawaye na sakko mata har aka turata cikin dakin. gaba daya jikinsu ya gama sanyi musamman Ummi da hawaye ya ki daina sakko mata, addu'a babu irin wacce batayi. Kusan 1 and half hour suna tsaye a wajen sannan Dr. Hisham ya fito, Abba ya kura masa ido yana kallansa, ya danyi murmushi yana kallan Abba ya ce "It was successful Sir, an samu cute baby girl" ajiyar zuciya suka sauke, a tare duk suka amsa da Alhamdulilah, Abba ya ce "Can we see her?" Ya ce "Not yet, za a mata allura ne bayan awa daya zata tashi, but u can see the baby, zasu kawo muku ita soon" daga haka ya wuce office dinsa yana cire hand gloves din hannunsa. Kafin a fito da Baby Mummy ta yiwa mutane sunfi 30 waya cewa tayi jika, bayan minti 10 nurse din ta fito da Baby a hannunta, sai kamshi take saboda yadda aka gyarata sosai, Ummi tayi saurin mikewa ta kar6eta sannan ta bude fuskar Babyn dake rufe da towel, sai da zuciyarta ya tsinke ganin kamannin Yusuf karara, ta sauke ajiyar zuciya ta mikawa Abba Babyn, shima same thing abinda ya gani, ya danyi murmushi ya kai bakinshi saitin kunnen Babyn ya mata kiran sallah hade da addu'a, hanging wayar Mummy tayi ta kar6a Babyn tana murmushi ta ce "Gata kamar shashashan ubanta kuwa" Abba dai ya kalli Ummi ya ce "Bari naje sallah na dawo" ta ce "Safe" Mummy ta ta6e baki ta ce "Wallahi da ana canza halitta dana canza miki kamannin Yusuf, dan bai kamata ki dauko kamarsa ba, baki sanshi ba bai sanki ba, banda ma hukunci na Allah taya zakiyi kama da Yusuf, uban me ya tsinana miki a rayuwa" goge dan hawayen idanta tayi ta ce "Allah ya taimakeshi watarana yazo yana kirarin shine mahaifinki, wallahi saina yaga masa rigar rashin mutunci, sai ya kwammace bai sanni a rayuwa ba, balle dangi na" Ummi dai bata ce komai ba, tasa tissue ta goge hawayen daya ke kokarin gangaro mata. Dakin da Rafi'ah take kwance suka shiga, bacci take sosai banda numfashi babu abinda take saukewa, Ummi ta kamo hannunta tana kallanta ta ce "Allah ya baki lpy daughter" Mummy ta ajiye Babyn a gadonta ta zauna gefen Rafi'ah tana mata addu'a. Kafin ta tashi mutane sunzo ganin Baby, makwabtan Mummy da Ummi sai kuma friends din Ummi, Anty Amina da 'yan gidansu sai daga baya suka zo, Ammi kam ita ce farkon zuwa ita da Sameer, Mami ma tazo sai murmushi take tana yaba kyan yarinyar kamar da gaske, duk da itama batasan Yusuf sosai ba amma taga kamanninsa da Babyn, Sameer dai ya dinga kallan Babyn dake kwance tana bacci, bayan 5 minutes Rafi'ah ta fara motsa karfarta, duk occupants din dakin suka dawo kallonta, ta fara bude ido a hankali tana salati, Ummi ta mike tana kallanta ta ce "Rafi'ah" kokarin tashi take amma ta kasa, Mummy ta dagata ta zauna ta ce "Sannu, kinajin ciwo ne?" A hankali ta nuna mata dai dai inda aka mata surgery din, Mummy ta ce "Sannu" limshe idanuwanta tayi ta budesu, sannan ta fara bin katon dakin da kallo, kowa na dakin take kalla amma bata ga Jawad ba, he once told her that duk lokacin data haihu tana bude idanta zata ganshi a gefe, but he is absent now, suna hada ido da Mami tayi saurin kawar da kanta gefe, the same thing daya faru lokacin data kalli Umman su Anty Amina, Ikleemah na zaune kan carpet tana ta danna phone dinta, jin Mummy ta ta6a ta yasa hankalinta ya dawo waje daya, ta sauke ajiyar zuciya kawai, Mummy ta ce "U didn't ask for ur Baby daughter" sauke kanta ta kara yi tana wasa da ring din hannunta, Mummy ta ce "Bari na dauko miki ita" kan gadon Babyn ta koma ta dauko Babyn, sai kallon towel din da Babyn ke ciki take, Mummy ta mika mata ita ta ce "Congratulation for having her, Allah ya kare miki ita daga sharrin masu sharri" zaro ido Rafi'ah tayi ganin fuskar Babyn, her eyes, lips, the fair skin, nose gaba daya is exact as Yusuf's own, fashewa tayi ta kuka ta rungume Babyn a jikinta kam kam tana fadin "Why didn't u resemble me Habibty, i was the one who take care of u since from the day i got u, i suffered for 9 months, i cried several times because of u dear, isn't all this a prove to resemble me dear? bana bacci da kyau, bana ci da kyau just because of u, meyasa ni baki yi kama dani ba" share hawayenta tayi ta kara kurawa Babyn ido, sai kuma ta kara rungumeta ta ce "Anywhere, i luv u Habeebty, ba wanda zai miki irin son da zan maki a duniya, i still remain ur mum and Dad, nice komai naki a rayuwa, if anyone's to blame, he's mistaken dear, i'm only yours, ke tawa ce ni kadai na, i luv u Habeebty" ta kara rungumeta tana kuka sosai da sosai, duk jikin mutanen dakin sai yayi sanyi, musamman Ammi data kasa tsayuwa sai ficewa tayi a dakin. _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _4_ Kar6an Babyn Mummy tayi a hannunta ta ce "Stop crying like this daughter, ke daya kamata ki godewa Allah kuma" hannunta tasa ta share hawayen daya sakko mata, Mummy ta zauna gefenta bayan ta kwantar da Babyn ta ce "Calm down and rest dear, what do u want to eat?" a hankali ta ce "Kunu zan sha" Mummy ta jawo basket din da Ammi ta kawo ta dauko flask ta zuba mata kunu cikin mug sannan ta mika mata, a hankali ta kar6a tana kallan Umminta dake zaune tayi shiru ta ce "Thank u mothers". Kwanan Rafi'ah uku a asibiti aka sallameta, kuma har suka koma gida Jawad baizo ba sakamakon tafiyar da aka sa shi yayi a wajen aiki, tin kwana daya da Rafi'ah ta haihu Mummy ta gaya masa hankalinsa ya kasa kwanciya, komai yake a wajen he's in a hurry, so yake ya gama komai ya koma kano a ranar amma hakan bai samu ba, dolensa ya kara kwana biyu. Da yamma Rafi'ah na zaune a dakin Ummi tana breastfeeding Babynta aka turo kofar, ta juyo tana kallan direction din kofar, Ummi ta shigo da flask a hannunta, ta ajiye a gefensu tana kallanta ta ce "Hope u are not in any pain, yace idan kinajin ciwo we should let him know" ta girgiza kai a hankali ta ce "Ni banajin komai, kawai dai wajen ne yake dan zogi" Ummi ta ce "Kina shafa maganin ne?" Ta ce "Eh" Ummi ta ce "To idan kun gama ki kawota gun Gwaggo sai ki huta" a hankali ta ce "Ohk zan kawota" Ummi ta mike ta ce "Abinci fa?" Tayi saurin girgiza kai sannan ta ce "Not now" daga haka Ummi ta fita ta jawo musu kofar, few minutes ta gama ta kwantar da Babyn a gefenta ta kwanta itama, jawota tayi very close to her ta rungumeta ta limshe ido, nan da nan duk sukai bacci, ganin shiru~shiru basu fito ba yasa Ummi ta koma sama duba su saboda yadda Gwaggo ta matsa a kawo mata Babyn, tana shiga dakin ta samesu suna bacci, Ummi ta kura musu ido cike da tausayi, sai kuma tayi murmushi ta juya, she never thought Rafi'ah zata so dan da zata haifa haka, tana sauka kasa Gwaggo ta ce "Ina jaririyar ne Zainab, idan ba'a so a bani ba sai na hakura ba, ni dama ba ita nazo dubawa ba jikata nazo gani na mata ya jiki" Ummi ta danyi murmushi ta ce "Hajiya Gawggo na samu sunyi bacci ne, kuma idan zan daukota zata tashi ne" Gwaggo ta ta6e baki tana kallan Mummy da Anty Salma ta ce "To sai a kira uban Rafi'ah ya maidani Bauchi yau, tinda dama daga cewa anyi haihuwa yaje ya daukomu muga 'ya, gashi kusan awana 1 ban dauki 'yar a hannuna ba" Mummy ta ce "Gobe fa zaku koma Gwaggo ai zaki dauketa harki gaji" Gwaggo ta mike ta ce "Ba sai nama dauketa ba, 'yar da akace da ubanta take kama, gara dai na ciccibi ita Rafi'an tinda itama bata fi a dauketa ba" Har Mummy zatai magana Anty Salma tayi mata alamar tayi shiru. Anty Anina ce kwance a parlorn ta ita da Anty Rahama suna hira, kamar an tsikareta ta mike ta ce "Ni kuwa Khadija tasan Rafi'ah ta haihu?" Anty Rahama ta girgiza kai ta ce "Ta ina zata sani, dama bamu zamu gaya mata ba, kuma kusan shekara bama waya da ita, ta ina zata sani to?" Anty Amina ta gyara zama ta ce "Bakisan Khadija ba kenan, zata iya sa ayi mata bincike, idan kuma taga dama zata watsar dasu ne kawai" Anty Rahama ta ce "Shiyafi mata sauki wannan, gaskiya yarinyar akwai kyau kam, kinga dazu da Yah Muhammad ya daukota, har ta danyi kiba, wannan da namiji ne cewa za'ai kakinta Yusuf yayi" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "Dama ai shine me kyau din, ita dai Rafi'ah fara ce amma bazata hada kanta da Yusuf ba, kwata kwata basu dace ba" Anty Rahama tayi dariya ta ce "Basu dace ba kam, gashi ai sun rabu" shiru Anty Amina tayi jin an bude kofar parlor, Ikleemarh ta shigo ta zauna gefensu tana turo baki, Anty Rahama ta mike ta ce "Waya ta6a ki?" Kuka ne ya kwace mata ta ce "Ba wannan kanwar Kakan su Rafi'an bace, naje wucewa ta dinga zagina wai harda cewa nima na kwaso ciwo, ai naga su suka fara ciwon kafin nayi" Anty Rahama ta ce "Share hawayenki, ai ciwo yanzu suka fara gani, ciwo ya wuce wata biyu a sako yarinya tazo gida ta haihu miji bai zo ba"... Kukan Babyn ne ya tasheta daga baccin da take, ta mike a firgice tana kallan Babyn, dagota tayi ta rungumeta tana share hawayen idanta, daga dan baccin nan data kwanta mafarkin Yusuf tayi yazo yana ce mata ta bashi Babynsa, ta limshe idanuwanta tana girgiza kai ta ce "It's impossible, she's only mine" daga haka ta gyara Babyna jikinta tana kallan idanta dake bude, silently ta ce "Ni kadai kika sani Habeebty, nine mamanki nine babanki kinji, inma akwai wani mahaifinki a duniya to Ya Jawad ne" hawayen idanta ta share ta sakko a kan gadon still holding her baby ta bude press dinta ta ciro wayarta ta kunna, raban data kunna ta tin ana gobe zata haihu, yau kwana 4 kenan, Ameera ma ta wayar Ummi suke waya, bayan wayar ta kunnu tasa hannu zata bude lock din kiran Jawad ya shigo, ta dan turo baki sannan tayi picking call din, Jawad yayi sallama, shiru bata amsa ba, ya sake sallama, nan ma shiru, a hankali yake jiyo sound din kukanta, ya danyi murmushi ya ce "I apologize dear, i'm on my knees pls do forgive me" dan turo baki tayi ta ce "Where have u been Yaya?" Ya ce "Kaduna, but i'm now in Kano, yanzu ina gidana zanyi wanka saina zo, hope my Baby is fine" a hankali ta ce "Yes, when will u come?" Ya ce "Just few minutes from now" ta danyi murmushi ta ce "Sai kazo to" ya ce "Alright dear" hanging call din tayi ta goge hawayen idanta sannan tasa hijab ta dauki babyn suka fito, tin suna sakkowa a stairs Gwaggo ke kallansu, bayan ta karaso ta ce "Ke ba haka ake bafa, kinbi kin kankame 'ya ko kunya bakyaji 'yar fari ce fa" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ajiyeta akan cinyar Gwaggo sannan ta juya zata shiga kitchen Ummi ta ce "Kinci abincin ne?" Ta ce "Zanci" daga haka ta shige kitchen. Mummy ne da Anty Salma sai Saudatu suna hada girkin dare, Rafi'ah ta dan tsaya gefe tama rasa ta ina zata fara, Anty Salma dake kallanta ta ce "Lafiya dai Rafi'ah?" Mummy ta juyo tana kallanta itama, girgiza kanta ta danyi ta ce "No, ba komai" Mummy ta ce "Ko kinasan wani abu?" ta kara girgiza kai, Mummy dai ta fahimci tana san abu amma ta kasa fada ne, hannunta ta wanke a sink sannan ta kalli Rafi'ah ta ce "Muje parlorn Abbanku" bin bayan Mummy tayi a hankali har suka shiga parlorn, bayan sun zauna ta ce "Tell me what's wrong with you, what do u want" sauke kanta tayi kasa a hankali ta ce "Dama Yayane yace wai yana hanya" Mumny ta ce "Wane Yaya, ko Sameer" ta girgiza kanta a hankali ta ce "Ya Jawad" Mummy dake kallanta ta ce "Yaushe ya dawo?" Ta ce "Dazu, yacemin yana gidansa wai daga nan zai taho nan" Mummy ta dinga kallanta kafin ta ce "Ohk, sai a kawo mishi abinci nan" daga haka ta mike ta fita a parlor Rafi'ah ta bita da kallo, ta jima zaune anan parlor ita kadai, horn din mota data ji ne yasa ta mike ta leka ta window, ganin motar Jawad yasa ta danyi murmushi ta koma ta zauna. Yana parking ya fito a motar da key dinsa a hannu, ya sha farar shadda, yayi wani kyau sosai sai kamshi yake, a hankali ya dinga takawa zuwa entrance din gidan, bayan ya danna bell yaja ya tsaya a gefe, Ummi ce kadai da Gawggo a parlor sai Saudatu da shigowanta kenen ta wuce ta bude kofar, a hankali ta ce "Bismillah" Jawad ya shigo parlorn kansa a kasa, kan carpet ya zauna yana murmushi, Ummi ta ce "Jawad ne? Yaushe ka dawo?" Ya ce "Dazu Ummi, ina yini" ta ce "Lafiya kalau Jawad, how is work?" Ya ce "Alhamdulilah, ashe an samu Baby girl" Ummi ta ce "Wallahi, gata nan a kwance tana ta bacci" kallan dan karamin bed din babyn yayi kafin ya ce "Allah ya raya ta da imani" Ummi ta ce "Ameen" kallan Gwaggo yayi data zuba masa ido tin shigowarsa, ya ce "Ina yini Hajiya" ta ce "Lafiya kalau yaro, kai din dan wane gida ne?" Ummi ta ce "Yaran Hajiya Hadiza ne" Gwaggo ta ce "Kishiyar Halima kike fada?" Ta ce "Ehh, shine babba" Gwaggo ta ce "Ba shakka gashi nan kamar honorable mahaifinsa, yayi aure ne?" Ummi ta mike ta ce "Aa baiyi ba tukunna, Saudat kaishi parlorn Abba" Saudat dake goge kan dinning table ta ce "Toh" mikewa yayi yabi bayanta har suka shiga parlorn, ta juya ta fita, a hankali ya ce "Nagode" kan carpet ya zauna ya dauko wayarsa a pocket yayi dailing number Rafi'ah, harta gama ringing bata dauka ba, ajiye wayar yayi ya dan juya, hangota yayi ta kifa kanta akan dinning table, ya mike a hankali yana murmushi ya karasa inda take zaune ya ce "How are u dear" kin kulashi tayi, ya kamo hannunta ya ce "Pls get up dear, ko so kike nayi miki kneel down?" Dago kanta tayi a hankali ta ce "U don't have to, but u broke the promise u made to me" murmushi yayi yana kallan face dinta ya ce "Aina ce maki a wajen aiki ne aka turani, amma kinsan da babu abinda zai hanani zuwa clinic ranar, now how are u feeling?" A hankali ta ce "Fine" ya kai hannunsa face dinta ya share mata guntun hawayen daya sakko, ta sauke kanta kasa ta ce "And u are not happy for seeing me" ya dan zaro ido yana murmushi ya ce "Who told u, i am more than happy Fatima" wasa taci gaba dayi da fingers dinta tana murmushi, ya koma kan carpet ya zauna yana kallanta ya ce "Most i tell u to bring her for me, ko rowa zakimin" ta tashi a hankali ta ce "No, ni ai bana rowa" daga haka ta fita a parlor, a corridor ta tsaya ta leka parlorn taga Ummi ce kadai, ta fito calmly ba tare data kalleta ba ta dauki Babyn ta koma parlorn Abba, gefen Jawad ta zauna ta mika masa Babyn ya kar6a, kallan fuskarsa kawai take lokacin daya kar6a Babyn, ya dago kansa yana kallanta ya ce "She's so cute, Allah ya raya mana cikin addinin islama" shiru tayi ta fara goge hawayen idanta, ya kamo hannunta ya ce "Why is it that kuka baya maki wahala Fatima, u waste ur tears too much, what makes u to cry, tell me now" cikin muryar kuka ta ce "Ni shine batai kama dani ba" ya danyi murmushi yana kallan yadda take tura masa baki as if shiya halicci Babyn, ya ce "So u thank God and stop crying dear, mu godewa Allah daya bamu this cute angel, is she not cute?" ta daga masa kai ta ce "She is" ya ce "Kamar ke ba, kinma fita kyau, just that ta fiki hanci" ta dan ta6e baki ta ce "Inma kace bani da kyau ni ina ruwana" daga haka ta fara kokarin tashi a gefenshi, ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "No, don't go pls dear, kin fita kyau, kawai na fada ne, do u think zance ta fiki kyau ne bayan kena fara sani na kuma fara..." Shiru yayi ganin yadda take kallansa, yaja hancinta ya ce "My stubborn Rafi'ah" ta kauda kanta gefe ta ce "Let me bring food for u" daga haka ta tashi ya bita da kallo. _08103810398_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _5_ Bayan few minutes Rafi'ah ta dawo da tray a hannunta me dauke da snacks sai exotic da glass cup a gefe, calmly ta ajiye a gabansa ta ce "Here it is Yaya" Jawad ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Thanks" mikewa tayi yayi saurin riko hannunta ta zauna gefensa ya ce "Ina zaki je?" ta ce "Abinci zan kawo maka" ya ce "No, wannan ma ya isa" ta juyo tana kallansa ta ce "Kace fa baka ci komai ba" Ya ce "Ai zanci wannan" ta dan matsa baya a hankali ta ce "Alright" kara matsowa yayi gefenta ya kamo hannunta, ya kalli Babyn dake bacci hankali kwance sannan ya kara kallanta ya ce "Are u with me Fatima?" Ta daga masa kai a hankali, silently ya ce "I just want to tell u that, right from the day i met u, i love the way u smile the way u laugh, and u know what?" Girgiza masa kai tayi kanta a kasa tana kallan hannunta dake cikin nasa, limshe ido yayi ya tattaro courage dinsa ya ce "I notice that it was lo..." Shiru yayi jin an bude kofar parlorn, tayi saurin jaa baya tana kallan Mummy dake kallansu, ta ce "Meye haka Jawad?" Kansa ya dan shafa ya ce "Ehh, dama abu ne ya fada mata a ido shine na hure mata" Mummy ta zauna akan kujera ba tare data kalli Rafi'ah ba ta ce "Yayi kyau, when did u came back?" Ya ce "Ban jima ba, banma je gida ba, but daga nan can zan wuce" ta ce "Ohk" ya danyi kasa da murya ya ce "Congratulations once again for the cute Baby" ta ce "Thank u, baza kaci abinci bane?" Ya ce "No, wannan dinma ya isa" sai lokacin Mummy ta kalli Rafi'ah dake zaune gefe tana jujjuya ring din hannunta ta ce "Kar6eta ki bashi waje yaci abinci" mikewa tayi a hankali ta kar6i Babyn sannan ta nufi hanyar fita a parlorn, Mummy ta mike tabi bayanta ta ce "Idan ka gama zamu wuce tare" ya ce "Ohk to" daga haka taja masa kofar. Cikin minti kadan ya gama cin abinda zai ci ya mike yasa phone dinsa a pocket sannan ya wuce sink ya wanke hannu ya dawo ya dauka key din motarsa, a parlor ya tarar da duk ilahirin gidan amma banda Rafi'ah, ya dan durkusa ya ce "Zan tafi Ummi Allah ya raya da imani" Ummi dake murmushi ta ce "Ameen" Gwaggo ta ce "To ni tinda nazo banga Hadiza tazo barka ba dama kuma..." Da sauri Ummi ta ce "Tazo mana Gwaggo, tin muna asibiti ai tazo" Jawad ya mike ya nufi kofar fita, Ummi ta ce "Allah ya kiyaye" Mummy da Anty Salma suka mike sannan sukai musu sallama suka tafi. Har suka isa gida Mummy da Anty Salma hirarsu suke, shi dai yana ta driving but zuciyarsa ya tafi wani tinani daban, what if Mami taga ya sauke su fa? ta kuma tabbatar tare suke? dan karamin tsaki yaja yaci gaba da tuki, Mummy ta dan kallesa ta ce "Lafiya da tsaki haka?" Ya ce "Ba komai" ta6e baki tayi taci gaba da bawa Anty Salma labarin yadda Rafi'ah ta sha wahala a rainon cikinta. Dai dai kofar gida Jawad yayi parking, Mummy ta ce "Ya zaka dire mu anan young man?" Ya dan shafa tilin gashin dake kansa ya ce "Eh, zan fita an jima kadan that's why" Mummy tayi masa wani kallo ta ce "Ko kana tsoron uwarka ba" daga haka ta fito a motar Anty Salma ma ta fito suka wuce ciki, sai bayan shigarsu da minti 10 sannan ya gyara motar ya danna horn, bayan an bude gate ya shigar da motar yayi parking sannan ya fito ya nufi entrance din gidan, Ikram ce kadai zaune a parlor tana kallo, ta mike a hankali ganinsa ta ce "Yaya sannu da dawowa" ya ce "Thank u, Mami fa?" Ta ce "Tana kitchen" daga haka ya wuce kitchen walking gently, a bakin gas ya sameta tsaye tana gauraya pepper chicken din da take, ya rungumeta ta baya yana murmushi ya ce "Mami" ta danyi murmushi ta ce "Ahmad, saukar yaushe?" Ya ce "Yanzun nan, aiki kike?" Ta ce "Kai nake yiwa pepper chicken, naga basan cin abincin gidanmu kake ba, kaga koka tafi dashi sai kai warming dinsa, ai kana da microwave ko?" Ya ce "Yes i have, thank u mother" ta ce "To kayi wanka kafin na karasa" ya ce "Alright to" daga haka ya fita a kitchen din ya nufi dakinsa na da, ba kowa a dakin amma a gyare tsaf tsaf, ya cire rigar jikinsa ya dauki towel ya shiga toilet. Kananun kaya ya saka sannan ya fito a dakin, yayi kyau sosai da sosai sai kamshi yake, ya leka kitchen yaga bata nan, hakan yasa ya wuce part dinsu yana balle botton din hannunsa, a parlor ya sameta tana zaune ta zuba masa papper a plate sauran kuma tasa a warmer, ya zauna gefenta ya ce "Is this all for me Mami?" ta ce "Sure" a hankali ya jawo center table din gabansa ya fara cin naman, kusan minti 10 ba wanda yayi magana a cikin, Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ahmad" dagowa yayi yana kallanta ba tare daya amsa ba, ta ce "Yaushe zakai aure ne Jawad? 37yrs kana zaune min a gida haba dan Allah, yanzu ko Sadeeq da yake shekara 25 ai zai iya aure, ya gama degree dinsa yana masters, amma kai ka gama komai kana aiki, kana da gida sai dai kawai kaje gidan kayi bacci ka tashi ba mace, gidanma yana maka dadi ne a haka?" Sauke kansa yayi daga kallanta ya ce "Very soon insha Allah, ki daina damuwa" ta ce "To a ina yarinyar take, menene dalilin da bazai sa akai tambaya gidansu ba, why not now?" a hankali ya dauki tissue yana goge hannunsa ya ce "Saboda ta haihu ne, so i have to wait sai ta gama shayarwa" zaro ido Mami tayi tana kallansa, lokaci daya taji zuciyarta na bugawa, cikin sauri ta ce "Wa kake nufi ne, a ina take?" Ya ce "Wata yarinya ce, mijinta Allah ya masa rasuwa, dama kuma tin kafin ya aureta muna tare, so iyayenta suka aura mata shi" Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya kyauta, amma meya kaika auran bazawara Jawad? Ga 'yammata kaca kaca a fadin duniyar nan ka rasa wacce zaka aura sai bazawara" ya ce "Ita nakeso Mami, idan kika ganta baza kiyi tinanin ta haifi diya ba, dan itama bata fi diyar ba, bata cika shekara 19 bama a duniya" Mami ta masa wani kallo ta ce "A ina take, and what's her name?" Ya gyara wristwatch din hannunsa ya ce "Sunanta Zarah, tana zaune a unguwar rimi, amma iyayenta ba anan garin suke ba" Mami ta sake sauke biyayyar ajiyar zuciya ta ce "Tinda haka ka zabarwa kanka Allah ya kyauta, ni dai bazan maka fatan sharri ba, fatana ka samu wacce zata kula da kai" a hankali ya ce "Insha Allah" Mami ta ce "Kaji Rafi'ah ta haihu ko?" Ya juyo surprisingly yana kallanta ya ce "When?" Ta ce "Kwana hudu kenan, ai tayi~tayi ta haihu da kanta ta kasa, kasanfa ba wayo ne, da wata babbace tsaf zata iya haihuwa, to yarinya dai sai data galabaita ko hannunta bata iya dagawa sannan aka mata CS aka ciro mata diya mace, tana nan duk ta kara karewa kamar ba a cikinta aka ciro wannan 'yar ba, kuma diyar sak kama da ubanta, nidai nace wannan mutumi ya bar mata babban tabo a rayuwa, ai nasan duk inda zata shiga da 'yar nan sai dai ace kanwarta ce, ba wanda zaice ita ta haifeta ta, shi dai ya cucesu ya maida musu 'ya bazawara" shidai shiru kawai yayi yana saurarenta, caan ya danyi tsaki ya mike, ta ce "Ina zuwa?" ya ce "Gidana" ta ce "Sai gadarar cewa gidana gida ba mata, Allah ya kiyaye, kuma wallahi ka rage wannan uban gashin" ya dan shafa kansa ya ce "Gobe insha Allah" daga haka ya dauki food flask din ya fita ta bishi da kallo. Few minutes ya kai shi gidansa dake old GRA, ya fito ya bude gate sannan ya shigar da motar yayi parking ya koma ya rufe gate din, key yasa ya bude kofar shiga gidan, ya zare key din sannan ya maida ta ciki ya tura kofar, kujeru ne masu kyau a parlorn sai TV sai kuma air-conditioner dake kunne, ya wuce upstairs ya shiga dakin dake farko ya rufe kofar, dakin tas tas ya sha farin bedsheed, ya kwanta saman gadon ya jawo wayarsa ya kira Aliyu, bayan ya dauka ya ce "Ka dawo ne Aumad?" Jawad ya limshe idansa ya ce "Ehh, na dawo dazu, kazo mana sai mu karasa magana" Aliyu ya ce "Sai na tashi a aiki kenan, kana gida ko?" Ya ce "Ina gidana, zan baka address" Aliyu ya ce "Alright then, saina gama zan ta6a ka" daga haka yayi hanging wayar, number Rafi'ah yayi dailing, sai daya kusan tsinkewa tayi picking, ya ce "Dear" a hankali ta ce "Yes, i hope u reach home safe?" Ya ce "Fine, how is my Baby" ta ce "She's sleeping" ya ce "Ki shafamin ita" ta ce "Ohk, dazu kana min magana kuma baka karasa ba" ya ce "Zan karasa but inaso sai ina kallanki kina kallona" ta danyi murmushi ta ce "Alright to, ya gajiya" ya ce "Ba wani gajiya, how are u feeling now?" Ta ce "Da sauki sosai" ya ce "Allah ya kara maki lafiya, i will call u ltr, don't off ur phone pls" ta ce "To, sai anjima" ya mike ya ce "Thanks Baby" daga haka ya katse wayar, kallan wayar ta dinga yi tana tinani, ko to bataji daidai bane, ko kuma ce mata yayi ta gaishe da Baby?, ta dan ta6e baki ta mike ta shiga toilet kar ruwan wankanta yayi sanyi. Da yamma Mami tasa Sadeeq ya kaita gidansu Rafi'ah kamar yadda Abi ya bada umarni, bata wani jima ba saboda surutun Gwaggo, bayan taga Baby da Rafi'ah ta mike ta musu sallama, Gwaggo ta kalli Ummi ta ce "Ya dai fi babu akan baka zo ba, ita kishiyarki tinda nazo banga ta shigo ba, ga dai baki ga hanci amma tsit kake ji" Ummi dai bata ce komai ba, ta gyarawa Babyn kwanciya sannan ta rufa mata net, Gwaggo ta ce "Shi Muhammad din a wajenta yake ne?" Ta ce "Ehh, tinda akai haihuwan ya koma caan, kinga baki suna ta zuwa, bai katura muba muma bamu takura shi ba" Gwaggo ta ce "To dama ana suna kice ya dawo dakinki, kuma saiya rama miki kwanakin da yayi acaan, aike ba dutse bace" Mikewa Ummi tayi ta ce "Bari na kaiwa Rafi'ah tea Gwaggo" Gwaggo ta ta6e baki ta ce "Zandamemiyar budurwa sai an kai mata shayi saboda ta haihu, naga ba haihuwa tayi da kanta ba, ciro yarinyar akayi, ke dai kawai kice kina mata bauta" tin tini Ummi tayi wucewarta ta barta zaune kusa da Babyn tana ta zance. Bayan su Mami sun bar gidan su Rafi'ah gidan Kawu suka wuce kamar yadda ta bada umarni, a bakin gate tace yayi parking saboda ba dadewa zasuyi ba, daga haka ta fito ta shiga gidan, Ihsan ce kadai a parlor tana cin abinci, ta danyi murmushi ganinsu ta ce "Ina wuni Mami, Ikram bata zo ba?" Mami ta ce "Tana caan tana baccin nata na jaraba, ina Hajiya?" Ihsan ta ce "Tana daki" Mami ta wuce daki ta bar Sadeeq suna magana da Ihsan, a bakin gado ta zauna tana kallan Hajiya Fatima ta ce "Yau dai nace bari nayi kokari na karaso, ku bada zua ba muma haka" Hajiya Fatima ta ce "Aikin kyauta, ya yaran da maigidan?" ta ce "Lafiya kalau, ina Kawu?" ta ce "Kawu tin safe bai dawo ba, sai kuma dare" tana rife bakinta Sadeeq ya shigo ya gaisheta sannan ya koma parlor, ta kalli Mami dake zaune ta ce "Ni kuwa ina Jawad ne?" Mami ta ce "Yana nan kinsan yanzu bada mu yake ba, ya koma gidansa zuwa yake yana gaishemu" Hajiya Fatima ta ce "To lallaikam, ko dai ya fara neman aure ne?" Mami ta ce "Dazun nan ya gama gayamin, wai yarinyar ta haihu shiyasa zai jira saita yaye dan" Hajiya Fatima ta ajiye kayan hannunta da take ninkewa tana kallan Mami ta ce "Rafi'ah zai aura kenan?" Wani katon ashar Mami ta saki ta ce "Tabbdi ai sai dai idan bana numfashi, sunan ita waccen Zarah fa, kuma yace ma unguwar rimi take, sannan kuma ita mijinta ne ya mutu" Hajiya Fatima tayi murmushi tana kallan Mami ta ce "Kije dai ki kara bincike, tin ba yau ba ninasan Jawad san yarinyar nan yake, kuma da kike kirarin sunanta Zarah ba sunanta Fatima ba? Koba ita ta haihu ba, kawai dai rainin hankali yake so ya miki, amma so kam yarinyar nan yake so" nan da nan zufa ya fara karyowa Mami, ta rasa abinda zata ce tana tinani, caan ta mike ta fara neman layinsa a waya, bugu biyu ya dauka ya ce "Mami" ta ce "Duk abinda kake koma menene ka bari ka dawo gida ka sameni" ya ce "Mami i have some important things..." A fusace ta ce "Cewa nayi duk abinda kake ka bari kazo gida, umarni na baka ba shawara na nema ba" daga haka tayi hanging wayar ta dauki hand bag dinta kamar zata tashi sama ta fita a dakin, Hajiya Fatima ta bita da kallo tana murmushi. Kallan Aliyu Jawad yayi ya ce "Kaga mun fara maganar guy din can kuma Mami ta kirani urgently, so bansan me yake faruwa ba, i have to go now" Aliyu ya ce "Ba komai, gobe ai Saturday koda safe zamu iya magana, i will call u idan naji wani bayani" Jawad ya ce "Alright thank u" daga haka duk suka mike suka fita a parlorn. _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _6_ Parking Jawad yayi dai dai gate din gidansu sannan ya fito a motar ya rufe ya shiga ciki, Ikram ne a balcony tana wanke hijab dinta na islamiyya, ta dago tana kallansa ta ce "Sannu da dawowa" a hankali ya ce "Sannu" daga haka ya murda handle din ya shiga ciki, Abi ne kadai a parlor yana kallan TV, Jawad ya danyi kasa da kansa ya karasa gefensa ya zauna akan carpet ya ce "Sannu da hutawa Abi" Abi ya ce "Thank u son, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya mike ya ce "Let me see Mami" da kai Abi ya amsa masa sannan ya wuce part dinsu, tana nan tsaye a parlor sai kaiwa take tana komowa, jin an bude kofar tayi saurin juyowa tana kallansa ta ce "Who was that girl u were talking about? I want to hear more about her" zama yayi akan kujera yana kallanta ya ce "But i have told u iyayenta baza su bari aje yanzu ba, sai ta gama shayarwa zan baku address din gidansu sai aje tamba..." A fusace ta ce "Ni zaka mayar 'yar iska Ahmad? Are u here to tell me what i'm suppose to do, kaika fini sanin sharudan aurene, ko ce maka nayi auranta zakayi yanzu, so nake na santa na san iyayenta, now give me her number or their home address" dagowa yayi kawai yana kallanta ganin yadda take tada jijiyoyin wuya, ya limshe idanuwansa kansa na mungun sara masa ya ce "I will u give Mami, but pls u calm down, just have a peace of mind even for some minutes" harara ta dalla masa ta ce "Ce maka akai hankalina ba a kwance yake ba, just give me their address before i show u the bad side of me" ta karashe maganar tana kafe shi da ido, jin an bude kofar yayi saurin mikewa yana kallanta ya ce "I will get it to u now" riko rigarsa tayi ta ce "Ba inda zakaje, ka fadamin da baki" karasowa parlorn Abi yayi yana kallan Mami ya ce "Why all this shout Hadiza, muryarki har parlorna ana jinki haka" ba tare data kalleshi ba ta ce "Nace ka bani ko!!!" Shi dai kansa kawai ya sauke kasa, Abi ya cire hannun Mami a jikin rigarsa ya ce "What is exactly happening Ahmad?" A hankali ya ce "Ba komai" Abi ya ce "Ba komai as in how, duk wannan ihun a banza take maka kenan" dan kallan Mami yayi ya koma gefe, Abi ya kalleta ya ce "have a seat" kin zama tayi still tana ta hararan Jawad, Abi ya ce "Magana fa nake miki Hadiza" Mami ta juyo tana kallansa ta ce "Jiransa nake ya bani address din gidan yarinyar da yake nema" da mamaki Abi yake kallanta ya ce "Me zakiyi to? Ke ina ruwanki kina mace a matsayinki na uwa, in dai wannan maganar ne kima barta, when the time comes zakiji komai, jeka abinka Ahmad" a hankali ya ce "Sai da safe" daga haka ya fice a parlorn Mami ta bishi da harara, zama tayi akan kujera ta fara share hawayen idanta cikin kuka ta ce "Meyasa kake min haka Honorable, sai kace bani na tsuguna na haifi Jawad ba, akwai wanda yake da iko dashi duk fadin duniyar nan idan bani ba, amma duk sanda nazo da bukata ta saika dinga sawa yana bijiremin" Abi ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce "Nasan ke kika haifeshi, kuma kina da iko akan Ahmad, ba wai ina sa shi ya bijire miki bane, yanzu menene naki na neman address din yarinyar da yake nema? So kike ki zubar da girmanki a gaban 'ya'yanki ne, Ahmad yana miki biyayya iya iyawarsa but wallahi am assuring u this duk ranar da kika kaishi karshe kar kiyi mamaki, banda abinki ki kyaleshi mana, shiba yaro bane yanzu, ya san duk abinda ya dace da wanda bai dace da shi ba, so duk abinda kika ga yayi ki masa addu'a kiyi fatan Allah yasa shine alkhairi a gareshi, amma ba ki zauna kina kara daga masa hankali ba" share hawayen idanta tayi ta ce "To shikkenan, na hakura amma wallahi idan wacce nake zargi yake so yama sa a ransa babu aure a tsakaninsu" daga haka ta mike ta shige daki Abi ya bita da kallo. _~The next day~_ Washegari ya kama jibi suna, Rafi'ah na zaune tare da Ameera a daki suna dan hira Ummi ta shigo, Rafi'ah ta mike tana kallanta ta ce "Munyi magana da Mummy dazu" Ummi ta ce "Kizo dakina yanzu" daga haka ta juya, kallan Ameera tayi kamar zatai kuka ta ce "Wai fa akan sunan Babyn ne, nina ce susa sunan duk wanda suke so, nasan ko nace asa sunan wacce nake so ba lallai asa ba" Ameera dake kallanta ta ce "Kamar ya? Ba dai su suka ce ki fada ba?" zama Rafi'ah tayi a bakin gado tana share hawayen idanta ta ce "Sunan Maman Doctor nakeso asa Ameera, but nasan they won't listen to me" daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta tana kuka, Ameera ta ce "U shouldn't think that Fatima, kika san ko zasu yarda" ta girgiza kai a hankali ta ce "Doctor have no prents alive, even one Ameera, ba shi da uwa ba shi da uba, sai Ammi kadai ce take son shi, ya sha fadamin in dai ya haifi mace zai sa sunan mamanshi idan Baby boy ne sunan mamanshi, i have to fulfill his wish Ameera, nasan ya min abinda bazan manta da shi ba harna koma ga Allah, amma at this time inaso na cika masa burin daya dade yana fata, and i don't think they will accept it" Ameera ta sauke ajiyar zuciya tana kallanta cike da tausayi ta ce "Ki gwada, idan sun ki then u accept whatever they say" mikewa tayi a hankali ta share hawayen idanta sannan ta bude press dinta ta dauko hijab ta saka ta fita a dakin Ameera ta bita da kallo, jikinta duk a sanyaye ta bude dakin ta shiga hade da sallama, Ummi dake duba abu a press dinta ta ce "Kije kawai Rafi'ah zata fita, anjima sai muyi magana idan ta dawo" har zata juya Mummy ta ce "Come here" karasowa tayi kanta a kasa ta ce "Gani" Mummy ta ce "Ya idanki yayi jaa?" A hankali ta ce "Ba komai" sai lokacin Ummi ta kalleta, bata dai ce komai ba taci gaba da abinda take, Mummy ta ce "U said nothing, amma kamar kinyi kuka?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "Kaina ne kawai yake ciwo" Mummy ta ce "Go and make sure u take your drugs" juyawa tayi bata ce komai ba ta fita a dakin ta koma dakinta. Jawad ne zaune a parlorn gidansa shida Aliyu, kowa da abinda yake tinanin, caaan Jawad ya danyi tsaki ya ce "Tabbas baya kasar nan, to amma wa kake ganin zai san inda yake?" Aliyu yayi shiru yana tinani, sai kuma ya ce "Idan fa akwai wanda zai san inda yake so definitely it most be me ko Mukthar, sai kuma wannan cousin din nasa Sameer" Jawad ya cire glasses din idansa ya ce "Kenan duk baku sani ba?" Aliyu ya ce "Ehh, ko ita maman Sameer din bata sani ba, dan kwana biyu da faruwan abun sun zo asibitinmu ita da mijinta ko zasu samu wani bayanai akansa amma babu" mikewa Jawad yayi yana zira hannayensa cikin pockets din wandansa ya ce "Kace baya shan komai?" Aliyu ya ce "Kyakkyawan sani nayi wa Yusuf, kaga dai shi kikita ne ko? Amma wallahi kwayar magani da kyar yake hadiya balle kuma har yayi shaye shaye, ni kaina abin mamaki ya bani, i don't know what comes over him, yana san matarsa fa wallahi" dan karamin tsaki Jawad yaja ya ce "To idan yana santa me zaisa ya saketa da ciki, almost a year harta haihu bai dawo ya ganta ba" Aliyu ya ce "Shine kuma abin dubawa, amma ina ganin koma menene ya faru da sa hannun mutanen gidansu, tinda duk tasu suka tafi, kuma suka tafi harda matar da suke so ya aura, Yusuf ba zai ta6a cutar da Fatima ba Ahmad, karkace nayi maka shishigi game da abinda kake, kai aikinka ne ni kuma ina fadan abinda nasan Yusuf zai iya ne, Yusuf ba shi da hali marar kyau Barrister sai dai kuma kasan dan Adam ta wani bangaren" a hankali Jawad ya zauna gefen shi ya ce "No, ai wannan ba shishigi bane, nima a nawa fahimtar banga alamun rashin gaskiya a tattare da shi ba, just that ni bana shiri da shi sabida wani dalili nashi" Aliyu ya ce "Yanzu menene abinyi kenan?" Jawad ya maida glasses dinsa ya ce "We should keep on praying, idan aka kasa gano abu sai ayi ta addu'a, but ina tabbatar masa duk ranar daya dawo he will be arrested kuma matar daya saka tayi masa nisa by then, dan tini ta auri wanda zai sota har abada" Aliyu ya ce "Allah ya za6a mana mafi alkhairi, ya kuma bayyana shi" a hankali ya ce "Ameen, thanks for ur time Dr. Aliyu" Aliyu ya mike yana mika masa hannu ya ce "Ur welcome Barrister, in dai naji wani abu i will let u know" Jawad ya ce "Nagode sosai" har bakin motarsa ya rakashi ya bude masa gate bayan ya fita ya rife ya dawo ciki, phone dinsa ya dauka ya kira Rafi'ah, tana fara ringing ta dauka hade da sallama, ya ce "How are u?" Ta ce "Fine" ya ce "What about my Baby" ta danyi murmushi sannan ta ce "She's fine too, sai kuma kuka takemin jiya i didn't slept well at night" ta karashe maganar tana turo baki kamar yana kallanta, ya dan shafa kansa yana limshe ido ya ce "To ki bani ita kawai" ta ce "To kazo ka kar6a idan zaka iya rikewa" ya bude idanuwansa ya ce "Sai dai idan tare duk zaku dawo gidana, kinga sai mu rike babynmu da kyau" a hankali ta danyi murmushi har yana jiyo ta sannan ta ce "Sai dai ita din dai" ya ce "A'a ni da Mummy da daughter nakeso" tayi dariya kawai bata ce komai ba, Jawad ya ce "Ya jikinki din ya warke?" Sai data kalli wajen CS dinta sannan ta ce "Saura kadan" ya ce "Allah ya sauwake" ta ce "Ameen" ya ce "I will call ltr, i'm going home, tin jiya banje na gansu ba" ta ce "Alright saika dawo" daga haka yayi hanging wayar ya dauka hula ya saka sannan ya dauki key din mota ya fito a gidan, garin is too cloudy sai iska da ake busawa me kura, sai daya rife duk windows din gidan kafin ya fitar da mota ya kulle gate din sannan ya dauki hanyar gida. Kafin ya iso gida an fara ruwa sosai da sosai, yana isa yayi horn aka bude gate sannan ya shiga yayi parking ya fito da sauri ya nufi entrance din gidan, ba abinda ya tsana irin yaji shi a jike, ba kowa a parlorn hakan yasa ya wuce dakinsa ya canza kaya sannan ya dawo part din Maminsa, Sadeeq da Ikram na zaune a parlorn suna cin abinci, duk suka masa sannu da zuwa sannan ya shige ciki, dakin ma ba kowa amma yana jiyo alamun mutum a toilet, hakan yasa ya kwanta kan gadon ya rufe kafafuwansa da blanket, after few minutes Mami ta fito a toilet, ta tsaya tana kallan kan gadon don dakin yayi duhu, a hankali ta ce "Sadeeq" ya bude idanuwansa yana kallanta ya ce "It's me" ta hade rai ta juya masa baya sannan ta nufi kofa ta fice a dakin, mikewa yayi da kyar dan sanyi yakeji sosai, ya fito a dakin ya shiga wanda ke opposite dinsa, yana shiga Mami ta mike daga zaunen da take ta ce "Uban me zan baka ne Jawad kake bina haka, cin mutunci da kayimin bai isheka ba kazo ka karamin wani ne?" a hankali ya ce "Dan Allah kiyi hakuri ki daina fishi dani Mami, i have no mother but u, ke fa kika haifeni idan banzo wajenki ba wajenwa kike tinanin zanje naji dadi Mami, pls forgive me Mami" tsayawa tayi tana kallansa ganin yadda ya kamo hannayenta duka biyu, sosai taji jikinsa yayi dumi, ta ce "Are u sick?" Ya ce "Kawai sanyi nakeji Mami" a hankali ta ce "Ka kwanta to" kwanciya yayi akan gadon yayi pillow da cinyarta, ta jawo blanket ta rufa masa, ya limshe ido yana jin wani dadi yana ratsashi, shafa gashin kansa ta shiga yi a hankali ta ce "I hope ba zazza6i za kai ba?" ya ce "No insha Allah" daga haka ta kura masa ido, duk cikin 'ya'yanta ba wanda take jin shi har ranta kamar Jawad, tasha wahala kafin ta haifeshi, after then sai da yayi shekara 11 kafin ta haifi Sadeeq, wani lokaci saita masa abu itama taji duk bata kyauta ba, sai dai kuma idan Rafi'ah yake so ta nan bangaren sai inda karfinta ya kare, kamo hannunta yayi ya ce "Mami" ta dawo daga tinanin data lula ta ce "Ahmad" ya ce "Kiyi hakauri" ta ce "It's ok" daga haka ta gyara masa blanket din tana kallansa. Abdul ne ya shigo dakin Rafi'ah rike da baby girl, tana zaune akan sallaya ta idar da sallan la'asar, ya ce "Anty Mummy na kiranki a dakin Ummi" ta ce "Ohk, be careful karka jefarta" ya danyi dariya ya ce "Aina fiki ma iya rikewa" ita dai bata ce masa komai ba ta mike ta nufi dakin Ummi, ita da Mummy ne kawai a dakin, ta nemi waje ta zauna tana kallan Ummi ta ce "Gani" Mummy ta ce "Akan maganar sunan Babynki ne, kikace asa sunan duk wanda aka ga dama ko" ta daga kanta a hankali ta ce "Eh, duk wanda kuka ga ya dace" Mummy ta ce "Kar mu tauye miki hakki ne daman, idan akwai wacce kikeso asa sunanta saiki fada" shiru tayi at first taki cewa komai, Mummy ta ce "Ina jinki" sauke kanta tayi kasa ta ce "Sunan Maman Doctor nakeso a sa" da mungun mamaki Ummi ta dago tana kallanta, sai kuma ta6e baki ta mike ta fita a dakin, Mumny dake kallanta cikin 6acin rai ta ce "Uban waye shi daza asa sunan uwarsa, shiya raini cikin? Ko shiya sha wahala dake" hawayen idanta ta share ta ce "Amma ai shi ne mahaifint..." Kafin ta rufe bakinta Mummy ta kifa mata mari, Rafi'ah ta fashe da kuka ta mike tana jaa da baya ta ce "Kiyi hkr pls Mummy" *_I want to see sweets and meaningful comments_* 🤗 _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _7_ A hankali ta durkusa kasa nan bakin kofa tana goge hawayen idanta ta ce "I don't mean to hurt u Mum, u said i should say out what's in my mind, kuma na fada miki ban boye miki komai ba, da nasan hakan zai 6ata miki rai wallahi i won't even say a word" daga haka ta kara fashewa da kuka, Abba ne ya bude dakin jin kukanta, ya kalli Mummy dake zaune har lokacin ranta a 6ace ya ce "What's going on? Why are u crying Mamana?" ita dai Mummy bata ce komai ba, Abba ya kama hannun Rafi'ah suka fita a dakin zuwa dakinsa, a bakin gado ya zaunar da ita yana kallanta ya ce "Keep quite and tell me what's wrong with u" a hankali tasa hijab dinta ta share hawayenta ta ce "Sunce na fadi sunan da za'a sama Babyn shine nace sunan..sunan.." Share mata hawaye Abba ya shiga yi ya ce "Feel free and tell me Mamana" sauke kanta tayi wasu sababbin hawaye na kara gangaro mata ta ce "Sunan Maman Doctor nace, Abba he has no one sai yarinyar nan, ai banyi laifi ba tinda shine dai mahaifinta, no matter how, ko kisa yake i can't change him from who he is, he still remain her father, but she slapped me Abba" cikin rarrashi Abba ya ce "Ya isa kiyi shiru, duk abinda kikeso shi za'ayi, ki kwantar da hankalinki kinji ko?" kai ta daga masa sannan ta mike ta ce "Nagode Abba" cike da damuwa ya ce "Ba komai Mamana" daga haka ta nufi kofar fita, tana bude kofar suka ci karo da Ummi, ta sunkuyar da kanta ta koma gefe, bayan Ummi ta shige ta fita ta jawo kofar. Tin daga ranar har ranar suna Ummi ko Mummy basu kara mata magana akan sunan ba, ita ma kuma bata ce komai ba, bata san kuma wane hukunci suka yanke ba, ranar suna tin da safe Mummy ta kira mai make~up ta mata, duk da haushinta takeji hakan bai hana ta shiryata ba, tsaf Mummy ta shiryata cikin tsadden lace dinta, tayi mungun kyau sosai da sosai, sai dai har lokacin bata san sunan da aka sawa Babyn ba, mikewa tayi kamar marar lafiya ta haura stairs Gwaggo ta bita da kallo, dakin Abba ta shiga ta rufo kofar, ta zauna gaban mirror tana karewa dakin kallo, tasan an kawo stickers jiya amma kuma bata gansu ba, mikewa tayi ta dinga bubbude drawer ko zata gani amma babu, daga kanta tayi ta hango bakin leda akan wardrobe, ta jawo stool ta hau kai sannan ta dauko ledan, zama tayi a bakin gado ta bude ledan, stickers ne masu yawa a ciki, ta dauko daya tana karantawa, ta saki wani murmushi ganin an rubuta *Fatima Yusuf Muhammad* ta limshe idanuwanta a hankali ta ce "Thank u Abbana, i know it's you, nagode sosai" jin an bude kofar yasa tayi still a wajen tana zare ido, Ummi ta karaso tana kallanta, mikewa tayi ta kulle ladan zata mayar Ummi ta ce "Sai ki tafi dashi kasa ki kaiwa Mummy za suyi amfani dashi, ai hankalinki ya kwanta tinda kin gani" bata ce komai ba ta wuce ta fita a dakin Ummi ta bita da harara, ko data sauka ta bawa Mummy ledan ta wuce parlorn Abba ta zauna, dan ita yanzu bata san shiga mutane kafin a fara mata bori. Da yamma liss gidan Ummi ya cika da baki, aka ci aka sha sannan akai hotuna, sunyi kyau sosai kowa ka gani yana cikin farinciki, Mami ma tazo gidan, Ammi dai bata zoba saboda itama gidanta a cike yake da mutane, Mummy kuwa duk wanda ya tambayeta sunan Babyn sai ta dan hade rai kafin ta fada, kusan magrib duk yawanci mutanen sun watse, sai 'yan uwa, wannan karan dai ba dangin Abba da suka kwana part din Anty Amina, a cewarsu a biki ma basu ji dadi ba, sabida haka basu ma zo da yawa ba. Wajen karfe 9 na dare Rafi'ah na zaune dakinta tana breastfeeding babynta Ummi ta shigo da flask a hannunta, ta dan sauke kanta kasa ganin har Ummi ta iso indan suke, tin data haihu bata yarda tayi breastfeeding a gaban kowa ba, ko dai ta koma daki ita kadai ko kuma tasa veil ko hijab da rufe jikinta, gaba daya she was uncomfortable, Ummi ta ce "Kije parlorn Abba Jawad yazo" ta ce "Ohk" Ummi na tashi ta turo baki ta jawo dan kwalinta dake kan gadon ta sannan ta kwantar da babyn ta dora dan kwalin tasa hijabi sannan ta dauketa suka fita. zaune ta sameshi a parlor ya sha manyan kaya, ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "U are welcome" ya ce "Thank u, ya hidima?" Ta ce "Alhamdulilah" bayan ya kar6i babyn ta kalli Cannula dake hannunsa, dan zaro ido tayi ta ce "Are u sick?" Ya ce "I recovered, nayi zazza6i ne" ta dan turo baki ta ce "But baka fadamin ba" ya ce "Is because is not that critical, idan muna waya ai bakya ganewa" ta ce "Yes, karfin hali kake kenan, amma ka rame ma" ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Mind not Rafi'ah, naji sauki sosai" shiru tayi tana wasa da fararen yatsunta, ya ce "Allah ya raya mana Fatima Zarah akan sunnah, mai suna ki kaiwa kanki shine ko kunya babu" ta danyi dariya ta ce "No, sunan Maman Doctor ne, kuma sunana, kaga taci sunan manya" ya ce "Hakane, i also like the name" ta ce "Really" ya ce "Yes" shiru ne ya biyo baya, ta dago kanta tana kallansa taga ita yake kallo, kara sauke kanta tayi, ya danyi murmushinsa me kyau ya ce "Let me ask u" ta ce "I'm all ears" ya ce "Shi Doctor bai fada miki inda zai tafi ba? bai kuma ta6a ce maki akwai kasar da yake son zua ba?" Kin dago kanta tayi jin hawaye ya gama taruwa a idanta, Jawad ya dago kanta yana kallanta, tayi saurin limshe idanuwanta nan kuma hawayen ya samu damar sakkowa, ya share mata hawayen ya ce "I didn't ask u to cry, tambaya fa na miki, or have u forgotten my profession?" Ta girgiza kai ta ce "No, ni bai ta6a fadamin ba" ya ce "But how was his reaction sanda ya baki takardan sakin?" Ta dan turo baki, sai kuma ta ce "He's somehow, hankalinsa kamar baya jikinsa, komai yi yake kamar ana controlling dinsa, but nasan ya tsaneni ne shiyasa, i don't know why bai nunamin true color dinsa ba sai dana aureshi, i regreat knowing him Yaya Jawad, nasan dai it's my destiny kuma raban na haifi wannan abin ne" Jawad ya kamo hannunta yana kallan cute face dinta data wanku da hawaye ya ce "Stop saying all this Fatima, kiyi ta addu'a kawai, idan shine alkhairinki kuma ba shiya cuce kiba, definitely one day zaku..." Shiru yayi yana kallanta, sai kuma ya goge mata hawayen idanta ya ce "Everything will be fine soon, and u stop calling my baby wannan abin" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "To Fatima" ya ce "No, she's bearing ur mother's in-law name, ba zamu kirata da sunan ba" ta bude hannayenta alamun bata sani ba, sai kuma ta ce "Ni bansan me zan ce mata ba" ya ce "Zamu kirata da *Imaan*" ta dan yi murmushi ta ce "Insha Allah" ya ce "Good baby girl, to kiyi min murmushi" ta sake yin murmushi sannan ta boye fuskarta tana dariya, mikewa yayi ya kwantar da babyn akan shoulder dinsa ya ce "I'm going, Allah ya raya mana Imaan" ta ce "Ameen Barrister" daga haka ta mike ta kar6a babyn, har compound ta raka shi sannan ta dawo ciki. Bayan ya karasa parking lot ya bude boot ya ciro babban trolley yana kallan Mustapha ya ce "Ka shigar da shi ciki, but ka budemin gate kafin nan" Mustapha ya ce "Angama oga" daga haka ya bude masa gate, Jawad ya koma mota ya tayar sannan ya fita a gidan. Jan trolley Mustapha yayi har cikin parlor, Gwaggo ne da wasu mata na zaune suna cin abincin dare, ya ajiye akwatin zai fita Gwaggo ta ce "Ke kuma fa?" Ya ce "Cewa yayi na shigo da shi" ta ce "Wa?" Ya ce "Wanda ya fita" Gwaggo ta ce "Ohh dan gidan Hadiza" mikewa tayi zata ja akwatin taji nauyi, Abdul da fitowansa a daki kenan ya tsaya kallanta ya ce "Ina ke ina daukar wannan Gwaggo" ta ce "Maza dauki ka kaiwa Zainab, muje tare dan naji akwatin da nauyi" Abdul yaja trolley suka haura stairs, Ummi da Mummy na zaune a parlor suna magana, ganin Gwaggo yasa sukai shiru, ta ce "Maza shigo dashi" Abdul ya ajiye akwatin a tsakiyar parlor ya ce "Gaskiya da nauyi" daga haka ya fice a parlorn, Ummi ta ce "Wannan fa Gwaggo?" Gwaggo ta zauna ta ce "Ina na sani, dan gidan Hadiza ne ya kawo yace a shigo da shi" Mummy ta ce "Wace Hadiza?" Gwaggo ta zauna gaban akwatin tana zugewa ta ce "Hadiza abokiyar zamanki mana, mu a danginmu akwai me irin sunan ne?" Nan da nan Mummy ta hade rai, Ummi dai kallan kayan cikin akwatin kawai take, pamper ne manya~manya sai kaya masu tsada iri iri da overall, wipes, tissue, baby soap, baby lotion, baby perfume, towels, earrings, rings, socks, vip, pants, duk wani tarkacen da ake bukata sai daya siya ya zuba, bayan Gwaggo ta gama ciccirosu ta kalli Ummi ta ce "Kinga idan ta gama shayarwa sai kawai ayi aure, dan tin ba yau ba nasan wannan yaran santa yake, wannan figigiyar jaririyar na cika wata tara dama ta yayeta, ai tama mata mutunci, naga ubanta tin cikinta bai fito ba ya gudu ya barta" Mummy ta mike ta wuce dakin Rafi'ah, fitowanta a toilet kenan, Mummy ta ce "Yaushe Jawad yazo gidan nan?" Ta sauke kanta kasa ta ce "Dazu, amma ya tafi" Mummy ta ce "Meye tsakaninki da Jawad Rafi'ah?" Ta dan zaro ido ta ce "Ni kuma" Mummy ta ce "Sai kizo parlor kiga abinda ya kawo miki" daga haka ta juya ta fita a dakin, hijab dinta ta saka sannan ta fito, ta tsaya caan bakin kofa tana kallan tilin kayan dake gaban Gwaggo, Mummy ta wuce dakin Ummi ranta a 6ace, Ummi ta mike tabi bayanta, a bakin gado ta sameta a zaune, Ummi ta ce "Karfa ki yanke hukunci baki tabbatar da abu ba" Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai bazai ma yiwu mu hada zuri'ah da Hadiza ba, yanzu ma ba abinda muka hada amma tabi ta takurawa Rafi'ah" Ummi ta ce "Allah ya kyauta" daga haka ta fita a dakin. Komawa daki Rafi'ah tayi ta dauka wayarta ta kira Jawad amma phone dinsa a kashe. karfe 10 da rabi Mummy ta kwashi 'yan kwananta suka wuce gida, tana parking ta fito suka nufi cikin gida, murda handle din Mummy tayi taji a rufe, Anty Salma ta ce "Ko dai sunyi bacci" a takaice ta ce "Akwai key a jakana" daga haka ta ciro key a hand bag dinta ta bude suka shiga. Washegari karfe 8 bayan sunyi wanka Mummy ta mike don ta samar musu abinda zasu yi breakfast, a parlorn Abi ta samu Mami tana hadawa Jawad tea, shi dai yana zaune akan kujera ya limshe ido, Mummy ta dan kalleshi sannan ta wuce kitchen, within few minutes ta dafa musu indomie ta juye cikin babban tray sannan ta kai wa su Anty Salma dakinta, dawowa parlor tayi tana kallan Jawad ta ce "Ahmad" ya bude idanuwansa a hankali yana kallan Mummy, ta ce "Ka shigo parlorna zamuyi magana" Mami ta ajiye serving spoon din hannunta ta ce "Ya za'ai kina gani bashi da lafiya kice masa ya tashi har wani ya shiga parlor ki" daga mata hannu Mummy tayi ta ce "Look, banfa yi dake ba, dashi nake idan kuma ba zai shiga ba, yayi wa kansa" mikewa Jawad yayi gently yana shafa gashin kansa, Mami ta ce "Koma ka zauna tinda nina haifeka ba wata ta haifamin kai ba" , zama zaiyi akan kujera Mummy ta ce "Ohk sbd bani na haifeka ba saika zauna kenan" ya dan kalleta sai kuma ya kalli Mami dake tsaye wajen dinning ta wani hade rai, Mummy ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Well, idan kaga dama ka zauna saboda ni ban isa na baka umarni ba, amma fa ka sani akwai abinda zaka zo kana nema a wajena, kana tinanin zan baka a haka?" Shiru yayi yana kallanta sai kuma ya sauke kansa kasa, Mummy ta juya ta shige part dinta, bin bayanta zaiyi Mami ta ce "Come back and sit down Jawad" ya juyo yana kallanta yama rasa abinda zai ce. 😄 *Jawad zai bi Mummy ko dai ya fasa ya bi umarnin uwa?* 🤭 _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _8_ Komawa Jawad yayi ya zauna akan sofa yana kallan Mami data kafeshi da ido, ya sauke kansa kasa ya ce "Is Abi out?" Harara ta dalla masa ta ce "Why won't u call him" daga haka ta wuce part dinta, mikewa yayi a hankali ya shiga daki ya zauna bakin gado, sosai kayan jikinsa suka masa kyau, ya mike yasa glasses dinsa sannan ya fito a dakin ya nufi part Mami, a parlor ya sameta suna zaune tana wa Ikram tsifa, ya zauna akan kujerar dake opposite dinsu, Ikram ta ce "Yaya dan Allah ka kaini gidan Baffa idan fita za kai" ya dan hade rai ya ce "Who is your driver?" Ta dan turo baki bata ce komai ba, Mami ta ce "Ina zakaje yanzu kaida ba jin dadi kake ba?" A hankali yana girgiza key din motarsa ya ce "My house" ta ce "To do what?" Ya ce "Yau zan koma tinda naji sauki" Mami ta ce "To Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen" mikewa yayi zai fita Ikram ta ce "Yaya na taso mu tafi dan Allah" ya ce "No, i'm not going that way, ki bari Sadeeq yazo ya kaiki" daga haka ya fice a parlorn ya rufo musu kofa. cikin quick light steps ya karasa part din Mummy ya murda handle din ya shige, ba kowa a parlorn ya zauna akan kujera yayi sallama in a low voice, Mummy ta fito rike da wayarta a hannu ta zauna tana kallansa ta ce "So u came?" Ya dan shafa gashin kansa ya ce "Yes, kiyi hakuri abinda ya faru dazu" Mummy ta ce "No, ba komai ai uwa ce, ni kuma kaga ban haifa ba" ya dan zaro ido ya ce "Noo, ba haka bane, ni duk na daukeku a matsayin iyayena" ta ce "Ohk, dama akan kayan da ka kai jiya ne, mungode Allah ya saka da alkhairi" silently ya ce "Ameen" Mummy ta ce "Amma do u have any feeling for her?" A hankali ya dago ya kalleta sai kuma yayi shiru, Mummy ta ce "Yes u have, but y kake ganin hakan zai faru Jawad? Ni dai bazan muku fatan tsiya ba, amma kafi kowa sanin halin mahaifiyarka, kuma ba lallai ne ta yarda ba, beside bama san zuwan Rafi'ah gidan nan take ba balle ace ta zama matar dan ta" shiru Jawad yayi yana jin Mummy, bayan ta gama ya ce "Ba abinda zai faru insha Allah" Mummy ta ce "Ohk Allah yasa, Allah kuma ya za6a muku duk abinda yafi alkhairi" ya ce "Ameen" ta ce "And then ni baza'a ji wannan maganar a bakina ba, idan ta amince kun fahimci junan to, amma duba da abinda ya faru da ita a baya bazan sake takurata tayi aure nan kusa ba" Jawad ya ce "No it isn't ur fault Mummy, ai kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa" ta ce "Hakane, but there is a reason" daga haka ta mike ta ce "Ya jikin naka?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Allah ya baka lafiya" daga haka ta shige daki, mikewa yayi ya karasa kofar parlor ya bude a hankali yana lekawa, ganin ba kowa ya fito ya fice a gidan da sauri. A ranar duk mutanen da suka halacci suna suka wuce, Ammi tazo da wasu 'yan uwanta mata biyu suka kawo akwatina guda biyu na kayan baby dana Rafi'ah, sosai Khairiyya ta makale Imaan a jikinta wai da ita zata tafi, bayan da suka tashi tafiya Ammi ta danyi mata nasiha daya sa gaba daya jikinta yayi sanyi, karshe dai sai da tayi kuka. Kwana uku da suna Ameera ma ta koma school, Ummi ta koma aiki, gidan ya rage daga ita sai Saudatu. *_3 YEARS LTR_* Tsaye take a kitchen gaban gas tana soya kwai, jin motsi a bayanta yasa ta juya da sauri, wani mungun bugawa zuciyarta tayi ganin irin tsayuwar da Imaan tayi, just as how Yusuf used to, a hankali ta ce "What's it?" yarinyar ta dan jaa baya ta ce "Ummi is calling u" juyawa Rafi'ah tayi tana taci gaba da abinda take, gaba daya jikinta yayi sanyi, tinda Imaan ta taso ta fara tafiya da magana kusan kullum sai zuciyarta ya buga, musamman idan taga ta jinginu a wani abu tayi folding hannayenta, ko kuma in tai wani abun sai Yusuf ya fado mata, a yanzu kuma kokari take taga ta manta dashi amma ga 'yarsa na kokarin dawo mata da ciwanta, a hankali ta share hawayen idanta ta juye kwan cikin plate sannan ta fita a kitchen din, Ummi na zaune a parlor da Imaan a cinyarta tana mata surutu, Rafi'ah ta ajiye plate din kwan a gabansu ta ce "Gani" Ummi ta ce "Dama Mummy ne ta kira wai ki kai mata Imaan idan zaki wuce school" ta wani turo baki ta ce "Ummi zanyi late fa, kuma test nake dashi" Ummi ta wurga mata harara ta ce "Sai ki kirata ki gaya mata" daga haka Ummi ta mike ta wuce parlorn Abba, kallan Imaan tayi ta ce "Will u eat?" ta karashe maganar tana nuna mata fried egg din dake ajiye gabanta, girgiza kai yarinyar tayi, Rafi'ah ta dan ja tsaki ta ce "Idan na ce bazanyi ba a takuramin gashi nan baci zakiyi ba" kallan Imaan tayi data zuba mata ido ta ce "Go and wear your scarf" ta mike a hankali ta wuce sama, dauke idanta tayi daga kallanta saboda zuciyarta da taji ya fara bugawa, ta kara yin tsaki sannan tabi bayanta, zaune ta sameta akan gado ta dauko tap dinta tana dannawa, ta kalli Rafi'ah da babu walwala a tattare da ita ta ce "Momma what's wrong with u?" bude press dinta tayi ta dauko mata hula ta karasa inda take zaune, zama tayi ta jawota jikinta tasa mata hulan ta ce "U stop talking anyhow dear, banasan kina magana sosai because u distract me sometimes" a hankali ta ce "Ohk" tashi Rafi'ah tayi ta dauka hijab dinta tasa sannan ta dauki laptop sai side bag dinta me dauke da biro da jotter, kama hannun Imaan tayi suka wuce dakin Ummi, ta bude dakin a hankali suka shiga, Rafi'ah ta ce "Zamu tafi" Ummi ta ce "Safe" ta dan yatsine fuska ta ce "To wa zai daukota?" Ummi ta juyo tana kallanta ta ce "Idan kin gama mana, ko kwana zakiyi kina lectures din" silently ta ce "To" daga haka ta juya, Imaan ta dagawa Ummi hannu ta ce "Bye bye Ummi" Ummi ta sakar mata murmushi ta ce "Bye bye dear" bayan haka ta juya tabi bayan Rafi'ah. Anty Amina da Anty Rahama ne zaune a tangamemen parlorn Ikleemah, sai washe baki suke suna karewa gidan kallo, dan tinda akai auran basu zo ba kasancewar kasar waje da mijinta ya dauketa suka tafi sai jiya suka dawo, da murmushi Ikleemah ta sakko daga stairs ta rungume Anty Rahama, Anty Amina ta kwalalo ido ta ce "Hummm Ikleemah kinga yadda kikai kyau" Anty Rahama ta ce "Gaskiya auran nan ya kar6eki, maza zauna kusa dani, shekara daya fa kenan ban ganki ba" Ikleemah ta danyi murmushi ta ce "Ammi nagode miki, kinga daga yin aikin nan yadda yake min kamar zai maidani ciki, matarsa ma tana gidansu" Anty Rahama ta saki wani shewa ta ce "Aina gaya miki zama daram zakiyi a gidan nan" Ikleemah ta danyi murmushi tana kallan Anty Amina ta ce "Ina labarin Rafi'ah?" Anty Amina tayi kasa kasa da murya ta ce "Tana caan tana galantoyin makaranta, yarinya dai girma take ga uban surutu, har yanzu kuma banji ana maganar aure ba" Ikleemah ta ta6e baki ta ce "Haka dai zata zauna har karshen rayuwarta" Anty Amina ta ce "Ba shakka kuwa". Dai dai kofar gidan Mummy Mustapha yayi parking, Rafi'ah ta fito sannan ta fito da Imaan suka shiga ciki, Ikram na zaune a balcony tana karatu, tana kallansu ta wani hade rai ta dauke kai, itama Rafi'ah bata kalli inda take ba ta wuce, ba kowa a parlorn suka wuce part din Mummy, tana zaune a parlor da wata kawarta suka shiga da sallama, Imaan tayi gudu ta dale cinyar Mummy tana dariya ta ce "I missed u Mummy" Mummy ta bata light kiss a forehead dinta ta ce "I missed u too Fatiti" Rafi'ah ta zauna akan kujera tana kallan kawar Mummy ta ce "Ina wuni Umma" ta ce "Lafiya kalau Fatima, ya Baby?" ta ce "Lafiyanta kalau" matar ta ce "Masha Allah gashi ta girma Allah ya raya ta" ta ce "Ameen" mikewa tayi tana kallan Mummy ta ce "Zan wuce Mummy" Mummy ta ce "Ohk, idan Jawad ya dawo sai ya kawota" ta ce "Ohk to, dama yace yau zai dawo" bayan haka ta nufi kofar fita, Imaan ta daga mata hannu ta ce "Bye Momma" a hankali itama ta daga mata ta ce "Bye sweetheart" daga haka ta bude kofar ta fita. Karfe 3 su Rafi'ah suka fito daga test, ta karasa inda taga Salma zaune ta ce "Kina nan ashe" Salma ta ce "Ehh wallahi, ina jiran Nadiya ta kawomin handout dina taje photocopy" Rafi'ah ta ce "Ohk" Salma ta ce "Ina Imaan?" Ta ce "Tana gida" Salma ta danyi murmushi ta ce "Inasan kanwarkin nan Fatima, musamman idan tana magana, tafa fiki kyau amma" Rafi'ah tayi shiru kawai tana murmushi, Salma ta yi picking call ta koma gefe, bayan few minutes ta dawo tana kallan Rafi'ah ta ce "Fatima ko zamuyi dropping dinki?" Ta girgiza kai tana murmushi ta ce "Mind not Salma, za'a zo daukana" Salma ta ce "Alright sai gobe, ki gaishe da Imaan" ta ce "Ohk thanks", bata wani jima awajen ba phone dinta ya fara ringing, tayi picking call din hade da sallama, Jawad ya ce "Banganki ba" ta dan turo baki tayi hanging call din sannan ta fito daga inda take, harta karaso kallanta yake with passion, ta bude front seat ta shiga ta zauna, ya ce "Ya akai Madam?" Shagwa6e masa fuska tayi ta ce "Ka barni inata shan rana" ya danyi murmushi ya ce "I'm sorry, ko gida banje ba yanzu nan na shigo gari wallahi" ta ce "So ya aikin?" Ya ce "Fine, Allah ya soki ban kara kwana ba" ta danyi dariyarta me kyau ta ce "Ba saina bika ba" ya ce "Ai zanso hakan, ina Imaan?" Ta ce "Tana gidanku" ya ce "Keba gidanku bane kenan?" Ta ce "Gidanmu ne, but amma ai gidanku zance" ya ce "U know what?" Ta ce "Saika fada" shiru yayi yana kallanta, sai kuma ya ce "What if aka turani zua Cyprus, sai dai in anyi auran na barki a nan?" Ta dan turo baki ta ce "Why" ya ce "Ur school, ai kin kusa gamawa, dama da year 2 kike da sai mu tafi, but kinga semester daya ya rage maki after this one" limshe idanuwanta tayi ta kwantar da kanta jikin kofa, gaba daya ji take kamar zai gudu ya barta irin yadda Yusuf yayi, jin hawaye na kawowa a idanta tayi saurin rife fuskarta da hijab din jikinta, Jawad yayi parking yana kallanta ya ce "Banfa ce miki zan tafi ba, tinda basu ma fada ba" ya kamo hannunta cikin sanyin murya ya ce "I will never leave u Fatima, banasan na daina kallanki even for some minutes, a yanzu kin zama wani bangare na rayuwana, bazan iya barinki ba, u mean alot to me, ina sanki so kuma bana wasa ba" Dago kanta tayi tana kallansa ta ce "I know, but i can't forget my past Yaya, ko Imaan na kalla sometimes inajin ba dadi" ta karashe maganar hawaye na sakkowa a idanta, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Mind not, dole ne tinda shine mahaifinta wasu dabi'unta da abunuwan da zatai ya zama irin nasa, but i beg u dan Allah for God sake, kiyi hakuri ki daina kuka, shima tinda ya manta dake why won't u forget him too" ta dan harareshi ta ce "Ni cewa nayi ina tinashi ne" ya ce "Ba gashi ba kullum kina kuka a kansa kusan shekara 4 kenan" ta turo baki ta juya masa keya, ya ce "Yess, ki cireshi a rayuwarki duka duka, Imaan kuma i still remain her Father, face ur future and forget ur past" a hankali ta ce "But how?" Ya ce "Ki daina tinawa kin ta6a aure a rayuwarki mana, ki manta dashi" silently ta ce "After i have a child with him" ya ce "Yes, it's possible, sai dai idan baki sa kanki ba" ta ce "To" hannunsa yasa ya goge mata sauran hawayen idanta, ya bude dashboard ya dauko tissue ya mika mata ya ce "Clean ur face" ta kar6a a sanyaye ta fara goge idanta sannan yaja motar suka wuce. _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _9_ Dai~dai bakin gate yayi parking ya juyo yana kallanta ya ce "U come down" ta dan turo baki ta ce "Kai zaka budemin" Jawad yayi murmushi yana kallanta ya ce "An gama Madam" daga haka ya fito ya zagayo ya bude mata ya ce "Ur wish is my command Baby" fitowa tayi a motor tana dariya zata rife kofar ya ce "Wait! Bari na karasa ladana" daga haka ya tura kofar motar ya rife, a tare suka jera suka shiga gidan, sai da suka kusa balcony ta dan ja baya ya wuce gaba sannan tabi bayansa, ya murda kofar parlorn ya shiga da sallama, Imaan najin muryarsa ta sauko a kan dinning da gudu ta nufeshi, ya dagata sama yana dariya ya ce "Is this my Imaan?" Ta washe masa baki ta ce "Yess Daddy, where have u been?" Ya bata light kiss ya ce "Momma bata ce miki nayi tafiya ba?" Imaan ta girgiza kai tana kallan Rafi'ah dake zaune kan sofa tana danna wayarta, Jawad ya juyo yana kallanta ya ce "Why Momma?" bata ko kalli inda yake ba ta ce "Ai nima saida ka tafi ka kirani" fitowa Mummy tayi a kitchen tana kallansu ta ce "Ha'a yana ganku tare?" Ya ce "Ita na fara daukowa, Ina wuni" ta ce "Lafiya kalau, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulillah" daga haka ya daura Imaan akan shoulder dinsa ya ce "Let me see Mami" ganin ya nufi part dinsu yasa Rafi'ah ta tashi tabi bayansa a hankali, da sallama ya shiga parlorn yana kallan Ikraam dake zaune tana kallo, ta mike zaune tana kallansu, sai kuma ta dan daure fuska ganin Rafi'ah ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Sannu" zama yayi akan kujera yana kallanta ganin taci gaba da canja channel ya ce "Ke" ta juyo tana kallansa, ya ce "Did u great her?" dan turo baki tayi ta ce"Who?" Ya ce "Your Aunt" kanta ta maida gefe kamar baza tai magana ba, sai kuma ta ce "Ina wuni" ba tare da Rafi'ah ta kalleta ba ta ce "Same" Jawad ya ce "Let's go inside Fatima" Rafi'ah ta mike ta ce "Ohk" daga haka tabi bayansa suka shiga bedroom din Mami. A tsaye take tana shirya gogaggun kayanta cikin press, da sallama suka shigo dakin, ta amsa tana kallan Jawad dake rike da Imaan ta ce "Har ka dawo?" Ya sauke Imaan a wuyansa ya ce "Ehh wallahi, ina wuni Mami" ta ce "Lafiya kalau, ya hanya?" Ya zauna bakin gado ya ce "Alhamdulillah" a kan carpet Rafi'ah ta zauna kanta a kasa ta ce "Ina yini Mami" ba yabo ba fallasa Mami ta ce "Lafiya kalau, ya karatu?" silently ta ce "Lafiya kalau" Mami ta kalli Jawad dake wasa da Imaan ta ce "Akwai abinci akan dinning" ya ce "Thank u, but i want to take my bath first" daga haka ya mike ya nufi hanyar fita, tashi Rafi'ah ma tayi ta ce "Sai anjima Mami" Mami ta ce "Mu jima da yawa" daga haka suka fita a dakin. Suna fita Rafi'ah ta wuce part din Mummy, Jawad ya ajiye Imaan ya ce "Follow ur Momma dear" ta tsaya tana kallansa kafin ta ce "Daddy are u leaving?" Ya ce "No, i want to take my bath sweetheart" hannu ta mika masa suka tafa sannan ta juya ta shiga parlorn Mummy, abinci Rafi'ah taci bayan tayi sallah sannan ta kwanta akan sofa tana kallan cartoon din da Imaan ke kalla, tana nan kwance har bacci ya fara daukanta, lokaci daya taji Imaan na bubbugata, ta bude ido a hankali tana kallan Jawad dake tsaye a bayan kujera, ya daga mata gira daya ya ce "Let's go" ta mike a hankali ta mayar da hijab dinta sannan ta shiga dakin Mummy, a zaune ta sameta tana waya, sai data jira ta gama sannan ta ce "Mummy zamu wuce" ta ce "Ohk daughter, sai yaushe kuma?" ta dan juya ido kafin ta ce "Exams zan fara ai Mummy, duk sanda na gama" Mummy ta ce "Ohk Allah ya kaimu, kin yiwa Mami sallama ne?" Ta girgiza kai ta ce "Yanzu dai" Mummy ta ce "Safe, ita wannan mai surutun fita tayi bako sallama ko?" Rafi'ah ta danyi murmushi ta jawo mata kofa, dan tin tini ta dale bayan Jawad sun fita, tana fitowa main parlor ta nufi part din Mami, ta shiga a hankali hade da sallama, Mami ta dago tana kalleta ta ce "Baku wuce bane?" A sanyaye ta ce "Ehh yanzu zamu tafi, mungode sai anjima" Mami ta ce "Allah ya kiyaye" juyawa Rafi'ah tayi ta fita a part din sabida bata iya hada ido da Mami yanzu, tin abubuwan da suka faru shekaru biyu baya da suka wuce wanda ya kai har Abi ya saketa tayi kusan wata 9 a gida, dan tsaki Ikram tayi ta ce "Mami wai yanzu kin hakura kenan Yayanmu ya auri wannan yarinyar?" Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Idan itace matarsa Allah ya sanya alkhairi Ikram, ni dai Allah na gani bana bin boka, nama tsani duk matar da xata kai sunan wata ko wani wajen boka, kina gani yadda na shiga jarabar rayuwa akan hana shi auranta, da kyar na samu nawa auran ya gyaru, saboda haka babu ruwana addu'a kawai zan bisu dashi Allah ya sanya alkhairi, na zagi 'yar mutane bansan ya nawa 'ya'yan zasu tashi ba, na mata sharri kala kala duk dan na cimma burina amma daga karshe Allah bai yi ba, to menene ribata anan Ikram? Allah ya yafe mana gaba daya kuskurene kam nayi shi, na tauyewa Jawad hakkinsa da yawa a rayuwa, badan uwa uwa bace nasan da wuya ya yafemin, amma ko sau daya bai ta6amin abinda zanji ba dadi ba, dan meyasa nima bazan so farincikinsa ba" Mami ta share guntun hawayenta sakamakon tuno baya da tayi, dauke kai Ikram tayi daga kallanta ranta a 6ace ta mike ta shige dakinta, Mami ta bita da harara ta ce "Haryanzu ke yarinya ce Ikram zuwa gaba zaki gane komai, bana fata na cuci wani yanzu balle watarana ya juyo kaina". one thousand Imaan ta fito dashi a pocket din wandanta tana nunawa Rafi'ah ta ce "Mami gave me this" Rafi'ah ta sauke kanta kasa ta ce "Kince kin gode?" Ta ce "Yes, ko Daddy" Jawad ya shafa kanta ya ce "Exactly" kallan Rafi'ah yayi data maida kanta gefe tana kallon titi ta window, a hankali ya ce "Dear" ta juyo a sanyaye tana kallansa, ya ce "What's wrong with u?" Ta ce "Nothing" cigaba yayi da driving lokaci lokaci yana kallanta ta gefen ido har sukaje gida, a waje yayi parking ta juyo tana kallansa ta ce "Meyasa anan Barrister?" Ya ce "Kinsan na tsani idan ba jimawa zanyi ba na shigar da mota" ta ce "Ohk" daga haka ta fito ta tura gate ta shiga, dauko Imaan Jawad yayi a shoulder dinsa suka shigo, a baya suke bin Rafi'ah har suka shigo parlor, ya ajiye Imaan sannan ya samu waje ya zauna a kan lallausan carpet, fitowan Ummi kenan a parlorn Abba ta tsaya kallansu, saam bata lura da jawad ba, sai da taji muryarsa yana gaisheta, ta saki murmishi ta ce "Lafiya kalau, yaushe ka dawo" ya ce "Dazu, ya aiki" ta ce "Alhamdulilah" daga haka ta koma parlorn Abba Imaan tabi bayanta, zama Rafi'ah tayi akan sofa tana kallansa ta ce "Me zan kawo maka?" Ya danyi murmushi yana shafa kansa ya ce "You" ta dan harareshi sannan ta mike zata wuce kitchen ya kamo hannunta, ta juyo a hankali tana kallansa ya ce "Kinsan yanzu fa naci abinci, so i'm going" ta ce "Ohk Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen, zakije school gobe?" Ta daga masa kai ta ce "Probably, but u know what Barrister?" Ya kafeta da ido ganin yadda take magana kamar bata sanyi, ya ce "Kina da damuwa Rafi'ah, what's that thing u are thinking of? Tin dazu kike behaving somehow, did anyone hurt u dear?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "Kaina ne yake ciwo, and my chest too, yanzu zan sha magani na kwanta karna samu attack" a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ohk, Allah ya sauwake, ki huta sosai" ta ce "Insha Allah, bye bye and i luv u" a hankali ya matsa kusa da ita tayi saurin sauke kanta kasa, ya bata very light hug ya ce "I luv u too" daga haka ya sake hannunta, daga masa hannu tayi ta ce "Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen" sannan ya fita ya jawo musu kofa ita kuma ta haura upstairs. Kwance yake a wani daki babba ya kama kansa dake masa mungun ciwo, dakin is well furnished, komai tsaf tsaf a inda yake, hannunsa na dama drip ne a ajiki dayan hannunsa kuma yawo yake tsakanin kirjinsa da kansa, idan yayi minti 2 dafe da kansa sai kuma ya maida kirjinsa ya dafe, mungun zafi zuciyarsa ke masa, gaba daya yayi mungun rama, sai haske daya kara sosai, idan ka kalleshi sau daya ba zaka gane Yusuf bane at once, Anty Khadija ne da Jiddah akansa suna tsaye, bayan 'yan mintuna Anty Khadija ta fito a dakin ta wuce dakin da Umma take, tsaye ta ganta tana ta faman dialing phone din Malaminta, tin jiya da suka dawo Nigeria take ta trying number amma yaki shiga, Umma ta zauna bakin gado cike da damuwa ta ce "Anya mutumin nan bai karya aikin nan ba Khadija? Ki duba fa kiga tin wata daya baya Yusuf baya bin abinda nace masa sosai, yanzu gashi satinsa daya a kwance baya magana sai juyi da yake" Anty Khadija ta karasa wajen Umma ta zauna ta ce "Ba shakka ya karya asirin nan Umma, da bai karya ba taya za'ai Alhaji Usman ya sakeni ya taho ya barni, sannan dama yace idan aka karya masa alkawari abin ba zaiyi kyau ba" Umma ta ce "Toba dole a karya alkawari ba Khadija, taya da auranki zaice ki dinga zuwa yayi lalata dake saboda asara ta mana yawa, anyi wanda akayi a baya amma yanzu kam naga ya isa haka, bazaki kara bashi kanki ba" Cike da damuwa Anty Khadija ta ce "Umma idan ba haka ba zai wargaza min duk wani shirina" Umma ta danyi murmushi ta ce "Ai kudi yana aiki Khadija, yanzu tashi zakiyi, ki dauki driver ki wuce Kano sannan kije kauyan nan ki sameshi, kudade kawai zaki bashi ya gyara komai, kinga ba wanda yasan muna da gida a Kaduna, bayan sati daya idan Yusuf yaji dama dama mu koma Egypt" Anty Khadija ta ce "Hakane Umma, shawara ce me kyau, yanzu bari nayi wanka na shirya, tin jiya da mukai landing nake taya Jiddah daga Yusuf ko wanka banyi ba gashi har kusan magrib" tana fadin haka ta wuce toilet, sai kuma ta juyo ta ce "Umma to a ina zan kwana a kano? kinsan dai ko hauka nake baxanje gidan mu ko gidan Yusuf ba?" Umma ta ce "Ai akwai hotels Khadija, ni dai fatana ki dace, ko nawa ya bukata zamu bashi tinda mu ba matsiyata bane" Anty Khadija tayi murmushi sannan ta shige toilet. A hankali Jiddah ta kamo hannun Yusuf dake saman kirjinsa, ya bude idanuwansa da suka dawo jajir yana kallanta, kuka ta fashe dashi ta rungumeshi ta ce "Pls talk Ya Yusuf, kusan sati daya baka magana dan Allah kace wani abu ko zanji dadi" shi dai kallanta kawai yake yana kwance, ta mike kamar mahaukaciya ta daga masa labule ta ce "Ka gani Yaya, jiya muka dawo Nigeria saboda condition dinka, kuma Umma taki bari a kaika asibiti sai dai a kira Doctor ya duba ka, ka gani Yaya nan Kaduna ne, mun dawo kasar mu" limshe idanuwansa yayi kamar yadda suke dazun, Jiddah ta fashe da kuka ta kara hawa gadon ta rungumeshi sosai ta ce "Nice Jiddan kafa Doctor, nice wacce kake cewa kullum kana sona tin tafiyarmu Egypt, ka manta bakaso kayi nisa dani? dan Allah kayi magana Habibina" bakinshi ya kai saitin kunnenta, har lokacin idanuwansa a limshe suke, ya dora dayan hannunsa da kyar a bayanta, da kyar muryarsa ke fita ya ce "Are u with me Rafi'ah?" Jiddah ta zabura ta mike tana zaro ido, sai kuma ta kwala ihu tana kiran Umma ta ce "Na shiga 3, ya tina ta wallahi Umma, ba Jiddah yace ba wallahi" Umma tayi kansa da sauri tana kallansa, kamar ba shi yayi magana ba, idanuwansa a limshe sai numfashi da yake saukewa daki~daki, number Doctor din daya dubashi daxu Umma ta fara kira, bayan ya dauka ta sanar masa ya tashi yace ga shi nan zuwa, Umma tayi hanging call din ta dago Jiddah zuwa jikinta ta ce "Kiyi shiru, Khadija na komawa komai zai daidaita Jiddah, yanzu haka shiryawa take kinji" muryarsa suka sakeji a hankali ya ce "Fatima" Jiddah ta kara sakin kuka ta ce "Yau na shiga 3 Umma dame zanji, da rashin lafiyarsa koda sunan waccen yarinyar daya ke kira" *The page is dedicated to the members of groups, i love u so much sisters, i appreciate ur comments love and support 🤗* _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _10_ A hankali ya kamo duvet din kan gadon yana kokarin tashi amma ya kasa, hakan yasa ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya, mikewa Jiddah tayi ta hau kan gadon tana kallan idanuwansa dake limshe kamar dazun, ta kai fuskarta kan nasa tana kuka kasa kasa, Umma ta mike ta koma dakinta inda ta samu Anty Khadija ta shirya da babban hijab dinta tasa nikab, Umma ta bata ATM card ta ce "Take care, kar ki sauka a hotel din dake kusa" Anty Khadija ta ce "To Umma, saina dawo" Umma ta ce "A dawo lafiya" daga haka Anty Khadija ta fita a dakin. Shiru Jiddah tayi tana sauraron yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri, ta mike a jikinsa ta sauka akan gadon da sauri tana kiran Umma, a bakin kofa suka ci karo, Jiddah ta rungume Umma ta ce "Na shiga uku Umma Yaya mutuwa zaiyi ya barni" kama hannunta Umma tayi suka koma dakinta ta zaunarta a bakin gado ta ce "Kinga yanzu na kira Dr kiyi shiru ki daina kuka zai samu sauki" Jiddah ta share hawayen idanta ta ce "To Umma yanzu idan yace ina Rafi'ah mai zamu ce masa, kinsan fa lokaci daya komai zai sake shi, i'm sure asirin ya bar jikinsa by now, kawai ciwansa ne ya tashi" Umma ta kamo hannunta ta ce "Asiri kam ya bar jikinsa amma Khadija ta koma ai, kuma bai manta da abinda suka faru a baya ba, yana sane da komai sai dai baisan meyasa yayi hakan ba, Allah na tuba da baya tuna komai ai sunanta ma bazai kira ba" Jiddah dake zare ido ta dan kalli Umma ta ce "To idan ya tambaya fa?" Umma ta ce "Barmin amsar a wajena" mikewa duk sukai jin ana knocking, Umma ta bude kofar parlorn tana kallan DR dake tsaye ta ce "Bismillah" ya shigo da sallama yana kallan Jiddah da idanuwanta sukai jaa suka kumbura, Umma ta ce "Ka shigo nan dakin" Dr ya bai bayanta zuwa dakin da Yusuf ke kwance, bayan ya duba shi sosai ya masa allurai sannan ya cire masa drip din da karewarsa kenan ya ce "Zai samu bacci na awa daya sai ya tashi, and i'm sure he will wake up fine" Umma ta ce "Ba wani matsala kenan?" Ya ce "Insha Allah, tinda anyi allura gobe da safe zan kawo magungunan da zai fara sha" Umma ta ce "Nagode sosai Dr, zan maka transfer yanzu nan" ya ce "Nine da godiya Hajiya" daga haka ya kalli Jiddah dake zaune gefen Yusuf ya ce "Madam Allah ya sauwake" kamar batasan magana ta amsa da Ameen, daga haka ya fita a dakin ya wuce. Rafi'a ce kwance akan sallayan data idar da sallan magrib, jin an bude kofar yasa ta mike a hankali, Ummi ta zauna bakin gado tana kallanta ta ce "Rafi'ah" a hankali ta ce "Na'am" Ummi ta ce "Kan naki bai daina ciwo bane?" Ta girgiza kai ta ce "Ya daina yanzu" Ummi ta ce "Toh Alhamdulilah u come down for dinner" ta ce "Toh" daga haka Ummi ta fita a dakin, kifa kanta tayi akan gado ta limshe ido, saam batajin dadin jikinta musamman yadda zuciyarta ke bugawa, mikewa tayi a hankali ta cire hijab din jikinta tasa hula sannan ta dauka phone dinta ta fita a dakin, kallan Imaan take dake zaune saman kujera tana bawa Ummi labarin Daddynta, Rafi'ah ta limshe ido ta wuce dinning ta zauna, Imaan ta sakko akan kujeran ta nufeta ta ce "My Daddy loves me so much ko Mom?" Rafi'ah ta dan kalleta bata ce komai ba, yarinyar ta dan hade gira tana kallanta ta ce"We just make call with Uncle Abdul, and shine yace wai Daddy baya sona wai shine yake sona, Daddy used to kiss and hug me, he bought ice cream for me, pizza and shawarma, he sometimes drop me to school or he picked me, Daddy loves me much ko Momma" daga mata kai Rafi'ah tayi ta share guntun hawayenta daya gangaro fuskarta, Imaan ta dan zaro ido ta ce "Are u crying Mom?" Girgiza mata kai tayi ta ce "No, something just enter my eye now" da damuwa Imaan ta rungumeta ta ce "Sorry, is it painful?" Ta girgiza kai ta ce "No, go and sit down" Imaan ta ce "I want to eat with u" Rafi'ah ta danyi murmushi ta daurata akan cinyarta ta ce "Alright dear" har suka gama cin abincin Imaan bata sake magana ba, saboda kullum Ummi na hanata magana idan tana cin abinci, sakkowa tayi akan cinya tana kallan Ummi ta ce "Ummi Momma didn't well" Ummi ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, kan kujera Ummi ta nunawa Imaan ta ce "U sleep there" Imaan ta hau kan kujeran ta kwanta, bata fi minti 10 ba tayi bacci, Ummi ta mike tana kallan Rafi'ah data kifa kanta akan dinning ta ce "Fatima" dagowa tayi tana kallan Ummi dake kokarin zama a kujeran dake gefenta, sauke kanta tayi kasa tana wasa da botton din doguwar rigarta, Ummi ta ce "Are u with me Rafi'ah?" Ta daga mata kai a hankali, Ummi ta ce "Duk wannan tinanin da kike ba shine mafita a gareki ba, sau nawa zance miki ki dinga addu'a ki manta da komai daya faru a baya, shekara 4 fa ba sati 4 bane, bazaki godewa Allah ki kar6i kaddararki a haka ba?" A hankali tayi wiping tears dinta ta ce "Na hakura Ummina, na kuma gode masa a haka, but ni Imaan used to makes me cry, musamman idan na tuna ba Ya Jawad bane mahaifinta, taya zanyi watarana na gaya mata haka Ummi" daga haka ta fashe da kuka, Cike da tausayinta Ummi ta ce "Shiyasa nace miki kowa da nasa kaddaran, ita nata a yadda yaxo kenan" Rafi'ah ta share idanta ta mike ta koma parlor zata daga Imaan Ummi ta ce "Ina zaki kaita?" Kanta na kasa ta ce "I want to spend the night with her" Ummi ta ce "To kisa tayi fitsari, sai ki shiryata" a hankali ta ce "Toh" daga haka ta wuce upstairs Ummi ta bita da kallo, a dakinta ta kwantar da Imaan saman gado sannan ta wuce dakin Ummi inda kayanta suke ta dauko mata kayan bacci da sucks da hula, rigarta ta fara cire mata sannan ta dagata suka shiga toilet, bayan few minutes suka fito ta saka mata kaya da socks tasa mata hula sannan ta kwantar da ita, cikin bacci ta ce "Ummi" Rafi'ah ta matsa gefenta tana shafa bayanta ta ce "It's me dear, do u need something" a hankali ta bude idanta tana kallan Rafi'ah ta ce "Dake zan kwanta?" Rafi'ah ta daga mata kai ta ce "Yes dear, is better u sleep with ur Mom, sai ki barmin Ummina ta huta" Imaan ta rungumeta ta ce "I love u momma" Rafi'ah na shafa bayanta ta ce "What do u want?" Ta ce "Water" kwantar da ita tayi sannan ta mike ta dauko ruwa ta tsiyaya mata sannan ta bata a baki ta sha, bayan ta ajiye cup din ta ce "Ki kwanta, zanyi sallan Isha" Imaan ta dan turo baki ta ce "That's not how Ummi used to makes me sleep" Rafi'ah dake kallanta ta ce "What do u want then?" Ta ce "She used to hug me nd we said a du'ah together" jawota tayi jikinta ta rungumeta sannan sukai addu'ah, suna a haka har tayi bacci sannan Rafi'ah ta zame jikinta a hankali ta sauka saman gadon ta shiga toilet. A hankali Yusuf ya bude idanuwansa saboda hasken wutan dake dakin, ya mike gently yana dafe da kirjinsa ya zauna, bin dakin ya dingayi da kallo ganin akwatinansu duk a tsakar dakin, mikewa yayi a hankali ya zura hannayensa cikin pocket ya tsaya bakin kofa, jin an bude toilet yasa ya juya da sauri suka ido hudu da Jiddah, ta sakar masa murmushi ta ce "How are u?" Silently ya ce "Fine?" Komawa yayi ya zauna a bakin gadon dan jiri yakeji kawai karfin hali yake, Jiddah ta zauna gefenshi ta rungumeshi tana murmushi, taji dadin ganin ya tashi kuma jikin da sauki, a sanyaye taji muryarsa ya ce "Sallah nawa nayi missing" ta dago tana kallansa ta ce "Tin dai na asuba da kayi shine jikinka yayi tsanani" ya dan kalleta ya ce "Wanda nayi a jirgi fa?" Ta ce "Isha na jiya kayi fa" ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya shiga toilet ta bishi da kallo, bayan few minutes ya fito ya shimfida sallaya ya tada sallah. Bayan ya rama duk sallolinsa yayi addu'a sannan ya mike, Jidda ta ce "In kawo maka abinci?" Ya ce "No" daga haka ta fita a dakin, a parlor ya samu Umma tana zaune, ya karasa gefenta ya zauna yana kama kansa ya ce "Umma" ta dago tana kallansa ta ce "Ya jikin?" Ya ce "Da sauki, is it true that na saki Rafi'ah?" Umma ta kafeshi ta ce "Ni kake tambaya ne kowa?" Ya zuba mata jajayen idanuwansa a takaice ya ce "Eh" ta ce "Shekararka nawa a Egypt?" Ya ce "Almost 4" Umma ta ce "To shekarun sakinta kenan" a hankali ya ce "Subhanallah, Umma mai tamin haka na saketa Umma, inasan matana wallahi" Umma ta ce "Kai zan tambaya wannan kuma" shiru yayi yana kallan Umma da itama shi take kalla, caan ya sake furta innalillahi kafin ya ce "Ni bansan me tamin ba, nasan dai by that time na tsaneta fiye da kowa, and i remembered when i divorced her, she's lying down on the floor and she's vomiting then, yes i remembered she was sick, but what comes over me?" Umma ta ta6e baki tana kallan Jiddah dake tsaye bakin kofa ta ce "Amma meyasa baka nemeta ba har tsawon wannan lokacin?" Ya ce "I don't know, nina manta da ita cikin rayuwa na Umma, all i know is ina tare dake da Jiddah da kuma khadija and nasan mun koma Egypt where i continue working with them with the help of ur classmate Alhaji Sunusi, after then rayuwana kawai nasa a gaba, ban ta6a tinata ba sai sau, Umma meyasa baku yi komai a kai ba kuka barni na saketa" Umma ta ce "To kace baka santa zan maka dole ne Yusuf?" Kama kansa yayi ya kara furta innalillahi wa inna~ilaihirraji'un, ya dago yana kallan Umma ya ce "Kenan shekara 4 tana gida? All i can remember is lokacin da muka je gidansu ziyara, i think she was 2 weeks in my house then, amma Umma ni bayan nan na manta ta a rayuwana ne" mikewa yayi kamar zaiyi hauka ya ce "Why Umma, muna zuwa Kaduna once in a year amma kuma baki ta6a tinamin ita ba, ban manta da kowa ba sai ita Umma, why? Meyasa haka ya faru dani ne?" Umma ta mike ta ce "Ni ina zan sani Yusuf, tinda ka saki yarinyar nan kana abu kamar kowa amma baka sake tambayarta ba, to zan maka dole saika dawo da ita ne" kifa kansa yayi akan dinning yana karanto addu'o'i ko zai samu saukin abinda yakeji, har yanzu he's so surprise da abinda ya faru da shi, duk yadda yake saan matarshi amma ya manta ta lokaci daya, shekara 4 bai sake maganarta ba sai yau, da karfi ya ce "Noo, it's impossible, i dont know what comes over me 4 years back" daga haka ya wuce daki da sauri yana kallan Jiddah ya ce "Where is my key?" Sai xare ido ta ke ta ce "Yanzu fa past 9pm kuma a Egypt kake da mota ba anan..." Wani mungun tsaki yaja ya wuceta ya fice a dakin ta biyo bayansa, lokaci daya yaji zuciyarsa ta buga, ya danne kirjinsa da hannunsa na dama yana furta subhanallah, anan wajen ya xu6e sumamme, Jiddah ta kwala ihu tana kiran Umma, da sauri Umma ta fito a daki ta ce "Faduwa yayi?" Cikin kuka Jiddah ta ce "Umma ya samu attack me tsanani, pls do help Umma, mu kaisa asibiti karya mutu, nima wallahi mutuwa zanyi, ganin Umma ta tashi ta shiga daki Jiddah ta mike ta fita a parlorn, dayan apartment din gefensu ta nufa, dayake dama gidan haya ne ta fara musu knocking kamar zata balla kofar. Anty Khadija na daga wayar Umma ta ce "Kin isa ne?" Ta ce "A'a Umma, sai gobe zan karasa ina cikin Kano a hotel" Umma ta ce "To da asuba zaki fita, ya tashi yana tambayar meyasa aka barshi ya saketa, yanzu dai ya samu attack ya sume gashi caan parlor, ki lalla6ashi ya gyara mana aikin nan Khadija, ki bashi ko nawa ya bukata" Anty Khadija ta ce "Toh Umma" daga haka tayi hanging call din. Koda Umma ta fito parlor neighbor dinsu harya sa Yusuf a mota, ta zura hijabi ta kullo kofar ta shiga motar suka tafi, wani nearest private hospital suka kaishi inda cikin gaggawa aka karbeshi. kusan awa daya su Umma na reception a zaune sannan akai kiransu, Jiddah banda kuka ba abinda take, Dr ya musu bayanin komai, cewar su kwantar da hankalinsu, amma anyi admitting dinsu zuwa gobe, daga haka ya wuce office dinsa, Umma ta shiga dakin da yake Jiddah tabi bayanta, yana nan kwance akan gadon idanuwansa a limshe, neighbor dinsu na kansa yana masa sannu, Jiddah ta kamo hannunsa cikin kuka ta ce " Karka maida abinda yake cikina maraya tin baizo duniya ba, dan Allah ka tashi Yaya, idan ka barni nima mutuwa zanyi" Umma ta kama hannunta suka fita a dakin ta ce "Ki daina kuka haka mana Jiddah, ko mutuwa yayi munada asara ne bayan duk dukiyarsa na hannunmu, da zarar Khadija ta dawo zai sake mance ta kuci gaba da rayuwarku" Jiddah dake kallan Umma ta kara share hawayen idanta cikin fishi ta ce "Eh ai saboda bake kika haifeshi ba zakice ya mutu, sannan bake kike dauke da cikinsa ba shiyasa xaki ce ya mutu, to wallahi Yaya ba zai mutu ba idan kuma ya mutu kema bazaki zauna lafiya ba saina tona miki asiri na gayawa duniya kece sanadiyyar mutuwar sa" Umma dake kallanta surprisingly ta ce "Jiddah ni kike dagawa murya haka? Ni zaki kalla kina nunawa da yatsa" cikin 6acin rai ta ce "An nunaki da yatsan nima ki kasheni ki huta, wallahi idan ba tashi yayi ba bazan yafe miki ba, duk kece silar abubuwan da suka faru" wanka mata mari Umma tayi, jiddah ta durkusa tana dafe da kuncinta ta ce "Ni kika mara?" Umma ta kara wanka mata wani marin ta ce "Gobe ki dinga dagamin murya kina nunani da..." Kafin ta rufe bakinta Jiddah ta wanka mata mari ta ce "Wallahi baki isa ki mareni ban rama ba" _08103810398_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _11_ Washegari misalin karfe 10 Yusuf ya tashi, ya bude idanuwansa da suka masa nauyi yana bin dakin da kallo, Jiddah da fitowanta a toilet kenan ta nufeshi tana fadin "How are u feeling now?" Silently ya ce "Fine, naji sauki" ta ce "Allah ya sauwake" kokarin tashi yake ta taimaka masa ya zauna, ya kalli idanuwanta da suka kumbura ya ce "Where is Umma and Khadija?" Ta dan hade rai ta ce "Umma went back home, Anty Khadija kuma tayi tafiya" ya limshe idanuwansa ya ce "Ohk" mikewa Jiddah tayi ta fita a dakin tana tino maganganun Umma kafin ta koma gida, dan cewa tayi idan Yusuf ya tashi sai ya sake ta, tana isa corridor ta hadu da matar neighbors dinsu da basket a hannunta, Jiddah ta danyi murmushi ta ce "Sannu da zuwa" matar ta ce "Sannu, ya mai jiki?" Jiddah ta ce "Da sauki, bismillah" daga haka ta juya matar tabi ta a baya, suna shiga dakin Yusuf ya bude idansa yana kallansu, matar ta ajiye basket a gefen gadon ta ce "Ina kwana" Yusuf ya ce "Lafiya kalau" ta ce "Ya karfin jiki kuma?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Allah ya kara sauki" ya ce "Ameen" kallan Jiddah tayi dake tsaye gefe ta ce "Zan wuce Allah ya sauwake" ta mike tana murmushi ta ce "Mungode, ayima baban Mu'azzam godiya" ta ce "Ba komai, Allah ya kara sauki, yaje aiki ne shiyasa bai shigo da safe ba" daga haka ta fita a dakin. Jiddah ta zauna gefensa ta ce "In zuba maka abincin?" Ya girgiza kai a takaice ya ce "No" bude kofar dakin akai wani likita ya shigo, ya kalli Yusuf dake zaune ya ce "Ya jikin?" Yusuf ya ce "Naji sauki, i hope u will discharge me today" Dr ya danyi murmushi ya ce "Idan munga ba matsala ba" Yusuf ya ce "There's not insha Allah" Dr ya ce "Allah yasa, but i'm giving u injection now" Jiddah ta dan kalleshi ta ce "But he didn't eat anything yet" ya ce "Ohk, idan yaci u let me know" ta ce "Toh shikkenan" Dr na fita Yusuf ya kalleta ya ce "How is ur own body?" Ta ce "Naji sauki, kawai banasan kamshin stew ne" ya limshe idanuwansa baice komai ba, ta sakko a hankali ta diba masa fatan dankali da kifi, ta zuba masa tea a mug sannan ta koma kan gadon, Yusuf ya girgiza kai ya ce "Tea kawai zan sha" mika masa mug din tayi ya kar6a ya rike a hannu, every minutes daya wuce daga tashinsa zuwa yanzu Rafi'ah kawai yake tinawa lokacin daya bata papern sakinta, yana tinawa by that time tana kwance cikin amai fuskarta da hawaye. Ta6a shi da Jiddah tayi ne yasa ya dawo hayyacinsa, ta ce "What are u thinking?" Ya ajiye mug din akan stool din dake gefensa ya ce "My wife" Jiddah ta dan kalleshi ta ce "Ni kenan" ya girgiza kai ya ce "Fatima na, ina tinanin da ciki na saketa, idan kuma ba ciki bane she was sick then" mikewa Jiddah tayi tana masa wani kallo ta koma kan kujera ta zauna ta wani hade rai, limshe idanuwansa ya sake yi inda hawayen dake makale a idansa suka gangaro, bude idanuwan yayi ya share hawayen ya dauki mug din ya fara shan tea din daya ke jinsa kamar gauta tsabar daci, ba dan alluran da za'a mishi ba da babu abinda zai sha, dan dai yasan akwai matsala ne idan akai baici komai ba, bayan five minutes ya sha half, ya ajiye mug din yana kallan Jiddah ya ce "Let him come" tashi tayi ba tare data kalleshi ba ta fita a dakin. Ba jimawa suka dawo tare da Dr, ya masa alluran sannan ya bashi drugs dinsa, bayan 30 minutes ya mike yana kallan Jiddah ya ce "An biya bill din?" Ta ce "Ehh" daga haka ya ce "We are going" ta tsaya tana kallansa ta ce "Ba suyi discharging dinmu bafa?" bai ko kalli inda take ba ya fita a dakin, ta mike tabi bayansa taga ya shiga office, ita dai a bakin kofar ta tsaya, bayan few minutes ya fito ta dori a bayansa suka fita a clinic din. Rafi'ah ce zaune a school dinsu tana jiran Jawad, sai bin mutanen dake wajen take da kallo, jin horn a bayanta yasa ta juya da sauri, ya sakar mata murmushi ya fito a motar yana kallanta, a hankali ta karasa inda yake tsaye ta ce "Yau dai kazo da wuri" yayi murmushinsa mai kyau ya bude mata front seat ya ce "Gudowa nayi a wajen aiki, kinga idan aka tashi kamani sai a hada harda ke" ta danyi dariya ta shiga motor ya rife, bayan ya zagayo yayi wa motar key yana kallanta ya ce "Yau kin gama da wuri" ta ce "Ai yau lectures daya mukai 8-10" ya ce "Good, ina Babynah?" Ta ce "Tana gida" ya ce "I missed her, jiya har mafarkinta nayi" ta ce "I see, yau kuma inaga kaida ka ganta sai dai da daddare idan kazo" ya ce "Why?" Ta ce "Khairiyya ta kirani zata zo, kuma nasan yini zamuyi" ya ce "Ohk, tinda aka bani ke dai wancen yayan nata ya daina daminki ko?" Ta danyi murmushi ta ce "Sure, sai dai ya kira mu gaisa, ba sosai yake zuwa ba" Jawad ya ce "Better, na tura miki abu ta Whatsapp idan kinje gida sai ki duba" ta ce "What's that thing?" Ya ce "U will see" ta sake murmushi kawai, kamo hannunta yayi cikin cool voice ya ce "I still don't know how much i luv u Rafi'ah, i face so much problems just because of u, har banaso na tuna abubuwan da suka faru two years back" a hankali ta ce "I also, but gashi amma ya wuce ba" ya ce "Sure ya wuce, shiyasa kullum nake ce miki ki dinga mantawa da abinda ya faru, just face ur future" ta ce "Insha Allah" har ya sauketa a gida hirarsu suke abin shawa'a, bayan ta sauka ya ce "Baki ce min abin ba yau" ta boye fuskarta kasa~kasa ta ce "I luv u so much" ya ce "I luv u too" juyawa tayi da sauri ta bude gate, ta dan juyo ta daga masa hannu sannan ta shige ciki. Cikin gaggawa Umma ta dauki karamar trolley tasa kayanta dana Anty Khadija, sai zufa take ta rufe akwatin, tinda aka kira daga police station hankalinta ya bar jikinta, ganin an sake kira ta daga wayar hankali tashe ta ce "Dan Allah Yallaboi ka bata muyi magana" DPO ya mikawa Anty Khdija wayar, cikin muryar kuka ta ce "Umma Alhaji Usman ya ganni yasa an kamani, yasa aka min duka sannan yace saina biyashi duk abinda ya min, Umma dan Allah kizo kar su kasheni maganarsa sukeji kamar shiya haife..." tsawar da wani dan sanda ya daka mata ne yasa tayi shiru, DPO ya kar6i wayar yayi hanging call din yana kallan Alhaji Usman ya ce "Insha Allah Alhaji zamu yi hukunci dai dai yadda ya kamata, dama mun jima muna neman irinsu" Matar Alhaji Usman dake tsaye a gefe ta wankawa Anty Khadija mari cikin kuka ta ce "Ta Allah ba taki ba makirar mata kawai, da Allah ya fiku sai gashi rana daya Abban Muhammad ya dawo, shekara kusan 4 bamu san inda yake ba, wallahi badan badan banzan iya shirka ba da nima naje wajen boka an rabaki da kowa naki, kin wulakanta a duniya" da sauri Alhaji Usman ya ce "Haba Hindatu, ya kike magana kamar baki da ilimi ne?" Ta ce "Aikin asirine wallahi, kuma muna nan da kai saita fada da bakinta, inba asiriba ya za'ai shekara 4 bakasan inda muke ba kake zama hankali kwance, wallahi baxan ta6a yafe miki ba saina tozarta ki an yadaki a media tsinuwar mutane ta biki" Alhaji Usman ya kama hannun matarsa suka koma gefe ya ce "Haba Hajiya, ba girmanki bane kamar ni matata ta dinga fadan irin wannan kalaman" hawayen idanta ta goge ta ce "Alhaji bakasan halin da muka shiga ba na rashinka, 'yayana dani kaina ba wanda ya sake jin dadin rayuwa sai wancen satin daka dawo, yanzu kuma Allah ya hadani da ita bazan ci ubanta ba, meyasa zakace in kyaleta" ya ce "Calm down pls, a hankali zamubi komai" daga haka ya dawo yana kallan DPO ya ce "A sata cell, idan mahaifiyarta tazo a kirani" DPO ya ce "An gama sir" daga haka ya tasa keyarta gaba, sai kuka take tana ta shiga 3. Umma bata fi minti 5 da fita a gidan ba su Yusuf suka iso, karfin hali kawai yake amma shiyasan abinda yakeji, Jiddah ce ta biya me taxi din sannan tabi bayansa suka shiga gidan, suna shiga parlor Yusuf ya dauka trolley dinsa ya fito, Jiddah ta tsaya kallansa ta ce "Where are u going Yaya?" A takaice ya ce "Kano" ta ajiye basket din hannunta ta ce "Nima ai binka zanyi" daga haka itama ta fito da trolley dinta, da sauri ta shiga kitchen ta wankewa Maman Mu'azzam warmers dinta da flask sannan ta fito ta kai mata ta musu sallama, har bakin kofa Maman Mu'azzam ta rakota sannan ta juya, Yusuf ya duba pockets dinsa ko zai samu kudi amma babu, ya kalli Jidda da shigowanta kenan parlorn ya ce "My ATM cards" ta ce "Duk suna wajen Umma, kuma da alama bata gidan dan ba dayan akwatin" ya ce "Akwai kudi a hannunki?" Ta ce "Ehh akwai 5 thousand, nasan zai kaimu Kano" ya ce "To saiki fito" daga haka yaja trolley dinsa ya fita a parlorn itama tabi bayansa da nata, a bakin titi suka hau cab ya wuce dasu park. Rafi'ah na zaune dakinta Imaan ta shigo da gudu, ta dago da sauri tana kallanta ta ce "Do u want to fall down Imaan?" Ta ce "No Momma, i just want to check if u are at home, banasan ki sake fita ki barni" murmushi Rafi'ah tayi tana kallan cute girl dinta ta ce "Ai bance maki fita zanyi ba so u feel free" Imaan ta juya ta fita a dakin ta ce "Bye Momma" Rafi'ah ta daga mata hannu ta ce "Bye" jawo phone dinta tayi ta shiga Whatsapp, bayan messages sun gama shigowa ta bude na Jawad wanda shine second to the last, pictures taga ya turo guda 8 sai a karshe ya rubuta "You choose two sets" bayan sun gama budewa ta kurawa akwatinan ido, duk cikinsu ba wanda bai mata ba, sunyi kyau sosai different design and color ko wanne guda 6, ta danyi murmushi ta fita a whatsapp din sannan tayi dialing phone dinsa, cikin cool voice dinsa ya ce "Wife" ta sauke kanta kasa kaman yana gabanta ta ce "I saw them, sunyi kyau duka" ya ce "Alright you resend me the one u choose, Anty Jamila zata dawo next week so ita zata taho dasu" Rafi'ah ta ce "Ohk to, Allah ya dawo da ita lpy" ya ce "Ameen, za muyi zama a court i will call u ltr" a hankali ta ce "Ayi adalci barrister" ya ce "Insha Allah Fatima na" ta sake yin murmushi ta ce "Alright then sai anjima" ya ce "Bye" daga haka tayi hanging call din, tana ajiye phone din Khairiyya ta shigo da Imaan a hannunta, Rafi'ah ta dan zaro ido tana murmushi ta ce "Graduate" Khairiyya ta sauke Imaan tana dariya ta ce "Ina wuni Anty Fatima" Rafi'ah ta ce "Lafiya kalau, kun gama Neco ko?" Ta ce "Ehh Anty" Rafi'ah ta ce "All d best" Khairiyya ta kama hannun Imaan ta ce "U are following me to our house ko Imaan, Ammi nata nemanki" Imaan ta ce "Noo, i won't leave my Momma" Khairiyya ta ce "U must, baki ta6a kwana mana ba" Imaan ta hau damfe tana buga kafa ta ce "I won't follow u" _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _12_ Karfe 1 da 'yan mintuna su Yusuf suka iso Kano, bayan an fitar musu da kayansu ya tare napeep a cikin park din, kamar bayasan yin magana ya ce "Sharada" mai taxi din ya ce "To bismillah Alhaji" Yusuf ya bude back seat ya shiga, Jiddah dake tsaye a gefe ta ce "Malam ga kaya fa" mai taxi din ya fito ya dauki trolley dinsu yasa a boot, sannan ya dawo ya kunna motar, kallan Yusuf tayi daya jingina da kujera ya limshe ido, tinda suka taso a Kaduna ko magana ba suyi ba har yanzu, ta danja tsaki a hankali ta dauke idanta a kansa, tafiyar minti 10 sukayi suka iso dai~dai gate din gidansa, bayan anyi parking Jiddah ta dan kalleshi ganin ya bude ido, bude motar yayi ya fito ya tura gate din yaji a rufe, ya juyo yana kallan Jiddah a takaice ya ce "Key?" Ta bude hannayenta alaman itama bata sani ba, Yusuf ya sauke ajiyar zuciya ya kara juyawa yana kallan padlock din dake jikin kofar, mai taxi din ya kalleshi ya ce "Yallaboi ko ana bukatar taimako?" Yusuf ya ce "Makulli nakeso wanda zai bude wannan kwadon" mai taxi din ya ce "To bari na kar6o a nan bakin titi" Yusuf ya kalli Jiddah dake tsaye tayi folding hannayenta ya ce "Ki bashi kudi" ta ciro 1k ta mikawa mai taxi din, mota ya koma ya kunna yana kallan Yusuf ya ce "Saina dawo" daga haka ya wuce, Jiddah ta juyo tana kallansa ta ce "What if he run away?" Yusuf ya kafeta da ido bai dai ce komai ba, kamar daga sam taji ya ce "Kansa yayi wa" ta juyo tana kallansa amma sai yayi kamar ba shi yayi maganar ba. Sun kusan minti 7 sai gashi ya dawo da key har iri buyu, ya fito yana kallan Yusuf ya ce "A cikin daya zamu dace insha Allah, hala kun manta naku makullin ne" Yusuf ya ce "Ehh" ana gwada na farko kuwa padlock din ya bude, Yusuf ya dan kalli Jiddah ya ce "Give him another 1k" daga haka ya kalli mutumin ya ce "Nagode" yaja trolley dinsa ya shiga ciki bayan mutumin yayi masa godiya, kamar bayasan taka kasa ya nufi entrance din gidan, ga wani jiri dake shirin dibarsa, shi dai kawai tafiya yake, tin daga tsakar gidan zaka gane anyi shekaru ba mutane a gidan, saboda duk datti ne ta ko ina, ga ganyen flowers din gidan da suka bushe sun zubo kasa. Yana murda handle din kofar parlor yaji a bude, ya bude ya shiga yana karewa parlorn kallo, ta ko ina kurane tin daga kan kujerunsa TV stand, TV, center table da kuma tiles din, ya nufi part din Rafi'ah ya samu ba komai aciki, sai kura a kasan tiles din, ya karasa dakunan ma ya leka, ko labule babu a ciki, hannunsa yasa ya share hawayen daya gangaro a idansa, ya tabbata kenan dai ya saki Rafi'ah kamar yadda yake tinawa, ya cije lips dinsa still hawaye na sakko masa ya fita a part din ya bude na Jiddah, itakam komai nata yana nan yadda suka barshi, wani abin ma kura ta lullubeshi, ya juya ya fito a hankali kamar bayasan taka kasa, yana fitowa parlornsa ya zauna akan 3 seater saboda jiri dake shirin jefar dashi, Jiddah da shigowanta kenan tabi shi da kallo, gaba daya ya 6ata farin kayansa dake jikinsa, caan bakin kofa ta tsaya tana karewa parlorn kallo, bayan minti 10 ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To yanzu a cikin kurar nan zamu kwanta yaya?" Bude idanuwansa yayi ya kalleta, yayi shiru yana tinanin taya zai fara zuwa gidan Ammi, da wani ido zai kalleta, mai zaice mata Rafi'ah tayi masa ya saketa? Maiyasa bai nemeta ba all this while? Sauke ajiyar zuciya yayi Jiddah ta ce "Doctor magana fa nake maka" ya kara dago kansa ya kalleta, ta ce "A haka zamu zauna dust everywhere?" A hankali ya ce "Ki gyara nan parlorn ki zauna" da mamaki ta ce "Bayan ina dauke da cikinka sannan kace nayi wannan uban gyaran ga kura, mutuwa zanyi kenan?" mikewa yayi gently ya ce "Then kije gidanku, duk ranar da zaki iya gyaran gidan sai ki dawo, i'm leaving too, dama na biyo nan ne na huta in other not to stress my heart again, tinda na samu relief tafiya zanyi" da mamaki ta ce "Ina zakaje to?" bai kalli inda take ba ya mike yana jaan trolley dinsa ya fita a parlorn ta bishi da harara. Umma ce zaune cikin cell ita da Anty Khadija dake faman kuka, babu abinda yake damunta sai rashin zuwa wajen bokan nan da tayi, tasan yanzu ko ta yaya Yusuf kokari zaiyi ya dawo gida, sauke ajiyar zuciya Umma tayi ta ce "Gaskiya bamu ta6a shiga kunci irin na yau ba, kema sai da nace karkije inda za'a ganki amma kika fita, yanzu ga shi nan kotu za'a turamu mu shiga 3" Anty Khadija ta kamo hannun Ummanta ta ce "Abin takaicin bai wuce dawowar Yusuf ba, wallahi Umma ko shekara 10 zanyi anan indai Yusuf zai shiga duniya ba damuwata bane, kuma na fito a hotel zan hau Napeep na tafi tasha kawai naga Alhaji Usman da matarsa, naso guduwa amma ya taramin jama'a Umma, mutane nata zagina haka aka taso keyata har nan, amma duk abin nan daya faru gara ninkinsa ya faru da Yusuf ya dawo" ta kifa kanta akan cinyar Umma tana kuka ciki ciki, Umma ta ce "Ai zamu fita ina nan dake sai na kadashi duniya" jin an shigo yasa Anty Khadija ba tai magana ba, dan sandan ya tsaya yana kallansu ya ce "Ance ku kira mutum daya cikin 'yan uwanku saboda jibi zaku fara zama a kotu, shi zai wakilce ku da wani abin daya kamata" Anty Khadija ta kalli Umma ta ce "Kawu na mararraba za'a kira ko?" Umma ta hade rai ta ce "Allah ya kiyaye wallahi, mutumin daya cimun mutunci gabanki rannan, wallahi gara nayi hayan dan uwa na kawo" Dan sandan dake kallanta ya jefa musu waya daya daga cikin wayoyi uku da suka kwace a hannunsu yayi tafiyarsa, Anty Khadija ta share hawayen idanta ta ce "Na shiga 3,yanzu fa idan asirinmu ya toni duk wasu manyan mutane da nake mingling dasu zasu gujeni, a gujeni wajen aiki, a gujeni a ko ina ma" fashewa tayi da kuka ta ce "Ga Yusuf na dab da bayyana Umma, nasan da an sallameshi zai dawo gida, Allah yasa ya rasa komai nasa a rayuwa, Allah yasa tayi aure mijinta ya kulleshi, ita kuma Jiddah data mareki Allah ne kadai zai rabani da ita wallahi" Umma ta ce "To ga shawara, ba sai mu kira Yusuf din muce masa gamu station ba, kinga yana zuwa zaiyi komai a gama, muna fita kuwa sai kauyen Marke mu kara kada shi" Anty Khadija ta ce "Kina ga zai zo?" Umma ta ce "Sai dai banyi kuka ba, amma muddin na nuna masa ina cikin tashin hankali zuwa zaiyi, kinga ba zai samu kwanciyar hankalin zuwa gidan kanwar uwarsa ba, nan zai taho direct" Dai dai kofar gidan Ammi aka sauke shi, ya zira hannu a aljihunsa ya ciro 100 naira daya gani dazu, ya mikawa mai Napeep din sannan ya tura kofar gate din ya shiga, zuciyarsa banda bugawa babu abinda take, da kyar yake takawa saboda yadda yakeji, a balcony ya sake trolley din ya fadi, ya murda handle din kofar ya shiga ciki, Ammi na zaune akan sallaya ta idar da sallan la'asar, ta juyo da sauri dan tinaninta Khairiyya ce ta shigo, Yusuf ta gani tsaye hawaye sun wanke masa fuska, ta zabura ta mike tana kallansa ta ce "Yusuf, is that really you?" Sai kuma ta fashe da kuka, a daddafe ya karasa inda take ya rungumeta sosai yana kuka ya ce "It's me Ammina, ki yafemin dan Allah bansan meya faru dani ba Ammi, i left without u knowing, i divorced my beloved wife, i lost my job, na rabu da duk masoyana na koma caan wani waje na kafa saban rayuwa, dan girman Allah ki yafemin it wasn't intentional Ammina, i have no one but u, kece komaina Ammi dan Allah ki gafarfeni kimin rai ko zan samu saukin abinda nakeji" Ammi kam banda kuka ba abinda take, jin ya sake jikinsa yana shirin faduwa yasa ta rikoshi da sauri tana jijjigashi amma ina ya sume a hannunta, anan tsakiyar parlorn ta kwantar da shi, ta dauka bottle water dake kan dinning ta zuba masa a fuska, yayi wata ajiyar zuciya ya bude idanuwansa da suka ciko da hawaye, Ammi ta dagoshi cikin tashin hankali ta kira Daddyn Sameer a waya ta fada masa abinda ke faruwa sannan ta katse wayar tana rungume da Yusuf still tana kuka tana kara godewa Allah hade da masa addu'a. *_2 hours ltr_* Kwance yake akan gadon Ammi, Sameer na rike da hannunsa yana masa sannu, Yusuf ya daga masa kai kawai yana kallan Ammi dake share hawaye har lokacin, a hankali Sameer ya ce "Zaka tashi ne" Yusuf ya daga masa kai, Sameer ya taimaka masa ya tashi zaune, zira kafafuwansa yayi kasa yana kallan Ammi ya kamo hannunta cikin sanyayyar murya ya ce "I know it's hurt Ammi, nasan nayi abinda ko a mafarki bakiyi tinani ba, Ammi ban tafi dan nayi rayuwa me dadi ba wallahi, ban gujeku dan bana sanku ba, no one loves u more than i did Ammi, bansan meyasa na tafi ba, i left my wife crying na tafi na barta cikin amai, wallahi Ammi it wasn't intentional, kin fitar da hawaye a kaina yafi a kirga, dan Allah kice kin yafemin Ammi" rungumeshi Ammi tayi tana share idanta ta ce "U never hurt Yusuf, nasan ba laifinka bane, nasan dole watarana zaka dawo indai kana raye, ai addu'ar iyaye bata faduwa banza" hawayen idansa ya share yana kallan Sameer dake hawaye shima, Daddy ya karaso yana masa sannu, Yusuf ya ce "Alhamdulilah" Ammi ta mike ta fita a dakin Daddy yabi bayanta, a parlor ya sameta tana zaune tana share hawayen dake gangarowa a idanta, ya ce "Aisha ai sai mu godewa Allah daya bayyana shi" Ammi ta ce "Mungode masa Engineer" Daddy ya ce "To dan Allah ki daina kuka haka nan, bari na kira mahaifin Fatima na sanar masa" Ammi ta ce "A'a dai tukunna, yanzu idan yayi wanka sai muje gidan gaba daya" Ya ce "To Allah ya kaimu" daga haka Daddy ya fita a parlorn, ana kiran Magrib Sameer ma ya fito a dakin, Ammi ta mike ta shiga dakin da Yusuf yake, fitowansa a wanka kenan, ta kura masa ido ganin yadda ya rame sosai, nan da nan kuma idanta ya kawo ruwa, Yusuf ya sauke kansa kasa ya ce "Naji sauki Ammi, u worry not" Ammi ta ce "Idan kayi sallah u meet me in my room" daga haka ta juya ta fita, kaya ya saka yayi sallah sannan yayi addu'a, karfin hali kawai yake amma shi kadai yasan abinda yakeji, mikewa yayi gently ya nufi dakin Ammi, da sallama ya karasa ciki ya zauna, ta ce "Kayi sallan?" Ya ce "Ehh" ta zauna gefensa ta ce "Ina ka shiga all this while Yusuf?" A hankali ya ce "Egypt" ta ce "You and who?" Ya ce "Umma, Khadija da kuma Jiddah" Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Where are they?" Ya ce "Jiddan na gidansu, but Umma da Khadija ban sani ba" nan ya bata labarin dawowarsu zuwa kwanciya a asibiti da yayi har tahowansu Kano, duk yadda Ammi taso ta danne kukanta kasawa tayi, ta dinga share hawaye, Yusuf ya sauke kansa shima yana goge hawayen idansa ya ce "Wallahi Ammi bansan meke faruwa dani ba, tin daga ranar dana tafi ban sake tina taba sai jiya, i cried alot Ammi, musamman idan na tuna yadda na tafi na barta" Ammi ta dago kanta tana kallansa ta ce "Kasan ka barta da ciki ne?" With shock ya dago kansa yana kallan Ammi ya ce "Ciki kuma? Nasan dai bata lafiya then, but bansan meyeke daminta ba" Ammi ta share hawayen idanta cikin sanyin murya ta ce "Ka barta da ciki Yusuf, she suffered alot har kamar ba zatai rai ba, haka tai ta rainan cikin har Allah ya kawo ranar haifansa, nan ma ta kasa sai CS aka mata aka cire mata yarinya" kuka ne ya kwace mata ta kasa karasawa, Yusuf dai still yayi yana kallanta, ji yake kamar ba dashi take ba, Ammi ta dago tana kallansa ta ce "Ur Baby is now 3 years old, ina tinanin idan akwai wacce zata yafe maka kaji dadi bai wuce Rafi'ah ba" mikewa yayi ya rasa abinda zaice, sai kuma ya zauna bakin gado yana furta innalillahi wa inna ilaihir raji'un,, ya dinga share hawayen dake zubo masa cikin kuka ya ce "I don't know she's pregnant Ammi, this was the biggest sin i have ever made, meyasa nayi haka" ganin kamar ba hayyacinsa yake ba yasa Ammi ta kamo hannunsa ta ce "Stay calm Yusuf, u know ur condition, karka samun attack pls" rungume Ammi yayi yana kuka ya ce "This is all my fault Ammi, nasan da wuya ta yafemin" Ammi ta share hawayen idanta ta ce "It's not your fault Yusuf, Allah zai tona asirin duk wanda yakesan yaga bayanka" saketa yayi ya mike yana share hawayen idansa, Sameer ne ya shigo dakin shida Daddy, Yusuf ya ce "Bani key din motarka" Ammi ta mike tana kallansa ta ce "Ina zakaje kuma?" Ya ce "I'm going to see my wife Ammi" ta ce "Amma kasan ba matarka bace a yanzu ko?" Ya ce "Na sani" daga haka ya fita a dakin suka bi bayansa. Rafi'ah ce tsaye a kitchen tana wanke hannunta, bayan ta gama ta goge hannun da towel ta fito tana kallan Mummy dake zaune a parlor ta ce "Nifa na kira wayar Ammi several times bata dauka ba, kawai mu fara sauke Khairiyya sai mu kaiki" Mummy ta ce "An fasa jiran Jawad din ne, naga yace yana hanya" Rafi'ah ta dan 6ata rai ta ce "Yanzu fa bayan magrib ne, kuma Ammi zatai fada Mummy, sai dai kuma idan zaki bari a fara sauketa" Ummi dake canzawa Imaan kaya ta ce "To ba sai a fara sauketa ba what's in it?" Rafi'ah ta ce "Allah sai Mummy tace sai mun sauketa sannan mu wuce" Mummy ta dalla mata harara ta ce "To badan Jawad ya matsa na jira ba da tin tini nayi tafiya ta, dama 'yar uwata nazo gani ba kowa ba, indan take da 'yarki ne ai bazan zo ba" Khairiyya ta danyi murmushi tana taya Ummi sawa Imaan takalmi, ita dai Rafi'ah tin data turo baki ta samu waje ta zauna, bata mike ba sai da taji horn, ta tashi ta saka hijab Mummy ta ce "To Zainab Allah bamu alheri, gobe dai a kaimin Imaan ta wuni" Ummi ta mike zata rakasu ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ta kalli Khairiyya dake saka shoes dinta ta ce "Kin dauki ledan karki manta" ta ce "Ehh gashi nan, nagode Ummi sosai" Ummi ta ce "Ki gaishe da Amminki" ta ce "To zataji" suna fita compound motar Daddy ta shigo gidan, Mummy ta ce "Bako kukayi ne, ashe ba Jawad din bane" tana rife bakinta motar Jawad ma ta shigo, Imaan ta wara ido ta tafi da gudu tana kiran "Daddy" dai dai nan Yusuf ya fito a motarsu ya kurawa cute girl din ido, Ammi ma duk suka fito a motar, Rafi'ah ta dafe kirjinta zata durkusa Ummi ta rikota, cikin 6acin rai Mummy ta nufi Yusuf ta shako shi tana fadin "Ubanme kazo yi gidan nan Malam, kazo ka karasa kasheta ne?" Shi dai Yusuf banda kallan Imaan ba abinda yake, harta dale jikin Jawad sannan ya sauke idansa a kansu, yana juyowa kuwa Mummy ta sauke masa mari a kumatunsa hawaye na sakkowa a idanta ta ce... _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _13_ Bude idanuwansa yayi a hankali ya fara bin dakin da kallo, Ammi dake zaune gefensa tayi saurin matsowa ta ce "How are u?" Silently ya ce "I'm fine Ammi, where is my daughter?" Ammi ta ce "Don't stress yourself again pls, everyone is fine, Rafi'an ma a jiyan aka sallameta tana gida" Yusuf ya dan kalleta ya ce "U said?" Ta ce "Rafi'ah" shiru yayi yana tina incident din jiya daya faru, Ammi ta ce "Pray first sai mu wuce gida" mikewa yayi a hankali yana kallan agogon dakin dake nuna karfe 7 saura, da taimakon Ammi ya shiga toilet yayi alwala sannan ya fito yayi sallah, idan ka ganshi zakace bashida damuwa saboda ya saki ransa yau ba kadan ba, sai dai kuma in kaga ramar da yayi. Kafin ya idar da sallah Daddy da Abi da kuma Abba da saukarsa a garin kenan suka shigo dakin, bayan sun gaisa da Ammi, Yusuf ya juyo a hankali yana kallansu, sai kuma ya sauke idansa kasa ya ce "Ina kwananku?" A tare duk suka amsa, Abba ya ce "Ya karfin jiki?" Ya ce "Alhamdulilah" Daddy ya kalli Ammi ya ce "Tinda an sallameku Sameer zaizo ya maidaku gida, sannan karfe 10 akwai meeting a guest house dina da akai organizing just because of this case, and i hope kowa zaiyi attending dan samun kwanciyar hankali" Ammi ta ce "Allah ya kaimu" Abi ya ce "Allah ya kara maka lafiya" daga haka suka fita a dakin, sauke kansa kasa yayi yana kallan Ammi ya ce "Good morning" Ammi ta ce "Morning too, ya karfin jiki?" Ya danyi murmushin karfin hali ya ce "Da sauki" ta ce "Allah ya kara sauki" shiru yayi yana san ya tambayi Imaan amma sai yaji nauyin hakan, jinginar da kansa yayi jikin gadon yana addu'a kasa kasa, sai daya ji an bude kofar dakin sannan ya dago yana kallan direction din kofar, wani dan uwan mahaifinsa ne tare da Sameer suka shigo dakin, Yusuf ya danyi murmushi yana kallan Kawun nasa ya ce "Ina kwana Kawu Umar" Kawu ya ce "Alhamdulilah, ya karfin jiki" ya ce "Da sauki Kawu" daga haka suka gaisa da Ammi, Sameer ya durkusa yana kallansa ya ce "How are u feeling now" Yusuf ya ce "Better" Sameer ya ce "Masha Allah, dazu Faruk ya kira zan hada ku ku gaisa kuma kana bacci" Yusuf ya ce "Ohk anjima sai muyi waya" mikewa Ammi tayi ta fara tattara duk kayansu ta bawa Sameer ya kai mota, sannan suka fito zuwa gida bayan sun kara siyan wani magani guda daya. Rafi'ah ce kwance akan gadon dakin Ummi tana faman goge hawaye, tinda aka sallameta a asibiti jiya da daddare bata rintsa ba har yanzu, Mummy dake zaune gefenta ta ce "Allah dai ya isa wallahi, yaushe raban da ciwanki ya tashi haka sai bayan dawowar wannan yaran" tana rife bakinta Abba ya shigo Ummi na biye dashi, ya zauna bakin gado yana kallan Rafi'ah ya ce "So u didn't stop crying, u forgot all i told u ko?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "No Abba, just that i can't control my tears" Abba ya ce "Try and control it then" daga haka ya kalli Ummi ya ce "Zamu je meeting din da sukayi organizing karfe 10" Mummy ta ce "Meeting din me kuma? bayan gamu da marar lafiya a gida" Abba ya ce "Wannan ba dalili bane Halima, u have to attend" Mummy ta hade rai ta ce "Aini banga wani meeting da za'ai ba, bayan ya saketa ai magana ta kare meye kuma za'a ce sai mun kara haduwa duk tamu" Abba ya dafa Imaan dake kwance tana bacci ya ce "For the sake of her, ya kamata ace an saurari bayani daga bakinsa, tinda koma menene shine mahaifinta, bayan an gama meeting din komai sai ya biyo baya, but we can seperata him with his daughter" Mummy dai bata ce komai ba a wannan karan, Ummi ta ce "Allah ya kaimu, sai dai bamusan wajen ba" Abba ya ce "Munyi waya da Jawad, zaizo ya kaiku sun bada address" Ummi ta ce "Allah ya kaimu". Khairiyya na zaune a parlor tayi tagumi su Ammi suka shigo, tayi saurin dauke kanta daga kallan Yusuf hawaye ya fara zuba a idanta, ba abinda take tinawa sai ranar daya saki Rafi'ah, ta mike da sauri ta wuce dakinta tana kuka sosai, dakin Sameer Ammi ta rakashi ta hada masa ruwan wanka ta ce "Bari na hada maka breakfast kafin ka gama" ya ce "To nagode Ammi" daga haka ta fita, dakin Khairiyya ta shiga ta sameta kwance tana kuka kasa kasa, Ammi ta zauna bakin gado ta ce "Kukan ne bazaki daina ba har yanzu?" Tayi shiru kawai tana goge hawayen idanta, Ammi ta ce "Kije ki gaishe da Yayanku sannan ki wuce kitchen ki fara feremin dankali, i want to bath first, banajin dadin jikina" mikewa tayi a hankali tana hade rai ta fita a dakin, direct kitchen ta nufa ta farayin abinda akace, duk bayan miti daya sai ta tsaya ta share hawayen idanta kafin taci gaba. Kafin karfe goma sun gama shiryawa, Ummi ta gama shirya Imaan ta ce "Go and call ur Momma for me" Imaan ta tafi da gudu zuwa dakin Rafi'ah, a bakin gado ta sameta zaune ta gama shiryawa tasa hijabi, Imaan ta rungumeta ta ce "Ummi is calling u" Rafi'ah ta rungumeta itama ta ce "I'm coming" daga haka ta mike ta kama hannun Imaan suka fita a dakin, da sallama suka shiga dakin Ummi, bayan sun zauna Ummi ta ce "Ki kwantar da hankalinki kinji ko, babu abinda zai faru insha Allah, saki ne ya riga daya sake ki, babu sauran alakarki da shi" Rafi'ah ta ce "To" Ummi ta ce "Ina Anty Halima?" Ta ce "Ta sauka tin dazu, suna tare da Yaya ne" Ummi ta ce "Ohk" juyawa tayi ta fita a dakin Imaan tabi bayanta, tinda suke sakkowa a stairs Jawad yake kallanta, ita kuma taki bari su hada ido, ta dan tsaya bayan kujera ta ce "Good morning" daga haka ta nufi hanyar fita ya bita da kallo, Mummy ta ce "Ai wallahi yayi attempting kar6an yarinyar nan kotu zamu kaishi" Jawad ya mike yana gyaran hulan kansa ya ce "Is better" daga haka ya fice a parlorn, parking lot ya duba baiga Rafi'ah ba, ya zagaya backyard ya ganta a zaune ta kifa kanta da gwiwowinta, ya karasa inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "Dear" kin dago kanta tayi, ya ce "Tashi ki gani" taki dagowa, hannunsa yasa ya daga kanta dake kan cinyarta ya ce "Are u still crying?" Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, ya shafa bayanta cikin rarrashi ya ce "Calm down pls, ur heart beats too fast, taba kiji" daga haka ya dagata a jikinshi ya dora hannunta saitin heart dinta ya ce "Kinji" ta daga masa kai, ya ce "Then keep quite, insha Allah alkhairi kawai zakiji, ki daina jin tsoro" ta turo baki ta ce "Ni banasan ganinsa kuma" ya ce "To bazan bari ya kalle kiba, aike ce duk kika jawo mana, kikace ke karatu zakiyi ba aure ba, kinga da munyi auran mu a acikin babban rigana zan saka ki ba yadda zai kallan min ke" ta danyi murmushi tana kallan shigar da yayi ta ce "Ya maka kyau sosai" ya ce "Ko? Kema kinyi kyau, just that idan nan ya kumbura kinyi kuka sosai" ta ce "Kuma inajin bacci ma" ya ce "Don't worry idan mun dawo sai kiyi baccin" ta ce "To" mikewa yayi jin muryar Mummy a parking lot ya ce "Karfa kibi bayana, ki koma ta kitchen" daga haka ya bar wajen, ta danyi murmushi ta tashi ta koma ta kofar baya ta shiga cikin gidan sannan ta kara fitowa ta parlor, duk suna tsaye a parking lot, yayi reverse sannan suka shiga motar yaja suka wuce. Suna isa katoton guess house din Daddy Jawad yayi horn aka bude masa gate, babban gidane sosai amma ba kowa a ciki, Jawad yayi parking yana kallan motoci hudu dake pake a wajen, da alama dai su kadai ake jira kenan, bayan duk sun fito Imaan ta daga masa hannu alaman ya dauketa, ya dagata sama sannan ya sauketa kan shoulders dinsa suka shiga ciki, duk ilahirin mutanen na zaune a wakeken parlorn, suka shigo da sallama sannan suka zazzauna, caan gefe Rafi'ah ta samu ta zauna kanta a kasa bata bari koda wasa ta hada ido da mutanen parlorn ba, Yusuf ya sauke idansa daga kallan Imaan ya wani sauke ajiyar zuciya, godiya ga Allah yake cikin ransa daya bashi this cute girl, kowa ya ganta yasan shine mahaifinta, Daddy yayi sallama sannan ya bawa Yusuf damar magana akan ya fadi dalilinsa na sakin matarsa sannan meyasa ya tafi ya barta almost 4 years ba'a san inda yake ba, shiru duk mutanen parlorn sukayi suna kallan Yusuf da kansa ke kasa, Rafi'ah ce kawai bata yarda ta kara kallansa ba, Cikin cool voice dinsa yayi musu bayanin komai, tin daga ranar daya farajin tsanar Rafi'ah har ta kai ga ya saketa sannan ya kara da cewa tinda ya tafi Egypt bai kara tina taba sai ranar, duk mutanen parlorn jikinsu yayi sanyi sosai, Kawu Umar ya ce "Ninasan wannan aikin Fatima ne, wallahi zata iya yin komai dan dai ta rushe farincikin yaran nan, yanzu ina take ita da 'yartata" Yusuf ya ce "I don't know Kawu, tinda aka sallameni a asibiti ban sake ganinsu ba" Kawu ya ce "Baka da number dinsu ne?" Ya ce "Ina dashi, sai dai banbi ta kan wayar ba, ga dai ta nan a pocket dina" Kawu ya ce "Kira mana ita" Yusuf ya ciro wayar ya danna yana kallan screen din, 25 missed calls ya gani, ya duba yaga kiran Umma ne, cire wayar yayi a silent sannan yayi dialing phone dinta, Kawu Umaru dake kallansa ya ce "Kar kace mata kana gida" shi dai shiru yayi yana kallan phone din dake ringing, bayan Umma ta daga yasa a hands free, ta ce "Yusuf" ya ce "Na'am" ta ce "Kana ina?" Yayi shiru sannan ya ce "Ina hanyar zuwa kano" Umma ta fashe da kuka ta ce "Yusuf gamu nan a cell wallahi, mijin da Khadija ta aura shiyasa aka kama mu, bayan ya saketa yace sai an biyashi duk kudin daya kashe mata, to nidai ga ATM's dinka dukka a hannuna ba damar ciran kudi, yanzu abinda nakeso da kai ka wuto station din ka kar6i ATM card ka ciro kudi a biyasu muma duk mu huta" Yusuf ya ce "To gani nan zuwa, a wani station ne?" Ta ce "Na nan unguwar Rimi, kusa da first bank" ya ce "To in zuwa" daga haka yayi hanging call din, Abba ya sauke ajiyar zuciya ce "Then sai muje station din ko?" Yusuf ya ce "Ohk to" Abba ya mike yana kallan Ummi ya ce "Ku wuce gida, mu zamu je staion din, koma me ake ciki i will call u" Ummi ta ce "Alright safe" Juyawa Abba yayi yana kallan Jawad dake gyarawa Imaan gashin kanta ya ce "U follow us too barrister" Jawad ya ce "Ohk" duk mazan mikewa sukai suka fita, Yusuf ya sauke kansa kasa ya fita Mummy ta bishi da kallo, itama duk jikinta yayi sanyi, Jawad ya nufi kofar fita Imaan tabi bayansa da gudu kamar zatai kuka ta ce "Zan bika Daddy" daukanta yayi suka fita a parlorn, Ammi ta kalli Khairiyya ta ce "Kije Sameer ya baki key din motar karya manta ya tafi dashi" Khairiyya ta mike ta fita bayan ta amsa da to, ba jimawa ta dawo da keys guda biyu, ta mikawa Ummi daya ta ce "Yaya Jawad ne yace in kawo, wai ya tafi da Imaan tana kuka saita bishi" Ummi ta ce "Ohk" Ammi ta kalli Mummy dake zaune tayi shiru ta ce "Kuyi hakuri dan Allah Hajiya Halima, nasan abubuwan da suke faruwa akwai ciwo, amma ba wanda ya wuce kaddararsa, Allah ya kaddara hakan zai faru, kuma indai aka sameshi da laifi nayi alkawarin zan bada goyon baya a hukuntashi dai dai da abinda kotu ta yanke masa" Mummy ta ce "Allah ya mana me kyau, amma kuwa idan matar caan ne tayi sanadiyar wargaza mana zuri'a wallahi Allah ne kadai zai rabani da ita, me muka mata? Me muka tare mata a rayuwa Aisha? Meyasa zata sa yarannan cikin wani rayuwa?" Ummi ta ce "Allah ya rufa asiri" Ammi ta ce "Ameen" sannan ta mike ta ce "Zamu wuce mu kam" Ummi ta mike itama ta ce "To sai anjima" daga haka su Ammi suka fita, Mummy ta dago Rafi'ah dake kuka tin tini ta ce "Kiyi shiru Rafi'ah, insha Allah duk wanda yakesan yaga bayanki ba xai ci nasara ba" ta kama hannunta suka fita a parlorn Ummi tabi bayansu. Tafiyar minti 6 sukai ya kaisu station din saboda dama a unguwar ne, Jawad na rike da Imaan suka shiga ciki, shima har lokacin basu hada ido da Yusuf ba, direct office din DPO suka shiga, kawu Umaru ya masa bayanin komai, DPO ya musu bayanin dramar da akai lokacin da aka kamo Anty Khadija, shi dai Yusuf na gefe duk jikinsa yayi sanyi, lokaci lokaci yakan kalli Imaan dake hannun Jawad tana wasa da hular kansa, DPO ya ce "To yanzu dai yace court za'a tura su dan sai anyi musu shari'ah" Kawu ya ce "To muma akwai case din da muka kawo a kansu, ina ga zamu rubuta statement sai a hada rana daya" DPO ya ce "Ba matsala insha Allah" juyawa Yusuf yayi ya fita a office din yana kallan dan sandan dake tsaye bakin kofa ya ce "Dan Allah akwai wasu mata da aka kawo jiya, inasan ganinsu" dan sandan ya ce "Ko kaine wanda suka kira" ya ce "Ehh nine" dan sandan ya nuna masa inda suke sannan ya dawo bakin aikinsa, a hankali Yusuf ya karasa wajen ya leka, suna nan zaune aka kasa dauro duk yaci ubansu sai susa suke, Umma ta taso da sauri ta ce "Dan Albarka, ga ATM din guda 4 bansan dai da wanne za akai amfani ba" Yusuf bai kalleta ba ya ce "Ohk, zaku fita nan yau insha Allah Umma" daga haka ya kar6i ATM cards din ya yasa a pockets dinsa ya juya, Umma na murmushi ta kalli Khadija dake zaune ta ce "Aina gaya miki zaizo, amma me zaisa zan kira Umaru, banda wa'azi ba abinda zaizo ya mana a wajen nan, karshe ma yasa a kaimu kotun". bayan an gama rubuce~rubuce Jawad yayi signing ya kuma tura case din zuwa court dinsu, ba 6ata lokaci akai printing takarar yasa a pocket dinsa, Abba ya ce "Yanzu akwai wani abu kenan?" Ya ce "A'a, idan naje office zan karasa komai sai asa date din da za'a fara zaman" Abba ya ce "To Allah ya kaimu" Daddy ya kalli Yusuf dake zaune kan bench kansa a kasa ya ce "Are u alright" Yusuf ya ce "Sure Daddy" kiran da DPO yayi wa Jawad ne yasa ya mike ya fita, sai lokacin Yusuf ya bishi da kallo, Imaan dake jikin Abba ta 6ata fuska kamar zatai kuka, Yusuf ya mike yana kallanta ya ce "Come" ta mika masa hannu ya dauketa suka fita a office din Daddy ya bisu da ido, fita sukayi a station din ya tsaya a ATM machine yayi withdrawing 30k sannan yasa a pocket dinsa ya tari cab, bayan sun shiga ya ce "Old GRA" mai cab din ya ja suka tafi, a hankali Yusuf ya kalli Imaan da tai collapsing ajikinsa ta rungumeshi, ya rungumeta shima yayi kissing kanta ya ce "I luv u daughter" _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _14_ Dai~dai kofar gidansa me cab din yayi parking, ya fito rike da Imaan a hannunsa ya ciro 1k ya mika masa ya ce "Nagode" daga haka ya juya ya tura gate din mutumin ya bishi da kallo harya rufo kofar, entrance din gidan ya nufa ya bude kofar parlor, gidan yana nan yadda suka sameshi ya karasa part din Jiddah ya bude, ba kowa a ciki da alama ta tafi kenan, Imaan ta yatsine fuska tana kallansa ta ce "Why is your house very dirty Uncle?" Yusuf ya danyi murmushi yana kallan cute face dinta ya ce "We are leaving now sweetheart" daga haka ya wuce dakinsa ya bude, sauketa yayi akan bed side drawer tana ta yatsina fuska, ya ce "Wait for me here" daga haka ya daga katifar kan gadon ya dauko wata babban leda ya ajiye gefe sannan ya maida katifar, jikinsa duk ya baci da kura, ya dauki ledan ya karkade sannan ya shiga toilet ya kunna tap ya wanke hannunsa ya kade wandan jikinsa daya 6aci, bayan ya gama ya dauki Imaan dake tsaye uncomfortable a wajen ya sata a shoulder dinsa dayan hannunsa na rike da ledan suka fita, bayan sun fito a gidan ya jawo kofar parlorn suka fita gate, sauketa yayi ya ciro padlock din dake jikin kofar ya datse kofar, bayan haka ya dauketa suka fara tafiya a layin har suka iso bakin titi, ya tare mai Napeep ya ce "Hamdala hotel" mai Napeep din ya ce "400" Yusuf ya shiga ya daura Imaan a cinyarsa sannan ya ajiye ledan hannunsa, ta dago tana kallansa ta ce "Where are we going Uncle?" ya limshe ido yana shafa bayanta bai ce komai ba, tafiyar minti 30 sukayi dan wajen da nisa sannan akwai hold up, bayan ya tsaya Yusuf ya bashi 500 sannan ya dauko Imaan da ledan gefensa suka fito, hotel din suka shiga ya tsaya a reception suka fara gaisawa da mutumin wajen, bayan sun gama ya ce zai biya kudin daki ne, mutumin ya tambayeshi kwana nawa, ya ce "2 days" ya ce "U pay the some of 50k" Yusuf ya ciro ATM card dinsa ya mika masa, ba 6ata lokaci akai making payment ta POS, suka bashi key da room number, matar dake gefen Mutumin nata kallan Imaan, bayan ta fada masa sama zasu hau taja hancin Imaan ta ce "Like father like daughter" Yusuf ya danyi murmushi yana shafa kan Imaan suka bar wajen zuwa upstairs, dakinsu shine na biyu by the left, yasa key ya bude dakin suka shiga ya rufo kofar, komai neat dakin sai kamshi yake, ya sauke Imaan akan gadon yana kallan fuskarta ya ce "Are u sleepy?" Ta girgiza masa kai, daukanta ya sakeyi ya dan cillata sama ta fashe da dariya, ya sake cillata ta kara fashewa da dariya, ya rungumeta yana shafa bayanta suka fita a dakin ya rife sannan ya zare key din yasa a pocket dinsa, downstairs suka sauka suka fita a hotel din, wani babban boutique dake gefen hotel din suka shiga, ya sayi kaya set 2 sannan ya siyawa Imaan set 5 da takalmi biyu, bayan ya biya kudin suka fito suka shiga provision store, ya kalli Imaan dake bin shop din da kallo ya ce "Do u take cornflakes?" Ta daga masa kai ya ce "What of custard?" Ta ce "No, biscuit instead", cornflakes da biscuits, da kuma chocolate sai milk na sachet, bayan ya biya kudin suka fito suka koma cikin hotel din, sauketa yayi a bakin kofa ya bude dakin sannan ya shiga ta biyo bayansa, ya ajiye kayan akan gado ya rufe kofar da key sannan ya jefa shi saman wardrobe, phone dinsa ya ciro a pocket ya kashe duka duka sannan ya dora akan gado, kallan Imaan yayi dake kallansa tin dazu ya ce "What?" Kamar zatai kuka ta ce "My Daddy" yaja dan karamin tsaki ya wuce toilet yayi alwalan azahar sannan ya fito ya shimfida sallaya ya tada sallah, bayan ya idar yayi addu'a sannan ya juya ya kalli Imaan dake kwance saman gadon ta rufe ido, ya kura mata ido yana murmushi ya mike ya karasa gefenta ya kwanta shima. Murmushi kawai Jawad yayi bayan Abba ya fada masa Yusuf ne ya tafi da Imaan, bayan sun iso gida Jawad yayi horn Mustapha ya bude gate din suka shiga, bude kofar Abba yayi ya ce "Sannu da kokari Barrister" Jawad yayi kasa da kansa ya ce "Ba komai Abba" daga haka Abba ya fito, ganin zai juya Abba ya ce "Ba zaka shigo kayi lunch ba?" Ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya juya motar Abba ya shiga cikin gida, yana fita gate ya nufi gidan Ammi, bayan ya isa yayi parking a waje ya fito ya shiga cikin gidan rike da key din motarsa, a parking lot ya samu Sameer yana kokarin rife mota, Jawad ya karasa ya bashi hannu, Sameer ya ce "Ya kokari?" Ya ce "Alhamdulilah, Yusuf yana ciki ne?" Sameer ya ce "No, muma dawowanmu kenan Ammi tace basu dawo ba, kuma bama wanda yake da contact dinsa na yanzu bare a kirashi" with surprise Jawad ya tsaya yana kallan Sameer, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Yana tare da Imaan fa" Sameer ya ce "Eh, shiya dauketa tin a station, may b lokacin suka taho" Jawad ya ce "Amma ina kake tinanin zan ganshi?" Sameer ya ce "Sai dai ko gidansa, ko gidan Ummansu" Jawad yasa hannayensa cikin aljuhunsa ya ce "Dan Allah ka rakani mana" Sameer ya ce "Ba damuwa" daga haka suka fara tafiya zuwa gate, bayan sun fita Jawad ya bude lock din motar suka shiga ciki yaja suka tafi. ba jimawa Yusuf ya tashi daga baccin daya sace shi, ya zame Imaan dake kwance kan kirjinsa ya shiga toilet, bayan few minutes ya fito ya zauna bakin gado, ya dinga kallan Imaan dake baccinta hankali kwance, ya durkusa dai dai goshinta ya bata light kiss, knocking da akayi ne yasa ya mike ya dauko key ya bude kofar, matar ta mika masa babban tray me dauke da fried rice da kaza sai chips a gefe, ya kar6a tray din ya ce "Thank u" daga haka ya tura kofar, ajiye tray din yayi yasa key a kofar ya zare shi ya maida inda yake, yana zama Imaan ta bude ido, ya dagota yana murmushi ya ce "Dear" ta ce "I'm hungry Uncle" ya dagata suka shiga toilet ya wanke mata fuska da baki suka fito, tray din abincin ya dauko ya ajiye a gabansu sannan ya cire transparent ledan dake kan abincin yana kallan Imaan ya ce "Kina cin wannan?" Ta daga masa kai, ya danyi murmushi ya ce "So u speak Hausa?" ta ce "Eh, very well" ya ce "That's good" spoon ya dauka ya fara bata abincin a baki tana ci, ganin tafisan shinkafan ya daina bata chips din, sosai taci ta koshi, ya bata ruwa ta sha sannan yaja hancinta ya ce "Zaki sha tea" ta girgiza masa kai ta ce "When are we going back home Uncle?" Ya dan bude ido yana kallanta ya ce "Meyasa kike cemin Uncle?" Ta ce "Is because Ummi tace duk babba in ce mishi Uncle" ya wara ido yana kallanta ya ce "Really" ta ce "Yeah" rufe abincin yayi ya ajiye a gefe ya dagata suka koma kan gado ya ce "From now henceforth sunana Papa" ta juyo tana kallansa ta ce "Why?" ya ce "Because i'm ur Daddy" ta dan kalleshi sai kuma tayi dariya ta ce "No, my Daddy is at home" ya ce "Nine Daddynki daughter" daga haka ya dauko ledan dazu ya ciro babban album din bikinsu da Rafi'ah ya bude, first picture hotonsu ne su biyu, ta wara ido tana kallan picture din ta ce "My Mum" ya nuna hotonsa ya ce "And who is this?" Ta kalli picture din ta dago ta kalleshi sannan ta kara kallan picture din ta ce "It's you" ya danyi murmushi ya rungumeta ya ce "Don't call me Uncle again" ta ce "Papa?" Ya daga mata kai ya ce "Tashi muyi sallan la'asar dear" ta mike tana nade dogon hannun rigarta ya tsaya yana kallanta with passion. Rafi'ah ce zaune a dakin Ummi tana ta trying number Jawad, sauke ajiyar zuciya tayi jin ya shiga, bayan yayi picking ta ce "Sweetheart" ya ce "Yes sweetheart, ya kike?" Ta ce "Lafiya, har yanzu baku gama bane naga almost 4 yanzu" shiru yayi yana jinta, ta ce "Hello, are u there?" Ya ce "Yes, inajinki kikace mene?" Ta ce "Baka dawo da Imaan ba" Jawad yayi kasa da murya ya ce "Abba bai fada miki bane, yanzun nan muka gama waya" kallan phone din take kirjinta na bugawa ta maida wayar kunnenta ta ce "Ni banga Abba ba, may b yana apartment din Antynmu, Yana tare da ita kenan?" Ya ce "No, mahaifinta ya tafi da ita, naje gidansa baya nan, naje gidan Ummansu nan ma baya nan ba kuma ya gidansu Sameer" mikewa tayi jefar da wayar ta fasa ihu, Ummi ta shigo da sauri jin ihunta ta ce "Lafiya Rafi'ah?" Rafi'ah ta kankameta tana kuka ta ce "My Imaan Ummi, Doctor ya tafi min da ita, dan Allah Ummi ku kirashi ya bani diyata wallahi baxan bashi ita ba, nice komai nata a rayuwa Allah bazan yarda ba" Ummi ta janyeta a jikinta ta ce "Keep shut now" tayi shiru tana goge hawayen idanta da yaki tsayawa, Ummi ta ce "Waya fada miki?" Cikin kuka ta ce "Ya Jawad ne, wai Abba ma ya sani" daga haka ta fashe da kuka ta ce "Nidai amin adalci a bani yarinya na, naji zan yafe masa komai amma ni ya barmin Imaan dina" ta sulale nan bakin kofa tana rera kuka, Ummi ta juya ta fita a dakin. Shiru Mami tayi tana sauraron bayanin da Jawad yake mata, bayan ya gama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To duk inda yaje ai dole zai dawo da ita" Jawad ya limshe idanuwansa ya ce "Nasan zai dawo, but Fatima ba lallai ta fahimci hakan ba, gani ma zatai nine na bashi ita" Mami ta danyi murmushi ta ce "Kunfi kusa kuma wannan" ya dan shafa kansa yana murmushi ya mike ya ce "Is Mummy back?" Ta ce "A'a ai inaga yau ma kwana zatai" daga haka ya juya ya fita a parlorn. Ammi na zaune a parlornta tana tinanin ina Yusuf ya tafi da Imaan, Sameer ya dago yana kallanta ya ce "Duk munje inda kike tinani amma baya nan" Ammi ta ce "The only way to have his contact shine ka koma station kace a baka numbersa" Sameer ya ce "Numbersa kuma?" Ammi ta ce "Ehh shiyafi sauki, tinda akwai numbersa a wayansu Khadijan ai, tin karfe 12 har 4 saura babu labarinsu" Sameer ya mike ya ce "Ohk bari na kira Barrister sai muje tare" daga haka ya fita a parlorn, Khairiyya ta ta6e baki ta mike ta bar parlorn, har yanzu haushin Yusuf takeji har cikin ranta. Abbane ya shigo parlorn da sallama yana kallan Ummi dake zaune ya ce "Ina Rafi'an?" Ta ce "Tana sama" Abba ya zauna kan kujera ya ce "Let her come" Ummi ta mike ta haura stairs, tare da Mummy ta sameta a dakin, har lokacin kuma kuka take sosai, Ummi ta ce "Kizo Abbanki yana nemanki" ta mike a hankali tasa hijabi sannan ta fita, Mummy dai na zaune bata ce komai ba har lokacin, Ummi ta fita a dakin itama, a tare suka sakko kasa, Rafi'ah ta zauna akan carpet kanta a kasa ta ce "Gani Abba" ya ce "Meya saki kuka?" Tayi shiru tana wasa da hijabin jikinta tana sauke ajiyar zuciya, Abba ya ce "Your daughter right?" Ta daga masa kai ya ce "To menene abin damuwa bayan tana tare da mahifinta? I see nothing in it, dole zasu dawo ai, ba guduwa zaiyi da ita ba" hawayen idanta ta share ta ce "But Abba dan meyasa zai dauketa bayan baima san ya akai na haifeta ba, shidai ne mahaifita amma Abba bata samu kulawars ba, batama san shi ba" Abba dake kallanta ya ce "Yanzu ai zata san shi, pls let's stop all this drama, zai dawo miki da ita u cool ur mind" daga haka Abba ya mike yana kallan Ummi ya ce "Abdul ya kira bai sameki ba" ta ce "Ehh, dazu munyi waya" Abba ya bude kofar ya fice a parlorn, kuka me cin rai Rafi'ah ta fashe dashi ta kifa kanta akan kujera. _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _15_ *The page is dedicated to my Phiaa 🤗 thanks for d alawan madara* 💃🏻 Da daddare Yusuf na zaune a daki da Imaan a cinyarsa yana mata wasa, ta kalli wayarsa dake kan gado ta ce "I want to play game" shiru yayi yana kallanta, ta ce "Ohh sorry Papa u warn me not to ask again" murmushi Yusuf yayi ya kai fuskarta saman nata ya ce "I will give u sweetheart, but sai idan kinci abinci" cike da jin dadi ta ce "Yesss, zan ci" daga haka ta sauka akan gadon ta zauna a gaban tuwan da aka kawo musu, lafiyyen tuwo ne da vegetable soup, sai kamshi yake yaji cow meat da crayfish, duk da bata ci amma saboda yace zai bata game ta kar6a, ya dinga bata tana ci amma ba a san ranta ba, ta danci sosai sannan ta kauda kanta gefe ya ce "Kin koshi?" Ta daga masa kai ta ce "Yes Papa, yaji ne da yawa" bottle water ya dauko a gefensa ya bude ya zuba mata ruwan a cup sannan ya bata a baki ta sha, bayan ta koshi suka mike a tare ya kama hannunta suka shiga toilet, hannu ya wanke mata sannan yayi mata brush suka fito, ya dauko ledan kayan da siyo mata ya dauki kayan bacci da socks ya cire mata kayan jikinta sannan ya canza mata, kayan sunyi mata kyau sosai da sosai, mikewa yayi ya rage AC dakin saboda garin ma akwai sanyi, yana zama Imaan ta bashi phone dinsa ta ce "U promised" ya kar6a wayan ya bude bayanta ya cire sim card dinsa sannan ya maida marfin ya kunna wayan, akan bed side drawer ya ajiye sim card sin, bayan wayan ya kawo ya dan zaro ido tinawa da yayi babu games a wayan, kuma idan downloading zaiyi sai yayi amfani da sim card, kallan Imaan yayi data kura masa ido tana jira ya bata, ya sauke ajiyar zuciya ya kara bude bayan wayar ya maida sim card din sannan yayi restarting wayar, bayan ya kawo yana kunna data kira ya shigo wayar, kallan number ya dinga yi amma bai daga ba harta katse, aka sake kira for d second time, yayi picking call din ya kai kunnne amma baice komai ba, Ammi ta ce "Yusuf" da kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce "Na'am" ta ce "Fisabilillahi ka kyauta kenan, ka daga mana hankali kasa mun fara wani tinani da ban" silently ya ce "I'm sorry, this is the only way dazan jawo ta jikina na kuma ganta, zan dawo da ita insha Allah" Ammi ta danyi tsaki ta ce "Baka kyauta ba wallahi, Dazu danaje kuka Fatima take kamar Imaan tayi sati bata nan" ya dan ta6e baki ya ce "Kiyi hkr" Ammi ta ce "Yanzu ina Imaan din? Kuma kuna ina?" Ya ce "Gata nan, muna hotel" Ammi ta ce "To dama gobe da safe ka dawo da ita, ana kokarin a kashe wata wutar amma kana kara jawo mana magana haba Yusuf, yarinyar nan ba wanda xai rabaka da ita idan kayi hakuri, kowa yasan kaine ubanta menene na daga hankalinka haka" limshe idanuwansa yayi ya ce "Insha Allah zan dawo da ita gobe" Ammi ta ce "Kar kuma ka sake kashemin waya" ya ce "Ohk". Bayan yayi hanging call din ya juyo yana kallan Imaan dake wasa da gashin kansa ya ce "Wane game kike so" ta danyi murmushi ta ce "Anyone" cikin few minutes yayi mata downloading games guda 4, ya bata wayar yana rungume da ita, mamaki ta bashi ganin ko wane game ta iya perfect, ya kalli time sannan ya kar6a wayan ganin quarter to ten, juyo da ita yayi tana facing dinsa ya ce "Wane sura kike?" Ta ce "Al-Humaza" ya ce "Karanta min" ba musu ta kwanta akan kirjinshi ta fara da bismillah sannan ta karanta har karshe, yayi kissing forehead dinta ya ce "Idan kina karatu zan saya maki tablet" ta wara ido ta ce "Ina dashi ai" ya ce "Waya siya maki?" Ta ce "My Dad" Yusuf ya rungumeta ya ce "Zan siya maki Laptop i know u don't have it" ta ce "Irin na Momma?" Ya daga mata kai sannan ya ce "Kiyi addu'a ki kwanta i'm also sleepy" a hankali ta fara karanto ayatul qursiyyu sannan tayi addu'an bacci tayi nasi da falaq, ta kwanta a jikinsa ta ce "Good night Papa" ya ce "Night daughter" daga haka ta rufe ido, ba jimawa kuwa tayi bacci, zameta yayi a jikinsa ya mike ya nufi bakin window yana kallan motoci da mutanen dake kasa. Washegari Rafi'ah na dakinta ta fito a wanka kenan phone dinta ya fara haske, ta leka screen din ta dauke kai taci gaba da abinda take, shiryawa tayi cikin atampa doguwar riga sannan tasa hijabi ta dauki laptop dinta da side bag ta fita a dakin, dakin Ummi ta shiga ta sameta zaune ita da Mummy suna magana, ta sauke kanta kasa ta ce "Zan tafi Ummi" Ummi ta ce "Allah ya bada sa'a, ki kwantar da hankalinki kiyi exams dinki da kyau, nothing is going to happen Mamana" a hankali ta ce "Insha Allah" daga haka ta kalli Mummy ta ce "Kafin na dawo kin tafi ko?" Ta ce "Eh, Allah ya taimaka" ta ce "Ameen" sannan ta juya ta sauko downstairs, tana fita compound phone dinta yaci gaba da ringing, ta maida ta silent ta shiga mota Mustapha yaja suka tafi. Karfe takwas Imaan ta tashi a bacci, tayi mitsi mitsi da ido tana kallan Yusuf dake zaune akan kujera, a hankali ta ce "Papa" ya juyo yana kallanta sannan ya mike ya karasa inda take ya dagata ya ce "How are u daughter" ta ce "I'm fine" daukanta yayi suka shiga toilet, bayan 10 minutes ya fito da ita a dukunkune cikin towel, kan gado ya direta ya goge mata jiki sannan ya saka mata kaya, tayi kyau sosai da sosai, ta dan kalleshi ta ce "U didn't comb my hair" ya ce "I don't have comb here" ta dan turo baki zatai kuka ya rungumeta ya ce "Don't cry pls daughter, idan munje gida Ammi zata miki" jin ya fadi haka ta dan saki ranta sannan ta ce "Baka samin perfume ba" ya kalli kan mirror sannan ya dauka perfume din daya gani ya fesa mata sau daya ya ce "Saura breakfast" ta sauko akan gadon tana kallansa ta ce "U look so handsome Papa" ya danyi murmushi kawai yajawo breakfast din ya fara bata a baki, bayan ta gama ya hada mata tea shima ya bata a baki, sai daya tabbatar ta koshi sannan ya ajiye mug din a gefe yana kallanta ya ce "So ur name is Imaan" ta daga masa kai, baima san sunanta ba sai jiya da Ammi ta fada, ya dauketa suka koma kan gado ya ce "Me ake ce maki a school?" Ta ce "Fatima Yusuf Muhammad" ya dan bude ido cike da farinciki ya ce "Whose name are u bearing?" Ta ce "My grandmother, haka Momma tace min" limshe idanuwansa yayi ya ce "Which class are u" ta ce "Nursery 1" ya ce "Good, which school?" ta ce "Prime College" ya danyi murmushi kawai yana kallanta, juyawa yayi jin phone dinsa ta fara ringing, ya dauka ya kai kunne hade da sallama, Jiddah ta ce "I have been expecting your call since yesterday but u didn't" ya ce "Ina busy ne that's why" ta ce "To yaushe zamu dawo gidan mu?" ya ce "Saina gama abinda nake" ta dan hade rai ta ce "Amma kasan ba kudi a hannuna ga cikin dake jikina sai wahala nake" ya ce "Zan maki transfer i'm sorry, how are u now?" Ta ce "Lafiya, amma dai inasan na ganka" ya ce "Ohk, kizo Hamdala hotel, room 32" dan zare ido tayi ta ce "Hotel kuma Ya Yusuf, me kazo yi Hotel?" Yusuf ya ce "I don't like noise much Jiddah, idan b zaki zo ba ki zauna it isn't by force, xan miki transfer din" ta ce "To ina zuwa" yayi hanging call din yana kallan Imaan dake wasa da button din shirt dinsa. _45 mins ltr_ Knocking kofar dakin Jiddah tayi, Yusuf ya mike ya dauka key ya bude mata kofar, rungumeshi tayi ta ce "Shine ka gudo nan ka barni kuma..." shiru tayi ganin Imaan tsaye akan gado tana kallansu, nan da nan zuciyarta ya hau bugawa, Yusuf ya janyeta a jikinsa ya tura kofar sannan ya dawo gefen gado ya zauna, cike mamaki da takaraso inda suke ta ce "Who is she Doctor?" Yusuf ya kalli Imaan sannan ya kalleta ya ce "My daughter" daaaamm taji kirjinta ya buga, ya ce "Yarinyar da Fatima ta haifa bayan na tafi" Jiddah ta zaro ido tana kallan Imaan, ita da take takama tana da ciki zata haifa masa diya ko d'a sai gashi da yarinyar da ta kai shekara 3 yace mata 'yarsa ce, nata cikinfa watansa biyu kacal, durkusawa tayi hawaye na bin fuskarta ta ce "Anya Doctor kaika haifi wannan babbar yarinyar, baka tinanin sun makala maka ita ne dan su cimma burinsu" Yusuf ya mike yana kallanta ya ce "Look, don't pretend like baki ga kamana da yarinyar nan ba, duk inda na shiga da Imaan kowa ya kalleta yasan jinina ne" Jiddah ta mike tsaye ta nufi kofa ta fita ya bita da kallo, Yusuf ya juyo yana kallan Imaan dake bin kofar da kallo ta ce "Who is she?" ya ce "Ur Aunt" bata ce komai ba ta fara tsalle akan gadon tana wasanta, wayarsa ne ta fara ringing yayi picking ya kai kunne, ahankali ya ce "Ina kwana Ammi?" Ta ce "Lafiya kalau, ya baku dawo ba har karfe 10" ya ce "Yanzu insha Allah" ta ce "Bari Sameer yazo ya dauko ku" ya ce "To, muna Hamdala Hotel idan yazo ya kirani" Ammi ta ce "To" daga haka ta katse wayar. Within some Minutes Sameer yayi parking a kofar hotel din, yayi dialing phone din Yusuf ya ce "Naxo" Yusuf ya ce "I'm coming" kallan Imaan yayi dake kwance akan gado ya ce "Dear, we are going back home" ta mike ta ce "Ohk, are we going with Napeep" ya ce "No" durkusawa yayi ta dale bayansa sannan ya dauki babban ledan da kayansu suke ciki suka fita a dakin, yasa key ya kulle bayan sun sakko ya basu key din ya nufi kofar fita, a parking space suka samu Sameer na tsaye, Yusuf ya karasa gefensa ya bashi hannu ya ce "Ya gida" Sameer ya ce "Lafiya kalau" daga haka ya bude musu back seat Yusuf yasa kayan sannan ya rufe ya dawo front seat suka zauna, Imaan ta kalli Sameer ta ce "Good morning Uncle" yaja hancinta ya ce "How are u beauty?" Ta ce "Fine" daga haka ta kwanta jikin Yusuf, har suka je gida Yusuf na rungume da Imaan, Sameer yayi horn aka bude mishi gate ya shiga yayi parking, Imaan ta kalli motar Jawad dake parke a gefe ta ce "Daddy" Yusuf ya juyo ya kalleta sai kuma tayi murmushi ta ce "I saw his car" bai ce mata komai ba suka fito a motar, ya kama hannunta suka nufi cikin gida, Ammi ce da Khairiyya sai Jawad a parlorn, ya shiga hade da sallama yana kallan Ammi ya zauna gefenta ya ce "Ina kwana" ta ce "Lafiya kalau" Khairiyya ta dauke kai ganin sun hada ido, mikewa Yusuf yayi ya bawa Jawad hannu ya ce "Morning" Jawad ya ce "How are u" ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya sake Imaan ya wuce dakin Sameer, Imaan ta bi bayansa da gudu Jawad ya bisu da kallo, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Alright yanzu zan masa bayanin komai insha Allah" Jawad ya ce "Ohk ba damuwa" mikewa Ammi tayi tabi bayan Yusuf, Khairiyya ta mike zata wuce dakinta Jawad ya ce "Come here" tsayawa tayi sannan ta juyo tana kallansa sai kuma ta sauke kanta ta kara 2 steps ta dan matso, ya ce "Sit down" ta zauna akan kujera, Jawad ya ce "Why didn't u great him?" Ta hade rai ta dago tana kallansa ta ce "Who?" Murmushi Jawad yayi ya ce "Your brother" _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _16_ A hankali Khairiyya ta dago ta kalleshi kafin ta ce "Zan gaishesa idan na shiga" Jawad ya shafa beards dinsa yana kallanta ya ce "Promise" ta daga masa kai daga haka ta juya ta koma ciki. A kan gado Ammi ta sameshi ya dora Imaan a cinyarshi, ta zauna bakin gado tana kallansu ta ce "Gobe insha Allah zamu fara zama a kotu" yayi kasa da kansa yana rike da Imaan ya ce "Allah ya kaimu" shiru ne ya biyo baya sai karan game din da Imaan keyi in a low volume, Ammi ta sake kallansa ta ce "Yaushe zaka maida musu da yarinyar?" sai lokacin ya dago kansa ya kalle ta ya ce "Gobe insha Allah but..." Shiru yayi ya kara sauke kansa kasa, Ammi ta ce "But what?" Da kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya ce "They're giving me my daughter Ammi" murmushi ta danyi ta ce "Why? Meyasa baza ta zauna inda ta saba ba" ya limshe idanuwansa ya ce "Zamu koma gidana tare, i don't think zan iya zama babu ita" Ammi dake kallansa ta ce "All these years da kai spending baka nan kasan da ita ne? Kaga karka sake jawomin wani rigimar Yusuf, ka barta kawai ta xauna da mahaifiyarta, sai dai kuma idan ita da Fatiman zasu koma gidanka" da sauri ya juyo yana kallanta ya ce "I don't think so Ammi, ita din dai ita ce mallakina so i'm going with her no matter how" sauke ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce "Allah ya za6a mana abinda yafi alkhairi, that's all my wish" a hankali ya gyarawa Imaan zama a cinyarsa ya ce "Ameen" Ammi ta mike ta nufi hanyar fita ta ce "Bari a kawo maka abinci" daga haka ta fita ta rife masa kofar, dakin Khairiyya ta shiga ta sameta zaune akan gado tana danna waya, Ammi ta ce "Are u done with the food?" Ta ce "Yes" Ammi ta ce "Sai ki kaiwa Yayanku" hade rai tayi ta ce "Nafa daura akan dinning Ammi, kuma yanzu 7 minutes past 12 ai lokacin lunch bai yi ba" Ammi ta dalla mata harara ta ce "Ai inada hannu ba sai na kai masa ba" daga haka ta juya, da sauri Khairiyya ta sauko akan gadon tabi bayanta, a wajen dinning ta samu Ammi zata dauki warmer tayi saurin riketa ta ce "Pls Ammi ki kawo zan kai" Ammi ta mika mata ta ce "Rashin hankali ne banaso, ba sai nayi da kaina ba wani abu ne" dan 6ata rai tayi ta nufi dakin Sameer da Yusuf ke ciki, ciki ciki tayi sallama ta ajiye warmer din a kasa ta juya ta fito, ta dauki dan karamin warmer da miyar ke ciki sai cabbage da cucumber cikin wani dan bowl shima ta kai, sake fitowa tayi ta dauki serving spoon guda 2 da spoon sai table water da plate hade da cup, duk akan plate din ta dora sannan ta koma dakin ta ajiye masa, har ta juya zata fita ya ce "Khairi" ta hade rai ta juyo tana kallansa ya ce "I need to talk to u" dawowa tayi ta tsaya caan gefe, ya ce "Zoki zauna" ta dan kalleshi sannan ta wuce ta zauna ganin kallan daya ke mata, ya ce "Mena miki da bakya kulani, or do u think saboda kin girma yanzu sai ki daina gaishe da mutane" tayi saurin saukar da kanta kasa ta ce "No" ya ce "To menene?" nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa, ya ce "Idan ba zaki magana ba u can go" share hawayen daya gangaro mata tayi ta ce "I'm seeing what u did to Anty Fatima up till now, anytime i saw u, or i heard ur voice inajin ba dadi, that's why banasan na ganka, i feel hurt deep down me" kallanta kawai yake baice komai ba, caan ya sauke ajiyar xuciya ya ce "After mun gama da court i will apologize insha Allah" da sauri ta juyo ta ce "Bana tinanin zata yafe maka Yaya" ya ce "I don't care, as far as ba laifina bane babu abinda zai dameni, koba laifina i will still apologize saboda Imaan, after all zan kar6i yarinyana suje suyi auransu" Khairiyya ta sake kallansa ta ce "Ai an kusa dama, baifi 2 months ba" ya mike yana gyarawa Imaan zama ya ce "Allah ya sanya alkhairi" daga haka ya nufi toilet yana nade hannun rigarsa, juyowa yayi yana kallanta ya ce "Zanyi alwala ne" daga haka ta mike ta fita a dakin tana share sauran hawayenta. Karfe 1 Rafi'ah ta dawo daga exams dinta ta samu Mummy ta tafi, duk ji tayi babu dadi gidan, ta wuce dakinta tayi wanka tayi sallah sannan ta sauko downstairs, abincinma kansa kasa ci tayi, ganin phone dinta na haske yasa ta jawo wayar tana kallan screen din, da kamar bazata dauka ba sai kuma tayi picking tayi shiru, on the orther side Jawad yayi sallama cikin cool voice, dan ta6e baki tayi sannan ta amsa, ya ce "After 26 miseed calls sai yanzu kika dauki wayana" nan da nan idanta ya cika da hawaye, ya ce "Ina waje" ta share hawayen daya sakko mata da bayan hannunta ta ce "I'm coming" daga haka tayi hanging call din, mikewa tayi ta xura hijabi sannan ta fita a parlorn, tana fita gate ya bude back seat yana kallanta ya ce "Bismillah" kamar iska zata dagata ta karasa inda yake ya ce "U come in" daga haka ya matsa mata ta shigo ta rife kofar, rife fuskarta tayi da hijabin jikinta ta ce "Where is my daughter Barrister?" daga haka ta fashe da kuka, Jawad dake kallanta ya danyi murmushi ya ce "Is that what makes u not to pick my calls?" Bude fuskarta tayi hawaye na sakko mata ta ce "Ai is all your fault, ka bari ya tafimin da yarinyana" Ta karashe maganar tana turo baki, ya kamo hannunta cikin rarrashi ya ce "Is not my fault sweetheart, na barta wajen Abba ne bayan DPO yayi kirana, i don't know how he managed to go with her" ta fara bubbuga kafa with serious ta ce "Allah saiya bani Imaan dina, ai ba shiya haifamin ita ba, ko yasan wahalan dana sha na haifeta ne" daga haka ta kara fashewa da kuka, rungumeta Jawad yayi unexpected, ya bubbuga bayanta ya ce "U stop crying love, ki barta a wajenshi ki gama exams dinki peacefully" ta dago kanta a kirjinsa hawaye na sakko mata ta ce "Did u said peacefully?" Ya ce "Yes" ta ce "Ni rashin ganinta shine yake sani kuka inajin ba dadi, kuma ai naga gobe zan gama exams din" kallan lips dinta yake dake motsi a hankali kamar ba magana take ba, ya ce "Nasan gobe zaki gama, sai kuma ki bari idan an gama zaman court sai ya baki idan har ya yarda, kinsan shine yake da iko a kanta bake ba" kuka ta sake fashewa da shi ta ce "After all i gone through sabida shi, wallahi bazan yarda ba, da kaina zanje na dauko yarinya na" jin bakinshi kawai tayi akan lips dinta, tayi shiru zuciyarta na bugawa da karfi, da sauri taja baya tana kallansa ta ce "Ni banaso" ya danyi murmushi yana shafa gashinsa ya sauke kansa kasa, wani mungun kunyarta yaji lokaci daya, ta ce "Pls help me and get my daughter back" jin yayi shiru ta kifa kanta jikin kujera tana share idanta ta ce "Pls Barrister i can't do without her, bata da mahaifin daya wuce kai wallahi, nina baka Imaan har abada" sai a lokacin ya dan kalleta yayi murmushi ya ce "Kin ta6a ganin anyi kyautar diya da ubanta?" Ta turo baki ta ce "Ni dai na baka" hannunta duka biyu ya kamo yana kallan cute face dinta data 6aci da hawaye ya ce "Let him go with her Fatima, wallahi court shi zata bawa yarinyar nan, sai dai kuma idan ta sameshi da wani hali wanda zai iya 6ata tarbiyyar Imaan, shine kadai abinda zaisa a baki ita" kwace hannayenta tayi ta fara rera kuka, ya matso gefenta ya bata light side hug ya ce "Bakya sona kenan?" Ta dago da sauri tana kallansa zuciyarta na bugawa, ya ce "Idan kina sona to ki yarda mu bashi Imaan, i promise u 2 weeks after our weeding zamu samo baby" ta dan wara ido tana kallansa saam bata manta da hawalan da tasha a cikin Imaan ba, ta maida kanta gefe, ya ce "Are u with me love, ko bakya so?" ta kara kauda kanta gefe bata ce komai ba, Jawad ya ce "Karfe nawa gobe zaki gama exams din?" Ta ce "12" ya ce "Alright zan dauko ki and we are going straight to the court" ta juyo tana kallansa kamar xata kara fashewa da kuka ta ce "I'm scared Barrister, banasan kallan Doctor again" murmushinsa me kyau yayi ya ce "Ba sai ki kauda kanki ba" ya kara kamo hannunta cikin rarrashi ya ce "Don't be scared Fatima, inaso ki zama barrister kema, idan kina tsoro ai bazaki iya ba" ta sauke kanta kasa ta zame hannunta a hankali ta ce "Ohk, kuma bazan dawo gida ba" ya ce "Ehh, kafin ki gama kowa yaje" ta dan 6ata fuska ta ce "My Imaan" ya ce "Goben zaki ganta ai" ta share dan guntun hawayenta ta ce "Kuma bata da kaya ko daya ma" Jawad ya kashe mata ido daya ya ce "Zai siya mata ai" ta turo baki ta bude kofar motar zata fita ta ce "Zaka zo da daddare?" Ya ce "Sure, insha Allah" ta danyi murmushi bayan ta fita ta ce "Kuma kayi kyau sosai" daga haka ta rife fuskarta ta juya ta shige gida ya bita da kallo yana murmushi, fitowa yayi a back seat ya koma gaba ya kunna motar ya bar layin. Anty Amina ce zaune a parlorn gidansu ta buga uban tagumi, Anty Rahama ta kalleta da kyau ta ce "Ba zakije gidan Ikleeman ba?" Anty Amina ta girgiza kai ta ce "Bazanje ba" Anty Rahama ta saki baki tana kallanta ta ce "Zaki kashe kanki fa Amina, kawai daga ji Yusuf ya dawo kin bi kin daga hankalinki, ni wallahi Jawad dinma shiri nake na kada shi yace ya fasa" Anty Amina ta juyo tana kallanta ta ce "Ai tinda ya dawo nasan asirin Khadija ya karye, kuma ni bani da numbernta bare na kirata, ni tinda Ya Muhammad yace min Yusuf ya dawo naji ba dadi, kuma bansan meyasa ba da fargaba nake kwana, karfa asirinmu ya toni Anty" Anty Rahama ta ta6e baki ta ce "To sai me? Ai wallahi ko kama su akayi tace dasa hannunmu koda rantsuwa sai mun kwaci kanmu, tinda dama sun nuna basanmu suke ba, kinga ko munce karya suke yarda za'a yi" Anty Amina ta ce "Kuma hakane, Amma jikina yana bani wani abu yana faruwa, tin bayan dawowar Abban Rafi'ah da nace zanzo gida ya barni, kinga yau kwanana 3 baice na koma ba, sai waya, kuma innace akwai abinda yake faruwa sai yace babu, abun daya fadamin shine Rafi'ah ba lafiya kuma Yusuf ya dawo" Umma dake kwance tana jinsu tayi murmushi ta ce "Yoo dama dole tayi ciwo mana, balle ma ga ciwan da yake daminta ai dole ya tashi idan taga bawan Allah nan, ki dai kwantar da hankalinki a gama komai caan ki koma gidan mijinki" Anty Rahama ta ce "Ai bazan bari tayi auran jin dadi ba, wallahi koda ta auri Jawad dinma sai ta fito, saina san yadda nayi ta kara fitowa" Anty Amina tayi murmushi kawai tana danna wayarta. _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _17_ Washegari karfe 8 Ammi ta gama breakfast ta dora akan dinning, dakin Yusuf ta shiga ta sameshi a tsaye ya goyi Imaan suna xagaye dakin, suna hada ido da Ammi ya sauke kansa kasa silently ya ce "Good morning" Ammi ta karasa shigowa dakin tana kallansu ta ce "How was your night?" Ya ce "Fine" Ammi ta kalli Imaan dake bacci a bayan Yusuf ta ce "Ai ta koma baccin ka kwantar da ita mana" murmushi kawai Yusuf yayi bai dai bari sun hada ido ba, Ammi ta ce "To ga breakfast a parlor kasan 11 ya kamata mu tafi court din" ya ce "Alright" Ammi na fita ya sauke Imaan a bayansa ya rungumeta, bude idanuwanta tayi a hankali tana kallansa, ya gyara mata gashinta daya sakko fuskarta ya ce "Sweetheart" ta ce "Papa" ya kara rumgumeta ya ce "Na goya ki har kin sake bacci" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Thank u" hannunta ya kama suka shiga toilet ya wanke mata baki da fuska sannan suka fita a dakin, a parlor suka sami Khairiyya tana zaune, ta juyo tana kallan Yusuf ta ce "Ina kwana" a takaice ya ce "Lafiya" bayan ya zauna ya daura Imaan a cinyarsa yayi serving dinsu. Cikin 10 minutes suka gama breakfast, Yusuf ya mike yana kallan Khairiyya ya ce "Ki mata wanka" ba tare data kalleshi ba ta ce "To sanda kuke hotel waya ke wankanta?" Dago kansa yayi yana kallanta ta mike a hankali ta kama hannun Imaan suka shiga ciki, yayi nodding kansa ya ce "I will surely deal with u" yana zama akan kujera Ammi ta fito a daki, ya ce "Zanje gidana" ta ce "Me za kai kuma?" Ya ce "Zan sa a gyaramin ne" Ammi ta tsaya kallansa ta ce "Why not after everything?" Ya dan shafa kansa ya ce "Ammi inasan na koma can ne" a hankali ta ce "To, sai kayi kokari ka dawo kafin time din yayi" ya mike ya ce "Insha Allah" daga haka ya nufi daki ya dauko key din gidan ya futo, dakin Nabeel ya shiga ya samu Sameer na kwance yana bacci, ya duba kan mirror ya samu key din motarsa ya dauka sannan ya fita, yana fita compound din gidan ya wuce parking lot yayi warming motar sannan yaja ya bar gidan. Cikin minti 10 ya isa gidansa yayi parking a waje sannan ya fito yasa key ya bude padlock din ya shiga ciki, bayan few minutes ya fito ya rife gidan sannan yaja motar ya bar layin, ba jimawa ya dawo da wasu samari su 2, suka fito a motar bayan ya bude gate din suka bi bayansa, bude musu kofar parlor yayi ya nuna musu broom da mop sannan yasa face mask dinsa ya bude part din Jiddah suka bishi a baya, yana tsaye bakin kofa suka gyara dakin tass sukai mopping, baza kace shine ya hada wannan kuran ba, rufo dakin yayi suka fara gyaran parlor, yana nan tsaye bakin kofa yana kallansu, da sauri yasa hannu a pocket dinsa ya ciro phone dinsa dake ringing, ya daga ya kai kunne hade da sallama, Jiddah ta ce "Naga kudin yau da safe, amma dai kasan ba zai isheni ba ko" limshe idanuwansa yayi ya ce "I will call u ltr, ina wani abu ne" daga haka yayi hanging wayar. Cikin 30 minutes suka gyara gidan, har part din Rafi'ah daba komai a ciki saida suka share sukai mopping, bayan sun gama suka fito tsakar gida suka hau sharewa yaja kofar parlorn ya rufe, cikin few minutes suka share tass suka fitar da sharan, Yusuf ya basu 4k yana musu godiya, suka masa sallama suna masa godiya suma suka fita, padlock yasa ya rife gate din sannan ya shiga motar ya dau hanyar gidan Ammi. Bayan yayi horn aka bude gate din ya shiga yayi parking, ya fito ya nufi entrance din gidan, da sauri Imaan ta fito a parlor fuskarta da hawaye ta nufeshi, ya dagata yana kallan idanta ya ce "I'm back sweetheart" cikin muryar kuka ta ce "You ran away Papa" ya shafa bayanta ya ce "I didn't dear, ba gashi na dawo ba" ta danyi murmushi tana kallansa ya shiga share mata idanta, suna shiga parlor Ammi ta ce "Tin dazu take mana kuka" Yusuf yayi murmushi yana kallan Ammi ya ce "Na dawo ai" daga haka ya ajiyeta akan kujera ya ce "Wait for me here" ya shige daki ya barta anan wajen zaune. Cikin kankanin lokaci suka shirya zuwa court, Daddy da Ammi da kuma Khairiyya a mota Yusuf kuma da Sameer sai Imaan, sai da suka biya suka dauko Jiddah a gidansu sannan suka wuce court din, sai kumbura take tana hararan Imaan, kuma tayi alwashin saita tonawa Umma asiri ta wulakanta, suna zuwa Jawad ya kaisu har inda zasu zauna, babban court ne sosai, ba kowa a kan stage din saboda kowa shirye shirye yake, ba jimawa su Mummy suka zo, Yusuf ya karasa har inda suka suka gaisa sannan su Ummi suka taso suka gaisawa da Ammi, karfe 11 da rabi Jawad ya dauki motarsa yayi school din su Rafi'ah, kafin ya karasa har sun fito a exams dinsu, bayan ya isa yayi parking ya fito yana kallanta, juyawa tayi da sauri jin alamar motsi, ta sakar masa murmushi tana kallan kayan jikinsa ta ce "Woow Barrister, kaga yadda kayi kyau, kayan ya maka kyau sosai" yau ne ranar farko data fara ganinsa da kayan sai dai kuma a hoto, ya ce "Thank u sweetheart, muje Fatima we don't have much time" daga haka suka shiga motar yayi reverse suka fita. Within 10 minutes suka iso court din an gama komai Rafi'ah kawai ake jira, tinda suka fara shiga zuciyarta ya hau bugawa kuma ta dauki alkawarin yau sai ta kar6i Imaan dinta, ta sunkuyar da kanta dan karma ta hada ido da Yusuf, Imaan ne ta dan wara ido ta ce "Papa here is my Mom" ta karashe maganar tana nuna masa Rafi'ah data zauna dan nesa dasu taki kallansu, sau daya ya kalleta ya dauke kai, Jiddah ta dallawa Imaan harara hakan yasa tayi shiru ta kwanta akan kirjin Yusuf, signing Jawad yayi sannan ya mikawa na gefensa takardar shima yayi signing, bayan haka Alkali ya bada unarnin a shigo dasu Umma, ba jimawa aka shigo dasu duk sunyi baki, Anty Khadija ta gwalalo ido ganin mutanen dake zazzaune, aka wuce dasu aka kullesu a inda aka tanada dan masu laifi irinsu, bayan komai ya kammala kotu ta bada dan brief na abinda ta sani akan su Umma, Alhaji Usman shima da iyalansa na zaune gefe guda, bayan haka Kotu ta bada dama Yusuf yayi introducing kansa da kuma takaitattcen labarinsa, da kyar Sameer ya rike Imaan dake ihu saita bishi, bayan ya karasa wajen yayi sallama cikin sanyi murya ya fara bada tarihin rayuwarsa daki daki har zuwa yanzu, bai rage koya kara komai ba akan abinda ya faru, harya gama kuwa Rafi'ah bata kalleshi ba kanta na kasa idanta ya cika da kwalla, bayan ya zauna ita ce next da aka kira itama ta taso duk jikinta yayi weak, Jawad da shine zai mata tambayoyi ya dan kashe mata ido daya, silently ya ce "feel free" ta shiga wajen ta tsaya kanta a kasa, itama cikin sanyin murya ta fada musu labarinta tin haduwarta da Yusuf har auransu da kuma rabuwarsu da yadda tasha wahala kan cikin Imaan har aka mata CS, tana kaiwa nan ta tsaya ta share idanta, sai lokacin Yusuf ya kalleta na seconds sannan ya dauke kai. A sanyaye ta koma ta zauna bayan an sallameta, daga nan aka kira Jiddah, dama Allah Allah take a kirata, babu 6ata lokaci ta tashi ta tafi Rafi'ah ta bita da kallo, tana shiga wajen ta fadi alakarta da Yusuf a takaice sannan ta danyi murmushi, hada ido sukai da Umma dake ta kifkifta mata ido amma tayi kamar bata ganta ba, Jiddah ta dan yatsina fuska tana kallanta ta fara bayani kamar haka "Wannan matar dake tsaye ita da 'yarta su suka jefani hanya karkatacciya, kuma su sukai sanadiyyar raba auran Yusuf da waccen yarinyar Rafi'ah, su suka san yadda sukai suka shiga suka fita yaji ba abinda ya tsana a rayuwarsa sama da ita" Jiddah ta danyi murmushi tana kallan Anty Khadija ta ce "Bazan manta ba, shekara 4 da suka wuce Khadija tazo gidana tace in hada mana kayanmu zamu bar kasar sun gama shirya komai, bayanta tafi Umma ta kira Yusuf ta umarce shi daya saki Rafi'ah, shi kuwa ganin a lokacin ba wacce yake jin maganarta sama da ita yayi abinda tace, kamar yadda ya fada ya tafi ya barta tana laulayin wannan yarinyar, a ranar da muka sauka a Egypt wani bawan Allah wai dan ajin su Umma yazo ya taremu ya kaimu masauki, ba mufi sati ba da taimakaonsa Yusuf ya samu aiki, ana haka ana haka duk bayan wata daya sai Umma ta turawa bokanta kudi saboda ya sake dora aikin karna baya ya warware, sannan ya kafa musu sharadi na cewa sai Khadija taje wajensa a shekara sau daya ya sadu da ita, to dai sau biyu ya faru ana ukun suka ki zuwa, duk karshen shekara muna dawowa Nigeria mu sauka a Kaduna amma Yusuf bai ta6a budar baki yace ina Rafi'ah ba, komai kuma normal yake amma cikin ransa ji yake babu mutanen daya keso sama damu, Kwatsam wata sati 3 da suka wuce Alhaji Usman ya saki Khadija, ana haka a karshen shekaran nan Yusuf ya fara ciwo sosai, harta kaiga baya iya magana, ganin haka yasa Umma ta tattaro mu muka dawo Kaduna, anan kuma muka fuskanci tinanin Rafi'ah ya dawo masa yayinda ya fara kiran sunanta, shine Umma ta tura Khadija da tazo wajen bokan ta bashi kudade danya maida mata aikin sabo kuma ta bashi hakuri akan batazo wajensa ya kwana da ita ba, to anan ne na samu labarin an kama ta, yayinda asirin Alhaji Usman ya bar jikinsa shima" tinda Jiddah ta fara magana Yusuf kansa na kasa sai data dasa aya hawayen idansa ya gangaro, nan da nan ya fara furta innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Jawad ya kalli Jiddah dake tsaye ya ce "Amma meyasa all this while da abubuwan suka faru baki zo kin sanar da kanwar mahaifiyarsa ba" Jiddah tayi kasa da kanta ta ce "Saboda nima ina sanshi, matukar nayi niyyar tona asirinsu zasu rabani dashi" Jawad dake kallanta ya girgiza kai ya kara ce wa "To yanzu wane dalili ne yasa ki kai magana?" A hankali ta ce "Saboda naga suna hannun hukuma kuma sannan tayi fatan Yusuf ya mutu saboda bata da asara, saboda taga ni nake dauke dauke da cikinsa, hakan yasa har mukai fada ta mareni nima na rama" with shock duk mutanen wajen suka tsaya kallan Jiddah, Abba ya girgiza kai ya maida kansa gefe yana addu'a kasa kasa, gaba daya tausayin Rafi'ah yakeji, lokaci daya suka canza mata rayuwa tin tanada karanci shekaru har zuwa yanzu, ita dai Rafi'ah ta kifa kanta akan kujerar wajen tana kuka sosai. Wani abokin aikin Jawad ne ya mike yayi rubutu a wata farar takardar sannan ya mikawa na kusa dashi ya ce "Zaki iya tafiya" Jiddah ta fito a wajen ta koma ta zauna, Yusuf dai na zaune kansa a kasa shima, tsabar bakin ciki kasa kuka sosai yayi, Jawad ya kalli Umma dake tsaye gefen Anty Khadija ya ce "Hajiya Fatima kin daiji abinda matar Yusuf tace, ko a maganganunta akwai abinda baki yarda kun aikata ba?" Umma tayi wulli wulli da ido ta rasa abin cewa, sai kuma ta ce "To idan tone tone ne ba sai ayi ba, aiba mu kadai mukai wannan aikin ba akwai wasu wanda suka bamu gudumawa kusan ma nasu yafi yawa" ganin abinda Alkali yayi yasa Jawad ya sauke kansa kasa irin yadda sukeyi alamar girmamawa sannan ya karasa wajen Alkali ya kar6i takardar hannunsa, duk sauran lawyers din wajen mikewa sukai suma, Jawad ya ce "Kotu ta daga shari'ah nan zuwa jibi wato 9 ga watan 9" police din dake gefe suka kara tasa keyar su Umma da hannunsu na daure da handcuffs suka wuce dasu. Mikewa Yusuf yayi ya saba Imaan a kafadarsa suka fita, Rafi'ah ta dago kanta ta kalli direction din da yake zaune taga bayanin, mikewa tayi da sauri ganin su Mummy na magana da Ammi, Abba yana gaisawa Daddy, fitowa tayi daga court din ta tsaya a compound tana kallan motocin dake parke a wajen amma bata gansu ba, hakan yasa ta nufi gate da sauri ta fita, tana fitowa a gate taga Napeep dinsu ya tashi, tayi saurin taran wani Napeep din ta shiga ta ce "Dan Allah wannan Napeep din zaka bi" daga haka ta gaya masa number Napeep din. A kofar gidansa aka sauke shi, ya bashi kudinsa sannan ya ajiye Imaan a kasa ya zaro key din gidan ya bude padlock din, daga haka ya tura gate din ya dauki Imaan suka shiga, da sauri Rafi'ah ta sakko a Napeep dinta ta bashi 500 ta juya da sauri ta shiga gidan, Yusuf ya juyo jin an bude gate din, da mamaki yake kallanta sai dai bace komai ba, hawaye na sauka a idanta ta ce "Nazo na tafi da Imaan, baka da wani dalili da zaka rabani da yarinyana" Yusuf ya mata wani kallo ya ce "I'm her Father, so u let me idan na yanke shawara zan baki ita from now till tomorrow" cikin tsawa ta ce "Stop saying u are her father Doctor, u don't know anything about her, idan ma akwai wanda ya dace ta kirashi mahaifi to Yaya ne" a hankali ya gyarawa Imaan zama a hannunsa ya ce "Tinda shiya miki cikinta sai kice masa yazo ya kar6a miki ita, and get out in my house now" daga haka ya juya ya bude kofar parlor ya shiga ya rufo kofar yasa sakata, yana zama wasu hawaye masu zafi suka sakko masa, bubbuga kofar da Rafi'ah keyi ne yasa ya mike ya share hawayen idansa ya bude kofar yana kallanta da jajayen idanuwansa cikin 6acin rai ya ce "What do u want then? get out and stop knocking my door before i show u the bad side of me" ya karashe maganar ransa a 6ace yana nuna mata hanyar gate. *DEDICATED TO MY GROUP MEMBERS ❣️* _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _18_ Kuka sosai ta fashe da shi tana kallansa, ya juya ya shiga zai rufo kofar tayi saurin tarewa ta ce "Pls don't do this to me Doctor, meyasa zaka rabani da farincikina, nina riga na yafe maka ka bani Baby na mu tafi for God sake" ta bude kofar ta shiga cikin parlorn ta dauki Imaan zata fita ya tare kofar, share hawayen idanta tayi ta ce "Let me go out pls" Yusuf yadan kalleta kafin ya ce "Idan kinaso ki fita ki ajiyemin daughter na" ta masa wani mungun kallo cikin tsawa ta ce "Stop calling her your daughter, she is not, wallahi kaiba mahaifinta bane, gara na bawa wani caan da bansan da shi ba, baka da wani maraba da mutumin da yayi raping mace baisan ta samu cik..." Wanka mata mari Yusuf yayi tayi saurin dafe wajen ta durkusa a kasa, ganin haka yasa Imaan ma ta fashe da kuka ta rungume mahaifiyarta, limshe idanuwansa yayi hawayen dake makale a idansa suka zubo, gaba daya ya rasa me yake masa dadi, maganar da Jiddah ta fada zaiji dashi ko kuma rashin hankalin da Rafi'ah ke masa, mikewa tayi ta gyarawa Imaan zama a jikinta ta ce "Wallahi saina tafi da ita, i'm going with her no matter how, ka matsamin na fita" ta karashe maganar tana kuka sosai, juyawa yayi yasa sakata a kofar sannan ya fisge Imaan a hannunta ya ajiyeta gefe yana kallanta ya ce "Idan kinasan tafiya kije ke dai" tayi kan Imaan zata dauketa ya fisgota ta fado jikinshi, daga ta yayi ta fasa ihu ya shiga da ita part din Jiddah ya ajiyeta akan kujera, yana jin Imaan na kuka haka ya rufe kofar yana kallan Rafi'ah dake kuka ya zauna gefenta ya ce "Sai ki fadamin abubuwan da kika mata yanzu yanzu na biyaki ki fita min a gida" ta dalla masa harara tana ci gaba da kuka, mikewa yayi yasa hannayensa a pocket dinsa ba tare daya kalleta ya fara magana cikin cool voice dinsa kamar haka "I thought you heard all what Jidda said, kinga ba laifina bane, su suka sa na tsaneki naji banasan rayuwa dake, nayi tinanin idan kikaji abinda ya faru kece mutum ta farko da zaki tausayin, kinsan yadda nake sanki more than anyone else, i can't betrayed u for no reason Fatima, nace maki ki bari gobe zan kai miki ita but u followed me and start shouting at me kamar wanda na miki sata, ko sata na miki ba zaki hakura da tsawan kimin magana a nutse ba, shekara nawa na baki a duniya Fatima? do i deserve such things, wane irin soyayyane ban miki ba kafin a shiga tsakaninmu? Or do u think i'm just pretending ba sanki nake ba?" Shiru yayi yana kallan yadda take kuka, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "And u are trying to said bani da maraba da wanda yayi raping mace baisan ta samu ciki ba, how do u call this a rape? nasan akwai wahala laulayin ciki da kuma haihuwa, but this doesn't mean ki zauna kina fadamin maganganu marasa dadi akan yarinyar dana haifa, at first ur Mum slapped me, she insulted me and she called me munafiki macicu azzalumi ta kara da cewa na cucesu Allah ya isa sannan na fita muku a gida kafin ta min illa, this words touch my heart more than u know" limshe jajayen idanuwansa yayi ya ce "Anywhere ki yafe min duk abinda na miki, it wasn't intentional na kuma gode maki with this cute Baby, Idan a zaman da mukai akwai abinda na miki bakiji dadi ba u pls forgive me, zan baki Imaan amma ba yanzu ba kamar yadda na fada miki a farko" bude idanuwansa yayi ya bude kofar parlorn ya fito, Imaan na kwance saman kujera harta fara bacci ya dagata ya goge mata hawayen idanta sannan ya sa6a ta a kafada suka shiga ciki, Rafi'ah na zaune a parlorn har lokacin tana goge hawayen idanta, ya wuce da Imaan daki ya kwantar da ita akan gadon sannan ya zauna bakin gado har yanzu mamakin Umma yake ba kadan ba, yasan bata kaunarsa amma baiyi tinanin zasu wargaza masa rayuwa irin haka ba, ajiyar zuciya ya sauke ya share hawayen daya gangaro a idansa. Kusan minti 10 Rafi'ah na zaune a parlorn, ta mike jikinta duk a sanyaye ta fito a parlorn ta bude kofar main parlor tasa shoes dinta ta fita a gidan, har ta isa bakin titi hawaye yaki tsaya mata, ta tare Napeep ta fada masa inda zai kaita, tana shiga kuma ta fashe da kuka sosai. Within 14 minutes suka iso gida, Mustapha dake zaune a kofar gida yayi saurin mikewa ganinta ya ce "Hajiya nata cikiyarki Rafi'ah" a hankali ta ce "Ka bashi kudinsa" daga haka ta shige ciki, tana bude kofar parlor suka hada ido da Ummi, tayi saurin sunkuyar da kanta Ummi ta ce "Daga ina kike, kinsa inata tambayar makwabta bakya nan, Mummy ma ta tafi caan gidanta bakya nan phone dinki kuma is off" a hankali ta ce "Naje gidansu Ameera ne, phone din kuma na motar Yaya" Ummi ta dinga kallanta kafin ta ce "Ohk, wuce ki rifemin kofa" tura kofar tayi ta wuce upstairs tana share idanta, tana shiga dakinta kuwa ta zube a tsakiyar gadon ta fashe da kuka. Ajiyar ziciya Mummy ta sauke bayan tayi hanging call din, ta kalli Jawad dake zaune gefenta ta ce "Ta koma gida yanzu, wai gidan su kawarta taje" Mami dake zaune gefe itama ta ce "To masha Allah" Mummy ta kara kallan Jawad dake zaune ta ce "Gaskiya mutanen nan sun cucemu wallahi, sun wargaza mana farincikinmu lokaci daya, ni yanzu wallahi kunyar hada ido da Yusuf nake irin abinda na masa ranar, kuma kaga yau ma har zuwa yayi ya gaishe mu, nidai dama zuciyata ne kawai a kusa na zazzageshi wallahi da nasan haka ne babu ruwana, dama ai baiyi kama da macuta ba, ga kunya da ladabi, Allah yasa dai ya yafemin" Jawad ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Irin cases din nan Mummy basu da iyaka, suna faruwa sosai, wani sai sihirin ya karye zakiga ya dawo, wani ma har abada ya tafi kenan shari'a kuma sai anje gaban Allah, to akwai matar da da kanta tayiwa diyarta asiri saboda wasu bukatu nata na duniya, so irin abubuwan na faruwa" Mami dai na zaune tayi shiru, ita kanta lamarin mamaki yake bata, Mummy tayi tagumi ta ce "Allah ya kara karemu, shiyasa ba'aso mutum ya shagala baya addu'a, at least ko abin ya sameka zaizo da sauki" Mami ta ce "Hakane kam Allah yasa mu dace" Jawad ya ce "Ameen" mikewa yayi ya nufi dakinsa ya ce "Sadeeq bai dawo ba?" Mami ta ce "Ya dawo, Kawu ne ya kirashi" ya ce "Ohk" daga haka ya shige ciki. Mikewa Yusuf yayi yana kallan agogon dake manne jikin bango sannan ya kalli Khairiyya dake cin fried rice cikin take away ya ce "Do fast dear" zama yayi akan kujera ya jirata ta gama sannan ya wanke mata baki suka fita a parlorn ya rife bayan sun fita gate ma ya datse da gwado, daukanta yayi suka karasa bakin titi suka hau Napeep zuwa gidan Ammi, After 10 minutes suka iso gidan, ya biya mai Napeep din sannan suka shiga ciki, Sameer ne kadai zaune a balcony yana waya, ya dan kauda wayar a kunnensa ya ce "Ka dawo" Yusuf ya ce "Ehh" daga haka suka shiga cikin gidan, Ammi ta dago kanta jin an bude kofar, Yusuf ya danyi kasa da kansa ya zauna ya ce "Sannu da gida Ammi" ta ce "Yauwa, ina kukaje haka?" Ya ce "Gidana" ta ce "Ohk, yaushe zaka maida musu Imaan ne?" Kallan Imaan yayi dake kwance ajikinsa ya ce "Idan an gama komai" ta ce "To dazu dai nacewa Umminta suyi hakuri zata dawo" kai kawai ya gyada mata, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Sannan abinda nakeso da kai shine karka saka komai a ranka, insha Allah duk wanda yake da hannu a lalacewar rayuwarka sai sun girbi abinda suka shuka, kaci gaba da addu'a insha Allah soon komai zai zama tarihi" a hankali ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya ajiye Imaan kusa da Ammi ya ce "Inasan hutawa ne" Ammi ta ce "Kana shan magani kuwa?" Ya ce "Ehh" Ammi ta ce "To Allah ya kara lafiya" daga haka ta shafa kan Imaan ta ce "Kinsha tea ne" ta daga mata kai ta ce "Since morning". Da daddare Jawad yayi parking kofar gidan Ummi, ya fito a motar ya nufi inda suka saba zama ya zauna akan daya daga cikin kujerun wajen, bayan sun gama gaisawa da Mustapha ya ce "Dan yi mata magana" Mustapha ya ce "To" sannan ya juya, bayan 10 minutes ya hangota ta tana tahowa da hijabinta har kasa, ya maida phone dinsa cikin aljihu yana kallanta harta karaso ta zauna a gefensa, ya ce "Ya kike?" A hankali ta ce "Alhamdulilah" ya ce "Dazu kuma sai kika tafi" ta danyi shiru tana wasa da fingers dinta ta ce "Ehh naje gidansu Ameera ne" ya ce "To meyasa baki bari kun dawo dasu Ummi ba" ta dan turo baki tana kallansa ta ce "Na gaji da zama ne kuma naga sunata magana" Jawad ya girgiza kai yana kallanta ya ce "This is not strictly true, kin daibi Yusuf ne ko?" Ta dago tana kallansa ta ce "Who told u ni ban bisa ba" ya danyi murmushi ya ce "Nayi karya kenan" ta ce "Ni bance maka ba" ya ce "To meyasa zaki bishi, bayan kinsan zai baki diyarki" ta dan hararshi bata ce komai ba, ya mika mata wayarta da side bag dinta sannan ya mike ya ce "Zan koma" ta ce "Bakaci abinci ba" ya ce "Na koshi, good night" daga haka ya bar wajen. *I'm much better today thanks for the care 🥰* _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _19_ Ranar Saturday karfe karfe 11 kowa ya iso kotu, kamar jiya yauma Yusuf sai daya je ya gaishe dasu Ummi, can gefe ya samu ya zauna yasa Imaan a cinyarsa, Rafi'ah dai na zaune ta turo baki fuskarta ko walwala babu, sau daya ya kalleta ya dauke kai, ba 6ata lokaci aka taso keyar su Umma aka kaisu inda aka tanada musu, bayan an gama komai Alkali yayi sallama ya kuma sanar da kowa cewa yau ne ranar da sukayi alkawarin cigaba da wannan shari'ah, bayan haka duk lawyers wajen suka mike tsaye kafin suka zauna, wani lawyer ne ya tashi yana kallan Umma da idanuwanta sukayi pulu pulu ya ce "Hajiya Fatima ta gamsu da laifin da tai ta kuma kar6a ba tare data bawa kotu wahala ba, sai dai a wancen zaman ta ambaci akwai wasu wanda suma dasa hannunsu" jin haka yasa Anty Amina tayi wuru wuru dama da kyar Abba yasa ta tazo, kuma ita ta titsiyeshi cewar saiya fadamata koma menene yake faruwa ita batasan boye boye, lokaci daya kuma tsoro duk ya cikata kana kallanta kasan she was uncomfortable then, Umma dake kallan kowa na court din ta ce "Hakane kam, akwai mataimaka a harkar da yawa" ya ce "To muna sauraronki Hajiya" tayi shiru sai kuma ta ce "Akwai kishiyar uwar Rafi'ah wato Amina da kuma yayarta Rahama, suma ba irin fadi tashin da bazasuyi ba don su hana wannan aure amma a karshe aure ya yiwu, kuma dasa hannunsu ta fito a gidanta" With much shock kowa na court din yake kallan Umma da kuma Anty Amina, Abba dai jin abin yake kamar a drama, Anty Amina ta mike cikin fishi da borin kunya ta ce "Ki rasa wacce zakiwa sharri sai ni Haiiya Fatima, wallahi karya take ina ruwana da yarinyar da zan mata asiri auranta ya kare, naga dai Rafi'ah koba aure tsakanina da ubanta 'yatace" ta karashe maganar tana nuna Umma da yatsa, wani ritaccen tsawa daya daga cikin manyan lawyers din yayi mata, with much serious ya ce "Malama nan fa ba filin dambe ne, idan baki nutsu ba muna da maganin irinku" hakan yasa tayi guum da bakinta ta zauna, Abba dai ya kasa cewa komai sai kansa daya dafe, lawyer din yana kallan su Umma ya ce "To akwai shaida da zai nuna mana suna da hannu cikin wannan laifin?" Anty Khadija ta ce "Ehh akwai a wayata" nan Alkali ya bada umarnin a bata waya ta nuna shaidar, handcuff din hannunta aka cire aka bata wayar, ba 6ata lokaci muryar Anty Amina ya bayyana cikin wayar lokacin da Anty Khadija taje mata, da kuma irin abinda takeso ya faru a rayuwar Rafi'ah, bayan ya kare Anty Khadija tasa wani sanda suka fara zuwa wajen bokan, ga muryarta nan radau kanaji tana bayani, mikewa Abba yayi ya hau kikkifa mata mari yana cankinta, Daddy da wani police suka rikeshi, nan itama aka saka mata handcuff akayi wajen su Umma da ita, sai kuka take tana sharrin shaidan ne, kukan Rafi'ah yafi na kowa kara a wajen, Ummi dai banda share hawaye ba abinda take, haka Mummy ma, shidai Yusuf na zaune kamar an dasa shi a wajen, duk Jawad ma jikinsa yayi mungun sanyi, rubuce rubucen da yake sai na gefensa ya bawa, lawyer din ya kalli Anty Amina dake kuka ya ce "Ke kuma menene dalilinki na yin hakan? Meyasa kika za6i ki raba ma'aurata" cikin kuka Anty Amina ta ce "Wallahi kishi nakeyi, ina bakincikin naga sun karu da wani abu, nafiso kullum na gansu cikin wahala, kuma gashi ni ban haihu ba kusan shekara 7 kenan yanzu, ko 6ari ban ta6a yiba, kuma ba irin magungunan da uwata bata bani ina sha amma shiru ba labari" Lawyer ya danyi murmushi ya ce "Yanzu kenan kun amsa laifinku a hannu" Anty Khadija na hawaye ta daga masa kai, bayan haka Alkali yayi rubuce rubuce ya mikawa wani daga gefe, mikewa mutumin yayi ya ce "Kotu tayi alkawarin kamo sauran masu laifin kamar yadda aka zayyana, sannan zatai musu hukunci dai dai da abinda suka aikata nan da sati daya, sannan kotu ta kar6arwa Yusuf Muhammad duk wani dukiyarsa dake hannun uwar rikonsa haka zalika zasu ci gaba da zama gidan horo har ranar da za'a yanke musu hukunci" kuka me karfi Anty Amina ta saki tana kallan Anty Khadija ta ce "Kin cuceni Khadija, duk ke kikazo kika kara rikirkita al'amuran, da baki zo ba nasan da bankai ga haka ba, wayyo Allah Ummana naga ta kaina" tasa keyarsu akai police suka fita dasu, Rafi'ah ta mike da sauri tayi wajen Abbanta ganin har rikeshi ake zai daki Anty Amina da zasu wuce, rungumeshi tayi ta fashe da kuka ta ce "Abbana" Abba ya rungumeta yana share hawayen idansa da suka ki tsayawa, tinda yake bai ta6a shiga kunci da tashin hankali irin na yau ba, Ammi ta dinga share idanta tana rike da hannun Yusuf daya kasa motsi sai hawaye dake gangarowa idansa, mikewa yayi a hankali ya nufi kofar fita da baya ma kallan gabansa sai duhu kuma idanuwansa a bude suke, basu ankara ba kawai sukaji yayi collapsing a kasa, Ammi ta mike da sauri tana jijjigashi hade da kiran sunansa, Sameer yayi kansu yana masa addu'a ganin ko motsi baya yi, kuka Imaan ta saki tana rike da hannunsa tana fadin "Papa wake up" da taimakon mutanen wajen aka fita dashi aka sakashi a mota, jin Rafi'ah tayi shiru yasa Abba ya dagota a jikinshi, a razane yake kallanta ganin suma tayi lokaci daya, ya dagata kamar Baby yana jijjigata suka fita da ita. _7 hours ltr_ Dawowansu kenan a asibiti bayan an sallamosu, Ammi na hada masa tea yana kwance akan 3 seater duk idanuwansa sun juya launi zuwa jaa sosai, ya limshe idanuwansa yana kallan Ammi ya ce "I want to bath first" Ammi ta ce "Ka sha tea din mana sai kasha magani, kuma alluran ma ai bai gama bin jikinka ba, da dai ka bari zuwa karfe 9pm sai kayi wankan" kai kawai ya gyada mata ya tashi ya zauna, ta mika masa tea din ya kar6a ya rike a hannu, Ammi ta zauna gefensa ta ce "Ka sha mana" a dole ya kai tea din bakinsa dan bashida appetite, da kyar ya sha kadan ya ajiye mug din kan center table ya koma ya kwanta, Ammi ta kamo hannunsa tana masa nasiha hade da kwantar masa da hankali. Washegari karfe 10am Rafi'ah ta fito a dakin Ummi bayan tayi wanka, ita kam jikinta da sauki sosai, sai ciwan ai kadan kadan, jikinta duk a sanyaye ta karasa parlorn da Abba ke zaune Ummi na gefensa, ta dayan side din kuma Mummy ce zaune taci kuka harta godewa Allah, a hankali Rafi'ah ta kalli Abba dake zaune yayi shiru, idanuwansa sun kada sosai, bata ta6a ganin Abbanta cikin tashin hankaki iri haka ba, murya caan kasa ta ce "Ina kwana Abba" ya dan kalleta cike da damuwa ya ce "How are u daughter?" Ta ce "Fine" Rafi'ah ta gaishe dasu Ummi ta zauna a wajen, kukan Imaan da sukaji a daki yasa Ummi ta mike ta shiga dakin, wanka ta mata tayi brush sannan ta shiryata suka fito, Ummi ta kalli Rafi'ah dake gefen Abba ta ce "Kije kiyi breakfast mana" mikewa tayi a hankali Ummi ta mika mata Imaan suka wuce. karfe 11 Abba ya ce "Suje su duba jikin Yusuf dan an maidashi asibiti ana kara masa jini" duk jikinsu yayi sanyi musamman Rafi'ah da idan ta tuna rashin kunyar data masa jiya sai kuka yazo mata, key din mota Abba ya dauka duk suka bi bayansa dama ko wacce da hijabinta, har suka isa clinic din baifi sau 3 sukai magana ba shima Imaan ne duk tayi causing, Bayan Abba yayi parking suka fito suka shiga ciki, Daddy ne da wasu 'yan uwan mahaifin Yusuf da suka iso da safe su 3, bayan sun gaisa Daddy yace su shiga ciki, a kwance suka sameshi yana bacci ana kara masa jini, gaba daya ya gama ramewa sai haske daya kara sosai, Ummi dai juyawa tayi ta fita, Mummy ta masa addu'ah itama ta juya, Imaan nata kallansa a tsorace sai dai ba tai magana ba, bayan few minutes Abba ya fita dakin ya rage daga shi sai Rafi'ah sai kuma Imaan, Hawayen idanta ta share ganin ko numfashi da kyau baya yi, taja kujera ta zauna a gefen gadon, bude ido yayi jin karan kujeran, suna hada ido ya maida kansa gefe hawaye na gangaro masa, daurewa tayi ta ce "How are u" da kyar ya daga mata kai, Imaan ta kalli Rafi'a dake kuka a hankali ta ce "Momma is Papa sick?" Juyawa Yusuf yayi ya kamo hannunta ya ce "But i recovered dear, i missed u yesterday" dan murmushi tayi ta ce "I missed u too" mikewa Rafi'ah tayi ta fita a dakin har lokacin kuka yaki tsaya mata. Har dare Yusuf yana asibitin, Ummi ta koma gida tayi dinner ta kawo musu, Mummy dai na tare da Ammi, sai Sameer da Rafi'ah, su Abba kam tintini sun koma da Ummi, tindaya farka da safe ya koma bacci bai sake tashi ba, jininma daya kare suka kara saka masa wani, karfe 9 Ammi da Mummy suka tafi salla, Sameer ma tinda ya fita sallan Isha bai dawo ba, Rafi'ah na zaune ta buga uban tagumi ta kuma yi nisa a duniyar tinanin data tafi, jin tarin da yayi yasa ta mike ta karasa kusa dashi, ta ce "Sannu" ya ce "Uhm" zama tayi a akan kujerar dake gefen gadon, silently ta ce "How are u feeling now?" Ya ce "Alhamdulilah" ta share dan guntun hawayenta ta ce "I'm sorry with what happened yesterday, i shouted at u which is not fair dan Allah ka yafemin" Yusuf ya mike da kyar ya zauna ya jingina da bango yana kallanta ya ce "Ba komai ya wuce, and u forgive me too, i cause too much pain in ur life" a hankali ta girgiza kai ta ce "They did but not u" shiru yayi yana kallan hannunsa daya kumbura saboda neman vains, a hankali ya ce "Imaan fa?" ta ce "Sun tafi gida da Ummina" ya ce "Ohk" juyowa yayi suka hada ido tayi saurin sauke nata idon, ya ce "Bani ruwa" ta mike a sanyaye ta nufi Fridge din dakin ta dauko bottle water sannan ta wanke cup din ta xuba masa, zama tayi a bakin gadon har ta kai cup din bakinsa sai kuma ta mika masa a dayan hannun, ya kar6a ya sha kadan sannan ya mika mata ta ajiye a gefe, komawa tayi gefe ta zauna kanta a kasa, Yusuf ya dan kalleta ya ce "Did u forgive me?" Da sauri ta kalleshi sai kuma ta daga masa kai tana share hawayen idanta ta ce "Yes i did, Allah ya yafe mana gaba daya" ya ce "Ameen" bude kofar dakin akai wani Dr ya shigo, suka gaisa da Yusuf ya masa ya jiki, ganin hannunsa ya kumbura ya ce "Bari a canza maka hannun ya huta" daga haka ya kashe ya maida masa dayan hannun sannan ya kunna yana masa sannu, daga haka ya fita a dakin, sun kai minti 5 a zaune kowa da abinda yake sakawa cikin ransa, ya dan kalleta ya ce "Pls help me with some water" ta mike ta dauko ruwan dazu ta mika masa, yana kar6a hannunsa yayi kasa cup din zai fadi tayi saurin rikewa, sai lokacin ta tuna hannunsa da ciwo, kamar baza tai ba kuma ta kai cup din bakinsa tana bashi ruwan, hakan yasa ta kauda kanta gefe bata bari sun hada ido ba, bude kofar dakin akai Jawad ya shigo rike da babban leda a hannunsa me dauke da fruits kala kala, yayi saurin dauke kansa ganinsu a haka, itama da sauri ta zare cup din a bakinsa ta ajiye a gefe kanta a kasa, Jawad ya karaso cikin dakin yana kallanta ya ce... _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _20_ Jawad ya karaso cikin dakin yana kallanta ya ce "Ya gama shan ruwan ne?" Ba tare data kalleshi ba ta daga masa kai, Ya ajiye ledan hannunsa yana kallan Yusuf ya ce "How are feeling now?" Yusuf ya ce "Alhamdulilah" Jawad yaja kujera ya zauna ya ce "Allah ya sauwake" ya ce "Ameen" zaro wayarsa a pocket yayi yana dannawa, kusan minti 10 suna zaune kafin ya mike yana kallan Rafi'ah ya ce "Ina Imaan?" ta ce "Tana gida" bude kofar dakin akayi Ammi da Mummy suka shigo, Jawad dake kallansu yayi murmushi suka sake gaisawa da Ammi ya ce "Ya mai jiki?" Ta ce "Da sauki sannu da kokari, Allah ya maka albarka" Sameer ne ya shigo dakin rike da ledan Apple, Mummy ta ce "Jawad muje ko?" Ya ce "Ohk to" kallan Yusuf yayi ya ce "Allah ya sauwake" Yusuf ya amsa da "Ameen" daga haka ya fita, Mummy ta ce "Hajiya sai gobe Allah ya yaye masa" Ammi ta ce "Ameen, Allah ya kaimu" mikewa Rafi'ah tayi tana kallan Ammi ta ce "Allah ya sauwake Ammi" ta ce "Ameen, mungode" ta gefen ido ta kalli Yusuf ta ce "Sai da safe" bata jira ya amsa ba ta fice a dakin Mummy tabi bayanta, a parking space suka sami Jawad yana zaune a mota, Rafi'ah ta shiga front seat Mummy kuma ta shiga baya, kallan Mummy yayi ta mirror ya ce "Yau kam gida zan kaiki ko?" Mummy ta ce "Aa sai gobe zan koma, danma jikin Rafi'ah da sauki" ya danyi murmushi yaja motar suka tafi ya ce "Mami tace ai yau zatazo duba Fatima nace bata gida" Mummy ta ce "Gobe idan ka kawota sai mu koma, shi dai Sadeeq bazai shiga mutane ayi komai dashi ba, kullum yana wajen abokai suna yawan banza" Jawad ya ce "Day before yesterday ma Mummy sai dana masa magana, bayasan shiga mutane saam" Mummy ta ta6e baki ta ce "To watakila zai daina, kai naka ada ai saida mukaita rokon Allah, gara shima yana shiga abokai" Jawad ya shafa kansa yana murmushi, ita dai Rafi'ah tana zaune tayi shiru, bayan 10 minutes suka karasa gida, Jawad yayi parking a waje Mummy ta fito ta ce "To saida safe" daga haka ta shiga ciki, kamo hannun Rafi'ah yayi cikin sanyin murya ya ce "Dear kinyi shiru" ta danyi murmushi ta ce "Ba komai" sai kuma ta sauke kanta kasa, ya gyara mata hijab din jikinta ya ce "Ohk, kici abinci sosai, sai ki kwanta" a hankali ta ce "Pls kayi hkr abinda nayi dazu, naga hannunsa da ciwo ne kuma..." Duk da baiji dadin abinda ya gani ba amma ya danyi murmushi ya daura Finger dinsa akan lips dinta ya ce "U don't have to explain, ba komai" murmushi ta sakar masa ta bude kofar zata fita ya ce "Good night" ta daga masa hannu ta rife kofar sannan ta shiga ciki. Washegari karfe 12 Yusuf na zaune akan gadon asibiti yana lunch Khairiyya ta fito a toilet, ta zauna gefenshi ta ce "Ya jikin Yaya?" ya ce "Lafiya lou" ta ce "Baka jin komai?" Ya ce "Naji sauki" dan murmushi tayi tana kallansa ta ce "Yaya Nabeel ya kusan dawowa, tare zamu koma inji Daddy, in fara makaranta shi kuma yana Masters dinsa" Yusuf dake jujjuya abincin hannunsa da spoon ya ce "Ina din?" Ta ce "America mana" girgiza kai yayi ya ce "No, ba dai keba, dan bazaki jeba" ta ce "But Daddy yace idan inaso inje fa Yaya" ya ce "Ki bari ki nema admission anan, i think it will be good for u, it's not safe mace karama irinki ta tafi wata kasa karatu" dan 6ata rai tayi ta ce "To ai angama bada admission Yaya" ya ce "Then u wait till next year" bata daice komai ba ta mike ta fara diban abinci tana hade rai. Kwanciya Imaan tayi saman carpet taki kar6an Apple din da Rafi'ah ke mika mata, Rafi'ah ta zare mata ido ta ce "Will u collect it like this or no?" kamar zatai kuka ta noke kafada ta ce "That's not how Papa used to gave me" cikin fishi Rafi'ah ta bar wajen ta shige dakinta, Imaan ta fashe da kuka tana shamba kafa hade da kiran Papa, Abbane ya fito a daki ya dauketa yana jijjigata ya ce "Me aka miki haka little Fatee?" cikin kuka ta ce "I want to eat Apple" Abba ya dauki daya daga cikin Apples din kan plate ya bata taki kar6a, ya ce "Ba kyaso ne kuma?" Ta dan turo baki ta ce "Daddynah yana yankamin ai, not that Daddy with Blue car, the fair one" sai kuma ta kara 6ata fuska ta ce "And he was sick" dakin Rafi'ah Abba ya bude ya sameta kwance tana waya, tayi saurin mikewa ganinsa, ya ce "Jeki yanka mata ki bata, ya za'ai ki barta kuma tana kuka mamana?" Hannun Imaan ta kama kamar zata fashe da kuka ta ce "To Abba sai tace ita sai abinda takeso, tin dazu nake mata hidima kamar wata baiwa" Ummi da shigowanta dakin kenan ta dalla mata harara ta ce "To karkiyi idan kinga dama, nan kika kafa mana kuka sanda ubanta ya dauketa, yanzu common ki yayyanka mata Apple zakice kina mata hidima, ai ke ba'a miki ba da kina karama girma kawai kikai" daga haka ta kama hannun Imaan dake share idanta, Abba ya ce "To menene abin fada anan kuma Madam?" Ummi ta ce "Saita zauna ai idan taga dama ta shekara tana kwance" daga haka ta fita da Imaan, Abba ya kalli Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "Are u happy with what u did?" Ta girgiza masa kai, ya ce "Ki daure kina mata abinda takeso kinji mamana, ke kinsan irin rigimar da kikai ne?" Ta danyi murmushi ta boye fuskarta da head tie dinta, Abba yayi saki murmushi ya nufi kofar fita ya ce "Allah ya miki albarka". Karfe 1:30 Mami tazo ta duba Rafi'ah, ta kawo mata fruits iri da kala, sun jima suna hira da Ummi kafin Sadeeq yazo ya dauketa, karfe 3 Ummi ta gama shirya basket din asibiti, Rafi'ah ta fito sanye da hijab tana kallan Ummi ta ce "Ke baza kije ba?" Ummi ta ce "Naga da safe naje, kuma munyi waya da Ammin tace may ba a sallamosu yau da daddare" Rafi'ah ta ce "Ohk" Ummi ta ce "Zaki tafi da Imaan ko?" ta wani hade rai tana kallan Ummi ta ce "Gaskiya ni zata takuramin Ummi, naga itama dazu da ita kikaje, yanzu mafa da kyar na samu na bata wayana kafin tayi shiru" Ummi ta ta6e baki taci gaba da kwashe abinci a warmer, Rafi'ah ta dauki basket din ta ce "Saina dawo" Ummi ta ce "A dawo lpy" daga haka ta fita zuwa parking lot Mustapha yaja suka bar gidan. Within few minutes suka iso asibitin, Mustapha yayi parking sannan ta fito ta shiga ciki, da sallama ta tura kofar dakin ta shiga, Sameer ya dago kai yana kallanta sannan ya amsa, Yusuf na kwance akan gadon yana kallan ceiling, by now babu komai a hannunsa jininma ya kare, ya mike a hankali ya zauna yana kallanta, sauke idanta tayi ta ajiye basket din a gefe ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya kalau" ta ce "Ya jikin?" Ya ce "Da sauki" kallan Sameer tayi dake danna wayarsa ta gaishe shi ya amsa mata da fara'ah ta ce "Ammi fa?" Ya ce "Basu jima ba suka koma gida ba ita da Khairi" ta ce "Ayyah" shiru tayi ta zauna caan gefe, wayar Yusuf dake gefenta ne ya fara ringing, ta kalli screen din sannan ta dauke kai, harya katse shima Yusuf baibi ta kan wayar ba, aka sake kira for d second time Rafi'ah ta ta6e baki ta kara kauda kai, Yusuf ya bude idanuwansa dake limshe yana kallan wayar ya ce "Pls help me with the phone" ta dauki wayar ta mika masa sannan ta koma kan kujeran ta zauna, a hankali yayi picking call din ya ce "Jiddah" ta fashe masa kuka ta ce "Wai meyasa baka kula dani ne Doctor, ko bakasan abinda ke cikina ne? u just left us aside kamar bamu da hakki akan ka" Yusuf ya ce "Banajin dadi we will talk ltr or tomorrow" daga haka ya katse wayar ya kashe phone din baki daya, mikewa Sameer yayi yana kallansa ya ce "Bari naje waje na huta Doctor" Yusuf ya ce "Ba komai, a huta lpy" daga haka Sameer ya fita, kusan minti 2 basuce komai ba, kowa yana zaune inda yake, Yusuf ya sauko a kan bed yana gyara zaman rigarsa ya nufi toilet a hankali, gaba daya jikinsa yayi weak, yana isa bakin kofar yayi saurin riko handle din jin zai fadi, Rafi'ah ta ce "Subhanallah" hannu ya daga mata alamar ba komai sannan ya shiga toilet din ya rufo kofar, bayan few minutes ya fito a toilet din, still dai he's not normal wani jiri yaji ya debeshi, Rafi'ah tayi saurin rikoshi ya fada jikinta, sai da sukai kamar zasu fadi sannan yayi karfin hali ya riko kujera suka fadi a nan wajen, bude kofar Jawad yayi ya shigo da sallama, Rafi'ah rayi saurin janye jikinta daga nasa ta matsa gefe, karasowa Jawad yayi yana kallan Yusuf ya ce "Are u ok?" Yusuf ya daga masa kai ya ce "U pls help me to my bed" Jawad ya kamashi ya mike sannan suka karasa kan gadon ya zauna, Rafi'ah na zaune kan kujeran kanta a kasa, kirjinta banda bugawa babu abinda yake, Jawad ya zauna a kan karamar kujera dake gefen bed din ya ce "Amma ya jikin?" Yusuf ya ce "Da sauki" Jawad ya ce "Masha Allah, yau an gama kama duk wani wanda yake da hannu a tafiyarka, sannan takaddun filayenka da gidajenka na wajen Umma yana office dina, dukda bincike ya nuna akwai abubuwa da dama da suka siyar, gobe insha Allah zan kawo maka takardun, abinda sukai amfani dashi ko suka siyar ka barsu da Allah, that's your own destiny in life, Allah kuma ya kara tsaremu daga sharrin masu hali irinsu, and i wish u quick recovery" sauke ajiyar zuciya Yusuf yayi ya kamo hannun Jawad dake gefensa ya ce "I don't know the words i will used to thank u Barrister, u have been there for me right from the beginning till end, jazakallahi khairan, u made so much to me which i can never pays u back, ka zamo gatan yarinyana a lokacin da take neman soyayyar mahaifi, ka bata gata wanda ko a wajena inaga da wuya ta samu kamarsa, u are a real man Ahmad, abinda ya faru a baya ka yafemin" Murmushi Jawad yayi me kyau yana kallansa ya ce "Allah ya yafe mana baki daya" Yusuf ya ce "Ameen" mikewa Jawad yayi ya basa hannu ya ce "Allah ya sauwake sai goben" daga haka ya nufi hanyar fita, yana fita Rafi'ah tabi bayansa da sauri, a parking lot ta sameshi tsaye yana kokarin bude mota, ta ce "Yaya zamu tafi tare" sau daya ya kalleta ya dauke kai, nan da nan idanuwanta suka cika da kwalla, ta ce "Kayi hkr, wallahi faduwa zaiyi shine na rikesa, i didn't do it intentional" ko ya daga kai ya kalleta, ta fashe da kuka ta dora kanta a bayansa ta ce "Wallahi i love u Yaya, i love u more than anyone else, pls don't leave me here" ta kankameshi tana kuka sosai and she didn't mind the way people are looking at them. _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _21_ A hankali Jawad ya zame hannayenta a jikinshi ya juya yana kallanta ya ce "And why are u crying?" Ba tare data kalleshi ba ta ce "Naga kamin fishi ne" ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Shiga mu tafi ya wuce" dan murmushi tayi ganin shima ya mata murmushi, ta zagaya ta bude front seat ta shiga sannan ya tada motar suka bar clinic din, juyowa Jawad yayi yana kallanta ya ce "U didn't wipe your face clearly" turo baki tayi tana kallansa ta ce "Na share mana" murmushi yayi yaci gaba da driving ya ce "Ohk, i called u but u refuse to pick" dan zaro ido tana goge sauran hawayen idanta ta ce "Why did u used the word refuse?" Ya ce "Uhum naga kamar yanzu bakyasan daukan wayana ne" girgiza masa kai tayi ta dan hade rai, ya sakar mata murmushi yana kallanta ya ce "To kiyi hkr, amma meyasa baki daukan wayana?" A hankali ta juyo tana kallansa idanuwanta tap da hawaye, kamar batasan yin magana ta ce "Is not like u think Barrister, jiya Imaan tayi tamin kuka ban kwanta da wuri ba, inaga sanda nayi bacci ka kira, yau ma kuma wayar na hannunta na taho" Ya ce "Ohk, how is she?" Ta ce "Lafiya take" daga haka ta share kwallan idanta. A bakin gate dinsu yayi parking ya jiyo yana kallanta ya ce "I will come back in the night" ta ce "Allah ya kaimu, baza kaga Imaan ba?" Ya ce "No, ina sauri zan koma office ne yanzu, idan nazo anjima zan ganta" ta ce "Thank u" ya ce "Mention not" fita tayi ta daga masa hannu sannan ta shige gate, ya danyi murmushi yaja motar ya wuce. bayan sallah Magrib aka sallami Yusuf, Daddy yazo ya daukesu suka koma gida, suna isa Ammi ta hada masa ruwan wanka ya shiga yayi, da towel ya fito a kunkuminsa ya zauna bakin gado, Khariyya ta bude kofar dakin ta shigo hannunta rike da fruits salad cikin dan bowl, zaro ido tayi ganinsa a haka ta juya da sauri, ya danyi murmushi ya tashi ya dauko kayansa ya shirya, kwanciya yayi akan gadon ya kunna AC ya limshe idanuwansa. Bude kofar dakin tayi a slowly tana lekawa, ganin ya shirya ta karasa cikin dakin ta zauna a gefensa tana murmushi ta ce "Yaya" ya bude idanuwansa yana kallanta, ta ce "Me zakaci na dafa? na hada maka fruits salad" murmushi yayi yana kallan bowl din ya ce "Thank u, ba sai an dafa komai ba wannan ma ya isa" ta dora hannunta akan goshinsa ta ce "Allah ya sauwake" ya ce "Ameen" daga haka ta ajiye masa bowl din a gefensa. Rafi'ah na zaune a dakinta tana shafa powder kiran Jawad ya shigo wayarta, ta danyi murmushi tayi picking call din, ya ce "Dear" ta ce "Uhm" ya ce "Nazo amma zan shiga mosque, an kira isha" ta ce "Ohk to sai ka idar" ya ce "Alright" katse wayar tayi ta ajiye a gefenta taci gaba da abinda take, sosai tayi mungun kyau sai kamshi take, ta dora dankwalinta sannan tasa hijabi tayi sallah, tana idarwa tayi addu'a ta cire hijab din ta yafa babban veil, call din Jawad ne ya kara shigowa phone dinta, tayi picking hade da sallama, ya ce "I'm done" ta ce "Ohk ka karasa BQ" ya ce "Why not inda muka saba zama?" Ta ce "Akwai sanyi a waje ai kuma da hadiri" ya ce "Ohk to" hanging call din tayi ta fita a dakinta zuwa dakin Ummi, a hankali ta tura kofar dakin ta shiga, suna zaune akan gado ita da Imaan, Rafi'ah ta sauke kanta kasa ta ce "Dama yazo ne?" Ummi ta ce "Waye?" Dago kanta tayi ta kalli Ummi sannan ta ce "Ya Jawad ne" Ummi ta ce "Ohk" mikewa Imaan tayi ta nufeta da gudu ta ce "Fita zakiyi?" Rafi'ah ta kama hannunta suka fita a dakin. Har suka isa BQ Imaan na tambayarta fita zasuyi, bude kofar parlorn tayi suka hada ido dashi, tayi saurin sauke kanta tana murmushi, Imaan ta nufesa da gudu ta dale jikinsa ta ce "I missed u Daddy" ya rungumeta yana kallan Rafi'ah dake tsaye ya ce "How are u beauty?" Ta ce "Fine Daddy" ledan chocolates din daya kawo mata ya mika ya ce "This is yours beauty" tana dariya sosai ta ce "Thank u Daddy" daga haka ta mike a jikinshi tana kallan Rafi'ah ta ce "Bari na nunawa Ummina" daga haka ta fice a parlorn. Kallan Rafi'ah yayi dake tsaye bayan kujera ya ce "Yau a tsaye zamuyi hiran ne?" Ta sauke kanta kasa bata ce komai ba, ya ce "Ko saina daukoki?" Taki kallansa kuma bata ce komai ba, ganin ya taso yasa tayi saurin zagayowa ta zauna akan kujera, ya zauna a gefenta ya ce "Kinyi kyau sosai" silently ta ce "Thank u" ya dan wara ido ganin ring din daya bata ne a hannunta ya ce "Ya maki kyau" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Bayan oversize ka bani sai kwanan nan yamin dai~dai" ya kamo hannunta yana kallan ring din ya ce "Uhm, ai ba laifi bane tinda dama bansan size dinki ba then, amma yanzu duk abinda zan siya ma..." Hannunta tasa ta rufe bakinsa ta ce "Ai naga dai ba kai na gayawa ba Anty Na'ima ne" zame hannunta yayi a bakinsa ya ce "Aita fadamin, kuma dani ake zuwa siyo komai" dan harara ta mishi ta kauda kanta gefe, ya danyi murmushi yana shafa kansa ya ce "Let me ask u something, banasan kuma ki fadamin abinda ba haka bane a zuciyarki" a hankali ta juyo tana kallansa, ya ce "Kinasan ki koma gidan Yusuf?" With shock ta kara kallansa sai kuma ta sauke kanta kasa, ya ce "Talk to me Fatima" fadawa tayi jikinshi ta fashe da kuka, ya bubbuga bayanta ya ce "I didn't ask u to cry, tashi ki fadamin" dago kanta tayi a kirjinshi ta ce "Ni banaso kuma" ya ce "Are u sure?" ta daga masa kai hawaye na sakko mata ta ce "Insha Allah i will finish my whole life with u, I thank God every time because He gave me you, ka sani farinciki a lokacinda bani da kowa, duk da ba laifinsa bane wallahi i can't stay with him anymore" ta kara maida kanta kirjinsa cikin sanyin murya ta ce "I had my heart broken during my first love, But when I think of it....." Kuka sosai ta fashe dashi, yana jin yadda hawayenta ke sauka a jikinshi, ya bubbuga bayanta ya ce "It's ok, ni bance kimin kuka bafa" silently ta ce "My future will be Good with u insha Allah, shima Allah ya bashi wacce zata so shi tsakani da Allah" sai kuma ta dago tana kallansa ta danyi murmushi ta ce "You are my first love and you will certainly be the last". Murmushinsa me yayi ya kara bata light hug ya ce "I luv u more" ta sakar masa murmushi ta matsa a gefensa ta ce "Dama kenan haushina kakeji ko?" Ya wara ido yana kallanta ya ce "No niba haushinki nakeji ba" ta dan turo baki ta ce "Hakane mana" matsowa yayi kusanta ya zaro handkerchief a pocket dinsa ya shiga share mata sauran tears dinta, bayan ya gama goge mata tass ta juyo tana kallansa ta ce "Inasan kamshin perfume din nan" silently ya ce "Nasa maki a kayan auranki ma" tayi saurin rife idanuwanta tana dariya a hankali, murmushi yayi ya mike ya ce "Zan tafi Baby, akwai abinda zanyi sannan kuma gobe karfe 6 zan fita" ta bude fuskarta ta ce "Safe, amma pls Yaya Anty Na'ima ta fada maka maganan da mukai da ita" ya ce "Ehh mana, ta fadamin komai" pillow ta wurga masa ta ce "To wallahi bada kai za'aje siya ba" ya dan shafa kansa yana murmushi ya ce "Na nawa kuma, har mun gama cika akwatin ma" pillow ta sake jefa masa ta ce "To nayi fishi ma" ya durkusa dai dai fuskarta yana dariya ya ce "Gobe da Yamma zamuje ki gaishe da Mami" ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ya nufi kofa tabi bayansa, har mota ta rakashi tana ta daga masa hannu ya tafi. Washegari Yusuf na zaune a daki bayan yayi breakfast Khairiyya ta shigo, ya dago yana kallanta ya ce "Ina zakije?" Ta ce "Kamar ya?" Ya ce "No naga kinyi kwalliya ne" ta danyi murmushi ta zauna gefensa ta ce "Yaya kasan menene?" Ya ce "Sai kin fada" rife idanuwanta tayi ta ce "Dama fa wanine na hadu dashi a wajen Jamb, he's so kind and humble so shine yace wai zaizo mu gaisa, na bashi address" tinda ta fara magana yake kallanta, ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce "Kin fasa yin karatun ne kika fara soyayya?" Bude fuskarta tayi ta ce "No ban fasa ba, amma yace wai zaijira na gama" Yusuf ya danja tsaki ya ce "Karya yake, ba namijin da zaice zai jira mace ta gama karatu bayan ba farawa tayi ba kuma nasan babbane" ta ce "Yess he's 33 but yace wallahi zai jirani" ya girgiza kai ya ce "That won't be possible, idan auranki zaiyi ya aureki sai kiyi karatun a gidansa idan kuma ba haka ba ya tafi ya kyaleki" da mamaki take kallansa ganin yadda yaci serious, ta ce "Amma Yaya ni sai nayi aure yanzu, i'm just 17 fa" harara ya dalla mata ya ce "And if u are just 17 what makes u to fall in love with someone" ta dan zaro ido sai kuma ta ce "To ai na kai" ya ce "Aurene baki kai ba kenan?" Ta ce "Uhm" mikewa tayi jin wayarta na ringing a dakinta, ta dan kalleshi ta ce "Amma pls Yaya karka gayawa Ammi, yau ne first day da zamu hadu kuma na kasa gaya mata" ya ce "Baza taji ba" daga haka ta juya tana murmushi ta fita, tana fita ya mike ya wuce parlor ya kulle kofar da key sannan yasa key din a pocket dinsa ya dawo ya kwanta, hanging wayar tayi ta yafa dan karamin veil dinta sannan ta fito a daki, leka dakin Yusuf tayi ta ce "Yaya saina dawo" ya daga mata kai yana murmushi ya ce "My regards to him" daga haka ta juya ta koma parlor, murda handle din tayi amma taji a rufe, ta duba taga ba sakata key ne, kamar zatai kuka ta koma dakin Yusuf ta ce "Dan Allah ka bani key din Yaya" ya ce "Key din me?" Ta ce "Na kofar parlor" ya ce "To bansan inda yake ba" ta tsaya tana kallansa irin na rashin yardar nan ta ce "Wallahi kaine ka rufe" ya mike tsaye yana kallanta ya ce "May be Ammi ce ta rife" ta kalli wayarta dake ringing ta ce "Na shiga 3 Ammi dake bacci kuma Yaya, daga nifa sai kaine Ya Sameer baya nan" ya ce "May b taji kina fada" ta durkusa a kasa tana hawaye ta ce "Yanzu ni mezance masa Yaya" ya ce "Bani wayar" ya kar6a wayar ya bar wajen ya koma parlor, picking call din yayi ya kai kunne, mutumin ya ce "Baby" Yusuf ya ce "U pls stay away from my wife, wani satin za tai aure sbd haka ka kyaleta karka sake kiranta, if not duk abinda ya faru fa kai is your fault" bai jira yaji abinda zaice ba yayi hanging call din ya koma daki, a zaune ya sameta akan carpet tana ta share hawaye, ya ce "Na bashi hkr" ta ce "Da gaske, ya kuma hakura?" ya daga mata kai ya ce "Ehh" bell sukaji an danna Yusuf ya mike ya fita parlor yaga ta biyo bayansa, juyawa yayi ya ce "Daukomin wayana a daki" ta ce "To waye Yaya?" Muryar Daddy sukaji yana fadin "Open the door Fatima" da sauri ta ce "Bari na tashi Ammi ta bani key di..." Ganin Yusuf ya zaro key a pocket dinsa yasa ta saki baki tana kallansa, bude kofar yayi Daddy ya shigo, Yusuf yayi kasa da kansa ya ce "Sannu da dawowa Daddy, ina kwana" Daddy ya ce "Lafiya Yusuf, naje morning meeting ne kana bacci" ya ce "Sannu da dawowa" kallan Khairiyya Daddy yayi ya ce "What's wrong with u?" _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _22_ 'Bata fuska Khairiyya tayi ta koma dakinta ranta a 6ace, Yusuf ya danyi murmushi yana shafa kansa, ganin Daddy ya shiga daki ya nufi dakinta yana dariya, a hankali ya bude kofar dakin ya hangota caan karshen gado tana kuka, ya maida kofar ya rufe ya karasa inda take yana murmushi ya ce "Ya akai Khairiyyan Yaya?" Fashewa tayi da kukan bakin ciki ta ce "Ni karka sakemin magana Yaya, mena maka daza ka hanani fita wajensa" side hug ya bata cikin rarrashi ya ce "It's not safe dear, naga baki sanshi ba, kullum waya kuke bakisan ya halinsa yake ba, watakila ma guduwa yazo yayi dake" ta dan zare ido tana kallansa ta ce "Guduwa kuma Yaya?" Ya ce "Uhmm, an gaya maki kidnappers suna da kama ne" jikinta ne yayi sanyi sosai, ta share guntun hawayenta ta ce "Kuma hakane, Allah ya kara karewa" ya ce "Ameen, kimayi deleting contact dinsa" ta daga masa kai da sauri, ya ce "kisa a black list ma" ta ce "Ohk" shiru tayi tana kallan Yusuf dake kallant ta ce "But Yaya what if he's innocent?" Ya ce "Just do what i said now" ta dan ta6e baki tasa number a black list sannan tayi deleting baki daya, duk yana kallanta harta gama, ta dago kanta tana kallansa ta ce "Yaya meyasa bazaka dawo da Anty Fatima ba?" Ya danyi murmushi yana girgiza kai ya ce "Kefa kika cemin ta kusan aure?" Ta ce "Yes, but nasan Ya Jawad zai hakura ya baka indai kaso hakan" kanta ya dora akan shoulder dinsa ya ce "Sankai kikeso nayi, ai Allah yace musowa 'yan uwanmu abinda muke sowa kanmu, kuma suna san junansu is hardly nace ta dawo ta yarda, and u know what?" Ta girgiza masa kai ya ce "Koda tace zata dawo bazan iya ba saboda Ahmad, he sacrificed alot Khairiyya wallahi da inada wani abin dazan saka mishi bayan Rafi'ah da zanyi, but haryanzu ina tinanin zan bashi Imaan idan har yanaso" Khairiyya ta danyi murmushi ta dago tana kallansa, sai kuma ta dan 6ata fuska ta ce "Yanzu shikkenan Yaya kun rabu?" Ya ce "No akwai zumunci Khairiyya, ga kuma Imaan sannan nima na cireta a raina by now, Allah ya hada auranmu tun farko saboda akwai raban Imaan tazo duniya, sannan auranmu shine silar kaddararmu" Khairiyya ta goge guntun hawayenta tana kallansa ta ce "Allah yasa haka shine mafi alkhairi" ya hade goshinsu yana kallan idanta ya ce "Ameen" jin an bude kofar yasa yayi saurin janye fuskarsa akan nata, Ammi ta kallesu sau daya ta kauda kai ta ce "Ka sameni a dakina" ya ce "Ohk to" mikewa yayi yana kallan Khairiyya ya ce "Till i come back" ta daga masa kai sannan ya fita a dakin. Da sallama Yusuf ya shiga dakin Ammi, ya nemi gefe ya zauna ya ce "Gani" Ammi ta ce "Toda farko dai mungode Allah daya kwatar maka 'yancinka ya kuma kubutar daku a hannun wannan mutanen" a hankali ya ce "Allah ya kara tsarewa" ta ce "Ameen, sai kuma maganar Rafi'ah, ka dawo kuma gashi tana shirin yin aure" a hankali ya dago yana kallanta sai kuma yayi murmushi ya ce "Allah ya sanya alkhairi Ammi, koda ba aure zata yi ba idan Allah ya kaddara zamanmu ya kare dole haka zamu hakura" Ammi ta ce "Toh fatanmu Allah yasa haka shine mafi alkhairi" ya amsa da "Ameen" Fitowa tayi walking slowly tana murmushi harta karasa kusa dashi, ya cire glasses din idansa ya ce "Amaryar Ahmad" ta sunkuyar da kai ta ce "Ina yini" ya ce "Lafiya kalau, kin shirya muje?" Ta daga masa kai ya ce "To bismillah" daga haka ya bude mata front seat ta shiga ta zauna, shima ya zagaya mazauninsa yayiwa motar key suka bar layin. Hannunta ya kamo yana kallan idanta ya ce "How is Imaan?" Ta ce "Tana nan lafiya" ya ce "Haka akeso" zame hannunta tayi a cikin nasa ta ce "Ummi tace za'a kaita wajen Babanta" ya ce "When?" Ta ce "Inaga yau" Jawad ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" shiru tayi tana kallan sajen fuskarsa daya kwanta sosai, ganin zai juyo yasa tayi saurin juyawa tana kallan window, murmushi yayi mai kyau ya ce "I caught you, me kike kalla a fuskana" ta danyi murmushi ba tare data juyo ba ta ce "Nothing" ya ce "There's" ta ce "To idan baka yarda ba shikkenan" ya ce "To zuwa zanyi na aske tinda bakyaso" tayi saurin juyowa tana kallansa ta ce "Nooo pls" ya juyo ya dan kalleta sai kuma ya maida hankalinsa ga titi, in a very low voice ta ce "Yana maka kyau sosai" ya juyo yana kallanta tayi saurin rife fuskarta da hijabi, ya ce "Wallahi wannan kunyan naki rana daya zan cire miki shi" bata dai dago ta kalleshi ba sai dariya take a hankali. Da sallama Ummi ta shigo parlorn Abba ta sameshi zaune yana rike da Imaan, kallanta kawai yake amma tinaninsa da hankalinsa na wani wajen da ban, jin bai amsa sallaman ba yasa Ummi ta kalleshi, ta sauke ajiyar zuciya ta zauna gefensa ta ce "Abbu Rafi'ah" ya juyo yana kallanta ya ce "Harkin gama ne?" Ta ce "Na dai kusa" ya ce "Ohk, Fatiman ina tafi ne? bamasan yawan fitan nan fa" Ummi ta ce "Taje gidan Anty Halima, kuma ta dade bata je bane shiyasa" Abba ya ce "Allah ya dawo da ita lafiya" ta ce "Ameen, dan Allah Abbu Rafi'ah kayi hkr da abinda ya faru karka sawa kanka wani ciwo" a hankali ya kwantar da Imaan akan kirjinsa ya ce "Ina kokarin yin hakan Zainab, amma kinsan abin da ciwo wani lokaci gani nake kamar mafarki ne" Ummi ta ce "Hakuri dai zakayi, tinda abinda ya faru ya riga ya faru, kuma dai koma menene 'yan uwanka ne, bazaka ta6a canzasu ba" Abba ya limshe ido ya ce "Hakane 'yan uwanane amma a yanzu da abin ya faru na cire hannuna akan lamarin su, ita Umma uwace a gareni sbd haka zanci gaba da kyautata mata kamar da, amma 'ya'yanta bani da sauran alaka dasu, abinda suka min suje suda Allah" duk jikin Ummi sai yayi sanyi, a hankali ta ce "Allah ya kyauta" ya ce "Ameen" daga haka ta mike ta daga Imaan dake bacci a jikinsa suka shiga daki. Jawad na parking Rafi'ah ta fito da sauri ta nufi entrance din gidan, bayan ya rife mota ya bi bayanta. A parlor duk ta samu ilahirin gidan, tayi saurin sunkuyar da kanta ganin sun hada ido da Mami, ta samu caan gefe ta zauna kanta a kasa ta ce "Ina yini Mami" cike da fara'a Mami ta ce "Lafiya kalau Fatima, ya karatu ana ta hutu ko?" Ta ce "Ehh" dai dai nan Jawad ya shigo rike da key din motarsa ya zauna kusa da Rafi'ah that wasn't comfortable, a hankali ta ce "Ina yini Mummy" Mummy ta ce "Lafiya kalau, yasu Umminki?" Ta ce "Suna nan lafiya" Ikram dake zaune ta ce "Ina yini Anty" a hankali Rafi'ah ta dan kalleta ta amsa, Sadeeq ya ce "Antynmu ina yini" kunya taji ta rife fuskarta da hijabi, Ikram ta mike tana dariya ta shiga kitchen, ba jimawa ta jerawa Rafi'ah different kind of fruits a gabanta, a hankali ta ce "Thank u" Ikram ta ce "Never mind Anty, tin jiya Yaya yake cewa zakizo wai sai Mummy ta miki dambu" ita dai kanta a kasa tana ta murmushi, ganin Mami ta tashi yasa ta mike da sauri ta shiga part din Mummy, Jawad ya danyi murmushi yana kallan Mummy ya ce "Sai ta zauna ita kadai ko? Dan mu yanzu anan muke yini" Mummy ta ce "Atoh idan ta gaji ta fito" Ikram ta dauki tray din tabi bayanta ta ce "Ni dai bazanbar Antynah ita kadai ba" daga haka ta shige part din Mami tana dariya. *1 Month 2 weeks ltr* Yau ya kama saura sati 2 bikin Rafi'ah kuma yau ne za'a kawo lefenta, tinda safe suna daki ita da Ameera sai yanzu da Ameera ta tafi sannan ta fito, lace ne ajikinta da yayi mungun kar6anta sosai, sai sheki take tana kamshi, bude dakin Ummi tayi ta shiga da sallama, suna zaune ita da Anty Salma da wata kawarta, Rafi'ah ta danyi kasa da kanta ta ce "In ayini" kawar Ummi ta amsa tana murmushi ta ce "How are u" a hankali ta ce "Fine" Ummi dake kallanta ta ce "Menene kuma?" ta ce "Dama Banci abinci bane" Ummi ta wurga mata harara ta ce "And who do u expect will bring food for u?" Sauke kanta tayi kasa tana wasa da fingers dinta, Anty Salma ta danyi dariya ta mike ta ce "Bari na kawo maki daughter" Ummi ta ce "To meyasa baza taje ta diba ba, bakinta ne a parlorn kasan" ita dai Rafi'ah murmushi tayi tabi bayan Anty Salma, dakinta ta shiga ta zauna a bakin gado, danna wayarta tayi taga message din Jawad, ta bude message din bayan ta gama karantawa ta danyi murmushi sannan ta masa reply. Karfe 3 motoci Hudu suka iso gidan Abba, cike da girmamawa aka tarye su suka shigo katon parlorn, duk yawanci 'yanuwan Abi ne saina Mami kalilan saboda su ba a gari suke ba, aka jera akwatina 12 a tsakiyar parlorn, wata babbar mata ce ta fara addu'a bayan an gama suka gaggaisa cikin mutunci sannan Ikram ta tashi ta bude ko wane akwati na parlorn, aka jejjera musu abinsha da snacks kala kala,,,, su Anty Salma nata yaba kayan suna Allah sanya alkhairi duk da dai ba daddagawa sukai ba, basu wani jima ba suka tashi tafiya, aka basu cartons din lemuka different types da kuma snacks suka tafi dashi, kowa ka ganshi yana cikin fara'ah da walwala. Bayan sun tafi Anty Salma ta shigo dakin Rafi'ah, ta sameta zaune akan sallaya ta idar da sallah, Anty Salma ta ce "Ba zaki sakko kiga kayan ba?" Sauke kanta tayi kasa ta ce "Anjima" Anty Salma ta ce "To ba damuwa, kin cin abincin dazun" ta daga mata kai, juyawa Anty Salma tayi ta fita a dakin Rafi'ah ta mike ta jawo wayarta dake ringing, a hankali tayi picking ta kai kunnen, Jawad ya ce "How are u?" Silently ta ce "Fine" ya ce "Kayanki sunzo ko?" kamar yana gabanta tayi saurin rife idanta bata ce ko mai ba, ya ce "Are u there?" Ta ce "Uhm" ya ce "Talk to me" ta ce "Ehh an kawo" ya danyi murmushi ya ce "Nasan an kawo, but how did u saw it?" rife idanuwanta tayi ta ce "Ni banma gani ba" ya ce "Why?" Ta ce "To 'yan uwan su Abba sun cika parlorn" ya danyi murmushi ya ce "Kema ai 'yan uwanki ne" ta ce "Uhm" ya ce "To anjima zamuyi magana, Mami ta kirani" ta ce "To nagode" ya ce "Thanks too, and never get tired of praying" ta ce "Insha Allah" daga haka sukai sallama. _08103810398_ *This page is dedicated to LUBABATU KASEEM & ZARAH MUHAMMAD, thank u sisters for the gift 😇 i appreciate the both of u 💃🏻💃🏻 Allah ya sanya alkhairi yasa ku gama lpy, my love for u is real and endless, thank u once again* 🥰❣️ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _23_ Daren ranar Yusuf na zaune a parlor yana kallo Ammi ta fito, ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Sannu da fitowa Ammi" ta zauna gefensa ta ce "Yauwa Yusuf, kaji an kawo kayan auren Rafi'ah ko?" Ya daga mata kai yana kallan TV ya ce "Eh, dazu munyi waya da Ahmad yake fadamin" Ammi ta ce"Bikinma sati biyu ya rage" ya ce "Duk munyi magana, Allah ya sanya alkhairi" Ammi ta ce "Ameen ya Allah" fitowa Khairiyya tayi a daki tana yatsine fuska ta ce "Ammi kinga ya kwacemin wayana tinda safe yaki ya bani" kin kulata Ammi tayi ta mike ta shiga daki, Khairiyya ta karasa gefensa ta zauna ta ce "Give me my phone" daga haka ta cusa hannu a pocket dinsa, hannayen gaba daya ya damke yana kallan idanta ya ce "Idan kika kwace na yarda zan baki" cije baki tayi ta dinga fincikan hannunta amma ta kasa kwacewa, shi dai sai kallan TV yake dayan hannun kuma yana kur6an tea, ya ce "Kin yarda ba karfinmu daya ba kenan" ta dan ta6e baki ta ce "Dama kai wannan katon ba dole kayi karfi ba" ya dan zaro ido ya ce "Nine katon?" Ta ce "Aiba kiba ba, kalli fa nan dinka babba" ta karashe maganar tana nuna kirjinsa, sake hannunta yayi ya mike ya ce "Keda wayarki sai kinyi aure idan na yarda na baki" daga haka ya shiga daki ta bi shi da gudu. Parking Jawad yayi a kofar gidan Abba sannan yayi dialing phone din Rafi'ah, tana kwance a daki kiran ya shigo, dan tinda aka kawo kayanta bata fito ba duk da mutanen sun watse sai Anty Salma kawai, picking call din tayi ta kai kunne hade da sallama, ya danyi murmushi ya ce "Are u sleeping?" silently ta ce "No" ya ce "Ohk i'm outside" a hankali ta mike ta ce "Toh" daga haka tayi hanging call din ta dauko hijab ta saka ta fita a dakin, a parlorn sama ta tadda Umminta da kuma Anty Salma, ta danyi kasa da kanta ba tare data kallesu ba ta fara sauka a stairs din. Very gentle take tafiya harta fito compound din gidan ta fita, tayi saurin sunkuyar da kanta ganinsa a tsaye yayi folding hannyensa ya jingina da mota, yayi mungun kyau sosai, ta karasa kusa dashi ta ce "Ina yini Yaya" ya ce "Lafiya kalau wife, how was today?" Ta ce "Fine" bude mata back seat yayi ya ce "Bismillah" ta shiga sannan shima ya shiga ya rife kofar, limshe ido tayi jin kamshin tirarensa daya hade da sanyin AC, kamo hannunta yayi ya ce "Kinga kayan?" Ta girgiza masa kai, ya ce "Why?" Ta ce "Babu" ajiyar zuciya ya sauke ya ce "How is everyone?" Ta ce "There are all fine, Abdul zai dawo ran Monday" ya ce "Allah ya kawo shi lpy" ta ce "Ameen" shiru ne ya biyo baya, ta daga kanta a hankali taga kallanta yake yana murmushi, da sauri ta sauke idanta kasa, cikin cool voice dinsa ya ce "Munyi waya da Yusuf dazu" ta dago kanta tana kallansa ta ce "Meya faru?" Ya ce "Nothing zumunci kawai mukai, na fada masa ranar auranmu kuma yau an kawo kaya" ta ce "Ohk" ya ce "And u know what?" Ta girgiza kai, ya ce "Ya bani Imaan har abada" with surprise ta dago kanta tana kallansa, sai kuma tayi murmushi ta ce "Allah na gode maka, dama ni abin na damuna yace zai kar6eta, inajin Imaan har cikin raina" ya ce "Shima haka yake ji, kuma ya bani ita saboda wasu dalilai nasa" ta sauke kanta ta ce "I'm so happy Yaya" ya ce "Really?" Ta ce "Yes" wayarsa ne ya fara ringing ya dauka ya kai kunne, kallansa kawai take harya gama, tayi saurin sauke kanta tana murmushi ta ce "I like your hair cut" ya ce "Thank u love, wane irin shiri kike na biki?" Ta bude hannayenta alamun bata sani ba ta ce "Ni kawai i don't like any event" ya dago fuskarta yana kallanta ya ce "To shikkenan, yadda kikeso haka za'ai" ta danyi murmushi ta zame jikinta, ya ce "To saida safe naga kamar kinajin bacci" ta ce "Ehh bacci nakeji sai anjima" ya ce "Alright i love u" daga haka ya bata light kiss a forehead dinta. *2 weeks ltr* Yau ya kasance friday ranar daurin auren Rafi'ah da Jawad, kowa ka gani yana cikin farinciki, gida ya cika sosai fiye da auranta na farko, Tana zaune a daki ita da Ameera Anty Salma ta shigo, ta zauna bakin gado tana kallan Rafi'ah dake zaune tayi shiru, Anty Salma ta bata side hug ta ce "Kiyita addu'a Fatima, ba wanda ya isa ya miki abinda Allah bai kaddara zai sameki ba" rungume Anty Salma tayi cikin kuka ta ce "Anty wallahi tsoro nakeji, gani nake kamar abinda ya faru 4years back zai sake faruwa" Anty Salma ta shiga rarrashinta ta ce "Ba haka bane daughter, insha Allah gidan zamanki ne na har abada" ta daga mata kai a hankali ta ce "I hope so Anty" Anty Salma ta shiga share mata idanta ta ce "Yanzu muka dawo daga gidanki mun karasa gyara komai, the house was so masha Allah, ki godewa Allah" dan murmushi tayi ta ce "Nagode masa Anty" tashi Anty Salma tayi ta ciro mata wani kaya ta ce "Yanzu mai make up din zata karaso, sai ki canza kaya kafin 'yan daurin aure su dawo" sauke kanta tayi kasa ta amsa da toh. Karfe 1 bayan an idar da sallan juma'a dumbum mutane suka shaida daurin auren FATIMA MUHAMMAD da AHMAD MUHAMMAD AHMAD, tinda Rafi"ah taji 'yan daurin aure sun dawo hankalinta ya kara tashi, batasan lokacin data fashe da kuka ba ta kankame Ameera cikin rawar murya ta ce "Ameera ina tsoro wallahi" Ameera ta ce "Bakiji abinda Anty tace ba kiyita addu'a babu abinda zai faru insha Allah" kuka sosai take tana addu'a cikin ranta, dan gaba daya ta girgiza da abinda ya faru da ita a baya. Da yamma liss aka shirya Amarya shiri na alfarma akai ta hotuna duk da fuskarta babu walwala sosai amma tayi mungun kyau, Khairiyya na gidan itama duk inda tayi Imaan na binta a baya, Mummy dai wannan karan tana bangaren ango, dan tinda aka fara biki bata leko gidan ba, suna caan suna nasu hidiman suma, karfe 7 aka kara shiryata cikin wani tsadadden lace da yayi mungun mata kyau, sai kamshi take ta ko ina, duk da gyaran jikin na sati biyu kawai akai amma sai sheki take, sosai da sosai Abba da Ummi suka mata fada, tana kuka haka aka dagata zuwa mota, shima Abdul duk yadda yaso kar yayi kuka saida hawaye ya xubo masa, hannunta ya kamo ya ce "Allah ya sanya alkhairi Anty" a hankali ta ce "Ameen" sannan ta shiga motar, motoci masu yawa ne suka rakata gidan Abi, ana parking a kofar gidan zuciyarta ya hau bugawa, aka fito da ita zuwa cikin gidan, fada sosai da naseeha Mami da Mummy suka mata, daga haka ta daga veil din da aka rife mata fuskarta dashi aka musu hotuna, Ikraam nata kallanta tana murmushi, ita dai taki yarda ta hada ido da kowa, bayan an gama komai daga nan aka wuce da ita gidanta, har dakinta Mummy ta kaita ba irin fadan data manta bata mata ba, tun tana daurewa harta fashe da kuka, bayan 'yan kawo amarya sun watse ya rage saura Ameera da Mummy sai Ikram da Anty Salma su suka kara gyara gidan yayi tass, bayan sun gama Mummy tace su tafi, ita tayi driving dinsu suka bar gidan. Rafi'ah na zaune taci kuka harta godewa Allah taji Karar shigowar message, jawo wayar tayi ta duba text message din, message ne na fatan zaman lafiya da kuma addu'o'i a rayuwar auranta a karshe ya mata fatan alkhairi, murmushi tayi ganin sunan Yusuf a karshe, tayi reply da "Thank u so much Yaya Yusuf i appreciate, and i wish u same" ajiye phone din tayi ta kifa kanta akan gwiwowinta, b jimawa taji an bude kofar dakin, ta dago kanta da sauri suka hada ido, sauke kanta tayi kasa, Jawad ya danyi murmushi ya zauna gefenta ya ce "I'm i not welcome wife?" Ta noke kafada hawaye na sakko mata, rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta ya ce "You stop crying Sweetheart" dago kanta tayi a hankali sai dai bata bari sun hada ido ba, ya ce "Kinajin yunwa ko?" Ta daga masa kai, ya ce "To muje parlor muci abinci sai muyi sallah" har lokacin jikinta rawa yake kuma ziciyarta na bugawa, dukawa yayi yana kallan jajayen idanuwanta ya ce "Ko in goya ki" ta rufe fuskarta ta ce "Ni bance maka ba ai" ya mike yana kallanta ya ce "To ki bari na daukeki" bai jira cewarta ba ya dauketa ya sata a shoulder dinsa suka fita parlor, akan kujera ya sauketa tayi saurin kifa kanta akan cushion ta ce "Ni banaso fa" ya ce "Ki bari sai anjima kice bakyaso" ta dago kanta tana kallansa ya kashe mata ido daya ya ce "Yes", plate ya dauko ya juye gasheshen kazar ya zuba fresh milk me sanyi cikin glass cup guda biyu ya ce "I want to feed u today" daga haka ya gutsuro naman ya fara bata a baki tana kar6a, ganin tana kunya yasa ya jawota jikinsa ya ce "Bari to na miki irin na babies" zame jikinta take sonyi amma ta kasa saboda rikon daya mata, haka dai ta hakura ta kwanta ajikinsa ya dinga bata, sosai taci kazar ta sha fresh milk dinta, ganin ta koshi ya daga plate din yana kallanta ya ce "To dagani na kai kitchen" a hankali ta sauka ajikinsa ta ce "Kai baka ciba" ya ce "Na koshi" daga haka ya wuce kitchen, yana dawowa ya sameta zaune inda ya barta, ya kai hannu zai dagata ta danyi kara ta ce "Nida kaina ne" ya ce "Ai banaso kisha wahala, let me just carry you" kin yarda tayi ta kara nokewa, ya ce "Then let me hold ur hand" hannunta ta mika masa ta ce "Sai dai na kama naka" ya ce "To gashi" ta danyi murmushi ta kama hannunsa suka wuce daki. Brush sukai sannan sukai alwala suka fito, ya jasu sukai raka'ah biyu sannan ya dinga musu addu'ar zaman kafiya har karshen rayuwarsu, tashi yayi ya ce "Bari naje kasa na kulle kofa" daga haka ya fita a dakin, mikewa tayi ta cire hijabin jikinta ta bude press dinta, night gown kala kala ta gani, ta dauko wata doguwa sannan ta cire kayan jikinta ta daura towel, ta dauko rigar zata sa kenan Jawad ya bude dakin, tayi saurin durkusawa ta ce "Wayyo Yaya ka fita na shirya mana" ya danyi murmushi ya karaso cikin dakin ya ce "Let me help u" daga haka ya dagota daga tsugunen da take, hannunsa yasa ya kashe switch din dakin, ta ce "Yaya kace tayani za..." Shiru tayi jin bakinsa akan nata, tayi saurin rintse idanuwanta zuciyarta na bugawa. *Firstly, my apology goes straight to TEAM YUSUF, u people shoul understand me here pls, a rayuwa ba komaine kakeso kuma kake samu ba, wani abin kana sanshi amma baka san ba shine alkhairi a tattare da kai ba, shiyasa akeso a kullum mutum idan yayi addu'a yayi fatan wannan abin shine alkhairi a rayuwarsa idan ba alkhairi bane Allah ya canza masa da mafi alkhairi, wannan shine fatanmu a koda yaushe Allah kuma yasa mu dace 🤲🏻 so inaso ku gane Allah ya kaddara zaman Rafi'ah da Yusuf ya kare ta dalilin wadannan mutunen, Allah kuma ya kaddara za'a haifi Imaan, furthermore littafina na gina shine akan Jawad da kuma Rafi'ah 🥰, thank u for reading 🤗* _08103810398_ *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _24_ Slowly ta bude idanuwanta tana bin dakin da kallo, ta mike a hankali ta shiga toilet, After few minutes ta fito daure da towel tana kallan agogon dake jikin wall, dan zaro ido tayi ta nufi press dinta ta dauko doguwar riga ta saka sannan tayi packing smooth hair dinta tasa hijab ta tada sallah, bayan ta idar ta jima tana addu'a sannan ta kifa kanta akan gado tana tuno rayuwarta right from the beginning till now, batasan lokacin da wasu hawaye masu zafi suka sakko mata ba, jin an bude kofar tayi saurin goge idanta ta limshe idanuwanta, Jawad ya karaso inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "How are u sweetheart?" ba tare data dago kanta ba ta ce "Fine, good morning" ya danyi murmushi yana dora hannunsa a kanta ya ce "Morning" dago kanta yayi yana kallan fuskarta ya ce "Open your eyes?" Ta noke kafada, ya dan shafa beard dinsa yana kallanta ya ce "Kunyana kikeji?" ta girgiza kai ta ce "No, just that..i'm not..feeling fine" yadda tayi maganar yasa ya danyi shiru yana kallan cute face dinta, ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Now tell me what's wrong with you" sai lokacin ta bude idanuwanta suna hada ido ta sauke kanta kasa, ya danyi murmushi ya kai bakinshi kunnenta yayi mata magana, daga masa kai tayi, ya bata light hug yana murmushi ya ce "Just like your first experience?" ta daga masa kai, ya rungumeta ya ce "I'm sorry, pardon me pls" ta zame jikinta a nashi ta mike ta ce "I want to sleep" ya mike yana kallanta ya ce "Breakfast fa?" Ta dan turo baki ta ce "I'm not hungry" ya zauna bakin gado yana kallanta ya ce "No u have to eat ko kadan ma, kinga tin dazu na tashi nake ta faman hada maki breakfast" kanta a kasa tana kallan dogayen yatsunsa dake kan kafarta, ya dan 6ata rai ya ce "So u won't appreciate?" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ya tashi tsaye ya dagata tayi saurin nokewa ta ce "Ai zan iya" ya ce "To naga kinaso na daukeki ne" ta dan turo baki tana kallansa ta gefen ido, ya kafe ta da ido ya ce "Kuma aciremin himar din nan" ta dan zaro ido ta ce "Yaaayaaahh" ya ce "Yes now, ni baza kimin yawo da himar a gida ba" ta zauna bakin gado ta ce "Tona fasa yin breakfast din" zama yayi gefenta ya ce "To naji tashi muje" mikewa tayi tana turo baki ta fita a dakin, ya shafa gashin kansa yana murmushi yabi bayanta. _3 weeks ltr_ Jawad ne zaune a parlor yana operating laptop, daga kansa yayi ya kalli time sannan ya mike ya haura upstairs, dakinsa ya bude ya samu Rafi'ah na kwance tana waya, suna hada ido ta turo baki tayi hanging call din ta juya masa baya, ya danyi murmushi ya karasa kan gadon ya ce "U haven't eat dear, ya jikin ki?" a hankali ta ce "Na koshi" ya dagota zua jikinshi ya ce "Are u still angry with me?" Ta girgiza masa kai a hankali sai kuma ta kifa kanta a kirjinsa tana sharar hawaye, cikin rarrashi ya ce "Ki bari next week sai muje i promise u this time around kinga shekaranjiya da zazzabi kika kwana" cikin muryar kuka ta ce "Ni wallahi na gaji u are always saying next week, 3 weeks banga Ummina ba banga Abba ba banga kowa ba sai Abdul daya zo min sallama ya koma school, ko Imaan sau biyu Khairiyya ta kawota" fashewa tayi da kuka ta kankameshi, shi dai kasa cewa komai yayi, caan ya dan bubbuga bayanta ya ce "Tashi ki shirya na kaiki, u meet me downstairs" daga haka ya janyeta a jikinsa ya dauki car key dinsa ya fita a dakin. Kwanciya tayi ta dinga share hawayen idanta bata kuma tashi ta shirya ba, bayan 20 minutes ya shigo dakin ya karasa inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "Are u not going?" Ta dago jajayen idanuwanta tana kallansa ta ce "Ba fishi kakemin ba" ya dan zaro ido ya ce "Niiiii?" ta ce "Ehh" ya ce "A'a niba fishi nake maki ba, kawai rigimarki ne tayi yawa, idan kinyi hkr ma na karasa da case din nan sai in kaiki gida harki kwana, amma kince ke bakyaso, then sai muje na kaiki anjima na dauko ki" sakkowa tayi akan gadon tana kallansa ta ce "Amma ba fishi kamin ba?" Ya daga mata kai yana kashe mata ido daya ya ce "In the next 2 weeks zaki koma school ma ai" toilet ta shiga ya bita da kallo yana dariya, fuskarta ta wanke tass sannan ta fito ta goge da clean towel ta fita a dakin zuwa dakinta, press dinta ta bude ta dauko atampa doguwar riga ta saka, sosai dinkin ya zauna mata tayi dauri me kyau tayi light make-up sannan ta yafa veil ta fashe jikinta da turare, tana juyawa suka hada ido da Jawad dake bakin kofa yayi folding hannayensa, ta sauke kanta kasa ta fara kwashe kayan data cire ta shiga toilet tasa a washing machine, a hankali ta karaso kusa dashi ta ce "Na gama" ya rungumeta yana limshe ido ya ce "U looks more beautiful wife" a hankali ta ce "Thank u" sakinta yayi ya kama hannunta suka sauko downstairs sannan yayi switching sockets suka fita ya rufo kofar, side hug ya bata suka karasa parking lot ya ce "Yaushe zan dauko ki?" Ta ce "Da daddare" ya ce "No ban yarda ba" ta ce "Allah Yaya zanyi hira da kowa sosai na dade fa bangansu ba" ya ce "After Magrib zanzo" ta dan tsaya tana kallansa ta ce "Why not 9pm or 10pm Yaya?" Murmushi yayi ya bude mata motar ya ce "Bismillah" bayan ta shiga ya rufe ya zagaya mazauninsa. Khairiyya ce kwance akan gadonta tana rokon Yusuf karya mata allura, gaba daya fuskarta ya wanku da hawaye, injection din hannunsa ya ajiye a gafe yana kallanta ya ce "It won't pain you lil sis, kinga jikinki yayi zafi" cikin kuka ta ce "Ai Daddy yace magani zan sha" ya ce "To bakiji sauki ba kinga sai allura kenan, bari na kira Ammi ta rike ki" sanin Ammi baza ta mata da dadi ba yasa ta danyi kara ta ce "Wallahi zata min fada dan Allah karkamin me zafi zan tsaya" ya ce "A hankali zan maki" daga haka ya dauki injection din ta juya jikinta na rawa, yana mata ta saki kara ta kankame hannunsa, yasa mata cotton wool a wajen yana murmushi ya ce "Allah ya baki lafiya" harara ta maka masa ta ce "Ba amin ba" ya fashe da dariya ya ce "Ameen din dai, in kuma kikaiwa kanki addu'an haka ni kuma naita maki allura" Ammi ne ta shigo dakin rike da cup ta ajiye a gefen gado ta ce "Anyi alluran?" Ya ce "Ehh" ta ce "Ga tea idan zaki sha" daga haka ta fita a dakin. Zama yayi a gefen gadon ya dauko tea din ya kai bakinta ya ce "Kar6i kisha" ta noke kafada tana jujjuya ido ta ce "Nina koshi" ya ce "To haka zamuyi auran kina harara na" ta ce "Aini ban harareka ba" ya ce "To kwanta kiyi bacci" a hankali ta zame jikinta ta kwanta ta ce "Yau kace zaka kaini na kaima Imaan abinda ka siya mata" ya ce "Not today, sai idan kin samu sauki" ta ce "Da yamma dan Allah" ya ce "Sai naga idan kin samu sauki kafin nan". Parking Jawad yayi a kofar gidan Abba yana kallan Rafi'ah ya ce "Mun karaso" kafin ya rife bakinsa ta bude motar ta fito ta shige ciki da sauri, tana bude kofar parlor ta dan ja baya ta wara ido ta ce "Saudat" Saudatu dake murmushi ta ce "Anty Rafi'ah" Rafi'ah ta zauna gefenta ta ce "Long time, sai waya kawai, ya mutanen garinku dasu mamanku, wannan babynki ce?" Rafi'ah ta dauki 'yar farar yarinyar da batafi 3 months ba tana jujjuyata ta ce "Masha Allah, ta girma sosai, me sunanta?" Saudatu na murmushi ta ce "Sunanku daya, nima wayana ne ya fadi banda numberku" Rafi'ah ta rungumeta ta ce "Allah ya raya ta da Imani, shiyasa bama saminki ashe?" fitowa Ummi tayi a kitchen Rafi'ah ta nufeta da sauri tayi hugging dinta ta ce "I missed u Ummina, ina Abba?" Ummi ta ce "Abba ya fita dazu, bakimin waya zaki zo ba, da yanzu zan sauke Saudatu a gidanki na wuce aiki" ta danyi murmushi ta ce "Nima ina shigowa kawai na ganta, i was so surprise ashe zata kawo mana ziyara" Saudatu dai ta danyi murmushi, Sakkowa Imaan tayi da gudu ta nufi mahaifiyarta ta rungumeta, Rafi'ah tayi hugging dinta tana kallanta ta ce "Kinga na samu wata babyn, do u like her?" Imaan ta daga mata kai, murmushi tayi ta koma kan kujera ta zauna Imaan ta zauna a gefenta, jin knocking yasa ta dan zaro ido, Ummi dake kallanta ta ce "Tare kuke ne?" Ta mike da sauri ta ce "Ehh" parlorn Abba Ummi ta shiga sannan Rafi'ah ta bude masa kofar, ya shigo hade da sallama ya zauna akan carpet, amsa gaisuwar da Saudat ke masa yayi, ya kalli Imaan dake kallansa ya ce "Come to me daughter" ta karaso da sauri ta rungumeshi harda hawayenta wai ya gudu ya barta, chocolate ya bata masu yawa hakan yasa ta hakura da mitan tayi shiru, bayan few minutes Rafi'ah ta masa jagora yaje ya gaishe da Ummi sannan suka fito, daga haka ya koma mota. Parlorn Abba Rafi'ah ta shiga ta zauna gefen Ummi ta ce "Dafa yini nazo kuma kince zakije aiki" Ummi ta ce "Why didn't u call me and ask? Test kuma zan musu, sai kije gidan Mummy ga Imaan nan, idan na gama zan biya na dauketa" ta dan hade rai ta ce "To, wani satin saina dawo" Ummi dai bata ce mata komai ba ta fita a parlorn, mikewa tayi itama ta fito a parlorn ta samu Saudatu na goya Babynta suna sallama da Ummi, ta ce "Tafiya zakiyi ne" ta ce "Ehh wallahi zanje gidan wata Innarmu anan zan kwana" Rafi'ah ta ce "To insha Allah zanzo miki kafin ki koma" ta danyi murmushi ta ce "Ina nan kwana 3 zanyi" ta ce "To sai kin ganni, ki gaishe da mutanen gida, bari na karba phone number ki" Saudatu ta ce "Ameen" daga haka ta saka mata number, Ummi ta ce "To bari na saukeki" ta ce "To ba komai" upstairs Rafi'ah ta nufa ta dauko kayan Imaan set biyu tasa a karamin jaka sannan tayiwa Ummi sallama suka fita, tinda suka fito Jawad yake kallanta yana murmushi, bayan sun shiga motar ya ce "Sai kyau kikeyi wife" ta dan turo baki ta ce "Ummina zata fita yanzu dan girman Allah next week ka kawoni" ya ce "Angama Madam" daga haka yaja motar suka tafi. Suna zuwa kofar gate dinsu yayi horn ya shiga yayi parking, Imaan ta fito da gudu ta nufi cikin gida, ita dai Allah ya gani yanzu bata wani sakewa idan tana tare da Mami, Ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "U look sick, ko har yanzu zazzabin ne" ta girgiza kai a hankali ta ce "Ni banajin komai kuma" daga haka yaja hannunta suka nufi entrance din gidan, da sauri ta janye hannunta ganin ba saketa zaiyi ba, ya juyo yana kallanta sai kuma yayi dariya ya bude kofar, Dukkansu suna zaune a parlor Mummy na yiwa Ikram kitso, Mami kuma ta dora Imaan a cinyarta tana fada mata tare da Daddy suka zo, da sallama suka shiga parlorn, Rafi'ah tayi saurin sauke kanta kasa ta zauna akan carpet, zama yayi a tsakiyar Mami da Mummy ya gaishesu, Ikram ta gaishesa sannan Rafi'ah ma ta gaishe su, Ikram ta ce "Anty ina wuni" sauke kanta tayi kasa ta ce "Fine" Mummy ta ce "Har yanzu zazza6in ne? Shekranjiya da mukai waya tace tana zazza6i" ya ce "Ehh amma taji sauki, dama yini daya ne tayi, data sha magani shikkenan" Mummy ta ce "To Allah ya sauwake, ya kuke ina babu komai" ya ce "Alhamdulilah ba komai" Tashi Ikram tayi ta jera mata abinci a gabanta ta ce "Anty ga abinci" ta girgiza kai ta ce "Na koshi Ikram, yanzu ai 10am ne, sai anjima" Ikram ta ce "To bari na tattara" da hannu Jawad ya mata alamar ta barshi ya ce "Zataci, bata ci komai ba" Mummy ta ce "To maiyasa Fatima, ko murnar zuwa gida ne?" Ta girgiza kai a hankali, Mummy ta ce "To dauki abinci kici" daukar warmer Ikram tayi ta shiga parlornsu ta ce "Zaki fi jin dadi anan, feel free pls" Mummy ta ce "To ki tashi ki bita" a hankali ta mike tabi bayan Ikram, Mami dai na zaune sai murmushi take tana shafa bayan Imaan dake kwance a jikinta. Zama Rafi'ah tayi akan carpet tana kallan Ikram ta ce "Pls i need a cup of tea" Ikram tayi dariya ta ce "Laa dama yunwa kikeji shine kikai shiru" murmushi tayi ta ce "Ba wani yunwa" Ikram ta fita tana dariya, bude babban warmern tayi taga chips ne da soayyan kwai, ta bude dayan taga farfesun kayan ciki, kauda kanta tayi gefe da sauri ta rife warmer ta fara jaa baya tana kokarin tashi, kafin ta karasa tashi ta fara kwararo amai a wajen, dai dai lokacin Mami ta shigo Jawad na biye da ita, yayi kanta da sauri yana dagata ya ce "What's wrong with u?" Magana zatai amma ta kasa saboda wani aman daya taho mata, Ikram da shigowanta kenan ta tsaya kallansu, Mami ta sauke Imaan ta karasa kusa dasu ta ce "Kace taji sauki?" ya ce "Ehh but bansan kuma meke damunta ba" Mami ta ce "To dadin meyake daminta?" ya dago yana kallanta sai kuma ya sauke kansa ya ce "It's malaria probably with typhoid" kama hannun Rafi'ah Mami tayi tana masa wani kallo suka shiga daki, toilet ta kaita ta wanke mata baki sannan ta kwantar da ita akan gado, tana bude kofa ta ganshi tsaye yayi folding hannyensa, ta ce "Kasan tanada ciki ka fito da ita a haka?" Ya dan shafa kansa ya ce "Mami ita ta takura saita fito, and i noticed she was pregnant day before yesterday" wuce shi tayi ta jawo kofar dakin ta ce "Da kace Malaria ne?" Ya ce "Uhm da farko haka Doctor yace min". _08103810398_ *Thank u all for your calls and messages i appreciate, Allah ya kara mana lafiya, wadanda basu da lafiya Allah ya basu lafiya 🥰 thanks for ur concern nagode sosai da sosai 💃🏻💃🏻* *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ _25_ Zama yayi akan kujera ya zaro wayarsa a pocket yana dialing phone din Aliyu, Mummy da shigowanta kenan ta wuce dakin Mami tana fadin "Ni dama tin dana ganta nasan akwai karamin ciki a jikinta" yayi saurin sunkuyar da kansa ya sake dialing phone din Aliyu, fitowa Mummy tayi tana kallansa ta ce "Wai tin yaushe ta fara laulayin me?" ba tare daya kalleta ba ya ce "Shekaranjiya ne" ta ce "To Allah ya raba lafiya, Allah kuma yasa kar tayi irin laulayin cikin Imaan" shidai baice komai ba yana zaune, gaba daya jikinsa yayi sanyi sosai, kallan Ikram dake gyaran wajen aman yayi ya ce "Sadeeq yana gida ne?" Ta ce "A'a" mikewa yayi ya wuce dakin Mami ya sameta tana canzawa Imaan kaya, a bakin gado ya zauna kansa a kasa ta ce "Wani taimako aka bata ne?" Ya ce "Nothing" ta dago kanta tana kallansa ta ce "Why? Bakuje asibiti bane?" Ya ce "Aliyu ne ya dubata a gida kuma na kirashi bai dauka ba yanzu" Mami ta ce "Allah ya bata lafiya" a hankali ya ce "Ameen" mikewa yayi zai fita a dakin ta ce "Ka kyaleta ta kwanta" a takaice ya ce "I'm not going to her" daga haka ya fita a dakin. Karfe 12 Rafi'ah ta farka daga nauyayyen baccin daya dauketa, ta bude idanuwanta a hankali tana bin dakin da kallo, jin an bude kofar yasa tayi saurin runtse idanuwanta dan tinaninta Mami ce, Jawad ya hau kan gadon ya daga blanket din jikinta yana kallanta, bude idanuwanta tayi suka hada ido, ya rungumeta lightly as if he don't want to, ya ce "How are u feeling now?" A hankali ta ce "Fine" ya bata kiss a forehead dinta ya ce "Me kikeji yanzu?" Ta ce "Nothing, kawai kaina ke dan min ciwo" ya kara rungumeta ya limshe idanuwansa ya ce "Quick recovery wife". Kusan minti 3 tana kwance a jikinsa kafin ta dago kanta a hankali ta ce "Pls Yaya i'm i pregnant?" Idanuwansa ya bude yana kallanta ya ce "Of course, are u not happy?" ta girgiza masa kai hawaye ya taru a idanta ta ce "No just that" shiru tayi ta kwanta ajikinsa tana sheshekar kuka, ya fara patting bayanta a hankali ya ce "What Baby?" Cikin kuka ta ce "Zan sha wahala" sosai ya jawota jikinshi ya ce "No, insha Allah baza musha wahala ba, God knows best ai kowani ciki da yadda yake ba lallai ya zama daya da wancen ba" a hankali ta ce "I hope so, banasan na tina wahalan dana sha last" ya shafa kanta ya ce "Ba komai, just keep on praying" kankameshi tayi ta fara sauke ajiyar zuciya, sai taji dadi yadda yake karfafa mata gwiwa, ya shafa bayanta ya ce "Are u still afraid?" Ta ce "No" ya rungumeta sosai a hankali ya ce "I love u wife, and i will still love u till my last breathe, Allah ya bamu cute babies kamar ke" murmushi tayi a hankali ta ce "Kamar kai dai" ya ce "Ehh zaki haifa duka, sai kin haifi 22" batasan lokacin data fashe da dariya ba, ya ce "Dariya na baki kenan?" Ta ce "I swear" bakinshi ya dora akan lips dinta tayi saurin juyawa ta ce "Yaya idan wani yazo fa?" Ya ce "Duk da kike kwance ajikina baki yi tinanin hakan ba?" zame jikinta ta farayi ya kankameta ya ce "Bazaki tashi ba" ta ce "Dan Allah kar Mami tazo" ya ce "And so" daga haka ya kashe mata one eye, ta fara kwace jikinta da karfi tana "Ni dai inada kunya wallahi bazan yar..." Shiru tayi jin an bude kofar dakin, Jawad ya dago kansa a hankali suka hada ido da Mummy, ta ce "To ka tashi dama ka dauki matarka ku bar mana gida, ai taji sauki Allah ya kara karewa" tana kai nan ta juya ta fita a dakin. Ajiyar zuciya Rafi'ah ta sauke jin muryar Mummy, ta mike a hankali ta sauko akan gadon ta dauka dankwalinta ta daura sannan ta juya tana kallan Jawad dake gaban mirror yana sa hula, ta kalli kan gadon ta ce "Yaya ka 6atawa Ikram gadon ta" ya ce "Zata gyara ai, danma bamu 6ata yadda naso ba" harara ta dan dalla masa yayi kanta zai kamota ta fita da sauri, parlor ta leka taga ba kowa ta dauka veil dinta ta yafa, rungumeta taji yayi ta baya, tayi saurin juyawa ta ce "Yayaaahh" ya ce "Muje dakin Mami muyi mata sallama" ta ce "To ka sakeni nikam" sakinta yayi ya kama hannunta ya ce "Muje to" ta tsaya tana kallansa ta fara hade rai, ya ce "Ha'a i'm i holding u?" Ta ce "But u are holding my hand" sake hannunta yayi ya wuce gaba ya ce "Zamuje gida ai" ta dan turo baki tabi bayansa zuwa dakin, suna zaune akan gado ita da Imaan, Jawad ya zauna bakin gadon Rafi'ah ta zauna a kasa ta ce "Zamu tafi Mami" Mami ta ce "To ko a yimiki kunu?" Kanta ta girgiza a hankali ta ce "Na koshi Mami" Jawad ya mike yana kallan Imaan ya ce "Sai anjima" Mami ta ce "Allah ya kaimu, Allah kuma ya sauwake" ya ce "Ameen" hannu Imaan ta daga musu, Rafi'ah dai mikewa tayi ta fita a dakin, Jawad ya daga mata hannu ya ce "Bye sweetheart". A kitchen suka sami Mummy da Ikram suna yiwa Abi tuwo, Rafi'ah ta dan tsaya a bakin kofa ta ce "Sai anjima" Mummy ta ce "Mu jima da yawa, Allah ya kiyaye" shidai Jawad murmushi kawai yake ya ce "Ameen" Ikram ta fito tana kallan Rafi'ah ta ce "Allah ya kiyaye Anty, sai nazo" ta ce "To sai kinzo Ikee" daga haka suka fita. Daren ranar Rafi'ah na kwance a iikin Jawad kiran Ummi ya shigo mata, tayi picking ta kai kunne hade da sallama, Ummi ta ce "Ya jikinki, Anty Halima tace baki da lafiya?" A hankali ta ce "Ehh amma naji sauki, Munyi waya da Abba dazu nace masa nazo ban ganshi ba" Ummi ta ce "To kin kyauta, sai anjima" tana hanging call din kiran Mummy ya shigo mata, ta dauka tana yatsine fuska ta ce "Ba koranmu kikai dazu a gidanki ba?" Mummy ta ce "Ba wannan ba kinji Ikleemah bata da lafiya ko?" Mikewa tayi a jikinshi ta ce "Meya sameta ni ban sani ba, yanzu fa muka gama waya da Ummina" Mummy ta ce "Mijin dai ya saketa wai ta samu ciki shi bayasan haihuwa, ya mata duka cikin ya zube, tana caaan tana kuka ga uwa da kanwar uwa a kurkuku, abundai abin tausayi jikinta duk duka ya farfashe" ita dai kasa cewa komai tayi ta ce "Allah ya kyauta" daga haka sukai sallama. *_Sorry for d short update, i'm very busy that's why_ 🙏🏻* *_...شريك حياتي..._* _{MY LIFE PARTNER}_ _[Part 2]_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._ _By FATIMA ✍🏻_ Washegari Rafi'ah na kwance a daki tana kallo a laptop Jawad ya shigo, ta juya tana kallansa ta ce "Wallahi Yaya naci abinci" hawa kan gadon yayi ya danna stop ya ce "Tashi muje kisha tea" ta dan zaro ido ta ce "Nafa sha" ya ce "Bangani ba" daukanta yayi kamar 'yar Baby suka fita a dakin zuwa parlor, ya ce "Oya show me the cup?" ta ce "I have washed it" daki ya koma da ita ya daurata akan gado ya ce "Let's fulfill our deal" ta zaro ido ta ce "Not now pls" ya rungumeta ya ce "Why Baby, i'm in need of u" shagwa6e masa fuska tayi ta narke ajikinsa ta ce "Let me finish watching my film plsss" bakinshi ya dora akan lips dinta in a low voice ya ce "Pls dear" ta fara shamba kafafuwa tana kuka a hankali, sosai ya kara hugging dinta ya fara bata hot kisses all over. Haka rayuwar Rafi'ah yaci gaba da tafiya gwanin dadi da kuma sha'awa, ba abinda ta nema ta rasa a wajen mijinta, kulawa na musamman yake bata ko nan da caan tare suke zuwa, yadda yake makalata a jikinsa sai kace cikinsa zai maidata, office ma idan yaje da wuri yake dawowa, sai dai kuma idan yana da case, shima kansa har kiba yayi ya kara kyau sosai, ko makaranta taje hankalinta baya kwanciya idan baizo da wuri ba, ta dinga turo baki tana masa shagwa6a saiya lalla6ata take saukowa. Bangaren Yusuf kuwa soyayya suke da Khairiyya na gani na fada, ko kadan bayasan abinda zai takura mata, kullum yana cikin frinciki musamman idan yana tare da Imaan dan yawanci zamanta ya dawo wajen Ammi ko kuma wajen Mami, bai kara shiga tashin hankali me tsananiba sai lokacin da aka kirashi Jiddah ta haihu amma yaron ya koma, sosai da sosai Khairiyya taji tausayinsa, Jiddah dai ba wai kukan rasuwar yaron kadai takeyi ba, kuka take saboda yanzu zamanta da Yusuf ya kare, dama da abin cikinta ya zauna shine zatai tinanin ko zai maidata, amma yanzu da babu d'an tasan kashinta ya bushe, ranar da akai sadakan uku ba irin kukan da Jiddah batai ba, ta rirrike Ammi wai dan Allah tasa baki, ita dai bata iya tace komai ba saboda tasan Yusuf bazai ta6a mayar da ita. Zaune suke akan gado ta mimmike kafanta yana mata massage, jin yana bata labari yaji tayi shiru yasa ya dago kansa yana kallanta, kar6e handout din hannunta yayi ya ce "Wai yanzu kam baki da lokacina ko Fatima?" Dan zaro ido tayi ta mike tana kallansa ta ce "Allah sarki Yayana, wallahi ba haka bane kaga final exams zanyi ga babynka kullum yayita damuna" ta karashe maganar tana turo baki, rungumeta yayi sosai yana shafa cikin ya ce "Soon zaku rabu Baby, 2 months ya rage mana" ta danyi murmushi ta ce "I hope so, ranar dana haihu zanyita bacci ko sweetheart?" Ya bata light kiss ya ce "Exactly Babynah" dan zabura tayi ta ce "Wait!! Honey did anyone came today?" Ya ce "Wa kenan?" Ta ce "Sadeeq tailor, yace zai kawomin dinkuna na" ya girgiza kai yana murmushi ya ce "Bai kawo ba, nidai ya kirani yace in baki hakuri" wayarta ta jawo akan bed side drawer yayi saurin kwacewa ya rungumeta ya ce "Me zakiyi?" A fusace ta ce "I want to call him, bayan shi yayi alkawari zai kawomin har gida, wallahi idan bai gama..." Bakinshi da taji a cikin nata ne yasa tayi shiru, ya fara bata hot and romantic French kiss, kusan 3 minutes suna a haka kafin ya zare bakinshi a hankali ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce "Ya kawo yana dakina" ta danyi murmushi ta rungumeshi ta ce "Da gaske Yayana" ya daga mata kai, ta sake sakin wani kyakkyawan murmushi ta ce "Dama ya za ai ina yayar Amare kanwar ango ace ba'a kawomin dinkuna na ba" dariya ya danyi ya ce "Kin dai girmi Khairiyya amma Ikram tafi ki" ta dan turo baki ta ce "Amma ai Yayanta nake aure sabida haka i'm her Aunt" collapsing tayi a jikinsa ta ce "Yaya Ikram dinmu zata sha girki, ance fa Ya Sameer baya awa daya baici abinci ba, he eats alot" shi dai murmushi kawai yayi hannunsa na kan cikinta ya ce "Da zaki zama kamarsa dana fi kowa jin dadi" ta zaro ido ta ce "Ni din" ya ce "Eh mana, nafiso kiyita cin abinci ki kara kiba" a hankali ta ce " To zan dinga ci" daga haka ta mike da kyar ta sauka akan gadon ta ce "Bari na dauko dinkin" ta fita ya bita da kallo, duk sai yaji tausayinta sosai ganin yadda cikin ya mata nauyi, ya sauke ajiyar zuciya yana addu'ar Allah ya rabata dashi lafiya. Washegari ya kama Saturday ba school, da sassafe Rafi'ah ta tashi ta musu breakfast sannan ta koma dakinta tayi wanka, sosai tayi wani sanyayyen kyau ga cikinta dan dass lol, tana cikin daura dankwali aka bude kofar dakin, ta juya da sauri jin kamshin turarensa, suna hada ido ta ce "Wooow, Yayana kayi kyau" ya karaso inda take yana murmushi ya durkusa dai dai cikinta ya bashi kiss ya ce "Good morning Baby" ya dora hannunsa akai, dan 6ata rai tayi ta juya kanta a hankali, ya mike ya rungumeta ya ce "How was your night" kamar batasan yin magana ta ce "It wasn't nice" ya dago yana kallanta da sauri ya ce "What makes it boring sweetheart" turo baki tayi bata ce komai ba, ya danyi murmushi ya ce "Ni dai ban yarda ba, ninasan yesterday night was so nice and sweet, ko in tuna maki" daga haka ya kai bakinshi saitin kunnenta yana magana yana murmushi, dan tura shi tayi ta ce "Ni dai banaso" ya ce "Then how are u?" Ta kara turo baki ta ce "I'm not fine" bakinshi ya kai saitin nata ya bata light kiss ya ce "Laifi na miki ne?" Kamar zatai kuka ta ce "Ba saida ka kula unborn dinka ba sannan ka kulani" ta karashe maganar idanta tap da hawaye, wani serious and tidy hug ya bata yana murmushi ya ce "I'm sorry sweetheart, ina sanki fiye da komai nawa, bama kece silar zuwansa duniya ba? I love u more than u think" ta danyi murmushi itama ta rungumeshi ta ce "I love u so much my Barrister" hannunta ya kama suka fita a dakin sukai breakfast, bayan sun gama ta dauko veil dinta da side bag tana kallansa ta ce "Let's go" ya ce "Nifa banasan a kallan min ke" ta kalli jikinta ta ce "Yaya to ai ba'a ganina" mikewa yayi ya gyara mata veil din ya ce "Cover my property" ya karashe maganar yana kashe mata ido daya, ta danyi murmushi ta kama hannunsa suka fita, key yasa a kofar sannan suka wuce parking lot, ya bude mata mota ta shiga ya zagaya nasa mazaunin ya kunna motar. Suna hawa bakin titi ya kamo hannunta ya ce "What gift do u want for ur convocation?" ta juyo tana kallansa ta ce "Saura 5 weeks fa Yaya" ya ce "I know, so nake na sani da wuri" ta danyi murmushi ta ce "Just anything sweety, i will appreciate what ever u give me" ya ce "Kin bani za6i kenan?" Ta daga masa kai, ya ce "Ohk angama". Few minutes ya kaisu gida, yayi parking ta fito tana kallansa ta ce "Sai dai ka bini a baya" ya danyi murmushi ya bi bayanta bayan ya rife motar, a balcony ta tsaya jin hayaniya a parlorn, bayan Jawad ya karaso ta kamo hannunsa ta ce "Kamar sunyi baki" shidai bai saketa ba kuma baice komai ba, ya murda handle din kofar, Khairiyya ce da Ikram sai Sadeeq suna buga uban musu, suna ganinsa duk sukai shiru sai Sadeeq dake dariya yana fadin "Baku da wayo ai, ku yarane" shigowa Jawad yayi yana rike da hannun Rafi'ah, ganin su Khairiyya ne yasa ta saki murmushi, suka taso da sauri suka rungumeta, Jawad dake kallansu ya ce "Ku kyaleta ta xauna" suka saketa kowaccensu na murmushi suka gaishe shi, a takaice ya amsa yana kallan Sadeeq ya ce "Kaima dai ka nemo mata aure zan maka" Sadeeq ya kwashe dariya ya ce "Allah ko Yaya" Jawad ya ce "Uhm" daga haka ya shiga part din Mami, Rafi'ah ta kalli Ikram dake zuba mata zance ta ce "Ku rakani wajen su Mami" hannunta Ikram ta kama suka shiga part dinsu, Mami na zaune ita da Mummy da uban kaya gabansu suna hadawa cikin akwati, duk kuma dinkakku ne, Rafi'ah ta zauna kanta a kasa ta gaishe su, Mami ta ce "Ya jiki kuma" a hankali ta ce "Da sauki" Ikram dake kallan Khairiyya ta ce "Kinga wai su Mummy suma harda anko, jiya sun cika wani akwati yau ma sun cika wani" ita dai Khairiyya murmushi kawai tayi, Mummy ta dalla mata harara ta ce "To kar muyi anko, kijimin iskanci banda bikinki sai kuma na Sadeeq idan yana da niyya, saboda haka gara muyi yadda muka ga dama" dariya sukayi Mummy ta ce "Ai gaskiya ne, idan kuwa Sadeeq yayi aure sai bayan shekaru kafin Abdul shima yayi, lokacin dai karfinmu ya kusan karewa, sai kuma na Imaan idan da kwanan mu" Jawad ya ce "Ni baza a yiwa yarinya na auren wuri ba" Mummy ta kama ha6a ta ce "Ikon Allah, ita wannan figigiyar matarta ka shekaranta 17 tayi auran farko, kaima kuma a shekara 21 ka aureta idan auran wuri ne ai bakayi magana ba" ya dan ta6e baki ya mike yana kallan Imaan dake bacci a kan kujera. Mikewa Rafi'ah tayi suka shiga dakin Ikram, bayan sun zauna Ikram ta ce "Anty ankawo mana dinkinmu bari kigani" Ikram ta jawo wani babban akwati ta ce "Sauran suna dakin Mami, anko zamu dingayi har a gama bikin" ita dai Khairiyya tayi shiru, dan harga Allah kunya take idan ta tuna wai Yusuf zata aura musamman a gaban Rafi'ah,,,, kaya kala kala duk bibbiyu iri daya Ikram taita fito dasu tana nunawa Rafi'ah, sunyi mungun kyau sosai, Rafi'ah ta ce "Masha Allah, Allah ya kaimu nan da 2 weeks din nan musha biki" daga haka ta kalli Khairiyya dake boye fuskarta a jikin gado, kamo hannunta Rafi'ah tayi ta ce "Zo muyi magana Khairi na" Khairiyya ta matsa kusa da ita a hankali ta ce "Gani Anty" Rafi'ah tayi murmushi ta bata side hug ta ce "Ki daina kunyana dan Allah, idan ba haka ba zan kira Yaya Yusuf na gaya masa kuma zance ko magana bakya min" ta dan zaro ido tana murmushi, Rafi'ah ta saukar murya caan kasa ta ce "Ko baki aureshi ba dole watarana zaiyi aure, kuma nima ba gashi nayi aure naba, ki saki jikinki ni ki daina kunyana haka nan, i pray ma in the next 1 year Imaan nada kanwa" tayi saurin runtse idanta tana murmushi, Ikram ta ce "Anty wallahi ke kadai takewa kunya, kinga wayar data dinga yi jiya da daddare" Rafi'ah ta ce "Na sani ai, yaushe suka zo?" Ta ce "Kwanan su uku yau, nima idan zasu tafi zan bisu nayi kwana biyu" Rafi'ah ta ce "Ina din?" Ikram ta ce "Gidan Ammi" Rafi'ah ta ce "Ehh lallai baki da kunya, kuma duk ana kallanki sai a barki kije" Ikram ta danyi baya sannan ta ce "Ehh mana, kema fa Anty da kina kwana a gidan nan, kuma ai abinda kuke keda Yaya yafi wanda nayi" pillow Rafi'ah ta jefa mata ta ce "Banasan sharri kuma, aini akwai yayar mamana a gidan, ke kuma wajen wa zakiji?" a hankali ta ce "Ya Sameer" sakin baki Rafi'ah tayi tana kallanta, ita dai Khairiyya sai babbaka dariya take tana daga kwance, Ikram ta dan harareta ta ce "To Khairiyya ma ta ban shawara, suyi hiransu muma muyi namu" ta6e baki Rafi'ah tayi ta mike da kyar ta ce "Ni bazan iya muku ba, bari naje parlor" Ikram ta ce "Ai kuwa duk inda kikai binki zamuyi" bude kofar dakin akai Imaan ta shigo da gudu ta rungume Rafi'ah, sosai ta kankame yarinyar tana bata kiss ta ce "I missed u daughter" Imaan ta ce "I missed u too Momma", daga haka ta dauko sabon Tablet dinta akan gado tana nunawa Rafi'ah ta ce "Papana ya siyamin sabo, harda laptop" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Masha Allah, kince kin gode ko" ta daga mata kai tana kallan Khairiyya ta ce "Ko Antyna?" Khairiyya ta ce "Ehh kin fada" kama hannun Imaan Rafi'ah tayi ta ce "Ko ruwa baku bani ba kun tsareni da surutu" mikewa sukai suka bi bayanta Khairiyya ta ce "Sorry Anty" daga haka suka fita a dakin. Abinci kala biyu suka jera mata a parlor taci tasha sannan suka ci gaba da hira, kuma duk hiran akan yadda bikinsu zai kasance ne, karfe 3 da rabi Jawad ya dawo gidan shida Yusuf da Aliyu, suna zaune a parlor suka shigo, Ikram ta mike tana kallan Khairiyya ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Yauwa sannu, ina fatan baku sata surutu da yawa ba" murmushi sukai gaba daya, bayan sun zauna Rafi'ah ta ce "Ina wuni Ya Yusuf" ya ce "Lafiya kalau our future Barrister" ta danyi murmushi kanta a kasa, sai boye cikinta take da hijabi, Jawad ya ce "Ba Ya Yusuf zakice ba ango zakice" ita dai murmushi tayi ta mike tana kallan Aliyu ta ce "Ina yini" ya ce "Alhamdulilah madam, ya gida" ta ce "Lafiya kalau" daga haka ta nufi part din Mummy, Khairiyya dai da kyar ta gaishesu dan kunyan Jawad take, ko yana waje bata fiye magana ba, itama kuma Ikram haka ne, tsoransa take gani take kamar zai iya dukanta idan tayi shirme. Hannun Khairiyya Ikram ta kama suka shiga part din Mummy, suna zaune a parlor ita da Rafi'ah suka shigo, Mummy ta ce "To kun kai musu abin sha?" Ikram ta dan ta6e baki ta ce "Khairiyya ki kai musu" wani kallo Khairiyya ta mata ta ce "Wallahi ke zaki kai" kasa kasa Ikram ta ce" Ai naga ba azo da Yaya Sameer ba" Khairiyya ta dan turo baki ta ce "Mummy kinji abinda tace ko" Mummy ta ce "Cewa nayi fa kuje ku kai musu abin sha, kuyiwa Mami magana nima yanzu zanje mu gaisa" daga haka ta mike, Rafi'ah ta ce "Mami tayi bacci ita da Imaan, bansan yanzu ko sun tashi ba naji an kira sallan la'asar" Mummy ta ce "Imaan ta koya mata baccin rana, da dai batayi" Rafi'ah ta danyi murmushi kawai, hijabi Mummy tasa ta fita a dakin, Rafi'ah ta kalli Ikram ta ce "Karku kai musu komai idan kunga dama mu yanzu zamu tafi" Ikram ta danyi murmushi ta ce "Allah sarki Antyn mu insha Allah a gidanki zamu ringa kwana da biki" mikewa Rafi'ah tayi ta dauki veil dinta ta shiga daki, ba jimawa ta fito sai tayi kyau sabida ta shafa powder da lipstick, Khairiyya ta kamo hannunta ta ce "Safe journey Anty, sai munzo next week" ta ce "To Allah ya kaimu, Ikee bye bye" hannu duk suka daga mata sannan suka fita tare, part din Mami ta shiga ta mata sallama sannan ta fito suka fita parking lot, Yusuf na shirin fita suka fito, Rafi'ah ta daga musu hannu ta ce "Safe Ya Yusuf" ya ce "Alright sis" daga haka ya kashewa Khairiyya ido yaja motar suka fita, da sauri ta dauke kai Ikram nata dariya. Bude hannaye Jawad yayi yana kallan Rafi'ah, ta karaso a hankali ta shige jikinsa, ya rungumeta, kallan su Ikram yayi ya ce "To mungode bye bye" kansu duk a kasa suka juya, Ikram ta dan ta6o Khairiyya kasa kasa ta ce "Yayanmu yanzu baya kunya" Khairiyya ta danyi dariya ta ce "Ya kai Yaya Sameer?" Duka ta kai mata tayi saurin kaucewa ta shige gida. _2 weeks ltr_ Su Ikram ne zaune a daki da friends dinsu suna ta pictures, sunyi kyau sosai cikin kayansu iri daya, bude dakin akai Rafi'ah ta shigo da warmer a hannunta, sosai tayi wani mungun kyau sai sheki take, ga cikinta ya fito sosai cikin gown din jikinta, juyawa Khairiyya tayi tana kallanta ta ce "Wooow Antyn mu u look so cute" Rafi'ah ta danyi murmushi tana amsa gaisuwar da friends dinsu ke mata ta ce "Ai kune da kyau Khairi, Amare irinku haka kyawawa" dariya suka danyi Ikram ta ce "Pls Anty Yaya ya fita ne?" Rafi'ah ta ce "Yana daki, is anything wrong" kamar zatai kuka ta ce "Dama zamuje Saloon ne kuma naji dazu yace baxamu sake fita ba sai za'aje kamu" murmushi ta danyi ta ce "Zan mishi magana, sai drivernsa ya kaiku, ga abinci nan kuci" daga haka ta juya ta fita, daya daga cikin friends dinsu ta ce "Woow Antynku ta birgeni Ikram, kyakkyawa ce" Ikram ta danyi murmushi ta ce "To ko zaki dawo ku zauna tare" dariya sukai sosai sannan Khairiyya ta jawo warmer da plate ta fara zuba musu abincin. Tana bude dakin ta sameshi gaban mirror yaci Ash shadda yana saisaita hular kansa ya juyo suka hada ido, ta danyi murmushi ta karasa gabansa ta ce "Masha Allah Yayana me kyau" rungumeta yayi yana shakan kamshin jikinta ya ce "I love u wife, inasan kullum in dinga jinki a jikina, i don't want to miss u even for a seconds" daga haka ya shiga kissing dinta passionately, bayan seconds ta zame jikinta tana dariya ta ce "Naki yawan" ya ce "Pls" juyawa tayi ta koma bakin kofa ta ce "No pls, Yaya su Ikram zasuje Saloon" ya ce "Let them, amma daga nan su dawo" ta ce "To, bakamin fishi bako?" Ya ce "Uhm" juyawa tayi tana murmushi ta fita a dakin, kasa kasa ya ce "I will caught u". Karfe 5 na yamma aka shirya amare tsaf cikin kayansu iri daya aka tafi wajen kamu, kowa da kowa ya tafi amma banda Rafi'ah dake hannun Jawad, tana zaune bakin mirror daure da towel tana turo baki ya fito a toilet, ta dauke kanta taci gaba da abinda take, kusanta ya karasa ya rungumeta ta baya ya ce "I'm sorry wife" kin kulashi tayi sai dai hawaye ya taru tap a idanta, ta zame jikinta a hankali zata tashi ya ce "Won't u pardon me Baby, yau fa throughout baki kula dani ba" kafin tayi magana hawayen idanta ya shiga sakkowa, ya rungumeta sosai yana jijjigata ya ce "Kiyi hkr dan Allah, bari na tayaki ki shirya mu tafi" ba musu ta zauna ya fara mata drying kanta yana mata combing dinsa, bayan sun gama ya dauko kayanta dake kan gado ya ce "Should i help?" Ta daga masa kai, daga haka ya tayata ta shirya, gaban mirror ta zauna ta fara make up shi kuma ya fita zua dakinsa, within few minutes ta gama make~up dinta me kyau, ta dora dankwalinta sannan ta feshe jikinta da turare ta dauka veil dinta ta shafa, woow masha Allah tayi wani sanyayyen kyau, side bag dinta ta dauka ta lankaya sannan ta fita a dakin, tsayawa tayi tana kallansa ganin yadda yayi kyau, ya sakar mata murmushi ya ce "Masha Allah, zamu haifa cute babies insha Allah" murmushi ta danyi ta dauko wayarta a jaka tana kallan screen din, ya ce "Who's calling?" A hankali ta ce "Ameera" daga haka ta dauka wayar, Ameera ta ce "Ban ganki ba" ta ce "Ina hanya Amarya" daga haka ta danyi murmushi tayi hanging call din, Jawad ya ce "Ta kusa aure ne?" Ta ce "In the next 1 month zatai aure" ya ce "Allah ya sanya alkhairi" ta ce "Ameen" daga haka ya bata side hug suka fita. Suna shiga wajen kallo ya dawo kansu saboda yadda sukai kyau, ta dan zame hannunta a cikin nasa ta nufi inda Ameera ke zaune, Imaan ta taso da gudu ta rungumeta ta ce "Look at Papa" ta nuna mata Yusuf dake gefen Khairiyya a high table, ta daga musu hannu tana murmushi sannan ta zauna tasa Imaan a cinyarta, Ameera ta ce "Kuma kika bar Ogan a gefe" juyawa tayi taga yana zaune gefen Aliyu suna hira, ta juyo sannan ta ce "Gashi ga abokinsa nan, ina Ogan naki ke?" Ameera ta ce "Ya tafi Kaduna kuma yayi niyyar zuwa wallahi" Rafi'ah ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya" ta ce "Ameen, wai yaushe zaki haihu musha suna?" Rafi'ah ta ce "bayan auranki da wata 1" Ameera ta ce "Kina nufin sauran wata 2" ta ce "Insha Allah" Sosai da sosai akaci akasha sannan akai hotuna kowa ya watse. Washegari ya kama Saturday karfe 1 aka daura auren Yusuf da Khairiyya da Sameer da Ikram, bayan 'yan daurin aure sun dawo akai hotuna sosai. Da Daddare kuwa bayan Isha aka fara shirye shiryen kai Amare, gida daya aka kaisu kowa da nata part din, gidan yayi mungun haduwa, suna kuka haka aka barsu kowa ya watse, Rafi'ah ta musu nasiha sosai sannan ta basu misalai kala kala ciki kuwa harda abinda ya faru da ita, sanda ta tashi tafiya saida suka sata kuka itama, da kyar ta daure ta karasa mota ta shiga, Jawad dake zaune yana jiranta ya ce "Allah ya basu zaman lafiya, muma muje muci namu amarcin" harara ta dan 6alla masa ta turo baki ta maida kanta gefe, yayi murmushi yana shafa beard dinsa yaja motar suka tafi. *4 YEARS LATER* Yara ne guda biyu a compound din gidan suna wasa akan keke, kana kallansu kaga twins ne saboda kamar da suke, fitowa Rafi'ah tayi tana kallansu ta ce "Oya you two should come in" macen dake kallanta ta ce "Momma we are not hungry" Rafi'ah ta dan harareta ta ce "I'm not talking of food, Oya Aisar carry your bike it's cloudy" sauka yayi akan keken yana kallan Aira dake turo baki ya ce "Wai kuka zakiyi?" Rafi'ah ta kalli cute girl dinta ta ce "What again daughter?" Kamar zatai kuka ta ce "I want to see my Papa" dan tsaki taja a hankali ta ce "He will soon come back" daga haka ta kama hannunsu suka shiga ciki. Suna zaune a parlor sunyi pillow da cinyar Rafi'ah sukaji horn, a tare suka mike suka fita da gudu ta danyi murmushi ta bisu da kallo. Parking lot suka nufa da gudu, suna tsaye suna ta tsalle har Jawad yayi parking, ya fito yana kallan Imaan dake faman turo baki ya ce "U close the car idan kin gama fishin" daga haka ya jefa mata key din motar ya nufi wajen kids, da gudu suka dale jikinsa suna dariya, ya ce "How are u my twins?" Suka amsa da "Fine" daga haka ya sauke su ya kama hannunsu, Aisar ya ce "Papa Anty Imaan bata sauko ba" ya ce "She will come in" daga haka suka nufi cikin gida, Rafi'ah na tsaye bakin kofa tayi wani mungun kyau, ya bata light hug sannan ya zauna ya ce "Sannu da gida" ta ce "Sannu da dawowa, ina Imaan?" Ya ce "Tana mota, fishi takemin na hanata zuwa birthday gobe" Rafi'ah ta dan ta6e baki ta ce "Ta gayamin dazu nace saita tambayeka" ya ce "Just forget, banasan fita yawo daga yanzu, duk da kaita za'ai but i don't want her to be going out anyhow" ta danyi murmushi ta ce "Allah ya kyauta, Mami na gaisheka" ya ce "Ke kika daukosu a school ne?" Ta ce " Dazu dana tashi a aiki naje na daukesu, Mummy tace a kaisu weekend" ya ce "Allah ya kaimu" ta ce "Abinci fa?" Ya ce "Let me bath first" daga haka ya mike, dai dai nan Imaan ta shigo rike da school bag dinta, fuskarta ko walwala babu tana ta faman turo baki ta nufi upstairs, kama hannun Rafi'ah Jawad yayi ya ce "Imaan kamar ke a da, saam halayanki ta dauko" ta danyi murmushi tabi bayansa suka haura stairs, dakinsa suka shiga ya juyo yana kallanta ya ce "Zaki tayani ko?" Ta dan zaro ido ta ce "Me din?" Ya ce "Wanka" ya karashe maganar yana kashe mata ido daya, ta ce "Noo, na bar kids dina downstairs" ya ce "Ba cartoon suke kalla ba, just let them" ta dan noke kafada ta ce "No, sai ka fito sweetheart" daga haka ta jawo masa kofarsa tana dariya, dakin Imaan ta shiga ta sameta zaune bakin gado tana danna laptop, Rafi'ah ta zauna a gefenta ta ce "Meyasa bakyaji Imaan, do u mind kiyi tasa Daddynki magana ne" ta dan girgiza kai a hankali ta ce "Ai dama cewa yayi na tambayi Papa kuma shima yace bazanje ba, Momma she's a good friend of mine fa" Rafi'ah ta kamo hannunta ta ce "That doesn't mean kiyi musu fishi, ki kira Daddy ki bashi hkr sannan ki samu Papa a daki anjima, be a good daughter pls" dan murmushi tayi ta rungumeta ta ce "Thank u Mum, and i love u" Rafi'ah ta dan bubbuga bayanta sannan ta mike ta fita. Da daddare Jawad na zaune a bakin gado yana aiki a laptop Rafi'ah ta fito a wanka, ya ce "Yanzu Imaan ta shigo" ta juyo tana kallansa ta ce "Meya faru?" Ya ce "She apologize, banda abin Imaan ma nawa suke da har zataje birthday, she's just 9 years fa" Rafi'ah ta ce "Ahaaa ai sun zama 'yammata, nan da few years zaka fara siyan gado" ya dan harareta ya ce "Karatu zatai" bata ce komai tana ta murmushi tasa night gown dinta, gefensa ta zauna ta dora kanta akan kafadarsa ta ce "Sweetheart Awara xanci" ya dan zaro ido ya ce "Awara Fatima?" Ta ce "Yes" rungumeta yayi ya rife laptop din ya ce "Ko dai mun sake samun twins ne?" Ta dan harareshi ta ce "Not now" ya hade bakinsu yana kissing dinta tayi saurin mikewa tana dariya ta nufi kofa ta ce "Good night Yaya i'm spending my night in the other room" daga haka ta masa gwalo, ya mike yabi bayanta ta juya da gudu kafin ta kai kofa ya rukota tana ta dariya ta ce "Wait wait let me close the door" yana dan saketa ta kara sauri ya kara rikota ya rungumeta, silently ya ce "I so much love u wife" _Alhamdulilah anan na kawo karshen littafina me suna *SHARIK HAYATY*, ina rokon Allah ya yafemin kuskuren da nayi 🙏🏻 abinda na rubuta daidai Allah yasa ya amfani al'umma._ *_My dear Ilham, Khadijah (KK) 😘 i luv u with full of respect sisters, wallah words only can't express how much i love u, u have been supporting me right from the beginning, wallah i luv u 🥰_* *_Our Sajeeda i luv u also 😊 And again Lubabatu Kaseem and Zarah can't forget with u people thanks for d gift sisters 😍 Finallay the members of FSM grp and LIFE PARTNER FANS grp, I so much appreciate with ur comment Fans, can't mention u oll, ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke, da wanda na sani dama wanda ban sani ba,, ni kaina i don't want to miss u, kusani a duk inda kuke FATIMA ZARAH na yinku over and over, oneluv* 💕 *💃🏻💃🏻 sanku na daban ne ina Kaunarku sisters, thanks for the support and comments 😘 can't mention u but i know u oll, Teemarh na sanku bila adadin 💗_* _08103810398_