Laifin waye...?, Laifin wayeeeeee Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai Ya Allah ka bani iƙon fara wannan littafi Lafiya in gama lafiya Allah ka ban iƙon Rubuta dai-dai da fatan da za'a ɗau darasin dake cikin Wannan littafi domin ya haɗa komai Inna CE komai ina nufin komai Gargaɗi!!gargaɗi!! Ban yarda wani ko wata ya canza min Labari ba ko mai da min document Ko masu YouTube channel su mai da Min audio duk wanda yayi haka Hmmm zai fuskanci fushin hukuma Wannan labarin kirkirarre ne duk duk wanda yaga yayi dai-dai to ya ɗauka Arashine....... *TSANANIN RAYUWA* *NA MARUBUCIYA *A'ISHA YAHAYA TANKO* _Wannan littafi yana ɗauke da abubuwan daban-daban na tausayi da Al'ajabi nasan idan ki/ka karanta sai ka zubar da hawaye😭😭_ Fatima da Sadiya ne zaune a ƙofar wani katafaren gida kallo ɗaya zakai musu kasan suna neman taimako. Na taka burki ina ƙoƙarin fitowa daga cikin motar naji sautin muryar ɗaya daga cikin su tana cewa. "Ke Sadiya mu gudu kar ya sace mu". Turus nayi jikina a sanyaye na jingina a jikin murfin kofar,ina saƙa abubuwa a zuciyata har na dena kallonsu saboda irin gudun da suke yi. _Wannan shine rashin sani wanda yafi dare duhu da kun tsaya zan taimake ku amma rashin sanin waye ni yasa kun yiwa kanku in sha Allah nayi alƙawarin zai taimake ku aduk inda kuke._ Inji Yusuf lokacin da yake furta wannan kalaman a cikin zuciyarsa. Yana gama faɗa ya shigewarsa mota ya tada ya fara tafiya a nutse yake toƙi har ya isa cikin gida a falo ya tarar da Amina tana kwance tan "Sannu sarauniyar mata,ana sana'anarne baki san bama nazo bare kizo ki tare ni ina yaran ne banji motsin su ba,ko basa nan ne?". Ta ɗago kai cikin sauri tace. "Sannu da zuwa Hubbi sun gama cin abinci sukai bacci nima kai nake jira to ya hanya ko duk gajiyar ce tasa na ganka haka ko yunwa ce?". Inji Amina. "Duk abinda kika faɗa akwai a tare dani yanzu inaso kafin ki kawo min abinci ki haɗa min ruwan dumi nayi wanka". "To Hubby duk abinda kakeso yanzu za'ai maka shi". Ga ci gaban Tsakanin Rayuwa Ta karashe Maganar tare da mikewa tsaye ta nuni bayan gida tana kokarin haɗa masa ruwan. Tunanin yaran nan ne ya dawo masa ji yai hankalinsa Yayi mutuƙar tashi saboda ganin karancin shekarunsa shin ta ina zai sami mafitar da abinda ya ƙudura acikin zuciyarsa ji yai an tsaya akansa ana magana da cewa. "Dama ni nasan akwai wani abu dake shirin ɓoye min shi yanzu alamu sun fara nunawa tunda ɗazu na jima akanka amma baka sani ba,to bama wannan ba yanzu ka tashi muje na gama haɗama ruwan wankan". Cewar Amina. Tashi yayi a sanyeye ba tare da yace uffan ba bakinsa ya gaza cewa komai Toilet ya dosa cikin ƙankanin lokaci ya kammala komai. Haka ya iske ta afalo ta haɗa masa abinci kala -kala nan ya kwasa. A can riga kuwa Fatima ne da Sadiya zaune cikin yana yin damuwa. Inna tace "Nifa bana san irin wannan shirman naku ai gashi nan kun dawo baku samo mana ko kanzo ba ga kawunku tunda ya fice har yanzu ba'aji duriyarsa ba ko yana raye ko yana mace Allah ne masani mi dai zan tsunduma cikin burni don na samo mana mafita wannan rigar tamu ba'a taimakon mu sai mun fito a dinga zunbe mu wai harɗo ya tafi ya bar mu cikin kunci da wahala". "Nifa Inna nayi alƙawarin a wannan lokacin zan samar miki da farin ciki amma inaso ki bari na dinga fita ni kaɗai saboda ki gane irin kwazo nah". Inji Sadiya. "Bana san rawar kai kinsan mutanen burni basu da kirki kar su sace ki kamar yanda suka sace kawunku harɗo ku dai yi haƙuri wata rana sai labari". A can gidan Yusuf kuwa yana kwance a falon Amina ta fito daga cikin ɗaki wai ka fasa zuwa rigar ne. "Cewar Amina. "Zanje hutawa nake ne Musa ne nake jira ya fini sanin ta kan rigar. Taku har kullum *A'ISHA YAHAYA TANKO* 💱💱💱 LAIFIN WAYE 💱💱💱 *Story and Writing By* *AISHA YAHYA TANKO*✍️ ~Page~ 2 Dogon suma Hauwa'u ta sake yi cikin sauri Baba Sa'a ta fara kokarin yayyafa mata ruwa cikin kidimiwa umar wanda tuni ya jima da suma a tsaye ji sukai an turo kofar dakin da karfi wanda gaba gaba yasa suka bi kofar da kallo likitoci suka shigo a gigice jin karar Hauwa'u da sukai sun tsaya a bakin gadonta suna tambayar dalilin da yasa ta haka Baba Sa'a ta nuna Umar da hannun ta. "Gashi nan shine yake so ya dawo muku da aiki naya tace bata san ganinsa a wannan wajen Amma yaki fita dan Allah ku fitar dashi daga cikin asibitin nan". Tana gama fadar haka ta maida dubanta ga Hauwa'u wadda ta dan fara bude idonta a hankali tana bin kowa da kallo, likitocin da suka bi Umar da kallon mamaki daya daga cikin su yai masa nuni da hannu akan ya fita daga cikin dakin fita Umar yayi jiki a sanyaye. Sannu Baba Sa'a ta shiga yiwa Hauwa'u fatana lafiyarki ta dore. Likitan dake tsaye ya dubi Hauwa'u wadda take kwance akan gado yace. "Ki rage damuwa karki fama ciwonki kinji, ki sani cewa a yadd kike din nan ba'a so ki kara shiga damuwa". Yana gama fada ya juyo da kallonsa ga Baba Sa'a inaso ki biyoni office yanzu zan miki tambayoyi. Ta amsa da toh suka fice daga cikin dakin tabi bayansu. Acan office din Likita na zaune akan kujerarsa yana yiwa Baba Sa'a tambayoyi. Baba Sa'a ta dan'nisa kadan' gaskiya laifina na shi wnnn mutumin dana ce ka Kora dazu shine wanda yai sanadiyar faruwar ciwon Hauwa'u dan'mijina ne tun Hauwa'u tana karama ya nuna yana santa, duk wasu abubuwa kala-kala na yara yake kawo mata duk abinda Hauwa'u take so shi zai mata tunda ni amana ce awajena yarinyar Kanwata ce tun da aka kawo ta yaye take hannuna har lokacin da Allah yasa ta kai shekaru 15 nan maza sukai nuna ra'ayinsu game da auren Hauwa'u ni kuma na tsaya tsayin daka akan naga ta amince da Umar ganin irin kulawarsa akanta ba yadda na gama komai na aurenta na shaidawa Mahaifinsa na tsaida ranar auren Umar da Hauwa'u.murna wajen Malam Sule ba'a cewa komai sai san barka ranar na kira Hauwa'u daki nai mata fada sosai akan ta bi mijinta shine aljannarta ta amince naji dadi nasa mata albarka muka kaita dakinta washe gari Umar ya shigo ya iskeni a tsakar gida na lura da fuskarsa ba kamar yand na saba gani ba muka dai gaisa a haka ya nufi wajen Mahaifinsa. da ya fito ne nake tambayarsa ina Hauwa'u nan yace. "Tana nan kalau". "ka gaisheta". Shine abinda na fada masa Amsamin yayi a dakile ya fice daga gidan naci gaba da aiwatar da aikina amma zuciyata cike da zullumi a haka na gama gudanar da aikina na wunin ranar. Aisha Yahya Tanko✍️ *AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻* ®️🪄 _(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._ *🗻A•W•A🗻* *KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬* ~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~ *NA MARUBUCIYA AISHA YAHYA TANKO✍🏻* *PAGE* 3 ```Rashin comment dinku yana sagar min da giwa, kodai book din baya muku dadi ne``` Na koma dakina na iske Malam Sule yana gabatar da sallah na sami waje na zauna daf da shi na jira ya idar yai addu'a muka shafa a tare yayi Jim kafin yayi magana na dan yi karfin hali nace. "Malam lafiya kuwa naga Umar ya canja kamar ba shi ba.ko dai akwai matsala ne?". Malam Sule yayi gyaran murya yace. "nima na lura da hakan amma nasan baze wuce gajiar biki ba, kinsan yaran yanzu sun san garce da yawa basa san wahala sosai". hakane malam. shiru na lokacin kadan'ina share kwallar data cika min kuncina. Likita ya zare glas din dake fuskarsa yana tsane gumi da hannusa zuciyarsa ta fara raya masa abubuwa da yawa Akan Hauwa' ya dubi Inda Baba Sa'a take tace. "naji dukkan bayananki amma har yanzu ba'a zo abinda nakeso naji....". Be karasa maganar ba wayarsa ta shiga ringing hankalinsa ya dawo kan wayarsa hannu yasa ya dauka ya kara a kunnensa ya fara magana. "eh ina office subhanallhi ganin nan zuwa karku taba shi ku bari na kara so". mikewa yai tsaye a gigice yana dudduba files da suke gabansa ya dubi Baba Sa'a ki koma wajen yarinyarki zan nemeki zuwa anjima kinji yanzu wani mara lafiya zan duba yana bukatar taimakon gaggawa. Allah ya bashi lafiya bari na koma wajenta ko zata bukaci wani abu. suka fito tare da Likita. Hauwa'u ta isheni tana bacci ta gyara mata kwanciyarta ta zauna a gefan gadon tana dubanta fuskarta cike da tausayawa murda kofar dakin akai ana kokarin shigowa Nurse ce ta shigo sanye cikin uniform hannunta rike da tulun magunguna ta tsaya abakin gadon tana ya nutse fuska " Haba baiwar Allah dama har yanzu ba'a gyarawa yarinyar nan jikinta ba ko so kike mu zamu gyarata to kiyi kokari ki gyara mata tun kafin ta doyi kina jina koh ga maganinta na kawo idan ta farka ki bata tasha amma ki tabbata sai taci abinci ta koshi". Tana gama fada ta juya ta fita. Godiya Baba Sa'a yi tana cewa insha Allah tana tashi zan gyarata bama sai an kara mgn ba. Hauwa'u ce ta bude idonta a hankali ta dubi Baba Sa'a "wai daman kina nan". yawwa w ai gwanda da kika farka inaso na gyara miki jikinki yadda bazan fama miki ciwon ba kinga an fara mgn akan rashin gyaran da ban miki ba. "Wallahi gaba daya jikina ciwo yake min kamar an min duka". Shine abinda Hauwa'u ta fada tana yamutsa fuska, taci gaba da cewa. "Dan Allah ki dena barin bakin kumurcin nan yana zuwa wajen a, na tsane shi zan ka she..... Hannu Baba Sa'a tasa ta rufe bakinta tana mamakin maganar data fito daga bakin Hauwa'u. "Haba Hauwa'u ' me yasa irin wadannan kalaman suke fitowa daga bakinki daga yanzu kar na sake jin kinyi maganar kisa wlh baki fini jin haushin abinda Umar yai miki ba ina jin abin a zuciyata tunda laifina ne, amma naga alamar nadama a fuskarsa kamata yayi muyi sama sassauci sannan mu roki Allah ya baki lafiya". Tana gama fadin hakan ta rike hannun Hauwa' tana kokarin tashinta zaune. Cikin shashshekar kuka tace. "shikenan Baba duk abinda kikeso shi za'ai amma fa zuciyata tana shiga damuwa a duk lokacin danai tozali dashi na kanji kamar na shakeshi kowa ma ya huta ki duba kiga tunda muka Asibitin nan babu wanda yazo duba ni daga bangarensa hatta Malam dana daukeshi a matsayin mahaifina shima be zo ba to iri-iren wadannan abubuwan sune suke da muna, ace dan' cikinka yayi barna amma ka kasa cewa komai". ki dai bar wnnn maganar idan sunzo lafiya zasu baki ko me duk ki ciresu daga ranki ki fuskanci abinda yake gabanki, ki tashi mu shiga bayan gida na wanke miki jikin ki. Cije lebe Hauwa'u ta kama gadon tana yunkurin mikewa tsaye Baba ta taimaka mata suka shiga bayan gida. ~kuna ina masu sha'awar siyan cup cake, birthday cake kai duk irin cake din da kuke so, zaku iya samu mu ta wannan number~ 👇 08169495093 *Aisha Yahya Tanko*✍️ *TSANANIN RAYUWA* *NA MARUBCIYA A'ISHA YAHAYA TANKO ❤️🌸🌷🪷* *PAGE 4* Haka ta daure zuciyarta ta shige cikin shagon saboda tsananin yunwar da ta addabeta amma ya zatai da kanta tunda ranta tunda sun rasa wadanda zasu taimaka musu, ko da abincin da zasu dinga ci acikin rigar su ko wanne yana ƙyashin yai musu komai duniya ina zaki damu ace mai hali ba ze taimaki marar hali ba,duk tana faɗin haka a ƙasan zuciyarta ji tai ana cewa. " haba ƴan mata ke kuwa wani irin tunani kike tun dazu na kawo miki abinci amma baki san na ajiye mkki ba, inaso ki sani komai yai zafi maganinsa Allah don shine yake saukar da ciwo a duk lokacin da yaga dama sannan kuma ya kawo maka sauki a cikin lokaci ƙanƙani". Cewar Matashi. Hawaye naji suna kwarara daga ƙasan kuncina hannu nasa na share ban wani bata lokaci ba naja kwanan gabana kafin kace maye tuni na share abincin nan na kora da ruwa sannan naji nutsuwata ta fara dawowa jikina nace araina. _Allah sarki ko su Inna da Fatima sun sami abincin da zasu ci dan ni daga nan zan ƙara nutsawa cikin birin har sai na cimma burina_ "Dan Allah inaso ki sanar dani sunanki, da kuma inda kika fito da kuma dalilin da yasa kika zaɓi barinki gida, nace miki ni har ga Allah zan taimake ki ne dan bana san rayuwarki ta shiga matsalar a yadda kike da ƙarancin shekaru kinji". Cewar Matashi. Wani irin ƙarfi naji ajikina da nace. "Ni wallahi na fito ne dan samar mana mafita nida Inna ta da kuma yar'uwata mun gaji da zaman yunwa acikin rigarmu,mun kasa samun wanda zai share mana hawaye tunda Babanmu ya gudu ya bar mu, gashi kuma an sace mana shanunmu balle mu siyar mu biyawa kan mu buƙata shine na yanke shawarar da zan faranta ran Innata". Shiru Salisu yayi yana tunanin ta hanyar da zai ganar da Sadiya yadda zata koma gida ba tare da wani ya ɓata mata rayuwa ba, duniyar yanzu babu gaskiya a cikinta burin masu kuɗi su ɓata musu rayuwa sannan su taimakeka. Salisu yace. " Ni dai atawa shawarar ki koma gida yanzu nayi alƙawarin in sha Allah zan dunga kawo muku abincin da zaku dinga ci sau uku a rana idan kin amince dani ni dai Alkairi nake nufinki dashi ba sharri ba zan rufe shigo ki muje rigar taku muyi magana da Innarta taki kinji". "To shikenan babu matsala amma dan Allah kar ka sace ni naji ance mutanen burni sata mutane suke yi, dan suyi kuɗi ni bana san kaima ka sace ni". A ɓangaren su Yusuf kuwa yana zaune akan doguwar kujerar yayin da Amina take shigowa da ƙwaryar nonon,bakinta yaƙi rufuwa dan murna ta zauna kusa dashi tana cewa. 'Habibi kaji garɗn Nono nan kuwa ba alamar tsami ko ɗaya, kasha kaji sai kace madara aka zuba a cikinsa". Yayi murmushi yace. "Ki kwantar da hankalinki ko yanzu kika shanye nayi alƙawarin zan koma na siyo miki tunda kina so". Cewar Yusuf. Wata irin ƙara tasa kamar zata tashi sama. " Da gaske kake Habibi na ai kuwa na gode sosai Allah ya bar kauna bari na dama ma fura kasha ka ƙoshi". tashi tayi cikin sauri ta nufi kichen. A bangaren gidan Alhaji me rumbun Allah ya isa kuwa yana zaune akan wata kujerarsa ya sa bakin glas yana karanta jarida yana lura da takun mutanen da suke wucewa da waɗanda suke neman taimakon sa amma yayi halin ko un kula dasu. A kan hanyar su Salisu da Sadiya kuwa tuni ya fara nuna gajiawarsa ta nisan tafiyar da suke ga kaya a hannunsa ita ko Sadiya ko ajikinta tunda ta saba tafiyar bata jin komai a haka suka ƙarasa cikin rigar,shigarsu ke da wuya suka fara karo da mutanen rigar kowa yana binsu da kallon mamaki masu zunde nayi masu dariya nayi suna Isa ne nan suka iske Inna tana shara duk ta haɗa gumi, Fatima kuma tana kukan yunwa ta dafe cikinta Inna ce ta saki tsintsiyar dake hannunta tana bin su da kallo. Taku har kullum. *A'isha Yahaya Tanko.* *LAIFIN WAYE* *AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻* ®️🪄 _(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._ *🗻A•W•A🗻* *KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬* ~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~ *NA MARUBUCIYA AISHA YAHYA TANKO ✍🏻* *PAGE* 5 *_______📖* Haka na k'araso cikin d'akin mu na iske Hauwa'u ta gaji da jirana har bacci ya d'auketa na sami waje na zauna a haka nima baccin yai awon gaba dani. washe gari ne d'aya Likitan ta shigo d'akin mu, ta tadda Hauwa'u tana zaune a bakin gado taji dadin haka rike hannunta tai tana cewa Allah mun gode, d'iyata ta sami lafiya saura kiris muyi sallama. ji sukai Hauwa'u tasa dariya wadda sautinta ya mamaye cikin d'akin gaba d'aya suka bita da kallo. Baba Sa'a taja tsaki tace "sakar kawai ai daman burinki kenan kina damuna da rigimar sai mun koma gida naga ajiyar da kikai duk kin cika mana kunne". Lkita ta dafa kafadarta Hauwa' ke yanzu idan kin koma gida ya zakiyi da ciwon naki wasa nake miki amma dai nasan nan da wata biyar ko shida zaki warware sosai daga nan ne zamu iya cewa ku koma gida". Nan da nan Hauwa'u ta hade rai idanuwanta suka kawo kwalla. bari na koma na duba naga ko ruwan dana sawa yaron nan ya kare tai musu sallama ta fice daga dakin. Baba Sa'a ta kalli Hauwa'u ai ke koh bakya jin magana naga uwar da zaki ci idan kin koma gdn, kin dai ji abinda tace idan zaki sawa zuciyar ki hakuri kisa ba ranar sallama yanzu aka fara zama ko kukan jini zakiyi kiyi na dena rarrashinki. "Wallahi Baba kun cuceni keda Umar kune sillar rugujewar rayuwata tunda kema kin bada gudun mawa Babbage". Nan hankalin Baba Sa'a yai mutukar tashi da jin kalaman Hauwa'u "Au sharri zaki yi min to na dauka, amma dan Allah ki bar maganar nan tun kafin wani ya shigo yaji abinda kike Fad'akar". Ji sukai an turo kofar dakin tare da yin sallama Malam ne ya shigo dakin hannunsa rike da leda baka ya ajiye a kasa yana duban Hauwa'u wadda ta kura masa ido kamar bata taba ganinshi ba. "sannu yarinyar kirki ya jikin naki". da k'yar ta amsa masa. "yau dai na sameki ido biyu dan Allah ki yafewa Umar kinji kuskure dai anyi shi". " Allah ne ya kaddara hakan" . Inji Baba Sa'a. Nurse ce ta shigo cikin d'akin tana ya tsune fuska kamar kullum hankalinta ya kai wajen Hauwa'u ta saki fuska ganinta tsaf akan gado tace. "ko kefa yau haka nakeso naganki kullum dama ke me kyauce kamar ke kikai kaki amma ake barinki da kazan take". Hauwa'u tasa hannu ta rufe fuskarta. zan miki allura yanzu guda biyu sannan zan sa miki jini roba daya kuma daga yanzu wake zaki dinga ci da ganye har tsawon wata guda. ta mai da dubanta ga Baba Sa'a dama kece Mamanta koh to ki kara lura da lafiyarta tana gama fada ta gabatar da aikin daya kawota dakin ta juyawarta ta koma office. Malam yai sallama dasu, Baba Sa'a ta zauna a gefan gadon tana Jan carbi Lokaci-lokaci tana kallon yadda jinin yake tafiya har bacci ya dauketa ahaka cikin bacci taji Hauwa'u tana kwalla mata kira akan ta kirowa Nurse su zare mata robar tunda ya kare. Mikewa Baba Sa'a tai a gigice har tana kokarin faduwa kasa. *AISHA YAHYA TANKO* ✍️ *LAIFIN WAYE* *AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻* ®️🪄 _(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantarw da Al'Ummah)._ *🗻A•W•A🗻* *KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬* ~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~ *NA MARUBUCIYA* *AISHA YAHYA TANKO ✍🏻* *PAGE* 6 *__________📖 washe gari Baba Sa'a ta gyara Hauwa'u tsaf ta zaunar da ita jikin gadon, ta koma gefe d'aya ta zauna tana Jan carbi. Likita ne ya shigo cikin d'akin yana sanye cikin k'ananan kaya fuskarsa cike da murmushi ya dubi Baba Sa'a cikin girmamawa yace. "sannu ya me jikin?". "Jiki kam akwai sauki ai dole a godewa likitoci irin k'ok'arin da kukeyi wajen ceton ran mutane". Inji Baba Sa'a. ya mai da dubansa wajen Hauwa'u sannu yarinya Allah ya baki lafiya kamar kowa inji likita. "wallahi likita ta uzzira sai anyi sallama mun koma gida saboda ta gaji da zaman asibitin nama rasa yadda zanyi dare yanayi take cikan kunne da kuka". Likita ya zare glas d'in dake fuskarsa ya matsa dab da gadon HAUWA'U yace. "haba ke kuwa kin kwa san matsalar da kike ciki da kin sani da har zaki zabi komawarki gida, ki sani cewa lafiyarki itace me amfani idan kin daure kamar yau ne zaku koma gida ai duk wanda Kika gani anan ba dadi ne ya kawo shi ba yazo ne kawai don neman sauki da mafita". Ta turo baki tana matse ido kamar me shirin kuka. "Dama baki k'arasa bani labarinta ba ya kamata kizo muje office ki k'arasa bani labari". yana gama fad'a ya fice daga cikin d'akin cikin sauri. Baba sa'a ta amsa masa to gani nan zuwa tafara kici-kicin gyara hijabinta. "Nifa yunwa nake ji amma shine kike k'ok'arin fita ki barnini kadai' koh" . Hauwa'u ke fad'ar haka. Ko kallonta bata yiba balle ta bata amsa. Acan office kuma Dr Nasir yana zaune akan kujerarsa yana sa hannu a farar takardar dake gabansa, yaji an murd'a k'ofar office ana k'ok'arin shigowa ciki d'aga kansa yayi yana duban me shigowa. Baba Sa'a ce ta shigo ta rabe jikinta a bangon office d'in. Dr Nasir yai mata nuni da hannu data zauna akan kujera, nan-da nan ta zauna dama jira take. Likita ya dakata da aikinsa ya numfasa ya fuskanci Baba Sa'a kafin yace uffan sannan yayi gyaran murya yace. "Ina fatan dai kinzo da shirin zama saboda kici gaba da bani labarin marar lafiyarki". Baba Sa'a ta gyara zama tace. "To Likita ai labarin Hauwa'u yana da tsawo nasan ko kwana zamuyi ina baka baze kare ba, amma kaima ka k'ara bud'e kunnenka kaji sannan ka shirya shirin kuka nasan kafin na k'are sai ka zubar da hawaye sannan kuma zaka tsaneni". Numfasawa tayi sannan taci gaba da cewa. "zaka kaso nabar wannan asibitin dan nasan zai iya zama rana ta k'arshe wadda zaka kyamaceni, bazaka so ka k'ara jin muryata ba saboda irin gudunmawar dana bayar wajen haddasa ciwon Hauwa'u" . Dr Nasir ya dafe kirji idanuwansa suka fiffito ya mike tsaye yana goge gumin dake tsatstsafowa a fuskarsa. "Yace........... *Aisha Yahya Tanko* ✍️. *LAIFIN WAYE* *AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻* ®️🪄 _(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._ *🗻A•W•A🗻* *KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬* ~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~ *NA MARUBUCIYA AISHA YAHYA TANKO ✍🏻* *PAGE 7* *__________📖 cikin Mamaki yake dubanta yace "kina tsammanin abinda kunnuwana suka ji gaskiya ne ko yaya?, amma idan haka zanso kiyi saurin k'arasa min labarin nan". inji Dr. Baba Sa'a idanuwanta suka kawo kwalla tasa hannu tana matsewa. "idan zaka tuna tun farko nace ma bani na haifeta ba,yarinyar k'anwatace sannan ba'a san ranta ba na aura mata Umar a haka dai rayuwarta ta kasance cikin bak'in ciki da k'unci a gidan mijinta Kowa yana bak'anta ran d'an uwansa gaba d'ayan su idan ka gansu a wannan lokacin zaka tabbatar suna cikin matsala, amma ba wanda yasan meye matsalar tunda sunk'i bayyanawa lokaci-lokaci nakan lekabsu don naga lafiyarsu haka zan tai mata dabarun mu na manya ko da zanji ta sanar dani halin da take ciki amma ina bata iya furtan komai haka zan futo daga gidan ina wasi-wasi". Baba Sa'a ta d'anyi shiru na lokaci kad'an kafin ta kara magana. Dr ya koma ya zauna akan kujerarsa yana ci gaba da sauraronta. Acan d'aki kuma Hauwa'u ce kwance kan gado ta daga kai sama tana cije baki sakamakon rad'ad'in daya taso mata. Likitace ta shigo cikin d'akin ta tsaya a kanta tare dayin magana. "Lafiya Hauwa'u na ganki haka ko har yanzu tunanin gidan kike, ki tausayawa kanki irin halin da kika shiga kinsan fa dole sai anbi a hankali sannan za'a cimma buried, ina Maman taki take?". cikin karfin hali ta d'an yunkura maganar ta bata iya fita saboda ciwo tace. " tana wajen Dr wallahi yau wajen zafi yake min ji nake kamar ana barkono ake zuba min". Subhanallahi inji Likita me ya kawo haka ko kin sosa ne kinsan ba'a san tab'a wajen. "Aa kawai dai yanzu naji yana min zafi. A can office kuwa Likita ne yaci gaba da sauraron Baba Sa'a, wayarsa tai k'ara yasa hannu ya dauka ya kara a kunnensa yace. " eh gata tana office d'ina to bari muzo yanzu". ya mike a gigice yana laluben glas dinsa. itama ta mike tsaye tana dubansa me ya faru lafiya naga duk ka rud'e ?inji Baba Sa'a. *AISHA YAHYA TANKO*✍️ *TSANANIN RAYUWA* *PAGE 8* *By AISHA YAHAYA TANKO ✍️👭😨* *INA ƘARA MIƘA TA'AZIYYATA GA IYALAN AMINU S BONO DA RASHINSA DA MUKAI LALLAI MUN YI BABBAN RASHI ACIKIN WANNAN MASANA'ANTAR TAMU😭😭* "Abban Walida ina ka samo waɗannan mutanen me zasu yi a gidan nan kuma?". Inji Amina. Dakatar da ita yayi tare da daka mata tsawa yace. "Ki iya bakinki, ki kuma sani nan gidana ne dan haka zan iya kawo kowa kar na sake jin bakinki ya furta wata magana game da su inaso ki bamu wajen zama ki kuma basu abincin da zasu ci su koshi nan zasu ci gaba da zama har sai ranar da Allah ya kawo tafiyarsu baki san irin ladan da zamu samo a wajen Allah ba, shi yasa kike haka ko kin manta *WANNAN TSANANIN RAYUWAR* da ake ciki a yanzu". Inji Yusuf. Tunda ake wannan maganganu Hama ta rakube ajikin mahaifiyarta tana tsoro. Nan dai Amina tayi dukkan abinda ya buƙata saboda ba yan da zata iya ta gyara musu sashen baƙi ta kaisu ta kuma dawo wajen Yusuf ta iske shi yana wasa dasu Walida tace aranta. ``` ko wannan mutumin kamar ba shine ɗazu yake ta faman yi mata faɗa kamar zai cinyeta``` Yusuf ya dubeta yace. "Sannu da ƙoƙari har kin kammala da baƙin kenan". Nan ya kwashe labarin ƙarya da gaskiya ya faɗa mata har sai da Amina ta fidda kwalla dan tausayi. A can ɓangaren Musa kuwa tun shigar sa cikin gida tunani ya addabeshi ya kasa zaune ya kasa tsaye ina tunanin irin badakalar da Abokinsa yake yi,Khadija ce ta iske shi a wannan halin ta tsaya tana dubansa kafin tace uffan,sannan tayi gyaran murya ta ƙaraso inda yake hannu tasa ta dafa shi tace. "Haba me gida na lura tunda kuka rabu da abokinka ka shiga cikin tunani shin meye? matsalarka,inaso ka sanar dani ko akwai shawarar da zan iya taimaka maka da ita amma rashin sanar dani baze zamar maka mafita ba sai dai ma ya ƙara maka, karuwa ni dai ina me rokonka daka sanar dani pls me gidana". Musa yaji daɗin kalamanta ya saki ransa ya zauna akan kujerar nan ya bata labarin duk abinda ya haɗu da Yusuf ya ƙara da cewa. " Nikam bazan iya zama inuwa ɗaya dashi ba, tunda baya jin shawara ko banyo tunani duk abinda yayi zai iya faruwa akan Walida tunda itama mace ce". "Hakane amma dai rabuwa dashi baze zamar maka mafita ba, ka daure kaci gaba da zama dashi har lokacin da Allah zai ganar dashi kasan fa irin su Yusuf basa jin kira tunda sunyi nisa addu'a kawai itace mafita dakuma ƙara tunatar dasu amma saurin fishi ba naka bane, tunda kowa ya sanka dashi haƙuri kawai zaka ci gaba da yi bari na kawo maka abinci kaci kayi wanka ko zuciyarka zatai sanyi". Inji Khadija. Nan ta mike tsaye ta nufi kitchen ta fara kici-kicin haɗawa Me gidan ta abinci da abin sha. A can ɓangaren su Sadiya kuwa sun ƙara shiga *TSANANIN RAYUWA* gaba ɗaya rigar ba me shiga harkar su balle a taimaka musu haka suke tafi da rayuwarsu cikin yunwa da talauci ba damar su leƙo sai kaji anai musu dan kira ana cewa. Talaucine ya sa Kawunsu guduwa ya barsu tunda ya gane su da Innarsu masu ƙashin tsiya ce haka suke jin irin wannan maganganun amma basa tankawa Sadiya ce take iya tanka musu. Inna ce zaune a bakin rigarsu bacci ya ɗauke ta saboda tsananin ciwon cikin daya turnuketa Fatima tana kwance kusa da ita basu aune ba suka ji saukar ruwa a jikinsu tamkar ruwan sama. *Taku har kullum A'ISHA YAHAYA TANKO ✍️* *LAIFIN WAYE* *AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻* ®️🪄 _(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._ *🗻A•W•A🗻* *KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬* ~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~ *NA MARUBUCIYA✍🏻* *AISHA YAHYA TANKO* *PAGE 9 *__________📖 Dr ya jima Akan Hauwa'u Yana dube-dubensa daga bisani ya umarci Baba sa'a data kirawo ɗaya daga cikin Likitocin Mata. Acan kuwa Likitocin Suna tsaye sunyi cirko-cirko a bakin ƙofar Suna sauraro. Baba sa'a ta iskesu a haka ta isar da saƙon Dr. ta biyo bayanta suka rankayo cikin ɗakin gaba ɗaya Suka tarar Dr Nasir Zaune gefe guda Yana girgiza kai fuskarsa cike da damuwa Mikewa tsaye yai Yana duban Hauwa'u "a gaskiya aikin nan ya dawo Baya Sakamakon Sosa wajen dan haka inaso Yanzu a gaggauta shiga da ita dakin tiyata nan da mintuna goma saboda gujewa matsala zanje na shirya kayan aiki kafin ku kawota". Yana gama fada ya ficewarsa daga cikin ɗakin. Baba sa'a ta kurma ihu wanda ya karaɗe Asibitin baki Ɗaya. Likita tai saurin rufe bakinta tace "idan baza kiyi shiru ba ki fita So kike yarinyarki ta ƙara samun matsala to ki kiyaye". "Shikenan nayi shiru Amma dan Allah karku kashe min ita wallahi ina kaunarta kuma ita kaɗai ce ya'ta" inji Baba sa'a. " Ai dama kashe mutane Muke yi da bakinki fa mukaji kince kinci Amanarta" inji Likita. Wayarta ce tai ƙara tasa hannunta acikin Aljihun rigarta ta zaro wayar ta kara a kunnenta "ok tohm gamu nan zuwa" inji Likita ta Fara kici-kicin daga Hauwa'u da taimakon Baba sa'a suka ɗagata. Acan ɗakin tiyata kuwa Dr Nasir ne sanye da kayan aiki Yana ta gyare-gyare yaji an turo ƙofa da ƙarfi tsayawa yai Yana kallon ikon Allah ganin yadda Hauwa'u ce kwance Akan doguwar kujera duk kamanninta sun sauya tausayin ta ya kama shi. *AISHA YAHYA TANKO✍️* *LAIFIN WAYE* *AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻* ®️🪄 _(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._ *🗻A•W•A🗻* *KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬* ~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~ *NA MARUBUCIYA✍🏻* *AISHA YAHYA TANKO* PAGE 10 __________📖 Nan da nan Dr. ya Fara kici-kicin yiwa Hauwa'u tiyata. Acan harabar Asibiti kuwa Baba sa'a ce take kai da kawo ta zama kamar tababbiya Saboda irin surutan data keyi yasa Mutane hankulansu ya dawo wajenta. Kafin kace kwabo Dr.ya kammala da Hauwa'u ya koma gefe guda Yana kallonta ya lalubi wayarsa ya daddana numbobi ya kara akunnensa ya kirawo Dr zahra. Dr zahra ta shigo cikin ɗakin hannunta riƙe file ahankali ta nufo wajen Dr ta miƙa masa file ɗin hannu yasa ya karɓa yana duddubawa. "Tab nifa lamarin yarinyar nan ya Fara bani tsoro Muna murna munyi nasarar aiki Amma yanzu ta dawo Mana da aiki Baya inji Dr zahra. ya numfasa ahankali ya gyara Zamansa, "Allah dai ya rufa asiri fatan mu Allah yasa daga wannan sai kuma sallama" inji Dr Nasir ya dubi Hauwa'u wadda take kwance kamar gawa. "innalillahi wa'inna ilaiyun raju'un Dr" inji Dr zahra gaba daya suka nufi karasa gadon da Hauwa'u take kwance Dr kifa kansa yai Akan gadon.yana salati hannu yasa Yana goge kwallar. A Nan na kawo karshen Labarin kashi na daya mai Suna LAIFI WAYE mu hadu a kashi na biyu ƙofa a buɗe take ga duk me san ƙarin Bayani ya tuntubemin Akan wannan number din 08173846034 *AISHA YAHYA TANKO* *LAIFIN WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO*✍️ *PAGE 11* Gaba ɗaya suka yo kan Hauwa'u a kiɗime suna ƙoƙarin lalubo ruwan dake gefanta. Dr ne ya yayyafa mata ruwan ta ɗan motsa kadan ta buɗe idonta " Allah na gode ma da kika farka ina ne yake Miki ciwo?". Hannu Dr yasa ya dakatar da ita ya nai mata nuni data fita ta basu waje su ƙara duba jikin Hauwa'u Baba Sa'a ta fice daga ɗakin jiki a sanyaye tana waige-waige kamar mara gaskiya tayi jigum a bakin kofar ɗakin tana share hawayen da suke kwaranyowa ta ƙuncinta tasa hannun ta share . A can ɗakin da Hauwa'u take kwance kuwa su Dr ne suke duba ta suna ƙoƙarin gano abinda yake damunta a wannan lokacin. Dr Zahra ce take rubutu a cikin file ɗin dake hannun ta. Dr Nasir ne ya dubi Hauwa'u yace. "Yanzu me yake miki ciwo a jikinki?". Ta ɗan numfasa cikin ƙarfin hali tace. "jikina ne yake ciwo ji nake kamar ana sassara min shi". tana maganar ne cikin ƙarfin hali. Murmushi yayi ya dubeta yace. "Sannu ga magani nai na rubuta miki za'a siyo miki shi yanzu kisha insha Allah zaki ji daɗin jikinki fatana dai ki kula da kanki ki ƙara hakuri har kiji sauki ki koma gida hankalinki ya kwanta idan mijinki yazo kice ina san ganinshi a office ɗina akwai tambayoyin da zan masa". Yana gama faɗa ya juya ya fice daga cikin ɗakin Dr Zahra tana biye dashi fitar su ke da wuya Baba Sa'a ta nufo su fuskarta cikin damuwa tace. "Dr ya jikin nata dan Allah ka fada min halin data ke ciki kar ka ɓoye min komai". Dariya yayi me ɗauke da nuna farin ciki yace. "ki kwantarki da hankalinki na gano abinda yake damunta kuma in sha Allah ba wata damuwa yanzu dai ga magani nan ki siyo yanzu ake san tai amfani da shi". Miƙa mata takardar yayi nufi office ɗinshi Dr Zahra ta juyo wajen Baba Sa'a tana cewa. "Ya kamata kiyi sauri ki siyo mata magani tasha yanzu kuma ki taho mata da abincin da zata ci". Tana gama magana tabi bayan Dr Nasir tana murmushi. Shigarsa office keda wuya ya zare glass ɗin dake idonsa ya zauna akan kujera yana duba file ɗin dake gabansa yaji an turo ƙofar office ana ƙoƙarin shigowa. Dr Zahra ce ta shigo office ɗin ta ƙaraso inda yake ta ɗan rusuna gabansa ta ajiye masa file ɗin tana murmushi kallon -kallo suka da Dr Nasir. Ta sakar mata wani irin kallo me dauke da abubuwa. *AISHA YAHYA TANKO*✍️ *LAIFIN WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO* *PAGE 12* _Ina Amare 'yan ƙwalisa ko masu sha'awar koyon kwalliya nazo muku da sabon albishir *Hafcy-beauty-kn*,07038455700 ta shirya tsaf don gyara Amare su fito tas ta tanadi kayan kwalliya kala -kala wanda ake kira mai da tsohuwa yarinya duk mai buƙata ya tuntuɓemu a wannan Number acikin farashi me rahusa Tana gyara Amare tana koyar da ɗalibai shima cikin farashi me rahusa._ *08173846034* Dr Nasir ne yai ƙarfin hali yayi ajiyar zuciya yace. " Dr ya akai ne ko akwai wani abu ne?". Cikin kissa take magana. " A'a Dr daman zuwa nayi muyi sallama kafin na wuce gida amma idan na ƙarasa zan nemeka a waya ina fatan wayar tana kusa dakai?". Ɗaga kai yayi alamar Eh bakinsa ya gaza furta komai tun shigowar Dr Zahra ya rasa abinda yake yawo a tsakiyar kansa komai ya tsaya masa. Dr Zahra cikin ɗaga sauti tace. "Dr ko baka ji abinda nace ba naga ka tafi tunanin Hauwa'u". A firgice ya ɗago kansa yana dubanta cikin inda_inda A'a Dr jinai kaina ya sarawa. Ta ƙara matsowa daf da shi tanai masa sannu fuskarta cike da tausayi juyawa tayi a hankali ta nufi kofar fita taji ya kira sunanta cikin muryar ta bata taɓa jin wani ɗa'na miji ya kira ba,tsayawa tai cak saboda yadda taji tsikar jikinta ta tashi ƙafafuwanta sunyi mata nauyi yadda baza su iya ɗaukarta ba. "Bazaki ki bari na ƙarasa wannan aikin ba na kaiki gida ba kinji". "Na gode da kulawarka amma a halin yanzu har an zo ɗaukata". Ficewa tai cikin sauri ba tare data jira amsar da zai bata ba. Miƙewa yai tsaye yana kai da kawo acikin office ɗin ya rasa abinda yake damunshi shin ina zai jefa rayuwarsa ko ya ƙarbi tayi Dr Zahra.to shin ina zai kai soyayyar da yake wa Hauwa'u wadda yake jinta har cikin zuciyarsa a haka dai yai ta tunanina daga ƙarshe ya yanke shawarar duk yadda zai yi ya ceci lafiyar Hauwa'u ya haɗa files din dake tule akan tebur ɗinshi ya sa glass ɗin idonsa ya dai shirya tsaf ya nufo kofar fita ya murɗata yaji kamar ana ƙoƙarin shigowa cikin office dakatawa yai yana jiran me shigowa Umar ya shigo fuskarsa cike da damuwa sallama yai wa Dr cikin ladabi Dr ya bashi wajen zama shima ya zauna suka fuskanci juna na 'yan daƙiƙai kafin suyi magana. "Dama cewa akai kana san ganina shine nazo naji ko lafiya?". "Ban fahimci abinda kake nufi ba ban shaidaka ba daga ina kake kuma waya turoka?". Wajena lokaci guda ya jero masa wannan tambayoyin. Ya ɗan ɗago kai yana shafa ƙeya gumi ya fara sallama a fuskarsa duk da sanyin Ac amma be hana gumi kwarara ajikinsa ba. "Ni sunana Umar ni ne mijin Hauwa'u". Ya zare glass ɗin dake manne a idonsa yana duban shi sannan yace. "Dama kaine mijin nata to masha Allah dama wasu 'yan 'tambayoyine zan maka idan bazaka damu ba kwanaki inaiwa Baba amma taki sanar dani takamaiman abinda yake damun Hauwa'u saboda akwai sila mudai a iya bincikenmu na likitoci mun gano abinda ya haddasa mata ciwon sai dai ƙarin bayanin da muke san ji daga gare ka ina sauraronka". Cikin kiɗima da fargabar ta ina zai soma yace a ransa ranar wanka ba'a boye cibi yau itace rana ta ƙarshe da zan bayyana maƙasudun ciwon Hauwa'u saboda aga *Laifin Waye* a ciki". Inji Umar. *AISHA YAHYA TANKO* *LAIFIN WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO* *PAGE 13* _Ga masu buƙatar talla su tun tu ɓemu ta wannan Number kamar haka 08173846034_ Wani irin kallo yake masa me ɗauke da tuhuma gyaran murya kafin yace wani abu ya ɗan numfasa yace. "To Malam Umar kai nake sauraro nasan kasan dalilin da yasa nake san ganinka amma ka gaza cewa komai". Ya ɗago kansa yace. "Ina maraba da duk tambayoyin da zakai min nima in sha Allah zan sanar dakai komai game da rayuwar mu da Hauwa'u". Dr Yayi murmushi me ɗauke da nuna jin dadi. Umar ya fara magana kamar haka. "Ni dai tunda na buɗi ido naga Hauwa'u a gidan mu nasan nayi matar aure daga wannan lokacin na ɗau san duniya na ɗora mata duk da lokacin kowa zai ɗauka ƙauna ce kawai ta wa da ƙanwa nake mata saboda duk abinda take buƙata nina ke mata shi, ko take san ci ni zanyi ƙoƙari naga na siyo na bata a haka har tai girman da zata fahimci soyayyar gaskiya nake mata daga nan ta fara jan baya dani ta kuma guji duk abinda zai fito daga hannuna tun ina ganin abun wasa ne har ya zama gaskiya,ni kuma kullum ƙaunarta ƙara shiga raina take ga samari a waje suna tururuwa a kanta a duk lokacin dana ga Hauwa'u da wani ji nake kamar na fille kansa na huta, abokaina suka bani shawara ko tana so ko bata so nasan yadda zai ai na aureta da zarar anyi auren zata fara sona naji daɗin shawararsu nabi duk hanyar da zanbi don naga na mallaketa nasami goyan bayan Baba Sa'a tai ruwa tayi tsaki hatta Babana dan kallo ya zama bayan anyi bikin mu ne sai matsala ta ƙara kunno kai Hauwa'u kwatata taki bani haɗin kai ni kuma abin yana damuna narasa wanda zan faɗawa kawai sai na yanke shawarar sanar da Baba Sa'a nan take ita ta nuna ɓacin rai a fili ta zo gida ta iske Hauwa'u tai mata nasiha ta tafi bayan ta tafi ne Hauwa'u ta nuna ita wannan nasihar bata shiga zuciyarta ba, ni kuma gashi nasha magani ƙarfin dana ke jina kamar matashin doki da shigata dakin na iske baccin ya fara ɗaukarta banyi wata-wata ba na haikefa wanda tun tana motsin yadda zata ƙwaci kanta har ƙarfinta ya fara karewa ni kwa ji nake kamar ana ƙara min wani sabon ƙarfin ajikina nan take naga jini ya fara tsattuwa ajikinta daga nan hankalina ya dawo jikina gabana yai mummunan faduwar ganin bata motsi ga jini be dena zuba ba na ɗauketa a suma na kawo ta wannan Asibitin naku na komagida na sanar da Baba Sa'a halin da ake ciki, itama hankalinta yayi mutukar tashi". Daga nan na tsorata na fara dana sanin abinda na akaita mata. Dr Nasir yace. "To ga irinta nan ka haddasa mata cutuka idan an sami sauki anan sai kuma wani abun ya ɓullo,har yanzu kana san zama da ita idan ta sami sauƙi?,ko yaya amma inaso ka gane itafa rayuwar aure sai anbi ahankali balle a wajen yara dudu shekarun Hauwa'u nawa da har zaka gwada mata karfi inaso ka sani cewa kaine sila ba kowa ba". _AISHA YAHYA TANKO✍️_ *LAIFIN WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO* _KASHI NA BIYU_ *PAGE 14* A can gida kuwa Dr Zahra ce ta gama ƙulluwa ganin irin kiran da takewa Dr Nasir amma baya ɗagawa ta kwanta akan doguwar kujera ta yanke shawarar idan har yana ganin kiranta be daga ba kuma be biyo kiran ba tasan me za tai masa saboda ya fahimci abinda take nufi yake shareta be san ita wace ba, shi yasa yake mata haka ta miƙe tsaye ta nufin toilet tayo alwala ta zo ta gabatar da sallah tare da yin addu'ar neman nasara akan Dr Nasir tashi wayarta tai ƙara da sauri ta ɗauki wayar ba tare da ta duba sunan ba muryar ƙawar Humaira taji akan wayar cikin karfin hali take bata amsa. "Haba Dr ina kika shiga ne kwana biyu gashi kuma yanzu naji muryar ki kamar baki da lafiya gaskiya akwai matsala. Wata irin dariya ta ƙaƙaro me ɗauke da sigar damuwa. "Wallahi Humaira kawai gajiya ce kinsan aikin namu sai a hankali fa, kedai Allah yasa mu dace". a haka sukai sallama ta ajiye wayar tana bin ta da kallo. A can office kuwa Dr ne zaune shi da Umar suna ci gaba da tattaunawa akan ciwon Hauwa'u Umar yace. "Naga tun ɗazu anata waya baka dagawa gwanda ka daga kaji ko lafiya". Ya dube shi yana murmushi yace. "Ba ruwanka da ko kira nawa za ai min ni dai fatana ka sanar dani tambayar dana ke ma akan Hauwa'u shin kana ganin zaman ku da ita ya ƙare ko zaka ƙara zama da ita idan taji sauƙi sosai ko yaya?". Yana maganar ne cikin tsare shi da ido daya yi. "A gaskiya ina mutukar ƙaunar ta amma bana jin da sauran zaman mu a gaba na gama yanke shawarar tana samun sauki zan sawaƙe mata amma ba'a san raina ba kawai ina ganin hakan shine zaman lafiyar mu". Inji Umar. Wata ajiyar zuciya yayi Dr Nasir yayi yace. "To shikenan Allah yasa hakane ya fi zama alkairi baki ɗaya ina ga tun da mun gama ni zan tafi gida sai kuma gobe in sha Allah nagode bisa haɗin kan daka bani yanzu mun gane _LAIFIN WAYE_. "Nawa ne ina fatan nan gaba zan ƙara irin wannan kuskuren da a baya ba". inji Umar. Suka Miƙe a tare suka fice daga office ɗin Dr Nasir yana gaba Umar yana biye dashi Dr ya nufin wajen ajiye motoci ya fara ƙoƙarin buɗe tasa kenan wayarsa tai ƙara hannu yasa ya ɗauka ya dubi sunan Dr Zahra yayi murmushi sannan ya ƙara a kunnesa yayi sallama cikin natsuwa yace. "Kiyi haƙuri Dr Zahra inata ganin kiranki amma ba damar ɗagawa na saboda wani dalili yanzu kin ganni sai yanzu nake shiga mota ina ƙarasawa gida zaki ji kirana nagode sai kin jini". ya kashe wayar yana dariya yace Dr Zahra rigima yana shiga motar ya tayar ya nufi get ɗin fita waje. Sallama Umar yayi acikin ɗakin jinya ya kalli inda Baba Sa'a take zaune yace. "Sannu Baba ya jikin nata naga kamar ta koma baccin koh naje na fayyace wa Dr komai game da halin da Hauwa'u take ciki kuma nasan LAIFI NA NE yai min nasihohi waɗanda suka shiga jikina daga ƙarshe na yanke shawara akan Hauwa'u idan Allah ya bata lafiya". Inji Umar. "Ɗan nan wacce irin shawarace Allah ya sa ta saki ce,dan ni a yanzu shine burina zan bata dama ta zaɓi irin mijin data ke so ba san raina ba". Inji Baba Sa'a. "Hakane dama kuskure ne kuma anyi shi da kuma ƙaddara saboda kowa na duniya akwai irin tasa". Inji Umar. Dama gida zan koma idan ta tashi kice ina dubata kafin na dawo gobe. ✍️ *LAIFIN WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO.* *PAGE 15* Wata irin harara ta zuba masa me ɗauke da tuhuma tace. "A'a kai zamanka ba sai ka dawo ba mun yafe". haka ya fice daga ɗakin cikin sanyin jiki. Iskar sa ke da wuya cikin gidan ya buɗe ɗakin ya cikin gajiya wa ya kwanta akan doguwar kujerar dake falon ya zare glas ɗin dake manne a fuskarsa ya lumshe ido yana tunanin abubuwan da suka wakana tsakanin sa da Umar daya tuno Umar yace. _zai sawaƙewa Hauwa'u yaji wani irin daɗi_ sannan ya mike tsaye ya nufi firij inda ya zaro ruwa me sanyi ya buɗe ya fara sha kenan wayarsa tai ƙara sai da ya gama shan ruwan ya dawo inda wayar take ajiye sunan Dr Zahra ya gani akan fuskar wayar yasa hannu ya ɗaga yace. "Sannu Dr ya kike yanzu nake shirin cewa sai na gama abinda nake zan kiraki ban jima da shigowa gidan ba ki dan kara haƙuri nan da lokaci kaɗan zan kiraki kinji ya kashe wayar yana ƙoƙarin sake kwanciya saboda irin gajiyar da yai cikin lokaci ƙalilan bacci yai awon gaba dashi be farka ba sai wajen 2: 00 na dare. Washe gari kuwa haka Dr ya tashi cikin ƙarfin hali yake shirya wa saboda gajiyar data gallabeshi ya gama shirya wa tsaf ya nufo wajen motarsa ya shiga ya tayar tafiya yake a hankali kamar ba'a kan titi yake ba har ya ƙaraso asibitin ya wuce office ɗinshi. A can ɗakin da Hauwa'u take kwance kuwa Baba Sa'a ce tana zaune a ƙasan gado tana jan carbi taji motsin Hauwa'u ta Baba Sa'a ta dubi inda take tace har kin farka ne sannu. Daga kai tai alamar Eh tai mata nuni data gyara mata kwanciyar Baba Sa'a ta tashi cikin sauri tana kicikici taji shigowar Dr Zahra. "Ki dai gyara mata a hankali karfi fama mata ciwonta". *AISHA YAHYA TANKO* *LAIFIN WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO* *PAGE 16* Ta gyara mata kwanciya ta koma ta zauna tana sauraron abinda Dr Zahra zata ce game da Hauwa'u Ta gama yan dube_dubenta ta dubi Baba Sa'a tace. "Masha Allah jikin Hauwa'u yayi kyau sosai muna sa rai nan da lokaci kaɗan zamu sallameku". inji Dr Zahra. Wata irin dariya Baba Sa'a tai tare da yiwa Allah godiya tace. "A gaskiya naji daɗi sosai burina ya cika kuma Allah ya saka muku da Alkairi yasa ku gama aikinku lafiya nagode sosai". Dr Zahra ta fice daga ɗakin tana murmushi Baba Sa'a ta kalli Hauwa'u tace sannu Yarinyar kirki. Acan office kuwa Dr Nasir ne yake duba files din dake gabansa yaji shigowar Dr Zahra ya kada da abinda yake yi yace. "Barka da zuwa Dr ashe har kin shigo". ya umarce ta data zauna. Taja ta zauna a kujerar data ke dab dashi tana murmushi tace. "Ai na jima da shigowa har naje na duba Hauwa'u kuma naga wajen ya fara kamewa masan nan da lokaci ƙalilan zata iya dawo normal kaga daga nan ma iya sallamarsu su koma gida taci gaba da shiga ruwan zafi". "Ƙwarai kuwa dama ranar da muke jira tazo kenan ɗazu naje can dakin naga wata me shigen matsalar ta itama inaso muje tare muga ta ina zamu fara da ita". Inji Dr Nasir. Dr Zahra tace to ba damuwa Allah ya bamu ikon sauke nauyin da yake kanmu,jiya bayan na barka a nan naga kayi busy daka koma gida ma haka. "Wallahi kinsan aikin namu ne sai a hankali Allah dai ya shiga lamarin". Bayan sun gama tattaunawa ne suka fara ƙoƙarin zuwa duba mara lafiyar. Acan ɗakin kuwa tuni farin ciki ya baibaye Hauwa'u lokacin data ji Baba Sa'a ta sanar da ita abinda Dr Zahra tace game da ita har ta sami karfin gwiwar cin abinci sosai tana magana. Suka ji shigowar Umar hannunsa riƙe da ledoji ya ajiye su kusa Da Baba Sa'a yana gaisheta Hauwa'u tuni ta haɗe rai kamar me shirin kuka yace. "Dan Allah ki saki ranki Hauwa'u ƙaddara ce ta riga ta faru Allah dai ya kiyaye gaba". Baba Sa'a tace hakane abu dai ya faru ni dai fatana ranar da muka fita daga Asibiti ka bata takardar saki shine abinda nake nema awajenka. *LAIFIN WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO* *PAGE 17* Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah Hauwa'u dai ta sami sauƙi har an salamesu daga Asibiti sun dawo gida Tun ranar da Dr Nasir ya buɗe yaga ba Hauwa'u a cikin asibiti komai ya dagule masa ya rasa inda zai sa kansa Dr Zahra ta rasa gane inda ya dosa har ta fara sawa zuciyarta haƙuri amma ba dan san ranta ba. Wata rana Hauwa'u tana zaune a tsakar gida kan tabarma tayi jigum tana tunanin rayuwarta a asibiti ne taji maganar BaBa Sa'a tana cewa. "ke kuwa Hauwa'u me kikeyi ne haka tun ɗazu na barki anan amma ba abinda kikai sai zaman tunani bayan kuma yanzu ba abinda ya rage miki sai fatan Allah ya kawo miki miji na ba irin Umar ba nazo miki da wani babban albishir amma sai kin min alkawari zaki dena wannan tunanin". Nan da nan Hauwa'u ta ɗago kai tana dariya ta nuna alamar zaƙuwar taji ko menene. Baba Sa'a ta zauna kusa da ita tace. "Umar dai ya sake ki". Wata irin ƙara da murna Hauwa'u tayi tace. "Dama wannnan ranar nake jira Baba Allah na gode ma daka bani lafiya ka kuma rabani da mutumin da yake kamar bakin maciji gareni ganinsa ya zame mun masifa". Kafin su ƙarasa magana suka ji sallama gaba ɗaya suka bi kofar da kallo cikin mamaki suka miƙe a tare Dr Nasir kaine agidan namu .Baba Sa'a sannu da zuwa nabban bako nasan wannan zuwan na Hauwa'u ne ƙaraso mana nan ma gidan ku ne. Hauwa'u ta kasa cewa komai ta kalli wannan ta kalli wannan shine kawai abinda take yi . Dr Nasir ya zauna bakinsa ya ƙi rufuwa ganin irin karɓar da akai masa. Baba Sa'a ta koma daki ta kirawo Malam suka gaisa. Ta bar Hauwa'u da Dr Nasir zaune a tsakar gida. "Tun zuwa na baki ce komai ba kuma ina ji Baba tace wannan zuwan naki ne ko nayi laifi inaso ki sani tun lokacin da aka kawo miki asibitin mu naji kin kwanta min ta nan ne na fara neman inda kuke zaune kuma gashi ban sha wahalar da mun gidan ba". Hauwa'u tace. "Nagode sosai bisa ƙoƙarin da kai akaina Allah ya saka da Alkairi". "Nazo da ƙoƙan barata ina fatan zaki bani dan Allah ina so ki bani dama idan kin gama idda muyi aure in sha Allah zan baki kulawar da baki samo ba". Inji Dr Nasir. "A'a ba zan taɓa amincewa dakai ba har abada na dauke ka Yayanah wanda zaka tsaya min a matsalata". "Kin san kwa me kike fada Hauwa'u ni bazan cutar dake ba nine mijin daya dace ki aura inaso ki bani hadin kai ki karbi tayin da nai miki nasan zaki ji dadin zama dani yana gama faɗa ya Miƙe tsaye ya zaro kudi acikin Aljihunsa ya ajiye mata ya fita cikin sauri daga gidan ba tare da ya jira amsar ta ba. ta zubawa kudin ido ganin yawansu BaBa Sa'a ta fito daga ɗakin tace. "Wallahi ke sakarai ce mara wayo ae duk ina jin abinda kuke fada ki sani cewa Dr Nasir shine mijin daya dace ki aura da zartar kin kammala idda kinsan baxan iya zama dake muna goga kafada ba sai kace uwar gida da amarya ba". _AISHA YAHYA TANKO_ *LAIFI N WAYE* *© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽* *BY AISHA YAHAYA TANKO* *PAGE 18* Ta gama balbalin faɗanta ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba tace. "kiwa kanki faɗa ki sani a yanzu bani da burin da ya wuce naga Allah yai miki sakayya daga wahalar da kika shiga abaya kullum addu'ar dana ke miki ita ce zaɓin Allah ada na tursasaki akan abinda bakyaso kuma kin bi amma yanzu na gane kurena naga faɗan dana ke miki ba shine mafita ba, na biki a hankali shine kawai dan Allah Hauwa'u ki karbin tayin Dr Nasir kinji". inji Baba Sa'a. Hauwa tace. "Baba kar ki damu zanyi dogon tunanin akan Dr Nasir in sha Allah zan sanar dake nan da kwana biyu". To shikenan ƴar albarka Allah ya shiga lamarin mu Baba Sa'a tace yawwa dama ina so ki shirya kayanki jibi gobe zamu kauye wajen su Inna Hama saboda suga jikin naki su tabbatar kin ji sauki kuma kinsan Mahaifiyarka tana fama da ciwon ƙafa ko tashi bata iya yi. Inji Baba Sa'a. Hauwa cikin zullumi ta miƙe tsaye bakinta yaƙi rufuwa dan murna tace to Baba bari naje na fara shirya kayan. "Haba ƴar nan kya dai bari kici abinci kar yai sanyi irin wannan murna haka kamar wadda akai mata albishir da zuwa Makka". Inji Baba Sa'a. "Tab Baba ai zuwana ƙauye dole nai murna yaushe rabon da naje yau kusan shekara uku fa ai kinga dole naji daɗi sosai ki bar abincin bana jin yunwa". A can asibiti kuwa mutane sun cika a kofar office ɗin Dr suna jiran zuwan sa isar sa ke da wuya yayi parking ya fito daga motar fuskarsa babu walwala yana ta saƙe-saƙen acikin zuciyarsa game da Hauwa'u har ya isa bakin office ɗin mamaki ya kama shi ganin yadda aka cika bakin office ɗin ya saki fuska yai musu sallama suka amsa duk suka miƙe tsaye tare da yi masa sannu da zuwa ya Amsa toh aka buɗe masa office ɗin ya shiga ya ganshi tsaf yayi addu'a sannan ya zauna akan kujerar sa ya fara ganin mutanen da suke zaman jiransa a haka duk ya gama da kowa ya ɗan kashingiɗe yaji wani ƙamshi ya bugi hancinsa ɗago yai yaga waye Dr Zahra ce tsaye bakin kofar ta kasa ƙarasowa inda yake yace. "ki shigo mana Dr ya kika tsaya Anan ko nayi laifi ne. Inji Dr Nasir. Dr Zahra tayi murmushi tace "ai kai baka laifi nice dai me laifi da har yanzu na kasa rabuwa dakai zuciyarka bata wajena tana wajen Hauwa'u amma duk da haka nake bibiyarka inaso ka sani duk halin dana shiga kaine silla". tana gama faɗa ta juya tana tafiya. Dr Nasir ya mike tsaye yana buga hannu yace "a fili wannan wace irin ƙaddara ce take nufin tunkaroni Allah yai min magani ya dawo ya zauna ya ci gaba da duba files din dake gabansa. Washe gari da sassafe tuni Hauwa',u tai wanka ta shirya tsaf ta zauna a kan wata tsohuwar kujerar ƙarfe tana jiran fitowar Baba Sa'a tasha kyau kamar bata taɓa aure ba idan ka ganta. Jim kaɗan Baba tta fito daga cikin dakinta itama ta shirya tsaf ta dubi Hauwa'u tace Allah yasa dai kin gasa jikinki kinsan dai likitoci sunce aci gaba da gasawa har sai kin dena jin ciwon ko yaya kar kilu ta jawo bau kina jina koh". Hauwa 'u tace haba Baba Sa'a ta ina zanyi wasa da lafiyata ai ban manta wahalar dana sha ba kullum sai na gasa wajen. Suka yi sallama da Malam suka fito suna hira har suka isa bakin titi inda zasu hau motar da zata kai su Ƙauye suka ga mota ta tsaya agabansu. _Aisha Yahya Tanko_✍️ Alhmdllh abin da na rubuta dai-dai Allah ya bani lada wanda nayi kuskure Ya Allah ka yafe min Mu haɗu a littafi na na gaba.......