[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *026.* Gaban ta ya fad'i k'irjin ta ya fara duka da sauri-sauri ta cire wayar daga kunnen ta ta kalla taga number sabuwa special mai sauk'in haddacewa ta sake mayar da wayar kunne ko zata ji an kuma magana amma shiru ba'a ce komai ba kuma har lokacin ba'a katse kiran ba. Sake cire wayar tayi ta kalla taga dai har lokacin tana tafiya ta sake mayarwa amma still shiru ba'a cewa komai. Ta bud'e baki zatayi magana aka riga ta ta hanyar fad'in, "Don't confuse yourself." Zak'in maganar sa take ji har sassan jikin ta hakan ya saka ta yin shiru ta kasa magana tana jin maganar sa na zaga ko ina na jikinta ta lumshe ido ta bud'e kafin ta daidaita kanta tace, "waye yake magana ban gane ba." Baice komai ba daman kuma bazai ce ba taji an yanke wayar ba tare da an sanar da ita ba tabi wayar da kallo har lokacin k'irjin ta bai daina bugawa ba. _Ina sonki._ abinda akace ya fad'o mata a rai ta sake kallon number zuciyar ta cike da mamakin wanda ya kira ta kuma bai fad'a mata waye ba ya kashe, tsaki taja tana so ta kawar da tunanin ko waye a ranta amma abin yaci tura ta zubawa waje d'aya ido kalaman da aka fad'a mata suna yi mata yawo a cikin kanta ta kasa kawar dasu daga kwakwalwar ta. Tana so ta tuna inda tasan muryar amma ta kasa tunawa dan kamar a waya ta banbanta da wacce ta sani a zahiri hakan ya saka ta kawar da tunanin daga kanta ta kwanta a hankali kalaman Anas nayi mata yawo a a zuciyar ta da gangar jikinta. ☆ "Mum yanzu me hakan yake nufi? Ana nufin ina ji ina gani Asad zai auri wata bani ba ba?" Jidda ta fad'a tana kallon Mum hankali a tashe. Mum tace, "nace ki kwantar da hankalin ki nice fa mahaifiyar ki, Asad bashi da wata mata in ba ke ba a duniyar nan." "Amma naji kina min wata magana daban." "Eh ya furta yana sonta amma asiri suka masa dan in kika ga yarinyar mai gadin gidan nan ma bazai d'auka ba balle Asad." Jidda tace, "Mama ban damu da kyanta ko munin ta ba kawai ki sanar dani ni an ajjiye a gefe kenan?." Mum ta fusata tace, "Na fad'a miki ki kwantar da hankalin ki kece matar Asad ba ita ba, yadda nake miki tanadin yadda zaki mallake shi ko uwar sa bata isa ba balle wata banza a gefe da ta shigo yanzu. Asad naki ne ke kad'ai daga ke sai dangin ki dan haka ki nutsu wannan auren ba mai yuwa bane ba." "Ta ya za'a fasa bayan kince yana sonta?." "Ita bata son sa ai." "A ganin ki Mum zak'i amincewa da tayin Asad ne?. Yana da kud'i, yana da kyau ga sarauta taya zata ki amince masa?." Mum tayi shiru kafin tace, "ko ta amince ko kar ta amince bata isa ta mallake shi ba, naki ne ke kad'ai zan iya yin duk abinda zanyi wajan ganin kin zama mallakin Asad koda kowa baya son hakan. Sai na juya Rabi'atu kamar yadda take juya mutane tafin hannun ki nake so Asad yazo ana zuwa wannan b'angaren zance ya k'are." Jidda tayi bata ce komai ba tana girgiza kanta dan ita maganar ba wata shigarta tayi sosai ba tunda taji ance yana son yarinyar take jin kishinta a zuciyar ta, k'wafa tayi kafin ta tashi ta bar falon ta hau sama. Da kallon Mum ta bita tana k'iyasata abinda zata aikata akan lamarin dan ko da tsiya koda tsiya-tsiya Asad bazai auri Rauda ba y'ar ta zai aura, ko yana so ko baya so. *◇◇* Hydar ne zaune a gaban mai martaba shi kuma yana duba littafi a hannun sa kafin ya ajjiye yace, "Ina jinka Hydar." Hydar yace, "Allah ya k'ara maka lafiya Mama tana neman hana Asad auren wacce yake so, tana k'okarin cusa masa ra'ayin k'inta duk da yana sonta ya sanar dani zai iya barin ta sabida Mama. Abba meyasa Mama take yiwa Asad haka dan ya kasance me yi mata biyayya a ko wanne lokaci?." Mai martaba yayi murmushi ya kashingid'a yace, "Mahaifiyar ku tana da wani hali wanda sai kuna taya ta da addu'a Allah ya cire mata shi daga cikin halayen ta in ba haka ba zata sha wahala yanzu ko nan gaba. Tana amfani da biyayyar da yake mata tana hana shi abinda yake so a ko wanne lokaci dan cikar burinta kawai, amma wannan karon bazan zuba ido ya rasa abinda yake k'auna ba wanda na tabbatar da alkhairin da yake cikin abinda yake so d'in zan nuna mata gaba da gaban ta. Kai ka tabbatar da yana sonta?." "Na tabbatar da wannan takawa, yana k'aunar ta sosai zan iya cewa itace mace ta farko da Allah ya d'ora masa k'aunar ta. A idanun sa in ana maganar ta mai martaba zai tabbatar da abinda nake fad'a, yana sonta so mai tsanani." "Ikon Allah kenan. Babu damuwa zan yiwa tufkar hanci kafin ta farga, sai dai ta farka daga dogon bacci ta tarar aikin gama ya riga da ya gama. Gobe kaje kazo min da mahaifin yarinyar zan sanar dakai inda zaka kai shi." Hydar yace, "Allah ya kaimu goben. A huta lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita mai martaba ya bishi da kallo. Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke ya kalli gefe guda abubuwa da dama sun cushe masa a kansa da kuma zuciyar sa, shi kansa zai so ayi auren Asad da gaggawa kodan ya cika mutum bashi mulkin ya huta gabad'aya, zai kuma tsaya wajan ganin Asad ya samu abinda yake so a karon farko in sha Allah. A b'angaren Mama lokaci d'aya ta fize ta rame sabida tashin hankalin da take ciki wanda ta d'orawa kanta, hankalin ta gabad'aya baya tare da ita tana zaune ta zubawa tv ido a zahiri sai ka d'auka kallo take amma ba kallon take ba ta tafi duniyar tunani. "Mama!." Suhaima ta fad'a daga bayan ta tana k'arasowa kusa da ita ta ta zauna a k'asa kusa da k'afar tana kallon ta. Bata amsa ba hakan ya saka Suhaima tace, "Dan Allah Mamana ta daina saka damuwa a cikin zuciyar ta dan Allah, in Allah ya rubuta yarinyar da ake magana a kai matar sace sai ya aure ta kenan babu amfanin damuwa akan lamarin. kuma....." Kallon da Mama tayi mata ya hanata k'arasawa ta tashi daga kusa da ita cikin tsoro ganin irin kallon da take mata tsaf zata iya bugeta. "Kar na sake jin wannan maganar a bakin ki matuk'ar kina buk'atar kwanciyar hankali na da naki kwanciyar hankalin, in kuma kina son b'acin raina ne sai ki fara daga yanzu. baza ta zama matar Asad ba da ganin wannan ranar gwara ganin ranar mutuwa ta!" Ta k'arasa fad'a tana kallon Suhaima. Suhaima tace, "Allah ya zuci zuciyar Mama, tuba nake" ta fad'a tana barin wajan tana waiwayon ta. Da sauri Mama ta d'auki waya ta kira layin Mum ana d'auka bata jira anyi magana ba tace, "ya maganar mu?." Daga can b'angaren Mum tace, "Da nace a bari sai zuwa jibi sabida kar ayi saurin gano muna da hannu a ciki." Mama tace, "A gano mana sai me?! Me zasu iya yi mana?, kiyi gaggawar aiwatar da komai a yau bana so a samu matsala, a b'atar da yarinyar nan daga duniya gabad'aya hankali na zai fi kwanciya!" Bata jima mai Mum zata ce bama ta yanke wayar tana wuci. Ta kwashe sama da awa biyu a zaune a wajan har dare yayi tana zaune ganin kiran Mum ya saka ta d'auka tace, "Good news please." Mum tace, "na tura wanda zasu shiga gidan, yanzu haka ma sun tabbatar min da suna cikin gidan sun samu mafaka jira suke dare yayi su aiwatar da komai." Mama tace, "kar ki kuma kirana sai an tabbatar an kashe ta" tana fad'a ta yanke wayar ta ajjiye a gefen ta. Suhaima da take jin komai gaban ta ya fad'i ta zaro idanu waje tare da dafe k'irjin ta ta wuce Maman da sauri ba tare da ta kula da ita ba ta fita zuwa b'angaren su Asad. A haukace ta shiga falon taga Hydar a zaune yana kallon ball ta kalle shi tace, "Yaya Hydar ina Yaya Deaf?." Kallon ta yake ganin ta a firgice yace, "meye kike neman sa?, lafiya kike?." "Mama ce ta tura a shiga gidan su yarinyar nan a kashe ta." "What!" Hydar ya furta yana wara idanu tare da mik'ewa tsaye yana kallon ta yace, "Wacce yarinya?." Suhaima tace, "Wacce Yaya Asad yake so." "Ke kin tabbatar da abinda kike fad'a kuwa bana son hauka" ya fad'a yana kallon ta a firgice jin abinda baiyi tsammanin ji ba. Girgiza kai tayi tace, "Allah abinda naji tana fad'a a waya kenan, dan tace kar a kuma kiran ta sai an tabbatar an kashe yarinyar. Kayi wani abu bro bana son hakkin kisa ya rataya akan Mama." Asad da ya shigo falon yaji abinda ake fad'a ya kalli Hydar kafin yayi magana ya juya da sauri ya fita. Da sauri Hydar yabi bayan sa amma kafin ya k'arasa ya shiga mota yaja har ya fita daga gate na biyu ya nufi na farko dole shima ya d'auki tasa motar ya shiga yabi bayan sa da gudu. yayi mamakin gudun da Asad yake yi domin bai ganshi ba alamun yayi nisa sosai dole shima ya ware motar yana binsa a guje. A can gidan su Rauda lokacin duk sun kwanta kasancewar sun saba baccin wuri har Baba ya kwanta kowa yana muhallin da yake. Rauda tana zaune a gefen gadon da suke kwana ita da Ummulkhairi ta saka dogon wando da riga tana zaune tayi tagumi gabad'aya bata jin dad'in komai tunda ta karanta message d'in Anas har lokacin bata dawo walwalar ta ba. Abu taji an buge a falo tayi shiru tana sauraro sai taji shiru sai ta kawar da tunanin kafin ta fara jin motsi a hankali, ta d'auka Baba ne hakan ya saka bata fito ba jin magana k'asa-kasa ya saka ta k'okarin tashi ta d'auki abinda yake taimaka mata wajan tafiya tana takawa a hankali sabida kar suyi k'ara ta k'araso jikin k'ofar, kokwanto take ta bud'e ko kar ta bud'e zuciyar ta duk ta cika da tsoro haka kawai bata san dalili ba. "Ban gane d'akin nata a nan ba kun san bama so a samu matsala." Abinda taji an fad'a kenan a hankali gaban ta ya fad'i ta zaro idanu waje kafin ta kuma ji ance, "Mu shiga kawai in kuga ba bata nan sai mu shiga wani duk wanda yaso yi mana gardama muga bayan sa." Rauda ta dafe k'irji a hankali tace, "Wa suke nema?." Tsoro duk ya bayyana a tare da ita tana jikin k'ofa ta kasa kunne babu zato taji an turo k'ofar tayi baya ta fad'i k'asa tare da yin k'ara. "Shiiiiiii" d'aya daga cikin su ya fad'a fuskar sa a kulle kafin ya kalli d'akin yaga Ummulkhairi a kwance tana bacci dan d'akin da haske yace, "Kika kuma yi mana ihu sai mun kashe kowa na gidan nan." Kai take girgizawa ta kulle hannun ta da baki tana kuka sosai jikin ta na rawa hankalin ta ya kai makura wajan tashi. d'aya ya kalli d'aya yace, "Mu aiwatar da aikin mu kafin azo a same mu." Ba musu d'aya yayi bayan Rauda ya saka mata igiya a wuya wanda yake tsaye a kanta yace, "Fad'i kalmar ki ta k'arshe domin kashe ki zamu yi." Bakin ta rawa yake hawaye na zubowa daga idanun jikin ta na kyarma ta kasa cewa komai sai ido da take bin su dashi ganin mutuwa kusa "baki da abin fad'a kenan, kai ja igiyar" ya fad'a yana kallon bayan sa. Tamke igiyar yayi a wuyan ta idanun Rauda suka k'afe sukayi ja sai kakari take amma babu damar yin numfashi sun tokare shi sai bak'in idonta ya juya baka ganin sa sai farin da ya koma ja kawai ake gani, k'afa take jurawa tana k'okarin rike igiyar d'ayan da yake tsaye ya rik'e hannayen ta duka. Su Asad kuwa duk yadda suka so shigowa gidan abin yaci tura an kulle gidan ta ciki gashi basu san hanyar da zasu bi su shiga cikin gidan ba, hankalin Asad ya tashi matuk'a har ya bayyana a tare dashi ya rasa abinda zaiyi ya shiga gidan gashi jikin sa yana bashi sun kashe ta ko suna gab da kashe ta. Tashin hankalin da yake ji tunda Allah ya kawo shi duniya bai tab'a jin irin sa ba, ji yake kamar ana daka naman jikin sa ana soya zuciyar sa a man da yake da mugun zafi. Mahaukacin dukan da ya yiwa gate d'in har su da suke ciki sai da suka ji suka tsorata wanda ya matse mata wuya ya sake ta da sauri ya k'arasa wajan taga ya bud'e yana kallon harabar gidan ya kuma jiyo dukan gate d'in da akayi. "Oga akwai mutane a waje fa ya kamata muyi sauri mu bar nan" ya fad'a yana kallon ogan nasu ya kalli Rauda da take kwance babu numfashi a tare da ita yace, "Muyi sauri mu fice" ya fad'a yana fita da sauri yana fitowa suka had'a idanu da Asad da yake tsaye bayan sa Hydar sai Baba da yake tsaye kusa dasu. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Baba ya fad'a hankali a tashe yana shiga d'akin da Rauda take ya ganta a kwance babu numfashi yace, "Shikenan sun kashe ta!." [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *027.* Kalmar da Baba ya furta ta girgiza Asad, wani irin yammmmm yaji yana shiga ko wanne b'angare na sassan jikinsa take yaji duniyar tana juyawa kansa ya sara zuciyar sa na bugawa kamar ana dukan ganga, gaban sa ya fad'i irin wanda bai tab'a yi ba tunda yazo duniya kamar an zare masa kuzarin jikin sa ya tsaya sak yana kallon k'ofar ba tare da ya aikata komai ba. "Bata mutu ba tana numfashi, da ranta" ya sake ji Baba ya fad'a bai san lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ba sabida wani k'aton dutse da yaji ya sauka daga k'irjin sa hakan ya bada damar saukar numfashin sa daidai. Mutanen Asad yake kalla ya gansu a zube a gaban Hydar ko wanne guiwa a k'asa ya kalli sauran mutanen falon yaga gabad'aya iyalan gidan su bayyana a wajan Rauda ce da mahaifiyar ta kawai babu da alama tana waja Rauda a d'aki, Baba ya kalli Asad ya kalli mutanen ukun da suke zube a wajan yace, "Kashe Rauda suka so suyi ban san dalilin su ba, me Rauda tayi muku zaku kashe ta? Kisa fa da muke kallo a film itace yau har gidan mu..? bazan lamunci wannan abun ba dole maganar nan taje kunnen hukuma sabida gaba." Asad ya kalli Hydar shima ya kalle shi suka kalli mutane ukun a tare babban ciki yace, "Ranka ya dad'e wallahi Allah turo mu akayi mu kasheta, batayi mana laifin komai ba alqawari aka yi mana in muka kashe ta za'a bamu kud'i masu yawa, ba'a san ran mu bane ba biyan mu akayi akace mu tabbatar bata numfashi." "K'arya kuke yi, wanne mak'iyi Rauda take dashi da zai aiko a kashe ta?, me take dashi da za'a aiko har cikin gidan su a kashe ta?. Ita ba y'ar film ko y'ar siyasa ba akan me kuke neman rayuwar ta?" Umma ta fad'a tana fitowa daga d'akin tana goge idanun ta cikin tashin hankali. D'aya daga ciki ya kuma cewa, "Hajiya Sadiya ce ta saka mu, itace tace muzo mu kashe Rauda kada mu bar wata shaida da za'a gane hakan. Mun jima a cikin gidan nan b'uya mukayi sai da dare yayi muka shigo nan." "Wacece Sadiya?" Baba ya fad'a yana kallon su shi kansa hankalin sa ya tashi. "Mu dai da haka muka santa bamu san sunan da zamu fad'a maka nata ba." Baba yace, "Zakuyi bayani a gaban y'an sanda dan wallahi sai nayi k'arar ku bazan zuba ido akan wannan lamarin ba dan ba k'aramin case bane ba." Hydar yace, "kwantar da hankalin ka Baba za'a yi musu hukunci daidai dasu baza mu bari su sha ba zamu tabbatar sun girbi abinda suka shuka. Abu na farko a d'auko ta a kaita asibiti a duba lafiyar ta." Umma ta kalle shi tace, "Bama buk'atar hakan mun gode basai anje asibiti ba ta farfad'o" Umma ta fad'a ranta a jagule tana kallon su. Shigowar y'an sanda guda biyu ya saka suka juya suna kallon su suka k'araso kusa da Asad suna yi masa alamun jinjina yace, "Ranka ya dad'e, Allah yaja zamanin ka, gani na fito kamar yadda ka buk'ata." Asad bai tanka masa ba sai Hydar ne yace, "wad'annan zaku tafi dasu a kaisu kotu a tabbatar anyi musu hukuncin da ya dace dasu, kisa suka so kisan ma akan mutum mai mahimmaci a wajan Asad." D'aya daga cikin su yace, "An gama ranka ya dad'e zamu tabbatar sun girbe abinda suka shuka. ku tashi muje shigar dare ce yau zakuyi" ya fad'a yana kallon su da suke durk'ushe akan guiwar su. "Dan Allah kuyi hak'uri wallahi ba laifin mu bane saka mu akayi akace muzo muyi amma ba aikin kaimu bane ba. Ku yafe mana dan Allah kuyi mana rai, wallahi zaman gidan yari babu dad'i dan Allah ku tallafa mana daga yau baza mu sake irin wannan kuskuren ba" D'aya ya fad'a yana kallon su kamar zai zubar da hawaye. D'an sandan yace, "yi mana shiru; k'aramin yaro ne kai ko kuma baka da hankali da za'a saka ka wannan d'anyen aikin kayi? Zaku girbe abinda kuka shuka gobe za'a tura case d'in ku kotu zaku gane baku da wayo, ku tashi muje" ya fad'a da tsaya ba shiri suka tashi suka tasa su a gaba suka fita. Sai a sannan Asad ya lumshe idanun sa ya bud'e yace, "Mama za'a a kaita asibiti." Umma tace, "Bama buk'ata na fad'a muku, abinda muke so a gare ka dan girman Allah ka janye maganar auren Rauda tunda ba itace mace ta farko a duniya ba. ban san dalilin ka na cewa zaka aure ta ba amma ni jiki na yana bani akwai dalilin ka nayin hakan domin ruwa ba sa'an kwando bane. In kana so za'a iya kawo maka mata d'ari koda dga k'asar larabawa ne in badan kana da wata manufa ba meyasa zakace sai ita?. Tunda ka furta maganar nan muke ganin tashin hankalin da bamu tab'a gani ba tunda muke har ya kawo da neman rayuwar ta akan abinda bata furta ta amince bama, dan ni nasan a akan ka akazo kashe ta in kuma tace ta amince kenan a ranar sai an k'ona ta da ranta kenan. Ina rok'on ka dan Allah ku janye maganar nan a bar Rauda ta huta da ranta da kuma lafiyar ta, bana son rasa ta dan Allah ka janye maganar nan a bar mu ji da talaucin mu" Umma ta fad'a tana hawaye tana kallon Asad. Nan take jikin Asad yayi mugun sanyi ya kalli Hydar shima ya kalle shi kafin suyi magana Baba yace, "Me kike cewa haka? Kin manta k'addara ne ko kin manta hukuncin Allah akan bayin sa?." Umma ta kalli Baba tace, "nidai a bar maganar kawai tunda ai ba ita kad'ai ce mace ba. Baka nan mahaifiyar sa tazo in kaji irin maganar da ta fad'a da ikirarin da tayi akan abinda zata yiwa Rauda in ta auri d'anta baza kayi sha'awar aura masa kazar gidan nan ba balle kuma ita. Kud'i ko mulki baya gaban mu mutunci da zaman lafiya muke nema, zamu rike kan mu suma su rik'e kansu kafin aje ko ina gashi an fara turowa a kashe ta, kisa fa kamar a film!, maganin kada ayi kada a fara gwara kowa yayi hak'uri daman daidai ruwa daidai tsaki" ta fad'a tana kallon Baba tana zubar hawaye har lokacin. Hydar yace, "kiyi hak'uri Mama hakan bazai sake faruwa ba in sha Allah; ba'a kyauta muku ba na sani, badan Allah ya kawo mu ba da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, amma ki tuna duk abinda ya faru da Rauda Allah ya rubuta zai faru da ita tun kafin tazo duniya babu wanda zai hana faruwar sa, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai samu Rauda in sha Allah." Inna tace, "Gwara dai a bar maganar kar muma a biyo ta kanmu nan gaba, tunda gashi har suka shigo cikin gidan bamu sani ba, in ma gidan ne ba'a so mu zauna sai mu tattara kayan mu mu tafi daman ba namu bane aro aka bamu." Asad ya dafe kansa yace, "kuyi hak'uri dan Allah duka" ya furta a sanyaye domin jikin sa ya gama yin sanyi gabad'aya. Rahma tace, "Kayi hak'uri mudai a bar maganar auren kawai tunda abin yazo da neman rayuwar Anty Rauda akan auren da in tayi ba rahama za'ayi mata ba, gwara ayi hak'uri a huta domin rai yafi komai a duniyar nan." Asad zaiyi magana Umma tace, "Dan Allah kayi hak'uri a hak'ura kawai maganar nan ta k'are a daren nan dukkan mu mu huta, mun gode da alkhairin ka a gare mu; k'afarta ta ma a barta a haka tunda tana tafiya mun gode Allah wasu ma yanke k'afar ake gabad'aya, gidan nan kuma zamu tashi mu koma namu tunda abin yazo da haka." Asad yace, "Shikenan Mama karki damu. Amma ku zauna nan har a gama aikin gidan, lafiyar ta kuma za'a cigaba da nema mata kamar yadda aka fara" ya furta cikin muryar sa ta koda yaushe da take a raunane amma ta lokacin har ta ninka na baya. Hydar yace, "kuyi zaman ku a nan babu wanda zai kuma takura muku, sannan in zaku kulle k'ofar gidan nan a dinga duba ko ina sabida wad'annan sun shigo ne kafin a kulle gidan dasu aka kulle, za kuma ayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata. Zamu kawo security da zasu dinga kula da lafiyar ku in sha Allah." Baba yace, "babu komai Hydar mun gode Allah ya saka da alkhairi, muje na raka ku." ya fad'a yana yin gaba Hydar ya tsaya yace, "Tana buk'atar ganin likita." Umma tace, "mun yafe dan Allah kuje kawai." Baba yayi gaba suka biyo shi a baya dan babu yadda zasuyi. A jikin mota suka tsaya Baba ya kalli Asad yace, "kayi hak'uri da abinda suka ce ransu ne a b'ace da kuma tsoro kaga hakan bata tab'a faruwa damu ba, a film ma muke ganin ana zuwa gidan mutane kisa bamu tab'a gani a gaske ba balle mu kawo hakan zai zo kanmu." Hydar yace, "Suna da gaskiya ba'a kyauta ba gabad'aya an kuma aikata babban laifi amma zamuyi maganin abun in sha Allah. Ka koma gida dare yanayi" ya fad'a yana bud'e tasa motar ya shiga Baba ya juya ya koma gida ya kulle gidan. Asad ya kasa motsin kirki ya hard'e hannayen sa k'irjin sa ya sunkuyar dakai yana kallon k'asa jikin sa yana ji kamar ana zare masa duk wani kuzarin da yake tare dashi, numfashi ya fesar ya kalli gidan ya lumshe ido yaso ya ganta ko zaiji dad'in zuciyar sa amma mutanen gidan basu bashi had'in kan faruwar hakan ba, baki ya jige ya mik'e daga jikin motar ya shiga mota yaja ya bar k'ofar gidan jikin sa a mace sosai. A falon ya sake tarar dasu Baba ya kalle su yace, "kuje ku kwanta mana kowa ya kwantar da hankalin sa komai ya wuce." Umma ta shiga d'akin da Rauda take Baba yabi bayan ta suma duka suka shigo suka ganta a zaune har lokacin bata dawo daidai ba sai tari take idon ta yayi ja sosai. Umma ta k'arasa ta zauna kusa da ita tace, "Ya jikin naki Rauda? Ya kike jin wuyan naki?." Rauda tana rik'e da wuyan ta har lokacin idanun ta ruwa yake yi ta kasa cewa komai. Baba yace, "Ki barta ta huta dan Allah." Umma tace, "ta yaya zan iya tafiya na barta bayan ga halin da take ciki? Bazan je ba gaskiya a nan zan kwana kusa da ita." Ya kalli Inna da Rahma yace, "kuje ku kwanta dare yayi, ke Ummulkhairi kema kwanta gobe kina da makaranta." Juyawa sukayi suka fita Ummulkhairi ta kwanta Umma na zaune kusa da Rauda da take sauke numfashi tace, "Sannu Rauda, Allah ya bi miki hakkin ki. Abinda muke gani a film shine yau yazo har gidan mu, Allah ya kare gaba." Baba yace, "ki ta magana kamar wata wacce bata san k'addara ba, a gaban yaran nan kike dinga wasu maganganu marasa dad'i duk d'awainiyar da suke damu baki gani ba." "Ina ruwana da wata d'awainiyar da suke damu? Ni na rok'e su nace kuzo kuyi d'awainiya damu ko su suka saka kansu?. Daman d'awainiya da Rauda a ka'ida a kansu yake tunda sune suka buge ta har ta samu matsalar k'afa, hakkin sune su kula da lafiyar ta har ta samu sauk'i. In sun ga dama su daina d'awainiyar da ita sai me su suka jiyo." "To duk bak'in cikin ki dai sai Rauda ta shiga gidan sarauta da izinin Allah." Baki sake Umma take kallon sa cikin mamaki tace, "Au wai duk abinda ya faru kaii baka cire rai da auran Rauda da yaron nan ba? Har gida fa aka aiko a kashe ta ko minti biyar ba'a yi ba duk baka gani ba idanun ka ya rufe akan kud'i?." Baba yace, "Kina da tabbacin sune suka aiko?." "In ba su bane su waye?." "Nida ke bamu da masaniya a kai dan haka baza mu yanke hukunci ba." "Baza ka yanke ba dai Malam; amma su kansu sun san daga gidan su aka aiko a kashe ta, yaje can ya nemi wata ya aura amma ba Rauda ba in Allah ya amince." Baba baice mata komai ya fita daga d'akin itama ba tace ba tana ta kallon Rauda da take a firgice har lokacin bata dawo daidai ba. B'angaren Asad a sanyaye yake jan motar kamar baya son tafiyar har ya isa gida lokacin k'arshe sha biyu na dare ta kusa ya faka motar direct ya wuce apartment d'in Mama duk da dare yayi.  Bai same ta a falo ba ya wuce k'aramin falo ya ganta a zaune tana kad'a k'afa hankalin ta na kan agogo da alama akwai abinda take jira. motsin da taji ya saka ta juyo tana kallon sa har ya k'araso sai ga Hydar a bayan sa ta bisu da kallo har suka k'araso. Idanun sa a raunace ya zube a k'asa ya kalle ta yace, "Mama meyasa? Kisa fa Mama!" Ya fad'a yana kallon ta. Gaban ta ya fad'i jin abinda ya ambata ta bisu da kallo tace, "ban gane kisa ba?." Hydar yace, "kashe Rauda da aka saka ayi na tabbatar kuma da sanin Mama Mum ta aika ayi." Mik'ewa tsaye tayi tana binsu da kallo tace, "an kashe ta d'in ne?." Hydar ya kalli Asad ya kalle ta yace, "Yanzu da gaske da saka hannun Mahaifiyar mu a cikin wannan aikin?." "Na fad'a masa na tsane ta bana sonta zan iya yin komai wajan ganin na raba su, meyasa yak'i ji ya nace sai ita?." "Kisa fa Mama!." "Bama ita kad'ai ba kaf dangin ta zan iya sakawa a kashe matuk'ar Asad bai fita daga sabgar ta ba, bana sonta bana k'aunar ta." Asad ya kalle ta yace, "Da an kashe ta fa?." "Dana kashe banza da wofi dan basu da abinda zasu d'auki fansar abinda nayi musu" ta fad'a tana kallon sa. "Allah fa?" Hydar ya fad'a yana kallon ta ransa a b'ace amma bashi da ikon bayyanawa. Shiru tayi Hydar zai kuma magana Asad ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kafin yayi magana ta riga shi tace, "Asad bana sonta, bana qaunar ta Asad, baka tab'a yi min musu akan komai nace bana so kana bari amma a kanta kake musu dani har kake cemin kai ita kake so. Ya kake so nayi Asad? Bana sonta bana k'aunar ta ko kad'an bana so ta rabe ka, Jidda nake so ka aura ba ita ba" ta fad'a da zallar b'acin rai tana kallon sa Asad yayi shiru yana kallon ta kafin ya sauke numfashi yace, "Mamana tana so na rabu da ita?." D'ago kai tayi ta kalle shi ta k'araso kusa dashi ta rik'e hannun sa tace, "Shine farin cikina, shine kwanciyar hankali na da nata kwanciyar hankalin." Asad ya numfasa yace, "Shikenan Mama, Zan rabu da ita amma ina neman alfarma guda d'aya." Mama ta fad'ad'a murmushi ta goge idanun ta da sukayi ja tana kallon sa tace, "Fad'i ko meye zan amince maka indai zaka rabu da ita." "Zan yi sabida Mamana kawai. Ina so Mama ta barni na cigaba da samar mata da lafiya komai zan mata na taimako kar tace komai akai; ni kuma zan cire ta a raina zan auri Jidda zab'in mahaifiyata" ya k'arasa fad'a yana kallon ta kafin ya sunkuyar da kanta. Da sauri tayi hugging d'in sa cikin jin dad'i tace, "Na amince Asad, na amince, Allah ya maka albarka." Numfashi ya sauke ya kalli Hydar da yake gefen sa yace, "Amin Mamana, zan iya hak'ura da komai akan farin cikin mahaifiyata." Ta bar jikin sa tana murmushi tana kallon sa sai ya murmusa kad'an yace, "Lokacin Hutum mama ne ko zata iya hutawa?" ya fad'a yana kallon ta fuska a sake. Kai ta girgiza ta juya tana tafiya kafin ta juyo ta kalle shi tace, "Kar ka canja abinda kace Asad, nasan ka baka sab'a alqawari ka tabbatar da maganar ka." Kai ya girgiza mata alamun to kafin ta shiga ciki shi kuma ya mik'e ya wuce ya bar Hydar a tsaye kafin ya biyo bayan sa. Gidan tsitt sai sautin tsuntsaye da yake tashi a gidan da motsin dokuna da kukan dawisu suka wuce zuwa apartment d'in su, a bud'e suka same shi hakan ya tabbatar musu da Aliyu yana nan basu bi ta kansa ba Asad ya shiga d'aki Hydar yabi bayan sa yace, "Me ka aikata?." Ya juyo ya kalle shi amma bai tanka masa ba Hydar yace, "meyasa kace ka barta Asad? Ka manta itace wacce kake so kake burin aure meyasa zaka ce ka fasa?. Indai zaka biyewa Mama baza ka tab'a samun abinda kake so ba a duniya." "Hydar ban tab'a ce maka ina so na aure ta ba, then zan iya barin kome nake so akan Mama u know dis." Hydar zaiyi magana yace, "Hydar zan barta kodan ta tsira da rayuwar ta akan ina sonta bazan bari ta rasa rayuwarta sabida ni ba,kana jin mai Mama tace a kanta why zan saka rayuwar ta cikin hatsari sabida ni?, indai da gaske ina sonta Hydar barin ta shine abinda yafi min alkhairi" ya fad'a yana jawo drawer ya d'auko passports d'insu Rauda yace, "Please a siyo min ticket ina so ayi mata aikin nan immediately" yana fad'a ya shiga toilet bai kuma kallon Hydar ba. Hydar ya fita jikin sa a sanyaye yana girgiza kai domin yasan daman Mama zata iya galaaba akan Asad amma ya kuma ci alwashin matuk'ar yana raye Asad bazai rasa Rauda ba sai ya mallake ta tunda yana sonta. Asad kuwa bayan ya kwanta duk sai yaji ya kasa nutsuwa maganar Umman Rauda da maganar Mama nayi masa yawo a cikin kansa sun hana shi sukuni gabad'aya, bai tabbatar haka yake son Rauda ba sai  a lokacin da ya furta zai barta nan yake jin wani abu na tasowa daga zuciyar sa yana taruwa a idanun sa da tsakiyar kansa ya cure waje d'aya. Bai san haka yake k'aunar ta ba sai yanzu da ya barta, bai san haka ta mamaye ko ina na jikin sa cikin lokaci kad'an ba sai yanzu da ya furta ya barta bai san soyayyar ta tayi masa mugun kamu ba sai yanzu da ya barta. Ya zama dole ya hak'ura kodan mugun nufin Mama a kanta tsaf zata iya sakawa a kashe ta tunda bata sonta, hak'ura da ita shine yafi masa alkhairi tunda bazai iya jurar ta rasa ranta ba. Numfashi ya fesar ya juya ya kwanta yana jin zuciyar sa na bugawa ya runtse idanun sa yana jin zafi tun daga cikin kansa har cikin idanun sa yake jin yaji da rad'ad'i na shiga cikin su zuciyar sa kuwa kamar zata fashe a wannan lokacin. [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *028.* Har safiya Rauda bata dawo daidai ba idanun ta har lokacin akwai ja sosai a idon ta har lokacin wuyan ta ciwo yake mata ga shatar igiya nan a ciki kuma ji take kamar an rik'e mata mak'ogwaro, firgici da tsoro da fargabar jiya bata sake ta ba sukuku take ko magana ta kasa sai binsu da ido kawai da take yi kamar wacce aljanu suka shafa, bata tab'a tunanin tsintar kanta a cikin makamancin wannan yanayi ba shiyasa take yin komai a sanyaye. Dukkun su suna d'akin da take har su Inna an kawo mata shayi mai madara da biredi mai yanka-yanka tana ci a hankali. Yaya Ummi ce ta shigo da Yaya Shamsiyya da babbar Yayar su wacce suke kira Yayar mu suka shigo a tare kamar gida d'aya suke, Umma ta amsa sallamar ta kalle su tace, "Kamar a gida d'aya kuke?." Dariya Yaya Ummi tayi tace, "a tare duka muka sauka daga mota kamar had'in baki. Ina kwana Inna, Umma ina kwana" ta fad'a a tare tana kallon su. A tare suka amsa suma suka gaishe su kafin Yaya Shamsiyya tace, "ita kuma me ya same ta haka?." Rahma tace, "Bari Yaya Shamsiyya jiya shigowa akayi da daddare za'a kashe ta." Yayar mu tace, "Kamar ya za'a kashe ta kamar a film?." Rahma tace, "wallahi da gaske muke badan Allah ya tak'aita ba da yanzu sai dai kuzo jana'iza domin har sun shak'e ta; kalli wuyan ta ma zaki ga shatar igiya." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" suka fad'a a tare suna yo inda Rauda take zaune tana shan tea a hankali. Yaya Shamsiyya tace, "Su waye su d'in to? Me tayi musu? Ya akayi shigo gidan nan?." Umma tace, "turo su akayi su kashe ta tun kafin mu kulle gidan suka shigo aka kulle dasu, badan Allah ya kiyaye ba da yanzu wata k'ila an kaita kushewa." Yayar mu tace, "To wa Rauda take dashi da zai turo a kashe ta?, bama y'an fashi bane ba kenan turo su akayi kawai dan suga bayan ta, waye ya turo ita da ba y'ar siyasa ba?. Amma dai an kama su ko?." Yaya Ummi tace, "Abinda yake raina kenan; wa Rauda take dashi mak'iyi da zai nemi kashe ta har haka? Me take dashi a duniya?." Umma ta tabe baki tace, "hmmm badai d'an sarkin Katagum ya furta zai aure ta ba; kar ku manta kuma shine mai jiran gado ko yanzu mahaifin sa zai iya murabus ya bashi sarauta shiyasa aka fara neman rayuwar ta sabida kawai ya furta ita yake so." Yaya Shamsiyya tace, "ikon Allah sai kallo, daga cewa kana so sai a fara yunk'urin kisa? Sai kace wacce d'an sarki Saudia yace yana so. Banda abinda akaje har gida aka yi muku?." Umma tace, "to ina dalili auren sa da gafara zai saka ayi mana ba? Ko gafarar ubangiji zaka samu ta hanyar auren sai kayi addu'a Allah ya kawo maka wata hanyar a bar wannan, yaje ya nemi daidai shi amma banda Rauda baza mu zuba ido a kashe ta a banza ba." Yayar mu tace, "wallahi fa, ina dalili daga zancen ana so sai a fara maganar kisa? Me yayi zafi shi ba wuta ba. Sannu Rauda Allah ya saka miki." Suka amsa da amin kafin Rahma tace, "Kuma abin haushi ma ko Yayar mu har yanzu babu wata maganar kirki da ta shiga tsakanin sa da ita, k'asaita da sarauta yake ji da ita ya kasa bata lokacin sa balle su fahimci juna." Umma ta sake cewa, "Wallahi shiyasa ban amince da soyayyar da yace yana yi mata ba ko kad'an, ni zuciyata fad'a min take akwai manufar da yasa yake sonta amma ba dan Allah ba." Yaya Shamsiyya tace, "Babu lallai kuma Umma shi had'uwar jini haka yake wanda baka d'auka zai saurare ka ba in Allah ya had'a jinin ku babu wanda zai ji yana so sai kai. Ita duniya ai haka take daidan wani karkataccen wani." Umma ta kawar da kai tace, "Kayya dai Shamsiyya." Yaya Ummi tace, "To me Baba yace?." "Me zai ce kuwa? Shi har yanzu bai saduda ba yana kan bakar sa ta aura masa Rauda sabida wani abun ya rufe masa ido baya ganin aibun hakan. Nidai na fad'a masa Rauda bazata aure shi ba." Shiru suka yi kowa yana juya abin a ransa daga baya aka cigaba da tattaunawa a kan maganar. Da misalin k'arfe sha biyu na safe Walida da Habiba suka kawowa Rauda ziyara lokacin ta d'an ware ba laifi ana hira da ita, ita kad'ai ce a d'akin suka shiga Habiba tana yi mata jinjina irin na sarakai tace, "Allah ya ja zamanin uwar gida kuma amaryar yarima Asad." D'an k'aramin tsaki taja suka zauna kusa da ita Habiba tace, "Ai na rantse da Allah babu amana, ace wannan abin alkhairin ya same ki sai dai naji na gari amma ko a waya baki kira kin sanar damu ba?." Walida tace, "Ai wallahi Rauda baki kyauta mana ba duk yadda muke dake." Rauda tace, "Sai abu ya dame ka ko yana maka dad'i sannan kake tunanin fad'awa wasu, ba auren sa zanyi ba kinga babu amfanin fad'ar" ta Fad'a a hankali tana kallon su. Habiba tace, "Akan me baza ki aure shi ba?, arzuk'i yazo miki har gida kisa k'afa ki ture shi." "Ba irin wannan arzuk'i ake nema ba Habiba." Walida tace, "irin wanne ake nema? Kamar a gaban ki aka fad'a mana halayyar wanda yace yana sonki d'in meye abin kin amincewa?." Rauda tace, "gidan sarauta bai dace dani ba Walida. A tak'aice ma ya akayi kuka san da maganar nan?." Habiba tayi dariya tace, "Ke kina wasa da lamarin gidan sarauta kina kuma wasa da lamarin y'an unguwa, maganar babu inda bata zaga ba wallahi." Rauda ta girgiza kai cikin mamaki kafin Habiba tace, "meyasa bai dace dake ba? Ke ba mace bace ba?." "Macece amma ba irin wacce ta dace taje can bace." Habiba tace, "kawai dai bakya ra'ayi amma ni banga aibun hakan ba." Rauda tace, "Daga furta zai aure ni abubuwa marasa kyau sai faruwa suke dani da iyalan gidan nan, har gida suka je aka dake ni da Ummana har aka ji mata ciwo a hannun ta har yanzu bai warke ba; suka d'aye kwanikan gidan mu kawai dan a wulak'anta mu.  Allah ya kawo shi Asad d'in da wanda ya buge ni aka kaimu asibiti daga nan suka kawo mu nan da sunan za'a gyara wancan ashe rushe su sukayi. Mahaifiyar sa tazo har gidan nan tana yi min gargad'i akan in na aure shi sai taga bayana, akan me zan kai kaina halaka?." Habiba tace, "bata da imani wannan babar tasa tsaf zata aikata, bana son talaka bata son talaka ya rab'e ta, amma in sha Allah sai kin shiga gidan nan matsayin matar sa in yaso ta mutu." Walida tace, "Ai na rantse da Allah zan so naji ace ta aure sa domin a nuna mata in Allah ya k'addara abu babu wanda ya isa ya canja." Rauda tace, "Nidai ku cigaba da yi min addu'a kawai amma ina cikin tsaka mai wuya. Kalli wuya na ku gani" ta fad'a tana d'aga kanta suka kalla ga shatin igiya a wajan tace, "jiya aka shigo har d'akin nan aka shak'e ni da igiya za'a kashe ni ashe sune suka aiko a kashe ni." Habiba ta dafe k'irji tace, "Mun shiga uku, daman ana irin haka a gaske?." "Nima dai abinda na gani kenan Habiba, kisa fa." Rauda tace, "To kunga meye amfanin shiga ta gidan nan matsayin matar sa?." Walida tace, "Babu wallahi." Rauda tace, "Kuma nida shi bawan Allah nan bai tab'a cewa yana sona ba, maganar sacan biyar bata had'a mu balle na tabbatar da yana sona ko akasin haka." Habiba tace, "Na fad'a miki dalilin sa baya iya doguwar magana haka Allah ya halicce shi ko ita babar tasa baya yi mata doguwar magana." Walida tace, "Amma matsayin wacce yake sonta yaci ace ya d'an yi mata magana kodan ya kafa gwamnatin sa a zuciyar ta. Itafa soyayya babu ruwan ta da wani mulki ko sarauta ko rashin maganar sa." Rauda tace, "gane min hanya Walida, babu maganar da ta tab'a had'a mu sai sau d'aya a haka zan aure shi shima?." Habiba tace, "haka ne amma dai kun san halitta mutum baya canja kansa. Mudai muna addu'a Allah ya tabbatar da lamarin nan." Rauda bata ce komai ba tayi murmushi suka cigaba da hira sama-sama. *☆☆* Hankalin Mama baya jikin ta jin labarin jikin mahaifin ta yayi tsanani wajan ciwo ba b'ata lokaci ta d'auki hanyar Kano ita da jakadiyar ta da Suhaima. Da taje nan taga duk yadda ake fad'a mata yanayin jikin nasa yafi haka duka y'an uwan ta suna nan na nesa dana kusa kowa ka kalla kasan yana cikin yanayi mara dad'i. Bayan sun baro inda yake suka ware kansu iya y'ay'an d'akin su kamar yadda suka saba tunda mahaifiyar su ta rasu basa shiga cikin y'an uwan su ware suke waje guda kamar ba jinin su ba. Suna tare su hud'u mata mazan guda uku suna nasu waje suke tattaunawa akan abubuwan da ya shafe su. Babbar cikin su itace mai hali d'aya da Mama ta kalle ta tace, "ya batun Asad kuwa?." Mama tace, "Hmm baki ga yadda na rame ba? Tashin hankali ya sako ni gaba akan auren nan nasa." Wacce take bin Mama tace, "Asad d'in aure zaiyi?." Mama tace, "Allah ya sawwake ai batun wannan aure an soke shi bai isa ya jawo min abinda fad'a a dangi ba." Y'ar autar su tace, "Abin fad'a a dangi? Auren shine zai zama abin fad'a?." Babbar cikin su tace, "To abin fad'a mana in kuka ji yarinyar da ya d'auko zai aura sai abin ya baku mamaki; kamar Asad ace ya d'auko y'ar talakawa yace ita yake so?." Mama tace, "Ai baki K'arasa ba, gata bak'a ga muni gata gurguwa gata mai tallan abinci a kan titi." Wacce take bin Mama mai suna Maimuna tace, "Shi kuma a ina ya gano ta?." Mama tace, "Bari kedai kawai, Hydar ne ya buge ta a mota kafin ya kwanta ciwo shi kuma ya nemo ta da niyar yi mata magani shikenan fa sai ga magana wai sonta yake yi, kina jin maganar nan kin san akwai asiri a lamarin." Y'ar autar su tace, "Ba wani asiri soyayya ce fa daga Allah ni banga aibu dan ya aure ta ba. Nidai nasan Asad bazai d'auko mara asali da ilimi ba, an fa daina wannan abun ace wai d'an sarauta sai y'ar sarauta indai Allah ya kulla kawai ayi." Maimuna tace, "Nima dai haka tunda har yana sonta ai zance ya k'are." Babbar cikin su tace, "Daman ku ai ba'a tab'a abin kirki daku. Yanzu namiji kamar Asad zaku goyawa baya ya auri yarinya mai kammin da aka lissafa?." "To meye a ciki da ya auri Jiddan da take so ba gwara ita ba, Jiddan nan bata da tarbiya ko kad'an ga shegiyar rawar kai a cikin ta. Meye abin so a Jidda? Kyaunta ne kawai yake rud'ar Mama amma me take dashi?." Babbar cikin su tace, "Ke malama bama son rashin kunya." Tab'e baki tayi suka tashi suka basu wajen yadda zasu fi jin dad'in tattaunawa. Ta kalli Mama tace, "Kar fa ki amince da auren nan amincewar ki daidai yake da fad'uwar darajar ki a idanun kishiyoyin ki wallahi, ki dage kai da fata wajan ganin auren nan bai yu ba in kuwa ba haka ba kina ji kina gani wata y'ar talakawa zata kwance miki d'an ki domin nan gaba in zaki ganshi sai kin neme ta sabida ta fiki kusanci dashi." Mama ta sake zuwa wuya tace, "Bari kawai Yaya zan san abinda zanyi." "Ya dai kamata" ta fad'a daga na suka cigaba da tattaunawa a kan lamarin jikin mahaifin su. A Katagum kuma da yamma mai martaba ya nemi ganin Baba kamar yadda aka tsara su biyu ne kacal a d'akin ganin bak'i na musamman mai martaba yana kan kujara shi kuma yana k'asa a zaune mai martaba yace, "Dalilin da ya saka nace a kira min kai akan batun auren y'arka da Asad, wanne mataki ake kai a yanzu ta amince ita yarinyar?." Baba ya gyara zaman sa yace, "Ranka ya dad'e ta amince; sai dai tana jin tsoron Fulani duba da abubuwan da suka faru bayan furta zai aure ta d'in da yayi." Mai martaba ya murmusa har cikin zuciyar sa yaji dad'in hakan domin kuwa shi kad'ai yasan alkhairin da ya gani a auren Asad da Rauda yace, "Ba abar tsoro bace; kamar yadda ta isa dashi muma mun isa da ita kar taji tsoro indai ta amince shine abinda nake so naji." Ba tare da tunanin komai ba Baba yace, "ta amince ranka ya dad'e, naso ma ta biyo ni sai ta nuna min baza ta iya zuwan ba shiyasa nazo ni kad'ai." Mai martaba yace, "Alhamdulillah. D'aurin auren nan kusa nake so ayi shi in yaso sai su tafi k'asar da za'a ayi mata aikin k'afar tare in sun dawo sai ayi biki a tare. Bana so ma yasan an d'aura auren sai bayan an d'aura in ba haka ba mahaifiyar sa zata iya canja masa ra'ayi lokaci guda. In Allah ya kai mu asabar jibi kenan ina so a d'aura musu aure da ita in da hali." "Allah yaja da ran mai martaba ai babu komai umarni kawai zaka yanke mu namu aikin mu bi." Mai martaba yaji dad'in kalaman Baba ya d'auko wata leda a kusa dashi ya mik'awa Baba yace, "kud'in na gani ina so, kud'in lefe da duk wani abu dake yiwa mace. Bana so a d'auki lokacin da za'ace sai an had'o kaya shiyasa na bada wannan kud'in ayi amfani dasu." Baba ya karb'a ya koma ya zauna kana yace, "Allah ya taimake ka, muna godiya Allah yaja da rai Allah yasa ayi damu." "Amin. Nine da godiya ai duk da abubuwan da suka faru aka amince aka bamu y'a kamar ta mai ilimin addini da tarbiyya." Baba dad'i yake ji har cikin b'argon sa yace, "Ranka ya dad'e dad'i mune ya kamata muji shi baku ba, Allah ya k'arawa mai martaba lafiya da imani muda aka had'a jini damu ai mune zamu gode." Murmushi yayi kana yace, "Aje ayi komai yadda ya kamata in Allah ya kaimu jibin koma gobe juma'a za'a d'aura musu aure da ita dan bana so wani abu ya jifta da za'a fasa." Baba yace, "Goben ma yayi ranka ya dad'e Allah ya nuna mana." Daga haka sukayi sallama da Baba ya yi godiya sosai ya tashi ya tafi zuwa gida zuciyar sa fari kallllll kamar an wanke masa ita haka yake ji. *sai Baba*💃🤣 [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *029.* Cikin tsantsar farin ciki Baba ya koma gida koda yaje bai sanar dasu komai ba ya adana kud'in a waje mai kyau ya cigaba da sabgar sa hankali kwance domin ya lashi takobin babu abinda zai hana auren Asad da Rauda koda bata so, daman Anas ya saka yake d'aga k'afa yanzu tunda babu batun sa ko ana muzuru ana shawo sai ya zama sirikin sarki mai jiran gado. Lokacin da ya shiga gidan da magariba suna zazaaune a waje d'aya har su Inna suna kallon tv ya samu waje ya zauna ya kalli Rauda yace, "ya jikin naki?." Rauda tace, "Da sauk'i." "Haka ake so. Wacce irin shawara kika yanke?." Rauda ta kalli Baba tace, "Akan me Baba?." "Auren ki" ya bata amsa yana kallon ta. Kai ta saukar k'asa kana tace, "Bana ra'ayin auren sa gaskiya." Baba ya d'aure fuska yana kallon ta yace, "Kamar ya bakya ra'ayi?." Rauda ta d'ago ido tace, "Eh Baba, bana son na aure shi." Baba yace, "To akan me bakya son auren sa? Wani abun kika fishi da bakya sonsa?." Umma ta bud'e baki da niyar bashi amsa ya d'aga mata hannu kana yace, "Kar naji bakin kowa a nan indai ba Rauda ba, da ita nake magana bada ku ba kar a saka min baki"ya fad'a a kausashe yana kallon ta. Dole tayi shiru ya mayar da kallon sa ga Rauda yace, "Ina jin ki." Rauda tace, "Ya fini komai Baba, kawai ni bana son auren sa ne sabida bana son sa." Baba ya gyara zama yana kallon ta yace, "ya kamata ki fara son sa kuwa domin auren ki dashi babu fashi." Rauda ta wara idanu tace, "Baba auren sa daidai yake da rasa rayuwa ta." "Nasan daman tsoron da kike ji kenan ai shiyasa kika ce bakya son sa, ki kwantar da hankalin ki a ko ina Allah yana tare da mai gaskiya, Allah bazai bari ya cutar dake ba tunda baki hakkin komai." Rauda tace, "Duk da haka Baba ni bai min ba." "Daman ai basai yayi miki ba tunda shi kinyi masa ai zance ya k'are. Zancen yayi miki ai bai tashi ba tunda shi har ya ganki yace yana so shikenan." Umma da take sauraren su ta kasa jurewa tace, "Auren dole kenan zakayi mata?." Baba ya kalli jama'ar falon yaga har su Khalil suna wajan sai ya fasa fad'ar abinda yayi niya ya tashi yana kallon su yace, "Kowa ya tashi yaje yayi sallah" yana fad'a ya fita daga falon bai kuma cewa komai ba. Babu wanda ya kuma magana aka tashi aka tafi sallah bayan sun idar da sallar i'sha a d'aki Rauda ta kalli Umma da take kan sallaya tace, "Umma kenan Baba auren dole zaiyi min?" Ta fad'a idanun ta na kawo ruwa zatayi kuka. "Babu batun auren dole tunda kince bakya so auren nan baza'a yi sa ba, abu mai sauk'i ne naje har fada na nemi ganin martaban na fad'a masa halin da ake ciki ai ina da k'afar zuwa, dan san abin duniyan mahaifin ki tsaf zai aurar musu dake." Rauda tayi shiru tana tunani tace, "Ina jin yawan fad'uwar gaba tsakanin kwanakin nan Umma." Umma tace, "Ai dole kiji fad'uwar gaba, har gida fa akazo za'a kashe ki in baki ji fad'uwar gaba ba ai baza kiji dad'i a zuciyar ki ba." Shiru Raudan tayi ganin kamar ta shiga damuwa ya saka Umma tace, "Ki kwantar da hankalin ki kome kika ga ya faru Allah ya rubuta faruwar sa tun farko, ki nutsu ki ta addu'a Allah zai kawo miki mafita." Kai kawai ta d'aga jikin ta a sanyaye Umma ta fita daga d'akin ita kuma ta samu ta lallab'a tayi sallah raka'a biyu ta karanta addu'ar da manzon Allah S.A.W ya bayar ta istikhara kana ta tashi ta kwanta badan tana jin bacci ba. Da safe jiki a sanyaye ta tashi sabida mafarkin da tayi wai ana bikin su da Asad shi da ita sai kuka suke amma da an gansu anga yanayin amarya da ango, gamsuwa take ji a zuciyar ta da gangar jikin ta na Asad shine mijin ta amma ta k'i barin hakan yayi tasiri a jikin ta sai kawar da tunanin take yi a dole baza ta bari yayi tasiri ba sai hakan ya haifar mata da sanyin jiki. Ko abinci bata iya ci ba tana zaune a d'akin tayi uban tagumi dana sanin ma yin istikhara take yi da tasan abinda zata gani kenan ko abinda zata ji a jikin ta kenan da bata yi ba. Tana nan zaune Umma ta shigo ganin yanayin ta ya saka tace, "Ke kuma lafiya kike ko lek'owa bakiyi ba?." Numfashi ta sauke kana tace, "Umma mafarki nayi." Umma ta zauna kusa da ita tace, "Mafarki kikayi kin auri Asad ko?." Rauda ta kalli Umma da mamaki kafin tace, "Umma ya akayi kika sani?." Umma ta dafa ta tace, "Nima nayi Rauda. A daren jiya ban kwanta ba sai da nayi ta addu'a akan nema miki zab'in Allah, na kuma rok'i Allah da ya nuna min zab'in da yayi miki ko a mafarki ne. cikin ikon Allah sai Allah y nuna min Asad shine mijin ki duk da mafarki ba gaskiya bane amma yana kasancewa wani lokacin Rauda. bazan ja da ikon Allah ba addu'ar kuma da nayi Annabin mune ya koyar damu ita sai nake ji a jikina yanzu na gamsu da auren ki dashi." Rauda ta rausayar da kai kana tace, "Umma akwai tarin abubuwa a gaba wanda shekaru na sunyi kad'an na fuskance su, ki duba ikirarin mahaifiyar sa a kaina, bana son auren nan ko kad'an Umma." "To Rauda nidai ban san me zance ba amma mu barwa Allah zab'i kawai, in ya zab'a miki shi ki saka a ranki shine alkhairin, in kuma akasin haka ya faru ki saka a ranki ba alkhairi bane ba. Ki tashi kizo ki karya" ta fad'a tana fita daga d'akin ta bar Rauda cikin zurfin tunani. *☆☆* A babbar fadar Katagum bayan sallar juma'a aka d'aura auren Asad da Rauda a kan sadaki naira dubu d'ari lakadan ba ajalan ba, babu mutane sosai daga mai martaba da Liman sai Wambai da abokan sa sai kuma Baba da k'annen Baba harda y'an uwan Umman Rauda sai kuma Hydar. Asad bai san me yake faruwa ba tunda yayi sallah ya fita daga gidan dan gabad'aya baya jin dad'in zaman gidan ko kad'an bai tsaya ba balle yasan abinda yake faruwa. A wannan lokacin suka samu labarin rasuwar Sarkin Kano mahaifin Mama, Asad yana zaune a guest house ya kashe wayar sa gudun kar a dame shi bai ma san me yake faruwa ba. Tv da take a kunne ana haska labarai itace ta sanar dashi rasuwar kakan nasa ba shiri ya taso ya dawo gida ya tarar dasu Hydar suna niyar tafiya dole shima ya shiga cikin su akayi tafiyar dashi. Da yake tafiyar mota ce basu isa ba sai bayan la'asar lokacin ana ta k'okarin tafiya kai shi makwancin sa an so a jira zuwa safiya sabida wanda basu iso ba amma ya'yan sa sunce suna so ya shiga a juma'ar kodan albarkar ta dole aka hanzarta komai aka tafi kai shi. Jana'izar ta had'a manyan mutane da mayan sarakuna da y'an siyasa kowa ka gani yana wane wannan, wannan yana na fika wannan ma yana nima na fika. Basu samu ganin Mama ba sai bayan sallar i'sha suka shiga cikin gidan aka nemo musu ita idanu sunja sabida kuka. Mai martaba sarkin Katagum ya mata gaisuwa y'ay'an ta ma suka yi mata gaisuwar rashin mahaifin ta da addu'a kafin Mai martaba yace, "ina babu damuwa a turo sauran muyi musu gaisuwa." Kai kawai Mama ta d'aga kafin ta tashi ta fita jim kad'an sai gata da y'an uwan ta mata suka gaisa sukayi musu gaisuwa kafin su tafi masaukin su. A Bristol hotel suka suka mai martaba yana zaune a personal room d'insa shi kad'ai su Asad da sauran makarraban sa kowa yana wajan da zai kwanta. Abinci aka kawo kamar ba'a so sabida yawa sa aka bawa kowa yaci ya k'oshi banda mai martaba dan su ba abincin kowa suke ci ba musmaman ma in yasan an san da zuwan sa kamar abincin dan shi akayi. A b'angaren Baba lokacin da ya bar wajan d'aurin auren bai koma gida har yaji labarin rasuwar yasan bai da k'afar zuwa da babu abinda zai hana shi zuwa yiwa sirikar sa gaisuwa ba to yana gudun abinda zai je yazo. Lokacin da ya koma gida suna zaune gabad'ayan su har y'ay'an da suke gidan mijin su sunzo ya shigo da sallama yana cewa, "yawon ku yayi yawa fa yaushe kuka zo harda zaku kuma dawowa yau?." Dariya sukayi dukkan su kafin su gaishe shi ya amsa kana yace, "nama ji dad'i dana ganku gabad'ayan ku." Umma ya mik'awa ledar hannun sa ta karb'a yace, "kud'in hannun ki kud'i ne na kayan lefe, da kud'in na gani ina so na y'ar ki Rauda." Gaban Umma ya fad'i ta kalli kud'in da tarin yawa ta kalle shi ta kalli Rauda da tayi sak tana kallon sa tace, "Malam ban gane ba." Baba yace, "Zaki gane yanzu ai" ya fad'a yana sake d'auko kud'i a aljihun sa ya mik'awa Rauda ganin tana kallon sa ya saka yace, "karb'i mana." Ba musu ta karb'a hannun ta na rawa yace, "Sadakin ki kenan jama'a sun shaida d'aurin auren ki da Asad ga goro da alewa" ya Fad'a yana fito dasu daga aljihun sa. Dammmmm k'irjin su ya buga ta kalli Baba da sauri ta kalli kud'in ta kalli Umma da take kallon sa itama ta kalli y'an uwan ta kafin tace, "Aure kuma Baba!?." Baba yace, "Eh aure Rauda. D'azun nan aka d'aura auren ku a fada ba'a masallaci akayi ba shiyasa baizo kunnen ki ba." Rauda tayi sak ta kasa furta komai sai Umma ce tace, "Malam wai da gaske ko wasa?." "Na tab'a yi muku irin wannan wasan ne?." Inna tace, "Yau dai ka fara Malam." Ya kalle ta yace, "ba wasa nake ba da gaske nake, da waliyan ta duka akayi d'aurin auren har da yayyen ki ma suma sun shaida" ya fad'a yana kallon Umma. Ganin sun kasa magana ya saka ya kalle su yace, "kud'in hannun ki kuyi mata siyayyar kaya dan tafiyar su Misra baza ta wuce wannan satin ba, ayi siyayya yadda ya kamata duk abinda zata buk'ata a siya ragowar kud'in kuma suna hannuna za'a yi wani abun dasu. Ke Rauda bani na hannun ki" ya fad'a yana mik'a mata hannu jikin ta duk ya saki ta mik'a masa ya saka a aljihu yana murmushi yace, "to ai kin gani, ana so a bawa yarinya sadakin auren ta a hannun ta shiyasa na baki, yanzu kuma za'ayi wata hidimar dasu." Yaya Ummi tace, "Baba dan Allah da gaske yanzu Rauda ta zama matar Asad halak malak?." "Mtswww! Wai makaryaci kuka mayar dani ne ko me?." "A'a Baba abin ne muka ji shi kamar a mafarki." "To kuji shi kamar gaske domin Rauda matar Asad ce a yanzu, wacce take ganin k'arya nake ta kira kawun ta ta tambaya" yana fad'ar hakan ya tashi ya fita yana tsaki. Dukkan su sun kasa motsin kirki kowa yayi shiru an rasa mai magana kafin wayar Umma ta fara k'ara, Ummulkhairi ce ta mik'o mata tana fad'in, "Baba Malam ne." Umma ta karba ta d'auka ta saka ta amsakuwa daga can b'angaren yace, "yanzu abinda kika yi mana kin kyauta? Ace yau za'a d'aura auren Rauda bamu sani ba sai a lokacin za'a sanar damu?, yanzu da mahaifin nata bai neme mu ba ke ko a jikin ki ko?. Ai kin kyauta." Jin wannan kalami na Yayan Umma sai Rauda ta tashi ta shiga d'aki tana kuka domin ta tabbatar da abinda ake fad'a gaskiya ne ba k'arya ba ita a yanzu matar aure ce. Kuka sosai take yi bata san yadda sukayi da Kawun ba sai ganin shigowar su tayi dukkan su suna tsaye a kanta hakan ya sake karya mata zuciya ta sake fashewa da kuka. "To meye na kukan kuma bayan aikin gama ya gama? Kiyi fatan Allah yasa alkhairi ne kawai ba kuka ba" Umma ta fad'a tana kallon ta. Yaya Ummi tace, "Dole fa tayi kuka Umma, shi wanda aka bata wata magana mai k'arfi wacce zata nuna da gaske yana son ta bata tab'a shiga tsakanin su ba kawai kuma sai a bashi ita dan kawai yana da kud'i da mulki?." Yayar mu tace, "to yanzu wa kike fad'awa haka? Kaf dai nan kin san babu wanda ya bada auren Rauda sai Baba shi ya kamata ki samu da wannan zancen." Tace, "Tsakani da Allah fa ba'a kyauta mata ba wallahi, an tauye ta auren dole za'a kira wannan ba auren soyayya ba." Yaya Shamsiyya tace, "Yanzu duka wannan ya wuce ai rarrashin ta ya kamata kiyi ba wannan maganar ba." Yaya Ummi zata kuma magana suka ji muryar Baba yana fad'in, "Duk wacce ta d'auki k'afa tace zata je fada da niyar sanar da mai margaba abinda ya faru Allah ya isa ban yafe mata ba, duk wacce ta zuga Rauda akan k'in karb'ar auren nan itama Allah ya isa ban yafe ba" yana fad'ar hakan ya juya ya fita Rauda ta sake rushewa da kuka. Raguwa akayi a d'akin aka barta da yayyen ta mata suka dinga rarrashin ta dak'yar aka samu tayi shiru tana goge idanun ta Yaya Ummi tace, "ko kefa, kina addu'a fa kina neman zab'in Allah ki saka a ranki wannan shine zab'in Allah gashi ya zab'a miki lokacin da baki kawo hakan ba daman haka ikon sa yake. Ki kwantar da hankalin ki ki kuma nutsu kita maimaita Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un zaki ji zuciyar ki tayi sanyi." Rauda tace, "Yaya ya zanyi? Baba ya zab'i kaini inda za'a kashe ni sabida kud'i kawai da mulki baya ta lafiya ta da rayuwata ta abinda zai samu kawai yake yi. Dame za'a kira auren nan? Auren cushe ko auren dole?." "Duka babu d'aya tunda shi ya fara ganin ki yace yana so babu zancen auren cushe a nan, kwantar da hankalin ki zakiyi ki kuma saka a ranki zab'in Allah kenan." Haka suka dinga rarrashin ta sai da ta dawo nutsuwar ta sannan suka k'yale ta amma kowa zuciyar sa babu dad'i. Da daddare gidan ya rage sai su kawai matan auren sun tafi a falon da yake na Umma Baba ya kira Umma da Rauda da har lokacin bata dawo daidai ba yace, "ke in zaki nutsu ki karb'i k'addarar gaban ki ki nutsu, aure an riga an d'aura shi na kuma fad'a miki koda wasa naji wata magana ban yafe ba." Hawaye ya sakko mata ta goge yace, "Kar kiga shiru babu mijin naki kakan su ya rasu suna can Kano gidan gaisuwa, da ya dawo nasan zai zo ku tattauna." Kai kawai ta d'aga tana goge idanun ta bata ce komai ba dan zuciyar ta a raunane take. Baba yace, "Ku fara siyayyar da wuri dan tafiya yi miki aikin nan da wasu kwanaki ne masu zuwa gwara ku tanadi komai kafin lokacin azo ana an manta wani abun." Nan ma bata amsa ba ya kalle ta yaga tana goge idanun ta sai ya sassauta murya yace, "Ita k'addara in Allah yayi nufin faruwar ta akan abinda baka zata ba Allah yake k'addaro maka ita, duk kuma abinda kake addu'a a kai kana neman yayi maka zab'in Alkhairi kaga ya zab'a maka koda baka so ka rungume shi domin shine alkhairin daka rok'a. Ki saka a ranki auren sa shine alkhairin kuma shine mijin da Allah ya rubuta zaki aura tun kina ciki, sannan kuma kiyi biyayya ga zab'in sa wannan koke-koken babu abinda zaiyi miki sai ciwo da zai saka miki aure dai an riga an d'aura shi." Kai ta d'agawa nan ma bata ce komai ba. Baba yace, "Tashi kije ki kwanta." Ba musu ta d'auki abinda yake taiamaka mata wajan tafiya ta tafi d'aki Baba ya kalli Umma yace, "Banji kince komai ba." Umma ta kalle shi ta tab'e baki tace, "me zance to? Me kake so nace?, hukunci ne ka yanke ka bawa y'arka wanda bata so, ka bawa y'arka wanda yafi k'arfin ta, ka kaita inda ake neman rayuwar ta, ka kaita inda za'a wulak'anta ta me zance maka kuma?." Ta fad'a a fusace tana kallon Baba da alama ranta a b'ace yake sosai. Ya lura da hakan a yanayin maganar ta yasan ranta a b'ace yake sai ya murmusa yace, "dad'in ta da kike maganar taki y'ata kike cewa tunda kuwa kin yarda y'ata ce ina da ikon yanke duk hukuncin dana so a kanta." "Eh shiyasa kud'i suka rufe maka ido ai ka siyar da ita, dan wannan siyarwa ne ba aurarwa ba. Ka manta abinda ya faru akan maganar auren idanun ka ya rufe kawai kud'in kake gani; har gida aka zo kashe ta sabida auren amma ka manta sabida an cika maka aljihun ka da kud'i. Ka siyo mata wulak'anci da kud'in ka duk abinda ya faru da ita nan gaba wallahi kaine sila, kuma sai Allah ya saka mata domin y'ay'a ma suna da hakki akan iyayen su" tana gama fad'ar hakan ta tashi ta bashi waje bai damu ba dan daman yasan za'ayi hakan shidai tunda burin sa ya cika kowa ma yayi ta fad'an ya gaji ya daina. A can Kano Asad bai san me yake faruwa ba har gari ya waye suka koma gidan rasuwar suka bar Mai martaba a hotel, a can suka zauna da rana tayi suka dawo masaukin su. Kira Asad ya samu daga mai martaba ya isa inda yake ya same shida Hydar a zaune Hydar yana matsa masa k'afar sa. Waje ya samu nesa dashi ya zauna kafin ya kalle shi yayi murmushi yace, "ba yau zaku koma ba ko?." Asad yace, "Eh Abba." Ya kyad'a kai yace, "Zamu koma yanzu shiyasa kafin mu tafi na kira na sanar dakai abinda ya faru a jiya wanda baka sani ba." Asad ya kalli mahaifin nasa baice komai ba mai martaba yace, "Aliyu ko nace Asad na lura da tarin soyayyar da kake yiwa yarinyar da ka furta kana so, tsoron halin mahaifiyar ka da biyayyar da kake mata ya saka kake tauye kanka a karo na babu adadi. A wannan karon nace bazan bari ka rasa abinda kake so ba kamar baya kuma na sanar da kai zan tsaya maka a ko ina wajan ganin ka samu abinda kake so koda ita bata so, jiya nida kaina na jagoranci d'aurin auren ka da yarinyar a fada ba tare da sanin ka ba, a yanzu haka matar kace kaima kuma mijin tane!." [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *030.*      Da sauri ya d'ago yana kallon fuskar mahaifin sa sai kuma ya saukar da idanun sa k'asa ya sake kallon sa yaga da murmushi a akan fuskar mahaifin nasa ya sake mayar da kansa kasa cikin sakannin da basu wuce uku ba fuskar sa washe sai kuma ta koma yadda take babu alamun walwala a tare da ita, wani abu yake ji yana shiga jikin sa zuciyar sa ta dinga bugawa da sauri ya kasa furta ko wacce kalma balle ya tabbatar da abinda aka fad'a masa gaskiya ne duk  da yasan mahaifin sa bazai tab'a yi masa k'arya ko wasa da irin wannan kalami ba. Ganin yayi shiru ya kasa furta komai sai Mai martaba ya sake cewa, "Asad baka ji me nace bane?." Asad ya d'ago raunannun idanun sa ya kalle shi yace, "Takawa ba mafarki nake ba?." "Ba mafarki kake abinda kaji nace gaskiya ne. Kai mijin Rauda ne ita kuma matar kace." Numfashi ya sauke ya kalli Hydar sai kuma ya had'd'iye saliva kana yace, "Amma Takawa....." dakatar dashi yayi ta hanyar fad'in, "Kana sonta ba?." Asad yayi shiru na wani lokaci kana ya d'aga kansa alamun eh sai kuma yace, "Mamaaaaa!" Ya furta a hankali a sanyaye cikin rauni. Mai martaba ya murmusa yace, "Kana sonta ita kuma Maman ka bata sonta shiyasa zaka hak'ura sabida ita haka ne ko?." Asad ya d'aga kansa alamun eh mai martaba ya kuma cewa, "wannan shine karo na babu adadi da kake son abu bata so kake hak'ura sabida ita, a wannan lokacin baza ka hak'ura ba zaka mallaki abinda kake so koda ita bata so d'in shiyasa na yanke hukunci ba tare da ka sani ba ko ita ta sani." Asad yayi shiru bai iya cewa komai ba mai martaba yace, "Ka kwantar da hankalin ka a wannan karon bazata raba ka da abinda kake so ba Asad ina bayan ka, in kun dawo gida zaku tattara kuje can inda za'a samar mata da lafiyar k'afar kuje kai da ita kuyi zaman ku har sai sanda na nemi ku dawo sai ka dawo." Kai ya d'aga bai iya cewa komai ba domin gabad'aya zuciyar sa a damalmale take baya jin farin ciki haka zalika baya jin bak'in ciki. Mai martaba yace, "ya naga baka murna ko baka sonta ne?, Hydar naga ya had'e fuska" ya fad'a yana kallon Hydar cikin zolayar Asad d'in. Murmushi Hydar yayi yace, "Takawa ai a zuciya yake farin cikin ni na sani." Murmushi yayi yana kallon Asad da har lokacin kansa yake a k'asa bai d'ago ba. Mik'ewa mai martaba yayi suka mik'e suma yana kallon Asad yace, "Tunda baza ka nuna min kana farin ciki da abinda nayi maka ba ai shikenan ni zan tafi." Sai a lokacin yayi murmushi shi kansa ya kasa gane halin da yake ciki a wannan lokacin shiyasa ya kasa dariya ya kuma kasa kuka. Tare suka fito suka raka mai martaba ya shiga mota sannan suka dawo masaukin su.  D'akin da Asad ya sauka ya shiga ya tarar da Aliyu yana niyar fitowa ya bishi da kallo shima kuma shi yake kallo alamun rashin gaskiya a tare dashi, ganin kallon da Asad d'in yake masa sai ya waske yace, "Oga deaf nazo duba ring d'ina ko a nan na bari ashe baya nan" ya fad'a yana ficewa ya bishi da kallo haka kawai yaji zuciyar sa bata amince dashi ba gabad'aya. Zama yayi a kan kujera ya jingina da kujerar yana kallon sama kamar mai son hango wani abun a saman, jin sa yake wani iri in ya tuna abinda mai martaba yace masa sai yaji wani iri tsigar jikin sa har tashi take, abinda ya tsaya masa a zuciya bai wuce Rauda na son sa ko bata son sa ba dan shi dai yasan baiga alamun tana son sa a tare dashi ba, cize bakin sa yayi a bayyane yace, "that's mean ta amince?" Shiru yayi yana tuna abubuwan da suka faru sai kuma yace, "No bana tunanin ta amince, but ta yaya akayi auren?" Ya fad'a yana dafe kansa da yaji yana sara masa. 'In bata sona fa aka aura mata ni? Ya zanyi da ita ya zanyi da Mama?, na riga na yiwa Mama alqawari zan barta yanzu kuma gashi na canja anya zata yafe min?.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan yana jin komai yana fita daga kansa ga k'irjin sa yayi masa nauyi sosai kafin ya shafa kansa yana jin sa kamar ba shi ba. Motsi yaji a bayan sa hakan ya saka ya kalli wajan yaga Hydar ne ya shigo yana amsa waya kafin ya kashe wayar ya zauna kusa dashi yana kallon sa yace, "Oga deaf as groom" ya fad'a da murmushi yana kallon sa. Asad da ya zuba masa idanu bai ce komai ba Hydar yayi dariya yace, "ka daina kallona idannun ka na rikita ni." Asad yace, "kai ka shirya komai?." "Yeah na san komai na kuma shirya komai Deaf. A karo na babu adadi bazan bari ka rasa abinda kake so ba musamman wannan da ta kasance abokiyar rayuwar ka." Ya sauke numfashi yace, "But ita bata sona." "Mahaifin ta da kansa yace ta amince kaga kenan tana sonka." "Bana tunanin da gaske ne." "Mahaifin ta ai bazai mata k'arya ba, ka ajjiye abinda kake jin tsoro babu abinda zai faru sai alkhairi." Ya sauke numfashi ya kulle idanun sa kana ya bud'e yace, "Rayuwar ta tana cikin hatsari a lamarin auren nan, u forgot abinda ya faru right?." "Ban manta ba Asad amma a wannan karon babu abinda zai faru, lokaci kad'an ma da zaku wuce Cairo Mama bata san anyi ba." Kai yake girgizawa cikin sanyin jiki alamun bazai iya aikata hakan babu sanin Maman sa ba, nan take yaji auren ya sake fita a ransa komai baya yi masa dad'i dan sai Mama nasan abu shima yake ji yana so. "Kar ka damu dan Mama bata sani bafa tunda Abba ya sani kuma shine ya yanke hukunci ai komai ya k'are." Asad ya sauke numfashi ya d'aga kai sama kamar mai son gano wani abun a saman. Hydar ya kalle shi yace, "Ka kira ta for the first tym as your lovely wife." Kai ya sake girgizawa alamun a'a Hydar yayi murmushi kawai ya daki kafad'ar sa yace, "kurma nawa, ina ji da kai sosai, zan iya yin komai dan samuwar farin cikin ka, zan iya barin komai da farin cikin ka" yana fad'ar hakan ya tashi ya bashi waje yana dariya zuciyar sa fess karon farko Asad ya mallaki abinda yake so ba tare da takurar Mama ba. Bayan kwana biyu. Ranar da akayi addu'ar ukun mai martaba sarkin Kano su Asad suka d'auki hanyar Bauchi suka bar Mama ita kad'ai a gida sai anyi addu'ar bakwai zata dawo ita,  bata san me ya faru ba har lokacin tana cikin alhinin rashin mahaifinta ba ta kan komai take bi hakan ya saka bata cika d'aukar waya bama balle a samu wanda zai sanar da ita bak'in labari a wajan ta. Bayan sun huta da daddare Asad na zaune a d'akin sa yanaa karatu Hydar ya kira shi a waya, bai d'auka ba sai da ya kira sau uku sannan ya d'auka baiyi magana ba ya kashe ya fito zuwa falo.  A tsaye ya tarar da Hydar d'in ya kalle shi alamun lafiya yake neman sa?. Hydar yace, "Takawa ya bada umarnin kaje gidan su matar ka yanzun nan shiyasa na sanar da kai" yana fad'ar hakan ya wuce ya barshi tsaye yana tunanin abinda ya kamata yayi. Yasan shirin Hydar ne sarai amma tunda ya ambaci mahaifin sa dole yaje babu yadda zaiyi. Shi bawai baya sonta bane yana sonta har lokacin kawai wasu abubuwa ne suke caja masa kai har yaji komai yana fice masa a rai shiyasa baya wani zumud'in hakan kwata-kwata. D'akin sa ya koma ya d'auki makullin mota a kan madubin d'akin har ya gota sa ya dawo yana kallon kansa a madubin, kayan jikin sa yake kalla riga da wando ne dogaye marasa nauyi a jikin sa sai yaji a zuciyar sa bai kamata yaje da kayan jikin sa ba. Ajjiye key d'in yayi ya shiga band'aki ba jimawa ya fito ya shirya cikin yadi fari mara nauyi mai shara-shara ya saka hula bak'a kalar aikin jikin yadin ya fashe jikin sa da turare masu sanyi ya tsaya yana kallon kansa a madubin bayan ya gama shiryawa. Shi kansa yasan yayi kyau sosai ya murmusa sai kuma ya cize baki ya d'auki key d'in motar ya fita a sanyaye. Da Aliyu suka had'u a falon har ya gifta Aliyu sai kuma ya dawo da baya ganin irin kallon da Aliyun yake masa ya wara idanun alamun kallon na meye?.  Aliyu yayi dariyar shak'iyanci ya cize bakin sa kamar yadda Asad d'in yake yi yace, "na tsaya ina kallon angon talakan yarinya, wow u look very beautiful deaf" ya fad'a yana tasowa yazo kusa dashi yana kallon sa. Asad baice komai ba ya fita shi kuma yayi dariya yana cize baki cike da mugunta sai da ya tabbatar Asad ya hau mota ya fita sannan ya shiga d'akin Asad d'in da yake a bud'e. K'arewa d'akin kallo yake yana girgiza kansa ganin sa tsaf dashi khamshin turaren Asad d'in ya cika d'akin wanda indai kasan Asad ka sanshi da wannan turare, a jikin bango ya jingina yana bin d'akin da kallo kamar me neman wani abun kafin ya girgiza kansa ya fita. Asad kuwa a sanyaye yake driving d'in motar gabad'aya jikin sa ya saki kansa take ji yana rasa masa sosai ga tunanin ta yadda zai tunkari gidan su Rauda as sirikin gidan duk sai yaji wani iri a jikin sa wallahi, Dak'yar ya iya kawo kansa k'ofar gidan ya faka motar yana kallon gidan amma ya rasa abinda zaiyi shiyasa ya zauna a motar kawai yana kallon gidan. Kamar wasa ya ganta tana nufar gidan ita da wani saurayi suna ta murmushi ita dashi har tayi tuntub'e zata fad'i yayi saurin rik'o ta ya gyara mata zaman sandinan nata suka cigaba da takawa har suka shiga cikin gidan da alama wani nata ne ta san shi sosai. Wani irin zafi Asad yaji yana taso masa daga zuciyar sa yana mamaye dukkan jikin sa har cikin idanun sa, cize bakin sa yake yana bin su da kallo har suka shiga gidan ya runtse ido ya kai hannun sa ya rik'e wuyan sa da duka hannayen sa biyun nan take yaji har fatar wuyan tayi zafi sabida zafin zuciyar sa har ya huda ya fito ya mamaye fatar sa. Ya sani yana da kishi Allah ya yishi cikin maza masu zafin kishi ko kad'an baya so yaga an rabi abinda yake so koda kuwa takalmi ne balle kuma matar sa. Idanun sa har sun fara canja launi daga fari zuwa ja ciwon kansa ya k'aru fiye da wanda yazo dashi dana sanin zuwa wajan ya mamaye masa zuciyar sa da ruhin sa ji yake ina ma baizo ba da baiga abinda zai d'aga masa hankali haka ba. Knocking d'in glass d'in ake yi amma bai iya kalla ba sai akayi kusan sacan ashirin sannan ya kalli gefen tagar ganin mahaifin ta ya saka shi daurewa ya bud'e motar ya fito waje. Baba ganin sa sai ya washe bakin sa yana jin farin ciki a zuciyar sa ganin kamar Asad ya kasance siriki a wajan sa me zaiyi in ba farin ciki ba?. Kafin Asad ya gaishe shi Baba ya riga shi furta, "Barka da Dare Asad." Sai Asad yaji wani iri ya dawo da nutsuwar sa jikin sa ya duk'a ya gaishe shi ya amsa baki a wangale kana yace, "ya karin hak'uri kuma?." Asad ya amsa da fad'in, "Alhamdulillah." "Allah ya jikan sa ya gafarta masa ya duba abinda ya bari." "Amin" Asad ya amsa a tak'aice domin baya jin dad'in yanayin sa gabad'aya. Baba yace, "ka k'araso ciki mana Asad kamar wani bak'o ka tsaya a waje." Babu yadda ya iya dole yabi bayan sa zuwa ciki , a k'aramin falon dake wajen cikin gidan ya zauna yana kallon sa yace, "Bara na turo maka ita ku gaisa" Baba ya fad'a da nishad'i yana kallon sa. Murmushi yayi kawai baice komai ba Baba ya fita shi kuma ya d'auko waya yana dannawa ko zai rage masa abinda yake ji a zuciyar sa. Ba jimawa yaji motsi tare da sallama a sanyaye ya d'ago ya kalle ta ya amsa shima a sanyaye, fuskar ta a tamke take babu alamun walwala ta k'araso ta zauna ta d'ago ido ta kalle shi tace, "Barka da dare." Bai iya amsawa ba sai zuba mata ido kawai da yayi yana k'arewa fuskar ta kallo ganin yadda fuskar tata tayi fresh duk da batayi kwalliya ba ko kad'an amma fuskar ta tayi kyau sosai bai sani ba ko shi kad'ai yaga hakan.   Jin shiru bai amsa ba ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido sai ya d'age gira guda d'aya ya basar kamar ba kallon ta yake ba muryar sa a ciki yace, "Ya jiki?." Rauda ta tab'e baki tace, "Alhamdulillah, ya hak'uri." "Alhamdulillah" ya furta daga nan yayi shiru itama tayi shiru. Shiru k'aramin falon yayi babu wanda ya kuma magana a cikin su kusan mintina uku suna a haka kafin yace, "waye shi?." A sama taji maganar ta d'ago da mamaki tana kallon sa kafin tace, "Wa kenan?." Bai bata amsa ba sai ido da ya zuba mata tayi saurin d'auke nata idanun ta kalli gefe amma batayi magana ba. "You're my wife ya kamata ki sam da wannan, I can't tolerate any kind of relationship tsakanin ke da wani" ya furta a sanyaye duk da maganar a kausashe take zuwa kuma a ciki alamun ba son maganar yake yi ba. Rauda da take jin sa ta kalle shi jfin kallon kama raina min hankali d'in nan tace, "ikon Allah, wai kana so kace kishi kake?, daman ana kishi without soyayya ne?" Ta fad'a cikin rainin hankali tana kallon sa. D'ago idon da yayi suka had'a ido sai ta sauke nata k'asa sai ya samu kansa da yin murmushi baice komai ba ya mik'e ya wuce ta kana yace, "Good night" abinda ya furta kenan ya fita ya barta zaune a wajan kamar wacce aka dasa a wajan. Idanun Rauda suka ciko da kwalla a bayyane ta furta, "Rainin hankali, Baba ga abinda ka jawo min nan na fara gani tun yanzu" Kafin ta mik'e hawayen ya zubo daga idanun ta tana k'okarin takawa da abinda yake taimaka mata take tafiya k'afar sandar ta zame zata fad'i ba tare da zaton ta ba taji an rik'ota ta fad'a jikin abu mai laushi da khamshi mai d'aukar hankali, sai da ta sauke numfashi sabida dad'in khamshin da taji kafin ta kalli abinda ya tare ta d'in ta ganshi tsaye yana rik'e da ita kamar bashi ba. Hawayen idanun ta yake kalla da mamakin abinda ya sakata kuka daga fitar sa haka yana so ya tambaya amma baya tunanin zai iya yin hakan sai ya cika ta ya kalle ta yace, "Be careful" yana fad'a ya k'arasa inda ya zauna ya d'auki key d'in motar sa ya fita daga falon bai kuma kallon ta ba. Jikin ta take bi da hancin ta gabad'aya khamshin turaren jikin sa take yi ta cize bakin ta takaicin ta ya k'aru ji take kamar ta rufe kanta da duka amma babu damar hakan ta fito tana hawaye ta nufi cikin gidan. Bata ga Umma a falo ba ta shiga d'aki ta zauna ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da tausayin kanta da rayuwar ta a gidan wanda baya sonta yayi amfani da k'arfin mulki da son kud'in Mahaifin ta ya aure ta. Muryar Umma taji a kanta tana cewa, "Meye na kukan kuma bayan kinyi min alqawarin baza ki kuma kuka akan wannan ba?, kince min kin amince da k'addara meyasa kike zubar da hawayen ki haka Rauda?." D'ago kai tayi tana goge idanun ta kafin tace, "Umma baya sona ban san wanne irin zama zanyi dashi ba ga tarin qalubalen dake cikin aure na dashi." Umma tace, "Ki daina cewa haka yana sonki Rauda in baya son ki bazai aure ki ba, in baya son ki bazai zo inda kike ba a yau, in baya son ki bama zaki sanshi ba Rauda. kita addu'a wannan kukan bazai amfane ki da komai ba." Dak'yar Umma ta rarrashe ta tayi shiru zuciyar ta cike da tausayin ta. Asad kuwa da farin ciki ya koma gida duk da fuskar sa bata gwada hakan ba amma zuciyar sa kamar an wanke ta da ruwa mai sanyi haka yake ji, abinda yake bashi tsoro sai ya tuna Mama sai taji fad'uwar gaba da tashin hankali a zuciyar sa. Lokacin da ya gama shirin sa zai kwanta sai ya tuno da kalaman Rauda sai ya murmusa a bayyane yace, "ko ta yaya zan tabbatar mata da ita son ta ban sani ba." Murmushi ya kuma yi ya kwanta yana jin nishad'i a zuciyar sa da kuma tashin hankali a wani b'angaren na daban. Aliyu yana tsaye a tagar d'akin sa yana kallo yaga dawowar Asad ya murmusa yana girgiza kai domin yafi kowa jin dad'in yin auren Asad da Rauda da akayi domin Allah kad'ai yasan abinda zai cimma da wannan auren shiyasa yake cikin farin ciki dashi yake kuma jin dad'in sa dari bisa dari. Dariya yayi mai sauti kana yace, "Zaku tafi Cairo amma kai baza ka dawo ba Asad ita zata dawo wajena matsayin kaine, zan cigaba da zama da ita a matsayin kai zuwa lokacin da zan kore ta daga cikin rayuwar gidan nan gabad'aya, sai na tabbatar na d'and'ana mata bak'in ciki a rayuwar ta sai tayi dana sanin kiran Aliyu da mahaukaci. zan cigaba da amsa sunan kai har abada kai kuma zaka kasance matattace a idanun duniya a yayin da ka koma Aliyu ni kuma na koma Asad. Ina godewa Allah da ya kasnace da kai nake kama bada Hydar ba zanyi duk abinda nake so da sunan Asad ne ba Aliyu ba, zan mallaki Jidda matsayin matata a matsayin kaine ba Aliyu ba, zan mallaki karagar katagum matsayin Asad ba Aliyu ba. Saura kiris hak'a ta ta cimma ruwa, wannan shirin nawa shi nake yiwa take da Kwantan b'auna" ya furta yana shafa sajen sa cikin tsantsar farin ciki da walwala. Dariya ya kuma yi ya tafa hannun sa lokacin da ya tuno dasu waziri ya cize baki ya girgiza kai domin shi kad'ai yasan makomar da ya tanadar musu da zarar komai ya dawo hannun sa zasu gane kuran su, zasu gane sunyi kuskuren bari yasan dukkan sirrkan su bama su kad'ai ba duk wanda ya kasance a k'ark'ashin garin Katagum sai ya san Aliyu yana mulki......... Tofa Aliyu ya k'ulla k'ullalliya🤔🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *031.* Washe gari ta kama ranar Talata akwai zaman fada da safe duk wani mai muk'ami a masarautar katagum ya hallara anyi gaisuwa kowa ya watse wanda zasu nufi office sun nufa. Bayan an tashi daga fada mai martaba ya nemi ganin Asad lokacin har ya tafi company ya dawo ya amsa kira, shi kad'ai ne a zaune kusa dashi kamar koda yaushe dan in zai gana dashi bai cika zama da wani ba ya kalle shi yace, "Asad akan batun matar kane anjima jirgin ku zai tashi zuwa Cairo ya kamata ka fara shiri." Gaban Asad ya fad'i dan baiyi tunanin abin zai zo da sauri haka ba ya furta, "Allah ya k'ara maka lafiya ni bani da visa Egypt." Mai martaba yace, "Na sani ai shiyasa na saka aka yi maka komai ta hannu Hydar, anjima da k'arfe hud'u zaku tashi kaje ka fara shiri itama ka sanar da ita na dai sanar da mahaifin ta amma yana da kyau kaima ka fad'a mata, gwara kuje a sama mata lafiya." Asad k'irjin sa duka yake kansa na k'asa ya kasa d'agowa shud'ewar wasu sacanni kafin yace, "Abba Mamaaaa!." Mai martaba ya zuba masa ido yana kallon sa cikin burgewa, ya jima baiga yaro mai k'arancin shekaru kamar sa wanda yake da tsananin biyayya ga iyayen sa kamar Asad ba, yana gujewa b'acin ransu ko kad'an baya so ba kuma ya k'aunar hakan ta faru ko kad'an, yana iya hak'ura da farin cikin sa sabida nasu farin cikin, yana yin abinda suke so koda shi ba shi yake so ba shiyasa a wannan lokacin yayi alqawarin samar masa da abinda yake so a karon farko a rayuwar sa. Cikin taushin murya kamar yace, "Zaki ka kwantar da hankalin ka komai zai zo da sauk'i Maman ka baza tayi fushi dakai ba, kaje kayi abinda nace kawai." Shiru yayi na wani lokacin kafin ya mik'e ya fita jikin sa a sanyaye matuk'a. Azahar tayi lokacin ya shiga masallacin cikin gidan yayi sallah kana ya koma ciki ya tsaya gaban kayan sa yana tunanin wanda zai d'auka domin tafiya dasu, numfashi ya fesar ya lumshe ido ya rasa ma abinda zaiyi. Kalaman Mama ne suke dawo masa cikin kansa ya koma gefen gado ya zauna ya dafe kai yana ji kamar ya kurma ihu sabida tsaka mai wuyar da yake ciki, Mama tace kar yayi Mai martaba yace yayi nawa zai d'auka nawa zai ajjiye?. Hydar ne ya shigo ganin a yanayin da yake bai kula shi ba ya jawo madaidaiciyar jaka ya fara zuba masa kaya da duk wani abun da zaiyi amfani dasu ya zuba a ciki kamar Asad d'in ne ya had'a ya zuge zip d'in jakar ya kalle shi yace, "ga automatic wheelchair a bayan boot d'in motar ka zaifi tayi amfani dashi sabida tafiyar Airport tunda ba private get zaku bi ba." "Hydar ta ya zan iya tafiya Mama bata nan? Ka sani Mama bata sonta ba kuma ta goyan bayan auren ta meyasa zan zab'e ta na bar Mama?" Ya fad'a a raunane yana kallon sa. Hydar yace, "ita wacece da zaka zab'e ta ka bar Mama? Ba zab'in ta kayi ba ka bar Mama ba ka d'auki abinda kake so ne kawai a karo na farko na tabbata kuma Maman zata duba wanda ka bari sabida ita na baya zata yi maka adalci a karo na farko." "U never understand" ya furta yana dafe kansa domin shi kad'ai yasan fitinar da hakan zai haifar. Hydar yace, "yanzu kenan umarnin Abba ne baza ka iya cikawa ba?." Kallon sa yayi shima ya kalle shi yace, "Yeah gashi kana k'okarin bijirewa bayan shima umarni ya baka." Jin hakan sai ya sauke numfashi ya tashi jiki a sanyaye ya ahiga band'aki shi kuma ya fita ya k'yale shi. Ya jima sosai sannan ya fito yayi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya suit black yayi kyau sosai kamar baturen America ya shiga d'akin karatun sa ya d'auki littafan da yasan zai nema ya zuba a jaka ya kalli agogo. K'arfe uku na yamma ya rage aww uku kenan jirgin su ya tashi, kan gadon sa ya kalla yaga Passports dinsa dana Rauda babu na iyayen ta bai damu ba ya d'auka ya saka a aljihu a lokacin Hydar ya shigo yana kallon sa yace, "Wow! Ango kayi kyau." Bai iya cewa komai ba Hydar ya d'auki jakar yace, "muje na saka maka a mota, tare ma zamu je in yaso sai na dawo da motar taka gida." Asad yace, "Ina Aliyu da Suhaima?." "Suhaima suna Kano da Mama Aliyu kuma kasan yana wajan y'an matan sa yanzu ai ko?." "Yanzu zan tafi ban yiwa mutanen gidan sallama ba?." "Haka Abba yace." Shiru yayi baice komai ba Hydar ya fita ya barshi dan yasna in ya biye masa sai su b'ata lokaci har ayi missing flight. Kulle d'akin yayi ya zare key d'in ya saka a aljihu yana juyowa Hafiz ya shigo falon yana fad'in, "Asad tafiya ba sallama?." Asad ya kalle shi yace, "urgently ne ban shirya ba." Hafiza yace, "Allah ya dawo da kai lafiya." "Amin" ya furta yana yin gaba shima yabi bayan sa. Mota ya shiga Hydar ya shiga mazaunin driver yaja suka fita daga cikin masarautar kewa tana mamaye zuciyar Asad ya juya ya kalli gidan yana ji a jikin sa kamar ya fita kenan har abada. Numfashi ya sauke lokacin da ya daina hango gidan ya lumshe ido yana jin jikin sa wani iri. Hydar ya kalle shi yace, "ya naga kana kallon gidan kamar baza ka dawo ba?." Baice komai ba suka d'auki hanyar gidan su Rauda yana jin sa wani iri kamar bashi ba har suka k'arasa k'ofar gidan suka faka. Hydar ya kalle shi yace, "muje ciki ko?." Asad kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fito Hydar ya bud'e bayan motar ya d'auko kujerar kome ya tuna kuma sai ya mayar da ita baya ya kulle boot d'in suka nufi cikin gidan. Suna zaune dukkan su da alama duka y'an gidan suna nan suka tsaya basu shiga ba sai ga Baba ya fito suka gaisa yayi musu iso zuwa ciki, da sallama suka shiga cikin gidan suka amsa gabad'ayan su Asad shi dai bai kalle su ba ya gaishe su dukkan su suka amsa daga nan yayi shiru baice komai ba. Hydar yace, "Mama zasu wuce Airport lokacin tashin jirgin su ya kusa kar lokaci ya k'ure." Umma ta sauke numfashi ta kalli Rauda da take zaune cikin doguwar riga ta Abaya mai mayafi cikin kayan da aka siyo mata da Baba ya bada kud'in fuskar ta a cushe baza ka banbance yanayin da take ciki ba lokaci d'aya. Umma ta kalli Asad da kansa yake k'asa tace, "Amana ce gata zan damk'a maka a hannun ka, na sani kafi k'arfin Rauda ta ko wanne b'angare amma kuma kana naka Allah yana nasa dukkan mu bamu tab'a kawo haka ba ko a mafarki sai gashi ta kasance ana kiran mu matsayin ma'aurata a yanzu. Dan Allah ka duba Allah ka rik'e Rauda hannu biyu kaine ka ganta kace kana sonta a haka kar wata rana ka tuna da asalin ta kayi mata wani abun. gata nan amana ce a hannun ka ka rik'e min ita dakyau dan Allah, kar ka bari wani abun ya same ta." Yadda Umma tayi magana da sanyi kamar zata zubar da hawaye sai zuciyar sa ta karye nan take yaji anya baiyi kuskuren nuna yana sonta ba duba da irin yanayin gidan da yake?, da ace baice bai furta ba da yanzu ba'a aura masa ita ba, tabbas yasan baza'a k'yale ta ba a yanzu haka baza'a rasa wanda suke neman su ga sun mata wani abun ba kawai dan a raba su. Sai yake ji a zuciyar sa ina ma ya danne bai nuna ba kodan ta zauna lafiya ita da iyayen ta, yanzu in wani abun ya same ta shi ya zaiyi kenan?. A sanyaye ya kalli Umman yace, "Ina sha Allah Mama ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru." Maganar sa ta fita kamar koda yaushe a tausashe kuma a k'asa in ba nutsuwa kayi ba baza kaji me yake cewa ba. Sosai Umma taji dad'in abinda yace tace, "na gode sosai, Allah ya bada ikon rik'e ta ya kawar da duk wani abun k'i a zaman ku na tafiyar da dawowar ku." Da amin Hydar ya amsa shi kam a ciki ya amsa Hydar ya kalli agogon hannun sa yace, "lokaci na tafiya yana dakyau muje." Tare aka mik'e shida Hydar suka yo gaba kafin su fito ma har sun shiga mota. Yaya Ummi ce take taimakawa Rauda tana tafiya fuskar ta duk ta jik'e da hawaye ta kuma kasa tantance kukan me takeyi, na farin ciki zata samu lafiya ko kuma kukan tausayin kanta take yi. Lokacin da suka isa bakin motar aka bud'e mata bayan motar ta shiga Hydar yace, "Ammmm basai ta shiga dasu ba akwai abinda zatayi amfani dashi in mun fita" ya fad'a yana kallon Yaya Ummi ganin zata saka sandinan a cikin motar. Yaya Ummi ta kalle ta tace, "Dan Allah ki daina Kuka Rauda kamar baki karb'i k'addara ba?. Da kanki kika cemin kin daina kuka meyasa kuma kikeyi yanzu?, dan Allah ki daina tafiya ce ta d'an lokaci zakuyi zaki dawo gida dan ba tarewa kikayi ba gabad'aya. Kiyi hak'uri ban san me kike ji ba amma nasan da ciwo abinda kike ji shiyasa nace kiyi hak'uri." Kai kawai Rauda ta d'aga bata iya cewa komai ba. Asad da yake tsaye ya kalli su Baba da murmushi a fuskar sa yace, "Sai mun dawo." Baba ya washe baki yace, "Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya ya bada lafiyar daka je nema." Da amin ya amsa ya bud'e gaban motar ya shiga suka ja motar suka bar k'ofar gidan a daidai wannan lokacin sautin kukan ta ya cika mota. Shiru motar babu mai magana sai kuka da take yi sosai babu wanda yace mata kanzil dan daman kuka dole tayi shi lokaci d'aya ba tare da ta shirya ba a raba ta da iyayen ta ai dole ta zubar da hawaye. Wayar Asad ce take k'ara duk hankalin sa baya jikin sa kukan da take yi har ta katse bai ji ba aka kuma kira Hydar ya kalle shi yace, "Relax Mr man, ana kiran ka." D'auko wayar yayi ya duba gaban sa ya fad'i ganin sunan Mama yana yawo a kan screen d'in wayar tasa. Daurewa yayi ya d'auka ya saka a kunne take cewa, "Asad kana ina yanzu?." Shiru yayi kana yace, "Ina hanyar Bauchi zanje airport." "Airport kayi me a can?." Shiru yayi bai amsa ba ta kuma cewa, "ko Kano zaka zo?." Nan ma bai bata amsa ba sai taja tsaki tace, "Bana son rashin hankali ina yi maka magana kayi min banza, wani lokacin shirun nan naka na iskanci ne in kaso maganar kana yi na lura da hakan." Ya bud'e baki zaiyi magana tace, "kome kaje yi a airport d'in ka tsaya yanzu jirgin su Jidda zai sauka ka kaisu gida ita da Mum dinta kar kace min kuma wani abun ya tsayar dakai" tana fad'ar hakan ta yanke kiran dan a tunanin ta ba k'asar zai bari ba dan tasan baya barin k'asar sai ta sani. Sauke wayar yayi daga kunnen sa ya kalli Hydar da yake tuk'in sa ya d'auke kai baice komai ba har suka isa airport d'in. Mintina talatin ya rage jirgin su ya tashi suka fito daga motar Hydar ya fito da jakunnan su ya fito da kujerar ya turawa Asad alamun ya fito da ita, bud'e gefen da take yayi har lokacin kanta na kan cinyoyin ta tana kuka mai sauti, ya kasa mata magana ya kuma kasa tab'a ta balle ta d'ago yayi mata alama ta sakko ya tsaya cak kawai yana kallon ta ya rasa me zaiyi. Hydar ganin yana b'ata lokaci yace, "Asad lokaci yana tafiya fa." Kamar bazai yi ba sai kuma ya mik'a hannu a hankali ya bubbuga kafad'ar ta tana jin sa tayi masa banza dan tayi alqawarin indai bai magana ba wallahi baza ta fito ba. "Raudaaaaaa!" Ya furta in sweet voice wacce ta ratsa shi kansa balle kuma ita da aka kira sunan nata ba shiri ta d'ago kanta tana kallon sa da idanun ta da suka jik'e sabida hawaye shima kuma ita yake kallo, yamutsa fuska yayi ganin yadda hawaye ya b'ata mata fuska idanun ta sunyi ja da hannu yayi mata alama da ta goge idanun ta ya nuna mata kujarar alamun ta sakko. Bata motsa ba sai kanta da ta mayar k'asa ya matsa sosai kusa da ita ya rik'e hannayen ta duka ya fito da ita ya zaunar da ita da kansa a kan kujerar ya kulle k'ofar motar ya danna madannin tafiya a jikin kujerar ta fara tafiya a hankali shi kuma yana bayan ta Hydar kuma yana jawo musu jakar su. Kusa dashi Hydar ya koma yana dariya yana fad'in, "Wannan ita ake kira da silent love." Bai kula shi ba har suka shiga ciki aka duba jakar su kamar yadda ake yi suka shiga ciki Hydar ya d'aga musu hannu yana murmushi zuciyar sa cike taf da farin ciki ya juyo. Wara idanu yayi lokacin da idanun sa ya fad'a kan na Mum da Jidda dukkan su a firgice da alama sunga wucewar Asad da Rauda sai ya basar ya maze ya d'auko izzar da ya ajjiye ya d'orawa zuciyar sa ya kalle su yace, "Mum kece?." Ta kalle shi tace, "Hydar wa nake gani kamar Asad?." Hydar yaja fasali kana yace, "shine." Jidda tace, "Ina waje? Kuma kamar shida wata nake gani wacce ita?." Hydar ya k'are mata kallo kana ya tab'e bakin sa yace, "ki tambaye shi" yana fad'ar hakan ya fita daga wajan ya barsu da tunanin wacece da kuma inda Asad zaije bayan Mama ta sanar dasu shine zai zo ya d'auke su. Ina yaje? Shida wace suka gani sun tafi....?. Babu mai basu amsa dole Mum tayi k'wafa suka fito suka tafi. Asad kuwa suna wucewa basu tsaya ba daman jirgin su yana k'asa motar da zata kai su ga inda jirgin yake suka suka ba jimawa sai gasu a inda jirgin yake, fitowa yayi ya fito da ita daman jakar su an auna ta sai sun je waccan garin zasu d'auke ta suna tafiya a hankali har suka isa steps na jirgin, kallon ta yayi yaga kamar a tsorace take sai ya rik'e hannun ta guda ya matsa ta d'ago ta kalle shi ba tare da yayi magana ba ya girgiza mata kai kawai ya saki hannu ganin mara lafiya ce kujerar ta baza ta hau ta steps ba sai aka nufi d'aya k'ofar da ita ta hau kai har cikin jirgi. Rauda duk ta rud'e ta gigice a tsorace take matuk'a ji take kamar ta saki fitsarin wando sabida tsoro, yana zaune kusa da ita yana kallon yanayin fuskar ta sai yayi murmushi haka kawai yake jin nishad'i ya rik'e hannun ta guda d'aya kamar d'azu itama sai tak'i kallon sa taushin hannun sa na ratsa ta amma ta jure bata kalle shi ba har aka sanar da tashin jirgi. Ihuuu da jirgi ya fara alamun tashi yaga ta runtse ido ta kwace hannun ta toshe kunnen ta da sauri ya d'auki abinda aka tanada dan toshe kunne ya saka mata sai taji bata jin k'arar sosai ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba a lokacin jirgi ya fara gudu a k'asa kafin ya d'aga ya lula sararin samaniya. Tashin da yayi tayi gefe ta fad'a kafad'ar sa ya rik'e ta a haka bai sake ta ba har sai da ya tabbatar sunyi nisa a sama sannan ya cika ta ta koma ta zauna tana raba idanu tana kuma hawaye har lokaci. A bangaren su Mum ko ta kan Hydar basu bi ba drop d'in mota suka d'auka zuwa katagum jikin Mum har rawa yake burin ta ta isa gida ta kira Mama taji ina Asad ya tafi sannan shida wa suka tafi. Tun a compound na gidan take mata waya bata d'auka ba har ta hau saman gidan ta sai a sannan Mama ta d'auka tana fad'in, "Sadiya kin san ina cikin jama'a." Mum tace, "abu ne na gaggawa Fulani shiyasa na dame ki da waya, ina Asad ya tafi na ganshi a airport a b'angaren international alamun k'asar zai bari? Sannan wacece wacce na gansu tare da ita?." Mama tace, "What! Asad da wata kuma sun bar k'asar nan? Anya kuwa shine?." "Shine mana bayan Hydar na gani shine ya kawo shi Airport d'in ma kuma na ganshi shima ya ganni." "Sadiya relax babu inda Asad zaije ba tare da ya fad'a min ba, sannan kuma wacece zaiyi tafiya da ita?, sai dai in Aliyu kuka gani amma ba Asad ba." Mum tayi shiru tana girgiza kanta cikin amincewa da maganar Mama tabbas Aliyu ta gani da wata budurwar tasa ba Asad ba Hydar ya raina mata hankali ne kawai, ajiyar zuciya tayi tace, "Haka ne fa kuma Fulani; duk na tsorata ne wallahi kar naje ko Asad d'in ne har wad'an can talakawan sun fara canja masa tunani yana yin abu baki sani ba." Mama tayi dariya tace, "K'arya su tasha k'arya, ai nafi k'arfin su wallahi tunda na yanke alaqar nan dake tsakanin su ta riga ta yanku, tunda nace a bari nasan an bari, tunda nace bana so nasan shima yanzu baya so. Ta ko wanne b'angare na mamaye ko ina ko kara na ajiiye Asad bai isa ya tsallaka ba sai na bada umarnin hakan, zancen waccan y'ar talakawan ai ki d'auka ya zama tsohon labari." Mum tace, "An gama ranki ya dad'e, mayi magana anjima ki huta lafiya" ta fad'a tana yanke wayar ta bita da kallo a bayyane tace, "Saura lokaci kad'an ya dawo a bayan hannun ki ba tafin hannun ki ba, in na fara sarrafa Asad baki isa ya saurare ki ba daga ni sai Jidda kawai zai dinga gani. Hmmmmm Rabi'atu kenan sai kin yabawa aya zak'in ta zumud'in zama uwar sarki zai bar zuciyar ki domin a zahiri zaki zama uwar sarki a bad'ini kuma nice uwar sarkin domin komai sai abinda nace za'ayi, zan nuna miki a wannan fannin na dame ki na shanye wallahi sai Jidda ta zamar miki ciwon ido a cikin gidan nan. ki kiyayi had'uwar mu" ta fad'a da murmushi tana kallon wayar ta kamar da Maman take magana..... *Nikam nace kun makara*🏃🏼‍♀️😂 [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *032.* *Four Seasons hotel Cairo.* D'aya daga cikin manyan hotels d'in da ake ji dasu kenan dake cikin birnin Cairo wato babban birinin dake cikin k'asar Egypt kenan suka sauka, duk da kasancewar dare yayi amma haske tarrr ko ina kamar rana fitulu sun haske ko ina baza kace dare bane sai ka kalli sararin samaniya. Babban falo ne guda d'aya mai d'auke da d'aki guda biyu manya babu abinda babu a cikin su girman su kuwa ba'a cewa komai. Tunda suka shiga falon take wara ido take kallon falon dan bata tab'a ganin irin sa ba a rayuwar ta gabad'aya shiyasa take kalla kodan ta kashe kwarkwatar idanun ta, yayi kyau komai na cikin blue hatta carpet da komai na cikin sa blue ne. Asad zama yayi a gefen kujerar dake d'aya daga cikin kujerun wajan ya shafa aljihun sa yana neman wayar sa amma yaji babu ita, ya mik'e tsaye yana duba jikin amma babu wayar sa a jikin sa. Dafe kansa yayi ya kalli Rauda da take k'arewa falon kallo har lokacin yaga wayar ta akan cinyar ta ba tare da yace komai ba ya d'auki wayar sai a lokacin ta kalle shi amma ba ita yake kallo ba ya danna number sa ya kira, a kashe yake jin sim card d'in nasa yaja k'aramin tsaki ya ajjiye wayar tata ya kama k'ugu ya rik'e yana kallon wani wajan daban dan yasan ya yar da wayar a wani wajan. Juyowa yayi ya kalle ta suka had'a ido ta d'auke kanta baice komai ba yaja jakar ta zuwa d'aki guda d'aya ya ajjiye yana fitowa ya nuna mata d'akin da hannu baice komai ba ya fita da sauri. Da kallo ta bishi ta sauke ajiyar tace, "Allah gani gare ka, ka kawo min d'auki da gaggawa" ta fad'a tana danna inda ya danna d'azu kujerar ta fara tafiya da yake ba tudu har tazo k'ofar d'akin, tsayawa tayi tana kallon kanta a k'aton mudubin da yake dogo tayi murmushi a bayyane tace, "Rauda a Cairo." shiga d'akin tayi lafiya wani abun bai tokare ta ba. "kan bala'i" ta furta ganin d'akin har yafi falon ma kyau ta bishi da kallo babu abinda ya d'auki hankalin ta sai wata taga ta glass doguwa wacce kake hango titi motoci suna ta wucewa ko kana zaune basai ka tashi ba. Kallon d'akin take tana tafiya a hankali har ta isa wata k'ofa da take tunanin band'aki ce ta bud'e girman sa dakyaun band'akin ta shagala da kallo kafin ta samu damar cire kayan jikin ta tayi wanka. Tana iya tsayawa da k'afa d'aya hakan ya saka a tsaye tayi wankan da k'afa guda d'aya sai dq ta gama taga towels da yawa a ma'ajiyar su sai khamshi suke yi ta d'auki d'aya ta d'aura tana fad'in, "Wai nima irin y'ar gayun nan, ikon Allah kenan Rauda ce yau a wata k'asar daba Nigeria ba." Zama tayi akan kujerar tata ta fito ta koma bakin gado ta sauka akan kujerar ta zauna gefen gado ta bud'e jakar ta tana dubawa, dogayen riguna masu mayafi da riga da wando shi Yaya Ummi ta zuba mata a ciki sai na bacci doguwa guda biyu sai k'ananu sauran, ta d'auki doguwar ta saka ta saka turare mai khamshi ta hau kam kujerar tana kallon d'akin da tunanin ko ina ne alqibla, wata takarda ta gani da take nuna gabas ta juya kujerar ta tayar da sallar magariba da i'sha. K'asaru tayi bayan ta idar taji bacci na k'okarin kama ta ga kuma yunwar da take ji a cikin ta, agogo ta kalla na d'akin taga k'arfe d'aya na dare tayi hamma ta koma kan gadon ta zauna sanyin a.c na rantsa ta amma rashin sabo da tsoro ya hana ta kwanciya. Wayar ta da take gefe ta gani ta d'auka tana duba number da ya kira d'azu ta danna number sai taga tayi kama da number da aka tab'a kiran ta ga kiran nan ma yana nan da adadin lokacin da aka d'auka ana wayar hakan ya tabbatar mata itace, ajjiye wayar tayi tace, "Kenan daman shine ya kira ni?." K'arar bud'e k'ofa ya saka ta kalli wanda ya shigo ta ganshi ya canja kaya zuwa k'ananu riga da wando marasa nauyi hannun sa rik'e da ledar abinci ya ajjiye mata a gefen ta ba tare da yayi magana ba ya juya zai fita tace, "Baka ji ba." Cak ya tsaya kafin ya juyo ya kalle ta ya d'aga gira alamun yana jinta tace, "Zan iya kiran Ummana yanzu?." Kai ya girgiza alamun a'a da hannu yayi mata alamun ta bari sai da safe daga haka ya fita baice komai ba. Tsaki taja tace, "Aikin banza shi a lallai ga d'an sarki, koma me kayi min dai Allah sai ya saka min" ta fad'a tana jawo ledar ta bud'e tayi karo da lafiyayyar shinkafa da kaza sai khamshi take zubawa ga ruwa da lemo a ciki ba shiri ta baje a kan gadon taci ta k'oshi tasha ruwa. Ta d'an jima a zaune kafin ta kwashe kayan ta zame ta kwanta cikin lokaci kad'an bacci ya d'auke ta. A b'angaren Asad yana zaune a falon yana cin nasa abincin hankali kwance babu tunanin an zuba masa wani abun a ciki ya gama ya d'auko kwalin sabuwar wayar da ya siya da sim card d'in k'asar ya kunna ya d'ora email d'in sa nan take komai nasa ya dawo kan wayar ya saka card d'in kana ya saka a chaji ya tashi domin bacci yake ji ya gaji, kallon d'akin da take yayi yaga haske har lokacin sai ya nufi d'akin k'irjin sa yana bugaw, yana bud'ewa ya ganta a kwance tana bacci ta cure waje d'aya da alama sanyi take ji. Murmushi yayi kad'an wani abu yana motsawa a ransa wanda bai san meye shi baya k'arasa inda take ya rufa mata bargon ya kashe hasken d'akin sannan ya fita daga d'akin ya shiga nasa d'akin ya kwanta zuciyar sa cike da tunani kala-kala bacci ya d'auke shi. Kiran asuba da ya karad'e d'akin da yake kwance ya farkar da Asad ya tashi yana yamutsa fuska dan rabon da yayi bacci mai tsaho irin sa babu farkawa har ya manta duk da ba wani mai tsahon bane amma a wajan sa mai tsaho ne, alwala yayi ya fito ya kalli d'akin da take yaga still babu haske ya k'arasa a nutse ya tura k'ofar d'akin sanyi ya dake shi yayi baya kad'an dan shi ba mutum ne mai son sanyi sosai ba, sake kutsa kai d'akin yayi har lokacin bacci take hankali kwance cikin bargo mai laushin gaske ta b'oye dukka jikin ta fuskar ta kawai ake gani. A hankali yake takawa a nutse har ya isa kusa da ita fuskar ta yake kallo cikin shaukin sonta da kuma k'aunar ta da yake ji tana shiga cikin jikin sa a hankali kamar a lokacin ya fara sonta haka yake ji, kamar zai kai hannun sa kan fuskar ta sai kuma ya fasa ya janye tsaya ya nutsu sosai kamar na shi ba sannan ya fara bubbuga gadon a hankali. Bud'e ido yaga tayi suka had'a ido sai da yaga bacci ya sake ta baice komai ba ya fice ita kuma ta bishi da kallo kafin ta kalli agogon bangon d'akin sai kuma taji kira alamun za'a tayar da sallah. Zaune ta mik'e tana goge idanun ta ta jawo kujerar ta zauna a kai zuwa band'aki tayi alwala ta fito ta tayar da sallah. Bayan ta idar d'auko wayar ta ta shiga application na karatun alkur'ani ta fara karantawa a zuciya amma bakin ta na motsawa. Bata jima sosai tana yi ba ta fara azkhar kamar koda yaushe har ta kai k'arshe ta ajjiye ta fara lazumi a zuciyar ta. Motsin sa taji a bayan ta ya k'araso inda take ya kalli a.c d'akin har lokacin tana aiki ga kuma sanyin d'akin yace, "bakya jin sanyi?." Kallon sa tayi kamar baza tayi magana ba sai ta tuna nasihar Umma tace, "Ina kwana." "Ya jiki?" Abinda yace kawai kenan ya ajjiye ledar hannun sa tace, "Da sauk'i." Baice komai ba itama haka ya fita ta bishi da kallon mamaki tana jin zuciyar ta na karyewa hawaye suka fara zubo mata bata hana kanta ba ta dinga kuka har ta koma ta kwanta tana kuka bata kuma duba ledar ba. Shima ya jima sosai yana karatun da ya saba yayi azkhar har k'arfe bakwai na safe yana zaune ya tashi ya shiga d'aki ya kwanta. K'arfe tara ya farka yayi wanka ya saka doguwar riga irin ta larabawa ya fito zuwa falon a lokacin ake danna door bell ya bud'e k'ofar ya karb'i abinci daga restaurant d'in hotel d'in ya mayar da k'ofar ya kulle. A kan table ya ajjiye abincin ya k'arasa inda ya jona ruwan zafi ya d'auko butar ya k'araso ya zauna ya had'a tea yana sha a nutse ya bud'e wanda aka kawo yaga kayan maiko ne kwai, dankali, planten, sai sandwich. Sandwich d'in ya d'auka guda d'aya yana ci bayan ya gama ya rufe sauran ya mik'e k'afa akan table d'in ya d'auki remote yana canja channel d'in TV. Ajjiyewa yayi ya d'auki wayar sa ya kira number Hydar dan yasan yana can yana neman sa, bai d'auka ba bai kuma kira ba sai ya kira layin mai martaba. D'auka akayi hakan ya saka shi ya nutsu ya sauke k'afar sa k'asa a nutse yace, "Assslamu alaikum." Daga can b'angaren Mai martaba yace, "Wa'alaika salam, Zaki ya kwanan Misra?." Murmushi yayi kana yace, "Alhamdulillah, Barka da safiya Takawa." "Barkan ka Asad, ya kuka tashi?." "Alhamdulillah." "Ka kira gidan su ka had'a su da ita dai ko?." Asad yayi shiru alamun baiyi ba Mai martaba jin yayi shiru sai yace, "Hakan bai kamata ba ai Asad duk inda suke yanzu hankalin su yana kanta suna so suji ya take, ka kira ka had'a su suyi magana." "In sha Allah" ya furta a hankali kafin Asad yace, "Abba Mamaaaa ta dawo?." Mai martaba yayi murmushi yace, "Bata dawo ba Asad, koda ta dawo kar ka damu komai zai zo da sauk'i kaji." Kai ya d'aga kamar yana gaban sa kafin yace, "Kayi gaggawar kaita asibitin ayi mata aikin nan, ka duba ina tunanin yau ne date d'in aikin da akayi booking za'a mata, ka duba dai Hydar yayi booking a Saudi German." Nan ma kai ya d'aga kamar yana ganin sa kafin yace, "In sha Allah za'a yi abinda akace." Daga nan sallama suka yi ya yanke wayar daidai nan kiran Hydar ya shigo ya d'auka. "Our groom, how was your first night? I hope you enjoy it" Hydar ya fad'a cikin tsokana. Tab'e baki Asad yayi ya murmusa kad'an Hydar yana bashi nishad'i ba kad'an b kana yace, "First night? With who?." "Your wife mana." "U are not serious Hydar."  Dariya Hydar yayi kad'an yace, "Oga Deaf as mijin aure, wallahi ganin abun nake kamar wasa fa." Bai bashi amsa ba yasan kuma daman bazai ce ba hakan ya saka ya kuma cewa, "U know what deaf? Kar ka bari kayi asarar wannan time d'in da kuka samu tare kayi k'okarin nuna mata kana sonta da gaske in ka lura zaka ga kamar gani take tilasta mata akayi ta aure ka, so Is better ka nuna mata kana sonta sosai sonta ya saka ka auro ta ba wani abun ba, ka gane ai abinda nake nufi ina nufin dai ayi komai." Baice komai ba Hydar yace, "Yeah kayi k'ok'ari before Mama ta gano komai ta dawo da kai gida." Gaban sa ya fad'i matuk'a ya sauke numfashi yace, "lemme call her, excuse me" ya fad'a yana niyar kashe wayar yaji Hydar yace, "Amma dai bada number nan zaka kira ta ba ko?." Asad yayi shiru bai magana ba Hydar ya kuma cewa, "Naga number Egypt kasan kuma bata san baka nan ba so gwara ka kira ta da layin ka in ba haka ba zata gane baka nan, daman jiya mun had'u dasu Mum sun ga wucewar ka." "Ohhh god! Hydar I lost my phone" ya fad'a yana dafe kansa. Hydar yace, "nayu mamaki dana ga number outside country dan nasan baka canja number kai da taka kake using a ko wacce k'asa, to yanzu ya za'ayi kenan gashi babu damar yin swap online dole sai kazo Nigeria, ga Mama indai ka kira ta da wannan number zatayi saurin d'agowa baka nan kuma kasan baka fad'a mata ba." Asad ya kasa cewa komai duk tsoro ya cika masa zuciya sam baya son abinda Mama zatayi fushi dashi gashi bazai iya jurewa har ya koma bai mata waya ba, beside bai san lokacin da zai koma Nigeria ba tunda ko aikin ma ba'a yi mata ba, laifi goma da shirin kenan ga laifin ya tawo babu izinin ta, ga laifin auren da yayi bata so, ga laifi rashin kiran ta waya sabida rashin layin sa bazai iya ba sam. Hydar ya katse masa tunani yace, "Ya za'ayi kenan Deaf?." Asad ya sauke numfashi kana yace, "bazan iya d'aukar wannan lokacin without nayi magana da Mama ba Hydar, I can't" ya fad'a a raunane kamar zaiyi kuka. Hydar yace, "Yaushe za'a yi mata aikin da akayi booking? Ina jin yau ne in akayi mata aikin kaga zata jima a kwance sai ka siyi ticket kazo kayi swapping ka koma a gani na hakan zai fi." Asad baice komai ba ya yanke kiran dan bai san me zaice masa ba. Shiru yayi yana kallon wani wajan daban dan Allah ya sani bazai iya jure har gobe ko jibi ba sannan yayi magana da Mama bazai iya jurewa ba sam. Motsin k'ofa yaji hakan ya saka ya juyo ya kalli inda yaji motsin ya ganta zaune a kan kujerar ta sanye da doguwar riga ta saka hula tayi kyau sosai kwana d'aya tal fuskar ta ta washe har annuri yake fitarwa, Kasa d'auke ido yayi daga kallon ta tana tawowa a kan keken wayar ta a cinyar da alama bata kula dashi bama. Idon ta takai inda yake suka had'a ido sai gabanta ya fad'i ta d'auke ido gashi tazo kusa dashi ya bita da kallo ji yake kamar ya jawo ta jikin sa gabad'aya ko zai samu sassaucin abinda yake a ji a zuciyar sa, kallon sa take shima yana kallon ta kafin ya fara janye idanun sa daga kanta ya mayar kan TV. Itama bata ce komai tayi shiru bata motsa ba taji maganar sa yace, "your breakfast." Bata motsa ba taji kuma me yace shi kuma yasan taji shiyasa ya share ta. Wayar sa ya d'auka ya kira number Baba aka d'auka suka gaisa ya mik'a mata wayar alamun ta karb'a, karb'a tayi ta saka a kunne jin muryar mahaifinta sai ta saki fara'a suka gaisa ta saka aka kaiwa Umma suka gaisa farin ciki ya cika zuciyar ta sun jima suna magana da Umma har ta fara kuka kafin ta kashe wayar bata bashi ba ta rik'e a hannun ta tana kuka sosai. Yana ji bai motsa ba yana kallon ta yana jin kukan nata wani iri a jikin sa ya lumshe ido ya bud'e a nutse ya kalle ta yaga ta d'ago tana goge idanun ta tana jan numfashi alamun kukan ya tsaya, wayar ta mik'a masa ya karb'a tace, "Na gode." Baice komai ba ya kalle ta suka had'a ido sai ya nuna mata abinci alamun taci ba musu ta zuba tea d'in tana sha a hankali. Mik'ewa tsaye yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita, ganin ya fita ya saka bud'e bowl d'in dankali ta fara ci da sauri tana ci dan yunwa take ji kawaici kawai take yi bata so taci a gaban sa shiyasa yana barin wajan ta fara ci da sauri-sauri, had'a ido sukayi dashi ya dawo sai tayi sak ta kasa cinye abinda ta zuba a bakin ta sai kallon sa da take yi sai taga yayi murmushi mai sauti kad'an ya d'auki wayar sa ya fita ya barta. Kunya taji kamar ta nutse dankalin da bata iya ci ba taji ya fita a kanta ta shanye tea d'in duk yunwar sai taji ta k'oshi ta ajjiye cup d'in tana raba idanu. Ba jimawa ya dawo ya kalle ta yace, "Wear your veil." Gani yayi tana k'okarin komawa d'akin ya dakatar da ita ya shiga da kansa yaga mayafin rigar a kan gadon ya d'auko ya bata ta yafa suka fita daga d'akin. Inda aka tanada dan ajjiye mota a hotel d'in suka k'arasa wajan farar mota babba mai tudu da kyau ya danna remote d'in motar sai ya kalle ta ya bud'e gaban motar ya rik'e ta ta shiga motar ya nad'e keken ya saka a bayan motar ya shiga yaja suka fita daga hotel d'in, kallon sa take a zuciyar ta tana mamakin inda ya samo wannan motar a k'asar da ba tashi ba. *Nigeria.* "Finally Asad ya tafi ya bamu waje lokacin da zamu gabatar da abinda muke so yayi yanzu" Fulani Hajiya ta fad'a tana kallon Waziri da yake tsaye a kusa da ita. Murmushi yayi kana yace, "Anyi mai wahalar kam, abinda ya rage a gaba yanzu shine....." kafin yayi magana yaji ance, "Duk yadda za'ayi kar a barshi ya dawo Nigeria nan kusa, kar kuma Mama tasan cewa baya nan in ba haka ba komai ya dawo baya" Aliyu ya fad'a yana shigowa yana binsu da kallo one by one. Dukkan su bin sa sukayi da kallo cikin tsantsar mamaki da tsoron ya akayi yasan inda suke har yazo ya kuma riski abinda suke cewa, ganin suna kallon sa da alamun mamaki sai ya murmusa yace, "Kar ku damu da ya akayi nasan kuna nan, ku san sani abu guda d'aya duk motsin ku a kan idona kuke yin sa a kuma cikin kunne na yake so kar ku yi mamakin ganina ba tare da kun sanar dani ba." Hajiya zatayi magana Waziri ya katse ta da fad'in, "Yanzu ya kake ganin za'ayi kenan?." Aliyu ya kalle su yace, "Ku san yadda zakuyi ku cire masa Mama daga zuciyar sa." Hajiya ta kalle shi tace, "Ban gane ba." "Bana son sake maimaita magana kema kin san da hakan. Indai har zai yi magana da Mama tabbas hankalin sa zai dawo Nigeria, indai zaiyi magana da Mama nan kusa Asad zai dawo zai kuma iya rabuwa da matar tasa, dole a cire masa Mama a ransa ya daina neman ta a waya ta haka shine zamu samu cikar burin mu." Cikin gamsuwa yake girgiza kai Waziri yace, "Very good idea our king, but ta yaya hakan zata kasance duba da irin son da yake yi mata?." Aliyu ya kalle shi yace, "Kuyi yadda kuka saba a raba shi da koda magana da Mama in ba haka ba aikin mu ya dawo sabo fil." Hajiya tace, "Wannan ba matsala bane, inda matsalar take aiki baya saurin kama Asad da sauri sai kaga ana ta abu d'aya babu nasara, bamu tab'a yin aiki munyi nasara a kansa ba ko sau d'aya." Aliyu ya kalle ta yayi murmushi mai sauti yace, "Wannan karon zaiyi tasiri ku gwada, ina tabbatar miki da zaiyi nasara" yana fad'a ya fita da baya yana kallon su suna kallon sa. Waziri ya kalle ta itama ta kalle shi tace, "kana ganin abinda yace za'ayi?." "Shi za'ayi mana ai maganar sa itace akan daidai." "Anya ba kan keken b'era yake d'ora mu?." "Wannan ba keken b'era bane gaskiya ce kuma abinda yace shi za'ayi." "Ta yaya zamu yi aiki ya kama Asad bayan ba tun yau muka fara ba?." Kallon ta yayi ya kalli k'ofa yace, "A wannan karon zamuyi nasara na fad'a miki, zamu cire k'aunar babar sa daga zuciyar sa zamu mayar masa da hankalin sa kan matar sa, daga wannan lokacin komai zaizo mana yadda muke so. Tabbas indai zaiyi magana da Rabi zai dawo Nigeria magana da itama tasiri ne a wajan sa ya zama dole mu dakatar da faruwar hakan" ya k'arasa fad'a da murmushi yana kallon ta itama sai tayi murmushin tana girgiza kai cikin gamsuwa da abinda yace. *Tofa*🤭😂 [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *033.* *SAUDI GERMAN HOSPITAL CAIRO.* Tun a farkon asibitin zaka tabbatar da girman sa da kyau da tsarin da yake dashi, iya tsayawa ka kalle shi ma abin burgewa ne balle kuma ka shiga cikin sa kana gani kasan ba'a k'asar ka kake ba tabbas kaje bak'unta wata k'asar Misra. Rauda tunda ya ajjiye motar take bin asibitin da kallo ya kalle ta yaga hankalin ta nakan asibitin sai ya d'auke kansa daga kanta ya kashe motar ya bud'e ya fita ya zaga inda take ya bud'e baya ya ciro keken da take kai ya kawo shi kusa da k'ofar da take zaune ya bud'e sai a lokacin ta kalle shi. Hannu ya mik'a mata alamun ta kawo nata tabi farin hannun nasa da kallo mai d'auke da azurfa guda d'aya kalar golden sai wani d'an abin hannu mai kama da jarbi bak'i a zagaye a tsintsiyar hannun sa na dama, hannun nasa ma kawai abin kallo ne, murza yatsun sa yayi suka bata sauti sai ta kalle shi ya motsa duka yatsun hannun nasa alamun ta tawo. A hankali ta d'ora hannun ta kan nasa tana kallo nan taga banbanci tsakanin fatar ta da tasa domin kuwa kamar an d'auko bak'in gawayi ne an d'ora shi a kan farar fulawa. 'In banda ikon Allah ina ni ina shi? Ji hannuna fa kamar na bokaye akan nasa hannun.' Ta fad'a a zuciyar ta a lokacin da ya fito da ita ta zauna akan keken suka shiga ciki har lokacin kallon asibitin take ganin sa hawa-hawa. Labarawa, turawa, Chinese, Japanese sune kawai suke kai kawo a cikin reception na asibitin wanda kallon sa ya kusa saka Rauda rud'ewa sabida ba komai ta gani a zahiri ba. Wajan eveletor suka k'arasa taga ya danna ya bud'e suka shiga ya kulle ya danna hawa na biyu ba jimawa suka je ya sake bud'ewa suka fita yana gaba tana bin sa a baya. A bakin wani office suka tsaya ya danna door bell d'in jiki ta bada sauti daga ciki suka ji an bada ikon shigowa ya tura k'ofar ya shiga ya bud'e mata ta shigo sannan ya rufe. Balaraben likitan yana ganin sa ya mik'e tsaye da mamaki da farin ciki ya tawo ya rungume shi yana murmushi shima Asad d'in murmushin yayi suka gaisa likitan cikin harshen larabci yace, "Sheikh Asad daman da gaske zaka zo d'in?." Asad ya murmusa ya shafa gashin fuskar sa cikin larabci shima yace, "gani kana gani." Likitan yace, "gaskiya nayi farin cikin ganin ka sosai dan uwana, zauna mana" ya fad'a yana nuna masa wajan zama da farin ciki a fuskar sa shima haka. Asad ya zauna ya saci kallon Rauda da gefen ido yaga duk ta rud'e sai ya d'auke kansa daga kallon ta ya kalli Dr Asif yaga ya tashi ya bud'e fridge yana d'auko ruwa da lemo da kayan motsa baki ya dawo ya ajjiyewa Asad a gaban sa yana ta murmushi har lokacin shi kuma Asad fuskar sa dai kadaran kadahan, "Bismillah" ya furta yana kallon Asad bai yi magana ba ya d'aga masa kai kawai sai yayi dariya yace, "Har yanzu kana nan da rashin son maganar ka kenan?." Murmushi kawai yayi bai amsa ba. Asad ya d'auki dabino d'aya yaci dan kar yaji babu dad'i ya bashi abu bai ci ba sannan ya nuna masa Rauda dake zaune yace, "ga patient d'in da mukayi magana dakai." Asif ya kalle ta ya kalle shi yace, "Ya sunan ta?." Asad ya kalle ta kana tace, "Rauda." Sai da gaban ta ya fad'i rana ta biyu kenan da taji ya ambaci sunan ta sai taji wani iri musamman yadda yake fitar da harafin R d'in kamar a bakin sa aka halicci harafin, ta kalli likitan dan ba larabci take ji ba ta dai d'an fahimtar abu kad'an irin dai na islamiyya dake koyawa. Dr Asif ya jawo computer gaban sa yana danne-danne kafin ya juyo ya kalli Asad yace, "bata iya tafiya ne?." Asad ya d'aga masa kai alamun eh ya d'aga kai ya danna wani abu a kusa dashi sai ga nurses mata guda biyu kyawawa sun shigo cikin uniform d'in su. Da harshen su yayi musu bayani da aje da Rauda ayi bincike k'afar ta, ba musu suka kalli Rauda d'aya daga ciki tace, "Muje" cikin harshen larabci ta fad'a kuma kalmar daman ba wani wahala ne da ita ba Rauda taji me tace sai ta danna madannin tafiya suka fita suna rik'e da keken ya bisu da kallo a zuciyar sa yana tunanin da wanne harshe zata yi musu magana in sun tambaye ta?. Kawai sai yaji bai gamsu ba ya kalli Dr Asif yace, "Zan bi bayan su" yana fad'a ya mik'e Dr Asif d'in ma ya biyo shi suka fito suka bi bayan su. D'aki aka shiga da ita babba mai d'auke da injina da na'uroro kala-kala suka kunna wata na'ura suka k'araso kusa da Rauda ita duk tsoro take ji ganin injinan harrrrr a idanun ta sai taji ta tsorata. Kan gado suka nuna mata alamun ta kwanta sai taji bazata iya ba sabida tsoron da take ciki ganin hakan ya k'araso kusa da ita ya kalli fuskar ta da take a kwab'e kamar zatayi kuka yace, "Relax." Ya furta a hankali yana rik'o hannun ta ya jingina ta da jikin sa ta runtse idanun ta suka matso da gadon ya kwantar da ita ta rik'e hannun sa gam idanun ta a rufe, k'arar na'urar taji kusa da ita taji an tattare rigar jikin ta an saka na'urar a k'afar ta nan take kasusuwan k'afar ta suka bayyana a jikin wani babban screen dake gaban gadon. Dr Asif yana kalla suna juya na'urar tana nuno ko ina na k'afar ra har inda matsalar take nan take ya gani ya bada umarnin a cire ta daga ciki har lokacin hannun ta na rik'e dana Asad, kashewa sukayi Dr Asif ya kalle ta yayi murmushi cikin larabci yake ce masa, "Tana da tsoro, amma tana da kyau irin na y'an Nigeria." Asad bai amsa ba ya share shi ya kuma cewa, "y'ar uwar kace? Kuma bakwa kama." Nan ma ya share shi baiyi magana ba ganin hakan sai Asif yaja bakin sa yayi shiru. Dr Asif ya kuma cewa, "In kun shirya za'a yi mata aikin yanzu ba wani mai wahala bane." Asad ya kalli Rauda da take kwance har lokacin ya sunkuya da kansa daidai kunnen ta yace, "za'a yi aikin yanzu, kar kiji tsoro" abinda yace kenan ya d'ago ya kalli Dr Asif ya d'aga masa kai alamun ayi kawai. Dr Asif ya kalli nurses d'in ya fad'a musu ayi shirin aiki shima ya fita, uniform suka ajjiyewa Rauda da hula da talamin da duk wanda zai kwanta asibitin yake amfani dashi suka fita suka bata waje dan ta shirya. Jin babu motsi sai ta bud'e idon ta ta kalle shi taga ita yake kallo yayi mata nunu da kayan da ido ta tashi zaune ya saki hannun ta ya fita. Sun jima basu dawo ba lokacin da suka dawo ta cire kayan ta saka wanda suka bata aka ja gadon zuwa d'akin tiyata yana bin su a baya har cikin d'akin, kallon sa da yaga tana yi sai ya k'arasa kusa da ita ya rik'e hannun ta gam yace, "Kar kiji tsoro." sai ta kulle idon ta akayi mata allura daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba. Cikin lokaci kad'an aka kammala aikin aka fito da ita zuwa d'akin da zata huta har lokacin bacci take a lokacin agogon Cairo karfe hud'u na yamma. Sai da yaga an fito da ita ta kwanta sannan ya samu damar yiwa mahaifinta message ya tura domin bazai iya doguwar magana ba ya fita zuwa masallaci yayi sallah. Bata san adadin lokacin da ta d'auka a kwance ba ita dai taga ta bud'e idanun tane ta ganta a kwance a kan gado haske ko ga ina kuma babu kowa a d'akin sai k'arar a.c kad'an da yake tashi a ciki. "Sannu Rauda" aka fad'a daga gefen ta ana murmushi ana kallon ta. Gaban Rauda ya fad'i idanun ta suka had'u dana wanda yake mata magana ta ganshi fari tas dashi kana ganin sa kaga balarabe amma taji yana yi mata hausa duk sai ta gigice tana jan ayatul kursiyu a zuciyar ta. A yanayin fuskar ta ya hango tsoro a ciki sai yayi murmushi yace, "Karki tsorata suna na Dr Khalifa ni bahaushe ne kamar ki." Duk da ta d'an ji dad'i amma bata nuna ba dan ba amincewa tayi da abinda yace ba kawai ita kallon aljani take masa. Murmushi yayi yace, "in kika ji tsoro kina kyau." Asad ta hango ya shigo yana amsa waya ya canja kaya zuwa riga da wando jajaye nasu kauri da tsaho dan rigar irin mai high neck ce kana ganin su kaga kayan sanyi. Dr Khalifa ya kalli Asad yace, "Asad da alama wannan sister naka kallon aljani take min dan taji ina hausa" ya fad'a yana murmushi ya k'arasa inda drip stand yake ruwan da yake shiga jikin ta ya tsayar dashi kana yace, "But tana dakyau." Asad baice komai ba ya k'arasa kusa da ita yana kallon k'afar da take cikin wani abu kamar akwati an d'aure ta da farin bandage a mike sanb'al. "Kina jin ciwo a k'afar taki?" Dr ya fad'a yana kallon ta. Kai ta girgiza kafin tace, "Akwai ciwon amma ba sosai ba." "Zai daina shima nan da anjima kad'an zaki daina jin komai." Kai ta d'aga kawai ya juya ya kalli Asad kafin yayi magana aka bud'e k'ofar aka shigo. Kyakykyawar matashiyar budurwa ce d'auke da rigar likitoci ta yafa karamin mayafi a kanta tayi kyau sosai duk da kana kallon ta kasan ba balarabiya bace amma ta had'a jini dasu. Asad ta kalla cikin mamaki tace, "dana ganka d'azu ban d'auka kaine ba shine nazo da kaina. Ohh Aliyu da gaske kaine?." Kallon ta yake yana so ya tuna inda ya santa amma ya kasa yadai san ya Santa a wani wajan ganin hakan sai ta kama k'ugu tace, "You forgot me right?." Nan ma bai amsa ba sai kallon ta da yake yi tace, "You forgot your school friend Muheeba?." Shiru ya kuma yi alamun yaso dai ya gane ganin hakan sai ta hard'e hannu a k'irji tana kallon sa da wani irin murmushi a fuskar ta kafin tace, "Muheebba!" Ta maimaita a hankali. Wara ido yayi sai kuma ya tab'e baki tunawa da ya san fuskar ta a wajan Aliyu lokacin da suna makaranta yace, "bani bane." Muhibba tace, "Lallai prince." Khalifa da yake jin su yace, "Dr wa kike nema ne ke?." Tace, "shine fa Prince Aliyu bin Nasir." Khalifa yayi murmushi yace, "Bashi bane wannan triples d'in Aliyu ne Asad." Wara idanu tayi cikin mamaki tace, "like seriously?." "Sure." Dawo da kallon ta tayi ga Asad tana binsa da kallo cikin mamaki da al'ajabi tace, "I see, kasan sai yanzu na gane Khalifa? Cos inda Aliyu ne da yanzu ya bani welcome hug, Wow Allah mai iko babu inda ya bar Aliyu." Khalifa bai bata amsa ba ta mik'a masa hannu tace, "nice to meet u prince Asad." Kallon hannun nata yayi sannan ya kalle ta sai ya d'auke kai a iya lab'ban sa ya amsa da, "Thanks" yana fad'ar hakan yayo gaban wajan gadon da take kwance ba tare da ya sake kallon ta ba dan Allah ya sani ya tsani mace mara kamun kai da nuna zaqewa a kan namiji da sunan wayewa. Muhibba kam kallon sa take da mamaki bata tab'a ganin kama irin ta Aliyu da Asad ba duk da Aliyu ya fishi kamar faran-faran musamman ga mata dan da shine yadda suka had'u d'in nan sai yayi hugging d'in ta amma babu ta inda ya barshi. Murmushi tayi domin ya burge ta sosai ajin sa ya burge ta matuk'a musamman lokacin da take masa magana yake d'aga girar sa sama yana kallon ta ya k'ayatar da ita har taji bata gaji da kallon sa ba. Khalifa ya kalle shi yace, "Deaf yana da kyau tayi sallah." Asad ya d'aga kansa ya kalle ta ya kalli agogon hannun sa lokacin asuba gab da take da yi amma bai ce komai ba. Muhibba tace, "she's your sister?" Ta fad'a tana kallon Asad ya runtse ido ya bud'e alamun ta dame shi baya son yawan magana amma ta kasa ganewa kafin ya bata amsa Khalifa yace, "Yeah, sister shi ce." "Woww! Amma basa kama, ya akayi kika bari yayan ki ya fiki kyau haka?. Kalle shi kamar arab in ya shiga cikin larabawan asibitin nan babu wanda zai gane shi" ta fad'a tana kallon sa da murmushi a fuskar ta. Rauda bata kula ta ba dan haushi ta bata ta lura irin matan nan ne masu shigewa maza ta saci kallon sa taga shima ba ita yake kallo ba, kusa da Khalifa ta k'arasa tace, "Baya magana ne kamar Brother d'insa? Naji kana ce masa deaf kuma naji yayi magana sau d'aya." "Baya son magana ko kad'an kinji wannan maganar da yayi miki babu lallai ya kuma yi miki wata har ki bar nan gwara ma kiyi shiru" ya fad'a mata a hankali a kunnen ta sai taji ya sake burge ta ta wara idanu tace, "Woww! He impressed me." Kallon Asad tayi tace, "Lemme help my sister tayi sallah before asuba" ta fad'a tana k'arasowa inda Rauda take tana kallon sa har lokacin. Da hannu Asad ya dakatar da ita alamun ta barshi ya kalli Khalifa shima shi yake kallo kafin Khalifa yace, "Kana kallona kasan ba ko yaushe nake gane me kallon ka yake nufi ba, ka yi magana abeg." Baice komai ba sai ya bar wajan ya fita daga d'akin jim kad'an sai gashi yazo da nurses d'in da alhakin kula da ita yake a wuyan su suna shigowa shi kuma ya juya ya fita. Dole suma suka fito dan su bar su suyi aikin su suka ganshi zaune akan kujera yana danna wayar sa a nutse bai damu da kowa ana wajan ba, yadda larabawa suke zirga-zirga sai ka d'auka shima balaraben ne hutawa yake yi sabida yadda ya dace da zama balaraben musamman shigar jikin sa da ta sake haska fatar sa. Muhibba ta k'arasa kusa dashi ta zauna a gefen sa tace, "Aliyu abokina ne a school yana ina yanzu? Ko zan iya samun number shi?." In kujerar da suke kai tayi magana tabbas shima yayi bai kalle ta ba wayar kawai yake dannawa. Zata kuma magana kawai ya mik'e ya bar mata wajan ta bishi da kallo cikin tsantsar burgewa har ya b'acewa ganin ta tayi murmushi tace, "I like his acting" ta fad'a tana murmushi sosai dan ba k'aramin burge ta yayi ba. A b'angaren Rauda sun bata ruwa tayi alwala a inda take sun nuna mata yadda zatayi sallah tayi duka wanda ake binta ta idar suka kawo mata tea tasha, yadda suke kula da ita baza kace mara lafiya bace abin ya burge ta duk da ta d'auka matsayin Asad shine ya saka suke mata haka dan taga duk sun sanshi bata san haka tsarin asibiti yake hatta na Nigeria kula da mara lafiya a wuyan nurses yake. Bata jima sosai ba akayi sallar asuba tayi sallah a zaune kamar d'azu bayan ta idar ta kalli gefen ta taga wayar ta ta d'auka ta shiga Islamic app ta fara karatu kamar ko yaushe. Bayan ta gama ta shiga wajan hotunan wayar tana kallon haukan su Khalil a wayar ta tana murmushi tana jin kewar su a zuciyar ta sosai.  Tana cikin farin cikin kallon y'an uwanta ya shigo ya canja kaya cikin suit fara tas tayi masa kyau sosai ya k'araso ya zauna a gefen ta yana kallon fuskar ta da take ta murmushi har lokacin ta kalle shi tace, "Ina kwana." Kafin yayi magana tace, "Da sauk'i. " Da mamaki yake kallon ta ta kalle shi tace, "nasan zaka ce ya jikina ne shiyasa na hutar da kai nace da sauk'i." Kyakykyawan murmushi yayi wanda ta jiyo sautin sa a inda take ta sake kallon sa da mamakin abinda ya bashi dariya haka shi kuma yadda tayi saurin amsa abinda bai tambaya ba shine ya bashi dariya wato tasan abinda zai tambaya kenan, sai ta sake burge shi sosai da alama dai tambayar bata mata dad'i shiyasa tayi saurin tare shi. "Ya kika tashi?" Ya furta in slow voice yana binta da fararen idanun sa masu d'auke da boyayyiyar k'aunar ta wacce shi kad'ai yasan da ita a zuciyar sa. D'ago kai tayi ta kalle shi cikin mamaki suka had'a ido har lokacin fuskar sa da murmushi a kai sai ta sauke kai k'asa tace, "lafiya lau." Murza yatsun hannun sa yayi suka bada sauti ta d'ago ta kalle shi ya nuna mata k'afar ta alamun ya take ji, "babu ciwo" ta fad'a a nutse tana kafe shi da nata idanun a son ranta sai dai ya d'auke nasa ita baza ta d'auke ba amma suna had'a ido sai ta sauke nata k'asa jin wani abu yana shigar ta. Waya ya d'auko daga aljihun sa yana dannawa ba jimawa ya mik'o mata ta karb'a a hankali dan tsoro take kar wayar ta sub'uce a hannun ta tayi masa asara gata da santsi, fuskar Baba taga ya bayyana akan screen d'in tace, "Lah Baba kaine?." Daga can b'angaren yace, "Nine Rauda, ya jikin naki ance anyi miki aikin?." Farin ciki ya bayyana a kan fuskar ta tace, "Babu ciwo Baba kamar ba'a yi min komai ba. Ina kwana." "Lafiya lau Rauda ya zaman misra?." "Lafiya lau, Ina Ummana?." "Gata ku gaisa." Fuskar Umma ta bayyana sanye da hijjabi ta sake fad'ad'a fara'ar ta tace, "Umma na ina kwana." Daga can b'angaren itama da fara'a a tare da ita tace, "lafiya lau Rauda, ya jikin naki?ance har anyi aikin k'afar taki." "Umma babu ciwo kamar ba'a yi min komai ba. Umma kinga yadda suke kula dani kamar ba mara lafiya ba kamar wata matar shugaban k'asa?, ga asibitin mai kyau Umma kamar ba'a duniya kake ba." Umma tayi dariya tace, "kedai shirman ki yawa gare shi Rauda, ya mijin naki?." "Mijina kuma? Au ashe fa ina da miji wallah8 mantawa nake Umma. Yana nan yadda yake Umma ko magana fa baya yi sai yaga dama daga ya jiki sai sannu shikenan, wani lokacin kamar na shak'o wuyan sa haka nake ji, yana da kayan haushi ni mantawa nake miji nane badan kin fad'a ba." "Lallai baki da hankali Rauda; duk fad'an da nayi miki bai shiga kunnen ki ba." Rauda ta share zancen tace, "Umma ina Ummulkhairi ina Khalil dasu Rahma? Wai Umma yaushe ma Baba yayi babar waya nidai nasan ba'a video call da k'aramar waya sai babba kuma dai nasan Baba bazai fitar da kud'i ya siya ba." Umma tayi dariya tace, "Mijin kine ya bashi kafin ku tafi sabida mu dinga ganin ki kema kina ganin mu." Rauda tace, "Allah sarki angode Allah ya saka masa da alkhairi." "Amin. Shiyasa nace ki dinga masa biyayya banda rashin kunya Rauda." Sai kuma tayi dariya sosai tace, "Daman dai nasan wallahi duk wahala Baba bazai siyi waya ba, da ya siya ai gwara ya ajjiye kud'in yana kallon su." Umma tayi tsaki kad'an tace, "In ya siya sai ki kwace." Rauda tace, "Ina k'annena suke Umma?." "Yanzu basa nan da sun dawo anjima sai ku gaisa." "Toh shikenan Ummana, nayi kewar ku wallahi sosai." "Muma munyi Rauda, Allah ya baki lafiya. A cigaba da biyayya banda rashin kunya Rauda banda tsiwa nasan halin ki." "Umma wai wa zan yiwa rashin kunyar?, Tabd'ijam wannan mutumin ba sai naga fuskar yi masa bama, kofa magana baya min sai yaga dama shima sau d'aya kawai in yace ya jikin ki basai sake cewa komai ba" ta fad'a bayan ta gwada muryar sa tana yamutsa fuska zuciyar ta na karyewa kamar zatayi kuka. Umma tace, "kina addu'ar dana fad'a miki? Duk da nasan ki bakya wasa da addu'a amma dai ki dage." "Ina yi sosai Umma" ta fad'a murya na rawa." "To meye kuma na kukan bayan alqwarin da kika yi min kin daina? Haba kodai daman alqawarin bai kai zuciya ba?." Ido Rauda ta goge bata ce komai umma tace, "Kuma kina jin komai na barin zuciyar ki?." "Eh Umma." Umma tace, "to ki dage nan gaba sai dai ki bada labari. Baki ga abinda ya aiko mana dasu ba ga ginin gidan mu an kusa gamawa baki ga ginin da akayi ba kamar ba'a unguwar ba, bamu da bakin gode masa ai sai addu'a ko iya haka aka tsaya, balle shi da yaga jinin mu yace yana so duk da tazarar da take tsakanin mu dashi, dan Allah Rauda ki cigaba da hak'uri." Rauda tayi murmushi bata ce komai ba kafin Umma tace, "ke ni na gaji sai anjima" ta Fad'a tana k'okarin yanke wayar da sauri Rauda tace, "Ina kewar ki Ummana, a gaida min dasu Khalil ace ina kewar su sosai, in Yaya Ummi tazo suyi min magana ta Whatsapp mu gaisa dasu." Da to Umma ta amsa ganin Raudan ta fara hawaye sai ta kashe wayar itama ta ajjiye wayar a k'irjin ta ta jingina da bango ta lumshe idanun ta cikin kewar y'an gidan su da k'aunar iyayen ta. Asad da yake jin ta duk abinda take yi yana kallon ta jin yadda take ta magana a kansa ta bashi dariya, wai baya magana daga ya jiki shikenan lallai da gaske ya jikin nan tana bata haushi. Murmushi yayi ya shafa kansa sosai ta bashi nishad'i da farin ciki sosai a zuciyar sa musamman in ya tuna yadda take kwaiwayon muryar sa sai ya sake yin dariya yana kallon ta dan yaga alama ta manta dashi a wajan shiyasa ta saki baki. "Waya ta" ya furta a hankali yana mik'a mata hannu. Da sauri yaga ta firgita tana kallon sa ta wara idanun ta alamun ta tuna da b'aranb'aramar da tayi kunya ta kamata ta kasa koda motsi ta d'auke kai daga kansa ba kuma ta bashi wayar ba, godiya take yiwa Allah da yasa bata furta bata son sa gaban idanun sa. Ganin hakan sai ya matsa daf da ita sosai har tana jin numfashi sa da khamshin turaren sa ya kai hannu k'irjin ta inda wayar take yana kallon ta yana sake matsar da hannun sa zuwa jikin ta. [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *034.* Hannu ya saka ya d'auki wayar sa a k'irjin ta yaja baya kamar bashi ba ya koma danna wayar sa hankali a kwance kamar ma bashi ne ya kalle ta ba, kunya ta da lullub'e Rauda tunawa da sakin bakin da tayi ta manta shaf yana zaune gefen ta sai ta kasa d'ago kai balle ta iya kallon sa. Bai kalle ta ba ya mik'e tsaye yace, "Byeee" abinda ya furta kenan ya d'aga k'afa da niyar fita sai kuma ya dawo da baya ya dawo kanta ya tsaya yana kallon fuskar ta da take a duk'e ya matso kusa da ita ya sunkuya a goshin ta ya sakar mata lafiyayyen kiss kafin ya kai ga d'agowa aka shigo d'akin. Muhibba da ta shigo taga abinda akayi amma bata kawo komai ba dan tasan Sister d'insa ce da yayi mata kiss a goshi ba komai bane ya d'ago ya sake tamke fuskar sa ta kalle shi da murmushi tace, "Morning Prince." In ya kalle ta ma ta gode Allah ya kalli Rauda suka had'a ido tayi saurin d'auke kanta ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba. Muhibba ta bishi da kallo tana lumshe idanun ta Allah ya sani yana burge ta sosai jan ajin sa yana d'aya daga cikin abinda yaja hankalin ta gare shi. Rauda ta kalla tayi mata murmushi tace, "ya jikin ki?." Rauda ta kalle ta tace, "Da sauk'i." Daga haka bata ce komai ba ta juya ta fita Rauda ta bita da kallon mamaki kafin ta tab'e baki ta saka hannu ta shafa saman goshin ta har lokacin tana jin sanyin lips d'in ta a kai sai abin ya bata dariya. *Nigeria* *3:00pm.* A wannan lokacin jirgin Asad ya sauka a Nigeria yana fitowa ya samu Hydar yana jiran sa ya k'araso ya shiga motar yana duba wayar sa, Hydar ya kafa masa ido yana kallon sa har ya tsargu ya kalle shi yayi masa alama da lafiya sai Hydar yace, "gani nayi kayi kyau kwana biyu kawai ga wani annuri akan fuskar ka." "Mtswww!" Shine abinda Asad ya furta kawai Hydar yayi dariya yaja motar bai tsaya a ko ina ba sai a mtn office. Suka shiga ciki shida Hydar direct wajan manager da suka wuce emergency akayi masa swapping na layin sa ko cikkaken mintina ashirin basuyi ba suka fito, zai shiga mota kenan yaji ance, "Prince Asad." Cize baki yayi ya dafe kai baiso a gan shi ba ya juyo a hankali ganin wacece takaicin sa ya k'aru sai ta saki murmushi tace, "Ashe dai na gane ka." Hydar ya kalle ta yace, "Jidda sauri muke kwa had'u a gida" ya fad'a yana shiga mota shima ya shiga suka ja motar suka bar wajan. Asad yaja tsaki kafin yace, "Mama bata dawo ba?." Hydar yace, "Ta kusa." Hotel mafi kusa da airport d'in suka samu Asad ya sauka yayi wanka yana hutawa dan jirgin safe zai hau ya koma Egypt. Awa d'aya na cika da yin swapping ya d'ora layin a kan wayar sa ya sauke Whatsapp d'in sa ya danna number Mama ya kira ta, bata tsinke ba ta d'auka daga can b'angaren tace, "Asad ina ka shiga kwana biyu wayar ka a kashe?." Asad yayi shiru shi ba ma'abocin k'arya bane hakan ya saka ya rasa abinda zaice mata jin shiru ya saka tace, "baka ji bane? Ko gurguwar ce ta d'auke maka hankali har ka manta dani?; ba kayi min alqawarin ka barta ba Asad?, ashe zaka iya yi min alqawari ka sab'a?." Mama ta d'aure Asad ya rasa me zaice komai nasa ya tsaya cak ya cize baki kana yace, "Barka da yamma Mama, ya karin hak'uri?." Jin ya canja maganar sai itama ta canja tace, "Alhamdulillah, amma zaku zo ranar Friday d'in ko? In yaso sai mu dawo tare." Asad ya girgiza kai kamar tana gaban sa yace, "Mamaa Abba ya sani aiki bazan samu dama ba." "Okay, dana dawo maganar ka da Jidda zata taso cikin watan nan nake so ayi bikin a gama." Ya had'd'iye saliva ya kasa furta komai kafin tace, "Ya gidan naku? Ba wani sabon abu?." Asad yayi shiru kafin yace, "Har yanzu dai." "Shikenan mayi magana anjima, kar kaga bana nan Asad ka canja maganar da mukayi da kai akan yarinyar can, indai kana sona ka cire yarinyar nan a ranka in kuma baka sona Asad kayi abinda kake so" tana gama fad'ar hakan ta yanke wayar ya bi wayar da kallo kamar ya kurma ihu. Dafe kansa yayi yana jin komai yana fita daga ransa tunawa da abinda ya cewa Mama sai yaji kamar yaci amanar tane da yayi abinda bata so bayan yace mata bazai yi ba. Shigowar Hydar d'akin bai saka ya d'ago ba Hydar ya zauna kusa dashi ya ajjiye masa ledar hannun sa yace, "Ya dai Deaf?." "Mamaa!" Ya furta a hankali yana d'ago ido ya kalli Hydar. Hydar ya gyara zama kana yace, "Amma kamar kun gama maganar nan da takawa ko? Meyasa shi baka gudun b'acin ransa sai na Mama kake gudu?." Asad ya d'auke kansa daga kallon sa ya d'auki ledar da ya shigo masa da ita yaga abinci ne da kuma kayan sa da zai saka ya d'auki ruwa a ciki ya sha ya jingina da kujerar yana kallon sama yace, "Ba haka bane but ina jin bazan koma ba." Hydar yace, "kenan baka jin maganar Abba ta Mama kake ji?." "Ohhh Hydar ya zanyi ne?" Ya furta yana dafe kansa da duka hannayen sa biyu ya rasa zab'in wa zaibi na Mama kona Abba. Hydar yace, "Kai dai ka sani, in kana ganin baza ka koma ba fine sai ka zauna kaga ka sab'a abinda Takawa ya nema a wajan ka a karo na farko, ni na tafi" ya fad'a yana tashi ta fita bai sake yi masa  magana ba. Kasa motsin kirki Asad yayi daga inda yake domin shi kam ya shiga tsaka mai wuya ya rasa yadda zaiyi yaji dad'i gabad'aya komai ya tsaya masa cak ya rasa tunanin da zaiyi wanda zai ji zuciyar sa ta gamsu dashi.  Ko fita bai iya yi ba haka ya zauna a d'akin sallah ma a nan yake yi har dare. Aliyu kuwa a lokacin suna tare da Waziri a falon gidan Wazirin Aliyu yana kallon sa shima yana kallon sa kamar bazai yi magana ba ganin hakan ya saka Waziri yace, "Kayi shiru baka ce komai ba, an tabbatar mana da maganin nan shine kad'ai zai ya manta dashi babar ku sai ya ganta hankalin sa zai dawo jikin sa kuma sai an shafa masa ina zamu ganshi?." Aliyu ya sake kallon sa ya d'ora k'afa kan d'aya sannann yace, "bani maganin." Ba musu ya mik'a masa ya karb'a yana kallon robar maganin kana yace, "fatar jikin sa ake so kawai ta tab'a right?." Waziri yace, "Kwarai kuwa an tabbatar min......" Aliyu ya d'aga masa hannu kana yace, "Ba wannan na tambaye ka ba, naji amsar tambaya ta" ya fad'a yana mik'ewa ya saka bak'in glass ya kalle shi kamar zaiyi magana sai ya fasa ya fita daga falon. Waziri ya bishi da kallo yace, "Allah ya tabbatar mana da nufin mu a wannan lokacin" ya fad'a yana binsa da murmushi. Aliyu yana fita ya shiga mota bai wuce ko ina ba sai hotel d'in da Asad ya sauka ya tsaya yana kallon sa sai kuma ya fara tunanin a wanne room yake...?, waya ya d'auko ba tare da tunanin komai ba ya kira number Asad cikin sa'a ya d'auka ya kara a kunne yace, "Meye room number d'in ka gani nazo hotel d'in." Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin ya yanke kiran ya nufi ciki. A bakin k'ofar ya tsaya ya d'auko man ya shafa a hannun sa sannan yayi knocking d'in k'ofar, Asad da yake zaune ya taso ya bud'e k'ofar suka had'a ido sai Aliyu yayi murmushi yana wara hannun sa yace, "Suprised" ya fad'a yana shigowa ciki yana kallon sa. Ya zare glass d'in idanun sa yana kallon Asad yace, "Har zaka shigo Nigeria kana niyar fita gobe without na sani Asad, a ganin ka hakan daidai ne?" Ya fad'a yana mik'a masa hannu alamun su gaisa. Asad da mamaki yake kallon sa amma bai nuna ba ya bashi hannu suka gaisa kafin Aliyu ya zame hannun sa ya rik'e tsintsiyar hannun Asad kana yace, "Ban san me nayi maka ba deaf baka sona kafi son Hydar" ya fad'a yana sakin hannun sa. Asad ya kalli hannun sa sai yaga kamar shatin hannun Aliyu kamar dai a hannun Aliyun akwai wani abu mai maiko ya kalli Aliyu ya sake kallon hannun nasa kamar zaiyi magana sai ya fasa ya koma ya zauna kana yace, "Taya zan ki ka?." Aliyu ya zauna a gefe d'aya yana kallon sa yace, "gashi nan kuwa baka nema na Hydar ne kawai naka." Asad baice komai ba daman shima Aliyun yasan bazai ce ba ya mik'e tsaye yace, "Shikenan ka gaida amarya in kaje" ya fad'a yana niyar barin wajan. Asad so yake ya tambaye shi ya akayi yasan yana hotel d'in bayan yasan babu wanda yasan yana nan amma ya share baya son doguwar magana musamman da Aliyu shiyasa kawai Aliyu ya fita da farin ciki domin abinda ya kawo shi ya samu ya aiwatar ba tare da Asad d'in ya lura da hakan ba. *Cairo* *8:00am.* Nurses masu kula da alhakin gyara ta sun mata komai hatta wanka an san yadda akayi tayi an canja mata uniform sun mata brush an kawo mata breakfast taci tana zaune tana charting da Yaya Ummi duk da zuciyar ta cike take da tunanin rashin ganin Asad awa ashirin da hud'u kenan. Sallama akayi aka shigo ta amsa tana kallon Dr da ya shigo tayi murmushi ta amsa ganin Dr Khalifa shima haka ya k'araso da tray na allurai a hannun sa yace, "Rauda ya jikin ki?." "Alhamdulillah da sauk'i." "Kina iya motsa k'afar taki?." "Sosai ma, ni ji nake kamar ba'ayi min komai ba." Yayi murmushi yana had'a allurar da zai mata ta kalli tray d'in dake gaban sa taga wata k'atuwar kwalbar allura da bata tab'a ganin irin ta ba ta kai hannu ta d'auka da mamaki ta ajjiye ba tare da tayi magana ba. "Mamakin girman ta kike ko?." Rauda tace, "eh, ban tab'a ganin kwalbar allura kamar ta ba." Dr Khalifa yace, "Wannan allurar da kike gani ana yiwa wanda ba'a so jikin su ya motsa ne kwata-kwata, kamar wanda za'a yiwa aiki haka duk dai ba'a amfani da ita sabida tana da hatsari sosai, in aka yiwa mutum ta kwana biyu tabbas jikin sa zai daina aiki har sai anyi masa wacce zata karya ta, itace wannan" ya fad'a yana nuna mata wata y'ar k'aramar kwalbar ta karb'a tana juyawa a hannun ta kamar wacce ta san ta kafin ta ajjiye tace, "Tabd'ijam, ita babba wacce zata karya garkuwar ta kuma k'arama." Yayi dariya yaja kujera ya zauna ya fara k'ok'arin neman jijiyar hannun ta yayi mata tata allurar yace, "Haka abin yake; kuma duk girman ta da anyi k'aramar nan za'a fara ganin canjin indai ba anyi ta da yawa bane." Rauda tace, "ikon Allah" daga nan taja bakin ta tayi shiru bata kuma cewa komai ba. Dr Khalifa yayi mata allurar kana yace, "Deaf bai dawo bane? Yace min jirgin safe zai biyo na d'auka by dis time ya iso." Rauda tayi shiru bata amsa ba domin bata san ma ita inda yaje ba. K'ofar aka bud'e ya saka suka kalli wanda ya shigo suka ganshi yana takowa cikin k'asaita da izza fuskar nan a had'e babu walwala a cikin ta hannun sa zube cikin aljihun wandon sa yana kallon su ta k'asan idanu yana juya kwayar idon sa yana bin ko ina da kallo. Gaban ta ya fad'i ta daina kallon inda yake ta d'auke kai Dr Khalifa ya mik'e yana fad'in, "Welcome back Prince, yanzu nake tambayar ta baka dawo ba ashe kana hanya." Hannu Dr ya bashi shima Asad d'in ya bashi suka gaisa kafin ya kalli Asad yace, "Sister nan naka tana da kirki sosai akwai saurin sabo ba irin ka bace." Banza Asad yayi masa shima kuma bai damu ba ya kwashi kayan sa ya fita Asad dake tsaye hannun sa cikin aljihu ya kalle ta ya kalli kujerar da Dr ya tashi ganin ta gab da Raudan ya sake kallon ta suka had'a ido tace, "Ina kwana." Banza yayi mata bai amsa ba ya zagayo inda kujerar take kamar zai zauna ya tsaya yana kallon ta yace, "last warning kar na sake ganin hakan." Da mamaki ta kalle shi taga ya sake tamke fuskar sa sai ta kasa tambayar sa me yake nufi ta sauke kanta k'asa ba tare da tasan akan abinda yake magana ba. Wayar ta taga ya d'auka yana juya ta a hannun sa kafin taga ya zare sim card d'in ciki ya raba shi biyu ya saka a shara ya d'auko sabuwar waya a aljihun sa ya ajjiye mata a kusa da ita ta hannun sa kuma yayi danne-dannen da zaiyi sannan ya saka a shara. Rauda kallon ikon Allah kawai take yi gashi ya had'e fuska yayi mata kwarjini ta kasa kallon sa balle tayi magana, kamar a mafarki taji yace, "in akwai sauran abinda kika san ya baki throw it away" ya fad'a yana kallon ta. Rauda tayi shiru cike da mamakin sa dan in ta fahimci me yake nufi kenan yasan Anas ne ya bata wayar shiyasa ya cillar?, yasan shine ya bata sim card d'in shiyasa ya karya?, kenan kishi yake da ita kome?. Shiru ya ratsa tsakanin su kafin a shigo d'akin Rauda ta kalli wajan banda Asad da ya fara danna wayar sa, "morning beautiful face" Muhibba ta fad'a tana kallon sa da murmushi a fuskar ta. Tsaki yaja domin shi ya tsane ta gabad'aya baya son ganin ta amma ta nace masa duk inda yaje sai tayi masa magana ya rasa dalilin hakan, bai d'ago ba balle ya amsa ta k'arasa kusa dashi tana k'are masa kallo tace, "how was your day?." Nan ma yayi mata Banza ta sake yin murmushi tace, "I like your acting  prince, ko baka ce komai ba indai zan kalle ka is enough." Tana fad'ar hakan ya fita daga d'akin ta bishi da kallo har ya b'ace ta kalli Rauda tace, "Ina son brother d'in nan naki Rauda, yayi min ta ko ina class d'in sa na burge nu over, I feel like naje nayi hugging d'in sa ko zanyi dad'i a zuciya ta." Kallon ta Rauda take yi itama ita take kallo tana murmushi Rauda taji babu dad'i a ranta amma in ta tuna wata k'ila shine yace musu y'ar uwar sace sai taji shi take jin haushi daman tasan ba sonta yake yi ba. Muhibba tace, "promise me zaki sanar dashi sak'ona zaifi sauraron ki a kaina dan naga yana ji dake, please sister help me before nayi loosing hankalina." Rauda ta k'ak'alo murmushi tayi amma bata ce komai ba ganin hakan ya saka muhibba tace, "Thanks you Sister, ina jiran feedback duk abinda yace ki sanar dani please. I'm coming" ta fad'a tana ficewa Rauda ta bita da kallo bata san lokacin da ta fara jin hawaye na sakko mata ba. Idanun ta ta goge ta hana kuka a zuciyar ta tace, 'Meye naki na kuka Rauda?, daman kin san ke ba tsarar shi bace ba irin su sune daidai dashi; ta ya zaki had'a kanki da ita...? kalli kyawun ta fa ba dole ma ya so ta ba, ke kuwa kalle ki kowa yasan baku dace ba gwara ki samarwa kanki lafiya kar kiyi asarar hawayen ki.' Bata san ya shigo ba sai ganin sa tayi a kanta a tsaye yana kallon fuskar ta da mamakin meya saka ta kuka lokaci d'aya. D'ago kai tayi ta kalle shi da hannu yayi mata alama da kukan me take yi, bata iya bashi amsa ba ta sake goge idanun ta tace, "Wacce ta fita yanzu Dr muhibba naji suna ce mata tace na fad'a maka tana son ka." Wara idanu yayi ya zauna a kan kujerar da take kusa da ita yana kallon ta sai kuma ya saki fuska annuri ya bayyana a kai yace, "Shine kike kuka?." Batayi zaton zaiyi magana ba ta d'auka zaiyi banza ne sai taji yayi sai ta kalle shi ta girgiza kai had'i da tab'e baki tace, "A'a wannan daban wancan daban." "Ohhh!" Ya furta ba tare da yace komai ba yana kallon ta. Duk sai ta tsargu ta kasa sakewa jin idanun sa a jikin ta sai ta sunkuyar da kanta jikin ta nayi mata wani iri abinda bata tab'a ji ba, hannun ta taji ya rik'e guda d'aya bata kalle shi ba sai abinda take ji a jikin ta taji ya k'aru. Baiyi magana ba itama batayi ba bai kuma ce komai bai kuma saki hannun ba yana rik'e dashi laushin hannun sa yana ratsa ta sosai, wani lokacin har bata so ya rik'e ta dan tasan zaiji hannunta da tauri ba irin nasa ba amma ya riga ya saba yana son rik'e hannun ta. Sun jima a haka kafin ya saki hannun nata ya koma danna wayar sa ba tare da yace komai ba itama kuma batayi karanbanin cewa ba. *Bayan Kwana biyu.* Haka suke zaman asibitin shiru babu wanda yake magana daga gaisuwa ya amsa babu abinda yake had'a su kuma kullum a wajan ta yake wuni har dare bata ma sanin lokacin da yake tafiya. Ranar saturday kwana biyar kenan da yi mata aikin k'afa sosai take jin dad'in ta bata jin ciwo ko kad'an a cikin ta har ji take ma zata iya takawa in aka barta, kula sosai take samu a asibitin tun ranar da sukayi magana da Muhibba bata kuma ganin ta ba sai taji dad'i a ranta domin har ga Allah haushi take bata. Tana kwance da safiyar asabar likita ya shigo tare da Asad bai yi mata magana ba ya k'arasa ya d'ago ta ta zauna sosai yace, "Zaki fara tafiya." Dad'i taji a ranta sosai ta rik'e hannun sa sosai ya mik'e da ita aka zare k'afar daga cikin abinda take ta tsaya da k'afar mara ciwo likitan cikin harshen larabci yake sanar da Asad da ta taka gabad'aya ta tsaya ya gani. Kasawa tayi sai a lokacin take jin zugi a k'afar wanda bata jishi sa ba farkon aikin Dr Khalifa da ya shigo yace, "Gwada tsayawa mu gani zaki iya." Ba musu take k'okarin mayar da nauyin jikin ta kan waccan amma ta kasa sabida zafi take mata. "Kina jin ciwo?" Dr Khalifa ya tambaye ta. Kai ta d'aga alamun eh Dr Khalifa yace, "sake gwadawa zaki iya." A hankali ta tsayar da ita ta tsaya sai kuma tayi saurin d'agawa ta jingina da jikin Asad ya rik'e ta yana kallon su, wani iri take ji in ta had'a jikinta da nasa duk sai ta rud'e daurewa kawai take. "K'afar tayi kyau amma zata dinga amfani da sanda before ta warware gabad'aya" babban likitan ya fad'a da larabci yana kallon Asad. Sandar aka kawo guda d'aya mai kyau a lokacin aka bata akace tayi tafiya da ita Asad ya koma gefe cikin ikon Allah sai gashi tana takawa da duka k'afar tata a hankali. Asad yaji dad'in hakan ganin anyi nasara k'afar ta ta dawo akace ta zauna amma ta dinga yawan tashi tana takawa, ita kanta murna take na dawowar k'afar dan bata d'auka zata dawo d'in ba sai murmushi take tana jin dad'i Asad yana lura da ita ganin nata farin cikin sai nasa yaji ya k'aru. *Nigeria.* Mama an sauka a katagum ita da Suhaima tun daren juma'a ta wayi gari asabar a gidan aka dinga zuwa ana mata gaisuwa wanda basu samu damar binta can ba. Hydar ya shigo Aliyu ya shigo amma mamaki take da bata ga Asad ba bata tambaya ba amma ta baza idanu tana jiran ganin ta inda zai shigo. Hydar ne ya kuma shigowa ta kalle shi tace, "Tun safe nake zaman jiran ganin Asad ban ganshi ba har azahar tayi, na kira shi bana samun sa yana ina?." Hydar yace, "baya nan Takawa ya aike shi." "Ina ya aike shi?." "Ban sani ba" ya bata amsa a tak'aice yana fita da mamaki ta bishi da kallo kafin ta mik'e ta kimtsa ta nufi b'angaren mai martaba dan bata amince da wannan batun ba.  Tasan daman weekend ne shi kad'ai yake zaune yana karatu kamar koda yaushe ta zauna bata ce komai ba har sai da kai inda zai tsaya ya kalle ta yace, "Ya akayi? Naga kamar akwai magana a bakin ki." "Allah ya k'ara maka lafiya wani abu ne ya d'aure min kai, Naga kowa ne banga Asad ba na tambayi Hydar yace min mai martaba ya aike shi amma bai san inda ya tafi ba shine nazo na tambaya naji in babu damuwa." Mai martaba yayi murmushi yace, "Kina son Asad sosai, bakya so ya matsa daga kusa dake amma kuma bakya son abinda yake so." Shiru tayi bata amsa ba yace, "K'warai Asad baya nan baya Nigeria gabad'aya na aike shi Egypt." Gaban ta ya fad'i jin ya ambaci Egypt ta kalli mai martaba tace, "Takawa me yaje yi Egypt?." "Aiki na." Tayi shiru tana jin abinda yace tunani ta rasa abinda zatace a haka ta taso ta fito haka kawai zuciyar ta bata amince da abinda yace mata ba. Da yamma tana zaune Suhaima ta shigo ta zauna a k'asan carpet tana kallon ta tace, "Mama wani abu nake ji a gidan nan ana fad'a but ban sani ba ko Mama ta sani." Mama tace, "meye shi?." "Ji nayi ana cewa Asad yayi auren sirri ya tafi Egypt shida matar tasa, haka ne?." Gaban Mama ya fad'i ta kalli Suhaima da sauri tace, "wa kika ji yana maganar nan?." "Jakadiyar Hajiya." Mama ta dafe kai tashin hankali ya bayyana a tare da ita tace, "Zai iya kasancewa tunda kika ji maganar daga bakin ta, kira min Hydar da gaggawa." Suhaima ta d'auki waya ta kira Hydar ba jimawa ya shigo yana kallon Mama yace, "Lafiya?." "Hydar da gaske ne abinda nake ji a masarautar nan?." Hydar da mamaki yace, "me ya faru?." Mama tace, "Da gaske ne Asad yayi auren sirri ya tafi da matar tasa Egypt?." Gaban Hydar yayi mugun fad'uwa har rud'ani yaso bayyana a fuskar sa yayi k'okarin dannewa gudun kar ta fahimta tayi saurin ganowa ganin yayi shiru bai amsa ba cikin tsawa tace, "Ka amsa min da gaske ne......?!." [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *035.* Shiru Hydar yayi ya kasa furta ko wacce kalma domin bai san me zaice mata ba duk tsoro ya dabaibaye masa zuciya har hakan ya bayyana akan fuskar sa. Ganin ya kasa magana ya saka ta girgiza kai tace, "abinda aka fad'a haka ne kenan ko?." Sai a sannan Hydar ya dawo hankalin sa ya kalle ta yace, "Mama ban sani ba, ni ban ma ji maganar ba in ba yanzu da Mama take fad'a ba; abinda na sani Abba ne ya aike shi." "K'arya kake Hydar! K'arya kake, bakin ku d'aya kai da Asad baya yin komai sai ka sani, ka fad'a min gaskiya kafin na gano da kaina ranka ya b'aci" ta fad'a tana nuna Hydar da yatsa. "Allah ya wuci zuciyar Mama, amma ban sani ba, Mama zata iya tambayar Abba wataƙila haka ne amma ni ban san da hakan ba in ba yanzu ba." Mama tayi k'wafa ta kalli Suhaima tace, "kira min number Asad." Suhaima ta d'auki wayar Mama tana kiran number Asad amma bata shiga ta sake gwadawa bata shiga ba ta kalli Mama tace, "bata shiga Mama." Mama ta kalli Hydar tace, "ka fad'a min inda kuka tura Asad, wanne aure ake zance yayi ban sani ba?." Hydar ya rausayar da kai yace, "Ban sani ba Mama, ban sani ba." Girgiza kai tayi ta wuce ciki a fusace Hydar ya fita da sauri ya d'auki waya yana turawa Asad message. Hankalin Mama ya tashi matuk'a ta kasa zaune ta kasa tsaye zagaye kawai take yi a d'akin ta a haka akayi sallar magariba, jikin Mama har rawa yake buri kawai take yi sallar i'sha ta nufi b'angaren Mai martaba taji abinda yake faruwa wanda yake k'okarin tarwatsa mata tunani. Ana idar da sallar i'sha Mama ta fito zuwa b'angaren mai martaba tana takawa a cikin taqama kamar koda yaushe. "Allah yaja da ran Fulani, Allah ya biya miki buqatun ki, Allah ya jiqan mai martaba sarki, ya jiqan Hajiya babba ya raya mana Asad, Aliyu, da Hydar da k'aramar su Suhaima" wani dogari ya fad'a bayan ya zube a gaban ta yana jinjina. Kallon sa tayi a hankali tace, "Amin." "Munji labari ashe yarima mai jiran gado ya angwance, Allah ya sanya alk....." cikin tsawa Mama ta dakatar dashi tace, "Kaii! K'arya ne wannan labarin k'anzon kurege ne kar na sake jin sa a bakin ka." Ya rud'e yace, "Allah ya wuci zuciyar ki." Tsaki taja tayi gaba da sauri tana zuwa b'angaren mai martaba ta shiga bata same shi a babban falon ganin bak'in cikin gida ba sai a turakar sa wanda babu wanda yake shiga sai matan sa sai kuma Asad da ya amince dashi. A k'aramin madaidaicin falo yake a zaune yana cin tufa ya ganta kamar an cillo ta ta zauna a gefe tana wuci bata yi magana ba. Bai kula ta ba ya cigaba da abinda yake yi dan yasan tatsuniyar gizo bata wuce da kok'i daman yasan labari baya tab'a b'uya a masarauta indai anyi sai ya fita wannan al'ada ce ta ko wanne gidan sarauta haka yake. Ganin bai saurare ta ba sai tace, "Ranka ya dad'e wani labari nake ji a masarautar nan wanda yake neman tarwatsa min lissafi da tunani na gabad'aya." Sai da ya kwashe sakanni baiyi magana ba kafin yace, "Ina jin ki." "Magana nake ji tana wayo wai Asad yayi auren sirri ya tafi Egypt haka ne?." Mai martaba ya kalle ta yace, "yanzu tutsiye ni kika zo kiyi?." Ta girgiza kai tace, "A'a ranka ya dad'e ba haka bane ina so na sani ne dan na samu peace of mind." Mai martaba yace, "babu lallai abinda zan fad'a miki yasa ki samu kwanciyar hankalin." Gaban ta ya fad'i ta kalle shi tace, "Kenan da gaske ne?" Ta fad'a tana dafe k'irjin ta da yake bugawa. Mai martaba yace, "Abinda kika ji gaskiya ne, d'an ki Asad nayi masa aure da wacce yake so a karon farko na tura shi wata k'asar yaje can ya huta." A firgice Mama ta mik'e ta dafe k'irji idanun ta a waje jikinnta har rawa yake yi tana so tayi magana ta kasa yi ta koma ta zauna ta dafe kanta tana ji yana juya mata sabida barazanar tarwatsewa da taji yana niyar yi. Ta jima a haka kafin ta sake kallon mai martaba dan dai tasan bazai mata k'arya ba amma tace, "dan Allah in wasa kake min ka daina zuciya ta zata iya bugawa wallahi." Mai martaba yayi murmushi yace, "Ba wasa nake miki ba Rabi'atu abinda kika ji shi na fad'a, Asad d'an ki yayi aure yana kuma tare da matar sa wacce yake so." Mama ta kalle shi a firgice tace, "Wacece wacce yake so d'in? Badai wannan gurguwar kake magana a kai ba?" Ta fad'a tana waro idanun ta waje jikin ta na tsuma sabida firgicin da take ciki. Mai martaba ya bita da kallo ganin yadda ta rud'e kamar wacce akace ya auri wata dabba ba mutum ba yace, "ita nake nufi, ba ita yake so ba?." Mik'ewa tsaye ta kuma tana girgiza kai tana ja da baya tana kallon sa hawaye na k'okarin sakko mata daga idanun ta tace, "A'a kar kayi min haka dan Allah, bana son yarinyar; na tsane ta bana son ganin ta kusa da Asad, ba tsarin sa bace na ajin sa bace, shi da ita sai dai taimako dan Allah ka daina fad'a. Yace min ya barta tunda bana so meyasa za'ayi min haka!" Ta k'arasa fad'a da ihu tare da durk'ushewa a wajan ta fashe da kuka zuciyar ta na bugawa da sauri. Mai martaba mamakin ta yake yi ganin yadda ta fita daga hankalin ta akan abinda bai kai ya kawo ba take wannan jan numfashi kamar wacce numfashin ta zai bar jikin ta ko mai ciwon zuciya. Kuka Mama take yi sosai guiwoyin ta a zube a k'asa tana jin zuciyar ta na tafasa gangar jikin ta kuwa kamar ana kwaro mata ruwan zafi tafasashshe. "Ta yaya za'a ce d'an dana haifa shine ya auri talaka, gurguwa, mummuna mai tallan abinci?. Anyi min adalci kenan yanzu matsayina na wacce ta kawo shi duniya?, meyasa ba'a yi shawara dani ba aka yanke hukunci babu sanina?, shin bani da hakkin zab'a masa mata ne?, bani da hakkin da za'a fad'a min abinda aka yanke?!." Yadda take maganar da d'aga murya da alama ta manta da wanda take magana shiyasa ya zuba mata ido kawai yana kallon ta ganin yadda ta rud'e gabad'aya ga fita daga hankalin ta kalaman ma da take yi bata san tana yi ba. "Bazan lamunci wannan abun ba zuciya ta zata iya tarwatsewa gwara na raba su koda nima za'a raba ni da duniya, babu ta yadda wuta da ruwa su had'u waje d'aya, babu ta yadda za'ayi zafi da sanyi su had'u waje d'aya, babu ta yarda za'ayi fari da bak'i su had'u waje d'aya haka babu ta yadda za'ayi Asad da ita su zauna waje d'aya. Sai na raba koda nima za'a raba ni da duk abinda na mallaka!" Ta fad'a da k'arfi tana dafe kanta da ya sara mata tana komawa da baya ta zauna tana cigaba da zubar da hawaye. Mai martaba ya cigaba da kallon ta yayi murmushi kana yace, "Koda kin raba su Rabi'a anci riba domin Asad ya samu abinda yake so a karo na farko a rayuwarsa, dole in aka kalle ta ace tsohuwar matar Asad ce kinga kenan koda kin raba su baki ci riba ba itace taci riba. Balle ma yau auren nasu ya wuce sati in ma rabo ne yanzu za'a iya samu kad'an daga cikin ikon Allah, kinga ta ko ina tayi miki fintinkau tasan sirrin d'anki wanda har duniya ta tashi ke baza ki san dashi ba. Raba su kuma baki isa kiyi ba Rabi'atu auren su ya zama mutu ka raba takalmin kaza." Dummm Mama taji a zuciyar ta ambatar ciki da mai martaba yayi ta d'ago da sauri ta kalle shi sai kuma ta dafe kai tana jijjiga kanta alamun sai yanzu tunanin ta yaje wajan, zabura tayi kamar mai tab'in hankali ta mik'e zata fita taji an rik'o hannun ta ya zaunar da a kan kujera zatayi magana yace, "Kar kice min komai, ke ba mai ja da ikon Allah ba? Har gidan su yarinyar kika je kika ciwa iyayen ta mutunci, kika tura a kashe ta, kika tura aka jiwa mahaifiyar ta ciwo; duka kinyi wad'annan abubuwan sabida ki raba su sai gasu tare shi da ita a inda babu ke a wajan, sai ki had'd'iye zuciya ki mutu domin indai ina da rai da lafiya babu abinda zai raba auren Asad da Rauda." "A'aaaaaaaa! Bazai yu ba!" Ta fad'a da k'arfi tana sake fashewa da sabon kuka mai shashshek'a kamar k'aramar yarinya. Mai martaba ya kalle ta yace, "ki kuma zauna a nan ban baki umarnin fita daga nan ba sai da safe." Hannayen ta ta had'e alamun rok'o ta zube a k'asa tana kuka sosai amma ta kasa magana. Tsaki yayi yana jijjiga kansa sam halayyar ta haushi take bashi a komai nata kanta kawai ta sani bata hangen kowa sai kanta, tauye kowa take indai ita zata b'ulle to kowa ma ya dawwama a wajan bata san komai ba sai son kai shiyasa ya nuna mata shima yana da iko da Asad kamar ita. "Asad d'ana ne meyasa za'ayi min haka?" Ta fad'a cikin kuka tana kallon sa. Baice mata komai ba ta had'a kai da guiwa tana kuka tana hasashen irin matakin da zata d'auka domin babu abinda zai hana ta raba auren koda nata auren zai mutu sai dai ya mutu bata damu, babu abinda zai hana d'aukar mataki koda za'a d'auki mataki a kanta itama, koda zai zama silar mutuwar kowa sai ta raba Asad da Rauda domin ruwa ba sa'an kwando bane ba. *☆☆☆*             _Asad Mama tasan komai a yanzu, kasan abinda zakayi kafin ta raba ku, ka cigaba da addu'a dan tabbas Mama bazata barku lafiya ba. Matsayina na d'an uwan ka ina baka shawarar ka amince da matar ka ka maida ta cikkakiyar matar ka kafin lokacin ya k'ure mana._ sake maimaita message d'in Asad yake yi kansa na sarawa ambatar Mama da yayi a cikin sakon da aka turo masa. Da sauri ya fita daga wajan message ya shiga call log da niyar kiran Mama amma sai ya tsaya cak ya dafe kansa a bayyane yace, "me ma zanyi?."    'Hydar.' Zuciyar sa ta bashi amsa ya danna number Hydar a maimakon ta Mama har lokacin hannun sa yana rik'e da kansa da yake ji yana yi masa ciwo. Hydar bai d'auka ba ya kalli Rauda a kan gado yaga tayi bacci ya tashi ya fita yana sake kiran wayar Hydar, a karo na biyu ya d'auka bai bari Asad d'in yayi magana ba yace, "Mama tasan komai Asad daga yau zuwa ko wanne lokaci komai zai iya faruwa, ban so taji labari da sauri haka ba amma kasan yanayin gidan namu ba ko wanne sirri ne yake b'oyuwa ba especially da ya kasance Aliyu ya san komai."     Asad ya dafe kansa kana yace, "Maamaaa!." Hydar jin sunan da ya ambata ya saka yace, "eh, lokacin da nayi maka message d'in nan ta kira ni kamar zata dake ni tana fad'a min bakin mu d'aya nasan inda kake nace ban sani. Asad ka rik'e matar ka i mean ku zama d'aya kai da ita kafin Mama ta raba ku da ita." Asad ya sake cize bakin sa kafin yace, "why nake jin wani iri in ka kira Mama? Why ban kira ta cikin kwanakin nan ba?, why in na d'auki waya zan kira ta nake forgetting Hydar?."     Hydar yace, "ban sani ba Asad, ka dai cigaba da addu'a kamar yadda ka saba amma akwai tarin qalubale a gaban ka, sai ka cire wannan rashin son maganar taka ka rik'e matar ka yadda koda za'a raba ku za'a sha wahala" Hydar yana gama fad'a masa haka ya yanke wayar bai jira mai zai kuma ce masa ba. Asad ya tafi duniyar tunani yana so ya gano dalilin da ya saka in ba ambatar Mama akayi ba mantawa yake da ita bayan a baya ba haka yake ba, inda akwai wacce yake tunawa a ko wacce dak'ik'a Mama ce, meyasa yanzu baya jin hakan a kanta a wannan lokaci?.      "Hello handsome." Muhibba ta fad'a a gefen sa tana tsayawa kusa dashi tana kallon sa. Bai kalle ta ba domin baya cikin yanayi mai dad'i ko kad'an daman itama tasan bazai yi magana ba tace, "zan iya taya ka hira?." Asad bai kalle ta ba ta sake yin murmushi tace, "na fad'awa sister ka sak'o ta fad'a maka I hope ta sanar da kai?." Kai ya dafe da hannun sa guda d'aya yaja k'aramin tsaki baice mata komai ba ya d'aga k'afa da niyar tafiya. Hannun sa ta rik'e hakan ya saka shi tsayawa cak ya juyo ya kalle ta sai ta saki hannun nasa tana kallon idanun sa tace, "I love you!." Bai ce komai ba ya bar mata wajan ita kuma ta bishi da kallo tana murmushin farin ciki, ita kallon sa ma kawai nishad'i yake bata balle kuma yayi mata magana.      Asad fita yayi daga asibitin yana niyar shiga mota yaga kiran mai martaba bai d'auka ba ya shiga motar ya zauna sannan ya d'auka ya saka a kunne yayi sallama muryar sa a sanyaye mai martaba ya amsa kana yace, "Babar ka tasan komai Zaki, kar hakan ya dame ka ka saka a zuciyar ka komai Allah ya rubuta sai ya faru, ko meye zai faru kar ka baro k'asar nan ba tare da umarnina ba kaji ko?." Asad ya d'aga kai kamar yana gaban sa dak'yar ya iya furta, "In sha Allah." "Ka cigaba da addu'a komai zaizo da sauk'i cikin ruwan sanhk, Babar ka bata isa tayi abinda Allah bai nufa ba komai ya faru Allah shine ya tsara faruwar sa." Baice komai ba Mai martaba yace, "a cigaba da addu'a" yana fad'a masa hakan ya yanke wayar Asad ya sake cire wayar da sauri da niyar kiran Mama amma sai ya samu kansa da nemo number Hafiz ya dafe kansa ya manta abinda zaiyi kawai ya kifa kan a kan sitiyarin motar yana furzar da iska mau zafi. *☆☆☆*        Mama kwanan zaune tayi ko kad'an bacci yak'i zuwar mata ido da ta kulle idon ta sai ta hango Asad da Rauda a kwance a waje d'aya sai ta bud'e ido a zabure tana cize bakin ta. Mai martaba yana lura da ita bai kuma ce mata komai ba. Asuba nayi yana fita masallacin cikin gida Mama ta zabura ta fito daga b'angaren sa ko sallar bata yi ba ta burin ta kawai ta ganta a b'angaren ta tana shiga a haukace hadiman ta na gaishe ta amma bata bi ta kansu ba ta shiga cikin d'akin ta ta kulle kanta. Hannun ta na rawa ta d'auki waya ta kira Asad amma wayar bata shiga ta canja akalar kiran ta kira Mum hankali a tashe, Mum bata d'auka ba ta cillar da wayar tana zagaye d'akin cikin neman mafita, tayar da sallah da taji anyi shine ya saka ta yin alwala sallar ma ba'a nutse tayi ta ba tana idarwa ta mik'e ta fita zuwa d'akin Suhaima. A bakin k'ofa suka had'u da alama zata je gaishe tane tace, "Barka da asuba Mama." Mama bata amsa ba tace, "sako hijjabin ki zamu fita yanzu." Suhaima da mamaki tace, "Mama Ina zamu je da asuba?." Kallon da tayi mata ya saka ta yin shiru tana bin maman nata da kallo ganin ta firgice kamar ba ita ba tace, "Mama lafiya naga kin koma wani iri?." Cikin tsawa tace, "Kiyi abinda nace kawai Suhaima, kije ki sako hijjabi zamu fita!." Da sauri Suhaima ta koma ciki ta sako dogon hijjabi akan kayan baccin jikin ta tana fitowa Mama ta bata key na mota tace, "ki fita da motar zan fito ta baya na same ki." "Mama amma Abba ya hana ni yin driving" ta fad'a tana karb'ar key d'in. Hannu takai da niyar marin ta Suhaima tayi baya da sauri ta fita tana mamakin abinda ya samu Mama haka. Duk a tsorace Suhaima take kar Takawa ya ganta dan ya hana ta jan mota balle kuma da asuba haka, a haka ta fita da motar zuwa can bayan gidan dan tasan ta nan Mamaa zata b'ullo tana zuwa kuwa ta ganta tsaye Suhaima na tsayawa ta bud'e gaban motar ta shiga Suhaima taja motar ba tare da tasan inda suka nufa ba. Tsoron yi mata magana take yi gashi bata san inda zasu je ba haka take mik'ewa kawai tana tafiya Mama kuma na gwada wayar Mum har lokacin bata d'auka ba, tsaki tayi ta kalli Suhaima tace, "kiyi kwana" ta fad'a tana nuna mata inda zata bi Suhaima ta bi wajan suka cigaba da tafiya. Sunyi tafiya mai nisa sosai domin Suhaima ta d'auka ko Mama ta manta hanyar ne amma babu damar tambaya tayi shiru har suka k'araso wata ruga ta fulani da babu mutane sai gidajen k'asa suma sai ka irga su ta bata umarnin tsayawa, bud'ewa tayi ta fita Suhaima zata fito tace, "kiyi zaman ki ina zuwa." Ta fad'a tana shiga cikin gidan da tazo da Sauri Suhaima ta bita da kallo. A zaune ta same malamin da yana jan carbi sallamar ta ya saka ya mik'e yana fad'in, "Ranki ya dad'e, Allah yaja zamanin ki, ya raya mana y'an uku yasa su mulke mu. Kece da kanki da sassafiya haka?." Mama bata iya amsawa ba ta zauna tace, "Ina cikin tashin hankali ne da dole na fito yanzu." Malamin ya zauna yace, "to ranki ya dad'e meya faru?." "Mahaifin Asad ne ya d'aura masa aure da yarinyar da muka zo wajan ka kwanaki ba tare da sanina ba." Malamin yayi murmushi yace, "Daman na fad'a miki auren su da wahala in bai yu ba, datse shi abu ne mai matuk'ar wahala." Tace, "Yanzu haka suna Egypt tare da yarinyar." Farantin gaban sa ya jawo ya fara duba k'asar gaban sa na wani lokaci kafin yace, "Tabbas suna can, yanzu haka gasu nan tare suna tafiya shi da ita amma kamar bata da lafiya na gani." Hankalin Mama ya sake tashi tace, "babu ta yadda za'a raba su ya dawo gida? Bana k'aunar ta ko kad'an." Ya sake bincikawa yace,  "akwai kuma babu, hanyar da za'a bi wajan raba su dole sai an jira lokaci domin kuwa akwai d'an katanga a yanzu da kafin a rusa ta dole sai an jira." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu ko kashe tane baza'a iya yi ba?." "Za'a iya ranki ya dad'e, amma a ganina abi wata hanyar domin kafin a samu wannan nasarar ma za'a jima dan na fad'a miki tana da rik'o da addini ba komai ne zaiyi saurin tasiri a kanta ba." Mama ta sauke ajiyar zuciya ta dafe kai maganar mai martaba ta fad'o ta kalle shi tace, "Kafin wannan a duba min aga akwai wata alaqa da ta had'a su da yarinyar, ina nufin auratayya ta had'a su ko a'a?." Malamin ya sake cigaba da duba mata kafin yace, "A dai yadda na gani babu abinda ya had'a su sai dai kin san ana samun tangard'a wani lokacin Allah yana yi mana hijjabi da ganin wasu abubuwan, sai mu gani muce anyi kuma ba'ayi ba, ko mu gani munce ba'ayi ba kuma anyi d'in." "Muje a bai had'a su d'in ba daman bana fatan hakan. Abinda nake so dakai ina so a yiwa Asad aiki a lalata masa mazantakar sa, ina nufin yadda bazai iya kusantar ko wacce y'a mace ba a wannan lokacin sai da nayi niyar hakan!" Ta fad'a tana kallon sa shima ita yake kallo da d'unbin mamaki....... [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *036.* Mamaki ya kama shi jin abinda ta furta ya girgiza kai yana jinjina tsantsar mugunta da rashin son yarinyar da take yi ya gyara zaman sa yace, "Ranki ya dad'e Asad d'in za'a yiwa aiki?." Ta kalle shi tace, "ashe kaji me nace." "Abin ne ya bani mamaki ranki ya dad'e, keda bakya so a yiwa Asad aiki da naji kince ayi miki shine nayi mamaki sosai." "Yanzu tunda kaji sai kayi abinda nace." Malamin yace, "yanzu ranki ya dad'e bakya hango matsala a cikin wannan lamarin? Ayi masa aiki a yanzu nan gaba in ya auri wacce kike so kuma fa?." Mama tace, "Sai a warware shi, kayi masa abinda bazai wahalar warwarewa ba amma bana k'aunar wani abun ya shiga tsakanin sa da yarinyar nan ko meye shi koda hannun ta bana so ya rik'e." Malamin ya girgiza kai yace, "wannan ba damuwa bane ba ranki ya dad'e, za'a yi kamar yadda kika ce." "Yau nake so ayi ba sai gobe ba." "Babu damuwa ranki ya dad'e." Ta d'an yi jimm kafin ta kuma cewa, "sannan ayi dai wani abun da za'a raba su bana son zaman nan nasu tare." Malamin yace, "babu damuwa ranki ya dad'e za'a yi." Bata ce komai ba ta mik'e ta fita ya bita da kallon mamaki kafin ya girgiza kai ya cigaba da abinda yake yi. Mota ta shiga Suhaima taja suka nufi gida jikin ta duk a gajiye yake sabida dogon tuk'in da tayi. Ta inda Maman ta fita tana nan ta shiga ta wuce b'angaren ta Suhaima ta ajjiye motar ta nufi zuwa ciki. A hanya suka had'u da jakadiya Babba tana ganin Suhaima tace, "Ranki ya dad'e barka da dawowa." Suhaima tace, "barkan ki." Har zata gota tace, "Mai martaba yana kira." Gaban Suhaima ya fad'i amma bata nuna hakan ba ta juya akalar tafiyar ta zuwa b'angaren mai martaba jikin ta a salub'e. Yana zaune shida Wambai kamar koda yaushe aka yi mata iso ta shiga da sallama ta tsuguna a k'asa tace, "barka da safiya Takawa, ina fatan an tashi lafiya." Mai martaba ya amsa kana yace, "Ina kika je naga kin fita da mota d'azu?." Shiru tayi kafin tace, "Na kai Mama unguwa." Mai martaba jin mai tace ya saka yace, "Shikenan jeki." "A tashi lafiya" ta fad'a da girmamawa ta fita a sanyaye. Mama kuwa tana shiga ta tarar da Mum a zaune tana jiran ta tayi tsaki tace, "Dake da Jidda wayoyin ku duka basu da amfani." Mum ta mik'e tsaye tana kallon ta cikin mamaki ganin yadda ta koma kamar ba ita ba tace, "Ranki ya dad'e lafiya na ganki haka?." Mama ta zauna tana zare hijjabin jikin ta tace, "a ko wanne yanayi ma ganina zakiyi indai a wannan lokacin ne, zauna." Ba musu ta zauna tace, "Me yake faruwa? Sarautar Kano aka bawa wani wanda ba namu ba?." Mama taja tsaki tace, "Inda sarautar Kano aka bayar d'in ma da naji dad'i domin yafi min sauk'i a kan abinda yake faruwa yanzu." "Me yake faruwa?." "Mai martaba ya aurawa Asad yarinyar nan yanzu haka suna Egypt." Firgici, tsoro, tashin hankali, mamaki, rud'ani, gigita duka suka had'arwa Mum a lokaci guda ta mik'e tsaye ba tare da tasan tayi hakan ba idanun ta a waje hannun ta dafe da k'irjin ta tace, "What!." Mama da take kallon ta tace, "abinda kika ji shi nace." Mum ta zauna tana kallon Mama tace, "Nasan dai baza ki min wasa da wannan maganar ba shiyasa na gigice." Mama tace, "na gigice ninkin wacce kika yi sau goma kiris ya rage na rasa hankalina, a fuskar ta kinga hakan ya bayyana." Mum ta sake rud'ewa tace, "Ta yaya?." "Ina can Kano." "To Asad ba anyi dashi ya hak'ura ba ya akayi maganar ta dawo?." "Mahaifin sa shine yayi komai, na tabbata Asad bazai aikata hakan ba tunda yasan bana so." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Fulani kice babban masifa ce ta kawo mana kai" Mum ta fad'a a rud'e tana kallon ta. Mama bata iya cewa komai ba Mum tace, "yanzu ya za'ayi kenan?." Mama ta bud'e hannun ta alamun bata sani ba Mum tace, "kuma kinyi magana dashi?." "Bana samun sa a waya kwata-kwata." "Shikenan! Har sun raba mu dashi, mun shiga uku" Mum ta fad'a cikin rud'ani da ya bayyana a tare da ita. Ba zato Mama taji tana hawaye tace, "Ban san me zanyi ba Sadiya bana son zaman su tare gashi mahaifin sa yace matuk'ar yana da rai da lafiya Asad bazai rabu da ita ba, nasan halin sa zai toshe duk wata hanya da yasan zamu yi magana da Asad, duk kuma abinda na saka a yiwa Asad ko ita yarinyar akan a raba su sai ya lalata shi. Kaina ya kulle Sadiya ya kuma ce in na sake na tafi Cairo raina sai ya b'aci" ta fad'a tana dafe kanta da hannun ta har lokacin hawaye take. Mum ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "dole mu san abinyi in ba haka ba burin mu bazai cika ba." Mama ta d'ago ta goge idanun ta tace, "wannan a rubuce yake dole ne na d'auki mataki na gaggawa kafin a kassara ni. Yanzu daga wajan Malam nake na bashi aiki ayi min za kuma ayi amma kafin lokacin ina so nayi wani abun da zan d'auke hankalin mai martaba daga kaina gabad'aya." Mum tace, "ya kamata kuwa in ba haka ba wallahi zasu cinye mana kurwar yaro, dan nidai nasan wannan ba aikin sa bane wallahi aikin asiri ne bata da abinda namiji zai sota dashi, sunyi nasarar asirce mana shi Fulani." "Zan warware shi Sadiya, ke kin san zan iya. Dan na aikata komai a duniyar nan wajan ganin d'ana ya dawo abu ne mai sauk'i, zan iya salwantar da komai dan ganin Asad ya dawo gare ni ya cika min burina." Mum tace, "haka ne ranki ya dad'e. Amma iyayen ta sun cuce mu iya cuta, tsakanin mu dasu sai Allah ya isa." "Hmmm" Mama ta fad'a dan maganar ma tak'i zuwa harshen ta. "Bakya ganin muje gidan su ayi yiwa iyayen ta barazana da kurari ko zasu ji tsoro suce ya dawo musu da y'ar su?." Mama tace, "ba aikin da hakan zaiyi mana, a baya munje ai me yayi?." Mum ta girgiza kai tayi shiru cikin tunanin mafita domin a ganin ta tafi Mama shiga tashin hankali. Mum tayi tagumi kana tace, "ni Jidda ma nake tausayi in taji labarin nan bana tunanin zata iya bacci yau." Mama ta kalle ta tace, "ya zama dole ta sani kodan ta taya mu da wani abun ta dage ta kwato mijin ta." Mum tace, "wannan abu dai sam baiyi dad'i ba ji nake kamar na fashe da kuka. In na tuna irin kalaman yarinyar nan a kan mu sai naga kenan itace tayi nasara a kanmu abinda ta fad'a yana neman tabbata." "Ki kwantar da hankalin ki Sadiya wallahi sai sun rabu." "Ba rabuwar ba ranki ya dad'e kar muje wani abun fa ya gifta tsakanin su, hakan tana faruwa wallahi mun cutu har abada. Koda basu had'a jini ba ta shiga jirin matan da zasu yi iddar auren Asad." "Nayi maganin wannan matsalar hakan bazai faru ba har a tashi duniya." Mum tayi ajiyar zuciya tace, "Allah ya tabbatar" ta fad'a tana goge idanun ta kamar wacce take kuka. Mama tace, "matakina farko akan mai martaba zan d'auke shi domin shine babbar matsalata a yanzu." Mum tace, "Shine abinda ya kamata ayi ranki ya dad'e, amma me za'ayi?." Mama ta kalle ta kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tace, "zan aiwatar dashi kowa kuma zai gani lokacin da zan dawo da Asad bai ma san nayi ba. Babban abinda yake gabana a yanzu na samu nayi magana da Asad gashi nasan ko da wasa bazai bari naje Egypt d'in ba." "Hydar bakin su d'aya a gani na shi ya kamata ki kira ya had'a ku a waya." Shiru Mama tayi kafin Mum tace, "Kenan dana gansu a airport daman shine ba Aliyu ba?" Ta d'aki kujera tace, "wallahi naji hakan a jikina amma kalaman ki ya saka na manta da maganar ashe sune da yanzu mun d'auki mataki." Mama taja tsaki ta furzar da iska ta tab'a wuyan ta tace, "Zazzab'i ne a jikina Sadiya." Mum tace, "dole kiyi Zazzab'i fulani, bara na kira Suhaima ta kawo miki magani" ta fad'a tana tashi ta shiga ciki wajan Suhaima Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jin zuciyar ta nayi mata zafi da rad'ad'i. *☆☆☆* "Ki taka slowly" ya furta mata daidai kunnen ta yana rik'e da ita hannun sa na zagaye akan shafaffen cikin ta domin ya karb'i sandar yace ta taka a haka. Gabad'aya ta kasa sakewa sabida hannun sa da yake zagaye da ita ga khamshin turaren sa da yake sanya mata kasala kanta na daf da kafad'ar sa hannun sa d'aya yana rik'e da hannun ta guda d'aya suna takawa a cikin asibitin a hankalin. Babu ruwan wani dasu tafiya suke tana takawa a hankali yana zamar mata garkuwa zuciyar sa na harbawa da sauri haka tata zuciyar ma. Dr muhibba suka gani a gaban su tana kallon su har suka zo daf da ita tace, "Sannu Sister ya k'afar?." Haushin ta Rauda take ji haka kawai hakan ya saka tace, "Da sauk'i" ta amsa a tak'aice tana kallon wani wajan daban. Gaban Asad ta tsaya tana kallon sa tace, "Handsome baka ce min komai ba, wallahi da gaske nake ina sonka. Sister baki fad'a masa sak'ona bane ba?." Gaban Rauda ya fad'i matuk'a bata san ta matsa hannun sa da k'arfi ba ta dai ga ya kalle ta amma bata san me ta aikata ba idanun ta a runtse suke sai ya d'an saki fuska kad'an baiyi magana ba ya taka da niyar barin wajan. "Handsome pls" ta sake tsawaya a gaban sa tana kallon sa kamar zatayi masa kuka. Kallon ta yayi na sacan d'aya, biyu, uku, kafin ya d'auke idon sa ya rab'a ta gefen ta ya wuce ta sake bin shi da kallo tana shak'ar khamshin turaren jikin sa. Rauda tayi kicin-kicin da fuska bata san taqamemen abinda yake damun ta ba har suka gama zagayen suka koma d'aki ta zauna a akan kujera tana kallon wani wajan daban ba tare da ta kalle shi ba. Shima bai damu ba dan bai d'auka zata ji haushi ba ya zauna na wani lokaci kafin ya tashi ya fita tabi bayan sa da kallo tana jin wani iri a ranta. Bayan kwana biyu. K'afar Rauda tayi kyau sosai har tana takawa babu sanda ba kuma tare da an taimaka mata ba tana tafiya sai ka lura zaka ga tana d'ingishi. Tayi kyau tayi haske fatar ta ta murje tayi kib"a amma ba sosai ba kana dai ganin ta kasan ta samu canji rayuwa sosai musamman a fatar ta da take kyalli tamkar chocolate. An basu sallama da magani a ranar sai zuwa da zata dinga yi ana duba k'afar sun fito da daddare zasu shiga mota zuwa hotel d'in da suka sauka babu mai magana a cikin su kamar koda yaushe shi yayi shiru itama haka. Yana bud'e motar tana tsaye tana kallon wani wajan daban Muhibba ta k'araso da sauri inda suke tsaye ta kalli Rauda tace, "Sis zaki tafi shine ba sallama?." Rauda ta kalle ta tace, "Ban ganki bane." Muhibba tace, "Saka min number ki ta Nigeria mu dinga gaisa." Rauda tayi jim tana kallon ta domin bata san sabuwar number da ya sake mata ba ita dai kawai tana kiran y'an gidan su amma bata tab'a dubawa ba. Muhibba ta saci kallon Asad da yake zaune a mota tace, "ki saka min ta yayan ki ma." Rauda ta kalle ta tace, "Wayata ta fad'i ban san inda na ajjiye ta ba." Muhibba tace, "Kuma baki haddace ba?." Rauda ta d'aga kai alamun eh Muhibba ta kalli Asad ta matso kusa da inda yake zaune tace, "Handsome zaka tafi ko goodbye baka ce min ba." Rauda ta zaga ta shiga gaban motar suna har loakcin bataji ya kula Muhibba ba, Rauda na rufe k'ofar motar shima yaja tasa zai kulle Muhibba ta rik'e tace, "Ka bani koda number kane please." Asad ya d'aga kai ya kalle ta yaja siririn tsaki yaja murfin motar ta saki ya kulle ta kalle shi tana murmushi har suka ja motar bata daina kallon su ba. Suna barin wajan Rauda tayi tsaki tace, "Bata da hankali gabad'aya yarinyar nan ta cika nacin tsiya, haushin ta nake ji" zancen zuci ya fito fili ba tare da ta san hakan ba. Kallon ta yayi kafin ya d'auke kansa ya cigaba da tafiya. Hotel d'in da suke dai nan suka koma d'akin yana nan tas dashi an gyara tana takawa a hankali ta shiga wanda ta sauka a ciki tana kallon sa tsaf dashi sai khamshi yake yi. Bata jima da zama ba ya shigo da ledar maganin nata ya ajjiye a gefen ta kanzil baice mata ba ya fita ta bishi da kallo kafin tace, "Ina ganin mulkin mallaka ni Rauda, magana ma ta dinga gagarar mutum kuma a haka ace wai yana tare da wacce yake so ne?, mtswwww" ta fad'a tana jin haushin hakan a ranta dan ita sam bata ga wata soyayya a tare dashi ba. Tana nan zaune ya dawo ya canja kaya zuwa jallabiya blue ya saka hular sanyi blue itama har kunnen sa ya rufe yayi kyau sosai khamshi na tashi a jikin sa ya kalle ta itama shi take kallo yace, "Zaki iya fita?." Kamar tace a'a amma sai ta amsa masa da eh baice komai ba ya juya ya fita. Zaman ta tayi domin baice mata ta taso ba bata d'auka shirun yana nufin ta tawo ba kusan mintina goma tana zaune tana jiran yace ta tawo su tafi. Gajiya tayi da jira ta fito falon bata ganshi ba kamar b'arauniya take takawa zuwa d'akin da ya sauka ta tura k'ofar ta shiga tana k'arewa d'akin kallo, kamar nata tsaf shima haka yake sai littafai da suke a kan gado na addini dana zamani. Burge ta d'akin yayi sosai ta taka tana k'are masa kallo a hankali domin ya had'u ga girma ga tagar d'akin nasa har tafi wanda take ciki kyau motoci kawai ake gani suna wucewa ta glass d'in. Har zata juya ta fita kan mudubin ta hango wani katin magani kamar nata da ya b'ata ta dawo da baya ta k'arasa inda yake ta d'auka ta bud'e shi taga katin tane wanda ta yar ranar da suka fara had'uwa dashi ta dawo da wajan mai magani, juya katin take yi kafin tace, "Me ya kawo shi hannun sa har ya tawo dashi k'asar nan?" Ta tambayi kanta ba tare da tasan amsar ba tana sake kallon katin ga sunan tana nan rad'au a jiki. "Maganin da aka zage ni aka wulak'anta ni a kansa, aka zage ni aka zagi iyayena dan kawai muna karb'ar bashi a kansa. Nifa kome ya faru dani a rayuwa silar gidan su ce" ta fad'a tana ajiiye katin maganin abinda ya faru yana dawo mata. 'Amma kuma ai an siya miki maganin har kika tawo baki daina shan sa ba, kinga kenan an wanke miki ciwon zagin da akayi miki' zuciyar ta ta bata amsa da sauri ta wara idanun ta a bayyane tace, "Kenan hakan yana nufin shine ya siyi maganin...? Anas yace bashi bane daman kuma shi muka d'auka ya siya yace bai siya ba kenan shine....?." Sai kuma tayi shiru tace, "ta ya zai siya kin magani daga ganina a hanya?." 'Kin manta abinda Khalil ya fad'a a lokacin? Hakan zai iya sakawa ya siya miki magani tunda daman yasan k'anin sane ya buge ki' zuciyar ta ta kuma bata amsa. Rauda ta fito daga d'akin har lokacin tunani take ta zauna a falo tace, "Kenan shine ya siya min magani, shine ya bawa Baba na keke napep, shine ya kawo mana kayan abinci kud'i kuma Anas ne ya aiko dasu. Amma meyasa d'an aike d'aya ne duka ya kawo? Ya akayi yasan kuma Baba na son napep tunda da Anas sukayi magana?" Ta fad'a cikin d'aure kai tana so ta gano bakin zaren. Bud'e k'ofar akayi aka shigo ta ganshi ya shigo da ledoji k'anana da alama har yaje ma inda yace zata je d'in ya dawo ta bishi da kallo har ya ajjiye ya zauna tace, "shine kaje ka dawo bayan nace zanje." Kallon ta yayi jin tama raina masa hankali wato zaman jiran ta zaiyi har sai sanda ta fito sannan zai tafi. "Baki son zuwa" ya bata amsa a tak'aice yana bud'e leda guda d'aya ya fito da ice cream a roba sai gumi yake sabida sanyi ya bud'e ya fara sha kafin ya tura mata d'aya ledar gaban ta sai tace, "Ina so naje mana na fito ban ganka ba kuma baka ce min nazo muje ba." "Oh sai nace kizo?" Ya sake fad'a ba tare da ya kalle ta ba tace, "Eh mana, ai da sai kace min tawo mu tafi sai kawai kayi tafiyar ka bayan nace zanje." Kai ya girgiza kawai baice komai ba ta bud'e ice cream d'in ta fara sha kamar yadda taga yana sha itama tayi shiru kamar yadda yayi shiru. Knocking d'in k'ofar akayi kafin ya tashi karanbanin Rauda ta riga shi mik'ewa dan tana so ta buɗe k'ofar yadda take bada sauti in an bud'e yana burge ta sosai tana bud'ewa suka had'a ido da Dr Khalifa. "Lallai patient k'afa yayi kyau" ya fad'a yana shigo yana kallon ta. Murmushi tayi domin sun saba dashi sosai tace, "Alhamdulillah." "Haka ake so ai" ya fad'a yana kawo hannu yaja kumatun ta yana murmushi itama haka. D'ago idon da zatayi suka had'a ido da Asad ya tsaya cak da shan ice cream d'in yana kallon su kafin ya d'auke kansa ya mayar kan TV. K'arasawa Khalifa yayi ya zauna kusa dashi yana kallon sa yace, "Prince ga ragowar maganin nata da ba'a karb'a ba d'azu, Sister zo na nuna miki duration d'in kar kiyi mistake." Ba musu Rauda tazo ta zauna ya nuna mata yadda zata sha da yadda zata shafa da ya gama ya bata duka tace, "na gode." Murmushi yayi yace, "haba chocolate colour you deserve anythings from me." Murmushi tayi bata ce komai ba Asad dai bai tanka musu ba Khalifa ya mik'e yace, "bye deaf dan nasan ba kula ni zakayi ba. Sister Allah ya k'ara lafiya" ya fad'a yana fita ta amsa da amin yaja k'ofar ta zauna ta cigaba da shan ice cream d'inta. Kallon da taga yanayi mata ne ya saka ta kasa sakewa da ta d'ago sai taga sun had'a ido in ta sauke idon ta ta sake d'agowa sai taga dai kallon ta yake sai ta rud'e ta fara juya cokalin ice cream d'in a cikin robar ba tare da tana sha ba ji take kamar ta tashi ta zura a guje sabida yadda take jin idanun sa a jikin ta. "Raudaaaa!" Ya kira sunan ta can k'asan makogwaron sa har lokacin idanun sa yana kanta. D'ago ido tayi ta kalle shi kana tace, "Na'am." Ya bud'e baki zaiyi mata magana sai kuma yayi shiru taga ya runtse idanun sa yana cize baki ya fara nuna ta da yatsa yana karkad' a shi kamar mai magana amma kuma ba magana yake mata ba. Duk sai taji tsoro ya mamaye mata zuciya ganin yanayin sa gabad'aya ya canja lokaci guda fuskar sa ta kuma d'aurewa fiye da d'azu. Fusata taga yayi yayi cilli da robar ice cream d'in ta daki bango ta b'ata wajan gabad'aya ta firgita ta kama jikin ta tana kallon sa sai taga yana had'd'iye saliva dak'yar har lokacin cizon bakin sa yake yi yana kuma kallon ta alamun magana yake so yayi baya son yi d'in ne kawai. Dak'yar ya fizgo maganar daga bakin sa yace, "He touched you a gaban idanuna...." Sai kuma yaja numfashi mai tsaho yace, "why.....!." Jin abinda yace sai ta gano inda maganar ta nufa kenan kishi yake dan Khalifa yaja mata kumatu wanda itama bata san hakan zai faru ba da zata dakatar da faruwar sa, zatayi magana ya d'aga mata hannu yana murza yatsun hannun sa amma bai ce komai ba ya mik'e ya shiga d'aki. Rauda sai ta kasa nutsuwa hankalin ta taji ya tashi ganin yadda yake nuna ta da yatsa fuskar sa duk ta canja hakan ya tabbatar mata da ba k'aramin abu yaji a ransa ba tunda gashi ya bayyana har ya kasa b'oyewa kuma laifin tane. Rauda tace, "to yanzu ya zanyi? Ni ban san hakan zata faru ba da ban bud'e k'ofar ba, sannan ban san zaiji haushi haka ba." 'Kije ki bashi hak'uri tunda ke kika yi masa laifi kuma matar sace ke, zunubi kika aikata babba barin wani namijin da ba maharramin ki ba ya tab'a ki kuma a gaban mijin ki. Kije ki nema ya yafe miki fushin sa gare ki ma illa ne' abinda zuciyarta ta fad'a mata kenan ta kuma gamsu da hakan ta mik'e da niyar zuwa sai kuma tace, "to naje nace masa me?" Dafe kai tayi cikin rashin sanin mafita. Nufar d'akin tayi bayan ta samo dabarar da zatayi amfani da ita zuciyar ta na bugawa kamar zata fito daga k'irjin ta. [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *037.*         A hankali take tafiya har taje k'ofar d'akin tana tunanin ta yadda zata shiga in ma ta shiga tace masa me..?. A haka tayi bismillah ta tura k'ofar d'akin da sallama a bakin ta ta hango shi a tsaye a jikin taga yana kallon motocin da suke wucewa yana sauke ajiyar zuciya da alama har lokacin bai wuce ba. Takowa take a nutse har tazo kusa dashi ta kalle shi shi kuma ba ita yake kallo ba tagar yake kalla tace, "Kayi hak'uri bazan sake ba, ban san zai tab'a ni ba da bazan bud'e k'ofar bama." Kamar jira yake tayi maganar ya sake fusata cikin maganar sa da bata fita sosai yace, "Ohh bud'e k'ofar da kikayi u think kinyi daidai?. I think tun a hospital nace miki bana son wannan shirmen da kuke yi dashi ko?." Taji tsoro sosai ranar farko da taji doguwar magana a bakin sa har haka kuma tana fita da k'arfi ba kamar yadda ya saba magana ba.        "I'm sorry" ta furta kamar zatayi kuka tana kallon sa ya d'auke ido daga kanta yana kallon tagar iska na kad'a shi yana ji kamar ya dira mota ta buge shi kowa ma ya huta. Baya son yaga wani ya rab'i abinda yake so ko kad'an balle ace ma mace macen ma matar sa har wani banza zai rik'e mata kumatu a gaban sa kuma matar bata hana faruwar hakan ba balle ta d'auki mataki. Ganin yayi shiru amma da alama bai wuce ba Rauda tace, "bai san ina da aure ba beside bai san ni matar ka bace, d'auka yake ni Sister d'in kace shiyasa." "Ke kuma u can't tell him, just because u feel ashamed to tell him that I'm your husband right?" ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba har lokacin kallon tagar yake yi. Rauda tace, "kaine baka bada damar hakan ba sabida baka nuna musu ni matar ka bace kace ni Sister kace, waccan likitan ma a gaban ka take cemin sistern kan but baka tab'a ce mata I'm your wife ba, why ni zan fad'a musu?. In na fad'a karyata ni ma zasuyi but ban dace da zama hakan ba shiyasa kaima baka nuna musu ni ba sabida kar kaji kunya."     Banza yayi mata bai ko kalle ta ba balle ya amsa tagar sa yake kallo kawai ganin hakan ya saka tace, "I'm stand here to tell u akwai mission da ya saka ka aure ni amma badan kana sona ba kamar yadda kace, ni nasan akwai abinda kake nufi dani amma bawai kana sona bane. Banga wani sigh da zai tabbatar min da kana sona ba, kayi amfani da power da kake dashi ka d'auko ni daga gidan mu ka ajjiye ni a nan kana k'inyi min magana. For how kake tunanin zan d'auka kana kishin wani dan ya tab'a ni for god sake?" ta fad'a with full confidence babu tsoro a tare da ita duk da gaban ta yana fad'uwa. Kallon ta yayi ya cize bakin sa ya girgiza kai kafin ya nuna msta k'ofa yace, "Out!." Murmushi Rauda tayi tace, "Zan fita, but stop pretending like u feel jealousy about me, I know your target ka kawo ni ne kawai dan kayi humiliating d'ina not love" tana fad'a ta fita ta k'yale shi kamar baiji me tace ba sai bayan yaji ta kulle k'ofa zuciyar take angiza shi akan ya fad'a k'asa kawai mota ta take shi ya mutu tunda har zata iya tsayawa a gaban sa ta fad'a masa haka duk da tarin son da yake mata. Zantuttukan ta ne suke tayi masa amsa kuwa a kunnen sa ya toshe kunnen sa ya bar jikin windown ya dawo ya zauna a gefen gado idanun sa a kulle. Shi kansa yana jin haushin rashin maganar da bayayi mta amma ya zaiyi halittar sace a haka baya iya magana kamar yadda mutane sukeyi. Yana sonta ya sani yana kuma son kasancewa da ita a ko yaushe amma baya iya furta mata hakan ko yaushe bakin sa nauyi yake yi ga kuma jinin sarauta da yake yawo a jikin sa abun sai ya zama biyu ga halitta ga kuma gadon sarauta komai sai ya k'ara tunzura. 'Ba mayafi taje ta bud'ewa wani k'ofa, tayi masa dariya har yana rik'e kumatun ta maimakon ta baka hak'uri da kalamai masu dad'i matsayin ta na matar ka sai taso yi maka rashin kunya? Tama raina maka hankali dan kawai taga kana sonta ne shiyasa ta furta abinda ta fad'a amma badan so ba da ita in akace tayi baza ta iya ba" zuciyar sa ta fad'a masa ya koma da baya ya kwanta yana sauke numfashi haushin ta dana Khalifa yana sake ninkuwa a zuciyar sa musamman ma ita.       A fusace itama ta koma d'akin da take har k'afar ta nayi mata zafi sabida takun da take yi da k'arfi har ta manta ma tana da ciwo ta zauna a kan gado tana wuci ita kad'ai ita a dole anyi mata laifi.  "An tab'a mutum haka bazai yi magana ba amma ya dinga nuna min iko dan kawai ya d'auko ni da kud'i?. In badan halin Baba na son kud'i ba dashi ya isa azo wannan matsayin? Kud'in sa ko kyau da mulkin sa duka basa gabana kulawa nake buk'ata a gidan aurena ba wannan ba, dan kawai yasan ta yadda ya d'auko ni sai ya dinga min abinda yaga dama, to wallahi bai isa ba daidai nake dashi na; na daina yi masa shiru zan nuna masa asalin wacece Rauda." Yadda take bayani ita kad'ai sai ka d'auka ita da wani take jawabin sai masifa take ita kad'ai a lallai ba'a kyauta mata ba. Tsaki taja ta jawo wayar ta ta d'auka ta shiga wps ta bud'e novel tana karantawa ko zai d'ebe mata kewa. Tana ta karatun ta tana yi in ta tuna taja tsaki a haka har akayi sallar asuba bata farga ba sai kira ta gani ta wayar ta ta ajjiye da sauri ta shiga band'aki tayi alwala ta tayar da sallah kafin ayi asuba. Tana idar da asuba bacci ya d'auke ta mai nauyi. Bata tashi ba sai azahar tana mik'ewa zaune abinda ya faru jiya ne ya fad'o mata sai kuma jikin ta yayi sanyi tunawa dafa laifin ta d'in ne ba nasa ba tunda a gaban sa wani ya tab'a ta koda baya kishinta baya sonta tunda akwai aure dole zaiji babu dad'i. A haka ta shiga band'aki tayi wanka ta fito ta d'auki riga da wando na Pakistan cikin wanda Yaya Ummi ta siyo mata ta saka ta d'aura d'ankwalin a kanta sukayi mata kyau sosai. Gyara gadon da ta tashi tayi ta had'e komai waje guda tana niyar fita taji wayar ta tayi k'ara sai kuma ta katse, k'arasawa tayi taga number Yaya Ummi ce tayi mata flashing ta zauna a gefen gadon ta kira ta amma bata d'auka ba sai kawai ta kira Umma. Sun sha hira sosai Umma tana tayi mata fad'a akan zama da mijin ta da yadda yanayin sa yake na rashin magana tayi mata nasiha kamar kullum kafin suyi sallama. Ajjiye wayar tayi ta tayar da sallar azahar kafin ta idar ta taso ta fito falon gabanta na fad'uwa matuk'a. Baya falon sai dai an gyara shi tsaf sai khamshi air freshener na yake yi ga khamshin turaren sa da ya had'e dana d'akin ga sanyin a.c da ya garwaye da khamshin sai yake bada kalar khamshi mai sanyi daban.  Mamaki take yi wai waye yake gyara d'aki da falon haka ita dai tasan bashi bane ba amma ko yaushe sai taga wajan tsaf kamar ba'a zama a ciki.       Kan table ta kalla taga abincin ta gashi nan sai ta kalli d'akin da yake taga k'ofar a kulle ta zauna ta fara cin abincin da yake a wajan. Taci sosai tana rufe bowl d'in ya shigo falon hannun sa zube a aljihu cikin riga da wando y'an kanti da suka yi masa bala'in kyau kansa da hular sanyi kalar rigar ta lura baya son sanyi sosai. Gaban ta ya fad'i ta d'auke ido daga kansa ya k'araso inda take baiyi magana ba taga ya d'auki wata leda ya ballo magani ya mik'a mata, hannu ta mik'a ta karb'a ya kalli ruwan da tasha ta rage sai itama ta kalla ta d'auka ya juya zai bar wajan amma bata sha ba. Juyowa yayi ya kalle ta sai ta saka maganungunan a baki ta kora da ruwa sai taga ya juya ya fita daga d'akin gabad'aya ba tare da yace mata k'ala ba. K'irjita dafe domin ba k'aramin bugu yake mata ba ta kalli inda yabi taga baya nan tayi ajiyar zuciya tace, "Allah sarki ni na manta ma da maganin ashe shi bai manta ba jira yake na tashi." Sai kuma ta tab'e baki tace, "To ba dole yaso na warke ba tunda d'an uwan sane silar komai" ta fad'a tana bud'e na shafawar tana shafawa. Bayan ta gama ta mayar dasu leda ta tashi kenan taji ana buga k'ofar sai tayi jimmm gudun kar ta bud'e a samu matsala jin ana ta bugu ya saka ta nufar wajan ta bud'e k'ofar. Balarabe ta gani sanye da riga fara wando bak'i da broom machine a hannun sa cikin harshen larabci yake mata magana amma bata gane me yake nufi ba. Asad ta gani a bayan sa sai ya juya suna magana da larabci kafin ya kalle ta, irin kallon da yayi mata basai yace mata komai ba ta fahimta tayi baya shi kuma balaraben ya wuce zuwa d'akin ta daman nan ne bai gyara ba. Asad d'akin sa yayi niyar shiga sai ya kalle ta da hannu yayi mata alama da ta shiga yayi baya ta fara shiga sannan shima ya shiga ya k'arasa inda kayan sa suke yana dube-dube. Rauda sai yanzu ta fahimci wanda suke yin shara tana ta girgiza kai tana jinjina aikin kud'i wato in akan da kud'i komai ma yi maka za'ayi. Asad kuwa yana d'aukar abinda yake nema ya fita dan ta sake bashi haushi bama d'an kad'an ba. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito ta shiga d'akin ta ganshi tass kamar kar ka daina kallon sa komai yayi kyau ta shiga band'aki nan ka kamar ka zauna kaci abinci sabida yadda yayi kyau. Falon ta fito ta zauna ta rasa me zatayi sai kawai ta fara karatun alkur'ani a fili. Ta jima tana yi sauk'in karatu ya d'auke tayi da yawa sosai sai da akayi la'asar ta tashi tayi sallah ta dawo ta cigaba da karatun dan bata san abinda zatayi ba.        Tana cikin karatun ya shigo bata ji shigowar sa bama tana ta karatu ya zauna kusa da ita yana saurarar abinda take fad'a yana kallon ta jin yadda take karatun da k'warewa kana ji kasan ba y'ar koyo bace ta iya sosai haddar ta zauna sosai a kanta. Lumshe ido yayi yana jinta tana k'aruwa a zuciyar sa fushin da yake da ita yana raguwa a hankali ya samu kansa da yin murmushi yana kallon ta har lokacin bata san yana nan ba. Sai da taje k'arshen aya sannan ta tsaya ta kalli falon ta ganshi a zaune amma ba ita yake kallo ba. Tana so tayi masa magana amma tana jin tsoron hakan gudun kar yayi mata banza dan ba son hakan take yi ba sai taja bakin ta tayi shiru amma nasihar da Umma tayi mata ce take mata yawo a kanta. Wayar sace tayi k'ara ya duba ganin sunan mai kiran sai ya share bai d'auka ba ya cigaba da kallo waje d'aya kamar me neman wani abu a bangon da yake kallo. Tashi yayi ya shiga d'aki ba jimawa ya dawo da laptop a hannun sa  ya zauna yana dannawa a hankali. Tasowa tayi cikin dauriya ta dawo kusa dashi kan kujerar da yake ta zauna ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba tace, "kayi hak'uri in nayi maka laifi." Cak ya tsaya da danna laptop d'in da yake yi ya juyo ya kalle ta ya d'auke kansa ya cigaba da aikin sa ba tare da yace komai ba, Rauda tace, "Bana so nayi magana ayi min banza Allah ya sani" ta furta cikin nuna rashin jin daɗin ta ga hakan kamar zatayi masa kuka. Nan ma yayi mata banza bai kula ta ba ta yunk'ura zata tashi ya rik'o hannunta ta tsaya ba tare da ta juyo ba ya dawo da ita ta zauna kusa dashi har lokacin bai cika hannun ta ba, baice komai ba ya cigaba da aikin sa wayar sa ta sake yin k'ara ya kalla yaga number Egypt yaja k'aramin tsaki ya d'auka ya danna a speaker ba tare da yayi magana ba. Daga can b'angaren Muhibba ta sauke ajiyar zuciya tace, "finally u pick my call. Ni ko baza kayi min magana ba indai nasan kana jina hakan yayi min, ina Sister na?." Gaban Rauda ya fad'i jin abinda take cewa bata san lokacin da ta kashe wayar ba ya kalle ta itama ta kalle shi tace, "Haushin ta nake ji." Sai ya murmusa kad'an baice mata komai ba itama tayi shiru bata ce komai ba. Suna nan zaune hannun ta yana cikin nasa ya rik'e yana murza tafin hannun ta a hankali ba tare da yace mata komai ba. Rauda wani iri take ji a jikin ta taja hannun ta zata kwace ya kuma riƙewa yak'i bata damar hakan sai ta kalle shi tace, "Meyasa baka ce mata ni matar ka bace?." Bai daina abinda yake yi ba kusan sacan goma da yin maganar tata kana yace, "Meyasa baki ce ba ke?." Mamakin abinda yace tayi ta kalle shi tace, "fad'ar a kanka yake ai bani ba sabida ban santa ba." Murmushi ya kumayi bai ce komai ba itama bata kuma magana ba amma taji dad'i da taga yayi murmushi. Sallar magariba ce ta tashe shi yaje masallacin hotel d'in yayi sallah bayan ya idar ya dawo yayi wanka ya saka doguwar riga fara sai kyalli take ya d'auko key na mota da wayar sa ya fito falon.      A zaune ya ganta da alama tayi wanka dan yaga ba kayan d'azu ne a jikin ta ba doguwar riga ce mai mayafi a jikin ta ya kalle ta yace, "Let go" abinda yace kenan ya fita ta bishi da kallo tace, "ko ina zamu je oho, bama ku fita d'in ba ya kasa yi maka magana" ta fad'a tana yafa mayafin tabi bayan sa ya kulle k'ofar suka shiga elevator suka sauka. Basu wuce ko ina ba sai The Egyptian museum Cairo, inda komai na tarihi yake tun daga kan gawar fir'auna har zuwa kayan tarihin da ya faru ka k'asar misra akwai shi a wajan. Sun sha wayo kasancewar sa babba d'an masu mulki kuma wanda yayi karatu a k'asar labarawa shugaban mai kula da wajan ya san shi har inda gawar fir'auna take ta asali sai da suka je, ba'a nunawa mutane ta asalin sai wacce sukayi creating suka ajjiye manyan mutane ake nunawa ta asalin Asad da Rauda sun shiga cikin su. Ana ta nuna musu Rauda sai d'aukar hoto take hannun ta yana cikin nasa ya lura da tayi farin cikin zuwa wajan shiyasa shima yaji dad'in zuwan. Rauda mamakin yadda aka sanshi kawai take yi wani b'angaren na zuciyar taji farin cikin hakan wani b'angaren akasin sa. Bayan sun gama da nan suka wuce shogun Japanese Restaurant baban gidan abinci a k'asar Egypt cikin garin Cairo, suka zauna a teburan da aka tanada har lokacin murmushi take yi ya kalle ta suka had'a ido sai yayi murmushi shima sai ta kulle fuskar ta. Yanayin garin larabawan yana burge Rauda ganin dare yayi amma kamar ba dare ba mutane sai zirga-zirga suke abin su.       Abinda suka yi order aka kawo musu suka fara ci juyawar da Rauda zatayi taga Muhibba a bayan su sai murmushi take musu, k'aramin tsaki taja ta dawo da kallon ta gare shi ya kalle ta alamun meya faru tace, "bakuwar kace." Muhibba ya gani ta k'araso ta zauna kusa dashi tana kallon sa tace, "banyi niyar zuwa joint d'in nan ba ashe rabon zan ganka ya fito dani." Baice komai ba ta kalli Rauda tace,  "Sister ya kike?." A dakike Rauda ta amsa mata ta sake dawo da kallon ta ga Asad tace, "Handsome kayi min magana please." Nan ma baice komai ba hannun sa guda d'aya da yake kan table d'in ta d'ora nata a kai yana kallon ta shi kuma ya tsaya cak da cin abincin. Kallon hannun nasa yayi ya kalle ta bata d'auke hannun ta sai murmushi da take masa tace, "please talk." Asad ya kalli Rauda yaga itama shi take kallo ya kalli Muhibba ya janye hannun sa kana yace, "Depriving me abeg." "I can't Handsome, I love you so much, I want to be your wife forever. Please allow me to show u how much I love you abeg." Yatsun sa ya murza ya nuna Rauda da yatsa yana kallon Muhibba yace, "She's my wife, so respect yourself and stay away from me." A tare k'irjin mata biyu ya buga Muhibba ta kalli Rauda itama Raudan kallon ta take yi kafin Muhibba tayi murmushi tace, "Nooo Handsome you must be joking, nasan baka da aure don kana sona rabu dakai kar kayi min k'arya." Banza yayi mata ya girgiza kansa  ta kuka cewa, "ba wasa nake ba ina sonka, ka kalle ni ina da kyau da ilimi zan dace da rayuwar ka. Please and please ka taimake ni." "Ina girmama mace that's why ban dakatar dake ba tun farko. Rauda is my lovely wife not my sister, so ko k'yaleni bana son takura" ya fad'a da alama ya fusata yana kallonta dan ya gaji da bibiyar sa da take yi shiyasa yayi maganin abun. Kallon Rauda take yi da mamaki ganin abincin ta take ci duk da yanayin ta ya canja daka kalle ta zaka ga haka ta nuna ta da yatsa tace, "Wannan abar ce matar ka? Ka daina irin wannan wasan Handsome baka dace da yin k'arya ba." Ba wanda yayi mata magana ta sake kallon Rauda tace, "take a look at her how com wannan abin zata zama matar ka for god sake?." Ta sake kallon Rauda sai tayi dariya tace, "nasan kana min wasa ne amma wannan sai dai tazo a housemate d'inka amma ba matar kaba. See her face abeg; she look like mon....." dukan table d'in da yayi k'arfi ya hana ta k'arasawa sabida yadda ta tsorata ya kalle ta yana cize baki yana nuna ta da yatsa cikin fushi da b'acin rai amma baiyi magana ba. Rauda ce ta mik'e tsaye shima ya mik'e bai kalle ta ba yayi gaba Rauda ta kalle bayan ya wuce tace, "Ni da kike rainawa na fiki sau dubu a wajan sa, da a bashi ke gwara a bashi matattaciyar dabba mara motsi, ki duba yadda yanayin sa ya canja da kika fad'a min magana ko a nan zaki tabbatar da matsayin da nake dashi a wajan sa, ki nemi wani wannan kam nawa ne ni kad'ai" ta fad'a tana wucewa ta barta a zaune tana kallon su. Muhibba ta mik'e tsaye tace, "Noo that can't be possible! babu ta yadda za'ayi wannan abar ta zama matar handsome kamar prince. I'll surely find out the truth ko meye zan gane."       A mota ta same shi ta shiga motar ta zauna yaja motar suka bar wajan kana kallon sa kaga ransa a b'ace yake sosai har suka koma baiyi magana ba, suna shiga d'akin sa ya shiga itama ta wuce nata jikin ta duk yayi sanyi a haka tayi wanka tayi sallar i'sha da take kanta ta shirya cikin kayan bacci riga da wando masu tsantsi ta fito falon. Agogo ta kalla taga k'arfe d'aya na dare ta nufi d'akin sa jikin ta duk a sanyaye ba tare da tasan abinda zai kaita can d'in ba ta tura k'ofar ta hango shi a inda ta same shi jiya. A hankali take takawa ciki har tazo daf dashi cikin murya mai sanyi tace, "Prince!." Runtse ido yayi jin sunan yayi har cikin bargon sa bai juyo ba bai kuma motsa ba ya dai yi ajiyar zuciya. Rauda tace, "ka fad'a min gaskiya, meyasa ka aure ni....?." A hankali ya juyo ya kalle ta ta d'ago masa kai tace, "ban dace dakai ba abinda likitan can ta fad'a gaskiya ne ban dace dakai ba da y'ar aikin ka na dace ba mata ba. Ina so nasan gaskiyar lamarin ko zan samu peace of mind sabida a zahiri ban dace da kai matsayin mata ba.  Meyasa ka aure ni?." Takowa yake a hankali yana kallon idanun ta itama kallon sa take duk da abinda take fani a idanun sa amma bata janye ido ba har yazo gab da ita yana kallon ta ya saka hannun sa duka biyun ya jawo ta jikin sa ya rungume ta tsam-tsam for the first time. [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *038.*              Yadda ya rik'e tsam a jikin sa a karona farko dukkan su sun tsinci kansu cikin bak'on yanayi mai wahalar fasarawa musamman zuciyoyin su da ta k'ara kaimi wajan gudu da bugu wanda basu tab'a riskar kansu a cikin yanayi irin sa ba. Gangar jikin su tayi sanyi ko wanne a cikin su ya kasa kwatar kansa daga wajan d'an uwan sa tafiyar wani abu suke ji a cikin fatar su yana zagaya har cikin gashin kansu. Ruwan soyayya suke ji ana kwararo musu daga sama tun daga kansu har Farcen k'afar su. Sun kwashi tsahon mintina biyar a haka ya manta k'afar Rauda har lokacin ba lafiya ne da ita ba tsayuwa mai tsaho tana sakawa ta sagewa ta fara yi mata ciwo, a daidai wannan lokacin k'afar ta rik'e ta d'aga ta sama ta furta, "k'afa ta." Yadda ta furta maganar a hankali har lokacin tana jikin sa ba k'aramin sabon yanayi ya sake jefa shi ba bai sake ba a haka yake tafiya da ita har kan gado ya zaunar da ita ya zauna gefen ta yana kallon ta idanun ta a rufe. Rana ta farko kenan da ya fara jin abinda yake ji akan wata mace shiyasa ya rud'e tsintar kansa da yayi a wani yanayi wanda ya kasance bak'o a wajan sa. Umarnin da zuciyar take bashi shi kawai yake bi hakan ya saka shi kafa mata idanu tare da rik'o hannun ta yana sake k'arewa fuskar ta kallo. A hankali ta bud'e idanun ta suka had'a ido ya saukar da nasa k'asa yana kallon hannun ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa sabon tunani ya d'arsu a ransa ya sake kallon ta ya sake d'auke kai alamun tunanin wani abu yake yi wanda yake son aiwatarwa amma kuma yana jiran umarnin zuciyar sa kafin ya tashi tsaye ya tasar da ita itama yace, "can we pray?." Kallon sa tayi yadda yayi maganar a hankali ta shige ta sosai ta tab'e baki ta d'aga masa kai alamun eh domin so take taga iya gudun ruwan sa kana ya bata amsar tambayar da tayi masa.        Sallah sukayi raka'a biyu kamar yadda addini da al'ada ta tanadarwa ma'aurata bayan sun idar ta tashi daga kan sallayar ta zauna a gefen gadon ta kalle shi muryar ta a sanyaye sosai tace, "baka bani amsa ta ba, ina so na sani domin nasan matsayina a wajan ka, duk da amsar a bayyane take amma ina so naji daga bakin ka zanfi amincewa." Tsam ya tashi ya d'auke sallayar ya ajjiye a mazaunin ta ya dawo kusa da ita ya zauna zuciyar sa na sake fad'a masa abinda zaiyi tana sake ingiza shi ga aikata abinda bai kawo shi a ransa kusa ba ya kalle ta yace, "meyasa kika tambaya?." "Ina so na sani na fad'a maka, ban dace dakai ba meyasa ka zab'e ni? Ban dace da rayuwar gidan ku ba meyasa ka d'auko ni? Ban dace da zama a cikin iyalan ku ba meyasa ka saka ni?. Ni ba kowa bace face k'ask'antacciya a cikin ku domin bazan had'a kaina daku ba ta ko ina kunyi min zarra wacce bazan kamo ku ba har abada. Sannan gani ni ba kyau gare ni ba sai......." d'uf bakin ta ya kulle sakamakon abu mai sanyi da khamshi tare da taushi da taji ya kulle mata bakin ta, ta zaro idanu waje ganin abinda take karantawa a novel take gani a American film da sauran finafinan k'asar waje ya faru a kanta. Cak numfashin ta ya fara k'ok'arin tsayawa jin abinda bata tab'a ji ba a cikin bakin ta yana yawo tamkar tafiyar maciji yana zaga ko wanne sak'o na cikin bakin ta yana tab'a duk wata halitta da Allah yayi a cikin sa. Shiru ya ratsa a wannan lokacin baka jin sautin komai a d'akin motsin kirki babu wanda yake yi a cikin su idanun su dukka a lumshe suna karb'ar bak'untar bak'on yanayin da yazo musu bazata ba tare da tsammanin zuwa sa ba. Dukkan su basu da nutsuwa wannan lokacin jikin su da zuciyar su tayi nisa cikin lokaci kad'an ba tare da sun shiryawa hakan musamman ga Rauda. Rauda bata farga ba taji sabon yanayi yana ratsa ko wanne sassa na halittar da Allah yayi a jikinta nan take jikin ta ya sake saki lokacin da ta tabbatar babu riga a jikinta, har lokacin bai cire bakin sa daga cikin nata ba sai ma tallafar kanta yayi da hannu guda d'aya yana cigaba da abinda yake yi zuciyar sa na sake k'arfafa guiwa.         Lokacin da hannun guda d'aya ya fara zagawa a kan fatar bayan ta sai da ta sauke b'oyeyayyiyar ajiyar zuciya jin hannun sa yana tab'a fatar bayan ta hakan ba k'aramin sake rud'a tunanin ta yayi ba, ba zato babu tsammani taji yana k'ok'arin kwantar da ita a kan gadon hankalin ta ya fara dawowa jikin ta ta yunk'ura cikin rashin k'arfin jiki zata tashi ya mayar da ita ta kwanta sai a lokacin ta sake tabbatar babu suttura a jikinta. Hasken d'akin taga ya kashe d'akin yayi duhu sosai daidai lokacin da ya cigaba da zagawa da hannun sa ko ina na jikinta ta sauke numfashi ta kulle idanun ta tana ji kamar ta kurma ihu sabida yanayin da take ji a jikin ta bana wasa bane. 'Kin sakar masa jikin ki yana niyar mallakar ki har abada ba tare da kin tabbatar da sonki da yake yi ba, ya gama abinda yane so dake k'arshe ya sake ki shikenan ya cuce ki ya mayar dake bazawara mai lasisi, baki da hankali ko?' Zuciyarta ta fad'a mata ta bud'e idanun ta tunawa da hakan tayi k'ok'arin kwace kanta a hannun sa amma ina ta makara a wannan lokacin babu wanda zai iya kwatar ta daga hannun sa domin yayi nisa baya jin kira kome zatayi a wannan lokacin tunda yayi niya sai dai ta jira ya kammala sannan ta aikata nata domin yadda yake jin zuciyar sa babu mai tsayar dashi a wannan lokacin. Ba zato babu tsammani ba tare da shiryawa hakan ba taji bak'on abu wanda bata tab'a jin irin sa ba tunda Allah ya kawo ta duniya yana shiga cikin jikin ta sai a sannan take jin muryar sa a hankali amma bazata tantance abinda yake cewa ba sabida ita kanta ba'a cikin hankalin nata take ba. (fan's kar ku manta fa Asad a cikin labarawa yake so akwai soyayya⛹‍♀️🤣😎) *After some minutes.*          Kuka take sosai wanda b'ata tab'a yi irin saba muryar ta har dashewa tayi sabida yadda take ware murya tana kukan sai ka d'auka iyayen ta ta rasa a lokaci guda. Tun bayan lafawar komai take wannan kukan har ta lallab'a tayi sallar asuba ta kwanta kuka take bata daina ba babu kuma niyar tsayawar tasa. Bawai kukan ciwon da take ji bane kukan tausayin kanta takeyi domin bata da tabbacin matsayinta a zuciyar sa gashi ya gama mallakar jikinta gabad'aya a cikin lokaci kad'an ta zama shi ya zama ita, ko a yanzu ya sake ta sunan ta bazawara ta k'arfi da yaji. Abinda yake tab'a mata zuciya take kuka kenan duk da tana jin ciwo a jikin ta ba kad'an ba amma bai dame ta ba dan tasan ciwon gado ne a wajan duk wata mace da takai mutuncin ta kan gadon mijinta, abin alfahari ne ciwon za'a kiran sa na alkhairi shiyasa bai dame ta sosai ba abinda ya dame ta matsayin ta a wajan sa. Asad tun yana rarrashin ta da kwayar idanun sa har ya zuba mata ido ya rasa abinda zaiyi mata gashi baya so yaji kukan nata ko kad'an amma kuma ya rasa me zaiyi. Kallon ta yake a cukwikuwiye cikin bargo sautin kukan ta kawai ake ji a d'akin ya runtse idanun sa yadda yake jin ta a ransa a wannan lokacin matsayin ta ya ninka na baya sau adadin da bai san iyakar su ba, yanayin da ya kasance da ita a lokacin da suka wuce ya saka shi sake bata wani babban matsayin da babu macen da take dashi a wajan sa, shiyasa kukan ta yake d'aga masa hankali gashi shi ba bakin magana sosai ba balle ya zauna ya fad'a mata kalaman da zasu kwantar mata da hankali. Jin kukan nata yayi yawa ya k'arasa kan gadon ya yaye bargon ds take ciki ya shiga ciki shima ya jawo ta jikinsa gabad'aya a kunnen ta yake furta, "Shiiiiii is okay please." Bata daina kukan ba sai ta kifa kanta a k'irjin sa tana cigaba da zubar da hawaye. Fatar jikinta yaji tayi zafi ya zare k'aramar rigar da ya saka a jikin sa yayi sallah ya had'e fatar jikin sa da tata kodan ta samu sauk'in zafin jikin nata, "I'm sorry Muwaddaty, ki daina kuka bana so naji ko kad'an!" Ya furta cikin sabuwar muryar da ya samo a lokacin yana shafa bayanta a hankali. Rage sautin kukan nata tayi sai kad'an-kad'an da take yi a k'irjin sa yana jin hawayen ta akan fatar jikin sa yana sauka ya sake cewa, "Kina so nayi kuka nima?." Bata motsa ba balle tayi magana hakan ya skaa shi yace, "So please ya isa, I'm sorry" ya sake fad'a mata a cikin kunnen ta yana matsa mata jikin ta a hankali. Yadda yake matsa mata jikinta sai take jin dad'in hakan domin tana buk'atar a matsa mata jikinta dan ko ina a sage yake kamar an mata dukan tsiya haka take ji. Lokaci kad'an bacci ya d'auketa kukan ya tsaya sai hawayen da yake fuskarta har lokacin, ya kalli fuskar ta ya saka harshen sa ya lashe hawayen fuskar ta ya mata kiss a goshi ya lumshe ido yana jin sa daban a kamar ba Asad na kwanakin baya ba. Sake matse ta yayi a jikin sa ya sake kallon fuskar ta ya sake mata kiss a lips d'inta yayi murmushi yana shafa kanta qaunar ta na sake yin nitso a cikin sa da zuciyar sa. *☆☆☆*           Haka kawai ta ta tashi da fad'uwar gaba da ta motsa sai Asad yazo mata ranta ta rasa dalilin faruwar hakan gashi gabad'aya kanta ya kulle ta rasa wanne irin tunani ma zatayi a kan abinda yake faruwa da ita taji dad'i. Waya ta d'auka ta kira shi a karo na babu adadi amma bata shiga ta cillar da wayar kan kujera tana dukan goshin ta cikin b'acin rai da takaicin rayuwar ta a wannan lokacin. Wayar ta sake d'auka ta kira Malamin ta ya d'auka da sallama ta amsa suka gaisa kana tace, "Malam aikin nan an gama shi kuwa?." Daga can b'angaren Malam yayi shiru bai bata amsa ba domin a zahirin gaskiya baiyi aikin da ta saka shi ba sabida rashin lafiyar da yayi fama da ita sai a yau yake da niyar yi amma sanin halin ta ya saka shi yace, "Kwarai ranki ya dad'e anyi aiki tun ranar da kika zo. Zancen da nake miki mun lalata komai babu macen da zai iya sani a wannan lokacin har sai mun karya shi." Mama tayi ajiyar zuciya cikin jin dad'i tace, "Naji dad'in hakan sosai ba kad'an ba, a cigaba da bincika min da zarar an samu damar da za'ayi aiki na biyu kawai ayi bana son b'ata lokaci ne ka sani." "In Allah ya amince za'a yi ranki ya dad'e." "Ka turo account number na saka maka na goro" tana fad'a ta yanke wayar tayi murmushi ko babu komai ta gama da wannan matsalar babu Asad babu sanin yarinyar da ta tsana matsayin y'a mace.        Hydar ne ya shigo d'akin da sallama ta amsa a ciki ba tare da ta kalle shi ba ya k'araso jikin sa a sanyaye ya zauna a k'asan ta yace, "Ban san laifin da na aikatawa mahaifiyata bata amsa sallama ta, hakan yana raunana min zuciya ina jin kamar na zubar da hawaye dan fushin Mama a gare ni ba k'aramin abu bane. Ina so Mama ta tuna bafa nine Asad ba akan me laifin sa zai shafe ni?." Mama ta kalle shi tace, "sabida bakin ku d'aya duk abind zai aikata ka sani, kaine kake bashi goyan baya akan duk abinda yake yi sabida kafi k'aunar sa a kaina. Hydar matuk'ar baka dawo min da Asad ba bazaka sake ganin farin cikina akan komai naka ba, nan gaba hatta magana sai ta daina had'a mu." Hankalin Hydar ya tashi yace, "ta yaya zan fifita a Asad a Mamana? Mamana itace komai nawa bani da wacce ta kaita ta wanne yanayi zanfi son Asad a kanta?." "Gashi a bayyane kafi son ya rayu da wacce na tsana a duniya, kafin son ya rayu da yarinyar da ta kalli cikin idanuna tace min sai ta auri d'ana koda zan mutu. Kuka munafurce ni kai da mahaifin ku kukayi abu ba tare da sani na ba sannan yanzu kazo kana cemin ba haka ba?." Yadda yaga ta fusata sosai hankalin sa sai ya kuma tashi ya durk'usa guiwa biyu a k'asa yace, "Ina neman afuwa ina rok'on Mama dan Allah ta yafe min, duk abinda mahaifiyata take tunani a kaina ba haka bane dan Allah ta daina fushi dani bana so naga ranta ya b'acia kaina" ya fad'a kamar zai zubar da hawaye. Ta kalle shi tace, "tashi tsaye Hydar" ba musu ya mike tace, "matuk'ar Asad bai dawo gidan nan ba wallahi baza ka sake ganin walwala ta ba, fushi kuma yanzu na fara yi da kai nan gaba zan iya sallama ka daga cikin y'ay'ana tunda abinda kake so kenan." Wara idanu yayi kamar zai zubar da hawaye yace, "Haba ya Mahaifiyata take fad'ar haka a kan d'anta Hydar? duk abinda ya faru ba yin Hydar bane umarnin Mai martaba ne babu abinda Hydar zai iya a kai, dan girman Allah ina rok'on Mama da ta yafe min." Tsaki taja ta kalle shi tace, "kanka ake ji kuma. Inda kasan abinda nake ji a zuciya ta baza ka aikata min abinda kayi ba Hydar, kaine kake bada goyan baya a koda yaushe badan kai ba da yanzu ba wannan maganar ake yi ba dan kaine silar had'uwar shi da yarinyar badan ka d'auki mota ka fita ba tare da sanina na ka buge ta da hakan bai faru ba. Kaine ka jawo komai ka kuma bada goyan baya a kan komai, ka tashi ka bani waje bana son ganin fuskar ka."    A hankali ya tashi tsaye daga durk'uso d'in da yayi yana kallon ta ita kuma ta kawar da fuskar ta gefe har zai fita tace, "Tsaya." Ya juyo da sauri har da murmushin sa ta kalle shi tace, "Kira min Asad da wayar ka." Hydar gaban sa yayi mugun fad'uwa ya kalle ta yace, "in na kira shi bata tafiya." "Gwada na gani." Ba musu ya d'auko wayar sa a aljihu ya fara neman number Asad a zuciyar sa yana ta jan salati ya kira, a speaker ya saka ta jima batayi magana ba kafin ta katse ta rubuta call ended. Ganin hakan sai yaji dad'i a zuciyar sa da hannu tayi masa alama da ya bata waje ya fita jikin sa gabad'aya a sanyaye yake amma b'angaren zuciyar sa yaji dad'in rashin samun wayar Asad. *☆☆☆*          Kuka take sosai cikin d'aga murya take fad'in, "Bazan jure ba Mum, bazan iya jurewa ba. Ke kika cusa min son Asad a zuciya ta meyasa yanzu kika kasa yi min komai game da hakan?. Yau kwana nawa da zancen auren nasa amma kin kasa komai a kai, zuciyata bazata jure ba Mum zata iya bugawa na mutu" ta k'arasa fad'a tana kifa kanta a cinyar Mum tana kuka sosai. Shafa kanta Mum take yi cikin sigar rarrashi da kwantar da hankali tace, "Haba Jidda ke kin san wahalar da aka sha kafin ta ambace ki matsayin wacce d'anta zai aura...? Ke kin san irin kud'in da na kashe kafin faruwar hakan? dak'yar aka sawo kanta ta ambace ki. Na san dole kina jin babu dad'i amma ya zamuyi? Ita kanta babar tasa kanta ya kulle sabida mai martaba da yake a tsakiya badan shi ba wallahi da yanzu ya yiwa yarinyar saki uku." Jidda tace, "yanzu shikenan ni sai dai na hak'ura ko?." "Haba Jidda, ai ko zan mutum a tafe wallahi sai kin mallaki Asad matsayin mijin ki; wannan alqawari nayi miki kuma zan cika miki shi da iznin Allah." "Allah yasa Mum, duk da jikina sai yake bani kamar bazan aure shi ba." Mum tace, "Kar ki kuma fad'a zaki aure shi ke kad'ai zai zauna da ita a matsayin matar sa bayan ke babu wata. Ki kwantar da hankalin ki komai ya kusa dawowa hannun mu nan bada jimawa ba, nan da wani lokaci kad'an Asad d'in kansa hannun ki zai dawo ba babar sa ba." Jidda ta goge idanun ta ta d'ago kanta tana murmushi tana kallon mahaifiyarta ta domin kalaman ta sun kwantar mata da hankali ba kad'an ba shiyasa take alfahari da ita. *☆☆☆☆* A b'angaren Hydar tunda ya bar wajan Mama jikin sa yake a sanyaye gani yake kamar bai kyauta mata ba goyan bayan auren Asad da yayi tunda bata son hakan matsayin ta na uwa kamar bai kyautu yayi mata haka ba. Hydar ya shafa kansa yana kallon wani waje daban yace, "Ina so ta daina fushi dani domin tafi kowa sona a duniya." Ya cize lips d'in sa yace, "Ta yaya zan dawo da Asad bayan yana tare da wacce yake so? Shima in nayi masa haka banyi adalci ba nafi kowa sanin waye shi, bashi da wanda yake so a duniya sama dani kodan na saka masa ya kamata nayi iya bakin k'ok'arina wajan ganin bai dawo yanzu ba." Yayi shiru kafin ya naushi hannun sa yace, "meya kamata nayi? Ya zama dole nayi wani abun kodan fushin Mama da yake a kaina, Yadda Mama bata son auren nan zata iya yi min baki akan cikar burin ta nasan babu abinda bazata iya ba balle babban burin ta da yafi ko wanne a duniya." Ya sauke numfashi ya shafa kansa yana cize baki yace, "Dole nayi wani abun!." _Tofa an shiga tsaka mai wuya._⛹‍♀️⛹‍♀️ [17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *039*             Bud'e idanun ta take yi wanda suka yi mata nauyi sabida kukan da tayi ba kad'an ba hakan ya haifar da nauyin idanun ta da kuma kunburi, Bud'e idon take a hankali kasancewar babu haske a inda take hakan ya taimakawa idanun nata wajan bud'ewa ba tare da wani abun ya kawo musu barazana ba.  K'arewa d'akin kallo take yi sautin agogo yana tashi a hankali, tik, tik, tik, hakan ya ja hankalin ta ga kai idanun nata kan agogon. Dafe kai tayi ganin lokacin sallar azahar har ya wuce ta rutse ido tana jin rad'ad'i a jikinta ga kanta da yake ciwo ga k'afar ta da take yi mata suka kad'an-kad'an. Yunk'urawa tayi ta mik'e zaune tana share goshin ta tana furzar da iska abubuwan da suka faru suna yi mata yawo a cikin kanta. Runtse ido tayi tunawa da abinda ya wakana tsakanin su ta cize baki ta d'aki gadon tana ji kamar ta d'auki ruwa ta wanke abinda ya faru ta daina tunawa ko zata daina jin abinda take ji a zuciyar ta amma hakan bazai yu ba. Idanun ta taji suna niyar kawo sabbin hawaye tayi aurin mayar dasu ta yaye bargon da ta rufa ta sauka daga kan gadon a hankali ta mik'e tsaye tana jin kamar ta kurma ihu sabida takaicin da take ji a zuciyar ta. A haka ta shiga band'aki ta watsa ruwan zafi a jikin ta ko zata ji dad'i ta gasa kanta sosai tayi alwala ta fito tana takawa a hankali sabida tana jin zafi tana daurewa ne kawai. K'arewa d'akin kallo sai kuma taja tsaki hawayen da take rik'ewa suka sakko mata towel d'in na jikin ta take takawa har taje bakin k'ofa ta bud'e ta fito falon. Babu kowa a falon ta wuce zuwa d'akin ta ta shiga yana nan yadda ta barshi ta saka kaya har lokacin kuka take bayan ta gama ta tayar da sallah har ta idar hawaye bai daina zuba daga idanun ta ba ta kwanta a kan sallayar tana cigaba da kuka. Taji motsin bud'e k'ofar amma bata motsa ba sabida haushin sa take ji bata so ta ganshi ko kad'an hakan ya saka tayi kamar bata ji shi ba.  A hankali ya k'araso inda take kwance yana jiyo sautin kukan ta ta cikin hijjabin da yake jikin ta wanda ta b'oye kanta a ciki ya durk'usa ya saka hannayen sa duka biyun ya d'ago ta zaune tayi luuuu zata koma ya rik'o ta yayi mata garkuwa da jikin sa ya zauna shima kamar yadda ta zauna gabad'aya tana kwance a jikin sa.        Shiru ya sake ratsa tsakanin su bata daina kuka ba shima kuma baice komai ba ya zubawa waje d'aya ido yana kallo amma ya rasa ta inda zai fara fad'a mata abinda yake zuciyar sa game da ita, ya rasa ta hanyar da zai bi ya fayyace mata sirrin zuciyar sa da yadda yake jinta a jikin sa ko zata fahimta ta daina wannan kukan. Ya kalle ta sai ya d'ago da kanta yaga kukan take har lokacin bakin ta har rawa yake yi ya matsa da fuskar sa kusa da tata yana kallon ta, tana jin hakan a zuciyar ta tasan kallon ta yake amma duk da hakan bai hana ta daina zubar da hawaye ba. A hankali ya had'e bakin sa da nata yana kissing a hankali a nutse babu tashin hankali, hawayen bai daina zuba ba hakan ya saka shi rik'e kanta da hannun sa guda biyu yana kissing yana kallon fuskar ta yana so yaga hawayen sun daina sakkowa. Bai d'auki lokaci mai tsaho ba cak kukan nata ya tsaya sai hawayen da suke kan fuskar ta tayi shiru tana fuskantar yanayin da ya kawo mata ziyara a karo na biyu, wani abu take ji a jikinta wanda baza ta iya jure masa ba hakan ya saka taja baya duk da ya rik'e kanta amma hakan bai tana ta zare bakin ta daga cikin nasa ba. Bai hana ta ba daman abinda yake so ta daina ta daina d'in ta kifa kanta a guiwar ta haka kawaj take jin wani abu mai kama da kunya yana zaga jikinta lokaci d'aya, tashi yayi ya fita jim kad'an ya dawo ya same ta a yadda take ya ajjiye abinda ya shigo dashi ya a inda ya tashi zauna yace, "kici abinci then Kisha magani." K'in d'ago kanta tayi ya saka hannu da niyar d'ago ta ta sake cusa kanta ciki sai ya k'yaleta ya jingina da gadon kamar yadda take yi ya zaro hannun ta d'aya daga cikin jikin ta ya rik'e yace, "I'm sorry!." Yadda ya furta kalmar sorry d'in ji tayi kamar an soka mata wani abu a zuciyar ta taja numfashi amma bata d'ago ba ya kuma cewa, "Amsar tambayar ki ta jiya ita na baki a jiyan, in baki amince u can cheek your phone, but kici abinci" ya fad'a a sanyaye yana jawo abincin ya d'auki tea d'in da ya had'a mata yana jiran ta d'ago kanta. Bata d'ago ba har lokacin ya zuba mata ido yana kallo jin shiru babu motsin sa sai ta d'auka baya wajan ta d'ago a hankali sai suka had'a ido ta firgita zata mayar da kanta yayi saurin rik'e kan nata yace, "Please" ya furta yana kai cup d'in bakin ta. Ido ta lumshe tak'i bud'e bakin shi kuma yak'i janye cup d'in, a hankali ta bud'e bakinta ya bata tea d'in ciki sai tayi saurin dawo dashi jin zafi hankalin sa ya tashi ya ajjiye na hannun sa yace, "I'm sorry ban yasan miki zafi ba, I hope bb damuwa?" Ya fad'a yana rik'o kanta ganin bakin ta a buɗe har lokacin sai ya sake mayar da bakin sa cikin nata duk dan kar taji zafin shayin. Mintina biyu ya sake kashewa kafin ya zame bakin sa ita kuma har lokacin idon ta yana kulle ya sake d'aukar tea d'in ya kai bakin ta ya bata tasha dan ya wuci. Sai da ta shanye tasss sannan ya ajjiye glass cup d'in ya mik'e tsaye.         Tashi yayi ya d'auko wayar ya ajjiye mata kusa da ita ya fita, tana jin rufe k'ofar sa tayi tsaki ta buɗe ido tace, "Iya abinda zai iya cemin kenan matsayina na wacce yayi disvirgin, ina so da k'auna a nan?. Allah ka bimin hakkina ba laifina bane laifin Baba ne badan shi ba da hakan bata faru ba" ta sake fad'a tana kuka sosai sai kuma taja wayar tata ta kunna nan tayi karo da notification ta danna taga godon message ta fara karantawa kamar haka.         _Heey Muwaddaty!. nayo miki wannan sak'on ne ba dan komai sai dan na bayyana miki the kind of love i have for you, and the reason why i have gotten married to you is because i love you muwaddaty believe me or not wannan shine gaskiyar abin dake cikin zuciyata,na aure ki ne dan ina sonki badan na wulak'anta ki ba, ban tab'a son wata y'a duniya kamar yadda nake sonki ba, ina sonki tsakanin da Allah ba dan wani abu ba . It's my nature rashin yin magana Rauda bake kad'ai nake yiwa hakan ba, ina so na koya kodan na fad'a miki sirrin da yake raina game dake but a duk lokacin dana shirya wa hakan sai naji na kasa, ina so ki sani d'an adam baya iya canja halittar Allah ne yaso ya ganni a haka nima bawai yin kaina bane. Kince you don't deserve to be my wife which i don't no what makes you think of that, that's why na nuna miki ke kad'ai na amince da ita ta zama matata kuma ta san sirrina, ke ce mace ta farko dana tab'a having sex da ita. Nasan wannan kad'a ya isa tabbatar miki dake nake so na zauna bada wata ba, inda ace bana sonki bazan taba bari hakan ta kasance a tsakanin mu ba Raudaaa. I'll never forget what happened between us Muwaddaty kin bani abu mafi qima da daraja wanda ni Asad bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata ta duniya, kece mace ta farko dana fara sani kamar yadda yake a wajan ki Nina mutum na farko da kika fara sani, you mean everything to me Muwaddaty zan iya yin komai because of you. Please muwaddaty i want you to stop thinking that i don't love, because it hurt me a lot. You're the first and last da zan so a rayuwata ina so ki sanya wannan acikin zuciyar ki._         Wani irin yammm take ji a jikin ta hawayen idanun ta sun tsaya cak hannun ta na rawa ta sake yin scrolling ta sake ganin another one ta cigaba da karantawa, _Ko wacce mace at her first night tana samun kalamai masu dad'i da kwantar da hankali but ta bangare na ba wannan because of my nature. A jiya Muwaddaty na zubar da hawaye najin haushin yanayina for the first time a rayuwata, ina sona nuna miki how much i care and how much i love you . I'm really sorry; na rashin Nuna kulawar da banyi ba akan, i promise to always be by your side duk runtse duk wuya, Sabida son da nake miki Muwaddaty I'm ready to face anythings for the sake of your love. You're my world wanda kaf duniyar nan ban tab'a jin wata a raina kamar ki ba, bazan barki ba in sha Allah muna tare ._ Bata san ta mik'e tsaye ba sabida zafafan kalaman da suke cikin rubutun sa sun saka ta mik'e bata sani ba, ba'a tab'a fad'a mata kalamai irin su ba tunda Allah ya kawo ta duniya hakan ya saka jikinta yake tsuma tana jin wani irin abu a jikin ta, sake scrolling tayi ta sake ganin cigaba,        _Yeah ni d'an sarki ne ta ko ina but kema matar d'an sarki ce ki daina tuna komai ni na ganki nace ina sonki. Muwaddaty da ban same ki ba ban san iya adadin abinda zai same ni ba ina jurewa ne kawai like i don't care about you amma deep inside my heart a ko yaushe kice maqale acikin ta. Finally na fad'a miki abinda yake raina i hope zaki goge duk wani tunani da kike a ranki ki zauna dani da zuciya d'aya, ina ji a jikina i can't live without u so please ki amince dani kar wani abun ya raba mu dake in hakan ya kasance ban san ya zanyi ba Muwaddaty. Thanks you for gave me the most important thing in your life, I really appreciate. And nayi alqwarin babu abinda zai faru ina tare dake bazan rabu dake ba ina fatan zaki amince. Kici abinci Kisha magani badan ni ba saboda Allah. I love u so much._       Hawaye taji suna is sakkowa daga idanun ta wanda ta rasa dalilin zuwan su a lokacin da taje k'arshe message d'in nata, tana d'ago ido ta ganshi a tsaye yana kallon ta da murmushi a fuskar sa itama kallon sa take yi ta motsa sai yaga ta runtse ido ya k'araso da sauri ya bata hut hug ya rik'e ta very tight yana sauke sigh idanun sa a kulle. Kunnen ta ya kai bakin sa in low voice yace, "I love you Muwaddaty!." Sai da ta zabura yayi saurin sake rik'e ta kam a jikin sa itama ta rik'e shi tana jin wani abu na shiga jikin ta game dashi ya sake shiga jikin sa tana sauke numfashi. Sun jima a haka kafin ya sassauta rikon da yayi mata ya d'ago da ita ya kalli face d'in ta su had'a ido tayi saurin kai idanun ta k'asa yace, "do u love me? And kin amince zaki zauna dani a haka?, I can't talk too much" ya fad'a yana fesa mata numfashi a fuskar ta ta lumshe ido ta sake mayar da kanta k'irjin sa ya kuma rungume ta tsam. Jikin ta yaji da zafi sosai ya d'ago ta ya k'arasar da ita kan gado ya zaunar da ita ya d'auki abincin a cikin bowl ya fara bata tana ci a hankali, kawar da kai tayi tak'i cin abinci ya kalle ta alamun lafiya tace, "bakina babu dad'i." "Sorry" ya furta yana cigaba da bata har taci rabin chips d'in ya ajjiye ya bata magani tasha ya sakko k'afar ta ya bud'e cream d'in maganin ta yana shafa mata a hankali yadda zata ji dad'in hakan. Kallon sa kawai take yi zuciyar ta tana fad'a mata wai daman haka ya iya kalamai masu dad'i? Daman haka yake sonta ko kuwa dai duka dad'in baki ne? Daman haka ya iya kula da mace ko kuma duk salon yaudara ne?. Ina mulkin yake yake bata abinci da kansa har yana shafa mata magani?. Bayan ya gama ya dawo kusa da ita ya zauna ta kalle shi sai ta d'auke kanta domin ita bawai ta gama amincewa dashi bane amma dai zata zuba ido taga iya gudun ruwan sa tunda babu mai bata amsar tambayoyin ta, yace, "Baki amsa ba." Ta sunkuyar da kanta k'asa tayi murmushi kad'an tace, "Kunyar ka nake ji." Murmushi taki yayi mai sauti ko tace dariya ma yana girgiza kai ya d'ago da kanta yace, "Meye kunya?." Kwace kanta tayi ta sake kawar da idon ta wani wajan daban ta lura shi kam baya jin abinda take ji. Ba tare da ta kalle shi ba tace, "in nace ina son ka zakayi da Maman ka? Kasan bata sona." Gaban sa yayi mugun fad'uwa kamar ta tsira masa allura ya d'auki wayar sa zai kirata amma sai ya kasa ya rasa me ma ya saka shi d'aukar wayar, ya dafe kansa ya d'ago ya kalli Rauda da take kallon sa yace, "wa nace zan kira ma?." "Mama" ta bashi amsa tana kallon sa yayi saurin mayar da hankalin sa kan wayar amma ya kuma mantawa. "Oh god!" Ya furta yana dafe kansa yayi shiru na wani lokaci kafin ya mik'a mata wayar yace, "kira min ita da sauri." Rauda mamaki ya kamata ta karb'i wayar tana dubawa taga sunan Mamana a jiki ta danna ta kira ta saka a speaker, kira d'aya biyu aka d'auka daga can b'angaren tace, "Asad d'ina yau kaine ka kira ni? Ashe zaka iya mantawa dani ka tafi ka barni ka zab'i wata mace a kaina Asad?. Meyasa zakayi min haka bayan kace min ka barta tunda bana so?, kenan kafi sonta dani Asad?" A jere take maganar burin ta ta isar b masa da sak'on dake ranta.       "Katse kiran Muwadda,disconnect it please!" Ya fad'a yana dafe kansa da duka hannayen sa Rauda ta bishi da kallo ganin ya gigice kamar ba shine yace a kira ba tace, "Prince Maman ce take magana fa." Cikin tsawa wacce bai tab'a yi mata ba yace, "I said disconnect!." Hannu na rawa Rauda ta katse kiran ta bishi da kallo hannun sa na rik'e da jijiyoyin kansa yana runtse ido yana bud'ewa. Me yake faruwa? Ta tambayi kanta tana kallon sa cikin mamakin canjawar sa lokaci guda sai kuma taga yana sauke numfashi a hankali yana komawa normal kamar bashi ba. Had'a ido sukayi da Rauda bayan ya dawo daidai ya sake kulle idanun sa ya sake kallon ta kana yace, "kina buk'atar hutu Muwaddaty, ki kwanta" ya fad'a yana kallon ta ta kalli agogo tace, "lokacin sallah yayi." Baice komai ba ya tashi har zai fita sai ya dawo ya tsuguna a gabanta ya tab'a wuyan ta yaji babu zafin sosai ya tab'a jijiyoyin kanta yaji suna harbawa alamun ciwon kai ya kalli cikin idon ta yace,"kanki yana ciwo." Rauda ta sauke ido k'asa tace, "Na sha magani zai daina." Shiru yayi ya d'an kulle ido na wani lokaci ya bud'e kafin yace, "Bb abinda yake damun ki?." Kai ta d'aga alamun eh ya mik'e ya rik'e goshin ta yayi mata kiss ya juya ya fita. Ta bishi da kallo tace, "ikon Allah! me yake faruwa dashi haka?." Babu mai bata amsa ta girgiza kai ta lallab'a ta tashi tayi alwala ta fito ta tayar da sallar la'asar. Tana idarwa kwanciya tayi bacci ya d'auke ta domin daman baccin take ji. *☆☆☆*         Lokacin da Asad ya datse kiran Mama duk taji abinda ya faru ba komai ya d'aga mata hankali ba sai jin muryar Rauda tana magana, zagaye take a d'aki hankalin a tashe jikin ta har rawa yake sabida tashin hankali da tsoro da ya mamaye mata zuciyar ta. _katse kiran Muwadda_ abinda taji ya fad'a ya fad'o mata gaban ta ya fad'i ta maimaita kalmar, "Muwadda! da hausa yana nufin Qauna" a bayyane tana jin zuciyar ta na buguwa kamar zata fito daga k'irjin ta. "Me hakan yake nufi kenan? Har sun samu kusancin da zai dinga kiran ta da wannan sunan ko me ake nufi?." Bazai yu ba wallail azim bazai yu ba!" Ta fad'a da d'aga murya tana d'aukar wayar hannun ta na rasa tana jin idanun ta yana kawo ruwa ganin kirikiri an raba ta da d'anta wanda take mutuwar so sama da komai. Malam ta dannawa waya ya d'auka kafin ma yyi magana tace, "Wai yarinyar nan wacece ita da baza'a kiya kashe ta ba?." Tana fad'ar hakan ya gano bakin zaren yace, "Ranki ya dad'e bawai baza'a iya ba za'a iya; kawai dai abin ne yana da wahala sabida tunda bata gari aiki kuma za'ayi mai kyau sai an samo wani abu nata kamar riga ko d'ankwali ko gashin kanta, kinga samun su zaiyi wahala shiyasa." Mama tace, "in aka samo ka tabbatar za'a kashe ta?." "Tabbas zamu zama silar barin ta duniya." "Za'a kawo maka zuwa dare a gobe nake so a aikata komai." "An gama ranki ya dad'e" tana fad'a ta yanke kiran ta kira layin Mum. Mum na d'auka kafin tayi magana tace, "Ta wacce hanya za'a bi a samo mana d'ankwalin kucakar can data asirce min d'ana?." Mum tayi shiru kafin tace, "abu ne mai wahala duk da baza'a rasa sauran kayan ta a gidan su ba amma shiga gidan a d'auko shine aiki." "Zai yu ko bazai yu ba?" Mama ta fad'a a fusace. Mum tace, "Zai yu, ki bani daga nan zuwa dare" tana fad'ar hakan Mama ta yanke kiran ta koma gefe tana wuci.          B'angaren Mum tana katse kiran key ta d'auka na mota da hijjabi ta sauka k'asa har zata gota kitchen d'in ta sai taga y'ar aikinta ta juya tana aikin nama ta k'are mata kallo tace, "Safiya." Ta juyo tace, "Na'am Hajiya." "Baki saka pad bane naga kayan ki sun b'aci da jini?." Gaban Safiyan ya fad'i tasan Mum bata san k'azanta tace, "Wallahi ban sani bane Hajiya." Mum tayi tsaki tace, "dallah wuce ki bawa mutane waje, abincin in baki dafa ba kar ki dafa in kuma kin dafa ku cinye iya ku kije ki sake wanka ki shirya kanki then kiyi mana wani abincin." Safiya tace, "To Hajiya." Mum har ta wuce sai wani tunani ya fad'o mata ta dawo da baya tace, "Jeki ki saka ki canja rigar jikin kizo." Da sauri ta wuce Mum ta shiga kitchen d'in ta bud'e fridge ta d'auko kwalbar flavor ta k'arasa wajan naman ds take wanke ta d'aga naman taga jini ta tsiyaya a kwalbar tana rik'e dashi ta fito har Safiya ta fito ta kalle ta tace, "kifa shirya kar ki b'ata min mota." "Na shirya" ta furta a sanyaye Mum tayi gaba ta bita a baya suka shiga mota suka fita. Tafiya suke har suka zo daf da gidan su Rauda daga can nesa ta tsaya ta kalle ta tace, "Karb'i wannan ki shafa a hijjabin ki ta baya." Karb'a tayi ta juyo da hijjabin tayi yadda tace ta kalle ta tace, "ki fita ki shiga gidan nan b'angaren haggu ki gaishe su kice dan Allah zaki gyara kanki ne kina hanya yazo miki baki sani ba, in sun baki hijjabi ko wani abun ki karb'a ki tawo ina nan ina jiran ki. In kika yi aiki mai kyau har suka baki kina da kyauta." Da to ta masa ta fita ta nufi cikin gidan Mum ta bita da kallo ganin yadda hijjab d'in ya lalace sai ka d'auka da gaske jinin ne. Da sallama ta shiga b'angaren Umma tana zaune ita kad'ai Umma ta amsa Safiya ta durk'usa tace, "Ina wuni Hajiya." Umma ta murmusa tace, "lafiya lau." "Taimako na shigo nema Hajiya, ina hanya ne naji zubar bak'on wata na ba tare da na shirya ba duk ya b'ata shine na shigo na gyara kaina in da hali." Umma tace, "Ayya, muje na kai ki band'aki" ta fad'a tana yin gaba tana binta a baya har d'akin su Rauda ta shigar da ita tace, "Ga band'aki nan ki shiga." "Na gode Allah ya saka da alkhairi" Umma ta amsa da amin ta fita. Kamar gaske Safiya ta shiga band'aki ta jika hijjabin jalaf duk a son ganin ta burge uwar d'akin ta ta fito ta saka shi a haka a wannan lokacin Umma ta shigo ganin haka ya saka tace, "Haba ke kuwa y'ar nan ina ke ina saka hijjabi mai danshi haka? Cire gana y'ata da bata nan kiyi amfani dashi yafi duhu koda wani abun ya zuba a jikin sa ma babu lallai a gane" ta fad'a tana bata maroon d'in hijjabi wanda tsahon sa ya wuce guiwa. Safiya ta karb'a tana godiya tace, "Allah ya saka da alkhairi Hajiya ya biya ki. Zan dawo da hijjabin da na koma gida in sha Allah." "Amin. Kar ki damu ki rik'e ma kema ai kamar y'ata kike. Ya sunan ki?." "Allah ya saka da alkhairi. Suna na Safiya." Umma tace, "Ashe kakata ce shiyasa kike tsohuwa." Safiya tayi dariya daga nan sukayi sallama Safiya ta fito ta nufi motar Mum. Tunda Mum ta hango ta da sabon hijjabin tayi ajiyar zuciya cikin farin ciki take kallon ta har ta shiga motar ta cire ta mik'awa Mum tace, "ga wannan ta bani tace na y'ar tane da bata nan." Mum tayi dariya ta karb'a ita kuma ta zauna babu hijjabin tace, "na gode Safiya, naji dad'in abinda kika yi min muna komawa gida zan baki kyauta ta ban mamaki." Safiya taji dad'i ta dinga murmushi a haka suka koma gida ta sauke Safiya ta sake buga motar ta sai gidan Sarki. Mama na kashingid'e a falonta na ciki taga shigowar ta ta bita da kallo tace, "ya kika yo nan kuma bayan aikin da yake kanki?." Mum tayi dariya ta ware hijjab d'in tana nuna mata tace, "Har na kammala ai, kin sanni indai akace a kan abinda ya shafe kine ba wasa." Mama ta tashi zaune sosai tace, "ban fahimta ba me kike nufi?." "Har na saka an kawo min hijjabin ta." "Bana son wasa Sadiya." Mum tayi murmushi tana zama tace, "Wallahi ba wasa nake ba ranki ya dad'e wannan hijjabin tane." Mama ta kalleta ta kalli Hijjabin tace, "ta yaya har kin samo ko cikakken mintina talatin bamuyi da maganar ba?." Nan Mum ta warware mata komai Mama tayi dariya tace, "Shiyasa a koda yaushe nake sonki Sadiya, basirar ki bata yara bace." Mum tayi murmushi tace, "da zafi zafi ake dukan k'arfe." "Gaskiya ne. Yanzu za'a kaiwa malam shi kuma ya aiwatar da aiki a kawar da ita har lahira." "Shikenan magana ta k'are mu huta da tashin hankali" Mum ta fad'a da murmushi Maman ma murmushi take na farin ciki kafin tace, "Wa zan samu ya mik'a masa yanzun nan?." Mum tace, "meye amfanina ranki ya dad'e? Bara kiga" Ta fad'a tana d'aukar hijjabin ta fita da sauri Mama tayi shewar farin ciki maganin matsalar ta yazo kusa-kusa. *Hajiya Mama kenan*😊 [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *040.*           Tunda Asad ya fita daga d'akin da take bayan an yanke kiran sa da Mama bata kuma ganin sa ba har akayi sallar i'sha, bayan ta tashi daga bacci wanka ta kuma yi kamar yadda Yaya Ummi take yawan fad'a mata akan yawan yin wanka, sosai taji dad'i zazzab'in jikin ta ya sauka sai ciwon kai kad'an ta kuma shan magani tayi sallah ta zauna a d'akin ta kira y'an gidan su suka gaisa. Bayan ta gama wayar ta gaji da zaman d'akin hakan ya saka ta fito falon ta zauna tana kallon tv. Remote ta d'auka tana dubawa dan ba sanin kan TV tayi sosai ba duba da bata taso da ita a gidan su ba ta canja ta mayar mbc bollywood suna haska film d'in kalank. Film din ya burge ta ganin na sarauta ne kuma ba'a jima da farawa ba ta fara gani tana fahimtar wasu abubuwan kad'an a ciki. Jingina tayi da kujerar dan gabad'aya bata jin dad'in jikinta sakayau take jin ta kamar an cire wata garkuwar da take tokare ta a jikinta.       Film d'in ya d'auki hankalin ta ganin an yiwa yarinyar labarin auren dole an kaita gidan sarauta tana kuka bata so, ji tayi kamar itace jikinta yayi sanyi ta cigaba da kallon film d'in yadda mijin baya nuna mata wata kula sai matar sa hakan ya sake karya mata zuciya amma bata fasa kalla ba ta cigaba da kallon bayan tayi tagumi. Ba zato taji an cire tagumin da tayi ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido ta d'auke idon ta ya zauna a gefen ta ba tare da yace komai ba itama haka ta cigaba da kallon. Shiru ya ratsa tsakanin su babu wanda yace komai kafin ya bud'e abincin da yazo dashi ya tura mata pack d'in shinkafa da kaza da kuma ice cream da burger da roll d'in shawarma, kalla tayi ta d'auke kai tace, "Bana jin yunwa" ta furta tana cigaba da kallon ta ba tare da ta kalle shi ba. Pack d'in shinkafar ya bud'e ya d'auki spoon d'in ciki ya cika shi ya kai bakin ta, kallon sa tayi ya d'aga gira idanun sa a cikin nata sai ta sauke kai k'asa Allah ya sani bata son kallon idanun sa bari ma yanzu da take jin kunyar sa.        "Na k'oshi fa" ta fad'a da shagwab'a idanun ta a k'asa. Bai janye abincin ba ta sake kallon sa taga still ita yake kallo ta sauke k'aramin numfashi ta bud'e baki a hankali ya zuba mata a baki tana taunawa a hankali gabad'aya bata jin d'andano daman kuma ga abincin larabawa babu isashshen maggi a cikin sa. Dak'yar ta had'd'iye ya sake debowa ya sake kai bakin ta ta sake karb'a tana yamutsa fuska kwata-kwata abincin baiyi mata ba. A karo na uku kafin ya debo tace, "dan Allah ka bari wallahi bana jin dad'in sa baki na babu taste ga kaina ciwo yake" ta fad'a idanun ta na kawo hawaye ta mayar da kanta cinyar ta hawaye na sakko mata. "Ohh Muwaddat! Meye na kukan?" Ya fad'a a sanyaye yana kallonta ta tashi ta goge idanun ta tace, "Ba kaine ba nace na k'oshi kana sake bani, bana jin dad'in bakina" ta fad'a cikin shagwab'a. Ture pack d'in yayi alamun shikenan an bari. D'an shiru yayi kafin yace, "muje kiga Dr" ya fad'a yana niyar tashi tayi saurin rik'e hannun sa ya kalle ta tace, "Basai munje ba." Da kansa yayi mata alama da meyasa tace, "Bana so ne kawai, kuma naji sauk'i." Komawa yayi ya zauna na wani lokaci kafin ya saka hannun sa ya rik'e kanta yaji ba sosai yake harbawa ba ya dawo da hannun sa wuyan ta yaji babu zazzab'i a jikinta ya kalle ta yace, "What do u want? Fad'a min ko meye I will give it to you." Lumshe ido tayi hak'ik'a in yayi magana kome girman ka da ajin ka sai kaso ya sake maimaitawa sabida yadda maganar take fita daki-daki da wani salo ba hayaniya sai kwantar da hankali da saka nutsuwa a zuciyar mai sauraron ta musamman ita da zuciyar ta take da rauni a kansa, bud'e ido tayi ta saukar k'asa bata ce komai ba itama.        Kallon ta yayi kamar zai kuma magana sai ya fasa sai yaga ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko maganin ta ta dawo ta zauna, k'afar ta yake bi da kallo sai yaga kamar tafiyar ta ba daidai take yi ba hakan ya saka shi binta da kallon har ta zauna kana yace, "Are you okay?." Kai ta d'aga alamun eh kafin yace, "but bakya tafiya daidai ko k'afar ki na ciwo?." Sai gaban ta ya fad'i ta bata ce komai ba domin bata san me zata ce masa ba.  "Answer me." Rauda tasha maganinta bata kalle shi ba sai da ta shanye kamar zatayi kuka tace, "Babu komai." Yadda ya kafe ta da idanu ko kiftawa bayayi hakan ya bata tabbacin bai yadda ba ta kalle shi sai ta kwab'e fuska tana shirin yin kuka tace, "Babu komai, dan Allah ka bar kallona kunyar ka nake ji wallahi" ta fad'a tana sake mayar da kanta cinyar ta. Sai yayi murmushi amma baiyi magana ba ya k'yale ta kusan mintina biyar yaga ta cigaba da kallon ta amma bata kalle shi ba. "Kina jin zafin still?." "Oh my god!" Ta furta a bayyane sai kawai ta fashe da kuka. Hankalin sa ya tashi ya jawota jikin sa gabad'aya ta dawo kan cinyar sa yana so yace wani abun amma kukan da take yi ya hana shi magana. "Please!" Shine abinda ya furta kawai yana shafa bayanta a hankali. "Ni ka daina min maganar kunya nake ji." Murmushi yayi ya mata kiss a kumatu yace, "is okay, sorry." Nishad'i yake ji a zuciyar sa in ya ganta a gefen sa sai ya rasa me yake masa dad'i kamar yayi ta kallon ta haka yake ji hakan ya saka shi cigaba da kallon ta kafin yace, "kina son zama y'ar jarida still?." Sai ta d'ago ta kalle shi ganin ba ita yake kallo ba ta wara idanun ta waje kafin tace, "ta ya akayi kasan ina son zama y'ar jarida?." Baice komai bai kuma kalle ta ba sai kallon tv d'in shima da yake yi. Tace, "Ina da tantama daman ina so na tambaye ka tun ranar nan da naga katin magani na a d'akin ka. Kenan ranar da muka had'u ka d'auka? Kaine ka siya min magani kenan har ka biya bashin maganin da ake bina. Ya akayi kasan Baba yana son keke napep ka siya masa?, yama akayi kasan gidan mu?, meyasa ka b'oye kanka a lokacin?" Bata kallon sa take maganar dan bata so su had'a ido yana jinta amma kuma baiyi alamun da zata gane ma yaji ba balle ta saka ran zai amsa mata.         Shiru ya sake ratsawa a tsakanin su tana jiran amsa shi kuma bashi da alamar bata amsa sai ya murmusa kad'an har taji sautin murmushin nasa ta kalle shi sai taga ya d'auki waya yana dannawa alamun bazai bata amsa ba kenan. Rauda ta d'auke kai bata ce komai ba amma zuciyar ta cike take da son ya bata amsar tambayar ta hakan ya saka tace, "Ka amsa min please, a lokacin da hakan ta faru mun d'auka Anas ne ya bayar sabida shine kawai yake taimaka mana musamman a........" shiru tayi ta kalle shi taga kuwa kallon nata yake kamar yadda taji a jikinta bayan ya had'e fuskar sa waje d'aya kamar ba shine yake murmushi ba.         "Don't call his name again please" ya fad'a yana kallon ta. Kai ta sunkuyar tana mamakin yadda yake nuna yana kishin ta amma a bayyane ya kasa nuna mata soyayyar da take so, dan ita Allah ya sani macece da take so a nuna ana sonta a kula da ita kamar kwai. Shiru tayi bata kuma magana ba amma taci alwashin sai ya bata amsar tambayar ta ko yaushe ne. "I'm sorry" ta furta a tak'aice tana cigaba da kallon ta. Wayar sa tayi k'ara ya kalla yaga sunan Aliyu ya sauke numfashi a bayyane yace, "Aliyu!." Har ta katse bai d'auka ba aka kuma kira sai ya saka a speaker ya d'auka daga can b'angaren yace, "Hii Asad baka nema na ko?." Asad ya sauke numfashi yace, "how was your day?." "I'm fine, ina missing d'inka ne shiyasa na kira ka." Asad yayi murmushi yace, "thanks you." Aliyu yayi y'ar dariya yace, "kar ka damu. A gaida Madam" yana fad'a ya yanke wayar shima ya ajjiye tasa. Ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba amma sai taji yace, "What up?." Kai ta sunkuyar ya juyo yayi y'ar dariya amma baice komai ba. "Maganar ku ma tana iri d'aya da Aliyu, ta yaya ake gane ku?" Ta furta ba tare da ta kalle shi ba. Ya shafa fuskar sa ya lura akwai ta da magana a haka ma wai bata da lafiya ya cize baki kamar bazai magana ba. Kallon ta yayi suka had'a ido sai ya mik'a mata hannu ta saka nata a ciki ya dawo da ita jikin sa gabad'aya ya hade hancin su waje d'aya yana goga nasa a akan nata idanun sa a buɗe ita kuma nata a kulle. Wuyanta ya yiwa kiss sannan yace, "Akwai different between Aliyu and i." Har lokacin hancin sa yana kan nata bai d'ago ba a haka yake magana khamshin vanilla flavor d'in da yasha na ice cream yana dukan hancin ta. Fuskar ta ya rik'e yace, "open your eyes please." Kai ta girgiza tace, "I can't." Murmushi ya sake yi baice komai ba ya kwantar da ita a k'irjin sa ya mayar da hannun sa ya kulle ya lumshe idanun sa. Bugun zuciyar sa take ji a k'irjin ta ta saka hannu ta dafe saitin zuciyar sa taji muryar sa yace, "sabida ke take beating very fast." Ya d'ago ya kalle ta suka had'a ido ya wara ido yace, "ana ahibbaki." Tasan me kalmar take nufi da hausa ta sake mayar da kanta k'irjin sa tana ji kamar ita kad'ai ce mace a duniya. Kusan mintina goma suna haka har bacci yana neman d'aukar ta jinta a jikin sa taji ya d'ago ta ya zare agogon hannun sa ya nuna mata wani bak'in zane kamar ciwo ya zagaye tsintsiyar hannun sa yace, "wannan shine banbanci na da Aliyu, duk lokackn kika ga wannan it's me not Aliyu ko Mama bata san dashi a hannuna ba because...." Sai kuma ya dafe kansa tace, "Sorry." Shiru yayi na wasu sacanni kafin yace, "Because ban jima sosai da samun shi ba, ciwo ne na same shi a madina shine banbancin kawai." Kallon hannun nasa take sai zanen ya masa kyau a hannu kamar irin mutum ya karce d'in nan wajan ya warke tace, "But voice d'inka dashi yana da banbanci wani lokacin." Ya girgiza kai ya sake mayar da ita jikin sa yace, "In yaso zai magana kamar ni ko Mama bazata gane ba." Rauda tace, "Ikon Allah! Ban tab'a ganin masu kama da juna kamar ku ba." Ya sauke numfashi kusan mintina biyu kafin taji yace, "Even me." Daga nan bai sake magana ba tana jikin sa kuma bai sake ta. *After two days.* *Nigeria.* Rana d'aya aka tashi da rashin lafiyar Mai martaba sarki hankalin iyalan sa ya tashi domin lokaci d'aya jikin sa ya birkice yayi tsanani sosai. Kasancewar litinin ce ranar zaman fada ce da safe ko wanne mai rawani ya bayyana a fada an cika mak'il ana jiran isowar sa. Ba jimawa ya bayyana Hydar yana rik'e da hannun sa suna takawa a hankali, take kowa ya mik'e tsaye masu kirari suna fad'in, "Barka da fitowa Dawisu sarkin ado, barka da fitowa dubu jiran mutum d'aya, barka da zuwa fari mai farar aniya. Allah ya watsa mak'iyan ka, Allah ya k'aro lafiya ya sake ninko ta fiye da wacce muke rik'a. Kauce ga inuwar alkhairi nan ya tawo manya da yara na gudu don shigar ta, kai kad'ai ne wallahi, wallahi kai kad'ai muka sani bayan kai babu wani. Wane mutum balle aljan? Aljan da kasa in kazo waje kaucewa sabida magana ake ta saurata da mulki da kuma k'asaita!" Da k'arfin gaske yake fad'a ko tsayawa baya yi har aka kare mai martaba ya zauna Hydar ya koma gefen sa ya zauna a kan carpet. Kusan mintina biyar aka d'auka kafin liman ya bud'e taro da Addu'a mai margaba kawai ake jira yayi magana ya kalle su d'aya bayan d'aya yace, "Alhamdulillah, yau shekarar mu talatin har da wani abun akan karaga, muna yiwa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana." "Allah ya k'ara lafiya, yasa a gama da duniya lafiya. Ya jikan mai babban d'aki ya raya mana zuri'a!" Aka sake fad'a mai martaba ya amsa da amin kafin ya d'ora da fad'in, "Shekaru sun ja k'arfi ya k'are ga ciwo da muke fama dashi, bamu san gobe ba amma Allah zai iya yin ikon sa a koda yaushe. Kamar yadda na ambata a kwanakin baya zan bayar da karaga mulki ga Asad a lokacin kuma duk kun bada goyan bayan hakan, ina fatan har yanzu kuna kan ra'ayi irin nawa?." Kallon kallo aka shiga yi idanun waziri sukayo waje ya share gumin da ya fara tsatstsafo masa kowa ya d'aga kai alamun suna nan kan matsayin su mai martaba yace, "To ma sha Allah. Duba da shawara da mukayi da makusanta da kuma yanayin ciwon bana so a bar talawa cikin rashin shugaba mai lafiya dan haka, A yau litinin zan mik'a kujera ga Asad duk da baya nan zan bada rok'on kwarya ga kawun sa da ya dawo a mik'a masa abin sa koda bana raye." Jin an ambaci kawun sa Waziri ya fara washe baki jikin sa ya fara tsuma yace, "Allah ya k'ara maka lafiya duk abinda kace namu shine mubi." Mai martaba ya d'aga kai kana yace, "in akwai mai magana ina so ya fad'a mana a wannan mataki da muke kai na lokacin k'arshe a kan karaga." Kowa ya kalle shi duk sai kuma ya basu tausayi zuciyar kowa ta motsa san k'ira ya sake kwalla kirari yace, "Bamu da tacewa sai dai muce  Allah ya k'ara maka lafiya, sai dai muce Allah ya saka maka, sai dai muce Allah ya faranta ranka ya dad'e kamar yadda aka faranta mana. Hakika bamu da bakin godiya domin anyi mana abubuwan alkhairin da baza mu manta dasu ba,  badan an yanke hukunci ba da munce muje a haka bama so muyi rashin adalin shugaba. Ka gama lafiya dan Toron guiwa gaban ka alkhairi bayan ka alkhairi." Mai martaba ya murmusa kana yace, "Team makers ku shaida Mubarak Wambai kenan shine zai yi rikon kwarya kafin dawowar Asad." A take gaban mutum biyu ya buga Wambai ya kalli Waziri shima ya kalle shi da alamun tashin hankali k'arara a tare dashi. Wambai ya kalli mai martaba yaga bashi yake kallo ba jikin sa duk yayi sanyi domin bai shiryawa hakan ba kwata-kwata. Mai martaba ya kalli Hydar sai Hydar ya mik'e ya fita jim kad'an ya shigo bayan sa jakadiya ce da babban tray an rufe shi da farin kyalle ta k'araso ta ajjiye bayan tayi gaisuwa mai martaba ya mik'e tsaye kowa ya mik'e tsaye aka bud'e tray d'in mai martaba ya kalli Wambai ganin haka ya saka liman yace, " Allah yaja zamanin Wambai bismillah." Jikin sa a sake ya tashi ya zauna a kan kujerar akayi kabbara tare da buga bindiga mai martaba sarki mai murabus ya singing akan takardar resignation letter Wambai ya saka hannu aka sake buga bindiga. K'aramar kujera wacce take k'asa da wacce wambai yake kaj Sarki mai murabus ya zauna yana murmushin farin ciki ko babu komai zai bar duniya da yak'inin al'umma zasu samu shugaba na gari. A wajan aka gabatar da komai na nad'in sarautar kasancewar rok'on k'warya ce a nan aka gama komai sai Asad ya dawo a nan za'ayi gagarumin abubuwa. Kowa ya watse zuciyar su cike da jinjina adalci da tausayin na k'asa irin na Mai martaba Nasir bin Sa'ad sab'anin wasu da suka tashi kamar ana yi musu bindiga a zuciya sabida bak'in ciki da hassada.          Cikin lokaci kad'an labari ya shiga cikin gida Mama na zaune tana kallon tv ta hakimce hadimai suna k'asanta a zazaaune jakadiyar ta shigo a guje ta zube a gabanta tana fad'in, "Allah yaja zamanin ki, Allah ya k'ara miki lafiya. Addu'ar mu ta karb'u yau mai martaba yayi murabus ya d'ora Wambai akan karaga kafin dawowar Mai martaba sarki Asad." Mama ta gyara zama ta kalle ta a firgice tace, "Me kike cewa? Kin san bana son wasa da hankali ko?." "Ni wacece da zan yiwa fulani wasa? Da gaske nake ranki ya dad'e a gaban yallab'ai Hydar akayi komai." Mama ta daki kujera cikin dunbin takaici zatayi magana sai kuma ta kalle su tace, "Ku tashi ku bani waje." Jiki na rawa suka mik'e suka fita Mama ta dafe kanta tace, "meyasa ba'a jira ya dawo ba za'a yanke wannan hukuncin? Meyasa za'a bada rik'on kwarya?" Ta fad'a tana mik'ewa tsaye hankalin ta duka a tashe yake. Agogo ta kalla taja tsaki domin tasan yanzu yana tare da bak'i da babu abinda zai hana bata bayyana a gare shi ba yanzun nan. "Ya zamar maka dole Asad ka dawo a cikin kwanakin nan, ko ya bada dama ko bai bayar ba zan dawo da Asad ya dawo ya karb'i mulkin sa. Bazan lamunci wannan zaman rik'on ba komai zai iya faruwa" ta fad'a da sauri tana shiga d'aki jikin ta na rawa sosai. Cikin gida gabad'aya ya d'auka aka ta bushe-bushe da kid'a domin kowa yaji dad'in zab'in mai martaba dukka su biyun ba abin yarwa bane koda Wambai d'in ne zai d'ore da mulkin abin murna ne ga talakawan sa. Fulani Hajiya kuwa hankalin ta yafi na kowa tashi har rama tayi a lokaci guda cikin ta ya juya ta shiga band'aki har sau hud'u ta sha magani tana sauke numfashi zuciyar ta na bugawa kamar zata fito daga k'irjin ta. Kiran Waziri take jira amma shiru hankalin ta ya tashi ta rasa inda zata saka ranta taji dad'i domin ba haka suka so ba sun so a bawa Waziri rik'on kwaryar ba Wambai ba. Baza ta iya jurewa zaman ba zuciyar ta zata iya bugawa ta fita ta d'auki driver ita kad'ai ya kai ta inda suka saba had'uwa da Waziri da Aliyu. Kamar yadda ta saba ta shiga ta same su a zaune Waziri hankali tashe jikin sa na tsuma ta kalli Aliyu da yake tsaye tace, "Meyasa ba'a sanar dani akwai meeting ba badan nazo na da anyi babu ni kenan?." Waziri yaja tsaki a harzuk'e yace, "Amma dai kin san dole a had'u duba da abinda ya faru ko?." Sai kuma yayi shiru yana tari yana dukan zuciyar sa da take masa ciwo. Aliyu bin sa yake da kallo kafin yace, "Nayi mamakin yadda ka tayar da hankalin ka na d'auka baza ka damu ba ai." Waziri ya kalle shi a harzuk'e yace, "a bawa Wambai kujerar karaga kace bazan damu ba?, kasan burina a akan wannan kujerar?, kasan adadin kwanakin dana d'auka ina jiran wannan ranar?." Aliyu ya bishi da kallo sai yayi murmushi yace, "Ohh kenan duk abinda kake fad'amin ba gaskiya bane kanka kake yiwa yak'i bani ba?." Sai a sannan ya dawo hankalin sa ya dafe kai yana jin yaji a idanun sa kuka ma yake so yayi amma ya kasa ya cize bakin sa Aliyu ya murmusa bai maimaita maganar ba dan baya so ya gano ya fahimce shi ba tun yau ba yace, "Bai kamata ku d'aga hankalin ku ba mu jira dawowar Asad d'in, kun manta da cewa daman shi muke so yau karagar? Ko kun manta plan d'in ne?."       Waziri ya rausayar da kai yace, "Sai yanzu na tuna, amma kana ganin Mubarak zai bari Asad ya dawo k'asar nan?." Aliyu yace, "Akwai Mama fa, duk wahala duk runtsi sai ta dawo da Asad cikin kwanakin nan. Kar kayi mamaki nan da kwana biyu zaka iya ganin sa domin in akace Mama akan burin ta an gama magana." Fulani Hajiya tace, "Kana ganin kuma zaiyi saurin amincewa shi Asad d'in?." "Ai zance ya k'are tunda har an riga anyi komai." Waziri yace, "na k'agu, na matsu, na damu, na tsanantu naga wannan lokacin Aliyu." Ya murmusa ya mik'e tsaye ya zuba hannu a aljihu yace, "Kar ka damu lokacin yazo" ya fad'a yana fita daga d'akin zuciyar sa fess domin burin sa ya kusa cika. Yana fita Hajiya taja tsaki tace, "nemo mana master planer muna buk'atar ta yanzu domin komai yana neman lalacewa." Waya Waziri ya d'auka take sai ga kira ya shigo yace, "Y'ar hakal" ya fad'a yana d'aukar wayar daga can b'angaren tace, "Na rasa dame zan fara jaje zan muku ko kuma farin ciki zan taya kanmu, abinda muke so ya kusa faruwa amma ba haka muka so ba." Waziri yace, "Mafuta muke nema Master in har Asad ya karb'i mulkin nan na shiga tara bama uku ba, ga wannan zararren da kika saka muka kawo cikin mu yana da wayo sosai bana tunanin zai bar wata gab'a da zan kwace mulki a hannun sa." Tace, "Zaman Aliyu cikin ku kariya ce domin shine next target d'in mu tunda abinda yazo da haka. Ta dole zamu kwace mulkin ai ba ta laluma ba kudai yanzu kuyi addu'ar dawowar Asad da wuri da zarar ya shigo Nigeria komai ya k'are." "Amma kin manta aikin da mukayi dan mu tura shi wata k'asar? Yanzu kuma muce ya dawo bayan kin san k'arfin aikin" Hajiya Fulani ta fad'a. Master tayi dariya tace, "Asad zai dawo yana nan tafe zai dawo, komai ma zai karye kuma Rabi'a zatayi nasarar raba shi da matar sa zai kuma dawo ya auri wacce take so ya kuma karb'i mulkin, mu kuma wannan itace last chances d'in mu." Waziri yace, "Ina jin tsoron hakan fa." Tace, "ka k'arfafawa kanka guiwa a taswirar k'addarar ka akwai mulki kuma yana nan tafe." "Allah ya tabbatar Master, in hakan ta faru zanfi kowa murna." Murmushi tayi tace, "Shine lokacin bayyana ta a gare ku. Ku koma kuyi mubaya'a kar ku nuna akasin haka kuyi farin ciki ni kuma ina gefe ina taimaka muku" tana fad'a ta yanke wayar. Waziri ya kalli Hajiya yace, "naji dad'in bayanan ta domin kuwa na tsorota da yanayin wannan makakken Aliyun, kansa akwai daud'ar kwaya da giya zai iya aikata komai." Hajiya tace, "Shiyasa ban so ya shigo team d'in kwantan b'auna ba gabad'aya." "Ki barmu dashi mun fishi iya tsara film aiki zamu dashi kafin shima mu ture shi gefe." Aliyu da yake tsaye yana sauraron su ya murmusa tare da cize bakin sa ya kad'a kai ya tab'e baki ya bar wajan domin kuwa ko aljani bai isa ya gano shirin sa akan su ba sai shi kad'ai yasan abinda yake tsarawa kuma k'iris ya rage komai ya bayyana...... Tofa masarauta ta rikice. Yanzu aka fara wasan⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️ [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *041.*        A gaban Dr Asif suke a zaune yana duba k'afar Rauda a cikin wani inji da yake nuna ko wanne k'ashi na jiki. Bayan ya kammala ta sakko ta zauna a kujerar da take kallon ta Asad Dr ya dawo shima ya zauna ya kalli Asad cikin harshen larabci yace, "Asad komai ya dawo daidai k'afar ta babu sauran matsala ta warke gabad'aya." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa Dr ya kalli Rauda yace, "Congratulations Madam." Murmushi tayi tace, "Thanks." Had'a ido sukayi da Asad sai ya d'auke kai kafin ya tashi suyi sallama da Dr Asif su fito daga office d'in. Suna fitowa suka hango Muhibba tana nufo su Rauda ta d'aure fuska hannun ta da yake cikin nasa ta rik'e nasa sosai har ya kalle ta sai yaga abinda take kallo shima ya d'auke kansa yayi kamar bai gani ba. K'arewa musu kallo Muhibba take yi kafin ta tab'e baki ta k'araso tace, "Ban tab'a karo da couples wanda basu dace da juna ba sai wannan, koda yake maybe akwai manufar da ya saka ya auri wannan abar amma ba so ba" tana fad'a ta wuce su babu wanda ya tanka mata jiran elevator sukeyi suna tsaye. Elevator ya danna suka shiga suka sauka k'asa suka fita daga asibitin suka shiga mota, yayi niyar su d'an yi yawo but baya jin dad'in jikin sa suka koma hotel suna shiga ya cika hannun ta ya shiga d'aki itama bata damu ba ta wuce inda take. Yana shiga wayar sa tayi k'ara ya duba ganin sunan mahaifinsa ya saka shi zama ya nutsu sosai kana ya d'auka da sallama. Bayan sun gaisa daga can b'angaren yace, "Zaki nasan zaka samu labari abinda ya faru a nan Katagum, yau dai Allah ya nufa na sauka daga kan karaga na kuma tamk'ata a hannun kawun ka Mubarak shi kuma da zarar ka dawo Nigeria zai baka domin rik'on kwarya aka bashi kaine shugaba ba shi ba." Gaban Asad ya fad'i har sai da ya runtse idon sa ya sauke numfashi a hankali jin hakan mai martaba yace, "ka zauna har matar ka ta samu lafiya Asad, in ka gama komai da ya kaika sai ka dawo kayi abinda nace." Cikin murya mai sanyi da rawar murya yace, "Amma Abba....." ya dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Kayi min alqawari zaka dawo ka karb'i karagar mulkin katagum, kayi min alqawari zakayi k'okarin sassauta wannan dabi'ar taka ta rashin son magana babu ta yadda za'ayi shugaba ya kasance a haka shiyasa nake makaa addu'a a ko wanne lokaci, nasan halittar kace amma zaka iya k'okarin ganin ka d'an gyara wani abun kana shugaba kamata yayi ka zama mai magana akan komai in ka kasance haka na k'asa dakai ya kenan?. Kayi alqawari min zaka canja; kayi min alqawari kome zai biyo baya baza ka hak'ura da karb'ar mulkin nan ba. Zaki kayi min alqawari zaka tafiyar da shugabancin katagum fiye da yadda nake tafiyar dashi, bana jin ka ta b'angaren abubuwa da yawa nasan talakawan ka zasu ji dad'in mulkin ka ko mutuwa nayi nasan na bar su a hannu wanda zai kula dasu ya taimaka musu ya kuma jiqan su. Abu biyu nake ji daman a tare dakai mahaifiyar ka da kuma wannan dabi'ar nan taka ta rashin magana. Babar ka zatayi k'ok'arin ganin ta takwara ka kayi abinda bashi kake son yi ba shima kayi min alqawarin kome zata zo maka dashi indai ya sab'a tsarin ka kar ka amince mata." Mai martaba yayi shiru kafin ya cigaba da cewa, "kana saurarona Zaki?." Asad muryar sa tayi sanyi yace, "ina sauraron Mai martaba." Mai martaba ya cigaba da fad'in, "komai zaka dawo ka tarar a katagum kayi hak'uri ka jure masa ka fuskanci abinda yake gaban ka. Asad duk runtsi duk wahala karka bari mulkin katagum ya sub'uce maka duk hannun wanda ya fad'a ba kai ba masarautar da wanda suke k'arkashin ta gabad'aya ta lalace, za'a shiga hali mara dad'i a duk sanda mulkin ya bar hannun ka, kayi min alqawarin duk dana roka a wajan ka?." Asad yayi shiru yana tunani ta Ina zai fara gudanar da abin baya so?, ta Ina zai fara mulkar al'umma?, wanne irin sarki za'ayi?, kurma ko bebe?. "Na Amince Takawa, nayi yiwa mahaifina alqawari in sha Allah zanyi iya bakin k'ok'arina nayi abinda akace, ina rok'on mai martaba daya taya ni addu'a Allah ya bani ikon gudanar da komai cikin ilimi da nutsuwa" ya furta a hankali. Takawa yayi murmushi yace, "Allah yayi maka albarka Zaki, Allah ya kare ka daga sharrin duk mai nufin ka da sharri, ya baka ikon bawa mak'iyan ka mamaki wanda suke ganin baza ka iya gudanar da sarauta ba ka basu kunya. Ka cigaba da addu'a Asad akwai wanda suna nan suna yi maka mummanan aikin da baza ka kuma dawowa Nigeria ba, amma mu da Allah muka dogara ka cigaba da rok'on sa zai baka kariya a ko ina." Jin farin ciki a muryar mahaifin sa sai yaji sanyi a zuciyar sa shima yace, "Amin Takawa. Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana." "Amin Zaki, ina jiran dawowar ka nan da wasu kwanaki." Daga haka sukayi sallama ya yanke wayar Asad yayi tagumi yana tunanin ta inda zai fara.        Bud'e k'ofar da akayi bai saka ya kalle ta ba ta k'araso tana kallon sa ganin gabad'aya ya canja kamar bashi ba tace, "Prince Lafiya?." Sai sannan ya kalle ta ya rik'o hannun ta guda d'aya ya dawo da ita kusa dashi ya zaunar da  ita a akan cinyar sa ya d'ora kansa a wuyan ta d'umin wuyanta yana shiga jikin sa idanun sa kulle yana jan numfashi yana saukewa. Gabanta ya fad'i domin tun ranar da wani abun ya shiga tsakanin su bai sake koda rungume ta da wata niya ba ganin abinda ya faru a yanzu sai taji fad'uwar gaba bashi yadda yake sauke mata numfashi a wuyan ta jikinta sai yayi sanyi. "Baba ne yace kwana biyu baku gaisa ba" ta furta a hankali ba tare da ta kalle shi ba dan kar ma ya d'auka wani abun ne ya kawota. Sarai ya jita amma bazai amsa bane ya zaga da hannun sa cikin ta ya rik'e ya sake had'a ta da jikin sa zuciyar sa na gudu sosai yana buk'atar rarrashi a halin da yake ciki. Lup dup, lup dup, lup dup, haka take jin bugun zuciyar sa a jikin ta ta kalle shi taga idanun sa a kulle suke har lokacin fuskar sa ta canja alamun akwai abinda yake damun sa. Kam taji ya rungume ta a jikin sa kamar zai b'alla mata k'ashin baya kafin jikin sa ya fara rawa a hankali zazzab'i ya mamaye fatar jikin sa, zafin taji yana shiga har cikin jikin ta kalle shi gashi ya matse ta sosai ta kasa motsin kirki a jikin sa. A hankali taji ya sassuta mata rik'on ta tab'a wuyan sa tace, "Jikin ka da zafi prince" ta fad'a da kulawa tana kallon sa. Ya sake ta ita kuma bata tashi ba ta saka hannu ta tallafi hab'ar sa tana kallon idanun sa da suke a lumshe tace, "Me yake damun ka?." Bai magana ba bai kuma bud'e ido ba ta saka hannu ta shafi gashin fuskar sa sai ya bud'e idanun sa da suka koma jajaye ta wara ido waje tace, "me yake damun ka dan Allah?." A hankali ya ya dawo da fuskar sa kusa da tata ya had'a goshin sa da nata ya furta, "Bana so! bana so!."  Yadda bakin sa yake motsawa ya saka tace, "meye baka so?." A wuyan ta ya sake kifa kansa yana juya fuskar sa kafin ya tsotsar fatar wuyan ta da zafi-zafi, lumshe idanun ta tayi duk da tana jin zafi kad'an-kad'an a fatar ta tana jin sa bata da abinda zatayi ta hana shi sai daga baya ya d'ago kansa ya kalli idanun ta yace, "Bana so, bana so su raba mu dake, kiyi wani abun kar su rabu. Ina sonki Muwadda." ya fad'a a sanyaye tare da lumshe idanun sa yana ji kamar yayi kuka. Nan take taji gabanta ya fad'i jin abinda yace baya so a raba su tace, "Waye zai rabu mu? Meye baka so?, kayi min bayani pls." Bai amsa mata ba yayi shiru ta sake cewa, "jikinka da zafi sosai kana buk'atar san magani." Kamar zaiyi magana sai yayi shiru ta kasa gane shi ba magani yake so ba kwantar masa da hankali yake buk'atar ayi ba magana ba, da baya ya kwanta ya zama daga k'ugun sa zuwa kansa na kwance guiwyoyin sa suna yadda suke a tsaye har lokacin tana zaune a jikin sa. Ganin yak'i magana sai tayi niyar tashi ba zato taji ya jawo ta ta fad'a jikin sa gabad'aya ya saka hannun sa yana tattare rigar jikin ta. Motsawa tayi zata hana ya sake matse ta sosai a haka ya zare rigar ya saka hannun sa a bayan ta ya b'alle hook d'in brezia ta ta cire ta baya. Bai juyo da ita ba ya sake matse ta sosai a jikin sa yana sauke numfashi a hankali hannun sa na fatar bayan ta ya rik'e ta gam kamar za'a kwance masa ita. Bata kuma yunƙurin kwace kanta ba tayi lup a cikin sa tana jin yana yawo da hannun sa jikinta. A hankali take jin saukar numfashin sa alamun yayi bacci ta kalli fuskar sa ta tabbatar yayi baccin sai taji ya bata tausayi a zuciyar ta domin bata gane abinda ya jefa shi a cikin wannan yanayin ba lokaci d'aya. So take ta tashi amma ya hana hakan har lokacin tana rik'e a jikin sa kuma bacci yake yi a haka sai ta mayar da kanta ta kwanta a k'irjin sa itama baccin ya d'auke ta.       Sun jima suna bacci sai da akayi la'asar ta riga shi tashi ta samu ta zare jikinta bata tsaya mayar da rigar mata ta fita bata son ya farka ya ganta. Wanka tayi ta shirya cikin riga da wando wanda basu kamata sosai ba ta saka dogon hijjabi tayi sallar la'asar bayan ta idar tayi azkar. Yunwa take ji sosai hakan ya saka ta fito falon nan ta same shi ya fito amma kafin su kai ga had'uwa ya fita. Tasan abincin ya tafi d'aukowa ta koma ta zauna sai kuma ta tashi ta had'a tea tana sha domin yunwar ta d'an kwanta kafin ya dawo.        Door bell taji an danna tayi k'ara kamar baza ta tashi ba sai kuma ta tashi ta k'arasa ta bud'e tayi karo da kyakykyawar balarabiya hannun ta da tray tayi mata murmushi itama ta mayar mata da martani kafin ta mik'a mata tray ta karb'a ta koma itama ta shiga ciki ta tura k'ofar da k'afa ta k'arasa ta ajjiye akan table ta bud'e ta fara ci daman yunwa take ji sosai. Taci ta k'oshi tasha magani sai ta tuna da abinda Muhibba ta fad'a ya fad'o mata a zuciyar ta, tsaki taja tana so ta kawar da tunanin amma ta kasa maganar yawo take mata a kanta gashi daman kuma abinda yake zuciyar ta kenan. Tana wannan tunanin taji kiran magriba ta tashi tayi sallah ta karanta suratul waqi'a kana ta tashi ta shiga d'akinta tana kallon k'atuwar tagar glass d'in dake d'akin, 'Rauda akwai dalilin da Asad ya saka ya aure ki, babu soyayyar da zata saka ya bar mahaifiyar sa sabida ke sai dai in akwai wani abun a k'asa, to meye shi?' Numfashi ta fesar ta kama k'ugu tana kallon tagar zuciyarta ta cigaba da bata labari, 'wataƙila wani aikin asirin za'ayi dake shiyasa aka auro ki bayan haka baki da wani amfani a wajan sa. Amma kin manta kalaman da ya fad'a miki lokacin da ya karb'i budurcin ki?.' A bayyane tace, "Wannan dad'in baki ne kawai amma tabbas akwai wani abun a k'asa." Ranta taji gabad'aya ya b'aci damuwa ta mamaye mata zuciya tana nan tsaye har akayi i'sha ta bar wajan tayi sallah tare da shafa'i da wutur ta kuma tashi ta koma bakin tagar ta tana kallo tana tunanin mafita da inda zata nemo gaskiyar dalilin kawo ta k'asar matsayin matar sa.         Ta baya taji ya rungume ta ya d'ora kansa a wuyan ta yana kallon tagar shima ba tare da yayi magana ba ta daure bata kalle shi ba ta cigaba da kallon tagar ta domin bata so zuciyarta kamu da soyayyar sa kar hakan ya zama mata babbar illa nan gaba, "kinyi kyau!." Yarrrrr taji a jikin ta kasancewar a kunnen ta ya fad'a ta sauke numfashi ta lumshe idanun ta sai ga hawaye suna sakko mata daga idanun ta. Kallon ta yayi ya sake ta ya dawo yana fuskar ta ya rik'e fuskarta ta saukar da kai k'asa tana kuka ya d'ago da fuskar ta sai ta kulle idanun ta hawayen na cigaba da zuba taji ya saka hannu yana share mata hawayen amma baice komai ba. Kallon ta kawai yake yi zuciyar sa na bugawa da sauri ko kad'an baya so yaga tana kuka amma ya lura dabi'ar da ta d'auko yanzu kenan ko dan taga baya so ne oho. Zaiyi magana yaji tace, "meyasa ka aure ni ka kawo ni nan bayan kasan ni ba sa'ar auren ka bace? Sam ban amince da kana sona ba har kawo yanzu zuciyata tana fad'in min akwai dalilin da ya saka ka aure ni, ka fad'a min meyasa kafin zuciyata ta buga na mutu ka huta" ta fad'a tana sake fashewa da kuka mai sauti. Numfashi ya sake saukewa yana kallon dan bai san me zai kuma ce mata ta amince da sonta yake yi ba wani abu ba, ya fad'a mata abinda ya kamata amma ya lura har yanzu zuciyarta tana rawa akan kalaman sa.         Zata kuma magana ya toshe mata baki da hannun sa ya girgiza mata kai yana juya kwayar idanun sa a cikin nata ya lumshe ido ya bud'e ya saka d'aya hannun ya jawo ta ya had'a ta da jikin sa sosai har lokacin bai saki bakin ta ba, goshin sa ya had'a da nata goshin ya kulle idanun sa kamar yadda ta kulle nata har lokacin kuka take yi bata daina ba. Bakin sa ya sanya a cikin nata bayan ya cire hannun sa daga kai ya rik'e kanta da hannu guda yana tsotsar bakin ta cikin k'warewa da son kawar mata da damuwar zuciyar ta. K'okarin kwacewa take yayi mata rik'on da ta kasa ko motsi sai juye-juye take wanda hakan yake k'ara masa jin dad'in abinda yake yi dan hakan da take yi kamar tana taya shi ne. Jikin tane yayi sak ta daina juye-juyen ta tsaya cak tana jin abinda yake yi mata har cikin jikinta. Babu zato babu tsammani taji ya gama b'alle duka mallaban gaban rigar ta ta bud'e ta gaba ta sake yunk'urin kwacewa ya sake rik'e ta babu yadda ta iya haka ta sake kulle idanun ta tana jin yadda yake mata abinda hankalin ta bazai d'auka ba, k'afar ta bazata iya d'aukar ba a wannan lokacin hakan ya saka k'afar ta fara rawa ta koma jikin sa gabad'aya ya d'auke ta cak ya k'arasa kan gadon ya kwantar da ita yabi bayan ta shima ya kwanta yana cigaba yana yamutsa mata jikin ta. "Me kike so nace Muwadda? Kina so kiga zuciyata sannan ki amince da ina sonki?" Ya furta a daidai kunnenta amma kuma yak'i bata damar magana. Tayi shiru ta kasa magana sai bugun zuciya da ya addabe ta har kunnen ta take jin bugun ta. "I love you so muchhhhhh!" Yaja kalmar much d'in a kunnen ta daga nan bata sake jin wata magana ba. *Shud'ewar wasu mintina.*         Yadda fuskar sa ta jik'e da gumi sai ka d'auka ruwa aka watsa masa rawa jikinsa yake yi hak'oran sa suna had'uwa da juna, gab, gab, gab haka jikin sa yake rawa har gadon amsawa yake sabida jijjigar da yake yi. Kansa sarawa yake yi yana ji kamar zai fashe ya tarwatse kwakwalwarsa ta watse a k'asa, marar sa ciwo take masa wacce bata tab'a yi ba tunda Allah ya kawo shi duniya sai a wannan lokacin ya cure a cikin bargo gumi na zuba a jikin sa kamar ruwa. Hankalin Rauda in ya kai dubu ya tashi duk da abinda ya faru tsakanin su tana jin zafin jikinta har lokacin kuma babu dad'i kanta ciwo yake amma ta nemi nata ciwon ta rasa ganin yadda yake jijjiga kamar mai manyan aljanu. Tun lafawar komai yanayin sa ya fara canjawa kansa ya fara ciwo haka jikin sa bata yi aune ba ta ganshi a wannan yanayin. Towel ta shiga band'aki ta d'auko ta d'aura ta haura kan gadon ta zauna ta d'ago kansa ta d'ora a cinyar ta tana kuka tana fad'in, "Asad me ya same ka haka? Meye yake maka ciwo?." Baya iya magana sai rawa da jikinsa yake yi da sauri hankalin ta ya kuma tashi ta fara tofa masa addu'ar da tazo bakin ta a fuskar sa. Gani tayi hakan baya aiki ta dire daga kan gadon dirowar da tayi taji ciwo sosai a jikinta ta d'an tsaya tana hawaye kafin ta k'arasa inda alkur'anin ta yake har zata d'auka sai ta tuna daga ita har shi basu da tsarki sai ta fasa ta fita da sauri ba jimawa ta dawo da ruwa a kofi tana tofa ayatul kursi da a'uzubika bi kalmatullayi tammat min sharri ma kalaq. Sai da tayi k'afa bakwai sannan ta koma inda yake ta fara zuba masa a fuska taga ya zubara kamar mai aljanu ta sake zuba masa taji yaja numfashi amma har lokacin jikin sa rawa yake yi, ta saka masa kofin a baki dan yasha amma yak'i sha ta rasa yadda zatayi dabara ta fad'o mata ta zuba a bakin ta ta zame ta saka bakin ta a cikin nasa tana d'ura masa masa ruwan yana dawowa tak'i cirewa duk da yadda jikin sa yake rawa bai saka ta cire ba sai da taga ya had'd'iye sannan ta k'yale shi ta cigaba da zuba masa tana yin ko wacce addu'a da tazo bakin ta. A hankali taga rawar jikin da yake na raguwa kafin taga ya daina gabad'aya bacci ya d'auke shi. Ajiyar zuciya tayi har lokacin kansa na cinyar ta ta shafa fuskar sa da duk ta jik'e da ruwa, tuno abinda ya faru take yi yadda komai ya gudana a tsakanin su da yadda yake k'ok'arin furta mata kalma mai dad'i da kuma lokacin da abin ya tsaya can bayan ya janye jikin sa daga nata. Numfashi ta sauke ta kuma kallon sa lokaci d'aya take jin k'aunar sa na shiga cikin zuciyarta da kuma tausayin sa wanda bata san dalilin hakan ba. Idanunta ta share ta zame kansa daga cinyar ta tana kallon gadon duk a jike amma babu yadda zatayi baza ta iya d'aukar sa ba balle ta d'auke shi daga wajan ta canja masa wani wajan. Tashi tayi tana cize bakin ta domin Allah ya sani tana jin zafi ta rashin lafiyar sane ya saka take daurewa ta shiga band'aki ta gyara kanta sannan ta fito ta saka doguwar riga ta zauna a gefe tana kallon sa kanta nayi mata mugun ciwo. A gefe ta kwanta tana kallon fuskar sa ta d'ora hannu akan fuskar sa tana shafa fuskar aa hankali har bacci ya kwashe ta. *☆☆☆*            Tunda ta shiga take a zaune bata ce komai ba shima kuma baice ba domin in dai batayi magana ba bata isa yayi mata ba, yadda take ji da sarauta haka yake ji shi ya mulki dubban jama'a ita kuwa a k'arkashin sa take. Kusan mintina goma haka kafin ta motsa k'afar ta tace, "Takawa daman magana ce akan dawowar Asad tunda ka bayar da sarautar bai kamata ace anyi sarki biyy a lokaci kad'an ba." Baice mata komai ba ta sake sauke numfashi tace, "Shine nace mai zai hana ka saka shi ya dawo domin ya karb'i sarautar sa da wuri." Nan ma bai kula ba ta kalle shi taga bama ita yake kallo ba ta sake cewa, "A ganina dawowar sa da wuri shine abinda ya kamata ayi, da ya dawo sai ayi bikin sarautar sa da bikin sa da Jidda." Nan ma baiyi mata magana ba ta kalle shi tace, "Takawa magana nake yi fa." Nan ma bai kula ba ya cigaba da kallon labaran da ake yi. Kamar ta kurma ihu haka take ji amma ya zatayi ita take nema dole tayi shiru tana kallon sa ta kuma cewa, "Allah ya taimake ka magana nake yi." Sai a sannan ya kalle ta yace, "Ina jinki." Ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido ta sauke kai k'asa tace, "yaushe akayi masa umarnin dawowa?." "Ba yanzu ba." "Amma meyasa ranka ya dad'e?." "Haka nayi niya." Ta taune bakin ta tace, "Amma Takawa bai kamata ayi hakan ba tunda har ka bayar da kujerar nan me za'a jira kuma?." Ya sake kallon ta yace, "to Rabi'a fad'a min abinda ya kamata sai nayi." "Allah ya wuci zuciyar ka." "Mtswww." Sake kallon sa tayi zatayi magana yace, "Ina da iko da Asad kamar ke, ina da ikon na saka shi yayi abinda nake so kamar ke, dan haka ki k'yale ni sai sanda naga dama zai dawo." Hawaye ya taru a idanun ta tace, "Yanzu fa Asad ko nema na bayayi matar da ka aura masa ta juyar masa da hankali daga kaina gabad'aya, rabon da naji muryar Asad har na manta, wallahi ina so na ganshi kayi min izinin zuwa naje can koda bazan dawo bashi" ta fad'a hawaye yana sakko mata. "Ban bada dama ba Rabi'a, indai nine wanda yake auren ki ban baki umarnin barin k'asar nan ba, in kuma kina ganin kin isa bismillah." Mama tace, "nidai gaskiya bazan zuba ido ina ji ina gani a raba ni da d'ana ba, dole naje inda yake." "Indai ina da rai da lafiya baki isa fita daga Nigeria ba Rabi'a, ke ko garin nan baza ki bari ba sai na bada damar hakan." Cikin kuka tace, "Shikenan yanzu ka sallamawa wata banza shi ta raba ni dashi ta raba shi da k'asar sa?." Bai amsa mata ba ta mik'e tsaye tana goge idanun ta ta gyara zaman alk'yabbar  tace, "Kayi hak'uri ranka ya dad'e amma sai na dawo da d'ana garin nan, sai ya dawo ya karb'i mulkin sa." "Kayi duk abinda kika ga dama Rabi'a" abinda ya furta mata kenan ta fita zuciyar ta na sak'a mata hanyar da zata bi wajan ganin tayi abinda take so domin matuk'ar yana raye tabbas bazai bata damar yin abinda take so kamar yadda yace, dole ta d'auki mataki bazata zuba ido wata bak'a mai mummnar fuska ta kwace mata shi ba dole ya dawo ya cika mata burin ta na zama sarki ya kuma auri Jidda........ [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *042.*          Da ciwon kai ya tashi zaune idanun sa har lokacin a kulle ya jingina da fuskar gadon yana sauke numfashi a hankali, ya jima a haka kafin ya bud'e idanun yaga d'akin babu haske ko kad'an ya zura hannu gefen sa ya kunna switch d'in wutar nan take haske ya bayyana a wani sashe na d'akin. Agogo ya fara kalla yaga k'arfe uku da arba'in na dare ya kalli d'akin gabad'aya abinda ya faru yana dawo masa a hankali. Lokacin da ya gama tuna abinda ya faru sai ya kalli kansa yaga babu riga a jikin sa amma akwai short niker, tunawa yayi da lokacin da abin ya faru ai babu komai a jikin sa ya akayi yaga boxer a jikin sa?. Kansa ya dafe jin yadda ya kuma sarawa har lokacin marar sa a d'aure take ya daure ya tashi tsaye yayi saurin komawa ya zauna jin jiri na neman kayar dashi sai da ya d'an huta sannan ya tashi yana takawa a hankali ya fito zuwa falon, duhu shima falon bai kula da ita a akan kujera ba burinsa yaje ya fara tsarkake kansa ya wuce zuwa d'aki ya shiga tare da kullo k'ofa. Band'aki ya shiga kai tsaye yana dafe da kansa har lokacin yayi abinda zaiyi a ciki ya fito d'aure da towel a jikin sa yana goge kansa da guda d'aya, shiryawa yayi ya saka doguwar riga mai santsi ya shinfid'a sallaya ya kalli gabas ya tayar da sallah. Ya jima yana sallah har akayi kiran farko na asuba sannan ya zauna yana lazumi yana cin sassuci akan abinda yake ji a jikin sa. Bayan an idar da asuba ya cigaba da lazumin sa yayi azkar kamar yadda ya saba ya d'auki littafan sa yana dubawa duk da baya jin dad'in jikinsa. Rufe littafin yayi yana kallon wani waje daman yana sake tuno abinda ya faru har ya tsinci kansa a yanayin da bai tab'a shiga ba tunda yazo duniya, "kenan ita ta saka min shortniker?" Ya furta a bayyane yana d'an wara idanun sa yana jin wani iri a jikinsa. "Wanne irin yanayi ne wannan? Meya faru dani?" Ya fad'a yana dafe jijiyoyin kansa da suke sarawa masa ya ajiiye littafin ya tashi ya fito falon. A zaune ya same ta itama tana karatun alkur'ani da ka ba tare da alkur'ani a hannun ta ba tana bin ko wacce aya daki-daki tana lumshe idanun ta alamun karatun yayi mata dad'i. A kan kujera ya zauna yana kallon ta kafin yaga ta kai k'arshe sura ta bud'e idanun ta ta kalli gefen da yake, had'a ido sukayi taga ya fad'a lokaci guda jijiyoyin kansa a mike har lokacin sai tace, "Ina kwana, ya jikin?" Ta fad'a a tare tana kallon sa. Da hannu yayi mata alama da tazo inda yake ta mik'e a hankali tana takawa har taje gab dashi juwa ta kwashe ta ta fad'a kansa gabad'ayan ta dan ita ba k'arfi gare ta ba. Zafi yaji a jikinta alamun zazzab'i ya cize baki yana kallon idanun ta kafin ta sauke nata k'asa, muguwar soyayyar ta yake ji tana sake shiga ko ina na jikinsa, son kasancewa da ita har abada yana sake ninkuwa sau babu adadi a zuciyar sa. Baya son rabuwa da ita domin yana sonta kuma ita kad'ai ce sirrin sa tunda gashi itace ta suturta masa jikin sa lokacin da yake kwance babu lafiya, ko mahaifiyar sa tun yana yaro rabon da ta saka mishi suttura to me zai saka rabu da ita bayan wannan babban matsayin da ta samu wanda babu wacce ta same shi?. "Jikin ki akwai zafi" ya furta yana kallonta. Jikinta har rawa yake a hankali tace, "Nasha magani." Shiru yayi baiyi magana ba sai kallon ta da yake yi yana jin kamar ya mayar da ita jikin sa ya huta da kewar ta da yake ji a ko wanne lokaci a zuciyar sa. In akace zai so mace kamar yadda yake sonta zai karyata faruwar hakan amma da yake Allah shine mai tsara komai sai gashi yana jin sonta fiye da komai a duniya. A kan kujerar ya ajjiye ta ya mik'e ya k'arasa inda butar shayi take ya kunna nan da nan tayi zafi ya had'a tea a kofi ya dawo inda take ya zauna ya mik'a mata yace, "take it." Kunyar sa take ji ba kad'an ba hakan ya saka ta mik'a hannu zata karb'a shi ya d'auka ta rik'e sai ya saki sai kuwa ya d'an zuba a yatsan ta ta yarfe hannu shayin ya zube a wajan, "wayyo Allah" ta fad'a tana yarfe hannun ta yayi saurin karb'ar hannun nata ya saka yatsan a bakin sa kamar alawa. Shiru tayi tana kallon sa shima ita yake kallo kafin ya zame shi daga bakin sa ya kalli yatsan nata sai kuma ya saki hannun nata ya tashi ya shiga d'aki. Jim kad'an ya dawo da wani cream dogo a hannun sa ya bud'e ya shafa a yatsan nata ya kalle ta yace, "Sannu, ko muje asibiti?." Kai ta d'aga zai kuma tashi ta rik'o shi tace, "Bana jin zan iya shan tea ka barshi kaima baka da lafiya." Bai fasa tashin ba ya k'arasa fridge ya d'auko lafiyayyen yogurt mara sanyi sosai ya k'araso kusa da ita ya zauna ya bud'e ya nufi bakin ta dashi. Ba yadda ta iya haka ta bud'e baki ya zuba mata ta shanye ya sake bata ta sake shanyewa a haka sai da yaga ta sha da d'an yawa sannan ya k'yale ta ya d'auko magani ya bata tasha ya sake tab'a wuyan ta yaji har lokacin da zafi. "Jikin ki akwai zafi still, meyasa bakya son ganin Dr?." "Ai naji sauk'i bana son fita ne yanzu." Da kafad'ar sa ta tayar da kai shi kuma ya rik'e hannunta, babu mai magana a cikin su kowa yayi shiru tana kwance a jikin sa yaji saukar numfashin ta alamun tayi bacci ya kalle ta yayi mata kiss a goshi ya tashi ya d'auke ta ya kaita d'akin sa ya kwantar a kan gado ya zauna gefen ta yana shafa goshin ta a hankali cikin k'auna da soyayyar ta mai tarin yawa. *☆☆☆*            "Mai martaba sarki mai murabus ne babu lafiya, yanzu haka ance jikin sa ko motsi bayayi yana kwance kamar gawa" hadimai suke suna tafiya suna tattauna maganar cikin jimami. A wannan lokacin Hankalin Hydar a tashe yake sosai sai shige da fice yake so yake private get d'in Asad da za'a d'auke shi a kaishi Germany ya zama ready domin yanayin jikin sa ya gigita shi. Dukkan iyalan sa suna zagaye dashi har y'ay'an sa mata da suke gidajen mazajen su sun hallara suna zaune an saka shi a tsakiya kowa yayi shiru ana yi masa tofi masu kuka suna kuka masu jimami suna jimami.  Fari siririn mutum ne zaune kusa dashi sanye da lab court kana ganin sa zaka fahimci likita ne sabida yadda yake yake ta had'a magani da allura yana yi masa ko za'a samu ya motsa amma abin yaci tura sai idanu kawai da yake bin mutanen d'akin dashi. Bayan ya kammala ya kalle su yace, "I'm sorry to say, na kasa gane abinda yake damun sa tafiya Germany d'in kamar yadda Hydar ya fad'a is better." Mai martaba sarki mai rik'on kwarya yace, "Dr jiya fa lafiya lau yake meya same shi da sauri haka?." Dr yace, "Allah ya taimaki sarki bana ce ba, kuma ita k'addara tana samun mutum ne a ko wanne lokaci koda bai shirya ba." Cikin gamsuwa yace, "Haka ne. Allah ya bashi lafiya." Dukkan su suka amsa da amin Hydar ya shigo yace, "Komai ya zama ready zamu iya tafiya yanzu." Mai martaba sarki mai rik'on kwarya yace, "Hydar dani ya kamata ayi tafiyar nan." "A'a Ranka ya dad'e, in hakan ta faru bamu ciki masa burin sa na k'in son a bar masarauta babu shugaba ba. Ayi hak'uri mu fara yin gaba daga baya sai a samu damar zuwa." Ya girgiza kai alamun haka ne waziri zaiyi magana hydar ya riga shi yace, "Nida shi kawai zamu tafi a yanzu, Mama ko Hajiya ko Ammi inda wanda wacce zata biyo bayan shi sai tazo daga baya, yanzu kam emergency muke son tafiyar" ya fad'a yana d'aure fuskar sa dan baya so ma ya bawa Waziri damar ganin dariyar sa balle yace masa zaije. K'arasawa wajan sa Hydar yayi yace, "Na shigo da mota nan mu fita dashi." Duka a tare suka mik'e da Hydar da sabon sarki da Dr suka d'auke shi aka fita dashi aka saka shi a mota. Hydar ne ya kuma dawowa ya shiga cikin d'akin sa Jim kad'an ya dawo da k'aramar jaka a hannun sa key d'in motar ya fad'i ya juya zai d'auka suka had'a ido da Mama. Irin kallon da tayi masa ya saka shi ya gano mai take nufi ta tashi ta fita daga falon ya fita shima ya saka jakar a bayan motar kasancewar doguwa ce a baya aka kwantar da mai martaba yabi bayan Mama da sauri, a k'aramin falon ta na biyu ya same ta ya shiga da sauri yace, "Mama sauri nake yi." Tace, "nasan saurin kake yi ai, tambayar ka zanyi ka kuma bani amsa kayi min k'arya Allah ya isa ban yafe maka ba Hydar." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mama me yayi zafi haka?" Ya fad'a a rud'e yana kallon ta taja tsaki tace, "kadai ji me nace ai." Jikin sa yayi sanyi yace, "in sha Allah bazan fad'i k'arya ba." "A wanne gari Asad yake a Egypt?." Gaban sa ya fad'i jin tambayar da tayi masa ya kalle ta yaga sai kallon sa take yi ko wanne yanayi nasa tana karanta ya sunkuyar da kai tace, "kayi min k'arya wallahi ban yafe maka ba Hydar. Nasan kasan komai raina min hankali kawai kake yi." Hydar yace, "dan Allah Mamana ta daina fad'ar haka a akan d'anta." "To fad'a min" ta fad'a tana kallon sa idanun ta a waje. Hydar ya sauke numfashi cikin rashin abinyi yace, "Cairo." "Wanne hotel ko wanne estate?." Hydar yaji kamar ya kurma ihu ya shafa kansa kafin ya kalle ta yace, "Four Seasons hotel." Ta girgiza kai tace, "Four Seasons hotel...!? Hotel mai tsada kuka sauki y'ar talakawa wacce bata tab'a kwana a a.c ba sai da kuka basu gida. Room number fa?." Hydar yace, "Special room 012." Kai ta girgiza tana kallon sa ganin hakan ya saka shi niyar fita ta dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Ka sake ka kira Asad ka sanar dashi ka fad'a min inda yake ban yafe maka ba, kuma kar ka saka ran zan yafe maka har a tashi duniya." Jikin sa ya sake yin sanyi ya tsaya cak bai juyo ba yana jin kamar yayi kuka domin yasan tabbas akwai abinda zai faru gashi baya son abinda zai raba d'anuwan sa da abinda yake so, ga kuma abinda Mama tace, ya juyo yace, "Allah ya wuci zuciyar Mama, ina rok'on Mama da tayi min afuwa a zuciyarta bani da laifin komai. Na wuce Germany ina neman albarka Mama" ya fad'a yana ya fita da sauri. Numfashi ta fesar tayi murmushi tace, "Suhaima!" Ta fad'a da d'an k'arfi. Suhaima da ta shigo lokacin cikin jimamin jikin mahaifinta tace, "Na'am Mama." "Kina da visa Egypt?." "Eh ina da ita, amma ina jin saura baifi sati biyu tayi expire ba." "Ki nema mana ticket nida ke na zuwa Cairo, in zai yu jirgin yau nake so da daddare in babu kuma na sassafe zakiyi booking." Suhaima ta bita da kallo tace, "To, amma Mama me zamu je yi can?." Ta kalle ta tace, "kiyi abinda nace malama, in baza kije ba ki nema min ni kad'ai ba lallai sai dake ba." Suhaima ganin ta fusata ya saka tace, "Allah ya wuci zuciyar Mama zanyi, wanne hotel zanyi booking?." Da hannu tayi mata alamar ko wanne Suhaima ta wuce ta shiga ciki zuciyar ta cike da tunanin abinda zai kai su Cairo. Mama ta sauke numfashi tana hasasho abinda zai faru a can domin tasha alwashin sai ta raba Asad da Rauda koda zata dawo babu rai, daman Mai martaba ne yayi mata katanga da hakan yanzu kuma katangar ta rushe zatayi duk abinda take so ba tare da sanin sa ba tunda ba lafiya yake da ita ba, tayi murmushi tace, "Gani nan zuwa Asad!!!."        *☆☆☆* Bayan Rauda ta farka taji dad'in jikinta sosai tayi sallah ta sake yin wanka ta fito falo bata ganshi ba amma akwai abinci ta zauna taci bayan ta ta kalli wani k'aton mudubi da yake falon, tashi tsaye tayi tana kallon kanta sanye take cikin doguwar riga mai fad'i ta saka hular ta tana kallon kanta. Ita kanta burge kanta take yi domin kuwa ita kanta tasan tayi kyau fatar ta ta murje sai shek'i take ga kib'a da tayi duk wata komad'a nama ya cike shi duk da dai daman bata da rama. Murmushi tayi tunawa da abinda ya faru sau biyu tsakanin ta da Asad sai ta saka hannu ta kulle fuskar ta tana murmushi shima da yake bayan ta murmushin yayi dan ya tabbata abinda ya tuna itama shi ta tuna. Shi kam baiga bak'i da munin da Mama take maimaitawa a kanta musamman da yaga fatar jikinta har tafi fuskar ta haske, kyaun ta yake gani shi kam fiye da komai baya ganin muni ko bak'i a tare da ita.      A hankali ya tako inda take har lokacin hannun ta na kan fuskar ta ya k'araso ya zura hannayen sa ya rik'e shafaffen cikin ta ya had'e bayan ta da jikin sa ya rugume ta tsam ta baya ya d'ora kansa a kafad'ar ta yana kallon ta mudubin har lokacin fuskar sa da murmushi har hakoran sa suna waje. Cak yaga ta tsaya tana bud'e idanun ta a hankali suna had'a ido tayi saurin kulle idanun ta ya yiwa kunnen ta kiss taji sautin sa har kwakwalwar ta. Ya lura ta fara sonsa kamar yadda yake sonta hakan ya saka yake jin farin ciki fiye da baya ya kalle ta yaga tana murmushi amma idanun ta a rufe. Juyo da ita yayi ta koma ta juyawa mudubin baya shine yake kallon madubin ya rugume ta very tight yana ji kamar wani ne zaizo ya raba su a lokacin. Sun jima a haka babu wanda yake yiwa wani magana kafin ya sassauta rik'on da yayi mata ya d'ago da fuskar ta yaga har lokacin idanun ta a rufe yake ya yiwa idanun nata kiss ya kai bakin sa daidai kunnen ta yace, "I'm in love with you Love." Yarrrrr taji gashin jikin ta yana tashi ta sake kwantar da kanta a k'irjin sa ta rik'e shi da hannayen ta da suke bayan sa shima ya rik'e ta kafin ya sake ta ya kalli doguwar rigar jikin ta yaga tayi mata kyau sosai ta haska ta kasancewar kalar ta jah ce sai khamshin humra take mai dad'i, mayafin doguwar rigar ya gani a gefe ya d'auka ya yafa mata ya rik'o hannun ta yaja ta sai yaga ta turje ta d'an kulle idanun ta alamun akwai abinda yake mata ciwo. K'are mata kallo yake yi tun daga sama har k'asa ya fahimci dalilin tsayarwa ta sai yace, "Ohh sorry, amma sai munje kinga dr." Rik'e hannun nata ya kuma yi a hankali suka fita daga d'akin ya kulle suka shiga elevator suka sauka, sai a nan ta tabbatar da ana rana a garin ganin rana ta kwalle sosai suka shiga mota yaja suka tafi.       Asibiti suka fara zuwa badan taso ba aka bata magani suka sake fitowa suka shiga motar. Kasuwa ya kai ta suka shiga ya kalle ta yace, "ki d'auki abinda kike so, then kiyi tsaraba." Murmushi tayi ta fara d'aukar dogayen riguna da riga da siket dana riga da wando dan iya zaman ta a k'asar tana jin dad'in saka su. Kad'an yaga ta d'iba ya kalle ta yayi mata alama da ta k'ara ai kuwa ta cigaba da d'iban abinda take so tana d'aukar su Umma ta cika basket taf bayan ta gama suka k'arasa ya biya kud'in aka cika musu manyan ledoji guda uku aka kai musu har mota suka shiga suka tafi. Gani yayi tana ta farin ciki sai kawai ya canja hanya suka wuce wajan wasan yara, sai da sukayi sallah sannan suka shiga nan Rauda ta dinga karo da y'ay'an larbaawa suna ta wasa tayi murmushi tana kallon wajan, ticket ya siya musu na lilo mai kyau wanda yake lulawa har sararin samaniya suka hau ganin yadda yake gudu a sama ta kwanta a jikin sa tana chukikwye masa riga daman shi haka yake so ya rik'e abar sa suna juyawa a sama. Ji take kamar kanta yana juyawa kasancewar karon farkon ta kenan suna sauka sai da ya rik'e ta dan kamar zata fad'i ya zaunar da ita tasha ruwa.         Suna barin wajan suka wuce wani lafiyayyen garden da masoya suke zuwa; suna shiga taga wasu shuke-shuke ga fitila a ko ina mata da miji suna zazaaune ko wanne da kalar soyayyar da yake nunawa matar sa, kallon sa tayi suka had'a ido tace, "wajan yayi kyau." Murmushi yayi mata ta zauna akan grass carpet ya zauna shima sai ta zame ta kwanta a cinyar sa ganin duk haka larabawan sukayi a wajan. Bai hana ta ba yana rik'e da hannun ta har wajan ya sunkuya da kansa yayi mata kiss a goshi aka kawo musu abin motsa baki bai sha ba itama haka suna nan zaune a nan sukayi i'sha sannan suka bar wajan. Magana bata had'a su sosai amma zuciyoyin su na amsar sak'on kowa musamman murmushin sa yana sakawa Rauda taji kamar zata fad'i sabida yadda yake ratsa ta. Katafaran restaurant suka shiga akayi order abinci suka ci shida ita basu jima a nan ba suka wuce home of ice cream, itace kawai tasha shi kam bai sha ba sai da ta shanye suka shiga mota ta sauke numfashi tace, "na gaji na kuma k'oshi." Baice mata komai ba da niyar sa su wuce sharaha amma jin ta gaji sai ya fasa suka d'auki hanyar hotel. Yana ajjiye motar ya saka ma'aikatan yi mata gaba da kayan ta su kuma suna takawa a hankalin hannun su sark'e dana juna ta kalle shi shima ya kalle ta sai ta b'oye fuska yayi murmushi suka shiga elevator.       Falon duhu sosai bata tsaya kunna haske ba ta shiga d'aki domin fitsari take ji bayan ta fito daga band'akin ta dawo falon, turus tayi ganin abinda yake falon ya d'auki hankalin ta ya kuma burgeta ta tsaya tana kallon ko ina. Lafiyayyun flowers ne jajaye da yalaye anyi ado dasu a falon ga balloon a barbaje a k'asa kid'a na tashi kad'an-kad'an irin wanda ake kira slow music sak irin decoration na india, wajan yayi bala'in kyau ta tsaya a tsakiya inda balloon d'in suke tana kalla tana dariya cikin burgewa dan ba gani ta tab'a yi a zahiri ba. K'ananun flowers sune a zube akan carpet d'in da ya mamaye falon ko ina yayi kyau sai khamshi da yake tashi a wajan ga fitilar da take kawowa ta d'auke kalar blue. _I wanna be in your life until the night is over, I wanna hold you so tight so tight, come in closer, it's been a hell of a ride forever single moment, you were there by my side. Whenever I'm broken u make me feel whole, whenever I'm lonely you're there for my soul, whenever you are girl that's where i call my home, whenever you doubt it i I'll lettin you know. Woahh girl i want to be dancing with you forever; you see through the storm and take me as I am, Baby it's magic anytime that we're together i make just love you and hold you for my hand, hold you for my hand, my hand, my hand._ wak'ar for my hand kenan ta burna boy itace take tashi a wajan a hankalu cikin dad'in sauraro. Daidai inda ake ce, 'i wanna hold u so tight, so tight come in closer' daidai wajan Asad yayi holding d'in ta very tight yana jera mata kyakykyawan kiss a wuyan ta wanda ya saka ta kusa zaucewa ta rik'e shi kam a jikin ta. Zuciyar ta bugawa take domin ta fahimci wak'ar sak'o ne yake bata cikin salo na nuna soyayya da kuma sanya nishad'i a zuciya hakan ya saka ta gigicewa ta rike shi sosai shi kuma yana ta mata kiss a duk inda idanun sa yaje. Cikin k'aramin lokaci dukkan su gangar jikin su da zuciyar su tayi nisa cikin soyayya da k'aunar junan su, shauk'i ne yake d'aukar su dukkan su ta rik'e shi kam shima haka yana yawo da hannun sa a jikin ta. Sakin ta yayi ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta yace, "Ki yarda ko kar ki yarda I love you for the sake of Allah." Yana kallon ta tana kallon sa yake furta mata kalmar da ta saka zuciyar ta jijjiga idanun ta yayi narai-narai kamar zata zubar da hawaye tana kallon sa shima kuma ita yake kallo. Hannu ta d'aya ya rik'e ya d'auko zobe mai kyau ya kama yatsan ta na kusa da k'aramin ya zura mata shi ya zauna cif a hannunta ya haska fatar hannunta. Kallon zoben take ta kalle shi sai ya d'aga mata kai yace,      "Do you love me Muwaddaty?." Rauda bata san lokacin da ta d'aga masa kai alamun eh ba sai kuma ta girgiza kai alamun a'a tunawa da qalubalen da yake cikin auren sa. Hannayen ta ya rik'e duka biyun yana cigaba da kallon idon ta amma ya kasa yi mata magana sai kallo. "Akwai tarin qalubale a cikin zamana dakai, bana son sai na saki jiki dakai zuciyata tayi nisa a k'aunar ka rana d'aya ka rabu dani. Abinda nake jin tsoro kenan prince shiyasa bana son sakin jikina dakai sabida nasan ban dace dakai ba" ta fad'a a hankali tana kallon fuskar sa. Yadda take magana muryar ta na shaking idanun ta na k'okarin sakko da hawaye ya saka shi matsar da bakin sa kusa da nata yayi kissing kad'an ya janye bakin sa yace, "babu abinda zai raba mu believe me. I will be always in your side forever." Kai ta girgiza tana kallon sa hawaye suka sakko mata tace, "Promise me u never leave me." Hannun ta ya rik'e yaja baya ya duk'a a kan guiwar sa duka biyun yace, "I promise you I will never ever leave you" Sai ya d'an cije baki yace, "Kome zai faru ina tare dake, ina sonki so mai yawa" ya furta a sanyaye muryar sa na yankewa alamu sun nuna maganar da yake yi tayi yawa. Bin sa tayi ta durk'usa itama tace, "are you sure that you never leave me?." Kai ya d'aga mata alamun eh ya matsa hannun ta yace, "I'm very much sure Muwaddaty." Kallon sa take yi da kai yayi mata alamun tana sonsa, sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai tace, "I love you." Jawo hannun ta yayi suka yi baya ta kwanta a jikin sa shima ya kwanta a kan carpet flat yana kallon ta tana kallon sa hannun sa yana zagaye da k'ugun ta. Juyawa yayi ta koma k'asa shi kuma ya dawo sama yana gefen ta yana kallon ta cikin blue light a hankali yace, "repeat it again" ya fad'a cikin muryar da ita kad'ai ce kawai zata ji. "I love you so mu......" bakin ta yayi shiru lokacin da ya fara kissing d'inta cikin sauk'in soyayya mai nuna tsantsar kewa da k'auna a bayyane. Wak'ar da take tashi ta sake jefa su cikin shauk'i sukayi nisa a cikin sabon yanayin da suka tsinci kansu, suna kwance cikin flowers masu kyau da khamshi k'auna da soyayya na sake narkar da zuciyar su cikin k'auna. Ya gigita Rauda tayi nisa a cikin duniyar da yake so taje shima yayi nisa a cikin ta. kamar an saka masa remote ya dakata da abinda yake yi ya dafe kansa da hannun sa ya koma gefe yana jan numfashi har lokacin hannun sa yana kansa yana sauke ajiyar zuciya. Rauda ganin yanayin da ya shiga sai ta janye jikinta ta tashi da sauri ta shiga d'aki tana sauke numfashi duk a tunanin ta ciwon da take dashi ne ya dakatar shi yin abinda yake niya. Ya jima a haka kafin ya tashi jikin sa a sanyaye ya shiga d'aki zuciyar sa cike da tsoro da tunanin dalilin yanayin sa da kuma abinda ya jawo tsayawar komai ba tare da ya shirya ba. _Gafa Mama a hanyar Egypt, ga Asad yayi Alqawari, ga kuma aikin Mama ya kama shi.😨_ [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *043.*           Zuciyarta bugawa take tana dafe da ita har lokacin idanun ta a kulle yake babu abinda take gani sai abubuwan da suka faru a lokaci kad'an da ya shud'e. Gani take kamar a mafarki ya faru ba gaske ba ta bud'e idon ta tana fuskantar kanta a mudubi tana kallon fuskar ta sai ta kulle idanun ta tunawa da abinda ta furta masa ta sake dafe zuciyar ta tana ji yadda take bugawa da sauri. 'Ke Rauda anya bakiyi gangancin barin gangar jikinki da zuciyar ki fad'awa tarkon soyayyar wannan bawan Allah ba?, kin sani shi ba daidai yake dake ba meyasa zaki bari rud'in kalaman sa suyi tasiri a kanki?. Kija jikin ki ki tuna matsayin ki sannan ki tuna wacece babar sa har kashe ki ta turo ayi dan kawai bata sonki, ki san abin yi kafin wankin hula ya kai ki dare.' Salon bugun zuciyarta tane ya canja ya koma na tsoro da fargaba domin abinda zuciyarta ta fad'a mata gaskiya ne ta tabbatar ba k'arya bane. Ita ba sa'ar Asad bace tabbas amma gashi tayi sake zuciyarta ta fara yin nisa a cikin k'aunar sa. Kanta ta dafe a bayyane tace, "Yayi min alqawarin bazai barni ba nasan kuma zai cika" ta fad'a tana dafe kanta da hannun ta. Numfashi take saukewa a hankali kafin ta tashi jikin ta a sanyaye ta shiga band'aki.       A b'angaren Asad tunda ya shiga d'akin yake zaune yana tunanin abinda yake faruwa dashi wanda hakan bai tab'a faruwa ba bai kuma tab'a tunanin zai faru d'in ba, kansa yake ji yana juyawa ya tashi zaune yayi shiru yana tunanin abinda ya faru har hakan ta kasance.  Tunanin yaga bazai yi masa ba ya shiga band'aki sharp-sharp yayi wanka ya fito ya canja kaya ya fita daga d'akin gabad'aya. Asibiti ya wuce kai tsaye ya kai kansa ya sanar dasu matsalar da ta faru aka shiga yi masa gwaje-gwaje a nan take amma babu wata matsala da aka gani a tare dashi, magani suka bashi wanda zaiyi amfani dashi jikin sa duk a sanyaye ya baro asibitin. Koda ya koma d'aki kawai ya wuce ya kalli agogo yaga dare ya raba yayi alwala ya tayar da sallah kamar kullum. Ya jima yana ibada har akayi asuba sannan ya nemi waje ya kwanta duk da ba baccin yake ji ba zuciyar sa a cushe take ya rasa tunanin ma da zaiyi gabad'aya damuwa tayi masa yawa zuciyar sa tana bugawa da sauri-sauri. *☆☆☆* *Nigeria.*          "Hydar ya jikin nasa? Me likitocin suka ce?." Hydar daga can b'angaren yace, "Ranka ya dad'e tunda muka iso aka karb'e shi yanzu haka har yanzu basu fito ba nima jiran su nake." Mai martaba sarki yace, "babu wani bayani da sukayi maka ko kad'an ne?." Hydar yace, "Babu." Mai martaba yace, "Hydar ina zargin wani abu akan lamarin ciwon nan nasa." Hydar yace, "kamar me kenan Takawa?." "Ina zargin da saka hannun wasu a ciwon nan, in ka duba shekaran jiya da daddare lafiyar sa lau har da babar ka sunyi magana dan tana fita ya naje wajan sa yake sanar dani fitar ta. Akwai wani abun da ya faru." Hydar yace, "haka ne. Baza'a rasa ba dan akwai wanda da dama hukuncin da ya yanke bai musu dad'i ba, to amma Allah yaja da ranka waye ko wace? Me suka aikata lokaci d'aya yayi tasiri haka?." Mai martaba yayi shiru yana tunanin Hydar ya katse masa tunani yace, "Ko akwai wanda mai martaba yake zargi?." "Tabbas akwai wad'anda zuciyata take zargi, bana so zargin nawa yayi nisa a kansu ne amma zan fad'ad'a bincike." Hydar yace, "Allah ya bada iko ya bayyana mana koma su waye suke da hannu a wannan ciwon nasa na farar d'aya." "Amin Hydar. Ka cigaba da kula dashi zan zo in sha Allah." Daga nan sukayi sallama da Hydar ya kashe wayar.          K'arfe shida na safe motar su Mama ta sauka a Tafawa b'alewa international Airport driver da ya kawo su ya juya ita da Suhaima suka shiga cikin Airport suna jiran jirgi domin k'arfe bakwai jirgin su zai d'aga zuwa Cairo. Suna nan zaune aka sanar da zuwan jirgi suka fita suka hau motar da zata kai su bakin jirgi, hankalin Mama bai kwanta ba sai da taji jirgi ya tashi ya lula sama ya d'auki hanyar k'asar Egypt sannan ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi. Awa biyar da y'an kaine suka kai Mama da Suhaima Cairo suka sauka daga jirgin a lokacin k'arfe d'aya na rana ta take sosai suka shiga mota direct suka nufi Four Seasons hotel ko hotel d'in su basu wuce ba kai tsaye inda Asad yake ta nufa.        A cikin hotel d'in Rauda na zaune a d'aki kamar ko yaushe tana waya da y'an gidan su tana ware kayan da suka siyo a daren jiya tana zubawa a jaka, katse wayar tayi bayan sun gama wayar ta kalli jakar tace, "kai tama yi kad'an ashe." Wata jar doguwar riga ce ta d'auki hankalin ta ta d'auka tana d'agawa sama tace, "rigar nan fa tayi kyau sosai, bara na gwada na gani" ta fad'a tana zame ta jikin ta ta saka jar ta d'aura d'ankwalin irin d'aurin nan mai v ta ta gaba gashin gaban kanta ya fito ta waje. "Kai amma tayi min kyau sosai" ta fad'a tana sake kallon kanta tana murmushi. Sai kuma ta tsaya cak tana kallon kanta har lokacin tace, "ko ina yake?." Bata da amsa ta jiyo motsi a falon ta bar kayan ta fito daga d'akin tana kallon fallon yana nan yadda yake jiya decoration d'in wajan kamar an sake sabunta shi. Wajan taga ya kuma burgeta tana nan tsaye taji sautin Camera alamun ana d'aukar ta hoto, juyawa tayi ta kalle shi yana zaune akan kujera da cup d'in lemo a hannun sa yana sha fuskar sa babu walwala amma kuma yana d'aukar ta hoto. Murmushi tayi ta sunkuyar da kai k'asa ya ajjiye kofin ya taso ya k'araso zuwa gare ta ya rik'e hannun ta duka biyun yana jin bugun zuciyar sa a bayyane yace, "you look so beautiful." Murmushi ta kuma yi fuskar sa tana nan yadda take bata canja ba ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta kafin ta sake sauke kanta k'asa. Yana so ya fad'a mata abinda ya same shi amma bai san ta inda zai fara ba domin shi ya gama amince mata bashi da abinda zai b'oye mata a duniya kuma ya kamata ace ta sani amma ya rasa ta inda zai fara cewa ga abinda ya same shi, yayi shiru na wani yana kallonta yana kuma rike da hannunta zoben da ya bata ya sake haska hannun sosai. Kallon sa tayi tace, "kayi min alƙawarin baza ka barni ba ko?." Ta d'ago ta kalle shi nan take taji gaban ta ya fad'i ya d'aga kai alamun eh tace, "dan Allah ka sake maimaitawa ina so na sake tabbatarwa." Numfashi ya sauke yayi shiru na wani lokaci kamar bazai magana ba har lokacin bai cika hannun ta ba sai daga baya yace, "ni Asad bin Nasir bin Sa'ad na yiwa matata Rauda alƙawarin bazan tab'a rabuwa da ita ba, duk wahala duk dad'i duk tsanani ina tare da ita" ya fad'a yana lumshe idanun sa a kan fuskar ta. Rauda ta sunkuyar da kai tana murmushi ta d'ago idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Na amince. Amma meyasa nake jin zuciyata tana rawa akan hakan? Sai naji kamar akwai abinda zai faru wanda zai raba ni dakai" ta fad'a k'irjin sa tana kuka tace, "Ina jin tsoro sosai, bana so a raba mu na saba dakai na fara sonka bana so son ya zamar min cuta nan gaba." Hannu ya saka ya zagayo dashi a jikinta ya rik'e ta sosai yana jin kukanta a k'irjin sa yana bubbuga bayanta a hankali amma baiyi magana ba, sun shima a haka kafin yace, "Ki daina kuka, Asad bazai barki ba kin zama shi ya zama ke babu abinda zai raba ki dashi dan yana sonki. Ki daina kuka bana son jin kina kuka" ya fad'a muryar sa na rawa kansa na ciwo sosai. D'agowa tayi ta kalle shi ta goge idanunta ya rik'e fuskar ta yana kallon idanunta yace, "Smile." Murmushin tayi duk da akwai hawaye a idanunta shima yayi murmushin yana girgiza mata. "Ya jikin ka?." Ya juya idanu ya kalle ta sai kuma ya kalli gefe ya sake kallon ta sai ya fasa maganar da zai fada ya rik'e hannunta suka je suka zauna. "Wacce country kike son kije?" Ya fad'a yana kallonta. Ta sake yin dariya tace, "Suna da yawa." Da hannu mata alamun yana ji tace, "Saudia, America, England kai nifa ko ina ma ina so naje, especially Dubai ma kodan na shiga national world Quran competition." Kai ya girgiza jin dad'in abinda take so ta shiga d'in amma baice komai ba. Kallon kanta yayi yace, "Zaki je saloon anjima kar kanki yayi ciwo" ya fad'a yana kallon gashin kanta da yake a tsefe. Murmushi tayi tana kallon zoben hannunta tace, "tohm." Hannun sa ta kalla babu agogo taga wannan zanen yana nan ta shafa zanen tace, "Ga shaida ta." Murmushi yayi ya kalli zanen ya kalle ta yace, "As my wife bazaki iya gane ni ba sai da sign?." Ta turo baki gaba tace, "Kuna da rikitarwa ne, kace fa Mama ma bata gane ku wani lokacin." Murmushi kawai yayi baice komai ba ya mayar da hankalin sa kan t.v. Zata kuma magana kenan aka danna door bell hakan ya dakatar da ita daga maganar kafin ya mike ya k'arasa kusa da k'ofar ya cire lock yaja handle d'in k'ofar ya bud'e. Wara idanu waje yayi ganin wanda suke tsaye ido cikin ido yake kallon su zuciyar sa na bugawa fat, fat, fat ya kasa furta komai sai kallo ya kasa furta komai. "Matsa min na wuce" Mama ta fad'a tana rab'a shi ta shiga ciki Suhaima ta biyo bayan ta. Had'a ido sukayi da Rauda gaban Rauda yayi mugun fad'uwa ta tsorata sosai har tsoron ya bayyana a fuskar ta taja baya tana cigaba da kallon Mama. Mama k'arewa falon kallo take tana girgiza kai gabanta na fad'uwa matuk'a ganin irin adon da yasha irin na gidan larabawa da India ne musamman lokacin da suke cikin nishad'in son kasancewa da iyalan su. "Mamana!" Asad ya furta with full love emotion yana k'araso da sauri yayi hugging d'in ta very tight. Hugging nasa back tayi tana jin sanyi da kwanciyar hankali na ratsa ta zuciyar ta na dawowa bugu daidai domin tunda Asad ya bar k'asar bata kuma jin zuciyar ta na bugawa daidai ba sai yanzu. Sakin ta yayi ta kalli face d'in sa tace, "Kar ka damu nazo gare ka tunda kai an hana ka zuwa inda nake" ta fad'a tana kallon Rauda da take wajan a tsaye kamar an dasa ta kanta a sunkuye. Dawo da kallon ta tayi gare shi tace, "Nasan raba mu akayi dakai shiyasa baka nema na bayin kanka bane aikin wannan bak'ar ashanar ne" ta fad'a tana nuna Rauda. Suhaima da take ta kallon falon tace, "Wow wajan nan ya had'u ya kuma tsaru sosai, Oga Deaf waye yayi planing wajan nan haka?." Kallon Suhaima yayi sai kuma ya kalli Mama gaban sa na fad'uwa matuk'a yaga Mama ta isa kusa da Rauda babu b'ata lokaci ta tsinke ta da mari. Da hanzari Asad ya k'arasa wajan yana kallon Maman ya kalli Rauda da hannun ta yake kuncin ta hawaye yana sakko mata idanunta a kulle tace, "Y'ar talakawa, mayya mai zubin mayu dangin mayu. Duk irin kashedin da nayi miki akan Asad baki ji ba sai da kika san yadda kikayi kika asirce min shi aka cuce shi aka aura masa ke kuka tawo nan. Gashi nan naga har canjawa kinyi anzo k'asar waje ana cin abinda ake so ke ga mai wayo ko?. Nafi k'arfin dangin ki ma gabad'aya balle ke y'ar k'aramar alhaki." Motsi Rauda batayi ba balle ta amsa hawaye ne yake zuba a idanun ta jikin ta yayi sanyi sosai tana ji a jikinta akwai abinda zai faru a wannan lokacin. "Kin raba ni dashi baya nema na baya min waya duk a tunanin ki kinyi nasara a kaina har abadah kamar yadda kika ce, to baki isa ba yarinya wanda ya riga ka kwana sai ya riga ka tashi baki isa kiyi nasara a kaina ba daidai da rana d'aya. In ma rik'e masa kurwa kikayi yau zaki sake shi domin banga abin so a jikin ba har da zai maqale miki, kin samu riba ai tunda gashi har kina taka k'afar ki tafiya tayi miki kyau. Anyi aure ban sani ba yanzu kuma na sani za kuma a warware shi." Asad ta kalla gaban sa ya fad'i ya saukar da ido k'asa zuciyar sa na rawa burin sa kar ta furta abinda zuciyar sa take aiyanawa domin bai san ya zaiyi ba, "Asad!." Jin yadda ta kira shi ya saka ya kalle ta da girmamawa yace, "Mama." "Wacece ni a wajan ka?." Kansa na k'asa yace, "mahaifiyata." "Na isa da kai ko a'a?." "Mamana itace isa da kanta." Mama tayi murmushi ta kalle shi tace, "umarni nake baka yanzu ba anjima ba ka saki yarinyar nan!." Runtse idanun sa yayi daidai lokacin da zuciyar sa ta buga da k'arfin gaske ya cize bakin sa ya bud'e ido ya kalle ta yaga shi take kallo sai ya sauke ido k'asa ya kasa cewa komai. Sautin kuka Rauda ya karad'e ko ina a falon kuka take yi sosai zuciyar ta nayi mata zafi ta kasa furta ko wacce kalma sai kuka sabida tashin hankalin da take ciki ba d'an kad'an bane. Mama ta kuma kallon sa tace, "Magana nake maka Asad indai ka d'auke ni matsayin mahaifiyar ka wacce ta haife ka ta raine ka ka sake ta, in kuma kana so ka nuna min ka zab'e ta a kaina bismillah Asad." Idanun sa sun koma jajaye haka fuskar sa ya d'ago ya kalle ta ya sake mayar da kansa k'asa yace, "Dan Allah Mamaaaaa!." Abinda ya iya furtawa kenan Mama tace, "Wallahil azim sai ka sake ta matuk'ar na isa dakai. Muryar sa har rawa take yi  har labb'an sa kana ganin yadda suke motsawa yace, "Allah da ya halicce mu shine ya halatta saki amma kuma baya son sa Mama, Mama tana da iko da Asad a koda yaushe amma dan Allah ta barni na gujewa abinda Allah baya so kar na aikata shi duk da kasancewar halak." Mama ta girgiza kai tace, "Da alama mallakar da aka yi maka har yanzu tana jikin ka kenan ko? To tunda nazo ko wanne irin asiri tayi maka wallahi sai na b'alla shi wallahi. Na riga na rantse ka sake ta Asad!" Ta k'arasa fad'a da k'arfi tana kallon sa. Zubewa Rauda tayi a wajan tana kuka sosai hankalin Asad ya kuma tashi zuciyar sa na bugawa a guje kamar zata fito daga k'irjin sa ya kasa furta komai ji yake kamar shima ya zubar da hawaye sabida rad'ad'in da yake ji a zuciyar sa. "Kana yi min biyayya a ko wanne lokaci meyasa kake son b'ata min rai akan wannan mujiyar? Ka fifita ta a kaina kenan?." Da sauri ya girgiza kai yayi alamun a'a tace, "to sake ta." Suhaima da take gefe tausayin d'anuwan ta ya kamata tace, "Mama dan Allah....." saurin dakatar da ita tayi tace, "ban saka ki a maganata ba." Ba shiri Suhaima tayi shiru Mama ta kalli Asad tace, "Zaka sake ta ko a'a?." Numfashi ya fesar ya had'd'iye yawu mai d'aci ya kalli Rauda da take zube tana kuka kanta na cikin cinyoyin ta ya sake sauke numfashi cikin tashin hankali da bugun zuciya.       "Baza kayi ba kenan ko? To ka sani matuk'ar baka sake ta a yanzu ba bazan yafe maka ba Asad sannan kuma wallahi sai nayi maganin ta da ita da dangin ta gabad'aya." Da sauri ya kalli mahaifiyar tasa ta d'aga masa kai tace, "eh kaji ai me nace, in baka sake ta ba bazan yafe maka ba Asad." Lumshe ido yayi cikin zafin da yake ji jiki sa har idanun sa yana ji kamar ya zubar da hawaye amma babu dama. Kai ya sunkuyar ya juya ya kalli Rauda da har lokacin kuka take ya sake kallon Mama da ta kafa masa ido ya cize bakin sa ya sake had'd'iye yawu bakin sa na rawa amma ya kasa furta ko wacce kalma. Dak'yar ya zame k'asa ya durk'usa yace, "Ni shugaba ne, Abba ya sanar dani komai Mama sakin aure hani ya kamata nayi dashi bana aikata shi ba. Dan girman Allah ina rok'on mahaifiyata da ta janye kalaman ta." Ganin yana b'ata mata lokaci ya saka taja tsaki tace, "Asad in bakayi abinda nace ba zaka had'u da b'acin raina wanda baka tab'a had'uwa dashi ba har abada. Ka sake ta ko na sallama mata kai har abada" ta fad'a a fusace domin ranta a b'ace a yake ganin yadda yake mata gaddama a gaban wata banza bare talaka yar talakawa. Rauda ya kalla bashi da zab'i sai bin abinda mahaifiyar sa take so yace, "I'm sorry.....!" Mama ta fusata kamar zata dake shi tace, "au sai ka bata hak'uri? Kenan itace wacce ka fifita sama dani Asad? Ashe zaka iya nuna kafi son wata a kaina Asad?." Ya kalli Maman cikin girmamawa yace, "Ban kai wannan matsayin ba Mama, Allah ya wuci zuciyar ki zanyi abinda kike so" ya fad'a jiri yana d'aukar sa. "To sake ta." Ya kalli Rauda ya tuna ko cikakken mintina asihrin baiyi da d'aukar mata alqawari ba gashi tun ba'a Je ko ina ba ya karya bai cika mata shi ba daman yasan abinda take tsoro itama kenan gashi kuma ya faru, zai zama makaryaci a idanun ta maci amana mara cika alƙawari yace, "Na sake ki saki d'aya!." A tare zuciyar su ta buga Rauda taja numfashi ta d'ago fuskar ta tana murmushin k'arfin hali hawaye yan zuba amma bata iya cewa komai ba. Mama ta sauke numfashi tayi ajiyar zuciya mai tsaho har tana dafe tace, "Finally mun rabu da k'aya, sai ki fita ki koma gidan ku kije can ku cigaba da zama cikin talaucin da kuka saba zama. Ina miki warning akan y'ay'ana bama Asad kawai ba, kar na sake ganin ki a kusa da k'ofar gidan su ma balle na ki shigo gidan, in kuma ba haka ba zan d'auki mummunan mataki a kanki dake da dangin ki. In kunne yaji jiki ya tsira kin taimaki kanki da iyayen ki, in kuma kink'i ji kin cigaba da yi masa asiri wallahi!, wallahi!!, wallahi!!! Sai naga bayan ki keda iyalan gidan ku gabad'aya." Rauda tana ji bata ce komai ba Mama ta kalle shi tace, "had'a kayan ka mu bar hotel din nan yanzu." Sai kuma ta kalli Rauda tace, "maza-maza tashi ki fita kije can ki karata ko yau a d'aura miki aure da wani dan nasan baki isa kiyi iddar d'ana ba." Rauda ta mik'e jiki a sanyaye dan hawayen ya tsaya cak Mama ta kalle shi tace, "Ina passport d'inta? Maza bata ta b'ace min da gani bana son ganin ta ko kad'an." Hankalin Asad yayi mugun tashi ya kalli Maman tasa yace, "bata san kowa a nan ba, bata an ko ina ba, ina zata je?." "Ta tafi ko ina ma bai dame ni ba." Rauda jikin ta ya gama yin sanyi ta fara takawa k'afar ta ko takalmi babu zata gifta su Asad yayi sauri ya zube guiwar sa a k'asa yana kallon Mama ya rik'e hannunta kamar zaiyi kuka yace, "Dan Allah Mama ki barta ta zauna a nan nayi abinda kika ce na kuma barta tunda shine farin cikin ki na cika miki burin ki na rabu da ita, kiyi min wannan alfarmar yadda Allah ya taimake ki ki taimaki d'anki mai rauni ki amince ki barta ta zauna a nan in ta bar nan ina zata je?, babu wanda ta sani babu inda ta gani a k'asar nan. Ki barni na mayar da ita gida kamar yadda na d'auko ta cikin aminci dan Allah." Mama kallon sa take da mamakin yadda yake magana kamar bashi ba kenan daman rashin maganar tasa iskanci ne yana sane tunda gashi indai akan lamarin tane yana magana yadda ya kamata hakan ya kuma fusata Mama tace, "Wallahi sai ta fita!." A daidai wannan lokacin Rauda ta fita daga falon ya saukar da kai kansa na mugun sarawa kamar zai fashe ya runtse idanun sa, zuciyar sa nayi masa ciwo tare da rad'ad'in da bai tab'a jin irin sa ba a rayuwar sa, ya d'ago kai yabi hanyar da ta fita da kallo ya sauke numfashi mai nauyin gaske.......... *Mama tayi mana yankan k'auna*😢 [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *044.*          A fusace ta juya ta kalle shi ta kama hannun sa ya mik'e tsaye tana binsa da kallo tace, "ban tab'a ganin raunin ka akan komai ba sai akan wannan kucakar yarinyar a lokacin raunin ka ya fara fitowa kan fuskar ka, ban tab'a ganin gazawa k'arara a fuskar ka ba sai da yarinyar nan da ta asirce ka. Duk wani ko wata da zai kawo min tangard'a a cikin cikar burina bazan barshi, ba'a san shugaba da rauni ba dan haka ka k'arfafa zuciyar ka ka manta da ita ka d'auka baka tab'a sanin ta bama a duniya domin ka barta kenan har abada." Kansa na k'asa bai ce komai ba harta gama bai ce komai ba sabida yadda yake jin zuciyar sa na tafasa bazai iya furta ko wacce kalma jikin sa kamar anyi masa allurai na sagar da gangar jiki bashi da kuzari ko kad'an kana kallon sa kasan yana cikin damuwa mara misaltuwa yana k'ok'arin kawarwa ne amma hakan yaci tura. Mama ta bar kusa dashi ta k'arasa d'akin farko ta tura k'ofar ganin nasa d'akin ne ta dawo da baya ta kalli Suhaima tace, "Zo ki tattara min kayan sa mu bar nan." Jikinta a sanyaye ta taka ta shiga d'akin sun d'an jima a ciki kafin su fito da jaka a hannun su hannu Mama da passport guda biyu ta kalle shi tace, "Wuce muje." A hankali ta tako yazo kusa da ita ya kalli Suhaima suka had'a ido cikin tausayin Yayan nata ta kalli Mama tace, "Mama akwai wasu kayan sa drawer da ban d'auko ba naga kuma kamar documents ne masu mahimmaci." Mama tace, "jeki ki d'auko" ta fad'a tana bud'e k'ofar ta fita ya biyo bayan ta. Da Suhaima ta fad'a d'akin da take tunanin na Rauda d'in ne ta had'a kayan da ta da ta gansu a wajan wanda zasu shiga wanda baza su shiga jakar ba ta barsu a wajan taga wayar ta a kan gado ta d'auko ta cusa magani a aljihun jakar ta jawo da sauri tana addu'ar Allah yasa Mama sun bar wajan. Tana fitowa babu Mama da Asad a wajan ta sauke numfashi ta hango Rauda a zaune a gefen wani d'aki ta had'a kai da guiwa sai passport d'in ta a kusa da ita ta k'arasa inda take tace, "Ga wayar ki ga kayan ki na bar wasu a ciki baza su shiga ba. Kiyi haƙuri da abinda Mama tayi miki na tabbata Yaya Asad yana sonki zai kuma dawo gare ki" abinda tace kenan ta ajjiye mata tabi bayan su da sauri ta shiga elevator ta sauka. Da kallo ta bi bayan ta ta kuma fashewa da kuka mai tsuma zuciya ta kwanta a wajan ba tare da tasan abinda zatayi ba. K'arar bud'e elevator taji bata d'ago ba taji anzo kanta an tsaya idanun ta sunyi nauyi bazata iya kallon ko waye ba hakan ya saka bata motsa ba sai ajiyar zuciya da take yi. Cikin harshen turanci taji ance, "Hotel d'in mu baya buk'atar zaman ki ki tashi ki fita ko mu kira miki y'an sanda su kama ki." Gabanta ya fad'i ta daure ta d'ago ta kalli wanda yake magana taga security ne ta tashi zaune ta dafe kanta da hannayen ta duka biyun zatayi magana akazo wajan bata iya kallon wanda yazo wajan ba taji ance, "A'a chocolatly lafiya kike a nan?" Dr Khalifa ya fad'a yana k'arasowa inda take kwance. Kallon security d'in yayi cikin harshen larabci yake tambayar sa lafiya, security d'in yace, "an sanar damu babbar mai aikata laifi ce daga Nigeria,.ta fita daga hotel din nan ko mu kaita wajan y'an sanda bama som zaman ta a nan." Da mamaki Dr Khalifa ya kalle shi ya kalle ta yace, "Chocolaty me yake faruwa haka? Ina prince yake?." Ta kasa magana sai rawar jiki da jikin ta yake yi hakan ya saka shi tab'a wuyan ta yaji zafi rau yace, "Subahanallah" ya kalli security d'in yace, "waye ya baku wannan masaniyar? Ina wanda suke tare da ita yake?." Security d'in yace, "bai dame mu ta tashi ko mu fitar da ita ta k'arfi." Dr Khalifa yace, "basai anje nan ba" ya kalli Rauda yace, "tashi mu tafi kafin su saka a kama ki kin san nan ba Nigeria bace tunda aka fad'a musu baza su amince dake ba." K'okarin tashi take yaga ta kasa ya kama hannun ta duka biyun ta tashi tayi baya zata fad'i tana dafe kanta yayi saurin rik'e ta yana fad'in, "Sannu." Jakarta yake jaya d'auki wayar ta da passport d'in ta suka shiga elevator suka sauka. Suna barin wajan Asad ya dawo yaga bata wajan ya bud'e d'akin duk yasan bazai ganta ba ya duba ya sake kullewa yana kallon wajan yana tunanin ina taje zuciyar sa na bugawa sosai fiye da d'azu. Komawa k'asa yayi ya koma reception wajan ma'aikatan wajan da harshen larabci yace, "Ina son ganin camera na wajan k'ofar d'akin 012 special room." Dannawa wanda yayiwa maganar yayi nan take akazo inda security suka je kanta da inda Dr Khalifa yaje kusa da ita har yadda ya rik'e ta suka tashi suka shiga elevator. Mummunan sarawa kansa yayi ganin yadda Khalifa ya rik'e k'ugun ta ga hannun sa a cikin nasa ya dafe zuciyar sa yana jan numfashi dak'yar yayi baya zai fad'i sukayi saurin tare shi ta baya suna jera masa sannu, zaunar dashi sukayi aka kawo mai ruwa mai sanyi amma bai iya sha ba abinda yake gani kawai a idanun sa shine yake sake tayar masa da hankali sai numfashi yake ja dak'yar kamar wanda zai bar jikin sa. "Asad!." Mama ta fad'a daga bayan sa ganin an zagaye shi ta k'araso wajan tana kallon ma'aikatan wajan tace, "me kake jira ne basu key d'in kenan?." Kai ya dafe ya zaro key d'in motar hotel d'in da yake amfani da ita ya basu ya tashi tsaye dak'yar yana jin jiri na d'aukar sa ma'aikacin da yake kula da computer yace, "akwai ragowar kud'i da bai k'are ba na d'aki da kuma na motar." Da hannu Asad yayi musu alama ya wuce Mama tabi bayan sa zuciyar ta a cushe tunanin ta kawai kenan baiyi niyar dawowa ba yana nan yana kashewa y'ar talakawa kud'i.        Taxi suka shiga Asad tunda suka shiga motar baice komai ba titi yake kallo yana jan numfashi dak'yar amma kuma a idanun sa Khalifa yake gani rik'e da k'ugun Rauda sai yaji kamar an soka masa mashi a zuciyar sa, _ina zai kaita? A ina zai ajjiye ta? Me zai mata da ya suka bar hotel d'in tare? Meyasa ya rik'e ta?._ Babu wanda zai bashi amsa ya sake kallon titi zuciyar sa ta kuma cewa, _meyasa ta bari ya rik'e ta? Meyasa ta bishi bayan tasan bazai iya tafiya bai nema mana mafita ba?, yanzu ina zasu je? Gidan sa zai kaita?, to su zauna ita dashi kenan?._ Tunanin hakan ya saka shi dafe kai tare da furta, "Hasbunallah!." Mama ta kalle shi batayi magana ba suka tsaya a hotel d'in da sukayi booking suka fita bashi da zab'in da ya wuce ya fita shimq duk da jirin da yake ji suka shiga ciki. Upstairs hotel ne dole suka shiga elevator zuwa d'akin da suka kama suka shiga ciki. Babban falo ne k'ofa biyu a cikin sa da alama shima dak'una biyu ne Mama ta bud'e d'aki na farko tace, "Shiga kayi sallah." Bai musa ba ya shiga ta kulle k'ofar ta kalli Suhaima da take kallon ta tace, "meye kike bina da kallo?." Ta langwabar da kai tace, "Mama bashi da lafiya fa kamata yayi mu wuce asibiti ba nan ba, jiri yake yi fa kamar zai fad'i." Ta tab'e baki tace, "Asirin ne yake sakin sa sai a hankali." D'aya d'akin Mama ta shiga zuciyar ta fesss tayi wanka ta da alwala ta canja kaya tayi sallah ta d'auki wayar ta tana neman number Mum amma bata same ta ba. Suhaima ma a d'akin ta shirya tayi sallah ta fita zuwa restaurant d'in hotel d'in ta debo musu abinci ta dawo d'akin ta kawowa Mama ta kalli abincin tace, "bara na duba sji" ta fad'a tana tashi ta nufi d'akin da Asad yake.      A zaune ta same shi da alama ko alwalar ma baiyi ba hannun sa a kansa yayi shiru ko motsin kirki bayayi, k'arasowa tayi kusa dashi zuciyarta na sake jin haushin Rauda da tsanar ta tace, "Taya bazan tsani yarinyar nan ba tayi maka abinda ko sallah ka kasa tashi kayi bayan ba haka kake ba?" ta fad'a tana isowa inda yake ya kalle ta da jajayen idanun sa kafin ya saukar da idanun sa k'asa. "Daurewa zakayi ka tashi kayi wanka then kayi sallah sai kasha magani ko muje asibiti." Baya son mata musu ko kad'an hakan ya saka shi ya tashi ta rik'e shi tace, "Sannu Zaki, sai a hankali asirin zai bar jikin ka." _Asiri_ ya maimaita a zuciyar sa cikin wani irin yanayi na tunani da mamakin kalmar ya shiga band'aki, fita tayi ta barshi. Lokacin da ya fito yaga jakar sa ta kaya ya ya bud'e ya saka doguwar riga kamar kullum ya tayar da sallah bayan ya idar ya zauna yayi shiru yana jin kewa a zuciyar sa kamar marayan da ya rasa iyayen sa a lokaci d'aya. Hawaye yaji suna taruwa a idanun sa zuciyar sa na bugawa sosai amma yak'i barin kukan ya sakko. Kamar ya tuna wani abu sai ya d'auki waya da sauri da niyar kiran ta yaji Mama tace, "In ka sake ka neme inda take zaka had'u da fushina Asad, bana so ka sake waiwayar ta daga nan har a tashi duniya indai na kasance uwa a gare ka." Ajjiye wayar yayi a gefen jikin sa a sanyaye ba tare da yayi kiran ba ya daure zuciyar sa da ta karaya yana ji idanun sa na kawo ruwa kamar zaiyi hawaye amma ya mayar dasu ya hana faruwar hakan dan farin cikin Maman sa. Abinci ta ajjiye tace, "d'auki kaci." Kai ya girgiza alamun bazai iya ba yana runtse idanun sa, waya ta d'auka yana dannawa kafin ta saka a kunne tace, "Suhaima kawo masa tea." Ba jimawa ta shigo dashi a kofi ta Mama ta karb'a ta bashi ya karb'a yasha kad'an ya ajjiye kofin Mama ta bashi maganin hannun ta tace, "sha zaka ji dad'in jikin ka." Ya karb'a yasha ta sake fita jim kad'an ta dawo ta bashi wani a kofi tace, "karb'i wannan ma." Shima baice komai ba ya karb'a yasha ta kuma kallon sa tace, "ka kwanta ka huta yanzu anjima in ka tashi zaka ji dad'in jikin ka." Kai ya d'aga ya tashi tsaye kamar yadda tace ya zauna a gefen gadon tayi murmushi kana tace, "Allah yayi maka albarka Asad, Yadda kake son abinda nake so Allah ya baka abinda kake so kaima." Sai ya kalle ta sai kuma ya sunkuyar da kansa a zuciyar sa yace, _Abinda nake so kin raba ni dashi Mama._ "Suhaima kin kira Hydar d'in ya jikin mahaifin naku?" Ta fad'a tana niyar fita sai kuma ta dawo tace, "Nasan baka san bashi da lafiya ba ko?, suna Germany da Hydar jikin sa ya rikice lokaci d'aya." Idanu ya lumshe sai yanzu ya fahimci yadda akayi Mama ta sub'uto ta tawo Cairo ashe mahaifin nasa bashi da lafiya. Bayan sun fita yaso ya kira Hydar amma bazai iya ba haka ya kwanta lamo yana jinyar zuciyar sa ya lumshe ido abubuwa da dama suna yi masa yawo a ido ya bud'e yana jin sautin muryar ta a lokacin da take cewa yayi mata alqawari. Wani irin nauyi yake ji a zuciyar sa karo na farko a rayuwar sa yayi alqawari bai cika ba nan take tashin hankalin sa ya sake ninkuwa. Wayar sa da take kusa dashi yaga kira na shigowa ya kalla yaga Khalifa ne yake masa waya ya sauke numfashi dan ya tabbatar maganar Rauda zaiyi masa shi kuma bai san me zaice masa ba haka ya share har ta katse. Numfashin sa ya cigaba da janyowa da dak'yar kafin kansa yayi mugun sarawa k'irjin sa ya fara up and down daga zazzaɓi ya rufe shi lokaci d'aya. Suhaima ce ta shigo ganin halin da yake ciki ta kwallawa Mama kira ta tawo a guje ganin kamar zai mutu ya saka su danna emergency bell nan take sai ga ma'aikatan hotel d'in sun bayyana aka d'auke shi zuwa asibitin hotel d'in. A b'angaren Rauda lokacin da suka bar Four Seasons hotel a mota ya saka ta yaja suka wuce estate d'in ma'aikata y'an Nigeria wanda suke aiki a garin irin sa. Gida ne mai kyau plat mai d'auke da ado tun daga wajan sa har ciki, fita yayi ya bud'e gate d'in sannan ya dawo ya shiga da motar ya kuma fita ya sake kulle gate d'in kana ya zagayo ya bud'e bayan mota dan tana kwance a bayan motar yace, "Zaki iya fitowa?." Kai ta d'aga alamun eh dan bata so ya rik'e ta ta fito dak'yar ta iya tsayawa tana takawa a hankali har cikin falon gidan ya gyara mata waje ta zauna. Fita yayi ya shigo da kayanta sannan ya ajjiye ya shiga cikin gidan Jim kad'an ya dawo da magani da allura a hannun sa, ajjiyewa yayi ya k'arasa fridge ya d'auko yogurt ya dawo ya mik'a mata yace, "karb'i kisha sai kin saka wani abu a cikin ki magani zai miki aiki." Kallon sa tayi tana so tayi magana sai kawai hawaye ya fara zubo mata sharr duk sai yaji ya damu yace, "Haba chocolaty wannan kukan da kike yi wai duk na meye ne? Koma meye yake damun ki ki adana shi a gefe kisha magani tukunna." Mik'a mata ya kuma yi yaga ta kalla tana goge idanun ta sai tace, "kaina." "Na san yana miki ciwo shiyasa na baki dan ki sha sai kisha magani." "Bazan iya sha ba." "Zaki iya, karb'i" ya fad'a yana sake mik'a mata ta karb'a ta kai bakin ta tayi kurba d'aya ta ajjiye shi a jikin ta bata kuma sha ba. "Bazan cutar dake ba Rauda, ina miki kallon k'anwata duk abinda zan yiwa k'anwata da muke jini d'aya shi zan miki. Ki kwantar da hankalin ki ki nutsu in ma zuciyar ki na rawa a kaina kar ki damu wallahil azim bazan cuce ki ba. Asad ya sanni farin sani in koda na cutar dake zai nemo ni duk inda nake" ya fad'a cikin sigar kwantar da hankali yana kallon ta. Bata tanka ba ta d'aga gorar nonon tana sha har ta d'an sha da yawa ta ajiiye ya bata magani ta sha ya kalle ta yace, "shiga wannan d'akin da yake kallon ki huta zan kira deaf d'in naji ina yaje ya barki security suka yi miki haka. Kayan ki suna ciki in zakiyi wanka. Matar gidan bata nan ne tana wajan aiki amma nasan tana hanya." B'oyayyiyar ajiyar zuciya tayi jin yana da aure sai hankalin ta ya kwanta daman tunanin ta ta inda zata zauna dashi a gida d'aya shi ba wani nata ba bata ma tab'a ganin sa ba sai da tazo k'asar. Bayan ta shiga d'akin kwanciya tayi wai ko zatayi bacci amma ina bacci ya k'auracewa idanun ta sai tunanin da tasan zai damu zuciyar ta, babban tashin hankalin ta in ta koma gida me zata cewa iyayen ta? Auren da bai cike sati hud'u ba ya mutu ko mutu ko kuma shiru zatayi da bakin ta?, sanar dasu zatayi ta zama bazawara ko kuma shiru zatayi?. Da wannan tunanin bacci ya d'auke ta dan a maganin da ya bata harda na bacci dan ta huta. Ta jima sosai tana baccin bata farka ba sai dare ta kuwa tashi ciwon kan ya tafi sai kad'an ta kalli agogo ganin sallah ta wuce ta sai ta mik'e ba shiri ta shiga band'akin tayi wanka tare da alwala ta fito ta bud'e kayanta, gabad'aya sababbin kayan aka zuba mata a cikin akwatin wanda taje dasu guda d'aya ce. Hawaye taji suna niyar zubo mata tayi saurin mayar dasu dan bata ga amfanin kukan ba ta d'auki wacce taje da ita d'in ta saka ta tayar da sallah. Bayan ta idar tayi addu'a kamar ko yaushe ta tashi ta koma gefen gado tana yamutsa fuska ji take gefen marar ta yana riƙewa, d'an k'aramin tsaki tayi dan tasan hakan yana nufin period d'in ta yana gab da zuwa. Tagumi tayi hannu biyu da tunanin abinda ya fad'o mata zata kawar dashi ta koma wani amma ta kasa sai da ta tuna. _i promise you I will never ever leave you no matter what!._ kalmar sa k'arshe kenan tsakanin su ta mayar da kwallar idanun a lokacin aka fara k'wank'wasa k'ofar d'akin. Sai da ta nutsu sannan ta amsa bai shigo ba yace, "In zaki iya ki fito ku gaisa da Madam." Ba musu ta tashi ta yafa mayafin ta ta fita falon ta same su a zaune suna cin abincin ta zauna da murmushin yak'e a fuskar ta kafin tayi magana matar tasa tace, "Sannu Rauda, ya jikin naki?." Ganin matar ta sakar mata fuska sai taji dad'i tace, "Da sauk'i. Ina wuni." "Lafiya lau, ya zaman bak'unta?." Rauda tayi murmushi bata ce komai ba tace, "kiyi hak'uri yau aiki ya min yawa shiyasa ban dawo ba kina ta zaune ke kad'ai. Ga abinci kici ko zaki samu k'warin jikin ki" ta fad'a tana tashi ta zuba mata dankali mai Romo da naman kaza a cikin sa an yanka shi k'ananu. Rauda tace, "da kin barshi bana jin yunwa." Ta kalli Khalifa tace, "kaji fa Dear wai bata jin yunwa" ta fad'a tana mik'a mata tana fad'in, "kici Rauda mara lafiya sai da abinci." Ba yadda zatayi ta fara ci a hankali bata jin d'andanon abincin gabad'aya dan tayi loosing appetite. Matar tasa ta koma kusa dashi ta zauna suka cigaba da hira harta ci iya yadda zata iya ta ajjiye. Khalifa ya kalle ta yace, "Rauda na kira shi bai d'auka ba nayi masa message still bai reply ba, kin gwada kiran sa ke?." Shiru tayi bata amsa ba ya kuma cewa, "Halin Asad ne sai shi wallahi, wataƙila yana can ya keb'e kansa yace baya son magana amma duk da baya baici ya barki ke kad'ai ba." Rauda ta kalle shi idon ta na kawo ruwa tace, "ni dan Allah kasa na koma Nigeria basai kayi magana dashi ba." Da mamaki yace, "meyasa zaki koma ba tare da sanin sa ba? Naga tare kuke kuma yayan kine yana dakyau yasan halin da kike ciki kafin ki tafi." Rauda idanun ta yayi rau-rau tace, "basai ka sanar dashi ba ko kayi masa maganar ma bazai saurare ka ba, dan Allah ka saka ni na koma gida na gaji da zaman nan ina son ganin Ummana." Kallon Ramla matar sa yayi itama ta kalle shi Khalifa yace, "kar ki damu zaki tafi Nigeria in sha Allah. Amma ina shi Asad d'in yake? Meyasa ya tafi ya barki?, ke ba k'anwar sa bace ba?." Rauda tayi shiru bata amsa Khalifa yace, "ko ke ba k'anwar sa bace?." A hankali tace, "k'anwar sace." "To ina yake? Kin kira shi ke da kanki?." Sai kawai ta fashe da kuka Ramla ta kalle shi ta girgiza masa kai alamun ya k'yaleta sai yace, "Yaushe kike son komawa Nigeria d'in?." "Gobe" ta fad'a murya na rawa. Khalifa yace, "Allah ya kaimu sai ki tafi." Ramla matar sa tace, "Ba jibi daman zaka tafi ba? Ta bari sai jibin sai ku tafi tare kaga ba wani sanin kan garin nan tayi ba bai kamata ta tafi ita kad'ai ba. Kema a bauchi kike?." Kai ta girgiza alamun a'a tace, "Katagum." Ramla tace, "bauchin kenan ai, shima a can yake abokin Yayan kine zai mayar dake har gida kinga ba saba tafiya kikayi ke kad'ai ba gwara ki bari in Allah ya kaimu jibin sai ku tafi." Rauda ta d'aga kai alamun to sukayi shiru dukkan su Ramla ta lura a takure take sai tace, "ki shiga d'akin ki huta." Kamar jira take ta mik'e ta shiga ciki tana goge idanunta. Ramla ta kalle shi tace, "Shine yace maka k'anwar sace?." Khalifa ya girgiza kai alamun a'a yace, "Nine dai nake ganin hakan amma bai fad'a min ba gaskiya." "Ni sai nake ganin kamar ba k'anwar sa bace." "To wacece d'in sa da zasu zauna waje d'aya shida ita? Kin san waye shi kuwa wajan kamewa?." "Ka sani ko matar sa ce?." Wara idanu yayi yana kallon ta yace, "Dan sarkin Katagum ne fa ta yaya zaiyi aure ba tare da an sani ba? Koma ace ba kowa bane ta yaya Asad zaiyi aure bamu sani ba?." Ramla tace, "to ka sani ko baya buk'atar a sani d'in ne? Kayi tunani yanayin ta bai gwada k'anwar sa bace in ba kuma ta tabbata ba k'anwar tasa bace wacece d'in sa? Budurwa sa kenan zamu ce?." Ya girgiza kai yace, "A'a Asad bazai tawo da budurwa wata k'asa ba nasan halin sa." "To kaga kenan indai har ba k'anwar ba bace ba to matar sace, yanayin yadda take magana kamar sun samu matsala ita dashi ne." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "na dai fi tunanin k'anwar tasa ce, abinda ya d'aure min kai ina yaje ya barta?. In ya kasancewa matar sace babu ta yadda za'ayi ya tafi ya barta ita kad'ai domin kishin sa bazai barshi ya iya barin ta ba. Shine fa wanda nake fad'a miki in ya nuna takalmi yace yana so tofa duk yadda kuke dashi kar ka saka wannan takalmin yadda yace yana so nasa ne shi kad'ai, in kuma ta faru ya bar maka shi baya so kiyi tunani ace matar sace ya abin zai kasnace?." Ta girgiza kai tace, "akwai dai wani abun a biye Dear amma ni ban yadda k'anwar sa bace ba kallon matar sa nake mata, matsala suka samu har hakan ta kasance amma bazai bar k'anwar sa inda ka ganta ba. Tunda ya kasance mai kishi dole yayi kishin k'anwar sa. Kuma k'anwar sace zai tawo da ita k'asar nan su biyu kawai har ayi mata aikin k'afa ba tare da mace ba? Ka tuna suna da kud'in da za'a tawo da masu jinyar ta bama guda d'aya ba amma aka had'o su su biyu kawai, in ba matar sa ba babu wacce zai zauna da ita daga shi sai ita." Khalifa girgiza kai yace, "to Allah ne dai masani, zan jira naga zai kira ni daga yau zuwa gobe in bai kira ba kawai sai na mayar da ita Nigeria d'in mayi magana dashi daga baya." Daga haka suka cigaba da hira kafin Khalifa ya fita. [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *045.*          B'angaren Asad yayi baccin sosai mai cike da sabbin mafarkai kafin ya farka dan sai da aka amsa allurar bacci sannan baccin ya d'auke shi. A gadon asibiti ya ganshi ya kalli hannun sa yaga ruwa yana shiga ya dafe kansa yana sauke numfashi a sannan Mama da Suhima suka shigo. Mama ta kalle shi tace, "Sannu Asad, kaji dad'in jikin ka?." Kai ya d'aga alamun eh sai ga likita ya shigo ya k'araso inda yake ya zare masa ruwan jikin sa ya sake auna bp sa ya kalli Mama cikin turanci yace, "bp nasa ya sauka saura kad'an, daman ya firgita ne dalilin da ya saka jinin ya hau kenan but yanzu in ya samu nutsuwa zai dawo daidai." Mama ta girgiza kai kawai bata ce komai ba tana binsa da kallo jin wai harda hawan jini akan kucakar yarinyar da bata wuce mai goge masa takalmi ba. A sannan suka koma cikin d'akin su ya shiga d'aki yayi alwala yayi sallah dan sosai yaji dad'in kansa ya rage ciwo sosai. Bayan ya idar da sallah Suhaima ta shigo ta zauna kusa dashi tace, "Kayi haƙuri Yaya Asad na bata passport d'in ta da wayarta da kuma kayanta in sha Allah zata koma Nigeria. Sai dai kuma babu kud'in ticket" Suhaima ta daki kanta tace, "na manta ban bata ba Yaya, yanzu da wanne kud'i zatayi amfani ta siya?." Asad sai murmusa ya cize bakin sa ya lumshe ido ba tare da yace komai ba. Suhaima tace, "kazo falo inji Mama" tana fad'a ta Mike ta fita jikin ta a sanyaye. Bai jima ba ya fito tunda ya fito daga d'akin take kallon sa har ya k'araso ya zauna a kusa da k'afafun ta bata daina kallon sa ba tace, "Asad kaga yadda ka rame lokaci guda kuwa?." Shiru yayi baice komai ba kafin ta share zancen itama tace, "gobe zamu koma Nigeria akwai abinda kake so ka siya ne? In akwai ka siya yanzu dan jirgin safe zamu bi." Dak'yar ya fizgo maganar yace, "Babu." "To yayi kyau, in muka tafi da safe nasan zuwa azahar zamu je bauchi mu shiga katagum zuwa jibi dai nake so sarautar ka ta dawo hannun ka a had'a shagalin da bikin auren ka da Jidda a huta." Baice komai ba ko d'agowa ma baiyi ba balle yayi magana. Kamar ya tuna wani abu sai ya kalli mahaifiyar tasa yace, "Ya jikin takawa?." Mama tace, "Bamu samu Hydar a waya ba har yanzu." Ya kalli Suhaima yace, "Wayana." Tashi tayi ta shiga d'akin ta kawo masa ya karb'a yana dannawa yaga message d'in Dr Khalifa a notification hannun sa na rawa ya danna ya bud'e yaga abinda yace kamar haka, _Prince ina kaje ne ina ta kiran baka picking call d'in?, sister ka tana gidana nazo hotel wajan ka na tarar da ita security suna neman arresting d'in ta. Ka kira ni in kaga message d'ina bata da lafiya ma._ _Tana gidana._ abinda ya sake dawo masa kansa kenan ya runtse idanun sa yayi saurin fita daga message d'in ya shiga wajan kira yana nemo Hydar zuciyar sa na zillo ya danna kiran wayar Hydar. Bai d'auka ba ya sake kira nan ma bai d'auka ba sai ya k'yale shi Mama tace, "Bai d'auka ba ko?." Kai ya d'aga alamun eh tace, "muma baya d'auka in mun kira, Allah yasa ba jikin nasa bane babu dad'i." "Wanne County suka tafi?" Ya tambaya muryar sa na shaking. "Germany" Suhaima ta bashi amsa da tausayi. "Zan iya siyan ticket naje Mama?." Ta kalle shi ya sunkuyar da kai tace, "A'a daga nan babu inda zaka je sai Nigeria, ka daina wani tunani in ba wannan ba." Ya girgiza kai kana yace, "Allah ya wuci zuciyar ki." Shiru ya ratsa tsakanin su kafin yace, "in an min izini ina so na sha iska." Mama ta kalle shi kamar baza tayi magana ba sai kuma tace, "jeka, amma in kayi abinda na haramta maka kasan sauran." "Godiya nake" ya furta a hankali ya tashi ya fita daga falon ya sauka zuwa reception ya fita ya tsaya a kan titi kawai yana kallon mototoci hannun sa hard'e a k'irjin sa. Wayar sa tayi k'ara ya d'auko yaga sunan Hydar ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Sorry Deaf ka kira ni muna tare da Takawa ana bashi magani." "Meyasa ba'a sanar dani bashi da lafiya ba?." "Shi ya hana a fad'a maka shiyasa ban fad'a ba. Ya kake naji maganar ka wani iri kamar baka da lafiya." Asad baice komai ba ya juya ya shiga hotel d'in ya zauna a reception kana datse kiran ya kira shi video call dan yana so yaga mahaifin sa, d'auka Hydar yayi fuskar sa ta bayyana a screen d'in wayar shima haka tasa fuskar tajewa Hydar daga can b'angaren Hydar yace, "Subahanallah! Deaf meya same haka? Naga ka rame sosai." Asad yace, "nuna min Abbana." Ba musu ya juya Camarar ta baya ya haska mai martaba da yake kwance cikin wata na'ura kamar mai bacci, har kusa dashi Hydar yaje yana sake haska masa shi yana cewa, "tunda muka zo yake a haka sunce nan da kwana uku zai farfad'o in sha Allah kuma za'ayi nasara." "Anya kunje asibiti mai kyau?" Ya furta a hankali cikin tashin hankalin ganin yanayin da mahaifin nasa yake ciki. Hydar yace, "kasan dai duk abinda zanyi dan ganin ya samu lafiya zanyi Deaf, likita har daga India munyo booking gobe zaizo, mun gayyato na nan  Egypt ma shima zai zo a had'u su a duba ko za'a gano matsalar dan nan har yanzu basu gano komai ba. Asad yayi shiru baice komai ba Hydar ya kuma cewa, "ka sanar dani dalilin wannan ramar taka Asad, ina ita Raudan take?." Shiru Asad ya kuma yi ya sauke ajiyar zuciya kana yace, "Komai ya k'are Hydar." Hydar ya kalle shi bayan ya dawo da camera front yace, "ya k'are akan me? Kar kace min Mama tayi nasarar raba ku?" Ya fad'a yana kallon sa da alamun tashin hankali. Asad yayi shiru baice komai ba yana kallon Hydar kafin ya janye idanun sa yace, "ka kula da Abba dan Allah, zanzo nan kusa in sha Allah" yana fad'a ya datse kiran ba tare da ya bashi amsa ba. Shiru yayi na wani lokaci yana kallon wani wajan daban kafin yaja siririn tsaki ya tashi ya koma ciki. Kamar yadda Mama ta tsara da safe suka dira a airport k'arfe bakwai da rabi na agogon Cairo jirgin su ya lula sama suka nufo Nigeria. K'arfe d'aya saura suka sauka tun kafin su taso an sanar da driver da zai d'auko su a airport d'in suka same su suna ganin fitowar su a guje suka k'araso aka karb'i kayan hannun su aka take musu baya, mota personal Asad ya shiga shi kad'ai Mama da Suhaima suka shiga aka d'auki hanyar katagum. Gudu suke sosai nan da nan suka shiga katagum aka isa gidan sarki aka bud'e gate motar su ta shiga cikin gidan, da sauri aka fito aka bud'ewa Mama k'ofa shi kam Asad kafin a bud'e masa ma ya bud'e ya fito yana kallon gidan sai yake ji ya zamar masa bak'o kamar ba'a nan aka haife shi ba. Ciki suka nufa Asad yayi hanyar da zata kai shi apartment d'in su ta kalle shi ta cigaba da tafiya, yasan ma'anar kallon ko bata ce ba yabi bayan ta a gajiye. Tana shiga apartment d'in ta aka fara kawo gaisuwa amma babu wanda take kulawa har taje k'aramin falon ta wanda ba kowa yake zuwa ba ta zauna a kan kujera ya zauna a k'asa Suhaima ta wuce d'akin ta, kallon sa tayi tace, "Ban amince da d'akin ka na da ba dan haka zaka zauna a nan kafin a kammala komai ka koma b'angaren ka, aiki yayi nisa ko nace an gama ma." Shiru yayi baiyi magana ba tace, "ko baka ji bane?." "Naji. Ina neman izini zanje can d'in na d'auko abinda zanyi amfani dashi." "Ban amince ba ka fara hutawa kaje anjima, tashi ka shiga d'akin da Hydar ya kwanta." Bai musa ba ya tashi ya shiga tare da kullo k'ofa.       B'angaren Fulani Hajiya tana zaune labarin dawowar Asad yazo kunnen ta bata nuna komai ba sai da ta shiga d'akin ta ta zauna a gefen gado tayi dariya tace, "ita a ganin ta dawo dashi d'in da tayi shine mafita a gare ta?, bata san lokacin mune zai fara ba" ta fad'a da farin ciki tana d'aukar waya ta danna kira. Daga can b'angaren aka d'auka tace, "Albishir babba na kira na sanar dakai, Asad dai yau ya dawo gidan nan." Yace, "wasa kike ko gaske? Kin ganni kin saka na tashi zaune ban shirya ba." "Da gaske nake wallahi ai ko mintina biyar basuyi da shigowa gidan nan ba. Na fad'a maka daman duk yadda Rabi'atu zatayi sai tayi wajan ganin ta dawo da Asad gidan nan tunda har aka furta maganar mulki wallahi sai ta dawo dashi shiyasa nake zargin ta a ciwon Takawa." "Meyasa kike zargin ta?." "Sabida shine kawai zai hanata dawo da Asad a kaf duniyar nan shine kawai zai dakatar da ita, inda yana nan da bata isa taje ta tawo dashi ba ya sanar da ita sai da izinin sa zai dawo. Daren ranar da zai kwanta ciwo itace ta shiga wajan sa ta kuma jima kafin ta fito." "In ma dai itace ko ba ita bace mu hakan yayi mana daidai domin daman jiran dawowar Asad muke kuma ya dawo, da zarar an tamk'a masa mulki a hannun sa a wannan lokacin zamu fara gabatar da aikin mu."     "Haka ne. Ka sanar da master duk abinda yake faruwa a sake nutsawa a cigaba da aiki." "Wannan ko baki fad'a bama sai anyi" ya fad'a yana yanke wayar tabi wayar da kallo zuciyar ta cike da farin ciki burin su ya kusa cika.         Asad bai fito ba sai bayan la'asar ya samu kiran sabon sarki baiyi k'asa a guiwa ba ya garzaya wajan sa domin amsa kira. Da girmawawa ya nemi izinin shiga wajan sa aka bashi dama yayi sallama ya amsa tare da fad'in, "Shigo mana Asad." Asad ya shiga ya zauna a k'asa yace, "barka da hutawa." Yayi murmushi ya shafa kansa yace, "barkan ka dai Asad. Ya hanya? Ina fatan an dawo lafiya." "Alhamdulillah" ya furta a tak'aice ba tare da ya kalle shi ba. Yace, "Maman ka taje ta tawo mana dakai mun huta jira." Murmushi kad'an Asad yayi har lokacin ciwon zuciyar sa bai warke ba yana daurewa ne kawai. "Naji dad'in dawowar ka kaga yanzu sai a saka ranar da za'ayi bikin baka karaga ka hau mulki ni kuma nabi bayan yayana naga ya jikin sa yake." Asad yace, "Allah ya taimake ka ina neman alfarmar a jinkirta komai naje naga jikin sa na dawo." "A'a Asad, mulki akwai dad'i akwai wahala iya kwanakin nan da nayi akan kujerar mulki ni kad'ai nasan abinda na tarar a cikin sa. Jiran dawawar ka ya saka aka bani to ka dawo yanzu kuma zan baka, juma'a mai zuwa in sha Allah za'a yi bikin nad'i da kuma bikin auren ka da wacce mahaifiyar ka saka aka nemo maka auren ta komai ya dawo hannun ka a huta." Bashi da bakin magana yayi shiru yana ji kamar ya kurma ihu sabida takaici mai martaba ganin haka ya saka yace, "kada ka damu fa zaka iya mulki fiye da wanda mahaifin ka yayi, hak'uri zaka k'aro dan zama shugaba ba abu bane mai sauk'i, ka k'aro juriya ka k'aro addu'a da nutsuwa. Sai wannan rashin maganar taka kayi k'okarin ganin ka d'an canja kodan sabida talakawan ka." Asad yace, "Zanyi kokarin hakan in sha Allah." Yayi murmushi ya kuma shafa kansa yace, "Allah ya bada ikon hakan. Kaje zan sanar da mutane ranar juma'a in sha Allah zaka mallaki kujerar mulkin garin katagum. Daman an sanar da governor yana jiran ka dawo ne ayi komai a gama." Asad yace, "Godiya nake, a huta lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita ya d'an tsaya ya dafe kansa sabida ciwon da yake masa kafin ya cigaba da tafiya. Babu wajan wacce bai shiga sun gaisa ba a iyayen nasa yaga k'annen sa maza da mata sannan ya nufi apartment d'in su dan akwai abinda yake so ya duba, da sallama ya shiga falon sai kuma yaja ya tsaya yana yamutsa fuska sabida warin sigarin da yaji falon yanayi. Gabad'aya falon a hargitse kamar ba'a rayuwa a ciki ya ga ragoye-ragoyen sigari ga tokar ta ga kwalbar giya da aka sha aka rage. Ya rasa ranar da Aliyu zaiyi hankali a rayuwar sa ya d'auki sab'on Allah ba komai ba ya mayar dashi ado in baka yi ma baya abota dakai gani yake kamar ba mutum bane ba, sanin mahaifin su baya nan Mama ma bata nan shine yake yin abinda yake so babu wanda zai hana shi. Tsaki Asad yayi cikin jin haushi da takaici ya wuce zuwa d'akin sa ya zaro makullin a aljihu ya bud'e d'akin ya shiga. Yana nan yadda ya barshi sai dai yayi k'ura ya tura k'ofar ya kulle ya k'arasa d'akin karatun sa ya shiga, ya jima a ciki har yamma tayi sosai sannan ya fito ya kulle d'akin zai bar falon kenan yaji maganar Aliyu yana cewa, "A'a yaushe ka dawo deaf?." Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya k'araso gaban sa yana kallon sa ya d'aga masa gira yace, "Mama taje ta tawo dakai kenan" sai yayi y'ar dariya kana yace, "ni daman nasan Mama bazata tab'a barin ka ba sai ta dawo dakai. To ya matar taka tana nan ko ta raba ku?." Asad bin sa yake da kallo babu ta inda ya barshi a kammani sak kamar su iri d'aya ce musamman yanzu da yake magana a tausashe sai ka rantse Asad din ne yake magana, halayya ce kawai ta banbanta dan in Aliyu ya shiga waje yayi shiru baya magana tsaf za'a d'auka shine sabida tsantsar kamar da suke da juna. Asad yace, "Yaushe zaka daina wannan halayen naka?." Aliyu yayi dariya yana nad'e hannun rigar sa yace, "Our uztaz  kar ka damu na kusa saura kad'an jira nake na zama shugaba sai na ajjiye." "In ka mutu fa.?." Aliyu ya wara idanu sai kuma ya juya idanun kamar yadda Asad yake yi kana yace, "mutuwa ai ba yanzu ba Asad, akwai burikan da nake gab da cimmawa dan haka bazan mutu yanzu ba." Asad ya kalle shi jin abinda yace kamar ran nasa a hannun sa yake sai ya girgiza kai zai wuce Aliyu yace, "Na manta congratulations zaka zama shugaban mu nan da wasu kwanaki kafin a shiga season two." Asad ya tsaya sai ya juyo ya kalle shi Aliyu yayi murmushi ya shafa kai yace, "kayi hak'uri d'an karamin tunani ne irin nawa." Asad yace, "meyasa baka bi Hydar wajan Abba ba?." Aliyu yace, "sabida ina da abu mai mahimmaci wanda yafi wancan." Kallon mamakin da yaga Asad yanayi masa ne ya bashi dariya yayi y'ar k'aramar dariya yace, "Kar ka damu wannan ba komai bane. Nace saki nawa ta saka ka yiwa abar son naka?. Naga ma duk ka rame baka nustuwar ka da alama duk soyayyar tata ce ko?." Asad bai kula shi ba ya fita ya k'yale shi a zuciyar sa yana tabbatarwa shaye-shayen da yake yi ya fara tab'a masa kwakwalwa. Aliyu ya bishi da kallo yayi murmushi yace, "Yanzu aka fara wasan Asad mu zuba mu gani aga nida kai waye zai hau karagar mulki, nidai bazan bar maka ba Mama kuma nasan bazata bar min ba amma dai zamu gani da alama a wannan season d'in za'ayi kashe-kashe" ya fad'a yana zaro waya a aljihu ya buda ya mayar ya fita. B'angaren Mama tana zaune bayan ta tashi daga baccin gajiya suna waya da Hydar Mum ta shigo ta zauna a kan carpet jikin ta nata tashi khamshin turare tana kallon Mama har ta gama wayar ta kalli Mum tace, "Wani lokacin wayar ki bata da amfani Sadiya." Mum ta duk'a tanayi mata jinjina tace, "tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar gimbiya fulani yar sarki jikar sarki matar sarki kuma babar sarki." Mama tayi murmushi tace, "Labari na kira ki zan baki daman tun ina can Cairo d'in." Mum ta zaro ido waje tace, "Har anje kenan ranki ya dad'e?." "Gani ma na dawo, na kuma tawo da d'ana." Farin ciki ya bayyana akan fuskar Mum ta gyara zama tace, "Ranki ya dad'e wannan ai labari ne mai dad'in ji, Allah yasa dai ta sakar masa kurwa asirin ya karye." Mama tace, "to gashi nan dai har yanzu bai dawo daidai ba har a asibiti ya kwanta a can jinin sa ya hau amma na haramta masa sake waiwayar inda take nasan kuma bazai yi ba." "Dakyau Fulani, shiyasa nake fad'awa Jidda a koda yaushe samun irin ki a mata wallahi yana da wahala, Allah yayi miki baiwar kwakwalwa kina fahimtar komai yadda ya kamata." Mama bata amsa ba sai murmushi da tayi tana jin kanta a sama Mum ta kuma cewa, "An rabu dai ko?." "An rabu da k'aya, na saka ya sake ta yayi saki d'aya da yake nasan babu idda a kanta ban damu ba." Mum ta fad'ada murmushin ta cikin jin dad'i kana tace, "Alhamdulillah, addu'ar mu bata fad'i k'asa a banza ba. Amma fa duk da haka ranki ya dad'e kada muyi sake muyi masa abinda zai tsane ta har abada da ita da dangin ta kar wata rana labari ya sake dawowa baya." Mama ta girgiza kai tace, "Maganar ki gaskiya ce, Malam Audu baya iya komai ne yanzu ki duba aikin da muka bashi akan kashe ta har hijjabi muka samo amma nice nayi aikin shi baiyi komai ba." Mum tace, "Ranki ya dad'e bashi da lafiya sosai, jiya naje wajan sa akan aikin na samu sai jiya ya fara fitowa ma sabida ciwon da yayi kwana biyu ko waje baya zuwa. Amma yanzu zance kar ya aiwatar da kisa yayi amfani da hijjabin nata ya saka masa tsanar ta data dangin sa mai muni ma, yadda ko ya ganta a hanya zai bi ta kanta da mota ya wuce hkan zai fi yi mata d'aci a zuciyar ta." Mama tace, "haka yayi ki fad'a masa yadda akayi sai ki sanar dani, a wannan karon kar ya bamu matsala dan Allah." "Shi d'in banza" ta fad'a tana murmushi. Mama tace, "Ya kamata a fara shiri fa dan nasan bikin nad'in nasa bazai wuce juma'a ba kuma kin san da bikin auren sa za'a had'a a huta, ki fad'a Jidda ta fara shirin zama mata ga sarkin Katagum" ta fad'a tana kallon Mum tana murmushi. Mum ta sake washe bakin ta tace, "Ai wannan maganar kamar a kunnen ta ranki ya dad'e, za'a sha murna kuwa dan kwana biyu kwana take kuka." Mama tayi dariya kad'an bata ce komai ba Mum tace, "ya tsarin zaman gidan yake a ina zata zauna ranki ya dad'e?." Mama tace, "Zata zauna a apartment d'in kusa dana mai martaba dan aiki ma an gama zance, an gyara inda mai martaba ya tashi itama an gyara mata nata su kawai ake jira su shigo." Mum tace, "Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Mama tace, "Amin." Daga haka taja bakin ta tayi shiru Mum tayi murmushi a zuciyar ta tana fad'in, _Lokaci yazo Rabi'atu, lokacin da zan kwace duk wata isar da kike ji da ita tazo, lokacin da komai zai dawo hannuna yazo, lokacin da zan zama uwar sarki a madadin ki yazo, lokacin da zan ajjiye ki a gefe ki koma tamkar hoto yazo, lokacin da y'ata zata zamar miki ciwon ido yazo. Asad zai zama tamkar k'aramin yaro ne sai abinda Jidda taso zaiyi, ita zata sarrafa shi yadda take so bazan yi sake ba nafi kowa sanin halin ki sai na tabbatar da y'ata ta zama sama da kowa a masarautar katagum._ Mama ta kalle ta taga tana ta murmushi ita kad'ai tana kuma d'an kad'a kai alamun tunani take yi tace, "tunanin me kike yi?." Ta kalli Mama tace, "tunani nake burin k'awata kuma shugabata ya kusa cika ina tuna irin farin cikin da zakiyi a duk sanda aka d'ora Asad a wannan kujera, tuna zaki farin ciki shine yake bani ninkin farin ciki." Mama ta murmusa tace, "gab burina yake da cika kam, zan mallaki abinda na jima ina fata, a bayyane Asad zai kasance sarki ne amma a b'oye zan kasance nice nake mulki domin kuwa sai abinda nace yayi sannan zanyi. Lokaci yayi da Rukayya da Sa'adatu zasu san ni ba sa'ar yin su bace." Kallon ta Mum take yi tana maganar tana bata amsa a zuciyarta tana fad'in, _K'arya kike wallahi kema baya zaki koma duk wannan jin kan naki sai na sauke shi domin komai naki a tafin hannuna yake, sai na nuna miki nima bata wasa bace ba._ A bayyane kuma sai tace, "Haka ne ranki ya dad'e, zamuyi abinda muke za kuma mu bar abinda muke so." Mama tayi dariyar nishad'i tana kallon Mum tana taya ta a zuciyarta tana fad'in, _Anzo wajan Rabi'atu!._ _Fan's nima nace Anzo wajan._👐🏼👨🏻‍🦯🤐[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *047.*           Takawa take a hankali tana k'arewa gidan kallo ganin harda wajan ajjiye mota guda d'aya, dan kyau gidan yayi kyau ta juya tana zagawa tare da d'aga kai tana kallon gidan. Kai ta girgiza gaban ta na tsananta bugawa a bayyane tace, "Ina amfanin wannan hidimar an wulak'anta maka diya?" Ta fad'a tana jan jakar ta zuwa k'ofar da ta gani tana kallon ta. K'ofar mai kyau kalar kofi ta tura ta ta shiga a lokacin Sammani yana niyar fitowa, kallon kallo suke yana kallon ta tana kallon sa da murmushi dan taga alamun bai gane ta ba, y'ar dariya tayi cikin k'arfin hali tace, "Sammani ya dai?." Sai kuwa yace, "La wallahi ita, Anty Rauda ta dawo!" Ya koma a guje yana faman kiran Anty Rauda ta dawo. Dariya tayi ta kalli inda ya fito taga tsakar gida ne babba gabad'ayan sa tiles ne a k'asan sa gefe ga matattakalan sama ita duka tiles tabi inda Sammani yabi tana jiyo ihun sa har lokacin.         "Anty Raudaaaaa!" Aka fad'a da k'arfi lokacin da ta shiga babban falo madaidaici mai kyau mai d'auke da kujeru madaidaita da carpet har da tv bango da a.c da fridge. Ummulkhairi ta gani a guje ta rungume ta tana ihu ta rik'e ta itama tana cewa, "Ke zaki yar dani." Ta d'aga ta tana kallon ta tace, "Anty Rauda kinga yadda kika koma kuwa? Kinyi kyau kinyi kib'a gashi kina tafiya." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta juya ta kalli Khalil da ya shigo shima ya rik'e ta yana ihu tayi dariya tace, "Ina Rahma take?." Ummulkhairi tace, "tana gidan Yaya Ummi, kinga gidan da muka dawo muma mun zama y'an gayu." Rauda tace, "Ina Umma da Inna suke kun barni Ina ta zuba ban gansu ba" ta fad'a tana yin gaba suka bita a baya Khalil yana jan jakar ta zasu shiga wajan Umma suna ga Inna ta fito daga wata k'ofa tana fad'in, "Ashe da gaske kece Rauda, Tabd'ijam wannan in a hanya na ganki ai bazan gane ki ba." Rauda tayi dariya suka gaisa cikin farin ciki kafin ta shiga wajan Umma. Ihun su ne ya tashi Umma daga bacci ta fito daga d'aki tana tambayar lafiya taga Rauda na shigo k'aramin falon Umman ta nufe ta da sauri ta fad'a jikinta tana fad'in, "Nayi kewar ki Ummana." Umma da mamaki da farin ciki tace, "Rauda! Saukar yaushe?" Ta fad'a da mamaki da farin ciki tana kallon ta. Rauda ta d'ago daga jikin ta tace, "Umma wallahi nayi kewar ki sosai." Umma tayi dariya tace, "Muma duka munyi kewar ki. Alhamdulillah lafiya ta samu Rauda kece kike tafiya da k'afafun ki?."       "Anty Rauda ina tsarabar mu?" Khalil ya katse su ta kalle shi Umma ta riga ta magana tace, "Kwa dai barta ta huta dai tukunna kwa tambayi tsarabar." Rauda tabi falon Umman da kallo ganin sa ba kai girman na farko ba amma mai kyau komai akwai a ciki sa kamar waccan Umma ta kalle ta tayi murmushi tace, "Ki huta duka za'a baki labari, shiga ciki kiyi wanka ki samu ki kwanta duk da tafiyar jirgi gani nake ai ba wata wahala sai dai zuwa nan daga bauchi." "Ummana Ina Baba?." Umma tace, "Ya fita amma nan da anjima zaki ganshi." Rauda ta shiga d'akin Ummulkhairi ta biyo ta da jaka duk suka mara mata baya gabad'aya dok'in ganinta suke yi gani suke kamar an canja ta. D'akin babba mai d'auke da kayan gado komai akwai harda carpet a tsakiya ga band'aki a ciki ta girgiza kai tace, "Lallai da gaske kike Khairi mun koma y'an gayu" ta fad'a tana shiga band'akin zuciyar a cushe. Wanka tayi da alwala ta fito har lokacin suna nan tayi dariya ita kanta taji dad'in ganin k'annen nata ta kalli Khairi tace, "Ina kayana na wancan gidan?." Khairi ta mik'e ta bud'e mata wardrobe tace, "gasu a ciki." Ta kalle su tace, "to ku bani waje zan shirya." Ba musu duk suka fita tayi dariya ta d'auko riga da zani cikin kayan ta ta saka ta tayar da sallar la'asar da take kanta bayan ta idar Ummulkhairi ta shigo mata da abinci. Karb'ar abincin tayi taci kad'an bada yawa ba kafin ta ajjiye ta kwanta amma sai ta kasa baccin. Babban tashin hankalin ta abinda zata fad'a musu in suka tambaye ta hakan ya saka ta dinga juyi a haka baccin ya d'auke ta. Sai magriba ta tashi tunda ta tashi take jin hayaniya ta k'aru bata fita ba sai da tayi sallar magriba sannan ta fito falon sai kuwa akayi ihuu Rahma ta tawo a guje ta rik'e ta tana murnar ganin ta, itama rik'en ta tayi tace, "Nayi kewar ki Rahma." "Nima haka Anty Rauda, kinyi kyau har fari kinyi ko bleaching kika fara a can?." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Rahma ta kuma cewa, "Kan uba! Kinji fatar hannun ki laushi kamar audiga." Ita dai bata ce komai ba ta tawo cikin falon dan taga Baba a zaune ta k'arasa ta durk'usa har k'asa tace, "Barka da dare Baba." Baba ya kasa rufe baki sai dashe hak'ora yake yi yace, "lafiya lau yar albarka. K'afa tayi lafiya ko?." "Eh Baba." "Ma sha Allah, haka ake so ai. Kinga gidan mu yadda ya koma ko ta dalilin ki?." Gaban Rauda ya yanke ya fad'i tayi murmushi kawai bata ce komai ba kafin Baba ya kuma cewa, "Tare kuka dawo dashi mijin ki?." Gaban ta ya tsananta bugawa tace, "Eh tare muke." Baba ya sake washe bakin sa farin ciki yake ji kamar ya goya Rauda sabida alkhairin da ta kawo masa kana yace, "Shi ya kawo ki nan?." Rauda had'd'iye yawu tace, "A'a ya saka a kawo ni ya wuce gida zaizo daga baya yace." Baba ya sake sakin murmushi yace, "Allah sarki d'an albarka." Rauda dai bata iya cewa wani abun ba kuma jikinta yayi sanyi har Umma ta lura da hakan Baba yace, "Bara na fita na samo miki gashashiyar kaza kici dan nasan bakin naki ya saba da cin kazar larabawa" ya fad'a yana fita Umma ta bishi da kallon mamaki.     Gabad'aya Rauda ta bar nutsuwar ta had'a idanun da sukayi da Umma sai ta d'an wayance tayi murmushi tana sosa kai k'annen ta suka fara bata labari wannan yace ga abinda ya faru wannan ma ya fad'a haka suka deb'e mata kewa har akayi sallar i'sha tayi sallah ta shiga d'akin da tayi wanka d'azu. Umma ce ta biyo bayan ta ta ganta a zaune tayi tagumi fuskar ta gabad'aya ta nuna damuwa k'arara ta zauna kusa da ita tace, "Rauda akwai wani abun ne naga kin canja gabad'aya?." Rauda ta kalli Umman cikin alamu na rashin gaskiya tace, "Babu komai Umma. Nayi mamakin gama gidan nan cikin y'an kwanaki haka Umma, ki duba yadda yayi kyau kamar anyi shekara anayi" ta fad'a dan ta kawar da waccan maganar.      "Banda abin ki Rauda in da kud'i meye baza'a yi ba? Ai aiki akayi bana wasa ba kusan kwana suke ana aikin gidan nan lokaci kad'an aka gama ya bada umarnin zuba komai na gidan nan da kike gani cokali namu bamuyi amfani dashi ba duka sabo aka zuba mana namu bayarwa muyi wasu muka siyar. Kayan abinci kuwa kamar kasuwa dan wallahi zan iya ce miki akwai kayan abinci na shekara a gidan nan, banda kayan miya da nama da kaji da ake kawo mana duk sati. Ai mahaifin ki yaga amfanin haihuwar y'a mace da kullum k'orafin sa bai ga amfanin haihuwar mace tazo a babba a gida ba." Rauda ta girgiza kai tana kallon gidan fanka tana ta juyawa a d'akin tace, "solar ce wannan ko nepa?." Umma tace, "Solar akayi mana Rauda, awa ashirin da hud'u da wuta a gidan nan sai dai mu gaji mu kashe. Ke y'an unguwar nan fa cewa suke wai mahaifin ku yankan kai ya koma shiyasa yayi arzuk'i lokaci d'aya, wasu kuma suce ya siyar dake ya karb'i kud'in magana dai kala-kala; kaf unguwar nan babu gida mai kyaun wannan fa." Kafin tayi magana Umma tace, "Duk ranar juma'a kuma da aiken da za'a yo mana kud'in cefane, abinci baya yankewa a gidan nan Rauda madara, milo dasu ake shan shayi a gidan nan, duk baki ga mun canja munyi haske ba?. Sai yanzu na gano Asad ne ya siya miki magani ba Anas ba."       Ambatar Anas da Umma tayi sai da gaban Rauda ya yanke ya fad'i tayi shiru bata ce komai ba Umma tace, "Bamu da abinda zamu biya yaron nan ai sai addu'a, yayi mana abinda bamu kawo zai faru ba cikin rayuwar mu ba." Rauda ta girgiza kai hawaye na neman zubo mata tace, "Haka ne Umma." "Ina Raudan take!" Yaya Ummi ta fad'a tana shigowa ganin Rauda ya saka ta tawo da sauri tana fad'in, "Mutanen Egypt." Umma ta kalle ta tace, "A daren nan kika fito Ummi?." "Shine ya kawo ni a machine Umma, bazan iya zama har gobe banga Raudan ba" ta fad'a tana rik'e hannun ta cikin kewa. "Kan bala'i, Umma kinji laushin da hannun Rauda yayi? Ke wai wankan madara kike a can ne naga gabad'aya kamar an sauya miki halittta." Dariya kawai Rauda tayi amma ta kasa cewa komai Yaya Ummi tace, "Zama dashi ya koya miki rashin magana kema ko sarautar ce ta shiga jikin ki?." Rauda tayi dariya tace, "Haba Yaya sai kace chajin waya?." Sukayi dariya gabad'aya tace, "to gani nayi sai maganar da kika ga dama kike bada amsa. Rauda kalli wayar hannun ki a k'alla ta kusa miliyan; yarinyar nan Allah ya yarda, Baba me cewa waye zai d'auke ki yazo yaga ikon Allah." Umma tace, "ya sakko ai yanzu, abin mamaki shine ya tafi siyowa Rauda kaza da kud'in sa." Yaya Ummi tayi dariya tace, "To Umma ai dole ki duba kud'in da suke shigowa hannun sa ta dalilin wannan napep d'in yana zaune sai dai a kawo masa balance. Me zamu ce da yaron nan mu in ba godiya ba? Abinci da gagarar ku yake a gidan nan, ga talla da yake d'ora musu ashe ta sanadin tallan Allah zai b'ullo mana da alkhairi." Rauda tayi dariya tace, "Baba akwai drama ai." Yaya Ummi tace, "k'afa ta warke Rauda." "Ta warke Yaya." "Alhamdulillah, bamu da abinda zamuce sai dai mu gode Allah Rauda. Ina tsohuwar wayar taki a bani?." Rauda ta kalli wayar hannun ta kafin tace, "Wallahi tun a lokacin da wayar da tsohon layin ya saka su a shara." "Shara! Meyasa to bai bar miki ba?." Rauda tace, "ban sani ba wallahi" ta fad'a a tak'aice dan kawai dauriya take. Umma tayi murmushi kawai bata ce komai ba Yaya Rauda tace, "kuma su a can babu wanda zai d'auka nasan bola za'a kai ba kamar mu Nigeria ba. Lallai yana da kishi dan nasan yasan Anas ne ya baki shiyasa ya yar da ita." Umma tace, "Da kika ce Anas sai kika tuna min, bayan tafiyar ki baifi da sati ba yazo neman ki yake shaida mana matar da zai aura Allah yayi mata rasuwa ya dawo wajan ki a karo na biyu muke shaida masa auren ki. Baki ga yadda ya gigice ba Rauda har kuka sai da yayi ya bani tausayi sosai a nan take kuma yayi tawakali yayi miki addu'ar samun zaman lafiya tun daga ranar kuma bai yanke zumunci damu ba Rauda yana yawan zuwa mu gaisa har ya zama ma da yazo zai shigo gidan nan kai tsaye." Rauda jikin ta duk yayi sanyi sun kasa gane bata son maganar sabida abinda take ji a zuciyar ta tace, "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata." Suka amsa da amin. Yaya Ummi tace, "Ina shi mijin naki wai?." Rauda tace, "ya wuce gida bai zo nan ba." "Ai gobe dole na dawo ko dan na ganshi dan nasan dak'yar in ba goben zai zo ba." Murmushin yak'e Rauda kawai tayi bata ce komai ba domin tasan bazai zo ba har abada. Umma tace, "Ummi tashi ki tafi dare yana kuma yi." Yaya Ummi tace, "ya zan tafi ba tsaraba? Ke Rauda yanzu baki tawo min da komai ba?." Umma ta rik'e baki tace, "Amma anyi yayar banza, ita da taje jinya ina ita ina yo tsaraba?." Rauda tace, "bara muga akwai dogayen riguna Allah yasa suyi miki naga kin zama k'atuwa" ta fad'a tana tashi ta janyo akwatin ta ta bud'e tana fito da kayan. Cikin ikon Allah duk wad'anda ta siyo musu matsayin tsaraba duka sune a ciki har dana Baba nata ne babu sosai sai guda biyu; ta d'auko ta Umma ta bata ta bawa Yaya Ummin ta sauran tace, "Gata Baba, gata Inna, gata Rahma. Wannan takalmin na Ummulkhairi ne dana na Khalil da Sammani, wannan doguwar rigar kuma ta Yaya Shamsiyya da Yayar mu da Yaya Nafisa da Yaya fariha." Umma tace, "Kice kud'i kika saka ya kashe haka." Rauda tace, "A'a Umma ni bance zan yi tsaraba bama shine ya saka ni." Yaya Ummi tayi dariya tace, "wannan doguwar rigar gobe da ita zan fito na yiwa talauci barazana ko babu komai na saka rigar Egypt. Allah ya barku tare Rauda ya k'ara muku zaman lafiya me d'orewa; shiyasa kake murna in k'anwa mace ta samu jin dad'i domin gabad'aya iyalan gidan kune suka samu." Umma tace, "Gaskiya kam. Allah ya k'ara muku zaman lafiya ya saka mutuwa ce zata raba ku." Sharrrr hawaye suke fara zubowa daga idanun Rauda tayi sauri ta goge Yaya Ummi da ta kula tace, "Dole kiyi kuka Rauda jin dad'in duniya kin same shi ke kam sai dai fatan ki samu na lahira." Murmushi kawai tayi zuciyar ta nayi mata ciwo tana sake goge idanun ta. Umma tace, "Ummi ki tashi ki tafi itama a barta ta huta dare yayi." Rauda tace, "Ai a can Umma ba'a bacci da daddare sai da safe dare shine lokacin zuwa kasuwa da yawo." Umma tace, "haka akace su can daman dare shine rana." Yaya Ummi ta mik'e tace, "Rauda na wuce gobe zan dawo da wuri na sha labari" ta fad'a tana ficewa Rauda tayi dariya kad'an. Umma ta kalle ta tace, "ki kai musu tsarabar sai kizo ki huta kin dawo Nigeria nan ba can bane." Tashi tayi ta kwashi kayan ta fita dasu ta kai musu suka dinga ihu ana murna, Baba ma a lokacin da ya shigo ta bashi tasa ya bata kaza yana ta saka mata albarka kamar bashi bane yake kiran ta da mujiya ba.       Lokacin da ta koma Umma bata d'akin ta zauna ta bud'e kazar da Baba ya bata amma sai taji ta kasa ci gabad'aya ta rufe Ummulkhairi ta shigo ta bayar ta bawa Umma. Kwanciya tayi a kan gadon tayi lamoo kamar marainiya hawayen da take riƙewa suka sakko mata ta fara kuka mai sauti ko zata samu sassaucin da take ji a zuciyar ta. "Me zance musu ni Rauda? Nace musu ya sake ni sabida Maman sa bata sona?. Suna ta fad'ar hidimar da akayi dasu sabida ni, suna tayi min addu'ar cigaba da zama dashi ya zasu ji in nace musu ya sake ni? Ya zasu ji in nace musu na zama bazawara a cikin sati hud'u kacal?, ya zasu ji in na fad'a musu irin wulaƙancin da akayi min?. wa'inna ilaihir raji'un, ya zanyi ni Rauda nayi shiru ko na fad'a musu?. Daman can nasan sai hakan ta faru dole ya rabu dani daman akwai dalilin yin auren" Ta kuma fashewa da kuka mai tsuma zuciya. "Anty Rauda kukan me kike yi?" Ummulkhairi ta fad'a tana shigowa tana kallon ta. Goge idanun ta tayi da sauri ta kalle ta tace, "kaina ne yake min ciwo kad'an, karb'o min magani wajan Umma in akwai." Da to ta amsa ta juya Rauda ta tashi ta goge idanun ta sosai Khairi ta dawo da magani ta bata tasha ta haɗa da ruwa, Ummulkhairi tace, "Ki kwanta to Anty zaki ji dad'in ciwon kan Umma tace gajiya ce." Ta amsa da to ta tashi ta canja kaya ta saka na bacci ta kwanta zuciyar ta cike da saqe-saqe. *☆☆☆*           _Love you girl no get holiday, I do am all day everyday uhmmmm I need no one like oh no no, love you girl i get pom pom shey if u go know how I want pom pom shey ooo  I need no one like i need you oh no no  mmmmm, shower body down and come my lover mmmmm make i dirty you well with my love la la la, and I say hop on my bed let's sin, baby coman good sin good sin, no be bad sin good sin good sin._ wakar da take tashi kenan tun daga farkon estate ake jin sautin ta da muryar y'an mata da suka had'a baki suna yi kamar karatu. Cikin harabar gidan y'an mata ne y'ay'an masu kud'i kai da ka gansu da wayoyin hannun su kasan ba y'ay'an talakawa bane. K'atuwar banner ce a manne a bango anyi mata ado da balloons a jikin banner d'in an rubuta _welcome to Jidda's bridal shower_ an had'a da k'aton hoton ta da yayi kyau sosai kanta babu d'ankwali kamar ba y'ar musulmai ba. An yiwa gidan ado an zuba kujeru ana kid'a ga kayan ciye-ciye da shaye-shaye kamar kamar an dad'e ana tsara abin. Rawa suke matan cikin pink d'in dogayen riguna amaryar kuma ta saka blue mai haske kanta babu d'ankwali ta nad'e gashin ta tayi bala'in kyau kamar ba ita ba sai chasar rawa suke ana hotuna da video. Tun k'arfe takwas suke rawa ana kid'a har k'arshe sha d'aya a lokacin suka fara watsewa da nufin sai gobe za'a kuma had'uwa masu decoration suka cire kayan su kowa ya kama gaban sa. Jidda da Eman  bayan sun cire kwalliya an kwanta a gefe ana ta sauke numfashi gajiya Mum ta shigo tana fad'in, "kun sha rawa ai dole ku gaji ai." Eman tace, "Sai ma gobe ai Mum, daman ma abin yazo mana a haka da wlh event biyar zamuyi." Mum tace, "Allah ya kaimu goben, tunda ba'a nan zakuyi ba kuje ku k'arata." Eman tace, "Mum muna so fa gobe Asad yaje dinner d'in kinga ba'a yi dinner babu ango ba." Jidda tace, "abinda yake raina kenan kika riga ni fad'a, in bai je dinner d'in nan gobe ba an gama wulaƙanta ni a idanun k'awayena." Mum ta rik'e k'ugu tace, "Amma dai kin san Asad bazai je wajan dinner ba ko? Kamar kin san halin sa basai an fad'a miki ba." "Amma Mum wannan ai bikin sane yana da kyau ya ajjiye duk wata halayyar sa ya bari ayi shagali, in fa ranar ta wuce baza ta sake dawowa ba har abada." Mum ta kalli Jidda da take maganar tace, "Kar ki sakawa zuciyar ki domin ba zuwa zaiyu ba na tabbatar, kar abin yazo ya dame ki gwara kar ki saka rai." Eman tace, "Sai mu had'a shi da Mama dan baza mu bari a dinga munafurcin bikin mu kamar yadda muke na wasu ba." Mum tace, "ku kuka sani dai nidai na fad'a muku" tana fad'a ta fita ta barsu. Jidda tace, "Eman bafa zan bari hakan ya faru ba gaskiya." Eman tace, "Ina bayan ki dole mu san abinda zamuyi." Daga haka suka cigaba da tsara yadda abu zai tafi kafin goben.       Kamar yadda suka tsara washe gari Thursday tun safe k'awaye ta suka cika gidan aka sake k'aramin event mai taken henna party aka yi musu henna zuwa azahar aka fara make up bayan la'asar sun shirya dukkan su magriba ake jira a tafi wajan event. Duk wata hanya da Jidda tasan zata bi Mama ta saka Asad yazo tayi amma hakan babu nasara domin ta sanar da ita bazai zo ba tayi taron ta ita kad'ai kawai gabad'aya hankalin ta ya tashi. Magariba tayi k'awaye aka fara tambayar zuwan ango duk taron ya fita a kanta ta fara k'ok'arin kuka sabida a ganin ta ba k'aramin wulaƙanci bane rashin zuwan sa. An firfito harabar gidan Jidda tayi kyau cikin gown ash colour an yi mata mayafi mai adon kalar fabric d'in  a jiki yana jan k'asa sosai, tayi kyau ba kad'an ba henna hannun ta red and black ya haska fatar ta in ka kalle ta sai ka kuma sabida kyaun da tayi, fuskar ta a cushe babu walwala kana gani kasan ranta a b'ace yake daurewa kawai take yi. Babbar k'awar ta Farha tace, "Jidda kince yana hanya yana ina? Ana can fa an cika jiran mu kawai ake yi?." Idanun ta suka ciko da kwalla zatayi magana kenan ash d'in mota kirar benz ta danno hancin ta cikin gidan ta haske su da fitar motar. Kowa sai da ya kalli motar sabida kyaun ta da yadda aka d'auki hankalin su aka k'i bud'e koda tagar motar Eman ta kalli Jidda itama ta kalle ta Eman ta fara takawa zuwa gaban motar ta kwankwasa glass d'in tana jira a sauke taga waye. Zuuuu aka sauke glass d'in motar ba Eman kad'ai ba hatta Jidda da take tsaye a baya sai da gabanta yayi mugun fad'uwa suka zaro idanun su waje cikin d'inbun mamakin wanda suka gani zaune a cikin motar.......... [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *048.*         Eman baya tayi farin ciki ya cika zuciyar ta da fuskar ta lokaci d'aya hakan ya bayyana a gare ta domin basu tab'a tunanin ganin sa a wannan lokacin ba ta kalli Jidda cikin iyayi da yanga da nuna sun isa tace, "Sis your groom is here." Jidda tayi b'oyayyiyar zuciyar nan take fara'a ta bayyana a tare da ita ta fara takawa a hankali da niyar nufar motar. K'awar ta d'aya ce ta rik'e mata hannu tace, "Eman kice masa ya fito muyi pics before muje can please." Eman ta kalle shi a lokacin glass d'in motar yake kallo tace, "prince can u come out please?." Agogon Rolex d'in hannun sa kalar golden ya kalla ya kalli Eman ya sake d'auke kansa alamun bazai fito ba. Eman ta kalle su tace, "yace dare yana yi kuzo in an je can ayi hotunan." Jidda ta tako ta bud'e gaban motar ta shiga k'awayenta suka gyara maza zaman mayafin nata suka kalle shi suka ce, "Ango harda sha mana khamshi? Duk da yadda bikin naku yazo without mun shirya komai muka zo akayi abu kamar an jima ana shiri amma shine baza ka fito ba?." Kallon ta yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yayi murmushi kawai da ya tafi da hankalin su dukkan su. Kulle k'ofar sukayi ko wacce ta shiga tata motar ya fara juya motar ya fita suka biyo bayan sa. Kallon sa Jidda take yi kawai cikin zallar mamakin ta yadda akayi ya amince har ya fitar da ita kunya haka amma ta kasa magana sai murmushi da take yi cikin farin ciki.  Shi kuma gabad'aya khamshin turaren ta ya addabe shi nema yake ya dagwagwala masa lissafi hakan ya saka baya kallon ta driving kawai yake hankali kwance.      Kallon sa ta kuma yi sanye yake da shadda fara sai maiko take tana d'aukar ido hular kansa brown kalar aikin jiki yayi kyau sosai ba kad'an ba kamar ka sace shi ka gudu.  Juyowa yayi suka had'a ido ya d'aga mata gira d'aya ya kyalkyale da dariya kana yace, "Amaryar Prince Asad ko nace his princess, kinyi kyau fa sosai ba kad'an ba but turaren ki yayi yawa" ya fad'a yana cigaba da tuk'in sa. Ras ras rasss gaban Jidda ya fad'i yadda yayi maganar ya tabbatar mata da Aliyu ne ba Asad ba ta dafe k'irji tana binsa da kallon mamaki tace, "Aliyu!." Ya kalle ta yace, "Yeah Jidda." "Daman kaine ba Asad ba?." "Yeah nine, kema kin san ko za'a sake haifo ki ne Asad bazai zo ba dalilin da ya saka Mama tace kiyi hak'uri kenan." Kai ta dafe fuskar ta ta canja gabad'aya ta kalle shi tace, "kai kuma shine ya turo ka kenan ko kai ka turo kanka?." Ya d'aure fuska kamar ba shi ba shine ya gama dariya ba yace, "ni na turo kaina dan na taimake ki, kamar ki ace anyi bikin ki dinner babu ango akwai disgracing da yawa a cikin lamarin, time d'in da kuke waya da Mama naji komai na kuma yi niyar taimaka miki but in bakya so zan k'yale ki ne." Jidda ta sauke numfashi tace, "Na gode ka taimake ni amma yau sak ka koma min Asad har acting din rashin maganar sa kayi." Yayi murmushi yace, "Ina sane nayi hakan." Hannun ta ya rik'e yana murzawa kafin ya kai hannun sa bakin ta yayi mata kiss a hannun ta k'wace tace, "nifa matar k'anin kace ka dinga controlling kanka mana." Murmushi yayi mata kawai ya cigaba da tafiya har suka zo inda suke so. A nan aka fito ya fito shima suka tsaya shida Jidda ana hotuna kamar daman hoton akazo yi, sai daga baya aka shiga wajan taro da ya cika da k'awaye da yayyen k'awaye Mum harda Suhaima tunda taga shigowar su tasan ba Asad bane sai dai Aliyu dan yanayin rawar kan kawai ya nuna mata hakan dan tasan ko za'a yi ruwa da kankara Asad bazai zo ba. Sun ci sun sha sun kuma sha rawa abinsu anyi hotuna kamar babu gobe kafin kace kwabo hotuna sun zaga duniya. Sha biyu na dare suka tashi kowa ya koma gida Jidda taji dad'in bikin domin kuwa kaf k'awayen ta tasan babu wanda ya d'auko kyau da kud'i da mulkin Asad sai ita kawai, sunga Aliyu sun rikice gabad'ayan ina ga sun ga babbar giwar Asad? Duk da kamar d'aya ce amma akwai banbancin class. Facebook, whatsapp, Instagram, Twitter da sauran su kafin kace kwabo hotunan sun yad'u kana bud'e wayar ka ka shiga da abinda zaka fara karo kenan hotunann Aliyu da Jidda a jikin ko wanne an saka prince Asad and his princess Jidda. Mum ma kafin su dawo a nan taga hoton tun da ta gani itama tasan sai dai aikin Aliyu bana Asad ba ranta ya b'aci matuk'a jira take Jiddan ta dawo tayi mata fad'a. Lokacin da suka dawo kamar jiya kwaliyya aka goge ana cire kaya ita dasu Eman da sauran cousins d'insu da suka tawo tare Mum ta shigo d'akin ta kira Jiddan ta fita. A d'aki Jiddan ta same ta tana fad'in, "Mum na gaji bacci zanyi fa." Mum tace, "ashe bki da hankali ban sani ba Jidda?." Da mamaki tace, "me nayi Mum?." "Baki san ma me kika yi ba kenan ko? Dan baki da hankali an fad'a miki halin Asad akan kishi amma kika gayyato Aliyu yaje ya tsaya a gefen ki kamar shi zaki aura ko? Kalli wannan hoton har hannun ki ya rik'e, meyasa bakya gudun matsala ne kewai?, kin san da yadda auren nan zai yu kuwa?." Jidda ta turo baki gaba tace, "Nifa Mum bani na gayyace shi ba shine yazo da kansa kuma da farko na d'auka Asad ne sai daga baya na gane shine, kuma Mum banda ku ai babu wanda yasan ba Asad bane ba." Mum ta sake fusata tace, "Amma nida ke na fad'a miki Asad bazai je ba, mahaifiyar sa ta fad'a miki bazai je ba meyasa zaki tunanin shine yazo? Ke yanzu in yaga wannan hotunan yace ya fasa auren naki Aliyu zaki aura ko wa?."        "Mum meya kawo maganar fasa aure? Kin san dai bazai yi magana ba dan nayi hoto da Aliyu tunda Yayan sane jinin su d'aya." "Dan jinin su d'aya sai kije ki aikata wannan haukan? Me ya shiga kanki ne?." Shiru tayi tare da turo baki Mum taja tsaki tace, "in zaki nutsu ki nutsu gobe zaki zama matar aure kuma matar sarki kuma dole ki shiga hankalin ki in ba haka ba wallahi zaki sha wahalar da bakiyi tunani ba. Matar sarki da nutsuwa aka Santa da aji da nuna mulki na irin ki ba" tana fad'a mata haka ta barta wajan itama ta koma d'aki dan ita bata ga laifin data aikata ba. *☆☆☆*            "Bana so yau ya kwana a raye duk yadda za'ayi a tabbatar anyi Asad ya bar duniya, bana so ya wayi garin gobe da rai da lafiya a tabbatar an kashe Asad, kada Asad ya rayu rayuwar sa barazana ce ga tawa rayuwar, a tabbatar an kashe shi har lahira!." Cak Asad ya tsaya daga wucewar da zaiyi ya dawo da baya kasancewar dare yayi sosai yake jin me ake cewa yana kallon inda yake jiyo maganar duk da dare ne akwai haske sosai a wajan amma baya ganin wanda yake a tsaye a wajan. Motsi yaji a bayan sa ya waiga yaga mage ce ta gifta ya dawo da hankalin sa inda yake jin maganar amma babu kowa. Bin wajan yayi har indai ya hango inuwar mutum a wajan amma bai ga kowa a wajan ba, k'irjin sa bugawa yake yi bai san dalili ba yaji tsoro ya dabaibaye masa zuciyar sa k'in k'aunar mulkin na sake shiga jikin sa ya juyo jikin sa a sanyaye ya nufi b'angaren Mama zuciyar sa cike da saqe-saqe yana sake tuno muryar yana so ya tabbatar da muryar wanda yaji yana maganar.          Duk da bashi da walwala da kuzari zuciyar sa cike take da tsoro da fargabar abinda zai faru komai cikin takun isa da nuna tsantsar jinin sarauta na yawo a jikin sa yake takawa ya shiga apartment d'in mahaifiyar sa ya wuce falon farko ya shiga na biyu ya same ta zaune tana kallon wayar ta tana murmushi jin sallamar sa ya saka ta amsa ta d'ago ta kalle shi tace, "Asad zo kaga wani abu." Ba musu ya zauna a k'asa kusa da ita ta mik'a masa wayar ta tace, "Kalli kaga." Karb'ar wayar yayi ya kalli screen d'in ya kalle ta ya sake kallo alamun shi bai fahimta ba tace, "Jidda ce fa matar ka ta gobe ita da Aliyu amma kowa d'auka yake kaine, nasan baza kaje ba shiyasa ma ban sanar da kai ba gaahi Aliyu ya fitar da ita kunya." Jin an kirata da matar sa ta gobe ya saka shi yake kallon hoton baice komai ba ya mik'awa Mama wayar ta karb'a tace, "Jidda tana da kyau sosai  shiyasa na zab'e ta matsayin matar ka." Nan ma bai tanka ba amma a zuciyar sa cewa yake, _kyau fuska kawai kika gani babu kyawun hali. Kuma baki nuna b'acin ranki akan abinda Aliyu yayi ba sai ma murnar hakan kikayi, ta ko wanne b'angare bata dace dani ba._ Kallon sa tayi tace, "Ya shirye-shiryen goben? Bak'i sun iso daga Kano a naka b'angaren fa?." Numfashi ya sauke kana yace, "Banyi inviting kowa ba Mama tunda kinyi gayyaar ki nima tawa ce." Murmushi tayi tace, "Haka ne, Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya." Ya amsa da amin kafin ta kuma cewa, "Akwai maganin da aka kawo maka daga Kano na ajjiye maka a d'aki ka tabbatar kasha maganin tsari ne da Abie yake bamu kafin ya bar duniya. Kasan yau akwai wanda suke fatan kar ka kai gobe nima kuma na shirya musu, kasha maganin akwai coal da kasko kayi turare akwai na wanka duka kayi amfani dasu kafin ka kwanta." Kai ya d'aga kana yace, "in sha Allah." Tayi shiru shima yayi shiru yana jiran ta bashi umarnin tafiya dan dare yayi sosai  ita kuma bata ce komai ba sai danna wayar ta da take yi.     Agogo ta kalla kana tace, "kaje ka kwanta dare yayi sosai kana da hidima gobe." Kamar jira yake yace, "A tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya wuce hanyar sabon d'akin da ta bashi yana tunanin sabuwar rayuwar zai fara gobe mai cike da sark'akiya da tarin qalubale da kuma wad'anda suke k'okarin ganin bayan sa. *☆☆☆*          A daren ranar Rauda gabad'aya bata jin dad'in jikinta tun safe haka ta wuni duk da yayyen ta sun zo ana ta hira amma bata sake ba haka har dare yayi ta k'ule a d'aki tana aikin tunanin da ya cushe mata zuciyar ta. Numfashi ta sauke ta d'auki wayar ta ta shiga contacts din wayar tata tana duba numbers d'in wayar gabad'aya basu fi goma ba daga ta y'an gidan su sai Khalifa da matar sa sai kuma number Asad da yayi mata saving da Husband. Numfashi take saukewa tana kallon number kafin ta danna ta goge ta gabad'aya daga wayar tare da goge hawayen idanun ta. Datar wayar ta kunna wacce tunda ya bata wayar akwai ta akai har lokacin bata san kuma taya zata duba ba balle tasan yaushe zata k'are ko zata expire, Whatsapp ta shiga kasancewar dare yayi babu jama'a online ta fita ta shiga Instagram tana scrolling. Gabanta yayi mugun fad'uwa karo da tayi da hoton Jidda da Aliyu a caption an rubuta prince Asad and his Princess, zaune ta tashi tana kallo tana zooming ganin da gaske shi d'in ne ta cigaba da kallon hotunan a nan ta tabbatar biki ake yi gashi yana ta walwala kamar bashi ba. K'irjin tayi yana zafi kamar ana soya mata zuciyar ta tayi saurin kife wayar tana zare idanu jikinta yana rawa ta sake fashewa da marayan kuka mai tsuma zuciya da gangar jikinta. _Kukan me kike Rauda? Kukan dan ya sake ki ya auri daidai shi kome? Kishin sa kike?._ Da sauri take goge idanun ta amma hawayen sunk'i tsayawa ga k'irjinta da yake mugun zafi maimakon hawayen ya tsaya sai kwanciya da tayi ta kuma fashewa da sabon kuka ta kasa tsayar dashi ta dinga kuka mai tsuma zuciya ita kad'ai a kwance a kan gado tana birgima. Sai da tayi mai isar ta ta dinga sauke numfashi kafin dabara tazo ranta ta tashi ta shiga band'aki tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah ko dan taji dad'in zuciyar ta. Ta jima tana sallah a kan sallayar bacci ya kwashe ta ba tare da tasan lokacin ba.     Haka ta tashi washe gari bata da wata walwala lokacin da ta farka duka yaran sun tafi makaranta tayi wanka ta saka riga mara nauyi ta fito falon nan ta tarar da Umma a zaune a akan carpet tana cin d'an wake. K'arasawa tayi ta zauna kusa da Umman tace, "Ina kwana Umma." Da kallo Umma ta bita ta tsayar da cin d'an waken tace, "lafiya lau, lafiya naga fuskar ki haka kamar wacce ta kwana tana kuka?." Ajiyar zuciya tayi tace, "na jima banyi baccin bane ba shiyasa." "Meya hana ki baccin?" Ta fad'a tana kallon ta. "Haka kawai na kasa baccin." Umma tace, "Zaki ci d'an waken ne ko shayi zaki sha?. Tashi nayi da sha'awar cin sa shiyasa nayi in zaki ci akwai ragowa." Rauda tace, "Bana jin yunwa ma Umma sai anjima." Umma ta bita da kallo kafin ta fuskance ta tace, "Rauda akwai abinda kike b'oyewa a zuciyar ki tun dawowar ki, fad'a min me kike b'oyewa har yake saka ki damuwa haka?." Gaban Rauda yayi mugun fad'uwa tsoro ya bayyana a akan fuskar ta ta daure ta cize tace, "Babu komai fa Umma." Umma tayi murmushi tace, "Labarin zuciya a tambayi fuska Rauda, yadda kika rud'e tsoro ya bayyana a tare dake hakan ya tabbatar min akwai wani abun a k'asa. Meya faru a can Egypt d'in? Meyasa har yanzu Asad baizo ba kuma bai yi miki waya ba? Na lura damuwar da kike ciki ta tattara ta dalilin sa ko wani abun da ya shafe shi." Hawaye suka fara sakko mata tayi saurin gogewa amma ina Umma ta gani kafin ta goge tace, "Babu komai Umma." Jikin Umma yayi sanyi sosai tace, "K'arya kike Rauda akwai wallahi kawai baza ki fad'a min ba gashi nan kina kuka. Kodai wani abun yayi miki kafin ki dawo?."  Rauda zatayi magana Baba ya shigo ya k'araso ya zauna Rauda ta goge idanun ta tace, "Baba ina kwana." Baba da murmushi yace, "Lafiya lau Raudan Baba, lafiya naga fuskar ki haka?." Rauda tace, "ciwon kaine yake damuna Baba." "Ki sha magani gajiya ce bata gama sakin ki ba." "Toh Baba zan sha." "Asad d'in shiru na d'auka jiya zai shigo amma ban ganshi ba, ya kamata ace yazo ai an gaisa kuma munji maganar tarewar ki kunyi waya?." Girgiza kai tayi alamun a'a sai kuma ta d'aga kai alamun eh Baba yace, "to meya ce miki?." Rauda tace, "Akwai abubuwan da suka tsayar dashi amma zaizo kayi hak'uri." Baba yace, "Ai shikenan sai yazo, in na kira shi bana samun sa a waya yanzu; ni da in mukayi magana hankalina yafi kwanciya." Shiru tayi bata amsa ba Baba ya tashi ya fita kafin Umma tayi magana Rauda ta mik'e da sauri ta shiga d'aki. Da kallo Umma ta bita gabanta yana fad'uwa fargabar abinda ya faru wanda bata sani ba ya dabaibaye mata zuciya domin kuwa ta tabbatar akwai abinda ya faru b'oye musu take yi amma akwai abinda ya faru, to meye shi?. Babu mai bawa Umma amsa ta sauke numfashi ta cigaba da cin dan waken ta. *☆☆☆*          K'arfe d'aya da arba'in na ranar aka d'aura auren Jidda da Asad, d'aurin auren da ya tara manyan mutane sarakuna da y'ay'an su da jikokin su. Duk wani mai ji da kud'i da mulki yazo d'aurin auren domin kowa yasan mahaifin Asad haka mahaifin amaryar shima ba k'aramin mutum bane ba, bayan a gama aka fara watsewa kamar yadda aka tsara na jiki suka fara wucewa gidan gwamnati inda a nan ne Asad zai karb'o sarautar sa. Gabad'aya bashi da walwala balle kwanciyar hankali fuskar nan tasa kadaran kadahan baza ka fassara yanayin sa kai tsaye ba a haka aka je dubban jama'a da kowa na garin da wajan garin duniya ta shaida Asad matsayin sabon sarki Katagum. Masu hotuna da y'an jarida nan da nan aka fara yad'awa cikin lokaci kad'an magana ta fita daga Katagum ta zaga ko wanne sashi na duniya domin ko wacce gidan jarida sun saka haka gidan radio da masu d'aukar hoto.       Tunda aka tabbatar dashi matsayin sarki yaji kamar an d'ora masa wani abu a kansa mai nauyin gaske ga rawanin da yake kansa an canja masa ado zuwa na sarakai gabad'aya ya sake girma da kwarjini a cikin su ya sake yin kyau k'uruciyar sa ta b'uya mayyanta ta bayyana a a kan fuskar sa. Kid'a ake ana busa ana tambari aka nemi Asad yayi jawabi dogarai suka tawo a guje aka kare shi da zai mik'e ya tashi tsaye yana takawa a hankali da sandar girma a hannun sa ya k'arasa inda aka tanadar ya tsaya yayi shiru bai ce komai ba. Harrrrr yake ganin mutanen duk da ya saba tsayawa gaban jama'a yayi magana amma ba kamar wannan da yake da wannan matsayin ba, ya lumshe idanun sa ya bud'e yayi gyaran murya a hankali kana yace, "A'uzubillahi minal shaidanir rajim bismillahir rahmanir Rahim. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah ala kulli halin." Yayi shiru na wasu sacanni baka jin komai sai zallar kirarin da ake masa a wajan nan take yaji sabuwar izza na sake ratsa jijiyoyin jikin sa da gangar jikin sa, izzar da take banbance tsakanin d'an sarki da sarki ita yaji tana bin ko wanne b'angare na jikin sa ganin dukka mutanen da suke wajan a k'asan sa yake in aka cire gwamna. "Mai girma gwamnan bauchi, kwamishinoni, sanatoci, da dukkan wanda suka samu damar zuwan wajan nan ina yiwa kowa barka da wannan lokaci, ina matuk'ar godiya da wannan damar dana samu aka zab"e ni a cikin dubban mutane aka d'ora min nauyin mutanen da suke cikin garin Katagum." Ya sake yin shiru yana sauke numfashi tare da lumshe idanun sa yace, "In sha Allah a mulkin da zamu gabatar ko wanne mutum da yake zaune a cikin garin nan zaiyi alfahari da kasancewar sa a garin bazai yi dana sani ba, zai kuma yi farin ciki da zama a k'arkashin inuwar wannan mulkin." Dak'yar yake fizgo maganar ya sake yin shiru na wani lokaci kafin yace,         "In sha Allah zamuyi iya bakin k'okarin mu wajan ganin bamu cutar da kowa ba ba kuma mu saka kowa zubar da hawaye ba, zamu tafiyar da mulki fiye da wanda mahaifina ya tafiyar dashi badan mun fishi k'warewa ba sai dan zamanatar da namu da zamuyi cikin ilimin addini dana zamani. Ina yiwa kowa fatan alkhairi da fatan komawa gida lafiya, ina rok'on Allah ya k'arawa mahaifina lafiya ya tashi kafad'un sa nan kusa, ya bamu ikon farawa lafiya ya bamu ikon gamawa lafiya, ya bamu ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu." Addu'a yayi da larabci yana yi yana tsayawa sabida yanayin amma sai ka d'auka wani sabon style d'in ne hakan sai ya sake burge mutane musmaman yadda yake magana da ilimi a cikin ta. Tambari aka buga sai da gaban kowa ya fad'i shamakin Katagum wanda ya kasance kowa yaushe yana gefe ya matso da sauri aka k'arasa aka gyara masa wajan zama ya zauna bayan an kare zaman nasa.      Jijiyoyin kansa ya rik'e domin harbawa suke sabida ciwo gabad'aya ya gaji ya galabaita jira yake kawai a tashi kowa ya watse ga sallar la'asar a kansa baiyi ba. Ba jimawa mai girma gwamna yayi jawabi kafin a watse a tafi raka mai martaba sarki Asad cikin gidan sa. Gudu ake a kan titi ana jiniya mutane da yawa sun fito kallo ana d'aga masa hannu duk sai yake jin wani iri sabuwar k'asaita tana shiga ilahriin jikin sa, a haka aka isa gidan sarauta ya shiga ta k'ofar da mahaifin sa ya shiga yana tafiya ana kirari ana takawa a hankali cikin rashin kuzari. Kida ake a gidan ana wasa da dawaki ana busa jama'a sun cika sosai na cikin gidan da wajan gidan. B'angaren Mamaa aka fara raka shi Mama tana zaune ita da y'an uwanta da k'awayen ta jakadiya ta shiga tana gud'a tana fad'in, "Ga farin wata nan ya tawo ya haske ilahirin duhun da ya mamaye gidan nan, ga bangon sikari nan ga fari ka zak'i, yadda yake fari fari haka zuciyar sa take fara tass, ga inuwar bishiya nan mai kud'i ya zauna talaka ya zauna. Allah yaja da zamanin Sarki jikin sarki, Allah ya k'arasawa sarki lafiya da nisan kwana. Shigo lafiya Angon Fulani Jidda....."      Duka mutanen Falon sun tashi banda Mama da take jin kanta a sama kamar zai fashe Asad ya shigo falon yana kallonta ta saki Murmushi ya k'arasa kusa da ita ya tsuguna a k'asa ta d'ora hannunta a kansa tace, "Allah ya yiwa rayuwa albarka, Yadda ka fara lafiya yau Allah yasa ka gama mulkin ka lafiya."      "Amin, Allah yaja da ranki ya baki tsahon kwanan ganin mulkin jinin ki" dogarai suka fad'a cikin d'aga murya. Mama tace, "ka gaji kaje ka huta." Kai ya girgiza domin bazai iya magana ba ya mik'e sai a lokacin ya kalli matan falon yaga dukkan su sun zube a k'asa kowa da farin ciki a kan fuskar sa. Fita sukayi daga b'angaren ana ta kid'a ana busa ana ta tambari an saka masa lema a sama yana takawa mata suna gud'a da addu'a ana ta d'aukar sa hoto shi kuma yana dogara doguwar sanda mai cike da ado yana takawa a hankali yana kallon kowa d'aya bayan d'aya, aka raka shi har inda ya kasance b'angaren sa kafin kowa ya watse ya barshi shi kad'ai domin ya huta dan bazai iya zaman fada ba. *The beginning.......* FitattuBiyar Nana haleema [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *049.*          "Rauda! Rauda!! Rauda!!." Daga can cikin d'aki tace, "Na'am! Baba gani nan." Jim kad'an ta fito daga d'akin hannun ta rik'e da d'ankwali ta fito inda Baba yake tsaye tace, "Baba gani" ta fad'a tana d'aura d'ankwalin. Ya nuna mata waje yace, "Zauna" ya fad'a yana zama shima ta zauna a kan carpet tana kallon sa yace, "Ashe yau aka nad'a mijin ki ya koma sarkin katagum amma shine koda wasa baki fad'a min ba?." Gabanta ya fad'i har sai da ta dafe k'irjin ta ta d'ago ta kalle shi zatayi magana yace, "Wannan ai wulaƙanci ne kin san da abu baki sanar damu ba ai ko Allah ya sanya alkhairi maje muyi masa ko bamu muje wajan nad'in ayi damu." Yadda yake magana da fad'a ya saka ta had'd'iye abinda yazo harshen ta Umma da take zaune tace, "Ke kin san za'ayi sarautar ne?." Kai ta girgiza alamun a'a ta mayar da kanta k'asa bata ce komai ba.       "K'arya kike, ta yaya za'ayi masa sarauta matsayin ki na matar sa baki sani ba?, nafa san take-taken ki tun farkon auren nan ba so kike ba keda uwar ki da take goya miki baya shiyasa tunda kika dawo kike neman hanyar da zaki bi ki datse igiyar auren tunda kin samu abinda kike so k'afa ta warke ko?. Rauda tayi shiru bata ce komai ba Baba ya kuma fad'in, "Ta yaya zaki ce baki sani ba banda rainin hankali...? ko kuma kishin ya k'ara aure kike yi shine ya mayar dake haka?." Lumshe idanun ta tayi ta bud'e su bata da abinda zata ce Baba ya fahimce ta gwara taja bakin ta tayi shiru a ganinta hakan yafi mata kwanciyar hankali, "ba magana nake miki ba? Kishi kike ko me?" Baba ya sake katse ta a fusace. "Kayi hak'uri Baba, duka abinda ka fad'a ban san anyi ba, tunda muka dawo yace min a kawo ni gida zaizo nayi hak'uri daga nan ban kuma ganin sa ba." "Ba kince kuna waya ba?."      "Eh muna waya Baba amma ba sosai ba" ta fad'a a sanyaye tana mayar da idanun ta k'asa. Baba yaja tsaki yace, "Zamu je muyi masa Allah ya sanya alkhairi matsayin sa na wanda yake auren y'ata." Rauda ta kalli Baba hawaye ya ciko idanun ta tace, "Baba basai kunje ba, da ace yana so kuje da zai sanar dakai."  Umma da take gefe tace, "Abinda na gani kenan nima dai. Bai sanar damu ba kawai sai a d'auki k'afa a bishi ayi masa Allah ya sanya alkhairi?."       "Daman ai ke ba son auren kike ba tun farko dole kice haka da yake dukkan ku baku san ya kamata ba, ai ko babu komai tsakanin su ko dan aikin da akayi mata ta samu lafiya aje ayi masa balle matar sace. Dole naje nayi masa fatan alkhairi matsayin sa na sirikina." Rauda ta runtse ido jin kalaman Baba na k'arshe zuciyar ta nayi mata d'aci da mugun ciwo tana bugawa tunawa da abinda ya faru. Umma taja bakin ta tayi shiru Rauda ta sunkuyar da kai tana wasa da hannun ta Baba yace, "In ma akwai wani abun a ranki kiyi gaggawar kawar dashi, auren ku babu rabuwa in sha Allah dan ya auri wata ba wani abun bane ba itace daman wacce babar sa take so ya aura tun farko, ki kwantar da hankalin ki ki kawar da ko maye a ranki tunda shi yana son ki zance ya k'are. Yauwa dan aure kam babu rabuwa da izinin Allah" yana fad'a ya tashi ya fita Rauda ta bishi da kallo ta sauke ajiyar zuciya.       Had'a ido sukayi da Umma tayi saurin d'auke kanta itama Umma ta d'auke kai Rauda ta tashi ta shiga d'aki jiki a sanyaye Umma ta bita da kallo tana k'iyasta kishin auren sane ya mayar da ita haka. Baba ne ya kuma shigowa yana fad'in, "Ku gyara Anas zai shigo ku gaisa." Umma ta mik'e ta d'auko mayafi ta yafa Baba yace, "Kira Rauda su gaisa" yana fad'a ya fita Umma ta shiga d'akin Rauda wacce jin motsi ya saka ta saurin goge idanun ta ta fara neman kaya kamar daman can abinda take yi kenan. Umma ta kalle ta tace, "ki ta b'oye damuwar ki a ranki Rauda ke zata dama bani ba, ke zata zamarwa ciwo a zuciyar ki bani ba, bazan kuma tambayar ki ba na gaji da k'aryar babu komai d'in da kike fad'a min bayan a bayyane ba haka bane ba. Ki sako hijjabi Anas zai shigo zaku gaisa" tana fad'a ta fita Rauda jikin ta yayi bala'in sanyi zuciyar ta ta karye hawaye suka cigaba da zuba, Umma ce abokiyar shawarar ta a ko yaushe amma yanzu ta kasa fad'a mata damuwar ta sai take jin nauyi a zuciyar ta, hannu ta saka ta share idanun nata sannan ta sako hijjabi ta fito gaban ta yana tsananta fad'uwa.       Da Umma ta tarar suna  gaisawa ya tsuguna har k'asa yana murmushin da ya saba koda yaushe ta k'araso wajan kanta a k'asa, Umma tana murmushi ta kalle ta tace, "K'araso mana ku gaisa, Anas ga Rauda ta dawo." A tare k'irjin su ya buga duka su biyun ya d'ago idanun sa ya kalle ta a lokacin itama ta kalle shi sai ya saki murmushi tayi saurin kawar da idanun ta jin yadda k'irjin ta yake bugu kamar ana doka ganga.          "Ma sha Allah Rauda an samu lafiya" ya furta a nutse yana murmushi har lokacin yana kallon ta. Dak'yar ta iya furta, "Ina wuni." "Lafiya lau Rauda, ya k'arfin jikin?." "Alhamdulillah." "Ma sha Allah. Allah ya k'ara lafiya." "Amin na gode. Allah ya k'ara hak'uri ya jikan wanda suka rasu." Sai da ya murmusa kad'an kana yace, "Amin ya rabbil alamin, na gode" ya mayar da kallon sa ga Umma yace, "Umma zan koma." Umma tace, "To Anas na gode sosai Allah a yiwa rayuwa Albarka." "Amin Umma, sai anjima." "Ka gaida mutanen gidan" ya amsa da zasu ji ya fita ba tare da ya sake kallon Rauda ba. Yana fita Rauda ta zauna a akan kujera ta d'ora hannu a kanta ta rasa abinda yake mata dad'i komai sake lalace mata yake a zuciyar ta. Umma ta kalleta ta kawar da kanta bata ce komai ba sai ma tashi da tayi ta bar mata wajan dan tayi alqawarin bazata sake tambayar ta damuwar ta ba, tunda ta zab'i ta b'oye tai ta b'oyewa ba ruwan wani.        *☆☆☆* Asad tunda aka raka shi b'angaren sa ya kasa kwanciya ma balle ya iya yin bacci yana zaune a kan kujera yana k'arewa d'akin kallo yana jinsa kamar a mafarki abin yake faruwa.   Numfashi ya fesar ya d'auki wayar sa ya danna number Hydar bata jima tana ringing ba ya d'auka daga can b'angaren yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, Allah ya k'arawa sarki lafiya da nisan kwana, Allah ya karya mak'iyan ka ubangiji yasa kaga bayan su badai suga bayan ka ba. Ranka ya dad'e mai martaba sarkin Katagum da kewaye." K'aramin tsaki Asad yayi jin dogon surutun da Hydar ya cika masa kunne dasu yace, "Ya jikin Abba?." Hydar ya sake cewa, "Allah ya taimaki mai martaba jiki gashi dai bama ce ba dan har yanzu babu cigaba, a taya mu da addu'a Allah ya kawo d'auki da gaggawa." Asad yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "zan zo nan da bada jimawa ba." "Allah ya kawo ku lafiya, ya tsare hanya." "Amin."       Hydar yace, "Ranka ya dad'e mun samu labarin an k'ara aure Allah ya sanya alkhairi ya kawo yara masu albarka." Asad yayi shiru bai amsa ba Hydar yayi murmushi jin bai ce komai ba shima yayi shiru kafin yaji Asad yace, "Call me Asad pls ka daina min wannan dogayen yaren kasan dai ba so nake ba." "Wane mutum ranka ya dad'e, Ramin kura ai sai y'ay'anta ina ni ina furta wannan babban suna...?." Shiru Asad yayi na wani lokaci kafin yace, "Hydar still ina ganinta a mafarkina cikin yanayi mara dad'i, ga abinda Mama tace a kanta ban san me ya kamata nayi ba, zuciyata ciwo take." Jin yadda yayi maganar cikin rauni sai Hydar yace, "Ina neman afuwa ranka ya dad'e zanyi magana kamar yadda nake yi da yayana." Sai ya canja murya yace, "kaje ka nemi yafiyar ta Asad, ban san ta yaya kuka rabu ba amma nasan bata hanya mai dad'i Mama ta raba ku ba, babu lallai ma ka kuma yi mata magana bayan kun rabu dan nasan halin Mama bazata bada wata dama da zaku had'u da ita kaga kumaa akwai cutarwa. Yana dakyau kaje ka bata hak'uri in hakan zai yu dan gaskiya ba'ayi mata adalci ba." Ya sauke ajiyar zuciya yayi shiru baice komai ba Hydar yace, "nasan it's very difficult kamar ka as emir of Katagum ka bawa wata hak'uri wacce ba matar ka ba but babu yadda ka iya akwai hakkinta da yake bibiyar ka dole ka dinga ganin ta a mafarkin ka domin anyi mata abinda wataƙila ma tana kwance cikin ciwo, zuciyarta tayi rauni over maybe jin maganar rabuwa dakai wani abun ya faru da iyayen ta." "Ya zanyi Hydar? Mama tace in na sake yin wani abun da ya shafeta bata yafe ba, ta yaya zan iya zuwa wajanta?."         "In kaje wajan ta neman yafiya ba wani abun bane ba maganar Mama bazata hau kanka ba, da ka zauna da hakkinta fa tana can wataƙila tana cewa bata yafe maka bafa?. Akwai hakkinta a kanka fa dan wallahil azim ba'a kyauta mata ba kaima kuma da laifin ka dole in tace bata yafe ba ya bika." Asad ya sake yin shiru baice komai ba kafin ya sauke wayar daga kunnen sa ya kashe ya lumshe idanun sa yana sauke numfashi. Ya zama dole yaje ta yafe masa komai zai faru sai dai ya faru amma bazai iya zama bai nemi afuwar ta akan abinda ya faru ba duk da shima ba laifin sa bane ba.           Ana idar da sallar magariba kyawawan motoci sama da guda hamshin suna jeru a k'ofar gate d'in masarauta an kawo amaryar mai martaba Jidda gidan ta, tun daga motar da ta fito ake mata tambari ana busa algaita ana kid'a har aka kaita b'angaren Mama. Bata jima sosai a nan ba aka kaita ko wanne b'angaren na matan gidan kafin a wuce da ita b'angaren ta wanda yake kusa dana Asad a ajjiye ta kowa ya tafi ya barta ita kad'ai zuciyar ta fari tassss.         "Allah yaja zamanin Fulani, Allah yaja zamanin uwar gidan mai martaba. Ina neman izinin shigowa" aka fad'a daga bakin k'ofa Jidda da take zaune ta fuskar ta a bud'e taji izza na shigar ta tayi murmushi tace, "Shigo." "Godiya nake" ta fad'a tana shigowa ta zube a akan carpet tana yi mata jinjina tace, "Allah ya taimake ki Sunana Hansa'u Jakadiyar mai martaba ana kirana da Jakadiya babba,  Fulani Mama ce ta aiko ni wajan ki." Kamar baza ta bata amsa ba tayi shiru sai da taga dama sannan tace, "Ina jin ki."     "Allah yaja zamanin ki an turo ni dan na raka ki turakar mai martaba." Jidda ta k'are mata kallo taga a sa'a jakadiyar zata yi sa'ar Mum in ma bata girme ta ba ta d'auke kai tace, "Wajan mijin nawa ma sai an raka ni?." "Ranki ya dad'e kin manta matsayin ki a garin nan? Ai dole a samu wanda zasu take miki baya duk inda zaki je dan bamu so ko kud'a ya hau kan fatar ki." Wani irin dad'i Jidda take ji kafin ta d'aga kanta tace, "Kiyi aikin ki." Yadda ta fad'a cike da k'asaita sai da jakadiya ta kalle ta tana jinjina mulkin da Jidda zata zuba a gida kafin ta taso zuwa inda take ta mik'a mata turare tace, "Ranki ya dad'e tace a baki wannan ki shafa a jikin ki." Jidda ta karb'a ta bud'e kwalbar ta tsiyaya turaren a hannun ta ta shafa a fatar hannunta da wuyanta da k'afar ta gabad'aya. Jakadiya ta fita jim kad'an ta dawo da alkyabba tace, "Ranki ya dad'e ki saka wannan sai muje." Bata karb'a ba hakan ya sak Jakadiya ta saka mata da kanta tace, "Zamu iya tafiya?."       Jidda tayi gaba tana binta a baya tana takawa cikin isa suka fita daga d'akin suka fito falo na biyu suka ratsa suka dawo na farko suka fito harabar b'angaren nata Jakadiya tace, "in babu damuwa ranki ya dad'e akwai hanyar da zamu bi ta nan" ta fad'a tana nuna mata Jidda tabi wajan itama tabi bayan ta. Babu jimawa suka bayyana a harabar b'angaren mai martaba ba tare da sun fita harabar gidan ba gabad'aya, duk inda suka wuce zubewa ake ana gaishe su Jakadiya ce kawai take amsawa hannun ta rik'e da jasan alkyabbar Jidda gudun kar taja k'asa. A kyayattacen falo suka bayyana wanda yake ta tashin khamshi ga hotunan Asad na d'azu da aka kafa a falon yasha ado da zanen sarauta sai kyalli yake yi ga haske tarrr kamar rana.       Falon babba ne iya ganin ka babu abinda babu a cikin sa hakan ya saka Jidda k'are masa kallo cikin burgewa domin ya burge ta matuk'a tana aiyanawa a ranta wani adon sai gidan sarauta. Jakadiya tace, "Allah yaja zamanin ki nan ne iyakata daga nan ba'a bani umarnin sake d'arawa gaba. In kin min izini zan iya juyawa na koma." Jidda ta kalle ta kafin tayi mata alama da hannu da ta tafi ta juya ta fita tana fad'in, "Godiya nake ranki ya dad'e, a tashi lafiya." Jidda ta kalli steps a can gefen falon kai tsaye ta nufi wajan cikin takun isa ta k'arasa inda steps d'in take tana takawa har ta bayyana a saman ta sake karo da lafiyayyen falo wanda sai ka sauka k'asa zaka shiga cikin sa yayi round sai khamshi yake ga sanyin a.c. falon har yafi na k'asan kyau da tsari girma na k'asan zai fishi ta da manyan kujeru na alfarma kasancewar sa na saukar bak'i. K'ofa guda d'aya rak ta gani a falon kai tsaye ta nufe ta ta bud'e sai gata a doguwar hanya wacce aka mata ado da fulawa na roba masu wuta da dogon carpet jah a jikin sa an rubuta sunan Asad.        "Woww!" Ta furta a bayyane domin da gaske ya burge ta bada wasa ba. A nan taga k'ofofi sama da guda biyu ta rasa wanne zata shiga a ciki tana wannan tunanin taji an bud'e ta farkon yana fitowa suka had'a ido da ita tana kallon sa yana kallonta, waya ta gani a hannun sa sai taji yace, "Na ganta." Daga can b'angaren Mama tace, "Yauwa nayi mamaki da kace bata k'araso ba, dan Allah Asad karka bani kunya kaga dai itace zab'ina abinda nake so kuma kana so kayi k'okarin ganin ka sauke hakkin ta da yake kanka, kar ka duba baka sonta ka duba ni ka kuma duba hakki ka tuna kai yanzu babban mutum ne lokacin da zaka fara tara y'ay'a yayi.      Da hannu ya nuna mata hanya ta rab'a shi ta shiga tana kallon sa da murmushi, baima kula tana murmushi ba tunanin sa ya tafi ga ciwon da ya same shi a Egypt wanda tun lokacin har kawo yau bazai iya d'aukar nauyin ko wacce mace ba bai kuma mayar da hankali sosai akan neman magani ba tunda suka baro can gashi ba jimawa yayi ba aka yi wannan auren, jin bai baice komai ba Mama ta kuma cewa, "Ina fatan babu wata matsalar dai ko?." "Babu" ya furta a kasalance domin bazai iya furta mata abinda yake damun sa ba gwara yayi shiru da bakin sa kawai tunda mai martaba baya nan ya yiwa kansa magani a hankali.        "Ka tabbatar babu matsala Asad?." Ya sauke numfashi yace, "Babu Mama." Yana jin sautin murmushin ta tace, "Allah ya tashe mu lafiya, karka manta kasha maganin dana baka na tsari ne suna da mahimmaci sosai domin Abie kafin ya rasu duka su yake sha." "In sha Allah. A huta lafiya" daga haka ta datse kiran ya sauke wayar daga kunnen sa yana kallon sa.        Jimm yayi yana kallon k'aton mudubin da yake facing d'insa ya sauke numfashi ya juyo sai ya tsaya cak yana binta da kallon mamaki, ta cire alkyabbar ta ajjiye a gefe daga ita sai rigar bacci bak'a wacce iyakarta guiwa tabi jikinta sosai kana ganin komai na jikinta. D'auke idanun sa yayi daga kanta yaja k'aramin tsaki Allah ya sani ya tsani mace mara kamun kai irin ta in ya tuno yadda suke cafkewa da Aliyu sai yaji takaici ya cika masa zuciyar sa. Wajan madubi ya nufa ya ajjiye wayar sa ya k'araso inda take ya wuce ta ya shiga band'aki khamshin turaren ta gabad'aya ta dagula masa lissafi, tsigar jikin sa tana tashi kansa na sarawa zuciyar sa na bugawa sabida d'akin da yake ji a cikin ta. Bai jima ba ya fito fuskar sa da ruwa da alama alwala yayi ya kalle ta sai yaga tana murmushi tana kallon sa ya sake kallon ta shi abinda yake nufi taje tayi alwala ita kuma ta d'auka burge shi tayi. "Barka da dare" ta fad'a cikin murya mai sanyi. Wuce ta yayi jin tama raina masa hankali tun d'azu bata gaishe shi ba sai yanzu zata wani ce barka da dare, a dak'ile yace, "Barka" daga nan yaja bakin sa yayi shiru bai kuma ce mata komai ba. Ganin zata b'ata masa lokaci baiyi sallar i'sha ba ya saka shi tsayawa a kan sallaya yana niyar tayar da iqama sai yaji tace, "Bara nayi alwala nazo muyi banyi sallar i'sha ba." Tana fad'a ta shiga band'akin ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba badan mahimmacin Jam'i ba babu abinda zai saka ya tsaya ta, jim kad'an ta fito ta saka alkyabbar da ta cire mayafin da ta yafa ta kuma yafawa suka tayar da sallah. Sun jima a tsaye yana karatu a bayyane tun tana daurewa har ta k'osa ta fara yamutsa fuska, dak'yar ta kai i'sha d'in nan kafin ya sake mik'ewa dan ta burge shi ta tashi itama taga sunyi raka'a biyu amma ita ba'a jima sosai ba yayi sallama. Shiru babu mai magana ita binsa take da kallo kawai dan Allah ya sani tana sonsa yana kuma burge ta sosai musamman bakin sa tana ji kamar ta kamo shi ta tsotse bakin sa. kallon yaji yayi yawa a jikin sa ya d'ago ya kalle ta sai ya nuna mata leda da hannun sa kafin ya mik'e tsam ya fita ya bar mata d'akin. Jawo ledar tayi ta bud'e sai taja tsaki ganin abinda yake cikita ture ita ba kaza take son ci ba shi take buk'ata kawai ba wani abun ba.        Gajiya tayi da zaman ta tashi ta zare alkyabbar ta zauna a gefen gado tana jiran ya shigo amma shiru babu alamun sa ta kasa daurewa ta tashi ta fita ta bud'e d'aya k'ofar ta ganshi a zaune yana duba littafi, k'arasawa tayi kusa dashi ta zura hannayen ta a kafad'ar sa cikin shagwab'a tace, "kazo mu kwanta." Rutse ido yayi ya cize bakin sa ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani iri a jikin sa. Dumin lips d'inta yaji a cheek d'insa a daidai kunnen sa tace, "Come on my king." Bai bari ta fahimci ya shiga yanayi mara dad'i ba ya d'auke hannun ta daga kafad'ar ta ta matso kusa dashi tace, "My king pls." Shiru yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya cigaba da duba littafin hannun sa turaren jikin ta gabad'aya ya hautsina masa lissafi. "I'm coming" ya furta cikin muryar sa mai sanyi ba tare da ya kalle ta ba, bubbuga k'afa ta fara tana turo baki gaba tace, "Please ka tashi muje tare tsoro nake ji na kwanta ni kad'ai."        Shiru yayi ya cigaba da abinda yake yi ganin yayi mata banza ya saka tace, "zanje ka tawo yanzu dan Allah." Bai bata amsa ba ta fita ya kifa kansa a kan littafin yana jan numfashi dak'yar yana k'ok'arin daidaita kansa. Bai jima a haka ba ya d'ago kansa ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya fita daga d'akin. Kallon d'akin da take yake yi yana tunani a zuciyar sa domin bai san me zai mata ba in ya shiga, ya fahimci abinda take nema gashi shi kuma bashi da abinda take so d'in babu amfanin shiga hakan ya saka shi sauka k'asa ba tare da ya shiga ba.    Jidda tunda taji sa shiru kawai taja tsaki ranta a b'ace ta kwanta zuciyar ta na rawa sabida b'acin rai a haka bacci ya d'auke ta. *☆☆☆*          Aliyu yana tsaye yana kurb'ar lemo a glass cup yana kallon taga wayar  sa tayi k'ara ya duba ganin mai kiran ya saka shi ya d'auka daga can b'angaren akace, "Ranka ya dad'e an aiwatar da komai kamar yadda kace, na zuba maganin kuma tabbas ya tsallaka a d'azu." Aliyu yace, "zaka ga alert yanzu, ka tuna in naji maganar a bakin wani....." bai k'arasa ba mutumin yace, "baza ka barni ba." "Good" yana fad'ar ya yanke wayar yana murmushi.       "Asad lokaci yazo, lokacin ka ya fara nawa kuma ya kusa fara aiki, nan bada jimawa ba labari zai sha banban da wanda aka saba ji a ko yaushe. Lokaci Asad" ya fad'a yana murmushi ya kurb'i lemon nasa. Wayar sace tayi k'ara ya duba ganin mai kiran ya saka shi ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Allah yaja da ran yarima akwai matsala a binciken mu na d'azu na kira ka ban samu ba sai yanzu."        "Meye matsalar?." "Yarinyar da Asad ya saki akwai yuwar dawowar ta masarauta kuma matuk'ar ta dawo komai ya lalace." "Ta yaya zata dawo?." "Shine abinda ban sani ba, amma binciken mu ya tabbatar min da akwai yuwar dawowar ta, cikin kashi d'ari akwai tabbacin kashi saba'in na dawowar ta dole a d'auki mataki." Aliyu yace, "Me kayi game da hakan?." Yace, "na fara aikin da zan saka ya manta da ita da dangin ta baki d'aya na sanar dakai ne sabida gudun matsala in akwai abinda zakayi a naka b'angaren sai a had'a k'arfi da k'arfe." Aliyu yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "ayi abinda ya dace nima zan san abinda zanyi" ya fad'a yana datse kiran wayar yana kallon tagar d'akin cikin sabon tunani. Murmushi yayi samo mafitar da yayi a zuciyar sa ya cize baki yana girgiza kai cikin gamsuwa da shawarar da zuciyar sa ta bashi yace, "Asaddddd!" Sai ya yi y'ar k'aramar dariya yana sake taune lab'b'an sa zuciyar sa cike da mugayen abubuwa wanda ya tsara domin kuwa kashe Rauda shine abinda ya fara zuwa zuciyar sa. *Akwai kura.* FitattuBiyar Nana Haleema. [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *050.*            A zaune take a gefen gado ta shirya cikin doguwar riga ta lace tayi mata kyau sosai fuskar ta a cushe babu walwala hannun ta rik'e da waya a kunne tana magana, yadda take maganar zaka gane da wacce take yi daga can b'angaren akace, "Ke Jidda bana son k'arya fa." Jidda tace, "Wallahi Mum da gaske nake; ni tunani nake ma anya za'ayi abin arzuk'i da mutumin nan?." Mum tace, "To meya faru haka? Nifa bana so a d'auki lokaci mai tsaho bai mayar dake cikakkiyar matar sa ba dan in hakan ta kasance akwai matsala wallahi." "Hmmmm ban san meye ba." "Amma mu bashi lokaci dan jiya ta wuce ai akwai yau ki san yadda zakayi ki tabbatar wani abun ya shiga tsakanin ki dashi kafin kwanaki bakwai d'in nan su wuce, suna da matuk'ar mahimmaci a zaman auren ki dashi bana so a samu matsala Jidda."        "To ni Mum ya zanyi? In bai neme ni bafa?." A fusace tace, "ke baza ki neme shi ba? Ai naga igiyoyi uku ne na auren sa a kanki kina da hakki a kansa, kin san kalar bak'ar wahalar da nasha kafin a samu azo wannan ranar?. Cikon burina kuma shine kasancewar ki cikakkiyar matar sa." Jidda tace, "Na fad'a miki abinda ya faru ma fa jiya Mum in ta sake faruwa fa me zan masa?." Mum tayi shiru tana tunani kafin tace, "Barni dashi ni nasan abinda zanyi amma duk da haka kiyi iya bakin k'okarin ki wajan ganin an wuce wajan matsala ce bana so Jidda." Jidda tace, "Zanyi." Mum tace, "ya dai kamata. Ga Eman nan ta tawo zata kawo miki magunguna da zaki sha ki shafa kiyi wanka dasu, ko wanne an rubuta yadda za'ayi amfani dashi a jiki ki karanta dakyau nasan halin ki bakya nutsuwa wani lokacin akan wannan maganin ki nutsu ki karanta sai kiyi amfani dashi." Jidda tace, "Mum duka maganin nan na meye kike d'ura min?." Mum tace, "baki da hankali, a kaf duniya ina d'aya daga cikin wanda suka san halin uwar mijin ki zatayi k'ok'arin ganin ta mallake ki a yanzu sai abinda tace zakiyi ni kuma badan haka na bari kika shiga gidan nan ba dan a nuna mata akwai iyakar ta ne, shiyasa nake dafa ki yadda ya kamata ta yadda komai zata turo miki bazai same ki ba." Jidda tace, "Ina so nima yadda yake fizge-fizgen nan yana k'in yi min magana nan gaba ya dawo sai abinda nace zaiyi." Mum tace, "to ki nutsu kiyi abinda duk na fad'a miki, babar sa tana da mugun wayo sosai da iya bakinta zata mallake ki sai kinyi takatsantsan." Jidda tace, "Toh Mum zanyi." Bud'e k'ofa akayi hakan ya saka ta kalli wacce ta shigo tayi murmushi kafin suyi sallama da Mum ta kalle ta tace, "Suhaima." Itama kallon ta take tace, "Amarya."        Y'ar dariya Jidda tayi Suhaima tace, "In kin gama wayar Mama tana neman ki a apartment d'inta." Jidda tace, "na gama muje." Tare suka fito daga falon suka fito daga b'angaren ta jakadiyar ta tabi bayan ta da sauri duk inda ta gifta ana zubewa ana gaishe su hakan ya k'arawa Jidda girman kai take jin kamar ita kad'ai ce mace ma a duniya.          A falo suka samu Mama tana zaune tana waya da Hydar akan jikin mai martaba suna k'arasa shigowa ta kashe wayar tana bin Jidda da kallon k'urilla tana son ta gano wani abu a tare da ita, a k'asa Jidda ta zauna tace, "Barka da Safiya Mama." Mama tayi murmushi tace, "Barkan ki dai Daughter, ya kwanan bak'unta? Duk da gidan ba bak'on ki bane amma mijin naki bak'on kine." Murmushi tayi kad'an kana tace, "Alhamdulillah." "To yayi kyau. Kinga masu yi miki hidima na tura miki ko?." "Eh Mama, na gansu har mun gaisa." "Sunyi miki ko a canja?." "Sunyi Mama ba laifi." Mama bata ce komai ba tayi shiru ranta ya b'aci domin kuwa ta fahimci babu abinda ya had'a Jidda da Asad a daren jiya.        "Asslamu alaikum" Eman ta fad'a tana shigowa falon. Suka amsa a tare Eman ta k'araso ta zauna a k'asa ta gaida Mama ta amsa fuska a sake tana tambayar ta gajiyar biki. Ta kalli Jiddan tace, "ku koma can sai kuyi hirar." Daman haka suke so suka mik'e suka fita suka koma b'angaren Jiddan. Suna fita ta d'auki waya ta kira number Asad amma bai d'auka ba sai ta share bata kuma kiran sa ba tana jiran ya kira ta taji dalilin da ya saka baiyi abinda tace masa ba.      Shi kuwa Asad da ciwon kai ya tashi mai zafi bayan yayi mafarki da Rauda tana kuka sosai tana bazata yafe masa ba tuna mafarkin shine yake sake yautsina masa lissafi hakan ya saka shi zama waje d'aya ba tare da yaje ko ina ba. Yana zaune yake jin k'arar wayar sa bai samu ya d'auka ba dan bata kusa dashi hakan ya saka bai san wanda yake kira ba gabad'aya baya tare da nutsuwar sa. Sake kiran wayar da akayi ya saka shi ya mik'e dakyar ya k'arasa inda wayar take ya d'auka nan yayi karo da sunan Uncle Mubarak yana yawo a kan screen d'in nasa.       D'auka yayi ya k'arasa ya zauna a akan kujera ya saka a kunne yace, "Barka da safiya Uncle." Yace, "Barka da safiya Ranka ya dad'e." Asad ya yamutsa fuska shi sam baya so yaji suna yi masa irin haka dan yana sarki ai gaba suke dashi kuma iyayen sane bai kamata su dinga girmama shi haka ba duk sai yaji wani iri, wannan dalilin yana d'aya daga cikin abinda ya saka ya tsani mulki.        "Uncle zamu iya magana dakai?." Daga can b'angaren yace, "Ina sauraro." "Uncle please ko zaka shigo cikin gida?." "Umarni za'a bayar aikin na cikawa, gani nan ranka ya dad'e." Asad ya sauke wayar ya kalli missed call yaga sunan Mama ya danna kira ya saka a kunne ta d'auka da sallama kafin yace wani abun tace, "Asad akwai damuwar data hana ka kasancewa da matar ka jiya?." _Hasbunallahu wani'imal wakil_ ya furta a zuciyar sa jin tambayar da take yi masa ya lumshe idanun sa ya bud'e baiyi magana ba tace, "Ba magana nake maka ba? Ko baka ji bane?." "Tuba nake Mama." "Fad'a min dalilin hakan." "Maamaaaa" yaja sunan ta sosai sai kuma yayi shiru tace, "Amma kace min babu matsala a daren jiya ko? Wulaƙanci ne ya saka ka aikata hakan kome?." "Kaina ciwo yake min Mama, Allah ya wuci zuciyar ki bada son raina ba nima." Numfashi ta sauke kafin tace, "Kasha maganin ciwon kan?." Kamar yana gaban ta ya d'aga kai kafin yace, "nasha." "Allah ya k'ara lafiya. Amma ka tabbatar ka sauke nauyin da yake kanka bana son a sake samun matsala matuk'ar kana son na daina yi maka maganar nan. Ko akwai matsala?." Ya girgiza kai alamun a'a kafin yace, "Babu." "To kayi abinda nace." Shiru yayi hakan ya saka tace, "Yaushe zaka yi zmaan fada ne?." "Ranar Monday in Allah ya kaimu." "To yayi, Allah ya kaimu. Akwai wanda ya kawo maka wani abun ne kaci?."           "A'a." Tace, "to ka nutsu da ka san abinda hannun wanda zaka dinga ci, masu abincin ka na ware su daban na amince dasu baza su cutar dakai ba in kuma matar kace zata dinga yi maka fine." Shiru yayi bai amsa ba jin bai bata amsa ba sai ta tuna yace yana ciwon kai sai ta yanke wayar ya sauke wayar yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudu. "Ya zanyi da Mama? Ya zanyi da yarinyar nan?" Ya furta a bayyane yana dafe kansa jijiyoyin kan suna harbawa. _Ina buk'atar neman magani_ ya furta a zuciyar sa yana shafa fuskar sa cikin rashin sanin abinda zaiyi.         Wayar sace tayi k'ara ganin mai kiran sai ya d'auka tare da tashi ya fita daga d'akin ya sauka zuwa falon k'asa ya tarar da Uncle d'in sa a zaune yana ganin sa ya mik'e tsaye Asad ya k'araso ya zauna a akan kujera Uncle zai zauna a k'asa yace, "dan Allah Uncle ka zauna akan kujera, bana jin daɗin hakan ko kad'an." Uncle ya zauna akan kujera yana murmushi yace, "to ya za'ayi ranka ya dad'e? Mu talakawan kane dole mu girmama ka yadda ya kamata. Baka ji karin maganar da ake cewa a banza wai talaka ya girmi mai mulki ba?." Asad yace, "Uncle i need your help." Wambai yace, "wanne irin taimako?." "Ka kasance a kusa dani ko yaushe Uncle, ban san komai na sarauta ba ina buk'atar ka a tare dani please" ya fad'a yana dafe kansa da suke harba masa sabida ciwo. Uncle yace, "bank'i taka ba zaki, amma ni bani da sha'awar cigaba da mulki gaskiya jira nake litinin tayi ranar da zaka fara zaman fada zanyi resining daga kujera ta zan bi d'an uwana naje naga yanayin jikin sa ko hankalina zai kwanta." Asad kamar zaiyi kuka yace, "Nima ina so naje jikina yana bani akwai abinda yake faruwa a can d'in, dan na amince da Hydar ne da zan iya cewa bai mayar da hankali wajan nema masa lafiya ba, gangar jikina ne a nan Uncle amma zuciyata tana tare da Abba." Yayi shiru yana had'd'iye yawu na wani lokaci alamun ya gaji da magana Uncle yace, "samu nutsuwa sosai, Sannu."         Ya cigaba da fad'in, "Ban san komai a nan ba Uncle in ka barni waye zai nuna min yadda abin yake? Ina so ka kasance a side d'ina always please." Uncle ya sauke numfashi yace, "Wannan aikin Uncle d'in kane Yahuza waziri kenan, shine yake da hakkin binka duk inda kake domin a sarautar ma daga sarki sai waziri." "Ta ya zan iya tafiya dashi Uncle? Kai d'in dai please." "Ai bazai yu bane Asad, na farko ni na ajjiye sarautar nan, na biyu kuma Yaya Yahuza shine yake da wannan hakkin." Asad yace, "Uncle nasan definitely Abban Suhail zai ajjiye sarautar nan sabida zai ce bazai yi mulki dani ba kaga sai ayi replacing dinsa dakai." Uncle yayi shiru alamun tunani Asad yace, "Please Uncle kar kace a'a dan Allah badan ni ba dan Allah, ina so mu cikawa Abba burin sa na inganta masarautar nan in ka barni ni kad'ai I can't." Uncle yace, "Shikenan Allah ya shige mana gaba." Asad yayi murmushi yace, "Amin. Na gode Uncle." Asad ya sake cewa, "Ban san me zance ranar Monday ba Uncle." Yayi murmushi yana kallon sa yace, "Kar ka damu duk abinda yazo zuciyar ka shi zaka aiwatar, kar kayi shayi ko tsoron kowa, kar ka d'auki shawarar kowa, kayi abinda kaga shine daidai a haka mulkin ka zai tafi yadda ya kamata." Asad yayi shiru Uncle ya kuma cewa, "yana dakyau ka had'a lunch a gayyato mutane da yawa azo a taya ka murna, dan ko iya ranar Monday din Allah kad'ai yasan adadin bak'in da zakayi." "Not now Uncle, mu fara gamawa da jikin Abba." "Hakan yana dakyau." Asad yayi shiru baice komai ba Uncle ya kalle shi yace, "kamar akwai abinda kake so ka Fad'a min." Asad ya sosa girar sa guda d'aya ya girgiza kai alamun babu Uncle yace, "Ma sha Allah haka ake so." Shiru suka kuma yi kafin Uncle yace, "in anyi min izini zan koma." Asad yace, "Thanks you Uncle." Murmushi yayi yace, "koda yaushe ina tare dakai. Ka huta lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita. *☆☆☆*            "Yanzu Daddy haka zaka yi mubaya'a k'aramin yaro kamar Asad sa'an d'anka ya mulke ka?" Suhail ya fad'a cikin zallar nuna b'acin ransa yana kallon mahaifin sa. Waziri yayi murmushi cikin kunar zuci yace, "Ya zanyi Suhail? In ban bishi ba ya kake so ayi?." "Ka ajjiye rawanin yafi ka dinga duk'awa masa bazan jure hakan ba ko kad'an." Waziri ya sauke numfashi yace, "Zan ajjiye Suhail daman banyi niyar yin tafiyar nan dashi ba, ba ta yadda za'ayi na kasance a k'ark'ashin baba sa sannan shima na kasance a k'arkashin sa bazai yu ba."        Suhail yace, "Daddy har yanzu babu wani cigaba da ake samu ne akan tafiyar nan?." Yayi murmushi yace, "Lokaci ya kusa Suhail saura kad'an, babban burina shine daman ya hau karagar mulkin kuma ya hau. Ni yanzu Suhail akwai abinda zakayi ka shiga jikin sa sosai? Naga abotar ku taja baya sosai ba kamar da ba." "Babar sace take hana shi mu'amala dani kasan kuma yana matuk'ar jin maganar ta shiyasa hakan take kasancewa amma shi har gobe ya amince dani, amma zanyi k'ok'ari naga na koma masa dan shi har gobe bai gano ni ba."        "Yauwa haka nake so, komawar ka kusa dashi zai bamu damar yin duk abinda muke so tunda ya amince dakai har abin hannun ka yana ci." Suhail yace, "zan koma Baba, Amma sai anyi maganin babar sa." Waziri yace, "Zamuyi wallahi, ita bata isa ba sai munyi abinda muke so, wannan shine lokacin mu ne." Suhail yace, "zanyi Daddy, sai nayi iya bakin k'ok'arina wajan ganin mulkin katagum ya dawo hannun ka, bazan bari Asad ya dinga juya ka yadda yake so ba matsayin sa na d'an cikin ka, lokacin da komai zai dawo hannun ka yayi." Murmushi waziri yake yi kana yace, "Allah ya yi maka albarka. Tabbas kai d'an dana haifa ne." Suhail yace, "in kayi min izini zan tafi." "Jeka duk inda zaka je." "A tashi lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita zuciyar sa cike da saqe-saqen yadda zai b'ullowa lamarin Asad.        *☆☆ 8:00pm ☆☆.*        Tun bayan magriba matar sarki Asad ta hallara a apartment d'insa tayi kwalliya cikin rigar bacci fara mai kyau wacce tafi ta jiya nuna jiki kanta babu d'ankwali gashin kanta ya kwanta luf bak'i sud'ik sai tashin khamshi jikinta yake yi tana zaune tana danna waya a falon saman. K'arar k'ofa taji hakan ya saka ta kalle shi ya fito daga d'akin karatu sanye jikin jallabiya maroon mai gajeren hannun hannun sa rik'e da wayar sa.  Cak ya tsaya ya d'auke numfashin sa sabida barazanar da turaren ta ya kawo masa ba tsammani ya jita kwance a k'irjin sa ta zagaya da hannun ta bayan sa ta rik'e shi gam idannun ta a kulle. Shiru yayi ko motsin kirki baiyi ba sai numfashi da ya sauke a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'e ya saka hannun sa ya janye ta daga jikin sa ya kalle ta na sakan 1,2,3, ya d'auke idanun sa daga kanta ya rab'a ta zai wuce tayi saurin sake rik'e shi tana fad'in, "my king wai laifi nayi maka baka kulani?." Kulle ido ya sake yi ya bud'e kana ya sake janye ta daga jikin sa ya kalle ta suka had'a ido yaga ta kwab'e fuska tana kallon sa bakin ta a gaba alamun shagwab'a. Wucewa Asad yayi ba tare da ya ce komai ba ya shiga d'aki ya ajjiye wayar sa ya cire agogon hannun sa ya shiga band'aki. Wanka yayi ya fito d'aure da towel a k'ugun sa da k'arami a hannun sa yana goge kansa da k'irjin sa. Without permission ta turo k'ofar ta shigo bai juya ba balle ya kalle ta ya cigaba da abinda yake yi.      "Subahanallah" ya furta a can k'asan makoshi lokacin da ya sake jin jikinta a jikin sa tana goga fuskar ta a fatar k'irjin sa muryar ta can k'asa tace, "My king......" hannu biyu ya saka ya d'ago ta daga jikin sa ya kalli face d'in ta yace, "leave me pls." "I can't, ina so na kasance dakai a ko yaushe" ta fad'a kamar zatayi masa kuka ya zagaye ta ya wuce ya bud'e inda kayan sa suke ya d'auko dogayen kaya milk colour ya juyo ya kalle ta suka had'a ido ya d'auke kansa domin shi kam bazai iya saka kaya a gabanta ba.        Kamar tasan tunanin da yake yi sai ta fita ya girgiza kansa zuciyar sa wani iri babu dad'i domin bai san ya zai mata ba baiga kuma laifin ta dan tana neman hakkinta a wajan sa ba dalilin da ya saka yake jin sa wani iri kenan kamar ya tauye mata hakki. Yana tsaka da shiryawa unexpected yaji an kashe hasken d'akin an fad'a jikin sa a guje an fashe da kuka mai tsuma zuciya. "Oh my god!" Ya furta a hankali yana jin yadda take shafa k'irjin sa sam hakan baya masa dad'i. Jin abin nata yana neman wuce gona da iri ya fincike ta daga jikin sa yace, "I said leave! Baza ki samu abinda kika so ba so please ki barni" ya fad'a yana kallonta yana k'ok'arin gifta ta ta rik'e hannun sa tace, "Why zan k'yale ka? Bayan kasan ina neman hakkina a wajan ka." "Nace baza ki samu ba, sorry please" yana fad'a ya fita ya k'yale ta ta zube a akan gadon tana girgiza kanta a zuciyar ta tayi aniyar bazata bari yau d'in nan ta wuce ta ba.        D'akin kusa da wanda ya fito ya shiga ya jingina da bango yana sauke numfashi haka kawai ana neman yi masa fyad'e, sai da ya daidaita kansa ya dafe kansa da yake masa ciwo duk abin nan da ya faru ko kaɗan baiji wani da zai tabbatar da yana cikin wani yanayi ba kawai haushin yarinyar yake ji shiyasa baya so ta rab'e amma bawai dan yana cikin yanayi da baya son hakan ba, ya furzar da iska yana kallon kansa a mudubi yana tuna lokacin da lalaurar ta same shi rana tsaka ba tare ya shiryawa haka ba. Zama yayi a kan stool na mudubi rigar sa da take hannun sa ya saka ya sunkuyar da kansa ya rasa tunanin ma me zaiyi. _Ko wanne yanayi take ciki yanzu?_ya furta a zuciyar sa sai yaja k'aramin tsaki ya dafe kansa da hannayen sa duka biyun, duk da baya sonta ko kad'an amma matar sace tana da hakki a kansa ko wanne yanayi ta shiga shine ya jawo gashi bashi da damar sauke mata wannan hakkin.  Bai san adadin lokacin da ya d'auka yana tunanin ba ya tashi yana so ya fita amma baya so su had'u dan bai san me zaice mata, fasa fitar yayi ya kwanta a kan gadon badan yana jin bacci ba.         *Monday.*      Babbar fadar mai martaba sarki Asad ta cika maqil da hakimai wajan fadar bak'i ne manya da yara an cika kowa yana neman hanyar da zai bi yaga sarki. Asad yana zaune a kan kujerar da babu wanda yake zama sai ka kasance sarki a wannan gari an cika gefen sa dogarai biyu ne suna yi masa fifita, k'asan sa shamakin sane d'aya b'angaren kuma babu kowa wajan zaman Waziri ne kuma ba'a ganshi a wajan ba. Camera ce a kansa ta ko ina yayi gyaran murya kowa yana sauraron abinda zaice yace, "Alhamdulillah, muna godewa Allah ya nuna mana wannan rana cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali. Ina rok'on Allah yadda ya nuna mana wannan rana lafiya ya had'a mu da alkhairin da yake cikin ta." Aka amsa da Amin yayi shiru kafin yace, "A matsayina na sarkin wannan gari nayi alqawarin d'aukar nauyin duk wani wanda yake k'arkashin garin nan. Mace, namiji, yaro da babba mai kud'i da talaka, bazan yi cuta ba bazan amince ayi cuta ba da izinin Allah." Shiru yayi jin yadda kansa yake bala'in harbawa ya lumshe idanu ya bud'e ga rawanin da yake kansa ya k'ara masa ciwon kai ga kayan zafi a jikin sa dan riga ma guda uku ce a jikin sa kuma manya hakan ya sake rud'a shi ba kad'an ba, "Allah yaja zamanin Sabon sarki, Allah ya karya mak'iyan ka ya datar dakai ga duka abinda ka saka a gaba!" Aka furta da k'arfin gaske daga can k'arshen fadar.         "Duba da yanayin da ake ciki na rashin abinci munyi alqawari da aljihun mu bada aljihun gwamnati ba zamu bunk'asa sadakar da ake yi kullum domin wanda basa samu su amfana, zamu rarrbawa mutane maza da mata jari dan su dogara da kansu, za'a bud'e makarantu na koyan sana'a ga mata da maza in sha Allah." "Allah ya amince maka amintattacen sarki mai zuciyar alkhairi, Allah ya dafa mata zab'ebben sarki mai zab'in alkhairi, Allah ya baka ikon ganin bayan mak'iyan ka!" Dogarai suka sake fad'a aka amsa da amin.       Yace, "Mata da za'a aurar dasu babu kayan d'aki k'ofa wannan masarauta a bud'e take wajan ganin an tallafawa wanda suka samu, baza mu ce duka zamu taimaka ba amma zamuyi iya bakin k'ok'arin mu wajan ganin mun taimakawa kaso saba'in bisa d'ari. Ga maza manoma wanda basu da gonar noma kuma suna son yi akwai bbar gonar masarauta wacce a qalla mutane sama da dubu zasu iya noma a cikin ta, zata bayar kyuata ga duk wanda yake da ra'ayin yi ya noma ya girbe ya kuma kai gidan sa ba tare da ya bamu koda kwaya d'aya na abinda ya noma ba. Muna fatan wannan mulki ya zama silar shigar mu aljanna" ya k'arasa fad'a a hankali muryar sa na shaking alamun yanayin sa yana gab da canjawa maganar tasa tayi yawa dak'yar ya iya k'arasawa dan ma abin yana ransa ne ya saka shi ya fad'a. Kirari ake masa ta ko ina ya kalli Uncle alamun ya k'arasa abinda zai fad'a Uncle ya k'arasa bayanin kamar yadda yace sannan ya sanar da matsayin Uncle ya koma Wazirin sa aka bawa wani sarautar Uncle a nan take akayi sabon nad'i don kowa ya shaida. A haka zaman fada ya tashi cikin farin ciki da walwala musamman mutane da suka ji dad'in kalaman Asad domin kuwa kowa ya burge shi musamman yadda yake magana cikin izza da k'asaita da kuma ilimi. Hotuna aka dinga yi dashi y'an jarida suna cigaba da d'auka ana watsa labaran a duniya kafin a gama Mai martaba ya nufi komawa gida a k'asa  ba tare da mota ba, shamaki ne a gefen sa na haggu waziri a gefen sa na dama sai mai rik'e da lema da masu fifita yana takawa a hankali ana cigaba da zubewa ana gaishe shi cikin girmamawa shi kam kai kawai yake d'agawa domin ya gaji matuk'ar gajiya.        "Allah yaja zamanin sabon sarki, Allah ya taimake ka ya bada ikon gudanar da mulki lafiya." Cak Asad yaja ya tsaya jin muryar wanda bai yi zato ba ya had'd'iye yawu mai d'aci ya juya yana kallon Baba suka had'a idanu Baba yayi murmushi shima Asad d'in murmushin yak'e yayi domin bai kai zuciya ba. Da hannu ya yiwa Baba magana da ya tashi daga durk'uson da yake yi sannan ya bada umarnin ya biyo shi ciki. Kan Baba ya fasu ya washe baki yana take masa baya har k'aramar fada ta cikin gida aka raka shi ya zauna yana sauke numfashi ya rad'awa shamaki wata magana nan take kowa ya fita har Uncle aka barshi shida Baba kawai. Asad ya kalli Baba yayi murmushi yace, "Baba barka da Rana." "Allah yaja zamanin ka" ya fad'a yana yi masa jinjina. Asad ya nuna masa kujera yace, "Bismillah." Ba musu Baba ya tashi ya zauna Baba yace, "Ina neman Afuwa anyi shagali babu ni babu dangina, ina fatan an yafe mana." Gaban Asad yayi mugun fad'uwa jin abinda yace zai zuciyar sa ta fara rawa ya daure yace, "Babu komai." Baba yace, "Allah ya bada ikon gunadar da mulki lafiya ya bada lafiya da tsahon rai, ya kare ka ya kuma tabbatar maka da duk abinda ka saka a gaba" ya amsa da amin Baba yace, "Mutanen gidan duka sunce a mik'a musu gaisuwa har ita uwar gidan." Dammm gaban Asad ya buga ya runtse ido domin zargin sa ya tabbata bata fad'a musu abinda ya faru ba nan take tausayin ta ya sake mamaye masa zuciyar sa har yana jin ruwa na taruwa a idanun sa yace, "Ina neman afuwa Baba, Amma in sha Allah yau zan shigo gidan da kaina."      Baba da farin ciki yace, "Mai martaba da kansa zai ziyarce mu..? Alhamdulillah wannan abin farin ciki ne babba da ya same mu muna dakon zuwan mai martaba, Allah ya bada ikon zuwa muna maraba da bak'untar mai martaba har inda muke." Murmushin yak'e yayi yace, "in sha Allah." Shiru fadar tayi kafin Baba yace, "Ina neman izinin tafiya domin naje na sanar da mutanen gidan baban bak'on da zai ziyarce mu yau." Asad yace, "A sauka lafiya, muna godiya." Daga nan sukayi sallama Baba ya tafi Asad ya tashi ya shiga cikin gida ta k'ofar da take fadar a nan ya tarar da hadiman sa suka rakaya suka bi bayan sa zuwa ciki yana jin zuciyar sa kamar ana tafasata saboda tashin hankali ga kansa yana ciwo. *Asad is coming*💃🤣 [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *051.*            Shigar sa babban falon sa na k'asa ya tarar da Mama a zaune a kan kujera ta hakimce fuskar nan tata a d'aure ganin wannan yanayin ta sai da gabansa ya fad'i ya k'arasa inda take ya zauna a k'asa kusa da k'afafun ta hadiman sa suka ja da baya falon ya rage daga ita sai shi. Ta kalle shi taga fuskar sa tayi y'ar k'arama jijiyoyin kasa sun tashi alamun kansa na ciwo sosai har bak'i yayi. D'auke kai tayi daga kallon sa hakan ya saka yace, "Allah yaja da ran mahaifiyata, da an sanar dani da nayi tattaki na amsa kira." Mama tace, "ba dole nazo da kaina ba kana neman kashe ni Asad." Da sauri ya d'ago kai ya kalle ta tace, "eh, kana neman kashe ni, daga fara gudanar da mulki kwana biyu yau har ka fara yanke hukunci ba tare da izinina ba?." Asad ya sunkuyar da kansa tace, "waye yace kace zaka bada babar gona ga duk namomin da bashi da wajan yin noma? Kasan burin da nake dashi a akan wannan gonar?."         Asad yace, "Mai martaba ya sanar dani nayi dukkan abinda talakawa zasu amfana shiyasa na yanke wannan hukuncin." "To a soke shi! Mallakina nake so wannan gonar ta zama dan haka bata aro bace. Gidan gona zan mayar da ita shine burina a kanta ba tun yau ba. Girman ta ya wuce tunanin ka k'afa bata iya zagata sai dai da helicopter." "Allah ya wuci zuciyar ki." "Wucewar zuciyata shine a soke abinda ka fad'a, kuma daga rana irin ta yau kar ka sake yanke hukunci ba tare da izinina ba." Asad yace, "Za'a yi Mama. Amma dan Allah ina neman alfarma badan ni ba badan kuma na isa ba, ki bari su amfana da wannan shekarar in lokacin ya wuce sai komai ya dawo hannun ki...." ya dafe kansa da yake masa mugun ciwo kana yace, "na riga na furta Mama, in aka canja maganar zasuyi tunanin wani abun za kuma su fara d'aukata mara cika alƙawari daga farawa. Kiyi min alfarman nan dan Allah." Numfashi ta sauke tayi shiru ganin hakan ya saka yace, "Godiya nake, Allah yaja da rai ya jiqan Abie da Ummi." Ta juyo ta Harare shi kana tace, "Meyasa ka kasa sauke hakkin yarinya da yake kanka yau kwana uku da auren ku?." Ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba yana jin maganar tayi masa mugun nauyi dan bata tab'a fad'a masa ita gata gashi ba sai dai ta fad'a a waya dalilin da ya saka kunya ta lullub'e shi ya kasa motsin kirki amma yaga ita ko a jikinta. "Magana nake maka." Ya sauke k'aramin numfashi ya d'ago idanu ya kalle ta yace, "Kiyi hak'uri." "Ba laifi nace kayi min ba tambayar ka nayi ka bani amsa." Nan ma yayi shiru ya kasa furta komai ta sake cewa, "Akwai matsala ne?." Ya girgiza kai alamun A'a ta bishi da kallon tuhuma sai kuma taji gabanta ya fad'i tunawa da abinda ta aikata a baya ta girgiza kai zuciyar ta na bata tabbacin wannan shine dalilin da ya saka komai ya tsaya. Kawar da zancen tayi a zuciyar ta kana tace, "Na samu labarin mahaifin wannan shegiyar yarinyar yazo har kuka gana kai dashi, wanne matsayi yake dashi a wajan ka da zaku keb'ance haka?." Asad ya d'ago kai yace, "Babu." "Meye dalilin aikata hakan to? Bana ce kar ka sake shiga abinda ya shafe ta ba?, kenan ban isa na hana ba ko?." "Allah ya wuci zuciyar ki." Taja tsaki kana tace, "wani lokacin kayan haushin ka kamar na shak'e ka haka nake ji Asad. Komai akayi ka bada hak'uri kuma baza ka tsaya ka yiwa mutane bayanin abinda aka tambaye ka ba." Nan ma shiru yayi bai amsa ba ta girgiza kai tare da yin k'wafa ta mik'e tsaye shima ya daure ya mik'e duk da ciwon da kansa yake yi masa tace, "Tunda abin naka haka ne zanyi maganin su dukkan su." Jin abinda tace ya saka yace, "babu wata alaqa da take tsakanina dasu, yazo taya ni murna ne bayan hakan babu komai." "To ya tsaya iya hakan! Magana bana so ta sake had'a ka da wani daga cikin y'an gidan su, ka san cewa yanzu kai shugaba ne kowa a k'asan ka yake ba ko wanne talaka zaka dinga yin magana dashi ba." Kai ya girgiza alamun zai kiyaye har tayi gaba sai ta dawo da baya tace, "naji batun kashe kashen kud'i da ka d'orawa kanka na jama'ar gari, shima ban lamunce ba komai zakayi ka tabbatar ka sanar in ka zartar da hukunci ba tare dana sani ba Asad ranka zai b'aci." "Zan kiyaye" ya furta a hankali burin sa ya daina magana gashi in tana yi bazai iya shiru ba dolen sa ya bata amsa. "Na tuna da batun uncle d'inka Mubarak, waye ya baka ikon bashi sarauta mafi kusa dakai Asad? Ban fad'a maka zan baka list d'in wanda zaka yiwa sarauta ba?." Asad ya lumshe idanun sa zuciyar sa cike da mamakin Mama ganin ita take so ta zama sarkin bashi ba yace, "Ina buk'atar sa a kusa dani ne Mama, ban san komai ba shi nake so ya nuna min komai dashi Abbana ya amince nima dashi na amince." "Munafuki ne, fuska biyu ne dashi ni nasan da hakan. Tunda ka riga ka aikata bani da abin cewa amma ka sani; daga wannan kar ka sake duk wanda kake ganin ya dace ka bashi sarauta kazo ka sanar in yayi min sai ayi." "In sha Allah." "Wa zaka bawa sarautar tasa?." "Wanda kika ce" ya furta kamar zaiyi kuka hakan ya saka ta kalle shi taga yana juya kansa sai ta yanke maganar tace, "Zan duba na gani, amma definitely za'a saka Aliyu da Hydar a ciki." Hanyar fita yaga ta nufa hakan ya saka yace, "A sauka lafiya." Tana jinsa tayi masa banza ta fita ya sauke ajiyar zuciya ya hau sama ya cire kayan zafin da yake jikin sa ya fad'a band'aki yayi wanka ya fito ya saka kaya k'ananu yasha magani ya kwanta domin Allah kad'ai yasan gajiyar da yayi. Wayar sace take ta k'ara yayi niyar sharewa amma ganin uncle ne yake wayar ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, ina neman afuwa kira ba tare da neman izini ba." Asad yayi shiru hakan ya saka Uncle yace, "Bak'i ne suka zo daga China sunje wajan babban malamin masallacin cikin gari suna neman ganin mai martaba in hakan zai yu." Asad yace, "A basu appointment amma banda yanzu na gaji bazan iya komai ba." Uncle yace, "Zuwa anjima sai mu iso, A huta lafiya." Asad ya yanke wayar ba tare da ya amsa ba. Kallon notification yayi yaga sunan Suhail yayi masa message ya bud'e message d'in yaga yace, _Allah yaja zamanin sarki, ina neman alfarmar ganawa mai martaba anjima._ Asad ya tura masa da Allah ya kaimu.        Message din Dr Khalifa ya gani bai bud'e ba ya ajjiye wayar ya kwanta yana sauke numfashi.  _Mutanen gidan duka sunce a mik'a musu gaisuwa, har ita uwar gidan._ kalaman Baba suka dawo kansa ya sake jin kansa ya sara k'irjin sa na harbawa da sauri maimakon yaji tausayin ta kamar d'azu sai yake jin wani abu mai kama da haushin ta ita da iyalanta gabad'aya. Yaja tsaki ya tashi zaune yace, "Ya zama dole na yanke alaqar mu da ita gabad'aya ko zan huta da abinda nake ji a raina, zanje anjima kamar yadda nace" ya fad'a yana kwanciya ya kulle ido dan so yake yayi bacci.       A b'angaren Mama data koma b'angaren ta a nan ta tarar da Mum a zaune tana jiranta ganin shigowar ta ya saka ta mik'e sai da Mama ta zauna itama ta zauna tana cewa, "Ranki ya dad'e barka da dawowa." Mama tace, "Sadiya yaushe kika shigo?." Mum tace, "Ina shigowa aka sanar dani fitar ki." Mama ta tashi tace, "Muje ciki." Tare suka shiga suka zauna a k'aramin falo Mama tace, "Naje wajan Asad ne yana neman fara tarwatsa min lissafi daga fara zaman fada yana yanke hukunci ba tare dana sani ba."      Mum tace, "naji a gidan jarida ana ta sanarwa tawowa ta a mota nima sai da nayi mamaki nace daga farawa har anzo nan." Mama tace, "Barni dashi kawai zanyi maganin abun. Ya akayi na ganki kwatsam ba notice?." Mum tace, "batu ne akan yarinyar nan da aka bada aiki za'ayi." Mama tace, "bayan kun ya kasa komai, yau d'in nan sai da Asad yayi magana da mahaifinta." Mum tace, "ai a yanzu aka gabatar da aikin a gabana an kuma tabbatar min da ya tsane ta kenan har abada, domin kuwa an bani tabbacin a yau zaiji babu wacce ya tsana kamar ta kuma zaiyi k'okarin yanke alaqa da ita." Mama tace, "Allah yasa hakan. Ni ina so nayi waya ma da Malam Audu a warware aikin da aka yiwa Asad kwanakin baya." Mum da mamaki tace, "Wanne aiki aka yi masa?." Mama tace, "Oh baki sani ba ashe, lokacin da suna tare da yarinyar can ne na saka akayi masa aikin da bazai iya kusantar ta ba koda yayi niyar yin hakan bazai iya ba. Aikin ya same shi shiyasa har yanzu tsakanin sa da Jidda ba labari amma zanyi magana dashi yanzu."         Gaban Mum yayi mumman fad'uwa ta wara idanunta waje tare da dafe k'irji tace, "What! Fulani da kanki kika bada go ahead d'in wannan d'anyen aikin akan sa?." Mama bata amsa ba Mum ta kuma cewa, "Ina laifin tun a baya kisa ace a yiwa yarinyar aikin da bazata burge shi bama kwata-kwata bazai ji wani abun a kanta ba balle ma ya kai ga aikata wani abun, amma sai kisa a yiwa Asad guda?." Mama tace, "lokacin kaina ya kulle neman mafita kawai nake yi, amma yanzu za'a warware komai ai ba wani abu bane mai wahala kar dai ki sanar da Jiddan." Mum tace, "Wannan ai tsakanin mune." Mama tace, "Good, yanzu zan kira shi da kaina sai muji yadda za'ayi." Mum tayi shiru bata amsa ba amma zuciyar ta a cushe take da tasan da wannan maganar ai da tuni ta saka an warware komai dan ita ko kusa ko alama bata wata tazara a tsakanin su so take komai ayi a gama shi a wannan lokacin kafin uwar ta farga.           *☆☆5:00pm☆☆☆* B'angaren saukar bak'i ya cika da manya manyan bak'i fararen fata da bak'aken fata suna ganawa da sabon sarki suna ta hotuna cikin burgewa. Yana jin larabci da turanci shiyasa ganawa dasu baya yi masa wahala ko wanne yare ka juya masa zai baka amsa, abokan sa larabawa sun iso taya shi murna sosai yaji dad'i a ransa sosai. Asad yayi kyau cikin kaya light blue komai blue hatta takalmin k'afar sa blue ne ga alkyabbar tayi bala'in amsar jikin sa yayi kyau matuk'a hakan ya saka sai hotuna ake masa kana kallo kasan ya saka dukiya a jikin sa. Sun jima kafin bak'in su tashi tafiya su bada kyaututtuka su tafi. Daga nan ya fara ganawa da mutanen cikin gida duk wani wanda ya shafe shi a wannan lokacin sun tattauna. A wannan shigowar Suhail yazo Asad yana zaune a kan karaga Suhail ya zauna a k'asa yana kai gaisuwa hadiman da suke k'asa suna fad'in, "An gaishe ka Suhail, mai martaba ya karb'i gaisuwar ka."     Suhail ya zauna a gefen sa yace, "Allah yaja zamanin mai martaba sarki." A tare suka amsa da amin Asad ya kalle shi yace, "Suhail." Suhail ya gyara zama yace, "Ranka ya dad'e." Asad ya murmusa kawai baice komai ba Suhail yace, "Allah yaja da ranka zuwa nayi na gaida mai martaba, ina fatan an karb'i gaisuwata." "Mai martaba yana godiya" suka had'a baki gabad'aya suka fad'a kafin ya sake yin gaisuwa ya tafi. Bayan kammala zaman fada Asad yana zaune shine da Uncle Asad yace, "Uncle ina so zanje Germany wajan Abban cikin week d'in nan." Uncle yace, "Allah ya k'ara maka lafiya sai a shirya komai nima daman ina so naje." Asad yace, "Uncle ya kake gani zamuyi da Suhail?." "Ban fahimta ba kamar ya kenan?." "Sai nake ganin a bashi sarauta mafi kusa dani." "Eh kuma a'a, abin ne a cikin duhu in ka duba waye mahaifin sa." "Na amince da Suhail tun ba yau ba." "In mai martaba yana ganin hakan babu matsala Allah ya shige mana gaba." Asad yayi shiru yana kallon wani wajan daban kafin suyi sallama ya hau saman sa ya samu Jidda a zaune a falon sama. Yana shiga ta taso ta k'araso kusa dashi ta zaga ta bayan sa ta zame allyabbar jikin sa tana fad'in, "welcome back my king." "Thanks" ya furta a tak'aice yana zare hannun sa daga alkyabbar, ta duk'a ta zare masa takalimin k'afar sa ya taka zuwa tsakiyar falon ya zauna. Ajjiye su tayi ta koma inda yake ta cire rawanin kansa shi kuma ya zare k'atuwar rigar da take saman shaddar jikin sa yana sauke numfashi dan ji yake iska na shigar sa ba kamar d'azu ba da zafi ya dame shi. Wajan fridge ta d'auko ruwa mai sanyi da glass cup ta k'araso kusa dashi ta zuba masa ta mik'a masa, kamar bazai karb'a ba sai kuma ya karb'a yasha farin ciki ya mamaye mata zuciyar ta ganin yasha ya ajjiye glass cup d'in ba tare da ya kalleta ba.       Tashi tayi ta shiga d'akin sa ya bita da kallo shi bai san me zai yiwa yarinyar nan gabad'aya bata burge shi ko kad'an bata cikin zuciyar sa ga tausayin ta yana ji ta wani b'angaren in ya tuna halin da yake ciki bazai iya sauke hakkinta da yake kansa ba dalilin da ya saka yake d'aga mata k'afa. Jim kad'an ta fito ta k'araso kusa dashi tace, "wanka fa." Bai amsa mata ba hakan ya saka tace, "na ajjiye maka ruwan wanka." Kai ya d'aga kawai kafin ya d'auki wayar sa yana dannawa suna charting da Hydar akan rashin lafiyar Abba sai kuma ya shiga Ig ya dinga karo da maganganun sa na d'azu da video da hotuna ana ta yabon abinda ya furta ya kashe data ya tashi ya shiga d'akin.   Tsalle ta buga bayan taga shigar sa tana murna tace, "ka fara zuwa hannu wallahi, wuuuu Allah yaja da ranki Mummyna dole na kira ki na baki labari" ta fad'a tana sauka da sauri. *☆☆☆*           Tunda Baba ya koma jikin sa yake rawa ya sanar Umma yadda sukayi da Asad ya tashi hankalin kowa na gidan akan a tashi a shirya masa abin motsa baki gabad'aya ya rud'a su. Rauda jikin ta duka a sanyaye take komai dan bata amince da zuwan wani Asad ba dan bata da yadda zatayi ne baza ta yiwa Baba musu ba shiyasa taja bakin ta tayi shiru kawai. A zaune ya shigo ya samu Rauda tana duba waya yace, "baza ki tashi kiyi abinda yake gaban ki ba sai yazo?." Umma ta kalle shi tace, "Dan Allah malam ka kwantar da hankalin ka basai an had'a masa komai ba dan ko an bashi ba ci zaiyi ba, ka manta matsayin da yake dashi ne a yanzu? Ba komai suke ci ko suke sha ba in aka basu." Baba ya zauna a akan kujera kana yace, "Eh kuma fa gaskiyar kine, amma ai nan gidan sirikan sane ba wani abun zamu bashi da zai cutar dashi ba." Umma tace, "Kaine kake ganin hakan." "Amma yanzu haka zai zo babu abinda zamu bashi?." "Sai a d'ora ai Malam" ta fad'a tana kawar da kanta gefe ba tare da tace komai ba.          "To ki tashi kije ki shirya sai wani sanyin jiki kike yi kamar ba mijin ki ne zai zo ba" Ya fad'a yana kallon Rauda bata musa ba ta tashi ta shiga d'aki shima ya fita Umma ta bishi da kallon mamaki, wato shidai duk inda akace kud'i a nan jikin sa yake rawa.        Rauda koda ta shiga d'akin bata iya aikata komai ba tsayawa tayi tana tunani kafin ta samu waje ta zauna ta rafka uban tagumi zuciyar ta na harbawa dan bata san me zai kawo Asad d'in gidan su ba. Sallah ce kawai take tashin ta a nan take zaune har akayi magariba babu Asad babu labarin sa har lokacin Baba bai sare da zuwan Asad ba ita kam daman tasan bazai zo ba. Wanka tayi lokacin ana kiran sallar i'sha ta fito ta saka doguwar riga ta bacci mai gajeren hannu jikinta yana rawa sosai kalar ja da bak'a ta saka hula ta d'ora hijjabi ta tayar da sallah. Bayan ta idar tayi shafa'i da wutri ta mik'e ta zare hijjabin kenan Baba ya shigo jikin sa har rawa yake yana cewa, "Ke Rauda yi maza-maza kije ga Asad d'in can yazo yana sitirum d'ina na waje." Gabanta yayi mugun fad'uwa ta dafe k'irji sabida yadda zuciyar ta ta buga fattt ji tayi kamar zata fito.       "Ba magana nake miki bane kin tsaya kina kallona? Dallah malama kiyi da jiki kije yana jiran ki an gaisa dashi ke kad'ai ake jira" Baba ya fad'a cikin fad'a hakan ya dawo da ita hankalin ta ta d'auki hijjabin data cire ta saka tana kallon Baba ta fita. A falo ta tarar da Umma ta wuce ta jikinta duk a mace gabanta yana cigaba da tsantanta bugawa haka ta wuce ta fita daga falon ta fito tsakar gida ta fita harabar gidan a nan ne set room d'in Baba yake. Tare da Baba suka fita ya tsaya a bakin k'ofa yace, "Shiga." Yawu ta had'd'iye ta saka kanta cikin falon nan take khamshin turaren sa ya bata tabbacin shid'in ne da gaske ba wasa bane. Kanta a k'asa take takawa jikinta yana rawa ta zauna a kan carpet har lokacin bata kalli inda yake ba gabad'aya tsoro ya gama mamaye mata zuciya. Tunda ta shigo yake kallonta k'irjin sa yana bugawa da sauri-sauri ya runtse idanun sa ya bud'e yana jin wani iri a zuciyar sa, shiru falon yayi babu mai magana tsabar bugawar da k'irjin ta yake yi ta kasa magana sai raba idanu da take a k'asa tana kallon k'afar sa da take sanye da takalmi ta mayar da kanta k'asa ba tare da tayi magana ba. Yadda tayi shiru haka yayi shiru baice komai ba kallonta kawai yake yi ta k'asan idanun sa domin tasan dai bazai mata magana ba sai dai in a kwana a haka. Gajiya tayi da zaman ga bugun da zuciyarta take yi ta yunk'ura ta tashi zata fita taji an rik'o hannun ta zuciyar ta ta cigaba da gudu ta runtse idanunta hawaye na ciko mata idanun ta, kwace hannun ta tayi daga rik'on da yayi mata sai a sannan tace, "Meya kawo ka gidan mu?." Hannayen sa duka biyun ya saka ya juyo da kafad'ar ta kanta na k'asa hawaye suna sauka daga idanunta ya d'ago fuskar ta suka had'a ido sa a sannan ta kalli fuskar sa ta ganshi sanye da face mask da kuma bak'in glass da alama yayi b'adda kama ya saka hannu ya zare glass d'in ya cire face mask d'in fuskar sa ta bayyana sosai ya lumshe idanun sa ya bud'e yana kallon fuskar ta da idanun ta suke zubar da hawaye har lokacin.         "Na mayar dake d'akin ki Muwaddaty! You're still my wife!" Ya fad'a a sanyaye yana bin fuskar ta da kallo yana so ya fahimci reaction d'inta. Wara idanun ta waje tayi cikin tsananin bugun zuciya tana k'arewa fuskar sa kallo ya d'aga mata kai alamun tabbacin abinda yace ya jawota ya had'a ta da jikinsa hannun sa na zagaye da k'ugun ta yace, "Yeah, you're still my wife!." *Tofa anya Asad yana cikin hankalin sa kuwa?*😱🏃🏼‍♀️ [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *052.*          Yanayin yadda yaga ta gigice ta zuba masa ido fuskar ta ta nuna tsantsar tashin hankali da mamaki had'i da al'ajabi a kai k'arara sai zare idanu take tana binsa da kallon da alama mamaki ya hana ta magana. Shima baiyi magana ba yana rik'e da ita har lokacin ganin kamar bata hankalin ta ya saka shi ya rik'e hannunta guda d'aya ya murza yatsun hannunta ta kalli yatsun nata ta sake kallon sa tana bin hannun nasa da kallo nan tayi karo da abinda take nema a hannun nasa ta sake kallon fuskar sa dan ta tabbatar shi d'in ne. "Nine a gaban ki kar kiyi tunanin wani abun daban" ya fad'a cikin maganar sa mai d'aukar hankali yana cigaba da kallonta. Sakin ta yayi ya kalle ta yace, "where is your phone?." Bata iya magana ba sai bin sa take da ido gani take kamar baya cikin hankalin sa in ta tuna yadda aka rabu bata d'auka zai dawo har yace ya mayar da ita ba. "Kin san yanayina bazan iya magana da yawa ba, amma I'm sorry." Wani irin abu take ji yana tasowa daga jikinta ta lumshe ido dan ji take yana tafiya kamar kiyashi yana zaga ko wanne b'angare na jikinta har cikin gashin kanta take jin maganar sa. Sake rik'e hannunta yayi duka biyun yace, "kace mace ta biyu a duniya dana bawa hak'uri because nasan na cutar dake, forgive me please." Numfashi ta sauke a hankali sai taga ya saki hannun ta ya juya gefen sa ya d'auki wata k'aramar leda ya ajjiye mata yace, "Is for u." Dafe kai taga yayi ya zauna yana runtse idanu alamun maganar da yayi da yana tana affecting d'insa ya lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya.  A nan ta tabbatar Asad ne domin kuwa yadda yake yatsine fuska da zanen hannun sa da yadda yake magana ya tabbatar mata shine, babar shaidar ma itace zanen hannun sa. "Na sake ki saki biyu!." Abinda taji ya furta kenan ta sake kallon sa a gigice taga ya mik'e tsaye yana mayar da abubuwan da suka hana fitowar fuskar sa gabad'aya yace,         "Na yiwa Mama alqawarin zan rabu dake gabad'aya har abada that's why na yanke duka igiyoyin aurena a kanki. Ki yafe min banyi dan na cutar dake ba sai dan na barki ki huta ki auri wanda kike so yake sonki. Ina sonki har gobe amma nafi son Mama akan komai, kiyi haƙuri" yana fad'a yana gifta ta zai wuce k'unar zuciyar ta na k'aruwa tayi sufa ta sha gabansa tana binsa da banzan kallo cikin tsanar data mayaye mata zuciya lokaci d'aya tace, "K'arya kake wannan ba alqawarin da ka yiwa Maman ka bane iya ita kad'ai harda zuciyar ka, na dad'e da sanin wannan ranar zata zo a cikin rayuwata, na jima da sanin za'a zo wannan gab'ar da saka wulaƙanta ni dan na kasance kaskantacciya a wajan ka." "Kayi abinda kake so ka mayar dani bazawara da k'aracin shekaruna, kasan babar ka bata sona meyasa ka aure ni? Kasan Babar ka bata sona meyasa ka b'ata min k'uruciya ta?." Kallonta yayi yace, "Ba'a san shugaba da sakin aure ba a wata masarautar an haramta hakan amma ya zama dole a wajena shine kwanciyar hankalina da naki." "K'arya ne wallahi, burin kane kawai kuma ka cika sai kaje ka k'arata daman Allah ya sani tun farko ba son auren ka nake ba k'addara ce ta had'a kuma ta raba, ban damu da kai waye ba amma ina so ka sani sai Allah ya saka min." Runtse ido yayi ya kalle ta ganin kamar an canja ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya cize bakin sa ya fita daga falon zuciyar sa na zafi shi kansa inda tasan abinda yake ji baza tayi masa wannan zargin ba, amma ya zaiyi umarnin zuciyar sa kawai yake bi maganar da yayi mata ma ya daure ne amma bala'in haushin ta yake ji.     Zubewa tayi a wajan tana kuka sosai zuciyar ta nayi mata ciwo ranta na suya haka take zubar da hawaye masu zafi, ta jima a wajan bata san adadin lokacin data d'auka a wajan ba taji an dafata ta baya, bata d'ago ba bata daina kukan ba kuma sai da taji muryar Baba yana cewa, "ke kuma lafiya kike yiwa mutane kuka? Ina mai martaban yaje?." Ta sake k'ara kaimi wajan kukan ta sai a sannan take ji a zuciyar ta komai ya faru da ita Baba ne silar komai da bai bada auren ta babu sanin ta ba da duk hakan bata faru ba.      Umma tace, "tashi muje d'aki ki daina wannan kukan." Umma ta d'aga ta ta jinginar da kanta a kafad'ar Umma suka fita Baba yaga ledar da aka ajjiye ya d'auka yabi bayan su jikin sa na rawa tsoro duk ya dabaibaye masa zuciyar sa. A falon Umma ya tarar dasu a zaune daga ita sai Umma tana ta kuka har lokacin Baba ya zauna kusa da ita yace, "meya faru ne wai?." Cikin kuka gabanta yana fad'uwa tace, "Baba tun a Egypt ya sake ni saki d'aya, yanzu kuma......" Sai kuma ta kasa k'arasawa ta sake fashewa da sabon kuka. Murmushi Umma tayi tace, "Daman nasan za'a rina ai, yanzu da yazo ya k'arshe guda biyun ko?." Rauda ta d'aga kai alamun eh tana sake cigaba da kukan ta. Baba cikin tashin hankali yace, "ban fahimta ba, mayar dake yayi sannan ya kuma sakin ki?." Kai ta d'aga alamun eh tana jikin Umma tana kuka tare da jan numfashi Umma tace, "Shine ya had'o ki da kud'i a jaka da yake ga kwad'ayayyiya wacce take neman kud'in hannun sa ko?." Baba ya buɗe jakar nan yayi karao da takardar doguwa fara ya d'auka ya warware yaga abinda ta fad'a a rubuce harda tambarin masarauta yaja tsaki yace, "K'arya kike wallahi kece kika yi silar da ya saka shi ya sake ki tunda daman tun farko ba so kike yi ba. Na tabbatar wani abun kika fad'a masa wanda ya b'ata masa har ya kai ga aikata abinda ya aikata. Kin cuce ni keda uwar ki kun gama dani gabad'aya, ina sirikin sarki guda fad'ar sirikin sarkin nan a baki ma dad'i ne dashi sai da kika saka k'afa kika b'arar da wannan sunan hankalin ki ya kwanta, kun kyauta ai keda babar ki burin ku ya cika sai ku zuba ruwa a k'asa kusha, gaki nan sai ta jika tasha ai. Ke ni ban ma amince ya sake ki d'in ba sai naji da kunnena domin shugaba baya saki." Umma tayi murmushin takaici tana kallon Baba tace, "ka duba takardar ka gani ka karanta ka tabbatar anyi sakin kace baka yarda ba?." Baba yace, "Nidai Allah ya isa ban yafe ba, dukkan wanda yake da hannu a cikin wannan lamarin bazan yafe masa ba wallahi, sai Allah yayi mana hisabi domjn an cuce ni an gama dani an b'arar min da duk wata dama da nake da ita."           Ran Umma ya b'aci matuk'a ta mik'e tsaye tace, "Nida itafa mu ya kamata muyi Allah ya isa ba kai ba domin mu aka cuta, son kud'in ka shine ya jawo ka bada y'arka badan tana so ba sai dan kawai kwai kud'i da mulki. Da Anas kake goyan bayan ta aura amma tunda kaga wanda ya fishi ka tsallake shi kace baka san zance ba duk tarin kyautatawar da yayi maka. Ka bayar da Rauda aure aka d'aura auren duk da abubuwan da suka faru a baya akan maganar auren ka manta ka shafawa idanun ka toka kana ji a ranka koda zasu kasheta indai kai zaka samu kud'i zance ya k'are. Har cikin gida akazo za'a kashe ta akan auren wanda ba komai ba tunda ba annabi bane ko sahabi amma duk da haka baka gani ba ka take kayi san ranka baka duba halin da zata shiga ba ta inda zaka fita kawai kake nema. To dan yanzu sakamakon abinda ka aikata ya bayyana sai kazo kana yi mana Allah ya isa? Ita yarinyar dan bazata iya bud'e maka zuciyar ta kaga abinda yake ciki ba shiyasa kake ce mata haka!?" Umma ta fad'a cikin d'aga murya tana kallon Baba da b'acin rai k'arara akan fuskarta.       Da mamaki Baba yake kallonta dan zai iya cewa karon farko kenan da ta d'aga masa murya a zamantakewar su ta aure su,ranar farko kenan da ta tsaya a gabansa yana fad'a tana fad'a har tana yi masa magana cikin fad'a kamar zata dake shi, "Binta ni kike yiwa magana kina d'agawa murya? Ni kike kallo kike cewa na siyar da y'ata sabida son kud'i?." Umma tace, "Na fad'a! ai ba k'arya nayi ba na sake fad'a ka bada auren ta sabida son kud'i irin naka. Har cikin gidan su yaro yazo ya sake ta sabida baka bata mahimmaci ba a lokacin daka ce ana sonta da ka nuna musu tana da daraja da abin zaizo da sauk'i. Yanzu kuma kake bud'e baki kake cewa baka yafe mata ba sabida ta rabu da wanda zai yanke maka talauci, ai ga kud'in nan ya sake had'o ta dasu sai ka d'auka ka rik'e tunda shine mutunci a wajan ka. Ya nuna maka y'arka iya matsayin ta kenan ya aureta ya saka bawai don ta zama matar sarki ba iya matsayin ta kenan; wacce take da wannan  matsayin tana gida a zaune da ita ya dace ba yarka ba, kud'i shine abinda take so gashi nan kuma ya bata tunda haka ka nuna musu."           Rauda hankalinta ya tashi karona farko kenan da taga iyayen nata suna cacar baki musmaman Umma da taga tana d'aga murya tana yiwa Baba fad'a kamar ba ita ba, rik'e Umma tayi tana kuka tace, "Dan Allah Umma kiyi hak'uri kiyi shiru, Baba kayi hak'uri dan Allah" ta fad'a tana kallon su idanunta na zubar da hawaye har lokacin. Kyakykyawan mari Baba yayi mata a fuska ta dafe kuncin tana kuka yace, "Duk ba kece sila ba? Da baki aikata abinda kika yi ba za'a zo wannan gab'ar ne?. yau a kanki uwar ki take kallon idanuna take cewa na siyar dake sabida kud'i, a kanki take d'aga min murya tana k'okarin tara min jama'a."      "Ni ya kamata ka mara ai ba ita ba tunda nice nayi maka laifin ba itace tayi ba, koda yake ai haushin sarki ya sake ta shine dalilin da ya saka ka mare ta to ka koma kaje kayi bikon sa mana in yaso sai ka had'a ta da wani suyi auren kisan wuta sai ka mayar da auren, ko kuma ka mayar haka sai ta koma can ta zauna" Umma ta fad'a cikin fusata sosai tana kallon Baba shima yana kallonta. Kuka sosai Rauda take yi ganin tashin hankalin da bata tab'a gani ba a gidan su kuma a kanta ake wannan fad'a tsakanin iyayen ta shiyasa hankalin ta ya tashi, zuciya ce take d'auka Baba in ya tsaya a wajan zai iya aikata komai abinda baiyi ba tun da zai iyayi a wannan lokacin a yadda yake jin zuciyar sa, yayi k'wafa ya juya ya fita ransa a b'ace yana wuci. Umma d'aki ta shiga Rauda tabi bayanta tana kuka tace, "Dan Allah Umma kiyi hak'uri, ki yafe min nice silar komai da ya faru" ta fad'a tana sake fashewa da sabon kuka. Umma tace, "ni baki min laifin komai ba ke aka yiwa laifi kuma ake tauye miki hakkin ki, dan nayi shiru kwanaki da suka wuce yanzu bazan yi shiru ba in yaga dama nima ya sake ni d'in sai na d'auke ki mu tafi gidan ubana na tabbata can zasu nemo miki mutuncin ki baza su siyar dake sabida kud'i ba. Dan ina yin shiru akan lamarin y'ay'ana ba hakan yana nufin bana son ku bane ko ban damu daku ba sai dan kawaici, to na lura bai san shi ba san anyi fito na fito." "Dan Allah Umma ki daina fad'ar haka tun tasowa ta ban tab'a ganin haka tsakanin ki da Baba ba meyasa yanzu zakuyi kuma sabida ni?." "Hmm" shine abinda Umma tace bata ce komai ba sai Rauda da take kuka tace, "badan Allah yasa Khalil da Khairi suna wajan inna ba da a gaban su hakan zata faru? Haba Ummana kamar ba ke ba?." Umma tace, "Tun zuwan ku Egypt d'in ya sake ki?." Rauda ta girgiza kai alamun a'a tace, "Sai ana saura kwana biyu zamu tawo, Maman sace tazo a gabana ta saka ya sake ni ta kuma kore ni daga hotel d'in badan abokin sa likitan da sukayi min aiki ba da yanzu ban san a ina nake ba. A gidan sa na zauna na kwana biyu matar sa ta d'auke ni kamar y'ar uwar ta shine ya dawo dani." Umma tace, "ba wani uwar sa da ta saka ya sake ki daman can shima akwai manufar da ya saka ya aure ki ba don Allah ba, daman can ban amince da wai yana sonki ba ina ke ina shi? Kwantan b"auna yayi ya lallab'a ya aure ki wataƙila sirrin  wani aikin ne akan sarauta akace sai ya auri budurwa mai irin suffar ki shiyasa ya nemo ki dan yasan halin mahaifin ki, yanzu da buk'ata ta biya ya zama sarki kuma ya dawo ya warware abinda ya rage dan kar ma wani tunani ya d'arsu a ranki nan gaba.' Shiru Rauda tayi bata ce komai ba sai kuka da take sharewa, Umma ta kuma cewa tace, "In kin kammala idda Allah ya baki miji kiyi auren ki kowa ya huta, ni ina jin ma na tura ki gidan Yaya Bilki can bauchi kije can ki huta da bala'in mahaifin ki, ko ki tafi gidan Baba Malam kiyi zaman ki."  Kallon Umma Rauda tayi itama ta kalle ta tace, "Nasan akwai idda a kanki Rauda tun dawowar ki idanun ki sun tabbatar min da kin zama cikakkiyar matar aure Rauda, kada ki damu k'addarar kice a haka komai zaizo da sauk'i nan gaba in sha Allah, wata rana sai labari zai wuce kamar bai faru ba." Rauda tayi shiru Umma ta kuma cewa, "Tun dawowar ki nasan akwai abinda kike b'oyewa zuciyata ta hasoso min hakan amma kika ce babu komai." "Umma ban san ta yaya zance muku an sake ni ba, ban san ta yadda zance miki auren satittika ya mutu ba shiyasa nayi shiru." "K'addarar ki kenan ki kwantar da hankalin ki." "Umma ki bawa Baba hak'uri dan Allah." Umma ta Harare ta har zatayi magana sai kuma ta fasa ta tashi ta shiga band'aki. Jikin Rauda a sanyaye ta tashi ta fita daga d'akin ta shiga nata d'akin tana, jingina tayi da bango ta lumshe ido hawaye suka sakko mata ta share a bayyane tace, "Tabbas Asad kayi min bazata, ka illata min k'uruciyata, ka jawo sa'insa tsakanin iyayena, ka raunana min zuciya, kayi wasa da hankalina, ka saka min ciwo a raina, ka lalata duk wani shirina, ka barmin tabo a zuciyata. Allah sai ya saka min" ta fad'a tana durk'ushewa a wajan ta fashe da sabon kuka tana dana sanin amincewa dashi har ta fara sonsa. _nayi miki alqawarin bazan barki ba ko meye zai faru._ kalaman sa da suka fad'o mata kenan ta runtse ido ta zube a wajan tana kuka sosai babu mai rarrashin ta. Tashi tayi tana kallon hannunta taga zoben da ya bata ta zare shi daga hannun ta ta buɗe kayan ta ajjiye dan k'ona shi zatayi da safe dan bata son tunawa da komai da ya shafe shi. Kama wacce ta tuna wani abun sai ta zabura da jajayen idanun ta ta fita zuwa saman Baba gabanta yana fad'uwa, a zaune ta ganshi yayi shiru alamun ransa a b'ace yake tayi sallama taga ya d'ago ya kalle ta bai amsa ba ta k'arasa ciki ta zauna akan carpet tace, "Dan Allah Baba kayi hak'uri, wallahi Allah ban cewa Asad ya sake ni ba shine ya sake ni tun muna Egypt sannan kuma ya dawo yau ya k'arashe saki biyun da suka rage na rantse da Allah babu laifina balle laifin Umma, kayi hak'uri ka yafe mana" ta k'arasa fad'a cikin kuka sosai dan zuciyar ta tayi rauni.       Shiru Baba yayi bai amsa ba ta kuma cewa, "Dan Allah Baba kayi hak'uri wallahi bani da laifi ko kad'an" sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ta kifa kanta a cinyoyin ta tana kuka. Baice kanzil ba ta jima tana kukan kafin ta goge idanunta ganin kallon ta baiyi ba ta tashi ta sauka daga saman nasa ta koma d'akin ta tayi lamoo a kan gado babu alamun bacci a cikin idanunta.                        *☆☆☆*         "Kin tabbatar kin zuba masa a cikin ruwan yasha?." Jidda rik'e da waya a hannunta tace, "Wallahi Mum yasha har na wankan ma dana zuba masa yayi wankan dashi, nayi mamakin yadda ya sauko lokaci d'aya haka." Mum tayi y'ar dariya tace, "k'yale Jidda tukunna ma kenan, ai na rantse da Allah sai Rabi tayi kuka da idanunta, sai ta gwammace bata bawa Asad kujerar sarautar nan ba." "Shiyasa nake yin Mum wallahi, Allah yaja da ranki." "Amin. Kedai kiyi duk abinda nace miki kar ya dame ki dan kinga baya neman ki akwai dalilin hakan sa kuma za'ayi maganin abun nan kusa." "To Mum." "To sai da safe ki tashi ki tafi b'angaren sa ki tabbatar ki shafe jikin ki da wad'an nan turarukan." "Okay Mum, Bye" tana fad'a ta kashe wayar tana farin ciki.        Shiryawa tayi kamar ko yaushe ta d'ora hijjabi ta fito jakadiyar ta tana take mata baya zuwa b'angaren mai martaba ta k'ofar cikin gidan dan farin ciki take ji dashi tafi so kowa ya ganta bazata bi ta inda baza'a ganta ba. Sunzo tsakiyar harabar gidan wutar gidan gabad'aya ta d'auke d'uf duhu ya mamaye duka gidan a guje ma'aikatan gidan akayi wajan wuta dan a gyara dan kowa yayi mamakin d'aukewar ta. Ba tsammani Jidda taji an jata wani waje an toshe mata baki zatayi ihu yace, "Shiiiii! Karki ce komai." Kallon sa take idanunta a waje tana so ta banbance Asad ne ko Aliyu ya kalle ta yace, "What are you thinking about?."         "Aliyu?." Ya d'aga mata kai yace, "Yeah it's me." Ta kwace hannunta da yake rik'o tace, "Meyasa ka kawo ni nan? Sai wani ya ganmu?." "Ki daina increase volume mana, i want to talk to you that's why na kashe wutar gidan." "Daman kaine ka kashe wutar?." "Yeah nine." "For what reasons?." Ya kalle ta yace, "stop shooting mana, ko ina kina so a ganmu ne?." Ta kalli bayanta taga babu wanda yayo wajan da suke tace, "Ina jinka." "Asad yyi having sex dake?." Idanun ta ta zaro tana kallon shima ya zaro idanun sa yace, "Answer me bana son wani kwana-kwana malama." "To ina ruwan ka da wannan kake tambayata?." "Because ina so na taimake ki ne in ba haka ba a haka zaki k'are a gidan nan babu wani cigaba sabida Asad yayi damage bazai tab'a yiwa kasancewa da wata ba; in fact bazai haihu ba." "What?." Ya wara idanu yace, "yes ke kin san bazan miki k'arya ba, in kuma kina tunanin wasa nake ki gwada ce masa kina son ya baki hakkin ki kiga me zai faru." "Wanne irin taimako kake fad'a zaka min?." "Ki fara tabbatarwa then sai ki neme ni, and......" ya fad'a yana lalubo aljihun sa ya d'auko wani magani ya bata yace, "karb'i." Ta karb'a yace, "Ki tabbatar kin bashi wannan magani yasha in kikayi sa'a zai samu lafiya iya na yau in kuma bai samu lafiya ba shikenan sai dai kiyi hak'uri." Kallon sa take kamar bata yadda ba ya rik'e hannun ta yace, "trust me bazan cutar dake ba, ina sonki ke kin sani that's why nake nema miki duk abinda kike so." Ta sauke numfashi tace, "ta yaya zan amince?." "U know bazan cutar Asad ba ko kad'an, I love him so much so bazan cutar dashi ba." Kai ta girgiza kana tace, "Okay I will try it now." Yayi murmushi tare da yi mata kiss a goshi yace, "That's my friend." Ya kalle ta yace, "Jeki, zan saka a dawo da hasken." Ta juya ta tafi yayi murmushi yana sosa gemun sa yana hango yadda zai same ta a b'agas ba tare da wata matsala ba. Tana dawowa inda take haske ya dawo ta nufi b'angaren Mai martaba ta hau sama ta same shi a zaune ya dafe kansa yayi shiru alamun akwai abinda yake damun sa, zama tayi kusa dashi tace, "akwai abinda yake damun sarkina?." Kallonta yayi ya girgiza kai alamun babu komai ta tashi ta kawo masa lemon da taga yana yawan sha wato five alive ta had'o da cup ta zuba masa tace, "take it pls."  Kamar bazai karb'a ba sai kuma ya karb'a yasha ya ajjiye cup d'in ta bishi da kallo sai taga ya tashi ya shiga d'akin karatu baice komai ba. Murmushi tayi ta girgiza kai ta tashi ta shiga d'akin sa ta shafe jikinta da turaren ta fito falo ta zauna. Bai jima ba ya dawo ya wuce ta zuwa d'aki ya jima da shiga tabi bayan sa ta ganshi da laptop a cinyar sa yana dannawa ta k'araso ta d'auke laptop d'in ta zauna a cinyar sa ta sak'alo hannun ta wuyan sa ta kwantar da kanta a jikin sa. Khamshin turaren ta ya bugar dashi sosai ta fara kissing d'in sa a wuya da fuskar sa a hankali. So yake ya daure ya kawar da ita daga jikin sa but turaren yayi tasiri a jikin sa sosai lokaci d'aya ya fara fita daga hankalin sa yana jin kansa yana sarawa sosai.      Kamar wanda ya tuna wani abun sai ya firgita ya ture ta daga jikin sa ya mik'e tsaye ta rik'e hannun sa tace, "Please My king." Ya sauke numfashi yace, "I'm sorry" yana fad'a ya zame hannun sa ya fita daga d'akin ta cure waje d'aya ta fashe da kuka dan a wannan lokacin ta kai mak'ura. Ta jima tana kukan ta kafin ta share hawayen ta ta d'auki hijjabin ta ta fita daga d'akin ta sauka ta fita daga b'angaren ma gabad'aya dan ranta ya b'aci. Gabad'ayan ta wani iri take jinta ta kasa jurewa tana shiga d'aki ta d'auki wayar ta hannu na rawa ta danna number Aliyu, ba jimawa ya d'auka tace, "i need your help Aliyu." Daga can b'angaren yayi kyakykyawan murmushi yace, "Zan taimake ki kar ki damu, ki nutsu zan miki duk abinda kike so ki daina kuka" yana fad'a ya yanke wayar yana bin wayar da kallo yana juyawa ta a hannun sa yana murmushi yace, "Lokaci ya fara Asad, bazaka iya yin komai ba duk abinda ka mallaka sai ya dawo tafin hannuna" yayi murmushi ya kwantar da kansa a jikin kujera yana murmushi zuciyar sa cike da farin ciki. FitattuBiyar Nana Haleema. [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *053.*            A zaune yake a k'asa kusa da k'afafun ta kamar koda yaushe in ya kai mata ziyara ta d'ora k'afa kan d'aya da file a hannun ta tana shan khamshi ji take kamar bazata iya magana ba sabida izzar da take ji da ita a wannan lokacin, file d'in ta mik'a masa tace, "Saka min hannu akai." Asad ya karb'i file d'in yaga akwai biro a ciki yana karanta takardar daki-daki har ya fahimci ta maye ya d'ago zaiyi magana tace, "Abinda na saka ka nace kayi ba magana ba." Ya d'an gyara zaman sa zuciyar sa cike da tunanin sanya a hannu a takardar amma babu damar musu, kallon sa take yi ganin yana juya biron tace, "baza kayi bane?." Ba yadda ya iya haka ya saka hannu ya rufe ya mik'a mata ta karb'a tana murmushi kana tace, "Sai abu na gaba, ina so filin can na baya a tasar min gini a cikin sa bazai yu ina matsayin babar ka na zauna waje mai iri d'aya da sauran ba, ya zama dole a banbanta ni." Asad yace, "in sha Allah za'ayi." Mama tace, "Sai batun bawa Aliyu da Hydar sarauta banji kace komai bafa." Asad yace, "Aliyu yace baya so Hydar kuma baya nan shiyasa ba'a yi komai ba." "To yanzu meye a gaba?." "Ina da meeting da shugaban k'asa gobe a Abuja, then zan wuce Germany wajan Abba daga nan zan shiga madina akwai taron da aka gayyace ni." Mama ta yatsine fuska jin yayi maganar mahaifin sa ita sam bata son ma abinda zai dawo da mahaifin sa kar yazo ya takura mata ya hanata rawar gaban hantsi gwara yaje can ya k'arata tace, "da matar ka zaka tafi?." Asad ya girgiza kai alamun a'a tace, "Meyasa bazaka tafi da ita ba?." Ya lumshe ido ya bud'e kana yace, "Bazan jima ba." "Allah ya kiyaye." "Amin. Godiya nake Allah yaja da rai" ya furta a tusashe cikin girmamawa matuk'a. Shiru ya ratsa tsakani kafin tace, "Zaka iya tafiya." "A huta lafiya" ya furta yana mik'ewa yana takawa a hankali ya fita daga falon aka take masa baya mutane sama da goma yana gaba ana binsa a baya ko tsuntu baya giftawa ta wajan sai in ya wuce sabida tsabar girmamawa. Mota ya shiga aka saki jiniya aka d'auki hanyar Bauchi kai tsaye airport suka nufa har gaban private get motar taje ya fito ya shiga jirgi shida shamakin sa da Uncle suka wuce Abuja.      A kan idanun Aliyu Asad ya fita yayi murmushin farin ciki ya fito zuwa b'angaren Mama ya same ta a zaune da file d'in a kusa da ita ya zauna a inda Asad ya tashi ta kalle shi tace, "Ya dai?." Ya saki murmushi bai ce komai ba ta kuma cewa, "Kamar akwai magana a bakin ka." "Babu komai Mama, tafiya zanyi shiyasa nazo na sanar dake zan jima sosai kuma in na tafi." Ta yatsine fuska tace, "Allah ya dawo dakai lafiya." "Amin Mamana, ina godiya." File d'in gefen ta yabi da kallo kana yace, "Wannan file d'in....." ya fad'a yana niyar d'auka ta d'auke bata bari ya d'auka ba tace, "Bana son bincke, tashi ka bani waje." Murmushi yayi kad'an yace, "A tashi lafiya" yana fad'a ya tashi ya fita yana dariya farin ciki na cika zuciyar sa domin akwai abinda zai aiwatar. A ranar Asad suka gama da president a ranar jirgin su ya d'aga zuwa Germany dan Allah ya sani ya k'agu yaga jikin mahaifin sa shiyasa ko hutawa ma baiyi ba suka wuce. Lokacin da suka sauka ko masauki basu je suka wuce asibitin direct ba tare da sanin Hydar ba. Hydar yana tsaye kusa da likitan da yake duba Abba ana saka masa ruwa har loakcin yana kwance baya ko motsin kirki suka ga an bud'e k'ofa a shigo, Hydar wara idanun sa yayi ganin d'an uwan nasa cikin kamala da shigar da in ka kalle shi sai ya kuma kallo kana ganin sa kasan ba k'aramin mutum bane ba, kana kallon sa kaga basarake mai ji da sarauta da isa da kuma ilimi. Hydar ya washe baki farin ciki ya cika zuciyar sa yace, "Barka da zuwa Ranka ya dad'e, bismillah ranka ya dad'e" ya fad'a yana bashi kujera yana kallon sa shima shi yake kallo. Zama Asad yayi ya kalli Dr cikin harshen turanci yace, "Likita ya jikin sa? Me yake damun sa?." Likitan ya kalle shi yace, "An rasa actual d'in abinda za'a ce yana damun sa, anyi scanning ba'a komai ba har yanzu, mu kan mu baza muce ga abinda yake damun sa ba." Asad ya sauke numfashi ya kalli Hydar yace, "In haka ne why ake ajjiye shi a nan? Meyasa baza mu koma India ba?." Hydar ya sosa kansa cikin girmamawa yace, "Ranka ya dad'e hakan naso yi sai mukayi waya da Uncle yace in bari yazo in anga abinda bazai yu ba sai a koma gida ayi na hausa a had'a da addu'a. " Asad ya kalli mahaifin sa ya tashi ya k'arasa inda yake yana kallon sa idanun sa a kulle ko ina na jikin sa ya saki ga rama yayi sai haske gashin fuskar sa kamar wanda aka fito dashi daga prison. Numfashi Asad yayi ya d'ora hannun sa a goshin mahaifin sa ya kalli Uncle sai Uncle yace, "Ranka ya dad'e yana dakyau aje a huta in yaso sai mu kamo bakin zaren." Asad bai iya magana ba ya sauke numfashi ya kalli Dr yace, "Ina so na gana da babban likitan asibitin nan." Likitan yace, "yana office, muje na raka ka." Asad yayi gaba likitan yabi bayan sa uncle ma yabi bayan sa haka Hydar zuwa office d'in. Abinda wancan likitan ya fad'a shi wannan ya maimaita haka suka fito suka tafi masauki gabad'aya jikin Asad a sanyaye yake zuciyar sa cike da nazarin mafitar da ya kamata ya samo.          A masauki shi kad'ai ne a d'akin ya yayi wanka tare da sallah ya zauna domin a gajiya yake sosai daga Abuja bai huta ba suka yo nan daga zuwan su kuma suka wuce asibiti, buga k'ofar akayi ya bada umarnin shigowa Uncle da kansa ya shigo hannun sa rik'e da babar leda yace, "Ranka ya dad'e ga abinci." Asad ya saunke numfashi yace, "Uncle bana tunanin zan iya cin wani abu." Uncle yace, "daurewa  za'ayi." "Yanayin jikin Abba ya dame ni musamman yanzu dana ganshi." "Dole a shiga damuwa ranka ya dad'e, amma ni a gani na a huta in yaso sai mu kamo bakin zaren." Asad yace, "have a seat Uncle."      Uncle ya zauna yana kallon Asad da ya dafe jijiyoyin kansa da suke harbawa kusan minti biyar kana yace, "I feel like basu iya aiki bane, ta yaya za'a ce an rasa abinda yake damun sa har tsahon wannan lokacin?." Uncle yace, "Ranka ya dad'e da alama an manta a inda muke, Germany ce fa cinbiyar da suka k'ware wajan duba marasa lafiya da k'wararrun likitoci." Asad kamar zaiyi kuka yace, "But why suka kasa yiwa Abba komai? Ka tuna yadda ya koma fa." "Abinda mamaki gaskiya, sai nake ganin mu koma gida dashi ayi masa maganin hausa da addu'a a ganina hakan zaifi. Tunda har akazo nan akace an kasa ganewa da alama ciwon nasa bana asibiti bane yana buk'atar maganin mu na gida da kuma addu'a." Asad yayi shiru baice komai ba ya cize bakin sa zuciyar sa cike da tunani Uncle ganin ya shiga tunani sai ya bashi waje Asad ya jingina da jikin gado yana aikin tunanin ta inda zai b'ullowa lamarin. Kasancewar da rana suka shiga bacci Asad yayi sai dare ya farka bai ma iya cin abincin ba sai bayan yayi wanka yayi alwala ya saka manyan kaya da babar riga wacce taji aikin sarakai ya saka hula mara girma ya kawo hirami ya d'ora a kai ya fito sak a babban malami. A sannan ya d'anci abincin kad'an ya fito suka shiga masallaci sallah daga nan suka koma asibitin. A nan suka sake tarar da Hydar kamar koda yaushe Asad baiyi ta kansa ba yaje ya nemi transfer daga asibitin zuwa asibitin madina, bayan ya dawo d'akin Hydar ya kalle shi shima shi yake kallo kamar zaiyi magana sai ya fasa ya fita shi kad'ai ya tsaya a harabar asibitin daga ciki Hydar ya biyo bayan sa yace, "Amma da ka barshi a nan a ganina zai fi samun kula duba da yanayin likitocin su." Asad ya sauke numfashi ya kalli Hydar kana yace, "can yafi safe." "Ta yaya yafi nan bayan su na can d'in ma nan suke kawo marasa lafiyar su?." Asad yayi shiru kamar bazai yi magana ba kafin yace, "Can akwai albarkar garin addu'a sai ta bashi lafiya." Hydar yace, "Haka ne. Wai Mama ko Hajiya babu wanda zaizo ya kula da Abba ne? Sai dai suyo waya itama sai sunga dama kamar farin ciki suke da ciwon nan nasa. Har gwara ma sauran akan Mama ita kamar ma abin bai dame ta ba." Asad yayi murmushin takaici ya cize bakin sa shi kansa yana yiwa kansa addu'ar Allah kar ya jarrabce shi da mata irin su Mama gabad'aya babu wacce ta damu da rashin lafiyar mijinta abinda yake gaban su kawai suke yi musamman ma Mama da kawai burin ta yayi abinda take so a k'arkashin mulkin sa.         "Kai baza ka iya kula dashi ba?." Hydar ya kalle shi yace, "Akan me bazan iya ba? Gani nayi ya kamata ace koda sau d'aya ne sunzo sunga jikin sa tunda har gobe miji yake a wajan su, har su Yaya sunzo sunga jikin sa amma su basu zoba. Aliyu shi kam ko waya, hakan yana k'ona min rai." Asad ya kawar da kai gefe baice komai ba Hydar yace, "Allah ya kyauta." Ya k'arewa Asad kallo sai yayi murmushi yace, "Asad ka koma babban mutum kamar ba kai ba, ka sake yin kamala kamar mai shekaru da yawa, fuskar ka ta koma ta manyan mutane ta k'aro kwarjini da sanin ya kamata." Bai bashi amsa ba kawai ya juya ya bar wajan Hydar yayi murmushi yana girgiza kansa shima ya juya yabi bayan sa. *☆☆☆*            "Amma dai bashi da kirki bashi da mutunci bai san mutunci ba, har gida dan tsabar ya raina mu yazo yayi mata saki uku! Haba dan Allah" Yaya Ummi ta fad'a kamar zatayi kuka tana kallon Rauda. Umma da take jinta ta tabe baki tace, "To ya za'ayi ne wai? Wannan cacar bakin da kuke yi nida ku babu wanda ya isa ya canja k'addarar nan Allah ya rubuta faruwar ta kuma ta faru." Yaya Ummi tace, "Amma dai duk da hakan akwai ciwo Umma, kwata-kwata nawa Raudan da take da za'a ce ta koma bazawara? Kalle ta fa sabida Allah bai cutar da ita ba?. Daman cana akwai manufar da ta kawo shi gidan nan neman aurenta ba soyayya ba." Umma tace, "kuma dai, sai yanzu kika fahimta ai da kema idanun ki ai rufe k'anwar ki zata shiga gidan sarauta." Rauda dai tana zaune bata ce komai ba tayi shiru kanta ciwo yake mata matuk'a bazata iya magana ba.       "Allah sai yabi miki hakkin ki Rauda wallahi sai yayi dana sanin abinda yayi miki sai kuma yayi kuka da idanun sa, aikin banza wanda ilimin sa bai amfana masa komai ba. Shine zai had'a ki da kud'i wato sune abinda kike so ko?." Rauda bata ce k'ala ba ta sunkuyar da kanta k'asa kawai amma batayi magana ba. Umma tace, "Nida Bauchi zan tura ta ma gidan Yaya Bilki taje ta gama iddar a can sai ta dawo. Babban farin cikina ma ni da ba kowa ne yasan anyi auren ba da yawan mutane sun san ance yana sonta ya kuma biya mata kud'in aikin k'afa amma basu san an d'aura auren ba a wancan lokacin na jiki ne kawai suka sani, naji dad'in hakan sosai ba kowa ne zai san sun rabu ba."         "A haka kamar mutumin kirki har ana yabon sa ace yafi kowa cikin y'ay'an mai martaba ashe shima da kashin sa a jikin sa, shiyasa aka d'aura auren a sirrance babu wanda ya sani kenan?. Kai ai bama iya shi kad'ai ne ya cuce mu ba har baban sa wallahi domin shine ya bada goyan baya." Umma tace, "wannan kumfar bakin da kike yi fa duk na banza ne, tunda Allah ya saka dai ta samu lafiyar k'afar ta shikenan mun gode Allah." Shigowar Baba shine ya hana Yaya Ummi magana ya kalli Ummi yace, "Ki taya y'ar uwar ki da addu'a shine yafi ba wannan d'aga muryar ba dan ba amfani zatayi miki na. Rauda baki da lafiya ne?" Ya fad'a a tausahe yana kallonta. Kallon sa tayi cike da mamakin yadda yayi mata magana tace, "Kaina ne yake ciwo Baba." "Dole kanki yayi ciwo kin kwana kina kuka, Kisha magani zai daina in sha Allah. Ki kwantar da hankalin ki kuma komai ya faru Allah ya k'addara faruwar sa tun kina ciki kafin kizo duniya, komai zai wuce tamkar bai faru ba. Kai ta d'aga zuciyar ta cike da jin dad'in yadda Baban yake mata magana cikin taushin murya da kalamai masu kwantar da hankali ba kamar jiya ba sai taji hankalin ta ya sake kwanciya ko babu komai tasan yanzu Baba bazai ga laifin ta akan sakin ba. Baba yaa kalli Umma yaga fuskar nan tata a d'aure ta kawar da kanta gefe yace, "Binta kawo min ruwan sha sama." Kafin tace wani abun ya fita Umma da tasan babu wani ruwa da za'a kai masa badan taso ba ta mik'e bata d'auki ruwan ba ta fita. Rauda tace, "Allah yasa su shirya, Yaya Ummi jiya naga tashin hankalin da ban tab'a gani ba Baba kamar zai daki Umma." Yaya Ummi tace, "da alama, a yanayin sa ai zaki ga ya gano bai kyauta ba shiyasa kika ga ya sauko har yana rarrashin ki. Daman banda abin Baba meye na fad'a?." Rauda bata ce komai ba tayi tagumi kawai tana kallon wani wajan daban.         Lokacin da Umma ta hau saman a zaune ta same shi ta shiga ta zauna itama batayi magana ba yace, "Binta nasan ban kwanta ba jiya ni kaina sai yanzu na gano kuskure na tun farkon maganar sa da Rauda nine na bayar da goyan bayan ko meye ya faru nine na bada k'ofar faruwar sa. Kiyi hak'uri ki d'auka k'addara ce abinda ya faru jiya ma kiyi hak'uri." Umma ta sauke numfashi tace, "Ya wuce." Baba yace, "itama Rauda ki bata hak'uri nasan ban kyauta mata ba tun farko, bata so akayi auren tayi biyayya ta amincewa abinda na zab'a mata ga kuma abinda ya faru na kuma d'ora mata alhakin hakan." "Ai babu komai kamar yadda kace k'addara ce babu wanda yake kauce mata duk inda kake sai ta bika ta same ka, mun karb'e ta hannu biyu in sha Allah nan gaba zamu ga alkhairin hakan. Ni sai nake ganin ko na tura ta gidan Yaya Bilki tayi iddar ta a can?." "Da idda a kanta ne?" Baba ya fad'a yana kallon ta da mamaki. Umma ta d'aga kai tace, "Akwai idda tun dawowar ta na fahimci hakan a tare da ita, ni burina ma Allah yasa ba ciki dan bana so wata alaqa ta sake had'a mu kar nan gaba suzo suce abinda ta haifa ba nasa bane, shiyasa na k'agu naga ta gama iddar hankalina zai fi kwanciya." Murmushi Baba kawai yayi kafin yace, "basai taje ko ina ba ki barta tayi iddar a nan babu wanda k'addara ta wuce fad'awa kansa." Umma tace, "haka ne. Allah yasa mu dace." Baba ya amsa da amin bata jima sosai ta sakko k'asa. *☆☆☆*           Washe gari su Asad suka tafi Madina aka kai Abba asibiti nan da nan aka karb'e shi aka fara k'ok'arin gano kan matsalar a sannan Asad ya bar Hydar da Uncle a wajan sa shi ya tafi hotel ya shirya cikin farar jallabiya ya saka huta fara k'arama a ciki ya d'ora hirami fari ya saka bak'ar alkyabba kamar yadda labarawan suke yi. Sak ya fito a balaraben Saudia ba b'ata lokaci mota tazo ta d'auke zuwa taron da aka gayyace shi. Bai dawo da wuri ba dan an tattauna abubuwa da dama ciki harda son da suke ya dawo Madina da zaka amma ya nuna hakan bazai yu ba, maimakon ya koma hotel sai ya nufi asibitin wajan su Abba. Kamar can a ranar dai ba'a ce ga abinda yake damun Abba ba Asad yace bazai koma ba ya zauna nan suka wuce ziyarar Rauda. Kwanan su biyu a madina amma shiru ba'a samu wani cigaba ba anyi iyakacin binciken da ya kamata amma ba'a ga wani ciwo ba dukkan su hankalin su ya tashi sosai. Asad yana zaune bayan an gama yi musu bayani ya dafe kansa ya kalli Hydar yace, "Hydar bazan bar Abba a nan ba zamu koma Nigeria dashi." Hydar yace, "Amma ranka ya dad'e da ka barshi a nan zai fi samu kula a akan can." Uncle ma yace, "Nima a gani na ranka ya dad'e gwara zaman nan d'in zai fi samu kulawa akan can, amma hukuncin daka yanke shine daidai." Asad ya shafa fuska sa kana yace, "muje dashi can" yana fad'a ya mik'e dukkan su babu wanda ya isa ya musa washe gashi jirgi ya d'auko su zuwa Nigeria. A katafaran b'angaren da aka gina mai kyau da tsari aka sauke Abba kafin la'asar an had'a duk abinda Abba zai buk'ata a cikin gidan an fara bashi kulawa a cikin gidan. Asad yana zaune a falo bayan an gama kula da mai martaba Mama da Hajiya da Ammi suka shigo da sallama. Mik'ewa yayi yana amsawa suka shiga inda mai martaba yake bai bi bayan su ba Jim kad'an suka fito Hajiya tace, "Amma sai nake gani zaman sa a can zaifi samun kula a akan nan." Asad yayi shiru bai amsa ba Ammi tace, "Gwara nan d'in yafi samun addu'a." Nan ma dai baiyi ba suka fita aka bar shi da Mama ta kalle shi tace, "meyasa bakayi shawara dani ba ka tawo dashi nan?." Ya d'aga ido ya kalle ta sai ya sunkuyar da kai tace, "dakai nake magana  meyasa?." Kansa ya dafe kad'an kafin yace, "Please Mama" yana fad'a ya hau sama ba tare da yace komai ba domin haushin su dukkan su yake ji ya barta a wajan a tsaye a tana kallon sa. Mamaki ya kusa saka Mama ta zube a k'asa a wajan ta bishi da kallo cikin tsantsar tashin hankali amma sanin babu abinda zatayi ya saka ta fita zuciyar ta cike da tashin hankalin da bata san dalilin sa ba. Bayan wasu kwanaki. [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *054.*          Waya ce a hannun Mama tana juya ta kana kallon yanayin ta kasan tana cikin tunani domin fuskar ta ta bayyana hakan kallo d'aya zakayi mata ka fahimci akwai damuwa mai tarin yawa a tare da ita duk da tana k'ok'arin b'oyewa. Sake kallon fuskar wayar tayi ta danna video call ta kira Aliyu, ba jimawa aka d'auka fuskar sa ta bayyana a kai ta kalle shi tace, "Aliyu kana wacce k'asa ne?." Aliyu da yake zaune ya kalle ta yace, "Bahrain." "Yaushe zaka dawo ne? Wannan wanne irin zama kake yi a wata k'asar bayan kasan ina buk'atar ka nan." Yace, "Mama zan dawo akwai abinda nake yi a nan d'in ne amma dana gama zan dawo nima nafi so na dawo nan d'in akwai dalilin zaman nan d'in." Yana bata amsa ta yanke kiran ta cillar da wayar a kan kujera ta dafe kai da duka hannayen ta. "Asslamu alaikum" Hydar ya fad'a a sanyaye yana shigowa falon ya zauna a kusa da ita. A ciki ta amsa ya kalle ta yace, "Akwai damuwa a tare da mahaifiyata, ko zan iya sanin dalilin zuwan ta?." Ta furzar da iska ta jima a haka bata bashi amsa ba kafin ta d'ago tace, "Hydar Asad! Ya canja yanzu gabad'aya kamar bashi ba." Hydar ya girgiza kai yace, "Allah yaja da ran Mamana akwai wani abu da ya aikata ne?."        "Meye ma bai aikata ba Hydar? Asad yanzu baya shawara dani yake aiwatar da komai sai dai naji labari a bakin Sadiya ko Jidda, Sadiya da Jidda sai sun fara jin abu kafin ni naji meyasa yake neman canjawa lokaci d'aya?." Hydar ya girgiza kai yace, "Allah ya wuci zuciyar ki; kinfi kowa sanin halin Asad kece kika haife shi kika kuma raine shi kinfi kowa sanin halin sa a kan kowa a duniyar nan. Duk yadda akayi yana da dalilin aikata abinda yake yi." "Dalilin sa na banza da wofi, duk yadda kake tunanin Asad a baya yanzu ba haka yake ba. Wacece Sadiya da zata riga ni sanin wani abu daya shafe shi?." "Allah ya wuci zuciyar ki, zan same shi da kaina nayi masa magana a kai in ma akwai wani abun da yake damun sa zan ji." "Jeka maza yanzu, yamma ce yana b'angaren sa." "A tashi lafiya" ya fad'a cikin girmamawa yana tafi ya fita direct ya wuce b'angaren Asad.         Asad yana zaune hannun sa rik'e da waya yana dannawa Jidda ta fito daga d'akin sa sanye cikin riga da siket y'an kanti kanta babu d'ankwali tayi kyau sosai tana zuwa ta yiwa kanta mazauni a cinyar sa ta kwace wayar a hannun sa ta ajjiye a gefe ta had'a goshin su waje d'aya tana kallon idanun sa. Shima kallon nata yake yi kamar yadda take kallon sa; shidai kawai yasan zuciyar sa tana sonta a wannan lokacin amma bai san yaushe hakan ya samo asali ba. Murmushi tayi masa shima ya samu kansa da mayar mata da martani khamshin bakin sa ya daki hancin ta ba shiri ta kai bakin ta kusa da nasa ta d'ora a hankali ta fara kissing d'insa slowly, bai hanata ba sai ma taya ta da yake yi hannun ta akan sajen fuskar sa tana shafa gashin tana sake rik'e fuskar tasa sosai. Kusan minti biyu suna a haka kafin ta zame bakin ta a hankali tayi dariya ta kwanta a k'irjin sa tace, "i love you my king." Idanun sa ya lumshe ya bud'e su a kanta muryar sa can k'asa yace, "Love you too." Wani irin dad'i take ji yana ratsa jijiyoyin jikinta tayi farrr da idanun tana jin kanta a sama in ta tuna Asad da yake fizge-fizgen yanzu shine a hannun ta sai abinda tace masa yake yi. Zatayi magana wayar sa ta fara yin k'ara, kallon screen d'in tayi taga Hydar yana yawo a kai taja tsaki ta danna ta kashe k'arar tana kallon sa bai hanata ba. Wata wayar ce ta sake shigowa ta sake ganin sunan sane ta d'auka ta saka a kunne Hydar yace, "Assalamu alaika, Ranka ya dad'e in an bani dama ina so na shigo mu tattauna akwai magana mai matuk'ar mahimmaci da zamu yi." Jidda ta yatsine fuska tace, "Bashi da wannan lokacin, ka jira gobe kwa tattauna a fada." Hydar da mamaki yace, "Jidda ina yake?." "Kar ka sake kirana Jidda, Fulani shine sunana. Gashi nan muna tare bashi da lokacin kane." "What! Kin sanar dashi nine nake waya?." "Shi ya bani na d'auka ai kaga ya fika sanin waye ya kira, kar ka takura mana yanzu please" tana gama fad'a ta yanke kiran ta ajjiye tana kallon sa kamar zai mata magana sai kuma taga ya fasa. D'aga shi tayi shi kuma ya mik'e ya shiga d'akin da ya kasancewa d'akin karatu, da kallo ta bishi tayi dariya ta shiga d'aki da sauri hannun ta yana rawa ta lalubo waya ta dannawa Mum kira tana d'auka tace, "Mum aiki yana tafiya yadda ya kamata, Asad ya dawo hannuna Mum ko Mama sai yaga dama yake zuwa inda take balle wani Hydar." Mum tayi dariyar farin ciki tace, "nasan wannan ranar zata zo Jidda na jima ina yi mata shiri mai kyau shiyasa da ta tashi zuwa tazo cikin dad'i da annushuwa. Kice yanzu Rabi ta zama y'ar kallo?." "Bari kawai Mum, sai fa yaga dama ma zaije wajan ta duk kuma abinda nace ina so shi za'ayi koda ba daidai bane ba kuwa." "Kar dai kiyi sake ina fad'a miki nasan babar sa sarai ta wuce tunanin ki. Babban burina ki samu ciki yanzu yadda zamu yak'e ta da makamai masu tarwatsa duniya." Jidda ta zauna a gefen gado tace, "An kusa samu Mum." Mum tayi siririyar dariya tace, "Dana fi kowa farin ciki in hakan ta kasance, akwai tarin abubuwa dana shirya Jidda yanzu baki fara ganin komai ba ki d'auka ba'a fara komai na." Jidda zatayi magana Mum tace, "Ina zuwa Daddyn ku nayi min waya" tana fad'a Jidda ta yanke kiran tana murmushi burinta guda d'aya tal a duniya daman ta mallaki Asad kuma ta mallaka sai yadda tayi dashi ko Mama bata kulawa balle wasu kuma.       Gaban tane ya fad'i tunawa da wani abu da ta binne tsoro ya fara shigar ta sai tayi saurin kawar da tuannin a bayyne tace, "Ta yaya zan bayyana?. Har abada bazai tab'a bayyana ba in sha Allah tunda ai Aliyun baya nan na tabbata bazai tab'a dawowa ba har abada."      Hydar jikin sa a matuk'ar sanyaye yake tafiya ana gaishe shi ma bai san ana yi ba ya wuce b'angaren da Abba yake ya samu d'akin daga shi sai Uncle a zaune likita yana yi masa allura an samu idanun sa suna bud'ewa cikin kwanakin kana fahimtar yayi bacci ko idanun sa biyu. Likitan ya fita Hydar ya zauna ya kalli Abba da shima shi yake kallo sai ya sunkuyar da kai yace, "Uncle me yake damun Asad ne?." Uncle yace, "kaima ka kaga canje-canjen dana gani kenan ko?." Hydar ya sauke numfashi yace, "yau ni mai martaba ya saka Fulani ta d'auki waya tana cewa bashi da lokaci na....?, ni Hydar fa Uncle? Ashe akwai ranar da zaice bashi da lokacin Hydar Uncle?." Uncle ya murmusa yace, "Itace babbar matsalar sa Hydar, matar sa kamar ta juyar masa da hankali komai nasa ya canja hatta yawan karatu da zikirin da yake yi ya daina sai yaga dama. In tak'aice maka labari sai mai martaba yaje wani taro ba tare dana sani ba sometimes sai ya d'auki Suhail bai d'auke ni ba. Ba k'aramin abu tayi masa ba shiyasa da ya tashi kama shi bai masa kamu ta sauk'i ba." Hydar ya girgiza kai cikin damuwa mai tsanani yace, "Tabbas Uncle Jidda itace matsalar Asad nima nayi tunanin hakan domin itace take sake assasa komai, Duk qaunar Asad da Mama baya zuwa inda take sai yaga dama. Hmmm Dole mu taya shi da addu'a kafin abun yazo yafi k'arfin mu." Murmushi sukaga Abba yayi a karo na farko tunda ya kwanta ciwo dukkanin su suka k'arasa inda yake da farin ciki Hydar yace, "Uncle murmushi naga yayi ko idanuna ne?." Yace, "Nima na gani ba kai kad'ai ba, Alhamdulillah lafiya tana samuwa tunda muka dawo Nigeria." "Gaskiya na jima banga abinda ya faranta min rai kamarwannan cigaban da aka samu ba, Alhamdulillah." Kallon su suka ga yanayi suma shi suke kallo sai kuma suka ga ya lumshe idanun sa hakan ya saka suka bashi waje kar suje hayaniya ce tayi masa yawa. Hydar wajan Mama ta wuce ya same ta a d'akin ta ita da Suhaima suna tattauna batun canjin da Asad ya samu ya shiga da sallama tun kafin ya k'araso ta tashi tace, "Ya kuka yi dashi?." Hydar ya sunkuyar da kansa kana yace, "Ki gafarce ni Mama, matar mai martaba Fulani ta d'auki wayar sa tace bashi da lokacin da zai saurare mu gabad'ayan mu, maganar da nake yi yanzu ban ganshi ba shima bai ganni ba." Mama ta dafe kai tana fad'in, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, me yake shirin faruwa dani ne haka?." Ta fad'a kamar zata fad'i Suhaima tayi saurin tare ta tana fad'in, "Mama!." Zaunar da ita sukayi ita da Hydar suka tsuguna a kusa da ita Hydar yace, "Allah ya sanyaya miki zuciya Mama, ina mai baki hak'uri a madadin sa in sha Allah komai zai dawo yadda kike so amma sai mun dage da addu'a sosai domin lamarin nasa ba mai sauk'i bane." Suhaima tace, "ita wacece da zata ce baza ka ganshi ba? Yaushe ta shigo gidan da zata fara yi mana mulkin mallaka....? Ina zuwa" tana fad'a ta tashi a fusace ta fita daga d'akin ta nufi b'angaren Jidda a zafafe.       A bakin babban falon ta tarar da dogarai maza guda biyu tana isowa suka bata waje suna zubewa a k'asa bata kula su ba ta shiga babban falon ganin bata nan ta nufi na biyun, jakadiyar ta da wata baiwa sukayi saurin tare hanyar suka ce, "Allah ya wuci zuciyar Fulani ina mai baki hak'uri sanar dake cewa Zakanyar mai martaba tace kar mu bar kowa ya shiga ba tare da izini ba." Da matuk'ar mamaki Suhaima ta girgiza kai a bayyane tace, "Zakanya!." D'aya ta duk'a tace, "kwarai da gaske ranki ya dad'e." Suhaima tace, "baki gane wacece bane?." Jakadiyar tace, "na gane ki ranki ya dad'e ina bin umarnin shugaba ta ne." Suhaima taja dogon tsaki tace, "in kuna da k'arfin hanani shiga sai na gani" tana fad'a ta zagaye su ta shiga babu yadda zasu yi mata dole suka bita da kallo kawai.         A falon kuwa Jidda na zaune tana waya cikin nishad'i tana dariya kawai taga Suhaima ta fad'o ta kalle ta ta d'aure fuska ta yanke wayar tace, "Lafiya Suhaima zaki shigo min falo ko sallama babu?." "Meye matsalar kine da zaki hana Hydar ganin mai martaba?." Jidda tayi y'ar dariya tace, "Sabida ni zakanyar sace." Kallon mamaki take mata hakan ya saka Jidda tace, "Baki gane bane? Shi zaki ni kuma zakanyar sarki, ko waye ko kuma wacece matuk'ar banga damar ya ganshi bazai ganshi ba ciki harda ku ." "Waye ya baki wannan matsayin?." Jidda ta mik'e tsaye kana tace, "mijina kuma uban yarana, shugaban ki kuma sarkin ki sannan yayan ki." Suhaima ta bita da kallo kafin tace, "ke yanzu har kina da wannan matsayin a wajan a ganin ki?." "Ai ba a gani na bane ba Suhaima, a bayyane yake in kina musu ki gwada ki gani." Suhaima tace, "Zanyi kuma baki isa ki hana ni ganin yayana ba dan baki da ko wanne matsayi a wajan sa face wacce Mama ta bashi matsayin ya aura badan yana so ba." Tayi dariya harda tafa hannu tace, "Zaki ga matsayina da zarar kin gwada hakan kuwa, a nan zaki gane cewa Mama ta bashi ni kuma ya karb'a babu wanda ya isa ya kwace ni." Suhaima ta harare ta tare da jan tsaki tana girgiza kai cike da jin tsanar Jiddan a zuciyar ta, Jidda kuma ta kira baiwar da tasan tana bakin k'ofa. Da sauri ta shigo jiki na rawa ta zube tace, "Allah yaja zamanin shugabata, Allah ya kare ki Allah ya taimake ki ya rufa miki asiri." Jidda tace, "ta wacce hanya kika bari Suhaima ta shigo min falo bayan na gargad'e ki game da hakan?." Jikin ta rawa yake sosai tace, "Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake, kaina bisa wuyana ki gafarce ni. Na sanar da ita umarnin ki tayi watsi dashi ta shigo bazan iya hanata ba." Jidda tace, "Zaki iya rabuwa da aikin kenan." "Allah ya wuci zuciyar uwar gidan mai martaba, afuwa nake nema a wajan ki ki yafe ni banyi dan na b'ata miki rai ba." Jidda ta kalli Suhaima da take tsaye tana kallon ta ta kalli baiwar tace, "Daga yau ko Fulani Mama ce tazo indai nace kar a bar kowa kika sake kika bari ta shigo a bakin aikin ki, kuma sai na saka an miki dukan tsiya kin kuma share turke.......!" [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *055.*          Ba iya Suhaima kad'ai ba hatta ita kanta hadimar sai da gaban ta ya fad'i ta zaro idanu har tana had'a ido da Jidda ba tare da tasan ta aikata hakan ba sai dan tsabar gigitar da kalaman Jidda suka jefa ta. "Kee! D'auke idanun ki cikin nawa" ta fad'a cikin tsawa ba shiri ta kai idon ta k'asa tana raba ido sabida tsoro jikin ta har rawa yake yi. Suhaima da ta k'ame a wajan tana kallon Jidda cikin d'ibum mamaki ta tab'e baki tace, "Ko mijin ki bai isa ya hana Mama shigowa nan ba balle ke karan kad'a miya matar cushe, ke bama wannan b'angaren ba ko wanne b'angare na gidan nan babu wanda ya isa ya yiwa Mama iyaka dashi balle kee y'ar talakawa jinin talakawa wacce bata da tarbiyya." Jidda ta murmusa ta kalli hadimar tace, "kinji me nace miki ai ko?." Ta girgiza kai alamun eh da hannu ta bata umarnin ta bata waje ta fita jiki na rawa Suhaima taja dogon tsaki ta fita ta barta a zaune zuciyar ta na fasa sabida b'acin rai. Murmushi tayi tana kallon inda Suhaima tabi tana wasa da hannun ta tace, "zaku d'and'ana kud'ar ku badai yanzu Asad din a hannuna yake ba....? Hmmmmmm muje zuwa" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki tana jin izza a zuciyar ta da gangar jikin ta.          Yarda Suhaima ta shiga d'akin Mama a firgice ya saka Mama tashi tsaye Hydar yana rik'e da ita tace, "Me tace miki Suhaima?." Suhaima tace, "Ki gafarce ni Mama amma Jidda ta wuce tunanin ki, kallon idanuna tayi ta kira hadimar ta take sanar da ita koda kece kika je kar a barki ki shiga matuk'ar ba ita ta bada umarnin hakan ba." "K'arya take! Wacece ita waye ubanta a garin nan? Yaushe ta shigo gidan nan har da take da bakin furtawa wannan mummanar kalma akan Mama..?" Hydar ya fad'a a fusace cikin b'acin rai yana kallon Suhaima kamar zai dake ta. Mama da take jin kanta yana juyawa tace, "yi a hankali Hydar bana so mutanen gidan nan su san abinda yake faruwa, ku barni da ita in anyi i'sha kuzo muje wajan Asad d'in dukkan mu koma meye yake faruwa zan gani zan kuma yi maganin abin a yau d'in nan, bazan bari abun yayi nisa ba dan ni zata cutar." Hydar yana rik'e da ita ta zauna ya kalli Suhaima yace, "Zo ki rik'e ta." Ba musu Suhaima ta zauna kusa da Mama ta rik'e ta ita kuma ta dafe kanta da yake mata ciwo zuciyar ta na harbawa da sauri tashin hankali na sake mamaye zuciyar ta. Kiran sallar magriba ya saka Mama ta tashi Suhaima ma ta fita zuwa nata d'akin domin yin sallah.         Fulani Hajiya na zaune cikin mayan y'ay'an ta mata su kad'ai ne a zaune bayan su babu kowa tattaunawa babbar cikin su wacce ake kira da Fulani Babba ta kalli Hajiya tace, "Hajiya mai martaba k'anina yana gari kuwa?." Ta tab'e baki tace, "Yana nan yayi wahalar gani yanzu gabad'aya halayyar sa ta canja kamar bashi ba." Wacce take binta biyun Fulani Jamila tace, "Haka Khaleesat take fad'a min gabad'aya yanzu an rasa gane kansa, daman ya za'ayi a barshi lafiya yayi sarauta..? Ba babar sace ta nace ba ai yanzu sai ta zuba ruwa a k'asa tasha." Fulani Babba tace, "Me ya same shi? D'azu da na shiga duba jikin Abba na d'auka zan ganshi wajan sai ban ganshi ba sai Hydar dalilin hakan ya saka na d'auka baya k'asar." Hajiya tace, "Ai bashi da wannan lokacin a yanzu, in ba Jidda matar saba bana tunanin ko ita Rabi'atu yana saurara, gabad'aya ya canja daga Asad ya koma wani daban." Fulani Babba tace, "Ya kamata kuwa a tashi tsaye a kansa domin in ba haka ba sunan gidan mu zai lalace, in ya lalace ba iya shi ya lalacewa ba harda mu." "Ina ruwan ki ya lalace d'in mana kece kika lalace? Ba babar sace take son hakan ba....? ai ga mulkin nan sai tayi abinda take so." "Allah yaja da ran Hajiya ai d'an uwana ne, kuma shugaban wannan gari yadda ake yabon sadaka da kyautar sa ga talakawa in muka bari hakan ta cigaba da tafiya ba iya shi ba har mu sai abin ya tab'a."       "To ban baki umarnin hakan ba, ki k'yale shi kome yake yi yana sane babu wanda ya kai Asad wayo a gidan nan kawai dan bashi da magana ne." Shiru sukayi dukkan su wayar Hajiya ta d'an yi k'ara kad'an ta duba kana tace, "magriba tayi ku tashi ku tafi gidajen ku." A tare suka duk'a suka ce, "Mun barki lafiya, a tashi lafiya" Suka fad'a suna tashi suka fita falon ya rage saura ita kad'ai ta d'auki wayar ta ta shiga can k'arshen d'akin ta. Tana shiga d'akin wayar ta sake d'aukar vibration tana d'auka ta saka a kunne tace, "Ina tare da yara ne sai yanzu suka tafi shiyasa ban d'auka ba." Daga can b'angaren yace, "Kiran ki na gani d'azu." "Kana da labarin yadda abubuwa suke lalacewa a gidan nan kuwa? Daga majiya mai tushe an sanar dani Hydar yaje ganin Asad an hana shi ganin sa." Dariya yayi irin ta rainin hankali kana yace, "nifa na kwanto kurar ta yaya kike tunanin ban san inda zan kamata ba? Kome yake faruwa a gidan nan na sani kuma ni na saka hakan ya faru. Rabi'atu kad'an ta fara gani sai tayi kuka da idanunta wallahi, sai tayi dana sanin bawa Asad mulki." Hajiya ta zauna a gefen gado kana tace, "A yanzu ma ta fara d'and'ana kud'ar ta tun ba'a je ko ina ba, amma meyasa yake fifita matar sa a yanzu akan babar sa? Karfa matar ta bamu matsala nan gaba." "Rabi ta amince da babar yarinyar ko wanne sirrin ta ta sani; ta wannan hanyar tayi amfani da sirrikan ta ta mallakewa y'arta Asad ta yadda sai abinda tace masa zaiyi. Ke banda Asad yana da addu'a da rik'o da salati ai wallahi da yanzu an jima da haukata shi, matsala kuma ko Rabi bata isa ta bamu matsala a yanzu ba balle wata matar Asad."         "Aliyu fa?." Yayi k'aramar dariya yace, "ke tunda yayi tafiyar nan kin sake jin d'uriyar sa?." "A'a." "To ya tafi kenan, Aliyu bazai sake marmarin dawowa Nigeria ba har abada na riga na tura shi bazai dawo ba sai dai in nine naso hakan. Nayi maganin Asad ma balle Aliyu k'aramin alhaki." "Amma ba haka aka tsara ba, karb'ar mulki a hannun Aliyu sai yafi sauk'i akan karb'a a hannun Asad, da ka bari anyi canjin yadda master ta tsara da yafi a ganina."        "Wannan ma master d'ince ta canja plan d'in kuma hakan shine daidai, barin Aliyu ya hau karaga babbar illa ce domin kin san halin sa yana da bala'in wayo bazai bamu wata damar da zamu tunb'uke shi cikin sauk'i ba. Yanzu kuwa kinga yana wata uwa duniya mun kafe shi a can mu kuma muna nan bai isa yayi wani abun ba tunda baya k'asar ma gabad'aya." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "Haka ne. Har naji dad'i daman babban tashin hankalina Aliyu amma tunda kayi maganin sa zance ya k'are." "Ai abun ne yazo mana yadda muke so ga mai martaba a kwance ba lafiya, Hydar da Mubarak hankalin su yana kan mai martaba da wannan damar zamuyi amfani mu cimma muradin mu kafin lokaci ya k'ure mana. Nan kusa zaki ji labarin da dole sai an sauke Asad a karagar mulki, badai halayyar sa ta canja ba....hmmmm" ya fad'a cikin zallar mugunta. Hajiya tayi dariya mai sauti cikin farin ciki tace, "Lokacin yazo ni na matsu nasan wacece master planer." Yayi murmushi yace, "Sab'anin tunanin ki itace Master planer, in kina jin labarin kwantan b'auna ki d'auka master planer itace kwantan b'auna da kanta ba aiki taba. Zan kira ki" yana fad'a yana yanke wayar tabi wayar da kallo. "Master planer! Wacece ita? A ina take? Ya akayi ya amince da ita.....?." Sanin babu mai bata amsa ya saka ta tashi ta shiga band'aki zuciyar ta cike da farin ciki wani b'angaren babu dad'i.       Bayan an idar da sallar i'sha kamar yadda Mama tace ita da Hydar da Suhima suka nufi b'angaren Asad tana gaba suna binta duk inda suka gifta aka zubewa a gaishe su har suka isa b'angaren nasa. Babu wanda zai dakatar da Mama ga shiga b'angaren dole kowa ya bata hanya ko yunƙurin hakan ma ba'a yi ba a babban falon k'asa suka zauna Mama ta kalli Hydar tace, "Kira min shi a waya." Kiran wayar da Hydar yayi amma baya d'auka ya kalli Mama yace, "Allah yaja zamanin Mama baya d'auka." Ta kalli saman ta mik'e tace, "muje saman" ta fad'a tana nufar stairs d'in ta fara takawa tana hawa gabanta yana fad'uwa matuk'a amma haka ta d'aurewa zuciyata tana hawa saman. Ita ta fara shiga falon ta ga Jidda a zaune tana kallon tv hannun ta rik'e da glass cup an zuba nono a ciki tana sha, kawai ganin Mama tayi a kanta ta d'ago ta kalle su ta mayar da hankalin ta kan TV kamar bata gansu ba sai kuma ta d'auki wayar ta tana dannawa. Kallon mamaki Mama take yi mata tace, "Jidda baki ganni bane?." Ta d'ago tare da k'ank'ance idanun ta tace, "Na ganki, jira nake kuyi sallama then sai na yi magana." Mama ta kalli Hydar suma ita suke kallo ta kalli Jidda tace, "ke duk abinda kike ji dashi ki tabbatar kin ajjiye shi gefe ki san wacce take gaban ki." Wani irin kallo tayi mata akan idon Suhaima hakan ya faru ta zabura tayo inda take tace, "Mama kike yiwa wannan kallon?." Ta kalli Suhaima tace, "Zaki dake ni ne?." "In na dake ki ya zakayi dani?." "Wallahi sai kin kwana a cell" ta fad'a tana kurb'ar nono ta ajjige glass cup d'in akan table ta tashi tsaye. Hydar yace, "Wai jidda me yake damun kine?." Ta kalle shi tace, "tambayi babar ku. Me yake damunta da zata shigo mana har nan babu neman izini balle sallama." Hydar ya zabura kamar zai dake ta Mama ta dakatar dashi ita kuma ta kalle shi tace, "me kake shirin yi?." Zaiyi magana aka bud'e k'ofar da take falon aka fito duk suka kalli wajan suka had'a ido da Asad da ya fito waya na kunnen sa ganin Mama ya saka shi sauke wayar daga kunnen sa da sauri ya k'araso inda take ya duk'a har k'asa yace, "Barka da dare Mama." Wani irin sanyi taji a zuciyarta ta lumshe ido ta sauke bayyananiyar ajiyar zuciya ta kalle shi tace, "Asad me yake damun ka kwana biyu?." Kansa ya saukar ya runtse ido yana jin sa wani iri daban yayi shiru bai amsa ba. A kan kujera ta zauna ya zauna a k'asa kusa da ita Hydar da Suhaima duk suka zauna a k'asa sab'anin Jidda da ta hard'e a kan kujera tana kallon su. Ba ta Jidda take ba dalilin da ya saka batayi mata magana ba tace, "Ina tambayar ka kayi min shiru ka bani amsa." Asad yace, "Mamaaaa...." shiru yayi ya kasa k'arasawa Jidda da take zaune ta fashe da kukan munafurci. Gabad'aya hankalin sa ya koma kanta ya juyo yana kallon ta tace, "Kamar ni Hydar zai ce zai daka, ina matsayin matar ka dan yana k'anin ka sai yace zai dake ni..?. Kenan nan gaba ma bawan gidan nan sai ya d'aga hannu ya dake ni tunda ka nuna musu bani da mahimmaci a wajan ka." Kallon Hydar yayi suka had'a ido ya kalle ta ya sake kallon sa da ido yake masa magana ya fahimta amma sai ya basar kamar bai gani ba domin haushin Asad d'in yake ji ba kad'an ba.         "Ni zaka kalla Asad ba Hydar ba." Kallon Maman yayi kamar yadda tace zaiyi magana Jidda ta sake katse shi tace, "shikenan ni an wulaƙanta ni kenan a banza? Ina matsayin matar sarki uwar gidan sa uwar y'ay'an sa wani yayi yunk'urin dukana a zuba masa ido daidai kenan...?." Mama ta fusata tace, "Kee Jidda! Bana son shirmen banza kin san halina, ko Sadiya bata magana in ina magana balle ke." Jidda tace, "Sai ita tak'i yi amma ni zanyi. My king ko a d'auki mataki akan Hydar ko kuma na bar gidan nan." Asad ya runtse ido ya kalli Hydar yayi shiru baiyi magana ba Mama tace, "Asad wai me yake damun ka? Kayi magana me ta baka kaci ka koma haka..?." "Abinda kika bawa mai martaba yaci ya koma yadda yake shi na bashi yaci, yadda kika mayar dashi haka nima zan mayar dashi wannan ba damuwar ki bace ba. ku tashi ku fitar min daga b'angaren miji lokaci shiga turaka......" babu zato taji saukar mari a kuncin ta. Suhaima ce a gabanta ta manta ma a falon wa take da kuma su waye a gabanta jikin tane kawai yake rawa jin yadda take fad'awa Mama maganar da tunda tazo duniya bata tab'a ji an fad'a mata irin ta ba. Mik'ewa tsaye Asad yayi idanun sa a waje yana kallon Suhaima da take kallon Jidda sai kuma ta kalle shi ta duk'a tace, "ka gafarce ni bazan iya zuba ido ana zagin Mama ba dole na d'auki mataki, nasan kuma mai martaba yana girmama mahaifiyar sa dan na d'auki hukunci akan wacce taci zarafin ta bazai bani laifi ba." Jidda da take dafe da kunci cikin mamaki dan bata d'auka hakan zai faru ba tace, "Ni kika mara Suhaima? Ina matsayin matar yayan ki, matar sarki, matar shugaban ki sama nake da kowa a gidan nan zaki d'auki hannu ki mare ni. My king kana gani kk?" Ta fad'a tana kallon Asad da yake kallon Suhaima baice komai ba. "K'asa kike da Mama shiyasa na hukunta ki." "Ko ita Maman sama nake da ita domin ita ta tako tazo inda nake ba nice nazo inda take ba, babu wanda ya fini a gidan nan koda kuwa itace!."      Shiru falon yayi ana jiran aga hukuncin da zai yanke dukkan su basuyi tsammani ba suka ga ya tsinkawa Suhaima mari abinda bai tab'a faruwa ba kenan tsahon rayuwar su. Mik'ewa Mama da Hydar sukayi ba shiri Mama ta kallli Hydar shima ya kalle ta suka kalli Suhaima da hawaye yake sakkowa daga idanun ta cikin bak'in ciki da k'unar rai. Hydar ya k'arasa inda yake yace, "Asad kana cikin halin ka? Mama ta zaga fa dan tayi mata hukunci sai ka dake ta?, kenan ka fifita ta akan Mama kenan?" Ya fad'a da alama ya manta matsayin da Asad yake dashi kallon Asad d'in da yake masa. Asad ya kalle shi yace, "Matata take, kuma sama take da kowa a gidan nan, sau d'aya tak baka tab'a ganin k'annen Abba sun daki Mama ba dan bazan lamunci gani anyi a gaban idanuna na k'yale ba." Hydar da ya zuba masa ido shima shi yake kallo cikin mamaki da tsoro Hydar yake girgiza kai Jidda tace, "wannan hukuncin yayi mata kad'an ina so ka saka ayi hukunci kamar yadda za'a yiwa baiwa in ta aikata kuskure da tayi." Mama ta matso kusa dashi cikin sanyin jiki ta juyo dashi da hannunta tana kallon sa shima kirr yana kallon idanun ta tace, "Asad anya kaine?" Ta fad'a tana d'ago kansa tana sake kallon idon sa ta tabbatar shine da gaske ba wani ba tace, "Meya same ka Asad? Wannan canjin daga ina yake haka?" Ta fad'a a tausashe tana kallon sa. "Mama a gaban ki ta mari Jidda baki hanata ba bayan hakan ba daidai bane" sake kallon sa take jin abinda yace tana girgiza kai. "Nifa my king kawai su sauka su bar wajan nan bana son ganin su, sannan ka saka a yiwa Suhaima hukunci indai kana sona kana qaunar zama dani!" Jidda ta fad'a tana kuka tana kallon sa suka had'a ido ya kalli Mama ya nuna musu hanya yace, "Mama ko zaku iya sauka?." "What!" Hydar ya furta yana kallon sa da mamaki jin abinda yacewa Mama idanun sa k'asa kuma kamar koda yaushe. Kafin su gama mamaki suka ji ya kalli Suhaima yace, "Ki tabbatar da sai an miki bulala goma nan gaba in kika sake....." Sai ya dafe kansa kana ya cigaba yace, "zan miki hukuncin da bakiyi tunani ba." Mama baki bud'e take kallon sa idanun ta sunyi ja sabida tashin hankali da tsoro hadi da al'ajabi da bugawar zuciya tace, "Asad kasan da wanda kake magana kuwa?." Ya runtse idanun sa ya dafe kai yace, "Na sani, na sani Mama! Don Allah ku barni kafin ku haukata ni bana son magana." Hydar ya sake kallon sa yace, "Asad kaine?." Cikin b'acin rai da fusata Asad yace, "Hydar i said out!" Ya fad'a da d'an k'arfi yana nuna musu hanya idanun sa a waje yana dafe kansa jin kamar zai fashe. Ba shiri Hydar ya kama k'afadun Mama suka wuce Mama na kallon Asad shi kuma idanun sa a kulle hannun sa dafe da kansa suka fara sauka daga steps d'in, "Suhaima ki tabbatar sai kin karb'i hukuncin ki domin bazan yafe miki laifin da kika aikata ba." muryar Jidda ta katse su suka juyo dukkan su suka kalle ta suka cigaba da sauka ko wanne zuciyar sa cike da tashin hankali. *Boom*💥😂😂 FitattuBiyar Nana haleema [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *056.*          Mama bata san sun isa b'angaren ta ba sai gani tayi Hydar ya zaunar da ita a gefen gado ya kawo mata ruwa mai sanyi a kofi ya mik'a mata ba musu ta karb'a ta shanye ko zata daina jin zafin da yake tasowa daga zuciyar ta amma babu canji, cillar da kofin tayi ya tarwatse a wajan ta dafe kanta da hannunta jikin ta yana rawa sosai dan tunda take bata tab'a shiga tashin hankali makamancin wannan ba. Zabura tayi ta kalli Suhaima tace, "Mik'o min wayata da sauri." Suhaima jikinta duk a mace har lokacin inda Asad ya mare ta zafi yake mata ta mik'a mata wayar hannun Mama na rawa ta kir  number Mum bata d'auka ba ta sake kira ba'a d'auka ba ta cillar da wayar a kan gado tana ji kamar tayi hauka sabida tashin hankalin da take ciki. Hydar yace, "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalin ki kin sani ba halin Asad bane abinda ya aikata akwai abinda yake faruwa a cikin lamarin nan." "Abinda yake faruwa ya wuce ta mallake shi?" Suhaima ta bashi amsa daga gefe idanun ta yana cikowa da hawaye.         Da hannu Mama tayi musu alama da su bar mata d'akin Hydar ya fita Suhaima ta kwashe glass d'in da ya fashe sannan ta fita kowa zuciyar sa babu dad'i akan abinda ya faru. Kamar mahaukaciya haka Mama ta koma so take ta samu mafita amma ta rasa inda zata samu ta d'auki waya ta kira babar yayar su amma wayar a kashe ta ajjiye wayar ta dafe kanta da duka hannayen ta. "Ni Rabi'a Jidda zata yiwa wannan wulaƙancin? Inaaaa bata isa ba wallahi ba kuma zata isa ba har abada" ta fad'a tana sake naushin iska cikin tashin hankalin da bata san iyakar adadin sa ba. Bata san ina adadin lokacin da ta d'auka tana a  haka ba ita dai tasan bata jin bacci ko kad'an ga abinda ya kuma tsaya mata a rai rashin kiran ta da Mum bata yi hakan ya sake tauar mata da hankali matuk'a. Bacci b'arawo ne ya sace Mama shima tana yi tana mafarkai tana farkawa. Washe gari. *☆☆*        "Rauda!" Umma ta fad'a tana tab'a ta tayi firgigit ta kalli Umma tare da sauke tagumin fuskar ta tace, "Na'am Umma, yaushe kika shigo?." Umma tace, "ta ya zaki san na shigo bayan kin shiga duniyar tunani?. Anya Rauda kina son samawa zuciyar ki salama kuwa? Kin mayar da tunani abokin ki koda yaushe kuna tare dan k'addara ta fad'o rayuwar ki?, meyasa baza kiyi tawakkali bane?." Ta sunkuyar da kai Umma ta kuma cewa, "da k'aracin shekarun ki zaki jawowa kan ki ciwo sabida d'a namiji, son sa kike har haka ne?." Ta kalli Umma ta sake sunkuyar da kai Umma ta kuma cewa, "kinyi gangancin bari soyayyar sa ta shiga zuciyar ki, kin sani ba tsarar ki bane daman akwai dalilin da ya saka shi auren ki ya samu abinda yake so kuma ya barki, kina saka damuwa a ranki shi yana can yana walwala yama manta da shafin ki a rayuwar sa ke kuma kina nan zaki kashe kanki da tunani. Ina rok'on Allah da na sanki da shi Rauda? Ina karatun alkur'anin da na san ki dashi duk ina suka tafi?."       Rauda ta share idanun ta tace, "Umma bawai ina sonsa bane kawai in na tuna ni a yanzu bazawara ce sai naji zuciyata ta karye." "Rashin karb'ar k'addarar kenan Rauda, dole ki damu amma bana tunanin zaki kaini damuwa domin nice mahaifiyar ki, addu'ar da nake yi babu dare babu rana shine ya sa kike ganin kamar ni abun bai dame ni ba amma na fiki damuwa. Ki cigaba da addu'a da rok'on Allah komai zai wuce ya zama tamkar ba'a yi ba, duk kin bi kin rame kin sake yin bak'i kamar ba ke ba." Rauda ta sauke numfashi tace, "In sha Allah Umma zanyi." "To yayi kyau. Kizo ga Habiba da Walida sun zo wajan ki" tana fad'a ta fita daga d'akin Rauda ta sauke numfashi ta tashi ta fito daga d'akin zuwa falo.  A zaune ta same su suna shan ruwa ta k'araso tana fad'in, "manyan manya maganin k'ananu yara." Dariya sukayi bayan ta zauna Habiba tace, "kodai kece manyan ba, ai wallahi baki da kirki gabad'aya bakya neman mutane ko a waya ma an daina samun ki. Nifa ban san ma kin dawo daga gyaran k'afa ba sai jiya." Rauda tayi y'ar dariya tace, "Bari kawai, wallahi kaina ne ya cushe ni ko fita bana yi, tsohuwar wayata kuma a can na cillar da ita ban sani ba. Ya kuke ya kwana biyu?." Walida tace, "lafiya lau, k'afa tayi kyau Allah ya kiyaye gaba." "Amin ya Allah. Ya su Gwaggo dasu Umma?." Habiba tace, "Gwaggo tana gidan sarki yanzu ma daga wajan ta nake." Rauda tayi murmushi kawai Walida ta kalli Habiba tace, "Sai da kika ce gidan sarki na tuna ina cewa zan tambaye ki, ance yanzu gidan ya sake damalmalewa ko?." Habiba tace, "Uhum bari kedai kawai. Asad d'in da muke ganin in ya karb'i sarauta zamu ji dad'i mu da muka rab'i aiki a gida yanzu ya canja gabad'aya,  da farko ya fara taimako da sadaka kamar yadda kowa ya san shi da ita, ba wulaƙanci sai girmamawa amma yanzu....." ta k'arasa fad'a tana rik'e hab'a. "Yanzu me?" Rauda ta samu kanta da tambaya ba tare da tayi niyar hakan ba. Habiba ta kalle ta tace, "Baya ganin k'imar kowa sai matar sa kawai wata shegiya kyakykyawar gaske kamar aljana, fatar ta har yellow take sabida haske gata bata da kirki ko misqala zarratun wulaƙanci a cikin ta kamar me. Duk soyayyar mai martaba Asad da Maman sa wallahi ta raba su." Walida tace, "ni naji dad'in hakan ai maganin babar tasa akayi dan ba kirki ne da ita ba." Habiba tace, "ke kin san ba'a binne sirri a gidan sarauta, jiya ita matar tasa gimbiya Jidda kun san Gwaggona tana daga cikin hadiman ta ita take fad'a min d'azu tace ko babar Mai martaba d'in ce tazo shiga wajanta indai batayi izinin a barta ba duk wanda ya barta ta shigo a bakin aikin sa." Walida ta bud'e baki tace, "Tooo! Lallai bata da kirki lamarin nata babba ne." Habiba tace, "duk inda kike tunanin rashin kirkin ta ta wuce haka. Amma fa itace daidai ita daman y'ar aminiyar tace farkon sarautar tasa sai abinda tace akeyi sabida tsantsar biyayyar da yake mata, yanzu kuwa an saka ta a gefe sai abinda matar take so akayi, babar tasa ma bata ma san meke faruwa bafa dan baya zuwa wajan ta." Walida tace, "Ikon Allah, amma dai asirce shi sukayi ko?." "Daman sai dai asirin ai ko nace tsafi ma dan yadda abun ya faru lokaci d'aya ke bakya ce zai faru ba." "Amma na d'auka asiri baya kama masu sarauta sabida dafa'in da yake jikin su." Dariya Habiba tayi tace, "Rauda kiji min walida dan Allah, akwai wanda asiri baya kamawa ne a duniya?. Ya kama annabin Allah ma balle wani sarkin katagum...?. Yana da ibada dan ibada kaf gidan babu mai ilimin addinin sa to abubuwan ne sunyi masa yawa, wannan ya jefe shi wancan ya jefe shi dan cikin y'an uwan sa ma ba kowa yake goyan bayan sarautar ba balle kuma y'an uwan mai martaba mai murabus. Ni wallahi har tausayi yake bani wani lokacin." Walida tace, "wataƙila silar hakan sai babar sa tayi hankali nan gaba ai."  Habiba tace, "To gata nan dai. bata da kirki fa baki ga sai da tasan yadda tayi ta raba tsakanin Rauda da Asad d'in ba?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalle su Walida tace, "Shiyasa nace Allah ya k'ara." Habiba tace, "Shine abin tausayin daman ai ba ita ba, bata tab'a yi masa abinda yake so ba komai zab'in ta yake bi babu yadda ya iya, ta ya zata bar shi da Rauda..? Wallahi daman sai ta raba su ke matar nan shaid'aniya ce, ita ake zargi a rashin lafiyar mai martaba dan zata iya yin komai akan sarautar d'anta gashi ya karb'a kuma tana neman ta zamar mata masifa, shi Aliyun tunda ya bar k'asar sun kafe shi a can yak'i dawowa, shi kuma Hydar yana kula da mahaifin su shi kuma mai martaba an juyar da tunanin sa." Walida ta kalli Rauda tace, "ni nama ji dad'i da Allah bai k'addara kin aure shi ba da Allah kad'ai yasan me zai faru tunda babar sa bata da imani." Habiba tace, "Wallahi fa,  hakan ma dan Rauda tana da rik'o da addu'a ne da sai tayi mata wani gib'i a rayuwar ta ko a halittar ta." Walida zatayi magana Rauda da take jin su tace, "Dan Allah mu bar maganar gidan sarautar na can suje da matsalar su muma muji da tamu. Bara na dafa mana taliya koda manja ne muci" ta fad'a tana tashi ta shiga kitchen. Jim kad'an ta fito tace, "Habiba wai ina saurayin ki?." Habiba tace, "yana nan yana min wasa da hankali, dana ce ya fito sai ya fara kawo min zancen da ba shikenan ba." "Ahh to ba son ki yake yi ba" Rauda ta fad'a tana zama. "Assalamu alaikum! Asslamu alaikum!!" Aka fad'a sau biyu daga tsakar gida Rauda ta amsa tare da tashi ta nufi tsakar gidan, yaro ta gani yace, "Ana sallama da mai gidan a waje." Rauda ta kalli saman Baba tace, "To bara nayi masa magana" ta fad'a tana komawa ciki ta sanar da Umma ta fito dan taje wajan sa. Zama tayi suka cigaba da hira jim kad'an suka fara jiyo hayaniya a waje ga kuma muryar Baba, Rauda ta saka mayafi suka fita su uku nan suka ga motar rushe gidaje da ta d"ibar k'asa ga dogarai sama da biyar a wajan alamun daga gidan sarauta suke. Muryar Baba taji yana fad'in, "Ban fahimta ba? Wanne irin filin talakawa anyi gini dashi?." D'aya daga cikin su yace, "tun bayan kwana biyu da suka wuce mun kawo muku notice na tashi daga gidan nan baku tashi ba, masarauta ta bada umarnin a rushe gidan nan yau domin fitarwa da talakwan da aka kwace filayen baya hakkin su." "Kamar ya kenan?" Rauda ta fad'a tana kallon sa. Ya kalle ta yace, "kamar yadda kuka ji na fad'a. Wannan gidan zamu rushe shine yanzu bamu damu da kun kwashe komai na ciki ba tunda an sanar daku ku tashi." "Akan wanne dalilin za'a rushe mana gida?" Ta fad'a tana kallon sa. Cikin tsawa yace, "umarnin masarauta ne!." Itama cikin tsawa tace, "Masarauta ai ba gwamnati bace, Gwamnati ce take da wannan ikon amma ba masarautar da take k'asan gwamnatin ba. Dan tsabar rainin hankali kawai ku kwaso mota kuce zaku rushe mana gida? Shi sarkin da ya turo ku gwamna ne shi kome?."       "Ke y'ar talakawa ki iya kalaman ki akan mai martaba" wani daga baya ya fad'a yana kallon ta. Ta kalle shi tace, "in nak'i na iya bakin nawa akwai abinda zakuyi min ne?. Dan kawai mu aka raina gida a lungu zaku zo kuce wai anyi gini a filin talakawa?. Banga wanda ya isa ya rushe gidan nan ba koda shi kansa sarkin ne zaizo wajan nan." Baba ya kalli Rauda yace, "Nutsu malama, uban me ya fito dake wajan nan?." ya dawo da kallon sa ga mutanen yace, "ta ina gidana ya zama filin talakawa bayan gidan nan nawa ne shekara da shekaru ina zaune a cikin sa?." Anas da ya faka daga baya mamakin mutanen yake yi ya fito daga motar ya k'araso wajan yaga Baba da Rauda a wajan ya k'araso yace, "Baba lafiya?." Rauda tace, "wani rainin hankali suka zo mana dashi wai zasu rushe gidan nan wai akwai filin talakawa, kuma wai daga masarauta dan tsabar sun mayar damu wanda basa fahimta." Anas ya kalle su yace, "wanne irin filin talakawa ana zaune lafiya?." "Masarauta ce ta bada umarnin hakan." "Masarauta ai ba gwamnati bace bata da wannan hurumin, gidan nan yafi shekara ashirin a wajan nan gyara shi kawai akayi tun lokacin ba'a ce akwai filin talakawa ba sai yanzu?." Babban cikin su yace, "Kaga malam umarni aka bamu dole kuma mu cika shi." Anas yace, "Ina plan d'in filin talakawan?." Ya mik'a masa ya karb'a ya ware yana dubawa Anas ya kalle shi yace, "ko zamu iya magana a gefe?." Ba musu yabi bayan sa sun jima suna tattaunawa kafin Baba yaga sun shiga mota sun bar wajan Anas ya dawo wajan Baba yace, "Baba mu shiga ciki." Ba musu suka shiga Habiba da Walida suka tafi cikin mamakin wannan lamari. A harabar gidan yace, "Baba sun k'i amincewa sunce umanini ne daga masarauta na lallab'a su sun k'ara kwana biyu." Rauda ta kalle shi tace, "Wai ban gane kwana biyu ba? Kana so kace sai an rushe gidan kenan?." Ya kalle ta ya d'aga mata kai ta wara idanu tace, "Akan wanne dalili kenan? Filin wa akayi gini dashi?." Baba ya kalle ta yace, "Shiga gida Rauda." Ba musu ta juya ta shiga gida Baba ya kalli Anas yace, "abinda ban gane ba meye had'in masarauta da ginin gidan nan? Filin me ake magana akai?." Anas yace, "Baba a ganina kawai wannan wata manak'isa daga masarautar, ana so a wulak'anta ahlin gidan nan ne kawai ba wani abun ba. In ba haka ba babu ta yadda za'ayi ace wai sunzo zasu rushe gida, ko gwamnati bata rushe gida sai bisa ka'ida balle su."Baba ya girgiza kai alamun gamsuwa da maganar Anas yace, "babu damuwa Anas, ina zuwa" ya fad'a yana shiga cikin gidan. Ba jimawa ya fito ya wuce Anas ya biyo shi yana cewa, "Baba duk inda zaka je zan ka basai kaje titi ba." Baba ya kalle shi yace, "Na sani Anas, ina so naje a motar hayan ne." Ya nufi kan titi ya hau abin hawa ya tafi gidan sarkin kai tsaye. Lokacin gab da sallar azahar ya shiga har cikin gidan masallacin cikin gida ya zauna yasan indai mai martaban yana gari tabbas zai fito sallah. Hakan ce ta kasance kuwa ana yin kiran sallah ya aka sanar da isowar sa bayan an tary gabad'aya, bayan an idar mai martaba ya fita Baba yabi bayan sa ya shiga cikin makarrban sa ya k'arasa gaban sa yana fad'in, "Barka da rana ranka ya dad'e." Cak ya tsaya ya kalli gefen da Baba yake sai kuma ya d'auke kansa bai amsa ba sai yayi ciki Baba duk da haka bai daina bin bayan sa ba.      K'aramar fada ya shiga Baba yana tsaye sai ga dogari yazo yace ya shigo suka shiga Baba yana baya shi yana gaba, a k'asa ya zube yana yi masa jinjina yace, "Allah yaja da ran sarki, Allah ya k'arawa sarki lafiya da tsahon rai, Allah yasa afi haka." Lumshe ido yayi ya bud'e shamakin sa da sauran dogarai suna amsawa da amin kafin wani dogari yace, "Fad'i matsalar ka." Baba ya gyara zama duk sai yaji wani iri ganin yanayin Asad din shima sai yasha jinin jikin sa yace, "Ranka ya dad'e kwana biyu da suka wuce aka kai mana takarda akace wai notice ne umarni daga gare ka mu tashi za'a rushe inda muke zaune, ban d'auki abinda mahimmaci ba amma sai gashi yau anje da motar rusau za'a rushe, shine nazo gare ka duba da ban san dalilin hakan ba." Asad yayi shiru zuciyar sa na bala'in harbawa amma kuma haushin Baban yake ji gabad'aya a zuciyar sa ba tare da ya shirya ba yace, "Ba iya gidan ku kawai bane, duk gidan da ya shiga hurumin talaka zamu rushe shi." "Wannan gaskiya ne, dan sarki kake jikan sarki kuma sarki" aka fad'a daga zaune cikin kirari. Baba jikin sa yayi sanyi ya kuma cewa, "Amma ranka ya dad'e gidana yafi sama da shekara ashiriin a inda yake gyare-gyare kawai aka samu ba samon gini bane, a duba lamarin ranka ya dad'e" ya fad'a a sanyaye zuciyar sa na bugawa. "Iya abinda zamu iya kenan" ya furta a hankali ba tare da ya kalli Baban ba fuskar Asad d'in a d'aure matuk'a. Baba ya kalle shi cikin mamaki ganin kamar bai gane shi ba hakan ya saka shi sake kallon sa cikin dunbin al'ajabi. "K'asa da idanun ka, Hattara Dattijo kallon idanun mai martaba yafi k'arfin ka." Baba ya saukar da ido yace, "Allah yaja zamanin mai martaba bamu da inda zamu koma in hakan ta kasance, kuma a ina neman afuwa amma rushe gida a k'arkashin gwamnati yake ba masarauta ba." "Hattara dattijo! Kasan a inda kake" aka fad'awa Baba cikin tsawa. Baba yace, "Tuba nake." Asad yayi shiru idanun sa a lumshe sam baya k'aunar ganin Baba ko kad'an a kusa dashi ya sunkuya ya rad'awa na gefen sa magana sai ya zabura ya mik'e yace, "Dattijo muje." Baba ya kalle shi ya kalli mai martaba ganin da gaske babu fuskar maganar sai yayi k'asa da kasa, "Tashi mana!" Aka sake fad'a da k'arfi Baba ya firgita ya mik'e ya fita jikin sa yana rawa zuciyar sa cike da zallar mamakin Asad da kuma tsoro........ [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *057.*           Mamaki ya gama dabaibaye Baba tafiya yake jiki a sanyaye kamar zai kifa kansa har juyawa yake sabida yadda lamarin ya cushe masa kai da kwakwalwar sa. "Baba!" aka fad'a daga gefe Baba ya kalli inda yaji an kira sunan sa yaga Hydar ne fuskar sa da murmushi yana k'arasowa inda yake. Baba ma murmushin k'arfin hali yayi yace, "Ranka ya dad'e." Hydar yayi murmushi yace, "ziyara aka zo mana kenan?." Baba ya numfashi yace, "kusan hakan, matsala ce aka je mana da mota za'a rushe mana gida wai anyi gini a filin marayu, shine nazo da kaina wajan mai martaba naji abinda ya jawo hakan dan kowa yasan gidana yafi shekara ashirin a wajan da yake gyaran da kuka yi mana shine kawai ya sauya shi." Hydar yace, "rushe gida kuma? To ya kukayi dashi?." Baba yace, "to bai ma saurare ni yadda ya kamata ba balle har yaji dalilin hakan, abinda yace min kawai iya abinda za'a iya kenan. Yanzu akan wanne dalili kenan za'a rushe mana gida? Mu ba'a kan hanya muke ba, ba'a kan titi muke ba rana tsaka azo ace za'a tashe mu ina zamu je?." Hydar ya furzar da iska zuciyar sa cike da bak'in cikin yace, "kayi hak'uri Baba, zan iya iya bakin k'ok'ari na wajan ganin hakan bata kasance ba in sha Allah. Ka kwantar da hankalin ka ya canja halayyar sane gabad'aya yanzu wani lokacin in yayi wani abun kamar bashi ba." Baba ya girgiza kai yace, "to na gode, sai anjima" abinda yace kenan ya juya zai tafi, Hydar ya d'auko kud'i yace, "Baba ga wannan ka hau mota." Baba ya kalli kud'in ya girgiza kai kana yace, "na gode" yana fad'a ya nufi hanyar fita Hydar ya bishi da kallo zuciyar sa sam babu dad'i ko kad'an. Fusata Hydar yayi ya nufi b'angaren Mai martaba yayi sa'a har lokacin bai tashi ba ya shiga kansa tsaye ya same shi shida makarraban sa kowa ya bishi da kallo har Asad d'in dan yadda ya ganshi yasan ransa a b'ace yake, ganin hakan Hydar yace, "Ina son ganawa da mai martaba ni kad'ai, ko zaka iya bamu waje?." Suka kalli Asad ya d'aga musu kai alamun suje auka Mike suna fad'in, "A tashi lafiya." Hydar ya kalle shi yana zaune yayi zaman sarkai akan kujera cikin shigar da ya saba in ba zaman fad'a zaiyi ba yace, "Amma kasan abinda kake aikatawa ba daidai bane ba ko?." Bai bashi amsa ba yasan daman bazai amsa masa ba yace, "Ina ruwan gidan su tsohuwar matar ka zaka saka aje a rushe musu gida? Duk kyautatawar da suka yi maka da abinda zaka saka musu kenan?." Asad ya sauke numfashi kamar bazai yi magana ba ya kalle shi yace, "Ina matsayin shugaba a gare ka zaka zo kana yi min ihu a kaina dan kaga ina k'yale?." Sai ya cize baki ya girgiza kansa kana ya kuma cewa, "Bana son su, bana qaunar ahlin su yarinyar gabad'aya sai me?." "Ka kyauta, kayi abinda kake so akwai limit d'in da za'a zo in akace kayi baza kayi ba." ya fad'a rai a b'ace yana kallon Asad da shima shi yake kallo cikin mamakin da ya kasa barin sa. Tashi Asad yayi ya shiga ciki ya bar Hydar a tsaye yana kallon sa har ya b'ace ya girgiza kai ya fito.           B'angaren Baba lokacin da ya shiga gida a babban falo ya samu matan sa sai Rauda da Rahma k'ananun sun tafi makaranta yanayin da ya shiga ya saka suka bishi da kallo har ya zauna ya cire hular kansa ya dafe kansa, Umma tace, "Malam lafiya?." Baba yayi kalle su kafin yace, "Wanne gida kuke ganin zamu samu haya daga yau zuwa gobe?."  Rauda tace, "Kenan sai mun tashin? Nifa bazan bari hakan ta faru ba wallahi zan iya shiga gidan rediyo akan maganar nan." Baba yace, "Dakata malama! Babu yadda zamuyi tashin ya zama dole dan yanzu ma daga gaban mai martaban nake amma nayi dana sanin zuwa tunda nake ban tab'a jin to tozarcin da ya tab'a min zuciya kamar wannan ba." Umma ta girgiza kai tace, "bai saurare ka ba kenan?." Baba yace, "Yace iya abinda zasu iya kenan, a tak'aice dai sai an rushe badan Anas bama ai da ba wannan zancen ake yi ba." Rauda ta zabura ta mik'e tace, "Akan wanne dalili wai za'a rushe mana gida? Me muka aikata?. Wallahi bazai yu ba dan kawai a tozarta mu kawai sai ace za'a rushe gida? Daman can ai ba mu muka ce su gyara gidan haka ba; sune sukayi niya da ra'ayi, fili namu ne dan haka basu isa suce zasu rushe mana gida ba wallahi. Ina zuwa" ta fad'a tana niyar fita Baba yace, "Kee Rauda, dawo nan." Ba musu ta dawo ta zauna Baba ya kalle ta yace, "Kome ya faru nine na jawo Rauda, na nuna musu ina son dukiyar su a kanki shiyasa suke yi mana duk abinda suka ga dama, kar naji kinje gidan wata radio akan wannan ku fara had'a kayan su zamu tattara mu bar gidan kar a wulaƙanta mu."     Rahma tace, "Amma Baba Anty Rauda tana da gaskiya banga dalilin....." baba ya dakatar da ita yace, "Rahma ya isa haka, kuyi abinda nace kawai" yana fad'a ya mik'e ya fita ya hau saman sa jikin sa a salub'e. Rauda ta runtse idanun sa sabuwar tsanar Asad take ji tana zaga ko ina na jikinta fiye da wacce take ji a baya, da ace tana da dama sai tayi masa abinda bai tab'a tunani ba a yanzun ma kuma bazata fasa ba sai ta nuna masa daidai take dashi. Umma tace, "Abin mamakin in dai ba shirin to tozarta mu akayi ba ina masarauta ina hurumin rushe gidajen mutane?." Inna tace, "Abinda na gani kenan, sai dai in anso a wulaƙanta mune kawai." Rahma tace, "In Allah ya amince baza mu wulak'anta ba sai dai yaga wulaƙanci akan sa." Rauda ta furzar da iska tana jin wani iri a jikinta gani take kamar ko meye ya faru itace ta jawo, jin dad'in tama dasu Walida suka tafi da bata san yadda zatayi ba kunya ba. *☆☆*         B'angaren Mama kwana d'aya ta rame sabida ciwon kan da ta kwana ta tashi dashi babban tashin hankalin ta kuma rashin kiran wayar da Mum bata yi mata ba har lokacin, duk ta damu hankalin ta ya tashi matuk'a kana kallon yanayin ta zaka fahimci hakan. Tana zaune dafe da kanta Suhaima na zaune a k'asan ta tana matsa mata k'afafun ta suka ji sallamar Mum tare da shigowa. Mama ta kalle ta Mum ta k'araso tana fad'in, "Tuba nake ranki ya dad'e,  Allah ya wuci zuciyar ki" ta fad'a tana k'araso ta zauna a kan carpet. Mama ta saki kanta ta kalle ta tace, "tun jiya nake kiran ki baki d'auka ba kuma baki kira ni ba." Mum tace, "Shiyasa nace tuba nake ranki ya dad'e." Mama ta kalli Suhaima tace, "Jeki." Ba musu ta tashi ta basu waje Mama ta kalli Mum tace, "akwai abinda yake faruwa a gidan nan kin sani?." Mum da alamun mamaki tace, "kamar me kenan ranki ya dad'e?."  Mama tayi tari kad'an kana tace, "Ki fad'a min gaskiya mai kuka yiwa Asad keda y'ar ki Jidda?." Mum ta zaro idanu tare da dafe k'irji tace, "kamar ya me muka yi masa ranki ya dad'e? Me kuwa muka yi masa?." Mama ta jingina da kujera tace, "Don't pretend like baki san komai baSadiya, kin san abinda nake nufi. Wanne malami kika samu ya mallake min d'ana haka?." Mum ta rausayar da kai tace, "Haba ranki ya dad'e wanne irin mallaka ana zaune lafiya? Ni ban yiwa Asad komai ba." Mama tayi mata kallon kin raina min hankali sannan tace, "Sadiya kin san karrr nake kallon ki, ki fito ki fad'a min abinda kika yiwa Asad tun muna shaida juna nida ke." Mum tayi murmushi ta gyara zama tace, "Irin malaman da kika samu suka mallake miki mijin ki da kuma y'ay'an ki, irin malaman da kika samu suka mayar da mijin ki tamkar gawa, irin malaman da kika samu aka mayar dake tauraruwa a wajan mijin ki wajan su nima naje." Gaban Mama yayi mugun fad'uwa tabi Mum da kallon mamaki tace, "Sadiya! Me kike cewa ne?." Mum tayi dariya ta tashi daga kan carpet ta dawo kan kujera ta d'ora k'afa kan d'aya tana kad'awa tace, "Abinda kika ji shi nace. An fad'a miki zan bar Jidda ta shigo gidan nan ba tare da na shirya ba duk da nasan halin ki? Kar ki manta nice fa Sadiya wacce kike fad'awa zaki mallake masarautar nan ko shi sarkin sai abinda kika ce masa, to kin fad'a min wannan ni da yake doluwa ce mara wayo sai na zuba idanu y'ata ta zama bora duk da kasancewar ta matar sarki?. Keda kike uwar sa ace kece zaki san komai kafin ita? Impossible kema kin san bazai yuwa ba ai Rabi" ta fad'a cikin murmushi tana kallon Mama. Mama ta kasa magana sai kallo da take binta dashi cikin tashin hankalim da ya bayyana a tare da ita tace, "Sadiya....!." Tayi farr da ido tace, "Na'am Rabi'atu. Kinyi saurin karaya bayan yanzu aka fara wasan ai, yadda kike tunanin mallake komai ni sai na riga ki mallakar sa, yadda kike juya kowa nima sai y'ata ta juya ki kina ji kina gani d'anki sai yafi k'arfin ganin ki." Mama binta take kawai da kallo cikin mamaki ta kasa cewa komai dan gani take kamar ba ita ba Mum ganin hakan ya saka tace, "kina ta kallona kamar baki san komai ba, tunanin ki kin amince min na butulce miki ko...? Hhhhhhh Rabi'atu kenan. Kin manta kema mijin ki ya amince miki kuma kika butulce masa har kika kai shi ga kwanciya dashi da gawa banbancin su kawai numfashi ne?. Yanzu aka fara wasan Rabi'atu burin ki na zama cikakkiyar mai iko nima shine burina, y'ata ta zama sama da komai da kowa a gidan nan kuma hakan zata kasance" ta fad'a tana mik'ewa tana kallon Mama. Mama ta kasa magana sai kallonta kawai da take yi baki a bud'e zuciyar ta na bugawa da gudu sabida tashin hankali kanta har rawa take ji yana yi sabida yadda yake mata mugun ciwo, Mum ta kalle ta tace, "na barki lafiya babar sarki kuma sirikar Jidda, kin kusa yin jika ma domin sirikar ki Jidda tana da juna biyu kin san kin samarwa mijinta maganin da ya samu lafiya yadda zai kasance da matar sa yadda ya kamata dan baki so tayi kuka. Magani yayi aiki kam domin zancen da akeyi yanzu har anyi ciki. Na barki lafiya Rabi na gode da kika yi iya k'okarin ki wajan ganin Jidda ta shigo gidan nan matsayin mata kuma matsayin sirikar ki, sauran aikin nawa ne" tana fad'a ta fita ta bar Mama a zaune kamar an dasa ta a wajan.         Mama kawai ganin ta tayi a d'aki ba tare da tasan lokacin da taje ba ta zube a kan tiles kawai taji idanun ta na zubar da hawayen bak'in ciki wanda bata shirya musu ba. Tunanin fa daman haka duniya take wanda ka amincewa shine yake k'ok'arin ganin ya cutar dakai....? Me ta yiwa Sadiya haka da ta yanke mata wannan d'anyen hukuncin lokaci d'aya haka. Kuka take yi sosai iyakar iyawar ta kafin wani lokaci zazzaɓi ya rufe ta ruf ga ciwon kai mai zafi da suka tarar mata. Suhaima ce ta shigo ganin halin da take ciki bata yi k'asa a guiwa ba ta kira likita ba jimawa ya k'araso aka yi mata allura aka saka mata ruwa nan da nan bacci ya kwashe ta Suhaima na kusa da ita haka Hydar ma. Bayan tayi bacci likitan ya fita Hydar ya kalle Suhaima yace, "Meya same ta ne lokaci d'aya haka?." Suhaima tace, "Wallahi a nan kawai nazo na ganta a kwance a kan tiles, nasan dai na bar su tare da Mum ban san lokacin da Mum d'in ta tafi ba." Hydar ya girgiza kai yace, "duk yadda akayi ciwon nata yana da alaqa da zuwan Mum, ki kula da ita ina zuwa" yana fad'a ya fita daga d'akin.         Mama bata farka ba sai bayan sallar la'asar ta tashi dak'yar har lokacin kanta yana ciwo ta shiga band'aki tayi alwala ta fito tayi sallah bayan ta idar karo na farko cikin addu'ar da take yi taji bakin ta yana furta, "Allah ka bawa mijina lafiya, Allah ka tashi k'afadun sa shine kad'ai zaiyi iya maganin Jidda da babarta, Allah ka dube ni ka fitar dani daga halin da nake ciki" ta fad'a tana kuka sosai ta shafa addu'ar ta tashi da hijjabi a jikinta duk da kanta da yake ciwo hakan bai hanata nufar b'angaren mijin ta ba. Babu wanda baiyi mamakin ganin ta a b'angaren mai martaba ba dan tunda ya dawo sau d'aya tak taje inda yake amma sai gata da yamma ta shiga ta samu Hydar da Uncle da sauran y'an uwan Abba su uku a ciki, ganinta ya saka suka fita aka barta daga ita sai shi idanun sa a bud'e alamun ba bacci yake ba ta k'arasa kujerar kusa dashi ta zauna ta rik'e hannun sa hawaye yana sakko mata tace, "Mijina sun raba ni da Asad d'ina, sun juyar masa da hankali daga gare ni Sadiya ta cuce ni ita da y'arta. Mamaki nake wai da gaske ne abinda yake faruwa ko mafarki nake? Yau nice aka mallake min yaron dana fi cin buri a kansa?." Bai motsa ba sai kallonta da yake yi hakan ya saka tace, "Kaina ya kulle na rasa me zanyi ka taimake ni mijina kar kwakwalwa ta ta fashe. Daga jiya zuwa yau na shiga tashin hankali mara iyaka dan Allah ka taimake ni. Allah ya baka lafiya da gaggawa ka taimakawa d'ana ya dawo hankalin sa zasu iya yin komai ganin sun raba shi da duniyar gabad'aya." Kuka take yi sosai a kan hannun sa hawayen ta na tab'a fatar sa sai da tayi mai isar ta sannan ta kalle shi tace, "zan fara nema masa magani ka taya ni fatan Allah yasa na dace." Ta jima tana kuka kafin ta saki hannun sa ta goge idanun ta ta fita jikinta a sanyaye ta koma b'angaren ta. Da Suhaima suka had'u da Hydar Suhaima tace, "Mama sannu." Kallon ta tayi tace, "Ina key d'in motar ki?." Suhaima tace, "yana d'aki." "D'auko ki kaini unguwa." Hydar yace, "Mama ina zaki je baki da lafiya fa?." "Yanzu zamu dawo Hydar" ta fad'a dafe kanta da har lokacin yake ciwo. Hydar yace, "to muje na kai ki." Mama tace, "Zamu je da Suhaima" tana fad'a Suhaima ta fito suka fita a babban falo hadiman ta zasu bita ta girgiza musu kai alamun su sha zaman su, ko jakadiya bata d'auka ba ita da Suhaima suka hau mota suka bar gida. Sunyi tafiya mai nisa suka isa gidan malamin Mama ta bata umarnin ta tsaya ta fita ta shiga ciki tace ta jira ta a ciki, da jama'a sosai ta samu a gidan amma sanin ita wacece yana sallamar ta gaban sa ta shiga ya mik'e yana kawo gaisuwa, zama tayi ta kalle shi tace, "Ya jama'a?." "Alhamdulillah ranki ya dad'e." Ta sauke numfashi tace, "babar matsala ce ta kawo ni Malam." Ya gyara zmaa yace, "To ina sauraren ki." Ta sauke numfashi tace, "dakai na amince nasan baka fitar min da sirrina kana kuma k'okari wajan yi min duk abinda nace ina so. Sadiya wacce muke zuwa tare ta butulce min sun juyarwa da mai martaba kansa gabad'aya baya jin maganar kowa sai tata data matar sa." Malam yace, "Ashsha! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, amma Sadiya tayi butulci ba kad'an ba. Tazo min da maganar kwanaki na amsa mata zanyi amma banyi ba sabida bazan iya cin amanar ki ba." Mama tace, "Meyasa a lokacin baka sanar dani ba?." "Kiyi hak'uri ranki ya dad'e naso fad'a miki sai kuma nayi tunanin kar na raba zumuncin ku." "Yanzu gashi ai komai ya lalace" ta fad'a tana dafe kanta shi kuma ya shiga duba mata abinda yake faruwa. ya jima yana yi kafin ya girgiza kai yace, "Tsakani da Allah ranki ya dad'e bak'in tsafi aka yiwa Mai martaba ba asiri ba, an bashi yaci ya kuma sha anyi amfani da makusantan sa anyi abin cikin sirri ba tare da ya sani. Hak'ik'a tsafin da yake jikin sa ba k'arami bane ba dan zan iya cewa ba'a k'asar nan akayi shi ba." Mama cikin firgici tace, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" ta fad'a tana dafe kanta da yake juyawa ya kuma cewa, "A halin yanzu yayi sakaci da rok'on Allah kamar baya shiyasa abin yake tasiri a tare dashi, bazan miki k'arya ba karya wannan tsafin na jikin sa ba abu bane mai sauk'i dole sai an had'a k'arfi da k'arfe wajan rok'on Allah, ma'ana sai an samu manyan malaman addini da dama an had'u ana yina addu'a sannan za'a samu nasara." Mama kamar zata zubar da hawaye tace, "Kafin wannan babu abinda za'a iya yi?." "Akwai ranki ya dad'e, zan bada ruwan rubutun da zai dinga sha amma sai dai a jira a rubuta a wanke a yanzu tunda ban san da zuwan ki ba in sha Allah zai rage wani abun tunda ayar Allah ce." "Wanne malamai kake ganin za'a samu akan wannan?." Ya sauke numfashi kana yace, "akwai wani babban malami sai dai ya tsufa sosai a cikin garin nan yake zaune Allah ya yi masa ilihamar iya karya tsafi ko asiri da ayoyin Allah da kuma maganin hausa." Mama ta gyara zama tace, "Ina zan ganshi?." "Zan bincika ranki ya dad'e in yana nan zan sanar dake sai aje wajan sa." "Ina jiran ka dan Allah kar kayi wasa." "In sha Allah ranki ya dad'e. Bara na saka ayi rubutun" ya fad'a yana mik'ewa ya fita. Ta jima sosai a gidan ta fito da jarkar rubutun tana jiri ta shiga motar Suhaima taja suka koma gida. *☆☆☆*       Baba ne ya lek'a d'akin Umma ya ganta ita da Rauda yace, "kuzo munyi bak'o" yana fad'a ya juya ya fita Umma da Rauda suka fito ko wacce ta saka hijjabi zuwa k'aramin setroom d'in baban. Hydar suka gani a zaune shida Baba ganin su ya saka shi yin murmushi yace, "Mai ciwon k'afa jiki yayi kyau sosai." D'aure fuska tayi ta zauna sai Umma ce tace, "Wallahi fa, jiki ya jima da warkewa ai." Ya kalli Umma yace, "barka da yamma." Umma tace, "ya mutanen gidan?." "Alhamdulillah. Rauda ya gida?" Ya fad'a yana kallon ta. Fuska a d'aure tace, "Alhamdulillah." Hydar ya numfasa yace, "kuyi hak'uri da abinda ya faru d'azu in sha Allah bazan bari hakan ta kasance ba, a tak'aice nayi maganin abun in sha Allah baza su sake zuwa gidan nan da niyar wani abun ba." Baba yace, "to ma sha Allah mun gode sosai. Amma dan Allah meye dalilin sa na sakawa ayi mana wannan wulaƙancin?." Hydar yace, "kuyi hak'uri kawai Baba, gabad'aya ya canja dana je na same shi akan maganar sai yace shi na bar maganar ya tsane ku ne baya son ku baya son dangin ku gabad'aya. Amma......" Rauda ta katse shi da fad'in,  "Amma me? Ka sanar dashi yadda ya tsane mu wallahil azim muma haka muka tsane shi bama son sa bama qaunar wani nasa. Har yana da bakin da zai ce ya tsane mu duk abinda aka yi mana mu bamu ce haka ba sai shii?. To ina so kayi masa albishir muma mun tsane shi dashi da dangin sa gabad'aya, dashi da babu ko nace dashi da banza duka d'aya suke a wajan mu, ka kuma tabbatar ka fad'a masa wallahi bai isa ya wulaƙanta ahlina na k'yale shi ba sai inda k'arfina ya k'are!" Ta fad'a a fusace tana kallon Hydar shima ita yake kallo da mamakin ta.......... [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *058.*           Jin yadda tayi maganar a fusace Baba ya kalle ta yace, "Rauda meye haka ne wai?." Shiru tayi tana girgiza kai jin abinda Baba yace Hydar ya cize baki yace, "Babu wanda zaizo ya sake cewa zai rushe gidan nan mun gama magana dasu babu abinda zai faru" ya fad'a yana mik'ewa tsaye Baba ma ya mik'e suka fita tare suna cigaba da tattaunawa. Da harara tabi bayan sa taja dogon tsaki tace, "Aikin banza aikin wofi." Umma tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta tashi ta shiga ciki ta bar Rauda a wajan tana faman cika da batsewa.          Baba ne ya dawo ya same ta har lokacin a wajan ya kalle ta yace, "ki dinga nutsuwa mana Rauda ko yaushe zuciyar ki a sama ki dinga sassautawa mana, nasan anyi miki ba daidai ba amma shi wannan meye laifin sa? Naga taimaka mana yayi ko?." Rauda tace, "Wallahi Baba gabad'ayan su na tsane su bana son su ko kad'an, mu da gidan mu ace sai alfarma akayi mana aka k'yale mu dan mu zauna? Wanne irin wulaƙanci ne wannan?." "Ya dai isa komai ya wuce yanzu ai." "To Baba" ta furta a sanyaye. Ya kalle ta yace, "Maman ki ta sanar dani lokacin Iddar ki ya k'are ko?." Gabanta ya fad'i ta d'aga kai ba tare da ta d'ago ba yace, "To Allah ya kawo miki miji na gari da gaggawa." Bata amsa ba ta canja maganar tace, "Baba indai zaka amince min a wannan lokacin ina so zan koma makaranta na cika burina na zama y'ar jarida." Baba yace, "me zai hana Rauda? Sai ki koma ai ba wani abun bane ba, da zaman gidan ai gwara ki koma. K'anwar ki Rahma ma in tana so duk sai ku koma d'in." Rauda taji dad'i sosai cikin mamakin Baba jin fad'a d'aya har ya amince kafin tayi magana yace, "Ba kuna da takardun sakandiri ba?." Tace, "muna dashi Baba, Jamb kawai zamuyi wannan shekarar in mun ci sai mu nemi makarantar." Baba yace, "Ba laifi, Allah ya taimaka" ya fad'a yana fita Rauda ta amsa da amin ta buga tsalle ta nufi d'akin Umman ta. "Ummana!, Baba ya barni na cigaba da karatu" ta fad'a cikin farin ciki tana kallon ta. Umma ta tab'e baki tace, "Na taya ki murna." "Umma wai me ya canja Baba ne lokaci guda haka? Ya daina yi min fad'a sosai, zancen makarantar nan fa ina fad'a masa baiyi musu ba ya amince." "Jeki ki tambaye shi ya baki amsa. Ni ba karatu nake so kiyi ba Rauda aure nake so kiyi Allah ya sani." Jikin Rauda sai yayi sanyi ta kalli Umman tace, "Umma meyasa bakya son karatun?." Umma tace, "Haka kawai, nafi so kiyi auren ki in yaso kyayi karatun a gidan mijin ki. Lokacin karatu a yanzu ya wuce tun a baya da ya amince kunyi da yanzu ba wannan zancen ake yi ba amma ya hana. Gobe in Allah ya kaimu gidan Baba Malam zan koma na karb'o maganin farin jinin da yake baki Allah ya fito miki da miji kiyi aure ko zaki wuce takaicin abinda aka yi miki. Zaman gida ba naki bane yanzu Rauda." Rauda jikin ta sai ya mutu murnar da take yi ta koma ciki ta kalle ta tace, "Ummana ai aure lokaci ne, ki duba wancan lokacin da yazo bamu shirya ba gabad'ayan mu sai da akayi haka wannan ma ko bamu shirya ba sai anyi. In na fara karantun in Allah ya kawo mijin ba shikenan ba?." Umma ta rausayar da kai tace, "To Allah ya bada sa'a." "Amin Umma, na gode." Fitowa tayi daga d'akin ta shiga d'akin ta taji wayar ta tana ihu tana dubawa taga sabuwar number da bata sani ba ta d'auka da sallama daga can b'angaren tace, "Sis Rauda kin manta dani gabad'aya ko?." Rauda tayi y'ar dariya da ta gane muryar tace, "Ni na isa? Wallahi kina raina Allah ne bai bani ikon kiran naki ba Anty Ramla. Ya na ganki da number Nigeria kuma?." "Ai mun shigo gari yanzu ma kiran ki nayi in kina gida mu shigo mu gaisa." "Dan girman Allah da gaske kike zaku zo?." "Wallahi da gaske nake, Dear yasan address d'in ki ai yanzu zaki ganmu yau in sha Allah zamu sauke alƙawarin da muka d'auka." Cikin farin cikin Rauda tace, "Lallai kam, ko yaushe ace min za'a zo sai yau Allah yayi. Ina gida sai kunzo." Dariya Ramla tayi ta kashe wayar Rauda ta ajjiye wayar ta fita da sauri zuwa d'akin Umma tace, "Umma!." Ta kalle ta tace, "Ke lafiya kuwa?." "Ina wanda na baki labarin sun taimaka min a Egypt lokacin da abin nan ya faru...? Ita tayi min waya gasu nan zasu zo mu gaisa." Umma tayi murmushi tace, "Lallai manyan bak'i ne, to ki samu ki dafa musu wani abun kafin su k'araso." Rauda tace, "Wallahi ban san me zan dafa bane ba Umma." Umma tayi hanyar fita tare tana fad'in, "ki musu abu mai sauki na hausawa tunda daga k'asar waje suke zasu fi sha'awar abincin mu." Da Baba suka had'u yace, "Su wa za'a yiwa abincin hausawa?." Umma tace, "Bak'i ne Rauda zatayi kuma a can k'asar da aka yi mata aiki suke zaune sai yanzu suka zo nan shine tace zata zo su gaisa." Baba ya kalli Rauda yace, "Ke a ina kika santa?." Rauda tayi shiru tana kallon Umma itama ita take kallo kafin tace, "Itace wacce nake fad'a maka mijin ta ya taimaki Rauda a lokacin akayi sakin nan a can misira, kaga ai manyan bak'i ne ayi musu abinci ko?." Baba ya girgiza kai yace, "Inda abinda yafi abinci ma ai a basu, tsayuwar me kike yi to kije ki samar musu abinda zasu ci. In sun zo kuma ki shigo da mijin nata har nan sai kiyi min magana mu gaisa" ya fad'a yana ficewa Umma ta shiga wajan Inna ita kuma ta nufi kitchen. Ba jimawa tayi musu lafiyayyen d'anwake kasancewar suna da kayan sa a hannu umma bata rasa yaji dakakke nan da nan ta gama ta zuba musu a flake sabo cikin wanda aka fara siya mata na tafiya gidan miji ta koma d'aki tayi wanka tana cikin saka kaya taji ana kiran ta alamun sun zo. Da sauri ta gama shiryawa ta fito taga Ramla a zaune da murmushi a fuskar ta ta k'arasa kusa da ita ta rugume ta tace, "Oyoyo Anty Ramla sannu da zuwa." Itama murmushin take yi tace, "Tunda kika gudu Nigeria sai aka daina jin ki sosai." Rauda tayi dariya tace, "Ina Dr yake?." "Yana k'ofar gida bai shigo ba." Rauda tace, "meyasa ya tsaya a waje?, Khalil!" Ta fad'a da d'an k'arfi Khalil yazo a kuje tace, "maza jeka kace wanda yake waje ya shigo." Ya kuwa fita a guje Rauda ta zauna suna cigaba da gaisawa da Ramla cikin fara'a. Ba jimawa ya suka shigo Rauda tace, "Yanzu dan Allah Dr sai ka zauna a waje?." Murmushi yayi ya zauna tace, "Ina wuni." "Lafiya lau Rauda, ya mutanen gidan kowa lafiya?." Rauda tace, "Suna nan lafiya. Khalil yiwa Baba magana yace in kunzo a sanar dashi zuwan ku bara na kira Umma" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki jim kad'an suka fito tare da Umma. Cikin girmamawa suka gaisa da Umma Baba ma ya shigo har da Inna suka gaisa cikin girmama juna kamar sun san su Baba yace, "Ta sanar damu duka taimakon da kukayi mata angode Allah yasa da alkhairi ya bar zumunci." Dr Khalifa yace, "babu komai ai yiwa kaine." Umma tace, "Ko ruwa baki kawo musu ba Rauda." Da sauri ta mik'e tama fad'in, "Murnar ganin Anty Ramla ce." ta kawo ruwa tare da abinda ta dafa musu lokacin da ta dawo su Umma basa nan. Dr Khalifa yace, "Su Umma suna da kirki sosai har sun fiki." Tayi dariya tana fad'in, "Musamman na dafa musu abincin nan Allah yasa kuna ci" ta fad'a tana bud'ewa Ramla tace, "kaii ai ko a k'oshe nake sai naci, favorite food d'ina ne fa" ta fad'a tana gyara zama Rauda taji dad'i ta fara serving d'in su ta basu ta zauna suna hira suna ci da alama kuma sunji dad'in sa. Bayan sun gama Dr yace, "Gaskiya kin samu lada Rauda, na jima banci d'anwake ba sai yau gashi yayi dad'i sosai da alama Umma ce tayi." Dariya ta kuma tace, "Nima naji dad'i da kuka ci wallahi." Ya kalli Ramla yace, "ya kamata muje magriba tayi" ya fad'a yana duba agogon hannun sa. Ramla ta kalli Rauda tace, "Yauwa Rauda, kin sani Baba Malam wani babban malami ance ya tsufa a garin nan yake amma bamu san wacce unguwa ba." Rauda da mamaki tace, "Baba Malam dai tsohon malamin nan da ake masa layi?." Ramla tace, "Shifa." "To ai Yayan Ummana ne, shine babba a d'akin su gobe ma naji tana cewa zata je wajan sa." Ramla ta kalli Khalifa da farin ciki a akan fuskarta tace, "Alhamdulillah, kice ta kwana gidan sauk'i ma kenan." Rauda tace, "ta kwana kam, ganin sa zakuyi?." "Eh Rauda." "Tabd'ijam ai kafin ku samu ku ganshi wallahi a kwana goma layi baizo kanku ba, amma yanzu tunda da Umma zai iya cewa goben ma kuzo tare da kunje kuma cikin gida zaku shiga zaizo da kansa inda kuke." Ramla ta rik'e hannun Rauda cikin farin ciki tace, "Na dad'e banji labari mai dad'i ba kamar yau Rauda, yanzu yaushe zamu ganshi?." Rauda tace, "Umma zata yi masa waya ta fad'a masa zai baku rana sai aje nasan in akace masa ba'a nan kuke ba zai bada ranar kusa." "Na gode Rauda Allah ya bar zumunci, kinga dad'in zumunci ko? Ta dalilin ziyarar da nazo miki ga abinda ya faru." Rauda tace, "Lah babu komai Anty Ramla kun wuce haka wallahi." Dr yace, "mun gode sosai Rauda, naji dad'i sosai wallahi." Rauda tace, "babu komai, yadda mukayi da ita anjima zan fad'a miki ko a chart." Daga nan sukayi sallama da Umma da Baba Rauda ta raka su k'ofar gida a nan Khalifa yake cewa, "Rauda ina Asad kuwa?." Gabanta ya fad'i matuk'a amma bata nuna ba tace, "Yana gidan su." Yace, "kwanaki munyi waya dashi, yanzu samun sa a waya sai kayi da gaske abubuwa sun masa yawa, ya zama shugaban katagum baki d'aya jan aji ya k'aru. " Shiru tayi bata bashi amsa ba ya d'an kalle ta sai yayi murmushi Ramla tace, "Sai munyi waya Sis. Ga wannan tsaraba tace" ta fad'a tana d'auko leda a mota, Rauda tayi musu godiya daga nan suka ja suka tafi itama ta koma gida.        Rauda tana shiga gida ta tarar da Umma da Ummulkhairi da Rahma a zaune su Rahma suna cinye ragowar d'anwaken ta kalle su tace, "Ku kam kuna da abin haushi, yanzu da zanci fa kuka cinye?." Umma tace, "Sai dai kiyi hak'uri ai." Ta k'arasa ta nunawa Umma k'aramar ledar tace, "Umma kinga abinda suka bani wai tsarabar Egypt." Umma tace, "kin gode, suna da kirki sosai kamar mun saba." Rauda tace, "mun saba sosai a waya Umma tunda na dawo ai ban yarda dasu ba muna zmuncin sosai. Kuma kin san wa suke son gani?." Umma ta girgiza kai alamun A'a Rauda tace, "Baba Malam suke nema an musu kwatancen sa basu san inda zasu ganshi ba." Umma tace, "Baba malam dai Yayana?." "Shifa Umma." "Allah sarki, sai nayi masa magana sai ya basu lokacin da zasu ganshi, sun huta bin dogon layi." "Haka nace musu, sai godiya suke yi." Umma tace, "Babu komai ai." Rauda ta kalli Falon ganin duk sun fita sai su biyu tace, "Kin san basu da yara kusan shekara bakwai da auren su bata tab'a samun ciki ba, har cewa tayi nayi mata addu'a ina jin matsalar ce zata kai su wajan sa." Umma tace, "Allah Akbar! Kice gwara da Allah ya hane ni d'azu k'iris nace musu ina yaran." "Wallahi fa Umma." "To in ma itace matsalar da zata kaisu Allah ya basu na gari in suna da rabon haihuwar." "Amin Umma" Rauda ta amsa Umma ta kuma cewa, "zan masa waya gobe in Allah ya kaimu yadda mukayi dashi sai na fad'a miki ki sanar dasu." Rauda tace, "To Umma." Rauda ta tashi ta shiga d'aki. *☆☆☆*           K'arfe sha d'aya na safe a garin Kano ta yiwa Mama ko gidan sarki ma bata je ba gidan yayar ta ta wuce kai tsaye tana zuwa bata zauna zaman hutu ba suka d'auki mota suka d'auki hanyar k'auyen kura. Isarsu kura ba wuya suka tsaya a k'ofar wani gidan k'asa da motoci manya a k'ofar gidan mata da maza suna ta shiga da fita suma suka fito suka shiga ciki. Basu jima da zama sosai ba aka kira su suka shiga wajan malamin yana ganin su yayi murmushi yana fad'in, "Barkan ku da zuwa." Zama sukayi kafin Babbar Yaya tace, "mun same ka lafiya malam?." "Lafiya lau ranki ya dad'e." Ta nuna masa Mama tace, "itace wacce na sanar dakai zuwan ta jiya, mahaifiyar sarkin katagum sarki Asad Nasir Sa'ad." Ya sake yi mata jinjina yace, "An gaida y'ar sarki mahaifiya ga shugaban Katagum." Babbar Yaya ta kuma cewa, "Zancen mai martaba Asad d'in ne d'anta gabad'aya an mallake mata shi yanzu ko inda take baya zuwa bayan da yana da tsananin biyayya a gare ta." Malamin ya fara istihara yana duba lamarin kafin ya kalle su yace, "Tsakani da Allah na jima banga bak'in aiki kamar wanda aka yi masa ba, wannan sai dai a kira shi da tsafi ma ba sihiri ba." Mama suka kalli juna hankalin ta ya tashi jin abinda akace mata a can an kuma maimaita mata Mama tace, "Karya shi nake so ayi da gaggawa." Ya sake yin shiru yana istihara kafin yace, "Karya shi ba abu bane mai sauk'i dole sai anyi da gasken gaske sannan za'a iya karya shi kuma dole sai an raba shi da matar sa sannan za'a samu abin yayi nasara, Matuk'ar suna tare bazata barshi shan duk wani magani da aka bashi ba." Mama ta gyara zama tace, "Wannan ba matsala bane zan saka shi ya sake ta koda baya so, duk da shugaba ne Bai kamata ace yayi saki ba amma dole yayi." Babar yaya ta kalle ta tace, "Kina ganin zai amince ya sake ta cikin sauk'i?." Mama ta kalle ta tace, "Zai yu." Malam yace, "Indai zai yu zan bada maganin da za'a bashi ya dinga wanka dashi, sannan akwai rubutun da zan bayar ya zama kamar ruwan shan sa koda yaushe ya dinga sha. Sannan akwai wani babban malami a can garin naku Allah ya bashi ilimin maganin gargajiya sannan yasan ayoyin alkur'ani yana karya tsafi komai munin sa indai Allah ya bashi iko." Mama tace, "waye shi? A ina yake?." Malamin yace, "A nan katagum d'in yake ana ce masa Baba Malam ya tsufa amma kuma akwai ilimi ba kad'an ba." Mama tace, "Wacce unguwa yake?." Malamin yace, "a nan gaban katsalle yake ni kaina in abu ya shige min duhu ina zuwa wajan sai kiga an samu nasara." Mama tace, "Zanje wajan sa da zarar na koma, yanzu bamu naka taimakon." Malamin ya juya yana had'o mata maganin kafkn yace, "Amma fa ganin sa yana da wahala sosai sai ka jera kwana goma layi bai zo kanka ba sai an jure. Baya duba mulki ko kud'i gaskiya in layi bai zo kanka ba bazai ganka ba." Mama taja k'aramin tsaki domin ita kam a ganinta babu wani wanda bai mata wahalar gani tana da kud'i da mulki kome take so zatayi. Maganin ya basu suka zube masa kud'i suka koma gidan Baban Yaya sai a sannan Mama ta samu ta huta ga zazzaɓin da yake cin jikinta sai da tasha magani sannan tayi bacci. Washe gari ta sauke d'aukar hanyar Katagum da sassafe, kafin rana tayi ta isa katagum tana takawa a hankali tana shiga cikin gidan tazo giftawa ta wani d'an lungu da ake aikin abinci a wajan taji hadimai mata d'aya tana cewa, "Bikin yarinyata yazo amma ban san da wacce fuska zan tunkari Mai martaba da maganar nan ba, ya canja gabad'aya ni tsoro ma yake bani shiyasa na yanke shawarar samun Fulani mai babban d'aki da maganar." D'ayar tace, "Me ta isa tayi a yanzu? Hmmm ai dama matar tasa kika samu Zakanyar Sarki in ta saka baki sai kiga yayi miki." D'ayar ta kuma cewa, "Allah mai iko, yanzu wai mai martaba ne baya zuwa inda Fulani take? Lallai duniya juyi-juyi. Amma fa maganin ta kenan kodan wulaƙanta mu d'in da take yi alhaki sai ya kamata." Da sassarfa Mama ta wuce wajan zuciyar ta na suya zazzaɓi na sake rufe ta ruf haka ta isa b'angaren ta.         Tana shiga falon ta hadimai suka zube ta kalle su tace, "Asad ya zauna a fada?." Hadima d'aya tace, "Eh ranki ya dad'e, amma ya shiga ciki yanzu." Bata ce komai ba ta shige ciki tana shiga d'aki tayi wanka ta shirya cikin shigar alfarma duk da bata jin dad'i sosai amma hakan bai hanata yin kwaliyya ba. Tana zama a k'aramin falon ta Hydar da Suhaima suka falon suka zauna kusa da ita Hydar yace, "Barka da dawowa Mama, da fatan an sauka lafiya?." Numfashi ta sauke kana tace, "Alhamdulillah. Ku taya d'an uwan ku addu'a." Hydar yace, "Muna yi masa Mama" ya fad'a yana dafe kansa ta kalle shi cikin tsoro tace, "Ya dai? Ko ciwon ne?." Girgiza kai yayi kawai ta koma ta zauna tace, "yana ina yanzu?." "Yana ganawa da bak'in da suka zo daga Cairo." Shiru Maman tayi bata ce komai ba. "Ina so na ganshi nasan bazai zo nan ba." Jin yadda tayi maganar cikin sanyi duk sai ta basu tausayi Hydar yace, "Allah wuci zuciyar mahaifiyar mu. Kiyi haƙuri komai tsanani yana tare da sauk'i." Tayi murmushin takaici kana tace, "Zanje da kaina" ta fad'a tana mik'ewa dole suma suka mik'e suka rufa mata baya zuwa b'angaren sa zuciyar su cike da tunanin abinda zai biyo baya a can.          Lokacin da suka je ya gama ganawa da bak'in ba hadimai gabad'aya yana niyar hawa saman sa kenan Mama suka shigo ya juyo yana kallon su, ya bada umarnin kar wanda ya shigo masa b'angaren amma babu wanda ya isa ya hana Mama shigowa yasan shiyasa aka barta ta shigo ya lumshe ido ya bud'e ya dawo da baya ya k'araso inda take ya duk'a har k'asa kamar ko yaushe yace, "Barka da Rana." Ajiyar zuciya tayi tana jin ruwa yana taruwa a idanunta ta dafa kansa da yake cikin rawani yellow wanda ya amshi fuskar sa tace, "Asad" ta fad'a tana d'ago k'afadun sa ya mik'e tsaye tana kallon fuskar sa sai taga ya sunkuyar da kai kamar yadda ya saba a wancan lokacin tace, "Asad kana lafiya?." Zaiyi magana kenan aka shigo b'angaren ko basu juya ba sun san wacece dan babu wanda zai shigo wajan daga su sai ita sai maganar ta maqale ya fasa Mama ta kalle ta ta ga ta d'aure fuska ta kalli Asad tace, "Wacece ni a wajan ka?." Yayi shiru na d'an lokaci kafin yace, "Mahaifiyata" yadda ya furta sai da suka kalle shi duka domin a sanyaye yayi maganar sosai. Mama ta sauke numfashi tace, "Na isa dakai kamar lokacin baya Asad?." Ya girgiza kai yace, "Matsayin mahaifiyata baya tab'a canjawa." Ta kalle shi ta kalli Jidda tace, "Nasan kai shugaba ne koyi ya kamata mutanen cikin gidan nan dana waje suyi dakai akan komai, amma dole ce ta saka zan saka ka aikata abinda zan fad'a domin zama da ita ba alkhairi bane a rayuwar ka, ban damu da maganar mutane ba indai zaka zamu lafiya shine burina. Dan haka Ina baka umarnin ka saki wannan yanzun nan!" Ta fad'a yana nuna masa Jidda da yatsan sa. Juyawa yayi ya kalli Jidda suka had'a ido yaga tana murmushi ya dawo da kallon sa ga Mama ya sake kallon Jidda sai ya kasa cewa komai ya sauke kansa k'asa zuciyar sa tana bashi umarnin aikata abinda Mama tace amma harshen sa da gangar jikin sa sun k'i bayar da wannan damar. Mama ta kuma cewa, "mahaifiyar ka nake shiyasa nace ka sake ta nasan baka tab'a tsallake umarni na a ko yaushe. Ina so ka sake tabbatar mata da na isa da kai yanzun nan ba anjima ba ka sake ta Asad." Kai ya saukar k'asa sosai ya sauke numfashi zuciyar sa naso ta furta amma maganar tak'i zuwa harshen sa, dak'yar ya iya tattaro abinda yake bakin sa yace, "Allah ya wuci zuciyar Mama na, bazan iya sakin ta ba!." [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *059.*            Yadda Mama ta k'ame 'kam tana kallon sa da alamun mamaki a tare da ita mai had'e da tsoro da firgitarwa da tashin hankali had'i da rud'ani take kallon sa, tashin hankalin da ya shiga jikinta har a kan fuskar ta ya bayyana k'arara ta kasa furta komai sai kallo da take binsa dashi shi kuma kansa yana k'asa baice komai ba. Bakin ta har rawa yake yi tace, "Asad....!." "I'm sorry Mama ina so na aikata abinda kika ce amma bazan iya ba, ina neman izinin tafiya" ya furta a sanyaye bai jira ta bashi umarnin ba ya juya ya hau sama ta bishi da kallo jiri yana d'aukar ta. Baya tayi zata fad'i Suhaima tayi hanzarin rik'e ta shi kansa Hydar ya daskare a wajan kallon inda Asad yabi kawai yake yi hankalin sa a tashe tsoro ya mamaye masa zuciyar sa, murmushi Jidda take yi daga gefe kafin ta k'araso inda Mama take tace, "Har abada bazai tab'a iya sakina ba, zai iya rabuwa da dukkan ku amma bazai iya rabuwa dani ba, In ma tunanin da kike kenan is better ki ajjiye shi sabida bazai tab'a faruwa ba ko yanzu ko nan gaba. Zaku iya tafiya zanje wajan mijina na taimaka masa yayi wanka ya huta." Mama idanun ta a lumshe yake bata iya magana ba Suhaima zatayi magana Hydar ya hanata dan baiga amfanin maganar ba suka rik'e Mama suka fita sabida mutane ma ta k'ofar baya suka bi zuwa b'angaren Mama dan har lokacin suna rik'e da ita jiri take yi.Kafin su isa zazzaɓi ya lullub'e Mama suna ajjiye ta falo Hydar ya kira Dr ya sanar dashi emergency yake son zuwan sa. Duk suna zaune kusa da ita ba jimawa yazo Hydar ya bada damar shigowar sa ya shigo ya fara auna BP Mama, sai da ya kammala ya bata magani ya kalli Hydar yace, "Ranka ya dad'e jinin Fulani ya hau sosai fiye da tunanin ka, inda akwai abinda yake damunta ayi gaggawar ganin ta rage damuwar ta in ba haka ba akwai matsala gaskiya." Sallama sukayi da Hydar bayan ya bata magani ya tafi ya dawo kusa da ita yace, "Mamana muje d'aki ki huta." Taimaka mata sukayi ta tashi zuwa d'aki ta kwanta a gefen gado idanun ta rufe sai a lokacin suka lura kuka ma Maman take yi. Basu iya cewa komai ba ta kwanta suka kullo mata d'akin ko wanne jikin sa a sanyaye. Hydar ya kalli Suhaima yace, "Wanne mataki kike ganin zamu d'auka akan Jidda?." Suhaima tace, "wanne mataki kenan Yaya Hydar? Mama fa ita take son Jidda ita ta saka ya aure ta ta raba shi da wacce yake so, ni daman wallahi sau da yawa na kanyi tunanin kamar akwai wata manufar da Mum take zaune da Mama a lokacin dana fad'a mata bazata amince ba sai dai ma raina ya b'aci. Yanzu kuma sun fito da asalin kalar su, waccen matar tasa yana sonta haka Mama ta raba su yanzu kuma gashi tana so ya rabu da wacce baya so yace bazai ba." "Kinga Suhaima wannan ya wuce, meye mafita yanzu da zamu taimaka masa?." "Addu'a mana, asiri suka yi masa wallahi dan in ba asiri ba banga abinda zai raba Mama dashi ba. Sai dai mu taya ta fad'awa Allah ya kawo sanadin raba su dan in ka lura yanzu ibadar sa ta ragu." Hydar yayi shiru yana saukar da numfashi yace, "Zan sanar da abokan sa na Madina su taya shi Addu'a nima zan nemo maganin da za'a dinga bashi ba ko Allah zai taimake mu ya warke, matsalar kuma in an nemo ma basha zaiyi ba." Suhaima tace, "in muna Addu'a zai sha wata rana ai. Kawai dai mu dage da addu'a in ba haka ba wallahi sai gidan nan ya gagari Mama zama wata rana, ka duba har jinin ta ya hau in aka cigaba ban san me zai faru da Mama ba." Hydar ya girgiza kai ya fita ya bar Suhaima a wajan. *☆☆☆*          "Mum kin san bata jima da fita ba na fito nazo nan wai ya sake ni." Mum tace, "What! Ya sake ki?." "Wallahi Mum, kuma yau yadda yayi mata magana cikin biyayya yayi mata ni na fara jin tsoro wallahi kar wata rana tayi galaba a kansa fa." Mum tace, "kice sai an sake nemo mafita kenan, in aka cigaba da haka wata rana zatayi nasara. Ta bazama nema masa magani yau ma daga Kano ta dawo wajan malaman su nacan akan matsalar in muka bari ana haka tabbas wata rana namu zai karye. Dole a samo mafita." Jidda tace, "abinda ya kamata ayi kenan Mum dan ni na tsorata wallahi, yadda yayi mata magana a sanyaye ya bani tsoro. wacce mafita za'a samu?." Mum tayi shiru tana kallon wani wajan daban zuciyar ta na kawo mata wani abun kafin tace, "Kashe ta za'ayi Jidda!." A firgice Jidda ta mik'e tsaye idanun ta a waje tace, "Mum kisa?." Mum ta kalle ta tace, "dallah malama zauna kar ki tara min jama'a" ta fad'a tana jan hannun Jiddan ta zauna har lokacin idanun ta a waje Mum tace, "Nutsu."  Jidda ta had'd'iye yawu cikin tsoro tana kallon ta Mum tace, "Dan nace a kashe ta kika wani firgita kamar nace ke za'a kashe?, in tana duniya wallahi wata rana sai ta raba ku dashi. Kar kiga shi shugaba ne a tsarin gidan sarauta sarki baya saki ke bama sarki ba ko wanda suke a k'asan sarki basa saki to wallahi sai ta nemo hanyar da zata raba ku, shu'uma ce duk yadda kike tunanin ta ta wuce haka." Jidda fuskar ta har lokacin da tsoro tace, "Duk da haka Mum kisa fa?, kisa sai kace cinnaka ko kiyashi? Nidai a bar maganar kisa Mum." "Mtsww sai kiyi ai, ke za'a taimakawa fa in aka barta da rai billahillazi sai kinzo kina kuka da idanun ki nan gaba domin ta wuce inda kike tunani, gwara mu yiwa tufkar hanci yadda zaki mulki gidan san ranki kiyi abinda kika ga dama in kuma ganin bakya son hakan fine Jidda daman ai ke za'a taimaka." Jidda ta rausayar da kai tace, "Yadda kika ce Mum, kawai ina jin tsoro ne." Mum tayi murmushi tace, "kar komai ya baki tsoro ni nasan yadda zanyi, ki bani nan da wasu kwanaki zanyi maganin ta." Jidda ta juyar da kai zuciyar ta gabad'aya a cushe haka kawai take ji bata so a kashe Mama amma bazata nunawa Mum ba dan duk abinda take yi dan ita take yi in ta nuna mata bata so bazata ji dad'i ba amma bata son aje ga kisa. Ta jima suna hira a gida har Daddy ya dawo suka gaisa sannan drivern ta da jakadiyar ta suka kwashe ta aka koma gida. *☆☆☆*          Waziri ne a zaune malami a gaban sa su uku ne a zaune a falon shi da malamin sai Suhail malamin ya kalli Waziri yace, "Ranka ya dad'e in ba'a gaggawa ba komai zai iya canja salo ya zama dole ayi abinda ya kamata." Waziri ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya yace, "Za'a yi cikin kwanakin nan kuwa in sha Allah." Sallama sukayi malamin ya tafi falon ya rage dashi sai Suhail ya kalli Suhail yace, "Meye shawarar ka?." Suhail yace, "ta yadda za'a raba shi da mulkin shine aiki." Waziri ya sauke numfashi yace, "kawo shawara dai."  Ya gyara zama yace, "a ganina shi shugaba ne kuma wanda ake yiwa kallon mai addini da sanin ya kamata, me zai hana mu samu baiwa mace a had'a baki da ita a biya ta kud'ad'e masu yawa a kuma ja mata kunne matuk'ar nan gaba ta furta abinda ya faru sai an kashe ta." Ya gyara zama yace, "Me za'ayi kenan?." Suhail yace, "Sharrin alfasha!." Waziri ya zubawa Suhail ido shima shi yake kallo kafin ya sauke kansa yace, "duk k'imar mutum alfasha tana zubar dashi, duk mulkin mutum alfasha tana sakawa a ganshi tamkar bawa, duk kud'in mutum alfasha tana sakawa a ganshi kamar talakan da bashi da cin yau bare na gobe. Duk yadda ka kai da ilimin ka da addinin ka indai alfasha ta shigo ciki ko kai kad'ai ne malamin da jama'a suke sauraron wa'azin su daga rana sun daina domin zasu ga abinda kake tsoratar dasu da kar su kusance shi kai kana kusantar sa. Sharrin Alfasha shine zai tarwatsa Asad ta k'arfi sai an sauke shi daga wannan karagar." Waziri ya girgiza kai cike da gamsuwa da maganar sa zuciyar sa cike da tsantsar farin ciki yace, "Na jima banji maganar data kwantar min da hankali kamar wannan ba Suhail. Kana da hangen nesa da sanin ya kamata kayi tunani mai kyau Suhail shawarar ka tayi dari bisa dari babu kuskure a cikinta, tabbas wannan shine zai tarwatsa sarki da dangin sa." Suhail ya murmusa ya shafa kansa yace, "Godiya nake ranka ya dad'e." "Tashi kaje zan neme ka anjima." "A tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya fita ya bar mahaifin nasa a zaune. Yana fita wayar sa tayi k'ara kamar jira ake ya fita ya duba ganin number da yake jira ya saka shi ya d'auka yace, "Kamar kin san jiran kiran ki nake yi master." Tace, "akwai update ne?." "Sosai ma kuwa." "Ina jin ka." "Maganar raba Mai martaba da kujerar sa ce an samo mafitar da zai barta koda baya so." "Meye ita?." Waziri yace, "Sharrin alfasha za'ayi masa, abinda nake nufi a kama shi da mace a d'aki macen ma baiwa." Tayi k'aramar dariya tace, "Sarkin za'a kama da baiwa a d'aki? Kana mantawa da sarki ne fa bafa hakimi ba?." Ta sake yin dariya kafin tace, "sam wannan shawarar batayi ba, babu ta yadda za'ayi sarki guda ace an kama shi da wata yarinya kuma baiwa a d'aki d'aya hankali ma bazai d'auki a wannan ba." Waziri yace, "Zaiyu mana, ba Zuciya ce fa." "To ta yaya ta shiga? Meya kaita d'akin sa? Me zata kai masa har d'aki?, daga kanta ya fara?, meyasa a baya ba'a tab'a jin makanancin labarin ba?. Bafa Aliyu bane Asad ne ya kamata ka gane." Waziri yayi shiru jin yayi shiru ya saka tace, "in zaki yanke hukunci kuyi wanda hankalin mutane bazai kai shiri bane kuyi abu kamar gaske, inda ace Aliyu ne dan munyi masa sharrin nan ba wani abu bane mai wahala kowa kuma zai amince da zai iya aikatawa tunda daman an san dabi'ar sace, amma Asad fa?. Kai koma Aliyun ne sarki ne fa taya zai nemi baiwar sa? In ma neman matan zaiyi ba'a gidan ba sai dai wani wajan daban." Waziri cikin gamsuwa yace, "Tabbas maganar ki gaskiya ce." Tayi murmushi tace, "tunda lokacin da muke jira yazo zan san abinda za'ayi amma wannan shawarar a ajjiye ta a gefe d'aya ba za'ayi aiki da ita ba kwata-kwata." "Me za'ayi?." "Zan sanar dakai in na gama shirya komai." "Batun yin cikin matar sa fa? Bana so ya ajjiye d'a a duniya domin zai iya zamar mana barazana nan gaba." "Shida haihuwa har abada, na gama da wannan aikin tun ba yau ba." Waziri ya sauke numfashi yace, "Zan so ki bayyana min fuskar ki ko sunan ki ni kaina ban sanki ba har gobe." Dariya tayi tace, "nan kusa" tana fad'a ta yanke kiran yabi wayar da kallo zuciyar sa na hasaso masa wacece master planer......? *☆☆☆*          Washe gari         Da wuri Rauda ta shirya tana jiran su Ramla dan ranar Baba malam ya basu suje su ganshi, k'arfe goma na safe suka bayyana a k'ofar gidan har gida Ramla ta shiga suka fito tare suka shiga mota suka tafi. A mota Rauda tace, "Ina kwana Dr." "Lafiya lau Rauda, mun fito dake da sassafe." Murmushi tayi kawai bata ce komai tana nuna musu hanya har suka je k'ofar gidan. K'arewa k'ofar gidan kallo suke yi ganin sa a cike da manyan motoci ga babura Dr ya kalli Rauda yace, "kalli jama'a kamar ana sadaka?." Ramla tace, "abin mamaki ba." Rauda tayi murmushi tace, "Dan ma yau asabar da jiya ne wallahi wajan nan babu waje." Kai ya girgiza suka fito Rauda tace, "shiga ciki zamuyi ai." Cikin gidan suka shiga suna wuce mata a zaune da maza wasu da hijjabi wasu kuma da mayafi wasu kuma da niqab.        A cikin wani d'aki Rauda suka sauka suka zauna sannan ta tashi ta shiga cikin gidan suka gaisa da mutanen ciki ta dawo ta zauna tace musu, "Yanzu zai shigo in sha Allah." Suna zaune kowa yana danna wayar sa babu mai magana a cikin su kusan mintina arba'in a haka kafin suji gyaran murya a bakin k'ofa. Da sauri suka mik'e dukkan su yana murmushi ya shigo yana fad'in, "Ku zauna mana, Babata zauna." Zama yayi akan wata kujera a d'akin suma suka zauna kafin su gaisa dukkan su ya amsa da murmushi ya kalli Rauda yace, "Babata kinyi min yaji ba'a ganin ki ko kad'an sai kinga dama." Murmushi tayi tace, "Muna gaisawa a waya ai Baba." "Ni ganin Babata nake so nayi ai ba waya ba, koda yake baki jima da fita daga idda ba ai." Murmushi kawai tayi tace, "Baba ga bak'in da Umma ta fad'a maka zasu zo munzo tare." Yace, "To ma sha Allah." Rauda ta mik'e tace, "bara na shiga ciki" ta fad'a tana shiga cikin gidan ta barsu dan su sake su fad'a masa matsalar su. Ta jima a ciki suna hira da y'an matan gidan har aka turo kiran ta sannan ta dawo ta shiga da sallama ya kalle ta yace, "Rauda." Ta zauna tare da fad'in, "Na'am Baba." "Gobe da yamma ko da daddare kizo ki karb'ar musu magani bani dashi a yanzu zuwa da asuba zan samo shi in sha Allah." "To Baba Allah ya kaimu." "Amin ya Allah. Kema akwai naki sai ki tafi dashi a goben gabad'aya." "To Baba." Baba ya kalle su yace, "Khalifa in sha Allah gobe za'a karb'ar muku maganin da izinin Allah kuma za'a dace, sannan kuma ku bi shawarwarin da na baku in sha Allah za'a dace, a kuma dage da rok'on Allah." A tare suka ce, "Mun gode Allah ya k'ara girma." Baba malam yace, "babu komai, zaku iya tafiya yanzu ina da bak'i." Dr ya d'auko kud'i masu yawa ya ajjiye masa Baba Malam ya girgiza kai yace, "Bana buk'atar kud'in sadaka daga wajan ku, mahaifiyar Rauda ta sanar dani taimakon da kuka yiwa mata kun cancanci fiye da haka daga wajan iyalan mu. Mu rama alkhairi da alkhairi" ya fad'a yana mik'ewa cikin murmushi fuskar sa sak ta Umma sukayi godiya sosai ya fita. Cikin gidan Rauda ta shiga tayi musu sallama suka fito suka fita, a k'ofar gidan suka ga dogarai maza guda biyu a bakin wata mota kana ganin motar kasan daga gidan sarauta ta fito yanayin number motar ya nuna hakan suka wuce abin su ba tare da sun kalli wanda yake ciki ba. A mota suna cikin tafiya Rauda na baya a zaune Ramla tace, "Gaskiya naji dad'i wallahi Rauda, badan ke ba wannan layin ai bamu san lokacin da zamu bar nan ba wataƙila ma layin bazai zo kan mu ba. Allah ya bar zumunci wallahi dan ji nake a jikina kamar har mun samu waraka." Dr yace, "Nima haka, ban tab'a jin wani yak'ini na samun magani kamar wannan ba, kuma ta inda ya burge ni da alkur'ani da hadisi yake amfani baya duba baya tsafi ko wani abun. Gaskiya Rauda kun dace samun babban mutum a dangi kamar sa ma rahama ne." Murmushi tayi kafin taji yace, "naji yana ce miki Babata sunan maman sane dake?." Rauda tayi dariya tace, "A'a kawai yana fad'a min ne sabida ina kama sosai da babar su Umman shiyasa. Umma tace kamar itace ta haife ni shiyasa yake ce min haka." Murmushi tayi kawai taji Ramla tace, "gashi duk matsayin ki sai kin bi layi baya tauyewa talakawan da suke zuwa wajan sa hakki akan masu kud'i. Yanzu ka duba motar da muka bari kamar ta gidan sarauta amma layi take bi." Dr yace, "Ai ba ganin Idanun Rauda ba ban tab'a ganin malami kamar sa ba." Ita dai murmushi kawai take yi Ramla tace, "Sis badan kar kice na cika tambaya ba dana ce daman kin tab'a aure ne?, naji yana miki zancen idda." Rauda ta sauke numfashi tayi shiru tana kallon hanya annurin fuskar ta ya d'auke gabad'aya ganin hakan sai Ramla tace, "Kiyi hak'uri dan Allah." Rauda ta wayance tace, "Lah babu komai fa Sis, abin ne in na tuna yana saka ni a wani yanayi mara dad'i. Na tab'a aure ban jima da fita daga idda ba Sis." Ramla tace, "kenan lokacin da kina Egypt da auren ki?." Rauda ta girgiza kai tace, "Eh, wanda muke tare dashi shine mijina. Hydar k'anin Asad shine silar samun matsalar k'afa ta shine ya buge ni a mota har k'afata ta samu matsala. Daga nan Asad ya nuna yana sona amma Maman sa ta hana hakan, da yake dai Allah ya rubuta sai na kasance matar sa ban sani ba Mai martaba mahaifin sa ya karb'i aurena wajan Babana akayi auren ba tare da Maman sa ta sani ba, bama iya ita kad'ai ba da yawa mutane basu san anyi auren ba muka tafi nan Egypt aka samar min da lafiyar k'afa ta. At the end dai auren bai wuce sati hud'u ba ya mutu wannan lokacin da Dr ya taimaka min har nazo gidan ki anyi sanki Maman sa tace kuma sai na fita" ta k'arasa fad'a muryar ta na shaking. Ramla ta kalli Khalifa shima ya kalle ta cike da mamaki da al'ajabi Rauda tayi shiru ta mayar da hawayen idanun ta tace, "Na d'auke ku y'an uwana shiyasa na fad'a muku dan Allah bana so maganar nan ta fita dan bani so mani asan nayi aure, yadda mutane basu san ya aure ni ba d'auke suke aikin k'afa aka yi min muka dawo muje a hakan kawai." Ramla tace, "in sha Allah babu wanda zaiji Rauda. Allah yabi miki hakkin ki domin dukkan su sun cutar dake daga shi har Babar tasa." Shi dai Dr baice komai ba zuciyar sa cike da mamakin abin har suka je gida suka sauke ta har  gida Ramla ta shiga ta yiwa Umma sallama sannan suka wuce. Bayan sallar la'asar Umma da Rauda suna zaune suna hira Baba ya shigo yana fad'in, "Rauda har kunje wajan Baba malam d'in?." Rauda tace, "Munje Baba tun d'azu muka dawo." Ya zauna yana fad'in, "To yayi kyau." Ya kalle ta yace, "Binta Anas yazo min da maganar yana neman izinin fara zuwa wajan Rauda mtsayin me neman auren ta a karo na biyu, tun jiya yayi min maganar yanzu kuma yazo yana can k'aramin d'akin can yana jiran ta." Gaban Rauda ya fad'i ta kalli Umma itama ta kalle ta sai taga Umma tayi murmushi tace, "Alhamdulillah, na jima ina jiran wannan ranar tun bayan kammala iddar ta. Amma Malam kaine ka sanar dashi ta gama idda?." Baba yace, "hira ce tazo har maganar ta shigo ciki ashe ya rik'e bai manta ba." Umma tace, "Allah sarki, wallahi ni daman can shi nake mata sha'awar aure Allah ma ya sani dan ka auri namiji mai sonka shine morewa." Baba yace, "in ya kasance mijin ta sai kiga anyi an gama kamar wancan." Ya kalli Rauda yace, "Saka hijjabin ki kije yana jiran ki zaku tattauna." Ba musu ta tashi ta shiga d'aki ta d'auki hijjabi ta fita Umma ta bita da kallo shima Baban kallon ta yake yi yana ji kamar komai ya faru da ita shine sila amma babu yadda zaiyi ba'a goge k'addara. Tunda ta doshi d'akin sai take jin fad'uwar gaba ta sauke numfashi ta shiga da sallama yana zaune cikin farar shadda anyi mata aikin bak'in zare sai khamshi yake yi ya amsa yana kallon ta, a gefe ta zauna tace, "Ina wuni." Yayi murmushi yace, "lafiya lau Rauda ta, ya naga kina jin kunya kamar bamu zama y'an uwa nida ke ba?." Murmushi tayi shima shi yayi ya gyara zama yace, "Nasan Baba ya sanar dake qudirina a kanki a karo na biyu Rauda, a karo na biyu na dawo gare ki ina neman auren ki Allah yasa zaki amince.: Ta d'ago ta kalle shi tayi murmushi tace, "Yanzu ba dah bane ba, kar ka manta na tab'a yin aure." Yayi murmushi yace, "Na sani ai, k'addarar auren kice ta zama silar raba mu har iyayena suka min zab'i da Allah yayi nufin dawowar ki sai ya d'auki ran wacce aka bani tun ban aure ta ba kema ya raba ki da naki mijin. In kika duba zaki ga Allah ya tsara mana faruwar hakan tun farko K'addara ki kalar tawa ce." Kai ta girgiza cikin gamsuwa da abinda yace iya tsara kalaman sa da nutsuwar sa yana daga cikin abinda yake burge ta a tare dashi tace, "Baka ganin a wannan karon ma zasu iya yi maka zab'in?." Yayi murmushi yace, "A wannan karon sun bani ikon zab'ar wacce nake so na riga na sanar dasu kece wacce nake so sun amince min yanzu taki amincewar kawai nake so. Bana so a d'auki lokaci nan da wata biyu nake so ayi bikin a gama bana so wata k'addarar ba fata nake ba ta sake kawo mana barazana tsakanin mu. Dan Allah Rauda ki fad'a min gaskiyar abinda yake ranki, kin amince na zama mijin ki? Kina sona a kafo na biyu ko A'a....?.Kar ki b'oye min abinda yake ranki." Shiru tayi ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta ta d'ago ta kalle shi tace,.......... [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *060.*             Shiru tayi kanta na k'asa sai kuma ta d'ago kai ta kalle shi ta fitar da sigh kafin tace, "zanyi tunani a kai a bani lokaci." Ya d'an wara ido yace, "Yanzu ashe ina da wani hali da sai anyi tunani a kaina?." Ta girgiza kai tana murmushi tace, "A'a ba haka nake nufi ba, kawai ina so nayi tunani ne a bani wannan damar." "An baki ranki ya dad'e, ina fatan dai baza'a d'auki lokaci ba." Tace, "Babu lokaci in sha Allah." "Godiya nake gimbiya." Sai tayi murmushi kad'an shima yayi murmushin tayi shiru bata ce komai ba kafin yace, "Ina sonki wallahi Rauda, duk abinda ya faru a baya ban tab'a jin sonki ya ragu a zuciyata ba. Har fa addu'a na dinga yi Allah ya cire min ke a zuciyata nasan kina da aure amma kuma na kasa daina sonki, ashe kina nan dawowa gare ni." Lumshe ido tayi ta bud'e ta kalle shi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tayi murmushi kawai shima sai yayi murmushin. "Naga alama yau sarautar kike ji da ita, shikenan to zan koma yamma tayi sosai." Ta kalle shi tace, "a gaida mutanen gidan." Yace, "Zasu ji in sha Allah. Zan fad'awa Mamana sirikar ta Rauda tana gaishe ta." Murmushi ta kuma yi kafin ya fita ita kuma ta ta shiga cikin gida fuskar ta har lokacin d'auke da murmushi. D'aki ta wuce ta zame hijjabin ta har lokacin bata daina murmushi ba Umma da ta shigo d'akin tace, "Rauda."      Juyowa tayi ta kalle ta tace, "Na'am." Umma ta kalle ta tace, "ya kike ji a zuciyar ki akan Anas?." Ta sunkuyar da kanta Umma tayi murmushi tace, "Allah yasa kin amince dashi dan ni wallahi ina miki sha'awar auren sa sabida yana sonki so na hak'ika sosai." Rauda tayi d'ago tace, "Umma indai kina son na aure zan aure shi." Umma ta wara ido tare da rik'e hab'a tace, "Ni zan zauna miki dashi da zan so ki aure shi Rauda? Kawai ina fad'a miki ra'ayina ne amma yankewa ai yana wajan ki." Tayi murmushi bata ce komai ba Umma ta sake cewa, "Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi, ki cigaba da addu'a" tana fad'a ta fita Rauda ta zauna a gefen gado tana murmushi ita kad'ai wanda bata san dalilin sa ba. Tunawa da kalmar Anas da yace sarauta take ji da ita sai fuskar Asad ta fad'o mata a zuciyar ta tayi saurin kawar da ita tare da runtse ido ta cize baki tare da dukan goshin ta a lallai sai ta kawar da tunanin da ya kawo mata ziyara ta tashi ta fita daga d'akin gabad'aya gudun ma kar tayi tunanin sa. Washe gari da yantsi Rauda ta shirya ta tafi gidan Baba Malam dan karb'o sak'on Ramla da kuma nata, kamar ko yaushe layi kamar babu gobe ta wuce zuwa cikin gidan mutane sai kallon ta suke wanda suka ganta jiya sun gane ta wasu kuma a ranar suka zo bata jima sosai ba aka sake ganin ta fito da leda a hannun ta alamun ta karb'i sak'on ta. Kusa da wata mota tazo wucewa sai ta wayar ta tayi k'ara ta d'auka ta tsaya a jikin tagar motar ta baya ta saka a kunne tare da fadin, "Kin kira a daidai Sis yanzun nan kinga sak'on a hannuna na karb'o miki." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tayi dariya tace, "Har na ganshi tuni ma, layi kam akwai shi har yafi na jiya ma wallahi." "Eh to mu had'u a gida sai ki karb'a" tana fad'a ta kashe wayar ta cigaba da tafiya. Mama da take zaune a mota ita da Suhaima ta kalli Suhaima tace, "Ita wacece yarinyar nan da naga jiya tazo bata jima ba ta tafi yanzu ma haka?." Suhaima ta kalli bayan Rauda tace, "Wataƙila ta san shine shiyasa." Mama ta kalle ta daidai lokacin da ta samu keke napep tace, "bita Suhaima muje ko wani abun ne a biyata ta kawo mu na gaji da dogon layin nan" ta fad'a tana dafe kanta domin ita kam bata saba bin layi ba. Suhaima tace, "Amma da an tura ance masa kece da kanki gani nake bazai ki sauraren ki ba." Mama tace, "Jiya an sanar dashi ashe shi baya alfarma. Banda dole me zai kawo ni wajan nan?, Sadiya ta cuce ni." Suhaima bata ce komai ba tabi bayan napep d'in da Rauda ta hau har k'ofar gidan su ta sauka ta biya shi sannan ta shiga. Suhaima jira take Mama tayi magana ita kuma ta rasa me zata ce ne, a zahiri tana son ganin Baba malam kodan bakin da yayi yawa akan aikin sa amma kuma bata tunanin zata iya neman alfarma a wajan wasu mutanen duba da matsayin da take dashi. Dan k'aramin tsaki taja kana tace, "Juya mu koma gida." Ba musu ta juya suka d'auki hanyar komawa gida. Bayan sun sauka direct b'angaren mai martaba Mama ta wuce kamar ko yaushe Hydar yana zaune a gefen sa idanun mai martaba a kulle alamun yana bacci. Zama tayi a inda Hydar ya tashi ya bata tana kallon mijin nata kawai sai ta fashe da kuka. Kuka take yi sosai Hydar yana tsaye yana ji kamar shima yayi mata kukan dan yasan an mata rauni a zuciyar ta ga rashin lafiyar da take fama da ita, ga Asad ga kuma Abba. Ta jima tana kukan kafin yazo ya dafa ta yace, "Dan Allah Mama kiyi hak'uri, Allah ya wuci zuciyar ki." Sassauta kukan nata tayi ta kalle shi ta goge idanunta sai kuma ta mik'e tana kallon sa tace, "Hydar me ya same ka? Badai ciwon kane zai tashi ba? Kayi min rai kar ciwon ka ya tashi in hakan ta faru ban san ya zanyi ba, ba Asad ba kai ba Aliyu." "Kiyi hak'uri Mama" ya fad'a a tausahe ta kalle shi tace, "Ina Asad?." Ya sauke numfashi yace, "Mai martaba ya tafi England shida matar sa." Runtse ido tayi bakin ta yana rawa tace, "ya tafi ban sani ba, meyasa yake min haka Hydar?" Ta fad'a hawaye na sake zubo mata Hydar ya rik'e ta sosai duk da ciwon da yake ji a zuciyar sa da kansa. "Ranki ya dad'e dan Allah ki daina kuka mutane suna shigowa ba girman ki bane" ya fad'a a tausahe ta goge idanun ta ta sauke numfashi ta juya ta fita daga d'akin. Numfashi ya sauke domin shima dauriya kawai yake yi mugun ciwo kansa yake masa zai iya cewa ciwon sa yana gab da tashi baya so ya nuna mata ne dan kar hankalin ta ya tashi. D'aki ta koma ta kwanta ta fashe da kuka mai tab'a zuciya kanta yana sarawa zuciyar ta na tsagaita bugawa, ta jima tana kuka kafin ta sassauta ta mik'e zaune kanta yana mugun sarawa ta dafe kai da hannu biyu sabida ji take kamar zai fashe. Wayar ta take ji tana ihu bata iya dauka ba sai da taji kiran yayi yawa ta mik'a hannu ta d'auka ba tare da ta duba ba taji ance, "Yaya Rabi'atu." Jin muryar k'anwar ta ya saka ta bud'e baki tace, "Uhumm." Daga can b'angaren tace, "Subahanallah Yaya meya same ki haka naji muyar ki kamar mai kuka?." Jin bata amsa ba ya saka yace, "Ko akan maganar da Yaya Babba ta fad'a mana ne? Nasan ma itace ta mayar dake haka Yaya daman maganar gaskiya kin sake da wannan Sadiyan da yawa, ko wanne sirrin ki ta sani bakya b'oye mata komai ba dole ta samu lagon ki da sauri haka ba. Yanzu ba wannan ba ya riga ya faru ki daure a bazama nema masa magani muma nan muna tayi ko za'a dace." Mama ta cize bakin ta tace, "Na rasa abinda zanyi." "Ki tuna, sai kin tuna sannan zaki aiwatar da komai wannan zaman naki bazai haifar da komai ba sai dai ma ya saka ki sake nisanta dashi. Mahaifin sa bashi da lafiya balle ya taimake ki dole ki dage." Bata amsa ba ta yanke wayar ta kwanta tana sauke numfashi zuciyar ta cike da tunane-tunane kafin kuma bacci ya d'auke ta. Data farka taji dad'in baccin sosai tayi wanka ta fito babban falon ta hadimai suna ta hidama ta zauna ta kalli Jakadiyar ta tayi mata alama da tazo, jiki na rawa ta k'araso ta zube a gabanta Mama tayi banza da ita kamar bata san wata wajan ba sai daga baya tace, "Kin san wani Baba Malam?." Jakadiya ta duk'ar da kai tace, "Allah yaja da ran fulani na san shi, kwanaki akwai matsalar sammu da aka yiwa dan wajena dana je na same shi cikin ikon Allah an samu waraka." Mama ta sake yin shiru kamar bata ji ba kafin tace, "Taya kika samu ganin sa?." Jakadiya tace, "Ranki ya dad'e ta hanyar Gwaggo da take b'angaren k'aramar Fulani na ganshi." Mama ta sauke numfashi tace, "Jeki ki kira min ita." "An gama ranki ya dad'e" tana fad'a ta mik'e ta fita da sauri Mama ta kwantar da kai a jikin kujera tana jiran dawowar su. Ba jimawa suka shigo su biyu suka zube a a gabanta Gwaggo tace, "Allah yaja zamanin Fulani, yaja da ranki ya k'ara miki lafiya." Mama tace, "Wa kika sani ya kai ki wajan wani malami Baba Malam?." Tayi mata jinjina kana tace, "Allah yaja zamanin ki akwai wata mahaifiyar k'awar y'ata Binta ita kuma k'anwar sace ta dalilin ta na ganshi har na yiwa Jakadiya iso wajan sa." Mama ta furzar da iska tace, "Abinda nake kuje gidan su kuzo min da k'anwar tasa nan." A tare suka amsa da fad'in, "An gama ranki ya dad'e" suka mik'e suka fita.           Suna fita mota suka hau zuwa gidan su Rauda suka same su kamar ko yaushe suna tare a zaune harda Inna ana ta hira suka shiga da sallama, bayan sun gaisa ne Gwaggo tace, "Rauda shugabar muce ta taso mu yanzu ta aiko mu." Umma tace, "Wacce kenan?." Gwaggo tace, "Fulani Rabi'atu mana mahaifiyar Asad.." Umma da mamaki tace, "To lafiya dai?." Gwaggo tace, "lafiya lau, cewa tayi nazo na tawo mata dake wajan ta."  Rauda tace, "Wacce shugabar taku kenan Gwaggo wai?." "Yanzu fa na fad'a Rauda, Shugabar mu gimbiya mana, matar sarki kuma babar sarki. Fulani Rabi'atu babar sarki Asad." Gaban Rauda ya yanke ya fad'i ta daure tace, "to me Umma zatayi mata zata ce a kai mata ita?." Jakadiya tace, "Kwantar da hankalin ki yarinya, tana son ganin Baba malam ne akan matsalar mai martaba duk da bata fad'a mana matsalar ba amma nasan akan sane zata je, to kunfi kowa sanin halin sa baya danne lokacin talakawa sabida masu mulki taje amma bata samu ganin sa ba shine take tambaya ta na sani nake sanar da ita na tab'a zuwa na ganshi ta dalilin Gwaggo itama kuma ta dalilin ku, shine tace muzo aje da Umman ki." Inna tace, "Kenan alfarma take so ayi mata?." Jakadiya tace, "Eh to kusan hakan zamu ce." Rauda tace, "Wallahil azim Ummana bazata je ba, in ita bazata tako k'afar ta tazo nan ta nemi alfarmar ba tasha zaman ta ita take nema ba mu ba." Jakadiya tace, "Hattara y'an mata magana ake ta Fulani Rabi'atu" ta fad'a tana murmushi tana kallon Rauda. Rauda tace, "in ma Asad d'in ne da kansa ba babar saba wallahi bazata je ba. Dan ma ta raina mana hankali tana neman alfarma kuma ace Umman ce ma zata je wajanta kamar itace take nema?. Itafa take nema bami ba in bazata zo ba tasha zaman ta Umma ce dai bazata ba." Gwaggo tace, "Haba Rauda sai magana kike baki bari munji ta bakin Umman taki ba." Umma tace, "Abinda Rauda tace shine daidai ai Gwaggon Habiba, zan iya yi mata alfarmar ganin Baba malam wannan ba komai bane amma sai dai tazo inda nake badai ni naje ba. Itace take nema bani nake nema ba dan haka bazan je inda take ba." Gwaggo ta kalli Jakadiya tace, "to kinji." Jakadiya tace, "ta yaya zamu sanar da ita wannan sak'on mai tsauri? Kinfi kowa sanin halin ta fa." Gwaggo tace, "koma meye haka zamu jure, tashi muje." Suka tashi suka yi sallama dasu suka koma. Da suka koma basu ganinta ba sai da yamma suka zauna a gabanta dukkan su tace, "Ina jin ku." Gwaggo tayi k'arfin halin cewa, "Ina neman afuwar fulani akan abinda zai fito daga bakina. Munje gidan amma sun tabbatar mana da sai dai Fulani da kanta taje ta nemi alfarma a wajan su amma su baza su zo ba, Tuba nake ranki ya dad'e" ta fad'a da girmamawa tana kallon Mama. Mama tayi k'aramin tsaki tace, "kun fad'a musu wacece ni?." Jakadiya tace, "kwarai ranki ya dad'e." Ta daki kujera tace, "Me ake yi da neman alfarma wajan talakawa...? Mtswww basu kai matsayin na nemi alfarma a wajan su ba. Ku bani waje" ta fad'a tana yi musu alamun su tashi da hannun ta suka fita jiki na rawa ita kuma ta shiga kiran number Asad. Bata samun sa haka ta hak'ura ta ajjiye wayar a gefen ta lumshe idanu abubuwa sun taru sun cushe mata kanta da zuciyar ta. Bayan sallar i'sha suna zaune ita da Hydar da Suhaima babu mai magana cikin su sai Hydar da yake dafe kansa sabida ciwon da yake masa yana zaune amma jiri yake ji sosai kamar ma zai kifa. Mama ce ta kalle shi tace, "Hydar ya dai?." Ido ya bud'e ya kalle ta sai kuma ya kulle ya furta, "Washhhhh" sai ya kifa kansa a kan kujera yana juya kansa. Mama tace, "Subahanallah, Hydar lafiya?." Ta fad'a tana tasowa tazo inda yake ta rik'e shi taji kansa yayi mugun zafi tana jijjiga shi amma sai taga yayi luf alamun ya suma. Suhaima hankalin ta ya tashi tana kusa da Mama ta jijjiga shi Mama ma haka, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Hydar! Ka tashi dan Allah kar ciwon ka ya tashi a wannan yanayin da nake ciki. Hydar! Hydar!!" Ta fad'a tana sake girgiza shi amma babu alamun motsi a tare dashi alamun ya tafi doguwar suman da ya saba tafiya lokaci zuwa lokaci. Hawaye take yi hakan ya saka Suhaima kuka itama ta tashi ta kira number Dr Yasir ta sanar dashi halin da ake ciki ya tabbatar mata da zuwan sa, ba jimawa ya bayyana a aka kwantar da Hydar kamar ko wanne lokaci aka Jona masa abubuwan da suke taimaka masa ko yaushe nan da nan zafin kan yake raguwa. Dr Yasir ya kalli Mama da take zaune duk ta fita daga hayyacin ta yace, "Ayi hak'uri ranki ya dad'e, wannan bai kai na baya ta'azzara ba zaiyi saurin dawowa hankalin sa in sha Allah. Kuma dan Allah Mama ta daina saka damuwa a ranta sabida itama bata da lafiya." Ganin babu wanda ya iya bashi amsa cikin su sai ya tafi ya kyale su. Suna nan zaune babu mai magana Mama tunanin ta ya tafi wani wajan daban ta rasa me zatayi komai ya tsaya mata duka y'ay'an nata babu wanda yake da amfani a wannan lokacin. Kafin wani lokaci labarin rashin lafiyar Hydar ta bazu a gidan haka aka kwana Mama bacci sai b'arawo tunda ta farka da asuba bata kuma komawa ba ta shiga wajan Hydar ta ganshi bata fito ba sai da gari ya waye rana ta bayyana sosai.       Tana fitowa jakadiyar ta ta shigo ta zube tana fad'in, "Barka da safiya ranki ya dad'e, Allah ya k'ara lafiya ya bawa Yarima lafiya ya tashi k'afadun sa." A labb'an ta ta amsa da amin kafin Jakadiya tace, "Fulani Hajiya da fulani Ammi suna neman Izinin shigowa." Mamaki ya kama zuciyar Mama amma sai ta danne tace, "suzo." "An gama ranki ya dad'e" ta fad'a tana mik'ewa ta fita. Da sallama suka shigo tana zaune akan kujera ta amsa a dak'ile suka k'araso suka zauna suna binta da kallo, mamakin ramar da tayi sukeyi suka kalli juna suna girgiza kai kafin Fulani Hajiya tace, "Sai muka ji labarin rashin lafiyar Hydar, Allah ya bada lafiya." "Amin" ta amsa a tak'aice tana shan khamshi. K'aramin tsaki Ammi tayi tace, "akwai gaisuwar da za'a je Bauchi mun shirya zuwa in zaki." Mama ta kalle su tace, "Waye ya bada izinin zuwan?." Hajiya ta kalle ta tace, "Sai an bamu izinin zuwa?." Mama tace, "nice nake da ikon bada umarnin aje ko kar aje." Hajiya tace, "A matsayin ki nawa?" Ta fad'a tana yi mata wani irin kallo na rainin hankali. Mama tace, "A matsayina na wacce take jagorancin gidan nan in shugaban gidan baya nan, a sama nake da kowa ni nake da bada ikon bada umarnin ayi ko kar ayi." Fulani Hajiya ta kyalkyale da dariya ta tafa hannu tace, "Allah shugaba?, kin manta ya kike a gidan nan ne? Kin manta matar Asad itace take mulki a gidan bake ba?." Mama zatayi magana Hajiya tace, "Kinga dakata malama, meye bamu sani ba ko dan kinga munyi miki shiru hakan sai yake nufin har yanzu kina da wani matsayi a wajan sa..?. Kamar ba shine ya koro ki daga b'angaren saba lokacin da kika je, kamar ba shi bane ya kalli idanun ki yace bazai rabu da matar sa ba, kamar ba shi bane ya tafi England bai sanar dake ba?. A haka kike da ikon? Yana ina to nuna mana mu gani." Mama ranta ya b'aci matuk'a tana wuci tace, "amma duk da haka d'ana ne nice na haife shi!." "To yana ina yanzu? Duka Y'ay'a ukun da kike tak'ama dasu kina d'ga kai y'ay'an ki sune manya kina da guda uku nuna mana amfanin su a halin yanzu mu gani. D'aya yana can neman matan sa wata k'asar, d'ayan da kika fi ji dashi kuma ya zab'i matar sa akan ki, d'aya kuma gashi a kwance dashi da gawa basu da maraba nuna mana amfanin su mu gani in akwai Rabi. Ko yanzu in ina buk'atar wani abun ina da wanda zan kira ya kawo min duk da kank'antar shekarun sa ke ina nakin suke...? Kinga kenan namu da ake rainawa k'anana sune suke da amfani ba naki ba. Nasha fad'a miki lokaci kad'an ne kawai naki in ya juye sai kinyi kuka gashi kuma kina gani, kina kallo wad'annan ukun sunfi k'arfin ki wallahi duk wata tak'ama da kike yi a banza da wofi kike yinta domin a tafin hannun mu kike" ta mik'e tsaye ta gyara zaman alkyabbar ta tace, "Zamu tafi gaisuwa ko kin bada umarni ko baki bayar ba sai munje duk da daman baki isa ki hana mu ba, nasan ke baza kije ba sabida abubuwan kanki ma sunyi yawa naji labari ance harda hawan jini. In baki kwantar da hankalin ki ba nan gaba har ciwon zuciya zai saka miki domin kuwa yanzu kika fara ganin abubuwan da kika aikata suna dawowa kanki. Rukayya muje" ta fad'a tana fita Ammi tabi bayan ta ba tare da ta tofa ko wacce kalma ba amma a zuciyar ta taji dad'in wanke ta da Hajiya tayi tasss. Mama kamar an dasa ta a wajan haka ta koma idanun ta suka ciko da ruwa tayi saurin mayar dasu zuciyar ta na bugawa a guje kalaman Hajiya na dawo mata cikin zuciyar ta. Tabbas gaskiya duka su ukun basu da amfani a wajanta a yanzu dasu da babu duka d'aya tunda gashi tana buk'atar su babu kowa a kusa da ita. kai ta dafe da hannayen ta duka biyun tana jin zuciyar ta fashe jikinta na rawa tace, "Ladidi!" Ta fad'a da k'arfin gaske a guje Jakadiya ta shigo ta zube a a gabanta tace, "Gani ranki ya dad'e." "Muje gidan dana aike ku jiya" ta fad'a tana mik'ewa ta shiga d'aki jim kad'an ta fito ita da Suhaima suka fita tare jikin Ladidi sai rawa yake haka aka shiga mota suka d'auki hanyar gidan su Rauda... *Fan's ga Mama zata je neman alfarma a gidan su Rauda.....*🏃🏼‍♀️🤣 [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *061.*         Mama dafe take da kanta har akaje k'ofar gidan su Rauda bata sani ba tiririn da take ji a zuciyar ta har cikin idanun ta hakan ya haifar musu da canja launi zuwa ja suka tara ruwa kamar wacce take shirin fashewa da kuka. "Allah yaja zamanin ki mun iso" Jakadiya ta fad'a tana nunawa Mama gidan. Ta jima bata d'ago ba sai daga baya ta kalli gidan ta kalle ta kamar zatayi magana sai ta fasa ta bud'e motar ta fita dole suka biyo bayan ta kai tsaye ta nufi cikin gidan. A guje Jakadiya ta rufa mata baya ta wuce ta ta bud'e mata k'ofar gidan ta shiga ta tsaya tana k'arewa gidan kallo, d'an k'aramin tsaki taja Jakadiya tace, "Ga hanyar nan ranki ya dad'e." Gaba tayi tana binta a baya har cikin falon gidan wanda suke a zaune Rauda da Umma da Anty Ummi suna hira da dariya da alama suna cikin nishad'i. Sallamar jakadiya ya saka su suka amsa tare da kallon bakin k'ofar wacce suka gani a tsaye a wajan ya saka Rauda mik'ewa tsaye tana kallon ta itama ita take da kallo da alama ta gane ta. Ran Mama ya b'aci matuk'a ganin wacce take a gabanta zuciyar ta na zugata ta juya ta koma amma wata zuciyar na hanata aikata hakan. Shiru babu wanda yayi magana a cikin su ita bata ce ba suma basu ce Rauda ta koma ta zauna nan taji muryar Jakadiya tace, "Sannun ku mutanen gidan nan, Fulani Rabi'atu matar sarkin katagum mai murabus, mahaifiya ga sarki mai mulki na yanzu Sarki Aliyu Asad." Yaya ummi tace, "Sannun ta da zuwa, bismillah ku zauna." Jakadiya ta kalle ta tace, "Allah yaja da ranki bismillah." Har lokacin idanun Mama yana kan Rauda wacce itama a kai a kai ita take kallo ba dan wani abun ba sai kamar Asad da take gani akan fuskar ta. Ta kasa motsawa kallon su take rashin kunyar da Rauda tayi mata yana sake dawo mata cikin kanta kamar a lokacin abin yake faruwa, ji take kamar ta jawo ta ta bawa dogarai su ta jibgar ta har sai ta daina numfashi. "Baiwar Allah ki zauna mana" Umma ta fad'a tana kallon ta itama ta kalle ta kamar zatayi magana sai ta daure ta fasa ta zauna d'in jakadiya ta zauna kusa da ita a k'asa Mama ta kalle ta alamun tayi musu jawabi. Zata fara magana Suhaima ta shigo da sallama suka amsa tace, "Sannun ku." Suka amsa da yawa ta tsaya a gefe tana kallon Rauda itama ta kalle ta amma sai ta d'auke kai. Suhaima mamaki take yi sosai har ta kasa b'oyewa tace, "Nasan fuskar ki." Kallon da Mama tayi mata ya saka ta yin shiru bata cigaba da maganar ba Jakadiya tace, "Kamar yadda muka shaida muku a daren jiya shugabar mu ta aiko mu wajan ku akan ganin Baba Malam gata da kanta tazo kamar yadda kuka ce." Umma tace, "to me take so ayi mata?." Jakadiya tace, "Tana buk'atar ganin Baba malam ne bata da hanyar ganin sa cikin sauk'i amma nasan in kika shiga maganar kamar anyi an gama ne." Rauda tayi murmushi cikin rainin hankali tace, "Kenan alfarma tazo nema?." A fusace Mama ta kalle ta tace, "Baku isa na nemi alfarma a wajan ku ba, su waye ku? Me kuke dashi?." Rauda ta d'an bud'e idanun ta kana tace, "To zaku iya komawa inda kuka fito" ta fad'a tana nuna musu hanya alamun su tafi.       Jakadiya tace, "Hattara y'an mata, macece a gaban ki macen ma kuma shugabar ki. Ki iya bakin ki har ya kai ki ya baro." Rauda ta tab'e baki tace, "Shugabar ki dai, ni ga tawa shugabar nan" ta fad'a tana nuna mata Umma da take zaune. Umma tace, "Rauda meye haka ne? Kiyi shiru bana son sake jin maganar ki." Umma ta kalli Mama tace, "Baiwar Allah ki fad'i abinda kike so in da dama zamu iya taimaka miki in babu dama sai mu baki hak'uri." _inda dama zamu iya taimaka miki._ abinda ya dawowa Mama kanta kenan cikin kalaman Umma wato ita zasu taimakawa ma dan wani dalili ya kawota wajan su suke k'okarin fad'a mata maganar banza. "Nafi k'arfin taimakon ku daku da dangin ku baki daya, abinda nake so Ladidi ta fad'a muku baku ji me tace bane?." Yaya Ummi tace, "To tunda kinfi k'arfin taimakon mu dana dangin mu kiji wajan wanda basu fi k'arfi ba mana kin sa sai su taimaka miki, kinga da baki sha wahalar zuwa nan ba. Kije ki nemi wanda baki fi k'arfi ba sai mu gani." Mama tayi shiru ta rasa me ya kamata tayi dan tasan ita ta kawo kanta, a ka'ida rashin mutunci ya kamata tayi musu ta bar gidan amma kuma tana buk'atar ganin Baba malam kodan bakin da yayi yawa a kansa hakan ya tilasta mata yin shiru badan taso ba zuciyar ta nayi mata mugun suya sabida b'acin rai.   Suhaima da take gefe a tusashe tace, "Mamana tana so zata ga Baba Malam ne tana so ayi mata hanyar ganin sa dan Allah." Umma tace, "Abinda za'a ce kenan fa tun d'azu ake jan maganar. Rauda shiga ciki ki kira shi a waya ki sanar dashi abinda yace sai kizo ki fad'a mana." Rauda kallon Umma take alamun mamaki kafin tace, "Wai Umma me kike cewa ne? Kina nufin alfarmar zaki yi musu?." Umma ta zare mata ido tace, "baki ji me nace bane kike kallona?." Tashi tayi ta shiga d'akin falon ya zauna shiru babu motsin kowa duk sunyi shiru Jim kad'an Rauda ta fito ta kalle Umma tace, "Yanzu bashi da lokaci yace amma zuwa dare bayan sallar i'sha zai jira ta. Bayan sallar i'sha ki dawo sai a had'a ki da wanda zai raka ki in hakan ta samu, in bata samu ba kuma abi wani sarkin" ta fad'a tana kallon Mama da kanta yake a sama amma tana jin me take cewa. Mama ta juyo ta kalli Rauda suka had'a ido ta jijjiga kai ta had'd'iye yawu mai d'acin gaske kalaman Rauda na sukar ta a zuciyar ta amma duk da hakan babu abinda zata iya sabida halin da take ciki taimakon take so dole. Umma tace, "Anjima in Allah ya kaimu zaku iya dawowa kamar yadda yace sai Rauda ta raka ku." Jakadiya tace, "Mun gode Allah ya bar zumunci." Umma tayi murmushi tace, "kar ki damu, ai mu zuciyar mu a wanke take tas da ruwan zamzam muna rama alkhairi ga sharri komai munin sa. Haka zalika muna rama alkhairi ga cuta komai yawan ta, haka zalika muna rama alkhairi ga cin zarafi komai d'acin sa. Mutane ne mu mun kuma san me muke yi muna taimakon kowa musamnan ma wanda ya kawo kansa" ta fad'a tana wani murmushi wanda kana kallon sa kasan akwai manufa a cikin sa. Mama ta kalle ta har lokacin da murmushin akan fuskar ta sai ta sauke k'aramin numfashi ta tashi ta fita jakadiya ta rufa mata baya Suhaima ta matso cikin falon tace, "Mun gode sosai Mama, Allah ya saka da alkhairi. Amma kamar na sanki" ta fad'a tana juya kallon ta ga Rauda da take tsaye. Rauda tayi murmushi tace, "Wataƙila mai kama dani kika sani bamu tab'a had'uwa ba." Suhaima ta tab'e baki ta d'aga kafad'a tace, "Maybe, sai anjima" tana fad'a ta juya ta fita.      Rauda kamar tayi kuka ta kallo Umma tace, "Yanzu Umma wannan matar kika yiwa alfarmar ganin Baba malam? Kin manta abubuwan da suka faru ne a baya? Kin manta zagi da cin fuskar da tazo gidan nan tayi mana?, har sakawa tayi a kashe ni har cikin gidan nan amma shine zata zo da guntuwar izzar ta wai da niyar neman taimako kuma ayi mata?. Kina gani fa ko neman alfarmar ta kasa sabida a ganin ta fad'uwa ne kuma mu kamar masu jin tsoron ta sai mu taimaka mata?." Umma ta kalli Rauda zatayi Magana Yaya Ummi tace, "Nima wallahi banji dad'in hakan ba, naso koda zamu taimake ta sai ta sauke izzar da take ji da ita ta rok'i alfarma da bakin ta in mun ga dama sai mu taimake ta. Kamar masu ji tsoron ta bata fad'i abu ba sai muyi mata." Umma ta kalle su tace, "to ku dake ni akwai ku wuce haushin ku." Jin hakan sai Rauda ta zauna tace, "ba batun duka Umma kawai dai bamu ji dad'i bane ba wallahi." Umma tace, "meye danrangamin ki da ita Rauda? Ni in nice ke wallahi bazan nuna na santa bama balle na d'aga ido na kalle ta, in ma na nuna mata b'acin raina kenan na damu da d'anta ma. Ina izzar take? Ina mulkin yake? Ina sarautar take? Ina k'asaitar take? Ina ji da kan yake?. Har cikin falon nan tazo fa neman alfarma koda batayi magana ba ai munyi nasara a kanta tunda yadda muka ce sai ta tako tazo sai da tazo d'in rashin maganar ta ba wani abun bane ba. Kuma dan ka rama alkhairi ga sharri ai babban aiki kayi ko yanzu tasan muna da amfani gashi tazo neman alfarmar da ta rasa wanda zaiyi mata sai mu d'in dai da take ganin mu k'ask'antattu." Rauda ta runtse idanun ta kafin tace, "Bata da kirki matar nan Umma. Ni ba ina magana akan saki ko wani abun ba; ki duba yadda tazo ta zauna kamar falon gidan su tana wani shan khamshi ita a lallai ga gimbiya maganar ma sai dai ayi mata." Umma tayi murmushi tace, "Mun sani amma babu abinda zamu cewa d'anta, ya zama silar abubuwa da yawa cikin rayuwar mu baki d'aya, badan shi ba da yanzu muna neman gidan zama lokacin da aka zo rushe mana wannan gidan kodan shi mayi mata dan mu ba butulu bane ba." Yaya Ummi tace, "Uhummm!." Alamun maganar bata wani ratsa taba kawai babu abinda suka isa su iya ne. Umma tace, "An koya mana rama alkhairi ga wanda ya nufe ka da sharri tun a gidan mu, in badan haka ba shi kansa Baba malam din bazai saurare ta ba dan ke y'ar sace duk wanda ya tozarta ki shi ya tozarta. Ki shirya anjima suzo ki raka su." Rauda tayi wani irin juyi tace, "Umma wai da gaske ni zan rakata?" Ta fad'a tana zaro idanu waje. Umma tace, "Ke zaki rakata Rauda" ta fad'a tana shiga d'aki. Rauda ma d'akin ta wuce tana ji a ranta ko za'a yi tashin hankali bazata raka Mama wajan Baba Malam ba sai dai duk abinda zai faru ya faru kawai.         Yadda Rauda take jin zafi a ranta haka Mama ma a haka suka koma gida ji take inama tana da bindiga ta harbe kanta kawai ta huta da wulaƙancin da ta jawowa kanta, tunda suka koma take a zaune fad'i take, "Sadiya kin cuce ni, kin cuce ni Sadiya, kin yaudare ni kinyi amfani da yarda ta a gare ki kin ci amanata. Jira nake nayi setling komai zan dawo gare ki, sai kin yabawa aya zak'inta keda y'arki. Ta dalilin ki naje neman alfarma wajan k'ananu mutane, kaiiii!" Ta fad'a tana sake dafe kanta ji take kamar zai fashe sabida abinda take ji a cikin sa. In badan neman taimako ba me zai kaita wajan su? Har su nemi fad'a mata magana sannan kuma suce wai ta dawo da daddare dan kawai sun raina mata hankali. Dogon tsaki taja ta tashi da sauri ta d'auki ruwan sanyi tana sha tana zubawa jikin ta dan ji take tiririn zuciyar ta na tab'a fatar ta. D'akin da Hydar yake ta shiga ta same shi a yadda yake a kwance kamar gawa ta cize bakin ta tace, "Aliyu shine babba baya nan ko samun sa waya bana yi yanzu, Asad da nake da buri a kansa ya watsar dani an raba mu dashi dani da babu duka d'aya a wajan sa" ta matsa kusa da Hydar ta dafa kansa tace, "Hydar da yake taimaka min a ko wanne lokaci yake k'aunar ganin ya bani farin ciki shima gashi a kwance dashi da gawa duka d'aya.  Gaskiyar Hajiya ne da tace ina amfanin maza ukun da nake tak'ama dasu...? Tabbas babu amfani. Har gwara su masu mata da yawa dan da ace nice da matan dana tura su wani abun nayi wani abun, ko basuyi wani abun ba zasuyi shawara" ta fad'a hawaye na zubo mata daga idanun ta. "Allah na roƙe ka ka bawa Hydar lafiya, ka dawo min da Aliyu gida ya bar banzayen dabi'un sa yayi hankali, ka karkato da hankali Asad kaina duk abinda aka yi masa ka karya shi ya Allah ka bashi ikon dawowa gare ni. Mijina ka bashi lafiya ka tashi k'afadunsa; tabbas da yana da lafiya abubuwa baza suyi min yawa haka ba, Allah ka dube ni badan halayya ta ba" ta fad'a tana kuka sosai mai tsuma zuciya nan take zazzaɓi ya rufar mata ta lallab'a ta fita ta koma d'aki tayi lamo akan gado bata da abokin shawara a kusa balle ta fad'a masa abinda yake zuciyar ta ko zata ji dad'i. Idanun ta ta d'aga nan tayi k'aro da k'aton hoton su su uku ranar da Asad yayi shagalin nad'in sarautar sa yana tsakiya Hydar yana dama Aliyu yana haggu dukkan su sunyi murmushi ba sunyi bala'in kyau. Murmushin itama take tana hawaye zuciyar ta na azalzalzalar ta akan dole ma ta bazama nemawa y'ay'an ta magani koda zata rasa ranta.     Ana idar da sallar i'sha Mama ta saka Suhaima a gaba sai wajan mota suka shiga aka tayar da motar zuwa gidan su Rauda. Motar na fita daga gate d'in farko kafin yaje na biyun wani dogari da yake tsaye ya d'auki waya ya shiga wani k'aramin d'aki da yake wajan ya danna wayar ya saka a kunne ya d'an yi jimm kafin yace, "Ranki ya dad'e an gama komai, nan da wasu mintina motar bazata sarrafu a hannun ta ba, zata kwace ni ta daki wani abun zasu mutu dukkan su." Murmushi wacce ake yin wayar da ita tayi tace, "Godiya nake, zaka ga kud'in ka kamar yadda nace maka." Yayi murmushi yace, "Nima godiya nake ranki ya dad'e." Ya yanke wayar yana dariya yace, "Kodan wulaƙancin matar nan ai nayi abinda zata mutu, bata d'auki kowa da daraja ba gwara ta mutu ma huta da k'yara da hantara."        Su Mama kuwa k'ofar gidan su Rauda suka tsaya daidai lokacin Baba yana niyar shiga ganin mota babba kamar wannan ta tsaya ya saka shi ya tsaya shima dan Umma ta sanar dashi komai yana ganin motar abinda yazo ransa kenan,  Suhaima ce ta bud'e gaban motar ta fito ta zaga ta bud'e maman ta baya ta kalle ta tace, "Mama mun zo." Shiru Mama tayi bata amsa ba Suhaima tace, "Sai da nace Mama ki zauna baki da lafiya amma kika ki." Mama ta d'an yatsine fuska tace, "Dan Allah jeki kiyi magana dasu ta fito muje." Suhaima ta kulle motar ta kalli cikin gidan taga Baba a tsaye ta k'arasa inda yake tace, "sannu." Yace, "yauwa. Fulanin ce a mota?." Suhaima tace, "eh" ta bashi amsa a tak'aice yace, "to bara na turo Rauda" ya fad'a muryar sa har rawa take ya shiga ciki ita kuma ta tsaya tana jiran sa. Kamar an cillo shi haka suka ganshi a falon Rauda na raka'ar k'arshe a sallah ya kalli Umma yace, "Ga Fulanin tazo tana waje tana jiran Rauda a mota taje su tafi." Umma ta kalle shi tace, "Shine kake rawar jiki haka Malam? Sallah take yi to." Ya kalli Rauda da take zaman tayya yace, "kiyi ki idar kar ki barsu suna jiran ki." A wannan lokacin Rauda tayi sallama yace, "Maza tashi kije ku tafi ki raka su ki dawo." Rauda kamar zata yi kuka ta kalli Umma ta dawo da kallon ta ga Baba tace, "Baba yanzu kana goyan bayan na raka su?." Baba yace, "kamar ya ina goyan baya?, zaki tashi kije ko sai nayi ball dake?." Rauda hawaye ya sakko mata ta kalli Umma da take kallon ta itama tace, "Umma bakwa jin tsoro in na bisu su kaini wani wajan da zasu kashe ni? Kun manta matar nan bata sona meyasa zaku ce na bisu?." Umma zatayi magana Baba yace, "Tashi ki wuce." Babu yadda ta iya tana hawaye ta fita da hijjabin da tayi sallah ta fita zuwa k'ofar gidan Suhaima na ganin ta sai tayi murmushi ta wuce gaban motar ta shiga ta lek'o ta taga tace, "Shigo nan." Rauda jikin ta a sanyaye ta share idanun ta ta isa gaban motar ta shiga suka d'auki hanya. Tafiya sukayi mai d'an nisa kafin su iso unguwar kasancewar ta shiru babu kowa sai haske wani b'angaren wani b'angaren kuma babu, suna isa k'ofar gidan suka ga akasin haka domin akwai mutane har lokacin ga wajan a cike dam Suhaima ta faka Rauda ta kalle ta tace, "Ina zuwa" ta fad'a tana fita ta shiga cikin gidan. Jim kad'an ta fito tana fitowa ta k'araso inda suke tace, "Kuzo muje" tana fad'a tayi gaba abinda Mama taji kamar ta jawota ta tsinka mata mari dole suka fito suka bi bayan ta baza kace Mama ta rab'i sarauta ba domin hijjabi ne a jikinta har k'asa. A k'aramin d'aki suka zauna Rauda tayi shiru kamar babu ita a wajan fuskar ta cike da b'acin rai kana kallon hakan zaka fahimta dan fuskar a d'aure take matuk'a, gyaran muryar Baba ya saka ta kalli k'ofa ya shigo ya zauna a kan kujerar da yake zama yace, "Babata ana ta saka ki aiki ko?." Murmushi tayi mai kama da yake tace, "babu komai ai Baba, bara na shiga ciki" ta fad'a tana tashi ta basu waje domin su tattauna.      Sun jima sosai har Rauda ta gaji da zaman sai daga baya aka aiko kiran ta alamun sun gama ta shiga d'akin ta samu Baba yana fad'in, "Bazan karb'i komai daga wajan ku ba, banyi dan a biya ni ba kowa yasan dan Allah nake taimakon kowa da aljihuna nake siyan ko wanne magani na kuma bayar kyauta. Nayi miki ne kodan shi shugaban namu na garin nan baza mu so rayuwar da aka jefa shi a ciki ba dole muyi iya bakin k'okarin mu wajan ganin mun taimaka ya dawo hanya ma daidaiciya duk da muma a wajan Allah muke nema." Mama tace, "Mun gode Allah ya saka da alkhairi" karon farko kenan da ta yiwa wata halitta godiya da irin wannan addu'ar. Baba yace, "babu komai ai yiwa kaine, in kika rik'e abubuwan dana baki da wanda shi za'a bashin nan da wasu kwanaki masu zuwa ko wanne irin tsafi ne zai bar jikin sa in sha Allah amma sai kin dage da addu'a sosai muma kuma zamu taya ki." Mama tace, "Amma dan Allah malam bana so mutane su san da maganar nan, amincewa dakai ya saka na kawo kuka na wajan ka in mutane suka san abinda yake faruwa ban san ya zanyi ba." Baba yayi murmushi irin na tsoffi yace, "Duk wanda yasan Baba malam yasan baya fidda sirrin wani ga wani, manyan mutane da suka fiki sunzo wajena kuma sun koma lafiya har yanzu babu wanda yasan me ya kawo su. Inda ina fitar da sirrin wani zuwa ga wani da ban kawo yanzu ba, kema da ba'ayi miki kwatance na ba." Mama tayi shiru ya kalli Rauda yace, "Babata kin kyauta abinda kikayi kar kiji a zuciyar ba'a kyauta miki ba abinda kikayi shine daidai. Ita rayuwa haka take akwai lokacin da baka so aikata abu ba In ka aikata sai ya zamar maka alkhairi, ki saka a ranki alkhairin kenan kuma ki taimaki wanda yazo inda kike." ya kalli su Mama yace, "na barku lafiya" ya fad'a yana tashi ya koma ciki suma suks mik'e hannun Mama rik'e da leda mai girma suka fita zuwa wajan mota kamar d'azu suka shiga mota suka d'auki hanya.       Tafiya suke yi shiru motar Suhaima ta d'an taka burki taji motar ta tsaya ta cigaba da tafiya ta sake taka burki ya sake tsayawa Mama tacee, "Tsayuwar meye?." Suhaima tace, "Burkin nake ji yana cizewa ne" ta cigaba da tafiya. K'atuwar mota ce tawo ta gaban su Suhaima tayi gefe mai motar ya danna horn ya gigita Suhaima tana k'okarin taka burki amma abin yaci tura hankalin Mama ya tashi ta kank'ame ledar da Baba malam ya bata tace, "Suhaima ki tsaya mana zaki kashe mu fa." Suhaima hankali tace, "Mama taki tsayawa, tak'i tsayawa wallahi." Motar ce take sake tunkaro su gashi suma tafiya suke babu sitiyarin yak'i juyawa yayi baya. Rauda ganin mutuwa kusa hankalin ta ya tashi tana kuka tace, "Mu fita a haka!." Kamar jira suke kuwa Mama ta bud'e motar duk da tafiyar da take yi ta fad'a gefe itama Suhaima tayi gefe Rauda ma ta fita ta buge da k'aton dutse a gefe hannun ta ya daki motar da take gudu akan titi ita kad'ai. Garam motar ta daki babbar motar wata motar daga bayan su a guje tayo kansu daidai saitin da Mama take  ba tare da sun farga ba, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mamaaaaaa!" Suhaima ta fad'a da k'arfin gaske cikin ihu tana yin inda Maman take a guje. *Mama ta ware fa*🤣🤣 [17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *062*          Da zafin nama Rauda ta jawo Mama da k'arfin gaske suka fad'i a k'asa motar ta wuce a guje ba tare da ta kalle su bama balle ta bada haƙuri, Suhaima ta k'araso inda suke ta d'ago Mama ta d'ago Raudan ma ta kalle ta tace, "Na gode, badan ke ba da yanzu mota tabi ta kan Mamana" ta juya ta kalli Mama tace, "Mama babu inda yake miki ciwo?." Mama kallon Rauda take yi suka had'a ido Rauda ta d'auke kai domin hannun ta zafi yake mata sosai ga kashin bayan ta da ya bugu fad'owar da tayi daga mota. Mama so take tace mata ta gode da ceton ranta da tayi amma ta gaza fad'ar hakan sai kallo kawai hannun ta k'amkame da ledar da Baba malam ya bata; ta bar wayar a cikin motar amma bata iya barin ledar ba sabida mahimmacin ta a wajan ta. Kallon motar Mama tayi ta ga gaban motar yayi kwatsa-kwatsa shi kuma mai babbar motar ya gudu ganin basu lura dashi ba. Suhaima tace, "Mama ina zamu je yanzu? Ban fito da waya ba balle na kira driver yazo ya d'auke mu, taki kin barta a ciki na tabbatar baza ta amfanu ba" ta fad'a tana dafe kanta dan itama ta bugu kanta ciwo yake sosai. Rauda da take hango gidan su tace, "Sai anjiman ku." Ganin ta fara tafiya tana rik'e bayan ta ga hannun da take yarfe shi kana gani kasan yana mata ciwo Suhaima tace, "bai kamata ki tafi ba asibiti ya kamata mu wuce a duba ki." Rauda ta kalle ta tace, "Babu komai" tana fad'ar hakan ta cigaba da tafiya. "Na gode." Ta tsinci muryar Mama a bayan ta hakan ya saka Rauda tsayawa cak ta juyo yanayin fuskar ta ya nuna tana jin ciwo a jikin ta tace, "Aikin musulmi na gari ceton rai ne ba d'aukar rai ba" tana fad'ar haka tayi gaba abinta ba tare da ta sake kallon su ba sai a lokacin take jin haushin kanta ji take ina ma ta bari motar ta markad'e ta kowa ya huta.         Mai keke napep Suhaima ta tsayar ta fad'a masa asibitin da zai kai su ta shiga tace, "Mama shigo muje." Mama ta kalle ta ta kalli napep d'in wai yau itace zata shiga keke napep lallai rayuwa ta fara canja mata baya. Babu yadda ta iya haka ta shiga suka tafi wajan Dr Yasir sukayi sa'a yana nan ya duba hannun Mama ya duba na Suhaima ma yaga duka buguwa ce ba ciwo bane ya basu magani da kansa ya d'auko su a mota zuwa gida. Duk da yanayin da Mama take ciki tana shiga b'angaren ta wajan Hydar ta shiga ta same shi yadda ta  barshi ta d'auko ruwan rubutun da malam yace a gidan shafa masa a fuska da tafin k'afa dana hannu ta shafa tana yi tana cize bakin ta sabida ciwon da jikin ta yake mata. Sai da ta tabbatar tayi komai yadda akace sannan ta shiga d'akin ta tayi wanka da ruwan zafi bayan ta shirya tana zaune a d'aki Suhaima ta shigo da sallama ta amsa ta k'araso ta zauna a k'asan ta tace, "Mama nifa tunani nake kwance min burkin mota akayi, na tura mechanic yaje a d'auke ta ya duba ta a yanzu ya tabbatar da kwance Birkin aka aka juyar da sitiyarin yadda bazai sarrafu ba." Mama tayi cak ta kalli Suhaima tace, "Kenan so akayi a kashe mu?." Suhaima ta d'aga kai mama ta sauke numfashi ta dafe fuska da duka hannayen ta biyu ita gabad'aya abubuwan nan sun fara fin k'arfin tunanin ta gab kwakwalwar ta take da daina aiki indai aka cigaba da tafiya a haka zuciyar ta ma zata iya bugawa ta mutu kowa ma ya huta Suhaima tace, "Waye zai turo a kashe ki? Su waye meye kuma dalilin su?." Shiru Mama bata amsa ba Suhaima ta kuma cewa, "Badan waccen yarinyar ba da yanzu bak'in labari ya gama karad'e masarautar nan, dole mu sake taka tsan-tsan da kowa Mama, yanzu kinga mu kad'ai ne daga ni sai ke bamu da mai taimaka mana" ta fad'a a sanyaye tana kallon Maman nata. Da hannu Mama tayi mata alama da ta bata waje ta tashi ta fita Mama ta bud'e fuskar ta tana so ta tuna waye zai bada wannan d'anyen aikin a aikata mata amma kanta ya cushe gabad'aya tama rasa wanda zaizo ranta. _Duk musulmi na gari ceton rai shine aikin sa ba d'aukar rai ba._ kalaman Rauda suka dawo mata zuciyar ta ta daki goshin ta a bayyane tace, "Kaiiii! Meyasa haka yake faruwa dani..?" Ta fad'a tana yin baya ta kwanta a kan gadon tana ji kamar tayi hauka. Kamar wacce aka yiwa allura sai kuma ta mik'e ta ta d'auki ledar da ta shigo da ita ta fita zuwa b'angaren mai martaba, yana kwance shi kad'ai idanun sa a bud'e da alama ba bacci yake ba ta d'auko maganin da aka bayar nasa tana shafawa masa tana kuka tana fad'in, "Mijina suna so su kashe ni, mijina haukata ni suke so suyi ban san me nayi musu ba. Dan Allah ka tashi ka taimaka min abubuwa sun yi min yawa suna neman fin k'arfin tunani na, kaine garkuwa ta a koda yaushe ka tashi ka taimaki matar ka mai rauni" ta fad'a tana hawaye tana zuba masa ruwan rubutun a bakin sa. Haka ta dinga soki burutsu a wajan sa kamar kanta ya kwance kafin ta koma b'angaren ta tana ji kamar ta kashe kanta ma kowa ya huta.       *☆* B'angaren Rauda lokacin da ta shiga gida dukkan su zaman jiran dawowar ta suke yi yadda ta shigo tana d'ingishi hankalin kowa sai ya tashi Umma tayo wajan ta tana fad'in, "Rauda lafiya? Meya same ki?." Rauda ta fara kuka tace, "Umma ba kun amince da ita kun barni mun fita tare ba...? Da yadda kuke zaunen nan sai dai kuji labarin mutuwa ta." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wani abun ta kuma yi miki? Ba'a son raina kika bita ba bazan ja da umarnin mahaifin ki ba Rauda ba yadda zan iya. Meya same ki?." Baba da ya shigo yace, "meya faru?."  Rauda tace, "Hatsari mukayi." "Hasbunallahu wani'imal wakil!, hatsari..? A ina?" Umma ta fad'a a gigice tana kallon ta. "A kan hanyar mu ta dawowa, motar ce tak'i tsayawa sai bud'ewa mukayi tana tafiya muka fita shine na buge da dutse a bayana" ta fad'a tana yamutsa fuska kamar zatayi kuka. Umma tace, "Wannan mata dai zuwan ta bai tab'a zamar mana alkhairi ba, tunda iyalan ta da ita kanta suka shigo rayuwar mu shikenan komai yake canjawa. Shine kuma suka barki kika tawo ko a kaiki asibiti a duba ki?. Su suna ina?." Rauda tace, "ban sani ba a wajan na barsu kawai nayi tawowa ta. Umma bayana" ta fad'a tana cize bakin ta domin ciwo yake yi mata ba kad'an ba. Rik'e ta Umma tayi tace, "Malam ya kamata muje asibiti a duba mana ita tunda su da suka fita da ita bata da matsayin da zasu kaita asibiti." Baba yayi shiru kawai baice komai ba dan yasan laifin sane da baice taje ba da hakan bata faru ba. Baba ya fita jim kad'an sai gashi ya dawo yace, "Kuzo muje." Tare suka fito wanda yake jan napep d'in Baba suka gani suka shiga zuwa asibiti na kusa, kasancewar private ne ba jama'a nan da nan aka dubata aka bata magani nasha dana shafawa dan itama buguwa ce kawai ba wani abun ba, Baba zai biya kuɗi kenan sai ga Anas a wajan ya kalli Baba yace, "Baba." Baba ya kalle shi yace, "A'a Anas." Ya duk'a ya gaishe shi kafin yace, "Waye babu lafiya a daren nan?." Baba yace, "Rauda ce ta samu k'aramin hatsari, amma Alhamdulillah komai yazo da sauk'i buguwa tayi a bayan ta kawai." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yaushe Baba?" Ya tambaya a gigice yana kallon Baba. Baba yace, "kwantar da hankalin ka, d'azu ne kuma da sauk'i dan yanzu dana biya kud'in nan ma tare zamu koma." Anas ya karb'i takardar yace, "Baba ka koma ka zauna zan gama komai." Baba yaji sanyi a ransa dan Allah ya sani baya son fitar da kud'i dan babu yadda zaiyi ne yasan shine yaja yace, "Ayi haka Anas?." Yayi murmushi kawai ya k'arasa inda ake biyan kud'in Baba kuma ya koma da baya zuciyar sa fes.       Bayan ya biya kud'in aka siyi magani Umma suka fito da Rauda Anas ya gaida Umma ta amsa Raudan ta gaishe shi ya amsa yace, "Ya jikin naki?." "Da sauk'i, maganin da suka bani nasha naji dad'in." Kallon da yake mata ya saka ta k'in had'a ido dashi murya a tausahe yace, "Sannu." A tare suka fito harabar asibitin Anas yace, "ku tsaya Umma bara na kawo motar nan." Baba yace, "Ai da adaidaita sahu muke." Anas yace, "bara na sallame shi sai mu tafi tare." K'arasawa inda motar sa take yayi ya bawa mai adaidaita sahun kud'i yace ya tafi ya shiga mota ya kawo ta inda suke tsaye Baba ya shiga gaba suka shiga baya suka tafi gida. A k'ofar gidan suka tsaya suka fito Baba yace, "Allah yayi albarka Anas, mun gode." Murmushi yayi kawai suka shiga gida yabi Rauda da kallo har ta shige ya sauke ajiyar zuciya Allah ya sani yana son Rauda da wannan tunanin ya shiga mota ya tafi. *Bayan wasu kwanaki.*         An shiga watan Ramadan an fita an shiga na sallah, tuni an saka ranar auren Rauda da Anas ya rage saura sati hud'u kacal ana ta shirye-shirye daman akwai kayan ta duk da aka siya lokacin auren ta da Asad k'arawa kawai akeyi tunda Allah ya rufa asiri yanzu. Amarya Rauda tana ta karb'ar gyara daga wajan yayyen ta kai da ka ganta kasan ta kusa zama amarya khamshin da yake fita a jikinta kad'ai zai tabbatar da hakan. A cikin satin za'a kawo lefe can gidan su angon ma shirye-shirye ake sosai bikin Babban d'a ba wasa bane. A bangaren gidan sarauta babu abinda ya canja anyi shagalin sallah yadda ya kamata mai martaba sarki Asad yayi hawan sallah fiye da wanda akayi a baya, yasha ado ya kashe kud'i dan dawakin da aka hau ma daga Germany aka zo dasu. Mama har lokacin bata kai matsayin da Asad zai zo inda take ba har gwara ma yanzu ya kan lek'a wajan ta ya gaishe ta amma bata san komai ba duk abinda zai faru sai dai ta gani kawai ya faru amma bata san anyi ba. Kullum Mama cikin shan maganin hawan jini take domin ya riga yayi mata illa dole sai da suka d'orata akan magani. Mama ta rame tayi bak'i abubuwa sun tarar mata iskanci kala-kala jidda take shinfid'a mata musamman yanzu da cikin Jidda ya tasa kana iya ganin sa a cikin riga sai iskanci yayi gaba dalilin samuwar ciwon ta kenan. Hydar ya warke ya cigaba da kula da mai martaba wanda ake samun cigaba a rashin lafiyar sa dan a yanzu yana motsawa sosai sai dai baya magana har lokacin kuma baya tashi. Aliyu kuwa har lokacin babu labarin sa tun ana samun a sa waya yanzu ta kai ta kawo an daina samun sa a waya har Maman ta gaji ma ta daina gwada kiran nasa, tayi addu'a a watan azumin da ya wuce taje umra zuciyar ta tana fad'a mata Allah ya masa dukkan abinda ta rok'a sai dai ta jira sakamako. *☆☆*         "Nifa na kasa gane abubuwan nan da suke faruwa, tun kwanakin baya kace min zaka san yadda za'ayi da Asad za'a haukatar dashi ya dawo daga England lafiya lau ya cigaba da mulkin sa babu abinda ya canja har kawo yanzu saima cigaba da yake samu. Kace min bazai tab'a iya haihuwa ba yanzu ga matar sa da ciki har ya fito ana ganin sa. Abu biyu ka fad'a ka cika shine b'atar da Aliyu da kuma gurb'acewar raywuar Rabi'atu bayan wannan shiru har yanzu ni na gaji. Kaida mastar d'in kun kasa komai lokaci yana ta tafiya da zarar yarinyar nan ta haihu shikenan abu ya sake dawowa baya" Hajiya ta fad'a tana kallon waziri da yake zaune. Yace, "kwantar da hankalin ki ni kaina nasan an d'auki lokaci amma me kika ce a maganar ki? Abubuwa biyu sun tabbata sauran ma zasu tabbata ne." "Yaushe? Kusan shekara ana abu d'aya ace har yanzu an kasa cimma komai." "Zamu cimma daman dole sai munyi hak'uri, in kuka tuna waye Asad ta b'angaren addini dole sai mun sha wahala. Suhail da muka tura shi jikin sa matar Asad bata yadda dashi ba tana k'okarin raba su ne kin san yanzu sai abinda tace shine nak'asun da muka fara samu tun farko." "Batun mai martaba fa? Kace bazai tab'a warkewa ba sai gashi yanzu ana samun cigaba har abinci yana ci." Ya dafe kai yace, "Baki amince dani bane?." "Da na amince amma yanzu amincewar tawa k'asa take yi sabida ka kasa yin komai kullum sai magana, itama master planer ta kasa komai. yar ficiciya Jidda ace ta gagare ku? Wannan ai abun kunya ne." Ya sauke numfashi yace, "wallahi sai munyi galaba akan Asad, babar matsalar a nan wanda zai shiga jikin sa shi muke so ta hanyar da zamuyi amfani dashi wajan tarwatsa shi to bamu dashi." "Gagarumin aiki za'ayi masa wanda zai saka shi yaso Suhail koda baya so, itama jiddan a saka ta so shi koda bata son hakan, sannana a zubar da cikin jikin Jidda, a sake kwantar da mai martaba kar a bari ya tashi in ya tashi komai ya dawo baya." Ya mik'e yace, "Abinda ya kamata ayi kenan kuma za'ayi." Itama ta mik'e tace, "in wannan damar ta kuma cewa gaskiya na fita daga tafiyar ku, bazan sake tafiya da ku ba zanyi tafiya ta ni kad'ai kawai" tana fad'a ta fice ya bita da kallo yayi murmushi yace, "A tunanin ki zaki fita daga cikin mune kuma mu barki da rai salon ki tona masa asiri Sa'adatu...? Lallai an gaishe ki" ya fad'a yana d'aukar wayar sa shima ya fita. *Bahrain.*         Kwanakin da suka gabata yake jin son komawa gida yana shiga zuciyar sa amma bai tab'a tasiri ba. Tunda ya farka yau yake jin zuciyar sa na sassautawa a hankali a hankali yake jin tunanin Nigeria yana dawo masa cikin kansa cikin mintina da basu wuce goma ba ya tuna komai, ya dafe kansa ya runtse ido yace, "me nake yi a nan ne? Ina mulki na? Kenan yana hannun su? Daman cin amanata suke yi...?" Ya fad'a yana tashi zunbur yana kalle-kalle. Jikin sane yake rawa tunawa da abubuwan da suka faru yayi k'wafa gano wanda suka yi masa wannan abun ya fara shirye-shiryen baro Bahrain ya dawo Nigeria a ranar. Sai da ya had'a kaya kaf sannan ya fita ya yanki ticket akayi sa'a ya samu jirgin da zai dawo Nigeria a ranar k'arfe goma na daren can jirgin sa ya taso zuwa Nigeria. *☆☆☆*         Ji yayi kansa yayi mugun sarawa lokaci d'aya ya dafe kai ya tashi zaune ya kalli Jidda da take gefen sa tana bacci ya tashi ya fito zuwa falo yana jin jinin jikin sa ana tafasa masa shi. Ji yake kansa yana juyawa hakan ya saka shi tsayawa gaban taga ya yaye labulen yana kallon k'asan gidan da haske ya haske ko ina ga bishiyu da suke kad'awa amma babu kowa sai maguna da suke yawo. Numfashi ya furzar zuciyar sa na bugawa da sauri jin sa yake kamar bashi ba sannan kuma ji yake kamar akwai abinda yake shirin faruwa dashi a b'oye ko a bayyane. labb'a ya taune ya kalli agogon bango falon yaga k'arfe uku na dare ya sauke numfashi ya shafa fuskar sa ya saki labulen ya koma kan kujera ya zauna tare da dafe kansa. Ji yake kamar ya jawo safiya haka yake ji gabad'aya hankalin sa ya gama tashi da ya rufe ido abinda ya jima da mantawa shi yake hangowa ya k'agara gari ya waye yaje ga abinda zuciyar sa take hasko masa a cikin daren, numfashi ya fesar ya kwanta da baya ya kulle idanun sa sai kuma ya mik'e zubur ya shiga d'aki jim kad'an ya fito ya hau carpet ya tayar da sallah.         *☆☆☆* Washe gari.             "Umma! Umma!! Kin san me?" Rauda ta fad'a tana shigowa d'akin ta da farin ciki akan fuskar ta. Umma tace, "Sai kin fad'a zan sani." Rauda tace, "Anty Ramla ce tayi min waya matar Dr nan da ya taimaka min har na raka su wajan Baba malam....." Umma tace, "na gane ta, meya faru?." "Umma yanzu take fad'a min tana da ciki na wata biyu, Umma sai kuka take tana gode min kamar nice na bata maganin." Umma taji dad'i a zuciyar tace, "Kai amma na taya ta murna sosai, Allah ya iganta yasa na gari ne, yasa kuma shine silar bud'ewar haihuwar ta." Rauda tace, "Amin Umma. Tace da zasu shigo Nigeria dole su koma suyi masa godiya sun jima suna shan magani amma babu wanda yayi musu sai na Baba, tace nace miki ta gode Allah yasa da gidan aljanna. Umma baki ji bafa yadda ta gigice kamar wacce aka bawa aljanna." Umma tace, "Amin. Shi Yaya Malam ai bashi ne ya bata ciki ba Allah ne, kawai ya taimaka mata ne cikin Ilimin da Allah ya bashi kuma akayi sa'a aka samu waraka. Murna kuma dole tayi murna ai Rauda, Allah kad'ai yasan tashin hankalin da take fuskanta a wajan dangin mijin ta dalilin rashin haihuwar nan, shi kansa mijin da an cigaba da tafiya a haka tabbas aure zai k'ara a hakan ma yayi mata adalci sosai." Rauda tace, "haka ne Umma, Baki ji yadda naji dad'i ba wallahi kamar nice." Umma tayi dariya kawai bata ce komai ba Rauda ta mik'e tace, "Zan tafi gidan Yaya Ummi d'in, ina sak'on da kika ce?." Umma tace, "gashi can a leda ki kai mata" Rauda ta k'arasa ta d'auka sannan ta fita. Shiryawa tayi cikin doguwar rigar da aka siya mata a Cairo, tunda suka dawo bata sake kallon kayan ba amma yau taji tana son sakawa ta saka wacce ta saka a can ranar da suka ci uwar soyayya ita da Asad. Tsaf ta shirya tayi mata kyau ta tsaya tana kallon kanta sai ta shafa cikin ta ta tuno yadda ya rik'e ta gam waka na tashi kad'an-kad'an. Saurin kawar da tunanin tayi taja tsaki ta d'auki waya da sak'on Umman ta shiga wajan Umma tayi mata sallama ta fita. Tana tsaye a kan titi ga rana babu abinda duk ta gaji ji take ma kamar ta koma gida taga mota ta tsaya a gabanta, sauke glass akayi ta kalli na ciki sai tayi murmushi yace, "ki shigo rana." Ba musu ta shiga gaban motar yaja suka fara tafiya ya kalle ta yace, "Ina amarya ta zata je haka ta tsaya rana tana dukar min ita?" Ya fad'a cikin kalar tausayi yana kallon ta. Murmushi tayi kad'an tace, "Zanje gidan Yaya Ummi ne fa, tun jiya take kirana." "Shine ko ayi min waya nazo nayi rakiya aka tsaya rana dan kawai ta saka min mata tayi ciwon kai ko?." Bata ce komai ba sai murmushi ya kalle ta yace, "kinyi kyau matata, ashe haka Abaya take miki kyau? Lallai dole a k'aro miki su a zuba a lefen ki." Had'a ido sukayi nan take sai gaban ta ya fad'i ta sauke ido k'asa tace, "Kaima kayi kyau sosai." Sai yayi y'ar dariya yace, "Ina kyaun a nan? Kina ganin duk nayi bak'i sabida zarga-zargar auro ki..? Sai yanzu na tabbatar auren matar manya yana da wahala sai ka jure, ki duba yadda na koma fa yanzu haka ma cafe zan wuce zasu buga min iv." "Wai matar manya, kodai mijin manya?." Ya kalle ta yace, "ni awa? Matar manya dai my love." "Har zaka buga Invitation? Ai yayi wuri naga." Ya wara ido kad'an yace, "Waye ya fad'a miki yayi wuri? Kin san irin adadin mutanen da zan gayyato ne..? Tabd'ijam ai in ban fara rabawa yanzu zan manta da abokaina da yawan gaske." Ta girgiza kai tace, "in ka raba yanzu su kuma zasu manta ba dan yayi wuri sosai." "In sun manta su suka jiyo babu wanda zai min k'orafin ban gayyace shi ba. Shima kuma nasa yazo banje ba." Tayi dariya kad'an ya kalle ta yace, "Rauda Allah ya sani na k'agu na mallake ki matsayin matata, gani nake sati hud'u yak'i zuwa dan yaga ina so yak'i yayi sauri. Sai zuciya take bani kamar akwai wata katanga da zata sake shigowa tsakanina dake shiyasa kawai nake so ayi a wuce wajan." Tayi murmushi tace, "babu wannan katangar in sha Allah, bata da gurbi a tsakiyar mu." Yayi murmushi ya dafe zuciyar sa yace, "Har naji dad'i wallahi, shiyasa akace kalma d'aya ta matar ka ta isa ta kwantar maka da hankali. Ina sonki matata." "Nima ina son ka mijina." Yayi murmushi ya kalle ta tace, "ka kalli gaban ka fa." Ya kalli glass d'in motar yace, "Ina ma kin zama mallaki na kika furta wannan kalmar, da babu abinda zai hana ban rungume ki a jikina ba My love" ya furta muryar sa a sanyaye yana kallon ta ta kasan idanun sa. Bata amsa ba daman yasan bazata amsa ba sau da dama in irin maganar nan ta fad'o tsakanin su bata bashi amsa har mamaki yake domin yasan yadda yawancin zawarawan yanzu suka lalace amma ita ba haka take ba dalilin da yake k'ara masa k'aunar ta kenan. "Kinyi shiru." Ta kalle shi tace, "to me zance?." Sai yayi murmushi jin me tace ya kai hannun sa ya rik'e hannunta zata kwace yace, "Rana ta farko dan Allah, ki bani dama na roƙi hannun ki kawai." Ta rausayar da kai tace, "Amma kasan babu kyau ko?." "Na sani My love, na kasa sarrafa kaina ne ina so naji dumin jikin ki a fatar jikina, ki bani wannan damar kawai dan Allah." Shiru tayi amma sai yaga ta d'aure fuska hakan ya saka shi ya saki hannun nata yace, "kiyi hak'uri." Bata amsa ba tana kallon titi har suka k'araso k'ofar gidan Yaya Ummi ya kalle ta yaga tana k'okarin bud'e motar sai ya saka mata lock ta juyo zatayi magana kenan taji saukar bakin sa a kumatun ta yayi mata kiss. Runtse ido tayi kafin tayi magana kuma ya rik'e hannunta gam yana kallon idanun ta yace, "na kasa jurewa ne My love, ina kasa sarrafa kaina in muna tare daurewa kawai nakeyi yau bazan iya ba ki bani dama na rungume ki dan Allah." Lallai ma ya raina mata wayo wato ta bashi dama ya rungume ta bayan ya rik'e mata hannu ta nuna bata ji dad'i ba shine zai k'ara gaba, zatayi magana yace, "Sau d'aya tak my love, sau d'aya kawai daga yau bazan sake ba sai kin zama mallakina." Kafin ta bashi amsa ma ya matso kusa da ita sosai ya jawo ta jikin sa kanta ya kwanta a k'irjin sa ya rik'e ta gam yana sauke numfashi a hankali. "Kar ki rabu dani my love, sonki zai iya yi min babbar illa. Ki zauna tare dani har abada, Ina sonki ina qaunar ki" ya furta har lokacin tana jikin sa idanun sa a lumshe.  Jin tana k'ok'arin kwacewa ya saka ya sake ta suka had'a ido ta sakar masa muguwar harara yayi murmushi ya danna lock d'in motar ta bud'e zata fita yace, "zan dawo na d'auke ki." Bata bashi amsa ba ta wuce ta barshi yana kallon ta har ta shiga gidan yayi murmushi ya kunna motar yaja yana jin nishad'i a zuciyar sa.         A zaune ta samu Yaya Ummi tana kallo ta shiga da sallama ta amsa tana fad'in, "Ga amarya, ga amarya." Dariya Rauda tayi kad'an ta zauna tace, "Yunwa fa nake ji." Tace, "to acici, sai kije ki zubo ai." Ba musu ta ajjiye ledar da mayafi ta fita ta shiga kitchen ta debo shinkafa da wake ta dawo ta zauna tana ci. Yaya Ummi tace, "Yarinyar nan kyau kike k'arawa wallahi, Anas zai more aure." "Kuma shine ya kawo ni fa." "Lallai, amarya ta ango yana ji dake sosai, gaskiya kinyi dacen me k'aunar ki tun baki wayewar haka ba." Yaya Ummi ta d'auki sak'on Umman ta bud'e kafin ta tashi ta d'auko wata leda ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "ajjiye abincin ga kaza nan ki cinye ta tassss." Rauda jin ance kaza ta ajjiye tace, "Yaya meyasa baki fad'a min ba kika bari na fara cika cikina da shinkafa?" ta fad'a tana fara cin kaza ta lumshe ido tace, "Dad'i na da Yayata ta iya dahuwar kaza." Tsaki tayi tana kallon ta tana ji kafin taga ga ajjiye tace, "na k'oshi wallahi." Yaya ummi tace, "Sai kin cinye tass Rauda dan ke aka yita ta gyaran amarya, maza daure ki cinye ki shanye romon." "Wallahi Yaya cikina ne zai fashe na kuma ci na k'oshi, sai dai anjima." Yaya tace, "to anjiman kya shanye. Yanzu kora da wannan ruwan in kin gama ga zuma nan ki sha koda cokali biyu ne." Daman tana buk'atar ruwan tasha ruwan zuma kuma abar kwadiyi ce tana ta lasa suna hira kafin ta ajjiye ta had'a mata a leda tace, "in kinje gida sai ki dinga sha, amma ko bari sai nan da kwana uku sai ki kuma sha kar yayi miki yawa. Kina shan kaninfarin dai ko?." Rauda tace, "eh." "Yauwa maganin sanyi ne kar kiyi sake." "To Yaya. Ni na gaji wallahi baku da hira yanzu sai ta wad'annan abubuwan da kuke d'irka min keda su Yaya Shamsiyya, dan Allah muyi wata hirar na gaji da wannan." Yaya Ummi tayi dariya tace, "to aure na biyu ne Rauda dole mu dage, in kika tuna auren ki na farko ai ba'a baki wasu abubuwan ba sabida lokacin budurwa ce ke in aka baki da yawa zaki cutu ne sosai. Allah ya isan mu ma da wancan ne ya sami budurcin ki a banza ina ma Anas din ne ya mallaka tunda shine mai sonki da kin sha qauna." "Hmmm!" Rauda tace kawai bata ce komai ba kafin su fara wata hirar su bar wannan. Bayan la'asar Rauda ta baro gidanta da bayan ta cinye kaza tass dak'yar take takawa dan bata d'auko sak'on nata bama tace ta kawo mata baza ta iya rik'ewa ba ta k'oshi. Tafiya take sai take ji kamar ana kallon ta ta juya sai taga babu kowa ta cigana da tafiya har tazo titin da ba'a samun jama'a sosai. Bak'ar mota ce ta tsaya a gaban ta har ga Allah ta d'auka Anas ne duk da taji dad'in ganin sa sabida wajan babu mutane amma sai ta basar ta kawar da kanta gefe sabida laifin da yayi mata, wuƙa taji an saka mata a baya ance, "kina yin ihu sai na soka miki ita a baya, shiga mota muje." Jikin Rauda ya hau rawa taga an bud'e bayan mota dole ta shiga a firgice a gigice aka ja motar da k'arfin gaske....... *Aliyu ya dawo, Asad yana k'ok'arin dawowa daidai, An sace Rauda, wacece master planer...?*🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ Zan iya cewa yanzu aka fara fa🤣🤣 [17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *063* Yadda suke kwarara gudu a kan titin hakan zai baka tabbacin basu da gaskiya Rauda na zaune tayi tsuru tana kuka gaban ta sai fad'uwa yake yi tsoro ya gama damalmale mata zuciya ta tabbatar sace ta akayi shikenan ta daina ganin Umman ta. Tuna hakan sai ya sake Sakata kuka hankalin ta ya tashi sosai cikin k'arfin hali tace, "Su waye ku? Meyasa kuka d'auko ni? Ina zaku...." duf tayi nuna mata wuƙa da na gefen ta yayi ta had'd'iye yawu ta sake fashewa da kuka. Basu jima sosai suna tafiya ba suka iso k'aton gida mai bak'in gate tafkeke suka danna horn da k'arfi aka bud'e musu gate d'in suma jefa motar cikin gidan suka faka suka fita aka bud'e mata wanda yake kusa da ita yace, "fito." Cikin kuka tace, "Bazan fito ba sai dai ka kashe ni." Cikin tsawa yace, "ki fito nace!." Ta sake cewa, "Sai dai ka kashe ni amma bazan fito ba." Wuƙa ya nuna mata yace, "in baki fito ba zan farka hanjin cikin ki yanzu." "In ka farka ka yanka ka soya kaci amma wallahi bazan fito ba." Hannu yasa zai finciko ta wanda yake bayan sa yace, "Kaii! Dakata mana." Juyowa yayi yana kallon wanda yake maganar yace, "kana jin abinda take cewa? Wai bazata fito ba." "To shine zaka saka hannu ka d'auko ta? Kai kasan wacece ita kake k'okarin yin wannan gangancin...? Wallahi hakan ta faru ka tabbatar ranka sai yayi mugun b'aci" ya kalli Rauda yace, "Dan Allah ki fito ranki ya dad'e baza mu cutar dake ba." Rauda tace, "Bazan fito ba!, bazan fito ba!" ta fad'a tana curewa a waje d'aya tana fashewa da kuka. Sake tausasa murya yayi yace, "Dan Allah ki daure ki fito wallahi baza mu cutar dake ba, ki amince damu bamu kawo ki nan da mu cutar dake ba." Bata kula su ba sai kukan da take yi sosai domin bazata fito ba sai dai duk abinda ya zasuyi mata suyi mata, shiru taji ba wanda ya kuma yi mata magana ta d'ago taga duk basa wajan ta juya taga babu kowa sai ita kawai a zaune a motar tsoro ya mamaye mata zuciya ta sake curewa a waje d'aya tana sake fashewa da kuka. K'ofar da take gefen ta taji an bud'e kafin ta kula da waye ko wace taji anyi sama da ita ta kurma ihu tana wuntsila k'afa hakan bai saka an ajjiye ta ba har cikin k'aton falo aka ajjiye ta akan carpet. Yunk'urawa tayi zata zura a guje taji an rik'e hannunta cikin kuka tace, "Dan Allah kayi hak'uri ka mayar dani gida me nayi maka aka kawo ni nan?." Juyowa yayi ya kalle ta amma bata gane waye ba domin gabad'aya fuskar a rufe take ya saka face mask kuma ya saka glass ga picap a kansa hakan ya saka bata gane shi ba. "Dan Allah kayi hak'uri ka mayar dani gidan mu dan Allah....." ta fad'a tana zubewa a wajan tana kuka shi kuma ya zuba mata ido kawai yana kallon ta duk da tarin haushin ta da yake ji a zuciyar sa amma ganin ta ya saka yaji nishad'i a zuciyar sa sosai. "Relax!" Ya furta a hankali cikin muryar sa mai d'aukar hankali wacce bazata manta da ita ba yana kallon ta. A firgice ta d'ago da idanun ta da suke jik'e da hawaye tana kallon sa jin muryar wanda ya daki kunnen ta, murmushi yayi kad'an ya zare glass d'in idanun sa ya cire hular ya cillar ya cire face mask d'in yana kallon idanun ta. Idanu ta zaro waje ta mik'e tsaye tana kallon sa shima ita d'in yake kallo fuskar sa tamke babu alamun walwala a kanta. Bakin ta rawa yake yi tana so tayi magana amma ta kasa sai kallon sa da take yi tana kifta ido cikin mamaki da tsoron da ya mamaye mata zuciya, kafin tayi magana yace, "Surprise." Kanta ta daka ta runste ido ta sake bud'ewa tana kallon sa ta tabbatar shi d'in ne a gaban ta ba wani ba. Fuskar sa a tamke yake binta da kallon sai yaga itama ta juya fuskar ta daga ta tsoro ta koma ta zallar rashin kunya tace, "Meye dalilin ka na kawo ni nan?." Wara idanu yayi yana girgiza kai jin tama raina masa hankali shi zata kalla ta yiwa wannan tambayar dan taga makwancin sa. Banza yayi mata ya samu waje ya zauna ya binta da ido itama shi take kallo tace, "Magana nake maka fa malam, meyasa aka akwo ni nan..? Me kake nufi dani eyeeee?." Kai yake girgizawa yana kallon ta cikin mamaki sai ya cize bakin sa ya murza idanun sa ya shafa sajen fuskar sa har lokacin bai daina kallon ta ba. "Mtswww in baza kayi magana ba ni bazan iya jira ba domin bani da lokacin ka ko kad'an ina da abin yi" ta fad'a tana juyawa zata fita taji muryar sa yace, "kar ki sake ki motsa daga nan." Juyowa tayi ta galla masa harara tace, "in nak'i fa akwai abinda zakayi min ne?." Kai ya girgiza dan shi mamaki ma take bashi ya kwantar da kansa a kan kujerar yace, "Okay, kiyi u shall see." Tsaki ta kuma yi ta k'arasa wajan k'ofar ta murd'a amma tak'i bud'ewa ta jijjiga duk da haka bata buɗe ba ta dawo da baya ta kalle shi tace, "Ka buɗe min k'ofa ina da abinyi, banga dalilin da zai saka ka kawo ni nan ka ajjiye kamar wata baiwar ka ba." Bai kula ta ba kamar bada shi take maganar ba ta sake zuwa wuya a fusace tace, "Asad!." Yadda ya d'ago idanun sa sai da gaban ta ya fad'i da gira ya amsa mata ta daure tace, "Ka bud'e min k'ofa na tafi gidan mu." Tab'e baki yayi ya d'auke kansa ya d'auki wayar sa ya fara dannawa kamar ba dashi take magana ba. Takaici ya cika mata zuciya ji take kamar ta shak'e shi ya mutu sabida bala'in haushin sa take ji ba d'an kad'an ba, kai ta juyar domin ko zama baza tayi ba dole ya buɗe mata k'ofa ta fita dan bata ga abinda zata zauna tayi masa ba. "Waye Anas?." Tambayar da taji kenan ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba ta sake banka masa harara tace, "Ina ruwan ka da sanin waye..? Haifa ta kayi ko kuwa aurena kake yi da zaka min wannan tambayar?." Sai kuma taja tsaki tace, "to sai me ma dan kaji waye..? Mijin da zan aura ne yau saura sati hud'u bikina dashi sai me? Me zakayi?." Kaf cikin kalaman ta babu abinda ya hasala shi kamar abinda tace ya d'ago a fusace ya mik'e tsaye ya matso kusa da ita tana ja baya yana sake matsowa tana sake yin baya har taje jikin k'ofa ya saka hannu ya tare ta yana kallon idanun ta da nasa idanun da suke waje suka fara canja launi zuwa ja sabida b'acin ran maganar ta. "Are mad?" Abinda ya iya furtawa kenan a zahiri kuma ba shine a zuciyar sa ba dogon jawabi yake so yayi mata amma babu wannan damar. Tace, "kaga ni ka barni nayi tafiya ta bana son wannan abin da kake min, meye had'in ka dani da zaka dinga min wannan kallon dan nace wanda zan aura ne?." Hannu ya saka ya murd'e mata lip d'in ta na k'asa tayi k'ara amma duk da hakan bai saki ba sai da yaga tana kuka sannan ya saki ya nuna ta da yatsa yace, "meya shiga kanki? Kin manta wacece ke?." Tana kuka tace, "Eh na manta, muje a na manta d'in ina ruwan ka dani dan Allah?. Babu komai a tsakaninmu meyasa zaka kawo ni nan?." _babu komai a tsakaninmu_ ya maimata a zuciyar sa ya kalle ta a zuciyar sa yace, 'Wannan yarinyar kodai tayi loosing memory ne ban sani ba? Tana cewa babu komai a tsakaninmu, babu komai fa me take nufi?' Kallon ta ya kuma yi yace, "What do u mean?." A fusace tace, "ka fini sanin me nake nufi, kafi kowa sanin abinda nake nufi meyasa kake min haka? Dan kawai kana da mulki da kud'i shikenan na zama sharar ka?." "Oh god!" Ya furta yana dafe kansa jin kansa yana sarawa wani abu yana masa yawo zir zir a jikinsa yana zaga ko ina a jikin sa tsigar jikin sa tana tashi kofofin gashin jikinsa suna buɗewa tana sake k'ara masa tashin hankali fiye dana baya. Shiru ya ratsa falon sai kukan ta da yake tashi ya d'ago ya sake kallon ta zaiyi magana sai ya fasa ya sake runtse idanun sa na wani lokaci kafin ya kalle ta yace, "meyasa kike magana irin haka? Bana son abinda kike cewa in wasa ne ki bari" ya fad'a cikin muryar sa ta ko yaushe maganar na fita a rabe. Rauda ta sake fusata tace, "me kake so nace maka ne dan Allah? Wanne abu zan fad'a ka fahimta ne?. Ka fini sanin duk abinda ya faru meyasa kake min haka ne wai dan Allah?" Sai hawaye sharrr suka sakko mata daga idanun ta. Hannu ya saka yana goge mata idanun nata yana girgiza mata kai ya rik'e hannunta ta ya had'd'iye saliva yace, "Nasan na cutar dake amma forgive me dan Allah, kin san komai meyasa kike min magana haka?" Ya fad'a yana kallon idanun ta itama nasa take kallo. Kwace hannun ta tayi ta bar jikin k'ofar tace, "Na yafe maka kake so sai ka barni na tafi..? Shikenan na yafe maka dan Allah ka barni na tafi kar ka sake waiwayo ni daga nan har a tashi duniya." "You're my wife taya zan barki?." "Ni ba matar ka bace, bazan tab'a zama matar ka ba har abada kar ka sake gangancin fad'ar wannan kalmar. Ni matar da Anas zai aura ce amma ba taka matar ba." "Ohhhhh! u said u forgive me right?." "Na yafe maka, amma ka barni na tafi dan Allah." Runtse ido yayi ya koma ya zauna ya dafe jijiyoyin kansa da suke harbawa a hankali yana ji kan na juyawa ga yanayin jikin sa gabad'aya yana canjawa zuwa wani daban, ya jima a haka kafin ya kalle ta yace, "You know you're still my wife right?." "Oh Allah, ta yaya zan zama matar kane wai? Meyasa kake raina min hankali ne ko an fad'a maka bani da ilimi ne da zaka yi galaba a kaina? Ko an fad'a maka kud'i da mulki zasu saka ni sabawa Allah ne..?." _Me take nufi ne?'_Ya tambayi zuciyar sa yana kallon ta da yasan irin abinda zatayi masa kenan da baizo inda take ba. Hannayen ta ta had'e waje d'aya tace, "Kafi kowa sanin ni ba matar ka bace, babu aure tsakaninmu meyasa kake mayar dani yarinya k'arama ne wai?" Ta fad'a tana kama k'ugun ta tana kallon sa. Kamar zai mata magana sai ta koma maganar ya sake dafe kansa tace, "Ni ba matar ka bace bazan tab'a zama matar ka ba, ka buɗe min k'ofa na tafi kafin nayi maka abinda bazaka manta ba. Kai sarki ne bai dame ni ba abinda yake gabana kawai na sani." Yarrrrr yake ji a jikin sa yanayin sa yana canajawa zuwa wani daban in ya kalle ta sai yaga ya dinga hango ta a yanayin su na baya nan take komai ya damalmale masa ya tashi tsaye da hanzari ya jawo k'ugun ta ya had'a ta da jikin sa yana kallon fuskar ta yana sauke numfashi a hankali yana kallon ta yace, "You're my wife." "I'm not, ka sake ni bana son irin haka bana so!." Zata sake magana ya sanya bakin sa cikin nata hakan ya saka dole maganar ta koma tana k'okarin kwatar kanta amma ina yak'i ya bata damar hakan ya rik'e ta gam yana jin yadda hawaye suke sauka a idon ta amma baya tunanin zai iya k'yale ta. Tun tana k'okarin kwacewa da k'arfin ta har jikin ta yayi saki sai kuka da take yi wani yana bin tana ture shi amma ina ta kasa tsanar sa take ji na zaga ko wanne b'angaren na jijiyoyi jikinta, tsanar sa sake nink'aya take a cikin zuciyar ta da gangar jikin ta. Ziiiiii taji ya sauke zip d'in gaban rigar ta rigar ta buɗe ta gaba dogon skin tried ya bayyana a jikin ta sai bak'ar vest k'arama. Dagewa tayi da k'arfin ta zata ture shi ya farga da nufin ta ya sake matse ta har loakcin bai zame bakin sa daga cikin nata ba. Abinda ya sake tayar mata da hankali jin hannun sa a cikin vest d'in ta ya balle hook d'in brazier ta yana yawo da hannun sa a cikin rigar kukan ta ya k'aru sosai zuciyar ta neman tsari daga shaidan take yi amma ina gangar jikinta ta fara karb'ar sak'on da yake bata tana so ta kawar amma abin yaci tura bata san sun zube akan doguwar kujera ba sai ji tayi yaja zame dogon wandon jikin ta har lokacin bai cika mata baki ba ta fara wutsil-wutsil ya saka mata nauyin gabad'aya ta koma tayi laqwas tana kuka sosai. Yadda yake murza ta yana shiga jikin ta sosai ta fara fita daga hayyacin ta tana karb'ar sak'on da yake mata jikin ta ya mutu murus yasan babu abinda zata iya sai ya zame bakin sa daga cikin nata ya kai shi wuyan ta yana sakar mata kisses da ya saka ta sauke numfashi bata shirya ba ta rik'e shi gam idanun ta a kulle amma duk da haka hawaye take yi. Bata farga ba batayi zato ba batayi tsammani ba taji yana k'ok'arin kaiwa inda yake nema a lokacin ta farga amma ina ta jima da makara yadda yayi niya bazai fasa ba. Baki ta bud'e zata kurma masa ihu ya toshe mata baki da hannun sa ta fara juya kai tana kukan kurame kamar ranta zai fita. *☆* Kuka take yi sosai ta cure akan kujerar ta yafa Abaya jikin ta tana kuka har numfashin ta yana up and down sabida kuka ji take kamar ta kashe kanta kawai ta huta da bak'in cikin da take ji, kukan bak'in ciki take yi da kuka kuma mugun ciwon da take ji a gabad'aya jikinta zazzaɓi nan take ya rufe ta ruf sai jan numfashi take dak'yar ta kasa koda motsin kirki. Wanka yake yana sauke numfashi yana fidda ajiyar zuciya jin sa yake sakayau kamar ba shi ba, jinsa yake kamar wanda ya amayar da abincin da ya jima yana damun sa a cikin sa haka yake ji. A haka ya fito daga wanka ya kalli agogon d'akin yaga har lokaci sallar i'sha yayi ya saka jallabiya tunawa da ko magriba baiyi ya tayar da sallah da sauri. Yana idar da magriba yayi i'sha ya lumshe idanu yana tuno yanayin da ya tsinci kansa a d'azu sai yayi murmushi yana girgiza kai tabbas yanayi ne mai dad'in gaske duk da bai shirya ba itama haka amma yanayi ne wanda bai tab'a tsintar kansa a cikin sa ba, yanayi ne da yake ji a take zai iya koma masa indai zai samu abinda ya samu a dazun. Mik'ewa yayi ya fito yana murmushi k'aunar ta yake ji sosai tana sake ratsa zuciyar sa yana fitowa ya ga ta mayar da kayan ta da alama ko wankan ma batayi ba yana fito ta kalle shi tana kuka jiri yana d'aukar ta tace, "Na tsane ka! Bana sonka bana son mai sonka ko waye!. Ban tab'a yin dana sanin sanin ka a rayuwata ba sai yau, ban tab'a tsanar kaina ba sai yau, ban tab'a jin duniya tayi min zafi ba sai yau. Me nayi maka kayi min wannan hukuncin..? Me na aikata maka bayan duk tarin abinda kayi min ni ban rama ba sai kaii?. Wallahil azimi na tsane ka bana sonka da za'a bani wuk'a yanzu babu abinda zai hana ban kashe ka ba. Ka saka na aikata sab'on Allah wallahi tunda nake ban tab'a Zina ba sai yau, meyasa zakayi min haka....meyasa ka zab'i ka cutar da rayuwa duk abubuwan da kayi min a baya....? Me nayi maka..?" Ta k'arasa fad'a tana kuka sosai tana ji kamar ta had'd'iye zuciya ta mutu. "Zina!" Ya maimaita a bayyana yana kallon ta da mamaki ganin yadda take kuka sosai da alama har zuciya maganar take fitowa. Ya matso kusa da ita ya rik'e kafad'ar ta yace, "What are you saying Rauda...? Kin san mayar dake bayan na sake ki a Cairo. Why kike kiran kasancewar mu da zina?." Ba tare da zato ba yaji ta d'auke shi da zazzafan mari ta ja baya ta nuna shi da yatsa idanun ta sunyi mugun ja baya da idanun ta jajaye tace, "Kar ka sake tab'a ni wallahi na tsane ka, ka matso kusa dani zan iya illata ka zan iya kashe ka Asad bana qaunar ka. Kun cika son kanku da yawa ku masu kud'i da mulki kanku kawai kuka sani bakwa duba lahira balle mu talakawan ku, kana yin abu kamar bakai ba. Allah ya isa tsakanina dakai wallahi bazan tab'a yafe maka ba har Allah ya tashi duniya" ta fad'a tana yin baya zata fad'i shi kam kallonta yake har lokacin saukar yatsun ta yake ji a fuskar sa abu kamar a mafarki. "Ka sani ko hakkina ne kawai ya rage in na yafe maka zaka shiga aljanna wallahi sai dai a kaita wuta, nayi danasanin sanin ka rayuwata, meyasa ka shigo rayuwata bayan kasan ka shigo ne dan ka tarwatsa ta?. Me nayi maka kayi min wannan hukuncin.....?" Ta fad'a tana dafa bango tana sake fashewa da kuka jiri yana sake d'aukar ta. Ya kasa koda motsin kirki kallon ta kawai yake rana ta farko da wata ta mare shi bayan marin da Mama tayi masa a kanta, nan take zuciyar sa ta harzuk'a yana jin d'aci a zuciyar sa yana binta da kallon da yake d'auke da ma'anoni kala-kala idanun sa sun juya sunyi jajur sabida b'acin rai. Kanta a kife a bango tana kuka mai tsuma zuciya kanta yana ciwo ga jirin da yake d'aukar ta tana jan numfashi dak'yar, d'ago kanta tayi ta sunkuya ta d'auki mayafin ta ta yafa bata sake kallon sa ba ta k'arasa wajan k'ofa kamar wasa tana murd'awa ta jita a buɗe ta juyo ta kalle shi tace, "Mazinaci bai dace da zama shugaban Al'umma ba, mai son kai bai dace da zama sarkin al'umma ba, banga nagarta da ake fad'a ba a tare dakai, banga ilmin da ake fad'a ba a tare dakai. Tirrr da masu hali irin naka ku kuma jira sakamakon ku tun a duniya Allah sai ya lalata rayuwar ku" ta share hawayen ta tace, "Bani da kud'in da zanyi Shari'a dakai a duniya amma ina da k'arfin guiwar yi dakai a lahira, sai ka fad'awa wanda ya halicce mu dalilin keta min haddi da kayi, wallahi sai Allah yayi mana hisabi nida kai Asad!. Na tsane ka tsana mai muni!" Tana gama fad'a masa hakan ta fita jiri yana d'aukar ta. A bud'e taga gate d'in ta fita cikin ikon Allah taga mai adaidaita sahu ta fad'a ciki jikin ta na rawa sabida zazzaɓin da yake jikinta suka tafi tana bin gidan da kallo tana hawaye tana ji a zuciyar ta har a tashi duniya bazata manta da gidan da ta aikata zina ba. *Tofa wai Asad ne ko kuwa Aliyu ne?.*🤔 [17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *064.*             Kamar an dasa shi a wajan haka yake a tsaye k'am har ta fita bai motsa ba yana wajan jinin jikin sa yana tafasa kamar an kwashe shi an zuba a wuta ana dafa shi haka yake jin zafin na karad'e ilahirin jikin sa. Mazinaci! shi za'a kallah a kira da wannan sunan mai muni da rashin dad'in ji. Sai a sannan ya zauna ya hard'e hannayen sa yana kallon wani wajan daban zuciyar sa kamar ana gasa a tukubar tsire. _Kayi gangancin bari ta raina ka, in ba raini ba ita har ta isa ta kalle ka ta fad'a maka wad'annan maganganun harda marin ka..? Mama ce kawai ta tab'a marin ka shima sau d'aya ne tak kuma a kan son tane sai ita. Wacece ita me take dashi da zatayi maka wannan cin fuskar? Dan kawai kana sonta ko me?._ Zuciyar sa tace take bashi wannan labarin ya furzar da iska ya jingina da kujera yana kallon fitilun da suke saman d'akin. _Ba'a tab'a ci min fuska kamar yau ba, ban tab'a danasanin aikata abu kamar yau ba, ban tab'a jin haushin kaina kamar yau ba, ban tab'a jin haushin wata halitta kamar yadda nake jin haushin ta yau ba. Mari fa...ta kuma kira ni da mazinaci, zina abinda na tsana a rayuwata dashi zata danganta ni?. Duk matsayin da nake dashi a garin nan dama duniya baki d'aya na sauke shi na nemi yafiyar ta akan abinda ya faru duk da ba laifina bane ta sani amma shine zata yi min wannan rashin hankalin?. Allah ya sani banyi niyar mata komai ba magana kawai naso muyi but lokaci d'aya nayi losing control ya kamata ta fahimce ni tunda tasan ina sonta, Ni Asad wata mace ta mara ta kuma kirani da mazinaci....!_ A zuciyar sa yake wannan maganar yana girgiza kai alamun abun ya tab'a shi sosai ba d'an kad'an ba. _Ni ba matar ka bace, har abada bazan zama matar ka ba, babu komai a tsakaninmu._ kalaman ta suka fad'o masa a zuciyar sa ya runste ido ya dafe kansa da duka hannayen sa yana mamakin dalilin ta na furta hakan bayan tasan lokacin da ya sake ta a Cairo ya mayar da ita. Suya ransa yake masa sosai amma yasan shine ya jawo da bai d'auko tama da duk hakan bai faru ba gashi a banza a wofi tayi masa abinda har duniya ta tashi bazai manta ba, kai yake girgizawa kansa na sarawa yace, "Is okay!" Ya furta sai kuma ya kwab'e fuska kamar zaiyi kuka ya daki kujerar da yake kai yana cize baki alamun kalaman nayi masa ciwo sosai.         Bai san adadin lokacin da ya kwashe yana haka ba sai agogo ya kalla yaga dare yayi ya tashi ya shiga d'akin ba jimawa ya fito ya rufe ko ina na fuskar sa ko waye kai baza ka gane fuskar sa ba ya fita daga falon gidan ya hau mota ya bar gidan gabad'aya.         Rauda kuwa kuka take a cikin adaidaita sahun kamar wacce dangin ta kaf suka mutu a lokaci d'aya, mai napep din ma ya d'auka mutuwa akayi mata sai ta bashi tausayi yace, "Kiyi hak'uri baiwar Allah." Bata saurare ba kuka take yi suna tafiya taji yace, "Mun zo unguwar baiwar Allah." Kallon wajan tayi tace, "ga layin.....can" ta fad'a muryar ta na rawa sosai ya k'arasa da ita ta sauka yace, "ki bar kud'in, Allah ya jikan wanda ya mutu" ya fad'a yana jan napep d'in sa ya barta ita kuma ta nufi gida gaban ta yana mugun fad'uwa ko ta kan mai napep d'in ma bata bi ba. Haka take takawa kamar wacce kwai ya fashewa a jikinta ta shiga cikin gidan ta same su a tsaye sun zubawa k'ofa idanu da alama ita suke jira, ganin hakan sai gabanta ya tsananta bugawa duk suka zubo mata ido harrrr sai taji ta sare ta tsaya cak a tunanin ta in ta k'arasa kusa dasu zasu ji wata alama da zata nuna ta aikata zina a wannan daren. "Malam! Malam!! Gata ta dawo" Inna ta fad'a cikin d'aga murya sai ga Baba ya sakko daga sama, Umma binta kawai take da kallo kamar mai son gano wani abun a tare da ita sai sake ware idanunta take akan Raudan kafin tace, "Ina kika shiga Rauda? Tun bayan la'asar Ummi tace min kin tawo ina kika tsaya haka har takwas na dare?." Hawaye sharrr ta durk'usa a wajan kawai ta fashe da kuka, dukkan su sai hankalin su ya tashi Rahma tayo wajan ta a guje tana fad'in, "Anty Rauda meya same ki?." Baba ya kalle ta yace, "Ana tambayar ki inda kika tsaya kina yiwa mutane kuka..? Ina kika je har dare yayi baki dawo ba sai yanzu?." Rauda bakin ta rawa yake yi ta rasa abinda zata ce dan Allah ya sani baza ta iya fad'a musu abinda ta aikata ba koda zata mutu. Kukan ya sake tsamari Umma taja tsaki tace, "ba magana ake miki bane zaki saka mu gaba kina yiwa mutane kuka? Gidan ubanwa kika je har dare yayi haka?." "Naje...gidan.....Farida y'ar ajin mu ta islamiyya na duba Maman su, da naje sai na samu Mamanta ta rasu a lokacin da muke hira da faridan kuma mun gaisa da Maman, shine na tsaya akayi jana'iza dani sai na tawo. Umma mun gaisa fa da Maman nasu amma tana shiga d'aki sai gawar ta aka fito da ita......." ta sake rushewa da kuka kamar gaske duk sai jikin su yayi sanyi Baba ya tausasa harshe yace, "Amma meye amfanin wayar ki da bazaki kira ki sanar damu ba? Kafin nan yaushe kika fara zuwa gidan su k'awa baki fad'awa Umman ki ba?."       "Kuyi hak'uri hanya ce ta bi dani sai na shiga" ta furta tana goge idanunta. Baba ya sauke numfashi yace, "to jeki ciki Allah ya jiqan rai, amma ko dan gaba kar ki sake aikata abinda kika yi kinji ko?." Ta d'aga kai alamun to ta mik'e tana jan k'afar ta ta shiga ciki ta kulle kanta a d'aki ta cillar da mayafin jikinta ta cillar da wayar ta cire doguwar rigar ta watsar tayi zaman dirshan a k'asa ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya. Had'a kai tayi fa guiwa ta cure waje d'aya tana furta, "Ka cuce ni, ka gama da rayuwata, ban tab'a aikata sabon Allah ba sai yau, me nayi maka kayi min wannan hukuncin? Me na aikata maka ka zab'i ka lalata min rayuwa...?" Ta sake fashewa da kuka tana jin yadda zazzaɓi ya rufe jikinta gabad'aya. Tunawa da tayi bata da tsarki sannan kuma batayi sallah ba sai ta mik'e dak'yar dan gabad'aya jikinta ciwo yake mata sosai ta shiga band'aki, ruwan band'akin yayi sanyi da yawa amma bazata iya fitowa tace zata dafa ba kar su zargi wani abun haka tayi amfani dana sanyin duk da zazzaɓin da da yake jikinta. Doguwar rigar da skin tried d'in da komai da ta cire ta cure su ta saka a leda bayan ta fito ta cusa can k'arshen wardrobe dan har abada bazata sake amfani dasu ba ta tsane su, _Meye na tsanar kaya Rauda bayan fatar jikin ki da ita aka aikata zinar?._ kalaman da suka zo ranta kenan ta buga kanta a jikin kwabar tana jin zafi a zuciyar ta sanyi yana ratsa jikinta. A haka ta daure ta saka kaya ta kalli gabas da niyar tayar da sallah sai take jin kunyar mahaliccin ta zuciyar ta na rawa a haka tayi sallar magriba tayi i'sha ta tayar da shafa'i da wutri ta kwanta a kan sallayar ta cure a cikin hijjabi tana jan numfashi. Buga k'ofar ake yi ta d'ago ta kalli k'ofar ta mik'e dakyar ta k'arasa ta buɗe k'ofar Ummulkhairi tace, "Anty Umma tace kizo kici abinci." Rauda tace, "na k'oshi, ki karb'o min maganin ciwon kai" ta fad'a tana komawa ta zauna a gefen gado. Ba jimawa Ummulkhairi ta dawo da p.c.m ta bata had'e da ruwan pure water ta bata tasha ta koma kan gadon tayi lamooo hawaye na sauka ta gefen idanun ta. "Rauda!." Jin muryar Umma a kanta sai ta firgita abinka da mara gaskiya ta kalle ta tace, "Na'am." Umma tace, "meya same ki?." Rauda murya na rawa tace, "Zazzaɓi ne Umma shima kuma kukan da nayi a gidan su Farida ne." Umma ta k'arewa fuskar ta kallo sannan tace, "Kin tabbata?." Rauda ta d'aga kai alamun eh. Hannu Umma takai ta tab'a wuyan ta taji zafi sosai tace, "Jikin ki akwai zafi sosai kin sha maganin?." Ta d'aga kai alamun eh Umma tace, "dukkan mai rai mamaci ne ai nima wata rana haka za'a fitar da gawata dole kuma kiyi hak'uri." Rauda ta sunkuyar da kanta k'asa  tana jan numfashi. Umma ta sake kallon ta tace, "Amma d'azu da kika gifta ni naji sabon khamshin turare a jikin ki wanda ban sanki dashi ba, yana da khamshi luma yana da k'arfi har yanzu ina jin tashin sa a jikin ki a ina kika same shi? Ko duk a gidan mutuwar kika shafa?."       Rauda ta rud'e ta gigice ta ta mik'e zaune tana waige-waige bakin ta yana rawa gashi Umman ta zuba mata ido alamun tuhuma ita kuma alamum rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, Umma tace, "Ya naga kin rud'e kamar mara gaskiya ne?, ko wani ne ya baki turaren?." Sai Umma ta kai fuskar ta wuyan Rauda ta d'ago tace, "Akwai khamshin sa sosai a wuyan ki, waye ya baki kika saka bayan fitar ki?." Rauda ta sosa kanta idanu na zubar da kwallah murya na rawa tace, "gidan....Yaya Ummi." "Ita ya baki ki shafa?." Rauda ta d'aga kai alamun eh, Umma tace, "To yayi kyau, kwanta Allah ya k'ara lafiya. Amma ki daina kukan in kina so kanki ya daina ciwo" tana fad'a ta fice Rauda ta koma da baya ta kwanta ta sake fashewa da kuka. Bata tab'a yiwa iyayen ta k'arya gashi a akan Asad ta fara, taya baza ta tsane shi tsana ta har abada ba? Ai ya gama cutar ta sai dai Allah yayi mata sakayya ranar alqiyama. Da wannan tunanin ta kwanta lamoo tana share hawaye ciwon kan yana raguwa a hankali, smun sassaucin ciwon kan sai bacci ya kwashe ta.         *☆☆☆.*       Jidda ce zaune cikin d'akin ta waya rik'e a hannun ta fuskar ta da gwada alamun damuwa k'arara a kai tace, "Mum wallahi yau gabad'aya fa tsoro ya bani, ya canja daga daren jiya zuwa yau d'in nan, zancen da nake miki ko tun d'azu ya fita har yanzu bai dawo ba gashi dare yayi, kuma shi kad'ai ya fita dan baza ma ka gane shi ba in ka ganshi." Mum tace, "Uwar sa ta dage ai lallai sai ta dawo dashi yadda yake a baya, amma kin san me za'ayi?." Jidda tace, "A'a Mum." "Za'a sake sabunta aikin da akayi ne da alama ya fara lalacewa sai mun kuma yin sabo." "Mum kika ce za'a kasheta, ai gwara a kashe d'in kawai a huta kinga da duk ba haka ba da bata raye." "Na gwada hakan yafi sau biyar amma babu nasara, amma za'a sake gwadawa a karo na shida." "Mum nidai ayi abinda za'ayi kar a raba ni dashi." Mum tace, "karfa ki damu tunda ina raye ai zance ya k'are, zan turo Eman yanzu ta kawo miki wani magani ki tabbatar ya kwanta dake yau bayan kin sha wannan maganin zai mana amfani sosai." Jidda tace, "toh Mum zanyi." Tana fad'ar hakan ta yanke wayar Jidda ta sauke numfashi tana kallon wayar zuciyar ta a cushe, burin ta kar a raba ta da Asad gashi an d'auko hanya shiyasa duk sai ta tsorata a iya yau kawai. Suhaima da take tsaye a k'ofar d'akin Jidda taji komai hannunta toshe da bakin ta take girgiza kai ta koma da baya a guje zuwa b'angaren Mama, da bak'i ta tarar da Mama hakan ya saka ta wuce d'aki tana ta zagaye burin ta bak'in su tafi duk minti biyu sai ta lekoo falon amma suna nan. Bak'in suna tafiya Mama Jamila k'anwar Mama ta shigo Mama ta kalle ta tace, "Jamy kina son tafiyar dare ke kam." Tayi dariya ta zauna tana fad'in, "tun d'azu fa muka zo mun sauka a guest house ne mun huta sai yanzu na fito. Barka da dare Mama." Mama tace, "Barkan ki, ya hanya?." "Alhamdulillah." "Ya kika baro mutanen Kano?." "Suna lafiya Mama, ina Suhaima?." Suhaima da dama jira take ta fito a gigice tana fad'in, "Mama!." Mama ta kalle ta tace, "lafiya?." Suhaima tace, "Naje apartment d'in Jidda naji tana waya tana cewa za'a sake sabunta aiki wanda aka yiwa Yaya Asad ya fara barin jikin sa, kuma wai gwara kawai a kashe ki in ba haka ba zaki sake lalata komai. Mama ina jin muryar Mum tana cewa ta saka a kashe ki har sau biyar babu nasara." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Suka furta a tare suna mik'ewa tsaye Mama Jamila tace, "Suhaima kin tabbatar da abinda kike fad'a gaskiya ne?." Suhaima tace, "wallahi da gaske nake small Mama, abinda naji tana cewa kenan." Mama Jamila tace, "kinji ko? Na jima da sanin Sadiya da y'arta amanar ki suke ci gashi yunk'urin kashe ki ma suke yi. Yanzu mr gari ya waya Maman Suhaima?." Mama kuwa tayi cak ta kasa cewa komai jikinta yayi sanyi ta sulale ta zauna akan kujera tayi tagumi da hannun ta duka biyun ta kulle idanun ta fuskar Mum tana gilma mata. Small Mama tace, "Bafa shiru zakiyi ba mataki za'a d'auka tunda Allah ya tona mata asiri dole tayi prison." Mama dai bata iya cewa komai ba tayi shiru da alama ta rasa ma abinda zata ce small Mama ta durk'usa a kusa da ita tace, "Maman Suhaima kallona zakiyi wannan tagumin babu abinda zai haifar miki sai zallar damuwa, ki bari muje muci ubanta sannan mu saka a kulle ta bata fimu da komai ba." "Jamy komai ya faru nice na jawo, nice na jawo komai Jamy, Da ban bata k'ofa ba da duk hakan bata kasance ba. Na fifita sama ta da kowa ko ku bana d'aukar shawarar ku kamar yadda nake d'aukar tata. Duk da karfafa zumuncin mu na had'a d'ana da y'arta na tsallake duka y'ay'an ku na raba shi da wacce yake so na bashi wacce nake so. Hasbunallahu wani'imal wakil" Mama ta furta tana tashi tsaye. Small Mama tace, "Wacce yake so kika saka ya sake ta ita kuma wacce kike so yace bazai yi ba." Mama ta girgiza kai tace, "Jamy ku k'yale ta in sha Allah bazata ga fad'uwa ta ba" tana fad'a ta shiga d'aki Jamila ta bita rai a b'ace domin bata ga dalilin da zai saka a k'yale wacce take son kashe ta. Tana shiga d'aki ta biyo bayan ta tace, "Akan me za'a k'yale ta? Kenan in ta kashe ki shikenan taci riba?." Mama tace, "bamu da hujja Jamy, dan Allah ku bani waje ina so na huta." Ba musu ta fita tana k'wafa ranta duk ya b'aci matuk'a. Bayan kamar awa biyu Suhaima ta shiga wajan Mama ta ganta a zaune batayi magana ba sai ta fita zuwa  kitchen ta had'o mata shayi mai zafi dan tasan bata ci komai ba ta tawo kawo mata. Hydar ta samu a wajanta ta zauna tace, "Allah yaja da ran Mamana, baki ci komai ba tun safe ki daure kisha tea d'in nan ko zaki ji dad'i." Hydar ya karb'i cup d'in yace, "Mama dan Allah kisha." Ta yamutsa fuska tace, "Hydar bana so." "Please Mahhh!" Ya furta a sanyaye yana kallon ta ta mik'a hannu ta karb'a ta rik'e a hannunta amma bata sha ba. Shiru basuyi mata magana ba ta kafa kai a kofin tasha ta sauke sai taji yayi mata dad'i yaji kayan khamshi hakan sai ya saka tasha da yawa ta ajjiye ragowar tayi tagumi, Hydar ya cire hannun ta yace, "Dan Allah Mama." Idanun ta ya ciko da kwalla tace, "Aliyu baya nan, Asad ya guje ni sai yaga dama yake zuwa inda nake, Sadiya tana so ta kashe ni, Jidda tana yi min wulaƙancin da take so, mutanen gidan nan gabad'aya sun raina nj ya kuke so nayi?. Bani da uwa bani da uba y'an uwana suna nesa dani me kuke so nayi in ban damu ba?." Shiru sukayi ganin tana hawaye Suhaima tace, "Amma ranki ya dad'e damuwar ciwo take saka miki, likita yace damuwar da kike sakawa tayi yawa ya kamata ki rage kodan lafiyar ki." Ta sauke numfashi tace, "Nafi buk'atar mutuwa ta a yanzu." Shiru sukayi jin abinda tace ko wanne kansa a k'asa zuciyar su duka a raunane. Cikin ta taji yana juyawa sai taji tana jin amai ta yamutsa fuska tace, "Hydar bani maganin ciwon ciki a cikin drawer." Ba musu ya juya yana neman maganin yaji ihun Suhaima tana cewa, "Yaya Hydar Mama!" Ta fad'a tana yin kanta suka ga tana shak'uwa idanun ta na juyewa suna komawa farare babu alamun bak'i a cikin farin abu na fita a bakin ta kafin Hydar ya k'araso tuni Mama ta zube akan gado babu numfashi. *☆☆☆*             "Ashe zaku iya cin amanata ban sani ba?" Aliyu ya fad'a yana kallon Waziri da hajiya idanun su sunyi fik'i-fik'i alamun marasa gaskiya. Gyara tsayuwa yayi jin sun kasa magana yace, "baza kuce komai ba?." Waziri yace, "Aliyu ka saurare ni." "Kace min me?." "Abinda kake tunani sam ba haka bane ba, mu kan mu bamu san meyasa ka maqale a wata k'asar ba." Ya harde hannayen sa a k'irji yana bin su da kallo yace, "Shine baku tab'a nema na ba?." Fulani Hajiya tace, "Na kira ka bana samun ka." Yayi murmushi mai kyau ya taune lips d'in sa yana jin d'aci a zuciyar sa yana girgiza kai. "Amma yanzu tunda ka dawo zamu d'ora daga inda muka tsaya ko Fulani?" Ya fad'a yana juyawa ya kalle ta ta d'aga kai tace, "Daman mun rasa wanda zai shafawa Asad maganin da zai bar karagar nan baki d'aya tunda ka dawo mu abin murnar mune ai." "Da ban dawo bafa? In kuka yi nasarar shafa masa maganin waye zai hau karagar kenan?." Alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dasu suks kalli juna Hajiya tace, "Ai bai ma farun ba, ka daina tuna baya dan Allah muyi abinda yake gaban mu yafi mana alkhairi." "Ai bazan kuma amincewa daku ba domin dukkan ku munafukai ne, kunce min matar Asad baza tayi ciki ba sai gata da ciki har ya bayyana ko bamuyi haka daku ba?." Waziri yace, "Sammatsi aka samu ne ranka ya dad'e amma yanzu zamuyi iya bakin k'ok'arin mu koda yaron yazo duniya zamu kashe shi dan baza mu bari y'ay'an sa su Shura ba." Ya murmusa kana yace, "Ita mamana me tayi muku kuke son kashe ta?." A tare suka wara idanu suka ce, "Kisa? Mu din?." Banzan kallon da yayi musu ya saka waziri yace, "bamu tab'a k'okarin kashe Rabi'atu ba, to akan me ma zamu kasheta muda ba ita muke hari ba?." Aliyu yayi murmushi mai kyau ya d'an sosa goshin sabaice komai ba waziri yace, "Yanzu ina tare da maganin da za'a shafa masa ayi maganin matsalar mun tura Suhail amma ya kasa yin komai, kai kad'ai ne zaka kawo k'arshen matsalar nan." Aliyu ya zuba hannu a aljihu yana kallon su d'aya bayan d'aya yayi shiru baice komai ba duk suka tsargu ganin irin kallon da yake musu yana murmushi wanda yake basu tsoro dan basu san shirin sa ba sun kuma san halin sa akwai dan bazan wayo, "well, ku kawo mu gani." Waziri ya washe bakin sa ya saka hannu a aljihu ya d'auko shi a kwalba ya mik'a masa ya kalla ya kalli wazirin sannan ya karb'a Waziri yace, "Kana shafa masa wannan an tabbatar mana da awa biyu bazata cika ba zai haukace kaga shikenan babu sarauta a hannun mahaukaci." Aliyu ya jinjina kai yana girmama mugunta irin tasu amma yafi su kaifin tunani dukkan su buga su zai dinga yi kamar ball shi kad'ai yasan mai ya tsaya da kuma abinda zai aiwatar yace, "Da an shafa masa shikenan an gama ka tabbatar?." Waziri yace, "An gama na tabbatar da wannan." Aliyu ya juya ya bar wajan ya shiga mota yaja ya tafi ba tare da yace komai ba. Hajiya ta kalle shi tace, "Ni nasan za'a yi haka sai da nace ka kashe Aliyun tun ba yanzu ba kak'i, wayon jaraba ne dashi zai iya lalata mana komai, dawowar sa barazana ce ga sarautar ka domin bazai bari kayi ba sai shi." Yayi murmushi yana kallon inda Aliyu yabi yace, "Barshi ya gama yi mana wannan aikin ya shafawa Asad d'in tukunna kiga yadda zanyi dashi, ai yadda ya shafawa Asad shima haka zan saka a shafa masa an fad'a miki k'aramin kaine dani?, duk wannan marairaicewar da kika ga ina yi ina sane tarko ne. Haka na tsara ko master planer da taji wannan sai da tace tsarin yayi ko ita iya abinda zata iya kenan." Fulani tayi ajiyar zuciya tace, "Har naji dad'i domin na tsani Rabi'atu tsana maimunin gaske,  haka na tsani y'ay'anta." Yayi murmushi yace, "Yanzu aka fara wasan fa, barni dashi kawai." Aliyu da yake tafiya ya saka bt a kunnen sa yana sauraron duk abinda suke fad'a ta cikin bt d'in ya murmusa ya daki sitiyarin motar yace, "Naku wasa ne tunda na dawo komai yazo k'arshe" ya fad'a yana sake take speed d'in motar  yana k'warara gudu akan titi. *☆☆☆*            Yadda babu wanda yasan ya fita haka babu wanda yasan shine ya shigo sai masu gadin k'ofar sa yana hawa sama bai nemi Jidda ba ya shiga d'aki ya kulle kansa abubuwa sun cushe masa kansa yama rasa wanne kalar tunani zaiyi yaji fad'i. Zama yayi a gefen gado yayi tagumi yana kallon wani wajan daban yaji ana buga masa k'ofa. Yasan Jidda ce domin shi bashi da lokacin ta a halin da yake ciki yana buk'atar kebe kansa amma yasan bazata gane ba, "My king pls ka buɗe magana zamuyi." "Jidda please leave, I need rest" ya fad'a a sanyaye yana kallon k'ofar. "Pls my king magana kawai zan maka fa." K'aramin tsaki yaja daman yasan bazata tafi ba ya kwanta a kan gadon ya lumshe ido kafin ya tashi ya shiga wanka. Yana ji tana dukan k'ofar yayi banza sai da ya gama shiryawa yayi sallah sannan ya buɗe ya same ta a tsaye yana bud'ewa ta fad'a jikin sa tace, "My king nayi maka laifi ne kake share ni?."  Ji yayi tana bashi mugun haushi ya runtse ido gabad'aya baya son ganinta kwata-kwata ya dafe kai ya d'ago ta daga jikin sa ta sake komawa ya sake d'ago ta ta sake komawa ya fusata ya fincike ta yace, "I said leave....!" Ya fad'a cikin murya mai amo wacce ta saka ta gigicewa tana kallon sa idanu a waje cikin zallar mamaki da al'ajabi. [17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *065.*          Kallon sa take da mamakin da ya cika mata zuciya ganin ita yake yiwa tsawa har cikin kanta kamar zai dake ta kuma yana kallon ta, sak tayi jiki yayi sanyi ta koma da baya shi kuma ya kulle k'ofar tabi k'ofar da kallo jikin ta a mace kawai ta sauka daga saman ta fita gabad'aya daga b'angaren. Kamar zata kifa haka take tafiya bata lura ma da jakadiyar ta ba kawai tafiya take tana shiga d'aki ta kulle kanta hannu na rawa take neman layin Mum amma bata d'auka ba ta sake kira bata d'auka ba ta ajjiye wayar tana kallon mudubi gabanta yana fad'uwa. Hankalin ta mugun tashi yayi ta rasa inda zata saka ranta zuciyar ta na bugawa ta dafe kai da hannun biyu tace, "Na shiga uku, me yake shirin faruwa ne? Yau My king shine ne yake min tsawa haka?" Ta fad'a tana zagaye a d'akin hankalin ta ya tashi sosai ji take kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan su. *☆☆☆*         "Dr ka saka mu a gaba baka ce mana komai ba, meya samu Mama wai?" Hydar ya fad'a yana kallon Dr Yasir shima yana kallon sa. Dr Yasir yace, "I'm sorry to say prince, guba Mama tasha." A tare suka wara idanu waje Suhaima tace, "poison..!." Dr yace, "Eh, kuma poison din ma ba kad'an ba da an sha kashe mutum take kai tsaye dan kunyi gaggawar kawo ta nan ne da babu abinda zai hanata kashe ta." Hydar ya kalli Suhaima sannan yace, "Amma a me tasha gubar Dr?" Ya tambaya cikin tashin hankali yana kallon sa. Dr yace, "Ba zallar ta tasha ba a wani abun aka zuba mata, inda zaku iya tuna abinda tasha na karshe ko zamu ga ragowar sa zamu iya duba shi wata k'ila a ciki gubar take." "Tabbas tasha tea, tana gama sha take cemin cikin ta na ciwo na juya na d'auko magani sai na ganta a yanayin da muka kawo ta nan." Dr yace, "To tabbas a cikin tea d'in poison d'in yake, amma dan mu tabbatar zamu iya zuwa mu d'auko ragowa in akwai sai gwada mu gani." Suhaima tace, "eh ta rage dan bata shanye ba ta ajjiye yana d'akin ta." Dr yace, "Zamu iya zuwa a d'auko mu gani." Hydar ya mik'e tsaye ya fita baice komai ba Suhaima tace, "Ina zuwa Dr" tabi bayan Hydar tana fad'in, "Yaya Hydar tare zaku je a d'auko?." Cak ya tsaya ya juyo yana binta da kallon tuhuma yace, "ta ya Mama tasha poison bayan kece kika kawo mata tea d'in?." Suhaima ta buɗe baki tana kallon sa da mamaki kafin tace, "Yaya Hydar zargina kake?." "Meyasa kika yi saurin kama kanki bayan bance ke kika zuba mata ba?." Suhaima ta rud'e tace, "Amma kasan dai babu yadda za'ayi na bawa Mamana poison ko?." "Shiyasa na tambaye ki ya akayi tasha poison bayan kece kika kawo mata tea d'in?." Suhaima ta fara hawaye tace, "Wallahi ko magen Mama bazan iya bawa guba ba balle Maman da kanta." Hydar ya fusata yace, "bance miki ke kika zuba ba malama, tambayar ki nake ya akayi tasha guba?!" Ya fad'a a k'arfi yana kallon ta idanun sa a waje. Kasa magana tayi kawai sai ta fashe da kuka yaja dogon tsaki ya barta a wajan ya fita ma daga asibitin gabad'aya zuciyar sa duka babu dad'i.  Suhaima d'akin da Mama take kwance ta shiga ta ganta a kwance an saka mata ruwa yana shiga jijiyar ta idanun ta a kulle farin abun ya daina zuba daga bakin ta, zama tayi a gefen ta ta rik'e hannun ta da babu allurar a jiki tana hawaye har lokacin d'aci take ji in ta tuna kalaman Hydar a kanta.        Bata san ya Hydar sukayi da Dr ba basu kuma had'uwa ba sai da safe sai da gari yayi haske ma Suhaima tayi sallar asuba duk ta k'agara ta koma gida sabida bata jin dad'in jikin ta ga makaranta zata je da azahar. Tana zaune a gefe taga Maman ta buɗe idanunta ta k'arasa wajanta a guje tana fad'in, "Mamana kin farka." Mama ta buɗe idanun ta sai ta fara tari da sauri Suhaima ta fita zuwa wajan Dr ta ganshi a tsaye dashi da Hydar tace, "Dr ta farka." Tare suka shiga da Hydar d'in ya samu Maman tana ta amai a kwance Suhaima ta sake fashewa da kuka tace, "Dr amai take yi fa." Dr yace, "kwantar da hankalin ki aman shine samun lafiyar ta daman shi muke so tayi ta amayar da poison d'in gabad'aya." Hydar ya kalli Maman ya kalli Dr yace, "yanzu ya aka gama binciken?." "Kamar yadda na fad'a maka a cikin shayin aka zuba mata poison d'in tasha, yanzu abinda za'a mayar da hankali wanda ya zuba mata poison d'in." Hydar ya girgiza kai yace, "Yanzu ya jikin nata?." Dr ya k'arasa kusa da Mama da ta mik'e zaune idanun ta a kulle yace, "Ranki ya dad'e ya k'arfin jikin?." Kai ta d'aga kawai tana cize baki hannun ta rik'e da cikin ta. Hydar ya kalli Dr yace, "Da alama cikin ta nayi mata ciwo." Dr yace, "Ai dole daman in ka duba a cikin ta poison d'in take, yanzu Suhaima ki taimaka mata ta tashi tayi wanka ta kuma sha tea mai zafi sosai." Kai kawai ta girgiza Dr ya fita ta share hawayen ta Hydar ya kalle ta yace, "Ga kayan Maman a jaka, a office d'in Dr sai ki karb'o mata tea" yana fad'a ya fita Suhaima ta bishi da kallo.         Taimakawa Maman tayi ta tashi tsaye dak'yar ta suka k'arasa band'aki ta fito ta barta Maman tayi wanka ta wanke baki ta fito ta shirya ta zauna tayi sallar asuba a zaune bayan ta idar Suhaima taje office d'in Dr ya nuna mata kettle ta d'ora mata tea ta had'a a cup ta tawo mata ta karb'a tasha dan taji k'arfi a jikinta. Tana cikin sha Hydar ya shigo ya zauna kusa da ita yana kallon ta ganin ta samu lafiya sai yaji dad'i da abubuwan sun masa yawa shima ga mai martaba a kwance ga Mama ga Asad ya zama abinda ya zama ga Aliyu baya nan. Mama tace, "Sannu Hydar, Allah yayi muku albarka." Suka amsa da amin Hydar yace, "Amin, Allah ya baki lafiya Mama." Mama tace, "Amin." Hydar yace, "Mama poison aka baki a tea fa kika sha." Tayi murmushin takaici tace, "na san za'ayi haka Hydar, masu neman su kashe ni ai suna da yawa." "Mama daman an san da hakan shine ba'a fad'a min ba? Da sun kashe mana ke fa shikenan." Mama tace, "kwantar da hankalin ka nasan shirin bazai wuce na Sadiya ba, Suhaima daman taji Jidda tana waya suna cewa sai an kashe ni, ku barsu su kashe ni d'in kawai ma yafii min zaman duniyar." Suhaima da Hydar suka kalli juna sannan suka kalli Maman Hydar yace, "Mama me kike cewa ne haka? Mun san da nufin ta a akan ki kuma mu zuba mata idanu?." Mama tace, "to muna da hujja ne?." "Zamu nemo hujjar Mama tunda har ta furta zata iya aikatawa, wataƙila jiyan ma ita ta saka aka zuba miki guba a tea ni kuma ina zuwa na d'ebo ban sani ba" Suhaima ta fad'a kallon Maman. Mama ta tab'e baki zuciyar ta na rawa tace, "a barshi dai kawai kome ya faru nice na jawowa kaina da ban bata dama ba da duk hakan bata faru ba. Asad baya son auren jidda na takura masa a kai wacce yake son zama da ita na raba su" ta dafe kanta da yake ciwo tace, "ku k'yale ta kawai abubuwan da suke gabana yafi wannan, burina Asad ya dawo hankalin sa, Aliyu ya dawo, mai martaba ya samu lafiya shine abinda na saka a gaba. Suhaima ina so ma zaki koma wajan Malamin nan da ya bamu maganin nan na k'arshe" ta fad'a tana dafe kanta cikin ta yana juyawa. "Baza'a bar maganar nan ba Mama!" aka fad'a daga bakin k'ofa duk suka juya jin muryar wanda basuyi zaton jinta ba suka ganshi a tsaye cikin k'ananu kaya fuskar sa babu walwala. K'arasowa ya yake yi ya canja yanayin fuskar sa yana murmushi ya durk'usa a gaban Maman yana kallon ta itama shi take kallo yace, "Barka da safiya Mama, ya k'arfin jikin ki?." Bakin ta rawa yake tana nuna shi da yatsa cikin mamaki da al'ajabi tace, "Asad ko Aliyu?." Murmushi yayi ta rik'e hannun sa yace, "Aliyun kine Mama, taya zaki ga Mai martaba da kansa da wannan shigar kuma shi kad'ai?."   Mama ta bayyana farin cikin ta tace, "Yaushe ka dawo? Ashe zan kuma ganin ka a duniya?." Murmushi yayi yace, "Gani na dawo Mama. abinda nake ji kuma baza'a bar maganar nan ba, babu wanda ya isa ya bawa mahaifiyar mu guba ya kwana lafiya." Ya kalli Hydar yana mik'ewa yace, "An tabbatar da tea d'in da tasha akwai poison?." Hydar da yaji dad'in dawowar d'an uwan nasa yace, "Akwai, bincike ya tabbatar akwai a ciki." "Suhaima lokacin da kika shiga kitchen wa kika gani?." "Babu kowa Yaya Aliyu, Amma ruwan a ajjiye yake a cikin kettle kawai dafasa shi nayi." "You're not serious Suhaima, baki san wanda ya zuba ruwan ba kawai zaki d'auka ki bawa Mama.....?" Sai ya dafe kai yace, "Oh god" ya fad'a yana runtse idanun sa. Suhaima tace, "Ina so naga taci wani abun ne a lokacin shiyasa." Aliyu ya kalle ta yace, "Duk abinda ya faru kece sila, kuma zaki shiga cikin wanda zan sakawa question mark." Mama da take ta kallon sa tana murmushi tace, "Sai kake min yanayi da Asad Aliyu, musamman yadda kake magana kana tsayawa kamar shine yake magana haka nake ji." Tausayin Maman nasu ya kama su dukkan su dan sun san tsananin kewar sa da take yi ne ya saka take jin hakan. Aliyu bai magana ba ya tashi kawai ya fita dan bazai bar wanda suka kusa kashe masa uwa su kwana lafiya ba. Dan shi kaf cikin plan d'in sa babu kashe Mama. Lokaci d'aya sai Mama taji dad'in jikin ta ganin addu'ar ta biyu ta karb'u har Allah ya biya mata saura guda biyu da take jiran tabbatuwar su. Basu jima sosai a asibitin ba tace sai an sallame su ganin taji sauk'i sai ciwon cikin kad'an-kad'an sai aka sallamo su suka dawo gida.         Aliyu gida ya koma sai a ranar ya shiga cikin masarauta ya tattara gabad'aya ma'aikatan b'angaren Mama ya saka su a gaba yana kallon ko waccen su yace, "Wacece k'arshen aiki a kitchen d'in Mama jiya?." Suna durk'ushe dukkan su duk sun tsorata dan sun san hali ba kirki ne dashi ba d'aya tace, "Nice ranka ya dad'e." Ya hard'e hannu a k'irji yana kallon ta sai ta sunkuyar da kai yace, "ke kika zuba ruwa a kettle d'in da ake dafa tea?." Kallon sa tayi suka had'a ido yayi mata mugun kwarjini ta sauke kai yace, "Duk wacce tayi min k'arya wallahil azimi saina hukunta, kun san halina." "Ranka ya dad'e nidai na gama gyara kitchen d'in amma ban zuba ruwa a butar ba" ta fad'a kanta na k'asa ya kalle su yace, "Wacece ta zuba a cikin ku?." Duk sukayi shiru ya girgiza kai yana kad'a k'afar sa yace, "in na sake maimaitawa sai kunyi kuka." D'aya daga ciki tace, "Nice ranka ya dad'e, amma wallahi ban zuba komai a ciki ba ruwa kawai na tara a fanfo na zuba na ajjiye kuma bada niyar wani abun nayi ba." "Nace daman an zuba wani abun ne?" Ya jefe ta da tambayar muryar sa a can ciki dan in baka nutsu nama baza ka san me yace ba yana kallon ta. Tayi shiru ya kuma cewa, "Bayan ku waye ya shigo?." Suka had'a baki suka ce, "Babu kowa." "Kenan dai a cikin ku wata ta zuba gubar a ruwan." Sun tsorata matuk'a jikin su sai rawa yake ya girgiza kai yace, "Better, zan saka a kulle ku yanzun nan then ayi muku bulala goma sannan ku share harabar gidan nan gabad'aya, in kun gama sai mu sake zama muji wacece tayi a cikin ku." Kafin suyi magana yace, "kana ina!." A guje dogarai biyu suka shigo yace, "aje ayi musu hukunci kar a k'yale su har sai rana ta fad'i" yana fad'a ya tashi zai bar wajan suka rushe da kuka d'aya tace, "Dan girman Allah ranka ya dad'e kayi hak'uri kayi mana rai, nidai wallahi ban san komai ba ban aikata komai ba kuma." Ko kallon su ma baiyi ba ya wuce abinsa aka tasa kewar su dan su karb'i hukunci ko wacce cikin su kuka take yi dan hukuncin da ya zayyana bamai sauki bane ba.      Ba jimawa su Mama suka dawo ta tarar b'angaren nata babu kowa hatta jakadiyar ta ladidi bata nan suna zaune a k'aramin falon Aliyu ya shigo ya zauna a kusa da k'afar ta kamar yadda Hydar yake a gefe tace, "Ina hadiman nan suke?." Aliyu yace, "na saka ayi musu hukunci sai sun fad'a min wacece ta zuba poison a tea." "Aliyu meyasa?" Ta fad'a tana kallon sa. Shima kallon nata yayi ya rasa me ya canja maman nasa lokaci d'aya itace take cewa meyasa aka yiwa Hadimai hukunci...? Baice komai ba ya kalli Hydar yace, "Ina so na had'u da Asad." Hydar yace, "Yana k'aramin falon sa yana tare da bak'i." Baice komai ba kawai ya mik'e ya fita Mama ta bishi da kallo zuciyar ta tana mata rawa a kansa dan gani tayi gabad'aya ya canja kamar ba shi ba kamar kuma shi ta girgiza kai tace, "Akwai alamar tambaya akan sa, meya canja Ali haka?." Hydar yace, "Mama ashe bani kad'ai na gani ba, tabbas Aliyu ya canja kamar bashi ba." Kai take girgizawa ta koma ta kwanta a jikin kujera dan har lokacin cikin ta ciwo yake yi mata. A k'aramin falon cikin gida kamar yadda akace Asad ya gama ganawa da bak'i yana kashingid'e yana duba wani littafi a hannun Aliyu ya shigo da sallama, amsawa yayi yana kallon sa shima shi yake kallo Asad bai san ya mik'e tsaye ba sai murmushi yaga Aliyun yayi yace, "Our king surprise" ya fad'a yana bashi hannu alamun su gaisa. Sai kuma ya janye hannun yace, "Oh sorry ba haka ake gaida ku ba" sai ya duk'a kamar yadda ake yiwa sarakuna yace, "Allah ya taimaki sarki ya k'arawa sarki lafiya." Asad ya saka hannu biyu ya d'ago Aliyu ya mik'e tsaye yana kallon sa da farin ciki a kan fuskar sa ya mik'a masa hannun alamun su gaisa, Aliyu daman abinda yake so kenan da sauri ya bashi hannu suka gaisa yana kallon Asad yana wani irin murmushi mai d'auke da ma'anoni da dama a cikin sa......... *karfa muje ya shafawa Asad maganin hauka Fans....*😨 [17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *066.*              Kallon kallo suke dukkan su baza ka iya fassara yanayin su ba duk da akwai murmushi akan fuskar ko wannen su amma yadda suke kallon juna hakan zai baka tabbacin akwai wani abun a k'asa a dinne wanda ba kowa yasan dashi ba. Asad ne ya fara janye hannun sa Aliyun ma ya janye Asad ya sake fad'ada murmushin sa yace, "Yaushe ka dawo?."         Jin yadda maganar Asad ta fita cike da iyayi ana bawa ko wanne harami na kalmomin hakkin sa sai abin ya bawa Aliyu dariya ya dara kad'an yace, "Ba'a jima ba ranka ya dad'e." Asad ya murmushi ya koma ya zauna Aliyu ya zauna shima a k'asa kamar yadda Asad d'in ya zauna kana Asad yace, "Barka da zuwa." Murmushi ya kuma yi yace, "Na gode." Shiru wajan yayi babu mai magana ko wanne da abinda yake sak'awa a ransa Aliyu ka katse shirun da fad'in, "In mai martaba yayi min izini zan shiga wajan Abba naga yanayin jikin sa." Asad ya kalle shi yace, "A fito lafiya." Tashi yayi yace, "A tashi lafiya our king" ya fad'a yana niyar tafiya har yaje gab da k'ofa sai kuma ya juyo yaga Asad d'in ma kallon sa yake yi sai suka saki murmushi a tare Aliyu ya fita.         Da wannan murmushi a fuskar sa ya shiga b'angaren mai martaba ya samu an zaunar dashi idanun sa a buɗe Uncle ya bashi alkur'ani yana karantawa, sallamar Aliyu ya saka shi kallon k'ofa Aliyu sai ya saki murmushi ya k'araso kusa dashi ya kalli Uncle yace, "Uncle barka da safiya." Uncle yace, "Aliyu yau kaine a k'asar tamu?." Murmushi yayi ya shafa kansa kafin ya kalli Abba da yake kallon sa shima ya rik'e hannun sa yace, "Ina farin ciki da naga mahaifina lafiyar sa tana samuwa, Allah ya tashi k'afadun mai martaba nan bada jimawa ba." Uncle ya amsa da amin sai mai martaba ya murmusa ya cigaba da karatun sa bai kuma kallon sa ba, Aliyu kallon gefen drawer yayi yaga allurai a ajjiye da yawa ya kalli Uncle yace, "wannan fa?." Uncle yace, "itace wacce ake masa duk sati." Aliyu ya girgiza kai ya d'auki allurar ya d'auka a waya ya ajjiye sai suka had'a ido da Uncle sai yace, "zan nunawa wani Dr ne naji ya ingancin ta." Uncle yace, "ba laifi." Aliyu yace, "Ina dawowa" ya fad'a yana fita daga b'angaren ya wuce tsohon b'angaren su wanda suke da d'akuna a can. Har zai gota b'angaren Jidda sai kuma ya tsaya cak ya kalli b'angaren nata yaga dogarai maza biyu masu gadin ta a tsaye a k'ofar da zata shigar da kai wajan nata, ba tare da wani tunani ba ya nufi wajan hango shi da sukayi sai suka mik'e suka zube a k'asa yana zuwa bai bi ta kansu ba kai tsaye ciki ya shiga.        A cikin falon kuwa Jidda na zaune ita kad'ai ta kori kowa na b'angaren nata waya na hannun ta kamar ko yaushe suna waya da Mum tana fad'in, "Mum naga Aliyu wallahi na ganshi ya dawo!, na shiga uku na lalace Mum komai zai lalace." Daga can b'angaren Mum tace, "Dallah malama ki nutsu, me Aliyun zai miki kika bi kika tsorata da dawowar sa haka? Mukayi maganin Asad sa balle shi karan kad'a miya." Jidda ta rausayar da kai tace, "Mum baza ki gane ba, Aliyu ya wuce duk inda kike tunani wallahi tsaf zai lalata mana shirin da muka jima munayi. Dawowar sa ba alkhairi bace ba a rayuwar mu meyasa ba'a kashe shi a can k'asar b......." cak maganar ta maqale baki bud'e ta mik'e tsaye tana kallon inda ta ganshi a tsaye ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta fuskar nan tasa a tamke babu alamun fara'a a cikinta.          A hankali yake takawo hannun sa na cikin aljihu yana Isowa kusa da ita ya saka hannu ya zare wayar hannun ta ya saka a speaker yaji Mum na cewa, "Waye Aliyu nayi maganin Asad da uwar su ma balle wani shi jiki duk neman mata...?. Ki  nutsu Malama ina so na gama da babar sune sannan na juyo kansa amma tunda naga kin tsorata sosai zan dawo da aikin kansa ko ba'a kashe shi ba za'a kulle bakin sa ko meye ma ya kasa fad'a. Nayi maganin Asad ma mai k'arfin ibada balle shi karan kad'a miya, ita kanta Rabi tana tsalle rijiya da baya ne amma gab nake da kawo k'arshen ita da yaran nata gabad'aya."      Jidda ta k'ame babu damar magana sai kallon sa da take yi yana sauraron abinda Mum take cewa da hannu yayi mata alama da ta bata amsa Jidda ta had'd'iye yawu murya na rawa tace, "Toh Mum." Mum tace, "Yauwa ki kwantar da hankali babu abinda zai faru ina tabbatar miki da hakan. Naji ya saka an kama hadiman babar sa akan yana zargin an zubawa babar sa guba zan gargad'i Ladidi kar ta bari sunana ya fito a cikin tuhumar su kome zai faru kar tace nice na saka ta dan Aliyun nan ba hankali ne dashi ba sai yayi min hauka." Mum tana gama fad'ar hakan ta yanke wayar Aliyu wayar da kallo suka had'a ido da Jidda ya saukar da idanun sa zuwa cikinta yaga ciki ya fito ya tab'e baki yana girgiza kai bace komai ba ya dire mata wayar ya fita.        Hannu Jidda ta d'ora a ka tace, "Na shiga uku! Shikenan ta faru ta k'are!" ta fad'a hannun ta na rawa sosai zuciyar ta a tsorace tana sake kiran Mum amma bata samun ta sai kawai ta d'auki wayar ta shiga d'aki ta saka babban hijjabi ta fito ta saka aka kira jakadiyar ta suka rufa mata baya zuwa inda mota take ajjiye driver ya shiga yaja su sai gidan Mum jikin ta har rawa yake sosai.          Aliyu yana fita b'angaren nasu ya nufa a kan hanyar sa ta tafiya yaga ana yiwa su Ladidi hukuncin da yace ayi musu duk sun galabaita sai kuka suke da hannu yayi musu alamun da su kawo masa su ya shiga falon ya zauna, a lokacin aka shigo dasu duk suka zube a k'asa dogaran suna baya yayi musu alama da su koma su suka fita yabi su da kallo dukkan su kuka suke yi har ita Ladidin. "Allah yaja da ranka kayi mana rai, wallahi ban aikata komai ba bazan iya cutar da Fulani ba ko sau d'aya" wacce take kula da kitchen d'in ta fad'a tana kuka. Da yatsa ya nuna su yayi musu alama da su fita su jiki na rawa suka mik'e duk da gab'ob'in su duk sun gashi suka ce, "Mun gode, Allah yaja da ranka yasa kafi haka." Sai da suka fita ya kalli Ladidi da take raba idanu rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita yace, "Bana son cin amana in na kama mutum da cin amana ina sakawa a b'atar dashi daga duniya ne ma'ana a kashe shi!" Ya fad'a yana kallon ta sai jikinta ya cigaba da rawa dan ta tabbatar ya gano ta ta rushe da kuka tace, "Allah ya taimake ka wallahi sharrin shaidan ne ban san kuma guba bace, Hajiya Sadiya ta bani tace maganin da zai ragewa Fulani zazzaɓi ne ni kuma ganin alaqar su sai na amince na zuba kamar yadda tace. Ka yafe min ranka ya dad'e nasan na aikata babban laifi amma bazan sake ba." "Ai sai kina raye zaki sake" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba yana danna wayar sa tana sharb'ar majina tace, "Dan Allah annabi Muhammad S.A.W kayi hak'uri ka yafe min ranka ya dad'e, kuskure ne kuma baza'a sake ba wallahi anyi na farko anyi na k'arshe. Nabi Allah na bika ranka ya dad'e ka taimake nj." Aliyu ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Zan k'yale ki amma da sharaɗi d'aya." Jikin ta na rawa ta nutsu taji yace, "yadda na gano ki cikin sauk'i kin san duk abinda kika kuma aikatawa bazai min wahalar gano ki ba ko?." Ta d'aga kai tace, "Kwarai ranka ya dad'e." Ya gyara zama yace, "bayan wannan Sadiyan ta tab'a baki wani maganin ki bawa Mama?." "Bata tab'a ba wallahi, jiya ne rana ta farko." "To ki nuna mana aiki kike mata har yanzu, duk abinda ta baki ki karb'a ki amsa kice zakiyi in kun rabu sai kizo ki bani duk abinda ta baki." "Na amince ranka ya dad'e, na amince wallahi zanyi." Ya girgiza yace, "Nawa ta biya ki?." Jikin ta rawa yake da hannu yyi mata alama da tayi magana tace, "dubu dari." Ya d'aure fuska tamau yace, "Akan dubu d'ari kika so kashe mana uwa?." Kuka take yi sosai tace, "Ban san na kisa bane, ban san kashe ta za'ayi ba wallahi." "K'arya kike Ladidi zan k'yale ki ne kawai. Zan ninka miki abinda ta baki sau goma matuk'ar kika yi abinda nace." "Ko baka bani komai bama zanyi ranka ya dad'e." Ya kwanta a jikin kujerar yace, "Kiyi abinda nace in naga yanayin aikin naki sai muga abinda zai faru" da hannu yayi mata alama da ta tashi ta bashi waje ta mik'e tana godiya sosai.        Bayan fitar ta ya tashi ya nufi d'akin sa har zai shiga sai ya fasa ya nufi k'ofar d'akin Asad ya murd'a handle d'in ya jishi a buɗe, "A'a bro yau kuma d'akin deaf zaka shiga?" Hydar ya fad'a daga bayan sa ya juyo ya kalle shi ya d'aga kai yana tura k'ofar d'akin yana kallon d'akin yace, "nasa zan dawo tunda ya wuce matsayin wannan yanzu." Hydar yayi murmushi yace,  "Yadda kake so, but akwai kayan sa da littafan sa a ciki" yana fad'a ya shiga nasa d'akin Aliyu ya shiga d'akin ya turo k'ofar yana kallon d'akin yana tab'e bakin sa kamar yaga kashi. Yana nan a gyare sai y'ar k'ura da yayi kad'an gadon a d'ame da alama babu wanda yake zama a cikin d'akin. Kamar an bashi umarni ya d'aga katifar gadon nan yayi karo da k'atuwar laya wacce bai tab'a ganin irin ta ba da wani bak'in gashi a nannad'e a jikinta ya saki katifar yana kallon layar. A gefe ya ajjiye ya koma ya buɗe kayan Asad yana kallon su a shirye sama da kala hamsin har sunyi k'ura sabida ba'a tab'a su. Murmushi yayi ya girgiza kai yace, "Allah sarki Deaf, dole abubuwa su canja" ya fad'a yana zura hannun sa can k'arshen wardrobe d'in ya zaro wata layar ya had'a da waccan ya jefa a drawer ya shiga band'aki domin bazai zauna da layoyi a d'akin ba dan shi yasan inda suke. A nan yayi wankan sa ya shirya tsaf da kayan Asad ya tsaya yana kallon sa a madubi yayi murmushi ya shafa gemu yace, "Like deaf." Murmushi ya sake yi domin shi kad'ai yasan abinda yake shiryawa a zuciyar sa, bayan Allah da ya halicce shi babu wanda ya isa ya gano shirin sa sai shi kawai ya fita daga d'akin. *☆☆☆*           "Ke Rauda tashi mana, wannan wanne irin bacci ne haka har azahar tayi baki tashi ba ko jikin ne?" Umma ta fad'a tana tashin ta daga bacci Rauda ta mik'e tana rausayar da kai Umma ta tab'a wuyan ta tace, "jikin ki babu zafi, tashi kiyi wanka kici abinci kiyi sallah bacci ciwo zai k'ara miki." Kai ta d'aga ta ziro k'afafun ta k'asa ta sakko daga kan gadon tana niyar mik'ewa sai tace, "Washh bayana." Umma ta kalle ta tace, "meya samu bayan naki? Naga tun asuba kina rik'e bayan ki." Rauda tace, "Haka nan ya rik'e min" ta fad'a tana shiga band'aki sai kuma ta fito tace, "Bara na d'ora ruwan wanka babu mai zafi." Umma tace, "Zauna a kawo miki." Ba musu ta zauna tayi tagumi Umma ta fita ba jimawa da kanta ta shigo mata da ruwa a bokiti bata k'arasa band'akin ba ta ajjiye mata bata ce komai ba ta juya. Tashi Rauda tayi ta d'auki ruwan ta shiga band'akin tayi wanka tare da alwala tazo ta tayar da sallar azahar, bayan ta idar tayi tagumi abinda ya faru da ita jiya yana yi mata yawo ba kamar irin kalaman da taji yana fad'a mata a lokacin da suke tsaka da sab'on Allah nan take tsigar jikinta ta tashi sai hawaye tayi saurin gogewa ta kwantar da kanta a guiwar ta.        Gudun kar Umma ta sake yi mata magana ta gano wani abun sai ta mik'e ta fito ta samu tasha tea kawai bata iya cin komai ba Rahma tazo suna hira da Umma ita kam bata saka musu baki tayi shiru tana kallon waje daya. Yaya Ummi ce ta shigo tana fad'in, "mara lafiya kin tashi ashe?." Ta daga kai tace, "Yaushe kika shigo?." "Kina bacci, ya jikin?." "Da sauk'i, Ina wuni." "Lafiya lau, Allah ya k'ara lafiya." "Amin Yaya." Umma ta kalli Yaya Ummi tace, "Jiya wanne turare kika bata ta shafa mai d'aukar hankali haka?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalli Yaya Ummi suka had'a ido ganin yadda ta rud'e lokaci guda sai Yaya Ummi ta d'auki haske tace, "Sabo ne,  Abban su Islam ya kawo min shine ta d'auka ta saka." Umma tace, "Tunda ke ya bawa bai kamata ki bata ba, yana da dad'in khamshi sosai amma matsayin ta na wacce bata da aure bai cancanci ta shafa shi ta fita ba, yana da k'arfi d'azu ma naji khamshin sa a jikinta ya rik'e fatar ta sosai, ki kiyaye koda nan gaba kema kuma kar ki saka ki fita waje" Umma tana fad'a ta mik'e ta fita daga falon Yaya Ummi ta kalle ta tace, "Tunda naga kina raba ido nasan baki da gaskiya, ke ina kika sami turaren?." Rauda tayi shiru ta rasa abinda zatace sai Yaya Ummi tace, "tambayar ki nake yi." Rauda tace, "a gidan su k'awata Farida ne na ganshi sai kawai yayi min dad'i na shafa, kin san in na cewa Umma haka fad'a zatayi min shiyasa nace a gidan ki na samu." Yaya Ummi tace, "Munafuka" ta fad'a tana yar dariya tana ta janta da hira ita dai bata iya bata amsa da ta kulle idonta abinda ya faru take hangowa duk ta koma wani iri lokaci d'aya.       Bayan la'asar Anas yazo bata so ma fita ba suka tilasta mata dole taje inda yake kamar ko yaushe yana zaune ta shiga ta zauna da sallama ya amsa ya kalle ta yace, "Amarya ta meya same ki haka kika rame a fuska?" Ya fad'a cikin kalar tausayi yana kallon ta. Murmushin yak'e tayi tace, "Ina wuni." Jin muryar ta na rawa sai yace, "Taya zan wuni lafiya bayan kina kwance ke baki da lafiya? Ji yadda maganar ki take shaking fa." "Zazzaɓi ne da ciwon kai shima naji sauk'i." "Anje asibiti?." "Basai anje bafa naji sauk'i." Yayi shiru yana kallon ta sai yaga kawai tana kuka hankalin sa ya tashi sosai ya matso kusa da ita yana fad'in, "Haba Rauda ya kike so nayi ne? Kukan na meye kuma?." "Kayi hak'uri!" ta fad'a murya na rawa sosai tana kuka. Hankalin sa ya tashi babban tashin hankalin sa bai wuce ace za'a raba su ba yace, "hak'urin na meye Rauda bayan ni ya kamata na baki hak'uri nayi miki laifi jiya? Hak'urin me zanyi? Ki sanar dani dan Allah kin saka min tsoro a zuciyata." Kai take girgizawa tana kuka duk ya rud'e hankalin sa ya tashi yana ta bata baki amma bata daina zubar da hawaye ba, wani yana bin wani haka take kukan hawaye na zuba sosai sun k'i tsayawa, jin bazata iya jurewa ba sai kawai ta mik'e tayi cikin gida a guje ta barshi a tsaye yana binta da kallo gaban sa yana fad'uwa. [17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *067.*           A guje ta shige su a falo zuwa d'aki ta fad'a kan gado tana kuka har suna jiyo gunjin kukan ta daga d'akin. Umma tayi murmushi tace, "Wai ka haifi yaro yace zai maka yawo, tun jiyan nasan akwai wani abun da yake damunta a zuciyar ta tana b'oyewa dan bata so mu sani." Yaya Ummi ta tashi ta bita d'akin lokacin tana fad'in, "Na tsani rayuwata bana son rayuwata, Allah ka aiko da mala'ikan mutuwa ya d'auki raina na mutu na huta da wannan bala'in da nake ciki." "Ban tab'a dauka ilimin ki ba bashi da amfani ba sai yau Rauda, da bakin ki kike wannan addu'ar bayan kin san yinta babu kyau?." Rauda jin muryar Yaya Ummi ya saka tace, "Yaya ya zanyi? Ji nake zuciyata kamar zata fashe na rasa wanne kalar tunani ma zanyi."  Yaya Ummi ta zauna a kusa da ita tace, "Fad'a min me yake damun ki? Wani abun Anas d'in yayi miki kike yiwa kanki wannan fatan?." Rauda ta fara jan numfashi alamun wacce taci kuka ta k'oshi Yaya Ummi tace, "Fad'a min mana meya faru, in baza ki iya sanar da Umma ba ni zaki iya fad'a min." Kallon fuskar Yaya Ummi take yi tana hawaye amma ta kasa cewa komai, taya zata iya fad'a mata ta aikata zina da tsohon mijinta? Taya zata iya ce mata tarbiyyar ta ta shekara ashirin da biyar ta watse a daren jiya? Ta zata ce mata ta aikata babban laifi a cikin mayan laifukan da Allah subahanahu wata'ala yayi hani da kusantar su duniya da lahira?. Ina baza ta iya ba gwara ta cigaba da barin sa a ranta koda zata mutu. Yaya Ummi ta tab'a ta tace, "Sanar dani ina jinki." Ta sunkuyar da kai tace, "ni tunda naga jiya babar su Farida ta rasu daga shiga d'aki bata sake fitowa ba sai gawar ta shikenan nake jin komai ya yatsa min cak Yaya, hatta auren sai naji bana so wallahi" ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Yaya Ummi tace, "Bayan shi akwai wani abun a ranki, me Anas yayi miki?." Rauda ta girgiza kai tace, "Wallahi bai min komai ba Yaya, abinda na fad'a miki shine a raina kawai." "Shine kike yiwa kanki wannan fatan?." "Yaya Ummi ji nake inda Ummana ce ta rasu haka jiya a ina zan saka Raina? Wanne irin hali zan shiga?, tuna hakan shine yake sakawa naji komai ya fita daga raina Yaya." Yaya Ummi tace, "Dukkan mai rai mamaci ne ai, yadda mahaifiyar ta ta rasu kema taki wata rana zata rasu, bama taki ba sai duniyar ta zama babu kowa a cikinta kaf sai mun mutu. Manzon Allah S.A.W yace muso duniya kamar baza mu mutu ba, sannan muso lahira kamar yanzu zamu mutu. In kika fahimci hadisin yana nuni akan abu biyu, kar tunanin lahira ya hana ki morar abinda Allah ya mallaka miki a duniya, haka kar shagala da abinda kika mallaka ya saka ki manta da lahira. Kiyi amfani da wannan hadisin sai kiyi rayuwar ki cikin sauk'i ba cuta babu cutarwa."      Kai Rauda ta d'aga alamun gamsuwa da abinda Yaya tace ta kuma cewa, "Haba kamar bake ba, ban sanki da kalamai irin wannan na marasa ilimi ba. Kaf gidan nan babu mai ilimin addinin ki ke Allah ya zab'a ya bawa haddar alkur'ani mai girma, haka duk gidan nan babu wanda Allah ya jarabta da k'addarorin da suke samun ki, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki sai kiga komai yazo ya wuce kamar bai faru ba. Maman Farida kuma indai kina son faridan kin kuma ji mutuwar maman nata a jikin ki addu'a zaki dinga mata ba wannan kukan ba." "To Yaya zanyi in sha Allah." Yaya Ummi tace, "Ina kika baro Anas d'in kika shigo a guje haka?." "A falo na barshi." "Haka kawai kin tayar masa da hankali sai ya d'auka ko fasa auren naku ma akayi. d'auki waya ki kira shi ki kwantar masa da hankali." Rauda tace, "Bazan iya ba yanzu." "Yanzu zakiyi, d'auki nace."         Ba yadda ta iya haka ta d'auki waya ta kira shi kamar jira yake ya d'auka kafin tayi magana yace, "Dan Allah nayi miki wani laifi ne Rauda?, meya faru kike bani hak'uri? Karki fad'a min abinda zuciyata bazata iya d'auka ba dan Allah." Kallon Yaya Ummi tayi sai Yaya Ummi ta tashi ta bata waje tace, "Kayi hak'uri babu abinda ya faru fa, zuciyata ce babu dad'i shiyasa kaga nayi haka, amma ka yafe min." Ajiyar zuciya ya sauke jin muryar ta a tausahe alamun ta gama kukan yace, "Alhamdulillah, har naji dad'i farin ciki ya mamaye zuciyata. Me yake damun ki haka?." "Rasuwa a gidan su k'awata Farida Maman su ce ta rasu bayan mun gama hira da ita shine abin yake tab'a min zuciya nake jin gwara na mutu kar hakan ta faru da Ummana Ina raye." Ya tausasa murya yace, "Duk mai rai mamaci ne My love, yau gare mune gobe ga wanin mu, dole sai an mutu ko muna so ko bama so sai mun mutu kinga gwara muso mu saka ta a ranmu mu kuma tabbatar da zuwan ta nan da wani lokaci kad'an mai zuwa. Allah ya jiqan wacce ta rasu ya bawa y'ay'an ta hak'urin rashin ta." "Amin" ta amsa tana lumshe idanu dan ita gabad'aya ma bata da wata k'awa Farida a duniya kawai sunan ne yazo zuciyar ta a jiya. "Kinga mutuwar ta saka kin k'ara imani." Murmushi tayi kad'an tace, "Sosai ma kuwa." "Shine aka so a jefa ni a wani hali na daban." "Kayi hak'uri." "Dolena ai na hak'ura, bakya laifi koda kin kashe dan masu gida." "Balle ma babu d'an mai gidan da har zan kashe shi" ta bashi amsa hawaye na zuba tana murmushi. Jin amsar da ta bashi sai yaji dad'i dan yasan ta dawo nutsuwar ta suka fara hira yana d'ebe mata kewa da kalamai masu dad'i har zuciyar ta d'an yi sanyi. *☆☆*         A zaune yake ya hard'e hannayen sa waje d'aya yana kallon k'asa yayi shiru yana saqa da warwara a zuciyar sa, shin me zaiyi? Wanne abu ya kamata yayi ne?. Shi kansa bashi da amsa hakan ya saka dole yayi shiru wai ko zuciyar sa zata sanar dashi abinda ya kamata d'in. Kansa ya kulle ta ko wanne b'angare a cushe yake cikin brain d'insa komai ya tsaya cak, da ya d'auko tunanin baya kai k'arshen sa sai yaji wani a zuciyar sa komai neman canja masa yake yi. "My king" jidda ta fad'a daga bayan sa ya runtse ido sam baya son jin maganar ta gabad'aya inda yake balle kuma yayi ido hud'u da ita sai yaji zuciyar sa kamar ana hautsina ta sabida takaici. K'arasowa tayi kusa dashi ta zauna tana kallon sa tace, "My king." Nan ma yayi mata banza bai amsa ba ta kai hannun ta kafad'arsa ta d'ora a kai tace, "My king ni ban san laifin da nayi maka ba kake share ni." Hannu ya saka ya cire hannunta daga kafad'ar sa ya kalle ta yace, "Please and please ki k'yale ni." "Akan me zan k'yale ka bayan ni matar kace? In banzo wajan ka ba wajan wa zanje?." Ya cize bakin sa yana jin turirin b'acin rai yana taso masa ya kulle idanun sa ta sake cewa, "Ina buk'atar kulawar ka kodan babyn ka da yake jikina." Iska ya furzar ya mik'e zai bar mata wajan ta rik'e hannun sa tace, "In nayi maka laifi ka fad'a min wannan horon da kake yi min bazan iya jurewa ba My king." Hannun sa ya kwace ya shiga d'aki tana nan zaune. Jim kad'an ya fito ya saka babbar riga ta blue d'in shaddar jikin sa ya saka hula ya d'ora hirami fari a kai taga ya nufi k'asa ta bishi da kallo kawai zuciyar ta na rawa sosai.         Yana sauka shamaki da zagin sarki da kuma Suhail suka mara masa baya yana gama suna bin sa a baya abin mamakin sai suka ga ya nufi b'angaren Mama kai tsaye, yana zuwa zai shiga ya juyo ya kalle su duk sai suka koma gefe har Suhail suna fadin, "A fito lafiya d'awisu gwanin ado, a fito lafiya sarkin sarakuna, kyau, mulki, kud'i sai sarkin katagum, ga kuma uwa uba ilimi da sanin ya kamata, wane mutum da zai kama kafar mai martaba?. Kaf sarakun arewa a karkashin mai martaba suke, ta tamkar da dubu. A fito lafiya."        Shigar sa falo na farko duk hadimai suka zube jiki na rasa suna kwasar gaisuwa ya amsa yayi ciki su kuma suka fita. A zaune ya tarar da Mama da Hydar da kuma Aliyu da Suhaima a zaune a k'asan carpet Mama na kan kujara Suhima tana matsa mata k'afar ta. Sallamar sa ya saka Hydar da Suhaima mik'ewa tsaye Mama da Aliyu kam ko gezau basuyi ba suna zaune, a ka'idar gidan sarauta rashin kunya Aliyu yayi ga shugaba k'arara dan bai bashi girma ba rashin mik'ewa tsaye da baiyi ba.        Yadda sauke a zube a k'asa shima haka ya zube duk suka zauna shima yana kallon Maman sa itama shi take kallo ta mik'e zaune sosai tana kallon sa tace, "Asad!." Kai ya saukar k'asa cikin taushin murya da rauni yace, "Allah ya k'ara miki lafiya da tsahon rai." Kallon Aliyu tayi ya kalle ta shima ta sake kallon Asad tace, "yau kaine a gabana kodai mafarki nake yi?." K'afar ta ya dafa yace, "Ba mafarki mahaifita ta take ba da gaske ni d'in ne a gabanta a zaune." Mama farin ciki ya mamaye mata zuciya har ta kasa b'oyewa  tace, "Alhamdulillah, Allah shine maji rok'on bawa a koda yaushe. Asad da gaske kaine?." Yayi murmushi cikin sanyi muryar sa ta ko yaushe yace, "Kwarai da gaske." Ya girgiza kai ta koma ta jingina da kujera tace, "Na jima ina mafarkin wannan ranar ashe zata tabbata ina da rai." "Akwai wacce zata zo nan gaba wacce tafi na baya muni" Aliyu ya fad'a a bayyane yana kallon k'asa. "Aliyu me kace?" Ta fad'a tana kallon sa sai a sannan ya tabbatar da maganar zuciya ta fito fili yace, "Afuwan ranki ya dad'e, wani tunanin ne a zuciyata." Mama ta sake kallon Asad ta mik'a masa hannu tace, "Zo ka rik'e hannuna Asad." Ba musu ya k'arasa inda take ya rik'e hannun ta ta sauke ajiyar zuciya tace, "Allah ya yiwa rayuwar ku albarka." Duk suka amsa da amin tace, "Meyasa kayi sakaci da rok'on Allah Asad?." Shiru yayi yana kallon k'asa baice komai ba tace, "Koma meye ka dawo kamar wanda na sani a da, karka bari shaidan ya sake jinyar zuciyar ka." Ya girgiza kai yace, "Ki yafe min Mama, nasan na sab'awa mahaifiyata sau babu adadi amma ina neman afuwar ki akan komai. Bana sanin nayi sai bayan abin ya faru in naso na baki hak'uri sai na kasa, mahaifiyata kuma tasan bazan tab'a iya juya mata baya in ina cikin hankalina ba, ki yafe ni Mama." Mama tayi murmushin farin ciki tace, "Babu komai Asad, ni nasan duka abubuwan da suka faru ba laifin ka bane aikin sirihi ne amma yanzu tunda ka dawo daidai Alhamdulillah." "Godiya nake Mamana, Allah ya k'ara miki lafiya." Suka amsa da amin dukkan su kafin ta kalle shi tace, "Ya akayi kake iya doguwar magana haka ba tare da ka huta ba Asad?." Yayi murmushi yace, "Ina k'okarin furtawa ne dan na roƙe ki afuwa akan abubuwan da suka faru a baya,na kuma tabbatarwa da Mamana Asad d'in da ta sani a baya ya dawo da izinin Allah amma sai Maamna tana taya ni da addu'a, ina ganin abubuwa sosai a rayuwata wanda k'iris ya rage su haukata ni." "Na sani Asad, rik'e ragamar masarauta ba abu bane mai sauk'i. Addu'a yanzu aka fara yi maka ita in sha Allah duk wani mai son ganin bayan ka sai dai kai kaga bayan sa. Baga shi nan yanzu kana iya magana ba babu laifi, ai duk cikin addu'ata ne da wacce mahaifin ka yake maka." Mama ta kalli Suhaima tace, "Suhaima kinga yana da kyau mu koma wajan Malamin nan baban yarinyar nan muyi masa godiya, maganin sa da addu'ar da ya bani tayi tasiri sosai akan duk abinda na saka a gaba." Suhaima tace, "tsohuwar matar mai martaba kike nufi?." Dummm gaban mutane hud'u ya buga a wajan, Asad, Aliyu, Mama, da kuma Hydar. Babu wanda gaban sa bai fad'i ba har ita Maman nan take annurin fuskar ta ya canja ta kalle ta tace, "Lallai sai kin danganta ta dashi kenan? Ko kin fini sanin tsohuwar matar sace?." Suhaima tace, "Allah ya wuci zuciyar ki. Gani nayi ta taimake mu badan ita ba da Mamana ta kwana biyu da rasuwa ta sadaukar da tata rayuwar sabida ta Mamana." Mama ta kalli Suhaima tace, "tashi ki bani waje tunda kin gama basu labarin abinda ya faru." Suhaima da take mamakin Maman nata tace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ki tashi lafiya" ta fad'a tana shiga d'akin ta ta barsu a zaune kowa yayi shiru a wajan.        Mama ta kawar da zancen tace, "Asad akwai abubuwan da nake so a aiwatar a cikin kwanakin nan." Asad yace, "Umarnin ki nake jira." "Batun canja min wajan zama da muka fara mgana tun lokacin baya aka fara ginin wajan aka tsaya ina so a cigaba nan da sati zan koma can. Sannan duk ma'aikatan gidan nan a tabbatar an biya su albashin su domin bana tunanin ana biya a watannin baya, abu na gaba kuma matar ka Jidda." Zirrrrr zirrrr zirrrr wayar Asad ta fara vibration ya kalli kiran yaga gwamna ne ya d'ago ya kalle ta sai tace, "Pick it." "Godiya nake" ya fad'a yana d'aukar wayar ya saka a kunne. Ya jima yana amsa wayar kafin ya sauke ya kalle ta yace, "Taro na gaggawa na majalisar d'inkin duniya ya taso a England yanzu zan bar k'asar nan." Mama tace, "Kai da wa zaku tafi?." Yace, "Nida shamaki da zagi sai Uncle." "Jeka" ta fad'a jin babu Jidda a lissafinta yayi godiya yace, "Mama a dinga taya ni addu'a ina manta wasu abubuwan dana aikataa baya, koda an fad'a min bana sani nayi." Kai ta girgiza ya tashi ya fita yana fita zuciyar sa cike da jin dad'in maganar Jidda da ta katse aka rufa masa baya da kirari zuwa b'angaren sa. Yana fita bai jima ba Aliyu ma ya fita Mama ta kalli Hydar tace, "halin Aliyu ya canja kamar bashi ba ka lura da hakan?." Hydar ya murmusa yace, "Na lura mama, abin farin ciki ne ganin hakan ko babu komai an daina mana gori da halayyar sa." Ta girgiza kai alamun gamsuwa kafin tace, "Allah yasa ba wani shirin yake yi mana ba." Hydar ya amsa da amin daga nan shima yy mata sallama ya fita. *Bayan wasu kwanaki.*        Sati d'aya Asad yayi a London ya dawo aka cigaba da gudanar da mulki a satin ya ziyarci wata saukar alkur'ani ya yiwa daliban kyautar kud'i da kuma na alkur'ani mai girma. Yana k'ok'arin canjawa sosai amma bai canja d'in ba sai ya d'auko hanya sai ya karkace dan tuni jidda ta sake kamo lagon sa tsawa ko hantara ya daina ya koma mata kamar da sai abinda tace ake yi amma yana zuwa wajan Mama duk d ba sosai ba.          Aliyu kuwa kowa yasan ya canja bama kasafai yake zaman gidan ba wata rana bama a nan yake kwana ba yayi shiru har lokacin babu abinda ya aiwatar bincike yake a sirrance yana kama duk wani wanda yasan hana da hannu abinda aka masa, su Waziri tun suna jiran sakamakon ganin Asad ya haukace har sun hak'ura in suka yiwa Aliyu maganar sai yace yana sane kuma yana sane d'in akwai abinda yake shiryawa wanda yafi nasu. Hajiya Mama an fara farfad'owa ginin da take so ayi mata an gama cikin sati d'aya har ta tare a cewar ta ba matsayin ta d'aya da ragowar matan gidan ba duk da girman kan ba kamar baya ba. Jikin mai martaba ana ta samun cigaba sosai duk da akwai wanda basa son farfad'owar sa. *☆☆☆*         Bikin Rauda ya rage saura sati biyu an kawo lefe akwati goma sha hud'u ko wacce cike taf da kaya komai akwatin sa akayi masa y'an uwa da abokan arzuk'i sai murna kawai ake yi. An ta jeren gidan amarya a unguwar Tatari Ali quarters   gida d'ankarere mai kyau da tsari kowa yaje sai ya dawo yana santin gidan.           Suna zaune ana ta shara yadda shagalin kamu zai gudana duka matan gidan ana zaune ana hira ita tana gefe tayi shiru domin mugun zazzaɓi take ji a jikinta, Yaya Fariha ta kalle ta tace, "Wai amarya lafiya kike ana hira kin yi shiru?." Rauda tace, "wallahi zazzaɓi nake ji sosai ga ciwon kai." Yaya Shamsiyya tace, "Muda muke da Fariha kun manta ta kusa magana karatun ta? Duba mana ita ki bata magani bana son wannan zaman nata shiru wallahi." Yaya fariha ta k'arasa kusa da Rauda tace, "Kodai malaria ko typhoid shine yake damun ta, abinda zai faru ina jin ina da sabon sring a aljihun jakata dana siya a makaranta muka gwada wani abu bara na d'auki jinin ki aje a gwada dan mu san meye" ta fad'a tana d'aukowa daga Jakarta.       Jinin Raudan aka d'iba ta yago takarda daga Jakarta tace, "Maza Rahma jeki nan baya ayi wannan test d'in" ta fad'a tana rubutu ta bawa Rahma da kud'i wacce take zaune.  Rahma ta karb'a ta mik'e ta fita tace, "kifa yi sauri kar jinin ya daskare."         Rahma na fita Baba ya shigo yace, "Ah lallai yau an zo za'a cinye min abincin gida, ko wacce ta kwaso yara an tawo zaman hira kawai." Da yake sun saba da halin mahaifin nasu dukkan su dariya sukayi kawai aka gaisa ganin su tare shima sai ya zauna ana hirar dashi. "Ke kuma lafiya?" Ya fad'a yana kallon Rauda. Yaya fariha tace, "Zazzaɓin nan dai, na bayar dai yanzu ayi mata test na malaria da typhoid yadda zamu gane wanne ne yafi yawa sai ayi maganin sa kai tsaye." Baba yace, "Yau dai naga amfanin karatun ki." Ummulkhairi da take gefe tace, "Baba nima in mukayi waec wannan shekarar shi nake so nayi." "Sai kiyi ai" ya bata amsa yana tab'e bakin sa kafin yace, "Itama mijin tane yake biya ki jira kiyi aure kema mijin naki ya biya miki." Yaya Shamsiyya tace, "Ai ko mijin ta bai biya ba Baba mu zamu biya mata, Allah yana rufa mana asiri dukkan mu yanzu Alhamdulillah." Baba yace, "Masalaha mai kyau." Umma da Inna dai kanzil basu ce ba suna dai zaune suna jin me ake yi.         Rahma ce ta shigo da sallama ta mik'awa Yaya Fariha takardar tace, "Ashe gwajin ba wahala, nan da nan akayi ashe ma uku yayi wai ya manta ya had'a da gwajin ciki." Yaya Fariha tayi dariya tace, "Yo ina ruwan mu da gwajin wani ciki ana zaune lafiya" ta fad'a tana warware takardar tana dubawa.          Dummmmm gabanta yayi mugun fad'uwa a gigice tace, "Ke anya jinin dana baki ya gwada kuwa? Kodai anyi had'e dana wani?." Rahma tace, "A'a Yaya, babu kowa ma fa a lab d'in ni kawai aka yiwa gwajin." Yayar mu tace, "Lafiya?." Shiru tayi ta sake kallon takardar hannun ta yana rawa tace, "Ba lafiya ba, bara na sake d'aukar sample d'in naje da kaina a sake yi na gani." Baba yace, "Fad'a mana abinda kika gani har ya tayar miki da hankali haka." Tace, "bara dai a sake yi Baba wannan bai nuna daidai ba." Yayar mu tace, "Dalla Malama ki  fad'a. Wani ciwon ne Raudan!?" Ta fad'a cikin tsawa tana kallon ta. Umma da take gefe tace, "K'anjamau ce ko me Fariha?." Duk sai suka rud'a ta tace, "Gwajin da akayi mata ne ya tabbatar akwai ciki a jikin ta na sati biyu......!" [17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *068.*           A tare dukkan su k'irjin sa ya bada sauti mai k'arfi da hakan ya saka wasu daga cikin su dafe k'irji tare da runtse ido firgici ya mamaye fuskar su da zuciyoyin su nan take suka ji abinda basu tab'a ji ba. "Kee Fariha wanne irin ciki ana zaune qalau? Gwajin jinin Rauda nefa ba naki kona Ummi ba" Yayar mu ta fad'a tana kallon ta itama da alaamun tashin hankalin a tare da ita.          Yaya fariha idanunta ya fito waje sabida tashin hankali ta sake kallon takardar ta kalle su tace, "Abinda sakamakon ya nuna kenan shiyasa nace anyi kuskure wajan yin gwajin, gwara a sake daukar sample d'in a sake yi sai a tabbatar." Baba da ya kasa cewa komai sai baki da ya buɗe zuciyar sa kamar ana doka ganga yace, "Ya dai kamata a sake yi amma har na cikin a sake gwadawa." Umma da taji hawaye masu d'umi suna sakko mata daga idanunta ta girgiza kai tace, "Basai an sake yin gwajin nan ba abinda aka gani tabbas hakan ne, na fukanci hakan a yanayin ta daga jiya zuwa yau gudun kar zagi ya shiga zuciya ta sai na watsar da abin na barshi a rashin lafiyar da take fama da ita ne kawai. Amma sakamakon ku gaskiya ne Rauda nada ciki!." "Wannan wacce irin maganar banza ce Binta? Da bakin ki kike cewa Rauda nada ciki?" Baba ya fad'a a fusace yana kallon ta kafin yaja tsaki yace, "Fariha sake d'aukar jinin muje tare a sake yin gwajin mu gani." Rauda da take zaune kamar an dasa bishiya sai idanu da take binsu dashi amma ko kad'an ta kasa fahimtar ma abinda suke cewa,  tunda aka furta kalmar ciki shikenan sai kwakwalwarta ta tsaya cak ta daina aiki gabad'aya, tana ji dai suna ambatar ciki amma bata san me suke cewa ba.         Har aka huda fatar ta aka saka k'arfe cikin jijiyar ta aka d'auki jini bata sani ba wani wajan kawai take kallo zuciyar ta kamar ana kid'an kwarya sabida duka. Baba da Fariha suka fita falon yayi shiru baka jin motsin kowa sai sautin kukan Umma kawai da ya cika falon dan ita zuciyarta ta tabbatar mata da gwajin da akayi gaskiya ne ba k'arya ba. Inna tace, "Haba Binta kin bani mamaki wallahi, na d'auka kece mace ta farko da zakiyi shaida halayen Rauda na kamun kai amma sai gashi kece kika fara furta kalma mara dad'i a kanta. Gaskiya baki kyauta ba bai kamata ki d'auki zugar shaid'an ba har ki furta wannan kalamai akan Rauda." Yaya Shamsiyya duk da k'irjin ta da yake bugawa tace, "Abinda na gani kenan Inna, Umma bai kamata kiyi saurin yadda da abinda akayi kuskure wajan yin sa ba." Umma dai kanzil bata ce ba Yaya Babba kuma Yaya Ummi da Yaya Nafisa sunyi shiru basa iya cewa komai kowa zuciyar sa cike da tsoro jiran dawowar Baba kawai akeyi. "Tana ina dan Ubanta!" Baba ya fad'a da k'arfin gaske yana shigowa hannun sa rik'e da zarbad'ed'iyar bulala ya k'arasa wajan Rauda da ta rasa hankalin ta na wucin gadi.         K'arfi ya saka ya finciko ta babu zato babu tsammani ya ta fara jin saukar bulala, dukan shine ya dawo da ita hankalin ta ta fara kuka yana dukanta duk ta inda yaso amma ta daure hawaye kawai take yi bata ihu. "Ni zaki tonawa asiri Rauda? Me kike nema kika rasa a gidan nan da zaki bari wani yayi miki ciki?. Bikin ki saura kwana goma sha hud'u ki rasa abinda zaki zo mana dashi sai ciki Rauda?" Ya fad'a yana dukan ta da iyakacin k'arfin sa ta ko ina ita kuma tana kuka. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!" duka matan suka fad'a suna mik'ewa tsaye Umma kuwa kukan tane ya k'aru Inna na zaune kusa da ita dan ta rasa ma bakin magana.  Sautin bulalar Baba kawai ake ji a falon ganin dukan da Baba yake mata yayi yawa zai iya jawo mata matsalar Yaya Fariha ta k'arasa ta rik'e bulalar tana kuka tace, "Dan Allah Baba ka bar dukan ta haka, zama ya kamata muyi muji taya aka samu cikin duka ba shine mafita ba." Baba yana wuci muryar sa na rawa yace, "Fariha ko ki sakar min bulalar nan kona had'a dake" ya fad'a yana fincikar bulalar ya cigaba da dukanta zuwa lokacin fatar hannun Rauda da bayan ta da k'afafun ta duk sun fashe suna jini amma bai daina dukan ta ba. Sai a sannan ta fara kuka sosai har muryar ta ta dashe sabida kuka Yaya Fariha ta shiga tsakiya wai ko Baba zai daina dukanta amma sai ya had'a da ita dole tayi tsalle ta koma gefe taga ya ajjiye bulalar ya rik'e fuskarta yana marin ta ta ko wanne b'angare. Bakin ta da hancin ta suka fashe amma Baba bai daina dukan ta ba ganin hakan ya saka matan tasowa a guje suka janyeta suka tura ta d'aki suka kulle k'ofar dukkan su kuka suke har babar Yayar su, Yayar mu ta kalli Baba tana kuka tace, "Kayi hak'uri dan Allah mu zauna da ita aji waye yayi mata cikin, wannan dukan zaka iya kashe ta." Umma da take zaune tace, "in ta mutu sai me? Mutuwar itace ta dace da rayuwarta a yanzu. Bikinta sati biyu fa kacal ya rage da wanne ido zamu kalli Anas muce masa ciki ne da ita? Me muka yi mata tayi mana wannan sakayyar? Me ta nema ta rasa a gidan nan da zata je ta bawa wani kanta?. Duk lokatun baya da suka wuce batayi ba sai yanzu da yake tana son......." kasa k'arasawa Umma tayi sabida kuka da jirin da take ji duk da a zaune tane.        A guje Yaya Nafisa tayi kan Umma ganin kamar zata kifa ta rik'e ta tace, "Dan Allah Umma ki daina kuka, k'addara ce ta same mu muyi rokon Allah ya bamu ikon cinye jarabawar."  Umma tace, "So take ta kashe ni kawai Nafisa so take taga an fita da gawata daga gidan nan, in ba haka ba me take so wanda bata dashi a cikin gidan nan?, ina tarbiyyar da ilimin nata suke?. Tsakanina da Rauda Allah ya......." da sauri suka dakatar da Umma wajan fad'in, "Kar ki furta Umma dan Allah kiyi hak'uri, ku tsaya muji uzurin ta wataƙila fyad'e akayi mata."        Baba ya cillar da bulalar yana wuci ya zauna a kan kujera ya hard'e yatsun sa waje daya yana kallon wani wajan daban yana maimaita kalmar ciki a zuciyar sa, "Rauda tana da ciki kuma cikin shege a cikin gidana, bikinta saura sati biyu taje tayo min ciki dan ta wulaƙanta ni a duniya" sai kuma ya zabura ya sake nufar k'ofar d'akin da suka saka ta da sauri sukayi saurin tarewa yace, "In baku bani hanya ba wallahi zan had'a daku na zane." "Kayi hak'uri Baba in ka sake dukanta mutuwa zatayi" Yaya Ummi ta fad'a tana kuka sosai. Baba yace, "ta mutu d'in mana daman raywuata bata da amfani a yanzu, gwara ta mutu nasan mutuwa tayi da abinda zai faru nan gaba." "Asslamu alaikum" aka fad'a daga k'ofa aka shigo duk suka kalli wajan aka amsa a ciki banda Baba da ko gezau baiyi ba balle ya juya, Kawu Badamasi ne da Kawu Mansur suka shigo Yaya Nafisa tace, "Gwara da kuka Baba zai kashe Rauda." Kawu Badamasi yace, "Adamu zo ka zauna ka bar wajan nan." Baba yace, "in ba kashe yarinyar ciki nayi ba hankalina bazai kwanta ba." "Kasheta ba shine mafita ba, kazo ka zauna kawai." Kai ya girgiza kai ya juyo da baya ya zauna akaan kujera suma duk suka zauna Kawu Mansur yace, "Nafisa ce ta kira mu ta sanar damu abinda yake faruwa shiyasa muka taso muka zo dan a kamo bakin zaren, duka ba shine magani ba a halin da ake ciki." Kawu Badamasi ya kalli Umma da take kuka yace, "Haba Binta kiyi hak'uri mana ki daina wannan kukan komai zaiyi daidai in Allah ya amince." "Meye zaiyi daidai d'in? Ciki fa tayi ba gwara a kashe ta d'in a huta ba." "Haba haba, me kike cewa haka kamar ba ke ba? Dan Allah ki kwantar da hankalin ki." Kawu Badamasi yace, "Adamu ba'a neman mafita da duka, ka sassauta zuciyar ka dan Allah a kira ta a tambaye ta wanda yayi mata cikin." Baba ya kalle shi yace, "Bikin ta saura sati biyu yau, da wanne ido zan kalli wanda zata aura nace masa ciki ne da Rauda dan Allah?" Baba ya fad'a muryar sa na rawa kamar zai yi kuka. Kawu Mansur yace, "in kuma cikin nasa ne fa? Rauda tana da wanda take saurara ne in ba shi ba?." Dukkan su gaban su sai da ya fad'i Baba ya girgiza kai yace, "Anas bazai tab'a aikata wannan d'anyen aikin ba na tabbatar da hakan, sai dai wani daban amma bashi ba." Kawu Badamasi yace, "Tana ina?." Yayar mu tace, "Tana cikin d'aki Baba yayi mata duka sosai." "Kuje ku bata magani tasha in anjima zamu dawo sai ta sanar damu koma waye yayi mata cikin. Dan Allah kar wanda ya sake dukan ta, kar kuma wanda yayi mata wata maganar ku k'yaleta taji da abinda take ji itama dan na tabbata babu wanda a cikin ku ya kaita jin ciwon abinda ya faru."      Rauda da take jin duk abinda da ake cewa kanta ya sake yin nauyi hawayen ma sun tsaya cak tana kwance a kan tiles tana jan numfashi dak'yar kamar zai bar jikinta, kalmar Allah ya isa da Umma taso furta mata tafi komai d'aga mata hankali ta juya idanu bakinta duk jini haka hancin ta zuciyarta na rawa. Me zatayi me kuma zata ce? Da wanne ido zata kalli iyayenta?, da wanne ido zata kalli Anas?. Sai hawaye sharrr tuna yadda yake ta shirin zuwan bikin nan yanzu ashe maaa tana da ciki. "Na shiga uku!" Ta furta kanta na bala'in sarawa gefen idanun ta yayi ja jini ya taru a ciki sabida marin da tasha wajan Baba.       K'ofar aka bud'e daidai lokacin da take kwara amai tana daga kwance da sauri sakayo kanta suka kamata suka ga tana son kwacewa Yaya Ummi tace, "wayyo ciwon jikin ki ko? Sannu" suka kamata zuwa kan gado suka zaunar, Yaya Ummi ta cire mata hijjabin jikinta Yaya nafisa ta d'ebo ruwa aka goge aman da tayi ta jingina a jikin Yaya fariha tana sauke ajiyar zuciya. Dukkan su kuka suke tausayin ta ya dirar musu a zuciya Yaya Fariha tace, "Jikinta yayi zafi fa sosai." Yaya Nafisa ta k'araso ta goge mata hancin ta da bakinta da suke a fashe tace, "Ki daina kuka Rauda komai ya faru da Allah jarabawa ce, Allah zai tona asirin wanda yayi miki fyad'e in sha Allah." Yaya fariha tace, "A bata magani tasha ko zazzaɓin zai sauka." Yaya Ummi tace, "Ina da sudrex a jaka ta bara na d'auko" ta fad'a tana mik'ewa. Yaya Fariha tace, "A'a Yaya Ummi in tasha sudrex zata iya yin miscarriage yayi k'arfi sosai sai dai normal p.c.m." Yaya Nafisa tace, "To ya zube mana, ni naso ma dukan nan da tasha ya zube wallahi kowa ya huta." Akan mudubi Yaya Ummi taga p.c.m ta d'auko aka bata tasha tana sauke numfashi jikinta duk ya fashe sabida duka.      Kuka ta fashe dashi ta kank'ame Yaya Fariha tana kuka sosai duk suma sai suka sake fashewa da kuka Yaya Fariha itama ta rik'e ta tace, "Ki daina kuka Rauda, ki daina kuka dan Allah." Kukan take sosai ta kasa magana sai kanta da yake harbawa tana jan numfashi kamar zai bar jikinta.     Yaya fariha ta kwantar da ita suka suka zauna a gefen ta suna ta rarrashin ta duk da ta kasa magana, Yaya fariha ta mik'e tace, "Bara na bawa Ummulkhairi ta siyo mata maganin ciwon jiki" ta fad'a tana fita falon. Kamar gidan makoki haka falon yake Umma na zaune zazzaɓi ya rufe ta Inna ta kalli Fariha tace, "zo ki duba Umman taku." K'arasowa tayi ta tab'a jin Umma tafi zafi zau ta d'auke hannun ta ta d'auki biro da takarda ta rubuta maganin da za'a siyo har da allurar da zatayi Umma. Ummulkhairi ta bawa tace taje ta siyo ta had'a su da Khalil tace ya rakata, jikin Ummulkhairi a sanyaye suka tafi suka je suka siyo a pharmacy da yake can bakin titi suka siyo duka abinda ta rubuta suka d'auko hanyar dawowa gida. Farar mota suka gani a ajjiye suka zo giftawa ta motar suka ji ance, "Khalil ko?." Juyawa sukayi dukkan su suka had'a ido da wanda yake zaune a ciki ya sauke glass kad'an ya kalle su da murmushi Ummulkhairi tace, "Ina wuni." "Lafiya" ya amsa a tak'aice Khalil yace, "Kai ba wannan ne sarki ba?, wallahi shine, Anty Khairi sarki ne fa" ya fad'a a rud'e yana kallonta. Murmushi yayi kad'an yace, "shiii" alamun yayi shiru ya daina magana. Khalil yana ta murmushi yaga sarki Asad ya sauke numfashi yana bin su da kallo kafin yace, "Ina kuka je?." Khalil yace, "Mun siyo magani za'a bawa Anty Rauda bata da lafiya, Baba yayi mata duka har bakinta sai da ya fashe. Kasan wai me akace?" Sai yayi shiru yana kallon sa. Hankalin sa ya tattara gabad'aya akan Khalil ya girgiza kai alamun a'a Khalil yace, "Ance wai tana da ciki shine Baba ya mata duka jikinta duk ya fashe" ya fad'a kamar zaiyi kuka. "Kai Khalil baka da hankali?" Khairi ta fad'a tana talle masa k'eya taja hannun sa tana fad'in, "Wallahi na sake ji ka fad'awa wani wannan maganar sai na fad'awa Baba ya zane ka kaima, banza mai surutun tsiya" ta fad'a suna yin gaba tana jan hannun sa. "Duka!" Ya maimaita a fili yana kallon su har sukayi masa nisa bai d'auke idanun sa daga kansu ba, ransa yaji yayi mugun b'aci nan take abinda ya fito yi a sirrance ya fita daga ransa ya ya d'aga bak'in glass d'in motar yadda duk nacin ka baza ka gane waye a ciki ba ya juya motar ya bar unguwar yana ji zuciyar sa na tafasa gabad'aya komai ya tsaya masa jin kalmar duka bayan ance tana da ciki kuma.        Bayan sun koma aka yiwa Umma allura aka bata magani sai tayi bacci itama Raudan suka lallab'a ta Allah ya taimaka tayi baccin gidan ya zama shiru babu wanda yake magana kowa da nasa tunanin a zuciyar sa.   Sai yamma Rauda ta farka jikinta yayi mata tsami ta tashi zaune babu kowa a d'akin ta kalli fuskar ta a mudubin d'akin fuskar ta ta kumbura sosai ga jini a idanun ta ya taru sabida marin da tasha a hannun Baba. Sakkowa tayi daga kan gadon amma sai ta kasa tsayuwa sabida k'afar ta bazata iya d'aukar ta ba tayi saurin dafa bango tana tafiya kanta ko d'ankwali zuwa d'akin Umma. A falo ta tarar dasu har Umma suna zaune a gefen ta suna ta bata hak'uri suka hango Rauda tana tafiya tana layi kamar zata kifa, fuskar ta da suka a kunbure shine ya sake karya musu zuciya ta k'araso gaban Umma ta zube maganar ta bata fita sosai tace, "Umma dan Allah ki...." Umma ta runtse idanunta tace, "Ki tashi ki bani waje Rauda wallahil azim bana son ganin ki, bana son kallon fuskar ki ki tashi kafin na saka k'afa nayi ball dake a wajan nan." Yayar mu ta taso ta d'aga Rauda daga wajan tace, "Koma ki huta ranta a b'ace yake sosai bazata saurare ki ba." Shigar da ita tayi d'aki ta zaunar da ita ta zauna itama a gefen ta tace, "Rauda waye ya miki ciki? Anas ne kowa?." Sai kawai ta kuma fashewa da kuka ta kifa kanta a kafad'ar Yayar mu tana kuka sosai ita kuma tana bubbuga bayanta a hankali tausayin ta na sake shiga jikinta dan su kam sun yadda da ita tunanin su fyad'e akayi mata ba yin kanta bane.         Yaya Nafisa ta shigo da abinci da shayi mai zafi ta zauna tace, "Rauda karb'i shayi kisha sai kici abinci." Kai take girgizawa tace, "bazan iya sha ba, bazan iya ba. Dan Allah ku fad'awa Baba ya kashe ni bana son rayuwata nima." Duk sai jikin su ya kuma yin sanyi suka dinga rarrashin ta amma baya aiki dan batayi shiru ba kuma bata ci komai ba. Wanka suka saka tayi da ruwa mai zafi sanda ta fito sai da suka tsorata da shatin bulalar jikinta duk bata da hasken fata amma fatar tayi ja sosai duk ta tashi wani wajan ya fashe. Kaya ta saka tayi sallar la'asar a zaune bayan ta idar ta d'ora hannun ta akan cikinta tunawa da tana da ciki sai taji kamar ta had'd'iye zuciya ta mutu da bak'in cikin da take ji a ranta har gwara ma ace ta mutu ta huta kawai. Basu barta ita kad'ai ba dan zuciya zata iya d'aukar ta yiwa kanta illah. Har magriba babu wacce ta tafi a cikin su bayan anyi sallah ne su Baba da Kawu Badamasi suka shigo aka kira kowa aka bada umarnin fito da Rauda. Suna rik'e da ita aka zaunar da ita a k'asa suma duk suna k'asa iyayen ne kawai a kan kujera. Kawu Badamasi yace, "Haba Adamu, wannan wanne irin hukunci ka yiwa wannan yarinyar? Kalli fuskar ta da idon ta yadda ya koma." Shiru yayi suma kowa yayi shiru Kawu Badamasi ya kalle ta yace, "Rauda!." Ta d'ago a hankali ta kalle shi yace, "Subahanallah haka idon naki jini ya taru? Gaskiya baka kyauta ba duka ba hukunci bane." Shiru aka kuma yi ba'a amsa ba yace, "Rauda tsakanin ki da Allah cikin waye a jikin ki?, kinga maganar bikin akeyi ga wannan abin da ya taso a yanzu babu maganar aure dan ba'a aure da ciki. Cikin waye a jikin ki." Shiru tayi ta kasa magana sai kuka Kawu Mansur yace, "ba kuka akace kiyi mana ba, tambaya ce guda d'aya kawai ki bamu amsa." Nan ma shiru batayi magana ba Baba ya fusata yace, "Kun gani ko? Bata jin ko wanne yare sai duka ku barni na b'alla ta in yaso sai tayi bayani." Kawu Mansur yace, "Dan Allah ka sakawa zuciyar ka salama, ka barmu zamu tambaye ta da kanmu." "Rauda ke muke saurare cikin waye a jikin ki?." Nan ma shiru ba amsa sai kuka Kawu Badamasi  ya kuma cewa, "Ko shi Anas d'in ne yayi miki?." Ta girgiza kai alamun a'a tana kuka Baba ya fusata ya mik'e ya k'arasa inda take ya d'aga hannu zai dake ta yaji ance, "Dan Allah Baba ka bar dukan ta haka!." Cak ya tsaya jin muryar wanda ya sani a kwanakin baya bai sauke hannun ba ya juyo yana kallon inda yaji maganar kowa ya zubawa k'ofar ido ana kallon wanda yake tsaye cikin zallar al'ajabi da tsoro da kuma mamaki........... [17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *069.*          A tsaye yake cak fuskar sa a bayyane duk da babu annuri a cikinta amma tayi haske sai shek'e take yi idanun sa akan inda Baba yake yana shirin dukan Rauda nan kawai yake kallo dan tunanin sa a wajan yake. sanye yake da manyan kaya na sakarai daga kallon aikin jikin su basai an fad'a ba kasan ba k'aramin mutum bane zaiyi wannan shigar sai wanda ya amsa suna basarake kuma mai abin hannu. Kansa yayi nadin buzaye ya zagaye fuskar sa da hirami kalar kayan jikin sa takalmin k'afar sa irin aikin jikin kayan sa ne yana tsaye cak cikin nustuwa da ta game ko ina na jikin sa yana kallon su. Dukkan su mik'ewa tsaye sukayi Baba ya juyo da sauri ya k'araso wajan yana jinjina yace, "Allah yaja zamanin mai martaba barka da zuwa, bismillah" ya fad'a yana bashi hanya alamun ya wuce shi kuwa Rauda kawai yake kallo dan yanayin ta ya bashi tsoro. "Barka da zuwa ranka ya dad'e" Kawu Badamasi ya fad'a yana kallon sa cikin girmamawa suke maganar. Sai a sannan ya d'auke idon sa daga kanta ya murmusa kad'an Baba yace, "Ranka ya dad'e tsayuwa ba taka bace, ayi mana alfarma a zauna dan Allah." Ba musu ya taka har tsakiyar falon da takalmi a k'afar sa gujerar da ta kasance babba a ciki ya zauna, Baba zai zauna a k'asa yace, "Dan Allah Baba" ya fad'a yana nuna masa kan kujerar kusa dashi alamun ya zauna. Baba yace, "Wane mutum" ya fad'a yana zama a k'asa duk kowa ya zauna a kasa sai ahi kad'ai ne a akan kujera.          "Barka da zuwa ranka ya dad'e, da fatan mai martaba yazo lafiya?." Shiru ya d'an yi kafin yace, "Alhamdulillah, fatan bamu zo a lokacin da bai kamata ba." "Ko wanne lokaci mai martaba yaso ziyara daidai ne a wajan mu, mai martaba ya ziyarce ka ma ai babban abin alfahari ne a gare mu baki d'aya" Kawu Mansur ya fad'a da girmamawa shima. Kwarjinin sa ya cika falon haka khamshin sa gabad'aya matan tunda suka gaisa sun kasa cewa komai har basa son dagowa ma su kalle shi sabida kwarjinin da yake musu kallon sama sai ka shirya balle magana. Shiru ya ratsa falon shi ya rasa me zaice nauyi yake ji a zuciyar sa ya kasa furta komai su kuma jiran yayi masa suke yi. Dak'yar ya iya had'a kalmar yace, "Ina neman afuwar ku dukka akan abubuwan da suka faru a baya, ina fatan za'a yafe ni." Baba yace, "Mai martaba da kansa yake neman afuwar mu? Mu su waye da har mai martaba guda zai mana laifi..? Allah yaja da ranka ai mu bamu isa mu rik'e mai martaba a zuciyar mu ba duk abinda ya faru mun d'auka k'addara ce kuma ta riga fata." Ya girgiza kai yana cize bakin sa yana kallon mutanen falon duka fuskokin su babu annuri ga Umma a zaune kamar mara lafiya sai yaji jikin sa ya sake jin sanyi. Ya d'an jima kafin ya kuma cewa, "Baba ina neman alfarma a wajan ka." Baba ya gigice ya gyara zama yace, "Allah ya kara maka lafiya ai umarni kawai za'a bani amma ina mai martaba ina neman alfarma a waje na." "Akwai ambulance a waje ina so za'a kaita asibiti" ya fad'a a sanyaye ba tare da ya kalli Baban ko ita Raudan ba. Baba yace, "Umarni ne ba alfarma ba, duk abinda mai martaba yace an gama." Asad yayi shiru ya d'auki waya yana dannawa jim kad'an sai ga nurses guda biyu mata sun shigo falon suka zube a gaban sa suka ce, "Mun amsa kira ranka ya dad'e." Da hannu ya nuna musu Rauda jiki na rawa suka k'arasa inda take suka duk'a sukace, "Ranki ya dad'e sannu" tare suka kama Rauda suka fita da ita zuwa waje, suka sake dawowa aka rik'e Umma suka sake fita Yaya Ummi da Yaya Fariha suka bisu dan sunji dad'in zuwan da kodan Rauda ta samu kulawa. Asad yaja numfashi ya lumshe ido ya buɗe zuciyar sa na dukan tara tara yace, "Nasan zakuyi mamakin ganina a nan, a fara samar mata lafiya komai zai biyo baya. Alfarma a gare ku gabad'aya dan Allah a bar maganar a nan." Kowa mamaki ya bayyana akan zuciyar sa sai kallon kallo suke yi kowa tunanin sa ta yaya yasan maganar? Kenan daman ita ta kawo shi kome?. Baba ya gyara zama yace, "Ranka ya dad'e abinda ya faru fa ita Raudan cikin....." da hanzari ya katse Baba yace, "Baba dan Allah wannan kalaman su daina fitowa daga bakin ka." Baba da mamaki yace, "Ranka ya dad'e bikin ta ya kasance saura sati biyu kawai, da wanne ido zan kalli shi wanda zata aura nace masa tayi cikin shege...?." "Hasbunallahu wani'imal wakil!" ya furta yana dafe kansa ji yake kamar ya toshewa Baba baya son abinda yake furtawa ko kad'an akan cikin da ya kasance na halak wanda aka same shi da aure, ga kuma zancen wani banza da yake masa wanda bazai tab'a mallakar abinda ya mallaka ba har abada shine ya saka shi yin salati ba tare da ya shirya ba. Jin hakan sai Baba yace, "Tuba nake ranka ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ka, na bar maganar sai ta samu lafiyar kamar yadda aka umarce ni." Kai Asad ya girgiza kai kafin ya kalli sauran ragowar matan yaga biyu sun ragu alamun sun bi su Umma sai ya dawo da kallon sa ga Baba yace, "Zan koma, amma zan dawo" ya fad'a yana mik'ewa tsaye duk sai suka mik'e shima har waje suka raka shi ana godiya ya shiga bayan mota ya sauke glass bayan ya shiga yace, "Baba duka ya k'are dan Allah" ya fad'a a tausahe yana kallon Baba. "An gama ranka ya dad'e, Allah ya kiyaye hanya." Glass d'in ya d'aga aka ja motar suka bar wajan kowa yabi motar da kallo da mamaki a zuciyar dukkan su. Ciki suka koma Baba ya zauna Kawu Badamasi yace, "Adamu mai martaba da kansa yazo gidan nan ya ceci Rauda daga dukan da kake mata, ya akayi yasan abinda yake faruwa har yazo ya cece ta? Abubuwan da suka faru a baya tsakanin shi da gidan nan ban d'auka zai sake waiwayo ahlin mu gabad'aya. Meyasa yake jin haushi dan kana kiran cikin jikin Rauda na shege?  Anya kuwa ba......" Sai kuma kawu Badamasi yayi shiru yana jijjiga kai jin girman abinda zai fad'a da kamar wuya ya kasance. Yayar Mu tace, "Abinda ya daure min kai kenan Kawu ya akayi yasan abinda yake faruwa? Bibiyar lamarin gidan nan yake ko me? In bibiya yake akan me to muda ba wata alaqa ce a tsakaninmu dashi ba?. Aure ne ya had'a kuma ya raba meyasa yazo a wannan lokacin har yake neman alfarma a haka duk da tarin matsayin da yake dashi?." Kawu Mansur yace, "Gashi mun tabbatar da saki a tsakanin su har takardar tana hannun Yaya Adamu dukkan mu munga takardar sakin a lokacin me hakan yake nufi?." Baba ya sauke numfashi yace, "ni nama rasa bakin magana wallahi, amma mu jira ta samu lafiya itace zata warware mana komai. Babban tashin hankalina shine Anas." "Mu bari zuwa gobe ai komai zai daidaita in yaso sai ayi maganar Anas daga baya." Baba ya kalli Yaya Shamsiyya yace, "Kira Ummi muji a wanne asibitin suke." "Na kira su bayan fitar ka wai asibitin da Rauda ta kwanta lokacin da akayi mata aikin k'afa suka nufa." Baba ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokacin kafin yace, "ku tashi ku wuce gida kuma anyi i'sha" ya fad'a suna tashi suka fita domin yin sallah.            Karb'ar gaggawa aka yiwa Rauda aka kwantar da ita nan da nan aka fara bata kulawa ta musamman wacce zatayi gaggawar taimakawa jikinta wajan dawowa daidai. Umma jinin tane ya hau itama aka saka mata ruwan da bp zaiyi k'asa nan da nan bacci ya kwashe su duka. Yaya fariha ta tafi gida Yaya Ummi ta yiwa mijin ta waya ta sanar dashi zata kwana ya kai y'ay'an ta gidan su wajan Inna. Asad tun bayan da ya koma guest house shi kad'ai ya zauna ya zuciyar sa cike da tunanin abinda ya faru gabad'aya ya rasa abinda yake damun sa farin ciki yake ji ko akasin sa bai sani ba, waya ya d'auka ya kira Dr Yasir babu b'ata lokaci ya d'auka yace, "Ranka ya dad'e, Allah yaja zamanin ka an gama komai an basu kulawar gaggawa dukkan su sun sami bacci." Shiru yayi bai amsa ba na wani lokaci. Dr Yasir ya fahimci karin bayani yake so hakan ya saka yace, "Allah yaja zamanin mai martaba komai lafiya a b'angaren k'aramar, hatta abinda yake jikinta yana nan lafiya babu abinda ya same shi." Sai a sannan ya sauke numfashi ya sauke wayar daga kunne sa ya ajjiye a gefe ya jingina da kujera yayi shiru yana kallon sama. Inda yasan ciki ne zai bayyana a abinda ya faru da bai bar hakan ta kasance ba duk da daman ba'a son ransa ba amma da yayi k'ok'arin rik'e kansa, k'aramin tsaki yaja tunawa da bikinta wai saura kwana sha hud'u a bayyane yace, "Bata da hankali ne." Sai kuma yayi murmushi tunawa da cikin sane fa a jikinta kuma silar sa dole a fasa auren ta da wani duk da ko babu cikin ma sai an fasa tunda matar sace, d'an dukan kansa yayi yana tunanin ta wacce hanya kuma zai bi ya cewa su Baba cikin sane a jikinta?. Numfashi ya sauke ya kalli wayar sa yaga tana haske ganin mai kiran sai ya d'auka ya saka a kunne, "Okay good" abinda ya furta kenan ya sauke wayar daga kunne ya mik'e tsam ya fita drivern sa yaja suka fita daga gidan gabad'aya. *☆☆☆*          Jidda na zaune a b'angaren sa a falon sa na sama duk ranta a b'ace yake hankalin ta kuma a tashe, ganin zaman bazai kai labari ba sai ta mik'e tana ta zagaye har ta fara jiyo takun sa ta juya ta ganshi ya shigo yana waya yana shigowa falon ya sauke wayar daga kunnen sa. Jidda ta matso kusa dashi tace, "My king ina kake zuwa a cikin kwanakin nan kai kad'ai? Ko dogarai baka d'auka fitar sirri kake yi kuma sai dare na kasa fahimta." Kallonta yayi ya sakko da idanun sa ga cikin ta sai yaji wani iri a zuciyar sa ya d'auke kai baice mata komai ba ya wuceta zuwa d'aki, ta d'aga kafa zata biyo shi ya d'aga mata hannu ya girgiza yatsa d'aya dole taja ta tsaya shi kuma ya wuce zuwa d'akin sa ba tare da ya sake kallon ta ba. Juyowa tayi ta sakko daga saman a guje ta fita zuwa b'angaren ta aka rufa mata baya masu rik'e alkyabbar ta gudun kar taja k'asa sai gudu suke sabida sauri take yi sosai. Tana shiga b'angaren ta ta dakatar dasu ta shiga falo na biyu ta tarar da hasken gabad'aya a kashe ta kunna idanun ta ya fad'a cikin na Aliyu da yake a kan kujera yana kad'a k'afar sa, tsoro ya mamaye mata zuciya ta firgita ya kalleta ta k'asan idanu sai yayi murmushi ya mik'e tsaye yace, "Meye shirin ku na gaba akan Mama?." Baya take ja tana girgiza kai tace, "bamu da wani shiri." Baki ya tab'e ya girgiza kai zuciyar sa nayi masa mugun ciwo yana cize bakin sa ya lumshe idanu ya buɗe baice komai ba kawai ya fita ya bar mata falon ma gabad'aya. "Na shiga uku na ni Jidda me na jawowa kaina haka?" Ta fad'a zuciyar ta na bugawa domin ita kad'ai tasan hatsarin kasancewar Aliyu a cikin gidan nan ba k'aramin tashin hankali bane a gare ta. "Mum!!" Ta furta da k'arfi tana zama jagwab akan kujera ta dafe kanta kawai sai ta fashe da kuka hankalin ta a matuk'ar tashe yake zuciyar ta karkarwa take yi sabida tsoro, kai take girgizawa tace, "dole nayi maganin sa da kaina, dole na kashe Aliyu bazan barshi ya zame min barazana a cikin gidan nan ba, dole naga bayan sa da kaina zan gudanar da wannan aikin" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki tana tunanin irin hanyar da zata bi dan ganin bayan Aliyu.       A b'angaren Mama tana zaune tana waya ita kad'ai a bedroom d'inta tana fad'in, "Ina kake zuwa ne Asad? Kwana biyu kana fita babu wanda ya sani ina kake zuwa kai kad'ai?." Shiru tayi alamun yana bata amsa kana tace, "yadai kamata ka cigaba da kulawa bana son wata matsalar ta sake faruwa koda nan gaba." Shiru tayi kafin ta datse wayar ta sauke numfashi tana jin farin ciki a ranta komai yana tafiya daidai sai kuma tace, "Mai martaba." Shiru tayi tace, "ya zama dole a hana bakin sa buɗewa in hakan ta kasance I'm in trouble" ta fad'a tana tashi da gaggawa ta saka alkyabbar ta ta nufi b'angaren sa. Tana shiga ta tarar da Dr da yake kula dashi ya kalle ta yace, "Good day madam." Da yake bature sai tace, "How was your work." "Fine ma'am." Kallon sa tayi suka had'a ido sai ta d'aga masa kai shima ya d'aga mata kawai sai ta juya ta fita shi kuma ya d'auko allura a aljihun sa ya balle kanta yaja a sirinji ya zuba Mai martaba a cikin ruwan da yake shiga jikin sa. *☆☆☆*       Washe gari. Rauda jikinta ta ya samu k'wari kumburin fuskar ya ragu sai dai har lokacin akwai shatin duka a jikin ta idanun ta kuma akwai jini a ciki amma ta samu k'arfi babu laifi. Umma ma taji sauk'i amma jinin yak'i sauka sabida bata cire damuwa a zuciyarta ba. Rauda kallon Umma kawai take a inda take kwance ita kuma tak'i kallonta gabad'aya hakan ne yake sake tayar mata da hankali taji gabad'aya komai baya yi mata dad'i. Tana shirin sakkowa daga kan gadon taje wajan Umma aka turo k'ofar d'akin aka shigo da sallama. Anas ne ya shigo shida Baba ya k'araso inda Umma take ya duk'a har k'asa yace, "Barka da safiya Umma, ya k'arfin jiki?." Umma sai taji hawaye yana k'ok'arin taruwa a idanun ta ta daure tace, "Jiki Alhamdulillah Anas." Yace, "ban san abinda yake faruwa ba sai yanzu muka had'u da Baba yake sanar dani duka baku da lafiya, Allah ya k'ara lafiya yasa kaffara ce." "Amin" Umma ta amsa a tak'aice muryar ta na rawa sosai. Mik'ewa yayi ya k'arasa inda Rauda take yace, "Subahanallah meya same ki haka?." Shiru bata amsa ba sai yace, "ya jikin naki?." "Da sauk'i" ta amsa idanunta na k'asa murya na rawa sosai. "Allah ya k'ara lafiya" ya furta yana binta da kallo gabansa hana fad'uwa haka kawai. Ta amsa da amin kafin ya kalli Baba sai yaga sun had'a ido ya sauke nasa k'asa yace, "Baba zan koma, Allah ya basu lafiya gabad'aya." Baba yace, "Amin Anas, da mun koma gida zan sanar dakai dan ina neman ka." Anas yace, "Baba amma dai lafiya dai ko?." "Kar ka damu lafiya lau" Baba ya furta ganin ya rud'e lokaci d'aya. "Shikenan Baba, Allah ya basu lafiya" ya fad'a yana yi musu sallama ya fita Umma ta bishi da kallo kawai sai ta fashe da kuka ita kanta Raudan Kukan take dan karamcin Anas a gare su bai cancani abinda tayi masa ba. Baba yace, "Zaki ci uwarki ai, yanzu kika fara kuka ai; wallahi matuk'ar baki fad'a min wanda kika bawa kanki wallahi sai kin bar min gidana." Baba kuma cewa, "Da wanne ido kike so na kalli yaron nan?, kawai sai nace masa kina da cikin shege Rauda....?. Kin cuce ni wallahi, kuma bazan yafe ba." Jin abinda yace sai ta k'ara k'aimi wajan kuka hankalin ta ya tashi ta diro daga kan gadon zatayi magana Baba ya fita bai saurare ta ba ta kalli Umma taga ta kulle idanunta alamun bazata ji ba sai kawai ta cure a wajan tana kuka. Nan da nan zazzaɓi ya sake rufeta da ciwon kai Allah ya shigo da nurse akayi gaggawar sake saka mata ruwa da allurai. Sai bayan sallar azahar ta farka taga y'an uwanta wasu suna nan wasu basa nan ana ta rarrashin Umma da alama kuka take tayi har lokacin. Sauka Rauda tayi daga kan gadon ta shiga band'aki tayi alwala ta fito ta tayar da sallah a zaune dan k'afar ta har lokacin ciwo take bazata iya sallah a tsaye ba. Tana sallah tana kuka bayan ta idar ne take jin sautin muryar Umma tana cewa, "me na yiwa Rauda tayi min wannan sakayyar? Ta rasa abinda zata saka min dashi sai cikin shege..." Sai ta sake fashewa da kuka. Yaya Ummi tace, "Dan Allah ki daina Kuka Umma kinga ance jinin ki yak'i sauka sabida damuwar da take ranki dan Allah kiyi hak'uri." "Nayi hak'uri fa kika ce, yanzu fasa aurenta za'a yi fa saboda cikin jikinta wanda bamu san waye uban sa kuma kice nayi hak'uri?. Fasa auren bashi ne matsala ba babbar matsalar shine cikin jikin ta." Shiru Yaya Ummi tayi ta kalli Rauda da take kuka itama tace, "Rauda ki sanar damu cikin waye a jikin ki dan Allah ko hankalin Umma zai kwanta." "Meye amfanin fad'ar Ummi? An riga anyi fa da ace ba'a yi bane sai a san wane dan a d'auki mataki sabida kar ayin to an riga da an aikata, ta rik'e a ranta koma waye karta fad'a kanta ta cuta" Umma ta fad'a tana goge idanunta. Yaya Ummi cikin tsawa tace, "Baza ki fad'i wanda yayi miki ba?." "Shineee!" Ta fad'a da k'arfi tana fashewa da kuka. "Shine wa?" Yaya Ummi ta tambaya da k'arfi tana kallonta rai a b'ace.  Rauda ta sake fashewa da kuka tace, "Shine!." "Akace miki shine wa? Anas?." Ta girgiza kai alamun a'a tace, "to shine wa?." Umma ta fusata rai a b'ace tace, "bazata fad'a bata so take taga na mutu an fitar da gawata kinga shikenan ai ta huta." Rauda ta runtse ido jin abinda Umma ta fad'a tana kuka sosai tace, "Asad.......!" Sai ta sake fashewa da kukan da yafi na d'azu fitar da sauti.[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks @nanahaleema11 *072.*          Numfashi yake saukewa a hankali yana kallon fuskarta da ta jiqe da hawaye ko kad'an baya k'aunar ganin kukan ta gabad'aya yana tayar masa da hankali sosai shiyasa kawai ya zuba mata ido yana kallo cikin rashin sanin abinda zai ce mata wanda zata amince dashi nan gaba. Sarawa kansa yake yi ya runtse ido ya kalli wayar sa da yaji tana vibrating yaga sunan Hydar yana yawo a kai ya d'auke kansa ya dawo da kallon sa a gare ta a daidai wannan lokacin tace, "ka daina bibiyata ka k'yale ni nayi rayuwata kamar yadda ka barni, kaje kaji da matar ka nima zanji da wanda zai aura kowa ya rik'e abinda ya mallaka bayan rabuwar mu, cewa matar kace ni da kake yi kai kasan ba gaskiya bane gwara ka daina dan k'arya ma haram ce" Sai kuma ta dafe kanta tace, "ka gama cucata, da wanne ido zan kalli Anas nace masa ina da cikin ka? Wanne kallo zai yi min?, fasiqa, mayaudariya ko kuma mazinaciya? Wanne zai d'auka a ciki?. Meyasa kayi min haka wanne laifi nayi maka ka yanke min wannan hukuncin mai d'aci?" Ta k'arasa fad'a murya na rawa ta zube a wajan tana kuka sosai. Kunnuwan sa babu abinda suke jiyo masa sai kalmar wanda zata aura Anas yafi komai d'aga masa hankali da tafarfasa masa zuciya, dukkan kalaman data fad'a akan sa baiji zafi ba sai sunan Anas data ambata nan take yaji kamar ana tafasa jinin sa idanun sa suka canja kala haka fuskar sa tayi ja sosai cikin muryar sa da bata da hayaniya yace, "Kar na sake jin kin ambace shi matsayin wanda zaki aura." A fusace ta mik'e tsaye tace, "Sai na ambata d'in ina ruwan ka dani! Duk cutar da kayi min har kana  bakin kallona kace kar na sake kiran Anas matsayin wanda zai aure ni? Ka manta wulaƙanci da kayi min a Egypt? Ka manta wanda kayi min a cikin gidan mu? Ka manta wanda kayi min a cikin gidan ka...?. Ka saka na aikata abinda ban tab'a yi ba, na sab'awa Allah da laifi mafi muni" ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Shi mamakin tsiwar ta yake yi bai d'auka tsiwarta ta kai haka ba duk da bata iya kallon idon sa tayi magana amma tana k'okarin fad'a masa duk abinda yazo bakin ta shi kuma ko kusa baya jin haushin ta dan yasan akan gaskiya take shima akan tasa gaskiyar yake. "Matata ce ke, na haramta miki ambatar sunan wani a gaban idona ko a bayan idona." Yadda yayi maganar cikin bada umarni da izza a cikin ta sai da ta d'aga ido ta kalle shi suka had'a ido tayi saurin d'auke nata idon tace, "Ni ba matar ka bace, a da na zama matar ka ta y'an kwanaki qalilan yanzu ni ba matar ka bace, ina so na shaida maka wannan tsinanen cikin wallahi sai na zubar dashi hankalina zai kwanta, bazan tab'a amincewa a fasa aurena da yake gabatowa ba." Cize bakin sa yayi ya lumshe ido ya lura bata jin magana ko kad'an ta kasa fahimtar dauriyar maganar yake amma shi kad'ai yasan irin ciwon da kansa yake yi masa, inda ya kasance mai saurin hannu da babu abinda zaj hana bai mare ta ba, idanun sa ya wara waje ya fiddo su dukka suka fito sun koma jajaye yace, "ki nutsu ki dawo hankalin ki ki san da wanda kike magana kar ki sake kuskuren yi min shouting." Banza tayi masa ta kawar da kanta gefe tana kuka ta zauna a akan kujera tayi tagumi ta rasa wanne ma irin tunani zatayi, "Tun farko Baba ne ya amince da aure na dakai ba nice na amince ba, ta silar ka abubuwan da basu tab'a faruwa dani ba sun faru. Ta silar ka na zama bazawara ban tab'a hango kaina a wannan matakin ba sai da ka shigo rayuwata, ta silar ka Ummana tayi min Allah ya isa..." Sai kuka yaci k'arfin ta ta kifa kanta akan cinyar ta tana kuka sosai mai tab'a zuciya. "Ya salam!" Ya furta a bayyane ya rasa meyasa take son yin kuka har haka, k'arasawa yayi inda take ya zauna a gabanta akan carpet yana kallon yace, "D'ago ki kalle ni." Kai take girgizawa tace, "Bana son ganin fuskar ka, na tsane ka bana sonka." Shiru yayi na wani lokaci yana jin d'aci da rad'ad'in kalmar bana sonka da tace ya sauke numfashi yayi tagumi kawai yana kallon ta. Muryar sa a sanyaye yace, "Dan Allah ki daina kuka kina k'ara min ciwon kai, bana so naga kina kuka please ki bari." Ta d'ago ta kalle shi tace, "kasan da hakan kasa na sab'awa Allah?." Kawar da fuskar ta take so tayi yayi saurin rik'e fuskar ta ta kulle ido yace, "Dan Allah ki bud'e idon ki." Bata bud'e ba ya jijjiga mata fuska ta buɗe idon a hankali suka had'a ido yace, "Kice bakya sona." Idonta ta saukar k'asa taji kamar an kulle mata bakin ta ta kasa magana ko kad'an kwarjinin sa ya mamaye duka ilahirin jikin ta nan take jikin ta yayi mugun sanyi. Ganin hakan ya saka ya saki fuskar ta ya rik'e hannun ta yace, "Na koyi doguwar magana tunda aka shiga wannan situation d'in Rauda." Hannun ta kwace tace, "ka daina rik'e ni, ka fad'a min abinda zaka ce ina so na koma gida." "Rauda ban sake ki ba." "Ka sake ni." Ya sauke numfashi ya dafe kansa da dukkan hannayen sa zuwa wani lokaci. Shiru sukayi dukkan su hannun sa na rik'e da kansa kusan mintina goma haka kafin yace, "A Cairo dana sake ki na mayar dake ko a'a?." Ido ta goge a fusace tace, "ka mayar dani. Amma ka kuma zuwa har gida ka sake ni kai da kanka kaga takardar da ka rubuta meyasa kake son yin wasa da hankalin mu ne dan kaga kai wani abu ne a duniya?." Kamar zaiyi kuka yace, "Rauda bani bane, ki yarda dani banzo gidan ku ba. Aliyu ne!" Ya fad'a muryar sa raunane yana kallon ta. Damm gaban ta ya buga jin abinda yace ta kalle shi da sauri sai kuma ta d'auke kai ta tsaya cak kwakwalwar ta tana tuno mata abinda ya faru a ranar da yazo da kamannin sa da maganar sa da komai nasa na Asad ne bana Aliyu ba. Murmushi tana girgiza kai tace, "Kai ka nuna min zanen hannun ka kace min dashi kad'ai ake banbance ku da Aliyu koshi bai san da wannan zanen ba a ranar da kazo naga wannan zanen a hannun ka. Kana so kayi wasa da hankalina ne kawai amma ta ya akayi Aliyu yasan da abubuwan da suka faru a Cairo?. Ya akayi yasan ka sake ni har yazo ya sake sakina?, ya akayi yasan saki d'aya kayi min yazk ya k'arashe biyun?. Ya akayi ya samu rubutun ka?, Ya akayi maganar Aliyu ta koma maganar ka sak har yadda kake magana shima yayi?, Ya akayi Aliyu yasan ma akwai iddar ka a kaina har yazo ya sake sakina?. Yace min Muwaddaty ya akayi yasan sunan nan? Baka tab'a fad'a a gaban sa ba balle ace ji yayi ya akayi ya san dashi?. Indai har ba kai bane ya akayi yasan da wad'annan abubuwan?" Ta fad'a tana kallon sa yayi shiru shi kuma baya kallon ta. Gabad'aya ta daure shi da jijiyoyin jikin sa tabbas duk abinda ta fad'a gaskiya ne shi kansa bashi da amsoshin tambayar tata hakan ya saka shi yayi shiru kawai baice komai ba yana sauraron abinda take cewa har ta kai k'arshe. Tayi murmushi tace, "Baza ka tab'a wasa da hankalina ba, a baya duk da abinda ya faru ina ganin mutuncin ka sosai kasancewar kaine shugaba a garin nan ina girmama hakan amma a yanzu ka zubar da wannan mutuncin in za'a ce min ga wuk'a na kashe wanda bana so tabbas kai zan fara kashewa. Ka daina k'ok'arin yawo da hankalina ko kace zakayi min wayo in iyayena sun amince dakai kai kasan ni bazan tab'a amincewa da kai ba, iya zaman da mukayi na fahimce ka daidai iyawata." Kallon ta yayi akayi sa'a tana kallon sa murya a raunane yace, "Bana k'arya Rauda a kanki bazan fara ba, bazan miki k'arya dan cikar burina ba bayan nasan haramcin da yake cikin abinda nake son aikatawa..." yayi shiru na wani lokacin kafin ya kuma cewa, "A kan gaskiyar ki kike banga laifin ki ba nima a kan tawa nake Muwadda, amma ina so ki sani bazan ce akwai aurena a kanki sabida wata manufa tawa; in kin fahimta dakyau cikin halin Asad babu son kai babu kuma k'arya...." ya sake yin shiru ya dafe kansa kana ya kuma cewa, "A matsayin da nake dashi bazan ce bazan yi k'arya ba amma tunda har na rantse yana dakyau ki amince. Tun bayan rabuwar mu ban sake ganin kia zahiri ba sai da rabon abinda yake cikin ki yazo bance lallai sai kin amince ba ki zauna akan ra'ayin ki shima daidai ne." Ya mik'e tsaye yana kallon wani wajan daban kana yace, "Amma ki sani bazan amince da sauraren wani namiji daban ba, bazan amince da maganar auren ki da wani ba, in kuma hakan ta cigaba da faruwa bake zan yiwa hukunci ba shi zan yiwa sai ya gwammace bai sanki ba.Maganar abortion da kike yi kiyi duk abinda zuciyar ki ta baki umarni daidai ne." Mik'ewa tayi zata gifta shi ta wuce ya jawota jikin sa sosai yana kallon fuskar ta itama haka,babu wanda yayi magana a cikin su kallon ta yake tana kallon sa har minti d'aya suna a haka kafin ya motsa bakin sa zaiyi magana ta riga shi tace, "Ya akayi Aliyu yasan da irin wannan rik'on da kai kad'ai kake min irin sa? Ko camera ya saka can Cairo d'in yadda zai dinga ganin duk abinda yake faruwa?. Ina jin dai camera ya saka shiyasa yasan da kayi min alqawarin baza ka rabu dani ba." Runtse ido yayi tashin hankalin sa ya ninka na baya ya matse ta sosai har sai dai kashin k'ugun ta ya amsa sabida matsar da yayi mata bata wsa bace har lokacin kuma bai bud'e ido ba fuskar sa a yamutse tana tattaro ja tana had'ewa waje d'aya. Rauda zafin rok'on take ji sosai ta kulle idon ta ta buɗe suka had'a ido yace, "Aliyu har rik'e ki yayi? Meyasa kika amimce hakan ta kasance? Ina hankalin da na sanki dashi ina yaje har kika bari hakan ta faru?, Aliyu fa ya rik'e ki like yadda muke yanzu....Hasbunallahu wani'imal wakil!" ya furta yana sakin ta sai ya koma da baya ya zauna a kan kujera ya dafe kansa da duka hannayen sa yana jin d'aci na mamaye masa kan harshen sa sabida tsananin kishi.         Wani irin abu taji a jikin ta ganin yadda ya koma lokaci d'aya ta bishi da kallo yana zaune a inda ya zauna har lokacin hannun sa yana dafe da kansa sai taji zuciyar ta na bugawa da sauri-sauri ba tare da tasan dalilin hakan ba. D'ago kai yayi yana kallon ta suka had'a ido sai ya cize bakin sa ya had'd'iye abu mai d'aci ya sake kulle ido ya bud'e cikin rauniyace, "Za'a kai ki gida, kije" yana fad'a ya tashi ya ya shiga ciki ta bishi da kallo har ya b'ace bai sake kallon inda take ba. Duk sai taji jikin ta kuma yayi sanyi sosai ta fita itama bata kuma kallon sa ba tana fitowa taga an bud'e mata mota ta shiga driver yaja basu tsaya a ko ina ba sai a k'ofar gidan su. Lokacin da ta shiga bata tarar da kowa a falo ba ta shiga falon Umma nan ta ga Umman a zaune ita da Khairi ta k'araso da sallama tana kallon Umma, a hankali ta taka inda Umma take kafin ta k'arasa ta fara kuka ga kanta da yake ciwo sosai, tsugunawa gaban Umma take niyar yi Umma tace, "Ummulkhairi rik'e ta ku shiga ciki kar ta fad'i." Ba musu ta tashi ta rik'e ta suka shiga ciki ta zaunar da ita a kan gado ganin yadda take rik'e kanta sosai sai Khairi ta d'auko mata maganin ta da ruwa tace, "Kisha Anty ko zai daina miki ciwo." Kai kawai ta d'aga mata Khairi ta fita Rauda ta ture maganin ta kwanta tana sauke numfashi koya ta kulle ido shi take ganowa da kalaman sa da suke mata yawo a cikin kanta har lokacin ta kasa mantawa. Umma ce ta shigo d'akin ta kalle ta bata ce komai ba ta fita jim kad'an sai gata ta dawo da ruwan tea mai kauri ta dawo kuaa da ita tace, "Tashi kisha shayi." Jin maganar Umma a tausashe a kanta kamar a mafarki sai ta zabura ta mik'e tsaye Umma ta ajjiye tea d'in ta zaunar da ita tace, "Meye na wannan zaburar kamar kinga dodo? Koma ki zauna? Ta fad'a tana zama kusa da ita. Kuka take k'ok'arin yi Umma tace, "Kar kiyi min kuka, ki mayar da wannan hawayen bana son ganin su." Ba shiri ta mayar dasu tana kallon Umma ta mik'o mata tea d'in tace, "karb'i ki shanye yanzun nan kisha maganin ki." Ba musu ta karb'a ta kafa kai duk dan ta burge Umma tana yi tana kallon ta. Bata sauke ba sai da ta gama shanyewa tass ta ajjiye kofin Umma ta bata magani da kanta tasha amma bata ce mata komai ba. Kallon Umma Rauda take yi ta sunkuyar da kanta k'asa murya na rawa tace, "Umma wallahil azim duk abinda ya faru babu laifina dan Allah ki yafe min." Umma ta sauke numfashi tace, "ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce yayi mana bayani kuma dukkan mu mun gamsu." Rauda ta kalli Umma tace, "Umma kema kin amince dashi kenan?." Umma tace, "Na amince har zuciyata Rauda, yanayin yadda yayi mana bayani ya tabbatar mana da kalaman sa gaskiya ne d'an uwan sa shine ya sake ki tun farko kin san shine wanda kuke fad'an nan bazai zo yaga kin rab'i dan uwan saba shiyasa ya yanke wannan hukuncin. Amma shi mai martaba Asad bashi ya aikata wannan sakin ba." Rauda tace, "Umma rubutun sane, kalaman sane, maganar sace, yanayin sane, hatta shaidar da ya nuna min yace da ita ake banbance su na ganta a hannun sa a ranar kuma ya sanar dani ba kowa yasan da wannan alamar ba ta yaya zai zama Aliyu ne bashi ba?." Umma ta sauke numfashi tayi shiru Rauda na k'ok'arin saka mata kokwanto a zuciyar ta amma har ga Allah ta amince da Asad dan yayi musu bayanin da dukkan su sai da suka firgita da lamarin masarauta. Umma tace, "Duk na amince da hakan Rauda amma bazai yi rantsuwa a kan karya ba." "Umma zai iya yi kodan ya samu abinda yake so. Yana k'ok'arin kare kansa ne daga fyad'en da yayi min amma babu aure tsakanina dashi Umma. Tabbas a Cairo ya mayar dani amma ya kuma sakina Ummaaaaa!" Ta fad'a tana can kalmar Umman cikin sanyi tana karyar da wuyan ta hawayen suka sakko mata. Umma tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Lamarin akwai d'aure kai Rauda." Rauda tace, "Na fad'a masa ya fita daga rayuwa ta wallahi bana son ganin sa ko kad'an na tsane shi na tsani ahlin su gabad'aya, yaje can ya k'arata kuma wallahi sai na zubar da cikin....." kallon da Umma tayi mata ya saka bata k'arasa ba ta sauke ido k'asa ta fashe da kuka tana fad'in, "Umma na tsani kaina bana son rayuwata, ta silar Asad kika ce min baki yafe min ba Umma, ina zan saka kaina naji dad'i bayan wannan furucin da kika yi a kaina?. Kallon fasiqa kike min Umma kuma wallahi ban tab'a zina sai a lokacin shima kuma fyad'e zan kira shi Umma. Ta silar sa Baba ya d'aga bulala ya dake ni har aka fasa min jiki, Umma ciki ne fa a jikina, ciki na haihuwa ba tare da aure ba. Bazan yafe masa ba Allah ya isa tsakanina dashi" ta fad'a tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya. Umma tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Allah kad'ai yasan abinda ya b'oye amma har zuciyata na amince dashi, badan yana sarki ko yana mai kud'i ba ke kin san halina ni ba irin mahaifin ki bace, dan haka na amince da cikin jikin ki na sunna ne bana shege ba. Zaki raine shi kamar yadda ko wacce uwa take rainon cikin y'ay'anta ki haife shi kamar kowa, kar na sake jin maganar zubar dashi a bakin ki balle ma ki aikata kona shege ne baza'a zubar dashi ba balle cikin sunna ne. Indai kina son farin cikina kar ki aikata makamancin hakan." Rauda bata daina kuka ba maganar Umma jinta take wani iri, wai ya zasu had'e mata kai kowa ya yadda cikin sunna ne bayan ita tasan ya sake ta? Meyasa suke mantawa da ita tasan shi tasan yanayin maganar sa ba Aliyu bane shine. Umma tace, "Bana son wannan koke-koken komai ya wuce, na yafe miki har zuciyata ki kuma yi hak'uri zargin ki da mukayi dukkan mu. Shi kuma Anas mahaifin ki zai sanar dashi komai dan ko babu aure tsakanin ki da Asad dole a dakatar da batun auren ki a yanzu." Kai take girgizawa ta d'ago tana fad'in, "Haba Umma ya zan yiwa Anas haka? Bayan dogon jiran da yayi a kaina tun ba yanzu ba yana gab da samuna kuma ace ya rasa ni?. Umma ke kike cemin daman kinfi sonsa da Asad sabida yana sona sosai ki tuna lokacin da na samu matsala a k'afata bai guje ni ba ya nuna zai aure ni a yadda nake. Umma bazan so na rasa Anas matsayin miji ba sabida k'aunar da yake min dan Allah kar kuyi min haka" ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Umma tace, "Dukkan mu babu wanda ya isa ya canja k'addara sai dai mu zubawa sarautar Allah ido daga nan har zuwa lokacin da zaiyi ikon sa akan dukkan mu. Bai rubuta Anas zai zama mijin ki ba tun farko shiyasa ake ta samun matsala akan auren ku, inda mijin kine babu abinda zai hana baki aure shi ba. Mu d'auka babu auren Asad a kanki amma akwai cikin sa a jikin ki kinfi kowa sanin ba'a aure da ciki kinga kenan auren ki da Anas ba abu ne mai yuwa ba." Zatayi magana Umma tace, "Ki daina wannan koke-koken ki kwanta babu abinda kuka zai k'ara miki sai ciwo" tana fad'a ta tashi ta bata waje ta fita daga d'akin. Hannu Rauda ta dunqule ta fara dukan cikin ta a zafefe cikin k'unar rai tana yi tana kuka sai kuma ta daina ta sake fashewa da sabon kuka. Ta jima a haka kafin kukan nata ya tsaya sai kuma ta zubawa waje d'aya idanu kalaman sa suna dawo mata cikin kanta sai taja tsaki ta toshe kunnen ta da duka hannayen ta biyu ta kwanta lamo a kan gadon. Bata san iya adadin lokacin da ta d'auka a haka ba maganin da tasha ya fara bin jikinta bacci ya d'auke ta. Umma data fita daga baya ta dawo ta tarar tayi bacci sai hankalin ta ya kwanta ta tafi wajan Baba dan su sake tattauna maganar nan, a zaune ta same shi shima da alama tunanin da yake yi kenan tayi sallama ta zauna tace, "Malam nifa gaskiya yanzu ina tantama, Rauda tace akwai abubuwa da dama wanda suka tattauna ita da Asad d'in kuma lokacin da yazo sakin ta ya maimaita mata su, in bashi bane ba taya Aliyun yasan dasu?." Baba ya sauke numfashi yace, "Wannan kuma duka zai bayyana tunda wannan d'in ya bayyana a yanzu. Abinda nake so ki fahimta a matsayin Asad bance bazai yi k'arya ba amma bazai yi k'arya irin wannan ba duba da yana da ilimin addini sosai yasan illar da take cikin zaman haramci." Umma tace, "Ni zuciyata tafi karkata akan shine ya sake ta d'in kawai lokacin baya cikin tunanin sane, ka tuna lokacin da kaje wajan sama mana akan rushe gidan nan ya kuka yi dashi? Ai bai nuna maka ya sanka bama gabad'aya." Baba ya girgiza kai yace, "Haka ne. Koda shi d'in ne yayi sakin tunda har baya cikin hankalin sa bata saku ba har yanzu matar sace." Umma tace, "ta ya ta zama matar sa bayan shi da kansa yazo gidan nan?, indai har baya cikin hankalin sa ya akayi ya kawo kansa gidan nan? Indai baya cikin hankalin sa ya akayi ya tuna da akwai matar sa a gidan nan? Indai baya cikin hankalin sa ya akayi yasan ya sake ta saki d'aya a baya yazo ya k'arashe ragowar?." Baba yace, "Ke baki san aikin sihiri babu abinda baya sakawa ba? Abinda nake so ki gane a nan Asad bazai mana rantsuwa a kan k'arya ba, ki tuna waye shi mana a garin nan." Umma tace, "Zai iya malam, zai iya kodan ya d'auke hankalin mu daga cikin jikin ta mu koma yi masa kallon cikin sunnah mu daina masa kallon cikin shege." Baba ya kalle ta yace, "Kina da matsala Binta, Rauda fa matar sace babu ta inda hakan zata kasance ba tare da aure a tsakanin su ba, yafa karantu yasan daidai da wanda ba daidai ba." Umma ta tab'e baki tace, "sai naga shaidan yana nasara akan kowa mai ilimi dama wanda bamai ilimi ba ya kamata ka tuna." Baba yace, "to nidai na amince da abinda yace, har yanzu Rauda matar sace ko yau yace zai tafi da matar sa zan bashi ita taje gidan sarauta a dama da ita. Anas kuma na kira shi da safe zai zo ya same ni muyi magana." Umma ta girgiza kai tace, "ya dai kamata a duba lamarin, komai ya faru da Rauda damu ya faru kuma hakkin ta yana wuyan mu dukkan mu sai Allah yayi mana hisabi da ita matuk'ar muka tura ta wajan sa ba tare da munyi bincike ba kamar mun tura ta taje tayi zina ne" ta fad'a tana mik'e ta fita ta bar Baba a zaune dan shi kam baiga abinda zai hana Rauda zama fulani matar sarki ba. Washe gari. *11:00 am.* Baba ne da Anas ne a zaune bayan sun gaisa Baba yayi shiru baice komai ba domin har ga Allah yana jin nauyin Anas d'in da babu yadda zai iya ne. Anas kam tunda yaji kiran jiya haka nan gaban sa yake fad'uwa dalilin da ya saka shi bai k'asa a guiwa ba ya tawo da safe dan yaji me yake faruwa ko hankalin sa zai kwanta. Baba ya numfasa yace, "Anas nasan zakayi mamakin kiran da nayi maka zuciyar ka zata dinga fad'a maka abubuwa da yawa akan kiran, ina so ka bani hankalin ka ka kuma saurari abinda zan fad'a maka dakyau." Anas ya gyara zaman sa yace, "to Baba." Baba yace, "Wato Anas akwai k'addarar da zaka ga ta gifta in Allah bai rubuta abu naka bane sai ya kubce ta silar wannan k'addarar da ta kusto kai. In hakan ya faru mukan d'auka daman ba rabon mu bane abinda muka rasa d'in tunda shi rabo hausawa sukace ko kana cikin mahaifiyar kane indai naka ne sai ya same ka." Baba ya sake d'aure Anas da jijiyoyin jikin sa jikin sa ya sake yin sanyi ya kalli Baba yace, "Baba ban fahimta ba." "Zaka fahimta yanzu Anas. Wato kamar yadda k'addarar auren ka ta raba ka da Rauda a wannan karon kuma k'addarar auren ta zata sake raba ku Anas." A firgice ya kalli Baba idanun sa a waje yana kallon Baba cikin tashin hankali, ganin hakan sai Baba yace, "Kwantar da hankalin ka Anas kaji bayanin da zan maka. Wato a kwanakin baya duka mun d'auka auren Rauda ya mutu har kai na sanarwa ka kuma nemi sake neman auren ta a karo na biyu har muka zo yau da auren ku bai wuce kwanaki goma ya rage ba. A cikin kwanakin nan abubuwa da yawa sun faru Anas ciki harda bayyanar mijin ta inda ya tabbatar mana da har gobe akwai auren sa akan Rauda bai sake ta ba." Baba ya kuma cewa, "Bayanan da yayi mana mun gamsu sosai dasu ita kanta Raudan ta tabbatar mana da ya mayar da auren ta bayan ya sake ta,  jin hakan ya saka na neme ka dan nasan kasan a yanzu auren ka da Rauda babu shi Anas!" Baba ya fad'a a tausashe yana kallon Anas da tashin hankali ya bayyana k'arara a kan fuskar sa gumi yana keto masa daga ko wanne kafofi na jikin sa cikin tashin hankali da bugar zuciya. [17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@ nanahaleema11* *074*            Hankalin Mum ya tashi sai zagaye take a falon tana dukan hannayen ta tana yi tana kallon Jidda da take zaune tana kuka sosai sai ta d'auke kanta ta cigaba da tafiya tana kallon sama zuciyar ta cike da tunanin mafita. Zama tayi ta kalli Jidda tace, "Jidda sanar dani abinda kika yiwa Aliyu, in baki fad'a min ba bazan taimake ki ba." Jidda tana kuka ta zube k'asa kusa da Mum tana fad'in, "Mum dan Allah a fara solving problem d'in then sai ki tambaye ni ni kuma zan fad'a miki, in aka tsaya tambaya a yanzu rayuwata tana cikin hatsari Aliyu zai iya aikata min komai, dan Allah Mum ki taimake ni kafin ya kashe ni" ta fad'a tana sake fashewa da kuka ta kifa kanta a cinyar Mum. Eman da ta shigo taji abinda suke cewa ta zauna a kusa da Mum tace, "abinda Mum take tambaya shi ya kamata ki fara bata amsa, me kika yi masa har kike tsoron hukuncin sa haka?." Mum hankalin ta da yake a tashe tace, "Abinda ya kamata mu sani kenan in yaso sai musan ta inda zamu b'ullowa lamarin, ki duba yanayin da take ciki fa kalli yadda ta rame ta lalace ga ciki a jikinta duk ta koma bak'a kamar ba ita ba. Me kika yi masa haka?." Jidda ta d'ago kanta daga cinyar Mum tace, "Mum kawar da Aliyu shine abinda ya kamata a fara yi ba wannan tambayar ba, in abinda nayi masa ya bayyana ba ni kad'ai ba hatta dangin ki da dangin Daddy sai abin ya tab'a su. Dan Allah ayi gaggawar kashe shi tun kafin shi ya kashe mu." Mum ta kalli Eman itama ta kalle ta kafin Mum ta kalli Jidda tace, "Ikon Allah! Bakin ki bazai iya fad'a laifin ba kenan kome?." "Fad'ar bata da amfani! Jinta sai iya tarwarsa kunnuwan ku Mum, ku tabbatar an kashe Aliyu in ba haka ba dukkan ku sai zuciyar ku ta kusa bugawa nan gaba" ta fad'a da ihu tana cigaba da kuka kafin ta baje a kan carpet tana kuka sosai tama manta akwai ciki a jikin ta. Eman tace, "ki sanar da mijin ki mana na tabbatar zaiyi maganin sa tunda sama yake da kowa a garin nan." Jidda da take kuka a kan carpet ta d'ago ta kalli Eman sai ta sake kwantawa tana cigaba da zubar da hawaye. Hankalin Mum ya kai k'arshe wajan tayi idanunta a waje take tunanin wanne irin laifi mai girma Jidda ta yiwa Aliyu haka da ta tsorata da hukuncin da zai mata...?         Jin yadda take kuka sosai ya saka Mum tace, "Taso nan Jidda" ta fad'a tana bata hannu ta rik'e ta mik'ar da ita ta zaunar da ita kusa da ita ta dafa kafad'ar ta tace, "Aliyu ne bakya so ki gani a raye ko?." Kai ta d'aga da sauri hawaye na sauka daga idanun ta wani yana bin wani tace, "Eh Mum, rayuwar sa barazana ce ga tawa rayuwar, zai tarwatsa min dukkan plan d'ina Mum." Mum ta girgiza kai tace, "Shikenan za'ayi maganin sa kar ki damu. Ko meye za'a yi akan a ga bayan sa indai hakan zai saka hankalin ki ya kwanta." Rungume Mum tayi tana kuka bata ce komai ba Mum tana shafa bayan ta zuciyar ta cike da zullumin ranar da laifin da ta yiwa Aliyun zai bayyana, yadda taga ta tsorata sosai abin ya bata tsoro tana da tabbacin akwai wani abun a k'asa, amma meye? Wanne irin laifi ne mai girma haka?. *☆☆☆.*          "Kai wallahi Fulani mai babban d'aki ce take tawowa, yanzu ya zamuyi gashi waziri yace kar mu bar kowa ya shiga b'angaren nan? Bamu isa mu hanata ba" mai tsaron k'ofar ya fad'a yana kallon d'an uwan sa wanda yaka tsaye a kusa dashi. Kafin suyi wani yunk'uri Mama ta iso wajan ita da jakadiyar ta a bayan ta dole suka zube a k'asa suna gaishe ta ta d'aga musu hannu ta nufi ciki jakadiyar ta ta tsaya a baya. Mama tana shiga d'akin da mai martaban yake kwance taga kan gadon wayam babu kowa a kai gabanta ya yanke ya fad'i ta dafe k'irji tana kallon d'akin aka bud'e k'ofa aka shigo, Uncle ne ya shigo ganin ta a tsaye duk sai ya rude yace, "Ranki ya dad'e yaushe kika shigo?." "Yanzu na shigo? Ina mai martaba?" Ta fad'a tana sake kallon gadon tana kallon sa. Kafin yayi magana mai martaba ya fito daga band'aki fuskar sa duk ruwa da alama alwala yayi suka had'a ido da Mama ta tsaya cak tana kallon sa shi kuma ya d'auke kansa ya zauna a gefen gadon ya d'auki wayar sa da take gefe yana dubawa. Kallon Uncle tayi ta kalli mai martaba ta sake kallon uncle ta sake dawo da kallon ta ga mai martaba da yayi kamar bai ganta ba yana zaune ya gefen gadon yana amsa waya. Ta juya ta sake kallon Uncle sai taga ya bud'e k'ofa ya fita ya kulle k'ofar ta sake kallon mai martaba da mamaki mai d'auke da tsoro hadi da al'ajabi. Takowa take yi zuwa kusa dashi shi kuma ya d'auke kansa tamkar ma bai san da wata hallita a wajan ba har ya gama wayar ya ajjiye wayar ta k'araso kusa dashi ta zauna kusa dashi tace, "Mijina kai nake gani ko kuma idona ne yake min gizo?." Idanun sa ya d'ago suka had'a ido ya d'aure fuska matuk'a sai ya sake d'auke kansa daga kanta. Idanun ta suka ciko da kwallah ta kwantar da kanta a kafad'ar sa tana hawaye tace, "Mijina kayi min magana dan Allah, kai nake gani ko mafarki nake yi." Hannayen sa ya saka ya d'agota daga jikin sa suka had'a ido yayi kamar bazai magana ba kafin yace, "ba mafarki kike ba nine dai da kaina." Sai ta rud'e ta rike hannun sa tana fad'in, "Tun yaushe mijina ya farka ban sani ba? Ka san adadin damuwar dana shiga akan rashin lafiyar nan taka amma shine har zaka tashi kana tafiya ba'a sanar dani ba?." Hannun sa ya kwace daga rik'on da tayi masa ya hard'e hannun a k'irji yana kallon ta yace, "Kina so na farka ne daman?." Yadda ya kafe ta da ido sai ta kasa magana ta diririce ta rasa me zatace ta sunkuyar da kai ta d'ago ta rasa me zata ce, ganin hakan sai yayi murmushi yace, "tashi ki koma inda kika fito, sannan umarni nake baki kar wani ko wata yasan da wannan labarin koda wasa, in kuma akasin hakan ya faru ranki ne zai b'aci dan nasan ke kad'ai kika sani." "Mijina ina zanje?." Ya kalle ta yace, "Inda kika fito nan zaki koma, bana son sake ganin ki a wajan nan har sai lokacin da kowa zai san na farka zaiyi. Asad, Aliyu, Hydar ban amince dukkan su su san da wannan maganar ba, in kuma naji a bakin su na tabbatar ke kika fad'a." Sai ta fashe da kuka tana kallon sa murya na rawa tace, "Mijina dan Allah ka yafe min nasan nayi abubuwa da yawa a bayan idanun ka, nayi ne sabida...." "Son zuciyar ki ko?" Ya katse ta da fad'ar hakan yana kafe ta da idanun sa masu kwarjini. Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana kifta idanu yaja dogon tsaki yace, "baki fara ganin komai ba Rabi'a, baki ga komai ba a cikin abubuwan da kika shuka yanzu kika fara girbar su. Tashi ki bani waje bana son ganin ki gabad'aya." Jiki a sanyaye ta mik'e tana tafiya kamar mara laka ta juyo ta kalle shi taga bama ita yake kallon ba tace, "Dukkan abinda na aikata nayi nadama bazan sake aikata makamancin su ba." Bai amsa ba dole ya saka ta fita yaja tsaki ya lumshe idanun sa dukkan abinda ta aikata suna dawo masa cikin kansa ya cize baki shi kam bai tab'a ganin mace makira kamar ta ba. Uncle ne ya shigo d'akin ya kalle shi yace, "Mubarak taya aka bar Rabi'a ta shigo a wannan lokacin?." Uncle yace, "Ranka ya dad'e na fita ta shigo su kuma masu tsaron k'ofa baza su tab'a iya hanata shigowa ba, da ace ina nan ne zan san yadda zanyi na dakatar da ita to bana wajan." Mai martaba yace, "Bana tunanin zata iya shiru da bakin ta ba tare da ta fad'awa y'ay'anta ba, fad'a musu daidai yake da lalacewar komai." Uncle yace, "Babu abinda zai faru in sha Allah mai martaba, Allah ya wuci zuciyar ka." D'auke kai yayi kana yace, "Ina Asad yaje?." Uncle yace, "Babu wanda yasan inda ya tafi." Abba ya sauke numfashi yana girgiza kai yace, "komai yazo k'arshe." Uncle ya amsa da fad'in, "Da izinin Allah."         B'angaren Mama kuka take sosai a kan gadon ta, bata tab'a jin dana sani akan abubuwan da ta aikata ba sai a wannan lokacin da ta tabbaatar mijin ta yasan duk wani target d'inta nasan ganin bayan kowa akan burinta.  Tunawa da wani abun sai ta zabura ta fara zagaye d'akin tana girgiza kai tana fad'in, "A'a bazai san ni na aikata wannan laifin ba, bazai sani ba, in ya sani na shiga uku na lalace" ta fad'a tana d'ora hannun ta a kanta tana cigaba da zaga d'akin hankalin ta a tashe tsoro ya bayyana a tare da ita. Sai ta koma kan gadon ta zauna tana kuka tayi tagumi, "shin ina y'ay'a mazan da nake alfahari dasu?" Ta tambayi kanta dan dukka su uku bata san inda suka suke ba balle ta neme su. Kai ta dafe zuciyar ta na farbawa da sauri-sauri zazzaɓi yana neman rufe ta tunda mai martaba ya farka bata da kwanciyar hankali dan tasan daidai yake da tonuwar dukkan asirin ta wanda ta jima tana b'oyewa. K'wankwasa k'ofar da akayi ya saka ta kalli k'ofar bata bada umarni ba aka shigo ganin Hydar ne ya saka ta mik'e ya k'araso inda take da sauri ta rik'e shi tana fad'in, "Mahaifin ku ya farka Hydar, naje na same shi a zaune yana magana har yana tafiya. Meyasa zai farka yanzu? Meyasa sai da komai ya lalace min zai tashi?" Ta fad'a tana rik'e Hydar shima ya rik'e ta dan yaga kamar bata hankalin ta. Gaban sa ya fad'i jin abinda tace ya zaro idanu yace, "Mama da gaske ya farka? Abbana ya tashi har yana tafiya?. Zanje na ganshi Mama" ya fad'a zai fita tayi saurin dawo dashi tace, "karka sake kaje inda yake, koda wasa kar ka nuna kasan ya tashi bana so yasan na fad'a maka ka rufa min asiri" ta fad'a tana kuka sosai ya rik'e ta hankalin sa duk ya tashi ya zaunar da ita yace, "Shikenan Mamana kwantar da hankali ki babu abinda zai faru, ki daina kuka dan Allah" ya fad'a yana rik'e da ita gabad'aya jikin sa yayi sanyi. Kuka take sosai yana rik'e da ita har sai da yaga kukan nata ya tsaya Suhaima ta shigo yace ta kula da ita shi kuma ya fita. Har zaije inda mahaifin na yake sai ya tuna mai tace masa sai ya fasa dan baya son abinda zai haifar mata da matsala kamar yadda tace. *☆☆☆*         "Inna da gaske fa ni ina sonshi zan aure shi indai kin amince" Rahma ta fad'a tana kallon Inna. Inna tace, "kin amince fa kika ce Rahma? Kuna jin abinda take cewa ko?" Inna ta fad'a tana kallon Yayar mu da Yaya Nafisa da Yaya Fariha da kuma Yaya Shamsiyya. Yayar mu tace, "To Inna tunda tace tana son sa shima kuma yace zai aure ta basai ayi ba. In kika duba Inna samari wahala suke yanzu, y'ay'an masu kud'i ma da kyau da komai suna zaune babu mijin aure ina ga mu y'ay'an talakawa?. Tunda har ya furta a bashi d'in kar mu bari ya sub'uce mana kinga har yanzu fa babu wanda yake zuwa wajan ta." Yaya Shamsiyya tace, "Nima dai abinda na gani kenan. Tunda kowa yasan asalin yaron nan me zai hana baza'a barta ta aure shi ba tunda dai yana so itama tana so?, mun san sai yafi son Rauda da ita tunda tun farko ita yake so amma duk soyayyar da yake mata in Allah ya rubuta Rahma ce matar sa babu wanda sai canja hakan." Yaya Nafisa tace, "Inna kawai a amince ayi abin nan, sai mu cigaba da mata addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Inna ta sauke numfashi tana kallon su tace, "dukkan ku kun goyi bayan ta aure shi kenan?." Yaya fariha tace, "To meye aibun hakan Inna?." "Amma kun san Rauda yake so ba ita ba, bakwa tunanin gori wata rana?." Yayar Mu tace, "Allah zai kiyaye babu abinda zai faru in sha Allah Inna." Inna tayi shiru kafin tace, "Yanzu dukka sai na fito na cewa y'an uwana zan aurar da Ita nan da kwanaki kad'an masu zuwa? Hakan ai abin kunya ne." "Babu kunya a ciki Inna, wacece bata da budurwa a cikin y'an uwan naki Inna? Ko wacce kuma burin ta taga ta kawar da ita daga gaban ta tayi aure; mu mun samu meyasa zamu watsar da samun gefe?." Inna tace, "Shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Suka amsa da amin Yayar Mu tace, "Zan sanar da Baba ta amince kema kin amince ayi komai a gama." Inna bata ce komai ba suka cigaba da hira kafin su je wajan Umma. *Bayan kwana biyu.* Biki ya gabato ya rage saura kwana biyu kacal d'aurin aure amarya tana ta shagali abinta tunda suka had'u da Anas sau daya bai sake zuwa ba dan jinyar kansa yake dauriya kawai yake yi yana zuwa amma bawai don son ransa ba. Da ya saka addu'a da neman zab'in Allah a kan gaba sai komai yake barin zuciyar sa a hankali yaji yana karb'ar Rahma matsayin mata a gare shi. A cikin kwanakin dai suna waya kuma babu laifi yana jinta a ransa yana k'ok'arin nuna mata yana son auren nata yana nuna mata ya karb'i k'addarar da Allah ya k'addaro musu itama kuma tana nata k'ok'arin. Rauda ta tattara komai nata Umma ta tura ta Bauchi gidan yayar ta tace sai an gama komai na biki ta dawo. Ana ta shagalin biki dangin Umma dana Baba dana Inna kowa yana nuna tasa bajintar daman gidan Amarya an gama zuba komai dan Umma bata ce uffan akan kayan Rauda da suke gidan ba tace dukkan su d'aya ne ita da Raudan. Ranar lahadi da misalin k'arfe sha d'aya na safe a masallacin cikin gari dubban jama'a suma shaida daurin auren Anas da Rahma akan sadaki naira dubu d'ari. Bayan d'aurin aure ya watse ango yazo gidan su amarya kamar yadda al'ada ta tanada yayi namijin k'ok'ari wajan kawar da komai a zuciyar sa duk da Raudan bata nan. Anyi shagali sosai kamar ba gidan Baba dan abinda Asad ya aiko dashi a bikin kad'ai ya isa ayi komai na bikin harda canji, aljihun Baba cike yake taf shiyasa da ance babu abu kaza zai bayar a haka aka gama taron biki aka kai amarya gidan ta kowa ya watse. *Matar mutum kabarin sa.*🥵🥵 [17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks @nanahaleema11* *73* Kallon Baba Anas yake yi bakin sa yana rawa alamun yana so yayi magana amma bashi da k'arfin guiwar yin maganar sai kallo da yake bin Baba dashi idanun sa kamar zasu fad'o kasa sabida tashin hankali da firgici. Ganin yanayin da ya shiga ya saka Baba sake tausasa murya yace, "Anas nasan dole kaji babu dad'i akan abinda na fad'a maka amma ina so ka fahimce ni wallahi bamu yi maka haka da wata manufa ba, Allah ya sani badan wannan maganar ba auren ka da Rauda yana nan babu fashi. K'addara ta riga fata Anas dukkan mu babu wanda yaji dad'in wannan abinda ya faru, amma babu yadda zamuyi da ikon Allah. Kayi haƙuri bamu yi dan mu wulaƙanta ka ba Anas." Runtse ido Anas yayi jin abinda Baba ya sake fad'a ya tabbatar masa da ba mafarki yake ba da gaske ne abinda yake faruwa, da gaske ne Raudan sa tana da miji babu damar ya aureta ya sake rasata a karo na biyu. Shiru yayi ya kasa magana jikin sa har rawa yake yi kansa na k'asa idanun sa sun cika da ruwan hawaye ya rasa abinda yake masa dad'i. Ba k'aramin tausayi ya bawa Baba ba zuciyar sa ta karye dan Allah kad'ai yasan abinda yake ji a cikin zuciyar sa a wannan lokacin hakan ya saka yace, "Sai hak'uri Anas. In kaga abu ya tunkaro bawa gadan-gadan zai same shi sai ya kubce to ka tabbatar ba alkhairi bane a tare dashi,  in kaga kana kaucewa abu Allah yana sake mayar dakai wajan koda baka so to tsaya a inda Allah ya kaika wataƙila alkhairi ne a gare ka. Kayi hak'uri nasan akwai ciwo kasancewar ka jima kana son Rauda amma Allah bai rubuta kai mijin ta bane shiyasa ake ta samun akasi a ko wanne lokaci." Kai Anas yake girgizawa nan take ruwan da ya taru a idanun sa ya sauko kan kuncin sa, hawaye yake wani yana bin wani kansa a k'asa har lokacin Baba ya zuba masa ido kawai shima ji yake kamar yayi masa kukan sabida tausayi zuciyar sa ta karye. Baba yace, "Abinda yasa banyi magana da wakilan ka ba na neme ka kai tsaye ina dan na sanar dakai da kaina kar kaji maganar a bakin iyayen ka kaga kamar an yaudare kane. Amma kayi hak'uri wallahi ita kanta Raudan tana sonka so mai tsanani, auren wani da yake kanta ya saka dole take k'ok'arin cire ka a zuciyar ta kodan gudun fad'awa fushin ubangiji." Muryar sa na rawa yace, "babu komai Baba, haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canja faruwar sa. K'addarata kenan zanyi......." ya kasa k'arasawa muryar sa ta sark'e ya sake saukar da kansa k'asa sabbin hawaye suka sake wanke masa fuskar sa. Baba yayi shiru yana kallon ikon Allah ganin namiji mai kyau da kud'i kamar Anas yana kuka da ya rasa y'ar talakawa Rauda. Lallai lamarin soyayya sai dai a barshi, duk wanda kaji yana cika baki a kan soyayya tabbas bai tab'a d'and'ana d'acin sa bane. Duk wanda yasan so yasan ya zafin sa yake, kana tare da wanda kake so d'in ma rad'ad'in sa yana damun zuciyar ka ina ga ka rabu dashi?. Sai da ya tsaigata kuka sannan ya share idanun sa yace, "Baba babu komai na d'auki hakan matsayin jarabawar ubangiji ina rok'on sa da kyawawan sunayen sa da ya bani ikon cinyewa." Baba yace, "Amin Anas. Kayi hak'uri haka Allah yake tsarin sa, babu ta yarda za'ayi jarabawar wanda ya halicce mu tazo mana da sauk'i dole sai ta tab'a mana zuciya da gangar jiki kodan mu k'ara imani dashi nan gaba. Jarabawar duniya ma wacce wani ne a duniya zai baka sakamako in ka shige ta hankalin ka yake kai kololuwa wajan tashi ina ga wacce mahaliccin kane zai baka sakamakon da kansa?. Kayi hak'uri!" Baba ya sake fad'a a tausashe yana kallon sa. Shiru yayi yana murmushin k'arfin hali kafin yace, "Babu komai Baba na d'auki k'addara." Baba yace, "Haka ake son dukkan mu'umi ya kasance Anas. Yanzu ya za'ayi da iyayen ka? A sanar dasu?." Anas yace, "A'a Baba, bazan so ace an sake fasa aurena ba a karo na biyu hakan bazai wa mahaifiyata dad'i ba, in na jure ita babu lallai ta iya jurewa. Na amince da tarbiyyar y'ay'an ka da kuma ilimin su Baba, tunda na rasa Rauda ina so a bani k'anwar ta guda d'aya." Baba ya washe baki farin ciki ya bayyana a tare dashi ya gyara zaman sa yace, "Banda abinka Anas wannan ai abu ne mai sauk'i, na kuma ji dad'in wannan kalami naka har sosai ba kad'an ba. Rahma k'anwar Rauda ce jinin tace sai ta maye gurbin y'ar uwarta a gare ka, wataƙila daman can Allah ya riga ya rubuta itace matar ka ba Rauda ba tunda dukkan lalube muke a cikin duhu." Anas ya girgiza kai yace, "Haka ne Baba" Sai kuma yayi shiru ya sake sunkuyar da kansa k'asa ya danne raunin da yake ji a zuciyar sa baya so ya bayyana amma ya kasa, Baba yace, "Na baka Rahma halak malak Anas, za'a cigaba da shirye-shiryen biki kamar babu abinda ya faru in Allah ya amince. Kayi hak'uri nasan har abada baza k daina jin ciwon da kake ji ba; amma ka jure wata rana sai labari." Anas bai amsa ba dan kansa sarawa yake yi zazzaɓi yana neman rufe shi bai san ya akayi bakin sa ya furta zancen k'anwar Rauda ba kawai taji ya fad'a ne hakan ya saka shi yin shiru bai ce komai ba. Baba yace, "Ya kake gani a sanar da iyayen ka abinda ya faru ko a'a?." Anas ya d'ago jajayen idanun sa ya kalli Baba yace, "A'a Baba, a cigaba da shiri kawai Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Baba yace, "A'a Anas in akayi haka kamar an mufurce su ne, kar nan gaba su samu labari suga kamar bamu kyauta musu ba." "Babu komai Baba, basai an fad'a ba bazasu tab'a sanin ba ita bace" ya furta a hankali idanun sa a lumshe. Baba yace, "To shikenan. Allah ya tabbatar da alkhairi yasa hakan ya samarwa da kowa farin ciki a zuciyar sa. Ya baka ikon jure abinda kake ji a ranka daga nan har lokacin da Allah zai kawo maka sassauci a zuciyar ka." Kai yake girgiza kai yace, "Amiin Baba." Mik'ewa Anas yayi yace, "Baba zan koma." Baba ma ya mik'e yace, "Anas naga yanayin ka ya canja gabad'aya, Anya zaka iya tafiya kai kad'ai?." Anas ya murmusa yace, "Babu komai zan iya. Sai anjima Baba" ya fad'a yana fita Baba yabi bayan sa sai da ya tabbatar ya shiga mota ya tafi sannan ya koma cikin gidan jikin sa a sanyaye matuk'a. Yana shiga wajan Umma ya wuce ya same ta ita da Inna ne a zaune Baba ya zauna yace, "Kamar kun san dukkan ku nake nema." Inna tace, "Lafiya na ganka a sanyaye haka?." Baba yace, "Yaron nan Anas shine ya karya min zuciya wallahi, kuka ya dinga yi k'aramar yaro k'arami jikin sa har rawa yake. Yana son Rauda amma Allah bai rubuta Rauda matar sa bace ba abin tausayi" ya fad'a a sanyaye yana sauke numfashi. Umma tace, "Malam dan ka dage ne amma ni banga dalilin sanar da Anas ba tunda bamu da tabbacin sakin nan baiyu ba a kanta. Allah ya sani ni hankalina yafi kwanciya da Anas wallahi." Baba ya kalli Umma yace, "kina son maimaita magana guda d'aya, aure ne akwai shi akan Rauda dan babu yadda za'ayi mutum kamar Asad yazo yayi mana k'arya kawai dan cikar burin sa. Kina so muyi mata aure akan aure ne? Koda ma ace babu batun auren haka zamu bawa Anas auren ta da ciki a jikin ta?." Jin Baba ya hasala sai Umma tayi shiru bata ce komai ba Baba yace, "Anas yayi tawakkali ya amimce da k'addara ni kuma na bashi Rahma a madadin Rauda dan haka biki baza'a fasa shi ba amma ya tashi daga kan Rauda ya koma kan Rahma" Baba ya fad'a yana kallon su. Inna ta bud'e baki tace, "Kamar ya kenan?." "Kamar yadda kika ji na fad'a. Ya amince da maganar Rahma shine ya fara nema ni kuma na bashi, dan haka duk wani shiri da kuke akan Rauda ya tashi ya dawo kan Rahma dan yau saura kwana tara auren ta da Anas." Inna ta kalli Umma itama ta kalle ta cikin mamaki tace, "Malam kenan auren cushe za'a yiwa Rahma kome?." Baba yace, "hukuncin dana yanke kenan babu ruwan ki dawai auren cushe ko akasin sa, Rahma Anas zata aura madadin y'ar uwar ta Rauda." Inna tayi dariya kad'an tace, "Ban damu da kud'in da Anas yake dashi ba abinda na sani shine wallahil azim babu wanda ya isa ya yiwa Rahma auren dole, in bata son Anas wallahi bazata aure shi ba dan ni ba ita bace da zan bari a d'auki y'ata a aurar ban sani ba sai dai kawai a kawo min sadaki" ta fad'a tana nuna Umma da take zaune tana kallon Baba da shima ita yake kallo. Baba ya girgiza kai ya kalle ta yace, "Lallai Asabe ni kike kallo kike fad'awa ban isa na aurar da Rahma ba, shikenan mu zuba nida ke kiga in ban aurar da ita d'in ba." Inna tace, "Oho dai, ni ba irin ka bace da son kud'i zai rufe min ido nakai y'ata inda zata wahala a dinga yi mata kallon matar cushe, wallahi bazata sab'uba bingida a ruwa." Baba ya mik'e yaja k'wafa ya ware muryar sa yace, "Ke Rahma!." Daga d'akin Rauda ta amsa ta fito jikin ta a sanyaye dan duk taji abinda ake cewa ta fito ta tsuguna tace, "Baba gani." Baba ya kalle ta yace, "Anas ya nuna yana son ki zai aure ki madadin y'ar uwar ki Rauda kin amince ko a'a?." Shiru Rahma tayi ta kalli Inna ta suka had'a ido ta dawo da kallon ta ga Baba tayi shiru bata amsa ba. Baba yace, "Malama magana nake miki kina kallona, kin amince a d'aura auren ki sati mai zuwa?." Rahma ta sunkuyar da kai k'asa tace, "Baba a bani lokaci nayi magana da Inna ta." "Babu lokacin da za'a baki malama, ki fad'i abinda yake ranki bamu da lokacin da za'a baki har kiyi magana." Rahma tayi shiru bata ce komai ba Inna tace, "Matuk'ar bata amince ba wallahi sai dai ka bashi Ummulkhairi amma badai Rahma ba, bazan lamunci auren dole a kanta ba haka kawai nan gaba bazai goranta mata yace ba ita yake so ba bashi ita akayi." Shiru Baba yayi yana kallon Inna yadda take fad'ar magana kamar ba shine yake mata magana ba yaja k'wafa ya fita baice komai ba. "Jeka, wallahi bazan amince ayi mata abinda aka yiwa Rauda ba gashi ana ta samun matsala har yanzu bamu da tabbacin da gaske akwai auren a kanta ko babu ga ciki kuma. Ina! ni wallahi bazan amince ba, ke Rahma tashi muje" ta fad'a tana kallon Rahma kafin ta fita itama tabi bayan ta. Murmushi Umma kawai tayi dan bata da ta cewa dan ta lura hak'urin ta shine yamr cutar da ita wani lokacin ya zama dole ita ta dage akan sai an tabbatar da auren Asad a kan Rauda in ba haka ba itama bazata koma masa ba. *☆☆☆*          Haka ya kwana babu walwala a tare dashi tunda yayi sallar asuba bai kwanta ba yana zaune yana lazumi har gari yayi haske sannan ya fara karatu bayan ya kammala yayi wanka ya shirya cikin shigar manyan sarakai yayi nad'in malamai akan hular da ya saka shigar ta amshe shi sosai ya sauko zuwa k'asa. Falon shiru babu kowa yana bin wajan da kallo yana tuna inda Rauda ta zauna jiya kafin ya janye idanun sa daga kallon wajan ya zauna a kan kujera ya d'auko waya yana dannawa, ajjiye wayar yayi a gefe ba jimawa aka danna door bell ta jikin k'ofar cikin maganar sa mai d'auke da isa da k'asaita yace, "Shigo." Da sallama ya shigo jikin sa har rawa yake yi ya zube a k'asa yana fad'in, "Barka da safiya Sarkin sarakuna, barka da tashi farar atafa, barka da fito taurarin sama sha ado. Allah ya k'arawa Sarki lafiya da tsahon rai, Allah ya k'arawa mai martaba lafiya yayi rik'o da hannun Fulani mai babban d'aki. Ranka ya dad'e" ya fad'a yana yi masa jinjina cikin girmamawa. Asad ya sauke numfashi a hankali ya amsa da amin kafin yace, "Sarkin mota." Jikin sa har rawa yake yace, "Ranka ya dad'e." "Kasan meyasa na zab'e ka a zaman gidan nan?." "Ban sani ba Ranka ya dad'e." "Sabida kana da amana, tun lokacin Abba na shaida hakan a tare dakai" yayi shiru kafin yace, "Bana son kowa yasan ina garin nan, bana so kowa yasan da abinda yake faruwa a gidan nan kana jina?." "Ina sauraron mai martaba, in sha Allah mai martaba bazai same ni da cin amana ba, zan riƙe amanar mai martaba daga nan har na bar duniya." Kai Asad ya d'aga yayi shiru na wani lokacin kafin yayi masa alama da hannu da ya tashi yayi masa sallama ya fita da sauri. Numfashi Asad ya fitar ya kalli sama yana kallon adon da aka yiwa rufin d'akin yana tunani, yana so Rauda ta dawo rayuwar sa a wannan tsaka mai wuyar da yake ciki ko zai samu sassaucin abinda yake ji a ransa amma kuma yana so ya bata hutu dan yasan akan gaskiyar ta take shima akan tasa gaskiyar yake. Hannun sa ya d'ora a kan cikin sa yunwa yake ji sosai amma baya tunanin zai iya cin wani abun da bashi da wannan nutsuwar ko kad'an. Ido ya sauke daga k'asa wayar sa yaga tana k'ara ganin mai kiran sai yaja k'aramin tsaki ya d'auke kansa sunan Jidda ya fad'o masa a zuciyar sa, runtse ido yayi zuciyar sa na bugawa ya mik'e ya fita daga falon zuwa harabar gidan, zaga gidan kawai yake yi shi kad'ai yana takawa har ya gaji ya sake komawa ciki ya zauna ya fara aiki a laptop. *☆☆☆* "Sau nawa zan fad'a nace maka Aliyu bazai mana aikin komai ba gabad'aya ya canja dabi'ar sa mu nemi wani ya bawa Asad wannan maganin da yanzu mun wuce wajan" Hajiya ta fad'a tana kallon Waziri da shima ita yake kallo yace, "Kwarai da gaske maganar ki haka take, gashi ya kasa yin komai har kawo yanzu. Wasa da hankali yake mana ya mayar damu tamkar ball ta ko ina buga mu yake yi son ransa, muma zamu buga shi son ranmu kuwa." "Shawara ya kamata a canja a sakawa Asad layar nan ya haukace kowa ya huta dan lokaci yana tafiya komai sake canjawa yake, matar Asad indai ta haihu komai ya riga da ya lalace dole mu san abinda za'ayi kafin hakan ta faru dan mu ne a ruwa." Waziri ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "Hakan za'ayi, abinda kika ce gaskiya ne a cikin kwanakin nan Asad zai sauka daga mulkin nan, k'arshen wahalar mu tazo lokacin nasara zai fara ina jin hakan a jikina wallahi." Ta girgiza kai tace, "Ina jin hakan a jikina nima." Kai ya girgiza shima kafin su rabu kowa ya kama gaban sa zuciyar kowa cike da kwarin guiwar samun nasaraa karo na babu adadi. [17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@nanahaleema11* *075*            A kwance yake a mik'e yana jan numfashi dak'yar hannun sa dafe da kansa yana juya kai da alama ciwon da kan yake yi masa ba d'an kad'an bane. Numfashin sa dak'yar yake sauka sabida ciwo ya rame lokaci d'aya yayi bak'i kansa ya taru da gashi haka fuskar sa kamar bashi ba. A zaune Mama take a gefen sa rik'e da hannun sa jikin ta yayi sanyi sosai ta kalli Hydar da yake tsaye shima tace, "Yaushe ne tafiyar taku ne? Kullum jikin sa sake gaba yake yi ya koma kamar bashi ba." Hydar yace, "an jima jirgin mu zai tashi zuwa India, amma ni Mama jikin Asad sai nake ganin kamar bana asibiti bane ba." Mama hawaye take ta dafe kanta tace, "Ban san me zance ba Hydar, mahaifin ku yace ciwon sa bana asibiti bane amma yak'i mayar da hankali a nema masa magani, dan Allah laifina sai ya shafi Asad? Duk soyayyar da yake yiwa Asad ace yana kwance a haka Abban ku baiyi komai ba kamar ma bai damu ba. Na shiga uku ni Rabi'a komai sake lalace min yake yi" ta fad'a tana sake dafe kanta da hannayen ta duka biyu. Hydar yace, "Za'a tafi India tunda kina so aje can sai muje in sha Allah zai samu lafiya." Hydar ya kalli Asad da yake kwance sai yaga kamar magana yake yi ya sunkuya da kunnen sa yana sauraron abinda Asad d'in yake cewa yaji yana fad'in, "Aliyu, Mama Aliyu." Hudar ya dago yace, "Mama Aliyu yake kira fa." Mama tace, "Wai ina yake tafiya ne? D'an uwan sa yana kwance babu lafiya amma shi yana can yawon duniya da y'an matan sa." Hydar yace, "Kiyi hak'uri Mama. Ina Jidda matar sa?." Mama ta dafe kanta bata bashi amsa ba dan bata san me zata ce ba. Kamar wacce ta tuna wani abu  sai ta mik'e tace, "Kafin ku tafi India akwai wajan wani malami da nake so naje na karb'o masa magani, maganin sa yayi tasiri sosai a kwanakin baya ka jira ni" ta fad'a tana fita ta sauka ta nufi b'angaren ta. Bata jira Suhaima ba ta nemi driver ya d'auke ta bai wuce ko ina da ita ba kai tsaye gidan su Rauda ta nufa. Dawowar Rauda kenan daga Bauchi tana zaune kamar ko yaushe jikinta a sanyaye ta rame sosai sai hasken ciki da tayi dan a lokacin cikin ta yayi wata d'aya harda kwanaki. Kasancewar bata laulayi baza ka fahimci ma ciki ne da ita ba sai ka sani. Umma na zaune kusa da ita gidan babu kowa duk an watse daga su sai su kamar ba shine akayi taro ba. Sallama sukaji anyi an shigo falon Umma ta kalli wacce ta shigo tare da amsawa, Rauda bata juya ba tana zaune hannun ta rik'e da ruwa wanda tasha ta rage ta rik'e a hannu bata kalli wacce ta shigo ba. Mama da take tsaye Umma ta kalle ta tace, "Bismillah ki zauna mana." Jikin Mama a sanyaye ta zauna ta kalli Umma tace, "barka da gida." Umma tace, "Yauwa sannu da zuwa" Umma ta fad'a da mamaki ganin yadda tayi magana kamar ba ita ba harda murmushi. Kallon Rauda tayi har lokacin bata san wanda ta shigo ba ta kalli Umma sai taji mugun nauyi ya danne mata k'irji ta sunkuyar da kanta k'asa a karo na farko da tayi hakan ga wank kafin ta d'ago ta sake kallon Umma tace, "Bata da lafiya ne?" Ta fad'a tana nuna mata Rauda. Umma tayi mata wani irin kallo kafin ta tab'e baki tace, "Eh bata jin dad'i." Mama tace, "Allah ya k'ara lafiya." "Amin" Umma ta amsa a tak'aice tayi shiru bata sake magana ba dan so take taji da me tazo kuma. Mama ta had'd'iye yawu dak'yar tace, "Alfar......" Sai ta kasa furta alfarma tayi shiru dan kalmar bata zauna a bakinta ba dan ba fadar ta take yi ba ta sake bud'e baki dak'yar, "Nazo neman alfarmar sake ganin Malam a karo na uku." Umma ta numfasa tace, "To ai ba'a gidan nan yake ba ko kin manta ne?." Mama ta girgiza kai tace, "Ban manta ba, iso nake so ayi min kamar wancan lokacin, ina son ganin sa da gaggawa ne." Umma tace, "Ai tunda kun gana wancan lokacin in kikayi masa bayani zai gane ki zai baki lokacin da zaki same shi." Mama a tausahe tace, "emergency nake son ganin sa, wanda zaiyi amfani da maganin India zai wuce anjima kad'an." Umma ta girgiza kai ta sauke numfashi tace, "To ga gidan namu shiru babu kowa balle a raka ki, sai dai in a neme shi a waya in ya bada dama sai kije ki ganshi." Mama ta girgiza kai tace, "Na gode." Umma ta d'auki wayar ta a gabanta ta kira Baba malam a waya ta katse bai d'auka ba ta sake kira a nan ya d'auka bayan sun gaisa ta sanar dashi dalilin kiran ya bata amsa sukayi sallama ta kashe ta kalli Mama tace, "Yace ganin sa yau bazai yu ba gaskiya, sai dai ki bari zuwa gobe in Allah ya nuna mana." Mama kamar zata zubar da hawaye ta kalli Umma muryar ta har rawa take yi tace, "Ina so na ganshi a yau d'in matsalar da take tare dani a yanzu har tafi ta baya." Umma tace, "To ga abinda yace ban san me zan miki bayan wannan ba." Mama tace, "a nema min alfarma a wajan sa dan Allah. Maganin sa yayi min tasiri matuk'a a kwanakin baya yanzu matsalar da Asad yake ciki har tafi wancan, dan Allah ki sake masa magana" Mama ta fad'a kamar da alama ta manta da talaka kamar Umma take magana jin yadda take karyar da murya baza ka d'auka ita bace ba, kana jin maganar ta kasan tabbas akwai damuwa sosai a tare da ita. Ambatar Asad da Mama tayi sai gaban Umma ya yanke ya fad'i amma sai ta jure bata nuna ba tace, "To ya kike so nayi miki? Nayi iya abinda zan iya tunda yace haka babu damar ganin naki ne a yau." Mama ta sauke numfashi jikin ta duk yayi sanyi ta kasa furta komai domin bata san me zata ce ba, duka burin ta akan maganin sane gashi bazata samu ba. K'arar wayar Umma ya saka Umma ta kalli wayar ganin mai kiran sai ta d'auka ta saka a kunne tayi magana kafin ta kashe ta kalli Mama tace, "Yace kije nan da mintina ashirin, kika wuce haka baza ki same shi ba." Nan take fuskar Mama ta washe farin ciki ya bayyana tace, "Yanzu kuwa zanje. Na gode sosai" ta mik'e tsaye ta kalli Rauda nan take sai gaban ta ya fad'i sosai amma bata nuna hakan ba tace, "Allah ya baki lafiya." Har lokacin bata kalle ta ba Mama ta fita zuciyar ta cikin farin ciki amma wani b'angaren na zuciyar ta mamakin kanta take yau itace ya nemi alfarma wajan k'ananun mutane kamar su Umma har tana had'a su da Allah. Tana fita Umma ta kalli Rauda tace, "Ke Rauda sai naji tace Asad ne babu lafiya, kenan wanda yake tare dake waye?." Nan take gaban Rauda ya buga ta d'ago ta kalli Umma itama ita take kallo ido cikin ido ta had'd'iye yawu tana kallon Umma. Umma tace, "Naji tace shine babu lafiya da alama jikin yayi zafi kuma ciwon duk yadda akayi bana asibiti bane ba duba da yadda ta tashi hankalin ta har take had'ani da Allah, kenan bayan ya daina zuwa wajan ki ya fara rashin lafiya ko kuma daman ba shi bane yake tare dake? Nifa jikina ya bani k'anin sane a tare dake bashi ba Rauda" Umma ta fad'a cikin tashin hankali tana kallon Rauda. Dumm gaban Rauda ya buga ta zaro idanu waje ta kasa magana ta rasa me zata ce tana kallon Umma itama cikin tsananin tsoro, Umma tace, "Bara baban ki yazo yana dakyau a bincika dakyau zuwan babar sa gidan nan ya saka ni a rud'ani, tunanina yana bani bashi ne a tare dake ba Aliyu ne." Rauda tayi shiru tana sauke numfashi hankalin ta har yafi na Umma tashi bata da kuzarin da zata nuna ne. Umma ta kuma cewa, "in kuma Asad din ne kenan bashi da lafiya? Babar sa bata san har yanzu da auren sa a tare dake ba kenan kome?. Tabd'ijam gaskiya akwai sauran rina a kaba." Ita dai Rauda shiru tayi amma yadda gaban ta yake fad'uwa Allah kad'ai yasan abinda take ji a zuciyar ta. Tashi tayi ta shiga d'aki kafin ta zauna wayar ta ta fara ihu ta kalli wayar taga Anty Ramla a kai sai ta samu kanta da yin murmushi har cikin zuciyarta ta samu waje ta zauna ta d'auki wayar ta saka a kunne, daga can b'angaren tace, "Amarsu ta ango, amarya kin sha khamshi." Y'ar dariya Rauda tayi kad'an kafin tace, "Ina kwana Anty." "Kin tashi lafiya Amarya? Ya kwanan amarci?." Rauda bata amsa ba sai tace, "Ina Dr fatan yana lafiya?." "Lafiya lau Rauda. Munyi miki laifi bamu shigo Nigeria bikin ki ba ko?. Wallahi Dr ne aiki ya masa yawa a asibiti ni kuma exams muke shiyasa baki ganmu ba amma dan Allah kiyi hak'uri, ki bawa Umma hak'uri zamu zo takanas dan ke." Rauda tayi murmushi tace, "Babu komai Anty meye na bada hak'uri dan Allah?." Ramla tace, "Ai dole na baki hak'uri duk yadda muke dake ace ban zo bikin ki ba ai babu dad'i." Rauda tayi murmushi tace, "Wallahi babu komai." Ramla tace, "To na gode da kika karb'i uzurina amarya" ta fad'a da niyar zolaya. Rauda murmushi ta sake yi kamar tana gabanta daga nan suka cigaba da hira kafin suyi sallama ta kashe wayar ta ajjiye a kan gado nan take kuma sai annurin fuskar tata ya d'auke ta lumshe idanun ta tana jin duniyar gabad'aya tana juya Mata komai yayi mata zafi kanta ya cushe. K'arar wayar tata ta sake ji ta d'ago taga sunan Rahma yana yawo akai nan take gaban ta yayi mugun fad'uwa kamar ta share sai kuma ta fasa ta d'auki wayar ta saka a kunne tace, "Asslamu alaikum." Daga can b'angaren Rahma tace, "Anty Rauda ashe kin dawo shine baki zo ba." Rauda tace, "Rahma kin san yanayin jikina ba lafiya ce dani ba." Rahma tace, "Haka ne, amma dai ya kamata ace kinzo." Ta sauke numfashi tace, "To zanzo in sha Allah. Amma ban ce ga rana ba zaki ganni dai kawai." "To ina nan ina jiran ki. Ya jikin?." "Alhamdulillah." "Kiyi hak'uri Anty Rauda." "Hak'uri name Rahma?." "Na komai ma." Rauda tayi murmushi tace, "to nayi akan komai d'in, bacci nake ji Rahma sai anjima mayi magana ko a whatsapp." Rahma tace, "shikenan sai anjima." ta fad'a tana yanke wayar ta ajjiye tana sauke numfashi k'irjin ta yana bugawa. Wai jinin ta Rahma ce matar Anas saurayin ta wanda suka jima tare suke burin yin aure ashe Allah bai rubuta ita zata aure shi ba ita ba duk wannan tsahon lokacin mijin Rahma ne ba mijin ta ba. Hawayen da take rik'ewa suka fara zuba a bayyane tace, "Meye makomar rayuwata? Cikin da ban san uban sa ba.....;eh ban san baban saba Asad ne ko Aliyu ban sani ba" ta fashe da kuka mai sauti harda shashsheqa. Umma da take tsaye tana kallon ta sai zuciyar ta ta karye itama hawaye ya ciko idanun ta dan ita kanta yanzu zuciyar ta tafi bata tabbacin Aliyu ne a tare da ita ba Asad ba. Da baya ta koma dan baza ta hanata kuka ba ta shiga nata d'akin ta goge hawayen idanun ta tace, "Meye amfanin mutum irin Malam? Meye ribar aure irin wannan, sabida kud'i kayi abinda ya saka jinin ka cikin wani yanayi wanda a shekaru ta yanayin ya girmi tunanin ta. Allah ka kawo mata mafita da sassauci" ta fad'a hawaye na sake sakko mata ta saka hannu ta share ta shiga band'aki. *☆☆☆*          Mama tayi sa'a taga Baba malam ta karb'o abinda zata karb'o ta koma gida, ana ajjiye mota aka bud'e mata ta fito taga sarkin mota ya shigo taja ta tsaya har ya ajjiye mota ganin irin kallon da take masa ya saka shi ajjiye motar da gaggawa ya k'araso inda take a guje. Yana zuwa ya zube yana kai gaisuwa ta kalle shi tace, "Kaine kake fita da Aliyu kwana biyu, ina kake kai shi?." Gaban sa yayi mugun fad'uwa rashin gaskiya ya bayyana akan fuskar sa ya had'd'iye yawu ya fara sosa kai yace, "Ranki ya dad'e" sai kuma yayi shiru. Mama tace, "Baza ka fad'a ba kenan?." Yace, "Tuba nake ranki ya dad'e, amma ni babu inda muke zuwa tare." Kai ta girgiza tace, "K'arya zaka min kenan ko? Shikenan jeka." Da sauri yace, "Tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ki. Tsakani da Allah gidan sa muke zuwa." "Mata kake kai masa ko?." "Ranki ya dad'e wata yarinya ce dai guda d'aya amma bayan ita babu ko wacce mace." Ran Mama ya kai matuk'ar wajan b'aci ta juya ta wuce ta shiga ciki ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na tsallake nata hukuncin sai na jira nasa kuma" ya fad'a kamar zaiyi kuka yana bin Mama da kallo dan da bai fad'a mata ba akwai matsala babba. Kai tsaye Mama b'angaren Asad ta wuce ta same shi da Hydar kamar yadda ta barsu tana shiga ta k'arasa inda yake kwance ta d'auko ruwan maganin da aka bata ta fara sha masa a fuskar sa da tafin hannu dana k'afa, ta saka Hydar ya d'ago shi ta zuba masa ruwan maganin a baki, kamar wanda aka bawa poison sai ya fara jijjiga idanun sa suna k'afewa suka firfito waje nan take. Hankalin Mama da Hydar yayi bala'in tashi suka rik'e shi dukkan su Mama na kuka tana kiran sunan sa amma har lokacin jikin sa rawa yake bai dawo daidai ba. Sai da yayi mintina biyu a haka kafin kuma ya lafa sai bacci ya d'auke shi Mama ta sauke ajiyar zuciya tana kuka. Kallon sa take yi ya koma wani iri kamar bashi ba a bayyane tace, "Lokacin da ya nuna min baya son sarautar nan da na k'yale shi da duk hakan bata faru ba, meye amfanin sarautar da babu lafiya a cikin ta? Asad ya koma kamar bashi ba kalli yadda ya koma kamar wanda ya shekara goma yana ciwo. Ka yafe min Asad" ta fad'a tana kuka sosai Hydar yana gefen ta yana goge hawaye. "Lokaci ya k'ure miki Rabi'atu!" Aka fad'a ana shigowa d'akin ita da Hydar suka kalli k'ofar dan sun san dai babu wanda ya isa ya shigo b'angaren. Mai martaba ne ya shigo da kansa bayan sa Uncle ne ya kalle su ita da Hydar sai yayi murmushi Hydar ya k'arasa inda yake yace, "Abbana." Kallon farin cikin da yake kan fuskar Hydar yayi sai ya girgiza kafad'ar sa yace, "Mazan gaske, sannu da k'ok'ari." Hydar yace, "Ina farin cikin samuwar lafiyar mai martaba, Allah ya k'ara lafiya." Uncle ya amsa da amin. Mama ta sunkyar da kanta k'asa ya Mai martaba ya kalli Asad da yake kwance a kan gado yace, "Hydar ban amince a fita da Asad wata k'asa ba zaman sa a nan nake so." Hydar ya kalli mahaifin nasa ya kalli Asad d'in da yake kwance amma babu damar musu sai yace, "duk abinda kace daidai ne." Mai martaba ya kalli Mama yace, "Ki daina saukar da kai Rabi'a lokacin saukar da kai d'in ya kusa amma ba yanzu ba. Bama ke kad'ai ba duk wanda ya shuka tsiya a bayan idanuna lokacin girbewar sa yazo." Shiru sukayi babu wanda yayi magana kafin yace, "duka mutanen gidan nan nake so a tattaro min duk wanda ya shafi gidan nan a had'o shi gobe in Allah ya kaimu ina son magana da kowa. Ina matar Asad?" Ya fad'a yana kallon Hydar. Hydar yace, "Tana gidan su wai bata da lafiya." Mai martaba yayi murmushin takaici yace, "Matar sarkin katagum guda ace tana gida bata da lafiya. An cutar da masarautar nan an b'ata mata suna an lalata garkuwar ta, amma yanzu lokacin gyaruwar tane." "Ina so aje azo da ita da mahaifiyar ta a goben, hatta tsohuwar matar sa wacce uwar sa ta raba su ina so na ganta a taron gobe ita da nata iyayen. Iya iyalan gidan nan nace a gayyato bance a gayyato min kowa ba, masu tunanin na nakasa bazan sake motsi ba gobe zasu tabbatar da har yanzu da lafiyata. Hydar kaji me nace?" Hydar yayi firgigit ya kalli mai martaba hankalin sa gabad'aya yana ga Asad yace, "Naji ranka ya dad'e, in sha Allah za'a yi abinda aka umarta." Kai ya d'aga ya k'arasa inda Asad yake ya dafa kansa yaji yadda kan yake harbawa a guje ya kalli Mama da robar maganin a hannunta ya girgiza kansa har zai magana sai ya fasa ya fita Uncle da Hydar suka take masa baya kowa da abinda yake cikin zuciyar sa hatta Mama da take tsaye wannan taro da za'a had'a ya tashi hankalin ta sosai ba kad'an ba. *Gobe akwai kura kenan*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼🤣🤣🤣 [17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@nanahaleema11* *076.*            Da kallo Mama tabi mai martaba k'irjin ta yana dokawa jin ya ambaci Rauda babban tashin hankalin ta bai wuce ita kuma me zatayi a taron da ya shafi iyalan cikin gidan su?. Bata da bakin magana haka ta juya ta kalli Asad da yake kwance ta zauna a gefen sa ta d'ora hannunta a kansa taji har lokacin yana harbawa. Numfashi ta sauke haka kawai fuskar Rauda ta fad'o mata a yadda ta tarar da ita sai ta samu kanta da fad'uwar gaba har ta dafe k'irjin ta a bayyane tace, "Fad'uwar gaban me nake ji akan yarinyar nan?." Ta dafe kanta da hannu biyu idanun ta a lumshe sai kuma ta d'ago kai tayi murmushi tace, "Rayuwa kenan." Sake juyawa tayi tana kallon Asad ta rik'e hannun sa tana jin wani irin d'aci a zuciyar ta.            B'angaren mai martaba yana fita daga b'angaren Asad jama'ar gida da suke so su  tabbatar shine kowa ya zube ana gaishe shi ana mamakin samuwar lafiyar sa lokaci d'aya ba wanda yayi tunanin hakan. Amsawa kawai yayi ya shiga b'angaren da yake bayan ya shiga d'aki Uncle yace, "Amma ranka ya dad'e sai nake ganin kamar anyi kuskuren bayyanar da samuwar lafiyar mai martaba ga iyalan gidan nan, akwai wanda baza su so hakan ba za kuma su so ace mai martaba ya sake kwanciya ciwo." Mai martaba ya zauna a gefe ya kalle shi yayi murmushi yace, "Mubarak kenan, dukka masu kawowa lafiyata farmaki a yanzu babu wanda ban gano shi ba, duk wanda yake a gidan nan kallon sa nake hatta Asad d'in ya bani mamaki matuk'a ban d'auka haka abin zai kasance ba da banyi gangancin damk'a amanar mutane a hannun sa ba." "Ranka ya dad'e amma sai nake ganin Asad kamar sharrin sihiri ne a tare dashi." Mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Akwai sharrin sirihi sannan kuma akwai....." Sai kuma yayi shiru sai yace, "Allah dai ya nuna mana goben akwai abubuwan da dama da zaku sani wanda zuciyar ku sai ta motsa da junsu, in ba'ayi sa'a ba wasu zasu suma na wucin gadi." Sai ya sake yin murmushi yace, "Akwai kuma wanda baza su so na kai goben da rai ba." Uncle yayi shiru kana yace, "Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya." Ya amsa da amin kafin yace, "Da zarar Aliyu ya shigo a sanar dashi ina neman sa, sannan ko waye yazo zai shigo b'angaren nan kar a bashi dama ko wace shima Aliyun sai dare nake neman sa." Uncle yace, "In sha Allah, a huta lafiya" ya fad'a yana fita yaja k'ofar ya bar mai martaba a zaune yana juya abubuwa da yawa a kansa.       B'angaren Fulani Hajiya tunda aka kawo mata labarin anga mai martaba da k'afar sa ya shiga b'angaren hankalin ta kai mak'ura wajan tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye, gabad'aya hankalin ta yakai makura wajan tashi ta shiga d'akin ta hannu na rawa take kiran number abokin shirin ta amma bai d'auka ba. Tsaki tayi ta kalli gefen gadon ta taga maganin da aka bata wanda take so ta bayar a masu dafa abincin b'angaren Mama su saka mata ta d'auke kai daga kansa dan yanzu ba shine a kanta ba so take ta same shi a waya su tattauna. Suhail ta kira yana d'auka tace, "Suhail mahaifin ka yana gida?." Daga can b'angaren ya bata amsa tace, "Zanje na same shi a can k'yale shi" tana fad'a ta yanke wayar ta sauke numfashi tana kallon agogo ganin la'asar ta kusa taja tsaki ta zauna. Sai yamma sosai sannan ta fita kai tsaye gidan da suke had'uwa dashi ta wuce jikin ta har rawa yake ta shiga falon kai tsaye sai kuma taja ta tsaya jin abinda take jiyowa daga ciki ana fad'a. Sak tayi jikin ta yayi sanyi ta wara idanun ta waje k'irjin ta yana bugawa sabida tashin hankalin abinda take jiyowa daga ciki. Muryar waziri taji yana fad'in, "Nasara munyi ta a akan Asad, munyi akan Aliyu sannan munyi a akan mahaifiyar sa. Asad lokacin haukacewar sa ne yayi domin an tabbatar min da tunda aka saka masa wannan layar da cikin kujerar zaman sa kuma ya zauna zance ya k'are ni hankalina baya tashi akan sa. Babban tashin hankalina yanzu Yayana Nasir da lafiyar sa ta dawo da kuma uwar gidan sa Sa'adatu." Muryar matar sa taji tana fad'in, "Ai tun farko sai da na fad'a maka bai kamata ka had'a kai da ita ba amma kace min tana da amfani yanzu gashi k'arshen abun yazo itama zata bamu tata matsalar, domin kasan baza'a yi maganin ta cikin sauk'i ba." Waziri yace, "tana da amfani ta taka rawar gani a cikin tafiyar nan, kinga master planer ta jaddada min tafiya da ita domin amfanin ta a cikin tsagin mu, tayi aiki yadda ya kamata amfanin ta ya k'are itama maganin ta zanyi." Matar tasa tace, "Me zaka yi mata?." Ya kalli matar tasa yace, "Zan saka a kulle mata baki ne yadda baza ta tab'a iya furta ko wacce irin kalma a kaina ba ko kuma na saka a kulle bakin nata har abada ya zama bazata kuma magana ba." Matar tasa tace, "Gaskiya dai ya kamata a d'auki mataki a kanta in ba haka ba zata zamar mana babbar barazana nan gaba." "Ko itama ayi mata irin ta Asad d'in ta koma ita ba mai hankali ba ita ba mara hankali ba, kinga kenan duk abinda zata ce babu wanda zai amince da ita." "Ko a ga bayan ta ba" matar ta fad'a tana kallon sa. Ya sauke numfashi yace, "nata duk daga baya ne, babban tashin hankalina yanzu dawowar mai martaba yafi komai d'aga min hankali ta wacce hanya zan daqile wannan kira na gaggawar da yayi?." Matar sa tace, "Ya dai kamata, a jikina nake jin wannan kiran bana alkhairi bane ba kira ne na tarwatsa dukkan plan d'in mu." "Allah ya tona asirin ka Yahuza!" Fulani Hajiya ta fad'a tana banko k'ofar falon ta shigo tana wuci tana kallon su. Dukkan su mik'ewa tsaye sukayi suna kallon ta da mamaki Waziri ya kalli matar sa itama ta kalle shi suka dawo da kallon su a gare ta babu alamun tsoro ko tashin hankali a tare dasu. "Nayi dana sanin had'a kai dakai akan komai, Yahuza ni kake k'ok'arin kashewa? Duk fad'i tashin da mukayi ko nace muke kan yi ashe daman hak'ar ka kake so ta cimma ruwa ka cillar dani a gefe?" Ta fad'a cikin d'aga murya tana kallon sa da mamaki da kuma tsoro. Waziri ya sassauta murya yace, "baki fahimci abinda nake nufi ba, amma zauna nayi miki bayanin komai." "Babu wani bayani da zakayi min naji komai da kunnena. Naji duk abinda kuke kitsawa kaida munafukar matar ka, ni kake shirin haukatarwa ko kashe ni dan ka rufe bakin tsanya babu wanda yasan abinda ka aikata ko?. Meyasa ma na amince dakai ne ni?" Ta fad'a tana dafe kanta da hannu d'aya tana cizon tsaya. Matar tasa zatayi magana tace, "Dalla rufe min baki, munafuka algunguma. Duk taimakon da na yiwa mijin ki ke kike bada shawarar kashe ni ya kamata ayi sabida kuyi mulki son ranku babu mai kawo muku barazana a cikin sa. D'ana ba mulki zaiyi a cikin shekarun nan ba amma na gwammace na had'a kai da mijin ki akan y'ay'an mijina. Nayi dana sanin bashi goya baya a rayuwata, ban tab'a aikata abinda naji na tsani kaina lokaci d'aya ba kamar wannan ba, kun bani mamaki matuk'a kun kuma koya min hankali kodan sabida gaba." Waziri yace, "Baki fahimci abinda nake nufi bane Sa'adatu ki zauna nayi miki bayani." Ta sake fusata ta nuna shi da yatsa tace, "Bazan kuma tab'a fahimta ba har a tashi duniya. Ka bani mamaki na kuma gano kuskuren dana aikata sabida kai, sabida kai na juyawa mijina baya kawai dan ka samu abinda kake so amma yau kaine kake tunanin hanyar da zaka ga bayana sabida kar nan gaba na tona maka asirin abinda ka aikata. Ka kyauta na kuma gano kuskurena ne tun farko dana had'a kai da mugu mai bak'ar zuciya irin ka. Inda na bar Asad d'in yana mulki lafiya lau ai da hakan bata faru ba amma na zab'e ka na barshi bayan bai tab'a aikata min wani abun mara kyau ba tun yana yaro." Waziri ya canja fuska yace, "kar ki yi k'ok'arin kawo min maganar banza dan kinga nayi miki shiru, bawai tsoron ki nake ji ba ya kamata kisan da hakan." "Nima kuma ba tsoron ka nake ji ba! Kai kasan nida kai kar ta san kar ne babu wani sirrin ka da baya tafin hannuna kuma lokacin da zan bayyana shi yazo, dan wallahi tunda niyar ka ta kashe ni ce sai na tabbatar ka rasa mulkin nan koda zan rasa raina ta dalilin hakan domin bazan barka kaci riba ba, sai na tabbatar da shiga gidan sarauta ya gagare ka kamar yadda ka saka ya gagari wasu daga cikin gidan. Duk wani shirin mu zanje na samu mai martaba na zayyana masa komai sai dai ya saka a kulle mu nida kai dan wallahil azim sai dai ayi tab'are!" Ta fad'a tana dukan kujera tana nuna shi da tsaya. Juyawa tayi zata fita Matar sa tayi saurin tsayawa a gaban ta tace, "Hajiya duk wannan tashin hankalin fa bai tashi ba dan Allah ki tsaya ki fahimci juna abin bai kai haka ba." Rai a b'ace Hajiya tace, "Zaki matsa min daga hanya ko sai na tsinke ki da mari? Ba kece munafukar da kike cewa gwara aga bayana ba..? To ni zan fara ganin naku bayan kafin ku kuga nawa, kud'irin ku akan mai martaba ne yanzu ai ko...? Ina tabbatar miki da zai ji komai tun kafin ku aiwatar da nufin ku a kansa dana y'ay'an sa" tana fad'a ta rab'a ta gefen ta fita a fusace. Matar ta dawo kusa daahi tace, "Ranka ya dad'e kayi wani abun kafin ta tarwatsa mana shirin da mukayi shekara da shekaru muna shiryawa, fitar ta ba k'aramar illa bace a gare mu kasan abinda zakayi." Ya kalli inda Hajiya ta fita yace, "Kyale ta zanyi maganin ta, ba burin ta taje ta sanar dashi shirin mu ba...? Ina tabbatar miki da baza taje inda take so taje ba." Matar sa cikin tashin hankali tace, "Ta yaya kenan?." "Ki yarda na fad'a miki, bazata isa gida lafiya ba kota mutu ko tayi mumman hatsari" yana fad'a shima ya fita tabi bayan sa da sauri suka shiga mota suka bar gidan. Bayan sallar magariba a cikin gidan Sarki aka sanar da mummanan hatsarin motar da Hajiya ta samu a kan hanyar ta ta dawowa gida, hankalin iyalan ta ya tashi sosai suka d'auki mota zuwa asibitin da akace tana can.         *☆☆☆*            Umma ce ta shiga d'akin da Rauda da take ta ganta kamar ko yaushe tana zaune tana aikin tunani bayan ta idar da sallah. Umma ta k'arasa ta shiga ta zauna a gefen gado tace, "Rauda." Rauda ta d'ago ta kalli Umma tace, "Na'am Umma." Umma tace, "tsohon sarki Katagum mahaifin Asad kenan shine ya aiko da sak'on yana son ganin ki bama ke kad'ai ba harda mu gobe." Rauda da take kallon Umma tana jin me take ji tace, "Neman na meye?." Umma tace, "Wallahi ban sani ba Rauda. Tunda y'ay'an sarkin nan suka shigo rayuwar mu suke buga mu kamar kwallo, wannan ya buga mu nan wancan ya tare, wannan ya sake buga mu can wannan ya tare. Rauda lamarin nan gab yake da saka min ciwon zuciya." Rauda tayi shiru kanta na k'asa tace, "To Umma basai muk'i zuwa ba." Umma tace, "bamu san abinda zai faru a can ba yana da kyau muje dan duk abinda zai faru nasan akan rayuwar kine. Rauda in cikin jikin ki ya tabbata na d'an uwan Asad ne ba nashi bane ya zanyi da raina? In ta kasance da gaske kuma Asad ya sake ki fa?. Wannan kwamachalar bata d'aukar hankali da tunani; zata iya barazana a gare mu." Rauda tace, "Kiyi hak'uri Umma." "Ba laifi kikayi min ba Rauda, nasan duk abinda ya faru k'addara ce daga Allah amma duk mahaifin ki shine sila." Rauda tayi shiru har Umma ta kai k'arshe sai ta rik'e hannun Umma ta d'ora a kan k'irjin ta tace, "Umma kullum ji nake zuciyata kamar zata fashe, Umma a kullum bana tunanin in na kwanta zan tashi da raina sabida a yanayin da nake kwanciya bana tunanin zan iya tashi. Umma in na tuna Allah ya isar ki a kaina sai nayi dama na mutu na huta" ta fad'a tana fashewa da kuka ta d'ora kanta a cinyar Umma. Umma ta sauke numfashi tace, "Ki cigaba da hak'uri komai yana gab da zuwa k'arshe in sha Allah. Rayuwar ki tana cikin rud'ani na sani amma haka Allah yaso jarabawa ce Allah ya baki ikon cinyewa Rauda." Kuka take a cinyar Umma sosai sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi Umma ta lalaba ta ta kwanta a akan gadon badan tana jin bacci ba. *☆☆☆* "Mum me za'a yi da akace ana kiran meeting? Nidai gaskiya bazan je ba sai daku kuje keda daddy" Jidda ta fad'a a rud'e tana kallon Mum. Mum tace, "Dole kuwa kije domin akan ki maganar take ba'a kaina ba, mahaifin ki baya nan dole nida ke d'in zamu je." Jidda ta girgiza kai tace, "Nidai bazan je ba Mum, bazan iya zuwa ba tsoro nake ji kar muje an gano komai." "Nima kaina tsoron nake ji Jidda amma ya zama dole muje in bamu je ba shima wata matsalar ce, zuciyata bugawa take yi sosai ban san me zan tarar a goben ba." Jidda ta fashe da kuka tace, "Nidai Mum bazan je ba zan iya mutuwa in akace sai naje, bazani ba." Mum binta take da kallo ganin yadda ta tsorata sosai kamar ita tayi wani babban laifin tace, "Jidda ni ya kamata naji tsoro bake ba, amma sai naga kin fini ma jin tsoron. Wannan yanayin naki yana sakawa na sake jin tsoro domin ban san me kika aikata ba." Jidda kawai ta tashi ta fita dan babu wanda zai saka ta tafiya gobe bazata je asirin ta ya tonu ta shiga uku ba gwara koma meye zai faru ya faru a bayan idanun ta ba a gaban idanun ta. *☆☆*         "Dole a san abinda za'ayi bana son Abba ya kai gobe da ransa ya zama dole na tabbatar ya koma rashin lafiya ko kuma ya mutu gabad'aya" ya fad'a yana hakki cikin tashin hankalin daya bayyana a tare dashi zuciyar sa har bugawa take yi sabida rud'ani da tashin hankalin zuciyar sa. Kamar an tsikare shi sai ta mik'e ya lek'a taga yaga dare ya fara mutanen gidan suna ta raguwa ya kalli d'akin Hydar ya tabbatar yana ciki ya sauke ajiyar zuciya yana sake girgiza kansa. Komawa yayi ya zauna yana girgiza k'afa tare da cize baki yana ji kamar ya jawo dare yayi sosai yaje ya aiwatar da abinda yake so ya aiwatar. Yana nan zaune k'arfe d'aya na dare ta buga ya zabura ya mik'e ya fita daga falon kai tsaye b'angaren mai martaba ya nufa ba tsoro a tare dashi balle fargaba. Masu tsaron k'ofar duk sunyi bacci ya shiga falon ya jishi shiru an kashe komai na falon baka ganni koda hannun ka sabida duhu, da yake ya haddace komai hatta hanyar da take falon ya haddace ta a haka ta k'arasa har k'ofar d'akin mahaifin nasa. Tunanin bud'e k'ofar yake dan yasan tabbas in ya bud'e zai iya ji gashi shi kuma baya son b'ata lokaci. "Sai me ma dan ya ganni? Mtsww" ya fad'a a bayyane yana jan tsaki ya tura k'ofar d'akin cikin dakewar zuciya da son idda nufin sa akan mahaifin nasa kai tsaye. Hasken a.c kawai ake gani a d'akin ya nufi kan gadon kai tsaye duk da baya gani sosai amma ya tabbatar da yana kwance a kan gadon a wannan lokacjn. Zagayawa yayi ta gefe ya d'auki pillow da yake gefe a ajjiye ya nufi inda yake hango tudun Abba daidai inda yasa kansa yaje ya danna pillow a kai da niyar toshe masa numfashi da k'arfin gaske. Ba zato babu tsammani yaga haske ya gauraye d'akin ya firgita matuk'a ya d'ago kai a firgice yana kallon inda switch d'in fitilun yake don ganin wanda ya shigo a lokacin da bai shiryawa hakan ba. [17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *077*            A tsaye yaga mai martaba hannun sa hard'e a k'irji yana kallon sa fuskar sa da murmushi da alama baiyi mamaki ko al'ajabi da ganin abinda yake shirin faruwa ba yasan daman hakan zata kasance, bai san pillow hannun sa ya sub'uce ba yayi baya kamar zai fad'i idanun sa kyam akan na mahaifin sa tashin hankalin da ya bayyana a tare dashi ba d'an kad'an bane ba. Murmushi mai martaba yayi ganin yadda ya firgice sai ya tako a hankali yazo inda yake yace, "Gani gaka zaka iya kashe ni in kana so." Baya yayi ya nisanta kansa daga kusa dashi jikin sa yayi bala'in yin sanyi duk ya dabarbace alamun rashin gaskiya amma babu alamun nadama ko kunya a tare dashi. Murmushi yayi ya sake cewa, "Kana tunanin ban san waye kai ba? Ko ina tunanin duk abinda yake faruwa a gidan nan ban sani bane ba?. In hakan kake tunani ka d'auka kayi babban kuskure duk abinda kuke aikatawa a tafin hannuna yake kuma k'arshen ku yazo ka tabbatar da komai ya kusa zuwar muku k'arshe." Zuciya ce take d'aukar sa akan kawai ya shak'e mai martaba ya huta in ba haka ba gobe zata zamar masa barazana ga rayuwar sa gabad'aya in ba kashe shi yayi ba hankalin sa bazai tab'a kwanciya ba, hannu biyu ya d'ago da niyar kaisu wuyan mai martaba sai kuma suka had'a ido ya fasa mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Kashe ni mana ya zaka fasa?." "Ba kai kad'ai kake son kashe ni ba a yau kuna da yawa wanda basa so gobe tayi, baku san me zan tattauna a  goben ba amma dukkan ku hankalin ku ya tashi kun manta da karin maganar da bahaushe yake cewa rana dubu ta b'arawo rana d'aya tak ta mai kaya. Dubun ku ta cika gobe lokacin girbar abinda aka shuka ne." Kamar wanda aka yiwa allura ya zabura ya kama wuyan mai martaba da k'arfin gaske ya matse yana fad'in, "Bazan iya bari ka kai gobe ba koda nima bazan kai ba, gwara na kashe ka in yaso nima a kashe ni" ya fad'a yana sake matse masa wuya da k'arfi. Shigowa d'akin akayi aka kwace mai martaba daga hannun sa Uncle ya tsinka masa mari ya sake marin sa ya bishi da kallon b'acin rai yana fad'in, "Ban tab'a d'auka rashin hankalin naka har ya kai haka ba sai yanzu, duk abinda ka aikata baya bai ishe ka ba sai ka had'a da kashe mahaifin ka." Mai martaba ya zauna gefen gado yana tari kad'an yace, "Mubarak kaje dashi a killace shi a wani wajan bana so ya gudu daga gidan nan, kuje a tabbatar an saka masa matakan tsoro yadda ya kamata." Da k'arfi Uncle ya jashi yak'i tafiya ganin hakan Galadima shima jashi suka fita dashi dak'yar. Mai martaba ya bisu da kallo bayan sun fita ya shafa wuyan sa hankalin sa ya tashi sosai zuciyar sa tayi rauni dan bai d'auka duk zafin kansa zai iya k'okarin kashe shi ba idon sa yana cikin nasa ba, ya d'auka zai tsaya yi a bayan idanun sa amma bai d'auka yana kallon sa shima yana kallon sa zai iya kashe shi ba. Ya sauke numfashi a bayyane yace, "Me ake da irin wannan haihuwar?."       Ba jimawa Uncle ya dawo ya k'araso wajan Mai martaba yana fad'in, "Ranka ya dad'e babu abinda ya faru dai ko?." Mai martaba yace, "Babu abinda ya faru, ina kuka ajjiye shi?." "Yana d'akin cikin b'angaren nan yanzu haka Galadima yana wajan sa an masa d'auri mai kyau. Mai martaba zufa yake a kunna a.c" ya fad'a yana d'aukar remote zai danna yayi saurin dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Kar ka kunna, yanzun nan na kashe ta akwai wanda suka zuba guba a cikin ta da zarar na shak'a zan mutu kamar yadda akayi a wancan lokacin." Uncle yace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, mutane me suke nema a duniya suka mayar da kashe musulmi ba komai ba?. Jinin ka shine yake son ganin bayan ka a koda yaushe meyasa duniya ta koma mai amana kad'an ne?." Mai martaba yace, "Dukkan su basa so na kai gobe dalilin da ya saka hakan kenan, suna nan da yawa domin ba mutum d'aya bane dukka kuma na san su d'aya bayan d'aya." Kai ya girgiza yace, "Ai gwara Allah ya tona asirin su kodan suji kunyar duniya su kuma jira jin ta lahira." Mai martaba yace, "Kaje ka huta Allah ya kaimu goben." "Bazan iya tafiya na bar mai martaba a a wannan yanayin ba." "Kar ka damu jeka" ba musu Uncle ya fita ya kulle masa k'ofa zuciyar sa babu dad'i. Washe gari.           "Rauda wai meye haka ne? Amma kin san dai na fad'a miki mai martaba shine yace yana neman mu ko?" Umma ta fad'a tana kallon Rauda da take a zaune a gefe. Rauda ta kalli Umma da jajayen idanun ta kamar ko yaushe tace, "To Umma me zanje nayi a can?." "Tunda ya neme ki me zai hana baza muje ba kika san abinda ya faru?." Rauda tayi shiru tace, "Umma gabad'ayan iyalan gidan su bana son ganin su duka, sun yi min mugun tabo a rayuwata bana son sake had'a ido da ko wanne su." Umma ta kalle ta tace, "Na sani Rauda duk abinda ya faru ai babu wanda ban sani ba, tun shigowar iyalan gidan su rayuwar ki komai yake lalacewa amma Allah ne ya rubuta hakan kuma shine zai gyara komai ai." Sunkuyawa tayi tana kuka Umma taga shatin dukan da tasha a hannu Baba a kwance a bayan ta sai jikinta yayi sanyi ta sauke numfashi tana kallon ta. Sai kuma ta d'ago daga kukan ta kalli Umma tace, "Umma Rahma ta takura min akan naje gidan ta har yanzu Allah bai bani iko ba, bana son zuwa sai naga kamar zuwana gidan ta bazai zama alkhairi ba" ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Umma ta zauna a gefen ta ta dafa ta tace, "Me zai hana shi zama Alkhairi Rauda? Daman fa ba kece matar Anas ba duk wannan fad'i tashin da yayi a kanki Rahma ce matar sa bake ba, Allah bai bayyana mana hakan bane sai yanzu da lokacin bayyanar tayi. Ki duba k'addarar farko da ta raba ku sannan ki duba wannan wacce ta sake raba ku in kikayi tunanin nutsuwa zaki tabbatar da daman ba shine mijin ki ba kuma kin sa baka tab'a auren mijin da ba naka ba kamar yadda baza ki shiga kabarin da ba naki ba, shiyasa hausawa suke cewa matar mutum kabarin sa." Kai ta d'aga ta goge siraran hawayen ta tace, "Haka ne Umma. Amma ina jin kunyar had'a ido dashi ita kuma kar taga kamar da biyu nak'i zuwa gidan." Umma tace, "babu komai ki bari ki samu lafiya sosai sai kije."  Rauda tayi shiru kanta a sunkuye Umma tace, "Me kike so kici yanzu? Tun safe baki ci komai ba."      Rauda bakin ta ya fara rawa tana so tayi magana kuma kuka ya hanata fad'a. Umma tace, "Wai sau nawa zaki kuka ne a rana Rauda? Bakya gudun idanun ki su samu matsala sabida zubar da hawaye?. Haba dan Allah ki d'auki k'addara mana kamar yadda muma muka d'auka, mun san kin fimu jin ciwo amma ya za'ayi fad'an da yafi k'arfin ka sai ka mayar dashi wasa, waye ya isa yaja da jarabawar ubangiji a cikin mu?." Rauda ta goge idon ta tace, "Umma ciki ne fa dani." Umma tayi murmushi tace, "Cikin halak ne ai wanda aka same shi da aure da meyasa kike damuwa aka sa?." "Bani da tabbacin cikin Asad ne Umma, zuciyata tana fad'a min cikin Aliyu ne bana Asad ba." "Ni jikina yana bani cikin Asad ne, zuciyata ta gamsu da Asad mijin kine cikin sane a jikin ki bana dan uwan sa ba." "Ni kuma in na tuna ance bashi da lafiya sai naji jikina yayi sanyi na sake tabbatar da cikin na Aliyu ne Umma, in hakan ta kasance na shiga uku na lalace." "Kar na sake ji kince kin shiga uku na fad'a miki komai ya faru da bawa daga rabbil alamina ne kema tak'i jarabawar shine ya jarrabo miki in kina furta irin wad'annan kalaman sai kizo ki fad'i, fad'uwar jarabawar ubangiji ba fad'uwar jarabawar duniya bace ba da zaka jure kace ka sake rubutawa, fad'uwa ce ta har abada domin kuwa imanin kine yayi rauni shiyasa kika fad'in." Rauda tayi shiru ta lumshe idanunta ta buɗe tana kallon bangon d'akin Umma tace, "Me kike so kici?." Rauda ta kalli Umma ta sunkuyar da kanta k'asa tace, "Shinkafa da miyar manja mai kifi." Umma ta mik'e tace, "Yanzu za'a kawo miki" ta fad'a tana fita zuciyar ta cike da tausayin Rauda d'in. Babu b'ata lokaci Umma ta had'a mata shinkafa da miyar manja kamar yadda tace ai kuwa taci sosai dan ta jima bata ci abinci mai yawan wanda taci ba dan taji dad'in ta musmaman da Umma ce tayi mata da kanta sai take jin wani abun na zuciyar ta na raguwa. Bayan sallar azahar aka aiko da mota daga gidan sarauta gidan su Rauda dan d'aukar su aje inda mai martaba yake neman su gabad'aya, Umma dak'yar ta lallab'a Rauda Baba ya dawo suka tafi a motar baza ma ka d'auka su bane da glass d'in ta bak'i ne sosai baka ganin na ciki sai dai shi ya ganka. Can wajen gari suka nufa dan a can ne za'a taru ba cikin gidan sarauta ba sabida abinda za'a tattauna baza'a yishi kowa yaji ba, babban gida ne ginin sarauta mai kyau da tsari tamkar masarauta haka yake sabida kyau da kuma zanen jikin sa. tunda suka doshe shi gaban Rauda yake fad'uwa haka kawai bata san dalilin hakan ba jikinta ya sake jin sanyi fargabar da take ciki ta saka take jin marar ta na ciwo kad'an-kad'an. A harabar gidan suka ga tarin motoci da alama mutanen da suka danganci taron duk sun hallara aka faka tasu motar drivern ya kalle su yace, "Ranku ya dad'e ciki zaku shiga." Da to suka amsa suka fito Umma ta rik'e hannun Rauda suka nufi inda ya nuna musu dukkan su zuciyar su rawa take. Duk takun da zasuyi da bugun zuciyar Rauda ake yin sa har suka bud'e wata k'ofar glass suka shiga sai ga mutane a zaune a falon dukkan su a k'asa, kan Rauda yana k'asa tana ji suna gaisawa dasu Baba ita kam bata iya kallon kowa ba kirjin ta bugawa kawai yake yi tashin hankali yayi mata yawa. D'ago ido tayi a hankali idon ta ya fad'a na Jidda da take binta da kallo ta d'auke kai ta kalli gefen ta taga Asad a zaune ya dafe kansa kana kallon sa kaga mara lafiya dan ya rame sosai. Nan take gabanta ya sake fad'uwa ta mayar da kanta k'asa zuciyar ta na tafiya a guje kamar zata fito sabida tashin hankali. Sallama sukaji dukkan su suka mik'e tsaye ganin hakan Rauda ma ta tashi mai martaba ya shigo yana kallon kowa da murmushi a fuskar sa ya zauna a akan kujera yana bin su dukka da idanun sa kafin ya girgiza kai yace, "muna fatan mun same ku lafiya dukkan ku." A tare aka had'a baki aka amsa yayi shiru kafin ya kalli Uncle yace, "a bud'e mana taro da addu'a." Uncle kalle su yace, "Salati ga annabi." Aka amsa gabad'aya kowa yayi shiru ana salati kafin Uncle ya kuma cewa, "A karanta suratul iklas k'afa uku da niyar saukar alkur'ani duk abinda muka saka gaba a taron nan Allah ya tabbatar mana dashi, duk sharrin da yake ciki Allah ya watsar dashi a wannan lokacin." Aka amsa nan ma akayi ya kalli mai martaba alamun an kammala. Mai martaba yace, "Alhamdulillah. Ina godiya ga Allah da ya bani ikon ganin wannan rana mai cike da rud'ani da farin ciki da tashin hankali da bayyanar wasu abubuwa a cikin ta, nasan akwai wanda basu so ganinta ba amma da yake Allah ya k'addara zuwan ta babu abinda mutum ya isa yayi a akan hakan." "Da yawanku baku san Malam Adam da kuma iyalan sa ba wasun ku suna ta mamakin me ya kawo su taron cikin gida to suma y'an gida ne domin y'ar sa itace tsohuwar matar Asad duk wani abu da za'a tattauna ya shafe ta domin kuwa tana cikin rud'ani itama tana so a warware mata duk abinda yake wakana a cikin tata rayuwar. Kowa ya d'ago yana kallon su ita dai Rauda bata kalli kowa ba mai martaba ya sake cewa, "Ina so dukkan ku ku kalli Asad da Aliyu ku nuna min waye Sarkin Katagum a cikin su." Mamaki fal zuciyar dukkan su kowa ya kalle su cikin mamakin tambayar mai martaba aka nuna Asad da yake zaune cikin manyan kaya har lokacin hannun sa na dafe da kansa. Mai martaba ya girgiza kai gani wanda suka nuna yace, "Rauda!." Gabanta ya fad'i ta d'ago kafin tayi magana yace, "Nuna min mijin ki a cikin su." Ta kalle su dukkan su duka babu wanda yake kallon ta a cikin su ta nuna Asad da yake zaune kamar yadda aka nuna shi d'azu. Mai martaba yayi murmushi ya kalli Mama da take a firgice matuk'a yace, "Rabi'a nuna min d'anki Asad kuma sarkin ku a cikin su." Mama ta firgita dan bata hankalin ta ta fara zare idanu cikin tashin hankali, "baki ji abinda nace ba?" Ya sake maimaitawa sai lokacin ta dawo nutsuwar ta ta nuna Asad da yake zaune kamar yadda kowa ya nuna. Mai martaba yayi murmushi yana kallon su shima kafin yace, "Duk wanda kuka nuna kunyi daidai shine Asad kamar yadda kuka sani amma fa kamar yadda ake nuna muku." Kowa ya kalli mai martaba alamun karin bayani dan basu fahimci kalmar sa ta k'arshe ba. Ganin hakan ya saka shi ya girgiza kai yace, "Wanda kuka nuna ba shine Asad ba, wanda yake zaune a gefen sa shine Asad duk wanna kuke nunawa yanzu Aliyu ne ba Asad ba!." [17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *078.*          A tare dukkan su k'irjin su ya buga nan take kowa ya d'ago kai yana kallon mai martaba ana kuma kallon Asad da Aliyu da suke zaune kowa d'auke da zallar mamaki da tsoro a tare dashi. Rauda firgitar da tayi sai da ta bayyana a gangar jikinta tayi baya kamar zata fad'i tayi saurin dafa carpet ta kai kallon ta ga wanda akace shine Asad idon ta ya shiga cikin nasa tayi saurin janye nata ta dafe k'irjin ta da yake bugawa tana raba idanu a kan carpet tsoron ta ya ninka na baya. Babban tashin hankalin ta da firgicin ta bai wuce da gaske cikin Aliyu ne kenan a jikinta bana Asad ba tunda gashi wanda duk suka nuna ba shine Asad d'in ba Aliyu ne, nan take hawaye suka fara wanke mata fuska jiri yana d'aukar ta tana jin kamar ta zube a wajan duk da a zaune take hakan bai hanata jin kamar iska zata kwashe ta ba, marar ta juyawa take kad'an-kad'an ta runtse tana cije bakin ta hankalin ta ya kai k'arshe wajan tashi. Babu wanda ya isa yayi magana sai an bashi umarni hakan ya saka kowa yayi shiru idanu a waje yana jiran yaji abinda mai martaba zaice. Mai martaba ganin dukkan su firgici ya bayyana a tare dasu sai ya murmusa yana kallon Asad da Aliyu yace, "Dukkan ku mamaki ya bayyana a tare daku, wataƙila ma wasu suna tunanin Anya abinda na fad'a gaskiya ne?. Abinda kuka ji gaskiya ne wannan shine Asad wannan kuma shine Aliyu" ya sake fad'a yana nuna su da yatsa kamar d'azu. Uncle da firgici ya dabaibaiye shi yace, "Ranka ya dad'e ban katse ka ba, amma bamu fahimci abinda ake fad'a mana ba. Asad shine Aliyu; Aliyu kuma shine Asad?." Mai marataba yayi murmushi yace, "Dukka wannan tunanin shine a ranku gabad'ayan ku na sani. Abinda nake nufi a nan wanda ya jima yana mulkar ku a garin Katagum Aliyu ne ba Asad ba!." A tare aka had'a baki wajan cewa, "Aliyu kuma ranka ya dad'e?.!" Dukkan su basu san sun fad'a ba tashin hankali ya bayyana sosai a tare dasu gabad'ayan su jikin su har tsuma yake burin su kawai suji k'arshen maganar da mahaifin nasu zai fad'a. Mai martaba ya girgiza kai yace, "Tabbas Aliyu ne yake mulkin garin nan a matsayin Asad, wanda kuke d'auka yana can k'asar Bahrain shine Asad ba Aliyu ba" ya fad'a yana kallon su dukkan su fuskar sa a sake yana karantar yanayin kowa daki-daki dan akwai abinds yake so ya zaqulo a fuskokin nasu. Kan kowa ya d'auki chaji sun kasa fahimtar inda maganar mai martaba ta dosa kansu ya kulle an rasa fahimtar inda zancen ya saka gaba balle ayi masa fashin bak'i a gane mai maganar take nufi. Mama da tafi kowa firgicewa a cikin su tace, "Ranka ya dad'e mun kasa fahimtar inda maganar ta nufa, muna so a warware mana ko hankalin mu zai kwanta. Aliyu matsayin Asad, Asad matsayin Aliyu ta yaya hakan zai kasance?." Mai martaba ya sauke numfashi ya sake kallon Asad da har lokacin hannun sa yake dafe da kansa ya kalli Aliyu da kansa yake a k'asa baice komai ba ya kalli jama'ar falon gabad'aya ya sake cewa, "Asad yayi mulkin katagum na y'an kwanaki kad'an, daga lokacin da ya kai min ziyara Germany Asad bai sake dawowa Nigeria ba, Aliyu ya dawo a matsayin shine sannan aka sanar daku Aliyu yana can wata k'asa yak'i dawowa, a zahiri kuma Aliyun dai dashi kuke tare Asad kuma shine a Bahrain." Waziri da zufa take tsatstsafo masa ya saka hannu ya share ya kalli Yayan nasa yace, "Mai martaba mun kasa fahimtar maganar nan har yanzu, muna so ayi mana dalla-dalla kafin zuciyar mu ta buga." Mai martaba yayi murmushi mai kyau yana kallon sa yace, "iya wannan maganar da kaji har zuciyar ka na barazanar bugawa? Lallai akwai aiki a gaban ka in kaji wacce take gaba zata iya zama silar d'aukar ranka gabad'aya." Waziri ya sunkuyar da kai k'irjin sa na bala'in bugawa hankalin sa a tashe yake sosai. Mai martaba ya sake kallon su gabad'aya yana cewa, "Wannan mai mayan kayan da yake zaune dafe da kansa ba Asad bane Aliyu ne shi kuke kallo matsayin sarkin ku tun lokacin da ya wuce, wannan kuma da yake zaune shine Asad wanda kuke yiwa kallon Aliyu kwanakin baya da suka wuce. Yanzu kun gane?" Ya fad'a yana kallon kowa yana nuna musu su kowa sai ya bisu da kallo cikin tashin hankali. Ganin su kasa magana mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Dukkan ku babu wanda yasan da abinda yake faruwa duka d'auka kuke Asad dai shine a garin nan Aliyu kuma shine baya nan, mutum biyu zuwa uku sune kawai suka san da abinda yake faruwa a gidan, ta farko itace matar Asad." Gaban Rauda ya fad'i ta d'ago kai da jajeye idanun ta mai martaba yace, "Hauwa'u Jidda, itace tasan bada mijin ta take tare ba da Aliyu yake tare. Haka ne ko Jidda?" Mai Martaba ya fad'a yana kallon ta jikin ta. Mugun rawa jikin Jidda yake yi zufa ta gama jika ta gabad'aya hawaye wani yana bin wani a fuskar ta yadda jikinta yake girgiza kamar wacce wutar lantarki take ja a wannan lokacin. Kowa kallon sa ya mayar ga Jidda ganin yanayin ta ya bawa kowa tsoro har numfashin ta ne yake mik'ewa kamar zai bar jikinta sabida tashin hankali. Bazata iya magana ba ji take kamar an sarqafe mata bakin ta da mukulli sai ido kawai da take binsu dashi fuskar ta tayi ja sosai har cikin jikinta girgiza yake sabida bala'in tashin hankali. Mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Bana so na fad'i ta biyun sai a k'arshen zaman nan. Ina so ku tuna dukkan abubuwan da suka faru daga zuwan Asad Germany; daga tafiyar sa duk abinda ya faru a bayan nan Aliyu ne yake aikata su ba Asad ba, ciki kuwa harda sakin ki da akazo akayi har gida Rauda, Aliyu ne ba Asad ba domin Asad baya Nigeria gabad'aya" ya fad'a yana kallon Rauda da kanta yake a k'asa. Rauda bata fahimci ma mai yace ba hankalin ta ya tashi tunanin uban cikin jikinta gabad'aya hankalin ta baya tare da ita kanta ya kulle so take azo gab'ar da zata fahimci cikin waye a jikinta shine kawai burin ta da kuma fatan ta. Mai martaba ya kalli Aliyu yace, "masu son ganin bayan Asad suke ta k'okarin ganin bayan Aliyu a tunanin su Asad ne har sukayi nasara a wannan lokacin suka juyar masa da hankali, wani lokacin ya kasance mai hankali wani lokacin ya kasance akasin sa duk a tunanin su Asad ne ba Aliyu ba. Amma ita Jidda tasan Asad take k'ok'arin ganin ta kashe ba Aliyu ba, dan ita Asad ne bata so a raye ba Aliyu ba, dan bazata so ta kashe uban cikin jikinta Aliyu ba sai dai ta kashe Asad kodan rana irin wannan" ya fad'a yana mayar da hankalin sa ga Jidda da numfashin ta yake gab da barin gangar jikinta. Mugun juyawa cikin Jidda yake yi marar ta na ciwo bayan ta kamar ana sara mata shi haka take ji, tayi k'ara mai k'arfi Luuuuu tayi ta sume a jikin Mum jin abinda ake fad'a wanda batayi tunanin jin su ba Mum ta rik'e ta tana girgiza ta cikin tashin hankali. "Jidda! Jidda!!, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'unn Jidda ki tashi kar ki mutu. Ranka ya dad'e jini take zubarwa kuma kaga ciki ne da ita" Mum ta fad'a tana kuka tana kallon Abba tana kuka. Mai martaba ya kalli Uncle yace, "Maza a kira sarkin mota a kaita asibiti karta rasa rayuwar ta." Da sauri ya fita jim kad'an suka dawo aka fita da Jidda da take bleeding aka saka a mota Mum tabi bayan su daman ita neman hanyar guduwa take kafin a tono nata a asirin. Inda jinin ya b'ata mai martaba ya kalla bayan sun tafi ya kalli Aliyu ya cize bakin sa yace, "Jinin d'an Aliyu kenan a jikin matar d'an uwan sa Asad!." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Takawa wai me ake fad'a ne haka? Ana so zuciyata tayi bindiga ne kome?. Taya hakan zata faru ban sani ba? Ta ya za'a ce Aliyu shine Asad?" Mama ta fad'a a firgice jin abinda mai martaba ya fad'a.           Mai martaba yace, "in kin kwatar da hankalin ki zaki ji komai ai, zaki ji wacce kika fifita sama da y'an uwan ki wato aminiyar ki Sadiya ita ta raba ki da d'anki Aliyu a tunanin ta Asad ne, ita take burin ganin bayan ki burinta taga ta kashe ki. Kwantar da hankalin ki yanzu aka fara bayani ai" sai mai martaba ya kawar da kai yace, "Koda yake banzo kan wannan batun ba tukunna har yanzu ina magana akan Aliyu da Asad ne." "Eh dukkan abinda Abba yake fad'a haka ne, ni ba Asad bane ni Aliyu ne!" Aliyu ya fad'a har lokacin hannun sa na dafe da kansa cikin murya mara dad'in ji mai amo da sauti mai firgitarwa dan da k'arfi yake maganar. Aliyu ya d'ago ya kalli Mama yace, "Mama bata iya b'oye son da take yiwa Asad a gaban koda a gabana ne, ina son mulkin garin Katagum amma Mama ta nuna ya haramta a gare ni sai dai Asad daga wannan lokacin nayi d'anmarar ganin bayan sa." Ya dafe kansa cikin ciwo yana k'ara mai k'arfi kafin ya dawo daidai yana sauke numfashi da sauri ya sake cewa, "nayi iya abinda zan iya a nan amma abubuwan sun cukud'e na kasa samun biyan buk'atar da nake so. Mama in zata tuna lokacin da akayi auren Asad na farko ya tafi Cairo nine wanda na raba su da ita ya manta da ita dan nasan matuk'ar Asad yana jin maganar Mama zai baro Cairo ba tare da ya shiryawa hakan ba. Lokacin da ya dawo Nigeria naje har hotel d'in da yake na shafa masa magani a tafin hannun sa tun daga wannan lokacin sai anyi maganar Mama yake tunawa da ita." Mai martaba yace, "Kai a tunanin ka wannan aikin kane yayi tasiri amma naka baiyi aiki ba, akwai na wad'anda yayi aiki amma ba naka bane, duk abinda kake aikatawa kana yin sane a k'ark'ashin su. Cigaba da jawabi" ya fad'a cikin bada umarni yana kallon sa. Aliyu da ya koma tamkar mahaukaci sai zare idanu yake yi ya cire hular kansa ya cillar yace, "Samun nasara ta ta farko kenan daga lokacin da Mama ta dawo dashi k'asar nan komai ya tsaya min, a lokacin da aka bashi sarauta kuma komai ya lalace min. Naje k'asar India na nemo masu tsafi na yiwa Asad a kan har abada babu shi babu Nigeria a lokacin da yaje Germany wajan Abba, aikina yayi kyau tun a can Germany d'in na koma Asad shi kuma Asad ya bar Germany d'in gabad'aya ya koma Madina. Daga wannan lokacin aka daina kirana da Aliyu sai Asad aka daina kiran sa da Asad sai Aliyu domin hatta wayar Asad itace a hannuna." Rigar saman kayan sa ya cire itama ya cillar yana zare manyan idanun sa kana yace, "Daga nan na dawo Nigeria na fara mulki matar Asad kuma Jidda ta cigaba da kasancewa matsayin Matata daman tasan komai tare aka shirya. Tasan komai lokacin dana dawo na sanar da ita bani bane na tabbatar mata da Asad ya tafi kenan har abada ta bada goyan bayan zama dani matsayin Asad har aka samu cikin jikinta." A firgice ya kalli Rauda yana nuna ta da yatsa yace, "Eh tabbas ni yazo gidan ku ba shine nan nazo, rubutun sa da kika gani a takarda computer ve ta d'ora a k'asar Dubai ina sane da duka abinda yake faruwa tsakanin ku a Cairo hatta magana in yayi miki ina jin me yake cewa domin kuwa na canja azurfar hannun sa na saka masa wacce take d'auke da na'ura a jikin ta a Kano lokacin da muka je jana'izar Abie, duk abinda yake fad'a ina ji a haka nasan dukkan abubuwan da suke faruwa tsakanin ku. an tabbatar min akwai yuwar dawowar ki masarauta kuma zaki iya zama barazana a gareni shiyasa nayi maganin ki tun kafin ki shigo dan bana son ganin wani abu da zai dakatar dani daga burina" ya fad'a yana zaro mata ido kamar zai dake ta. Mama da take gefe ta mik'e hankali a tashe tazo inda Aliyu yake ta rik'e shi tana kuka tace, "Aliyu me kake fad'a haka?." Ya kalle ta ya wara idanun sa waje yace, "Eh Mama nine na sake ta, sannan kuma nine na zauna da Jidda matsayin Asad cikin jikinta kuma nawa ne! Domin kuwa babu abinda ya tab'a had'a su da Asad na bata maganin da zata lalata masa mazantarka sa kuma ta bashi yasha ya kuma yi aiki, kamar yadda kikayi aiki aka lalata a lokacin da yake Cairo tare da matar sa!. Ni ne na shirya komai nine nan na tsara kuma nake tafiyar dashi yadda nake so!" Ya fad'a da ihu yana kallon Mama da take rik'e da wuyan sa ruwa har sakkowa yake daga cikin idanun sa. "Nayi k'ok'arin iya komai na Asad duk da wani lokacin ina yin ba daidai ba" ya kalli Mama ya nuna ta yace, "Kin tuna lokacin da kika ce min na canja kamar bani ba? Eh tabbas ba Asad d'in bane nine ina yin iya yadda zan iya ne wajan ganin nayi tamkar Asad amma ban iya yi ba wani lokacin. Dalilin sakaci da addu'a ta k'awar ki ta samu galaba a kaina a tunanin ta Asad ne. Dalilin ni ba Asad bane shiyasa kika kasa samun abinda kike so a wajena, Asad mai biyayya ne kina juya shi yadda kike so ni kuma bazan lamunci wannan biyayyar ba shiyasa kike ganin canji da yawa cikin lamari na. Ni na shirya, na tsara nake kuma aiwatar dashi yadda nake so." "Ba kai bane Aliyu, d'auka kake kaine ka shirya kake kuma aiwatarwa amma baka d'auki kashi d'aya a cikin kaso d'ari na cikin abinda suka aikata ba. Kai kanka a k'asan su kake baka san komai ba kana yin komai bisa umarnin su" Mai martaba ya fad'a yana kallon sa shi Kuma yana kallon Mama. Mama tace, "A'a k'arya kake Aliyu ba gaskiya kake fad'a ba, ka daina cutar kanka kana fad'ar abinda ba gaskiya ba." *Wai! To su waye wad'annan?🏃🏼‍♀️* [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *079* Mai martaba ya murmusa jin abinda Mama tace yace, "Koma ki zauna zaki ji komai." Jikin ta a salub'e ta zame hannunta daga jikin Aliyu ta koma ta zauna tayi tagumi zuciyar ta na bugawa sosai.  Mai martaba yace, "Cigaba da bayani Aliyu." Aliyu yace, "Daga wannan lokacin ni kaina bazan ce ga abubuwan da suke faruwa ba, na rasa tunanina bana gane komai sai Jidda kawai. Daman akwai plan d'in daina kirana da Aliyu sai dai Asad da yake tana so sunan ya shiga bakin ta ko sau d'aya bata tab'a kuskuren nunawa ba Asad bane ba ni" ya fad'a yana dafe kansa tare da runtse ido. Mai martaba yayi murmushi mai kyau ya girgiza kansa yana kallon kowa da yake zaune a falon. Zaiyi magana kenan aka turo k'ofa aka shigo ganin wacce ta shigo ya saka gaban Waziri fad'uwa ya kasa d'auke ido daga kanta ganin ta garau da ita babu alamun ma tayi hatsari sai yaji tsoro gaban sa ya fad'i. "Munafukin Allah dole ai kaita kallona ka so kashe ni Allah baiyi ba" Hajiya ta fad'a tana kallon sa itama. Dawo da kallon ta tayi ga Mai marataba tace, "Allah yaja da ranka zan fad'i dukkan abubuwan da muka k'ulla nida Waziri da wata boyayyiyar abokiyar shirin sa, ya saka a kashe ni a daren jiya dan kar wannan ranar tazo bai san ina sane na saka likitan yace ace muku naji mummunan ciwo ba dan kawai ya sakankace bani da lafiyar da zan halarci wannan zaman ba." Kowa ya kalli waziri da yake zare ido aka kalle ta Mai martaba yace, "An baki fad'i duk abinda yake bakin ki." Ta nemi waje ta zauna tace, "Duk wani abin da yake faruwa a cikin masarautar nan nida shi mune muke k'ullawa dan cikar burin mu kawai, burina kar jinin Rabi'atu ya mulki garin nan shi kuma burin sa ya mulki garin nan. Burin mu iri d'aya ne shiyasa muka had'a kai wajan ganin bayan y'ay'an Rabi kodan cikar burin mu." Mama da take jin me take cewa ta runtse ido tace, "Daman ku biyun nan na jima da sanin shirin ku na kashe min y'ay'a tun suna k'ananu, na jima da sanin kuna bak'in ciki da kyautar su da Allah ya bani. Shiyasa lokacin da kika so kashe shi ta hanyar bashi guba a zogale......" Hajiya ta katse ta tace, "Bani na bashi guba ba a wannan lokacin yana da kyau ki amince da nayi tabbas zan fad'a a yanzu dan yau lokacin fad'ar komai ne" ta dawo da kallon ta ga Mai martaba tace, "Ban san wanda ya bashi guba ba, abinda na sani munyi shirin hakan yafi sau babu adadi Allah bai bamu sa'a ba. Tabbas da tace tun suna yara nake so na kashe su haka ne domin ranar da aka haife su sai da naje wajan malaman tsibbu suka bani tabbacin dukkan su zasu tashi basu da amfani a masarautar sannan hankalina ya kwanta." Fulani Hajiya ta kuma cewa, "Nida shi da wata wacce ake kira master planer wacce ni ban santa ba shima kuma bai santa ba, sai kuma d'ansa Suhail wanda yake bamu gudunmawa sosai wajan ganin bayan Asad. Mun bawa Suhail laya ya sakawa Asad a k'asan katifa ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, mun bashi ya bashi a ruwa yasha ya kuma ci a abinci duka burin mu na ganin bayan sa amma babu nasara. Akwai wani lokaci da daddare da Asad ya jini ina waya ina zancen a kashe shi da naga yaji a take na saka a busa masa yaji a idanun sa yadda bazai ga wacece ba. Asad ya amince dani amma munci amanar sa koda yake Aliyu ma yana cikin tafiyar mu" ta fad'a tana kallon mai martaba. "Ban sani ba ko shirin sane kwanciya rashin lafiyar ka domin kuwa yana aikata abubuwa wanda ban san dashi ba amma ni bani da hannu a ciki wallahi, abinda na sani kawai mun saka Suhail ya shiga jikin sa ta k'arfi yana saka shi duk abinda muke so a kuma lokacin da muka so. Shirina gabad'aya akan Asad ne da y'an uwan sa amma banda Mai martaba da mahaifiyar sa" ta fad'a kanta a k'asa idanun ta na cikowa da kwalla. Ta kuma cewa, "Tunda naji da kunne na yana niyar kashe ni naji komai ya fitar daga cikin raina, a lokacin da ya saka a daki motar da nake ciki daga nan na sake tabbatar da cewa ramin mugunta kurarrare ne kuma rana d'aya ta b'arawo rana d'aya tak ta mai kaya. Naso ganin bayan Asad sai ban ga bayan sa ba wanda muke k'okarin ganin bayan wani tare dashi ashe nima yana k'ok'arin ganin nawa bayan. Na sanar da mai martaba komai abinda yake faruwa ko wanne hukunci da ya cancanci ayi min a shirye nake dana karb'e shi." Falon yayi shiru babu wanda yake magana a cikin su sai mai martaba da yayi murmushi yana kallon su kafin yace, "Dukka shirin ku na sani Sa'adatu, keda Yazuha da wacce baku sani ba hatta Suhail d'in na sani. Ko Suhail?" Ya fad'a yana kallon Suhail da yake zaune a gefe ya tankwashe k'afar sa kansa a k'asa. Murmushi Suhail yayi kawai baice komai ba kafin mai martaba ya kuma cewa, "Yazuha wacece master planer?." Waziri da ya dabarbarce ya fara zare idanun sa gumi yana keto masa kana kallon sa kasan yana cikin tashin hankali sosai ba kad'an ba, ganin ya kasa magana sai ya d'auke kansa ya kalli Asad da yake zaune yace, "Asad akwai magana a bakin ka, ka k'arasa warware abubuwan da suke faruwa dan mu sani." Asad ya sauke numfashi ya kalli mutanen falon gabad'aya ya lumshe ido ya buɗe cikin muryar sa mai taushi da kwantar da hankali yace, "Kamar yadda kuke d'auka Suhail yana cutar dani ba haka abun yake ba, duk wani shiri da kuke dan ganin bayana Suhail yana sanar dani ne yana kuma taimaka min dan ganin na tsira daga dukkan shirin ku shiyasa baku tab'a nasara ba domin kuwa kafin ku aiwatar na sani ni kuma na d'auki mataki. Yana amfani da kune yana jin sirrin ku da abinda kuke k'ullawa a kaina amma bai tab'a cutar dani ba" ya furta cikin muryar sa ta ko yaushe a tausashe yana kallon Waziri da Hajiya. Hajiya tace, "kar ka amince da dad'in bakin Suhail wallahi dashi ake k'okarin ganin an kashe ka." Asad yayi murmushi yace, "a zahiri kenan, amma a bad'ini baya tare daku yana tare dani. Na amince da Suhail fiye da yadda ba amince da y'an uwana na jini." Mai martaba yace, "kuna so kusan wacece master d'in da ku kanku baku Santa ba? Kuna so kusan wanda ya jefa ni a cikin rashin lafiya sabida son zuciyar sa?." Kowa ya zuba masa ido masu sunkuyar da kai duk suka sunkuyar da kai ganin hakan sai mai martaba yace, "ban san me zance bane, ban kuma san me zanyi ba. Rabi'atu ta cutar da y'ay'an ta dukkan su sabida son zuciyar ta da kuma burin da ta d'auka ta d'orawa zuciyar ta." Nan ma falon yayi shiru sai kukan Mama da ya fara tashi tace, "Nasan nayi duk abinda akace nayi dan ganin y'ay'ana sun zama sune gaba a masarautar nan, amma ban tab'a yunƙurin kashe wani ba, ban tab'a yunƙurin ganin wani ya cutu ta dalilina ba." "Har matar Asad Rauda?" Ya jefa mata tambayar yana kallon ta. Kai ta sunkuyar k'asa ta kasa magana ganin hakan sa yace, "ki amsa mana, kince baki tab'a yunƙurin kisa ba shine na tambaya har ita?." Nan ma shiru Mama tayi ta kasa amsawa sai hawaye da take tana sauke numfashi a hankali cikin tashin hankali. Mai martaba ya kuma cewa, "Nasan baza ki amsa ba daman dan kin san kin aikata ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, ita kuma yarinyar tayi miki alkhairi ba sau d'aya ko biyu ba, domin ina so kowa yasan ta silar ta na samu lafiya har nake tafiya yau kuka ganni a zaune a gaban ku." Asad ne ya kalle shi alamun mamaki yace, "Eh Asad, nasan kaima baka sani ba dan babu wanda ya sani daga ita sai Mubarak sai kuma Yayan mahaifiyar ta Baba Malam, ta silar sa da tata silar na samu lafiya. Ina so kusan duk dare sai anzo an kaini wajan sa yana min magani wanda nake jin dad'in sa sosai ba kad'an ba, duk cikin maganin da ake bani ban tab'a jin dad'in ko wanne ba sai nasa. akwai ranar na same ta a can gidan an kaini ita kuma Kawun nata ya kirata ta kawo ruwan da za'a bani magani a lokacin akwai allurar da ake min a hannu Mubarak ta nuna ta san allurar lokacin da suka je can Cairo nema mata lafiya ta nemi k'arin bayani a kanta an kuma tabbatar mata ana yiwa mutumnin da ba'a so ya motsa ne, kamar wanda za'a yiwa aiki ko kuma wanda ake som cutar dashi ta hanyar allurar" ya dakata da magana yana kallon yanayin fuskar kowa da yake wajan. Mai martaba ya kuma cewa, "Nan take duk da dare ne ta kira likitan da ya sanar da ita a can ta d'auki hoton allurar ta tura masa ya tabbatar itace ya kuma turo mana maganin ta a lokacin ya kuma ce kar a sake yiwa wanda ake yiwa ita domin nan gaba zata kashe masa gab'obi ne dan bata sanar dashi nine ba, daga wannan lokacin aka daina yi min wannan allurar aka koma yi min wacce ta kasance maganin da take karya ta. Ta silar ta na samu lafiya ita da dangin ta domin badan ita ba da yanzu wataƙila ina kwance har yanzu." Kowa yayi shiru babu wanda yake magana sai Suhaima tace, "Muma munje wajan sa ta silar ta Abba, domin munje ba sau biyu bama samun ganin sa sai da muka je har gidan su Mamata ta saka ta raka mu ya bamu magani lokacin da muke d'auka Aliyu Asad ne, mun karb'o masa magani mun kuma karb'o maka mun karb'owa Yaya Hydar ma. A hanyar mu ta dawowa akaso kashe Mama  badan tayi hanzarin janye Mama ba da yanzu Mama ta jima da rasa ranta. Itace ta cece Mama a wannan lokacin ta silar ta Mama take zaune yanzu badan haka ba da yanzu mota ta markade ta tuni.' Mai martaba yace, "Ta yaya ta iya zuwa gidan su neman alfarma bayan tarin abubuwan da tayi musu a baya? Ta yaya ta iya had'a ido da y'ay'an gidan har ta iya shiga ciki?. Koda yake jiya ma taje cikin gidan nasu ta silar Mahaifiyar ta ta sake karb'owa Aliyu magani gashi har zaune ana magana dashi, ko ina izza da raina na k'asa da ita d'in suka tafi oho" ya fad'a yana kallon ta Mama ta runtse idanun ta. Falon ya sake yin shiru babu wanda ya kuma magana a cikin su Asad ya kalli Rauda suka had'a ido sai tayi saurin d'auke idonta daga kallon sa gabanta yana fad'uwa sosai ita har yanzu bata tabbatar da cikin wanda yake jikinta ba. "Aliyu yayi mulkin katagum na watannin da suka wuce, Asad ya kasance baya tare damu a yanayin da muke d'auka shine a tare damu Aliyu ne baya nan, Aliyu ya goge duk wata alamar da ake gane su da tsakanin sa da Asad hatta k'aramin yankan allurar da yake hannun Asad wanda babu wanda ya san dashi daga shi sai matar sa Aliyu yayi irin sa dashi ya yiwa matar sa barazana har ya sake ta a madadin Asad ita kuma ta amince. Ta hanyar azurfar hannun Asad tana nan yaji lokacin da yake fad'a akwai alamar shi kuma yayi amfani da wannan damar da ya dawo yaga a hannun da yake shima yayi irin sa. Asad ya dawo shi kuma sai ya koma muku Aliyu duk dan sabida ya aiwatar da komai cikin sauk'i duk da Aliyu yasan shine haka Jidda ma amma basu nuna ba duk tunanin su hankalin sa ya bar jikin sa, babu wanda yasan ba Aliyu bane daga shi sai Aliyun sai matar sa Jidda sai kuma y'an bayan fage." Ya kalli su waziri yace, "Dashi kuke meeting d'in kashe shi, badan shi ba da yanzu mahaifiyar jidda ta kai ga kashe Rabi shine yayi maganin abun dan ya gani da jakadiyar ta Ladidi suke yin komai. Shi Jidda taso a kashe bata san yasan shirin ta ba dan Asad d'in yanzu bana da ba bane ba." Ganin kowa ya kasa motsi sabida abinda suke ji kamar almara ya saka yace, "Lokaci yayi da ya kamata kusan wacece master sannan kuma su waye wad'anda nake kira y'an bayan fage."  Ya kalli k'ofa yace, "A shigo min dashi." Nan take aka shigo da Hafiz duk an d'aure shi jikin sa duk ya b'aci haka fuskar sa tayi bak'i matuk'a sabida wahala. Umarni ya bawa wanda suka kawo shi da su koma suka koma suna godiya ya kalli kowa yaga kowa kallon Hafiz yake yi. Mai martaba yace, "Nasan kowa yana mamakin ganin Hafiz, kowa yasan Hafiz da Asad abokai ne shine manager director a company sa, shine yake k'okarin kare shi daga masu son ganin bayan sa a zahiri kenan. Tsakanin sa da Suhail ba'a shiri a zahirance Hafiz yana nunawa Asad Suhail yana so ya cutar dashi ne shiyasa baya so ya ganshi a kusa dashi, amma a bad'ini shine yake k'okarin cutar da Asad shiyasa baya so yaga Suhail a kusa dashi. Suhail yayi kwantan b'auna dan cimma nasara a b'angaren kare lafiyar abokin sa na yarinta Asad. A yayin da Hafiz yayi kwantan b'auna ya cimma cutar da abokin sa na yarinta Asad." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Aka fad'a baki aka fad'a gabad'aya ana kallon Hafiz. Mama da take kuka tace, "Hafiz! Hafiz kai da kanka?." Ya d'ago ya kalli Mama cikin muryar sa da ta d'an yi k'asa yace, "kar kayi mamaki mama, jin wad'anda zan ambata yanzu sai yafi jefa zuciyar ki cikin mamaki." "Kenan yasan master planer?" Fulani Hajiya ta fad'a tana kallon sa. Yace, "Kwarai na Santa domin ita nake yiwa aiki, ku bakwa ganin ta ni kuma kai tsaye nake magana da ita, bama iya ita kad'ai ba hatta wanda suka bayan ta na sansu." "Fad'a mana muji wacece" ta fad'a tana kallon sa. Yayi murmushi yace, "kun shirya jin wacece master planer?." Mai martaba yace, "Fad'i abinda yake bakin ka kai tsaye." Ya kalle su dukkan su ya saukar da ido k'asa yace, "Duk wad'annan abubuwan da suke faruwa ba kowa ne yake shirya su ba face...........!" Guess who?🏃🏼‍♀️🤔😂 [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *080*           K'irjin kowa motsawa yake a cikin su burin su suji abinda Hafiz zai fad'a dukkan su sun zuba masa ido suna kallo hankali a tashe tsoro da al'ajabi ya bayyana k'arara akan fuskar su.  Hafiz ya sake yin shiru ya kalle su dukkan su yace, "Kuna tunanin wacece master planer..? Hmm abinda ya dace kuyi tunani shine waye master planer dai domin ba mace bace namiji ne." Fulani Hajiya tace, "kar ka raina mana hankali mana, ta yaya zai kasance namiji bayan ni nasan macece." Hafiz yace, "murya kike ji amma kin tab'a ganin ta a zahiri?." Shiru tayi ta kalli waziri suka had'a ido ta dawo da kallon ta ga Hafiz tace, "Ban tab'a ba." Hafiz yace, "ta tab'a amincewa kunyi video call?." Ta girgiza kai alamun a'a ya sauke numfashi yace, "Shiyasa nace miki namiji ne ba mace ba." "To waye ka fad'a mana ka tsaya kana rainawa mutane hankali, ka fad'a way......." "Hydar ne!" Ya katse Mama da ihuu yana kallon ta idanun sa a waje. Dummmmm zuciyar kowa ta buga a wajan nan duk suka juya suka kalli Hydar da yake zaune kansa a k'asa tunda aka fara wannan abin baiyi magana ba kuma bai d'ago kansa ba har lokacin, mamaki kwance a fuskar su dukkan su Mama ta kalli Hydar ta kalli Hafiz tace, "Wanne Hydar d'in kake nufi?." "Hydar da kika sani Mama, Hydar da yake tare dake a ko yaushe, hydar da yake kwanciya rashin lafiya, Hydar d'in Asad, Hydardai naki shi nake nufi" ya fad'a yana kallon ta itama kuma shi take kallo idanun ta a waje gabad'aya. Suhaima ta kalli mahaifin su dan tana so tayi magana amma tana jin tsoro shima ya kalle ta yace, "kowa yana da ikon yin magana a wannan lokacin." Jin hakan ya saka Suhaima tace, "K'arya kake! Kwatankwacin wannan abinda aka lissafa Yaya Hydar bazai aikata shi ba. Kowa ya shaida son da Yaya Hydar yake yiwa Yaya Asad bazai cutar dashi ba, ko yaushe ciki bashi kariya yake taya zaka ce shine master planer?." "Da kariyar yake amfani yake cutar dashi a ko yaushe, Hydar ya wuce tunanin ki yadda kuke kallon Aliyu mai wayo da makirci Hydar ya dame shi ya shanye" ya sake fad'a yana kallon Suhaima da itama shi take kallo fuskar ta ta jiqe da hawaye.  Fusata Mama tayi ta zabura ta mik'e ta tsinke Hafiz da mari ta nuna shi da yatsa tace, "In ka sake furta magana makamanciyar wannan a kan Hydar sai na saka anyi maka hukuncin da har ka mutu baza ka manta ba." Hafiz yace, "Mama sai dai kiyi min duk abinda zakiyi amma bazan fasa fad'ar abinda yake gaskiya ba, duk wani tuggu da ake k'ullawa a gidan nan Hydar ne sila shine yake shirya komai duk su Waziri, Aliyu, Jidda da duk wani mai son ganin bayan Asad umarnin sa suke jira." Mama ta sake tsinke shi da mari ta juyo ta kalli mai martaba tace, "Taya mai martaba yana ji yana fad'ar kalamai mara sa dad'i akan Hydar zaiyi shiru" ta dawo da kallon ta ga Asad tace, "Baka ji me yake cewa bane ba Asad? Hydar d'inka fa yake jifa da wannan kalamai masara dad'in ji." Asad ya d'ago ido ya kalle ta sai yayi murmushi yace, "Mama duk abinda yace ba K'arya yayi ba gaskiya ce. Duk wani abu da ya faru a gidan nan Hydar ne sila, shine ya shirya komai yake kuma bada umarni." Mama tayi baya zata fad'i Suhaima tayi saurin tare ta suka zauna jikin ta yayi sanyi kamar wacce aka zarewa rai kanta yana sarawa kamar zai rabe gida biyu. Hafiz yace, "Duk wani abu da ake tunanin Suhail ne ya saka na cutar da Asad nine nayi ba Suhail ba, in Mama ta tuna lokacin da na same ta nace an zubawa Asad abu ya tsallaka yana ciwo ba wani ne yayi ba nine ina sane nake saka Suhail a ciki dan a ture shi gefe ni a amince dani dan tabbas Asad ya yarda da Suhail. Yadda ya amince dashi bai amince dani ba shiyasa nake jin zafi da d'acin hakan. Da ina aiki da Aliyu ne amma da na gano Hydar shine babbar giwar sai na koma tsagin sa badan komai ba sai dai abin duniya." Hafiz ya sake cewa, "Duk son mulkin da Aliyu yake dashi Hydar ya fishi; iya taku shine ya saka yake nuna ko a jikin sa amma yafi kowa d'aga hankalin sa a kai. Ko Mama tasan da cewa gab da Asad zai dawo Hydar ya kwanta ciwo wannan ciwon bana gaskiya bane na shiri ne...? Yayi amfani da cutar da take damun sa ya kwanta ciwo ya aiwatar da dukkan abinda yake so hankalin kwance babu wanda ya kawo komai a ransa. Hydar yasan Aliyu ne yake mulki ba Asad ba sai kuma abinda yace masa yakeyi. Na fad'a muku abinda zai fi haka gigita ku..?" Ya fad'a yana kallon su dukkan su. Ya cize baki yace, "Hydar shine silar kwanciya Abba ciwo, shine silar da dukkan gab'obin Abba suka daina motsawa. Yana sane tsarin sane yayi hakan da Mama ta dawo da Asad shi kuma ya aiwatar da duk abinda yake so, ya kuma tabbatar matuk'ar mai martaba yana da lafiya wani abun bazai kasance ba shiyasa na aikata abinda ya aikata ko nace yake kan aikatawa. Lokacin da Asad yana Cairo yana sane yak'i sanar dashi rashin lafiyar Abba ya tafi dashi Germany ya hana ko wanne likita ganin sa in ma sun duba shi da zarar sun fita zai masa allurar da ita Rauda ta bada maganin ta." Ya kalli Aliyu yace, "A tunanin ka maganin da suka baka ka shafawa Asad a fatar hannun lokacin da ya dawo daga Cairo don yayi swapping layin sa a tunanin ka shine silar da ya saka ya manta da Mama? Hmm ba shine bane domin a abincin da yaci ni da kaina na karb'o maganin da aka zuba masa a ciki a wajan matsafan k'asar turkey. Nasa ne yayi aiki ba naka ba yana sane yayi hakan duk dan ya sake tunzura Mama da take ta dawo dashi. Waye ya fad'awa Mama inda Asad yake a Cairo? shine yayi hakan yana sane a wannan lokacin burin sa ya dawo." "Aliyu kaima kana naka aikin a wannan lokacin amma aikin Hydar yafi naka k'arfi, kaine kaje gidan su Rauda ka sake ta amma kuma turawa a rushe musu gida ba kai ka yishi ba shine yayi badan komai ba dan ya sake tunzura tsanar Asad a zuciyar ta dan kar tayi marmarin sake waiwayar sa har abada; duk inda muka je ana fad'a mana akwai yuwar dawowar ta kuma barazana ce a gare mu, gashi kuwa daga dawowar tata komai yana bayyana." Hafiz ya kalli Hajiya yace, "kina ta kokwanton waye ya zuba guda a zogalen da kika bawa Asad ko? Ba kowa bane yayi Hydar ne, yana sane dan a jefa zargi a kanki a kawar da hankali daga shirin sa ya kuma jefa kin." Ya sake kallon kowa na falon yace, "Zuwan Asad Germany ya takura sai an dawo da Abba a wannan tafiyar ya shirya canja Asad inda ya yiwa Aliyu zazzafar message ya tsara masa komai shi kuma ba tare da tunanin komai ba ya hau kan plan d'in ya zauna daman neman mafita yake yi. Duk wani likita da zaku gani a gidan nan indai Hydar ne ya kawo shi yana karya garkuwar jikin Abba ne ba lafiya yake samar masa ba, ya shirya komai nasa tsaf amfani yake da Aliyu so yake da zarar an haukatar dashi sai shi ya maye gurbin kujerar ya mulki kowa son ransa." "Duk soyayyar da yake nunawa yana yiwa Asad ta bogi ce a zuciyar sa babu wanda ya tsana sama da Asad, kullum b'acin ransa ta ya Asad ya kasance abin so a wajan iyayen su shi ya koma baya? Ta ya kowa yake zancen Asad bashi ba? Ta yaya za'a ce shida Aliyu suna da makusa shi bashi da ita...?." Shiru falon babu mai motsin kirki a cikin su kowa yayi shiru yana kallon Hafiz Mama kam ji take zuciyar ta tana gab da bugawa. Mai martaba yace, "ko kun san jiya da daddare Hydar ya shigo har d'akin da nake da niyar kashe ni? Ko kusan ya zuba min poison a a.c dan kawai na shak'a na mutu na bashi waje yayi abinda yake so, bai so yau tazo ba badan tonuwar asirin sa ba sai dan bai shirya kowa yasan waye shi ba dan bai gama tsara abinda yake so ya tsara ba. Hydar yayi kwantan b'auna ya kuma cimma nasara akan abubuwa da yawa amma lokacin bayyanar komai yanzu yayi." Hafiz yace, "shine master planer, shine yake tsara muku komai a duk sanda yaso shiyasa nace dukkan ku a k'asan sa kuke. Yana amfani da voice changer yana magana daku matsayin mace ku kuma da yake kowa ya saka cuta a zuciyar sa babu wanda ya kawo tunanin da wa kuke magana kawai kun amince dashi. Ku in ba na cikin gida ba taya za'a dinga kawo muku labaran cikin gida wanda na gidan ma basu sani ba?" Ya fad'a yana kallon su dukkan su suma kuma shi suke kallo. "Mallake Aliyu da Jidda tayi tafi masa dad'i fiye da kowa shiyasa in Mama ta tura shi da magani ya kai mata sai ya zubar ko shi ya shanye amma bazai kai masa ba. Da ace Abba ya bar Hydar ya tafi da Aliyu wata k'asar a jiya tabbas da sai dai gawar Aliyu amma bashi ba, sannan ya dawo kan Asad domin kuwa dukkan ku sai yaga bayan ku harda ke Mama domin kina k'okarin bashi matsala zai kawar dake dan cikar burin Hydar yafi masa komai a duniyar nan." "K'arya kake Hafiz! K'arya kake Hydar d'ina bazai tab'a aikata abinda kake fad'a ba, taya Hydar d'ina yaga lafiyar da zaiyi abinda kake cewa shida yake kwance cikin ciwo a ko wanne lokaci?. Hydar yana son Asad bazai tab'a cutar dashi ba, Hydar yana son mahaifin sa bazai tab'a aikata abinda kake fad'a ga mahaifin sa ba, Hydar yana sona bazai tab'a yunƙurin yin abinda kake fad'a min ba. Na amince duk abinda kuka fad'a Aliyu zaiyi tabbas ya aikata shi amma banda Hydar K'arya kake bazai tab'a yin abinda ake cewa zaiyi ba" hawaye sharrrr daga idanun Mama sai kuma ta dafe kanta tace, "Ta ya ma Hydar zaiyi haka? Ta wacce hanya duk abinda ka fad'a za'a ce Hydar ne shi kad'ai ya aikata ta yaya hakan zata kasance banda K'arya?!" Ta fad'a cikin kuka tana kallon Hafiz da take ji kamar ta bindige shi. Hafiz yace, "Ya aikata fiye da haka domin kuwa har laya ya saka Asad a kujerar zaman a office duk dan yayi masa Farraqu daga gidan nan amma Allah bai bashi sa'a ba. Hydar ya wuce tunanin ki Mama a gaban sa nake fad'ar komai nasan kuma komai domin tare ake shirin dani. Duka wannsn tunanin naku akan sa shiyasa yake cutar daku domin dukkan ku kun amince dashi amma shi kuma ta b'angaren sa ba haka abun yake ba. Shiyasa yayi nasara akaan Asad sabida yasan dukkan lagon Asad yasan abinda yake so yasan wanda baya so, yasan abinda yake ci yasan wanda baya ci. Da ace maqiyin ka na kusa dakai gwara yana nesa dakai domin maqiyin kusa yafi na nesa sharri." Suhaima da take rik'e da Mama tace, "dan kai kana aikatawa hakan ba yana nufin ka yiwa Yaya Hydar wannan mummunan kazafin ba, wallahi K'arya kake Yaya Hydar babu ta inda zai iya aikata abinda ake fad'a, yana son yaya Asad karen Yaya Asad Bobby Yaya Hydar bazai iya cutar dashi ba balle kuma shi." "Mama, Suhaima ya kamata ku daina rantsewa duk abinda kuka ji an fad'a ku amince dashi domin kuwa Hydar zai iya aikata abinda yafi haka ma. Kuna yiwa Hydar kallo a baibai ne amma Hydar ya wuce duk inda kuke tunani, dukka abinda aka fad'a yanzu kad'an ne daga cikin shirina kuma har gobe ina kan bakata ban sauka ba!" Muryar sa ta karad'e falon cikin kaushin murya mai fita a zafafe da nuna tsantsar isa da izza da kuma zallar mugunta a cikin ta. Hydar!🤒🏃🏼‍♀️ [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *081* Dukkan su juyawa sukayi suna kallon sa ya d'aga gira guda biyu yayi murmushi mai kama da dariya kafin ya sauke numfashi ya kalli kowa na falo sai kuma ya tab'e baki har lokacin murmushi yake yi ya mik'e tsam ya zuba hannu a aljihu yana kallon su d'aya bayan d'aya yace, "Ki daina rantsewa Mama kar azumin kaffara yayi miki yawa a kanki, k'anwata ki bar kuka" ya fad'a yana kallon Suhaima kafin ta taka zuwa tsakiyar falon yana kallon kowa. Mama suman tsaye tayi ta kasa motsi sai kallon Hydar da take yi da ya juye mata ya koma tamkar wani cikakken d'an ta'adda a kamannin sa. Hydar ya kalle su yace, "Eh duk abinda kace nayi na aikata gaskiya Hafiz yake fad'a ba k'arya ba" ya fad'a yana kallon Hafiz d'in yana murmushin rainin hankali. "Nine master planer, kun jima kuna so ku ganni yau gani a tsaye a gaban ku kunyi murnar ganina?" Ya fad'a yana kallon su tare da wara musu hannayen sa. Ganin duk sun kasa magana sai ya kyalkyale da dariya ya dafa hannun sa sai ya kalli mahaifin sa yace, "Ina so mahaifina yasan AliyuHydar baiso kashe shi ba, inda yaso ganin bayan sa tamkar yadda zan take kiyashi haka zan take duk wanda naso. A wannan tafiyar babu nufin kisa sai dai za'a sha wahala." Ya kalli Asad da yake kallon sa yace, "Ina sonka Asad kamar yadda nasan zuciyar ka tana zafi a wannan lokacin kana ji inama mafarki kake ba gaskiya ba, yadda kake qaunar Hydar baza kaso hakan ta kasance ba amma ta kasance domin ba mafarki kake yi ba. Kai kana tunanin a banza na goya maka baya ka auri wannan?" Ya fad'a yana nuna Rauda da yatsan sa ba tare da ya kalle ta ba har lokacin Asad yake kallo. Sai kuma ya sake yin ya cize bakin sa yace, "Nayi ne sabida mafita tawa badan wai kana sonta ba sai dan ta silar soyayyar ta Mama ta tsane ka tayi maka baki ta daina fighting akan baka kujerar mulkin garin nan. Amma sai naga Mama bata saduda ba hukuncin ta akan yarinyar ne a kanka ba shiyasa na canja shiru. Tun dawowar ka nasan waye ya dawo kake raina min hankali wai matsayin kaine Aliyu baka san Aliyun ma a tafin hannuna yake ba balle kai, ka tuna yar da wayar ka da kayi a Cairo? Koda yake a yanzu nasan kasan nine na cire ta daga jikin ka dan nisanta ka da Mama." "Duka abinda yake faruwa na sani, ka dawo ka koma Aliyu kake fita daga gidan nan matsayin Aliyu wasu suna d'auka da gaske Aliyu ne dan ko sarkin mota ya d'auka Aliyu yake d'auka yake fita dashi har yake kai masa wannan" ya fad'a yana sake nuna Rauda da yatsan sa sai yayi murmushi yana cize bakin sa yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya. "Duka ku kwnatar da hankalin ku ai yanzu aka fara kuna tunanin wai komai yazo k'arshe ne? Hmmm hatta wannan zaman da akayi yau yana daga cikin plan d'in master planer akwai na gaba wanda zai gigita ku gabad'aya ku. In har Hydar bai zauna a kan kujerar katagum ba babu wanda zai zauna ya kwana lafiya, ku rubuta wannan ku ajjiye!. Wannan yana nan tafe kuma zai zo in bai zo ba kuma ba sunana Hydar ba" Yana fad'a ya fita da baya kamar walqiya basu sake ganin koda kalar rigar jikin sa ba. Luuuuuu Mama tayi ta zube a wajan a sume Suhaima tayi kanta a guje Asad ya taso shima da sauri ya rik'e ta amma ina ta suma ko numfashi bata yi, Fulani Rukayya da take zaune tana hawaye ta girgiza kai tace, "Dole ki suma Rabi'atu, abin suma ne ya same ki. In ma da abinda yafi suma kyayi abubuwan sun wuce tunani." Asad da yake hankali a tashe ya tara yatsun sa a kofofin hancin ta yaji bata numfashi hankalin sa ya kuma tashi sosai yace, "Muje asibiti" ya fad'a yana tallafo Mama. "Asad ka bar Suhaima da Suhail su kaita asibitin ina buk'atar zaman ka a wajan nan, sannan a bincika inda Jidda take a ji ya yanayin jikin nata" Mai martaba ya bada umarni jin hakan Suhail Asad da Suhaima suka kai Mama mota suka tafi shi kuma ya dawo duk jikin sa a sanyaye da zai samu dama ya keb'e kansa babu abinda zai hana bai fashe da kuka ba. Dawowa yayi ya zauna mai martaba ya kalle shi ya kalli Aliyu da yake a kwance idanun sa a kulle yayi murmushi yace, "Asad ka zama namiji ka danne zuciyar ka bana son ganin rauni a tare da kai ko kad'an." Mutanen falon ya kalla gabad'aya yace, "Ban amince wani hadimi ya samu wannan labarin ba dalilin da ya saka nace kowa yazo nan kenan, bana so maganar nan ta fita in kuma ta fita na samu labarin wanda ya fitar da ita akwai mummunan mataki a kansa. Yadda kowa yake d'auka Asad ne yake mulki aje a hakan bana so kowa yasan da canje akayi, bana so!" Ya sake fad'a da kakausar murya. "Sa'adatu dake da Yahuza da Hafiz babu abinda zance muku haka zalika babu abinda zan yi muku, kowa ya aikata alkhairi ya sani haka kowa ya aikata akasin sa ya sani. Aliyu da yake kwance a k'asa yanzu hankalin sa yana barazanar barin jikin sa ya zamar muku abin kallo da darasi domin tare kuke shirya komai ga kuma abinda ya same shi nan, abinda ake kira qaiqayi koma kan masheqiya kenan anyi zalincin da Asad sai kuma ya k'are a kanku. Shi Allah haka yake ikon sa baya cutar da wanda bashi da hakki yana bayan mai gaskiya a koda yaushe yana kuma bashi kariya daga mutane irin ku. Kai kayi abinda kayi sabida kanka ita kuma tayi ne sabida kawai ra'ayin tane, ina so ku jira sakamakon ku wajan Allah domin bazai barku ba, hakkin cutar da wannan bawa da kuka yi sai yayi masa sakayya ko yanzu ko nan gaba. Ta inda Allah ya taimake ku babu ran wanda aka d'auka da wallahil azim babu abinda zai hana ban saka an yanke muku hukuncin kisa ba." Dukkan su sunyi shiru suna jin abinda yake cewa Fulani Hajiya kuka take sosai nadama tana shiga zuciyar ta a yanyin da Waziri ya d'auko wayar sa jin kiran da ake masa yayi yawa, mai martaba ya kalle shi yace, "Amsa kira, ka kuma sakata a amsakuwa." Ba musu kuwa yayi yadda yace daga cikin wayar akace, "Ranka ya dad'e tun d'azu muke neman wayar waziri bamu samu ba, gida ne babu lafiya Mai sunan Hajiya mai babban d'aki da mai sunan mai martaba aka same su a kwance a falon Waziri dukkan su kumfa na zuba daga bakin su. Labari mara dad'i ranka ya dad'e dukkan su Allah karb'i rayuwar su." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Dukka jama'ar falon suka fad'a shi kuwa katse kiran yayi ya kulle idanun sa a daidai lokacin aka kwalla kiran sallar la'asar. Bud'e idanun sa keda wuya ya fara zubar da hawaye kamar k'aramin yaro yana kuka sosai mai had'e da hawaye jin lokaci d'aya y'ay'an sa guda biyu wanda yafi so a duniya sun mutu. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, muna rok'on Allah ya jiqan su ya gafarta musu ya sa sun huta ya kuma karb'i baquncin su. Abinda ya kamata ayi yanzu in an idar da sallar la'asar za'a kai su makwancin su. Taron nan dole ya tashi a yanzu" Mai martaba ya fad'a cikin maganar mai d'auke da taushi a cikin ta. Zabura Waziri yayi ya fita da sauri duka mutanen d'akin kowa ya fita ya bada umarnin a tafi da Aliyu gida Uncle suka fita dashi dan zuwa lokacin ko motsi ma bayayi sai numfashi kawai da yake fitarwa. Falon ya rage daga Asad sai Abba sai kuma su Baba da suke zaune suna jin abu kamar almara kansu duk ya kulle. Abba yace, "Malam Adam da iyalan ka ina yi muku godiya akan dukkan abubuwan da suka faru, ina fatan kuma dukka ku kun fahimci abinda ya faru an kuma tabbatar babu hannun Asad a dukkan abinda ya faru. Hakika naji dad'in yadda kuka karb'i k'addarar nan hannu biyu na sake tabbatarwa a zuciyata itace matar Asad ta cikin mafarkin sa. Y'ata Rauda ina fatan kin tabbatar da har gobe kina matsayin matar sa ne ko?." Rauda hawaye take yi sosai a lokacin ta kasa magana mai martaba yayi murmushi yace, "Kar ki damu ki daina kuka ita daman rayuwa haka take, wanda ka bawa amanar kanka da rayuwar ka shine yake cutar dakai a wani lokacin. Shiyasa amana tayi karanci ba kowa ne yake tamk'a amanar wani abu nasa hannun mutane ba balle kuma rayuwar sa. Asad yaso Hydar sosai har gobe yana son sa kaf y'an uwan sa yafi son Hydar yanzu ga abinda Hydar yayi masa. Kuyi haƙuri dukkan ku abubuwan da suka faru a baya yanzu komai ya wuce in sha Allah." "Ta silar ki komai ya bayyana y'ata shiyasa dukkan su baso son dawowar ki domin ke tamtar Inuwa kike a gare shi tun a mafarki ya sanki yake kuma rayuwa dake. Ke alkhairi ce a cikin gidan nan ta silar ki abubuwa da yawa sun bayyana wanda ba'a yi tunanin bayyanar su ba. Allah yayi muku albarka dukkan ku ya albarkaci rayuwar ku yasa kufi k'arfin dukkan maqiyan ku." Baba ya gyara zama ya amsa da Amin kafin yace,"Allah ya taimake ka babu komai, komai ya wuce sai dai muyi fatan alkhairi nan gaba." "Ma sha Allah. Yanzu abu na gaba da zamu fuskanta shine dawowar ta cikin gidan sarauta matsayin matar sa, ina so ayi gagarumin biki da dukka jama'a zasu shaida matar sarkin katagum ce. Ba kuma naso a d'auki lokaci nan da kwanaki uku zuwa hud'u nake so ayi komai a gama dan ina so a dawo da martabar katagum da aka rasa. Ina fatan babu takura a cikin lamarin." Baba ya sake cewa, "Duk abinda mai martaba yace shine daidai a wajan mu, Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya." Mai martaba ya amsa da amin ya kalli Asad yace, "banji kace komai ba? Ko na k'yale ka sai kaje can gidan?" Ya fad'a cikin zolayar Asad d'in. Murmushi ya kubce masa wnada baiyi niya ba ya shafa kansa yana jin nauyi da kunyar mahaifin nasa. Shima murmushin yayi yace, "Muje muyi sallah ayi jana'izar yaran da aka rasa" ya fad'a yana mik'ewa kowa ya mik'e ya kalli Baba yace, "Malam ya kamata a tsaya a samu ladan jana'iza in yaso sai su matan su tafi gida." Tare suka fito yana gaba Asad yana bayan sa har lokacin yak'i kallon inda Rauda take balle ma yayi mata magana. Mota Umma da Rauda suka shiga aka tafi dasu gida su Baba kuma aka shiga masallaci akayi sallah. *☆☆* A b'angaren Waziri lokacin da ya koma gida ya tarar har an musu suttura har lokacin kumfar bata daina fita daga bakin su ba, wani abu yaji mai nauyi ya tsirga masa ya tsaya a tsakiyar zuciyar sa ya fita da sauri zuwa falon nasa da akace a nan aka gansu. Shigar sa keda wuya yayi karo da kwalbar turaren da aka bashi wanda akace masa matuk'ar mai martaba da Asad ya shek'e su ya gama zaman gida kenan domin guba ne a cikin sa bana wasa ba. Kai ya dafe yana kallon kwalbar dan yasan Y'ay'an sa guda biyun da suka rasu akwai su da son turare tabbas sun shigo sun ganshi sun buɗe da nufin jin khamshin sa ya zama silar barin su duniya, zama yayi a kan kujera ya dafe kai maganar mai martaba ta fad'o masa inda yake cewa akwai sakayya ko yanzu ko nan gaba. Bai san ya kuma fashewa da kuka ba zuciyar sa na k'una tashin hankalin sa ya nikku dan ya tabbatar shine ya kashe y'ay'an sa a dalilin son zuciyar sa. Bai san lokacin da ya d'auka a haka ba sai buga k'ofar yaji ana yi yana d'ago kai suka had'a ido da Suhail da idanun sa shima yayi ja alamun yasha kuka shima yace, "Ana jiran Abba dan gabatar da jana'iza" ya fad'a da girmamawa kansa a k'asa. Haka ta taso jiki a salub'e badan yaso ba yayi gaba Suhail yana bin bayan sa limamin garin Katagum yaja sallar gawar aka sallace su daga nan aka wuce dasu gidan su na gaskiya. _Son zuciya hausawa suka ce b'acin ta. Allah kasa mufi karfin zuciyar mu Amin._😭😭😭 [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *082.*             Tunda aka shiga da Jidda d'akin da za'a duba ta Mum take safa da marwa hankalin ta ya tashi abubuwa biyu sun cushe mata zuciyar ta a wannan lokacin, tunanin abinda ya faru da kuma rashin lafiyar Jidda sun d'aga mata hankali sosai ta kasa nutsuwa ko kad'an. Daddy ne ya k'araso wajan ya kalli Mum d'in yace, "Sadiya lafiya? Meya faru da Jiddan haka?." Mum bata iya magana ba dan bata da nutsuwa a wannan lokacin nuna masa d'akin tayi yaja ya tsaya shima yana kallon d'akin zuciyar sa na harbawa cikin tsoron abinda zai biyo baya. Tun suna tsaye sai da suka zauna jikin Mum har rawa yake yi so take ma ta zubar da hawaye ma ta kasa sabida bala'in rud'anin da take ciki. Buɗe d'akin da aka shigar da Jidda akayi likita da nurses biyu suka fito Mum ta mik'e ta k'arasa wajan sa tace, "Dr ya jikin nata?." Likitan ya kalli Daddy ya kalli Mum d'in sannan yace, "Ta haihu." Da mamaki Mum ta kalli Daddy shima ya kalle ta ta dawo da kallon ta ga likitan tace, "Kamar ya ta haihu? Yi min bayani ban gane ba." Dr yace, "Eh ta haihu, ta haifi yaro namiji d'an wata bakwai wanda ake kira bakwaini." Daddy yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "Haihuwa Dr?." "Eh yallabai, tsoro da firgici da tashin hankalin da take a ciki ne ya jawo haihuwar da gaggawa, inda ace cikin k'arami ne bai zama mutum ba da zai zube ne sabida ta firgita sosai." Mum tace, "Yanzu ya jikin nata ita?." Dr yace, "gaskiya jikin ta babu dad'i, jinin ta ya hau sosai ga kuma haihuwa ga zuciyar ta da take bugawa very fast har yanzu unconsciously take. Babyn kuma yana inda aka tanada domin cigaba da rainon sa." Baya Mum tayi ta zauna a wannan lokacin Eman tazo wajan ganin yanayin da Mum take ciki ya skaa ta rik'e ta tana fad'in, "Mum meye faru da Jiddan?." Zama tayi kusa da ita Daddy ma ya zauna ya kalli Mum yace, "Ki sanar dani abinda ya firgita Jidda haka dan nasan kuna tare, sannan ya banga mijin ta ko wani nata a nan ba sai ke kad'ai?. Ba taro aka kira ku a gidan sarki ba?." Kuka Mum take yi sosai babu alamun zata tsayar dashi balle kuma ta iya masa magana ganin hakan sai ya tashi ya fita daga asibitin ma gabad'aya ya barsu a wajan dan firgice shima yake jin ance tsoro ya saka ta haihu. Duk yadda Eman taso rarrshin Mum abin yaci tura kuka take kamar wacce aka yiwa rasuwa itama sai ta fara kukan duk da bata san abinda ya faru ba amma kukan Mum d'in ya sakata kuka dan tasan akwai wani abun a k'asa. *☆☆*           Kuka Suhaima take yi sosai ganin Mama a kwance ko motsin kirki batayi an saka mata abinda zai taimaka mata wajan yin numfashi amma duk da haka numfashin baya fita yadda ya kamata a kirjin ta yake tsayawa baya sauka ciki. Tana zaune a kan kujerar kusa da gadon Maman tayi pillow da gadon tana cigaba da zubar da hawaye. "Yaya Hydar, Yaya Aliyu meyasa kukayi abinda kuka yi? Meyasa baku duba halin da Mama dani kaina zan shiga ba kuka zab'i son zuciyar ku akan farin cikin Mama?. Allah sarki Yaya Asad ya zaiji? Duk qaunar da yake yiwa Yaya Hydar amma da abinda zai saka masa kenan?. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta fad'a a bayyane tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya bata tab'a shiga kwatankwacin rud'ani kamar wannan ba. Tun daga bakin k'ofar ake jin sautin kukan Suhaima Dr Yasir ya shigo da sauri yana kallon ta murya can k'asa yace, "Suhaima please ki daina wannan kukan baki ga a gaban patient kike bane ba? In kika tashe ta fa?." Maimakon tayi shiru sai ta nuna masa Mama tana kuka tace, "Mama ce fa a kwance a haka, kalli Mamana ita kad'ai ba Yaya Hydar babu Yaya Aliyu babu Yaya Asad a tare da ita. Ya Mama zataji in ta farka ta ganta ita kad'ai babu su a tare da ita?. Bazan iya yin shiru ba ka barni nayi kukana bazan iya daina kuka ba." Ganin yadda take maganar kamar bata cikin hankalin ta hakan ya saka shi fita da sauri suka shigo da nurses mata guda biyu aka d'auke Suhaima daga wajan suka fita da ita zuwa wani d'akin daban aka yi mata allurar bacci suka saka mata ruwa dan itama tana buk'atar magani. *☆☆☆*                    Ciwon kai mai tsakani ya saka Rauda a gaba tunda suka koma gida ko buɗe ido bata son yi sabida yadda kan yake mata mugun ciwo ga zuciyar ta da take bugawa tunda take a duniya bata tab'a jin tashin hankali kamar wanda take ciki ba, ji take zuciyar ta na fizga sabida bala'in rud'ani jikinta har rawa yake yi. Umma da take zaune a gefen ta a zaune ita kuma ta jingina da kujera ta rik'e kai da hannu biyu tana kallon sama. Umma tace, "Sannu Rauda, kodai muje asibiti wannan ciwon kan bana k'are bane ba." Kai ta girgiza alamun a'a Umma tayi shiru tana girgiza kai in ta tuna irin abubuwan da suka ji sai taji amana ta k'are a duniya kowa ma ba abin yarda bane. Umma ta kalle ta tace, "Gwara muje asibitin kar kiyi b'ari, dan abinda kike ji a zuciyar ki a yanzu tsaf zai iya sakawa cikin jikin ki ya zube." Lumshe ido Rauda tayi ta d'ago kai ta kalli Umma ta mayar da idon ta ta kulle. Umma ta mik'e tsaye ta mik'ar da ita itama tace, "Muje ki kwanta ko zaki samu sauk'in abinda kike ji." D'aki Umma ta kai Rauda ta kwantar da ita ta bata magani tasha ta zauna a gefen ta har sai da bacci ya d'auke ta sannan ta fito ta k'yale ta. Baba bai dawo ba sai magriba har lokacin Rauda bacci take yi kai tsaye b'angaren Umman ya nufo yana zuwa ya same ta ta idar da sallah tana lazimi a kan kujera ita kad'ai Ummulkhairi da Khalil suna wajan Innan su. Da sallama ya shigo ta amsa tana sauke numfashi ya k'araso ya zauna yace, "Ya jikin Raudan?." Umma tace, "bacci take har yanzu, dak'yar baccin ya d'auke ta shiyasa ko sallah ban tashe ta ba." Baba ya girgiz kansa yace, "Ai gwara ta samu baccin, irin wannan tashin hankalin sai ya saka zuciyar ka ta buga." Umma tace, "ita da take da k'aramin ciki ma sai ya zube, wacce ya girma ta fad'i tana zubar da jini ina ga wacce bai girma ba?" Ta fad'a tana tagumi domin abubuwan da suka faru ganin su take kamar almara. Baba ya girgiza kansa yace, "Wato Binta tunda Allah ya kawo ni duniya ban tab'a jin tashin hankali kamar wanda naji yau ba, ace wanda kuke ciki d'aya uwa d'aya kuma uba d'aya sune suke k'okarin ganin bayan ka akan abinda ba kaine ka bawa kanka ba?. Ke duniya ina zaki je damu? Amana tayi k'aranci kowa ba abin yarda bane ba." Umma ta girgiza kai tace, "Har yanzu nutsuwa ta tak'i dawowa jikina, kaina jinsa nake a cushe bana fahimtar komai wallahi. D'an uwa na jini uwa d'aya uba d'aya amma akan mulki ya nemi salwantar da jinin sa? Meye abin so a mulkin?." Baba yace, "Baki san dad'in mulki bane shiyasa kike fad'ar haka, duk wani mai mulki da ya lashi zumar sa baya so ya daina lasar ta har abada, shiyasa hankalin su yake tashi in suka rasa kujerar su wasu kiga kamar ma zasuyi hauka. Mulki babu abinda baya sakawa ayi dan a d'auki rai a neman mulki abu ne mai sauk'i." Umma tace, "Ni kuwa nasan abu ne mai sauk'i tunda gashi naji da kunne na. Babu wanda ya bami tausayi sai Asad d'in da mahaifin sa, duk irin abubuwan da mahaifiyar sa tayi mana amma wallahi sai nake jin zuciyata tana tausaya mata dan Allah kad'ai yasan halin da take ciki a yanzu. Y'ay'anta da take alfahari take tutiya ace d'aya ne kawai mai amfani a cikin su? Muguntar wannan tana wane ta wannan, kowa a cikin su burin sa ya kawar da d'an uwan sa?." Baba yace, "Hydar d'in shine abin mamaki, ki tuna yadda yake shigewa Asad d'in gaba a akan komai hatta auren sa da Rauda shine ya assa shi ashe yana da manufar yin hakan badan Allah ya aikata ba. Yafi kowa bani mamaki ya kuma fi kowa bani tsoro, domin kaji tsoron maqiyin ka mai fuska biyu gwar wanda zai nuna maka kai tsaye baya sonka da wanda zai dinga yi maka kwantan b'auna." Umma tace, "Shi mai martaban ya zaiji?. K'anin sa uwa d'aya uba d'aya, matar sa kuma uwar gidan sa, ga ita kanta babar Asad d'in, ga y'ay'an sa guda biyu. In ba namijin gaske mai dakakkiyar zuciya ba sai ya yanke jiki ya fad'i ya had'u da lalurar shanyewar b'arin jiki. Ace duk wanda ya aikata maka sharri jinin kane da matan ka?." Baba yace, "Allah baya cutar da bawa akan laifin da bai aikata ba, duk wanda ya kasance mai yawan addu'a da neman zab'in Allah Allah bazai barshi da kansa ba sai ya shiga cikin lamarin sa. Yanzu ki duba shi Wazirin cikin lokaci kad'an Allah ya nuna masa sakayya babu b'ata lokaci y'ay'an sa biyu sun rasu a lokaci d'aya. Ni na d'auka ma yara ne fa ashe dukkan su babu wanda bai kai munzalin aure ba babu kamar namijin ma da ya girma sosai. Abin mamaki da d'aure kai turaren da aka bashi da nufin kashe Asad da baban sa suka d'auka sukayi amfani dashi su suka mutu. Dan Allah in baka ji tsoron Allah a lamarin nan ba tsoron me zaka ji?. In bakayi imani da Allah ba dawa zakayi imani?. Kai Allah kasa mufi k'arfin zuciyar mu." Umma girgiza kai kawai take yi cikin rud'ani zuciyar ta ta karye tace, "Kaji tsoron wanda aka zalunta in Allah ya tashi saka masa, yanzu kalli cikin lokaci kad'an Allah ya nuna masa bai isa yayi abinda bai nufa ba. Ita kuma uwar gidan garin son a kashe wani kaso kashe ta in mai hankali ce iya wannan ya isheta ishara, kalli ita mahaifiyar tasu duk alfaharin da take dasu da nuna talaka ba komai bane sai gashi alfarmar talakan taci kuma y'ay'an nata guda ukun d'aya ne kawai mai amfani a ciki. Shi Aliyun da ake nufin kashe d'an uwan sa dashi har ana so a saka shi hauka sai gashi......." umma bata k'arasa ba sai tace, "Kai Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ya hayyu ya qayyum ka saka mufi k'arfin zuciyar mu, ka tsare mu ka kare mu a duk inda muke kasa mu rinyaji zuciyar mu ba ita ta rinjaye mu ba" Umma ta fad'a tana d'aga hannun ta sama. Baba ya amsa da amin sukayi shiru dukkan su kafin Baba yace, "Ni daman nasan babu ta yadda za'ayi Asad ya rsntse yace bashi ya saki Rauda ba akan k'arya, ashe duka aikin d'an uwan sane." Umma bata ce komai ba girgiza kai kawai take yi kafin ta sauke numfashi tace, "Duka haka Allah ya nufa ya kuma k'addara, shekara har ta kusa zagowa da bikin sai yanzu ake samun sassauci a lamarin auren nasu. Ni wallahi yanzu abin yafi na baya bani tsoro, kaga Hydar d'in nan gani nake kamar bazai bar Rauda ba dan babu alamun nadama fa a tare dashi." Baba yace, "yadda Allah ya kare Asad da mahaifin sa haka Allah zai kare ta, zuciyar ta a wanke take bata tab'a nufar wani da sharri ba Allah bazai bari a cuce ta ba." Umma ta d'aga kai kawai Baba ya tashi ya fita zuwa masallaci dan yaji kiran sallar i'sha itama ta tashi ta tayar da sallah. Sai bayan ta idar ta duba Rauda ta ganta a zaune da alama ma tayi sallah itama ta koma ta kawo mata abinci da kanta ta tilasta mata taci badan taso ba dan ita har yanzu zuciyar ta bata amince cikin Asad ne a jikin ta ba. *☆☆☆*           Cikin awa da bai wuce uku ba an chanja komai na b'angaren mai Martaba Asad hatta carpet an cire shi an saka wani dan mahaifin sa yace bai amince da komai na ciki ba. Dukka kayan sawar Asad dana Aliyu an fito dasu daman mai martaba ya bayar da order dinki da alkyabba manya-manya ta Asad duk an kawo an saka ya koma sabo dal. Yana tsaye a jikin window yana kallon jama'ar gidan da suke ta kai kawo ya sauke numfashi ya juyo yana kallon falon ba komai ne yake fad'o masa ba sai zaman Jidda a cikin sa ita da Yayan sa. Tsaki yaja ya d'auke kansa yana cize baki, "Hydar!" Ya furta a bayyane yana lumshe idanun sa da suka kankance sabida tashin hankali da b'acin rai. Zuciyar sa bugawa take yi Allah ya sani yana qaunar Hydar da zuciya d'aya duk abin nan da fari baiji son sa ya fita daga zuciyar sa ba saima cutar dashi da son yake so yayi. Barin jikin window d'in yayi ya k'araso cikin falon yana niyar sauka yaga mahaifin sa na yawowa saman. Dole ya koma da baya ya bashi hanya ya wuce ya zauna ya k'araso ya zauna a k'asan carpet yace, "Barka da zuwa." Mai martaba yace, "Ina kake niyar zuwa haka?." Asad yace, "Zanje wajan Mama ne hankalina yak'i kwanciya ina so na ganta." "Ban amince da fitar sirrin nan da kake yi ba kayi fitar da ko wanne saraki yake yi." Asad yace, "In Allah ya amince zanyi abinda akace." Mai martaba yace, "Ya batun matar ka Jidda?." Gaban sa ya fad'i matuk'a ya d'ago yace, "Allah ya k'ara maka lafiya ni ba matata bace ba." Mai martaba yace, "Matar kace Asad, shari'a ta baka d'an cikin ta duk da ba naka bane. Ka tambayi ya lafiyar ta take?." Asad yace, "Ina neman afuwar ka dan ni gaskiya indai dan igiyar aurena da yake kanta ne na jima da datse ta, na sake ta!" Ya furta a sanyaye yana kallon mahaifin nasa da shima yake kallon sa da nasa mamakin. "Ka sake ta fa kace Asad? Waye ya fad'a maka shugaba yana saki?. Kaifa sarki ne shugaba ne da zaka daqile yawaitar sakin aure da ake yi amma da kanka kake furta ka sake ta?." Asad yace, "Allah ya wuci zuciyar mahaifina, bazan iya zama da ita ba mahaifina ya shaida ita d'in fasiqa ce taya zan iya zama da wacce tayi alfasha da auren ta tana sane?. Daman can zab'in Mama ce nayi biyayya ne na aure ta badan ina so ba sai dan gudun b'acin ran Mama, yanzu kuma ga abinda ya biyo baya zama na da ita ya haramta har abada. Batun da da mai martaba yake yi jinin Aliyu jinina ne zan iya rik'e masa y'ay'a d'ari indai akace jinin sane koda ba y'ay'an sunnah bane ba, amma bazan iya zama da ita ba." Mai martaba da yake jin sa yasan gaskiya yake fad'a masa amma yana gudun zubewar k'imar gidan dan in akaji labarin Asad ya saki Jidda ga d'a kuma sunan gidan da tarihin gidan gabad'aya ya lalace. Duk sanda aka bud'e ido akaga baby Jidda sai Rauda kowa zai ta tunanin inda take k'arshe a fara mumman zato a kan hakan. Yace, "Asad nasan gaskiya kake fad'a, amma ina so ka duba yanayin gidan da kake da kuma matsayin da kake dashi, me mutanen gari dama jama'ar gidan nan da basu san abinda ya faru ba in akace ka saki matar ka bayan tana da cikin ka?." Asad ya kalli mahaifin sa jin ya ambaci ciki sa sai mai martaba yayi murmushi yace, "Nasan ba jinin ka bane amma cikin Aliyu naka ne, abinda yayi ka shine yayi Aliyu. Kowa yasan Jidda matar kace ya kenan in akace yau babu Jidda a gidan sai wata daban me hakan yake nufi?." Asad yace, "Ban tari numfashin mai martaba ba, amma ina so a duba lamarin wallahi bazan iya zama da ita ba, kuma ni na riga na yanke hukunci gashi na sanar da mahaifina bana tunanin zan iya yin wani hukuncin da ba wannan ba, ina neman afuwar ka akan wannan bazan iya ba wallahi" ya fad'a yana kallon k'asa zuciyar sa na rawa in ya tuna abinda ya faru sai yaji jikin sa kamar ana kwashe masa kuzari sa gabad'aya komai sai ya tsaya masa cak. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *083.*          Mai martaba kallon sa yake yi ganin yadda jikin sa yayi sanyi ya sauke numfashi yasan daman abu ne mai wahala amma ya za'ayi dole ayi wani abun dan b'oye wani abun. Yace, "Asad bank'i ta taka ba, amma yanzu ya kenan in mutanen gari suka ji ka rabu da matar ka?." Asad yace, "Allah ya taimaki Abba ni a yanzu ba matata bace, tasan na saketa na fad'a mata baki da baki tun lokacin da take kirana da Aliyu." Mai martaba yace, "Sai kace min ka gama yanke hukunci ma tuni. Mahaifinta yazo d'azu bayan jana'iza da alama bai san duk abinda yake faruwa ba amma kawun ka yayi masa bayanin komai tashin hankali ya bayyana a tare dashi amma an sanar dashi ya kwantar da hankalin sa komai zaizo da sauk'i, kai kuma gashi yanzu ka lalata komai Asad." Shiru yayi ya sunkuyar da kansa k'asa Mai martaba ya kuma cewa, "Ya kake so ayi yanzu?." "Abba in ana so na d'auki abinda zata haifa zan d'auka har abada bazai san bani na haife shi ba, bayan wannan Abba bana tunanin akwai abinda zan iya." "Yanzu kenan kana so kace ta fita daga cikin gidan nan matsayin ba matar ka ba?, ka tuna fa kowa kallon matar ka yake mata in akace yau bata nan me mutane zasu d'auka? Shugaba mai sakin aure ko kuma me?." Asad yayi shiru ya kasa bashi amsa Mai martaba yace, "Mahaifinta ya sanar dani tayi haihuwar wata bakwai sabida rud'anin da ta shiga, kaga kenan yanzu auren ku ya k'are; koda yake daman babu idda a kanta." Shiru Asad yayi ya kasa magana kansa yana k'asa. Mai martaba yace, "Yanzu ya za'ayi da ita Jiddan da mahaifiyar ta?, tayi yunƙurin kashe mahaifiyar ka ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, ita kuma Jiddan taso kashe ka kuma taci amana ta kuma aikata alfasha wanda inda za'a yi mata hukuncin addini da za'a jefe tane har sai ranta ya bar jikin ta." Asad ya gyara zama yace, "A ganina bazata amince da hukuncin addini ba, ni a shawarata kawai a k'yaleta yadda Allah yaji da Uncle Abban Suhail suma zai ji dasu." Abba ya d'aga kai yace, "Hydar fa?." Asad ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya d'ago idon sa ya kalli hasken da yake falon ya sake mayar da kansa k'asa yace, "Ina son Hydar Abba, kaf cikin y'an uwana bani da wanda nake so nake ji dashi kamar Hydar. Zuciyata tana min ciwo in na tuna abubuwan da Hydar ya nufa a kaina sai naji da ina da iko dana goge su" yayi shiru alamun yana so ya d'an huta ne kafin ya cigaba da cewa, "Ina ganin kamar wasa duk abinda suka faru Hydar ne ya shirya sai naji zuciyata tana rawa Abba, bazan iya yiwa Hydar ko wanne hukunci ba a ganina a barshi shima Allah zaiji dashi kamar yadda yaji da Aliyu" ya k'arasa fad'a a sanyaye idanun sa yana cikowa da kwallah. Tausayin sa ya kama Mai martaba ya d'ora hannun sa a kansa yace, "Zuciyar ka mai kyau ce Asad, shiyasa nake farin ciki da katagum ta mallaki shugaba kamar ka. Kayi hak'uri k'addarar ke kenan y'an uwan ka da kuma babar ka sune k'addarar ka kayi addu'a Allah ya kawo k'arshen wannan k'addarar domin ka samu sauk'i a zuciyar ka. Nasan kana son Hydar shi kuma yayi amfani da son da kake masa ya cutar dakai, har gwara Aliyu daman kowa yasan ba shiri kuke ba amma Hydar naka ne, kayi haƙuri ka fuskanci abinda yake gaban ka domin Hydar bai kyale ka ba." Hawayen idon sa ya mayar ya danne zuciyar sa yak'i bari yayi kukan yace, "Haka ne Abba. In sha Allah zanyi abinda akace bazan bari tasirin wannan ya hanani gabatar da abinda yake gabana ba. Duk da ina jin tsoro mulki ya sake barin zuciyata, Allah ya k'ara maka lafiya ina ganin kamar mulkin nan zai kawo k'arshen rayuwata ne, bama kaina nake ji ba ina jin Muwadda zasu iya cutar da ita sabida ni" ya fad'a a sanyaye kansa yana k'asa. Jin sunan da ya kira yasan Rauda yake nufi sai yayi murmushi yace, "Dukkan ku babu abinda zai same ku in sha Allah. Zata dawo gidan nan kwanaki kad'an masu zuwa babu abinda zai faru da kai ko ina da izinin Allah komai ya k'are. Babban tashin hankalina in maganar nan ta baza gidan nan ban san ya abin zai kasance ba. D'ana Aliyu yayi zina da matar aure ya zauna da ita tamkar matar sa, d'ana Aliyu ya had'a kai da maqiya domin ganin bayan mahaifin sa da d'an uwan sa, d'ana Aliyu yayi abubuwa da yawa wanda basu da dad'in ji balle dad'in saurare. D'ana Hydar yaso kashe ni da d'an uwan sa, ya aikata abubuwa masu muni, ya mutane zasu kalli wannan?." Asad yayi shiru zuciyar sa babu dad'i sosai ya lumshe ido ya bud'e yaji Mai martaba yana cewa, "Amma baza'a bar Hydar ba yayi ta'asar da yaga dama ba, kuma in aka kyale shi yaci banza kenan, in za'a kyale kowa baza'a k'yale Hydar ba dole ayi maganin sa domin har yanzu babu nadama a tare dashi. Shi kuma Aliyu za'a yi masa magani in sha Allah duk sihirin da yake cikin sa zai warware." Asad yayi shiru mai martaba ya kalle shi yace, "Soyayyar da mahaifiyar ka take yi maka itace ta jawo maka tsana a wajan y'an uwan ka." Asad ya girgiza kai yace, "Allah ya k'ara maka lafiya Mama tafi son Hydar a kaina, tana son Hydar matuk'a shiyasa abinda ake fad'a ya saka ta suma. Burin ta take so na cika mata amma bawai tafi sona bane." Mai martaba yace, "Kuma ka kasance mai biyayya shiyasa take tauye ka a koda yaushe, bata duba abubuwan da ka bari sabida ita burinta kawai kayi abinda take so." Mai martaba ya mik'e tsaye shima dole ya mik'e yana binsa a baya Mai martaba yana cewa, "kaje duba maman naka in ka dawo kazo dai ina neman ka." Ya amsa da girmamawa Mai martaba ya tafi shi kuma ya koma da baya dan ya shirya. Shigar buzaye yayi riga da wando da babar riga ya nad'a rawani kalar kayan ya fito ya sauka k'asa nan ya tarar da masu zaman jiran sa ciki harda Suhail ya bada umarnin mota biyu kawai yake so banda kuma jiniya haka akayi kuwa ya shiga mota suka nufi asibitin. Lokacin da suk shiga d'akin Suhaima na zaune hannun ta da canular ta dafe kanta, sallamar da akayi ya saka ta d'ago suna had'a ido dashi ta taso a guje ta fad'a jikin sa ta rik'e shi gam sai ta fashe da kuka. Kallon Suhail yayi da yake gefen sa ya kalli Suhaima zuciyar sa ta karye ya saka hannun sa a bayan ta ya bubbuga kad'an yace, "Ki daina kuka Suhaima." Ta d'ago ta kalle shi tace, "Mama Yaya Asad, har yanzu bata farka ba ko motsi batayi. Babu kai babu Yaya Aliyu babu Yaya Hydar a kusa da ita,in ta farka taga haka zuciyar ta bazata yi mata dad'i ba." Yadda take kuka sosai ya saka shi ya rik'e kafad'ar ta yace, "calm down Suhaima! Babu abinda zai samu Mama Ina tare da ita a ko ina, relax please" ya fad'a yana wuce ta ya k'arasa gaban gadon Mama yana kallon ta. Gani yayi gabad'aya ta canja kamar ba ita ba ya rik'e hannun ta da babu ruwa a jiki ya zauna a gefe yace, "I'm sorry Mama." Likita ne ya shigo ganin Asad ya saka ya k'araso yana fad'in, "Barka da zuwa ranka ya dad'e." Asad ya kalle shi yace, "Me yake damun Mama?." Ya kalli Mama yace, "jinin tane ya hau sosai har yanzu bai sauka ba, sannan zuciyarta na bugawa sosai har bugun yayi yawa har yanzu bai daidaita ba hakan kuma matsala ne ga zuciyarta. Akwai firgici sosai a tare da ita shiyasa dole aka yi mata allurar bacci dan ta samu hutu" ya nuna Suhaima yace, "Itama sai da aka bata magani dan ta firgita sosai sai da tayi bacci ta samu lafiya." Asad ya girgiza kai yace, "in aka fita da ita outside country fa?." "Ranka ya dad'e ban tari numfashin ka ba, amma duk inda akaje hutu zasu bata dan shi take buk'ata a halin yanzu." Asad ya girgiza kansa yana kallon Mama da take bacci ya kalli Suhaima yace, "Zauna." Ba musu ta zauna Dr yace, "tak'i zama yadda ya kamata, tana buk'atar hutu itama sosai amma tak'i zama ta huta d'in." Asad ya kalle ta alamun meyasa hawaye ya zubo mata tace, "Bazan iya kwanciya na huta Mmaa tana cikin wannan yanayin ba, zuciyata bugawa take in na tuna abinda aka fad'a d'azu akan Yaya Hydar da Yaya Aliyu. Bazan iya jurewa ba" ta fad'a tana fashewa da kuka. Likitan ya fita Asad ya rik'e hannun Suhaima duka biyun yace, "Ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce." Kai ta d'aga yace, "wipe your tears." Ba musu ta goge hawayen ta yayi murmushi dan shi yaga k'okarin tama in shine a matsayin ta gani yake sai ya suma sau goma. Suhail ya kalle shi yace, "Ranka ya dad'e sai nake ganin kamar akwai matsala barin Mama ta kwana da Suhaima tunda dukkan su babu lafiya." Asad ya girgiza kai dan tabbas gaskiya ya fad'a amma bai amince da kowa ba balle ya d'auko hadima d'aya ta zauna dasu, ga y'an uwan Mama duka a nesa balle ya nemi wata a cikin su. Suhaima ta kalle shi tace, "Babu abinda zai faru zan iya." Asad ya kalle ta yace, "kin tabbatar?." Kai ta d'aga alamun eh yace, "duk abinda ya faru ki kira ni." Ta amsa da to shi kuma ya yi waya aka kawo security mata da maza wanda zasu kula da Maman ya yiwa Mama addu'a suka fita zuciyar sa duk babu dad'i musamman halin da ya tarar da Maman a ciki. Tunda ya shiga mota ya dafe kansa baya ganin inda suke nufa kawai yayi shiru zuciyar sa na sake hargitsewa in ya tuna abubuwan da suka faru sai yaji kamar ya d'auki bindiga ya harbe kansa, yadda yaga Mama ya sake dagula masa lissafi kuka kawai yake son yi amma babu dama. Tsayawa yaji anyi duk da hakan bai d'ago ba sai ji yayi Suhail yana fad'in, "Allah yaja da ranka Hydar ne ya tare hanyar." Jin hakan ya saka Asad d'ago kai ya kalli kan titin duk da baya ganowa sosai amma yaga mutum a tsaye ya tare musu hanya. Suhail yace, "Ranka ya dad'e zan ji dashi." Asad yace, "K'yale shi yazo." Suhail ya tsorota yace, "Amma ranka ya dad'e....." ya d'aga masa hannu dole yayi shiru ya fita yaje inda Hydar yake sai gashi ya tako yazo inda Asad yake zaune ya bud'e motar ya shiga ya zauna kusa da Asad d'in shi kuma ya bada umarnin kowa ya basu waje sannan ya kalli Hydar shi kuma yace, "Kasan sai ana neman izinin ganin ku, ranka ya dad'e" ya fad'a yana yiwa Asad jinjina yana kallon sa ido cikin ido. Kallon sa Asad yake yi shima haka sai Hydar yayi dariya kad'an yace, "oga deaf." Asad ya basar ya b'oye raunin kan fuskar sa yace, "me yake tafe dakai?." Hydar ya wara hannayen sa yace, "kashe ka." Asad ya murmusa yace, "gani gaka." Hydar yace, "Ina so kisan ya zama na musamman ne gaskiya, kamar yadda nida kai muke na musmaman ko a gidan mu haka nake so komai ya kasance." "Gani gaka duk abinda kake so zaka iya." Hydar ya kalli Asad yace, "Ina sonka har gobe Deaf amma nafi son kujerar katagum a kanka, naga yanzu ai ka koyo magana ba kamar da ba" ya fad'a yana dariya sai ya kuma cewa, "banfa yi niyar kashe ka bane tun farko da ba maganar ake yi yanzu ba, to lamarin ne naga sai an had'a da kisan sannan za'ayi nasara. Wannan matar taka ma cikin jikinta yana da kyau ace babu shi dan bana so ka bar baya." Asad ya kalle shi sai ya kyalkyale da dariya yace, "Har face d'in ka ta canja na ambato Muwadda a lamarina, karka damu cikin tane kawai bana so ba ita ba kar ka manta nine na bada support d'in auren ta bazan mata komai ba." Asad ya kalle shi yace, "Babban kuskuren da zakayi a duniya shine tab'a ta ko abinda yake jikin ta." Hydar ya girgiza kai yace, "Woww! Deaf fa ya koma mai magana yanzu ta dole ya koma Aliyu" sai kuma ya d'aure fuska yace, "In na tab'a ta d'in akwai abinda za'ayi min ne?." Asad ya jingina sosai da kujera yace, "Baka sanin abinda zai faru sai ka aikata abinda aka hane ka." Hydar yace, "Zan kuwa so naga abinda zai faru gaskiya dan haka zan aikata kodan na gani d'in, kai kasan ni akwai son rigima. amma fa sai na fara kashe ka sai na koma kan d'anka daman na hannun jidda ba naka bane bani da damuwa da wannan" ya fad'a yana zaro bindiga daga aljinun sa ya saita ta ya kalli Asad sai ya sake fashewa da dariya yace, "Deaf nawa, ina ji da kai har yanzu, kayi hak'uri wannan zata ratsa zuciyar ka ta fasa k'aunar Rauda ta fito daga ciki ta tsiyaye a k'asa tabi rariya." Asad yayi murmushi mai kyau ya gyara zaman sa yace, "Go ahead Hydar, kashe ni in zaka iya." "Me zai hana na iya? Indai akan kujerar katagum ne zan iya yin komai." "Bismillah!." Hydar ya saita bindiga a daidai zuciyar Asad yace, "silences gun ce babu wanda zai san ka mutu dan ba k'ara zasu ji ba. Ka fad'i abinda kake so na fad'awa Muwadda kafin ka mutu ina so nayi mata baban albishir." Asad baiyi magana ba bai motsa ba kallon sa yake yi ganin hakan ya saka Hydar yaja kunamar bindigar yace, "Baka da abin cewa kenan Oga deaf? Say goodbye" ya fad'a yana  dariyar mugunta tare da harba bindigar. #NanaHaleema #FitattuBiyar [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *084.*         Kallon idon Asad yayi sai kuma ya kyalkyale da dariya ya jiya bindigar a hannun sa yace, "Relax our king babu bullet a cikin bindigar, taya zan kashe ka Abba yana raye? Ai kamar na kashe maciji ne ban sare kai ba. Sai na gama da Abba na gama da babyn cikin Rauda then sai na dawo kanka" ya fad'a yana kallon bindigar yana dariya. Asad yayi murmushi shima ya kalli taga kafin ya dawo da kallon sa ga Hydar yace, "Hydar babu abinda zaka iya yi min, wani nawa ma baza ka iya yi mashi komai ba balle ni." Hydar ya sake yin dariya yana girgiza kai yace, "Asad d'in Mama, babu dalilin da zai saka na kasa ganin bayan ka, burina shine na d'auki ran kowa ciki harda naka ran" ya fad'a yana kallon sa. Asad baiyi magana ba Hydar yace, "Ya jikin Mama? In ta farka kace ina gaishe ta ka kuma sanar da ita ina kan cika burin ta ne dan naga kai babu abinda zaka iya" ya fad'a yana kallon idanun sa. Kallon sa shima yake yi Hydar ya d'aga riga ya sake yin dariya yace, "Asad nasan kana jin Hydar a zuciyar ka" ya dafa kafaɗarsa yana bubbuga ta yace, "Hydar ina son Asad amma kuma yafi son mulki a kanka." "Lokacin da na dawo Nigeria zan yi swapping sim card me ka bani abinci naci?" Asad ya tambaya yana kallon sa. Dariya Hydar ya sake yi yana tafa hannu kana yace, "Y'ar dabara ce irin tamu ta k'ananun yara ba wani abun bane ba" ya fad'a yana kallon sa har lokacin fuskar sa da murmushi. Asad baiyi magana ba Hydar yace, "kana da yarda da yawa shiyasa a ko yaushe ake cutar dakai, nasan tun a Germany ka gano ni musamman lokacin da ka dage akan a kai Abba India nak'i tun a sannan nasan ka saka min question mark baka nuna min bane ba amma kar ka manta harara Asad yayi nasan me yake nufi, shiyasa tun a lokacin nayi maganin ka." Ya sake kallon Asad d'in suka had'a ido sai ya d'an yi k'aramin tsaki yana runtse ido yace, "idon ka yana saka ni jin wani iri a jikina ka daina kallona haka bafa sata nayi maka ba."  Kafin Asad yayi magana ya kuma cewa, "in kuma ba haka ba a juya akalar auren ka da Rauda ya dawo kaina, cikin sauk'i zan raba ku na aure ta daman can tawa ce. Kaga sai ayi 2_0 Aliyu ya rik'e Jidda ni har da albarka an samu ni kuma na rik'e Rauda" ya fad'a yana d'agowa ya kalle shi. Asad ya lura so yake ya hasala shi ransa ya b'aci sai yayi murmushi yace, "Hydar!." Hydar ma yayi murmushi yace, "Asad! Sai fa kayi haƙuri na shirya wasu abubuwan da yawa za'a rasa rai za kuma a rasa lafiya. Tabbaci nake baka akan cikin jikin matar ka sai ya zama babu shi dan in zan k'yale komai bazan k'yale cikin ba, ka shammace ni ban san za'ayi ciki da sauri haka ba dan ban bari an zo wajan ba. Duk d'auka nake har yanzu abin sautin ya daina d'aukar sauti ashe ya gyaru har amo yake fitarwa ba iya sauti ba" ya fad'a yana kallon sa shima shi yake kallo. Hydar yace, "Ashe sitiyarin motar ya dawo da aiki yadda ya kamata na d'auka tunda Mama ta lalata shi bai dawo daidai ba ashe nine nake haukan banza tunda gashi harda ciki." Asad ya sau ke numfashi yace, "Ko a mafarki kar ka d'auka wannan abinda kake fad'a zai kasance." Hydar ya hard'e hannu a k'irji yace, "to muyi deal mana, in na zubar da cikin ta me zaka bani? Ni kuma indai ban zubar da cikin ba ka saka a kashe ni."  Asad yace, "bani da lokacin da zan tsaya yin deal dakai Hydar, bana da lokacin da zan saurari shirmen ka mai kama da tatsuniya. In kayi nasara a kaina a kwanakin baya tabbas yanzu ni zanyi nasara a kanka." Hydar ya murmusa yace, "Kana nan yadda na sanka confidence d'inka yana nan, to in ban tabbatar da shirina a kanka ba ai ba sunana AliyuHydar ba." Asad yace, "fitar min a mota." Hydar yace, "Daga na ambaci Rauda sai a kore ni daga mota? Ayi haƙuri tuba nake ranka ya dad'e ba wani abun nace zanyi da ita ba ai" ya fad'a yana yi masa jinjina kafin ya sake kyalkyalewa da dariya yace, "Zan fita Asad koda baka ce ba, amma ina so kasan zan dawo gare ka bazaka tab'a zama lafiya ba matuk'ar ina raye sai na raba ka da komai da ka mallaka ni na mallake shi ciki kuma harda matar ka da kake so. Zamu had'e nan bada jimawa ba, ina nan zuwa gare ka" yana gama fad'ar hakan ya fita daga motar ya shiga tasa motar yaja a guje. A lokacin escorts d'in sa da Suhail suka dawo Suhail ya shiga motar uana fad'in, "Ranka ya dad'e fatan komai lafiya? Naga bindinga a hannun sa." Asad ya masa alama da su tafi kawai driver yaja motar kai tsaye gida suka wuce. Shiru Asad yayi suna tafiya tunani yake yi ta ko ina Hydar ya gama gano lagon sa, ta ko wanne b'angare ya karance shi sosai shiyasa cutar dashi bazai yi wahala ba. Tambayar da yake yiwa kansa itace anya Hydar zai iya kashe shi? Yasan har yanzu Hydar yana sonsa anya zai iya kashe shi?. Bai gama nemo amsar tambayar ba suka iso cikin gidan kai tsaye b'angaren sa ya wuce. Suhail yana bayan sa bayan sun shiga falon yace, "Suhail a tabbatar an sake k'ara tsaro a kaf gidan nan, inda babu camera ina so a saka" ya fad'a yana dafe kansa. Suhail yace, "An gama ranka ya dad'e. Allah yaja zamanin ka Fulani Hajiya ce take neman izinin ganin ka." Asad ya sauke numfashi a wahale yace, "Suhail bana jin zan iya ganin kowa. Suhail na gaji sosai." "To ranka ya dad'e sai a sanar da ita" ya fad'a yana juyawa zai koma. "Tazo" ya fad'a a hankali Suhail ya amsa ya fita. Zama yayi a kan kujerar da take mallakin sa ba jimawa Hajiya ta shigo da kaf y'ay'anta mata da namiji ganin hakan sai ya mik'e tsaye suka k'araso yace, "Hajiya da an sanar dani da nazo da kaina." Hajiya tace, "Mune ya kamata muzo da kan mu ranka ya dad'e." Zama yayi ya nuna musu waje su zauna duk suka zauna Hajiya tace, "Ranka ya dad'e nazo da kaina ne neman afuwa akan abubuwwan da suka faru a baya, shiyasa na tawo da duka iyalana dan su taya ni baka haƙuri da kuma neman yafiyar ka." Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah Hajiya a bar maganar nan ta riga ta wuce." "A'a Asad bata wuce ba, an cutar dakai da yawa ko nace mun cutar dakai Asad. Nayi abubuwa a kan ganin bayan ka ni kaina ban san adadin su ba tun ba'a je ko ina ba na fara ganin sakayyar da Allah yayi maka akan Yahuza. Wallhi tun ranar da kazo duniya nake son ganin bayan ka Allah bai tab'a bani nasara ba. Ina had'a ka da kyawawan sunayen Allah kayi hak'uri ka yafe min abubuwan dukka da suka wuce" ta kalli y'ay'an ta tace, "Ku taya ni rok'on sa." Babbar yayar su tace, "A madadin iyalan Hajiya muna neman afuwa abinda ya faru a baya ranka ya dad'e, abinda aka aikata wanda aka fad'a da wanda aka aikata ba a fad'a ba muna rok'on mai girma sarki da ya yafe mana mun yi alqwari in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba." Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah ku daina wannan maganar bana son ji, komai ya wuce ban rik'e kowa a raina ba." Hajiya tace, "Da gaske mai martaba sarkin mu ya yafe min?." "Na yafe duk da daman ban rik'e ki ba Hajiya. Ina miki kallon mahaifiyata." Zata fara godiya yace, "Dan Allah kar kice komai, uwa kike a gare ni bazan jure ganin kina zubar da hawaye ba. Komai ya wuce dan Allah a daina kuka." Ba musu ta goge idanun ta tana murmushi ya kalli y'an uwan nasa gabad'aya dukkan su fuskar su a sake yace, "Ina rok'on ku dukkan ku in akwai abinda ya faru a baya wanda ba'a ji dad'in saba a yafe. Sannan ina so duk inda akaga wani abu ba daidai ba a ciki da wajen masarautar nan ayi hanzarin sanar dani." Dukkan su da farin ciki suka amsa kafin suyi sallama duk su tafi shi kuma ya tashi ya wuce saman sa Suhail yana bayan sa. A falon Suhail ya tsaya shima yana tsaye yace, "Ranka ya dad'e Hydar fa barazana ne ga rayuwar mai martaba bai kamata a sake dashi ba." Asad ya sauke numfashi yace, "kar ka damu babu abinda zai faru." "Haka muke fata, a kwana lafiya" ya fad'a yana juyawa ya sauka shi kuma ya wuce bedroom d'in sa. D'aki ya shiga sai ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa kafin ya runtse idanun sa yana jin d'aci a zuciyar sa. _ni kuma in ban zubar da cikin jikinta ba na amince ka kashe ni._ kalaman Hydar suka fad'o masa ya cire rawanin kansa ya kalli wayar sa ya d'auka da niyar kiran ta sai kuma ya ajjiye yaja k'aramin tsaki ta ko wanne b'angare haushin ta yake ji a zuciyar sa shiyasa yayi banza da ita bai sake waiwayon ta ba har yau. _Yana dakyau ka neme ta kodan abinda Hydar yace._ Zuciyar sa ta fad'a masa ya runtse idanun sa a bayyane yace, "In sha Allah babu abinda zai faru da ita, ina tare da ita a ko yaushe." Fuskar Mama ta fad'o masa sai ya d'auki wayar sa ya kira Suhaima tana d'auka yace, "Mama." Suhaima tace, "Har yanzu bacci take." Datse kiran yayi ya kama k'ugun sa sosai kansa yake masa ciwo har jiri yake ji yana d'aukar sa. "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a bayyane yana zama a gefen gadon ya dafe kansa lokacin da Jidda ta saka a kashe shi har ya kamata tana waya ya fad'o masa. Saurin kawar da tunanin yayi ya tashi ya shiga wanka. Wankan ma da ruwan magani ya yishi bayan ya fito ya shafa mai da magani ya fesa turare mai magani ya saka kaya wanda aka turara su da magani. Hannun sa ya d'ora a cikin sa baya jin yunwa ko kad'an gashi shidan yasan tun daren jiya bai sake cin komai ba. _Wallahi na tsane ka bana qaunar ganin mazinaci._ kalaman Rauda suka fad'o masa abinda yaji a zuciyar sa sai da ya datse labban sa da hakorin sa ya runtse ido yana sauke numfashi zuciyar sa na rawa. Bai san adadin lokacin da ya d'auka a haka ba sai da dare yayi sosai ya sauko kai tsaye b'angaren mai martaba ya shiga. Kamar yadda yayi tunani yana zaune akan sallaya ganin hakan sai ya koma ya shiga d'akin da Aliyu yake kwance. A zaune ya same shi shima a kan gado idanun sa a waje ya yaga rigar jikin sa yayi tagumi ya zubawa waje d'aya ido kamar mai kallon wani abun. Ganin Asad ya shigo ya saka Aliyu zabura yana kallon sa har ya k'araso inda yake ya zauna ya dafa kafad'arsa yace, "Allah ya baka lafiya Aliyu." Kai Aliyu ya fara girgizawa yana fad'in,  "Ba sunana Aliyu ba sunana Asad, ni sarki ne ina hawa doki ana zagawa dani, ina zuwa na bawa yara y'an islamiyya allo a lokacin bikin sauka. Ka daina cemin Aliyu zan iyawa yin komai akan hakan." Asad ya runtse idanun sa ya buɗe yana kallon Aliyu cikin tausayin halin da yake ciki ya zuba masa ido kawai baiyi magana ba. K'arar buɗe k'ofa yaji hakan ya saka shi ya juya ganin mahaifinsa sai ya mik'e tsaye har ya k'arasa ya dafa kafaɗarsa sa yace, "me ya fito da kai a daren nan?." Asad ya nuna Aliyu yace, "hankalina yak'i kwanciya." Mai martaba ya kalli Aliyu yace, "zai samu lafiya da iznin Allah shiyasa na zab'i a barshi a nan yana karb'ar magani." Asad ya girgiza kansa yace, "Abba jikin Mama ma babu dad'i." Numfashi ya sauke yace, "dole ta samu gigita da rud'ani a wannan yanayin da ake ciki amma itama zata samu lafiya." Mai martaba ya kalle shi yace, "Zuciyar ka a wanke take Asad kyakykyawar zuciyar da kake da ita Allah bazai bawa kowa damar cutar da kai ba." Asad yyi shiru ya sunkuyar da kansa mai martaba yace, "Ka koma kaje ka huta gobe akwai zaman da zaka gabatar domin gyara mulkin ka. Bana son a sake samun matsala a wancan karon ma kaine ka bada dama ka dinga karb'ar duk abinda babar ka tazo dashi. A wannan karon bazai faru ba." Kai ya girgiza kai kafin yayi masa sallama ya wuce ya koma yana ji kamar ana tura shi in yana tafiya sabida jiri. *☆☆☆*        "Duk abinda kuka aikata yazo kunnena Sadiya, duk yadda kuke da Rabi'a ta d'auki aminci ta baki tun kuna makarantar secondary a Kano kuke tare amma ki rasa abinda zaki saka mata sai da cuta, cutar ma kuma wai kisa Sadiya? Yaushe kika zama y'ar ta'adda ban sani ba?" Daddy ya fad'a da alamun bacin rai a tare dashi yana kallon Mum. Mum tana kuka sosai tace, "Ambassador ka tsaya nayi maka bayanin abinda ya faru, banyi hakan da....." dakatar da ita yayi ta hanyar fad'in, "Rufe min baki domin baki da wani kalami da zaki fad'a min na amince. Sabida tsabar son zuciyar ki aminiyar ki kike k'ok'arin kashewa bayan kin rabata da d'an da ta haifa sabida wani banza burin ki na iska. Kin d'ora y'arki a tafarkin zina da aure a kanta take zmaan fasiqanci da Yayan mijinta kuma duk kina sane kikayi shiru sabida cikar burin ki." Mum tace, "Wallahi ban san ba Asad bane, bata fad'a min ba, ban san zaman fasiqanci sukeyi da Aliyu ba ka yarda dani." "Babu abinda zaki fad'a na yarda dashi, kin cutar dani kin kuma cutar da kanki da rayuwar yarki. Baxan lamunta ba wallahi bazan iya cigaba da zama da mata irin ki ba, daga asibitin nan kar ki sake ki koma min gidana kije can ku k'arata dake da y'ar taki da kuma d'an shegen da ta haifar miki da aure a kanta, wannan bak'in zunubin bazai zauna a gidana ba domin wata rana kar fushin Allah ya shafe ni." Hankalin Mum ya sake tashi ta zube a k'asa tace, "Kar kayi min haka Daddy wallahi duk abinda ya faru bada son raina ba ka tsaya nayi maka bayani." "Ni na tsaya na saurare ki? Har abada bazan tsaya ba domin ban san me kika k'unso kike so ki kashe ba nima dan tunda kikayi yunƙurin kashe Rabi baki duba alaqar ku babu wanda zaki bari a duniya. Ga takardar sakin y'arki nan an bani sai kije da ita ku k'arata ko babu komai tahiri ya kafu a kanta wanda baza'a manta dashi ba a duniya. Mace ta farko da tayi zina da yayan mijinta y'ar kice, mace ta farko da taso kashe mijin ta sabida karta rabu da yayan mijin nata y'ar kice, mace ta farko da sarki guda shugaban al'amma ya fara sakin ta. Kar ki sake ki dawo min gida bazan iya zama da dake da kuma y'arki ba" ya fad'a yana cilla mata takardar hannun sa. Har ya juya zai tafi yaga Eman na kuka sosai ya damk'o hannunta yace, "muje kar kema ta lalata min ke da bak'ar zuciyar ta!" Ya fad'a yana jan Hannun Eman suka bar wajan tana kuka sosai Mum tana kuka. #FitattuBiyar #Nanahaleema [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *085.*        Zubewa Mama tayi a k'asa tana kuka sosai mai tsuma zuciya Mai cike da tarin dana sani da nadamar duk abinda ta aikata domin gashi ya k'are a kanta da y'arta. "Mum!." Da sauri Mum ta juya tana kallon Jidda jin muryar ta ta fita tana kallon ta itama ita take kallo. Shafa cikin ta tayi ta sake kallon Mum tace, "Mum ina cikina?." Mum ta mik'e ta taso tazo kusa da ita ba tare da tunanin komai ba ta chakumi wuyan Jidda tana girgiza ta kafin ta cire hannu ta tsika mata mari tana fad'in, "Jidda kin cuce ni kin gama dani. Me na aikata miki kika zab'i kiyi min wannan hukuncin? Me nayi miki kike k'okarin saka zuciyata ta buga eh Jidda?." Jidda ta sake fashewa da sabon kuka duk da ciwon da yake tare da ita tace, "Mum ba laifina bane laifin kine Mum, kece kika d'ora ni akan hanyar aikata duk abinda na aikata. Bana son barin gidan sarauta bana son a daina kirana matar sarki shiyasa na amince da Aliyu tun farkon kaini gidan matsayin matar Asad ba. Ban san wannan ranar zata zo ba da na kashe kaina kafin zuwan ta." "Ko baki kashe kanki ba ni zan kashe ki Jidda. Na tsane ki wallahi bana son ganin ki dan kin aikata zunubin da ban tab'a ganin wanda ya aikata shi ido da ido ba sai kee!." Jidda ta tashi zaune dak'yar tana cize baki tace, "Da nace a kashe Aliyu da an kashe shi duk wannan bata zo ba, a lokacin in nace miki a kashe Aliyu Asad nake nufi domin munyi agreement da Aliyu akan bazan sake kiran sunan sa Aliyu ba sai dai Asad shi kuma Asad nace masa Aliyu. Mum duk laifin kine da baki d'ora ni akan cuta ba da yanzu ina tare da mijina Asad, ke kika koya min son kai, ke kika koya min kisa, ke kika koya min dukkan abinda na aikata a wajan ki na iya...." a haukace Mum tayo kanta ta fara dukan ta ta ko ina. Nurses ne suka shigo a guje aka kwace Mum amma tuni Jidda ta suma itama Mum d'in baya tayi ya zube a k'asa suka d'auke ta aka shiga bata nata taimakon haka Jiddan ba. *☆☆☆* Washe gari ta kama ranar litinin an gabatar da zaman fada mai aji wanda Asad ya gabatar da zafafan hukuncin da ya yanke wanda zai sake farfad'o da martabar masarautar sa. Duk wani abu da ake yi ba daidai ba an dakatar dashi an sake d'ora masarautar akan tafarkin addinin musulunci da kuma kyawawan ayyuka masu kyau da tsari. Ranar kowa sai da Asad ya burge shi domin yadda yake maganar ma abin burgewa ne balle kuma hukuncin da ya yanke akan komai ya tsara komai yadda ya kamata. Bayan an tashi daga zaman fada asibitin da Mama take kwance ya wuce ana tafiya ana jiniya mota hud'u a gaba sannan wacce yake ciki sai hud'u a baya ana gudu akan titi. Duk a k'ofar d'akin suka tsayaa shida Suhail ne kawai suka shiga ciki tunda ya hango Maman sai kuma gaban sa ya fad'i ganin ta dai tana nan yarda ya barta jiya. Suhaima ya kalla yaga ta rame lokaci d'aya tayi duhu idanunta ya fad'a ya kalle ta yace, "Suhaima meyasa bakya jin magana?." Ta rausayar dakai dan ta gaji da yin kuka tace, "na kasa bacci ne." Ya furzar da iska a bakin sa yace, "Mama bata farka ba?." Kai ta d'aga alamun eh ya girgiza kansa ya kalli Suhail kamar yasan me yake nufi sai ya tashi ya fita jim kad'an sai gashi da Dr sun shigo. Dr Yasir ne ya gyara tsayuwa yace, "Barka da zuwa ranka ya Dade." Asad bai amsa ba yace, "ya jikin Mama?." Ya sake saukar da murya cikin girmamawa yace, "Ranka ya dad'e jinin Mama ne ya hau sosai, sannan zuciyar Mama tana bugawa da sauri har muna expecting heart attack ya kama Mama but bamu yi confirming ba. Akwai firgici sosai a tare da Mama dalilin da ya saka har yanzu jinin ta baiyi daidai ba har yanzu zuciyar Mama a firgice take." Asad ya sauke numfashi ya kalle shi sannan ya kalli Suhaima Dr ma ya kalli Suhaima yace, "Allah ya k'ara maka lafiya itama Suhaima akwai firgici a tare da ita shine ya haifar mata da zazzaɓi amma tak'i zama ayi mata treatment." Asad ya kalle ta ya kalli Dr din sai ya kalli Suhail gnin kallon sai yace, "Ayi mata yanzu Dr duk abinda ya kamata ayi. Sannan zuwa yaushe Mama zata farka?." Dr yace, "in sha Allah zuwa gobe zata farfad'o, muna so bp d'in nata ne yayi k'asa kafin allurar ta sake ta." Suhail yace, "Ayi duk abinda ya kamata Dr." "In sha Allah ranka ya dad'e." Asad addu'a ya yiwa Mama sosai kafin a kawo gado a kwantar da Suhaima a kai a saka mata ruwa a gaban sa bacci ya d'auke ta. Security aka k'aro mace mai uniform aka ajjiye ta da kula da Mama aka saka maza biyu a bakin k'ofa ya bada umarnin ko waye yazo kar a barshi ya shigo suka amsa da girmamawa sannan suka fito suka koma gida. *☆☆☆*        Yadda waziri yake kuka sai ka d'auka k'aramin yaro ne har majina ce take zuba daga hancin sa matar sa na tsaye a kansa itama cikin kuka da tashin hankali tana fad'in, "Na rantse da Allah sai ka fad'a min matsafan da ka bawa y'ay'ana suka tsafe akan son mulkin ka na banza da wofi. Wallahi bazan bar maganar nan ba zan kaita gaba wajan human right domin su kwatar min hakkina." Kuka sosai yake yi zuciyar sa tana bugawa yayi tari yana dukan k'irjin sa kana ya d'ago jajayen idanun sa ya kalle ta muryar sa har rawa take yace, "Yanzu ni kike kalla kike sanar dani na kai y'ay'ana anyi tsafi dasu?." Ta kalle shi tace, "Na fad'a, ai nasan zaka iya ne akan son mulkin ka babu abinda baza ka iya aikatawa ba. Ko ka saka a dawo min da y'ay'ana ko na kai ka k'ara" ta fad'a tana fashewa da sabon kuka ta zube a wajan. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, kaicona ni Yahuza kaico da masu hali irin nawa na son duniya da k'ok'arin ganin bayan wani.  Yanzu me gari ya waya a gare ni? Na rasa y'ay'ana har guda biyu akan abinda ba addini ba" ya fad'a yana kulle fuskar sa yana kuka mai tsuma zuciya. "Ban amince da wannan jawabin naka ba, wallahi Allah sai an karbar min hakkina sai an saka min abinda akayi min nida y'ay'ana, bazan amince ba wallahil azim sai bazan bar maganar nan ba kaji na rantse, jira nake a share makoki in kai maganar gaban hukuma" tana fad'a ta tashi ta fita bai iya kallon ta ba ya cigaba da kuka sosai. Bai daina kuka ba dan kukan daga zuciyar sa yake zuwa shiyasa hawayen idanun sa suka ki tsayawa kuka yake sosai kana kallon sa kasan yana cikin rad'ad'in zuciya da tashin hankali. Ya jima a haka kansa yana sarawa yana yi masa ciwo ya kwanta yana kallon sama. "Assalamu alaikum, ranka ya dad'e anyi baki daga Kano" wani dogari ya fad'a daga bakin k'ofa. Bai iya d'agowa ya kalle shi ba da hannu yayi masa alama da yaje ya juya ya tafi ya jima kafin ya tashi ya shiga band'aki ya wanke fuskar sa ya fito. Sai da yazo gab da mutanen da suka zo masa gaisuwa jiri sai ya kwashe shi nan take ya zube a wajan a sume. *☆☆☆*           Falo na musamman suke a zaune Asad ya kalli mahaifin sa murya a sanyaye yace, "Abba ina neman alfarma." Mai martaba ya ajjiye abinda yake hannun sa ya kalle shi yace, "Ina jinka." "Ranka ya dad'e alfarma nake nema a madadin Mama, ina rok'on mahaifina da ya yafe mata kuskuren da ta aikata a baya, tana jin jiki yanzu daga can nake har yanzu bata san a inda take ba." Mai martaba yayi murmushi yace, "Asad babu kai a cikin maganar dake tsakanina da mahaifiyar ka, ina so tayi nadamar dukkan abinda ta aikata da wanda take son aikatawar wannan abun ya faru. Ina so tayi nadamar abubuwa da yawa ta wanke zuciyar ta dukka halayen ta marasa kyau ta ajjiye su a gefe." Asad yayi shiru har Abba yakai k'arshe kafin yace, "A duba dai Abba." "Ai kad'an ta fara gani Asad abinda ta aikata ko hakkin matar ka Rauda bazai barta ba balle hakkin sauran mutane. Ni sai ka tuna min ma batun matar taka jibi juma'a za'ayi bikin dawowar ta gidan na shugaba guda bazai yu ya zauna a gidan nan babu mata ba." Asad yayi shiru baice komai ba Mai martaba yace, "Munyi magana da mahaifinta d'azu sun san da batun dawowar ta jibin an gama gyara b'angaren da zata zauna komai an tanadar mata ita akwai ake jira ta dawo dan cikar martabar ka." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa kafin yace, "Allah ya taimake ka ba'a ce komai akan Maman ba." Yayi y'ar dariya yace, "wato hankalin ka yana kan Maman ka ba matar ka ba, zanje naga yanayin jikin nata kawun ka ma an sanar dani d'azu a wajan zaman makoki ya yanke jiki ya fad'i an kaishi asibiti." Asad ya girgiza kai yace, "Ina godiya mai martaba Allah ya k'ara lafiya, Allah ya bashi lafiya shima." Ya amsa da amin kafin Asad yace, "Abba Aliyu." Mai martaba yace, "Zai samu lafiya in sha Allah ka kwantar da hankalin ka sai a hankali komai zai wuce. Kun had'u da Hydar ne?." Ya d'aga kai alamun eh yace, "Akan hanyar mu ta dawowa daga wajan Mama jiya muka had'u." "Kar hankalin ka ya tashi a duk abinda zaice yana neman hanyar da zai fusata kane shiyasa zai fad'a maka maganar da ranka zai b'aci, ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai faru." Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan lamarain gidan ciki da wajen sa. Da daddare Asad ya kira Suhail bayan ya d'auka ya sanar dashi yana neman sa ba jimawa kuwa ya bayyana a falon Asad ya bashi umarnin zuwa sama ya hayo ya same shi a tsaye yace, "Suhail zamu je wajan Mama, but bana so kowa yasan zamu fita ina nufin nida kai kawai." Suhail yace, "Amma ranka ya dad'e fita babu jami'an tsoro akwai ganganci duba da yanayin dake ciki yanzu." Asad yace, "Haka nake so." Suhail zaiyi magana ya d'aga masa hannu dole yayi shiru yace, "Allah ya wuci zuciyar ka" ya fad'a yana komawa k'asa shima ya sakko k'asan yazo da mota har k'ofar b'angaren sa ya shiga bayan motar suka fita. Yadda suka barta d'azu haka suka kuma ganin Mama sai dai Suhaima taji sauk'i ita ta samu kuzari ya umarci Suhail da ya barshi a nan yaje aka siyowa Suhaima abinda zata ci da abinda zata sha ya dawo ya same shi. Basu jima sosai ba suka baro asibitin suna tafiya a kan titi Asad baice komai ba ya zubawa titi ido kawai ba tare da yayi magana shi kad'ai yasan abinda yake zuciyar sa. Abinda ya gani shine ya firgita shi ya kalli Suhail ya masa alama da ya tsaya yaja ya tsaya yana kallon gefe inda yake kallon abinda yake haddasa masa bugun zuciya. Rauda ce a tsaye a wajan mai siyar da kayan marmari hannunta rik'e da leda da alama ta gama siya ma tana bashi kud'i, ransa yaji yayi mugun b'aci ya zuba mata ido kawai yana kallon ta ya saukar da glass d'in K'asa kasancewar akwai duhu a wajan ba kowa ne zai gane shi ba.  Suhail ganin abinda yake kalla sai shima ya kalli wajan ya ganta sanye da dogon hijjabi har k'asa fuskar ta a buɗe tana k'okarin tsallaka titi. Titin ta tsallaka ta tsaya tana yatsine fuska alamun gajiya a tare da ita tana kallon titin, Suhail ya kalla baiyi magana ba sai ya juya kan motar yaje daidai da ita ya tsaya amma basu sauke glass ba. K'aramin tsaki taja tayi gaba tana sake kallon hanya Suhail ya sake yin gaba ya sauke glass lokacin ta juyo take idon su ya had'u dana Asad. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *085.*        Zubewa Mama tayi a k'asa tana kuka sosai mai tsuma zuciya Mai cike da tarin dana sani da nadamar duk abinda ta aikata domin gashi ya k'are a kanta da y'arta. "Mum!." Da sauri Mum ta juya tana kallon Jidda jin muryar ta ta fita tana kallon ta itama ita take kallo. Shafa cikin ta tayi ta sake kallon Mum tace, "Mum ina cikina?." Mum ta mik'e ta taso tazo kusa da ita ba tare da tunanin komai ba ta chakumi wuyan Jidda tana girgiza ta kafin ta cire hannu ta tsika mata mari tana fad'in, "Jidda kin cuce ni kin gama dani. Me na aikata miki kika zab'i kiyi min wannan hukuncin? Me nayi miki kike k'okarin saka zuciyata ta buga eh Jidda?." Jidda ta sake fashewa da sabon kuka duk da ciwon da yake tare da ita tace, "Mum ba laifina bane laifin kine Mum, kece kika d'ora ni akan hanyar aikata duk abinda na aikata. Bana son barin gidan sarauta bana son a daina kirana matar sarki shiyasa na amince da Aliyu tun farkon kaini gidan matsayin matar Asad ba. Ban san wannan ranar zata zo ba da na kashe kaina kafin zuwan ta." "Ko baki kashe kanki ba ni zan kashe ki Jidda. Na tsane ki wallahi bana son ganin ki dan kin aikata zunubin da ban tab'a ganin wanda ya aikata shi ido da ido ba sai kee!." Jidda ta tashi zaune dak'yar tana cize baki tace, "Da nace a kashe Aliyu da an kashe shi duk wannan bata zo ba, a lokacin in nace miki a kashe Aliyu Asad nake nufi domin munyi agreement da Aliyu akan bazan sake kiran sunan sa Aliyu ba sai dai Asad shi kuma Asad nace masa Aliyu. Mum duk laifin kine da baki d'ora ni akan cuta ba da yanzu ina tare da mijina Asad, ke kika koya min son kai, ke kika koya min kisa, ke kika koya min dukkan abinda na aikata a wajan ki na iya...." a haukace Mum tayo kanta ta fara dukan ta ta ko ina. Nurses ne suka shigo a guje aka kwace Mum amma tuni Jidda ta suma itama Mum d'in baya tayi ya zube a k'asa suka d'auke ta aka shiga bata nata taimakon haka Jiddan ba. *☆☆☆* Washe gari ta kama ranar litinin an gabatar da zaman fada mai aji wanda Asad ya gabatar da zafafan hukuncin da ya yanke wanda zai sake farfad'o da martabar masarautar sa. Duk wani abu da ake yi ba daidai ba an dakatar dashi an sake d'ora masarautar akan tafarkin addinin musulunci da kuma kyawawan ayyuka masu kyau da tsari. Ranar kowa sai da Asad ya burge shi domin yadda yake maganar ma abin burgewa ne balle kuma hukuncin da ya yanke akan komai ya tsara komai yadda ya kamata. Bayan an tashi daga zaman fada asibitin da Mama take kwance ya wuce ana tafiya ana jiniya mota hud'u a gaba sannan wacce yake ciki sai hud'u a baya ana gudu akan titi. Duk a k'ofar d'akin suka tsayaa shida Suhail ne kawai suka shiga ciki tunda ya hango Maman sai kuma gaban sa ya fad'i ganin ta dai tana nan yarda ya barta jiya. Suhaima ya kalla yaga ta rame lokaci d'aya tayi duhu idanunta ya fad'a ya kalle ta yace, "Suhaima meyasa bakya jin magana?." Ta rausayar dakai dan ta gaji da yin kuka tace, "na kasa bacci ne." Ya furzar da iska a bakin sa yace, "Mama bata farka ba?." Kai ta d'aga alamun eh ya girgiza kansa ya kalli Suhail kamar yasan me yake nufi sai ya tashi ya fita jim kad'an sai gashi da Dr sun shigo. Dr Yasir ne ya gyara tsayuwa yace, "Barka da zuwa ranka ya Dade." Asad bai amsa ba yace, "ya jikin Mama?." Ya sake saukar da murya cikin girmamawa yace, "Ranka ya dad'e jinin Mama ne ya hau sosai, sannan zuciyar Mama tana bugawa da sauri har muna expecting heart attack ya kama Mama but bamu yi confirming ba. Akwai firgici sosai a tare da Mama dalilin da ya saka har yanzu jinin ta baiyi daidai ba har yanzu zuciyar Mama a firgice take." Asad ya sauke numfashi ya kalle shi sannan ya kalli Suhaima Dr ma ya kalli Suhaima yace, "Allah ya k'ara maka lafiya itama Suhaima akwai firgici a tare da ita shine ya haifar mata da zazzaɓi amma tak'i zama ayi mata treatment." Asad ya kalle ta ya kalli Dr din sai ya kalli Suhail gnin kallon sai yace, "Ayi mata yanzu Dr duk abinda ya kamata ayi. Sannan zuwa yaushe Mama zata farka?." Dr yace, "in sha Allah zuwa gobe zata farfad'o, muna so bp d'in nata ne yayi k'asa kafin allurar ta sake ta." Suhail yace, "Ayi duk abinda ya kamata Dr." "In sha Allah ranka ya dad'e." Asad addu'a ya yiwa Mama sosai kafin a kawo gado a kwantar da Suhaima a kai a saka mata ruwa a gaban sa bacci ya d'auke ta. Security aka k'aro mace mai uniform aka ajjiye ta da kula da Mama aka saka maza biyu a bakin k'ofa ya bada umarnin ko waye yazo kar a barshi ya shigo suka amsa da girmamawa sannan suka fito suka koma gida. *☆☆☆*        Yadda waziri yake kuka sai ka d'auka k'aramin yaro ne har majina ce take zuba daga hancin sa matar sa na tsaye a kansa itama cikin kuka da tashin hankali tana fad'in, "Na rantse da Allah sai ka fad'a min matsafan da ka bawa y'ay'ana suka tsafe akan son mulkin ka na banza da wofi. Wallahi bazan bar maganar nan ba zan kaita gaba wajan human right domin su kwatar min hakkina." Kuka sosai yake yi zuciyar sa tana bugawa yayi tari yana dukan k'irjin sa kana ya d'ago jajayen idanun sa ya kalle ta muryar sa har rawa take yace, "Yanzu ni kike kalla kike sanar dani na kai y'ay'ana anyi tsafi dasu?." Ta kalle shi tace, "Na fad'a, ai nasan zaka iya ne akan son mulkin ka babu abinda baza ka iya aikatawa ba. Ko ka saka a dawo min da y'ay'ana ko na kai ka k'ara" ta fad'a tana fashewa da sabon kuka ta zube a wajan. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, kaicona ni Yahuza kaico da masu hali irin nawa na son duniya da k'ok'arin ganin bayan wani.  Yanzu me gari ya waya a gare ni? Na rasa y'ay'ana har guda biyu akan abinda ba addini ba" ya fad'a yana kulle fuskar sa yana kuka mai tsuma zuciya. "Ban amince da wannan jawabin naka ba, wallahi Allah sai an karbar min hakkina sai an saka min abinda akayi min nida y'ay'ana, bazan amince ba wallahil azim sai bazan bar maganar nan ba kaji na rantse, jira nake a share makoki in kai maganar gaban hukuma" tana fad'a ta tashi ta fita bai iya kallon ta ba ya cigaba da kuka sosai. Bai daina kuka ba dan kukan daga zuciyar sa yake zuwa shiyasa hawayen idanun sa suka ki tsayawa kuka yake sosai kana kallon sa kasan yana cikin rad'ad'in zuciya da tashin hankali. Ya jima a haka kansa yana sarawa yana yi masa ciwo ya kwanta yana kallon sama. "Assalamu alaikum, ranka ya dad'e anyi baki daga Kano" wani dogari ya fad'a daga bakin k'ofa. Bai iya d'agowa ya kalle shi ba da hannu yayi masa alama da yaje ya juya ya tafi ya jima kafin ya tashi ya shiga band'aki ya wanke fuskar sa ya fito. Sai da yazo gab da mutanen da suka zo masa gaisuwa jiri sai ya kwashe shi nan take ya zube a wajan a sume. *☆☆☆*           Falo na musamman suke a zaune Asad ya kalli mahaifin sa murya a sanyaye yace, "Abba ina neman alfarma." Mai martaba ya ajjiye abinda yake hannun sa ya kalle shi yace, "Ina jinka." "Ranka ya dad'e alfarma nake nema a madadin Mama, ina rok'on mahaifina da ya yafe mata kuskuren da ta aikata a baya, tana jin jiki yanzu daga can nake har yanzu bata san a inda take ba." Mai martaba yayi murmushi yace, "Asad babu kai a cikin maganar dake tsakanina da mahaifiyar ka, ina so tayi nadamar dukkan abinda ta aikata da wanda take son aikatawar wannan abun ya faru. Ina so tayi nadamar abubuwa da yawa ta wanke zuciyar ta dukka halayen ta marasa kyau ta ajjiye su a gefe." Asad yayi shiru har Abba yakai k'arshe kafin yace, "A duba dai Abba." "Ai kad'an ta fara gani Asad abinda ta aikata ko hakkin matar ka Rauda bazai barta ba balle hakkin sauran mutane. Ni sai ka tuna min ma batun matar taka jibi juma'a za'ayi bikin dawowar ta gidan na shugaba guda bazai yu ya zauna a gidan nan babu mata ba." Asad yayi shiru baice komai ba Mai martaba yace, "Munyi magana da mahaifinta d'azu sun san da batun dawowar ta jibin an gama gyara b'angaren da zata zauna komai an tanadar mata ita akwai ake jira ta dawo dan cikar martabar ka." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa kafin yace, "Allah ya taimake ka ba'a ce komai akan Maman ba." Yayi y'ar dariya yace, "wato hankalin ka yana kan Maman ka ba matar ka ba, zanje naga yanayin jikin nata kawun ka ma an sanar dani d'azu a wajan zaman makoki ya yanke jiki ya fad'i an kaishi asibiti." Asad ya girgiza kai yace, "Ina godiya mai martaba Allah ya k'ara lafiya, Allah ya bashi lafiya shima." Ya amsa da amin kafin Asad yace, "Abba Aliyu." Mai martaba yace, "Zai samu lafiya in sha Allah ka kwantar da hankalin ka sai a hankali komai zai wuce. Kun had'u da Hydar ne?." Ya d'aga kai alamun eh yace, "Akan hanyar mu ta dawowa daga wajan Mama jiya muka had'u." "Kar hankalin ka ya tashi a duk abinda zaice yana neman hanyar da zai fusata kane shiyasa zai fad'a maka maganar da ranka zai b'aci, ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai faru." Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan lamarain gidan ciki da wajen sa. Da daddare Asad ya kira Suhail bayan ya d'auka ya sanar dashi yana neman sa ba jimawa kuwa ya bayyana a falon Asad ya bashi umarnin zuwa sama ya hayo ya same shi a tsaye yace, "Suhail zamu je wajan Mama, but bana so kowa yasan zamu fita ina nufin nida kai kawai." Suhail yace, "Amma ranka ya dad'e fita babu jami'an tsoro akwai ganganci duba da yanayin dake ciki yanzu." Asad yace, "Haka nake so." Suhail zaiyi magana ya d'aga masa hannu dole yayi shiru yace, "Allah ya wuci zuciyar ka" ya fad'a yana komawa k'asa shima ya sakko k'asan yazo da mota har k'ofar b'angaren sa ya shiga bayan motar suka fita. Yadda suka barta d'azu haka suka kuma ganin Mama sai dai Suhaima taji sauk'i ita ta samu kuzari ya umarci Suhail da ya barshi a nan yaje aka siyowa Suhaima abinda zata ci da abinda zata sha ya dawo ya same shi. Basu jima sosai ba suka baro asibitin suna tafiya a kan titi Asad baice komai ba ya zubawa titi ido kawai ba tare da yayi magana shi kad'ai yasan abinda yake zuciyar sa. Abinda ya gani shine ya firgita shi ya kalli Suhail ya masa alama da ya tsaya yaja ya tsaya yana kallon gefe inda yake kallon abinda yake haddasa masa bugun zuciya. Rauda ce a tsaye a wajan mai siyar da kayan marmari hannunta rik'e da leda da alama ta gama siya ma tana bashi kud'i, ransa yaji yayi mugun b'aci ya zuba mata ido kawai yana kallon ta ya saukar da glass d'in K'asa kasancewar akwai duhu a wajan ba kowa ne zai gane shi ba.  Suhail ganin abinda yake kalla sai shima ya kalli wajan ya ganta sanye da dogon hijjabi har k'asa fuskar ta a buɗe tana k'okarin tsallaka titi. Titin ta tsallaka ta tsaya tana yatsine fuska alamun gajiya a tare da ita tana kallon titin, Suhail ya kalla baiyi magana ba sai ya juya kan motar yaje daidai da ita ya tsaya amma basu sauke glass ba. K'aramin tsaki taja tayi gaba tana sake kallon hanya Suhail ya sake yin gaba ya sauke glass lokacin ta juyo take idon su ya had'u dana Asad. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *084.*         Kallon idon Asad yayi sai kuma ya kyalkyale da dariya ya jiya bindigar a hannun sa yace, "Relax our king babu bullet a cikin bindigar, taya zan kashe ka Abba yana raye? Ai kamar na kashe maciji ne ban sare kai ba. Sai na gama da Abba na gama da babyn cikin Rauda then sai na dawo kanka" ya fad'a yana kallon bindigar yana dariya. Asad yayi murmushi shima ya kalli taga kafin ya dawo da kallon sa ga Hydar yace, "Hydar babu abinda zaka iya yi min, wani nawa ma baza ka iya yi mashi komai ba balle ni." Hydar ya sake yin dariya yana girgiza kai yace, "Asad d'in Mama, babu dalilin da zai saka na kasa ganin bayan ka, burina shine na d'auki ran kowa ciki harda naka ran" ya fad'a yana kallon sa. Asad baiyi magana ba Hydar yace, "Ya jikin Mama? In ta farka kace ina gaishe ta ka kuma sanar da ita ina kan cika burin ta ne dan naga kai babu abinda zaka iya" ya fad'a yana kallon idanun sa. Kallon sa shima yake yi Hydar ya d'aga riga ya sake yin dariya yace, "Asad nasan kana jin Hydar a zuciyar ka" ya dafa kafaɗarsa yana bubbuga ta yace, "Hydar ina son Asad amma kuma yafi son mulki a kanka." "Lokacin da na dawo Nigeria zan yi swapping sim card me ka bani abinci naci?" Asad ya tambaya yana kallon sa. Dariya Hydar ya sake yi yana tafa hannu kana yace, "Y'ar dabara ce irin tamu ta k'ananun yara ba wani abun bane ba" ya fad'a yana kallon sa har lokacin fuskar sa da murmushi. Asad baiyi magana ba Hydar yace, "kana da yarda da yawa shiyasa a ko yaushe ake cutar dakai, nasan tun a Germany ka gano ni musamman lokacin da ka dage akan a kai Abba India nak'i tun a sannan nasan ka saka min question mark baka nuna min bane ba amma kar ka manta harara Asad yayi nasan me yake nufi, shiyasa tun a lokacin nayi maganin ka." Ya sake kallon Asad d'in suka had'a ido sai ya d'an yi k'aramin tsaki yana runtse ido yace, "idon ka yana saka ni jin wani iri a jikina ka daina kallona haka bafa sata nayi maka ba."  Kafin Asad yayi magana ya kuma cewa, "in kuma ba haka ba a juya akalar auren ka da Rauda ya dawo kaina, cikin sauk'i zan raba ku na aure ta daman can tawa ce. Kaga sai ayi 2_0 Aliyu ya rik'e Jidda ni har da albarka an samu ni kuma na rik'e Rauda" ya fad'a yana d'agowa ya kalle shi. Asad ya lura so yake ya hasala shi ransa ya b'aci sai yayi murmushi yace, "Hydar!." Hydar ma yayi murmushi yace, "Asad! Sai fa kayi haƙuri na shirya wasu abubuwan da yawa za'a rasa rai za kuma a rasa lafiya. Tabbaci nake baka akan cikin jikin matar ka sai ya zama babu shi dan in zan k'yale komai bazan k'yale cikin ba, ka shammace ni ban san za'ayi ciki da sauri haka ba dan ban bari an zo wajan ba. Duk d'auka nake har yanzu abin sautin ya daina d'aukar sauti ashe ya gyaru har amo yake fitarwa ba iya sauti ba" ya fad'a yana kallon sa shima shi yake kallo. Hydar yace, "Ashe sitiyarin motar ya dawo da aiki yadda ya kamata na d'auka tunda Mama ta lalata shi bai dawo daidai ba ashe nine nake haukan banza tunda gashi harda ciki." Asad ya sau ke numfashi yace, "Ko a mafarki kar ka d'auka wannan abinda kake fad'a zai kasance." Hydar ya hard'e hannu a k'irji yace, "to muyi deal mana, in na zubar da cikin ta me zaka bani? Ni kuma indai ban zubar da cikin ba ka saka a kashe ni."  Asad yace, "bani da lokacin da zan tsaya yin deal dakai Hydar, bana da lokacin da zan saurari shirmen ka mai kama da tatsuniya. In kayi nasara a kaina a kwanakin baya tabbas yanzu ni zanyi nasara a kanka." Hydar ya murmusa yace, "Kana nan yadda na sanka confidence d'inka yana nan, to in ban tabbatar da shirina a kanka ba ai ba sunana AliyuHydar ba." Asad yace, "fitar min a mota." Hydar yace, "Daga na ambaci Rauda sai a kore ni daga mota? Ayi haƙuri tuba nake ranka ya dad'e ba wani abun nace zanyi da ita ba ai" ya fad'a yana yi masa jinjina kafin ya sake kyalkyalewa da dariya yace, "Zan fita Asad koda baka ce ba, amma ina so kasan zan dawo gare ka bazaka tab'a zama lafiya ba matuk'ar ina raye sai na raba ka da komai da ka mallaka ni na mallake shi ciki kuma harda matar ka da kake so. Zamu had'e nan bada jimawa ba, ina nan zuwa gare ka" yana gama fad'ar hakan ya fita daga motar ya shiga tasa motar yaja a guje. A lokacin escorts d'in sa da Suhail suka dawo Suhail ya shiga motar uana fad'in, "Ranka ya dad'e fatan komai lafiya? Naga bindinga a hannun sa." Asad ya masa alama da su tafi kawai driver yaja motar kai tsaye gida suka wuce. Shiru Asad yayi suna tafiya tunani yake yi ta ko ina Hydar ya gama gano lagon sa, ta ko wanne b'angare ya karance shi sosai shiyasa cutar dashi bazai yi wahala ba. Tambayar da yake yiwa kansa itace anya Hydar zai iya kashe shi? Yasan har yanzu Hydar yana sonsa anya zai iya kashe shi?. Bai gama nemo amsar tambayar ba suka iso cikin gidan kai tsaye b'angaren sa ya wuce. Suhail yana bayan sa bayan sun shiga falon yace, "Suhail a tabbatar an sake k'ara tsaro a kaf gidan nan, inda babu camera ina so a saka" ya fad'a yana dafe kansa. Suhail yace, "An gama ranka ya dad'e. Allah yaja zamanin ka Fulani Hajiya ce take neman izinin ganin ka." Asad ya sauke numfashi a wahale yace, "Suhail bana jin zan iya ganin kowa. Suhail na gaji sosai." "To ranka ya dad'e sai a sanar da ita" ya fad'a yana juyawa zai koma. "Tazo" ya fad'a a hankali Suhail ya amsa ya fita. Zama yayi a kan kujerar da take mallakin sa ba jimawa Hajiya ta shigo da kaf y'ay'anta mata da namiji ganin hakan sai ya mik'e tsaye suka k'araso yace, "Hajiya da an sanar dani da nazo da kaina." Hajiya tace, "Mune ya kamata muzo da kan mu ranka ya dad'e." Zama yayi ya nuna musu waje su zauna duk suka zauna Hajiya tace, "Ranka ya dad'e nazo da kaina ne neman afuwa akan abubuwwan da suka faru a baya, shiyasa na tawo da duka iyalana dan su taya ni baka haƙuri da kuma neman yafiyar ka." Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah Hajiya a bar maganar nan ta riga ta wuce." "A'a Asad bata wuce ba, an cutar dakai da yawa ko nace mun cutar dakai Asad. Nayi abubuwa a kan ganin bayan ka ni kaina ban san adadin su ba tun ba'a je ko ina ba na fara ganin sakayyar da Allah yayi maka akan Yahuza. Wallhi tun ranar da kazo duniya nake son ganin bayan ka Allah bai tab'a bani nasara ba. Ina had'a ka da kyawawan sunayen Allah kayi hak'uri ka yafe min abubuwan dukka da suka wuce" ta kalli y'ay'an ta tace, "Ku taya ni rok'on sa." Babbar yayar su tace, "A madadin iyalan Hajiya muna neman afuwa abinda ya faru a baya ranka ya dad'e, abinda aka aikata wanda aka fad'a da wanda aka aikata ba a fad'a ba muna rok'on mai girma sarki da ya yafe mana mun yi alqwari in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba." Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah ku daina wannan maganar bana son ji, komai ya wuce ban rik'e kowa a raina ba." Hajiya tace, "Da gaske mai martaba sarkin mu ya yafe min?." "Na yafe duk da daman ban rik'e ki ba Hajiya. Ina miki kallon mahaifiyata." Zata fara godiya yace, "Dan Allah kar kice komai, uwa kike a gare ni bazan jure ganin kina zubar da hawaye ba. Komai ya wuce dan Allah a daina kuka." Ba musu ta goge idanun ta tana murmushi ya kalli y'an uwan nasa gabad'aya dukkan su fuskar su a sake yace, "Ina rok'on ku dukkan ku in akwai abinda ya faru a baya wanda ba'a ji dad'in saba a yafe. Sannan ina so duk inda akaga wani abu ba daidai ba a ciki da wajen masarautar nan ayi hanzarin sanar dani." Dukkan su da farin ciki suka amsa kafin suyi sallama duk su tafi shi kuma ya tashi ya wuce saman sa Suhail yana bayan sa. A falon Suhail ya tsaya shima yana tsaye yace, "Ranka ya dad'e Hydar fa barazana ne ga rayuwar mai martaba bai kamata a sake dashi ba." Asad ya sauke numfashi yace, "kar ka damu babu abinda zai faru." "Haka muke fata, a kwana lafiya" ya fad'a yana juyawa ya sauka shi kuma ya wuce bedroom d'in sa. D'aki ya shiga sai ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa kafin ya runtse idanun sa yana jin d'aci a zuciyar sa. _ni kuma in ban zubar da cikin jikinta ba na amince ka kashe ni._ kalaman Hydar suka fad'o masa ya cire rawanin kansa ya kalli wayar sa ya d'auka da niyar kiran ta sai kuma ya ajjiye yaja k'aramin tsaki ta ko wanne b'angare haushin ta yake ji a zuciyar sa shiyasa yayi banza da ita bai sake waiwayon ta ba har yau. _Yana dakyau ka neme ta kodan abinda Hydar yace._ Zuciyar sa ta fad'a masa ya runtse idanun sa a bayyane yace, "In sha Allah babu abinda zai faru da ita, ina tare da ita a ko yaushe." Fuskar Mama ta fad'o masa sai ya d'auki wayar sa ya kira Suhaima tana d'auka yace, "Mama." Suhaima tace, "Har yanzu bacci take." Datse kiran yayi ya kama k'ugun sa sosai kansa yake masa ciwo har jiri yake ji yana d'aukar sa. "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a bayyane yana zama a gefen gadon ya dafe kansa lokacin da Jidda ta saka a kashe shi har ya kamata tana waya ya fad'o masa. Saurin kawar da tunanin yayi ya tashi ya shiga wanka. Wankan ma da ruwan magani ya yishi bayan ya fito ya shafa mai da magani ya fesa turare mai magani ya saka kaya wanda aka turara su da magani. Hannun sa ya d'ora a cikin sa baya jin yunwa ko kad'an gashi shidan yasan tun daren jiya bai sake cin komai ba. _Wallahi na tsane ka bana qaunar ganin mazinaci._ kalaman Rauda suka fad'o masa abinda yaji a zuciyar sa sai da ya datse labban sa da hakorin sa ya runtse ido yana sauke numfashi zuciyar sa na rawa. Bai san adadin lokacin da ya d'auka a haka ba sai da dare yayi sosai ya sauko kai tsaye b'angaren mai martaba ya shiga. Kamar yadda yayi tunani yana zaune akan sallaya ganin hakan sai ya koma ya shiga d'akin da Aliyu yake kwance. A zaune ya same shi shima a kan gado idanun sa a waje ya yaga rigar jikin sa yayi tagumi ya zubawa waje d'aya ido kamar mai kallon wani abun. Ganin Asad ya shigo ya saka Aliyu zabura yana kallon sa har ya k'araso inda yake ya zauna ya dafa kafad'arsa yace, "Allah ya baka lafiya Aliyu." Kai Aliyu ya fara girgizawa yana fad'in,  "Ba sunana Aliyu ba sunana Asad, ni sarki ne ina hawa doki ana zagawa dani, ina zuwa na bawa yara y'an islamiyya allo a lokacin bikin sauka. Ka daina cemin Aliyu zan iyawa yin komai akan hakan." Asad ya runtse idanun sa ya buɗe yana kallon Aliyu cikin tausayin halin da yake ciki ya zuba masa ido kawai baiyi magana ba. K'arar buɗe k'ofa yaji hakan ya saka shi ya juya ganin mahaifinsa sai ya mik'e tsaye har ya k'arasa ya dafa kafaɗarsa sa yace, "me ya fito da kai a daren nan?." Asad ya nuna Aliyu yace, "hankalina yak'i kwanciya." Mai martaba ya kalli Aliyu yace, "zai samu lafiya da iznin Allah shiyasa na zab'i a barshi a nan yana karb'ar magani." Asad ya girgiza kansa yace, "Abba jikin Mama ma babu dad'i." Numfashi ya sauke yace, "dole ta samu gigita da rud'ani a wannan yanayin da ake ciki amma itama zata samu lafiya." Mai martaba ya kalle shi yace, "Zuciyar ka a wanke take Asad kyakykyawar zuciyar da kake da ita Allah bazai bawa kowa damar cutar da kai ba." Asad yyi shiru ya sunkuyar da kansa mai martaba yace, "Ka koma kaje ka huta gobe akwai zaman da zaka gabatar domin gyara mulkin ka. Bana son a sake samun matsala a wancan karon ma kaine ka bada dama ka dinga karb'ar duk abinda babar ka tazo dashi. A wannan karon bazai faru ba." Kai ya girgiza kai kafin yayi masa sallama ya wuce ya koma yana ji kamar ana tura shi in yana tafiya sabida jiri. *☆☆☆*        "Duk abinda kuka aikata yazo kunnena Sadiya, duk yadda kuke da Rabi'a ta d'auki aminci ta baki tun kuna makarantar secondary a Kano kuke tare amma ki rasa abinda zaki saka mata sai da cuta, cutar ma kuma wai kisa Sadiya? Yaushe kika zama y'ar ta'adda ban sani ba?" Daddy ya fad'a da alamun bacin rai a tare dashi yana kallon Mum. Mum tana kuka sosai tace, "Ambassador ka tsaya nayi maka bayanin abinda ya faru, banyi hakan da....." dakatar da ita yayi ta hanyar fad'in, "Rufe min baki domin baki da wani kalami da zaki fad'a min na amince. Sabida tsabar son zuciyar ki aminiyar ki kike k'ok'arin kashewa bayan kin rabata da d'an da ta haifa sabida wani banza burin ki na iska. Kin d'ora y'arki a tafarkin zina da aure a kanta take zmaan fasiqanci da Yayan mijinta kuma duk kina sane kikayi shiru sabida cikar burin ki." Mum tace, "Wallahi ban san ba Asad bane, bata fad'a min ba, ban san zaman fasiqanci sukeyi da Aliyu ba ka yarda dani." "Babu abinda zaki fad'a na yarda dashi, kin cutar dani kin kuma cutar da kanki da rayuwar yarki. Baxan lamunta ba wallahi bazan iya cigaba da zama da mata irin ki ba, daga asibitin nan kar ki sake ki koma min gidana kije can ku k'arata dake da y'ar taki da kuma d'an shegen da ta haifar miki da aure a kanta, wannan bak'in zunubin bazai zauna a gidana ba domin wata rana kar fushin Allah ya shafe ni." Hankalin Mum ya sake tashi ta zube a k'asa tace, "Kar kayi min haka Daddy wallahi duk abinda ya faru bada son raina ba ka tsaya nayi maka bayani." "Ni na tsaya na saurare ki? Har abada bazan tsaya ba domin ban san me kika k'unso kike so ki kashe ba nima dan tunda kikayi yunƙurin kashe Rabi baki duba alaqar ku babu wanda zaki bari a duniya. Ga takardar sakin y'arki nan an bani sai kije da ita ku k'arata ko babu komai tahiri ya kafu a kanta wanda baza'a manta dashi ba a duniya. Mace ta farko da tayi zina da yayan mijinta y'ar kice, mace ta farko da taso kashe mijin ta sabida karta rabu da yayan mijin nata y'ar kice, mace ta farko da sarki guda shugaban al'amma ya fara sakin ta. Kar ki sake ki dawo min gida bazan iya zama da dake da kuma y'arki ba" ya fad'a yana cilla mata takardar hannun sa. Har ya juya zai tafi yaga Eman na kuka sosai ya damk'o hannunta yace, "muje kar kema ta lalata min ke da bak'ar zuciyar ta!" Ya fad'a yana jan Hannun Eman suka bar wajan tana kuka sosai Mum tana kuka. #FitattuBiyar #Nanahaleema [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *086*            Gabanta yayi mugun fad'uwa ganin da wanda suka had'a ido ta sauke ido k'asa bata motsa ba shi kuma bai daina kallon ta ba da alamun b'acin rai a tare dashi. Suhail ne ya fito daga motar ya bud'e mata baya da hannu ya mata alamar ta shiga kafin yace, "Ranki ya dad'e bismillah." Ba musu ta shiga ya kulle musu k'ofar ya tsaya a bakin motar ba tare da ya koma ba. Shiru babu wanda yayi magana cikin su ita shi yake kallo cikin tsantsar b'acin rai da takaicin abinda ya gani, d'ago kai tayi ta kalle shi suka had'a ido ta sunkuyar dakai k'asa ta sosa kanta kad'an kana tace, "Barka da dare." Banza yayi mata yana kallon ta ba tare da ya bata amsa ba sai tamke fuska da yayi yana hararar ta. Kusan mintina biyu suna haka kafin yace, "Daga ina kike?." Ta d'ago ta kalle shi ta shagwab'e fuska tace, "na rako Yaya Ummi titi." "Da izinin wa?." A sama taji maganar ta d'ago ta kalle shi taga tamkar bai tab'a yin dariya ba a duniya sai taji tsoro ya mamaye mata zuciya tace, "Ba kowa." Ya sauke numfashi ya jingina da kujerar yana kallon ta ji yake tamkar ya tsinka mata mari sabida yawan haushin ta da yake a cikin zuciyar sa, ya d'auki sacannin baice komai ba kafin yace, "Zaman kanki kike kenan?." Gajiya tayi da bashi amsa cikin k'osawa tayi tace, "A'a." Kai ya girgiza ya kalli titi kafin yace, "Shine kika tsaya bakin titi kina siyayyar banza da wofi?." Kai ta kawar domin bazata bashi amsa ba itama sai dai yayi duk abinda zaiyi yadda yake jin haushin ta itama nasa haushin take ji sosai bai kuma isa ya juya ta ba, ganin ta juyar da kai bata bashi amsa ba itama ta d'aure fuskar ta sai ya share ta ransa ya sake b'aci bai kuma kallon ta ba ya kira number Suhail yana ganin kiran ya shigo motar kai tsaye gidan su Rauda aka nufa. Babu wanda yake magana a lokacin da yake babu tafiya sosai lokaci d'aya akazo gidan su Rauda ya tsaya ya bud'e motar ya fita ya sake barin su. Buɗe motar zatayi taji an saka lock ta koma ta zauna tana kallon gidan nasu da yake tarr da haske tamkar ba dare ba. Mota ce ta tsaya a k'ofar gidan Rahma ta fito daga gaban motar Anas ya fito shima yana yi mata magana kafin Rahma ta shiga ciki ta barshi a wajan a tsaye. A tare Rauda da Asad suka kalli juna ta sake kallon Anas da yake taaye ta sauke numfashi kafin tace, "Ka Buɗe min motar zan shiga gida." In motar da suke ciki ta amsa tabbas shima ya amsa yayi mata bama ita yake kallo ba wani wajan yake kallo zuciyar sa kamar ana bulbula mata kalanzir ganin Anas a tsaye a k'ofar gidan su. Kamar tayi kuka sabida takaici tace, "Ka buɗe min." Nan ma yyi mata banza ta kalle shi idanun ta ya taru da hawaye amma bama ita yake kallo gabad'aya. Itama banza tayi ta juya hawaye ya sakko mata ta girgiza kai tana cize bakin ta dan tasan babu abinda zata iya, kusan minti biyu suna a haka kafin ta juyo ta kalle shi tace, "Ka bud'e zan shiga gida bacci nake ji" ta fad'a cikin muryar kuka tana kallon sa. Juyowa yayi ya kalle ta ya d'aga gira sama ya tab'e bakin sa ya sake mayar da kallon sa ga wajen gidan. Ganin kiran mai martaba yana shigowa ya saka shi kallon ta yace, "In kika sake kika kula wancan sai ranki ya b'aci" ya fad'a yana danna lock d'in ya buɗe ta fita daga motar bayan ta d'auki ledar kayan ta. Yana kallon ta har taje kusa da Anas d'in sai yaga tayi saurin shiga gida bata tsaya ba sai a sannan ya d'auke ido daga kan gidan Suhail ya shigo suka tafi bai san itama bata son had'a ido dashi dan kunyar sa take ji. Akan hanyar su ta tafiya Suhail yace, "Ranka ya dad'e zan iya magana?." "Uhum" ya furta yana danna wayar sa. Suhail yace, "ayi haƙuri zan shiga abinda bai shafe ni ba, amma ranka ya dad'e bai kamata a dinga barin fulani tana fita ita kad'ai ba, akwai tarin mak'iyan da suke nufin kawo mata hari ko a mutanen gari y'an unguwa akwai wanda baya qaunar ta yake neman hanyar cutar da ita, barin ta tana fita ita kad'ai akwai matsala. Allah ya taimake ka bawai zan koyawa mai martaba abinda zaiyi bane amma yana dakyau ace tana da personal driver wanda aka amince dashi before ta dawo gidan sarauta." Asad yana jinsa yasan kuma gaskiya ya fad'a ya girgiza kansa alamun gamsuwa amma baiyi magana ba daga nan bai sake mgana ba shima ba suka cigaba da tafiya.         A b'angaren Rauda rai a b'ace ta shiga falon Umma ta samu Rahma a zaune suna gaisawa da Umma ganin ta sai ta d'an saki rai Rahma ta mik'e ta rungume ta tana dariya tace, "Yanzu nake tambayar ki, duk da fushi nake dake Anty Rauda har yanzu baki je inda nake ba." Rauda tayi murmushi tace, "Banda son wayo Rahma ina ke ina fitowa yanzu?." Umma tace, "Nima haka nace Rauda, amma dai baki kyauta ba da baki je ba." Rauda ta zauna kafin tace, "Allah zan zo." Rahma tace, "to ya zanyi ina nan ina jira, bara na shiga wajan Inna" ta fad'a tana fita Rauda ta bita da kallo ganin tayi haske har kib'a tayi ta juyo da kallon ta ga Umma da itama ita take kallo. Umma tace, "Ina kika je kika dad'e haka daga rakiya?." Rauda ta fito da ledar gefen ta tace, "Wallahi masu kayan marmari na gani a gefen titi na tsaya na siya" ta fad'a tana d'auki apple guda d'aya ta fara ci. Umma tace, "bakya jin magana Rauda, ina ke ina tsayawa akan titi kina siyayya? Kin manta matsayin da Allah ya baki? Ko kin manta abubuwan da aka fad'a a gaban ki ke kanki kin san baki wuce a nemi kashe ki a wannan yanayin ba." Rauda ta sauke numfashi tace, "sha'awa suka bani wallahi shiyasa na tsaya." Umma tace, "Wannan ba inda zaki dinga tsayawa siyayya bane malama, ki nutsu ki fuskanci abinda yake tankaro ki domin kuwa jibi ake zancen komawar ki gidan sarautar." Rauda ta tsaya da cin apple din da take yi ta wara ido waje tace, "Wacce jibin Umma?." Umma tace, "Juma'a." Rauda ta dafe k'irji tace, "Kuma Umma sai kuka amince?." Umma ta bita da kallo tace, "to sai muce A'a? Daman ba ranar muke jira tazo ba ki koma gidan ki kema a daina miki kallon bazawara?." Rauda idon ta ya ciko da hawaye tace, "Amma Umma jibi yayi kusa, kamar wata y'ar tsana za'a ce wani jibi zan koma." Umma ta bita da kallo kafin tace, "ke zmaan gidan bai ishe ki ba Rauda?." Tayi shiru ta sunkuyar da kanta k'asa Umma tace, "in ke bai ishe ki ba ni ya ishe ni Rauda, bawai don bana sonki ba sai dan kin wuce zaman gida zaman gidan miji shine ya dace dake. A unguwa da y'an uwa ana ta yawo dake a baki bakya jin tsoron bakin mutane?." "Wanda suka san shi mijin kine sun sani domin ni babu wanda zan fad'awa komawar ki daga ke sai y'an uwan ki ayi komai a gama Allah yasa kin shiga a sa'a ya d'ora ki akan dukkan maqiyan ki dana mijin ki ya baku zaman lafiya mai d'orewa." Rauda ta sauke numfashi bata ce komai ba ta tashi ta shiga d'aki ta bar kayan marmarin a wajan dan ji tayi sun fita daga ranta. D'aki ta shiga ta cire hijjabin jikinta ta cillar tace, "Aikin banza, bai san nima haushin sa nake ji ba zai dinga wulaƙanta ni shi a lallai ga shugaban al'umma. Aikin banza ni gabad'aya haushi yake bani ya cika nuna isa." Zama tayi a gefen gadon tana tunani kafin taja tsaki ta tashi ta shiga band'aki ranta duk a jagule. *☆☆*          B'angaren Asad lokacin da ya koma a fusace yake bayan ya kammala shirin sa na kwanciya yana zaune yana aikin jan tsaki zuciyar sa cike take da b'acin ran abinda ta aikata. 'Ta tsaya a kan titi tana siyayya kamar wata namiji, anyi mata magana kuma ta yiwa mutane banza da yake bata da kunya, da ace ta yiwa wannan banza magana da sai na b'ata mata rai sai tayi dana sanin kula shi din da tayi' abinda yakr fad'a kenan a zuciyar sa cikin fad'a. "Aikin banza" ya furta a bayyane yana jan tsaki gabad'aya ransa a b'ace yake a haka ya kwanta zuciyar sa babu dad'i yana ta fad'an sa shi kad'ai. Bayan kwana biyu. Tun daga bakin gate d'in masarautar ta zaka san ana gagari min biki domin tambari ne yake tashi da busa algaita da abubuwa masu dad'i. Duk da babu jama'a da yawa a gidan amma kana ganin kasan akwai abinda ake gabatarwa a cikin sa. Da yamma aka tura da babbar mota da jiniya aka d'auko Rauda daga gidan su zuwa gidan sarauta bayan tasha adon lalle da duk abinda ake yiwa amarya an mata itama y'an uwanta suka rako ta zuwa gidan. Babu b'angaren da ba'a kaita ba har na Mama duk da bata nan amma y'an uwanta sun zo tarbar Rauda cikin mutunci da girmamawa suka karb'e ta kafin a zaga da ita ko ina daga baya aka kaita b'angaren da ya kasance nata. A wannan lokacin jakadiyar ta mai suna Samira da bayin ta da komai suka gabata a gaban ta ita dai bata yi musu ba sai Yaya Ummi ce ta sallame su suka tafi itama kafin su barta dukkan su su watse suka barta ita kad'ai tana kuka kamar yarinya k'arama. Sai da akayi sallar i'sha tana zaune a gefen gadon da ya kasance nata bayan ta idar da sallar i'sha akayi sallama a k'ofar d'akin tare da fad'in, "Barka da hutawa ranki ya dad'e." Rauda ta kalle ta dan ita bata saba da irin wannan maganar ba hakan ya saka tace, "Barka." "Fulani Hajiya ce ta aiko ni da kanta domin na raka Fulani b'angaren mai martaba." Rauda ta sauke numfashi kamar tace bazata je ba sai ta d'aga kai tace, "ki jira ni ina zuwa." Jiki na rawa ta mik'e ta fita Rauda tafi minti biyu bata tashi ba kafin ta tashi tayi wanka ta saka kaya da dogon hijjabi ta bata umarnin ta shigo. Jiki na rawa ta shigo ta k'araso da sauri ta tsaya a bayan ta Rauda ta kalle ta tace, "Kece zakiyi gaba ai ni da ban san wajan ba." Hadimar tace, "Wane mutum, ranki ya dad'e ni wacece da zaki bi bayana? Sai dai ni na biyo naki bayan." A guje ta zabura ta kwasowa Rauda takalmi ta skaa mata da kanta sannan tace, "Ranki ya dad'e zamu iya tafiya?." Gaba kawai Rauda tayi ta biyo bayan ta suka fito harabar b'angaren Rauda ta nan suka shiga wata k'ofa sai gasu sun bayyana a harabar b'angaren Asad d'in sai da ta rakata har bakin falon sannan ta zube a k'asa tace, "A fito lafiya ranki ya dad'e." Da amin Rauda ta amsa duk tana jinta wani iri domin bata saba wad'annan abubuwan ba mace ta haife ta ta dinga zube mata a k'asa. Kai tsaye falon ta shiga babu kowa ta tsaya tana k'are masa kallo in akace had'uwa to falon ya had'u carpet d'in kamar jikin mage, numfashi ta sauke tace, "Ko ina zan bi kuma oho." Tayi k'aramin tsaki ranta sai taji ya sake b'aci haka kawai komai ya dagule mata ta rasa ma abinda zatayi. Ciki ta sake shiga ta sake ganin wani falon amma bai kai wancan girma ba amma shima babba ne akwai kyau duka hotunan Asad d'in a manne a jikin sa dana mahaifin sa, stair d'in ta gani kai tsaye ta nufe su ta fara takawa zuwa saman ba tare da tsoron komai ba. Wani falon ta sake shiga mara kayan da yawa amma ya tsaru shima a nan hoton  mahaifin sa da dukkan su har Mama yake a manne baza ka gane shi a jikin hoton ba domin kaya iri d'aya ne a jikin su. Kai ta d'auke daga kan hoton ta kalli hanyar d'akunan kamar bazata shiga ba sai kuma kai tsaye ta nufi d'akin farko ta buɗe, girman d'akin ya bata tsoro domin gadon kamar ba'a saka ba gashi tafkeke a tsakiyar d'akin amma kamar babu sabida girman d'akin, har zata kulle sai ta hango hoton ta a kan bedside drawer wanda aka d'auka lokacin da suna Cairo. Fita tayi daga d'akin ta dawo falon ta zauna tayi shiru domin ta tabbatar baya nan sai ranta ya sake b'aci haushin sa ya ninku a zuciyar ta tayi shiru ta rasa abinda zatayi.           A b'angare Asad sun fita shida mahaifin sa da Suhail da kuma Uncle kai tsaye wajan Mama suka wuce suka same ta tana nan dai yadda take sai Suhaima da taji sauk'i sosai jikin ta ya warware. Tun shigowar su Suhaima ta mik'e tsaye security d'in da take kula dasu ta fita mai martaba ya kalli Suhaima yace, "Autar Mama ya jikin naki?." Sai kawai ta fashe da kuka tana fad'in, "Abba jikin Mama baya sauk'i ko kad'an." "Waye yace miki baya sauk'i? Kira mana likitan muji." Ba musu ta fita sai gata da likita sun dawo ya gaishe su gaisuwar girmamawa kafin ya mai martaba yace, "Wanne cigaba aka samu akan ciwon nata?." Dr yace, "an samu cigaba a da bp ta baya sauka amma yanzu ya sauka ya dawo normal jiran farkawar ta kawai yake yi." Asad yace, "bugun zuciyar fa?." Dr yace, "Shima ya ragu amma bai dawo daidai ba har yanzu, amma in sha Allah daga yau zuwa gobe zata iya farkawa." Asad ya k'arasa kusa da ita yana yi mata addu'a har lokacin da oxygen a hancin ta, a wannan lokacin k'annen ta suka shigo mata su biyu ganin su mai martaba suka gaishe shi yace, "Ya mai jikin?." Ta kalli Mama kafin tace, "Alhamdulillah gata nan a kwance." Ta kalli Suhaima tace, "Suhaima ki tafi tare da Antyn ki kije gidan ta ki huta zan zauna da Maman a nan in yaso gobe sai ki dawo kema baki da lafiya." Fuska ta kwab'e zata musa Asad yace, "Ki tafi." Dole tayi shiru bata ce komai ba a nan su Asad suka bar su suka fita kai tsaye mai martaba yace su wuce asibitin da Waziri yake. Shima yana kwance har lokacin bai farfad'o ba suka yiwa iyalan sa ya mai jiki da addu'ar samun lafiya, har zasu juya su fita matar sa tace, "Allah yaja zamanin mai martaba daman ina so zan kawo k'ara." Abba yace, "To k'ara wacce iri?." Tace, "Akan sane ina so a bi min hakkina dana y'ay'ana sakamakon kashe su d'in da yayi, bazan bar maganar nan ba shiyasa nace zan sanar dakai ko na kai k'ara human right." Kai Mai martaba ya girgiza kafin yace, "Ya kashe miki y'ay'a kamar ya kenan?." Tace, "Ta son zuciyar sa da neman duniyar sa mana, ya karb'o abu dan ya ksshe wani ya k'are a kan y'ay'ana ni kuma wallahi bazan yarda ba." "Shikenan ki jira ya samu lafiya sai ayi maganar gabad'aya, banda batun kai k'ara zamuyi maganin matsalar da kan mu." "Na gode Allah ya k'ara girma ya k'ara lafiya" suka amsa da amin kafin su sake fitowa suka shiga mota amma babu wanda yake cewa kanzil.          A can gidan lokaci d'aya wutar gidan ta d'auke duhu ya mamaye ko ina aka rasa daga inda matsalar take, Rauda na zaune taga haske ya d'auke duhu sosai ya mamaye inda take sai tsoro ya shige ta hannu na rawa ta kunna hasken wayar ta amma kamar bata kunna ba iya inda take kawai take ganin hasken. Motsi ta dinga ji a bayanta gabanta yayi mugun fad'uwa ta kasa juyowa balle jira take kawai taji an shake ta ta baya. "Hiii Gambia Rauda!" Aka fad'a daga bayan ta ana dawowa ta gaban ta. Wayar hannun ta ta sub'uce ta fad'i k'asa jikinta ya soma rawa har lokacin bata kalli waye ba. Dariya yayi sosai ya kunna tashi fitirar ya haske kansa yace, "K'anin mijin kine Hydar, kar kiji tsoro." Maimakon tsoron ya ragu sai ya sake k'aruwa jikinta ya cigaba da rawa tana kallon sa amma bata iya cewa komai. Yace, "Zauna ki nutsu magana nazo muyi dake ta fahimta, zauna" ya fad'a yana zama shima dole itama ta zauna tana kallon sa. "Magana ce nazo muyi dake ta fahimta wacce zaki tsira mijin ki ma ya tsira. Ba zama nazo yi ba balle surutu magana nake so muyi guda biyu ko nace zab'i ne zan baki guda biyu ko guda uku wanda kika amince dashi zamuyi amfani. Na farko ga magani yanzu ki karb'a Kisha a gabana cikin jikin ki ya fita, na biyu ko ki amince dani a wannan daren mu kasance da juna nida ke, na uku ko na kashe mijin ki. D'auki d'aya a ciki da sauri ba b'ata lokaci nazo yi ba." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Shine abinda Rauda take fad'a kenan jikinta yana rawa zuciyar ta na bugawa sosai ta zuba masa ido ta rasa abinda zata yi. Jin tayi shiru ya skaa shi daka mata tsawa yace, "Baki ji me nace bane?!." Ta sake firgita tace, "Naji" murya tana rawa sosai. Yace, "iskanci ne ya saka kika yi min banza kenan? Babu wanda zai kwace ki a yanzu domin dukkan su basa nan zan iya yin duk abinda nake so dake a yanzu kuma kisha maganin ta k'arfi kuma na kashe mijin naki babu abinda kika isa kiyi. Na baki zab'i ne dan kawai ina ganin mutuncin ki amma in kina ganin baza ki zab'a ba..." ya fad'a yana tasowa yayo kanta ta zabura ta mik'e tayi baya tace, "Zan zab'a! Wallahi zan zab'a ka tsaya." Kuka take yi tana maganar ya tsaya yace, "Ina jinki." Tace, "bani maganin zan sha, amma kayi min alƙawarin in nasha zaka kyale mu." Hannu ya wara kafin yana kallon ta ta hasken fitilar wayar ya mik'a mata tablet d'in da ruwa a k'aramar jarka hannunta yana rawa ta b'alla amma ta kasa sha sai kuka da take yi. Hannu taga ya mik'o zai jata jikin sa bata san lokacin da ta cilla maganin bakin ta ba ta kafa kai tana shan ruwan a haukace a daidai lokacin motar su Asad ta shigo cikin gidan. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *087.*          Kamar walqiya sai ta neme shi ta rasa nan take haske ya mamaye d'akin duk ta jiqe da gumi sai numfashi take saukewa k'irjin ta yana sama da k'asa ruwa duk ya zubar mata a jikinta. A kan carpet ta zauna ta cure waje d'aya tana sauke numfashi tsoro yaka sake mamaye mata zuciya. Motar su Asad tana tsayawa haske ya mamaye gidan Uncle yace, "Da me ya samu wutar gidan haka?." Babu wanda ya amsa Mai martaba ya kalli Asad yace, "to sai da safe bance ka biyo ni duba Aliyu ba." Amsawa yayi cikin gamsuwa Suhail ya raka shi har b'angaren sa. Kallon Suhail yayi sai yaga yana ta murmushi ya kalle shi yace, "Murmushin na meye?." Suhail ya sosa kai yace, "A'a ranka ya dad'e wani abun na tuna." Asad yayi k'aramar dariya ya kawar da kansa yana jinjina kai kafin yace, "Fad'a min as your friend." Suhail ya kalle shi sai ya sauke kai k'asa yace, "Ranka ya dad'e wannan labarin baya ne ni yanzu ko iya kallo fuskar mai martaba ma bana iyawa." Asad ya murmusa ya shiga ciki Suhail ya juya ya fita. Kai tsaye saman ya hau dan shi yama manta an kawo Rauda gidan hankalin sa yana wajan Mama yana hawa ya hango mutum a cure a waje d'aya sai gaban sa ya fad'i ya tako ya k'araso wajan yaga robar ruwa a wajan a yar ga tablet na magani a kwali ya kalli inda take amma baiyi magana ba. Jin motsi ya saka Rauda d'agowa ganin sa ya saka ta zabura ta mik'e ta k'araso inda yake ta rugume shi sosai tana kuka cikin tsoro har lokacin jikinta rawa yake yi. Hankalin sa ya tashi ganin yadda take hakan ya tabbatar masa akwai abinda ya faru ya d'ago ta daga jikin sa ya rik'e ta yana kallon fuskar ta da ta jiqe da hawaye yace, "Lafiya kike?." Numfashin ta sama da k'asa yake yi bakinta yana rawa tace, "Hydar! Hydar ne yazo nan, tsoro nake ji" ta sake fad'a tana sake komawa jikinsa jin abinda ta fad'a sai ya rik'e ta sosai hankalin sa kai k'arshe wajan tashi burin sa yaji abinda ya faru. Zaunar da ita yayi a kan kujera yana kallon fuskar ta yayi mata alama da kansa meya faru, muryar ta har lokacin rawa take tace, "Yazo nan bayan an kashe hasken gidan" ta tsaya tana jan numfashi a hankali ya furta, "Nutsu ina tare dake" ya fad'a yana goge mata hawayen fuskar ta ta rik'e hannun sa k'am tana kallon hanya tace, "Yazo nan! Yazo wallahi na ganshi." Ganin a rud'e take har lokacin akwai tsoro a tare da ita sai ya d'auki wayar sa da hannu d'aya ya rubutawa Suhail message ya sanar dashi Hydar yana gidan a tabbatar an nemo shi kafin safiya, ajjiye wayar yayi ya sake rik'e hannunta yana kallon ta sai hawaye take yi. "Ya bani wancan maganin yace in ban sha ba sai ya kashe ka!" Ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Dumm k'irjin Asad ya buya ya d'auki kwalin maganin  yaga sunan sa nan take ya d'auki wayar sa ya shiga Google yana duba maganin na meye abinda ya gani ya saka shi firgita yace, "Kin sha?." Kai ta d'aga masa alamun eh tana kuka, ya sauke numfashi mai tsaho ya furta, "Why!." Muryar ta na rawa tace, "Yace dole na zab'i d'aya ko na sha ko ya kashe ka ko yayi min fyad'e, dak'yar na gudu yana so ya tab'a niiii" ta fad'a tana sake fashewa da kuka ya rungume ta sosai a jikin sa zuciya sa na wani irin bugu mai k'arfin gaske. "I'm sorry naje wajan Mama ne" ya fad'a yana shafa bayan ta gagarumin tashin hankali yana sake mamaye masa zuciya musamman da ta ambaci fyad'e ji yake kamar ana soka masa mashi a zuciyar sa sabida bala'in kishi da zafin da yake ji a ciki. Tashi yayi zai fita tayi saurin rik'e shi ya dawo ya zauna tace, "Kar ka barni ni kad'ai zai dawo, tsoro nake ji dan Allah kar ka fita." Komawa yayi ya zauna ya sake rik'e ta a jikin sa hankalin sa yakai mak'ura wajan tashi haka zalika ransa yakai k'ololuwar b'aci so yake yaje ya samu masu tsaron wajan su fad'a masa aikin me sukayi har da za'a shigo b'angaren sa har saman sa matsayin sa na shugaba babu wanda ya sani. Hannun sa ya d'ora a kan cikin ta ya runtse ido har lokacin kuka take yi tana jikin sa yace, "Meyasa kika sha? Meyasa baki amince an kashe ni d'in ba?. Tashi mu tafi asibiti." Kai take girgizawa amma batayi magana ba sai daga baya tace, "Bazan iya ba, bazan iya bashi kaina ba, bazan iya gani an kashe ka ba, gwara cikin ya zube" ta sake fad'a tana kuka sosai. Bayan ta yake bubbugawa alamun rarrashi duk da har lokacin haushin ta yake ji amma bazai barta cikin wannan hali bai rarrashe ta ba babban tashin hankalin sa Hydar dan yasan zai dawo kuma wajan ta zaizo ba wajan shi ba. Tablet d'in ta buɗe a hannunta tace, "Ban sha ba, ya d'auka nasha a lokacin hankalin sa ya tashi yaji ana buɗe gate alamun kun dawo sai na neme shi na rasa." Tablet d'in ya d'auke daga hannun ta ya mik'ar da ita tsaye tak'i barin jikin sa har lokacin ya kaita d'akin sa ya zare hijjabin jikinta ya ajjiye a gefe ya kwantar da ita yace, "Ki huta." Zai fita ta sake rik'e shi tana girgiza masa kai ya sauke numfashi dole ya zauna a gefen ta tana rik'e da hannun sa tana sauke numfashi alamun taci kuka ta k'oshi. Wayar sace tayi k'ara ganin sunan mahaifinsa ya saka shi ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Asad da gaske Hydar yana gidan nan?." Asad ya girgiza kai kawai kamar yana gaban sa dan bazai iya magana ba b'acin ran da yake ji a zuciyar ba bazai barshi magana ba. Jin yayi shiru Abba ya sake cewa, "Kayi magana Suhail ya sanar dani kace a bincika yana nan, kenan shine ya saka aka kashe wutar gidan?." Asad ya sauke numfashi yace, "Abba yazo har wajan ta." Jin yadda maganar Asad d'in ta fita yasan akwai tarin b'acin rai a tare dashi alamun wani abun ya faru Abba yace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma dai lafiya ko?." Asad yayi shiru yana runtse idanun sa ya kalle ta yaga itama shi take kallo ya d'auke kansa yana girgiza kai kana kallon sa kasan ransa b'ace yake. Jin bai amsa ba ya saka Abba yace, "In zaka iya sauko kasa Uncle ka zai zo kuyi maganar sabida a san abinda za'ayi kar abun yayi nisa." Datse kiran Asad yayi ya mik'e zai fita ta kwab'e fuska tana kallon sa tare da girgiza kanta ya zauna ya dafa goshin ta yana kallon ta amma baice komai ba kafin ya zame hannun sa ya tashi ya fita. K'asa ya sakko tun daga nesa da Uncle da Suhail suka hango shi suka san ran maza ya b'aci domin kuwa fuskar sa har ja tayi sabida b'acin rai annuri kona sisi babu akan fuskar sa yana k'arasowa ya kalli Suhail yace, "An same shi?." Suhail ya tsorata da yanayin Asad yaja baya yace, "ranka ya dad'e an duba ko ina amma ba'a samu Hydar a gidan nan." "Meye amfanin ma'aikatan gidan nan har da Hydar zai shigo har nan har sama babu wanda zai ganshi? Meye aikin su?" Ya fad'a cikin fad'a sosai yana kallon Suhail har sai da ya tsorata dan bai tab'a jin muryar sa da amo haka ba. Suhail yace, "Allah ya wuci zuciyar ka ranka ya dad'e tuba nake, dukkan su hankalin su ya tafi tunanin abinda ya d'auke wutar gidan a yadda akayi bincike an tabbatar shine ya kashe wutar gidan." Uncle da yake kallon Asad yanayin b'acin ransa ya tabbatar da an yiwa matar sa wani abun ya kalli Suhail yace, "Meya amfanin cameras gidan din gidan nan da aka saka? Meyasa basu mayar d ahankali wajan kula da duk wanda zai shigo gidan ba?." Asad ya murza yatsun sa na tsakiya da babba suka bada sauti ya kalli Suhail yace, "Aje a duba a tabbatar an gano ta hanyar da ya shigo nan" yana fad'a ya juya ya koma Suhail ya fita ya kalli Uncle yace, "Gaskiya akwai abinda ya faru da ya b'ata ran mai martaba haka, dole a nemo inda Hydar yake nan gaba ba'a san me zaiyi ba." Uncle yace, "Ya kamata." Asad lokacin da ya ya same ta a tsaye a falon ta kasa nutsuwa ganin sa ya saka hankalin ta ya kwanta ya rik'e hannun ta suka koma ta kwanta ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa ya cize bakin sa. Ya jima a haka kafin ya dawo nutsuwar sa yace, "Ki nutsu babu abinda zai faru." Kai ta girgiza yana zaune a gefen ta har bacci ya d'auke ta ya d'auki waya ya fita yana neman Suhail. A daren sai da aka tabbatar da ta inda Hydar ya shiga b'angaren sa da ta inda ya fita sannan hankalin sa ya kwanta aka tara meeting na ma'aikatan duk a dare aka yiwa kowa warning akan kula da aikin sa duk suka amsa da zasu dage Suhail ya sanar dashi sai a lokacin yake jin nutsuwa a zuciyar sa. Yana zaune bayan sun gama waya da Suhail kawai yaga kiran Hydar yana shigowa ba tare da tunanin komai ba ya d'auka ya saka a speaker kafin yayi magana Hydar yace, "To dan ka saka an nemo ta inda na shiga apartment d'inka ai ba wani abu bane mai wahala, ka sani masu tsaron ka ina da yaran da in nazo zan shiga zasu bar wajan suyi kamar wani aikin ne ya taso musu. Ina da mutane da yawa a gidan nan ko me naso yi zanyi lafiya lau babu damuwa." Asad baiyi magana ba hakan ya saka ya kuma cewa, "Na samu matar taka ai a zab'in da na bata na d'auka zata ce a kashe kane sai naji gwara ta bar babyn ta ya salwanta da dai kai ka bar duniya, amma fa naso ta amince dani mun kasance yau d'in nan kasan ance mace mai k'aramin ciki sirri gare ta" sai ya kyalkyale da dariya yace, "Kwantar da hankalin ka ko hannunta ban rik'e ba tunda dai tasha maganin shine burina, zan juyo kanka daga baya." Asad ya runtse ido ya buɗe murya a kausashe yace, "Ka kiyayi had'uwar mu Hydar!" yana fad'a ya yanke wayar ya cillar akan kujera ya dafe kai da duka hannayen sa. Bai jima a haka ba ya tashi ya shiga d'akin yayi wanka ya saka kaya ya kwanta a gefen ta amma ko kad'an bacci yak'i zuwa idanun sa sabida b'acin rai, tsaki yayi ya d'aura alwala ya tayar da sallah. Washe gari da wuri Rauda ta bar b'angaren ta koma nata dan ita take son dinga yi masa abinci ba ma'aikata ba, duk da akwai kitchen a saman nasa amma bata tsaya yi a can ba ta sauko k'asa. Da kanta tayi duk abinda ya kamata sannan ta saka aka d'auka suka tafi tare aka kai har lokacin bai fito ba kasancewar asabar ce babu zaman fada. Hadimar ce ta koma ita kuma ta tuna wayar ta na saman sai ta hau saman da sallama ta shiga falon ya amsa ta ganshi a zaune amma bai kalle ta ba, k'arasowa tayi ta zauna tace, "Barka da rana." Kai kawai ya d'aga mata ta tab'e baki ta duba wajan da wayar ta fad'i ta hango ta a can k'arshen kujera har chajin ya k'are saboda fitila da take a kunne tama manta ita. Kallon sa tayi taga ya wani d'aure fuska yana zaune da manyan kaya kansa babu hula yana ta aikin kad'a k'afa ya d'ora d'aya kan d'aya, "Breakfast yana k'asa" ta fad'a tana niyar mik'ewa kallon da yayi mata ya saka ta fasa tashin ta koma ta zauna ta kawar da kanta gefe itama ta d'aure fuska ta fara kad'a tata k'afar. Sai ta bashi dariya ma amma baiyi ba ya danne ganin yadda ta wani basar ta d'aure fuska itama ya jinjina kai yana girmama k'arfin hali irin na mace, in ba ita ba waye yana zaune a kan kujera zai zauna? Waye zai wani d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa a gaban sa?, lallai ba'a yiwa mace mulki in taso nata mulkin sai yafi na ko wanne shugaba. D'auke kai yayi daga kallon ta ganin yayi mata banza ya skaa ta kalle shi taga bama ita yake kallo ba waya yake dannawa suna chart da son MD d'in sa na company akan sabon aikin da suka samu. "Ina da abin yi fa" ta fad'a ba tare da ta kalle shi ba. Sarai ya jita sai yayi kamar ma baiji ba ta sake cewa, "Ina da bak'i ni zan tafi." Kallon ta yayi sai ya d'auke kansa daga kallon ta ya sake yi mata banza. Ganin hakan kawai sai ta mik'e zata bar wajan taji yace, "Dawo." Sai ta fara yi mata dara tana buga k'afa a k'asa kamar zatayi kuka tana cewa, "Nace maka ina da bak'i kana ji kuma ina magana kayi banza dani." Nan ma banza yayi mata kafin ya d'ago ya kalle ta ya hard'e hannu a k'irji ya juya kansa yana k'are mata kallo kafin ya mata alama da hannu taje. K'aramar harara ta sakar masa yana kallon ta ta juya ta sauka shi kuma yayi dariya kad'an dan ta bashi dariyar sosai. Tunda ta bar wajan sa basu sake had'uwa ba tana wajanta tana ta amsar bak'i daga waje daban-daban na gidan har Habiba da Walida kawayen ta yadda suke mata sai ta dinga jin nauyin su. Waya sukayi da Umma take ce mata taje ta duba Mama kar abinda ya faru a baya yayi tasiri a zuciyar ta duk abinda zatayi ta dinga tuna Asad d'in. ta gamsu da abinda Umma tace bayan sun gama waya ta kira number Asad, bai d'auka ba har ta katse bata sake kira ba ta ajjiye wayar. Kusan mintina ashirin da kiran ya kirata ta d'auka ta saka a kunne tayi sallama bata jira ya amsa bama tace, "Ammmmm daman ina so naje duba Mama ne." Shiru yayi kamar bai ji ba itama tayi shiru dan tasan yana jinta sai da aka d'auki lokaci sannan yace, "Suhail zai kaiki" yana fad'a ya datse kiran tabi wayar da kallo tana harara kamar shi take harara. Ba jimawa hadimar ta ta shigo ta sanar da ita zuwan Suhail ta bada umarnin ya shigo ya shigo yana fad'in, "Allah yaja da ran Fulani." Dariya kawai tayi dan bawai ta iya wad'annan abubuwan bane tace, "na taso ne?." Suhail yace, "zamu iya tafiya." Ita da Jakadiyar ta suka tafi Suhail yaja motar suka je asibitin har lokacin Mama bata farka ba taga jikinta suka gaisa da Suhaima da kannen Maman kafin ta dawo gida dan da fitar da dawowar ba'a yi mintina talatin ba. Da daddare Hydar ya kaiwa Mama ziyara a lokacin babu kowa a wajanta sai security ya shiga har gaban gadon da take kwance ya zauna yana kallon ta kafin yace, "Mama nasan wataƙila kina jin abinda zance; nazo dan naga lafiyar ki na kuma shaida miki abubuwan da suke raina." "Wato Mama nasan kaf cikin y'ay'an ki kinfi sona tabbas nasan da wannan amma kinfi nuna k'aunar Asad a kaina tunda shi kike yiwa burin zama shugaba bamu ba, baki tab'a tunanin hakan zai k'ona mana rai zai kuma iya sakawa mu dauki mataki ba, kawai abinda yake zuciyar ki kike fito dashi bakya duba da yanayin da hakan zai jefa mu tunda muma jinin sarauta ne. Kullum zancen ki Asad ya mulki garin nan ko kara baki tab'a yi mana ba shin mu babu jinin sarautar a jikin mu ne? Ko kuma Asad ne kawai ya gaji sarauta banda mu?." "Mama a duk sanda kika fad'i haka ina jin kamar na bawa Asad guba yasha ya mutu sabida banbancin da kike nunawa k'arara a kanmu, bakya tunanin komai sai shi kawai bayan muma y'ay'an kine muna da hakki a kanki ko sau d'aya ki ambace mu dukkan mu babu wanda baya son sarautar amma maganar d'aya ce kullum Asad!" Ya fad'a cikin fusata yana dafa gadon da take kai kafin ya cigaba da fad'in, "Na shirya abubuwa da yawa akan ganin bayan duk wanda zai hanani mulkar garin nan koda kece Mama, ina nan akan baka ta duk abubuwan dana shirya a baya baza su zama a banza ba sai na aiwatar da kudurina. Jiya na bawa matar Asad maganin zubar da ciki amma na fahimci tayi min wayo ne bata sha maganain ba to ai in tasan wata bata san wata ba zanyi maganin ta cikin k'aramin lokaci." "Mama ban hak'ura da mulkin nan ba ina nan ina shirin yadda zan ga bayan Asad da mijin ki, koda kece zan iya ganin bayan ki a duk sanda naso indai burina zai cika. Kiyi haƙuri Mama amma bazan iya hakura ba sai na tabbatar da burina ya cika hankalin kowa zai kwanta. Ina baki hak'uri in kika farka kika samu bak'in labari ba laifina bane laifin kine." Buɗe k'ofa akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo yaga Suhaima ce kawai sai ya mik'e ya fita bai mata magana ba a daidai lokacin da Mama ta fara wani irin numfashi k'irjin ta yana sama da k'asa. Hankalin Suhaima ya tashi ta fita a guje suka dawo da likita aka yiwa Mama allura  amma har lokacin numfashin baiyi daidai ba dak'yar aka samu numfashin ya tsaya tana kuka ta kira number Asad ta sanar dashi halin da ake ciki. A daren suka fito shida Suhail suka tawo hankalin sa a tashe, lokacin da suka zo ta koma bacci likita yake sanar dasu an fad'a mata maganar da ta tayar mata da hankali ne shiyasa hakan ta kasance in aka cigaba da hakan kuma zuciyar ta zata iya bugawa. Nan take Asad ya saka dokar ko waye kar a sake barin sa ya shiga sai Suhaima kawai da kannen Mama in basu ba kar a sake barin wani yazo inda take. Ransa a b'ace ya koma gida yaga Rauda a saman sa ko ta kanta baibi ba ya wuce itama bai isheta kallo ba balle ta kalle shi ta tab'e baki ta cigaba da hira da Yaya Ummi a wayar ta domin tayi alwashin nuna masa itama fa bazata d'auki wulak'anci ba sai dai duk abinda zai faru ya faru. Bayan kwana biyu. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *088*         Cikin ikon Allah a cikin kwanakin duk wani abu da Aliyu ya b'ata da ya shafi masarauta Asad ya gyara shi da taimakon Abba, duk wata sadaqa da aka daina yanzu an dawo da ita komai yana tafiya bisa tsari Asad yna k'okari ganin komai ya tafi bisa tsarin addinin musulunci. Ma'aikatan gidan su kansu sun san an samu canji sosai kowa farin ciki yake yi don sakaqa da taimako ya dawo. A cikin kwanakin Rauda da Asad babu abinda yake had'a su magana ba sai anga dama tun tana zuwa ma b'angaren sa har ta share ta daina daman sabida mutane take yin wani abun to ta gaji da wulaƙancin itama ta watsar dashi sai a kwana a wuni ma a sake tashi basu had'u dashi ba balle magana. Jikin Mama yayi sauk'i sosai duk da batayi magana ba tunda ta farka amma jikinta ya warware sosai sai dai an kafa mata sharud'a akan ahiga damuwa da yawan tunani. A ranar da ta kasance ranar laraba da safe aka sallamo Mama ta dawo b'angaren ta bayan an gyara mata b'angaren nata. Tun safe ake karb'ar bak'i amma har lokacin batayi magana ba Asad kawai take son gani amma shiru bai shigo ba duk ta damu. Shi kam bayan an tashi daga zaman fada kai tsaye wajan ta yayo tunda aka hango shi aka fara bada hanya ana kirari sosai saman sa da lema har ya k'araso k'ofar falon Mama. Sauke Lemar akayi ya shiga ciki su kuma duk suka tsaya a waje ya shiga ya same ta zaune ita da k'annen ta mata biyu wanda suke wajan ta. Tunda yayi sallama ta mik'e har ya k'araso ya tsuguna a k'asa yace, "Barka da dawowa Mama." Sai a sannan bakin ta ya buɗe bakin ta yana rawa tace, "Asad!." Kowa yayi mamakin jin maganar ta farin ciki ya cika zuciyar su har lokacin bai tashi ba. Zama tayi akan kujera shi kuma ya zauna a k'asa kusa da ita tana ta kallon sa kafin ta fashe da kuka. Hankalin Asad ya tashi ya kalle ta yana kallon fuskar ta yace, "Zubar da hawaye bai kamaci mahaifiyata ba, dan Allah Mama ta daina kuka nima hakan yana cutar dani." Mama ta dinga kuka kafin ta share hawayen ta ta kalle shi tace, "Asad kayi haƙuri." Kai ya dafe yana kallon ta kamar zaiyi kukan shima yace, "Subahanallah! Dan Allah mamana ta daina furta wannan kalmar dan Allah" ya fad'a yana dafe kansa da yake sarawa. Mama tace, "Dole na baka haƙuri Asad na cutar dakai akan abubuwa da yawa dan ka kasance me yi min biyayya na dinga tauye maka hakki, kayi haƙuri ka yafe ni" ta sake fad'a cikin kuka sosai. Ya kasa magana sabida shi kansa sarawa yake yi Mama Jamila tace, "Haba Maman Suhaima, dan Allah ki daina wannan kukan kinga kin saka Asad din cikin wani yanayi mara dad'i. Ga abinda likita yace" Ta kalle su tace, "Dole nayi kuka Jamila, na cutar da Asad iya cuta duk abinda ya nuna yana so sai na raba shi dashi bana duba halin da zai shiga kawai cikar burina nake so. Ban tab'a addu'ar in mulkin nasa ba alkhairi bane Allah ya hana shi kullum alkhairi nake hangowa ban tab'a fad'awa Allah yayi min zab'i ba. Na raba Asad da aikin sa, na raba shi da burin sa, na raba shi da duk wani abinda yake so hatta matar da yake matuƙar qauna na raba shi da ita kawai dan na samu cikar burina." "Wacce nazo na tilasta shi ya aura sai gashi ita da babar ta suke so su kashe ni, daman yasha fad'a min Mama bata dace dani ba amma nak'i ji nace ko baya so dole ya aureta, ya aure ta d'in ya hak'ura ya zauna da ita ya fara mulkin da nake so na fara saka shi yana yin duk abinda nake so koda shi baya so koda kuwa ya sab'awa shari'a. In ban nemi yafiyar Asad ba me zanyi?. Ta silar mulkin da baya so aka masa kurciya ya bar k'asar nan ya koma wata k'asar amma da ya dawo sai ya cigaab da fafutukar neman ganin bayan makiya na" Ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Asad yayi shiru ya kasa magana Mama ta kuma cewa, "Hydar da Asad yake so sama da komai a duniya dashi kad'ai ya yarda ya kuma aminta amma shine yake cin dunduniyar sa yake neman kashe shi duk ta silata kuma, da ace ban nuna k'arara Asad nake so yayi mulki ba da hakan duk bata faru ba. Ga Aliyu ma da yaso kashe Asad....Kai na cutar da Asad cuta mai tsanani" ta fad'a tana dafe kanta ta sake fashewa da sabon kuka. Murya na rawa ta fara cewa, "Hydar! Aliyu!. Hydar d'ina shine yake so ya kashe Asad Hydar fa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.  Duk abinda ake shiryawa ashe Hydar ne sila shine yake komai amma a zahiri sai ya nuna bai san komai ba, ya zanyi da rayuwata?. Y'ay'ana biyu duka babu na zab'e." Ta sake fad'a tana sake fashewa da sabon kuka ta kwanta a kan kujerar. Asad ya tashi akan guiwar sa ya rik'e ta yace, "Mama likita yace kar ki shiga damuwa dan Allah ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce." "Ta ina ya wuce Asad? Bayan Hydar ya tabbatar da bai gama d'aukar fana a kanka ba yana nan zai dawo, in ya kashe ka ya zanyi Asad?. D'an uwanka jinin ka wanda kuka fito duniya lokaci d'aya ace shine yake neman d'aukar rayuwar dan uwan sa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ina ma na mutu kafin wannan ranar. Meye amfanin maza ukun da nake alfahari ina dasu? Makisa, makirai, masu son kansu, masu son duniya akan D'anuwan su?, meye abin alfarahin da zanyi dasu? Basu da wani amfani dukkan su ina ma Allah ya d'auki rayuwar su gabad'aya na huta." Mama Jamila tace, "bai kamata kina fad'ar wannan kalmar ba Mama, dan Allah kiyi haƙuri. Ya kike so Asad d'in yayi shida a lokaci d'aya ya rasa y'an uwan sa da babar sa suka juya masa baya? Ya kike so yayi lokacin da aka kwantar da mahaifin sa mai share masa hawaye?." Mama ta tashi zaune ta dafe kai da hannun ta tace, "Duka ta silar Hydar wad'annan abubuwan suka faru, da kuma son tawa zuciyar badan na bayyana burina ba da duk hakan bata faru ba, da yanzu suna nan tare shida Hydar kamar da." Asad yace, "Dan Allah Mama ki daina kuka kodan lafiyar ki." "Ka yafe min Asad, kace ka yafe min dan Allah." "Mama dan Allah" ya fad'a a raunane yana kallon ta kamar zai zubar da hawaye shima. Mama tace, "ku taya ni rok'on yafiyar sa dan Allah kar na mutu da hakkin sa a kaina." Asad yace, "Mama baki min komai ba, kina da iko dani har yanzu; ko yanzu kika ga abinda baki so a tare dani zaki iya cewa na hak'ura kuma na hak'ura domin kin isa." Mama ta girgiza kai tace, "A'a Asad, bazan sake hana ka abinda kake so ba har abada duk abinda kake so shi nake so, su wanda nake bawa abinda suke so d'in sune suke k'okarin ganin bayana kai da nake tauyewa kaine kake k'okarin ganin na rayu kake tsaye a kaina kana nema min lafiya. Naji dad'i da ya kasance Aliyu yana cikin yanayin hauka da lafiya saura Hydar shima Allah zai hukunta shi daidai da abinda ya aikata." Mama ta kalli su Mama Jamila tace, "Ku kira min Suhaima tazo ta raka ni wajan matar sa na bata haƙuri." Asad yace, "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalin ki baki da cikakkiyar lafiya fa." "Nidai a kaini inda take na bata haƙuri nayi mata abubuwa da yawa a rayuwa wanda bazata manta dani ba." Mama jamila ganin yadda Mama ta rude lokaci d'aya sai tace, "Ranka ya dad'e a kira Fulanin taka tunda hakan take so ko dan sabida jikinta." Asad ya kalli Suhaima da ta fito da kai yayi mata alama da ta kira Rauda ta amsa ta fita. Ba jimawa suka dawo tare da Rauda ta zauna akan k'asa kamar yadda Asad d'in yake tace, "Barka da dawowa Mama." Jin muryar Rauda sai Mama ta kalle ta tace, "Tun kina asibiti lokacin da Hydar ya buge ki ban tab'a ganin ki ba amma na d'auki tsanar duniya na d'ora miki, na saka aka kore ki daga asibitin ta silar hakan kika samu matsalar k'afa,  ta silar hakan abubuwa da yawa suka faru dake wanda na samu labari da wanda ban samu ba. Na saka akazo har gidan ku aka ci muku mutunci aka daki mahaifiyar ki, daga nan ban hak'ura ba na sake dawowa da kaina na sake ci miki fuska akan kud'urina wanda Allah ya riga ya rubuta ke matar sace. Na sake turowa har gidan ku a kashe ki Rauda, kisa nayi k'okarin yi a kanki a karo na farko a rayuwata" ta fad'a da kuka sosai ta kasa cigaba da magana. Dukkan su shiru sukayi kafin Mama ta cigaba da cewa, "Allah ya nuna min ikon sa akan aure ku akayi ba tare da na sani ba amma maimakon na hak'ura na d'auka haka k'addarata take sai na sake sakawa ana yi miki aikin da zaki bar duniya, har hijjabin ki an tura an samo a gidan ku dan ayi miki aiki a kashe ki amma Allah bai nufa ba duka ban hak'ura ba na skaa aka yiwa Asad aiki...." Sai ta sake fashewa da kuka Asad yace, "Dan Allah Mama ya isa haka duka komai ya wuce ki daina kuka Mama bana so" ya fad'a yana rik'e hannunta idanun sa sunji ja sosai. Mama tace, "barni na fad'a, har abada bazan yafewa Sadiya ba dukkan abinda ya faru itace take shiryawa haka kawai bana iya tsallake maganarta komai tace sai nayi bana iya tsallakewa ban san meyasa ba. Nayi abubuwa da yawa akan ka da kuma matar ka Asad, inda ace nasan akwai idda a kanta da a lokacin da na saka ka sake ta bazan bari ta fita ba sai ka yanke igiyoyi biyun da suka rage ba, amma da yake Allah yana so ya nuna min in ya rubuta abu ban isa na goge ba sai gashi matar kace har yanzu ko a wannan yaci ace na fuskanci ikon Allah akan bayin sa." "Duk wad'annan abubuwan da nayi miki keda iyayen ki baki rike shi ba kika tura min anniyata nazo har gidan ku neman alfarma maman ki ta tashe ki kika raka ni inda na samowa Asad da mahaifin sa da kuma Hydar, a kan hanyar dawowa akaso kashe ni kika cece rayuwata. Ban sani ba ashe kece kika kawo silar samuwar lafiyar mai martaba, tabbas kin turo min aniyata gata nan kuma ina gani tunda gani a zaune babu lafiya y'ay'ana biyu dukka sun zama y'an ta'adda. Ki yafe min Rauda dan Allah iya hakkin ki bazai barni na zauna lafiya ba dan nasan nayi miki abinda babu wanda ya tab'a yi miki shi a duniyar nan." Rauda hawaye take yi ta girgiza kai tace, "Babu komai Mama ni komai ya wuce a wajena kin wuce neman alfarma a gare ni, ki yafe min in na tab'a b'ata miki rai nima." Mama tace, "Baki tab'a ba Rauda ba kuma zaki tab'a ba, babban burina kice kin yafe min dan Allah." Rauda tace, "Na yafe Mama." Mama tace, "Na gode Rauda Allah ya saka miki da alkhairi ya raba ki da abinda yake jikin ki lafiya." Ta kalli Asad tace, "Na dawo kanka banji kace ka yafe min ba Asad, kaga y'ar albarkar matar ka ta yafe min saura kai." Asad yace, "Mama baki min komai ba dan Allah ki daina fad'ar haka, in ma kinyi na yafe miki Mama." "Na gode Asad, tabbas zaka cigaba da ganin sakamakon biyayya a rayuwar ka, Allah yayi maka albarka ya kare ka daga y'an uwanka masu nufin ka da sharri a duk inda kake." Aka amsa da amin kafin ya tashi tsaye ya tasar da Mama ya kaita har cikin d'aki yana rik'e da ita ta zauna ya bata maganin ta da kansa ta kwanta yace, "Ki huta Mamana, dan Allah ki daina saka damuwa a ranki ina tare dake har abada." Hannun sa ta rik'e yana zaune a gefen ta a haka bacci ya d'auke ta. Sai da ya tabbatar baccin yayi nisa ya fito bai samu Rauda ba sai kannen Maman ya kalle su yace, "Mama dan Allah a kula da ita." Tace, "in sha Allah ranka ya dad'e zamuyi iya bakin k'okarin mu." Daga nan ya fita dan baiga Rauda ba. Kai tsaye b'angaren mahaifin sa ya wuce ana take masa baya kamar d'azu shi kad'ai ya shiga ya same shi zaune dashi da Uncle yana shigowa Uncle sai ya tashi ya shiga ciki Asad ya zauna a k'asa yayi ahiru baice komai ba, Mai martaba yace, "Fuskar ka akwai damuwa a tare da ita Asad, meye yake faruwa?." Asad yace, "Abba dan Allah ka yafewa Mama, wallahil azim tayi nadamar dukkan abinda ta aikata yanzu har Rauda ta saka aka kira ta bata haƙuri. Dan Allah ka yafe mata Abba." Abba yayi murmushi yace, "Dole tayi nadama ai koda bata so na dan in ma batayi ta tsakani da Allah na duniya ta koya mata hankali, taga ishara akan Sa'adatu da Yahuza da kuma Aliyu, ta tabbatar itama ta cigaba da tafiya a haka irin wannan k'arshen zatayi. Kaf ma'aikatan gidan nan basa son ta sabida halin ta na wulaƙanta na k'asa da ita a ganin ta Allah ya fifita ta akan su, y'ay'an ta har biyu dukkan su y'an ta'adda masu bak'ar zuciya da bak'ar aniya da mugun nufi ai dole tayi nadama. Duk taqamar ta akan y'ay'an da take yi sai gashi dukan su samun su ba alkhairi bane in aka cire ka, Rauda kuma da take magana badan ita ba da yanzu har yanzu ina kwance har yanzu ana cigaba da yi min allurar karya garkuwar jiki, silar kawun ta komai yazo k'arshe ba dole ta bata haƙuri?." "Ka manta har kisa ta aika aje ayi a gidan su? Duk tunanin ta wannan ranar bazata zo ba sai gashi tazo tana kuka da idanunta. Ta gode Allah ma tana da bakin rok'on bata mutu tun farko abin ba da sai a lahira Allah ya tsayar dasu yayi musu hisabi. Taje ta raba ku da yarinyar nan duk a tunanin ta taci riba bata san Allah ya riga ya kulla alaqar ku ba." Asad yayi shiru baice komai ba har sai da mai martaba ya gana fadn sa sannan yace, "Yafiya nake nema mata Abba, nasan duka ta aikata amma sabida Allah sabida ni Mai martaba ya yafewa Mamana iya abinda take ji a zuciyar ta ma ya ishe ta." Mai martaba ya sauke ajiuar zuciya yace, "ni na yafe mata ai; na yafewa Sa'adatu ma balle ita? Na yafewa Yahuza ma balle ita? Na yafewa dukka ire-iren su balle ita?. Taci darajar ka na yafe mata." Asad yace, "Na gode mai martaba, Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana." Ya amsa da amin kafin ya kalle shi yace, "Akwai gajiya a tare dakai yana dakyau kaje ka huta." Asad yace, "zan duba jikin Aliyu ne." "Ana samun cigaba sosai a rashin lafiyar tasa, basai ka shiga ba tafi kaje ka huta. Shi kuma Hydar da yak'i saduda Allah zai mana maganin sa." Asad baice komai ba ya fito aka rufa maaa baya aka raka shi b'angaren sa kafin kowa ya watse. Zai hau saman Rauda zata sakko idanun ta yayi ja alamun kuka tayi ta dawo da baya ta bashi hanya ya wuce bata ce komai ba  ta sauka ta fita ya bita da kallo kafin ya wuce ciki shima.        Da daddare ta kawo masa abincin dinner har sama ta same shi zaune da k'ananun kaya masu laushi kalar milk yana aiki da laptop yayi shiru baka jin sautin komai sai na keyboard. Ajjiye masa abincin tayi ba tare da zatayi magana ba ta juya ya kashe laptop din yace, "Tsaya." Ba musu ta tsaya ta juyo tana kallon sa ya mik'e tsaye yazo kusa da ita yace, "Me kike ji dashi ne? Me kike d'aukar kanki?." Rauda ta kalle shi itama fuskar ta kamar tasa fuskar a d'aure tace, "Abinda kake ji dashi nima shi nake ji dashi. In taqamar kai sarki ne ni matar sarki ce, in taqamar ka kai dan sarki ne nima sirikar sarki ce, in taqamar ka kai jikan sarki ne nima sirikar jikan sarki ce. Duk abinda kake ji dashi nima shi nake ji dashi" ta fad'a tana kallon sa shima ita yake kallo. Kai yake girgizawa yana kallon ta kafin yace, "ba kece sarkin ba ashe matar sace?." "Eh daidai nake da sarkin tunda nice matar sarkin!. Dan an kawo maka ni gidan nan sai ka dinga wulaƙanta ni kana yi min abinda kaga dama dan kaga kawai ina sharewa? In haushina kake ji nima ka sani haushi ka nake ji wallahi domin ta silar ka abubuwa da ya suka faru dani a rayuwata wanda bazan manta dasu ba har abada." "Ta silar ka Ummana tayi min Allah ya isa" sai muryar ta ta soma rawa ta fara kuka tana fad'in, "Dukkan k'addara ta a kan kane duk abinda ya faru dani ta silar kane kaine ka jawo komai da baka shiga rayuwata ba da hakan bata faru ba. Ni banji haushin ka ba sai kai zaka dinga jin haushina kana share ni dan kawai kana taqama da wani abun kana ganin kamar power da kake dashi ne ya saka ni dawowa ko auren ka. To ba haka bane baza kayi min abu kuma ka fara fushi ba sannan ni na sauka k'asa ba bazai yu ba, a baya an dake ni an hana ni kuma amma a yanzu bazan lamunta ba wallahi, ina k'okarin sauke hakkin ka da yake kaina matsayin ka na mijina Allah yana gani in ka kula kanka in ma baka kula ba kanka" tana fad'a ta juya ta sauka ta barshi a wajan a tsaye yana kallon hanyar da tabi zuciyar sa na rawa sosai. *Duk mulkin namiji bawan mace ne.*🫡 [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *089*           Da kallo ya bita har ta sauka ya furzar da iska ya juya ya hard'e hannayen sa a k'irji ya runtse idanun sa. _Sudai mata duka halin su d'aya basa damuwa da damuwar ka kansu suka sani kawai_. Ya fad'a a zuciyar sa yana sauke numfashi ya zauna akan kujera yana jin zuciyar sa na bugawa. Baya so kalaman ta suyi tasiri a ransa dan zasu b'ata masa rai ne hakan ya saka bai ma kalli abincin ba ya tashi ya barshi a wajan ya shiga d'aki a zuciyar sa yana aiyana dole ma gobe ya bar garin tunda Mama ta samu lafiya dole ya basu waje ya huta tunda ba son ganin sa zai basu waje tunda babu tausayi a zuciyar ta bata ganin yanayin da yake ciki take sake k'ara masa damuwa. B'angaren Rauda a fusace ta shiga b'angaren ta ranta duk a b'ace haka take jinta sai girgiza kai take yi ita kad'ai komai ya tsaya mata. "Bashi kad'ai yake ji da kansa ba nima ina ji da kaina, ni mutum ce kamar shi wallahi bazan d'auki wulaƙancin dana d'auka a baya ba" ta fad'a a bayyane tana dafe kanta tana zaune a gefen gado. Sai kuma ta rasa me yake mata dad'i sai kawai ta mik'e ta nufi b'angaren Mama dan ta sake duba jikinta. A zaune ta same ta a falo sanye da hijjabi da carbi a hannunta tana ja ita da Suhaima tana b'are mata ayaba tana bata amma kafin ta cinye guda d'aya ma aiki ne. Da sallama ta shiga Maman ta amsa ta saki murmushi tana kallon ta Rauda kuma ta sauke kanta k'asa ta zauna tace, "Barka da dare Mama." "Barka dai Fulanin Asad, ina aka baro mai martaban kuma?." Jin yadda Mama tayi mata magana da barkwanci sai ta d'ago ta kalle ta sai taga tana ta murmushi ta sunkutar dakai k'asa tana murmushin itama. "Nazo na sake duba jikin Mama ne kafin na kwanta." Mama taji dad'i har zuciyar ta tace, "Jiki Alhamdulillah, daman tarin hakki ne yayi min yawa yanzu kuma duk da kuka yafe sai nake jin ina ta samu lafiya." Rauda bata ce komai ba tayi shiru Suhaima ma batayi magana ba. Mama tace, "Kije ki huta dare yanayi." Rauda ta mik'e tace, "A kwana lafiya." Daga haka ta juya ta fita tana ji a zuciyar ta badan Umma tace ba wallahi bazata zo ba ta yafe mata amma tana jin haushin ta. Mama ta kalli Suhaima tace, "Raka ni b'angaren su Sa'adatu" ta fad'a tana mik'ewa Suhaima ma ta mik'e tace, "Mama bakya jin dad'in jikin ki fa." Mama tayi murmushi tace, "zan iya zuwa." Gaba Mama tayi Suhaima na binta a baya da jakadiyar ta har b'angaren Hajiya. Mama ta manta rabon da ta shiga b'angaren ta hakan ya saka taga ya canja mata amma bata nuna ba hadiman Hajiya suka mik'e ana gaishe ta da Mama ta amsa kafin a sanar da Hajiya zuwan ta su shiga ciki. Tana ganin Mama ta mike tana fad'in, "Rabi'atu da kanki keda baki da lafiya?." Mama ta zauna itama ta zauna tace, "Jiki Alhamdulillah na samu lafiya." Hajiya tace, "Haka muke fata." Mama ta kalle ta tace, "Nazo neman afuwa akan abubuwan da suka faru a baya wanda nasan na aikata a abubuwa da yawa wanda baau kamata ba, ayi haƙuri dani." Ba k'aramin Mamaki Hajiya tayi ba ta kalli Mama ta girgiza kai kana tace, "Haba babu komai mune mukayi laifi bake ba." Mama tace, "Nima nayi." "Amma ba kamar ni ba, nayi abubuwa da yawa a bayan idanun ku wanda baku sani ba, tuun ranar da aka haifi su Asad nake tsaye a kansu dan ganin dukkan su babu wanda za'a mora a cikin su har girman su. Adadin abubuwan da na aikata dan dakushe su bazasu irgu ba dole na nemi afuwar ki nima Rabi Asad ya yafe min saura ke." Mama tayi murmushi tace, "Duk abinda kuka aikata nice na jawo, halina ne ya jawo badan halina ba da duka baku aikata ba, da kun rik'e su tamkar y'ay'an ku amma nine na raba na nuna kuda su akwai banbanci." Hajiya tace, "Duk da haka ai ke baki nufe mu da sharri ba mu kuwa fa?." Mama tayi murmushi tace, "haka ne, nidai na yafe ko meye ina fatan a yafe min nima." Hajiya tace, "Naji dad'in yafiyar ki nima kuma na yafe miki koma meye, Allah ya bawa Asad ikon cigaba da mulkin sa cikin aminci da lafiya, Allah ya bawa Aliyu lafiya" ta fad'a muryar ta rawa sosai sabida kuka da yake so ya kwace mata. Mama ta Mike tace, "Na gode sosai. Ki huta lafiya" ta fad'a tana tashi ta fita itama ta biyo bayan ta har k'ofar waje sukayi sallama ta shiga wajan Ammi. Nan ma dai maganar d'aya ce Ammi tace bata rik'e ta ba sukayi sallama tace da Suhaima ta koma zata je b'angaren mahaifin su haka akayi ita ta koma ita kuma ta nufi b'angaren kai tsaye. Babban falon ta shiga baya nan kai tsaye ta shiga d'akin da tasan yana nan, nan ma baya nan ta fito ta shiga d'ayan nan ta ganshi zaune kusa da Aliyu yana bashi magani. Sallamar ta ya saka shi ya juyo tare da amsawa ya d'auke kai ya cigaba da bashi maganin ta tako a hankali ta tsaya tana kallon Aliyu. Yana zaune yana binta da ido ya rame yayi wani iri sai ido kawai da yake binta dashi kamar ba Aliyu d'an gayu mai ado ba, kusa dashi taje ta rik'e hannun sa shima ya rik'e alamun ya ganeta tace, "Sannu Aliyu." Kallon mahaifin sa tayi sai taga ya tashi ya fita ta zauna a gefen Aliyu ta rik'e fuskar sa tace, "Haba Aliyu meyasa ka aikata dukkan abinda kayi? Meyasa neman duniya ya rufe maka ido kake k'okarin cutar da d'an uwan ka?." Kamar yana jin me take cewa ya sunkuyar da kansa k'asa sai ta fara kuka tunawa da tuni Asad ne a cikin halin da hakan ta faru bata san ya zatayi ba. Bacci taga yana neman yi ta kwantar dashi tayi masa addu'a ta rufe shi ta kashe mishi haske ta nufi d'akin mahaifin sa. Waya ta samu yanayi da governor Kano ta samu waje kusa dashi a k'asa ta zauna har ya kammala wayar suka had'a ido ya d'auke kansa tace, "Barka da dare." "Ya jiki?" Ya fad'a a tak'aice ba tare da ya kalle taba.  Ta goge idanunta tace, "da sauk'i." Daga nan yayi mata banza bai sake magana ba ta gyara zama tace, "Dan Allah kayi hak'uri." Kallon ta yayi yace, "Me kikayi min?." Ta ja numfashi tace, "Komai ma." Tab'e baki yayi yace, "kome kika aikata ai kanki kika cuta Rabi'atu, yanzu ba gashi y'ay'an naki da kike taqama dasu  meye amfanin su yanzu?. Ace jinina wanda na haifa d'an cikin gidan nan shine ya dinga Zina da matar aure matar auren kuma matar k'anin sa, shi kuma d'ayan har d'akin nan yazo kashe mahaifin sa sabida son zuciya da bak'ar aniya. Yanzu meye amfanin wad'annan guda biyun?." Ta goge idanunta tace, "Babu, ina rok'on Allah ya d'auki ransu dukka na huta domin ganin su kawai bak'in ciki yake k'aramin." "Ganin kanki baya saka ki bak'in ciki? Kin manta kece silar jefa Aliyu da Jiddan wannan hali?, ko kina tunanin ban san aikin da kika yiwa Asad lokacin da yana Cairo dan kawai kar yayi auratayya da matar sa?." Gaban Mama ya sake fad'uwa ta runtse ido bata ce komai ba yayi murmushi yace, "Alhakin abinda suka aikata yana kanki, da ace Asad d'in a lokacin da lafiya a tare dashi da bata bawa Aliyu had'in kai ba amma kin dakushe lafiyar tasa sabida kawai nufin ki Mara kyau akan y'ar mutane, dan haka kanki zaki fara tsana ba su ba." "Ina jin haushin kaina domin na cutar da kaina da y'ay'ana. Asad da ya kasance mai yi min biyayya nafi cutar dashi sama da komai." Yace, "Yanzu me gari ya waya? Da kin bar son mulkin da kike a zuciyar ki duk da ba haka ba, amma ji kika dinga yi kamar ki kunna min huta na k'one dan cikar burin ki. Baki tab'a addu'ar in Mulkin Asad bazai haifar da alkhairi ba Allah kar ya bashi baki tab'a ba kawai ke son kanki da yadda zaki wulaƙanta abokan zaman ki shine kawai a gaban ki. Akwai jinin sarauta a jikin ki na sani amma duk abinda kike ji dashi nima ina ji dashi dan ni nayi mulki ke kuma baki yi ba iyaye ki da mijin kine sukayi; amma yadda nake zaune da Jama'ar gidan nan ke ba haka kike ba. Kika d'auki burin duniya kika saka akan Asad akan burin ki har kokarin kashe wacce yake so kika yi, akan burin ki tsallake umarnina kinyi kin tafi Cairo kin saka ya saki matar sa dan akwai bani da lafiya. Da farko na zarge ki a rashin lafiyata domin nasan zaki iya indai akan burin kine amma daga baya sai naga anyi amfani da damar da kika bayar ne dan ace kece." "Abun kunya kuma d'an cikin ki shine ya aikata hakan dan ki fad'a ramin da ya hak'a kuma kin fad'a dan kaf mutanen gidan nan duka ke suke zargi akan rashin lafiya ta hatta d'anki Asad. Kin aura masa wacce kike so sai gaahi suma suna k'okarin kashe ki har sai da kika je gidan su wacce kika saka ya rabu da ita d'in kika nemo alfarmar Kawunta. Kin jawo min abubuwa da yawa wanda bazan manta ba Rabi'a, kin saka anyi cikin shege a cikin gidan nan bayan kin san tun farko yarinyar ba tarbiyya ce da ita ba kika nace sai ya aure ta, kin saka an aikata min abubuwa da dama wanda har k'asa ta rufe idanuna bazan manta dasu ba." Ya sauke numfashi yace, "Amma ta dalilin Asad na yafe miki kamar yadda na yafewa Yahuza dalilin Suhail, amma ki jawa Hydar d'anki kunne wallahil azim idona idon sa sai yayi zaman prison, ya bar ganin na k'yale shi ya d'auka yaci bulus ina nan sane dashi sai na saka an masa hukinci daidai da abinda ya aikata. Shi Aliyu Allah ya hukunta shi saura shi." Kuka Mama take yi sosai muryar ta har dashewa take sabida kuka tace, "Nayi nadama, wallahi nayi nadamar dukkan abinda na aikata. Na nemi yafiyar Raudan ita yafe min domin na cutar da ita cuta mai yawan gaske. Duk abinda ya faru tabbas nice silar komai, ya Allah ka yafe min" ta fad'a tana sake fashewa da kuka yayi mata banza bai kula ta ba. Sai da ta gama kukan ta son ranta sannan ya kalle ta yace, "Kije ki huta nima zan huta." Kai ta d'aga ta mik'e tsaye ta dafe kanta tayi baya kamar zata fad'i yayi hanzarin rik'e hannun ta har ta tsyaa daidai yace, "Kiyi a hankali." Kai ta d'aga ta nufi k'ofar fita ta fita ya sauke numfashi yana jin ciwon abubuwan da suka faru a zuciyar sa. Washe gari. Rauda koda ta tashi girki abinci tayi masa duk da ranta a b'ace bayan ta gama tana shirin kaiwa Suhaima ta shigo ita da Khaleesat da sallama, tana tsaye da tray akan table ta amsa da murmushi tana fad'in, "Barkan ku da zuwa." Sukayi dariya Suhaima tace, "Khamshi muke ji ya cika ko ina na gidan nan shiyasa muka shigo muci girki." Dariya Rauda tayi kad'an tace, "Bismillah ku." Khaleesat tace, "Dole ai mu zauna muci wannan khamshin bazai bar mu ba." Suhaima tace, "A haka ma fa wai dan mai martaban baya nan ne da ace yana nan abincin da zamu samu sai yafi wannan." Khaleesat tace, "ashe fa ya tafi Abuja d'azu, ai naga alama Fulanin mu akwai iya girki ga iya kula da yayan mu kuma shugaban mu.: Murmushi tayi kawai amma bai kai zuci ba zuciyar ta cike da zallar b'acin rai da kuna jin wai ya tafi Abuja kenan ya mayar da ita banza kenan a gidan bata da wani amfani tunda har zaiyi tafiya bata sani ba. Daurewa tayi tace, "Bismillah kuci zanje wajan Mama na kai mata nata" ta fad'a tana kiran Hadimar ta ta shigo a guje ta d'auki tray d'in tayi gaba tana binta a baya. Suhaima ta bita da kallo tace, "Yayan mu yayi sa'ar mace ki kalla abincin ma ba y'an aiki ne zasuyi ba itace zatayi" ta fad'a tana tashi ta k'arasa kan table d'in Khaleesat ma ta taso tana fad'in, "Gaskiya dai tana da kirki gashi tana son Mama." Suka zauna suna cin abincin. Rauda lokacin da suka shiga Mama tana zaune ita kad'ai tasha magani ganin Rauda da abinci ya saka ta yin murmushi aka ajjiye abincin hadimar ta fita Rauda ta zauna tace, "Barka da safiya Mama." Mama ta bita da murmushi tana kallon ta tace, "Barkan ki, ya k'arfin jikin k?." Rauda tace, "Alhamdulillah. Ya jikin Maman?." "Naji sauk'i sosai. Wannan aikin duka ke kikayi?." Rauda ta girgiza kai tana murmushi Mama tace, "Allah yayi miki albarka ya baku zaman lafiya me d'orewa." Rauda tayi murmushi ta amsa da amin kafin Mama tace, "Yace min zaki bishi Abuja anjima gwara kije ki shirya kar azo ana jiran ki." Rauda ta kalli Mama da mamaki amma bata da bakin musawa ko babu komai bata nunawa Mama bata san ma baya nan ba. Rauda tace, "a tashi lafiya." Daga nan ta fita Mama ta bita da kallo tana jin kamar ta wanke zunubai masu yawa cikin wanda ta aikata.          A fusace Rauda ta koma b'angaren ta sai da ta shiga falon ta tuna dasu Suhaima a zaune suna ganin ta Khaleesat tace, "Fulanin mu wallahi abinci yayi dad'i sosai, da ace mai martaba yana nan yaci abincin nan yau kin gama dashi, daman Yaya Asad da son abu mai dad'i." Murmushi tayi tace, "Santi kuke yi kawai. Ina zuwa" ta fad'a tana shiga d'akin da sauri tana jiyo Suhaima tana fad'in, "Mun wuce wajan Ammi." Mayafin jikinta ta cillar a kan gado cikin zallar b'acin rai tana zaga d'akin tana fad'in, "Rainin hankali mai lasisi kenan, ni zai yiwa irin wannan rainin wayon dan kawai ya raina ni ya raina yadda ya d'auko ni? Wato harda fad'awa Maman sa zan bishi bayan ban san ma yayi tafiyar ba? To wallahi bazan je ba sai dai duk abinda zai faru ya faru." Wayar ta taji tana k'ara kamar bazata duba ba sai ta kalla taga sunan Umma ta d'auka ta zauna a gefe ta saka a kunne tace, "Umma barka da safiya." Umma tace, "Barkan ki Rauda, ya naji maganar ki wani iri haka?." Rauda tace, "Babu komai Umma. Ya mutanen gidan?." "Alhamdulillah. Daman sanar dake zanyi y'ar wajan kawun ku Lawan ta haihu sai ki kirata kiyi mata barka kafin kije." Rauda kamar tana gaban ta ta d'aga kai kafin tace, "in sha Allah Umma, Allah ya raya." Umma tace, Amin. Amma akwai abinda yake damun ki fad'a min ina jinki kar kice min babu." Rauda ta fashe da kuka jin hakan sai Umma tayi shiru gabanta yana fad'uwa kafin tace, "Nutsu kiyi min bayani, meya faru?." Rauda murya na rawa tace, "Umma na gaji da gidan nan gabad'aya." Umma tace, "Meya faru?." Rauda tace, "Umma baya sona gabad'aya sai a kwana biyu ban ganshi ba shima bai ganni ba kuma hakan bai dame shi ba, yau tafiya yayi zuwa Abuja amma ban sani ba sai a bakin k'annen sa nake ji Umma." Umma tayi shiru kafin tace, "Tsayar da kukan tukunna." Rauda taja numfashi ta goge idanunta sannan Umma tace, "Shine zai neme ki kenan ba kece zaki neme shi ba ko Rauda? Wato kece mijin shi kuma shine matar ko?." Kafin tayi magana Umma tace, "duk irin qalubalen da ya tsallake da rijiya da ya tsallake da baya duk baki gani ba sai kin sake d'ora masa wata damuwar? Zuwan ki gidan wacce gudunmawa kika bashi wacce zata kore masa damuwar da yake ciki?." Rauda tayi shiru kafin tace, "Tsakani da Allah Umma ni banyi komai ba, hasalima ni bana zuwa inda yake indai ba abinci zan kai masa ba." Umma tace, "Baki da hankali ashe ban sani ba Rauda?." Rauda tace, "Umma haushin sa nake ji kin sani, ta dalilin sa fa kika......" Umma ta katse ta tace, "Dake da haushin nasa da kike ji kunci uban ku, shi baice yana jin haushin ki ba sai kece zaki ce kina jin haushin sa?. Ki tuna mahaifiyar sa kwanciya rashin lafiya tayi, ya rasa soyayyar y'an uwan sa guda biyu dukkan su suna son ganin bayan sa, ya rasa lafiyar mahaifin sa a baya, ya rasa komai hatta ke ya rasa, a wannan gab'ar yana neman wacce zata share masa hawaye ta yaye masa damuwa ta taushi zuciyar sa ta rarrashe shi kodan ya rage zafin da yake ji a zuciyar sa. Ki tuna Hydar ke kanki da Hydar kika sanshi amma me Hydar yayi masa? Ke wannan an fad'a miki abu ne mai sauk'i? Kin san zafi da k'unar da zaiji a ransa ace k'anin sa uwa d'aya uba daya shine yake neman kashe shi?. Ki tuna yayan sa da suke ciki d'aya shine ya dinga Zina da matar sa har tayi ciki wannan ma ba damuwa bace? Ke wacece da zai saurare ki yana cikin wannan yanayin bayan baki taimake shi wajan ganin an kawar da damuwar ba?." Yadda Umma take mata fad'a sai taji fad'an yana shiga zuciyar ta abinda take fad'a kuma gaskiya ne sai ta sake nutsuwa taji tana cewa, "Ke kad'ai ce zaki d'auke masa damuwa kuma kin share shi to me kike so yayi miki? Zuwa zaiyi ya durk'usa akan guiwar sa yace miki Rauda ki rarrashe ni?." Nan ma Rauda tayi shiru Umma tace, "Zaki ragewa kanki matsayi da k'ima a wajan sa, duk soyayyar da yake miki wannan banzar dabi'ar taki zata d'auke ta cillar da ita a gefe domin baki da amfani a wajan sa indai baza ki wanke masa damuwar da take ransa ba. Na tabbata yana buk'atar ki a kusa dashi ko in kula d'in ne da kike nunawa ya saka shima ya watsar dake, to dan yayi tafiya bai fad'a miki ba kuma sai kiji haushi? Naga ke kika zab'arwa kanki hakan ai ko?. Ai sai kije ki tayi Rauda tunda haka kika zab'a Allah ya bada sa'a kina zaune zai k'ara aure daman sarakuna basu zama da mata d'aya" tana fad'ar hakan ta yanke wayar bata jira Rauda tace komai ba. Rauda tabi wayar da kallo k'irjin ta yana bugawa matuk'a cikin tashin hankali da gano zallar laifinta da kuma wautar da ta tafka a cikin lamarin, babban abinda yafi d'aga mata hankali bai wuce kalmar kishiya da Umma tace ba nan take hankalin ta ya sake tashi matuk'a...... [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *090.*        Da kallo tabi wayar jikinta kamar an zare duk kuzarin jiki ta ajjiye ta a gefen ta ta sauke numfashi ta tallafi hab'ar ta da duka hannayen ta ta lumshe idanu tare da jan numfashi ta sauke sannan ta buɗe idanunta tana jin babu dad'i a zuciyar ta. Bata kai ga yanke tunanin da zatayi ba wayar ta ta sake yin k'ara ta duba ganin sunan Yaya Ummi ya saka ta d'auka kafin tayi magana ta rufe ta da fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba hakan ya saka ta tayi shiru tana jin me take cewa. "Wallahi Rauda ban d'auka shirmen ki ya kai haka ba, duk ina jin yadda kukayi da Umma kin bani kunya da mamaki wallahi. Duk abinda yayi miki wannan halin da yake ciki ai yaci ace kin ajjiye naki fushin ki taya shi korar nasa kodan samun sasauci a zuciyar sa. Wa yake dashi da zai rarrashe shi Hydar ne yanzu kuma yana ina?." Rauda bata iya magana ba Yaya Ummi ta kuma cewa, "Kiyi gaggawar samun sa yanzu in da yadda za'ayi ki bishi inda ya tafi in babu hali kuma ki jira ya dawo ki gyara kuskuren ki in ba haka ba zakiyi dana sani" tana fad'ar hakan ta yanke wayar Rauda ta sake ajjiye wayar tana jin zuciyar ta na rawa sosai. Duk sai hankalin ta ya tashi ta rasa inda zata saka kanta tunawa fa da duk abinda kace mata gaskiya ne gashi bata san ya zatayi ba,yanke shawarar kiran sa tayi a waya sai kuma ta fasa ta kira number Suhaima. Suhaima tana d'auka tace, "Babar Yayar mu." Rauda tace, "Sister number Suhail zaki tura min." Ta amsa da to ta kashe wayar jim kad'an sai ga number ta shigo ba tare da shawara ba Rauda ta kira number. Bata jima tana ringing ba aka d'auka tayi sallama ya amsa kafin tace, "Dan Allah Suhail ne?." Ya amsa da fad'in, "Eh shine." Rauda ta sauke ajiyar zuciya tace, "Rauda ce take magana." Jin abinda tace sai yace, "Ranki ya dad'e, da kanki Allah yasa lafiya?." Rauda ta d'anyi shiru kafin tace, "Ina so zaka kai ni inda Sultan yake dan Allah." Suhail yayi murmushi yace, "Haba ranki ya dad'e umarni kawai zaki bani sai a aiwatar, yanzu zan k'araso in sha Allah." "Na gode" ta amsa tana yanke wayar kafin ta tashi jikinta duka babu dad'i. Rasa ma abinda zatayi tayi gabad'aya zuciyar ta babu dad'i ta koma ta zauna tayi tagumi kawai tana tuno fuskar sa a jiya da daddare yadda yake kallon ta da alamun maganar ta ta shige shi sosai. Furzar da iska tayi tana k'arewa d'akin nata kallo cikin rashin sanin abinda zatayi. Tashi tayi ta shiga band'aki tayi sabon wanka ta canja kaya ta saka dogon wando ta saka vest mai k'aramin hannu ta zuba turare a jikinta kafin ta d'auko abaya cikin kayanta ta saka a jikinta ta nad'a mayafin tayi kyau sosai cikin shigar ta d'auki zoben da ya bata a Cairo ta cire ta saka a daidai lokacin da Suhail ya kira number ta. D'aukar wayar tayi kafin tayi magana yace, "Ranki ya dad'e na iso, a ina zan same ki?." Rauda ta sauke numfashi tace, "Kazo kawai bakin apartment d'in nan zan fito." Ya amsa ta kashe wayar ta fito falon tare da kulle d'akin ta ta zare key d'in ta fito k'aramin falon ta dukka babu kowa ta fito babban nan taga hadiman ta ganin ta duk suka mik'e tsaye Jakadiyar tana fadin, "Barka da fitowa uwar gida ga mai martaba sarki katagum, takawar ki lafiya mara mai farar aniya, zuciyar ki wankakkiya fuskar ki wankakkiya. Allah yaja zamanin ki ya baki dukkan abinda kike so." Kanta taji ya fashe sosai tana jinjina dad'in mulki domin kuwa ba k'aramin girma taji ta k'ara ba fad'ar wad'annan kalaman da suke yi. Tace, "Zanyi tafiya zuwa wani waje amma bazan jima ba a kula da komai." Jakadiyar ta tace, "Zamu iya raka mai girma fulani?." Rauda ta girgiza kai tace, "A'a zanje ni kad'ai." "Allah ya dawo dake lafiya, ya tsare gaban ki da bayan ki, ya kare ki daga mak'iyan ki ya baki nasara da rinjaye akan komai." Amsa tayi ta fita Jakadiyar ta ta kulle b'angaren gabad'aya dukkan su suka fita. A daidai k'ofar fita daga apartment d'inta ta ga motar kai tsaye Jakadiyar ta da take bayanta ta buɗe mata baya ta shiga Suhail yaja suka fita daga gidan. Sai da suka fita sannan yace, "Barka da safiya ranki ya dad'e." Rauda tace, "an tashi lafiya." "Lafiya lau Alhamdulillah." Daga nan sukayi shiru yana jan motar duk a tunanin ta garin zasu bari. Gaban wani gate d'in gida taga yayi slow ya danna horn aka lek'o ganin shine aka buɗe masa ya saka motar a ciki sai da ya faka sannan ya juyo yana kallon ta yace, "Afuwa ranki ya dad'e ban miki bayani ba. Mai martaba yana cikin gidan nan ya sanar dani kar na fad'awa kowa yana garin nan har Abba ya d'auka yana Abuja, na sab'a umarnin sane sabida kece babu yadda zanyi na iya b'oye miki inda yake. Ki rok'a min afuwa a wajan sa nayi laifi." Rauda ta kalli gidan sai ta tuna tazo gidan a daren da Yaya Ummi ta rakota da daddare ta juyo ta kalle shi tayi murmushi tace, "Na gode." Murmushi yayi yace, "nine da godiya da aka amince min. In babu damuwa zan iya cewa wani abun matsayin abokin Mai martaba?." Rauda ta d'aga kai alamun eh yace, "Tsakani da Allah ranki ya dad'e yana tare da damuwa sosai yanzu maganar da nake yi akwai Dr Yasir ya saka masa drip a ciki sabida jikin sa babu k'arfi, da aka auna jinin sa bp d'in sa ya hau fiye da tunani shiyasa aka sama masa ruwa dan a samu ya sauka da wuri. Yana da damuwa ranki ya dad'e zuciyar sa a cushe take Hydar ne abokin shawarar sa yanzu babu shi ke kad'ai kika rage masa, dan Allah ki taimaki rayuwar sa kar ciwo ya kashe shi da k'arancin shekarun sa." Yadda yayi maganar a nutse sai ta sauke nunfashi cikin tausayin sa mai yawa da dana sanin abinda ta aikata ta girgiza kai tace, "in sha Allah. Na gode." Ya fito ya buɗe mata motar yace, "in kika wuce falon farko akwai na biyu dana uku, a cikin na ukun akwai underground nan zaki bi yana ciki." Kai ta d'aga ta nufi cikin kai tsaye zuciyar ta na bugawa. Babu kowa a falon farkon sai haske da hotunan sa da suke cikin glass gabad'aya falon adon farin glass akayi komai fari hatta kujera da carpet gasu karr kamar ba'a takawa. Ciki ta wuce kamar yadda yace ta sake ganin wani falon mai step d'in da zaka hau sama ta sake wucewa nan ta sake zuwa wani falon da yake da underground d'in. K'asa ta dinga yi tana bin steps d'in har ta k'araso wata doguwar hanya mai kyau da haske da mudubi ta ko ina da adon fulayoyi kafin ta iso falon. A zaune ta hango shi ruwan da yake shiga jikin sa ya k'are an cire Dr Yasir yana zaune yana had'a masa magani, "Assalamu alaikum." Ta fad'a cikin muryar mai dad'i Dr Yasir ya amsa yana juyawa yana kallon ta. Ganin ta ya saka Dr Yasir yace, "Barka da zuwa ranki ya dad'e." Kai ta d'aga bata ce komai ba shi kuma ya cigaba da had'a masa maganin. Maganin ya bashi yasha tana tsaye har lokacin kafin Dr ya tashi ya fita daga falon bayan yayi mata sallama cikin girmamawa. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta k'araso inda yake jikin ta a sanyaye tana kallon sa ganin ya rame a fuska da wuyan sa da k'aramar riga ce a cikin sa dogon wando. Kamar bai san da mutum a wajan ba ta zauna a gefen sa tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba wani wajan daban yake kallo fuskar sa a d'aure. "Sultan!." Ta furta a hankali tana kallon sa sai da ya rufe ido ya bud'e sunan da yadda ta fad'e shi sun shige shi sosai amma baya tunanin zai iya kallon ta. "Ya jikin ka?" Ta sake fad'a tana kallon sa amma bai ma kalle ta ba balle ya amsa mata. Ganin hakan sai ta zago ta dawo kusa dashi ta jawo stool d'in tsakiyar d'akin ta dawo dashi daidai da fuskar sa tace, "I'm sorry." Sai a sannan ya d'ago ido ya kalle ta suka had'a ido ta sauke nata k'asa sai ya sake d'auke kansa baice komai ba. Hannun sa ta rike duk da kirjin ta yana bugawa tana kallon hannun da babu agogo a jiki zanen bak'in shaidar sa ta fito ta kalle shi tace, "Kayi haƙuri Sultan." Hannun sa ya zame daga cikin nasa ya sake kawar da kansa gefe tare da dafe kanta baice komai ba. Sake komawa inda fuskar sa take tayi zatayi magana yace, "Please" ya furta a hankali yana dafe da kansa. Shiru tayi ganin ya dafe kai ta d'auke kai daga kallon sa tayi shiru tana wasa da hannun ta, a fakaice ya kalle ta gabad'aya khamshin turaren ta ya dame shi ya d'auke kai tare da sauke numfashi yana sake jin zafi a ransa jin khamshi na tashi a jikinta kuma a haka ta fito daga gida. Mik'ewa yayi sai kuma ya d'an tsaya jin kansa na ciwo kafin ya fara tafiya zuciya cikin d'akin da yake cikin falon, da kallo ta bishi sai ta d'auke kai sai take jin ina ma bata kawo kanta an wulaƙanta ba da tayi zaman ta ya neme ta da kansa duk da ba haka ba.  Kiran sallah taji na azahar a wayar ta ta kalla taga sha biyu da y'an mintina ta ajjiye wayar tana sauke numfashi. Ta jima a nan a zaune har ta tashi taga wata k'ofa a falon ta buɗe taga band'aki ne ta shiga tayi alwala ta fito ta sake d'aukar wayar ta ta nemi alqibla a falon ta nuna mata ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta kalli k'ofar da ya shiga bazata iya sake zuwa inda yake ba gwara ta tattara ta koma inda ta fito zaifi mata alkhairi akan ta zauna yana share ta. _Amma kuma bashi da lafiya_ zuciyar ta ta fad'a mata sai ta tashi ta nufi d'akin a sanyaye. A kwance ta same shi alamun har yayi sallah ya kwanta ya kashe hasken d'akin gabad'aya sai sanyin a.c da da yake tashi a hankali, d'akin ba sanyi sosai kuma babu zafi. K'arasawa tayi kusa dashi ta kalli fuskar sa sai taga idon sa a kulle ta juya ta fita ta k'yale shi. Yunwa take ji tana damun ta taga ragowar yogurt da ya rage ta d'auka tasha sai taji dad'i a cikin nata ta jingina da kujera tana kallon robar drip d'in da aka cire a haka itama bacci ya d'auke ta.       Yunwa ce ta sake tashin ta daga bacci ta tashi tana juya wuyanta ta sabida ya sage ta kalli tangamemen agogon bangon mai d'auke da hoton sa taga k'arfe uku daidai ta kalli falon tana neman abinda zata ci, tashi tayi duk k'ofar da ta gani sai da ta buɗe amma babu kitchen gashi tsoron komawa baya take dan girman gidan tsoro yake bata ga zurfi tsaf za'a yi mata wani abun ma bai ji ba. Yunwa ta dame ta sosai ji take kamar ana nad e mata hancin ciki ta zauna duk ta jigata sabida yunwa tana runtse idanunta, hannu ta saka ta kulle fuskarta kawai ta fara kuka, kukan yunwa da kukan k'in kulata da yayi. Duk abinda take yi yana tsaye a bakin taga yana kallon ta ya rigata tashi ya fito yaga tana bacci ya koma, fitowa yayi bata ji ba ya wuceta bai jima ba ya dawo da pack na abinci yazo kusa da ita ya mik'a mata tare da cewa, "Me kukan yunwa." D'ago fuska tayi ta kalle shi ta kalli hannun sa sai ta turo baki ta goge idanunta ta karb'a ta buɗe ta fara ci ko wanke bakin ta ma batayi ba sabida yunwa. Sai da ta cinye tass har lokacin yana tsaye a kanta ya hard'e hannun sa a k'irji yana kallon ta, kwarewa tayi ta fara tari ya bata ruwa ta karb'a tasha ta ajjiye pack d'in tana sauke ajiyar zuciya dan sai lokacin taji ta dawo daidai. Kallon kanta tayi sai a sannan taga babu roiling din mayafin da tayi sai hular kanta kawai tasan shine ya zare da tana bacci hakan ya saka bata damu ba ta sunkuyar da kai k'asa bai magana ba ya juya ya tafi. Da kallo ta bishi ta sauke ajiyar zuciya  tana murmushi ganin ya d'an samu lafiya ba kamar d'azu ba ya kuma ya d'an sarki rai fuskar sa bata kai d'azu d'aurewa ba. La'asar akayi ta sake tashi tayi alwala tayi sallah a falon tana zaune akan carpet d'in ya fito yayi wanka ya saka k'aramar riga fara da farin wando wanda ya wuce guiwa kad'an rigar mai k'aramin hannu gabad'aya hannun sa a waje yake. Mik'ewa tayi tana kallon sa shima ita yake kallo da idanun sa har sai da ta sauke nata k'asa ganin kallon yak'i k'arewa sai kuma taga ya juya ya nufi barin falon. Da hanzari ta bi bayan sa dan bazata iya zama ba taga ya koma wancan falon ya shiga wani d'aki ta zauna tana jiran sa. Ya jima sosai har ta gaji da zama ta tashi ta lek'a taga karatu yake yi ya tara uban littafai a gaban sa sai ta sake komawa ta kulle masa k'ofa. Sai da akayi magariba ya fito yana kallon ta ta tashi tana rik'e da bayanta ya sake komawa ta sake bin bayan sa. Tare sukayi sallah bayan an idar tana nan zaune a kan sallar ta sake jin yunwa tana damunta, kamar ya fahimta ya sake kawo mata abincin da Suhail ya tulo masa taci sosai ta sauke numfashi. Babu wanda yake magana a cikin su har akayi i'sha suka sake yin sallah bayan an idar ne tayi shafa'i da wutur shima haka kafin ta tashi ta fara nad'a mayafin ta ta gama tsaf ta kalle shi tace, "Kayi haƙuri nazo inda baka gayyace ni ba, na jure wulaƙancin naka na wani lokaci amma na kasa jurewa zan koma inda na fito" ta fad'a tana kallon sa tare da soka filled d'in jikin mayafin ta. Tashi yayi yazo gab da ita yana kallon ta sai ta tsaya daga abinda take yi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sauke numfashi amma bai daina kallon ta ba, a hankali ta kalle shi murya na rawa a tausahe tace, "Na baka haƙuri kak'i ka hak'ura" ta fad'a hawaye na sakko mata ta goge. Yatsu biyu ya saka ya d'ago fuskar ta yana kallon ta sai kuma yaja baya kad'an yace, "kinyi laifi ne?." Jin abinda yace sai tace, "Eh nayi, kamar yadda akayi min amma na hak'ura nake bada hakuri kuma ake wulaƙanta ni." Murmushi yayi mai sauti jin abinda tace ya girgiza kai dan yana mamakin ta gabad'aya bata jin shakkar fad'ar abinda yake ranta yace, "to me kike so ayi miki?." "Gida zan koma." "Ni na kawo ki?." "Suhail ne kuma yanzu zan kira shi ya mayar dani" ta fad'a tana d'aukar wayar ta da niyar kiran sa. Wutar gidan ce ta d'auke gabad'aya tayi k'ara ta saki wayar ta nufe shi a guje ta fad'a jikin sa ta kank'ame shi tana sake b'oye kanta a k'irjin sa. Ajiyar zuciya ya sauke babu ta yadda zai iya fushi da ita yana sonta son da bai son adadin yawan sa ba, yayi kewar ta kewar da bai san yawan ta ba, yana son kasancewa da ita fiye da tunanin ta. Cikin lokaci kad'an sai kuma hasken ya dawo ta buɗe ido a hankali tana kallon falon ta mik'e da niyar barin jikin sa amma ya rik'e ta ta baya yana kallon fuskar ta sosai. "Fada min haushina da kike ji" ya furta yana kallon ta cikin murya mai dad'i. Tayi shiru batayi magana ba dan yadda ya rik'e ta yana yi mata magana ya fara canja mata yanayi, dak'yar ta iya cewa, "Kaina kake nuna ko in kula akan lamarin na, gabad'aya baka tani sai a tashi a wuni baka neme ni ba bayan kasan kayi min laifi tun a baya amma baka damu da baka rarrashe ni balle ka bani haƙuri." murmushi yayi ya cize baki yace, "Ya kike so nayi miki Muwaddaty? Bani da nutsuwa ko kad'an, bani da wanda zai bani shawara ke kuma kin nuna bakya son zama dani bazan miki dole ba." Ta kalle shi shima ita yake kallo tace, "To ba kai bane baka son nazo inda kake in nazo sai ka share ni, tun ranar da Hydar yazo baka sake rarrashi na ba sai ma share ni da kake yi dan kawai baka so....."yatsan sa ya d'ora akan lab'b'an ta ya girgiza masa kai yana kallon idanun ta yana lumshe ido tare da bud'ewa. Shiru yayi kawai kallon ta yake yi ta sauke saukar da ido k'asa tana jin wani iri a zuciyar ta sai daga baya yace, "Muwaddaty abubuwa sun min yawa baki gani ba? Nida ke waye ya kamata ya yayewa wani damuwa?." Tayi shiru tana jin wani irin abu na zaga jikinta musmaman lokacin da ya dawo da hannun sa cikinta ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi cikin murya mai sanyi tace, "Nice, shiyasa nazo nace kayi haƙuri amma sai naga baka so ganina ba." Zip d'in doguwar rigar ta gaba ya sauke gabad'aya tayi k'asa vest d'in jikinta ya bayyana ya d'aga vest d'in yana shafa cikinta a hankali yace, "waye yace bana so na ganki?." Ta kwanta a jikin sa tana lumshe ido tace, "gashi nan ko kula ni kak'i kayi." Numfashi shima ya sauke yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "Nima kiyi haƙuri, shikenan?."  Sai ta shiga jikin sa sosai tace, "Iya nan na haƙura banda na baya." Yayi murmushi tare da yi mata kiss a goshi baice komai ba yana sake rik'e ta gam. "Ina sonki Muwaddaty." Ta rik'e shi kam tana jin soyayyar sa data binne tana tasowa amma bata amsa ba. A daidai kunnen ta yace, "anythings for me?."  Juya kanta take a k'irjin sa yayi murmushi ya zare hannun sa daga cikinta ya rik'e ta a jikin sa ya d'auke ta kai tsaye sai cikin d'akin da yake. Kwantar da ita yayi a hankali yana kallon idamun ta da yake a kulle yace, "I really missed you" ya fad'a yana kwanciya kusa da ita ya jawota jikin sa gabad'aya ta dawo saman sa shi yana k'asa, fuskar ta ya girgiza alamun ta buɗe ido ya goga hancin sa akan nata yace, "Buɗe idon ki." Kanta ta mayar jikin sa sai kuma taji yace, "Zina!." A hankali ta bud'e ido suka had'a ido duk da babu haske amma tana kallon hasken idanun sa ta shagwab'e fuska zaiyi magana ta hana shi ta hanyar jefa bakin ta cikin nasa dan bata son abinda zai dakatar dashi a wannan lokacin. Sai kuma taji nauyin aikata hakan musmaman da idon ta yake a buɗe tana kallon sa yana kallon ta tayi k'ok'arin zamewa ya hanata yana sake binta da idon sa da yake kashe mata jiki a ko wanne lokaci.......... The love birds 🐦❤️ [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *091*        Tare suka fito daga bathroom hannun ta rik'e da kanta da kuma bayan ta ta wuce kan stool d'in mudubi ta zauna ta kifa kanta a akn mudubin tare da furta, "Wayyo Allah na." Kallon ta yake ganin kamar bata da lafiya ya saka shi ya k'araso ya tsaya a bayan ta yace, "Baki da lafiya?." Bata d'ago ba ta d'aga masa kai alamun eh kafin ta d'ago tace, "Kaina na ciwo dai bayana da ya rik'e." "Let me call Dr" ya fad'a yana k'ok'arin wuceta ta rik'e hannun sa ta juyo ta kalle shi tace, "Zan ji sauk'i basai ka kira shi ba, dare yayi fa kalli kaga sha biyu har ta kusa; na gaji ne kawai." Da kansa ya mata alama da ta tabbatar tace, "Eh babu komai." Ta fad'a tana sake kallon kanta a mudubin ta gashi sosai bayan ta kamar zai cire tasha wahala a hannun sa ba kad'an ba, yadda marar ta ta dinga k'ullewa ta d'auka ma cikin zai zube. Kallon ta taga yana yi ta madubin sai ta sake sauke kanta k'asa ta kifa kai akan madubin tana murmushi, ya tako ya tsaya a bayan ta yana kallon gadon bayan ta da rabi yake a bayyane kasancewar towel ne a jikin ta. Tabbai ya gani guda biyu dogaye sun zagaya wuyan ta har kafaɗarta ya saka yatsan sa yana binsu a hankali. Kamar tafiyar maciji haka yake yi da hannun sa fatar ta hakan ya saka ta d'agowa suka had'a ido ta madubin yace, "Kinji ciwo?." Tasan tabon yake nufi sai tayi murmushi ta girgiza kai tace, "Ba ciwo bane." Da ido yayi mata alamar to meye. Ta sake yin murmushi tace, "Duka ne." Wara ido waje yayi ya sake kallon tabon ya sake kallon ta yaga tayi murmushi ta sunkuyar da kanta yace, "Duka fa." Ta d'aga kai tace, "Uhum. Baba ne ya zane ni lokacin da cikin nan ya bayyana duka jikina ya fashe, sauran tabon sun baje wannan ne dai dashi zan tafi lahira" ta fad'a tana d'agowa amma bata kalle shi ba. "Oh Allah!" Ya furta a bayyane yana lumshe idanun sa ya buɗe ya koma kan gefen gadon ya zauna yana kallon ta amma baice komai ba cimin tsananin tausayin ta. Jin yayi shiru sai ta share itama tana zaune bata motsa ba balle tayi magana wasa take da zoben hannunta ba tare da ta kalle shi ba. "Muwaddaty!." Jin yadda ya kira sunan ta sai ta kalle shi ya yafito ta da hannu alamun tazo inda yake ta taso tana takowa a hankali tana k'arasowa ta zauna kusa dashi tare da fad'in, "Cikina Sultan." Hannun ta d'aya ya rik'e ya d'ora daya akan cikin ta yace, "ciwo yake miki? Me kike ji a cikin?. Ki fad'a min na kira Dr" ya fad'a a rud'e yana kallon ta. Hannun ta ta d'ora akan nasa da yake kan cikin tana kallon sa tace, "ciwon kad'an ne basai yazo ba." K'aramin tsaki yaja ya d'auki waya zai kira Dr, bata hana shi ba ya kira aka d'auka yace, "Yasir kana clinic?." Shiru yayi alamun yana bashi amsa kafin ya kalle ta yace, "Ina da patient." A speaker ya saka wayar taji Dr yana cewa, "Me yake damun ta?." Ya kalle ta yayi shiru bai magana ba sai zuwa wani lokacin kafin yace, "Ciwon ciki." Dr Yasir yace, "Ranka ya dad'e sosai cikin yake ciwo? Wai dan nasan da wanne irin magani zan tawo mata dashi." Ya kalle ta suka had'a ido sai tace, "Ba sosai bafa Dr, kawai bana jin dad'i ne basai kazo ba yunwa ce ma." Kallon sa tayi taga ita dai yake kallo bai d'auke ido daga kanta ba sai ya yanke wayar tace, "Bafa ciwo bane ba daka sani baka kira shi ba, babu abinda zai faru tunda wad'acan ranakun suka wuce banyi miscarriage ba bana tunanin akwai abinda zai saka ni yanzu. Yunws ce kawai." ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.  Hannun ta ya rik'e yana murza goben da ya bata a Cairo yayi shiru na wani lokaci baice komai ba kafin yace, "Wanne lokaci?." Ta kalle shi tace, "Lokacin da Baba yayi min duka akan cikin, lokacin da Umma ta dinga min fad'a har tace bata yafe min ba, lokacin da nake confusing akan tsakanin ka da Aliyu waye mamallakin cikin nan. Rana ta k'arshe da Umma ita kanta ta d'auka cikin zai fita shine ranar da Mai martaba ya kira mu. Sultan tunda cikin nan bai fita a cikin wad'annan kwanakin dana lissafa ba bana tunanin zai fita yanzu, ban tab'a shiga tashin hankali a rayuwata ba kamar na wad'annan ranakun." Idon ta yake kallo tana magana sai yaga hawaye suna taruwa a ciki ya girgiza mata kai alamun kar tayi kuka ya furzar da iska yana sake murza yatsan hannun ta yace, "I'm deeply sorry Muwaddaty!." Batayi magana ba itama sai murmushi da tayi kawai ta d'aga kai tana kallon sama kamaar me neman wani abun. A kafaɗarsa ta kwantar da kansa ya zaga da hannun sa ya rik'e k'ugun ta hannun sa d'aya yana cikin nasa, kuka yaji ta fara a hankali kafin tace, "Na shiga tashin hankali Sultan, nayi dana sanin zuwana duniya gabad'aya." Numfashi ya sauke ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta yace, "Ban tab'a alƙawari na sab'a ba sai sau d'aya, shima a kanki ne nace wa mama na barki amma Abba ya bani zab'ina tunda yason ina sonki" yayi shiru yana sake kallon ta kafin yace, "Tunda na d'auki alƙawarin bazan barki ba Muwaddaty bazan tab'a barin ki ba kawai kafin nazo inda kike ne za'a jima but ina tare dake ko yaushe a kuma ko ina." Tana kallon idanun sa tace, "Nayi tunanin hakan, tun  can Cairo lokacin da kuka fito kai da Mama ina zaune naga kayi mata magana ta barka kazo inda nake na d'auka zaka yanke igiyoyi guda biyun ne sai naji ka furta ka mayar dani har yanzu ni matar kace, kafin na farga naga ka tafi tun a sannan na saka a raina kamar baza ka karya alƙawari ba amma daga baya sai kawai naga kayi min haka ne dan ka wanke min zuciyata amma bawai dan zaka dawo gare ni bane." Kai ya girgiza ya goge mata hawaye cikin muryar sa mai sanyi yace, "Bana alƙawari na sab'a Muwadda, in na barki a wannan lokacin da kika fara qaunata na cutar dake har abada Allah bazai yafe min ba kema kuma haka." Cize bakin sa yayi ya kulle ido ya buɗe yana kallon ta idanun sa sun koma jajaye itama kallon sa take. Matse hannun ta yayi a cikin nasa tana kuka tace, "Shiyasa na kasa fad'a a gida, zuciyata tana rawa ne wani b'angaren yace na sanar dasu ka sake ni wani b'angaren yace kar na fad'a tunda ka mayar dani duk da nasan mayarwar bata da wani amfani sabida Mama. Umma ta lura da bani da walwala ta tambaye ni nak'i fad'a mata har na b'ata mata rai tace bazata kuma tambayata ba." Ta sake kwanciya a kafaɗarsa tace, "A lokacin da abin ya faru badan Dr Khalifa ba ban san inda zanje ba ga security sunce saina fita ance musu ni mai laifi ce ga kaina yana min ciwo" ta fad'a da kuka tana cusa fuskar ta a kafad'arsa.  Shiru baiyi magana ba yana bubbuga bayanta a hankali shud'ewar wasu mintina kafin yace, "Haushin ki na farko dana fara ji kenan Muwaddaty, meyasa kika bi Khalifa bayan kin san bazan tab'a tafiya na barki ba? Meyasa kika bari Khalifa ya rik'e ki a lokacin da zaku bar wajan?. Kin san zafin da naji a raina kuwa?." "Bani da zab'i ne sai na binsa Sultan, in ban bishi ba ina zanje? Ban san kowa ba ban kuma san ko ina ba sai kai kawai gashi an raba ka dani ina zani?. Dole ce ta saka na bishi gidan sa kuma rik'e ni da yayi ban sani ba Sultan sabida bani da lafiya a lokacin." Shiru ya sake yi na wani lokaci yana sauke numfashin sa kafin yace, "Muwadda baki sanshi ba sai da kika je Cairo, meyasa kika amince har ya kaiki gidan sa? Da yayi miki wani abun fa?" Ya furta a kausashe yana d'ago da ita daga jikin sa yana kallon ta tare da rik'e hannayenta duka biyun. Idon sa take kallo ta saukar da nata k'asa tace, "Ni kaina hankalina bai kwanta ba sai da matar shi ta dawo, Sultan in ban bishi ba wa zanbi a wannan lokacin? Bani da kowa fa sai kai kad'ai ina zanje?." Kai yake girgiza mata yana rik'e da hannunta tana kallon sa ya cize bakin sa ya sauke ajiyar zuciya idanun sa sun tara ruwa kamar zaiyi kuka amma baice komai ba. Shiru ya sake ratsa su kafin yace, "Naji wannan. Meyasa kin san da aurena a kanki kike kula wancan banzan mijin k'anwar taki? Kina da aure fa kike sauraron sa hards maganar aure tsakanin ku, meyasa Muwaddaty?." Tace, "Sabida ban san da aure a kaina ba a lokacin na kammala iddar ka ta saki ukun da kayi min, kar ka manta a lokacin na d'auka kaine kazo ka bani takardar saki biyu ban san Aliyu bane ba. Ummana tana so taga nayi aure sabida abinda ya faru dani wata d'aya da yin aurena ya mutu na dawo gida da zama ana ta wayo dani a dangi da unguwa daman kwad'ayi ne da son abin duniya in ba haka ba ina kai ina ni?, harda wanda suke tarar Ummana face to face suna cewa Allah ya k'ara dalilin da ya saka na amince zan aure shi kenan." Kallon ta yake yi hakan ya saka tace, "Ban san ba kai bane ba, duk wani abu da zai tabbatar min kaine na ganshi a tare da Aliyu Sultan, hatta wannan zanen daka nuna min na hannun ka na ganshi a hannun sa. Ya kira ni Muwadda cikin voice d'in da kake fad'ar sunan, na fad'a maka komai dana san nida kai kawai muka san dashi ya fad'a taya zan d'auka ba kai bane ba? Hatta yadda kake hugging d'ina yayi" ta fad'a murya na rawa. "Subahanallah!" Ya furta yana cize bakin sa jin kalaman ta na k'arshe ya sauke numfashi mai k'arfi ya matse mata hannu sosai yana jin kamar ya goge kalmar da ta fad'a cikin tarihin rayuwar su amma bazai yu ba. Rauda ta kuma cewa, "Ba nice na haife ku ba dole na d'auka kaine yadda yayi min magana da rauni sai na sake tabbatarwa kaine Sultan domin ta ko wacce fuska a yanayin ka yazo. Dalilin dawowar sa rayuwata kenan da niyar aurena a karo na biyu bani da zab'in da ya wuce amince masa dan ni da farko ban so ba makaranta naso na koma Umma ta nuna min auren take so nayi shiyasa na amince." Ya sauke numfashi yana kallon sama yayi shiru itama tayi shiru tana goge hawayen idanun ta. "A ranar kika tsane ni ko?." Jin yadda yayi maganar sai ta kalle shi ya juyo shima ya kalle ta ta d'aga masa kai tace, "Tabbas a ranar naji ina ma ban tab'a sanin mai iri Sunan ka a duniya ba, nayi dana sanin sanin ka na kuma yi dana sanin mallaka maka kaina da nayi a wannan lokacin, na tsinewa zuciyata da ta fara son naji kamar na cire zuciyata na cillar sabida abinda nake ji a cikinta. Na haƙura na mik'awa Allah komai abinda ya sake b'ata min rai rushe gidan mu daka aiko ayi, na fusata sosai tsanar ka ta ninku a raina nake ji da ina da iko dana zo har cikin fadar da kake na tsinke ka da mari na fita. Hydar shine ya daidaita komai a lokacin amma duk da hakan ban daina jin haushin ka ba." Yayi murmushi kad'an yana kallon bango tare da lumshe idanun sa amma baice komai ba sai dai yana sauraren dukkan abinda take cewa. Shiru itama tayi ta goge idanunta ta mayar dasu ta kulle yana ajiyar zuciya. "Duka kinyi min hukunci ba'a kan laifina ba, bazan iya rabuwa dake ba Muwaddaty, bazan iya sakawa a yiwa kowa abinda Hydar ya saka ayi akan gidan ku ba balle ke, ko babu ke Umma da Baba ina musu kallon iyayena bazan iya ganin an yiwa wanda ya shafe su ba balle ke Muwadda" yayi shiru yana ajiyar zuciya idanun sa a kulle sannan yace, "Kika tsane ni kina jin haushina duka kuma bani nayi miki laifin ba, in na tuna kin tab'a tsana ta a duniya ina jin duniyar tayi min zafi" ya fad'a yana rik'e jijiyoyin kansa da suke harbawa da sauri sabida halin da yake ciki. Rauda tace, "Ban san ba kai d'in bane ba Sultan a ganina kabi umarnin Mama ne ka yanke duka alaqar dake tsakanin mu dalilin sakin da sake yi min kenan." Ya sake kallon ta na wani lokaci ko kifta idanun sa bayayi kafin ya janye idon sa ya sake sauke numfashi yace, "Tunda kika baro Cairo duk motsin ki na sani Muwadda, ko fita kikayi kikaje wani waje sai an sanar dani. Ko lokacin da na bar Nigeria na koma Bahrain da zama ina bibiyar ki, abinda akayi min ya karye da tasirin addu'a da kuma tasirin aure da naji ance zakiyi, hankalina ya tashi sosai har sai da na dawo Nigeria shine na saka aka d'auko min ke Muwaddaty." Jin yayi shiru sai sake matse ta da yayi a jikin sa ya sakata sauke ajiyar zuciya itama kusan minti biyu suna a haka kafin yace, "Amma da kika zo sai naga kin canja kina ta min fad'a da rashin kunya na rasa gane me kike nufi Muwaddaty, a wannan lokacin banyi niyar maki komai ba wani dalili ne ya gifta har hakan ta kasance." Ta kalle shi tace, "wanne dalili ne?." Ya sauke numfashi ya kalle ta  ya rik'e fuskar ta yana kallo yayi shiru kamar bazai kuma magana ba. Har ta fitar da rai bazai ce komai ba sabida d'aukar lokacin da yayi baice komai ba kafin ya kai bakin sa idanunta yayi musu kiss kafin ya sake rik'e hannunta yace, "Ranar da na sake sanin ki a karo na biyu a Cairo Muwaddaty wani ciwo ya same ni wanda bazan sake iya sanin wata mace ba shine dalilin wannan ciwon da kika ga nayi." Rauda ta mik'e daga jikin sa tace, "Amma wannan ciwon da aljanu yayi kama fa, yadda nake maka addu'a kana firgita aljanu ne." Yayi murmushin takaici yana girgiza kansa ya kalle gefe guda d'aya ya sake yin shiru kamar bazai ce komai ba kafin ya sake kallon ta yace, "Aikin aljanun ne Muwadda, duk dan a raba ni dake." Rauda tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma mutane basu da tausayi da imani, ina ruwana a wannan lamarin da za'a cutar dakai? In ba'a so ka zauna dani basai ka rabu dani ba lallai sai an cutar dakai?. Ni na rasa abinda mutane suke nema a duniya suka mayar da cutar da d'an uwan su musulmi ba koman komai ba." Jin kalmar da ta fad'a mutane basu da tausayi da imani sai ya sake yin murmushi yana sauke numfashi yana kallon hannunta kamar me ganin wani abun a hannun nata dan ya kula lokacin da Abba ya fad'i wasu maganganun a taron da akayi duk bata ji ba da alama bata hankalin ta a lokacin kafin yace, "Mama ce!" Ya fad'a yana kallon ta sai yaga ta sauke idonta k'asa bata ce komai ba. Murmushi yayi yana jin kansa na mugun ciwo amma baya so yayi shiru yace, "Inda tasan akwai idda a kanki a wannan lokacin saki uku zata saka ayi ba saki d'aya ba, dogoranta akwai aikin shine ta amince da saki d'aya" ya fad'a yana murmushi kana kallo kasan murmushin takaici ne da bakin ciki. Shiru ya sake yi itama tayi shiru aka rasa mai magana a cikin sa yayi baya ya kwanta ya dafe kansa da guda hannayen sa yana ji kansa yana juyawa amma yafi so ya bayyana mata komai ko hankalinta zai kwanta ta daina jin haushin sa shiyasa ya zab'i ya cutar da kansa ta hanyar yin magana mai tsaho badan yana so ba. "Naso na sanar dake a can ban samu dama ba Mama tazo, daga nan ban sake samun lafiya ba sai da naje Madina daga Bahrain nayi addu'a a Rauda nasha maganin karya asiri da dama a can, manyan malamai suka bani magani da addu'ar tsari a wannan lokacin na fara jin sauk'i a jikina ina jin son dawowa gida yana shiga raina a hankali." Shiru ya sakeyi ta kafa masa ido tana kuka sosai yana jinta amma bazai hanata ba shima kukan yake so yayi hakan ya saka shi yin shiru kawai baice komai ba. Ya sake d'aukar dogon lokaci kafin yace, "Ranar da abin ya faru shine ranar da aikin ya karye a kaina gabad'aya, a sannan na tabbatar na samu lafiya amma sai kika d'auki abin ba daidai ba, kika kirani mazinaci Muwaddaty, har kika d'auki hannu kika mare ni." Ta kalle shi yana kwancen idanun ta suka cigaba da zubar da ruwa zatayi magana ya d'aga mata hannu ya sake tashi zaune ya hard'e hannayen sa waje d'aya yana kallon k'asa kafin yace, "Naji zafin kalmar Muwaddaty ba'a tab'a kirana da makanmanciyar ta ba tunda nake a duniya sai a kanki, banji ciwo da zafin marina da kika yi ba amma naji zafin kalmar ki, naji b'acin rai sosai a ganina kina sane baki da wata hujja kin fad'a ne dan ranki yana b'ace akan abinda nayi miki. Daga ranar nace bazan sake neman ki ba tunda kika ce min haka......" yayi shiru ya furzar da iska daga bakin sa ya kulle idanun sa na wani lokaci. Shiru ya sake ratsa su sai jan numfashin Rauda ake ji ya juyo ya kalle ta ya d'auke kansa ya sake yin shiru kamar bazai yi magana ba kafin yace, "Ina sonki dalilin sonki ya saka na kasa daina neman ki, na shirya ba tare da kowa ya sani ba na tawo gidan ku amma sai na kasa zuwa sbd kunyar su Baba, a nan naga kannen ki k'aramin Khalil shine yake fad'a min abinda ya faru." Ta kalle shi shima ya kalle ta sai yayi murmushi ya d'ora hannun sa kan cikinta ya matso sosai kusa da ita har tana jin numfashin sa mai zafi da yake fita ya dafe kai da hannu d'aya, hannun sa ta cire ta d'ora akan fatar goshin sa taji zafi sosai jijiyar kan tana ta harbawa ta kalle shi taga ya had'd'iye yawu yace, "hankalina ya tashi da naji yace Baba yana dukan ki dalilin zuwana kenan dan nasan nine silar komai." Kai ta sunkuyar hawayen ta na zuba akan hannun sa ya shafi hannun sa yana murza ruwan hawayen nata yayi shiru baice komai ba tana kuka tace, "Ban d'auka akwai auren ka kaina ba a wannan lokacin Allah ya sani, banyi dana ci maka fuska ko naci mutuncin ka ba; wallahil azim da gaske na d'auka na aikata Zina ne shiyasa hankalina ya tashi na rasa me yake min dad'i. Ban tab'a sanin kowa ba sai kai ka rabu dani kuma na ake sanin ka sai nake jin k'yamar kaina na gwammace ma wai daban ne ba kai ba. Kayi haƙuri!" ta fad'a tana kuka sosai ta kifa kanta akan hannun sa. Murmushi yayi yace, "Na zama silar abubuwa da yawa a rayuwar ki Muwaddaty, tun farkon shigowata rayuwar ki abubuwa suke faruwa dake marasa dad'i, sau da dama ina jin ina ma ban shigo rayuwar ki ba na barki ki huta kamar kowa amma k'addara ta riga fata. Abinda ya sake k'ona min rai na rantse da Allah akan ban sake ki ba amma kika shafawa idanun ki toka kina ganin kamar zan rantse akan k'arya ne sabida wani burina." "Kayi haƙuri, dan Allah ka yafe min wallahi banyi ina sane ba duka nayi ne dan kare mutuncin kaina amma bawai dan na wulaƙanta ka ba. Kayi haƙuri ka yafe min dan Allah!." Yayi murmushi kad'an jin yadda take kuka ya cize baki yace,  "Akan gaskiyar ki kike Muwaddaty banga laifin ki ba ina fad'a miki abubuwan da banji dad'in su bane amma badan ina jin haushin ki ba." "Kaima akan gaskiyar ka kake Sultan nice na kasa fahimtar ka duk da dole kaina ya kulle sabida abubuwan da suka faru bazan yi saurin fahimta da wuri ba. Kayi haƙuri ka yafe min dan Allah. Ka kuma yi min duk abinda kasan zaka wuce akan marin da nayi maka wallahi nayi dana sani." Fatar cikin ta ya murza yana murmushi kad'an amma bai ce komai ba tace, "Kanka akwai zafi sosai fa, ka daina maganar ka huta dan Allah kar ya jawo maka matsala." "Rabon samun abinda yake cikin ki shine silar faruwar duka wannan k'addarar. Tun farkon had'uwa ta dake abinda ya faru wanda Mama tayi miki ko ni nayi miki dan Allah ki yafe mana dukkan mu." Kai take girgizawa tace, "Ka daina rok'ona Sultan ni ya kamata na roƙe ka afuwa nayi maka abubuwa da yawa, na kira ka da kalma mara dad'i na jefa ka da munanan kalamai sabida rufewar idanuna, na d'aga hannu na mare ka matsayin ka na shugaba ban duba wannan ba, kayi hak'uri ka yafe min Sultan bazan sake aikata makanancin haka ba in sha Allah." Janta yayi zuwa jikin sa ya rungume ta sosai a jikin sa ta sake fashewa sosai da kuka yana shafa fatar bayan ta yace, "Ya isa ki bar kuka, amma ki yafe min ki yafewa Mamana, ki yafewa Aliyu ma Muwaddaty dan Allah." "Ni na yafewa kowa ma har Hydar na yafe masa, kaima ka yafe min." Jin ta ambaci Hydar sai ya matse ta a jikin sa yace, "Ina son Hydar Muwaddaty, ina Qaunar Hydar, ban saba da kowa ba sai Hydar, bani da aboki sai Hydar, bani da d'an uwa sama Hydar. Shine abokin shawarata shine abokin kukana, amma Hydar......!" Sai ya kasa maganar ya kulle idanun sa yana furzar da iska sannan yace, "Har yanzu ina son shi." Tausayi ya bata sosai ta d'ago daga jikin sa tana kallon sa ganin gabad'aya ya canja tace, "kayi haƙuri duk tsanani yana tare da sauk'i, ka yiwa Hydar addu'ar shiriya da fatan samun nutsuwa da sassaucin abinda yake zuciyar sa. Nasan zaka ji ciwo sabida nima da Hydar na sanka amma kayi haƙuri, haka rayuwa take koda hakan bta faru ba wata rana zaka mutu ko shi ya mutu dole wani ya tafi ya bar wani a cikin ku. Ka kwantar da hankalin ka kaga jinin ka ya hau saka damuwa ba naka bane ba. Na tabbatar shima yana sonka wani abun ne kawai ya rufe masa ido amma in kana mas addu'a sai kaga ya dawo Hydar d'in da ka sani a baya." Numfashi ya sauke yaji dad'in kalaman ta sosai a ransa ya matse ta sosai ya kulle ido yace, "Ina sonki Muwaddaty, ki daina nisa dani in ba haka ba zan iya rasa raina abubuwa sunyi min yawa kece maganin damuwana. Dan Allah ki zauna tare dani." "Ina sonka Sultan, ina sonka sosai bzan sake yin nesa da kai ba in sha Allah, kullum ina tare dakai daga ban har aljanna." Yayi murmushi ya sassauta rik'on da yayi mata yana kallon ta ya share mata hawayen fuskar ta da hannu yayi mata alamun da tayi murmushi tayi shima yayi murmushin kafin tace, "Yunwa nake ji, kaina na ciwo." Mik'ewa tsaye yayi sa kuma yayi saurin dafe kansa tare da dafa bango tayi hanzarin Mik'ewa itama tace, "Ka zauna Sultan baka da lafiya." Kai ya girgiza ya kalli agogo yaga k'arfe d'aya na dare harda wani abun ya k'arasa inda kayan sa suke ya buɗe kaya ne a ciki kamar a gidan yake rayuwa ya d'auko doguwar rigar sa ya k'araso ya saka mata towel d'in ya fad'i ya d'auke ya saka mata hular ta da tazo da ita ya rik'e hannun ta yace, "muje na miki girki." Jan hannun ta yayi ta turje tace, "Baka da lafiya Sultan, ka dawo ka zauna dan Allah kanka yayi zafi sosai fa." Kai ya girgiza mata ya sake jan hannunta ta sake turjewa ya juyo yana kallon ta ya kama k'ugu zatayi magana ya d'auke ta cak suka fita daga d'akin kai tsaye kitchen d'in gidan suka nufa. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *093*            Tana jin fitar Suhail ta fito ya kalle ta yaga ta b'ata fuska suka had'a ido sai ya d'aga mata gira yaga ta sake d'aure fuska sai yayi dariya kad'an ya tashi ya d'auki abincin da Suhail ya buɗe yaga abinci ne har kala uku, kallon abincin yaga tayi alamun sun bata sha'awa ya d'auki wanda yaga tana kallo ya kalle ta taga tana kallon sa sai ya mik'a mata hannu ba musu ta d'ora hannun ta man nasa ya zaunar da ita a cinyar sa. "Baza kisha tea ba?." Ta kalli abincin tace, "Wannan kawai nake so naci." Baiyi musu ba ya ware spoon din da yake nannad'e a tissue ya fara bata tana ci sai yaga ta tsaya kuma tana kallon sa tana yamutsa fuska, da ido yayi mata alama da ya dai sai ta mik'e daga jikin sa tayi wajan sink a guje ta fara shara amai. A hankalin sa ya tashi sosai ya k'araso inda take ya rik'e ta har ta gama aman ta d'ago ta dafe kai ya rik'o ta suka dawo ta zauna tace, "Abincin babu dad'i." Asad ya bita da kallon tausayi yace, "Sannu." Ta kwanta a jikin sa tace, "Ina jin yunwa Sultan amma bana son duka wannan abincin." "Me kike so?." "Farfesun dankali da hanta." Waya ya d'auka zai kira Suhail ta rik'e wayar tace, "Ni kai nake so ka dafa min." Wara ido yayi yace, "Muwaddaty babu komai na girki a nan taya zan iya miki abinda kika ce?." Kawai sai ta fashe da kuka tana fad'in, "ni shi nake son ci in banci ba zan iya mutuwa" ta fad'a tana dukan k'irjin sa tana kuka. "Oh my god!" Ya furta a bayyane kafin yace, "Is okay!." Suhail d'in ya kira daga can b'angaren yace, "Allah ya taimake ka." "Suhail potatoes nake so." Suhail mamaki ya kama shi yace, "Ranka ya dad'e akwai dankali a abincin dana kawowa mai martaba." Asad yaja tsaki ya kashe wayar ya rubuta masa text dan ya fahimci baya ganewa. Kuka take yi har lokacin yace, "Ya isa mana Muwaddaty yanzu Suhail zai kawo." Tace, "Ni kai nake so ka dafa min." Kai ya d'aga yana jiran kiran wayar Suhail. Tsaki yaja ganin mintina biyar Suhail baizo ba ya tashi ya kwantar da ita yace, "Ina tare da Suhail kar ki fito" yana fad'a yayi gaba da sauri. A falon suka had'u da Suhail ya shigo yaja tsaki yana kallon Suhail yace, "Tuba nake ranka ya dad'e,  akwai abinda ya bani wahalar nema shiyasa." Kitchen ya wuce dole Suhail yabi bayan sa ya same shi ya hard'e hannu a k'irji Suhail ya ajjiye kayan yana kallon sa amma baiyi magana ba. "Ranka ya dad'e akwai abinda ake so?." Asad ya kawar da kai ya dawo da kallon sa ga Suhail yace, "Dafa min zakayi." Suhail ya kalli dankalin da yake a leda yace, "An gama. Soyawa za'ayi ko farfesun sa za'ayi?." "Na k'arshen" ya fad'a yana kallon sa Suhail yace yanzu za'ayi a gama. Suhail ya d'auko wuk'a yana feraye dankalin Asad yana tsaye yana kallon sa ganin yana yi a hankali, wayar sa da take hannun sa yaji tana k'ara yaga sunan ta ya dafe kai yace, "Oh Muwaddaty! Suhail kayi sauri mana tana jin yunwa babu abinda taci fa" ya fad'a ba tare da ya d'auka ba ya ajjiye wayar ya d'auki wuk'a shima yana yin yadda yaga Suhail d'in yanayi. Suhail dariya yake b'oyewa  ya yanka dankalin ya d'auko kayan miya daman a markad'en su suke ya d'auki tukunya ya d'ora akan gas ya kunna nan da nan ya fara had'a mata abinda take so. Asad yana tsaye yana kallon sa ya k'agu a gama ya kai mata ya kalli Suhail yace, "I'm coming" ya fad'a yana ficewa Suhail ya kyalkyale fa dariya harda rik'e ciki. Ya jima yana dariya sosai domin yadda Asad din ya rud'e shine abinda ya bashi dariya yagirgiza kai yace, "Lallai a gaida mace, yanzu badan ni ba ko taya zai iya girki oho, nidai nasan babu abinda ya iya sai had'a coffee shima bai jima da iyawa ba da muna makaranta sai dai a dafa a bashi." Motsin sa yaji a bayan sa hakan ya saka shi yin shiru Asad ya k'araso yana kallon tukunyar Suhail yana juyawa. D'an tsaki Asad yayi yana kallon sa yace, "in banda dole ina ita ina cin abincin wannan." Suhail ya sake fashewa da dariya kafin yace, "Afuwan ranka ya dad'e an kusa gamawa." Yana nan tsaye Suhail ya gama ya d'auko bowl ya zuba a ciki ya saka spoon yace, "An gama ranka ya dad'e." Asad ya karb'a yace, "Allah yasa da dad'i, jira ni" ya fad'a yana sake fita Suhail yayi murmushi yana cin wanda ya rage dan sosai girkin nasa yayi masa dad'i. Tana kwance ya kai mata ta tashi zaune ta karb'a tana murmushi tace, "Na gode Sultan" ta fad'a tana fara ci. D'an yamutsa fuska tayi tace, "Yayi yaji, amma babu laifi ya d'an yi dad'i" ta fad'a tana ci. Yana zaune yana kallon ta har ta cinye tass ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya koma wajan Suhail ya ganshi a falon a zaune. "Ka cika yaji" ya fad'a yana kallon sa Suhail da ya mik'e tsaye yayi murmushi ya sosa kai yace, "Afuwa ranka ya dad'e, a haka na siyo kayan miyan wataƙila suna cika yaji." Asad yayi murmushi yace, "Na gode Suhail, banda kai ba ban san ya zanyi da ita ba."  Suhail yayi murmushi yace, "Haba ranka ya dad'e meye abin godiya?." Asad yayi murmushi ya dafa kafaɗarsa sai kuma yanayin sa ya canja alamun ya tuna Hydar. Suhail ya sassauta murya yace, "Sai haƙuri ranka ya dad'e, dukkan matakin nasara a rayuwa akwai qalubale, qalubalen kuma shine sirrin nasarar a rayuwa gabad'aya." Asad ya d'aga kai kafin ya juya ya koma shi kuma ya fita. Lemo ya same ta tana sha ya zauna kusa da ita ya nuna mata leda ta buɗe taga undies ne sama da goma a ciki harda doguwar riga ta kalle shi tace, "A ina aka samo?." Tab'e baki yayi ya wara hannun sa alamun bai sani ba tace, "Har kwana nawa zanyi a nan ne na gansu da yawa?." Nan ma baiyi magana ba ta kalle shi sai ta d'auki ledar tace, "Bara naje na saka baa......." da baya ya dawo da ita ta fad'a jikin sa gabad'aya ya girgiza mata kai alamun A'a. "Allah Sultan bana jin daɗin zama haka" ta fad'a yana kallon sa shima kallon ta yayi ya rad'a mata abu a kunne tayi dariya ta kifa kanta a k'irjin sa tana b'oye fuskar ta. "Ina kika samo Sultan?" Taji ya tambaya a sama ta kalle shi tace, "Sultan shugaba kai shugaba ne a ko ina, nima shugabana ne kai." Tab'e baki taga yayi sai ta kalle shi tace, "Ko baiyi maka ba?." Ya juya idanun sa yace, "It's not a romantic name." "Wanne kake so nace?." Ya cizi bakin ta yayi murmushi ganin sai ta sake kwanciya a jikin sa shima ya rik'e ta. Wayar ta taji tana k'ara ta d'ago ta mik'a hannu ta d'auka ta kalli wayar ta kalle shi tace, "Kaga number outside country ce." Ya kalla yaga number Saudia ce yace, "pick it." Ta wara ido tace, "Na sani ko scammers ne? Wa nake dashi a k'asar waje?." Da kai yayi mata alama da ta d'auka tana kallon sa ta d'aga wayar ta saka a speaker. "Rauda Umman kice!." Jin muryar Umma a cikin wayar sai ta zabura ta mik'e daga jikin sa ta zauna tana rik'e da kafad'arsa sa tace, "Ummana?." Umma tace, "Na'am Rauda, kinga number Saudia ko? Ai jiya muka tafiya gabad'ayan mu yanzu haka muna Madina." Rauda ta kalle shi sai taga ba ita yake kallo ba tace, "Umma Saudia kuma? Wai da gaske Ummana kece nifa gani nake kamar bake bace ba." Muryar Yaya Ummi taji tana cewa, "Sai nayicmagana zaki tabbatar itace?." "Lahh Yaya Ummi? Harda ke? Nifa kun kulle min kai dan Allah kuna ina?." "Ke Rauda wallahi da gaske muna Madina gabad'aya y'an gidan mu keda Rahma ne kawai babu." Rauda tace, "Amma shine zaku tafi ko a sanar dani ai da nazo munyi sallama ko?. To wai waye ya biya muku dukkan ku kuka tafi ban sani ba?." Yaya Ummi tace, "Mijin ki mana, akwai wanda zai biya mana ne in bashi ba Rauda?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalle shi sai ya d'aga mata kai tace, "Amma Yaya Ummi ban sani ba." "Mijin kine yace kar mu sanar dake shiyasa mukayi shiru, yanzu kin ganmu har mun fito daga Rauda munyi gaisuwa a kabarin annabi mun koma masaukin mu." Rauda ta lumshe ido hawaye suna sakko muryar ta na rawa tace, "Har su Yayar mu?." Yaya Ummi tace, "Na fad'a miki gabad'ayan mu ne, kin gan mu zaune ma gama cin abincin mu kenan." Rauda ta fashe da kukan farin ciki Yayar mu da take jin komai tace, Kaji min Rauda da shashanci, to meye na kukan keda zakiyi farin ciki ki taya mu godiya sai ki fara kuka kuma?." Datse kiran Rauda tayi ta kwanta a k'irjin sa tana kuka sosai, shiru yayi yana sauraron ta dan yasan babu lallai ta daina in yace ta daina tana jikin sa baice mata komai ba. Sai da tayi mai isar ta sannan ta d'ago ta kalle shi tace, "Shine ko ka fad'a min." Yayi murmushi yaja kumatun ta amma baice komai ba. Bud'e baki tayi zatayi masa godiya ya d'ora hannun sa bakin ta ya girgiza kansa yace, "Bana son jin komai." Rauda tace, "Addu'a zanyi maka." "Kiyi a zuciyar ki. Tashi muyi sallar la'asar" ya fad'a yana sauke ta daga jikin sa ya rik'e hannun ta suka shiga d'aki. Alwala sukayi sukayi sallah ita dai har suka idar ji take wani iri wai iyayen ta da y'an uwan tane duka a Saudia ta dalilin ta, me ya kai wannan dad'i da farin ciki a duniya? Ace ta dalilin ka iyayen ka sunje Saudia ai abin murma ne. Yana lura da ita ganin zata sake yi masa kuka ya saka yace, "Bana son kuka Muwadda kin sani." Tace, "Farin ciki ne yayi min yawa Sultan, na rasa inda zan saka raina sabida farin ciki ji nake kamar bani bace. Ta dalilina iyayena suna Saudia sai naji kamar ana wanke min zuciyata sabida farin ciki Sultan shine yake sani kuka." Idanun take gogewa ta matsa kusa dashi ta kwanta akan cinyar sa bai hanata ba ya fara karatun alkur'ani a bayyane ba tare da alkur'anin ba. Nan da nan ta d'auka itama suna yi tare a hankali duk da kira'ar ba iri d'aya sukeyi ba amma yana k'ok'arin yin irin tata suna tafiya a hankali. Sunyi sama da izu biyu a haka sai da yaji muryar ta tana rawa zatayi masa kuka ya saka shi ya dakata yace, "Haddar ki ta zauna sosai, kina ganin zaki iya national world Quran competition?." Da sauri ta tashi daga kan cinyaar sa tana kallon sa tace, "Zan iya Sultan, shine burina ina so nayi koda bazan ci ba ace na shiga shima nasara ne." Ya girgiza kai alamun gamsuwa ya dawo da ita jikin sa ta jingina da kafad'ar sa yace, "Zakiyi." "Thanks you Sultan. Allah ya kare min kai a duk inda kake, ya yaye maka dukkan damuwar da take zuciyar ka, ya saka maka da gidan aljanna yasa mu rayu tare nida kai a can. Ina sonka Sultan" ta fad'a tana jikin sa baice komai ba sai sake rik'e ta da yayi. Itama shiru tayi bata ce komai ba sun d'auki lokaci a haka akwai hango en gidan su a Saudia take yi taji yace, "Naso na had'a dake ku tafi gabad'aya sai na fasa" ya kalle ta yace, "Maje tare dake ko?." Ta girgiza kai tana murmushi shima murmushin yayi domin farin ciki ne kwance a kan fuskar ta daka gani zaka gane basai ka fad'a ba. Shiru tayi tana murmushi ita kad'ai ganin ta a farin ciki saka shi farin ciki yake sai yaji dukkan damuwar sa tana yayewa kamar bashi ne wanda yake da damuwa a kwanakin baya ba.  Sun jima suna a haka babu mai magana a cikin su ko wayar sa baya d'auka in an kira sunyi shiru basa magana. Cikin ta taji yana shafawa ya kalle ta sai ta mik'e ta jawo abincin tace, "Tunda kaci dan kad'an banga ka kuma ci ba" ta fad'a tana buɗewa takai bakin sa tace, "Kaci abinci." Bai mata musu ba yaci tana yi tana d'auke kanta daga kan abincin dan bata son khamshin hakan ya saka ta tashi ta d'auki ledar kayan ta shiga d'aki. Bayan sallar i'sha tayi wanka ta saka riga da wando na bacci wanda ya siyo mata a cikin kayan ta saka hula sunyi mata kyau shima ya saka nasa riga da wandon suka fito suna zaga cikin gidan hannun sa na sark'e da juna. Kallon gidan take tana girgiza kai tace, "Sultan!." "Sultana" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba tace, "Ban tab'a ganin gida irin wannan ba tunda nake." Yayi murmushi suka tafiya yace, "Badan Abba ya d'ora min nauyi ba da a nan gidan zamu zauna." "Tsarin ginin gidan larabawa akayi gabad'aya." Baice komai ba suna cigaba da tafiya tace, "Wai kuna waya da Dr Khalifa kuwa?." Cak taga ya tsaya ta kalle shi sai taga ya canja gabad'aya kamar ba shine yake murmushi ba sai jikin ta yayi sanyi tace, "I'm sorry." Tafiya suka cigaba da yi bata ce komai ba shima baice ba. Kallon sa tayi taga har lokacin fuskar a d'aure take sai tace, "Sultan yaushe zan fara makaranta? Ina son zama y'ar jarida." Banza yayi mata kamar baiji ba suna tafiya har ta fitar da rai zai amsa sama da mintina goma kafin taji yace, "Ki haƙura." Ta kalle shi jin abinda yace sai ta sauke kai k'asa bata sake cewa komai ba. Gama zagayen sukayi suka zo zasu koma ta tsaya yana kifta masa ido ya kalle ta tace, "Na gaji, ka goya ni." Cikin ta ya kalla itama sai ta kalla sai tace, "Bafa abinda cikina zaiyi." Yak'i magana ta fara bubbga k'afa tana cewa, "Nidai na gaji ka d'auke ni bazan iya tafiya ba." Hard'e hannu yayi a k'irji yana kallon ta kamar bazai saurare ta ba sai kuma ya sunkuya ya d'auke ta suka cigaba ciki. Har cikin d'akin ya ajjiye ta baiyi magana bai kuma yi murmushi ba ya juya ya fita, biyo bayan shi yayi ta same shi a zaune yana danna waya da alama aiki yake yi ta k'arasa inda yake ta wara hannayen sa ta shiga ciki ta mayar ta rufe ta kwanta a jikin sa. Baice mata kanzil ba ya cigaba da danna wayar sa dan yasan ba yunwa take ji ba taci abincin da Suhail ya kuma kawo musu, "Sultan!" Ta furta a hankali tana kallon sa. Bai kalle ta ba ta kuma cewa, "Sultan nayi maka laifi?." Nan ma baice komai ba ta sauke numfashi tace, "Kayi haƙuri." "Kar kiyi min kuka" ya fad'a bai kalle ta ba jin muryar ta fara rawa ta mayar da hawayen ya cigaba da abinda yake yi. Sun jima a haka kafin yace, "Nasan kin san Khalifa har kina da number sa meye naki da zaki tambaye ni? Tare kika ganmu ko?." Ta d'ago ta kalle shi tace, "Kayi haƙuri ban fad'a da wata manufa ba, Khalifa ya taimake ni kuma muna zumunci da matar sa. In baka son hakan zan daina." K'aramin tsaki yayi baice komai ba ganin hakan duk sai jikin ta yayi sanyi tace, "Kayi haƙuri dan Allah bazan sake yin maganar sa ba." Nan ma bai kulata ba tayi shiru bata ce komai ba shima kuma baice ba. Sun jima a haka babu wanda yake magana sai danna waya da yake yi ita kuma tana kwance a jikin sa. Wayar tace tayi k'ara ta d'auka ba tare da ta bar jikin sa ba ganin Rahma ce take waya tace, "Hajiya Rahma." Rahma tace, "Anty Rauda nida wallahi fushi nake dake har yanzu baki zo ba gashi su Umma sunyi tafiya sai ni kad'ai." Rauda tayi dariya tace, "Kiyi hak'uri ki daina fushi in sha Allah zanzo gidan, bazata zan miki sai dai kawai ki ganni." Rahma tace, "Allah ya kawo ki. Shima jiya yake cewa kink'i kizo mana ko sau d'aya nace nasan kina hanya yace shi ai yayi fushi." Ta sake yin murmushi  tace, "Ki basa haƙuri zaku ganni in sha Allah in nazo sai kun kore ni." "To Anty Allah ya kawo ki. An yiwa su Umma da Inna abin alkhairi fa Allah ya biya mai martaba ya saka masa da gidan aljanna. Kinga yadda y'an uwa suke murna da wannan abun da ya faru kuwa? Ai Anty Rauda addu'ar da kika sha dake dashi ba y'ar kad'an bace." Rauda tace, "Amin Rahma. Ban ma sani bafa ni sai yanzu da Yaya Ummi take sanar dani, ashe har sun kwanaa d'aya." "Wallahi kuwa Anty, abu ai yayi mugun dad'i. Harda Baba malam fa." Rauda tace, "Au harda shi? Ni da yake ban ma gama jin labarin ba na kashe." "Wallahi harda shi." Rauda tayi murmushi tace, "sun tafi sun bar mu daga ni sai ke." Rahma tace, "Lahh nima passport dina ne bai fito ba da ya fito zamu tafi nida shi." Rauda tace, "Ma sha Allah. Ina taya ki murna." "Na gode Antyna." Daga nan sukayi sallama ta yanke wayar tana fad'in, "Nidai naga ranar da zanje gidan ki Rahma, in sha Allah zanje ko zan huta da gorin nan da ake min." Gaban ta ya fad'i ganin kallon da yake mata ta had'd'iye yawu tana kallon sa yace, "D'aga ni." Jin yadda yayi maganar ya saka ta mik'ewa ya tashi ya shiga d'aki ta bishi da kallon mamaki ganin ya sake birkicewa. Sai da ta bari ya d'an jima da shiga sannan ta tashi tabi bayan sa ta ganshi a zaune yayi shiru ba tare da  yana wani abun ba. Ta zauna kusa dashi tana kallon sa tace, "Sultan kayi haƙuri naga ranka ya b'aci." A fusace ya kalle ta yace, "Waye shi d'inki da zaki je gidan shi? Waye a wajan ki da zaiyi fushi dan baki je gidan sa ba?. Har abada baza kije ba!" Ya fad'a yana tashi tsaye ya juya mata baya ba tare da yace komai ba. Yanzu ta gano laifin ta wato maganar gidan Anas da maganar Khalifa itace laifin da tayi masa sai ta tashi ya isa inda yake ta rugume shi ta baya ta kwanta akan bayan sa tace, "I'm sorry Sultan bazan sake ba in sha Allah. Rahma k'anwata ce dan naje gidan ta a ganina ba wani abun bane dan ita naje badan mijin ta ba amma tunda baka so bazan je ba, kayi haƙuri dan Allah." Shiru yayi bai amsa ba yana jin zafin kishi yana taso masa daga cikin zuciyar sa yana sauke numfashi ta dawo ta gaban sa tace, "Dan Allah kayi haƙuri Sultan, bana so kana fushi dani hankalina yana tashi. In baka so zan daina kula Khalifa ko gaisawa zamu daina." Ya sauke numfashi yana kallon ta in ya tuna yadda ya rik'e ta a Cairo sai yaji haushin sa yake ji gabad'aya shiyasa wani lokacin ko wayar sa baya d'auka sabida haushin hakan. Amma kuma ya taimake ta haka kuma Rahma k'anwar tace bazai raba su ba amma baya so yaga ta rab'i Anas balle taje gidan sa dan yasan tabbas zasu had'u shi kuma baya son hakan ko kusa. Jin ta fara yi masa kuka ya saka ya kalle ta tana jikin sa yace, "Shikenan ki bar kuka." "Ka yafe min?." Kallon sa tayi shima ya kalle ta ya rik'e hannun ta ya d'ora a saitin zuciyar sa yace, "Bana son naji kina maganar wani Muwaddaty, ina ji kamar zuciyata zata fashe." "Bazan sake ba in sha Allah, kayi haƙuri ka yafe min dan Allah bazan kuma ba." Rarrashin ta yake yana bubbuga bayanta ba tare da yayi magana ba. "Ina sonki Muwaddaty! Sonki a jinina yake, na fara sonki tun a mafarki" ya furta yana sauke numfashi ya rik'e ta sosai a jikin sa. D'agowa tayi tace, "Mafarki?." Ya d'aga mata kai alamun eh tace, "Ka bani labari." Murmushi yayi ya girgiza kai alamun a'a ya jata kan gado suka zauna ya kashe hasken d'akin ya jata suka kwanta zata sake magana ya fara kissing d'inta dole taja bakin ta tayi shiru ta fara taya shi a karo na farko. Bayan kwana biyu. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *092.*            A kan stool d'in dake tsakiyar make makeken kitchen d'in ya ajjiye ta da yatsan sa yayi mata alama da ta zauna ta gani, binsa take da kallo taga ya dafe kai kad'an ya runtse idon sa zatayi magana ya karkad'a mata tsayan sa dole tayi shiru tana binsa da kallo. Sai da ya daidaita kansa sannan ya tsaya yana kallon kitchen da tunanin abinda zai dafa mata taci. Kettle ya kunna bayan ya zuba ruwa a ciki ya d'auko cup ya d'auraye shi da ruwa ya buɗe drawer ya d'auko coffee ya had'o da madara da sugar ya ajjiye a gefe. Kallon sa take yi yana sanye da rigar wanka wacce da kad'an ta wuce guiwar sa farar k'afar sa a bayyane a cikin takalmi yawo a cikin gida sai d'aukar ido k'afar tasa take hatta farren k'afar sa abin so ka kalla ne. "Yawan kallo yana saka mutum ya fad'i." Abinda taji yace kenan tayi murmushi ta sunkuyar da kanta k'asa ya kalle ta shima sai yayi murmushin shima ya kashe switch d'in ruwan ya zuba coffee d'in da sugar ya zuba ruwa kad'an ya d'auko coffee maker ya jona ta itama ya saka a cup d'in yayi making coffee yayi kumfa sosai ya cire ya ajjiye, madarar ya zubawa ruwan zafi a wani kofin daban sannan ya zuba akan coffee d'in nan take yayi sama kamar zai zube sai ya dakata da zubawar ya d'auko ya kalle ta yana nuna mata cup d'in. Jinjina tayi masa yayi murmushi ya fita ya kai coffee d'in falo ya dawo tana inda take ya d'auke ta kamar yarinya har inda ya ajjiye coffee d'in ya zaunar da ita akan kujera ya jawo coffee d'in ya kai bakin ta ta buɗe tasha ta yamutsa fuska ya kalle ta ya d'aga gira tace, "Babu laifi." Murmushi yayi ya d'auki cake a leda cikin wand Suhail ya kwaso masa ya b'are mata ya mik'a mata ta karb'a taci ta kalle shi tace, "kaima kaci." Wara ido yayi ya girgiza kai baice komai ba tace, "Allah sai kasha." Ya kalle ta na wani lokaci ya lumshe ido ya furzar da iska amma baiyi magana ba tace, "in fa baka karb'a ba nima na fasa." Ya sake kallon ta yace, "In nasha coffee bazan iya bacci ba." "Ka karb'a kasha a hakan." Ya kalli agogo ya nuna mata itama ta kalla tace, "Nidai kasha kawai." Sha d'in yayi kamar yadda tace ya d'aga girar sa sama ya kalle ta ya kalli coffee d'in alamun yayi dad'i, ta tab'e baki tace, "Ba laifi dai, na tabbatar shi kad'ai ka iya shima dan kayi zaman garin larabawa ne." Murmushi yayi yana bata tana sha shima yana sha a haka suka shanye cup d'in. Ta jingina da kujera shima haka ya rik'e hannun ta suna kallon tv ba dan tana kunne ba tace, "Na fara jin bacci." Ya kalle ta yace, "Na fad'a miki bana iya bacci ko?." Tace, "Aini zanyi baccin ba kai ba." Ya zuba mata ido har sai da ta kawar da fuskar ta tace, "in kana kallona wani iri nake ji a jikina, idanun ka bana iya kallon su sosai" ta fad'a tana buɗe ido taga fuskar sa daidai tata yace, "me kike ji?." Yadda yayi maganar ya sakata yin shiru tana kallon sa ya d'aga mata gira alamun ta bashi amsa sai tak'i magana ta sauke ido k'asa, "kince nasha abinda bazan bacci ba nasha, so dole kema bazaki ba." Ta kalle shi ya girgiza mata kai alamun abinda yace kenan tace, "To in na zauna me zanyi ga dare yayi?." Kafin tayi magana taji saukar bakin sa a wuyan ta ta kulle idanun ta tace, "Sultannnn!." "Sultanaaaa!" Shima ya furta ba tare da ya d'ago daga jikinta ta ba. "Na gaji fa Sultan." Rigar ta yake tattarewa ta k'asa tayi saurin rik'e hannun sa tunawa fa da babu komai a jikinta sai rigar kawai tace, "Sultan dan Allah." Bai bari ba ya kwace hannun sa ya kai hannun sa kan fatar cikin ta yana shafawa a hankali. Shiru tayi dan ya kashe mata baki gabad'aya, daga shafa cikinta taji yana kai hannun sa sama ta sauke numfashi tace, "Sultannnn!." Yadda tayi maganar ya saka shi juyo da fuskar ta ya hanata sake magana ta hanyar saka bakin sa cikin ta dole tayi shiru badan taso ba. Bata san ya akayi ba sai akwai ganin ta tayi a kan gado zata kuma magana ya sake hana ta dole tayi shiru tana jin sabon yanayi yana sake yin nink'aya a cikin jikin ta, "Say something Sultanaaaa! Ina so naji kinyi magana" ya fad'a a kunne ta amma babu damar yin maganar a wannan lokacin idanun ta a kulle suke gabad'aya ta kasa cewa komai.           *☆*  Tana cikin bargo a jikin sa gabad'aya tana kukan shagwab'a tana fad'in, "Sultan ka b'alla min bayana, wayyo k'afana, cikina zai cire Sultan." Duk ta rud'a shi hankalin sa ya tashi yace, "to ki daina kuka, I'm sorry Sultana." Ta sake shigewa jikin sa tana fad'in, "nidai na gaji bayana ciwo yake min." "Shiiiii!" Ya furta a kunnen ta ta sauke numfashi jin yana mata tausa a bayan dan da gaske ciwo yake mata sai tayi shiru ta lumshe idanunta bacci yana k'ok'arin d'auke ta. Sai da yaji ta fara bacci sannan ya k'yale ta ya zame ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta ynaa murmushi. Allah ya sani yana son wannan baiwar Allah, yana Qaunar ta fiye da tunanin mai tunani, baya so yaga tayi nisa dashi hakan yana sakawa yaji kamar shi kad'ai ya rage a duniya sabida kewa. Kiss ya mata a goshi ya tashi ya shiga band'aki. Alwala yayi ya fito ya saka doguwar riga ya shinfid'a sallaya, "Sultan ina so nayi sallah nima amma bazan iya ba." Yaji ta fad'a ya juya ya kalle ta sai ya k'arasa kusa da ita ya zauna yana shafa kanta yace, "Zan miki duk addu'ar da kike so, kiyi bacci." Kulle ido tayi baccin ya sake d'auke ta ya gyara mata abinda ya rufe ta ya tashi ya koma kan sallayar ya tayar da sallah. Har akayi asuba yana sallah sai da ya idar da sallar asuba ya k'arasa inda take ya zauna ya yaye abinda ta furta yana matse mata hancin ta, bata buɗe ido ba dan bacci take sosai ya sake matse hancin ta nan ma bata buɗe idanun ta ba. Sunkuyawa yayi ya cizi kunnen ta yana jan sa da hak"oran sa. Buɗe ido tayi idanun ta sunyi nauyi sabida bacci ta kalle shi yace, "Sallah Muwaddaty" ya fad'a yana yaye bargon gabad'aya ya d'auke ta bai sauke a ko ina ba sai a band'aki. A gefen bathtub ya ajjiye ta yace, "lokaci yana tafiya." Idanun ta har lokacin akwai bacci sosai ga kanta yayi nauyi hakan ya saka shi zuba ruwa a hannun sa ya shafa a fuskarta, ta yatsine fuska tana shafa fuskar ta ta d'ago ta kalle shi ya d'aga mata kai. Fita yayi ya barta bata jima sosai ba ta fito tayi alwala cikin kayan sa riga da wando marasa tsaho masu kama jiki sai sukayi mata kamar nata, tana fitowa ya bata abayar ta ta jiya ta saka ta yafa mayafin ta tayar da raka'atanul fijir, bayan ta idar tayi sallar asuba dak'yar ta iya karanta ayatul kursi bayan ta idar ta mik'e ta zauna a kan gadon tana kallon sa yana karatu. "Barka da safiya Sultan" ta fad'a tana kwanciya ta sake lullub'e jikin ta yayi murmushi dan yasan dole taji bacci badan baya so ta rasa sallah bama da bazai tashe ta ba yace, "Barka da safiya Sultana." Bata sake magana ba bacci ya d'auke ta. Sai da gari yayi haske sannan ya kashe hasken d'akin shima ya kwanta a bayan ta ya dawo da ita jikin sa gabad'aya a haka shima bacci ya d'auke shi. *☆☆☆*                Yadda take kuka sosai sai ta baka tausayi jaririn d'anta da bai gama zama cikakken mutum ba har lokacin take kallo tana zubar da hawaye tana fad'in, "Ina son shi a haka, dan Allah ya tashi kar ya mutu ya barni." Mum da take jingine a gado ta rame gabad'aya ta koma kamar ba ita ba saboda rama ta firgice lokaci d'aya, maza ne a tsaye a kanta sai Eman da take kuka ta saka hannu ta karb'i yaron ta mik'awa mazan tace, "Ki daina kuka Allah ne ya baki kuma ya karb'i abin sa, ki bari a kaishi makwancin sa." Mazan suka fita da yaron a hannun sa Jidda ta sake fashewa da kuka ta rik'e hannun Eman tace, "Eman na cuci kaina na cuci rayuwata, Mum ta lalata min rayuwata gabad'aya ta gurb'ata min tarbiyya da addini na. Wallahi badan Mum ba da zuciya d'aya naso zama da Asad ita take zuga ni akan sai na mallake shi Eman." Eman kuka take itama tace, "Kiyi haƙuri k'addarar ki kenan." Jidda tace, "Ba k'addara bace Eman nice na jawowa kaina, nice na biyewa son zuciya da son mulkin da Mum ta dasa min a zuciyta na biyewa Aliyu muka aikata sabon Allah da auren k'anin sa a kaina. Wallahi Asad ko hannuna bana tunanin ya tab'a riƙewa sai dai ni na rik'e shi amma Aliyu tamkar shine Asad haka ya koma wajan mu'amalar aure dani bana jin tsoron Allah haka nake biye masa dan kawai na kai kaina matsayin da Mum take fad'a min." "Na raba Aliyu da babar shi duk a tunanin su Asad ne nida shi ne kawai muka san ba Asad bane Aliyu ne...... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, na shiga uku Eman a ina zanga Asad ya yafe kin?" Ta fad'a yana sake fashewa da kuka sosai. Eman ta rik'e ta tana kukan itama bata ce komai ba Jidda ta kuma cewa, "Sabida Mum ta mayar da kisan rai ba komai ba nima na koya na dinga k'okarin kashe Asad kawai dan kar asirina ya tonu Eman, Mum ta cuce ni wallahi itace ta koyar dani hanyar da za'a kashe mutum domin mun sha yunƙurin kashe Babar Asad d'in kawai dan kar ta bamu matsala akan kudurin Mum. Dole ma hakkin Mama dana Asad ya dinga bibiyar mu gashi nan Daddy ya barmu kema ya raba ki damu babu wanda yake zuwa wajan mu dan abinda muka aikata ba k'aramin sabon Allah bane." Eman ta girgiza kai tace, "Daddy fushi yayi amma In ya wuce zai dawo Jidda." "Gwara karya dawo Eman domin mu ba irin wanda za'a rab'a bane nan gaba kad'an shi d'in ma Mum zata iya kashe shi. Eman ina so na kai kaina kotu a yanke min hukuncin da musulunci ya tanadarwa Irina na karb'i hukuncina tun a duniya kafin naje wajan mahalicci na." Eman tace, "Jidda za'a jefe kine fa har sai kin mutu shine hukuncin wanda ya aikata Zina da aure a kansa." Jidda tace, "Meye amfanin rayuwata Eman? Gwara ace na mutu d'in kowa ya huta dan rayuwata bata da amfani Kwata-kwata. Mum ta gama cutata sai Allah ya tsayar dani da ita yayi mana hisabi." Kuka take Mum d'in ma haka, sun cika d'akin da kuka babu mai rarrashin wani kafin Jidda tace, "Ina so naga Asad ya yafe min wallahi na tuba, na kuma taya shi murna da bai zauna da mace Irina ba Allah ya kawo masa mafita da yake ya kasance mai bautar Allah. Mu kuwa da babar mu ta d'ora mu akan turba mara kyau ga inda k'arshen mu ya kasance a wulaƙance a lalace. Eman koda an jefe ni na mutu kar ki biyewa son zuciyar Mum ki bi Allah da abinda ya umarta wanda yace a bari ki bari Eman in ba haka ba zakiyi k'arshe irin nawa mara kyaun gani da kyaun ji." Rungume ta Eman tayi tana kuka sosai itama tana kuka Mum ma tana kuka sosai, Jidda tace, "Tun Mama da Mum suna makarantar secondry school a Kano aminan juna ne har sukayi aure a waje d'aya suka cigaba da aminci, Mama ta amince da Mum amma ita kuma cutar da ita take yi. Ina ma kafin ta haife ni cikina ya zube na huta da wannan bak'ar rayuwar da ta saka ni a ciki." "Eman ki cewa Mama ta yafe min, ki cewa Asad ya yafe min dan Allah nasan babu lallai na kuma ganin su dan yau d'in nan zan kai kaina inda za'a jefe ni na mutu." Eman tana kuka matuk'a itama haka. Mum da take gefe tana kuka tace, "Kwarai son zuciyata ne ya jawo min, tabbas nice na jefa ki a wannan hali Jidda kiyi haƙuri ki yafe min dan Allah." Jidda tace, "Babu yafiya tsakanin mu Mum, sai Allah yayi mana hisabi nida ke." Eman tace, "haba Jidda meyasa kike cewa haka? Yanzu kike cemin na fad'awa su Asad su yafe miki meyasa ita bazaki yafe mata ba?." Jidda tace, "Haka ne kuma, na yafe mata Eman amma ta cuce ni wallahi." Tari Jidda ta fara tana dukan k'irjin ta ganin yadda idon ta yake k'afewa ya saka Eman fita a guje ta kira likita ya shigo a guje aka fitar da Eman aka rufu akan Jidda dan ganin a ceto rayuwarta dan yanayin nata yayi muni sosai ba kad'an ba amma abin yaci tura rai yayi halin sa lokaci ya riga yayi tafiya ko baka shirya ba sai kaje. Fad'a musu ta rasu Eman ta zube a sume Mum ma bata sake sanin inda take ba. Daddy aka kira aka sanar dashi duk da abinda yake ji a kansu sai da hankalin sa ya tashi rasuwar Jidda ta tab'a shi gama jana'izar abinda ta haifa kenan itama ta bishi, ya rud'e sosai haka akazo aka d'auki gawar ta a safiyar akayi jana'izar Jidda wacce ta tara mutane dama dan shi kansa Daddy bai san za'a cika haka ba aka kaita makwancin ta Mum bata sani ba Eman ma tana sume. *☆☆☆*           K'arar wayar sace ta tashe shi ya tashi yana yamutsa fuska ya kai kallon sa kan agogo yaga k'arfe d'aya daidai na rana ya wara idanun sa ya sakko daga kan gadon ya zauna ya d'auki wayar ganin mai kiran ya saka shi ya d'auka ya saka a kunne, "Zaki ina ka saka waya haka?." Asad ya gyara murya yace, "Barka da safiya Abba." "Safiya! Da alama yanzu ka tashi kenan." Asad ya dafe kansa yace, "Na kwana bana jin daɗi ban samu bacci da wuri ba. Ina fatan Abba ya tashi lafiya." Mai martaba yace, "Alhamdulillah. Ya zaman Abujan?." Asad ya shafa kansa yace, "Alhamdulillah." "Ina ta kiran ka tun d'azu na sanar dakai rasuwar matar ka Jidda da ita da abinda ta haifa duka Allah ya karb'e su." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yau akayi jana'izar ta?" Ya furta cikin bugawar zuciya. "Tun safe akayi ana ta mamakin rashin ganin ka." Asad yace, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Allah ya gafarta mata ya yafe mata yasa tana aljanna. Abinda ta haifa yasa ya kasance mai ceton ta." Abba yace, "Amin ya rabbil alamin. Babar ta da K'anwar ta har yanzu basu farfad'o ba suna sume, ita kanta babar ka mutuwar ta tab'a ta sosai." Asad yayi shiru yana girgiza kai kafin Abba yace, "In ka kammala abinda kake yi dai zuwa gobe ko jibi ka dawo akwai abubuwan da suka taru suna jiran ka dawo ka aiwatar dasu." Asad yace, "In sha Allah." Daga nan sukayi sallama ya kashe nan ya duba yaga missed call d'in Mama dana Suhail. Mama ya fara kira ta d'auka yace, "Barka da rana Mama." Mama tace, "Barka Asad." "Ina neman afuwa ban d'auki kiran Mama ba." "Babu komai Asad. Ka samu labarin rasuwar Jidda ko?" Ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Kafin yayi magana tace, "Asad duka abinda Jidda ta aikata nima ina da hannu a ciki gashi ta rasu bata yafe min ba ya zanyi?." Jin tana kuka sosai sai hankalin sa ya tashi ya sassauta murya yace, "Kiyi haƙuri Mama ki mata addu'a" ya fad'a dan bai san me zaice ba kuma. Kuka take sosai yana jinta sai da tayi kusan mintina bakwai tana kuka a waya shi kuma yayi shiru bai kashe ba yana jin kukan har zuciyar sa kafin yace, "Kiyi haƙuri Mama haka Allah ya rubuta abinda zaiyi silar rasuwar ta kenan." Yana ji ta sauke ajiyar zuciya kafin tace, "Ka gaida Rauda" tana fad'a ta yanke wayar yabi wayar da kallo zuciyar sa tana bugawa sosai. Mutuwar yaji ta a jikin sa sosai bazai manta lokacin da suka je dubata ba duk da abinda ya faru yana yi mata fatan samun rahamar Allah, Rauda da tunda ya fara waya ta tashi tana jin duk abinda ake cewa tace, "Waye ya rasu Sultan?." Kallon ta yayi ya sauke numfashi yace, "Jidda ita da yaron ta." Rauda ta mik'e zaune tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yaushe?." "Yau" ya bata amsa a tak'aice. "Allah ya gafarta mata yasa yaron ya zama mai ceton ta." Numfashi ya sauke yace, "Amin. Mama tana gaishe ki" ya fad'a yana mik'ewa tsaye. "Ina amsawa" ta fad'a jin wani iri wai Mama tana gaishe ta lallai duniya ta ishi kowa riga da wando harda babbar riga. Agogo ta kalla ganin d'aya ta wuce sai ta sakko daga kan gadon ta tsaya itama kamar yadda yake a tsaye bai motsa ba sai k'asa da yake kallo, numfashi taga ya sauke ya juyo ya kalle ta ya mik'a mata hannu yace, "Wanka." Kafaɗar ta nok'e tace, "Zanyi ni a wani d'akin kayi kai a nan." Duk da babu walwala a fuskar sa haka ya tako inda take ya rik'e hannun ta bai magana ba ya jata har cikin band'akin babu yadda zatayi dan babu fuskar musawa a tare dashi. Tare sukayi wankan suka fito ta zauna gefen gado tana kawar da fuska har gobe kunyar sa take ji shi kuma taga ya sakawa idanun sa toka baya jin kunyar ta ko kad'an kamar ba shine sarkin Katagum ba. Sabuwar doguwar riga taga ya d'auko mata a leda irin mai laushi da babban mayafi ya mik'a mata ta kalli doguwar rigar tace, "Bani da undies fa." Tab'e baki yayi baice komai ba ya k'arasa inda take ya zira mata doguwar rigar ta sama ya zame towel d'in jikinta yace, "Sallah." Shima doguwar rigar ya saka suka tayar da sallar azahar, bayan sun idar ya kalle ta yaga sai yanutsa fuska take ganin yana kallon ta tace, "Wallahi bana jin daɗin zama haka babu komai a jikina, ni zan koma gida kawai yau." Bai tanka mata ba taga dai ya d'auki waya bata san me yayi ba taga ya ajjiye sai kuma ya kuma d'auka ya kira Suhail. Yana d'auka yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, Allah ya kiyaye mai martaba ya kare shi." "Suhail" shine abinda ya furta kawai. Suhail yace, "Allah yaja zamanin ka ina cikin gidan tun safe na kawowa mai martaba abinda yace a kawo." Kai kawai ya girgiza kafin ya yanke wayar ya kalle ta yace, "Ina zuwa." Ya tashi tsaye itama ta tashi tana kallon sa tace, "tsoron gidan nan nake ji fa bazan iya zama ni kad'ai ba, nidai zan bika muje inda zaka gaka." Kallon ta yayi sai yaga kamar ana ganin komai na jikin ta dan yadda ta motsa komai na jikinta motsi yake tunda babu komai a jikin nata, d'aure fuska taga ya sake yi amma duk da hakan bata hak'ura ba zai wuce ta tace, "Wallahi tsoro nake ji." Ganin a tsorace take sosai sai ya kira Suhail yace ya k'araso falon ya fita ita kuma ta zauna a d'akin. Suhail na ganin sa ya mik'e tsaye har ya k'araso ya zauna Suhail yace, "Barka da fitowa ranka ya dad'e. " zama Asad yayi ya nuna masa kujera shima ya zauna kafin Suhail yace, "Ina fatan mai martaba ya samu lafiya." Asad yace, "Alhamdulillah." Suhail yace, "Sai aka tashi da rasuwa, Allah ya jikan wanda suka rasu." Nan ma ya amsa da amin kafin Suhail yace, "Ranka ya dad'e ga abincin, ga kuma list d'in matan da aka kawo wanda za'a aurar babu kayan d'aki. Ga kuma yawan takardun masu neman aikin da muka samu. Na bibiyi gidajen y'an matan da za'a aurar kuma na tabbatar da gaske auren zasuyi wasu abincin gidan ma yana gagarar su balle kayan d'aki." "Su kuma samari masu neman aikin na tabbatar dukkan su babu aiki babu kuma Sana'a, a cikin su wasu babu mahaifi sai mahaifiya da y'an uwa nauyi ya hau kansu amma babu halin saukewa." Karb'ar takadar Asad yayi yaga sunayen mata sama da hamshin ya girgiza kai yace, "A siyi kayan ko a basu kud'in?." Suhail yace, "A siyi kayan ranka ya dad'e." Asad ya girgiza kai ya mik'a masa yace, "Duk abinda ya kamata ayi, a had'a da kayan abinci ga kowa a d'ora kud'i." "Kamar nawa kenan ranka ya dad'e? Abincin kuma kamar ya za'a saka?." Asad yayi masa alama da yayi komai Suhail yace, "In sha Allah. Allah ya k'ara arzuk'i yasa a d'auki alkhairin da ake a duniya a gidan Aljanna. A zuciya ya amsa da amin kafin Suhail yace, "Su kuma masu neman aikin zan rarraba wasu a company mai martaba wasu kuma za'a basu jari." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa kafin Suhail ya kuma cewa, "akwai bak'i da suka zo suna son ganin mai martaba na sanar dasu mai martaba yayi tafiya sun kafe akan zasu jira shi ya dawo." Yayi k'aramin tsaki yace, "bazan koma yanzu ba." Suhail yayi murmushi Asad ya kalle shi ya d'aga gira sama yace, "Fad'i abinda yake ranka." Suhail ya shafa kai yana murmushi yace, "ni na iya ranka ya dad'e? Babu abinda yake raina sai alkhairi."  Asad yayi murmushi shima dan yadda yaji dad'in kwana d'ayan nan bazai koma ba sai sun kwana biyar cif. Asad yace, "Hydar bai shigo ba?." Suhail yace, "tun kwanaki ban sake ganin gilmawar sa a gidan ba." Ya girgiza kai kawai baice komai ba dan ya tabbatar akwai abinda yake shiryawa shiyasa yayi shiru kamar babu shi. Wayar Suhail tayi k'ara bai d'auka ba Asad yace, "pick it, akwai abinda za'a baka ka kawo min." Jin hakan sai Suhail ya d'auka ai kuwa masu delivery ne ya fita yaje ya karb'o kayan a leda babba ya shigo dasu ya ajjiye. Suhail yace, "Ranka ya dad'e in anyi min izini zan iya tafiya?." Asad ya d'aga masa kai ya mik'e sai Asad ya kalle shi yace, "Wai yaushe zakayi aure ne?." Suhail bai sam dariya ta sub'uce masa ba shima Asad d'in dariyar yayi Suhail yace, "Ranka ya dad'e an kusa in sha Allah." Maimakon yayi magana sai ya sake yin dariya yana cize bakin sa kafin yace, "yafi dai." Suhail yana dariya suka had'a ido sai yaga Asad d'in ya d'aga masa gira ya sake yin dariya yace, "Zan zo wajan mai martaba a nema min mata dan naga giyar auren har saurin warkar da marasa lafiya su warke." Asad yayi dariya mai sauti amma baice komai ba. Suhail yace, "Na barka lafiya, a gaida Fulani." Kai ya d'aga masa yana murmushi har lokacin Suhail yana jin farin ciki a ransa dan yaga shugaban nasa yana farin ciki shi kuma yana so yaga yana farin ciki domin yana da ciwo a zuciyar sa sosai farin ciki shine kawai maganin ciwon. [17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11 *094.*         Yadda ta rame ta lalace kallo d'aya in kayi mata sai ka sake kai duba a gare ta sannan zaka tabbatar itace, tayi bak'i babu gayu a tare da ita balle ado da kwalliya. Fuskar ta ta jeme kamar an saka sirinji an kwashe albarkar fuskar ta ta koma y'ar k'arama kamar wacce ta shekara tana jinya. Tana zaune kusa da Mama tana kuka wanda ya zamar mata abokin hira tun bayan rasuwar Jidda har ta hawaye basa tsayawa a fuskar ta ko yaushe cikin zuba suke. Itama Maman kuka take amma bai kai na Mum dukkan su sun kasa magana ga Eman a gefe itama ta rame sosai idanun ta yayi bala'in ja. Dak'yar Mum ta iya had'a kalmomin a kan harshen ta ta kalli Mama tace, "Na rasa ta wacce kalma zanyi amfani na nemi afuwar ki Rabi'a, na rasa wacce irin kalma zan furta wacce zata nuna miki nayi nadamar cin amanar ki." Sai ta sake fashewa da sabon kuka zuciyar ta nayi mata kuna da ciwo tace, "Kin amince dani na ha'ince ki, babban burina naga bayan ki na mallake dukkan abubuwan da kike taqama dasu ke na raba ki dasu badan komai ba sai don son zuciyata da rashin k'aunar Allah da kuma zallar cin amana. Gashi yanzu dalilin mugun halina na kashe y'ata da kaina domin badan na d'ora ta akan turba mara kyau ba da duk hakan bai faru ba." Mama ta girgiza kanta tace, "Sadiya laifina ne, da ban nuna miki burina akan sarautar ba da kema baki saka ranki a kai ba, dan nuna miki tsantsar son kai ba da kema baki yi wannan tunanin ba, da ban nuna miki in y'ar ki ta shigo gidan nan zan mayar da ita tamkar baiwa ba da kema baki tunanin d'aukar mataki ba, da ban nakasa Asad akan banzan burina ba da bata kai kanta ga Aliyu ba, da ban nuna nice nake so nayi iko da komai ba da baku mallake Aliyu ba. Duka wad'annan abubuwan nice naja nice na bada k'ofar da aka shigo aka aikata su, nice na bada dama nice na bada lasisin aikita dukkan abinda aka aikata shiyasa kike k'okarin kashe ni. Ni ya kamata na nemi yafiyar Jidda domin badan abinda na saka aka yiwa Asad ba da yanzu tana matsayin matar sa." Mum ta girgiza kai tace, "Duk da haka ban zauna dake da zuciya d'aya ba, tabbas nasan yawan cewa a kashe wane da wance da kike cewa shine ya d'arsa min son kashe ki shiyasa na  saka aka kwance burkin motar Suhaima ta yadda zaku mutu gabad'aya amma Allah ya tseratar dake. Na sake bada guba aka saka miki a shayi shima Allah ya kubtar dake. Dan girman Allah kiyi hak'uri Fulani naga sakamakon aikata sharri tun kafin naje lahira, naga sakamakon mugun nufi tabbas naga amfanin karin maganar da hauwasa suke cewa in zaka hak'a Ramin mugunta ka yishi daidai kai." Kuka suke dukka su biyun kafin Eman tace, "Mama kafin Yaya Jidda ta rasu ta bani sak'o na sanar dake ki yafe mata abubuwan data aikata miki, dan Allah ki yafe mata ko zata samu salama a cikin kabarin ta." Mama ta kalki Eman da take hawaye tace, "Na yafewa Jidda, nima naso tana raye ta yafe min dan ina da hannu a halin da ta shiga." Eman tace, "Mai martaba da matar sa tace na nema mata afuwar su Mama, a ina zan gansu?." Mama ta share hawaye tace, "Asad da matar sa basa nan sunyi tafiya amma na tabbatar sun kusa dawowa. Allah ka yafe mana abubuwan da muka aikata dan tabbas duk cikin mu babu wanda baiga sakayyar Allah ba tun a duniya, shi waziri da ya tashi y'ay'a biyu ya rasa lokaci d'aya.....Allah ka yafe mana." Mum tace, "Baki ce kin yafe min ba Fulani." Mama tace, "Na yafe miki, kema ki yafe ni." "Na yafe miki nima. Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a tana sake fashewa da kuka dukka su ukun kuka suke har Suhaima ta had'u da take gefen su. *☆☆☆☆* Cikin kwana hud'u da Asad da Rauda sakayi sun yishi cikin soyayya da nuna tsantsar kulawa ga junan su, ko gate basa fita ko yaushe suna cikin gida duk abinda suke so Suhail zai kawo musu ko yaushe suna tare da juna. Sunyi haske Asad har kib'a yayi dan ya samu mai kwantar masa da hankali bata barin sa cikin tunani da taga ya zauna shi kad'ai zata dawo kusa dashi tana bashi labari.          Tsaf ya shirya cikin manyan kaya shadda kalar ash colour babbar rigar har k'asa take tasha aiki kai da ka kalla kasan aikin bana k'ananun sarakuna bane, aka kawo alkyabba kalar shaddar aka d'ora akai aka saka rawani kalar aikin shaddar takalmi kalar shaddar da aikin da yake jikin ta. Ba sai ance yayi kyau ba kana kallon Asad kasan yayi kyau sosai yana tsaye a jikin madubi yana sake gyara rawanin kansa. Rauda da take tsaye a bayan sa tana kallon sa tace, "Sulatan." Ta madubin ya kalle ta tace, "In ka saka kayan nan sai ka koma tamkar babba, kuruciyar ka sai ta b'uya sai manyanta ya bayyana akan fuskar ka. Kana kyau da kayan nan kamar daman dan kai aka yi su." Yayi murmushi ya juyo yana kallon ta ta tako zuwa inda yake tana kallon sa itama kamar zai mata magana sai ya fasa ya juya yana cigaba da abinda yake yi amma har lokacin fuskar sa a sake take. Sai daga baya sannan yace, "Muwaddaty banso tafiya yau ba, amma ya zanyi dole na amsa kiran Abba in ba haka ba sai mun kwana bakwai a nan" ya juyo yama kallon ta yace, "Na jima ban samu farin ciki kamar na kwanakin nan ba." Hannunta ta zaga dashi a jikin sa ta rik'e bayan sa tace, "Ai a can d'in ma muna tare ko yaushe." Yayi k'aramin tsaki ya girgiza kai yace, "ba kamar nan ba, can hayaniya tayi yawa." "Abba yayi kira dole mu amsa, amma nima bana so mu tafi zaman nan yafi na can dad'i. Kasan ni ban saba da wannan kirari ga abubuwan da ake min ba sai naji wani iri" ta Fad'a tana kwanciya a jikin sa ya rik'e ta shima idanun sa a lumshe. Jin yayi shiru ya saka tace, "Sultan baka ce komai akan makarantar tawa ba." Bai sake ta ba kuma bai magana ba yayi shiru suna tsaye a haka kamar baiji me tace ba jin yayi shiru itama sai tayi shiru. "Kin tab'a ganin mace irin ki tana karatu a wata makaranta?." A sama taji maganar da bata d'auka ma zai sake maganar ba ta d'ago ta kalle shi tace, "To ai neman ilimi ne Sultan, kuma ina so shine burina a rayuwa." "Badai a Nigeria ba sai dai in zaki iya a outside country" ya furta yana kallon ta sai yaga tayi murmushi tace, "Zan iya mana Sultan." Yayi murmushi baice komai ba ta bar jikin sa ya kalle ta yaga doguwar rigar jikinta bata nuna jiki ba kwata-kwata domin mai fad'i ce sosai ya rik'o hannun ta zuwa falo daga ita sai wayar ta kamar yadda tazo dan kayan da tazo dasu a jikin ta ma an ajjiye su a gidan. Yasan amsar sa take jira shiyasa ya share dan abinda zaice ba dad'i zai mata ba ganin tana ta kallon sa ya saka yace, "In kina so zakiyi, amma dole a samu wacce zata zauna dani a nan in yaso duk sanda na samu lokaci sai naje can wajan ki. Ba'a barin shugaba a wani waje babu mata sai dai su zama biyu, akwai a nan akwai a can" ya furta yana kallon ta. Take annurin fuskar ta ya d'auke ta ta bishi da kallo tace, "Kana nufin sai dai matan ka su zama biyu, ni ina can ina karatu ita tana tare dakai a nan? Sai lokacin da ka samu dama zaka je inda nake?." Ya d'aga girar sa alamun haka yake nufi sai yaga ta sake d'aure fuska gabad'aya walwalar da take fuskar ta ta d'auke tace, "Dole ne karatun?." Mamaki yake jin tambayar da tayi masa sai ya tab'e baki ya wara hannayen sa alamun oho. Ranta gabad'aya ya b'aci ko kallon inda yake ta daina shima kuma bai kalle ta ba dan haka maganar take dole sai dai hakan ta faru inda tana son karatu. A haka Suhail ya k'araso Asad ya bashi umarnin ya fara mayar da ita gida suka tafi har lokacin ranta a b'ace sai bayan ta tafi yayi dariya kawai. Ba jimawa ya dawo aka d'auki Asad suka wuce gida kai tsaye. Rauda taga dawowar sa tasan b'angaren sa zai wuce ranta gabad'aya a b'ace yake a haka ta yi sallar azahar ta fito dan taje ta gaida Mama. A zaune ta tarar dasu kamar gidan mutuwa tayi sallama duk suka d'ago suna kallon ta sai ta sunkuyar da kanta ta k'arasa ta zauna tace, "Barka da Rana Mama." Mama ta fad'ad'a murmushi tana kallon ta tace, "Barkan ki. Kun dawo lafiya?." "Alhamdulillah. Ya karfin jiki?." "Jiki yayi sauk'i, ya naki jikin kema?." Rauda tace, "Alhamdulillah. Mun samu labarin anyi rasuwa Allah ya jikan wanda suka rasu ya gafarta musu." Mama ta amsa da amin kafin Rauda taji muryar Mum tace, "Barka da shigowa Fulani." D'ago ido tayi ta kalli Mum tace, "Ya karin hak'uri?." Mum tace, "mun gode Allah." Rauda tace, "Allah ya gafarta mata, abinda ta haifa kuma ya saka ya kasance mai ceto." "Amin" ta fad'a sai ta fashe da kuka tace, "Ki yafe min ranki ya dad'e dukkan abubuwan da aka yi miki nice nake kawo shawara ko nake bada goyan baya, dan Allah kiyi hak'uri da duk abinda ya faru wanda kika sani da wanda baki sani ba ina neman afuwar ki." Rauda ta sauke numfashi tace, "Babu komai ya wuce, Allah ya yafe mana baki d'aya." Mum tace, "Amin ya Allah. Na gode ranki ya dad'e Allah ya saka da alkhairi." Rauda jikin ta duk yayi sanyi ta amsa da amin kafin Eman tace, "Yaya Jidda ta bani wasiya akan in nema mata yafiya a wajan ki, dan Allah ki yafe mata ranki ya dad'e ko zata samu sassauci a wajan wanda ya halicce ta." Rauda taji idanun ta ya ciko da kwalla tace, "Na yafe mata ina yi mata addu'a samun rahama a wajan Allah." Mama tace, "Allah ya saka miki da alkhair. Kin haifu kin nuna mana dukkan mu baki d'auki sharrin da akayi miki a bakin komai ba domin dukkan mu da muke nufin ki da sharri gabad'aya kan mu ya dawo." Rauda tace, "Dan Allah Mama ta daina fad'ar wannan kalaman bana son sake maimaita su sun riga sun wuce." Mama tace, "Haka ne. In da dama suna son iso wajan Asad." Rauda ta d'anyi jimm sai taji nauyi abinda Mama tace matsayinta na mahaifiyar sa ace itace zata nemawa babbar aminiyar mama iso a wajan Asad sai ta kasa magana jin abun wani iri lallai dan hakin daka raina shine yake tsone maka ido wata rana. Suhaima ce tace, "Yanzu ya dawo sai dai ko su jira zuwa yamma ko dare." Mum tace, "Ko gobe ne zamu jira har sai mun ganshi in sha Allah." Ita dai Rauda tana nan zaune ta kasa magana sai daga baya ta mik'e tayi musu sallama ta fita duk suka bita da kallo zuciyar su na tariyo musu dukkan abinda suka aikata. Rauda sai yamma tayi abinci kamar kullum aka tafi kaiwa mai martaba ta canja kaya zuwa atampa doguwar riga ta d'ora mayafi babba kamar ko yaushe dan ita ba son saka alkyabbar nan take ba zafi isar ta yake yi. A saman sa ta ajjiye tray d'in yana zaune ya canja kaya shima yana kad'a k'afar sa waya na kunne sa yana amsawa. Zama tayi jin da larabci yake wayar bayan ya kammals tace, "Akwai Maman Jidda tana son ganin ka tana nan tun d'azu." Abinda tace kenan ya kalle ta yaga fuskar a d'aure sai ya tuna yadda suka rabu. Had'a ido sukayi yayi mata nuni da ta bashi abincin ta tashi ta zuba masa ta mik'a masa ya karb'a ya rik'e hannun ta ta zauna ya cika cokali ya kai bakin ta. Bata da zab'i dole ta buɗe bakin ya bata sannan shima yaci baice mata komai ba, a haka suka ci abincin ya d'auko ruwa da kansa ya bata tasha shima yasha ya sake share ta kamar ma baiji me tace a d'azu ba. "Fushin duk na meye Sultana?." Jin sunan da ya kira ta ya saka ta kalle shi tace, "Muwaddaty sunana ba Sultana ba." Yayi murmushi yace, "Ohh sorry Muwaddaty, fushin na meye?." Ta girgiza kanta tace, "Ba kai bane daga yin maganar makaranta sai ka kawo min zancen da zai b'ata min rai, in baka so nayi ai sai ka fad'a min ba sai ka fad'a min maganar da zatayi barazara ga zuciyata ba" ta kalle shi tace, "Wallahi Sultan zuciyata bugawa take yi ji nake kamar zata fashe" ta fad'a tana kallon sa kamar zatayi kuka. Yayi murmushi ya rik'e hannunta amma baiyi magana ba sai daga baya yace, "Na fad'a miki gaskiya ne Muwadda, ba tsarin gidan sarauta bane tafiya karatu ka bar miji a wani garin" ya fad'a yana kallon idanun ta. Shiru tayi dan tasan akwai k'arashen maganar raba maganar yayi sai ya gama hutawa yana ja mata aji zai fad'a. Shiru ya sake ratsawa kafin yace, "A wata masarautar zama da mace d'aya haramun ne a al'adar su, a nan ba lallai bane amma ki duba Abbana kiga matan sa nawa." Kallon sa tayi tace, "me kake nufi? Me kake so kace min?." Yayi dariya mai sauti ya girgiza mata kai ya jingina da bangon kujera yana kallon ta amma baice komai ba, sai da suka d'auki mintina goma a haka sannan yace, "Babu abinda nake nufi, ina fad'a miki ne in kina son karatu har matakin PHD zakiyi Muwaddaty, ki zab'i duk inda kike so zan kaiki amma ki sani zaki bar wata a nan ke kina can duk sanda na samu lokaci zanzo wajan ki." Sai kawai ta fashe da kuka ya runtse ido yasan daman sai anyi haka tace, "Kawai kace min kana so ka k'ara aure basai kana yi min magana cikin magana ba, wayyo Allah na shiga uku" ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Bai kulata ba sai da ta gaji da kuka tayi shiru ta mik'e zata tafi taji yace, "In ina da ra'ayin a baya a yanzu na sauke, ki duba abubuwan da suka faru a gidan nan bazan so su faru da abinda zaki haifar min Muwaddaty." Ta juyo ta kalle shi yace, "Beside bana da wannan ra'ayin ke kawai kin ishe ni rayuwar zaman duniya, bazan iya had'a ki da kowa ba ke kawai kece." Dawowa da baya tayi ta zauna ta rungume shi tana dariya yayi dariyar shima amma baice komai ba. "Har naji dad'i da ka saka naji tsoro, indai haka ne na fasa karatun bazan sake maka maganar sa ba na hak'ura." Baice komai ba ta d'ago ta kalle shi taga yana kallon ta yayi murmushi ya dungure mata kai a zuciyar sa yana aiyana tabbas zatayi karatun tunda tana so. Basu fito ba sai magariba suka wuce wajan Abba tare suka gaishe shi kafin su rabu ta koma ta barshi tare dashi. Abba ya kalle shi yace, "Naji dad'i da naga kana farin ciki Asad, hak'ik'a naji dad'in da ka samu mace mai tarbiyya wacce zata d'ebe maka kewa a koda yaushe." Asad ya kalli Abba nasa yace, "Abba yanayin jikin ka ya canja." Mai martaba yace, "Jiki yak'i dad'i  cikin kwanakin nan Asad, shiyasa na ce ka gaggauta dawowa duk da daman kana cikin garin nan na sani na kyale kane ka huta kamar yadda kake buk'atar sa. Jikina yak'i dad'i gabad'aya daman jikin tsufa sai a hankali kullum mutuwa sake gabato mu take." Jikin Asad yayi sanyi ya kalle shi sai gaban sa ya fad'i Abba yace, "Ka yiwa iyayen Jidda gaisuwa kuwa?." Asad yace, "Munyi da mahaifinta a waya mahaifiyar ta kuma tana wajan Mama daga nan wajan ta zanje." "Duniya kenan, wacce suka so su kashe sai gata itace take rayuwa dakai wacce suka so ta rayun itace ta bar duniya, in baka ji tsoron Allah a a duniya babu inda imanin ka zaije." Asad yace, "Abba ya jikin Aliyu?." Abba ya murmusa yace, "Asad kenan, Allah yayi maka albarka, Allah yasa ka cigaba da ganin albarka a rayuwar ka daga nan har ka bar duniya. Kana son y'an uwanka da zuciya d'aya su kuma suna yi maka zagon k'asa." Asad ya amsa da amin kafin Abba yace, "Jikin ana samun cigaba sosai, Allah ya yiwa Kawun matar ka baiwa ta sanin magani a ayoyin alkur'ani da kuma maganin gargajiya. Jikinsa yana kyau sosai wani lokacin ma har magana yanayi." Asad ya sauke numfashi yace, "Abba Hydar kuma shiru ban sake jin labarin sa ba, jikina yana bani kamar ciwon sa ta tashi a wani waje daban." Mai martaba yace, "wataƙila kuma yana can yana shirya hanyar da zai kawar da kai dan ba abin yarda bane ba." Shiru Asad yayi kafin Abba yace, "Asad ka kula da y'an uwan ka maza da mata dukkan su kaine babba a cikin su kai Allah ya zab'a ya bawa matsayin da bai bawa wani a cikin su ba, ka kula dasu kar ka bari wani abu mara dad'i ya sake faruwa a masarautar nan, da kai kad'ai na amince zaka saita koma bisa addini kayi haƙuri da duk qalubalen da zaka fuskanta shine matakin nasarar ka." Asad ya kalli mahaifin nasa jin yana masa magana kamar wasiya kafin yayi magana ya kuma cewa, "kayi mulkin ka tamkar yadda ka fara cikin ilimi da kuma taimakon na k'asa Asad, kar kayi hange akan wata masarautar kace kaima bara ka gwada abinda suke yi kayi naka tsarin yadda ta hanyar mulkin ka zaka shiga aljanna. Kar ka had'a kai da ko wanne d'an siyasa ka tsaya iya matsayin ka duk wani d'an siyasa da yake burin taimakon talakawa shine naka shima kuma kar ka zak'e da yawa." Asad yayi shiru yana jin rauni na mamaye masa zuciyar sa baice komai ba Abba yace, "Hydar!." Jin yadda ya ambaci sunan Hydar ya skaa ya kalle shi yaji yace, "Kada a sassauta masa ayi masa hukinci daidai da abinda ya aikata, kar kaji tausayin sa kayi masa hukunci Asad yin hakan shine cikar k'imar ka shine zai saka kowa ya fara shayin aikata laifi sabida zasu ga k'anin ka mafi soyuwa a gare ka yayi baka raga masa ba." Asad ya girgiza kai yace, "Abba dan Allah ka daina irin wannan maganar sai naji kamar kana bani wasiya ne." Abba yayi murmushi yace, "ita nake baka Asad, bani da tabbacin kaiwa gobe a raye shiyasa nake fad'a maka abinda yake raina, ka kuma yi k'okarin cika abubuwan dana fad'a maka. Kar ka amince da kowa daga Mubarak sai Suhail sai kuma matar ka, hatta mahaifiyar ka ba abar yadda bace wanda na lissafa masa sune zasu tsaya ganin sun kare ka daga duk abinda zai same ka, sune kawai zasu iya sadaukar da ransu sabida kai." Asad yaji yana k'ok'arin yin hawaye yaji Abba yace, "Kar kuka ya zubo daga idanun ka Asad, kai jarumi ne ka rik'e wannan jarumtar Kar ka bari zuciyar ka ta karye." Asad ya kasa magana mai martaba ya cigaba da fad'in,  "Addu'a kar kayi wasa da ita, nasan baka yi kana iya k'okarin ka amma ka k'ara a yadda kake yi d'in Asad! Itace ta kawo ka matakin da kake kai ka daure ta sake kaika na gaba. Na amince dakai Asad dukkan dukiyata dana mallaka suna hannun ka bayan na rasu d'an autan ku bana so yayi kuka balle kuma y'an uwan ka mata, ka zamar musu mahaifi ka zamar musu Yaya ka zamar musu shugaba." Ya rik'e hannun Asad yace, "Nasan indai kana raye babu wanda zaiyi kuka Asad, bana so iyalai na su tarwatse sabida rashin kula kayi min alqawarin kula da komai yadda ya kamata." Asad ya kasa magana sai zuciyar sa da ta karye yayi shiru baice komai ba Abba yace, "Nasan kayi Asad bani da haufi akan alqawarin ka nasan zaka cika dan baka cikin mutane masu sab'a alqawari. Allah ya albarkace ka dakai da abinda matar ka zata haifa, Allah ya kare ku a duk inda kuke yyi maka katanga da alkhairi ya raba ka da sharri." Shiru falon yayi Asad ya kasa cewa komai jikin sa yayi sanyi sosai Abba yace, "Tashi kaje ana kiran sallar i'sha." Ya kalli mahaifin sa sai yaga yayi murmushi yace, "Muje tare muyi sallah." Jiki a sanyaye Asad yayi sallar i'sha bayan ya idar ya koma b'angaren sa ya zauna shiru ya kasa furta ko wacce kalma maganar Abba nayi masa amsa kuwa a kunnen sa. Wayar sa yaji tana k'ara ya duba number Mama bazai iya k'in d'auka ba ya d'auka jin abinda tace ya saka shi sauke numfashi ya jima a zaune kafin ya taso ya sakko zuwa k'asa. A nan ya same su dasu Mum ganin hakan sai ya daure yace, "Mama da an kirani dana zo da kaina." Kallon sa kawai tayi ta tabbatar akwia abinda yake damun sa amma bata muna ba tace, "Sadiya da Eman ne suke so su ganka." Zama yayi Mum tana k'asa ya kalle ta yace, "Ya karin haƙuri?." Mum sai ta fashe da kuka tana fad'in, "Alhamdulillah." Kafin yayi magana tace, "Dan Allah kayi haƙuri ka yafe min nayi maka abubuwa wanda ni kaina ban san adadin su ba." Ya dakatar da ita a hanyar fad'in, "Ko ban san adadin su ba Allah ya sani kuma zai yafe miki domin ni na yafe miki dukkan ku, har ita Jidda na yafe mata ina yi mata fatan samun rahmar Allah." "Na gode Asad, Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka abinda kake." Ya sauke numfashi yace, "Amin ya rabbil alamin." Mama ta kalle shi suka had'a ido sai ta sauke kai k'asa maimakon shi ya sauke idanun sa k'asa suka tashi suka fita duk sai yaji wani iri a zuciyar sa. Komawar sa sama babu wuya Rauda tazo inda yake ganin yanayin da yake ciki sai bata yi masa magana taga ya keb'e kansa ita kanta ranar kasa gane kansa tayi duk da tayi k'okarin ganin damuwar ta ragu amma ko kanzil baice mata ba sai dai ya bita da idanu kawai a haka suka kwana kowa zuciya babu dad'i. *Bayan wasu kwanaki.*