*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS _No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ *DISCLAIMER* This is a work of fiction. All characters, names, and events are products of imagination and are not intended to depict any real persons, living or dead, or to actual events or locales is entirely and purely coincidental. May Allah make this story a source of benefit and lessons, and forgive me for any shortcomings. Ameen. *DEDICATION* To Fatima Hassan Yakubu, This journey of words is for you. Life may write different stories for people, but if any line feels like yours, take it as a sign from Allah, thank you for your love, your loyalty, and your light. May our sisterhood never fade 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim CHAPTER 1: Not just the beginning! "Jannat ki buɗe kunnuwanki ki saurare Ni da kyau!" Abuya da ke zaune kusa da Ummi ya faɗa muryarsa a kausashe yana nuna ni da yatsa yayin da nake durƙushe gabansu kaina ƙasa "Matsawar ina da daraja a wurinki kuma kin yarda ni na haife ki to dole ki amince da zaɓin da na miki, auren ki ke da Khalil babu fashi matuƙar dai ina numfashi a doron duniyar nan, wajibi ne, dole ne ki rabu da so called Doc Wani mugun kallo Ummi ta aika min tare da dungure min kai tana faɗin "Wallahi Jannat, kin ji na ce wallahi ko? Matsawar za ki take umarnin da muka gindaya miki na auren Khalil, wallahi zan iya yafe ki cikin ƴaƴana, ke in ba da ma ƙaddara me Khalil zai yi da ke? Ba Ni na haifi Khalil ba amma ya fiye min ke sau dubu miliyan, don ina da tabbacin cewa ko Ni nan in na shata masa layi ba zai take ba, ke fa? Um?" Wani irin kuka na saki da da ran za su tausaya min, irin kukan nan da ake wa laƙabi da marayan kuka, kukan da duk wanda kunnuwansa suka jiyo sautinsa ba makawa tausayi da kuma rangwame za su mamaye zuciyarsa, amma kash, ban da Ummi da Abuya, wanda cikin kwanakin nan da suka fahimci alaƙar da ke tsakanina da BB suka riƙe min wuta kamar ba su suka haife Ni ba. Cikin muryar tawa mai haɗe da fitar Kuka na ce "Ummi, Abuya, wallahi ku kuka haife ni na san wannan, ku ne kuka min gata har na kai yanzu, don Allah Ummi na roƙe ku kada ku ruguje min rayuwa ta hanyar aura min BB, wallahi ba shi ne wanda...." Hannu Ummi ta kai min za ta buge bakina, Abuya ya yi saurin riƙo hannunta ya dawo da ita mzauninta, cikin ƙunar rai da takaicin abun da na ce ta aiko min da wani mugun kallo da ya sa ƴaƴan hanjina juya, sauƙe kaina ƙasa na yi babu shiri. Ummi ta ce "Ba shi ne wanda kike so ba ko? To ƙanin uwarki kike so um?" Abuya kam numfashi ya sauƙe yayin da yake Ƙoƙarin saisaita ɓacin ransa, cikin wata irin murya da na gagara gane manufarsa ta ce "ba sai kin sa hannu kin dake ta ba Amina, rabu da ita, idan har ta san wata ai ba ta san wata ba, aure kuma da Khalil na faɗa miki babu fashi, idan ya so ki kashe kanki in an aura miki shi, yarinya ƙarama da ke ba za ki lalata mana zumunci Ni da ɗan'uwana ba don ke a sama na same ki, shi kuwa da shi muka yi gwagwarmayar rayuwa har muka kawo matakin da muke ba tare da an taɓa jin kanmu ba, ke a wankin ce za ki zo min da banzar magana Jannat?" Abun da ya maƙale masa a maƙoshi ya haɗiye sannan ya ce "Ko bayan raina Jannat, ban amince ki auri wani ɗa namiji ba in ba Khalil ba, kin ji abin da na ce ko?" Cikin shesheƙar kuka na ce "Don Allah Abuya kar ka min hak..." "Za ki rufe min baki a nan ko sai na ɗauko bulala na fara bugun ki?" cewar Ummi wacce ranta ya gama ɓaci da rashin ta ido da nake sheƙa musu. A tsorace na ɗan ja Baya ganin kamar Ummin za ta dake ni. "Shashasha kawai! Madadin ma ki fahimci inda muka dosa jeji kike ƙara nausawa, anya kuwa kan ki ɗaya Jannat?" Abuya ya faɗa cike da kokonton sabbin halayen da nake displaying a ƴan kwanakin nan. Hausawa suka ce Abun da babba ya hango, ko dutsen dala yaro ya haye ba zai iya gani ba. To kamar haka ce take faruwa a wannan gida, duk wata hanya ta lallami Abuya da Ummi sun bi wajen ganin na karɓi soyayyar ɗan'uwana amma abun ya ci tura, na dage dole sai Dr. Junaid, mutumin da ba ma ɗan garin ba ne a binciken da Abuya ya sa aka yi akansa. Yadda nake ke kuka gaban su Abuya kamar raina zai fita ya sa ran Ummi ƙara ɓaci, cikin hargagi ta ce "Ɓace min da gani kafin na zuciya na miki dukan da sai kin yi zaman jinya, wawuyar yarinya kawai" Da mugun sauri kamar wacce ke zaune gaban dodo na fara ƙoƙarin barin gaban nasu har ina dungurawa, cikin kaɗewar hankali da na samu na tashi sai na ruga da mugun gudu har ina cin tuntuɓe kamar zana faɗi har lokacin sautin kuka na na fita. Ɗakina na nufa kai tsaye tare da faɗawa kan lallausan gadona wanda a yanzu nake jinsa tamƙar ƙaya, kai ba ma gadon ba, gidan kansa a yanzu ya gama isata, ba Ni da wani buri a yanzu ko fata irin a ce an ɗaura min aure da Dr. Junaid mun tare a gidanmu Ni da shi, rufe fuskata na yi da tafukan hannayena biyu ina mai ƙurawa chandelier da ke sarƙafe jikin farin POP ɗin da ke ɗakin ta tsakanin ƴaƴan yatsuna. Kukan na ci gaba rairawa tun muryata na fitar da sauti har ta dashe, tun hawayena na zubowa har suka daina zuba ya zamana kukan da nake yi na fita ne daga zuciyata har wata irin ƙuna nake ji daga can cikin ƙirjina. Tabbas ina cikin mawuyacin hali a yanzu, iyayena da ya kamata su nuna min kulawa a wannan yanayin sun juya min baya akan mutumin da ya raine n da tsantsar ƙiyayya da mugunta, mutumin da bai ƙi igiyar numfashinmu Ni da ƴar'uwa Rafi'at ta datse ba tun muna yara ƙanana, mutumin da bai taɓa dubanmu da idon rahama ba bare kuma tausayawa sai zallar son ganin hawayenmu. "Ta yaya suke tunanin zan so shi?" Na ayyana hakan cikin raina daidai lokacin da nake sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya, Zaune na miƙe tare da jingina kaina da fuskar gado, cikin dasasshiyar muryata da ke fita da ƙyar kuma cikin sauti mara amo na ce "Don kawai ya buɗe baki ya furta min kalmar soyayya sai na yarda da shi? Babu yadda za a yi maƙiyinka ya ce yana sonka rana ɗaya! So na da yake a yanzu ba zai canza komai ba, don har yanzu ba na jin zan iya mance duk wata nau'in izaya da cutarwarsa gare ni ba." Ba wai ban yarda yana son nawa ba ne a yanzun, a'a Ni kaina ina iya ganin tsantsar soyayyata cikin ƙwayoyi idanuwansa amma dai, zuciyata ta riga da ta gama soyewa, ta bushe ƙayau, ta ƙaiƙashe, kai ta ma zama gari in dai akan ta so shi ne, ji nake a raina ba zan taɓa son BB ba, so dai so irin na soyayya kam, ba na jin zuciyata za ta ji shi akansa, kai ko a mafarki ba na tunanin hakan, bare kuma kuma a zahirance, har babban al'amari wato aure ya shiga tsakaninmu, Dr. Junaid shi ne zaɓin raina, shi ne wanda nake muradin rayuwa tare da shi a ƙarƙashin inuwar aure, don haka babu gudu babu ja da baya, Dr. Junaid shi ne wanda zan ta aura ko da kuwa gaba ɗaya duniya za su juya min baya ne. Sulalewa na yi daga jinginon da na yi na kwanta tare da Juyi ina mai dafe kaina da ke mugun ciwo sakamakon kuka da kuma rashin cin abinci da na saka gaba wanda nake ganin kamar shi ne mafita gare na, ina ganin ta iya wannan hanyar ne in na ɓullo Abuya da kuma Ummi za su janye tsumagiyar da suka ajiye mata kan hanyata tare da cika min muradin da nake jin bayan shi na gama samun duk wani farin ciki, jin daɗi da kuma walwala a rayuwata, tunanin yadda zan samu Wayar da zan yi magana da Dr. Junaid nake amma babu wata dama, Ya Sadiq ne dama hope ɗina, shi ma kuma a yanzu na san cike yake da matsanancin haushinna, ko da kuwa zan shura ne ta mutu na san ba zai ba ta wayarsa na kira wani ba ma, bare kuma Dr. Junaid da a yanzu na tabbatar illahirin gidanmu babu wanda bai tsane shi ba, domin gani suke kamar ya yi min wani abu ne shi yasa nake behaving so strange about him. Rafi'at ce ta faɗo min a rai. Hakan ya sa Ni miƙewa zaune ina furta sunan Rafi'at ɗin cikin dasasshiyar muryata "Rafi'at?" saurin girgiza kaina na yi ina faɗin "Nooooo, Ban da Rafi'at, ta yaya ma zan iya kallon tsabar idanuwanta na ce mata ta ban wayarta na kira Dr. Junaid after all ido cikin ido na ce mata ba na son ɗan'uwanta?" Na ƙarashe ina girgiza kaina, duk da cewa dai Rafi'at ba ta juya min baya akan abun da ke faruwa ba sai dai kuma Ni kaina ina da yaƙin cewa cikin ranta tana tsananin jin haushina, ko ba komai BB ɗan'uwanta NE, ƙyamarsa da na nuna kaɗai ya isa ya yanke alaƙata da Rafi'at, amma abun sai bai zo a haka ba, ko a fuska ba ta nuna min hakan ba tun daga ranar da ta fuskanci abun da ke kai kawo tsakanina da kuma Yayanta, ko ma dai meye, ba shakka alaƙar da ke tsakanina da Rafi'at alaƙa ce mai ƙarfi da ake wa take da Mutu ka raba!. Ban kai ga samarwa kaina mafita ba na jiyo sallamar Rafi'at a parlour suna gaisawa da Ummi. A kunnena na ji Ummi na ce wa Rafi'at ɗin "Tana ciki tana fama da baƙar zuciyar tata irin ta kafuran farko, Ke ma dai na rasa wace irin mace ce maras kishin kanta, yarinyar da ta nunawa duniya ba ta son ɗan'uwanki ita ce kike yi wa jinyar zuciya? Iska dai tana wahalar da mai kayan kara wallahi" Murmushi kawai Rafi'at ta yi wa Ummu sannan ta ce "A yi haƙuri Ummi, bari na shiga na duba ta." Babu kunya bare tsoron Allah ina jin Rafi'at na sanya ƙafarta cikin ɗakin na wani juya mata baya. Cikin sassanyar muryarta ta ce "Ni kika juyawa baya Jannat?" Banza da ita ma yi, ina jin ta sai da ta ƙara cewa "ba za ki juyo ki kalle Ni ba ko?" "Shi ke nan na fahimta. ƙiyayyar da kike yi wa BB Nima a yanzu dai ta shafe kasancewa ta jininsa ko?" Motsawa na fara yi da niyyar juyowa, a hankali na gama juyowa sakamakon yadda kaina ya min wani mugun nauyi kamar an ɗaura min ƙaton dutse akai, kallo ɗaya na yi wa Rafi'at daga nan na kawar da kaina gefe, tsare ni da ido Rafi'at ɗin ta yi. Cikin sassanyar muryarta ta ce "Yanzu ke Jannat abun da kike yi kina ganin shi ne daidai?" Ko kallo Rafi'at ba ta samu daga gare ni ba bare ta yi tunanin zan tanka mata. "Hukunta kanki da yunwa da kuma kuka ba shi ne mafita ba, ya kamata a ce ƙwaƙwalwarki ta fayyace miki komai Jannat, wai shin wace irin zuciya ce a ƙirjinki? Wace irin ƙiyayya ne kike yi wa BB um? na san cewa BB ya wahalar da mu da izaya iri-iri a baya, amma in za mu dubi hakan da buɗaɗɗiyar zuciya wallahi tsantsar ƙaunarsa gare mu ce ta sa shi yin hakan, meye aibun BB um Jannat? Shin ko don Ni bai cancanci ki masa alfarma ki so shi ba? Ina da tabbacin cewa BB ya ɗara Dr. Junaid ɗin da kike tinƙaho da shi ta kowanne fanni..." Saurin katse ta na yi yi cikin dasasshiyar muryar tawa da ke fita a hankali na ce "Ya isa haka Jannat, idan har abun da ya kawo ki ke nan, gara tun magariba ba ta miki ba ki koma gida, ya kamata Ku fahimci cewa soyayya da kuma yafiya akwai banbanci, Ni ban ce ban yafewa BB ba, amma dai son shi ne kawai ba zan iya ba, saboda ina da wanda nake so, akwai wanda zuciyata take muradin yada shi, amma ku kun gagara fahimtar hakan, yaya kuke so na yi ne? Na haƙura da zaɓin zuciyata na bi naku zaɓin ke nan?" Ta ƙarashe tana ɗan ɗaga muryarta da ba wani sosai take fita ba saboda kukan da ta ci. Kasancewar Rafi'at mai raunin gaske ya sa ta fashewa da kuka tare da ƙarasowa kan gadon, ba tare da na aune ba na ji ta rungume da Ni tana kuka mai cin rai, sanyi sosai jikina ya yi da hakan, iya sanina, tsawon. mu'amalata da Rafi'at tun yarinta Ni ke cutar da ita, kusan duk wani hukunci da BB zai mana a baya ma Ni ce ke jaza mana laifin don kuwa ita Rafi'at babu ruwanta, irin mutanen nan ne masu bin doka da ƙa'ida. A hankali na tsinci kaina da fara shafa bayan Rafi'at, can dai na ji ta tsagaita da kukan tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai. A hankali ya raba jikinta da nawa tare da kallonsa, sanya idanuwanta cikin nawa ta yi sannan ta ce "Ina da yaƙinin cewa wanda kike so ba ya miki kwatankwacin soyayyar da BB ke Miki, ki nutsu Jannat, kada ki biyewa don zuciyarki wurin yankewa BB hukunci, duk da na San irin tsanarsa da kika yi da wuya ki iya tuna alkhairansa gare ki, ba wai ina goranta miki ba ne, at least i'm just telling you the fact, wannan shi ne alaƙar gaskiya, Ina so ki nutsu ku yi tunani, shin alkhairansa kaɗai ba su kai ki masa alfarma ki so shi ba?" Duk da cewa maganar tata ta so yin tasiri a cikin zuciyata don ba kaɗan ba ta buge ni, a hakan dai na ƙara haɗe fuskata kamar ban ma fahimci ina ta dosa ba, ganin ban kula ta ba ko ma na nuna alamun ina sauraronta ya sa ta sauƙe numfashi tare da faɗin "Shi ke nan. Zan ba ki wuri Jannat, zan je na yi jinyar zuciyar ɗan'uwana, Amma ina ba ki shawara, ki nutsu ki yi tunani, ba na fatan ki aitaka Kuskuren ƙin amincewa da auren ɗan'uwana, idan kuma muka yi hakan, ki sani ya zama min wajibi nima na rabu da naki ɗan'uwan!" Dim! Gabana ya bayar da wani irin sauti, gaza ɓoye halin da zuciyata ke ciki na yi sai da na waro idanuwana da suka yi ja suka kuma kumbura saboda kuka, sai yanzu ma na tuna ashe Ya Sadiq da Rafi'at suma soyayya suke yi, sanin irin tsananin yadda Ya Sadiq ɗin ke ƙaunar Rafi'at ya sa ta dafe ƙirjina, na san waye BB, mutum ne mai juriya da kuma ƙarfin hali. Tabbas Rasa Ni da BB zai yi na san zai shiga wani hali sai dai ina da tabbacin na wani lokaci ne ƙalilan. Amma Ya Sadiq fa? Tabbas idan har Rafi'at za ta iya aikata abin da ta faɗa. Wato ta ta rabu da shi zuciyarsa za ta iya bugawa nan take. Idanuwana na ɗan waro ina jinjina girman al'amarin a zuciyata ban gama wannan nazarin ba na ɗago don na lallaɓa Rafi'at sanin cewa ita mace ce mai haƙuri da sauƙin kai, sai dai me? Ta riga ta fice a ɗakin. Ajiyar zuciya na sauƙe ina tunanin yadda duniya ta juya min baya lokaci guda. A yanzu dai ba Ni da wani buri da ya wuce na auri Dr. Junaid saboda yadda nake ji a raina idan har ba ta same shi ba numfashina zai iya rabuwa da gangar jikina wanda hakan zai iya zama silar rasa rayuwata, takunkumin da su Abuya da Ummi suka sa min ya yi min tsanani, sun ƙwace wayata, system ɗin ma da take ɗebe min kewa sun karɓe ta sun ba wa Jadeed, ga shi yanzu har mai gadi an masa gargaɗin kada ya kuskura ya bar Ni na fita waje, haka nan kuma sun gargaɗe shi da ya sanar da su idan wani ya zo wurina, to yanzu saboda ni Ummi ma ta koyawa kanta zaman parlour Wanda da ba ta fiye yi ba. Cikin wannan yanayi wani ɓarawon bacci ya sace ni, kasantuwar jikina na tsananin buƙatar baccin ya sa na yi shi hankali kwance, ba ni na tashi ba sai wuraren magrib sakamakon karatun da sauraye ke raira min cikin kunnuwana, wani irin juyi na yi ina sakin wani kasalallen nishi sakamakon rashin ƙarfin jiki da nake ji ga kuma yadda kaina ya ƙara min wani irin nauyi ga yadda jijiyoyin idanuwana suka wani matse wuri guda. A daddafe na iya tashi na nufi toilet, alwala kawai na yi na fito ina bin bango, da ƙyar na iya kawowa gaban gadona na faɗi rigijib kamar tarin kayan wanki sakamakon jirin da ya ɗebe ni. Idanuwana nake ƙoƙarin buɗewa amma abun ya ci tura, da ƙyar na iya buɗe su a wahalce sai dai me? ba abun da nake iya gani sai duhu. Tsoro ne da kuma fargaba suka ziyarci Ni lokaci guda, ƙoƙarin ƙara ware idanuwan nawa na kuma yi, but same, ganina ya ɗauke ba abun da nake gani ban da duhun da ya mamaye ko ina. Wani irin wahalallen ihu na saki ina kiran sunan Ummu, daga nan ban ƙara sanin inda nake ba. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 2: Sunana Jannatul-Firdaus Sulaiman Shirama, mazauniyar unguwar Gandun wambai kuma haifaffiyar garin AZARE da ke jahar Bauchin Najeriya. Tun ina ƙarama na kasance yarinya maras ji mai shegen rawar kai, hakan ya sa ko kaɗan ba ma shiri da mahaifiyata wacce muke kiranta da Ummi, haka zalika mahaifina Abuya, sai dai ta nashi ɓangaren akwai sassauci saboda ba ya bugu na, kawai dai shi ko yaushe yana cikin yi min faɗa ne. Mahaifina Abuya, su huɗu ne a wurin mahaifinsu, Wansa babba, shahararren attajiri ne, Alhaji Abubakar Shirama, wanda muke kira da Daddy, Abuya shi ke biye wa Daddy, sai ƙannensu biyu, Hajiya Bara'atu wacce ke aure a garin Misau, muna kiranta da Mommyn Misau, autarsu ita ce Hafsatu, tana aure ne a ƙaramar hukumar jama'are, ita kuma muna kiranta da Mommyn Jama'are, Abuya da kuma Daddy gida ɗaya suke, ban da Kakarmu mahaifiyar su Abuya, wacce sam ta ƙi zaman Azare, a cewarta, ta fi so itama ta mutu a inda mijinta ya mutu, tana zaune ne a gidanta da Abuya ya gina mata a Misau. Gaba ɗaya gidan su Abuya kansu haɗe yake, don kuwa duk wani hali da ɗayansu zai shiga, imma na rashi ko samu, suna kasancewa a tare da shi, Abuya da Daddy da suka kasance maza, tare suke yanke hukunci akan ƴaƴansu, though kusan ragamar yanke hukuncin a hannun Daddy take, kasancewar shi ne babba, hakan yana matuƙar burge Ni idan naga Abuya na bai wa Daddy girmansa, su dai tsakaninsu sai son Barka. Wani ƙarin abun burgewar bai wuce yadda matansu suka haɗe kansu ba. Don kuwa tsakanin Hajiya Turai (Mommy) da Hajiya Amina (Ummu) sai son Barka, kai, bare kam ma in ya gansu sai ya yi tunanin ƴan'uwan juna ne kamar dai mazajensu, Ni kaina ban da dai muna zuwa wurin danginsu da ba zan san da hakan ba. Mommy ƴar asalin ƙaramar hukumar Shira ne, yayin da Ummi kuma ta kasance haifaffiyar garin Giade. Daddy na da ƴaƴa biyu ne, shi kuma Abuya uku. Ibrahim Khalil shi ne babban ɗan Daddy, muna kiran shi da BB, wato Big Bro, sai kuma mai bi masa, Abubakar Sadiq, ɗa na farko wurin Abuya, muna kiran shi Yaya Sadiq, tsakanin Yaya Sadiq da kuma BB akwai ratar shekaru huɗu, hakan ya sa da wuya ka gan su tare wuri guda, kasancewar BB mutum Mai Kamun kai. In ka gan su tare, to wata muhimmiyar magana za su yi, ko kuma dai shi Ya yana buƙatar wani abun wurin BB. Unlike Habib farouq mutum ne mai son barkwanci da raha, baka rasa shi da abun dariya kuma ko yaushe fuskar shi dauke da murmushi take, yanzu haka yana aiki ne asibitin koyarwa da ke garin Azare (Fuhstha). Rafi'at ƙanwar BB ce, ta girme Ni da shekara guda. Amma dai tare muke komai namu tun muna yara, hatta Bacci wuri guda muke yi Ni da ita, ita ɗin matsayin da take da shi gare Ni suna da yawa, ƴar'uwata ce, aminiyata kuma Abokiyar shawarata kafin BB ya faɗo cikin duniyata da maganar soyayya. Ni ce mai biyewa Rafi'at, sai kuma ƙanina Ayman, ɗan kimanin shekaru takwas a yanzu. BB, kamar yadda sunan nashi ya nuna ya cancanci a kira shi da hakan, domin kuwa mutum ne mai matuƙar kamun kai da jan aji, la'alla ko don kasancewarsa kyakkyawa ne? Allah kaɗai ya bar wa kanshi sanin hakan. Kyakkyawa ne kam ajin farko, fatar shi nada haske amma ba irin dau ɗin nan ba, siririn hancinshi da ke a tsakiyar fuskar shi tamkar ajiye shi aka yi, lips nashi basu fiye girma ba sai dai suna da dan kauri, sama black na ƙasan kuma pinkish, ga uwar cikakkiyar girar shi da ta ƙara bayyana ainihin kyau na guy din. Sajenshi na da ɗauke da wadataccen kwancaccen gashi da ya yi luf ya manne jikin fatarsa, Sumar kansa kuwa ta kasance baƙa siɗik sannan kuma a yalwace take, shi ya sa kusan ko yaushe za ka ga kansa tsaf-tsaf yana ƙyalli, yau this hairstyle and tomorrow that hairstyle. BB mutum ne mai izza, isa, da kuma taƙama, ko kaɗan ba ya ɗaukar raini a wurin ko ma waye ne, bai ma shiga sabgar mutum ba bare ya samu damar raina shi, yadda BB yake a waje na ya fi sauƙi akan a cikin gidan musamman ga mu ƙannensa, tun muna yara yake cin ƙwal ubanmu, yadda muke shakka da tsoronsa ko iyayenmu ba ma yi jin hakan kansu, slight mistake za mu yi ya ba mu punishment ɗin da sai mun kwana mun yini muna jin jiki, abun da ma na lura da shi shi ne, ya fi takura mana Ni da Rafi'at, lafiya lau za ku gani shi yana yi wa Ayman dariya kamar wani abokinsa, amma mu kam ina! BB kamar dodo yake a gare mu. Duk yadda zan kwatantawa masu karatu halayen BB, zai yi wahala su fahimci irinsa, don ko a cikin jerin jaruman litttattafa, ba a taɓa yin kwatankwacinsa ba. Ta ko ina BB is perfect with life. Yana da matuƙar Sa'a da nasara a rayuwarsa, don kuwa duk wani abu da ya sa gaba in Sha Allah sai ya same shi cikin sauƙi, a lokacin da BB ya cika shekaru goma sha takwas a duniya, ƙofofin nasarorin rayuwa suka fara buɗe masa, kasancewar shi mutum mai so da kuma ƙaunar motsa jiki da ƙwallon ƙafa don har gym room yake da shi a gida a wannan lokacin. Wannan hub ɗin da yake da shi a wannan fanni ya sa shi samun wani irin experty a fannin. Nasararsa ta farko a fannin ƙwallon ƙafa ta fara ne a shekarun nan, ya samu damar bugawa ƙasarsa ƙwallo har ya yi nasarar lashe musu kofi, wannan ne ya ba wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban daban son samun shi a matsayin ɗan wasansu, wanda da ƙyar ya amince ya kuma ba su dama, a shekarar ba ƙananan kuɗaɗe ya samu ba, a hakan kuma bai daina samun tayi daga wasu clubs ɗin ba. Su Daddy sun yi matuƙar farin ciki da ire-iren nasarorin da BB ke samu a wannan fage. Amma can ƙasa, Daddy, ya fi so BB ya zama jami'in tsaro ne, ko dai ɗan sanda, soja, ko dai wani aikin ɗamara, bayan tattaunawa da Kaka da suka yi ne Abuya ya tunkari BB da maganar, babu musu ko taurin kai kuwa ya amince, Daddy ya nema masa Form a makarantar aikin sojoji, cikin ikon Allah ya tafi domin samun horo da kuma gwaji a wannan fage, alhamdulillah, nasrun minallah, sunan BB ya fito na biyu ne a jadawalin waɗanda suka yi nasara a wannan gwaji da aka musu, take Gwamnatim ƙasa ta ɗebe su aiki a matsayin ƙananun sojoji. Ƙwazo da yanayin kuzari da kuma kazar-kazar irin na BB ya taka muhimmiyar rawa wurin ƙara buɗe masa matakan nasara, wata rana bayan artabu da suka yi da wasu ƴan fashi da makami ya samu lambar girmamawa, da shi da wani abokin aikinsa da suka haɗu, Khalid Usman Usman sun kuɓuta da rabon ƙara karatu, wanda hakan ba ƙaramar dama ba ce suka samu, da yawa sun buƙaci hakan ba su samu ba, wani abun burgewa da ƙarin karatun da za su yi shi ne, za su ƙara samun matsayi ne da kwalin wannan karatu. Cikin farin ciki da addu'ar iyaye BB ya tafi ƙasar Cairo shi da mutumin da ya nace sai ya shiga rayuwarsa, wato Khalid, Ba na mantawa lokacin muna primary school, boarding school aka saka mu ta ƴaƴan masu hannu da shuni, gari gari har Bauchi, abun ka da makarantar ƴaƴan masu hannu da shuni, babu mai takura mana a Dolphin Maria college, hatta salla sai mun ga dama muke yi, wanda hakan ya sha banban da tarbiyyar gidanmu. Daga Ummi har Mommy tsayayyu ne akan ibada, suna kuma tsananin saka mana ido wurin ganin salla ba ta kuɓuce mana. Tsautsayi ne ya faɗa kanmu wata ranar hutu, Daddy da Abuya duka ba sa gari. Ga shi kuma ko da wasa ba a saka Driver ya ɗauko mu daga school, Daddy ne ko Abuya mafi aksari suke ɗauko mu. Wannan Ranar ta zo da wani irin arashi, ranar BB ya dawo daga ƙasar Canada bayan sun je buga wani wasa, yana dirowa ko hutawa bai yi ba Mommy ta tare shi da batun ɗauko mu daga makaranta. Though ko kaɗan bai ƙaunar abun da zai haɗa shi da mu haka ya amsa da to, daga nan ya fito Mommyn na saka mishi albarka. Daga cikin motocin da ke packing space BB ya sa aka goge masa ɗaya, sannan ya shiga ya ja motar ƙiiiiiiiiii ya bar gidan. Cikin nutsuwa motar ke tafiya kan titi yayin da BB ya ke sauraran karatun surah al'anbiyā' cikin muryar babban ƙari'i Muhammad ayyub yayin da yake bi a hankali da irin muryar, so Masha Allah, kamai nashi na musamman ne. Yana isa Dolphin Maria college securities suka gama checking motar daga nan ya samu damar harba motar zuwa titin dan da zai sada shi da dormitory ɗinmu. Bayan ya magantu da securities na wajen ne aka fara fito da bags da trolleys ɗinmu, yayi da muke biye da masu ɗaukar kayayyakin namu shi kuma BB already ya wuce zuwa cikin motar yana jiran shigowarmu. Ba mu tsaya ɓata lokaci ba ganin mutumin da ya zo ɗaukarmu, ya sa ba mu tsaya ɓata lokaci ba, cikin rawar jiki muka shiga ciki, Ni na faɗa buɗe seat ɗin baya na zauna, hakan ya sa Rafi'at buɗe front seat ita kanta zauna sanin halin BB tsaf zai CE mu fita mishi a mota ya ja ya tafi kayan shi. Cikin rawar muryar da ban taɓa tunanin Ni kaina ina da ita ba na ce “BB sannu da sauƙa fatan ka dawo lafi..” ban kai ga ƙarasa faɗin abun da zan ce ba na ga ya daga min hannu ba tare da ya juyo ya kalle Ni ba, hakan ya sa na ja linzamin bakina na tsuke shi.. “ina yini BB” Rafi'at ma ta gaida shi gudun yin wani laifin a wurinshi. Ko samun kallon arziƙi ba ta yi ba ita ma bare ta yi tsammanin zai amsa mata, dama kuma ba mu yi expecting amsawar daga gare shi ba. Shiru ne ya wanzu cikin motar har muka isa garin Azare , gidanmu da ke unguwar gandun wambai muka nufa, cike da ɗaukin ganin iyayenmu da muka yi kewa muka fara murmushi, yana parking na sa hannuna na taɓo bayan Rafi'at, ƙin juyowa ta yi haka ya sa Ni dole tsayawa jiran umarnin BB ganin itama ba ta fita ɗin ba. Wani mugun kallo BB ya juyo ya aika mana daga Ni har Rafi'at, take hantar cikinmu ta kaɗa don a lokacin har wani ƙugi cikina ya yi saboda tsananin tsoro. "Jira kuke sai na ce ku fita um?" Ya faɗa cikin kaushin murya tare da jan tsaki. Ai bai gama rufe baki ba jiki na rawa muka fice daga motar. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 3: Driver na ganin mu ya ƙaraso wurin motar tamu tare da tsayawa wurin da BB ke ciki har lokacin bai fita ba. Glass ya sauƙe yana gaida Driver, driver ya amsa tare da faɗin "Ƙaramin Alhaji a buɗe Boot na ɗebi kayan yaran" Trolleys da bags ɗinmu ɗaya bayan daya ya miƙa ma kowa zuwa part ɗin da ya dace da shi. Part ɗin Mommy muka nufa da gudu har muna ture juna, ganin parlourn wayam ya sa ni ƙwala kiran "Mommy! Mommy" “Mommy your angels are....” ban kai ga ƙarasawa ba na ji tsawar shi ta dira cikin kunnuwana, take kayan cikina suka fara juyawa ina tausayawa kaina. Rafi'at kuwa da gudu ta nufi bedroom ɗin Mommy, ganin hakan ya sa na ɗaura mata baya shi kuwa yana ganin mun yi ciki ya juya zuwa part ɗin Ummi. Mommy dake zaune bakin katafaren bed din ta ne Jin muryar angels yasa ta yi ƙoƙarin fitowa, cin karo tayi da su kan hanyar su ta shigowa hakan ya Tabbatar mata habib yayi musu halin. Hugging din ta suka yi tare suna ihun murna “mommynmu! Mun yi kewar ku da yawa” janye mu tayi daga jikinta ta riƙe hannayenmu muka dawo parlor, a tsakiyarmu ta zauna sannan muka fara 'yar hirar kwana biyu “kai Mommy don Allah miyasa kika tura BB ɗauko mu bayan kin san sam baya ƙaunar mu" Rafi'at CE ta tambaya tare da ƙarashewa muryarta a shagwaɓe. “nikam ma na san da wuya in ciki na bai ɓaci ba Ummi, irin tsoratarwar da ya mana hmm” na faɗa ina jinjina kaina Mommy kuwa haɓar ta ta riƙe sannan ta bi mu da kallon mamaki. “yaushe na Zama abokiyar ku da zaku ke questioning na akan wani Abu? ” ta ƙare tana jifanmu da wani irin kallo. Hannu muka haɗa wuri guda muka marairaice fuska cikin sigar a tausaya mana muka ce “Allah ya huci zuciar Mommynmu tuba muke” “shikenan ya wuce amma ku kiyaye bana son irin maganganun nan” Da “toh” muka amsa, na ce “mommynmu ko gaisawa dai ba mu yi ba, Ina yini ya gidan" “lafiya ƙalau ɗiyata ya jarrabawar kuma da karatun?” “Alhamdulillah mommy” fadin Rafi'at tana shirin miƙewa “toh Allah ya Ba ku sa'a " “amin” muka furta a tare sannan Rafi'at ta ja hannuna “ki tashi mu je wurin Ummina mana” “ke ki je ni ban gama Jin ɗumin mommyna ba” na fada ina ƙara shigewa jikin Mommyn. Part ɗin Ummie Rafi'at ta tafi, ganin baby ayman na ta rarrafowa yana tunkaro trolleyna da alamun son ta'adi yake yi ya sa ta ɗaga shi sannan ta fara mishi 'yar waƙar “baby Ayman baby Ayman. Baby Ayman farin jinin kowa mai gidan Dada!" Gwalatu da kuma dariyar ayman da kuma muryar Rafi'at yasa ta fito don gani. Da gudu Rafi'at ta yi hugging Ummi tana faɗin “Ummina” “yarinyar kirki” ta fada tana zuba uban murmushi. Parlor suka dawo suka gaisa sannan sai ga shigowar Jannert, bayan sun gaisa da Ummi suka fara 'yar hirar da duk rabin ta shirme CE “Ummi wallahi duk na ƙagu nagan ni a secondary school din nan na ji me ake ji a ciki” Fadin Rafi'at kenan yayin da na yi caraf na ce mata “worry not dear, mu mun kusa zama manya ai" “ai kam manya, gashi har yanzu ɗabi'unku na yara ne" Maganar Ummi yasa muka kwaɓa fuska kamar za mu yi kuka. “haba Ammie kiga fa gashi mun ƙara ɗan tsayi ma fa” “uhm ai na gani, Rafi'at dai tafi kama da mai hankalin amma ke kam Jannert ban San yaushe zaki yi baƙi hankalin ba” kwaɓe face na yi kamar zan yi kuka na fara buga ƙafata ina sakin kukan sbagway “kai Ummi! Damah can ba so na kike yi ba amma ai na fi wannan nunar ranar hankali" na faɗa ina pointing Rafi'at. Dukan da Ummie ta kawo min ya sa na goce cikin zafin nama ina dariya alamun ko ba komai dai na rama. “kuna dai sallah a can din ko dai marasa yi kuka zama a can din" Tambayar da Ummi ta mana yasa muka fara kallon juna muna ƙiƙƙfta idanuwanmu. Rafi'at CE tayi ƙarfin faɗin “e Ummi muna yi amma ba kullum ba fah” Baƙi ta hangame tana kallon su yayin da dukkanmu muka sha jinin jikinmi “shikenan na gane, ƙarfi da yaji makarantar nan so take ta mayar da ku su ngozi da Emanuella koh?” kanmu muka kaɗa alamar a'a. Ummi ta tsare mu da ido sannan ta ce “toh in ba haka ba ku fada min naji, kun san cewa annabi yace *_tsakanin mutum musulmi da shirka da kuma kafirci shine barin sallah_* duk wani musulmi da ya daina sallah ki kuma yayi wannan ya tsallake wannan toh wallahi bari na fada muku he's at risk of transforming himself to Christianity!” Jikinmu ne yayi sanyi yayin da muka sunkuyar da kawunanmu ƙasa “sannan kun san dai duk wani kafiri babu shi ba aljanna ko?” muka gyaɗa kai. Ummi ta ce “yauwah toh kuna ji na ko? Daga yau sai yau ko Ina kuka tsinci kanku sallah ba sai ance kuyi ba kunji?" “eh Ummie mun ji, in Sha Allah toh amma wanda bamu yi ba na baya mun manta guda nawa ne ta yaya zamu biya?” “kada ku damu shi Allah mai yafiya ne, da kun tuba kun gyara shi kenan ba sai kun biya na da ba” Kanmu muka jinjina alamar gamsuwa. Rafi'at da ta fi ni jin wa'azin duk ta fi tsorata “in sha Allah zan ke yin salloli na a cike saboda Ina son shiga aljanna” “nimah haka” “yauwah yaran kirki Allah yayi muku albarka ya ƙara shirya mana ku” “Ameen Amen Umminmu” Kiran sallar maghrib yasa muka miƙe tsaye muka cr “bari mu yi sallah Ummj" “nifa da nayi sallah part din Mommy zan wuce saboda na san BB a nan zai yi dinner, zaman lafiyarmu muna yi mu face can” na faɗa ina wawwaigawa kada na je yana jin mu, domin kuwa yawanci duk lokacin da za mu yi maganrshi sai dai mu gan shi a kanmu. Muna yin alwala muka koma part din Mommy muka nufa. Muna yin salla muka yi ta roƙon Allah yafiya zuciyarmu fal nadama, daga nan muka fito parlour wurin Mommy da ke kallo. *____NOTE!!!____* Na daga cikin sauƙe haƙƙoƙin yara a kan iyaye tarbiyyar su. A matsayin ki na uwa, kiyi iyakar iyawar ki wajen ganin kin bawa yaranki tarbiyya mai kyau, ba wai duka ne zai sa yaro ya shiryu ba dole sai kin haɗa da yi musu addu'ah saboda ke ɗin garkuwarsu CE. Idan kika ga yaran ki sun yi ba daidai ba, ki ja su a jiki ba wai ki ɓare baki kina masifa da zagi ba, hakan ba zai haifar da ɗan mai Ido ba gaskiya, sai dai ma maimakon ya gyara shima zagin nan da kikaye haddace su zai yi kuma ya fara kwatantawa, kinga kuwa a garin Neman Ido in ji hausawa, wai an rasa gira ko? Yaya ta, ki ja su a jiki, ki nuna musu ainihin rashin kyan abun da suka aikata tare da sanar da su uƙubobin da Allah ya tanadar ma mai yin irin hakan, hakan zai sa tun suna yara su tashi da tsoron Allah da kuma azabobin shi. Sannan a matsayin ki na uwa ya kamata ki kikaye yin duk wani Abu da yaro bai kamata ya gani ko yaji ba, don kuwa su yara ƙwaƙwalwar su na da son gwada duk wani Abu da suka gani, so don Allah mu kikaye. Ubangiji ya kula mana da tarbiyyar yaran mu su tashi su zama ababen alfahari garemu. Kan lallausan carpet ɗin da ke shimfiɗe a parlorn muka baje kamar wasu kaya. Murya ƙasa ƙasa muke maganar sabodsy in case kafa mu je BB ya shigo ba mu sani ba, mun san halinsa tsaf zai saka mu gaba da punishment don kawai muna magana, shi fa duk yadda mutum ya kai ga kiyaye tone ɗin Muryarshi sai ya ce an dame shi. “wallahi Jannat ɗazun nan hanjin cikina babu wanda bai gaisa da ɗan uwan shi ba” dariya na yi sannan nace “ke nifa cikina har ya ɓaci wallahi, BB ba ƙaramin dodo bane wallahi” “matar shi ta shiga uku, don ni har tausayawa mata nake yi” “ammah a haka fa duk an fi son shi, ko Dada da take takwarata ba ta ƙaunata kamar wannan jikan nata” “haka Ummi ma duk tafi son shi wallahi” “toh ya zamu yi duk yayi mana babakere” na faɗa ina wani kanne idanuwana, lokaci guda kuma na ware su a tsorace. Ƙamshin _imperio majeste_ da ya gauraye ɗakin har ya gurguntar da ƙamshin freshener ne ya dawo da mu cikin hankulanmu, babu shiri muka miƙe tsaye yayin da muka duƙar da kawunanmu ƙasa, ba mu yi yunƙurin ɗaga ido mu kalle shi ba saboda yadda muke tsakanin tsoronshi, Rafi'at kam jikinta har wani ɓari yake, Ni ma mai taurin zuciyar a dai lokacin kam na saddaƙar kashinmu ya bushe har ya hura wuta. A ɗan dake ya ƙara kallonmu yayin da ya maida hankalin shi kan phone din shi dake hannunshi yayin da mu kuma muka sandare wuri guda zukatanmu na luguden irin hukuncin da zai mana in dai har ta tabbata yaji hirarmu da kyau sai dai abun mamaki juyawa yayi ya wuce part Ummi. Wata iriyar ajiyar zuciya muka sauƙe muna ƙara gode ma Allah da ya tseratar da su daga wahalar BB. Sallar ishâ da aka fara kira muna muka gabatar daga nan muka dawo parlor muka kunna kallo, Bayan mun yi Dinner, ba tare da yin wata hira ba muka miƙe zuwa bedroom ɗinmu na part ɗin, brush muka yi sannan kowa ya nemi makwancin shi. ************** Can ɓangaren BB kuwa yana dawowa daga masjid can part din Ummi ya nufa, dama shi ɗan ɗakin ta ne ai, don kuwa hardly ka ga ya ci abinci gurin Mommy, Ummi kuwa bata gajiya haka take yi mishi girki duk da cewa akwai mai abinci sai dai shi da Abuya sun fi son cin girkin Ummin. Kasancewar Abuya ba ya gari sun je wani workshop so Ummi da kanta tayi serving BB sannan ita ma ta zuba nata, bayan sun kammala kuwa kowa part ɗin shi ya nufa, baby ayman kuwa tare da Ummi suka wuce abun su. BB na tashi bedroom din shi ya nufa kai tsaye, brush da wanka yayi sannan ya ɗauro alwala. Ɗaure da towel din shi white color ya fito yayin da yake fitar da ƙamshin daddaɗan shower gel din shi yana tsane jikin shi, gashin kanshi da ya jiƙe da ruwa sai ya ƙara wani kyau tambmkar wani baindiye, tsane gashin yayi sannan yayi drying nashi da hand dryer dake kan morror din, a nutse yake shafa creams din dake kan mirror din har ya kammala, sannan ya miƙe ya tunkari closet din shi, ƙamshi kuwa daga ciki baa magana, wasu milk colour pyjamas ya ɗauke yayi da ya sanya wando da rigan a nutse. Shi komai nashi daban ne fah! Yana kammalawa ya dauko turarurruka kusan kala biyar ya fesa yayin da jikin shi ke fitar da wani daddaɗan ƙamshi. Praying mat ya shimfiɗa ya gabatar da sallar shafa'i da witri sannan ya dan rera alƙur'an kafin ya nufi shimfiɗar shi ya kwanta addu'ah yayi sannan bacci ya ɗauke shi. Ƙarar da agogon bangon ɗakinsa ke yi yasa shi yin miƙa yana mai furta "La ilaha illallah Muhammadur Rasulullah...ah, alhamdulillahil Lazi ahyana ba'da ma amatana wa ilaihin Nushur!" A hankali ya fara buɗe idanuwansa tare da ƙara mayar da su, kusan mintuna huɗu da hakan ya tashi ya zauna sannan ya zuro ƙafafunsa ƙasa, toilet ya nufa can ya fito sanye da bathrobe da alamun ba iya alwala yayi ba har da wanka, bai wani ɓata lokaci ba ya goge sumarsa da ta ɗan jiƙe sannan ya sauya zuwa wata jallabiyar, a hankali ya fice zuwa Masallaci. Bayan idar da salla ma ya ɗan jima a Masallacin har gari ya soma haske kafin ya koma gida, Kai tsaye part ɗin Mommy ya nufa, Murda handle ɗin ƙofar bedroom ɗin mu ya yi a hankali, ganin hasken ɗakin a kashe ya tabbatar masa da zarginsa, numfashi ya sauƙe sannan ya mayar da ƙofar a hankali ya rufo, fridge ɗin da ke parlour ya buɗe ya Ciro ruwan jarka mai sanyi sosai sannan ya koma ya sake buɗe ɗakin, a tunaninsa zai tarar sun tashi saboda sautin buɗe ƙofar tasa (Mutumin da ba ya son hayaniya ta yaya zai yi making high pitched sound da zai tayar da wasu?. Switch ya shashima ya kunna haske, ga mamakinsa har lokacin baccinmu muke hankali kwance, mun wani bararraje, ƙafafuna kusa gaba ɗaya suna kan Rafi'at, Siririn tsaki ya ja sannan ya buɗe bottle ɗin tare da nufar gadon namu kai tsaye, shaaaaaa babu ko tausayawa ya sheƙa mana ruwa mai ɗan karen sanyin. Babu shiri Rafi'at da ba ta gigin bacci ta miƙe zaune tana murza ido, Ni kam juyi na yi ina faɗin "Rafi'at sai na faɗa ki da Mommy, Allah ya isa na" Jin abun da na faɗa ne yasa Rafi'at da ta gama tantance waye gabanta ta sulale ta nufi bayi yayin da na ci gaba da baccina hankali kwance. Ruwan ya ƙarasa sheƙa min, jin Rafi'at ta ci gaba da watsa min ruwa ya sa na miƙe zauna a firgice ina tura baki. Cikin takaicin katse min bacci da ta yi ya sa ma ce "Wallahi yau mai raba Ni da ke Rafi'at sai Al...." Hannuna na yi saurin ɗaurawa kan bakina ganin BB gabana a madadin Rafi'at , Wani irin tsalle da ban san na iya ba na yi ba dire da gudu na nufi bayi ba tare da tunanin ko Rafi'at na ciki ba na kai hannu zan murɗa handle ɗin. "Ke! Where the hell are you going e?" Ya dakatar da n a tsawace, diri-diri nayi ina zare idanuwana, kasa magana na yi saboda tsoratar da na yi yayin da Rafi'at ta fito da sauri ta shimfiɗa Sallaya. "Make sure You people pray, and then" Ya numfasa "After that! Ku tabbatar kun yi muraja'a zuwa seven, daga nan ku wuce kitchen ku taya su aiki, if not!" Ya jinjina kansa alamun warning tare da ficewa cikin takunsa mai cike da ƙasaita. Wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya Rafi'at ta saki tare da yin kabbara, Ni kuma da ƙyar na haɗiye yawun da ya maƙale min a maƙoshina sannan na nufi bayi cikin raima ina da na sanin zuwanmu hutu lokacin da BB ke gida. Bayan na yi alwala salla nayi, lokacin Rafi'at kuma na karanta Alqur'ani, cikin murya ƙasa-ƙasa na dubi Rafi'at sannan na ce "Ke nifa baccin bai ishe Ni ba." "Me kike nufi?" Itama ta ba Ni amsa cikin raɗa. "Tun da ya tafi kawai mu samu wuri mu kwanta abunmu, ki saka mana alarm battery a wall clock, da zarar seven ta yi sai mu fice, ya kika gani?" Rafi'at da itama baccin bai wani ishe ta ba kawai tace "E kuwa" ba tare da wani tunani ba. Rufe Alqur'aninta tayi sannan muka naɗe jiƙaƙƙen bedsheet tare da shimfiɗa sabo wanda ko toking nasa ba su yi ba suka lulluɓu da duvet, take wani daddaɗan bacci ya kwashe mu. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 4: A can ɓangaren BB kuwa yana barin ɗakinmu part ɗin Ummi ya nufa sannan ya nufi nashi bedroom ɗin ya shimfiɗa Sallaya ya fara raira karatun Alqur'ani cikin muryarsa mai daɗin gaske da yake kwaikwayon irin ƙira'ar Sheikh Muhammad Ayyub (Rahimahullah), sai wuraren seven thirty ya rufe Alqur'anin tare da mayar da shi muhallinsa ya kuma naɗe praying mat ɗin, jallabiyar jiknsa ya cire ya sauya zuwa wasu kaya da alamun motsa jiki zai fita, bayan ya sauƙo ƙasa har ya nufi ƙofar fita ko me ya tuna sai ya nufi kitchen, to his suprise, yaran can ba sa nan, ko da ya tambayi Salaha wacce ke taya Ummin girki tace ba su shigo ba, sosai ransa ya ɓaci, cikin ransa kamar wadda ake hurawa wuta yace "Lallai yaran nan sun gama raina Ni, zan mugun saɓa musu kuwa." Kai tsaye part ɗin Mommy ya tafi, ɗakinmu ya nufa, ko da ya buɗe ƙofar sosai ransa ya ƙara ɓaci ganinmu sai sharar baccinmu muke a ƙudundune a cikin blanket, kansa ya jinjina sannan yayi maza ya fice ya ƙara ɗauko ruwa mai sanyi bottles biyu wannan karon, tun kafin ya shigo ya buɗe su, sai da ya daidaita kowaccenmu ya kifa su shaasss, a matuƙar firgice muka tashi zaune kowacce na ƙoƙarin yaye bargon ta nata ɓangaren. Bayan gwagwarmayar da muka sha daga ƙarshe muka cilla bargon gefe muna zazzare ido. Rafi'at ce ta samu ƙarfin guiwar faɗin "Wallahi BB Jannert ce..." Bai bari ta kai aya ba ya dakatar da ita da faɗin "I don't need any elaboration, kun raina Ni Ko?" Idan aka ce tashin hankali, to fa ba a sa masa date, Idona da na ji Rafi'at na shirin mayar da laifin kaina take ya yi zuru-zuru yayin da cikinna ke bayar da wani irin sauti. "Zan wuce gym, ku tabbatar yanzun nan kun wuce kitchen ku taya Salaha haɗa breakfast, after that." Ya dube mu fuskarsa haɗe ya ce "Ku tabbatar kunyi watering duka flowers ɗin gidan nan, today no breakfast for idle girls like you, ku kuma tabbatar kun same Ni a garden by nine, kada ku kuskura ku bari ba ku gama komai ba before nine, wallahi wannan karon ba zan muku da daɗi ba, silly girls!" Yana gama faɗar haka ya fice tare da banko mana ƙofa ya nufi gym room abunsa. Kallon kallo muka fara aikawa juna tsakanin Ni da Rafi'at yayin da kowacce ta kasa magana mun kuma kasa aiwatar da umarnin BB. Rafi'at da itama ke tsiryace tace "Wallahi Jannert duka laifinki ne, har na fara karatuna kika ce na ajiye mu kwanta, ga shi kin jaza mana bala'i wurin BB, mukan mun gama yawo yau" "Ke dallas ki bar mu da halin da muke ciki tunda dai nima ba ware Ni yayi ba, kuma da kike cewa Ni na jawo miki ai ban ce dole ki yi baccin ba, Ni dai fatana Allah sa kar ya ba mu wannan mugun punishment ɗin nasa da Gara duka akansa." Na faɗa ina ƙarasawa cikin wata irin murya mai cike da tsantsar tsoro. "Mu ci gaba da zama Jannert, in ya ƙara dawowa ya tarar da mu wallahi sai dai a a ƙara haifarmu in ana yi, Gara ma ki lallaɓa mu je mu yi abun da ya saka mu kafin lokaci ya cika." Ai kafin Rafi'at ta rufe baki na dire daga gadon ma nufi ƙofa, bayana Rafi'at ta bi. Kai tsaye kitchen ɗin muka nufa muka fara abun da ya kai mu, ita kam Salaha hakan sosai ya burge ta don kuwa ta san wannan aikin Big Brother ɗinmu ne, yana mugun burge ta kasancewarsa tsayayye akan yaran, tabbas samun tsayayyun yayye irinsa sai an tona, ga shi da dai a shekare ba wani girma gare shi ba, amma kuma hankalinsa, tunaninsa da kuma hangen nesa irin nasa ko a masu shekaru sai an tona. Da Ummie ta shigo kitchen ɗin sosai itama tayi mamakin ganinmu a kitchen ɗin ta kuma tabbatar da aikin waye, bayan mun gaishe ta tace "Yau kuma angels ku ne a kitchen?" Juna muka kalla ba tare da mun ce komai ba, Ummie tace "Daga dawowa ba za ku huta ba?" Nan ma shiru "To shi ke nan, ku koma ku kwanta kawai tun da baccin bai ishe ku ba" Ai a haɗe kamar karatu muka ce "Laa, Ummie za mu ƙarasa, ga shi saura ma kaɗan ko Mama Sala (Kamar yadda suke kiran Salaha). "Ƙwarai kuwa Hajiya, yanzu za a kammala ma." "Ma sha Allah" Ummie ta faɗa tana mai ficewa abun ta cikin ranta tana ƙara yi wa BB albarka don kuwa ta san ko da bayan ransu ne, zai kula sosai da tarbiyyar yaran. Bayan mun kammala haɗa breakfast mun jera kai tsaye muka fice daga sashen Ummi muka biya mu gaida Mommy wacce ta gama haɗa nata breakfast ɗin, sosai Mommy ta yi mamakin ganinmu sassafe haka, mutanen da ke tashi daga baccin safe ƙarfe sha biyu in ba tashinsu aka yi ba su ne a waje? Kasa shiru tayi sai da ta magantu "Yau ku ne da tashi da wuri Yarinyata?" Wani irin zare ido waje na yi kafin na ce "Yau so muke mu yi aiki Mommy, daga yau sai mu fara hutawa ko?" Ƴar dariya tayi irin ta manya kana tace "To ku zauna ku karya yanzu sai ku ƙarasa aikin." "Laaa, Mommy ai mun riga mun yi breakfast a part ɗin Ummie" na faɗa ina shafa cikina da ke neman ɗauki saboda yunwa. "To shi ke nan, a ɗau harama" ta ba mu amsa tana mai wucewa upstairs. Ni da yunwa ke shirin Kaini ƙasa ne na dubi Rafi'at nace "Me yasa rai Allah ya dawo da BB gidan nan lokacin hutunmu, nikam na ƙosa a fara registration mu samu mu koma." "Kin ga tafiyata Jannert, ba za ki jaza min wani laifin ba, ki zauna kina surutu bayan kin san lokaci ya ba mu ga kuma tulin flowers ɗin da za mu ba wa ruwa." Rafi'at ta faɗa tana ficewa abunta, kallon agogon da ke bango nayi, takwas da mintuna, hakan yasa na bi bayan Rafi'at da gudu. Sosai muka sha wahala kafin mu gama watering flowers ɗin kasancewar yawan da suke da su don gaba ɗaya farfajiyar gidan flowers ne tun daga bakin gate, iya hanyar da aka bari ne ta wucewa da mota zuwa parking space, hatta canopy ɗin da baƙi ke zama ko su idan za su huta a kewaye yake da flowers ɗin, zuwa bayan gininnika, sai kuma babban garden ɗin gidan da shi ma yake cikin lissafin BB. Mun matuƙar ligirta kafin mu gama saboda rashin sabo da yunwa da muka yi, gara ma Rafi'at wasu lokutan akaina, ganin in muka ce za su wuce wurin BB za mu iya mutuwa don ba mu san kalar punishment ɗin da zai ba mu ba yau yasa muka yanke shawarar cin abinci, ko ma wani irin punishment ne, la'alla ma iya ɗauka idan tunbinmu ya ɗiba, yanke shawarar ci a part ɗin Ummie muka yi, fatansu ko da BB ya shigo ya ganmu In mun canki Sa'a ya haƙura idan Ummie ta musu magana. Da wannan shawarar muka ba wa cikinmu hakkinsa duk da cewa a ɗaɗare muke kada ya shigo ma ya tarar da mu. Lokacin da cikinmu ya ɗauka ne muka fice don zuwa karɓar sakamakonmu, garden muka nufa kai tsaye, tun daga nesa muka hango shi hakan ya sa zukatanmu fara luguden tsoro, kamar an jiƙa tsumma saboda yadda jikinmu yayi lirif, a haka muka nufi wurin da yake yana sipping hot tea ɗinsa hankali kwance yayin da mu kuma ya bar mu cikin tashin hankali. Sallama muka yi, ba tare da ya ɗago ba ya amsa mana sallamar yana ƙara sipping tea ɗin. "BB ga mu" Rafi'at ta faɗa tana wani irin lanƙwasa harshe tare da fatan ko zai tausaya mana. Tsawon wasu daƙiƙu ya share ba tare da ya ƙara duban yadda muke ba, in bacin amsa sallamarmu da yayi da sai mu ce bai ma san da zamanmu ba ne. Ganin yadda ya banzatar da wanzuwarmu ne yasa Ni tunanin ko dai ya manta da su ne? Hakan yasa na yanke shawarar yin Magana da fatan ko zai tuna da mu. Cikin murya mai ɗauke da tsoro nace "BB..." hannu ya ɗaga min, take ta gimtse bakina na kuma yi wa kalamaina sakatar fita. Don kansa ya gaji da shan ƙamshinsa can ya ajiye cup ɗin hannunsa a gefensa tare da dubanmu. Fuskarsa ya ɗaure kamar wani soja a filin daga kana yace "Wato ku kun raina Ni Ko?" Da sauri muka fara jijjiga kai a tare muka ce "Wallahi a'a BB" "Good" ya faɗa yana mai gyara zamansa "Na ma ce muku ku same Ni a nan by nine shi ne kuke so ku nuna min cewa wuyanku ya kai ko?" Kanmu muka fara girgizawa yayin da muka gama tsorata, tsoronmu ɗaya dai Allah yasa ba ƙara lokaci muka yi ba. "Da ku nake kuma wani jijjiga min kai, ba ku da baki ne?" Ya faɗa a ɗan tsawace "A..a...a BB, muna da shi" na faɗa, cikin raina ina da na sanin komawa baccin da muka yi. "Tun ba yau ba na ga yadda kanku yake rawa, musamman ke Rafi'at" ya faɗa yana nuna Rafi'at, Allah sarki, take hawaye suka fara zarya daga eyes ɗinta, ta san suna da rawar kai don ba iya BB ke faɗa ba amma dai duk rawar kanta ai ba ta kai Ni ba. Wani kallo ya aika mata take ta share hawayen da hannunta "Na duka ki ne kike min kuka?" Ta ba shi amsa da "A'a" "Then kar na ƙara ganin ko da drop ɗaya ne na hawayen, ok?" Kai tayi saurin gyaɗawa. Bai ƙara kallonmu ba ya janyo wayarsa da ke gefensa ya kunna tare da juyo mana da screen ɗin yana fuskantarmu "Ku duba what's the time and tell me yourselves " Ƙwalalo idanuwa muka yi ganin mun ƙara kusan 30minutes. Kasa samun mai magana a cikinmh aka yi, hakan kuma ba ƙaramin ƙara fusata shi yayi ba. "Are You people deaf?" Ya tambaya a fusace "N...no" "Duk cikin rainin ne ko?" "No?" Muka ba shi amsa da sauri a wannan karon "Shi ke nan, I'll make sure that you people get to know how to mind yourselves." "Don Allah BB ka yi haƙuri ba za mu ƙara ba" "Don Allah wallahi ba za mu ƙara ba" Kallonmu yayi yace "Ya isa! Kar ku sa min ciwon kai." Kamar haɗin baki dukkanmu muka ɗaura index finger ɗinmu kan lips. Gyaran murya yayi can yace "Anya ma kuna Salla a school ɗin?" Kallon kallo muka aikawa juna, Ni na yi saurin faɗin "Wallahi tun da muka dawo Mommy ta yi mana faɗa, kuma mun ɗauka asubar ce aka samu akasi." "You called it Akasi right?" Jikina ne ya fara karkarwa yayin da na fara juya abun da ta faɗa a ranina ina tunanin me ye ba daidai ba a ciki. "Shi ke nan, za mu zauna a nan ne da ku, in kun shirya yin bayani sai ku yi na ba ku punishment ɗinku." Kamar mu ɗaura hannu a ka mu zunduma ihu haka muka ji, tabbas mun san sun zo hutu tare da BB, ga shi tun ba a je ko ina ba ya sako su gaba, rama kam mun riga mun saddaƙar mun yi ta ma don in dai yana nan hatta magana a hankali muke yin ta, abu kaɗan sai yace laifi ne. Ni ce a wannan lokacin nace "Wallahi BB mun shirya, dama can a school ba ko yaushe muke sallar ba, muna yin azahar, magriba kullum sauran ne dai ba ma yi, wallahi jiya Mommy ta mana nasiha mai ratsa zuciya har mun sauya wallahi, asubar ma rashin sabo da tashinta ne amma mun maka alƙawarin za mu gyara don Allah ka mana haƙuri in ba mu gyara ba ka mana duk abun da kaga dama ko ba haka ba Rafi'at?" Da sauri Rafi'at ta fara gyaɗa kai tana faɗin "E wallahi BB, mun tuba mun bi Allah don Allah ka mana rai wallahi yanzu ma mun ji jiki." Murmushin gefen baki yayi kana yace "Ba dai ba ku saba da salla ba? Karatun Qur'ani fa, izunku nawa-nawa?" Idanuwa muka zaro a kunyace Rafi'at tace "Babu ƙarya wallahi BB iya wanda Ummie da Mommy ke mana ne muka yi, amma shi ma za mu koya?" Ya jinjina kai yace "Good! Ba za ku kuma komawa boarding ba, a nan gida za ku zauna, gobe goben nan ku shirya duk Islamiyya zan kai ku, wato ku ko damuwa ba kwa yi ko? Ba ku iya komai ba a addini, Allah ya sa sallar ma kun iya" "Wallahi mun iya!" Muka haɗa baki muka ba shi amsa da sauri. Jinjina kansa yayi yace "Sure?" Muka gyaɗa kai yace "Ok, yanzu kuzo ku yi a gabana, duk wani supplication da ake karantawa kuma ku yi a fili." "Innalillahi!" Abun da na iya furtawa ke nan a raina don har ga Allah ba komai na iya ba. Ganin babu wanda ya motsa cikinmu yasa ya haɗe fuska yace "I'm talking to human beings?" Kanmu muka gyaɗa tare da miƙewa jiki ba ƙwari muka fara kwatanta sallar munna fatan Allah yasa kar ya ce ba haka ba ne yayi mana asarar komawa Dolphin kamar yadda ya fara faɗa don ba ƙaramin buri muka ci ba. Kamar ba mu yake kallo ba saboda yadda ya lumshe ido amma a gaskiya mu ɗin yake kallo, ganin ya lumshe Idanuwansa yasa muka sauƙe ajiyar zuciya a tare, sai da ya bari muka gama tukunna ya dube su yace "Haka aka koya muku?" Raurau muka yi da idanu tare da kallon juna cikin ranmu muna masu saddaƙar da cewa shi ke nan. "Ku dawo ku zaun.." kafin ya kai aya mun zauna damas gabansa. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ _No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 5: "Ba abun da kuka yi sai shegiyar rawar kan tsiya, saboda haka, ku sa a ranku ma day school za a nema muku, za kuma kuna zuwa islamiyya don ba zai yiwu mu zauna gida da masu duhun kai ba, ɓata min lokaci kuma da kuka yi, za mu haɗu ne, for now, ku je ku yi breakfast ku yi wanka, sannan in kuka ga masu aiki sun shiga kitchen ku bi su ku taya su, idan kuka saɓa abun da na faɗa," sai kuma yayi shiru yana cije gefen lips dinsa alamun mun san sauran. Da sauri muka haɗa baki muna faɗin "Mun gode BB, Allah ya saka da Alkhairi." Daga haka kuma muka wuce sai sauri muke kada mu je mu ƙara yin wani laifin ya ƙirawo mu. Sai da yaga ficewarmu daga garden ɗin tukun ya miƙe ya nufi part ɗin Ummie, wanka ya samu yayi ya shirya cikin wasu ƙananan kaya da suka amshi jikinsa yayin da ya fito hannunsa riƙe da wayarsa sai zuba ƙamshi yake yi. Babu kowa a dining lokacin, hakan yasa ya zauna tare da ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya ya fara danna wayar tasa cike da isa da mulki, Mama Sala ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe da wani bowl, ganinsa yasa tayi saurin ƙarasowa tana faɗin "A'a, har ka fito ke nan." Fuskarsa ya ɗan saki don kuwa sosai yake mutunta Mama Sala, "Na fito Mama, yaran nan kuwa sun shigo kitchen ɗin nan?" "Ƙwarai ai tare muka haɗa karin kumallo da su, ga abun karyawarka." Ta idasa tana ajiye masa bowl ɗin da ke ɗauke da sliced fruits of different kind. "Na gode Mama" ya faɗa tare da kai hannunsa ya jawo bowl kamar wanda dama shi yake jira, Bismillah yayi ya fara sha a hankali har ya gama, bayan ya sanye yayi hamdala, mintuna biyu yayi zaune ya miƙe ya nufi bedroom ɗin Ummie don yana da tabbacin cewa tana ciki. Knocking ƙofar yayi kafin ya murɗa handle ɗin ƙofar, Da sallama a bakinsa ya shiga, jin babu response yasa ya tabbatar tana bayi, hakan yasa ya wuce part ɗin Ummi. A mutunce suka gaida da Ummi ta gabatar masa da fruits itama, babu yadda ya iya haka ya karɓa ya taɓa don ba zai iya ce mata a'a ba tun da can dama kullum in yana garin a nan ɗin yake sha. Kaɗan ya taɓa sannan yayi hamdala. Cike da kulawa Ummi ta dube shi tace "Khalil" Amsawa yayi da "Na'am Ummi" "Kun gaisa da Daddynku ne?" Ya jijjiga kai "Ok" kawai tace tayi shiru, dubanta yayi yace "Ummi nace wai yaran nan kuwa ba za su dawo day school ba?" An taɓo wa Ummie abun da ke mata ciwo hakan yasa tace "Ba dai su Jannat ba?" Ya gyaɗa mata kai "Wallahi Khalil Nima ba na son wannan boarding ɗin irin tasu, yara duk sun tashi sakaka, dama Daddy ne ya nace amma Abuya ma bai so, nima gaskiya ina ga yanzu kam ya kamata a sauya hanya." "Haka ne kam Ummi" ya faɗa yana gyara zama "Gaba ɗaya rawar kai ta musu yawa, common sallah ba iyawa suka yi ba bare kuma suke yi, Alqur'ani kuwa babu, zan yi magana da Daddy in na dawo, gobe zan kai su islamiyya, idan result nasu na Common entrance ɗin ya fito sai a nema musu wata school haka mai kyau." Murmusawa Ummi tayi tana ƙara yabawa BB, tunaninsa na manya ne, ra'ayoyi nasa da yawa sun zo daidai da nata shi yasa tun yana ƙarami ya fi zama da ita fiye da Mommynsa. "Ma sha Allah, Allah yayi albarka Khalil, ya ƙara girma" Da "Amin" ya amsa mata, nan suka taɓa ƴar hirarsu kafin yayi mata sallama. Addu'a ta masa sannan ya wuce, part ɗin Mommy ya wuce, lokacin kam tana bedroom ɗinta hannunta riƙe da wani littafin addini yayin da ta sanya farin glasses ɗinta wanda ke taimaka mata wurin gani. Gaisawa suka yi yake tambayarta yashe Daddy zai dawo, tace masa yau, daga nan sallama ya mata ya fice, bai bi ta kan driver ba ya wuce abunsa. A ɓangaren mu tun da muka samu muka bar garden muka saka a na kare sai part ɗin Mommy, ba mu tsaya ko ina na muka nufi ɗakinmu, muna shirin shigo muka jiyo Mommy na faɗin "lafiyar ku kuwa kuke wanann uban gudun??" Dif muka ci birki kamar abun hawan da aka tsayar, kamar munafukai muka juya muka tsaya gaban Momyn. Kallo Mai cike da tambayar da Mommy ke aika mana yasa Ni saurin faɗin "ga mu Mommy" "Lafiyarku kuwa?" Ta tambaya tana mai ƙara nazartarmu. Da sauri Rafi'at ta saita muryarta tace "Laa Mommy ƙalau muke fa, mun dai ɗana bayin flowers ne mun gaji, wanka muke son yi ba mu lura ma da ke ba ne ko Jannert?" Ƴar dariyarsu tayi irin ta manya kana tace "To, ku je ku yi wankan" sai da suka wuce ta jinjina kai kana ta ce "Lallai dodonsu ya dawo kam, dubi yadda suke rarraba ido. yanzu duk za su bi su rame, Gara ya gama hutunsa ya wuce, ko kuma su wuce wurin Dada in ya wuce sa dawo in ba haka ba sai ɗan buzunsu, su da rashin ji, shi kuma da tsaurin rai." Muna shiga ɗakinmu Rafi'at ta dube ni tace "Kai gaskiya yau da Sa'a muka tashi, ki ba BB bai haɗa mu da punishment ba, Allah mun gode maka" ta wani sauƙe ajiyar zuciya kamar wacce ta tsira daga hannun ƴan boko haram. "Ke?" Ni da na fi ta shan wahala nace "Ni zan ce miki mun taki Sa'a, yanzu dai mu samu mu gasa jikinmu don wallahi na gama yawo nikam, ko breakfast ba zan yi ba baccin wahala zan yi, ki tashe Ni don Allah idan Mama Sala ta fara aikin lunch." Da sauri Rafi'at tace "Kan bu! Idan kin isa na tsaya a nan, yadda kika gaji wallahi na fi ki, don haka ki tabbatar in kika kwanta Ni ba zan tashe ki ba, don wallahi barin ki zan yi in yazo ya ganki ke ɗaya ya ba ki kashi." Marairaice fuska na yi ina faɗin "Allah sarki, yanzu Rafi'at yaushe kika fara kware min baya? Don Allah ki taimaka min ki bar Ni na kwanta." "Can ta matse miki, kin ga shiga ta toilet" Rafi'at ta ba ta amsa tana mai shigewa bayi abunta. Bayan mun yi wanka dining muka nufa, Sauran abincin da ya rage muka ci, daga nan muka tafi part ɗin Ummi don yin abun da ya dace da mu a yanzu. Tare muka yi lunch aka jera a dining ba mu tsaya ci ba muka dawo part ɗin Mommy gaba ɗaya jikinmu a gajiye. Sallar azahar muka samu muka yi don har ga Allah nasihar da Mommy ta mana jiya ta ratsa mu, kai ko ba don wannan nasiha ba, abun ka da yara. Wallahi gani muke kamar BB na ganin mu. Whatever the case may be, da alamun sauyi dai ya fara samuwa a tattare da mu. Rafi'at na kalla bayan mun yi sallar azahar na ce "Allah sarki, mu kan mun gama yawo Rafi'at, yanzu haka za mu yi ta rayuwa har hutunmu ya ƙare?" Rafi'at ta dube Ni ta ce "To ya za mu yi? Allah na jarrabar kowa, mu tamu jadrabawar BB ne wallahi" Na marairaice fuska kamar zan yi kuka na ce "Hmm, Ni kaɗai na san me nake ji a tattare da shi, Rafi'at Wani lokacin ko sunanshi aka faɗa wollah ina firgita sosai, Allah dai ya sanyaya ran BB ya yi rayuwa irin ta mutane" "Amin fa." Rafi'at ta faɗa tana sanya idanuwanta cikin nawa "Wai kin ji islamiyya zai kai mu, kuma za a cire mu a Dolphin a mayar da mu wata daya school haka" Kamar na cilla ihu haka na ji, mun saka rai sosai kan in min shiga secondary mu ma za mu yi enjoying kamar yadda muka ga ƴan secondary ke yi, mun tsara abubuwa mabanbanta da rayuwarmu za ta tafi kai. Kwanciya muka samu muka yi. Take wani wahalallen bacci yayi abin gaba da mu, Rafi'at ce ta fara farkawa jin ana kiran sallar la'asar, tashi na ta yi, muka yi salla, daga nan muka nufi part ɗin Ummi. Sallar magrib da iska ranar suka min yi muna yin dinner kuwa da wuri wuri muka kwanta don har lokacin jikinmu tambayarmu yake kasancewar aikin da muka yi ya girmi shekarunmu ga kuma rashin sabo a ciki. Washe gari ma BB ne ya tayar da mu daga Bacci sannan ya wuce masallaci, da ya dawo ya tarar mun koma ya ƙara tayar da mu daga Baccin ya ce Mu yi karatu zuwa wayewar gari sai mu je kitchen mu ga yadda su Mama sala ke girki, mu tabbatar mun taimaka musu da abubuwan da za mu iya. Hakan ce kuwa ta kasance, bayan mun kammala muka koma part ɗin Mommy. Kamar yadda na faɗa muku dama, Mommy mace ce mai sanyin hali, ai bayan mun je haka ta tsare mu ta ce Lallai sai mun faɗa mata dalilin da ya sa muke shigewa ɗaki ba kuma ma walwala, da ta matsa akan sai ta sani ne nan muka faɗa mata komai, kai kawai ta jinjina tace zai shigo ya same ta. A ranar da Azahar BB ya kwashe mu ya nufi da mu wata makaranta Bilal academy, da take lokacin makarantar iya yadda ake yi, sai da ya gama mana cuku-cukun komai kafin ya koma, da yamma kuma bayan an tashi ya zo ya ɗauke mu. Duk wannan abu da ya faru cikin Ummi da Mommy babu wanda ya san da aukuwarsa, sai da muka koma ne muka shiga part ɗin Ummi take tambayarmu "ina kuka ɓuya? Ko dai kuna can muna baccin asarar ne?" Ni da abun ya ci damuna na ce "Ummi BB ne ya kai mu islamiyya wai ba mu iya komai da ya danganci Musulunci ba, yanzu Ummi mu da muka zo hutu muke shirin komawa me ya sa za a kai mu islamiyya don Allah?" Bakina Ummu ta buge tana bi na da kallon takaici "Ba za ki taɓa yin hankali ba Jannat! Don ubanki idan ya shigo ko tare shi ki faɗa masa abin da kika faɗa min kin ji?" Tana gama faɗin haka ta ƙara kawo min duka tana faɗin "Na rasa yaushe za ki yi hankali Jannat, ke shi ke nan sai dai ki yi rayuwa sakaka haka kike so? To bari ki ji, ungulu ma da ta rasa mafaɗi kashi take ci. Haka kika ga ƴar'uwarki tana yi? Ina ce dai duka tare aka saka ki a islamiyyar? Kin ji ita tana ƙofafi ne?" Bakina na turo gaba, ba tare da na aune ba na ji sauƙar hannun Ummi akai ta buge min shi. Kukan shagwaɓa na saka ina damfe, yadda na ga ya yunƙuro za ta cafko Ni ya sa na ruga a guje sai part din Mommy. Bayan tafiya ta Ummi ta dubi Rafi'at sannan ta ja ta jikinta ta ce "Rafi'at kina yi wa wannan ƴar'uwar taki nasiha, na ras game ko iskokai ne da ita ko me? Islamiyyar da Khalil kuma ya kai ku an jima in ya dawo da ke da Jannat ku ne ku masa godiya, ƙaunarku ce ta sa ya muku hakan, duk wanda ya ke nuna maka hanya yake faɗa maka gaskiya ko da yaushe son ka yake da rahama, wanda ba ya son ka kuwa ko zargin Allah za ka yi ba zai ce maka uffan ba, zai zuba maka ido ne ka yi abun da ka ga dama." "Kina faɗa mata gaskiya kin ji Rafi'atu?" Rafi'at ta gyaɗa kai sannan ya ce "Na ji Ummi" Ummi ta dube ta ta ce "na san hankalinki ya yi tun ta ai tun da ta tafi, je abun ki, ki tabbatar kun ke kun masa godiya kin ji?" "E" Rafi'at ta ba ta amsa tana bin bayana. A part ɗin Mommy muka haɗu, Mommy ta dubi Rafi'at da ta shigo ta ce "Yanzu Jannat ke faɗa min wai Khalil ya kai ku islamiyya ko?" Rafi'at ta gyaɗa kai tana faɗin "e Mommy" "Shi ne ku kuma kuka wuce kuka tafi ba ku faɗa min ba" "Mommy dai kin san halin BB ba ya son a ɓata masa lokaci, yanzu kam ai ga shi mun faɗa miki " Mommy ta ce "To ai ban yi tunanin yau zai kai ku ba ma, Allah dai ya saka masa da alkhairi" Ni dai "Amin" kawai na ce cikin raina kuwa baƙin ciki nake da yadda kowa bai ganin laifin BB, Mommyn ma da nake tunanin za ta yi magana akan saka mu islamiyyar da ya yi jin ta masa albarka ya sa na yi saurin miƙewa zan tafi ɗakinmu. Muryarta ne ta doki kunnena ya sa na tsaya "E Jannat, ku je kam ku ce masa kun gode, don ba ƙaramin jahadi ya yi ba" Ba tare da na juyo ba na ce "To Mommy" daga nan na wuce ɗaƙinmu zuciyata na tuƙuƙin dalilin da ya sa aka fi son sa a kanmu da kuma dalilin da ya sa komai ya yi ake ganin daidai ne. Zuciyata nake ji wani iri, haka kawai nake jin kamar ba na ƙaunar BB, ta iya yiyuwa yarinta ne take ɗawainiya da Ni, amma a babin gaskiya na san da gaske nake har cikin raina ina ƙinsa. Washe gari su Abuya suka dawo daga tafiyarsu, shi ya gama nashi workshop ɗin, daga shi har Daddy Babu wanda bai mana tsaraba ba, mun ji daɗin hakan ƙwarai da gaske. Dawowarmu daga islamiyya Daddy ya mana kyakkyawan albishir na zuwan Dada ta yi kwana biyu a gidanmu. Murna sosai nake saboda ko ba komai zan yi rashin ji na son raina ba tare da Dadan ta bari wani mahaluki ya taɓa Ni ba kasancewar ni ɗin takwararta ne. Murnata gaba ɗaya ciki ta koma lokacin da na tuna BB na nan, duk zai kwashe ƴar kulawar da zan samu daga wurin Dadan. Da daddare muna part ɗin Mommy bayan an yi Dinner Daddy ya kawo zancen islamiyyar da BB ya saka mu. Nan ya ja hankulanmu akan mu nutsu mu koyi abin da aka mana, ya faɗa mana cewa Alqur'ani na da falala sosai, har ya faɗa mana irin falala da darajar da mahaddaci sa ke da shi a wurin Allah a duniya da kuma ranar gobe ƙiyama, wannan bayani na Daddy shi ne ya sa na ɗan ji sanyi kaɗan a cikin zuciyata ina addu'ar Allah ya sa dai nima na shiga sahun mahaddatan, kuna mamakin dabi'u na ko? To babin gaskiya abun da ya sa nake wasu abubuwan Ni kaina na san rashin zama kusa da iyayenmu ne, tabbas da a gabansu muke karatu na tabbata za mu kasance nagartattu kamar dai yadda suke. Bayan an gama cin abinci ne Daddy ya dube mu ya ce "Ibrahim ya ce Ku shirya da wuri gobe, akwai inda za mu je?" "BB Kuma?" Na furta ina zaro idanuwana waje. Daddy ya tabbatar min da shi ɗin dai. Nan dai na tafi ɗaki raina wani iri, daga nan Bacci ma ya kwashe Ni ba tare da na San yaushe Rafi'at ta dawo ba. ********** Kamar yadda BB ya Fara sabar mana da tashin asuba, yau ma kafin ya wuce masallaci sai da ya biyo last ɗin Mommy ya tayar da mu, bayan ya dawo ma ya biyo ya duba mu, gaishe shi muka yi ya amsa, ganin Alqur'ani a hannayenmu muna karatu ya sa shi ficewa ya koma part ɗin Ummi. Sanin cewa ya ce Mu shirya ya sa muka shirya da wuri, kasancewar muna tsoron yin laifi a wurinshi. Ko giftawarsa ba mu gani ba sai wuraren tara na safe, kamar ko yaushe sassanyan ƙarmshin sa ne ya ankarar da mu da shigowarsa parlourn, gaishe shi muka yi a ladabce, da "Lafiya" kawai ya amsa daga nan ya wuce bedroom ɗin Mommy, lokacin da ya fito mun riga mun fice muna tsaye jikin motar da zai fita da ita, ko da ya ƙaraso shigewa ciki ya yi ba tare da ya ce mana komai ba, dama ba mu yi expecting hakan daga gare shi ba. Sai da muka yi sallama tukun muka shiga, abun mamaki ya amsa sallamar, Ni ce a front seat sai kuma Rafi'at a back seat. Mun share kusan mintuna biyar cikin motar bai tayar da ita ba bai kuma yi mana magana ba, wannan ɗabi'ar tasa na daga cikin abun da ke ƙara ba Ni mamaki akan shi, mutum ba zai iya buɗe baki ya yi magana ba sai ka ce Ubangiji ya haramta masa? Ganin dai ba mu fahimci komai ba shi ma ya gaji da tsayuwa ya sa ya ja siririn tsaki Sannan ya ce "Gidan uban wa za ku je da mayafi?" Ai kafin ya rufe bakinsa ma mun fara kiciniyar buɗe mota mu fita, sai da muka sanyo hijabi tukun ya ja motar. Ban taɓa jin takaicin BB ba irin na ranar ba domin wata makaranta ya kai mu wai Ummul Qura science academy, makarantar Boko ne da islamiyya a haɗe, in aka tafi tun safe sai ƙarfe biyar ake dawowa. Haka ya baro mu a can, wuraren sha biyu Driver ya kawo mana abincin rana, ƙarfe biyar ɗin daidai BB ya zo ya ɗauke mu ya mayar da mu. Kwana uku ya jera yana jigilar kai mu da ɗauko mu yayin da Driver ya ɗauki ragamar bayan tafiyar BB wurin Dada, kwana biyu ya yi a can ya dawo, daga nan ya wuce abun gabaɗaya, kar ku so ku ji irin farin cikin da na tsinci kaina da tafiyarsa, na so yin gardamar ƙin zuwa makarantar da ya saka mu amma gargaɗin da ya mana kafin ya tafi shi ya hana Ni. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ _No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 6: Kwanci tashi, in ji bahaushe wai asarar mai rai, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ba mu samu halartar graduation party ɗinmu na Dolphin ba, wanda hakan ya sa na ji ba daɗi sosai, a ɓangarenmu da Ibada sai dai mu ce Alhamdulillah don yanzu kusan babu sallar da ba ma yi, asuba da kanmu muke tashi, idan mun idar sai mu tisa haddarmu ta Makaranta, gari na wayewa muke shirya wa saboda gudun makara, don in mutum ya makarar ba ƙaramin bugu yake kwasa ba daga perfects ga kuma shara da za a ba shi ya yi, musamman ma mu da muke juniors, tun da BB kuma ya koma Cairo Bai ƙara zuwa gida ba. Alhamdulillah, cikin iko da sahalewar Ubangiji muka kammala aji ɗaya na secondary, tarin nasarori kan mun fara artabu da su a rayuwarmu don wani lokacin har tunani nake dama muma muna da Sa'a a rayuwa haka ne? Lallai a yanzu muna enjoying karatunmu a sabuwar makarantar da yanzu muka saba da ita, Rafi'at ce ta karɓi kyautar ta ɗaya Ni kuma ta biyu a wannan shekara ga kuma best subjects gifts da muka kakkarɓa, hakan ya sa ahalinmu yin farin ciki sosai, shi kam Abuya ƙarin farin cikinsa bai wuce nasarar da muka samu a fannin addini ba, mun kammala littattafai da dama, fagen hadda kuwa ma sha Allah, don makarantarmu ba baya ba a wannan babin ma, ga shi mun tashi da tagomashin haddar hizifi biyar masu kyau da ingattaciyar hadda. A haka muka shiga aji biyu, uku har muka yi jssce, izunmu talatin talatin lokacin. Muna aji ɗaya na Babbar sakandare ne girma ya fara riskar mu, cikin ƙanƙanin lokaci muka yi wani irin girma na ban mamaki musamman Ni, domin in ka gan mu za kayi tunanin mun kai shekaru sha bakwai bakwai a duniya while bamu wuce sha huɗu huɗu ba. A lokacin ne kuma girma ya riske mu, kasancewar dama tuntuni muna da ilimin akan al'amarin ya sa komai ya tafi yadda ya kamata sai ƴan shawarwarin da Mommy ta ƙara mana da su. Rayuwar duniyar ke nan, a yanzu haka ajinmu uku na babbar sakandare, gaba ɗaya mun sauya kamar ba mu ba, mun samu damar haddace Alqur'ani mai girma, a yanzu haka muna gab da fara jarrabawoyin fita, don mun riga mun yi registration na jamb, waec da kuma neco though a ra'ayin Abuya da Ummu kawai da zarar mun kammala secondary kawai mu yi aure ne don ya lura Ni ina da rawar kai. A tsukin wannan lokacin ne Daddy ya saya mana wayoyin hannu Ni da Rafi'at, wannan ne ya fara buɗe min damar fara yin soyayya a rayuwata, to a yanzu dai soyayya nake fafa, duk wanda ya ce yana so na amsawa nake mu yi soyayyar mu tun da ina da waya, ita dai Rafi'at babu ruwanta da wannan dabi'a hasali ma dai Banda Ya Sadiq Babu wanda take kulawa, wasu lokutan nima takan yi min nasiha kan na daina biyewa samari sai na ce mata ta rabu da Ni, Murmushi kawai take in na faɗa mata haka ta ce "Allah ya shirya mana ke Jannat, tashen balagar tsuntsaye ke ɗawainiya da ke" Nima dariyar nake yi kawai daga nan sai mu bar zancen, duk da yadda nake kule-kulen mazan nan ko kaɗan ba na wasa da karatu na, a haka muka fara rubuta jamb ɗinmu, bayan sakamako ya fito na ci maki 134, Rafi'at Kuma maki 230, dama can Ni medicine and surgery na cika, ita kuma law, wannan sakamako shi ne ya rage min karsashina har ma Fara tunanin gyara ɗabi'ar da na lulluɓawa ruhina ita. Ɓangaren su Abuya babu wanda ya ce min komai da sakamakon jamb ɗina, wannan dalilin ya sa na fuskanci cewa zuru suka yi min, daga nan kuwa na ajiye samari a gefe na dawo kan hanya yadda ya kamata. Yau ta kama Litinin, tun dama tashi daga Bacci nake ji na wani irin, bugun zuciyata ya hauhawa haka nan fitar numfashi da shaƙarsa, shima da sauri yake fita, na tabbata da zan je na gwada daga bugun zuciyar zuwa numfashi na yanzu sun sauƙa a layin daidai, addu'o'i na ci gaba da yi cikin raina ina roƙon Ubangiji da ya kawo min komai da sauƙi yayin da na yi sukuku kamar ba Ni ba, tun Rafi'at na tambayata ina share ta har ta gaji ta yi fushi tare da zuba min idanuwa. Har dare haka nake ji na wata irin kamar an sauya Ni, ina yin sallar isha' ban tsaya cin abinci ba na wuce ɗaki na kwanta, a maimakon Bacci ya ɗauke Ni sai tunani ya yi wa zuciyata ƙawanya, tsaki na ja tare da ƙara tuƙuiƙuye kaina cikin bargo ina fatan baccin ya ɗauke Ni. Rafi'at ce ta shigo ɗakin, kallon mamaki ta bi Ni da shi kafin ta wuce toilet, ko da ta fito ba ta kula Ni ba, itama sai ta samu wuri ta kwanta, duk yadda aka yi haushina take ji ba kaɗan ba, ban ba ta haƙuri ba ita ma ba ta kuma tambayata me ke damuna ba, har wuraren goma idona biyu Ni da na shigo tun ƙarfe takwas da niyyar Bacci. Rafi'at kam tuni ta fara barcinta har da minshari, ajiyar zuciya na sauƙe tare da niyyar sauƙowa na yi alwala na yi salla, vibrating ɗin da wayata ke yi ya sa na sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya Tare Da miƙa hannuna na ɗaga pillow na ɗauko wayar ina mamakin mai kira na a irin wannan lokaci. Baƙuwar lamba na gani, har na ji kamar kada na ɗaga sai kuma na duba farkon numbern, a maimakon na ga irin lambobinmu na gida Nigeria sai naga akasin haka, tdantsar mamaki ne ya bayyana akan fuskata, har wayar ta katse ban samu damar ɗagawa ba, saurin shiga Google na yi don duba wace ƙasa ne ke da county code mai +1... Ban kai ga searching ba kiran ya sake shigowa a karo na biyu, ba tare da wani tunani Ba kawai na yi picking tare da karawa a kunnena ina faɗin "Hello" Shiru ba a amsa ba, na ƙara faɗin "Hello" still ba a amsa ba, jinjina kaina na yi kafin na ce "Wai waye ne? Idan mutum ya san ba magana zai yi ba dalla can meye na kiran, aikin banza kawai" na ja tsaki na kashe kiran ina jin takaici sosai cikin raina. Washegari ma da daddare an ƙara kirana da wannan numbern jiyan, ko da na ɗaga ba a yi magana ba, hakan ya matuƙar tunzura ni na balbale mai kiran da masifa duk da cewa ba Ni da tabbacin yana jin Yaren nawa duba da cewa mamallakin numbern mazauni ko kuma ɗan ƙasar Canada ne. Haka kawai na kasa yin Bacci daren ranar ina tunanin waye wannan yake kirana? Na farko dai danginmu ba wani yawa ne da su ba, hasali ma daga Kaka sai Mommyn Misau da Mommyn Jama'are, to bayan su da iyalansu ba mu da wasu dangi na kusa haka, ƴaƴansu suma gaba ɗaya suna cikin ƙasar, babu wanda ya ƙeta hazo, to waye wannan ya samu number ta har yake kirana after all numbern ma sabuwa ce?" Kamar wata mahaukaciya haka na sauƙo daga kan gado ina kewaya ɗakin, gaba ɗaya na kasa gano wannan mai kiran nawa, tsaki na ja a bayyane sannan na ce "To miye abun ɗaga hankalin bayan nan san wane ne ba? Ya kamata na manta da ko ma waye ne na maida hankali na ga abubuwan da ke gabana" Ina faɗin haka na gyara zaman hular da ke kaina na koma na kwanta. Zaune nake a garden Ina shan iska yayin da na langwaɓar da kaina jikin kujerar da nake zaune, Shekaru shida ke nan cikakku yau da tafiyar BB, tun da ya tafi ban ƙara tunawa da shi ba sai yanzu da na ga date a jikin wayata, tsaki na ja kafin na ce "Mugu mai baƙar zuciya, Allah ya sa kar ya ƙara dawowa" na faɗa cike da tsantsar kiyayyarsa da nake ɗorawa kaina nake kuma ƙoƙarin ganin jikina da ruhina sun aminta da hakan. "Ko ya yake rai?" Na tambayi kaina yayin da nake yamutsa fuskata, tun da ya tafi ba mu ƙara magana da shi ba, ba kuma mu jin ana zancensa ban da sau ɗaya da Kaka ta zo mana hutu, ita dai kam tana yawan yin zancensa wani lokacin har na ji kamar na kai mata duka saboda takaici. Duk yadda na yi na yage tunanin BB da yake shirin maƙalewa zuciyata, kamar mai taɓin hankali haka ma wani kwaɓe fuska tare da miƙewa tsaye, screen ɗin wayata na zubawa ido kafin na tunkari hanyar fita, karo muka ci da Rafi'at. Kallo Mai cike da tarin tambayoyi ta jefa min Ni kuma na kawar da kaina gefe da niyyar in raɓa gefenta na fita kafin ta fahimci wani abun. "Meye hakan kike yi Jannat?" Rafi'at ta faɗa yayin da ta riƙo hannuna tana ƙoƙarin ganin idanuwanmu sun haɗu "Sai wani avoiding ɗina kike? What's wrong with you um?" Ajiyar zuciya na sauƙe kafin na ce "kin ga Rafi'at, sake Ni na fita, babu abun da yake damu na, kawai dai yawan magana ne ba na so a halin yanzu." Ina rufe baki Rafi'at ta ce "Ƙarya kike Jannat! Akwai abun da yake damunki mana, kar fa ki raina min hankali" ta faɗa tana tsare Ni da ido Janye hannuna na yi na wuce ina faɗin "Sai kuma ki yi ai, Ku bar mutum in Yana cikin yanayin nan don Allah, haba mana" da ido Jannat ta bi Ni har na shige, ta sauƙe ajiyar zuciya ta biyo bayana. A parlour na tarar da Mommy, kallo ɗaya ta min itama ta fahimci cewa ba daidai nake ba, ba ta iya ɓoyewa ba ta ce "Zo nan Jannat" na amsa da "To" Sannan na ƙarasa na zauna kusa da ita. "Ba ki da lafiya ne?" "Lafiyarta ƙalau Mommy Amma dai wani abun na damunta" faɗin Rafi'at wacce ta shigo yanzu, harara na Banka mata kafin na ce "To uwar kanzagi, nima ai ban ce ba Ni da lafiya ba, Mommy" na mayar da kallo na gare ta "Lafiyata ƙalau, kawai yawan magana ne ba na so yanzu" Mommy ta ɗan murmusa sannan ta ce "Iyeeeee?" Murmushin nima na yi ina faɗin "Allah Mommy, yanzu ba na son yawan magana ko kaɗan ita kuma Rafi'at yanzu kamar wata aku haka take, ta dinga damuna ke nan" Mommy ta ce "Haka abun yake? To ke Rafi'at kin ji me ɗiyata ta ce, in kin san na za ki iya kiyaye abun da ba ta so na salin alin ki bar part din nan" Hararata Rafi'at ta yi tana faɗin "bari na haɗa kayana na koma part ɗin Ummi, idan kin koma daidai na dawo" "Ki fi ruwa gudu" na faɗa ina juya idanuwana. Da daddare yau ma an kira Ni da wannan numbern ta ƙasar Canada amma dai yau Ban ɗaga kiran ba, ko da aka kira a karo na biyu ma ban ɗauka ba, sai ma kashe wayar tawa gaba ɗaya da na yi na ajiye a ƙasan pillow na kwanta. Sati guda ke nan ana damu na da kira da wannan numbern, abun takaici yanzu da safe na sai an kira Ni, ga shi kuma ba a magana in na yi picking, wannan dalilin ya sa nake ta tunanin blocking number sai dai da na shiga kan numbern sai wani abu ya shiga kaina na manta abun da zan yi. Tsakanin Ya Sadiq da Rafi'at soyayya ce ta ƙullu, shima yanzu yana ajinsa na ƙarshe a matakin karatun jami'a, yanzu haka yana Gamawa zai fara housemanship ɗinsa, daga nan kuma zai zama cikakken likita, sai kuma ya yi residency na shekaru bakwai don zama consultant. Tun ranar da Ya Sadiq ya furtawa Rafi'at kalmar soyayya ta sanar da Ni, sosai Na ji daɗi ko ba komai ɗan gida ne, kuma ina da tabbacin zai riƙe min ƴae uwata amana, ba wai don ya kasance jinina ba kawai, sai don sanin kyawawan halaye da Dabi'un da yake da su, uwa uba sanyin hali da tausayi ba kamar BB ba. "Ko ina yake rai?" Na furta a bayyane ina riƙe haɓata Fuskata na yamutsa na ce "Matarsa ta shiga uku, Allah ma dai ya sa ya samu wacce za ta so shi" "Kamar ya samu in Sha Allah" Faɗin Rafi'at wacce shigowata yanzu ta zauna gefe na, idanuwana na zaro cike da mamakin yadda maganar ta fito fili. Dafa Ni Rafi'at ta yi kafin ta ce "Wani ya sani ma ko ke ce matar tasa?" Da wani irin ƙarfi na runkuɗa ta gefe har sai da ta kusa faɗuwa, dariya ta saka tana sanya idanuwanta cikin nawa ta ce "Irin wannan hasala haka miss Jannat? Don kin auri BB ɗin wani abu ne?" "Tuf" na yi kamar mai zubar da miyau kafin na fara yamutsa fuska "Allah ya sauwaƙe min wannan wahala Jannat, to wahala mana zan ce don wallahi duk wacce ta aure shi wahala ta kwasa" Bugu Rafi'at ta kai min sannan ta ce "lallai ba ki da mutunci Jannat, to meye aibun Yayan namu?" Caraf na ce "Aibubbuka dai Rafi'at, ke ce kawai ba kya gani saboda ɗan uwanki ne" Ta ce "Gaskiya dai ba lallai na ga aibunsa ba Ni kam, kema kuma bai kamata ki gani ba, BB mutum ne mai kyan dabi'u ke kan ki kin sani" Nace "tab, kyan fuska dai in kin ce yana da zan yadda, don na tabbata matar da za ta aure shi ma Kyan fuskar ta gani" "Ashe dai???" Na ce "Ko ma meye, Ni dai ki daina min fatan auren BB, hasali ma ba ya da siffofin irin mijin da nake so, All I need is a caring husband ba wai irin BB mai cunkusasshiyar zuciya wanda na tabbata ita kanta zuciyar tashi yana takura mata" Dim, na ji dundu a bayana, a hasale na ce "Wallahi ba ki isa ba Rafi'at, don na faɗi gaskiya sai ki wani sa Ni gaba da duka, wa ma ya san yanzu ya BB ya koma, yana da ƙarancin shekaru ma yake mugunta bare kuma girma ya kama shi?" Rafi'at ta kwashe da dariya tana faɗin "Ɗazu Na ji Ummi na waya da shi, kamar wai zai dawo wata mai kamawa" Wata irin zabura na yi na miƙe tsaye tare da zurawa Rafi'at da ta yi magana zararrun idanuwana. Cikin yanayi mai kama da rashin hankali na ce "What? BB ɗin ne zai dawo?" Rafi'at ta jinjina min kai. Kamar wata zararriya na ce "Shi ke nan mun shiga uku kuma, don Allah ki roƙa mana Ummi ta roƙe shi ya zauna a can mu mun yafe musu shi wallahi" "Wasa ma kike yarinyar nan" "Wallahi mun yafe musu shi, da dai ya zo ya sauƙe muguntar shi ta shekarun nan masu yawa, ga shi yanzu soja ne ma ba wai ɗan ƙwallo ba, mun shiga uku Rafi'at" na ƙarashe a ɗan kiɗime don iyakar gaskiya wannan maganar ta buge ni sosai. Ita dai Rafi'at dariya kawai take yayin da take nuna Ni da yatsa Cikin fusata na ce "Dalla Malama Ni ki daina wani dariya, wannan ba abun dariya ba ne abun mu jajantawa kanmu ne" Ko a jikinta ta ce "To meye abun tashin hankalin, duk tafiya in ya dawo na san Mommy a gaba za ta saka shi ya yi aure, da zarar ya yi aure kuma shi ke nan" "Allah sarki wacce ƙaddarar auren BB za ta faɗo kanta, ina jiye mata" Rafi'at ta ce "sai aka ce miki yadda ya mana haka zai wa matarsa? You must be out of your senses jannat, AI Ina faɗa miki irin mazan nan idan suka yi aure wasu sololi suke zama" "Sololi kuma?" Na tambaya ina jiran amsarta *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 7: "Ƙwarai kuwa, sololi, soloɓiyo, ina nufin masu sanyi, kar ki sha mamakin kiga yadda mace za ta juya BB" "Allah Rafi'at?" Ta gyaɗa kai tana faɗin "ƙwarai kuwa" "To ke duk wannan a ina kika sani?" "Ke ba kin ce karanta Hausa novels shirme ba ne? To wallahi akwai abubuwan amfani da yawa a ciki, kuma kin san me?" Na girgiza kai "Wallahi irin masu halin BB ɗin nan su ake sawa a matsayin taurari, kin ga yadda yake muguntar nan ko? Wallahi akwai littafin da na karanta kamar da BB ake." Cikin zaƙuwa na ce "Ikon Allah " Rafi'at ta ce "ba ki ji komai ba ma, kuma wani abun ma, yawanci jaruman auren haɗi ake musu, shi yasa ma nake tunanin la'alla BB ma a haɗa shi da ke, ko kuma Nasman Misau " "Sai dai Nasmah " na faɗa da sauri. "Um ai ba daga nan ba, da kina karanta littattafai da yanzu ke kanki kin samu mai kwatankwacin rayuwarki, tsari, buri da kuma dabi'u duk iri ɗaya sai ki ga kamar labarinki ake bayarwa" Cikin cunkushewar zuciya na ce "tura min guda ɗaya na gwada ko zan ji dadinsa" Rafi'at ta ce "Akwai littattafan team WOW FIVE WRITER'S HUB da na saya, zan na karanta mana in an yi update, ki fara da Yarima Bahjat, in ya miki sai na na ki gaba ta zo baya, sai waheeda da kuma Noor Ayn, Kuskurena NE zan ba ki ƙarshe" Numfashi na sauke tare da faɗin "To, amma kafin nan ki ba Ni wani complete na karanta kafin a gama waɗannan ɗin da kika ce kin saya" ta ce "To ban wayar taki" Nan dai Rafi'at ta tura min Novels masu yawa daga marubuta mabanbanta, littafin da na fara da shi shi ne saran ɓoye, Ni da ba na karatun littattafai sai ga shi na kammala littafin kafin dare ya yi, hakan ya sa na shiga littafi na gaba, cikin dan lokaci sai ga shi na ji ƙaunar karatun cikin raina, ina mamakin ashe dai haka masu karatun litattafai suke ji? Lallai marubuta ƴan baiwa ne haƙiƙa. Tun daga wannan rana da na samu litattafai a wurin Rafi'at damuwoyina da yawa suka gushe, da shike muna zuwa practicals makaranta da zarar mun dawo zan hau kan karatun Novels salla ce kawai take ɗaga Ni. A haka muka fara waec. Jarrabawarmu ta farko was a bit calm, practical Chemistry muka yi and alhamdulillah muna san ran samu sakamako mai kyau a cikinta, washe gari ba mu da exams hakan yasa ba mu fita ko ina ba, nikam Banda karatu ba abun da nake yi, surutu kuwa yanzu ba na yi, to dama rashin abun yi ne yasa nake yi yanzu kuma na samu abun yi, domin kuwa ina ƙara samun wayewar kai cikin litattafan da nake karantawa sosai. Ranar da muka kammala waec BB ya dira a ƙasarshi ta haihuwa sai dai sanin cewa ba za mu samu ganinsa ba ya sa ko su Abuya ba su je tarbansa ba, sai da ya gama da wurin aikinsa tukuna ya kira Abuya, ai kuwa cikin wani irin farin ciki Abuya ya nufo hanyar Bauchi ya ɗauko BB. Tun da muka dawo daga makaranta yau ina dakinmu ina karatun wani littafi Mai suna RUFAFFIYAR AJIYA (my next book) I was a kinda happy and excited saboda littafin ya zo da wani salo na musamman, Ni kaɗai ce a ɗakinmu Rafi'at na part ɗin Ummi, Ni dai ba Ni da masaniyar akan dawowar BB ɗin, ita dai ta sani saboda tare da Ummi suka shirya masa ƙayatattun abinciccika kamar wadda za a yi gayya. Ina zaune a parlourn Mommy na kwanta akan kujera mai mazaunin mutum uku yayin da TV ke kunne amma Ni hankali na gaba ɗaya yana kan littafin da nake karantawa a wayata, ina cikin karatun ne na ji sassanyan ƙarmshin da ko Bacci nake ba zan manta mai shi ba ya doki hancina. Idanhwana na lumshe tare da sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya kana na ci gaba da karatuna, ko layi ɗaya ban karanta ba na ji an dungure min kai. Cike da mamaki na ɗago don har ga Allah ban yi tunanin shi ba ne, ƙamshin da na ji kuma na san kawai gizo ne, amma dungure kaina da aka yi ya sa Ni miƙewa zaune na ɗago kaina don ganin waye. A zahiri na furta "Fatabarakallahu ahsanul Khaliqina" yayin da sautin bugun zuciyata ke fita da matsanancin sauri, kasa furta komai na yi bayan haka sai na lumshe idanuwana, BB ne tsaye akaina tabbas, ya ƙara tsayi da kuma ƙirar jiki, ya ƙara kyau da kuma cikar kamala, babu wani saje a fuskarsa saɓanin lokacin da ya tafi, amma duk da haka da wuya idon mace ya sauƙa kansa kuma ta iya ɗaukewa lokaci guda ba tare da jin son ƙara kallonsa a karo na biyu ba, Wannan shi ne abun da ya faru da Ni ma. Gyaran muryarsa ce ta sa ni dawowa daga duniyar da tunanina ya yi hijira gare ta. Cikin rawar murya na fara buɗe bakina trying to say something meaningful sai dai me, abun da na iya furtawa shi ne "Ka ka dawo ke nan?, so you're back now" Ƙoƙarin ɗaga idanuwana na yi don na kalle shi, to my surprise sai na ga wayam, ajiyar zuciya na sauƙe ina wawwaigawa ko dai kawai hasashe nake yi? Ko, ba hasashe nake yi ba, idan hasashe kuma nake da ya kamata ƙamshin turarensa shi ma ya ɓace ɓat. "Then Ina yake?" Na tambayi kaina cikin kiɗima, shigowar Rafi'at ya sa Ni dubanta, wata irin ajiyar zuciya na kuma sauƙewa, wurina ta ƙaraso tana faɗin "Jannat, BB ya dawo" fara'a sosai na gani shimfiɗe kan fuskarta haka kawai sai na ji ba daɗi kuma. "Kin ga yadda BB ya ƙara girma ya ƙara kyau..." "Um" na faɗa a gajarce tare da miƙewa zan nufi ɗakinmu. Wata irin sautin dakakkiyar murya ne ya dira cikin kunnuwana, cikin wani irin tsoro da fargaba na juyo, tsaye yake ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yayin da ya tsare Ni da idanuwansa. "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" A rarrabe na ce "E am na na iya, ina kwana ina yini" kansa kawai ya girgiza tare da tsura min idanuwansa da ke ba Ni tsoro tun muna yara, yadda ƙafata ke shirin kasa ɗauka ta ya sa na ƙara ƙanƙame jikina, cikin sanyin murya na ji ya ce "Disperse from here" Da wani irin gudu na kwasa na nufi bedroom ɗinmu, Ina isa na dafe ƙirjina tare da ƙamewa wuri guda, sai da na shafe mintuna kusan biyar a jikin bango kafin na faɗa kan gado ina sauƙe numfashi da sauri da sauri. Idanuwana na lumshe Sannan na ce "More handsome than he's before" sai kuma na tura bakina gaba. "Sai shegen haɗe fuska kamar..." Shiru Na yi na kasa ƙarasa abun da na yi niyyar faɗa, can dai da na dawo cikin right senses ɗina na Fara laluɓa wayata. Ganin ba ta gabana ya sa na tabbatarwa kaina cewa na bar ta a parlour ne, siririn tsaki na ja sanin cewa ban isa na koma parlour ɗauko waya ba har sai na tabbatar ya tafi, a wurin na kwanta tare da lumshe idanuwana na lula zuwa wata duniyar ta tunani. A can ɓangaren BB kallo ɗaya ya min ya gane ni, ko da ya ga yadda na saki baki da hanci ina kallonsa sai ya wuce ciki kawai don ya tabbatar at that moment ba lallai na iya ba shi amsar abun da tambaya ba, lokacin da ya tsayar da Ni kuma haka ya ci gaba da kallona har sai da na ji kamar zan faɗi, a nashi ɓangaren hakan ya so dama to amma yanayin firgici da tsoron da ya gani akan fuskata ya sa shi lumshe idanuwansa, kan laɓɓansa ya ce "She'll never change" sai kuma ya murmusa ya fara nufar hanyar fita, vibration wayata ta yi, har zai wuce sai kuma ya juyo, hango wayar akan kujera da ya yi ya sa ya dawo ya ɗaga yana mamakin wayar waye rai da yake wayar ba ta shiga lock ba hakan ya ba shi damar accessing ɗinta, yatsarsa ya saka akan secreen ɗin har ya koma bedroom ɗinsa, zama ya yi bakin bed sannan ya Fara bin screen ɗin which was still unlocked da kallo, a hankali ya fara karanta abun da yake gani cikin ransa, duk da ya sha wahala sosai kasancewar he's not used to karatun Hausa amma dai ya fahimci dai littafin soyayya ne irin wanda ƴanmata da kuma matan aure suka ba wa amanna a yanzu. Kansa ya jinjina kafin ya ce "Lallai yaran nan, nawa ma suke da za su fara karanta Irin litttattafan nan kalan duk su fitsare?" Sanin ba mai ba shi amsa ya sa ya jinjina kansa kana ya shafa kan nasa da babu gashin kirki duk sumar an aske ta. Wayar ya ajiye a wardrobe ɗinsa daga nan ya miƙe don yin sallar. Sai da Rafi'at ta dawo daga part ɗin Ummi na samu tabbacin ba ya nan, wannan dalilin ya sa na fito don ɗaukar wayata sai dai ga mamaki na babu wata babu alamar ta, a ɗan ruɗe na tambayi Rafi'at ta ce ba ta gani ba, ita tun fitar ta ɗazu ba ta ƙara dawowa ba sai yanzu, take zuciyata ta fara bugun tara-tara fatana ɗaya Allah ya sa ba BB ba ne ya ɗaga ba, idan shi ne ai kashina ya gama bushewa. Washe gari ban matsa da cigiyar wayar ba, Rafi'at ta kira amma ba a ɗagawa, mun duba saƙo da lungu babu wayar, hakan ya tabbatar min da cewa BB ne ya ɗage ta, gashi yau yini guda ko giftawarsa ban gani ba, gobe kuma muna da exams ɗin maths, ban san ya yake so nayi ba. Ganin bani da wata mafita da ta wuce na tunkare shi ya sa na aro jarumta na yafa wa kaina, da misalin ƙarfe tara na dare na nufi sashen Ummi, kai tsaye hanyar ɗakinsa na nufa.atre da cin birki a bakin ƙofar ɗakin ina tunanin knocking ko kuwa, can dai na yanke shawarar knocking ɗin sau uku na bufa daga nan na janye hannuna na kara kunnena a jikin ƙofar ina jiran a ce na shiga. Kusan minti biyu na kwashe ina jira ban ji ko da motsi ba, ba tsammani na ji an buɗe ƙofar hakan ya sa na bi ƙofar luuuuu kasancewar a jikinta nake, runtse idanuwana na yi don na tabbatar ba abun da zai min shamaki da faɗuwa ƙasa, matashin da na ji gangar jikina ta yi da Abu ya sa Ni sauƙe ajiyar zuciya Tare Da sakin wani gauron numfashi. "Ke!" Na tsinkayi amon muryarsa mai taushi cikin kunnena, saurin buɗe idanuwana na yi cikin rashin Sa'a na sauƙe su akan kyakkyawar fuskarsa wacce babu wani yanayi da ya bayyana kanta na daga garin ciki ko akasinshi. "Meye kike a nan?" Ƙoƙarin fara janye jikina na yi daga nashi da nufin na tsaya da ƙafafuna sai dai bai ba Ni damar hakan ba sai ma gyara min kwanciyar da ya yi akan hannayensa. "Am I not talking?" Kaina na kawar Sannan na ce "Wurinka na zo" sai lokacin ne ya samu damar sauƙe Ni ƙasa ya tsayar da Ni akan ƙafafuna, kallo Mai cike da tarin tambayoyi ya aiko min hakan ya sa ba shiri na fara ƴan kame kame "dama, dama dama BB wayata da ka ɗauka jiya gobe muna da exams" Cikin isa da ƙarfin halin da ya ban mamaki na ji ya ce "Ba zan bayar ba." "Don Allah..." "Shhhh" ya ɗaura yatsarsa kan lips ɗina sannan ya Fara magana cikin raɗa "I don't want to hear anything, just go away" Kasa cewa komai na yi hakan ya sa na fito jikina ba ƙwari, haushin kaina na fara ji don me ya sa zan biye masa, take wani littafi da na karanta ya faɗo min a rai, wanda jarumin da kuma jarumar alaƙarsu kusan irin tamu ne, shi ma ya je ƙasashen ƙetare ne ya yi karatu sai ya dawo, nan ya fara mannewa jarumar kasancewar ya saba da mu'amala da mata a can. Saurin kawar da wannan tunanin na yi sannan na wuce part ɗin Mommy, Ina ji Rafi'at na tambayana ina na je na yi banza da ita na koma na kwanta, sai dai baccin ya ƙi zuwa min sakamakon tunaninsa da ya yi wa zuciyata ƙawanya. A sannu zuciyatata fara gwaɓa ta akan yakice tunaninsa a raina. Washe gari bayan mun dawo daga school, wanka muka yi kana muka nufi part ɗin Ummi, shi kaɗai muka tarar a parlour kwance akan 3 seater yayin da ya lumshe idanuwansa kamar mai Bacci, cikin raina nake ayyana irin yadda ya ƙara kyau da kuma kwarjini, sai nake ganin ma kamar shuɗewar kowacce rana ƙara kyau yake yi. Ganin idanuwansa rufe ne ya sa muka yi tunanin Bacci yake hakan ya sa na yi wa Rafi'at alamun mu wuce ciki kawai a hankali, takunmu hurhuɗu muka ji gyaran muryarsa, babu ɓata lokaci muka dawo gabansa muka tsugunna. Tashi ya yi ya zauna, kamar masu rige-rige haka muka gaida shi, bai amsa ba sai ma bin mu da kallo da ya yi. Sai da ya ƙare mana kallo kana ya ƙira sunanmu ɗaya bayan ɗaya. "Jannatul Firdaus, Rafi'atu!" Jiki na rawa muka amsa, fuskarsa ya haɗe lokaci guda, take muka sha jinin jikinmu. Cikin Muryarsa mara hayaniya ya ce "Dama aure kuke so ashe?" Na ɗago na kallo Rafi'at, itama ta kalle Ni sai muka sunkyar da kanmu ƙasa ba tare da mun iya cewa komai ba. "Aure kuke so ashe?" Ya ƙara maimaitawa cikin halin ko in kula. Cikin kame-kame muka fara faɗin "A'a e a'a BB" Yatsarsa ya ɗaura kan lips ɗinsa sannan ya ce "shhhh, don't say anything, aure kuke so, in Kuma ba haka ba to yaya ne" Shiru muka yi daga Ni har Jannat muna wasa da yatsunmu. Ƙara haɗe fuskarsa ya yi tamau kafin ya dube mu ya ce "Idan ba auren kuke so ba meye?" Raurau na yi da ido sanin cewa da Ni yake wannan maganar, cikin rawar murya na ce "Don Allah ka yi haƙuri kar ka faɗawa Abuya, wallahi ba aure muke so ba, karatu muke so" A dake ya ce "fine, wa ya siya muku waya ma? Kema kina da ita ko Rafi'atu?" Rafi'at ta ce "Ka yi haƙuri BB Daddy ne ya siya mana saboda exams" "Sai ya ce kuke karance-karancen iskanci ko? Na sha jin malamai na magana akan Littattafan hausan nan, a ciki ake lalata muku tarbiyya" Cikin ƙarfin hali na ce "BB wallahi ka karanta ka gani, wallahi wannan littafin babu iskanci a ciki" "O kin san akwai iskancin a ciki kuma kuke karantawa ke nan?" A ɗan kiɗime na ce "Wallahi ba haka nake nufi ba, don Allah ka rufa mana asiri BB, wallahi ba zan ma ƙara karantawa ba" Shiru ya yi can ya ce "Fine, yanzu dai tun da aure kuke so kun ga kun hutar da mu, bari sakamakon jarabawar ya fito sai ku turo samarin naku gida..." *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 8: Hannu muka haɗe muka fara masa magiya, can dai ya ce "Na haramta muku karatun Littattafan Hausa at your early stage, idan kuma kuka ci gaba wallahi na lahira sai ya fi ku jin daɗi, kar ku ga kamar kun girma, har yanzu ƙananan yara nake kallonku, wallahi in na kama yarinya ko? Hmm" ya wani cije leɓensa. Rige-rigen gyaɗa kai muke, BB ya ƙara da faɗin "Kuma wallahi ko da wasa na ji labarin kuna kula samari ko? Wallahi ku da karatu sai dai ku ga ana yi, ko kuma in ce sai a gidajen mazajenku " Cikin rawar murya muka ce "in sha Allah za mu kiyaye ma" "Ku ba Ni waje" Tsaye muka miƙe muna faɗin Mun gode daga nan kuma muka juya za mu tafi, sunana ya kira cikin wani irin sauti da ban taɓa jin an furta sunan da shi ba har sai da zuciyata ta yanke, juyowa na yi, Rafi'at ta wuce abun ta, na koma gabansa na tsugunna. "Yaushe za ku kammala exams ɗin?" Na ce "Neco ce ta rage, next week za mu fara itama" Shiru ya yi can ya ce "How about your jamb results?" A kunyace na ce "I scored 134, Rafi'at Kuma 230" Sai da ya gama isar tasa ya ce "ma sha Allah, Dama me kuka yi applying?" Na ba shi amsa da faɗin "Ni MBBS, ita kuma Law" Kansa ya jinjina can ya ce "Karatun littattafan nan ne ya sa kika ci low score a jamb ɗinki ko?" Na girgiza kai Ya ce "To mene? Ga shi yanzu Rafi'at ma ta fi ki ci, garin yaya?" Cikin sanyin jiki na ce "Haka Allah ya ƙadarto" Ya ce "shi ke nan, amma kin san cut off mark na MBBS ko?" Na gyada kai ya ce "Good, zan bincika na ji me ya kamata a nema miki, itama Rafi'at ta haƙura da law ɗin ta zaɓi wani abun, don ba za ku yi karatu a wajen gari ba beside ma rawar kanku ta yi yawa" Ni dai ban ce mishi komai ba, haka na sunkyar da kaina ƙasa kamar wata mai ɗaukar karatu. "Karɓi nan, Jannat" sai da na karba ya ce "Kada na ƙara gani ko jin labarin kuna karance-karancen hausan nan kin ji ko?" Na ce "e" Ya ce "fine, you can depart" Kamar abun da nake jira na ji ya faɗa da sauri na miƙe zan tafi ya ce "Come back" Na dawo na tsugunna gabanshi "Wato yanzu kin yi girman da ba za ki iya godiya ba ko?" Na ce "Ka yi hakuri na gode" Ya sauƙe numfashi tare da nuna min hanya da hannunsa jiki ba ƙwari na wuce nima. Tun daga wannan rana na fara wasan ɓuya da BB don kk kaɗan ba na son abin da zai haɗa Ni da shi, ba don komai ba sai don abun da na fara ji dangane da shi mai kama da so, wanda barin wannan yanayi ya ci gaba da girmama cikin zuciyata zai iya zama babban KUSKUREN da zan aikata a rayuwata, beside BB is not a kinda guy I want, ba na son mutum mai ji da kansa ko kuma dai miskilanci, i want someone very simple Wanda komai na yi masa zai min uzuri ya za Ni a turbar yarinta. Lura da hakan da ya yi ya sa shi zama a part din Mommy ranar, sai dai abun da bai sani ba muna makaranta lokacin, bayan mun dawo kuwa ya tsare mu, muka gaishe shi, Ni dai kunya gaba ɗaya ta ishe Ni, bai ce mana komai ba muka shige ciki, shi ma tun daga ranar ya sauya mana ya koma ainihin BB ɗinsa, Wanda ba ya wasa da mu, wanda burinsa mu yi laifi ya jibge mu. Yau ma kamar ko yaushe mun dawo daga makaranta ke nan muka shiga part ɗin Ummi, bayan mun gaishe ta ne take shaida mana cewa ba ta jin daɗi, ko za mu yi wa BB girki, Ni dai kamar na ce ba zan yi ba, amma babu dama. Haka muka cire uniform muka shiga kitchen, ba don na so ba haka muka yi girkin muka zuba a flask, sai da muka tafi haka kawai zuciyata ta raya min in dawo in ƙara yaji a abincin sanin cewa ko kaɗan BB ba ya ƙaunar yaji. Cikin sanɗa na baro Rafi'at a sashen Mommy na taho part ɗin Ummi, a hankali na lallaɓa kitchen, na Fara binciken containers ɗin da Ummi ke ajiye reserved pepper powder a ciki, cikin ikon Allah kuwa na hango ta a sama, ai da sauri na ɗauko stool na haye Sannan na fara ƙoƙarin ɗauko ta, alhamdulillah, har na ɗauko ban ji motsin kowa ba, na sauƙo na ciko spoon na pepper powder ɗin na zuba cikin pepper soup ɗin kayan cikin da muka yi ba ɗauko wani spoon na gauraya da kyau, na ƙara ɗebo spoon of pepper powder ɗin na buɗe jallop ɗin taliyar da muka masa mai ruwa ruwa na zuba nan ma na gauraya, ƙara ɗebo wani na yi na ƙarawa taliyar zuciyata fal farin cikin abun da nake aikatawa, komawa na yi na haye stool ɗin sannan na mayar da container na sauƙo, sai da na ɗan ɗebi pepper soup ɗin na zuba a hannuna na ɗanɗana, waro idanuwana na yi jin uban yajin da ya yi, da gudu na nudi dispenser na samu na sha ruwa tukun na dawo na rufe pepper soup ɗin na dawo kan taliyar itama na yi tasting, kan balai, ai saura kadan asirina ya tonu don yajin da ya ziyarci ƙwaƙwalwata sai da na kusa cilla ihu, da sauri na toshe bakin nawa Sannan na rufe na ƙarasa gaban dispenser na sha ruwa sosai tukun na zo na gyara jeren abincin, ina kammalawa na kaɗe jikina ina sakin wata irin dariyar mugunta don na san yau BB idan ba Sa'a ba sai mun ji ihunsa, to dai nima da na kasance Gwanar cin yaji wallahi ba zan iya cin wannan abincin ba, in na yi good three spoons ma wallahi da ƙyar. Bedroom ɗin Ummi na nufa na sanar da ita cewa mun kammala, ta ce "Allah ya muku albarka, ki miƙa masa bedroom ɗinsa kafin ki tafi" Na amsa da "To Ummi" fuskata sake samun abun da na riga na ƙulla masa. Ina fitowa daga bedroom ɗin Ummi na dauƙo tray ɗin da na jera flasks ɗin kai na nufi ƙofar bedroom ɗinsa, a ƙasa na ajiye na yi knocking Sannan na murɗa na ɗan tura kaɗan sai na ɗauko tray ɗin na nufi ɗakin bakina ɗauke da sallama, kasancewar ba ya ciki ya sa na sauƙe wata irin ajiyar zuciya tare Da godewa Allah da ya ara min such a golden opportunity. Ina dire abincin na fito tare sauƙe numfashi ina wani rolling eyes ɗina cikin wani irin salo daga nan na koma part ɗin Mommy da ƙudirin ba zan fito ba ko sau ɗaya, ba kuma zan bari ko da wasa BB ya ganni ba. Ina fita a ɗakinsa ya fito daga bathroom, yana gama goge jiki yayi routine ɗinsa sannan ya zura jallabiya abun sa. A bakin gado ya zauna nan ya hango abincin da na kawo, wani cute smile ne ya yi escaping akan lips ɗinsa, cikin ransa yana ƙara jin ƙaunar Ummi a ransa. Wani medium sized carpet ya shimfiɗa sannan ya ɗauko tray ɗin ya dire. Fridge ya buɗe ya ɗauko drink ya ajiye gefe da kuma bottle water sannan ya samu wuri ya zauna yana ambaton sunan Allah. Ɗaya bayan ɗaya ya buɗe girkin, daddaɗan ƙamshin girkin ne ya buge shi take ya wani ja dogon numfashi yana mai lumshe idanuwansa, the scent, the aroma, ya Allah, was very good smelling. Serving kansa ya yi da paper soup ɗin tare da yin bismillah ya fara ci, alive ɗin farko na naman da ya kai bakinsa ya waro idanuwansa jin yaji sosai, a haka dai ya daure ya tauna ta haɗiye sannan ya yi saurin buɗe lemon ya kai bakinsa, sai da ya sha kusan rabin lemon tukunna ya sauƙe yana sauƙe ajiyar zuciya, this food definately no be Ummi's, ko dai masu aiki suka yi ko kuma dai, masu aikin nema, ya faɗa cikin ransa, rufe flask ɗin pepper soup ɗin ya yi tare da janyo spaghetti ɗin without knowing that, yajin da aka ƙara mata ma ya fi na farkon da ya ci. Kaɗan ya zuba a plate itama sannan ya yi bismillah ya kai one spoon bakinsa, wannan karon kan kasa haɗiyewa ya yi tsabagen abun da ya ji ya ziyarce shi ba nau'in yaji, tuni ya nufi toilet, kusan mintinsa biyar ashe dai da ya yi brush ya fito har lokacin amma zafin yajin yake ji. Gaba ɗaya abincin ya fice masa daga rai, hakan ya sa ya rufe flask ɗin ya ture shi gefe ransa na masa ba daɗi da abincin ga shi kuma yunwa yake ji don tun breakfast bai ƙara cin komai ba. Sallar la'asar ya fita Masallaci ya yi da ya dawo ya tarar da Ummi a parlour, gaishe ta ya yi har zai wuce kuma ya dawo ya ce "Ummi me za ki ci a yi order?" Ummi ta ɗan dube shi fuskarta na ɗauke da tambaya Ta ce "Ban gane ba, order kuma? Ai akwai sauran abincin da su Jannat suka maka ɗazu, bari ma na saka su su maka dinner" Saurin ce mata "A'a" ya yi ta ce "Why? Ko dai girkin ɗazun bai maka daɗi ba?" Ya ɗan sako fuska ya ce "A'a Ummi, bari zan kira su da kaina ma" Ba tare da kawo komai a ranta ba Ummi ta ce To, BB ya ce bari na je. Yana fitowa bakin apartment ɗin Ummi ya jinjina kai tare da jinjinawa mugunta irin ta yaran nan, duk yadda aka yi ya tabbatar da sani suka masa haka sun sani sarai ba ya son yaji ko kaɗan, lallai kuwa yau zai koya musu hankali ƙwarai. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 9 Part ɗin Mommy ya nufa, ita kaɗai ya tarar a parlour, gaishe ta ya yi sannan ya ɗan dudduba, kamar zai wuce ya janyo su da duka sai kuma ya girgiza kai ya ce "Mommy ina yaran nan?" "Waɗanne yara kuma?" Ya ce "Waɗannan yaran nake nufi, su Rafi'atu " "Suna ciki, Rafi'at! jannat!" Mommy ta ƙwala musu kira daga yadda take kwance. "Na'am" muka amsa a tare, cikin daƙiƙa biyu suka fito, Rafi'at gaba ina bayanta, a lokcin da idanuwana suka sauƙa kan halittar da ke tsaye take na ja Baya da wani irin sauri ina dafe ƙirjina, "Allah dai ya sa ba shi ke kiranmu ba" na faɗa cikin raina. "Ya kika tsaya baya?" Mommy ta faɗa tana kallona, wanda maganar Mommyn ita ta sanar da shi kasantuwa ta a wurin kallona ya yi ya jinjina kai wanda hakan sosai ya sa kayan cikina juyawa, na riga na tabbatar in dai har ya ci abincin to ya zo hukunta mu ne "ni kam na gama yawo" na faɗa cikin raina ina aro wata ƴar jarumta na ƙarasa wurin Mommy ina faɗin "Mommy ga mu, ina yini BB" Mommy ya ce "Yayanku ke nemanku" ai wani irin ƙwalalo idanuwana waje na yi ina mai dafe ƙirjina. "Lafiya?" Mommy ta tambaya tana mai tsare Ni da ido, saurin girgiza kai na yi, Mommy ta ce "Anya?" Cike da shakku "Ko dai laifi kuka masa?" "A'a e a'a Mommy ba mu yi komai komai ba" na ba ta amsa ina ƴan kame-kame. Mommy ta ce "Shi ke nan, sai ku bi shi ai, kafin ku ƙara wani laifin don waɗannan idanuwan naku sun nuna tsantsar rashin gaskiya. Sai lokacin na samu damar mayar da dubana ga bigiren da yake, ganin ba ya nan ya sa na ja jiki a saɓule na bi bayan Rafi'at wacce ta riga ta yi gaba, Ni kaɗai na san halin da nake ciki a yanzu, tsoro da firgici sun lulluɓe Ni, Ni dai kawai na san yau na gama yawo wurin BB, Allah dai ya sauƙaƙa haɗuwarmu da shi. Har sai da muka isa bakin part ɗin Ummi Rafi'at ta juyo ta kalle Ni sannan ta ce "Ana ganinki an ga marar gaskiya, wace masifar kika kuma jaza mana wurin BB?" Na ce "oho, in kin je kya ji" tsaki ya ja sannan ta ce "Wallahi kika sa aka bani punishment akan ki zan rama" tana faɗin haka ta shige part ɗin Ummin a ɗan fusace, Ganin haka ya sa na taɓe baki nima na shiga ciki. A parlour muka tarar da shi ya hakimce akan kujera, Rafi'at ta yunƙura za ta tsugunna ya ce "Tashi" a matuƙar fusace. "Cikinku waye ya yi girki ɗazu?" "Mu mu mu ne BB" Ta ba shi amsa muryarta na rarrabewa. Ya ce "Ku wa?" Na ce "Ni da ita ne" Ɗagowa Ya yi ya kalle Ni sannan ya ce "wacce ta kai min bedroom ɗina ta je ta ɗauko ta kawo shi nan" A saɓule na wuce kamar wata Munafuka na ɗauko abincin na kawo gabansa na ajiye. Wani irin mugun kallon da ya aiko mana sai da hanjayen cikinmu suka yi colliding da juna hakan ya sa muka sunkyar da kanmu ƙasa. Murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ku ɗago ku kalle Ni" Jiki na rawa muka ɗaga kanmu sai dai kwarjininsa ya hana mu sanya idanuwanmu cikin nasa. Mun kai minti uku a wurin shi bai ce komai muma haka, can dai ya numfasa ya ce "A cikin wace ce ta yi girkin nan?" Muka haɗa baki wurin faɗin "Tare muka yi" ya ce "Ok, ku buɗe shi yanzun nan ku cinye shi" Ba musu Rafi'at ta janyo tray ɗin ya buɗe flask ɗaya na buɗe ɗaya, and luckily mai pepper soup ta buɗe Ni kuma mai taliya. A ɗan zafafe wannan karon Ya ce "Ku zauna ku cinye shi tas kafin na ba ku punishment ɗin da ya dace da ku" Tun da ya ambaci punishment na Fara ambaton Allah cikin raina ina addu'ar Allah ya shigo da Mommy don ɗazu ta ce za ta shigo ta duba jikin Ummi. Allah sarki Rafi'at da ba ta san komai ba ta ambaci sunan allah tare da sanya hannunta cikin flask ɗin pepper soup ɗin yayin da Ni kuma na zubawa taliyar gabana ido ina tunanin ta ina zan iya cinta tun da na riga na san masifar da ke cikinta. Lomar farko da Rafi'at ta kai take ta juyo ta kalle Ni tana zaro eyes ɗinta, da ƙyar ta iya haɗiyewa Sannan ta kwaɓe fuska, da Yaren kurame ta ce min "ya haka?" Na ɗage kafaɗata, duk abin da muke ashe BB na ganinmu, hakan ya sa shi gama tantance wacce ke da kaso mai tsoka wurin cika yaji a abincin amma bai nuna mana ba, sai ma tsawar da ya saka min ya ce "Ke kin fi ƙarfin ci ne?" Yadda tsawar ta dake Ni ya sa Ni tsoma hannuna cikin taliyar ba tare da na aune ba nan na fara kai lomar farko bakina, sai lokacin na tabbatar ashe ɗanɗanawar da na yi lami na ji, yanzu ne na ji asalin ɗanɗanon abincin, cikin dakiya na kai loma ta biyu na yi ta uku, ai take nima na fara kuka, irin voluntary kukan nan da ke zuwa da kansa, juyawa na yi na fuskaci Rafi'at, itama kukan take, cikin raina na ce "Don ma naki bai kai nawa masifa ba." Koma shida na yi tuni na gigice kamar ba Ni ba, yunƙurin miƙewa na yi na nemo mana abun sha na ji ya daka min tsawa, "Zauna ki ci gaba da ci" ba shiri na zauna, ya ce "Sai kun cinye shi tas kafin na ba ku exact punishment ɗin da ya dace da ku" Rafi'at da azaba ta mata azaba ne ta ce "Na rantse da girman Allah BB bamu saka yaji haka ba, akwai sauran abincin a kitchen" ta ƙarashe numfashinta na cikewa yayin da hawaye ke bin kuncinta, tausayinta ne ya kama ni ganin yadda take karɓar hukuncin abun da ba ta aikata ba, hakan yasa Ni dole magantuwa cikin fitar hayyaci na ce "Wallahi Ni ce! Ban da ita.." ƙafarsa ya sa ya shure flask ɗin gaban Rafi'at ya nuna mata fridge da hannu sannan ya min alamar na matso kusa da nawa flask ɗin. Tun daga lokacin na san cewa nikam tawa ta ƙare, Ko da Rafi'at ta dawo ce mata ta yi ta je abun ta ya kuma gargaɗe ta kan kada ta faɗawa Mommy, a guje ta fice ta bar Ni ina ta jefa abincin a cikina, ko rabi ban ci ba na fita hayyacina sosai, ganin hakan ya sa shi sakin murmushin mugunta Sannan ya ce "Ni aka so na shiga wannan halin ko? Ci gaba da ci maza, da sauri" "Numfashina sama sama na ce "Don Allah! Zan mutuuuuuu" Ya ce "ki mutun mana, sai kin cinye shi tas" Kaina na girgiza don yanzu kalaman ma ba sa iya fita, ture nawa flask ɗin ya yi, amma bai ce na tashi ba, raɗaɗin da na ji bayan na daina cin ma Ni ya fi min cin wahala bai sani ba, idan kuma ya sani to ba shakka shi ɗin ya cika ƙaton mugu, sai da BB ya ga ina shirin shurawa haiƙan tukun ya miƙo min lemon peach da ke hannunsa, da wani irin sauri na karɓa sa of my life totally depend on it, murmushin mugunta ya saki ganin yadda nake shan lemon, sai da ya ƙare tas na ɗage gorar amma har lokacin zafin yajin na nan kamar wadda aka sabunta shi. Abun da ya ban mamaki ko tausayina BB Bai ji ba haka ya ajiye Ni gabansa lokaci bayan lokaci yana sakin murmushin mugunta, sai da ya tabbatar na azabtu tukun ya dube Ni ya ce " Jannat" na ɗago na dube shi, ya ce "yanzu har ƙiyayyar da kike min ta kai wannan matsayin da za ki iya cutar da Ni?" Ni haushinsa ne ma ya turnuƙe Ni, yana ganin halin da nake ciki ba zai ce na tafi ba zai tsaya min wani bayani? "Har yanzu ku ɗin yara ne shi ya sa nake daga muku, amma tun da kun nuna min wuyanku ya isa yanka shi ke nan, mu zuba mu gani, ɓace min da gani." Cikin wani irin hanzarin da ban taɓa tunanin ina da shi ba na miƙe da shirin tafiya ya dakatar da Ni "Ki je ki faɗawa Mommy kin ji?" Yana faɗin haka na wuce abuna sai part ɗin Mommy. Ina zuwa na nufi kitchen, Ina shiga da niyyar duba kunu NA ga madara, a haukace na buɗe gwamgwanin madarar na ɗauko cup na zuba a ciki, ruwa na tara a dispenser ko gaurayawa ban yi ba na kai baki, sai da na shanye tas tukunna na ajiye kofin, ajiyar zuciya na sauƙe tare da jinjina kaina. Lallai yau na taka siraɗin mutuwa Allah ya cece Ni na kuɓuta, bedroom ɗinmu na nufa, Allah sarki Rafi'at har lokacin kuka take yi sosai Na ji jikina ya yi mugun sanyi, wurinta na ƙarasa da niyyar lallashinta, a fusace ta ture Ni gefe tana faɗin "Ki har Ni na mutu don Allah Jannat, miye abun da kika aikata haka? Baya na ɗan ja ina ƙare mata kallo, after all the hard punishment da ɗan'uwanta ya ba Ni tanada da gut ɗin da za ta ce Wani abu. Cikin ɓacin rai nima na ce "Tambayata ma kike Rafi'at? Bayan duk azabar da ɗan'uwanki ya gana min kina da bakin tambayata me na aikata?" Kaina na fara girgizawa ina faɗin "wato kin zaɓe shi fiye da Ni ke nan?" Rafi'at ta ce "Haba Jannat, abun da kika yi kema bai dace ba, ramin mugunta kika gina masa sai kika janyo mu kika jefa mu ciki." Wurin na bar mata don ita kanta wallahi haushinta nake ji a lokacin, shi kuwa BB ya gama fice min daga rai da wannan izayar tasa. Washe gari da safe muna breakfast na ji Mommy na sanar da Daddy tafiyar BB ɗin wai zai koma bakin aiki can Abuja, daɗi ne ya kama na ji kamar na tashi na taka, ko ba komai za mu samu salama da nutsuwa. Tun da BB ya tafi wani irin walwala muke abun mu, a haka har muka kammala Neco ya zama babu inda muke zuwa. Wata Guda BB ya yi sannan ya shigo Azare, ko kaɗan ban ji daɗin hakan ba, duk da cewa yanzu ba na iya juran abubuwan da yake mana, wasu lokutan idan ya ɓata min rai har akan fuskata yake gani. A wannan dawowar ganin babu yadda muke zuwa ya sa BB yi mana register da wani catering school Wanda da farko da cewa nai Ni ba na so, Ummi har bugu na sai da ta yi akan haka ta yi min faɗa sosai wai ana min gata ba na gani. Yau juma'a, da wuri muka kammala karatun kasancewar practical ne, gani na yi a madadin tsayawa jiran BB gara kawai mu tsari mai keke ya kai mu, da kyar Rafi'at ta amince Don ita har yanzu tsoron BB da take yana nan, unlike me da nake jin yanzu duk abun da ya min nan ji daɗi ba sa na rama ta wata hanyar. Muna cikin tafiya ne wata danƙareriyar mota ta faka gefenmu, mai motar ga sauƙe gilashin motar sai dai ko kaɗan ba mu yi gigin tsayawa ba don mun san hakan ba koyarwar gidanmu ba ne. Gaba muka yi abun mu kamar ba mu ganshi ba, mun ɗan yi tafiya kaɗan muka ji an ce "Hi" Rafi'at wacce take a tsorace ta ce "Malam mu matan aure ne, don Allah ka tafi abun ka" Kyakkyawan saurayin ya yi ƴar dariya sannan ya ce "Lallai kam, na ga matan aure a nan, to ko za ku shekara kuna ce min ku matan aure ne Ni ba zan yadda ba idan ba mazajenku na gani ba, kai ko na gansu ma Ni da ƙyar na yadda" Wani ƙayataccen Murmushi na yi sannan na ce "To shi ke nan, idan ma mu ƴanmata ne inaga bai kamata ka tsayar da mu akan hanya ba, beside ba shigar banza ka gani jikinmu ba bare ka ce ka ga alamun rashin kamewa a tattare da mu" Kamar dai kalamaina sun yi tasiri akan shi, ya sosa sumar kansa sannan ya ce "Haka ne, ku yi haƙuri don Allah, na san cewa ban kyauta ba, amma ku sani babu yadda zan yi ne shi ya sa na tsayar da ku, don Allah ku yi haƙuri, ku ba Ni 11 digits ɗinku sai na tafi" Na jefe shi da wani kallo, ya marairace fuska ya ce "Haba sister, duk da cewa na ga ƴar'uwar tamu na kunya ke kam ya kamata ki ba Ni ai, in kin ba Ni kin ga shi ke nan, ba zan kuma muku magana akan titi ba sai dai na kira na tambaye ku gidanku sai iyayena su zo" Ƴar dariya na yi sannan na ce "Kawo wayarka na saka maka" Ya ce "To" da sauri yana miƙo min wayarsa ƙirar iPhone 16, na karɓa ina bin wayar da kallo Sannan na zuba masa numbern wayata. Bayan na gama na miƙa mishi muka yi sallama, har ya juya zai wuce sannan ya juyo ya ce "Amma dai bai kyautu a ce kuma bin titi haka ba, ku shigo na sauƙe ku mana" Na girgiza kai na ce "A'a, kar ka damu, za mu tari abun hawa ai" Ya ce "Ai ba lallai ku samu ba in dai a wannan titin ne, tafiyar kuma da yawa hala" Rafi'at ce ta ja veil ɗina ta ce "ki ci gaba da biye shi, Ni dama sai da na ce miki ba zan taho ba zan jira BB kika ce sai mun taho" Na ɗan harare ta sannan na dubi saurayin na ce "Shi ke nan, mu je" Waro eyes Rafi'at ta yi kafin ta ce "Ba ki da hankali ne jannat?" "Wow! Jannat, Nice name from sweet voice, na roƙe ki ba don Ni ba ki shigo kin ji?" Rafi'at ta ce "I'm not going with you guys, ku je, Ni zan koma na jira BB" Ba tayi tsammani ba na ja ta zan nufi da ita wurin da motar guy ɗin take Na ji an daka min tsawa. Ai take na shiga taitayina don ko ina cikin magagin mutuwa ba zan mance sautin Muryar nan ba. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 10: Da sauri na saki Rafi'at ina ja Baya kaina ƙasa. BB ne tsaye cikin wasu ƙananun kaya da suka amshi jikinsa, cikin zafin nama na ga ya tunkari guy ɗin ya tsaya gabanshi. "Kai ba ka da hankali ne za ka tsayar da Mata akan hanya?" Guy ɗin ya yi dariya sannan ya ce "Kaima hala tsayar da su ɗin za ka yi, to na riga ka, ka jira sai na zaɓa tukun na bar maka..." Taf! BB ya ɗauke guy ɗin da mari cikin ɓacin rai ya nuna shi da yatsa "You must be out of your senses Man! Do you know who am I to them? O ya asked them" ya juyo inda muke, ai tuni mun nufi motarsa muna zazzare idanuwa. Ganin hakan ya sa guy ɗin saduda ya ce "Yi haƙuri Yaya, wallahi na yi zaton kai ɗin ma kamar nine, wallahi Ni ba mutumin banza ba ne kuma da aure nake so ƙanwarka ba wai cutar da ita zan yi ba..." "Ya isa, kar ka ƙara ko da kallon ɗaya daga cikinsu ne" yana faɗin haka ya bar shi tsaye ya nufo motarsa, misalta muku yanayin da na ji a wannan lokacin ma abu ne mai wuya, domin na tsorata ainun da wannan al'amari kasancewar kullum faɗan da BB ke mana yana cewa Duk ranar da ya kuskura ya ganmu da saurayi to daga ranar mun yi sallama da karatu sai aure. Bai kula mu ba har muka isa gida, Ni na fara yunƙurin buɗe ƙofa zan fita na ji ta kulle, ban yi yunƙurin kallon yadda yake ba sai ma wasa da yatsuna da nake yi, muryarsa ce ta doki kunnuwan mu "Ku ba Ni wayoyinku" jiki na rawa Rafi'at ta miƙa Ni kuma na ce "Don Allah ka bar mana wayoyinmu BB.." "Jannat!" Ya ƙira sunana da wani irin sauti wanda ya sa Abdominal contents ɗina cin karo da juna. Ya miƙo min hannunsa ba tare da ya ce komai ba, duk irin yadda nake jin tsoro haka na ɗan dake na ce "To me muka yi?" Ni kaina sai da maganar ta fita na zaro idanuwa ina mamakin kaina, ina ga Rafi'at da ke mintsinina ta ƙasa ta min alamar na bayar? Shakkuna ne ya ɗarsu mata a rai har ta gagara ɓoye hakan ya magantu duk da cewa a gaban BB muke. "Jannat?" Na ce "What?" Cikin halin ko in kula amma fa cikin raina Ni kaɗai na san me nake ji, don nadama in akwai maras iyaka na yi ta a ciki, to amma ina so yau dai mu ɗan yi ta da BB ko zai rage takura mana da yake. Tsabar yadda ransa ya ɓaci take hasken fuskarsa ya sauya tuni kalar fatarsa ta sauya zuwa jajajaja, ko ban kalla ba na san idanuwansa ma a wannan lokacin sun yi jawur. Cikin ɓacin rai ya yi unlocking motar ya ce "Ku fice min a mota" Jiki a sanyaye Rafi'at ta fara fita, nima na fita, muna fita ya langwaɓar da kansa a kujerar motar tare da lumshe eyes ɗinsa yayin da zuciyarsa kuma ke zafi da ƙunar abun da na aikata, tunani ya fara cikin ransa, a duk lokacin da wani sashe na zuciyarsa ya yi ƙoƙarin fahimtar da shi cewa zallar rashin kunya da tsauri ido na masa sai ɗaya sashen ya ce masa ba haka ba, may be aljanu sun shafe Ni ne, cikin wannan yanayi ya zauna cikin mota har lokacin salla ya yi ya fito sannan ya yi alwala a tap ɗin da ake bayi da shi daga nan ya wuce masallaci. Ba shi ya dawo ba sai da ya yi sallar isha', ranar ko dinner Bai yi ba yana ɗaka, Gaba ɗaya bacci a daren ranar ƙauracewa idanuwansa ya yi, banda saƙe-saƙe da since-since babu abin da zuciyarsa ta kwana ta yi. Har muka isa part ɗin Mommy babu wanda ya kula ɗan'uwansa daga Ni har Rafi'at, haka har muka yi sallar magrib muka yi isha kowa ya kwanta. Washe gari da safe ma Rafi'at ba ta min magana ba abun ya ɗan dame Ni gaskiya, hakan ya sa na riƙo hannunta bayan mun gama breakfast za mu koma bedroom ɗinmu, janye hannunta ta yi, na ƙyale ta har ta shiga ɗaki nima na shiga sai na janyo ƙofa na rufe. Na dubi Rafi'at a raunace na ce "Haba ƴar'uwata" saurin ɗaga min hannu ta yi hawaye na bin fuskarta ta ce "Ke ba ƴar'uwata ba ce, ba haka ƴar'uwata take ba, zan faɗawa Abuya anjima a kira Malam ya cire aljanar nan daga jikin ƴar'uwata.." Jikina ne ya ƙara sanyi nima sai ga hawaye ya fara bin kuncina, ban yi ƙasa a guiwa ba na nufe ta xan yi hugging ɗinta sai ta ja Baya "A'uthubillahi minasshaiɗanir Rajiim, idan har ba ki bar jikin ƴar'uwata ba tabbas Abuya zai sa a cire ki, kin sauya min ita..." Kuka ne ya ci ƙarfinta, cikin don fahimtar da ita na miƙa hannu zan riƙo nata ta janye tana girgiza kai, na ce "Ni ce Jannat, Rafi'at Ni ce Wallahi" Ta ce "Ba ke ba ce, wallahi an sauya ki, ke aljana ce kin ɗauke mana Jannat ɗinmu kin kawo mana kanki, ba ma son kiiiiii" ta ƙarashe tana jan karshen maganar tare da faɗawa kan bed tana muka mai tsuma zuciyar" Ƙasa ƙarasawa kusanta na yi sai na ja gefe na zauna nima na haɗe kai da guiwa ina kukan. Mun shafe kusan 30minutes muna aikin kuka har Bacci ya ɗauke Rafi'at, sauƙar ajiyar zuciyarta da nake ji akai akai ya sa na fahimci hakan, kwanciyarta na gyara mata sannan nima na kwanta gefenta. Wuraren ƙarfe ɗaya muka tashi muka yi salla, bayan mun idar na sulale na nufi part ɗin Ummi don gudanar da abun da zuciyata ke Umarta ta da na yi, sanin cewa Ummi ba mai zama a parlour ba ne ya sa na shiga hankalina kwance, haka kawai na tsinci kaina da nufar dining ba buɗe flask ɗin da ke jere, daga nan na jera wasu akan tray ɗin na ajiye wayata akai na nufi ɗakin BB. Knocking na yi sannan na murɗa door handle daga nan na cusa kaina ciki bakina ɗauke da sallama, maimakon na fito sai na zauna gaban abincin duk da cewa ban gan shi a ɗakinba, ƙarar buɗe ƙofa ya sa na dubi hanyar toilet, shi ne tafe yana shafa sumarsa da ta ɗan jiƙe sama-sama bai ma san da Ni ba sai da ya matso kusa. Buɗe baki na yi da nufin gaida shi na ji ya ce "Can You Please excuse me?" Cikin sanyin jiki na ce "I'm sorry BB, don Allah ka yafe min, ban san me ya shiga kaina na aikata hakan ba, but I'm really sorry, don Allah..." "Nope, Kar ki damu, yanzu na san limit ɗina ai, na san yanzu ƙanwa ɗaya nake da ita a madadin da da nake tunanin su biyu ne" Yana gama faɗin haka ya raɓa Ni ya zauna bakin bed, Ni dai rasa abun da zan yi na yi, haka ya sa na sunkyar da kaina ƙasa, ina ji idanjwansa na yawo a kaina, kamar daga sama na ji ya ce "Kin zo ƙarasa Ni ne da abinci mai yaji bayan baƙin cikin da kika ƙunsa min Jannat?" Jiki na rawa na ce "A'a, a'a, wallahi ba haka ba ne BB, don Allah ka yi haƙuri" Ya ce "Shi ke nan, zan ci da yajin, zan kuma mutu sai ki ji daɗin yin rayuwa cikin salama tun da dama can Ni takura Miki nake" Kaina ƙasa na ce "Wallahi ba haka ba ne Ummi ce ta yi girkin ba Ni ba, abun da ya faru jiya was not intentional BB, don Allah take heart to forgive your..." Ya ce "Shhhh" ba musu na ja baki na yi shiru ya ce "Kar ki damu, kin nuna min ban isa da ke ba ai, Allah ya so ba a gaban saurayin naki kika min hakan ba, da na gama jin kunya ba shakka" Wallahi tsabar kunya kasa magana ma na yi, sai da ya yi shiru Na Sa hannuna na ciro wayata da ke kan tray na miƙa masa na ce "Ga shi ka yi haƙuri" BB ya girgiza kai ya ce "Ki riƙe abun ki, itama ki ce mata ta zo ta karɓi Tata, na daina takura muku, ku yi rayuwarku yadda kuka so" Kukan ƙarya na fara sanin cewa ba ya son kuka, ai kuwa yana jin ƙinƙishin kukan nawa ya juyl ya dube Ni "Kin ga, kar ki ƙara min wani ciwon, can You Please excuse me?" Ina kukan na ce "Don Allah BB, wallahi na yi regretting, it won't happen again in Sha Allah, Please forgive your..." "Not mine, kin nuna min I'm not...." "Wallahi sharrin shaiɗan ne" Abu kamar wasa sai kukan da nake ya koma na gaske, hankalinsa na ga ya tashi ya ce "Fine, fine, yi haƙuri ki tafi, komai ya wuce" Na ce "Then ka karɓi wayar" Ya ce "No go with it, maza je ki" ya ɗaga ni tare da nuna min ƙofa na fita. Bai san na ajiye wayar ba na tafi abuna, Lokacin da na koma Rafiat ma ta tashi, damar kam da kyar na shawo kan Rafi'at ta haƙura. Tun daga ranar nake ɗan kaffa-kaffa da yi wa BB rashin kunya, wa Ummi ya ba wa wayoyin namu ta na mu, kwana biyu BB ya ƙara Sannan ya koma Abuja. Wani abu da ban sani ba shi ne, duk wannan takura da izayar da BB ke min wai so na yake. Don da ya koma Abuja haka Ya Khalid ya saka shi gaba kan cewa ya bayyana ƙudirinsa gare Ni, amma ya yi banza da shi. Ya Khalid ya ce "Haba Friend, wallahi gara ka bayyana ƙudirinka before it's too late for you" BB ya lumshe ido ya ce "I'll never be late a inda nake fata K, beside na tabbatar itama tana so na ɗin" "Wa ya faɗa maka tana son ma bayan irin haɗe fuska da bugun da kake musu?" Ya ce "Ba sai na faɗa ba ai" Ya ce "Ya kamata dai ka furta mata tun yanzu Khalil, don wallahi yaran nan a tsorace suke da kai fa" Miƙewa zaune BB ya yi daga kwancen da yake yace "WHO told you?" Ya Khalid ya ɗage gira BB ya ce "I'm telling you Jannat ta fara raina Ni yanzu, ka san me ta min zuwan nan da na yi?" Ya Khalid ya girgiza kai, nan ya ba shi labarin rashin kunyar da na masa, Ya Khalid ya kwashe da dariya ya ce "Tab, ai dama abun da ake gudu ke nan, ka ga mutumina" Ya dafa ƙafaɗar BB "Yanzu ne ya dace ka bayyana RUFAFFIYAR AJIYAR da ke zuciyarka tun kafin lokaci ya ƙure maka" BB ya ce "Sai faman cewa kake lokaci ya ƙure min, lokaci ba zai taɓa ƙure min ba K " Ya Khalid ya girgiza kai cikin ƙoƙarin son ya fahimtar da BB ya ce "Ba ka fahimce Ni ba, ka ga Ni I'm expert in love related appears" BB ya ɗan ɗage gira yana ganin kamar wasa Ya Khalid ke masa. "I'm serious Khalil, su mata ba a musu haka ka san an ce mace Allura ce cikin ruwa..." "To Na ji, Ni dai na san ba yanzu ne lokacin da ya dace na tunkare ta da maganar nan ba in dai kuma ba wani rainin kake so na jawo wa kaina ba" Ya Khalid ya kwashe da dariya kafin ya ce "Wane raini kuma bayan kama son ta?" BB ya haɗe fuska sannan ya ce "Yarinta na damun Jannat ga kuma rawar kai, I'm sure in na yi exposing mata Sirrin nan, surely za ta raina Ni fiye da kima, Rafi'at kanta sai ta samu kafar yi min rashin kunya" Ya Khalid ya ce "Ba za ka gane ba, kai komai raini raini, to bari in faɗa maka iyayenmu mata suna da ƙananun shekaru iyayenmu maza suka aure su, su ba su yi zancen raini ba sai kai?" "To ai nasu generation ɗin daban, kana ganin yaran yanzu da shegen rawar kai?" Ya Khalid ya jinjina kai sannan ya ce "Ni ba ka faɗa min dalilin karɓar wayar tasu ma da ka yi ba fa" BB ya harare shi sannan ya ce "Zai wuce rawar kansu kuwa, ganinsu na yi wani guy ya tsayar da su a hanya, in ba da iskanci sai su kula shi kamar ba..." Ya khalid ya dakatar da shi yana dariya "To kar su kula shi ke nan? Kana ji, a wannan stage ɗin da dole ne a yi ta attacking ɗinsu, shi ya sa na ce maka ka gaggauta yin abun da ya dace wallahi in ba haka ba kana nan wani ya sace zuciyar Jannat..." Duka BB ya kai wa Ya Khalid yana harararsa ya ce "Kana faɗan alkhairi ko kuma ka yi shiru" Ya Khalid ya shafa kansa sannan ya ce "Ai Gaskiya na faɗa maka, idan har ba ka yi abun...." "Na ce maka ya isa haka don Allah, duk ka sa Ni na jigata da surutu" Ya Khalid ya ce "Akan Jannat kam ai ba ka gajiya da surutu har musu ka iya, da dai a ce wata maganar ne ko zan mutu ina maka magana ba za ka taɓa biye Ni mu yi ta a mutumce ba sai ka ƙona min rai da miskilanci" BB ya ja tsaki, ya Khalid ya yi dariya sannan ya ce "Mood swapping sunan wani condition, yanzu dai an ɗauke Khalil ɗin Jannat an ajiye Captain Ibrahim Abubakar Shirama" BB Bai kula shi ba, shi ma sai ya miƙe ya bar kishi ɗakin. BB da ya Khalid jininsu ya samu jituwa ne tun da suka tafi karatu bayan samun gurbi a hukumar sojojin ƙasa, da fari BB Bai ba wa Ya khalil shiga rayuwarsa ba duk yadda shi ɗin ya so hakan har sai da wata rana suna Canada Ya haɗa shi da Mami da Abbansu, su suka ƙara ƙarfafa alaƙar bayan damƙa amanar Ya Khalid ɗin a hannun BB, wanann dalilin ya sa wasu lokutan idan Ya Khalid zai ishi BB da surutu sai ka ji ya ce "Ɗan'amana zan faɗawa su Mami fa" To duk irin shaƙiyyyanci da ya so yi BB na faɗa masa haka zai haƙura kasancewar shi Allah ya yi shi mutum mai raha da don mutane kamar ba soja ba, in ka ga yadda yake dariya kai ka ce me, amma da yake alaƙar tasu haɗin Allah ce tuni ta yi ƙargo har wasu lokutan shima BB in Yana video call da Ummi ko Mommy ko kuma Abuya ko Daddy yakan haɗa su su gaisa, har yanzu da nake faɗa muku ba su taɓa kallon Ya Khalid a zahiri ba, amma dai Mami da Abban Ya Khalid sun san BB tsaf tun ranar da suka dawo Nigeria, yanzu haka a gidansu Ya Khalid BB ke zaune instead of barrack, duk da cewa shi hakan ya so Mami da Abba suka ce ba su san zancen ba, har godiya su Ummi suka yi wa su Mami tare da alƙawarin za su zo in sha Allah. BB ba shi da matsala da kowa a gidan daga Mami har Abba, haka kuma younger sis ɗin Ya Khalid, Nimrah, ita ma tana girmama BB sosai don ita ma dai ba za ta wuce sa'ar mu ba, Big Sis ɗin Ya Khalid kuwa ba a magana, yadda take ji da BB ma yanzu ba ta ji da ƙanin nata itama gidanta a nan Abuja yake, unguwar Maitama, mijinta na da kuɗi sosai, yaranta biyu, Sophie da Mufeed, yara masu shiga rai da son mutane, lokuta da dama Big Sis (Safinatu) kan gayyaci ƙannen nata cin abincin dare gidanta, and to be sincere, she's very kind, BB finds her very amazing to be part of his life. Sakamakon WAEC ne ya fara fitowa, gaba ɗaya results ɗinmu sun yi kyau, cikin farin ciki Rafi'at ta kira BB ta faɗa masa, ya sa ta yi snapping ta tura masa a Whatsapp, abun mamaki sai ga voicd note ɗinsa yana faɗin "Ma sha Allah mu sisters, you did well, Allah ya sa albarka, ban da kula samari kun ji, Where's Jannat? Make sure that Kin ba ta ta ji, sannan in an yi fixing date ɗin Speech and price giving day ɗinku you guys should inform me ok?" *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 11: Mamaki sosai muka yi jin yadda ya yi wannan dogon bayanin kuma cikin sassanyar murya babu wannan ƙuncin nan, da alamu dai ya yafe min abun da na yi masa nima. Tsakanina da Rafi'at sai son Barka, sati guda da fitowar WAEC result, Neco result ma ya fito, aka kira mu daga makaranta kamar yadda aka yi a lokacin da WAEC yi ta fito, bayan an cirewa kowa aka ba shi copy ɗaɗɗaya, daga nan aka ce za a nemo mu batun shirye-shiryen sauƙa da Speech kamar yadda makarantar ke shiryawa, sosai iyayenmu suka yi farin ciki da sakamakon da muka samu, daga nan suka fara tunanin abun yi, a son ran Abuya dai mu fitar da mazaje ne a mana aure, Ummi ma ba ta da matsala da hakan, amma kuma Daddy na son mu yi karatu gaskiya, ko da suka zauna a junansu wata rana da muka je Jama'are gidan Kaka sun samar da matsayar a ba mu dama mu kawo mazaje in Babu sai mu fara makarantar gaba da sakandare, idan mijin ya zo ko muna farawa ne to ba makawa za a aurar da mu, tun da muka ji wannan bayani kowaccenmu ta ce ai ba ta da saurayi, Daddy ya ce shi ke nan za a nema mana admission Amma bai ce a kaza ba. Ɓangaren BB haka ya ci gaba da dakon soyayyata yayin da ya ci gaba da ɓoye ta ba tare da ya bayyana min ba, bayan zuciyarshi da kuma Big Sis sai Ya Khalid ne kaɗai suka san da wannan babban sirri, hatta su Mommy da Ummi babu wanda ya sani. Watan Oktoba aka saka ranar Speech and prize giving day ɗinmu da kuma memorization Walimah ɗinmu, ba mu yi nauyin baki ba muka samar da BB ta wayar Rafiat don Ni dai ba Ni da ko da numbern shi bare kuma na kira shi, ya tambayi exact date muka sanar mishi. A week to the graduation BB da Ya Khalid suka dira a Azare, Tarba ta musamman suka samu wurin Ummi, muka taya ta shirya musu abinciccika iri-iri har nake mamakin yawan abincin, ashe saboda zuwan Ya Khalid ɗin ne. A mutunce maka gaisa da BB fuskarsa babu yabo ba fallasa yayin da Ya khalid kuma ya amsa mana a sake har yana tambayan wace ce Jannat cikinmu, wani iri na ji, na ce hala dai ba BB ya ba shi labarin rashin kunyar da na mishi ba ne yake son ganina, a sukwane na bi Rafi'at muka koma part ɗin Mommy. A tunanina kwana biyu BB zai yi ganin da baƙo suke, sai na ga sun zarce hakan, bamu ji wata magana daga wurin BB na game da shirin da muke, mu dai ba abun da muke shiryawa, haka ma iyayenmu mata, ana saura kwana biyu Speech and prize giving day BB ya samu shiryawar ba zata, a tare da shi da kuma Ya Khalid, sannan Ni da Rafi'at ya ɗauke mu ya kai mu wani katafaren wurin gyaran jiki, abun mamaki kuma ya ce a mana duk wani abu da ya kamata sannan ya ce In an gama se should let him know ya zo ya yi settling bills sai ya mayar da mu gida. Banbaraƙwai, wai namiji da suna Hajara, mace da suna isa, wallahi sosai muka sha mamaki har sai da muka tattauna a tsakaninmu, nikam abun da ya zo raina ma na yi tunanin Ya Khalid ɗin ya yaba da wata a cikinmu ne, Ni dai addu'a ta Allah ya sa Ni ce Don kuwa ya yi min, yana da dukkan siffofin mijin da nake so, tun daga kyau, thought ko kama ƙafar BB Bai yi ba a wannan fagen, kuɗi ma sha Allah don na tabbata shi zai biya wannan ɗawainiyar ma, uwa uba fara'a Da faran-faran daga gani goga ne da zai iya fafatawa a fagen soyayya irin ta bugawa a jaridar nan. Ni dai da wannan tunani da hasashen cikin raina aka mana gyaran gashi, sai da ba a kitse shi ba, an mana both Jan lalle da baƙi bayan an wanke mana ƙafafu da hannayenmu da yanzu ke da wani irin sihirtaccen taushi da kuma laushi. Kusan ƙarfe biyu aka gama mana, Rafi'at ta kira BB ta sanar da shi, suka zo suka ɗauke mu tare, hakan ya ƙara tabbatar min da zargi na, cewa Ya Khalid na son ɗayarmu, dole ma ba da himma don ganin na samu wannan dama tun da ita Rafi'at already Ya Sadiq na sonta. Abun mamaki BB sai gwaɗa lallen namu yake a hanya though ban ma tunanin ya gani ma, ga shi kuma ya sake mana fuska kaɗan har da yin dariya, Ni kam sai na ji abun banbaraƙwai don ba sabun ba ne, wai tinkiya da gilashi, kafin mu koma gida sai da muka biya ta wani Bakery, BB da Ya khalid suka shiga suka ce Mu jira su, bayan sun dawo muka ƙarasa gida, Ummi da Mommy suka yi ta saka masa albarka, Ni dai na ja bakina na tsuke ban ce ba shi ya biya kuɗin ba Ya Khalid ne, ashe Gara da ban faɗa ɗin ba shi ɗin ne ya biya. Washe gari ba mu je ko ina, though da mun tambayi Ummi Driver ya kai mu gidansu wata ƙawarmu Amina Zubair Mu tambayo ta me da me yake shiryawa muma mu dawo a mana, Ummu ta ƙi amincewa, saboda haka muka haƙura tare da zubawa sarautar Allah idanuwa. Daren ranar wani zumuɗi muke ji, haka muka yi ta surutu ba mu yi Bacci ba har wuraren asuba, Ganin haka ya sa muna yin salla muka yi wanka, na ɗauko kaya zan saka Rafi'at ta dube Ni ta ce "Ke lafiyarki?" Na ce "Me kika ga?" Ta janye kayan daga gabana ta mayar da su closet "Tsabar zumuɗi ne za ki saka kaya tun yanzu? To ba za ki sa ba" Babu yadda na iya sai da muka yi breakfast tukunna, nan ma ta ce ba zan saka ba sai 8:00 ta cika, sai da ta cika ya bar Ni, muka shirya cikin sabuwar atamfar mu da Mommy ta ɗinka mana. Da mun so bin motar Baba Driver ne, sai da ga mamakinmu BB da abokinsa sun hakimce cikin wata sabuwar motarsa da ba na ce Ga ranar da ya saya ba, ƙarasawa muka yi muka gaida su, Ya Khalid ya ce Mu shiga tare da mu tafi, su Mommy za su biyo su Daddy, ba musu muka shiga, tun da motarmu ta shiga cikin makaranta idanuwa suka yi kanmu, bayan ya paka a wurin da aka tanada domin ajiye motoci muka fito, na nuna musu canopy ɗin guests, suka zazzauna, muma muka nufi sashen da aka tanada dominmu. Muna isa ƙawayenmu suka fara murnar ganinmu suna yaba kyan da muka yi, musamman Ni da kalar Hijab ɗin namu ya haska sosai, kafin ka ce me mutane sun zozzo, manyan baƙi sun zauna a rumfarsu, organizers tuni sun daidaita komai ana jiran ƙarfe takwas da rabi ta cika a fara komai. A ƙa'idar taro a makarantarmu, ana buɗe shi ne da opening recitation daga students ɗaya namiji ɗaya mace sannan a yi national anthem, sauƙa ita ce agenda ta farko da za a fara. Nan aka jera mu ɗaya bayan ɗaya mata na fuskantar maza, sannan aka bayar da amsa ƙuwwa guda biyu wa mata biyu wa maza, cikin ƙwarewa da kuma bayarwa harrufa haƙƙoƙinsu Malam Misbahu ya fara yi mana ja a cikin Alqur'ani muka ɗauka muka yi, can ya dakatar da mu ya mana sabon ja, shi ma muka yi shi, ja biyar ya mana, na shidan kuma ya ja mana surorin ƙarshe na Alqur'ani, daga ahad zuwa ƙasa, nan kam haɗa baki muka yi tare da shi har muka kai -Minal jinnati wannas!" Nan wasu daga cikinmu suka fashe da kukan farin ciki, ciki kuwa har da Ni, bayan an kammala sauƙa aka ba wa kowaccenmu certificate na shaidar ta haddace Alqur'ani tukuna muka koma wurin zaman mu. Taro ne aka yi mai ƙayatarwa, mun kuma ji daɗin yadda ya tafi a nutse babu hanyaniya, manyar mutane sun yi Speech kala-kala masu muhimmanci da taɓa zuciya, haka hukumomin tsaro, ɗaliban primary section sun yi drama, presentations and debates also by students, sai kuma farewell speech da head boy ya yi sannan aka kira sunana a matsayin headgirl nima na yi. Bayan mun kammala da wannan sashen aka ba mu prefectship certificate, daga nan aka fara raba kyaututtuka. An shafe awa guda a wannan sashen daga bisani aka kammala aka dawo sashen outgoing students, kyaututtuka huɗu na karɓa, Rafi'at shida, na karɓi kyautar best in Qur'an, best in mathematics, best in Chemistry da kuma best in Agriculture yayin da Rafi'at ta karɓi kyautar best in History, most obedient student, most punctual student, da kuma best in Government da geography. Kusan duka kyaututtukan mu muka kwashe su, hakan ya matuƙar sanya iyayenmu alfahari, a haka aka kammala taro lafiya, aka fara daukar hotuna, BB ya kira wayar Rafi'at ya ce ta kira Ni, ga mamakina hotuna wai za mu ɗauka, hotuna a tare da BB da sauran mutanen gidanmu, hotuna sosai aka cire mana masu kyau daga nan BB ya faki idonmu ya yi wani wajen, ashe zuwa ya yi ya karɓi details ɗin malamin da ya sauƙar da mu da kuma asusun makaranta, yana dawowa muka tafi gida. Yana ajiye mu ya ƙara fita, da yamma muka shirya domin zuwa walimar da makaranta ta shirya mana, bayan an kammala jawabai aka fara raba souvenirs, mu kam babu abun da muka yi, muka ja gefe abun mu, muna tsaye wayar Rafiat ta fara ringing, tana dubawa ta ce "Ke BB ne" na ce "Don Allah?" Ta gyaɗa kai tare da ɗaga wayar ta kara a kunnenta, ban san me yace mata ba sai gani na yi ta washe baki tare da daka tsalle ta ce "To ga mu nan zuwa" tana sauƙe wayar ta ce "Ke ki zo mu je, Allah ya sa wani abun su Ummi suka bayar ya kawo mana, gaba ɗaya sai yanzu na ji dama mun karɓi kuɗi wurin Daddy mun yi hidimar mu" Na ce "Mu je dai yanzu kam" Muka fita, a gefe can muka hango motarsa, ta can baya yake jingine da motar ya yi kyau abunsa, muna isa Ya Khalid ya fito sannan ya ce "A'a, ƴan gatan BB kin iso ke nan?".na kalle shi na jinjina kai cikin raina na ce, ba ka san ƴar tsamar da ke tsakaninmu ba. Boot ya buɗe mana, ya nuna mana Boot ɗin da hannunsa, waro idanuwana na yi saboda mamaki ban san lokacin da na ce "Dukka wannan ɗin miye?" BB ya amsa da "Idon matambayi, malamai in za ku ɗauka ku ɗauka in ba ku so kuma na shiga na kira ƙawayenku na ba su kyauta" Ai bai rufe baki ba muka sa hannu don mu janyo buhuhhuna guda biyun da ke ciki but ba mu da ƙarfin hakan, ya Khalid ya ƙaraso ya ce "Kada ku damu, mu je za mu shigo muku da su" BB ya harare shi ya ce "Mu ɗin bayinsu ne?" Ina ji Ya Khalid ya ce "To ai watarana hakan ne, haba babban yaya " Wata irin murna na ji ta kama Ni, na ta'allaƙa hakan ne Ni kuma da kalaman Ya Khalid na watarana hakan ne, ke nan da gaske yana son ɗaya daga cikinmu, a yanzu fatana shi ne Allah ya sa na zamto wannan mai Sa'a, ya kuma sa ya furta min wanann abu a yau ɗin nan. Wannan shi ake kira da neman nema, shi BB yana nan yan dakon soyayyata Ni kuma ina nan ina dakon ta abokinsa. Har ciki suka shiga mana da kayan, ƙawayenmu da ke rabo suka ƙaraso suna gaida su duk da ba su san matsayinsu wurinmu ba, kowacce sai wani maƙale murya take, hakan ya ban haushi tare da fatan Allah sa dai ba wacce ta burge Ya Khalid cikinsu, suna ajiyewa suka juya, nan muka hau rabo muma, kaya ne sosai BB ya sa aka mana, souvenirs masu aji, kowacce jaka akwai sallaya, hisnul Muslim, counter, callender, mug, meme da kuma biro mai ɗauke da sunanmu sai kuma wata takeway rubber da aka saka half chicken, doughnuts biyu cake ɗaya da puff² biyu, sai lemon jarka guda. Lallai dole mu jinjinawa Babban Yaya, yau kam ya nuna mana cewa shi ɗin babban yayanmu ne, don ya fitar da mu kunya, hotuna muka dauka bayan kammala rabo mazanmu da matanmu coz wannan me dama ta farko da makaranta ta ba mu na yin hakan a tare da Opposite classmates ɗin namu. Sai da aka fara kiraye-kirayen sallar magrib muka fito, alhamdulillah mun samu mai keke ba ɓata lokaci muka shige abunmu sai gida, a hanya BB ya kira Rafi'at yana tambayarta muna ina? Ta ce masa mun kusa isowa ya ce shi ke nan ya kashe kiran. Muna komawa gida wanka muka yi muka sauya kaya sannan muka yi salla, daga nan muka nufi part ɗin Ummi kasancewar Kaka ma na can, ana ta taɗi sai albarka kaka ke saka mana. A can ɓangaren BB tun da suka koma daga kai mana souvenirs Ya Khalid ke takurawa BB kan ya fitar da sirrin zuciyarsa a wannan rana yayin da BB ya ce shi sam bai san zancen nan ba, ai zan raina shi, yanzu ma ya aka kaya, shi dai zai ƙara haƙuri na ƙara hankali tukun na. Cike da takaicinsa ya khalid ɗin ya dube shi ya ce "Wallahi ka mugun ba Ni mamaki Khalil, wai kai ba ka tunanin mai zai je ya dawo ne?" BB ya ƙi kula shi, cikin ɓacin rai ya ce "Wallahi ina jiye maka kada wani ya maka shigar sauri, wallahi in ta kamu da son wani babu abun da ka isa ka yi, don na tabbata Daddy ba zai taɓa bari a takura ta ta so ka ba wai don kana ɗan'uwanta" BB ya juyo ya Kalli Ya Khalid ya ce "Ni na san ba kuskure a cikin shirina K, na tabbatar maka cewa, Jannat tawa ce duk wuya duk rintsi, she'll forever be mine, mine alone! Kuskurenta ne kuma ta ƙi karɓa ta a matsayin miji, amma dai na san ita ɗin matata ce, kuma in Sha Allah hakan za ta tabbata" "Ina fatan hakan, shi ya sa nake nuna maka illar jinkiri wurin fitar da sirrin zuciyarsa, hakan kuskure ne babba " BB ya lumshe idanuwansa sannan ya ce "Allah ya zaɓa mana mafi alheri" daga nan bai kuma ƙara cewa komai ba. A namu ɓangaren da wuri muka yi bacci saboda gajiya, washe gari da misalin ƙarfe goma muka taru a part ɗin Mommy, da Ni da Rafi'at, BB da Ya khalid, Mommy day Ummi, Daddy da Abuya da kuma Hajiya Kaka. Tattaunawa aka yi amma an fi karkata wurin nuna mana muhimmanci aure a wannan gaɓar, la'alla don Abuya ne ke bayanin, don da Daddy ne yanzu batun boko zai kawo, ai kuwa bayan ya karɓi jawabin batun da ya yi magana kansa ƙarshe shi ne karatunmu, ya yanke shawarar nema min admission a school of nursing, ita kuma Rafi'at ta je ta yi change of institution ta yi Bsc Economics, ba ta ji daɗin hakan ba amma babu yadda ta iya, haka ta amince, washe gari BB da kansa ya kai ta café aka mata change of institution zuwa Aminu Sale College of Education Azare, ya biya ya siya min Form ɗin Basic Midwifery a Adamu Adamu College of Nursing Sciences, Azare, sai dai ya samu bayanin cewa sai December suke fara sayar da fork ɗin Midwifery. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 12: Two months BB ya yi sannan ya dawo kuma takanas saboda mu ya dawo, ai kuwa lokacin an fara sayar da fork ɗin Midwifery ya siyo da kansa bayan ya kai Rafi'at ta yi online screening a ASCOE azare. Bayan sun dawo gida aka cike min Form aka yi submitting, ranar da za a yi entrance exams BB ya koma, Driver ne ya kai Ni, bayan na gama ya dawo da Ni. Bayan kwana biyu aka kira Ni aka ce na ci wannan sashen, za mu je mu yi oral interview, zo ku ga farin ciki akan fuskata, a ranar da kaina na karɓi numbern BB na sanar da shi, ya taya Ni kurma ya kuma min fatan Allah ya ba Ni sa'ar cin oral interview ɗinma. Yana sauƙe wayarsa Ya Khalid ya dube shi ya ce "Irin wannan farin ciki haka Babban Yaya?" BB ya ɗan harare shi kana ya ce "Jannat passed the first step, yanzu za su yi oral interview" Ya Khalid ya ɗan kwaɓe fuska ya ce "Khalil" BB ya dube shi Ya ce "Har yanzu ba ka ganin abun da nake gane maka ko?" BB ya ce "Me ke nan?" "Yanzu ka yarda ta tafi Makaranta kafin ka furta mata muradinka?" BB ya ɗage kafaɗa, Ya Khalid ya ce "Try to understand my friend, wallahi akwai illa sosai hakan, za ta yi interacting da mutane daban daban, You know how special she's, Ba abu mai wahala ba ne wasu mazan su yi ƙoƙarin samun kusanci da ita ba..." "Na yarda da ita" BB ya faɗa a gajarce. Ya Khalid ya ce "Fine, idan kai ba ka san ina ke maka ciwo ba Ni zan kira ta na faɗa mata komai" Da wani irin sauri BB ya miƙe yana bin Ya Khalid da wani irin kallo, ya Khalid ya kashe masa ido sannan ya ce "Ya dai?" BB ya wani kwaɓe fuska ya ce "A beg friend, don't spoil this fun, In Sha Allah wani juyin da za Ni sai na mata maganar ko?" Ya Khalid ya ce "To, Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri" BB ya amsa da "Amin". Ranar oral interview Rafi'at ta raka Ni, muka shiga layin waɗanda za a yi wa interview ɗin, har aka tantance mu na bar Rafi'at a reception, muka shiga, kasancewar ina cikin mutane na farko da aka fara yi wa da wuri na fito, na nemo Rafi'at muka wuce guda tun da dama Ba Driver na jiranmu. Washe gari ita ma na raka ta ta yi physical screening daga nan muka dawo gida. Yau Laraba tun da na tashi jikina ke min ciwo hakan ya sa ban fita ko ina ba ina kwance, A yanzu dai ba na ce komai ba dangane da BB, ba na jin haushinsa kuma ba na jin sonsa amma dai abu ɗaya da na sani shi ne, yana da matsayi na musamman a cikin rayuwata kuma ina girmama hakan cikin raina, har yau ban cire tsammanin kira daga Ya Khalid ba, sai dai ganin shirun ya yi yawa ya sa na fara ba wa zuciyata haƙuri tare da tunanin hala Rafi'at yake so, kuma ya faɗa mata ta ce tana da wanda take so. Tsaki na ja na ƙara jan bargo na lulluɓe, ƙarar shigowar saƙo na ji a wayata, hakan ya sa na laluɓo ta, baƙuwar number be, har zan ajiye wayar sai kuma na shiga saƙon, me zan gani "congratulations, Dear Jannatul-Firdaus, you've been offered an admission in to Adamu Adamu College of nursing sciences...." Ko ƙarasa karantawa ban yi ba na cilla wani ihun murna, Rafi'at ta shigo a ɗan kiɗime."lafiya Jannat?" Na mika mata wayar na ce "Ki ga, ki ga, na samu admission ɗin" Itama ihun ta ɗan yi tare da rungume Ni tana faɗin "Congratulations, Allah ya sa albarka, mu je mu faɗawa su Mommy" Nan muka ɗunguma muka je muka nuna ma Mommy sannan Ummi, addu'a da fatan alkhairi suka yi min, na dawo na yi forwarding message ɗin wa BB. Bai kira Ni ba sai dare, na masa uzurin aikinsu, ɗagawa na yi na gaida shi a mutunce, ya ce "Ma sha Allah, I've seen your message" Na ce "uhmm" Ya ce "Congratulations, Allah ya sa albarka" Na ce "Amiin" Ya ce "Gobe sa ki karbi admission letter ɗin, ki yi snapping ki tura min sai na tura wa Ummi kuɗin ta ba mu Atm card ɗinta ki ciro ki yi registration ɗin" "Na gode na..." "Ya isa, ina da abun yi." Yana faɗin haka ya katse kiran, wayar na bi da kallo na ce "oh, mutum sai shegen faɗin rai kamar wani ƙaramin mutum" Washe gari Baba Driver ya kai Ni na karɓo admission letter na, muna dawowa na yi snapping na tura masa. Washe gari Ummi ta kira Ni sashenta, da na je ta miƙa min atm card ɗinta ta ce "Yayanku ne ya ce a ba ki, ya tura 250k a ciki na registration da sauran abubuwan da za ki yi" Na karɓa na ce "Allah ya saka da alkhairi " ta amsa da "Amin" Har na tashi zan fita Ummi ta ce "Dawo ki zauna nan jannat" na dawo wurin data nuna min Shiru ta yi can ta ce "Kina ji na Jannat?" Na jinjina kai, ta ce "Ni na haife ki Jannat, ina kuma so yau na tunatar da ke wani abu game da rayuwa" Ta ɗan yi shiru sannan ta ci gaba "Kin ga Khalil ko?" Na gyada kai "Ba Ni na haife shi ba, amma dai ina jinsa a jikina fiye da ɗan da na haifa ba don komai ba sai don yadda yake mutunta Ni yake kuma ba Ni girma, yake so na yake son ƴaƴana, kin ga tun da nake da Khalil bai taɓa saɓa umarnina ba, bai taɓa yin musu da wani hukuncina ba, ko kuma a zo batun rashin ɗa'a, bai taɓa ƙin ba Ni matsayin mahaifiya ba, yadda yake yi wa ƙannensa hidima haka yake wa ƴaƴana, kin ga Mommy, Mommy ba ta taɓa nuna rashin jin daɗinta ga yadda muke da shi ba, saɓanin wasu matan da za su iya tunanin ko mallake shi na yi ta hanyar asiri, Mommy mutuniyar kirki ce, haka Daddy, Ina da tabbacin halin dattakon Khalil daga wurinsu ya koya." Ni dai shiru ba yi ina sauraron Ummi tare da tunanin ina maganganun nata suka dosa. "A duniyar nan ba ki da tamkar Khalil Jannat, Ko bayan ranmu Ni da Abuya, ina da tabbacin zai ci gaba da kulawa da ke kamar yadda yake yi a yanzu haka Mommy, na tabbatar ko bayan raina za ta ci gaba da ba ki kulawa a matsayin mahaifiya." Ummi ta numfasa, Ni dai zuwa yanzu kalaman Ummi sun fara ba Ni tsoro, sai ka ce mai bayar da wasiyya? Na faɗi hakan cikin raina. "Jannat, ina gargaɗinki kuma ina mai ba ki umarni, ko bayan raina kada ki kuskura ki ce za ki saɓawa mutane masu karamcin nan, saɓa musu kamar saɓa min ne biyayya gare su kamar yi min biyayya ne" Kalaman Ummi sun taɓa rauna ainun sai da ƙwalla ta zubo daga idanuwa, Ummi ta ce "Kina ji na ko?" Na ce "E Ummi" Ta ce "To, Allah ya miki albarka ya sa wa karatun da za ki yi albarka, ki tabbatar kin kira shi kuma kin masa godiya" na ce "To Ummi " "Za ki iya tafiya " Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na miƙe na koma part ɗin Mommy Ina ta nanata kalaman Ummi cikin raina. Wanka muka yi muka fita tare da Rafi'at, ba Driver ya ajiye mu muka ciri cash sannan muka tafi AACNS, tas muka gama registration muka zauna jiran Baba Driver da ya fito siyo stationaries, yana dawowa muka yi submitting na yi signing, daga nan na tambayi wani mutumi da ban da waye shi ba when za mu fara zuwa, ya ce "in the next two weeks" na jinjina kai daga nan na karɓi tai sets na uniform muka taho, a hanya muka tsaya na sayi hard cover Notebook manta, da kuma school bag rinɗimemiya, Rafi'at sai dariya yake min wai wannan jakar ai za a iya jefa mutum a ciki. Da haka muka koma gida duk na ƙagu da mu fara zuwa jami'a, a wannan ranar ce wani abun farin cikin ya ƙara riskarmu, itama Rafi'at ta samu admission, itama dai cikin satin muka je ga yi registration bayan BB ya Turo kuɗin, ranar Monday muka je Branch na FCMB muka buɗe account aka mana atm kamar yadda BB ya ce Mu yi. Alhamdulillah rabbil alamin! Dukkan godiya da jinjina ga mahalicci suke, kuma duk wani mataki na rayuwa da bawa zai taka sai da sahalewarsa, ina cikin farin ciki a yanzu, walwala kuwa ba a magana, a yanzu dai ba Ni da wata damuwa da ta wuce na fara karatuna, batun wani ƙalubalen rayuwa har yanzu Ni Jannat ba na ce na sani ba, abun da ban sani ba shi ne, fara karatuna shi ne zai fara buɗe min wasu muhimman darussa na rayuwa da ban san su ba a baya. Satin da muka fara zuwa makaranta aka mana orientation, bayan kwana uku muka fara lectures, alhamdulillah kawai zan ce, ina fahimta sosai, da na dawo gida kuma zan ƙara bitar abun da aka mana a makaranta, hakan ya sa har abokan karatu da lecturers ɗinmu sun fara fahimtar ƙwazo da basirata, hakan ya sa aka naɗa class Rep. Sati ma biyu Rafi'at ma ta fara zuwa lectures, tare muke fitowa tun 6am saboda samun front seats, da abinci muke fitowa da kuma isassun kuɗi don BB ya saka mana 50k each a account ɗinmu, su Rafi'at 3pm suke gama lectures mu kuma 3:30pm, idan sun tashi sai Baba Driver ya ɗauko ta ya biyo ta school ɗinmu by that time muma min tashi. A yanzu ba mu da wani tunani da ya wuce n karatu, duk da Ya Sadiq yanzu damun Rafi'at yake kan ta bar shi ya sanar da su Abuya alaƙar da ke tsakaninsu amma a ta ƙi, a cewarta sai nima na samu wanda muka daidaita tukun. Ranar wata juma'a mun gama first period lectures ɗinmu na fito don siyan wani abu na ci saboda yunwar da nake ji, ina cikin tafiya don zuwa shagon Mukhtar, wanda ke kusa da area class ɗinmu, karo muka ci da wani senior ɗinmu da ke ND nursing, da sauri na ja Baya ina faɗin "I'm sorry please" Ya wuce na wuce ba tare da ya ce komai ba, bayan na koma class wata colleague ɗina Hamra wacce kusan tare ma muke karatu da ita kuma muna yawan zama seat ɗaya da ita ta zo gefena ta ce "Shirama guess something" na ce "wetin?" Ta ce " Yanzu na ji ana gurmin wai kin ci karo da Abbas Hashim Toro" na ce "ban gane ba" Ta ce "To ai yanzu ma an tura a Whatsapp group abun da ke trending yanzu ke nan" Na ce "kamar ya, Ni fa ban fahimce ki ba" Ta gyara zamanta Sannan ta ce "Abbas Toro shima student be, yana HND nursing ne, set 1, na ji maryam saddiqa na cewa tun kafin ta shigo school ɗin nan take jin labarinsa wurin yayarta" Na ce "ikon Allah" "E, an ce guy ɗin is fine, shi yasa yake da rashin mutuncin, he's arrogant, ga masifar wulaƙanci" Cike da ƙosawa da zancen nata na ce "Hamra Please, can You excuse me in ci gaba da kwafan note ɗina?" Ta ce "To ai ban faɗa miki abun da na zo faɗa miki ba, ki ga" ta nuna min wayarta, idanuwa na saka don ganin mene ne, hotona ne da nasa lokacin da muka ci karo, da Caption ɗin "Finally Mrs. Arrogant was taken" Na ce "Waye wannan ɗin ya dauki hoton har da turawa a group?" "Wallahi ban san waye ba, kin san channel ne kuma ban san su waye ke da ita ba" Cikin halin ko in kula na ce "Allah ya kyauta" sannan na ci gaba da kwafan note ɗina. Ina gani mutane na shigowa time to time su kalleni sai su fita, a haka har lokacin break ya ƙare, bayan gama second lectures muka yi closing, Baba Driver ya yi picking ɗina saboda yau Ni kaɗai ce Rafi'at ba ta da lectures. Tun da na fito ake ta nuna Ni amma na kafse kamar ban san suna yi ba na nufi motar gidanmu na shige ciki, wani abu da ba su sani ba Ni ba Ni da lokacinsu, karatu ne ya kawo Ni kuma shi na zo yi, hatta Whatsapp group iya official group nake shiga wanda akwai lecturers a ciki kuma ta ciki ake tura mana note, don haka duk wani abu da suke ma Ni ban san ana yi ba. Ranar Monday da na koma makaranta ma haka aka yi ta nuna Ni ana ƙus³ Ni kuwa ina ruwana, sai na ƙara yi kamar ban gansu ba, saboda yadda ake nuna Ni ya sa ko fita waje ma ban yi ba, Allah ta taimake Ni na taho da ruwa, ko dana ci abinci na sha ruwa da lokacin sallar azahar na fita, shima cikin zugar ƴan class ɗinmu na fita. Bayan na yi salla class na dawo, Ni kaɗai ce sauran duk suna waje, ina zaune na yi shiru ina tunanin rayuwa tare da fatan Ubangiji ya yi wa rayuwata albarka. Tsayuwar mutum na ji a kaina, babu shiri na ɗago, ban gane shi ba, kasancewar ko ranar da muka yi karo ban ga fuskarsa ba haƙuri kawai na ba shi na wuce. Ban ce uffan ba sai ma kwantar da kaina da na yi akan desk na juya masa baya. Hayaniyar dana fara ji ne ya sa na ɗago da sauri, colleagues ɗina sun shisshigo ajin, shi kuwa har lokacin yana tsaye a wurin. Dakewa na yi na dube shi na ce "Mallam lafiya ka min tsaye a ka? Ko na ci bashinka ne?" Mutanen da ke ajin suka saka ihu, ya murmusa tare da zagayowar ta ɗaya barin ya zauna a wurin zaman Hamra fuskarsa ɗauke da Murmushi, ai babu shiri na miƙe don rabona da zama kusa da namiji haka tun ina dolphin Maria college. Ihu aka ƙara sakawa a ajin Ni kuwa na fice har sai da na ga Nurse. Salim sai shigo na dawo, haka ta sa dole Abbas ficewa, kowa ya koma mazauninsa aka ci gaba da gulma. Yanzu kam abun ya ɗan dame Ni, I'm not ready for any relationship now, karatu na zo, don haka ba zai yiwu a ɓata min shiri na ba, don haka na ƙudiri aniyar Duk ranar da guy ɗin nan ya kuma zuwa inda nake zan yi casting ɗinsa sai ya rasa wannan class ɗin da ya samu a AACNS. In ban da ma iskanci babba da shi ya zo yana yin irin abubuwan nan? *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 13: Ai kuwa ranar nan na ƙara ganinsa a kaina ina zaune a cool down, sai dai sa'ar da ya samu Ni ɗaya ce a wurin, a gefena ya zauna, na ɗago da niyyar yi mishi rashin mutuncin sai na kasa, ya dube Ni ya ce "Da alama ba ki san Ni ba ko?" Na ce "e" Ya ce "I'm Abbas Hashim Toro, popularly known as Abbas Toro, Ina HNd class, kina wani avoiding dina after all Ni senior ɗinki me, I deserve some respect, Abi?" Ban ce komai ba, yace "Fine, ba wani abu ya sa nake son Miki magana ba, I'm here just to earn the certificate, already Ina aikina a Companyn Daddyna, and na ji an ce you're SS (Kamar yadda muke faɗa, serious student) shi ya sa na ce zan taimaka Miki with tutorials a duk wani course da ke miki wahala" jikina ne ya yi sanyi na ce "Thank you, I'm very sorry for the other day, ban kyauta ba" ya yi Murmushi ya ce "Don't worry, I'm Abbas, and u?" Ya miƙo min hannu alamun mu gaisa, na girgiza masa kai ina Murmushi na ce "I'm Jannat, jannatul Firdaus" Ya ce "wow! What a nice name" Na ce "thank you" Tun daga wannan rana muke mutunci da Abbas Toro, mutane har mamaki suke idan suka ga yadda yake mu'amalanta ta, wasu kuma da suka jima suna son samun irin damar sai kushe Ni suke suna faɗin albarkacin bakinsu, sosai muka dinke abun mu, yana min tutorials akan FON (Foundation of nursing) da kuma Anatomy and physiology, and alhamdulillah, hakan yana taimaka min sosai, a haka muka cinye watanni uku a academic block, aka yi posting ɗinmu hospital for clinical experience. Sunana ya faɗo cikin waɗanda za su yi posting ɗinsu ne a orthopedic ward, na yi farin ciki sosai kasancewar shi a orthopedic ward a old site yake. Ina dawowa gida ranar da list ɗin nan ya fito na tarar BB ya zo gida, amma an ce ya tafi gidan Hajiya Dada, hakan ya sa ban samu ganinsa ba sai washe gari asabat da yamma da ya dawo, na gaishe shi ya amsa fuskarsa babu yabo ba fallasa, ya tambaye Ni ya karatu na ce masa "Alhamdulillah" ya ce "Best wishes of luck" na ce "Thank you". Har na tashi zan tafi ya ce "An ce course ɗinku ba maza" na gyaɗa kai ya ce "Fine, ban da kula samari dai, har yanzu You guys are too young ki fara kula samari, idan lokaci ya yi zan ba ki damar hakan da kaina" Na ce "To BB" Ya ce "You can go" Na tafi ina mamakin maganarsa, wai mun yi ƙanƙanta da kula samari, na yi dariya na ce "Don ba ka san tarin samarin da na yi ba ina ss 2 zuwa 3, kwanan nan kuma zan samo mijin aurena ma na huta, Rafi'at already ta kama na ta GT ɗin (guarantee" Ranar Sunday, da yamma BB ya ɗauke mu muka je Annor cosmetics, muka yi shopping ɗin turaruka da mayuka da kuma sauran kayan gyaran jiki, Ni kam Duk abun da na ga ana tallarsa a facebook sai na ɗauke shi, Ni ce facemask, Ni ce showergel, scrub, face cream, body lotion, face wash, body oil,cbody soap, sunscreen da sauransu, bayan mun gama wannan shopping ɗin muka nufi check 'N' buy, nan ma muka yi siyayya, daga nan muka tafi Ayzan Fun pack. Ƴan gayu sosai muka gani a wurin, iceream ya mana order muka sha, muna shirin fita wani saurayi ya tsayar da mu, Rafi'at ta wuce Ni kuma na tsaya, tunawa da waccar ranar da BB ya ganmu da wani na yi ba shiri na bi bayansu zuwa wurin da muka yi packing. Saurayin ya biyo bayanmu da sauri, ina shirin shiga Mota na ji ya ce "Haba Baiwar Allah, ko minti biyu ne don Allah ki ba Ni" ban kula shi ba na shige cikin mota, kawai sai na ga BB ya buɗe sashensa ya fito, kai tsaye ya tunkari mutumin, Ni dai ido na waro ina duban Rafi'at wacce ta kawar da kanta tana faɗin "Ke ko kaɗan ba kya gudun magana" Na ce "Haba Rafi'at, me kuma na yi? Ban fa kula shi ba, beside in na kula shi ma ba laifi ba ne tun da Ni ba Ni da wanda yake so na, ko don ke dillalinki ya shiga inuwa?" Ta ɗago ta banka min wani irin kallo "Amma kin san BB dai ba ya so ko?". Na ce "To in ba ya so shi zai aure Ni ne?" Saurin rufe bakina na yi da hannuna jin abun da na faɗa. A ɓangaren BB fitarsa ba don ya gan Ni da wani ba ne, fita ya yi zai yi takeway wa su Mommy, ji ya yi an dafa ƙafarsa ana faɗin "Yauwa Yayanmu, ashe ka gan Ni?" Sai a lokacin BB ya dubi saurayin ya ƙare masa kallo shi dai bai san shi ba gaskiya a iya tunaninsa. Saurayin ya ce "Yayanmu ka taimaka ka ba Ni ƙanwarka don Allah, wallahi aurenta zan yi, ta ƙi kula Ni" Wani irin haushinsa ne ya cika zuciyar BB ji ya yi kamar ya sa shi tsallen kwaɗo sai kuma ya sauƙe numfashi ya dubi guy ɗin yadda yake wani roƙonsa, a taƙaice ya ce "Matata ce ba ƙanwata ba" "Habaaa Yayayana wallahi kamanninku sun yi yawa da za a ce matarka ce Don Allah to ka faɗa min unguwarku sai na turo iyayena, wallahi ta shiga raina" Tsawa BB ya daka masa, ba shiri ya sake shi "Kar ka sake fadin wata magana akan matata! Miyasa ku mutane ba ku da hankali ne?" Yana faɗin haka ya juyo bai ma ƙarasa ya yi abun da ya fitar da shi ba. Allan da ya taimake Ni BB Bai ji abun da na faɗa ba, sosai Na ji sanyi a raina tare da marairace fuska ina kallon Rafi'at, ta cije gefen lips ɗinta daga nan muka wuce Baby Ayman sai surutu yake yi. Da daddare Ya Khalid ya kira BB, bayan sun gaisa ya tambayi lafiyar kowa sannan ya jaddada masa ya bayyana min soyayyarsa, nan fa BB ya sauƙe ɓacin ran da wancan mutumin ya ƙunsa masa, shi kam Ya Khalid dariya ya yi ya ce "To ai dama na faɗa maka, ka ma godewa Allah da a gabanka ne ka lalata komai, ina kuma ga in ba ka nan? Kana tunanin za ta yi rejecting duk wanda ya zo mata da kalmar soyayya ne saboda kai? To ai ba ta san ma kana yi ba K". BB ya numfasa sannan ya ce "Hmm" "Kar ka tsaya sanya Friend, kawai ka faɗa mata cewa kana son ta, I'm sure za ta amince, da zarar hakan ta faru ba ka da wata fargaba, komai zai tafi maka yadda ya kamata" BB dai bai ce komai ba, daga nan suka yi sallama, BB ya sauƙe numfashi yana tunanin abun yi. Ranar Monday muka fara zuwa asibiti, da yake Ni A FMC old site nake ya sa ana sauke Ni na kira ƙawayena da muke tare ina tambayarsu a ina za a taru, suka faɗa min da yake ban san wurinba na tambaya aka nuna min, da misalin ƙarfe takwas daidai clinical instructors ɗinmu suka iso wurin aka yi orientation sannan aka sada kowa da ward ɗinsa aka damƙa mu ga head of units tare da posting letter. Sati guda muna zuwa, ranar wata juma'a muna tsaye ana ward round sai consultant Dr. Ɗin ya yi mana tambaya dukkanmu har da OTOC Dr, gaba ɗaya aka yi tsuru kowa na tunanin amsar, caraf suka ji na bayar da amsar daidai, Consultant Dr ɗin ya ba Ni kyautar 10k, shima Dr. Junaid ya ba Ni 5k. Tun daga ranar ya fara shige min, haka kawai zai ware Ni daga cikin colleagues ɗina Wai zai min lectures, tuni su Sa'adatu Muhammad suka fassara mu wai soyayya muke, Ni dai na san ba soyayyar da muke yi da shi kawai karatu yake min. A hankali tun ba na damuwa da shi har na Fara jin shi cikin raina duba da irin gudunmawar da yake ba Ni wajen ganin na iya abubuwa, su Sa'ada kuwa tuni sun fara jin haushina, a haka muka ƙarar da four weeks ɗin da za mu yi a clinics muka koma academic block. Karatun 1 month muka ƙara daga nan aka fara shirye-shiryen fara exams, kasancewar da kaya sosai gabanmu ya sa na mayar da hankalina kwacakom ga karatuna, ko a gidan ba sosai nake kallo ba, chat kuwa yanzu na yage shi, Abbas Toro ma na ja masa layi saboda karatun exams kuma ya fahimce Ni. Har zuwa Lokacin kuma BB Bai ƙara zuwa gida ba a haka muka yi weeding exams cikin amincewar Ubangiji, and luckily we were able to make it, mun samu clear pass, sosai Na yi farin ciki, na kira BB na sanar da shi, a wannan lokacin su Rafi'at suna second semester ɗinsu saboda su 3months suke per semester unlike mu da muke 6months. Tsakanina da Dr. Junaid kuwa iya gaisuwa ne coz na riga na ba shi numberna kuma yakan kira lokaci bayan lokaci, Ni da shi kuwa ba mu ƙara haɗuwa ba tun da muka bar clinical environment muka koma area class, wata rana ina zaune ina jiran zuwan baba driver sai ga kiran DR. Junaid, na yi picking call ɗin muka gaisa cikin mutuntawa, ya tambaye Ni ya studies. Na ce "Alhamdulillah" Ya ce "Ma sha Allah" sai kuma ya yi shiru "Kina school ne?" Na amsa masa da "E, wani abu ne?" Ya ce "A'a, dama na shigo school ɗin naku ne na ce Ko zan zo mu gaisa" A ɗan tsorace na ce "Ai mun tashi ma, yanzu haka Driver nake jira zai zo mu wuce" Caraf na ji ya ce "To ai ga Ni nan, sai na kai ki gidan ko?" Na ce "A'a, so kake Abuya ya min shegen duka in ya gan Ni da kai?" "Shi ke nan tun da ba kya so na zo" Wani irin na ji, ko ba komai dai bai kamata na masa haka ba after all shima kamar tutor yake a wurina, wannan dalilin yasa na ce "Shi ke nan sai ka zo" Yace "thank you" Ko mintuna goma ba a ƙara ba Dr. Junaid ya zo, ina waigawa na hango shi jingine jikin wata lafiyayyar mota yana laluɓen numberna, ban bari ya gama kiran ba na ƙarasa wurinsa kasancewar ba mu da wani nisa da shi. Na ƙarasa wurinsa ina yin sallama, ya amsa min fuskarsa ɗauke da Murmushi. Ya ce "a'a kina kusa ma ashe" Na yafa Murmushi kan fuskata na ce "E, a can nake " na ɗan waiga na nuna masa cool down ɗin da nake zaune. Ya ce "fine, ya na ga kin ƙara kyau ne" Na ɗan kwaɓe fuska jin ta yadda ya ɓullo, ban iya ce masa komai ba saboda na ji zancen wani banbaraƙwai, ya ce "Ya kika yi shiru RM. J?" Na girgiza kaina na ce "Babu komai" Ya ce "Shi ke nan, in kin amince zan na zuwa muna gaisawa a nan tun da ba ki so nake zuwa gidanku shi ya sa ma kika ƙi yarda na mayar da ke" Na ce "a'a wallahi ba haka ba ne, kuma ka san tsarin school ɗin nan, tsayawa da saurayi ma is an offence" Da sauri ya ɗago eyes ɗinsa ya dube Ni yana faɗin "Am i your boyfriend?" Zaro eyes ɗina ma yi na ce "Ban ce haka ba Dr. As far as Kai ba ɗan gidanmu ba ne then saurayi za a kira ka" Ya ce "ke dai ba za a ci ki a zance ba, an bar miki, how studies?" Na ce "Alhamdulillah" Ya ce "ma sha Allah" Horn ɗin motar da na ji gefena ya sa na waiwayo and to my surprise motar gidanmu ne, hakan ya sa Ni dole na yi mishi sallama na wuce abuna. Ina shiga motar Baba Driver ya ja muka wuce, Rafi'at ta dube Ni ta ce "Sannu ko?" Na ce "Yauwa"daga haka na ja bakina na tsuke saboda ba na son maganar da za ta min, muna isa na ajiye jakana a bedroom ɗinmu na watsa ruwa, Rafi'at ma ta watsa Tukun muka nufi dining, muna cin abinci na dawo na yi sallar la'asar, ina ganin yadda Rafi'at ke bi na da wani kallo Mai kama da tuhuma Ni dai na ƙi ba ta damar yin magana saboda ina idar da azkar ɗina na jawo school bag ɗina tare da fitar da Anatomy and physiology textbook. Kusa da ni ta dawo ta ce "Jannat" Na dago na kalle ta ba tare da na ce mata komai ba, ta ce "Na san kina ji na" A ɗan fusace nima na ce "tun da kin san ina jinki ai sai ki faɗi abun da ke ranki" Ta jinjina kai sannan ta ce "Duk masifar da za ki yi kuwa ba za ta hana Ni tambayar taki ba, da wa na ganki a school ɗazu?' Na ɗago na dube ta na yatsina fuska sannan na ce "Toooo Mommy ce Ko Ummi? " Ta ce "idan ma ba su ba ne yayarki ce Rafi'atu" Dariya na kwashe da ita sannan na ce "Afwan Yaya Rafi'atu, amma babu ruwanki da wanda kika ganni tare da shi, beside I'm not a kid, I'm an adult, ko ban kai na tsaya da namiji ba ne?" Tace "Amma kin san dai BB ya gargaɗe mu da kula samari a waje, ba ma wannan ba mu muka zaɓi karatu akan aure" "Sai na ce miki Ni kuma aure zan yi yanzu?" "Kin san ba auren za ki yi ba kike kula saurayi?" Na ce "Ba saurayi ba sai dai bazawari, ke Ni fa ki ƙyale Ni haka nan, karatu zan yi" Tace "shi ke nan, Ni dai na riga na fita hakkinki da na faɗa miki gaskiya" Kallonta na kuma yi kana na ce "To Hajiya, kema sai ki daina kula ya Sadiq " "Hmm" kawai ta ce daga haka ba ta ƙara ce min komai ba. Washe gari sai ga BB ya dawo. Ni dai ba na ce ban so ya dawo ba ba kuma zan ce na yi farin ciki da dawowarsa ba, lokacin da muka dawo daga school mun biya gaida ummi muka ganshi kwance akan sofa Yana bin azkar ɗin da ake yi a Sunna TV na yammaci, sallama muka yi, muka gaida shi ya amsa a gadarance, Ni dai a raina na ce "Ka ji da shi dai, sai shegen son mulki kamar wani basarake " Bayan mun gaida ummi muka wuce part ɗin Mommy, da daddare muna kallon wani series a Bollywood Sai ga BB ya shigo part ɗin Mommyn, Ni dai ban ji komai ba dangane da shakka ko tsoronsa, ina ji Rafi'at na raɗa min cewa "Ga BB nan, ke Ga BB " Banza na mata na dake har ya shigo, haka kawai nake jin yanzu kam zan nuna mishi rashin tsoronsa la'alla mu samu zaman lafiya da shi. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 14 Gaida shi ta yi, Ni kuma na yi kamar ban ga shigowarsa ba, ya ƙare min kallo Sannan ya kira sunana" Na ce "Na'am, a BB ban san ka shigo ba, ina yini" Kallon kin raina Ni ya aika min cikin raina na ce "Mai halin tsiya da na kirki, in ya juye akwai kirki, ya birkice kuwa ya fi tsohuwar mota iya iskanci" Kamar zai ce wani abu sai kuma ya ya juya ya nufi bedroom ɗin Mommy. Yaya Sadiq ne ya shigo, na gaida shi daga nan na miƙe na ba su wuri shi da abar ƙaunar tasa. Bayan kwana biyu wani abu bai ƙara haɗa mu da BB, don kuwa muna ƙoƙarin ganin mun kiyaye duk wani abu da zai haɗa mu da shi ɗin muma, yau ta kama juma'a, bayan mun dawo daga school muka yi wanka muka yi kwalliya kamar masu fita wani wuri, ƙananan kaya muka sanya, da yake sun Kama jikinmu sai muka ɗaura kimono akai muka yi rolling veils ɗinmu, tsakar gida muka fito muna snapping pictures, ba mu ankare ba har BB ya shigo gidan muna ta yin videos abun mu. Hankalinmu na can gefe muna ta iye kawai muka ji Muryarsa kusa da mu, da wani mugun speed Rafi'at ta filla a guje sai part ɗin Mommy, Ni kuma na dake na fara tafiya a hankali, takuna huɗu na ji ya kira sunana. Ba tare da wani tsoro Ba na amsa ina mai zuwa gabansa na tsaya, ya duba Ni ya ce "Wato ke ko a jikinki ko jannat?" Na ce "To Ni me na yi BB" maganar tawa ta fita cikin sigar shagwaɓa. Hararata ya yi kana ya ce "Wai ke ba ki jin magana ne kam? Ba ki san me da me ya dace ba ba kuma ki san abun da bai dace ba?" Na girgiza masa kai, ya ce "Jannat" na ɗan saci kallonsa Sannan na mayar da kaina ƙasa "Ba wai don ba na sonku ba ne nake faɗa muku gaskiya ba, hasali ma soyayyar ce ta sa nake faɗa muku amma na san ku gani kuke kamar ina takura ku ko" Shiru Na masa, ya ce "Har yanzu ku yara ne Jannat, ba za ku fahimci me nake nuna muku ba har sai kun yi hankali" Bakina na ɗan tura gaba jin ya kira mu da yara, wai shi kam me yake nufi da mu ne? Shekarunmu sha takwas takwas har mun shiga ta sha tara amma still he's calling us kids, ban san sai yaushe ne za mu girma a wurin BB ba. "Jannat" ya ƙara kiran sunana a karo na ba adadi har sai da na ji inama bai san sunan ba musamman yadda yake yawan faɗinshi kamar mai jin daɗin hakan. Amsa masa na yi, ya ce "Yanzu wannan abun da kuke yi ɗin kuma ganin kuma kyautawa kanku ne?" Na yi shiru ban ce komai ba Ya ce "Ki dubi kayan da ke jikinku, sai ka ce ba ku san kun fara girma na Uhm?" "BB me ai...." "Rufe min baki dalla, tun da ba ku da hankali kuwa ina za ku san meye aibun kayan? Ke ga ki maras kunya da rashin tsoro kina ganina kika tsaya saboda ki nuna min ke yanzu kin fara girma ko Jannat? Tun ba yau ba nake ganin abubuwa iri-iri a wurinki, ke ce kula samari, ke ce saka ɗamammun kaya kina hotuna sai wani lallanƙwasa jiki kike yi" Cikin masifa yake maganar don har jijiyoyin kansa ana iya gani, huci ya fitar sannan ya sauƙar da Muryarsa ya ce "Na ga yadda kanku ke rawa kwanan nan daga ke har Rafi'atu, so kuke mu saka ƙafar wando ɗaya da ku kuma wallahi hakan ba zai zo muku da kyau ba, ku sani har yanzu yara nake ganinku, kar ku ga kuna higher institutions ku yi tunani kun girma, duk yarinyar da ta yi abun da bai kamata ba babu abun da zai hana na zane ta" Dariya na ji ta kama Ni for his last statement, Wai zai zana mu? I was like lallai kam cikin raina ina jinjina kaina, yayin da a zahiri kuma na fara tarin ƙarya wanda na tabbata shi kanshi ya fahimci dariya nake, bai ƙara bi ta kaina ba ya wuce abunsa, na bi shi da kallo cikin raina ina mamakinsa, just like a chameleon, yau ya zo a mai kirki gobe kuma a ƙaton mugu, yanzu in ban da neman magana da kuma takuri irin na BB meye laifin kayan jikinmu? Mun ji sun matse mu to Kimonon da muka ɗaura akai fa?, siririn tsaki na ja sannan na wuce abuna nima. Da daddare a parlour muka baje tare da Mommy ana kallon wani Film 172 days a wayar Rafi'at, Mommy kam da na iya karanta subtitles ɗin take yi ba saboda sun ya ƙanana yasa ta mana sai da safe ta wuce, Rafi'at ma da ta gaji ta bar min wayar ya zamana Ni kaɗai nake kallon. Abu ɗaya da na sani shi ne, Film ɗin na soyayya ne mai taɓa zuciya, don tun ba mu yi nisa ba na fara hawaye ga shi kuma ƙarshensa ya ƙara karya min zuciya haka na yi ta zabga kuka har da jan hanci. A ba zata na ji Muryarsa don kuwa Ba na ce na san lokacin da ya shigo ba. Sunana ya kira, gagara amsawa na yi sai yunƙurin tashi da na fara ina sauƙe ajiyar zuciya, tsugunnowa ya yi daidai fuskata har ina iya jiyo numfashinsa, ƙamshin da jikinsa ke fitarwa ya sa na sauƙe wani numfashi tare da lumshe idanuwa. "Jannat!" Ajiyar zuciya na ƙara sauƙewa Sannan na gyaɗa kaina Cike da kulawa ya ce "me yake damunki?" Da ƙyar na iya cewa "Babu" coz har yanzu kukan bai gama sakina ba. BB ya ce "Tambayarki nake Jannat, na shigo kusan 20 minutes back, you were busy shedding tears har da shesheƙa, tell me what's wrong with you, ko ba ki da lafiya ne?" Na girgiza kai, ya ce "To me yake damunki?" Na ce "Babu" ya ce "Ƙarya kike, za ki faɗa min ko kuwa?" A hankali na ce "Kallo nake shi ne Film ɗin ya ban tausayi" Galala ya yi yana kallona can ya iya buɗe baki ya ce "Are You in love Jannat?" A wani irin ba zata tambayar tasa ta zo min, hakan ya sa na dube shi sai kuma na kawar da kaina gefe? Cikin wani yanayi da ba zan iya fassarawa ba ya ce "kina soyayya ko Jannat?" Na girgiza kaina ina faɗin "A'a" "Then why kike kuka while watching just a movie?" Na ce "Mutuwa ya yi ya bar ta, shi ne nake kuka" Da sauri ya ce "Waye ya mutu?" Na ce "Amir" Ya jinjina ka ya ce "That proved me right you're in love Jannat" Saurin girgiza kai na yi ina faɗin "BB am not, it's that the film is heartouching and emotional" Ya Gyaɗa kai sannan ya ce "Fine, tashi ki je ki yi alwala ki kwanta" na gyaɗa masa kai sannan na miƙe ina faɗin "Sai da safe" ga mamakina sai na ji ya ce "Allah ya tashe mu lafiya" ɗaƙinmu na nufa, shi kuma bai yi abun da ya kawo shin ba ya koma abunsa. Daren ranar kasa rintsawa BB ya yi don kuwa abun da idanuwansa suka gane masa ya tsaya masa cak a rai, da dai ya ga alamar tabbas ba zai iya baccin ba kawai sai ya tashi ya ɗaura da salla yana addu'ar Allah ya kawo masa komai da sauƙi, washe gari BB ya koma Abuja bayan ya saka mu gaba ya mana faɗa sosai, har mun tashi da mu tafi ya ƙira sunana, hakan yasa na dawo. Ya dube Ni ya ce "Jannat" Na amsa ina gyaɗa kaina Ya ce "Kin ji abun da na faɗa muku ko?" Cikin raina na ce Ni ba kurmiya ba ai na ji, amma a zahiri sai na ce "E" Ya ce "ko da wasa kada ku kuskura ku aikata ɗaya daga cikin abubuwan da na lissafa muku, ban da kula samari, Engagement in to social media, iya Whatsapp na amince muku shima saboda hidimar karatu ne, ban da biye ƙawayen banza da kuma yawo, ki kula Jannat, abun da ya sa na ƙara jaddada miki na san kin fi kowa taurin kai a gidan nan, ko kowa ya kiyaye dokata ke ce mai kunnen ƙashin taka ta, wallahi Jannat wannan karon zan ba ki mamaki na ji labarin kin yi wani abu da bai kamata ba, kin ji ko?" Na ce "e" ya ce shi ke nan, je ki abun ki. Nikam kamar an tsoma Ni a aljanna haka na rinƙa ji da tafiyar BB duk da cewa Ummi sai da ta min faɗa akan yadda ta ga ina murnar tafiyar tasa, amma dai ko ma meye dai ai ya tafi, mun samu freedom. Ko da na shiga part din Ummi bayan tafiyarshi a parlour na ganta, gaida ta na yi ta amsa, na ce Ummi ina Ayman? Ta ce "Shekaranjiya da Khalil zai je Misau ya tafi da shi wurin Mommyn su Mu'awwaz (Ƙanwar su Abuya). Kwaɓe fuska na yi na ce "Ummi me ya sa mu ba kwa barinmu mu je wurin Family? Ki duba fa bai fi sai uku na taɓa zuwa Giade ba, duka ƴan'uwanki ban da Uncle Munir da Uncle Sagir ban san su ba, su ɗinma in ban da Maza ne suna zuwa ai da ba zan san su ba." Hararata ya yi ta ce "Kin taɓa cewa kina son zuwa wurinsu ne? Tabbas da Inna na da rai ne ma za ki san yan'uwana sosai, nima kin ga sai ƙarshen shekara nake zuwa ai" Kamar zan yi kuka na ce "To Ummi yaushe za ki je da Ni?" Ta amsa min da "Sai dai ku shirya ke da Rafi'at ku je idan kun samu hutun makaranta, dama na so ku zaga dangi sosai sanda kuka gama Ummul Qura to hakan kuma ba ta kasance ba, amma dai tabbas ya kamata kuke leƙawa wurin ƴan'uwa kar su ce mu muke hana ku" Na jinjina kai na ce "Haka ne kam" Ummi ta ce "kin gani ai, zan yi wa Yaya Turai magana akan hakan". Shiru muka yi can kuma na ce "Wallahi duk BB ne ya janyo ba ma ziyarar ma, da ba a mayar da mu..." Gwaɓe min baki Ummi ta yi ta ce "Oh saboda ya tafi ne kike faɗin haka ko? Don ubanki a duniyar nan ba ki da kamarsa in faɗa miki, yarinya kamar mai tosasshiyar ƙwaƙwalwa?" Na tura baki gaba na ce "Haba Ummi, wai shi BB ɗin nan..." Ummi ta daka min tsawa ta ce "Rufe min baki, sakarya kawai" Bakina na kuma turawa na ce "Gara ma da ya tafi Abujan, in ya je ma ya yi zamansa a can mun yafe musu shi" bugun da Ummi ta kawo min ya sa ba shiri na fita daga parlourn a guje. A can ɓangaren BB daren ranar da ya koma bakin aiki na gagara Bacci ya yi wuraren ƙarfe biyu Ya Khalid ya farka ya gan shi zaune ya jingina na pillow yayin da fuskarsa ke lafe akan fuskar gado. "Are You alright K?" BB ya ce "Babu komai, just thinking on how to confront that girl, na ga alamun bari ya wuce zai iya kawo rabon wani" Ya Khalid ya zauna gefensa tare da dafa kafaɗarsa Sannan ya ce "my friend ya kamata kam ka san abun yi" BB ya ɗan yamutsa fuska jin yadda kanshi ke sarawa, zamansa ya gyara kafin ya ce "Kana ji Khalid, ban fiye son yi gaggawa akan al'amuran rayuwata ba ne saboda mafi aksari gaggawa na iya karewa da da na sani wanda ba na fatan hakan, ka ga kuma ba wai Mommy da Daddy sun damu da rashin aurena ba ne yanzu bare na ce zan gaggauta fitar da maganar, kuma Ni ba na so na jawo mata wani tsaiko cikin karatunta" Ya Khalid ya murmusa sannan ya ce "Lallai abokina maganganunka gaskiya ne dukka, amma kuma abun da za ka duba shi ne, shirunka akan al'amarin nan babu alkhairi ciki, ka san da Hausawa sun ce, a bari ya huce, shi ke kawo rabon wani, kuma sun ce da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, tun ba yau ba nake nuna maka fa'idar sanar da ita yarinyar tun kafin wani ya riga ga fada mata kalmar soyayyar amma kai ka ce A'a, na yi tunanin ka yi abun ɗaya kamata wannan zuwan naka gida ashe ba ka yi ba, to wallahi bari ka ji, in ka tsaya sanya wani katon ne zai riga ka kuma ka ga babu yadda ka iya ba za ka mata dole ba" BB ya jinjina kai tare da faɗin "Haka ne kam, amma.." Ya Khalid ya daga BB sannan ya ce "Look my friend, the only solution you get shi ne ka sanar da yarinyar nan Jannat, ka ajiye duk wani ji da kai da ƙi faɗinka gefe, kana son ta, ka san hakan, then why za ka ci gaba da wahalar da kanka ne Uhm?" BB ya ce "Wannan zuwan nawa na fuskanci wani abu game da ita, ba na fatan a ce hasashena ya zama gaskiya." Ya Khalid ya ce "Ai kuwa dai in har kana sonta you've to save yourself and confront her, Ina tsorace maka aikata kuskuren da za ka zo kana nadama daga baya, kawai ka faɗa mata tun kafin ta kamu da son wani, ka ga a wannan gaɓar dole ka haƙura da ita.." "wannan shi ne mafi munin labari kuwa da zan taɓa riska a rayuwata, Ni tsoron da nake ji ma yanzu shi ne, na sama da ita ta yi rejecting ɗin soyayyata, for sure zan iya rasa rayuwata" Daga shi Ya Khalid ya kuma yi, cikin sigar lallami ya ce "Ba ma fatan hakan, burinmu shi ne mu cika mota mu tafi Azare bikin Captain Ibrahim Abubakar Shirama da kuma Jannat ɗinsa" Wani ƙayataccen Murmushi BB ya saki har sai da haƙwarensa suka fito. Daga nan ya ji wani irin nauyi na zuciyarsa ya ragu masa, tabbas aboki irin Ya Khalid gare shi babbar ni'ima ce daga mahalicci, Faransa shi ma Allah ya ba shi damar yi masa abun da zai yi alfahari da shi wata rana. A nawa ɓangaren bayan tafiyar BB abubuwa da yawa sun fara sauya wa a tare da Ni biyo bayan wani taɗi da muka yi Ni da wata colleague ɗina Halima Madaki, wacce kowa a ajinmu ya san yadda idanuwanta ke buɗe, duk wani social media handle in ka leƙa za ka ga Sady-Madaki tun daga facebook, Whatsapp, Instagram, tiktok da sauransu. Yarinyar wayayya ce ta ƙarshe, Ni da ba na kula ta yau ma ƙaddara ne ta kai Ni seat ɗinta na tarar ana taɗi kasancewar lecturern mu na Behavioural sciences bai zo ba, nan fa ana taɗin Novels da irin mazajen Novels na ce musu ai ina da yaya shi ma haka yake, suka fara zuga Ni kan kar Na sake na bari ya kuɓuce min, Ni kuwa cikin halin ko in kula na ce "Ai ko kaɗan BB Ni bai burge Ni, mun san saboda me?" Suka ce A'a Na ce "Saboda tun ina yarinyar yake cin ƙaniyata, suka babu irin wanda ban sha ba, punishment kuwa ba a magana, kun san sojojin nan ba su da tausayi" "Ai soja ne ma?" wata a cikinmu ta tambaya Na ce "ƙwarai kuwa, mugu ne kuwa na ƙin ƙarawa though he's very kind at times, tun da ƙofar samu ta buɗe masa shi yake sponsoring karatunmu, har Yayanmu Dr. Sadiq, za mu gani shi a Labour ward ko kuma Post Natal ward" Khairat ta ce "Wai dama Dr. Sadiq yayanki ne? Sai yanzu ma na ga kamar" Na ce "Yayana ne, daga shi sai Ni, sai ƙanina Ayman" "AI guy ɗin nan akwai ƙwaƙwalwa in ji sister na, kin san su sun fara speciality posting, hotunansa da yawa a wayata ban san a ina ta samu ba, tana crushing mass over" Na ce "Ai kuwa shi kam an bayar shi" Muka sheƙe da dariya gaba ɗayanmu, Ni na fara tsagaitawa na ce "Da gaske, bestie na kuma cousin sis ɗina yake so, ƙanwar wannan Boss ɗin gidan namu" Sady-Madaki ta ce "To amma ke meyasa ba ki son shi" Na yamutsa fuska na ce "A matsayin ɗan'uwana shi ɗin na daban ne, amma ina jin ko da a ce shi ya ce yana so na ba zan iya soyayya da shi ba, kun san saboda me?" Suka ce A'a na ce "na rasa me ya sa duk lokacin da zuciyata za ta hasaso Ni a wannan ɓigiren sai na ji na fara tuna izayar da ya mana, gaba ɗaya sai tsanarsa ta cika raina" Khairat ta ce "Wai! Da aiki gabanki class Rep, wallahi za ki so shi, don kuwa tsaf a gidanku za a ce za a haɗa ku aure" Na waro idanuwana tare da rufe Mata baki da palms ɗina sannan na ce "Bakinki ya sari guntun kashi. Ina na isa na auri BB, Ai BB sai miskila irin shi su je can su kwaɗa mugun halinsu su cinye" Su Sady-Madaki suka yi dariya, Khairat ta ce "Sai ka ce jaruman meye ma sunan novel ɗin? Oho, na manta a tiktok dai na ga ana recommending a je a karanta" Cike da mamaki na ce "Ku kam kuna tiktok abunku" Ta buɗe baki tana kallona, na ce "ya dai? Kallon kuma na miye?" Ta ce "To ai dole na kalle ki class Rep, sai kina nufin ke ba ki yi? Mukam muna ɗanawa, Instagram, Twitter Dukka muna taɓawa, followers ba adadi nake da su, ke kuwa da kina yi yadda kike kyakkyawar nan, hmmm" Na ce "Ai ko app ɗin ba Ni da shi, BB ya hana mu, iya Whatsapp ya yarje mu yi amfani da shi" Shewa su khairat suka yi kafin Sady-Madaki ta ce "Lallai hasashe na ya zama gaskiya, wallahi Jannat wannan BB ɗin naku son ki yake" *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 15: Idanuwana na zaro Sannan na ce "Rufa min asiri don Allah kar ki min mummunan fata, wallahi duk Kyan nan nasa Ni bai burge Ni, beside mijin da nake fata ma ba irin qualities ɗin BB gare shi ba" Khairat ta ce "Kar ki ce Ban faɗa miki ba, muna nan da ke zai ce miki yana son ki ".na ce "Wai Ni?? Zan mutu kuwa ashe, ku duk bayanin da zan muku ba za ku gane ba, BB ya wuce tunaninku, wallahi shi fa har yanzu yara yake ganinmu" Suka jinjina kai, Sady-Madaki ta ce "Lallai kuwa, to Allah ya kyauta, ko account dai kwa buɗe a handles ɗin ko don ganin updates ko ba za ku yi amfani da shi ba, amma zandama zandaman ƴan mata kamar ki a ce ba ki da media handles? Sannu Saratu" Na ce "ko garajen buɗewa ba zan ba Sady-Madaki, zan jira in ya gama isar tasa ya ba mu dama sai mu buɗe" Ta ce "Tab, ai sai kin ga dama zai ganki, ki buɗe da wani suna mana" Na ce "kuna ganin ba zai gane Ni ba?" Suka ce ,"Ta yaya zai gane in dai ba wayarki za ki ba shi ya gani ba" Na ce *shi ke nan, ku buɗe min yanzu" na miƙa musu wayata suka buɗe min account a IG da tiktok, tare da ƙara wayar min da kai kan yadda zan yi amfani da su. Sady-Madaki ta ce "Ko ke fa?" Na murmusa na ce Hmm. A hankali na gama koyan yadda zan yi amfani da waɗannan handles ɗin wasu lokutan har nakan yi amfani da tiktok ma na yi hotuna a school sai na sauya privacy zuwa only you, hakan ta sa BB Bai fahimci komai ba game da Ni to ta yaya ma zai fahimta bayan da Noor Saddam na buɗe? Ranar wata juma'a da ba zan manta ba ne muka yi wanka muka ci gayu Ni da Rafi'at sannan muka fito tsakar gida muna hoto da tiktok filters masu mai da mu larabawan gaske, na ba wa Rafi'at ta min ita ma na karɓa na mata, wani abu da ban sani ba shi ne, lokacin da Rafi'at ta karɓa za ta min nan san cewa ta cire only you ba, hoto kam ya tafi public. Bayan mun gama hotunanmu mun koma cikin gida kowa ya kama harƙar gabanshi. Da daddare ina kwance wayata ta fara ringing, Ina dubawa na ga sunan BB ɗaro-ɗaro akan screen ɗin wayar, ɗan zaro eyes ɗina na yi sannan na tura bakina kaɗan na ce "Ko me ya sa yake kira na rai?" Rafi'at da ke gefena ta ce "Waye?" Ban kula ta ba coz lokacin na yi picking call ɗin, sallama na yi na gaida shi, bai amsa gaisuwar tawa ba na ji ya ce "Ke wato Jannat kina so ki nuna min cewa kin fi ƙarfina ne ko me?" Na ce "BB me ya faru?" Ni dai iya sanina babu abun da nayi. "Tambayata ma kike ko? Didn't I warned you people not to engage yourself in any social media platforms bayan Whatsapp?" A ɗan tsorace na ce "BB Ni kuma? Ba na komai fa, wallahi..." Cikin ɓacin rai na ji ya ce "Will you shut that your big mouth ko sai na ɓata miki rai? Ki yi laifin tsabagen kin raina Ni za ki ce min ba ki yi ba? Am I your mate?" Na girgiza kai kamar ina gabanshi na ce "No" Ya ce "Ki tabbatar in na dawo sai na sauya miki kamanni perhaps hakan ya ladabtar da ke ki daina yin hotuna kina ɗaurawa a media" Yana faɗin haka ya katse kiran. Ai nima kamar jira nake ya katse kiran na fara lalumen buɗe IG da tiktok ɗina amma kash, IG ɗin ya ƙi loading alamun data na ya ƙare, Rafi'at na kalla wacce hankalinta kwance take kwance sai chat ɗinta take, ɗaka mata duka na yi ina faɗin "Wai ke ina cikin tashin hankali ke kuma hankalinki kwance ma chat kike?". Tashi ta yi ta zauna tana hararana. Na ce "Don Allah wayar taki da data ki ban aro?" "Me zaki yi da shi?" Cikin tashin hankali na ce "Ni in za ki ba Ni kawai ki ba Ni Malama" Yatsina fuska ta yi ta ce "To na ga dai ba assignment za ki yi ba" "To kar ki bayar dalla, ki cinye abunki?" Miƙo min ta yi, da har na ce zan yi zuciya sai kuma na miƙa hannu na karɓa na yi connecting hotspot, nan da nan na shiga IG na Fara laluɓa account ɗina ban ga komai ba, na shiga tiktok account ɗina me zan gani? Hotona da Rafi'at ta yi min jiya ne wanda na yi kyau sosai. Ɗaka mata duka na yi na ce "Shi ke nan kin kashe Ni Rafi'at." Na ƙarashe ina zuba mata idanu. "Me na miki za ki maka min wannan dukan?" Na miƙa mata wayata na ce "Duba ki gani, a rashin iya amfani da tiktok kin je kin posting min hotona har BB ya gani, Rafi'at kin kashe Ni!" A razane itama ta tashi ta zauna tana zazzaro idanuwa "Na shiga uku, garin yaya hakan ya faru? Ke ɗin yaushe kika buɗe account a tiktok?" Maimakon ta taya Ni nemo maslaha sai ta jefo min tambayar yaushe na fara toktok, tsabar kaicinta da ya cika Ni sai na ce "ban sani ba" Ta ce "shi ke nan, sai ki tanadi abun da za ki ce masa ai" Tana faɗin haka ta fara ƙokarin komawa ta kwanta, cike da masifa na ce "To an gaya miki shi ɗin mala'ika ne da zan ji tsoronsa? Ke kuma in kin isa ki kwanta na yi kwantai, ki tashi mu samo maslaha tun da ke kika yi posting hoton" Kallon ba ki da wayo ta aika min kafin ta ce "taki ake ji kuma, Ni sau nawa kina jefa Ni a uƙubar BB bayan kuma ba Ni da laifi?" Ganin yadda ta ɗau zafi itama ya sa na sauƙar da murya na ce "Haba Rafi'at, yanzu haka za mu yi da ke?" Dariya ta yi sannan ta ce "Ai na ɗau kema BB ɗin ce, ashe kin iya magana politely haka?" Ban biye ta ba na ce "koma dai mene ne yanzu mu san abun yi kafin ya dawo" Ta ce "to, kin goge hoton ina de?" Na ce "A'a, ya riga ya gani, ba ki ga har comment ya yi ba akai?" Ta ce "what? Mu gani" Na mika mata wayar, kai ta jinjina na ce "Mun mutu" Na ce "wallahi ba mu mutu ba, bari dai na goge yanzu" Deleting post ɗin na yi sannan na ce "Haba! Wannan wace irin masifa ce wannan Rafi'at, wane irin hali haka BB yake da? Wannan ai abun ƙi ne a ce mutane na fargabar ko da ganinka ne, amma shi ina? Don Allah don Annabi at this stage of Life da muke miye Aibu don mun yi social media?" Rafi'at ta jinjina kai ta ce "To ya za mu yi, kin san ko iyayenmu ba su da say akan hukuncin BB" Na ce "Gara ma Daddy da Mommy, ammma Ummi da Abuya kam su suke ƙara ɗaure mishi gindi yana maida mu kamar ƴaƴansa, Ni wallahi na fara gajiya da rayuwar takura irin ta BB, duk ta silar shi ga shi ko dangi ba wani saninsu muka yi ba." Rafi'at ta ce "Ni fa kin ga, Mommyn Misau ma ba wani saninta na yi ba, in ban dan albarkacin zuwa gidan Dada ai da ba za mu taɓa saninta ba tun da ita mijinta ba barinta yake tana yawo ba, ƴaƴanta kam ba na ce zan tuna wani cikinsu ba" Na jinjina kai na ce "Allah dai ya kyauta, Ni yanzu har na Fara gajiya da zaman gidan nan, Gara ma na yi aurena na huta da fargabar wannan bawan Allahn" Rafi'at dai ba ta ce komai ba, komawa ta yi ta kwanta abunta bayan ta karɓi wayarta, shigowar saƙo cikin wayata ya sa na duba, Data aka saka min amma ban san waye ba, damuwar halin da nake ciki yasa ban ma damu da na San koma waye ne ya tura ba. Washe gari da na je school ma Dr. Junaid ya zo wurina a school and lucky to him, mun samu lokaci sosai. Haka kawai yau na ji in saki jiki da shi muka yi hira sosai, hirar da ta min dadi ba kaɗan ba though kusan dukkanta shi yake riƙe da akalarta. Tabbas yau na ƙara fahimtar Dr. Junaid fiye da tunani, da haka ta min sallama ya wuce abunsa. Yana tafiya kuwa baba Driver ya iso, na shiga mota cikin walwala muka koma gida, ina fitowa daga mota ban bi ta kan Rafi'at ba na wuce part din Mommy a madadin sashen Ummu tun a bakin kofa na ji zuciyata ta yanke, school bag ɗina na yi dropping sannan na cire uniform ɗin jikina tare da watsa ruwa na saka wata riga maras nauyi, fitowa a toilet ya yi daidai da shigowar Rafi'at ɗakin, ta dube Ni ta ɗan taɓe baki sannan ta ce "Da ba ki jira Ni ba kin kyauta" Ba tare da na kalle ba na ce "A'a, to zafi ne ya addabe Ni dole kin ga na cire wadannan uniform ɗin kafin na ji sanyi." Ina faɗin haka na fice tare da nufar dining,ajiyar zuciya na sauƙe bayan buɗe flask ɗin da ke jere ɗaya bayan ɗaya tare da yamutsa fuskata, gaba ɗaya girki da ke jere babu wanda ya min, kitchen na nufa don dafa ko da noodles ne idan na taɓa sai na je part ɗin Ummi na dubo me ta yi. Ina tsaye ina tunanin guda nawa ne za su ishe Ni wata irin fargaba ta mamaye ruhina sakamakon ƙamshin turarensa da na ji ya kaure kitchen ɗin. Da wani mugun speed na juyo ai kuwa idanuwana suka sarƙafe cikin nasa, wani irin waro idanuwana na yi yayin da ƙafafuna suka saki har suna shirin kasa ɗaukata sai ma wani ɓari da suke yi. Cikin raina na ce "Shi ke nan, na gama yawo" Murmushin da BB ya saki ya sa Ni ƙara shiga wani tashin hankalin da ya ninka na baya, don na gama tabbatar da cewa wannan murmushin ba na Allah da Annabi ba ne. Cikin takunsa na ƙasaita ya fara takowa kusa da Ni, yayin da na kasa ɗauke idanuwana daga gare shi na kuma kasa ko da motsa wata gaba a jikina. Gyaran murya ya yi, hakan ya sa Ni dawowa cikin hayyacina, saurin girgiza kaina na yi trying hard to be normal yayin da na shaƙi wata iska tare da fesar da zazzafar iska. A hankali na ce "Sannu da dawowa BB" Ya dube Ni tun daga sama har ƙasa sannan ya wani yamutsa fuska. "Me kike girka mana ne?" Ban san lokacin da na ɗago idanuwana na sanya su cikin nasa ba jin maganar da ya yi amma ga mamakina babu wani reaction akan fuskar tasa da ya wuce ma kwanciyar hankalin da na gani shimfiɗe kanta. Kansa da babu wata wadatacciyar suma ya shafa kana ya juya, ajiyar zuciya na yi saurin sauƙewa tare da jinjina kaina, sai da ya kusa barin kitchen ɗin sai kuma ya dawo, Ni dai har lokacin ina tsaye wurin da ya bar Ni, kitchen cabinets ɗin ya fara buɗewa ɗaya bayan ɗaya kamar mai neman wani abu, taɓe baki Ni dai na yi tare da sauƙe numfashi tare da juya masa baya ina jiran ficewarsa. Kamar a mafarki na tsinkayi Muryarsa na kiran sunana, I tried to hesitate Kar na je sai na juya kuma ba kiran nawa ya yi ba. "Hey!" Muryarsa ta ƙara sauƙa a kunnuwana. Saurin juyawa na yi ina faɗin "Na'am BB" Cike da isa ya ce "Come here" Yana illustrating circle da yatsarshi, ba musu na ƙarasa kusa da shi tare da tsayawa a wurin da ya nuna min yayin da kaina ke ƙasa "Take this" Ɗagowa na yi don ganin mene ne, wani ɗan ƙararramin cup ne irin extra gift da ake samu a pack ɗin wani abu kamar maggi, da sauransu. Hannu na da na karɓa tare da riƙe cup ɗin. "Follow me" ya faɗa yana mai fara stepping cikin takunsa na ƙasaita, har sai da ya isa parlour ya zauna kan kujera tukun ya kai dubansa gare Ni. Zaro wayarsa ya yi tare da faɗin "Ɗauko min bucket" Da sauri na juya na nufi kitchen tare da dauko bucket ɗin na kawo gabansa na ajiye ina faɗin "Ga shi" Ya dube Ni ya ce "Using this cup da ke hannun ki, lemme check the time" wayarsa ya duba yayin da ya bar Ni tsaye ina jiran jin cikakken bayanin nasa. "It's five minutes past five, Ina duba lokaci ina kika wuce 30 minutes ko?" Ya jinjina kai sannan ya ce "Hmm" tare da cije lips ɗinsa. Cikin rawar murya na ce "ehm, e, ehm BB me za a yi?" "Kina zuwa kitchen sink kina ɗebo ruwa da cup ɗin har ki cika min bucket ɗin nan" ya ƙarashe yana nuna min bucket ɗin da yatsarsa. "What?" Na fada cikin raina yayin da na zaro idanuwana da suke cike da tsoro waje. Gira ya ɗage min sannan ya ce "Your time already start Jannat" Gagara tafiya na yi tsabagen yadda na firgita sai na cup ɗin hannuna da na duba Sannan na ƙara duban bucket ɗin, yanzu fisabilillah ta ya zan iya cika bucket ɗin nan da wannan ƙararramin cup ɗin beside ya san ruwan a hankali yake zubowa ai. Ganin na ƙi motsawa ya sa BB daka min tsawa ta ce "Za ki wuce ki fara ne ko sai jikinki ya faɗa miki?" Bai kai ga rufe baki ba na ɗiba a guje na nufi kitchen, duk ƙarantar cup ɗin sai da na kusa minti guda tsaye tukunna ya cika sakamakon yadda ruwan ke zuwa a hankali, haka na fito na zo na juye cikin bucket ɗin sannan na juya da gudu saboda na samu na yi akan lokaci kafin na ƙara yin wani laifin. Haka na yi ta jido ruwan nan yayin da BB ke zaune yana daddana wayarsa ya wani harde ƙafarsa ɗaya kan ɗaya kamar wani basarake. Na yi ya kai sai ashirin Amma yadda kuka san cup ɗaya na zuba a cikin bucket ɗin, Ni dai nake ganin ma ko kwana aka ce na yi ina zuba ruwan nan da cup ɗin da ya ba Ni ba lallai bucket ɗin ya cika ba gashi gaba ɗaya jikina ya yi tsami, ga yunwar da nake ji ta ƙara dawowa sabuwa kar, halin da nake ciki is a true definition of TSAKA MAI WUYA. Yanke hukuncin ba shi haƙuri na yi idan na kawo wannan san, hakan ya sa bayan na juye na fashe da kuka ina faɗin "Don Allah BB ka min afuwa wal..." Katse Ni ya yi ta hanyar faɗin "Will you wipe these your crocodile's tears and keep doing your tasks or?" "Don girman Allah BB na tuba na bi Allah..." *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 16: "Kin san dai lokacinki kike ci ko?" Ya ba Ni amsa cikin halin ko in kula. Sanin cewa magiyar tawa ba za ta yi amfani ba a wannan lokacin ya sa na goge hawayen nawa na juya na ci gaba da ɗiban ruwan. Sai da na kusa isowa wurinshi kawai na yi tuntuɓe da spoon na faɗi, take ruwan nawa ya zube. Daga wurin da yake ya aika min wani mugun kallo ya ce "Duk wurin da kika ɗisar da ko da drop me na ruwa ko tabbatar in kin gama cika bucket ɗin nan za ki goge shi tas" Cikin raina na ce "Lallai BB ba shi da imani, yanzu dai ke nan sai na cika wannan bucket ɗin yake nufi kafin ya bar Ni? Kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka na miƙe zan ci gaba da ɗebo ruwan na tsinkayi Muryar Mommy na faɗin "A'a, ba ka wuce Misau ɗin ba ne?" Daidai isowarta wurin BB ɗin ta ce "bokiti a parlour kuma? Wa ya kawo shi hala?" Kallonta BB ya yi sannan ya ce "na fasa, sai Allah ya kai mu gobe" Mommy ta ce "To Allah ya kai mu" Hannu ta sa za ta ɗage bucket ɗin BB ya ce "Ni na kawo shi" Da kallon mamaki Mommy ta bi BB ɗin da shi Sannan ta ce "Ikon Allah" Bai ce komai ba shi dai, hakan ya sa Mommyn miƙewa za ta koma ɗaki, juyowar da za ta yi Ni kuma na ƙaraso ba ta san da Ni ba sai kuwa muka ci karo cup ɗin da na ciko da ruwa ya faɗi ƙasa, idanuwana na waro tare da tsugunnawa don ɗauko cup ɗin wanda ni a yanzu shi ne a gabana ma ba komai ba. Ɗago Ni Mommy ta yi ta ce "A, ke Lafiyarki?" Cikin inda inda na ce "E, am e" idanuwana na kai na duba shi sai na ga ya kau da nashi gefe, kaina na jinjina ina ƙara mamakin taurin zuciya irin ta BB, wato Kar ma na kalle shi Mommy ta fahimci wani abun ya sa shi kau da kansa gefe ko. "Miye hakan kuma?" Na ce "a'a Mommy ba komai ba, yi haƙuri ban kula da ke ba" BB ne ya yi saurin faɗin "Mommy kina da saƙo Misau ɗin ne?" Kallon BB Mommyn ta yi sannan ta kalle Ni trying hard to figure out what's fishy between us Amma BB ya ƙi ba ta wannan damar, ganin hakan ya sa zuciyata saurin yanke shawarar samar min mafita, take na yi saurin barin wajen na nufi kitchen Ina Allah Allah cup ɗin ya cika na dawo na zuba tare da addu'ar Allah ya sa har lokacin Mommy na wurin. Cikin Sa'a cup ɗin na cika ba taho da sauri ina sakin murmushi ganin Mommyn na tsaye da alamu wani abun suke tattaunawa da BB ɗin. Ina ƙarasowa kuwa na juye ruwan a ciki, ai kuwa a idon Mommy, tafa hannayenta ta yi ta ce "Ikon Allah, me zan gani haka Khalil?" Kamar ba zai tanka ba kuma ya ce "Mommy..." "Kar ka ce min komai ai na gani da idona" Jin Mommy ta shiga zancen ya sa na fashe da kuka ina ƙanƙame jikina, Mommy ta duba Ni sannan ta mayar da kallonta ga BB tana aika masa wani kallo da ita kaɗai ta san fassarar shi. Janyo Ni jikinta ta yi sannan ta ce "Yi haƙuri Daughter, je ki watsa ruwa, Rafi'at! Rafi'at" Mommy ta ƙwalawa Rafi'at kira "Ki kai wa Jannat Abinci ɗaki, maza je abun ki, zan yi maganin Yayanku" Ido na faka na kalle shi ya wani yi kici-kicin da fuska ya haɗe girar sama da ta ƙasa, gwalo na masa tare da wucewa abuna bayan tabbatar da cewa ya gan ki, kansa ya jinjina sannan ya fara ƙoƙarin miƙewa. Mommy ce ta tsayar da shi tana faɗin "Haba Khalil, wai dama har yanzu ba ka daina ire-iren waɗannan punishments ɗin ba uhm? Yanzu meye ribarka na wahalar da ƙanƙanuwar yarinyar nan, ko ba ka raga musu Kasancewasu ƙannenka ai ka raga musu kasantuwarsu mata" Cikin ransa ya ce "Mommy ke kike ganinta ƙaramar yarinya, ita ganin kanta take ta isa a yanzu" "Magana nake maka Khalil, ka wani zuba min ido kamar ba ka ji na" Saurin shafa kansa ya yi tare da faɗin "I'm sorry Mommy, In Sha Allah ba za a ƙara ba" "In kuwa aka ƙara ma ba lamunta zan yi ba, don ba zai yiwu ina ji ina gani ka lahanta min yarinya ba, ire-iren punishments ɗin nan ba nasu ba ne Khalil, ban hana ka hukunta su ba amma a yi komai daidai ruwa daidai tsaki, Please take note" Ya amsa da "In sha Allah Mommy" daga haka ya fice yana cije gefen lips ɗinsa tare faɗin "She's safe now, Amma za mu haɗu" daga nan BB Bai tsaya ko ina ba sai part ɗin Ummi. A nawa ɓangaren ɗakinmu na nufa tare da zubewa kan bed, Rafi'at da ke shirin fita ta ce "Ke Lafiyarki kuwa?" Ganin ban kula ta ba ya sa ta ƙaraso ta zauna bakin gado tare da kai hannunta jikina tana taɓawa. "Ƙalau muka dawo fa, kin dafa indomien ne? Uhm tun da ba za ki kula Ni ba bari na je na haɗo mana golden morn in mun sha na je part ɗin ummie na ɗebo mana wani abun" tana faɗin haka ta fice. Blanket na shashimo tare da ƙudundune wa ciki ina sauƙe ajiyar zuciya, gaba ɗaya ƙafafuna ciwo suke min kamar wacce ta shekara tana aiki, na dai danganta hakan da yunwar da ke cin jikina yau ne. Cikin raina na ja wa BB Allah ya isa ta kai cikin randa don kuwa na gama fuskar da ba ya son jin daɗi na ne gaba ɗaya after all ban tare mishi komai ba rayuwa ba, tunanin laifin da na masa daga dawowata zai tarbe Ni da wannan mugun punishment ɗin nasa na yi, amma iya hangena na kasa gane dalilin hakan, hakan ne ma ya sa na ƙara ka masa Allah ya isa a zahiri yayin da nake ƙoƙarin stretching ƙafafuna da nake jin su kamar ba a jikina ba. Shigowar Rafi'at ɗakin ya sa Ni tattara sauran ƙarfin daya rage min na miƙe zaune, cup ɗin da ta dama min golden morn na amsa tsabagen yunwar da ke cikina spoon ɗin na cire na kafa kai. Bayan na shanye shi tas ne na dubi Rafi'at na ce "Don Allah ki dubo mana wani abun a part din Ummi na san ba za a rasa ba tun da ɗanlelen nata yana nan" Kallo Mai cike da tambaya Rafi'at ta aiko min sannan ta ce "Ban gane ba?" Na ce "ba ki gan Ni ba ne? Yaya Zalimu ya dawo wallahi, yau ban tashi da Sa'a na gaba ɗaya" na ƙarashe ina marairaice murya Hannunta ta sa ta rufe bakinta jin sunan da na faɗa, sai da na gama maganar kana ta ce "Wai BB ne ya dawo?" Na jinjina mata kai "Ƙwarai kuwa, Ni kam har tsaraba sai da ya ba Ni" "Me?" Na ce "Ke dai in za ki dubo mana ki je ki dubo mana" Ta ce "Tab, in ba za ki ba nima ba zan je ba, Gara na je na daga noodles" "To ki dafa mana tare don Allah, wallahi ji nake kamar ƙafafuna ba a jikina suke ba" Cikin raɗa ta ce "Wane punishment ya ba ki ne?" Ta ƙarashe tana ɗage min gira. Na amsa mata da faɗin "Hmm, fill the bucket, kuma wai daga kitchen sink zuwa parlour" Rafi'at ta zaro ido kasancewar tun muna yara na ma yana ba mu wannan punishment ɗin, lokacin kuwa kayan wasanmu yake cewa mu ɗauko sai ya ga smallest cup ko bowl ya ce da shi za mu cika. Kanta ta jinjina sannan ta ce "Tab! Lallai kin jikkata, bari na je na dafa mana da ɗan yawa sai mu ajiye a ɗaki ba zai mun fita ba" "To" kawai na iya ce mata, daga nan na mayar da kaina kwance ita kuma ta fice. Bayan Rafi'at ta dafa mana noodles ba mu ƙara fitowa ko da parlour ba har dare, washe gari kuwa bayan mun shirya za mu wuce school a ɗaɗɗare muka biya muka gaida Ummi cikin ranmu kuwa addu'a muke Allah ya sa kar mu haɗu da BB, wata nannauyar ajiyar zuciya muka sauƙe a tare bayan mun fito ba tare da mun gan shi ba, Daga nan kuma muka wuce aka fara dropping Ayman daga nan aka ajiye Ni sannan Rafi'at. Bayan mun dawo daga school cikin Sa'a muka shiga part din ummie muka fito ba mu yi arba da Yaya Zalimu ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya mana ba. Muna shiga part ɗin Mommy muka tarar da ita zaune a parlour tana kallon maimaicin shirin bayyinat da ake yi a Sunna TV. Jikin Mommy na shige ina faɗin "Sannu da gida Mommy" Cikin fara'arta mai yalwa ta ce "Sannu ƴata, an dawo" Na gyaɗa kai Mommy ta ce "Sannunku da dawowa" Na amsa da "Sannu Mommy" Bin bayan Rafi'at da ba ta tsaya ba na yi, a ɗaki na iske ta tana shirin shiga wanka, da Allah na haɗa ta kan ta bar Ni na fara shiga don wallahi yunwa nake ji sosai. "To ya zan yi ai sai ki shiga" Ni dai ban ce mata komai ba tun da har ta min alfarma hakan ya sa na shiga na samu na watsa ruwa, kallonta na yi ganin tana daddana waya sannan na ce "Na fito" Ta ce "ok" Daga nan ban ƙara bi ta kanta ba na saka kaya marasa nauyi Sannan na fito parlour har lokacin Mommy na zaune. Dining ba nufa na fara buɗe food warmers ɗin, wani irin dogon numfashi na shaƙa ganin gurasa, hannu na rawa na yi saurin zubawa a plate na tsiyaya zoɓo a cup sannan na dawo parlor na baje kan carpet kusa da Mommy. Mommy ce ta dube Ni ta ce "Hala jiya kam laifin me kika yi ne daga dawowarku Khalil ya tisa ki da punishment?" Gurasar da ke bakina na haɗiye sannan na ce "Hmm, wallahi Mommy ban san me nayi ba, dawowarmu ke nan daga school na shiga kitchen zan daga noodles ya ba Ni aiki" Mommy ta jinjina kai sannan ta ce "Shi ya sa ba na so ya dawo gidan nan wani lokacin, kuma ya kamata Ku yi ƙoƙarin kiyaye duk wani abu da kuka san zai haɗa ku da shi bare har ku keta dokokinsa." Na jinjina kai sannan nace "In sha Allah Mommy" Sai da na kusa cinye tawa Gurasar Rafi'at ta fito, itama nan ta ɗebo Jallop rice ta zauna inda na gama ci ta fara cin nata, miƙewa na yi na nufi ɗakinmu tare da ɗauko wayata a cikin jakana. Missed call Na gani, Dr. Junaid NE ya kira Ni, taɓa baki na yi na ce "Ko me rai zai ce min?" Dialling numbern nashi na yi har ta gama ringing bai ɗaga ba, ina ƙoƙarin ajiye wayar kiransa Ya shigo , hakan ya sa Ni picking kiran tare da ƙara wayar a kunnena. Gaisawa muka yi daga nan na ja bakina na yi shiru ina jiran jin dalilin kiran nawa da ya yi. Shi ma shirun ya yi, ganin muna ɓata lokaci ya sa Ni faɗin "Hello" Ya ce "Ina jinki" Cike da mamakinsa na ce "Kai fa ka kira" Ys ce "na sani, dama akwai maganar da nake so mu yi ne" Na ce "alright, I'm all ears" "Ba ta waya ba ce maganar, I'll like to see you in person" Ban iya ɓoye mamakina ba na ce "Ikon Allah" Ya ɗan murmusa sannan ya ce "ikon gaske" ɗan pause ya ci Sa'annan ya ce "To be sincere I want to see you, akwai maganar da nake so mu yi, to amma na san da kamar walaha ki kwatanta min gidanku" Na ce "Gidanmu kuma Dr.?" Ya ce "E, ita personal issue that's why nake so my yi maganar a gida" Murya ƙasa-ƙasa na ce "BB is home, Babu yadda za a yi wani ya zo wurina, idan kuwa hakan ta faru na tabbatar ko wata ba lallai na ƙara ba za a aurar da Ni" Dariya mai sauti Dr. Junaid ya yi kafin ya ce "And so? Ba ki kai auren ba ne ko me?" Na ce "hmm" "Meye Hmm? A beg my friend ki daina wani tsoro, wai shi wannan BB ɗin?" Shiru ya yi sannan ya ce "Ina tunanin fa" sai kuma ya ƙara yin shiru Tsintar kaina na yi da tambayar "me?" Ya ce "Babu komai, zan samu alfarmar zuwan ko kuwa na haƙura sai gobe na zo school ɗin naku?" A kasalance na ce "Da dai zai fi" Ya amsa min da "Fine, hakan ma na gode, see You tomorrow " Na ce "Ok, bye" Ya ce "Take care" Daga haka kiran ya katse, na jima tsaye ina mamakin Kiran na Dr. Junaid yayin da zuciyata ke ƙoƙarin gano dalilin son ganina da yake yi, numfashi na sauƙe Sannan na samu bakin gado na zauna ina zame hular da ke kaina, gashina da ya zubo har gadon bayana na shafa sannan na taɓe baki na ce "What a personal issue is he talking about?" Rashin mai ba Ni amsa ya sa Ni jan siririn tsaki na ajiye wayar tawa a gefena sannan na ɗan kishingiɗa, ban aune ba Bacci ya ɗauke Ni. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 17: Kamar daga sama na jiyo muryar Rafi'at na faɗin "Kar Allah ya sa ki tashi, wallahi zuwa zan yi na ce masa kin ce ba za ki zo ba" Juyi na yi tare da miƙa a lokaci guda. Cikin Muryar Bacci na ce "Meye?" Ta ce "kar Allah ya sa ki tashi, BB ne ya ce Na kira ki yana part ɗin Ummi, ki tsaya ɓata lokaci ya ƙara miki wani punishment ɗin..." Ai kafin Rafi'at ta rufe baki tuni na miƙe zaune ina sosa idanuwana. Dariyar mugunta ta yi na ɗan harare ta, kallona ta yi ta ce "Kya ki da shi, Ni dai na isar da saƙona" Miƙewa na yi na shiga toilet na wanke fuskana sannan na ja hijabi na saka tare da ficewa zuwa part ɗin Ummie. A parlour na gan shi zaune ya ɗaura ɗaya akan ɗaya, sanye yake cikin wasu soft rugs da wando kamfanin Adidas yayin da ya wani hakimce yana daddanawa waya, sallama na yi, akan laɓɓansa ya amsa ba tare da ya ɗagoeya kalle Ni ba. Zama na yi a gabansa kamar mai karɓar sadaka, cikin cool voice ɗin da ba na sanin ina daura sai gabansa na ce "BB ga Ni" Sai da ya shafe kusan three minutes Tukun ya ɗago ta duba Ni, daga nan kuma ya ƙara ɗage kansa, kamar ba zai ce komai ba ya ajiye wayarsa gefe sannan ya kira sunana. "Jannat" Amsawa na yi ina faɗin "Na'am" Ya ce "Haushina kike ji ko?" Na girgiza kaina a zahiri while deep down in my heart haushin nashi kam ina jinsa ba kaɗan ba. Ya ce "Kina jin haushina mana, is it because Ina takura muku ko? Ina tauye muku haƙƙoƙinku ko?" Cikin raina na ce ƙwarai kuwa, amma a zahiri sai na ce "A'a" Ya ce "Ki daina cutting ɗina idan Ina magana" numfashi ya sauƙe sannan ya ce "Na gama fuskantarki Jannat, na san cikin ranki ganina kike kamar wani mugu wanda bai son ganin farin cikinku, and it's not like that, Ina ƙara faɗa muku, duk abun da nake muku ke da Rafi'at soyayya ce ba wai ƙiyayya ba, yarinta har yanzu na ɗawainiya da ku shi ya sa ba za ku taɓa fahimta ba, musamman ke jannat, amma with time, wata rana ko da ba a gabana I'm hundred percent sure that Za ki faɗi haka a lokacin da hankali ya zo miki." Shiru BB ya yi, Na ma yi zaton ya gama magana sai kuma na ji ya kuma kiran sunana, kaina na ɗaga ba saci kallonsa Sannan na mayar da shi ƙasa. "Me ya sa in na saka doka ke kike fara ƙetare ta Jannat?" Kaina na ƙasa na ce "me kuma na yi?" Kasancewar cikin raina na yi maganar ya sa bai ji me na ce ba. "Saboda kin raina Ni Jannat Ko kuma kina ganin ban isa ba?" Murya ƙasa-ƙasa na ce "A'a " ina girgiza kaina. Ya ce "Haka ne mana, idan ba haka ba ne why kike son ɓata min rai ko yaushe? Why kike aikata abin da kika san zan iya hukunta ki akansa?" Ikon Allah, na faɗa cikin raina don ban ga dalilin yin duk waɗannan maganganun da yake yi ba. Kallona ya kuma yi ya ce "Na ce muku ba na son ganin ku a social media, Amma kin nuna min cewa ban kai na kafa Miki doka ki bi ba" Zaro idanuwana na yi don har ga Allah na manta da wannan batun, kuma har ga Allah ai ba wani abu nake yi da bai dace ba, beside na ma goge account ɗin nawa tun ranar da ya kama Ni. Kafe Ni ya yi da idanuwansa, jikina ne ya ɗan yi sanyi. "Kin yi shiru, ko so kike ki ƙara ɓata min rai?" Kaina na girgiza ina faɗin "A'a " Ya ce "Kin san dalilin da ya sa nake restricting ɗinku from all those kind of socialization?" Na girgiza kai ya ce "Na san cewa ta this stage of Life da kuke kanku na zafi, idan har ba a saka muku dokoki da kuma tsare-tsaren rayuwa ba za ku tashi ne ƙara zube kamar wasu dabbobi, I know you've so many rights da kuke ganin you're eligible and entitled to them, you see, these social media stuffs da na hana ku wallahi gata nake muku, za ku ga kamar ina daƙushe ku wuri guda amma ba haka ba Ni, kun ga social media nan ko, duk wasu tarin fa'idodi da muke ganin tana da, it has a lot of challenges and disadvantages Wanda ba kowa yake hange ba, idan har aka ce za a bar ku ku yi abun da kuke so to da an samu matsala babba, but tun da kin nuna ke hakan da nake muku ba ki so, fine, I'll give you the opportunity to do as you like, in dai duniya ce, za ki koyi darrussa da dama cikinta" Kamar ba zan ce komai ba sai kuma na ji zuciyata ta ɗan yi sanyi, cikin sanyin murya na ce "I'm sorry BB, ka yi haƙuri kar ka cire hannunka a kanmu" Kallona ya yi yana nazarin maganganun nawa tare da auna su a wani mizani, can kuma ya ce "You can go jannat" Simi Simi na miƙe after saying thank you na koma part ɗin Mommy. Tun da na koma Rafi'at ke tambayata me BB ya ce min amma na kasa faɗa mata. Washe gari muka je school, daf da lokacin tashi sai ga kiran DR. Junaid, gaba ɗaya na shafa'a da cewa jiya mun yi magana da shi cewa za mu haɗu yau, siririn tsaki na ja sannan na ɗaga ina ƙara wayar a kunnena. "Hello Jannat" Na amsa da "hi" Ya ce "Ina yini ya lectures?" Na ce "Alhamdulillah" Ya ce "Ma sha Allah, Allah ya sa dai kun fito daga lectures " "Umm" Ya ce "Ma sha Allah, ina jiranki a cool down ɗin da ke bayan classes ɗinku" "To" kawai na ce, daga haka na yake kiran tare da ɗaukan stuffs ɗina na nufi wurin da ya ce min yana can. Hango shi na yi tun daga nesa yana zaune, ko fa na ƙarasa sai na tsinci kaina da kallonsa, kyakkyawa ne sosai, sanye yake cikin ƙananan kaya kamar ko yaushe, sai da yau babu labcoat akan shigar tasa. Ƙarasawa na yi na zauna akan kujerar da ke fuskantarsa sannan na ajiye stuffs ɗina kan table ɗin da ke tsakaninmu ina faɗin "Wash" Cike da kulawa Dr. Junaid yace "Sannu Jannat" Na amsa "Da yauwa, an yini ƙalau Dr.?" Ya ce "Lafiya lau, Allah ya sa dai ban takura Miki ba" Murmusawa na yi na ce "A'a" Shima murmushin ya yi sannan ya ce "Ma sha Allah, ya lectures din?" Na ɗan yamutsa fuska sannan na ce "Alhamdulillah" Ya ce "ma sha Allah" sai kuma ya yi shiru "Jiya fa i thought za ki ce na zo gidan" Da ɗan mamaki akan fuskata na ce "To me ya sa sai ka zo gida za mu yi Maganar?" Yamutsa fuska ta yi kafin ya ce "Just! Ina son a San Ni a gidan, ko ba komai yanzu ai mun zama ɗaya" Na ce "as in?" Wayancewa ya yi ya ce "E, ke fa kamar ƙanwata kike, kin san fa Ni ba ɗan Azare Ba ne, babu wanda ba sani a nan, family na suna Katsina" Ban ce komai ba sai ma mayar da hankali na da na yi wajen gano inda maganganun nasa suka dosa. Katse min tunanin da nake ya yi da faɗin "Bayan ke ba na kula wata macen Jannat, ko yaushe I'm feeling loneliness in me, babu wani ɗan uwa ko ɗaya a kusa" Murmusawa na yi sai dai ban ce komai, kallona ya yi ya ce "Don Allah ki bar Ni na je gidanku mu gaida da su Mommy, ki ga fa ko Rafi'at ba ta san Ni ba" Mamakinsa ne ya cika min rai, ko me yake nufi only God knows. Haka dai ya yi ta kawo min irin excuses ɗin nan, Ni dai kawai jinsa nake don ko giyar wake na sha ba zan bar Dr. Junaid ya zo gidanmu ba, na kawo shi a matsayin wa? Ai ba zan ma Fara ba, ba da Ni ba, wai gaɗa a kotu. A haka muka ɓata lokaci har aka zo ɗaukana daga nan muka yi sallama na wuce don na ga kiran Rafi'at wanda ya tabbatar min sun zo ɗaukana. Sallama muka yi da Dr. Junaid, ya miƙo min wani ɗan medium giftbox, ƙin amsa na yi sai da na ga ya matsa tare da nuna rashin jin daɗinsa Tukun na karɓa ina mishi godiya, daga nan muka rabu, ya nufi motarsa nima na nufi yadda ta gidanmu ke ajiye. A gajiye na koma gida hakan ya sa ban samu damar ko da tuna wani sashe na hirar tamu da Dr. Junaid ba, sai dare ne na na je ɗauko handout ɗina zan yi karatu na ga giftbox ɗin da ya ba Ni. Zaro idanauwa na yi don har ga Allah na manta da shi, hannuna na saka na ɗauko giftbox ɗin, tsintar kana na yi da son buɗewa na ga meye a ciki, a hankali na fara ware zaren da aka naɗa jiki, baya na ware na buɗe gift box ɗin. Ban san lokacin da na furta "wow" ba Ba komai ba ne a ciki sai wani abu da akayi wrapping cikin wrapping sheet sai kuma card ɗin da ya ja hankalina wanda sosai ya burge Ni, karanta abun da ke jiki na yi ins Murmushi, daga nan na fara ƙoƙarin buɗe gift ɗin da ke ciki. Me zan gani? Chocolates ne iri-iri, haka na bi su ɗaya bayan ɗaya ina dubawa, kusan dukkansu abun da na fahimta sunayensu na da alaƙa da soyayya, kuma idan na fahimta, irin wannan kyautar ana yi ma wanda ake so ne kawai. To amma ai Dr. Junaid ba so na yake ba, its a sisterhood relationship tsakaninmu for now kamar dai yadda ya yi requesting. Tattara komai na yi na saka a drawer daga nan na wuce parlour wurin Mommy. Muna zaune Ya Sadiq ya shigo parlourn. Bayan mun gaida shi ina ganin yadda ya yi wa Rafi'at magana da ido, ganin hakan ya sa na saki wani Murmushi, sosai hakan ya min daɗi, ko ba komai na san sister na ta yi dacen abokin rayuwa. Fuskata na ɗan kwaɓe ina tuna cewa nifa ba Ni da mai so na a yanzu, tsaki na ja har sai da Mommy ta tambaye Ni lafiya, wayancewa na yi na ce mata babu komai, daga haka na fice daga ɗakin na bi bayan ya Sadiq da ya fita yana jiran masoyiyar tasa ta fito. Kallonsa na yi na ce "Ya Sadiq don Allah gobe da yamma za ka ɗan zaga gari da mu?" Fuskarsa ya ɗan haɗe sannan ya ce "Ni ɗin ne zan fita da ku?" Kafe shi na yi da idanuwana tare da faɗin "Kai Ya Sadiq, kaima so kake ka zama kamar BB ko?" Dariya ya yi sannan ya ce "Don na ƙi fita da ku? To ai shi yana fita da ku na gani, Ni jiya kam me ya haɗa ku da mutumin, Rafi'at ta ce min ya..." "Wato sai da ta faɗa maka? Lallai za mu haɗu" Cikin lallashi ya ce "Kin ga, ki yi haƙuri kar ki ce za ki mata magana, kiranki na ce ta yi shine ta ce kina can kwance BB ya ba ki stress" Marairaice fuska na yi na ce "Ai nikam na rasa me yasa BB Bai ƙaunata Ya Sadiq" "Shhhh, waye ya faɗa miki haka, Jannat ai duk yadda nake son ki wallahi ko rabin yadda BB ke sonki nan yi" "Me yasa ka ce haka?" Ya Sadiq ya ce "Ba za ki fahimci hakan ba Jannat, mai iya jurar rashin kunya da rawar kanki sai iya BB ɗin" Kwaɓe fuska na yi kamar zan yi kuka, ganin hakan ya sa shi faɗin "I'm sorry, but I'm saying the fact, ba Kya ji ko kaɗan sister, shi kuma BB kin san ba ya juran rashin ji" "Kaima kana bayansa ke nan?" Na fada kamar zan yi kuka Ya ce "to ai dole na, shi ne limaminmu fa" Na ce "shi ke nan ai" Ya Sadiq ya ce "Yaya Khalil is such a simple man like everyone else, musamman ga wanda ya fahimce shi, da a ce kema za ki fahimce shi Jannat, you're going to find him as the nicest person ever" Waro idanuwana na yi ina faɗin "Tab, wai BB?" Ya Sadiq ya Gyaɗa min kai, gyaran Muryar Rafi'at ta sa ba shiri na juyo ina faɗin "Bari na ba ku wuri ko, a baiwa flowers ɗin ruwa da kyau" na ƙarashe sounding rude Ina ɗan ɗage musu gira. Kasancewar akwai haske da yawa ya sa Ya Sadiq ganin abun da na yi, daƙuwa ya aiko min yana faɗin "Zan yi maganinki ne Sister " Ban tsaya biye shi ba na koma parlour muka ci gaba da kallon wa'azi tare da Mommy yayin da Na bar Rafi'at da Ya Sadiq a waje, suma ba su jima ba coz Rafi'at a tsorace take hakan yasa ta ƙi ba wa Habibyn nata cooperation su yi soyayyar, babu yadda ya iya haka ya sallame ta ta dawo ciki shi kuma ya wuce abunsa. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 18: Kwanan BB uku ya ƙara komawa bakin aikinsa, tsakanina da Dr. Junaid ba a magana, alaƙa ta ƙullu tsakaninmu kai ka yi tsammanin ƴan'uwan jini ne mu idan har ba faɗa maka na yi ba, hatta ƴan class ɗinmu yanzu sun san shi, komai nawa Yaya Doctor, Yaya Doctor, cikin waɗanda suka yarda cewa shi ɗin Yayana ne har sun fara takura min akan na haɗa su suna son shi, this and that, a ɓangaren ƴar'uwata Rafi'at kuwa na rasa me ya sa ba ta son alaƙata da Dr. Junaid after all ta san ba soyayya muke yi ba, kullum tana cikin kushe shi da duk wani abu da ya danganci shi, hatta Abu idan ya kawo min ba ta ƙaunar ko da kallon abun ne, tun ina ɗaukan hakan a ba komai ba har dai na fara tunanin wani abun na daban, na gama lura da ita ko gaisawa za ta yi da Yaya Doctor kanta sama, wanda hakan ba ya min daɗi ko kaɗan don shi ma ya fahimci cewa Rafi'at ɗin ba ta son alaƙarmu da shi, da ya kawo min irin zancen nan sai na yi ƙoƙarin kawo wani zancen don kore wanda muke yi ɗin. A ɓangaren BB bayan ya tafi ma yakan kira mu mu gaisa, zafin nan nashi sai nake ganin kamar ya fara raguwa though ban yi na'am da hakan ba saboda sanin halinsa, yanzu zai iya sauyawa zuwa wani iri daban. Yau gaba ɗaya gidansu Ya Khalid in ka cire Mami da Abba dukkan suna gidan big sis, ciki har da BB. Shi dai BB tun da Sophie da Mufeed suka zo jikinshi sai zuba mishi surutu suke. Sophie ce ta sauƙa daga jikinsa ta nufi wurin Nimrah, yayin da Mufeed ya saki safiyar farin ciki hana faɗin "Ai gara da kika bar min Uncle ɗina" Daga cinyar Nimrah Sophie ta ce "Ai sai ka cinye Uncle ɗin, kuma nima a wurin Mommy Nimrahh zan zauna, idan Uncle ya tafi za ta yi min baking cakes, plenty ones, ko ɗaya ba zan ba ka ba" Yaron ne ya kwaɓe fuska sannan ya dubi BB ya ce "Uncle ina za ka Kaini Bakery nima a min?" BB ya saki wani ƙayataccen Murmushi tare da faɗin "Rabu da Sophie my boy, za mu je Bakery in ba ka son na bakery ma in na je Azare Jannat za ta maka masu daɗi" Kukan shagwaɓa Yarinyar ta saki tana faɗin "Ai dai na Mommy Nimrahh ya fi daɗi, kuma idan Mom ta fita Aiki babu kowa iya Ni za ta yi wa abinci, ko Mommy?" Nimrah da ba ta ce uffan ba tun da yaran suka fara rikicin nasu ta murmusa tare da gyaɗa kanta. Ganin yadda suke shirin ɓata daren da rikicinsu ya sa Ya Khalid faɗin "K, ya kamata mu tafi fa" BB ya ɗan kane wuri guda ba tare da ya ce komai ba, satar kallonsa Nimrah ta yi tare da sakin wani ƙayataccen Murmushi wanda caraf ta yi shi akan idon Big Sis. Basarwa ta yi ta ce "Yanzu sai yaushe ke nan?" BB ya ɗan saki fuska ya ce "Ni kam ina tunanin next week zan wuce Azare, i don't think if we'll have another chance to be here kafin nan" Big sis ta ce "Kai Haba Bro, ka ce dai kana so ka koma wurin Jannat" Da biyu big sis ta yi maganar don ta lura da ƙanwar Tata yadda take satar kallon BB ɗin, ai kuwa Big sis na faɗin haka Nimrah ta ƙara satar kallon BB don ganin face reaction ɗinsa, ganin ya saki Murmushi ya sa ta haɗe fuska ta miƙe tsaye. Big sis ta ce "Ke kuma ina za ki je?" Nimrah ta ce "Ruwa zan ɗauko a fridge" "Shi kuma wannan ruwan dake gabanku da?" "Mai sanyi nake so big sis" tana faɗin haka ta yi saurin barin wurin kamar za ta faɗi, big sis ta jinjina kai tare da dawo da hankalinta wurin su BB. Ya Khalid ya ce "ke dai Big Sis ki bari kawai, mutumina Ya yi ambaliya a tekun soyayya, kuma har yanzu kin san bai faɗa mata cewa yana son ta ba?" Big sis ta dubi BB ta ce "To me kake jira Bro?" BB ya ɗan sosa kai ba tare da ya ce komai ba, yayin da Ya Khalid ya ce "Kin san shi fa, kin san halin mutumin da shegen jin kansa, wallahi kusan shekara yanzu ake nufa ina nuna masa illar rashin faɗa mata ya ƙi ji" Duk abun da ake Nimrah na tsaye tana jinsu, ita ta kasa ƙarasowa ciki ta kuma kasa komawa don gaba ɗaya ta shiga shock da wannan tattaunawar da ake yi. Big sis ce ta dubi BB cikin ido sannan ta ce "Haba ɗan ƙanina, to meye na ƙin faɗa matan kuma? Ai Gara tun wuri ka yi magana kafin wani ya maka shige layi, ka san da zafi-zafi ake dukan ƙarfe ga" "Rabu da shi Big Sis, wallahi duk yadda zan yi K ya faɗawa yarinyar nan yana son ta ya ƙi, ga shi yarinyar Allah ya mata farin jini kamar me" Ya Khalid ne ya faɗi hakan yana ɗagewa BB gira, wani irin banzan kallo ya jefi Ya Khalid da shi, a tare big sis day Ya Khalid suka sanya dariya. "To be sincere bro, zan ba ka shawara ka yi maza ka bayyanawa Jannat soyayyarka, haka kawai nake jin ina son yarinyar tun da kaima kana son ta, ka san mu mata ba ma gane kurman yare, ko da a ce ta san kana son ta In har ba ka faɗa mata ba wallahi za ta iya take soyayyarka ta amshi ta wani, Allah ya kiyaye" "Amiin" suka haɗa baki wurin faɗi. BB ya ce "Thank you Big sis in sha Allah zan ƙoƙarta na ga komai ya tafi yadda ya kamata" "I'll be glad if they happened" "Now are we good to go?" BB ya faɗa yana sauƙe Mufeed daga jikinshi. Tare suka miƙe shi da Ya Khalid wanda yake faɗin "Ina Nimrah kuma?" Big sis ce ta ƙwala kiran Nimrah tana faɗin "Wai shan ruwan ne har yanzu? To ki zo za ku wuce?" Kamar wacce aka jefo Nimrah ta shigo parlourn tana gyara rolling ɗin veil ɗinta "Ayya big sis, na tsaya na ƙara chips ɗin nan ne shi yasa " Murmusawa kawai big sis ta yi tare da miƙewa don yi ma su BB rakiya, har parking space suka rako su BB ya ɗauko wrappers na 1k guda biyu ya damƙawa Mufeed da Sophie kowa a hannunshi Yana faɗin "Sai na dawo ko?" Cikin farin ciki yaran suka nufi Big sis suna nuna mata kuɗin "Mommy kin ga Uncle ya ba mu kuɗi" Big sis ta ce "kun ce wa Uncle Kun gode ne?" Yaran suka ruga suka nufi wurin BB tare da faɗin "Thank you Uncle " Sunkuyawa ya yi ya ja kuncinsu ɗaya bayan ɗaya, ita dai Nimrah kallonsu kawai take gwanin burgewa har take ji a ranta kamar ƴaƴanta ne da babansu, Murmushi kawai ta saki tare da nufar tasu tana faɗin "To big sis, mu kwana lafiya, my baby, next time in zan zo I'll bake some cakes for you" Sophie ta daga tsalle tana faɗin "Thank youuuuuuu" cikin farin ciki. Mufeed ne ya kwaɓe fuska tare da faɗin "Uncle Nima" BB da ya rufe mota bayan ya shiga ne ya bude tare da ɗagawa Mufeed hannu alamun rarrashi." Tayar da mota da Ya khalid ya yi ya sa yaran suka fara ɗaga musu hannu, nan motarsu ta fice zuwa gida. NIMRAH Nimrah ita ce Autar Mami, yarinya ce kyakkyawa son kowa, fara ce, siririya, kana ganinta ka ga bafulatana Usul, bayan kyanta abu na gaba da yake jan hankalin mutane gare ta shi ne nutsuwa da kuma kamun kai, hatta tafiya idan Nimrah na yi abun kallo ne don kuwa ko irin sautin takalmin nan ba ka ji idan tana tafiya, komai nata tana yin shi ne cikin natsuwa, Nimrah na da ilimin addini sosai, ga haddar Alqur'ani kamar me, yanzu haka tana gab da tafiya musabaka ne ƙasar Egypt don wakilta ƙasarta najeriya, a fannin karatun boko ma Alhamdulillah, ta kammala secondary shekaru kusan biyu da suka wuce. Interest dinta akan ilimin addini ya sa ta ci gaba da zuwa makarantun hadda a madadin jami'a. Wani abu da babu wanda ya lura da shi bayan big sis shi ne, Nimrah son BB take, ta lura da hakan ne tun BB Bai jima da fara zama gidansu ba, ranar ita ma ta je yinin gida ba ta mantawa, yadda Nimrah ke bin duk wani motsi na BB hakan ya sa ta dasa Ayar tambaya akan ƙanwar Tata, to yanzu ta gama tabbatarwa don kuwa ko makaho ya ga yadda ta miƙe babu shiri ɗazu daga ji an ambaci Abokiyar takararta zai fahimci inda ta dosa. Sati guda da zuwan su BB gidan big sis BB ya dawo gida, wannan karon sosai ya ba wa kowa mamakin sauyawarsa. A ranar da ya dawo ya sa aka kira mu, kowa da tsarabarshi tun daga kan Abuya, Ummi, Mommy, Daddy, Ya Sadiq, Rafi'at, Ni da kuma auta Ayman. Bayan siyayyar ƴan gida har da na su Mommyn Misau da Mommyn Jama'are, abu dai gwanin burgewa, abun da ya daure wa kowa kai bai wuce ganin tsaraba ta ta fi ta kowa yawa ba, sai dai babu mai bakin magana ciki kuwa har da Ni kaina da tsarabar tawa ta mugun ba Ni mamaki. Washe gari da safe, da yake muna hutun semester ta biyu a aji ɗaya ya sa ban tashi da wuri ba har Rafi'at ta wuce school. Bayan na tashi na yi wanka na fito muka gaida da Mommy da Daddy, sannan na wuce na gaida Ummi, abuya ya tafi wani conference na malaman addini na ƙasa, hakan ya sa na fito da niyyar komawa part ɗin Mommy don gaba ɗaya na manta da cewa BB is home. Har na kusa fitowa daga bedroom ɗin Ummi na ji ta tsayar da Ni "Kun gaisa da Khalil ne?" Na ce "Tab, wallahi har na manta da ya dawo" Ummie ta ce "Dole ki manta ai duk rashin mutuncin da kike masa da ya tashi kawo tsaraba ai bai manta da ke ba, taki ma ta fi yawa" Bakina na ɗan tura gaba, cikin raina na ce "Ai ba Ni Na ce ya kawo min ba" daga haka na fara takawa zan fice, ina ji Ummie na faɗin "Ki tabbatar kin je kin gaishe shi kin kuma yi masa godiya kin ji?" Ban samu damar amsa mata ba ina tura baki na fito, ai kuma sai muka kusa cin karo da shi. A hankali na ce "Ina kwana BB" Kansa ya gyaɗa tare da nuna min kujeru alamun na jira shi, ɗakin Ummie ya shiga can sai ga shi ya fito, Ni kuwa ina tsaye akan carpet kamar wacce ta haɗiyi taɓarya, ina ganinsa har ya ƙaraso ya zauna akan kujera mai zaman mutum ɗaya, sai da ya zauna tukun ya ce "Ba ki iya zama ba ne?" Na ce "Ni?" Ya ce "a'a Ni" Ƙoƙarin zama na fara yi kan carpet na ji ya ce "have a seat" kusan daskarewa na yi saboda mamaki coz tun da nake ji dai ban taɓa zama wuri guda da BB ba, kai ko lokacin da muke yara idan yana sama ba na hawa sama, sai dai ƙasa. Saurin girgiza kaina nayi cikin son dawowa cikin hayyacina, nan na ranƙwashi kaina da yaƙinin cewa kunnena ba su ji min daidai ba, hakan ya sa na ci gaba da ƙoƙarin zama a ƙasa. Muryarsa da ta doki kunnena a wannan karon ita ta sa Ni fahimtar cewa tabbas ɗazu abun da kunnena ya ji gaskiya ne, ɗagowa na yi da niyyar na kalle shi cikin rashin Sa'a idanuwanmu suka sarƙafe da na juna, duk ƙoƙarina na ganin na ɗauke nawa idon abun ya gagara don kuwa ji na yi kamar an manne nawa da nashi wuri guda. Mun shafe kusan daƙiƙu uku kafin na iya janye nawa idanuwan a kunyace ina mai sauƙar da kaina ƙasa Cikin sassanyar Muryarsa ya ce "Can You have a seat ko sai.." Bai ƙarasa faɗin abun da zai ce ba na miƙe na ɗosana mazaunaina akan kujerar da ke fuskantar shi. "Ki zauna da kyau mana, sai ka ce kina gaban wani aljani" Mamaki kalaman nasa suka ba Ni ban iya ɓoye haka ba sai da na saci kallonsa sai dai ga mamakina hankalinsa kwance yake zaune babu wani alamu na ya fadi wani abu da bai kamata ba. Kallona ya yi yayin da ya ciro wayarsa daga aljihu sannan ya ce "Ina Rafi'at?" Na ce "ta tafi schol" "Ke me ya hana Ni zuwa?" Na ba shi amsa da "Muna hutu" Shiru ya yi can ya ce "Fine, ya karatun?" "Alhamdulillah" "Ma sha Allah, Allah ya taimaka" Shiru muka yi can dai na ce "BB mun ga kaya, mun gode Allah..." Katse Ni ya yi ta hanyar faɗin "Allah shi ne abun godiya" Kasa na yi da kaina ina jiran jin abun da zai ce, har na cire tsammanin zai yi magana sai kuma na ji ya ce "Yau za mu fita da yamma, idan Rafi'at ta dawo ki faɗa mata, ku shirya da wuri kun san ba na son African time ko?" Kai Na gyaɗa tare da faɗin "In sha Allah" Ya ce "You can go" kamar wacce ke zaune akan allura haka na miƙe na fice daga parlourn ina haɗawa da sassarfa, wani irin dogon numfashi na shaƙa bayan na fita tare da dafe ƙirjina. Anya wannan BB ne? Yau shi ne har da gaisawa da Ni haka a mutunce? Lallai kayan mamakin BB ba ya ƙarewa. Da wannan tunanin na koma part ɗin Mommy, gaba ɗaya na kasa manta abun da ya faru. Around 3:50pm Rafi'at ta dawo daga school sai da ta yi wanka ta ci abinci Tukun nake faɗa mata ce za mu fita tare da BB anjima, kasa ɓoye mamakinta ta yi tare da faɗin "ikon Allah, anya kuwa ba Ya Sadiq ne ya ce Miki za mu fita ba?". harararta na yi sannan na ce "Tun da dusa ne a idona ban san Ya Sadiq ɗin ba" "To abun dai ya ba Ni mamaki" Na ce "ki tsaya mamaki kina tunanin Ya Sadiq ne zai fita da mu ki yi African time ki karɓi baki punishment ɗin" Dariya Rafi'at ta yi kana ta ce "Kan ki ake ji kuma, duk muguntarki ta ƙare akan ki" Dariya mu biyun muka yi, daga nan kowa ya ci gaba da danna wayarshi. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 19: Ƙarfe huɗu daidai muka fara shirin fita, kwalliya sosai Na yi har Rafi'at na tsokanata wai zan je taron miss world ne nake irin wannan ƙwalliya, laces ɗinmu da BB ya saya mana lokacin graduation muka saka, laces ne masu kyau da tsada da duk yadda mutum ya wulga da shi sai an samu masu yabawa. Ɗinkin doguwar riga ne a sake, ya sha stone kamar an yi ɓarin shi, wanda hakan ke ƙarawa kayan wani irin Aji na musamman, mayafin da zai tafi da kayan kowaccenmu ta ɗauka, muka ɗauki luxury hand bags ɗinmu sannan muka feshe jikinmu da turare. Bakin gado muka zauna muna yaba Kyan junanmu. Wayata ce ta fara neman agaji, ganin sunan BB akan screen ɗin wayar ya sa na yi saurin ɗagawa na kara a kunne ina yi mishi sallama amsawa ya yi sannan ya ce "Hope kun shirya" Na ce "e" ya ce "Ku faɗawa Mommy za mu fita, ina jiran ku a parking space" Na amsa da "To BB" Daga haka ya katse kiran, na dubi Rafi'at na ce "Ke tashi mu yi wa Mommy sallama" Ta amsa da "ok" tana mai ci gaba da danna wayarta, ban bi ta kanta ba na wuce bedroom ɗin Mommy. Mommyn na ganina ta ce "A'a, irin wannan gayu haka Jannat?" Na murmusa na ce "Mommy za mu fita da BB ne" "To, to, Allah ya kiyaye, sai kun dawo" Da "Amiin" na amsa daga nan na fito ina taku cike da ƙasaita. A maimakon na biya mu fita tare da Rafi'at sai na wuce parking space Kai tsaye, farar matarshi da na gani tana shining na tabbatar yana ciki, front seat na buɗe tare da faɗin "Ina yini BB" Ya amsa "Lafiya lau" yana ƙare min kallo. Tsarguwa da na yi da kallon nasa yasa na fara ƙoƙarin rufo murfin motar "Ina Rafi'at?" Ya faɗa yana tsare Ni da ido Sai lokacin ma na tuna na bar ta a ɗaki tana danna waya, cikin ƙiƙina na ce "E, am tana fitowa, Mommy ce ta sa ta aiki" Bai ce komai ba, hakan ya sa Ni saurin ciro wayata na tura mata saƙo, ko minti uku da shigar saƙon bai yi ba na hango ta sai uban sauri take ta nufo inda muke. Back seat na buɗe na shiga, tana zuwa da ta ga front seat wayam ta harari back seat sannan ya yi ƙwafa ta shiga front seat ɗin tana gaida BB. Amsa mata ya yi fuska babu yabo babu fallasa, daga nan ya tayar da motar, tun da muka fara tafiyar na lura da yadda ya kafe Ni da idanuwansa ta cikin madubin motar yayin da sassanyan sautin waƙar Auta Waziri ta "Matata" ke tashi a hankali. Haka kawai na ji yanayin ya fita daban yayin da nake zuciyata ta min saƙayau, time to time nake ɗaga kaina ina satar kallonshi sai dai abun mamaki duk kallon shi da zan yi sai idanuwanmu sun harɗe cikin madubin motar, duk wanda wasa da ake bugawa Rafi'at ba ta sani ba coz she's busy chatting with love of her life. Yaji and grill muka fara zuwa, muka samu seat muka zazzauna, sai da ya tambaye me muke so Tukun aka kawo mana, wani suya da ya sa aka kawo mana mai shegen daɗi muka ci, shi dai kam ba wani ci ya yi ba, ya dai riƙe bottle ɗin peach Yana Sha a hankali yayin da yake kallona a sace, wanda da wuya mutum ya iya fahimtar satar kallon yake yi ba. Idanuwansa ya lumshe yayin da ya ga yadda nake cin suyan hankalina kwance, cikin ransa ya ce "Stubborn jewel" Bayan mun gama BB ya yi settling bills daga nan muka nufi check 'N' buy, tare muka jera da Ni da shi yayin da Rafi'at ke gabanmu, duk layin da muka wulga sai an kalle mu ƙasa ƙasa bakan jiyo wasu na yana yadda muka dace, Ni dai cikin raina cewa nake su daina min fatan kasancewa da BB matsayin couples. Wurin agoguna da turaruka na tsaya, duddubawa na fara har idanuwa suka sauƙa kan wani luxurious wristwatch white colour, hannuna na saka zan ɗauko ai kuwa hannunmu suka haɗu ashe shima shi zai ɗauka, saurin janye nawa hannun gefe na yi, tare da yin gaba da sauri. Wurin chocolates na nufa na fara haɗa pack, Ina cikin ɗauka na ji an min sallama, waigawar da zan yi na ga Yaya Doctor, da sauri na saki fuska ina faɗin "A, Yaya Doctor." Fuskarsa sake ya ce "Sis Jannat, kwana biyu" Na ce "Wallahi ƙalau" Jiya na kira ki kusan sau goma ba ya tafiya, yau ma na yi ta gwada wa still not going, I'm worried Allah dai ya sa lafiya" Murmusawa na yi na ce "Lafiya lau, amma ai wayana a kunne yake" Yaya Doctor ya ce "Ba Ni Na duba" Ba tare da wani tunani Ba na miƙa mishi wayar tawa, yana karɓa Rafi'at ta ƙaraso wajen, ɓata fuska ta yi kamar za ta yi kuka ganin Yaya Doctor, shi kuwa bawan Allah fuskarsa ya saki yana faɗin "Yayarmu ina yini?" Yamutsa fuska ta yi har sai da na ji babu daɗi can dai ta ce "Lafiya" sannan ta dube Ni "Madam ko za mu iya wucewa? Kin san dai da wa muke tafe kika wani kafe ke da ƙato kuna hira " Sosai kalaman Rafi'at suka ɓata min rai coz na lura da gangan ta yi, kunyar Yaya Doctor NE ta kama Ni kamar na toni rami na ɓuya. "Shi ke nan, ki je zan biyo ki" "Za ki wuce ne ko sai na ɗauke ki da mari a nan?" Da wani irin sauri na waiwaya jin Muryar BB a bayana, kafin na juyo tuni Rafi'at ta wuce abun ta, ya rage daga Ni dai Yaya Doctor sai kuma BB. Kallo Mai cike da gargarɗi ya aiko min, babu ɓata lokaci na bar wurin ko wayar tawa ban tsaya karɓa a hannun Yaya Doctor ba. Kallon mamaki Yaya Doctor yake bin BB da shi kasancewar bai taɓa ganinsa ba, ya dai san Ya Sadiq ba shakka. "Haba bawan Allah, don tana budurwarka sai aka ce ba za ta kul..." "Will you shut your big mouth and give the phone ko sai na ɓata maka rai!" BB ya faɗa cikin zafin rai wanda hakan ya haddasa zuwan ma'aikatan wurin don ganin me yake faruwa. "Na'am" yaya Doctor ya faɗa cikin shaƙiyyanci, lallai yau akwai daga in dai ba a raba wannan fitina ba, don kuwa duk wani ji da kan BB wani lokacin gani nake kamar yaya Doctor ma ya fi shi. A harzuƙe BB ya sa hannu ya fizge wayata daga hannun Yaya Doctor ya buga ta da ƙasa har dai da ta tarwatse, daga haka kuma bai ji ta kan mutanen da ke tsaye ba ya dubi Yaya Doctor cike da gargadi ya ce "Kar ka ƙara ganinka da ita, If not! I'll surely make this life miserable to you" Yana Kai wa nan ya bangaje shi ya nufi reception, wayarsa ya ciro ya ƙira Numbern Rafi'at, jiki na rawa ta yi picking. Cike da masifa ya ce "Ni kuke jira na bi na harhaɗa kayan da kuka ɗauka na kai a musu kuɗi?" Ai da sauri Rafi'at ta fito, Ni kam kin fitowa Na yi don kuwa irin ɓacin ran da na gani akan fuskarsa ya sa na shiga wani irin hali da ya zarta a kira da fargaba ko tsoro, dukka Kayan Rafi'at ce ta kai su, yana gama settling bills din ya dube ta ya ce "Saura ki ɓata min lokaci" Wani daga cikin ma'aikatan wurin na gani ta ce "Ɗan uwa don Allah ka taimaka min na fita da kayan nan kar Na ƙara wani laifi" Haɓarsa ya rike ya ce "niiii? Rufa min asiri, wannan mijin naku tsalle ɗaya zai yi a kaina zan daina numfashi" Kamar za ta yi kuka ta ɗauki wasu ta fita da su, sannan ta ƙara dawowa ta ɗauki sauran na kai su Boot. Duk jidon kayan da Rafi'at ke yi nikam ina cikin mota na hakimce duk da cewa cikin raina a mugun tsorace make don kuwa cikina har wani irin kuka yake yi alamun yana son ɓaci, haka muka yi ta zama da Ni da shi har Rafi'at ta gama shigowa da kayayyakin, tana gamawa ta shiga front seat ta zauna. Da wani irin speed BB ya ja motar, muna isa gida kowaccenmu ta buɗe motar, cikin hanzari na bar wurin na nufi sashen Mommy yayin da na bar Rafi'at a wurin, tsayar da ita BB ya yi ya ce "Ni zan fitar muku da kayan?" Mamaki ne ya kamata ganin ita ba da laifi ba ita da kwasar ganimar laifi. Babu yadda ta iya haka ta kwashi kayan ta shiga mana da su ciki. Bayan mun fice daga motar BB ya sauƙe wani dogon numfashi tare da sakin wani zazzafan huci, kansa da ke masa ciwo ya dafe tare da resting kan jikin seat ɗin motar. Akan saman laɓɓansa ya ce "Ya Rab! Help me" Kusan mintuna biyar ya shafe a wannan yanayin kafin ya samu damar ɗaga kansa ya kuma buɗe idanuwansa da suka yi ja. Hannunsa ya ɗaura akan saitin zuciyarsa tare da rintse idanuwan nasa Cikin raunin murya ya ce "Surely her love will kill me one day!" Kansa ya girgiza cikin jimami ya ce "What a terrible love is this? Me ya sa Ubangiji ya jarabce Ni da ƙaunarta ne haka?" Idanuwansa ya lumshe Sannan ya haɗiye abun da ya tsaya masa a maƙoshi. Tambayar kansa yake dalilin da ya sa maza ke chasing abun da yake so after all shi ya raini abun ne domin ya mallake shi, ya inganta abun ne domin yana ƙaunarsa. Why will guys be chasing his heart's desire so cruelly beside shi bai taɓa yi wa wani hakan ba. Kansa ya jinjina cike da ƙarfafawa kansa guiwa ya ce "The game must have reached its end! Now it's my right time to play and win!" Hannunsa ya dunƙule tare da naushin iska sannan ya ce "Idan har ban bayyana mata soyayyata ba for sure zuciyata za ta yi bindiga ita kaɗai, all the dreams I've been wishing to fulfill will went in vain" Saurin girgiza kansa ya yi ce "that's not even possible! She's mine, mine alone! And I love her!" Tsintar kansa ya yi da lumshe idanuwansa, a cikin wannan yanayin ya share kusan daƙiƙu biyu kafin ya iya buɗe idanuwan nasa. Numfashi ya sauƙe sannan ya shafa kansa, ɗan waigawa ya yi kamar wadda ya tashi daga ciwon hauka ya kai hannunsa kan fuskarsa ya shafa. "What the heck am I doing?" Hannunsa ya kai ya fito daga motar, direct part ɗim Ummie ya nufa, TV da ya gani kunne ya sa shi girgiza kansa sanin aikin waye, kashewa ya yi daga nan ya shige bedroom dinsa. Akan lafiyayye gadon nasa ya baje yana sakin nishi. Kansa da har yanzu ke Sara mishi lokaci zuwa lokaci ya ɗan dafe tare da sauƙe ajiyar zuciya, idanuwansa ya lumshe kana ya ce "I love her! Madly in love with everything about her from day one I took her on my hands!" Cikin rashin ƙarfin jiki wanda ya gauraye da kasala ya yi furucin, a wannan yanayi ya ci gaba da kasancewa na shauƙi da kuma kishin bar ƙaunarsa kiraye-kirayen sallar magrib ya sa shi miƙewa duk da cewa har lokacin yana jin kansa da nauyi sosai. Toilet ya shiga ya yi Tsarki sannan ya ɗauro alwala, daga nan ya fice masallaci, ba shi ya dawo gidan ba sai baya sallar isha' suka dawo tare da Abuya wanda ya matsa mishi a hanya da tambayar Ko lafiyarshi ƙalau. Numfashi kawai BB ya sauƙe tare da ƙara jin ƙaunar ɗan'uwan mahaifin nasa cikin ransa, shi kansa wani lokacin ya kan yi mamakin irin ƙaunar da ke tsakaninsa da waɗannan mutane, wato Abuya da kuma Ummi, a duk lokacin da hakan ta faru yakan tabbatarwa kansa cewa ƙauna da min indillahi, domin kuwa yadda Ummi da Abuya ke girmama sha'aninsa Mommy da Daddy Sam ba su yi, Ni kaina wasu lokutan a lokacin da ƙuruciya ta min yawa tunanina duka ya tafi ne kan cewa Abuya da Ummi su suka haifi BB, yadda Ummi kuwa ke hukunta Ni idan na yi wani abu duk ƙarantarsa sai na ga kamar dama can ita ɗin ba mahaifiyata ba ce girma da hankali da na yi ne na fahimci cewa ita ɗin dai ita ta haife Ni, ko da iya kamannin da muke yi za tabbatar da hakan. Abincin dare ma da kyar BB ya iya ci hakan ma saboda yadda yaga Abuya da Ummi sun nuna damuwarsu akan shi ne, babu yadda ya iya haka ya taɓa daga nan ya wuce bedroom ɗinsa. Wanka ya yi ya sauya zuwa kayan baccinsa, wasu tsadaddun riga da wando masu taushin gaske, turaruka ya fesa sannan ya ɗauko Alqur'aninsa ya karanta wasu shafuka daga ciki, daga nan ya mayar ya ajiye bayan ya yi tawassul da karatun da ya yi tare da roƙon Ubangiji ya sauƙaƙa masa soyayyata da ta kanainaye zuciyarsa, ya sanyaya masa ita kada ta zamo solar mutuwarsa. Kwantawa ya yi akan gadonsa tare da lumshe idanuwansa. Take tunanin abar ƙaunar tasa ya yi wa zuciyarsa ƙawanya tare da hana shi sakat, saɓanin wasu lokuta a baya da in har wani invador ya shiga rayuwar Jannat yakan kasa yin Bacci ne sakamakon ɓacin rai da kuma haushin Jannat ɗin, yanzu sam bai jin haushin nata sai dai haushin intruders ɗin. Tun da muka dawo ban kuma barin ɗakinmu ba, kayan ciye-ciyen da muka siyo muka ci bayan mun bawa Kowa abun da muka sayo mishi. Washe gari da yamma na yi wanka abuna na sanya wata doguwar rigar material ɗina Mai kyau. Fitowa Na yi don na je part ɗin Ummi kasancewar yau kwata-kwata ko gaisuwar safe ban samu na shiga mun yi ba saboda lokacin da na tashi ban tarar da Rafi'at a gida ba. Bayan na je na gaida Ummi na fito zan koma part ɗin Ummi, vibration ɗin da wayar Rafi'at da na fito da ita ke yi hakan ne ya sa Ni tsayawa cak ina duba sunan mai kiran. Idanuwana na zaro ganin sunan BB akan fuskar wayar, take memoryn jiya ya dawo min, har na yanke shawarar ƙin picking sai kuma na tuna da cewa zan iya janyowa Rafi'at ɗin matsala wurin BB, hakan ya sa na ja siririn tsaki a bayyane, ganin wayar na shirin yankewa ya sa Ni dole ɗaga wayar tare da kara ta a kunnena zai famar zazzare idanuwa nake kamar ina gabansa. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 20: Wani abu da ya tsaya min a wuya na samu na haɗiye kafin na iya furta sallama cikin sanyin murya, amsa min ya yi a nashi ɓangaren cikin wata cool voice, saurin gaishe shi na yi, ga mamakina na ji ya amsa a sanyaye kamar dai ba shi ba, ajiyar zuciya na sauƙe cikin raina na ce "Don bai gano da wa yake magana ba ne" Ina jin sa yana "Hello, Hello" na yi banza da shi, sai kuma na yi sauri yanke kiran tare da taɓe baki, cikin raina na ce "oh! Babban Yayanmu Mai halin tsiya da na kirki ke nan" yayin da a zahiri kuma na fara ƙoƙarin komawa don na san definitely he's going to call back tun da bai gama faɗin abun da zai ce ba. Shigowar wani kiran nasa ne ya ƙara min karsashin haɗawa da sassarfa, sai dai ban kai ga isa ba kiran ya yanke, hakan ya sa Ni jan tsaki na ce "Duk ya sa ina ji na wata iri saboda rashin wayata a hannuna." Part ɗin Mommyn na shige, Mommy da ke parlour ta zube Ni ta ce "Daughter unguwa za ku fita ne yau ma?" Na ce "A'a Mommy, daga part ɗin Ummi nake" "To" kawai Mommyn ta ce, daga haka na wuce ɗakinmu, Rafi'at da ke kan sallaya na duba na ce "Hajiya ga wayarki, masifaffen yayanmu ne yake kira, Ni kuma kin san yanzu ga akuya ga kura muke da shi" Dariya Rafi'at ta yi sannan ta ce "After all duk akaina yake sauƙe fushin ba?" Na ce "Um, can dai ta matse masa" Rafi'at ta ce "Ta matse muku dai, daga ke har shi, tun da ku kuka yi abun mu" Na so ba ta amsar da ta dace sai kuma na ga ta kara wayar tata a kunnenta, ganin haka ya sa na haɗiye maganar in ta gama na faɗa. Ƙoƙarin haye gado nake na ji tana faɗin "ki karɓa Jannat" Juyowa na yi na dube ta, ƙasa ƙasa ta ce "Cewa ya yi na ba ki, ƴar raunin wayo" Kamar ba zan karba ba sai kuma na karɓi wayar tare da kara ta a kunnena. Sallama na yi, ya amsa, sai kuma na jinya ce "kina ji?" Na amsa masa da "E ina ji" Ya ce "Ki same Ni a garden yanzu, kar ki ɓata min Lokaci kin ji?" Kai Na Gyaɗa kamar ina gabansa, take na ji wayar ta katse alamun ya gama faɗin saƙonsa, cikin kwaikwayon Muryarsa na ce "Ki same Ni a garden yanzu, kar ki ɓata min lokaci kin ji?" Fuskata na yamutsa sai kuma na ji dariya ta kama Ni, sai da na yi mai isa ta Tukun na taɓe baki na ce "he always sounds authoritative kamar yana filin daga. Idanuwana na yi rolling kafin na iya gyara hulana da ya zame. "Uhm" abun da na iya fadi ke nan daga nan fara ƙoƙarin amsa kiran BB gudun kada na janyo wa kaina wani lukutin laifin bayan na jiya kuma. Miƙa ma Rafi'at wayarta na yi wacce ke mitar wai ta gaji da ara min waya. Ƙoƙarin fita nake na ji ta ce "idan kin je ki ce ya biya ki taki da ya fasa miki " Daga yadda nake na ce "Za kuwa ki gani." Mommy da ke parlour na wuce, kai tsaye garden ɗin na nufa zuciyata na bugun tara-tara tare da addu'ar Allah ya sa mu wanye lafiya da shi. Can nesa kaɗan a favourite spot ɗin shi na hango shi, ƙoƙarin daidaita kaina na yi ina mai jan dogon numfashi. Ƙarasawa wurin na yi na masa sallama. Sau ɗaya ya ɗago ya kalle Ni ya ce"Wa'alaikumus Salam" Waskewa na yi na ce "BB ga Ni" Da hannu ya nuna min kujerar da ke fuskantarshi, ba musu na zauna kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna. Wayarsa da yake dannawa ya ajiye kan table ɗin da ke tsakaninmu sannan ya dube Ni. "Janaat" ya ƙira sunana cikin wata tausasasahiyar murya, ɗagowa na yi na ɗan kalle shi ina faɗin "Na'am" Shiru ya yi kamar bai da niyyar magana can kuma ya ƙara kiran sunan nawa, Ni dai ban amsa ba wannan karon don na riga na lura da cewa sunan nawa na mishi daɗin furtawa ne. "Ki nutsu magana nake so mu yi" Dim! Na ji zuciyata ta buga da wani irin ƙarfi jin ya ce zai yi magana da Ni, abu ɗaya da ya zo min rai bai wuce tsoron kada ya tayar da maganar Yaya Doctor ba ne. "Kina ji na ko?" Na gyaɗa kai ina faɗin "E" "Jannat ki faɗa min gaskiya a tambayoyin da zan miki, hakan shi zai sa ki samu rangwame akan hukuncin da na yanke a kanki, kika min ƙarya kuma kin sani, zan gane" Dim na ji gabana ya kuma bugawa. "Jannat kina karatu yadda ya kamata kuwa?" Wata irin ajiyar zuciya na sauƙe jin tambayar tasa, a hankali na ce "E BB" Ya ce "shi ke nan. Amma me yasa ko yaushe kike son yin abubuwan da na hana ku?" Shiru Na yi ina tunanin amsar da zan ba shi, can kuma na ce "Kawai ƙaddara ne, amma ina kiyayewa BB" Kansa ya jinjina ya ce "Fine, kina gani kamar na tsane ku ko?" Na girgiza kai, ya ce "Haka ne mana, kina ganin kamar ina hana ki enjoying rayuwarki ko?" Kaina na kuma girgizawa, Murmushi ya yi wanda ya so bani mamaki kana ya ce "Haka ne mana Jannat, komai da nake yi saboda gobenku ne, ina so ku yi rayuwa mai kyau wacce ku kanku za ku yi alfahari da ita, rayuwar da ba za ku yi nadama Ba, wani da yake rayuwa da ku ma ba zai yi Allah wadai da ku ba." Kaina na jinjina tare da ƙara mayar da hankalina ga saurarensa. "Idan har kuna so na fita sha'aninku don Allah kada ki ɓoye min Jannat, kada ki rufe kanki ki faɗa min" Kaina na girgiza na ce "Don Allah BB ka yi haƙuri, wallahi muna ƙoƙarin kiyaye dokokin da kake gindaya mana, ajizanci ne irin namu a wasu lokuta" Cike da gamsuwa ya jinjina kai sannan ya ce "Jannat ki faɗa min wani abu da nake muku wanda ba kwa so, kuke ganin ya kamata na gyara" Wannan furucin na BB ya mugun ba Ni mamaki har ban san lokacin da na ɗago idanuwana na kalle shi ba kansa ya jinjina tare da faɗin "E, ki faɗa min don Allah" Cikin raina na ce, ai kai din ne ba ka da alƙibla ɗaya BB. "Kin yi shiru" Na ce "Babu komai" Ya ce "akwai fa, ki faɗa min kar ki ji tsoro, ba abun da zan miki, beside Ni na tambaye ki" Ajiyar zuciya na sauƙe kana na ce "Babu komai fa, kawai dai, muna so ka zama so friendly kamar Ya Sadiq." Harara ta ya ya ce "Ai Ni da shi ba ɗaya ba ne, wato kun fi so na yi ta wage muku baki kamar wani sakarai ko?" Dariya na ɗan yi sannan na ce "a'a, kawai dai muke hira irin ta ƴan'uwa " Ya ce "Fine, iya abun da kuke so na sauya ke nan?" Na ce "E" haɗe da gyaɗa kaina. Shirun wasu sakanni muka yi gaba ɗayanmu. BB ya ce "Ya studies?" Na ce "Alhamdulillah" Kansa ya jinjina ya ce "Yanzu saura shekara nawa ku kammala?" Kaina na ɗaga alamun lissafi nake sannan na ce "2 years ya rage" Idanuwansa ya ɗan waro kana ya ce "Shi ke nan, study hard please, ban da biyewa samari" Kaina na gyaɗa fuskata ɗauke da Murmushi na ce "In sha Allah " Shiru muka yi kowa na yin zance da zuciyar shi, Ni dai har yanzu na kasa daina mamakin yadda BB ya sauya Lokaci guda, na yi tsammanin zai kawo zancen yaya Doctor sai na ji shiru. Ke nan dai ya min zuru ne? Na tambayi kaina, yanke shawarar yin shiru Na yi kamar yadda shi ma ya yi sai dai zuciyata ta ƙi aminta da hakan yayin da take ingiza ne ga ba shi haƙuri kawai a wuce wurin. "BB" na kira sunanshi a sanyaye. Gira ya ɗage min alamun yana ji na, hakan ya sa kai tsaye na ce "I'm sorry for the other day" Kamar bai gane me nake nufi ba ya ce "For?" Na ce "For Dr. Junaid, ba wani abu ba ne tsakani...." "Shhhh, ya wuce, now we're friends" Da mamaki na kalle shi jin kalamansa, kansa ya jinjina cike da tabbatarwa ya ce "Yes! But if you abide by my rules, in Kuma kuka sauya I'll Surely change also" Ƴar dariya na yi na ce "Deal!" Ya jinjina kansa sannan ya ce "For your phone, I'm sorry, in Sha Allah I'll buy you another one" Kaina na sunkuyar na ce "Thank you" Ya ce "don't mention" Shiru muka yi, can ya ɗago ya dube Ni ya ce "Za ki iya tafiya" Na ce "to na gode BB" Daga haka na miƙe na bar wurin. Ko da na iso bakin part ɗin Mommy tsayawa na yi ina wawwaigawa ko ina kamar wata maras gaskiya, sai da na tabbatar babu kowa tukun na saki wata ajiyar zuciya ina jinjina kaina. "Wai anya BB ne wanna kuwa?" I asked myself, rashin mai ba Ni amsa ya sa na jinjina kai tare da shigewa sai wani Murmushi nake saki. Ko da na shiga ɗakinmu ban cewa Rafi'at uffan ba sai ma kwantawa da na yi gefenta ina lumshe idanuwa Ni kaɗai sai Murmushi nake saki. Waseh gari da safe bayan Rafi'at ta fita school BB ya aiko Ayman ya kira Ni, ko da na je bayan mun gaisa sai wani fara'a yake min kamar ba shi ba, ban yi mamakin hakan ba sai dai na ƙara tabbatarwa kaina cewa ya sauya sosai. "Ko za ki taimaka ki girka min White spaghetti da sauce Amma da jan mai?" Dariya na yi na ce "BB manja ake cewa ba jan mai ba" Ya ce "Lallai ma BB" Har na juya zan fita ya ce "Saura ki saka attaruhu da yawa, I'm going to deal with you" dariya na kwashe da ita ina faɗin "To" *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim CHAPTER 21: Daga haka na nufi kitchen na dafa masa kamar yadda ya bukata sannan na yi preserving nakai mishi ɗakinsa. Godiya ya yi min daga nan na fito ina ƙara mamakin BB. Duk wannan haushi da tsanar tasa da na yi ta ji a baya yake na ji sun yaye kamar ban taɓa ba, Ni kaina hakan ba ƙaramin mamaki ya ba Ni ba, amma dai na danganta hakan da ƴan'uwantaka ne a kuma gudanuwar jini ɗaya a gangar jikinmu. Yinin ranar haka na yi shi cikin farin ciki na rasa dalilin hakan, haka Rafi'at ta saka Ni gaba ta tambayar Ko Lafiyata ƙalau don ta kama Ni several times Ina smiling Ni kaɗai wanda nima kaina ina mamakin hakan. Ko da ta ga na share ta sai ita ma ta watsar da zancen daga nan ta shafa min lafiya. Yau ta kama juma'a, na je gaida Ummie da safe muka haɗu da BB, gaishe shi na yi ya amsa fuska sake, daga nan na shiga muka gaisa da Ummi wacce ke kitchen da alamun baking take yi don ƙamshin gashin nata gaba ɗaya ya addabi ƙofofin hancina har ina jin kamar na ci babu, ina fitowa daga kitchen ɗin na ga BB tsaye ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa cikin wata irin tsayuwa irin ta dakakkun mazan nan masu jini a jika. Shirin wucewa na yi na ji ya ce "Jira Ni mu fita" Ba musu na tsaya, taku ɗaya ya yi ya iso Ni, take wannan sassanyan ƙamshin nasa da ban taɓa jinsa a jikin wani mahaluki ba bayan shi ya doki ƙofofin hancina, idanuwana na lumshe yayin da bugun zuciyata ya fara fita da sauri sauri. A jere muka fita daga parlourn, ba tare da ya kalle Ni ba ya ce "Ya kika yi shiru?" Na ce "Ai ba ka son surutu" A ba zata na ji ya ce "Ban da naki surutun" Saurin tambayar sa na yi don tabbatar da abun da na ji, maimakon ya maimaita min sai na ji ya ce "Ba ko yaushe ba" Wani Murmushi ne ya suɓuce min, a tare muka shiga parlour lokacin shima murmushin yake yi. Mommy ce ta kalle mu fuskarta dauke da Murmushi ta ce "A'a, ku kuma daga ina?" Cikin jin kunyar mommyn na ce "Na je gaida Ummie ne shi kuma ya ce zai zo nan" Na yi saurin faɗin hakan ne gudun kada Mommyn ta kawo wani batun cikin ranta. Satar kallonsa na yi, ganin wani ƙayataccen Murmushi akan kyakkyawar fuskarsa ya sa na ɗan sunkuyar da kaina ƙasa tare da wucewa ɗakinmu. Gaisawa BB suka yi da Mommy, its dai Mommy sosai ta yi farin ciki da ganinmu tare har ma ta fara ƙisssima abun da na ƙi a cikin ranta. Abun ku da manya tuni Mommy ta hasaso wani abun tsakanina da BB Wanda ya samarwa kanta tabbacin cewa ɗan nata ya faɗa tarkon soyayyata ne, ko da BB ya fita murmusawa Mommyn ta yi ta ce "Allah ya tabbatar musu da alkhairi" ko ba komai tana sa ran cewa ina har wannan hasashen nata ya zama gaskiya to fa ba ƙaramin dacewa muka yi da juna ba, wani abu da ba ta sani ba shi ne, Ni dai kam ba na jin wani abu mai ko da kamanceceniya da soyayya ne dangane da BB ɗin cikin raina. Ba dai kai tsaye zan ce ba na ƙaunarsa ba, idan na ce haka na san ƙarya ma nake, don ko a da da babu wani kusanci tsakaninmu ba wai na tsane shi ba ne, sai dai kuma ina jin haushinsa ba shakka. Abu ɗaya da zuciyata ke haska min akan alaƙata da BB shi ne ƴan'uwantaka, ina jinsa yanzu kam a jikina sosai, domin wannan zumunci da yanzu muka fara ya taka rawar gani wajen samar masa da gurbi da musamman cikin zuciyata. Wuraren ƙarfe huɗu da rabi na yamma bayan Rafi'at ta dawo daga school, muna zaune akan gado muna taɗin zuwa Misau. Kallona Rafi'at ta yi ta ce "Ke labari da ɗumi ɗuminsa" Kusa da ita na matsa ina faɗin "Ba Ni Na sha" Ta ce "Ke dazu da safe na je gaida Mommy BB ya yi zance Dani" "Zancen me?" Ta ce "Wallahi kamar ba shi ba, har da tambaya na ya school? Ina maida hankali kuwa? Ke har Murmushi ya min" Ajiyar zuciya na sauke na ce "Um, lallai kin ciri tuta" Ta ce "Wallahi kuwa, To shima ai da haka yake mana ai za mu fi jin dadi" "Uhm" kawai na ce, ban kuma ba ta labarin tawa dramar da shi ba, haka kawai na ji ba sai na faɗa mata ba. Washe gari dukkanmu muna gida daga Ni har Rafi'at. Da daddare wuraren ƙarfe takwas na dare muna gama dinner muna zaune a parlour muna kallon wani Korean series Mai sunan perfect crown a wayar Rafi'at when suddenly her phone rang. Tsaki na ja saboda an zo wurin rashin hankali kawai aka kira, murya ƙasa-ƙasa Rafi'at ta ce "Ke BB ne, bari na ɗaga" Ban ji me ya ce mata ba sai na ji ta ce "To BB, e, yanzu ma" daga haka kuma ta sauƙe wayar. Kallona ta yi ta ce "BB na kiranki, wai ki same shi a parlourn Ummi" Tura bakina gaba na yi, Rafi'at ta kalle Ni ta ce "Kya ji da shi ai" Banza na mata daga nan na zari Hijab ɗina na fita hankalina kwance cikin raina ina mamakin irin wannan kira da BB ya min Wanda a tarihi zan iya cewa hakan ba ta taɓa faruwa ba. Zaune na tarar da shi a parlour ya yi zaman naɗe a kan carpet yayin da ya yi resting kansa jikin kujerar idanuwansa na lumshe kamar mai bscci. Sallama na yi, ya amsa ba tare da ya motsa ba, ɗan nesa da shi na zauna tare da gaishe shi, sai lokacin ya sauƙe kansa ƙasa tare da gyara zamansa, fuska sake ya amsa min yana faɗin "Na yi tunanin ai kin yi bacci" Na ce "Tukunna dai, kallo ma muke" "Me kuke kallo?" Na ce "K drama ne" Kansa ya jinjina sai dai ga mamakina bai ce komai ba, Nima shirum na hi, ganin bai da niyyar magana ya sa na ce "Rafi'at ta ce kana son ganina" Cikin Wata kasalalliyar murya ya ce "E" Na ce "To Allah ya sa lafiya" ya amsa min da "Amiin" "Jannat!" Na ji muryarsa ta kira sunana cikin wani irin salo da zan iya cewa ya kere duk wani wanda ya yi amfani da shi a baya. Shiru ya yi kamar mai tattara kalaman da zai yi amfani da su ya ce "Ina so ki ban aron hankali da kuma lokacinki, there's something important I want to discuss with you" Kaina na jinjina tare da ƙara nutsuwa wuri guda duk da cewa deep down my heart I'm wondering what is he discussing with me right now da ba zai bari sai gari ya waye ba. "Jannat" ya ƙara kiran sunana tare da gyara zamansa "Ina so ki fahimce Ni, kuma ki ɗauki duk wata kalma da zan furta a yanzu a matsayin wani sirri da ke fitowa daga ƙarƙashin zuciyata wanda na jima ina ɓoyonsa" Duk da cewa maganar tasa ta zo min a wani irin bauɗe hakan bai hana gabana faɗuwa ba. Wani irin dogon numfashi ya ja da Ni kaina sai da na saci kallonsa. Ƙasa ya ƙara yi da muryarsa kamar mai raɗa ya ce "Ba komai nake son sanar da ke ba Jannat, illa iyaka ina ƙaunarki, ina sonki kuma ina so na rayu da ke zuwa numfashina na ƙarshe" A ɗan firgice na ɗago kaina tare da kallonsa sai dai yanayin fuskarsa da na gani ya cire min shakkun tunanin da nake akan kalamansa da suka min sauƙar ba zata a cikin kunnuwana. Ganin kamar a rikice nake ya sa shi ƙara faɗin "Yes Jannat, i love You, ina son ki, ina ƙaunar ki, sannan ina so na rayu da ke tsawon numfashina" Wannan karon kallon wadda ya fice daga hayyacinsa nake masa, don na san ko a mafarki hakan ba za ta taɓa faruwa ba matsawar dai BB ɗin na cikin hayyacinsa, gaba ɗaya kaina na ji ya cushe na kasa yin ko da kyakkyawan tunani ne, anya kuwa BB ya san me yake faɗi? Anya kuwa ya san da wa yake magana? Saurin girgiza kaina na yi ina ƙara tabbatarwa kaina abun da zuciyata ke raya min. Tabbas wannan ba BB ba ne, ba dai wannan miskilin yayan namu ba ne da izza da kuma taƙama suka gauraye jinin jikinsa, idan kuma har shi ne to tabbas ba ya cikin hayyacinsa. Wani sashe na zuciyata ne ya yi saurin tunatar da Ni cewa shi ne, yayin da ɗaya sashen ke faɗin Ko dai ya sha wani abun ne? A'a, BB ba ya shan komai, ko sigari da ake cewa sojoji na sha zan iya shaidar Yayanmu ba ya sha. Kamar ya san me nake zantawa cikin raina kwatsam na ji ya ƙara kiran sunana. "Kar ki yi mamakin abun da na faɗa miki, Ni ɗin dai Ni ne, ban sha kayan maye ba bare ki yi tunanin ba na cikin hayyacina, hasali ma Ni na kira ki Saboda fallasa wannan daɗaɗɗen Sirrin da na jima ina adanawa gudun kada wata rana riƙe shi ya yi ajalina." Ɗan dakatawa ya yi kafin ya ci gaba "Na san kina cikin ruɗani da kuma fargabar kalamaina, kina da buƙatar tabbatar da su sakamakon ban taɓa ajiye wata alama da za ta sa ki fahimci hakan ba" "Jannat! Ina son ki ba batun wasa ba, duk wata takura da kike ganin ina muku saboda ke ne, saboda ƙaunar da nake miki ne, saboda ina son matar da zan aura ta kasance bar kwatance wurin kyawawan ɗabi'u, ta'ammali kuma da wasu maza a waje da nake ƙoƙarin yi muku Shamaki da shi Jannat, saboda ina tsananin kishinki ne, a duk wata rana da zan yi arba da ke wani namijin bayan Ni na magana dake nakan kasa rintsawa, zuciyata takan yi nauyi sosai har nakan ji kamar za ta daina aiki." Ni dai a wannan lokacin ba zan iya banbance halin da nake ciki ba saboda tsananin mamaki, na yi ƙoƙarin auna kalaman nasa a wani scale, zuciyata ka sa yadda cewa shi yake furta min su, to idan ma shi ne babu shakka kawai yana faɗa ne don Ni matsayin tatsuniya ɗaya da wannan jawaban masa da yake min. Shiru ya yi don ya huta sannan ya ci gaba "Jannat, kin san tun yaushe na fara sonki?" Kamar wata wacce ta rasa tunaninta na girgiza kai, wani irin sihirtaccen Murmushi ya saki wanda ke ɗauke da wasu sirrika da Ni ban iya fahimta kana ya ce "Tun ranar da aka haife ki! A ranar babu kowa a gidanmu daga Ni dai Ummi, Ni ne nan mutum na farko da na fara daukar ki a hannunsa bayan Ummi, Ni ne wanda ya fara sanar da ƴan'uwa samuwarki, tun daga wannan ranar da na ɗauke ki Jannat! Daga ranar Ubangiji ya dasa min matsananciyar so da kuma ƙaunarki ta yadda har nake jin zan iya sadaukar da komai nawa saboda ke." Kansa ya shafa, sannan ya ce "A lokacin ba ki da wayau, amma iyayenmu sun shaida wannan ƙauna da na nuna Miki, sun shaida sadaukarwar da na yi ta yi saboda ki yi farin ciki ki kuma rayu cikinsa na har abada, ki sani da soyayyarki na girma har na kai wannan matsayin da nake ciki a yanzu." Sunana ya kira a sanyaye kafin ya ce "Ki saka idanuwanki cikin nawa" kasa yin hakan na yi sai ma ƙas da kaina da na yi, ba tare da ya ɗauke nashi idon a kaina ba ya ce "ba zan taɓa takura ki ki so Ni ba, zan ba ki zaɓi ki yanke hukuncin da kika yi na'am da shi, ba zan taba fitar da wannan sirri ba har sai lokacin da kika yi na'am da Ni, don fitar da shi kan iya jawowa iyayenmu su Miki dole ko da kuwa ba kya so na, ba zan aikata wannan KUSKUREN ba, Zan ba ki lokaci, ki nutsu kuma ki yi tunani, fatana da kuma roƙona ɗaya shi ne, ki dubi dakon ƙaunarki da na yi na tsawon shekaru kada ki duba abubuwan da na Miki a baya wanda na riga na miki bayaninsu yanzu, ki yi min adalci wurin yanke hukuncin Jannat" Shiru ya yi, nima kuma a nawa ɓangaren shirun na yi yayin da kaina ke ƙasa ina wasa da ƴan yatsuna. Ƙoƙarin miƙewa ya fara sannan ya ce "Tashi mu je na raka ki, dare ya fara" Ba musu na miƙe tsaye, ya yi gaba Ni kuma na take masa baya, har bakin part ɗin Mommy ya raka Ni tukun ya ja gefe ya ba Ni hanya na shiga, ganin zan wuce ba tare da na ce da shi wani abu ba ya sa shi faɗin "Ba za ki tsaya mu yi sallama ba?" Babu yadda na iya haka na tsaya, abu ya miƙo min ya ce "Karɓi wannan" Leda ce fara ban san meye ciki ba, hannu na saka na karɓa tare da faɗin "Na gode" Ya ce "Sai da safe ke nan?".kaina na gyaɗa "Shi ke nan, ki yi bacci mai daɗi, sai da safe" Simi simi na wuce kamar wacce ta kamu da matsalar ƙwaƙwalwa, juyowa na yi a lokacin da na isa bakin ƙofar ɗakinmu to my surprise Yana tsaye a wurin, hannu ya ɗaga min, daga haka na yi saurin shigewa ciki. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 22: A ɓangaren BB yana ganin Jannat ta shige ɗaki ya sauƙe ajiyar zuciya, ko ba komai bayyana wa Jannat wannan shirin ya sa ya ɗan samu relief a zuciyar shi, ko ba komai yau ya samu damar amayar da abin da ke cikin zuciyar shi na wasu shekaru masu yawa. Part ɗin Ummi ya koma sannan ya rufe musu don tuni Abuya ya dawo gida bai kuma ƙara fita ba, bedroom ɗinsa ya shige tare da samun bakin gado ya zauna yana sakin murmushi. Akan laɓɓansa ya ce "Farin ciki sai ranar da Jannat ta mayar min da martani cike da tsantsar so na da kuma ƙaunata" ko me ya tuna yana faɗin haka ya miƙe tsaye tana shafa kansa. Tunawa ya yi da yanayin Jannat a lokacin da ya isar mata da wannan saƙo, bai wani ga wata alama ta farin ciki ko akasinshi akan fuskarta ba, sai dai ba zai yiwu yanzu ya iya yanke hukuncin cewa tayi na’am dashi ko akasin hakan ba tun da ba ta ba shi tabbacin hakan da kanta ba. Abu ɗaya da ya sani shi ne Idan har Jannat ta yi accepting ɗinshi a matsayin wanda take so kuma za ta rayu da shi, to ba shakka ya tabbatarwa kansa cewa ya samu farin cikin da ya daɗe yana fatan samu, kenan idan taƙi accepting ɗinshi da? Hakan na nufin ke nan zai samu akasin farin ciki?, ya sani, rasa soyayya da kuma amincewar Jannat gare shi na nufin rasa jin daɗi da farin cikin da yake fata ne, zaunawa ya yi damas akan gado jin kamar ƙafafunshi ba za su iya ɗaukarshi ba. Baya fatan hakan ta kasance gare shi saboda bai san halin da zai shiga ba in ya rasa ta, ajiyar zuciya ya sauƙe shi kanshi na mamakin irin yadda soyayyar Jannat ta yi wa zuciyarshi mummunan kamu da har yake jin ba zai iya rayuwa babu ita ba, ko kuma in ya samu ya rayun ma ba zai yi rayuwa mai daɗi ba. Ko da na shiga ɗakin Rafi'at na kwance aka gado tana latsa wayarta da alamun dai ta yi nisa a chat ɗin da take yi tun da ba ta farga da shigowar tawa ba, ledar da BB ya ba Ni Na ajiye a bedside drawer, daga nan na ja gefe na tsaya kamar wata gunki na ma rasa abun yi saboda ƙwaƙwalwa ta riga ta cakushe wuri guda, duk wasu neurons da ke aikin sarrafa saƙo sun tafi juyin wani lokaci, na share kusan mintuna uku a tsaye sai da na tabbatar zuwa lokacin BB ya bar bakin ƙofa na fita na rufe ƙofar parlourn da bismillah Sannan na dawo. Toilet na shiga na watsa ruwa, ina fitowa Na tsane jikina, kamar wacce ba ta da lafiya haka na shirya cikin kayan baccina, turare na shafa daga nan na haye kan bed ɗin, ba da sani na ba na ɗan murtsuke yatsun ƙafar Rafi'at ai kuwa ta wani zabura ta miƙe. Ɗauke da mamaki akan fuskarta take kallo na kafin ta ce "Ke kin tsorata Ni, yaushe kika dawo?" Da ido kawai na bi ta coz a lokacin ma na gagara yin ko da magana ne."Ai na yi ta jiranki na ga shiru, har Ya Sadiq ya zo shi ma ya daɗe, da har na ce zan biyo shi ik duba ki ya ce min a'a, kuma tare da BB. Gaba ɗaya na damu kar Na je ko punishment zai ba ki" Da ƙyar laɓɓana suka iya motsawa, a hankali na furta "Uhm, I'm ok" Idanuwanta ta zura min kamar mai son gano wani abun, fuskewa na yi na ce "Meye hakan? Cinye Ni za ki yi?" Hararata ta yi sannan ta ce "Oho, kya ji da shi, na ɗauka wa wani abun ne ke damunki, shit!" A ɗan fusace ta koma cikin blanket ɗin yayin da ta bar Ni zaune ina bin ta da aikin kallo. Hannayena biyu na saka tare da rufe fuskata yayin da jikina ya yi wani irin sanyi ƙalau, maganganunshi ne suka ci gaba da yi min yawo a ƙoƙon kaina, haka na kwashe kusan rabin daren ina tafka muhawara da zuciyata yayin da wani ɓarin ke son gaskata kalaman BB ɗaya ɓarin kuma na min kashedi akan hakan, ba Ni Na samu damar rintsawa ba sai gab da asuba don ina jin ko wasu mintuna ashirin ba yi da kwanciya ba na fara jin kiraye-kirayen sallar. Da kyar na iya tashi na gabatar da sallar asubahi a daddafe, akan sallayar bacci ya kuma yin awon gaba da Ni, ba Ni Na tashi ba sai wuraren ƙarfe tara da ɗori. Juyi na yi tare da yin miƙa yayin da wata makararriyar hamma ta kufce min, addu'ar tashi daga Bacci na samu na furta tare da ƙoƙarin miƙewa, bayi na nufa sannan na wanke fuskata tare da wanke bakina. A daddafe na nufi parlour kamar wata ƴar maye saboda har lokacin ma baccin bai gama sakina ba sai famar lumshe idanuwana da nake yi. "Ina kwana Mommy" Mommy ta amsa min da lafiya ƙalau yarinyata. Rafi'at na kalla na ce "Yau ba za ki je school ba ba ne?' Tea ɗin da ke hannunta ta kurɓa sannan ta ce "yau Saturday fa" Na ce "Au! Haka fa" Cike da kulawa Mommy ta ce "Akwai abinci a dining, ki samu ki karya" kaina na gyaɗa daga nan na nufi dining na ja kujera na zauna. White spaghetti aka yi da sauce ɗin manja, bayan na zuba a plate na gyara zama zan fara ci, kalaman BB na jiye ne suka dawo min a zuciyata, jujjuya Fork ɗin na Fara yi ina yamutsa fuska. Me BB ke nufi kalaman nashi, ko kuma kai tsaye in CE tatsuniyar tashi don kuwa zuciyata ta gagara yin amanna da maganganun nasa. Anya kuwa BB na cikin hayyacinshi da zai tunkare ni da wannan tsadaddiyar kalma mai wuyar furtawa? Kaina na girgiza in a confusion way na ce "But je sounds serious" "Will you mind that chameleon on his words? He can easily change" wani sashe na zuciyata ya yi saurin ankarar da ni. Haka na shafe kusan 20 minutes zaune a dining ɗin ba tare da na kai ko da loma ɗaya ne cikin bakina ba. Muryar Mommy da na jiyo tana kirana ya sa Ni ba shiri fara cusa abincin a bakina duk da cewa tashe ɗin abincin gaba ɗaya bai min daɗi ba. Ko tea ban tsaya haɗawa ba na baro dining ɗin na koma ɗakinmu. Ajiyar zuciya na sauƙe tare da jinjina, na shiga damuwa sosai Na rashin sanin dalilin da maganganun shi suka tsaya min a zuciyata, ban kuma san dalilin da yasa na kasa gasgata maganganun nashi a raina ba duk da nasan har zuciyar shi yake faɗin su. Abu na gaba da na kasa tantancewa shi ne rashin marhabun da kalmomin BB da zuciyata ta yi, "shin hakan na nufin kenan bana son shi?" Na faɗa yayin da na faɗa kan gado ina ƙufundune kaina cikin blanket. Da sauri na ɗago sakamakon shawarar da kyakkyawar zuciyata dake son BB ta ba Ni "Kada ki yi gaggawar yanke hukunci Jannat, ta yiwu zuwa gaba ki so BB ko da ba Kya son shi" Saƙon da ya ba Ni daren juya da ya rako Ni na hango akan bedside drawern da na ajiya, cikin son sanin miye a ciki na miƙa hannuna na janyo ledar, kafin na ƙarasa jawota abubuwan ciki sun zubo. Idanuwana na waro ganin wata, wayar ma mai ɗan karen tsada. Hannuna na rawa na saka na tattaro kayan da kuma ledar gaba ɗaya. Wayar na ɗaga na ƙara kalla sai famar jujjuyata nake a hannuna kamar mai son gano wani abun, wani kyakkyawan Murmushi ne ya suɓuce min har sai da haƙwarena suka fito. Ajiye wayar a gefe na yi kana na zazzage sauran abubuwan da ke ciki ledar, envelope ɗin da ya faɗo na buɗe cikin ƙaguwa da son ganin mene ne a ciki. Idanuwana na wato ganin wrapper na ₦1k wanda a iya kallo sun kai 20k, shirin mayar da su nake na hango wata takarda a ciki, da sauri na janyo ta hannuna na ɓari na fara warware ta, cikin haɗaɗɗen rubutunsa na fara karanto abun da ke cikin cikin raina. "Assalamu alaikum, how're you and how are you doing? Hope you are doing well, wayarki da na fasa miki a dalilin kishinki da nake You can use this one a madadinta, and for the money, you can buy phone accessories sannan ki yi swapping SIM card ɗinki, do that as soon as possible please so I can reach you. Sannan put me in your prayers we have a serious operation to carry out this time around and your prayers matters. I end with love, thank you, and have a great day." Papern na fara jujjuyawa, yanzu kam da gaske BB ya daina ba Ni mamaki, don na fi masa ganin wanda ba ya cikin hayyacinshi. Tattara komai na yi na ajiye a cikin drawer ta sannan na dawo na zauna bakin gado trying hard to find out the best and perfect solution for this situation. Ni kaina na san cewa BB ya kai namijin da duk wata ƴa mace za tayi fatan ya so ta domin kuwa Ubangiji ya masa ni'ima sosai da ya haɗa masa abubuwa da dama da mace mace ke buƙata daga ɗa namiji, BB na da ilimin addini da kuma na zamani, kuɗi daidai misali yana da shi, uwa uba kuma kyau, kyau ɗinma mai ɗaukar hankali don na tabbata ko a cikin maza dubu BB ya fita daban, duk da muna takun saƙa da shi, hakan ba zai hana ni bayyana irin nagarta da kuma kyawawan halayen da yake da shi ba, matsalata da shi guda ɗaya ce zuwa biyu, mugunta da kuma miskilancinshi. To banda wannan komai na BB zan iya ba shi 100%, sai dai kuma wannan abubuwa biyu da ba na so a dangane da shi sune suke taka rawar gani wajen ruguje duk wata hujja da sashen zuciyata da ke son ƙulla alaƙa da shi, ina da ra'ayin auren namiji so friendly Wanda za mu mori rayuwarmu da shi, namijin da in na yi ba dai-dai ba ma a wasa zai gyara min, to Amma ina ganin BB ba irin wannan ba ne. Ina nan zaune ina ta karanta wasiƙar da ban gama warware ta ba Rafi'at ta shigo ɗakin sai dai zurfin da na yi a duniyar tunani ya sa ban sam na ta shigo ba har ta zauna gefena, zabura na yi a lokacin da hannunta ya sauƙa kan kafaɗata. "Lafiyarki kuwa Jannat?" Ta tambaya cike da kulawa yayin da ta kafe Ni da idanuwanta. Murmushi na ƙirƙiro tare da faɗin "A, lafiya, lafiya nake, me kika gani?" Kanta ta rausaya kafin ta ce "Akwai abun da ke damunki Jannat, wallahi akwai abun da ba ki so na sani" Shiru Na yi ban ce komai ba, yayin da zuciyata ke gargaɗi na kan kada na faɗawa Jannat wannan babban al'amarin da nake son daƙile shi tun wuri kafin ya fita har manyanmu su sani, don na san hakan ta faru zan shiga wani irin hali na ƙaƙanikayi don kuwa ko ban amince da BB ba na San magabatanmu za su yi yadda za su yi su ga wannan alaƙa ta gama ƙulluwa tsakaninmu. "Me yake damunki Jannat?" Murmushi na kuma ƙaƙalowa na yafa akan fuskata tare da janyo hannun Rafi'at da ke kan kafaɗata na damƙe "I'm ok Rafi'at, kawai na yi mafarki ne na ban tsoro, gaba ɗaya yanzu ba na jin daɗin jikina" Ba don ta yadda ba ta ce "Shi ke nan, ki ɗauko Alqur'ani ki karanta in sha Allah za ki ji daidai kin ji?" Kaina na gyaɗa tare da miƙewa na ɗauko Alqur'ani, shafin Farko na Suratul ankabut na buɗe don kawar da duk wani abu da zai ƙara kawo zargi tsakanina da Rafi'at, tana ficewa a ɗakin na dafe ƙirjina tare da furta sunan Allah. Alqur'anin da ke hannuna na mayar sannan na fita parlour. Ganin Rafi'at kwance akan kujera ya sa na ce "Zan je part din Ummie" Ƙokarin tashi ta fara ta ce "Jira Ni" Tare muka je muka gaishe da Ummin wacce ke famar soya snacks, muna shirin ficewa ta ce "Ina za ku je kuma? Dawowa za ku yi ku taya Ni mu samu mu ƙarasa, na Yayanku ne" Wata irin ajiyar zuciya na sauƙe jin kalaman Ummie, tsabar daɗin tafiyar tasa da na ji ai ba shiri na kama aiki, wuraren ƙarfe goma muka haɗa komai aka saka mishi a cikin wata jaka wanda kusan ko yaushe in zai koma Abuja a ciki Ummin ke jera masa snacks ɗin. Muna gamawa muka koma part ɗin Mommy. *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 23: Wuraren ƙarfe Sha ɗaya na ji shigowar BB ɗakin, hamdala na yi da ya kasance ba na parlour, Ina ji suka gaisa da Mommy Rafi'at ma ta gaishe shi. Sallamar da na ji ya yi wa Mommy ya sa Ni jin wani sanyi a raina duk da cewa zaman da muka fara yanzu da shi ya min daɗi ƙwarai amma tun daga daren juya nake jin cewa nasanta kaina da shi shi ne kaɗai maslaha gare Ni. Addu'o'i Mommy ta ringa yi masa, bayan ta gama nata Rafi'at ma ta ɗaura da nata. Har ya juya zai fita sai kuma ya dawo sakamakon rashin sukuni da zuciyarsa ke ciki na rashin ganin Abar ƙaunar tasa hakan ya sa shi dawowa ya dubi Rafi'at ya ce "Ina jannat?" Ta ce "Tana ciki, ina tunanin Bacci take" Ba don ya so ba ya ce "Fine, Mommy na wuce" Mommy ta amsa mai da "Allah ya tsare hanya" daga haka ya fice cike da takaicin rashin ganin Jannat ɗin. A ɓangarena ajiyar zuciya na sauƙe jin amsar da Rafi'at ta ba shi akaina. Ina kwance idanuwana lumshe na miƙe zaune, sauƙa na yi daga kan bed na nufi bakin drawern da na jefa wayar da ya kawo min, tsintar kaina na yi da ɗauko lettern da ya bar min ina ƙara karanta ta. Jin motsin shigowar mutum ya sa Ni ba shiri mayarwa na rufe. "Wai dama idanuwanki biyu?" Rafi'at ta tambaya hannunta na riƙe da labule Fuska na yamutsa tare da juyawa ina fuskantarta "E" Kina ji "BB na nemanki kuma kika yi shiru?" Na ce "To sai me, bayan kin ce ina Bacci so kike na fito kuma?" "Kya ji da shi kuma" A ɗan hasale na ce "To ai da kin zo kin ja Ni kin kai Ni na masa sallamar tunda Ibrahim Shirama ne" Kafe Ni ta yi da ido jin ta yadda ba ɓullo, cikin sanyinta ta ce "Abun bai kai ga haka ba Jannat, Allah ya ba ki haƙuri" Na ce "In ya ba Ni Ki ƙwace" ba ta amsa min ba ta fice a ɗakin. Ganin ta fita ya sa na ja dogon tsaki kana na ce "Daga mutuncin ƴan kwanaki da ya mata har ta manta irin muguntar da ya shata mana" Kan gado na koma na kwanta tare da yanke shawarar kada na sanar da ita komai batun BB, sannan kuma na ranƙwashi zuciyata tare da shawarar watsar da komai da ya danganci kalaman BB, mafitar da na samu shi ne duk lokacin da ya tayar da maganar kawai na ce da shi ban gama shawara ba ya ƙara min lokaci. Da wannan shawara na ji kamar an yaye min wani tulin nauyi da ke kaina. Tare da Ya Sadiq suka tafi, har Bauchi ya kai shi sai da jirginsu ya tashi ya dawo gida. Tun da BB ya shiga jirgin gaba ɗaya ya kasa sukuni wanda hakan na da nasaba da rashin ganin Jannat kafin ya tafi, ga shi ya tafi ya bar ta, bai san wa da waye za su kula ta ba, uwa uba kuma rashin sanin nashi stand ɗin, wanda hakan ya sa shi lumshe idanuwansa. Jawabin da ya ji ana yi gare su game da saka belt ya sa shi aiwatar da hakan, babu jimawa jirginsu ya tashi. Ya Khalid ne ya zo ɗaukarsa tare da Nimrah. Jakarshi Ya Khalid ɗin ya saka a Boot, shi kam bai ma san da Nimrah aka zo ba sai da ya gyara zamansa a cikin motar zazzaƙar muryarta ta sauƙa akan kunnuwansa tana gaida shi. Amsawa ya yi daidai lokacin da Ya khalid ya ja motar. "Sannu da Hanya Yaya Khalil" Ba tare da ya juyo ba ya ce "Yauwa Nimrah, yaya islamiyya?" Ta amsa mishi da "Alhamdulillah" cikin muryarta wacce ke fita kamar balarabiya sakamakon sabo da harshenta da ya yi da karanta Alqur'ani tare da bashi duk wasu haƙƙoƙinsa. Ya Khalid ne ya dubi BB ɗin ya ce "Ai ba ɗauka Jannat ba za ta bari ka dawo ba" Harararsa BB ya yi ganin yadda ya kawo topic ɗin a gaban Nimrah wanda ya rasa dalilin da ya sa idan tana wuri yakan ji shi uncomfortable sai dai ya danganta hakan da Kasancewarta nutsattsiya kuma mai kamun kai, ba kamar sauran matan da ya yi ta cin karo da su ba. Suna isa BB ya samu kyakkyawar Tarba daga Mami da kuma Big sis, Mufeed da kuma Sophie Wanda suka zo yinin gida, zo ka ga yadda suke nan da nan da shi kamar za su cinye shi, shi kansa kowanne lokaci yakan ƙara godewa Ubangijin da ya haɗa shi da Ya khalid da kuma familynshi da suke tsananin ƙaunarshi, jakar snacks ɗin ya ajiye musu yana faɗin "Bari na je na watsa, wanan Ummi ce ta ce a kawo" "To madalla! Madalla" Tare da ya Khalid suka nufi ɗakinsu sai Uwar zuba Ya Khalid ɗin ke yi. A nan ɓangarenmu yau ne muka karɓi baƙuncin Mommy Misau da kuma Nasmah, wanda suka zo da kuma alamun za su yi kwana biyu, farin cikin zuwan nasu ne ma ya sa na ƙara yasar da batun BB. Kwanana uku ina ajiye da wayar da ya kawo min sai a rana ta huɗu na fito da ita tare da nunawa Rafi'at da Nasmah a taƙaice na ce musu yanzu Ummi ta ba Ni, wai BB ne ya siya min a madadin wayar da ya fasa min. Nasmah da Rafi'at ne suka kalli juna tare da kashewa juna ido, cikin haɗin baki suka ce "Iyyyeee" Fuska na yamutsa Sannan na ce "Ai shi ya fasa min tawa akan abun da bai taka kara ya karya ba" Nasmah ta ce "garin yaya" Nan Rafi'at ta ba ta labari tas, Nasmah ta dube Ni ta ce "Sister anya kuwa ba sonki BB yake ba?" Gabana ne ya bada wani irin sauti, a ɗan tsorace na ce "ba dai sun gano wani abun ba!" Cikin raina na yi maganar hakan ya sa ba su ji Ni ba, Rafi'at ce ta kwashe da dariya sannan tace "Wallahi kuma Nas, kema sai kya faɗa, Ni wallahi gani nake ma kamar raina mana hankali take soyayyar suke yi, ki ga fa waya don Allah! Kuma kin san me?" Saurin rufewa Rafi'at baki na yi tare da harararta "Wai ke lafiyarki kuwa?" Duban Nasmah na yi na ce "Ke kuma ki zauna tana ɗaura miki karatun ƙarya, ku kanku kun sani Ni ba na soyayya, beside ko zan yi ma kun sani tsarina, ba namiji irin BB zan so ba" Nasmah ta taɓa baki sannan tace "Lallai yarinyar nan, to wallahi yau in aka ce kin samu ya BB wallahi kin gama morewa" "Rabu da ita dai, Yayana ai sai mace mai Sa'a" Rafi'at ta faɗa tana ɗagewa Nasmah gira" "Ikon Allah" na faɗa cikin raina "Na gode Allah da ban faɗa musu cewa BB na so na ba, tabbas waɗannan biyun will do whatever to see su samar mishi da soyayyata which I'm not hoping for" Ya zama min dole na yi taka tsantsan da takuna kafin su gano hakan. Washe gari bayan na dawo daga school kasancewar washe garin tafiyar BB muka koma su Nasmah suka raka Ni Wani shago na yi sim swap Sannan na sayo charger, Bluetooth da sauransu, sauran kuɗin dubu takwas na saka su a opay ɗina. Da daddare na gama saita da waya tsaf, na ɗaura Whatsapp ɗina a Kai. Ƙarfe takwas na shiga ɗaki na bar su Nasmah a parlour suna hira da Ummi da Mommy da Mommyn Misau da kuma Rafi'at. Ina cikin chat a Whatsapp sai ga Salam daga wata number, abunku da wacce ta yi welcome back numbern ba su na. "Wslm" na yi typing na tura ba jimawa aka ce "Ykk" Na ce "Kalau, and You?" "Ƙalau nima, how studies?" Na tura "Alhamdulillah" "Ma sha Allah" ko da na buɗe na ga ma sha Allah sai na fice na bar Mai numbern a blue ticks, ba jimawa naga ana typing, sai kuma aka Turo Abu buɗewa na yi "Me ya sa ba ki kira Ni ba bayan na ce ki kira Ni, ko ba ki ga saƙo na ba?" Gaba ɗaya ban kawo cewa BB ba ne a raina, hakan yasa na tura "Ban gane ba" Emojin Murmushi aka turo min da kuma "You'll never change, Captain Ibrahim Abubakar Shirama ne, your big bro" Emojin surprise na tura sannan na ce "Yi haƙuri BB ban gane ka ba ne, ka san in mutum ya yi swapping SIM ɗinshi yana rasa contacts ɗinshi me" "No problem " shi ne abun da ya Turo. Murmusawa na yi tare da gyara kwanciya ta na tura masa "Thanks, ka isa lafiya? Ya mutanen gidan" Ya Turo min "Lafiya lau, suna ma gaishe ku" Na ce "Uhm, muna amsawa, amma sun sanmu ne? Ina Ya Khalid?" Ya Turo min "Lafiya ƙalau yake, shima ya ce a gaida ki" Surprise emoji na tura tare da faɗin "ina amsawa" "Ok, kun koma school ko?" Na tura mishi da "Yes" Ya ce "Fine, Allah ya ba ku Sa'a, a yi karatu da kyau Banda kula samari da ƙawayen banza" tsintar kaina na yi da sakin Murmushi sannan na fara typing "in Sha Allah" Ya turo min da "Kar Na takura Miki, bari na bar ki kiyi Bacci kar ki makara da safe" Stockern Murmushi na tura masa, ina ƙoƙarin kashe data sai ga message ɗinshi ya shigo. "As the stars shine above, my heart only beats for you 💞. The night feels empty without your words or your voice to soothe my soul 💌✨. You are the dream I want to hold onto forever, the reason my heart smiles even in the dark 🌹. Mi corazon, before you close your eyes, Remember you’re always on my mind, and my heart belongs to you tonight and forever, Sleep peacefully, Good night." Saurin kashe data na yi sakamakon rashin sanin amsar da zan tura mishi, ƙara shiga chat ɗin namu na yi na sake karantawa daga farko zuwa yadda muka tsaya, murmusawa na yi na ce "Hmm" daga haka na shige cikin blanket, ba jimawa Bacci ya kwashe Ni. A ɓangaren BB ganin Jannat ta yi viewing last chat ɗin nasa amma ba ta yi reply ba ya sa shi jan siririn tsaki, Wani irin takaici ne ya kama shi sai ya ji dama bai dawo ba, kuma dai yanzu ne ya kamata ya jawo jannat jikinsa, su samu fahimtar juna ta yadda za ta kamu da son shi kamar yadda yake ɗawainiya da tata soyayyar. Kashe datarsa ya yi daga nan ya ɗauro Alwala ya kwanta ba tare da ya kira Ya Khalid da ke yin waya a parlour ya dawo ciki ba. Satinmu guda da komawa school aka mana speciality posting na tsawon 2 months , sosai Na ji daɗi ko ba komai ma huta da uban note ɗin da ake ɗirka mana da kuma zaman lectures. Gynae emergency aka kai Ni, kuma wannan karon muma students Za mu yi shifting kamar yadda staffs suke yi, a ranar aka mana roster, zan yi morning na seven days, sai na yi 3 days off, daga nan na fara night na seven days, sai na yi seven days off, in na dawo kuma sai na yi evening na seven days four days off, haka kuma sai mu yi rotating mu koma post Natal ward. Kwanana biyu ina zuwa morning sosai aikin ke min daɗi, a kwana na huɗun ina zaune Ni da Maryam Muhammad Mahmud, da kuma Joanna John, dama tare muke shift da su, muna cikin zaune lokacin aiki ya tsagaita sai ga Dr. Junaid ya zo, gaishe shi muka, ya amsa daga nan ya ƙarasa nurses station, ban san me ya cewa Nurse on duty BA na dai ji ta ta ce "To babu damuwa" Daga nan ya dawo wurinmu ya dube Ni ya ce "Jannat" *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 24: Ɗagowa na yi na kalle shi ya ce "Can i see you in person?" Kai Na Gyaɗa tare da miƙawa, ina ƙoƙarin zuwa na ɗauki permission ya ce "Don't worry na gama da wannan" yana faɗin haka ya fita waje, bayansa na bi gaba ɗaya kunyarshi nake ji don tun ranar da muka haɗu da shi a check 'N' buy har BB ya fasa min waya bai ƙara ji daga gare Ni ba, ko da na yi swapping SIM ɗinma Babu numbernshi bare na kira shi. Daidai reception na ANC clinics yadda ake awo ya tsaya, kujerun da ke jere ya nuna min, ba musu na zauna, shima zaman ya yi, sannan ya dube Ni cikin wani yanayi mai kama da damuwa ya ce "Where have you been Jay?" Wayancewa na yi na ce "Ina lafiya Yaya Doctor, wayata.." Katse Ni ya yi da faɗin "In kin san tun farko za ki iya rabuwa da Ni me yasa kika sa na saba da ke Jannat? Do you know how much it pains?" Kallonsa na yi cikin ido yayin da na karanto ainihin gaskiyarsa da yake faɗi "Kin bar Ni cikin tunaninki, shi ya sa tun farko na ce ki bar Ni na san gidanku, ko ba komai idan irin haka ta faru na san yadda zan ji Lafiyarki" A hankali na ce "I'm sorry Yaya Doctor, ban san ma ta ina zan fara ba, ka yi haƙuri akan abun da BB..." Katse Ni ya yi ta hanyar faɗin "Ya wuce Jay, and please kada ki ƙara min irin haka, idan kuma ba haka ba notice ɗin mutuwata za ki ji" Da sauri na ɗago idanuwana na dubi Yaya Doctor Jin kalamansa da suka min dirar mikiya, kasa ɗauke idanuwana daga nashi na yi, trying very hard na fahimci yadda maganganun nashi suka dosa sai dai bai ba Ni damar hakan ba. "Yes, zan iya mutuwa idan kina nesanta kanki gare Ni, fi you know how much I care Jay?" "I'm sorry Yaya Doctor," na ba shi amsa a sanyaye. Ya ce "ki koma, I'll call you in kin koma gida" Na ce "ok, thank you" Daga haka muka yi sallama, yana tsaye a wurin na koma ward ɗinmu Ina mamakin inda kalaman nashi suka dosa. Ko da na koma ward an kawo wata patient mai incomplete miscarriage za a yi MVA, ƙarasa wurin na yi, har sai da aka gama muka dawo da ita bed ɗinta muka yi fixing mata IV fluid, daga nan muka ɗauki excuse muka tafi masallaci muka yi Sallah, bayan an ida sallar Ni kam kaina na haɗe da guiwa ina tunanin maganganun Yaya Doctor na ɗazu, taɓa Ni da Maryam Muhammad Mahmud ta yi ya sa na miƙe muka koma ward. Vitals muka yi wa patients ɗinmu, daga nan muka yi medications under supervision na nurses on duty yayin da suke mana bayanin komai, abun da ba mu gane ba kuma mu tambaye su su faɗa mana. Ba mu wani jima ba staffs na evening duty da students suka zo, aka yi musu handing over muka tafi, kasancewar yanzu lokacin tashina da na Rafi'at sun banbanta ya sa na tsari napep na wuce gida. Ina isa gida na watsa ruwa, na ci abinci daga nan na koma ɗaki na kwanta. Maganganun Yaya Doctor NE suka faɗo min a rai, ba shiri na tashi na zauna tare da jingina da fuskar gado. Yatsata na cija sannan na ce "Me yake nufi da zai iya mutuwa?" Saurin girgiza kaina na yi tare da faɗin "Nooo, ba lallai abun da nake tunani ya zama gaskiya ba" Ringing ɗin da wayata ke yi ya sa na sauƙe ajiyar zuciya Tare Da janyo wayar tawa, picking call ɗin na yi duk da cewa numbern ba suna. Dakakkiyar Muryarsa ne ta sauƙa akan kunnena yayin da yake min sallama cikin nutsuwa. Amsawa na yi ina mayar mishi amsa da gaisuwa. "Kin koma gida lafiya?" "Lafiya ƙalau" na ba shi amsa. "Ya yi kyau, ya su Mommy da Daddy?" Na ce "Lafiya lau suke" "Ina Abokiyar faɗa na?" Na ce "wa ke nan?" Ya ce "Rafi'at mana" baki na taɓe na ce "Tana school" Ya ce "To Allah ya taimaka." Na amsa masa da "Amiin" Shiru ya yi can kuma ya ce "Me kika cewa Daddy ya siya miki sabuwar waya?" Kamar ina gabansa na jinjina kaina tare da faɗin "Ba shi ya siya min ba ai, bai ma san BB ya fasa wancan ba" "Uhmm, Mommy ne ta saya ke nan" Na ce "A'a, BB ne saya min wata" Dif! Na ji Yaya Doctor ya ɗauke wuta. Wannan dalilin yasa Ni saurin faɗin "Ka san shi ya fasa wancan, in bai biya Ni ba kuma, zai sha faɗa wurin Mommy" Ɗan Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce "Hmm, Ni miye ma alaƙarku da shi?" Na ba shi amsa da "Cousin brother na be" "Uhmmmmm, akwai aure tsakaninku ke nan?" Na ce "Kamar Yaya?" "Kamar dai yadda na faɗa, idan ya ce yana son ki ai za ki aure shi" Na ce "Tab, ai ba za mu zauna wuri guda ba, mutumin da kullum cikin azabtar da Ni yake?" "Saboda yana son ki ne?" Wani irin bugawa zuciyata ta yi, me yasa kowa sai ya ce saboda BB na so na ne yake azabtar da Ni?" Kamar ya san me yake raina ya ce "ƙwarai Jay, BB sonki yake" Nace "Gaskiya ba haka ba ne" Murmushi mai sauti ya yi har ina iya jiyowa sannan ya ce "Ta yaya za ka ce haka?" "Na gani da idona a ranar da muka haɗu a check 'N' buy, da gaske Jay BB yana ƙaunarki, zallar kishinki na gani a cikin idanuwansa " Cikin sanyin jiki na ce "Amma dai Ni ba na son shi ai, kuma shi ma bai ce yana so na ba" "Kika san ko ta sama zai biyo Miki?" Cikin raina na ce inaa ba zai yiwu ba. "Da gaske nake Miki Jay, idan har kin san ba kya son shi tun wuri Ya kamata ki ba wa wanda yake son ki dama, in ba haka ba za a kai ƙadamin da iyayenku ba za su duba cewa ba ki son shi ba su aura Miki shi a dole" Na ce "Tab" Ya ce "ƙwarai kuwa, shawara dai na ba ki" Ni kam ban wani fahimce shi ba, ashe wai hannunka mai sanda yake min na fahimci inda ya dosa. Hirar muka sauya zuwa wata daban, ba mu wani jima ba muka yi sallama. Miƙewa na yi na nufi part din ummie sanin cewa Nasmah na can, ba mu wani jima ba na janyo ta muka dawo. A ɓangaren BB tun wannan chat ɗin da suka yi da Jannat ɗinshi ba su ƙara ko da waya ba sakamakon abubuwa da suka mishi yawa don kuwa shirin tafiya wani operation suke yi a jahar Sokoto, sai dai wani abun mamaki ko da sau ɗaya bai taɓa mantawa da Jannat ba in fact duk wani motsi nashi da tunaninta a cikin ranshi. Tsaye suke a barrack shi da Ya khalid da alamun wucewa ma za su, Ya Khalid ne ya dube shi ya ce "Mutuniyarka ta ce a gaida ka" BB ya ce "Jannat?" Harararsa Ya Khalid ya yi ya ce "ita ɗin kuma saƙonta ta hannuna zai shigo?" "Then who?" Ya ce "guess who?" Tsaki BB ya ja zai wuce, Ya Khalid ya ce "Doctor Suhaima dai, ƴar gidan Senator Hashim Barde." Wani tsakin BB ya ja ya ce "Wai ita ba ta manta da Ni ba ne?" "Ga dai alamu" ya Khalid ya ba shi amsa "ta ce a sanar da kai ta gode sosai, ko wayar tata ba la iya dauka" Harar ya Khalid BB ya yi kana ya ce "Kaima ba ka da abun yi da kake karɓan saƙon irin matan nan, after all ka san cewa Ni akwai wacce nake so, mace kuma in ba Jannat ba na yafe, beside ka san ba na ra'ayin macen da za ta fara furta min tana so na, ko da na yi niyyar na so ta sai ta fice min a rai" Dariya Ya Khalid ya yi sannan ya ce "Our unique Captain, komai naka daban yake, anyways Allah dai ya ba ka Jannat mu sha biki " Murmushi ne ya sauka akan kyakkyawar fuskarshi, ya Khalid ya ce "Mu kam namu auren ba jimawa, kuma za ka sha mamakin wacce zan aura" Cikin halin ko in kula BB ya ce "Fine " Daga haka suka nufi mota abun su. Ko da suka koma gida Ya Khalid ya lura da BB kamar yana cikin damuwa hakan ya sa shi tsayawa kusa da shi don ganin ya rage masa yawan tunanin da yake ganin in ya ci gaba zai iya taɓa aikinsa. "K, yanzu yaushe ne takamaimai tafiyar ne kam?" BB ya ce "On Monday " Ya Khalid ya ce "To Allah dai ya kai ku lafiya, muna nan muna muku addu'a ku yi nasara ku dawo mu sha biki " "Hmm, Ni wallahi Ni nake ma kamar na je a cire Ni cikin mafi tafiyar" har cikin ransa ya yi maganar yana shafa kansa. "But why" Kamar zai yi kuka cikin wata raunatacciyar murya ya ce "saboda ba ta bani amsar tana so na ko akasin haka ba, yanzu duk wani abu da nake gudanarwa ina yi ne da rashin sanin madafar a wani matsayi nake domin Ni na san lamume a duhu nake, Friend, ina son ta, yanzu abin da yafi damu na shine ban san yaushe za mu dawo ba, Ni ɗin zan dawo ne ma ko a can tawa za ta ƙare ba tare da samun soyayyar Jannat ba" Damuwar da ta bayyana ƙarara a fuska da kuma Muryarsa ta sa Ya Khalid tausayawa abokin nasa, lallai so ya wuce tunaninsa yanzu kam, bin shi da kallo kawai ya yi cikin rashin sanin ta ina ma zai fara lallashin abokin nasa, ya yarda so gaskiya ne, kuma mutum kan iya canzawa akan abun da yake so,, wai yau K ne ya zauna yana doguwar Magana akan mace, zai iya tsayawa ya shaidawa duniya cewa mata ba sa gaban K, amma yanzu gashi yana faɗin irin son da yake ma ƴar uwarshi Jannat, lallai so guba ne mai kama da madara. Cikin taushin murya ya Khalid ya ce "Kana ji abokina, ka mayar da al'amuranka ga Allah, ka ba shi zaɓin ya zaɓa maka abun da ya fi alkhairi, idan son Jannat alkhairi ne gare ka, ga addininka, ga kuma rayuwarka, to Ubangiji ya karkato maka da hankalinta, idan kuma akasin haka ne Allah ya zaɓar Maka mafi alkhairinta." BB ya amsa da "Amin" Ya Khalid ya dafa kafaɗarsa Sannan ya ce "So relax your mind my man, za ku dawo lafiya cikin aminci ba tare da ko ƙwarzane ba." BB ya Gyaɗa kai, daga haka Ya Khalid ya ce "mu koma parlour a yi hira, ko za ka ɗan ware" Tun daga ranar da Yaya Doctor ya ƙira Ni muka ƙara ɗinkewa wuri guda, idan ba ma waya to muna online, sosai wata irin shaƙuwa da ta fi wacce muka samu a baya ta ƙullu tsakaninmu, haka kawai nake jin daɗin mu'amala da shi coz he's very friendly to me, ga kuma yadda yake nuna min kulawa kamar zai cinye Ni. Satin su Nasmah guda suka koma Misau, sosai Na yi kewarta don kuwa mun yi sabo sosai da ita. Ranar da suka koma muka Hajiya Dada ma ta zo. Hakan ya sa gidan ƙara armashi, part ɗin da Daddy ya gina ba jimawa nan ta sauka bayan an saka mata duk wani kayan buƙata, fatan Daddy da Abuya shi ne Dadan ta ji daɗin zaman ta haƙura su zauna tare. Tun da Dada ta zo kuma na kwashe na koma wurinta, ba na yini a part ɗin Ummi ganin yadda Rafi'at ta saka min ido akan yawan waya da chat ɗin da nake, galula titsiyen da take min wai sai na faɗa mata da uban da nake waya.. Bacci ne kawai yake dawo da Ni part ɗin Mommy, tun daga nan na samu salama a wurin Rafi'at ɗin, though can sashen Dadan ma in na je cikin faɗa muke don shegen surutu ne da tsohuwar. Yau ta koma lahadi zan fara night shift ɗina. Ƙarfe bakwai da ƴan mintuna ba Driver ya miƙa Ni asibiti bayan na tattari duk abun da zan buƙata ciki har da abun taɓawa. Wuraren 10 muka gama TDS medications ɗinmu, 12 kuma 6 hourly medications, daga nan nursed on duty suka ce za mu iya kwanciya tun da babu abun yi so far. Wayata na Kama Ni kam ina chat da Yaya Doctor, ba mu muka yi sallama sai 3:07am, ba jimawa kuma Bacci ya ɗan ɗauke Ni a zaune akan kujerar, around 4am hayaniyar cleaners ta sa na tashi. Da safe wuraren shida sai ga kiran Yaya Doctor. Bayan mun gaisa ya ce Don Allah na jira shi in mun yi closing, lucky to be dama ban faɗawa Baba Driver lokacin tashi ba, ya dai ce In ya kai Rafi'at yana dawowa Sai mu tafi. 7;30am muka yi handing over ma staffs ɗin safe, daga nan kuma na zauna ina jiran Yaya Doctor. Ba jimawa ya kira Ni ga sanar da Ni cewa na same shi a bakin amenity ward, ba jimawa kuwa na isa kasancewar wurin ba nisa da ward ɗinmu. Tsaye na gan shi jikin motarsa cikin shigar manyan kaya akasin normal shigarshi ta yau da kullum, kayan sun karɓe shi ba kaɗan ba, tun da ya hango Ni ya saki wani kyakkyawan Murmushi wanda har na ƙaraso bai gushe ba akan fuskarsa. Kaina na sunkyar da na ƙaraso tare da faɗij "Good morning" Fuska sake ya ce "Morning, how's your night?".harararsa na yi tare da faɗin "After I spent it all with you" Dariya ya yi tare da shafa kansa ya ce "Haka da, I'm sorry, hope Kin fito da kayanki ko, ina nufin jaka da kuma.." saurin gyaɗa kaina na yi Ya ce "Bai kyautu mu tsaya a nan ba kowa ya zo wucewa ya ganmu musamman ke da kike sanye da uniform, Mu shiga Mota, in mun gama maganar sai na ƙarasa da ke" Idanuwana na zaro tare da faɗin "Kai, ba Driver fa na zuwa" *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* *TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB* ~Paid novels~ https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS *No 04* *KUSKURENA NE* _(From the choice I made)_ *©® Fatima Adamu Hassan* _(Diamond Bhatool 🦋)_ 07061707238 Bismillahir Rahmanir Rahim . CHAPTER 25: Fuskarsa ya haɗe kafin ya ce "Za ki fara ko?" Da sauri na ce "Shi ke nan, mu je" na idasa ina bin bayansa. Motar muka shiga duk da cewa wata zuciyar na kwaɓa ta amma sai na ji ina, ba na son ɓatawa Yaya Doctor Rai. Kallona ya yi sannan ya ce "Ba wani abu zan Miki ba Jay, magana za mu yi" Kaina sunkuye na ce "ina jin ka" Gyaran murya ya yi sannan ya ce "To kai tsaye Jannat zanso na sanar da ke dalilin kiranki da na yi." Da wani irin sauri zuciyata ta fara gudu ina fatan dai a ce so na yake, ko ba komai hakan zai tseratar da Ni daga auren BB ko da kuwa ta kana dole. Tunanina ya katse ne jin muryarsa ya ce "Shekarar ki nawa Jannat?" Na amsa mishi da "nineteen " Ya jinjina kansa sannan ya ce "Fine, you're an adult right?" Ban iya ba shi amsa ba ya fara magana cikin nutsuwa da kuma kamala irin tashi "Da Ni da ke dukka ba yara ba ne, za mu iya yankewa kanmu shawarar da ta dace da mu." Wani irin faɗuwa gabana ya yi Yaya Doctor NE ya ci gaba da magana "Yauwa, to Cut it short Jannat, kafin wannan lokacin ban taɓa yarda da wani abu wai shi so ba despite yadda naga mutane da yawa na shiga wasu matsaloli saboda shi ba, har na Fara karatu na kammala zuwa yanzu Ban taɓa yin soyayya ba, saboda a littafin rayuwata babu ita a ciki, but now, na yi developing duk wani feeling da ake danganta shi da soyayya kuma ina da tabbacin cewa I'm in love, with an assurance that wacce nake so, will surely love me in return" Tsabagen fargaban kalaman Yaya Doctor ban san lokacin da na fara wasa da yatsuna ba yayin da na ji numfashina na fita da sauri da sauri Agogon hannunshi ya duba tare da faɗin "Kar Na ɓata Miki lokaci a fara nemanki a gida, Jannat, From the very beginning, no one has ever compared to you. You hold a place in my life no one else could ever touch. Even my mother sees the way my eyes light up when I speak about you. She told me to come to you honestly with my whole heart open and tell you how serious my love truly is. I love you Jannat! I love you!" Magana ta gaskiya na shiga shock da kalaman Yaya Doctor duba da cewa sun zo min a ba zata kamar dai yadda kalaman BB suka dake Ni a wancan lokacin! Gaba ɗaya na shiga tsaka mai wuya, take kalaman BB suka dawo min lokacin da yake confessing soyayyarshi gare ni lokacin da yake faɗin " Jannat, i love You, ina son ki, ina ƙaunar ki, sannan ina so na rayu da ke tsawon numfashina" Ga kuma yanzu da Yaya Doctor ke faɗin "even my mother sees the way my eyes light up when I speak about you. She told me to come to you honestly with my whole heart open and tell you how serious my love truly is. I love you Jannat! I love you!" Lallai wannan shi Bature ke kira da Dilemma! Yanzu to ya zan yi da raina? Ga BB ga kuma Yaya Doctor. Ban so wannan al'amari ya min a haka ba to amma haka Ubangiji ya rubuta zai faru babu yadda na iya. Idan na ce ba na jin yaya Doctor a raina, to ba shakka ƙarya nake yi, don kuwa from day one we met, from the rumors from my friends, I started to develop feeling for him, sai dai kasancewa mace mai wayo da kuma kamun kai ya sa ban taɓa nunawa ba, Gashi dai yanzu na samu damar samun kusanci na har abada da Yaya Doctor, Amma rashin sanar da BB nasa matsayin ya sa dole sai na fara kashe wutarshi kafin na amincewa Yaya Doctor. Tunanina ya katse ne jin Yaya Doctor na kiran sunana. Ɗagowa na yi sai dai ban bari idanuwanmu sun haɗu ba. "To Cut it short, Jannat, im very simple game da sha'anin rayuwa, ba zan takura Miki ki so Ni ba, zan kuma ba ki dama har zuwa lokacin da ya yi Miki ki sanar da Ni matsayina, in har kin san ba ki so na, feel free and tell me, za fahimce ki kuma zan Miki fatan alkhairi, na san cewa babu wanda zai auri matar wani." Ajiyar zuciya na sauƙe jin bayani sa, cikin sanyin murya na ce "Shi ke nan, I'll think over it" Ya ce "To Allah ya sa na ji alheri, mu je na sauke ki ko?" Shiru Na yi ban ce komai ba, ya dube Ni ya ce "Ko ba ki so?" Saurin girgiza kaina na yi, hakan ya sa shi murmusawa daga nan ya tayar da motar tasa, muna tafiya ina nuna mishi hanya har muka zo danƙareren gidanmu, a bakin get ya ajiye ni muka yi sallama da shi, na shige ciki. Wanka na samu na yi kana na saka wata doguwar riga maras nauyi, maganar Mommy da na jiyo ya sa Ni fitowa waje gaishe ta na yi, cike da kulawa ta amsa tare da faɗin "Yau kam an yi night Duty, Yaya aikin dai?" Na ce "Alhamdulillah" Ta ce "ga abinci a dining " Cike da girmamawa na ce "To Mommy" Ina ganin Mommy ta koma bedroom ɗinta na sauke ajiyar zuciya, part ɗin Ummi na ne na gaishe ta, daga nan na wuce na gaishe da Hajiya Dada. Abincin na ɗiba na shiga da shi bedroom ɗinmu, sai dai haka na sa shi gaba ina jujjuyawa na kasa ci, ganin haka ya sa na fito da shi na ajiye a kitchen daga nan na dawo na kwanta akan gado da niyyar rama Bacci da ya kuɓuce min. Kalaman Yaya Doctor NE suka fara dawo min, saurin toshe kunnena na yi ina girgiza kai ganin kamar zan zauce. Tabbas ina da buƙatar abokin shawara a wannan situation ɗin da nake ciki, to da wa zan yi shawarar? Ba Ni da wanda ya kamata na yi shawara da shi sama da Rafi'at, domin ita kaɗai ce wacce nake jin zan iya faɗawa damuwata mu haɗu mu magance ta, to akan wannan sabga kuma na yanke shawarar ƙin sanar da ita domin na tabbatar Rafi'at za ta bi bayan ɗan'uwanta NE NI kuma ga shi tun ba a je ko ina ba zuciyata ta fi karkata ga Yaya Doctor akan BB. A hankali na ce "Ya Sadiq?" Saurin girgiza kaina na yi "He'll never support my decision, na tabbata matsawar ya san cewa akwai wata alaƙa tsakanina da BB to zai yi forwarding zancen ne kai tsaye ga magabatanmu musamman idan ya kasance ina da wani zaɓin bayan BB. "Then yaya zan yi?" Rashin sanin abun yi ya sa na fara auna BB da kuma Yaya Doctor akan mizani, kowanne quality da Yaya Doctor ke da shi in na duba sai na ga BB ya kere shi ba kaɗan ba, ida kyau ne, ilimi gayu, wayewa na tabbata sai an kira BB, to Amma ni na rasa dalilin da ya sa har rana mai kama ta yau na kasa jin wani abu mai kama da so dangane da shi, gashi dai na san ba shi da wani aibu ko kushe. Zuciyata ce ta yi saurin ce min "Me zai hana ki yi haƙuri ki ranƙwashi kanki ki so BB, ko ba ki jin komai akan shi ki karɓi soyayyarsa, ba kya tunanin wata rana za ki fara son shi ne? Kuma wannan jahadi da za ki yi wa BB zai ƙara danƙon zumuncinku beside BB ne ya fara confessing love ɗin shi before Yaya Doctor kuma har yanzu jiran samun amsarki yake, ki yi adalci tsakanin su biyun jannat!" Mu evil Heart ce ta ce min "Kul jannat! Yanzu za ki haƙura da muradin zuciyarki ne ki auri wanda ba kya so? Idan kika yi haka kin cuci kanki don kuwa babu wanda ya ce Dole sai kin so BB beside AI ba ki ba shi amsar cewa kina son shi ba" Da shawarar evil Heart na yi amfani yayin da nake jin zan iya fito na fito da duk wanda zai takura min akan sai na auri BB. Na dai san tabbas matsuguni na musamman cikin raina BB ya riga ya same shi Amma batun auren kam, babu shi a lissafi na tun da har na samu wanda zai zama Shamaki tsakaninmu da shi. Hakan ya sa na ƙudiri aniyar Turawa BB message tare da ban haƙuri kan cewa ya min haƙuri ina da wanda nake so duk kuwa hakan na san da ciwo amma Gara tun wuri Ya san stand ɗinshi. A haka muka kammala night shift ɗinmu kowanne dare chat muke, in an tashi zai kai Ni har gida though ban taɓa ba shi damar shiga cikin gidan namu ba. Waya da chat kuma suka ba ma yi da BB. A can ɓangare BB sun tafi operation ɗin a can wani ƙauye a jahar Sokoto da ƴan ta'adda ke shiga su yi ta karkashe mutane, kasancewar garin babu network ma ko kaɗan ya sa har suka yi kwanaki bakwai ɗin bai neme Ni ko wani a gida ba, haka suka share sati biyu Tukun suka kammala cikin ikon Allah kuma sun samu nasarar daƙile waɗannan ƴan ta'adda, an kama waɗanda ke da rai an taho da su Abuja yayin da wasu daga cikin sojojin kuma suka raunata, ciki har da BB Wanda aka harɓe shi a hannu. Suna dawowa aka ba su taimakon gaggawa, ranar kuma night na ƙara fita sakamakon waɗanda ke night ɗin ɗaya mayar aure ce ta ce Don Allah a cire ta a sa ta parmanent morning shi ne aka yi replacing ɗinta da Ni, a daren ranar na hau Whatsapp na ga Yaya Sadiq, Daddy, su Nasmah, Rafi'at da sauransu sun yi sharing flyer mai ɗauke da hoton sojoji a kwakkwance yayin da hoton BB ya fito boldly, jikin flyer an rubuta "An samu nasarar daƙile kashe-kashen da ƴan ta'adda ke yi a ƙauyen gidan kare da ke ƙaramar hukumar tureta ta jahar sokoto. Jami'an tsoro da dama sun raunata, ciki har da shugaban tawagar atasayen, Captain Ibrahim Abubakar Shirama." "Innalillahi wa innaa ilaihi rajiiuna" shi ne kawai abin da na iya furtawa, take na kira numbern Rafi'at, tana picking na ji tana kuka cike da fargaba na ce "Rafi'at me nake gani a status ɗinku?" Abunka da mace mai rauni cikin kukan ta ce "Kin ji su BB sun dawo? Amma an harbe shi a hannunsa" Na ce "What? Yanzu yana gida?" Ta ce "A'a, suna can Abuja ana ba shi taimakon gaggawa, gobe da safe ma Abuja da Ummi za su tafi" Cikin rashin sanin abun da zan ce na ce "Ubangiji ya taƙaita ya ba shi lafiya" daga haka na katse kiran. Lalumen numbernsa da har yau ban saving ba na fara, nan na danna mishi kira sai dai bai yi picking ba. Washe gari da safe bayan mun ji handing over Yaya Doctor ya zo maida Ni gida, ganin damuwa akan fuskata ya sa shi tambayata ko lafiya nan na fashe masa da kuka, da kyar na yi shiru. "Now tell me what's wrong, ba ki da lafiya ne? Na girgiza kai "Wani ya ɓata Miki rai me?" Na ƙara girgiza kai "then what's happening?' Na ce "BB ne..." "Ya Miki wani abun ne?" Na ce "A'a, harbinsa aka yi" Numfashi ya sauƙe tare da faɗin "That's why you're crying like that " Galala na yi ina bin shi da kallo gira ya ɗage min, na ce "BB is my eldest brother so far, shi ɗin garkuwarmu ne, duk abun da ya same shi ba zan ji daɗi ba" "To ai shi ke nan, sai in ya dawo ki yi jinyarshi" Ganin tsagwaron kishinsa akan wannan ƙaramin abun ya sa Ni jin ba daɗi, a hankali na ce "I'm sorry" bai kula Ni ba ya ja motar har muka isa gida fita na yi bayan na misi godiya daga nan shige gida ina mamakinsa, idan har ba fahimce shi ba ya son wata alaƙa tsakanina da BB bayan kuma ya san shi ɗin ɗan'uwana ne ko ba aure Akwai zumunci. Ko da na dawo su Abuyan ba su tafi sakamakon Abban Ya Khalid da ya kira ya ce ba sai wani ya zo ba don Allah. Allah sarki Nimrah, sosai ta shiga damuwar wannan al'amari kai ka ce Yaya Khalil ne abun ya samu, daga Mami, Abba har Yaya Khalid ɗin sai da suka saka har tambaya kanta, musamman da suka san cewa ita ɗin ba mai saka damuwa a ranta ba ne. Kwana uku su BB suka yi suka sassamu sauƙi, sai lokacin aka dawo musu da wayoyinsu, tarin missed calls ɗin da ya gani ya sa shi lumshe idanuwansa. Ya Khalid ne ya dawo da shi gida, bayan ya yi wanka ya ci abinci aka ba shi wuri Ya ɗan huta. Abuya ya fara kira sosai suka nuna kulawa da tsanatsar damuwar da suke ciki shi da Ummi, nan ya kwantar musu da hankalin daga nan ya kira Daddy, a nasu bangaren ma haka ne. Ni ce mutum ta gaba da ya kira lokacin ina shirin tafiya asibiti, da sauri na ɗaga tare da ƙara wayar a kunnena. Sallamarsa ce ta sa zuciya fara bugawa da sauri, amsa mishi na yi a sanyaye tare da tambayarshi ya jiki, cikin sanyin muryarshi marar hayaniya ya ce "Alhamdulillah, I'm ok" "Harbin da zafi ko, hope kana shan analgesics?" BB ya ce "Bai kai zafin nesanta da ke da na yi ba" Sauri buɗe bakina na yi alamun mamaki, don yanke wannan magana ya sa na ce "Zan tafi asibiti, let's chat in na isa" "Haka ake kula da patient ɗin?" Ya faɗa a shagwaɓe "Ni gaskiya zan tattaro na dawo ki yi jinyata" yadda ya yi maganar sai na ji abun banbaraƙwai, wai namiji da suna Hajara. Shi da yin shagwaɓa Ni da jiye mishi kunya. Shiru Na yi ina tunanin me zan ce, can na ji ya ce "me za ki yi a asibiti?" Na ce "An yi posting ɗinmu ne" "Har shifting kuke yi?" Na gyada kai ina faɗin "e" Ya ce "Fine, ki je kawai, zan kwanta na huta gobe da safe sai mu yi waya" Na ce "to" "To ki faɗa min wani abu sai na kwanta" Rasa inda zan sa kaina na yi, kamar zan arta a guje haka nake ji. "Kin yi shiru" Na ce "To Ni me zan ce?" "Say anything you think will comfort me to have a nice dream" Zaro idanuwana na yi kana na ce "To Allah ya ba ka lafiya BB, ya tashe mu lafiya" Ba wai don haka ya so ba kawai ya ce "Amiin, i love You!" Ya fadi kalmar i love You ɗin ne cikin raɗa har sai da na ji tsikar jikina ta tashi. Saurin katse kiran na yi daga nan na yi wa su Ummi sallama na wuce. *To jama'a akwai ƙura fa cikin wannan labari namu mai taken KUSKURENA NE domin kuwa yanzu ne muka fara kutsa kanmu cikin labarin.* *Masu karatu na san kuna da tarin tambayoyi akan littafin* *To Jannat dai ta shiga tsaka mai wuya a tsakanin soyayya guda biyu wanda kowacce na da muhimmanci gare ta, Idan har ya guji BB tabbas ba ta kyauta masa ba domin shi ɗin masoyin gaskiya ne, to matsalar ɗaya ita ce, tana son cikawa zuciyarta muradinta na auren Doctor Junaid!* *Shin me kuke tunanin zai faru idan aka san cewa BB na son Jannat? A tunaninku su Abuya za su bai wa na waje ne bayan ciki bai ƙoshi ba ko kuma za su cikawa ƴar tasu muradin zuciyarta?* *Idan komai ya tafi yadda ya kamata cikin Jannat, da kuma BB waye ya tafka kuskure a cikin zaɓin da ya yi?* *Dukka amsishin ku na tare da alƙalamina!* *Alhamdulillah rabbil alamin! Dukkan yabo da jinjina su tabbata ga mahaliccin sammai da ƙassai da ya ba Ni ikon fara wanna littafi na kuma kammala shi lafiya, duka duka a nan muka kawo ƙarshen littafi na ɗaya wanda na alƙawaranta shi matsayin kyauta, ga masu don karanta littafi na biyu, za su biya Naira ₦3000 kacal, domin samun littattafan namu da suka fito a matsayin 5 in one! idan kuma iya littafin KUSKURENA NE za ku daya ₦1000 ne kacal.* *Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.* *TEAM WOW 5 WRITERS HUB* 1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup) GABA TAZO BAYA 2-Harira Salihu Isah Uwar Batoorl YARIMA BAHJAT 3-Zainab yahaya Amzah NOUR AYN 4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool) KUSKURENA NE 5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul) WAHEEDA Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan. Guda ɗaya 1k Biyu 1500 Uku 2k Huɗu 2500 Biyar 3k Account Number 9126022777 Bank: Opay Suna: Ummulkhair Sani Panisauu Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇 09023907030 09161720046 +20 150 885 6397 09065856251 07061707238 *Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.* ©®2026 Under Women of Words Writer's Association, team WOW 5 writer's Hub.