*💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®Fa'iza Almustapha Murai Daga Alkalamin✏ 👄FA'EEH BG👄 💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18💎A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai ya Allah ina tawassali da sunayenka tsalkaka Allahu,Arrahmani,Alwadudu Yaa ubangiji kabani ikon kammala kk story lafiya kamar yadda kabani ikon wallafa shi cikin kuzarin jikina da ƙwaƙwalwalta. _______________________________________ 💋KK💋Story ƙirƙiraren labari ne,duk wani abun da ke cikin labarin ƙirƙira ne, Idan kuma yayi shige da rayuwar ki kiyi haƙuri a kasine ,banyi rubutuna dan cutar da kowa ba,sai dai nayi ne dan kawo Sauyi ga alumma da cigaba...... *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* 👄FA'EEH BG👄 *(FirstLady🙌)* -------------------------------------------------------------------- Littafan marubuciya A MAFARKI NASANTA RAYUWAR MU A YAU ------------------ *BOOK ONE* Free pages👌 P.0️⃣1️⃣ The story is all about ........ *# Destined* *# Jeoleus* *# Arrogant* *# Love and romance* *# Hatred* *# Politics* *# Sympathy* *_THE BEGINNING_* *SULEJA* Daji ne dake cikin garin suleja wanda ake kira ƙare kukan ka. Babu abun da ke tashi sai kukan tsuntsaye kala kala sai kuma yana yin yadda itatuwa ke kaɗawa suna bada iskan hunturu mai daɗi kasancewar lokacin sanyin da ake ciki. Matashiyar budurwa ce ke tafiya cikin dajin a hankali da wani irin tulelen ciki a jikin ta da alama cikin zai kai kamar wata shida haka ko bakwai.Hawaye ne jage jage a kan fuskar ta ga idanun ta sunyi wani irin jaaa tafiya ce ta ke yi wadda bata san inda take jefa ƙafafun ta ba.Yadda take tafiyar kai kan ka zaka shaida a gajiye take kuma a galabaice.Kukan karnuka da taji a bayan ta ne hakan ya sa ta fara sauri tana ƙarawa tafiyar ta sauri kafin ta haɗa da gudu domin kuwa ko ba,a faɗa mata ba ta san ko suwaye kuma suka cimma ta rayuwar ta na cikin galalari domin kuwa kisa ne mai zafi zasu aiwatar akan ta domin yadda suka yi neman ta a chan nan ma hakan ne zai kasance.Cikin wani irin gudu haka take kutsa ƙafafun ta cikin ramukkan dake gaban ta da tulelen cikin na ta ga wata irin Hajijiya da ke kama ta wadda ba ta san mafitar ta ba.Sai dai tana fatan da irin wannan yanayi gwara mutuwar ta domin kuwa wata irin azaba ce ke ta so mata na gudun da take yi dan gudu ne bana wasa ba.Tana kawowa dai dai bakin wani ƙaton rame mai kama da kogo ta faɗa nan domin tsira da rayuwar ta da abinda ke cikin na ta tana sauke haki kafin kuma kan ta ya buge da wani irin ice da bata lura dashi ba A cikin kogon wanda hakan ya sanya ta fara ganin dishi dishi kafin kuma Numfashin ta ya ɗauke ɗiif. *** *A WALA* Sararin samaniya ne da ya ke bada wani irin kala mai kyau da ke ƙara Haska gari tare da ranar da take Kutsowa a lokacin wanda a lokacin ne kowannenn mai fita nema yake fita dan samar wa kan sa abun saka wa a bakin salati,fita irin ta yau da kullum. Ƙauye ne mai tarin hikima kowane irin yare ya haɗa Fulani,Fulani Hausa, wuri,sai dai Fulani sun fi yawa.ƙauye ne wanda ke ɗauke da manyan mutane masu al'adu da ban daban masu hikima,Sannan ƙauye ne da mutanen cikin sa suke yin ta ka tsan tsan da tarbiyyar yan matan su kuma suke ƙoƙarin bawa ya yan su ilmi na Addini da na boko gwargwado... *** Gudu take a hankali kamar wata zakanya a cikin dajin har da wani irin tsalle kamar wadda ke gurin yaƙi yanayin yadda take tsallakar itatuwan da suka yi mata kawanya da abun harin ta.Ba,a iya ganin fuskar ta sai dai bayan ta da yake ɗauke da dogon gashin ta.Dai dai ta isa inda zata ɗana kibiyar ta kenan taji ana furta.. " Adda shatu,Kiyi Sauri ki kama kar ki bari Baffa na ya riga ki " . Saboda yadda suka hango abin farauta yana ta ƙara falla gudu. Da jin wannan furuci na wannan yaro aiko ta ƙara ƙaimi wurin saita abun harin ta wanda ke gudu daga nesa domin tsira da ransa. Ganin kamar tayi gaba da yawa hakan ya sa ta dawo baya da sauri inda ta ja da baya kamar yadda kuka san Actors na yi a film irin na farau ta haka ta ja daaga ta ƙara saita abun harin ta inda ta juya a hankali ta kalli gefen ta tana kallon mutumin da nake tunanin shine Baffa na ganin da tayi yana shirin sakin ta sa kibiyar hakan ya sa ta sakin murmushi kafin a hankali ta saki nata a tare kibiyoyin nasu suka kama hanya suna bin abun harin na sua jere.Wani irin tsalle ta buga tana ɗaga hannayen ta sama tana furta. " Baffa na ka riga ni zuwa kuma ina ga na cinye ka ta wa ta fara isa ". Juyowa tayi tana tare yaron da ya kawo kusa da ita wanda kamar ba zasu wuce sa,anni ba sai dai da ka gani zaka iya tantance wanda ke babba a cikin su.inda ya rungume ta cikin farin ciki, ita ma Rungume shi tayi kamar yadda ya rungume ta sannan suka saki juna suka fara gudu a tare cikin nishaɗi sai dai basu wuce mintuna biyar ba suka isa inda dabbar take domin kuwa ƙatuwar dabba ce suka samo yau kamar yadda suka saba fita farautar su itadah mahaifin ta da ɗan uwan ta wani lokacin ma ita ke fita ita kaɗai duk da yadda take shan magana akan fitar ta ita kaɗai,ko kuma da wannan yaron wanda da alama shi ne ƙane sai dai duk da hakan da gani ka san babu wata tazara tsakanin su dan sai ka yi zaton Yan biyu ne ma. Suna zuwa bakin ƙatuwar Dabbar da ke kwance yashe,Tsalle suka fara wanda yayi dai dai da zuwan wani dattijon mutun kamar bafulani domin fari ne tass wanda kamar su ke sak da yaron.Wata uwar zabira ya Fiddo daga cikin wata yar jaka tashi Sannan ya sai ta wuƙar sa mai kaifi a Wuyan kurar ya yi Bismillah ya yanka inda take jini ya ƙara ɓalle wa a wuyan ta, 'yan murje murjen da take yi take ya tsaya Chak.Bata ƙara shurawa ba. Yana gamawa ya ɗago ya kalli Yar Matashiyar yarinyar da aka kira Adda Shatu wadda a ƙiyasi shekarar ta bata wuce goma sha biyu ba ko sha uku ba sai kuma shi yaron bazai wuce goma ba ko sha ɗaya ba kamar dai saanni suke. " Shatu na ta kashe kura,gaskiya ya kamata a baki kambun girma,maza da yawa ba su iya samun abun harin su kai tsaye amma shatu na take ta ke bin shi da kibiya na jinjinawa Yar Inna Adda ta,Kuma Adda Shatou bace wa Baffa ya yi ki zauna gida ki huta ba shine kika fito,ya ma akayi Inna ni tabar ki kika fito ne?? "....Matashin yaron ya kai ƙarshen furucin yana kallon ta yana ƙara tsalle cikin murna Haka ma Baffa na murmushi yake yi kawai yana kallon ta bayan zare kibiyar ta da ta ture ta sa......... * A gajiye take saboda ta aikatu yau matuƙa duk sai da suka cika komai na gidan gashi daga gurin jidar ruwan akwai nisa,Sannan tare da mahaifiyar ta suka yi ayyukan gidan har aikin gyaran gefen dabbobin su Baffa na da Bibu ke yi.Kafin kuma ta bi bayan mahaifin ta da suka fice tun ɗazu bayan yin karin kumallon su,duk yadda ta so hana ta haka ta barta saboda kukan da ta sanya mata har da murje murje.Tunda ta fito take gudu kamar bazata daina ba saboda nisan wajen da zata isa a cikin ƙungurmin dajin da suka saba farauta ita da mahaifin na ta. Duk wani mai kiran sunan ta bata ko sauraren sa babu abinda ta ke son gani face ta isa inda ta san zata same su.Wasu kai tsaye suke kiran ta da mara kamun kai saboda yadda take tsalle tsallen ta dan ta ɗebo gadon mahaifinta takan saci hanya ta fice ita kaɗai basu ko duba ƙarancin shekarun ta,sai dai a sanar da mahaifin ta an ganta ita kaɗai ta fice farauta,wanda hakan mutanen ƙauyen sai suke faɗe faɗe akan ta wasu har mahaifin ta suna yiwa magana kan yadda ya ke barin ta shiga daji farauta duk iya ƙoƙarin sa shida mahaifiyar ta ga ƙarancin shekarun ta kuma da alama bata tsoron kowa duk da bata shiga harkar kowa,sai an Jata. Bata samu jin ta dai dai ba sai da ta isa dai dai inda zata same su sannan ta dakata.Dukkanin su da suka gan ta Murmushi kawai suka yi dama sun san za,a rina,Saboda yau weekend ce babu makaranta,ta allon ma ta su yau ba,a zuwa.Shiru tayi bayan tuno yadda ta fito kafin ta ƙara sakin murmushi ba tare da ta bashi amsar tambayar sa ba ganin yadda yake ta murna kafin ta ƙara ɗana wani mashin ta jefi tsuntsuwa da tayi fira daga kan iccen Mangwaro a yanzu aiko cikin sa,a sai gata ƙasa tana bille bille da sauri Baffa ya yanke wuyan yar kurciyar yana murmushi ganin yadda ta ƙara cilla ta ya san shatu da namiji ce anan gaba da tafi shi ƙwarewa akan harbi duk da ko yanzu tana nuna masa iyawar ta duk da tana da ƙananan shekarun ta. Tsalle ta daka " Na ƙara samun sa,a Bibu " tayi furucin tana kallon yaron. murmushin farin ciki yaron ya saki yana tsallen murna shima a karo na biyu. Murmushi mutumin da suke kira Baffa na yayi wanda yake matsayin mahaifin su. A haka suka haɗa komai na su na farauta sannan suka doshi wani ƙaton rafi aka gyaran naman tsafff sannan suka kama hanyar gida kai tsaye kasancewar sun yi sa,ar fita yau lokaci ɗaya sun yo farautar Babban Kamu. Sai da suka yi tafiya mai tsawo daga cikin jejin sannan suka iso dai dai wani ɗan madaidaicin gida na ƙasa da ya ji fenti fari sai kuma wasu yan bukkoki dake cikin sa tare da wasu ginukan ƙasa da ake iya hangowa ta ciki saboda rashin girman katangar. Da sallama ɗauke a bakunan su suka shiga cikin gidan. Yar matashiyar matar dake zaune a kan tabarmar kaba ce wadda kamar ta take kamar an tsaga kara da Shatou saboda ita ta biyo bata wani kama da Baffana ta amsa Sallama fuskar ta cike da murmushi tana kallon su musamman Shatu dake ta tsallen murna na irin ƙwazon da tayi a yau ɗin duk da dama tana yawan samun abun harin ta awurin farauta amma na yau ya banbanta saboda Babban kamu tayi ba irin ƙananan dabbobi bane. " Maraba lale maraba ". Ta yi furucin bayan amsa Sallamar su miƙewa tayi da ɗan sauri ta riƙa ma Baffa kayan dake riƙe a hannun sa cikin sakin fuska. Murmushin ya saki shima tare da sauke ƙwaryar naman da suka feɗe a bakin wani rafi. "Sannu da dawowa Baffan su." "Yawwa Sannu A'i " "Kin san yau Mutuniya ta tayi muna babban kamu".Ya ƙara yin furucin yana murmushi. Murmushi ta yi tana mamaki mai girma da wannan lamari nan Shatou gashi bata san yadda zata raba ta da Farautar nan ba. A hankali ta kalli kuma ta kalli Shatu dake ta murmushi ta furta " Su Hajiya rigima an yi sa,a,Kuka fa ta zauna ta na mini harda murje murje,Allah da na same ta da sai ta ci na jaki yan nema shekara sha biyu cikin ta uku babu wayau sai rigimar tsiya,ko Bibu na yafi ta hankali ". Murmushi Baffa na yayi yana furta " Sai gata kuwa,na so ace ta zauna ta huta,bana son yadda mutanen ƙauyen nan ke magana akan guje gujen ta ". " Allah dai ya shirye ta indai Shatu ce sai Addu,a,Allah ya shirya maka ita ". Inna ni tayi furucin " Amin A'iie ". Baffa na yayi furucin yana sakin murmushi yana kallon Shatu da ta turo bakin ta gaba ganin Bibu na dariya ƙasa ƙasa ance yafi ta hankali. Sallar la,asar kawai kowa yayi yi suka huta suka ci abinci sannan suka zauna a tare suka yi aikin yanke naman tsaff ita da su Bibu da shatu yana yi yana bata labarin yadda komai ya wakana a chan dajin.Ita ko tana mitar guje gujen da zuwa farautan na ta da yawan fita ma da take yi a sace da take ƙokarin hana ta.Amma abu ya gagara. A haka har suka gama zuwa lokacin ta hura wuta da yangan ice da shatu tayo jiya Har aka kusa Sallar magriba suna nan zaune suna taɓa fira tare da ƙara rura wuta akan tukunyar dahuwar naman su,wanda suke dafa wa a matsayin abincin daren su. Wanka kowannen su yayi Sannan mazan suka wuce Masallaci dan gabatar da sallahn magriba.Suna dawowa dai dai naman yayi rugu rugu,Inna ni ta gama shirya komai da taimakon Shatu suka zauna suka ci suka ƙoshi kowannen su yayi nak. Sannann Aka yiwa su Shatu bitar karatun su.Sallar Isha'i ce ta tashe su gaba ɗaya Sannan kowannen su ya wuce wajen sauƙe Haƙƙin Allah dan har yaran iyayen su sun sabar musu da yin Sallah a lokacin ta. Tun da aka gama Sallolin Isha bayan dawowar su Baffa da Bibu Inna ni kamar yadda suke kiran ta,take jiran fitowar Shatu daga ɗan madaidaicin ɗakin na ta da yake kamar yar bukka saboda ba wani mai girma bane, sai dai wayam shiru babu labarin fitowar ta.A zaton ta ma sallar ce bata gama ba amma sai gashi har aka gama sallolin mazan suka shigo gidan babu labarin ta,sai dai dan tabbatar da zargin ta bayan shigowar ta su ya sa ta faɗa dakin na ta yadda taji shiru haka ɗakin yake babu mai kama da shatu sai yan kayan ta da yar tabarmar ta dake da ɗauke da zanen shimfiɗar ta ko ina tsaf sai dai ga kayan da ta cire nan yanzu a watse ta chanza wani. Shiru tayi bayan fitowar ta daga ɗakin kafin ta nisa ta girgiza kan ta.Yawon shatu tsoro yake bata data samu dama sai ta fice daga gidan duk irin faɗan da take mata a banza gashi wata rana harda bugu take haɗa mata mata dashi dan ma Baffa na, na hana ta da kullum sai ta jibge ta. " Ta fice ko "??? Baffa ya yi furucin yana girgiza kan sa shima fuskar wanze da Murmushi dan ko ɗazu kafin su fice sallah sai da ya ce mata " banda fita Shatu a zauna gida a huta a haka yau anyi farauta Babba." Ashe bata shiga kunnen ta ba maganar. Kai kawai Inna ta iya ɗaga masa tana zama akan sallayar da ta sha jiki wadda ta shimfiɗa akan Tabarmar kaba da take kai. Charbin ta da take jaa ta cigaba da jaaa sai dai hankalin ta na kan yar ta tsoron ta ɗaya kar ta jawo musu abun magana saboda Mafaɗaciya ce ta ƙwarai shatu koda yaushe cikin kawo ƙarar ta ake gidan ta yiwa wani, wani abun daga cikin warin ta ko wayen da basu kai ta ba har manya ma in suka shiga gonar ta sai ta rufe ido ta yi rashin mutum ci shi yasa bata shiga sabgar da bata shafe ta ba saboda bata da haƙuri idan ka taɓa sai ta rama a kullum Addu,ar iyayen ta kenan samun hankalin ta na wannan yawan faɗaɗace faɗacen, idan ka mata kallo ɗaya zaka hango natsuwa a tattare da ita amma ana taɓa ta zaka san akwai ruwan rigima da suke ɓoye a cikin ta,wanda Tsokanar ta ke iya tsokalo su. "Baffan su,wai ni Shatu ba igiya zan fara saka mata ba,tsoro nake ji ta jawo muna wata rigimar domin ban manta karon ta da ɗan gidan mai gari ba da yan zu ya illata ta ga tsoro ga ban tsoro kura,bana son fita wasar nan ta Dare". Murmushin Baffa yayi jin Furucin Inna ni kafin ya sauke Kan sa ƙasa Yana kallon Bibu dake jin kamar ya saka kuka jin mahaifiyar su ta fara zancen ɗaure Adda shatu. " Baza,ayi haka ba ai ". " Na san abun da zanyi A'ie." Bata iya furta komai ba ta miƙe daman bata yi shafa'i da wutiri ba ta kabbarta Sallar ta,.Sai dai Ranta a jagule yake matuƙa.Kusan kullum sai ta mata faɗa Dan shi Baffa bai son ana mata faɗan ma ko kaɗan idan tayi sai yayi ta Rarrashin ta yana mata faɗan cikin hikima a cewar sa yarinya ta ce,kuma ya san duk wanda ta taɓa shine ya fara tsokanar ta.Bibu kuwa da Baffa cigaba da bita karatun Alqur'anin suka yi a tare hankali kwance duk da rabin hankalin su na kan Shatoun su. A ɓangaren Shatu kuwa tunda ta samu ta fice ta ke fanfala gudu kamar wadda take harin abu farautar ta a daji bata tsaya ba sai inda suka saba tsaya wa suyi wasannin su ita da sauran ƙawayen na ta. Sai dai yau anyi rashin sa,a duka basu taru gurin ba sai ita sai mazan dake wajen yan na iya masu zuwa kallon su. Wuri ta samu ta zauna zaman jiran su saboda zasu kai su goma amma manyan ƙawayen ta su uku ne kuma kan su komai tana iya yi mafi yawan rigimar ta akan su ne su aka taɓa saboda kowa na tsoron shiga sabgar ta. " Yan mata ".!! Duk yadda take jin sautin na shiga kunnen ta bata jin zata ko kalli mai maganar Dan bata da lokacin sa,saboda ta raina sa tun asali,kuma ta san kowane ne.Ibro ne ɗan gidan mai gari da yake ta Bibiyar ta.. Like and share. Ku ta yani Sharing saboda Allah.🙏 Daga Alƙalamin✍️ Firstlady🙌 (Fa'eeh BG) GIMBIYAR TASKIRA 👑 08069059746 For more information👆 UPDATE👇 https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0 Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®Fa'iza Almustapha Murai Daga Alkalamin✏ 👄FA'EEH BG👄 💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎 *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* ______________💔 _Wannan Shafi naki ne baki ɗaya masoyiya ta AMMYN LAYLAH 😘💞 Ina godiya da kulawar ki a kaina da wannan labari,Ina roƙon Alkhairin Allah ya kai Miki A duk inda kike,kuma ya raya muna Love(Layla).🥰🤲🏾_ ______________💔 _Daga marubuciyar littafin_ *A MAFARKI NASANTA* *RAYUWAR MU A YAU* '''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''’''' *BOOK ONE* Free pages👌 P..0️⃣2️⃣ Shiru ta masa tana fatan kar ya ƙule ta ta masa rashin mutunci kamar na ranar Da ya tashi kaɗe ta, ta fahimci bai da zuciya bai ji kashe din da aka musu ba a tsakanin su.Tunda har zai iya Binta a karo na biyu.Ganin ya dawo ta gaban ta yasa ta ƙara ɗauke kanta tare da rufe Hancin ta irin na wari yake yi dan ta ɓata masa rai da siffar wulaƙanci duk da ba warin yake yi ba. Shiko Iro murmushi kawai ya saki na yaƙe sannan jiki mace ya ja baya yana komawa cikin yan uwan sa da suke masa dariyar abun da ta yi masa duk da ya san laifin sa ne,amma zai yi maganin ta zai cire mata girman kan dake kan ta. " Ya kamata fa ake ce raini dake tsakanin ka da Yar shilar chan yarinya ba komai a ƙirji sai ƙwailanci amma kana ta Bibiyar ta tana dizga ka,yaro mai ilmi duk ƙauyen nan kana Buz guy,gaskiya Iro ka yi tunanin abin yi dan ni waccan yarinyar tsafff zan iya karya ta karass na watsa ƙasusuwan ta a rafi " Wani daga cikin Abokan na sa ya faɗa kai tsaye bayan tsaida dariyar sa ta ƙeta ganin iro na masa kallon bana son haka. Iro dai sauraren sa kawai yake yi sai wani cije baki da yake yi yana jan yaji irin na ɓacin rai wanda ya taso masa yanzu.Musammman da ya tuno rashin mutuncin da tayi masa a ranar da ya so buge ta da mashin ɗin sa mara shalan sa da ya addabi ƙauyen da shi wanda ya zo dashi bayan gama JLC ɗin sa da yake faɗin degree ce da ya kwashe yan shekaru a A birni.Anan ƙauyen ma ana secondry school bayan primary wanda kuma nan iya bokon na su yake ƙarewa bakin SS3 wasu ma basu kaiwa ake musu Aure wasu kuwa sukan fitar da ya yan su birane masu kuɗi kenan sai su cigaba da karatun su.Kamar dai Iro ɗai daga cikin ya yan mai gari wanda bai ma fara karatun a nan ba ya fara karatun sa a birni tun Daga jss1 zuwa jss3 bayan gama primary ɗin sa wanda rabi da kwata yawon banza ne da kashe ma matan hanya kuɗaɗe da tangaririya a cikin gari sai ya dawo ƙauyen yana fafa da sunan Jami'a yake yi har ya ci wasu shekaru a chan bai haɗa ko Takardar gama secondry ba sai ƙaryace ƙaryace duk da kuwa yana da ƙananan shekaru shima dan bai wuce sha shidda ba amma Allah ya zuba masa ƙarya ga ɗan ruwan da ya iya ɗan watsawa na mutumen ƙauye da ya je birni shi ya sa mutanen ƙauye suke ji dashi haka ma mai gari da aka rufe da wasu takardun bugi shima ya zauna akan ɗan sa ya haɗa degree yayi karatu mai zurfi a yanzu haka ya na nema masa aikin yi ne da takardun sa,kuma idan aka yi baƙo a ƙauyen shine mutun na farko da ake kira gudun kar a haɗu da Bature wanda bai jin Hausa su kasa iya communication.Ga kuma Case na biyu daga bata Shawara bai daddara ba dan ya san guje gujen ne nata suka sa yayi niyyar kaɗe ta sai komai ya juye.Wannan kenan. 'Zuwan yara ne su biyar da basu wuce shekarun ta ba yan sha uku sha biyu ya sa ta miƙe tana washe baki hankalin ta kwance ta tare su itama da gudun nan na ta kamar yadda suka zo a guje gurin dan dama sun san ta iso tun da har gidan su sun leƙa basu gan ta ba.Sannan suka fito a guje kafin Inna ni ta gan su ta riƙe su gidan kamar yadda take musu idan sun biyo mata haka wanda daga ƙarshe dole Shatu ta baro wajen dan ta san muddin bata gan su ba har lokaci ya cika suna gurin Innar ta tana musu fira Dan bata son fitar kwata kwata ta Shatu wanda kuma da shatu ta ga haka take komawa gida baki kunbure na rashin yin wasar daren da basu yi ba.Abu kamar jaraba. 🤭 Yo Shatu wasan Dole ne.Bari dai nayi shiru kar amini rashin mutunci😂 " Shatu ! Shatu ! Shatu " ! Shine abun da suka haɗa baki gurin faɗi dai dai isowar su kusa da juna cikin washe baki itama bakin ta washe ta riƙo hannun Babbar ƙawar ta Amina daga cikin su ƙawayen nata tana furta " Nidai na zaɓi Abokiya ta ".Kallon ta kawai suka yi babu mai bakin magana a cikin su dan sun san kullum aka zo haka take musu wayau kuma har Amina ta saba duk da tana da ɗan tsoro shi ya sa kafin su iso sai sun gargaɗe ta ko da an zo tace bata son Shatu matsayin Abokiyar haɗin ta.Amina dai bata iya cewa komai ba sai ɗan murmushi da ta ƙaƙalo kafin ta koma gefen Shatun tana ƙara washe bakin ta. Su kuwa sauran ƙawayen na su kowacce kama Abokiyar ta tayi cikin jin haushi kafin su fara gabatar da wasan na su duk da sauran ƙawayen na ta na amana biyu suna cike da jin haushin abun fifikon da Shatu ke Nuna wa a tsakanin su.Wasannin su suka fara kamar yadda suka saba irin dai wasannin nan na dare da yara ke yi na tsalle tsalle da yar goye goyen nan,wanda yar goye goyen ce ma ke saka Shatu zaɓar Amina saboda sune basa da jiki amma duka sauran sun fi su girma ita cewa take bazata iya ɗaukar ƙatuwa ba.Dan shi take zaɓen Amina kai tsaye bata ma bari ayi wasan a fitar da wanda zai goya wani.Sun yi wasannin su cikin nishaɗi sai dai me suna gab da kammalawa kowa ya watse mazan da ke gurin su Iro kenan suka yo cikin su suna hudi irin abun nan na iskanci suna shigewa cikin su duk wadda ka samu ka rungume.Cikin rashin sa,a Iro ya faɗa hannun Shatu bada sanin sa ba Aiko tana jin yadda ya ke ƙoƙarin rungumar ta ta yi masa mugun cizo a hannun sa da iya ƙarfin ta har sai da ta ja sosai fahimtar shine dama da Haushin shi take matuƙa na ƙazafin da yayi mata kwanan baya wai ta zage shi ta zagi mai gari da ga kawai ya ma ta faɗan ta daina guje guje,bayan rashin mutuncin da ta masa ranar da ya tashi kaɗe ta,bata kula sa ba,dan bata son shigar shigula,ko ranar ma rayuwar ta yayi niyyar illatawa da mashin ɗin sa shi ya sa ta masa tass,Alhalin kuma ƙarya yake mata bata zage sa ko ranar dan daga ƙarshe ma da ya ishe ta sai ta masa tsawa,shine da ya ji Haushi ya je ya faɗa ma Mahaifin ta shine aka mata faɗa ta ji haushi ta gan shi kan hanya ta ƙara gaggaya masa magana cikin rashin tsoron sa.Haka magana tun tana ƙarama har ta zama Babba ta kai ga mai gari an taɓa ɗan gaban goshin sa hasken ƙauyen su,ya tara zaman ba,a si,sai dai mutane sai faɗar suke itace bata da gaskiya saboda a gaban jama'a ta yi masa rashin mutunci kamar sakon ta,kuma sun lura da lalama ya mata maganar guje gujen na ta,haka aka yi zaman babu daɗi daga ƙarshe aka yi sulhu aka tsayar da kowa matsayin sa.Tun daga wannan rana kuma duk da kashe din dake tsakanin su yake bibiyar ta dan shi burge shi take yi musamman ma faɗan na ta ɗan ƙaramin bakin ta ya ke son ganin yana motsi saboda yana burge sa,shi ya sa yake ƙara shisshige mata musamman da ya ke ji da kan sa shima sai yake ganin yafi ƙarfin ta ma dan haka yake da ya gan ta yake mata magana kamar wanda ya bata ajiya ita kuma tana share sa dan mugun tsanar sa take ji dan kan shi Baffa yayi mata faɗa sosai Inna ni ma ta so ta dake ta,da ƙyar ta sha kuma itace mai gaskiya... Ƙarar da Iro ya sanya ce ta ankarar da mutane halin da yake ciki,kan su aka yo kafin su an kara Shatu ta falfale a guje wasu daga cikin ƙawayen Iron ne Musa da isaka suka bi bayan ta sai dai kafin su an kara ta ɓace ma ganin su saboda mugun gudun da take yi gashi ɗan jikin ba wani ba kamar balbela.Haka suka dawo suna cizon baki da wassafa yadda zasu ci uban Shatu in suka riƙe ta Iro bai so matsawa ga re su ba amma suka matsa masa gashi sun ja masa wahala dan ya cizu.Haka suke kallon sa cikin tausayi sun zagaye sa,suna masa fifita tare da mayar da bakin yadda aka yi. Su kuwa Su Amina kowaccen su gida ta nufa bayan samun kuɓuta daga hannun Mazan hankalin su a tashe dan sun tsorata basu taɓa musu haka ba sai yau.Kuma sun ji daɗin abun da Shatu tayi ma ɗai daga cikin su duk da basu san kowaye ba dan ta cece su matuƙa. Hannun sa da ya fara tartsar da jini wani ya yanki gefen hannun rigar sa da ta ji jiki yana furta " Yarinya kamar mayya duba yadda ta fasa maka hannu wallahi sai taci uban ta yarinya mai Shegen tsiwar tsiya wallahi Iro kabar ni da ita Sai na koya masu hankali shegiya dangin Mayu masu farautar naman mushe ". Ya kai ƙarshen zancen yana ɗaure masa hannun da ke masa zuji shiko Iro Wata irin kunya ce ta dabaibaye shi da baƙin ciki lokaci ɗaya yadda zai wulaƙan ta rayuwar Shatu kawai yake hangowa.Shi da ya san ita ce ai ba zai faɗa mata ba,Amma wallahi zata gane kuren ta sai zaman ƙauyen ya gagare ta haka yake ta tunani kala cike da baƙin ciki dan a cikin a bokan na su akwai masu masa dariya ƙasa ƙasa musamman da suka ga yana jin jiki sosai ya wahala matuƙa. Suna barin wajen direct gidan mai gari suka wuce maimakon su wuce ɗan ƙaramin chemist na ƙauyen a bashi maganin rage raɗaɗi. " Keh Adda lafiya kika faɗo muna gida a hargitse keda kike shigowa a sace yau sai gaki a guje da alama wayen nan idanun naki basu da gaskiya Adda Shatu". Bibu yayi furucin yana kallon ta bayan kiciɓus da suka yi saboda ganin bata dawo da wuri ba shine zai saci hanya yaje neman ta.Sai gata a guje tana neman kai shi ƙasa tana zarar ido kamar karen da yayi ƙarya. Hararar wasa ta sakar masa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta yi masa raɗa a kunne tana sakin ƙaramar dariya. Idanu Bibu ya zaro cike da tsoron abun da ta faɗa masa kafin ya riƙo hannun ta da sauri ya shige ɗakin sa da ita yana kallon ƙofa. Ba,a fi mintina biyar da shigar su ɗakin na sa ba sun yi jugum sai ga Ƙatuwar Muryan Wani Babban yaron mai gari ya'yan Iro mara kunya yana rabka sallama cikin hargowa.Ƙirjin ta ne ya buga da sauri kafin ta shanye tsoron da ya shige ta domin ita yanzu mahaifiyar ta take tsoron ta ji abun da ta yi duk da ta san da gaskiyar ta duk inda za,aje amma ta san da wanchan mugun ba zai faɗi shine mara gaskiya ba ko a yanzun. Da sauri Baffa na dake ɗakin sa ya fito haka ma Inna ni da sauri ta fito nata ɗakin dama a tsame take hankalin ta na kan Shatun ta. Jikin ta na bata sai ta zo musu da wata rigimar. " Na rantse da Allah sai na kakkarya Shatu kosongo shegiya mara tarbiyya " Laƙanin da wasu daga cikin mutanen ƙauyen suka mata kenan,kuma daga bakin Iro ya fito saboda guje gujen ta da Shegen gudun da Allah ya bata,sai suma mutanen gari suka ɗauka,A ɓoye Dan ya taɓa ganin wata dabba mai Shegen gudu mai suna kosongo shine ya kira sunan gaban abokan sa yana kaman ta Shatu dashi sai suka ɗauka suna kiran ta dashi.Amma saboda fitinar ta ba kowa ke iya kiran ta hakan ba saboda bata shiga sabgar kowa Shatu yarinya ce mai halin manya dan Shegen wayau ne da ita duk faɗan da ake mata tana takatsan tsan amma da zaran an Jata sai tace katt,musamman irin su Iro yan na iya. " Iro ta ciza har sai da ta fasa shi yanzu haka yana chan hannun na sa yana zuza yana kuka, saboda ta saka masa mugayen haƙoran ta masu kama da na kura sun zabci naman daji har sun gaji wallahi sai na lallasa ta kafin ma mai gari ya yi maganin ta ko shi iro Ni zan yi " Ya kai ƙarshen zancen ganin Baffa na ya zuba masa idanun sa yana kallon sa cikin mamakin yadda yake zagin yar sa gaban sa babu kunya harda wani Shegen suna da suka mata wanda shi bai taɓa jin sa ba sai yau. A jiyar zuciya Baffa na ya sauke kafin ya ja numfashi Yace " Zaidu a riƙa tausasa harshe koba komai Ni mahaifin Shatu ne ba komai ya kamata ka faɗa a gaba na ba,kuma na san Shatu na bazata iya aikata abin da ka faɗa ba ba tare da an tsokane ta ba wannan halin ta ne na sani,Dan haka ba zan gaji da bada haƙuri ba kamar ranar ayi mata haƙuri yarinta ce ke damun ta duka duka Shatu shekarar ta Sha biyu cikin ta sha Uku Zamu je yanzu na kai shi a duba hannun "..Baffa na ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi.Dai dai kuma lokacin ne saƙon mai gari ya iso masa na neman Shatu da iyayen ta. Mai bada saƙon Yana gama sanar da Baffa ya wuce cikin mamakin abun da Zaidu yake yi anan amma ya san bai wuce takakka ce ya kawo gidan ba saboda ɗan uwan sa. " Wallahi aja mata kunne ko na lafira ya fi ta jin daɗi wallahi yau ta leƙo barzahu ta gane mana asarori ".Zaidu yayi zancen yana barin wajen shima. Inda ya bar Baffa na cike da takaici na rashin mutun cin sa da kuma neman da mai gari yake masu.Tunanin yadda case ɗin zai ƙare ne ya fara a tsaye ganin tsayin bazai amfana masa komai ba ga dare na yi hakan ya sa ya juya ya koma cikin gidan inda ya isko Inna ni tsaye ƙofar ɗakin Bibu ga Shatu daga ciki tana ta kuka kamar wadda aka yanka kafin ma ta taɓa ta dan duk ta ji komai da ya faru kuma tana da tabbacin Shatun ta dawo gida dan haka ta leƙa ɗakin ta sai dai babu ta ciki hakan yasa ta koma ɗakin Bibu Tun kafin ma ta shiga taji ƙusƙus ɗin su Bibu na ce mata kar ta ji tsoro ai itace mai gaskiya waya sa ya taɓa ta ai ya taɓa jin akwai lokacin da Inna ni tace mata kar ta riƙa bari maza su taɓa jikin ta koda hannun ta ne kar ta bari Indai ba Bibu ba sai Baffa na.Hakan da Inna ni taji ta tabbatar da yar ta ce mai gaskiya hakan ya sa ta dakata da ga shiga ɗakin sai dai ta ɗaga murya cikin kaushin murya tana kiran Sunan Shatun,ita kuwa Shatu cike da tsoro ta fara kuka dan ta san yau sai kashin ta ya bushe A hannun Inna ni. Baffa na bai cewa Inna ni komai ba ya shiga ɗakin ya riƙo hannun Shatu yana share mata hawaye cikin Tausayin ta kafin ya tambaye ta ta faɗa masa gaskiyar abun da ya haɗa ta da Iro a karo na biyu idan har itace da gaskiya zasu tsaya mata a bata gaskiya komai wahalar samun gaskiyar. Cikin kuka ta sanar masa da komai dake faruwa.Ɓacin rai ne ya bayyanar masa hakan ya sa rai ɓace ya ja hannun ta suka fice daga gidan ba tare da ya cewa Inna ni komai ba da ma shi ya san akwai dalilin da yasa Shatu ta masa haka. Inna ni ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Bibu da yaji Tausayin yar uwar ta sa shima ya fara hawayen dan bai yi tunanin zata sha ba ko yanzu ma bai jin Inna ni zata ƙyale Shatun sa..... Ba zamu daɗe muna free pages ba gaskiya zaku iya fara payment... 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga wannan sati bazan ƙara posting a weekend ba gaskiya saboda ranar Hutu ce.🙏 Ƙarin bayani. 08069059746 Daga Alƙalamin ✍️ Gimbiyar taskira👑 FirstLady 🙌 React and Share, Comment PLS 🙏 *UPDATE* https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0 *Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®Fa'iza Almustapha Murai Daga Alkalamin✏ 👄FA'EEH BG👄 💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎 *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* _Daga marubuciyar littafin_ *A MAFARKI NASANTA* *RAYUWAR MU A YAU* '''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''''’'''"""""""" *_𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭_* Best kayan kwalam 09025859622 or 09163353050 *END OF DISCUSSION PACKAGE* Now available in- candies package stop in and stock up on a sweet piece of summer! 🍬🍔🧆 𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭: ce ta shirya tsafff domin kawo muku. Samosa Spring rolls Filled doughnut Glazed doughnut Puff puff Shawarma Cupcake Birthday cake Bento cake Egg roll Milk cake Candy's Alewar madara Gullisuwa Tsami gaye Coconut laddo Milky gireba Albishir Mandula Sayen daya ko sari muna aikawa ko ina cikin aminci muna karɓar order bikin suna ko aure Location zamfara state ,gusau What's no :-09025859622 or 09163353050 Hajiya karki bari wannan garaɓasa ta wuceki domin taken mu shi ne 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝘿𝙀𝙇𝙄𝙂𝙃𝙏 Koda kuɗinka seda Rabonka... Se kun zo _______________&&&& *BOOK ONE* Free pages👌 P..0️⃣3️⃣ 💦💦💦 Ɗaki ta juya ta shige zuciyar ta cunkushe.Shi ko Bibu a sace yabi bayan su. A ɓangaren su Baffa na da Shatou kuwa har suka isa Fadar mai gari yana Rarrashin ta dan ta kasa tsaida kukan ta Muryan da mahaifiyar ta tayi amfani da ita wajen kiran sunan ta ne abun da ke ƙara tayar mata da hankali. Dai dai sun kusa isa Fadar ta mai gari ne ta tsayar da hawayen ta chak tare da haɗiye fuska dan kar ma a ga ruwan ta a samu damar yi mata rainin wayau ko ta muzan ta tana kuka gaban shi yayi zaton tsoro ne. Zama suka yi a gafe kamar yadda Iro da abokan sa suke zaune.Gayar Da Mai Gari Baffa na yayi,sannan yayi shiru bayan ƙare ma su Iro da kowannen su yake cike da batsewa jira kawai suke yi a basu dama su illata shatou sai abun ya bashi dariya da ya kalli girman Shatun sa da kuma yan matasan da ke ta cika suna batsewa kan ta ,wani ko cikin Hancin sa zai iya tura ta amma nan dama suke jira su ci zarafin ta,ƙila har su karya masa yaaaa. Ba su ɗauki mintina uku da zuwa ba sai ga duka abokan nan wasan na su Shatou an tattataro suma tare da iyayen su. Gaggaisawa suka yi da mai gari kafin kowa ya samu guri ya tsaya masu zama kuma suna zaunawa. Gyaran murya mai gari yayi tare sallama ga kowa dake wajen har da wayen da ba,a gayyata ba a wajen yan ganin ƙwamm. Sannan ya cigaba da magana... " Shatou Iro ya kawo ƙarar ki,kumaa na samu shaidu da dama anan dan ga abokan sa sun tabbatar da ke kika aikata masa wannan ɗanyen aiki,ki duba ki ga yadda hannun ya kumbura lokaci ɗaya,sun ce bai Miki komai ba kika aza masa haƙora haka ". Ai da sauri Shatou ta ɗaga idanun ta tana zuba ma mai gari da ya sauke ayar zan cen da ya ɗauko.Ido cikin ido ta ke kallon sa kafin kuma ta ɗauke idanun ta tana mayar da su kan Zaidu da yake furta " Uban kike kallo haka ". Samun kan ta tayi da sakar masa murmushi irin na baka da hankali kafin ta furta ƙasa ƙasa ta yadda shi kaɗai zai iya gane abun da ta furta masa " Ubanka dai " Idanu zai du ya zaro da sauri yana ƙoƙarin yin kan ta aka riƙe sa inji wani daga cikin ya yan mai garin mai suna Ali wanda duk yafi su hankali kuma yaga lokacin da Shatou ta furta masa amsar da ta bashi,wanda sai da ya saka sa murmusawa da mamakin ƙarfin halin shatou.Ciccika Zaidu yake yi yana cije bakin sa ran sa ɓace ji yake ina ma akwai wuta ya jefa Shatou ya futa dan wata irin tsanar ta yaji jin yadda ko tsoron sa babu a idanun ta ta basa amsa. Ita kuwa Shatou Hararar sa tayi tare da kallon Baffa na da yake kallon ta ganin tana Hararar Zaidu gashi yaga ana riƙon sa wanda kuma yana jin sa yanzu ya gama zagin ta a gaban sa,gashi kamar kan ta yake son ya zo.Kan sa kawa ya girgiza yana mamakin abinda ya ƙara harzuƙa sa haka.(Niko nace yar ka ce Baffa na 😂) Kafin ya bata damar magana da idanun sa sannan ya furta " ki faɗi gaskiya kinji Shatou na ".kai ta gyaɗa masa tana sakin ajiyar zuciya. Kamar ba zata yi magana ba ta buɗe bakin ta cikin rashin tsoro ta ce " Dukkanin abokan sa munafukai ne wallahi mai gari shine bai da gaskiya,Sun dai rufe zancen da ƙaryar su,maƙaryatan banza ko kunya baku ji gashi malam Habu yace wuta ake saka mai ƙarya da badan bawa bai isa ya yanke wa bawa hukunci ba da dan an muna karatun da tuni nace yan wuta kuke dukkanin ku Tarin dolaye kawai,Bari kaji mai Gari wallahi a tambayi su Amina a ji Haka kawai suka yi cikin mu muna wasa suka kama faɗawa jikin mu,Ni kuma gashi Inna ni ta ce kar na bar kowa ya taɓa ni,sannan malam Habu ma ya muna karatun shine na cije sa kuma ni ban ma san cewa Iron ka bane da sai dai na gudu ba zan taɓa maka shi ba ".Tana kai ayar zancen tayi shiru.Inda Fadar mai gari tayi wata irin hargitsewa lokaci ɗaya Abokan Iro kamar zasu cire bakunan su wasu na zagin Shatou wasu na tsinema ta,wasu na ƙarya ta abun da ta faɗa duk sun cika wajen da Surutun su,inda da ƙyar aka samu suka lafa dan har wasu suna son kai hannu kan Shatou sai da Baffa na yayi da ƙyar da sun taɓa yar gaban goshi.Maganganun Shatou sun yi tsauri gare su take wani Haushin ta ya da muguwar tsanar ta suka fara kutsa su ji suke kamar su kashe ta take gurin. Baffa na da hankali ya kwanta ya ce " Allah ya ƙara ma lafiya mai gari ni na san cewa SHATOU ba zata taɓa yin ƙarya ba a bincika a tabbatar". Ɗan jim mai gari yayi badan komai ba sai dan yadda zantukan SHATU suka shige sa dan yayi mamakin yadda ta iya zaro irin wannan kalamai kamar ana tsara mata. Sai da ya gama ƙare ma Iro da sauran abokan sa kallo sannan ya dawo da kallon sa ga su Amina da suke tsaye cirko cirko. " Gaskiya ne abun da Shatou ta faɗa "? Mai gari yayi furucin yana kallon su Amina, Ramatu,Jawariyya Manyan ƙawayen na Shatou.Kame kame suka fara gaba ɗaya kowaccen su na son faɗin gaskiya sai dai tsoro ya cika musu zukata ganin yadda iro yake bin su da wani irin kallo da Zaidu ga kuma sauran abokan na sa da suke jifar su da mugun kallon nan na idan kuka faɗi gaskiya zaku gane kuren ku. Amina ce da tafi su Tsoro ta buɗe bakin ta da ƙyar bayan kashe din da Iro yayi mata yanzu ido cikin ido ta furta " A'a ba haka bane,Suma sun shiga ayi wasan da su ne wai ".takai ƙarshen zancen jikin ta na rawa Muryan ta ma na rawa kamar mazari. Wani irin mugun kallo SHATOU ta jefa mata kafin cikin ta kaici ta ce " Wallahi ƙarya ya faɗa,Wallahi tsoron su take ji,ki rantse idan ba jikin ki suka je taɓawa ba " Ta kai ƙarshen zancen cikin takaici wasu irin hawaye suna zubo mata na raɗaɗi da baƙin cikin amsar da Amina ta bada dan ta ji zafin amsar tata fiye da abun da su Iro suka mata dan ita kam ta rage zafin abun da iro ya mata dan ta bar masa dafin da bazai ƙara gigin kai hannun sa kan ta ba. Kuka take yi wiwi Saboda yadda ranta ya ɓa ci musamman dasu Ramatu suka ƙara tabbatar da zancen na Amina haka ma sauran abokan wasan na su. Baffa na ne yake Rarrashin ta da bata baki inda da ƙyar ya samu ta yi shiru. " To ka dai ji kai da kake nuna ka yarda da yar ka ɗari bisa yaran yanzu ai ba abun yarda bane,suna da wayon da kai kan ka zasu iya sayar da kai inba kayi hankali ba,yanzu dai SHATOU ƙarya kika yiwa Iro ni dama na san ba za su iya aikata wannan aiki ba ƙazafi ne kawai ". Shiru Baffa na yayi ran shi yayi matuƙar ɓaci amma da yake mutun ne mai haƙuri matuƙa sai yayi ƙoƙarin shanye ɓacin ran sa. SHATOU kuwa samun hawayen ta tayi sun ƙafe ƙaff kafin cikin wani irin kakkausar murya ta furta " Mai gari nice mai ƙarya ko,wallahi bana ƙarya,a tambayi Baffa na amma tunda kace shi ne mai gaskiya naji na yarda, amma ku sani wallahi kune maƙarya ta gaba ɗaya wannan shari'ar ta ƙarya ce,kuma wallahi sai Allah ya saka mini badai kunce ƙazafi na masa ba,wallahi sai haƙƙi na ya fita nan kusa,Ku kuma su Amina daga yau babu ni babu ku kowa ya tsaya kan sa ni ba mutuniyar banza bace maƙarya ciya.Zan bashi haƙuri kamar yadda aka ce ".Sannan ta kalli Iro tace Kayi haƙuri Muryan ta a sanyaye cikin wani irin baƙin cikin da ya mamaye mata zuciyar ta. " Baffa tashi muje ".Tayi furucin bayan ta miƙe tana jan hannun rigar ta da ya saɓule kaɗan saboda rashin jikin ta gashi kwana biyu tayi yar rashin lafiya ta faɗa. Ƙaramin kallabin ta, da ta cire yanzu ta sanya a kan fuskar ta goge hawayen baƙin cikin da ya silalo mata a ɓoye. Baffa na bai iya cewa komai ba ya miƙe ya riƙe hannun yar sa suka bar fadar bata re da jiran jin wata magana daga bakin mai gari ba. Mai gari haka kawai ya samu kan sa da zuba ma yarinyar ido wadda yake mugun jin Tausayin ta saboda yanayin da rayuwar ta take ,sai dai ya san bata jin magana kuma shi akan iro zai iya ɓatawa da kowa ma dan haka Tausayin ta yake yin ƙasa ya kasa aiwatar da ƙwaƙƙwaran bincike,ya rasa mai yasa suke yawan samun matsala da Iro duk da shima ya ja masa kunne akan ta. Kalaman ta ne suka sanya jikin sa yin mugun sanyi sannan da kalmar haƙuri da ta bawa Iron da babu wanda yayi tsammani acikin su sun zata sai sun kwana wajen ko shi mahaifin ta bai yi zaton haka ba saboda yasan kafuwar ta akan gaskiyar ta,ya so ya ƙara cewa wani abu amma saboda ganin yadda ta nuna tana son barin wajen ya sa ya amince idan shine farin cikin ta. A ɓangaren SHATOU kuwa bata nuna komai akan fuskar ta ba sai dai akwai ɓacin ran da take ɓoyewa wanda shi mahaifin ta ya hango sa. Haƙuri ya yi ta bata da rarrashin ta har suka iso gida. A ƙofar gidan suka tarar da Bibu wanda aka yi komai gaban sa yana ganin sun ta so ya bi hanya mafi sauri ya ya riga su zuwa gida ranshi jagule amma ya san tunda tayi Allah ya isa lallai Allah zai isar mata haka ma kuma ba lallai haƙurin da ta bada ya tabbata ba har zucin ta ba akwai dalilin ta. " Adda SHATOU kundawo,Baffa na adda ta aka bawa gaskiyar ta koh "? Yayi furucin yana riƙo hannun ta. Hararar wasa Baffa na ya sakar masa yana cewa " Bayan ka gama laɓen ka ai na ganka Malam Habibu,hanyar ma daka biyo na san ta ". Yakai ƙarshen zancen yana murmushi tare da shafa kan sa. Shiko Bibu yar dariya yayi irin ta yara cikin yar kunyar ganin sa da Baffa na yayi ya ce " Allah Baffa na ka ganni " Yayi zancen cikin yar dariya. Dariya Baffa na yayi yana gyaɗa masa kai. Ita kan ta SHATOU sai da ta ɗan murmusa dama ta san sai ya je gurin koda Inni ni ta hana sa. " Dama na san dole zaka je Sarkin wayau " Baffa na ya ƙara faɗa yana dariya. Dariya Bibu yayi sannan yace " Wallahi Allah Baffa na sai Allah ya isar wa Adda SHATOU an cuce ta ga gaskiya ƙarara amma sun danne haka ranar aka yi wanchan case ɗin,Wallahi bamu yafe ba tunda suka saka Adda ta zubar da hawaye gaban su,mugaye ".Ya kai ƙarshen zancen yana sharar hawaye masu zafi na jin Haushin abinda aka yiwa yar uwar sa. " Kuyi Haƙuri kunji kuma SHATOU A riƙa tausasa harshe kinji gaban manya wata rana mai gari zai iya saka a zane ki ba zai dubi ƙarancin ki ba ".Cewar Baffa na. Baki ta turo gaba tana cewa " Allah ni ba ƙarama bace Baffa na Sai dai Bibu dan yafi Ni tsawo ne ma yake jin shi kamar Babba " . SHATOU tayi zancen tana tura bakin ta gaba irin na sakuwa.Dan in tana cikin su ji take kamar yau ta zo duniya. Dariya Bibu yayi yace " Baffa na ai in tsawon Banza ne wani yayi mugani Adda SHATOU guntuwa yar ƙarama,kuma ma ai Baffa na tace ma Inna ni bata son ta girma haka take son zama yar ƙarama kamar yar gidan mai gari saratu" Ya na kai ƙarshen zancen yayi cikin gida da gudu yana dariya cikin farin cikin yadda SHATOU ta saki fuskar ta. Yadda ta zaro ido waje ne ya san ya tsokano rigima hakan ya sa ya gudu ciki yana dariya.Saboda bata son ya na ko kaman ta ta da saratu yar tsohon mai gari wadda take Wada domin haka halittar ta take. Baffa ma dariya yayi ganin yadda ta bishi a guje tana cewa " Wallahi Allah ya raba Ni da zama saratu Wada miyan ka ya tsallaka rafin maliya ya wanke tass ".. Ciki Baffa ya shige shima yana sayo gidan na su bakin shi washe kamar ba yanzu dukkanin su suke cikin zafi ba amma gashi har Bibu ya sa sun manta musamman Shatou koda yaushe yana ƙara ƙaunar soyayyar dake tsakanin junan su,yana Roƙon Allah ya shirya masa su ya daɗa haɗa masa kan su. Tun shigar Bibu Inna ni ta fito wadda ke zaune kamar a ƙaya cikin ɗakin na ta tana jiran Dawowar su,sai leƙe take ko zata hango su,ta sako hijabi kuwa yafi sau biyar ganin sun daɗe tana son ta isko su sai ta kasa zuwa ta ji nauyin zuwa wajen. Numfashi ta sauke a hankali ganin Shatou ta shigo a guje tana dariya Wanda ya kwantar mata da hankali a tunanin ta an bawa shatoun Gaskiya ne. Cirko cirko Baffa na ya isko su tsaye. Cikin kwantar da hankali Baffa na ya kalli Inna ni yace " Komai ya wuce ki kwantar da hankalin ki yar ki ce mai gaskiya kuma anyi sulhu ba zai ƙara shiga gonar ta ba,ko ta shiga ta sa ".Baffa ya faɗa mata bayan ya kora su Shatou ɗakunan su tare da basu umurnin kowa ya kwanta yayi Addu,a. A jiyar zuciya ta ƙara saukewa Jikin ta sanyaye kafin ta masa sai da safe ta shige ɗakin ta tana sayo shi. Tana zama akan ɗan madaidaicin gadon na ta wasu irin hawaye masu zafi suka silalo mata kafin kuma ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai tsuma zuciya kuka irin na bege da tausayi,sai da tayi mai isar ta sannan ta miƙe ta ɗauro Alwallah ta yi raka'a biyu ganin tunani zai addabe ta sannan ta kwanta bacci wanda ya kwashe ta da ƙyar.Baffa na da ke laɓe bakin ƙofar ne ya shige ɗakin sa cike da tausayi dama ya san sai ta koka ya rasa yaushe zai raba ta da wannan kukan yana son cika mata burin ta amma babu dama.Haka ya kwanta shima cikin Tausayin ta da na Shatoun.da su kan su gaba ɗaya. A ɓangaren mai gari kuwa haka taron ya watse kowa zuciyar sa babu daɗi sai suka ji kamar sun aikata babban Zunubi.Amina da su Ramata kuka suka yi tayi har suka isa gidajen su tare da iyayen su da su kansu basu san abinda ke faruwa ba sai yanzu kuma sai gashi ya yan su sun ƙarya ta zancen Shatoun.Gashi sai koke koke suke yi ba ma kamar Amina da zantukan na shatoun suka mata wani irin zafi sai taji kamar ta rabu da ita har abada Dagasken. 🌷🌸🌸🌷 *KADUNA* Ya rane mata sa da ba za su haura sha ba suka zagaye wata yarinya dake zaune Dirshan a ƙasa tana kuka kamar ranta zai fita sun kasa Rarrashin ta sai kallon ta suke yi kowa na tsoron abun da kan iya zuwa ya dawo idan ya taɓa ta ko hana ta kukan. " Kutumar uban nan uban wa ya taɓa ki REENA "?? Wata yar mitsitsiyar yarinya ce kamar dai wadda ke zaune ƙasa tayi zancen tana doso gurin bayan jin kukan yarinyar da nake zaton yar uwar ta ce. Matsawa baya dukkanin su suka yi suna kallon ta dama tsoron su ɗaya su taɓa ta ace sune yanzu suji ajikin su dan dukkanin su sun halin ta.Yanzu sai su ci na jaki kan yar uwar Tata.Cikin ɗan tsoro suka fara mata bayanin nan suka ganta zaune tana kukan haka. Hannun yarinyar ta riƙo tana kakkaɓe mata uniform ɗin jikin ta da suka yi duhu saboda ƙasar da ta kwanta tayi murje murje kamar yar goye. Hanya ta kama tare da ita hannun su ruƙe da na juna.Dama Driver suke jira bai zo ba shine ta nemi yar uwar Tata bata gan ta ba tayi zaton ta tafi ta bar ta kamar yadda ta saba ko sai ta wahalar da ita da driver neman ta,tafiya suka yi sai da suka ɗan ja kaɗan kusa da yaran ta sake ta tana Hararar ta tana cewa " Amma wallahi REENA ke wawuya ce wai har yanzu kin kasa yin hankali ji yanzu dan ubanki yadda kika yiwa uniform ɗin ya kike son a kalle mu idan mun koma ne so kike Ummah ta ji Babu daɗi ne a ce kullum ya yan ta ne marasa jin magana ƙazamai ". " Wallahi LINA kar ki ƙara ce mini Wawuya nikammm yanzu da Banyi haka ba ai ba zan gan ki ba me Shegen yawon tsiya kawai ".REENA tayi furucin. " ohh wai dama saboda ni kika kwanta ƙasa kika kashe jiki haka kamar kura saboda baki da wayau ". Wadda aka kira LINA tayi zancen tana Dariya irin ta yarinta tana kallon jikin yar uwar ta ta,kafin ta fara dariyar da ta san tana ƙular da yar uwar ta ta. Aiko kafin kace me REENA ta far mata da duka tana kuka na sangar ta dan LINA tafi ta wayau,dambe suka kaure dashi LINA ta haye abarta tana jibga kamar kullum da suke dambe duk da tsananin soyayyar dake tsakanin su amma in ɗaya ya taɓa ɗaya sai an yi rigima,babu ma kamar LINA da take cikin tsokanar ta koda yaushe,Duk yadda REENA take da sanyi haka take biye ta suyi tayi gata ba wani ƙarfi ba.Ga LINA da Shegen jan magana ko ka tsokane ta ko baka tsokane ta ba ita sai ta yi domin yar rigima ce ta ƙwarai dan REENA haƙuri take matuƙa da ƙarfin hali ita kawai ka bar ta da rigimar ta ga LINA wanda ba kullum take kula ta ba sai rashin son maganar ta da yake nature nata da yar shagwaɓar ta.Da sauri Mutumen dake cikin danƙareriyar motar da yayi parking kusa da su ya fito yana furta " Subhanallah LINA me ta Miki ". Da sauri ta ɗaga ta tana nishin Masifa. Ita kuwa REENA kuka ta fashe dashi cikin azaba dan ta jibgu.Kafin ta furta " Allah ya isa na Wallahi kuma sai na faɗa ma Abban mu,kuma sai na faɗa ma Ya Bilal muguwa kawai ". Jin sunan ƙarshe da REENA ta kira ya sanya hankalin LINA mugun tashi har tsigar jikin ta na tashi.Kafin ta fara zarar idanu kamar kazar da ta sha ruwa. Riƙo hannun ta Drivern na su yayi yana furta " Baki kyauta ba LINATU babu wani dalili kika ma yar uwar ki wannan mugun duka Yanzu ya kike son fuskantar Yallaɓai Bilal idan har ta faɗa masa ". Ɗan Dattijon Drivern na su da ya isa haihuwar su ya furta yana Rarrashin REENA dake cigaba da rera kuka harda na shagwaɓa.... " Bafa haka kawai na dake ta ba Baba Adamu itace ta kawai daga na yi mata dariya ta hau ni da duka ni kuma naji bazan iya ƙyaleta ba shine na hau ruwan cikin ta na rama ". LINA tayi zancen tana turo bakin ta gaba ga wata irin Fargaba da ta mamaye ta jin sunan wanda aka ambata yanzu duk da kuwa baya kusa amma ta san kowane irin lokaci zai iya zuwa Dan ganin shi kawai suke yi tsulum a cikin gidan ba tare da sun shirya ma zuwan sa ba. " To yanzu dai ke REENATU ki yafe wa yar uwar ki,kar ku shiga gida kuna faɗan nan kun ji ko "..yayi zancen yana ɗan kallon motar ta sa. Kai REENA ta gyaɗa tana furta shi kenan na yafe mata. " Ni dai ta bani haƙuri sannan na yafe mata ai itace ta fara kai min duka Wawuyar yarinya ". Zaro ido malam Adamu yayi jin abinda LINA ta furta kai tsaye cikin haɗe rai bare yayi zaton wasa take yi tunda an kashe case ɗin. Cikin sauri da rarrashi ya furta " haba " Ya ta LINATU ,na ce fa ku daina ba kya son Mahaifiyar ku ta samu salama ne kullum kuna cikin rigima tana fama daku ". Shiru LINA tayi kafin ta furta " Ni ba LINATU nake ba fa,Baba Adamu LINA nake ".Tayi zancen tana tura baki gaba. Kafin kuma kamar mai tashin iska ta wuce fuu ta take ta shigewar ta bayan motar ta su. Hararar bayan ta REENA tayi ta yi ƙyafci sannan ta bi bayan ta. Malam Adamu kan sa kawai ya girgiza yana musu Addu,ar shiriya.Yana bin bayan su da sauri dan ya san wanda ke cikin motar yanzu haka ya gaji da jira. LINA da bata lura da shi bane ta waiga da sauri jin ƙamshin turaren da ke razanar da ita.Shi ɗin ne dai cikin sauri ta fara ƙoƙarin ficewa daga motar jikin ta na wani irin rawa.... Su waye LINA,REENA BILAL??? Daga Alƙalamin Fa'eehbg ✍️ Gimbiyar taskira 👑 (FirstLady 🙌) Ba zamu daɗe muna free pages ba gaskiya zaku iya fara payment... 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt *08069059746* Daga wannan sati bazan ƙara posting a weekend ba gaskiya saboda ranar Hutu ce.🙏 Ƙarin bayani. 08069059746 Like share and comment pls 🙏 Rashin yin REACT zai sa na daina yin Update kullum.✍️ Idan kuna son cigaba LABARIN KURMAN ƘADDARA Ku riƙa comment da react. *UPDATE* https://chat.whatsapp.com/BzXaAD3pB6yJ1wBBrkE4V0 *Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®Fa'iza Almustapha Murai Daga Alkalamin✏ 👄FA'EEH BG👄 💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎 *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* _Daga marubuciyar littafin_ *A MAFARKI NASANTA 1&2(paid)#500* *RAYUWAR MU A YAU complete (free)* ____________________________________ *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 ___________________ _Wannan page kacokam Sadaukar wane gare ki Hafsat Bature(BOSS BATURE)💔💋 Nagde ƙwarai da kulawar ki akan wannan Book Allah ya bar zumunci,🤲dan kin yi mun abun da wasu suka kasa yi,Ina Alfahari dake🌹🥰KK story na godiya_ *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣4️⃣ 🌬️🌿🌲 Sai dai me kakkausar Muryar sa ce ta shiga Kunnuwan ta yana cewa " Don't dare try to move " Numfashin ta ne take jin yana shirin yin sama bayan tabbatar da shi ɗin ne.Tsinewa Malam Adamu ta fara yi a cikin zuciyar ta tun kafin ta iya dawowa cikin natsuwarta,dan mugun tsoron yayan na su take yi matuƙa saboda yadda ya saka mata ƙahon zuƙa saboda rashin jin ta.Zama tayi kamar kace ƙyar ta gudu musamman da ta san bata da gaskiya.Da ta san yana cikin motar Nan da tuni ta bar faɗan nan har haƙurin ma zata iya bawa REENA har ƙasa ma ta duƙa mata idan ta kama. REENA da ta shiga gaba itama da sauri ta juya tana kallon bayan motar bayan jin ƙamshin na sa cikin farin ciki take kallon sa tana " Wel come back Ya B. " Shima da Murmushi ya Kalle ta yana furta ya " How are you girl ". "I'm fine ". Ya studies ya mata ta amsa masa cikin sakin fuska kamar ba yanzu ta gama kuka ba.Shima haka ya saki ta sa fuskar. Shiru ne ya ratsa motar bayan gama gaishe gaishen na su. " LINA wai baki ga Ya B. Ba kika yi shiru ". REENA tayi zancen kai tsaye ita har ta manta da faɗan da suka yi ma murnan ganin ya'yan na su ya gusar mata da zafin jibgar da tasha. LINA murmushi ta ƙaƙalo kafin ta ce " na gansa ai har na gai da shi,amma bari na ƙara masa sannun da zuwa ".Ta yi zancen a ɗar ɗar.REENA bata ƙara tankama ta maba sai ma sautin ƙira'ar Alqur'ani da ta fara bi da ya ke tashi daga cikin motar kaɗan kaɗan. Ganin kamar hankalin sa bai kan ta hakan ya sa a hankali ta furta " Ya .B Barka da dawowa Ina wuni ". Yi yayi kamar bai ji abun da take faɗa ba ya share ta har sai da ta ƙara maimai ta sunan na sa kamar zata yi kuka cike da Haushin da ta ƙunsa na share ta da yayi. " Kunnuwa suke ji ba " Kuma kika saka mini kuka na ci uban ki yanzu wajen nan ƙatuwar banza mara hankali ".Shiru tayi kamar ruwa ya cita jin yadda ya jefo mata magana kamar jiran ta yake yi dama kuma ta san za,a rina tun da ya gan ta da idanun sa kan ruwan cikin REENA yar gaban goshin sa tama jibgar ta kamar ta samu aikin yi. Ɗiff tayi kamar ruwa ya cita tana turo baki gaba haɗe da gunguni tana kallon glass ɗin mota da suka ɗai suke iya hango na waje tinted ne glass ɗin motar shi yasa basu lura da Bilal ɗin a cikin motar ba. Har suka isa gida babu wanda ya ƙara furta komai sai dai hankalin LINA ya ƙi kwanta wa ko kaɗan burin ta ta samu ta gan ta kusa da Ummah lokacin ne zata san ta tsira.Wata ƙatuwar mension ce mai tsari da burge wa wadda take cike da gidaje na alfarma masu kyau motar ta kutsa Hancin ta bayan wangale mata gate. Tsarin gurin gwanin burge wa irin yadda kuka san estate take ko ina ƙalƙal sai sojojin da ke wulgawa kaɗan kaɗan saboda a ciki saboda mai gidan su da yake gari.Ganin sojojin da yawa ya ƙara tabbatar mata da ya dawo kenan,kuma da alama zai daɗe gida,dan ƙwarori ne suke tsaron estate ɗin amma daka gansu da yawa to yana gari. Dai dai mazaunin motar ya yi parking motar wanda ko ida dai dai ta parking bai yi ba ta fara kiciniyar fita motar da iya ƙarfin ta.Baba Adamu da ya fahimci saurin na ta sai ya cire lock ɗin yana sakin guntun murmushi.Aiko kamar jira LINA take yi ta banka aguje cikin wani gidan da yake ɗan kusa da parking lots ɗin.Yana dai dai ta Parking ɗin REENA da ke ta sakin murmushi tana jiran ya'yan nasu su fita tare yana fitowa itama ta fito tana tsalle tsallen ta tana jin kamar yanzu ta ga ya yan nasu da ya kan ɗan kwana biyu bai garin saboda yana yin aikin sa Kasancewar sa Land army na ƙasa bai cika zama ƙasar ba ma. Guntun Murmushi ya saki yana kallon REENA kafin ya riƙo hannun ta ganin yadda take ta tsalle tsalle sannan ya furta " Ki Nutsu kinji " Natsuwa kuwa tayi kuwa tana cigaba da sakin murmushi.A tare suka shiga cikin ƙaton falon jakar ta sargafe a bayan ta ga datti jikin ta duk ya bayyana. Da gudu ta faɗa jikin Matar da ta fito daga kitchen tana kitchen tana amsa waya Fara ce tass kamar Bilal da REENA sai dai kama Bilal ya fi kama da ita sosai bisa ga su LINA da suke kama sosai da mahaifin su. " Ummah I miss You "REENA tayi furucin tana dariyar farin ciki. " Oh ni Barirah bint Usman Wai yaushe SAREENA ta zata yi hankali ne ALINA ta shigo a hargitse,REENA kuma ta dawo da datti me ya ɓata jikin ki haka ne,Ke da kika fita tsafff ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin murmushi mai cike da natsuwa Tana zare ma REENA school bag ɗin tana kallon Bilal dake murmushi shima jin mahaifiyar su ta kira cikakken sunan ta. " Ummah Faɗuwa nayi " REENA ta furta itama cikin murmushi. Hararar wasa Ummah ta sakar mata kafin ta furta " naƙi wayon Wannan akwai alamar rashin faɗuwa jibi yadda kika yi busu su fa gashi idanun ki sunyi rau rau kamar sun yi kuka,anya kuwa ba halin kuka yi awaje ba keda wacchan shiryayyar ". Kallon Bilal tayi tana tsoron ta faɗa wa Ummah ya kama LINA ya daka duk da ta san may be ya riga ya gansu. Bilal kuwa yi yayi kamar bai san maganar da ake yi ba ya mayar da hankalin sa kan wayar sa. " Ummah faɗuwa fa nayi,shine LINA ta mun dariya na yi kuka ".Ta kai ƙarshen zancen tana yar shagwaɓarta. Murmushi kawai Ummah ta saki tana furta " to jeki ki watsa ruwa idan kuka yi sallah sai ku fito yin lunch ga ya yan ku nan bai ci komai ba ya dawo ya matsa sai ya fara ganin ku jeki, kuma LINA ta tabbatar ta fito yin lunch ".Ta san tsafff zata ƙin fitowa tunda basa ba maciji da ya yan na su.Duk yadda ake firar sa kullum baya nan da ya dawo sai ta fara ɓoye ɓoye na rashin gaskiya. Dariyar farin ciki ce ta kama REENA jin ya yan su bai ma iya yin lunch ba sai ya fara ganin su hakan ya sa da gudu ta bar falon tana tsallen murna ya nason su sosai. Idanun sa ya bita da su yana sakin murmushi a hankali kafin ya maida kallon sa ga Umma ya ce " Ummah Barka da hidima " " Barka da dawowa Soja,na san kaga komai da ya faru faɗan suka yi ko ".? Tayi mishi zancen cikin sanyin da jikin ta yayi ta sigar tambaya tana zuba masa idanun ta. Idanun sa ya ɗauke daga na mahaifiyar sa yana sakin ajiyar zuciya saboda ya san sune Raunin ta matuƙa waɗannan yan biyun ya yan na ta ya rasa abinda yake damun su musamman LINA kamar mai ƙwanƙwammai haka take wasu abubuwan wata rana ma kamar mai taɓin hankali dan so da yawa ya sha kama ta tana wasa ita kaɗai tun bata fara kai haka ba,ita kuwa REENA sangar ta gashi saboda mugun faɗan su abun ya zamar ma mahaifiyar su faɗe a cikin familyn da kishin samrin ta da kuma kishiyoyin ta ta rasa yadda zata yi maganin matsalar amma abu ya faskara sai gaba yake yi. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta a hankali cikin natsuwa " UMMAH dambe suka yi " nan ya labarta mata abun da ya gani da idanun sa. Kai UMMAH ta jinjina kafin ta sauke ajiyar zuciya " tana furta kwana biyu naga an samu zaman lafiya amma ashe abun gaba yake yi ,Allah ya shirya mini su,Dan ALLAH Karka dakar mini "Yaa Kaji Soja,Addu,a kawai zamu cigaba da saka ta,gaba ɗayan su ma ". Kai ya jinjina yana furta " Amin " Amma tabbas da badan Mahaifiyar su ta hore sa ba da sai ya hora LINA sai tayi kamun kunne wanda zata daɗe bata yi rigima ba,tuna cewa ya sha hora ta amma bai yi aiki ba sai Shegen tsoron ta ya sa shi girgiza kan sa kawai yana tuno wani lokaci da ta yi wa REENA wani irin duka kamar zata raba ta da duniyar ta kan kawai ta sanya hular ta tace ta cire bata cire ba.Ai ko ya wahalar da ita kamar yadda suke yi a wurin training na sojoji ta wahala sosai harda jinya amma bai hana ta koma ba.A.lokacin kaɗan ya rage ya sha mari ga UMMAH dan Abba faɗa kawai yayi masa na ya riƙa haƙuri,ƙucuciyar ta ce haka, LINA taci baƙar wuya da ƙyar take iya tafiya a lokacin har sai da tayi kusan sati bata iya tafiya lokacin suna da shekara takwas ciff a duniya. miƙewa yayi bayan Sun gama maganar shima ya wuce na sa sashe dake part ɗin duk da yana da ɓangaren sa kuma achan yake sauka idan ya zo ko sashen Abba Babba duk da gidan ba kowa a cikin sa. Zama tayi jagwab akan gadon tana sauke ajiyar zuciya kafin ta saki guntun murmushi tana kallon wayar ta da ta gama amfani da ita yanzu bayan shigowar ta ɗaki. Wani kiran ne ya sake shigowa akan wayar hakan ya sa ta ɗaga da sauri tana furta " Abban su Barka " Bayan amsa Sallamar sa. "Sun dawo school ko,Injin ba,a yi halin ba " .Kai ta girgiza kamar yana gaban ta kafin tace ''Basu yi ba yanzu haka ma sun fito yin lunch "Murmushi yayi mai sanyi yana jin wani irin farin ciki na mamaye sa.Itama murmushin ta saki kafin suka ƙara yin maganar dawowarsa dan yaje yayi attending wani business class a Morocco wanda yana yawan tafiye tafiye kasancewar sa ɗan kasuwa Babba,A halin ma gaba ɗaya tunda ga kakan su Yan kasuwa ne familyn basa wani aikin gwamnati face kasuwancin su in ka cire Bilal da yake da muradin aikin soja wanda shima yana taɓa Business ɗin sosai bai saki gadon gidan na su ba. SHATOU Yau ta tashi da wani matsanancin ciwon kai wanda ya hana mata zuwa makarantar allo ta safe a safiyar lahadin,tare da ayyukan da ta saba ɗan jagwalgwalawa mahaifiyar ta,tunda ba wani iya wa tayi ba ita dai barta da aikin gidan ta horu da iya share share da yan goge amma ta fannin girki ba,a cewa komai. Baffa yau ya ma kasa iya fita farauta ko kaɗan,Bibu ma da ƙyar ya iya tafiya makarantar.Kula take samu ta ko ina Baga Baffa ba Baga Inna ni ba ita kuwa an samu abun yi sai ƙara lanƙwashe wa take yi,dan ko abin karin daƙyar ta tsakura ta sha magani ko shi sai da INNA Ni tayi daƙyar. Sai zuwa maraice ya ciwon ya lafa mata dan ba kasa fai take kwanciya ciwo ba tun dai wanda ta sha yi lokacin tana ƙarama saboda rashin samun kulawa ta uwa dan Inna ni tayi wata rashin lafiya sosai Alokacin Baffa na bai ma taɓa tunanin zata iya samun lafiya ta koma dai dai ba. Da ƙyar Baffa na da Bibu suka iya fita shi ya wuce farauta shi ko ya wuce makaranta,wadda sai da aka rarrashi shi sannan ya wuce harda yan hawayen sa. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba jikin Shatu ya ƙara rikicewa Hankalin Inna ni ya tashi matuƙa musamman ganin yadda jikin ta yake jijjiga tsoro abun ya bata wanda ya sa ta zuba ma yar Tata idanun ta kawai tana kallon ta,tana fatan abun ya tsaya nan, kafin wasu hawaye masu zafi su zubo mata dan ko rantsuwa tayi bazata yi kaffa ra ba tsohon ciwon ta ne ya tashi na matsalar jinnu da tayi fama dasu shekaru uku da suka wuce dama shine abinda take gudu tun safiyar yau da ta tashi da matsanancin ciwon kan cikin ɗarr take na abinda kan iya zuwa ya dawo.Riƙo hannun ta tayi.tana tofa mata Addua,a kafin cikin wani irin kuka Shatou ta fara magana ƙasa ƙasa ganin bata jin abun da take faɗa hakan ya sa ta kara kunnen ta a bakin ta " Suna cikin matsala rayuwar su na cikin hatsari,Kuyi wani abu zasu hallaka su,zata samu sauƙi zata samu waraka zata sami lafiya ". Tana gama furucin kuma sai wani irin bacci ya kwashe ta,mai Nauyi. Wani irin kuka ne ya ƙwacewa Inni ni wanda ya sa ta durƙushe wa nan tana rungume yar ta cikin wani irin baƙin ciki mara misaltuwa itama take jikin ta ya ɗau zafi saboda kukan da ta yi gashi babu mai rarrashi......... Meye matsalar Inna ni wai ??? Haba na san a rina shatou ku ba ita kaɗai take ba ahe 😂😂Mai gari ya mata uzuri🚶🚶 Wasa farin girki✍️✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan N#1000. Yanzu muna kan free pages, kuma baza,a same su da yawa ba gaskiya dan haka kuna iya fara yin payment. 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt *08069059746* Daga Alƙalamin ✍️ GIMBIYAR TASKIRA 👑 FA'EEH BG ✍️ FIRSTLADY 🙌 LIKE,REACT, COMMENT sune kawai nake buƙata,shine zai nuna mini yadda kuka karɓi book ɗin..✍️ _*Typing*_ Update 👇 https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *Masu son ganin ƙarshen labarin sai suyi following channel ɗita.👇* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®Fa'iza Almustapha Murai Daga Alkalamin✏ *FA'EEH BG* 💎Sadaukarwa ne ga class mate ɗina ɗalibban GGC T/MAFARA,ZAMFARA STATE SET 2K18.A duk inda kuke Alkhairin Allah ya kai muku.🤲💎 *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* _Daga marubuciyar littafin_ *A MAFARKI NASANTA 1&2(paid)#500* *RAYUWAR MU A YAU complete (free)* ____________________________________ *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 ___________________ *MUNA TALLATA HAJA KOWACE IRI CE A FARA SHI MAI SAUƘI...* *BOOK ONE* free pages👌 P...0️⃣5️⃣ Sai da tayi mai isar ta Sannan ta share hawaye ta tare da gyara ma Shatou kwanciyar ta dan baccin take mai nauyi kuma da alama yayi mata daɗi.Dan rage ma kan ta tunani ne da yake son kutso mata ya sa ta janyo wata tsohuwar saƙar da ta fara ta cigaba da yi tare da ƙara sautin redion da yake fitar da sautin Qira'a mai daɗi ta Sheikh sadiqu Sadiq Gusau. Tana nan zaune har aka kira sallar la,asar sannan ta miƙe ta gabatar da sallah tare da jerawa Ubangiji damuwowin ta da suka cike zuciyar ta.Tana gamawa ta tsakuri abinci kaɗan Dan bata jin ɗanɗanon sa ko kaɗan saboda yadda zuciyar ta take harbawa tun bayan kalaman da suka fito daga bakin Shatou suka shiga kunnen ta.Duk ta tuno da zantukan sai jikin ta yayi wani irin mugun sanyi sai ta ƙara jin wani irin rauni ya ta so mata.Bata da mafitar da zata iya yin komai akan zancen da Kunnuwan ta suka jiye mata face ta miƙa lamurran ta ga Ubangiji shine wanda ya san damuwowin ta.Zama tayi a kusa da SHATOU tana zuba mata idanun ta wasu irin hawaye masu zafi suka silalo mata wayen da bata ma shirya wa fitowar su ba.A hankali ta ware idanun na ta da suka bayyanar da yanayin rashin lafiyar ta ta sunyi wani irin garai garai ta zuba su kan fuskar Mahaifiyar ta ta da ɗigon hawayen ta ya ɗigar mata a kan fuskan ta, da ta ƙara yin fayau tsantsan yarinyar ta ta ƙara fitowa ƙarara dan Shatou da ace irin gidajen masu kuɗi ne masu sangarta yara da har yanzu babu aikin da ta iya saboda shekarun na ta da kuma girman ta bata da wani girma haka take yar firit da ita. " Inna ni " Cikin sanyi Sautin ya shiga Kunnuwan Inna ni da ke duƙushe gaban shatoun.Idanun ta ta share da sauri tana goge hawayen da ke ƙoƙarin sake fito mata.Da murmushi ta zuba ma Shatou idanun ta kamar yadda ta zuba mata nata tana ƙaƙalo dariyar farin ciki ganin shatou ta tashi garass babu wani ciwo à jikin ta da alama zazzaɓin ya sauka ma gaba ɗaya." Sannu kin tashi ya jikin,ina yake Miki ciwo yanzu " Inna ni ta jera wayen nan tambayoyin tana shafa fuskar Shatou cikin Tausayin ta. Kai SHATOU ta gyaɗa mata tana kallon ta cikin ido ganin yadda idanun ta suka yi jaa kaɗan na kukan da tayi a ɗazu. "Inna ni kawai dan ban da lafiya kika yi kuka haka,?Ashe haka kike so na ban sani ba ".Shatou tayi zancen kafin kuma ta ƙara sa zancen Baffa na dake tsaye a gefe ya sauke Numfashi tare da girgiza kan sa cikin tausayin su.Sannan ya ƙara so ciki yana maimaita wata sabuwar Sallamar dan tun ɗazu ya shigo tun lokacin da Inna ni ta durƙushe ƙasan idanun ta na tsiyayar da hawayen da bai san dalilin zubar su ba a wannan karon duk da ya saba da irin wannan yanayin nata. Amsa masa sallamar sa suka yi a tare cikin washe baki Shatou tayi masa Barka da dawowa tana miƙewa daga kwance cikin ɗan ƙarfin da ya rage mata.Washe bakin sa yayi yana kallon ta yana furta " Shatou na ta murmuje sosai ko dan da alama Kwana kika yi mai daɗi ". Murmushi tayi tana gyaɗa masa kai dan ita kam iya sanin ta tunda su Baffa suka fita bacci ya kwashe ta sai yanzu.Kuma gashi baccin ya tafi da ko wane ciwo na ta. " Masha ALLAH,Allah ya ƙara sauƙi Shatouwa ta ". Ya furta yana cigaba da murmushi mai cike da natsuwa.Baki ta Turo gaba jin ya kira ta da Shatouwa sunan da bata so,kuma shine ƙaɗai ya ke kiran ta da wannan Sunan. Kayan farautar ta sa ya ajiye a ma,ajiyar su sannan ya zo ya zauna yana ƙara yi ma Shatou ya jiki tana Amsawa fuskar ta a washe.Inni ni kuwa abun farautar ta sa da ya ajiye ta miƙe ta ɗauka ta ajiye shi a inda ya dace zuciyar ta cunkushe da tunani kala kala. Baffa na dai idanu kawai ya bita da su yana jin wani Tausayin ta na mamaye shi kafin ya sauke idanun sa ƙasa yana tasbihi Sannan ya mayar da kallon sa kan SHATOU " Baffa Banyi Sallah ba fa,Inna ni bata ta da ni nayi Sallah ba ta bar ni ina ta barci ".Kan ta ya sha fa a hankali sannan ya furta " Inna ni bata kyauta ba gaskiya tashi kiyi Alwallah ai lokacin ta bai wuce ba ''. Cikin ɗan kuzarin ta kuwa ta miƙe tana washe baki Ruwan da ya ajiye mata yanzu a buta ta ɗauka ta zaga makewayi sannan tana fitowa ta ɗaura Alwallah ɗakin ta ta shige ta ɗaura zani mai girma ta kabbara Sallah. A tsakiyar gida kuwa Bayàn Tabbatar Da Shatou ta shige ɗakin ta ne Baffa na ya kira sunan Inna ni a hankali. Sannan ya ce " Kiyi Haƙuri A'ie ban matsa Miki ba ki faɗa mini abinda yake damun ki yake yawan saka ki kuka ba,Duk da na san raba ki da kuka yana da wahala a wannan lokaci amma ina son ki sani Komai yana da lokacin sa ki cigaba da Addu,a Allah zaiyi mafita a duk abunda ya tsananta a gare mu,Kuka ba shine maganin matsalar mu ba,Sannan ba zan gaji da faɗa Miki ki faɗi wata alama da zata iya bamu mafita ba,ina son sanin komai da yake faruwa kin ƙi bani dama bare a samu mafita,Àmma duk da haka bazan matsa Miki ba zan bar ki sai ranar da kika buƙaci hakan,Sannan na roƙe ki kar ki taɓa bari Shatou ta san wani abu shekarun ta basu kai na lokacin da zata iya sanin abin da ba zata ji daɗin sa ba,". Yana gama furucin sa ya shige ɗakin sa ya bar Inna ni dake zaune jikin ta ya mutu mutus domin ta san ba tun yau ba,yake son tace wani abu amma ta kasa sannan duk wasu zantukan da shatou ke yi a lokacin da iskan ta suke tashi bata taɓa faɗa masa ba,tun tana farkon samun ciwon dan sun fi tashi a lokacin da suke daga ita sai ita a gidan.Shin ta ina zata fara ita kan ta ba ta san ta ina zata fara ba bata san komai ba duk yana yin da take ciki tsintar kan ta kawai tayi,wasu lokuttan ta kan rasa tunanin da zata yi amma ta san tabbas duk abinda Mutantanin Shatou suke yawan faɗa mata basu yi mata ƙarya ba,duk wani lokaci sukan faɗi ƙarya,zancen su shine kawai abinda ke natsar da zuciyar ta yake kwantar mata da hankali kuma yake tayar mata da hankali.Numfashi ta sauke mai Nauyi cike da nauyin da ya maƙare zuciyar ta wanda bata san ranar da zai gushe ba. Shatou Kuwa bayan ta gama sallah sai tayi ajiyar zuciya tuno yadda ta ga fuskar mahaifiyar ta amma kan ta bai iya kawo komai ba sai ma murmushi da ta ƙara saukewa tana jin daɗin wai Inna ni na son ta sosai ashe faɗan ne kawai take mata tana son ta.Sai ta ji zata rage ɓata mata rai ta daina abinda bata so amma fa muddin wani ya taɓa ta sai ta nuna masa ya taɓa ta.dan bata yarda a raina ta kamar yadda aka raina Amina ba. Miƙewa tayi tana sakin murmushi jin muryoyin su Amina da su Ramata suna sallama duk sun cika gidan ai ko burumm sai gata tsakar gida tana washe baki har ta manta abun da ya faru jiya sai dai tana haɗa idanun ta da su sai ta wani irin shan kunu kamar taga kashi tana bin su da kallo ɗai ɗai sai ta kama Hanyar ɗakin ta tana neman komawa ɗakin ta tino yadda suka kunya ta ta jiyan ƙiri ƙiri suka goyi bayan ƙarya wanda ko da asuba sai da tayi hawaye na baƙin cikin abun. " Yau na ga shegan taka Shatou ba gurin ki suka zo ba kika kare musu kallo kuma kika shige ɗaki,Kamar ba su Aishan ki ba,wata sabuwar tsirfa ce haka ko me?" Inna ni tayi furucin bayan tagama ansa gaisuwan da suke mata suma bakunan su washe kafin kowaccen su ta sauke idanun ta ƙasa na rashin gaskiya dama da ƙyar suka zo saboda cike suke da tsoro ko yanzu dan ta kama dole ne rashin lafiya ne da Bazasu iya tunkarar ta ba saboda yadda kowaccen su ke cike da tsoron ta. Baki ta turo gaba tana zama Kusa da shinfiɗar tabarmar da Inna ni ta musu. " SHATOU Ya jikin ki,Bibu yace baki ji daɗi ba ". Kai ta gyaɗa musu kawai tana shan ƙamshi. " Allah ya baki lafiya,yasa ki ji sauƙi ƙwarai " suka haɗa baki wajen faɗa suma cikin rashin sakewa ganin yadda duk ta haɗe rai sai bai musu daɗi ba sun zo baki washe amma fuska ta sauya saboda yadda ta sha fuska. " Amin " Inna ni ta amsa cikin murmushi tana bin su da kallo haka ma Baffa na da ya shiryo har ya chan za kaya shima murmushi yayi yana furta " A yafe musu haka Manya, sun ji gata kin ga suma sun san basu kyauta ba ai ".Yayi furucin yana kallon Amina da ta ƙara yin ƙasa da kan ta cike da nadama ga kuma sanyin da jikin ta yayi dan ta tsani ɓacin ran aminiyar ta ta dukkanin su ma haka suke dan ko rigima suka taro itace mai tare musu ko wanda yafi karfin ta ne tana tare wa,dan shi suke mugun ji da ita a tsakanin su,amma kuma idan faɗan su ya tashi a tsakanin su ba,a mai kyau dan shatou bata raga musu. Murmushi ta saki tana cunno baki gaba.Hararar su tayi musamman Amina da ta zuba mata idanun ta tana jiran jin amsar ta dan ƙirjin ta har bugawa yake yi dan tana azabtuwa matuƙa jiya ko bacci. Kirki bata yi ba har da kuka ta saka wa mahaifiyar ta yau da safe wai shatou fushi take da ita,mahaifiyar ta ta ce taje gidan su ta ka sa,tace sai dai ita taje, ta ce bazata je ba,haka dai ta shirya tayi makaranta tayi shiri da wuri dan ta samu ta haɗu da shatou sai dai cikin rashin sa,a Bibu kawai ta gani wanda ya sanar mata da rashin lafiyar ta Shatou. " Na yafe musu badan halin su ba saboda Kai Baffa na " Tayi furucin tana jefe ma Ramata Harara,dake washe bakin ta da duk yayi datti dattin da shatou take addabar ta da bakin ta wari yake yi,sai ta gyara ta fara wanke sa yanzu kuwa saboda kwana biyu bata sako ta gaba ba cikin ƙawayen su sai ta koma yar gidan jiya dan yanzu haka bakun yellow yake. " A'a Shatou ki ya fe musu Saboda Allah kin ji sai ki samu lada,ki riƙa yin abu saboda Allah shine wanda ake yi dan shi a bari dan sa ". Baffa na yayi furucin yana murmushi. Kai ta gyaɗa masa na zancen ya shiga kunnen ta da zuciyar ta. Haka su ma su Amina kai suka gyaɗa kamar da su yake magana. " Na yafe muku saboda Allah,amma wallahi kuka koma sai na chan za ƙawaye ,kun yarda".Tayi furucin kamar irin Dagaske. Inna ni kai kawai ta girgiza tana sakin murmushi ganin yadda duk suka haɗa baki waje furta eh suna gyaɗa kai kamar ƙadangarru.Addu,ar shiriya ta musu baki ɗayan su tana sauke numfashi tana kallon su tana jin wani abu a ranta mai girma da raɗaɗi musamman da su ka rage su huɗu kawai a wajen saboda sauran su sun wuce manyan ƙawayen ne suka zo jinya.Hawayen da ta ji suna neman silalo mata ne ya sa ta shige ɗakin ta da sauri ta bar su kan tabarmar suna bawa Shatou labarin karatun da aka yi musu a yau.Na Al'ada wanda malamin ya sanar musu da duk wacce ta fara ganin jini zata iya ɗaukar ciki su riƙa kama kan su dan daga lokacin sun girma zasu iya haihuwa.Haka dai suke bata labarin tana sauraren su tana dariya kafin ta furta '' Wai Jini to ai mu ba zamu taɓa yin sa ba ma har yanzu yara muke,kuma ma taya ciki zai zauna a wannan shafaffen cikin na wa ".Ta kai ƙarshen zancen tana shafa shafaffen cikin ta.Sannan ta ƙara furta " Ai Babu ruwan mu da maza mun san halin mutanen ƙauyen nan ba zan manta abinda aka yiwa yar gidan malam Shehu ba ".Tayi zancen cikin yarinta. Kai suka gyaɗa mata suma kafin suka yi shiru Baffa na ne ya fito daga ɗakin sa bayan gama cin abinci yana furta " A'i na fita sai na dawo " adawo lafiya ta masa duk da tafiyar bata wuce majalisar su ce zai je. Amina ce ta riƙo hannun Shatou jikin ta a sanyaye bayan sun yi ma Baffa na a dawo lafiya, tana furta " Dan Allah shatou karki daina ƙawan ce damu kin ji bazamu ƙara ba ".Ta kai ƙarshen zancen kamar zata yi kuka. " Ai naji kunya ƙwarai da kuka ƙarya ta ni gashi malam Habu yace ƙarya haramun ce,amma kuka rufe ido kuka tozarta ni da girma na " Ta kai ƙarshen zancen da ya sanya Inna ni dariya dake zaune tana cigaba da yan ka naman da Baffa na yayi farauta.Saboda Bata da R sai yana yin furucin na ta na ƙarshe da ta furta ya ƙara bayyanar da rashin R ɗin ta fili.Ƙara jinjina kalmar Inna ni tayi wai da girma na hakan ya sa ta ƙara sakin murmushi tana kallon yar ta ta yar firit da ita amma ita ke zancen da girman ta kamar wata babba. Ai kin ta cigaba da yi tana sauraren su suna ƙara ba shatou haƙuri wanda bata san abin da ya faru ba sai yanzu dan har yanzu Baffa na bai sanar da ita yadda komai ya wakana ba.Ajiyar zuciya kawai ta sauke bata shiga zancen su ba har suka gama suka chan za firar ta bikin gidan su maraƙisiya da zasu je mamarta ta haihu kuma bikin jibi ne dan yau jiye ne ta haihu da dare.Murna Shatou tayi ta yi dan dama bata gan ta ba cikin su ashe mamar ta ce ta haihu, farin ciki ne ya kama shatou matuƙa wanda har ya bawa Inna ni mamaki dan sosai ta yi murna musamman da ta ji mace aka samu sai ta ji ina ma Inna ni ce ta haihu.Tana cikin wannan mamaki ne ta tsinkayi SHATOU na furta " Ni Inna ni wai yaushe zaki haifa mini Yar ƙanwa Allah ina son samun yar ƙanwa Nida Bibu,kin ga da kin haifa muna ita Allah na daina fita wasa sai muyi Wasar mu cikin gida anan tare ". Shiru Inna ni tayi kamar ruwa ya cita kan ta ya rufe ɗiff sai kuma cikin ɗan murmushin da ta ƙaƙalo ta furta " Ai Ni shatou na tsufa baki ga harda furfura ba a kaina,kuma kin san tsofaffi basa haihuwa ". " Laaaah Dagaske Inna ni ai Ni ban taɓa ganin ta ba,Inna ni kan ki fa baƙi wulik yake ai ina buɗe shi na taɓa wata rana idan kina bacci saboda daɗin taɓa sa nake ji taushin sa kamar kayi ta bacci ". Waro idanu Inna ni tayi tana sauke ajiyar zuciya da firar ta su ta sauya. Kafin ta furta " Ohh ni Indo gashin nawa ke saka bacci kuma Shatou,ai ga naki nan da baki son a taɓa sai ki riƙa taɓa shi dan naki yafi nawa taushi nesa ba kusa ba kawai na wa kika zuba ma ido ko,zan ma aske shi saboda ke ". " Wallahi Inna ni ba zaki aske shi ba ki saka naji kunya har fa labarin shi na ke bawa su Amina ko ". Kai su Amina suka gyaɗa suna murmushi dan suna shan labarin jin yadda gashin Inna ni yake da silɓi wanda suko suke ganin bai kai na Shatou ba saboda akwai ranar da ɗan kwallin ta ya cire bayan sun yi dambe da wata yar aji biyar ta yaga mata hijabi har ɗan kwalin ta ya cire wajen Masifa daga nan suka san shatou ma nada gashi dan bata son ana ko taɓa kan na ta bare a ga abun da ke cikin sa kitso daƙyar inna ni take ma ta shi kuma bai wuce kalaba itace kawai ta iya. Dariya Inna ni tayi wadda ta ƙara bayyanar da kamar ta da shatou har yar wushiryar su ma iri ɗaya ce. Itama shatou murmushi tayi mai haɗe da dariya ganin dariyar Inna ni wadda ba kullum take yin ta ba. " Inna Dan Allah a bar maganar wasa kar ki aske shi wallahi kika aske shi ba zan ƙara fita ƙauyen nan ba dan gori za,a mini ace Inna ta Tal kwabo gare ta ". A wannan karon Inna ni daƙuwa ta jefa wa Shatou tana dariya. Itama shatou dariya tayi tana chafke daƙuwar tana shigewa cikin su Amina da suke ta dariya suma gwanin burgewa ganin yadda shatou ke wasa da mahaifiyar ta. " Allah ya shirye ki Shatou ya baki hankali " Inna ni ta furta tana girgiza kan ta Dan ta fahimci idan ta biye wa shatou haka zata lalace wajen. Shigowar Bibu ce ɗauke da Sallama a bakin sa ya dakatar da su da dariyar da suke yi.Zama yayi cikin su cikin farin ciki yana furta " Adda shatou kin ji sauƙi sosai naga kina farin ciki sosai,Naji daɗi ". Dariya tayi tana furta " Naji sauƙi sosai Bibu baka ga har ƙiba na ƙara da girma ba " . Dariya yayi sannan ya ce " Wallahi Adda SHATOU ba wata ƙiba kin ga yadda kika rame,girma kuma ai kince bakya son ki girma,dan Baffa na ya ce kar na miki addu,a da sai na Miki Addu,a ki zama Saratu Wada ". Ai ko su Amina me zasu yi in ba dariya ba ganin yadda ta bata fuska saboda sun san yadda ta tsani sunan.Bibu kuwa shima dariyar yayi yana tserewa bayan Inna ni yana furta Inna Barka da aiki ". Amsa masa tayi tana furta" Sarkin jan magana ko Allon an kasa ajiyewa sai tsokana na san da ba kai bane da wani ne yake haɗa wacchan rigimammar da saratu da tuni wani zancen ake yi ba wannan ba" ta kai ƙarshen zancen tana kallon shatou dake Hararar Bibu kamar idanun ta zasu faɗo. Dariya yayi tare da tsalle yana furta " Sai ni na Adda SHATOU guntuwa ". Yana gama furucin ya shige ɗakin sa da gudu yana dariya. Har ta miƙe,kuma ganin cewa in ta biye masa haka zai ta ƙara kiran ta ya sa ta dawo ta zauna tana dariya tana furta " Ai in ba tsoro ba mutun ya zo ya faɗi gaba na ". Inna ni ce ta karɓe zancen tana furta " Ai maza ba sa tsoro,bare Habibullah na ai jarumi ne ". Baki Shatou ta turo gaba bata ce komai ba. Inna ni kuwa murmushi tayi kawai tana cigaba da yin aikin ta.Tana jiyo dariyar Bibu daga ciki.Sai taji sanyi dan hankalin sa tashe ya bar gida sai gashi daga shigowar sa ya samu nishaɗi. Su shatou kuwa firar su suka cigaba da yi kamar babu abinda ya shiga tsakanin su. Daga ƙarshe ma Inna ni aka tashi aka ƙara ƙalƙalewa gida.Ita kuwa sai kallon su take yi tana murmushi cike da wasu irin tunani ka iri iri. ***GTR👑👑👑 Kafin fitowar ta su wajen lunch ɗin sai da aka kusa yin dambe saboda LINA bayan gama yin wankan ta ƙin fitowa tayi daga toilet ɗin saboda dama tana shiga chan ta yi tsinke,Jin shiru ya san ya REENA buɗe toilet ɗin kai tsaye dan babu motsin ruwa. Zaune ta isko LINA gaban madubin toilet ta na ta kallon kan ta tana Murmushi tare da jan dogon gashin ta da ta jabga ma ruwa yanzu. Cike da haushi ganin jikin ta ya ma bushe tana ɗaure da towel tayi zaman ta gashi Ummah tace su fi to da wuri saboda ya'yan su,amma ita har ta zama ta bata kamar ba ɗazu a school ta gama faɗar yunwa take ji ba bayan ta gamo faɗace faɗacen ta. " Mutun ba wani kyau ba sai iyayi ". Tayi furucin tana nufar inda set na towel ɗin su suke jere gwanin burgewa.Ko ina tsafff ba zaka taɓa cewa ƙananan yara ke aiki dashi ba,saboda yadda ake kula da tsaftar su.Komai na su tsaf dashi. " Damar abun kamar mu ɗaya idan ma rashin kyau ne Kinga har ke baki da shi ". LINA tayi furucin tana wani juya ido gaban madubi tana mayar da gashin ta baya kamar wata ba indiya. Sai kuma chan kamar an dawo da sense nata ta ta so da sauri tana yowa kan REENA tana furta " Uban wa ne mai iyayi " . " Wallahi da ba Abba zan zaga ba da sai nace uban ki ". " Hehehe " tayi wata irin dariya ta na yaƙunar fuska sannan ta ƙara furta " wallahi kin zagan kuma Abba ya dawo sai na faɗa masa,Wawuya kawai ". Take idanun REENA suka cika da hawaye baƙin cikin ta ɗaya kalmar Wawuya da LINA ke yawan kira mata bata son ta ko kaɗan Dan bata ga inda take wawanci ba amma abu kaɗan sai LINA ta kira mata wawuya abun na ƙona mata rai dan tun bata san ma, anar kalmar ba har ta gane ba mai daɗi bace. " Wallahi ma rufa Miki da nayi sai na faɗa ma Yaya Kin tafi yawo bayan an tashi breakfast,har sai da aka kusa tashi kika dawo ". Zaro idanu LINA tayi kafin ta zo da sauri tana marairaice wa kamar ta duƙa ma REENA tana furta " Ki rufa mini asiri ba zan ƙara ce Miki Wawuya ba REENA " Murmushi REENA tayi abun ka ga zuciya mai sauƙi take ta ce " ai ba zan faɗa masa ba na rufa Miki,da zan gaya masa tun ɗazu ai da na faɗa masa ma ". Numfashi LINA ta sauke har da dafe ƙirji Dan wasu maza tayi dambe dasu su uku bayan school kawai dan sun yi Gulmar ta maganar ta dawo kunnen ta shine ta aika musu da saƙon su haɗu lungun kaci uwa ka idan basu tsoron ta wanda da ƙyar wani security na su ya raba faɗan har suka bashi cin hanci ganin Dagske zai kai report wa school a hukunta su sannan a kira iyayen su. Gaba tayi zuciyar ta na yin sanyi tana fatan kar wata rana Surutun REENA ya tashi ta faɗa ta san ranar sai ya kakkarya ta tayi faɗa da maza ko matan ya ta ƙare in zancen ya zo kunnen sa. " Ummah ta ce mu fito da wuri muyi lunch tace har ke ki fito kuma ". Tana gama sauraren zancen na REENA ta fice daga toilet ɗin tana yatsinar fuska ganin kamar an takura mata dan bata so fita ba, ta so akawo mata abun ta nan hankalin ta kwance amma yanzu da ta haɗa ido da Ya B. Ta san Harara ce zata ƙosar da ita. Ta shirya da wuri amma itace last fitowa dan zaman ta tayi sai da tayi ta tunanin zaman dinning saboda ta san haushe yake da ita tunda gaban shi ta daki yar gaban goshin sa, gashi bata da gaskiya ganin take ko wane irin lokaci asirin ta zai iya tonuwa dan ta san REENA gaɓa ce wata rana tsafff zata iya kawo zancen idan fira tayi daɗi. Zama tayi tana ƙaƙƙyafta idanun ta kamar wadda tayi ƙarya.Rabi mai aikin Ummah a asashen dafa abinci dake tsaye gefe, da sauri kuwa tayi serving nata bayan ta zaɓi abinda take buƙata.Sauƙin ta ma babu wanda ya kula kan ta dan sun saba da rashin fitowar ta ta da wuri sai taga dama Dan haka suke fara cin abincin su ba tare da sun jira ta ba idan ka gan ta ta fito da wuri to Abba ya dawo ne kafin shima a cire marmarin sa. Tun da suka fara cin abincin babu wanda ya cewa kowa ƙala dan sun saba da rashin yin magana idan ana cin abinci sai dai koda magana kaji to bakin LINA ne kuma Abba na kusa.Shirun ne ya ishe ta gashi har yanzu babu wanda ya tashi tsakanin Ummah da BILAL hakan ya sa ta yin ɗan tari na farko babu wanda ya Kalle ta na biyu ma haka ana uku ne UMMAH ta miƙa mata ruwa cikin kulawa shiko BILAL spooon ɗin hannun sa ya ajiye yana zuba mata idanun sa da suke saurin kaɗa hantar cikin ta,Tana kafa bakin ta a ruwan kuwa jikin ta ya fara tsuma ganin kallon da yake mata wanda ya sa ta sarƙewa Dagaske idanun tane suka firfito take suka yi jaaa na azaba. Hawaye REENA ta fara tana miƙa mata ruwa cikin Tausayin yar uwar Tata. Itama umma da rarrashi take ɗan bubbuga bayan ta tana furta mata kalmar sannu.Shiko BILAL Allah ya ƙara kawai ya iya furta wa A hankali yana Hararar ta wanda dama da gangan yayi saboda ya fahimci tarin munafunci ne,miƙewa daga gurin yyi yana yin falo ba tare da ya bi ta kan su ba.. Rashin Chaji ya sa baku samu page jiha ba saboda biyu ya kamata a samu.✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan N#1000. Yanzu muna kan free pages, kuma baza,a same su da yawa ba gaskiya dan haka kuna iya fara yin payment. 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt *08069059746* Daga Alƙalamin ✍️ GIMBIYAR TASKIRA 👑 FA'EEH BG ✍️ FIRSTLADY 🙌 LIKE,REACT, COMMENT sune kawai nake buƙata,shine zai nuna mini yadda kuka karɓi book ɗin..✍️ _Typing_ *💋KURMAN ƘADDARA💋* ©®*FA'EEH BG* *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣6️⃣ ''''"""$""""$""""" *Contact dis line👉08069059746 for advert.* *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn 💋💋💋 Hawaye ne suka silalo mata masu zafi na azaba cike da Haushi da baƙin cikin sa na furucin da yayi mata cikin rashin tausayi ta matsa gefe tana sakin kuka Itama REENA zama tayi gefen ta kafin kuma ta rungume ta suka haɗe kai waje ɗaya. Ummah murmushi kawai tayi cike da ƙaunar ya yan nata ta furta " wai duk saboda kin samu chocking ne zaku mayar muna da gida gidan kuka,Allah idan baku daina ba zan bar ku dashi kun san sauran ". Shiru suka yi kamar ruwa ya cisu dan kamar sun manta waye yake zaune cikin falon. REENA ce ta riƙo hannun yar uwar ta da idanun ta suka yi jazir na azaba. Fisgewa LINA tayi tana barin dinning ɗin tana gunguni wanda ba kowa zai iya cewa ga abun da ta ke faɗa ba. Har ta kusa shigewa lungun da zai sada ta da bedroom ɗin su dake ƙasan ta taji saukar Muryan sa " Wallahi kika shiga ɗakin nan sai kin yi tuman kwaɗɗo ɗari " Cikin sauri ta juyo tana share hawaye kan ta ƙasa saboda fushi take yi dashi ta zo ta zauna kusa da REENA da ke zaune kusa dashi ta yi shiru tana kallon Cartoon da ya kunna mata bayan dawowar su Falon ita da Ummah.Ummah da ta gama bawa masu aikin na ta umurni ne ta zo ta zauna cike da kulawa ta furta " Soja ya hanya ya kuma aiki,tunda ka ƙi bari mu ko gaisa sai ka fara ganin ƙannen ka ". Sunan Soja itace kawai ke kiran sa dashi.Murmushi yayi yana kallon mahaifiyar ta sa Abar son sa sanyin idaniyar sa sannan ya furta " Ummah Alhamdulillah komai lafiya lau". " Amma baka cin isasshen abinci ko Soja,dan wannan karon ban ga kayi wata ƙiba ta arziki ba ". Murmushi yayi kafin ya ce " Ummah ai idan nayi ƙiba aikin zai min wahala,Gudu ma sai ya gagare ni " Idanu ta zuba masa tana ƙara ƙare masa kallo kafin cikin cire Muryan wasa ta furta " Dagaske fa nake yi Soja ka yi rama a wannan karon,me yake damun ka ". Shiru yayi zuciyar sa na wani irin chanza sauti kafin ya samu damar bata amsa yana furta " Ummah aiki ne kawai,kin san munje wani mission na sati biyu to Bama samun isasshen abinci achan ko daga ni har ya ra na kowa kika gani zaki ga ya chanza saboda yanayin wurin da muka samu kan mu " . Kai ta girgiza masa kamar ta yarda kafin ta sauke ajiyar zuciya da ita kaɗai ta san ma,anar ta. A ɓangaren sa ajiyar zuciya ya sauke a ɓoye yana rufe idanun sa bayan ƙare ma LINA kallo da ke zaune kamar wadda an ka yiwa mutuwa fuskar nan Tata ta sauya ta wani karkace kai irin bata son magana da kowa ma. Ammah ce ta ƙyafato ta bayan sun haɗa ido yanzu ganin har yanzu ranta a ɓace yake ta furta " Zo nan ". Zama LINA tayi a kusa da ita wanda ya ƙara tabbatar mata da fushi take yi da kowa dagasken.Dan da ba haka ba kan ƙafafun ta zata haye. Murmushi tayi tana ɗago face ɗin tace " ALINA my baby girl waya taɓa min ke,waya taɓa sanyin idaniyar SS family ne ''Tayi zancen tana janyo ta jikin ta duk da ta san kan wa ake fushin. Kuka LINA ta fashe da shi mai cike da shagwaɓa tana furta " Ba Yaya Bilal bane ya min Allah ya ƙara ai dama na san baya sona,ya fi son REENA ai ban manta ba yace ni ba ƙanwar sa ba ce bai haɗa komai dani ba ". Buɗe idanun sa da suka masa nauyi yayi saboda bacccin da ke cin su yayi yana sauke su kan ɗan ƙaramin bakin da ke zuba kalaman da baka taɓa tunanin ta iya zaro su saboda yarintar ta. Murmushi kawai ya saki yana kallon REENA da ta zuba masa idanu tun ajiyar zuciyar da ya sauke wanda kaɗan ya rage tace masa Yaya Ba ka lafiya ne naji ka yi ajiyar zuciya.Sai kuma ta dakata saboda Ummah ta katse mata zancen na zucin ta da take son fito dashi ta hanyar yiwa LINA magana. Jinjina kai yayi yana furtawa azuciyar sa Lallai LINA bata da mantuwa shi da yayi zancen ya daɗe da mantawa kuma lokacin tun tana yar shekara bakwai ne a duniya lokacin tana cikin ganiyar rashin jin magana babu wanda bata addaba ba cikin estate ɗin ita faɗa da wanchan yau gobe da wani wanda shi kuma ya sako ta gaba dan ya tsani rashin jin magana dan duka yaran familyn suna tsoron sa sosai itace kawai mai kunnen ƙashi ya rasa dalilin rashin jin na ta gashi kullum abun nata gaba yake yi,shi ya sa ya ke matsa mata kamar yadda take cikin rashin ji kullum yake hukuntata sai dai banza dan Tsoron nasa ma bai wuce shekara uku da ta fara yin sa ba.May be ko saboda suna gida ɗaya ne bata jin maganar sa Oho. Hararar sa Ummah tayi bayan sun haɗa ido. Kafin ta furta " Soja kar ka ƙara ta kura ma sanyin idaniyar gidan SS kaji ka iya bakin kaji abun da aka yi tun shekara huɗu Bata manta ba abun na ran ta,yanzu dai kar ka ƙara dakar min Yaa kuma ka bata haƙuri ,ko muci ga da fushi da kai ". Idanu ya zaro yana furta " Ummah Haƙuri fa,ai ita ya kamata ta bani haƙuri,a gaban ido na nagan ta tana dakar REENA kamar Allah ya aiko ta,sai kace ba yar uwar ta ba,kamar ba ciki ɗaya suka fito ba,wannan wane rashin ji ne idan har tayi wa wasu dake waje ai bai kama ta ta yiwa REENA ba,bana son yawan faɗan nan na su abu kullum kamar gaba yake yi,kuma a duk lokacin da za,ayi rigimar itace fa mara gaskiya fa Ummah ". Shiru yayi dan har ransa ya ɓaci tuni bayan tunano irin rashin jin da tayi tayi a baya dan bata ragawa kowa a cikin yaran gidan ga rashin kunya ga manya sai in bata ga damar ka ba,ko bata ga dama tana yi sai dai a dake ta tayi kukan ta ta share hawayen ta.Ta sha yin dambe iri iri da yan matan har haƙora ta taɓa cirewa Ninah ɗiyar ƙanen mahaifin su.Shi yasa har yanzu ba wani shiri take yi da ita ba. Kan sa ya sauke ƙasa cike da haushi yana ƙara furta " Allah Ummah ke kike ƙara wa aya zaƙi kamar kina goyon bayan yarinyar nan akan abun da take yi,ace mutun bai son zaman lafiya,kowa ya buɗa baki sai ya faɗi mara daɗi kan sa,ni bazan lamun ta ba gaskiya Ummah,ba zan iya jure shirmen ta ba ".Ya kai ƙarshen maganar matuƙar ransa ɓace.Jikin sa har ya fara ciccira LINA dake hango sa ƙara shan jinin jikin ta tayi tana rufe idanun ta saboda tsoron da ya ƙara kama ta ganin yadda ya'yan na su ya juye lokaci ɗaya da alama zuciyar sa ta ke son motsawa dan Allah ya zuba masa zuciya dan haka baya son a kawo masa wargi sannan bai cika shiga harkar yaran gidan ba,bare ma kuma duk tsoron sa suke yi. Ganin yadda ko ƙanwar sa da suke ɗaki ɗaya bai raga ma ba. Murmushi Ummah ta sauke kafin ta kalli fuskar LINA da idanun ta suke a rufe.Kan ta ta ɗauke kan ta ,tana mayar wa kan REENA da take cikin tsoro ji take kamar a ce ƙyat ta ruga ganin yadda ran yan maza ya ke son motsawa LINA zata janyo musu Masifa da rana tsaka.Dan idan yana irin wannan yanayin ko Ummah da ƙyar take tanƙwasa sa bare ma Abba da yake ba zama yake yi sosai ba saboda harkar business ɗin sa. Kai ta girgiza kafin ta furta "SSB" dan wata rana haka take kiran sa. " Ni nake ƙarawa aya zaƙi Soja " ta furta tana jin jina maganar. Shiru yayi jikin sa sanyaye jin furucin ta kafin ya ɗago ya Kalle ta,fahimtar kalaman na sa kamar sun mata tsauri tun da ya san itama fama ta ke da su yace cikin Muryan nadama da ladabi " Kiyi haƙuri " bata tan ka masa ba sai ma cigaba da magana da tayi. " Ka cigaba da shan ragin ruwan Alwallah wannan zuciyar taka na zata ta tafi a she tana kusa,yanzu lallashi SAREENA dake gefen ka, kasaki fuska Karka sabauta mini Yaa ".ta kai ƙarshen furucin tana kallon REENA da idanun ta suka yi rau rau alamar kuka a kowanne irin lokaci zai iya zo mata.Samun kan sa yayi da sakin guntun murmushi kafin ya janyo ta jikin shi yana tsokanar ta.Kasa sakewa tayi sai da ya kunna wayar sa ya kamo Pics nasu lokacin suna yan dagwai yake nuna mata wanda take ta fara dariya,tana furta " LINA nafi ta kyau,Ji bi bakin ta a tsakiyar haƙoran ta kamar ta ga " tayi zancen tana kallon ƙaton giɓin su da yake bayyane saboda sun washe baki ne a dariyar. LINA da tayi likimo ne kamar bata san akwai wasu a falon ba ta ɗago tana furta " Wallahi baki fi ni kyau ba,mu ma ga pics ɗin " Tana zancen ta sauko jikin Ummah da sauri ta na komawa bayan kujera kusa da Bilal da REENA ɗin.Ammah kai kawai ta girgiza ganin har ta sauko lokaci ɗaya,gata bayan wanda ake faɗan ma dashi ana neman yin sabuwar fitinar domin idan ba Allah ya tsayar ba sai an yi rigima,dan LINA ta tsani REENA ta kira mata mara kyau duk da da wasa take mata dan kamar su ɗaya a jiki da fuska da komai ba za ma ki iya banbance su ba idan ba sanin su kika yi ba,ko shi ta gefen natsuwa da REENA ta fi LINA ɗin. miƙewa Ummah ta yi bayan ta sauke numfashi kamar wadda aka tsakura ta miƙe ta shige bedroom ɗin ta da yake sama.Ba tare da ta bi ta kan su ba. Gidan kamar sauran gidajen yake dan dukkanin su tsarin su ɗaya in ka cire na BILAL dan shima yana da na sa PART anan amma dukkanin su haka suke babu banbanci a tsakanin su,gida ne fankacece mai ɗauke da ƙaton falo mai ɗauke duk wata duniya acikin sa daga ƙasa su REENA suna da bedroom ɗaya daga sama kuwa kusa da bedroom ɗin abban su suna da ɗai ɗaya kowacce nada nata shaƙe da kayan ɗaki na alfarma irin samfurin na yara da komai da ya shafi yara,dan har da sashen karatu kowace an ɗebe mata an ɗaura komai na buƙata.Ɗakin Ammah biyu ne tana da ɗaya ƙasa kamar su LINA tana da ɗaya sama kusa da na su LINA ta gefen dama.Abba yana da bedroom ɗin sa ta ɗaya a ƙasa shima mai ɗauke da babban ɗakin tarbon baƙi dan bayan guest house da suke dashi a gidan suna da ɗakin tarbon baƙi a kowanne sashe,ɗakin masu aiki akwai shi chan sashen kusa da kitchen nan nasu yake,duk da suna da part na su a chan maza da mata kowa nashi daban amma bai hana aka ware musu ɗakuna a falon ba dan idan suna da aiki mai yawa suna iya yin komai a nan kafin su koma gefen su.A sama ma ɗakin ABBA yana kusa da ɗakin su LINA ta hagu BILAL kuma nasa bedroom ɗin a ƙasa yake gaba ɗaya ta wani gefe chan dan sai kin yi yar tafiya kafin ki isa part ɗin sa daga cikin gidan,sai ba,a ware masa na sa ba saboda yadda ya nuna ƙin hakan duk da manyan bedroom da falos da ke a achan upstairs ɗin dan ƙoƙofi ne birjik ta wanchan ɓangaren.Gidan dai ya tsaru iya tsaruwa,komai Masha ALLAH ba sai an faɗa muku irin dukiyar dake cikin sa ba. Hoton ta kalla bayan REENA ta miƙo wayar daga sama dariya ta ƙyaƙyace da ita tana furta " Yy Dan Allah giɓin waye yafi kyau,wallahi nawa yafi naki kyau Allah duba fa,wannan ƙofar ta me ce,ƙofar mata ce ko ta ɗan agundi ". " Allah bari na cewa "Ummah a mayar dake Kano Ƙofofin haƙoran ki duk na su ne," ta kai ƙarshen zancen tana ƙyalƙyata dariya tana kallon ƙaton giɓin na su kowaccen su ta sha doguwar riga yar guntuwa ƙafafun su sake sai walƙiya suke yi.Sun yi kyau sosai dan kayan su iri ɗaya ne a duk hoton da za,a wuce. REENA shiru tayi kamar ta ƙwage tana ɓata fuskar ta. Jin bai bata amsa ba ya sa ta ɗagowa tana ƙara maimai ta tambayar " Dan Allah yaya a faɗi tsakani da Allah na wa yafi a lokacin " ? Ɗan buɗe idanun sa da ya rufe yayi yana sauke su akan ta kafin ya mayar da su ya rufe sannan ya furta " na REENA man ".ai tafi ki kyau nesa ba kusa ba duk da kamar ku ɗaya ai abun bayya ne " Ya yi zancen bayan ƙare ma REENA da tayi sagado cike da Haushin zancen LINA.Tsalle ta fara bayan jin furucin sa kafin ta faɗa jikin sa ta rungume sa tana cewa " Ai yaya dama na san na fi ta kyau,ai duk da fuskar mu ɗaya dole za,a ga wanda yafi wani kyau,nafi yar wata kyau yelun"Ta kai ƙarshen zancen tana Hararar LINA da ta ɓata fuska idanun ta har sun sauya alamar kowane irin lokaci tana iya zubar da ƙwalla. Ta gefen ido ya Kalle ta ya karanci yanayin ta dan ba zai iya ba ma da rigimar Tata ya miƙe yana karɓan wayar sa hannun ta yana barin falon gaba ɗaya bayan kashe din banda faɗa da ya musu. " LINA an fara saka sabon tomm and Jerry zo mu kalla kin ga yanzu na gan sa ". REENA bata lura da yanayin LINA ba tayi furucin sai dai kafin ta ankara ta kai ma fuskar ta bugu cike da Haushin ta ita da ya yan su. Baƙin cikin ta ɗaya wai REENA tafi ta kyau. Fitowar Ummah daga ɗaki kenan ta ga faruwar abun kafin rigima ta kaure tsakaninsu da ƙyar ta raba su REENA sai kuka take yi ita kuwa kamar wata samna. Ammah kan ta ji tayi kamar ta ƙarawa REENA abu kaɗan sai kuka shi yasa LINA ta raina ta,ta mugun Tausayin REENA saboda yadda rayuwar ta take mai sauƙi gashi irin wannan kana cin wahala a mutane Bama REENA ba kowa na gidan ganin bata son fitina suna ƙoƙarin shige mata ga hanci sai da LINA tayi maganin kowa sannan suka shafa mata lafiya,dan ita in zata chasa ta sau goma bata damuwa amma idan wani yayi ko sau ɗaya tana jin baƙin ciki,inda take shigewa faɗan.Ko kuka taga yar uwar ta nayi idan dai ba ita ta san ta saka ta ba akwai matsala.Haka suke gudanar da rayuwar su mai cike da abun sha'awa cike da soyayyar junan su. Rarrashin ta Ummah tayi kafin ta yi shiru. Neman ba,a sin faɗan tayi inda cike da haushi LINA ta faɗa mata. Zuba mata idanu Ummah tayi kafin ta furta " oh ni bint Usman,SOJA ka haɗa mini faɗa a gida, yanzu wannan shine abun faɗa kuma LINA da zaki saka mini yaa a gaba haka,yanzu duk faɗan da Soja ya Miki,a banza, a gaban ki nan kika ji yadda yake hawa ya ke sauka idan na barki dashi a lokacin ƙalla mun ke kawai zai yi,amma shine bayan ɓacewar sawun sa kika koma,nide Allah ya shirya mini ke ALINA ban san yaushe zaki yi hankali ba may be sai kirji ya cika an zama yan mata,Allah dai ya shirya mini ku "Ta kai ƙarshen zancen tana girgiza kan ta tare da sakin murmushi. Ganin yadda LINA ta turo baki hakan ya sa ta ƙara furta " In ban da abun ki ALINA kamar ku ɗaya fa ni kaina da nake mahaifiyar ku da ban yi da ƙyar ba ko bazan iya gane ku ba ko lokacin da kuna ƙanana haka nayi ta fama bana gane ku sosai amma da yake ni na haifa a buna take nake gane ku,tun ran da kuka fito ciki haka kuka fito kala ɗaya babu mai banbanci atsakanin ku kyawun ku iri ɗaya ne,kun kwaso kyakkyawar fuskar iyayen ku,Kyawawan Idanun ku duka nawa ne yanayin shape na fuska na mahaifin ku ne ,yara masu kyau ai duka familyn SSS babu kamar ya'ya na a fagen kyau " haka tayi ta koɗa su kafin ka ankara fuskokin su suna cike da murmushi har da mai kuka. Samun kan ta tayi da sakin yar ƙaramar dariya kafin ta janyo hannayen su waje ɗaya ta zauna tare da su. Tana ƙara furta " Kune hasken idaniyar mu,ya yan Gata,LINA soyayyar da ya yan ku yake Miki dai dai take da ta REENA kawai rashin jin maganar ki ne ke haɗa ku,da zaki daina zaki gani,gashi harda yarin ta ya sako mini ke gaba babu abinda zaki iya fahimta " " Allah ya shirya mini ku ya sa naga yan matan cin ku naga Auren ku Allah ya muku Barka ". " Amin " Suka haɗa baki suka faɗa suna murmushi.Kan su ta shafa itama cikin murmushi kafin tayi musu peck a goshin kowacce.Fira suka fara yi suna bata labarin school suna cigaba da kallon Cartoon ɗin su tana biye musu cike da so da ƙauna,har waya suka kira Abba suka yi dashi cike da farin ciki da kewar sa mai haɗe da ƙaunar mahaifin na su. *** Hajiya ɗazu naga fitinannun yaran chan sun dawo daga makaranta ɗayar baki ga jikin ta ba kamar tayi faɗa da kura,Da alama dai halin suka ƙara yi a waje,tun da sun zama yan dambe. Murmushi Babbar matar dake zaune a kan kujerar alfarma tayi irin murmushin nan na masu aji da wata manufa. Kafin ta ɗan muskuta sannan ta ce " Ina son zan tura ki wani waje ma dan akwai aikin da nake son yi dan na fara hango matsala babba dole na sake sabon shiri,Ba zan lamunci ina kallo ba kasuwa ta watse dani babu riba" " LINA rigimammar kan ta ce da kika sani luba,shi ya sa nake son yarinyar " Sai ta ƙara sa zancen tana sakin murmushin da ita kaɗai ta san ma,anar sa. Dariya itama yar dattijuwar matar da aka kira luba tayi tana yiwa uwar ɗakin na ta kirari ganin ta miƙo mata bandir na yan dubu dubu guda uku. Fitowar yar tace ƙwaya ɗaya tal mai suna Hamrah ya sa juya wa tana kallon ta fuskar ta cike da murmushi tana furta " Yar gwal an fito " Baki yarinyar ta cunno gaba irin na sakuwa kafin ta faɗa jikin mahaifiyar ta tana rungume ta... " Momy na gaji da ya wallahi tun da na dawo school ƙafafu na suke ciwo gashi bakya nan bare ki rarrashe ni,Yawwa Momy kin sa wai su REENA yau dambe suka ƙara yi a schl kwana biyun chan ba su yi ba,har naji daɗi amma yanzu kin gan yadda suke dambe,ni dana ga ba,a zo ɗaukar su ba na san halin LINA nace wa yusuf driver kawai ya wuce ba sai na rage musu hanya ba,dan malam Adamu bai je ɗaukar su da wuri ba ". Murmushi matar tayi kafin ta furta " Ya yan ku ne ya dawo shine ya tsayar da shi,suka je ɗauko su tare,nima duk yanzu Luba take faɗa mini " Ai bata bari ta rufe baki ba ta dire ƙasa cike da wani irin tsalle tana furta " Momy nayi part ɗin Ummah na ga Yaya ". " A'ah karki je a haɗa dake gashi da baki kin ce dambe suka yi na san shi ma BILAL ɗin ba zai rasa ji ba ko gani,ba zan lamunci ya haɗa dake ya sakar muku ƙarfin sojoji ba,ki bar su chan da yawar su ". Tabbatar da zancen mahaifiyar ta gaskiya ne hakan ya sa ta dawo jiki mace ta zauna kusa da Mahaifiyar ta tana ɗaura kan ta a bisa kafaɗar ta tana rungume ta,dan tayi kewar ya'yan na su. Dariya Momy tayi haka Luba dan sun san Hamrah da Shegen tsoro. Miƙewa luba tayi ta mata sallama tana ficewa daga part ɗin gaba ɗaya,cikin son isar da saƙon uwar gijiyar ta ta da ta san ko saƙon me ne ne.✍️ INA ƊAN FAMA DA ZAZZAƁI NE SHI YA SA KUKA JI SHIRU,KUMA IRIN ZAZZAƁIN NAN NE MAI TAKURA🥲😔.ALLAH KA BAMU LAFIYA MAI AMFANI.🤲 Masoyan SHATOU a yi haƙuri zamu koma gefen ta a next page in sha ALLAH. Like share,and comment 🙏 Wannan littafi na kuɗi ne. Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya.. Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *TAFIYAR TA DABANCE SAI AN BIBIYA AKAN GANE HAKAN.✍️* _Typing_ *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣7️⃣ >>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>> *CONTACT DIS LINE 👉08069059746 FOR ADVERT.* *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* Channel link https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y Posting room link https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* 🎀🎀🎀 ***Sai da suka ci girkin Inna ni sannan suka watse kamar kar su rabu. Dare nayi hankalin Inna ni ya fara tashi ta san cewa SHATOU dole sai ta fita, fira suke yi amma hankalin ta na kan ta har suka ɗauko abun karatun su Baffa na ya fara bita musu bata natsu ba.Kamar kullum sallar isha'i ce ta sanya su miƙewa domin gabatar da sallah akan lokacin ta,musamman ta isha da take mai nauyi. A tsakar gida tayi Sallah tare da Inni amma duk da haka hankalin ta ba a kwance yake ba,Suna gama wa Nan bacci ya ɓingire ta wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar inni ni ganin baccin take yi Dagaske.Gyara mata kwanciya tayi ta ɗan sha iska kafin su tashi ta mayar da ita ɗakin ta. Addu,oin ta ta cigaba da yi bayan ta gabatar da shafa'i da wutiri. A haka su Bibu suka dawo daga masallaci suka tarar da ita tana baccin ta cike da natsuwa. Murmushi Baffa na yayi yana gyara mata hannun ta ɗaya daya lanƙwashe. Sannan ya furta " Shatouwa da bacci da wuri yau,halama dai A'ie Addu,a kika mata ta bacci da wuri ".? Inna ni dariya tayi tana furta " gata nan dai,nikamm babu ruwa na Allah dai ya dubi zuciya ta ya kwantar muna da ita da wuri yar neman,dan haka karku ƙalubalance ni" Ta kai ƙarshen zancen tana Murmushi tana miƙewa ta zubawa Bibu abincin sa da ya bai ci ba ɗazu yace ya ƙoshi sun ci abinci a makaranta kuma cikin shi ya cika sosai. Dan haka kowa yaci nashi ba dashi ba. Fira suka taɓa kaɗan kafin aka mayar da Shatou ɗakin ta,Sannan dukkanin su kowa ya koma na sa ɗakin bayan sunyi wa juna sai da safe. Kamar ko da yaushe bayan dukkanin sawu ya ɗauke ta miƙe bayan tabbatar da Baffa na yayi bacci ta miƙe ta haɗe kai da gwiwa ta fara wani irin kuka mai tsuma zuciya,kuka ne mai fitowa daga ƙasan zuciyar ta wanda yafi na ko yaushe,yau zantukan SHATOU sun ƙara mata wani irin rauni a cikin zuciyar ta,ta kusa ɗaukar Awa tana yin wannan kukan mai cike da rauni da kewa sannan ta share hawayen ta ganin tana neman jazawa kan ta ciwon kai. Miƙewa tayi ta fita da zummar wanke fuskar ta sai dai Turus ta ja ta tsaya domin kuwa bakowa taci karo dashi ba face Baffa na fuskar shi cike da tausayi idanun sa sunyi jazir dan akwai farin wata sosai. Kan ta ta sauke ƙasa,ta raɓa shi tayo alwallah.Shi ma bai ce mata ƙala ba har sai da ta kusa shigewa ɗakin na ta sannan ya ambaci sunan ta cike da tausayin ta. " Komai yayi tsanani maganin sa Allah,hakan da kika yi shine dai dai, Sannan ba zan gaji da maimaita Miki ba A'ie ki fito ki faɗi wata maganar da zata sa mu fahimci wani abun da yake damun ki,zancen da kika bani a baya ba zai iya saka a fahimci komai ba,har a san abun yi,amma kiyi tunani ina son sanin komai dake faruwa,amma ba zan matsa Miki ba ina jiran ranar da kika tashi faɗa zan saurare ki ". Yana gama maganar sa ya shigewar sa ɗakin sa dake kusa da nata kaɗan. Jikin ta ne ya ƙara mutuwa wani sabon kukan na son ta so mata dan Dagske tana cikin damuwa,kuma tana buƙatar mai Rarrashin ta. Shigewa tayi ta shimfiɗa sallaya ta tayar da sallah sai da tayi raka'a shida sannan ta fara kai kukan ta ga Ubangiji hawaye na kwaranya a cikin idanun ta. " Allah idan har abun da mutanen Shatou suka faɗa gaskiya ne Allah ka kare mini su,a duk inda suke,Allah ka bata lafiya,Allah ka yaye mata,Allah bani da tsimi bani da dubara Allah ka yaye mini damuwa ta,Allah ka kawo mini mafita,Allah ka kare mini rayukkan su a duk inda suke " Kuka ne ya ƙwace mata mai zafi da raɗaɗi da ƙuna sai da tayi mai isar ta anan sannan ta kwanta nan kan sallaya bacci ya kwashe ta mai nauyi. Baffa na dake tsaye bakin ƙofar ɗakin ne da ya ji komai da take faɗa ya koma ɗakin sa da sauri cike da tambayoyi a cikin zuciyar sa ya je da zummar ƙara bata baki ya ji abinda bai san inda zai saka kalaman na ta ba da ba komai ya fahimta ba sai dai ya sanya su a cikin zuciyar sa cike da mamakin mutane shatoun da ya ji ta faɗa wanda shi dai duk iya sanin sa da yar ta sa ba ta da wasu mutane tun da basu taɓa tashi ba bare a gan su. Addu,ar kwanciya bacci yayi bayan ya ƙara tofekke su Shatou da Addu,a ya sayo gidan sannan ya kwanta shima cike da tunani a haka har bacci ya kwashe sa jiki mace. Yau Litinin hakan ya sa tun da suka tashi sallar asuba basu koma bacci ba,saboda yin ayyukan gidan da wuri da kuma zuwa makaranta akan lokaci tsaf suka shirya bayan sun jido ruwa tare da yiwa Inna ni share share,karin kumallo suka yi sannan suka fice a tare bayan yiwa iyayen na su mun tafi.Addu,a suka bisu da ita.Ba a ɗau lokaci ba shima Baffa na ya fice kasuwa dan yana da ɗan ƙaramin shago a kasuwa yana siyar da kayan farauta duk wani nau'in kaya na farauta,da kuma Ganyen shayi ko wane iri ne ana samun sa a wajen sa. Tun da suka isa makaranta tsirarun yaran da ke wajen ke kallon su musamman shatou sai su kalle su suyi dariya sai suyi gaba.Tun abun na bawa shatou mamaki har ya daina bata.Bata ce ma Bibu komai ba haka shima sai dai kowa ya shigewar sa aji cike da mamakin kallon da ake musu. Da shigar ta Ajin su ta ji ƙana nan maganganu na tashi sama sama gashi sai kallon ta suke yi.Kamar ance ta kalli allo saboda ta iya karatun Hausa tsafff ta zaro ido tana kallon Allon da ya ƙunshe da rubutu kamar haka " daga yau ni Shatou suna na ya koma Kosongo,ko shatou kosongo ". Abun gugar allo ta ɗauka tana furta " Uban wa yayi wanann rubutun nayi imani da Allah ko waye yayi shi sai ya ɗan ɗani azaba ta sai ya gwammace Ni shatou banzo duniya ba ". Tana yin maganar cikin ɓacin rai da haushi tana gugar rubutun,su dai sauran yan Ajin su kowa zuba mata ido yayi wasu kuwa dariya suke yi ƙasa ƙasa ba damar a fitar an san halin ta. Sai da ta goge Allo tass sannan ta dawo tana nishin Masifa tana kallon yan Ajin na su,Amina ta hango daga gefe wadda tayi tagumi dan ta san yau akwai matsala taso ta goge rubutun wasu yan Ajin suka hana ta,ashe ma a banza dan kowane aji dake makarantar anyi rubutun,rubutun da ma yake chakuɗe kamar na yan koyo. " Amina wa yayi rubutun nan,waya tsokano fitinar da tafi ƙarfin sa,na rantse da Allah idan kin san kowaye karki ɓoye ni,dan idan na gano wallahi sai na bar ƙawance dake " Tayi hakan ne dan ta san yadda Amina ta tsani kalmar ta san dole in ta sani ba zata taɓa ɓoye mata ba. Idanun Amina cike da hawaye ta ce " Wallahi na yi miki rantsuwa da Allahn da ya halicce ni ban san wanda yayi shi ba nidai ko da na zo na tarar dashi na so na goge suka hana ni,Kuma Kiyi haƙuri gaba ɗaya ajujuwan makarantar nan aka yi rubutun amma ni da su Ramata mun goge shi wanda koda muka goge wasu sun riga sun gani ". Ran shatou ne ya ƙara ɓaci kamar ta fasa kuka dan da gaban su Inna ni ne da ta yi kuka sosai yadda ran ta yake ɓace ko zata rage hasahi. Zama tayi bata cewa kowa ƙala ba har su Ramata da suke son cewa wani abu,amma bata basu dama ba. Ajin sai kallon ta suke yi kowa na son ya maimaita sunan yana gudun ruwan masifa dan daga Mazan har matan su babu wanda take shakku. Har malamin su ya shigo yayi karatu bata sauko ba duk yadda yake jan ta da magana saboda tana cikin ɗalibban Ajin masu hazaƙa tana da kai, sosai take gane karatu both Arabi da boko. Har aka tashi makaranta shatou bata wani gane ma kan ta ba saboda yadda ta sanya son gane wanda yayi rubutun ta rasa wanda zata hasasowa gaba ɗaya kan ta har ya fara ciwo saboda tunani. Ko ba,ayi ba daga makarantar ta kama hanyar gida,daga zuwa fitsari,da shigar ta ko sallama ba tayi ba ta shige ɗakin ta, littafan ta na makaranta ta janyo tun na aji ɗaya da suke ɗauke da sunayen halittu a bayan su saboda Amina ta faɗa mata ance mata wata dabbace ake kira haka mai Shegen gudu. Tana cikin dubawa kuwa taci karo da ita mummunar halittar dabbar ran ta ne ya ƙara ɓaci har wani numfashi ta ke sauke wa na yadda zuciyar ta take cike da Masifa.Kuka ta fashe dashi na yadda aka haɗa sunan ta da dabbar.kukan ta ne ya ankarar da Inna ni Dawowar ta, kasancewar tana sallah koda ta shigo.Kuma cikin natsuwa ta shigo babu guje guje. Cike da mamaki ta faɗa ɗakin na ta zaune ta isko ta haɗa kai da guiwa ta na ta darzar kuka. " Ke lafiya, , wa ya mutu ne,ina kika baro mini yaro na " Inna ni ta jero kalaman cike da son samun amsar su. " Yana makaranta ni dawowa nayi saboda kaina na ciwo yake ". " Shine saboda kan ki na ciwo shatou sai ki zauna kiyi ta kuka".takai ƙarshen zancen cike da tausayin ta dan a tunanin ta Dagske zazzaɓin ne. Ficewa tayi sai gata ta dawo tare da magani da ruwa. Ɓalla mata tayi ta bata babu musu kuwa ta karɓa dan ta san halin inna ni yanzu sai ta hasala dan tana da saurin hasala dan kamar duk ita ta biyo. " Sannu,yanzu ki tashi ki watsa ruwa sai ki samu ki ci abinci ki kwanta ko ". Kai shatou ta gyaɗa kafin ta miƙe ta cire kayan jikin ta nan gaban Inna ni ɗin ta koma daga ita sai ɗan kan fai dan babu ruwan ta Indai ta so cire kayan jikin ta kowa ke wajen tana iya wa sai dai bazata cire gaba ɗaya ba,gaban Inni ni kuwa zama take da ɗan kanfai.Inna ni tayi faɗa amma ta kasa bari,har gaban Bibu wata rana ta kan cire kayan jikin ta. Shi ko yayi ta tsokanar ta da "Adda SHATOU ƙatuwar banza mai cire kaya a gaban mutane ". Daga haka kuma suyi ta zagayen gidan har su gaji. Kai Inna ni ta girgiza tana murmushi ganin yadda ƙiren dangin na shatou suke maƙale a jikin ta,lallai girma yana hanya. Jikin ta ne ya mutu mutus hakan ya sa ta fice daga ɗakin tana share hawayen da suke son silalo mata masu zafi cike da tausayi Shatou. Ruwan wanka ta haɗa mata ta kai mata makewayi. Shatou na fitowa ta san cewa ta kai mata su chan hakan ya sa ta wuce makewayin. Sallamar su Amina ce da Bibu ta cika gidan. Amsa musu Inni ni tayi fuskar ta wanze da murmushi ta furta " Ya na gan ku fuskokin ku kamar babu lafiya ". " Eh dama Shatou ce " .... Amina ce ta fara maganar sai kuma ta yi shiru. Cigaba da maganar ki. Nan ta kwashe komai ta faɗawa Inna ni. Kai Inna ni kawai ta girgiza ita sai ma abun ya bata dariya wai shatun ta ce ake kira da kosongo sunan ma abun dariya. Yar dariya tayi kafin ta furta " Oh ni indo kowa ye da wannan ɗan yen aiki " ita kuma shine ta dawo ta zauna tana rusar kuka saboda sakalci ". Ku tafi kawai sata sauko kunji. " Toh " suka haɗa baki wajen faɗa kafin suka bata jakar ta suka fice daga gidan. " Inna ni,Adda Shatou fa na san bazata bar zancen nan ya tafi ba sai ta nemo wanda yayi aikin nan ".Furucin Bibu. Kafin ta basa amsa sai ga shatou ta fito tana bin su da kallo dan taji duk taji komai. Alwallah tayi bata ce komai ba ta shige ɗakin ta. Da kallo duk suka bita ganin yadda ran ta yake jagule har yanzu. Murmushi Inna ni tayi tana furta "Lallai ran maza a ɓace yake,Bibu kuka fa ta zauna ta shara,dole na taka mata burki ta haƙura. Ɗakin ta bi shatou tare da jakar ta sallah ta tarar da ita tana yi,aje mata jakar tayi tare da zaunawa har sai da ta gama sallar tayi Addu,oin ta, Sannan ta kamo hannayen ta,ta ce " Shatou na kiyi haƙuri kinji koma wane ne ki bar shi da Allah,zai saka Miki,kuma ma shatou ai ba abun tashin hankali bane tun da bakalar dabbar zaki koma ba.Ta kai ƙarshen zancen tana sakin yar guntuwar dariya tana kallon yar Tata cike da ƙauna. Kallon Inna ni tayi kafin ta furta " Toh " tana cewa haka bata ƙara cewa komai ba. " Allah yayi Miki albarka " Inna ta furta cike da murmushi tana ficewa daga ɗakin tare da sanar da ita abincin ta Bibu zai kawo mata idan ta ci ta kwanta ta huta kafin lokacin makarantar su yayi.✍️ *** " Hhhhh ki bar wannan aikin kawai an riga ki,kuma anyi aikin mafi hatsari,aiki ɗaya za,a Miki yanzu shine ƙara hana su kusantar juna,wannan shine kawai zaki yi " Cike da mamaki take kallon Bokan na ta da ke zaune kamar wani malami sai buge buge yake yi a ƙasa. " Amma Boka Gangaro yaushe hakan ya kasance dama an daɗe da yin aikin ne ". Matar da ke zaune gaban sa tayi kamar wata baiwa tayi Furucin tana sanye cikin kayan alfarma da mayafin ta na manyan mata,mai tsada. " An daɗe da yin sa,ya fi ƙarfin shekara goma,anyi shi tun kafin zuwan su duniya,kuma yana nan yana bibiyar su gaba ɗayan su,ki bar aikin a hakan karki shiga cikin wannan gamami aiki ne babba da ya ci shekaru dan haka ki fitar da hannun ki ". " Boka Gangaro ko zan iya sanin wanda yayi aikin ". " A'ah karki matsa kar ki jamin bala'i,aiki ne na duhu baƙaƙen Aljannu ke riƙe da shi ,Idan kika matsa zamu halaka mai aikin fitinanne ne,ki iya tunanin ki kar ki ƙara maganar kuma kar ki sanar wa da wani ki bar shi a cikin ki domin zaki iya shiga haɗari,ke kan ki,aiki nane ya cece ki da tuni an gama dake ". Idanu ta zaro cike da tsoro kafin ta miƙe bayan karɓar yan ƙulle ƙullen na boka Gangaro sannan ta fice da baya daga ruɓaɓɓiyar rumfar sa,bayan ta ajiye masa manyan kuɗaɗe kamar yadda ta saba. Sai da tayi tafiya mai nisa Sannan ta fice daga cikin ƙungirmin dajin.Motar ta,ta hau ta tada tana ƙara jan Niƙaf ɗin ta. Sai dai zuciyar ta cike take da mamaki da al'ajabi me ya sa bata taɓa sani ba sai yau.To waye ne yayi mata rigaye gashi ya ce aikin ya daɗe wane mara imani ne wannan.Lallai dole ta ƙara riƙe Boka Gangaro kar ta rasa rayuwar ta. Wal, iyazubillah 😭 Hmmm.🙄 Hmmmmm Kuna ganin haƙurin nan, na Shatou ya kai zuciya kuwa ? Wa kuke tunanin ya aikata wannan aiki ? Gaskiya duk wanda ya tado muna da rigima bai kyauta ba.🚶😂 Like share,and comment 🙏 Wannan littafi na kuɗi ne. Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya.. Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *TAFIYAR TA DABANCE SAI AN BIBIYA AKAN GANE HAKAN.✍️* *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣8️⃣ >>>>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>>>> *CONTACT DIS LINE👉08069059746 FOR ADVERT.* *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* Channel link https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y Posting room link https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* 🤳🤳🤳 Har ta isa aka wangale mata ƙaton gate ɗin gidan zuciyar ta cike take da mamaki mai yawa.Ta so kiran ƙawar ta ta sanar da ita sai dai ba zai yiyu ba saboda gargaɗin da Boka Gangaro ya mata dan haka ta kame bakin ta tayi shiru. *** A ɓangaren su LINA kuwa bedroom ɗin su suka koma kasancewar lokacin makarantar islamiyya yayi suka yi shiri kafin Yayan su ya kora su da kan sa dan ya saba musu hakan idan suka buga latti saboda mafi yawan lokutta suke tsayar da yan uwan na su,kasancewar a tare ake kai su makarantar islamiyya dan dama dalilin raba su shine fitina da suke yawan yi a mota. A jere suka fito cikin shirin su kowacce riƙe da jakar ta mai ɗauke da Alqur'ani da sauran littafin sanin addini saboda makarantar suna karatu sosai gashi ana zube kuɗaɗe masu tsoka a cikin ta. Gwanin burge wa kowaccen su ta sha niƙab da Safa saboda bin ƙaidar dokar makarantar amma duk da haka LINA wata rana haka take shiga makarantar,ko yanzu ma bata ɗaura nata ba,ƙiri da muzu wai takura ta yake yi tun malamman basu fahimci halin ta ba har suka fahimci haka take idan suka ce su tilasta ta mata saka wa dole za,a samu matsala domin zata iya hinjire musu shi yasa suka saka mata ido sai gashi abun ya zame mata shan ruwan tsuntsaye wata rana ta saka wata rana ko ta ƙi sakawa. Ya'u ne driven su shine mai haƙƙin kula da kai yaran islamiyya hakan ya sa ya ke shirin sa da wuri amma duk da haka sai sun ɓata ma kan su lokaci da shi.Yau dai Allah ya taimaka saboda kasancewar wanzuwar ya yan nasu hakan ya sa kowaccen su tayi shirin ta da wuri.Koda suka fito sun tarar da Hamrah,da Nina kowaccen su ta hakimce a kujera suna taɓa fira kaɗan kaɗan. Cikin washe baki REENA ta ambaci sunayen su,suma haka cike da ƙuruciya suka amsa mata suna matsa mata space alamar ta shigo bayan kusa da su duk da motar irin mai seat da yawa ce prado new design.Da sauri kuwa ta shige tana zama tsakanin su. Ita kuwa REENA bata cewa kowaccen su ƙala ba haka su ma sai ma wani haɗe rai da tayi tana bin su da Harara daga cikin niƙaf ɗin da ta saka yanzu,dan duka haushin su take ji akan su Yaya B ya taɓa tabkar ta.dan ko wancan zuwan na sa ya tabke ta akan Hamrah da ta zaga kafin kuma ta hau ruwan cikin ta tana ta nusa.ba,a ma zancen Nina da basa ga maciji dan itama fitinanniyar kan ta ce duk da wata rana tana shayin REENA dan ta taɓa cire mata haƙori a achan baya,Allah ya taimake ta lokacin suna fira ne. Tana zama ya'u ya Kalle ta yana washe baki yana ɗan gyara sumar kan sa a madubi kasancewar sa saurayi mata shi ya furta " Yan matan Ummah yau waya taɓa mu " Dan shi dai haka kawai Allah ya ɗaura masa son REENA tana matuƙar burge shi yana son mace yar tujara,kamar ta. Mugun kallo ta jefa masa kafin ta taɓe bakin ta ta mai da fuskar ta kan glass tana ƙarewa haɗaɗɗiyar estate ɗin ta su kallo da koda yaushe ƙara kyau take yi kamar kullum ake renovation nata. Murmushi ya ƙara saki kafin ya furta "Allah ya huci zuciyar Hajiya ALINA SS ". Murmushi ne ya suɓuce mata jin ya kira ta da sunan manya wanda ya sanya ta jin kanta yayi wani ƙato. Sai dai bata kalli ko gefen da yake ba ta cigaba da kallon wajen. Haka ya tada mota yabar estate ɗin bayan wangale masa ƙaton gate da aka yi. Wani tunanin da ya shige sa ne ya san ya shi jan mugun tsaki yana bin motar da ƙwafa dan duk abinda ke faruwa a ciki Yana gani saboda ba tinted glass bane da motar ta su.Lallai dole ya taka wa wannan Drivern burki ya fara wuce gona da iri akan ƙannen na sa. Shigewa yayi part ɗin da babu kowa a cikin sa sai kayan dake zube na alfarma a ciki da wani irin ƙamshi. Da shigar sa ya nemi waje ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,abubuwa da dama suna dawowa masa aƙwakwalwa hawaye ne masu zafi suka silalo masa kafin ya yi ƙarfin halin share su yana ambaton sunayen Ubangiji zuciyar sa na cigaba da ƙuna da raɗaɗi wanda ya daɗe yana dunƙula na rashi,shekara da shekaru a duk lokacin da ya tuno da abun da idanun sa suka gane ma sa sai yaji wata iriyar zafi ta mamaye zuciyar sa baida tabbacin abinda ya gani.Dan haka tsawon wannan shekarun ya rasa wazai tun kara da wannan maganar wa zai masa fashin baƙi akan ta.Sai dai kunya da nauyin maganar sun sa ya kasa iya kallon kowa da ita kuma ya hana zuciyar sa saka masa mugun dafi mai illa a tsakanin makusan tan sa.Kuka ne ya ƙwace masa mai zafi sai da yayi mai isar sa sannan ya miƙe ya shige wani haɗaɗɗen bedroom da yake ƙal ƙal saboda kullum cikin gyaran sa ake,saboda umurnin sa ne. Kwanciya yayi akan gadon inda take bacci ya kwashe sa anan cike da tunani iri iri mai cike da mafarkayya masu daɗi da marasa daɗi. Shine bai farka ba sai ana kiraye kirayen sallar la,asar a Babban Masallacin dake cikin estate ɗin. Miƙewa yayi da sauri ya faɗa toilet wanka ya ɗauro tare da alwallah sannan ya chanza kaya saboda yana da wasu sutura anan.Wani ƙaramin frame yayiwa kiss sannan ya fice zuwa masallacin da ke cikin estate ɗin ta su. Bayan fitowar su Sallah kuwa sai Alokacin ya fara kame kame ganin yadda Mai gayya Alhaji Sada tsohon Arziki wanda dukiya ta ƙara wa tsufan sa kyau yake kallon sa yana taɓe baki.Kafun ya ɗauke kan sa daga idanun sa yana mayarwa kan Junaid da yake gayar da shi cike da girmamawa. Murmushi ya ƙaƙalo dan ya san cewa yayi laifi tun safe ya shigo bai neme sa ba sai yanzu da sallah ta haɗa su.Babu ma.wanda yaje ya gayar a cikin iyayen na sa duk da ya san suna nan kuma yana da niyyar yin haka zuwa dare. Junaid ma cike da farin ciki ya matsa kusa da ɗan uwan na sa da ya lura da shi yanzu ya rungume sa yana masa sannu da zuwa kasancewar ya ga alamar sa a cikin estate ɗin ga sojojin sa na birjik. Waye Alhaji Sada Saleh( SS ) *TUSHE* SS Babban ɗan kasuwa ne da yayi gwagwarmayar rayuwa da turawa iri iri a fannin kasuwan cin sa kuma shine magini na arzikin wannnan zuri,a,shida ɗan uwan sa. Sada Saleh,Haifaffen garin Kaduna ne su biyu suke ga mahaifin su shida ɗan uwan sa,Usman Saleh tun farkon asali mahaifin su yana ƙaramin kasuwan cin sa a ƙofar gida irin na ƙaramin shago haka kafin A hankali Allah ya buɗe masa ya cigaba ya mayar dashi kasuwa daga nan ne komai ya fara chanza wa cigaba ya samu mai yawa.A lokacin kuwa Sada da ɗan uwan sa basu wuce shekaru bakwai, shidda a duniya ba,dan babu tserewa a tsakanin su mai yawa, dan haka suka taso cikin Gata saboda sune ƙwal a gun iyayen su,sune kyautar da Allah yayi masu bayan barowar su mahaifar su,dan Saleh mata ɗaya yake da ita Aisha,Sada Saleh shine Babba sannan Usman Saleh.Iyayen su irin fulanin nan ne da suka baro garuruwan su saboda tsaro suka fara gina kan su a cikin birni cike da gwagwarmayar rayuwa. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ana ta samun cigaba ta ko ina,su Sada da Usman kuwa suna cigaba da samun ingantaccen kulawa da ilmi mai kyau.Kwatsam ana zaune wata rana Saleh Ya tsiro da zancen ƙarin Aure A'isha bata tada hankalin ta ba kasancewar ta mace mai alkunya da haƙuri duk yadda yake ɗarare da zancen amma ganin yadda ta kwantar da hankalin ta dan shi kan shi bai san abun da zai sanya shi ƙarin Auren nan ba saboda idan ya ce A'isha ta rage shi da wani abu yayi ƙarya.A haka har aka yi Auren kuma gwargwado sun haɗa kan su suna mutunci sosai a tsakanin A'isha da amaryar ta sa Ruƙayya.Ya haɗu da Ruƙayya ne a kasuwa tana kai masa tallan Nono mai kyau.Cikin aminci suka cigaba zaman su babu hayaniya har amarya ta samu rabo ta samu yar ta mace.Aka saka mata sunan Yar uwar Saleh mace ƙwaya ɗaya tal da suka fito ɗaki ɗaya da ita mai suna Sakina wadda yayi kukan rabuwa da ita saboda ya neme ta bai gan ta ba bai san inda ta faɗa ba dan da alama ɓacewa tayi,basu lura bata cikin ayarin ba sai da suka samu kan su a cikin jama'a,kuma har yanzu bai cire rai da sake ganin fuskar yar uwar shi ba.Sakina ta ɓata ne a lokacin da suka yi gudun hijira daga asalin mahaifar su a chan wani ƙauyen Adamawa. Sakina ta samu kulawa ta ko ina ga yayyen na ta ga kuma mahaifin ta da A'isha da suke kira Mama. A haka yarinya ta fara girma da wayo har ta gane dukkanin yan uwan ta itama ta tashi cike da gata. Ana nan kwatsam sai Allah ya ɗauki ran Ruƙayya da tayi fama da masassara ta kwana biyu. Mutuwar Rukayya ta taɓa kowa a cikin gidan babu ma kamar Sakina tayi kuka matuƙa saboda ta fara yin wayau sosai.Su kan su su Sada da Usman sun ji mutuwar haka ma A'isha da ta saba da Ruƙayya sosai kamar ya'ya da ƙanwa haka zaka ga suna mu,amalar su.Bayan rasuwar Ruƙayya Ciwo ya sako Sakina itama da ƙyar ta sha cikin yardar Ubangiji ta samu lafiya.A hankali ta fara sakewa cikin yan uwan ta tana samun kulawa fiye da wadda mahaifiyar ta take bata haka suka taso cikin so da ƙauna Sakina yarinya mai shiga rai da tarbiyya. Akwana a ta shi rayuwa ba wuya yau kusan shekara biyar da rasuwar ruƙayya kuma a yau ne Alhaji Saleh ya kwanta dama,sunyi kuka sun ƙoshi cike da kewar bangon su,ana haka kuma Babban shagon sa dake kasuwa ya kama da wuta,babu abinda aka tsira da shi,a kuma dai dai lokacin da iftila'in ambaliya ya afkawa gidan su,cikin ikon Allah sun tsira da rayuwakan su,amma babu maganar kayan inganta rayuwa.Rayuwa tayi wa su A'isha da su Sada zafi babu duk tarin dukiyar su ta bi ruwa sun koma basu da komai sai kayan jikin su da rayuwar da Allah mai rahama ya bar musu.lokaci ɗaya suka fara fita hayyacin su saboda rashin bangon na su ga yunwa da take son sako su gaba.Gashi suna zaune cikin gidan kamar dole saboda yadda yake dawo musu da moment tare da mahaifin su. Karatun su,na boko na Arabia komai na su ya tsaya chak domin ko taimakon su babu wanda ya iyayi sai wani bawan Allah da yake maƙwabcin Saleh a kasuwa shine mai basu hatsi.A haka rayuwa ta fara tafiyar wa da Su sada babu daɗi koda yaushe cikin ƙunci.ƙara fahimtar rayuwa da suka yi ganin babu mai taimaka musu hakan ya sa suka koma neman na kan su suka shige kasuwa suka bazama nema dama ance zafin nema baya kawo samu to haka dai suke kalato wanda zasu saka a abaki ko bai ishe su ba koda mahaifiyar su ce kawai da Sakina za su yi farin ciki dan sun san sune mafi buƙatar kulawa yanzu.. A haka suka jin gine karatun su suka cigaba da shiga kasuwa suna yin dako da dai duk wani aikin ƙarfi,tun basu iya jurewa har takai ta kawo suna iya yin aikin su babu tsoro zuciyoyin su sun riga sun bushe da neman na kai da abun da zasu rufawa kan su asiri da mahaifiyar su da yar uwar su Abar son su. Sada da yake babba shine mai ƙoƙarin sauke nauyin gidan duk da shima Usman yana yi amma saboda ba hankalin su ɗaya ba a lokacin.Cikin ikon ubangiji Allah ya fara buɗawa Sada yana samu gwargwado har ya buɗe yar ƙaramar kwntena ta kayan wasan yara cikin hakan ya samu ya saya musu kayan amfani masu yawa tare da yan kayan abincin da zasu iya kai su yan kwanakki. Sannan ya saka Sakina makaranta tare da mayar da Usman makaranta,sai dai dukkanin su ta gwamnati ya mayar da su.Shi ya jingine ta sa a haka rayuwa ta cigaba da tafiya cike da gwagwarmaya Har Allah ya sa suka fara tsallake wani mataki na cigaba ya ƙara gyara musu gidan su kafin ma gaba ɗaya suka bar unguwar saboda shima Usman yana samu a wajen yan buge bugen sa shima take Allah ya fara buɗe ma sa.A tare suka wuce makarantar gaba da jami'a.Ita kuma Sakina Alokacin tana aji shidda cikin ikon ubangiji suka gama,suka karɓi kwalin su da suka ci gwagwarmaya a fannin business Administration dukkanin su shi suka yi.Ga kasuwan cin su komai dai dai yadda suke so.A haka rayuwa tayi ta tafiya Har Allah ya ƙara sakawa Kasuwancin na su Albarka ya faɗaɗa sosai nan ne suka yanke shawarar sayen ƙaton fili suka yi ginin da bai wuce sashe biyu ba na su wanda kowannen su zai zauna da iyalan sa sai kuma na mahaifiyar su da take tare da Sakina.Ba,a shanye shekara ba dukkanin su suka yi Aure dan babu tserewa a tsakanin su saboda yadda Mama ta sha musu kai.Sada ya auro wata bafillatana yar Borno shi ko Usman ya Auro yar garin Adamawa a lokacin dukkanin su sun haɗu ne da su a wajen yawon kasuwan cin su.Anan ƙasar mu. Shekara na zagayowa Allah ya albarka ci matar Sada ta samu namiji inda aka saka masa suna Sadam.Yaro ya taso cikin Gata da kulawa ta ko wane gefe musamman ta gefen Sakina da matar Usman yana shan kulawa sosai.Matar babu ruwan ta tana da kulawa sosai sai dai har Sadam ya girma ita bata da komai.Mama mace ce mai saurin fahimta hakan ya sa bata taɓa nuna wa sarakuwar ta ta komai ba ta san Allah ne mai bada wa Alokacin da ya so.Ana haka sai ga wani cikin a gun Matar Sada mai Suna Hajara suna kiran ta hajo haka suka yi ta renon cikin gaba ɗayan su cikin yardar Ubangiji ciki ya taso har ya kai lokacin haihuwar sa.Cikin ikon Allah tana haihuwa sai ga wani santatelelen Namiji Wanda ya kwaso kamar sakina sak yaro ya zo cikin gata ranar suna yaro ya ci sunan sa Saleh. Haka suka cigaba rainon yaron cikin kulawa.Har zuwa lokacin da yaron yayi wayau Allah bai kawo wa matar Usman mai suna Ramlat ba suna kiran ta Uwani saboda haka dangin ta ke kiran ta dan ta ci sunan mahaifiyar mahaifin ta. Ana haka sai ga wani ciki ya bayyana ga Hajo kasancewar Saleh yayi shekara ɗaya sai bata damu ba ta cire shi ta cigaba da rainon cikin ta.Lokacin haihuwar sa na yi ta haifi ɗan ta santatelele namiji mai suna Ibrahim tunda ta haifi Ibrahim kuma sai komai ya tsaya chak dama kuma a lokacin tana neman hanyar da zata dakatar.Sunyi farin ciki sosai da samun ƙaruwar haka yaro ya tashi cikin gata kamar sauran yan uwan sa.Hajo dake cike da tausayin Uwani tayi magana da Sada dan ya amince mata ta basu sadam tun da ta ga yadda suka shaƙu da Uwanin shima kasancewar yana Tausayin matar ɗan uwan na sa da ɗan uwan na sa ya amince Sadam ya koma sashen su baki ɗaya.Farin cikin Usman a wannan rana bai da adadi shida Uwani har kukan farin ciki sai da suka yi haka suka rungumi Sadam da ya fara tasawa suka fara mishi gata.A lokacin itama Sakina anyi nata bikin tana gidan ta.Inda ta Auri wani Babban ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa mai suna Aliyu Bukar mai Billions haka ne laƙanin familyn sa yake.Ya ga Sakina daɗewa ne tun a wani taro da suka zo na ganawa tsakanin manyan yan kasuwa anan gidan tare da su Sada ta zo kawo musu abun sha ne tare da Ma,aikata tun da ya ƙyalla ido ya sa a ransa har yayi yadda yayi ya samu shigowa tun da abun ba mai wahala bane sun san juna.tunda ya zo da zancen aka sanar da sakina take ta murmushi,wanda koda bata ce komai ba sun san abun da murmushin na ta yake nufi dan sun san ta da kunya hamdala suka yi cike da farin ciki sannan aka fara shirye shiryen biki ba a ɗau lokaci ba aka yi bikin aka kai Amarya cikin katafaren gidan ta dake cikin Ƙaton gidan na su dan A Bukar mai Billions babban family ne mai ji da kuɗaɗe suma ya samo asali tun da ga ka kan su ne har zuwa mahaifin su Bukar mai Billions,dan Alokacin ma sun fi su SS family yan chanji duk da suma sun tara sosai dan har sai da ya kai ko ina an gine a ƙaton filin na su anyi gini na alfarma da koda yaushe ake cikin sake gyara sa. Amarya ta shiga cikin dangin ango babu tsangwama ko ƙyara.Sai da ta share shekara biyar zuwa shidda sannan ta samu ciki inda haihuwar farko ta haifi yar ta mace ta ci suna Barirah sunan mahaifiiyar Aliyu.Kafin samuwar cikin kuwa ta fara ganin sauye sauye acikin dangin na mijin ta dan maganganu sunyi ta dawowa kunnen ta akan rashin haihuwar ta,bata ta ɓa faɗawa Aliyu ba sai dai ta sha kukan ta ita kaɗai,sannan ta kan sanar da Uwani saboda itace ta san raɗaɗin da take ji,Uwani sai dai ta rarrashe ta,dan har zuwa lokacin bata samu komai ba duk da sun yi yawo asibiti amma an nuna musu babu komai kawai Allah ne bai kawo ba sai maganukkan da ake bata da zasu iya taimakawa. Kowa yayi farin ciki da samuwar Barirah yarinya ta samu gata ta ko kowane ɓangare,cike da kulawa.Yarinya bata ko haura shekara da watanni ba sai ga wani sabon cikin wanda ya ƙara sanya zuri'ar Bukar mai Billions farin ciki dan kamar tare ma suka cigaba da rainon cikin Sakina ta samu farin ciki matuƙa ita kan ta kuma ta gode Allah da Ni,imar da yayi mata dan cikin yardar Ubangiji duk wani da ya fara mata magana mara daɗi da barin gefen ta sun dawo Gata da son mutane.Aliyu yayi farin ciki sosai haka ma Mama tayi farin ciki ita da Su Sada.Lokacin haihuwa nayi Aka kwashe ta aka yi asibiti da ita saboda jaririn da yaƙi fitowa, dan wancan haihuwar gida ce,da kan ta ta haihu kuma bata wahala ba kamar wannan. Ana zuwa a asibiti cikin yardar Ubangiji ta haifi yar ta mace kyakkyawa mai kama da ita sak yarinya mai shiga rai kowa ya gan ta sai yayi Masha ALLAH.Gaba ɗayan familyn biyu sun tsincin kan su cikin farin ciki.Yarinya an mata zanen suna da A'isha taci sunan mama mahaifiyar su sada.Sai dai wani irin tashin hankali ne ya same su suna shirin barin asibiti sai ga ɓallewar jini ta samu Sakina.Cike da tashin hankali kowannen su yake su kan su likitotan ma dan sun kasa tsayar dashi gashi basu samo silar shi ba.Da ƙyar suka gama binciken suka tsayar da jinin ta da rasa sosai dan idan har ba,a yi gaggawar saka mata wani ba zata iya rasa ran ta.Cikin ikon ubangiji aka sanar da su an samu tsaida jinin da doguwar naƙuda ta jawo mata zubar shi. A Bukar dake zaune ya haɗa zufa farin ciki ne ya mamaye sa shida su Sada da suke zaune a wajen jugum mama ma da ƙyar suka samu ta yarda aka mayar da ita gida.Haka ma Hajiya Barirah mahaifiyar su A bukar.Jini aka saka mata da aka ɗiba ga mijin ta da ɗan uwan ta Usman dan na su ne iri ɗaya.Sai dai duk da haka abin da aka gujewa shine ya auku idan lokaci yayi babu makawa babu maɓoya sai an tafi dan ba,a fi mintuna goma da saka mata jinin ba sai ta fara fisge fisge. A bukar da ke waje dafe da kai ne hawaye suka silalo masa saboda kalmar da ta faɗa masa yanzu kafin fitowar sa wajen na ta da ta kasa barin tunanin sa. " Kamin alƙawari idan na bar duniya zaka bawa Yaya Usman riƙon Barirah da A'isha,yanzu ko wata rana zuwa lokacin girman su " idanu ya zuba mata cike da faɗuwar gaba yana niyyar yin magana kawai ya lura tayi bacci kuma da alama ya mata daɗi.Hakan ya sa ya baro ɗakin bisa umurnin likita. Sai dai kwatsam yanzu Kunnuwan sa suka jiye masa abun da Likitan da ya baro wanda yake shine Babba a team da suke kula da ita yana furta " Allah yayi wa Sakina Saleh Rasuwa " inda ya sanar musu da samun tsinkau tsinkau ɗin da yayi ajalin ta tare da basu haƙuri. Riff haka suka ji faɗuwar a bu a ƙasa bakowa bane face A bukar.Kan shi suka yi cike da koke koke kowanne su zuciya a ruɗe wasun su ma basu yadda da rashin na Sakina ba...✍️ ALLAH YA JIƘAN WAYEN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA.😭😭 Wanda bai gane bayanin ba ya samu rufaida yogurt ya sha mai sanyi zai fahimci bayanin🚶🚶🤭😅Ni kaina wani wajen ba fahimtar sa nake yi 😬😁 Dan Allah,kuyi,sharing da comment shine ƙarfin rubutun mu. 🙏 A Wasu lokutan shike sagewa marubuci gwiwa ya kasa iya baku page a kullum. Wannan littafi na kuɗi ne. Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya.. Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* free pages👌 P..0️⃣9️⃣ >>>>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>>>> *CONTACT DIS LINE👉08069059746 FOR ADVERT.* *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* Channel link https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y Posting room link https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* 🍃🍃🍃 Haka aka kwashi A bukar sai gadon asibiti. Har aka yi komai aka rufe margayiya Sakina bai farka ba sai dai Yan uwan ta ne suka yi jagora aka rufe yar uwar su. A wannan rana wannan ahali biyu sun shiga tashin hankali matuƙa dan har zuwa lokacin A bukar bai farfaɗo ba.Haka ma jikin Mama ya tashi ita ma sai da ta ga likita dan Bpn ta ya tashi wanda ya same ta tun rasuwar mijin ta Saleh. Su Sada sunyi kuka matuƙa haka ma A Bukar da ya farfaɗo a kwana na biyu yayi kuka kamar zai rasa ransa na rashin mata mace mai haƙuri da alkunya,da Biyayya wadda yake ganin ba zai taɓa samun maye gurbin ta ba a gare sa. Bayan anyi zaman makoki Bukar ya sanar da Wasiyyar da Sakina ta bar masa duk da bai ce zai cika mata ba amma ya ji a zuciyar sa idan wannan zai saka ta farin ciki dole sai ya aiwatar ya cika mata burin ta.Dan ya san wannan shine burin ta tun farko ta bawa ɗan uwan na ta ya guda idan su samu rabo mai yawa sai gashi yanzu ta roƙi a ba su duka. Bai nuna komai ba haka duk dangin suka amince mahaifiyar sa ma ce ta so ta hana wanda aka shirya da ƙyar idan sun yi wata ɗaya zuwa biyu za,a mayar da su wajen su ɗin. Farin ciki kuwa Familyn Saleh sunyi shi kuka Uwani da Usman Saleh suka zauna suka ɓarza cike da kewa da Tausayin yar uwar su da zafin rabuwa da ita dan mace ce mai ƙima da daraja alkunya haƙuri.Haka Sadam da su Saleh, Ibrahim sun yi kuka matuƙa saboda shaƙuwar da ke tsakanin su da ƙanwar mahaifan ta su. A haka yara suka taso cikin Gata da kulawa ta kowane ɓangare suna cika wata ɗaya kamar yadda aka tsara aka damƙa su hannun Uwani kamar yadda mahaifiyar su ta nema Uwani itace ta cigaba da shayar da Aisha da suke kira Maamaaa dama chan madara a ke bata.Barirah kuwa take ta sake dan bata fahimci komai ba ko chan baya koken ne da ta ga kowa nayi sai neman mahaifiyar ta ya sa ta kuka amma ba dan ta fahimci akwai wani abu ba,sai dai duk dare sai tayi kukan mahaifiyar ta.A haka har suka share watanni ta ƙarasa sakewa.Aka cigaba da rainon su a gidan Usman Saleh wanda tare da Sadam ake yiwa Maaamah komai saboda ƙaunar da yake yiwa jinjirar.Haka Barirah tana matuƙar son yar uwanta.A haka rayuwa ta cigaba da tafiya yara suna ta girma musamman ma Maammaa da take ta sowa itama gwanin burge wa kowa na ƙaunar su ita da Barirah sai dai tafi Barirah samun kulawa sosai saboda tafi ta saurin shiga rai.Da kuma sabo da sakewa ga mutane da faranfaran.Sunyi karatu na Arabia da boko a ƙarƙashin mahaifin Su da suke mugun so da ƙauna tun bayan fahimtar shine asalin mahaifin na su kasancewar ba,a bar shi baya ba gurin kula da ya'yan na sa abun son sa haka ma duka dangin na sa.Dan haka Suka ta so cikin gata basu san wani abu shi maraici ba.Kuma Basu taɓa nunawa Uwani da Usman Saleh basu ne suka haife su ba suna musu kara matuƙa musamman maama bata taɓa zancen mahaifiyar ta gaban Uwani saboda tana da fahimta da wayau,tana fahimtar yanayin da Uwani take shiga suka nuna damuwar rashin mahaifiyar su,suna kiran Uwani da Ummu,kamar yadda su Sadam ke kiran ta.Haka suka cigaba da rayuwa cikin yan uwan su har girman su. Shekaru sun shuɗe dan lokacin Sadam ya gama karatun sa da ya yo akan kasuwan ci.Ita ma kuma Barirah ta kammala Tata makarantar a secondry. Mama da Sada suka yanke hukuncin haɗa Auren zumunci a tsakanin Sadam da Barirah tare da shawarar mahaifin su dan dama su matan su basa karatu mai zurfi dan ko sakina da ƙyar suka barta tayi diploma a economics.... Lokaci mai jaaa idan akwai rayuwa a yanzu Saleh Sada ne mai tarin dukiyar da ko shi kan sa bai san kan ta ba,A yanzu yana da mata uku ta farko itace Hajiya Asma'u suna kiran ta da (momy)tana da yaaa ƙwaya ɗaya itace Hamrah,mai shekara goma sha ɗaya da rabi tana a ji ɗaya a junior sec,Dan su Reena suna gaban ta dama kaɗan dan dama sun girme mata kaɗan. Sai mai bi mata Hajiya Sa,ada ita bata samu rabo ba har yanzu.Suna kiran ta Mamy Sai kuma Hajiya Barirah ita tana da ya'ya uku na farko shine Bilal ma,aikacin soji ne yana matsayin Captain shekarar sa Ishirin da biyar sai yan biyu Alina da Sarina,suna da shekara goma sha uku suna aji uku a junior sec sch,Ibrahim Sada kuwa yana da Mata biyu ta farko Sunan ta Maryam Suna kiran ta (Hajiya)tana da ya'ya uku Maza,na farko shine Samir,yana aiki a Custom service,yana da shekara ashirin da huɗu,Sai na biyu Abdul jabbar,yana da shakara sha tara yana Ug II I a Wata Babbar University dake nan jahar su wadda ake zube ma Naira,sai Ayman mai shekara goma sha biyar yana aji Biyu ne a University wadda Abdul jabbar yake yi.Sai matar sa ta biyu sunan ta Ramlat suna kiran ta Momcy tana da ya'ya biyu Junaid,mai shekara sha tara yana aji biyu a University tare da su Abduljabbar suna mataki ɗaya sai dai kowa field ɗin sa daban.Sai Amina (Ninah) mai shekara sha uku suna matakin karatu ɗaya da su Reena. 🍃🍃🍃 *MU KOMA LABARI.* Suna gama gaisawa da Junaid ya matsa kusa da tsohon yana rusunar da kan sa ƙasa yana cewa " kaina a ƙasa Sir S S ".Saboda haka suke kiran sa da Sir gaba ɗaya jikokin na sa. Murmushi Yayi yana jan kunnen BILAL yana furta " wane SS ɗin ne uban ka ko ni " "Ouuch Sir pls " Ya furta yana ɓata fuskar shi. Murmushi yayi yana cewa " Laifi muka yi ne da za,a shigo aka sa zuwa wajen mu ka san yanzu ƙarfe nawa ne,ohh kana sane ma". Ya furta jin yana bashi amsa da 4:30pm. Sakin shi yayi yana riƙe hannun sa na dama yana furta " Ya aikin " ? " Alhamdulillah Sir ya tsufa ".? "Tsufa ai sai ku BILAL mu yanzu muke Tashe na bai fi naka ƙwari ba ne " Dariya Bilal yayi yana furta " Haka ne Sir ai yanzu kake tashe ma " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntuwar dariya. Dai dai isowar su Abdul Jabbar da Ayman a wajen suma fuska cike da farin ciki suka rungume Bilal ɗin suna haɗa baki wajen gaishe sa.Shima cike da murmushi ya amsa musu yana musu yan tambayoyi game da karatu suna amsa masa gaba suka yi bayan sun ɗan yi barkwanci tare da gaida Sir. Har Sashen sa ya kai shi anan ya tarar da Hajo zaune tare da mama da tsufa ya mayar da ita kamar yarinya komai sai anyi mata Uwani da ita suna ƙoƙari akan su duk da yadda su kan su tsufan ya taso musu amma suna ƙokarin faran ta ran surukar ta su. "Ja'iri sai yanzu ka ga damar shigowa ko,ai ko Badan mu ba kana shigowa ka ga Uwar ka " Tayi zancen tana Murmushi tana nuna Mama da ke tauna goron da Hajo take daka mata a wani ƙaramin dutse mai kyau guda biyu wanda aka sawo mata shi tun da ga saudia kuma idan ka ji kuɗin sa zaka jima kana mamaki,shi an yi shine kawai saboda tsofaffi irin su da ba komai suke iya taunawa ba saboda yadda haƙoran su suka yi taushi,suka koma kamar dasashi irin dai na yaro ƙarami. Ƙasa yakai yana murmushi tare da riƙo hannun Mama yana furta " Tsohuwa mai ran ƙarfe,Allah ya ja da rai da nisan kwana,ya ƙarfin jikin ". Fuskar shi ta shaafa tana furta " Ɗan ga ne,ka dawo me ka yo mini tsara ba,ya aikin ka ". Ta jero zantukan da sai ka kwantar da hankali zaka ji fitar su a bakin ta. "Ina nan Mama".Yayi zancen yana riƙo hannun ta. " Me ke kika so dan ban siyo komai ba,irin na ki keda Hajo ma,da Sir " Da ƙuwa Hajo ta sakar masa tana furta " Ai mu bamu yi wannan tsufan ba,baka gan mu garass ba ko goro Bama ci ". Ta kai ƙarshen zancen tana tauna goron da ke hannun ta wanda bata daɗe da fara cin sa ba. Dariya yayi yana kallon Sir da ke zaune yana kallon su yana murmushi musamman mahaifiyar sa da ke ta mamular bakin ta tana tauna goron da Hajo ta ke daka mata tana Murmushi tana sauraron abun da BILAL yake faɗa. Itama Hajo murmushin ta saki. " Ina son kilishi Samiru baya nan dama shi yake sayo mini shi "." Bani son na nan gidan bai min daɗi " Ta kai ƙarshen zancen tana ƙara damƙe hannun sa. " Kilishi kike so Mama,gashi ance likita ya hana ki cin jan nama Ba zaki haƙura ba ". " A'ah nidai ka sawo mini Likita bai isa ya kashe ni ba,sai lokaci na yayi,Koh Sada ". Kai Sir ya girgiza kawai saboda sun yi sunyi su hana ta abun ya gagara saboda tana fama da sugar likitota suka yi suggesting tabar cin nama jaa. Ga su da naman kowane iri a gida har kilishin da sabo da tsoho kullum sai masu kula da Sashen nama sun yi shi dan haka akwai sabo akwai tsoho.Amma bata son shi saboda rigima sai na waje. " Sir me ya sa kuke barin ta,lafiyar ta fa na iya ragwanta ". BILAL ya yi zancen yana kallon Sir . Numfashi Sir ya sauke shima cike da Muryan tsufa ya furta " Ya zamuyi har kuka take sakawa sauƙin ta ma shi kaɗai take nema,dan ta san Samir na sayo mata shi ya sa da ya zo sai ta Masa zancen ".Sai ya sayo mata a sace tun bamu gane ba har muka gane aka masa faɗa amma da ta buƙata sai kowa ranshi ya jagule sai ta yi ta kuka,gashi bata cin na gida ko bata aka yi ta san ba wanda take ci bane ". Numfashi BILAL ya sauke kafin ya furta " Mama zan nemo Miki shi kin ji ki kwantar da hankalin ki,dan saboda tana jin abun da yake faɗa har ta fara hawaye saboda bata da wuyar kuka. " Yawwa yawwa nagode Bulal Allah ya jiƙan magabata ". Ta kai ƙarshen zancen kuka na sake mata. Jikin su ne yayi sanyi suma babu ma kamar BILAL saboda wani giɓi ne ta soso masa da yake zagaye da zuciyar sa. Miƙewa yayi ya musu sallama bayan ya rarrashe ta tare da ƙara tabbatar mata da tabbacin kawo mata kilishin na ta. Sashen Uwani ya fara shiga bayan fitowar sa daga part ɗin Hajo cike da farin ciki ta tarbi Jikan ta tana tsokanar sa bayan sun gaisa. " Ango na na kaina,Allah ya sa babu ƙari da gani,idan kuma ka ƙara mini na kashe baka damu ". Murmushi yayi yana cewa " Nifa kin mini tsufa Uwani yawwa,ina Ni ina tsohuwa ai Ni na yarinya ne ". Daƙuwa farin Dattijon da ya fito yana murmushi ya sakar masa yana cewa " Ja'iri ai kar ka ƙara kira mini Mata da Tsohuwa dan yarinya ce shakaf haka nake nake kallon ta ".Ya kai ƙarshen zancen yana zama kusa da BILAL ɗin. Dariya BILAL yayi kafin ya ce " naga alama ai,Ya tsufa " ? Dariya yayi kafin ya furta " Tsufa gashi nan muna jaa yau ma ban samu na fita sallah ba ƙafafun suka tasar mini da ƙyar na samu yanzu na motsa yanzu ma da zan fito ". " Ayyah Sannu Dada " Dan haka suke ce masa. " Allah ya ƙara afuwa ya sa kaffaran jiki ne,ashe shi ya sa bangan ka ba a masallaci ina ta duban ka ". " Amin " " Eh Ai sai yanzu shima Yaya muka yi magana dashi ya kira ni bai ganni gurin Sallah ba ". Fira suka taɓa irin ta ƙauna tsakanin Kaka da kika kafin ya musu Sallama ya fice. Sashen Hajiya ya nufa kai tsaye bayan fitowar sa,Da sallama ɗauke a bakin sa ya shige haɗaɗɗen falon da yake ta tashin ƙamshi. Masu aiki ne kawai suke ta kai kawo a falon ko ina tsit. Har ƙasa mai aikin ta da ke kula da tarbon baƙi tayi,kuma wadda bata ma shamaki da komai na ta kasancewar bata da mace sai ta sake mata.Ruwa aka aje masa masu sanyi da lemu sannan ta gayar da shi. Sama tayi ta kira uwar ɗakin ta ta. Bayan fitowar ta da yan mintuna sai gata ta fito.Babbar mace ce mai ji da wanka ta fito. Tun daga chan take sakin murmushi Ganin wanda ke zaune a wajen kasancewar ta samu labarin Dawowar sa ga su Abdul Jabbar kafin su wuce makarantar islamiyya. Ƙasa ya rusuna shima cike da murmushi ya gaida ita. " Ya aiki ya kuka baro legos ɗin ". " Lafiya lau Hajiya,na same ku lafiya ". " Muna lafiya BILAL ai shekaran jiya ma da muka yi magana da ɗan uwan ka yace kana hanya zaka zo ashe ko ka samu shigowa ". Murmushi ya saki a hankali kafin ya ce " eh mun ɗan yi maganar kwana biyu,shima aikin na sa yana ɗaukar zafi yace sai a hankali ". Murmushi ta saki kafin ta furta " Allah ya taimake ku ya bada nasara ". " Amin " ya amsa cike da jin daɗin Addu,ar ta ta. Dan Hajiya mecece mai karamci ga kula ga na ta da wanda ba na ta ba ma. Sallama ya yi mata ya fice.Bayan sun ɗan taɓa fira kaɗan da ta shafi ta aikin su. Yana fita wani sashen ya shiga kamar dai wanchan sai dai funitures ne suka bambanta da kuma yanayin kalar ƙamshin da kowacce take da shi. Zaune ya same ta cikin falon tana kallon wani series da murmushi ta tarbe sa inda take ta saka aka cika masa gaban sa duk da ya ƙoshi da yake sanar mata. Cike da girmamawa suka gaisa. Suna fira cike da kulawa " Ai ɗazu ninah take faɗa mini sun koma yin halin a hanya ,ashe ma kana kusa,nidai nace Allah ya shirya muna su tace Reena haka ta dawo kacha kacha da ita,gaskiya Barirah na haƙuri Allah ya ƙara shirya muna ". Gyaran murya yayi yana son katse zancen sai gashi ta katse abun ta ta hanyar furta " Ai Junaid ya sanar da ni ka dawo ". Kai ya jinjina mata yana Murmushi tare da miƙewa yayi mata sallama. Ajiyar zuciya kawai ya sauke yana jin Tausayin mahaifiyar sa dama wannan shine abun da take gudu yadda kowa yake buɗe baki yayi zancen yanayin su Reena ɗin. Sashen momy ya fara shiga suka gaisa cike da kulawa yayi mata sallama. Itama take sanar mishi ashe Su Reena faɗa suka cigaba da yi a titi abun har yayi girma dambe a titi dan Hamrah ta faɗa mata lallai dole ya ƙara tayar musu tsaye kar abun ya kai inda ba,a so.Shi dai bai ce mata komai ba sai ma in sha ALLAH da yake faɗa na zai ƙara saka musu ido. Sannan ya shiga sashen Momcy itama dai sai da ya zauna zaman jiran ta dama ya saba da hakan kuma bai taɓa damuwa ba saboda halin ta ne idan ka zo wajen ta sai ka jira ko kai waye. Ya daɗe yana duba a gogon hannunsa saboda yana da abin yi kafin ya ji takon ta cike da ƙasaita ta fito tana bin shi da kallo. Zama tayi tana ɗaura ƙada ɗaya kan ɗaya cike da izza irin ta manyan mata ta furta " Ashe an dawo ". Ƙasa ya durƙusa ya gayar da ita cike da kulawa.Amsa wa tayi tana tambayar sa ya aiki shiru falon yayi babu wanda ya ƙara cewa komai tun Gaisawar da suka gama suna gamawa ya miƙe ya yi mata sallama. Bin shi tayi da kallo kafin ta galla ma bayan sa Harara tana jan mugun tsaki tana furta " Dangin jaraba " . Mai aikin ta ta ƙwalawa kira ta kawo mata abun taɓawa hakan ya sa da sauri saboda ta san halin ta ta kawo mata su ta ajiye mata.Dama fruit ɗin sun zama ready tun ɗazu ta yi cutting na su yadda take so. 🍃🍃🍃 A ɓangaren shatou kuwa nan bacci ya kwashe ta bayan ta gama cin abin ci,sai dai a cikin bacccin harda mafarkin wanda ya rubuta sunan na ta a allo ta yi sai dai bata ga fuskar sa ba ta dai gansa yana rubutun.Dan haka tana farkawa babu abun da ta fara sai tunanin yana yin shigar sa da ta gani sai dai ta kasa tunawa hakan ya sa ta miƙe ta fito wajen anan ta isko baffa na ya dawo shi ko Bibu yayi makarantar Allon.Buta ta fara suntuma fahimtar ba,a tada ita tayi Sallah ba.Dan Baffa na ya hana saboda ta samu sauƙin ciwon kan da tace saboda Inna ni ta faɗa masa duk abun da ke faruwa.Sai dai duk da ya taɓa jin sunan bakin Zaidu bai nuna ya taɓa jin sunan ba a bakin wani saboda ya san halin yar ta sa. Tana gama Sallah la,asar ta miƙe ta yo waje tana furta " Inna ni,Ni me ya sa yau baki tashe ni ba,gashi na rasa makaranta,kuma nayi lattin Sallah " Saboda duk rashin jin ta tana son karatu gwargwado. " Ga Baffa na nan shi zaki tuhuma bani ba " Inna ni tayi Furucin tana kallon ta. Baki ta cunno tana furta " ai Baffa na zaka min ƙari ko ". Kai ya jinjina mata cike da murmushi. " Baffa na gobe ina zuwa Farauta ". Ta ƙara furtawa. " Keda wa "? Cewar Baffa na saboda ya san gobe akwai makaranta. " Da kai " Ta bashi amsa tana Murmushi. Kai ya girgiza cikin alamar rashin wasa ya furta " A'a makaranta zaki je Shatoun Baffa na " Shiri tayi bata ƙara cewa komai ba. Murmushi Inna ni tayi kawai tana girgiza kai bata shiga cikin zancen ba ganin yadda yayi Furucin in serious wanda dole ta natsu ta ƙi tada maganar.Yayi hakan ne dan ya san cewa idan ba haka yayi mata ba sai ta addabe su ƙila ma ta tafi ba,a sani ba.Ko ta same shi chan daga makaranta. Ficewa Baffa na yayi ya musu sallama yayi majalisar su. Azkar ɗin ta Inna ni ta sanya ta ɗaukowa saboda tana son ta ƙara dagewa da addu,in kariya. Ɗaukowa tayi fuskar nan a cushe ta ji Haushin hana ta da Baffa na yayi kuma bata ga alamar wasa ba bare ta fice dan kan ta.Ga shi yanzu abinda aka mata Makarantar boko ya dawo mata cikin ikon Allah mafarkin da tayi na kalar kayan wanda yayi rubutun ya dawo mata a ido.Dan haka yau taci alwashin sai ta fita ko Allah zai sa ta samu mai irin shigar da kalar kayan mugun da ya disga ta cikin makaranta. Hmmmmm Allah ya baki nasara ta hannun damar Baffa na 🤭🤭😂😂Lallai akwai case yau muddin ta gano mai kayan nan yau sai mun yi kallo. Ina masoyan SHATOU ku kawo a gaji kar ta janyo wata rigimar 🚶🚶💃🤣 Wannan littafi na kuɗi ne. Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya.. Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* free pages👌 P..1️⃣0️⃣ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting room link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* 👅👀👂Ka tsarkake wayen nan ɗan uwa. Na farko_harshen ka.(Magana mara daɗi,mai iya jefa ka haɗari ) Na biyu _Ganin ka.(Daga haramun) Kunnuwan ka _ Jin ka.(Daga Haramun ) Idan ka kiyaye waɗan nan kaga ma samun natsuwa ta duniya ɗan uwa. 🌻🌱🌻🌱🌻🌱🌻 A ɓangaren su LINA kuwa tun da Ya'u ya hau titi babu wanda ya cewa ɗan uwan sa ci kan ka tsakanin ta da su Ninah ɗin.Har suka sauka gaban ƙatuwar gate ta makarantar kai da ganin ta kasan Naira ce ke aikin ta dan haka malammai ma suke iya yin su saboda yadda iyayen yara suke zube kuɗade makudai dan samun ingantaccen ilmin Arabia na ya'yan su kamar na boko kamar dai Familyn SS da suke da wannan babu gefen da suka saki dan akwai wayen da duniyar kaɗai suka saka gaba. Firfitowa suka yi suka shige cikin makarantar kasancewar basu yi latti ba kai tsaye kowaccen su tayi na ta aji dan an rabasu gaba ɗayan su waccan an kai ta Faslul A'isha R.A wacchan Usman R.A kowacce da nata sai dai duk a bu ɗaya ake koya musu. Zaman ta ke da wuya wata ƙawar ta da halin su ya zo kamar ɗaya mai suna Anisa ce ta zo da sauri kasancewar ta ga shigowar su tana wani ajin tana faɗa da wani yaro da ya buge ƙanwar ta.Anisa da Lina kawancen su ya fara ne lokacin da kowaccen su ta gano kanwar kasa ce ita,dan farkon zuwan su LINA itace kaɗai take nuna rashin tsoron ta har dai suka saba,kuma itace ta fi kowa sake mata saboda yadda kowa yake shayin ta saboda agaban su ranar da aka kawo su tayi dambe da REENA ta daddaki kayan ta.Shine silar haɗa kan su amma duk da haka ko yanzu ta haɗa su sai an raba su kare jini biri jini suke yi. " Ke lafiya nagan ki kamar a tsorace " LINA tayi zancen tana kallon ta. " Isah na dako,da ya daki Rahima ". Ta bata amsa kai tsaye tana cigaba da zare ido. " To shi ko zare idon na me ye " ?Ta ƙara yin zancen tana Hararar ta tana ciro qur'anin ta a jaka. " Wallahi ina kai shi ƙasa na fara nusa naji tsitt ashe Ustaz Babba na tsaye yana kallon na " Shine duk ajin suka natsu bayan ganin tsayuwar sa. " To sai me dan ustaz Babba ya ganki,ba bulala ce ba kawai sai ki tsaya a Miki ki tashi ki kakkaɓe hannun ki da hijab ". LINA tayi zancen tana buɗe shafin da zata bada yau. " Hmmm ba zaki gane ba bane ustaz Babba ya fi kowa iya Bulala a makarantar nan,kin zata irin dukan su Uztaz ne da kike kakkaɓe ma hijab ". " Shi kuma Isah sai yayi bayani bari a tashi,haka kawai zai kama ta ya daka saboda yana shugaba ". LINA tayi Furucin ba tare da ta tan ka ma Anisa ba. Shiru suka yi tana cigaba da karatun ta cikin sauti mara ƙara dan duk abunta ta wannan fannin akwai natsuwa da mai da hankali,dan ta tsani ta je karatu tayi ta kure a na mata gyara.Dan duk littafin ta na karɓan hadda jaidan ne ke tashi a rubuce. Kasancewar Ustaz na ajin na su ya zo ya sa suka natsu karɓan hadda ya fara a hankali ta kowane ɗalibi kuma gwargwado ajin kowannen su yana ƙokari. Su LINA ne seat na baya a sashen mata kuma itace ta ƙarshen seat itace ta ƙarshe a karɓa.Cikin ƙwarewa da iyawar da Allah ya bata ta yi ta tayi ta rera karatun ta a cikin suratul kahfi ustaz na su sai gyaɗa kai yake yi yana jinjina kai saboda yadda take tafiya babu wani kuskure. Haka har ta gama ta miƙe bayan an mata kabbara kamar yadda aka yiwa kowannen su. Ƙari aka musu gaba ɗaya saboda tare suke tafiya gaba ɗaya ajin. Sallamar Ustaz Babba ce ta sanya ƙirjin Anisa bugawa da ƙarfi kafin ta lafe a kan kujerar su tana sauke niƙab ɗin ta. Gaisawa suka yi da Ustaz.Kasancewar Duka malamman na su Suna kiransu da ustaz Babban da suka ƙara na shugaban makaranta ne shine banbancin.Suna banbanta wa ne kuma a lokacin da magana ta shigo sai su faɗi ustaz wane da da sunan sa. Da Larabci yayi wa Ustaz na su bayanin komai harda sunan Anisa kasancewar kowannen su yana jin Yaren sai suka fara waigen Anisa da take zaune cikin ta ya ɗuri ruwa kamar kace ƙyat ta yi gaba saboda a kunnen ta Ustaz Babba ya faɗi komai. Kallon ta Ustaz na su yayi kafin ya ce " ta'al ta'al Anisa " Jikin ta ne ya fara rawa dan ta san yau sai ta ci na jakuna ganin yadda ran ustaz na su ran shi ya ɓaci ganin sa duk irin ƙoƙarin da yake kan su ace wai ɗalibar sa ce dambe da maza,inda ma Isah ƙarami ne amma da kallon ta kasan ya girme mata koda shekara biyu ne. Ta sowa tayi tana jin kamar tafiyar gaban Allo ta ƙara tsawo. Niƙab ɗin ta Ustaz ya sa ta ɗage wanda idanun ta sun cika da hawaye har sun fara zuba,kafin ya fara mata faɗa dai dai lokacin da bulalar da Ustaz Babba ya aika a ɗauko masa ta iso.Saboda Har Isah yayi wa hukunci itace ya bari ta samu damar karɓan hadda. Sai da ya gama faɗan sa Sannan Ustaz Babba ya yi mata bulala Goma a ƙafafun ta.Kowa sai da ya tausaya mata kuka ta ke tayi amma hakan bai sa Ustaz Babba ya ƙyale ta ba. LINA ta tausaya mata matuƙa dan haka ta sha alwashin sai ta yiwa Isah bugun wahala dan zasu yi same age dashi,Wanda ko nan gaba aka ce ya taɓa wani ba zai ƙara ba. Da ƙyar ta rarrashe ta tana jin zafin abun da aka yiwa ƙawar Tata.Duk da bugun da aka yiwa Anisa bai sa LINA jin tsoron aiwatar da wani a bu dan Anisa da ƙyar ta iya taka ƙafafun ta sunyi jaaa sosai dan sai ka cire socks. Ana tashi Ya'u ya zo ɗaukar su,tare da Anisa da ƙanwar ta suka wuce ganin ba,a zo ɗaukar su da wuri ba gashi sai kuka take yi,hakan ya sa LINA shigar da ita tasu su sauke su gidan su sannan su wuce na su. Har gida suka ajiye Anisa tare da yiwa Maman su bayani sai dai mahaifiyar su Anisa faɗa tayi ta mata na dambe da maza da ta fara.Su dai su LINA dama ita da REENA suka shiga da ita,Sallama suka yi mata. Koda suka fito suka shiga Mota Ninah sai faɗan an bar su zaune a mota take yi su sun gaji har da cewa Ya'u ya tafiyar sa. Sai dai ya ƙi saboda ya san inda rigimar zata ƙare kan sa. Babu wanda ya tanka mata cikin su sai dai LINA da ta yi kamar bata ji ta ba ta ce " Ke bafa shirun kura ya zamo tsoro bane,wallahi yanzu sai na lallasaki gurin nan,Uban wa zaki ɗagawa murya mtsww ". "Ke ɗin ko kema kin zata tsoron ki ake ji da da yan zu ba ɗaya bace wallahi sai dai muci uban juna ".Cewar Ninah. " Uban wa kike zagi " ? LINA ta yi Furucin tana ƙoƙarin baro gaban motar da take. Ya'u ne yayi parking motar yana cewa " Dan Allah Hajiya ALINA Kiyi haƙuri kinji ku bari nidai na kai ku gida lafiya,ku tausaya wa abinci na yanzu idan wani ya taɓa wani ya ji mashi ciwo cewa za,ayi laifi na ne da ban raba ku ba,dan Allah kiyi haƙuri,REENA ki bata baki ". Hararar sa tayi tana jan ƙyafci REENA da ta buɗa bakin ta tana furta " Kefa LINA saurin ɗaukar zafi gare ki ". " Rana ce " LINA ta bata amsa tana Hararar ta " kuma wallahi kika matsa mini sai na haɗe ku duka na ci ƙaniyar ku ".Ta ƙara furta wa REENA Hararar ta kawai tayi tana jan mugun tsaki kafin ta ce baki iyawa wallahi. LINA saboda kawai ya'u da ya roƙe ta ya sa ta share ta da sai ta yiwa bakin nan aiki ta cika sa da jini. Shiru motar ta ɗauka babu wanda ya ƙara furta komai itadai Hamrah shiru take saboda tsoro gare ta ta san halin LINA ƙwarai bata manta yadda ta sha wahalar ta chan da bata san halin ta ba. Yana dai dai ta parking ta fito tare da wartar jakar ta.Koda ta shiga ta tarar da su Ummah da BILAL zaune a falon sai kuma Hamida yar wajen Ƙanen su Ummah.Wadda ta girme ma su LINA sosai dan ita budurwa ce duk da bata cika irin cikar nan ba.Amma a shekaru zata yi shekara sha Shida. Duka da ido suka bita Hamida dake kiran sunan ta shiru tayi dan ko juyowa bata yi ba duk da ta gane Muryan ta duk da bata lura da ita ba kan ta sama yake. Kai Kawai BILAL ya girgiza kafin ya ce " Ummah kin gani ko ". Numfashi ummah ta sauke kafin ta kalli Hamida da tayi shiru sannan ta furta " Hamida kin san halin mutuniyar taki sai ahankali ƙila wani ya taɓa ta awaje tun da kina nan har an jima zata sauko ". Kai Hamida ta gyaɗa tana sakin murmushi kafin suka cigaba da taɓa fira rabi duk ta jikin kakan su A bukar ce da yake ɗan fama da jiki kwana biyu dan ita Ummah bata ma sani ba sai yanzu a bakin Hamida dan yace kar a faɗa ma kowa ba wani ciwo bane tsufa ne kawai.Dan dama baya da Isasshiyar lafiya abubuwa biyu sun ƙara Raunata sa ga tsufa. Shigowar REENA ce ta sanya su kallon ta cike da murmushi kamar yadda fuskar ta take washe. " Oyoyo yaya Hamida,shekaran jiya ma sai da nayi wa LINA maganar muje muga Baban Billions amma tace mu bari sai week end muje mu yi shi chan ". Murmushi Hamida tayi fuskar ta washe itama kafin ta furta " ai nayi fushi gashi ni na zo da kai na duk da haka ". Cike da shagwaɓa REENA tace" Uhmm karki yi fushi Yaya Hamida ni yanzu ma idan Ummah ta bar ni sai muje tare na ga su Ammah ". '' To naji yanzu dai je ki cire uniforms ɗin ,kizo muyi fira " . Ummah murmushi tayi haka ma BILAL "Ummah Barka da wuni,yaya Barka da wuni"Ta furta tana sakin murmushi. Jin " BILAL na furta " Mu ba,a gan mu bane ". Da sauri ta wuce bayan duk sun amsa har ta kusa take wa upstairs zuwa bedroom ɗin ta saboda ta ga yanayin yar uwar ta. Ta san tsafff zata jan ta rigima su yi ta faɗa ta jiyo Muryan UMMAH na tambayar ta me ya sa LINA ta shigo kamar ran ta ɓace dawowa tayi da baya tana tsayuwa dai dai ta zayyane duk abinda ya faru. Kai kawai su Ummah suka girgiza kafin Ummah tace " tafiyar ki bedroom naki barta kinji na san yadda take jin zafin chan tsafff zata lallasa mini ke,ohh na man ta ya yan ku na kusa ". Ta kai ƙarshen zancen tana sakin guntun murmushi.BILAL dai bai ce komai ba kuma babu wata alamar ko damuwa akan fuskar sa ta sa ko ya ji abun da ake faɗa amma yaji komai duk da wayar sa yake taɓawa. " Wai Ummah har yanzu LINA bata daina rigimar nan ba,naga kwana biyu an samu sauƙi dan ko chan suka je ba sa yi ashe halin na nan ".Hamida tayi zancen cike da damuwa. Cike da damuwa Ummah ta ce " Lamarin LINA sai Addu'a Hamida haka take kwanan nan abun ya dawo,addu'a kaɗai zamu cigaba da yi musu ita kaɗai ce abun da ke shiryar wa,duka ko zagi ba ya kawo sauƙin rashin ji face hinjirar wa da yake yi, Shi ya sa nake cewa Soja ya daina dakar mini yaaa". Kiraye kirayen Sallah ne ya dakatar da ita daga abun da take son furtawa tana furta "Alhamdulillah" BILAL miƙewa yayi cike da natsuwa yayi wa Ummah Sallama yayi ficewar sa masallaci dan gabatar da Sallah magriba akan lokacin ta. Bayan gama Sallolin kuwa Falon dukkanin su suka dawo har LINA da Hamida ta fito da ita da ƙyar da rarrashi dan suna ɗan sawa da ita wadda basu shiri itace yayar ta Samira. Shiru tayi suna ta fira amma ta ƙi yin magana ta haɗe fuska waje ɗaya har aka yi Sallah isha'i suka ɗaga bata saka bakin ta ga firar ta su ba. Bilal bai dawo ba sai da ya siyo ma Mama kilishin ta sannan yayi sallar Isha ya shigo cikin part ɗin. A chan ya yi Dinner ɗin sa yaci Tuwon dawa da Hajo tayi wa Sir dan yafi son na ta,idan yayi ra,ayin sa ita ke shiga da kan ta ta girka masa. Koda ya shigo suma sun gama Dinner ɗin su,da zummar idan ya zo sai ya ci na sa dan ya faɗa ma mahaifiyar ta sa inda zaije sashen Hajiya.koda ya zo suna ta aikin Rarrashin LINA da ta ƙi cin abincin ta kafe da ta ƙoshi. Sallamar sa ce ta sanya ta miƙewa da sauri tana nufar dininng bai ce komai ba shima sai bin bayan ta da yayi saboda ya ji komai ya san tsafff zata iya ƙin cin abincin ta miƙe haka dan haka ya zo da kan sa yayi serving ɗin ta yace Rabi ta wuce. Tura mata yayi gaban ta.Da sauri tayi ta turawa saboda so take ta tashi ta shige ɗaki bata buƙatar ganin kowa haka kawai yanzu take jin jikin ta wani iri kamar an sassara naman ta,ga zuciyar ta da take mata rawa kamar tana cikin damuwa ko matsala. Bai hana ta cusa abincin ba sai da ya tabbatar da ta ƙoshi sannan ya miƙe yana bin bayan ta kasancewar ta riga shi miƙewa. Direct ɗaki ta nufa bai hana ta ba sai ma zama da yayi yana kallon agogon hannun sa cike da kulawa ya furta " Hamida Dare ya soma ya kamata ki koma gida ". Kai Hamida ta gyaɗa tana furtawa cike da shagwaɓa " Allah da Badan school ba da zan zauna anan sai na yi sati ɗaya ". Ummah murmushi tayi tana furta " Lallai kam ki tsaya kiyi Rarrashin mutuniyar ki naga yau fushin da ban ne ban san dalili ba,gashi dai ba ma faɗan aka yi ba mai muni ". Miƙewa tayi tana furta " bari na kira driver." " No bari na kai ki ba sai kin kira shi ba ". BILAL yayi Furucin. " Nagde yaya ". Hamida ta furta tana shigewa ɗakin na su LINA tayi mata sallama tare da ƙara Rarrashin ta.bata iya furta komai ba sai ma a hankali ta furta " Allah ya tsare Anty Hamida,ki gayar da Ammah da Baba B " tayi Furucin Ganin bata kyauta mata ba na share ta,dan bata saba mata haka ba. Cike da murmushi Hamida ta fita tana furta "Amin, Zasu ji in sha ALLAH ". Sallama tayi da su Ummah sannan ta fice daga dan har BILAL ya zari keys daga inda suke ajiye. Kasancewar dare yayi Ummah ta ce REENA ta je ta kwanta saboda schl gobe kar ta makara. " Ummah sai da safe ". REENA ta furta." Allah ya bamu Alkhairi,kar a manta da addu,ar kwanciya bacci ". " Amin,in Sha ALLAH ".ta furta ta wuce sama zuwa bedroom ɗin ta. Itama Ummah miƙewa tayi ta tayi sallama da Rabi da wasu daga ma'aikatan masu kula da tsaftar part ɗin. Ɗakin Su LINA ta faɗa kwance ta isko ta idanun ta rufe bacci ya fara ɗibar kwasar ta. Murmushi tayi kafin ta matsa ta tofa mata Addua sannan ta rufo mata bedroom ɗin. Bedroom ɗin ta ta nufa sai da ta fara leƙa bedroom ɗin REENA da ita ma ta yi shirin baccin cikin yar guntuwar riga da wando kamar na LINA dan itama tayi shirin baccin har hular ta ta sanya. Murmushi tayi ta shafa kanta tare da ƙara shafa mata Addua,a sannan ta fice. Bedroom ɗin ta ta wuce itama direct toliet ta wuce,wanka ta,ɗauro tana fitowa dai dai lokacin da wayar ta take rurin neman taimako.Da sauri ta ɗaga tana Murmushi cike da farin ciki. Sallama tayi cike da kulawa da natsuwa. A chan ɓangaren ne a aka furta " Ina yan biyu ko sunyi bacci,ya suke ? ". " Haba Abban su Ni ba zaka yi ta tawa ba sai ta ya yan ka,Ni nayi ma fushi ". Murmushi aka yi daga chan ɓangaren kafin ya furta " A gafarce ni Uwar Soja ai kina raina,ban samu 'okaci bane ko yan uwan ki duk yanzu nake son kiran su,ya kike Amaryar ta ya gdn "? Shiru tayi jin furucin sa kamar bazata amsa ba.Sannan ta sauke Numfashi tana haɗiye wani abu mai nauyi tana furta " Duka muna lafiya,ya aikin ". Haka suke cigaba da firar cike da kulawa sai da suka yi kusan mintuna talatin sannan suka yi sallama rabin firar kuma duk ta su LINA ce da yadda yayi kewar su " .Sallama suka yi cike da kulawa sannan ya yi hanging kiran. Yana mai da kiran kan Momy. Numfashi ta sauke wani abu na sauka mai nauyi acikin zuciyar ta,wanda ya ke maƙare da maƙoshin ta tun lokacin da firar ta su tayi tsawo. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta miƙe ta saka kayan barcin ta yi shirin ta tsafff,Addu,ar kwanciya bacci tayi bayan ta sanar da BILAL idan ya dawo ya rufe part ɗin ta shige. Wuraren sha ɗaya na dare ta farka tana lalaba gefen ta sai dai wayam babu komai a wajen buɗe idanun ta tayi da sauri tana bin ɗakin da kallo tana duban inda zata ganta.Miƙewa tayi ta buɗe toilet sai dai babu ta ciki.Fahimtar ba nan ta kwana ba hakan ya sa ta ta saka bedroom silifas na ta ta fito dan ta san inda zata same ta.Dan baya iya kwana ita kaɗai sun saba da kwana a tare da juna komai faɗan da aka yi,idan sama suke son yin Bacci sai sai su kwana na ɗaya jibi na ɗayar su. A falon ta tarar da dashi yana wani aiki a system ɗin sa akan business idanun ta ta murza ganin dai shi ɗin ne hakan ya sa bata ce komai ba ta raɓa shi ta wuce idanunsa ya sauke da sauri bayan abinda idanun sa suka ƙyallo masa,ya cigaba da aikin sa yana girgiza kan sa dan shi har ya nzu mamakin yar uwar ta sa yake yi yadda faɗa baya damun ta. Bedroom ɗin REENA ta faɗa tana kunna haske ganin ta tayi tana sharar bacci ta hankali kwance.Hararar ta tayi kafin ta kashe hasken ta kwanta kan gadon bayan REENA.Ta na kwantawa kuwa bacci mai nauyi ya kwashe ta. A ɓangaren BILAL kuwa bai tashi daga aikin ba sai kusan ƙarfe ɗaya na dare sannan ya miƙe ya cire system ɗin sa daga Chaji sannan ya wuce sashen sa dake cikin part ɗin. 🍃🍃🍃 Aɓangaren SHATOU kuwa tun da aka yi Sallar Isha take ta mutsuniyar yadda zata samu ta fice saboda dukkanin su suna zaune a tsakar gida suna shan Iska.Inna Ni na lura da ita dan haka ta ka sa ta tsare cike da kulawa.Har wani jan jiki take ƙara yi saboda kawai ta ƙi fitar dan ta fahimci yan kame kamen da take yi da salo. "Inna ni yau zan je makarantar dare Su Amina sun ce zasu biyo mini kuma basu zo ba ". Murmushi irin na yarinya yarinya Inna ni tayi mata dan ta fahimci nufin ta.Sannan ta furta " Sai ki haƙura kawai " " Na haƙura fa Inna ni Kinga mun kwana biyu bamu je ba ya kamata mu koma " " To yanzu ya za,a yi kenan ". Cewar Inna ni. " Ki bari mu tafi tare da Bibu kawai Inna ni ko Baffa na " Tayi zancen tana kallon Baffa na da Bibu. Murmushi Baffa na yayi dan ya fahimci shirin ta sannan ya furta " Ya kama ta kam SHATOU na ".Ya san Indai da Bibu za,a je to rigimar daƙyar ayi ta. Numfashi kawai Inna ni tayi kafin ta furta " Kuje kuma idan an taso kar ayi biye biye nan dare ne yanzu ba rana ba banda rigima ". Tsalle SHATOU tayi tana murna tana cewa " to Inna ni ". Bibu da bai so fita ba baccin sa ya so yayi ya miƙe yana saka takalmin sa. Babu littafin karatu babu komai haka ta fice kuma Inna ni ta gani sai dai kawai ta girgiza kan ta tana fata da Addua,a Allah ya dawo mata da su lafiya babu wata rigima.Dan ta san asalin inda za.,aje ba makarantar ba kawai. Makarantar daren suka fara zuwa basu ko yi mintuna goma ba ta nemi izinin zuwa gida wai kan ta ke ciwo haka aka saka Bibu ya raka ta. Tun a makarantar yake kallon ta yana son ya ce wani abu sai da ya bari sun fita sannan ya ce " Adda SHATOU ƙarya fa kika yi,kwanan nan sai zuba ƙarya kike yi ". " Eh nayi ai ƙarya akwai inda ta halasta " " Yawwa Bibu fili zamuje in zaka je idan kuma ba zaka je ba ka ce Baka da lafiya sai kayi gida kace shine ya sa ka dawo,ni kuma sai na zo daga baya " " Kuma dan Allah Karka faɗawa Inna ni na tafi Filin wasa ". Baki Bibu ya turo gaba kafin ya ce " Ai tare muka zo tare zamu koma Ni bazan koma nikaɗai ba mu tafi na yi kallo ko na shiga nima kuyi dani ". Dariya tayi tana laƙƙamo hannun ta wuyan sa shima ya laƙƙaama na sa sannan tace " Yawwa Bibu na kusa zama SHATOUn birni haka nake jin kamar zan tafi,kuma Allah Dagske haka nake ji ". Dariya yayi kafin ya ce " Babu inda zaki je Adda SHATOU,to me zaki je yi chan ". " Oho Nima ban sani ba,Allah ya sa alkhairi ne na siyo maka Raken birni mai ƙara wa kan ta zaƙi da ragewa ". Dariya Bibu ya ke ce da ita yana furta " Kai Adda SHATOU ya sifn ban yadda akwai wannan raken ba ke har kin yarda da maganar Iro ,ance shi ya kawo zancen nan wai akwai wannan raken ". " Mtsww" taja tsaki jin an ambaci sunan maƙiyin ta kafin ta furta. " Eh lallai ƙarya ne Bibu amma zan maka tsara ba mai kyau kana so ko ". Kai ya jinjina mata cike da Murmushi haka suka cigaba firar su har suka isa chan firar wata shirme wata dai dai. Koda suka isa filin cike take yara na ta wasa sai yan manya irin su Iro gefe ɗaya suna shan rake suma taɓa firar su suna kallon abun da ke waka na. Cike da farin ciki sauran yaran suka tarbe ta suna kiran sunan ta. Wasar yar jari ri bisa gado suka cigaba da yi inda aka yiwa SHATOU ta4fna ta dariya sai dai rabin hankalin ta na na ga kan jama'ar dake wajen dan akwai hasken kara da aka kunna. Bibu ma cikin maza irin sa ya shige suka cigaba da wasa. Ita kuwa SHATOU a jirgi na tara ne da aka wulla ta baya a lilon da suka koma yi yanzu ta hango dai dai kalar yaguwar dake ga rigar da ta gani a barcin ta.Hakan ya sa cike da sauri ta ce su ajiye ta dan tabbatar da abun da ta gani.Wanda ke sanye da rigar ya juya baya yana Marmara gyaɗa.Cikin azama suka sauke ta ganin yadda take ta ɗaga musu murya dan har sun tsorata.A hankali take sanɗa dan fara ganin wanda yayi aikin da kyau.Aiko sai aka yi sa,a dai dai lokacin da ya juyo da fuskar sa...✍️ Wannan littafi na kuɗi ne akan1000 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* *~Paid~* *Second to the last free pages*👌 P..1️⃣1️⃣ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting room link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* _*A MAFARKI NA SANTA*_ _*RAYUWAR MU A YAU!*_ _*SHAGALI💃💃💃💃nace!! Ina yan kasuwa manyan Hajiyoyi masu Capacity nace ga damar ku tazo domin kuwa muna tallata muku hajar ku,kowace iri ce a farashi mai sauƙi idan ki/ka na buƙata,sai ku tuntuɓe mu wannan lambar +234 808 750 4734 dan tallata hajarku.Sai kun zo.*_ 🪐🪐⚡🪐🪐⚡🪐🪐 A hankali take sanɗa dan fara ganin wanda yayi aikin da kyau.Aiko sai aka yi sa,a dai dai lokacin da ya juyo da fuskar sa yana kallon ta jin sauran Abokan su na maganar nufowar ta wajen su dan yace kowannen su ya fita iskan ta sai an manta sai su rama abun da ta musu.. Idanu ta ƙara buɗewa da kyau dan tabbatar da zargin ta shi ɗin dai ne dan tass haka fuskar shi ta bayyana gare ta.Cike da wani irin haushi da baƙin ciki take kallon sa sai dai ta kasa cewa komai sai ma Riƙe ƙugu da tayi ,tayi tsaye tana ƙarewa dukkanin su kallo.Bibu ne ya matso gurin da sauri gudun faruwar wani abun hakan ya sa ya riƙo hannun ta yana furta " Addah SHATOU lafiya ".?? Ƙin bashi amsa tayi sai bin hannun ta da ya fara jaaa da kallo tayi kafin ta yi murmushin da ita kaɗai ta barwa kanta sani.Su Amina ma duk zuba mata idanu suka yi haka ma sauran abokan na Iro sai Surutun su suke wasu suna hayayyaƙo mata na lafiya kallon da ta ke yiwa Iro,Wanda wasun su har sun fara kiran ta mayya mai cin naman mushe Indai Iro ne kurwar sa tafi ƙarfin ta. Bata tan ka ma kowa ba har ta daina ganin duhun jama'ar wajen dan kai tsaye Bibu hanyar gida ya nufa kuma bata hana sa ba dan ta riga ta sha alwashin ta ƙara tabbatar da shi ne sai ta masa wulaƙancin da bai zata ba. Sai da suka kusa isowa gida ne suka lura da su Amina a bayan su.Ashe tun ɗazu suna biye da su.Dakatawa tayi tana furta " Ku kuma lafiya kuka sako mu gaba ".? Amina ce cikin ɗan ƙarfin hali ta furta " Dama mun ga kamar ba lafiya ba ne SHATOU shi ya sa nace bari mu biyo bayan ku " "Idan na faɗa muku kuna iya ɗaukar mini mataki "? Tayi furucin tana kallon Amina. Kai Amina ta girgiza kafin ta furta " Indai wanda bai fi ƙarfi na ba zan iya SHATOU Ni kaɗai ma ". Murmushin na samu banza SHATOU tayi kafin ta furta " Yawwa Iro nake son Ki tsaya gaban sa ki zazzage sa saboda ya ci mutun cin ƙawar ki ". Idanu Amina ta zaro ba ita ba har Bibu da ke kallon Shatoun.Haka ma su Ramata. " Adda SHATOU kin san dai abun da ke tsakanin ku da shi,to ma ai bai Miki komai ba kuma naga yanzu bai ma kula ki ba ". Hararar Bibu tayi sannan tace " Shine fa yayi rubutun nan a makarantar mu,kuma wallahi ba zan yafe masa ba sai na rama dan ma kar wanda ya dakatar da ni Gara ma Karka faɗa a gida kayi shiru da bakin ka ". Ta kai ƙarshen zancen a hasale kafin ta ƙara furta " Mafarkin sa nayi jiya,da kayan da ke jikin sa,Dama neman mai kayan nake yi sai gashi a she shine dai dan da farko nayi zargin sa. Idanu da baki dukkanin su suka saki suna kallon ta kafin Amina cikin ƙarfin hali ta furta " SHATOU mafarki fa ba gaskiya bane,sheɗan na iya zuga ki Shine ya nuna Miki Iro,nidai Dan Allah kiyi haƙuri ki bar zancen nan ko kuma ki bari mu tabbatar da gaskiyar ta fili ". Kallon Amina tayi tana gyaɗa kan ta,ta san gaskiya take faɗa amma tabbas tana buƙatar Son yin maganin sa idan dai har shi ne.Dan haka zata yi binciken kamar yadda ta tsara tun farko da ta tabbatar da shi ɗin ne sai ta masa wulaƙanci. " Naji " kawai ta furta ta cigaba da tafiyar ta har ta shige gida babu wanda ya ce ƙala a cikin su sai dai suna mamakin yadda zaka ga abu a mafarki kuma kace zaka yarda da abun da ka gani.Gashi Malamin su ya sha faɗa musu bakowa ne mafar ki ne gaskiya ba wani mafarkin sharrin shaiɗan ne kawai. Sallama Bibu yayi musu ya wuce gida sannan suma suka juya suka yi gida kowace zuciyar ta cike da zullumi. Jawairiyya ce ta furta " Ni dai ko da an ƙara kirana shaidu zance ban da lafiya gaskiya dan na san sai an yi rigima babba akan wannan zancen dan ba barin sa zata yi ba ". " Nidai tsoro na kar su bata kashi,na san idan dukkanin su suka dake ta mutuwa zata yi " Amina tayi furucin tana jin hawaye ya cika mata ido. " Ke Amina ba dai daga magana ba har kin fara hawaye " Cewar Ramata dake kallon ta cikin hasken farin wata. Dariya ta kece da ita tana furta " shi ya sa duk SHATOU ta fi raina ki wallahi ". Tsokanar ta suka dinga yi har suka iso gida kasancewar gidajen su suna kusa da juna kowaccen su tayi shigewar ta. Koda suka shigo Inna ni ce kawai zaune a tsakar gida tana jiran su hankalin ta ba kwance ba ganin lokacin ta shin na su yayi amma ba su iso da wuri ba. Numfashi ta sauke mai nauyi bayan shigowar SHATOU gidan sannan Bibu. Bata ce musu komai ba sai umurnin kowa yayi Alwallah ya je ya kwanta tare da tunatar da su mahimmancin Addu,ar kwanciya bacci. Haka suka shigewar su ɗaki kowa ya kwanta bayan yin Addu'a. A ɓangaren Inna ni itama da baffa na sai da safe suka yiwa juna kafin suka yi Sallama. Guraren Ƙarfe Biyu ta buɗe idanun ta da suka gagara rufuwa da bacci,dan ta daɗe haka kwance.Miƙewa tayi zaune tana kunna fitilar ɗakin na ta.Idanun ta da suka yi nauyi ta ƙara buɗewa kafin hawaye suka silalo mata masu zafi.Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin Kuka ya kubce mata mai tsuma zuciya kamar ko yaushe sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta. Tana nan zaune yadda take bacci ya kwashe ta. " Yadda suke kuka suna ƙoƙarin rungume ta ne ya sa ta zuba musu ido tana kallon su ta kasa rarrashin su wata mata ce da baƙin mayafi fuska a rufe ta zo da sauri ta janye su jikin ta da ƙarfi wanda ita kan ta har da zabura tayi " Wanda ya sa ta miƙe firgigit daga zaunen da take tana buɗe idanun ta daga nannauyan baccin da ya ɗebe ta.Duk yadda take son tuno fuskokin da ta gani yanzu a mafarkin na ta a bin ya gagara dan haka ta miƙe ta fice alwallah ta ɗauro ta sallah tayi addu,oi sannan ta miƙe ta koma kan ɗan madaidaicin gadon na ta. Yau an tashi da abun farin ciki a cikin kauyen kasancewar zasuyi manyan baƙi domin ɗan gidan babban ministar ne na Abuja zai zo duba yadda tsarin makarantun su yake kafin a fara wani abun.Dan haka yau ta ko ina su SHATOU basu samu sauƙi ba tun da suka je makaranta sai aikace aikace suke yi.Tana son guduwa gida abu ya gagara dan yunwa take ji dan haka saboda Abar ta taje ta san malamin su ba zai hana ba idan ta tafi tare da su Ramata ta san zai yarda zata dawo.Da ƙyar da rarrashi ta roƙe sa ya bar su suka fice daga makarantar da zummar zasu dawo. Sai dai Shatou ba yunwar kaɗai ba ce ke damun ta ta gundura da aikin ne kawai a cewar ta dan wani banza zai zo sai a saka su aiki kamar tumakai dan duk da aikin nata na shan ruwan tsuntsaye ta cire jin Haushin aikin da aka tataro musu ba, dan har da su cirar yana da cire ƙananan hakukuwa,duk yadda prefect suke matsin lamba da malammai amma ita tana gefe tana ragwanci bakin ta ture kaɗan take jira ayi ta ruwan masifa tsakanin ta da prefect ɗin sai dai fahimtar halin da take ciki sai suka fita iskan ta bayan malamin su ya basu umurni kuma ko ba dan haka ba sun san halin ta. *** " REENA kin san jiya mafarkin me nayi,mafarkin fuskokin mu nida ke nayi,muna kuka muna miƙa hannayen mu ga wasu hannayen da ba,a ganin fuskokin su wai muna kuka suma suna kuka ". LINA ce ta yi Furucin bayan sun gama sallar asuba. Kai REENA ta ɗaga alamar tunani kafin ta furta " Me yasa baki bari kika ga ko su waye ba kafin ki farka ".ta kai ƙarshen zancen cike da yarinta kamar yadda LINA tayi zancen. " Mtsww ke fa Wawuya ce waya ce Miki ana iya saka wani abu a mafarki,kai ba sai dai ka gani ba ne ". LINA tayi Furucin tana cigaba da tofa Addu'a. " Mtsww Ni dai ba Wawuya ba ce wallahi,idan kin san Wawuya nake mai ya kawo ki bedroom ɗina ai da sai ki tsaya naki". REENA ta kai ƙarshen zancen tana ɓata fuska kamar zata yi kuka. " Uban me zai shigo da ni nan ni ma ban san wanda ya kawo ni nan ba,da ba zan kwanta a wannan banzan gadon ba " Ta kai wa bed ɗin bugu kamar irin zai ji. Kuka REENA ta fashe dashi kafin ta furta " Wallahi ki ka ƙara dakar mini bed Allah ya isa na muguwa ". Dariya LINA ta ƙyalƙyace da ita kafin ta miƙe ta na wani irin ja baya sannan ta kai wa bed ɗin mugun shuri da ƙafar ta,ta dama har da yin suluka kamar wata Chinese sannan ta haye bed ɗin. Kuka ne ya ƙara ƙwace wa REENA har da murje murjen ƙafafu an daki gadon ta. Tana furta " bai yafe ba wallahi,kuma sai na rama ma sa ". Miƙewa tayi tana cire hijab ɗin ta dogo har ƙasa kafin ta haye gadon ta faɗa kan LINA da ke ta tsalle tana dakar bed ɗin tana dariyar ƙeta jin REENA na ƙara giyar kukan ta. Tana hayewa kan gadon kuwa kamar dama LINA jiran ta take ta faɗa mata aiko ta hau dakar abar ta har sai dai ta kai tun REENA na ƙara ta kai Muryar ta bata fita kafin ka a an kara ta sume ga jini ta bakin ta yana gangara kaɗan. Ummah da take jin hayaniyar su ƙasa ƙasa ne ta leƙo tana tambayar lafiya. " Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un " " LINA me nake shirin gani,Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un LINA kashe kashe mini ita zaki yi ".? Ummah tayi furucin Ganin Yadda LINA take jibgar REENA dake kwance a Kasan ta bata motsi kuma duk da haka bata daina jibgar ta ba kamar Allah ya aiko ta. LINA da bata fahimci aika aikar da tayi ba ne saboda yadda idanun ta suka rufe ta juyo da sauri tana kallon Ummah kafin ta mai da idanun ta kan REENA dai dai zaro idanun ta da faɗuwar ƙirjin ta ganin yadda jini ke zuba bakin yar uwar ta hannu ta aza a kai ganin babu numfashi a jikin ta.Miƙewa tayi tana sauka daga kan ta kafin kuma wata irin juwa ta kwashe ta ta faɗi ƙasa yaraff babu numfashi. Ummah dake riƙe da REENA hankalin ta ƙara tashi yayi hakan ya sa ta miƙe cike da sauri tafi ce tana ƙwala kiran Sunan Soja. BILAL da bai daɗe da shigowa bane bai ko isa sashen sa ba ya ji kiran mahaifiyar ta sa cike da tashin hankali.Juyowa yayi da sauri yana dosar sama dai dai lokacin da itama ta iso ƙofar ɗakin REENA ta nuna masa da sauri ta ma kasa magana. Shigewa yayi da sauri cike da tambaya sai dai bata bashi amsa ba. Abun da ya ci karo da shi ne ya tayar masa da hankali ganin REENA kwance kamar gawa fuskar ta ta kumbura lokaci ɗaya ta chanza kamanni kamar wadda ta yi dambe a filin dambe. Kan ta yayi da sauri yana ɗan marin fuskar ta yana kiran sunan ta sai dai ganin bata motsa ba ya sa shi tunani wata mafita kallon bedroom ɗin ya fara kafin ya hango LINA itama yashe a ƙasa idanun sa ya waro wani sabon tashin hankalin na mamaye sa ga tambaya rass dafe da zuciyar sa babu amsa.Ummah ce ta shigo da ruwa mai sanyi a hannun ta.Hankali tashe ruwan ta yayyafa ma LINA har sau biyu sannan ta miƙe a razane sabo da tashin hankali ne ya kai ta ƙasa da tsoro. Miƙa ma BILAL ruwan ta yi ya yayyafa ma REENA baiwar Allah tana jin sanyin ruwa ajikin ta ta buɗe idanun ta a galabaice sun yi jawur da su na azaba. Hawayen ma sun ƙafe.Zama take son yi amma ta kasa, fahimtar hakan ne ya sa BILAL miƙa ta hannun Ummah bayan ya ɗago ta, toilet ya faɗa ya haɗa ruwan masu ɗan ɗumi da zasu taimaka mata sannan yadawo ya ɗauke ta ya shige toilet ɗin da ita. Bayan shi Umma ta bi cike da tausayin REENA babu wanda ya kula halin da LINA take ciki dan kuka take ta rizga harda shiɗewa. Ganin Ummah bayan sa ya sa shi ɗan kallon ta ƙasa ƙasa kafin ya baro toilet ɗin yana mamakin wasu halaye da Ummah take nuna wa duk da alƙawarin da ya ɗaukar mata a chan shekarun baya da suka wuce. Ummah kuwa kan REENA tayi bata ma kula da shi ba.Cike da tausaya wa ta ke ɗan gasa mata fuskar ta da ruwan ɗumi bata fito daga cikin bahon ba sai da tayi kusan mintuna goma sannan Ummah ta chanza mata wasu ruwa tare da yi mata wanka ta ɗaauro mata towel suka fito. Koda suka fito BILAL ya fita ɗauko first aid kit.yana shigowa kuwa kallo ɗaya yayiwa LINA da ta ta kure waje ɗaya alamar bata da gaskiya.Zama yayi bakin gadon yana Fiddo da maganin kashe zafi da su pain relive na oral,Tare Da maganin da zai taimaka mata tayi bacci dan ta bugu,BILAL duk da bai san abun da ke faruwa ba amma zuciyar sa ta riga ta gama amince masa aikin LINA ne musamman yadda ya ga ta takure gefe ɗaya sai satar kallon sa take yi tare da REENA da ke ta sauke nishin azaba. Shayin da Ummah ta haɗa mata yanzu ta sha kafin ya miƙa mata maganin ta sha kamar zata dawo dashi dan itama bata wani son magani.Duk da tafi LINA ita da wuya a bata magani bata zubar ba,ko ta ɓoye. Kwantawa tayi ya lulluɓe ta da blanket yana mata sannu.Kai kawai Take iya ɗagawa sai hawaye da suke sauka kaɗan a gefen idanun ta.Cike da tausayin ta ya fice daga bedroom ɗin. Fitar BILAL ta sa LINA jin sauƙi a zuciyar ta,dan wata irin masifa ta hango cikin kwayar idanun sa a kallon da yayi ƙara yanzu kafin fitar sa. Ummah kuwa yana fita ta fara mata faɗa cike da ɓacin rai ta inda take shiga bata nan take fita ba.Shigowar BILAL ce da wata iriyar bulala mai harshe biyu ya sa Ummah yin shiru tana kallon sa kafin ta furta me zaka yi BILAL.... ______________ 🍀🌻🍀🌻🍀 A ɓangaren SHATOU kuwa gidan su ka wuce suka ci suka ƙoshi kafin suka fito suna firar su da wasannin su a hanya harda yan guje guje,Suna tsaka da tafiya su huɗu manyan danƙararrun motocin da ke ƙoƙarin mamaye yar hanyar suka ratso kusa dasu dai dai wata babbar mota mai walƙiya kamar an ƙera ta da zinari wacce duk tafi sauran kyau kuma itace a tsakiya tayi wa su Amina da Ramata, jawairiyya wanka da ruwan kwatar dake zube a wajen saboda akwai kwata wajen dan ƙofar gidan suna niƙan injin na ruwa ko wane kala sai ya zama wajen ya tara ruwan kwata,gashi ba,a tsaftace sa. " Kutumar Uban nan,Amina kunji wanki ". Ta furta ganin yadda duk aka wanke musu jiki ita kaɗai ce ruwan bai sama ba.Amma taji kamar itace dan cike da masifa da ɓacin rai tayi zancen ganin ko ta kan su ba,a bi ba kamar ba mutane aka yiwa haka ba. " Yau ko uban waye sai ya yi bayanin abun da ya aikata sai ya baku haƙuri ko shine ɗan gidan Shugaban ƙasar Nigeria,na rantse da Allah sai ya yi dana sanin zuwan sa ƙauyen nan,Amina kun jin yadda kuke wari wallahi haƙƙin ku ba zai ta fi banza ba sai ya san ya taɓa ƙawayen SHATOU ". Sai dai bata rufe baki ba wata motar tayi mata wankan kwata a fuska sage hannuwan ta ta yayi tana runtse idanun ta cike da hargagi tana tofar da yawu take furta " Allah ya isan mu,Allah ya isan mu Azzalumai ɓarayi,masu kuɗin jini ". Cikin dabara ta samu ta goge fuskar ta dake ta wari sauƙin ta ma basu kai cikin baki ba ruwan iyakar su akan leɓen ta. kafin ta yanka da gudu ta cimma asalin motar da ta watsa wa Su Amina kwata da tarin duwatsu a hannun ta da ta tsinta a yanzu cikin hasala da wani irin zafi da zuciyar ta ke na wulaƙanci da aka musu ba,a kuma tsaya aka basu haƙuri ba ......✍️ # MMG# # SHATOU# # IRO# # LINA SSS# # REENA SSS# # BILAL SSS# # SAMIRA MAI BILLIONS. Wannan littafi na kuɗi ne.akan farashin 1000 Page ɗaya ya rage a free pages da na muku alƙawari dan haka duk wadda ta shirya yin payment ga details a ƙasa.👇 *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Idan ba shaida kika tura ba kar kimini wani zance pls serious one nake buƙata,ga komai nan a sama na ajiye muku. Last free page on Monday. Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ *BOOK ONE* __Paid__ *_Last free pages👌_* P..1️⃣2️⃣ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting room link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn *LITAFFAN MARUBUCIYA* *A MAFARKI NA SANTA* *RAYUWAR MU A YAU!* _*Ina yan kasuwa Manyan Hajiyoyi masu Capacity ga damar ku tazo domin kuwa muna tallata muku hajar ku a farashi mai sauƙi idan ki/ka na buƙata,sai ku tuntuɓe mu wannan lambar +234 808 750 4734 dan tallata hajarku.Sai mun ji ku.*_ ✨🕳️💦🕳️💦✨ Cike da masifa ta fara ƙoƙarin jifar motar sai dai bata kai ga yin jifar ba aka daka mata tsawa inji ɗai daga cikin garda garda dan masu tsaron sa dake tare da shi wanda suka diro daga kan buɗaɗiyar motar su su biyu kasancewar sun hango abun da take shirin yi. Zare mata idanu suka yi suna jifar ta da mugun kallo. " Hey girl what are you up to ? " Wani daga cikin su ne yayi tambayar yana kallon hannayen ta da suke rawa jiran take ta samu dama ta jefi motar yadda zata yiwa na ciki rauni. Aiko cike da rashin tsoro itama zaro idanun ta dan bata fahimci abunda ya faɗa ba.Hararar su ta dinga yi ɗaya bayan ɗaya kafin ta faki idanun su ta yanka a guje ganin haka ya sa suka bi bayan ta tana isa dai dai ta wajajen motar ta ja baya ta saita danƙon kafin ta saki dutsen na ta da ta saka a kan danƙon da ta fito dashi a ɓoye wanda ita kan ta bata san dalilin da yasa ta ɗauko shi ba ta saka aljihun.Sai yanzu. Tasss haka glass ɗin ya bada ƙarar tsagewa saboda yadda dutsen ya dake sa na farko kafin na biyu ya ƙara hawa kan sa sai da tayi harbi uku sannan taga ta tarwatsa glass ɗin ta dakata ganin sun kusa isowa wajen ta dan ta musu nisa. Dariyar farin ciki ta kece da ita cike da jin daɗi dan ba haka ta so ba ma so tayi ta ta zubar da shi duka ta ga asalin ɗan ikon da ke ciki zaune wanda da alama babba ne dan ta ga yadda ake ƙoƙarin kare sa tun da ga waɗan chan gardawan. Motocin chak suka tsaya dai dai saitin ta kasancewar umurnin da suka samu na dakatawa. Dai dai lokacin su Amina sun ƙaraso cike da tsoro sai zare ido suke yi ganin abun da ta aikata dan su kan su basu san ta fito da danƙo ba.Tun da gardawan nan suka biyo ta. Ƙoƙarin kama ta bodyguard ɗin suke yi dan hasale suke sai dai maimakon ta gudu sai ma riƙe ƙugu da tayi tana jifar su da kallon banza cike da masifa ɗayan ya ɗaga hannu yana batun kai ma ta mari sai dai ƙamshin turaren sa da yaji a akusa da su ne ya sa shi dakatawa yana kallon sa cike da mamakin uban gidan na su dan bai ma san fitowar sa ba. Itako SHATOU bata juya ba sai ma rufe idanun ta da tayi tana jiran saukar marin da take ganin idan aka yi shi sai kowa ya mutu cikin su saboda yadda zata addabi rayuwar su.Duk da taji ƙamshin wajen ya sauya da wani daddaɗan ƙamshi hakan bai sa ta yi ƙoƙarin juyowar ba still sai ma buɗe ƙofofin Hancin ta da tayi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin tana jin ta kamar ta faɗa wata duniyar dan take taji bacci na son ƙwace mata ta gurin. Sanyayyiyar Muryar sa ce mai cike da Izza ta daki zuciyar ta yana furta " Bike Stop this She's young ".Yayi zancen yana ƙare mata kallo ta ƙasan ido cike da mamakin rigimar ta ta dan tun farkon fara rigimar yake ɗan hango su ta madubi. Dai dai lokacin ne kuma ta buɗe idanun ta tar akan sa kasancewar ya dawo gaban ta yanzu. Ƙirjin ta ne yayi muguwar faɗuwa ganin mutumen dake gaban ta Bature sak har wani kashe ido yake yi yana sanye da baƙin yadi mai taushi sai dai babu hula akan kwantaccen gashin sa da ya sauka har akan wuyan sa.Kyakkyawa ne fari mai ɗan jiki kaɗan bai wani tara irin muscles ɗin nan ba dan da alama yanzu yake tashe yaro ne shakaf wanda ba zai wuce Shekara ishirin ba da uku a duniya. Yana da tsawo sosai da faffaɗan ƙirji,Kyakkyawa ne dai na asali,Irin asalin kyawon nan na turawa masu kyau da suka samu surki da fulanin mu,Yana ɗauke da manyan idanu masu haske da gashin gyara wanda yake cike tabb akan gyaran sa ga dogon Hancin sa da ya ƙara ƙawata Kyakkyawar fuskar sa bakin sa na ɗauke da red lips masu kyau da suka ƙawata ƙaramin bakin sa.Sai da ta gama ƙare masa kallo sannan ta sauke numfashi dan ya ɗan bata Tsoro,ganin sa take kamar ba mutun ba,Samun kan ta,tayi da galla masa harara bayan haɗa idon da suka yi yanzu tuno da shine cikin motar da ta yiwa su Amina wankan kwata. Masifar ta ce ta dawo sabuwa inda ta fara girgije girgije kamar wadda ke ɗauke da wani abu aƙirjin ta tana furta " Wallahi sai kun ba su haƙuri sannan zan haƙura na bar ku ku wuce ko na ƙara sa fasa muku glass ". Idanun sa ya lumshe a hankali yana ɗauke idanun sa a kan ta dan tsafff yake kallon ta ta gefen ido yana kallon duk abun da take yi. " Is that all " ? Ya yi tambayar yana ya mutsa kyakkyawar fuskar sa da rana take ƙarawa haske gashi ranar ma ta ishe sa dan haka yake son su gama abun da ya kawo su subar garin dan tun asali bai yi niyyar zuwa ba Aka tilas ta masa. SHATOU da bata fahimci komai ba ta cigaba da faɗan ta tana furta " Babu ruwa na ko turawan duniya zaka tara nan,kai ko mamamar ka elibabeth da donath trup wallahi sai kun bamu haƙuri babu ruwan mu da masu jajayen kunnuwa ". Yanzu kam ido cikin ido yake kallon bakin ta da ke zaro zancen kafin ya koma kan kyakkyawar fuskar ta,ta ƙuruciya da take fitar da wani haske fess.Kalmomin ta sun so saka shi dariya amma shi ba ma,abocin dariya bane dan haka yadda ta ambaci su Elizabeth da donald trump suka sa shi ɗan lumshe idanun sa dan sun bashi dariya matuƙa,sai dai babu dariyar. Hangame baki tayi tana kallon sa yadda zararan eyelashes ɗin sa suka kwanta akan fatar idanun sa,gashi taga kamar fuskar ta sake ba zata iya kiran abun da yayi da murmushi ba ko wani abu daban. Ƙirjin ta ne ya ƙara bugawa haɗa idon da suka yi ayanzu karo na biyu kai ta sauke ƙasa jin ƙafafuwan ta sun sanyi. Lemar da aka lulluɓe sa da ita har ta shiga ciki ce ta kalla kafin ta kalli ƙafafun sa dake sanye da sandals na maza masu shegen kyau da ɗaukar ido da suka ƙara haska farar fatar ta sa saboda suma black ne.Mere bakin ta tayi ganin ƙafafun na sa da ko ita da take mace nata basu kamo na sa haske da tsafta ba cikin zuciyar ta kuwa mai bilicin kawai ta furta sai dai bata san cewa zancen ya fito fili ba Kawai ta tsinkayi Muryar sa yana furta " Hey bana bilicin,Amma ke kin yi kama da su ai". Ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi saboda bai cika magana sosai ba hasalima bai cika yin ta da cikakkiyar Hausar mu ba amma yau an saka shi dole. Ido ta waro cike da masifa kafin hawaye ya wanke mata fuska duk da mamakin jin Hausa a bakin sa " Wallahi bana bilicin nima,Allah ya isa na duk wanda ya ƙara ce mini ina kama da masu bilicin ". Bai ce mata ƙala ba sai ƙara lumshe idanun sa da yayi yana ja baya ya bar ta cikin rana dan lemar sa tayi mata rumfar dai dai itama. Da ido yayi ma sauran alama da suke kallon ikon Allah su wuce ya rage daga shi sai wanda ke kula da motar dashi na hannun da man sa wanda suke mota ɗaya dashi. Wucewa suka yi kowannen su cike da Haushin da ya ƙunsa dan sun so su nunawa Shatou ƙarshen rashin jin ta,su yi maganin ta dan gobe idan sun dawo ba zata ƙara gigin shiga sabgar mai gidan su ba. " Mubarak ka ba wa yarinyar nan haƙuri ". Yana gama zancen ya shige motar sa aka rufe.Bayan ya jefa mata kallon da ta kasa fassara shi dan ƙafafun ta sagewa suka ƙara yi. Bata samu damar yin magana ba har sai da motocin da suke gaba suka tada motocin sun fara tafiya sannan ta ce cikin ɗaga murya " Wallahi ni ba yarin ya bace kuma ban karɓi haƙurin ba dan kai nake so sai ka bamu haƙuri,kuma Allah ya isa na,mai bilicin kawai ". Mubarak mai kula dashi wanda ya girme masa sosai kuwa haƙuri ya bata murmushi ɗauke akan fuskar sa sai dai ko kallon gefen da yake bata yi ba dan kalmar yarinyar da ya kira mata ta ɓata mata rai. Da sauri da ɗan gudu ya koma motar su yana mamakin halin wannan yarinya da uban gidan na su da yakan yi sati bai yi magana ba sai dai alama ta ido yau gashi da yin magana ta kusan seconni,a tsakiyar rana. Daga chan cikin mota kuwa bayan sa ya jingina da seat yana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya dan kansa ya fara sara masa da hayaniyar ta ga rana ya san sai ya kwanta ciwo wannan ranar da ya shiga mai zafi. Kalaman ta ne da suka gama ratsa kunnen sa suka sake dawo masa " Wallahi ni ba yarin ya bace kuma ban karɓi haƙurin.... ".... Katse tunanin yayi yana jan mugun tsaki kafin a hankali ya furta " witch " saboda haɗa idon da suka yi babu abun da ya hango face Zallar masifar da take son sauke musu da bai jin zai iya ɗaukar ta dan yanzu haka kan sa ya fara juya masa. Idanun sa ya lumshe a hankali yana cire duk wani tunani a kan sa,yana janyo wata hadaddiyar kwalba kamar zinari sai walƙiya take yi tana ɗauke da shisha flavour,ya fara zuƙar ta yana ja da sauri kamar zai haɗiye hayaƙin gaba ɗaya. Mubarak dake gaban mota kallon sa kawai yayi ta madubin yana girgiza kan sa. A ɓangaren Shatou kuwa kuka ne ya ƙwace mata saboda yace mata yarinya kuma yadda yayi zancen cike da rainin wayau hakan ya sa ran ta ya ƙonu matuƙa dan haka ta fashe ma su Ramata da kuka abun da basu ta ɓa gani ba sai yau tattare da SHATOU kowaccen su ta kasa iya furta komai sai ma yar kallon kallon da ake yi tsakanin su kowaccen su ta kasa furta komai. Jawairiyya ce ta yi ƙarfin halin furta " SHATOU kiyi haƙuri idan ma dan haƙurin ne mun yafe masa ". Wani irin kallo ta jefawa Ramata da hawayen ta jage jage a kan ido kafin ta ce " wallahi ba su ci ban za mugu kawai mai jajayen Kunnuwa dama an ce Turawa mugaye ne basu son baƙar fata ". Tayi zancen tana share hawayen ta da suka tsaya chak. " Ai nida ke ba baƙaƙe muke ba inda ma su Ramata kika ce ". Amina tayi zancen tana kallon SHATOU. Suko su Ramata kallon ta suke yi cike da harara.Itako murmushi kawai tayi dan ta san gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba. " Yanzu dai muje fara zuwa gidan su Ramata daga nan kowa ta je gida ta chanza kaya Ni na wanke fuska ta kar malam ya muna faɗa bamu dawo da wuri kar baƙin su zo muna nan,dama ina son na ga wani Shegen ne aka saka mu wahala saboda shi ". Ranka ya suka yi zuwa gidan sai dai kafin su isa Shatoun sai jini take yi wai kamar ita wani mai jajayen kunne zai kirama yarinya ita da Inna ni ta daɗe da yaye ta. Nan dai su Amina suka fahimci kalmar ce ta saka ta kuka.Suko sai yaba kyaun sa suke yi cike da santi kowa na faɗin albarkacin bakin sa,har da faɗin ba su zaci yana jin Hausa ba.Ita kuwa tana kushe sa tare da zagin uwayen sa da ta manna masa su Elizabeth da donald trump wayen da ta ɓa jin su a wani karatu da aka musu ana bada tarihin ƙasashe shine ta riƙe sunayen kuma sai aka yi rashin sa,a ba dai dai ta riƙe sunayen ba. A gidan mahaifiyar Ramata da suke kira Inna faɗa tayi ta musu na rashin kallon hanya gashi garin haka sun jawa kan su wanka da ruwan kwata kwata dan basu yi mata bayanin asalin abun da ya faru ba sun ce mai mashin ne ya zo wucewa ya taka kwatar ta wanke su duk da haka bata yarda ba duk da SHATOU ce ta bada labarin.Wanda su basu san amfanin hakan ba,ita kuwa kar faɗan yayi yawa ne ya sa ta ce haka. Babu ɓata lokaci suka fito saboda suma sauran sun chanzo kayan makarantar su ramata ce kawai suke jira dan ta fi wankuwa da ruwan dole sai da ta watsa ruwa. Ficewa suka yi bayan sun mata sun tafi ta musu addu,a da tuna musu da kiyaye hanya. Tunda suka fito suka yi ta fanfalan gudu dan sun san sun buga latti daga zuwa cin abinci wanda ba ma bari ake yi ba amma suka yi sa,a aka bar su. SHATOU ce a gaba cikin su dan tafi su gudu nesa ba kusa ba basu dakata ba sai tsakiyar makarantar su dan a sake take babu ko ƙofa bare gate sai filin Allah da take zagaye dashi.Turus ta ja ta tsaya tana ƙarewa motocin kallo ƙirjin ta na sama yana ƙasa tana tuno abun da ya faru ɗazu,tana tsoron a ce sun faɗa ta san in haka ne dole za,a dake su,dan ta san tabbas ƙarar su ce suka kawo,sai dai ta san bugu bai kashewa dan haka ta kwantar da hankalin ta..Haka suma su Amina tsaye suka yi cike da macewar jiki, malam Yusi ne ya hango su daga chan gefe aiko ya taso da sauri bai ce musu ƙala ba sai alamar ido da yayi musu,su shigo a hankali yana nuna musu haɗaɗɗiyar kujerar da yake zaune ya haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ita bata ma san akwai irin wannan kujarar a ƙauyen ba bare ma cikin makarantar.Cike da mamaki take bin bayan kujerar da kallo sannan ta na ƙarewa mai riƙe da lemar sa kallo ganin kowannen su a natse,kamar wani abu ya kawo su ba abun da take zargi ba, sai A lokacin kuma ta tuno da baƙin da zasu yi kenan shine baƙon ta faɗa a cikin zuciyar ta. Gaba ɗaya yaran kowa zuba ma Shatou idanu yayi ganin yadda suma kan su masu tsaron na sa da sauran jama'ar da ya zo da su suke kallon su musamman SHATOU. Shi dai bai lura da komai da ke faruwa ba saboda hankalin sa na kan abun da yake dubawa, sai da ta tsayu agaban sa, saboda dama tana cikin wayen da ake ji da su anan makaranta ko mai gari zai zo ko baƙo tana cikin ɗalibban da ake ajiyewa gaba saboda tana da tsafta,da ilmi gwargwado ko yanzu tsaf take sai fuskar ta da har yanzu take nuna alamar an jiƙata da ruwa da kuma ɓacin ran da ya taso mata na sa. Ido cikin ido suka haɗa ido dai dai lokacin da ya gama kallon duk bayanin makarantar da abun da ake buƙata na bayanin da p.a ɗin sa da suka tattara a yanzu bayan gama zagayen da su ka yi yanzu. Lumshe idanun sa yayi yana sake buɗe su sai yanzu ma ya lura da uniform ɗin makarantar ashe kalar nata ne.Haɗe fuska r sa yayi ganin yadda take buɗe manyan idanun ta alamar ƙiriss take jira tayi rashin kunya nan gurin tun da ta ga ba,a mata komai achan ba. Su Ramata shan jinin jikinsu suka yi suma kowaccen kamar an tsamo ta a rame tsoro ya cika zukatan su,su tsoron su ace Dagske ya bada labarin abun da ya faru ko ƙarar su aka kawo dan su har yanzu ba su yi zaton shine baƙon ba ganin sa yaro ne ba irin babba da ake magana ba. Iro ne ya shigo da tawagar sa an sha coat hoƙaƙƙu sun sha guga sai buɗawa ake yi shi ga ɗan gayu,dan shi mai gari ya wakilta anann makarantar da kuma zagayen guraren da za,a kafa ma famfon ruwan sha,bai samu zuwa ba sai yanzu saboda ba,a goge masa kayan da wuri ba da ya aro a wani ƙauye. Tun da ya shigo SHATOU ta ɗauke idanun ta daga kan sa ta mayar da su kan Iro tana sauke masa wata irin muguwar harara mai birkita Idanu ga wani irin zafin sa da ya taso mata.Sai dai dariya ce ta so ƙwace mata ganin yadda yake ta wani lanƙwashe wa,ta ayyana a ranta baka ga wannan ɗan izzar ba daka raina kan ka. Tana rufe baki kuwa ya kawo dai dai gurin yana ƙare masa kallo.Haɗiyar yawu yayi ganin ko gaba da gaban ta dan sai da ƙirjin sa ya buga dan ya san idan wannan yayi turanci sai dai ya bishi da ido turanci Nigeria ya yaji da shi bare na Nigeria,to amma ai ba turawa aka ce zasu zo ba minister ne da kan sa,wannan shine minister ɗin ake nufi ko me.?ya tambayi kan sa.Maganar zucin sa ne ya katse lokacin da SHATOU ta saki wata irin mahaukaciyar dariya tana ƙara bin Iro da kallo daga sama har ƙasa da ke ta zancen zucin da bai da mai basa amsa,Cike da raina ta sa shigar sai yaji ya muzan ta musamman ganin irin dariyar da SHATOU ke yi kuma ya san dashi take ba shakka.Ran sa ne ya ɓaci take ya bawa Malam yusi umurnin a fitar da ita a hukun ta ta.Haka kuwa aka yi malam Bello dake tsaye ransa ya gama ɓaci da shatou ya taso rai ɓace ya fizgo hannun ta har sai da ta kusa faɗawa jikin sa bai dangane ta da ko ina ba sai ƙasa faɗuwa tayi kamar zata ci ƙasa a gefe har sai da ta sanya hannayen ta,ta riƙe ƙasar. Tunda ta fara dariyar Tata yake bin ta da kallo Cike da mamaki dan shi farko ya zata ma spirit ne da ita suka tashi sai dai a hankali ya kalli gefen da ta ke kallo a lokacin ne ya ga Iro kuma ya tabbatar da shi take. A kan idanun sa komai ya faru har yadda malamin su ya fisgi hannun ta yana kallo ta ƙasan idanun sa.Amma bai tan ka ba sai ma lumshe idanun sa da yayi dan dariyar har cikin kan sa ya ji ta.Jin gina da kujerar yayi yana jin kan sa na ƙara sara masa. Mubarak ne ya matso da sauri ya ɗan sunkuya yayi magana ƙasa ƙasa wadda bansan abun da ya ce masa ba.Idanun sa ya buɗe yana sake lumshe su dan idanun sa har sun fara sauya wa saboda hayaniya da kuma rana. Miƙewa yayi ba tare da ya kalli kowa ba cike da izza da sanyin tafiyar sa ya kama hanyar shiga motar sa baya Mubarak ya take masa. Malam Bello da yake principal na makarantar da Iro suma da sauri suka bi bayan sa.Dakatawa yayi bayan ya cire sun glasses na sa da ya sanya bayan ta sowar sa ya ƙyafato malam yusi Cike da sanyin murya ya ce " Don't let them to hurt her,mace ce ".Malam Yusi da ba wani gane turancin yake ba ya ɗan fahimta hakan ya sa ya gyaɗa kan sa cike da girmamawa. Da ido yayi wa Mubarak magana.Mubarak cikin aiwatar da zancen sa ya ce " masu construction zasu zo su duba komai,tare da masu ginar ruwa in Sha ALLAH,zasu zo a gobe,kuma idan mun samu time zamu dawo ". Yana gama zancen ya shige mota shima dan dama shi ya shige tun bayan gama maganar sa har ya rufe sa. Glass ɗin gefen da su Iro suke tsaye cirko cirko ya buɗe kafin ya Jefa musu wani irin kallon da suka kasa gane na meye. Sannan ya danna madanni glass ɗin ya rufe.Sai da suka ɗan tsaya na mintuna kafin ya bada damar tafiya.Yadda motocin suka shigo haka suka bar makarantar ɗauke da daddaɗan ƙamshin sa da ya garwaye ko ina. Malam Bello da Iro da suka ji duk bayanin da Mubarak yayi ne suka ce Masha ALLAH cike da farin ciki sai dai dukkanin su suna mamakin izzar wannan yaro dan daga nin sa yaro ne da kaɗan zai girmi shi Iron.Sai zancen da yayi na farko da basu gane komai ba,dan lafiyayyen turanci ne yayi amfani dashi ko shi Malan yusi dan yana ɗan ganewa ne kaɗan ya fahimta.Kalmar mace ce kawai suka iya ganewa su ko. Dan haka suka zuba ma malam Yusi ido dake murmushi dan jin ko zai yi wani bayani.Amma gudun jin kunya musamman shi principal yaji kunya bare ma Iro mai Degree.🤭 MANYA🤣 # MMG # SHATOU J FARAUTA # IRO # LINA SSS # REENA SSS # BILAL SSS # UMMAH SS # SAMIRA M BILLIONS Wannan littafi na kuɗi ne.akan farashin 1000. Mun gama free pages👌duk wadda ta shirya yin payment ga details a ƙasa.👇 Zan baku kwana goma ko biyar zuwa lokacin na san duk mai niyyar biya ya biya.Dan mufa ra sa da wuri kafin school ta mini ɗauri. Masu tambayar document bani dashi a ƙasa.✍️ Amma zan cigaba da update a Arewa Books mai buƙata sai taje chan tayi following ɗina ta saka kuɗi ta karan ta. Handle ɗina a Arewabooks shine👇 Arewabooks *@Fa'eeh bg* Whatsapp dai sai kun shirya,sai mu fara Ngde🙏 Idan ba shaida kika tura ba kar ki mini wani zance pls serious one nake buƙata,ga komai nan a ƙasa na ajiye muku.. *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh 💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ P..1️⃣3️⃣ *BOOK ONE* ~PAID~ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow my account* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ༼✿☯⁠‿⁠☯⁠✿༽ Bulalar Ummah ta riƙe ganin ya fara zubawa LINA ita,kafin ta rufe baki, idanun sa a rufe dan ko amsar tambayar ta ya kasa bata.Cike da ɓacin rai itama ta ƙara dafe bulalar tana furta '' Me kake shirin aikatawa,duk hukuncin da kake yi mata bai yi ba sai an haɗa da bulala yau she ma ka samo wannan ne,me ya sa ba zaka saka ta kamun kunne ba kamar yadda ka saba ". Sakin Bulalar tayi tana kallon sa idanun sa sun kaɗa sunyi Jawur zuciyar sa ta motsa dan har jijiyoyin kan sa sun tashi kamar wanda yayi faɗa da mazaje, ta gefe ɗaya LINA kuka take tayi,na abun da ta aikata bama bulalar da yayi mata ba dan bata jin zafin bulala sai ta ɓace,ta takure waje ɗaya,ita kuwa REENA baccin azaba ya kwashe ta tuni dan haka hayaniyar ma ba ta ji ba. Ƙasa Iya furta komai yayi sai ma sauke kan sa ƙasa kafin ya faki idon Ummah ya cigaba da zuba mata ita a duk inda ya ga shuɗin ta saboda yadda idanun suka sake rufewa dan bai ga alamar taji jiki ba. Cike da tashin hankali Ummah ta yanka masa marin da sai da ya kusa ɗauke wuta.Amma ko gizau sai ma rufe idanun sa da yayi yana sauke ajiyar zuciya,yana haɗiyar baƙin ciki bibbiyu zuciyar sa ji yake kamar tayi bindiga ta fasa ƙirjin sa asan baƙin cikin dake mamaye da ruhin sa. Bulalar ta ƙwace da sauri ran ta ɓace tana batun bashi damar fita kawai ya sa kai ya fice cike da mugun sauri kamar zai yi tuntuɓe.Kukan LINA har tsakiyar zuciyar sa sai dai bai da damar hana kan sa hukunta ƙanwar ta sa saboda abun na ta yayi yawa lamarin ya fara bashi tsoro ace yan biyu ciki ɗaya kamar Annabi da kafiri babu wani sassauci ko ragi. Part ɗin ya bari gaba ɗaya yana tafiya kamar ya tashi sama. Bai zame ko ina ba sai asalin na sa part ɗin.Cike da zafi da ƙunar rai ya sakarwa kan sa shower yana sauke ajiyar zuciya tare da huci mai zafi da raɗaɗi.Sai da ruwan suka shiga jikin sa sosai har kayan jikin sa sun fara ɗiga sannan ya kashe yana ɗauro wanka tare da fitowa sharp sharp yayi shirin sa cikin uniform na sa da suka ƙara masa kyau bai yi sallama da kowa ba ya haɗa abun buƙatar sa ya fice tare da sauran yaran sa.Dan gaba ɗaya ji yayi baya buƙatar ganin komai daya danganci estate ɗin musamman ya san Ummah sai tayi fushi da shi dan haka ba zai iya jura ba Gara yayi gaba yayi ba zai iya jurar abubuwa da dama ba. A ɓangaren Ummah yarda bulalar tayi cike da tausayin LINA ta rungume ta dan ta daku kukan ma ta daina sai zubar da hawaye da take yi a galabaice dan ta ma fi REENA da kuwa.Toilet Ummah ta faɗa kamar zata zubar da hawaye ta haɗa mata ruwan wanka masu ɗan ɗimi sannan ta tada ita da taimakon ta suka shige toilet ta bar ta ta yi wanka da kan ta dan taƙi yadda Ummah ta mata wanda sai abun ya ba ummah dariya wanda ka raina da hannun ka gashi har yanzu bai wuce wanka ba shine da ɓoye ɓoye kamar wani girman tayi.fitowa Ummah tayi ta bar ta tayi wankan Sannan sannan ta haɗa mata shayi mai kauri tare da bada umurnin kawo mata bread da sauran kayan karin kumallo masu kyau. Tana fitowa ta sanya kaya masu ɗan nauyi saboda zazzaɓi da ya fara saukar mata a jiki na azaba.Da dabara Ummah ta shayar da ita shayin saboda sai wani sabon babin kuka ta buɗe mai cike da shagwaɓa.Maganin da Ummah ta bata kuwa ta kanne shi ƙasan harshe ita kuwa Ummah ganin ta kora ruwa bayan ta saka maganin ba tare da wani musu ba duk da tayi mamaki sai ta ji daɗi dan ta san yadda ake rigima da ita kan magani.Rufa mata tattausan duvet Ummah tayi bayan ta hau gadon da ta so ta zille wai ɗakin ta take so da ƙyar Ummah ta rarrashe ta ta zauna kusa da yar uwar ta zata ji daɗi idan ta farka.Fitar Ummah keda wuya ta buɗe idanun ta tare da ciro ƙwayar maganin da ta ɓoye a ƙasan harshen na ta.chan ƙasan katifa ta ɗaga kaɗan ta sanya shi dan har ya fara watsewa.Ya ƙune fuskar ta tayi kafin ta miƙe ta shige toilet ta kuskure bakin ta. Sai a lokacin ta kallo kan ta gaban madubi yadda jikin ta yayi Jawur abunka ga fata mai haske ko ina shatin bulala ne.Hawaye ta ji sun silalo mata masu zafi da ƙuna,babu ma abun da ya ƙara gudun kukan ta tuno yadda ta mayar da REENA cikin ƙanƙanin lokaci ita kan ta abun ya bata tsoro dan idanun ta a rufe suke bata san ta aikata ba sai dai Allah ya kawo Ummah da ƙila sai dai ta kashe yar uwar ta,da ita ma ko sai dai ta kashe kan ta.Ta bawa kan ta amsa daga tunanin na ta. Sai da tayi kukan ta na ƙuruciya da tausayin yar uwar ta kafin ta fito ta je ta kwanta take bacci ya kwashe ta mai nauyi. ***" Ɗan Baiwa Wallahi ina cikin farin ciki dan haka na kasa haƙura na same ka,ɗan baiwa aikin nan bai wargaje ba yana nan,babu abun da ya chanza,da kace sun je Hutu, na kasa yarda ashe dagaske ne,lallai na yarda dakai Ɗan baiwa na yi imani da kai,Lallai kai abun ruƙo ne dole na zube maka manyan chanji yau dan nuna murna ta " " ga na ka gana jajayen aljanu da baƙaƙe a yi musu yan ka a zubda jini su sha su ƙoshi yau ranar su ce hhh ta kece da dariya ". Macen da ke durƙushe gaban wani yaƙususasshen mutun mai zubin bokaye take zancen, dan babu inda yayi kama da mutanen kirki ko daga inda yake zaune zaka fahimci cewa Boka ne mai saɓon Allah mara imani dan bukkar da yake kai ita kan ta Abar kallo ce Dan upside down take kuma duk da haka rana bata kan musu sai ma wata irin inuwa da ke zagaye da rumfar mai cike da wasu irin surƙulle ɗaure ɗaure gwanin ban tsoro,ga wani irin sauti mara daɗi dake fita shi ba kuka ba shi ba dariya ba,amma matar nan babu alamar tsoro atattare da ita dan da alama ta saba da gurin kuma gurin zuwan ta ne. Dariya ya kece da ita kafin ya natsu amma dariyar ta cigaba da tashi itama kamar sabon kamu ta riƙa dariya,dariya ta ƙeta harda hawaye. Wata irin ƙwarya ya nuna mata abun da ta gani ne ya sanya ta ƙara sakin wata irin mahaukaciyar dariya harda kwantawa ƙasa. Miƙewa tayi zaune jin yana furta " Natsu " Cikin wata birkitacciyar murya mai ban tsoro. Idanun ta ta zuba masa daga cikin baƙar abayar da take saye da ita da baƙin niƙab da idanun ta kawai zaka iya hange a ciki.Cike da rashin tsoro haka take bin shi da kallo cike da azarɓaɓin son jin abun da zai furta. " Ai na faɗa Miki ta Baiwa,kin ƙi yarda,sai ma kin so ki watsa muna ƙasa,dan har sun hasala sun so a cire Miki aikin zana,amma tun da kin yi imani da mu kin sha haka muke so mu ɓace tare hhhhh ". " Kinga yadda kika ga haka haka zasu koma a duk inda suke,mai iya cire wannan aikin sai ni hhh aikin mugaye kenan,ki kwantar da hankalin ki,zai kai ga ci ". " Sai abu naga ba akwai wani duhu da yake bibiyar ki,shima zamu Miki aiki kan sa,zamu cire sa kar ki damu,Zamu bi hanyar da ta dace idan ta kama muyi farfesun ɗan sabon jariri da naman alade dan mu haska wannan duhun muga abun da ke cikin sa " "Ungo wannan" Ya furta yana miƙa mata wata irin gora tana ɗauke da fararen ruwa sai dai ga wasu irin halittu nan na yawo a cikin su kamar tsutsotsi. " Kin san abun da zaki yi da wannan ɗin ba sai an maimaita Miki ba ki tabbata komai ya tafi yadda ya dace ". " An gama Ɗan Baiwa,ɗan gado kafi gado,ko waya ja da kai sai ya bar duniya aikin ka ya ci dubu,babu abun da ke karya ka sai ikon ka,shine ajalin ka ". Tana gama zancen ta juya bayan ta ta ɓace ɓatt tana sakin wata irin dariya ta ban tsoro. 。⁠☬☬⁠。☬。⁠☬☬⁠。 Tun da ya dawo daga ɗakin motsa jiki yaga fitar sa tare da yaran na sa cike da mamaki ya ke bin motocin da kallo har suka bar harabar gidan aka wangale musu gate.Kai ya girgiza dan ya san bai saba hakan ba yayi kwana ɗaya ya wuce ba tare da yayi wa kowa sallama ba.Tunanin da ya shigo sa na ƙila kiran gaggawa ne ya samu hakan ya sa ya cigaba da tafiyar sa yana sauke gajiyar da ya kwaso tare da ta tsufa da take tattare da jikin sa.Hankalin sa ne ya kasa kwantawa hakan ya sa yana shiga Sashen na su bayan ya zauna ya ce " Uwani bani waya ta ". Miƙa masa wayar tayi tare da ruwan sha da ta ajiye ɗauko masa masu ɗan ɗimi saboda an hana sa shan abu mai sanyi haka ma an saka shi yawan motsa jiki saboda sugar dake barazana a jikin sa. " Ina kwana Yaya ". "Lafiya lau,An tashi lafiya ya ƙarfin jiki " Sir ya amsa daga chan ɓangaren dan ba su samu haɗuwa masallaci ba ɗazu. " Alhamdulillah yaya jiki sai na tsufan mu na ji sauƙi ". Murmushi Sir yayi yana furta " Allah ya sa mu yi kyakkwan ƙarshe ya raya muna zuri'ar mu ". "Amin" Ya amsa harda Uwani da ke gefen sa dan wayar handsfree take. " Yawwa Yaya nace ko Lafiya,naga BILALU ya fice yanzun nan bayan na baro wajen ɗan motsa jikin Nan da Turawan chan suka tilas ta mini,kuma kamar tafiyar sauri ce zai yi " " Shi BILALUn ai bai yi Sallama da kowa ba tun da har kai ma ba ka yi magana dashi ba,to Allah ya sa lafiya,ta yuyu tafiyar gaggawa ce a ka kira sa,amma na san ko ta waya ya na sanar wa ko ɗayan mu ne,bar shi zuwa anjima zan kira sa muji ko lafiya idan bai kira ba. " Sallama suka yi kowa na fatan Allah ya sa lafiya ce ta fitar da BILAL gidan tun da safe ba tare da yayi sallama da kowa ba... 乁✿༼✿☯⁠‿⁠☯⁠✿⁠༽✿ㄏ A ɓangaren Ummah wanka ta fito tsaf ta shirya cikin shigar ta mai kyau da ke ƙara fitar da ainihin kyaun ta da kamala. Falo ta dawo cike da bada umurni take bawa su rabi umurnin abun da take son a girkawa su REENA wanda ta san favorite na su dan in ba haka ba ta san da ƙyar su ci abin ci. Class teacher ta su ta kira bayan ta zauna akan cusion cike da mutun ta wa suka gaisa sannan tayi mata bayanin rashin zuwan na su LINA school sun tashi babu lafiya gaba ɗayan su.Cike da tausaya wa malamar ta musu Allah ya sauƙaƙa tare da furta dama yan biyu haka suke ai ciwo lokaci ɗaya suke yin sa bare su da suke Identical.Sallama suka yi ta ajiye wayar. Miƙewa tayi tana barin wayar nan tare da shigewa kitchen dan ganin yadda suke gudanar da komai dan ta san BILAL bai da jimirin yunwar safe. 🕳️🪐🕳️🪐 A ɓangaren SHATOU kuwa da ido tsaitsaye take kallon motocin har suka fice daga makarantar, kallon da ya jefa mata yanzu bayan miƙewar sa na dawo mata,duk da kallo ne na ƙasan ido ta san na rainin wayau ne bai san dama shima cike take dashi ba,Hararar bayan sa tayi wanda shi Mubarak ya gani kai kawai ya girgiza lamarin yarinyar na bashi tsoro bata da tsoro ko kaɗan,sai dai abun da bai sani ba Hararar a kan idanun sa ta sauka saboda ya ɗan juya kaɗan yana kallon yadda take durƙushe babu tsoro akan fuskar ta,kuma ya san cewa dole zasu iya hukun Tata tun da malaman ta ne. Suna fita ta miƙe tana kakkaɓe hijab ɗin ta cike da ɓacin rai take furta " Wallahi Iro bai isa ya saka ni abu nayi ba ko yanzu biyayya ce nayi ga Malan Bello,amma wallahi Indan iro ne sai dai a yi gunduwa gunduwa da nama na ". Duka zuba mata idanu suka yi musamman ma iro da malam Bello da bata taɓa haɗa sa da ita ba yana dai jin labarin rashin jin ta idan wasu daga cikin ɗalibbai suka shiga gonar ta koda kuwa wayen da suka wuce ta da aji ne. Iro da ke cike da Haushin ta ne har yanzu gashi malam Yusi ya ƙi cewa komai ya ce " Dan Allah a hukun Tata,bata jin magana,Ni bari muje na isar da saƙo ga mai gari ". Yana gama zancen yan gayar sa su huɗu da ya zaɓo ya zo da su suka take masa baya yana ƙara bubbuɗawa yana ƙwambo yadda kuka san marigayi ɗan Ibro na yi in ya fito mai kuɗi.Har wani doro yake yi. Sai dai ko tako biyar bai yi ba yaji ta kece da wata irin dariyar wadda ta fi ta ɗazu domin har da kwanta wa tayi tare da dafe ciki.Tsaye yayi kafin ya juyo ya Kalle ta ya je fa mata harara tare da ƙyafci sannan ya gyaɗa kai irin na zamu haɗu. Ita kuwa SHATOU da ta ɗago ta ƙara kallon sa ne ta ƙara sakin wata dariyar tana nuna sa.Dan harda ƙeta take haɗawa saboda abun da yayi mata ko ta hakan ta bar shi ta san ta rage hasahi,dan haka take yi ta ƙure sa.Dan tun bata nuna kai tsaye dashi take ba har ta fito fili harda nunen sa da tayi yanzu. Malam Yusi shi kan shi ya dara Badan komai ba sai dan ita kan ta dariyar ta Shatou abun a dara ce musamman idan ka kalli wanda take yiwa dariyar sai ka kasa riƙe dariyar ka yadda yake zuba ƙwanbo da kuri da yayi masa yawa harda wani aski aka yi mai kama da ci chan ci chan gefe gefe an chanye aka bar tsaka da yar suma sai dai ba da yawa ba. Barin makarantar iro yayi ran sa jagule su kuwa yan zugar sa sai zuga sa suke yi na yayi maganin ta,ko ya basu dama in suka gamu da ita hanya su karya ta.Sai dai bai ce musu komai ba shi kaɗai ya san irin abun da yake tsara wa a ransa da zai yi mata. Ita kuwa SHATOU yana fita ganin tabar hango ƙurar sa ta miƙe tana mayar da sauran dariyar da ta yi mata saura kafin ta fashe da kuka dan ta san tsaf za,a iya hukun ta ta gata da tsoron bulala bata son abun da zai taɓa fatar ta. Malam yusi da su Malam Bello da duk wanda ke gurin idanu suka zuba mata ganin ta fashe da kuka na ƙwarai lokaci ɗaya kamar ba ita ta gama dariyar ƙeta ba yanzu.Sai abun ya bawa Malam Bello dariya ma dan haka ya cewa malam Yusi a bawa SHATOU aiki kawai gobe tayi shara.Hankalin malam yusi kwantawa yayi dan dama bai san ta yadda zai hana malam Bello zane ta ba dan bai iya duka ba in yaro ya shiga hannun sa gashi shi an bashi saƙo mai kama da amana. Sauran ya ran kuwa gida aka ce kowa ya koma dan sun aikatu.SHATOU kawai aka bari kafin itama aka sallame ta bayan malam yusi ya rarrashe ta. Idanun ta ta goge kafin ta sakarwa malam Bello harara ta gefen ido wanda malam yusi ya gani sai dai kawai ya girgiza kan sa. A chan bakin makaranta ta tarar da su Amina da Bibu da ya kasa tsaye sai zagaye yake yi hankalin sa tashe. Fitowa tayi tana Murmushi kamar ba ita ta gama kuka ba.Zuba mata idanu suka yi kowannen su na kallon ta baki sake kafin suma su saki murmushi.Haɗe rai tayi ganin dukkanin su suna murmushi basu ma ji Haushin abun da aka yi mata ba kenan. Gaba tayi bata kula kowa suko cikin sauri dukkanin su,suka bi bayan ta suna kiran sunan ta kafin ta zunduma a guje,suma suka mara mata baya shi Bibu ma sai da yayi dariya kamar kar ya daina sannan ya bi bayan su dan lamarin yayar ta sa na yau dariya yake ba sa mace kamar mai aljanu...✍️ *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ P..1️⃣4️⃣ *BOOK ONE* ~PAID~ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow my accounts* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* Tunda suka kamo hanyar barin ƙauyen yake jan hayaƙin Shisha kamar zai shanye sa duka. Mubarak ne ya Kalle shi ta cikin madubi cike da ɗan girmamawa kamar yadda shima yake basa na sa girman ya furta " Hayaƙin nan yayi yawa zai iya tada maka da ciwon ka fa ".Idanun sa ya ɗago ya kalli Mubarak kafin ya lumshe idanun sa sannan ya cigaba da zuƙaar abun sa dan kan sa yake jin yana cigaba da sara masa kamar zai rabe gida biyu. Sai da ya zuƙa iya zuƙa sannan ya cire ta ya tura ta mazaunin ta inda ya Fiddo da ita. " Yallaɓai MAHAJ " Mubarak ya ambaci sunan sa dan ganin ko lafiya ganin yadda yake sauke numfashi. " My name is MAHAJ not yallaɓai MAHAJ ". Ɗan shiru yayi kamar ba zai yi magana ba sannan ya ƙara cewa cikin shaƙaƙƙiyar Muryar sa mai sanyi dan ta cikin maƙoshi yayi zancen. " This is the last time da zan gyara maka sunan nan Muby,I really don't like yallaɓai,yallaɓai is for the elders, Right". Mubarak dai murmushi yayi kawai yana satar kallon sa ta madubi kafin ya furta " noted sir ". Idanun sa ya ware ya kalli Mubarak da ke tuƙin sa hankali kwance,yana Murmushi. Rufe idanun sa kawai yayi bai furta komai ba.Dan ya fahimci Mubarak ba zai iya kiran sa da sunan sa ba,duk da kuwa ya girme sa dan zai bashi shekara kusan biyar,amma bai da abokin magana bayan mahaifin sa,sai Mubarak,sai ko ɗan uwan sa idan yana ƙasar,ko in sun haɗu duk da ba magana yake yi ba sosai daga uhmm Yes,sai ok,a'a,sune kalaman da yafi an bata,sai abun da yafi ƙwarewa da shi zancen kurame dan tun Mubarak bai gane wa har ya fara ganewa kuma ya fahimci haka halin sa yake na miskalanci. Haka suka isa cikin garin Abuja a cikin a katafaren gidan na su dake cikin ministers estate ginukan ne na alfarma sun tsaru iya tsaruwa kamar ba Nigeria ba ko ina Naira ta zaunu.Babu bincike ganin tambarin motocin aka bar su suka shige ana ɗaga masa hannu dan sun san ko waye ne ya shigo,dama dokar estate ɗin ce in ka fita ka dawo sai an bincike ka,ko baƙo aka yi sai ya sha bincike har ya gaji kafin a bar shi ya shiga.Dokar kenan amma saboda shine Babu mai tare sa dan sun san fitinannen yaro ne da baya daukar raini ko kaɗan Dan yanzu sai ya ce fitowa zai yi ya sa a chanja musu gurin zama,dan ɗan gata ne ta ko ina duk wasu ministoci dake zagaye da su suna ji dashi saboda akwai basira da dattako a gare sa duk da baida wasu shekaru kuma a hakan yana da na sa share a cikin estate ɗin dan babban ɗan kasuwa ne bai zauna haka ba,ganin mahaifin sa na dashi,ya tara dukiyar da shi kan sa yanzu ba bi ta kan ta yake yi ba a wannan shekarun na sa.Yanzu haka yana karatu ya kusa haɗa masters ɗin sa na farko,duka a fannin business dan dama burin sa ne yin business dashi ya tashi tun yana ƙarami,har ya samu goyon bayan mahaifin sa,ta fannin karatun sa.Mubarak shine wanda mahaifin sa ya taɓa haɗuwa dashi a wata tafiya da yayi yana cikin halin taimako sai ya taho dashi nan ya taimake sa, sai ya damƙa masa kula da Mahaj da kasancewar su tare tun yana shekara sha biyar a duniya a haka har suka fara sabawa tun bai sake dashi ba har ya sake dashi,kuma kowannen su na girmama wanin sa da bashi matsayin sa,mafi yawan duk tafiyar da zasu tare suke yin ta har ta karatu mubarak dashi a school ɗaya suka yi,sai dai shi Mubarak tun da ya haɗa degree na sa yace ya gama boko duk yadda ko MAHAJ ɗin ya so ya ga yayi ya ce kan sa ba zai iya ɗauka ba. Dai dai wani ƙaton gate mai kama da wata duniya guda aka wangale musu gate bayan ganin motocin na su ta cikin CCTV dake aiki anan wajen da ciki wanda duk wanda zai shigo ana kallon sa kafin a tantance sa. Haka motocin suka shige cikin ƙaton compound ɗin na alfarma dake ɗauke da shuke shuke masu kyau wasu ganyayyakin daga nin su Bama na ƙasar nan bane yanayin ginin yayi kama dana turawa komai atsare dai dai motocin sun gama parking ya fito ba tare da ya jira ma an buɗe masa ba.Bai yi magana da kowa ba sai kallon Mubarak da yayi kafin ficewar sa a motar dan haka kai ya sunkuyar kawai alamar ya gane.Cikin ƙaton falon ya shige da yar ƙaramar Sallamar sa yana ya mutsar fuskar sa mai cike da rashin annuri da ta haɗe tun bayan shigowar su cikin estate ɗin.Raɓa su yayi ya wuce cike da izza Ganin hakan ya sa bai iya ce masa komai ba sai ma cigaba da maganar sa da yayi da mutanen da yake tare dasu,ba kowa bane face abokan sa yan siyasa da suke tattaunawa kan wani isssue na harkan siyasar su." Ko zaka je ka duba sa kamar ba lafiya ba Hon gagara " ? Babban mutumin da ke zaune daga cikin mutanen uku ya furta ganin hankalin sa ya rabu gida biyu.Numfashi farin mutumin da aka kira Hon Gagara ya sauke a hankali yana bin bayan sa da murmushi.Kafin ya furta " ƙyale sa gajiya ce kawai kasan yadda abun yake,Nima ina son na ɗan huta shine na tura sa,dan dama ya kama ta ya fara shiga mutane ina tsoron wani abu ya kamu da wani ciwo ne kasan Indai ya zo ƙasar nan Hutu haka nake fama dashi baya iya zuwa ko ina ". Shigowar Mubarak ce ta dakatar dashi daga maganar da yake yi. Har ƙasa Mubarak ya duƙa ya gaishe su cike da girmamawa.Cikin jin daɗi Hon Gagara yayi masa sannu da zuwa tare da yan tambayoyin ya komai ya wakana nan take kuwa Mubarak ya zayyane masa komai dan ya san dama shi ne zai yi aikin ba dai shi ba. " Dama kuma shine zai yi aikin a cikin aljihun sa amma yace kar a faɗa maka ". Mubarak ya kai ƙarshen zancen yana kallon ƙofar inda ya san zai iya ɓullowa kasancewar ɗakin sa yana da ƙofofi daban daban. " Kai Masha ALLAH " Hon Marafa ya furta yana cewa " Allah yayi albarka gaskiya koda yaushe ina taya ka farin cikin samun wannan yaro,dama zai iya shiga siyasar mu da munci riba sosai dan daga nin sa zai iya da kowane Shege ".Ya kai ƙarshen zancen yana dariya. Hon Gagara da fuskar shi ta kasa daina bayyanar da murmushi ne ya girgiza kan sa cike da ƙaunar ɗan na sa ya furta " Baya ra'ayin ta da a ce yana da dama Ni kaina ba zan yi ta ba,sai dai yana girmama abun da nake so kamar yadda nake girmama na sa a matsayi na na mahaifin sa dan haka ma tun farko ban taɓa kwaɗai ta masa ba tunda ya nuna mini nikaina baya son ta da ni ". Su ma sauran murmushi suka yi suna jinjina kai. Mubarak kuwa miƙewa yayi cike da Murmushi. Yayi musu sallama Sannan ya miƙe ya bi bayan Mahaj ɗin da wayoyin sa a hannun sa.Upstairs ne na alfarma mai kyau ya take da ɗan sauri. Wata haɗaɗdiyar ƙofa ce ta alfarma ya bi inda sai da yayi yar tafiya sannan ya isa dai dai wata ƙofar mai kyau da tsari.Buɗe ta yayi a hankali.Ƙamshin ɗakin ne da ya daki Hancin sa ya san ya sa rufe idanun sa dan jin kamar an yi masa buɗaɗen turare bayan fitar su,wanda bai rasa na saba da yawan gyaran da yake samu daga wani daga cikin masu kula dashi. Sanyi ta ko ina lif lif sai tashin ƙamshi yake yi.Kasancewar babu wani shamaki tsakanin su hakan ya sa ya shige ciki da sallama ɗauke a bakin sa,bayan buɗe ƙofar. Tsitt haka ɗakin yake dama bai yi zaton zai same sa nan ba hakan ya sa ya a jiye masa su nan ba tare da ya neme sa ba. Ajiye komai yayi sannan ya fice bayan ya rufo masa ƙofar. 🔏🔏🔏 SHATOU bata da kata ba sai da ta yi gudu mai nisa Sannan ta dakata tana sauke numfashi tare da bin su da kallo daga nesa dan ta musu nisa sosai,kawo War su kusa da ita ya sa ta sakin dariya cike da ƙuruciya ta shammace su ta ƙara falfalawa a guje tana waigen su.Su Amina kuwa a gajiye kowannen su ya dakata suna kallon juna,Kafin suka mara mata baya suna dariya.Dan sun fahimci yan wasar ne suka motsa take son wahalar da su.Dan ta kan yi musu haka a wasu lokuttan.A ɓangaren SHATOU kuwa ɗan wannan lokacin ta ji ta tsinci kan ta cikin nishaɗi kamar ba ita ta gama kuka ba ɗazu.Da gangan ta bi gefen da ta san abokan Iro suna zama duk da ba hanyar ta bace aiko aguje ta biyo hanyar tana kururuwa " Kura! Kura ! kura! " da farko basu tsorata ba sai dai ganin yadda take waigen bayan ta sai suka yi zaton wajen farauta ta kuskure ta biyo ta,duk da sun gan ta da uniform,A guje suka miƙe dukkanin su ganin Dagske take yi dan har da hawayen ƙarya irin na tashin hankali, A guje suka miƙe har wasu na faɗawa kan wasu ba su kaɗai ba har majalisar dattawa dake chan wata rumfa zaune a guje ko wannen su ya fara neman hanyar gudu dan tsira da rayuwar sa,tun da har ita yar mafarauci ta iya gudu su mai zai su tsaya a guje, aiko akayi ta kururuwa ana faɗawa gidaje.Iro da ya kamo hanyar zuwa majalisar ta su bayan isar da saƙon ga mahaifin sa ya an kara da abun sa ke faruwa ganin mutane na ta gudu ana kura ta gudo daga daji ta biyo SHATOU da farko tsaye yayi bai yarda ba sai dai bayan hango ta a guje itama kan ta hakan ya sa ya auna a masifar gudu yana waigen bayan sa cike da wani mugun tsoro da ya dirar sa tare da tsine ma shatou da ta jaji ɓo musu bala'i.Shatou kuwa da ta hango sa ƙara ƙarfin gudun ta tayi tana sakin ƙarar neman taimako tana haɗiye dariyar ta wadda take saki idan ta faki idon jama,a masu gudu.Mai gari da jama'ar sa dake ƙofar gida cike da farin cikin saƙon da ya same sa ya ga Iro a guje yana faɗin kura ta yi ɓatan hanya daga daji ta biyo SHATOUn Jibril farauta yadda zasu gane kai tsaye aiko ko rufe baki bai yi gaba ɗaya suka runtuma a guje suna neman gurin ɓoyo. Daga mai gari har yan fadar sa wani ɗaki suka rufe suka shige duk uban zafin da ake tsulawa a gari.Tsit haka garin ya koma kamar anyi mutuwa. Cike da natsuwa ta shiga gida cike da murmushi a kan fuskar ta kamar an biya mata aikin hajji dan wani daɗi take ji musamman ganin yadda ta rama abun da Iro yayi mata cikin ruwan sanyi duk da har yanzu nata huce ba amma kina komai ta saka shi tiƙar gudu.. Ummah ce ta ke ta kallon baki sake kafin ta iya furta wani abu sai ga su Bibu sun faɗo a guje su huɗu. Amina ce ta baya saboda ta gaji sosai. Shessheka suka dinga yi a gajiye.Inni da ɗai ɗai take bin su da kallo ganin yadda kowannen su yake a hargitse cike da tsoro gashi da alama gudu ne Suka yi bana wasa ba. Kallon SHATOU suka dinga yi harda leƙen ta suna cigaba da sauke numfashi. " Me yake faruwa ne,ku ka shigo gidan wani hargitse kuma daban daban " .? Inna ni tayi tambayar kafin su bata amsa sai ga Baffa na ya shigo fuskar sa cike da tashin hankali mai girma.Dan ko sallama bai samu ya yi ba sai ganin sa suka yi. Idanu ya zuba ma SHATOU ganin ta hankali kwance sai murmushi take saki, kafin ya mayar da idanun sa kan su Bibu suma sai dai su tasu a tashe take sai nishi suke saukewa. "Allah yasa lafiya,Baffan su "?Cewar Inna ni Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " Babu komai dama na zo duba wani abu ne ". Yayi zancen yana shigewa ɗakin sa da sauri cike da jiran ta kwana dan yasan magana ce Babba shatou ta janyo dan yana kasuwa yaga ana guje guje.ya tambaya lafiya aka sanar masa da yar sa ce kura ta biyo yanzu haka kowa neman wurin ɓuya yake yi dan haka babu ɓata lokaci ya rufe yayo gida cike da tashin hankalin da ya kasa barin ƙwaƙwalwar sa da mamaki dan ya san dai Shatou na makaranta ya za,ayi ta je gurin farauta duk da ya san halin ta tana iya zamewa ta tafi tun da wani lokacin ta kan yi hakan,wannan tunanin yasa ya zo gida cike da sauri. Sai dai bayan shigowar sa gidan ya gan ta zaune kan yar guntuwar kujera hankalin ta kwance ta cire hijab ɗin,tana wasa da jelar gashin ta da ya sauko har kan kafaɗun ta. Su ko su Bibu kowanensu su shima hankali tashe kamar yadda yake.Numfashi ya sauke yana neman mafitar wannan case ɗin domin kuwa ya sa akwai matsala Babba saboda SHATOU garin ta taɓa gaba ɗaya yau. A tsakar gida kuwa kallon tuhuma dukkanin su Inna ni take bin su dashi tana son karantar wani abu kafin a hankali jikin ta mace ta ce " Amina me ta aikata " ? Shiru Amina tayi fuskar ta cike da damuwa ganin yadda SHATOU ta marairaice mata ta san faɗin zai iya zame mata illa. Kan Ramata Inna ni ta koma dan ta ji ko zata samu amsar tambayar ta sai dai itama ɗin shiru ce sai kai da ta sunkuyar ƙasa ita fuskar ta na son bayyanar da dariya saboda tuno yadda ta ga mutane nata guje guje harda manya masu ƙaton tumbi na ƙauyen su,koda suka iso hanyar da shatou ta bi basu ga ƙurar ta ba sai dai sun samu labarin kura ta biyo ta daga wajen farauta,dan haka tun chan suka fara sheƙa dariya dan duk sun san ƙarya ne,tun da tare suke da ita.Sai dai saboda sanin da suka yi akwai matsala ya sa suka yo gida cikin sauri dan sun san akwai rigima Babba zasu yiwa SHATOU abun da zai saka ta farin ciki dan haka suka yanke shawarar abun da zasu ce,ba zasu taɓa ƙarya ta ta ba,ba kurar bace zasu ma bada shedu. Ƙatuwar murya ce take rangaɗa sallama a ƙofar gidan hakan ya sa da sauri Inna ni ta kalli gefen SHATOU dake zaune hankalin ta tashe fuskar ta na cigaba da bayyanar da kyakkyawan murmushin ta dan dariya ce ke cin ta matuƙa amma tana ɓoye ta saboda Inna ni sai take mazewa tayi murmushi babu wanda take tunowa face Iro yadda ta hango sa yana gudun ceton rai yana kururuwa shima a tsorace ta san ko haka ta tsaya wallahi ta gama da case ɗin shi dan haka take ta sakin murmushi kafin ta samu damar zubar da kwandon dariyar itada su Amina dan duk ta san akwai dariya a cikin ta. Wata Sallamar ce aka ƙara rangaɗawa kafin aka sanar da saƙon mai gari " mai gari na son ganin Jibril Farauta da yar sa a gaban fadar sa yanzu yanzu ,idan kuma ba,a zo tare da ita ba,akwai hukunci mai tsanani bayan wanda aka tanadar mata " Shine abun da mai kawo saƙon ya furta yana gamawa ya juyawar sa fada sanin cewa saƙon ya isa dan har maƙota ma wasu sun leƙo yan gulma a ji abun da ta sake yi yanzu kuma. Baffa na cike da sauri ya fito dama a shirye yake ita kuwa SHATOU da komai ya shiga kunnen ta bata motsa ba illa ma satar kallon Inna ni da take yi wadda fuskar ta ta sauya lokaci ɗaya tashin hankali ya bayyanar mata wanda ta rasa gane dalilin da ya sa duk case ya haɗa da ita sai ta zamo abun tausayi. Hannun ta Baffa na ya riƙo ya miƙar da ita tsaye ya saka mata hijab ɗin ta kafin bai cewa Inna ni komai ba ya fice daga gidan suma su Amina bayan su suka bi dan tabbatar da alƙwarin da suka yi na fitar da ita. *** Koda su rabi suka gama jera komai na breakfast ɗin a gaban idon ta,sannan ta fice ta tayar da su LINA da kowaccen su jikin ta yayi tsami babu ma kamar LINA. Wanka ta taimaka musu suka sake yi kafin suka shirya suka fito.Falon sai dai cikin su babu wanda ya kula wani ita REENA lamarin LINA tsoro ya bata dan haka ta sha jinin jikin ta cike da tsoron sake shan wani dukan,ita kuwa LINA tana son yi mata magana sai dai ganin kamar fushi take yi da ita sai ta kasa. Wayar sa take ta faman kira bata shiga dan haka ta aika REENA ta kira sa daga sashen sa azaton ta yana chan,duk da tayi mamakin abun da zai hana sa samun Chaji su da suke da wuta koda yaushe dan ta su ce ta kan su bata gwamnati ba,Babban injin na su babu inda baya bayar da isasshen wuta mai kyau koda yaushe. Miƙewar REENA da yar kumburarriyar fuskar ta zata je kiran na sa sai ga Rabi tana furta " ai ina ga Ƙaramin mai gida ya koma gurin aikin sa dan zan shigo nan na gan sa an da ƙatuwar jakar da yake zuwa da ita nan,suka shiga Mota shida wayen nan sojojin nasa,an buɗe musu gate sun fita,tafiyar ma kamar ta sauri ce dan motocin a guje suka fice ". Idanu Ummah ta sakar mata kafin ta furta " kin tabbatar da abun da kika faɗa kuwa rabi". " Allah na gani da ido na,ki ma tambayi Baba Tsoho na Uwani kiji "Kai ta jinjina cike da mamaki kafin cikin sanyin da jikin ta yayi ta bawa REENA Umurnin dawo wa ta zauna.Ita kan ta REENA Jikin ta yayi wani mugun sanyi taji kamar ta saka kuka lokacin. LINA kuwa ji tayi zaman dinning ɗin ya gagare ta dan dama bata so fitowa ba amma saboda tsoron hukuncin sa ya sa ta fito,yanzu kuma gashi saboda ita ya bar gida ba tare da ya gama hutun sa ba,ko tsararabar su basu karɓa da yake basu bayan kwana biyu da Dawowar sa ba. Hawaye ne suka cika mata ido dan itama tasan wannan karon a bun yayi yawa dole yayi fushi da ita. Serving nasu rabi tayi ƙamar yadda ta san kowa na buƙata kafin ta bar gurin tana komawa kitchen cigaba da ayyukan dake gaban su. Kowanne su babu mai jin test na komai dan LINA har ta miƙe ummah ta mayar da ita dan haka baki ture tayi ta cusa bread da ƙwai a baki suka ɗai ta ci duk tarin abun da ke kan dinning dan bata cikin mood ji take ya'yan na su ya ƙara tsanar ta fiye da koyaushe akan wannan case dan zuciyar ta take mata wani irin ƙunci da zafi.✍️ WANNAN LABARI NA KUƊI NE A MANHAJAR WAHTSAPP *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Commente,and like pls 🙏 *_Typing_* *💋KURMAN ƘADDARA💋* *©®Faiza Almustapha Murai* *FA'EEH BG*✍️ P..1️⃣5️⃣ *BOOK ONE* ~PAID~ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* Tun da suka kama hanyar zuwa fadar mai gari take ta waswasin yadda zata tsara mai gari a yarda a zancen ta dan ta san wasu munafukai sun je sun ƙarya ta maganar kurar. Har suka isa bata tantance ba saboda tunani da ta take ta faman yi yadda zata fita ba tare da an gane ba. Zama suka yi gurin da yake cike da jama'a dan mutanen gari sun cika wajen saboda har da su suka kawo ƙarar ta dan sun samu labarin ƙarya ce tsantsarta SHATOU ta ke yi hasalima daga makaranta take bada ga wurin farauta ba. Kan ta ta sauke ƙasa bayan ƙarewa duk jama'ar dake wajen kallo kafin ta saki wani Shegen Murmushi tuno da yadda ta sako su gaba manya da ƙanana ana ta Guje guje kamar yan gudun hijira.Kafin kuma wata irin dariya ta kubce mata mai ƙarfi irin wadda ta yi wa Iro aɗazu. Ba Baffa na ba har mai gari zuba mata idanu suka yi suna kallon ikon Allah kafin kuma,wani ɗan kazagin mai gari ya furta " ke yar talakawa Yar mafarauci,ki guji ɓacin ran mai gari,shirmen ki ya isa haka,da ace ba yarinya kike ba da tuni na sheƙa Miki bulaliya ta "Ya kai ƙarshen zancen yana Hararar ta tare da nuna mata ƙatuwar bulalar sa da ya Fiddo yanzu. Ƙasa da sama SHATOU ta ƙare masa kallo kafin ta zunɓure baki tana tsayar da dariyar ta badan kuma maganar sa ba sai dai kallon da Baffa na yayi mata tare da girgiza mata kan sa alamar dai yana roƙon ta daina ta natsu. Natsuwa kuwa tayi kamar ba ita ke dariya yanzu ba. Su Amina kuwa suma dariyar ke cin su sai dai ganin bulalar ya sa duk suka natsu kowa zuciyar sa cike da tsoro,dan har ɗan ƙwarin guiwar da suka zo dashi suna jin yana neman guje musu yanzu. Shiru wajen ya ɗauka tsitt ganin mai gari ya ci mur fuskar sa babu annuri kafin ya fara magana cike da ɓacin rai yau ko sallama bai yi ba da jama'a. " Malam Jibril farauta yar ka ta sanya mutanen gari na shiga duniyar tsoro mafi muni,shin ya abun yake ne,gaskiya ne ko ƙarya domin na samu labarin ba daga gurin farauta take ba daga makaranta take ,Kuma ba kowa ya sanar mini ba face Iro domin shine ya tarbi minister Kuma ya gan ta chan,babu yadda za,a ce har ta fito daga makarantar ta shiga daji "... Ya kai ƙarshen zancen yana jiran amsar da yake son samu dan wannan karon sai ya hukunta SHATOU dan shi kan sa ya ji jiki har da zawo yayi cikin wando yanzu haka yana gudawa kowane irin lokaci zai iya miƙewa gurin ya rage zafi. Da sauri Shatou ta kalli gefen da Iro yake yaci mur dan sai da ya samu gurin ɓuya sannan ya tuna da cewa makaranta ya bar SHATOU ba zai yiyu ace har ta wuce gurin farauta ba,gashi baƙi a kayi yau.Dan haka take zuciyar sa ta ayyana masa ƙarya take yi,Sai gashi ma yana cikin sanar da mai g Mai gari su buɗe ɗakin ƙarya ne wanda Alokacin mai gari ya buɗe ɗakin da wari ya cika sa fadawan sa sai shaƙar hanci suke yi sai dai babu damar nuna alamar sun ji wani abu.Sai ga mutanen gari suna cewa ƙarya ne a hukunta SHATOU da ta sanya su guje Guje domin ya yan su sun ce daga makaranta take bada ga wajen farauta ba,kuma itace ta ƙarshen fitowa makaranta,saboda ana hukun Tata.Gashi kuma har yanzu babu wanda yayi ido biyu da kurar. Numfashi Baffa na ya sauke kafin ya ce " Allah ya taimaki mai gari Shatou ba zata iya yin ƙarya ba,a dai bincika lamarin na fi tunanin daga makarantar ta wuce chan dan ta saba haka,sai ta ci karo da ita ta tsorata ne sosai dan haka ta shigo gari a hargitse saboda a kwai yarin ta kan ta ka sani,ina rokon a sassauta ma Shatou ko dan asalin yadda rayuwar ta take,ƙuruciya ce Kowane yaro da kalar ta sa ". Yana gama furucin yayi shiru zuciyar sa jagule,yana fatan ɗan mashin da ya soka ma mai gari a kai kace ya sauka dai dai inda ya ke buƙata. Mai gari shiru yayi yana kallon SHATOU kafin ya nisa yace " Kin tabbatar da kin shiga Dajin Dagske " ? Kai ta gyaɗa masa tana marairaice wa kamar irin da gaskiyar ta.A ƙasan zuciyar ta kuwa dariya ce mai ƙarfi. " Kina da shedu "? Mai gari ya ƙara furtawa yana kallon ta. Kai ta ƙara gyaɗa wa kafin ta juya ta kalli su Amina dake tsaye cirko cirko. Kallon su mai gari yayi kafin ya furta " Kun tabbatar da cewa bada ga makaranta take ba '' ? " dan idan na samu ƙarya cikin zancen ku zan sa a hukunta ku da laifin ƙarya a bulale ku,kamar yadda za,a yi mata ". Kallon kallo aka fara tsakanin Amina da su jawairiyya kowa zuciyar sa na rawa har ta Bibu sai dai yafi su ƙarfin hali dan haka ya gyaɗa kai alamarsun amince. Numfashi SHATOU dake jin kamar ta hau su da duka tayi dan yanzu su kaɗai ne zasu kashe mata case ɗin,ya kasu saboda tare take da su dole za,a yarda. " Eh ta tafi Daji dan duk da mun riga ta fita, sai da muka jira ta,kuma tana fitowa ta kama hanya,zuwa daji kuma dama tace yau zata je wajen farauta,sai nace mata kar ta je saboda za,ayi baƙi kamar yadda na samu labari a makarantar,shine da aka tashi ta wuce,mu ma muka biyo bayan ta,zuwa gida,Sai dai hankali na bai kwanta ba,dan haka na yi niyyar bin ta dajin nace su Amina su wuce gida,nabi bayan ta sai dai kafin ma na ƙara wani tako muka hango ta a Guje,kuma na san duk abunda ya saka Adda SHATOU a tsoro babba ne,dan ta yuyu mafaɗaciyar kura ta haɗu da ita ta tsorata shine ta yo gari ".Yana kai ƙarshen zancen yayi shiru. Kowa dake wajen ya ji ya gamsu sai yan kaɗan daga cikin su irin su Iro da su Zaidu . Amina ce ta ƙara da cewa" ai ni na riƙa mata jakar ta gata nan wajen har da kayan farautar ta na ciki ma da ta manta da su ". Ta Fiddo da kibiyar tana nunawa mai gari. Su jawairiyya Nana ta zancen suka yi irin na Bibu.Kafin wajen yayi tsit bayan ɗan cecekucen da aka fara.Wasu na furta Baffa na ya daina barin ta ai bai dace ba tana mace ma tana shiga daji farauta ,yanzu da kurar ta mata illa fa masu tausayi ke wannan zancen musamman ganin yadda SHATOU ke hawaye irin na tana cikin tsoro har yanzu. Kafin ta kware ɗan ƙaramin bakin ta ta fashe da kuka tana furta " Baffa nidai mu bar garin nan,kar kurar nan ta zo har gida ta chanye ni,dan ta ga fuska na " . Wata sabuwa Baffa na ya furta a ransa duk da ya san shirme ne irin na ta da rashin jin da yake hawa kan ta yanzu. " Yi shiru ba zata dawo ba kinji zan je na farauto ta hankalin ki ya kwanta shikenan ". Kai SHATOU ta gyaɗa tana share hawayen ta.Su ko su Amina da su Bibu dariya ce ke cin su sai dai babu halin yi dan sun san tayi duk wannan dan kawai mutane su ƙara yarda da ita.Shiru tayi ta makure kamar yar Marainiya.Sai kuma ta bawa mai gari tausayi musamman tuno da zancen Baffa na.Jikin sa ne yayi sanyi dan haka ya yi shiru shima kafin wurin ya ƙara samun natsuwa sannan ya furta " Daga shaidun da muka samu na tabbatar da SHATOU a kan gaskiyar ta take dan haka daga yau Jibril kar ka ƙara barin ta shiga daji,haƙƙin ka ne kare wannan yarinya kamar yadda ka ɗaukar wa Allah ya yan mu amana ne a gare mu,Dan haka ka kula da kyau,Na san ko ban bincika ba A'i na cikin tashin hankali a yau dan haka a kula da kyau,Shatou a daina shiga daji kinji Allah ya tsare gaba ". Zancen mai gari. Tun da ya fara zancen Baffa na yake murmushi cike da jin daɗi dan haka ya ɗago yayi masa godiya cike da girmamawa. Ita kuwa SHATOU dariya ke cinta marar control dan haka ta cije bakin ta gamm ta ƙi cewa komai sai kai da take langaɓewa irin na tausayi ɗin da wanda yake cikin tsoro.Sai kuma Haushin mai gari da ya kira sunan Inna nin ta a gaban jama'a. Miƙewa suka yi bayan furucin mai gari da ya furta " Na sallami kowa ". Sake da baki Iro ke kallon SHATOU da ta sakar masa muguwar harara da Gwalo dan cike take dashi jin shine munafikin da ya ƙarya ta ta ashe.Dan haka yanzu ƙyat take jira ta masa rashin mutunci cikin ruwan sanyi duk da har yanzu bata haƙura da sunan da yayi mata ba ya tozar ta ta,dan ma tsaye take da sunan ya bita dan kowa na shakkar ta ne da tuni ba shatou take amsa wa ba. A ɓangare ɗaya kuwa zuciyar sa kwata kwata bata yarda da zantukkan su Amina ba.Dan haka yake bin su da kallon tuhuma yana son su Kalle sa cikin ido sai dai kowaccen su tayi ƙasa da kan ta ta ƙi bashi dama. Ƙyafci yayi wanda ya sauka a cikin Kunnuwan SHATOUn kuma ta san da ita yake dan haka ta ƙara sakar masa muguwar harara kamar idanun ta zasu zube gaba ɗaya sannan tayi gaba a bin ta su Baffa na a bayan ta. Haka taron ya watse wanda kafin ma ya watse mai gari ya miƙe dan zagawa. Dariya take ta wangala tana tsallen murna in ta rungumi Amina ta rungumi Bibu Takoma ta rungumi Jawairiyayya,Ramata,sai yanzu dukkanin su suke sauke kwandon dariyar dake cikin su.Baffa na da suka baro Baya kallon ikon Allah kawai yake yi tare da sakin murmushi dan shi kan shi ya san babu gaskiya ko ɗaya a zancen su bai ma san sadda aka saka kibiya a jakar ta ba,mamakin ma.wayon su yake yi yana musu kallon haka haka yara masu cike da ƙuruciya dukkanin su dan har bibun bai yi tunanin zai iya tsaro zance haka ba wanda ba,a yi ba. Har suka kawo gida suna dariya tare da gwada irin yadda wani ɗai daga cikin masu kuɗin garin su ya ke gudu ciki ture sai su ƙara tintsirewa da dariya suna cigaba da kwaikwayon sa,Tafiyar Iro ce ta ƙwanbo ta faɗo ma SHATOUn arai hakan ya sa ta ƙara sakin wata mahaukaciyar dariya dai dai ta shiga gidan babu ko sallama sai gata ƙasa tana dariyar ƙeta tana ambaton Iro tare da yin tafiyar ta sa wadda ba SHATOU ba har su Amina da Inna ni da ke kallon ikon Allah sai da ta dara haka ma Baffa na dariya yayi kaɗan kafin ya samu kujerar roba da suke da ita gidan ƙwaya ɗaya ya zauna yana sauke numfashi. Inna ni da ta tsinci kan ta cikin nishaɗi ganin farin cikin yar ta hakan ya sa ta cigaba da sakin murmushi fuskar ta na washe wa da ga Damuwar da ta ke ciki wadda suka bar ta ciki tun fitar su. Ruwa ta ɗebo ma Baffa na masu sanyi a randa ta ajiye masa.Ɗauka yayi ya sha yayi hamdala. " Ke wai uban me kuke yi wa dariya haka kamar wayen da suka kode eh,babu sallama haka kuka faɗo mana cikin gida " Cewar Inna ni.Tana son tambayar Baffa na amma ta san ko ta tambaya idan bai ga damar faɗa ba ba faɗa zai yi ba.Haka ma su Amina ta san idan har SHATOU bata basu dama ba,ba faɗa zasu yi ba sai dai ayi ta yar kallon kallon tsakanin su. Shiru SHATOU tayi tana dakatar da dariyar ta har su Bibu ma kafin cike da murmushi tace '' Babu komai Inni ni dama Iro ne ". Sai ta kwashe labarin yadda yayi ta ƙwanbo a ɗazu.Inni da ta gama jin komai dariya tayi mai isar ta sannan ta ce " Allah ya shirye ki Shatou ". " Amin,Inna ni ta " SHATOU ta amsa. Baffa na dai murmushi yayi kawai yana ƙara mamakin wayan Shatou yanzu ƙiri ƙiri ta ɓoye wanchan laifin dan ta san halin Inna ni yanzu sai dariyar ta koma kuka. " Yanzu dai kuzo na zuba muku abinci kuci sai kowa yaje yayi wanka a fara shirin makarantar islamiyya ". Cewar Inna ni wadda take mamakin wayon SHATOU dan ba wannan zancen ta so ji ba dalilin kiran mai gari take son sani,amma ƙiri ƙiri Shatou ta kawo mata maganar da ba ita ba.Kuma ta san cewa dagan gan tayi dan ta ɓoye wancan zancen kuma tun da aka yi haka zai yi wahala ta san abinda ya faru waje.Amma zata bincika ko mene ne dan mai gari baya kira banza musamman kiran Shatou.✍️ Ayi haƙuri ba yawa. *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Commente,and like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P..1️⃣6️⃣ *BOOK ONE* PAID *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* 🕳️🕳️🕳️ Tun da suka isa bai fito ba ko nan da falo ne.Babu abun da ya taɓa tunda ga abincin rana har dare da ke jere a kan dinning da aka shirya masa saboda sun san da zuwan sa AB ya sanar da Dawowar su.Ganin hakan ya sa suka kasa haƙura ganin shirun yayi yawa gashi ya kashe duka wayoyin sa dan haka suka kira Ummah kai tsaye tsakanin wadda itama hankalin n ta tashe dan ma su Sir sun kwantar mata da hankali zai neme su dan ta basu labarin abinda ya faru,dan suma sun jinjina lamarin na su Reena. Cike da tashin hankali Ummah ta kalli agogo dake nuna ƙarfe goma na dare gashi dama suma sun yi kiran na sa layuka shiru har su Sir sun gwada dukkanin su dai hankali tashe dan yayi abin da bai saba ba.Ya tafiyar sa babu Sallama. Gashi bayan haka sai da su Reena suka ƙara kwata wani damben gurin bada haƙuri da Ummah ta saka suyi wa juna,su yafewa juna.LINA uwar rashin haƙuri daga kawai REENA ta share ta shikenan ta fara ƙoƙarin kaima ta duka,A fusace,duk da tana cike da tausayin ta,kuma tana son bata haƙurin Allah ya sa Ummahn tana kusa,sai faɗan ya tsaya nan, sai dai har yanzu babu mai yiwa wani magana a cikin su sai gidan ya koma babu daɗi daga ita sai su Rabi ne suke ɗan sakewa suma ba wai suna jin daɗin bane saboda dama su LINA ke ƙawata gidan yau gashi kowaccen su kamar an mata mutuwa. Ga tashin hankalin yadda ya yan na su yake ciki dan haka estate ɗin ta koma ko ina shiru dan tun rana suke kiran layin sa daga ƙarshe suka bar shi haka tun da sun binciki yaran sa since lafiya lau yake. Yana bacci koda suke kiran bayan isar su,sunyi hakan ne suma ba tare da suna da tabbacin bacccin yake yi ba. " Yanzu ya za,ayi a fito dashi ina tsoron kar ace wani abun ne ya same sa,bari na kira Abban su kawai AB ". Ummah ce ke zancen cike da wani irin raunin ta da ya bayyana. AB yana niyyar ƙara furta wata magana sai ya ga an buɗe ƙofar bedroom ɗin dan haka ya ce ma Ummah " Ya fito he's fine " kafin ya katse kiran yana sara masa (Solidarity)cikin girmamawa. Numfashi Ummah ta sauke mai nauyi kafin ta ja ajiyar zuciya tana tunanin yadda zata kira Abban su ta tada masa da hankali duk da ta san shima ɗin zai iya kira kowane irin lokaci ƙila ma ya kira bai same sa ba. Daga chan ɓangaren kuwa kallon AB yayi kafin ya ɗauke kan sa dan ko bai tambaye sa ba ya san da wa yake waya ganin yadda ya natsu dan suna mugun girmama Ummah suna jin ta kamar mahaifiyar su saboda mutuncin ta ga kowannen su sun ɗauke ta kamar uwa. Direct kan dininng ya nufa tea ya haɗa kawai mai kauri ya sha sannan ya miƙe ya dawo falon yana sauke numfashi.Tashar labarai ya kunna ko hakan zai rage masa Damuwar da yake ciki.Mayar da hankalin sa yayi ga labaran da ake haskawa a tashar sai dai ba wani fahimta yake ba,dan hankalin sa na ga su REENA yana son ya ji ya ƙannen na sa suke amma ya san yanzu sun isa yin Bacci saboda da wuri suke kwanciya bacci saboda school. Ganin babu abinda zai fahimta a cikin tvn hakan ya sa ya miƙe ya koma bedroom ɗin sa.A chan ma ya daɗe zaune kan cusion kafin ya miƙe ya doshi bed ɗin sa, zuciyar sa daƙushe.Dan tunda suka iso ɗin ya shige ya rufe kan sa saboda damuwa,chan yayi sallolin sa,ko abinci bai ci ba sai shayin da yasha yanzu ko shi saboda yaji yunwa na neman illata sa ne.Duk ya tuna da yadda ya daki Lina sai zuciyar sa ta yi zafi saboda ya san bata kai ta samu irin wannan ba duk da chan baya yayi bugun ta amma chan bata yi hankali ba yanzu kuwa ta san zafin jikin ta.Dukkanin su rarrashi suke so saboda yarinta ce dukkanin su ke damun su amma ba yadda zai yi dashi har mahaifiyar su haka, Allah ne ya basu nasu yan biyu ɗin haka.Numfashi ya sauke mai karfi yana kawar da duk wani tunani tare da yin addu'ar bacci take kuwa bacci ya ɗauke sa mai nauyi. *** Tun da ya shigewar sa bedroom ɗin na sa ya faɗa toilet saboda haka kawai yake jin jikin sa babu daɗi yar tafiyar nan da suka yi ko ina tsami yake masa saboda yanayin tafiyar hanyar duk da manya motoci ne ba gane yanayin hanya suke yi ba amma shi duk ya gaji haka yake ji dan haka ya cika ƙaton bathtub ya faɗa ciki da ruwa masu ɗumi da ƙamshi yayi haka ya kai sau uku kafin ya fito bayan ya ɗauro wanka tare da yin alwallah. Tsaye yayi gaban mirror madaidaicin jikin sa mai cike da ƙira wadda take mummurɗe ya ke ƙarewa kallo kafin ya fara murza mayukkan sa masu ƙamshi yana bin ko ina na jikin sa da su a hankali. Turarukkan sa ya shafa masu ƙarfi da kyau.sannan ya tada Sallah bayan ya saka Jallabiya mai kyau da tsari. Cikin natsuwa ya gabatar da Sallah azahar da ta fara gota lokacin ta saboda ya daɗe toilet bai lura da lokacin ba. Yana gamawa duk da yunwar da yake jin akwai ta acikin sa dan ko breakfast bai yi ba haka ya haye lafiyyayen gadon sa bayan cire Jallabiyar da yayi ya koma da ga shi sai short, duvet ya yi cover dashi mai taushi fari ƙar dashi kafin ya ƙara gudun ac daga kwancen sannan ya rufe idanun sa take bacci mai nauyi ya kwashe sa. Mubarak da ya san tabbacin sai yayi baccin nan na Hutu dan haka shima ya wuce na sa gefen ya huta kamar yadda ya huta ɗin dan shi ma ya ɗan gaji dan su suka yi yawon ma,sai dai duk ya tuna da Shatou da mai gidan na su sai yayi guntun murmushi ya girgiza kan sa ya rasa dalilin da ya sa yarinyar ta kasa fice masa arai amma ya san tabbacin MAHAJ ya manta da wata halitta ita Shatou dan sun ji sunan ta bakin Iro.Ya rasa har yanzu dalilin da ya sa ya kula yarinyar shi da ko su Sajida da Salma da ba su ishe shi kallo ba duk da kuwa gida ɗaya suke zaune dasu kuma yan uwan sa ne.Amma ita har ya kula ta gata wata figaggiya da ita dan ya san a ƙalla ba zata wuce shekara goma ba ma a duniya dan bai tunanin ta ma hau da sha ɗaya saboda yadda take yar cukul da ita ga rashin tsawo ga rashin jiki. "Amma Ya MAHAJ ya dawo fa tun ɗazu " Wata yarinya ta furta mai matsakaicin jiki sai dai ita ma a kallo ɗaya zaka san tana da yarinta dan zata kai shekara sha uku. Kallon ta matar da aka kira Amma tayi kafin ta furta " shine bai shigo ba kuma har yanzu Samra " " Amma akwai gajiya kin sani ko Amma ai na san zai shigo dan bana jin ko gefen Ayya ya shiga,Nima ga Yaya Muby na gani yanzu yace ai sun dawo ". Kai matar ta gyaɗa kafin ta ce " Sun kwaso gajiya kamm gashi ko breakfast ɗin sa bai yi ba gashi har lunch ya gota,ban san ƙiyayyar sa da abinci ba,haka yayi tafiyar nan ". Ta kai ƙarshen zancen tana cigaba da ɗan duba saƙonni dake shigowa a wayar ta. Yarinyar da aka kira da Samra kuwa ɓata fuska tayi tace " Amma dagaske bai yi breakfast ba,kuma shine har yanzu bai fito yayi lunch ba ". Murmushi Amma tayi kafin ta ce " To Sarkin kuka kar ki fara yi mini kuka gurin nan idan kuma Ayya ta isko ki babu ruwa na ke da ita ne,wanda kike Tausayin ko ajikin sa hasalima ɗabi'ar sa ce hakan,gwara kiyi shiru yadda muka saka masa ido ki saka masa,idan ya ga dama zaki gan sa ya fito yanzu ". Takai ƙarshen zancen tana share ma Samra hawaye dan har sun fito kuwa dan tana mugun son ɗan uwan ta da Tausayin sa shi ya sa a duk lokacin da yazo nan take cikin farin ciki duk da basu wata magana dashi amma wulgawar sa na saka ta farin ciki.Ko fitar nan ba ta so ba saboda ta san zai sha wahala, Allah ya ɗaura mata ƙaunar ɗan uwan ta,Ammah har cewa take yi ta fi son sa fiye da ita sai tayi dariya dan ita ta san tana son kowa a cikin yan uwan ta bare ma mahaifiyar ta. Miƙewa Samra tayi da sauri. " Ina zaki je Samra kuma ba dai gurin shi zaki je ba " Cewar Ummah ganin ta miƙe tsaye kamar an tsikare ta. " Gurin Ayya zani ko zata iya Fiddo da Ya MAHAJ ya yi lunch kar yunwa ya kama sa " Shiru Amma tayi kamar zata hana ta sai dai ta san ko ta hana ta tunda tayi niyya sai ta kai jiki dan haka ta ce " Samra ki bari zai fito kinji ba sai kin je wajen Ayya ba ". Ai ko Samra bata ma jira ta kai ƙarshen zancen ba ta falfala da gudu tana dariya. Da sallama ta shiga wani ƙaton falo wanda ƙofar shi take a cikin ƙaton falon na Amma dan ƙofofi ne gasu nan birjik wasu sama wasu ƙasa ta Ayya tana ƙasa saboda tsufa. " Ke lafiya kika faɗo mini falo babu Sallama,ita Maryam bata ga fitowar ki haka bane,kamar zaki je gasar Guje Guje " Yar dattijuwar tsohuwar da Hutu da kwanciyar hankali ya ratsa ta tayi furucun,sai dai daga nin ita fitinannun tsofaffin nan ne masu rigima.Dariya Samra tayi kafin ta haye kan rugs na ƙaton falon na Ayya sannan cike da tausayi ya yan na ta ta ce " Ayya Yya MAHAJ yau gaba ɗaya bai saka abinci a cikin sa ba fa,gashi sun yi tafiya sun dawo kuma bai nemi abinci ba,dan Allah ki je ki tado dashi ko bacci yake yi ".Ta kai zancen tana ɓata fuskar ta tare da riƙe hannun Ayya ɗaya. Ayya kuwa da sauri ta kaɓe hannun ta tana furta " ke tafi chan yar neman ga,Wanda bai san ciwon kan sa ba zaki saka kan ki dole kula dashi,shekarar sa nawa,Mahajjaci ai ba yaro bane,ada na wahala dashi amma yanzu babu garjejen ƙaton da zan wahala akan sa ta tafi ta bar mana jaraba,duk halin uwar shi ya gado " mstww taja mugun tsaki tana juyar kan ta gefe taana cigaba da kallon tsohon Film na hanyar Kano da ake haskawa a tashar ta Saira movie tana jan charbi a hannun ta. Samra hawaye ne suka wanke mata fuska nan ta fashewa Ayya kuka,dama ta san ba lallai ta samu magana mai daɗi ba amma ta san yadda yake mugun jin maganar Ayya akan takowa a gidan.Ba ta san dalilin da ya sa Ayya take tsangwamar sa ba tun bata gane abun da ke yi wa ya yan na ta ba daɗi har ta kai ta fahimci inda ta dosa dan kai tsaye take nuna bata son sa duk da irin biyyayyar da yake mata saboda rabin rayuwar sa a hannun ta yayi ta,kuma tun yana ƙaramin sa yake cikin matsin Ayya har bai gane ba ya gane dan haka dai dai da rana ɗaya bai taɓa nuna damuwa saboda kallon uwa yake mata koda yaushe. Miƙewa tayi da sauri bata ƙara cewa komai ba ta fice daga sashen tana Sharar hawaye.Sai dai tsaye tayi ganin wanda ya ke tunkare gaban ta,ta tare da jin ƙamshin sa da ya mamaye ko ina.Shi ɗin ne dai ya ke saukowa yana zuba ƙamshi ya sanya wasu irin kaya masu kyau da tsari kamar dai na sport riga da wando ash color da suka ƙara haska farar fatar sa mai sheƙi da ɗaukar ido.Cike da murmushi take bin shi da kallo har ya sauko.Ɗan sake fuskar sa yayi dake ɗaure kafin ya sakar mata lafiyyayen Murmushin sa yana shafa kan ta cike da son yar uwar ta sa da yake jin mugun Tausayin ta saboda yadda ta ke damuwa da lamurran sa dan ta kawai wasu lokuttan yake fitowa ya saka ma cikin sa wani abu dan ya san ta da naci yanzu haka ma.da ya ga hawaye a fuskar ta ya san daga inda ta fito dan haka babu tambaya,ya nuna mata shafaffen tumbin sa da kai kace bai taɓa samun wani abu a cikin sa ba.Fahimtar alamar da yake mata ya ci abinci ya sa ta sakin yar dariya ta jin daɗi ko bata tambaya ba ta san Chocolate ya ci saboda akwai shi da shegen son kayan zaƙi fridge ɗin sa duka sune shaƙe aciki babu kalar da babu.Ficewa yayi saboda yayi shirin sa tsafff dan zai ɗan motsa jikin sa ne da yake jin har yanzu yana masa babu daɗi.Dan haka yana tashi daga bacccin mara nauyi,ya ƙara watsa ruwa dan akwai wanka kamar moɗa.Chan baya inda field ɗin wasa yake ya nufa yana ɗan haɗawa da ɗan gudu.Dai dai lokacin suma su Salma da Sajida sun fito daga gurin sun gama buga ball kowaccen su da ɗan guntun wando.Kai ya ɗauke daga gare su tun kallon da yayi musu na farko.Su ko tsaye suka yi cike da jin haushin sa na share su da yayi gashi har haɗa baki suke yi wajen faɗin Sunan sa dan basu san ya dawo ba sai yanzu da suka gan shi.✍️ Duk abinda kuka gani kuyi Haƙuri ko editing na tafi ɗaya tafi uku nayi saboda yau ban samu na zauna ba.ngde WANNAN LABARI NA KUƊI NE A MANHAJAR WAHTSAPP *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Commente,and like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P..1️⃣7️⃣ *BOOK ONE* PAID *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* Not edited🥺 ✨✨✨ Cike da murna ta faɗa ɗayan falon na Amma da yake ta upstairs ɗin da yake gefen hagu.Ganin ta hakan ya tabbatar ma Àmmah da ta samu abun da take so dan haka ta girgiza kai cike da murmushi dan ba ma sai ta mata bayani ba ta fahimci komai. Ƙaramin tsaki Sajida ta saki,ita kuwa Salma murmushi ta yi na farin ciki ko ba komai ai sun samu ganin sa tunda tsada yake yi dan shi ma suke yawan fitowa wajen wasannin basu san dalilin da yasa bai sake musu fuska kamar yadda yake sakewa Samrah ba har Sajida zata bi bayan sa Salma ta riƙo hannun ta tana girgiza mata kai.Kallon ta tayi kafin taƙwace hannun ta tayi gaba hasale dan ta ji zafin wulaƙancin da yayi musu,ita ba kowane ta ke ɗauka ba dan ma bata ga fuskar raini ba da tuni MAHAJ ya ga rainin ta. *** A ɓangaren SHATOU yau ta tashi da wani irin mahaukacin ciwon ciki da ya ke neman ganin bayan ta,duk murnan bikin sunan da zasu tafi na maman ramata bata sami zuwa sabo da yadda ciwon ya sako ta gaba ko maƙiyin ta sai ya tausaya mata. Ta zama Abar Tausayin Inna ni da Baffa na iya kar ƙoƙarin su kawai suke yi har ɗan chemist da suke dashi ya je ya siyo maganin ta sha banza dan yana lafawa da mintuna ƙalilan yaƙara tashi dan haka suka zuba ma sarautar Allah ido domin kamar ciwon bai jin magani gashi baiwar Allah duk ta ƙara lanƙwashewa.Shatou tayi Kwana kusan huɗu tana fama da wannan ciwon babu wani sauƙi sai ana biyar ne ta samu da ƙyar ta miƙe ta shige toilet wajen fitsari bayan ya ɗan lafa mata sai dai,me ƙara ta saki ganin abinda yake fita a jikin ta bayan fitsarin.Inna Ni dake tsakar gida cikin ɗan jin daɗin miƙewar da tayi ta taso da sauri dan ita kaɗai ce a gidan,sai SHATOU. " SHATOU lafiya kuwa,ko jikin ne ".Inna ni ta furta bayan samun kan ta tsakiyar makewayin. Miƙewa tsaye Shatou tayi dan kamar an zare mata ciwon jikin ta lokaci ɗaya haka ta ji sai ta ɗan samu sauƙi. Idanu Inna ta zaro cike da farin ciki kafin ta riƙo hannun ta tana ayyana wa aranta wata sabuwa.Dan wani sabon aiki ne ya same ta bata taɓa tunanin Shatou zata iya shiga wannan yanayin yanzu ba ta yi tunanin sai shekarun sun ƙara yin gaba duba da yanayin ɗan jikin na ta. " Ji rani nan " Inna ni ta furta fuskar ta cike da murmushi.Kafin ta fice daga bayin. SHATOU kuwa hawaye ne har yanzu suke silalar mata duk da yanzu ta tuno da wani karatu da wani malamin su yayi musu kan wannan abun da ya same ta sai hankalin ta ya ɗan kwanta yanzu ƙyanƙyamin kanta take yi sosai dan haka take tsaye hawaye na silalar mata musamman ganin yadda jinin ke bin ƙafafun ta saboda na farko ne yana mugun rushing sosai. Ɗauke da wando ta shigo tare da Wani ƙaton tsumma da ta yanko wani zanen ta wanda bai ji jiki ba. Nan ta kimtsa Shatou da ke ta hawaye bayan ta bata izinin yin wanka dan har da ruwan wanka ta haɗo mata tana gama yin wankan ta saka komai gaban ta kamar yadda ta nuna mata.Ganin hawayen yaƙi tsayawa ya sa Inni ni furta " Ni fa kin ishe Ni,haba,Girma fa ne ya kama ki,dama so kike ki ƙara girma ai, yanzu zai zo lokacin sa yazo,tunda baki son ana ce Miki ƙarama " Ta kai ƙarshen zancen tana sakin yar guntuwar dariya.Baki Shatou ta turo gaba tana jan majina.Kafin tayi gaba ta baro Inna ni cikin toilet ɗin tana wanke kayan ta da ya lalace wando da rigar. Ɗaki shatou ta shige ta yi kwanciyar ta saboda duk jin ta take yi a takure kamar an manna mata wani mugun abu ganin take yi motsi kaɗan zai iya saka abun ya faɗo dan haka ta takure waje ɗaya. Maganganun Inna ni kuwa da ta yi ta jera mata suna dawo mata kan kunne.Zantuka ne masu cike da gargaɗi da tsoratar wa.Dan haka taji ko wajen bata son fita domin Inna ni ta nuna mata kuskuren da ke ciki koda ace hannun ka ka bari wani ya taɓa wanda ya wuce Bibu da Baffa na. Duk dai wani yanayi da kuka sani farin shiga yana samun kan sa ciki haka SHATOU ta tsinci kan ta cikin yanayin mai takura.Tana cikin tunanin zantukkan ne wani irin bacci ya kwashe ta. Inna ni kuwa cike da tausayi haka ta wanke kayan na Shatou ta cigaba da ayyukan gaban ta dan ta samu ɗan kwanciyar hankali ko ba komai ciwon ya tafi tunda dama wannan ne dalilin wahalar ta ta ita bata ma lura ba tunanin ba bai zo ga kan ta ba a tunanin ta ko ma wani abun ta ci a waje basu sani ba. A haka koda Baffa na ya dawo shida Bibu sun ji daɗi sosai ganin Yadda Inna ni ta sake Sosai babu wata damuwa kan fuskar ta hakan ya tabbatar musu da Shatou ta samu lafiya,dan haka ya jikin ta kawai suka ƙara yi mata sannan.Nan ta sanar musu da ta ji sauƙi ta samu bacci ma suna tsaka da zancen kuwa sai ga ta ta fito tana yaƙune fuska tana wani haɗe ƙafafu.Duka zuba mata idanun su kayi cike da tausayinta ganin yadda ta ƙara yin fayau da ita har ja ta ƙara yi kamar wadda aka kwalhewa jinin jiki. " Ya jikin SHATOU "? Cewar Baffa na. Cike da murmushi ta amsa masa tana zaro ido jin kamar abinda ke fita jikin ta zaya zubo ƙasa saboda yadda yake mata rushing. " Adda SHATOU lafiya kuwa kike zaro ido haka kamar wacce ta yi ƙarya,gaban mai gari " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ɗan guntun murmushi. Hararar sa ta yi kafin ta mayar da kallon kan Inna ni da take ta kallon ta tana tsoron ta ce musu wani kan halin da take ciki dan haka ta zuba mata idanu tana fatan kar Surutun ta ya kai ta sanar da su duk da ta san dole ma zasu iya sani wata rana.Duk da ba abun ɓoyo bane. Kai Inna ni ta juyar gefe kamar bata ga yadda take zaro ido ba yanzu dan ta fahimci halin da take ciki dan haka tace " Wuce ki samu waje ki zauna " Sai dai bata kai ga rufe baki ba Shatou ta faɗa Makewayi a Guje bayan ta runtumi buta.Sai da ta ɗan jima sannan ta fito tana ɓata fuska dan sabon tsumma ta chan za tana jefar da wanchan dan nan Inna ta ajiye mata kayan ta san zata buƙace su. Inna ni kai kawai ta girgiza kafin ta zubo musu abincin a waje ɗaya dan wasu lokutan tare Baffa na yake cin abin cin sa da ya yan na sa. Koda Shatou ta fito har sun fara ci sun yi fiye da rabi da sauri ta nemi waje kusa da Baffa na ta zauna.Sai dai har ta ɗora hannun ta akan filet ɗin ta cire tana ya ƙunar fuska wasu daga cikin spoon da Inna ni take da su ta ɗauko ɗaya cikin su duk da kasancewar su yan ƙanana.Babu wanda ya ce mata ƙala daga Inna ni har Baffa na da yake nuna musu cin abinci da hannu ya fi lada da albarka. Tare suka cinye abincin sai dai suna cinye wa itama ta miƙe dan jin cikin ta famm duka kallon ta suka yi cike da mamakin ɗan abincin da take cewa ta ƙoshi kan sa. Bibu ne ya ka sa haƙuri yayi wa Baffa na rigaye da yake son yi mata magana " Adda SHATOU wannan ɗan abincin zai ishe ki keda bakya zama sai kinji ko ina tab". Ya kai ƙarshen zancen yana kallon ta yar Hararar wasa tayi masa dan Dagske dai ta ƙoshi ɗin bata jin ma zata iya cin abincin dare dan ji take ko ina yayi mata baƙebaƙe.Inna Ni dai bata ce komai ba dan ta san hakan bai rasa na saba da yanayin da take ciki dan haka mutun yake komawa kamar mai lauyayi a wannan lokacin bare mata shine farkon ta.,dole zata samu ire iren waɗannan abubuwan. Ganin Dagske ta ƙoshi ɗin dan kai tsaye ta cewa Bibu " Wallahi Allah Na ƙoshi ko Baffa n,a shafa ciki na kaji ". Ta na sauke ayar zancen tare da kamo hannun Bibu da yake kusa ƙwace hannun sa.Yana ɓata fuska saboda ganin ya kw yi kamar har yanzu jikin ne dan duk da yake bata da lafiya da ta farfaɗo sai ta ɗan zubawa cikin ta ko ba da yawa ne,amma gashi yau ta ji sauƙi sosai ta kasa cin abincin. Baffa na ne yayi Murmushi tare da shafa kan Bibu yana cewa " Habibullah bafa koda yaushe mutun yake zaune akan halayyar sa ba a wasu lokuttan ya kan iya aro na wani,dan haka ka daina damuwa Addan ka zata samu ta samu lafiya,gata nan komai tanayi,akwai abinda ya sauya mata cikin ." Kai Bibu ya gyaɗa cike da tausayin yar uwar ta sa. Ruwa ta sha kafin tayi gyatsa tare da yin godiya ga Wanda ya ƙara tabbatar musu da ƙoshin ta. zaman ta nan gurin tayi tare da Inna ni da ta rage a wajen saboda sun tafi cire kaya su watsa ruwa su huta. A ɓangaren su ALINA kuwa yau kusan kwana biyar babu mai iya yiwa wani magana acikin su dukkanin su sun koma kamar wayen da basu da lafiya saboda yadda suke azabtuwa da rashin kula junan su, ALINA tana son yiwa REENA magana sai ta kasa musamman dan ta bata haƙuri da Auntyn su tace ta bata saboda itace ƙarama idan ma faɗa su kayi komai zai wuce kasancewar an ga sun dai na ko chachar baki ne a aji babu mai kula kowa.REENA tsoro ne maƙil a zuciyar ta ga Tausayin yar uwar ta da ta san ya damuwar bugun da BILAL yayi mata a matsayin ya tsane ta ta tabbatar ko kashe ta zai iya yi in ya samu dama a ƙuruciyar ta dan haka ta sha alwashin babu ita babu magana da ya'yan na ta idan ma ya zo ba zai ƙara ganin ta ba har ya koma gurin aikin sa,tun da bai son ta,dan a zuciyar ta cewa take yi bada gangan tayi wa REENA haka ba ita kan ta bata iya cewa ga yadda aka yi ta mata wannan dukan abun da kawai ta sani shine ta hau ruwan cikin ta da faɗa ya fara. Yau ne suka ɗan sake dan kowaccen su ɗakin ta take bacci ita ɗaya a wahalce Umma tayi rarrashi ta saka musu ido. Tana son sanar da Bilal sai dai shima har yanzu ba wani sakewa yayi ba duk daya kira kowannen su daga kakanni na sa har iyayen sa ya basu haƙuri na rashin sanar da tafiyar sa,ya sanar da su tafiyar gaggawa ce ta same su. Sai shige da fice suke yi an chaɓa ado idan ka Kalli fuskar Ummah sai ka ƙara kallawa tayi kyau har ta gaji saboda tarbon mijin na ta dan yau sashen ta yake kafin ya yi tafiyar itace dan haka kai tsaye nan zai sauka kafin ya zagaya ya gano sauran.Ko Ina ya amsa a estate ɗin SSS zai dawo kowana cike da farin ci,sai kai komo suke yi ana ta gyare gyare dan kowane sashen suna cike da farin cikin Dawowar sa. Su ALINA ma sun sha kyau matuƙa cikin shigar jeans da t shirt shigar ta su iri ɗaya dan duka kayan su iri ɗaya ne.Sun yi kyau sosai idan ba ka sansu ba zai yi wahala ka iya tantance ALINA ko SARINA a tsakanin su kamannin su suka ƙara bayyana masu cike da kyau da haiba da zallar Hutu da yake ƙara musu kyau da annuri.Koda kowaccen su ta ga iri ɗaya suka saka sai aka koma kallon kallo murmushi ne ya suɓuce ma Rina bayan ƙare ma yar uwar ta kallo dan ta riga ta fitowa.Ita kuma boss ɗin ɗaure fuskar ta tayi dan kar ta raina ta,dan tunda Umma tace ta riƙa sassauta mata kodan saboda tana babba ba ƙarfin su ɗaya ba.. Ummah ma murmushi ta yi tana janyo hannayen su ta zauna tare da su bakin ta washe kamar gonar Auduga. *** " Hmmm wai kin san Hamida duk saurin nan da nake yi na gama exams na je Hutu wajen Ummah ashe ya koma gurin aiki tun daren da ya kawo ki da safe ". Matashiyar budurwa ce ke zancen wadda a ƙalla zata kai shekaru ishirin a duniya tana zaune akan makeken gadon royal mai kyau Murmushi Hamida dake zaune gaban fankacecen madubin da ya ƙara ƙawata ƙaton bedroom ɗin na su ta ce " Yaya Samira ke dai ba zaki raba kan ki ba ko,kin fi son Ya BILAL yana disga ki,kin san dai abun da kike yi baya so ". Budurwar da aka Kira Yaya Samira ce ta galla ma Hamida Harara kafin ta ce "Ai Ummah na so dan bata taɓa ce mini komai duk da ta lura da abun da nake yi dan haka babu ruwan ki,idan kika matsa mini kuma yanzu na sassaɓa ki kina haɗa ki da Ummu " ta kai ƙarshen zancen tana jan mugun tsaki. " ai da na sani da ban faɗa Miki ba,kuma ma gashi ya koma sai kije ki ƙara "... Hamida ke zancen ƙasa ƙasa. " Me kike faɗa " Cewar Samira. Baki Hamida ta turo gaba bata tanka ma Samira ba. Ƙara jan dogon tsaki Samira tayi tana saka earpiece a kunnen ta. *** " Amoh ta ƙi karɓan abincin ta nayi nayi ta ƙi karɓa har Sagir ya shiga ya bata ɗazu ta ƙi karɓa,gashi Nurse ɗin ta bata zo ba ". Shiru Babbar matar da aka kira Amoh tayi wadda ke zaune cikin ado na alfarma daga nin ta ka san akwai dukiya a jikin ta,Numfashi ta sauke sannan ta furta " Suhaila kodai kiran Suhail ɗin zamu yi duk da na san akwai ayyuka gaban sa,yau suna ganawa da patient ". " Bari na gwada idan bata karɓa ba sai musan abunyi dan yunwa zata iya yi mata illa,gwara ya bata ko zata karɓa ". Kai matashiyar budurwar da aka kira Suhaila ta girgiza fuskar ta cike da damuwa. Tare suka kama hanyar wani lungu sai gasu tsaye ƙofar wani ɗaki mai duhu ko ina lif lif babu hayaniya. Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Sai monday idan Allah ya kai mu. Ina alfahari da ku masoyan wannan labari 🥰💋 Comment and like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P..1️⃣8️⃣ *BOOK ONE* PAID *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* 🌙🌙🌙 Zaune take ta takure waje ɗaya jin hasken da ya gauraye ganin ta ya sa ta zabura da ƙarfi tana neman hanyar gudu.Saboda bata son haske ko kaɗan a cikin sa ne take ganin wasu irin halittu kala kala da ban tsoro shi ya sa ta ke natsuwa a duk lokacin da take cikin duhun.Cike da tausayin ta Amoh ta kashe hasken tana jin hawaye na wanke mata fuska kamar Bazasu tsaya ba.Haka ma Suhaila.Ɗaki ne dai mai kyau ko ina tsaf dashi sai tashin kanshi yake yi. Haka wacce ke zaune ta da kan ta yake hargitse yana walƙiya cikin shigar kaya mara sa nauyi saboda akoda yaushe yana samun kulawa.Dan wasu lokuttan abun yana sakin ta amma a lokacin da duk abun ya motsa ɗakin ma sai ta hargitsa sa da ita kan ta dan kayan jikin ta gaba ɗayan su take yaga su bana ta ba har wanda ya matsa kusa da ita.Kwana biyu an samu sauƙin abun na ta ciwon ya kwanta.Sai dai yau ɗin nan akwai alamar tashin ciwon duk lokacin da taƙi karɓan abinci hannun kowa sai ciwon ya motsa Suhail ne yake mata dole shi kaɗai take shakku a cikin halin da take ciki dan duk tafi sabawa dashi a gidan,idan bata yi niyyar karɓa ba ko Daddy ya zo bazata karɓa ba sai Suhail dan Haka Amoh ta ce bari ta gwada in zata karɓa kafin a tado da Suhail ɗin daga aikin sa. Ƙara ƙankame jikin ta tayi waje ɗaya tana rufe Kunnuwan ta da take jin wani irin sauti a cikin su kamar na kukan jarirai da wasu halittu.Cike da tashin hankali suka yi kan ta ganin idanun ta na lumshe wa alamar suma zata yi kamar kullum idan abun ya motsa.Sai dai kafin suyi wani abu Numfashin ta ya ɗauke ɗaff da sauri cikin wasu irin hawaye da suka silalo ma Suhaila ta nemi wayar ta dan muddin babu wani namiji a kusa tana farfaɗowa zata ji ma kan ta ciwo ta hargitsa ko ina kuma ta riƙa neman guduwa. Cike da tashin hankali tayi masa bayani wanda ko jin ƙarshen zancen ta bai yi ya damƙa aikin duba marasa lafiya ga colleques na sa dan suna da ɗan yawa kar ya bar su zaman jiran sa.Bai san ranar Dawowar sa ba suma cike da tausayin sa suka yi masa a dawo lafiya sanin abun da ke faruwa dan muddin ciwon ƙanwar ta sa ya tashi dole sai ya je gidan. A chan kuwa koda suka yayyafa mata ruwa a fisge ta miƙe tana faman yin wani irin gurnani tana watse komai dake kan madubin babu abin da ke tashi da ke ƙara juyar da ƙwaƙwalwar ta face ƙarar kwalabe. Da Inna ilaiihi wa Inna ilaiihi raji'un da su Amoh ke ambata da sunayen Allah.A lokacin kuma wani ƙarfi ke ƙara tarar mata a jiki kamar wani ƙato dan haka bayan ta gama watse komai na kan madubin ta koma kan jikin ta gaba ɗaya ta yaga kayan jikin ta duk yadda suke ƙoƙarin hana ta amma abun yaci tura Saboda tafi ƙarfin su ƙarshe ma kan Suhaila ta koma tana jibgar ta kamar Allah ya aiko ta tana sakin wata irin dariya dake nuna bata lafiya bace dan mai cikkakken hankali ba zai yi ta ba.Dai dai lokacin Nurse ɗin ta ta shigo kasancewar wani uzuri ya riƙe ta dan ita ke kula da komai na ta har wankan ta,sai kuma wadda take kula da ita idan bata nan itace Nana itama tun da ta ga alamar yanayin na ta yau ta ɗauki uzuri tayi gaba bayan shirya ta. Rasa abun yi tayi dan abun yafi karfin ta saboda tana da ɗan tsoro Ta juya da sauri kenan dan kiran security sai ta yi kici ɓus dashi fuskar nan tashi tayi Jawur kamar jan tumatir Matashin saurayi ne tsaye da aƙalla zai kai Shekara Ishirin da uku ko da Huɗu a duniya sai dai yana da cikar jiki dan haka zaka iya cewa ma ya wuce shekarun sa,ko zai kai da biyar.Fari ne tass irin farin nan na Fulani kamar sa dai sak irin ta Suhaila da Amoh dan ita suka biyo Rayyan ne ma ya ɗebo mahaifinsu,dan shi bai yi farin su ba.Fatar sa dai kamar ta wadda ke a cikin halin haukar. Idanun sa ya runste da ƙarfi cike da ƙunar rai bayan ya haɗa ido da ita a lokacin da take ƙoƙarin yaga rigar Suhaila dake ta dambe ta ƙwace kan ta.Ta shammace ta ta cije rigar a bakin ta da haƙoranta wanda kuma babu alamar zata sake su.Zuba masa idanu tayi jin ƙamshin turaren sa da ya garwaye ɗakin wanda ya hana mata yaga rigar sai ma ɗago kan ta dan ganin inda zata gan sa.Murmushi tayi mai kyau kamar yadda ta saba sauka daga yanayin wasu lokuttan cikin ruwan sanyi.A hankali ta zare rigar daga bakin ta tana ɗagawa kan Suhaila tana komawa gefe ta takure waje ɗaya kafin kuma ta saki wani irin mahaukacin kuka mai tsuma zuciya mai cike da sambatu. Amoh dake jin kan ta na sarawa ne saboda damuwa ta raɓa Suhail ɗin ta wuce haka ma Suhaila cike da wani irin kuka na Tausayin da yar uwar ta ke ciki ta yi anyi magani abu sai gaba yake yi kullum sai zagayen asibiti ake bincikar ƙwaƙwalwar ta da hotuna dan ita yanzu ba likita bace amma har ta haddace yadda hoton kan ɗan adam yake. Nurse ɗin ta itama jiki mace ta fara ƙoƙarin gyara wajen a dubarance dan cikin kwalaben ta koma ta zauna sai anyi da dabara sannan yanzu za,a chan za mata waje tare da kayan jikin ta. Numfashi ya sauke mai nauyi kafin ya raɓa ya shige wata ƙofa wadda take haɗe da hanyar da zata sadaka da part ɗin sa.Bai daɗe ba ya fito yana fitowa da syringe a hannun sa wanda yake ɗauke da ruwan Allurar ta dan haka cike da dabara ya shammace ta ya soka mata a damtse cikin kukan azaba ta saki wani marayan kuka mai tsayawa a zuciya.Kafin ta fara fisge fisge tana son ƙwace jikin ta saboda ya bata yar runguma yadda zata natsu kafin ya mai da ita kan gado.A haka bacci ya kwashe ta mai nauyi dan haka chak ya ɗauke ta ya mayar kan gado tare da gyara mata kwanciya.Sannan ya kunna haske dan ya taimaka ma Nurse ɗin ta kula da komai yadda ya dace. " Mira Komai na hannun ki a gyarata idan ta farka ki sanar dani,Ta samu ta yi lunch ". Kai Nurse mira ta gyaɗa cike da murmushi tana mugun kaunar yadda Suhail da sauran yan uwan sa da mahaifiyar su suke bawa Yar uwar su kulawa da wasu ne irin yadda take dukan nan ko inda take ba zasu iya matsawa ba. Amma su koda yaushe cikin bata kulawa suke kuma sun kasa haƙura da kashe mata maƙudan kudade dan an rasa gano abinda ke cikin ƙwaƙwalwar ta ta tun fara ciwon na ta dan tun tana da ƙanana shekarun ta aka fara ganin sauyin yadda yara suke abubuwan su wata rana zaka ga tana Harare harare ita kaɗai ko kaga tana huci ko magana ita kaɗai Tun abun bai damun su har ya fara damun su dan harda dariya ta fara yi ita kaɗai nan suka fara bincike asibiti aka tabbatar musu da lafiyar ta ƙalau kuma an kira mai raƙiyya shima babu Aljannu,dan har yanzu kuwa babu wani cigaba na asalin abun da ke damun ta,Kuma hakan bai hana da Anji wani sabon consultant ba mai kula da sashen ƙwaƙwalwa su mata booking aje a duba ta koda kuwa ba ƙasar nan bane... Tsafff ta gyara ɗakin da sauri saboda kowane irin lokaci tana iya farkawa saboda Alluran ba su wani tasiri a jikin ta. Dan haka tayi sauri ta gyara komai ta chanza mata kaya tare da gyara mata gashin ta da yaƙara hargitsewa saboda bata bari a taɓa shi ko wankin kan da dambe suke ƙare sa da ita,ita kan ta bata son taɓa kan na ta,bare wani. Kashe hasken tayi bayan ta gama kimtsa ta.Sannan ta nemi waje ta zauna tana sauke numfashi.Nurse Mira wajen aikin su ɗaya da Suhail shima ya nemi alfarmar ta dan ta riƙa kula da lafiyar ƙanwar ta sa dan tayo special course under sashen brain da kuma abinda ya shafi psycho haka ya roƙe ta tare da albishirin linka mata albashin ta dan haka take ta amsa masa koba komai ai aljihun ta ya ƙara cika,Sannan ta samu shiga Babban gida irin wannan gida na Babban minister. Cike da wani irin sanyi ta tashi kasala mai nauyi na saukar mata dama haka Allurar ke mata dan haka a hankali ta sauko daga kan gadon tana rakuɓewa a inda ta saba zama.Cikin ɗan hasken da ke akwai a ɗakin wanda ita kan ta Nurse Mira ta saba dashi dan haka ta hango ta dama idanun ta kan ta suke bata motsa ba ko hana ta saukowa sai ma jiran ta zama dai dai ta matso mata da abincin ta.Wanda mafi yawan sa madara ne ko shinkafa da tea. Su tafi karɓa... Cike da dabara ta matso kusa da ita tare da kayan shayin da ta haɗa mata mai kauri wanda ya ɗan huce kaɗan. Zama tayi kusa da ita kamar yadda ta zauna,ta fuskance ta.Ɗago idanun ta tayi ta zuba mata idanu kafin ta ɗauke su kan ta tana sakatar akaifar ta ɗaya daya da ɗaya wanda take tsaftace kuma ba mai yawa ba. Murmushi Nurse Mira ta saki kafin ta kamo hannun ta.Sai dai da ƙarfi ta ƙwace sa tana zabura tana neman miƙewa tsaye dan ganin ta tayi ta koma mata wata halitta musamman murmushin da ta yi mata yanzu. Ganin haka ya sa Nurse Mira miƙewa tana jaaa baya.Hakan da tayi ya bata damar komawa ta zauna mazaunin ta. " Ni ce ko Isha" Bata Kalle ta ba sai ma haɗe ƙafafun ta da tayi waje ɗaya tana saka kan ta ciki alamar bata son ko kallon ta. Nurse Mira kuwa da ta gane abinda take nufi hakan ya sa ta ɗau wayar ta ta danna ma ñumban da tayi Saving da Dr.Suhail kira. Ba,a daga ba har ta gama ringing sai dai ba,a wuce minti biyu da gama kiran ba sai gashi ya ɓullo ta ƙofar da ya bi ɗazu yana sanye da kaya marasa nauyi na shan iska. Cup ɗin ta miƙa masa dan dama ta san tunda ta ga bai ɗaga kiran ba ta san cewa yana hanya.Dan wasu lokuttan haka yake yi. Karɓa yayi cike da natsuwa ya matsa kusa da ita ɗago kan ta ta ke son yi amma saboda ta tuna zafin allurar da ta san shi yake mata ita hakan ya sa ta ƙi ɗagowa ɗin wanda ke nuna alamar fushi take yi dashi. Murmushi ya saki a hankali sannan ya riƙo hannun ta ɗaya. Ya furta a hankali " MA'ISHA " ɗagowa tayi ta zuba masa idanun ta da suka ciko da ƙwalla dan shi kaɗai ne yake kiran ta da cikakken sunan ta ko shi kuma ba kullum ba sai lokacin da take cikin irin wannan yanayi,dan tun bata fahimtar shine kaɗa ke kiran ta da sunan har ta gane.Koda kuwa tana cikin ciwon ne tana gane cikakken sunan na ta da kuma ƙamshin turaren sa. Hawayen ya share mata cike da tausayin ta yana jin kamar ya saka kukan shima. Cup ɗin da ya ajiye gefe ya ɗauko ya ɗaura mata a baki take kuwa ta fara sha kamar zata haɗiye harda cup ɗin bai hana ta ba,dan ya fahimci tana jin yunwa ne sosai. Sai da tayi rabi sannan ta tsaya kafin ta jaan yo hannun sa tana jan yatsun sa tana dariya cike da yanayin rashin lafiyar ta. Nurse Mira dariya itama tayi cike da farin ciki. Sakin hannun sa tayi ta koma kan cup ɗin da ke hannun sa ta juya shi kan bakin sa dan ya san abun da kan iya biyo baya hakan ya sa babu gardama ya ɗan kurɓa kaɗan hannun ta ta haɗa waje ɗaya ta taɓa kafin ta juyo dashi bakin ta ta sha tana leƙo fuskar sa,tana dariya. Shima yar dariyar yayi sannan ya kafa bakin sa kaɗan ya kurɓa ya mayar mata cije kofin ta yi ta hana shayin shiga bakin ta dan haka duk ya ɓata mata kaya rabi ya bi ta wuyan ta ya ɓata mata kaya.Haka dai aka gama bata shayin rabi shi rabi ita rabi jikin ta.Suna gamawa kuwa da dabara ya miƙe dan wasu lokuttan tare take cewa zasu miƙe dole sai ta bishi gashi bata son haske ko kaɗan ko yanzu ɗan hasken da suka saba dashi ne suke kallon ta cike da tausayi haka itama.Ruwa ya bata wanda ke ɗauke da ƙwayar maganin bacci suma sai da ya sha kaɗan sannan ta sha tana kallon sa tana dariya har da lakato tsinin hancin sa. *** Tare dukkanin su yaran aka je airport tarbon Sa cike da farin ciki babu ma kamar su LEENA da REENA. Babban mutun ne mai natsuwa da nagarta wanda Hutu ya zauna masa sosai da ganin sa ka ga cikakken ɗan boko mai ji da dukiya,dan ba zaka taɓa cewa ya ajiye Bilal da su LEENA ba,da Hamrah ba. Cike da farin ciki Suka rungume sa suna haɗa baki wajen faɗin Abba.Shima cike da murmushi da farin ciki ya shafa kan REENA yana furta " my Baby kece kika ƙara girma haka" .Fuska LEENA ta ɓata kafin ta kawar da kan ta gefe Murmushi ya yi mai kyau yana ayyana wa aransa dama na san arina uwayen rashin haƙuri,dama tsokana ce yayi.Sai gashi ta faɗa.Dan su Hamrah da Ninah ba su nuna komai ba sai murmushi da suke yi suna zagaye dashi. Amma ita har ta ɓata fuska kuka ma take batun saka wa. Janyo ta yayi ganin tana neman barin wajen kafin ya rungume ta yana furta haba " Babyn SSS,Abban ta Yar gaban goshin Ya BILAL SS ". Ai kamar ya tsokano inda ke mata kaiƙayi take kuwa idanun ta suka kawo ruwa sai kuka.Dariya yayi saboda ya san case ɗin da aka yi dan yana da labarin komai dake faruwa amma bai nuna ma Ummah ba saboda ya san yanayin da take ciki shima bata son ya shige sa shi ya sa bai nuna mata ya sani ba kwata kwata. Share mata hawayen yayi dan Abba mutun ne mai barkwanci. Shiru tayi tana sauke numfashi suko su Nina ga dariya ga tsoro sai dai suka kalli junan su kawai suka yi murmushi.Junaid ne,Ayman,Abdul jabbar suka matso suma cike da murmushi da girmamawa suka yi wa Abba sannu da zuwa dan sun tsaya ne matan su fara gama yi masa sannu da zuwan.Sai dai ganin shiriritar LEENA bata ƙarewa ya sa suka matso. ✨✨✨ A ɓangaren MAHAJ kuwa ɗan motsa jiki yayi kaɗan kafin ya wuce masallaci,ya fara gabatar da sallah a cikin jami'in ta kasancewar lokacin ta da ya riga ya kawo.Cike da ƙwarewa ya yi ta buga Basket ball ɗin sa shi,kaɗai sai da ya ji jikin sa ya saki, dai dai lokacin aka fara kiraye kirayen Sallah ta magriba dan haka cike da kuzarin da ya ɗan samu na motsa jikin da yayi ya wuce ɗakin sa direct wanka ya shiga ya ɗauro wanka da alwallah da sauri sannan ya sako Jallabiya mai santsi da taushi maroon color Direct masallaci ya wuce achan ya haɗu da mahaifin sa cike da girmamawa ya gayar dashi,Shima cike da Murmushi ya amsa masa.Mubarak kuwa kai yake ta sunkuyar wa ƙasa ganin irin kallon da yake masa,na tuhuma, wanda shi kaɗai ya san yana yi masa shi saboda ya san duk wani Motsi nasa.Ganin ya dalla masa Harara yanzu bayan sun haɗa ido ne ya sa shi sakin guntun murmushi kafin ya bi bayan su shida Hon Gagara.Da suke yiwa laƙabi da Abbu.✍️ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Na rage kuɗin ne saboda complain ɗin wasu daga cikin ku masoya na,saboda irin ƙaunar da nake muku,na rage🥰.Na tabbata kuma in sha ALLAH zaku karɓe shi a hakan,Nasan rage su da nayi ba yana nufin na rage darajar labarin bane.. Masu niyyar saye🥰😘✨ Allah ya bada iko. Wayen da suka saya dan Allah kar ku fitar mini da littafi.Hakan shine kawai soyayyar da zaku nuna mini.Zan baku littafin amafarki na san ta, ga wayen da basu karanta ba a matsayin Naira 300 ɗin ku Ngde.🙏 Sai kuma labari mafi daɗi💃💃💃💃da zan sanar da ku zan baku complete book one free saboda soyayyar da nake muku,Book two kuma 800.Ongoing kenan. Complete book Idan an haɗa 1k.✍️ Ina godiya da shawarar ki Maman Abba🥰😘.Uwa ta ta gari Allah ya bar zumunci.🤲 Kk story daban yake,Ba zan ce yafi na kowa ba amma dai zance muku da ban yake.Ku dai kar ku bari Abar ku a baya. Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Comment,share,like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P.....1️⃣9️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* P...1️⃣9️⃣ Direct Sashen sa ya shige duk da ya san Mubarak na bayan sa hakan bai sa ya juya ba sai ma cigaba da tafiyar sa da yayi inda bai daka ta ba sai da ya tsinci kan sa a ciki ƙaton falon na sa.Zama yayi yana ɗan sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗago idanun sa da suka ƙara yin haske ya zuba su kan Mubarak dake tsaye yana sakin murmushi shi kaɗai dan ya kasa manta badaƙalar da aka sha da SHATOU.kan sa ya kawar bayan ɗan yi masa kallon yan mintuna.Wanda ko bai tambaya ba ya san abinda kallon ke nufi dan haka kai tsaye ya furta ' Eh dama Yarinyar nan ce na tuno da ita a ƙauyen da muka je ". Sarai ya ji shi kuma take ya fahimci inda yake nufi dan in bama yanzu da ya tuna masa ba shi ya manta da wata halitta Shatou a rayuwar sa. Bai ce komai ba dama Mubarak bai yi tunanin zai amsa masa ba.Dan haka ya ƙara furta " Dama cewa nayi a gafarce ni,na faɗawa Abbu maganar nan naga bai kamata a ɓoye masa ba shine,na ga ka fahimci komai daga yanayin Abbu ɗin shi ya sa naga Gara na faɗa maka karka ce na munafunce ka !"Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntun murmushi. MAHAJ kuwa idanun sa ya ɗan ƙara buɗewa a zuciyar sa yana ayyana gayen nan ya ma raina mini da wayau a fili kuwa ɗan kallon gefen ido yayi masa ganin yana Murmushi hakan ya sa bai ce masa ƙala ba,dan dama ya fahimci cewa ya riga ya matsi bakin sa da bai gajiya da magana idan ya tashi. " I know this will happen " Ya furta a hankali kamar mai tsoron magana.Mubarak kan sa ya shafa kawai kafin ya miƙa masa wayoyin sa da ya ajiye masa tun ɗazu sai dai ya san bai ko bi ta kan su ba har yanzu yadda ya ajiye su haka ya gan su. Ajiye mai su yayi nan kusa dashi kafin yayi masa Sallama bayan ya nemi ko yana buƙatar wani abu. Bayan fitar Mubarak MAHAJ numfashi ya sauke kafin ya miƙe da wayar sa wadda yafi amfani da ita ahannun sa,Babban falon ya fita Sashen Amma ya fara shiga anan ya tarar da su Sajida da Salma da Samrah dake ta buga game hankalin ta yayi nisa.Bayan sun gama sanar da ita irin wulaƙancin da yayi musu yau. Da murmushi kwance a kan fuskar ta ta amsa masa kamar bata ji komai bakin su Salma ba dan bata cika ɗaukar zancen su serious ba dan ta san halinsa ne,hakan ko samrah saboda tana little sister na sa ne yake ɗan sake mata,kuma duk wannan rashin sakewar ya samo asali daga irin kular da ya samu. Zama yayi cike da girmamawa anan ƙasa yana cewa " Amma Barka da dare " Cikin sakin fuska ta amsa masa. Ya hanya ta yi masa ya amsa da Alhamdulillah kafin yayi shiru ya rufe bakin sa ruf. Shiru falon ya ɗauka.Su ko Su Salma ganin yanayin sa ya sa suka kasa yi masa magana dan fuskar sa babu alamar akwai wasa acikin ta.Ƙarshe ma idan suka takura sai dai irin wulaƙancin ɗazu ya biyo ko makamancin sa dan sun fuskanci ɗabi'ar ya yan na su ce rashin son takura. Miƙewa yayi zai fice Amma tace " MAHAJ ba zaka ka yi Dinner ba,Abbun ku ba zai ji daɗi ba,idan kana zama da yunwar nan " Ɗan shiru yayi kasancewar ya dakata yana sauraren ta sai dai bai juyo ba. "Nop I'm full " ya furta mata a taƙaice kafin ya fice cike da natsuwa.Bayan yayi mata sai da safe.Dan ita da sake ganin sa sai in ya fito zaije Sallah,ko Allah ya Fiddo dashi cin abincin idan yayi ra,ayi. Da Harara dukkanin su suka bi bayan sa babu ma Kamar SAJIDA Salma kuwa mugun tsaki ta ja cike da ƙunar rai,sun rasa abinda suka kashe masa da bai iya ko amsa gaisuwar su sai ya ga dama a iya binciken su sun kasa gano laifi guda da suka yi masa da ya saka bai kula su ko dan basu haɗa jini dashi ba kamar Samrah.Haka dai suke ta yiwa kan su tambayoyin nan sai dai su gaji suyi shiru sannan Amma ta rarrrashe su. " Ku riƙa zuba masa ido tunda bai buƙatar magana da ku,kun san halin mutun dan me zaku riƙa damar da kan ku ne,na sha faɗa Miki Sajida ku fita iskan sa bakwa ji dan haka Ni kar wacce ta ƙara kawo mini ƙarar sa " . Baki suka Turo gaba ba tare da sun ce ƙala ba sai dai abun na ransu ba sa jin zasu bar zancen haka.Sun fi son ya je ga Abbu. Sashen Hajiya ya faɗa cike da natsuwa Sai dai bata cikin falon hakan ya sa kai tsaye Bedroom ɗin ta ya wuce dan ya san chan ne kaɗai zai same ta dan haka direct ya tsayar da ƙafafun sa ƙofar tare da ɗan yin knocking.Shiru ba,a amsa ba ba,a basa izinin shiga ba,Ƙara maimaita Sallamar sa yayi cike da sanyin da Muryar sa ta ƙara yi,dan ya san tabbas tana jin sa wata rana haka take masa. Ya ɗan jima tsaye kafin ta bada izinin shigowar sa fuskar ta babu annnurin murmushi.Sai ma karkace kai da take faman yi gefe jiki mace ya durƙusa ƙasa ya gayar da ita. " Ayyah Barka da dare,Ina wuni " "Barka,Lafiya " Kawai ta bashi amsa ta cigaba da jan charbin ta.Zaune yayi ya ta ƙwashe ƙafafun sa wajen kan sa sunkuye.Ya ɗauki kusan mintuna goma a haka bata ce masa ci kan ka ba.Cike da rashin damuwa dan ya saba da hakan yana shanye duk wani abu da zata masa,tun ba yanzu ba tun yana ƙarami,kuma yana mata uzuri ne dan itace ya buɗe ido ita da mahaifin sa ya sani sune uwa uba na sa.Tun chan farko ya san bata bashi kulawar da ta dace duk da itace ta riƙe sa.Amma a koda yaushe bayan yin wayan sa yakan yi tunanin dalilin da ya sa wata rana take juye masa izuwa wacce bata son shi,wata rana kuma ta nuna masa ƙauna fiye da komai kamar yadda ya taso hannun ta ya taso cikin wayen nan fuskokin biyu nata sai dai har yanzu ya kasa samun dalilin ta ɗaya,da take nuna masa haka,A duk lokacin da ya tambayi Abbu kuma ya kan nuna masa babu komai ƙila yanayin tsufa ne.Ya kan ji nauyin sanar da shi dalilin da bai zamo abun da zata ɗaura masa ƙiyayya ba.Yace masa me akan me.Sai dai wasu lokuttan yana ji tana dan gan ta abun akan mahaifiyar sa da bai san fuskar ta ba sai a hoto,wadda kuma bata ma cikin duniyar mu gaba ɗaya. " Idan zaka riƙa cin abinci ka riƙa ci,dan babu ruwa na ciwo ya kama ka ace ban riƙe amana ba ahto ". Daga wannan furucin Ayya bata ƙara furta komai ba.Sai ma miƙewa da tayi ta shige wata ƙofa ta bar shi nan zaune. Wani abu ya haɗiye mai nauyi da ɗaci kafin ya miƙe jiki a sanyaye ya bar bedroom ɗin. Yana fita Sashen Abbu ya nufa. Abbu dake duba wata tsohuwar jarida ne da yake adanawa a duk bayan lokaci ya kan ɗauko ta ya yi ta kallo yana Murmushi bayan karanta abinda ta ƙunsa. Yau ma kamar kullum ya same sa riƙe da ita ahannun sa sai dai shigowar ta sa ya sa ya mayar da ita gefe da sauri yana ɗaura wayar sa akai yana ƙakalo murmushi. MAHAJ da ya ga komai dan ya riga ya saba da ganin hakan dan haka ya nemi waje ya zauna ƙasa kusa da Abbun yana sauke ajiyar zuciya domin wani mashi da ya soke zuciyar sa na kewar mahaifiyar sa,A duk lokacin da Ayya ta masa wani abun mahaifiyar sa ce abu farko da yake fara tunowa da sai yaji wani irin rauni ya ƙara mamaye zuciyar sa. Lumshe idanun sa yayi yana buɗe su kan Abbu da ya zuba masa idanu kamar ya samu Tv.Dan kobai faɗa ba ya san daga inda ya fito.Tabbas yana ji da Ayya ba mahaifiyar sa ba ce da tuni ya sata ta bar rayuwar ɗan sa amma uwa ce har gida ya so chanza mata ta yadda babu yadda za,ayi taga MAHAJ ɗin abu ya gagara rabi da kwata ahannun ta ya tashi amma har yanzu ta kasa ajiye makaman ya ƙin ta wadda take yi dan ta ta fi,amma hakan bai sa ta chanza ba,bai da dabara baida iko dan haka ya zuba ma Ayya idanu tare da fatan Allah ya kawo haske a cikin rayuwar ɗan sa.Farin cikin da ya rasa Allah ya kawo masa cika makon sa. Murmushi ya ɗan ƙakalo kaɗan kar ya sanya Abbu a cikin damuwa ko ya ƙara masa ita.Abbu shima murmushin yayi da yake ƙara bayyanar da kamar su ta asalin fatar su da take iri ɗaya sak dan ba zama kace jinin Ayya bane dan ita chocolate ce. Abbu fatar Mahaifin sa ya biyo ta sak asalin Bature na Australia sai dai duk da kasancewar sa Bature ya banbanta da saura kamar yadda muka san ko ina akwai musulmi akwai Christian.Domin kuwa kakan Abbu Musulmi ne kuma ba Nigeriye,kakar sa ce Baturiya..Wannan kenan. " Kaci abinci kuwa " Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke jin Furucin na mahaifin sa. Kai ya girgiza masa a sanyaye."But" Miƙewa Abbu yayi ya cire kan sa dake kan ƙafar sa,bai bari ya furta abun da yake son furtawa ba, ya bi wata ƙofa sai gashi ya shigo da fruit wayen da aka yayyanka,da wayen da ba,a yanka ba.Tare da ruwa mara sa sanyi. Inda Abbu yabi yake kallo har ya ɓacewa ganin sa kafin ya sauke ajiyar zuciya yana ƙara lumshe idanun sa. Fitowar sa ce ta sanya shi ware su kan sa.Yana sakin guntun murmushi a cikin zuciyar sa. Zama Abbu yayi kusa dashi yana murmushi sannan ya miƙa masa pock da ya ɗauko wani irin apple mai kyau daga nin sa kasan zai yi daɗi. " Haaa " Haka Abbu ya ce harda buɗe na sa bakin kamar zai cida ƙaramin yaro. Murmushi ne ya suɓuce masa wanda bai yi niyyar yi ba wanda kuma bai wuce na jin daɗi ba saboda,hakan da abbu yake masa sai yake tuna masa lokacin da yake ƙaramin sa.kafin ya kai haka. Ɗan Buɗe bakin sa da yayi Abbu ya shammace sa ya ɗaura masa shi kan Leɓen sa.Idanu ya ɗan zaro a hankali kafin ya buɗe bakin gaba ɗaya ya tura apple ɗin yana zare shi daga pork ɗin.Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Abbu koba komai ya saka ɗan sa farin ciki a yau ko iya wannan murmushin zai gani akan fuskar sa yakan ji daɗi matuƙa rayuwar da ya taso mai cike da kewa yana rage ƙunci. Taunawa yake yi a hankali yana lumshe idanun sa dan ba zai iya nuna wa Abbu cewa bai da ra'ayin cin abincin ba.Dan chocolates ɗin da ya ci sun ishe sa dan haka bai rabuwa da su a cikin fridge na sa. A haka Abbu yayi ta cida MAHAJ kamar wani ƙaramin yaro.Ya ɗan ci kaɗan su kankana da su abarba apple ɗin sannan ya janye bakin sa.Bayan Abbu ya miƙa masa gwanda da ta nuna sosai sai tashin ƙamshi take yi. Sai da ya janye bakin sa Abbu ya lura da abun da ya ɗauko shi ya mama manta ya sako da ita.Shi ko MAHAJ Har tsikar jikin sa ta tashi.Gefe abbu yayi da ita. Ruwa ya ke kallo sai dai bai furta komai ba. Hakan ya sa Abbu fahimtar abinda yake nufi dan haka ya tsiyoyo masa ruwan da suke da ɗan ɗimi kafin ya miƙa masa cup ɗin karɓa yayi babu musu ya sha rabi sannan ya ajiye cup ɗin. Murmushi Abbu yayi bayan ya miƙa masa tissue ya goge bakin sa. Sannan ya shafa kan sa a hankali yana furta " Ni wai ba zani zan nema na fara goya ka ba MAHAJ ko yaushe ɗan ye shakaf kake komawa shekaran ka fa cikin na ishirin da ɗaya zaka shiga idan ban yi ɓatan lissafi ba ". Murmushin gefen baki yayi kafin ya ce " I'm still your little son " . Dariya Abbu yayi kaɗan sannan yace " Na tabbata hakan,bari na fara neman zanin goyo,ƙila kai da girma sai ka tara iyali MAHAJ,Allah ya kawo muna haske a cikin rayuwar ka ". Bai ce Amin ba sai ma rufe idanun sa da yayi bayan yayi wa Abbu kallon ƙasa ƙasa dan duk lokacin da yayi zancen nan yakan ji wani iri dan baya jin akwai wannan burin na tara iyali nan kusa,dan bai shirya ɗaukar duk wata hayaniya ba yadda yake rayuwar sa ta private life haka yake son ya cigaba da gudanar da Abar sa babu takura. Abbu dake lura dashi hannun sa ya riƙo yana furtawa a sanyaye. " Baza ka ce Amin ba MAHAJ "? Idanun sa ya ware kan abbu kafin cike da rashin son takura ya gyara bakin sa sannan murya ƙasa ƙasa ya amsa. Abbu sai dai hango yadda jajayen laɓɓansa suka motsa yayi. Samun kan sa yayi da yin murmushi kafin kowannen su yayi shiru. Kiran Sallah ne na Isha ya tayar da su Alwallah kowannen su ya ɗaura sannan suka fice daga part ɗin zuwa masallacin estate ɗin kamar wani wa da ƙane dan abbu har yanzu jikin nan na sa bai chan za ba sai kaɗan baka taɓa cewa ba ya'yan MAHAJ bane saboda yadda Hutu ya ratsa sa. *KAR KU SHAGALA KUNA KARATUN LITTAFIN KURMAN ƘADDARA*✍️ Tare da Fa'eeh BG. (Firstlady 🙌) Gimbiyar taskira👑 *** A ɓangaren su Abba kuwa ranka ya suka yi zuwa gida fuskokin su cike da farin ciki,bayan ya Rarrashi LEENA.Tare da Masu tsaron sa da come boy na sa da suke cike da kewar sa suma.Ma'aikatan masu kula da kamfanonin sa,dan suma sun zo tarbon Sa. Cike da farin ciki dukkanin ahalin suka tarbe sa,Har su Hamida sun zo da iyayen su dan Abba ya ɗauki yan watanni chan.Farin ciki Sir da Hajjo da su Uwani bai ɓoyuwa dan Abba mutun ne mai kula duk da kuwa baya nan yana ƙoƙarin kiran yan uwan sa da iyayen sa,surukan sa. Ƙaton dinning dake babban falon na Ummah aka baje masa komai da akayi masa duk wani wanda yayi masa abun tarba nan aka kawo masa shi.Dan faranta masa yana mugun son yaga ko ina ahalin sa ne dan haka har su Sir aka zauna akayi ci aka ƙoshi kafin aka ƙara yi masa ya hanya,ya kuma baro Germany ɗin dan chan ya tafi. Su LEENA da su REENA take aka fara mantawa da wani faɗa aka cigaba da bawa Abba kulawa.Ummah bakin ta kamar ya yage saboda farin ciki sai dai ta wani ɓangaren tana kaƙalo murmushi ne kawai bata san dalilin da ya sa bata son ganin kishiyoyin na ta a part na ta ba.Amma gudun abun magana sai take ƙoƙarin haɗiye komai gashi an shedeta da haƙuri dan Ummah mace ce mai haƙuri da kau da kai.Dan kafin ma kaji ance wani abun ya haɗa su da wani sai an bincika.ta san ta kan ta bata bari kishin ta ko kaɗan ya fita har ya zame mata illa.. Sai da aka watse gaba ɗaya sannan abba ya samu ya je ya watsa ruwa sannan ya dawo falo cikin ya yan sa.Cikin su ya zauna yana biye musu ana bashi labari rabi duk shirme ne dan REENA ce mai bada labarin idan ta faɗi wani abun sai dai yayi dariya ita ko LEENA sai ta galla mata harara.Cikin Surutun nan ne na ta wanda indai tana gaban mahaifin su bakin ta bai iya shiru duk da rashin hayaniyar ta ta sanar da shi Damben da suka yi aschl shekaranjiya. Yi yayi kamar bai sani ba ya tsaya ya saurare ta kafin yace " Amma ALEENATU Baki kyauta ba gaskiya,Yar ƙaramar ƙanwar taki zaki daka,baki san kin girma ba ". Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntun murmushi tunda abun ya wuce. Ɓata fuska Leena tayi kafin ta ce " Ai Abba itace sai ta dinga yin abu kamar bata da wayau Ni kuma sai na dinga jin haushi ". Kai Abba ya girgiza yana mai da kallon sa kan REENA da ta ke ta Hararar Alina sannan ya furta " Laaa laaa daina kin ji yar gaban goshin Umman ta,harara Anty kike yi,ita wannan Munbar wa BILAL S S ƙanwar sa " ya nuna Alina,nufin sa ita. Ya ɗan yi gefe da kan sa kamar bai ga yadda idanun ta suka cika da hawaye ba. " Allah Abba,Ni ta gaban goshin Familyn SSS ce gaba ɗaya nice hasken idaniyar ku,Ni bana son na zauna gaban goshin ya Bilal a bar Ni da kai da Sir da KaKa,Kuma inada Baba Mai bIllions a gefe na ". Ta kai ƙarshen zancen ran ta ɓace cike da ƙuruciya. Dariya Abba yayi yana son su tado da zancen sai dai sun ƙi dan haka bai ƙara tada zancen ba. Sai ma shiru da yayi yana kallon Ummah da tayi shiru kamar mai tunani fuskar ta babu annuri ta zuba ma waje ɗaya ido kamar hankalin ta bai kan su sai dai kuma duk abinda suke yi tana jin su,hasalima wata kalmar da Abba yayi ce ta ɓata mata rai. " Ai kuma REENA ce ta gaban goshin ta Abba bani ba ka tambayi Ummah kaji ". Zancen Leena ne ya shiga kunnen sa hakan ya sa ya ɗan juyo da kallon sa kan ta yana furta " ai kema ta gaban goshin sa ce ". Ummah ce tayi karaf ta amshe zancen cikin sakin Murmushi tana furta " Ai dukkanin ku na gaban goshin sa ne,his precious girls,kawai rashin jin maganar nan ne ke haɗa ku,idan kika daina zaki ga Kun shirya ". Ta kai ƙarshen zancen tana dariya. Abba dake jin ta kuwa wani guntun murmushi ya sauke kawai bai ce ƙala ba sai ma miƙewa da yayi,ya kama hanyar barin falon dan bacci yake ji saboda kwana biyu bai samu ya runtsa ba saboda yana shirin baro ƙasar.. " Zanyi bacci Barry,kar a tashe ni kowaye ya zo " . Ya ce wa Ummah.Dan haka yake kiran ta ko kuma Umman su. " Abba ko Yaya BILAL ne ya dawo " Reena tayi zancen tana Murmushi. Kai ya girgiza shima yana son yin dariya hango yadda Leena ke ta Hararar ta. Saboda jin wani sabon sakar ci.wanda ita bata ɗauke shi komai ba. yadai suɓuto bakin ta kuma ta fitar. " Ko shi ne SARINA ai ya san inda na fito ba zai so a tashe da Abban sa ba yana hutawa ". Hayewa yayi da ɗan sauri Ummah da ido ta bishi bayan ta amsa " TOH a fito lafiya " wani irin abu na tsaya mata arai. Kafin ta sauke numfashi. Miƙewa itama tayi ta shige ta kama hanyar bedroom na ta ba tare da tace wa su Lina komai ba. Ganin haka ya sa suko suka fito suka yi Sashen Uwani. A chan suka yada zango duk sun cika kaka da surutu gashi ba wata Isasshiyar lafiya amma haka yake biye musu,shida Uwani sai dai suna ta ƙoƙarin ganin an rabu lafiya gudun kar su fara faɗace faɗacen na su dan haka da an kwata Uwani zata tare. Su waye suka yi missing rigumar Shatou 🤗🤣😂Kar ku damu Nima ina kewar ta zamu je sashen ta next part in Sha ALLAH. Da ga yanzu update ya koma duk bayan kwana ɗaya. Saboda na koma school lecture sai a hankali.Allah ya sa zaku fahimce ni.ngd. _FA'EEH BG✍️_ Book one free Book two paid#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Comment,share,like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣0️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* 👑👑👑 ___________________Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a ɓangararen.Yau da daɗi gobe babu daɗi.Faɗan su Leena yanzu har gaban Abba yi suke yi sai dai yayi ta faɗa shida Ummah.Tun da haka yarintar su take babu abinda zasu iya yi Musu sai fatan shiriya. BILAL ya samu kwanciyar hankali shima ya duƙufa aikin sa kasancewar hutun da ya samu ya ƙare masa achan ya ƙarar dashi.Sai dai har yanzu baya neman Leena ko ya kira waya baya zancen ta.Haka itama babu ruwan ta dashi fushi take yi dashi mai zafi dan haka a gaban ta zasu yi waya da Reena bata taɓa cewa a bata su yi magana,wata rana a gaban ta har video call suke yi kuma tana fitowa zai gan ta sai dai bata kula ko nuna cewa ta san abun da suke yi,abun na damun Bilal ɗin sai dai ya zuba mata idanu kawai ya ga iya inda fushin zai tsaya,Ummah kuma da Abba sun zuba musu ido a cewar su sun fi kusa da ya'yan na su zasu ma sauko ne,kowa yayi mamakin fushin na ta dan tana da saurin sauka bisa ga ma Leena da bata da faɗan amma tana da wahalar sauka idan tayi fushi. Duk abun da ƙannen na sa suke ciki yana sane dan har case ɗin Anisa da ta shiga ta yi dambe da Wanda ya daki ƙanwar Anisa ɗin,kamar yadda ta ce sai ta koya masa hankali, wanda kan hakan ya sa Uztas Babba ya zane ta tare da mayar da ita gida suspension na rana ɗaya.Sai da tayi kusan kwana biyar hakan ya sa aka bawa Nina takarda ta kai gida saboda gaba ɗayan su har ita har REENA ya ji suka yi sai dai sun ce hutun kwana biyu aka ba su ana su ajujuwan dan haka Ummah da Abba suka yarda.Sai dai bayan hutun ya ƙare har sun ƙara wani Ummah ta sha kai da zancen komawar su makaranta.Ana cikin haka sai ga Nina da Hamra sun zo da takarda suka ci sa,a Abba ranar a sashen yake dan haka suka damƙa masa aiko ya tara su su duka biyun ya yi ta musu faɗa dan babu abun da aka ɓoye a takardar ga cikakken sunan Leena nan.ALINA SALEH SADA. Har Reena haka na ta yake rattafe an rubuta nata rashin zuwa makarantar wanda shine laifin ta kawai. Da haka aka tasa ƙeyar su bayan an musu faɗan da ya bi taɗa yan kunnen leena ya bi ta ɗaya ya fita... ••••••••••••A ɓangaren SHATOU kuwa duk yadda Inna ni take ƙoƙarin ɓoye wa Baffa na sai da ya fahimci cewa yar sa ta girma dan haka addu'o,i kawai ya bita da su cike da farin ciki da mamakin ɗan mutun girman sa babu wuya idan akwai rayuwa wanda ya sa har ya tuno da wani shuɗaɗɗen lokaci da bai taɓa tsammanin shatou zata zama mutun ba. Sai dai mutuniyar taku babu abinda ta ɓoyewa su Amina.Suka dinga murna suma sun kusa girma kamar Shatou tunda Inna ni tace ta girma nan gaba kaɗan zata zama Babba. A ɓangaren rigimar ta da Iro sai abun da yayi gaba domin sai da ta rama cin kashin da yayi mata bayan ta tabbatar shine dai wanda yayi rubutu akan allunan makarantar su. Dan haka ta fashe masa tayun keke gaba ɗaya,fashi kuma irin na babu gyara. Koda Iro yayi bincike ya gano Shatou ce dan haka ya ƙullaci sai ya wulaƙanta ta,tare da ɗaukar zugar ƙawayen sa.Yanzu haka yar ɓuya ake yi tsakanin su.Dan ita da kan ta ta san tayi masa illa babba wadda kuma take farin ciki har cikin ranta. Inna ni kuwa mugun daɗi take ji a tunanin ta shatoun ta yi hankali tun ganin kwana biyu bata ɓallo masu wata rigima ba da iro tunda shine abokin faɗan ta. Sai dai kamar haka ne dan ta rage yawon Sosai,ko farauta yanzu ba kullum take bin su ba. Tafe Suke a hanya su huɗu,sun kaiwa Maman ramata aiken da ta musu,suna tsalle tsallen su na yara masu ƙuruciya.Ta furta "So nake Ɗan gidan elibabeth ya dawo na rama cin kashin da yayi mini dan ban manta ba " Kai Amina ta ɗan juya tana dariya saboda ta san maganar ramuwa ce dan kwana biyu da suka wuce Shatou kullum cikin jini nin sa take in ta haɗu da shi sai ta masa wulaƙanci,kamar yadda ya wulaƙan ta ta.Tana batun furta wata kalma akan zancen na zuwan sa sai kawai taga SHATOU na sakar mata harara da ta sakata haɗiye maganar ta.Kafin kuma tayi gaba tabar su nan cirko cirko. Da sauri suka bi bayan ta har da haɗawa da ɗan gudu,kamar yadda ta fara gudun itama. Ramata ce ta furta " ki jira mu Don Allah shatou " Chak ko ta tsaya saboda jin sunan Allah da Ramata ta ambata,saboda SHATOU akwai taƙawa duk abinda ka haɗa ta da Allah kan sa kagama dan haka su Ramata da sun fara abu ta zille sai su haɗa ta da Allah sai kiga ta sauko anyi komai cikin natsuwa. Suna isowa kusa da ita suka jera suka cigaba da tafiya kowannen su na sauke numfashi dan sai da suka haɗa da gudu. Turus tayi ganin Wanda ke gaban ta,kamar an jefo sa, cike da masifa take kallon sa dan duk da ta san ta masa rashin mutunci bata jin zata nuna masa ta ji tsoro dan bai isa ba. Kallon kallo aka fara tsakanin su,suko yan zugar abokan sa sai wani ciccira suke yi jira suke yi kawai ya basu umurni su hau ta da bugu dan bulali ne hannun su masu girma,ashirye suka zo bayan samun labarin an ga Shatou ta wajajen Layin Audu mai chemist itada su Amina. Su ko su Amina tsoro ne ya mamaye musu zukata musamman ganin wayen nan bulolin sai hankalin su ya ɗaga matuƙa babu ma kamar Amina. " Yau dai na kama ki bayan gama ɓoye ɓoyen ki,ke Ni zaki wulaƙanta,yau Bama zan jira hukuncin mai gari ba da kaina zan hukunta ki,kuma in kin isa ki rama ". IRO yayi zancen cike da gadara da rashin mutun cin da ya zo da shi. Hanɓare baki tayi bayan ta kyaɓe sa tana galla masa harara cike da rabin tsoron ta.Sai kuma ta saki guntun murmushi irin na rainin wayau kafin ta riƙe ƙuguu tana cewa " Ai dama jiranka nake yi,mu haɗu fuska da fuska,dan na shaida maka cewa ba zan taɓa yafe maka ba,abunda nayi maka bai cire mini zafin abubuwan da kayi mini ba,wai har Ni zaka ƙaryata kai da wayen nan ban zayen abokan na ka,saboda son ranku baka san abun na raina bane ko me,Sannan ka koma ka yi mini wani suna chan da bai da daɗin faɗa ma,kuma ka sake ƙarya ta ni,ai nikaina wannan karon ba sai an je gun mai gari ba " Duka Idanu suka zuba mata sake da baki ƙaramar yarinya na zaro zance cike da rashin tsoron ta yadda ma take juya ɗan ƙaramin bakin ta yake kallo wasu miyau iro ya haɗa yana ƙarewa Shatou kallo daga sama har ƙasa irin kallon da bai taɓa yi mata shi ba. Idanun ta da take ƙara juyawa cike da masifa yake ƙara bi da kallo. Sai dai kafin ya iya cewa wani abu ya ji saukar bulala bulalar nan ba jikin kowa ta sauka ba face jikin Shatou wani daga cikin su ne mara haƙuri wanda yake mugun jin Haushin ta ya far mata saboda ta kira su da wawaye dama wanchan karon cike yake da ita.Cike da Masifa Shatou ta kai ƙasa tana kururuwa kafin ta kwaso ƙasa ta fara auna musu a jiki idanun ta a rufe cike da masifa. Dai dai lokacin kuma manyan motocin da ke ratsa hanyar suka wuce su.Su Amina kuwa cike da tashin hankali ganin an fara da Shatou suka fara neman hanyar gudu itako babu alamar zata motsa sai dai cikin ikon Allah tayi musu wankan ƙasa yadda take so musamman wanda ya dake ta dan gaba ɗaya idanun sa sun rufe da ƙasa dan bai ankara ba ya jita kamar yadda itama bata zaci jin bulalar ba.Iro dai da ya ga Kamalu ya riga ya gama aikin da bai bashi dama ba hakan ya sa ya kakkaɓe ƙasar da ta gama musu wanka da ita wadda ya cire ta idanun sa da ƙyar sannan ya ce " muje kamar baƙin nan sun shigo fa " Yana yi yana kallon suturar jikin sa da tayi buɗuɗu.Yana ma tunanin yadda zai je wajen haka yaron nan ya masa kallon banza.Basu kula Shatou dake Masifa ba tana Allah ya isa kuma yanzu yanzun nan sai ta je ta samu mai gari da cin fuskar da suka mata bata musu komai ba dan ta riƙe shatin bulalar da ya ɗan kwanta mata. Basu kula ta ba suka miƙe hanyar da suka ga baƙin motocin nan sun wuce saboda inda za,a fara aikin ne yau ne ranar ƙaddamar da shi. Ita ko shatou cike da masifa ta miƙi hanya bata zame ko ina ba sai fadar mai gari sai dai ta tarar da ya tafi chan gurin dan haka ta nemi ƙofar gidan na sa ta zauna tayi zaman nan na duk wanda ya tara ya samu dan jira take wani ya mata ko kallon banza ne ta masa rashin mutunci.Kamar ko sauran ya yan mai gari sun sani duk wanda ya zo da yayi mata kallo ɗaya ya shigewar sa gida Mutun ɗaya ne Abu shine ya tsaya tambayar ta me take yi zaune cikin wannan rana.Sai dai kamar yadda bangon da take jingine da shi ba zai iya magana ba haka itama bata tanka masa ba.Yar ƙaramar dariya yayi kawai ya shige cikin gida dan ya san ɗayan biyu baza a rasa da wani a gidan take rigima ba ko Zaidu ko Iro da ya rasa dalilin da ya sa yake biyewa yarinya yar firit da ita amma ya biye mata shi idan shine da tuni ya fita iskan ta.Dan shi Mutun ne mai daraja mutane ba halin su ɗaya da Iro ba da Zaidu dan ko Iro rashin jin na sa sai ta kama yake yin sa ko ta Shero masa. A dai dai lokacin da SHATOU take ƙara cika tana batsewa kuma alokacin ne aka ƙaddamar da fara aikin Gina manyan bohole da kuma fanfuna tare da aikin makarantar su Shatou. Cike da farin ciki mai gari ya kamo hanyar gida tare da jama'ar sa tare da manyan motocin nan a bayan su saboda yadda mai gari ya Matsa da akwai babbar kyautar da zai basu dan haka babu musu Abbu da ya samu zuwa yau ɗin saboda MAHAJ ya koma schl akan wani uzuri na gaggawa shi ya sa bai samu dawowa ba dole Abbu ne ya gabatar da aikin cike da farin ciki da alfahari. Isowar su gurin ya bawa jama'ar dake tare da mai gari gyara wajen shimfiɗar cike da farin ciki dan abu ne da basu taɓa tsammani ba domin sun ji farin ciki sosai ba,a taɓa samun wani mai muƙami da ya kula da su ba kamar sa,koda suka kai koken na su ba suyi tunanin zai karɓu ba dan suna ɗan fama da matsalar ruwa kaɗan saboda a rafi ake ɗebo su kuma bohole ɗaya da suke da ita da wata ƙungiya mai zaman kan ta ta gina da daɗewa itama bohole ɗin sai a hankali Saboda ya tsufa kun san halin ƙarfe da ta tsufa sai dai a yi ta haƙuri. Sai da duk suka Zazzauna masu zaman gurin yan fadar sa sannann aka fara jawabin godiya tare da fito musu da ƙwaryan Nono mai kyau,da zuma da duk wani kalar abu da ake samu a ƙauye,Zuma ta fito daga wajen Baffa na ne saboda ya san inda ake samun zuma dan haka ana samun mai kyau a wajensa saboda haka mai gari ya masa magana da wuri dan haka aka tana de ta mai kyau da ita da uwar saƙar ta babu haɗi.Haka aka jere Musu su cikin boat ɗin motar da Abbu yake ciki. Ganin irin kayan da aka fito da su ne ya sa Abbu fitowa daga cikin danƙararriyar motar ta sa da ya ke hakimce a bayan ta.Cikin wata dakakkiyar shaddar sa fara da ta ƙara fallasa asalin kalar fatar sa,Shaddar sa sai maiƙo take yi, ya fito yana zuba ƙamshi fuskar sa cike da murmushin da ke nuna farin cikin sa da kuma kasancewar sa mutun mai sanin darajar ɗan Adam da girmama sa bai ji Dar ba ya nemi waje tare da gyaran babbar rigar sa ya zauna hakan sai ya ƙara masa ƙima a idon al ummar garin. Godiya ya fara yi musu da karamci su cike da farin ciki. Sai dai me kamar Shatou jira take yi ya sauke zancen sa,dan bata tsaya tantance mai maganar ba ma ta ce " Baba Mai gari ina da magana ".Tsit wajen yayi jin yar ƙaramar Muryan ta dan babu wanda ya lura da ita a wajen dan har Baffa na na wajen saboda suna cikin manyan ƙauyen. Zuba mata idanu yayi kasancewar bai san da ita wajen ba dan mutane sun rufe ta saboda taron harda ƙananan yara da suka biyo motocin cike da burge wa. Kallon ta mai gari yayi jin yau har da Baba mai gari ake kiran sa dan haka yayi murmushi yana fatan ba rigima ta kawo ta ba. " Ina jin ki SHATOU " Magana ta fara " wallahi su iro ne suka ci zarafi na shida abokan sa kuma ban musu komai ba,kuma wallahi sai an rama mun idan ba haka ba kuma wallahi ban yafe musu ba wuta balbal" Kuka ne ya ci ƙarfin ta hawaye suka wanke mata fuska kowa dake wajen kallon ta yake yi kowa na son tofa albarkacin bakin sa sai dai mai gari bai bada damar hakan ba. Babu wanda ya dakatar da ita daga kukan har sai da ta dakatar da abun ta sannan ta yi shiru. " Ikon Allah ke ko Shatou bugu dai,dame suka buge ki,sannan dawa dawa aka yi aikin,faɗa mini su yan zu su ji hukunci,dan lalle tabbas basu kyauta ba " Mai gari yayi zancen cike da nuna alhini sai dai a kasan zuciyar sa dariya abun yake bashi shi har ya gaji da case ɗin ta. " Kamalu ne sauran kuwa dariya suka dinga yi mini kuma bai bani haƙuri ba dan haka bulalar zasu nemo Nima na rama,dan da bulala ya dake ni,kama ga inda suka buge ni nan har an fasa mini naman jiki na,harda jini gashi jini na litre kusan biyar ya ƙare kwanan baya,duk ya tafi saura kaɗan gashi kuma sun ƙara zubar mini da abu na ".Ta kai ƙarshen zancen tana sakin kukan sangarta.Dariya wasu daga wajen suka fara dan abun ma na dariya ne,wai sun ƙarar.mata da jini.Mai gari murmushi ya saki cike da basar da dariyar da yake son yi ya ce " Subhanah har da jini suka zubar miki muga inda ya zuba ". Hannu ta miƙa masa inda shatin bulalar ya zauna kaɗan shima sai ka matsa ne sosai zaka iya gane shatin dan ma tana fara ne shi ya sa wajen yayi jaa kaɗan. Kai mai gari ya jinjina cike da alhini harda ɗan rufe ido kamar irin ya ga inda jinin ya zuba alhalin babu alamar gurin ya zubar da jini. " Ka gani ko,Wallahi sun zalince ni matuƙa dan haka nake son ka bi mini haƙƙi na ". Ta kai ƙarshen maganar tana share ƙwalla . Baffa na da ke zaune a nan kaɗan da ita ya sauke numfashi yana ɗauke idanun sa akan ta cike da wani irin Tausayin ta dan ya san tunda tace an dake ta yi anyi ɗin. A yanzu mai gari Baffa na ya ɗan kalla kafin ya ce " Kamalu me ta yi maka " Bayan ya kallo gefen da suke cirko cirko. Tsaf suka kwashe komai suka faɗa masa,har kasar da ta musu wanka da ita wanda ga alama nan kowannen su bususu babu ma kamar Iro da kamalu da idanun sa suka yi jajizir saboda ƙasar da ta shiga cikin su dan har yanzu yana jin ta sai zuji suke masa yana jin ƙasa na ɗawafi a cikin idanun.Ƙare musu kallo yayi ga dariya babu halin yi. Kanta ya dawo tambayar Dalilin da ya sa tayi musu hakan cike da wani irin mugun Haushin su har mai gari ta zayyane masa komai ƙarshe ta kasa faɗin sunan da ya saka mata aka yi aka yi ta faɗa ta kasa faɗa. Sai Amina ce aka tambaya da suka zo wajen ba da daɗe wa ba ta sanar da mai gari.Nan take da wasu suka dinga dariya shi kan shi mai gari yayi dariyar sunan babu halin fitar da dariyar sa,dama kowa yana son darawa su Iro da ita kan ta uwar kawo ƙaran. " Yanzu kin san abun da za,ayi zan hukunta su da hannu na,tun da har kin rama Kinga ko hakan nan ai kin rama abun da suka Miki,duba yadda kika mai da su kamar kuran daji, ".Ya kai zancen ƙarshe fuskar shi da ɗan murmushin " kar ki damu,na fahimci gaba ɗaya laifin Iro ne dan haka da kaina zan rama Miki bugun da suka miki,ba sai kin wahala ba har ki ƙara zubar da jinin ki,ayi haƙuri Hajiya Shatou,ƙasar nan ma hukuncin ta yayi " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ɗan murmushi. Ita kuwa SHATOU wani gingiririm kan ta yayi mata cike da jin daɗin har da Hajiya yau ta samu sunan da ake kiran yan birni da shi dan haka ta ce " A ƙara masa kashe di da zugar abokan hi dan Wallahi suka ƙara shiga gona ta sun san sauran sai na musu abun da basu zata ba " Dai dai ta gama furucin idanun ta suka faɗa a cikin na Baffa na.Baki ta tura gaba tana ƙyafƙyafta idanun ta.Alamar rashin gaskiya da kuma mamaki.A hankali ta fara bin sauran jama'ar dake wajen.Dai dai ta tsaida kallon ta kan Abbu da yake ta sakin murmushi tun lokacin da ta fara magana ya zuba mata idanu kamar ya samu tv wani irin lamari mai girma na ɗarsuwa a cikin zuciyar sa akan SHATOU. Murmushi ya sakar mata mai sanyi ganin yadda ta zuba masa idanu kafin ta sauke kallon ta kan Mubarak da ke ta sakin murmushi shima dama ya hango ta ɗazu da suka shigo sai dai bai yi zaton faɗa ake yi wajen ba yayi zaton ma taɗi ne suke yi irin na ƙauye tunda ya san da wuri suke yi wa ya yan su Aure daga Mazan har mata.Samun kan ta tayi da mayar masa da murmushin,tana mayar da idanun ta kan Mubarak karo na biyu kafin ta galla masa harara dan tsaf ta gane sa, idanu ta ɗan ƙara warewa ko zata hango uban gidan na sa da ta tara kalolin masifar da zata masa sai dai babu alamar sa a gurin fahimtar hakan ya sa Mubarak Shafa kan sa cike da murmushi ya girgiza mata kai.Harara ta ƙara jefa masa duk da cewa ta fahimci abinda yake nufi ɗin.Ita koda ta ga manyan motocin bata san sune suka dawo ba.A zaton ta wasu baƙin aka yi daban dan bata ji zancen ba ko ga su Baffa na ne saboda kwana biyu tana samun yawan bacci tun fara yin al'adar ta dan ko fita rage yi tayi.Koda taji Iro na maganar baƙi sun zo ta yi zaton sababbi ne ashe sune dan sai yanzu ma da ta ga Mubarak ta ƙara tuna cin kashin da take faɗa ya mata,dan kwana biyu ta watsar da shi da lamarin sa,sai dai ta daɗe tana tsara irin abun da zata masa na ramuwa a,a chan farko har bacci ranar da aka yi abun bata yi ba,kusan kwana uku,a cewar ta ai ko Dagaske shi ɗan gidan elibabeth ne sai ta rama sai dai ya tarkato dangin sa turawa ayi faɗa dan ita da Bibu da Baffa na sun ishe su. ___________Hoo uwayen rigima🤭🤣 _FA'EEH BG✍️_ ~👑GTW👑~ ________Kallon ta yake ƙarayi ganin ta yar cukur da ita kamar ka hura iska ya kwashe ta,gata ba wani tsawo ba. Hannun rigar ta sai faɗuwa yake tana mayar da abun ta dan mayafi ne hannun a jikin ta,dan haka aka dawo dashi a hannu kun san dai irin shigar mu ta ƙauye duk da haka dai ita taɗan banban ta dasu dan babu ruwan ta da wannan damɓare damɓaren powder da su Ramata suke yi da Sauran ƙawayen su dan itama Amina tana shafawa sai dai ba kullum ba. " Daga yau Iro,Kamalu,Rabilu,Saminu,Dauda .... Babu ruwan ku da shiga sabgar Shatou kun ji na na faɗa muku ko,dan na fahimci cewa kune baku da gaskiya,kun ji ko,maganar wankan ƙasa da tayi muku kuyi haƙuri kun Kaita ƙul kar wanda ya ƙara saka mata hannu da sunan bugu ko ba ita ma ba kar ku ƙara bugun wata a ƙauyen nan." Maganar mai gari ta dawo da hankalin ta kan sa tana cire idanun ta daga Mubarak da take ta aikawa da harara kamar taga uban gidan na sa shiko sai murmushi yake saki abun sa. Haka ma Abbu sai kallon ta yake yi ya kasa miƙewa su wuce har yanzu mamakin ta bai bar sa ba na yadda take ta zance haka kamar wata babba kuma.dudu shi gani yake Bama zata wuce shekara goma ba,idan ma ta kai su. Allah Abbu idan ta jika kana kiran ta Yar goma zaku yi rigima,da ka san rigimar da ke tsakanin ta da ɗan ka hm🚶🤣 Kai su Iro suke gyaɗa masa kamar ƙadangaru,sun kasa iya furta komai kamar an musu dabaibayi, ga mamakin munafurcin yarinyar da suke yi dan haka suka ƙara kullatar ta azukatan su sai dai shi Iro wani lamarin ne yanzu da ban a cikin zuciyar sa wanda ya fi na baya kamar yadda dama chan yake ƙoƙarin ganin ya cusa kan sa gare ta,sai abun ya ƙara zama mai girma gare sa dan haka ya amsawa mahaifin na sa anatse babu wata damuwa akan fuskar sa,kamar bashi ba. Suko cike da hasala suke kallon ta suna jin ina ma da wuta su kaɗa ta su huta ta zamar musu ala ƙaƙai yanzu ko an zo wajen mai gari ita ake bawa gaskiya.Musamman ma Kamalu. " Kema Shatou ki daina shiga sabgar su kinji ko,mace kike bai kama ta kina biye Musu ba,idan sun ja ki kawo mini ƙara ko bama su bane,ki bar ɗaukar hukunci da kan ki kinji ko " Kai ta gyaɗa masa cike da sanyin da jikin ta yayi saboda tana jin idanun Abbu akan ta,idanun da ta ke hango su sak na mutumin da ko sunan sa bata sani ba,Dan haka take jin cewa da alama suna da zumunci tunda ta gan shi shima tare da Mubarak ɗin.Ƙila ya'yan shine ta ayyana aranta. Kafin ta kalli mai gari ta ce " Ai dama Ni babu ruwan na da su dama Inna ni tace na daina kula kowane namiji idan ba Baffa na ba ko Bibu,A yanzu ma nan sauri nake na fita gurin nan ". Murmushi Mai gari yayi yace " To Allah ya sa mudace kinji A kula sosai,Banda faɗa kinji nida kaina zan yi Miki maganin su " Kai ta gyaɗa masa kafin ta fice daga wajen. Chan ta ɓulla inda zata iya ganin Baffa na da kyau ta Kalle shi cike da murmushi kamar ba ita ta gama kuka ba ta ce " Baffa na, na jira ka,ko na wuce wa ta,?." Zuba mata ido Baffa na yayi ganin Dagske amsar tambayar take nema dan haka ya samu kan sa da sakin Murmushi yana girgiza kan sa. Sannan a hankali cikin sake fuska ya ce " Shatouwa Ai ba tare muka zo ba,ki tafi kawai ". Baki ta tura gaba kafin ta ɗan saci kallon gefen da Su Abbu da Mubarak suke tare da masu tsaron sa da suke zagaye da gefen na su kamar jira suke yi,suma securites din kowannen sa fuskar sa babu annuri kamar dai yanayin masu kula da MAHAJ ɗin. Murmushi ta mayar ma da Abbu cike da wani irin yanayi da kallon na sa ke sakata dan sai taji guiwoyin ta sun riƙe.Shi ko Mubarak Wata Hararar ya ƙara samu.Juya wa tayi ta kalli Gefen da su Amina,ramata,Jawairiyya,Ta banka musu harara kamar idanun ta zasu zube sannan ta yi gaba abunta tana tsalle tsalle. Idanun sa ya sauke yana girgiza kan sa kaunar yarinyar na ƙara samun waje a cikin zuciyar sa natsuwar da ya hango ta ɓoye ya ke ƙara jinjina da kuma baiwar hankali da take dashi a yan shekarun ta na ƙuruciya. Hmmm Abbu ina hankali anan🤭 Mai gari ma murmushi ya saki kafin ya maida kallon sa kan Abbu yana bashi haƙuri tare da ƙara yi masa godiya. Abbu kuwa cike da murmushi yayi musu sallama bayan ya miƙe yana ƙara gyara zaman Babbar rigar sa.Ƙarewa Baffa na kallo yayi kafin ya miƙa masa hannu kasancewar duk haka yayi musbaha da yan majalisar.. " Baffa na,Ina ji kamar kabar mini yar nan taka,na tafi da ita, tana da abun dariya da bada nishaɗi" Murmushi Baffa na yayi kafin yace " SHATOU haka take Ranka yadaɗe ƙuruciya kowa da irin ta sa,ita haka Tata take,ai kalar mu ce ba zaka iya da rigimar ta ba " " Haka ne lallai ita Tata mai kyau ce kamm dan tana da hankali,da tarbiyya,ina son yaro haka mai sake wa da ƙarfin guiwa " Murmushi Baffa na ya ƙara saki karo na biyu kafin cike da jin daɗin yabon irin sa yayi masa godiya. Jinjina hannun sa Abbu yayi da hannun sa ɗaya kafin ya sake sa suka shige mota. Hannun Baffa na ya kalla da ya darmaƙa masa manyan kuɗaɗe masu yawa,yan Bandir na Naira dubu. Yana ƙara nanata abinda ya furta masa sama sama kafin barin sa wajen " Abawa Hajiya Shatou " Baffa na kuwa dubawa yayi idan babu mai ganin su dan haka ya sauke numfashi,dan kowa hankalin sa yanzu yana ga motocin da suka fara reverse, yana mamakin dalilin da zai sa ya bawa Shatou kuɗi dan bai da ikon mayar wa saboda sun riga sun shige mota hakan ya sa dole ya cusa su a cikin aljihun sa saboda kar abun ya zama ƙananun magana a cikin ƙauyen..✍️ _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣1️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ___________Tunda suka kama hanyar barin ƙauyen yake ta sakin murmushi yana ƙara jin wani lamari na ginuwa a zuciyar shi game da Shatou.Shi kan shi Mubarak Murmushin yake saki a gaban mota yana driving hankali kwance yana ji ina ma ace tare da MAHAJ suka zo ya ƙara ganin Abokiyar rigimar sa dan ya san har yanzu abun na ranta daga Hararar da ta ta sakar masa. Ƙasa haƙuri yayi ya ce " Mubarak Ka san wannan yarinyar ne,hala,naga yadda take ta jefa maka Harara a ɗazu ɗan shafa kai Mubarak yayi kafin ya furta " eh wanchan zuwan da muka yi sai da aka yi rigima da ita da MAHAJ ".Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ƙaramar dariya.Abbu kuwa idanu ya ɗan waro cikin mamaki yana furta " shi Mahaj ɗin ".Kai Mubarak ya gyaɗa masa kafin ya fara bashi labarin yadda komai ya faru.Kai Abbu yake girgizawa fuskar shi cike da murmushi babu ma abun da yafi bashi dariya furucin ta na ko shi ɗan gidan waye ne,ko ɗan gidan elibabeth da donath trup.Dariya ya ƙara saki mara sauti yana ƙara mamakin yadda Mahaj ya biye mata har da mayar mata da amsa ya kira ta mai bilicin.Ji yayi ya so ace a gaban shi komai ya faru dan haka next time ya ƙudurta wani abu a ransa. " Baku kyauta ba ai da ya bada haƙurin amma na san ba lallai ma ta samu kalmar ba lallai MAHAJ ya haɗu da dai dai shi waton duk rashin son maganar ɗana sai da ta saka shi magana " Ya kai ƙarshen maganar ya na ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi. Shi ma Mubarak Murmushin ya saki kafin ya ce " abun da ba zai taɓa yuyuwa ba kenan Dady ". Kai Abbu ya girgiza yana jingina kan sa da sit ɗin kafin ya sauke numfashi da ajiyar zuciya a hankali ya cigaba da karatun jaridar sa sai dai duk bayan ɗan lokaci zai saki murmushi wani irin nishaɗi yake ji a ran sa. Baffa na kuwa gida ya wuce shima cike da jimamin lamarin da ya ke gani kamar alamara haka kawai abawa yar sa kuɗi irin wannan bai taɓa riƙa irin wayen nan kudaɗen ba kuma a hakan ma basu burge sa ba dan sai yake ganin kamar ba dan Allah Abbu yayi ba,ya san halin yan siyasa ance suna bada kuɗin tsafi,kuma suna bada kudaden su Badan Allah ba sai dan wata rana su nemi wani abu a wajenka,shi bai hango hakan gun Abbu ba dan a ɗan zaman da suka yi ya hango nagartarsa da kuma mutuncin sa da addinin sa da suka kai shi matsayin da yake kai yanzu domin a kallo ɗaya zaka shaida Abbu mutumin kirki ne mai nagarta. Har yaje gida yana juya kuɗaɗen cikin aljihun sa. Tun da ya shiga ya kafe Shatou da idanu yana kallon ta ita kuwa tunda ta ma sa sannu da dawowa ta cigaba da yan wasannin ta na kitson ɗiyar a guro ta toton rake tana kitson tana labta ma kan mai kamar na mutun,tunda ta fara Inna ni tayi mata faɗan ta daina saka mai,kar ta ƙarar musu dashi,ta amsa da, to ta tashi ta mayar da kwalbar,sai dai ashe ta ɗibi wani ta saka a saman ƙafar ta. Dan haka Inna ni bata lura ba,tayi zaton ta mayar da shi dan haka take yin abun ta hankali kwance,hankalin ta ya ɗauku dan haka bata kula da kallon da Baffa na yake Binta da shi ba. Inna ni ce ta lura bayan fitowar ta daga ɗakin ta yanzu kai tsaye ta ce " lafiya Baffan su kuwa ? " Kai ya jinjina mata yana ƙawata fuskar shi da murmushi kafin ya ce " Babu komai A'ee kawai Shatou nake kallo naga sai girma take ta ƙarawa da hankali " . Ba shatou ba har Inna ni murmushi tayi ita kuwa SHATOU wani daɗi ne ya mamaye ta dan haka ta ɗaga idon ta ta kallo Baffa na Sannan ta ce "Allah Baffa na Dagske " ? Kai ya gyaɗa mata kafin ta miƙe cike da wani irin tsalle tana furta " Yee na kusa yin Aure Nima " Ido Inna ni ta waro kafin ta rarumi mabur kaki ta bi Shatou da shi aiko a Guje Shatou ta shige ɗakin Baffa tana Dariya dan ta san nanne kawa zata shiga ta tsira.Ai ko Inna ni bata matsa ba sai murmushi ta saki tana hararar ta saboda Baffa na ba zai barta ta taɓa ta ba saboda a ƙofar ɗakin ya zauna kan yar kujerar sa. Murmushi ya saki yana furta " A'e kar ki karye mini ƙashin ya da wannan abun " Yayi zancen yana nuna maburkakin. Kai Inna ni ta girgiza kafin ta sauke a jiyar zuciya idan ta tuno da furucin Shatou. Shi ko Baffa miƙewa yayi yana furta " fito yar albarka ". Fitowa tayi tana Dariya.Bibu ma dake gyaran wasu tsofaffin fitilu da ya fara koyon aikin ya ƙara sakin dariya yana cewa kedai Adda SHATOU Allah ya kai damo ga harawa,Allah Ranar Auren ki akwai bidiri a ƙauyen nan ". Dariya ta saki tana wani farfar da idanu inna ni da ta gani kai kawai ta girgiza tana yiwa SHATOU Allah ya shirya a cikin zuciyar ta. Ita kuwa zama suka yi suka fara tsara yadda za,ayi bikin na ta ita Bibu suna dariya kamar yadda kuka san wadda take da tsayayyen saurayi. Inna ni da take jin su bata kula su ba sai ma wani abun in an faɗa tayi dariya ta ji hawaye sun wanke mata fuska wanda take kaikaitar idanun su ta goge. Har Baffa na ya ƙara fita bayan kiran da aka yi masa zancen da suke yi kenan. Daga karshe da suka ishi Inna ni Sai ta watse firar ta sanya su shirin makaranta dole haka suka shirya suka wuce gashi yanzu lokacin zuwan bai ƙara sa cika ba ma amma saboda sun ishe ta ta ce su tafi kar suyi lattti.Haka ko suka fito suka wucewar su kowa fuskar sa turneƙe babu ma kamar Bibu dan bai gama gyaran da yake yi ba aka ce su tashi su wuce dan sallah kawai sai abinci da suka ci ya sa ya tashi daga aikin ita kuwa sana,a guda domin kuwa ɗiyan toton rake ɗin sun kusa goma kuma duka nata ne,haka take bin su layi layi kamar an zo gidan kitso tana kitse musu gashin wasu ayi musu hannu biyu,wasu zane. Yau tun asuba haka ta tashi da a hargitse Saboda ciwon ya motsa gashi ta rufe ɗakin,Babu wanda ya ankara da halin da take ciki sai Nana da take kwana da ita a ɗayan wani ɗaki dake cikin bedroom ɗin dan ƙofar shi Anan take.Kamar ta dai irin hanyar da Suhail yake biyowa daga part ɗin. Duk yadda Nana take kururuwa babu wanda ya ji ta saboda ɗakin a rufe yake,ta kasa buɗe nata ta kawo mata ɗauki saboda tsoro duk da ta na jin yadda take faffasa komai da ya ke na fasawa da wanda bana fasawa ba a ɗakin.Gashi sai wani irin Dariya take ban kawa tana cigaba da aikin hargitsa ɗakin dan abun da bai wuce mintuna goma ba ta lalata komai da ke cikin ɗakin.Ta daɗe hakan kafin Nana ta ji shiru dan haka koda Nana ta ji haka cike da tausayin ta ta buɗe bedroom ɗin na ta tana leƙowa sai dai a matuƙar razane ta saki wata irin Mahaukaciyar ƙara domin kuwa Ba kowa ta gani gaban ta ba face Ishaa Tsaye fuskar ta jina jina sai soshe soshe take yi tana ganɓalan dariya,ga kayan jikin ta duk sun lalace nan kwalba ta shige nan ta fasa ko ina ta ji ma kan ta rauni. Ai kamar jira take yi dama shine tsayin da tayi ta faɗa cikin bedroom ɗin kamar an jefa ta sai ga Nana ƙasa tana neman agaji domin haye ruwan cikin ta tayi tana nusar ta,bugu na fitar hankali cikin abun da bai wuce mintina uku ba ta mayar da Nana kamar ta dan har kayan jikin ta ta yayyaga. Rayyan da ya shigo ta ƙofar bayan ne ya ji kamar sautin kuka na ta shi sanin cewa suna da mara lafiya a gidan hakan ya sa babu tsoro ya fara ƙoƙarin tura ƙofar sai dai kamar an buɗe Kunnuwan sa tarr ya ji kukan Nana,dai dai lokacin da Nana take sakin wata irin ƙara kuma a lokacin ne Allah ya bashi ikon sanya spare key dake maƙale a chan kan wata yar fulawa mai kyau ta yan gayu da ya zaro. Da Inna lillahi ya matsa wajen yana cigaba da Nana ta sunan Allah domin kuwa wuƙa ce Ishaa ta ke riƙe da ita wadda bai san inda ta samo ta ba.Cike da tashin hankali ya ambaci sunan ta " Ishaa "Ganin ko juyowa bata yi ba ta kalle sa hakan ya sa ya ƙara furta " MA'ISHA " shiru ta masa sai dai tana nan tana yaƙen nan da wasu marasa hankali suke yi.bata juyo ba sai da yayi mata kira biyu sannan ta juyo tana saita mishi wuƙar da take ta sheƙi dan da ganin ta sabuwa ce dall. Dariya ta ɓalle da ita kafin ta ce " Sai na kashe su,sai na kashe su dukkanin ku,bana son su ". Kafin gurin ƙara riƙe wuƙar da kyau ta yanke hannun ta.Jini yana ɗai daga cikin abinda yake bugar da ita a duk lokacin da ta gan shi yana zuba haka da sauri idan an samu ozzz sai kan ta yayi ta sarawa ko a cikin haukar take ta asali ko sama sama.Dan haka cikin abun da bai fi secconi ba sai gata ƙasa luuuu.Da sauri Rayyan ya taro ta yana ƙwala kiran sunan ta cike da tausayi ƙanwar ta su.Hawaye ne suka wanke masa fuska ganin yadda jinin yake zuba wani ƙaton ɗan kwalin Nana da yake yashe gefe ya yajawo ya ɗaure mata hannun sai dai babu sauƙi dan haka babu wani kuzuri jikin sa jin kamar bata numfashi.Sun kasa saboda ciwon MA'ISHA sun kasa aminta bata taɓa samun lafiya, kasancewar ba,a san dalilin ciwon ba har yanzu bare a yi maganin sa. Da ita ya faɗo Babban falon Amoh yana share zufan da take keto masa. Da Suhaila ya fara cin karo wadda ta fito ɗaukar wani abu ta saka ma cikin ta dan bata da jimirin yunwa tun fil azal. Ƙara ta saki mai tada hankalin mai hankali kafin ta sulale wannan ƙarar kuwa itace ta ankarar da Amoh da Alhaji Sardauna.Wanda suke kira Dady. ALHAJI IDRIS SARDAUNA. Shine cikakken sunan Dady,ana kiran sa Hon Sardauna daga abokan aikin s,da kuma wajen gari,Saboda kasancewar sa Minister mai kula da har kar Noma,a gida ya'yan sa suna kiran sa Dady,Amoh Cikakken sunan ta Amina yara da dangin ta suna kiran ta da Amoh. Amoh nada yaya Biyar Babba shine Suhail sai mai bi masa Suhaila,sai kuma Rayyan sai Kuma ƙaramar su MA'ISHA Wadda suke yiwa wani irin mugun so sai dai lalura ta musu shamaki sai dai duk da hakan suna iya kar ƙoƙarin su na bata kulawa yadda ya dace yadda bazata cutu ba bare ta cutar da wani,Amoh ko da yaushe cikin kukan zuci take na damuwa da ɗimuwa yanayin da yar ta ke ciki.Haka Dady kowa dake gidan yana ji da MA'ISHA sosai.Dukkanin Wannan a hali suna zaune ne A buja a cikin Ministers estate inda su MAHAJ suke.Suhail yana da ya kammala degree ɗin sa a fannin likitanci tun shekarar da ta gaba ta wanda Bama aƙasar nan yayi karatun ba,Yanzu yana aiki a wata Babbar private hospital dake nan Abuja, Suhaila kuwa yanzu take kusan kammala degree ɗin na farko,Sai Rayyan shi yana ug 2 ne a jami'a tare yake da Suhaila a school ɗaya,MA'ISHA ba,a ma zancen ta dan bata samu ilmi ba saboda yanayin ciwon ta ko school ba,a saka ta ba,saboda yadda abun ya taɓa ta dan tun tana ƙarama take da abun kamar yadda muka sani tun farko.Dan haka kowannen su yake jin mugun tausayin ta.Duk da haka kuma Suhail yana iya ƙoƙarin sa dan shi ya koyar da ita sign kamar na kurame kafin ta samu damar iya yin magana dan wasu lokuttan har bakin na ta bai iya yin magana,Kuma yayi ƙoƙarin sanya mata Abcd sai dai ba lallai yanzu ta iya kawo su ba.Su Suhail sun taso cikin Gata kamar yadda iyayen na su ke ƙokarin faranta musu,da basu tarbiyya gwargwadon ta Addinin Musulunci... Da wani mugun sauri suka sauko daga benen kowannen su fuskar sa cike da tashin hankali babu ma kamar Amoh da duk guiwowin ta sun Sage saboda tashin hankalin abun da ta hango dan kuwa Kuka Rayyan yake yi kamar ƙaramin yaro ya kasa yin komai ga Suhaila kwance ƙasa a sume ga kuma hannun MA'ISHA na reto alamar babu rayuwa a jikin ta.Daddy Ma koda ya iso wajen hankalin sa yayi matuƙar ɗagawa da abinda idanun sa suke gane masa dan ga alama ta bayyana babu lafiya dan ko ina na jikin ta jini ne wani wajen shatin kwalba sai inda yafi tada musu da hankali inda ta yanke dan ɗan kwalin da ya ɗaure ne yake ta tsiyayar da jini saboda yadda ya tsuma. Daddy bai tsaya wata wasa ba ya zari car keys dama a shirye yake da Jallabiya jikin sa saboda basu jima da dawowa daga masallaci ba. Hannun Rayyan ya karɓe ta da sauri dan shi kamar ya zama hoto haka ya koma sai dai ya kalli MA'ISHA ya kalli Suhaila ya ƙara ɓarkewa da kuka. Bayan Daddy ya bi da kallo yana ɗan dawo wa hayyacin sa ganin Suhaila da Amoh ta watsawa ruwa ta dawo dai dai tana sauke numfashi kafin ta ɓarke da wani irin kuka mai ban tausayi da katse zuciya. Riƙota Amoh tayi kafin ta taimaka mata ta zauna sannan ta juya da sauri ta koma sama ta ɗauke hijab Babba ta ɗaura akan kayan Kwanan dake jikin ta. Shafa bayan Suhaila tayi da ta rafka ta gumi kafin ta fice sai dai bata karasa ficewa ba sai ga Rayyan ya dawo yana furta " Amoh Nana,aje duba halin da take ciki ".Cikin sauri Amoh ta juya ta koma zuwa ɗakin a sume ta isko Nana da ta yi zaton kwanan ta sun ƙare.Ruwa ta Yayyafa mata bayan ta kunna hasken ɗakin kan ta ta dafe da wani irin sauri da ya sara mata saboda ganin yadda komai ya koma upside down.Hawaye ne ta ji sun silalo mata.Ta sanya Nana ta kwashe Kayan kwalaben nan, amma bata san yadda ake dawo da su ba dan toilet ko cikin lockers nan aka ce a mayar da su saboda yadda zasu iya zama illa a gare ta.Saboda sun lura idan so ɗari za,a cika madubin sai ta hargitsa komai kuma hakan bai taɓa damun su ba sai ma ƙara son ganin sun gyara rayuwar yar su. Tuno yadda ta ga kwalabe duk sun soke ta hakan ya sa ta runtse idanun ta da ƙarfi tana share wani hawayen da ya zubo mata mai zafi.Wani rauni ne ya ƙara bayyanar mata ta san muddin da ace Suhail yana nan sai ya fi kowa shiga tashin hankali dan haka ba zata bari ya san da zancen ba,saboda duk yafi shaƙuwa da Ishaan ta. Dan haka ta sauke ajiyar zuciya bayan dawowar Nana cikin hankalin ta tana ta sauke numfashi tana jan Ajiyar zuciya. Nana kuwa a tsorace ta miƙe tana neman guduwa tana cewa " Dan Allah MA'ISHA ki min rai bani bace wadda kike nema,bani ce ba kar ki kashe ni "...Ta kai ƙarshen zancen tana ɓarkewa da kuka bayan Amoh ta janyo ta tana bubbuga bayan ta. Kafin tace. " me kike nufi da bake bace wadda take nema "? " Ta ambaci sunan wani ne hala " " Ehh kamar haka " Nana ta bawa Amoh amsa jikin ta na rawa saboda tsoro tana mugun tsoron yanayin MA'ISHA sai dai tana kaunar ta matuƙa Allah ya ɗaura mata son ta,dan haka ko ta so ta ajiye aikin sai ta kasa dan haka take kula da MA'ISHA da zuciya ɗaya cike da so da ƙauna kuma ba yaune ta fara yi mata irin hak baa,sai dai na yau ya bata tsoro ganin ta da yuƙa sabuwa. " Tou Ikon Allah Sunan wa kika ji ta kira Nana " ???✍️✍️ # Wannan labari na kuɗi ne #800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣2️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ____________________"Banji ba sosai Saboda na suma a lokacin amma kafin na ƙarasa fita hayyaci na,naji tana ƙara nanata sai ta kashe su,sai ta kashe ta,sai kuma bakin ta da na ga yana motsi a hankali tana faɗan wani suna nidai na kasa kawo shi Amma kamar yana tashi da Ta...,daga nan ban ƙara sanin abun da yake faruwa ba." Nana tayi furucin cike da kalamai masu nuna tausayi dan Dagske tana jin Tausayin Ishaa Matuƙa. Amoh ɗan numfashi ta sauke bata jin daɗin rashin jin ƙarashen sunan ba dan ta so ta ji sunan wa ta kama dan su har yanzu basu yarda da ciwon Ishaa ba saka hannun wani bane saboda yadda suke fafutika kan neman maganin ta amma abun babu gaba babu baya.Sai dai basu matsa ba sun dage da yin addu'a da miƙa lamurran su ga Allah shi ya jarabce su kuma shi ne zai yi maganin matsalar a lokacin da ya so. Taimaka ma ta Amoh tayi suka fice a tare dan itama tana buƙatar ganin likita saboda yadda ta ji raunuka. Suhaila ta yi driving na su dan su Rayyan da Daddy sun wuce. A Chan a sibiti kuwa saboda sanin mahimmancin su Dady da matsayin da yake dashi da irin shares da yake da ita kaso biyu,na asibtin,aka karɓi Ishaa cikin sauri da karrama wa,da kulawa aka fara bata taimakon gaggawa domin dama duk sun san ƙaunar Dr.Suhail ce wanda sun san da ace yana nan shi zai kula da ita a gida ma ba sai anzo nan ba sai in abun ya ɓace.Cikin ikon Allah an samu ƙwararrin likitota suka hau kan ta sun ɗauki kusan awa ɗaya suna duba ta kafin suka samu Dawowar Numfashin ta da dai dai tar bugun zuciyar ta.Alluran bacci suka yi mata mai ɗan karfi saboda yadda jinin ta yake dan zata iya farkawa yanzu ba tare da tayi mata wani aiki ba. Haka Ita ma Nana an karɓe ta anyi mata treating raunukan ta kamar yadda aka yiwa Ishaa nata aaka tsaftace mata jikin ta. Tunda aka sanar da su halin da take ciki yanzu suke sauke nunfarfarshi kowa fuskar sa babu yabo babu fallasa sai dai tana cike da damuwa mai tarin yawa wadda suke jin babu ranar gushewar ta sai ranar da suka samu lafiyar yar su. Rayyan ne ya sauke waya akan kunnen sa bayan ya gama waya da ɗan uwan sa da ya kira shi hankalin sa tashe saboda samun labarin halin da take ciki da Wani daga cikin friends ɗin sa Doctors ya sanar masa an kawo ƙaunar sa ciwon ta ya tashi,ta ji ma kan ta ciwo .Bawan Allah take hankalin sa ya tashi seminar da yaje yi yaji zai iya barin ta duk da kasancewar ta mai matukar Amfani dan International seminar ce sai dai a nan Nigeria za,a yita,Lagos.Kwantar masa da hankali Rayyan yayi kafin suka yanke kiran sai dai ya san cewa bai lallai ya saurare sa cewar da yayi masa da sauƙi ba. Dan haka kai tsaye ya sanar da Daddy halin da ake ciki. Shiru Daddy yayi kafin ya ce " kira mini shi ". Babu musu kuwa Rayyan ya danna ma ñumban ta sa da yayi saving Yaya Suhail. Ringing biyu ya ɗaga dan baya wasa da lamarin ahalin sa musamman abun da ya shafi Ishaaa saboda yadda suke mugun Tausayin ta. Miƙa wa Daddy wayar yayi ba tare da yayi Magana ba.Shiru yayi jin Dady na kiran sunan sa yana furta " Na san halin ka,kar ka baro abun da ka je yi zamu bata kulawar da ta dace,kaji ko,ta samu lafiya sai abun da ba,a rasa ba,Allah ya taimaka " . Ɗiff ya kashe wayar,Dan bai son ya masa wata magana,duk da ya san bazai Musa ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye wayar bayan ya gama ƙare mata kallo kamar zai ga komai a cikin ta.. Numfashi ya sauke yana komawa ya zauna daga tsayen da yake bakin window yana shaƙar iskan da yake kaɗawa mai daɗi yana ji kamar yayi tsuntsuwa ya samu kan sa a cikin asibitin.. Dady Saboda yana da wani meeting da zai yi hakan ya sa ya bar su Amoh nan sai dai yana fitowa yayi murmushi ganin securites nasa da suke tsaye cogai cogai. Bata re da yace komai ba ya shiga motar da ya tuƙo da kan sa sai dai a wannan karon wani daga cikin su ya tuƙa ta. Amoh ma gida suhaila ta matsa mata ta koma saboda yana yin jikin ta ga ciwon ƙafafu da take fama dashi dan haka kai tsaye aka mayar da ita gida inji ɗai daga cikin securites da aka bar musu. Nurse Mira da bata san abun da ke faruwa ba ta zo gidan sai dai tun abakin gate ta samu labari ga securites cewa an fita Ida Ishaa amma Hajiya da Alhaji sun dawo dan haka cike da tashin hankali ta faɗa gidan.A kitchen ta tarar da Amoh tana bawa masu kula da girki umurnin abun da zasu yi wadda bata daɗe da shigowa ba. Amoh fuska cike da damuwa ta faɗa mata duk abun da ke faruwa,kamar yadda Nana ta mata bayani yadda ta fara,Hawaye ne suka wanke mata fuska cike da tausayin Ishaaa. " Bari na je na gyara komai kafin su dawo da ita,kuma fa na cire duka kwalaben turaren nan na mayar da su toilet ban san wanda ya dawo mata da su ba anan kan mirror ". Tayi zancen tana mamaki gashi Itama Nana ta ce wa Amoh ba ita ta jera su ba.Dan haka sai suka yi ta mamaki da tsoro domin sune abinda suke ji mata ciwo a tashin farko idan ciwon ya tasar mata. " Nikaina abun yaɗaure mini kai ". Amoh tayi furucin fuskar ta cike da damuwa. Nurse Mira da ta rasa abun cewa ne ta ce " Allah ya bata lafiya,Amoh bari na yi sauri,ina son naje a asibitin " . Kai Amoh ta gyaɗa mata tana wucewa itama tana wuce wa bedroom ɗin ta. Wani irin hawaye ne ya ƙara wanke mata fuska ganin yadda ɗakin ya ƙara hargitsewa komai ya farfashe ya koma kamar ba,a taɓa zama a cikin sa ba har ta mirror ta fasa shi ga kwalabe nan zube an farfashe wanda ita kanta idan bata yi ta ka tsantsan ba zata jima kan ta rauni.Dan haka babu jira ta cire hijab ɗin ta ta lankafe sannan ta koma ta ajiye jakar ta a ɗakin Nana da shima farkon shi a hargitse sai da ta shiga ciki ma ne shima ta ga ga kaya nan a watse. Cike da rashin kuzari na Tausayin Ishaa ta fara gyara komai bayan ta kwashe kwalaban turaren da suke masu kuɗi saboda manya ne dukannin su babu karami sai Shegen ƙamshi da ɗakin yake ta yi saboda yadda turarukkan suka watse akan carpet da ta mahe ɗakin. Tsaf ta gyara ɗakin ta sanya sabon bedsheet dan wanda aka cire ko kwana biyu bai yi ba.Dan jiya Nana ta saka mata shi.. Dai dai ta gama Amoh da masu girki sun kimtsa komai dan ba wani abu mai wahala aka yi ba irin wanda zata iya ci ne ruwan zafi sai masan ƙwai da irish da suka soya mata irin mai haɗe da kayan miya da kuma ƙwai a cikin sa. Nurse Mira kuwa kwasar kayan tayi ta fice da su inda dama bata saka motar ta a garage ba dan haka ta jata ta fice. Koda ta isa Nana ta ɗan wartsake saboda ruwan da aka ƙara mata ta samu ɗan ƙarfin jiki.Sannu ta yi mata cike da tausayin ta tare da furta Allah ya tsayar nan da tsare gaba ya bawa Ishaa lafiya. Da Amin duk suka amsa mata har Suhaila da ke zaune jugum dan yanzu ta baro sashen da Ishaa take har yanzu ta lura ko motsi bata yi,babu abun ke raba ta da gawa face ɗan ƙirjin ta dake ɗagawa tayi fayau da ita gashi dama ba wani auki ne da ita ba. Haɗa ma Nana shayi tayi ta haɗa mata duk abun da ta san zata buƙata,Babu musu dama yunwar take ji dan haka ta fara cin abin ta hankali kwance dan ta saba mafi yawan lokuttan da ta kwana gidan a tare da mutan gidan take breakfast sai dai in ya kasance Suhail na kusa ita kan ta gizagon sa take gani dan haka take ka sa iya motsi duk yadda za,a ce ta zauna bazata zauna ba sai dai a saka akai mata ɗaki,har ya kai ta saba mafi yawan lokutta a tare da Ishaa suke yin breakfast ko lunch wanda ake kare shi alalala ce dan ita Ishaa babu hankali ita kuwa sai ta yi ta biye mata,suyi ta haukar a tare. Cike da kulawa Nurse Mira ta isa ɗakin na ta cikin tausayi ta ƙare mata kallo tare da share ƙwalla sannan ta mata Addua ta rufo ɗakin. " Ta Baiwa kin halaka,arniya,Ta Baiwa baki da imani,ta Baiwa magajiyar baƙin aljani,baƙin duhu ba naki bane " ..Ya kai ƙarashen zancen yana gaggaɓan dariya mai tsoratar wa dan duk wani cikakken mai lafiya dariyar tsafff zata iya mayar da shi mara hankali dan abun tsoro ce. Kamar ko yaushe zaune take gaban shi ta tanƙwashe ƙafafun ta cikin baƙar a baya da uban niƙab wanda yake fallasar da manyan idanun ta dake ciki,sai dai ba su bayyana sosai ba dan wanda ya santa ma sai yayi da ƙyar ya gane ta. Dariyar take gaggaɓa itama wanda ya Kaita har ƙasa kwance kafin a cikin yar bukkar ta sa da kullum take upside down sai dai inuwa ta ko ina duk da ranar da ake watsawa a cikin ƙungurmin dajin. Sai da tayi mai isar ta tana taya shi sannan ta yi shiru ganin ya sha fuska,ban sani ba ko dama dariyar limit gare ta Amma haka wajan yayi tsit har kukan tsuntsaye ma babu a wannan karon. " Ta bai wa faɗi damuwar ki da bakin ki,ke nake son jin yadda abun ya dame ki,duk da ɗan duna,da baƙi sun faɗa mini komai,faɗi Damuwar ki a yaye miki,ina son ki ta Baiwa ke ta amana ce, imani da aiki na shine ke ƙara mini ƙaunar ki ta Baiwa tare zamu halaka "... Ya saki kukan jarirai mai ban tsoro wanda sai kayi zaton ba shi ke yi ba dan kukan bana jariri ɗaya ba ne. Cike da ƙwarin gwiwa da rashin tsoro da rashin damuwa ta ce " Ɗan Baiwa maganar gizo ce bata wuce ta ƙoƙi kuma na san kasan da haka,abun na ƙara ƙuntata ni,Yau naga haske gobe na ga duhu,ya kamata ayi wani abu dan bana buƙatar mai mai ta magana ɗaya Ɗan Baiwa,a wancan karon har su duna na bawa a shayar da su jini amma ban ga wani Haske ba sai duhu da yake ƙara da baibaye ni " . " Ni yanzu Babbar Damuwa ta ma,kan wannan munfukar matar ne a yi mini maganin ta ta cika shige mini hanci da yawa ". Ta kai ƙarshen zancen tana jan dogon tsaki. " Hhhhhhh ta Baiwa ke makakka ce,ai irin su ba da wuri ake kame su ba,ita kan ta ba tsaye take ba haka nan,Rame mara zurfi ba wurin ɓoyon ɓera bane,ki riƙa nazartar wasu abubuwan,zan Miki maganin ta,zamu saka yan jajaye su karya ta,idan har tana taƙama da wani abu ". Ya kai ƙarashen maganar yana ganɓalan Dariya. Ita ma dariyar take yi tana " ho na Baiwa Ho Na Baiwa " tana yi kamar tayi masa Sujjada. Muryan sa ce ta katse ta yana cewa " Ta Baiwa ban riƙe ba kar ki mini Sujjada " . Dariya tayi kafin tace " Ɗan Baiwa ko ita kake so zan maka,nidai burina ya cika,ya kasance daga Ni sai shi zamu mallaki komai muyi rayuwar mu mai cike da jin daɗi da soyayya,dan ba zan yarda aiki na na shekaru ya tafi a banza ba " " Duhun da yake bi na Ɗan Baiwa a cigaba da neman hanyar Haska shi,ya kama ta muga abun da ke ɓoye ". " Idan har wata matsalar ce sai mu rufe ta da wuri ". " Kar ki damu ta Baiwa,aiki an gama duhun nan bana matsala ɗaya bane ,kuma ina ga dunƙulallun Abubuwa ne a cikin sa,amma zamu cigaba da bincike,waccan matsalar kuma an kusa kai ƙarshen ta,komai zai zamo tarihi,Haihuwa da shi kamar anyi an gama duk wanda yayi wannan kutsen ya ci nasara amma zamu warware aikin dole zaki samu Magaji,ko ajiyar aljanu ce sai kin haifa " Yana kai ƙarshen zancen ya ƙara sakin wata mahaukaciyar dariya kafin ya jawo ƙwarya ya ƙara nuna mata abun da ya nuna mata ranar wanda ya ƙara sanya ta farin ciki mai girma. Cikin farin ciki bayan ta gama kece Wa da dariyar ne ta bude wata yar jakar ta ta ciro masa bandir na manyan kuɗade yan dubu rafa biyar kamar dai zasu kai dubu ɗari biyar. Wani ruwan ya ƙara bata a gora tare da wani irin turare mai ƙarfi dan da ta shaƙe shi sai da ta lumshe idanun ta kan ta ya ɗan sara saboda kaifin ƙamshin sa. Haka ta cusa komai acikin jakarta tare da wasu irin ƙulle ƙulle da ya bata ta fara sakin dariya tana zagin shi tana yabon shi. Tana cewa " Shege,Shege ne,ɗan iska, ɗan iska ne,Ɗan gado ka wuce gado,Baiwa ta Allah ce,Amma kai mai nasara ne,nayi imani da kai kaine haske a cikin rayuwa ta Ɗan Baiwa kar ka bari nayi ƙwalla,Kar ka bari yar Baiwar ka ta zubda ƙwallla hhhh " ta kece Da dariya sai gata iya karta kaɗan da tafiya bakin bukkar ta sa ta ɓace ɓatt. Dariya ya kece da ita yana cewa " ta Baiwa kin Halaka kin halaka " .Kafin ya ɓace ɓatt daga shi har bukkar ta sa wurin ya koma filin Allah fallau kamar ba,a taɓa zama wajen ba ga wata irin rana da ta buɗe ta yi wani irin tsayi. " Ninah zo ki dubo mini Junaid na aike sa ya nemo mini magani na ina jin kamar Bp na na son ya tashi,na duba ashe maganin ka sun ƙare mini ". " To Ummah amma na Ga kamar kina cikin damuwa me yake damun ki ". " Bana son yawan tambaya Ninah zaki nemo mini shi ko naje da kaina ". Ɓata fuska Ninah tayi kafin ta miƙe ta bi wata hanya da ta shiga kamar lungu. Kasancewar yau weekend ce dukkanin su suna gida lokacin islamiyya bai yi ba..✍️ *To fa jama'a wace ce wannan Ta Baiwa bari na sha cuppy na ɗan samu relief tunani ya min yawa kar brain tayi Bosting wajen zaƙulo muku wacece ta Baiwa,Allah na ƙagu na san wacece wannan mata.🚶😮‍💨🚴🚴🚴🚴* Me kuke hasashe akan ciwon ISHAA. wai chakwakiya....🚴🚴 # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣3️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ☘️☘️☘️ Junaid kallon ta yake yi bayan ya kawo mata maganin ta sha gaban sa. Numfashi ya sauke kafin ya ce " Momcy wai me yake damun ki ne,Babu dalili BP yayi ta hawa,kuma anyi tambaya kice babu komai dan Allah idan wani abu na damun ki,ki faɗa mini Momcy ". Hajiya Ramlat kai ta sauke ƙasa bayan ta gama ƙare ma Junaid kallo da saurarar furucin sa kafin ta ƙara kallon sa tana galla masa Harara. Sannan cikin shan toka ta ce " Wai ni,Junaid ba zaka rage yawan yi mini tambaya ba,na sha faɗa maka babu abinda ke damuna,amma da alama baka yarda,Hawan jini ba ciwo bane da Allah ka jarabtar bayin sa da shi,ko ance maka sai akwai damuwa yake samuwa ". Ta kai ƙarshen zancen tana jiran jin amsar sa bayan ta ƙara zuba masa idanu. Junaid bai ce komai ba sai kai da ya sauke ƙasa cike da natsuwa ya ce " Allah ya baki haƙuri Momcy,kuma ya baki lafiya ". " Amin " ta furta ba tare da ta ƙara bi ta kan sa ba kasancewar ya miƙe jiki a sanyaye ya bi hanyar da zata sadaka da nashi bedroom. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana haɗiye wani irin abu mai nauyi a cikin zuciyar ta wanda take faman haɗiya shekara da Shekaru tun shigowar ta gidan. Tsaki ta ja mai ƙarfi tana furtawa a fili " Dole na ƙara sanin abun yi ba zai yuyu ba wallahi na zuba ido,idan har na ga babu cigaba a aikin da ya zo a ɓagass,ba zan taɓa yarda na faɗi warwass ba,dole na ƙara buɗe wuta ". Ta kai ƙarshen zancen tana ƙara jan mugun tsaki da yafi na daa girma. Miƙewa tayi a ɗan gajiye ta shige ɗakin ta kasancewar bata daɗe da fitowa ba ma daga cikin sa dalilin fitowar ta rashin ganin maganin ta ne da ta lura ma sun ƙare. Reena shiru tayi tana tura bakin ta gaba da Leena tayi wa mugun bugu a yanzu bayan ta ce mata Allah ya isa saboda ta taɓa mata littafin da take yan zane zane saboda tana son zane sosai, sai dai har yanzu bata wani ƙware ba. Hawaye ne suka silalo mata a hankali kafin ta buɗe bakin ta ta ƙara furta " Allah ya isa na ". Aiko Leena da ke ciccika kamar jira take yi ta ƙara kaima bakin na ta bugu inda take ya fashe da jini Kuka Reena ta saka ganin jini bayan ta shafo bakin aiko giyar kukan na ta ta ƙara tana ƙoƙarin kaiwa Leena bugu.Abba ne da ya shigo yanzu ya katsa musu tsawa dan hakan ne kawai zai an kararar da su da faɗan da in suka fara sai ka tsorata dan ma yanzu an samu sa,a Reena na ɗan ƙwatar rabon ta dan haka kare jini biri suke yi sai dai duk da haka itace mai shan wahala dan ƙarfin ba ɗaya ba,Leena kamar ƙarfin maza haka take damben babu ji babu gani,ranar da suka fara yin irin damben Gaban Abba sai da ya shiga tashin hankali matuƙa dan sai dai ya ji labarin anyi bayan sun ɗan fara tasawa,basu cika yi gaban sa ba. Sakin juna suka yi kowace na ciccira kamar ta kashe yar uwar ta.Reena ga bakin ta har yanzu jini yake yi kuma bata fasa shesshekar kuka ba.Wanda yake ratsa ƙwaƙwalwar Leena saboda daɗi dan yanzu mugun jin daɗin take ta ga tana kuka,in ta buge ta sai dai har yanzu idan wani ya taɓa Reena daga waje rigima ake yi Babba. Tsitt falon yayi sai numfashin su dan ko Reena yanzu ta yi shiru ganin yadda Abba ya zuba musu idanun sa ya rungume hannuwan sa. " Kowaccen ku ta je ta ɗauko mayafi na baku mintina biyu ". Ya furta musu cikin tsare gida. Babu musu kuwa suka wuce kowaccen su ta yi bedroom ɗin ta.Ba,a jima ba sai gasu a shirye Leena ce ta farko,kafin Reena saboda ta tsaya goge bakin ta da kuskure sa.Tare da wanko fuskar ta. Mayafi ɗaya dukkanin su suka saka dama shigar iri ɗaya ce,ta riga da siket yan janyo masu kyau. Bayan sa suka bi bayan ya gama ƙare musu kallo yana sauke Ajiyar zuciya da numfashi. Drivern sa ne ya taso da sauri ya buɗe masa bayan shigewa yayi itama Reena shiga tayi bayan sai dai a tsorace take da Abban yau. Ita kuwa Leena gaba ta shiga fuskar ta a ɗaure da ka gan ta kaga ruwan masifa dan haka driven da ya san halin kayan bai ce mata ƙala ba dan yana ɗan tsokanar ta wani sa'in. Securites ɗin Abbu da suke kula da shi ne suka taso su uku zasu shiga Mota ya hana su yana furta " Ba nesa zamu je ba ". Daga haka driven ya ja motar suka bar haɗaɗdiyar unguwar. Sun yi tafiya mai ɗan nisa har suka bar unguwar ta su kafin suka shiga wata unguwa itama dai gwargwado mutanen ta akwai dan hali a ciki ga jama'a nan sai harkokin gaban su suke yi. Dai dai wani ƙaton gate Drivern ya dakata bayan bin umurnin Abba. Fitowa yayi suma haka bayan an buɗe masa kofar. Wani ɗan dattijo ne da ya ke ɗauke da gemu mai ɗan tsawo fari ya fito daga yar ƙaramar kofar gate ɗin da alama fita zai yi ganin Abba ya sa ya washe bakin sa yana cewa " A'ah Saleh yau kaine a nan " . " Ehh malam " Abba ya faɗa cike da girmamawa. " Madallah to ku wucekke,har da manyan baƙi ake yau ". Murmushi Abba ya sake yi yana kallon su Reena da suke ɗan satar kallon Abba ɗin su ga ko ya chan za fuskar sa da take haɗe. Sai ko Gashi yanzu sun ga ya saki dan haka suka fara samun natsuwa a zukatan su.Suka fara sakin jiki babu ma kamar Reena Ita dai Leena bata wani saki fuskar ta ba. Zama suka yi a wani Madaidaicin falo da yake ɗauke da tarin littafan addini ya sha gyara sai ya zama ko ina yayi haske dakin babu hayaniya daga kujeru sai carpet da littafan addini da suke a tsare jere gwanin burge wa. Gaisawa suka yi cike da girmama juna.Har yana tambayar Abba Ina Sir da yake abokin su Sir ne da Dada sun yi gwagwarmaya tare anan.Malan Sunan sa shine Hambali.Ana kiran sa malam ne gaba ɗaya yanzu saboda ya zamowar sa Babban Malamin Addini shi ya sa da wuya kaji wani ya ambaci sunan sa sai dai malan ɗin. Gaisuwar su Leena ce ta maido da hankalin sa kan su.Zuba musu idanu yayi kamar yana karantar wani abu akan su kafin ya saki ɗan murmushi yana amsa musu Gaisuwar cike da sakin fuska. Yana cewa " Yan biyu an girma " Yayi zancen yana sakin ɗan murmushi.Baki Reena ta washe cike da jin daɗi tana gyaɗa masa kai. Ita kuwa cike da jin haushi ta sakar wa Leena harara bayan sun haɗa ido ganin ta ɗaga masa kai. Abba ne ya fara magana yana cewa " Dama Malam ya ran nan ne abun yake damuna shine nake son ka ƙara dubamin su idan ta dace ko raƙiya a musu a gani,Ni lamarin su tsoro yake bani,babu mai son ɗan uwan sa ya shiga inuwar sa,chan baya mun zo kace babu komai Malam dan Allah ina son a kara duba mana yanzu ko akwai iska a kan dayan su ". Abbu ya haɗiye wani abu mai ɗaci yana ajiye ayar zancen wanda ke nuna maka yadda abun yake damun sa. Kai Malam ya gyaɗa dan an taɓa kawo masa su chan baya kuma ya duba su kuma tun a wancan lokacin ya ga abun da suke tare da shi sai dai bai sanar ma da kowa ba ya ce babu komai a tare da su. Wanda bamu san dalilin sa nayin hakan ba.Zuba musu ido ya sake yi musamman Leena kafin ya saki guntun murmushi ganin tana ɗauke idanun ta akan sa bayan sun haɗa ido. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalli Abba dake jiran jin yace akwai iska akan Leena ɗin dan ayi mata ruƙiyar. Sai dai jin ya ce " Babu komai kawai ƙuruciyar su ce haka,kar ka damu da sannu zasu daina in Allah ya yarda ". Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana fatan hakan ya tabbata tun da wanchan karon ma haka Malam yace masa dan ko wancan lokacin shi ya kawo su da kan sa. Har malam ya ce masa idan ta sake faruwa ya kawo su nan a gani ko akwai ɗin dan yan zu babu alamar komai a tare da su lafiyar su ƙalau. A yanzu ma Malam ne ya katse masa tunani da tausayin ya yan na sa da ya ke so fiye da shi kan sa a cikin duniyar nan.Yana cewa " Idan abun yayi ƙamari ka ƙara kawo su sai a basu magani na miyagu,kar ka kai su wani wajen a wahalar da su kaji,Saleh zasu daina in Sha ALLAH ". A jiyar zuciya Abba ya sauke dan haka aka yi a wancan karon kafin ya ƙara tsintar Muryan malam da yake magana da ita anatse cikin natsuwa da kamala ya furta Yanzu zan basu ruwan Addua, kowaccen su ta sha sai ta shafa ". Wata ƙatuwar Jarkan zam zam ya jawo daga gefen sa sannan ya bude ya tsiyaya a wani ɗan ƙaramin cup sai da ya cika sa tab sannan ya rufe Jarkan yana mayar da ita inda take. Ya daɗe yana tofa ma ruwan Adduo,i kafin ya ɗago kan sa ya ɗauki ruwan ya raba biyu inda ya zuba a wani cup irin wannan Sannan ya miƙa ma kowaccen su cike da murmushi yana cewa suyi Bismillah su sha.Amsa suka yi sai dai kafin su amsa sai da Leena ta zuba ma ruwan idanu kamar ta ce bazaa ta sha ba sai kuma ta karɓa jikin ta na yin sanyi ƙalau Bismillah tayi ta kafa kai bata tsaya ba sai da ta shanye komai sannan ta sauke cup ɗin tana yatsinar kyakkyawar fuskar ta mai cike da ƙuruciya. Malam ma Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya kafin ya ɗan matsa kusa da su ya fara tofa musu Addu,oi sai da ya daɗe yana yin su sannan ya shafa ma Reena akai ita kuwa Leena A ƙafafu.Hakan da yayi sai ya bawa Abba mamaki amma sai dai ya kasa tambayar sa dalilin yin hakan.su kan su su Leena sun ga abun da yayi sai dai basu kawo komai ba saboda ƙuruciyar su basu ɗauka akwai dalili ba. Godiya Abba yayi wa malam kafin ya sauke masa manyan kuɗaɗe yace a yi sadaka. Duk yadda malam ya nuna ya bar su haka Abba ya tule masa su yana Murmushi tare da ƙara yin godiya. Har gate ya raka su tare da yiwa Abba kyautar zuma mai kyau wadda sai da ya shiga Mota sannan ya bawa driver saboda ya san halin sa ba lallai ya karɓa ba."Ka gaishe mini da Sada da Usman".Malam ya furta yana ɗaga musu hannu ta glashin motar. Hannu suma suka ɗaga masa kafin driver ya tada motar suka bar bakin ƙofar gidan. Numfashi Malam ya sauke da ajiyar zuciya kafin ya furta wa kan sa a hankali murya a karye cike da tausayin Saleh da Su Leena " Ba yanzu ne lokacin da zaka ka san komai ba,Saleh bana jin zuciyar ka na iya ɗaukar wannan ƙaddarar a karo na biyu,a sannu komai zai warware kan sa,tabbas ya' yan ka suna cikin matsala Babba amma faɗar matsala ce a cikin rayuwa ta, ka gafar ce ni Saleh,amma muna ta ya ka yaƙi muna kai wa Allah duk dare,komai zai zama tarihi za,a wayi gari mai aikata wannan aika aikar ya bayyana da kan sa,kafin mu" Ya kai ƙarashen zancen yana sauke ajiyar zuciya yana komawa cikin gida jin kan sa na sarawa dan ya ji fitar ma ta fita ransa.Abubuwa da dama na dawo masa a kai har bai son yana tunawa saboda yadda zuciyar sa take tsinkewa da rayuwar duniyar. Abba kuwa umurni.ya bawa Driven na sa ya kai su Wani haɗadden mall Inda ya zuba musu Leena siyayya kamar bai san darajar kuɗi ba saboda adalci haka ya siya wa su Hamrah harda Ninah da ba yar sa ta cikin sa ba.Siyyaya su kayi mai Shegen yawa kafin ya biya kuɗin aka saka musu kayan a mota.Sannan suka yi gida kowaccen su tana ta faman sakin murmushi dan kwana biyu ba su je ba dama yaya Bilal ne yake kai su sai Abba wata rana amma ya kan daɗe.Cike da farin ciki suka yiwa Abba godiya Saboda koyar war Ummah ce wannan. Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana zuba ma Reena idanun sa wadda ta ke ta faman shan ice cream ɗin ta hankali kwance bai san dalilin da ya sa yake jin ƙirjin sa na faɗuwa ba idan ya tuna yadda malam ya shafa ma ƙafafun ta Addu'a sai ya rasa samun natsuwa sai dai bai jin zai iya maganar da kowa saboda haka kawai yake jin akwai wani ɓoyayyen lamari da yake a jiye a duhu da Allah kaɗai ya bar wa kan sa sani,ba zai zargi malam ba amma zuciyar sa sai kai kawo take yi akan maganganun malan. Kallon sa ya mayar kan Leena itama dai anatse take shan ice cream ɗin ta tana sakin murmushi.Murmushin ya samu kan sa da yi yana jingina kan sa da seat. Tare da rufe idanun sa wani shuɗaɗɗen lokaci na dawo masa a kai samun kan sa yayi da sakin murmushi a karo na biyu kan sa ya girgiza sannan ya buɗe idanun sa ya shafa kan Reena. Dai dai sun kawo gida inda aka wangale musu ƙaton gate ɗin. Shigowa motar tayi bata tsaya a ko ina ba sai bakin sashen Hajiya Asma'u. Kayan Hamrah da na Ninah suka fito da su inda suka shige ciki.Ba tare da sun jira Abba ba. Hamrah dake falon tana kallo ne tare da mahaifiyar ta ta daka tsalle tana murna ta karɓe kayan.Tana tambayar waya siyo muna. Reena ce ta bata amsa baki washe tana faɗin " Abba ne ". Hajiya Asma'u dake zaune ce ta ɓata fuskar ta tana haɗiye wani irin ƙololon baƙin ciki kafin ta saki fuskar ta ganin Abba ɗin ya shigo. Gayar da ita su Reena suka yi cike da bata girma,sai dai ita Leena gaisuwar bata ma yi niyyar yin ta ba.Haka kawai jinin ta bai haɗu da na Momy ba. Zama Abba yayi yana sauke numfashi kafin ya amsa gaisuwar da Momy ke masa wadda kowa ya san itace mace ta farko a gidan na sa sai.Ita ce uwar gida.Sai dai ya ɗaya gare ta. " Abban su daga ina haka,sai ga yara sun shigo da kaya Masha ALLAH "? Murmushi Abba ya ɗan saki kafin ya furta. " Sun raka ni,na gano malam shine sai na biya da su aka yo siyayyar nan ". Wani irin raɗaɗi zuciyar Momy ta ƙara yi jin yana faɗin rakiya dan son kai ai ya san yar ta Na nan mai ya sa bai je da ita ba ta yo siyayyar da kan ta sai yan son sa,zata yi maganin sa da shi har uwar su take ayyana wa a ranta.Inda maganar Abba ta katse mata shirun na ta yana cewa " Kuje ku kaiwa Ninah nata ku dawo ko ".Kai suka jinjina masa kafin suka miƙe cike da murna suka fice har Hamrah tare da kayan Ninah ɗin a hannun su. Bayan fitar su kuwa Momy cike da kisisi na ta miƙe tana furta. " Angode ƙwarai Abban su,Bari na kawo maka ruwa " Dan bata saka kowa aikin mijin nata ita take yi da kan ta komai yawan sa. Kai ya jinjina mata yana yin balance akan kujerar da yake kai fuskar shi na sauya wa da damuwa dan har yanzu ya kasa sanin tunanin da zai yi. Ruwan ta tsiyayo masa sannan ta zo da lemu na kwali mai tsada haka ta ɗauro kayan akan tiren da ta ɗauro su.Lemun ne take ta faman girgizawa. Tana ɗan satar kallon Abba da ya rufe Idanun sa.. "Abban su anya kuwa lafiya lau kake naga kamar fa akwai damuwa akan kyakkyawar fuskar nan taka" ? Ta furta tana ɗan nuna damuwar ta. Murmushi ya saki kafin ya buɗe idanun sa . Yace '' Babu komai Asma'u,Bacci ne kawai nake ji jiya ban kwanta da wuri ba saboda ayyukan da na ke son na kammala a office da ban samu nayi ba ".kai ta jinjina tana fara miƙa masa lemun mai sanyi da tsiyaya masa. Karɓa yayi yana kaiwa bakin sa cike da Bismillah. Cije baki Momy tayi kafin ta tsiyaya masa ruwan suma tana sakin Murmushi ganin ya shanye duka. Ajiyar zuciya ya sauke jin yadda sanyi ya ratsa sa. Bai ma sha ruwan ba ya miƙe yana faɗin " bara naje na ɗan kwanta kafin a yi sallah ko kan zai rage mini ciwo su idan sun dawo kice musu na wuce ". Kai Momy ta gyaɗa kafin ta sauke ajiyar zuciya tana masa sai anjima. Duk da anjima kaɗan zai dawo part ɗin na ta saboda itace da shi anjima,har nan da kwana biyu. Murmushi ta saki wanda ita kaɗai ta san ma'anar sa sannan ta kwashi kayan da aka kawo na Hamrah ɗin bayan ta gama sakar musu harara kamar sune Abba ɗin da su Leena ƙwafa tayi tana wuce wa Bedroom ɗin ta. A part ɗin Momcy kuwa Ninah kawai suka tarar anan falon itama cike da farin ciki ta karbe kayan tana tambayar wa ya siyo musu. " Abba ne " suka haɗa baki wajen faɗa aiko cikin daka tsalle da murna ta ke furta " thanks you Abba ". Hayaniyar ta ce ta sanya Hajiya Ramlat fitowa wadda har ta ɗan fara bacci bayan shigar ta. " Ke lafiya kika cika mini gida haka "? Kayan ta ke nuna mata fuskar ta wanze da murmushi. Washe baki Momcy tayi kamar ta yage sa dan murna dama mace ce mai shegen son banza. Karɓan kayan tayi tana dubawa dukkanin su babu ƙarami kaya ne masu tsada dan kowace riga da wando zasu kai kusan dubu arba'in ko fiye da haka takalmin ma masu tsada ga chocolates nan suma zube masu yawa. Fuskar ta cike da murmushi ta ce " Abba ya kyauta kamm yana ji da ya yan sa,kuce an gode Allah ya saka da Alkhairi " " Bari ma na haɗa ku da faten wake da nayi ɗazu na san yana son sa sai ku kai masa ". miƙewa tayi ta shige kitchen bayan gama maganar ta jima a ciki sai gata ta fito bakin ta washe hannun ta rike da yar wata kula mai kyau ta silver da ta haɗa da golden.Miƙa musu tayi suka karɓe kuwa Ninah ma ta karɓa sannan suka fice daga part ɗin. Koda suka shiga Part ɗin Momy basu tsaya jiran komai ba ganin baya nan haka ya tabbatar musu da ya koma part ɗin Ummah sai Reena ta karɓo Coolern saboda Hamrah ta san halin mahaifiyar ta sai ta mata faɗa saboda bata, bata izninn fita ba. Ganin bata falon ya sa ta miƙa ma Reena Ita ta wuce bedroom ɗin Momcy ta ƙara ganin kayan ta dan ta san suna wajen ta... 'Tunda suka dawo daga makarantar ƙirjin ta yake wani irin bugawa ba tare da ta san dalili ba dan in ka lura da kyau zaka iya ganin yadda ɗan hijabin ta yake ɗagawa. Duk yadda su Amina suke son ta saki jikin ta ta kasa ƙarshe ma kuka ta saka musu abinda bata cika yi ba.Bibu hankalin sa tashi yayi shima ganin yadda take kuka wiwi kuma a iya sanin su babu abinda aka yi mata har aka tashi daga makarantar.Da ƙyar suka rarrrashe ta suka samu ta yi shiru sannan ta miƙe suka cigaba da tafiya wadda ake yin ta yau kamar masu koyo dan Shatou bata iya cewa ga inda take saka ƙafar ta.Su suke kula da duk tafiyar ta ta har suka iso gida zuwa lokacin magriba ta gabato.Sak Inna ni tayi ganin yadda SHATOU ta koma kamar marainiya dan ko lokacin da ta samu kan ta acikin baƙon wata a matsayin farin ta, bata yi hakan ba,cike da mamakin yanayin na ta take kallon ta cikin ɗan hasken da ya rage.Kafin ta iya furta wani abu sai ga Baffa na ya shigo cike da sallama.Bibu ne ya amsa masa sai Inni ita kuwa SHATOU kuka ta ƙara fashewa da shi tana dafe ƙirjin ta,da yake cigaba da bugawa tana durƙushewa wajen kan ta Bibu da Baffa na suka yi cike da kulawa.✍️ Anya kuwa Momcy 🚴🚴🚴🙆‍♀️Wannan matar nason kunce mini ɗaurin kaina. Malam ma haka jama'a me yake faruwa wai🤨an bar mu cikin duhu.🚶🚶😂🚴🚴 Shatou me yake faruwa hiliss ki daina karya muna zuciya.🥺 # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣4️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* # Shatou # Baffa na # Iro # Leena SS # Reena SS # Mamy # Samir IS 🍂🍃🍂🍃🍂🍃 ***Kukan ta sake ɓarkewa dashi kafin ta lafe jikin Baffa na dake tambayar ta lafiya bayan ya rugume ta jikin sa yana share mata hawaye shida Bibu.Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sauke kallon ta kan Inna ni da ta gama furta Bata son sakalci Kafin ta furta a hankali. " Inna ni zuciya ta fa nake jin kamar zata faso ta fito,duba yadda riga ta ke ɗagawa,Allah kamar zuciya ta bata da lafiya,baki ji yadda take bugawa ba,kamar ana kaɗa ganga". Ta kai ƙarshen zancen tana ƙara dafe ɗan ƙirjin na ta da yake ɗauke yan ƙanana halittun da suke manne akai. Sai hawaye shar suka zubo mata.Dan son tabbatar wa hakan ya sa Inna ni ɗaura hannun na ta a dai dai in da ta dafe kallon ta tayi kafin ta ce " Ki riƙa Nanata Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un da ambaton sunan Allah ". Kama wa kuwa ta yi a hankali tana faɗa bakin ta yana ɗan motsawa ahankali cikin yardan Ubangiji kuwa sai taji sauƙin yanayin idanun ta,ta ɗan rufe a hankali ta buɗe tana kallon A halin na ta da duk fuskokin su suke cike da da damuwaa babu ma kamar Baffa na dan fuskar shi ta fi nuna zallar damuwar da yake ciki. Miƙar da ita Baffa na yayi yana sauke ajiyar zuciya yana furta. " Shatouwa ki riƙa Addu,a kinji Allah ya sa alkhairi ne ke tun karo ki damu baki ɗaya ''Kai ta jinjina itama tana sauke numfashi. Ganin lokacin Sallah ya na neman gotawa wasu har sun fara sallame sallah hakan ya sa Baffa na da Bibu suka yi sauri suka fice bayan sunyi Alwallah aka bar Inna ni da shatou suma ɗin alwallah suka yi dan shatou yanzu wuta Inna ni ke saka mata akan ibada ko da ma chan tana matsa mata bare yanzu,kuma shatoun gwargwado tana iya iya ƙoƙarin ta,tana tsayar da biyar ɗin nan sai dai wasu lokuttan musamman da asuba sai Inna ni tayi Dagske bayan ficewar su Baffa na masallaci. Kamar tambayar arziki bayan gama sallahn su Shatou ta kalli Inna ni cike da ƙuruciya ta furta " Wai yaushe zaki haifa mini ƙanwa Inna ni,ni nikaɗai ce mace gidan nan fa " ? Zuba mata idanu Inna ni tayi kafin ta ce " Ni kuma wando kika ga ina sakawa ba ". Dariya shatou ta kece da ita dan haka kawai ta hango Inna ni cikin wandon Baffa na hakan ya sa ta ƙara tintsirewa da dariya har sai da ta kai ƙasa. Inna ni kuwa murmushi kawai ta saki ta cigaba da jan charbin ta tana jin wani sanyi Aranta ganin yadda shatou ta koma lokaci ɗaya,sai dai kuma ƙasan ranta tambayar ta shatou na ɗaga mata hankali dan ta san ta da shegen nacin tsiya yanzu ko Baffa na idan ta ga dama zata iya tsirewa da wannan tambayar,batun yau take maganar ayi mata ƙanwa ba sai dai Inna ni ta watsar da ita da shirmen ta Amma har ƙasan ranta tana jin tsoron wani mataki da za,akai shatu ta iya fahimtar wani abu,ko ta samu Baffa na da zancen. Sai da ta gama tun tsutsar dariyar ta sannan ta ƙara furta wa cike da ƙuruciya " Nidai Inna ni idan ba zaki mun ƙanwa ba Allah ya sa na haifu da ciki na na samu ƙanne sai na haifa Miki goma " " Ke uku ,Ni biyu,Baffa biyu,Bibu biyu ,Sai kuma biyu na ".. Sai ta yi ɗan alamar tunanin wanda zata bawa. Baki taɓe dan babu wanda ya faɗo mata a rai face MAHAJ. Sai ta ce a zuciya (" Wallahi bazan ba masu jajayen kunnuwa "ya 'yana ba koda kuwa kuwa masu kyaun sa ne ") Tsakin da ta ja a fili ne da murguɗa baki bayan katse maganar zucin ya sa Inna ni da ta zuba mata idanun ta da suka sauya ne lokaci ɗaya sauke numfashi kafin ta iya furta komai sai ta kara tsinkayar Muryar Shatou na furta " Mai gari ɗaya,Amina,da Jawairiyya ɗaya,dan ba zan ba Ramata ba ta saka musu warin baki ". Ta kai ƙarshen zancen irin Dagske take zancen ta kuma kallon da Inna ni ta mata ta fahimci daga ƙasan zuciyar ta zancen ya fito dan haka cike da son danne abun da ke ta so mata ta ce " Ke fa Shatou wani sa'in sha sha kike,Wani cikin ne zaki haifa yaya goma dashi a lokaci ɗaya,kuma da uban me zaki shayar da biyun da zaki riƙa " ? " Gashi nan " Ta buɗewa Inna ni shafaffen cikin ta da yake fari sol sai walƙiya yake yi kamar wadda take gyaran jiki dan dama haka duka jikin ta yake kamar na Inna ni kafin ta fara ƙokarin kai rigar sama kan yan ƙiran dangin ta sai kuma taƙi buɗesu tayi murmushi irin na kunya ta ce " Wannan zan basu " Kai Inna ni ta girgiza tana ɓalla mata Harara,Ga kayan haushi ga abin dariya dan wannan shirmen na shatou abun dariya ne musamman yan ƙiren dangin da ke manne chan da ake cewa sune za,a shayar da ya yan da su. Kafin Inna ni ta sake cewa komai ta ƙara tsinkayo maganar Shatou "Nidai Inna ni kimin Addu'a Allah ya bani yan goma ".ta faɗa da iyakar gaskiyar ta. Baki Inna ta saki tana ƙara ware idanun ta akan shatou a karon farko. " Shin a ruwa zaki sha cikin ne da zan Miki addu'a dan uban ki da kika fara isa ta da Surutu ". Cike da Hasala Inna ni tayi zancen. Baki shatou ta tura gaba kafin ta ce "eh ai a ruwa ake shan sa dama,ba dole sai ka matsa kusa da maza ba tun da mamassu Ramata basu da maza gidan har baban su ramata baya nan,sai dai ya shigo ya bar ƙauyen amma ta haihu a bun ta kuma a ruwa Ramata tace ta sha ".Ita ana ta tunanin tun da an musu karatu da su daina kula maza suna matse musu dan da kin balaga kina iya haihuwa shine ta ɗauki zancen.Ba tare da fahimtar komai b. Salallami Inna ni ta ɗauka tana fatan kar su Baffa na su shigo su ji wannan magana dan haka babu alamar wasa akan fuskar ta,ta kira sunan ta. ........."Shatou!" Kallon ta Shatoun tayi wadda ke ta sakin murmushi kafin tayi karaff tace. " Addu'ar ce zamu yi Inna ni " ?? Ta ɗaga hannayen ta sama cike da jin daɗi a iya tunanin ta addu'ar samun yan goma ɗin Inna ni zata mata.Tun da ta san amakarantar Arabia da boko ance Addu'ar iyaye karɓaɓɓa ce. Inna ni bata tan ka mata ba sai ma. Kai data girgiza kafin kuma ta mai da kallon ta kan shatou ɗin da kyau. Ta ce " Shatou ke wata rana sai na ganki kamar mai hankali,Wata rana sai ki zama babu komai akan ki,bana son zancen cikin nan daga yau tun da ke sha sha ce,anan ƙauyen idan baki sani ba,Duk aka samu mace da ciki koda na ruwa ne korarar ta wasu daga jama'a suke yi musamman idan ya kasance a lokacin da ake gab da damina ne,manoma sukan kori kowacece ,Dan haka sai in kina da Aure ne aka gan shi dashi ba,a ce Miki komai koda na ruwa ne bana son ko kaɗan naji zancen ƙannen nan,keda kike da tarin ƙanne da yawa ke kika faɗa da bakin ki ". Shiru Shatou tayi ba wai dan ta fahimci wani abu mai ma'ana ba amma dai ta ɗauki gargaɗin Inna ni,dan tana jin tsoron rabuwa da iyayen na ta dan haka dole ta bar zancen. Shiru Inna ni tayi ganin shatou na kallon ta kafin ta ce . " Tarin ƙan nai kuma ".? Fahimtar suɓutar bakin da Inna ni tayi ne ya sa ta furta " eh ina nufin Bibu da Amina ai kin ce kamar dubu suke a gare ki ". Murmushi Shatou tayi tana gyaɗa kanta kafin ta ce " Ba zan ƙara maganar ba nikam,Bana son ƙannen ma ". Tayi zancen da iya kar gaskiyar ta.Sai dai a lokacin ƙuruciyar ta bata damar tunanin tambayar Inna ni dalili ba. Kallon ta Inna ni tayi tana sauke Ajiyar zuciya kafin ta saki murmushi ganin yadda SHATOU ta narke fuska. Sallar Isha'i ce da aka kira ta sanya Shatou miƙewa dan chanza Alwallah dama Inna ni taji warin tusa dan haka da yake su biyu ne ya sa bata ce mata ƙala ba dan ta san itace.Tana zuba ido taga idan lokacin Sallah yayi ko zata miƙe tayi.Sai ko ta miƙe. (" Mai gari ɗaya,Amina,da Jawairiyya ɗaya,dan ba zan ba Ramata ba ta saka musu warin baki ".) Murmushi Inna ni tayi tuna wayen nan kalaman da suka fi bata dariya duk da ƙirjin ta na ɗagawa akan yadda kwana biyun nan Shatou take addabar ta yau zancen Aure gobe haihuwa,dudu shekarar Shatou nawa da zata fara wannan shirmen koda yake wasu yaran haka ƙuruciyar su take da jajiɓe jajiɓe idan ba shirmen Shatou ba yaushe haihuwar ta zama mara wahala da zata haifi yan goma,abu kamar wasan yaran ai bata mata fatan samun yan goma ko nan gaba ne.Shi Raino harda mai gari..Ta ƙara furtawa acikin zuciyar ta kafin ta saki yar ƙaramar dariya a bayyane dai dai lokacin da Shatou ta same ta,kallon ta tayi ta ce " Inna ni me kike yiwa dariya halan "? " Babu komai Shatou,Addu'a kawai nake yi Allah ya shirya min ke,Ya sa naga Auren ki,ke da yan uwan ki (...da bani tabbas akan su ") ....ta kai ƙarshen zancen cikin zuciyar ta cike da wani irin raunin da take ɓoyewa a lokutta da dama musamman a gaban Baffa na. Sai kuma ta ɗago Afili ta cigaba da cewa. " Amina,Ramata, Jawairiyya Habibu na ga kuma Yar gaban Goshin Baffa nan ta ". Tana sauke zancen ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye. " Amin Inna ni,har da nasu Iro ma Allah ya nuna miki ". Shatou ta furta babu kunya cike da ƙuruciya. Inna ni kuwa cike da dariyar da ta bayyanar da wushiryar ta yar ƙarama irin irin ta shatou,cike da mamakin ƙuruciyar Shatou ta kalli yar kyakkyawar fuskar ta da take ɗan ya sharaff da alama zancen har zuci tayi sa wanda ya nuna ma Inna ni cewa shatou bata da riƙo yanzu gashi har da Abokin faɗan ta a cikin wayen da take fatan Inna ni taga Auren ta cike da murmushi ta ce. " Yar mafarauci manya,har da iro alamarin". Kai SHATOU ta gyaɗa kafin Inna ni ta koma sakin murmushi dan yau firar ta da yar ta ƙayatar da ita take yi matuƙa tana samun farin ciki duk da akwai shirme ciki. " Tomh Allah ya nuna muna,ya sa muna da rai da lafiya ". " Amin " Shatou ta ƙara furtawa tana sakin murmushi. Ita ma Inna ni murmushin ta saki kafin ta kalli Shatou tace " ki kabbara Sallah ". Tana gama zancen ta tayar da sallah. Itama shatou haka ta tayar da ita cike da natsuwa kuwa ta gama sai dai duk da Inna ni ta riga ta farawa ta riga ta gamawa. Inna ni kai kawai ta girgiza bata ce mata ƙala ba bayan gama sallahn Tana jin ta tana Yin Addu'a wadda rabi da kwatan sa duk Inna ni ake yiwa da Baffa na. Murmushi Inna ni ta samu kan ta da yi dai dai lokacin da ta gama jan charbin ta tace. "Ke ma fa kina buƙatar Addu,ar nan Shatou,kiyi wa kan ki bamu kaɗai ba da Bibu ". Fuska ta ɓata sannan ta ce " Nidai Inna ni na fi son ku na riga ku mutuwa,Dan nafi son na riƙa ganin ku kusa dani,idan bakwa nan kuma Ni na san bazan ma iya rayuwa ba ". Shiru Inna ni tayi tana zuba mata ido ganin yadda take zancen cike da ƙuruciya da gaskiyar ta, kafin ta saki guntun murmushi cike da tausayin Yar Tata abun son ta wadda take kallo a matsayin sanyin idanun ta wadda bata son damuwa ko ɗigo ce ta gan ta atattare da ita,akwai dalilai da dama da suka saka Inna ni bawa Shatou wani waje na musamman a cikin zuciyar ta,mai cike da tausayi wanda ita kaɗai ta bar wa kan ta sani sai lillahi.Ita kan ta Abar tausayi ce sai dai Shatou take ji ma wa. " Allah ya sa mu mutu Muna masu imani kowa ta ɗauka a tsakanin mu duk ɗaya ne dama lokaci kawai muke jira " Shiru Shatou tayi bata bi maganar Inna ni ba wadda ta sauke a jiyar zuciya tana haɗiye wani irin ɗaci a ƙasan zuciyar ta mai girma da ciwo. Shatou kuwa shiru tayi sai dai ta zuba ma Inna ni idanu tana Murmushi kafin ta ce. " Amin " Murmushi itama Inna ni tayi. Sallamar su Bibu ce ta katse ma Shatou wata maganar da take son yi.Dan haka cike da murmushi ta gayar da Baffa na. Amsawa yayi shima cike da sakin fuska da murmushi yana ƙara bin ta da kallo kamar yau ya saba ganin shatoun. Inna ni ce da ta lura ta ɗan yi gyaran murya hakan ya sa ya juya yana kallon ta kafin ya sauke a jiyar zuciya yana sakin murmushi. Zama suka yi a kan ta barman da Inna ni ta shimfiɗa musu tun ɗazu a bincin su ta sauke musu nan kafin ta dawo ta zauna bayan ta tabbatar komai ta ajiye na buƙata dan ta san tare zasu ci abincin dan haka bata wahalar da kan ta da raba musu shi ba. A haka suka ci abincin tare ita Inna ni bata ma ci na ta ba sai dai Baffa na bai ce mata ƙala ba.Cikin natsuwa suka ci suka ƙoshi suka wanke hannayen su kafin Baffa na ya ƙara bita musu karatukan su,kowannen su yayi bita sannan ganin dare yayi suka fara ƙoƙarin miƙewa dan lokacin tara ta buga. Sai dai Shatou na miƙewa Ta tsinkayi Muryan yaro na Sallama wai ana yiwa SHATOU Sallama yadda ta zuba ma yaron da ake tsaye ido haka ma Inna ni, Baffa na ji yayi kamar an masa dabaibaiyi jikin shi ya sauya lokaci ɗaya ya tsinci kan sa cikin wani irin tashin hankali dan haka da ƙyar ya zaƙulo a bun da zai iya furtawa " Wa ya ke kiran ta ".? " IRO ne ɗan gidan mai gari ". "IRO"! Suka haɗa baki wajen faɗa cike da mamaki ita kuwa SHATOU da farko daɗi ta fara ji an fara zuwa wajen ta zance sai dai jin sunan Iro ya sa ta ɓata rai tana Hararar yaron cikin ɗan hasken fitilar da Inna ni ta kunna musu. Inna ni kuwa samun kan ta tayi da sakin murmushi kawai kafin ta bar su nan ta shige ɗakin ta dan ita sai abun ya bata dariya zillau (wai ana yiwa SHATOU Sallama,)sai lamarin ya bata kunya. Ajiyar zuciya Baffa na ya sauke mai nauyi ganin shatou ta wuce fuuu bayan ta furta " Ka ce masa nayi Bacci,idan wani abu na masa ya bari mu haɗu fadar mai gari ".Ta kai ƙarshen zancen tana jan tsaki,irin ita Babbar budurwan nan. Bibu dariya yake ta saki yana kallon Shatou ɗin wadda ta galla masa Harara ya san yadda take yawan faɗin za,a ga saurayin ta kyakkyawan gaske ranar da ya fara zuwa ƙofar gidan nan sai kowa ya suma saboda kyaun sa amma daga ƙarshe sai aka ɓuge da ganin Iro abokin faɗan ta dan haka yake ta sakin dariya yana tuno kalaman na ta. 'Harara take ta galla musu sai dai babu wanda ya kula ta, su dai abinda ya kawo su suka yi suka samu waje suka zauna,cike da rashin damuwa da yanayin na ta. Tun da kuma suka gaida ita dan amsawar ma ciki ciki ta amsa musu ita dan haka bata ƙara bi takan su ba,dan dukkanin su umurnin Ummah suke bi dan ita ke turo su dole daga su har Bilal gaida matan uban na su da sauran matan yan uwan sa koda kuwa ba su so dan akwai inda suke jin daɗin shiga kamar sashen Hajiya Asma'u da sashen Hajiya Ramlat da sashen Hajiya Maryam mahaifiyar su Samir wadda suke kira Hajiya.Ba su damu da halin ta ba sun saba dan ita kai tsaye take nuna musu tsana dan shi kan shi ma Abba ya sani kuma bai takura mata da dole sai ta so ya yan na sa ba wulaƙanci dai ne bai ɗauka ga kowannen su akan ya yan sa da suke ganin kamar ya fifita su da yar guda ɗayar Momcy da ma su Ninah. Dalilin da ya sa Ummah ta tura su kuwa ganin sun shiga kowanne sashen bayan dawowar su daga shashen Momy da faten waken da ta ce akaiwa Abba wanda Ummah ta karɓa sannan ta ce su juya su je su gaida Hajiya Sa,ada Mamy itama su gano ta kamar sauran. Dan haka da turin baki suka juya.Abba da bai shige ba tukunna ya yi yar ƙaramar dariya yana jin wani irin kaunar Ummah a ransa duk da ya san Yadda Hajiya Sa,ada Ke rashin kulawa da ya yan Ummah bai taɓa ganin damuwa kan fuskar ta ba kai ita ko abokin faɗa bata dashi cikin abokan zaman na ta dan haka yake ƙara girmama lamarin ta duk da suma sauran ba,a cika kama su ba dan suna yin kishi mai tsafta sai dai duk da haka kowaccen su akwai abun da ke ranta tsakanin Mamy, Momcy. Sai da suka kusan share mintuna talatin suna zuba wa tv ido sannan Leena ta zunguri Reena da tayi balance dan ta saki jikin ta sai kallon Cartoon take yi da ta sauya ita kuwa Hajiya Leena da take jin ta kamar a ƙaya ta ɗaure fuska ta mau dan tana jin hararen hararen nan har cikin jikin ta dan haka ta kasa ko ƙara kallon gefen da Mamy take zaune.Dan Umurnin Ummah ne ta ce Sai sun tsaya sun ta ya ta fira saboda ita dai tausayi take bata babu wani yaro na ɗebe kewa a sashen ta daga masu aiki sai ita kaɗai dan haka take tura su sosai a sashen sai dai Allah bai saka ma Mamy ƙaunar su da su har uwar ta su ba,duk da kuwa tana da son yara amma bata kula su ko kaɗan.Tun Ummah bata gane ba har ta gane amma duk da haka baiwar Allah sai ta tura su wannan rashin albarka ba su ba har Bilal yiwa take yi dan ta sha barin sa a falo shi kaɗai ta ƙara gaba shi ko ga sharaɗin Ummah dan haka yake zaunawa har a ɗan ja lokaci sannan ya fice,to yau ma sun ci sa,a ta zauna kuma ta amsa musu sallama. Hajiya sa,ada mace ce irin matan nan masu kaifi ɗaya idan bata son ka bata son komai na ka dan haka saboda rashin kaunar da ta keyi wa Ummah sai ta shafi ya yan ta,Sannan mace ce da bata damu da shiga sabgogin mutane ba sai dai tana da sakewa idan ta ta shi da kuma wanda ta ga dama dan idan ta shiga sashen surukan na ta bama zaka ce ita bace ko a gaban mijin ta,dan suma suna ƙoƙarin bata kulawa Musamman Uwani da ta san zafin rashin haihuwa tun da ta ɗan ɗana itama wanda har yanzu suke cikin raɗaɗin. (Masu neman haihuwa ido rufe Allah ya basu.Rashin haihuwa tabo ne Babba mai raɗadi da ke samun zukatan wayen da suke cikin wannan yanayi,yara abun so ne ga kowa musamman naka kana kallo kana jin daɗi,shi ya sa sai inyi ta mamakin Mazan da ko matan da basu son haihuwa abinda wasun su suke nema ido rufe.Suna nan Dare da rana suna kai kukan su ga Ubangiji.Amma sai kaga ciki ya tasa an hana sa shaƙar iskar duniya saboda son rai.Kyautar da kai baka isa ko wanin ka ya baka ita ba.Allah ka bawa masu neman haihuwa,Iri mai albarka.Amin✍️) Miƙewa Leena tayi wanda ya sa Reena kallon ta kafin ta ɓata fuska tana miƙewa. Dan ta so ta cigaba da kallon ta dan ita fa ko a jikin ta. Ficewa suka yi bayan sun mata sallama sai dai bata ce musu ƙala ba duk da tana jin Reena na nanata Mamy mun tafi. Sai da suka fice sannan ta juya ta harari bayan su tana furta " Ya yan Mayu kawai duk zan yi maganin ku har uwar ta ku uwar munafukai ". Mtsww ta ja dogon tsaki tana kara waya akan kunnen ta. Suko su Leena suna fitowa Sashen Hajiya suka faɗa ganin wata dallaleliyar mota Parkey a gurin wadda ko ba,a faɗa ba sun san ta waye har rigen gen suke yi cike da farin ciki da mamakin yaushe ya dawo haka suka an taya ƙaton falon babu ko sallama,kowaccen su fuska washe babu ma kamar Reena.✍️ # 2025 # Hausa novel # Love,and romance story # Zumunci mai ban mamaki *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Commente,and like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣5️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ☘️☘️☘️ Da murmushi kwance akan fuskar sa ya tallabi Reena ta dake gaba juya ta yayi kamar yar kaza suna ta dariya haka ma Leena dukkanin su dariya suke yi cike da farin ciki mai tarin yawa mai cike da kewar ya'yan na su.Matashin saurayi ne kyakkyawa kamar dai yanayin sa da Bilal sai dai Bilal ya ɗan ɗara sa ko daga yanayin fata dan shi ta sa mai duhu ce kaɗan. Samir kenan ma'aikacin Custom service kamar yadda muka sani shine ɗa na farko a wajen Hajiya Maryam Uwar gidan Ibrahim Sada Saleh. Samir yana aiki a kano kuma ya kan shigo gida ya ga yan uwan sa idan sun samu hutu ko ya ɗauko hutun. " Yaya Sannu da dawowa, shine ranar da muka yi waya da kai a wayan Ummah,ka ce ba yanzu zaka dawo ba sai bayan an gama a zumi ". Reena ce tayi zancen tana shige wa jikin sa bayan sun zauna a tare a kan ɗai daga Cikin manyan kujerun dake a cikin ƙaton falon. Hajiya Maryam dai da suke kira Hajiya murmushi ne ta ke ta yi cike da dattako da tsantsar ƙaunar ta ga yaron na ta da yan uwan sa take kallon su. " Yanzun ma Reena ba zama na zo yi ba na zo ganin Baby ta ne,nayi kewar ku baki ɗayan ku ". Ya yi zancen yana kallon Leena da taɓata rai,dan a tunanin ta Hamrah yake magana dan itace bata kusa tun da duk yana kiran su haka,sai dai ita yafi kiran ta hakan. Yar ƙaramar dariya yayi kafin ya mai da kallon sa kan mahaifiyar sa da take cewa bazai je ya watsa ruwa ba ya dawo ta san rigimar su da Leena yanzu idan aka fara babu ranar ganawa. "Hajiya bari ba lallashi Baby na tayi fushi " Ya bawa mahaifiyar sa amsa yana sakin murmushi. Hannun Leena ya riƙo da kyau yana mata raɗa a kunne ban san a bun da ya furta mata ba take ta washe baki tana furta " Allah Yaya " Kai ya jin jina mata shima cike da sakin murmushi. Hajiya dai bata ce komai ba sai ma murmushi kawai da ta saki tana kau da kan ta bata re da ta damu da shiriritar ta su ba dan ba yanzu aka fara ba tun kan su kai haka,yake biye wa Leena dan sun fi shaƙuwa da shi a cikin yayyen na su,shi ne komai Leena dan haka ta ji zai dawo ta kama murna kenan a wasu lokuttan harda kitso da lalle take matsawa Ummah sai anyi mata saboda Ya Samir zai dawowa idan ya sanar musu, tasan school ɗin su ba,a barin lalle amma haka zata je ayi mata idan ta je su zane ta shi ko Samir da ya gane hakan sai ya daina sanar musu idan zai dawo dan haka har yanzu akan turban yake. Tafawa suka yi da juna kamar wasu sa'o'i. Ita ma Reena rigima ta aza sai ya tafa da ita dan haka cike da farin ciki suka tafa da ita. Shigowar su Abduljabbar ce da Ayman,da suka fita wajen ball suka shigo cike da murna ganin motar sa sai ga Junaid shima a bayan su wanda ya fito yanzu da niyyar fita sai ya ga motar ya yan na su. Cike da farin ciki da girmamawa suka masa sannu da zuwa yana amsa musu da sakewa da murmushi haka suka gama gaisawa yana ɗan musu tambayoyi suna Amsawa kafin kowannen su ya kama gaban sa musamman su da suka dawo daga wajen ball suna buƙatar saka ma jikin su ruwa zafi ya taso musu duk da sanyin Ac dake ta aiki a ƙaton falon. Shima Junaid ficewa yayi yana zuwa kuwa ya sanar ma Ninah cike da farin ciki ta baro sashen Mahaifiyar ta da ta baro da kayan da Abba ya saya musu wanda ta ke ta fama gwaggwadawa ai ta na jin cewa ya Samir ya dawo ta cire kayan da sauri ta fito daga sashen tana dosar sashen Hajiya. Dai dai yana cewa " Girls Bari na watsa ruwa na zo muyi fira dan ba zan ma yi baccin ba sai na sha labari ". Da gudu ya tara Ninah da ta shigo itama a Guje tana kiran sunan sa. Baki washe ya tarbe ta yana rungume ta kafin itama ya ɗaga ta sama yana lilo da ita tare da faɗin " Little naga kin ɗan ƙara girma,Keda Reena,Baby na kawai naga babu wani chanji gata nan yar firit ". Dariya duka suka yi sai Leena da ta tura baki gaba kafin ta fara hawaye tana ɓata fuska tace " Ba yaya B bane ya sako ni gaba gashi harda karya mini kashin baya na yayi,kuma Ni ban yiwa ma Babyn sa komai ba,amma aka mun ƙazafi ". Ta kai ƙarshen zancen kamar Dagaske jawabin nata. Waro idanu yayi shima ya ɓata fuska yana cewa "Wai meya sa ya'ya Bilal ya saka mini Baby gaba,Ni na san baki taɓa Leena ba ai,ke da babu ruwan ki ko yatsa aka saka Miki a baki na san ba zaki ciza ba " " Gaskiya bai kyauta ba,kuma zan masa magama kar ya ƙara shiga sabgar Baby na ". Duk da akwai tazaran shekara ɗaya a tsakanin su hakan bai hana su mu'amala da juna yadda ya dace ba duk da shi Bilal bai da irin muguwar sakewar nan kamar shi Samir ɗin. kai ta lanƙwashe tana Murmushi tana jin. wani daɗi a ranta jin zai masa magana duk da ta san Bilal ne Babba amma ta san zai saurare sa saboda kamar ƙawaye haka suke tare suka tashi su biyu. Ita kuwa Reena ka sa haƙuri tayi dan haka ta ce " Yaya fa bugu na tayi har ta sumar da ni,shine fa yaya ya dake ta kuma har yayi fushi da ita,yanzu ma duka faɗa take yi dashi,shima yaya B babu ruwan sa da ita ".Ta kai ayar maganar Tata cike da damuwa kamar zata yi kuka. Uwar Harara Leena ta makawa Reena taana ji kamar ta jawo ta ta ƙara jajjagawa,sai kawai ta buga ƙyafci dan taji Haushin Reena ta ƙarya ta ta tunda ta san bai son tana faɗa ce faɗacen nan kamar dai Bilal shi bugun ta kawai bai yi sai dai ya yi fushi da ita. Shi ko Samir murmushi kawai yake yi saboda ya san Gaskiya ya san komai dake faruwa ya ji a bakin Bilal ɗin,kuma ya roƙe sa ya daina dukan ta ƙuruciya ce,dan haka bai nuna musu ba kawai ya share zancen Reena ta hanyar furta " Ku jira na zo,ku bani labaruka " " Hajiya ta bari naje na watsa ruwa na dawo yunwa ma nake ji " Ya na zancen yana shafar ɗan tumbin sa.Kai Hajiya ta gyada masa wadda ta fito daga kitchen yanzu tana Murmushi cike da jin daɗin ganin su Leena a arha dan ba su cika shigowa sashen na ta ba sai ko gaisuwa idan ta kawo su dan ita bata da mace ko ɗaya duk maza ne. Su Leena kuwa kowaccen su waje ta nema ta zauna bakunan su ɗauke da murmushi sai kuma aka koma fira da Hajiya da take tambayar su ya Ummah take dan kwana biyu ba su haɗu ba koda wajen gaida sarakkan su ne dan itace kawai Ummah bata cika sakewa da ita ba. Yau kwanan ta ɗaya biyu a asibitin dan riƙe ta Suhail ya sa aka yi ta ƙara samun sauƙin raunukan ta,sai ka sallami rabi kawai sannan suka Bata hutun kwana biyu.Dan haka suke bata allura mai ƙarfi bayan lokaci zuwa lokaci dan brain ɗin ta ta samu hutu mai kyau.Tunda ta buɗe idanun ta ta ga haske tar ko ina ta fara kiciniyar ƙwace kan ta idanun ta na rikiɗewa suko ma jajir da su kamar an baɗa mata barkono.Babu kowa ɗakin dan haka ta samu ta ɓalle duk jone jone dake a jikin ta Wanda Likitawa suka yi.Su Suhaila dake waje basu san abunda ke faruwa ba sai dai ganin mutun kawai suka yi ya fito a guje,cikin kiɗima da razana suka bi bayan ta cike da tashin hankali ita kuwa gudu take ta rusa akan babban coridor ɗin da zai fitar da kai daga sashen su.Ta ke hular kan ta,ta zare gashin kan ta ya barbaje har akan fuskar ta saboda kafin su zo nan an walwale kan ba,a samu aka kitse ba aka bar shi haka dan ba ta ma bari aka taje shi ba. Dabb haka kan ta ya bugi ƙirjin sa,ɗan rufe idanun sa yayi kafin ya buɗe su,ita kuma a lokacin ta samu ta zare jikin ta ƙara fallawa a Guje sai lokacin ya an kara da su Suhaila dake kuka sun zo sun gifta ta sa ita da Nurse Mira sai nurses guda biyu mace da namiji su ma a bayan su ɗan yanayin gefen fuskar ta da ya ɗan gani yake son hasasowa tare da tunanin wace ce cike da tausayin ta yanayin ta dan yanayin da take ciki ya nuna Zallar Hauka ce,yanayin da ya samu kan sa ne a lokacin da jikin su ya haɗu ya san ya shi sauke a jiyar zuciya da numfashi yana mamakin abun da ke tattare da wannan mara lafiya da tausayin ta ya dabaibaiye shi kiran wayan shi da aka yi ne ya sa ya cigaba da tafiya ba tare da ƙara kawo tunanin komai ba sai dai zuciyar sa cike take da tausayin take,haka kawai ya ji ina ma yaga fuskar ta. Gaba yayi yana amsa waya hankalin sa kwance. A ɓangaren su Suhaila kuwa da suke cikin tashin hankali da gigicewa dan yaune rana ta farko da ta samu damar yin irin wannan gudun wanda take nuna alamar ɓacewa daga gida dan tana nuna son guduwa sai dai yau ne kawai ta samu dama dan chan iyakar ta compound saboda tsaro. Da wani irin karfi ya fisgota bayan ta ɗan gota shi kaɗan daga tsayen da yake,dan ya daɗe tsaye wajen yana kallon tafowar tata a inda yake saboda bai daɗe da shigo wa ba sai dai a ƙafa yake dan taxi ta sauke shi a bakin gate dan ƙa'idar su ce ba,a shiga da ita,dan dawowar ta sa bai sanar ma da kowa ba bare a je ɗaukar sa ko driver ban sa bai sanar ma ba. Ƙammmm haka ya rungume ta a jikin sa yana sauke a jiyar zuciya cike da tausayin ta ga wasu hawaye masu zafi da ciwo da yake jin suna neman sauka akan fuskar sa.Su ko su Suhaila chak suka tsaya zukatan su na musu wani irin raɗaɗi da ƙuna ga su kowaccen su fuskar ta tayi haja haja saboda kuka da fita hayyaci dan sun san muddin ta hau hanya su kan su ba su san yadda za,a iya kama ta ba. Numfashi suka sauke ganin wanda ba su zaci gani ba a lokacin,Nurse Mira Murmushi ta saki haka ma Suhaila Rayyan ma da ya shigo yanzu murmushi yayi cike da farin ciki dan ya na shigowa ya hango su a Guje itace gaba kafin ya san abun yi sai aka yi sa,a shima Ya na kusa. Kiciniyar ƙwace kan ta take yi sai dai ya ƙi bata damar hakan dan riƙo yayi mata bana wasa ba. Daga ƙamshin turaren sa ta fahimci shine sai dai a idanun ta a wannan yanayin babu abun da suke da buƙatar gani face ta tsince ta a inda take ganin kan ta a cikin idanun na ta.Addu,oi yayi ta tofa mata dan ƙara take ta saki ta na gaɓɓatan dariya kafin kuma a hankali hawaye masu zafi suka silalo mata suka sauka aƙirjin sa idanun sa ya rintse da ƙarfi da suka yi jaaa abun ka da farar fata fuskar sa tayi jaa na damuwa da baƙin ciki na yanayin da ƙanwar ta sa take ciki. Jin da yayi jikin ta ya saki hakan ya tabbatar masa da cewa tayi bacci dan haka ya durƙusa ya ɗauke ta dai dai nan aka kawo kujerar marasa lafiya daura ta yayi ya gyara mata zaman kafin ya bi bayan Nurses dake kula da ita. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa sannu da zuwa da Rayyan yake masa. Su Suhaila ma sannu da zuwa suka masa bayan sun isa inda Sashen na masu ciwon ƙwaƙwalwa yake. " Captain manya yau nake ganin idon ka ". Murmushi matashin da aka kira captain yayi kafin ya shafa kan sa.Hannu suka haɗe waje ɗaya cike da murmushi. " Wallahi ko ayyuka sun yi yawa yanzu ma dole ce ta kawo ni nan Yaqub ". " Kuna da patient ne anan halan " ? "Eh wallahi wani ma'aikacin mu aka kawo sun samu accident to abun kamar ya taɓa brain ɗin sa shine na shigo,idan ka lura tafiyar ma ta wa ce ni kaɗai " Kai yaqub ya jinjina kafin yace " Allah ya bashi lafiya,Nima na zo ganin Patient ɗin mu ne ta kwana biyu nan Ni sai yau Allah ya kawo Ni dan bana ƙasar na yi tafiya kwana biyu,Yar wajen Yaya na ce itama tana fama da matsalar ƙwakwalwa abun ba,a cewa komai gashi na ta tun tana yarinya har yanzu babu wani cigaba " Ya karasa zancen cikin alhini. Cike da tausayi saurayin da aka kira Captain ya ce " Allah ya basu lafiya ya sa kaffara ne ya kawo karshen wahala ". " Amin '' Yaqub ya amsa " Bari kawai muje na gan ta sai na wuce tunda har mun haɗu sai ayi zumunci ". Kiran wayar sa ne ya katse maganar da Yaqub zai yi. Cike da ladabi ya gama wayar kafin ya sara yana kashe wayar.ya kalli yaqub da ke jiran sa su wuce yaga patient ɗin ta sa ya ce " Sorry Yaqub Wallahi na samu kiran gaggawa sai wata haɗuwar idan kuma na samu time zan zo na ga mara lafiyan ,Allah ya bata lafiya " " Amin bakomai Captain sai mun yi waya " .Hannaye suka tafa kafin suka yi Sallama kamar kar su rabu,dan an kwana biyu ba,a haɗu ba. Matashin da aka kira yaqub Shima gaba yayi yana caɓa car keys sama yana ɗan waigen Motar Captain da ta bar asibitin yana murmushi cike da kewar abotar ta su da suka yada kwana biyu kasancewar su class mate suna ɗan chat sai dai yanzu sun jaa baya. Tsaye ya isko su cirko cirko Ganin Rayyan a kusa ya sa shi cewa " Lafiya Rayyan ko Jikin Isha ne ya tashi kuma ? Na gan ku cirko cirko ". "Sannu da dawowa Uncle,Wallahi Uncle shine yanzu abun ya motsa mata ta fita ba tare da sanin kowa ba Allah ya taimaka Ya ya Suhail ashe ya dawo yau shi ya tare ta da bamu san inda zata je ba inda Allah ya takaita sai ya zamo a kwai mutane a kusa ". Rayyan yayi zancen cike da damuwa da raɗaɗin da ke maƙare da zukatan su. Cike da damuwa ya dafa kafaɗan sa yana cewa in sha ALLAH zata samu lafiya komai zai zama tarihi ganin hawaye sun kwaranyo a idanun Rayyan. " Ina Suhail ɗin " ? Ya tambaya ba tare da amsa sannu da zuwan da yayi masa ba. " Yanzu ya wuce office ɗin sa " . Kai Ya gyaɗa kafin ya matsa ya gaisa da su Suhaila da Nurse Mira ya musu ya mai jiki tare da ƙara musu ƙwarin guiwa dan kowa chan gida haka ya baro Amoh sai a hankali damuwa ta mata yawa dan ma sun hana ta zuwa ne da tana wajen. Da Sallama ya shiga office ɗin yana samun wajen zama dai dai shima Suhail ɗin ya fito daga toilet yana gyara hannayen rigar sa da ya tattare hannayen da danshin ruwa da alama alwalla yayo. Cikin ɗan sakin fuska ya ce " Uncle Yaqub yaushe garin,? Ina wuni " ya faɗa cike da girmamawa duk da Uncle ɗin ba zai wuce ya bashi shekara ɗaya ba. Murmushi yaqub yayi kafin ya ce "lafiya lau,ai Jiya na shigo tafiyar dare nayi dan haka ban faɗa ma kowa ba ". " Naje gida ganin ku aka ce baka nan,suma su Rayyan suna hospital tare da Suhaila Saboda jikin Ishaa da ya tashi ". Zama Suhail Yayi Yana Sauke Numfashi " Ai da sauƙi ma dan yanzu tana samun isasshen bacci yanzu ma bacccin aka mayar da ita amma zuwa anjima zan mayar da ita gida kawai dan ma akwai wani likita da zai taimaka mini mu haɗa hannu mu cigaba da lura da yanayin nata sai dai ba nan ƙasar bane Canada yake dan haka nake son muje da ita idan mun gama shirye shiryen,ban ma yi magana da su Daddy ba ". " Allah ya bata lafiya,jarabawa ce kowanne bawa da kalar ta sa ita wannan ce ta ta damu baki ɗaya,Allah ya bamu ikon cinye wa ya kuma bada ladar ɗawainiyya Allah kuma ya saka muku da Alkhairii ". " Amin Uncle Yaqub ya hanya,kuma " ? Suhaila ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya mai cike da wani irin rauni wadda Uncle ya ji ta sai dai bai wani damu ba dan ya san akwai damuwa sosai a yanayin sa zuciya dole sai ta hakan take rage nauyi musamman ga re su maza tun da basu cika zama su yi kuka ba............. Koda ta shige ɗaki ƙaramin tsaki ta ja tana Hararar bango kamar Iro ɗin ne gaban ta Cike da Haushin sa yau ita da take ce ma su Amina da Bibu ga kalar saurayin ta da zai fara zuwa fira amma sai a ka rasa wanda zai zo sai Iro,to amma ai faɗa ma suke yi dashi kodai ba fira ya zo yi ba. Wata zuciyar ta yi maganar da alamar tambaya ?wata zuciyar ta bata amsa da ba fira ya zo yi ba, tsaki ta ja a bayyane kafin a fili ta ce " To uban me zai sa ya ce a kira ni wallahi idan ma soyayya ce ta kawo shi sai na masa mugun wulaƙanci,ni kamata zai ce yana yiwa sallama ". Tsaki ta ƙara jaaa sai kuma ta yi ƙyafci ta kwanta kan katifar ta, mai ta tuna sai kuma ta miƙe daga kwancen,tana miƙewa kuma ta fito waje tare da yafo ɗan mayafin ta,ta suri ta kalmi, su Baffana da ke tsaitsaye su ka gan ta kawai ta bi gaban su ta wuce. Baffa na idanu ya waro yana ji kamar ya janyo ta ta dawo dan wani irin tashin hankali ne ya ji ya mamaye masa ilahirin jiki gabas ya kalla da kudu kamar mai tsoron yanayin da yake ciki ya bi bayan Shatou shiko Bibu dariya yake yi kafin ya fara rera waƙar masoya ya shige ɗakin sa. Dai dai Iro na juyawa bayan ya tsaya jira ya tabbatar da zargin saƙon yaron da ya aika shin ita tace Dagske bata zuwa,ko,ko wanda dama ya san hakan zai iya faruwa saboda yar tsamar dake tsakanin su. Gaban shi ta sha,ta tsaya tana riƙe ƙugu.Shi ko kamar Gaula ya sakar mata idanu yana murmushi Harara ta ƙara maka masa ganin yadda ya ƙara washe baki.✍️ # 2025 # Hausa novel # Love,and romance story # Labari mai tafiyar saƙar gizo gizo # Soyayya mai tsayawa a zuciya # Kaddara mai cike da ƙalubalen rayuwa # zamba ma yar aike ce. # Cuta mai mai ban tsoro. # Mummunan Zuciya kai bawa mahalaka # All in one story ~*KURMAN ƘADDARA*✍️~ # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣6️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* 💞💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞 💞💞💞💞 💞💞💞 💞💞 💞 " me ya kawo ka waje na " ? Ta furta masa tana haɗiye fuska ta re da girgiza ƙirji kamar wata cikakkiyar budurwa. Shi ko Har zuwa lokacin murmushi yake yi dan haka kawai ya ke jin kamar an ƙara masa wani mashin son ta da yake sukar sa ya ƙara ƙarfi a ɗan lokacin nan dan haka ya kasa haƙuri sai da ya same ta kozai cire abun da yake ji. Sai da ta ƙara maimaita masa cike da tsiwa shiko kamar Gaula kamar ba Iro ba ya ɗan yi ƙasa da kan sa kamar Ba fade a gaban Sarkin sa ya ce " Dama zuwa nayi kawai na ganki ". Baki ta taɓe tana hararar sa kamar idanun ta zasu zube ƙass.Shiko murmushi ya ƙara saki kafin ya ce " Wallahi Dagske ganin ki kaɗai nazo yi Shatou" Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta sauke idanun ta ƙasa da ga mugun kallon da take masa ta ce " da ka ganni kuma sai me ye " " Ajiya ka bani ne,ko na tsokane ka,ba ma an yi muna kashe di da juna ba " Shiru Iro yayi kafin ya sauke ɗan ajiyar zuciya sannan ya ce " Babu ko ɗaya " " To kama hanya ka wuce gidan ku,ko na haɗa ka da Baffa na ". Ta yi maganar tana nuna masa hanya Murmushi yayi ya ce " Toh an gama sai da safe " Ya wuce yana waigen ta kamar sakarai yana sakin murmushi.Ita kuwa muguwar harara ta bishi da ita kafin ta miƙi hanyar shiga gida fuuu kamar iska zai kwashe ta cike da Haushin Iro da mamakin wannan lamari na sa sai kace ajiya ya bata da zai ce ganin ta ya zo yi. Ƙaramin tsaki ta ƙara ja tana juyawa ta harari hanyar da ya wuce wanda har ya shanye kwana.Daf haka goshin ta ya bugi kafaɗar Baffa na dake tsaye yana jin duk abunda ke faruwa da kallo murmushi ya sakar mata bayan ya sauke a jiyar zuciya mai haɗe da numfashi.Bata ce masa ƙala ba ta yi yar dariya dan haka kaiwa ta ji kunya sannan ta shige gida tana ɗan mirza goshin ta shima Baffa na murmushi kawai yayi kafin ya bi bayan ta yana sakaya gidan. Ya ɗan daɗe tsaye tsakar gidan kamar mai tunani komai ya tuna kawai ya shige ɗakin sa zuciyar sa cike da wani irin tsoro da shakku da halin ƙaƙanikai. A ɓangaren Shatou tana shige wa ta haye gadon ta sai tayi ta tuno yadda ta ke gatsa masa magana amma bai mata komai ba hakan ya tabbatar mata da babban dalili ne zai saka Iro yin sanyi haka.Dan haka sai jikin ta yayi sanyi wai ita Iro zai ce ya zo gani akan me ?.Ta tambayi kan ta. Akan yana son ki wata zuciya ta bata amsa.Kai ina ba zai yuyu ba wallahi ta bawa kan ta amsa tana jan ƙaramin tsaki. Adduar kwanciya Bacci tayi bayan ta rage kayan jikin ta sannan ta juya kwanci kafin kace me sai bacci. A ɓangaren Inna ni kuwa zaune take,tayi ta gumi tuninika iri iri ke addabar zuciyar ta ta rasa yadda zata kwatanta ma Baffa na abinda ke cin ranta shekara da shekaru,dan haka Damuwar tayi mata wani irin riƙo a zuciya wanda dama cikin ta take damuwa ta san bata rabo da ita sai lokacin da Allah ya iyakance. (" Suna cikin matsala rayuwar su na cikin hatsari,Kuyi wani abu zasu hallaka su,zata samu sauƙi zata samu waraka zata sami lafiya ".) Wayen nan kalamai na Shatou dama wasun su sune ke ta amsa kuwwa a cikin Kunnuwan ta.Ta ina zata fara shin zata yarda da abun da iska suke faɗa mata ne zata gasgata su bayan kuma su ɗin sun kasance masu ƙarya mafi yawan zancen su ƙarya ne,idan har abun da Shatou ta faɗa gaskiya ne tabbas zancen alaƙar sa da wannan tabbatatta ce me zata yi me ya kama ta tayi ta tambayi kan ta.Addu,a shine abinda zuciyar ta ta faɗa mata hakan ya sa ta sauke numfashi mai zafi kafin hawaye masu mugun zafi da raɗaɗi suka silalo mata duk yadda take son dannewa ta ka sa hakan ya sa ta sake wani irin kuka mai fitowa daga ƙasan zuciyar ta sai da ta yi mai isar ta sannan ta kwanta saboda ta na fashin Sallah ta yi addu,a ta kwanta.Cikin ikon Allah sai kuwa bacci mai nauyi ya kwashe ta sai dai daga nin yadda take kwancen ka san a cikin damuwa take.Baffa na ma a ɓangaren sa ya kasa barci dan haka ya ke kai kawo shima ɗin kamar akwai abunda ke damun zuciyar sa sai dai shi kaɗai ya sani sai mahaliccin sa.Ya daɗe haka kafin ya koma ya buɗe wata yar jaka ta shi ta ajiyar abubuwan sa masu amfani sannan ya jefa wata leda baƙa a ciki yana zuba mata ido kamar mai tsoron abun da ke ciki.Haka ya rufe ta yana sauke ajiyar zuciya.Sannan ya je yayi Alwallah yayi Addu'a ya kwanta shima kuma cikin yardan Ubangiji bacci ya kwashe sa dama an kwashi gajiya.Bibu ma tun da ya shige babu labarin sa da alama yayi bacci dan shi baya wasa da duk wani abinda ya shafi Hutu na sa. Asuba ta gari shatoun Baffa na. Cikin ikon Allah Bata farfaɗo ba har sai da yayi discharge na su dan haka tare suka koma gida da ita. Har dare yayi yana kan ta shi ya zauna zaman kula da ita dan haka ma ya ce Mira ta wuce gida kawai Nana tunda ta samu sauƙi sai ta dawo haka kuwa aka yi. Cikin ikon Allah kuwa Ishaa bata farka ba sai da safe kuma cikin yardan Allah ta tashi babu hayaniya sai dai kamar a tsorace take da kowa dake gidan dan ta ki sakin jikin ta sai tayi ta kakkamewa kamar yadda take yi ta makure waje ɗaya babu ci babu sha sauƙin ta ma Suhail tana karɓan na sa shima ganin ko na shi kwana biyun nan sai ta ga dama take karɓa rabi duk ta zubar hakan ya sa suke ƙara jin Tausayin ta dan tana azabtuwa matuƙa sosai. Dan haka suke kara bata kulawa fiye da wadda suke bata saboda yanayin da take ciki dole ka tausaya mata,a ɓangaren fitar da itama suna nan suna shiri dan Suhail ya tun kari iyayen su da maganar kuma sun aminta tare da nuna jin dadin su da sanya masa albarka. Koda ya fito duk suna nan zaune suna kallo wanda an kwata faɗa yayi kusan sau biyar Hajiya na tare wa ta raba.Haka Samir koda ya fito cikin shirin sa na kaya marasa nauyi ya same su Leena sai aikawa Reena harara take yi kamar idanun ta zasu zube murmushi kawai yayi ya ƙaraso wajen yana furta "Take it easy My Baby ".Kunya ta ji dan haka ta sauke kan ta ƙasa tana Murmushi shi shiko Dariya yayi kafin ya miƙar da ita tsaye haka ma reeena da Ninah suna dariya.Yadda ya tallabo kamar wasu yan teddies.Tare suka isa bakin dinning da dama An riga an shirya sa shi kaɗai ake jira dukkanin su ka zazzauna har su Ayman da ake firar da su dan sun riga shi ma fitowa.Cike da sakewa su Leena da aka zubawa ko wacce nata suka fara cin abincin hankali kwance.Sai dai Leena ko rabi ba tayi ba ta koma kusa da Samir wai na shi take son ci babu musu kuwa yana murmushi yace ta wanke hannun ta da gudu kuwa ta wanke hannun a nan cikin robar da aka ajiye ta wanke hannun saboda Samir da yake cin abinci da hannu a mafi yawan lokuttaa yanzu hakan ma shine kawai ke cin abincin sa da hannu hankali kwance. Cike da murna ta zauna suna cin abincin tana kallon sa tana Murmushi shima murmushin yake yi Reena dai bata tanka mata ba sai cin abincin ta take yi a haka suka yi ta shirita wajen cin abincin kafin suka koma Falo su Abduljabbar da Ayman Sai tsokanar ta suke yi ta yiwa Hajiya ya ji yau tunda Samir ya dawo ta zo harda zama, idan ba ya nan kuwa gaisuwa kawai ke kawo ta,ko ita ba kullum ba Haka suka zauna suna ta fira suna bashi labari yana kwasar dariya dan harda labarin islamiyya aka taɓo masa harda dukan da Ustaz Babba ya yi mata ta bashi labari tana dariya tana nuna yadda wai cikin ustaz Babba yake motsawa idan ya ɗaga bulala.sai da ya gama cin dariya sannan ya ce " Yanzu Leena Uztaz Babba mai makaranta gaba ɗaya shine kike kwaikwayo "? Dariya tayi itama kafin ta ce " To Ai shi ya dake ni yaya ai da faɗa kawai yayi mini kamar yadda kai da su Ummah kuke mini ". Ta kai ƙarshen maganar tana turo ɗan ƙaramin bakin ta gaba. Dariya yayi kafin yace " Gaskiya ba,a.kyauta mini ba an sako mini Baby gaba ". " Ai wallahi yaya wannan da kake gani sai dai Allah ya shirya shekaranjiya fa wani ta gani yana jan wata mota mai kuka kamar mataccen injin kawai ta saka mishi dariya tun bai gane da shi take ba har ya gane,haka fa ta tura kan ta a glass tana kwasar masa dariya,shi ko fahimtar da shi take ya hau zagi harda kira ma Su Abba ɓarayin gwamnati ". Ayman ne yayi zancen. Dariya Ce ta kama Samir kafin ya ce " ohh ina kuka je hala ?" " Mun je aikar Sir Ni da ya'ya Abdul Shine fa kafin mu fice ta ganmu ta ƙalla sau ta tace sai ta bimu,muka ce ba zamu je da ita sai kuka,sai aka sa,a Dada ya fito ya motsa jiki shine ya saka mu dole muka fita da ita aiko munyi dana sani dan mutumin nan ya ji haushi sosai yana fama da kan sa shi kaɗai ya san halin da yake ciki amma yarinyar nan saboda rashin ta ido ta fara sakar mai dariya tana nuna yadda motar ke rawa " . Har Hajiya da bata wani shiga firar ba bayan zaman ta wajen yanzu dariya tayi tana furtawa A ranta Allah ya shirye ku Albasa bata yi halin ruwa ba Leena mahaifiyar ku mutuniyar kirki koda yake ba haushe yace kana haihuwar ɗane baka haifi halin sa ba addu,a ta cigaba binsu da ita duk su duka tana rokon Allah ya ƙara shirya musu zuri,ar su. Samir bayan ya tsagaita da dariyar sa ne ya kalli Leena da ta haɗe rai tuno yadda Ayman ya janyo ta ya rufe glass kafin ya balbale ta da faɗa dan haka tun da suka yi mata haka dan shima Abduljabbar ya taɓa faɗan ta rufe komai. Hannayen ta ya riƙo kafin ya kalli fuskar ta yana jan kumatun ta take kuwa ta washe baki tana dariya kamar Ba ita ba dan tana mugun shiri da Samir sosai idan ka ga dariyar ta da ya Samir ne a irin mabanbanta lokuttan. Ƙarar wayar shi ce ta sanya shi dakatawa yana kai duban sa ga screen murmushi ya saki kafin ya ɗaga kiran. Da sallama ɗauke a bakin sa ya ɗaga tsadaddiyar wayar ta sa ya saita a kunne. Daga chan ɓangaren Amsawa aka yi kafin cike da barkwaci ya ce " Allah ya taimaki soja ni na 'isa " " ai Reena mutuniyar kirki ce gasu nan ma kusa muna fira ,kuma an kawo mini ƙarar ka daga jarumar gidan nan ". Ban san abinda aka faɗa masa ta chan ɓangaren ba naga ya saki murmushi yana shafa kai kafin ya kalli Leena ya ce " Mu dai Dan Allah kar a ƙara taɓa mu kaga ka sa ka mu fushin ka da yawa " Fahimtar da wa ake yin waya hakan ya sa Leena ɓata fuska sai hawaye kafin ta miƙe tana shirin fita daga part ɗin gaba ɗaya hannun ta ya riƙe da sauri yana girgiza mata kai.Kafin ya kafa mata wayar a kunne. " Kin gama fushin,ko da saura na ƙara miki lokaci " ? Shiru tayi tana haɗiye kukan ta jin yadda yayi magana cikin kakkausar muryan sa da babu wasa a cikin ta kafin ta ce komai ta kara tsinkayar Muryan sa yana cewa " Sakaryan yarinya kawai,Mara hankali,zanyi maganin ki duk abun da ke kan ki sai na cire Miki shi mark my word " kafin ya ja karamin tsaki yana kashe kiran . Ai Leena bata san ta saki wayar ba tana ɓarkewa da kuka kafin ta kai ƙasa harda murje murje kamar yar shekara huɗu.Kan ta suka yi ganin abun na ta kamar mai Aljannu dan ta birkice dagaske hankalin su ne ya ɗaga jin tana kuka kamar ranta zai fita,sai an samu ta rage sautin kukan bayan ya dago ta ya rungume ta kaɗan sai kuma da ta tuna kalaman sa sai ta ji wani irin baƙin ciki tana ji ina ma ba Ya Bilal Bane ta masa rashin mutunci kuka tayi mai isar ta ana Rarrashin ta.Shiko Samir hankalin shi duk ya ta shi dan haka ya ce " B da yace zai bada haƙuri ashe wata rigimar zai tsokano mana ya bar mu da rigima ". " Cewa fa yayi na baki ya rarrrashe ki ya baki hakuri ". " To ba ce min yayi Sakarya ba kuma wai duk abin d ke kaina sai ya cire mini,kenan yana nufin ina da aljanu Ni wallahi lafiya lau nake,wai sai yayi ta haɗa Ni da Aljannu " ta ƙara fashe wa da kuka cike da sangarta itama Reena ganin kukan Leena abun ka da ɗan uwa tuni ta fara tsiyayayar da hawaye itama kafin ta ɓarke da kukan haka suka jeru su biyu Ninah babu batun dariya ga abun dariya dan haka ta zuba musu ido kawai kamar ta samu tv. " A yafe ma yya B kinjin my baby shi fa big brother ne duk abinda yakeyi saboda ke ne da samun kammaluwar ki,You should not be like that hakuri zaki yi kinji Babyn SS kin san Ya ce ke ce matar ta sa Farko ba Hajo ba " Cike da barkwanci Samir ya kai maganar ƙarshe.Dariya duk suka sanya kafin suka tsinkayo Muryan ta tana shesshekar kuka bayan gama yar dariyar da tayi yanzu tana cewa bata son Sir ya mata tsufa " Ya Samir fa harda mara hankali ya kira mini wallahi kuma Ni ba mahaukaciya bace ai dai ka sani ko " Kai ya ɗaga mata kawai har ta gama maganar ta yana murmushi ganin hawaye sun ƙara silalo mata hakan ya sa ya ƙara janyo ta jikin shi ya yi wiping tears ɗin.Yana furtawa common is ok chill up my baby a hankali. Su ko Su Abduljabbar da Ayman yar dariya kawai suke yi wa Reena da ta lafe gefen sa itama idanu sun yi jazir wanda har yanzu idanun ta hawaye suke yi sai dai basu kai na Leena ba.Ta tsani ganin yar uwar ta cikin damuwa ko ƙalilan ta dan haka kukan ta bai da wahala akan abun da ya shafi Leena ɗin. A haka suna nan aka kira Sallan azahar dan haka suka miƙe kowa yayi wajen Sallah ,Su ko Su Leena Sashen Ummah suka koma da niyyar zasu dawo haka ma Ninah tare suka fice tayi na su sashen. " Na ra sa yadda zanyi da matar nan wállahi ta san bana buƙatar ganin ko ɗigon jinin ta ne a kusa dani amma wallahi saboda muguwar gulma da munafunci musamman take Turo su gaisuwa waje na har Babban su,Shin dole ne bana so wallahi bana kaunar ta ko kaɗan da ina inada yadda zan yi da ita da tuni nayi ". Hajiya Sa'ada ce ke zancen tana kishingide kan mahehen gadon ta na alfarma daga ita ɗan towel wanda ya rufe mata jiki da alama daga wanka ta fito sai hular wanka akan ta. Ban san abinda aka furta mata ta chan ɓangaren ba na ga tayi dariya kafin ta sake cewa " Ki bar Ni da ita wallahi zan yi maganin ta,ke ni har mai gidan ma yanzu mugun Haushin sa nake ji yayi tafiya Lagos kwana biyu da suka wuce da ya dawo ɗaki na ya kamata ya sauka amma wallahi Sashen matar chan ya sauka da na kalubalance shi sai ce mini yayi ai ya'yan sa kawai ya je gani da yayi kewa kiji munafunci fa,Sai yanzu nake jin dana sani matuƙa akan ƙwayoyin hana haihuwa da na yi ta bankawa kaina,wallahi tunda likitota suka ce sai an cire mahaifa ta ta lalace nake cike da tashin hankali haryanzu da aka zare ta bana samun isasshen bacci mai daɗi Mabaruka " Handsfree ta saka wayar ta sauko ta zauna kan mirror da ke wadace da kayan gyara fata sannan ta cigaba da sauraren maganar da ake yi ta ɗayan ɓangaren " Sa'ada sai da nace Miki kar ki yi,amma kika rufe ido bakya son haihuwa da wuri yanzu gashi nan ai mu kan mu kin barmu cikin damuwa, kuma nace ki karɓa yara ko na dangi ne yan ƙanana ki raina kin kasa kin fison baƙincikin Barirah da wannan su kai ki ƙasa,ki na kallo zata kwashe komai ita da ya'yan ta ga dukiya har ba a san iyakar ta ka ba amma babu magajin ki ai na yi baƙuncikin wannan lamari ". " Hmmm Ba zaki gane ba ne,Bana son sai na gama wahala da yaya su koma gun mahaifiyar su ne su bar Ni da ciwon zuciya da ƙunci shi ya sa kawai na karɓi kaddara ta hannu biyu,kuma bana fatan wata rana Saleh ya san da wannan maganar tunda bai san komai ba akan hakan sanin sa kawai bana haihuwa dan haka na haɗa baki da likita ya faɗa masa " " Allah ya kyauta ai Bama zai sani ba '' " Yanzu dai zamu yi magana zuwa gobe in Sha ALLAH idan na samu time zan shigo sai mu ga abun yi dan matar nan da alama ba tsaye take ba Bayan saye zuciyar shi da ya'ya har da wani sharrin da ban Dan Barirah da ganin ta nan macijin sari ka noce ce,zan shigo dai zamu yi magana " " Tau yayi yar uwata Nagode ki gaida Alhaji Mamman da yara " " Zasu ji in sha ALLAH bye " Daga haka suka yanke kiran. Tsaki ta ja tana cigaba da mirza mayukkan ta hankali kwance. Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya tun bayan sauke wayar kunnen sa yake kallon wayar yana jin sautin kukan nata har tsakiyar kan sa.Murmushi ya saki a hankali kafin ya furta " Ni kowa ye zai kwashe mini wannan rigimammiyar ƙanwar ta wa,hankali sai baya yake yi " " Allah ya shirya mini ku twins " Miƙewa yayi ya shige rooms ɗin sa dai dai nan Ab ya shigo da Aiken da yayi masa. Wayar sa ya kira hakan ya sa ganin Ab ne ya ɗaga " shigo " Kawai yace masa ya katse kiran. Cikin haɗaɗɗun Rugs dake wadace da falo mai kyau da ya ji dark purple light rugs and curtain komai sai san Barka ko ina tar ga wata haɗaɗɗiyar tv dake ta aiki. Sara masa yayi kafin ya miƙa masa wata yar takarda. Karba yayi yana dubawa ya ja tsaki bai ce ma AB komai ba yayi gaba ya shige Bedroom ɗin sa, Ab kan sa kawai ya girgiza ya fice dan shi kam bai san amfanin aikin da ogan sa ya saka shi ba shi inda ma ya ga yarinyar da zai iya ma binciken ƙwaƙwaf amma ba kowace asibiti ne suke iya bada bayan nan mara lafiya ba,saboda doka ce bare Babbar asibitin SHAHABS ta manyan mutane. Aiken da BILAL yayi wa Ab kuwa shine tura sa asibitin ne ya nemo masa bayanan wannan mara lafiya ɗin dan mugun tausayin ta ne ya ɗar sa masa lokaci ɗaya ya kasa samun natsuwa yana son tallafa mata ya kai ta wajen wani Babban likita a Chaina,kafin su koma Lagos ya so su gama komai da ya dace.Sai dai yanzu bayan zuwan AB ya samu labarin an sallame ta sannan sun hana bayanai dan komai nata da ban yake hakan ne ya sa ran BILAL sosuwa ya ta shi ya shige daki yana jan tsaki mara sauti da tunanin shisshigin me zai kai sa dan haka take ya watsar da maganar bin ta da addu'ar samun lafiya. Shiru ya zuba ma wani hoto guda biyu da ke a jiye da bandan ɗaya na mace ne tana sanye cikin farar abaya ta yane kan ta da veil ɗin sa tayi kyau sosai a kallo ɗaya zaka mata san cewa Babbar mace ce sai na biyu hoton shima dai Hoton Matashin magidanci ne sanye da ƙanana kaya yana ɗauke da briefcase yana murmushi an masa hoton kamar dai wajen taro aka ɗauke shi ma a hoton. Wani irin abu ya haɗiye mai kauri a maƙoshin sa wanda yake ta kai kawo tun zuba ma hotunan biyu idanu.Hawayen da suka cika idanun sa ne ya shafe kafin ya fashe da wani irin kuka mai cike da kewa da raɗaɗi da baƙin cikin da yake jin ba zai taɓa gushe masa ba,wazai tun kara ya warware masa wannan lamari,me ya sa sai shi mai ya sa,zuciyar sa ta kasa gasgatawa me ya sa ya furta a bayyane da ƙarfi yana buga kan sa da kan gado kafin ya mike cike da ƙunar zuciya ya shige toilet kan sa ya sakarwa ruwa yana yi hawaye na silalar masa wani irin raɗaɗi a zuciya na sake mamaye sa. *Wani irin kaɗawa iskan wajen keyi tana bada wani irin ƙamshi mai narka zuciya da ruhi yadda wajen ya wadatu da shuke shuke da yanayin ruwa dake gudana a ƙasa zaka tabbatar ta Babban waje ne baida hayaniya ko kaɗan a wajen kowa yana harkan gaban sa ne babu ruwan kowa da kowa,a gefe akwai hadaɗden restaurant dake tsare gwamnin burge wa. Zaune yake daga shi sai guntun wando ya mike ƙafafun sa ɗaya akan ɗaya kan yar rumfar da yake cikin ta ya ɗaura hannayen sa kan ƙeyar sa idanun sa kuwa sanye da wani irin faskeken rado mai kyau black wanda ya ƙara bayyanar da ainahin zubin kyaun sa. Wayar sa ce tayi ringing kusan sau uku kafin ya ɗan ɗago ya zuba mata idanun sa wani kiran ne ya sake shigowa dan haka a hankali ya miƙa hannun sa ya zari wayar. Abbu shine abun da ya furta a ƙasan laɓɓansa sa. Goshin sa ya ɗan dafa dan bai yi zaton Abbu bane yayi zaton Mubarak da zai zo yau ne yayi zaton ya iso yana tunanin ya je ya dauko sa ne kamar bai san hanya ba. Sai da kiran ya katse sannan ya bi bayan sa. " Assalamu alaikum Abbu " Shine abinda ya furta kafin yayi shiru. Abbu cike da farin ciki ya amsa yana sauke ajiyar zuciya tare da sakin Murmushi mai sanyi. " Shine bazaka neme ni ba yau kusan kwana biyar MAHAJ kamar ba ka ma yi kewa na ba ". Murmushi ya saki mai sanyi kamar yana gaban Abbu sannan ya ce " Abbu kana lafiya ai Mubarak yana faɗa mini komai na shiga busy ne saboda mun fara preparations na presentations ɗin da zamuyi " shiru yayi har Abbu ya fidda rai da zai kara magana ya ce " Abbu ai kana raina daga ku har su Ayya ". Murmushi Abbu yayi sai kuma ya ji hawaye sun tarar masa na tausayin ɗan na sa da yake cikin kewa ta kulawar mahaifiya da bai samu ba. Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke dan shi da Badan mahaifin sa ba sai Samrah da babu abun da zai saka shi yawan komawa gidan ma Hutu sai dai yayi zaman sa nan.Amma ko yaya ne yana duba farin cikin da zai gani akan fuskokin Wayen nan mutanen guda biyu. " Aikin Ƙauyen ne an fara shi tun kwana biyu da suka wuce,na san kana da labarin komai ". Shiru yayi ma Abbu hakan ya sa Abbu sakin guntun murmushi dan ya san ba tan ka masa zai yi ba. " Allah ya sa ka da Alkhairii,ya sa matar Auren ka ta zame maka ta gari,ya baka yaya masu albarka da maka biyayya kamar yadda kake yi mini ". Haka kawai ya ji bakin sa yayi masa nauyi dan haka ya kasa Amsawa da Amin.A duk lokacin da mahaifin sa yayi masa irin wannan addu'ar wani yanayi yake tsintar kan sa ko yanzun dai hakan ya samu kan sa.Yana jin kamar yana yiwa mahaifin sa zagon ƙasa domin duk wannan zancen na mahaifin sa babu shi Aran sa ko nan da shekara goma ne,ba zai so rayuwar da ya ta so ta kaɗaici ya yan sa su yi ta ba dan haka bai shirya ma zuwan kowa karƙashin sa ba hasalima private life ɗin sa itace yake ganin tafi dacewa dashi har ƙarshen rayuwar sa saboda yadda ba ya son takura. Abbu bai ji komai ba na kin amsawar ta sa , sai murmushi da yayi bai yi masa maganar ya amsa ba yau kamm, shi kan sa Mahaj murmushi kawai ya yi cikin mamaki ya ɗan sauke wayar sai kuma ya tsinkayo Muryan sa yana furta " Mubarak zai sauka in the next thirty minutes in Sha ALLAH ka tura a ɗauko sa ko kaje da kan ka ". Baki ya tura gaba kamar Abbu na ganin sa jin shirun sa ya sa Abbu dariya kaɗan ya ce " kun fi kusa,ka kula da kan ka bye,Allah yayi maka albarka". " Amin " ya furta a ƙarƙashin laɓɓansa sa da suka ƙara yin jaaa sosai dan sai ɗan taunar su yake yi a hankali miyan bakin sa na ƙara musu sheƙi da nuna Zallar yadda suke a taushi. Headphones ya makala dake gefen sa bayan ya sauke ajiyar zuciya yana ƙara zuba wa wayar ta sa manyan idanun sa. Ɗan lemu dake gefen sa kan wani table ya ɗan yi sipping wanda ke a kan wani haɗaɗɗen cup yanayin dai na turawa haka irin wanda ake saka mocktail,jaaa yayi kaɗan da straw ɗin ya ajiye yana mai da idanun sa ya rufe ruff iskan da ke shiga jikin sa na ƙara masa wani jin daɗin wajen dan yadda ta garwaye da turaren sa mai Shegen ƙamshi sai kayi zaton shine mallakin wajen gaba ɗaya. A ɓangaren shatou dukkanin kwanakkin nan da suka shuɗe kullum sai Iro ya tare ta a hanyar makaranta ko aika,har ta kai yanzu ba ta son fita farautar ma da ta ke yawan matsawa idan ba,a je da ita ba yanzu bata zuwa,su Baffa na sun sakawa ikon Allah ido dan kowa ya fahimci Iro dai son Shatou yake yi duk da taƙi barin sa ya faɗa ɗin ma dan ga tsau ga tsau haka take jefa masa magana mara daɗi amma duka ya shanye.Yau ma daga wajen farauta ta fito saboda ta gaji sai ta baro su Baffa na chan Ita dai saboda gajiyar da ta kwaso bata san cewa akwai mutun bayan ta ba hakan ya sa ta ke tafiyar ta hankali kwance dan ta rage guje gujen yanzu. Ta kawo wajen wata bishiya kenan kawai ta ji mutun bayan ta ya ce "keeeh " Irin abun nan na ka bawa mutun tsoro cikin soyayya shine Iro ya yi mata aiko ta zabura ta zunduma a Guje ko waigen sa ba tayi ba, shima bayan ta ya bi yana ƙwala mata kira yana dariya cike da nishaɗi. Fahimtar shine hakan ya sa ta ƙara giyar gudun cike da Haushin sa.Su Ramata ne suka tare ta da Amina suka shaaa gaban ta hakan ya sa ta dakata dan har ta yi niyyar wuce su.Sai kuma ta ci burki tana Hararar su.Dai dai nan shima Iro ya iso wajen yana sauke numfashi yana cewa " Haba Shatou ke ko tausayi na baki ji kin fa gane Ni amma kike cigaba da gudu na haba Shatou na". Wata uwar Harara ta jefa masa kafin ta kalli su Amina da suka yi tsuru tsuru suna kallon Iro ganin yadda ya ƙara komawa kamar ba shi ba abokin faɗan Shatou wai yau shi ke kiran Shatou da shatoun sa. Dariya suke son yi babu dama dan shatou bata ƙaunar ko tsayuwar su ne duk sun shaida hakan yadda take tserewa kafin a tashi makaranta saboda shi har wajen wasannin su ta daina zuwa sosai saboda shi dan duk wata hanya da ya san zasu haɗu sai ya bita,ƙofar gidan su idan ya je zai gaji da tsayi yayi gaba. '' Nifa wallahi Iro ka fara isata wallahi zan kai ka ƙara wajen mai gari haba duk ka bi ka ta kura mini kamar bani da gata saboda jarabar ka ko kofar gida ta daina burge ni,ni kan wallahi ga mai gari zan kai ka ya ƙara mana kashe di "ta kai ƙarshen zancen kamar zata saka kuka musanman da ta ga ko ajikinnsa sai ma Murmushi da yake ta saki dan shi wata dama ya hango a nan take wajen.✍️ # 2025 # Hausa novel # Love,and romance story # Labari mai tafiyar saƙar gizo gizo # Soyayya mai tsayawa a zuciya # Kaddara mai cike da ƙalubalen rayuwa # zamba ma yar aike ce. # Cuta mai mai ban tsoro. # Mummunan Zuciya kai bawa mahalaka # All in one story ~*KURMAN ƘADDARA*✍️~ # Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣7️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* ♣️♣️♣️ Fuuu haka ta wuce ta bar su nan shi da su Amina ana kallon kallo kafin ya ɗan bi bayan ta da sauri sauri sai dai kafin ya an kara ta zunduma a guje dan ta fahimci muddin ba haka ta yiwa Iro ba,ba zata zauna lafiya ba.Dan bata taɓa jin zata iya tsayuwa dashi. Koda ta shiga gida babu sallama Inna ni na aikin wanke kayan da ake zubawa shanayen Baffa na abinci wayen da suka yi datti.Dan tun safe bayan Shatou ta gyara musu wajen su ta ce ta wanke su amma bata yi ba saboda shiriritar ta,sai ta ɓuge da bin su Baffa na Farauta. Kai kawai Inna ni ta girgiza bata iya ce mata komai ba sai cigaba da aikin ta dan ko bata tambaya ba ta san cewa Iro ne ta ke yiwa wannan guje gujen.Ta rasa dalilin da ya sa shatoun bata ƙaunar Iro ko kaɗan domin ga alama nan ko tsayu wa ta arziki ta ka sa yi da shi,itama wani farin ciki take ji duk da bata jin zata yi mata auren wuri kamar yadda ake yi a Ƙauyen na su duk da ƙalubalen da zasu fuskanta tana son Shatou tayi karatu mai zurfi ta taimaki mutanen wannan ƙauye ta mayar da kyauta da karamci. Zaune ta kai daɓass tana huci da sauke numfashi kafin ta ce ''Inna ni dubi dan Allah yadda Iro ya sako ni gaba wallahi na kusa kai shi ƙara wajen mai gari " " Aah ba ayi haka ba,kefa matsala ta dake rashin wayau shi iron ne meye dalilin zuwan sa wajen ki " ? Ƙin bata amsa Shatou tayi dai zumɓura baki. Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " to tunda kin san abinda ke kawo ɗan mutane ai sai ki bari ki ji abun da zai faɗa daga baya sai ki san abun ce masa,kuma banda wulaƙan ta wa Shatou rayuwa bata da tabbas karki wulakanta kowa domin baki san ɓoyayyen Alkhairii sa gare ki ba,sannan baka san mai taimakon ka ba dan haka idan ma tsayawa ne ba kya son yi dashi ki gaya masa ke an hana ki tsayuwa da kowa a gida faqat ". Bakin dai ta ƙara tun zurawa gaba bata ce komai ba. Chan kuma kamar an tsakure ta,ta mike tsaye ta kalli Inna ni ta ce " amma ai ni Inna ni bana son sa kuma ni ba a ƙauyen nan zan yi aure ba miji na birni yake shi ya sa bana kula shi duk ga su Amina nan amma sai ni da ya raina ". " Sannu matan ɗan birni,Haba SHATOU Soyayya ce fa " Baki ta kara turawa sai kuma kunya ta kama ta tayi kasa da kan ta tana dariya da ɗan murmushi Inna ni dai bata ce mata ƙala ba. Sai kuma ta matsa ta fara ɗauraya wa Inna ni kwanonin tana yi tana langaɓe kai maganar Inna ni na bata dariya wai Sannu matar ɗan birni,soyayya ce fa. A haka suka gama aikin tare. Su ko su Amina gaba suka yi kowacce su tayi gida suna ƙara mamakin Iro suna zuwa gida kuwa kowaccen su ta fara bawa innar ta labari suna dariya suma iyayen na su dariya abun ya basu duk da sun san haɗin mai wahala ne sai suka bi Su da addu'ar fatan Alkhairi. " Ina su Baffan naku,ba tare kike da su ba " ? " Ni na gaji ne shi yasa na tafowa ta " " Shine wanchan uban nacin ya biyo ni". Shatou ta bawa Inna amsa tana ƙara tura baki gaba. Komai Inna ni bata ce ba sai karɓe wanda yayi saura a hannun Shatou dan ta kasa dauraye shi sai juya shi da ta keyi har ta fara jiƙe kayan jikin ta. A tare suka kaiwa Shanayen da sauran dabbobin abincin su dan tun da safe sunyi gyaran wajen ita da Bibu saboda babu makaranta yau ɗin. Mubarak kuwa ya sauka ƙasar Beijing china lafiya dan sanin da yayi wa Ogan na sa kuma aminin sa da yake ma kallon ɗan uwan sa na jini ko ya kira sa ba lallai ya samu zuwa ɗaukar sa ba hakan ya sa koda ya fito daga cikin jirgin bai yi gigin kiran sa ba sai ma ƙokari tare taxi da yake yi. Sai dai kamar an ce ya juya ya hango sa jingine da wata irin lafiyayyar mota mai ƙirar Naira ya harɗe hannayen sa cikin ƙirjin sa haka ƙafar sa ɗaya ya ɗan karkata ta da take sanye da kafiyayun baot masu kyau,yana sanye cikin kaya mara sa nauyi kamar shigar ɗazu guntun wando mai kyau da wata yar riga armless sai uban rado dake kan fuskar ta da wanda har yanzu bai cire shi ba daga nesa gashin sa sai sheki yake yi wanda yake shan gyara. Murmushi Mubarak ya ɗan saki kafin ya taka izuwa inda yake. Yana kaiwa wajen da yake ya shafa kan sa yana furtawa a hankali " thank you sir " Ko kallon sa MAHAJ bai yi ba sai koma wa da yayi bayan motar yayi zaman sa kamar yadda ya zo dan yana da driver da ke kula da shi idan Muby baya nan dan ba kullum yake tare da shi ba saboda shine yake taimaka masa a wajen kasuwancin sa nan da yake gudanarwa. Buɗe masa drivern yayi ya shige yana masa godiya kafin suka bar filin jirgin. Koda suka isa masaukin su dan wani Babban apartment ne mai dauke da gidaje masu kyau irin tsarin ginukan Chinese masu kuɗi komai ya ji tabarkallah.A wani irin Babban fili na ajiyar motoci suka yi parking cike da ƙasaita ya fito bayan driver ɗin ya buɗe masa. Ficewa yayi ba tare da ya magana da kowa cikin su ba. Shima Mubarak da ya bude da kan sa murmushi kawai yayi yana ayyana wa a ransa miskillancin na asali ya motsa dan haka ya karɓi jakarsa hannun Drivern da ya Fiddo masa a boot godiya yayi ma ba chinen mutumin kafin ya shige ƙofar da na ga ya shiga mai ɗauke da wadattacen glass,sai da akayi scanning na sa sannan ya shige bayan ta wangale. Ƙaton Falo ne na alfarma da yake ɗauke da komai hanyar upstairs ya kalla kafin ya saki murmushi kawai sannan ya Miki hanyar.Tafiya yayi kaɗan ya iso wata ƙofa mai ɗan kyau itama ta glass sai da ta gama scanning ɗin sa sannan ya shige kayan sa kawai ya ajiye ya faɗa toilet domin samun damar sauke gajiyar da ya kwaso. Duk da tafiyar jirgi ce amma yana jin jikin sa yama da tsami dan sun ɗauki a wanni da dama a saman iska. A ɓangaren Mahaj kuwa ƙudundune yake cikin ƙaton duvet sai dai bai rufe jikin sa ba gaba ɗaya dan kana iya hango fresh skin ta sa da take ta sheki kasancewar babu riga a jikin sa yana shigowa ya zare ta. Wani irin kwalba ne kamar na gold mai cycle sai ƙyalli yake yi ajiye yake a gefen sa kan bed side drower ta makeken gadon na sa dake ɗauke da bedside lamp a kowanne gefe gefe da gefe. A hankali ya lumshe idanun sa da yake jin sun masa nauyi saboda rashin samun isasshen bacci tun dawowar sa ya maida hankali akan presentation ɗin domin zai wakilci school ɗin su ne su uku aka zaba shi daya daga Nigeria sai wani dan China da wani dan america guda dan haka ganin Makarantar ta nuna bukatar kulawar su yake iya ƙoƙarin sa wajen yin research mai ma,ana da gamsar wa. Zuƙar hayaƙin flavour shi shi yayi yana jin wani iri a kan sa da yadda yake jin hayaƙin nan na kawar masa da komai da yake damun zuciyar sa. Zuƙa yake yi a hankali sai dai irin zuƙar nan mai ja da yawa dan da ganin yadda yake shan ta kasan ya saba da ita,zuƙa yake yi sosai wanda take hayaƙi turneƙe ɗakin, tari ya fara a hankali yana jan numfashi lokaci ɗaya idanun sa suka yi jaa. Mubarak da yayi wankan sa ne ya fito ya faɗa wa MAHAJ ɗin saƙon Samrah ya faɗa Bedroom ɗin da sauri cike da tashin hankali bayan ƙofar ta wangale.Aiko da wani irin mugun sauri ya kunna na'urar da ke korar hayaƙin abun ka da kasar da ke da technologia take ya fara ɓacewa da sauri ya matsa ya fisge shi shi ɗin dan har yanzu tarin yake yi kuma ya ƙi daina zuƙar ta. Kashe ta yayi gaba ɗaya cike da damuwa ya ke kallon mahaj da ya zuba masa idanun sa da suka rikiɗe yana kallon sa irin na ban son shisshigi. Mubarak yi yayi kamar bai fahimce sa ba dan haka ya sauke kan sa ƙasa dama ba kasa fai yake haɗa ido dashi ba duk da yana masa maganar bai son munafunci ya daina masa hakan amma saboda girmamawa yake kasa wa sai irin wayen nan lokuttan. Bai ce masa komai ba sai ficewa da yayi da kwalbar yana jin babu daɗi a zuciyar sa dan ya san muddin ciwon sa ya tashi a kwai matsala kafin a samu farfaɗowar sa sai ya ci wahala gashi har yanzu babu wanda ya san yana da wannan ciwon sai shi Mubarak ɗin da Ayyah Abbu bai san komai ba saboda ciwon bai taɓa ta shi a gaban sa ba,a mafi yawan lokutta zuciyar sa ma idan ta motsa tana tayar dashi dan haka Mubarak yake kaffa kaffa da shi dan daga baya ciwon ya bayyanar masa sai chan baya ayyah ta san yana tasar masa dan ta taɓa kai shi asibiti aka faɗa mata matsalar harda maganin sa tunda kuma ya tashi ya san abinda ke damun sa yake saurin danne fushin sa,sai gashi ta silar wannan hayaƙin yake shirin tado ma kan sa da lalurar da yayi kwana biyu babu ita dan ya manta ma da yana da ita ta daina ta shi sosai chan baya harda damuwa take ƙara mata ƙaimi kuma duka Mubarak ne yayi kula dashi a lokacin yana school tare dashi kuma suka ɓoyewa Abbu itama Ayya abun bai wani dame ta bata taɓa faɗawa Abbu ba a cewar ta ba zata kashe ɗan ta ta raya na wata ba saboda ta san yadda Abbu ya tsani ciwon ko kan ƙani ne a jikin MAHAJ ɗin sa take yake sauyawa saboda damuwa Bpn sai ya tashi. Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanun sa da suka garwaya daga asalin farin madarar su. Ƙofar da Mubarak ya banko ce ta sanya shi ya mutsa kyakkyawar fuskar sa kafin ya ɗan harari ƙofar yana sakin murmushi a zuciyar sa dan haka yake ƙara jin ƙaunar Mubarak saboda kyawawan ɗabi'un sa yana bashi kulawa kamar ta mahaifin sa da mahaifiyar sa yana iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya riƙe amanar da Abbu ya basa dan koda ya fahimci MAHAJ na shan shi shi bai matsa masa da dole sai ya daina ba yayi dai koƙarin ganin ya yi yadda zai yi ya rage har Allah ya sa a samu ya daina tunda itama shan ta baida fa'ida dan hayaƙi ce itama yadda taba zata cutar haka itama zata taɓa huhu.Sannan bugu da ƙari cutar da yake fama da ita. Jan jikin sa yayi ya kwanta yana yana sauke numfashi ya san Mubarak yayi fushi daga jin yadda ya banko masa ƙofa. Kasancewar dare ya riga yayi dan a gogon ƙasar har ya nuna sha biyu na dare wanda gari yake kamar rana hakan ya sa ya tofa addu'oin kwanciya bacci kafin ya miƙe ya kashe haske ya bar bedside lamp wanda itama ta gefe ɗaya kawai ya kashe ya bar ɗayar tare da rage ta.. A haka barci mai daɗi ya kwashi ɗan Abbu. Mubarak da ya dawo yanzu ne ya tura ƙofar a hankali ganin ya kashe haske ne ya san cewa yayi barci hakan ya sa ƙatuwar TV dake aiki a hankali wadda take dai dai da saiti gadon ya kashe ta kafin ya matsa ya kashe masa Hasken bedside lamp tare da rage masa gudun Ac saboda ita kan ta illa ce a gare sa amma haka ya ke ƙure ta.Dan haka yake fama dashi a kullum idan suna kasar nan. Baya shigo masa Bedroom sai yayi barci ko ya same sa a irin haka amma iyakar sa Falo. Ficewa yayi bayan ya gyara masa kwanciyar ta sa dan filon mai taushi ya bar kan sa sai ya zama na ya aza kan sa a kan hannayen sa da suke ta shinning da alama zasu yi taushi dan Jawur haka suke sai alamar taushi da suke da shi a bayyane kamar na sabon jariri. Kyakkyawar fuskar sa da take Baby face wanda zaka tabbatar jikin ne kawai amma yaro ne shakaf MAHAJ matashi mai tasowa cike da burikan rayuwa da wani irin raunin zuciya da ya rayu dashi,wanda yake fatan wata rana ya sauke wannan nauyin ya samu farin ciki. Murmushi yayi cike da tausayin sa sannan ya fice daga ɗakin take kuwa ƙofar ta rufe ruf wadda take kamar ta Karfe kamar kuma glass dan itama sai ta bincike ka tsaf amma idan ta saba da ɗaukar baya nan ka kana zuwa take buɗe maka ka shiga. Shima kasancewar ya kwaso gajiya hakan ya sa yana dawowa ya nemi waje ya kwanta shima cikin haɗaɗɗen bedroom ɗin sa mai kyau sai dai duk da haka na MAHAJ ya fi sa nema ba kusa ba. Asuba ta gari. " Ta baiwa ki cigaba da aiwatar da komai cikin natsuwa muna samun nasara an kusa Haska duhun da ke bai baiye dake yanzu kawai jini za'a ƙara ba wa su ɗan duhu zasu bazama kuma suna son na sabon jariri da na mai ciki dan haka aiki ne Babba " " Sirrin ki naki ne yana nan ɓoye bana son ki ƙara mini magana akan sa,Babu wanda zai taɓa zargin ki koda kuwa ya ga wata alama mun toshe kowace ƙofa,ki yarda da mu, ba zamu taɓa bari aikin shekaru da dama ya tafi a banza ba,kin mance sharaɗin mu da Sarkin Aljannu muddin muka kuskure su ɗan duna da ɗan duhu suka halaka akan wannan aiki Ni dake duk mun halake dan haka ba zan taɓa wasa da wannan aikin ba na toshe kowace ƙofa " " Na yarda da ku Dan Baiwa,Kawai dai wata rana sai nake jin kamar akwai wanda yake da wani sani akai kuma yake cikin kokwanto akan abun wanda wata rana kaɗan zan fallasa,Yanzu dai shi kenan bari na tafi dan dama wata yar dama na samu na fito sai na sake dawowa ". Kudade ta ajiye masa masu yawan gaske kafin ta miƙe tana zagin sa yana zagin ta sannan tana juyawa ta ɓace ɓatt kamar yadda ta saba yi kullum idan ta zo shima ɓacewa yayi kamar bai taɓa zama wajen ba.✍️ Ta Baiwa 🥵 Ta baiwa 🥵 Ta baiwa 🥵 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________2️⃣8️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* _____________" Umma Ya Samir ya dawo " Reena ce tayi zancen tana washe bakin ta kamar gonar audiga. Ita kuwa Leena zama tayi tana haɗe rai kamar wacce aka yiwa mutuwa. Murmushi Ummah ta saki kafin ta ce " Masha ALLAH,yau ya samu zuwa kenan,shi kam kamar ana korarar sa da gida shida Soja ko hutun basa son zuwa ". Ta yi zancen tana kallon Leena da ta ke shiru.Hannun ta ta riƙo tana furta " Wa ya taɓa wannan kayan ita kuma ta shigo min haka ".? Dariya reena ta ɗan yi wadda ke ƙara wasar da idanun ta da suka fara ɗan sauyawa dan tun shigowar su Ummah ta lura sai dai ba ta tambaya ba kawai tana jiran su faɗa da bakin su,amma ta lura ba faɗar za,ayi ba dan giwar a cike take. " Yaya B ne ya ɓata mata rai " Kyaɓe baki Umma tayi a hankali kafin ta ce kunfi kusa cikin zuciyar ta tana Murmushi amma a fili sai ta ce " Kai BILAL bai kyauta mini me ya sa ya taɓa mini yaaa yaushe ma aka shirya bamu sani ba ".?Takai ayar zancen tana jiran amsar su fuskar ta sake. Baki Leena ta tura gaba ita kuwa Reena dariya ta saka ganin yadda Ummah tayi da fuska tana kallon Leena. Cike da ɗan irin mamaki. " A ina kuka samu yin magana da shi ne " ? " A Wayan Yaa Samir ne " Reena ta bawa Ummah amsa. " Ku bar ni da shi zamu garwaya ba faɗa masa bana son yana takura wa ya ya na amma naga alamar bai jin magana sai na fara zane shi da bulal.. ". Ai ko kafin Ummah ta kai ƙarshen zancen Leena ta fashe da dariya haka Reena dan sosai suka dinga dariya wai sai Ummah ta zane shi garsheshen ƙato dashi har ta hango Ummah na dukan shi yana kuka. " Ummah kina iya zane sa,yafi ki ƙarfi fa " ? Leena da ta saki fuskar ta tayi zancen tana kallon Ummah da fuskar ta ke cike da murmushi na farin ciki ganin yadda suka saki fuska lokaci ɗaya musamman Leena da ta haɗe ta gabas da yamma wanda ko bata tambaya ba ƙara ce ta kawo mata shi ya sa aka shigo aka yi mata zugumm kamar kurma yayi faɗa,dan ta san dole zata tambaya in ita bata faɗa ba Reena zata faɗa. " Sosai ko har yayi kuka harda karya sa ma zan iya a ƙafa ". Dariya Leena da Reena suka ƙara fashewa da ita kafin Leena ta miƙe kamar wadda aka tsikara ta fara tafiyar gurmunta ta irin in ƙafar ka na ciwo haka tana nuna yadda ya B ɗin zai yi idan Ummah ta karya sa. A wannan karon Ummah sai da ta dara kaɗan tana girgiza kan ta dan shashancin su Leena abun dariya ne har yanzu basu yi wani mugun wayau ba kullum yan jiya suke koma mata,kamar lokacin da suke cikin zane. Shiru tayi bayan wani tunani da ke shirin kutsowa a cikin ƙwalƙwalwarta na abinda ya faru shuɗaɗɗen lokaci hakan ya sa ta miƙe daga zaunen da take tana cewa " ku tashi ku je kuyi Sallah kafin Abban ku ya dawo naji yana neman ku kafin ya wuce masallaci " Cike da dariya kuwa suka miƙe suna cigaba da yin tafiyar sai dai itafa Reena dariyar ce kawai take amma tasha alwashin sai ta fadawa ya B kar ya zo gida Ummah zata karya shi. Ita kuwa Leena wani irin nishaɗi take ji jin Ummah zata rama mata kuma ta san tana iyayin hakan dan haka ta saki fuskar ta take ta manta da abunda akayi mata. Ummah sama ta haye da sauri tana ɗaukar kiran da ya shigo wayar ta tana Murmushi da dariyar su Leena. " Haba B tin yaushe nake kiran ka baka ɗagawa bana jin daɗin abinda kake mini samm wallahi,sai ka riƙa ware Ni kamar ba yar uwar ka ba nifa ina kiran ka ne mu gaisa amatsayi na na yar uwar ka,zuwan da kayi kwanan baya har na shirya na zo gidan aka ce ka koma,Wallahi banji dadi ba,na so mu gana ". Shiru yayi bayan jin ta aje aya tana Sauke numfashi dan tun da ya ɗaga wayar take ta uban surutu ko gaida shi bata yi ba ta fara zuba masa zance.Dama haka take bata ko gajiya da kiran na sa. " How is Hamida and Momma " ? Shiru tayi kafin a hankali jikin ta mace jin bai ma bata amsa akan maganar da tayi ta zuba wa ba kamar an buɗe famfo sai ma tambayar Hamida da Momma. Wani takaici ne ya turneƙe ta sai dai ta san halin sa hakan ya sa cike da wani irin haushi ta ce Tace " They are fine,Amma B baka ji abinda nace ba,duk maganar da nayi "? Uhhm ya ce kawai dan har yanzu bai jin dadin jikin sa tun ruwan da suka dake sa a toilet yanzu haka koda ya fito sai da ya sha pain relieve Dan wani irin ciwon kai ya taso masa da sanyi da ya saukar masa yana son ya huta ita kuma uwar nacin son zumunci tana son addabar sa dan shi duk da ya fahimci inda ta dosa duk da bata taɓa faɗa masa ba yake ƙokarin kawar da faruwar wata magana a tsakanin su yafi son ta bar shi a matsayin Zumuncin take bi. " Samira ina jin headache pls I want to hang up the call,want to sleep and rest " " Ki gayar da su Bb Mai Billions duk da minyi magana dashi jiya da su Ammah,ki gaida Abba da kowa da kowa,Bye ". Ya yanke kiran yana ajiye wayar tare da jan guntun tsaki. Sage da baki Samira ke kallon wayar kafin ta Saci kallon gefen da Hamida take kwance hankalin ta kwance tana danna wayar ta kamar hankalin ta bai kan ta. Wulaƙancin yau yafi na koyaushe take gani dan haka wasu hawaye ne suka silalo mata masu ciwo kasa jurewa tayi dan haka ta miƙe da sauri ta fice daga ɗakin tana ɓare baki kamar ƙaramar yarinya. Ita kuwa Hamida duk da dariya na son ka mata amma ta ji Tausayin yar uwar ta matuƙa dan haka duk da haka dai sai da ta dara ta girgiza kan ta dan ta daɗe tana cewa yayar ta ta raba kan ta amma taƙi ji dan ita duk da yarinya ce ta fahimci Ya B baida bukatar yayar ta Samira yanzu ga irin ta nan tace wa Momma ta daina goya mata baya amma dukan su sun nace kamar Auren zumunci dole ne kowa ta tsiya ake ci a cikin sa gashi Samiran ta ƙwallafa rai ga ya yan na su. Samira na fita da kuka ta faɗa jikin wata Babbar mace da ta fito daga wata ƙofa da alama bedroom ne. Kallon ta tayi ganin hawaye jagaga bayan ta ɗago fuskar ta kafin ta ce " Samiran Momma lafiya kuwa " ? " Waya taɓa mini ke " ? " Momma ba B bane ya ya yi mini wulaƙanci ". Ta bawa mahaifiyar ta su amsa tana jan wani sabon kukan. Murmushi matar tayi kafin ta riƙo hannun ta suka zauna anan kan ɗai daga cikin hadaɗdun sofas dake ƙawace da falon. Hawayen ta fara share mata kafin ta sauke numfashi ta ce " Nifa ban ce ki matsa mishi da yawa ba, ba sai na riƙa Nana ta Miki halin Mazan nan ba Samira wata rana sai naga kamar Hamida tafi hankali ma,a hankali a hankali ake tafiyar da komai Hamida na min zancen na ce ki daina ta kura masa,sai dai ina yi mata ne kamar bana jin ta amma Ni na san Indai kika matsa zai gundura dake,Ki bi komai a hankali na miki alkawarin sai kin samu Bilal zumunci kawai muke son mu karfafa dan koshi Baba Mai B na ra'ayin hakan dan na taɓa masa zancen ya ce a bari har gaba to yanzu dai ga gaban ta fara zuwan ki kwantar da hankalin ki,Ni Rashida sai na ƙwato Miki Soyayyar BILAL ba dai mahaifiyar shi na so ba kar ki damu Abban su kuma na san bazai taɓa musawa ba haka ma duka a halin dan ba zasu taɓa manta da halaccin da Baba Mai Billions Yayi musu ba dan ance ko kafin Shima Baba Bukar ya rasu ya nuna yana son haɗin zumunci a wannan a ahali dan haka na san Baba Mai B ba zai hana faruwar hakan ba ki saka a ranki kin Auri BILAL SSS kinji kin zamo surukar Ummah surukar Abba ".karshe sai ta fara rera mata waƙar nan " ƙanwata kiyi Haƙuri ..... Dariya suke yi bayan ta kai aya cike da farin ciki a haka Momma ta sharewa Samira hawayen suka koma dariya kamar ba ya da mahaifiya ba gwanin burge wa suna ta barkwancin su har Hamida anan ta same su ta zauna aka cigaba da fira da ita kafin lokacin ya ƙara shigewa kowa ya watse saboda dare ne ba,a dade da ga ma Sallahn Isha ba.Su na nan zaune sai ga mahaifin su ya shigo Alhaji Ahmed Aliyu Mai Billions Sannu da dawowa suka yi masa dan sun san inda ya fito yana sashen Mahaifin na sa.Ammah da kuma A Bukar. Fira suka cigaba da yi cike da kaunar juna kafin su kayi Sallama da juna. A ɓangaren su Leena ma koda Abba ya dawo duk sunyi sallolin su anan suka zauna gaba ɗayan su har su Samir da suka shigo suka yi ta fira kafin lokacin islamiyya yayi suka shirya suka wuce ya'u ya kai su kasancewar weekend ne sai bai zauna ba ya dawo gida time nayi ya dauko su ya dawo da su,sai dai fa ko a mota sai da aka tashi kwata wata rigimar domin Ninah da Leena ta kama tana Hararar ta dan ita ta so shiga gaban mota shine tayi karaff ta shige shine dalilin faɗan na su,da ƙyar ya'u ya raba faɗan. Koda suka dawo gida ma suna cire uniforms ɗin su suka yi sashen Sir da duk yau ba su shiga ba wajen Maaama Da Hajjow har da su Uwani ma da Dada. A chan suka yada zango sashen kakannin na su dan wajen Ummu aka fara zuwa da Dada kafin suka yi sashen Hajjow suka ta sa ta gaba tana biye musu itada Sir cike da ƙaunar Jikokin na su da suke musu wata irin ƙauna da su kan su Bazasu iya bayyana ta ba. Shigowar Abba ce a ƙaton falon na Hajjow ya san ya Reena miƙewa da sauri tana masa oyoyo tare da amsa Sallamar sa kamar ba ɗazu suka rabu ba. Shi ko Murmushi yake ta saki yana kallon su tare da iyayen na sa kafin ya kara sa wajen su har ƙasa ya kai yana gayar da Hajjow tare da Sir sai kuma Maama da ke ɗan jingine da wani tintimi kamar filo sai dai mai mugun taushi saboda jikin tsufan ta shi ya sa suke samar mata da duk abu mai taushi da zata ji daɗin jikin ta. Zama yayi kusa da Mamaa yana cewa " Wai ke tsohuwar nan yaushe zamu ci dafa dukan ki " ? Kuka ta fashe da shi tana furta " ka jiya ko Sada,Kana jin shi ko ". Daƙuwa Sir yayi masa yana furta " Babana Karɓi nan,nace gyatumar ka Uwani,Nace ka daina saka mana uwa a gaba baka bari sai ka karasa muna ita muna lallaɓa a bar mu,Ai ga na kan nan sun tsufa su ya kamata ka fara cin dafadukar su ". Dariya Abba yayi dan haka yake Indai ya shigo Sashen sai ya Tsokano Kakar ta sa su yi ta rigima ta yi ta kuka tana cewa bai son ta.Sir ne yake shige mata ko Hajjow amma Abba ya riga ya saba sai ko su BILAL da su Samir da take mahaifiyar su tunda tattaɓa kunnen ta ne, sai su yi ta ɓata fuska idan Abba na yi ma Mamaa haka a gaban su,duk in sun tashi suna tsokanar ta. Ita dai Hajow dariya kawai take yi saboda kawaicin ɗan farin da take yiwa Abba a yanzu.Kamar yadda Mamaa take yiwa Sir wanda sai yanzu da tsufa ya kamata take kiran Sada da sunan sa. " Wallahi Sada wannan ba Saleh na bane wai jairin Ni yake yiwa fatan mutuwa " Kuka ta ƙara fashewa da shi wiwi.wiwii Dariya kuwa su Leena kamar sun samu abun yi.Kukan na ta cike da tsufa da abun dariya dan harda yar majina ake fyacewa da ɗan tisssue dake gefen ta da ake ajiye mata a kusa da ita.Idan ta tara sai Hajow ta kwashe tun da ita take kulawa da ita basu saka kowa ba da ita da Sir da sauran ahalin suke kula da ita cike da tausayi ta da ƙaunar ta. Hannun ta, ya janyo cike da sakin murmushi yana cewa " Haba Maama ta ai ni mijin ki ne fa ba sunan kawai na ci ba,ai Sir shaida ne ,shi na biyo dan dai tsufa ya cinye muna ke ai kema kin san da haka ". A wannan karon Hajow kasa hakuri tayi ta masa daƙuwa.Dariya yayi cike da farin ciki.Kafin ya ce " Ai ina son Mamaa Gashi harda kilishi na tana do Miki mai daɗi ". Baki washe kuwa kukan ya tsaya nan hawaye ta fara sharewa tana Murmushi dama haka suke kullum kuma Indai yana gari shida Ibrahim sun dinga rigima ta kaka da jika kenan suna tsokanar ta. Ƙarshe anan wasan yake ƙarewa dan duk sun san yadda take ƙaunar kilishin duk da Babu wasu haƙora sai an buga mata shi.Sannan sun san an hana ta cin irin wannan Jann nama amma saboda tsufa da tausayin su ke jin Gara su bata abinda take so kar gaba suna kallo gashi babu ta gabansu shi ya sa shima Sir d dada suke ƙyalewa yanzu sun san ba,a mutuwa sai lokaci yayi kuma Mahaifiyar su ai tayi tsufa mai kyau tun har takan iya cin abu mai nama nama ba ruwa kawai ba.Shi ya suke ƙara gode ma Allah. "Kaji ɗan Albarka,Allah ya jiƙan magabata,Allah ya jiƙan Dam rayuwa " Sai kuma ta fashe da kuka.Jikin su ne yayi sanyi har su Leena tunda sun san wanda take cewa Dam duk da basu yi rayuwa da shi ba amma sun san shi a bakin a halin gidan kuma sun san hoton sa dan suna ganin sa asasan gidan. Rarrashin ta yayi da ƙyar kafin jiki mace jin ta tado masa da wani Miki haka cike da ƙarfin hali haka ya fara daddaka mata kilishin sai da yayi rugub akan haɗaɗɗen dustsen da ake daka mata irin wayen nan abubuwan kafin ya fara bata ya na cewa " Ya isa Maama ci " Yana saka mata acikin bakin ta da ke ɗauke da da sa shi kawai sai yan haƙora da basu wuce biyar ba tsufa duk ya sauke mata su dan haka ko maganar ta ba irin sosai ake ganewa ba sai su da suka saba da ita.Ta nata magular abun ta. Hajow tunda Mamaaa ta fara maganar ta miƙe tsamm ta shige ɗakin ta. Shi kan sa Sir ƙarfin hali yake yi. Abba da ya lura da yanayinsu bai matsa ba ya cigaba da bawa Maammaa tana ci suna taɓa fira har da su Leena tare aka cinye kilishin dan wanda suka rage mata kaɗan ne.Koda su ya gama bata dai dai an fara kiran Sallah hakan ya sa ya miƙe yana sanar da ita zai wuce amma zai dawo sai su wuce tare da su Leena ɗin.Dan Sir shima ya bar falon ya bi bayan matar sa. Dai dai shima Sir ya fito haka ma Hajow a bayan sa sai dai babu wanda ya bari Ya haɗa ido da Abba.Numfashi kawai ya sauke bata re da ya ce komai ba sai dai ya saka mahaifin sa gaba suka fice a tare zuciyar sa cike da wani irin ƙunci mara daɗi da duk lokacin da Mamaa tayi maganar Dam sai dukkanin su sun tsinci kan su a damuwa dan kafin su warware sai an ci lokaci Abubuwa da dama ke dawo musu a tunani soyayyan su da suka rasa ne suke musu riƙo a zuciya mara wuyar sauka saboda dukkanin su kamar wani irin bango ne ko ginshiƙi a gare su na farin ciki. Anan Falon Hajow ta yi Sallahn Isha tare da su Leena haka ma Mamaa da take yin Abar ta zaune saboda ƙafafun ta babu lafiya yau dan duka haka suke fama da su har Hajow ɗin Dada ma sune ciwon sa ko Sir ma haka sai dai na shi bai kai nasu ba dan in ya tashi ko tafiya ba su iyawa Uwani ce kawai da suke kira (Ummu)take da lafiyar ƙafafu. " Nidai yunwa nake ji Inna ni ". Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " kin ji abinda zaki ce Malama ba wani gajiya ba ke da farauta ɗaya biyu zaki zo min da zancen kin gaji ". Dariya SHATOU ta kece da ita dan harda dungure kan ta Inna ni tayi. " Akwai sauran abincin Baffann ku na nan ki ɗauko tun da bamu kai ga na rana ba,dan yau ma tuwo ne zanyi". Ido Shatou ta ƙwalalo waje kamar wadda ta ga wani mugun abu ko ta ji ta ce " Inna ni tuwo,nikam dai ba zanci tuwo ba yanzu ma fa shine zan ci ragin ɗumame wai so ake yi sai Na zama kamar tuwo ne a riƙa kira na tamalmatu ". Dariya Inna ni ke son yi sai dai ta fuske abunta ta cigaba da saƙar kaba da take yi Shatou na gefen ta tana haɗa mata kayan hadin dan tunda suka gama wanchan aikin ta ɗaura girki lokacin ita Shatou ta shiga ɗaki ta duba wani aikin gida da aka basu hankalin ta ya ɗauku. Kuka ta sakawa Inna ni Dagaske bata cin tuwo ko anyi shi yau dan ba zata yarda ta zama tamalmatu ba dan ta taɓa jin labarin mai sunan an ce daga cin tuwo ta zama haka an mu su irin wannan ta tsuniyar a makaranta inji wani prepect. Lalllai kammm Sai prefect 🤣 " Wallahi Zan kira Almajiri na bashi ya cinye shi yanzu " " Ke kuma idan kin gama shiriritar ki sai ki ci na rana ". Kafaɗa take girgizawa tana cigaba da yin kukan duk da ta na jin sarai abun da Inna ni ke faɗa,miƙewa Inna ni tayi kamar Dagaske take yi dan Muryan Almajirin ta ji a maƙota tunda ta kangar su babu wata girma gare ta dan ma duk haka gidajen na su suke na ƙasa dan ma Baffa na ya ƙara ma ta su girma sai suka ɗan banbanta. Aiko cike da sauri ta miƙe tana ƙara sautin kukan ta. Gefen madafar su ta ɗauke shi a inda yake killace cikin wata yar Samira. Inna ni dariya ke cin ta sai dai bata nuna a fili ba tayi a zuciya sai dai kawai a bayyane ta girgiza kan ta cike da ƙaunar yar ta. A wannan karon kammm sai da ta yi Murmushi a bayyane ganin yadda SHATOU ke cin Tuwon kamar tana cin kashi sannan ga hawaye jage jage akan fuskar ta.Ga kan ta da take ta langaɓewa gefe cike da Sangarta irin ta ta tana yi tana Sharar hawaye. Chan kuma mai ta tuna ta ture kwanon baki ture cikin shesshekar kuka ta ce " Ni Bama zan ci wannan ɗin ba,haka kawai a yi ta bawa mutun tuwo,Ai Baffa na suna wajen Farauta na san zai zo da kaya masu yawa shi ya sa nafi son aje farauta saboda mugun Tuwon nan ". Ta yi zancen tana share hawaye tana Hararar Tuwon Inna ni da yayi kyau na dawa ne sai ƙyalli yake yi ya tuƙu sosai kuma yayi taushi ya sha miyar mu ta kuka mai kyau. Baki sake Inna ni take kallon ta jin tana kira ma Tuwon ta mugu aiko da sauri ta ƙwala kiran Almajirin.✍️ Damm🤔 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________2️⃣9️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* Almajiri kuwa dake kusa da sauri ya kwaɗa sallama bayan jin kiran da Inna ni tayi masa. Zuru haka Shatou tayi da manyan idanun ta da suke ta wani maiƙo na hawaye tana dakatar da kukan na ta tare da zuba ma Inna ni idanu ganin in da gaske zata aiwatar da ƙudurin ta,ita kuwa Inna ni ba tare da ta ƙara bi ta kan ta ba, ta ɗauke Samiran ta karɓi roban Almajirin ita da kan ta,ta juye masa shi fuskar ta haɗe. Shatou kuwa Wani sabon babin kukan ya buɗe haka ta zauna ta cigaba da rera kukan ta dan an kyautar da Tuwon da ba lallai ma ta cisa ba Inna ni ta san da hakan amma shine take ta uban kuka haka,Inna ni kuwa har lokacin Sallah yayi bata kula ta ba dan ta lura yan taɓarar sun ƙara motsawa. Da maburkaki ta kora ta wajen Sallah ai ko tana gama sallahn ta ɗaura daga inda ta tsaya ta zauna inda ta tashi ta cigaba da kukan na ta abun dariya.A haka su Baffa na suka same ta shida Bibu Sai rusar kuka take yi kamar wadda aka yiwa mutuwa. " Wa ya ta ɓa mini Shatouwa ta matar ɗan birni " ? Baffa na ya tambaya saboda yanzu firar ce suke yi da Bibu yana sanar masa ta ce bata son Iro ita matar ɗan birni ce dan haka bata ma son ko ganin Iro wai ya zo da sunan ko ganin ta ne shi ya sa take ta guje gujen ta cike da ƙuruciya. Hawayen da suka ƙara silalo mata ta share kafin ta kalli Inna ni tana ɓata fuska sannan a hankali cikin shesshekar kuka tace " Ba Inna ni ba ce ta bawa Almajiri Abincin da ka rage mini,shine nace ina jin yunwa na fara ci ta bawa Almajiri ". Ɗan murmushi Baffa na yayi kafin yace "A'ie baki kyauta mini ba,yar amanar tawa zaki yiwa haka ko Tausayin mu ba,a ji " Ya kai ƙarshen zancen yana share mata wasu hawayen da suka silalo mata. Inna ni dai bata ce musu komai ba sai ma yar madafar ta su da ta shige tana cigaba da aikin ta fuskar ta a sake dan kamar murmushi ke son fita sai dai ta ƙi bashi dama saboda shirmen na shatou a bun dariya ne. " Share ta kin ji nama gasasshe ma yau zaki ci dan kamar mun sani muka tsaya muka gasa abun farautar mu tun a chan ungo gashi ". Wata leda ya Fiddo da ita daga jakar da kayan na farautar su ke ciki da Bibu ya miƙo masa.Wata irin gaashi ce Baffa na suka yi dan dama har gashi suna yi idan sun je chan yunwa ta riƙe su sosai sai su gasa rabin abunda suka samu,yau ma hakan ne dan gashi suka yi na musamman akan abun farautar ta su, tsarkakakken nama ne kamar na kaji kamar kuma na tsuntsaye an banƙare su sun ji gashi mai tsafta sai tashin ƙamshi yake yi. Take bakin Shatou ya fara motsi jin ƙamshi ya bugi hancin ta tun kafin a ciro shi daga ledar ita sai yanzu ma ta fahimci ta ji ƙamshin tun shigowar su rigimar ta ta hana ta ta tabbatar. Guda ɗaya Baffa na ya ajiye mata akan wani ɗan madaidaicin filet da Bibu ya ɗauko yana murmushi ganin yadda hawayen Shatou suka ƙafe ƙaff. Miƙa mata yayi yana furta " Yi Bismillah kici ki ƙoshi wannan duka na ki ne ". Wani ya Fiddo da ban sannan ya ce " Bibu wannan na Innar ku ne ". Miƙa ma Inna ni naman yayi cike da fara'a karɓa ta yi tana furta " Angode " dai dai lokacin ta fito daga yar madafar ta su kamar dai ta rumfar kara haka da aka ɗan shinge. " Inna ni dan Allah mu ji naki ko yayi daɗin nawa " Mara zuciya ya ji haushi Inna ni ta furta acikin zuciyar ta tana murmushi. A fili kuwa cewa ta yi " Zo gashi kwaɗayatu " Cike da jin daɗi kuwa shatou ta matsa ta miƙa ma Inna ni nata zata saka mata baki.Ɗan kallon ta Inna ni ta yi kafin ta ɗauke kan ta ta ce " ɗibi na wan kawai tunda naki baya isar ki " '' Nidai sai kin ci nawa sannan ki ji yadda gashin sa yake nawa gashin ya fi daɗi " Babu musu kuwa Inna ni ta yago kaɗan tana neman kaiwa bakin ta. Karaff Baffa na da ya fito yan zu daga ɗakin sa bayan shigar sa yace " A'ee kar ki janyo ma kan ki rigima ƙyale ta naman ta na farar tantabara ne " " Naki kuma na ɓaƙa ne,barta ta ci ". Cike da tsoro kuwa Inna ni ta mayar maa Shatou da shi a cikin filet ɗin tana zuba masa idanu kamar ta ga abun tsoro. Baffa na kuwa bai ƙara cewa komai ba ya faɗa wajen wanka da ruwan da ya ɗiba yanzu.Ba tare da ya wahalar da Inna ni ba dan wasu ayyukan yana yin abun sa ne ba tare da damuwa ba dan haka ita har ta saba. Shatou kuwa kallon Inna ni tayi ganin yadda ta tsira ma naman ta Idanu hakan ya sa '' Ta ce Bafa duka zan cinye yanzu ba zan ajiye wa su Amina ne " Numfashi Inna ni ta sauke kafin ta fara tsakurar nata naman da ya ji gashi mai kyau dan har da kayan gashin akwai a cikin sa ba Zallar naman ba ne. Bibu ma ɗakin sa ya shige ya canza kayan jikin sa kafin ya fito yana bawa shatou labarin yadda suka yi farautar yau dan harda gasa suka yi da wasu yan farautar kuma su suka yi nasara tana ta murna tana cin naman ta sai da ta ga ta ci rabi sannan ta ce " wannan na su Amina ne, Ramata Jawairiyya " Haka ta raba naman a ledar kowannen da gefen sa ana yi ana suɗar hannu. Inna ni ma ta tsakuri nata jin cikin ta ya ƙoshi ma hakan ya sa abin cin da take neman zubo musu ta ke neman samun murfin samira ta rufe sa saboda tunda suka yo gashin nan ta san sun ƙoshi dan haka babu buƙatar tambaya,amma saboda tantance wa ta ce " Habibu na na zubo maka abincin ". Cikin sa ya shafa yana cewa " Wallahi ji nake kamar ma zanyi Amai Inna ni a dai bar shi sai anjima ". Kai ta jinjina. Baffa na da ya fito kuwa shima ta tambaye sa lokacin yana alwallah kai tsaye ya ce " Wallahi Mun ƙoshi sai dai anjima " " Ai dama ɗana ya ce kun taƙe cikin ku,na dai tambaya ne kawai " Murmushi Baffa na yayi kafin ya ajiye butar da ya gama alwallah da ita a mazaunin ta. " Assalamu alaikum Wai ance ana Sallama da shatou " Wani yaro ne ya shigo yana zancen bayan yin Sallama wadda ko amsa masa ba ayi ba ya jero kalamin. " Inji uban wa "? Shatou ta tambaya cike da Hasala dan ko ba,a faɗa ba ta san nataccen ta ne. " Wai inji masoyin ta Iro ". Yaron ya bada amsa kamar yadda aka umurce sa. Wani irin ƙololon baƙin ciki ta haɗiye kafin cike da masifa ta ce " tafi kace masa ba zan zo ba nama nake ci,kuma wallahi ko ya fi ɗan ƙuje kwaɗayi ba zan sammi shi ba ". Bibu kuwa mi zai yi idan ba dariya ba yana kallon ledar naman na ta da ta kusa cinye rabin da ta ajiye wa su Amina dama bai ji a jikin sa zasu samu ragin ba dan adda shatou akwai son nama bare kuma ba irin Tattabara mai irin girman nan ce sosai ba,ta ta wadda aka san zata iya cinye wa aka haɗa ta da ita. Inna ni ma dake saka marafe ga samirun abincin kuwa murmushi kawai ta ke yi ta re da girgiza kan ta abun haushi abun dariya. Azo hira wajen ka kana cewa saurayi nama kake ci kuma ba zaka samma shi ba,ai ko bata faɗa ba ya san bata Rabo da cin nama tunda yar mafaraucin daji ce.Dariya ta yi ta gefen baki tana ƙara auna kalaman na shatou da take kallon su da shir me tsantsa. Baffa na dai tun fara zancen yaron ya samu kan sa da yin tsaye waje ɗaya ƙirjin sa na bugawa duk lokacin da za,a ce ana yiwa shatou Sallama wani irin abu mai kama da nauyi ne ke ɗaure masa jijiyoyin jikin sa su kan hana sa sarrafa harshen sa da gangar jikin na seconni. Sai dai duk da yanayin da yake ciki kalaman SHATOU sun mugun bashi dariya matuƙa. Dan haka ya murmusa kaɗan yana cewa " ai ko baki faɗa ba shatou na ya san Gidan nama kike ". Baki ta tura kafin ta ce " Bibu ta shi ka raka ni wajen mai gari,yasin Inna ni kar ki hana ni,ai shi Baffa na ba zai ce komai ba tunda ya san bana son sa ". Miƙewa tayi da sauri ta shige ɗan ɗakin ta bata daɗe ba ta fito da wani ɗan guntulallen hijab na ta da aka yi mata kusan shekara biyu da suka wuce,tana mugun son hijab ɗin dan haka ba kullum ake saka shi ba gashi har ya gundule mata kuma ta ƙi bari a bada shi wa wasu. Baki Sake Inna ni da ta fito daga ɗakin ta take kallon ta.Ita kuwa shatou hannun ta ta ke wankewa cike da alamar da ke nuna sauri take yi Dagaske wajen mai garin zata je. Baffa na ta kalla kafin ta ce " Baffan su kana kallon wannan shirmen ba zaka dakatar da ita ba " . Numfashi Baffa na ya sauke kafin ya saki ɗan guntun murmushi yana kallon Shatou da ta laƙƙama kafadar Bibu da yake ɗan waigowa yana kallon Inna ni yaga yanayin fuskar ta dan ya zille ma rakiyar.Sai dai Inna ni, sake fuskar ta, ta samu kan ta da yi jin Baffa na ya ce " Karatu ya dace da shatou ba Aure ba yanzu,kuma yafi dacewa ne a lokacin da gari yayi haske duhu ya yaye raunin zukata ya sauka ". Wayen nan kalamai na Baffa na da Inna ni ta fahimce su sarai hakan ya sa ta sakin fuskar ta wani irin raunin ta na bayyana a fili wanda take ta ƙokarin ɓoyewa a koda yaushe. Baffa na ya lura da yanayin da ta shiga sai dai bai bi ta kan ta ba sai ma ficewa da yayi ya bi bayan Su shatou sai dai shi masallaci zai je saboda an fara kiran Sallah Asr dan gabatar da sallah akan lokacin ta, da zummar idan ya fito ya bi bayan su Shatou dan shi a gare sa zuwan case ɗin chan mai sauƙi ne dan haka ya ƙi hana shatou ɗin ta fiya. A ɓangaren su shatou kuwa Yaron na fita suka bi bayan sa ita da Bibun anan suka tarar da iro ya ɗauko wanka irin wanda ya ɗauko ranar da Mahaj ya ziyar ce su. Ya banbaɗa humra ta mata sai wani buɗawa yake yi. Ai ko kallo ɗaya shatou tayi masa ta watsar tayi gaba dan haka fahimtar inda zata je hakan ya sa cike da alfahari da wani irin farin ciki dan tana kwana gidan sauƙi ya bi bayan su. Dan haka koda Baffa na ya fito ya hango bayan su ne sai shi Iro da ke bayan su yana ta buga ƙwanbo. " Haba Captain Wai har zaku bar nan ɗin gashi ko ziyara ban samu na kawo maka ba ". Ta ɗayan ɓangaren ake zancen. " No Yaqub kar ka damu dama wani aiki muka zo yau zan koma amma ai zamu dawo ko meeting haka,nikaina na so a ce na zo naga patient ɗin ku,amma next time zan shigo in Sha ALLAH " " Ko yanzu wani issue ne ya taso daga Lagos ɗin ai da ba zan bar Abuja yau ba sai na ƙara ɗan huta wa dan nan ɗin nafi samun Hutu Sosai ". " Ok captain Allah ya taimaka A dinga zumunci yanzu fa ban gan ka ba da ban ma sanin ka shigo Abuja ". Ɗan shafa kan shi yayi yana gyara zaman belt ɗin sa da hannun sa ɗaya dake ta walƙiya yace " Haba Yaqub Ai wannnan duka laifin mu ne,Allah dai ya bamu ikon gyarawa ". Dariya yaqub yayi ta chan ɓangaren kafin ya ce " waton dai ba zaka yarda laifin ka ne ba " ? Dariya shima yayi mai ɗan faɗi ya ce " Haba na isa,ai Indai gardama ce an bar maka Yaqub dan haka na yarda,dama ko school su Samir ne masu riƙa maka " Dariya Yaqub ya kece da ita yana tuna rayuwar su a Thailand ɗin mai cike da tarihi sai dai basu watsar da taren ba ta su ba har yanzu dan nisan da ke tsakanin ne kawai amma suna communication ko shi ba sosai ba saboda commitment da yayi wa kowa ya wa. " Allah ya tsare Captain na gode sai mun yi magana ". " Amin thanks you " Kafin suka yi Sallama wayar ya ajiye.Yana sauke ajiyar zuciya. Wata ƙatuwar jakar sa ya ɗaura a bayan sa yanayin ta sojoji kafin ya kwaso duk wani abu nasa na irin na'urori ya zuba a cikin wata yar ƙaramar jaka itama.Sannan ya kashe hasken Bedroom ɗin ya fice daga ɗakin yana rufo shi. A dai dai ƙofar bedroom ɗin ya samu AB na jiran sa wanda shima yake sanye da na sa uniform ɗin cike da girmamawa haka ya sara masa tare da ƙokarin karɓan jakar sa da take goye a bayan sa. " Nop " Kawai ya furta tare da Katar da Ab ɗin gefe kuwa ya koma ya bashi hanya ya shige gaba kafin ya bi bayan sa. Haɗaɗɗun motocin da ke a wajen suka shiga sai dai mota uku kawai suka yi dan su biyar ne suka zo kawai yin meeting ɗin da minister of defence akan wani case da ya shafi tsaron Nigeria.Kasancewar Train suka yi booking saboda shine available hakan ya sa babu wata drivern ya kai su Train station ɗin ba,a jima ba kuwa jirgin ya tashi. Koda su Sir suka dawo Daga masallaci tare suka shigo su huɗu sun saka Abba tsakiya sai jikan su a gefen Dada Samir kenan, suna ta tsokanar sa yana tsokanar su har Abba na masa jan ido ya daina rena musu iyaye. Sai yayi dariya ya ce " Ai Abba haka kake yiwa Mamaan mu tsohuwa mai ran ƙarfe". Sai Ya dungure masa kai dan Abba akwai barkwanci matuƙa shida ɗan uwan sa haka suke da son wasa. Cike da murna Reena ta faɗa jikin Dada tana cewa " Oyoyo Dadan Ummu Uwani ". " Wai wace Ummu ɗin ta ku yar nema " ? Dada yayi maganar yana lakace Hancin Reena dake wasar haƙora. Ummun su Umma Umman mu ce " " Aaa ga Umman ku chan " " Amma mata ta bata isa haihuwar irin ki ba ga dai iyayen ku nan " Ya nuna Ibrahim da suke kira Abba ƙarami. Murmushi Abba ƙarami yayi yana karasa shigowa ciki dan baya nan bai daɗe da dawowa ba daga tafiyar kwana ɗaya da yayi,dan haka yau koda ya dawo bai samu shiga Sassan iyayen na sa ba, sai a masallaci suka haɗu da sir yana son yaga mahaifiyar su,da rigimammar kakar ta su dan haka ya fara shiga sashen Ummu Uwani ya gaida ita sannan ya yo nan. " Abba ƙarami ina wuni " Leena ta faɗa kamar wata mai hankali ita kuwa Reena hannun sa ta maƙalkale tana dariya tana cewa " Abba Wai Ummu Uwani bata haife Ni ba ".Dariya yayi ya shafa kan ta kafin ya ce " kin ga ummun ku chan,waccan tsohuwar mara haƙora,gashi kun ƙi saka mata artificial ta samu na cin kilishi ". " Wacchan ta chan ta mu ce " Dariya ta yi haka kowa dariya yayi yadda Abba ƙarami ke bayanin kamar irin yana mata wani karatu ne da ake buƙatar demonstration dan fahimtar ɗalibai. Hajjow ma murmushin ta yi tana masa daƙuwa. Kan sa ya shafa kafin cike da girmama ya gayar da Su Sir,Dada ,Hajiya Sannan cike da girmama Ya gayar da Abba shima cikin basa girman sa na Babba. Amsa gaisuwar Samir yayi yana hararar sa.Dariya Samir yayi yana shafa kan sa dan ya san dalilin hararar ta sa bai shiga Ya masa sannu da dawowa ba dan sashen Momcy ya sauka chan,sannan bai faɗa masa zai dawo ba.Sai dai ganin sa yayi ɗazun a masallacin Sallahn la,asar shine har yanzu bai huce ba. Matsawa yayi kusa da Maama cike da tsokana ya ce " Yar tsohuwa mai ran ƙarfe an buga dake an barki,ni da Yaya Sai zancen Jallof ɗin ki mu ke yi " Yanzu kam Maaama bata yi kuka ba sai wata harara da ta sakar masa tana ɗauke kan ta da tura baki gaba kamar dai yadda kuka san Leena na yi. Dariya duka suka sanya har su Hajow haka suka cigaba da tsokanar ta Samir na karewa yana juya abun kan Su Sir Abba ƙarami na masa daƙuwa shida Abba. Lafiyayyar Dinner ɗin da Mai aikin Hajjo ta haɗa suka zauna gwanin burgewa kowa ya ci ya ƙoshi suna gamawa suka fara taɓa ɗan fira kaɗan wadda ke nuna shaƙuwar dake tsakanin a halin kafin suka yi sallama a tare Abba ƙarami da su Leena da Samir suka fito daga sashen harda Dada sai dai kowa na sa ɓangaren ya nufa. Ummah da ke zaune falon ce ta rafka ta gumi kamar wadda ke cikin damuwa ta ga shigowar ta su idanu ta zuba musu cike da so da ƙauna kafin ta yiwa Abba sannu da zuwa yana zama kuwa ta miƙa ta shige kitchen ta haɗo masa shayin sa da yake sha asashen ta kusan kullum dan ta san sun ci abinci chan kamar yadda suka saba yi idan sun tafi Sashen Hajow ko Dada ɗin,sai bata tambaya ba. Su Leena kuwa kasancewar akwai school gobe Abba ya ce kowa yaje yayi brush yayi alwallah ya yi wanka ya kwanta dan su tashi da wuri haka kuwa ya kasance babu musu suka wuce sama bayan sun yiwa iyayen na su sai da safe.Daki ɗaya suka shiga na Reena dan ita giwar shiga na ta rigima ne da matsala ga Reena ɗin dan duk abun da ta taɓa sai an yi faɗa kan sa amma ita idan shekara za,ayi akan na Reena ko a jikin ta haka ita mai ɗakin bata taɓa damuwa ko kaɗan sai ma ta ka tsaan tsan da take yiwa halin yar uwar ta ta,tun da ta fahimci saurin fushin ta akan ta yake. Abba na shan shayin suna taɓa fira a hankali cike da so da ƙauna basu ko share awa ba wajen suka miƙe suka wuce sama a tare suka shige bedroom ɗin Abba dake sashen wanka ko wannen su ya yi suma kafin suka bi lafiyar gado shi dai Abba bai daɗe ba bacci ya kwashe sa rungume da matar sa a jikin sa. Amma Ummah ta daɗe tana juye juye Kafin bacccin ya kwashe ta mai nauyi. Chan ba,a haura ko awa ba ta miƙe a firgice tana sakin ƙara wadda ke nuna alamar tsoro miƙewa Abba yayi yana Nana ta Inna lillahi wa Inna ilaiihi raji'un yana kunna bedside lamp dake gefen ta ai ko ta haɗa zufa sharkaf. Addu'a yayi ta tofa mata kafin ta samu natsuwa ta fara sauke numfashi. " Lafiya kuwa Bary mugun mafarki kika yi ne " ? Kai ta girgiza masa tana ɗan sakin murmushi sannan ta ce " Wai fa yanzu baccin ya kwashe ni,shine naji kamar kenkeso a cikin jiki na yana mini ya wo shine fa na tashi a firgice ka sanni da tsoron coacroch " Abba dai zuba mata idanu yayi cike da tausayi dan ya san mafarkan da ta saba yi ne a chan baya wanda har yanzu ta ƙi bayyanar masa da asalin abun da take gani so ɗaya ne zai iya cewa ya ji ta yi wani furuci a cikin mafarkin wanda ya ɗarsa masa mugun tausayin ta,da na sa tausayin dana ya yan sa baki ɗaya, wanda kuma yana tunanin har yanzu bata tuna mafarkin ba,saboda bai taɓa jin ta masa zancen sa ba sai dai yana ganin ta cikin damuwa a wasu lokuttan ya san cewa abun ne ke damun ta matuƙa,dan haka kasancewar shi shirme ya ɗauki abun ya watsar dashi nan inda ya ji shi dan ya san wanda ya mutu baya taɓa dawowa duniyar nan ya tafi kenan dan haka mafarkin nata aikin shaiɗan ne musamman irin wannan.Ko yanzu ya san bai da na saba da irin wancan da ya ji dan haka yake cike da wani irin mugun tausayin ta da na su Leena. " Kiyi abunda ya dace,Allah ya sauƙaƙa ya yaye muna damuwoyin mu " A hankali ta furta " Amin " Kafin ta juya gefen hannun ta na dama dama ta kuskure ne ta kwanta a na hagu. Ta ƙara shafa addu'oi sannann ta rufe idanun ta. Abba ma numfashi ya sauke kafin ya fara yin sabuwar Addu'ar ya tofa mata ya shafa mata sannan ya shafe ma jikin sa cike da kulawa. Bai daɗe ba bacci ya kwashe sa. Ita kuwa Ummah baccin ne ya gagara sai ma wani dogon tunani da ta lula a hakan bacci mai daɗi ya kwashe ta. " Wai Ni Samir abokin wasan ka na koma eh " Abba ƙarami ne riƙe da kunnen ɗan na sa na fari Samir yake zancen bayan fitowar su daga sashen Sir inda suka sosai sashen Hajiya mahaifiyar su Samir ɗin dan Sashen ta ya koma da daren nan kwanan ta ya fara. Yar ƙara Samir ya saki kafin ya ce " Abba ƙarami na fa kira ka ba ka ɗaga ba kwana biyu da suka wuce niko na zata ka shiga busy shi ya sa ban neme ka ba ". Dun gure masa kai Abban Yayi kafin ya shafa kan sa yana murmushi ya furta " Na yarda ka barranta ". Dariya Samir yayi yana shafa kan sa da murza kunnen sa yana ɗan ɓata fuska. Hajiya da ta fito yanzu jin motsin su ta saki murmushi kafin tace " Sannu da dawowa Abban su,Yawwa mar atussaliha" Murmushi ta saki haka ma Samir dake shafa kan sa dan ya san halin mahaifin sa babu ruwan sa a gaban su yake yabon matar sa kuma eh ai Hajiya ta chanchanta rayuwar su da Ummah abun burgewa ce a gare sa dan haka yake son koda zai yi aure matar sa sai ta koyi dabarun zama da jama'a a da miji a wajen Ummah da Hajiya dan rayuwar su na burge sa. " A kawo muku Dinner ɗin nan ne " " Kwantar da hankalin ki,kin dai ci kin ƙoshi ko keda zarata na ". Kai Hajiya ta gyaɗa ma sa tana murmushi kamar yar yarinya. Shima murmushin yayi ganin yadda ta bashi amsa. Samir kan gaba yayi yana musu sai da safe. " Mun ci abin ci sashen Sir da su Yaya " Kai ta jinjina kafin ta mayar da komai inda ya dace sannan ta dawo ta kama hannun mijin na ta suka wuce na su Bedroom ɗin su. Koda suka isa Lagos lokacin magriba yayi dan dama tafiyar maraice ce suka yi manyan motocin na sojoji ne suka zo suka kwashe su cike da tsari sai a salin ƙaton gidan sa da ke nan. Shaf shaf suka yi alwallah suka yi masallaci dan gabatar da sallah wadda har an wuce su da raka'a ɗaya. Bai fito daga masallacin ba sai da ya gabatar da sallahn Isha sannan gaba ɗayan su suka fito kafin suka yi sallama da ogan na su dan sun san da ya shige ya shige bare sun yi tafiya yana bukatar hutawa. Kayan sa da Ab ya jera masa su a inda ya dace ya kalla kafin ya girgiza kan sa dan sai da ya ce masa kar yayi ya bari ya zo zai yi komai da kan sa. Wanka kawa yayo ya bi lafiyar gado babu wani tunani bayan yin addu'a bacci yayi gaba da shi. Tun da Baffa na ya fita ta bi bayan shi da kallo ta kasa ɗauke fuskar ta da idanun ta har ya fita yana jin idanun ta akan sa Wani abu ya tuna hakan ya sa yayi astagfirullah a cikin zuciyar sa ya shige masallaci. Ita ma Inna alwallah ta yi bayan ta sauke a jiyar zuciya sannan ta shige ɗaki dan gabatar da Tata sallahn akan lokacin ta. A ɓangaren su Shatou kuwa koda ta isa mai gari ya shige masallaci tare da jama'ar sa dan haka ta samu daga ta ja ta tsaya tana tokare ƙafa shidai Bibu tsoro yake ɗan ji amma babu halin nunawa saboda ya san rigimar Addan ta sa. Shi ko Iro ya koma gefe sai sakin murmushi yake yi ji yake kamar ace a ɗaura masa Aure da shatou dan dama jibi ne bikin Musa ɗai daga cikin abokan sa to haka yake ji kamar a haɗe bikin yau a Daura a fadar ta mai gari dan wata irin ƙaunar Shatou ce ke ƙara huda jinin sa. Koda jama'ar mai gari suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya haka suke bin Shatou da kallo kowa na tunanin da wace aka zo yau har suka gama fitowa kuwa babu wanda ta ce wa ƙanzil harda masu ɗan tsokanar ta sai dai ta ture bakin nan gaba. Bibu ne mai ƙokarin gayar da duk wanda ya fito. Mai gari da ya fito da ita ya fara sauke idanun sa chak ya tsaya yana zuba mata idanu kamar yau ya saba ganin ta.✍️ Ku gafar ce ni ji na da kuka yi jiya shiru jikin ne babu daɗi ulcer ya sako ni gaba shi ya sa ko Online ban samu na leƙo ba jiyan.Amma a hakan dan na faran ta muku na matse da ƙyar na muku word 400 da wani abu.Ina baran Addu,an ku. Allah ya bamu lafiya baki ɗaya. Ngde da kulawar Ku. Masoyan wannan labari na nesa da na kusa ina godiya ina alfahari da ku.allah ya bar ƙauna mai ɗaurewa. Fa'i bg Heart ❤️ u o'll💞🙏🙏🙏 Masu ganin Bama sauri kuyi Haƙuri muna kan hanyar inda ya kamata mu isa idan nace nayi rushing ginin labarin zai rushe. Amma tabbas wasan yanzu aka fara ku ƙara ɗaure ɗamara akwai dubbanin abubuwan da suke ƙulle a kan mu da zamu warware.Wannan kuma tare da ku kawai ne zan samu ƙwarin guiwar hakan ngd.🙏 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣0️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Wannan shafi na ku ne rankatakaff in ji Bahaushe💃💃🥰💕Maman Abba,Ayeesha Abdullahi,HS,Feenat Ahmad,Hajara kawu gana,Na'eemart Collection,Zainab Ishaq,Habibah Yusuf,Huudatu Umar,Aishatul humaira,Clothing,Zeinabousmaneidi,FB graphics Queen,His Queen,Meryama,Husaina Baby Mohammed,Ummigambonbala, Hauwa'u Musa yeldu,Oumsamha410,Sadiya ka'oje ,Adama Ahmad,teemah beauty,Suhaila,Miss Abdul,Rocky handsome (Lady)😇da sauran su.Ina miƙa saƙon gaisuwa a gare ku. Allah ya ƙara yiwa rayuwa albarka,ya bar zumunci.I heart😍💕 you all ✨ 🤲* _________________ ___________ _______ ____ __ _ Sai da ya gama ƙare mata kallo na kusan seconni goma kafin ya janye kallon sa daga kan ta yana sakin ɗan murmushi. Ƙarasowa yayi inda take tsaye cike da yar tsokana yace " Yau da me aka zo mana Hajiya shatou " Baki ta ƙara turawa gaba kafin ta ɗan taka kaɗan ta ce " Wallahi Iro ne ya addabi rayuwa ta shine na kawo sa ƙara" " Kuma dai me ya haɗa ku ". Mai gari ya furta yana sakin murmushi. " Wai so na yake yi yanzu duk inda zanje haka yake bi na kamar tare Inna ni ta haife mu,kuma nace masa ya daina bi na ya ƙi ya daina,Ni kuma shine na ce bari na kawo shi ƙara a masa magana tunda Ni ba ya jin ta wa ". Ta kai ƙarshen zancen tana ɓata kyakkyawar fuskar ta. Tun da ta fara zancen fuskar mai gari ta haɗe kamar bai taɓa dariya ba ko Murmushi duk wani annnurin fuskar sa shi ya kau dan haka kallo ɗaya yayi wa Iro dake gefe yana sakin Murmushi sai dai kallon da Mahaifin sa yayi masa ya sa shi shanye Murmushin da duk wani ƙwarin guiwar sa abun da bai tsammana ba a gurin mahaifin sa. Zama yayi a cikin yar kujerar sa ta zaman fada kafin ya sauke numfashi.Dan murmushi ya saki yana ƙyafato Shatou a hankali kuwa ta ɗan matsa chan kusa da shi ta tsaya tana sauke kan ta ƙasa dake nuna alamar ran ta ɓace yake da abun da Iro yake yi mata. " Tafi gida zan yi magana dashi kinji daga yau ba zai ƙara Miki magana ba ". Kai ta gyaɗa masa kafin ta yi gaba ba ta ko kalli Bibu ba dan ta ga yadda yake a tsantance kamar tsoro yake ji dan haka ya bata haushi. Su ko sauran mutanen fadar murmushi kawai suke yi suna kallon shatou da ta wuce kamar bata son taka ƙasa dan kamar an rufe mata baki haka ta ji bata yi jayayya da mai gari ba ko kaɗan dan haka kowa dake wajen yake murmushi na mamaki da hango alamar hankali ya fara samuwa A tattare da ita. Shi ko Bibu bayan ta ya bi yana ɗan sauri da haɗawa da gudu yana ƙwala mata kira amma bata ko waiwayo ba ko ta nuna ta jishi. A ɓangaren Iro kuwa hankalin shi ya ɗan tashi dan bai fahimci ma'anar kallon na mahaifin sa ba mai kama da gargaɗin gaske. Numfashi mai gari ya sauke yana bin bayan Shatou da kallo ɗauke da murmushi kafin ya koma mayar da kallon sa kan Iro wanda ya sha jinin jikin sa musamman yanzu ganin irin kallon da Mahaifin na sa ya ƙara jefa masa. Sum sum haka ya bar wajen yana kama hanyar majalisar su ba tare da ya gabatar da Sallahn La,asar ba cike da damuwa akan fuskar sa. Mai gari kuwa da ido ya bi shi ganin damuwa ta bayyana akan fuskar sa wanda ke nuna masa Dagske yake yi ɗin maganar shatou babu gyara cikin ta. A ɓangaren SHATOU kuwa da sauri Ya sha gaban ta,zille masa tayi ta na haɗe rai murmushi yayi yace " Ke Adda SHATOU duk akan mene ne wannan haɗe ran "? Ƙin tanka masa tayi sai yin gefe da ta ƙara yi,fuska ya ɓata kamar zai yi kuka.Kama hanya tayi ta cigaba da tafiyar ta kamar bata ga Bibu na neman yin kuka ba. Juyawa yayi cike da damuwa ya Kalle ta kafin ya bi bayan ta. Ta ɗan tattaka kaɗan sannan ta tsaya ta juyo tana fuskan tar sa, yar tsintisyar hannun ta ta ɗaga ta masa alamar ya zo. Ɓata fuska yayi kafin ya taka da sauri yana murmushi. Sai da ta tabbatar ya saki jiki ya kusa cimmata dan ya tabbatar zata jira sa ɗin kuma ta sauko Ai ko ta yanka a guje tana dariya. Kamar yar balbela haka Bibu ya hango shatou aiko cike da dariya shima ya bi bayan ta yana ƙwala mata kira ta jira shi su yi gasa aga wanda zai riga isa gida. Bata saurare shi ba da alama ita har ta fara gasar shima ƙaimi ya ƙara dan haka sai ya zamo ya riga ta jefa ƙafa a tsakar gidan na su. Baffa na da ya gansu ne a hanya ya bisu da ido yana murmushi kafin yayi gaba. " Wallahi ba zan yarda ba ". Sai kuma ta fashe da kuka tana ƙaƙalo hawaye. Inna ni da ta fito daga ɗakin ta yanzu ne ta saki baki tana kallon su Ita Shatou na cigaba da ƙaƙalo hawaye da kukan da ke nuna tsantsar sakarci. Da mamaki ganin alamar yanzu suka shigo hakan. Inna ni ce " Wai lafiya kuka shigo muna gida haka babu ko sallama ''? " Wai daga kawai nace muyi gasa shine muka yi na riga ta saka ƙafa anan, shine take kuka wai ba zata yarda ba " Cewar Bibu yana cigaba da yin dariyar sa. Salallami Inna ni ta hau kafin ta ce " na shiga uku ni Indo yanzu wannan ne abun kuka Shatou ke da kullum ba kya girma dan uban ki ƙanen ki ma ya fi hankali wani sa'in ". " Daga yau ma kaine wa na karɓe daga gare ta,idan tayi laifi ka zane ta a matsayin ka na babba ". Tunda Inna ni ta fara zancen yake wasar baki yana dariya. Ita ma Inna ni dariyar take yi ƙasa ƙasa ganin yadda hakimar ta haɗe rai kamar an mata mutuwa ga hawaye sun wanke fuskar ta ta a wannan karon Dagaske. Tsalle Bibu ya daka yana murnar sa ita ko shatou kamar ance mata Inna ni ce ta mutu ko Baffa na ko shi Bibu da su Amina ta cigaba da sakin kukan ta mai ƙara. " Amma dai anyi ƙatuwar banza SHATOU " Inna ni ta ƙara furta wa. Matsawa ta yi kusa da SHATOU ɗin tana dariya sai kuma ta juya ta shiga madafar su sai gata ta fito da maburkaki a hannun ta, fuskar ta haɗe dan ta lura lamarin na Shatou sai a hankali. Aiko Shatou na hango ta,ta miƙe tana shigewa ɗakin ta tana waigen Inna ni. Dariya Bibu yayi kamar zai kai ƙasa kafin ya yi alwallah ya fice masallaci yayi Sallah. Inna ni ma kan ta,ta girgiza tana sakin guntun murmushi tana furtawa a ranta kura ga tsoro ga ban tsoro. A ɓangaren Baffa na kuwa koda ya isa fadar mai gari gaisawa kawai yayi da mai gari da sauran jama'ar fadar yayi gaba,Mai gari da ya fahimci dalilin zuwan sa ya wuce ɗin bai ce masa komai ba sai sakin murmushi da ya ɗan yi ta gefen baki kulawar Baffa na ga yar sa na burge sa. A ɓangaren shatou kuwa tunda ta shige ɗakin ta,ta ke sauke ajiyar zuciya kafin ta tura baki gefe ta miƙe tuna bata yi Sallah ba.Koda ta fito tsakar gidan babu kowa dan haka tayi alwallah ta wuce ɗaki tayi sallah anan bacci ya kwashe ta bata farka ba sai gab da magriba.Cike da mafarkaii haka ta tashi tana zarar idanu addu'oi tayi tayi a zuciyar ta kafin ta samu su fito fili har ta buɗe idanun ta tar akan Inna ni dake kan ta wadda itace ta tada ita daga baccin na ta ganin shiru har su Baffa na sun yi masallaci bata fito ba shine ta zo duba lafiya ta same ta tana bacci dan ta yi zaton ma a ɗazu ta fice gidan su Amina ko Jawairiyya sai Bibu yace mata ai tana nan ya dubo ta lokacin da Baffa na yake zancen ina take kafin ya sake ficewa,dan haka ta fita iskan ta dan ta san ƙila wani abun ya ɗauke mata hankali kamar aikin aji da sauran su dan baya ma yi zaton bacci take yi ba. Inna ni zuba mata idanu tayi ganin tana zare ido alamar har yanzu tsoron abinda ta gani a mafarkin bai sake ta ba dan ta fahimci mafarki tayi dan haka tayi ta tofa mata addu'a, itama da ta fahimci ta farka daga mugun mafarkin ta fara addu'oi Inna ni na taya ta a hankali kuwa ta fara sauke dogon numfashi tana ya mutsar fuska cike da son tuna yanayin mafarkin na ta sai dai duk yadda take son tunawa ta kasa dan haka ta kalli Inna ni da idanun ta da ke cike da hawaye da suka taru lokaci ɗaya dan zata iya tuna mafarkin ba mai kyau bane duk abun da ta gani a cikin sa akwai tashin hankali a cikin sa mai girma. " Mafarkin me kika yi haka Shatou " ??? Inna ni ta faɗa tana zuba ma yar Tata idanu cike da wani irin rauni da ya dabaibaiye ta ganin hawayen yar ta wanda suke tabbatar da cewa har zuci lamarin babba ne na abunda zai karya mata zuciya haka a game da mafarki wanda kuma kowa ya san kaso goma kashi uku duka ƙarya ne mafarki. Kuka ta ta fashe ma Inna ni dashi rarrashin ta Inna ni ta dinga yi kafin ta samu ta lafa ta yi shiru. Cike da wani irin ɗan tsoro tace " Mafarkin na kasa tunawa fa shine nake ta son na tuna amma na kasa Inna ni kuma fa abun da na gani ba mai kyau bane,Harda kuka nayi a mafarkin " Sai kuma ta fashe da kuka " Ya isa barshi kawai kinji duk ranar da kika tuna sai ki sanar mini yanzu dai ki dage da addu'a ƙila da zaki kwanta baki yi addu'a bane ba ko ? " Kai shatou ta gyaɗa mata. Ɗan murmushi Inna ni ta ƙaƙalo kafin tace " Yawwa yanzu anyi Sallah tashi kinji ". Miƙe tayi da taimakon Inna ni suka fice daga ɗakin. Ruwan Alwallah ta zuba mata sannan ta miƙa mata ita kuma ta shige nata ɗaki kafin ta fito da littafin azkar ɗin ta dan kwana biyu ba su zauna zaman karatun azkar ɗin ba. Tabar mar dake shinfiɗe ta gyara mata abun Sallah kafin ita ma ta kabbara Tata Sallahn akan abun Sallahn da ta shimfiɗa ma kan ta,hijabi shatou ta ɗauko ɗakin ta itama mai ɗan girma ta tada Sallah a natse , abun mamaki yau Inna ni ta riga Shatou gama sallah. Inna ni dai ikon Allah take ta kallo da wani shakku akan yanayin shatou da mamakin wannan wane irin mafarki ne ya lallasa jikin Shatou haka komai babu kuzari take yin sa. Tun Inna ni na mamaki ta daina dan shatou bata gama Sallahn ba sai da a ka kusa kiran Sallahn Isha shima tana gama magriba ɗin ta hau yin Ba,adil magrib.Inna ni dai ga mamaki ga kuma wani irin karye wa da zuciyar ta ke yi na yanayin yar ta ɗin. Ƙarshe sai dai ta girgiza kai tana sakin murmushi tana tuna wani lokaci da ya shuɗe lokacin da tana amarya ta dinga rafka sallah tana amarya bayan ango ya tafi Rakiyar abokai har ya dawo ya same ta haka,sai yanayin ya dawo mata da komai sabo ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi zuciyar ta na fara wani irin rawa kamar ana daka sakwara ga wani irin ɗaci da ya maƙare zuciyar ta da ruhi wani duhu da ta fara gani na damuwa ne da baƙin ciki hakan ya sa ta fara ambaton sunan Allah da neman agaji take kuwa ya kawo mata ɗauki ya hana yanayin da zuciyar ta ke neman shiga yin tasiri a gare ta. Bayan ta samu natsuwa ne ta juyar da kallon ta kan Shatou da tayi zugum tana kallon ta ganin yadda take ta rintse ido tana dafe ƙirji. Murmushi ta ƙaƙalo dan bata son ta fahimci komai bare ta dame ta da tambaya har Baffa na ya fahimci wani abu. Aiko tambayar da ta guda itace ta ratsa dodon kunnen ta. " Inna ni me kike dafewa ƙirji da rufe ido ko bakya da lafiya "? Murmushi ta ƙara saki ganin shatou na gama furucin ta ƙara zuba mata manyan idanun ta alamar amsa take jira dan haka ta ce " Babu komai shatou gajiya ce kawai " " Irin yadda naji ranar ne kika ji ko Inna ni ai nima haka na dafe ƙirji na har kika ce mini sakarci ne kawai " Murmushin inna ni ta saki kafin ta ce " Eh fa shine ai na fahimce ki fa,ranar gajiya ce ta saka ki jin haka,Nima itace dan haka yau da wuri ma zan kwanta ". Kai shatou ta jinjina cike da gamsuwa kafin ta cigaba da addu,oin ta ita kuwa Inna ni ɗan murmusa wa tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya. Dan bata san mai zata ce mata ba dan ko ita ta ta faduwar ƙirjin a wancan ranar abun ya tsaya mata a rai ta san tabbas babban abu ne zai kawo wa yarinya ƙarama irin wannan matsalar sai kuma idan an haifi ya ro da hawan jini ko ya samu tsoro mai girma.To bare ita da ta san ainahin ta ta damuwar,da ta kasu kashi kashi wanda ta san hankalin shatou ba zai taɓa iya ɗauka ba,ba yanzu ya kamata ta fuskanci komai ba.Ƙaddarar ta wani babi ne da take ganin shafin sa ɗaya bayan ɗayan akan yar ta kuma Garkuwar ta,da ƙaddarar su take tafiya a tare da rayuwar su.Numfashi ta ƙara sauke wa tare da su jan ajiyar zuciya wanda har sai da Shatou ta waiwayo sai dai bata ce mata komai ba ta cigaba da yin addu'a tana jerawa su Inna ni Addu'oi tun rana yi a zuci har ta fito fili hakan shi ya sanya ya zuciyar Inna ni yin sanyi tare da sakin murmushi tana karɓawa da Amin.✍️ Ku GAFARCE Ni hiliss mutane kirki na san na muku laifi wallahi na shiga.Busy kwana biyu dan haka typing ya gagare ni.🙏 Jama'ar facebook ma da muka wuce sosai gashi a jiye basu samu update ba ayi haƙuri ✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 https://chat.whatsapp.com/H5xKfOMK5QE2YtMirvcsat?mode=r_t _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣1️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* ADVERTISING! ADVERISING!💃💃💃 KHADSEEN'S COLLECTION GIDAN KAYAN ADO 👜👛👝👡👠⌚👗🛍️ BABBAR YAR KASUWAR NAN TA KU TA MATA MAI SUNA KHADSEEN'S COLLECTION TA ƘARA KAWO MUKU HAJAR TA MAI KYAWON KALLO DOMIN KO BAKA SAYA BA ZAKA GAMSU DAGA KALLON SU.💃💃💃 TANA DA DUK WANI NAU' I NA KAYAN ƘAWA NA KWALLIYAR MATA DA MAZA,MASU KYAU KAMA DAGA TOTE BAGS,COMFY BAGS,DUBAI MATERIALS,LUXURY BAGS,LUXURY ABAYAS.FLAT SHOES.Da sauran su. WANI ABU SAI A KHADSEEN'S COLLECTION💃💃💃💃💃💃WO HOHO HAJIYA TA, KE DAI GARZAYA KI CIKA KAPACITYN 💃 KI A KHADSEEN'S COLLECTION Wa.me//. 8149484562 ZA,A IYA TUN TUƁAR TA TA WANNAN LAMBA DAKE SAMA👆 SAI KUMA LINK NA GROUP NA TA A SAMA 👆A CHAN ZAKU GA KAYAN KECE RAINI,KUDAI💃💃 KU GAR ZAYA KU CIKA KAPACITYN KU MANYAN MATA MASU ADO👜👛👠KHADSEEN'S COLLECTION NA AIKAWA DA KAYAN TA A KOWACE NAHIYAR DUNIYA CIKIN GAMSAR DA ABOKAN KASUWAN CI TA.🛍️🛍️🛍️ https://chat.whatsapp.com/H5xKfOMK5QE2YtMirvcsat?mode=r_t _________________ A haka su Baffa na suka same su suna karanta azkar bayan gama addu'oin kasancewar su Baffa na sun tsaya masallacin sauraren wa,azi. Kamar kullum a tare suka ci abincin daren su su uku.Suna gamawa suka fara taɓa yar fira kafin suka yi Sallama kasancewar gobe Akwai makaranta gashi yanzu shatou na zuwa latti kuma ansha mata faɗa bata denawa saboda kullum da faɗa take zuwa dan bata son karatun yanzu ko kaɗan tilasta mata kawai take jin ana yi dan haka kullum yanzu sai tayi faɗa da Inna ni Baffa na yayi ta Rarrashin kayar sa,Bibu na Dariya a haka da lallaɓawa ake samun tana tafiya,kuma ko taje a banza. A ɓangaren Baffa na tambayoyi ne bakin sa game da amsar da mai gari ya bawa shatou sai dai kuma ya share zancen kan wani dalili na sa. A haka Kowa yayi alwallah ya shige suka yi wa juna sai da safe. Dukkanin su sai da Inna ni ta tabbatar da sunyi addu'oin su kafin ta ƙara shafa musu Sannan ta shige tare da abincin ta da bata ci ba. Zaune ta kai kan wata yar tabarmar kabar ta dake shimfiɗe a ɗan tsakiyar ɗakin da yake da ɗan siminti da ya fara ciccirewa saboda rashin isasshen suminti a cikin sa. Abincin ta zubawa ido kafin ta haɗiye wani irin ɗaci A maƙoshin ta.Zuciyar ta ta mata wani irin zafi.Hawayen da take ta dannewa ne suka silalo mata kafin ta ji saukar su akan wuyan ta,hawaye ne masu ɗumi dake nuna tsantsar damuwa da baƙin cikin abin da yake tabbas a gare ta wanda ya bar ta cikin kokwanto. Kuka ne ya ƙwace mata tuno da wani lokaci da ya shuɗe na rayuwar ta,da ta yi cikin gata da soyayya.Sai da tayi mai isar ta sannan ta Share hawayen na ta.Abincin ta fara turawa A hankali tana jin shi kamar tana haɗiyer magani mai ɗaci saboda ƙunci da kewar da ke dabaibaiye da zuciyar ta mai cike da rauni da bege da kewar da bata san adadin ta ba. Sai da taci rabi sannan ta sha ruwa kafin ta yi addu'a ta nemi waje ta kwanta kan ɗan gadon ta. Wani sabon tunani ne ya ƙara kutso mata dan haka ta kai shi gefe ta rufe idanun ta tana ambaton sunayen Allah.Cikin yardan Ubangiji Kuwa Bacci mai nauyi ya kwashe ta. Baffa na ya daɗe yana Zarya a Cikin Dakin sa ya kasa bacci,dan ya so ya ji ya ta kaya tsakanin mai gari da shatou ɗin duk da ya san abu ne mai sauƙi amma lamarin na Bashi tsoro shi bai shirya kai yar shi gidan kowa ba yanzu,Sannan yana da dalilin sa mai ƙarfi akan wannan maganan,dan haka duk yadda ya so ya share ya kasa duk da abun ya san mai sauƙi ne. Numfashi ya sauke kafin shima ya koma kan gadon sa yayi addu,o I ya kwan ta cike da yar damuwa. Shatou ma babu kwane kwane bacci ya kwashe ta saboda an sha ƙiriniya sosai,haka ma ta ɓangaren Bibu dan shi dama baya wasa da bacci ko ƙanƙani ne. " Oummm !Oummm! Oummm " Wannan sauti shine ke shiga cikin Kunnuwan ta yana karya duk wasu gaɓɓan jikin ta wani irin zubawa yaran tayi idanu daga bakin bishiyar da take zaune ta jingina bayan ta da alama iska take sha,tana bin su da kallo kamar ta ga sabuwar halitta. Sai dai murmushi ta samu kan ta da sakar musu cikin mamakin kiran ta da sunan da suka yi. Tana ƙokarin riƙo hannayen su ne ta ji an fisge su da ƙarfi ana ƙoƙarin jefa su a wani rami mai zurfi cike da tashin hankali ta ke ƙoƙarin ganin mai shirin yin wannan aika aikar da hana afkuwar hakan cike da tashin hankali...A zabure ta tashi tana mai nana ta Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un fuskar ta jage jage da hawaye na tausayi ga wata irin rawa da zuciyar ta keyi kamar ana kaɗa ganga mai taushi. Mafarkin take ta, tariyo wa sai dai mamaki ne fal a ranta na wannan suna da suka kira ta da shi. Fuskokin su take ƙoƙarin hasasowa sai dai ta kasa amma duka muryoyin sun zauna a cikin ƙwaƙwalwarta wanda har yanzu sautin yake ƙara hargitsa tunanin ta tare da girgiza naman jikin ta. A jiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana shafe zufan da yake tsiyayar mata na tashin hankalin abinda ta gani yake shirin faruwa kafin ta miƙe Tayo Alwallah Nafila tayi gwargwadon iyawar ta sanann tayi Addu'oin ta ta koma bacci sai dai abun ya gagara dan bacci ya ƙi kwasar ta wanda bata samu, ya kwashe ta ba sai gangar asuba. Yau kusan wata guda kenan Iro bai ƙara tuntuɓar Shatou da wata magana ba Shatou bata san abinda mai gari ya ce masa ba amma ko mene ne taji daɗi sosai dan haka ta cigaba da rayuwar ta hankali kwance cikin rashin damuwa, haka ma Baffa na.Yayi matuƙar farin ciki.Yanzu hankalin Shatoun sa ya kwanta. Bawan Allah in suka haɗu kan hanya yayi ta kallon ta cike da mamakin abun da zai sa mahaifin sa yi masa kashedi da dakatar dashi da soyayyar sa ga shatou duk iya tunanin ya rasa madafa. Sai dai ya ƙwallafawa ran sa sai da ya samu shatou ko ta ƙarfi ne kuma zai nemi soyayyar ta ko mai gari bai so ba dan shi Dagaske yanzu,son ta yake yi har cikin ran sa,kuma idan har bai samu Shatou ba sai dai abin da ake gudu ya faru a ƙauyen,dan ba zai bar kowa ya same ta ba ya sha wannan alwashin ya fi a ƙirga. A ɓangaren shatou ƙiriniya yanzu sai abinda yayi gaba ga karatun yan zu idan an tura ta sai ta yi daji wajen farauta tun Inna ni da Baffa na na faɗa har sun zuba ma sarautar Allah ido dan ƙiriri take nuna rashin son karatun na ta yanzu Addu,a kawai suke bin ta da ita. A ɓangaren Aikin da ake yiwa ƙauyen an samu cigaba sosai aiki na ta kan kama babu kama hannun yaro abun ka ga an zube kuɗi ƙasa. " Ummahhh " ! REENA ce ta zo da kuka tana sanye cikin wando da t-shirt masu kyau gashin ta ya sha gyara kai da ka gan ta kasan suna cikin gata.Kuka take tana nunawa Ummah ɗin hanunn ta wadda ta sha ado itama cikin wata dakakkiyar shadda ta yi kyau har ta gaji. Dan yanzu ta fito da ga kitchen ta ɗan duba abubuwan da aka jera kan dinning. Hannun Ummah take kallo, ganin ta sangaye shi kamar ya samu rauni da yawa. " Me ya samu hannun ta furta a natse cike da yar damuwar kukan na REENA " " Hannu na LEENA ta karya daga kawai na taɓa nata chocolates na tsarabar Yaya Samir ita bata shanye nata ba shine na ɗauka zan sha ko fasawa ban yi ba ta murɗe mini hannu tana kira mini ɓarauniya ".Ta kai ƙarshen maganar tana fashewa da wani sabon kuka. Ɗan jimm Ummah tayi kafin ta sakin iska mai zafi cike da wata sabuwar damuwa yanayin alamar ɓacin rai na bayyana akan fuskar ta. Hannun ta riƙa wata ƙara LEENA ta saka tana batun sumewa Ummah wajen saboda ta taɓa dai dai wajen da yake mata ciwo. Cike da damuwa da tashin hankali Umma tayi kan ta tana rungume ta kafin ta riƙo hannun ta ɗaya mai lafiya, zauna wa da ita tayi kan kujera har lokacin tana rusar kuka. Rarrashin ta Ummah ta fara yi wadda take tunanin REENA ta samu Bone dislocation Wayar ta,ta fara ƙoƙarin dannawa domin kiran Abba sai ga REENA ta fito tana faman cin chocolate hankalin ta kwance. Fuskar nan Tata ɗaure kamar an mata mutuwa musamman yau da take jin Haushin kowa saboda dawowar ta Bilal dan har yanzu basu shiri tun maganar da suka yi akan wayar Samir ba su ƙara magana ba,bata nemi shi ba shi ma haka ya fita iskan ta,Ummah da Abba duk suna lura sai dai babu wanda ya shiga cikin faɗan sun san daya dawo gidan zata sauko dan shi sun san ayyukan gaban sa,yanzu haka ya ma manta da suna faɗa dan duk yayi waya da ɗayan su yana yawan tambayar ina LEENA da REENA Sai dai duk Suka yi waya da REENA itama takan ce ga LEENA ita kuwa da ta fahimci dashi Reena ke waya sai ta bar wajen dan dashi har Reena ɗin haushi suke bata dan cewa take yafi son Reena. Sai dai cikin Wannan ɗan lokaci abun ya ɗan yi sanyi sai dai sukan yi sati basu yi magana ba sannan kowaccen su ta na Bedroom ɗin ta sai kwanan nan ne ma aka samu dai dai to bayan Ummah ta shiga lamarin ita da Abba. Kuma hakan bai da na saba da ƙoƙarin Samir dan kafin ya wuce daga hutun na sa da ya ɗauko ganin yawan faɗan na su ya tayar masa da hankali hakan ya sa ya sanya aka yi musu sauka dan samun saukin wannan lamari wajen Ubangiji da ya jarabce su dan yanayin da suke ciki ɗin jarabawa ce Babba Yadda suke hantarrar junan su ko kashe juna suna iya yi ga dambe take hakan shi ya ɗaga hankalin Samir ba tare da ya sanar wa kowa abun da yayi ba ya aiwatar cikin yardan Ubangiji kuwa aka samu sassauci sai dai gabar haka kawai da suke yin ta babu dalili LEENA zata ɗaurewa Reena, yar uwar ta tayi ta bibiyar ta jin meta mata,ita kuwa bata faɗi sai ta share ta dan babu dalili,sai wata rana da Reena ta matsa kai tsaye LEENA ta ce mata ta tsane ta duk da ƙarancin shekaru irin na REENA ta ji zafin kalamin sai dai bata faɗawa kowa ba amma ya zauna ranta duk da ta san cewa yar uwar ta ta faɗa ne kawai bada wata manufa ba,kuma ba tana nufin abun da ta ce bane a gare ta.Kuma tun daga lokacin itama Reena sai ta fita iskan ta dan haka kawai ta ji ita kan ta bata buƙatar magana ko da Leena ɗin ne bare zama inuwa ɗaya dan haka kowaccen su ta koma ɗakin ta dake sama. "Ina tunanin SARINA ta samu Gocewar ƙashi Abban su,gashi sai kuka take yi" REENA da jin haka kuwa ta ƙara fashewa da kuka dan sun taɓa Rakiyar Hamrah da ta goce aka yi mata gyara sai da ta yi fitsari a wando saboda a zabar da taji su kan su sai da suka koka duk rashin jituwar Leena da Hamrah ɗin sai da tayi mata kuka bare ma ita Reena uwayen kuka. Yanke wayar ta yi cike da damuwa kafin ta ƙwalawa Rabi kira wadda ke kitchen suna aiki. Da sauri rabi ta zo. Sai da ta gama sauraren Maganar Ummah kafin ta ce " Subhanallah Alinatu baki kyauta ba samm ji bi yadda yar uwar ki ke kuka ". Tana jin abinda Rabi ke faɗa amma bata ko kalli sashen da take ba sai ma cigaba da cin chocolate ɗin ta,tayi tana turo baki gaba wanda ke nuna tana jin ta sarai. Ummah ce ta katsa mata tsawa hakan ya sa ta ɗan zabura dan ta fahimci iskancin LEENA gaba yake yi. Sai kuma ko me ta tuna sai ta sassauta murya cike da Rarrashi ganin yadda LEENA tayi Narai Narai da idanu alamar kuka zata yi. " Haba ALINA dubi yadda kika ji ma yar uwar ki,yanzu kenan nasihar da na ke muku a ban za,ace akan chocolate da gashi nan a ko ina an saka muku shine kika karya mini hannu Yarinya, Alina kin kyauta kuwa,Dubi yadda take kuka ita kaɗai ta san zafin da take ji dubi yadda hannu ke walƙiya har ya fara Kumburewa ". " Ummah ai Chocolate ɗin ya Samir ne kuma itama ai ya bata nata shine ta shanye nata,kuma zata shanye nawa mayyar ". Bakin ta Ummah ke ƙoƙarin kaiwa bugu Rabi ta hana dan ta ji Haushin kalmar mayyar da ta kira wa Reena ɗin. " Wato ke Bakin ki bai da saiti ALINA,kin cewa Ya ta Ɓarauniya gashi ko biro ba bata taɓa ɗaukar min ba,yanzu Idan Bilal ya dawo sai ki masa bayani ,dan a wannan karon ba zan raba ki dashi ba tun da na gane har yanzu kin kasa yin hankali ko Tausayin ta ba kya ji kin ƙara daɓa mata wannan muguwar kalmar,kuma kar naji,ko na ƙara gani kin kira wa SARINA wayen nan sunayen ko makaman tan su,ko Abban ku wannan karon bana fatan ya ɗaga Miki ƙafa sakarya " " Rabi riƙa ta ku tafi Driver ya kai ku bari na ɗauko kuɗin gyaran ". Miƙewa Ummah tayi ta haye upstairs da ɗan sauri ko kallon Sashen da Leena take tsaye bata yi ba wadda ko gizau bata yi ba hawayen ma yaƙi sauka idanun ta sun bushe babu ko alamar hawaye a idon ta ko ɗigon Tausayin Abin da ta yiwa Reena dan a cewar ita ta nema tun da ta taɓa mata abun ta. Rabi kuwa riƙa Hannun REENA tayi bayan ta karɓi kuɗin hijabin ta da ɗauko ta sanya tare da ɗaurawa LEENA gungun mayafi da Ummah ta ɗauko mata daga bedroom ɗin ta. " Baba Rabi Zanje ". LEENA Ta furta cike da ƙuruciya da rashin damuwa. Rabi saƙaƙe tayi tana kallon ta ganin ƙarfin halin ta kafin kuma ta ce " fito muje ". A zuciyar ta kuwa tana mata addu'ar shiriya daga ita har Reena da samun haɗin kan yan biyun. " Wallahi babu inda zata bi ku,ta zauna gida,gashi ma BILAL ya min saƙo ya iso lafiya,ina son ya karya da ita dan uban ta,bari ma na masa saƙon abun da tayi yana isowa yayi mini maganin ta sha sha shaar yarinya ". Rabi kuwa jin Ummah ta rantse ga ɓacin rai da ta gani kwance akan fuskar ta hakan ya sa babu musu ta fice tare da REENA ɗin. Wadda ke cigaba da rera kukan azaba. Junaid ne suka ci karo dashi zai shiga Sashen su kuma sun fito ganin yanayin da REENA ke ciki hakan ya sa ya bi su tare a gaban sa aka yi komai dan kuɗin ma shi ya biya duk da rabi ta nuna masa Ummah ta bada kuɗin. REENA ta sha kuka ƙiris ya rage ta yi fitsari a wandon ta saboda azaba. Dukkanin su sun tausaya mata matuƙa fuskar ta, take tayi jaa idanu suka yi sutu sutu gwanin ban tausayi. Junaid yayi ta tambayar Rabi matsalar ta auku.Sai dai ta yi ta masa kame kame. Hakan ya sa ya share bai ƙara tambaya ya fahimci bata son sanar masa. A ɓangaren LEENA kuwa Haushin maganar Ummah ta ji dan haka ta kwasa da gudu tana fashewa da kuka ta shige Bedroom ɗin ta ta saka lock.Sai da ta rushi kukan ta na rashin dalili kafin Bacci yayi a won gaba da ita.Dan haka koda BILAL ya dawo bata sani ba. Ita kuwa Ummah cigaba da ayyukan su suka yi tare da sauran masu aikin da ke ta kai kawo suna haɗa duk wani abu na buƙata kasancewar BILAL da Ummah ta sanar musu ya iso ya kafin ya shigo tana son komai ya zama ready. Koda Su Rabi suka dawo sun tarar da motocin su B ɗin ga kuma yawan sojojin da aka samu a estate ɗin. A kafaɗa Junaid ya ɗaura REENA dan tayi baccin a zaba sauƙin ta ma sun bi ya wani Babban Pharmacy an siya mata pain relieve anan kuma ya saka ta dole ta sha sannan suka yo gida tare da yar siyayyar chocolate da yayo mata. Da sallama ya shiga a Babban Falon Na Umma. Sauke ta yayi akan doguwar kujerar da Bilal yake zaune a gefe ya gyara mata kwanciya tare da ɗaura hannun inda ya dace da ya sha ɗauri sai walƙiya yake yi an shafa masa magani. Sannan ya ajiye magungunan a kusa da ita,tare da ledar chocolates ɗin. Cikin ɗan kamewa B da ya kasa haƙuri ya kalli Junaid dake gayar dashi cike da girmamawa da yi masa sannu da zuwa ya furta. "Me ya same ta ne naga an ƙudundune hannun haka,kamar wanda ya samu dislocation"?. Cike da girmama Junaid yace masa eh shine sai dai shima bai san inda ta samu raunin ba dan Baba Rabi ta kasa faɗa masa. Tunda ya ji cewa Rabi ta ƙi faɗa ya san inda matsalar ta afku sai dai cikin mamaki yake ƙara kallon REENA da fuskar ta tayi jaa idanun ta sun kumbura wnada da gani na azabar da ta sha ne. Ya ce " OHk " Sai a Sannan ya karɓa gaisuwar Junaid da ya ƙara maimaita masa dan ya san ya'yan nasu baya ɗaukar wasa. Cike da kulawa yake amsa masa da masa tambayoyi yana bashi amsa cikin basa girman sa. Dai dai nan Ummah ta fito Gaisawa suka yi da Junaid ɗin kafin ya fice dan ya samu kiran Abba ƙarami da alama aikar sa zai yi ko abinci za,a kai masa office,dan haka suke yi dukkanin su daga shi Har Abba idan aiki yayi musu yawa sai a dafa akai musu ba sai sun ci na cafteria"n ma'aikatar ta su ba ko na restaurant.Duka wannan sabon Matayen su ne,Ummah da Hajiya dan sun fi sauran kulawa duka a gurin mazajen su duk da suma sauran nayi amma na su na dabanne.. Ficewa yayi yana musu Sallama tare da ƙara yiwa Reena Addu'ar samun lafiya. Ummah da ta ga Bilal dan bata san har ya dawo ba ta zata idan yayi fresh up ɗin tunda ya cika tun bin sa ya ɗan kwanta ya ɗan huta sai ta gan shi zaune fuskar nan cike da masifa da ko bata tsaya bincike ba ta san ya gane inda matsalar take,dama tun wajen cin abinci yake ta tambayar Inda suke Ummah tace Leena bacci take yi Sarina kuwa sun fita da rabi sai bata faɗa masa ba,dan haka ya kasa yin Bacci ya zo ya ga ƙannnen na sa da yake jin ya shekara bai saka su a idanun sa ba yayi kewar su. Dan haka yanzu bata ce komai ba sai ɗaukar Reena ta yi ta haye sama da ita ta kwantar akan bed ɗin ta.kan ta,ta sha fa kafin ta tofa mata Addua sannan ta rufa mata blanket mai taushi ta fito tana sayo mata bedroom ɗin. Rabi ce tsaye tana masa sannu da dawowa cikin girmamawa haka ya amsa mata shima yana sauke kan sa kafin ya ce '' Me ye silar gocewar SARINA ". Rabi ta fahimci bada wasa ba jin yadda ya kira Sarina ɗin dan bata cika jin ya kira su da cikakken sunan su ba. Cikin ɗan damuwa ta ce '' Ba wani abu bane ba fa Alhaji ƙarami dama chan wajen wasar sune da yar uwa .." .. Shiru Rabi tayi ganin kallon da ya sauke mata. Hakan ya sa ta yi shiru ta kasa ƙarasa zancen. Shima komawa ya jingina da kujerar yana sauke numfashi da ajiyar zuciya wani irin damuwa na dabaibaye shi ya rasa wace irin Masifa ce wannan ke bibiyar rayuwar ƙannen sa shi har ya fara zargin lamarin na su. Rabi kuwa kuɗin da ta zo kawo ma Ummah ne na aikin da Junaid ɗin ya biya ta koma kitchen da sauri dan ta ga zuciyar sa ta motsa idanun sa har sun garwaya sun rikiɗa. Yadda jijiyoyin kan sa suke harbawa hakan ya ƙara tabbatar wa Ummah da ta ke ƙare masa kallo tun saukowar ta. Ta san cewa ya tabbatar da aikin na Leena ne Ita ma ajiyar zuciya ta sauke cike da damuwa. Kafin ta zauna kusa da shi cike da so ta kamo hannun sa ɗaya da ya dafe goshin sa dashi da yake ɗan sara masa. " Soja " Ta kira a hankali Muryan ta ƙasa ƙasa. " Kai kake ƙarfafa mini kai da Abban ku,kune na farko wajen ƙarfafa mini akan yara na,me ya sa yanzu zaka bayyanar da taka Damuwar da zata iya linka mini ɗimbin Damuwar da nake ciki,ya ra na suna cikin wata irin jarabawa mai tsani, ban taɓa sanin yan biyu na tsanar junan su ba sai akan na wa,ban taɓa sanin suna cutar da Junan su irin haka ba sai akan nawa shin me ya sa,me ya sa BILAL, Wannan wace irin jarabawa ce ".?? Kuka ne ya ci ƙarfin ta cike da wani irin ɗaci ya rungume ta ya fara rarrashin ta. " Me kake tunanin mutane zasu faɗa akaina akan tarbiyyan su,ina jin tsoro Mai girma akan rayuwar da suke yi mai ban al'aja.." Kuka ne ya ci ƙarfin ta a karo na biyu Shi kan sa BILAL hawayen ya share masu ɗan ɗumi. Ya cigaba da rarrashin Mahaifiyar sa Abar son sa yana haɗiye wani irin dutse mai ƙarfi na baƙin ciki mai girma da ya tsaya masa a maƙoshi.. Shiru falon yayi sai Shesshekar kukan Ummah gwanin ban tausayi. Abba ne da ya shigo tun ɗazu yayi gyaran murya.Shima idanun sa sun kaɗa sun yi jazir wani irin yanayi yake jin zuciyar sa ciki wanda ya daɗe da shuɗe masa wanda yake haɗe da damuwar ya yan sa da yanayin da suke ciki da har yanzu ya kasa natsuwa da zantukan malam Hambali sannan yana tsoron kuskure masa kasancewar ya san Malam babban Malami ne masanin Addini ya san ba zai mishi ƙarya ba duk inda zai je dai maganar ɗaya ce ko kuma ya samu aka sin ta makaman ciyar ta amma har yanzu abunda malam yayi yana ransa na rarraba shafa ruwan addu'ar a tsakanin su Leena,yana jin tabbas akwai abinda malam yake ɓoye masa.✍️ Nifa kaina cigaba da yake da ƙullewa🚶🥺 Amma dai muje zuwa zamu🚴🚴 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣2️⃣➖3️⃣3️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* Ba tare da ya ce komai ba ya haye upstairs jiki a saɓule daga ganin yadda yake tafiya sun san yanayin da zuciyar sa ke ciki kai Ummah ta ɗauke daga kallon sa tana sauke a jiyar zuciya kafin ta miƙe ta bi bayan sa. Guntun murmushi ta sakar wa Bilal kafin ta bar wajen bayan ta ɗan bubbuga kafaɗar sa. Numfashi ya sauke mai zafi tare da ajiyar zuciya kafin ya miƙe ya bar Sashen gaba ɗaya domin wani irin sarawa kan sa ke masa. Sashen sa ya shige dake iri ɗaya da sauran ginukan. Zaune ya kai kan Corner seater da ke kusa da ƙofa yana sauke numfashi. Ganin damuwa na neman dabaibaiye shi hakan ya sa ya miƙe ya shige Bedroom ɗin sa da babu wata hayaniya a cikin sa so simple sai ƙyalli yake Saboda ana gyaran sa duk bayan ɗan lokaci. Hayewa yayi kan gadon na sa bayan ya zare rigar sa Gudun Ac ya ƙara ta hanyar remote ɗin sa kafin ya rufa tafkeken blanket mai taushi dake ƙawace da bed ɗin. Addu'a yayi ya tofa kafin a hankali bacci ya fara fisgar shi,sai ya fara bacccin ya farka kuma a firgice kamar mai jin tsoro da alama akwai shuɗaɗɗen lokacin da yake tunowa ko yake gani a idon sa a wannan ɗan baccin dake fisgar sa.Addu,oi ya cigaba da yi,Har kuma a hankali bacccin ya ɗauke sa mai nauyi dan tafiyar safe ce yayo. " Na daina damuwa fa Abban su Alina,Kawai dai ina cikin wata irin damuwa ce akan yanayin su Twins,Zuciya ta na shiga ƙunci a duk lokacin da na gan su haka,Abubuwa da dama nake tunawa, abu mafi muni ace naka sa tarbiyyantar da ya ya na " Hawaye ne suka silalo mata masu zafi kafin ta kalli fuskar Abba da ta yi jaaa Shima idanun sa kamar sun tara ruwa. " Ƙarfin gwiwar da kike bani itace nake kai Bary,da Badan yadda kike ƙarfafa mini ba da bana tunanin zan kai wannan lokaci bary me ya sa ƙaddara ta mana haka,wace irin jarabawa ce yaya na suke kai ".Shiru yayi,Ɗumin da ya ji a gefen idon sa ya shafo hawaye dai ne masu ɗumi ɗan murmushi ya yi yana haɗiye sauran kafin ya shafe ma Ummah na ta da suke cigaba da kwaranya. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi wadda har shi kan sa sai da ya ji ta dan haka ya zuba mata idanu. Sanin ma'anar ajiyar zuciyar ta ta da tayi ne,dan haka a hankali ya furta " ina ƙara baki haƙuri Bary ki cigaba da haƙuri komai zai wuce jarabawar mu ce hakan ina iyakar ƙoƙari na gurin nema mana sauƙi wajen Ubangiji abinda yake damuna ya yaye muna baki ɗaya ". " Kuma in sha ALLAH Allah zai yaye muna zai dubi zukatan mu masu kyau ". " Komai zai zama tarihi ki cigaba da haƙuri Sannan ba zan gaji da neman gafarar ki ba." Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi bayan jin ta akan ƙirjin Abba wanda yake sauke numfashi a jejjere kamar wanda yayi tsere dan a duk lokacin da ya samu kusanci da Ummah haka ya kan ji sauyin yanayi a jikin sa sai dai yana iya ƙoƙarin sa na dannewa. Sun jima a haka kafin ya sake ta yana rintse idanun sa. Miƙewa yayi ya shige toilet ruwa ya sakar ma jikin sa kafin ya zare kayan jikin sa ya ɗauro wanka. Ummah kuwa idanun ta ta rufe tana jin gina da gadon tare da sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ta buɗe idanun ta ta zuba ma ƙofar toilet ɗin idanu. Ɗan murmushi ta saki a hankali kafin ta share wani hawayen da ya silalo mata. Sannan ta fice daga ɗakin tana shigewa nata. Kayan jikin ta ta cire itama kafin ta shige toilet wanka. *Tsut haka ta bayyana gaban sa kamar yadda ta saba zuwa wajen sa a koda yaushe cikin shigar ta da ta saba. Hahahhahhha Dariyar shi ta karaɗe ilahirin dajin. Wadda take fita iri daban daban. " Ta Baiwa yar Baiwa Uwar Mugaye yau da wace aka zo,ki faɗa da bakin ki aiki ya fi ci haka ". Gyaran zaman ta tayi kafin ta gyaran zaman mayafin abayar ta cikin wata murya dake nuna damuwa ta fara magana " Hankali na ya kasa kwantawa ne Dan Baiwa,Har yanzu gani nake kamar babu abun da zai ci da kyau game da aikin mu duk da akwai wasu alamomi da suke bayyane,Sannan Duhun nan da ka yi magana akan sa ya kamata na san me ne ainahin abunda ke cikin sa,haka kawai nake jin kamar akwai matsala ". Dariya ya fara gaggaɓa yana kallon ta idanun sa na wani irin fitar da hucin zafi na kalmomin ta da take fitarwa kamar bata yi imani da shi ba kamar yadda ta faɗa baya.Dan haka cike da wani irin haushi ya ce " Ta Baiwa kin halaka,kin halaka ". "Mun halaka Ɗan Baiwa,ka wuce gado,ba gaba da gaba ko ta baya sai an shirya,Sarkin mugaye uban su ɗan duhu da duna ". Ta yi Zancen itama hankalin ta kwance dan ta san zai sauko saboda ɓacin ran da ya shiga yanzu. Laƙwass Haka Ƙaton bokan nan yayi kafin ya kece da Dariya har sai dai ya kai ƙasa yana mulmulawa jikin nan na sa kamar tsohuwar ƙwarangwal.Abun dariya abun haushi. Sai da ya gama sannan ya miƙe ya ce " kwantar da hankalin ki Lallai sai na bincike wannan abun da ke cikin duhun nan,Bana son ki koma damuwa akan sa,maganar hankalin ki tashe yake ki ƙara imani zai kwanta Ta Baiwa,aikin mu yana nan yana tafiya dai dai kedai ki cigaba da zuba ido ki gani zaki ga kammaluwar sa dai dai lokacin da ya kama ta " . Kai ta gyaɗa masa kafin ta kece da dariya kamar zararrriya ta furta "Lallai nayi imani da kai Ɗan Baiwa na san zaka cika mini buri na,Ka ƙara mini maganin masu mini kutse na fara hango cigaba ". " Hhhhh Ta Baiwa ta Ɗan Baiwa Mai ja dake sai ya shirya,Son zuciyar ki na burge Ni,Rashin imanin ki shine ya ƙara wa su ɗan duhu ƙarfin Miki aiki lallai kin ci lambar yabo nan gaba kaɗan za,a Miki naɗin Uwa ta su ɗan duhu aiki ɓagass,ki saka ki hana ". Wal iyazubillah😭😭 Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un 😭 Masu halin ta baiwa fa suna da yawa wallahi suna nan atsakankanin wannan duniya suna aikata ɓarna son ran su.Ba tare da tunanin yau da goben su yadda zata kasance ba,ba tare da tunanin hukuncin da Ubangiji ya tanadar ma masu aikata shirka ba,Lallai Allah mai jin ƙaine ga bayin sa.Haƙurin da ubangijin mu yake yi damu wani bawan sa ba zai iya yin sa ba.Mukan yi laifi mai muni,mu yi mu maimaita mu nemi gafarar sa ya yafe muna,Lallai ubangiji Mai Rahama ne,Dan haka masu zuwa wajen bokaye ko malaman tsibbo ku ji tsoron Allah ku tuba ku nemi gafarar Ubangiji. Allah mai yafiya ne da jinƙai ga bayin sa. Allah ka yi mana shiriya ka hana muna zuwa wajen da zamu haɗa Allah da wanin sa.Da duk wani wajen saɓon Allah,Allah ka bamu ikon tsarkake zukatan mu.Amin. Dariya ta kece da ita tana gyara mayafin ta kafin kuma ta ce " Na tafi ɗan Baiwa sai wata haɗuwar ". Ta ɓace ɓatt anan wajen. Shima kamin ƙayfatawar ido babu alamar zaman sa wajen dan itace ta fito da shi dama. Allah ka yafe mana zunubban mu.😭🙏 A yau ne ake ta shirye shiryen zuwa da MA'ISHA waje kamar yadda suka gama shirye shiryen su dan Daga Suhail za,a je sai Suhaila da kuma Nurse Mira Duk wani shirye shiryen su an gama sa.Su Dady da Amoh sun Bisu da Addu'ar samun nasara cike da kewar ya'yan na su musamman MA'ISHA da tausayin ta ya gama mamaye zukatan su.Abba Saboda ayyukan office da suka masa yawa Suhail yace ba sai ya je ba shi kaɗai ma ya isa ita Amoh ba,a maganar ta saboda ciwon ƙafafu da take fama dashi. Jirgin su ya tashi daga babban filin tashi da saukar jirage na Abuja. In da bai yi tsinke a ko ina ba sai a Canada. Sun sauka a wata asibiti mai suna British Family Hospital Canada Kasancewar asibitin sun san da zuwan su an riga anyi follow up aka tarbe su cikin karrama wa. Da zuwan su aka karɓi Ishaa dake ta bacci na Allurar Baccin da aka yi mata kafin barowar su Nigeria dan har aka shirya ta bata san ana yi ba. An mata gwaje gwaje aranar sai dai kamar koda yaushe bayanin irin ɗaya ne da sauran asibiton ke nuna wa dan basu ga komai ba duk da sun yi mamaki saboda ƙwararru ne ke kula da ita asibitin ma gaba ɗaya dan shi kan sa Suhail ba baya ba amma yana son wasu su ƙara bincika masa,ko za,a dace su san inda matsalar take.Dan haka suka bawa Suhail haƙuri tare da masa alfarmar zasu mata wannan checkup ɗin na wata ɗaya a gani ko za,a dace. Cikin Tausayin ta ya amince ganin lokaci ne mai tsawo ya sa yace Nurse Mira ta koma gida aka bar Suhaila kasancewar akwai ƙwararrun likitotan Jinya dan haka Mira ta koma gida ta cigaba da aikin ta kafin dawowar su da suke fatan kafin lokacin an gano matsalar. Amoh da ke zaune lokacin da Suhail yake yiwa Dady bayani a waya saboda handsfree take, wani irin hawaye ne suka silalo mata ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta isa wajen yarinyar ta amma ina. Kuka ne ya ci ƙarfin ta haka Dady ƙarfin hali yayi dan lamarin Ishaa ya fara bashi mamaki matuƙa mamakin ma na ra sa abun yi amma duk da haka addu,a yake cigaba da bin ta da ita cikin zuciyar sa yana share ma Amoh hawaye da girgiza mata kai wadda kuka ya ɓalle mata. Wanda da ƙyar ya samu ta natsu bayan ya bata baki wanda shima kan sa ƙarfin halin ne kawai yake yi. A haka suka share wata ɗaya A Canada sai dai tsit kake ji babu wani bayani ƙarshe ma Dr Barack da yake abokin sa shi ya kira Suhail gefe ya bashi haƙuri dan sauran sun kasa tun kararr sa. Cikin lafiyayyen turancin ya sanar masa " I'm sorry gaskiya ba zan ɓoye maka ba Dr.Suhail yarinyar nan ƙwaƙwalwar ta lafiya lau yake bata da matsalar komai,Ku cigaba da yi mata addu'a kuna kainta church,or mosques ana mata addu'a dan bamu ga komai ba ". Shiru yayi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya bayan gama sauraren sa.Dan haka godiya kawai yayi masa tare da amsa addu'ar samun lafiya da yake ta yi mata acikin harshen turanci tare da ambatar Jesus kamar yadda bakin su ya saba. Koda ya isa ɗakin ta da take jin ya wanda itada Suhaila kawai ke cikin sa komai akwai shine kawai yake cikin otel ɗin da ke cikin Asibitin mai Shegen tsada da kyau dan saboda mafi yawan mutane suna zuwa hospital ɗin neman lafiya saboda ƙwarewar su. Kwance ya tarar da ita kamar koda yaushe dan bai fi sau Biyar ba ne yake samun ta ido biyu saboda yanayin ta da yake son hutu hakan ya sa likitotan suke bata Alluran barci wadda bata cutarwa dan haka ta ƙara samun Hutu tayi wani irin kyau fatar ta sai sheƙi take yi dan ko abinci suna bata shi a cikin drip abun da zai hana ta saurin jin yunwa da ciko mata cikin ta kafin ta farka ta saka wani abu a cikin ta,kuma gwargwado idan ta farka tana shan madara da fruit ɗin suma da ƙyar kafin a gama ta ɓata jikin ta gaba ɗaya dan zuwan su Canada ma ta rage duk wani haukar irin ɓatattar nan so ɗaya ta yi ta wan sahaken da suka zo ta farka cikin na'urar da ke Binciken ƙwaƙwalwa gashi ko ina tar take ta hargitse musu kasancewa su ƙwararru cikin yan daƙiƙu suka mayar da ita yanayin natsuwa dan haka ta koma sai yadda suka yi da ita idanun ta ƙwar akan su ga hasken da take ji har tsakiyar kwanyar ta,ga abubuwan da take gani a cikin hasken kamar an ƙara musu yawa dan haka hawaye suka yi ta silalar mata a gefen ido koda aka dawo wa Suhaila da ita kuka ta zauna ta darza tana kallon Ishaa a wannan yanayi gashi da haske amma ta kasa ko motsi sai hawaye da take yi ta kafe Suhaila da ido. A bu ɗaya ne matsalar hasken nan da bata so likitota suka matsa da kullum Abar hasken ɗakin kunne.A hakan har ta fara rashin damuwa da shi sannan duk wata rigima ta rage ta, zata yi shiru dai ta zuba ma waje ɗaya ido kafin kaga kuma ta ɗauke kallon ta wajen,Sai kuma hawaye,chan sai kaga tayi dariya ko surutai mara sa kan gado kamar wani yare daban wanda Suhaila bata taɓa sanin akwai shi duniya ba.Kuma yanayin ta hakan yana sanya su Farin ciki ganin kamar wata nasara ce ko wannan maganar tata da take yi cikin Muryan ta ƙarama.Wannan kenan. Idanun sa ya rintse da ƙarfi yana buɗewa kafin ya ja ajiyar zuciya yana barin ɗakin bayan ya sanar da Suhaila su shirya yau zasu bar ƙasar da dare. Kai kawai Suhaila ta gyaɗa masa tana haɗiye wani sabon kukan da ya ta so mata bayan wanda ta gama yanzu,dan ta san tun da bai ce mata komai ba babu wata nasara. Sai da ta darji kuka sannan ta haɗa musu komai na su dama a haɗe komai yake. Da taimakon Nurse suka chanza mata kayan jikin ta daga rigar asibitin... Ƙarfe takwas dai dai na dare suka hawo jirgi sai Nigeria kafin suka sauka ƙarfe bakwai na safe.Driver ne yaje kwaso su tare Amoh har da Dady da Rayyan a mota ɗaya. Su ne suka fara fitowa fitowa tare da ma'aikatan jirgin guda biyu da suka tuƙo gadon da Ishaa take kai. Hawaye ne suka Silalo ma Dady na tausayin Ishaaa, A hankali ya shafe kar amoh ta gani,ita kan Amoh ba,a ma maganar ta.Dan kuka ne ya ƙwace mata ji take kamar ta dawo da yanayin Ishaa akan ta. Driver motar da Rayyan yake ciki ya buɗe wa Suhail ya sanya Ishaa ciki a baya sannan shi ya shige gaban motar. Ita kuwa Suhaila Gaban motar su Dady ta shiga da driver ya tuƙo su. Duk yadda Amoh ke son cigaba da daurewa kamar yadda Suhail ya rarrrashe ta, ta kasa haƙuri dan ko yanzu suhaila baki take ta bata kamar ta yi kuka, ita ganin ta yi kamar ma Ishaa ɗin ta bata numfashi, Badan Suhail ya sanar mata da ran ta bazata yarda ba,ga kuma suhaila da take ta bata ƙwarin guiwa, baiwar Allah hankalin ta duk ya tashi lokaci ɗaya. Dukkanin su sai suka matsu su isa gida dan bai sanar musu da komai ba kuma ya gargaɗi Suhaila ɗin dan haka take ta kame kame ta ƙi yin magana. Dan haka yana cewa zasu dawo gobe hankalin su ya koma ga jin yadda lafiyar ta ta take sai dai ya datse kiran tare da kashe wayar sa hakan shi ya hana musu sanin komai har Rayyan dan Ya san halin sa da zuciya kamar ta mata zai iya tsorata ya furta wata magana kusa da Amoh ya tayar mata da ciwo duk da ko yanzu fama take yi da kan ta. Hankalin Amoh ya kwanta sosai jin cewa an gano matsalar har an bada maganin ta tare da zuwa duba ta duk bayan wasu yan lokutta.Kasancewar Dady ya gargaɗe sa kar ya sanar mata bayan saukar su gama breakfast ɗin su sai ya keɓe da Dady ya fara sanar masa dan haka ya gargaɗe sa dan dama shima ko kwonton faɗa mata yake yi. Dukkanin su kallon Amoh kawai suke yi dake ta farin ciki tana ta faman lailayar Isha dake ta baccin ta har yanzu.Wani sanyi ta ji labarin da Suhail ya kawo mata,itadai Suhaila murmushi kawai take yi tun da ta ji ya'yan ta ya ɓoye ta san cewa saboda Amoh ɗin ne dan haka ta ja ta ƙara tsuke bakin ta,kamar farko. MA'ISHA kwanan ta ɗaya kafin ta farfaɗo,Yanayin ta na shiru shiru ya dawo ta yi sati haka,kafin suka tashi da wani sabon tashin hankalin da suka shiga domin kuwa yanayin da take ciki ya dawo sabo na haukar ta da har yafi na da domin kuwa kayan jikin ta yanzu babu wanda yake kalluwa duk ta musu fata fata ta yaga kamar yankan reza kuma duk wanda ya matsa wajen ta sai ta masa illa.Amoh harda kwanciya asibiti duk da yadda aka kwantar mata da hankali da cewar likitotan ta sunce dole zata yi hakan kafin komai ya fara yin ƙasa.Dan haka suka samu ta ɗan kwantar da hankalin ta. Yanzu har ta kai Ishaa Ɗaure ta ake yi saboda yadda take azabtar da kan ta.Cikin ɗan wannan lokaci wannan a hali sun shiga tashin hankali matuƙa,sai dai sun duƙufa wajen faɗawa Ubangiji ba dare ba rana,sun san shi ya ɗaura mata wannan lalurar shi ya jarabce ta da ita kuma shi zai yaye mata.. Zaune yake gaban wani haɗaɗɗen Glass mai kama da bango guda,wanda ke ta walƙiya yana haska yanayin da garin yake ciki.Sama ya zubawa ido yana kallon yadda Rana take ƙara haska garin Beijing,mutanen garin kowa sai harkar gaban sa yake yi wasu kan mota,mashin,Keke,wasu ƙafa.Komai cikin tsari gwanin burgewa. Idanun sa ya ɗan lumshe a hankali kafin ya buɗe su yana sauke ajiyar zuciya a hankali da numfashi a lokaci ɗaya. Wuyan vest ɗin sa da ke ta shinning fara ƙar da ita da ta haɗe da fatar sa ya gyara.Dan ita kaɗai ce jikin sa sai Short daga bakin guiwar sa bai ma kai chan ba dan haka Santala Santalan ƙafafun sa da suke ɗauke da gashi suke bayyane sai walƙiya fatar ke yi tana kashe ido. kasancewar yau yana Hutu ne zuwa gobe zasu gudanar da Presentation ɗin su dan haka yake zaune wajen yana hutawar sa. Yar sofa ɗin da yake kai mai zagaye wadda ke ɗauke da Haɗaɗɗen center table shima a kusa da ita inda take ɗauke da ruwa da glass cup mai kyau da tsada. Ƙoƙarin tsiyaya ruwan yake yi a hankali cike da natsuwar sa jin maƙoshin sa ya bushe,Sai dai katawa tayi jin basu da maraba da ruwan zafi hakan ya sa shi jan ƙaramin tsaki yana Hararar ƙofa kamar yanzu Mubarak ɗin ya ajiye masa ruwan dan ya san zai buƙace su.Duk da ya san fushi yake yi dashi amma bai hana tun da safe ya zo duba yanayin da yake ciki ba,ganin sa nan zaune ya sa hankalin sa ya ɗan kwanta dan haka bayan gaisuwa bai ce masa komai ba,ya ɗauko masa ruwa ajiye yayi gaba. Wanda har ya fita da gefen ido yake kallon sa,yana mamakin wannan fushi sai kace rayuwar sa zai ra sa.Rufe goran ruwan yayi da kyau.Miƙewa yayi ya matsa wajen wata na'ura kamar dai hot and cool sai dai ita wannan magana take yi abun ka da technologia sannan ga ta dai kamar na'urar Haɗa cupy amma ba ita bace. Ƙaramin tsaki ya ja jin yadda na'urar ta cika masa kunne shi ya sa bai cika damuwa da taɓa ta ba ya fi gane wa ya ɗauko na fridge,ciwon sa ya san bai son sanyi dan haka yake takatsantsan yake kamantawa yana shan masu ɗan ɗumin sanyi,amma shi Mubarak muddin zai ajiye masa ruwa basu da ɗigon ko na sanyi kamar wani mai zunubi, shi gani yake ma kamar mubeey ɗin na ɗunama ruwan. Dawowa yayi ya zauna bayan ta tsiyayo masa ruwan da ta saka shi magana,inda ya sanar mata masu sanyi. Dan haka ya sirka da wayen da Mubarak ya ajiye masa kurɓa biyu yayi ya ajiye. Wayar sa ce tayi ƙara kobai bincika ba ya san cikin biyu ko Abbu,ko Samrah,ko abokan kasuwan cin sa irin masu naci da suke matsa dole dashi suke son yin tsare tsare ba Mubarak ba.Dan haka kullum yake sauya layi saboda ya tsani takura. Abbu ne ya bayyana akan screen ɗin sa dake ɗauke da wani hoto na mace Black beauty da kamala hoton da yayi kyau har ya gaji wanda bai daɗe da samun hoton ba a cikin takardun Abbu,Tare da sunan Mahaifiyar sa a bayan sa dan haka ya adana shi sai kwanan nan ya sa aka wanko masa hoton ya ƙara yin kyau kamar yau aka ɗauke shi.. Cike da girmamawa ya yi sallama kafin Abbu ya fara jan sa da fira yana amsa masa sama sama. " Abbu bari na mayar video call "Ya faɗa a hankali kamar mai tsoron maganar. Abbu cike da farin ciki duk da ya san ba wata maganar kirki amma ganin fuskar sanyin idaniyar shi na saka shi farin ciki dan fuskar mahaifiyar shi yake gani a tattare da shi kuma ita take ɗebe masa kewa. Zuba masa idanu Abbu yayi cike da so da ƙauna kafin ya ce " Wai Ni ko kana cikin abinci kuwa MAHAJ?,Dubi yadda idanun ka suka Zurma ,me yake damun ka ".? Gaban shi ne ya faɗi jin tambayar da Abbu yayi masa dan shi kan sa yan kwana biyun nan ya san ya faɗa ko Mubeey bai samu dama bane da ya sha tambaya jiya. Ɗan murmushin gefen baki yayi kafin ya ce " Abbu Stress ne ". Ɗan shiru yayi tare da shanye idanun sa da suke ta walƙiya da maiƙon nan na su. A hankali ya ƙara furta " kuma bana samun isasshen bacci ne saboda presentation ɗin nan ". Ganin yadda Abbu ya zuba masa ido cike da damuwa. Numfashi Abbu ya sauke cikin yarda da maganar sa ya ce '' Allah ya taimaka ya bada nasara,a riƙa cin abinci yan samari har da shi na ramar mini da kai,nafi son ka yi ƙiba ka tara damtse ". Murmushi ya saki mai sanyi yana shafa ɗan wadataccen Gashin kan sa da na gaba yafi ya wa kamar dai irin na india haka ko turawa. Samrah ce ya hango ta shigo da sallama sai dai ganin MAHAJ wanze akan screen ɗin wayar Abbu mai tsada hakan ya sa ta rugo da gudu bata ma ƙarasa Sallamar ba kasancewar Abbu na sai ti ƙofar ne ya bada baya daga zaunen da yake yana karatun jarida a haɗaɗɗen falon na sa. Kai MAHAJ yake ta gyaɗa mata sai uhmm tun bayan yar tambayar ya ya take da yayi mata cike da sakewa da ƙaunar yarinyar. Fira suke ta masa ita da Abbu cike da ƙauna shi dai iyakar sa uhmm uhmm a haka suka yi Sallama ganin da Abbu yayi kamar ya gaji da Surutun Samrah sai dai shi a nasa ɓangaren bai gaji da kallon wayen nan fuskokin ba Surutun ne kawai da zasu zauna haka da ya ji daɗi yayi ta kallon su,dan haka wasu lokuttan yake a jiye wayar ko system yana jin firar tasu sama sama wata rana kuma yayi muting yayi ta Murmushi daga ƙarshe Abbu ne mai datsewa saboda ya san halin kayan sa. Miƙewa yayi gaba ɗaya ya bar wajen cike da tafiyar nan ta sa ta ƙasaita. Babban falon sa ya koma yayi zaman sa yana chan za tashar labarai.Cartoon yake kallo kamar wani ƙaramin yaro ya mai da hankalin sa kacokan kan su yadda ya mayar da hankalin su kan su ka san yana son kallon toon ɗin. A haka har lokacin Sallah yayi alwallah yayi ya fice, a masallaci suka haɗu da mubeey sai dai bai ce masa ƙala ba haka shima sannan ana gama sallah yayi gaba ya ma riga mubeey ficewa. Mubarak kuwa da yake son yi masa magana ne ganin ya fice kamar ya ɗau fushin da ya fi na sa hakan ya sa ya saki murmushi yana shafa sumar kan sa da take shan gyara itama yanayin ta sa dai irin ta matasan mu ta cikakkun Hausawa. " Ɗan Abbu rigima " Ya faɗa a fili kafin ya kalli gefen sa kamar akwai wanda zai ji ko MAHAJ ɗin na kusa.Yar dariya yayi kafin yayi gaba. Abin cin da ake kawo musu kullum wanda sun riga sun yi ordern sa irin abincin nan ne na Chinese da kuka sani dai kayan Ruwan nan,na halittun ruwa (Sea food )sai snacks sune abincin su idan ba su ra,ayin cin na China ɗin,duk da akwai Restaurant mai kyau dake kusa da su da ake kala.kalan abincin Nigeria sai ka zaɓa.Amma saboda sun saba da na China ɗin suke cin abun su.Idan sun je Nigeria su ci na gida. Ganin shi da yayi har an ajiye hakan ya sa ya ɗauki na MAHAJ wanda ya san zai iya ci yanzu ya shiga falon bayan ƙofar ta masa Surutun ta na koda yaushe na maraba musamman shi da ta san shi harda ɗan chat take gwada yi da shi saboda gulma😂,kamar dai yanzu. Haka ya ji tana furta Sir MAHAJ is watching TV toon channel. Na'urar ƙofa mai GULMA sai a KURMAN ƘADDARA 🚴🚴😂Kai fa'eeh shariii🚴 Murmushi yayi kawai ya shige ba tare da ya bata amsa ba. Shi ko MAHAJ da ke zaune bai ma ji shigowar Mubeey ɗin ba dan hankalin sa yayi nisa sosai,Baki sake Mubeey ke kallon sa kenan dai Dagaske na'urar chan ke yi shi yayi tunanin ko tsohon labari ne waton har yanzu yana kallon toon ɗin lallai da aiki gaban sa garjejen ƙato da kallon Cartoon ina lafiya,shi bai ɗauke sa normal ba kana namiji kana kallon cartoon kamar wani Baby. Ɗan gyaran murya yayi hakan ne ya farkar da MAHAJ da ya saki jiki yana enjoying kallon sa. Chanza tashar yayi zuwa ta wrestling da sauri saboda tun chan baya ya taɓa ganin sa sau ɗaya yace masa kayan yara ne fa wannan yallaɓai har ya rika masa tsokana dan haka ya dena kallon su kusa da mubeey ɗin. Mubarak kuwa shanye dariyar sa yayi kafin ya ajiye kayan kan haɗaɗɗen Centre table dake ƙawace da falon kamar dai kujerun.✍️ Jama'a Allah ya shirya muna TA BAIWA.🥺🤲 Shatou i miss You🥺Ta gida na.😍😁 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣4️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* Muryan sa mai sanyi ce ta da katar da Mubarak ɗin daga ƙoƙarin yin serving ɗin sa,bayan ajiye kayan,yana furta " I'm full may be later " Ɗan kallon sa ya yi kafin ya sauke kan sa ƙasa abun ma dariya ya bashi ganin yadda ya ƙara tsuke fuskar sa. Kai Mubarak ya jinjina kafin ya ɗauke komai daga wajen ya kai shi inda ya dace. Sannan ya fice yana girgiza kan sa da mamakin ƙiyayyar Mahaj ɗin da abinci. Shi ko yana tabbatar da Mubey ya fice ya harari bayan sa kafin ya sauya tashar yana maida ita zuwa asalin inda yake inda yafi enjoying.( Kowa da kiyon da ya karɓe sa "🤗 Anan wajen bacci ya kwashe sa kamar wani Baby. Mubarak kuwa ya zama ya ci,ya ƙoshi yana kallon wani series Chinese films da ake haskawa a iQiyi mai suna Hidden Love,Duk da yadda film ɗin ya ɗauke masa hankali saboda yadda yayi kyau amma da ya tuna da mai kallon Cartoon sai yayi murmushi da girgiza kan sa a hakan aka kira Sallahn la,asar Kafin ya fice wajen Sallah kasancewar ya san MAHAJ baya wasa da Sallah dan haka kai tsaye ya wuce masallaci ya san zai gan shi a chan. A ɓangaren Mahaj kuwa bai farka ba sai da lokacin Sallahn La,sar yayi sannan ya farka Alwallah kawai ya yi sannan ya wuce masallaci. A sahu ɗaya suka tsaya ana gama Sallah bayan gama addu,oin sa ya fito cike da natsuwa. Mubarak ma fitowa yayi chan ya hango sa dan haka ya taka da ɗan sauri dan yan zu yana son yama sa bayanin Yadda komai ya wakana a zuwan su ƙauyen su Shatou har da son kawo masa Gulmar shatou,Dan Abbu ya ce ya riƙa sanar masa da duk abinda yake wakana koda bai tambaya ba. A jere suka isa Babban falon. Zama yayi yana kallon dinning alamar sai yanzu yayi ra,ayin cin abincin dan haka Mubarak fahimtar abinda yake nufi hakan ya sa ya haɗo masa komai na buƙata ya kawo masa. Sai da ya gama shan ƙamshin sa alamar har yanzu fushin ne sannan ya fara cin abincin mai tsada wanda ko China sai masu kuɗi ne ke cin irin sa, halittun ruwa ne masu tsafta da wasu irin sinadarai yadda dai kuka san abincin su yake. Ya taɓa snacks kaɗan sannan ya ci asalin abincin na China dan ya ma fi cin sa Sosai,dan ko da safe cuppy kawai ya sha. Yunwa ta tarar masa dan haka ya ɗan tsakura babu laifi. Yana gamawa Mubarak ya kwashe komai ya mayar dashi inda yake kasancewar gidan na'urori ne ta ko ina take kayan da yayi amfani da su take ya wanke komai tare da tsaftace sa ya mayar dashi mazaunin sa sauran abincin ya saka fridge . Zama yayi kaɗan nesa da MAHAJ ɗin ya ɗan mayar da hankalin sa kan Hidden love ɗin da ya mayar yanzu dan cigaba da kallon sa. Mahaj da ya san cewa magana ce bakin Mubarak ɗin yayi dan ya karance sa take taken sa gyaran murya yayi a hankali,irin na ina jin ka. Kallon sa Mubeey yayi kafin ya saki guntun murmushi. Mahaj ya ga murmushin dan haka ya share sa. " Eh dama ina son maka magana ne akan aikin ƙauyen su yarinyar chan Shatou mutuniyar ka ". Wani irin kallon ban fahimce ka ba Mahaj yayi masa. Kan sa ya shafa ganin kamar bai gane ba saboda sunan da ya ji ya ambata,duk da kuma sarai ya san wadda yake magana yana ji a jikin sa ya fahimce sa.Rainin hankali ne kawai. Idanun sa ya ƙara zuba masa alamar ƙarin bayani. Dan haka ya furta " Yarinyar da kuka yi faɗa da ita a zuwan mu ƙauyen a wala ". Idanu Mahaj ya lumshe irin dai yadda kuka san yanayi kafin ya buɗe su tar akan Mubeey ɗan kallon sa yayi na daƙiƙa kafin ya ɗauke kallon sa kan sa yana sauke ajiyar zuciya tare da ƙara shigewa cikin kujerar kamar wani Basarake. Mubarak kuwa fahimtar cewa ya fahimce sa ne ya sa ya cigaba da magana yana sakin guntun murmushi yadda yake tuno badaƙalar su. " Aiki ya fara,komai Abbu ya saka hannu an gabatar ranar ma mutuniyar ka wani ya jogano ta ta kai shi ƙara gurin mai gari tana ta kuka ". Kalaman Mubarak yake saurare da farko ya mayar da hankalin sa kan sa sai dai jin sunan mutuniyar ka da ya maimaita masa ya kuma tabbatar da wadda yake cigaba da alaƙantawa dashi hakan ya sa ya miƙe yana Jefawa Muby wani irin kallo kafin ya ja mugun tsaki yana furta " ka daina alaƙanta ni da wanchan stubborn girl ɗin ".Yayi zancen iya kan laɓɓan sa kamar baya son Mubeey ɗin ya ji shi ko Mubarak sarai ya ji shi dan haka yayi kamar bai ji ba ya ƙara ɗaga murya yana furta " Tayi ta neman ka ". Chak ya dakata daga tafiyar da ya fara domin lamarin Mubarak ya fara shige masa hanci ya fahimci kamar ya fara wuce masa gona da iri duk da wasu lokutan haka suke saboda sabon da ke tsakanin su. " Tayi ta auna mini harara,tana ɗaga kai ganin inda zata gan ka ". Ɗan lumshe idanun sa yayi kafin ya janye daga kan mubeey da ya ɗan waiwayo yana kallo. Shi ko mubeey ganin kamar kallon na sa na neman ƙarin bayani ne hakan ya sa ya cigaba da maganar sa. Ƙaramin tsaki ya ƙara jaa kafin ya bar wajen cikin ɗan sassarfa. Mubeey kuwa ƙaramar dariya yayi yana cigaba da kallon sa hankali kwance haka kawai yake son ƙara ganin haɗuwar MAHAJ ɗin da shatou. Kayan jikin sa ya tuɓe duka kafin ya shige haɗaɗɗen toilet ɗin,tun da ga sama har ƙasa ruwan yake dukan sa bayan tsayuwar sa wajen sabod Shower ɗin irin na'urar nan ce mai amfani da tsayuwar mutun ne kana jayewa kuma zata ɗauke ta kashe kan ta. Sai da ya ɗauki lokaci a cikin toilet ɗin kafin ya fito mayukan sa masu tsada ya murza ma jikin sa kafin ya sanya wasu kayan mara sa nauyi riga da wando yan Companyn apple rigar armless jacket ya ɗaura kai bayan ya ƙara gyara haɗaɗɗen gashin kan sa da be san adadin abun da yake kashe masa ba. Turarukan sa masu tsada ya feshe jikin sa da su kafin ya fice daga bedroom ɗin yana ɗaura p_cap a bisa lallausan gashin sa. Ƙamshin sa ne ya fara bayyana kafin isowar sa wajen dan haka Mubarak ya zuba ma wajen da zai ɓullo ido shi ɗin ne dai ɗauke da system a hannun sa sai tsadaddiyar wayar sa. Kunnuwan sa duka biyun maƙale da Bluetooth fari ƙarr kamar kayan da ke jikin sa dan har Wandon irin buɗaɗɗen nan ne kamar pallazo sai dai shi guntu ne yayi kyau matuƙa kyau iya kyau. Ɗauke idanun sa yayi da ga kan sa. Kafin ya miƙe ya zari keys ya bi bayan sa. Kasancewar ya san bai wuce fita zai yi ba gashi Abbu bai son yana driving a cewar sa bai isa fara driving ba duk da ya san ya iya amma yana tsoron yadda dokokin ƙasashen ƙetare suke su,gashi ko kuskure basu sani ba kar wata rana ƙaddara ta hau kan ɗan gaban goshin sa dan haka ya ce Mubarak ya daina barin shi yana tuƙi duk da kuwa gwanewar da yayi. Gaba ya shige bayan Mubarak ya buɗe motar wanda ya ke ƙara jinjina hali irin na MAHAJ yana haka i na ga nan gaba ya san maganar kurame zasu komawa yi gaba ɗaya. " School Auditorium zamu je "Ya furta cikin muryan sa mai nuna yanayin sanyin sa. Kai tsaye Mubarak ya fahimci inda yake nufi dan haka ya ja motar suna ficewa bayan wangale musu katon gate da aka yi. Sunyi yar tafiya mai ɗan nisa kafin suka isa haɗaɗɗiyar makarantar ta su.SHINHWA University Babbar makaranta ce da take da manya manyan sassa kama daga primary secondary har zuwa tertiary,sannan makarantar biyu ce akwai ɗaya a Korea komai ɗaya da wannan bayan haka suna da sassan su a cikin zagayen Beijing da sauran garuruwan Ƙasar. Makaranta ce ta masu kuɗi da mulki domin duk wani mai maiƙo yana cikin wannan makaranta. Bakin Wani ƙaton Hall yayi parking. Shi ya buɗe da kan sa kasancewar shi kaɗai suke jira dan bai so zuwa ba ma amma saboda jin wani yanayi a jikin sa kamar kasala ya sa ya yanke shawarar zuwa wajen ko dan ya wartsake. Shigar su wajen ne ya ƙara bayyanar mini da girman da wajen yake da shi waje ne mai Shegen kyau ya Tsaru iya tsaruwa komai na sa red kama da kujeru har zuwa curtein komai ya yi kyau ga wasu irin haɗaɗdun kujeru masu kyau,kai daga nin yadda komai yake tsare kasan makaranta ce ta manya board ɗin su ma abun kallo ne. Tun da suka shiga ka fara jin shin shin na tashi a tsakanin su musamman Mubarak da ya fi sakewa.Abun ka da Chinese.Shi ko iya ka ya gyaɗa kan sa da ɗaga hannu ga wayen da ke ta faman furta masa nî háo?.(how are you) A chan ƙasan maƙoshi kawai yake amsa wa da fine yana zama fuskar nan dai sai sa sai sa. Haka suka fara gudanar da Rehersal Presentation ɗin su saboda sun gayyace shi ne ko zai taimaka musu da wani abun duk da gobe ne za,a yi. Mutun uku yayi yan China kafin ya miƙe kamar an masa dole yayi ya yi musu yan gyare gyare sannan ya rufe da xié xíe (Thanks you) Dukkanin su tafa masa suka yi. Godiya suka masa kafin suka watse taron cike da jin daɗi dan yana cikin ɗalibai masu ƙwazo sun san zai tallafa musu sosai duk da suma ba baya ba. Wajen wani gidan shaƙatawa suka nufa bayan ya sanar ma Mubarak ɗin dake ta murmushin jin daɗi dan baiwa irin ta Mahaj na burge sa. Ya san dole gobe ya burge manyan professors. Sun jima wajen kafin ya gama hutawar sa sannan ya fito ya samu Mubarak da yayi zaman sa cikin mota ya ɗan kwantar da seat ya kunna ƙira,a yana saurare tare da bin babbar hanyar titin da kallo mai cike da tsari mai kyau kowa sai harkar gaban sa yake yi. Yana shiga ya rufe motar hakan ya sa Mubarak sanin shigowar sa. Babu wata magana yaja motar dan ba yau ya saba da halin sa ba. Gida suka wuce direct koda suka isa ana kiran Salloli kasancewar dukkanin su da alwallan su ya sa kai tsaye suka shige masallaci ana gamawa kuma kowanne su ya fito dan mahaj ya riga fita ma kafin Mubarak.. Yau ko zaman falon bai yi ba ya zarce war sa sama. Wayar sa ya zuba ma ido yana kallon ñumban Ayya da yayi kewar ta sai dai ya san ko ya kira magana ce mara daɗi zai samu kamar koda yaushe. Numfashi ya sauke mai ɗan fita da hayaƙi na yanayin weather ɗin garin kafin ya danna mata kira. Saboda Allah ya saka masa ƙalahucin Ayya Saboda ita ya buɗe ido ya gani uwa duk da rashin mutuncin da take masa yakan ji kewar ta,kuma bai cika ganin baƙin ta ba kan hakan dan ya san tana da dalilin ta wanda ya rasa gane dalilin da ya sa har yanzu da ya girma fentin bata goge masa shi ba,yana jin tana yawan saka mahaifiyar sa cikin zancen kuma ya san wata rana dole zai san inda Ayya ta dosa. Laifin me kuma mahaifiyar sa ta yi da ta chanchanci yaɓin magana a gurin Ayya duk da cewa ta na ƙasa kwance.Idanun sa ne suka sauya sako wannan tunanin da yayi.Iska ya ɗan furzar kafin ya maƙala Bluetooth ɗin sa a kunnen sa. Ringing daya ba,a ɗaya ba sai ana biyu aka ɗaga. Shiru aka yi ta ɓangaren Ayyah kafin a hankali cikin Muryan sa mai sanyi ya furta " Ayyah Barka da dare ". " Barka " Ayyah ta amsa kamar an mata dole. " Kin wuni lafiya " ? " Da ban wuni ba ne zaka ganni,ja'irin yaro mai mugun hali,halin ne na uwar ka zaka nuna mini hi'illanci,ka ji murya ta garas nake,ina ruwan ka ma da yini na ne, kake tambaya na akan wuni lafiya,to nace ban wuni ba ka haɗa taro kayi party mtsww mugun iri kawai,Ragin dashin ɓarayi,an dai cuce ni wallahi " ƙyatt ta kashe wayar tana ƙara jan mugun tsaki. Tun da Ayyah ta fara magana ya rintse idanun sa da ƙarfi mafi munin kalaman da ya ji na ƙarshe su suka ƙara ta fasa jinin jikin sa wani irin rawa jikin sa ya fara kamar mazari zuciyar yan maza ta motsa. Yafi ƙarfin mintuna biyu a haka kafin a hankali ya sauke a jiyar zuciya wani irin rauni na bayyanar masa idanun sa ya ware da suka chanja launi kafin ya zuba ma wayar idanu. Kalaman na Ayyah na yau sun fi na koyaushe yin nauyi a gare sa.. me take nufi da ragin dashin ɓarayi,me take nufi da mugun iri wace irin cuta ce take cewa an musu ... Haka ya jero wa kan sa wayen nan tambayoyin sai dai babu mai bashi amsar su.Duk iya dogon tunanin sa ya kasa gane inda aka dosa. Kan shi ne ya fara sara masa hakan ya ƙara sanya jikin shi yin sanyi idanun sa ya rufe cike da tunani iri iri.Kiran Sallahn Isha ne ya tayar da shi daga wajen. A ɓangaren Ayyah kuwa sai da ta gama wayar ta gama yaɓa maganganun ta sannan ta lura da wanzuwar Abbu a wajen da ya shigo tun kafin ta ɗaga kiran ta fara mita. Da farko har ta nuna alamar ɗan razana sai kuma ta taɓe bakin ta tana kallon ƙwayar idanun sa da suka sauya daga fari zuwa jaa ɓacin rai da baƙin ciki da damuwa sun mamaye su jijiyoyin kan sa sun miƙe kamar yadda na MAHAJ suka ɗaga saboda yadda zuciyar Shi ta motsa. Yafi mintuna shida wajen tsaye a gefen ta yana kallon ta kafin ya ji saukar furucin ta. " Ka ɗaga mini akai kar ka jagula ni,haka kawai ka saka wa kan ka damuwa har ta kai ka da hawan jini ina dalili,ka san kai kaɗai nake gani ita wacchan gantalalliyar daɗi miji ta bar ni nan dan haka ka natsu ka samu lafiya,shi wanda kake ji ma tausayi bai ji ma kan sa duk wata magana tawa bana ganin tasirin ta gare shi,ɗan neman mai zuciya irin ta uwar shi ". Ajiyar zuciya Abbu ya sauke domin wani irin Tausayin ɗan sa da ya saukar masa dan a gaban sa ya fara maganar, maganar ma na da ko shi da yake mahaifin sa ba kullum yake samun irin haka ba ya rasa wace irin ƙauna MAHAJ yake yiwa Ayya da ya kasa share lamurran ta duk da musgunawar da take masa. Yadda ya ji Muryan ɗan na sa cike da ɗan farin ciki yake gayar da Ayya ɗin hakan ya ƙara karya masa jiki domin a handsfree Ayyah ta saka wayar abun ka da tsufa sai tace bata ji sosai. " Ayyah ba ya da laifi na sha faɗa Miki,daga shi har margayiya Zainab Basu da laifi,nine ɗan ki mai laifi,Ayya me ya sa ba zaki haƙura ba naga dai ta tafiyar ta fa,sannan ko Allah muna yiwa laifi ya yafe muna,bare Ayya ba laifi Margayiya zainab ta Miki ba,me ye lafin ta ƙaddarar ta ce haka,ko ince tamu,shin wani laifi ta yi ne, babu fa,na roƙe ki Ayya ki saurarawa MAHAJ haka ". Baki da hanci Ayya ta saki tana kallon sa kamar irin tana sauraren sa maganar na shigar ta aiko yana kai aya ta aza masa kuka wiwi bai son ta ya fi fi ta ta da ɗan sa da matacciyar matar sa,wai har ita zai dinga wa faɗa saboda ɗan sa lallai zainab tayi nasara dama ai dangin tsafi ta fito,dole a rina,shi yanzu ko Tausayin ta bai ji bata da kowa sai shi. Wayen nan kalamai su suka ruɗar da Abbu har bai san ya kai kusa da ita ba ya rungumo hannayen ta. Hawayen ya fara share mata kafin ya rarrrashe ta da ƙyar yana taushe wani irin dutse mai ɗaci a maƙoshin sa na damuwa da ɓacin rai da ɓakin ciki. Sai dai bai da abun yi akan wannan ƙiyayyar da Ayya ta ɗaura wa MAHAJ babu wani ƙwaƙƙwaran dalili. Da ƙyar ya yi shiru hakan ya sa bai ƙara furta komai ba bayan kalmar haƙuri ya fice daga bedroom ɗin na ta sashen ma gaba ɗaya.. Zarya ya ke ta yi bayan ya koma bedroom ɗin sa yana son kiran MAHAJ ɗin sai dai ya san shi ba zai iya taushe yanayin da yake ciki ba,ya san MAHAJ zai taushe amma shi ba zai iya ba take raunin sa da Damuwar sa zasu iya bayyana.Haka yayi ta tunanin abun da ya dace yayi inda Daga ƙarshe dai ya haƙura da kiran na sa har zuwa da safe. Haka Ammah ta same shi zaune cikin damuwa da ƙyar ya iya ce mata babu komai sai dai duk yadda ya ke ƙokarin ɓoyewa ta gane komai dan haka bata ce komai ba ta ja bakin ta tayi shiru cike da tunani a cikin zuciyar ta,dan ko abincin da tace aka wo masa saboda bai ci abincin dare ba cewa yayi aa dan haka ta zuba masa ido daga ƙarshe ma wanka ya faɗa bai daɗe ba ya fito a gurguje ya kimtsa ya yayi addu'a ya haye kafcecen gadon sa yayi kwanciyar sa cike da damuwa yana rufe idanun sa. Am mah inda saboda ta saba da wannan ɗabi'a ta Abbu a lokuttan da yake cikin damuwa hakan ya sa cikin rashin nuna damuwa itama tabi sahun mijin na ta kasancewar a shirye ta shigo dama tayo Sallama da ya'yan ta dan kayan bacci ne jikin sa. Tun da suka haɗu bayan anfito Sallah ya san cewa akwai matsala ganin yanayin fuskar ta sa, ta ƙara chanzawa ta haɗe irin na mugun izzar nan da iko da kuma yar damuwa da take bayyane. Cike da tausayin sa haka ya bishi da kallon har ya ɓace wa ganin sa kafin ya bi bayan sa. Bai same shi ƙasa ba dan haka shima ya wuce sama. A chan ya same shi sai dai ya saka lock a ƙofar bedroom ɗin sa duk yadda Mubarak ya so na'urar nan ta cire masa makullin ta ƙi haka ya juya yana fatan komai ya zo da sauƙi dan ya san duk ya sha shishar nan da yawa yadda yake hasale haka zai iya yiwa kan sa illa ta kai shi kwance saboda Illar hakan a jikin sa. Shishar kuwa ya ke sha dan gani yake ita ce maganin kawar da Damuwar sa,haka yake ta zuƙar ta kamar yadda ya saba sai da ya ji ya fara tari sannan ya ajiye. Wani locker ya buɗe ya janyo sweet mai ƙamshi ya jefa bakin sa yana sauke Numfashin ajejjere. Sai da ya ja yan mintuna kafin ya miƙe ya saɓule kayan jikin sa ya faɗa da ɗan toilet ɗaure da ɗan ƙaramin towel da yayi masa ɗaurin a zaz zarge kamar ya faɗi. Bai jima ba ya fito ɗaure da wani sabon towel ɗin a jikin sa,ga danshin ruwa a jikin sa,da alama wanka ya ɗauro,sai kam sa na ɗauke da ƙaramin towel white kamar na ɗaure a ƙugun sa.Kayan barci ya saka masu taushi da santsi maroon color da suka ƙara bayyanar da hasken fatar sa irin na turawa.. Turaruka ya fesa masu ƙamshi sannan ya haye gadon sa yana jingina bayan sa da kan gadon yana sauke numfashi. Ya daɗe zaune haka kamar mai wani tunani kafin ya yi addu'a ya rage haske da ƙara gudun A.c. Lallausan duvet ya rufa jikin sa da shi yana lumshe idanun sa.. Mubarak da ke ta faman zagaye sai da ya tabbatar da yayi bacci babu motsin sa sannan shima ya shige. A hankali a hankali bacci ya kwashe sa mai nauyi. Asuba ta gari ɗan Abbu jikan Ayya... Sanye yake cikin Suit blue and white ya sha kyau har ya gaji farin madaran fatar sa sai ƙara kashewa masu manyan guntayen mutanen nan ido yake yi,da jajayen fata,Ga kan shi ya sha gyara Masha Allah sai ƙamshi yake zubaawa.Miƙa masa hannun da ake ta yi ne inji manyan mutanen da aka gayyata a wajen presentation ɗin suna jinjina masa na da nuna irin ƙwazon da yayi,Musamman kasancewar sa ɗan Nigeria dan ba su cika samun yan Nigeria a irin wannan presentations ɗin ba wannan ne karo na biyu dan haka ya samu jinjina wa matuƙa dan tunda ya fara har ya gama tafi ne ke tashi na nuna jinjina da yabawa. Duk yadda yake daurewa da hayaniyar wajen abun ya gagare sa, dan haka ya zubawa Mubarak ido da ke ta washe baki kamar shi yayi presentation ɗin nan ya ji daɗi matuƙa dan yadda ake yabon ɗan Abbu abun farin ciki ne a gare sa ya san Abbu zai ji daɗi matuƙa idan ya san cewa Ɗan sa ya yanke kowa shi ya zo na farko. A ward ɗin sa ma Mubarak ya karɓo sa tare da na makarantar ta su inda su suka yo na farko a cikin gaba ɗaya presenter ɗin kuma shi ya zo na farko. Kallon sa Mubarak yayi dan shi ba yanzu ya so su wuce ba har sai jama'a sun fara ragewa masu taya sa murna. Amma ya san halin uban gidan na sa hakan ya sa ya miƙe shima yana gyara Suit ɗin sa baƙi kamar na sauran mutanen da ke wajen dan suma mafi yawa duk baƙi suka saka Abin kamar haɗin baki mahaj ne kawai mai sanye da blue and white. Taro yayi kyau matuƙa. Ficewa suka yi daga Ƙaton Hall ɗin na gwamnatin China da aka gudanar da taron.. A gajiye ya zauna bayan motar da mubey ya buɗe masa yana jin kan sa na sara masa ga kasala ta gajiya da ta saukar sa,da doguwar maganar da yayi,duk da taƙaitaccen bayani ne yayi,Sannan Gashi Surutun wajen yayi yawa musamman na Chinese ɗin da ke tana faman yawo da shin shin😂✍️✍️ Idanun sa ya lumshe tare da sauke ajiyar zuciya ta gajiya.Ya na ƙara shigewa cikin seat.Tare da yin balance yana untighting necktie ɗin sa. Har suka isa haka yake hakimce bayan mota kamar wani Babba ɗan shekara talatin.Ya sha kyau matuƙa yau kamar ka sace shi ka gudu komai na sa a kallo ɗaya zaka san mai tsada ne. Nima dai nace Nimên hoa ma (How are you All )👋🚴🚴🚴 Wân ãn..(Sai da safen ku) Allah ya bamu alkhairi. Wai me yake damun Ayya ne ? Me take nufi da kalaman ta hmmm 🤭 Ya kamata wani ya samo muna inda ta dosa haba.Ace jikan ki guda kike tsangwama gaskiya ayyah akwai zama 🥺😔 Inda ku ka ga kuskure ku yi haƙuri wallahi cikin bacci na yi editing ɗin sa.🥺 Kumin Addu'a Allah ya bani ikon kammala book one kafin mu fara exams nan da 15 sept dan na kusa tafiya Hutu,na ma yi jinkiri saboda ku a wannan karon,amma in sha ALLAH ina hanya🤗🚴🚴za,a ɗan yi jira na.✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P________3️⃣5️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* Cikin farin ciki Abbu ya kira shi bayan sanar da shi da Mubarak ya yi. Fitowar shi wanka kenan yana tsane jikin shi.Ya ji ƙarar wayar sa tana fitar da sauti mai daɗi kuma a hankali cikin sauti mara tashi.A hankali ya sauke numfashi mai haɗe da ɗan murmushin gefen baki yana furtawa a kan Leɓen sa Abbu. Wayar ya saka a speaker sannan ya cigaba da goge jikin sa da tsaftaccen towels na sa. Gashin sa ya fara drying da na'urar busar da gashi. Kafin a hankali ya danna wa Abbu wani kira bayan kiran na sa ya katse. Cike da farin ciki yaji Muryan Abbu ta ratsa kunnen sa yana masa sallama. Amsawa yayi shima muryan sa ɗan sake alamar babu wata damuwa a tattare dashi a wannan lokaci. " Congratulations,an kawo mini albishirin yaro na ya goge wa sinawa da turawa Hadda ". Murmushin da bai yi niyyar yi ba ne ya suɓuce masa.Jin furucin Abbun. Jin saukar murmushin sa da Abbun yayi ya ƙara tsintar kan sa cikin farin ciki domin abinda ya faru jiya ya saka masa waswasi da tsoron kar ya hana MAHAJ ɗin gudanar da abun da ya dawo da shi school ɗin yi.Dan haka koda ya kira Mubarak ya ji ya su ke ya sanar masa da lafiya lau,gashi har MAHAJ ɗin ya shirya zasu tafi.Addu'a kawai yayi masa kawai dan yanzu idan ya kira sa ya ji yanayin Muryan sa zai ji babu daɗi dan ya kasa cire damuwar a ran sa. " Kayi ƙoƙari,Allah ya taimaka,I'm so proud of you ''. " Thanks you best father ". Ya furta a hankali kamar bai son wani ya ji. Murmushi Abbu yayi kafin ya ya ɗanyi jin sannan ya furta. " I hope baka saka Damuwar wani a bu a ranka ba game da Ayyah " ? Shiru MAHAJ yayi duk da ya ji zancen Abbu ɗin. A jiyar zuciya Abbu ya sauke sai ya ji dama bai masa maganar ba ganin Damuwar ya ɓoye ta amma yana son ya rage taushe ta ne ya na rage zafin zuciyar sa idan ya na sanar wa wani. Shiru ne ya ƙara ratsa tsakanin su. Abbu ne ya katse shirun na su ta hanyar chanza magana,yana furta. " Yanzu yaushe zaka dawo ? ya kamata kaje ka duba yanayin aikin nan ka ga gashi Ramadan na gabatowa ba lallai ka iya zuwa lokacin ba,Gara ka je yanzu kaga yadda komai yake tafiya ". Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke kamar wanda ya sharɓi kuka. Dan Maganar Ayya da Abbun yayi sai da ya dakatar da duk abinda yake yi dama mai ne yake ta faman shafawa jikin sa dole ya dakata yana kallon wayar da idanun sa da suka sauya,jikinsa na yin sanyi domin ya san cewa Abbun yaji abun da ya faru tsakanin sa da Ayyah wannan zancen na sa shine tabbacin hakan,kuma shi ba haka yake so ba dan duk abinda zai saka mahaifin sa damuwa baya so kamar Yadda baya son komai ya shafi Ayyah ɗin sa.Ya san tabbas jiya Abbu ba lallai ya iya bacci ba,sai yanzu ya gano dalilin ƙin kiran sa da bai yi ba da safe. Abbu da ya ji saukar ajiyar zuciyar ta sa ne ya ji wasu irin hawaye suna neman zubo masa. Haɗiye su yayi jin MAHAJ ɗin na furta " Zan huta Abbun na ɗan lokaci zuwa kafin a zumin zan shigo na ƙarasa Hutu na Nigeria ". Murmushi Abbun yayi jin ya sauke numfashi na doguwar maganar da yayi. " TOH Allah ya bada iko,ka kula mini da kan ka Kaji ɗan Albarka ". Kai ya gyaɗaa kamar yana gaban Abbun tare da ɗan sakin fuskar sa. Kasancewar Abbu ya san yana buƙatar hutawa hakan ya sa babu wata fira yayi masa Sallama. " Komai ya kusa zuwa ƙarshe MAHAJ zaka samu farin ciki in sha ALLAH ". Abbu ne yayi Furucin yana ƙawata fuskar sa da murmushi wanda yake fitowa daga ƙasan zuciyar sa, Murmushi ne mai cike da ma'anoni da ban daban da shi kaɗai ya bar wa kan sa sani. A ɓangaren MAHAJ kuwa Jerarrun Ajiyar zuciya yayi ta sauke wa bayan yanke War da Abbu ya yi,tun ɗazu yake son sauke ajiyar zuciyar na abun da abinda yayi masa tsaye a maƙoshin sa. Dai dai ya gama murje jikin shi ko ina tare da saka manyan turarukkan sa masu tsada da suka riƙa bedroom ɗin na sa da duk wani abun amfanin sa da yake taɓawa yau da kullum idan yana ƙasar. Wani wando ya saka mara nauyi kamar na jersey sannan ya haye gadon sa bayan ƙara gudun Ac da yayi tun daga kan sa har ƙafafun sa ya rufe da tattausan duvet kafin yayi addu'a bacci yayi a won gaba da shi. Kamar yadda MAHAJ ya sanar da Abbu haka kuwa aka yi domin kuwa sai da suka sha hutun wata ɗaya sannan ya haɗo kayan sa tare da Mubarak suka dawo Nigeria. * " Wallahi ni dai Ban yafe ba,duba ki ga yadda ya tulɓe mini fata,Wallahi Allah ya isa na ". Ta kai ƙarshen zancen tana jan majina fuskar ta tayi Jawur ba kowa bace kuwa face Shatou da ta yi fashin islamiyya malam Abu ya zane ta,wanda su su Inna ni ba su ma san cewa ta yi ba dan tana fita da zummar zuwa makaranta,wanda su sai yanzu suke jin ashe laɓewa take yi bakin makarantar bata shiga dan haka yau da dubun ta ta cika malam Abu ya kama ta ya zane. Inna ni dai zuba mata idanu tayi fuskar nan Tata cike da damuwa ganin yadda take kuka kamar za,a zare ran ta ga Allah ya isa da take ta jifan malam Abu. Numfashi ta sauke kafin ta ce " Ai shine dai dai dake dan uban ki tun da baki jin magana ta,bare ta mahaifin na ki da yake ɗaure Miki yake bi dake ta Rarrashi,ai Ni ya ci Ni goro,ungo Habibullah kai wa malam sadaka,Allah ya biya shi ". Ta miƙawa Bibu Naira dari biyar ɗin tana jan ƙaramin tsaki tare da haɗe fuskar ta. Baffa na dan guntun murmushi kawai yayi jin furucin Inna ni kafin ya kamo hannun shatou dake cigaba da kuka tana ƙara masa giya Saboda kalaman Inna ni da suka bata haushi. Rarrashin ta ya dinga yi tare da Bibu da ya faki idon Inna ni da ta shige ɗaki ya ƙi fita daga hanyar da ya nufa. " Baffa na kalli hannun ta fa Wallahi Adda shatou kin daku,Kuma bamu yafe wa Malam Abu ba.". Cewar Bibu. Kallon hannun ta,ta yi inda shatin bulala ya kwanta kan lafiyayyar fatar ta. Cike da sangarta ta ƙara ɓare ƙaramin bakin ta. Tana yi tana kallon gurin tana sake fashewa da kuka. Baffa na hankalin sa duk ya tashi dan haka ya cigaba da rarrashin ta. Sai da suka tabbatar ta yi shiru sannan Baffa na ya furta a hankali " Karki ƙara yiwa malamin ki Allah ya isa kinji shatou malamai sune magada annabawa kinji,haka kaima Bibu kar na ƙara jin haka ". Kai suka ɗaga masa ganin babu alamar wasa kan fuskar sa. Miƙar da Shatoun zaune yayi kafin ya ce " Ki riƙa zuwa makaranta kinji ko,bana son ana dukan ki,gashi ma Makarantar boko sai karar ki ake kawo wa dan Allah ki daina kin ji , Mahaifiyar ki bata jin daɗin haka bare ni,Ki mayar da hankalin ki kamar yadda Bibu ke son zama ba kin ce Yar sanda kike son zama ba " ? Kai ta gyaɗa masa.Cikin tabbatar wa. Murmushi yayi kafin ya ce " Yawwa sai kin dage dan karatu shine gaba su ma ba haka Kawai suka saka kayan Yan sanda ba ". Dan Shatou tunda Abbu ya zo tare da masu kayan yan sanda taga harda mace cikin to tunda ta ƙyalla ido ta sha wa Baffa na kai irin wacchan matar da ta gani ga wannan mutumin mai kyau take son ta zama nan ya ce mata yan sanda ne ta ce ta ji har da aikin su ya faɗa mata ta ce ta ji ta gani.Da farko dariya abun ya bashi sai da yaga dagiyar tayi yawa da nacin tambaya hakan ya sa ya gane da gaske take yi.Shi ya sa yake biye mata a je hakan kawai shi ya san babu wani yar sanda da zata zama suna sake ko suna ɗaure,ai Bama nan gizo ke saƙa ba.Hmm Numfashi ya sauke yana ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi kafin ya ce " dan haka ki dage kin ji,Allah ya baku sa,a gaba ɗaya,shi Bibu ya ce mai Shari'a yake son zama kamar yadda mai gari yake yi ". Dariya ta saki kaɗan jin wai bibu mai Shari'a yake son zama kamar Mai gari yana nufin irin yadda idan an kai wa mai gari ƙara yayi sulhu ya bawa mai gaskiya gaskiyar sa.Chab lallai ita kam yar sanda take son zama sai ta saka wayen nan uniform ɗin ko dan ta kama irin su MAHAJ masu rainawa talakawa suna musu yadda suka so. Sunan MAHAJ da ya shigo cikin zancen zucin ta ne ya sa ta jan guntun tsaki. Har sai da Baffa na ya Kalle ta ganin ta haɗe rai tare da sakin tsakin. " Lafiya dai ko ".? Ya tambaye ta yana kallon ta. Ƙara taɓe fuska tayi tana turo baki gaba ta gyaɗawa Baffa na kai kawai. Murmushi yayi kawai tare da girgiza kan sa.Yana mamakin halin shatou wasu lokuttan tayi ta abu kamar mai tashin iska. A ɓangaren Iro kuwa abun duniya ya sha masa kai dan gargaɗin mahaifin sa yake tunowa sai dai har yanzu bai jin ya bar zancen dan haka yau ɗin nan ya shirya tare shatou idan Allah ya Fiddo da ita dandali dan yanzu ba kullum take fita ba sai tayi sati bata fita ba.Kuma hakan mugun yiwa Inna ni daɗi yake yi dan haka yanzu bata wani mata faɗan fitar saboda ko ta fitan tana dawowa da wuri kuma tare da Bibu suke tafiya dan gaba take saka shi.Sai dai Kullum Inna ni cikin Bin ta da Addu,a take ta kariya daga shaiɗan da aljan,da mutun. Kamar kuwa ya sani yau Allah ya fitar da Shatou tun daga nesa ya hango ta tana yankar gudu dan haka bakin shi washe ya tare ta yana zuba mata idanun sa. Turus ta ja ta tsaya ganin sa. Ɗan zuba masa idanu tayi na ɗan lokaci kafin ta ɗauke idanun ta daga kallon sa tana taɓe bakin ta ganin duk yayi duhu ya faɗa kamar wani mai aikin wahala,bayan kuma A iya sanin ta mai gari bai barin sa ko noma ne saboda gata. " Haba Shatou idan babu yaƙi me ya kawo gaba " ? Harara ta sakar masa kafin ta ja ƙaramin tsaki sannan ta ce " Yaƙi kuwa tsakani na da kai ai baya ƙarewa tunda haka kake so yanzu me ye na tare mini hanya ta idan ba neman faɗa ba ". Ta faɗa tana hura hanci irin an dame ta ga cikakkiyar budurwa dan hannuwan nan zaune suke dam a gefen ƙugu. Shidai Iro kamar Gaula haka ya zuba mata ido dan shi duk wani abu da shatou zata yi yanzu burge sa yake yi Kamar kar mahaifin sa yayi masa kashedi da ita ya ji duk duniya babu wanda ya isa ya raba shi da Shatou sai Allah. Ya sha shan alwashi iri iri akan ta tun bayan da ya fara son ta har izuwa yanzu haka yake dan ya sawa ran sa idan har ba shine mijin shatou ba kuwa sai dai yayi mai hisshe sa wadda zata saka dole a duba masa ko ba,a so.Dole na so ki yar Abar nan ga Shegen kyau kamar hindiya. Numfashi ya sauke yana ajiye maganar zucin sa,yana murmushi da yake bayyana haƙoranta sa da suka fara yin jaa saboda rashin wanke bakin. " So ne fa ba komai ba ya kamata Babies ki gane ". Wata uwar Harara ta ƙara sauke masa tana ƙara hura hancin ta musamman jin sunan Babies da ya kira ta dashi dan ya mata daɗi amma bata yarda ta nuna masa ba kar ya ga damar ta ko ya zaci wani abun. Shiko Iro cike da iyayi yake ta ƙara Nana ta haba Babies. Wai tsaya 🤔🤭ko dai yan matan da yawa suke gaban iro bamu sani ba.Koda yake degree ce ga Manya🤣 Gaba tayi aiko Sarkin nacin ya ƙara cin gaban ta. Cike da tsiwa ta fara sauke masa Masifa sai dai abun haushi har ta gama murmushi ne yake saki. Abun da ya fara sage mata gwuiwa kenan domin babu rashin mutuncin da bata juye masa ba a wannan lokacin mai gari ne kawai bata zaga ba har sunan dabba ta kira sa dashi amma sai dai fuskar sa babu alamar damuwa. Tsaye tayi tana kumbure fuska cike da haushin masifar da ta gama.Ji take kamar ta tsinka masa mari ko ta yanke kan sa yadda ba zai ƙara ganin ta ba. Ganin dai bazata taɓa rabuwa da shi ba ta hakan ba ya sa a hankali wata dabara ta faɗo mata ta sauke kan ta ƙasa tana ɗan sakin fuskar ta kafin ta ce. " Yanzu dai muje dandalin ". Tayi gaba tana haɗe rai tare da hararar shi ta gefen ido. Shi ko kamar Gaula haka ya bi bayan ta yana jin kan sa sama musamman da suka jera a tare sai yake jin kamar an biya masa kujeran makka,ko an masa kyautar manyan kuɗaɗe. A haka suka isa dandalin a tsawalle take domin yana yi yana Kallon ta gashi bata wani saba ma hakan da kowa ba sai Bibu ko Baffa na amma yau ɗan anace ya saka ta jerawa da shi dan dole,dan haka take ta cika tana batsewa ba tare da sanin sa ba. Oho shikan ina ruwan sa ai gaba tayi da shi.. Kallo ne ya koma kan su, su Ramata har gwara kai suke yi da Amina wajen ƙara kutsa idon su wajen da suke dosowa da ɗan farin wata ya haske su. Take guri ya amsa kuwwa samari na ta dariya ta irin burge su da Iro da shatou suka yi, dan sai suka ga muguwar dacewar su tare gashi sai ka zata wasu masoyan na ƙwarai ne dan ta sake fuskar ta tana yi tana kallon Iro da yake ta yaƙar baki sai dai ta ciki na ciki ji take kamar ta kai masa mari ga Shi sai tsine masa take yi ƙasan zuciyar ta. Abokan Iro da ke wajen kuwa sama suka ɗaga sa suna cillawa saboda murna shi ko sai kwasar dariya yake yi yana ƙara jin kan sa sama. Ita kuwa Shatou tana samun sun janye sa ta fara jan mugun tsaki wanda ya sa su Ramata Kallon juna. Amina da ta fahimci komai murmushi kawai tayi dama ta san babu komai sharrin shatou ne. Aiko bata gama tunani ba ta ji ta tana furta " Allah ya raba ni da Auren mummuna ƙazami ".Ta tofar da miyau tuno da haƙoran Iro. Sannan ta cigaba da furta " Ni sai ɗan birni mai kyau,amma ba mai kyaun Aljannu ba,wanda idanun sa suke da mugun tsoro " Dukkanin su idanun su suka zuba mata sanin inda zancen ta ya dosa. Ganin yadda suke kallon ta ne ya sa ta furta a hankali " Kai lafiya kar ku cinye wa Inna ni da Baffa ba kyau na ". Amina ce kawai ta yi murmushi suko su jawairiyya shiru suka yi mata musamman Ramata fuskar ta dake haɗe tun dosowar su wajen bata saki ba su kan babu wanda ya lura cikin su sai shatoun ce ma ta lura sai ta basar da ita,dan ta san dai bata mata komai ba. A hakan suka fara wasannin su sai dai ba,a je ko ina ba dambe ya kaure tsakanin Shatou da wata ana tsaka da wasan wai saboda bata mata riƙon dai dai ba ta faɗi dan haka ya sa ta ci ƙasa shine tana tashi ta kama yarinyar da kokawa abun da ta ɗan jima bata yi ba. Aiko da ƙyar aka ƙwaci yarinyar nan. Yarinya ta ji azaba sosai, dan haye ta Shatou tayi yarinyar gata Barakallah kamar ni 🤭😂amma haka ta haye kayan ta dan a girme ma zata bawa shatou shekara biyu. Kukan ta ne ya ankarar da jama'ar wajen musamman maza da suke chan gefe wayen da basu lura da abun da ke faruwa ba. Shi ko saurayin yarinyar dan har an musu baikon su irin na ƙauye jin Muryar ta hankalin sa ya tashi gashi babu mutucin aiko ya zo da azama zai kama shatou ya kakkarya sai yayi rashin sa,a dan Iro ya ce bai san wannan zancen ba zai yi maganin sa musamman jin irin zagin da yake jifan Shatou da shi bayan zagi harda kiran ta da Sunan yar tsintuwa,mara asali yar karuwa.Wayen nan kalamai sun yi tasiri ga zuciyar Shatou duk da ƙarancin shekarun ta,dan take taji kamar a bar ta ta yi maganin sa sai dai su Amina sun san bazata iya faɗa da shi ba gashi ma ba faɗa take yi da maza ba baki ne kawai.Shi ya sa yau suka ji daɗin kasancewar Iri iro wajen dan yau da sai buzun shatou. Dambe ne ya kacha me mai rai da lafiya kowa na tashen balaga.Aiko da ƙyar aka raba , dan Iro sai da ya zubarwa yaron nan da jini.Anan taron wasa ya ƙare,domin kuwa faɗa ne ya ƙara kachamewa tsakanin abokan Iro da na yarinyar duk da dai dama abokai ne wasu ƙungiya daban bayan na iro dan yaron ɗan wani mai kuɗin ƙauyen ne shima jin kan sa yake yi sosai. Da ƙyar aka raba faɗan bayan wasu sun je sun gaya wa mai gari da bai tashi daga fadar sa ba. Koda aka isa da su wajen mai gari da ya turo daga fadar sa,cike da mamaki yake kallon su kafin ya iya yin magana jin bahasin rigimar koda ya bincika ya ji cewar Shatou ce sai ya shiga mamaki dan ya san dai ya raba Shatou da Iro,gashi kuma zagin da iro yace yaron ya mata ya girgiza sa sai dai bai nuna ba ya dai tsawatar musu,a hakan ya samu ya raba case ɗin aka watse sai dai shi kamm Saurayin nan mai suna Shamsu bai bar zancen ba,ya sha alwashin sai ya rama ma Nazihwa budurwar sa bugun da shatou ta mata. A ɓangaren shatou kuwa dukkaninn su hanyar gida suka nufa a tare,gudun kar wani abu ya faru su Amina basu bar Shatou ba sai bakin ƙofar gidan Baffa na suka ajiye ta saboda yau dai babu Bibu a tare da ita ya ce kan sa ke ciwo. Duk da ta ce su tafi amma haka suka ƙi sai da suka ajiye ta sannan suka juya kowa zuciyar sa maƙare da tsoro na damben da aka yi sai dai ita giwar babu ko ɗar a jikin ta.Hasalima ta watsar da komai kofar gidan. Koda Inna ni taga shigowar ta bata ce mata ƙala ba bayan amsa mata sallama Sululu kamar wadda tayi ƙarya haka ta shige ɗakin ta. Inna ni ajiyar zuciya ta sauke kawai ta shige ɗakin ta bayan ta tabbatar mata da ta tabbatar sai tayi addu'a kafin ta kwanta daga chan ta amsa da toh. Tana cire kayan jikin ta ta ɗaura zani saboda zafin da ta ji ya taso mata. Baffa na dai da dake biye da shatoun tun fitar ta har Dawowar ta,yana biye bayan su iya da su Amina faɗan ma ya ji komai da ya faru,duk da yana nesa kaɗan aka yi shi,a hankali ya sauke ajiyar zuciya da numfashi yana shigewa gidan tare da sakaya shi bayan yayi basmalah. Yau sati ɗaya da dawowar su MAHAJ wanda ya kama kuma saura Sati uku a zumi dan haka ya zama ko ina sai shirye shiryen tarbon baƙo ake yi ta ko ina sai gyare gyare ake yi.✍️ A GAFARCE Ni na so yafi haka jiya ban yi da yawa ba sai na tsaya na ƙara muku,yayi tsawo to abun ya gagara exams on next Monday gara nayi focusing kan karatu kar na kwaso carryovobibi🤣Father yace a ajiye rubutu. Zan tafi Hutun wata ɗaya zuwa october zan dawo in Sha ALLAH.Idan muna cikin masu gani idan Rabbi ya lamunce mini. Zan dawo mu cigaba da wannan tafiyar mai ban mamaki da al'ajabi da rikitarwa. Na san zaku ji rani ko nan da shekara ne.Dan haka nake alfahari da ku.🥰💯✨🙏 Allah ya bar kauna.🤲🤲 Dan Allah ku saka Ni a cikin Addu'oin ku.Allah ya bani sa,a da duk wani mai rubuta jarabawa. Shin Iro zai samu Shatou kuwa ? Shatou zata zama yar sanda kuwa kamar yadda take buri? Ina labarin Alina,Sarina ????? Yan biyu masu abun mamaki da tsoro. Ina labarin ta baiwa ? Ina labarin Mai zuwa wajen boka gangaro? Me ye abun da Ayyah ta tsana akan mahaj game da mahaifiyar sa ? Shin wane irin abu ne yake damun rayuwar Bilal Me malam Hambali yake ɓoyewa ? Ya tushen wannan labari ya ke,ina asalin sa,hmmmm mu haɗe a nan da October in Sha ALLAH ✍️✍️ Akwai abubuwa da yawa bayan wayen nan da ya kamata na warware muku kafin zuwa na Hutu sai dai Allah bai nufa ba.Dan haka ku sha kurumin ku zan dawo da zafi zafi 💃💃💃ba tare da tsaiko ba In Sha ALLAH.Ngd.yan amana ta.✨✨🥰 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣6️⃣ *BOOK ONE* *_FREE._* _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* _________________________ Alhamdulillah, all praise be to Allah, the Most Glorified and Exalted, who granted me the opportunity to return from the short journey I undertook.I appreciate the support you all showed me by waiting patiently throughout these past days. I’m proud of you, my beloved ones both near and far, those I know and those I don’t.May Allah preserve our love and strengthen our bonds of kinship. I also pray to Allah to not let me face disgrace and to grant me the ability to complete this book successfully without any obstacles. My sincere gratitude goes to my readers,📚 because this name Fa’iee🥰😍✨wouldn't have had meaning without you lovelies 💕. Thank you so jazakallahu khairan.🙏Kurman ƙaddara na godiya ƙwarai Dagaske kun nuna masa ƙauna matuƙa kuma na ji daɗi kamar in taka 🤭😍💃💃💃 Endless thanks to my family,may Allah bless us, increase us in unity and strengthen our ties of kinship. Ameen.🤲 🕊️🕊️🕊️ Yau kwana biyar da samun gocewar ƙashin REENA Kuma har yanzu B bai yiwa LEENA maganar ba kuma ya zuba mata ido da mamaki musamman ganin ta cigaba da harkokin gaban ta,bata nuna wata muguwar damuwa ba akan yanayin yar uwar ta da take fama dan kwanaa biyu Bata ma samun bacci isasshe, sai Ummah ta yi mata addu'oi ta shafa mata akan ƙafar da ke mata zugi haka Sir shima da Dada sai da suka dage da shafa mata addu'a Sannan a hankali ta fara samun sauƙin ƙafar kuma duk wannan yanayi na azaba da Reena take ciki bai taɓa tadawa leena Hankali ba hasalima koda sau ɗaya bata taɓa nuna nadama akan fuskar ta ba,ko damuwa dan haka Ummah da B suka zuba wa sarautar Allah ido. Yau ta kasance Laraba sun shirya tsaf zuwa gaida kakan su dukkannin su tsohon arziki,su uku suka shirya suka tafi dan BILAL ɗin ne ya saka su gaba zuwa wajen Baba Mai Billions ɗin da yake ɗan fama da jiki. Har suka isa babu wata sakewa a tsakanin su.Tsitt suke zaune a cikin tangamemen falon na sa Badan komai ba sai dan Yadda Fuskar Bilal take haɗe kamar wani kumurcin maciji dan tun abinda Leena tayi wa Reena ya kasa sakewa da su fuskar sa ta zamo kullum a ɗaure Ummah kullum cikin masa faɗa take Badan komai ba sai dan samun sakewar Reena da take ɗan raɓewa gefe na jinyar da take yi ta ƙafar kafin ta warke gudun abu biyu yayi mata yawa.Sai dai yana bata kulawa Sosai,kamar yadda kowa yake iya ƙokarin sa. " Ni nayi fushi ace ace sai yau kuke zuwa gaida mai gidan na ku kamar baku son shi " Farin dattijo ne yake yin zancen yana saukowa daga matattakalar benen fuskar sa ƙawace da murmushi kallo ɗaya zaka masa kasan shine mahaifin Ummah dan babu inda ta baro shi. Da sauri Reena ta miƙe tana tura ƙafar ta da ta ke ɗan mata ciwo kaɗan ta isa gaban sa tana dariyar farin ciki. Ba tare da ta tuna gargaɗin Bilal ba na natsuwa da yace kowaccen su tayi wanda kuwa ya yi furucin ne ba dan kowa ba sai dan Leena kuma maganar ta shiga kunnen ta dan ta natsu tayi shiru sai satar kallon sa take yi daga gefe har fitowar dattijon da matar sa wadda suke kira Kaka tayi kiran sa dan sun tarar da ita asashen na sa. Murmushi ƙawace akan fuskar sa yake kallon Reena yana shafa kan ta cike da tausayin ta da wani irin yanayi na kewar abun da yayi masa nisan kiyo. " So ake na huce da wuri haka ne,ake rungume ni " ? Yayi maganar cikin dattako yana shafa farin gemun sa da ya ƙawata fuskar sa. Kai Reena ta gyaɗa masa tana kallon fuskar sa. " Ya jikin B B " Reena ta furta tana Murmushi. Murmushi yayi mai sanyi ya ƙara shafa kan ta kafin ya furta cike da jin daɗi " Na ji sauƙi mata ta " Sannan ya ƙyafato Leena yana furta " waton ke wannan ja'irar matar ta wa baki yi kewa ta ba "..Ai ko kamar jira take yi ta washe baki ta matsa kusa da shi da ɗan gudu tana dariya tana girgiza masa kai. Dariya yayi yar ƙarama sannan ya ce " to me zai sa a share ni,sai na yi magana,ga ɗayar mata ta harda mini ya jikin tsufa ". Ido ta ɗaga ta ɗan saci kallon B Dake zaune yana ɗan taɓa wayar sa fuskar sa kwance da murmushi na ganin dattijon ya samu lafiya dan kwana biyu yana yawan zuwa duba sa kusan kullum sai ya zo duba sa tun da ya dawo musamman ma da ya tarar jikin sa, sai a hankali Ummah ma tana zuwa duba mahaifin na ta duk bayan ɗan lokaci Haka Abba ma da su Dada,Sir suna ɗan leƙawa dan basu yar da Zumuncin ba duk da yar uwar su ta tafiyar ta amma ai Zumuncin su na nan ya riga ya haɗu gasu harda jikokin su jini ɗaya. Fahimtar cewa BILAL ya gargaɗe su ne ya sa Baba mai Billions bai ƙara cewa komai ba sai ma shafa kan ta da yayi yana murmushi yana tofa musu addu'oi na kariya ba ta re da sanin su ba sai da ya gama sannan ya samu waje ya zauna tare da kowaccen su a gefen sa. " Ya Mahaifiyar ta ku,tana lafiya ko ".?? Ya tambaya bayan Bilal ya gayar da shi da jiki cikin girmamawa duk da wasan jika da kaka da suke yi hakan bai hana sa bashi girman sa ba da daraja sa kamar yadda yake bawa sauran manyan mutanen da bai san su ba. " Ai jiya Abban na ku yazo ya jima nan bayan fitar ka ". Murmushi BILAL yayi yana jin daɗi har cikin ran sa. " Ke yar gurguwa ya ƙafar da sauƙi ko ?" Ya faɗa yana kallon REENA da take ta murmushi dan indan kewar sa sunyi kewar sa dan tun da ta kwanta ciwon ƙafa basu leƙo shi ba gaba ɗayan su Bilal shi kaɗai yake tahowar sa. Baki ta tura gaba fahimtar da ita yake Kafin hawaye suka cika idon ta tuno azabar da ta sha kafin ƙafar ta samu sauƙi " Ya isa haka Allah ya tsare gaba a ƙara kulawa da hanya " Ya furta yana wanzar da guntun murmushin sa kasancewar ya san komai duk da Bilal ya ɓoye masa amma ya ji komai gurin Samira jiya da ta zo gai she da shi itama gurin Hamida ta ji komai dan ta je gidan wayewar safiyar da abun ya faru ne ta ji komai bakin Ummah. " Yaushe zaka koma aiki na san hutun na ka ba mai yawa bane ko " ? Yayi maganar yana kallon Bilal da ya ajiye wayàr ta sa yana kallon kakan na sa. " In sha Allah zuwa farkon azumi zan koma,duk da hutun ba mai yawa bane dama na ɗauko ". Kai Baba Mai Billions ya gyaɗa yana murmushi kafin ya kalli Leena ya ce " Matas shirun dai yau babu magana " Murmushi tayi kafin ta ce " Akwai magana man mun kusa zama manya daga wannan shekarar sai wata zamu je senior section " Ta kai ƙarshen zancen tana Murmushi. Reena kuwa dariya ta yi itama mai haɗe da murmushi tana furta " Muma mun kusa zama irin su Anty Hamida da Samira mu riƙa fita mu kaɗai ba tare da kowa ba ". Dariya mai nuna jin daɗi Baba mai Billions yayi yana kallon su. " Ashe amare na sun kusa tare wa, na ku sa zama Sabon Ango na yar da Kaka tsohuwa " Shigowar Kaka dai dai tsakiyar falon ne da ta shige Bedroom ɗin ta bada jimawa ba ya kai ƙarshen maganar yana sakin murmushi. Murmushi Kaka tayi tana ɗan hararar Baba mai Billions cike da murmushi ta furta " ai mu tsohuwar zuma ce,sai dai ayi da mu a bar mu,idan muma aka matsa mana sai muyi sabon Aure,ga ango na nan a hannu ",ta nuna Bilal dake zaune yana murmushi fuskar sa sai sa. Dariya Baba mai Billions yayi yana furta " Tsohuwar zuma sai da wuta".Dariya Kaka tayi tana zama kusa da Leena. " Ni ba zan iya Auren Tsohuwa ba,na bar wa Baba mai Billions yayi ta kaya mu sai masu jini a jika ". Hararar shi tayi haka ma Baba mai Billions dariya ya saki yana kallon su. Kafin ya furta " Ko dambe aka haɗa mu sai mun chanye ka Indai gasa ce,dan mu rainon tuwon dawa ne bana ice cream da indomie ba " Dariya Bilal yayi haka ma Reena ganin yadda B B yayi da hannun sa alamar yana da ƙarfi irin mugun ƙarfin nan.Ita ko Leena kallon su kawai take yi dan ta kasa sakewa. Haka suka cigaba da ta ɓa fira cike da barkwanci da sakewar su har Hamida ta shigo aka cika taro da ita tare da Samira wadda ke ta rawar ƙafa tana bawa BILAL kulawa yana share ta ko kunyar su Kaka bata ji.Sun daɗe a wajen sa kafin suka shiga suka gayar da Mahaifiyar su Samira da sauran jama'ar gidan sannan suka yi Musu Sallama. *** Ƙamshin sa ne ya zagaye makeken falon kafin ta kon tafiyar shi mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ya fara shiga kunnen Abbu da Mubarak da ke zaune suna magana wanda baka jin abinda suke faɗa sai kukan Ac da ke tashi haɗe da sanyin turare mai daɗi da yake garwaye da falon, dan musamman Abbu yau ya tare falon bayan ya tado sa dan in bai fito ba ya koma ya sako shi gaba,dan tun safe yake son ya fito da shi zuwa ƙauyen su Shatou duba aikin da ake yi ya san halin shi tsaf zai kasa yin tafiyar kamar kwana biyu da suka wuce ya zille wa tafiyar wadda sai yau Allah ya nufa za,ayi ta dan Abbu da kan sa ya shiga bedroom ɗin sa ya tado shi dan haka kyakkyawar fuskar nan ta sa take a ɗaure dan gaba ɗaya ji yake an takura masa ba yanzu ya so yin tafiyar ba.Murmushi Abbu yayi yana kallon sa ganin yadda ya tura bakin sa gaba kamar wani ƙaramin yaro ɗan goye.Sanye yake cikin wasu haɗaɗdun riga da wando masu kyau yan Companyn le vanor tsadaddu yana sanye da riga ruwan shuɗi da Black blue jeans sai p cap da yaɗaura akan sa mai ɗauke da rubutu kamar haka ANGEL.cikin tsari mai kyau da burgewa kwantaccen gashin kan sa ya kwanta luff agefe da gefen cap ɗin sa Black blue,sai takalmin sa rufaffu suma masu tsada da kyau blue Black. Murmushi Mubarak yayi ganin yar hararar da ya sauke masa ta gefen ido wadda ba kowa zai iya lura da yayi masa ita ba. Abbu cike da sakin fuska da murmushi ya furta " Masha ALLAH bayan ya gama ƙarewa ɗan na sa kallo ya so ace shigar manyan kaya yayi amma ko hakan babu laifi ɗan na sa kyakkyawa ne Masha ALLAH. Cike da ƙasaita da natsuwar sa ya ƙara sa saukowa fuska ya shagwaɓe a hankali yana zama kusa da Abbu da yake ta murmushi. Kan sa ya shafa a hankali sannan ya ce " Masha ALLAH,Allah ya tsare muku hanya yayi albarka ya baku iyalai masu albarka " . Cike da farin ciki ya amsa da Amin sai dai Abbun ne kawai ya ji shi dan akan laɓɓan sa yayi ta. Addu'ar Abbu ta ƙarshe kuwa bata samu amshi ba sai ma lumshe idanun sa da yayi hakan da yayi ya sa Abbu girgiza kan sa kawai yana cigaba da murmushi shiko Mubarak cike da jin daɗi yake Amsawa da Amin yana yin ƙasa da kan sa a addu'ar ƙarshe ta Abbu da ya ɗan jima kunya. Miƙewa yayi a hankali bayan ware idanun sa sannan a hankali ya furta " Abbu sai mun dawo ". " Allah ya tsare hanya banda rigima da ƴaƴan mutane ". Abbu ne yayi Furucin yana sakin ƙayataccen murmushi wanda MAHAJ da maganar ta bashi mamaki yake ɗan satar kallon Abbun na zancen sa mai haɗe da murmushin sa da ke nuna farin cikin sa a fili,kan shi ne ya ɗan ɗaure masa yana mamakin yadda aka yi Abbu ya sako wannan zancen sai dai kamar zai ce wani abu bayan ɗan ƙara waigowa da yayi ya ɗan ƙara satar kallon Abbun,sai kuma ya sa kai ya fice yana baza ƙamshin sa a ko wane saƙo da lungu. Muby kuwa ƙaramar dariya yayi fahimtar inda furucin Abbu ya nufa kafin shima yayi wa Abbu sallama tare da bashi tabbacin zasu kula da hanya.Addu,a ya ƙara bin su da ita yana Amsawa da Amin har ya fice daga ƙaton falon gaba ɗaya. Murmushi ne ya cigaba da wanzuwa akan fuskar Abbu kafin ya ɗan girgiza kan sa ya miƙe yana gyara zaman hular sa door ɗin da zata sadaka da part ɗin Aiyah ya shiga da Sallama ɗauke a bakin sa. Zaune ya same ta kan darduma tana lazimi dan gama sallar walhan ta kenan dan Aiyah akwai ibada matuƙa. " Aiyah Barka da safiya " Abbu ya furta a natse yana mai tanƙwashe ƙafafun sa kusa da sallayan ta mai taushi da take kai. Kasancewar ta saba bayan gaisuwar bayan Sallahn Asuba idan zai fita irin wannan lokaci dole zai shigo yayi mata ina kwana tare da mata ya fita ta yi masa addu'a. Shafe addu'a tayi tana sakin fuskar ta a hankali ta amsa masa tana furta " Har za,a fita ".Da murmushi kwance akan fuskar ta. " Eh Aiyah zamu yi meeting da shugaban ƙasa ne by 10" Kai Aiyah ta jinjina cike da sakin fuska ta ce " Allah ya taimaka ya bada nasara ya sa awanye lafiya ". " Amin ya hayyu ya qayyum " Abbu ya amsa cike da jin daɗi kafin a hankali kuma murya cike da raunin da yake ɓoyewa ya furta " MAHAJ ma sun fita ƙauyen chen duba aikin nan da ya fara ". Ya kai ƙarshen zancen kamar mai jin tsoron ƙarasa zancen ko tsoron abinda Aiyah zata tai masa. Aiyah kuwa take fuskar ta ta chanza ta haɗe rai kamar an mata saƙon mutuwa shiru ƙaton Falon na Aiyah da ya ke tsit ya ƙara ɗauka sai sautin AC da ke ɗan tashi.Kafin a hankali jiki mace Abbu ya miƙe ganin bata da niyyar cewa komai. " Na tafi sai na dawo " Abbu ya furta a hankali jikin sa mace. " A dawo lafiya ". Aiyah ta furta ba tare da ko ta kalli fuskar Abbun ba dan ta tsani ganin Damuwar sa ko kaɗan shi ya sa ma take ragawa mahaj a gaban idanun sa. Har ya cire rai da tsammani ya kai tsakiyar falon jikin sa mace yana gyara Babbar rigar sa ya tsinkayo Muryan Aiyah na furta " Allah ya sanya albarka ". Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya furta Amin yana ficewa daga sashen gaba ɗaya dan ya san da wa take wannan addu'ar,wanda ita kan ta Addu'ar ya san bata da zaɓi ne yanayin sa ta duba Damuwar da ta wanzu akan fuskar sa. Sashen Ammah ya shiga bai jima ba sai gashi ya fito dan dama sunyi Sallama ya shiga ya ƙara duba jikin Samrah ne da take fama da mura kwana biyu na sanyin ice cream da MAHAJ ya ke ɗan fita da ita tana jido shi. Direct yana fitowa ya shige ɗai daga cikin danƙara danƙaran motocin sa da suke Parkey a gefe gwanin burgewa.Bayan motar ya shige kamar ko yaushe bayan bude masa motar kafin suma suka fice tare da mota ɗaya ta sauran masu kula da shi da suka rage. A ɓangaren MAHAJ kuwa yana fita mota ya faɗa yana gyara zaman sa tare da jingina da seat dan dama masu wankin motocin sun gyara komai an kimtsa sa da duba lafiyar su dan fitar ta su da ta Abbu ɗin. Muby kuwa da zuwan sa shima fuskar sa kwance da murmushi ya shige motar tare da kunna ta suka bar harabar compound ɗin tare da mota uku sai budaɗdiya guda da Abbu ya tilasta masa fita da su dan kariyar lafiyar gudan jinin sa abun son sa da farin cikin sa. A jere suka fice gwanin burgewa bayan wangale musu ƙaton gate ɗin da aka yi koda suka iso dai dai fankacecen gate ɗin estate ɗin take aka wangale musu shi ganin tambarin motar ta sa da duk inda ta shiga sun san mallakin ta duk da ƙarancin shekarun sa ko Amma suna bashi girma sosai kasancewar sa mutun mai tsare gida da kame kan sa ga kowa bayan mahaifin sa. ***A ɓangaren Shatou kuwa yau tun safe ta tashi da fitina dan abinda bata taɓa yi ba yau shi ta yi dan tun gama ayyukan gidan na su da suka zama na ta ne ta shirya ta fice makaranta,makarantar da aka fita da Haushin malam Abu,da Haushin faɗan da Inna ni ta yi mata dan Bibu ta samu ta narka abinda bata taɓa yi ba tun fara wayon ta ko kan ta ta hana dukan Bibu bare wani yau sai gashi daga kawai ya tsokane ta da wasa ta fara jibgar sa bayan kai shi ƙasa dan ma ta shan ma ce sa ne dan Bibu Badai jiki ba yana da ƙirar ƙarfin sa gwargwado,shima da abun ya bashi mamaki sai ya sakar mata jiki ta yi ta kilma da ya ga dai abun na yi ne hakan ya sa ya saki kukan azaba ta yadda Inna ni da ke kusa ta jiyo ta yo kan su cikin mamaki take kallon su kafin ta ɗaga Shatou jikin sa ta na mata faɗa cike da ɗaga murya da ɓacin rai da tsoron da ya dabaibaye ta na wannan sabon abun da ya faru. " Daga kawai na ce mata nan gurin Shanaye bai sharu ba shikenan ta hau ni da bugu,kuma ma tsokanar ta nake yi ". Inna ni kai ta girgiza bayan gama sauraren Bibu da ya kai ƙarshen zancen yana Shesshekar kuka. Ita kuwa bata ce ƙala ba har Inna ni ta gama faɗan ta kafin ta bar wajen,ta wuce ɗakin ta tana kumburan baki. Inna ni kuwa da ke jin kamar ta riƙo ta ta kai mata bugu ko ta jibge ta kai kawai ta girgiza dan ta san ba lallai shatoun ba ce haka kawai jikin ta ke nuna mata kamar ba asalin shatoun ta bace sai dai bata da ikon yarda da hasashen ta dan haka ta Rarrashi Bibu ta taimaka masa ya shirya ya wuce makaranta dan yau bai ko tsaya jiran Shatou ba Inna ni tace ya wuce,ita kuwa tana gama shiryawa cike da kumburin ta,ta bar gidan ba tare da tayi wa ko Inna ni sallama ba,sauƙin ta ma an gama mata ayyukan ta. Dan shi Baffa na yau da wuri ya fita kasancewar yau ranar kasuwa ce. Wannan kenan. Tunda ta isa makaranta bata kula kowa ba har su Amina duk yadda suke ƙoƙarin jan ta jikin su amma abu ya ƙagara dan haka suka zuba mata ido ganin abun bana wasa bane kamar harda cika take tana batsewa kuma hasale take rigima take nema ido rufe dan haka kowa ya sha jinin jikin sa cikin su cike da tsoron abinda zai je ya dawo. Koda aka tashi tara ƙin fita tayi ta hakimce akan yar kujerar su koda suka dawo su Amina ta cinye kusan filin mutun biyu kuma fuskar nan a haɗe babu alamar zata iya sauraren maganar wani,dole suka bar mata seat ɗin gaba ɗaya. Malaman su duk wanda ya shigo yayi Magana bai samu kulawa ba sai su fita iskan ta.A haka aka tashi makarantar sai dai koda aka tashi duk itace ta ƙarshen fita su Amina bayin Allah kusan ƙarfe uku haka suka zauna zaman jiran ta kamar abun dole.✍️ Update zai riƙa sauka a koyaushe harmu kammala Book iñ sha ALLAH. Sai kunyi haƙuri yanzu yadda kuka san mai Aljannu barci haka nike kamar kar mu gama exams da ciwon da na tashi wallahi yanzu da anyi sallahn isha Bani kai 😹🥺labari sai barci dan haka kuka ji shiru shekaranjiya.Wayan ma sai dai mother ta kwashe ta in kwana ya debeni ba ayi hakuri da duk yadda page ɗin ya zo naso ace yafi haka yawa. Ina alfahari da ku.💃👌🤝✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣7️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* 🕳️💕🕳️💕🕳️ Koda ta fito haka ta yi gaba ta bar su tsaye kafin cikin shakkar ta suka bi bayan ta,shima Bibu kasa tafiya yayi,har sai da Shatou ta fito sannan ya bi bayan ta abun ka da ɗan uwa sai gashi ya jera da ita har ya manta abun da ya faru ɗazu kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kan ta. A gida kuwa hankalin Baffa na da ya dawo ya tarar babu kowannen su gida kasancewar lokacin tashi yayi hankalin sa ya tashi,dan koda yayi wa Inna ni zancen rashin dawowar ta su su biyu da wuri wanda itama tana cike da tashin hankali musamman da ta san yanayin da Shatou ta fita sai dai tayi ƙoƙarin dannewa tana kwantarwa da Baffa na hankali. Har fita yayi niyyar yi zuwa nemo su Inna ni ta hana tace suna hanya. Su Amina kuwa jikin su a sanyaye suke bin bayan Shatou da Bibu da Tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kai kamar taga kashi tunda ga lokacin jikin shi yayi mugun sanyi dan haka ya haɗe dariyar da ya zo da ita da murmushi a haka suka cigaba da tafiya kafin kuma yaji ta ja tsaki ta ja burki kallon ta suke yi dan tunanin abun da zata yi kafin su ankara ta yanka a Guje sai dai ƙurar ta kawai suka hango Bibu haɓa ya riƙe sai dai bai yi mamaki ba dan ba yau ne farau ba sun saba sai dai yanayin na ta akwai ban mamaki da tsoro a cikin sa dan ko magana bata yi da kowa ba tun wadda suka yi da safe ta koma Kurman karfi da yaji. Su Amina ma da su jawairiyya basu yi mamaki ba sai dai su Abin ya basu dariya mace kamar mai Aljannu sai dai yau sun ƙara tabbatar da hasashen su Shatou na da iska akan ta dan gaba ɗaya yanayin nata da masu ƙwankwanmai yayi kama dan haka basu bi ta ba suka cigaba da tafiyar su kafin kowaccen su ta iso kofar gidan su ta shigewar ta rai jagule. Bibu kuwa shima ta fiyar shi ya cigaba da yi a tsakanake yana mai cigaba da mamakin sabon halin Addan sa Shatou sabon hali man dan bugun da ta masa da safe bata taɓa masa shi ba tun suna wasan ƙasa na yara kuwa bare yanzu da suka fara hankali da wayau irin na manya. Koda Shatou ta isa gida haka ta faɗa babu sallama tana nishi sai dai tana shiga ta yanke jiki ta faɗi cike da tashin hankali Baffa na da Inna ni suka yi kan ta,Inna ni cikin zuciyar ta kuwa take ayyana dama ta sani sai dai tana fatan kar shatou ta furta komai a gaban Baffa na dan bata shirya Son ya san wani abu ba game da abinda bata da tabbacin shi a yanzu, abinda ta ke yiwa kallon labarin ƙanzon kurege,labarin hikaya,domin kuwa har yanzu kan ta ya kan cigaba da ƙullewa a duk lokacin da ta tuna da zantukan Shatou ɗin sai dai zuciyar ta na bugawa da damuwa a duk sa,a da daƙiƙar da ta tuna kalaman nan taya zata gasgata su,taya zata gasgata zancen Mutanen ɓoye,Halittar da suke da muguwar ƙarya a doron duniya,dan kaso ɗari cikin maganar su kashi biyu ƙarya ce. Numfashi ta sauke mai zafi tana cire wa Shatou Guntun hijab ɗin ta bayan Baffa na ya ɗaura ta akan tabarman da yake kai bayan ya tallabo ta. Hankali tashe Baffa na yake kallon Shatou cike da mamakin yanayin ta da bai saba gani ba sai yau kuma bai taɓa ji ba ko a bakin Inna ni dan su ɗin ma basa zuwa a gaban sa. Idanu ya zuba mata yana ƙare mata kallo kafin ya sauke a jiyar zuciya da numfashi yana jin jijiyoyin jikin sa na kuncewa da ɗai ɗai musamman na kansa da tunani yake neman tarwatsawa a dai dai wannan lokaci.. "akwai matsala,Indai har abun da nake zargi ne ". ya furta a ƙasan zuciyar sa wani irin damuwa na bayyana akan fuskar sa.Addu,oi ya fara tofa mata ganin yadda idanun ta suka kakkafe lokaci ɗaya sannan jikin ta ya ɗauki ciccira kamar mazari.Inna ni wasu hawaye ne take dannewa gudun kar ta nuna damuwar ta fili raunin da take ɓoyewa ya bayyana Baffa na ya fahimci wani abu hakan ya sa ta rintse idanun ta da ƙarfi tana haɗiye ajiyar zuciya ran ta a jagule wata sabuwar damuwa na samun matsugunni a cikin zuciyar ta wadda take ƙara girmama a duk lokacin da Shatou ta samu kan ta a wannan yanayi.A hankali bayan Baffa na ya yayyafa mata ruwan addu,an da yayi yanzu jikin ta ya fara lafawa daga girgizan da yake yi sai dai jikin na ta ya gashe kamar ana rura wuta a cikin sa har hucin yana dukan fuskokin su. Cike da tausayin ta Baffa na ya shafa ma idanun na ta da suke kafe Ruwan Addu'a kafin suka koma yadda suke sai dai basu rufe ba gaba ɗaya suna ma ɗan yin blinking kaɗan. " SHATOU wa tahh " Baffa na yayi zancen cikin sanyin murya mai haɗe da damuwa. Ko motsi bata yi ba duk da cewa ta ji cewar Baffa na ne dan da alama bata dawo hayyacin ta ba har yanzu. Baffa na ganin haka ya sa ya ƙara furta cikin son tabbatar da zargin sa. " Wace ce domin na san wannan ba shatou bace zaki yi magana ko sai an ɗauki mataki yanzu ". Ya kai ƙarshen zancen yana kafe Shatou da ido.Aiko yana aje ayar zancen ta Gwale manyan idanun na ta masu haske ta ɗaura kan sa kai daga nin yadda take zare su ka san ba lafiya ba. Murmushin gefen baki ta saki kafin ta juyar da ƙwayar idanun ta kan Inna ni da take makure idanun ta Sun rikiɗe sun sauya ga hawaye kwance cikin su wanda kowanne irin lokaci tana iya fashewa da kuka. Idanu Inna ni ta saka cikin na Shatou ɗin duk da idanun na ta kallon su ciki da ciki akwai tsoro domin ko ƙyafta su bata yi. Kai Inna ni ta girgiza mata,bayan hango bakin ta na motsi kamar kullum idan sun zo da magana.Sai dai ba zata so ta ji komai ba a gaban Baffa na ba domin dole ne ya san abun da ta furta mata. Aiko kamar ta fahimci abinda Inna ni ke nufi sai kawai ta ɗauke idanun ta,ta mayar kan Baffa na sai da ta masa kallon yan seconni kafin a hankali ta mayar da kan ta gefen Inna ni sai kuma ta fashe mata da kuka. Wani irin bugawa ƙirjin Inna ni yayi wanda har sai dai Baffa ba ya ga alama dan idanun ta sun fito waje sosai na tashin hankalin da ya bayyana a gare ta domin kuwa ta san kukan na Shatou Ko tace mutanen Shatou bana lafiya bane,kuka ne da ke nuna akwai matsala daga abun da take faɗa mata wanda har yanzu ta ka sa gasgata lamarin dan bata san ta inda zata fara ba,domin kuwa abune mai ɗaure kan mai tunani da hankali. Baffa na kuwa haka kawai ya samu kan sa da kafe Inna ni da idanun sa yana kallon yanayin ta da karantar sa kafin a hankali ya ɗauke kallon sa daga gare ta yana sauke numfashi sai dai zuciyar sa ta fara masa wani zancen kamar na da walakin akan yanayin da Inna ni ta shiga dan bai taɓa ganin ta a wannan yanayin ba tun bayan Samun lafiyar Shatou ɗin da ita kan ta na doguwar jinyar da tayi. Kuka ne Shatou take yi wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyar ta jikin ta har girgiza yake yi gashi an kasa samun mai rarrashin ta a haka Bibu ya same su kowa yayi jigumm ga shatou na ta darzan kuka. " Adda shatou "! " Me yake damun ki,?Baki da lafiya ne,ina yake Miki ciwo " ? Wayen nan sune tambayoyin da yake ta jerawa Shatou bayan shigowar ta sa hankalin sa ta she ya matsa kusa da ita kamar zai fashe da kuka shima idanun sa har sun cika da hawaye na Tausayin yar uwar ta sa. A jiyar zuciya dukkanin su suka sauke ganin tayi shiru bayan zaman Bibu kusa da ita.Dan kuwa shima idanun ta zuba masa har sai da ya ɗan tsorata kafin ta janye su kan shi hannunn sa ta riƙo " kafin a hankali ta ƙyafato shi tana nuna masa ya karo kunnen sa kusa da bakin ta dan da alama shaƙaƙƙiyar murya ga re ta ko gare shi Dan har yanzu Inna ni bata san wane jinsin bane na mace ko namiji amma tafi masu kallon mace. Karo kunnen na sa kuwa yayi kafin a hankali ya tsinkayo yar ƙaramar Muryan ta da bai fita sosai ciki ciki take sai ma kana da lafiyayyen kunne zaka ji ta furta. " Ka yi haƙuri ba da gangan na dake ka ba,kuskure ne,Kar ka sanar wa da Baffa na abunda nace amma kana iya faɗawa Inna ni,idan kuwa ya matsa yana son ji ka faɗa masa ". Hawaye ne suka cika idon Bibu a take kai ya girgiza mata share hawayen sa yayi kafin ya yi kokarin riko ta, ta tashi zaune sai dai kamar dutse haka ya ji dan haka ya sake ta yana sauke a jiyar zuciya fuskar sa cike da damuwa dan duk shi ganin yake yi duk shiru shirun da ta koma abun da ta masa ne ke damun ta. Idanun ta ta mayar kan Baffa na kafin a hankali ta masa wata alama kamar ta kurame.Sak kuwa ya fahimta alamar zasu tafi ne suke masa dan haka bai ce komai ba.Kan Inna ni suka juya kafin suka ƙara kallon ta sannan ta fara rufe idanun ta bayan ta sakar wa Inna ni murmushi mai nuna tabbacin akwai damuwa sai dai tunda ta fahimci Inna ni bata son sanin komai ne ne gaban Baffa na sai ta haɗiye komai shine dalilin sakin kukan na baƙin cikin duk da ta san ko faɗawa Inna ni tayi babu abinda zata iya,amma ta san addu'ar ta kamar dafi ce akan abinda ta zo dashi. A haka bacci ya kwashe Shatou jikin ta ya saki sai numfashi da ta fara saukewa a hankali. Baffa na ganin haka ya sa ya sauke ajiyar zuciya kan shi kuwa da yake har yanzu a kulle ya dafe kafin ya miƙe ya fice daga gidan jin kiran Sallah la,asar da ya karaɗe ƙauyen bayan ya sanar da fitar ta sa. Inna ni ma numfashi ta sauke da ajiyar zuciya mai nauyi kamar wadda ta haɗiyi zuciya damuwar ta na sake dawowa sabuwa Badan komai ba sai dan rasa jin abinda suka zo da shi a yau ɗin wanda ta tabbatar babu lafiya tunda ga yanayin Aljannun na Shatou.A haka ta gyara mata kwanciya ta miƙe tare da ɗaga Bibu tana cewa. " Muje ka watsa ruwa kayi Sallah kaci abinci ka kwaso yunwa,Addan ka ta samu bacci ". Babu musu kuwa ya miƙe yana share hawaye. " Baccin ta samu fa kuma zata tashi kaji ". Inna ni ta furta jikin ta a sanyaye ganin yadda Bibun ya kasa sakewa. Kai Bibu ya ɗaga kafin ya shige ɗan ɗakin sa ya cire kayan sa ya canza da wasu sannan yayi alwallah ya wuce masallaci yana dawowa sannan ya shiga ya watsa ruwa yana gama shirya wa ya zauna cin abinci kuma har lokacin Shatou bata farka ba yana yi yana kallon ta har ya gama cin abincin sa. Baffa na kuwa wani uzuri ya hana sa dawowa gidan bai dawo ba sai Gab da magriba kuma yana shigowa ana kiran Sallah dan haka kai tsaye ya yi alwallah ya wuce masallaci tare da Bibu da ya ke ta yiwa Shatou Fifita tana shan baccin ta hankali kwance. Dai dai fitar su kuma Shatou ta fara motsi alamar tashi a hankali kuwa ta fara ware manyan idanun ta da suka ƙara girma da haske tar kuwa ta ware su akan Inna ni dake zaune akan yar zuƙunno ta buga ta gumi tana kallon ta. Ya mutsa kyakkyawar fuskar ta tayi da ta ƙara yin fayau farin ta ya ƙara bayyana sai shinning take yi kamar yadda kuka san fatar nan ta yan Korea mai walƙiya kamar suna wanka da mai na madara. Murmushi ta sakar ma Inna ni kafin ta miƙe zaune cike da kuzarin ta,tana jan doguwar miƙa tare da Nanata addu,ar tashi daga bacci. Inna ni ma Murmushin ta sakar mata tana jan ajiyar zuciya tare da riƙo hannun ta ɗaya.Bata ce mata komai ba sai da ta dangane ta da ɗakin ta,da taimakon ta shatou ta cire kayan jikin ta Sannan ta ɗaura zanen da take wanka dashi. Fitowa Inna ni tayi ta haɗa mata ruwan wanka ta kai mata makewayi. Ɗan leƙawa tayi bayan ta kai mata ruwan ta ce. " Kije ki watsa ruwa na kai Miki ki samu ki yi Sallolin ki,dan ban samu ta da ke daga bacci ba ". " Touh ". Shatou ta furta a hankali babu musu kafin ta fito daga ɗakin,makewayin ta shige ba tare da ta ce wa Inna ni komai ba da ke alwallah. Sallah ta kabbarta bayan gama alwallah. Koda Shatou ta fito Inna ni na Sallah bata ko gama magriba ba. Ruwan Alwallan da ta zuba mata a wata ƙaramar buta ta ɗauka kafin ta yi alwallah sannan ta shige ɗakin na ta.Bata jima ba ta fito ta sanye da wata yar kodadddiyar riga da take mugun so ta roban gwanjo da Baffa na ya taɓa siyo mata da yayi tafiya.Dan rigar da jan ta take yi amma yanzu ta ɗan shige mata dan haka take jan ta tun Inna ni na dariya idan ta sako har ta daina. Kusa da Inna ni ta tsaya ta sanya hijabin ta ta kabbara Sallah lokacin Inna ni ta sallame magriba zata fara nafilan bayan magriba. Magriba ta fara yi kafin ta ranka la,asar A tsanake tayi Sallolin ta koda ta gama su Baffa na sun shigo suna zaune gefe shida Bibu akan yar tabarmar kaba sun zuba mata ido babu ma kamar Baffa na sai dai fuskokin su cike suke da annuri ganin ta zaune harda sallah.Samun kan ta tayi da sakar musu murmushi haka suma. " Ya jikin ki Adda shatou " ? Bibu yayi maganar yana kallon ta. Kai ta girgiza masa kafin ta ce a hankali " Lafiya ta lau fa barci ne kawai ya kashe n,kuma Inna ni bata tashe Ni Sallah ba,gashi sai dai nayi ranko ".Tayi zancen kamar zata fashe wa da kuka dan bata son fashin sallah ko kaɗan ta san zunubin da mutun ke samu wasu malammai ma sunce ba,a karɓanta.Haka malamin su ya sanar musu dan haka take jin tsoron fashin sallah wanda zai saka ta tarikussalah ba tare da dalili mai ƙarfi ba.Na daga cuta,ma,ana rashin lafiya ko tafiya.d.s. Shiru gurin yayi Baffa na kuwa ajiyar zuciya ya sauke domin kuwa abun da yake zargi ne ya ga ya tabbata dan har yanzu ko kwanto yake yi. Inna ni kuwa ba tace komai ba itama sai cigaba da jan charbin ta da tayi tana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Shatou kuwa daga gama maganar Addu'oin ta, ta fara yau babu wanda ya ji abinda take cewa dan cikin zuciyar ta take yin abarta. Yau Baffa na sai ya ga kamar ta ƙara hankali dan haka ya ke satar kallon ta kafin a hankali murmushi ya ɗan suɓuce masa na gefen baki. Bibu shiru yayi yana mamakin ta kafin kuma ya miƙe ya ɗauko Kitabul azkar na su bayan Baffa na ya bashi umurni sannan ya dawo ya zauna. Baffa na ya cigaba da bita masa haka Shatou jikin ta har rawa yake yi ta zo ayi karatun da ita aiko tana gamawa ta dawo kusa da Baffa na bayan ta gayar da Inna ni da ta amsa mata fuska sake. Haka shima Baffa na tayi masa ina yini duk mamaki suka yi dan ba kasafai take wannan gaisuwar ba Ƙiriniyar ta bata barin ta gaisuwar maraice ta safe ce kawai wannan babu fashi dan Bibu yafi ta ƙoƙarin musu ina yini bayan Sallahn magriba. Daga shi har Inna ni murmushi suka yi Acikin zukatan su dan mamakin ta sai dai sun shanye abun su ba zaka taɓa ganewa ba. A haka Baffa na ya cigaba da bita musu azkar ɗin suna sakawa akan su har suka yi wanda ya wadata kowannen su ya bita da kan sa zuwa lokacin kuwa an kira sallahn Ishai.Baffa na da Bibu masallaci suka wuce su kuwa suka tada Sallahn su anan take. Koda suka gama Sallah Shatou ka sa haƙuri tayi dan haka ta buɗe bakin ta tace " Inna ni wai banda lafiya ne,naji Bibu nace wa wai Ya jiki na,kuma lafiya ta ƙalau bacci kawai na sha ". " Sai kuma kema ɗazu da na tashi naga kamar kinyi kuka wani abu ya shigar Miki ido ne " ? Haka ta jerawa Inna ni tambayoyin wadda ke jan charbin ta hankali kwance. Ɗan kallon ta Inna ni tayi kamar bazata tanka mata ba sai chan ta ce " wai dukan da malam Abu ya Miki ne ya ke Miki ya jiki kan sa,Nima kuma ɗazu wani abun ya faɗa Mini ido kamar kin sani da ƙyar ya fita ido na ". Kai shatou ta gyaɗa cikin yarda ta ce " Sannu " cike da tausayin mahaifiyar ta ta. kafin kuma ta ƙara furta " Inna ni Zanje Dandali yanzu ". " Da wuri haka ". Inna ni ta furta tana jin babu daɗi dan bata son fitar ta gaba ɗaya kwanan nan an ma yi sa,a yau ta tambaya da sai dai a neme ta a rasa ta ja Bibu sun fice. " Ehh wasan gala gala zamu yi,kuma yau bana son Rakiyar Bibu yayi baccin sa ". Kai Inna ni ta jinjina tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ce. " Abin cin kin fa ba,ba kya jin yin wa ne " ? " Eh na ƙoshi sai na dawo ". Kai Inna ni ta girgiza kawai kafin a hankali ta furta. " Ki kula in kika fita kuma banda yin dare ". Cike da farin ciki Shatou ta ce. " Tau zan kula ". ko gama Addu,an bata yi ba kuwa ta miƙe ta chanzo riga yar doguwa ta atamfa da ta ɗage mata sannan ta ɗauro ɗankwali irin dai shigar da kuka san matan ƙauye na zuwa dandali da ita ta fice bayan ta yiwa Inna ni sai ta dawo. Koda ta fita Inna ni ajiyar zuciya ta ƙara saukewa tare da bin ta da addu'ar kariya. A ɓangaren Shatou kuwa tana fita gidan su Jawairiyya ta fara shiga da ke kusa da su maman Jawairiyya da gama sallahn ta kenan ta kalle ta da mamaki ta ce. " Wai dandali za,a je yanzu da wuri haka,Amma dai A'i bata gan ki bata san kin fito ba ko,wannan irin sako haka " ? " Sai da na tambaye ta sannan ". Shatou ta bata amsa tana cunno baki gaba. Kai maman Jawairiyya ta gyaɗa bata ƙara cewa komai ba dan dama ita bata tauye yar ta abu ɗaya ne bata so shine ta yowar dare,dan ma dai kawai ta san dalilin da ya sa Inna ni take yi wa Shatou katange ya sa yanzu tayi mamakin fitowar Shatou haka da wuri dan haka ta shanye mamakin ta da amsar da shatoun ta bata. A haka suka shirya cike da murna da sakewar da shatou tayi haka suka fice da Jawairiyya daga gidan, gidansu Amina suka wuce nan ma maman ta sai da ta magantu amsa ɗaya ta bata itama dan haka itama Amina da take cike da tunanin shatoun ta yi ta murna maman ta kuwa abun har mamaki ya yi ta bata dan da ta dawo harda kuka tayi mata na yadda Shatou ta share su sai gata kuma ishain farin ta zo da sakin fuskar ta kamar ba ita ba. Suna fita suka yi gidan su Ramata chan ma basu jimaba sun same ta har sun gama sallah dan haka a take su ka yi dandali su hudun su a jere suna wasannin su har suka isa duk da suna ɗan shakkun Shatou ɗin amma sun sake ganin yadda ta wartsake musu kamar ba ita ba. Sune farkon wayen da suka buɗa dandalin yau dan haka suka samu waje suka zauna suna yan wasannin su na hannaye a haka wajen ya fara cika da jama'a yan yara matasa irin su kafin suma Mazan su fara zagaye wajen suna zama akan ɗan dakali da ke wajen wasu akan kara wasu jingine a kan bangon dake kusa da wajen na tsohon gidan mai gari. Waje na cika dan har su iro sun cika wajen suka fara wasannin su cike da nishaɗi da burgewa. Ita da Nazihwa kamar ba su yi faɗa ba suka sake ma juna aka cigaba da wasa sai dai shi Shamsu fa ya riga ya ƙullaci Shatou da gaske dan haka ya ke Binta da ido duk motsin ta yana kallo dan yau ya sha alwashin sai yayi maganin ta cikin daren nan dan bata isa ta taɓa masa Nazihwa ba ya ƙyale.Shi ko Iro ganin an ɗan kwana ya sa ya share da zancen Shamsu dan tunanin sa ya bar maganar duk da ya san halin sa mugun mutum ne Shamsu ko tsakanin su ta haɗa su sai anyi da ƙyar yake saki maye ne ɗan Bala'i dan sun tabbatar da ace Shamsu maye ne duk wanda ya kama sai buzun sa. A haka suka yi wasannin su cikin sakewa cikin ikon Allah yau har an ka gama ba,ayi rigima da kowa ba an wanye lafiya. Suna gamawa kowaccen su ta kama hanyar gida Iro hankalin sa ya ɗauku saboda wata gardama da suke yi a tsakanin su har Shatou da yake ta bi da ido ta bar wajen bai lura ba, yau ba ma hanya ɗaya suka bi da su Amina ba kowa ta sa ya kama dan haka tafe take tana juya ɗan karen dawar ta,da ta samo a wajen dandalin tana yan waƙe waƙen ta.Sai dai Turus ta ja ta tsaya ganin mutun gaban ta kamar an jeho sa. Wata irin ƙatuwar sanda dake hannun sa ta tsirawa ido kafin ta kai kallon ta kan fuskar sa da take babu annuri ko magana bai yi ba ya ɗaga ƙatuwar sandar yana neman Kaita jikin Shatou wadda ta waro idanun ta da ƙarfi ganin da Dagske a jikin ta zata sauka ga wani tsoro da ya saukar mata ganin bata da mace ci sai Allah bata kuma da abun kare kan ta sai dai ba zaka taɓa gane cewa a tsorace take ba ta shanye harda riƙe ƙugu irin in ka isa ka taɓa ni,ai kuwa akan ta ya sauke sandar da wani irin ƙarfi sai dai wani abu ta ji ya tokare mata akai sandar bai sauka akan ta ba hakan ya sanya ta buɗe idanun ta da ta rufe ruff tana jiran tsintar kan ta wata duniyar mai cike da wahala. Iro ne ta gani gaban ta yana zare ido cikin ɗan hasken farin watan da ke zagaye da su ga hannun sa ɗaya akan ta riƙe katuwar sandar Shamsu da ya fara kiciniyar sai ya sauke ta jikin Shatou ɗin ran sa ɓace dambe ne ya kachame tsakanin su ita kuwa Shatou cike da mamakin yadda akayi Iro ya san ta nan ta biyo ta matsa baya tana haɗiye tsoron ta tare da ɗan jin sanyi a ranta na zuwan Iron dan ta san da yau sai su Baffa na sun yi kukan rasa ta. Ganin yadda dambe ya kachame tsakanin su hakan ya sa da baya baya ta fara tafiya kafin ta ɗaga ƙafa ta yanka a Guje tana ɗan waigen su. Su ko su Iro abokan sa ne da suka biyo bayan sa suka raba faɗan dan dama wani daga cikin su ne da bai je da wuri ba ya sanar da Iro ya ga shatou a wannan hanyar da zai taho nan dan haka ya biyo bayan ta sai sai dai kuma ya tarar da shamu ya tare ta yana batun mata illa dan ya san ya aje wannan sandar ta sa jikin shatoun sa sai ya mata illa ƙila ma ya karya mata ƙashin baya. Da ƙyar suka raba faɗan abun ka ga ƙarfi da ƙarfi sai da suka yi da ƙyar suka raba dan kowannen su yaji jiki babu wanda yake baya wajen ƙarfi da rigima. Gida suka wuce da Iro sai dai ya zille sai bin bayan Shatou da yayi yana huci. Sai dai har ya kusa isa gidan su bai ga mai kama da ita ba dan haka ya tabbatar cewa ta isa gida lafiya.Sannan ya wuce gida yana jin yar natsuwa na saukar masa. Shiko Shamsu wata sabuwar gobarar ƙiyayyar Shatou ce ta ƙara ruruwa a cikin zuciyar sa nan yayi ta shan alwashin illa ta ta, ta hanya da ban da ban.Sai da ya zage ta tass ita da Iro kafin ya wuce gida yana ƙara jin zafin ta har Iron musamman ganin bakin san ya fashe dan ya shafo jini ga shi yana jin zugi kaɗan kaɗan. A ɓangaren shatou kuwa a Guje ta faɗa gidan Baffa na da ke zaune yana duba wasu littafan sa dan jiran Dawowar ta saboda hankalin sa da ya ƙi kwanciya ya ɗaga ido ya Kalle ta dan abinda Inna ni tayi bai masa daɗi ba amma ya san tana da dalilin barin ta fita gashi ba ta ma san rigimar da aka yi shekaranjiya ba.Dan ya san da ta sani da ba zata barta ta fita ba gashi shi da na shi dalili mai ƙarfi da bai son yawan fitar ta ta dan haka ya ke ƙoƙarin saka mata ido akan komai da take yi. Inna ni da ta fito wanke hannu kasancewar tana ɗakin ta ne ta ɗauke kallon ta daga kan Shatou da ta gama ƙare ma kallo wadda ke ta sauke numfashi daga inda take tsaye. Sai kuma a hankali kamar wadda aka matsi bakin ta,ta ce " Lafiya kika faɗo haka babu sallama ".?Ta yi mata tambayar ba tare da ta kalli ƙwayar idon ta ba. " Inna ni faɗa fa ake yi da Iro da Shamsun mai guru ". Sai da ta yi zancen sannan ta rufe bakin ta tana zare ido dan ta san dole za,a tambaye ta dalilin faɗan na su wanda dole zata ce itace sila gashi Inna ni bata san farkon rigimar ba,haka ma Baffa na wanda bata san ya san komai ba. Hmmm kawai Inna ni tayi kamin ta ce. " Ki wuce ki kwanta ki tabbatar kinyi addu'a kafin ki kwanta,abincin ki na nan ki tabbata kin ci ". Kai ta gyaɗawa Inna ni kafin ta wuce sum sum alamar rashin gaskiya.Inna ni idanu kawai ta bi ta da su tana girgiza kan ta haka ma Baffa na ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani tunani akan wannan rigimar na ɗarsar masa.A haka ya gama duba littafin na sa ya shige bayan sun yi sallama da shatou da ta masa sai da safe haka ma Inna ni dan Bibu yayi baccin sa tuni tunda suka dawo ya ji labarin shatou ta fice kuma ta ce ta yau bazata je da shi ba yayi alwallah ya shigewar sa yayi baccin sa hankali kwance bayan ya ci abincin daren sa. Miƙewa Baffa na yayi ya saya gidan kamin ya shige shima. Sai da yayi ta juye juye kamin bacci ya kwashe sa, ya daɗe yana tubka da warwarar yadda zai yi da rigimar da ta shiga tsakanin Shatou da shamsu sauƙin ta ma ta samu mai tare mata duk da bai son wannan shisshigin na Iro amma yakan ji daɗi da kariyar da yake bata. Inna ni yau ma ta daɗe zaune kafin ta kashe haske ta kwanta bayan ta yi addu'a cikin yardan Ubangiji kuwa bacci ya kwashe ta mai daɗi sai dai bacci ne mai cike da mafarkai. A ɓangaren shatou kuwa bayan ta gama cin abincin ta,wanda ta ci kadan ta sha ruwa,ta kwanta,ta daɗe tana tunanin wannan ƙarfin hali na Iro duk da ta ji daɗin yadda ya shige mata faɗan matuƙa dan ta san ko giyan wake ta sha bazata iya dambe da Shamsu ba. A haka cikin tunanin bacci mai nauyi ya kwashe ta kasancewar tayi Addu'an kwanciya bacci. ***Yau Shatou a sake ta tashi cike da fara,a dan haka suka yi duk wasu ayyukan da suka saba yiwa Inna ni ita da Bibu kafin suka fice makaranta bayan sun yi wa Inna ni da Baffa sai sun dawo kasancewar Baffa na yau bai fita da wuri ba ya ɗan tashi da ciwon kai. Koda suka isa makaranta kowa ya san yau Shatou ta dawo ta asali ba shatoun jiya ba ce. Dan haka kowa yake kokarin shige mata aka cigaba da yadda aka saba farin cikin Amina ya kasa ɓoyuwa dan koda ta zo makarantar a tsorace take ta yi zaton Shatou ta chanza musu sai ta tarar da aka sin haka dan haka take jin daɗi kamar ta goye shatoun kuma Shatou ta fuskan ci hakan da dukkanin su ma sai dai bata tambaye su ba ta share. A haka aka tada su tara suka fito gida kowannen su gida yayi dan an basu dama yau ɗin dan haka Shatou tana cikin masu zuwa gidan su Amina kuwa duk basu je ba dan sun san dole zasu yi latti a zane su Gara ita sun san bata jin tsoron bulalan sosai dan tana mazewa kar a raina ta. Gidan ta wuce sai da ta ci abinci Inna ni nata mita sannan ta fito ganin tana neman yin latti. Koda ta fito gida ta ci karo da Iro.Yana ganin ta ya washe baki.Gaba tayi kamar ba zata tanka masa ba da sunan ta da ya kira. Har ta ɗan yi gaba ta tuno da taimakon da yayi mata jiyan sai ta ɗan ji Tausayin sa hakan ta sa ta ja burki tana juyowa tana kallon sa,sama da ƙasa ta gama ƙare masa kallo kafin ta yatsine fuskar ta sannan kuma ta sake ta. Sannan a hankali ta amsa da " Na'am " bayan ya ƙara kiran sunan ta har da wani haɗawa da ta.Na nata sunan ta yi wai Shatou ta sannan ta ja ƙaramin tsaki iya laɓban ta shi ko sokon sai ya ga kamar tayi masa wani ɗan style na murmushi daya ga ya ƙara mata kyau. A haka suka jera suna tafiya Iro na jin kan sa sama sai washe jajayen haƙoran sa yake yi.Dan Shatou hakan ne kawai take ganin mafitar rabuwa da iro lafiya,musamman da ya fara yi mata amfani ko dan haka yanzu dole ta ƙara sake masa dan ya dagargaji maƙiyan ta dan shatou ba dai wayau ba shi ya sa yanzu ta saki fuska tana sauraren labarin faɗan su na jiya da yake bata wani abun tayi murmushi wani ta ɗai juya kai. *A ɓangaren su MAHAJ kuwa kasancewar suna da lafiyayyun motoci basu wani jimaba suka iso ƙauyen. Kasancewar ba baƙi suke ba Mubarak da sauran drivers sun san inda ake aikin ya sa basu tafi wajen mai gari ba direct suka kama hanyar wajen. Jingine yake da seat ɗin motar kamar yadda suka fito da Bluetooth a kunnen sa yana sauraren ƙira'ar minshawi idanun sa a lumshe p cap ɗin sa ya juyar da kan ta baya ya sanya haɗaɗɗen radon sa baƙi wulik mai kyau da ya ƙara wa fatar sa armashi da kyaun sa da yake fitar da wani annuri na haske na Hutu,arziki,da lafiya. Gudun motar ta su Muby ya rage kasancewar ya hango ta tun daga nesa haka kuma ya gane wanda take tare dashi ɗin dan haka ya ɗan saci kallon MAHAJ ta glass ganin bai lura da ita ba ya sa da gangan Muby ya ci wani irin burki wanda ya saka MAHAJ dake jingine kamar baya numfashi buɗe kyawawan idanun sa masu haske yana sauke su akan Muby ɗin. " Sorry ina gudun rigimar yarinyar chan ne kar mu tada mata da ƙura ya sa na rage gudun motar sai kuma ta nemi kubce mini dole na taka burki da sauri ". Muby ya faɗa yana danne Dariyar sa tuno farkon haɗuwar su da ita.Da mamakin ta gata yar mitsitsiya tana fira shi gaulan sai sakin baki yake yana kallon ta. MAHAJ da bai wani fahimci wace yarinya yake zance ba ya ɗauke idanun sa daga kan sa yana lumshe su kamar yadda suke sai dai kuma jin Muby ya tsayar da motar ya ƙi cigaba da tafiya ne ya sa ya zare space ɗin sa a hankali yana bin Muby da kallo na zargi. Sai dai bai iya yin kallo mai tsawo ba hakan ya sa ya ɗauke idanun sa daga kan sa. Ya ƙara lumshe idanun sa tare da mayar da glass ɗin na sa. Tafiya Muby ya cigaba da yi a hankali yana fatan Allah ya sa idon Mahaj ya kai inda yake buƙata yaga Abokiyar faɗan sa.koda suka gota su ya ji haushi na rashin ganin ta da Mahaj ɗin bai yi ba. Sai dai abun da bai sani ba dai dai sun iso wajen MAHAJ da ya ke ƙara mamakin abinda Muby yayi ya ware idanun na sa da ƙyar ta cikin rado ɗin na sa ta yanda mai zato ba zai taɓa zato ba ya ɗan saci gefe da gefen motar sai dai kamar an ce ya ɗaga idon sa ta gaban su sai gashi ya sauke ganin sa kan ta a hankali kafin Iro,tana ta washe bakin ta abunda bata saba yi ba da kowa idan ba Bibu ba da su Amina. Dan dai dai lokacin ne Iro yake gaya mata Yadda ya yaga bakin Shamsu ya san harda jini yayi. Yana bata labarin yana dariya itama haka dan ta ji daɗi ta ji ƙeta.Aiko Iro sai kallon ta yake yi har ya shagala ganin yadda dimples ɗin ta yau suka wani bayyana haɗe da yar ƙaramar wushiryar ta suka ƙara mata kyau na musamman. Idanun sa ya ɗauke da sauri kamar wanda ya ga kashi dan dukkanin su ya gane su tsaf,kuma idan ba mistake yayi ba abinda Muby yayi,yayi hakan ne dan ya ja hankalin sa.Ƙaramin tsaki ya ja a ƙasan laɓɓan sa wanda shi kaɗai ya ji fitar abun sa. Har suka gota su bai ƙara ko tada kan kan sa ba hasalima idanun sa a lumshe suke. Ita kuwa Shatou haka kawai ta dakatar da dariyar ta tana bin danƙara danƙaran motocin da kallo a hankali kasancewar haka kawai ta ji alamar kamar ana kallon ta ganin bata ganin komai har suka wuce ya sa ta janye idanun ta kan su. Shi ko Iro da ya shagala da kallon ta sai da suka matsa nesa da su kaɗan sannan ya lura da motocin...✍️ Yau dai da alama mutanen zasu ƙara haɗuwa fa 🚴🚴🚴😅 Ohni yar babanta Shatoun ku rigima gare ta.Arado Allah ya sa ta bar mana Mahaj ɗin mu kar ta saka mana ciwon kai.🚴🚴🚴💃💃😂 Page biyu ba haɗe muku na jiya da na yau.🙏🙏🙏🚴🚴🚴 Typing 🥺🥺🥺A samu wata hiliss ta muna typing 🚴🚴 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ Book one free Book two and three paid N#800 an samu discount. Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya. *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣8️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ Not edited😴 _____________ " Lallai fa kamar baƙin nan ne suka zo masu aiki zasu duba aikin ina ga kamar motocin su ne ". Iro yayi zancen yana ƙara ƙure motocin da kallo da suka ɗan yi nesa da su kaɗan kamar zai hango wanda ke cikin motar. Shatou kuwa bakin ta,ta mere bayan ta ɗauke idanun ta daga kallon motocin. Iro kuwa da gama furucin ya cigaba da bata labarin faɗan nasu kafin ya koma bata wani labarin daban.Shatou tayi zaton zai wuce sai dai ta ji ya cigaba da tsiyaya surutu kamar fanfo dan haka tun tana ƙaƙalo murmushi har ta kai ta haɗe fuskar ta dan dole fahimtar hakan ne da Iro yayi alamar ta gaji hakan ya sa ya fara ɗan kame kame yana ƙyafce ƙyafcen ido. Haka ta cigaba da tafiya kafin ta fara zabga sauri tun Iro na cimmata har ya kai tafiyar ta su ta rabu dan ta yi gaba. Kafin kuma ta runtuma a Guje sai kuma ita da kan ta abun ya bata dariya ta cigaba da ƙyalƙyala dariyar ta ita kaɗai tana gudu tana waigen Iro da shima ya biyo bayan ta yana dariyar sa kamar wani wawa yana kiran sunan ta da alamar ta tsaya,sai kayi zaton wasu masoya ne na asali yadda suke yi.Har ta zo ta gota mutanen da ke tsaye gurin bata lura ba duk da ta ji yadda wajen ya gauraye da ƙamshin daddɗan turare. Bata tsaya ba sai da ta tsinci kan ta cikin makarantar sannan ta dakata tana nishi. Malam Bello dake nan yana duba wasu takardu daga tsayen da yake ya ɗago idanun sa ya kalle ta,ganin Shatou ce ya sa ya galla mata harara.Ita kuwa shatou sanda ƙirjin ta ya buga ganin malam Bello dan ta san halin sa duk da haka kuwa ta shanye tsoron ta.Baka taɓa ganewa sai dai idanun ta da take ta ƙyaftawa,alamar rashin gaskiya,dan ta san bata da gaskiya ta yi latti ta san dole zata iya samun hukuncin sa tunda mugu ne. Malam Bello kuwa cike da faɗa bayan gama sakar mata harara,Ya furta " Zo nan " .Babu musu Shatou kuwa ta zo ta tsaya kusa da shi kaɗan tana tura bakin ta gaba ga ƙirjin ta dake bugawa kaɗan na ɗan tsoron bulalar sa. " Uban me ya hana ki dawo wa da wuri har aka shige aji " ? Shiru ta masa taƙi ko ɗaga ido ta kalle sa. Ran malam Bello ne ya ɓaci dan haka ya ce " Sun kuya nan ". Bakin ta, ta ƙara turawa gaba kafin ta kai guiwowin ta ƙasa tana yin kneeldown. Malam Bello yayi zaton ta bashi haƙuri sai dai shiru har bayan ɗan lokaci hakan ya ƙara tunzura shi dan haka ya ƙara sanya ta ɗaga hannuwan ta sama tare da rufe idanun ta. A ɓangaren shatou ƙafafun ta sun fara ciwo matuƙa amma saboda taurin zuciyar ta kasa ce masa yayi haƙuri. Ga wata zuciya da take jin tana ta so mata kamar ta miƙe ta yi gida,taana ji duk wanda ya tara ya samu. Kuma ta sha alwashin ba zata taɓa bada haƙuri indai har malam Bello ne. A ɓangaren su MAHAJ kuwa suna zuwa bakin inda aka gina ruwa tare da sanya manyan tankuna na ruwa da ake akan aikin su, nan suka dakatar da motocin na su.Da ƙyar uban gayyar ya fito daga mota. Ko shi sai da ya gama shan ƙamshin sa sannann ya fito yana gyara zaman p cap ɗin sa da ya juyar da ita. Bakin motar da ya fito ya jingina bayan sa yana ƙare wa wajen kallo da sauran filayen ƙauyen dake zagaye da wajen. Bai ɗaga daga nan ba har su Muby suka fara zagaya wajen. Tare da jama'ar garin da suka ɗan taru a gurin,suna satar kallon MAHAJ ɗin da gaida shi wanda sai dai ya ɗaga musu hannu kawai fuskar sa sanye da glass ɗin sa da yake ta ƙara yiwa kyakkyawar fuskar sa armashi. Mafi yawan jama'a sun bi bayan Muby da yake duba ayyukan dan ogan ya gincire anan ya ce su je kawai. Yana ɗan ganin komai daga nesa. Sai ya zamo daga shi sai masu tsaron sa aka bari sai yan tsirarun mutane da ke bin sa da kallon ƙurilla. Da kallon ya ishe sa sai ya juyar da jikin sa yana facing motan tare da ɗaura hannuwan sa jikin kan motar yana jan ƙaramin tsaki.Na kallon da yake jin ya dame sa dan shi mutun ne wanda ya tsani a yi masa kallon da ya wuce ɗaya ya tsani kallo yana daga cikin abinda ke takura masa. Ya ɗan daɗe tsayen inda a hankali a hankali yake jan tsakin da bai san dalilin jan sa ba yanzu ga idanun sa da suke a lumshe ta cikin space ɗin. Gajiya da tsayin da yayi ne abun ka ga ɗan Hutu ga yar ranar da ta fara yin zafi da haske tana kasar masa fata hakan ya sa ya juyo a hankali da niyyar komawa cikin motar da bawa masu tsaron na sa umurni. Ɗan kallon gefen sa na dama yayi a hankali sai dai kamar haske hakan ya hango ta tana falfala gudu kamar wata balbela,Bakin ta sake tana dariya,Sai ga Iro bayan ta shima yana dariya kamar wani wawa. Kallo ɗaya dukkanin su yayi musu ya ɗauke idanun sa yana yatsine fuskar sa kamar wanda ya ga kashi da jan ƙaramin tsaki da ya tsaya iya laɓɓan sa. Hakan ta wuce a Guje kuwa ta gaban su ba tare da ta kalli ko ɗayan su ba kasancewar hankalin ta ba nan yake ba kawai ta tsinci kan ta makaranta take buƙata dan ta san ta yi lattin dawowa sannan bata son wanchan nataccen ya ƙara tsayar da ita,dan ita kaɗai ta san yadda ta ji tsayuwar dashi mugun Haushin hakan take ji bata da yadda zata yi ne dan hakan kawai take ganin mafita wa kan ta. Ta ƙasan ido ya bi ta da kallo bayan shuɗawar ta gaban sa. A jiyar zuciya ya sauke da numfashi na gajiya da tsayuwar sa kafin ya buɗe seat ɗin baya da kan sa ya shige motar ya rufo murfin yana sauke numfashi tare da jingina bayan sa da seat ɗin sa, p cap ɗin da ta yi wa lallausan gashin kansa mai taushi rumfa ya cire ya ajiye gefe ya zamo kyakkyawar fuskar sa ta bayyana gaba ɗaya.Wadda take ɗaure kamar wanda bai taɓa koda murmushi ba bare dariya. A hankali ya duba wristwatch ɗin sa mai tsada da kyau ya ɗan kalla a hankali wanda ke ɗaure akan tsintsiyar hannun sa,Kallo ɗaya yayi ya ɗauke idon sa yana jan guntun tsaki,ganin lokaci ya ɗan ja. Bai jima da shiga Motan ba sai ga Muby da Sauran jama'ar. Shisshiga motar su kayi babu ɓata lokaci dan ya san ogan na sa a cike yake dan bai son jira ko kaɗan duk da aikin sa ne ya bar masa. Sannan haka kawai zuciyar sa ke ayyana masa MAHAJ ya ga wucewar Shatou da jelar ta da ya dakata daga nan. Motsin sa ne ya sanya MAHAJ dake zaune shiru kamar kurma ya ɗan buɗe manyan idanun sa dake cikin glass ɗin kafin ya ƙara rufe su. Shiru ne ya ratsa domin kuwa Mubarak ya san cewa ya na jin sa yan ikon ne ke kai dan haka yayi shiru shima yana ɗan satar kallon sa ta madubi tare da nazartar yanayin sa sai dai bai gane komai ba daga abinda yake son gani saboda Glass ɗin da yayi wa kyakkyawar fuskar sa kawanya. " Idan ba zaka iya driving ɗin ba let me take over " Maganar sa ce da Mubarak ya tsinkayo cikin natsuwa hakan ya sa ya ɗan juya ya kalle sa kafin ya furta " Zamu shiga waccan Makarantar ".Kafin ya tada motar dama already sauran na gaba sun tada na su. Har suka ɗaga daga wajen bai cewa muby komai ba. Shi ma kuma muby bai ƙara cewa komai sai dai nanata Muryan da ta fitar da sautin maganar sa ta ƙarshe yake yi da amon ta saboda son gano ƙwaƙƙwafi da wani hange na sa da yayi da bai san ma yadda hakan zai iya faruwa ba. A ɓangaren shatou kuwa haka ta kasance a wajen saboda taurin zuciya duka malamai sun taru kan ta ta bada hakuri ta ƙi dan shi ya ce da ta bada hakuri ta amsa tayi kuskure zai sake ta. Baiwar Allah fuskar ta tayi jaaa na wahala ga ƙafafun ta da hannuwan ta sun yi mugun sanyi da ciwo na gajiya. Suna hakan kuwa sai ga motoci sun fara kutso kai ta cikin makarantar sai dai daga Gefen sabon ginin da ake musu domin kuwa kwangilar ta koma ta sababbin building bata renovation ba wannan kuma duka aikin MAHAJ ne shi ya bada umurnin hakan sai dai Abbu ya hana ya shiga aljihun sa dole sai nasa dan haka dole ya amince aka shiga ƙarƙashin aljihun Abbun badan ya so ba. A wannan karon bai wani jima ba ya fito da kan sa bayan buɗe masa motar da muby yayi domin kuwa yana son ganin yadda aikin ke tafiya. Da p cap ɗin sa ya fito a hannu kafin ya ɗaura ta akan sa muby kuwa ganin yadda yake ta yatsinar fuska saboda ranar da ta buɗe ne ya koma cikin motar ya ciro lafiyayyen umbrella ta kare rana ya buɗe masa. Jin yadda ranar ta sauka daga kusa dashi ne ya sa ya ɗaga kan sa ganin lema ruƙe hannun muby ya sa shi ɗan ƙare masa kallo kaɗan ta cikin glass ɗin da muby ke ta Allah Allah ya cire sa ƙwayar idon sa yake son gani fili. Idanun sa ya lumshe a hankali yana ware su wanda shine ke nuna alamar yaji daɗin abun da muby din yayi kuma hakan godiyar sa ce ya nuna masa duk da kula da shi aikin sa ne alƙawarine da yayi Abbu har gaban abadan. A hankali suka fara zaga wajen ma'aikatan wajen na na gayar da shi yana gyaɗa musu kai kamar ƙadangare,wasu kuwa ɗaga hannu,wasu ma idanu kawai yake lumshe musu sai kayi zaton wulaƙanci ne ma. Wata dai ta ce haushi kake bata my crush 🙄😏🚴 Kar ku man ta kuna karanta littafin KURMAN ƘADDARA ne tare da Marubuciyar ku ta amana fa'i.💕✨ Kar ku yi sanya wajen BIBIYAR wannan labari dan samun warwaran zare da abawa,wannan tafiya, tafiya ce mai cike da abun burgewa, Soyayya, ƙauna,darasin rayuwa. ______Kafin su gama zagayen kuwa mai gari ya iso wajen bayan samun labarin zuwan su daga Iro da wasu daga cikin mutan gari dan haka ya saɓo babban riga daga Majalisa suka yo nan. Haka ma malaman makarantar su shatou suma rabi da kwata duk sun yi gefen,ayi komai gaban su musamman da kowa ya san MAHAJ ɗin na raba kudi dan ko wancan zuwan ya kashe kuɗaɗe haka ya damƙa su ga muby yabawa malamman su Shatou suka raba da wasu daga cikin jama'ar da suka dabaibaiye sa.duk da basu san asalin wanda ya zo ba amma suna fatan ya kasance shi ɗin ne.Dan haka wajen yake ta cika dan sai yanzu wasu da suka samu labarin abinda yayi wancan zuwan suke samun labarin zuwan sa. Sun zagaya ko ina a gajiye ganin ko ina yayi masa yadda ya ke so ne ya sa yayi ce su tafi yanayin sallama da mai gari dake ta washe baki kamar gonar aufiga Sai Iro biye dashi kamar jela, shima na sa bakin washe. Suna gama Sallamar da mai gari da yake ɗan bawa amsa da ido sai ya juya ya shige motar sa. Muby ma shigewa yayi wanda yayi ɗan jimm yana kallon tsakiyar makarantar ta su Shatou hango yarinya tayi kneeldown Haka kawai zuciyar sa ke ayyana masa itace dan ya sa halin ta da rigimar ta. Sanin halin uban gidan sa ne ya sa ya faɗa mota yana girgiza kan sa.Sai dai Har ya shiga ya kasa share zancen dan haka bai cewa MAHAJ komai ba dake pressing phone ɗin sa a yanzu karo na farko tun fitowar su wanda koda ya ji fitar muby sarai amma ko ɗaga kan sa bai yi ba. Cikin yar Sassarfa ya matsa bakin inda malam Bello yake. Ban san abinda ya yi wa malam Bello ba chan na hango sa yana wasar baki kasancewar gefe ya ja sa suka yi magana tare jin bahasin abinda tayi domin kuwa bayan zuwan sa wajen ya ƙara tabbatar da ita ɗin ce dai kamar yadda ya zarga duk Tausayin ta ya kama sa gashi basa shiri a uban gidan sa bare ya ce ta zo a kai ta gida sabida ƙafafun ta da suka yi sanyi ga gajiya.✍️ Babu ƙorafi😂😏😂Yau har sai an gaji da karatu page ya cika.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________3️⃣9️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ ✿⁠☉☉✿⁠☉☉✿⁠☉☉ Godiya malam Bello yake masa kamar zai duƙa masa bayan jin hannun sa da ya damƙa masa kuɗaɗe a cike. Wajen ya bari cikin Sassarfa yana komawa cikin motar. Shi ko MAHAJ tun bayan shirun da ya ji bayan fitar Mubarak yake ta mamakin inda ya je tunanin abinda ya fita yi ne bayan ya san sun gama abinda zasu yi hakan ya sa ya a jiye wayar sa a hankali ya zuba ma mirror ido kasancewar yana facing ɗin su Mubarak ɗin dan haka ya hango sa dai dai lokacin da ya damƙa ma malam Bello kuɗaɗe. Idanun sa ne suka ƙara sauka a kan yarinyar dake duƙe ta ɗaga hannayen ta sama ɗan luuu yayi da idanun sa bayan ya ɗan zuba mata idanun sa. Kan sa ya mayar yana jingina da bayan sa tare da jan guntun tsaki na mamakin Gulmar da ta fitar da muby ɗin. Mubarak kuwa yana shiga motar ya rufe ba tare da ya kallo mahaj ba ya tada motar suma sauran motocin na su suka tayar. Tafiya suka fara yi a hankali ɗan satar kallon sa Mubarak yayi ta madubi ganin ya buɗe idanun sa dan ya zare space ɗin yanzu.Waje ɗaya ya ga ya zuba ma ido kafin a hankali ya lumshe idanun sa yana jan ajiyar zuciya a bayyane. Buɗe idanun sa yayi a hankali kafin su sauka akan na muby da sauri kuwa ya janye na sa yana furta " Tuba nake yallaɓai "Wani Shegen kallo yayi masa ya ɗauke idanun sa yana shigewa cikin seat tare da rufe idanun sa. A jere motocin suka cigaba da tafiya sai dai sun ɗan yi tafiya kaɗan mai gari ya dakatar da su ta hanyar ɗaga musu hannu. Glass Mubarak ya sauke a hankali yana sakin murmushi cike da murmushi mai gari ya roƙi alfarmar da su je fadar sa su karɓi saƙon Abbu.Babu musu kuwa suka juya aka lar motocin na su kasancewar ya san fadar.Shidai gogan bai ce komai ba yana hakimce a bayan motar bai ce ƙala ba duk da ya ji komai.Har suka iso fadar mai gari idanun sa a lumshe suke kamar mai bacci sai dai ba baccin yake yi ba. A ɓangaren Shatou kuwa malan Bello na barin wajen Muby ya koma wajen ta bakin sa washe ya ce " Shatou tashi kin ji ai ban san kina da ƙashin arziki haka ba ". " Kuma ba zan kasa faɗa Miki ba ki rage wannan taurin kan ba dan da ban samu masu gidan rana ba sai kin kai maraice haka ". Yana gama furucin sa ya kama hanyar ɗan office ɗin su. Shatou kuwa da take jin sa da sauraren ta wadda ke sauke numfashi a hankali cike da wahala ta sauke hannayen ta jagab tana shanye wasu hawaye da suke son Silalo mata na azabar da hannuwan ta suke yi da ƙafafuwan ta da jikin ta ma baki ɗaya. Zaune ta kai kasancewar ta kasa miƙewa dan har juwa juwa take gani bayan buɗe idanun ta da suka ɗan sauya kasancewar har da su yace ta rufe daga baya. Hawayen da take ƙokarin riƙewa ne suka Silalo mata wanda ta kasa haɗiye su share su tayi bayan ganin gari ya washe mata dan buji buji take gani a idonta. Ta ɗauki kusan mintuna huɗu babu wanda ya ce mata ƙala domin kuwa Dukkanin su suna chan wajen rabon kuɗin da Mahaj ya sanya wani daga cikin masu kula dashi ya basu a matsayin wata yar sadaka nan da ya saba ba su. Ta jima zaune ta haɗe rai tare da miƙe ƙafafun ta sai da ta ji sun sake mata sannan ta miƙe tana ƙara haɗe duk wani annnurin fuskar ta saboda yadda ta ji Haushin abunda take ji da wahalar da ta sha. Sai dai tunanin zantukan malam Bello da yayi bai bar kan ta ba saboda mamakin abinda ya sauya shi. Ajin su ta faɗa babu ko sallama ana tsaka da musu karatu. Ganin yadda ta galabaita ne malamin da ke karatu baice mata komai ba. Dan haka kai tsaye kujerar su ta nufa su Amina dake Binta da ido cike da tausayi suka matsa mata ta zauna. Har aka tada su bata cewa komai ba dan yau ma da wuri aka tashe su saboda masu aiki da zasu duba makarantar da tsarin ta zasu yi aune aune. Dan haka sha biyu na bugawa dot aka ta she su. Koda aka tashe su kuwa shatou fuskar nan a haɗe take sai dai ba irin yanayin jiya ba daka kalle ta dai kasan a galabaice take sannan kuma masife take saboda jira kawai take yi wani ya taɓa ta cikin yara ta sauke masa. Su Amina kuwa zagaye ta suka yi suna bata haƙuri sai dai babu wanda ta tace wa ƙala sai ma idanun ta da suke ɗan walƙiya alamar ruwan hawaye. Hanya suka kama suna tafiya a tare kamar an musu mutuwa.Bibu ma shiru yayi cike da tausayin yar uwar sa. A ɓangaren Su MAHAJ kuwa fadar mai gari sun isa lafiya inda suka tsaya jiran isowar dafaffiyar madara da zuma da bata iso ba.Domin kuwa sha tara na arziki mai gari yayi musu da nufin saƙon Abbu.Sun jima bakin fadar mai gari domin Mahaj yaƙi fita daga motar muby ne kawai ke ta godiya ana sakawa mota da taimakon sa. Koda Baffa na ya kawo zuma sanya wa aka yi kasancewar ita kawai ake jira dafaffiyar madarar an kawo ta daga gidan mai gari. Isowar Baffa na wajen ne ya sanya MAHAJ ɗan sauke space ɗin sa kasancewar Muby ya shiga Mota zasu tada motar bayan saka komai.Lafiyayyen shanu ne Baffa na ya miƙa wa Muby a cikin wata tsaftatacciyar jarka, ta glass ya miƙa masa fuskar sa cike da murmushi bayan ya ɗan ƙare ma bayan motar kallo dai dai kuma lokacin da Mahaj ya cire glass ɗin sa ɗan satar kallon sa ya yi kafin ya janye idanun sa daga kan sa yana rufe idanun sa ruff. Yana ji koda Baffa na suka yi sallama da Muby cike da girmamawa. Sallama suka yi musu kafin suka bar fadar har zuwa lokacin kuma MAHAJ bai ƙara ko dogon motsi ba hasalima baccin gajiya ne ke ɗan fizagar sa. Su Shatou kuwa rabuwa suka yi da su Amina bayan sun kawo hanyar da kowaccen su zata je gida.Sai ya zama na daga Bibu sai Shatou kuma shine yake ta rarrashin ta yana bata baki dan sai cika take tana batsewa,ga kyakkyawar fuskar ta tayi jaaa na azaba da hasalar da take ciki. Tun daga nesa ya hango ta tare da yaro mai kamar sa,ar ta dan haka suna kusa isa inda suke kasancewar yar guntuwar hanya ce dole sai ta inda suke zasu bi. Horn muby ya fara buga musu a hankali yana murmushi. Sai dai Ko waige bata juyo ba Bibu ne ma kawai ya matsa yana cewa itama ta matsa su wuce kar a taka ta tunda sun san mutanen birni. Tafiyar ta ta cigaba da yi kamar bata ji ba duk da kuwa sai nanata wa yake yi kuma ya san tabbas tana jin sa sarai sanin halin ta ya sa bai damu ba. A ɓangaren Shatou kuwa zuciyar ta ta kawo wuya a hasale take matuƙa dan haka take jiran taga Wane isasshe ne zai nuna musu mota yake tuƙi ya cika mata kunne kamar wadda ta cika masa hanya. Mahaj kuwa tun da sautin ƙarar horn ɗin ya fara damun sa yake ta faman ya mutsar fuska sai dai bai ce komai ba. Jin Muby ya ƙara yin wani horn ɗin ne ya sa shi buɗe idanun sa yana sauke kallon sa akan glass ɗin motar da suke ganin komai tarr zuba mata lumsassun idanun sa yayi wayen da suke narke kullum kamar mai jin bacci.Kallon yan daƙiƙu yayi mata yana ɗauke kallon sa daga kan ta yana jan guntun tsaki kamar yadda ya saba. Sai dai tsakin na sa ya fita fili dan har muby sai da ya ɗan kalle sa ta cikin madubi sai dai idanun sa rufe ya same su. A ɓangaren shatou kuwa tafiyar ta ta chanza salo sillo sillo kamar wata hawainiya dalilin hakan ne ya san ya Mahaj jan tsaki saboda akan idanun sa ne ta fara iya Shegen na ta kamar ta san cewa sune a cikin motar sai dai ta zargi cewa ta gane cewa sune dan haka ya kashe motar ya fito dan rarrashin ta, ta lala ma ko zata janye. Koda Muby ya fita ta ƙasan ido Mahaj ya bi shi da kallo wanda ya ƙara tsumewa a kan seat kamar mai bacci. " Shatou "! Muby ya ambata yana sakin murmushi yana ɗan Gyara tsayuwar sa daga bayan ta . Ɗan juyowa tayi a hankali ta sauke duban ta kan sa a kallo ɗaya ta gane shi dan haka ta ƙara tsuke fuskar ta.Ta ƙara haɗe rai. Ɗan kallon motocin tayi na kusan daƙiƙa ɗaya kafin ta mere baki ta juya ta cigaba da tafiyar ta tana gunguni da jan tsaki a cikin ran ta,da mamakin yadda aka yi wannan mutumen ya san sunan ta. Murmushi Muby yayi ya ƙara ɗaga ƙafa ya bi bayan ta. Bibu dake gefe matsowa yayi yana furta " Adda SHATOU dan Allah ki janye kar su taka ki mutanen birni ne ". Ya kai ƙarshen zancen yana riƙo hannun ta,fisge hannun ta yi ta ɗan harari Bibu. Kafin ta ce a hasale " Nifa ba zan janye ba tunda ƙauyen mu ne kuma ba nan ne kaɗai hanya ba ai da za,a takura Ni sai na matsa na bada hanya ". Ɓata fuska Bibu yayi da jin furucin ta ita kuwa ko a jikin ta duk da ta lura da Muby dake ta sakin murmushi daga gefen ta amma taƙi bari su haɗa ido. " Dan Allah ki bamu hanya mu wuce Shatou" Muby ya faɗa kamar wani wanda yake magana da wata Babbar mace yarinyar da bata wuce ya ɗauke ta ya jefar gefe ba. Wani ne daga cikin masu tsaron sa ya sauko daga motaa yana zare ido kasancewar sune baya sai an fita wajen garin sai kowannen su ya koma mazaunin sa shida yake tsakiya ya koma tsakiyan dan haka suka biyo hanya shigowar su nan ne ya suka sauka wannan tsarin ko shi saboda yace suje hakan. Sheƙeƙe Shatou ke kallon basamuden mutumin wanda ko kaɗan bata manta fuskar shi ba shine wanda ya tashi zane ta a haɗuwar su ta farko aiko cike da rashin tsoro jin yana furta wa da turanci " Sir let us deal with her " " Babu uban da ya isa ya saka na bar hanyar nan Ni da ƙauyen mu " Ta kai ƙarshen zancen tana Hararar sa duk da bata san abinda ya ce ba amma jin her ta san cewa da ita yake. Aiko basamuden nan bai jira ta kai cike da jin Haushin ta ganin ƙaramar yarinya na raina musu hankali domin shima bai manta abun da ya faru a wancan lokacin. Hannun sa ya sanya yana ƙoƙarin ɗaga ta sama ya ajiye gefe sai dai chik haka ya ji an ruƙe hannun na sa kafin ƙamshin turaren sa ya bayyanar da wanzuwar sa wajen sai kuma Muryan sa mai sanyi da amo da ya furta " Don't touch her " Cikin kakkausar muryan da sai da Muby ya zuba masa ido haka yaron na sa ma. " Sir yarinyar ta cika zama stubborn ". Ya faɗa yana ƙara zare idanun Sa.Wani kallo Mahaj ya jefa masa dan haka ya yi shiru daga wani sabon furucin da yake ƙokarin yi dan ji yake kamar ya kamo Shatou ya karya yarinyar da ya isa haihuwar ta sai rashin kunya take zuba wa an kasa yi mata komai. Ƙasa haƙuri yayi ganin yadda take hararar sa ya ƙara miƙa hannun sa zai kamo nata tsintsiyar hannun sai dai hannun na sa bai kai ba ya tsinkayo Muryan sa na furta " This is a last warning akan haka " Yayi maganar da wata irin murya da basu san sa da ita ba a karo na biyu sannan gashi da ƙarfi yayi zancen wanda ke nuna ɗan Abbu ya fara Hasala dan shi mutun ne da yake tsanar duk wata musgunawar da za,a yiwa mace muddin gabansa ne ba zai bari ba. Gefe wannan mopol ɗin ya koma yana jin mugun ɓacin rai na dabaibaye sa. Jin Mahaj ɗin na furta masa a natse a wannan karon duk da duk maganar da yake anatse yake yin ta." she's a still a young girl so don't let your anger hurt her ". Muby dai bin su kawai yake yi da ido kamar ya samu tv yana nazartar duk wani motsin Mahaj ɗin da shatou dake ta Harare Harare har ta mai kare ta ɗin bata bari ba. Abun na ta abun dariya har da riƙe ƙugu kamar mai shirin dambe. Yo kodai da ƙaton mopol ɗin nan zata yi U bar ta dashi 😅🤭 *Bibu dai sai kallon mahaj yake yi yana mamakin me wannan baturen kyakkyawa ya zo yi a ƙauyen su.Gashi yana kare Addan su da fitinar ta domin ya san wancan mopol ɗin ko karya ta yana iya yi in aka barshi da ita. Ɗan satar kallon ta yayi ta ƙasan ido daga cikin glass ɗin sa da ya manna kafin fitowar sa. Sannan a hankali ya kalli muby ya ce " ka ce ta bada hanya i'm so exhausted " Kai Muby ya jinjina yana son sakin murmushi kafin ya labarta masa yadda suka yi kafin zuwan sa sai dai duk da turanci suke zancen har ya ƙara masa da " Yarinyar na da taurin kai ko zaka yi mata magana da kan ka ko zata ji nauyin ka ". Yar guntuwar harara mahaj ya masa kafin ya sauke numfashi karo na farko ya sanya idanun sa cikin na ta ya mata kallo na kusan minti ɗaya sai dai ba zaka ce ita ɗin yake kallo ba a cikin space ɗin na sa idanun sa ya sauke daga kan ta yana yatsine fuskar sa kafin ya furta a hankali " Ki bamu hanya mu wuce ko na saka wanchan ya ɗauke ki daga nan " Ya yi zancen a natse kamar bada ita yake ba.Yana sauke numfashi na yar doguwar maganar da yayi. Sheƙeƙe ta kalle sa ta kafe idanun ta tar akan glass ɗin sa da idanun ta wan da take jin kamar yana bin ta da kallo ta cikin sa ne, kafin kuma ta jaa guntun tsaki wanda ya sauka kunnen sa sak sai dai ko alamar hakan bai nuna ba duk da sai da ya ga Zallar ƙarfin halin yarinyar da har yanzu bai riƙe sunan ta ba. " Ba zan janye ba,turatu uban turai masu tura ma turai,turanci,shine sai da ka gama zage ni nida ƙane na sannan zaka ce mu sauka daga hanya,nida ƙauyen mu dan haka ba zan janye ba a soye ni, kuma bana jin tsoron sa ko wanda ya fisa ka fito zan iya karawa dashi na tumurmushe sa " Idanun sa ya lumshe a hankali jin yadda yar ƙaramar Muryan ta ke ratsa kwantaresa chau chau da ita ga ta chan ƙasa sai rigima duk da yaga ta ɗan chanza kaɗan. Ajiyar zuciya ya sauke na gajiya da tsayuwar kafin ya furta a hankali cikin sanyin murya " Haka kika ce,yar ƙauyen ƙayau " ? Kai ta gyaɗa masa tana cigaba da Hararar sa na kiran ƙauyen su da ƙauyen ƙayau wanda bashi da komai dan haka ta fassara shi. Muby kuwa murmushi yake ta saki yana dariya cikin zuciyar sa wadda bashi da ikon fitar da ita. Da hannu Mahaj ya ƙyafato Wannan mopol ɗin da yake ƙara cika yana batsewa ganin yadda uban gidan su yake ta rarrashin Shatou magana cikin sanyi. " Adda shatou ki yi wa Allah ki zo muje gida ki Basu hanya kar wancan mutumen ya kashe mana ke " Bibu yayi Furucin kamar zai saki kuka ganin abinda Mahaj yake shirin yi.✍️ Masu comments da likes nuna godiya sosai. Sai kunyi hakuri dan bacci ke cikin ido na na san za,a ga kura kurai mau be ayi haƙuri.🙏da zuwan sa late. Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣0️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ ******💕 ****💕 ***💕 **💕 *💕 Da sauri wannan mopol ɗin ya matso yana jin sanyi a ran sa na damar da yake shirin samu ya yiwa yar ƙaramar yarinyar da bata wuce gwiuwan sa ba hankali. MAHAJ kuwa gyara zaman rado ɗin sa yayi yana ƙara tsuke fuskar sa. Muby ne cike da sakin fuska ganin yadda mopol ɗin nan ke ta ƙara haɗiye rai haka ma uban gidan na sa duk da ya san ba lallai ya aikata abin da ya faɗa ba. " Haba Malama Shatou dan Allah ki matsa mu wuce mai gida na baya son rana tana saka shi zazzaɓi yanzu haka in kin lura ya mutsar fuska yake yi ki taimaka mana ba sai an kai yadda ba,a so ba kar jama'a su tarar mana nan " Ya kai ƙarshen zancen yana haɗiye dariyar dake neman kubce masa ganin yadda take ta hurar hanci da girgiza ƙirji da Harare kamar zata zubar da idanun ta kuma duka akan sa ne kafin ta koma kan Mahaj dake tsaye hannayen sa maƙale a cikin aljihun sa.Ba zaka iya tantance ainahin yanayin da yake ciki ba sai dai fuskar nan a haɗe take dan ya gaji da lamarin shatou.A ɓangaren Bibu kuwa ganin bata saurare sa ba dan fisge hannun ta tayi tana ce masa barni ka tafiyar ka sai na ga karshen rainin hankali, hakan ya sa ya bar wajen da sauri yana haɗawa da gudu wanda da alama wani zai kira ya raba wannan rigimar. " Wannan ne uban gidan naka,wannan ɗan Yaron ko ni fa na girme sa kawai dan bana girma ne shi ya sa yafi ni zama ƙato,kuma ma na tuna Bature ance dama haka suke girma kamar biredi hhh " ta kai ƙarshen zancen tana nuna Mahaj tare da ƙara sakin wata yar dariya ta yarinta da rainin wayau da sakarci. Baki sake Mopol ɗin da ke jiran izini yake kallon ta haka ma Muby sai da ya ƙwalalo idanun sa yana kallon ta tare da furta anya wannan ba aljanna bace a ran sa ga dariyar dake ƙara ta so masa ji yake ina ma a ce Abbu yana kusa ya sha kallon wannan dramar ta su. Ɗan satar kallon MAHAJ yayi da yake tsaye kamar bai san abinda ake yi ba dan ya ma juyar da kan sa gefe ya san cewa ran sa ya fara ɓaci ne sai dai yana ƙoƙarin shanye wa dan shi mutun ne mai shanye komai ba kasafai kake gane yanayin sa ba musamman ma yanzu da shatou ta zamo mace babu yadda zasu yi da ita dan shi kawai yake lallaɓa ta. " Kai dube ka garjejen ƙato da kai kake kiran wannan abun mai gidan ka chab " Ta yi zancen irin bani da damuwa da kuma mamaki. Wannan karon muby murmushi ya saki wanda ya fi na ko yaushe sannan ya ce " Ba wannan ba dan Allah ki yi Haƙuri ki jaye gefe mu wuce ". Ƙugu ta ƙara dafewa tana hararan Mahaj. Musamman ganin yadda ya ɗan saka hannun sa akan sa ya cire p cap ɗin sa. Sai kuma ya taka gaban ta a hankali wanda ya zamo ɗan tazarar dake tsakanin su dan kaɗan ne. Sai da ya ɗan mula hannun sa ɗaya a aljihu.Ya ɗauki mintuna biyu tsaye gaban ta.Ita kuwa shatou baya ta ɗan ja kafin ta furta " Wallahi Ni ba yar iska bace dan haka ka matsa,ko in fasa maka kai da dutse " ta duƙa ta ɗauki dutsen. Ƙara takawa yayi inda take dan ganin ƙarshen iskan cin na ta. Baki ta tura gaba bayan ta zuba masa ido Ganin kammanin Abbu Mutumin kirki ƙiriƙiri a gare sa dan tun ɗazu ta ke hango su wanda sai yanzu ta ƙara ganin su bayyane saboda kusan cin da suka samu,kuma ta tabbatar lallai ya yan sa ne dan shima fatar ta su ɗaya ce sai dai a yanzu ta mahaj tafi ɗaukar ido,ɗauke idanun ta daga kan sa tare da hararar sa ganin sa gaban ta a karo na biyu kafin ta ankara wanda sai da ya ɗan razanar da ita sai dai ta haɗiye dan a cewar ta bata tsoron girman biredi,Cikin zuciyar ta,tayi zancen sai dai bata san cewa ta fito fili ba sak haka maganar ta shiga kunnen sa " Ni bana tsoron Girman biredi ". Kafe ta yayi da idanun sa ta cikin glass ɗin sa kafin ya ja ƙaramin tsaki da ya sauka kan kunnen Shatou.Wanda ya sa ta ƙara maka hararan da tafi sauran. " Ai watar da abun da kike shirin yi " Haka zancen sa ya shiga kunnen ta cike da wani irin isa da kaushin dake nuna ya fara gundura da tsayuwar ta su. " Zan jefa ka ". Ta faɗa tana hararan sa tare da turo baki gaba. Glass ɗin sa ya zare a hankali tare da mayar da hulan sa a kan sa yana zuba mata idanun sa wayen da ya kafe mata har tsakiyar kai yana ƙare mata kallo a fakaice. " Zan jefe ka fa,ka matsa kafin na ƙirga goma " Ta kai ƙarshen zancen tana rufe idanun ta. " Ɗaya,Biyu,uku,huɗu Biyar..." Ɗan buɗe idon ta ɗaya tayi ganin ko ya matsa sai dai yana nan tsaye kamar dutse ya zuba mata idanun na sa. Haɗa idon da suka yi ne ya sanya ta ƙara tura bakin ta gaba tana buɗe idanun na ta gaba ɗaya, hannun ta ta ɗaga kamar zata jefa masa dutsen. Sai kuma ta saki ɗan guntun murmushi wanda ya bayyanar da yar ƙaramar wushiryar ta, murmushin kai da gani ka san akwai Zallar ƙuruciya kan ta babu Damuwar komai a kan ta kamar ma ta mayar da komai shirmen ta. Ɗauke kallon sa yayi daga kan ta a hankali yana lumshe idanun sa kafin ya ware su Dai dai nan kuma Baffa na ya ƙaraso wajen wanda ke cike da tashin hankalin labarin da Bibu ya kai masa yana kuka kashirɓan ga Addan sa chan zata yi faɗa da mutanen birni zasu kashe ta. Sai dai yana ƙarasowa wajen ganin Muby sai ya ɗan yi jimm yana kallon sa dan ya gane sa tun da tare suka zo kwanan baya da Abbu, kafin ya mayar da idanun sa kan MAHAJ dake tsaye yana kallon ƙasa kamar mai nazari. Yan ƙafafun Shatou yake kallo yan ƙanana da su da suke da ɗan datti a cikin silifass ɗin ta,Wani murmushi ne ya nemi suɓuce masa sai dai ya hanawa kan sa hakan. Ita kuwa shatou dutsen ta yar ƙasa bayan ɗan juyawan da tayi ta kalli Baffa na dake tsaye yana kallon MAHAJ bayan sun haɗa ido da ita. " Ka ci sa,a Baffa na ya zo wajen nan,Sannan da kuma kaci sa,ar ya yan ka mai mutunci da kamar da kuke yi da sai na fasa maka kai gobe ba zaka ƙara raina ni ba ka zata na manta abun da ya faru ko wai har ni zaka kalla kace mini yarinya,kuma kai da ke bilicin Ni zaka cewa nake yin bilicin ai da ganin ka an san farin bilicin ko ka zata ban san yan bunni na bilicin ba ai Baffa na ya bani labari akwai masu farin mai kuma kaima shi kake shafawa ji fa fatar ka kamar ƙosan iya " Ta kai ƙarshen zancen tana ƙyaƙyata dariya. Idan ba kuskure yayi ba ya ga alamar murmushi akan fuskar sa wanda sai idan ko lura sosai ne zaka iya fahimtar hakan. Dan haka ya zuba ma Uban gidan na sa ɗan uwan sa ido. Ga mamakin furucin Shatou wanda ya tabbatar ba kowa take nufi ba face Abbu shi take kira da ya yan sa.Lallai wannan yarinya Boss ce ya furta a cikin zuciyar sa yana sakin murmushi. Numfashi ya ɗan sauke Da ke nuna gajiyar sa dake bayyane kafin ya ɗan ja baya kaɗan bayan ya samu haɗa ido da Baffa na da ya zuba masa ido yana Kallon sa kamar ya samu tv.Ga shirmen Shatou da shiga kunnen sa wanda ya ji kamar ya kame bakin ta ya hana ta yin furucin wanda har nauyi tasa ya ji bayan wanzuwar sa wajen. Kan sa ya ɗauke daga kallon kowa kafin ya kalli wannan Mopol ɗin ya furta masa " is Okey let her be ". Cije baki mopol ɗin nan yayi wanda kafin yanzu ya yardan wa kan sa shatou bata da lafiyan ƙwaƙwalwa daga yanayin yadda take abubuwan ta. Dan haka sai lamarin na ta ya so ba shi dariya dan har wani kaso daga Haushin ta ya ragu ganin wanda yake yi dan sa ko ajikinnsa kamar ma yana biye mata su yi ta ƙuruciyar tun da duk kamar sune. Mota ya koma tare da sauran da suka zagaye su jira kawai suke yi a basu dama su yi wani abu akan Shatou. Juyawa tayi ta kalli Baffa na ta yi Murmushi tana barin wajen tana komawa gefen Baffa na ɗin. Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke tare da ɗan shanye narkakkun idanun sa yana kallon Shatou da take ta ya mutsar gashin Bibu tana dariya kamar har ta manta da rigimar da ta gama Badan komai take yi masa haka ba sai dan ganin yadda yake cikin tsoro kamar zai yi wani kuka har yanzu a tsorace yake yana zaton wani abu zai same ta ne kafin su iso. Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke idanun sa kan su. Juyawa yayi a hankali ya fara tafiyar sa cikin ƙasaitar sa da natsuwa sai dai ko tako biyar bai yi ba ya juyo a hankali ya ɗan saci kallon Baffa na kafin kuma ya juya ya cigaba da tafiyar sa ko kafin ya isa bakin motar wani ya buɗe masa da sauri. Shigewa yayi suka rufe sa.Jingina bayan sa yayi da seat ɗin yana sauke Jerarrun Ajiyar zuciya tare da numfashi kan sa ne ya ɗan sara masa na gajiyar magana da tsayuwa cikin ranar da yayi.Wani madanni ya danna a hankali inda ya buɗe wata yar ƙofa sai ga drinks ɗin sa wayen da suke favorite na sa a ciki sun ɗauki sanyi mai yawa.Dan wajen kamar fridge ne. Ɗaya ya ciro kafin ya zuba masa ido kamar mai karantar wani abu a cikin sa,Har ya fara ƙoƙarin buɗe murfin sai kuma ya dakata tuna lafiyar sa da yanzu in ciwon sa ya tashi Abbu ne mai shiga damuwa matuƙa dan haka ya ajiye shi gefe har ya sha iska,ya rage sanyi. Jingina ya ƙara yi da seat ɗin yana ɗan kallon gefen damar sa sai kuma ya juyo a hankali ya ƙara ɗaga wani abun sai ga wannan yar kwalbar da take ɗauke da shishan sa. Zuƙa ya fara yi a hankali yana lumshe idanun sa yana fitar da hayaƙin da wani irin style na ƙwarewa. Idanun sa ya ɗan ɗaga ya kalli gaban motar. A ɓangaren Muby kuwa dariya yayi wadda tun ɗazu yake riƙewa sai dai yar ƙarama kafin ya matsa wajen Baffa na ya miƙa masa hannu cike da girmamawa suka gaisa. Baffa na haƙuri ya basa na aika aikar da shatou tayi na ɓata musu lokaci. Ya ƙara da furta " Ƙuruciya ce ita Tata haka take sai haƙuri Shatou kuma in sha ALLAH zata daina wata rana ka bashi hakuri ". " Babu komai Baba ai mun ga alama kamm Shatou Badai rigima ba,Zata daina in sha ai komai lokaci gare sa " Baffa na ya ji ɗan sanyi a ransa duk da har yanzu yana jin wani iri a ransa na ganin MAHAJ ɗin da yake fuska babu annuri. Kuɗi Muby ya zaro daga aljihun sa ya damƙa ma Baffa na sai dai yaƙi karɓa,kuma a dai dai lokacin ne Mahaj ya sauke idanun sa kan su daga cikin motar kallon su yayi na yan seconni kafin ya ɗauke idanun sa kan su yana cigaba da jan shishar sa,yana ƙara shanye idanun sa tare da kumshe su kamar mai jin bacci,duk da akwai bacci a idanun sa amma hakan Halittar Mazan take nature na sa ne. Duk yadda Muby yayi Baffa na ƙin karɓan kuɗin yayi wanda kafin ma su lura Shatou sun yi gaba ita da Bibu da gudu suna dariya saboda tace ayi yar rigen gen kuma akan idanun Mahaj suka yanka a Guje. " Runner girl " Shine furucin da ya fito daga bakin sa a hankali ba tare da ya shirya wa hakan ba wanda ya fita a iya laɓɓan daga bakin wanda ba kowa zai ji ba koda yana kusa da shi ne kuwa, sai kuma ya ja tsaki na bayyane wanda ya sauka a kunnen Muby da ya riga yayi sallama da Baffa na yana ƙara jin jina ƙuruciya da rigimar Shatou yana sakin murmushi. Zama yayi da kyau kafin ya kunna motar bayan ya saci kallon MAHAJ ɗin da har yanzu yake zuƙar hayaƙin dan har motar ta fara turneƙewa ga hayaƙi da illa ko wani yake zuƙan taba ko wani abun hayaƙi zai iya cutar kai.Dan haka ya kunna abun hurar da hayaƙin da sauri,wanda ke zuƙe sa take. A ɓangaren MAHAJ kuwa tari ya fara kafin ya ajiye shishan yana rufe ta ya ajiye gefen sa tare da ƙara shigewa seat na motar yana sauke numfashi jin yadda awazzun sa suka fara riƙe masa. Tafiya motocin suka yi suna barin wajen ajere gwanin burgewa. Baffa na bai ɗaga daga wajen ba sai da ya daina ganin su sannan ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana kama hanyar gida. Su Shatou kuwa koda suka isa gida kowannen su na dariya da sauke numfashi kasancewar a tare suka shiga.Inna ni dake saƙar kaba ce ta ɗago ta kalle su kafin ta ce " lafiya kuka faɗo muna haka yau har da kai Bibu da nake gani mai hankali ". Yar ƙaramar dariya yayi yana furta " Inna ni mun gaji " " To dan kun gaji sai aka ce ku ƙi yin sallama mai ya haɗa gajiya da sallama " " Kai ku koma kuyi Sallama ko na saɓa muku " Baki Shatou ta tura tana sauke nishin gajiya kafin ta juya ta bi bayan Bibu. Sallama suka yi suka shigo bayan Inna ni ta amsa musu. " Me ya faru yanzu a bani amsa Bibu " ? Ta ƙara tambaya kasancewar bata san komai ba domin A kan hanya ya haɗu da Baffa na ya fito daga gidan, Zashi fadar mai gari. " Wai fa Shatou ce Inna ni ta tare wa yan birni hanya da sun ture ta sun take ta da mota da ace ban kira Baffa na ba da sun kashe mana ita,kuma har da rashin kunya ta yi ta musu har da wani ƙato ta so yin faɗa ". Sai da ya kai ƙarshe ayar zancen sannan ya daɗe bakin sa da sauri yana zare idanu kamar wanda yayi ƙarya domin kuwa ya san halin Inna ni yanzu sai ta zane Shatou,tana dadewa bata buga ba amma duk ta Hasala sai ta buge ta take jin sanyi in ta kai ta ƙul bare ma ta sha mata faɗa akan rashin kunya wanda kuma ba kowa take yi wa ba sai wanda Allah ya jefa komar ta kan sa,ta samu waje wanda kuma ma ita bata ɗauke sa komai ba a ta ta ƙuruciyar. Shiru Inna ni tayi ta zuba ma Shatou idanu ƙirjin ta na bugawa da wani irin sauri jin zancen mutanen birni ga maganar Bibu ta tsakiya da ta ƙara sanya ta kiɗima da yace da sun ture ta sun take ta da mota,sun kashe mana ita. Ganin kallon da Inna ni take bin ta da shi ne daga sama har ƙasa ya sa Shatou ɗan shan jinin jikin ta. Ta sowar Inna ni ce daga zaunen da take ta kaɗa hanjin Shatou take ido ya raina fata rashin gaskiya ya bayyana ƙara rara gare ta, ganin Inna ni na tun karo ta ne ....✍️ 🙏🙏🙏🙏 Ayi manage haka pls.🙏 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣1️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕 💕💕💕💕 💕💕💕 💕💕 💕 Ganin Inna ni na tun karo ta ne hakan ya sa ta koma bayan Baffa na da yake tsaye yana kallon su bayan shigowar sa yanzu,domin kuwa koda bai tambaya ba ya tabbatar da ta ji komai. Ɗan murmushi yayi yana kama hannun Shatou ya riƙe gamm ganin Inna ni ta tayi tsaye waje ɗaya idanun ta sun sauya na damuwa lokaci ɗaya. " Ayi haƙuri mun san munyi laifi " Ya faɗa yana ɗan kallon Bibu dake hawaye domin ya san duka laifin shi ne da yayi subutar baki. Ajiyar zuciya Inna ni ta sauke domin kuwa wani sabon tunani ne ya shigo kan ta tun bayan jin zancen. Wanda shima Baffa na ya tsinci kan sa a wannan tunanin da ganin yanayin Inna nin ɗin. Ɗaki ta shige ba tare da ta furta komai ba. Ɗan numfashi Baffa na ya sauke yana dawo da Shatou gaban sa wadda take ta zarar ido tana ƙyaf ƙyafta su. " Ki daina irin haka kin ji Shatouwa Wayen nan mutanen,mutanen kirki ne,Wannan mutumin da kika taɓa gani mai kama dashi a fadar mai gari mahaifin sa ne ba hamman sa bane,Kinga ko dan shi bai kama ta ki masu hakan ba su ci darajar shi,bana son hakan ki daina kin ji gashi na ga kinyi hankali kuma sai ki ƙara komawa gidan jiya " Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntun murmushi irin na manya mai ma'anoni da dama da shi kaɗai ya bar wa kan sa sani. Shatou kuwa idanu ta ƙwalalo tana kallon Baffa na jin zantukan sa wai ba Hamman sa bane chab ita kam ta zata wa da ƙane ne ashe mahaifin sa ne,lallai kuwa Baban sa (Abbu) bai tsufa. Niko nace Yo to mutumin da Hutu da Naira suka ratsa ya za,ayi a hango tsufan sa take.🤭 Wannan sai talaka bawan Allah. Allah ka azurta mu da arziki mai albarka.🤲 Kai ta jinjina tana Murmushi bayan Baffa na yace mayar da idanun to,kar su zube. Bibu kuwa kallon Baffa na yayi da shatou yana share hawaye, Shatou ɗan hararar shi tayi bayan haɗa idon da sukayi,dariya ta ɗan saki kaɗan ganin yana matsar hawaye.Baffa na neh yace " haba kai ko Habibullah maza ba a san su da saurin kuka ba duk ka komawa Inna nin ku kamar Shatou ". Baki shatou ta turo gaba tana furta " Ai ni na girma dan na san na girmi Bature nesa ma shi da yake da girman biredi dan haka na bar wa Bibu kuka ba zan ƙara yin kuka Bama ". Zuba mata ido Baffa na yayi yana kallon ɗan ƙaramin bakin ta dake magana chau chau.Murmushi ne mai faɗi ya samu kan sa da yi yana girgiza kan sa domin kuwa ya san wa take magana kai. " Allah ya sa " Shine abun da Baffa na ya furta kawai yana cigaba da murmushi kan wani al'amari dake shiga zuciyar sa akan lamarin shatoun na yau. '' Ki daina yiwa mutane rashin kunya yanzu Kinga Innar ki ta Hasala dake ". Ganin yadda ta ɓata fuska ne ya sa ya furta. " Zamu cigaba da bata hakuri karki damu shatoun Baffa nan ta ". Ya kai ƙarshen zancen yana shafa kan ta tare da ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi. Itama sakin fuskar ta ta tayi tana sakin guntun murmushi. Bibu kuwa zuwa lokacin ya share hawayen sa yana shesshekar kuka. "Adda shatou kiyi haƙuri wallahi ba ƙarar ki na je kawo wa ba,baki na ne ya yayi maganar ban sani ba ". Yar guntuwar harara ta ƙara sakar masa ta wasa tana riƙo hannun sa tace " Ai ban ce ban yafe maka ba da zaka yi irin wannan kuka,kuma baka ga Inna ni bata dake ni ba " Ta kai ƙarshen zancen tana ɗan kallon ƙofar ɗakin Inna ni. Baffa na ne ya ce " kowa ya wuce yayi Sallah kafin ta wuce dan tana hanya " Dan haka suka rabu kowa ya shige ɗakin sa bayan yayi alwallah. Cire kayan jikin ta tayi ta sanya wata yar rigar ta, ta a tampa ta,ta da Sallah. Shiko Baffa na ficewa yayi daga gidan gaba ɗaya. A ɓangaren Inna ni kuwa ta jima zaune bakin ɗan gadon ta tana dafe ƙirji da ƙoƙarin hana tashin hankalin ta bayyana fili.Sai da ta samu natsuwa bayan nanata sunayen Allah sannan ta fito daga ɗakin tana cigaba da ayyukan gaban ta sai dai ta sha al washin ko ranƙwashi ne sai ta yiwa Shatou da ta tayar mata da hankali ko ta rage zafi da raɗaɗin abun da ta ji. Shatou na gama sallah bayan ta yi addu'a ta cire rigar jikin ta ta ɗauro zanen ta na wanka sannan ta fito tana sakin yar doguwar Hamma ta yunwar dake naniƙar cikin ta. Tsaye tayi ganin Inna ni zaune sai kuma ta fara susar kai tana furta " Inna ta ina Yini " Ɗan ɗagowa Inna ni tayi ta Kalle ta ta ɗauke kai. Ɓata fuska shatou tayi kafin ta matsa kusa da ita cikin ɗar ɗar cikin yin ƙasa da kai ta ce " Na fa daina wannan ma saboda sun taɓa yi muna wulaƙanci ne, saboda ina da Haushin su shi ya sa na musu rashin kunya,kuma kar ta san kar ni da su babu abinda zasu iya mini dan ogan na su ma girman biredi ne " . Ta kai ƙarshen zancen tana dariya harda ƙyalƙyatawa.Inna Ni dake sauraren ta sai yanzu ta ɗaga kai ta kalle ta kafin ta saki guntun murmushi tana girgiza kan ta a cikin zuciyar ta kuwa faɗi take mai hali baya fasa halin sa yanzu a wannan yanayin har ta samu damar dariya irin haka. Ganin murmushin Inna ni ya sa shatou ƙara gyara zama tana cewa " Kuma fa Inna ni baki san abinda suka mini ba kwata fa suka watsa wa su Amina " Ɗan shiru tayi ganin Inna ni ta kalle ta sai ta ƙara furta " Ai har da ni,Ni kuma shine yanzu na rama ". Kai Inna ni ta girgiza bayan gama zancen Shatou wadda ta yi shiru tana ɗan leƙen fuskar Inna ni da ta juyar da kan ta dan ganin ko ta saki fuskar gaba ɗaya. Dai dai nan kuma Bibu da ya gama ta sa Sallah ya fito yana furta " Inna ni yun wa nake ji,Ina abincin mu ". Kallon sa Inna ni tayi da murmushi kafin ta ce " Habibullah kamar dai yau ka sauka gidan nan ". Shima dariya yayi dan sun san inda take ajiye musu abincin su. Amma yau shine da tambaya duk da wata rana ita ke zuba musu ta kawo musu. " To ai Inna ni kin fi saba mana da ki kawo mana da kan ki ". Shatou tayi zancen. A wannan karon Inna ni Murmushi ta yi wa shatou kafin ta ce " To yanzu sai ku je ɗaya ya zuba muku sai kuci tare ,dan tuwo ne ma na dawa yau muka yi gidan ". Ai ko rufe baki bata yi ba shatou ta fashe da kuka tana furta " Allah Ni ba zan ci tuwo ba haba,jiya ma fa shi muka ci,yau ko yar murjin nan Ace ba,a dafa mana ba " Ta ƙara ɓarkewa da kuka " Shikenan sai mutun ya dafe shima,ai in mutun na cin tuwon dawa kullum baƙi yake yi dan haka Ni dai ba zan ci ba Allah kuwa sai dai na zauna da yunwa na idan Baffa na y zo ya siyo mini tsiren Sharehu " Ta kai ƙarshen zancen tana shesshekar kuka tare da ƙara taɓe baki na sangar ta. Ƙala Inna ni bata ce mata ba sai da ta gama har ta fara share hawayen ƙaharun sannan ta ce " Habibullah shiga ka ɗauko mini Bulalar nan da nake ta ajiya ƙasan gado na,dama ta tsuma sosai jini kawai take jira ta ɗiba,sauri zaro mini ita". Aiko shima Bibu baki ture ya kama hanyar ɗakin yana kallon Shatou da ta ke ƙoƙarin maƙalkale Inna ni aiko yana shigewa ta shige jikin Inna ni kamar zata koma ciki tana furta " Ai na ce na daina kuka fa yanzu ma baki ga dariya nake yi ba " Ta fara ɓallan dariya ga hawaye na Silalo mata dake nuna dariyar ƙarfin hali ce kawai da Shegen tsoron ta tunda ta san Baffa na baya kusa dan haka ta yiwa kan ta wannan dubaran dan fidda kai. Inna ni kuwa ikon Allah take kallo tana son tayi dariya amma ta haɗe ran ta. Sai dai cikin zuciyar ta sai da ta dara musamman da ta kalli fuskar shatoun ta da hawaye keta silalowa tana gogewa tana ƙara cewa " Dube ni fa na daina kukan nan ai haka na cewa Baffa na ko Bibu " Ta kai ƙarshen zancen tana kallon Bibu dake tsaye bakin ƙofar ɗakin Inna ni Hannayen sa ɓoye a bayan sa. " Kawon bulalan ". Inna ni ta furta wa Bibu bayan ta ƙare masa kallo daga tsayen da yake. Kuka shatou ta ƙara fashewa da shi kafin ta ce "Na fa daina wallahi Na tuba Inna ni ki mini afuwa ina son shiga aljanna zan dinga jin maganar ki ". Jin Inna ni na furta kin shigo hannu mai kunnen ƙashi bayan gama furucin ta na farko.Kuka kasharɓan shatou take yi wanda ya sanyaya jikin Inna ni da ta haɗe mata hannaye waje ɗaya,alamar Dagaske dakan ta zata yi kamar yadda shatou take zato da Bibu da idanun sa suka cika da hawaye. " Bani bulalan,ko sai na zo gurin " Inna ni ta ƙara furtawa zuciyar ta ƙuntace domin kuwa wata irin damuwa take tsintar kan ta a duk lokacin da shatou take cikin yanayi mara daɗi tunanikan baya ke dawo mata marasa daɗi da masu daɗi da wayen da ya kamata su zauna mata akai da wayen da basu kama ta ba. " Dan Allah ki yafe mini Inna ni ina son shiga Aljanna zan dinga jin maganar ki,kuma idan nayi kuɗi zan kai ki Umrah da hajji ke da Baffa na ".inda ta kai ƙarshen zancen tana ƙokarin ƙara fashewa da kuka. Wani irin rauni ne ya bayyana gare ta ƙarara sai da idanun ta suka cika da hawaye sai ta shanye abun ta gudun kar yaran su gani duk da ba lallai su fahimta ba. " Nace ka bani bulalan fa " Inna ni ta ƙara furtawa tana ɓoye murmushin ta da ya fi kuka ciwo.Duk da ta san cewa Bibu bai ɗauko komai ba hasalima bata da wata bulala dan ta samu ta rage fitinar Shatou ne da ita kan ta ba son bugun ta take yi ba. " Inna ni idan ba kya sona zan bar gidan nan kawai ni nama yarda a mini Aure kawai ". Cike da sakin fuska Inna tace " Dagaske ". Kai shatou ta gyaɗa mata tana sharar hawaye. Yar ƙaramar dariya Inna ni tayi kafin ta ce " kai Masha ALLAH,to waye mijin dan mu kai ƙarshe kafin zuwan Baffan ku ". " Ni kawai Zan Auri iro tun da yana sona idan na zama yar sanda zan je da shi birni ya riƙa wanke bakin sa,Idan na zama Babba kuma sai na sake shi ya dawo ƙauye yayi sabon Aure " Wannan karon dariya Inna ni tayi da ta bayyanar da wushiryar ta irin ta Shatou mai kyau kafin tace " Kai masha Allah wannam abun alkhairi ne Bari Baffa nan ku ya zo sai aje neman Aure da wuri da kan mu ma zamu je na dangin mijin zasu zo ba sai a fara daga yar mafarauci ". Shiru Inna ni tayi bayan fitowar wannan furuci da ta ji ya mata wani iri a baki kafin ta ɓatar da yanayin da zuciyar ta ke hauhawa tana ƙara sakin dariya. Ita kuwa Shatou baki ta tura gaba tana sauke ajiyar zuciya. " Ai na yafe Miki shatoun Baffan ta ". Hawayen ta,ta ida sharewa tana sauka daga jikin Inna ni. Bibu kuwa yar ƙaramar dariya ya fara yi tun bayan fara maganar ta Aure. Ɗauko muku abincin ku yau faten dankali ne muka yi,abincin mutuniyar ka ". Ai ko shatou take ta wartsake ta miƙe jin abinda Inna ni ta furta nan ta fahimci Inna ni tsokanar ta take yi shi ya ƙara sakar mata da jiki tabbatar da cewa ta haƙura. " Yeeehhh Dankali dankali " Shatou ta furta cike da farin ciki miyan ta har katsewa suke yi.Saboda yadda take son sa. Lokaci guda ta manta abun da ya faru yanzu.Murmushi Inna ni tayi cike da farin cikin sakewar shatou tana cigaba da saƙar ta tana yiwa ya yan nata addu'ar shiriya.Bibu da sauri kuwa ya ɗauko musu abincin tare suka zauna suka ci suka ƙoshi kowanensu na ta zuba santi.A ɓangaren Baffa na kuwa fadar Mai gari ya wuce a chan ya tarar da mai gari ana ta fadanci da jama'ar sa ana ta yaba irin ƙokarin Abbu da Mahaj.Ganin sa da mai gari yayi kuwa dai dai wannan lokaci ya ce " Malam Jibril Sai yanzu ". Murmushi Baffa na yayi kafin ya ce " Eeh wallahi na samu kira tun ɗazu sai dai rikicin Shatou ne kasan ba ƙarewa yake yi ba shine ya tsayar da ni,nan ya labarta ma mai gari komai " ai ko mai gari ya yi dariya Sosai wanda har ya bawa jama'ar fadar mamaki shi kan sa Baffa na Murmushi yake yi. Sai da duk jama'ar suka watse kasancewar mai gari ya ce kowa ya zai iya tafiya. Sannan ya kalli Baffa na ya sake yin murmushi. " Tabbas Farauta Haske zai samu a cikin duhu a cigaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da Alkhairiin sa a ko da yaushe ". Amin Baffa na ya amsa yana ƙaƙalo ɗan murmushi da bai kai ciki ba. Sai kuma suka miƙe suka shige wani ɗan ɗaki na mai gari ban san abinda suka tattauna ba amma sun jima sannan Baffa na ya fito zuwa lokacin an fara kiraye kirayen Sallah la,asar. A ɓangaren su Mahaj kuwa suna fita Babban titi suka koma yadda suke kafin suka fara sharara gudu kamar zasu tashi kasancewar Umurnin Ubangidan na su ne. Basu daka ta ba sai da suka samu waje suka yi Sallahn azahar da ke neman wucewa,Sannan suka kama hanyar asalin Abujar.Koda suka isa anyi Sallan La,asar dan haka kai tsaye masallaci Suka sauka suka fara sauke farali. Babu kowa cikin Babban falon dama bai tsammana ba dan haka kai tsaye ya shige Sashen sa.Kai tsaye wanka ya faɗa bayan tuɓe kayan jikin sa.Ya daɗe ruwa na sauka jikin sa masu ɗumi kafin ya ɗauro wanka. Ɗaure da guntun towel ya fito fari ƙar wanda yayi wa ɗaurin saɓu saɓu ga kan sa na ɗigar da ruwa kaɗan kaɗan kasancewar ya ɗan goge sa da towel a cikin toilet ɗin.Bakin fankacecen mirrorn sa da ya kusa ma he rabin bango wanda yake shaƙe da kayan gyara masu tsada da kyau da inganci ga lafiyar fata da kuma turarukkan sa masu Shegen ƙamshi da ƙamsasawa wayen da suka kama bedroom ɗin sa sai kace wani Company na turare. Hand dryer ɗin sa mai kyau ya kunna wadda take a jiye a waje mai kyau ya busar da gashin kan sa tass kafin ya kashe ya koma murza mayukkan sa sai da ya bi ko ina na jikin sa da man sa mai kamshi sannan ya koma gyara gashin sa da ke ta shinning kamar an masa ruwan mai aiko take ya ƙara yin wani irin haske da shinning har wani kashe ido yake yi. Sai da ya gyara sa tass sannan ya taje ya koma ya bi jikin sa da Haɗaɗɗen body spray na sa.Haka kan sa ma sai da ya ji na sa turaren sannan a ɗan gaggauce saboda baccin da ke idanun sa ya bar bakin madubin yana komawa gaban sip ɗin sa kasancewar sip ɗin ta sa mai taya ce kafa kawai ya saka ta buɗe da kan ta ƙananan kaya ya zaɓa mara sa nauyi daga cikin dubannin kayan dake tsare cikin ta cikin tsari mai kyau gwanin burgewa komai dai irin na luxury life babu ƙaramin abun a ciki. Saka kayan yayi wanda suka kasance guntun wando ne na mai santsi mai haɗe da vest fara ƙal kamar yanayin wandon. Yana gama kimtsawa ya saka turarukan sa masu ƙamshi.Masha Allah, yayi kyau kamar wanda zai je wani taro ɗan tsaye yayi bakin mirrorn ya ɗan zuba ma kan sa ido kafin wani tunani ya shigo ƙwaƙwalwar sa hakan ya sa shi jan guntun tsaki mara sauti kafin ya ɗaga ƙafa a hankali ya kwanta kan gadon sa bayan ƙure gudun A C,da rage haske. Yana kwantawa kuwa bacci mai daɗi ya kwashe sa duk da ya ɗan yi ta juye juye Kafin ya kwashe sa. Muby kuwa Bai zame ko ina ba sai part ɗin Abbu cike da zumuɗi. Koda yayi sallama tare da knocking a ƙofar falon Abbu,Abbu na zaune yana duba wata tsohuwar jarida ya zuba mata idanu bazaka taɓa iya tantance yanayin da yake ciki ba sai dai daga yanayin fuskar sa zaka shaida ba mai kyau bane,domin kuwa jikin sa a sanyaye yake dan tun bayan dawowar sa meeting da Mr president ya ke aikin karatu ko muce na zarin wannan jarida dan yau ko Amma bata gane wa kan sa ba abinci ma bai saka a bakin sa ba wanda kuma bata damu ba domin inda sabo ta saba da wannan yanayin na sa dan haka ta share sa kafin ya dawo dai dai. Koda Abbu ya ji knocking kuwa ɗan zuba ma ƙofar idanu yayi dan hankalin sa na kan su Mahaj ɗin sa dan haka yayi zaton shi ne ya dawo,miƙewa yayi ya mayar da wannan jarida cikin wata locker mai kyau sannan ya saka makulli ya rufe ta yana saka keys ɗin a cikin bedside drower. Sai da ya ɗan sanya wa kan sa jarumtar ɓoye yanayin da yake ciki kafin ya bada izinin shigowa.Cike da Sallama Muby ya buɗe ƙofar yana kutsa kan sa ciki bakin sa dauke da murmushi,cike da girmamawa ya duƙar da kan sa ƙasa ya gayar da Abbu da yi masa Barka da gida wanda ke zaune a kan kujerarar sa ya ɗan miƙe kafafun sa akan Centre table. Cike da farin ciki Abbu da yayi zaton Mahaj ɗin ne wanda sai yanzu ya tuna da sai ya huta yake zuwar masa idan ma har yanzu suka dawo. " Kun dawo kenan ya hanya ". " Lafiya lau Abbu " " Masha ALLAH Allah ya sanya albarka " " Amin " " Y komai yake tafiya ta ɓangaren ayyukan " ? " Lafiya lau Abbu suna ƙokari sosai " " Masha ALLAH Allah yayi mana jagora ya sa amizani " " Amin " Muby ya furta yana ƙara sakin murmushi. Murmushi Abbu yayi kafin ya ce " An sake wata draman kenan ". Baki washe Muby yace " Sosai Abbu". Cikin sakin yar ƙaramar dariya Abbu ya ce " Sha fa mini na ji,ai na manta da recording na nace ka mini " Ya kai ƙarshen zancen yana ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi jin wani yanki na damuwar sa na raguwa tun kafin ya ji abinda ya faru. Muby kuwa gyara zama yayi daga ƙasan da yake zaune ya labartawa Abbu komai da ya faru bai ɓoye masa komai ba.✍️ To jama'a Abbu zai kwashi romon drama 🤣🤣🤣🤣🤣Kai Allah ya shirya mana Amarya Shatou uwar gida a gidan Iron mai gari.🤭🤭🤭An bar muku kayan ku mutanen Shatou saura shan buki💃💃💃🚴🚴🚴🚴🚴🚴😂😂😂 Zanje ganawar sirri da (INAYATH KHALIL) Sir ZAFIN KAI.😏my next Novel,idan na dawo sai a bani labarin yadda ɗaurin auren ya kasance da malam Iro🚴🚴🤭🤣 Amma fa Muby akwai ɗan munafunci 😏 Ya zai mana haka.🙄 Kar ku ji komai Ni ɗin ce dai ta ku muna tare har ƙarshen wannan tafiya.In sha ALLAH.🤗🤗💃💃 Ku kasance tare da yar mutan Zamfarawa dan gane wa idon ku ƙarshen wannan labari mai abin mamaki da al'ajabi,sarƙaƙiya,ruɗani,cin amana yaudara.All in one story📚Kurman ƙaddara. Na gaishe ku na amana ta.🔥✨💕 Labari yanzu yake ku dai cigaba da Bibiya ta.🔥🔥🔥🔥🔥🔥 Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 Book one zai kare a page 50 Dan haka wadda ta shirya sai ta saka kuɗin ta dan babu wanda zamu jira zamu cigaba da wannan tafiya in sha ALLAH.🙏🙏🙏 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 2️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕 💕💕💕💕 💕💕💕 💕💕 💕 Tunda Muby ya fara bashi labarin yake ta sakin murmushi yana ƙara jin wani irin farin ciki a ran sa shi haka kaiwa yake samun kan sa a farin ciki idan suka haɗu waje ɗaya. A kallo ɗaya zaka san cewa Abbu yana cikin farin marar misaltawa. Domin kuwa fuskar shi ta da ɗaɗa sosai murmushi kawai yake saki yana gyaɗa kan sa tare da girgiza sa cike da jin wani irin farin ciki. " Lallai kuwa na yi missing ya zama dole na saya maka Camera ko dan ɗaukar rahoto ". Cewar Abbu bayan Mubarak ya gama zayyane masa komai. Yar ƙaramar dariya Muby yayi yana shafa kan sa. Yana gamawa yayi wa Abbu sallama bayan sun ƙara tattaunawa akan yadda komai yake tafiya. Koda Muby ya fita Abbu kasa zama yayi ya miƙe ya fito Bai zame ko ina ba sai bedroom ɗin Mahaj koda yayi knocking ya ji shiru sai ya fara tunanin abun da zai ce masa dan haka yayi tsaye kafin kuma ya juya fuskar sa cike da farin ciki. Sai dai koda ya koma falon sa kasa zama yayi ji yake ina ma ace a gaban sa aka yi komai ya samu abun tsokanar mahaj ɗin sa tun da ya samu dai dai shi wadda duk miskillancin sa sai da ta saka shi magana mai ɗan tsawo.A haka wannan yini ya zo wa Abbu cikin farin ciki dan koda Amma ta same shi gab da Magriba sake ta samu fuskar sa wanda ya sanya ta ɗan mamaki duk da ba abun mamaki bane hakan a gare sa.... ***A ɓangaren su Alina kuwa yau sun tashi da wani irin mahaukacin ciwon kai gaba ɗayan su wanda ba abun mamaki bane irin haka a gare su domin kuwa sukan yi rashin lafiya wani sa'in tare. Dan haka aka kira family doctor na su ya duba su ya basu ɗan taimakon gaggawa saboda Leena da jikin ta ya fara ciccira. Cikin ikon ubangiji yana basu taimakon gaggawa da ya dace bacci ya kwashe su mai nauyi.Hankalin Ummah da B ya tashi sosai babu ma kamar Abba domin shima yar ƙaramar ciwo yayi saboda damuwa dan kwanan su uku haka. Sai yau ne suka fara samun sauƙi,sai dai Reena ce kawai jikin ta ya fara sauƙi dan dai Leena ba,a cewa komai amma dai itama ya rage mata ba kamar kwanakkin da suka wuce ba... * " Hahaha Lallai ta baiwa ke Masifa ce,da sannu zaki ga yadda aikin mu ke ci ke shaida ce Ɗan Baiwa baya aiki kawai dan haka ki ƙara kwantar da hankalin ki wayen nan alamomi ne na cikar aikin mu ".Ya kai ƙarshen zancen yana gaggaɓan dariya. Inda itama ta fara dariyar kamar wata zararrriya. " Hankali na ya fara kwanciya Ɗan Baiwa buri na ya kusa cika komai ya kusa dawowa hannu na daga ni sai shi dole mu ƙara zage damtse a ƙara bawa su ɗan duhu jini su ji ƙarfi a jikin su su aiwatar da aiki cikin kuzari,nayi imani da kai ɗan Baiwa na san ba zaka taɓa bani kunya ba ". Ta ƙara sakin dariya ta na kai ƙarshen maganar. Cike da rashin imanin ta. " Hhhhhh ta Baiwa kenan,kibar wuƙa da nama a hannun mu zamu ɗaukar Miki fan sa har da riba dole komai ya koma hannun ki ". Miƙewa tayi kamar yadda suka saba tana zagin sa yana zagin ta kafin ta yi layar zana ta ɓace ɓatt. Ɓacewar ta shima ya ɓace ɓatt kamar bukkar sa bata taɓa zama wajen ba. " Ummah jiya fa mafarki nayi mara kyau akan LEENA amma na manta wallahi Ummah ina dai tuna kukan ta ne da na ji " Reena ce ke zancen idanun ta na cika da hawaye. Idanu Ummah da ke kallon ta zuba mata wadda ke kallon ta bayan fara maganar. Numfashi Ummah ta sauke cike da ƙaryewar zuciya ta " Ta ce ki yi mata addu'a Allah ya bata lafiya da ke baki ɗaya,amma wane irin mafarki ne kika yi haka " ? " Na faɗa Miki Ummah na manta fa ". Kai umma ta girgiza kawai zuciyar ta cike da rauni kafin a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana furtawa a fili Allah ya baku lafiya ya ya na. Amin Reena ta furta tana gyara zaman ta kan doguwar kujeran da take kai wadda take kallon ta Ummah. Dai dai nan LEENA ta fito tana ya mutsar fuskar ta da ke nuna har yanzu tana jin jiki sai dai akwai alamar sauƙi ya fara samuwa itama. Zama tayi kusa da Ummah tana shagwaɓe fuska. " Ya jikin na ki " ? Ummah ta faɗa tana taɓa wuyan ta. Jin da zafi sai dai ba sosai ba hakan ya sa ta jan ajiyar zuciya tana ƙara rungume ta jikin ta bayan ta gyaɗa mata kai. " Aleena ya jikin ki " Yar hararan Reena tayi jin ta kira ta da complete name na ta kafin ta rufe idanun ta tana ƙara ya mutsar fuskar ta. " Ummah Leena itama ta fara samun sauƙi ko " ? Kai Ummah ta gyaɗawa Reena wadda ta ƙara yin tambayar ta kulawa da yar uwar ta. Dai dai nan Abba ya shigo wanda ya dawo yanzu daga office. Dan yanzu ya fara samun damar leƙawa kwana biyu ciwon ya yan na sa ya tayar masa da hankali matuƙa. Ɗauke da murmushi akan fuskar sa ya zauna kusa da Reena yana ƙara ƙawata fuskar sa bayan amsa masa Sallamar sa. " My babies sun samu lafiya ". Cike da murmushi Reena ta ce " Eh Abba mun samu lafiya, Leena ce kawai yanzu take ɗan jin ciwon kan ta ,Amma itama Ummah ta taɓa jikin ta temperature na ta ya sauka." Murmushin Abba ne ya ƙara faɗaɗa cike da jin daɗi ya shafa kan Leena yana furta " Allah ya ƙara muku lafiya ya kare ku daga sharrin maƙiyi da sharrin Aljan da duk wani abun cutarwa da muke gani da wanda bama gani ". " Amin " Reena da Leena suka haɗa baki wajen faɗa dan suna matuƙar ƙaunar Addu,an Abba haka ma Bilal da ya shigo yanzu ya amsa a hankali yana sakin ɗan murmushi. A ɓangaren Ummah kuwa ido ta zubawa Abba kafin ta sauke kallon ta daga kan sa tana Amsawa da Amin ganin yadda ya ɗan faɗa wanda sai yanzu ramar ta ƙara fita. Ajiyar zuciya ta sauke yar ƙarama tana shafa kan Leena. " Barkan ku da yini,Ummah da Abba " Cikin sakin fuska Ummah ta amsa masa kafin ta ƙara sakin murmushi na jin yar kunya.Jin Abba na kiran " Momyn Yara yau babu sannu da zuwa ga masoyi sai ta ya yan ki kike yi ".? '' Ya jikin Leena ɗin ".? Ya ƙara faɗa yana ta sowa daga kujerar da yake kusa da Reena yana komawa zuwa kusa da ita. " Sannu da dawowa,Abban su,Leena ta samu lafiya itama ". " Murmushi yayi ganin yadda Ummah ke soke kai kafin ya shafa kan Leena yana dawo da ita jikin sa fuskar ta ya shafa a hankali yana ƙara jin Tausayin ta na ƙara mamaye sa musamman da ya ji ɗan zafi a jikin ta sai dai bai kamar na ɗazu ba da safe. Idanu Leena ta ɗan Lumshe kamar mage tana ƙara shigewa jikin Abba kafin ta ce a hankali " Abba sannu da zuwa ". " Yawwa ya jikin,?kin samu lafiya ko "? Kai ta gyaɗa masa tana sakin gun tun sanyayyen murmushi. Kan ta Abba ya ƙara shafawa kafin ya sakar mata kiss a goshi. Yana cewa." Allah ya baku lafiya ". Amin suka haɗa baki wajen faɗa. Miƙewa yayi ya haye Sama bayan ya gaisa da Bilal ɗin da sai yanzu suka haɗu shima dan da wuri ya fita shima ya fita wajen motsa jiki. " Babu komai a tattare da su kamar yadda na faɗa maka,amma dai abun da kawai zan ce maka shine ku ƙara da gewa da Addu,a akan su nima a ta gefe na zan dage sosai dare da rana zan taya ku nema musu kariya wajen Ubangiji,yanzu ƙuruciya kawai ke damun su ". " Ungo wannan ka ba su,su sha sannan kuma ka tabbatar ka shafa wa kowaccen su a kai da ƙafafu ". " Kar ka yarda da kowa yayi wannan aikin ka tabbatar kayi shi da kan ka " Sallamar Ummah ce ɗauke da jakar sa a hannu ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga na zantukan malam Hambali dan yanzu daga wajen su yake daga office ya wuce chan har yanzu kalaman malam suna masa shawagi "Babu komai a tattare da su ....." Shin me hakan ke nufi kenan akwai wani abu a ƙasa sannan me zai saka malam yin wayen nan zantukan " Ka tabbatar kayi shi da kan ka ....." Numfashi ya sauke da ajiyar zuciya bayan zaman Ummah ɗan kusa da shi kaɗan. Zuba masa ido Ummah tayi ganin yadda ya yi shiru kamar ya ƙara komawa duniyar tunanin da ta same sa. Numfashi ta sauke kafin a Hankali cike da yar damuwa ta ce " me yake damun ka Abban yara ". Murmushi Abba ya ƙaƙalo kafin ya ce " Babu komai Barry kawai dai ciwon yaran chan ne yake damu na,ina tsoron wani abu ya same su ". Hawaye ne ya wanke fuskar Ummah cike da wani irin raunin ta dake bayyane ta ce " Abban su,ka cire damuwa komai zai wuce,zasu samu lafiya,sannan duk wasu rigimar su zasu daina ". " Kune ƙwarin gwuwaita Abban su dan Allah ku daina sage mini gwiwa ". Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana ɗan samun sanyi a ran sa,ko ba komai ya samu ƙwarin gwiwar da ya ke jin yana neman rasawa. " Kar ki damu Barry,amma akwai wani hanzari wai Ni kaɗai nake hasashen yaran nan kamar akwai sihiri a jikin su ". " Tunani ne ke faɗa mini hakan Barry na kan ka sa yardar wa kai na babu wanda ya ke bi mini ya ya da bita da ƙulli ". Wata irin faɗuwar gaba ce ta saukar wa Ummah cike da tsoro ta ce " Abban su Sihiri me za,a tsinta a jikin ya yana,me suka yi wa wani babu abun da suka sani fa,bamu da wani maƙiyi Abban su,kai gaskiya Abban su Wannan hasashe ne kawai Dan Allah Abban su ka daina irin wannan maganar wallahi ka tayar mini da hankali innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un " Ta kai ƙarshen zancen tana fashe masa da kuka. Jikin Abba ne ya ƙara yin sanyi ya ji dama bai yi maganar ba a hankali ya ɗan rungumo Ummah jikin sa ya fara rarrashin ta. "Ba cewa nayi Dagaske ba hasashe na ne kawai,kuma sai yanzu na tabbatar da hasashe na ba gaskiya bane domin kuwa bamu da wani maƙiyi bare su na fili da na ɓoye duk abinda kika faɗa ba gaskiya ne". " Allah ya basu lafiya,ya sa komai ya zamo muna tarihi mu da su,ya dawwamar da mu cikin farin ciki ". Amin Ummah ta faɗa a hankali bayan tsaida kukan na ta. Tana share hawayen ta tare da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. " Zamu kai kukan mu ga ubangiji a koda yaushe mu masu miƙa wuya ne,dan haka Abban su ka ɗauka jarabawar mu ce wannan mu da su,Amma bana son ka raunata imanin ka ta hanyar yin wannan hasashen Abban su,Shekaran jiya ma na saka anyi musu saukan Alqur'ani,yanzu ma zan bada kuɗi a ƙara musu wata ". Murmushin Abba ne ya fito da wani irin farin ciki ya washe fuskar sa daga damuwa. Hannun ta ya riƙo a hankali yana fuskan tar ta kafin ya ce " Allah yayi Miki albarka Barry,Allah ya saka Miki da Alkhairi ya ƙara Miki ƙarfin renon ya yan mu da basu tarbiyya ". " Amin " Ummah ta amsa tana sakin murmushi. Jakar ta sa ya amsa bayan ya miƙe daga zaunen ya saka ta inda yake ajiye jakar sa. Tuno da abun da malam yace masa dan haka ya tura jakar cikin lockern sa kamar yadda Ummah ta saba yi masa. Kallon sa ta dinga yi ganin yau da kan sa yake ƙokarin ajiye jakar ta sa. Kafin ya ta ce " Abban su Yau ko kayi mantuwa wannan ba aikin ka ba ne ". Murmushi Abba yayi yana juyowa kafin ya ce " kar ki damu na ga kina gajiye ne ga kula da marasa lafiya shi ya sa na ke ƙokarin yin komai da kaina ina son ki huta ne ". Murmushi ta ƙara saki na jin daɗi. Wanka ya faɗa yana furta" bari na shiga na sake jikin nan nawa". Kai Umma ta gyaɗa kafin ta miƙe ta fice kasa wajen haɗa masa abincin sa,ta san Abba baya wa sa da cikin sa. A ɓangaren Abba kuwa bai daɗe ba ya fito daga cikin toilet ɗin tsaf ya kimtsa cikin kaya mara sa nauyi na zaman gida. Jakar sa ya janyo kafin ya Fiddo da yan gorunan ruwan addu,an da malam Hambali ya ba shi. Zuba masu idanu yayi gora biyu ce ciff yanda malam yace a ba su na kwana biyu. Har ya ɗauki ɗaya ya fita da ita sai ya tuna maganar malam hakan ya sa ya mayar da ita cikin jakar yana ficewa daga ɗakin. A ɓangaren Bilal kuwa bayan wucewar su Ummah cike da yar kulawa ya dubi Leena. Yace " Y jikin na ki ".Naji sauƙi. Ta bashi amsa. Daga haka bata ƙara cewa komai ba sai shigewa cikin kujera ta ƙara lafewa lafe. Ita kuwa Reena jikin shi ta shige tana cewa " Ni ya ya B baka mun ya jiki ba ". Ɗan guntun murmushi ya saki yana kallon fuskar ta da tayi fayau kafin ya ce '' Na ga ba kya buƙatar tambaya ne Reena,gashi kina da ƙarfin jikin ki har kin samu damar surutu ". Ya kai ƙarshen zancen yana shafa kan ta. Yar dariya tayi tana cewa " eh na ji sauƙi y B " A wannan karon murmushin ya ƙara saki kafin ya ce " Ta ci abinci ". Fahimtar wadda yake magana hakan ya sa ta ce " Eh ta ci chocolate,kuma tace ta ƙoshi haka ta cewa Ummah ". Kai ya gyaɗa kafin ya ce " Je ki Kice wa Inna Rabi ta haɗo mini tea mai kauri ". Miƙewa Reena tayi jikin ta sanyaye dan har yanzu da Sauran rashin ƙarfi a jikin ta itama. Dai dai fitowar ta dai dai lokacin da Ummah ta ke saukowa daga step steps fuskar ta babu yabo babu fallasa..... Sai dai fuskar ta kamar da danshin ruwa da alama sai da ta shiga bedroom ɗin ta,ta wanko fuskar ta. Kallon B tayi dake zaune ya zuba wa Leena idanu yana kallon ta wadda idanun ta ke rufe da alama bacci ya fara kwasar ta. Ɗan jimm tayi kafin ta karasa saukowa tana giftawa ta gaban sa hakan ya sa ya ɗauke idanun sa kan ta yana jin wani mugun tausayin Ƙannen na sa na sukar zuciyar sa. Zama Ummah tayi kafin ta shafa kan Leena ta ce " Baiwar Allah ta fara samun barci ". Kai B ya gyaɗa kafin ya ce " Ashe bata ci abinci ba ". " Eh wai ta ci chocolate ta ƙoshi ". Ummah ta bashi amsa. " Ummah Chocolate ai ba zai yi ba shi ya sa jikin na ta ya ƙi yin ƙarfi ". " To ya za,ayi Soja basa jin dadin komai ne itama Reena da ƙyar ta yarda ta ci coslow ko shi kaɗan ". Reena dake zaune ce ta ce " Ummah ai na ƙoshi ". Kai Ummah ta gyaɗa mata tana Murmushi kafin ta ce wani abu sai ga Inna Rabi ɗauke da cup a kan ɗan ƙaramin ti re mai kyau. To subscribe yours contact this number 08069059746 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 3️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕💕 💕💕💕💕💕 💕💕💕💕 💕💕💕 💕💕 💕 Wani table ne dake kusa da Bilal ta ɗaura tiren Saboda Reena ta faɗa mata saƙon sa ne. Gaisawa suka yi kaɗan sannan ta ƙara yiwa yan biyu ya gajiya sannan ta bar falon tana amsa umurnin Ummah dake tabbatar musu da a ƙara kimtsa dinning tunda sun gama aikin Su da wuri ita da masu aikin. Miƙewa Ummah tayi tana cewa " Kuma fa ina ga har da yunwa ke ƙara nuƙurƙusar ta fa,da zata iya ai da an haɗa mata abu mai sauƙi ta sha". Cike da yar natsuwar sa da kulawa ya ce " Ummah ai wannan ita aka haɗawa ko kaɗan ne sai ta sha ". Kai Ummah ta jinjina kafin ta ce "Eh yayi hakan bari na tashe ta ". " Alina,! Alina ! Alina ! " Haka Ummah ta jera mata sunan na ta inda kafin a hankali ta fara buɗe idanun ta da suka fara mata nauyi.Ya Mutsa fuskar ta tayi kafin ta ce " Ummah na fi son kwanciya ".tana batun sakar mata kuka. Ummah cike da kulawa tace " yi hakuri ki tashi zaune,kin ji ki saka wa cikin ki wani abu ". Ɓata fuskar ta tayi kafin ta ce " Ummah ai na faɗa Miki na ci chocolate fa,kuma na ƙoshi,Dubi fa ciki na " Ta kai ƙarshen zancen tana buɗe shaffafen cikin ta. Bilal dake kallon su ne ya janye idanun sa da sauri yana kallon shayin dake ta tururi. Ɗan fara feta shi yayi da spoon yadda zata ji saukin shan sa. Ummah kuwa rarrashin ta ta fara kafin tace " Ni dai yanzu ke da ya yan ku bari na je na ɗauko waya na,kafin Abban ku ya fito ". Miƙewa tayi ta haye steps tana jin yadda Leena ke ta ƙoƙarin sakin kuka. Ita kuwa Reena kallon ta kawai take yi. " Ya B ka rarrrashe ta,ko Ni na sha shayin makon ta ". Ɗan murmushi yayi yana jan table ya zauna ya miƙa wa Leena ɗin tea ɗin yana haɗe kyakkyawar fuskar sa. Ɓata fuskar ta tayi kafin ta karɓi cup ɗin da ya dungura mata. A hankali ta fara sha ganin tana sha da wasa hakan ne ya sa ya karɓa ya fara bata da kan sa haka take karɓan tea ɗin kamar ɗaci duk da ta ji daɗin saukar sa a cikin hanzayen ta. Motsin Abba ne ya sa shi ɗan kallon steps din. Abba ne kuwa ke saukowa fuskar shi cike da murmushi yana kallon su wani irin farin ciki na mamaye sa kulawar da Bilal yake bawa yan uwan sa na sanyaya masa zuciya ya san cewa ko ba sa duniya Indai har yana raye zasu samu kulawa bayan ta kakannin su. " Ai dole sai da hakan dan tun da na shigo na ga alamar bata ci wani abun kirki ba ". " Ka kyau ta Allah yayi muku albarka ". " Amin Abba ". " Yawwa Ina Umman ku ". Dai dai nan kuma ummah ta fito riƙe da wayar ta a hannun ta fuskar ta ƙawace da murmushi. Yau Abba Dinning Abba ya wuce bayan hango an jera komai a chan. Bayan sa Ummah ta bi bayan ta yiwa BILAL kallo ɗaya da Leena. Reena kuwa hankalin ta ta mayar kan Tv tana cigaba da kallon ta shar toon. *** " Ba zai yuyu ba gaskiya Boka gangaro ya kamata dai ka ƙara duba mini lamarin nan babu yadda za,a ce komai yana faruwa haka ba tare da kasan wayen da ke wannan aikin ba ". " Hmmm ba zaki gane bane ai shi rame da ƙarami yake farawa kafin ya yi girma na sha faɗa Miki ki fitar da hannun ki cikin wannan rigimar wannan abun daɗaɗɗen aiki ne yanzu ya fara ci,bana son Ni dake mu shiga Masifar da zata yi muna wahalar fita,Masu wannan aikin ba ƙananan Azzalumai bane suna aiwatar da shi ne cikin kuzari domin kuwa su ɗan duhu kowa ya Sani ba su san inda imani ya shiga ba,ba wani sanin su ne ban yi ba,a wancan karon na ji tsoron su ne hakan ya sa na ɓoye mikisaboda yadda na tsorata da abun da na gani,na dai shaida Miki ki fita wannan sabgar aikin ki ɗaya kuma yana kan ci,muna aiwatar da shi,duk da an riga ki aiwatar da shi amma zamu iya loda na mu koda ace wanchan ya sauka ". " Hakan shine zai kawo mana salama Ni dake ". Ƙaramin tsaki matar dake zaune itama cikin shigar ta ta alfarma sai dai fuskar ta rufe ruff da wani irin liƙab irin na zamani wanda sai kayi da kyau zaka iya hango idanun ta domin rufe yake ruff. " Naji yanzu ga wannan Ni dai a yi mai yuyuwa kuma zan yi ƙokarin kwantar da hankali na,tun da haka kake so,amma muddin na ga cigaban da na gani ya tsaya zan dawo kayi aikin nan ko na chan za waje ". " Ba sai an kai chan ba shegiya yanzu dai zube muna kuɗin mu kiyi gaba ". Itama tsaki ta ja dan ta tsani zafin ga da yake mata wasu lokuttan duk da kasancewar sa boka ji take kamar ta kai masa bugu sai dai tana da tsoro dan tana mugun tsoron aljanu dan haka take raga masa kar ta kai kan ta ta baro. Kuɗaɗe ne ta Fiddo da su masu yawa ta a ajiye masa aiko ya kwashi abun sa yana gaɓɓatan dariya kamar wani zararre. Miƙewa tayi ta fice da baya baya tana zagin sa yana Amsawa,sannan ya na ramawa. Haka tayi ta ta fiya da baya baya har sai da tayi masa Nisa kamar kullum sannan ta juya tana cigaba da tafiyar ta hankali kwance. Fitowar ta bakin titi ne inda ta parker motar ta ta shige tana tada ita sai dai tunda ta shiga motar take jan tsaki ita kaɗai.... " Shiru haka take zaune ta kafe waje ɗaya da kallo ga idanun ta cike da ƙwalla ta sha igiyoyi a jikin ta na ɗauri saboda kwanakkin nan da suka shuɗe tun bayan dawowarsu Canada abun ya ƙara hauhawa sai ta ƙara ƙaimin ji wa kan ta ciwo akwai lokacin da ta yanke gefen cikin ta glass wanda har yanzu ba,a san inda ta same shi ba, wanda da ƙyar aka ceto ranta kasancewar ba sosai ta samu yan kan ba amma duk da haka ta zubar da jini sosai. Komai na jikin ta ya sauya saboda yanayin jikin na ta. Wani irin kuka ta fashe dashi tana rufe idanun ta,tana sake buɗe su. Tana ƙokarin nuna inda ta kafe da idanun ta sai dai hannuwan nata a ɗaure suke baiwar Allah daga ɗauren ta fara buga kan ta da bango haka kake jin sautin ƙuu ƙuu tana gwara kan ta a bangon fillern da aka ɗaure ta akai,dai dai lokacin ne kuma ya zo kawo mata abinci domin kuwa yanzu shine kawai yake iya shigowa batare da tayi har gowa ba,domin tsoron kowa take yi dan ko su Amoh da Dady sai ta samu bacci da su Nurse mirra suke zuwa duba ta da tsaftace mata jikin ta,cikin wani irin sauri ya buɗe ɗakin da key da ya zo da shi kafin ya shige da sauri cike da tausayin ta da tsoro gudun kar ta yiwa kan ta illa duk ya san ba lallai ta iya ko dogon motsi bane saboda yadda Uncle Yaqub ya ɗaure ta dan shi kasawa yayi haka ma Dady dan Tausayin ta suke ji sosai kowannen su ji yake kamar ya da wo da lalurar ta jikin sa,Amoh kuwa tun da jikin Isha ya ƙara rikichaɓewa itama jikin ta ya tashi,yanzu haka tana fama da Bp. Wasu irin hawaye ne yake jin suna neman sauko masa sai dai kasancewar sa namiji mai ƙarfin hali da zuciya hakan ya sa ya shanye ya matsa kusa da ita yana ajiye wayar sa akan gadon dake ɗan nesa da ita kasancewar an chan za mata ɗaki yanzu tana kusa da Suhaila ga ƙofar ta gata ta. " MA'ISHA " ! Ya ambata yana haɗiye wani irin abu mai ɗaci a cikin zuciyar sa kafin ya fara ƙoƙarin kunce ta dan bayan ɗago fuskar ta da tayi kacha kacah da hawaye tayi jawur ya ji ya kasa jurewa ganin ta hakan,sai dai yana fara kunce ta, ta fara kai masa bugu da ƙarfi tana cigaba da kuka mai tsuma zuciya.Idanun sa ne suka yi jazir kuma ya kasa hana ta dukan na sa ganin yake yi kamar shin e abun da zai rage mata raɗadi. Uncle Yaqub da ya shigo gidan yanzu ne ya zo direct nan dan ya gan ta kasancewar suhaila tace masa Suhail na nan aiko cikin sauri ya matsa ya riƙe ta yana katsawa Suhail tsawa mai girma ganin abun dake faruwa domin ya san tsaf zata iya ji masa domin ba acikin hankalin ta take ba,maimakon ya hana ta bugun sa shine ya saki jiki tana ta jibgar sa gata da ƙarfi kamar na maza goma. Da ƙyar Uncle Yaqub ya ɗaure ta yana furta " Are you in your right sense Suhail , What's this " .? Ɗagowa Suhail yayi ya kalle sa da idanun sa da suka ƙara rikiɗewa na damuwa da tausayi dan shi kwata kwata bai ji zafin dukan da ta masa ba. Rufe idanun sa yayi da yake jin sun masa wani irin nauyi. Babu abun da ke ƙara hargitsa tunanin sa irin jin kukan ƙanwar ta sa dake ratsa dodon kunnen sa. " Gaskiya baka cikin hankalin ka Suhail so kake kai da ita ku zama ɗaya ne,me ye wannan,ita fa ba,a cikin hankalin ta take ba,Amma kai fa ".?karamin tsaki yaja kafin ya ƙara furta " Gaskiya kaima kana buƙatar Ganin likita Suhail because what you did,person that's has normal sense can not do it Wallahi,yanzu kai ne kadai take sakewa da kai idan ka bari wani abu ya same ka ita kan ta da take a wannan yanayi ba zata taɓa yafe maka ba Suhail haba ". Kara ɗago jajayen idanun sa yayi ya zubawa Uncle Yaqub. " Yes kalle ni da kyau na ce ba zata taɓa yafe maka ba,Suhail dan Allah ka kula da lafiyar ka taka ita zata taimaka mana mu samu ta Ishaaa,domin ka san abinci ma kai ne ka wai ke iya saka ta cin sa ,to idan ka samu rashin lafiya duk wazai yi wannan zata zauna cikin damuwa da rauni na jiki da na zuciya." Miƙewa Suhail yayi yana cigaba da jin faɗan da Uncle Yaqub ke masa na kwance ta. Allura ya haɗa wanda tunda ta hango yana haɗa ruwan ta fara sakin wani Marayan kuka mai tsumaa zuciya tana girgiza kan ta,alamar bata so.Duk yadda yake jin Tausayin ta haka ya cije ya zube mata ruwan nan tare da taimakon Uncle Yaqub ko minti ɗaya bata yi ba kuwa bacci ya kwashe ta wuyan ta yayi gefe. Tare wa yayi ya jinginar da ita ga ban gon yana ƙ ara zuba mata idanu.Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya miƙe ya fita tare da abincin da yazo mata dashi dan ya san yau ba za ta iya saka komai ba a cikin ta saboda baccin da zata yi ta yi har wayewar gari,ko kuma tsakar dare.✍️✍️ Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800 Book one zai kare a page 50 Dan haka wadda ta shirya sai ta saka kuɗin ta dan babu wanda zamu jira zamu cigaba da wannan tafiya in sha ALLAH.🙏🙏🙏 # _FA'EEH BG CE✍️_ *PAID BOOK 800* Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin✍️ FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 4️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💕💕💕💕💕 Amoh ce zaune idanun ta sun sauya na Zallar Damuwar da take ciki. "Amoh ki yi Haƙuri kin ga ko ɗazu sai da Yaya Suhail ya ce ki rage ya wan damuwa Bpn ki yana hawa yana sauka ". Ɗan kallon Suhaila Amoh tayi dake maganar kafin ta sauke numfashi ta ce " Suhaila yaushe Ya ta zata samu lafiya,yaushe Auta zata zamo kamar kowa,a koda yaushe ina yin mararin wannan mafarkin sai dai kamar abu ne mai matuƙar wahala,Ya Allah ka yaye wa baiwar ka, ka sa iya kar wahalar kenan,Allah ka bata lafiya ''. Amin Suhaila ta amsa jikin ta sanyaye. " Amoh zata samu lafiya in sha ALLAH,jarabawa ce,Ke kike faɗa mana Allah yana jarabtar bayin sa ta hanyoyi da ban daban lallai mu tamu jarabawar kenan,Allah ya bawa Ishaa Lafiya,ka nuna mana ranar da zamu zauna muyi fira da ita ". Kai Amoh ta girgiza cikin karyewar zuciya ta ce " Amin ". " Allah ya sa " Shigowar Suhail ce ta sanya Amoh zuba masa idanu. Kawar da kan sa yayi daga kallon ta shima yana zama kusa da ita,jikin sa sanyaye. " Ta samu bacci ai " Ajiyar zuciya Amoh ta sauke tana cewa " Allah ya bata ikon farkawa cikin aminci " Amin dukkanin su suka amsa. Uncle Yaqub ne da ya gama masa faɗa bayan fitowar su saboda shima yana da mugun jinini kuma ganin sa a bunda Suhail yayi wauta ce kawai da rashin hankali dan haka gudun kar ya maimaita yake ta nanata masa illar abun da yayi. Zama yayi kusa da kujerar da ke kallon ta su Amoh. Yace " Amoh ya ƙarfin jikin ki,ki yiwa Yaron nan magana ya riƙa kulawa da lafiyar sa ". Ɗan Hararan sa Suhail yayi da ya ɗaura kan sa jikin Amoh. Yana sauke ajiyar zuciya jin Uncle Yaqub bai tona sa kai tsaye ba. Yar ƙaramar dariya uncle Yaqub yayi. Amoh kuwa ce wa tayi " ka riƙa kulawa sosai Baba na ka ji ".Tana shafa sumar kan sa. Kai Suhail ya jinjina mata yana ƙara shigewa jikin amoh. Ko da Dady ya dawo haka ya isko su kowa dai zugum sai a hankali tun daga nan ya fahimci akwai matsala dan haka bai tambayi kowa ba ya dai yiwa yar sa addu'a cike da tausayin ta bayan ya leƙa ta window ya gan ta cikin yanayi na tausayi dan har da ƙwalla ya fitar mata. 💫💫💫 *A ɓangaren Abbu bai samu ganin Mahaj ba sai bayan sallan Magriba. Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga room ɗin sa kasancewar ya gan sa masallaci kafin ya ƙara sauke kallon sa kan sa ya ɓacewa ganin sa. Dan haka ya kasa hakurin ya isko sa ya same sa da kan sa. Kunya ce ta kama Mahaj ganin Abbu dan haka ya sunkuyar da kan sa ƙasa bayan yiwa mahaifin na sa kallo mai ɗauke da soyayya da ƙauna irin ta ɗa da uba. Dan shi da ya ji knocking a tunanin sa Mubarak ne. Zaune yake kan ɗai daga cikin rugs dake ƙawace da Falon na sa ya sha baƙar jallabiya yar Moroccco Black color ta masa kyau matuƙa kyau ya haɗu da kyau. Sai da Abbu ya gama ƙare masa kallo sannan ya saki ɗan guntun murmushi dai dai lokacin da Mahaj ya ɗaga idon sa ya kalle sa ganin bai zauna ba har yanzu ga shi yana jin idanun mahaifin na sa akan sa. Ɗan lumshe idanun sa yayi a hankali ya buɗe yana zubawa mahaifin sa su da bashi da na biyun sa a wannan duniyar mamakin murmushin da yake ta saki yake yi gashi ya kasa magana bare shi kan shi ya yi magana dan murmushin ya bashi mamaki taya za,a yi mutun yayi ta Murmushi haka babu dalili duk da ya san abbu mutum ne mai sakin fuska amma ya san akwai wata ƙasa.Anya kuwa Abbu lafiya yake zuciyar ta furta masa. Shima kan sa murmushin ya jefa shi wani irin yanayi sai dai ba zaka iya gane hakan ba kai tsaye dan fuskar sa babu wani alamar murmushi a cikin ta sai dai a sake take.Kasa haƙuri yayi cikin sanyayyiyar Muryan sa da take fita cike da natsuwa da sakewa irin ta ɗa da mahaifi da yar chakuɗaɗɗiyar Hausar sa ya ce " Abbu wani abu ya faru ne " ? Kai Abbu ya girgiza yana ƙara faɗaɗa murmushin sa kafin a hankali shima ya ce " Kawai farin cikin ganin ka nake yi nayi kewar ka ,shine da ka dawo daga masallaci mai makon ka fara zuwa ka ga sanyin ranka ka shige ". Murmushin gefen baki ya saki wanda Abbu ne kawai yake samun sa yana yin ƙasa da kan sa. Riƙo hannun sa Abbu yayi wanda ya san ba zai ce masa komai ba a bazata kuwa ya ji ya ce " I'm sorry bayan isha'i na so naje wajen ka ". Murmushi ne ya ƙara fita akan fuskar Abbu. " Bani labari ya komai yake tafiya " Cewar Abbu kafin ya ƙara furta " Da abun da ya faru da wanda bai faru ba " Ɗan kallon sa Mahaj yayi yana zuba masa idanu kamar mai nazari kafin ya janye idanun sa akan Abbu. Abbu kuwa ya lura dan haka ya ce " Kai nake jira malam ".Ya na haɗiye dariyar sa.Ganin kallon da yake masa. Shiru ne ya biyo baya kowa da tunanin da Yake a ransa Abbu na jiran amsar da ya san ba samu zai yi ba har a zuciyar sa ya sani babu abin da zai faɗa masa. Shi ko mahaj haka kawai zargin Muby ya ɗarsa masa amma sai ya haɗiye komai bai nuna ya ɗan fahimci abun da Abbu ke son ji ba. Abbu kuwa cike da tsokana ya ce " Ni fa yarinyar nan shatou nake son jin labarin barafasar da kuka sha,Ance ...." Shiru Abbu yayi yana rufe bakin sa domin ya san kai tsaye zai zargi Muby ɗin.Wanda bai sani ba tuni hakan ya faru dan yana jin sunan ya fito bakin abbu sai da ya furta a cikin zuciyar sa I know. Ɗan lumshe idanun sa yayi kafin ya buɗe su ya ce " Wa yace Abbu " ? Ɗan shiru yayi kafin kuma ya ce " Wace ce Shaaaa touuu " Ya kai ƙarshen sunan A rarrabe kamar mai tsoron kiran sunan. Yana sauke Numfashi. Abbu kuwa zuba masa ido yayi sai dai murmushin sa ko kaɗan bai bar kan fuskar sa ba mai cike da kamala da dattijan ta ka. " Manta kawai ". Cewar Abbu. " Shatou kake tambaya ta,ai ka fi ni sanin wace ce hakan,ko ba haka ba ".? Shiru yayi wa Abbu yana ƙara yin ƙasa da kan sa.Sai dai Abbu na lura da shi domin kuwa bakin shi ya tura gaba da jan guntun tsakin kan leɓɓen sa na tuna riginar su da shatou ɗin yanzu,wanda Abbu ya ji fitar sa a kunnen sa dan haka ya tabbatar da rainin hankali ne kawai na ɗan sa tun da ya mayar da shi abokin wasan sa dan haka ya share zancen yana cigaba da sakin murmushi inda ya canza wani zancen daban. Mahaj kuwa tunda Abbu ya chan za magana ya ɗan saki jikin sa suka fara yar fira irin ta ɗa da uba wadda ta shafi rayuwar su ta baya da ta mahaifiyar Mahaj ɗin. Suna a hakan a ka kira sallan Isha'i a tare suka fice kasancewar dukkanin su sunada Alwallan su. Suna gama Sallah muby ya riga kowa fitowa daga masallaci haka kawai baya son haɗuwa da mahaj ɗin musamman yanzu da ya ganshi tare da Abbu. Ai ko MAHAJ da yake lura dashi bai ce masa ƙala ba har ya fice yana gama addu'ar sa kuwa shima ya fito. A nan Babban falon dukkanin su suka hadu har Aiyah da take dan jifar shi da harara.Dinner zasu yi wadda dama haka suke yi Shine kawai yake tsame kan sa saboda wasu dalilai bayan takurar idanun Aiyah a kansa da na wasun ta dan mutun ne da ya tsani kallo yana cikin dalilin da ya sa baya shiga mutane sosai bayan rayuwar kaɗai ci da ya ratsa jikin sa. Ɗunguma suka yi zuwa kan Dinning hannun sa riƙe da na Abbu shi da kan sa ya ja masa kujera ya zauna yana furta " Yau ɗure zanyi wa wani babu ruwa na " Shi kuwa sai ƙara ɓata kyakkyawar fuskar sa yake yi dan ji yake cikin sa cike yake saboda ya sha chocolate a ɗazu bayan ya farka daga bacci kafin aka kira sallah ya fice bayan yayi brush da watsa ruwa,bayan tashin sa daga baccin wuraren ƙarfe shida da yan mintuna. Abbu kuwa ko a jikin sa kuma bai damu da idanun Aiyah da yake ji kan sa ba. Dan shi ganin Mahaj yake yi yana rama bai sani ba ko idanun sa ne kuma ya san cewa rashin saka abinci ne isasshe a cikin sa. Kasancewar ya san yanayin tsarin cin abincin sa ya zuba masa kunnun gyaɗa mai kyau da basa rabo dashi a koda yaushe kan dinning saboda Abbu da yake mugun son sa duk da shima Mahaj ɗin yana son sa amma saboda bai damu da cikin sa ba anfi yiwa abbu dan haka koda yaushe ake masa shi a duk girkin da masu aiki zasu yi sai sun yi shi. Ajiye masa cup ɗin yayi gaban sa yana furta " Shaaa yanzu kuma bana son ganin komai sai cup idan ba haka ba zan saka Samira da Salma su matse mini kai na yi maka ɗuri ". Haɗe rai yayi jin sunayen da Abbu ya ambata yana tura bakin sa gaba kamar yaron da ke shan nono. Yar ƙaramar Dariya Samrah ta yi wadda ta warke har ta koma ayyukan gaban ta dan har school ta koma. Yar hararan ta yayi kafin ya ɗauki cup ɗin ya na zuba masa idanu,daddaɗan ƙamshin sa ne ya daki hancin sa hakan ya sa ya ja ɗan numfashi yana kai cup ɗin bakin sa bayan yayi bismillah.cike da kulawa Amma ta ce " Yau dai wani zai ci dole ". Ɗan kallon ta yayi bai ce komai ba bai kuma nuna alamar ya san da shi take ba. Inda sabo Ammah ta saba da hakan dan haka cike da rashin damuwa ta kalli fuskar Abbu dake ta sakin murmushi yana kallon MAHAJ dake shan kunun sa a hankali. " Kuna damuwa da wanda ko ciwon kan sa bai sani ba,idan yunwa zata masa illa me ye naku a ciki da har ake maganar yiwa garjejen ƙato ɗura ". ta kai ƙarshen maganar tana jan ƙaramar tsuka. Furucin Aiyah ne ya sa shi ɗan dakatar da shan kunun sa kafin ya ɗan saci kallon ta dan haka kawai kwana biyun nan yake shafa ma kan sa lafiya ya daina leƙa wajen ta kwana biyu kuma cike take dashi a kan hakan jira take ta samu dama ta masa tass shi da uban sa dan a cewar ta shi ya ɗaure masa.Abbu ɗan ɓata fuskar sa shi yayi sai dai bai ce komai ba. Dan baya da amsar bata sai dai ya san shi ke da komai a ciki kuwa domin shine wanda zai fi kowa fita hayyacin sa idan ciwon yunwa ya kama masa ɗaan sa abin son sa farin cikin sa. Shiru wajen yayi kasancewar kowa ya fara cin abincin sa da aka yi serving ɗin sa. Su Samira da Salma kuwa dukkanin su wani irin kallo ne suke jifan MAHAJ da shi wanda Ni dai Ban gane ma kan sa ba kuma yana ɗai daga cikin dalilin da ya sa baya son zaman kan dinning ɗin tare da su. Yana jin idanun su jikin shi sai dai bai nuna yama lura da su wajen ba koda Abbu ya saka su cikin zancen sa kuwa bare yanzu. A haka aka gama dinnern inda shi ya riga kowa ta shi duk yadda Abbu ya so ya ƙara saka wani Abbu ya ƙi dan kuka yake neman ma sa a cewar sa ya ƙoshi da ƙyar ma yake numfashi. Ganin hakan ya sa Abbu bai matsa masa ba ya masa sai da safe yayi hayewar sa. Koda ya shige ɗakin direct jallabiyar ya cire dan dama bai fita da wayan sa ba towel ya ɗaura ya shige wanka bai jima ba ya fito bayan ya ɗauro Alwallan kwanciya bacci. Wasu riga da wando ne ya saka na bacci silky masu kyau guntun wando maroon color kafin ya ƙara gudun Ac ya hayewar sa kan bed ɗin sa bayan kashe hasken ɗakin da barin bedside lamp na gefe ɗaya. Bacci dai ya ƙi zuwa duk yadda ya shirya yin sa yanzu kasa ɗaukar sa yayi domin kuwa sai juye juye yake yi wanda shi kan sa bai san dalilin ba ƙaramin tsaki ya ja yana jan ƙaton duvet na sa mai taushi blue color mai kyau ya rufa jikin sa tun daga kan fuskar sa har ƙafafu yana turje turje shi kaɗai tare da jan tsaki. zaune ya miƙe yana hargitsa gashin kan sa dake ta walƙiya A hankali ya furta " Ya rabb.." Idanun sa ya lumshe a hankali wata sabuwar Addu'ar ya ƙara yi kafin ya kashe light ɗin gaba ɗaya. Ya kwanta babu abin da ke tashi a dakin sai ƙarar aikin na'urori da sanyayyen ƙamshin sa dake maƙale da ɗakin yana a hakan bacci ya kwashe sa rungume da filon sa wanda inda sabo ya saba hakan tun bayan da ya zamana yana kwana shi kaɗai ya saba wa kan sa da hakan ko da ya manta ne sai ya farka ya rungume filon sa yana jin hakan a matsayin cewa kamar mahaifiyar sa ce ya rungume duk da bai waye ta ba. A suba ta gari ɗan Abbu.✍️ Mun kuwa komawa in da muka fito. Masu niyyar fara payment su fara ba zamu jira kowa ba wayen da suka biya sun yi hakuri matuƙa dan haka babu jira in sha ALLAH. Kuna da wani page an jima In Sha ALLAH. Na yau kenan wannan bashin jiya ne.🤭🙏🙏 Kuna ƙwarin gwiwata readers Allah ya sakawa kowa da Alkhairi. Masu bibiyar wannan labari na cikin group da na waje,mutanen facebook,mutanen Wattpad,mutanen Arewapens ina yiwa kowa fatan Alkhairi.💔🙏✍️💫 To subscribe yours contact this number 08069059746 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 5️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ *Wannan shafin naki ne kacokam Uwata* *_(Maman Abba)_*💕💕🥺kiyi yadda kike so dashi.Shatou na godiya.🙏🙏 *** A ɓangaren Abbu ma sai da safe kawai yayi wa Aiyah ya shige da matar sa. Yau ko yar firan da suke taɓawa as a family ba,ayi ta ba saboda yadda Aiyah ta ɓata mood ɗin Abbu. A ɓangaren shatou kuwa suna gama cin abinci kowa ya watsa ruwa kafin suka fice zuwa makarantan islamiyya.Abin mamaki yau bata tsokani kowa ba har aka tashi dan sai da Inna ni ta mata kashe di ashe kuwa ya shiga kunnen ta. A haka aka rabu lafiya da su malam Abu. Bayan sun dawo makaranta kuwa sun samu Baffa na baya gida yana kasuwa dan haka suka shirya suka same shi Chan kasancewar an kusa Magriba hakan ya sa ya sako su Gaba suka yo gida yana jin daɗin firar su da ya yan na sa musamman shatou.Wadda ke bashi labarin yadda taga malam Abu na zare ido wanda ke jiran tayi masa laifi yau ya dake ta. Alwallah kawai Baffa na yayi ya wuce masallaci shi da Bibu bayan isar su gidan. Ita kuwa shatou tare da Inna ni suka yi sallama kafin suka cigaba da aikin da suka tarar Inna ni nayi na fige ganyen zogala da Baffa na ya tsinko musu daga daji. Shigowar su Baffa na ce ta dakatar da su inda dama Kowa Inna ni ta ajiye Musu abincin su a tare suka ci suka ƙoshi sai dai ita kamar koda yaushe bata ci nata nan ba a ɗaki ta ci abin ta kafin ta fito suka cigaba da taɓa yar fira. A hakan Kiran Sallahn Isha'i ya same su kowa ya yi wajen Sallah. Suna dawowa kuwa karatu Baffa na ya ƙara bita musu sai da ya tabbatar kowa ya iya sannan ya bar su. A ɓangaren shatou hankalin ta ya rabu gid a biyu domin kuwa tana son fita dandali tana tsoron abun da kan iya biyo wa baya kan rigimar ta da shamsu maƙiyinta. Wata zuciyar ta ce mata kije da Bibu shiru tayi kafin wata zuciyar ta bata amsa da zai iya masa illa idan ke bai same ki ba. To ai kina da mai kare ki baga iro nan ba. Wata zuciyar ta ƙara furta mata. Kafin ta yi shiru jin ɗayar zuciyar na ce mata ki rufa ma kan ki asiri yanzu idan baku haɗu da iron ba ke dai zauna gida bari ƙura ta lafa. " Ke lafiya ,me kike tunani haka " ? Inna ni ce da ta zuba mata ido tun ɗazu ganin ta lula wata duniya abun har mamaki yake bata wai kamar shatou da tunani.Me take tunani wata zuciyar ta tambaye ta dan haka ta furta mata tambaya kai tsaye. Bayan zuba mata idanun na ta. "Babu komai Inna ni " Shatou ta furta wadda maganar zucin ta tsaya chak kan tambayar da Inna ni ta mata. Murmushi ta ƙara saki tana Kallon Inna ni da tayi alamar rashin yarda ga shatou ɗin. Dan kai kawai ta girgiza. Baffa na da ya lura bai ce komai ba sai yar dariya kawai da ya saki. Yau shatou da wuri bacci ya kwashe ta ko firar basu gama ba dan ta bi maganar zuciyar ta.Aiko ba,a daɗe ba bacci ya ɗebe ta Inna ni ce ma dole ta tashe ta ta kai ta tayi fitsari saboda tana da gigin Bacci kafin ta taimaka mata tayi tsarki ta kai ta ta kwanta tayi mata Addu,a ta shafe ta ta ko ina, bisa ga Bibu da yaje da ƙafafun sa dan idanun sa biyu shikam. ---------Abba na gama cin abincin sa ya miƙe ya dawo falon dai dai lokacin da Leena ke fashewa da kuka kasancewar ta ƙoshi amma B ya ƙi daina bata sai ɗura mata tea yake yi ta kasa samun fuskar da zata masa magana kai tsaye. Dan haka Ganin Abba sai ta fashe da kuka tana furta " Abba na ƙoshi ".cike da shagwaɓa Murmushi Abba yayi yace '' Ai bani zaki faɗawa ba ".ya nuna mata B dake ƙara haɗe fuskar sa ganin abun da ya rage kawai cikin cup ɗin wanda ya kamata a ce ta shanye sa. Zuwan Ummah ne wajen wadda ta tsaya kimtsa dinning ɗin tare da taimakon masu aikin ta. Ya ƙara bawa Leena damar fashewa da kuka ganin bata ci nasara wajen Abba ba. " Ummah zan mutu idan na shanye wannan abun,Dan Allah Kice Abar shi haka ". Ummah cike da kulawa ta matso wajen da sauri tana furta " oh ohh my Baby yanzu wannan hawayen duk na tea ne" ta kai ƙarshen furucin tana shafo hawayen dake silala.Cike da tausayin ta ganin ta ɗaga kan ta ta ce " Soja ya isa haka kar ka saka mini ya amai " Ta rungume Leena jikin ta. Shiru Leena tayi tana sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin sanyi a ranta. Idanu suka haɗa da B da ya haɗe fuskar sa yana Hararar ta yana kallon cup ɗin aiko da sauri ta rufe idanun ta tana sauke numfarfashi a jere. Abba cike da tausayin yar sa ya yi dariya ya ce " Kun fi kusa ai ". " Ni ba zan iya saka baki a rigimar da bata shafe Ni ba " dalilin da ya sa bai kula ba dan ya san tana bukatar abun da zata sanya wa cikin ta ne dan suna bukatar abinci bayan kulawa Saboda yanzu da ka kalli fuskokin su da ke sanya shi a wani irin yanayi mai cike da kewa bege wanda baya da maganin sa sai hakuri zaka san sun faɗa sun yi yar rama kowaccen su tayi fess da ita hasken su ya ƙara fitowa haka ma manyan idanun su. Yau ta kama laraba Abba da kan shi ya shirya ya kai ya yan sa makaranta domin kuwa nan ne yake samun damar basu ruwan da malam yace dan haka yace ya hutar da Drivern su sai dai duk da haka cikin dabara yake yin komai tunda har da su Hamra da Nina yadda ba zasu taɓa ganewa ba dan har su ya haɗa tun da Addu,o,I ne na kariya.kwana biyu yana kai su sai da ya tabbatar da ya cika maganar malam gaba ɗaya sannan ya bawa driver damar cigaba da kai su makaranta. Ummah ma da B sun ɗan shiga mamaki saboda kowa ya san hidimomin dake gaban Abba ta harkar business ɗin sa sai dai sun ji dadi sosai musamman ganin yadda su Leena da ta fara ɗan samun ƙarfin jiki ta na ta murna Abba da kan sa yake driving na su. Drivern sa tare da security na sa a bayan su. Kowaccen su murna take yi sosai dan haka basu taɓa kawo wa kan su komai ba daga ruwan da Abba yake ba su idan sun fita kuma koda wasa babu wacce ta taɓa yin maganar koda da Ummah ne ko wani na cikin gidan dan basu ɗauke shi a komai ba. Cikin ikon Ubangiji kuwa jikin kowaccen su ya samu ƙarfi sun koma asalin su sai rigima ta dawo sabuwa har kamar ma ta yanzu ta fi ta da dan basu ko shaƙar inuwar ɗayar su ɗan abu kaɗan sai ƙokarin illa ta juna. Sabo da hakan ya sa yanzu Ummah take sassauta murya wajen yi musu faɗa tun da ta san faɗa da ɗaga murya ba zai taɓa shirya mata ya yan ta ba,sai Addua,a. Dama B ne kuma ya koma Lagos. Abba ma yayi tafiya satin da ya gabata dan haka take lallaɓa abun ta,tana jan su jiki sai faɗan ya ɗan fara raguwa dan tana zaunar da su ta musu nasiha mai ratsa jiki,wadda wani lokaci ta shiga wani lokaci tafita. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya ta kowanne ɓangare yau da daɗi gobe babu daɗi.A kwana a tashi ba wuya wajen Ubangiji yau ake cika sati Uku daga lissafin zuwan Ramadana da ake yi kuma cikin ikon Ubangiji yau ne ake dibon wata idan an gan sa za,a tashi da azumi idan ba,a gan shi ba za,a duba zuwa gobe. Cikin ikon Ubangiji kuma an samu ganin wata mai alfarma a saudia wanda har an gabatar da sanarwar anan Nigeria. Baffa ne ya shigo bakin sa cike da farin ciki yana furta " Anga wata fa gobe sai tashi da azumi ". Shatou dake zaune fuskar ta kamar zata yi kuka dan tun da aka ce yau ake dibon wata ta koma marainiya ta ce " yanzu da gaske Inna ni duk azumin da kuke yi shi zanyi Ni fa sai in ga kamar ban isa ba wallahi dube Ni fa kalli ɗan ƙirji na shamfal " ta kai ƙarshen zancen tana jin kamar ta saki kuka kasancewar wannan shine lokaci na farko da zata yi azumi goma ma a jere a chan baya iyakar ta biyar ko shida a rarrabe har Ramadan ya ƙare Inna ni ta yi faɗa Baffa na ya tare wa shatou ya ce ta huta har lokaci ya zo.Wanda sai yanzu ta fahimci lokacin gashi yanzu tana jin kamar bata iya yin su duka gashi Kuma idan ta ajiye babu laifin komai, tana da babban laifi gurin Ubangiji Allah zai hukunta ta,Sannan ƙofar da aljanna da ake buɗewa masu azumi bada ita ba gashi kullum Baffa na da malam Abu suna faɗa musu ni'imar Aljannar fiddausi har da Inna ni idan yan maganar ta na kai. *Allah ya saka mu aljanna baki dayan mu,Ni da ku masoya wannan labari na nesa da na kusa.Allah ubangiji kuma ya nuna muna zuwan Ramadana na 2026 lafiya,Allah ya yafe mana kurakuran mu,wayen da muka aikata a cikin sanin mu da wayen da muka ba,a cikin sanin mu ba.🤲🤲🤲* " A,a ni zan Miki " Cike da Haushin surutun na shatou da take shaƙa da babu sayi bakin ta inna ni tayi furucin,Ita kuwa shatou muryan Inna ni ce katse mata tunanin ta. Bakin ta tura gaba Kafin ta kalli Bibu da ko a jikin sa dan shi ko waccan shekaran azumi ishirin yayi duk da da ƙyar ya kai shi wanda ko shi Baffa na da Inna ni sun yi sun yi ya bar shi a goman da suka ce yayi ya ƙi. Yace na sa goma sauran ladar goma na su ne. Sun ji daɗi sosai ita ko Giwa girman banza da rigima ake kai shi da sanya idon Inna ni dan ta san halin ta tsaf zata iya shan ruwan ta ta lankahe mata ala dole ƙisa take ji duk da haka kuwa Inna ni ta san Allah dai ya kyauta.A zumin manya. " Yanzu Bibu kai ba zaka taya ni a zumin ba ". Yar dariya yayi yace zan Miki kema ai wannan karon. Dariya tayi kafin ta ce " kai kammm ka huta " Baffa na dake kallon ta yar dariya yayi yana girgiza kan sa kafin ya ce " Ke ma kin huta ai ". " Baffa na wai Yanzu Dagaske dai Nima tare daku zanyi a zumi kuma duk saboda wannan jin..." " Ke ban son shirmen banza dan uban ki,azumi ne sai kin yi shi wallahi kona sassɓa Miki,idan kuma kina wasa na ji ko naga koda wasa kin saka wani abu a bakin ki bayan wucewar lokacin sahur,Sakarar yarinya kawai ". " Ke kar ma na ƙara jin maganar a zumin nan bakin ki ibada ce ta zama dole gare ki,dan haka ki rufe mini shi ko na haɗa dake da shi na zane ". Inna ni ta kai ƙarshen zancen tana haɗe fuska. Shatou kuwa ganin tana neman tono rigima hakan ya sa ta yin shiru tana ƙyafƙyafta idanun ta tana ƙara cunna bakin ta gaba. Baffa na dai murmushin kawai yayi. " Ke zo nan ma na huta da shirmen ki riƙa mun aikin nan ". Cewar Inna ni dake aikin Yankan ganyen Alayyahu na miyar sahur. Baki tunzure ta miƙe ta matsa ta ɗauki kabewa ta fara feɗewa sai dai Inna ni na lura da ita yan kan kabewar da ƙeta ake mata shi dan cizgar ta take yi kamar Allah ya aiko ta da wuƙa mai kaifi da aka heƙo musu ɗazu dan haka duk ta kusa zabce rabi da nufin tana ferewa ita kuwa Inna ni kai kawai take girgiza wa tana mamakin yadda za,ayi ace kamar Shatou bata son yin A zumi duk da ba laifin ta ba ne na mahaifin ta ne domin kuwa da ace ya saka mata hannu tun chan da,ai da tuni ta gwane,ta saba da juriya Amma yanzu budurwar yarinya da jinin ta da komai balagus duk wata ace a tana rakin a zumin da ko ɗaukar sa ba,a yi ba.Har take iƙirarin ba zata yi ita dai ba. Kai Inna ni ta girgiza tana sakin murmushi a cikin zuciyar ta idanu ta zaro da ƙarfi ganin yadda aka mayar mata da kubewa yar ƙarama yar cika aiki ta zabce rabi aiko babu arziki ta ce " Ta shi je kai geron dawo na furan gobu, wannan aiki dai babu niyyar yin sa Nagde " . Summ summ haka shatou ta saka hijab ɗin ta, tana turar baki tare suka fice Da Bibu sai dai ko kafin su isa ta wartsake ta saki jiki fushin ma na Inna ni ya sauka.✍️ Maganar gaskiya ba zan ɓoye muku ba Maman Abba na so na ƙwarai da gaske.🥺 Ita kawai ta damu da shiru na na kwana biyu.Ta zata ko ciwon na wa ne ya tashi lallai wannan itace soyayya ta gaskiya. Naji daɗi sosai lokacin da naji muryan ta. Ina godiya sosai uwata rubutu ya bani mutane masu daraja da ƙima a rayuwata. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana ya raya Miki zuriyar ki.I Love you uwata wallahi ina jin ta kamar mamata da ta haife ni Allah ya bar mu tare har a gidan aljanna.✨🙏❤️❤️💕 To subscribe yours contact this number 08069059746 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 6️⃣↔️4️⃣7️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💫✨💫✨💫 # Shatou/Iro # Aiyah # Mahaj # Abbu # Faiza Almustapha murai# # fa'i✍️ Suna kai geron suka kamo hanyar gida. A tare suka shigo gidan Bibu a gaba ita a baya suna dariya. Da gardamar wanda zai je ya karɓo dan Bibu ne yaɗauki geron yanzu da zasu fita. Ganin su haka ya sa Inna ni shanye murmushin ta na yar maganar da suke yi da Baffa na dan kar shatou ta samu damar ta.Ta ƙara samun damar wata magana. " Inna ni mun dawo " Cewar Bibu. Ɗan kallon sa ta yi ta saka murmushi kafin ta ce " Allah yayi muku albarka ". " Amin Inna ni ". Shatou ta amsa da ƙarfi tana sakin murmushi. Inna ni dai bata bi ta kan ta ba sai yar hararar da ta sakar mata.Kafin ta ce " Kamar fa jiya ne aka gama Ramadan Baffa na,Yau gashi cikin ikon Allah wani ya sake zuwar muna lallai lokaci babu wuya wajen Ubangiji,Allah ya nuna mana ƙarshen sa lafiya,ya yaye muna damuwowin mu ya kawo muna ƙarshen su ". Ta kai ƙarshen zancen cikin wata raunatattaciyar zuciya wani shuɗaɗɗen lokaci na dawo mata da take ta ƙoƙarin ɓoyewa kan ta. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan ƙaƙalo murmushin ya ƙe jin shatou na furta " Kuma Allah ya sa Inna ni ki haifa mini yar ƙanwa ".Ta kai ƙarshen zancen tana dariya.Haka ma Bibu. Baffa na ma ɗan numfashi ya sauke fahimtar duk inda addu'ar ta ta nufa da kuma abun da yake masa kai kawo a kullum da take ɓoyewa da yake ƙara shigar da ita damuwa. Amin ya amsa cike da tausayi. Kiran Sallah ne ya fitar da su daga gidan shida Bibu.Basu dawo daga masallaci ba sai bayan Sallahn Isha'i sannan suka dawo . Koda suka dawo Su Inna ni sun gama komai har tuwon ta tuƙe abun ta wanda ta sha fira har ta gaji dan shatou kamar an buɗe bakin ta. Sai kuma ta koma firar kayan Sallahn su da ke wajen ɗin ki da kuma irin wankan da zata yi ranar. Kafin kuma aka koma bata labarin Mahaj da ake kira Bature tana yi tana Harare Harare " Wai ni zasu yiwa turanci,nace musu turatu uwar Turai ai nima na iya"... Shiru tayi jin Inna ni na cewa " You are not serious shatou ".Kafin kuma a hankali ta ƙara furta " You are too funny ". Zuba ma Inna ni ido tayi kamar yau ta saba ganin ta kafin kuma ta buga tsalle ta ce " Inna ni turanci kika yi fa kema yau ". Wani farin ciki ne ya ƙara bayyana kan fuskar shatou ita kuwa Inna ni ɗaure fuskar ta tayi kamar ba ita tayi furucin ba kafin tace " ke ban son shashanci,ni da ko aji ban ta ɓa zama ba ina zan ji Yaren Bature ai sai ku ". Ɓata fuska shatou tayi kafin ta ce " Na fa jiki Inna ni ". " A gidan wa kika ji ni shatou ".? " Me na ce " ? " Ce wa kika yi yom no siriyes sai kika saka suna na gaba " Shatou ta yi maganar tana dariya dan ta kasa faɗa,itama ta san shirme ne ta haɗa duk da kalmar ta ɗan shiga kan ta. Dariya ce Inna ni tayi wadda ta jima bata yi ba. Kafin kuma ta ɗaure fuska ta ce cike da tausayin Shatou " Gaskiya ba ki ji dai dai ba shatou ". Ɓata fuska shatou tayi jin furucin Inna ni. Shiru tayi kamar mai nazari chan kuma sai ta ce " Haka fa kika ce to sai in Aljannun ki ne ko Inna ni ". Baki sake Inna ni ke kallon ta kafin ta ce. " Yau naga ta kaina ni matar salihin Bawa yau ni ce ake cewa mai Aljannu ". Tsuru tsuru da ido shatou tayi wadda ta san ta kwafsa,tana tsoron Inna ni ta riƙo ta,dan haka ta zuba mata ido tana sauraren Inna ni dake ƙara furta " to wai gidan wa na same su " " Ai ni ban ce fa kina da su ba,a gefen ki ƙila suke tsaye ". Ɗan ja baya Inna ni ta yi kamar irin ta ji tsoro aiko shatou ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa " Wallahi Inna ni kina da su " Ance duk mai tsoro yana da aljanu ". Inna ni ma Murmushin kawai ta yi kafin ta girgiza kan ta sannan ta ce " Lallai ko ƙila sune kan,kiyi addu'a to". Ai ko addu'ar ta fara dai dai lokacin kuma su Baffa na suka dawo nan suka zauna suna shan iska suna taɓa yar fira shatou na fara saka maganar firan su da inna ni akan turanci da ta ji ya fito bakin ta Inna ni dake lura da ita sai ta tare ta hana kuma duk wannan abun baffa na,na lura sai dai bai san me Inna ni take ƙoƙarin hana shatou faɗa ba,dole haka shatou ta haƙura,suka cigaba da wata firan har lokacin kwanciya bacci yayi kowa ya watse,kafin lokacin ma ta watsar da komai. Koda lokacin Sahur yayi shatou da ƙyar Aka samu aka tashe ta sai da tayi nak sannan ta nemi waje ta kwanta. Yadda kuka san taliya a wannan rana ta ɗai ga watan Ramadana haka Shatou tayi ta lauɗin yunwa kuma Inna ni na saka mata ido sosai ta lura shatou akwai tsoron Allah dan ta ga alamar bata sha komai ba ko cin wani a bu dan yau ma da asuba sai da ta ƙara nusar mata. Yadda kuka san yini biyu haɗe haka shatou ta ga wannan rana. Kowa ya kalli shatou sai ta bashi dariya dan haka ranar babu abinda ta tsinana wa Inna ni tun da suka dawo makaranta take sheme tana jin jiki. Salloli ma da ƙyar take iya miƙewa ta yi su Ita dai Inna ni kai kawai take gyaɗawa cike da takaicin shatou.Da mugun tausayin ta da kullum yake ɗar suwa a ran ta. Koda aka sha ruwa kasa miƙewa tayi saboda yadda ta shaƙe cikin ta tab Da ƙyar ta samu ta yi Magriba da isha'i ai ko,ko Fira yau bata yi ba bare ayi ashamm bacci ya kwashe ta yau ma da taimakon Inna ni ta kwanta,kamar jiya. A ɓangaren Ishaa kuwa tun daga ranar ta ƙara zama shiru shiru babu ko alamar lafiya ajikin ta sai dai ta zuba wa waje ɗaya ido har Suhail da take ganewa yanzu ta daina kula shi dan haka yan kwanakkin nan duk ta fara ramewa saboda kafiya bata karɓan abinci ko kaɗan bare kallon sa.Idan aka matsa mata haukan ta ya ƙara ta shi tuɓuran.Dan haka yanzu komai da dabara ake lallaɓa ta domin babu wanda a yanzu baya yar ƙwalla saboda Tausayin MA'ISHA.Taimako kuwa babu wanda ba,a nema mata wanda ake mata amfani da shi cikin dabara... A ɓangaren MAHAJ kuwa sun koma China kasancewar chan yake a zumi dama mafi yawan lokutta saboda karatun sa. Sai dai ya kan dawo duk bayan ɗan lokaci kafin fitar Ramadana wasu lokuttan kuma ya na yin sa gida. A kwana tashi ba wuya wajen Ubangiji Ramadana ya zo ƙarshe, su shatou an karɓo ɗin ki sai murna ake yi. " Inna ni wallahi kayan nan sun mugun yin kyau ba zaki gane ni ba ranar Sallah ". Murmushi Inna ni kawai tayi tana girgiza mata kai. Tana furta " da wannan ƙashin na ki na wuya sai kace wadda tayi a zumi talatin ciff ". Dariya shatou tayi tana taɓa wuyan ta ta ce " ai ana gama azumi zan cika sa ". " Allah ya sa " Inna ni ta furta tana Murmushi. Bibu ma murna yake ta yi yana gwada kayan na sa kala biyu...Kamar na shatou da hijab ɗaya. Cikin ikon Allah an ga wata yau gobe ake hawan idi ta kowa ne bangare murna ake yi da yi wa juna Barka da Sallah. Mahaj ma gida yayi Sallah sai dai tun da aka dawo Idi ya shigewar sa duk yadda Abbu ya so ya fito ya ƙi fitowa. A ɓangaren masu aiki kuma sun kammala gyara sabon ɓangaren makarantar su shatou a bun ka ga harkar Naira,sannan an samar musu da hanyoyin ruwa masu kyau da tsafta bisa ga inda suke zuwa ɗebo ruwan su. Dan haka Abbu ya saka ranar ƙaddamar da aikin dan fara amfani da shi sallah da sati biyu. A cikin wannan lokaci na bukukuwan Sallah shatou an sha tangaririya ita da su Amina da su Ramata da Bibu dan duk inda za,a je da shi ake zuwa. Kowaccen su ta sha ado ta labta jan baki a baki da ja gira babu ma kamar su Ramata da Jawairiyya. Sai dai A wannan karon itama shatou ta sha Jan bakin ta da Ja gira ta yi kyau a irin kwalliyar ƙauye Inna ni dai in ta kalle ta sai dai tayi murmushi kawai ta girgiza kan ta,da ta so hana ta yi sai ta ga rashin amfanin hakan dan haka ta bar ta ta kashe fuskar ta sai gashi ta ɗan mata kyau,dan kafin su fita Tv ta mayar da ita har sai da Shatou ta kai ga cewa " Inna ni nayi kyau ko" ?.Kai Inna ni kawai ta gyaɗa kafin ta ce " Sosai kuwa kamar amaryar kauye ". ".a'a nikam Amaryar Birni ce ba zan yi aure a ƙauyen nan ba ni da ma zan zama yar sanda Aure na ba yanzu ba ". Inna ni dai a yanzu ma Murmushin tayi kafin ta ce " Allah ya ce " Har suka fice tana kallon Shatou tana Murmushi kafin hawaye kuma ya wanke mata fuska,daga nan ta shige ɗaki ta saki wani irin kuka mai ciwo da ƙunar zuciya sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta daga nan barci ya kwashe ta kasancewar ita kaɗai ce a gidan.Sai su shatoun........ " Uban wa na kama " Muryan sa ta daki kunnen ta ba ita kaɗai ba har ta da su Amina sai da ƙirjin su ya buga jin muryan sa dan tunda aka fara a zumi ko hanya basu ƙara haɗuwa da shi ba wanda sai daga baya suke jin ya shiga birni kai rake. Tsuru shatou tayi da ido tana kallon sa. Shima haka. " Yarinyar nan sai yar shila kike zama ". Maganar sa ta ƙara ratsa Kunnuwan ta. Ya kai ƙarshen zancen yana lasar baki kamar wani maye. Hararar sa ta samu ƙarfin yi sannan ta ce " kai muje " Bibu da ke a tsorace ya riƙe hannun Shatou gamm. Kara shan gaban su yayi kallon kallo aka fara tsakanin ta da su Amina kowa na tunanin abin yi dan sun ma fita tsorata. Dariya abokan sa dake tare da shi suka sanya ganin yadda shatou ke ta zarar ido. Hararar su ta ke ta yi tana jan tsaki. Wani mai zafin nama ne ya ɗaga hannu da zummar kai ma bakin ta bugu Sai dai bai samu damar yin hakan ba domin kuwa hannun sa aka kama da ƙarfi. Ba kowa bane kuwa face Iro da ya sha shaddar sa yellow sa ka wanke sai walƙiya take yi kamar an mata ruwan mai. Wani sanyi ne ya ratsa Shatou.Tana gode ma Allah. " Wallahi da ka taɓa ta sai zaman garin nan ya gagare ka ". Iro yayi zancen yana Harare Harare,Wanda ya je gidan su Shatou aka ce bata nan dan yaje gwada mata wankan san na yau dan yanzu ta ɗan fara sake masa sai dai yana ganin wulaƙanci kuma hakan ya ke shanye wa dan shi burge shi hakan ke yi saboda yana shiga birni,sai yake ganin kamar tana masa irin yadda yan matan birni ke yiwa matan su ganin sa abun da take masa yan ga ce. Hannun sa ya janye yana huci kafin ya ce " To uban ya zai sa ta mana tsaki,ita fa wannan yarinyar ji take kamar uban ta ya gina ƙauyen nan,ke ba yar kowa ba babu asali mai kyau amma ke har kin samu damar raina mana mu da ƙauyen mu,wallahi kin cin sa,a da mun Miki figar kaza, Ni da ace nine kika yiwa budurwa ta wannan bugun da tuni na jeme ki amma ko yanzu ba zan bar Shamsu yayi wannan yaƙin shi kaɗai ba ,zaki gane kuren ki ". Ya kai ƙarshen zancen yana jan mugun ƙyafci wanda ke nuna a hasale yake. " Ka kashe ta idan ka ta shi ". Iro ya furta shima cike da hasalaaa. Shatou dai ganin cacar baki ta kaure tsakanin su ne hakan ya sa ta ja hannun su Amina suka yi gaba.Tana ji yo muryan Shamsu na zagin ta da aiban ta ta,da kalmomi mara sa daɗi wayen da yarintar ta ba zata iya bata damar tantance su ba da ma,anar su. " Wallahi sai na mata mugun wulaƙancin da bazata taɓa mantawa da shi ba,ba dai kai ka ɗaure mata ba daga kai har ita sai na jefa ku a masifa,zaka san ka shiga hurumin Shamsu,Shatou sai ta zamo a bar tausayi ka rubuta ka aje ". Wayen nan sune kalmomin da suka mata wani irin tsayi a kunne da zuciya dan dakatawa tayi tana juyawa kadan ta kalli Shamsu dake maganar wanda ya ke zancen yana ƙure ta da kallo yana huci saboda yadda Iro ya tare hanyar ta sannan ya ce idan ma mutun ya cika Shege ya matsa ya taɓa ta sun san halin sa hakan ya sa kowa ya yi cirko cirko,shi ko Shamsu ya ce aka mo masa ita,Amma duk sun ƙi matsawa dan haka ran sa ya mugun ɓaci ya ƙara ƙulla masifar da ke cin zuciyar sa ta ƙiyayyar shatou da ya ɗaurawa kan sa. Haka kawai jikin shatou yayi mugun sanyi har ta ji kafafun ta sun kasa ɗaukar ta. Yawon Sallahn da ba,ayi ba kenan yau dan jikin ta ya mutu mutuss ta kasa ko tafiya da kuzari tayi sauri bare gudun da suke yi idan sun ga ji kafin su samu mafaka su huta suna dariya. Gidan su Amina suka wuce har Bibu. A chan ta ɗan wartsake har ta saki maganganun Shamsu suka cigaba da wasannin su na ɗiyar kara.Sai kusan Magriba suka yi gida ita Bibu kuma ta ce Bibu kar ya faɗi komai game da abun da ya faru yau,ɗan kallon ta kawai yayi bai ce komai ba dan duk da shima ba wani girma gare sa ba ya ji kalmomin na Shamsu sun ratsa kan sa dan haka ya ƙara tsorata ta da shi,tsoron sa idan ba kashe masu shatou zai yi ba.Dan haka yake jin kamar ba zai iya shiru ba sai ya fadawa Baffa na.Sai dai tuna cewa Inna ni zata iya ji kuma sai ta daki Shatoun hakan ya sa ya ji zai iya kame bakin sa. Koda suka isa gida Baffa na bai dawo ba shima daga fadar mai gari. Sun tarar da Inna ni tsakar gida tana sauraren rediyo ana zaɓen Barka da Sallah na gaishe gaishe na sallah ga yan uwa. Suna saka waƙoƙin soyayya na zamani. " Inna ni ma idan na yi Aure wata rana haka zance ina gaida Inna ta ina mata Barka da Sallah da ita Baffa na da Bibu da su Amina,Amma idan nayi Aure nesa ". Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " Ohh amaryar Iro ko kin manta an gama zancen ne ko dan kin ji nayi shiru ne ai magana ta kan kama tuni baffan ku har ya fara zancen kuɗin Aure zai karɓo jibi tunda ke kika bada dama a nemo Miki ". Idanu Shatou ta ƙwalalo ta ce " Dagaske Inna ni " ?Tayi maganar tana dariya. Baki sake Inna ni ta Kalle ta kafin ta ce " Dagaske dai kina son yaron nan ".? " Allah ya raba ni nikamm wallahi sai ɗan birni ". Kai Inna ni kawai ta girgiza tana ɓoye dariyar ta. Ganin yadda ta haɗe rai. " To ai na ga ko ɗazu angon naki ya zo neman ki " " Eh ai kawai gaisawa muke yi Ni bana son sa ina da miji na ɗan birni ". " Dagaske wane ne wannan mai sa,a ". Baki washe shatou tace " ban san shi ba amma dai ɗan birni ne,kuma zai zo nan ya kwashe mu tare da ke da Bibu da Baffa na,kin san Inna ni na taɓa mafarkin na je birni,ƙila ma shi zai zo ya kai ni makarantar yan sanda ". "Hmmm to Allah ya bada mai albarka " Cewar Inna ni idanun na ja sauya wa daga farin madarar su izuwa duhun damuwa da ya fara lulluɓe su. " To me ya sa ki ka bar ɗan mutane a tsaye oh ni Indo ". " Ai shi ne naga yana mun amfani shi ya sa,amma Ni kam bana son sa wanda ko bakin sa baya wanke wa,duk wari yake yi sauƙin ta ma shima yana saka dan turare ko kaɗan ne,Kai saka turare sai Batu.." Shiru tayi ta ƙi kai ƙarshen maganar sai kuma ta ja guntun tsaki ta ce " Maye " A bayyane. " Waye maye kuma " ? Cewar Inna ni. " Da wannan Baturen nake wallahi Inna ni ba a daɗe ba na gan sa a mafarki na kusan sau uku wai yana riƙo hannu na na zo mu tafi ". Cewar shatou. " To fa ku je ina " ? Inna ni ta tambaya. " Waya sanar masa,ai ni da zan ƙara ganin sa da nace masa wallahi yayi wa aljanin sa magana duk na ƙara ganin sa sai na ƙona su,har dashi,dan na san Aljannun sa ne ƙila ".Tayi maganar da iyakar gaskiyar ta. Inna ni dake sauraren ta murmushi kawai ta yi. " A,a shatou mutanen birni kike ƙokarin faɗa da su ki rufa mini asiri ki bar natsuwar da nake da ita yanzu ta zauna kar ki fara kin ji ki bar ni da sauran farin ciki na". Shatou dai sauraren ta kawai tayi ba tare da ta fahimci komai ba na inda zancen Inna ni ya kaɓa. Shiko Bibu sai dariya yake yi yana kallon Shatou dake maganar cike da ƙuruciya yana tunanin taya za,ayi ta iya faɗa da aljani bayan ga Shamsu ma ba ta iya karawa da shi duk yadda take cika baki idan ta gan sa zata masa rashin mutun ci. Inna ni dai bakin ta kawai take kallo tana dariya. Dan labarin yadda ta tare musu hanya ta basu kafin kuma koma bada labarin yadda Mopol ɗin nan yake tafiya da yadda Ogan su yake wani shan ƙamshi harda kwaikwayon tafiyar sa. Daga ƙarshe dai bayan Inna ni ta gama shan dariya ta mata nasiha da kulawa da barin raina manyan ta.Tana bin ta da addu'ar shiriya. Sannan ta ce ta cigaba da Addu'a rashin Addu'a ne ka saka ta yawan wannan mafarkin. Salloli da aka fara ne ya tayar da su daga firan da suke yi ta bikin sallah da suke bawa Inna ni yadda wasu suka yi kyau wasu basu yi ba,wasu ma basu samu ɗin kin ba take ce musu su gode wa Allah. Masallaci Bibu ya wuce. Tare suka dawo da Baffa na aka sha fira kafin kowa ya wuce makwancin sa. Sai dai fa shatou maganganun Shamsu sun sako ta gaba ji take kamar yanzu yake nana ta su,sai kuma maganar Auren ta da Iro da Inna ni tace mata wasa take yi mata ko maganar bata yi da Baffa na ba ganin ta matsa mata da tambayar bayan sun gama sallah wai dagske take yi.,Bacci ɓarawon ne ya kwashi shatou a yau bayan ta gama Addu'a.Dan musamman maganganun Shamsu sun mata tasiri ƙwarai da gaske.. Yau Sallah kwanan ta goma sha biyu ciff inda ya kasance saura kwana biyu Abbu su shigo wajen ƙaddamar da ayyukan da aka kammala. Shatou ce zaune ta buga ta gumi idanun ta sun zubawa waje ɗaya ido kamar hankalin ta baya jikin ta. Inna ni ce ta fito tana cewa " wai baki wuce wajen Sallahn ba har na gama na fito " Ganin shatou bata ma nuna ta san da ita take ba hakan ya sa ta ƙare mata kallon ƙwass ga wani irin tsoro na kama ta domin kuwa ta lura da shatou cikin yan kwanakkin nan tana yawan yin shiru ko ta makure gefe ta zubawa waje ɗaya ido ga shi ta ƙara yin wata irin rama kamar mai ciwon yunwaaaa... Ajiyar zuciya Inna ni ta sauke kafin ta matsa kusa da ita ta dafa ta ta kira sunan ta. "SHATOU"! Ai ko da sauri shatou ta kalli gefen irin a tsorace take babu zaton nan.zuba mata ido Inna ni ta ƙara yi kafin ta ce " Me ya ke damun ki wai,ke ba Damuwar komai ba amma ki zauna ki yi mini shiru ga ramar da kike ta yi,me yake damun ki ". Kuka ta fashewa Inna ni dashi wanda ke fitowa har ƙasan zuciyar ta sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru Inna ni bata samu damar rarrashin ta ba domin mamaki abun ya bata da tsoro dan tsoron ta kar ace wani abu ya faru da shatou bata sani ba duk yadda take saka ido akan ta. " Me yake faruwa wai ko sai na ƙara saka ki kukan yin kukan mai dalili ". Ajiyar zuciya shatou ta sauke kafin ta ce. " Inna ni ji nake kamar zan mutu kowane irin lokaci,sannan ƙirji na ke bugawa da ƙarfi kullum, taɓa ki ji fa,Ni na san tafiya zan yi na bar ku,ban ga kin haifa mini yar ƙanwa ba ".Ta kai ƙarshen zancen ta na ƙara fashewa da wani irin kukan da ya fi na ɗazu. Ita kuwa Inna ni wani irin rintse idanun ta tayi jin yadda zuciyar shatou ke mugun bugawa da kuma kalmomin ta da suka jefa ta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici duk yadda ta so ta hana hawayen ta zuba a wannan karon gaban shatou sai da suka silalo suka sauka akan kafaɗar shatou da ƙirjin ta yake cigaba da mugun bugu mai hana jiki da ruhi zaman lafiya. Chak ta tsayar da kukan na ta kafin ta ce " Inna ni kin ji ko " " Dan Allah ki mini Addu'a Allah ya sa ba mutuwa zanyi ba,bana son na mutu yanzu na Barki ". Wasu hawaye ne ke ƙoƙarin ƙara sauka akan fuskar Inna ni indata haɗiye su, Shatou kuwa jin hawayen Inna ni jikin ta sai ya ƙara karya mata zuciya sai take ganin kamar Dagaske mutuwan zata yi itama Inna ni ta ji tunda har ta ji danshi kamar kuma hawaye a kan fuskar ta. Kuka ta ƙara fashewa dashi. Wanda da ƙyar Inna ni ta rarrrashe ta tayi shiru.. " Je ki kiyi Sallahn ki in sha ALLAH ba zaki mutu ba sai kin haifa mini jikoki ". " Ba zaki tafi ki barni ba cikin wannan duniya mai abun tsoro shatou ina ji a jiki na kece haske na,da zai yaye mini duhun da nake ciki ke ce zaki kai mu ga hasken da zamu yi farin ciki a tare ".Ta yi wannan furucin na biyu a cikin sauti mara fita wanda shatou bata ji ba. Shiru shatou ta yi tana sauke ajiyar zuciya tana jin wani sanyi a ranta. " Ki cigaba da na na ta Innalillahi wa Inna ilaiihi raji'un kinji wannan abun da kike ji zai daina babu komai in Sha ALLAH Alkhairi ne,bana son wannan yawan shiru shirun yanzu idan kin gama Sallah kije ki same su wajen farautar " Aiko da sauri shatou ta washe baki tana furta " Dagaske Inna ni "? Kai ta gyaɗa mata itama cikin Murmushi mai haɗe da wani irin rauni da mugun tausayi. Aiko cike da ɗan kuzarin da shatou ta samu ta yi alwallah sannan tana gama sallah ta yi addu'a Sannan ta fice dan dama tace zata je Inna ni ta hana saboda bata son tana Guje guje kuma ta san muddin suka fita sai ta yi gashi dai ta fara zama yar budurwa duk da ƙirjin na nan shafe har yanzu sai tsawo da take ɗan yi. Da kyawun ta dake ta ƙara bayyana fili makerin kyau na ta aikin sa. Ficewa tayi daga gidan bayan ta yiwa Inna ni sai ta dawo,yanzu bata ma yin fargaban fita saboda ta san Iro na kare ta dan duk inda ya san Shamsu yake yana bibiya.Da ya ji labarin zai je wajen ta sai ya tare shi su yi ta rafka artabu tsakanin su. Kuma tun daga wannan rana sai Shatou ta saki jikin ta,saboda yadda maganar Inna ni ta mata wankin Damuwar da take ji a jikin ta da wani irin tsoro da ke shigar ta. Duk da wani gefe akwai ɗan tsoro sai dai mara yawa. " Wallahi ni bana jin tsoron ka,dan haka baka isa ka kashe ni ba,sai lokaci na yayi ". Kallon ta yayi da kyau ganin yadda ta riƙe ƙugu.Babu tsoro ko ɗar akan fuskar ta ko da chan tana shanye abun ta bai ta ɓa ganin Zallar tsoron sa ba a idanun ta Wata muguwar dariya ya saki kafin ya ce " Ke ni zaki saka a tozar ta gaban abokai na ". " Wallahi sai na illata ki,sai na cusa Miki baƙin ciki ". Dai dai nan Iro ya bayyana yana furta " Allah kaɗai ah haka ". Kallon sa Shamsu yayi kafin ya ja tsaki yana jefa masa muguwar Harara. Cikin rashin damuwa da son ƙara ƙure Shamsu ya ce. " Shatou na ina zaki je ne " Baki ta fara turawa gaba jin sunan da ya kira ta da shi da ta mugun tsana wai shatou na.Mugun jin zafin sunan take yi bata da yadda zata yi ne da ta hana shi kiran sunan ta ma gaba ɗaya. " Wajen Baffa na zanje farauta ". Ta bashi amsa. " To tafi,kuma ki kula da hanya ". Ya furta mata yana sakin murmushi yana ƙara washe bakin sa ganin ta gyaɗa masa kai kamar irin yana da mugun iko da ita. Hmmm.😏 IRO yan love manya.LOl🤪 Bari dai nayi shiri kar shatou's fan su wullo mini daƙuwa.😂🤗 ...Bai bar wajen ba sai da ya ga shatou ta ɓace ma ganin su haka ma Yaga hanyar da Shamsu ya bi wanda ya cika ya batse. A ɓangaren shatou kuwa take ta saki komai da ya faru ta cigaba da falfala gudun ta har ta isa wajen su Baffa na aikuwa take ta ƙarasa wartsakewa tana ta tsalle tsalle harda gasa suka yi da Bibu wanda ya cinye ta kasancewar kwana biyu ya daina zuwa Farauta,aiko tana ta matsar hawaye Baffa na kuwa murmushi kawai yake yi yana kallon su Bibu kuwa dariya yake ta mata. Daga ƙarshe itama nan ta saki jiki har suka yaɗa zango suka gasa wani ƙaton Zomo na daji su ka ci nan sannan suka yi wa Inna ni guzuri suka yo gida. ***Yau an tashi da shirye shirye, su mai gari sai kai kawo ake yi da su Baffa na a fadan mai gari ta shirye shiryen zuwan su Abbu domin ƙaddamar da ayyukan cike da farin ciki domin kuwa abun fari ciki ne Babba a gare su da cigaba a ƙauyen su,kowa ka kalli fuskar sa zaka gan ta sake saboda farin cikin samun wadattun ruwa domin mafi ya wan su chan suke yini suna kallon wajen suna jin daɗi. A ɓangaren Abbu kuwa suma sun shirya tsaf dan zuwa wajen ƙaddamar da ayyukan sai dai duk yadda ya so suje tare da Mahaj ya ƙi hasalima Bacci yake sha kuma Abbu baya son ta dashi dan haka ya cigaba da shirin sa suje tare da Mubarak. Suna gama shirya wa suka fice kowannen su cikin shiga mai kyau babu ma kamar Abbu yadda kuka san wani sabon ango. A ɓangaren MAHAJ kuwa bayan fitar su daga kwancen da yake ido rufe kamar mai bacci ya miƙe yana sauke numfashi da a jiyar zuciya. Ƙaramin tsaki ya ja wanda ya tsaya iya kan laɓɓan sa kafin ya miƙe ya zare kayan jikin sa ya ɗaura towel ya shige toilet bai jima ba ya fito yana tsane jikin tsaf ya shiryawar sa cikin wata irin shiga ta alfarma yau kayan mu na Hausa ya saka Black jampa da takalmi masu kyau da tsada white color,sannan ya ɗaura agogon sa mai kyau ya fesa turare mai ƙamshi sannan ya kwashi wayoyin sa ya fito. Tun da ya doso ƙamshin sa ya mamaye ko ina har ya fice ya dawo ya zari wani a bu a wata yar kwalba sannan ya shige sashen Aiyah. Zaune ya same ta ta miƙe ƙafafun ta kan doguwar kujeran ta tana kallon tashar labarai. Sai wata lafiyayyen madara dake kusa da ita a cikin wani cup na tangaran mai kyau. Haɗe fuska ta yi dan gaisuwar ma ciki ciki aka amsa mishi ita.Duk da dama shi take zaman jira yau bai shiga gai da ita ba jiya, tana jiran ya cika na uku ta musu tass shi da uban shi dan ko chan baya kafin a zumi sai da ta zazzaga ma MAHAJ ta yaɓa ma MAHAJ mugayen kalamai mara sa amfani,wasu ma ita kan ta bata san amfanin faɗar su ba. Daga gaisuwar nan kuwa bata ƙara ce masa komai ba haka shima. Miƙewa yayi ya na mata sallama. " Ga madara nan ko zaka sha ". Ta furta masa ba ta re da ta kalle sa ba. Ɗan kallon madaran yayi wadda yake ta satar kallo tun shigowar sa saboda ya san tana da madara mai kyau da take sa ake nemo mata,yana son ta sosai lokacin da yana ƙarami har shan ta yake yi a sace bata sani ba. *WAIWAYE,MU KOMA FARKON LABARI* Daji ne dake cikin garin suleja wanda ake kira ƙare kukan ka. Babu abun da ke tashi sai kukan tsuntsaye kala kala sai kuma yana yin yadda itatuwa ke kaɗawa suna bada iskan hunturu mai daɗi kasancewar lokacin sanyin da ake ciki. Matashiyar budurwa ce ke tafiya cikin dajin a hankali da wani irin tulelen ciki a jikin ta da alama cikin zai kai kamar wata shida haka ko bakwai.Hawaye ne jage jage a kan fuskar ta ga idanun ta sunyi wani irin jaaa tafiya ce ta ke yi wadda bata san inda take jefa ƙafafun ta ba.Yadda take tafiyar kai kan ka zaka shaida a gajiye take kuma a galabaice.Kukan karnuka da taji a bayan ta ne hakan ya sa ta fara sauri tana ƙarawa tafiyar ta sauri kafin ta haɗa da gudu domin kuwa ko ba,a faɗa mata ba ta san ko suwaye kuma suka cimma ta rayuwar ta na cikin galalari domin kuwa kisa ne mai zafi zasu aiwatar akan ta domin yadda suka yi neman ta a chan nan ma hakan ne zai kasance.Cikin wani irin gudu haka take kutsa ƙafafun ta cikin ramukkan dake gaban ta da tulelen cikin na ta ga wata irin Hajijiya da ke kama ta wadda ba ta san mafitar ta ba.Sai dai tana fatan da irin wannan yanayi gwara mutuwar ta domin kuwa wata irin azaba ce ke ta so mata na gudun da take yi dan gudu ne bana wasa ba.Tana kawowa dai dai bakin wani ƙaton rame mai kama da kogo ta faɗa nan domin tsira da rayuwar ta da abinda ke cikin na ta tana sauke haki kafin kuma kan ta ya buge da wani irin ice da bata lura dashi ba A cikin kogon wanda hakan ya sanya ta fara ganin dishi dishi kafin kuma Numfashin ta ya ɗauke ɗiif. Wani irin zabura tayi ta miƙe daga kan haɗaɗɗen royal bed da take kwance Numfashin ta na wani irin sama yana ƙasa kamar zai tafi da rayuwar ta ga zuciyar ta dake wani irin bugawa kamar zata faso ƙirjin ta lokaci guda ta haɗa wani irin zufa. Sunan ta da aka kira ne cikin ɗan tsoro da tausayi yasa ta fara samun natsuwa tana lumshe lulu eyes ɗin ta da suka tara ruwa kamar na hawaye sai dai ba su kai ga saukowa ba. "ALEESHAT ''!!! Zubawa matar idanun ta tayi da taƙara kiran sunan ta,tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika mata ido sai dai abun ya ci tura domin kuwa a hankali ta ɓarke da wani irin kuka mai tsumaa zuciyar mai saurare.Dafa ta Babbar matar tayi wadda ke sanye da shiga ta ado ta alfarma ita ma idanun ta sun sauya jikin ta yayi sanyi alamar damuwa.✍️ Rikicin cim kenan yau kuma ina muka samo Alishat.🤔? Shin ya kuke jin tasirin maganganun Shamsu ? Wace irin manakisa yake shiryawa Shatou? Lallai zamu tsunduma filin watse Gara ku gyara zama.💃💃💃💃💃💃💃💃 Zaku fahimci komai,a hankali zamu war are komai na san zaku yi mamakin yadda aka yi muka koma farko,haka tafiyar take haka labarin ya zo,muna ni da ku. Fatan zaku jure mu cigaba da wannan gwagwarmaya a tare.Allah ya biya kowa da gidan aljanna.🤲🤲🤲 Ba zan gaji da faɗa muku ba mun kusa kammala Book One,two and three paid ne.Ongoing 800 Complete book idan mun gama 1k Masu buƙata Ga numban da zaku tuntuɓa *08069059746* Ko ki saka kuɗin direct to my opay 8069059746 Sai ki tura payment receipt naki ta Wannan ñumban. *+234 808 750 4734* Note : idan kin san ba zaki iya jurewa karatun shafi shafi ba Ban ce ki saka kuɗin ki ba,kar ki zo kina matsa mini da yaushe za,a gama ku raba mini hankali biyu.Na kasa concentrating akan gyara muku labarin na yi ta sauri mu kashe tafiyar a zo a yi ta zagina.Lol✍️ *FA'EEH BG CE✍️* SHARE FISABILILLAH.... REACT AND COMMENT PLS 🙏🥰💕 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣8️⃣↔️4️⃣9️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Second to the last free page.* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ # Alishat # Asad # Mamma # Alhaji Mamman # Fa'eeh BG # ✨✨✨ Rarrashin ta matar ke yi cike da tausayin ta. Sai da tayi shiru ne sannan ta sake ta ta juya ta ɗauko mata ruwa mai sanyi a cikin wani ƙaramin fridge dake a cikin bedroom ɗin ta ba buɗe mata. Ruwan ta miƙa mata babu musu kuwa ta kafa kan ta a hankali ta sha dan su ta fi buƙata a yanzu,a hankali ta sauke a jiyar zuciya da numfashi a tare tana sauke goran a bakin ta jin sun ratsa ta ta ko ina. Lumshe idanun ta tayi tana buɗe su. Yaron da ke gaban ta da ya dunƙule waje ɗaya ta kalla wanda a ƙalla zai kusa kai shekara biyar a duniya. Baccin sa yake sha hankali kwance kusa da ita dan ajikin ta ma rabin jikin sa yake. Itama matar shi ta kalla kafin ta ce " Sannu mafarkin ne ? ". Kai Budurwar da aka kira Alishat ta ɗaga kafin ta ce cikin natsatsiyar Muryar ta mai sanyi da taushi " Mamma me ya sa wannan mumman tarihi ya kasa barin idanu na da tunani na,me ya sa zan dinga mafarkin sa haka? ". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta yi shiru tana sauke numfashi jin wasu Sahabban hawaye na neman sauko wa tare da wani sabon kukan da ke bayyanar da ƙunar da zuciyar ta ke yi. " Ki cigaba da Addu'a In Sha ALLAH daga wannan ba zaki ƙara yin sa ba da yardan Ubangiji,kuma hakan ba komai bane sai yadda tsoron yanayin ya shige ki,kuma ki yi ƙoƙari ki daina tunawa kar ki haifar wa kan ki wani sabon ciwo kin san dai yadda kike fama idan ciwon ya tashi ". Matar da aka kira Mamma tayi furucin. Ajiyar zuciya Alishat ta sauke kafin ta ɗan shafa kan yaron da ya fara motsawa kasancewar lokacin sallar Asuba yayi ta zo ta tada yaron su wuce masallaci shida mai gidan na ta.Alhaji Sama'ila da suke kira Abbi wanda kuwa Ba kowa ta ya raɗa masa shi ba sai Wannan yaron. " Asad ! Asad ! " A hankali kuwa ya fara washe manyan idanun sa dake cike da bacci kasancewar jiya bai kwanta da wuri ba sai da ya yi ta rigimar da ya saba wadda har yanzu sun kasa samo masa mafitar ta.Dan haka wasu lokutan tare suke shan kukan su ita dashi abun tausayi dan ita kan ta da take mahaifiyar sa ba zata iya yi masa abun da ya ke nema ba hasalima ba ta san inda ta dosa a abin da yake buƙata. Zuba wa Alishat ido yayi yana kallon ta wadda ko makaho ya shafa ya san ɗan ta ne amma ba zaka taɓa cewa ita ce ta haife sa ba. Kiran sunan sa da ta ƙara yi ne cikin murya mai taushi ya sanya shi ɗan Lumshe idanun sa masu cike da bacci kafin ya ɓata fuskar sa ganin tana Murmushi tana nuna masa Mamma dake tsaye tana murmushi itama tana kallon sa. Da sauri ko ya ja tattausan duvet dake kan gadon ya rufe fuskar sa. Aiko da sauri itama ta riƙe duvet ɗin tana Murmushi mai bayyanar da side dimples ɗin ta. Jan sa ta yi baya tana furta wa a hankali cike da Rarrashi " Come on my baby wake up pls ". " Ummieeey ". Ya furta kamar ya fashe da kuka ɗaga shi tayi tana Murmushi. Mamma ce ta ce " Asad Abbi na jiran ka fa kaga an fara Salloli ". " Mamma Basshi ". Ya bata amsa kamar zai saki kuka. Yar dariya tayi ganin ya tsayu kan ƙafafun sa da taimakon mahaifiyar sa. Alishat ce ta furta " Mamma ce Abbi ya tafi kawai kar ya makarar da shi ". Murmushi Mamma tayi kafin ta ce " Ɗan nema yau Abbi fushi zai yi da kai ". Ta fice tana Murmushi. Shiko Asad jikin Alishat ya shige daga tsayen da suke. Hannun sa ta riƙa tana Murmushi sannan suka shige toilet guntun wandon dake jikin sa kawai ta cire masa ta masa wanka da brush sannan suka ɗaura Alwallah tare suka fito bayan ta ɗaura masa towel karami. Koda suka fito short kawai ta saka masa na yara mai kyau da tsada sannan ta saka masa jallabiya mai kyau itama ta saka ta ta a bayan akan rigar ta ta barci mai tsawo da take da ɗan buɗaɗɗen gaba wanda har albarkatun ƙirjin ta da suke a tsaye chik suka bayyana.Ɗan kwallin ta yana akan ta kafin suka kabarta Sallah a tare a natse daga ita har shi suka yi sallar sannan suka sallame,a tare suka yi addu,a gwanin burgewa. Karatun Alqur'ani ta fara bita masa yana Amsawa bayan sun yi azkar a tare na safe. Sai da suka karanta kusan page biyu sannan suka rufe qur'ani. Dai dai lokacin kuma Momma ta shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakin ta murmushi kawai ta saki kafin ta ce " Allah ya sa yau an muna Addu'a ".? Ɗan guntun murmushi Asad ya saki kasancewar ya san da shi ta ke kafin ya ce " Na Miki kuma har da Dady na ma ". Ya kai ƙarshen zancen yana washe bakin sa da yake ɗauke da yan tsirarun haƙoran sa da suke fara re sol kasancewar yana fira. Zuba masa ido dukkanin su suka yi babu ma kamar Alishat ƙirjin ta da ya buga ne ya sa ta haɗiye wani abu mai nauyi a zuciyar ta kafin ta sauke numfashi ba tace komai ba sai ma Wayar ta da ta ɗauka a gefen bedside drower da ta sanya Chaji da dare. Zama tayi bakin gadon tana kunna wayar ta ba tare da ta ƙara kallon gefen da Asad yake tsaye ba dan a duk lokacin da zai yi maganar mahaifin sa jikin ta mutuwa yake yi ta kan ji wata irin kunyar sa kunya mafi hana motsi domin kuwa duk duniya yanzu ba ta da kamar sa shine kawai abun da take kallawa tayi farin ciki sai kuma su Mamma da suka zame mata bango.Domin bata san ainahin abun da zata ce masa a kan mahaifin sa ba. Mamma kuwa numfashi ta sauke kafin ta saki murmushi ta ce " Me ka roƙa mini " ? Ta tambaya tana kallon kyakkyawar fuskar sa dake shar da ita. " Na ce Allah ya sa kar ki tsufa " Dariya Mamma tayi kafin ta ce " Yau wannan na samu kuma, toh nagde,Amma fa Asad tsufan nan sai ya zo wa Mamma ". Shi dai murmushi kawai yake yi yana kallon Mamma dan shi yaro ne da bai cika hayaniya ba. Ummiee yau ba zan je school ba ko "? Ya furta yana mayar da kallon sa ga Alishat. Ɗan ɗagowa tayi a hankali ta Kalle sa da idanun ta da suka ɗan sauya kafin ta ɗan yi luu da su kamar zata rufe sannan ta buɗe ta girgiza masa kan ta tana sakin guntun murmushi. Ɓata fuskar sa yayi hakan ya sa itama ta ɓata Tata fuskar kafin ta ce " Asad yau fa akwai wasa ". Cike da murna Asad yayi tsalle yana furta " yeeeh zan yi wasa da su Chuchu ". Dukkanin su dariya suka yi mai Sauti. Sai lokacin ne kuma Alishat ta kalli Mamma cike da murmushi ta ce " Mamma good morning ". " Wannan yaron naki Mamma ya sa na manta bamu gaisa ba ". Dariya Mamma tayi tana riƙo hannun sa ta ce " Shi ɗin ma yau bai gayar da Mamman sa ba ". Murmushi Alishat ta saki a hankali tana kallon su musamman Asad dake ta miƙa ma Mamma hannu ta ɗauke sa. Yana furta " Mamma Good morning ". Cikin yar maganar sa ta yara da har yanzu bakin sa magana bata wani zauna ba. Ɗaga shi Mamma tayi tana Murmushi kafin ta ce " Fine,good boy, hope ka yiwa kan ka Addu'a kai ma ".? Kai ya jinjina mata kafin ya ce " eh kuma har da Dady na na yiwa Addu'a ". Kallon sa Mamma tayi tana Murmushi kafin tace " good,Allah yayi maka albarka ". " Amin " Ya amsa yana jan jelar jallabiyar sa. Ficewa da shi Mamma tayi zuwa na sa ɗakin dan shirya sa kamar koda yaushe. Har suka fita yana ɗagawa Ummieen sa hannu yana murmushi sai kace wanda zai je wani wajen.Itama murmushi kawai ta Bisu da shi kafin ta ajiye wayar ta kwanta kan gadon tana sauke ajiyar zuciya ta tsirawa pop dake shimfiɗe a rufin ɗakin. Wayar ta ce da ta ɗan yi ƙarar shigowar saƙo ne hakan ya sa ta ɗan kalli inda ta jefa wayar kusa da ita kafin ta janyo ta a hankali. Ƙaramin tsaki ta ja tana wurgar da wayar kafin ta rufe idanun ta tayi shiru kamar mai yin Bacci. Miƙewa tayi zaune kamar an ce mata ta shi zaune. Wayar ta janyo ta duba notification na saƙuna da suke kan shigowa wayan rutu tu da su musamman na new numbers. Wani saƙo ne da ya shigo yanzu ta zubawa ido '' Yau ina son haɗuwa dake Dan Allah, wallahi ina son ɗanɗana zumar ki,ko nawa ne zan zube Miki,zan sakar Miki Naira kinji tauraruwa ta" Sai daga ƙasa aka rubuta Alhaji Mamman. Wani irin murmushi ta saki kasancewar ya fi sati biyu yana bibiyar ta kuma har yanzu ma ta kasa yin saving number sa,A hankali ta shiga what'sapp ɗin ta ƙara kalla saƙon da kyau.Tana jan Numfashi. Fitowa cikin chat ɗin tayi inda ta fara bin sauran saƙunan da suke kamanceceniya da wanda ta karanta yanzu. Sai da ta gama karance su tsaf sannan ta a jiye wayar gefe. Alhaji Mamman kuwa dake zaune ya saka tumbin sa gaba a ƙaton bedroom ɗin sa ne yana jiran reply na ta ya ja ƙaramin tsaki yana fatan ganin wani alama bayan na duba saƙon da ta yi ma sa sai dai har ya ci zaman sa bakin gadon har ya miƙe ya fara Zarya babu alamar zata bashi amsa hakan kuma Bai dame sa ba domin kuwa ya ji labarin ta tsaf da izzar da take da ita da jan ajin ta dan bata hurɗa ma da ƙananan mutane sai manyan Alhazzawa dan ko yanzu labarin ta a bakin wani abokin sa ne minister ne na security. Kuma tun da ya ga ƙirar ta shekaranjiya ya ji gaba ɗaya ya kasa zama kurumm dan haka yayi duk yadda zai yi har ya samu ñumban ta da bayanan ta shi ji yake ma zai iya auren ta idan ta bashi dama tun da Ance bazawara ce mai lasisi ba dole sai ta bariki ba. Wayar ta sa yayi wurgi da ita kafin ya miƙe ya faɗa toilet har ya saka wa jikin sa kumfa ya fito da sauri jin motsi a ɗakin kuma ya san bata wuce matar sa ce ba aiko da kumfa da komai haka ya fito yana bin bango tare da kiran sunan matar ta sa yana furta bani wayata kasancewar wayar ta shi bata da password a kan ta dan haka ya yi azamar fitowa gudun tonon asirin sa. Sake da baki matar ta sa ke kallon sa data zo sanar masa da lokacin breakfast yayi ta zata bai ma tashi ba. Salati ta rafka kafin ta kalli wayar dai dai lokacin shima ya sanya wata Babbar rigar sa pitch color ya rage kumfar. Wayar ya janyo jikin sa na rawa,sannan ya juya hanyar toilet jikin sa na ra wa. Hakan kawai jikin ta yake nuna mata akwai matsala mijin na ta bai da gaskiya. Dan haka ga zuba masa ƙofar da ya bi da kallo. Ƙyafci ta yi kafin ta ce " Alhaji breakfast ya zama ready ". Daga chan ya amsa mata da ya ji. Hakan ya sa ta ficewar ta Alhaji Mamman dake tsaye bakin ƙofar toilet ne ya buɗe ƙofar ya leƙo ganin Babu kowa a cikin hakan ya sa ya fito da sanɗa ya ajiye wayar ya koma. Aiko yana shigewa ta fito babu wahala sai gata cikin saƙonnin sa na what's app. Aiko ƙirjin sai da yayi muguwar daka kamar zai fito daka ƙirjin ta sunan take ta nanata wa. A bakin ta. " Leesha " Inda ta taɓa jin sunan take son tunawa sai dai ta kasa dan haka jin motsin alamar fitowa zai yi hakan ya sa ta yi sauri ta ajiye ta fice cikin sanɗa tana nazarin sunan da ya tsaya mata a ƙirji. Kitchen zata koma amma ta kasa dan haka bedroom ɗin ta,ta koma ta ɗauki wayar ta wata number ta yi dialing ringing ɗaya biyu aka ɗaga cike da azama bayan sun gai sa ta ce " Anty Ruƙy wai ni ko kamar na taɓa jin kuna labarin wata yarinya yar bariki haka na ga sunan a wayar Alhaji da chat da yayi mata,shine nake son tabbatarwa idan ita ce ". Daga chan ɓangaren ne aka furta " Leesha kike magana kenan "? Wani irin faɗuwa gaban ta ya cikin mazarin baki ta lailayo ashar ta sauke kafin " tace ita fa,ita nake nufi ". Murmushi ta wanchan ɓangaren a kayi kafin ta ce " Makiyya ki raba kan ki da yarinyar nan dan bomm ce ina faɗa Miki zata iya rabaki da Alhaji Mamman wallahi rabuwa ta har abada,ki bi komai a hankali a rabu lafiya,duk yadda kike tunanin yarinyar nan ta wuce haka,ita nata jawarcin mai lasisi take da barikin ta,dan haka ki bar komai hannu na". " Wai ni me take dashi haka suke ta tura kan su gare ta haba wallahi dole mu ɗauki mataki ". Hajiya Makiyya ta yi furucin a hasale. Ta ɓangaren Anty ruƙy kuwa numfashi ta sauke kafin ta iya furta " Wallahi da kika sani Alhaji sai da na kauce sannan na samu ya rabu da ita,saboda yarinyar ta haɗu ko ni da nake mace na sara ma baiwar da Allah yayi mata ta sura bayan haka ga kyau kamar wata ɗiyar aljanu wallahi sai dai kin gan ta a fili zaki iya fahim ta ta,kuma duk masifar nan taki wallahi ta na iya shanye ki,dan magana guda zata faɗa Miki ta kashe Miki motsin zuciya saboda zafin ta ". " Yanzu me ye abun yi Anty ruƙy ".? " Abun yi kawai shine kema ki bi hanyar da na bi ki jaye shi wajen ta kafin ki rasa shi ". Numfashi Hajiya makiyya ta sauke kafin ta ce " An jima zan zo gidan ki Anty ruƙy wallahi yau ba zan iya barci ba sai na san abin yi dan ba zan yarda ina ji ina gani wata shegiya ta jaye mini miji ba a bariki ba, ko ta karɓe mini shi ". Sallama suka yi tana a jiye wayar tare da jan tsaki tana haɗiyar wani baƙin ciki bayan tuno da saƙon da ta gani wanda mijin ta ya rubuta shi da kan sa cikin salon roƙo,gashi sai ja masa aji ake yi. Tsinewa Leesha ta dinga yi kamar ta cire bakin ta. Kafin ta miƙe ta haɗiye komai ta fito ta cigaba zaman jiran fitowar Alhaji Mamman ɗin wajen breakfast saboda yana fita da wuri majalisa yau,tare burin aiwatar da maganar Anty ruƙy da tace kar ta yadda ta nuna masa ta ga wani abu a wayar sa. A ɓangaren Mamma kuwa shayi kawai ta haɗawa Asad mai kauri ta bashi ya sha. Sannan ta ƙara masa wani sabon wanka ta shirya sa tsaf cikin shigar sa ta uniform dark blue masu kyau da necktie ɗin su.Kayan sun masa mugun kyau kamar koda yaushe yau ma Mamma sai da ta zuba masa idanu tana kallon sa dan koda yaushe wani kyau yake ƙarawa a idanun su.Turarukan sa dake shaƙe akan madubin sa ta fesa masa tare da gyara masa kan sa dake shan kayan gyara kafin suka fito daga bedroom ɗin na sa dake kusa da na Alishat ɗin sai dai na shi ta ko ina kayan wasan yara ne masu tsada da kyau. Da sallama Mamma ta shiga bedroom ɗin na ta tare da Asad riƙe a hannun ta yana kumbure kumbure. " Ummieey,Mamma wai ba jata bani ice cream ba na sha ". Maganar sa da ta shiga kunnen ta cikin barcin da ya fara fisgar ta ne hakan ya sa ta buɗe manyan idanun ta a hankali a kan sa tana ɗan Lumshe su tare da sakin guntun murmushi wanda daga shi sai Mamma da Abbi ke samun sa. " Asad yau an tashi da sanyi ka bari sai anjima idan ka dawo school ". Jin wannan magana ta sanya shi fashewa da kuka take dukkanin su hankalin su ya mugun tashi idanu Alisha ta zuba masa kamar ta saka kukan itama,saukowa daga kan gadon tayi a hankali ta janyo shi jikin ta,ta rungume ta fara rarrashin sa.ƙin shiru yayi sai da ta ɗaga shi sama ta fara juyawa dashi tana masa chakulkuli take kuwa ya sake ya fara ƙyalƙyata dariya kamar ba shi ba itama kan ta dariyar take yi cike da jin daɗi da farin cikin da take samu a gurin ɗan na ta. Mamma kuwa kallon su kawai take yi cike da tausayin su. Bakin wata locker ta je dashi rungume akan kafaɗun ta wata jaka ta janyo ta saka hannun ta ciki sai gata da chocolate guda uku masu tsada jakar sa dake kan wata yar hanger mai kyau ta buɗe ta zuba masa su a ciki dan ta san halin sa da shan chocolate kamar dan shi aka yi su bakin sa ya san kwaɗayi kwarai da gaske,haƙorin sa ɗaya har zaƙi (cin Zuma)ya fara kama sa sai fira (giɓi)Ya cire sa.Bakin sa washe yana murmushi yake kallon mahaifiyar ta sa cike da ƙauna kafin ya sakar mata kiss gefen kumatun ta ya ce " thanks you Ummmiey " cikin yar Muryar sa ta yara. Murmushi ta saki mai sanyi kafin ta sakar masa kiss a goshi itama sannan ta sauke sa ƙasa.Tare suka fito falo har da ita bayan ta ɗauro wata doguwar hijab akan rigar baccin jikin ta,da ta a za rafa akan sa.Tare da keys a hannun ta,dan ita ke Kai sa ta ɗauko sa. Mamma ce ta Kalle ta kafin ta ce " Lafiya hala baki fita yau ".? " Zan fita amma sai zuwa 10 ko 11 Mamma ". Kai Mamma ta jinjina kafin ta miƙa ma Alishat lunch box na Asad ɗin.Kasancewar baya breakfast mai nauyi tun da safe. Abbi ne ya fito cikin shirin sa na karya wa yana gamawa ya fice daga nan. Har ƙasa Alisha ta gayar da shi. Shiko Asad da sauri ya faɗa jikin sa yana dariya ɗauke sa sama Abbi yayi kafin ya ce " yoo my boy,Yau ka yi missing lada mai yawa,kar ka bari gobe ka rasa ka ji,ina son mu shiga aljanna tare ". " Abbi zamu sha Ice cream ko mai yawa ko ". Kai Abbi ya gyaɗawa Asad cike da murmushi. Dukkanin su murmushi suka yi kaɗan sun san inda ya dosa. Dariya yayi mai kyau da take fitar da haƙoran sa dake a ware wasu duk sun fita ma saboda firan sa da yake kai yanzu. Mamma ce ta ce " Ɗan nema ice cream ɗin nan dai ba zai fita bakin ka ba ". Dariya yayi bai ce mata komai ba sai faman shafa chocolate da Abbi ya basa yake yi yana jin daɗi dan Indai chocolates ne babu wanda ke masa shamaki da su Amma abun da ya shafi su Ice cream sune ake hana masa saboda yanayin ciwon sa. Sai da ya gama firan sa da Asad sannan ya ce " Yau ba da wuri za,a fita ba kenan " ? Ya furta wa Alisha wadda ya karɓa gaisuwar ta kafin ɗaukar Asad. Kai ta ɗaga masa kafin ta ce a hankali " Sai zuwa 10 haka ". " Allah ya taimaka ".Cewar Abbi. " Amin " Suka amsa har Asad. Miƙa mata shi Mamma tayi bayan saukar sa jikin Abbi. Bye bye yake musu har suka fice shi daga gidan Alishat dai sai ɗan murmushi take saki a hankali tana kallon Asad ɗin da ta tashi da mugun tausayin sa da ta kwana da shi,wanda yake maƙale ƙasan zuciyar ta koda yaushe. Suna fita tsakiyar compound ɗin wata lafiyayyar mota suka nufa ta buɗe,ta saka lunch box da school bags da ta fito da ita,bayan ta sanya su ta buɗe ma Asad extra sit sannan ta rufe ta koma mazaunin driver ta shiga. Kunna motar tayi kafin ta bata wuta suka fice gidan bayan wangale musu gate da aka yi na gidan... Gudu take a hankali na zallar kwarewar ta akan kwaltar.karatun Qura'ani ta kunna musu,ƙira'ar Sheikh Afif inda take bita wa a hankali,sai Asad da ke ta tsalle tsalle kan sit yana bitar dan inda ya iya ne ta kunna masa,wanda har ta gaji da furta ya zauna ya ƙi. Suna isowa dai dai makarantar ta su dake ɗauke da tambarin S&A Staff school Abuja. Ta dakata ta juyo tana kallon Asad da ya hargitse gashin kan sa da ya sha gyara. Ɗan zuba masa idanun ta tayi tana jin wata irin kasala na saukar mata domin a duk lokacin da zata yiwa Asad kallo na ƙwas dan ganin ainahin kamannin ta da shi da kuma tantance irin ta sa kamar da zubin da har yanzu take mamakin yadda hakan ya kasance.Sai ƙirjin ta yayi ta bugawa har ta ji Numfashin ta na neman barin gangar jikin ta. Yanzu ma hakan ce ta kasance sa ita dan haka da sauri ta janyo ruwa kusa da ita ta sha sannan ta rufe idanun ta jingina da sit tana sauke numfashi. " ummieey mun iso fa ". Muryan Asad ta sauka cikin kunnen ta yana furucin. Yana kallon gate ɗin na su da ake ta wuce wa da yara cikin sa dan an buɗe sa sosai. " Yes maa boy I know,I just want you to have a good small rest ". Dariya yayi mata yana furta " Yes Ummieeey na "Murmushi tayi tana shafa kan sa. Sai da suka ɗauki mintuna biyu kafin ta ce a hankali cikin Rarrashi " Asad don't fight anyone pls,Ka kula da kan ka,kayi karatu sosai idan ka dawo ka koya mini ". Kai ya jinjina mata cike tabbatar mata da zancen ta ya shiga kunnen sa. Sai dai tana fatan haka dan wata rana shima ɗan rigima ne,na kwarai da ya shiga cikin yara sai ya zama mafaɗaci a gida kuwa ba zaka taɓa cewa shine haka ba. Hannuuwan su suka dunƙule suke ware tare kafin suka tafa gwanin burgewa tana furta " promise,and deal " Shima ya furta " Yes Promised,deal accept d" Kiss ta sakar masa a goshi sannan ta buɗe motar. Fitowa tayi daga cikin motar ta ɗauko lunch box na sa da school bags ɗin sa kafin ta rufe bayan,sannan ta buɗe masa ta fito dashi ta ƙara taje masa kan sa da ƙara gyara masa zaman necktie ɗin sa. School bag ɗin sa ta goya masa kafin suka yi addu'a a tare suka kama hanyar cikin makarantar suna shiga kuwa yara aka zuba musu ido ana kallon su har da wasu daga cikin malammai ma da suka iso. Har a jin su Na nursery two ta kai sa ta damƙa sa hannun malamar su sannan ta fito da ƙyar dan kullum haka suke sai yayi kuka muddin ta zo komawa gida. Kuma haka zai ƙi sakin jiki sai ya ga dama sannan wani lokaci har a tashi baya kula kowa mutun ɗaya ce yake kulawa Chucu sai ya yan ta wanda yake primary one ko su ba sosai yake sakewa da su ba.... Gida ta koma cike da kewar sa dan duk lokacin da zata bar sa wani wajen sai ta ji kamar kar ta bar sa ko wani abu zai iya samun sa dan ita yanzu tsoron duniyar ya shige ta sosai. Koda ta koma gida Abbi har ya fita Mamma ce kawai a gidan sai masu aiki. Ita ma ɗin Mamma na ɗakin ta,da alama ta koma bacci ne. Bedroom ɗin Asad ta shiga da zummar tayi bacccin ta chan sai dai tarar da mai gyara musu ɗakuna na aikin ta duk da ba wani datti ke a cikin ɗakin ba wanda ana masa gyara uku a rana hakan ya sa ta juya nata bedroom ɗin wanda aka gyara shi tsaf sai wani irin ƙamshi da yake yi mai daɗi ko ina ƙal ƙal ƙal dama kuma a tsaftaccen sa yake kamar na Asad ɗin. Toilet ta shiga direct bayan ta zare kayan jikin ta ta ɗauro wanka da haɗaɗɗun bath lotion ɗin ta.Masu ƙamshi da tsada. Tana gama wankan ta ɗaura guntun towel da ya tsaya iya tudun Hips ɗin ta zuwa ƙasan laps kaɗan. Dogon gashin ta da wanke da shampoo masu kyau da tsada ta ke gogewa kafin ta fito daga toilet ɗin tana jan guntun tsaki jin ƙarar wayar ta dake kan gado. Bata kula ta ba sai da ta gama busar da kan ta da hand dryer sannan ta murza mayukkan ta masu kyau da tsada skin care product masu kyau sannan ta,taje kan ta da ya ji mayuka masu kyau,na gyaran gashi da ƙamshi,sannan ta sanya masa band mai kyau ƙwaya ɗaya ta kama shi da ƙyar. Jelar gashin dake kwance a bayan ta buzu iska na ɗan kaɗa shi kasancewar window na baya dake a ɗan buɗe da mai aikin ta buɗe da zata fara gyaran ɗakin,kuma ta manta bata rufe ba. Kame shi tayi da ƙyar kamar farko ta fara masa kalba tana sauke numfashi da tura bakin ta gaba kamar wadda aka yiwa laifi kuma bada kowa take ba sai gashin na ta wanda kusan kullum haka take akwai lokacin da ta ce wa Mamma zata je ama ta aski Mamman ta hana dan haka take ta fama dashi gashi sai ƙara haukar sa yake yi ga tsawo ga yawa.Sauƙin ta ma ya na da taushi irin na Fulani ne,mai santsi da walƙiya. Da ƙyar da numfashi aka ɗaure jelar gashin da ya sauka a tsakiyar bayan ta Dan Allah ya mata albarkar gashin kai mai kyau.Dan ko Asad da mace ne da anyi gashi ko yanzu kan sa a cunkus yake kamar ka kama ka kitse abun ka,ɗan shigar da shi tayi kaɗan ya zama kamar an yi mata donut ya kuwa zauna da kyau a ƙasan kan ta dan parking na ƙasa tayi. Tayi matuƙar kyau kyakkyawar fuskar ta ta ƙara yin sharr da ita kamar wata yar Baby Masha ALLAH jiki duk madara kai daga nin yadda fatar ta ke shinning ka san cewa gyara ne take samu na musamman. Turarukan ta ta murza masu ƙamshi tun da roll on,body spray,oud masu tsada haka ta bi kowane saƙo na jikin ta da kamshin nan take bedroom ɗin ta ya ƙara haɗewa da ƙamshi ta ko ina. Babu abun da tayi wa fuskar ta face shafa Kajol da ɗan lipbalm mai kyau da ƙamshi. Bakin gadon ta nufa bayan ta gama ƙarewa kan ta kallo wanda akoda yaushe lamarin Ubangiji take dubawa bata taɓa saran zata koma haka ba,zata tsinci kan ta a wannan rayuwar ba sai gashi Allah mai iko da buwa,ya mayar da ita haka wanda wasu lokuttan ita kan ta ta kan kasa gane kan ta,shi ya sa a koda yaushe take godewa Ubangiji. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jin wani irin tunani da ya ke kutso kan ta wanda bata rabo dashi a cikin zuciyar ta sai dai bata da madafa akan komai dan haka ta barwa Allah komai yayi mata zaɓi. Wayar ta ɗauka ta na kallon missed call ɗin.Ɗan ya ƙuna fuskar ta tayi kafin ta " Mayar da kiran ". Ringing ɗaya aka ɗaga kasancewar an san halin na ta,sai ta kashe wayan gaba ɗaya. Shiru tayi bayan ɗaura wayan akan kunnen ta " Leesha ki zo school yanzu an bamu Presentation kuma yanzu ake buƙatar mu kammala sa muyi submitting " " Waye ya bada ".? Ta tambaya cike da sanyin ta da kuma ko in kula. " Prof Maitama ".Aka bata amsa. "Okey I'm on my way ". Daga haka ta katse kiran. Bata re da ta jira ko zai ƙara yin wata magana ba. Shiru tayi tana zubawa ñumban ido wadda tayi saving da Course mate. A chan ɓangaren sa kuwa yana gama wayar ya sauke ajiyar zuciya domin wani irin sanyi ne ya ratsa shi jin tattausan muryan ta da tayi amo a cikin kunnen sa,duk yadda ta ke nuna masa kamar bata san inda ya dosa ba amma kullum soyayyar ta ƙaruwa take a zuciyar sa. Ya ɗan jima zaune a cikin capterian kafin ya fito yana komawa department na su na LAW dan fara gudanar da aikin na su kafin zuwan ta. A natse ta fara shirin ta,tana jan ƙaramin tsaki. Wata Jeans ne ta sanya ƙirar Companyn Dolce and Gabbana sai rigar sa fara mai buɗewa wadda ta ɗan saukar mata baya gaba kuma ta ɗan datse kaɗan. Masha ALLAH domin kuwa kwalar rigar ta zauna mata haka ma dogayen hannuwan rigar sun yi kyau sosai dan kamar yadda rigar take mai botir haka hannuwan suke. Black blue jersey veil ta yana a kan ta tare da sanya takalman ta hill masu mugun kyau da tsada wayen da suka ƙara yiwa kafar wani irin mugun kyau kamar dai yadda kuka san turawa na saka su sun zauna musu. Turarukan ta,ta ƙara saka sannan ta ɗauki wayar ta da duk wani abun bukatar ta ta fito falo bayan ta duba kan ta a cikin madubi da ƙara gyara zaman mayafin ta. Ficewa tayi da yar ƙaramar jakar ta a hannu tana tafiya tana baza ƙamshi.✍️ Idan an ga typing error a yi haƙuri cikin bacci na yi aikin. Kuma ina baku hakuri rashin update jiya,munyi yar hidima ne ta haihuwa🙏✍️ Book one na ta sallama.💃💃💃 Gobe ne last page namu na free in sha ALLAH. Kar ku ji wai daga gobe mun gama samun free book one ya ƙare. Dan haka ku hanzar ta shiga cikin wannan tafiya kar a yi babu ku kar ku bari wannan labari mai cike da abun mamaki nishaɗi,rikitar wa,ruɗani son rai ya wuce ku. Labarin da ban yake kamar yadda salon ma da ban yake.🤗🤗🥰ku dai ku zama cikin shiri kuma ku sanya juriya. Ban ce ki sayi littafi na ba idan baki da juriyar jiran page page kar ki zo ki Adda be ni ba update yau,yaushe za,a gama 😏🤭😅 Komai a hankali yake tafiya dole na san komai dade wa inda rai da lafiya zamu kammala labarin nan in sha ALLAH. Allah ya bamu iko ya ƙara muna juriya da Ni da ku yan ( KK CONVERSATION ROOM PAID & KURMAN ƘADDARA BOOK)Allah ya bar min ku na amana ta. Saƙon gaisuwa ga duk ɗaukacin member na wannan gida ina muku fatan alheri. To subscribe yours contact this numbers 0806 905 9746 0808 750 4734 FA'EEH BG CE ✍️✍️✍️ SHARE FISABILILLAH. LIKE,REACT,VOTE AND COMMENT PLS 🙏 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________5️⃣0️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *LAST FREE PAGE* Wannan shafi Sadaukar wa ne ga ɗaukacin masoya wannan littafi.📚 Jinjina gare ku,da gaisuwa mutanen kirki.. Maman Abba Ayeesha Abdullahi(ta kwaran shatou)😜 Na'eemart Collection H.S Ammiey Layla oumm Amjad Boss Bature Sadiya ka'oje Nainarh KD Zee Dodo Ibnatu Umar Oum Zainab (Diamond lady) Fauziyya yakubu ɗan Bello. Hudatu Umar Zainab Ishaq. Hajara kawu gana Habibah Yusuf Hausa Novel Audio and documents.(Rewa Novel Bilog). Maman Abdullah Mhiz bareemat. Hauwa Musa yeldu. Fatima A Bello Aishatul humaira. Maman Hanifah Pretty Minal Kuna da yawa fa har wayen da ban lissafo ba ina miƙa gaisuwa da jinjina.🙏🙏🙏💕Allah ya bar tare. _______________________________________ *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ # Asad # Aleeshat # Kamal Yarima # Doctor Mahuta # Part one ending # Faiza Almustapha murai# # Fa'eeh BG#✍️ 💦💦💦 Turuss tayi bakin ƙofar barin falon jin muryan Mamma da ta fito bada jimawa ba tana furta. " Breakfast fa ". Ɓata kyakkyawar fuskar ta tayi tana ɗan juyowa tana kallon Mamma. Mamma dai guntun murmushi tayi kafin ta ce. " Haba Hajiya ta dake ɗan naki ban san wanda yafi wani ƙiyayyar abin ci ba,yanzu da haka zaki fita da ciki a kwashe ". " Dawo ki karya,zaki fi samun ƙarfi a jikin ki ". " Mamma ba daɗe wa zanyi ba ai ". " Ahaf ai sai kiyi ". Ɓata kyakkyawar fuskar ta ta ƙara yi kafin ta dawo cike da yar shagwaɓa ta kama hanyar dinning da komai yake kai. Mamma Murmushi tayi kafin ta ce " Wa kunbo wa kayan ta ". Ɗan guntun murmushi Aleeshat tayi kafin ta zauna ta haɗa ma kan ta shayi mai zafi shi kaɗai ta saka ma cikin ta inda tayi ta sipping ɗin sa a hankali tana duba tsadadden a gogon hannun ta.Har ta shanye sa dama kaɗan ta haɗa dai dai cikin ta. Tana gama wa ta miƙe bayan ta ɗan goge bakin ta da tissue sannan ta ce a hankali " Mamma na tafi sai na dawo ". Ta kama hanya tana Amsawa da Amin jin addu'ar da Mamma take yi mata. Mamma da ido ta bita cike da tausayin ta domin kuwa ta san yanzu sai sun gan ta sai kuma idan lokacin tashi school na su Asad yayi idan ta dawo ta kan ƙara fita sauƙin ta ma yanzu saboda ya fara wayau ta rage fitar,da sun yi ƙokarin hana ta fita koda yaushe abu ya gagara har sun zuba ma sarautar Allah ido domin kuwaa duk lokacin da suka so hana ta fita musamman ta dare ita da su wani yanayi suke shiga domin haka take koma musu kamar zata haukace musu da magiya tace ita kaɗai ta san abinda take ji a jikin ta a duk lokacin da suka yi yunƙurin hana ta fita.Sauƙin ta ma yanzu ta rage sosai. Numfashi Mamma ta sauke kafin ta kama hanyar da zata sada ta da ɗakin ta. A ɓangaren Aleeshat kuwa cike da takon ta na rausaya kamar tarwaɗa haka ta isa kusa da motar ta,wata ce daban ta buɗe ta shiga yanzu kamar irin BMW ɗin na Black mai kyau. Wuta ta bawa motar bayan ta kunna ta inda aka wangale mata gate ɗin ta fice. A Guje kamar zata tashi sama dan dama ta saba da gudun ta ba Damuwar ta ba ce duk inda zata shiga cikin Abuja a high speed take gudun ta,sai ko idan Asad na aciki ne ta ke yin gudu kaɗan. Ba ta haura mintuna arba'in ba sai gata a iconic University Abuja branch parking ɗin motar ta dai dai ta, ta fito.Koda ta fito idanu ne kan ta kamar ƙasa dama kuma sun san wacece domin ita kaɗai ce Dalibar da ke yin parking na motar ta a parking space na staff ba tare da an mata komai ba.Ita ce kawai mai wannan capacity ɗin. Kawar da kan ta tayi daga kallon sa dan da shi ta fara haɗa ido kasancewar bakin department na su ne tayi parking. Ba tare da ta ce masa ƙala ba ta rufe motar tare da locking ɗin ta sannan ta cigaba da tafiyar ta inda ta san zasu haɗu zai iya yuyuwa chan ne inda team ɗin suke dan ba ta jin zata masa wata magana daga inda yake ko ta isa wajen sa. Shiko Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan shafa kan sa dan ya shagala da kallon ta dan koda yaushe kyawun ta ƙaruwa yake a idanun sa ba ma shi kaɗai ba kowa ya san Leesha yar gayu ce ƙwarai ga kyau da zubin halitta da Allah yayi mata,a awasu lokuttan yakan ji kishi mai yawa ya rufe masa idanu sai dai bashi da yadda zai yi ne,domin wata shigar da take yi shikan sa fitina ce a gare sa bare wanin sa. Gashi manyan Alhazzawa ne ke bibiyar ta da sunan soyayya masu dukiya tana wulaƙan ta su bare shi da yake ɗan talakan sa duk da suna da kuɗi gwargwado amma bai kai na wayen da take kulawa ba.Abin na ƙona masa rai matuƙa baya da yadda zai yi ne da tuni ya furta mata kalmar da sauran mazan suke furta mata da suke shan wulaƙanci asalin sa.Bayan ta ya bi yana ƙarewa halittar ta kallo yadda hips ɗin ta ke juyawa cikin rigar.Numfashi ya sauke kafin ya janye idanun sa a kan ta,da suke dauke da wani mugun kishi. Aleeshat kuwa bata damu da duk kallon da ake mata ba daga student har teachers haka take ratsa mutane tana baɗe su da ƙamshin ta. Bakin Audit ɗin su ta dakata dan ya zo ya nuna mata inda suke kai tsaye ba tare da ta wahala ba. Bata daɗe da tsayuwa ba sai gashi ya iso Murmushi ya saki kafin ya ce '' Ran ki ya daɗe Barka da isowa ". Ɗan kallon sa tayi jin wani sabon kilin bibin da ya zo mata dashi na kiran ta da ranki ya daɗe. Ɗan sake fuskar ta tayi kaɗan ba ta nuna komai ba " yawwa Kamal " Daga haka bata sake cewa komai ba. Sai ma janyo wayar ta da tayi tana kokarin yin kira. " Muje " ya furta Fahimtar dama abun da take jira kenan.Bayan yayi wani murmushi na jin daɗin yadda sunan sa ke fita bakin ta cikin wani salo wanda ita ba da wata manufa tayi sa ba.Gaba yayi kafin ta bi bayan sa.Chan ƙarshe suka nufa sai dai tun da ta shigo idanun kowa ya koma kan ta musamman mazan da ke ciki suna karatu.Har da matan ma masu jin haushin ta suka fara zagi da Harare gare ta sai dai a banza babu wanda ta kalli gefen sa cikin su. Suma sauran team ɗin idanun duk suka zuba mata sai dai tun da tayi sallama bata ƙara cewa komai ba. Suma babu wanda ya ƙara yin magana cikin su. Sai ɗan satar kallon ta suke yi mazan, macen dake wajen ita ɗaya,kasancewar suna ɗan gaisawa ta saki fuska suka gaisa, anan suka haɗu da Nafisa sai dai duk yadda Nafisa ta so su jone a bu ya gagara kusan yan zu shekarar su ta uku da fara karatun Law.Nafisa Hamza Indabawa itama yarinya ce yar wanka da gayu mai kirkiri ita kanta bata ɗaukar raini dan haka ya sa ma take sake mata kaɗan.Dan ta fahimci itama ba ƙyalliyar ta bace,kowaccen su nada nata aji gwargwado. Abun da ya tara su,suka fara kafin kowa ya riƙa bada ideas na sa ita ce ƙarshe wadda ta kawo Tata idea. Har ta gama bayanin ta a tsanake cikin ƙwarewa da basira kowannenn su idanu ya zuba mata,kafin ta dasa aya tayi shiru,kuma take suka karɓa dan kan ta na mugun jaaa dan tun da suka fara wannan program tana cikin wayen da ba su taɓa yin carry over ba,ba a class na su. Daga nan suka fara haɗa bayanai suka haɗa komai Aleeshat ma tun kafin a tashi kiran Alhaji Mamman ya fito da ita wanda bata ma yi niyyar ɗagawa ba amma saboda yadda wajen ya dame ta sai tayi amfani da damar kar su ga kawai ta fita bata cewa komai ba. Aiko tana fito wa ta yanke kiran Alhaji Mamman da kan ta.Tana jan mugun ƙaramin tsaki. Sai ga kira ya shigo wayen ta daga teacher ɗin su.Asad. Cike da sauri da wani irin mugun tashin hankali ta faɗa motar ta kafin ta kunna ta, ta fige a tsiyace ta bar school ɗin baki ɗaya bayan yanke kiran. Idanun ta ne suka rikiɗe lokaci ɗaya damuwa ta bayyana ƙara ra akan fuskar ta sa. Gudu ta ke tsugawa bana arziki ba dan cikin abun da bai wuce min tuna goma ba ta isa bakin gate ɗin wata haɗaɗɗiyar asibiti da ta amsa sunan ta asibiti dan asibiti ce ta a manya sai dai ko talaka gwargwado zai iya kai kan sa Amma tabbas asibitin manyan mutane ce kama da ga yanayin zubin ta da Nairan da aka kashe mata. MMG Hospital shine sunan wannan asibiti a taƙaice. Kamar kullum sashen yara ta nufa bayan yin parking motar zuciyar ta na wani irin rawa da harbawa kamar Ance mata Asad ɗin ya Mutu. Idanun ta har dushi dushi suke gani saboda tsabar tsoro da firgici da ya shige ta da tashin hankali. Kafaɗan wani da ta buga ce ta sanya ta ɗan dawowa hayyacin ta kafin ba tare da ta tsaya kula wanda ta buge ɗin ba ta cigaba da tafiya,cikin kiɗima. Su biyu ne a tare ɗaya da kayan likitota ɗaya kuma sanye cikin kaya na alfarma mutun mai kamala da natsuwa daga nin sa dai ba ƙaramin mutun bane. Ɗan juyawa yayi ya Kalle ta kafin ya ɗauke idanun sa kan ta.Yana furta astagfirullah a cikin zuciyar sa. " Sorry M Ina ga tana da patient ne a ciki shi ya sa, hankalin ta na kan sa ".Ya kai ƙarshen maganar yana sakin murmushi ganin yadda Mutumin ya nuna babu komai yana sakin guntun murmushi kafin ya ce " Babu komai na ga alama kammm,Allah ya basu lafiya ". Amin wannan likitan ya furta. " Ammm Jibi zai shigo ko gobe,zamu yi magana in sha ALLAH idan ya amince,Ba abun damuwa bane Mahuta. ". Godiya wannan Dr da sunan shi ke maƙale a jikin rigar sa shine Dr Sada sabo Mahuta,Amma an fi kiran sa da Doctor Mahuta.Kayan sa da suka zube suka duƙa suka kwashe tare kafin suka yi musabaha da wannan likitan sannan ya raka shi har mota suna ƙara tattaunawa kan maganar da suke yi ɗin kafin su fito yanayin su dai kamar a bokai ko mutanen da suka shaƙu da juna sai dai akwai ɗan nuna girma ga likitan zuwa ga mutumen da ya kira M.Yana barin asibitin shi kuma ya juya ya koma cikin asibiti. Haka kawai yake jin ƙirjin shi ya buga da ya tuno da yanayin gefen fuskar ta da yayi arba da ita duk da ba sosai ya gani ba saboda saurin da take yi. Wani tunani ne ya shigo masa akai sai dai da sauri ya furta " No impossible gaskiya ". Haka ya cigaba da tafiya har ya isa inda zai je. A ɓangaren Aleeshat kuwa kasancewar ta san room no.nasa dan komai Anty prise ta sanar mata a waya hakan ya sa ta tura ƙofar jikin ta na rawa. Ko Sallama babu haka ta faɗa ɗakin ,wannan Aunty ta su Asad mai suna Anty Prise sai ganin ta tayi tsaye kan ƙafafun ta.. Zuba ma Asad idanun ta tayi da suka sauya kamannin su sai ga wasu hawaye Sun Silalo mata musamman ganin sa haka kwance marabin sa da gawa numfashi,gashi numfashin na sa ma har yanzu bai dai dai ta ba. Bacci yake yi kai daga nin sa kasan ya na shan baƙar wahala. Kujerarar da ke kusa da shi ɗayar ta zauna tana haɗiye kukan da ke shirin ta so mata. Tana taɓa hannun sa dake maƙale da drip. Kan ta ta kife akan cinyar ta saboda ta kasa jurewa musamman ganin sa yayi wani sharr da shi kamar wanda baya da jini a jikin sa.Ɗan ɗagowa tayi ta duba ɗakin tsitt wanda har Malamar ta tafi kasancewar dama mahaifiyar sa take jira duk da suna da clinic a school Amma na sa ciwon bana treating bane clinic dan wanccen karon clinic aka kai shi dan abun ya fara ta sar masa a makaranta gadan gadan,sai dai na yanzu ya fi worse,dan haka suka nemi asibiti mai kyau mafi kusa.Duk da lokacin da ya na ɗan shekaru biyu ya yi ciwon ya fara nuna alamar sa a jikin sa. Sai dai ba su taɓa kawo cewa abun zai zamo haka ba dan dukkanin su tsorace suke tun karɓan report na sa na farko da aka yi masa bincike a school clinic... Numfashi ta sauke mai nauyi kafin ta ɗago kan ta ta ƙara kallon Asad da har yanzu ko motsi bai yi ba. Wasu hawaye ne masu zafi suka ƙara biyo wa ta fuskar ta damuwa ta ƙara bayyanar ma ta da tashin hankali. Sai alokacin ta lura Aunty prise ta wuce.Shiru ta yi cike da tunani kala kala tana kallon Asad zuciyar ta cike da wani irin zafi da ƙunci.Tana nan zaune sai ga nurse ta shigo ta sanar da ita Dr na neman Iyayen Asad Jibril. Aiko babu musu ta fito bayan ta yi wiping tears nata da wata hanky ɗin ta mai kyau fara tass. Asad kuwa ta bar shi hannun Nurse dan dama jinyar mutun ɗaya ke yin ta,idan ya kasance ku zaku yi jinyar abun ku ba nurse ba. Cikin sanyin muryan ta tayi Sallama zuwa cikin office ɗin. Ɗago idanun sa yayi ya zuba mata ido dan koda basu ga fuskar ta ba ya gane shigar ta. Masha ALLAH ya furta a cikin zuciyar sa sai da ya ƙare mata kallon tsafta sannan ya ce " Bismillah ga seat ".Ya furta yana nuna mata seatt ɗin. Aleeshat kuwa babu musu ta nemi waje ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,haka kawai take son jin wani abu da ban bayan report na farko na Asad ɗin dan haka ta ƙagara ya sanar da ita komai ta san halin da Asad ɗin ta yake ciki. " Ammm ke wacece a gurin Asad F Jibril ".? Yayi mata tambayar duk da cewar ya ga yanayin kamannin su amma yana son tabbatarwa ko ƙanen ta ne ko ɗan ɗan ta dan daga yanayin shigar ta baiga alamar matar Aure bace ko kaɗan. Ɗan jimm tayi tana wasa da zoben ta na azurfa mai kyau da ya ƙara yiwa yatsun ta kyau ta ce " Ɗa na ne " . Daga haka bata ƙara ce masa komai ba. Kai ya jinjina yana saka record ɗin a system dake gaban sa.Sai dai mamaki ya kashe shi daga zaune,sai dai ya shanye abun sa tun da su likitota ne sun saba ganin abun mamaki wanda ya fi wannan su haɗiye. " Kece Mahaifiyar sa kenan miss " Kai ta jinjina masa. " Sunan ki fa ".? " Aleeshat Jibril Farauta ". Ta bashi amsa.Cike da fara jin ta ta kura daga yanayin tambayoyin da yake mata gashi tana jin ɗan kallon da yake mata ƙasa ƙasa.Dan abun da ta tsana shine kallo a yanzu. Shima kan sa ya jinjina mata kafin ya ce " Wa yake da Ashthma a cikin a halin ku ko na mijin ki "? Wani irin bugu ƙirjin ta yayi mai mugun zafi dan numfashin ta ne yayi yunƙurin ɗaukewa na wuccin gadi da taimakon Allah da taimakon da ya bawa wanin sa dama ta samu dai daiton numfashin ta domin kuwa wannan tambaya da ta sako kalmar mijin ta,ta girgiza ta matuƙa wani irin tsoro ne da tashin hankali ya bayyana kan fuskar ta.Take idanun ta suka sauya kala. Asthma ta na na ta akan laɓɓan ta kafin ta ji wasu irin hawaye na neman wanke mata fuska domin kuwa abun da suka gani kenan a binciken farko da aka yi masa a makarantar su. Hawayen da take ƙoƙarin riƙewa ne ya silalo mata ƙoƙarin ciro hanky ɗin ta take yi a daga cikin jakar ta sai dai ta ji saukar wani Hanky a hannun ta mai taushi yana ta ƙamshi. Ɗan kallon sa tayi,shima ita yake kallo kafin ya jinjina mata kan sa. Bata yi masa musu ba Ganin handky ne lafiyayyen mai tsafta kamar sabo hakan ya sa ta fara goge hawayen. Sai da ta goge su tsaff sannan ta sauke numfashi. Dr Mahuta na kallon ta kafin ya yi gyaran murya sannan ya ce " Yana ɗauke da Asthma ne kun san da hakan ko kuwa sai yanzu " ? Kai ta jinjina masa da tabbatar masa da sun sani. " An taɓa bamu report na sa a school na su ". " A lokacin bamu yarda ba gaskiya ". " Duk da a lokuttan baya mun ga wasu daga cikin alamomin irin cutar a gare sa ". Dan bazata manta ba lokacin yana shakera ɗaya da wata takwas yayi ta samun matsalar ɗaukewar numfashi,tun ma dai yana jaririn sa da wannan matsalar ta fara ganin sa Numfashin sa samaa sama bata taɓa zaton zai rayu ba sai gashi Allah yayi ikon sa. Numfashi ta sauke a hankali tana kawar da tunanin baya dake da alaƙa da maganar ta su. Kai Dr Mahuta ya jinjina mata yana ɗauke kallon sa daga kan ta ganin yadda take ɓata kyakkyawar fuskar ta alamar kallon na damun ta.Murmushi ya saki kaɗan sannan ya cigaba da rubuce rubucen sa. Ɗan ɗagowa ya ƙara yi kafin ya ƙara maimaita tambayar da ta fi komai ɗaga mata hankali " Mahaifin sa ke da Asthma ko ke ,idan shine ya kamata ya zo nan ".?Wani irin faɗuwa ƙirjin ta ya ƙara yi cike da wata irin rauni ta ce " Mahaifin sa ne, Asthma itace silar mutuwar sa ".Ta kai ƙarshen zancen hawaye Masu zafi na Silalo mata.Wani irin Tausayin ta ne ya ƙara kama Dr Mahuta.Ita kuwa kuka ne ta ɓarke da shi a hankali na ƙaryar da ta yi wadda bata taɓa sanin cewa ta iya ta ba yanzu.Wadda rashin mafita ya saka ta furtawa bata re da ta shirya wa hakan ba.Zuba mata ido yayi kafin ya sauke numfashi ya ce " Ayyah Sorry may his soul rest in perfect peace ". Bata tanka masa ba sai kukan ta dake cigaba da fita a hankali cikin wani irin rauni da ƙuncin zuciya." Calm down Miss Aleeshat Jibril Farauta.,Ba wani abun tashin hankali bane Asad zai samu lafiya idan an ƙara dagewa da bin dokokin mu ". ✍️ A hayyyye inji ɗan Daudu😅💃💃💃💃Biki buduri yau dai cikin Yardan Uban giji mun samu kammala Book One cikin iyawar ubangiji.. Ƙanwa ta tace ɗan da ƙyar😏😏😅🤣🙏 Ina godiya gare ku masoya wannan labari na nesa da na kusa.Ƙaunar da kuke nuna mini da goyon bayan ku shine ƙwarin guiwata.Allah ya sakawa kowa da Alkhairii.Allah ya kuma haɗa mu a gidan aljanna baki ɗaya. Sai mun haɗe book two and three. Na amanata.🙏🙏🙏🙏 Kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke tafiya ce mai ban mamaki,al'ajabi,tausayi zazzafan soyayya mai cike da ƙauna,sadaukarwa,Zamba,cuta mai ban mamaki,zumunci mai abun burgewa. Lallai kar ki bari a yi babu ke 💃💃💃💃💃Takwaran Shatou dai ta ce " Ko da bashi sai na shiga paid group " 😂😂😂🤔Niko nace hmm😇😒😏😂 Jama'a kar in cika ku da surutu.🤗 Na san akwai tambayoyi masu yawa a bakin ku dan haka paid group ne mafitar ku.😎💁 INA LABARIN SHATOU,WAIT WAIT IDAN SHATOUN MU TA ZO BIRNI TA YAYA,TANA INA ?KO TA CIKA BURIN TA NA ZAMA YAR SANDA 🤭🤭 SHIN KO SHAMSU YA CI GALABA KAN MUGUN BURIN SA. WAYE MAHAIFIN ASAD ? INA LABARIN SU INNA NI..? WACECE ALEESHAT? INA LABARIN SU ABBU DA ƊAN SA ? INA LABARIN TA BAIWA MAI CAPACITY 😏😒😂? INA LABARIN MA'ISHAT,TA WARKE KO TANA NAN HAR YANZU CIKIN CIWON TA ? ME YAKE SANYA BILAL YAWAN DAMUWA ?Ina ma labarin sa ? WA KUKE GANIN YAKE YIWA SU ALEENA,SARINA MAƘARKASHIYA ? Me malam Hambali yake ɓoyewa ga Abba???? Na san akwai wasu tarin tambayoyi a cikin zukatan ku..🤎😇🤔 HMMM WANI ABU SAI A PAID GROUP.Da Naira #800 sai ki samo amsoshin ki 😇😇☺️😌🥰 ZAKU IYA SAKA KUƊIN KU TA 8069069746 OPAY FAIZA ALMUSTAPHA. SAI KU TURA SHAIDAR BIYAN KUDIN KU TA WANNAN NUMBER. 0808 750 4734 Mutanen NIGER(500 CFA) ZAKU IYA MAGANA DA WANNAN LAMBAR.08069069746 Dan biyan kuɗin ku,ko tura shaidar ku. Koda katin Airtel ne za,a karɓa.Mungode! Note:idan kika tura kuɗin ki ta vtu,ko kati kin yiwa Fa'eeh sadaka.Babu refunding.😜 And ba zamu jira kowa ba zamu cigaba da update.Idan kin shirya sai ki saka kuɗin ki. Masu neman complete Book yanzu muke typing. A taƙaice babu complete book. Idan mun gama zaku same sa complete book 1k✍️ Allah ya haɗa mu da Alkhairi.🙏 Fa'eehn ku ta amana,na godiya mai tarin yawa.Love You all my esteem fans 🥰🥰💕🌹 FA'EEH BG CE ✍️✍️✍️ SHARE FISABILILLAH. LIKE,REACT,VOTE AND COMMENT PLS🙏 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels