Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 7 complete by Novels Elite Admin May 15, 2024 Sponsored Link _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القدر💋✊🔥 ~Takun Ƙarshe🔥~ قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace"Ina da banbanci dasu, Har Yau har gobe sunƙi mantawa da matsayina a gidan ku, Suna yi min kallon ƙasƙantacciya Ƴar aiki, babu abunda Ya canza" Ya fahimci baƙaramin jin shakkarsu ta ke yi ba, muryarshi a kausashe ya furta"kamar ba matar Sir mubarak ba, kin bani kunya, wlh daga yau zan baki last warning, idan na kuskura na sake ganin kin zubda hawayen ki ko kina jin tsoron wani acikin su, sai na sa6a maki" ƙiris ya rage ta fashe mashi da kuka, jin yadda yake mata magana da faɗa. Zare mata ido yayi"ina fata kin fahimce ni"? Muryarta na rawa furta"yea..h" ruƙo hannunta yayi acikin nashi, yaja ta a hankali suka nufi katafaren falon gidan, ko da su ka shiga masu yi masu hidima suka taras sai kai komo su ke yi a cikin falon, ganin sir mubarak yasa suka yi saurin gaishe su cikin girmamawa bayan ya amsa masu ya tambayi ina gimbiya mujeedat. Ɗaya daga cikin hadiman ce ta bashi amsa da cewa"su na a garden" Damƙa mata hannun Turai yayi wadda tuni jikin ta yayi sanyi lakwas. Cikin kuwala yace da hadimar "she's my wife, inaso ki rakata wurin su, ki bi min ita a hankali' murmushi hadimar tayi aranta ba karamin burgeta yayi ba, daga gani yana daraja matarshi "In sha Allah yalla6ai" ta faɗa tare da ruƙo hannun mom Turai suka nufi ƙofar fita daga falon, tana tafiya tana waiwayon shi, kamar yadda shima yake kallon ta har sai da ta 6ace ma ganin shi kafin ya nufi ɗakin prime minister. Jin motsin shugowar Sir Mubarak ne Yasa shi Buɗe idanunsa Yana dubanshi Daga gefen gadon shi Ya zauna Yana fadin"ƙanina Ya Gajiyar tafiya," miƙewa Hateem Yayi da wata irin kasala Ya zauna Yana fuskantar Sir mubarak "Gajiya tabi Jiki, yayana nakaina, kaima ya gajiyar taka" Da zolaya Sir mubarak Yace"nifa Sojane tafiyar da mukayi bata isa ta gajiyar dani ba" murmushi Hateem Ya sakar mashi Cikin kulawa Sir mubarak Yace"Meke damunka? Naga yanayinka ya canza ko baka Jin dadine"? Cikin sanyin Murya Yace"lafiyana lou" ya fada yana kokarin danne damuwarshi "Nifa Yayanka ne Hateem, baka Isa ka 6oye min damuwarka ba, dan Allah ka faɗamin, Idan ba haka ba hankalina bazai kwanta ba, na fahimci tun da kazo ƙasar nan ka canza gaba daya" Ruƙo hannun sir mubarak Yayi acikin nashi ya damƙe shi sosai. Muryarshi ƙasa ƙasa Ya furta"bansan ya zanyi ba da ƙaunar yaron nan na wurin Owais, shine silar duk wani hali da nake aciki, Har mafarkin shi nake Yi" ya faɗa yana mai sanyaya muryarsa. "Allah Ya jarabce ni da son shi, bani da alaƙa da shi amma sai nake jin kamar ni na haife sa, na faɗa maka ne saboda kana ɗaya daga cikin waɗanda suke fahimtana" Tun da ya fara magana Sir mubarak yake binshi da kallo mai nuni da tausayawarsa gare shi, yasan bakomai ke damun shi ba face rashin samun ɗa namiji, shiyasa ya kwallafa rai akan yaron da owais ke ruƙo. "Ban ta6a ganin shi ba, amma saboda kai In sha Allah zanje har gidan owais ɗin In ga Yaron zuwa Gobe In Allah Yakaimu" "Yana kama dani, tamkar Anyi photocopy din fuskana, hasken fatane kaɗai Ya banbanta mu da shi, Fatarshi farace Sol, tamkar Nazli, Dalilin dayasa kaga nashiga halin nan, bana son inbar ƙasar nan batare da yaji saukin lalurar shi ba, ina matuƙar son mu gana dashi, sai dai na rasa wannan damar da nake da ita, baba ya hanani kusantar shi, Gidan Owais dinma An hanani zuwa saboda shi, dole In hakura" cikin karyayyar murya ya faɗa yana faman sauke numfashi. Lamarin ya ɗaurewa Sir mubarak kai, yana neman rudar dashi, Aranshi Ya ayyana wannan wata irin kaunace haka? Abu kamar aikin asiri Allah na tuba. Lallashin shi ya somayi yana kwantar mashi da hankalin shi, Har saida Yaga yafara sakewa tukunna suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su. __________________✍️ Lokacin Da Hajiya Turai, Ta shigo garden din tare da Hadimar data rakota, Tunkafin Ta ƙarasa inda su Gimbiya mujeedat suke, Hajiya laurat ta rafka salati tana fadin"wa nake gani kamar Harriet ƴar aikin gidan baba obie" ta kira ta ne da ainihin sunan ta, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, Hadimar data rakota Harta Juya ta nufi hanyar komawa gidan, Jiki asanyaye turai take tafiya tana tunkarar su. Wani irin Matsiyacin kallo Hajiya laurat da Hajiya saratu suke watsa mata. Tuni tasha jinin jikinta, da hannu Hajiya laurat ta nunata"ke! meya kawo ki nan? Ko kinga sa'ar Yin ki ne" Shiru tayi bata tanka mata ba, Hajiya saratu ta kwashe da dariya Tana fadin"shisshigine da kutsu irin na ɗan talaka, malama wani tsautsayinne ya kawo ki wurinmu? Ko aiko ki akayi don ki yi mana hidima ne"? Cike da shaƙiyanci her excellency Muhibbat tace"jibarta kamar wata mutuniyar kirki, ita kanta ta raina kanta shiyasa take jin shakkar shiga cikin mu, Ni wlh bansan me mubarak Ya gani a jikinta da har Ya aureta ba, in banda hasken fatarta da gashin da take da shi, Mace kullum kamar ana ɗibar namanta ana miya da shi, babu ƙiba babu tsawo, Duk arziƙin da take ci," Dariya suka sanya, mutun ukune basu tanka mata ba, Gimbiya mujeedat da hajiya malikat sai Hajiya madina. Sauran sune hatsabiban. Hajiya Jamila tace"ai auran nata da yayi bana Allah da annabi bane wama yasani kota asirce shine, saboda Sir mubarak yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, Babban gorone, Shiyasa ta nace mashi don aci arziƙi, don Ma Allah Yasa bata ta6a haihuwa da shi ba, sai dai taci ta zubda.... " Hankalin turai ba ƙaramin tashi yayi ba, Jin cin mutuncin da suke Yi mata, Tuni hawaye sun soma wanke fuskarta. Hakan ba ƙaramin daɗi yayima hajiya laurat ba, Ita dama burinta takala Ya ƙuntata. "Nifa Har yanzu ban daina zargin Yaron nan nata shege bane, tun da bashi da uba, ahaka tazo da shi aiki gidanmu daga ƙasar england, matar nan muguwar munafuka ce, babu Allah aranta, Allah kadai Yasan maƙarƙashiyar da take kulla mana" zaro ido waje Hajiya turai tayi jin abunda Saratu take fadi, Maganar ta ƙona mata ranta, zuciyarta har wani tafarfasa take Yi sam takasa buɗe baki ta dakatar da su, sai dai binsu da take Yi da idanu. "Gobe kada in kuskura Inga ƙeyarki awurin taron shagalin dinner din da za'ayi na Hateem, Idan ba haka ba agaban idon kowa zan watsa maki ruwan lemu akan fuskarki" Hajiya laurat ce ta fada tana nuna ta da cup din hannunta. "Dake da wannan ɗayar munafukan meye ma sunanta"? Da sauri hajiya saratu tace"hajjaty" hajiya laurat tace"yawwa ita nake nufi, uwar iyayi, mai shafa turaren ƴan bori, ku biyun nan bamu buƙatarku a family din nan don kawai ba yadda zamuyi daku ne amma very soon zamu yi maku korar kare" ta faɗa tana sakar mata shu'umin murmushi. Fashewa Turai tayi da kuka mai cin rai, kamar an ruƙe mata ƙafafuwanta takasa tafiya tabar wurin su. Gyaran murya Gimbiya Malikat tayi masu, gaba ɗaya suka kalleta. "Ba girmanku bane, kun bani Kunya, ni banga amfanin maganar da kuke gaya mata ba, ku kama mutunci ku mana" rai 6ace ta furta maganar, babu wasa a fuskarta. Sai lokacin Gimbiya Mujeedat ta buɗe baki cikin nutsastsiyar muryarta ta furta Sunan turai. Baiwar Allah muryarta na rawa ta amsa mata da na'am. "Zo ki zauna kusa dani" ta fada tana nuna mata gefenta. rai a6ace Laurat da muhibbat suka miƙe tsaye suna fadin Allah Ya kiyaye su haɗa kafada da ita, Indai turai zata zauna sai dai su su tafi" ko kallon su mujeedat batayi ba. Muryar turai da shessheƙar kuka tace"bazan Iya zama ba Aunty mujeedat, bana so na shiga tsakaninku, ni zan tafi kawai, dama yaya mubarak ne Yace in zo wurinki don inyi maki bangajiyar tafiyar da ku ka yi, don haka zan tafi tun da naganki..... " tana ƙarasa maganar, ta juyawa da sauri ta nufi hanyar fita daga garden din. Zuciyar Gimbiya mujeedat ta sosu, ranta ya 6aci da kalaman da Su laurat sukayi ma Turai. Yunƙurawa tayi tare da miƙewa tsaye tana gyara rigarta, Har suna hada baki wurin tambayarta ina zataje? Batare da dube su ba tace"zan shiga cikine, nagode da ziyara sai mun haɗu gobe idan Allah yakaimu" Ta fada tare da kallon Gimbiya malikat tace"mu shiga daga ciki," miƙewa hajiya malika tayi suka ruƙe hannun juna atare suka nufi cikin gidan. Bayan tafiyar su, Tsoki Hajiya laurat taja tana fadin"wannan munafukar matar duk itace taja mana, Muna zaman mu lafiya, ta tarwatsa mana farin cikin mu" Hajiya Jamila tace"Halin talakan kenan, Yanzu gashi tasa Ran gimbiya mujeedat Ya 6aci" Hajiya saratu tace"banji dadi ba wallahi, amma nasan ta inda zan rama, Allah yakaimu gobe lafiya, Idan har matarcan ta kuskura ta zo dinner din ya hateem jikinta zai gaya mata sai nayi mata abun da bata ta6a tsammani ba" ta faɗa tana faman haɗe fuskarta, Sun jima a garden din kafin daga bisani kowaccensu ta shiga motarta suka nufi gidajensu. Baiwar Allah Hajiya turai tana azaune cikin motar Sir mubarak, tasha kuka tamkar ranta zai fita tayi danasanin zuwa gidan prime minister, kalaman su sun ƙona mata rai, musamman da hajiya saratu ta ambaci jazz da sunan shegene, tayi alkawarin bazata fadama sir mubarak abunda suka gaya mata ba, don kuwa idan yaji sai sun yabama aya zakinta. _______________________✍️ Baka jin sautin komai a falon tamkar babu mutane acikinsa, alhalin nan kuwa Suna zaune kowa Ya hakimce abun sa, tsabar miskilanci ne Yasa basa iya buɗe baki su tanka ma Junan su, Kowannan su da abunda Ya ɗauke mashi hankali, fitowa Dr jazz yayi daga bedroom dinsa ya kimtsa kanshi cikin shadda launin blue sky abunka ga farar fata ta ƙara fiddo mashi da hasken shi, ga wani daddaɗan ƙamshin turarensa dake fesowa, Ya gyara sumar kanshi hannun shi ɗaya ruƙe da key din motarsa, wani irin annurin farin cikine akan kyakkyawar fuskarshi ga dukkan alamu akwai wani abu daya faranta mashi rai. kafin Ya ƙarasa cikin falon, Idanunsa suka hango ma sa Matasan Samarin Family din dake zaune saman sofas Har sai da gabanshi Ya faɗi da idanunsa suka yi mashi tozali da su, Baisan da zuwansu ba, aranshi ya ayyana to fa ashe yau muna da manyan baƙi a gidan na mu ba, meyasa Ibad bai faɗa min sunzo gidan nan ba? Ya ƙarasa zancen zucin nashi cike da jin fagabar tunkararsu, Ya kasa motsa ƙafafuwanshi Ya tsaya atsaye kamar wanda aka yi mashi Iyaka da shiga falon, ɗaya bayan ɗaya ya soma bin su da kallo, Zaki Yana a azaune saman 2 seater Yayin da Apple Laptop dinsa ke akan Table din gabansa, Gaba ɗaya ya tattara hankalin shi akanta yayin da yake operating dinta atsanake, Short ne a jikin shi tare da Denim shirt tabi shape dinsa, Kau da idanunsa yai daga kan Zaki Ya mayar da su kan Wani Matashin saurayi fari Sol, fatarshi ko ƙwarzane babu, Ga wata nannaɗaɗɗiyar sumar kai dark brown, kai daga ganinsa wani shege ne mai ji da naira, Allah yayi shi da kyau mai jan Hankali, Jallabiya ce a jikin shi launin grey, ta zauna mashi sosai, bakowa bane wannan face Captain YASEER ɗan gidan His Excellency Abdul Razak da Her Excellency Muhibbat shuwa arab ne kamannin shi sak dana su Chief Owais, banbancin su launin fatane dana Ido, hannun shi ruƙe da Expensive phone dinsa da yake daddanawa da zira ziran yatsun hannunsa, yayin da Justice Nadeem ɗan gidan His excellency Deen Yake a kishingide kan doguwar Sofa, Ya zagayo da hannun shi ɗaya saman forehead dinsa, idanunsa suna a lumshe tamkar mai yin bacci. Ziyad ne kaɗai yake a zaune saman lallausan Carpet din dake a shimfiɗe tsakiyar Sofa set din falon, faffaɗan farantin da aka kawo masu fresh fruit acikinsa ya tasa a gaba yana shan kayan marmari, duk acikin su Ziyad yafi su sauƙin kai kasancewarshi ɗan jarida da son labari, A yanzu haka da yake a zaune cikinsu A takure yake jin kanshi sunƙi sakar mashi fuska su yi fira kowa Ya kama harkar gabanshi shiyasa ya sauko kan carpet yaci gaba da shan kayan marmari. Ƙamshin turarensu Ya gauraye Falon, Jazz dake kallon su ba ƙaramin burge shi su ke yi ba, ba tun yau ba Yana son Yaga jikokin Baba Obie sun haɗu suna sada zumunci aranshi sai yaji inama ace shima Jikan Baba obie ne da Allah ne kaɗai Yasan irin Farin cikin da zaiyi a duniyar nan. Ganin basu lura da shigowarshi falon bane yasa shi yin saurin tafiya cikin sanɗa Ya nufi ƙofa Ya fuce daga ciki Yana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri Ya nufi Harabar Ajiye motocinsu, Ya buɗe motarshi Ya shiga daga Ciki, tare dayi mata key, zuciyarshi acike fal da tunaninta, fatan shi Allah yasa wannan karan ta kula shi. Yana driving fuskarshi dauke da annurin farin ciki, A haka Ya nufi Gidan baba obie. Ganin shirun nasu bamai ƙarewa bane, Yasa shi miƙewa, Ya nufi Zaki Ya sanya hannu ya ɗauke laptop din da yake dannawa, Ya juya Ya nufi Captain Yaseer Ya kar6e wayarshi, kafin Ya tunkari justice Nadeem Ya sanya hannu Ya kamo Hancinshi Yaja Shi da karfi har sai da Justice Nadeem Ya buɗe idanunshi dake dauke da bacci Fuskarshi adaure yake kallon Ziyad. Harara Ziyad Ya watsa masu Ranshi a6ace yace"wai meke damunku ne? Kullum muka haɗu kamar wasu kurame babu mai magana kowa ya kama harkar gabansa? Haka ake zumunci? Ni banga amfanin kirana wurin nan donmu haɗu ba.... " gaba ɗaya sun ɗaura idanunsu kan fuskarshi babu alamun zasu tanka mashi. Guntun tsoki Yaja"kun wani zuba mun idanu kuna kallona wato ni ga shashasha" Yamutsa fuska Zaki yayi tare da miƙa mashi hannu yace"Bani laptop dina ziyad" "Ta ƙarfi ce zoka kwata" A faɗace Ya faɗa Yana haɗe mashi fuska. Murmushi gefen fuska Zaki Ya sakar mashi. "Meye damuwarka"? Ya tambaya yana faman lumshe idanunsa. "Damuwata shine ku bani aron hankalin ku muyi fira kan abunda ya shafi rayuwarmu, daga gobe fa shikenan kowannanku zai koma inda Yake rayuwarsa, yawanci ba akasar nan kuke zaune ba why ba zamu kula juna yadda ya dace ba? Bamu da tabbacin ko zamu sake haduwa da junanmu" Yanayin yadda yayi masu maganar Ya ta6a zuciyoyinsu, In a calm voice Zaki Ya furta"In sha Allah zamu sake haɗuwa, Yanzu dai ka yi haƙuri, Ka zauna mu yi fira" Ta6e baki Ziyad yayi, kafin Ya koma Ya zauna, Batare daya miƙa masu Kayansu daya kar6a ba. "Bro, Ni bansan ta yadda zan fara firar bane, ko zaka taimaka mana da abun da zamu tattauna akai"? Captain ne Ya faɗa Tamkar baison furta maganar, justice Nadeem dake a kishingiɗe tuni Ya gyara zama saman Sofa Yana duban su "Me zai hana Mu yi magana dangane da matayen da muke da burin aure"? Acewar ziyad. kallon Harara Captain Ya watsa mashi"mu yi magana kan abu mai mahimmanci, Idan ba haka ba zan ja baki na nayi shiru"! "Aure shi yafi komai mahimmanci domin kuwa Sunna ce mai karfi ta Manzon Allah SAW, Allah Ya bamu komai da zamu buƙata, Kowannanmu Yana da aikin yi, Aure shi ya rage mana yakamata ku yi tunani yanzu fa lokaci ne da zamu more rayuwarmu, mu ma yi aure mu hayayyafa kamar yadda Iyayen mu suka yi.... " Ziyad ne ya kora masu jawabi. "Look, Ni aure baya a gabana yanzu, har yau banga macen data kwanta min arai na ba, tun lokacin dana rasa wadda nake da burin aure naji matan ma sun fitarmin araina" Justice Nadeem dake kallon Captain Ya saki murmushi tare da cewa"Ai ba ita kadai bace mace a family dinmu ba, Kai ma kaso ka wahalar da kanka, Ai ni tun lokacin dana fahimci macace mai izza da ji da kai, na sanyama zuciyata salama, saboda bana son macen da namiji bai isa yayi iko da ita ba, ba zata yi dadin zaman aure ba, kwara wadda zaka Iya juyawa son ranka ba wadda zaka dinga jin fargaban tunkararta ba" Ziyad yace"ka faɗi gaskiya mutumina, ita fa gaba ɗaya namiji ma baya agabanta, bata da burin yin aure, kai ma mai yaja maka yin dakon soyayyarta? Bayan Ga matasan ƴan mata nan masu jini a jika a family namu.... " kafin Ziyad ya ƙare maganar, Zaki yai gyaran murya tare da cewa"wai kuna Nufin Nazli"? Ɗaga mashi gira Nadeem yai, matashin murmushi ya saki kafin yace"Kuna nufin bakusan alaƙar dake a tsakaninta da chief Owais namu ba"? Atare suka haɗa baki wurin furta meke nan"? Jim ya ɗanyi kafin Ya furta"Uncle Hateem, Ya riga daya mallaka mashi ita, bata da wani miji daya wuce shi a duniyar nan, tun kafin tazo duniya, wannan alƙawarine dake atsakanin Uncle sharafudeen da uncle Hateem, zasu haɗa auran ƴa'ƴansu... " da mamaki suke kallon shi Ziyad yace"amma ni banta6a ganin alamun suna kula junansu da sunan soyayya ba, Ko ranar Birthday din grandfa da suka haɗu ko kallo ba su wa junansu ba" "Dama taya za'ai su kula juna?bayan kowannansu Yana ji da kanshi daga ita har shi Owais din, duk abunda take taƙama da shi shima Yana da shi, gaskiya Uncle sharafudeen da Hateem basu yi tunani mai kyau ba, bayan sanin cewa Izza A jinin su take, tayaya Nazli zata yi mashi biyayya amatsayin matarshi? Justice Nadeem ne yayi maganar. Captain da ke sauraransa fuskarshi babu annuri babu walwala ya furta"da ace nasan da zancen nan da tuntuni na cireta araina, dama ni ba Iyawa zanyi da ita ba, owais din shi yafi dacewa da ita, suje can su ƙarata," Ya faɗa tare da jingine kanshi jikin Sofa. Shiru suka yi na ɗan wani lokaci, babu wanda Ya furta magana sai daga bisani Justice nadeem Ya furta"Zaki Ina budurwarka ta Canada Kyakkyawar balarabiyar nan" Da zolaya ya faɗa yana duban shi. Kallo ya jefa mashi mai kama da harara kafin Ya furta"ta koma gidan su" Zaro ido justice Nadeem yayi"me? Kana nufin tabar gidanka" Ɗaga mashi gira yai alamar eh, "But why"? Bai cika son tada maganarta ba, saboda hakan Yana fama mashi raunin dake a zuciyarshi. Cikin sanyin murya ya furta"bansan meyasa ba, rana ɗaya ta haukace min ta soma kokarin juya min ba, badan naso ba nabarta ta dawo Nigeria" Justice Yace"banji dadi ba, me zai hana ka nemi gidansu inyaso saika gabatar da kanka wurin Iyayenta"? Murmushin takaicin Zaki yayi"tana da aure har da ƴarta, ban ta6a fada maka bane" Jin wannan maganar Yasa Captain ware manyan idanunshi, hatta Ziyad dake sauraransu saida Ya zaro ido da alamun mamakin kalaman Zaki A ruɗe justice Nadeem ya maimaita maganarshi"tana da aure har da ƴa? Amma ta zauna a gidanka tsawon shekaru tamkar ma'aurata? Kafin Ya ƙare maganar Captain Yace"tayaya hakan zai yiwu? Nima fa nasan Matar duk lokacin da zanje canada a gidan ka nake taras da ita, nayi tsammanin Ƴar aikin ka ce, shiyasa ban ta6a kawo ma raina wani abu ba," Girgiza kai Zaki yayi"ba ƴar aikina bace, Taimakon ta nayi, na ruƙe ta agidana saboda ta nuna min bata da kowa bayan mun fara shaƙuwa take bani labarinta, Hankalina Ya tashi jin cewa tana da aure, amma agidana mijinta ya tura mata da sakon saki, ganin hakan yasa muka cigaba da yin rayuwarmu, naso ta amince min in aure ta saboda bani da burin daya wuce na mallake ta, nasan tana sona sai dai tafi ƙaunar takomama mijinta saboda ƴarta da tabar mashi" Gaba ɗaya sun lura da canzawarshi, hakan Ya ƙara tabbatar masu da irin kaunar da yake yi mata. Miƙewa yayi da sauri Ya nufi bedroom dinshi, Da sauri justice Yabi bayanshi, Yana Shiga Ya zura hannayenshi cikin aljihun short dinshi, Yayin da zuciyarshi ke cigaba da tafarfasa "Bana so hakan Ya dame ka, Yarinyar nan ko tana so ko bata so, Kai ne mijinta, Saboda kafi cutuwa, Tsawon shekara goma sha shidda kuna rayuwa agida ɗaya tamkar ma'aurata? Ka raineta ka kashe mata maƙudan kudi, Idan har ta butulce maka Allah ma bazai barta ba" Justice ne yayi maganar, yana daga tsaye abayanshi "Duk abunda nayi mata nayi ne don Allah..." kafin Ya ƙare maganar justice yace"nasan don Allah kayi mata amma wallahi bazan bari ta karya maka zuciya ba, tun da nake da kai baka ta6a nuna kana son wata ƴa mace ba, sai akanta, don haka dole ta aure ka, shi kuma mijinta Ya haƙura ya nemi wata, nasan ma yayi auranshi tun da jimawa" Juyawo Zaki yayi idanunsa akan justice Yace"nagode da kulawarka agare ni, amma mubar maganar, saboda hakan bamai yiwuwa bane, Ni bazan tursasa mata akan ta so ni ba, ta ɗauke ni tamkar yayanta tana girmamani, tun da nake da ita ban ta6a nuna mata inasonta da aure ba itama haka " "Ita ai ba makauniya bace, in ba kaiba wani namijine zai dauki dawainiyar baligar mace kamarta almost 16years, idan bazan manta ba, lokacin da naje gidanka a canada, ina lura da duk wani motsinku, Idan ka shiga daki da dare zaka kwanta tana binka bata fitowa har saita tabbatar da kayi bacci take fitowa, kaima kuma haka, sannan baka Iya cin abinci idan ba atare da ita ba, itama haka, kana nufin wani abu bai ta6a shiga tsakaninku ba"? ya faɗa yana bin sa da kallon tuhuma. "Nadeem, Ba abunda kake tunani bane, nasan nayi kuskure na ajiye macen da ba muharramata ba a gidana, amma wallahi ban ta6a shigarta ba..... " muryarshi na rawa ya ƙare maganar, wani irin yanayi yake jin kanshi tunawa da rayuwarshi da ita. Numfashi yaja kafin yaci gaba dacewa"Ta saba min da kanta, komai ita take yi min, bansan menene so ba sai akanta, ban fara muradin yin aure ba sai akanta, ashe ita din ba rabona bane...." "Da ace kuɗi zasu Iya siyamin ita, wallahi har dukiyata zan iya salwantarwa saboda ita, bana tunanin zan samu macen da zata Iya maye min gurbinta, Ni ita kadai nakeso Nadeem" kwallar dake taruwa a cikin idanunsa har sun fara kokarin gangarowa saman kuncin sa. Hankalin Justice Ba ƙaramin tashi yayi ba, ko a mafarki bai ta6a tunanin mace zata Iya tanƙwara zuciyar Zaki ba. Dafa kafadunsa yayi da hannayenshi "Inaso ka faɗamin shi mijinta tsawon shekara nawa su ka yi atare"? In a low voice zaki Ya furta"ƙasa da 2 years, ta faɗa min aranar data haifa mashi baby tabar gidan badan bata son shi ba, kawai taji ya futar mata arantane" "Kasan mijin nata"? "Taya za'ai nasan shi? ni ko sunan shi ban ruƙe ba, saboda kishinta da nake ji" Murmushi justice yayi tare da ruko hannun Zaki, suka zaune gefen gadon shi. "Iyayenta masu hali ne"? ya jefa mashi tambayar. "Yeah, mahaifinta ya ta6a ruke mukamin Governor a jihar joss, amma bai jima a mulkin ba ya sauka sakamakon ciwon kafar dake damun shi, bayan haka Ƙanin Mahaifinta Former president ne Na nigeria, Alhaji Musa wadata, Yayan Matar Uncle sharafudeen Hajiya Laurat, nima a wurin ta naji labarin ta" jinjina kai justice yayi"Ƴar masu Hali ce, Alhaji musan nan Yana ɗaya daga cikin wadanda suka fi kowa kuɗi a africa bayan family dinmu, amma nayi mamakin da har ta gudu tabar nigeria basu nemo ta ba, meyasa tabar mijinta da ƴarta? Shine abun tambayar" "Naikaina Labarinta Yajima Yana ɗaure min kaina, Sonta ne Ya makantar dani shiyasa ban mayar da ita ga Iyayenta ba, saima na taimaka mata wurin 6oye kanta agidana, naci gaba da bata kulawa" Justice ya ce Labarinta Akwai ruɗani Acikinsa, Ta fito daga babban family, ga ta kyakkyawa da ita amma ahaka har ta gudu daga gidan mijinta? Akan wani dalili? Me ta nema tarasa?" Ya faɗa yana kallon Zaki, "Nayi kokarin nemanta don inji ya ta koma gidansu? Iyayenta sun kar6eta ko kuwa? Shine fargabana sai dai bani da hanyar da zan Iya kiranta, tabar min wayarta a hannuna, bansan kowa nata ba, in ba hajiya Laurat ba" Numfasawa Justice yayi kafin yace"kada ka damu ɗan uwana, zan iya yin komai akanka, gobe Idan Allah yakaimu a family dinner zanyi magana da hajiyar laurat din dangane da ita Yarinyar," har cikin ranshi yaji dadin maganar justice, ya kwantar mashi da hankalin shi sosai harya fara tunanin yadda haduwarsu zata kasance da ita, sun jima adakin suna tattaunawa daga bisani suka dawo falo wurin su Captain. ______________________✍️ A hankali Motar Dr Jazz Ta ƙaraso bakin Entry Hall na shiga gidan baba Obie, Bayan yai parking ɗinta ya fito ya nufi cikin gidan, A katafaren Main Falo din gidan Ya taras da Twins zaune saman sofa tare da wani matashin saurayi kyakkyawan gaske kallo ɗaya zaka yima fuskarshi ka shaida ɗan uwan Justice ne, gaba ɗayan su wankan suit ne a jikin su, Cike da jin fargabansu Ya nufe su, Cikin sanyin murya yace"barkanku da hutawa" Ko kallo bai ishe su ba, Kamar Yayi magana da bango, kuma sun ganshi. Kusan sau uku Yana maimaita maganar da yayi masu amma babu wanda Ya amsa mashi, hakan Yasa shi yanke shawarar Tafiya yabar wurinsu Har Ya ɗaga ƙafa zai tafi muryar Zayn takatse shi. "Kai zo nan"! da kakkausar Murya Ya faɗa tare da yafuto shi da hannu, Irin kiran da akeyima kananin Yara, Jazz baiji komai aranshi ba Ya nufi Zayn. Yamutsa fuska zayn yai yayin da yake binshi da kaskantaccen kallo Yace "Kai makaho ne? Baka gan mu bane zaka wuce batare daka gaishe da mu ba"? Fuska adaure yayi mashi maganar. Cikin sanyin murya Jazz yace"Nayi maku magana kusan sau uku babu wanda Ya kula ni" Harara Zayn ya watsa mashi, Dr. nawaz dake a kishingide yana duban su Yace"zayn dama har yanzu wannan kwandon sharar Yana agidan nan? Nayi tsammanin Uncle Mubarak Ya saki babarsa sun koma kasarsu" Ta6e baki Zayn yayi"gayanan dai kana kallon shi, baida banbanci da masu gida, Har yafi mu jin daɗi, Uncle Mubarak ya ɗaure mashi wurin zama" Yamutsa fuska Dr.Nawaz Yai"Kaci sa'a ba'a ƙasar nake zaune ba, da tuni nasa anyi watsi dakai, donni bana son bare ya ra6i Ahlinmu," Jazz dake atsaye yana sauraron Rashin mutuncin da suke yi mashi, tuni idanunsa sun cicciko tab da kwalla. "Ya isa haka!" Zaid ne Ya faɗa tare da kallon Jazz, Da hannu Yayi mashi alamar Ya tafi, bawan Allah Jiki asanyaye ya nufi Hanyar kitchen din gidan, tunkafin Ya karasa Able ta fito daga ciki hannunta ruƙe da tray na kayan marmari, ganin jazz yasa ta dakata da tafiya fuskarta da fara'a tace"Jazz Ya jikin naka"? Fuskar shi babu walwala Yace"da sauki" "Allah Ya kara lafiya" ya amsa mata da ameen, ganin Yana ƴan kalle kalle Ne yasa ta fahinci akwai wani abu da yake nema don haka tace"ko akwai wani abu da kake bukata ne"? Ɗaga mata kai Yai haɗi da cewa"Eh, Ina neman Faryat ne," "Muje na raka ka, Nima wurin su zanje kai masu Kayan marmari," amsa mata yayi da toh, ta yi gaba yabi bayanta, aranta ta ayyana ko me zai kai shi wurin faryat? Tantiriyar Yarinyar nan da babu Allah aranta" Upstairs suka hau, bayan sun sauka third floor, suka nufi Balcony dake acan sama,Tsayawa fasalta kyawun wurin 6ata baki ne sai wanda Ya gani, tunkafin su karasa Jazz Ya hango Su zazzaune saman wasu hadaddun Kujeru Bugun Dubai, Matasan Ƴan mata ne masu ji da kansu, A kalla sun kai su uku Kowaccensu Ta dauki wanka na kece raini, Kamshin turarensu tuni Ya soma Cika mashi hancinshi. Kaitsaye idanunsa suka sauka akan Faryat, wadda ke asanye da mini skirt ya matse jikinta, daƙyar skirt din Ya wuce Ass dinta, Rigar jikinta kuwa Ko cibinta bata rufe ba, ta bayyana shape din kirjinta hatta nipples dinta kana iya ganin tsininsu, babu mayafi akanta Kitson kalabar da akayi mata ne mai kyan gaske ansanya mata sparkling stones masu jan hankali saman gashin kanta, yatsun hannunta yana asanye da gold knuckle rings, Haka zalika Hancinta na amanne da nose ring, wata ziririyar sarka ce a kafarta, Yarinyar karshe ce wurin Iya barikanci, Hatsabibiyar gaske bata jin magana ko miskala zarratin, sai dai fa akwai kyan sura, komai nata irin na hajiya saratu ne banbancinsu girman jiki da shekaru. Matashiyar dake a gefenta, Yusra ce Ƙanwar Yaseer, Kallo ɗaya zakai mata saika sake kallonta, Tsabar haɗuwarta, itama fara ce sol, kamanninta sak dana mahaifiyarta Her excellency Muhibbat, gata doguwa tubarkalla, bayan ita sai Zulaihat kanwar Ziyad Wankan tarwaɗa ce alaunin fata tana da saukin kai ko a fuska ka kalle ta, babu wanda Ya lura da Jazz A cikinsu Hankalinsu na akan firar da suke Yi. able ce tayi masu sallama, Tare da ajiye masu tray din kayan marmarin saman round table din dake a tsakiyar kujerun su, juyawa tayi da sauri ta fuce tabar wurin. Wani irin shakkar Yi masu magana Yake ji, Sai faman bin Faryat Yake Yi da kallon ƙurulla. "Na jaraba kiran layin Sister Hindu bata yi picking ba, may be ko bata a kusa ne da wayar, ita dai Yazrin nayi mata uziri, saboda tafiyar da suka sha nasan haryanzu gajiyar tafiya bata sakesu ba" Zalaihat ce tayi maganar tare dakai hannu ta dauki tufa tana ci "Ina ga mezai hana mu shiga gidan yi masu bangajiyar tafiya, Su mommy ma suna acan" "Ni dai ba inda zanje, sai zuwa gobe idan mun haɗu wurin Dinner din daddy Hateem" Acewar Faryat Tana faɗa tana farfari da idanunta. "Gobe akwai shagali, zamu yi sharholiyarmu son ran mu, Har nakagara goben nan tayi," Yusra ce ta fada tana karkaɗa kafarta. Har Faryat Ta buɗe baki daniyar tayi magana, Sautin ringing din wayar Jazz Ya dakatar da ita, Kusan atare suka wurga idanunsu kan fuskarshi, nan take yaji gabanshi ya faɗi rass saboda kwarjinin da suka yi mashi. Yamutsa fuska Yusra tayi tare da kau da idonta Zulaihat kuwa Murmushi tasakar mashi "Dan uwa, Tun yaushe kazo wurin nan ne? Yana faman Kame kansa Yace"tare da abla muka zo" "Amma meyasa bakayi mana magana ba jazz," cikin kulawa ta fada tana dubanshi Ta fuskanci Hankalin shi ba kwance yake ba "Wa kake nema ne"? Kallon Faryat da yayi ne yasa ta gane ita yake son gani" Murmushi zulaihat tayi, Faryat dake kallon shi, wani irin shu'umin murmushine akan fuskarta, yunƙurawa tayi ta miƙewa ta dubi su Yusra"ni zan shiga ciki, bazan jima ba yanzu zan dawo" Yusra dake harararsa tace"faryat kin bani kunya, Ki rasa wa zaki kula sai wannan halittar" ta fada tana nuna shi da yatsa Zulaihat tace"Please Yusra, babu ruwanki da shiga sabgarsu" Ta6ebaki Yusra tayi Ba tare daya ankare ba, Faryat ta ruƙo hannunsa tare da jan shi suka soma tafiya atare, wani sanyine yaji ya ratsa zuciyarsa, duk da yasan ba lallai Faryat ta sassauta mashi ba, Ya riga daya san halin ta. Kaitsaye suka nufi bedroom dinta dake a gidan, adai dai bakin kofar shiga Dr.Jazz Ya dakata da tafiya, da sauri ta kalle shi hadi da kashe mashi ido ɗaya tace "my babe meyasa ka dakata da yin tafiya? Let's go inside," ta fada tana matse hannunsa dake acikin nata, har cikin zuciyarshi yake jin matsar da take yi mashi. Muryarshi ƙasa ƙasa Ya ce"basai na shiga ciki ba, mu koma falo mu yi magana" Ɗaure mashi fuska tay "Jazz, you will lose your chance to talk to me if you don't go in," she warned. "If you don't go in, don't expect to see me again"! *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga D Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 8 by Novels Elite Admin May 23, 2024 Sponsored Link _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القدر💋✊🔥 ~Takun Ƙarshe🔥~ قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Tana ƙarasa fadar hakan ta sanya hannu ta ture ƙofar ta shiga ciki, A ƙalla Yafi karfin mintuna biyar a bakin kofar yana yanke shawara da zuciyarsa, haƙiƙa Yana matuƙar jin tsoron Allah, bayason zama daki ɗaya da macen da ba muharramarsa ba, hakanan ba tare da wata lalura ba, balle kuma faryat da ta kasance tantiriya, sai dai baya jin zai iya rasa wannan damar, Allah ya jarabce shi da tsananin ƙaunarta, Itace mace ta farko da ya fara jin tsantsar sonta tun lokacin daya mallaki hankalinsa, ya mutu akan kaunar faryat yana son yarinyar duk da kasancewarta mara jin magana. Numfasawa yayi kafin ahankali ya tura kofar dakin nata ya shiga daga ciki, katafaren dakin kwana ne, kamar na ƴar sarki, tsabar haduwar furniture din dakin, Komai na cikinsa Launin black pink ne. Bayan shigarsa dakin, Sanyayyan sanyin A.c ne mai haɗe da daddaɗan kamshin turaren faryat ya ratsa hancinsa da fatar jikinsa, Lumshe idanunsa yayi slowly ya buɗe su akan faryat dake a tsaye gaban dressing mirror, ta juya baya kitson kalabar kanta ya sauko har mid back dinta, ta cikin madubin ta ke jifar shi da shu'umin kallo. Ganin yaƙi ƙarasowa gare ta, yasa ta juyo ta nufe shi, dab dashi ta ɗaya suka soma jefa wa junansu kallo. Ba zai iya jurar shaƙar ƙamshin turarenta ba da kallon surar jikinta hakan ba ƙaramin jefa shi yanayi ya ke yi ba, Muryarshi na rawa ya furta"Am.. umm.. tun da naganki zan tafi" ba zato ba tsammani yaji ta ɗaura hannayenta saman kirjinshi, muryarta da shagwa6a ta furta"Ni ban gaji da kallon ka ba, My honey, tsawon lokaci bansanya ka a idanuwana ba, nayi kewar komai naka jazz.. " kafin ta ƙare maganar, jazz ya tari numfashinta da cewa"Faryat tayaya zan yarda da kalamanki? Bayan ke da kanki kika faɗi cewa bazaki ta6a sona ba, kuma ba zaki iya aure na ba" Juya mashi baya tayi haɗi da goya hannayenta saman kirjinta kafin ta soma magana. "Jazz, I won't hide it from you. Nothing has changed. I love you, but I can't marry someone who has no origin", (Jazz bazan 6oye maka ba, Har yanzu babu abun da ya canza, Inasonka amma bazan Iya auran wanda bashi da asali ba,)" ta faɗa tana girgiza kanta, kafin ta ɗaura da cewa. "kaima ka sani jazz mommyna da daddyna ba zasu ta6a yarda mukasance atare ba, jazz I come from a wealthy family. How can I love someone like you who has no origin? What is your family status?" ta jefa mashi tambaya ba tare da ta jira amsar shi ba taci gaba da magana "Ta ya ya zan auri ɗan tsohuwar mai aikin gidan mu" tun da ta fara magana sai yanzu ta juyo ta fuskance shi, Jikin shi yayi sanyi lakwas, hawaye tuni sun soma taruwa a cikin fararen idanuwansa, kalamanta sun kashe mashi kwarin gwiwarshi, sai yajima gaba ɗaya ya tsani kan shi, ta fahimci halin da ya shiga sai dai ko kaɗan bata ji tausayin shi ba. "Jazz Hamshaƙan masu kuɗi suna rububi akaina, waɗanda duniya tasan da zamansu, How can I choose a meaningless future for myself when I could have so much more?" a tsiwace ta faɗa tana zare mashi kyawawan idanuwanta masu dauke da zira ziran eye lashes. Hawayen da suka cika idanunsa tuni sun wanke fuskarshi Cikin karyayyar murya yace"Nasan ni bakowa bane faryat, bani da asali, amma inaso ki sani, ina son ki tsakani da Allah badan wani abu naki ba, ba lallai ki sami wanda zai so ki kamar yarda nike sonki ba, nayi maki alkawarin zan baki kyakkyawar kulawa idan har kika amince da soyayya ta, ba zaki ta6a danasani ba faryat"! Shu'umin murmushin gefen fuska tasakar mashi, wani irin kyawuntane Ya kara bayyana. Matsawa tayi tare da shige mashi, Har takaiga mumfashinsu na kokawar fitowa, hannayenta biyu ta ɗaura saman waist dinsa, da sauri ya yi kokarin kwace kansa daga gareta sai dai taki bashi damar yin hakan, gaba ɗaya ta kashe mashi jikin shi. "Jazz ka daina wahalar da kanka akaina, cos I will never marry you. Owning me is not an easy thing, idan mommy taji zancen kana neman soyayyata kai kasan me zai biyo baya, shiyasa nake rufa maka asiri, saboda ina da buri akanka," lumshe idanunsa yayi cikin jin ƙunar rai, Allah ne kadai yasan Irin azabtuwar da zuciyarsa take yi mashi akan soyayyar faryat, zai iya jure komai amma bazai juri ya rasa ta ba. Jin motsin hannunta akan Trouser dinsa ne yasa shi yin saurin buɗe idanuwansa a hanzarce ya buge hannunta Yana faman fitar da huci... Kashe mashi ido ɗaya tayi tare da zuro harshenta waje ta lashe pink lower lips dinta, cikin jin shaukin shi ta furta"jazz, har yanzu ban canza ra'ayina akanka ba, ka bani dama, in ɗebe maka kewa, kaga babu mai kallon mu daga ni sai kai, zan faranta maka rai, sannan inyi maka abun da zai zautar dakai ya gigita ka" ta faɗa cikin jin shauƙin shi tana kokarin tura mashi boobs ɗin ta da suke acike fam. Jikin shine ya soma kakarwa a ruɗe ya furta"bani da wannan ƙazamin tunanin araina, dan Allah ki daina fadamin kalaman nan, Hakan Yana karya min zuciyata, Ni tsakani da Allah nake sonki, Idan babu mai kallon mu Allah Yana kallon mu faryat, Bazan bari mu sa6a mashi ba, " Harara ta jefa mashi"matsalata dakai kenan, Har yanzu bakauyene kai, sai kace ba bature ba, sam baka da wayewar nan irin ta zamani, Daga anyi magana sai ka ambaci sunan Allah kamar kafi kowa tsoronsa, Ay Allah gafurirrahim ne, Idan mukayi sai mu roƙi rafiyarsa... " tunkafin taƙare maganar yace"Idan kuma muka mutu muna cikin aikatawa fa"? Murguɗa mashi baki tayi"nima bansani ba, tun da baka buƙatana ka tafi kawai, zan nemi wanda zamuyi da shi" ta fada tana ruƙe qugunta. Wani irin kishine ya ziyarce shi, tamkar Ya haɗiyi zuciya haka yake ji "Faryat ba ki jin kunyar fadin hakan agabana ba"? Ɗaga mashi gira tayi "Yeah i can sleep with someone in front of you. tun da kai bazaka bani abun da nakeso ba, jazz bakason farin cikina, na jima ina sha'awar son kasancewa dakai amma kaƙi bani haɗin kai" cikin rauni na murya yace" idan kina son kasancewa dani ki aure ni mana, zan zama naki ke kadai, Mallakin ki, ko da yaushe kike bukatana zan kasance atare dake", Girgiza mashi kai tayi"A'a nidai kawai kayi min abun da nakeso, ay na fada maka bazan iya auranka ba, sai dai mu kwanta in baka kaina" Lamarin faryat ba karamin mamaki yake bashi ba, A shekaru bazata wuce 22 Years ba, Mace har mace sai dai babu kunya ko kadan. Ganin Ya tsareta da idanunsa ne yasa ta fara tunanin ko ya amince mata ne, ɗaura yatsun hannayenta tayi akan wandonsa da niyar ta zame masa shi, A hanzarce Ya buge hannunta, da sauri jiki na rawa ya nufi kofar dakin zai fuce, da gudu tabi bayanshi tayi hugging dinshi, ta soma raira mashi kukan shagwa6a, hakan baƙaramin yanayi ya jefa shi ba, baisan da wani yare zaiyi mata magana ta fahince shi ba, ya riga daya gane faryat tana sonshi, Rashin asalin shine yasa take gudin shi. Muryarta da shessheƙar kukan ƙarya take fadin"Jazz, kada ka tafi kabarni, Ina buƙatarka Jazz, Ina son kasancewa tare dakai, dan Allah ka amince min muyi nayi maka alkawarin bazan faɗama kowa ba, Idan ma kana fargaban wani ya gan mu, sai mu je hotel in kama mana room, ko muyi a cikin motana" ta faɗa tana murza mashi mararshi da hannayenta, gaba ɗaya tagama susutar dashi wata irin zuface tasoma wanko fuskarshi Muryarshi da matsananciyar kalasa sautinta ke fita "Bazan iya sabama mahaliccina ba faryat, Ina jin tsoron Allah, kiyi haƙuri, Nima inajin abun da kike ji amma bazan iya ba, Kina bani wahala faryat, kema kuma kina cutar dakanki, saboda kina sona, Kina son kasancewa dani, amma kin haramta ma kanki aurena akan wani dalili naki mara ma'ana, Meyasa bazaki tausaya mana ba daga ni har ke? Faryat ki cika mana burinmu na ganin mun raya soyayyarmu, kada ki bari shaidan Yaci galaba akanki, ki fi karfin zuciyarki faryat, ki zauna kiyi tunani... " daƙyar ya ƙare maganar muryarshi na sarƙewa ya daddage ya 6an6are hannayenta daga ruƙon da tayi mashi, da sauri ya ruƙo handle din ƙofar ya fuce daga dakin A jikin kofar Ya jingina kanshi hawaye masu ɗumi suka shiga zarya akan kuncinsa. Sautin shessheƙar kukan faryat ne ya cika kunnuwansa, baisan ya zaiyi da ita ba, yasan da irin mugun sha'awar dake gareta sai dai shi bazai amince mata su aikata sabo ba, saboda babu ɗa'a ga abokin halitta wurin sa6ama mahalicci Allah! Bazai juri sauraron kukanta ba, zuciyarshi karaya take yi, da sauri Ya sauko down stairs Cikin takun sauri Ya Nufi part din baba Obinna, zuciyarshi na cigaba da tafarfasa, Abakin kofar dakinsa Ya tsaya da yin tafiyar Ya zaro hanky, Ya goge kwallarsa, Kafin ya daidaita nutsuwarsa, sallama yayi mashi. Daga Ciki Ya jiyo muryar baba obie "Shigo daga ciki" Buɗe kofar yai tare da shiga Ciki, adai dai lokacin Baba Obie, Yana zaune saman darduma hannun shi ruƙe da cazbaha. Ba zato ba tsammani, Yaji saukar Jazz saman bayanshi, gaba ɗaya ya rungume shi tare da cusa fuskarshi saitin kafadarsa, Hakan ba ƙaramin ɗaga mashi hankali yayi ba, saboda a duk lokacin da jazz yayi mashi irin wannan rungumar to an 6ata masa raine," Yana Iya jiyo sautin fitar numfashinsa, dakatawa yayi da jan cazbahar, Ya ruƙo hannun Jazz Ya zagayo da shi ta gabanshi, tare da rungume shi ya kwantar da kansa saman kirjinsa tamkar ɗansa na cikinsa ko jikansa. Cikin sigar lallashi yake bubbuga bayansa batare daya furta masa ƙala ba, har saida Yaji alamun Ya fara samun nutsuwa tukunna Ya soma magana "Waya ta6a min shalelena"? Muryarshi adisashe Ya furta"Baba ka ta ya ni da addu'a, ita kadai nake bukata daga gare ka" ya fada batare daya raba jikin shi daga na Obie ba. "Jazz kasan bana son damuwarka, Ka fada min koma menene nayi maka alkawarin indai baifi karfina ba wallahi zanyi maka shi," babu wasa a kalamansa Jazz yayi fatan ace zai iya fada mashi abunda ke damunshi amma bazai iyaba, Yasan muddin baba obie yaji zancen Yana son faryat sai ya aura mashi ita, koda kuwa Iyayenta basa so, shi kuma abunda yake gudu tada husuma, saboda ba lallai hajiya saratu da Pravin su amince mashi ya aureta ba, komai zai iya faru. Shafa bayanshi baba obie yaci gaba dayi yana fadin"Ina sauraronka, Fadamin meke damunka rabin raina" Ɗagowa yayi da fuskarshi wadda tuni ta jiƙe sharkar da hawaye, cikin rauni na murya yace"baba, Bana jin daɗin yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba"? Zuciyar baba obie ba karamin karaya tayi ba, nan take ya gane gori akayi masa, bawan Allah tsantsar tausayinsa ne yakama shi. Cigaba da yin magana yayi"Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya buɗi baki sai yace ni ɗan mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba" daƙyar ya kare maganar wani irin kukane Yaci karfinsa da sauri Baba obie Ya janyoshi zuwa jikinshi sosai Ya rungune shi, Yana lallashin shi. "Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani ɗan adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi ƙaddarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin ƙaddararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita" nasiha mai ratsa zuciya baba obie Yaci gaba dayi mashi har saida yaji ya daina kukan tukunna Ya raba shi daga jikinshi Cikin kulawa yace dashi"Yanzu fada min wanene Ya tsokane ka"? Shiru yayi batare dayace komai ba, baba obie ya fahimci bayason ya sanar da shi, hakan yasanshi cewa"Ko da yake basai ka fadamin ba, ni da kaina zan binciko wanene, kuma zan hukuntashi" ya fada yana daure fuskarshi alamar ranshi ya 6aci. "Baba," Kallon shi obie yayi ina sauraronka "Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family ɗinka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina ɗaya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa" Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskar baba obie. "Jazz baka ɗauke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance" yayin da baba obie ke yin maganar, wani irin sanyi da daɗi ne ke tsuma zuciyar jazz, har abada bazai ta6a mantawa da halaccinsu agare shi ba. Ganin Ya faranta masa raine yasa baba obie cewa"namanta ban tambayeka ba, Ya jikin naka"? Fuskarshi dauke da murmushi Yace"naji sauki, nagode na kulawarka agareni" Jinjina kai baba obie yai"gobe idan Allah yakaimu, Ina fata zaka halacci Dinner din Hateem" Jim ya ɗanyi harga Allah baison zuwa kodan gudun a ci mutuncinsa, amma saboda yana son ya faranta ma baba obie yasa shi cewa "In sha Allah tare dani za'a buɗe taro" Murmushi baba obie yai masa"Naji dadin jin hakan rabin raina. Jan shi da fira baba obie yai, kamar wani abokinsa, tuni jazz ya saki jikin shi. *💋 UMMIN AMERICA❤* Duk Yinin Yau Bata fito daga ɗaki ba, ta killace kanta tun safe bata jin daɗin zuciyarta, duk ta ƙuntata kanta, tayi jiran zuwansu unaisah su shigo don su ɗe6e mata kewa sai dai shiru babu alamarsu, tuntana sa ran ganin su har ta fidda ranta, ta ƙundundune kanta cikin lallausar bargonta, Sallah ce kaɗai take tada ta daga saman gado Har ta fara nutsawa cikin baccinta kwatsam wayarta dake ajiye kan nightstand ta soma yin ruri, da wata irin kasala ta ɗago da kanta, sumar kanta duk ta hargitse babu gyara, laluba Hannu tayi ta kamo wayar batare data duba sunan mai kiranta ba tayi picking tare da kara wayar a kunnanta. Sautin Muryar NATASHA ne ya Daki Dodon Kunnanta"nayi fushi Kin manta dani ko"? ta faɗa cikin harshen turan ci. Muryarta da kasala Ta furta"ba haka bane Natasha, Kina araina, dake nake kwana dake nake tashi" "Ban yarda da kalamanki ba Ummi, Idan Dagaske kinyi kewata meyasa baki kirani ba? Sai da na kira ki ni da na damu dake ko"? Shiru tayi na ɗan wani lokaci har sai da Natasha Ta furta Naji kinyi shiru tukunna taja numfashi tana faman sauke ajiyar zuciya tace"bansan yadda zanyi maki bayani ba NATASHA, ni kaɗai nasan halin da nake aciki, ina cikin damuwa, Ina cikin kaɗaici, Rayuwata a ƙuntace take natasha, bani da wani ƴan ci, ba wanda Ya damu dani, tun safe bana jin daɗin jikina babu wanda ya leƙo ɗaki na don Yaga awani hali nake aciki.... "Muryarta na rawa ta ƙare maganar, tamkar zata fashe da kuka, hakan Ba ƙaramin ɗaga Hankalin Natasha Yayi ba, Jin sautin miryar aminiyarta da alamun matsananciyar damuwa.. Cikin saurin mirya ta furta"Ummi, muyi magana ta video Call, Inason naganki ko hankalina Ya kwanta" "Toh, amma kafin nan zan shiga toilet, Ƴan mintuna kaɗan Idan na fito zan kiraki" natasha ta amsa mata da toh, bayan ta yi rejecting Kiran, ta daura wayar kan drawer, kafin Ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6a da shi, Jallabiya ce a jikinta launin dark ash, saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet, After Some minutes ta fito fuskarta da alamun lemar ruwa, Laptop dinta dake ajiye kan desk ta dauko ta koma kan gado ta zauna daga tsakiya ta ajiyeta agabanta, kafin ta buɗe ta soma sarrafata, Natasha ta kira video Call nan take ta ɗaga, kallon juna suka soma yi tamkar suna a wuri ɗaya, Natasha tana a kishingiɗe saman beach chair dake a ga6ar teku, babu suturar mutunci a jikinta, dama ita bata cika son sanya suturar da zata rufe mata tsiraicinta ba, tafi sha'awar ta sanya pant da bra. cikin harshen turanci suke yin magana. "Yanayin fuskarki Ya tabbatarmin da bakyajin dadin Ummi, Ki faɗamin meke damunki? Waya ta6a min ke"? Yamutsa fuska Ummi tayi tamkar batason furta maganar tace"kamar yadda na faɗa maki bana jin daɗin jikina, narasa gane meke damuna, amma ina da tabbacin hada kaɗaici, ban ta6a ƙuntataba Irin na Yau, Jin kaina nake tamkar Ina a prison" Cikin kulawa Natasha tace"meyasa ba zaki janye aikin da Commender Ya baki ba? Ummi dama ni nasan bazaki Iya jurewa ba, tuntuni naso In gargaɗeki saboda ba zaki Iya ba, mu da muka saba da yawo kullum sai mun fita wurin abokan harkar mu, taya zaki Iya jure rayuwar kulle"? Ta faɗa tana mai dubanta, Dafe kai Ummi tayi da hannu ɗaya"Har yanzu banyi danasanin kar6ar aikin kula da yaran nan ba, Saboda Inaji araina akwai wani alkhairi atattare da zamana da su, shiyasa bana danasani, ni kawai abunda ke damuna rayuwar kullance ke banaso, Yana ƙuntata Rayuwana, hada ƙarin Yaran da suke ɗebe min kewa basu zo wurina ba yau, ni kuma nakasa tashi naje gare su" fuskarta a yamutse tayi maganar "Har Yanzu ba zaki fahimce ni ba Ummi, Ni inaso na kwatarmaki ƴan cinki ne, Inason farin cikin ki, Kina buƙatar abokan Harka, kefa ba irin matan da za'a ƙuntata ba ne...' tunkan Natasha ta ƙare maganarta, ummi tayi saurin tarar numfashinta da cewa "Akwai labari mai daɗi, nasan idan na fada maki zakiyi mamaki" Ta faɗi hakan ne don batason Natasha taci gaba da yi mata zancen Ajiye aikin da take Yi. "Naƙosa naji labarin nan fadamin mana" ta fada tana sakin murmushin shaƙiyanci. "Mutumin Ya ziyarce ni Har cikin gidan da nake," Waro idanu waje natasha tayi da mamaki ta furta kina nufin Big Boss? Ya ziyarce ki? Ɗaga mata gira ummi tayi alamar eh. "Amma ya akai ya iya shigowa gidan Jami'an Isod, bayan kin faɗamin acikin sharuddan da suka baki, babu shige babu fuce basu buƙatar wani naki yazo inda kike, har zuwa lokacin da kika kammala Yi masu aikin su" ta faɗa a kagare da son jin ƙarashen xancen. Dariyar shaƙiyancin Ummi tasaki tamkar babu damuwa aranta"kinsan mutumin na dabanne, ni kaina bansan tayaya akai ya shigo gidan ba, Har tambayarshi nayi sai yace min idan na yarda dashi indaina tambayarsa.... " dariya natasha tayi cike da nishaɗi tace"Namijin Duniya, Nayi kewarshi ummi, kullum cikin begen ganinsa nake yi, yayi min nisa yanzu, ba kamar lokacin da nake yi mashi rainon babynsa Pretty ba, tun da Ya kar6i Yarinyar sai nayi dagaske nake ganin shi, ko wayana baya picking... " kafin Natasha ta ƙare maganar Ummi tayi hanzarin tarar numfashinta da cewa"wai ina yarinyar take ne? Na jima ina son na tambayeki ita, nayi missing dinta, tun ranar dana fara Yin tozali da ita naji kaunarta ta shiga raina, duk da bata jin magana amma tana da kyau" Natasha tace"hmmm, Ummi Ya raba ni da ita, tsawon watanni, duk idan na tambayeshi ina baby Pretty na sai yace min ya mayar da ita wurin mamanta, har alfarma na nema awurin shi akan ya amince min inbiyo shi nigeria saboda ina son ganinta amma Ya hanani.... "muryarta na rawa ta ƙare maganar idanunta sun cicciko tab da kwalla. "Ummi Inason yarinyar nan, Ina ƙaunarta, nayi fatan ace ni na haifeta ko dan saboda mu kasance atare har abada, mun shaƙu da juna, na saba da ita, Amma yayi min yankan ƙauna.... " tunda tafara magana ummi ta natsu tana kallon fuskar Natasha ta cikin screen din laptop tamkar suna awuri ɗaya. "Ummi nasan zaki Iya taimaka mani, tunda Yana kaunarki, Yasha fadamin ke kadaice kike Iya sarrafashi son ranki, please kiyi amfani da damar da kika da ita, Ki lalla6a shi Ya dawo min da baby pretty" cikin sanyin Murya ta ƙare maganar, Ummi dake kallonta tuni tausayinta Ya kamata, bata ta6a ganin Natasha tana zubar da kwallarta akan wani ɗan adam ba sai akan babyn da take mutuwar so, tasan da irin kaunar da take yima yarinyar a lokacin baya. Cikin kwantar da murya ummi ta furta"Am sorry, Kinsan bana son ganin hawayenki, zan Iya yin komai akanki, saboda halaccin ki agare ni, Kin wuce ƙawa a wurina sai dai ƴar uwa, saboda kin kaunace ni a lokacin da kowa yake guduna, abun da nakeso dake ki kwantar da hankalin ki, zanyi kokarin ganin na shawo kanshi don ya dawo maki da babyn ki" Murmushin farin ciki natasha tasaki tana fadin"thank u ummi, nasan zaki iya yin komai saboda farin cikina, shiyasa nake ƙara kaunarki, ina nan ina shirye shiryen zuwa Nigeria saboda ke" Martanin murmushin ummi ta mayar mata, "Ina handsome boy din nan, namanta ban tambaye ki shi ba" "Bashi da lafiya, Yana a kwance" Yamutsa fuska Natasha tayi"najiye mashi ba dadi, Allah Ya bashi lafiya, har yau ban manta da fuskar shi ba" Murmushi Ummi tayi mata" dama ke ay bakya mantawa da abu mai kyau, naga kin kirani da layinki Na england, hakan na nufin kin koma gidanki"? Ɗaga mata gira tayi alamar eh. Jinjina kai ummi tayi, shiru sukayi na wani lokaci yayin da suke kallon juna batare da ƙyaftawa ba. "Kin tsareni da ido Kina kallona, Kamar akwai wani abu da kikeson fadamin" acewar natasha ta faɗa tana ɗage mata gira. Dariya Ummi tayi, Harta Buɗe baki da niyar furta magana, Sautin knocking ƙofar da akayine Yasa ta fasa yi mata maganar, "Zan Kiraki Anjima Ki kula min da kan ki" "Bangaji da jin muryarki ba ummi, amma shikenan zan jira zuwa anjiman inma kin manta baki kirani ba, Ni zan Kira ki, ki kula min da kanki and pls ki daina sanya damuwa aranki" a hankali ummi ta furta mata"toh, nagode da kulawarki agare ni" bayan sunyi sallama, Ta kashe video Call din, ta sauko tare da laptop din a hannunta, ta nufi desk ta ɗaurata, kafin ta shiga wurin closet dinta, mayafi ta daura akanta. ɗaga Murya ta yi Wanene"? Daga waje tajiyo Muryar Batool Tana fadin"aunty Ummi ni ce" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta jin muryar Batool. "Ki shigo daga ciki," turo ƙofar batool tayi tare da shigowa ciki, tana bin dakin da kallo kafin ta ɗaura idanunta akan fuskar Ummi, Murmushi suka sakarma juna "Nayi fushi Batool, sai yanzu zaki tuna dani? Nayi tsammanin kece mutun na farko da zaki zo gare ni idan kika ji shiru ban fito ba, amma sai naji shiru babu ke babu unaisah" tafaɗa tana haɗe mata fuska alamar ranta Ya 6aci. "Aunty ummi am sorry, Kina araina, tun ɗazu nake taso in shigo wurin ki' Miƙa mata hannu Ummi tayi da sauri Batool ta ƙarasa gabanta tare da faɗawa kan chest dinta, sosai Ummi tai hugging dinta. "Nayi missing dinki My babe, kun barni a daki ni kaɗai inata kewarku, Ina unaisah ne"! Ta faɗa batare data raba jikinta daga na batool ba. "Nima bansan inda take ba, ɗazu muka rabu" "Okey,ina fata kina lafiya, " ɗago dakai Batool tayi"Lafiyata lou, amma ke kamar baki da lafiya" Shafa gefen fuskarta ummi tayi"bana jin dadi, amma kada hakan Ya dame ki, ganinki da nayi ya faranta raina" ta ƙare maganar tare da ruƙo mayafin Pakistan din batool"kayan sunyi maki kyau sai naga kinyi min kama da wata Old friend ɗina da muka rabu da dadaɗewa, kamar ita ta haifeki, Itama doguwace fara, Mom dinta balarabiya ce" Murmushi batool tayi"amma ni da Unaisah nake kama" Girgiza kai Ummi tayi"No, baki kama da Unaisah kun dai yi yanayi da ita" Kwa6e fuska Batool tayi saboda ita tafison ace tana kama da Unaisah, ummi ta fahimci hakan sai tayi saurin cewa"wasa nake maki, dama don in ga reaction dinki ne, gaskiya kuna kama da ita sosaima kamar twins" jin hakan yasa batool sakin dariyar farin ciki, ummi dake kallonta batayi mamakin hakan ba ta riga data fahimci tsantsar ƙaunar da suke ma junansu. "Mu zauna ki tayani fira, Ko baki gaji da tsayuwa bane" "Aunty ummi, nasan kina jin yunwa, ki tafo muje falo zan sama maki abunda zaki ci" wani irin kallon ƙauna ummi keyi mata ba ƙaramin dadi take ji ba idan Batool ta nuna damuwa akanta. Ruƙo hannunta ummi tayi acikin nata atare suka fito daga dakin. Sautin Muryoyinsu Naufal ne Yajawo Hankalin Ummi Ga kallon su, tun Dazu suna a falo, Tare da Boss Man, Sun tasa shi gaba sai surutu suke zuba mashi. Jin takun Takalmansu Yasa su dagowa suka kalli su Ummi dake saukowa down stairs, Har suna haɗa baki wurin ambaton sunanta Aunty Ummi. Saukowa Jamimah da azeeza su ka yi daga kan sofan da suke zaune, da gudu suka nufe ta, Hannah da Parveen ma suke miƙe suka nufe, wani irin daɗi taji aranta, Ɗaya bayan ɗaya ta soma rungumarsu a jikinta, "Aunty Ummi, Yanzu kika tashi daga bacci"? Azeeza ce tayi mata tambayar Girgiza mata kai tayi alamar a'a Parveen tace"Ko dai baki lafiya" Harara Ummi ta jefa ma Parveen tare da cewa"kun damu dani ne? Meyasa ba ku zo bedroom ɗina kun duba ni ba? Shiru sukayi sai jamimah ce tai kokarin cewa"mantawa mu ka yi" Jan kumatunta Ummi tayi da hannu"Aku sarkin ɗumi, Na riga da nage baku kaunata, Shiyasa baku damu dani ba" ta faɗa haɗi da marairaice masu fuska, "Wallahi aunty Ummi Muna ƙaunarki, kuma mun damu dake" Hannah ce tayi maganar "Ni dai Inasonki aunty Ummi, kiyi hakuri idan mun 6ata maki rai," murmushi ummi tasakar ma Azeeza da tayi maganar. Ruƙo hannunta Jemimah Tayi"Aunty ummi nima ina sonki" "Naji na Yarda kuna sona, Yanzu mu shiga ciki," ta fada tare da Jan hannun Batool suka nufi ciki tare da su Hannah Tunkafin Su ƙaraso, Boss man Yake Kallon Ummi, sam ya manta da ita. "Barka da hutawa Yalla6ai, Fatan ka wuni Lafiya, Ya iyali" A hankali Ya furta"Lafiyalou Ummi, Ina fata kema haka"? Ɗaga mashi gira tai alamar eh, ta faɗa tare da samun wuri saman Sofa ta zauna, suma sauran duk suka zauna. hankalin Sajeed na akan screen din wayar Unaisah, Haris da javed suna zaune gefe da gefen shi tare da naufal sai kallon Game din da Yake bugawa suke yi, baijima da sauke shi akan wayar ba. Gyaran Murya Ummi tayi masu atare suka dago suna kallon ta. "Sannunku, ba hello ba Hi kun samu Waya kunata danna waya baku ita ne" "Ta Unaisah ce," Acewar Sajeed Da mamaki Ummi tace"Unaisah ke da waya iphone15pro? Amma ban ta6a ganinta ba" "Dr Laurace ta bata Kyautarta, ɗaya daga cikin Likitocin da suka yi jinyarsu a america" Boss man ne Ya bata amsa, Jinjina kai tayi. "Ina ita Unaisah dinne"? Tayi tambayar tana kallon su Boss Yace"Bansan meya tsayar da ita ba, tunɗazu da muka shigo tare da big guy Ya tafi da ita zai nuna mata kitchen din gidan nan ban ƙara ganin ta ba, ba mamaki ta tsaya taya masu aiki girkin dinner" "Dan Allah ka nuna min kitchen din, Inaso In kar6o ma aunty Ummi abinci, Yunwa take ji" acewar Batool. Murmushi boss man Yayi yana dubanta yace"kin damun da auntyn nan naki da alama, kada ki damu, bari na kira big guy awaya, idan suna a kitchen din zansa akawo mata abincin.... " kafin Ya ƙare maganar, Parveen tayi saurin cewa"Dan Allah Nima zanci" dariya sukayi gaba dayansu. Ummi tace"foodie, Baki Gajiya da cin abinci, shiyasa kika fi sauran ƴan uwanki jiki" Kwa6e fuska tai"ay bani kadai bace me cin abincin ba, Ki kalli kumatun jamimah sunyi manya manya da su" maganarta ta basu dariya. Harara jemimah ta watsa mata"ay dai ban kaiki Cin abinci dayawa ba, Ni madara da bonbita nake sha, Sai dafaffan kwai da Fika fikin Kaza," boss dake kallonsu murmushine dauke akan fuskarshi, Firarsu ba karamin nishadi take sanya shi ba Wayarshi Ya zaro daga aljihu Ya danna ma Big guy kira, Bugu uku Yayi Picking Miƙewa yai da sauri Ya nufi cikin falon nesa da su ya tsaya saboda hayaniyarsu. "Malam Ina ka shiga ne? Ka tafin mun da rabin raina" On the other hand sautin dariyar Big guy ta karaɗe Kunnuwansa, "Nifa Yanzu Haka Ina daki kwance saman gadona" "Bana son Iya shege, To ita ina kabarta? "Ka riga da kasan Halin Jarin naka, yarinyarce da kiriniya, Tunfa dazu dana nuna mata kitchen din nace mata ta dawo cikin yan uwanta, bayan na fada mata hakan na wuce room dina, yanzu haka bata wuce kitchen din, Cikin kattai" ya karasa maganar Yana dariya. Daure fuska boss yayi tamkar Yana agabanshi, "Zamu hadu dakai ne, Allah idan wani abu Yasamu Yarinyar nan jikinka ne zai gaya maka dan rainin wayau" ya fada tare da yin rejecting kiran, Cikin takun sauri Ya nufi hanyar zuwa kitchen din, ba laifi akwai tazara tsakanin kitchen din da main falo, Lokacin da Ya Isa katafaren kitchen din gidan tamkar a restaurant tsabar haɗuwarshi, kai kace ba wurin Girka abinci bane saboda girman shi da ƙawatuwarshi, An zuba kayan aiki masu tsada da inganci, gaba ɗaya masu girka abincin Gidan Jami'an Isod ne cikin chef'uniform, matasan samari masu jini a jika, daga ganin Yadda suke aiki zaka shaida kwarewarsu a 6angaren catering, ko mace bazata nuna masu Iya sarrafa abinci ba, A ƙalla sunkai su Bakwai, Babu wanda Ya lura da shigowar Taj acikinsu, Gaba ɗaya Hankalinsu na akan Unaisah, dake agaban kitchen island tana Yanka masu kayan Lambu, abun da ya ɗaure ma taj kai, ganin Yadda sukayi mata rumfa kamar zasu haɗiyeta tsabar yadda suke binta da mayataccen Kallo, Ta saki baki sai Labari take basu su kuwa sun Kasa kunne suna sauraron daddaɗar muryarta, Tunda suka kafe ta da idanunsu ko kyaftawa basa yi kamar zasu haɗiyeta. Gyaran Muryar da Taj yayi masu ne Yaja Hankulansu ga dubanshi, kamar sunga wani mugun abu, A gaggauce su kayi saurin barin Inda Take, kusan atare suka buga ƙafa Haɗi da sara mashi. Kallon Harara Ya watsa masu, Cikin harshen turanci Ya furta"wannan wani irin gangancine zaku bar Yarinya tana amfani da wuƙa? Kun wani tsareta da idanunku kamar zaku lashe ta" Sunnar dakai su kayi Suna faman sosa keya suka hada baki wurin furta"sorry Sir, ba laifin mu bane, Itace ta buƙaci damu koya mata girki, munyi kokarin Hanata amma saita sanya mana rigima" Wurga eye balls dinsa Yayi akan Unaisah dake Kallon shi, Har ta ajiye wuƙar hannunta, nufo shi tayi fuskarta da murmushin Yaƙe tace"ay ni nace su bani In tayasu aiki, Kuma dama Na iya ba yar koya bace" ta fada tana ruƙe qugunta da hannu. Wani kallo Ya jefa mata me kama da harara, bakomai Yake tunawa ba face lokacin da tana yar ƙaramarta, ranar daya tafi aiki yabarta a gida tana jin yunwa taje ta kunna cooker gass da sunan zata yi girki, wuta ta kama a gidan, wai yau itace take mashi kurin ta Iya girki ba yar koyo bace? Girgiza kai Yayi haɗi da yin murmushi tacikin face mask dinshi "Daughter, ƴan uwanki sunata nemanki, Yakamata Kizo Mu koma falo" maƙe mashi kafaɗa tayi"ay bamu gama girkin ba" "Bana son gaddama, zo ki wuce mu tafi" Marairaice mashi fuska tai"dan Allah kabarni wallahi inason In Iya girki kala kala," "Kada Ki damu, zansa a koya maki amma ba yanzu ba, dokar Aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, baki ga maza bane a kitchen din"? Cikin lallashi yayi mata maganar Yana nuna mata chefs din dake tsaitsaye cirko cirko suna kallon su "Yalla6ai, da dai anbarta ta koya tun da ta nuna tana so, kuma ni aganina maca ce ita, wata rana zataso tayi ma mijinta.... "Tunkafin chef din daya dauko Maganar Ya karasa boss Yayi mashi wani kallo mai nuni da kashedi, Hakan yasa shi yin saurin Katse maganar, Janyo hannun Unaisah Yayi dakarfi Ya fito da ita daga kitchen din, Chefs din basu ji dadin zuwan Shi ba, Ya raba su da Yarinyar data ɗe6e masu kewa yau, zuwanta Ya faranta masu rai, sunji dadin surutun da tadinga yi masu, komai nata burgesu Yake yi. Ranta Ya 6aci, Ganin yadda ya janyota daga kitchen din, da sauri ta fusge hannunta tana fadin"Ni ka ƙyale ni, in tafi da kaina" Ta faɗa tana daure mashi fuska, Sam Yakasa ce mata komai sai dai kallonta da yake yi. "Bansan meyasa ka takura rayuwata ba, girki fa kawai na roƙa kabarni In tayasu amma ka hanani, dan Allah menene alaƙata dakai ne? Na lura so kake kana Yin iko dani, Idan don saboda taimakon da kukayi mana ne ay dan Allah ku ka yi ko"? A fadace ta faɗa tana zare mashi gray eyes dinta tamkar zata rufe shi da bugu, Har saida Yaji gabanshi Yaɗan fadi, sauƙinta ma yasan halinta, "Meyasa ni kadai kake ma haka? "Saboda ke jini na ce" a zuciyarshi Ya furta maganar "Kiyi haƙuri Idan na 6ata maki rai, bana son 6acin ranki, Ƴan uwanki ne suke ta nemanki, bayan haka kamar yarda na fada maki dokar aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, waɗannan chefs din da kike gani dukansu a lokacin baya ba mutanan kirki bane, Dayawansu Ƴan shaye shaye ne da masu bin matan banza, wasun su mugayen ƴan ta'adda ne wadanda suka gagari Iyayensu da hukuma, Ire iren su chief Yake kamowa Ya koya masu hankali, Idan suka shiryu sai ya maida su Jami'an Isod..." Waro ido waje tayi jin Ya ambaci mugayen ƴan ta'adda. "Ba Zanso abun da zai cutar min dake ba, Haƙƙina ne kula da rayuwarki Unaisah dan Allah kada ki hanani Yin aikin lada... " in cool voice ya faɗa... Wani irin kallo yaga tana bin shi da shi, kamar akwai wani abu da take son ganowa Muryarta na rawa ta furta"dan Allah ka cire min face mask din fuskarka inason ganinka" Girgiza mata kai yayi"zaki ganni amma ba yanzu ba, amma meyasa kike son ganin fuskata"? "Saboda muryarka, tayi min kama da ta daddyna wallah sai nake ji kamar daddyna ne kai, duk da nasan ma ba shi bane, ina ji araina baya araye ma" idanunta har sun ciko da kwalla. "Kina ji aranki ni daddyn ki ne" ɗaga mashi kai tayi alamar eh" "Ki ƙaddara aranki cewa Ni ne" ya faɗa tare da ruƙo arm dinta, Ya janyota jikin shi, haɗi da kwantar mata da kanta saman kirjinsa, wani irin sanyine taji ya ratsa zuciyarta, lumshe idanunsa yai a hankali ya sanya hannu tare da zame face mask dinsa, Sumbatar head dinta yai, kafin da sauri ya maida mask din fuskarsa. Tsawon mintuna biyar cuf suna manne da juna, sai daga bisani ya raba ta da jikin shi, baiwar Allah jikinta yayi sanyi tamkar an watsa mata ruwan sanyi, Shafa gefen fuskarta yayi da tafin hannunsa"Ina sonki my daughter" murmushi tayi mashi"Nima ina sonka daddy na" *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *(Kaɗan daga cikin na sati mai zuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya, unaisah zatayi waya da Benazir😍 Garkuwa zaiyi tashin bazata, kada ku bari abaku labarin walimar hateem😂🤣 Ni kaina zumuɗin ta nake yi🔥🔥🔥)* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 9 Complete by Novels Elite Admin May 24, 2024 Sponsored Link _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القدر💋✊🔥 ~Takun Ƙarshe🔥~ قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Har Ya ruƙo hannunta za su shiga ciki sai kuma Ya dakata yana faɗin "Au namanta, Auntyn ku ummi tana buƙatar abinci ban sani ba, ko akwai abunda chefs suka gama girkawa yanzu"? ya tambaya yana duban ta. "Akwai naga sun kammala Rice and chicken stew tare da coleslaw hada zobo ma ... " kafin ta ƙarasa lissafa mashi yace"Okey, Ki jira ni, bari na shiga ciki in kar6o mata" amsa mashi tayi da toh. Bayan shigarsa kitchen din ta soma tunanin ko awani hali Garkuwarsu ya ke a ciki? ta yi matuƙar damuwa da shi, ganin shi da take yi a mawuyacin hali ba karamin karya mata zuciya ya ke yi ba, rabon da ta sanyashi a idanunta tun da asuba da su ka shiga yi mashi addu'a, da tunanin shi ta wuni ta bari sai da anjima ta shiga duba shi. "My babe, I'm back" Muryar Boss man ce ta fargar da ita, da sauri takai dubanta gare shi, Hannayen shi ruƙe da handle din wooden tray mai faɗi, daga saman shi haɗaɗdun warmers ne babba da ƙarama tare da plates da sauran tarkacen kayan abinci" Miƙa mata yayi kar6i nan, ta sanya hannu ta kar6a cikin kitchen din Ya koma jim kaɗan Ya dawo hannayen shi ruƙe da wani madaidaicin faranti mai ɗauke da mixed drinks masu sanyi. Ganin tana kallon shi yasa shi kashe mata ido ɗaya, murmushi tasakar mashi, a tare suka jera zuwa cikin falon. Jikin Batool Har Kerma Yake Yi wurin mikewa da wani irin sauri ta nufi Unaisah zata rungumeta, ganin Tray a hannunta yasa ta dakata tana faman ɗaure mata fuska tace"Ina kika shiga inata nemanki" "Ina a kitchen fa, Girki Na tsaya taya masu aiki" ta faɗa tare da wucewa ta sauke tray din hannunta saman Carpet, Parveen tun da tayi tozali da Abinci takasa samun sukuni, Tafi kowa zalama. A Plate Batool ta zuba ma Ummi abincin ta hada mata da pineapple juice ta miƙa mata, fuskarta da fara'a ta kar6a tana fadin nagode My babe," a tsanake ta soma Ci. Ɗaya bayan ɗaya unaisah ta soma kasa masu abincin tana miƙa masu a plate, bayan ta gama da su itama ta zuba nata tare da Boss man a plate ɗaya, suka zauna suna ci gwanin ban sha'awa, falon Yayi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke ci... "Ummi Ina son Yin magana dake bayan sallar magrib" Boss ne yayi mata maganar, amsa mashi tayi da toh. "Amma wannan ɗin abincin daren mu ne"? Acewar Parveen, Harararta Naufal Yayi. "Kusan ƙarfe shida na marece, A haka Har kike tambaya, toh abincin dare ne, mu da cin wani abincin sai gobe da safe in Allah yakaimu" javed ne Ya bata amsa Yayin da yake kur6ar lemu me sanyi. "Ba'a magana idan Ana cin abinci," Boss ne ya faɗa yana duban su. "Dariya fa da murmushi suma ba'ayi"? Jemimah ce ta jefa mashi tambayar yayin da take cunkusa abinci abaki tana tauna. Dariya suka sanya gaba ɗayansu cikin raha. "sajeed Ina wayata" Dafe kai Yai da hannu ɗaya"Am sorry sister, Na cinye maki chargy, bansan ko kina da charger ba" "Akwai charger bani wayar" da sauri ta miƙe taje gaban sofa din da yake a zaune, Wayar Ya zaro daga trouser pocket nasa ya miƙa mata ita. Tasa hannu ta kar6a, kafin ta nufi bedroom dinsu, shigarta keda wuya wayar hannunta ta soma ringing, tana kokarin ɗaga Wayar ta kashe kanta kamar tayi hauka saboda ta gane number da suka kirane ita da sajeed.' Cikin takun sauri ta nufi backpack din su, ta buɗe ta dauko cazar wayar ta jona a socket, akan idonta wayar tayi haske alamar ya ɗauka, lumshe idanunta tayi tare da jingina bayanta jikin gadon, zuciyarta a cike fal da tunanin shi. *💋NAZLI👑* Sautin daddaɗan kiɗa ne da ke tashi a katafaren gym room (ɗakin motsa jiki) da ke a gidan prime minister, an ƙawata shi da manyan injinan motsa jiki, a tsaye take saman thread mill tana gudu cikin shiga ta kayan motsa jiki, sport bra tare da short launin black colour, sunyi bala'in yi mata kyau, sun bayyana farar fatarta sol ko kwarzane babu, tamkar bata ta6a yin rarrafe ba arayuwarta saboda hasken fatarta harta gwiwar ƙafarta tayi jawur da ita, dirar mace doguwa ga kyan sura, ta ɗaure lallausar baƙar sumar kanta sai salƙi take yi da sheƙi ta sauko har saitin waist din ta, gaba ɗaya ta tattara nutsuwarta akan abun da take yi, sautin music din ba ƙaramin ni'ima yake samar mata ba, kyawawan idanunta na akan tanƙameman madubin dake manne da bango, zufa ce ta soma tsastsafo mata ta ko'ina ta jiƙe sharkaf da ita, babu alamun gajiya atattare da ita, daga gani ta ƙware a 6angaren gym. Bakomai ne acikin zuciyarta ba, face zallar begensa, duk yadda taso ta hana kanta tunawa da shi abun yaci tura, tayi tunanin zata iya sarrafa zuciyarta wurin hana ta tunaninsa sai dai abun yaci tura, a kowani daƙiƙa son shi ƙara ninkuwa yake yi a zuciyarta, ga dukkan alamu Nazli batasan menene So ba, ko da yake girman kai da izza sun hana ta gane cutarwar da take yima kanta, shiyasa ta kasa miƙa wuya" Tunanin shi ne ya haifar mata da jin Kasala, ba arziƙi ta dakata da motsa jikin, ta kai hannu ta ɗauki short towel fari ƙal ta soma tsane jikin ta da shi, bayan ta kammala fitowa tayi daga gym room din ta nufi bedroom dinta, kai tsaye ta shiga bathroom domin yin wanka. Shigowa ɗakin Yazrin tayi cikin shiga ta riga da wando black and white, tayi rolling veil akanta, hannunta ruƙe da wayarta. Ganin babu ita a dakin yasa tayi tsammanin ko ta fita ne har zata juya ta juyo motsin ta a toilet da sauri ta la6e a bayan labule. Gently ta zuro ƙafafunta dake sanye cikin slippers, bathrobe ce a jikinta fara ƙyal, hannunta ɗaya ruƙe da towel sai faman tsane sumar kanta take yi. Yazrin dake a la6e bayan labule, wayarta ta danna ta shiga camera ta ɗage labulen a hankali ta soma ɗaukar Nazli video batare da sanin ta ba. Dressing mirror ta nufa cikin takun qasaita, wasu tsadaddun mayukan gyaran jiki ne asaman mirror din, bayan ta zauna ta soma bin ko'ina tana shafe shi a tsanake, kafin ta dauko bakhhoor burner ( turaren wuta) ta soma turara jikinta da sumar kanta, komai nata cikin aji take yin shi, Nazli macece mai tsafta ga son gayu, kuma ma'abociya son ƙamshi. Duk wani motsinta, Yazrin na kallonta ta cikin camera, bayan ta gama gyaran jikin nata, closet ta nufa jim kaɗan ta fito, har ta canza kayan jikin ta zuwa kimono robe, yazrin da ke ta daukar ta video kayataccen murmushi ne kan face dinta, aranta ta ayyana ukhty Nazli badai iya gayu ba, bata gama zancen zucin nata ba, taga Nazli ta haye saman Royal bed dinta hannun ta ruƙe da wayarta, bakomai take kallo ba face hotonsa, har zooming dinshi take yi da zira ziran yatsun hannunta, hoton da take kallo tsohuwar ajiyace a kalla yakai shekara biyar, lokacin yakai masu ziraya a canada, ba tare da sanin shi ba ta dauki hotan, dama duk in yaje basa jituwa da Nazli, har ya bar ƙasar basa sakarma juna fuska kai kace makiyane, Yazrin ce kadai suke mutunci da juna, kuma a lokacin suna matuƙar ƙaunar junansu, amma izza ta hanasu bama juna kulawa sai dai su yi magana ta text message, tamkar basa a gida ɗaya. fita tai daga gallery ta shiga wurin messages dinsu Har ta rubuta "I miss u.... ' sai kuma ta goge, zuciyarta na raya mata zubda aji ne ta nuna ta damu dashi, shi ne yakamata yafara yi mata magana Jefar da wayar tayi gefenta, tare da kai hannu taja lallausan duvet dinta ta lullu6e fuskanta, ganin hakan yasa Yazrin fitowa daga bayan labulen cikin sanɗa ta nufi gadon, tare da hayewa ta janyo wayar Nazli cike da fargaba cikin sa'a ta ɗauko ta batare da security din wayar ya shiga ba, hakan ba karamin dadi yayi mata ba. Whatsapp dinta taso ta shiga sai dai kash password Ya hanata, tunani ta soma yi me Nazli ta rubuta a matsayin password dinta? Gudun kada ta tayi mistake ta samu matsal Zurfi tunani ta shiga, can zuciyarta ta raya mata cewar ta jaraba rubuta date of birth din Aki Owais saboda ta ta6a ganin ta rubuta shi a diary din ta amatsayin rana mafi mahimmanci agare ta. Wani irin tsalle ta daka ganin Ya buɗe, da sauri ta shiga nutsuwarta tana leƙen Nazli, wadda tuni bacci yayi awon gaba da ita Yazrin tayi mamakin ganin tsawon lokacin da suka dauka ba suyi magana wa junansu ba, Ranta ya sosu bata ji daɗi ba, ji take kamar ta dauki pillow ta bubbuga mata akanta tsabar haushin da taji. "Ƴar bakin ciki, In sha Allah baki da miji a duniyar nan daya wuce big bro, bazan zauna na zuba maki ido kina cutar kanki ba, Akhi Owais shi ya dace ya mallake ki, nayi maki sha'awar auran shi saboda samun miji nagari irin shi ba abu ne mai sauƙi ba, Ina son kiyi rayuwar farin ciki yar uwata, dole na shirya tsakaninku.... " acikin zuciyarta ta furta maganar tare da cigaba da danna wayar, daga wayarta ta tura video din data dauka, kaitsaye ta yi mashi sending, shaf shaf ta rubuta mashi text message da harshen turanci kamar haka _Nayi kewarka bugun zuciyata, ina mai baka haƙurin nuna halin ko'in kula da nayi, ba'asan raina ba, nayi danasanin hakan don ba ƙaramin cutuwa nake yi ba na rashin jin ɗumin jikinka a kusa dani, ka duba whatsapp in ka, na tura maka video dina don ya ɗebe maka kewar rashi na, nasan zaka ji dadin kallon shi_ fuskar yazrin dauke da murmushin mugunta ta tura mashi message din, bayan ta gama ta ajiye mata wayarta, ta nufi kofar fita daga dakin tana faman sakin dariya, ta riga da tasan me zai biyo baya muddin Nazli taga aika aikan da tayi mata ba ƙaramin husuma zata tada ba, zata ce ta zubda mata aji awurin chief owais. *A GIDAN UNCLE ƊAN IYA* Kusan Atare Su ka yi Parking din motocin su, Mahboob ne Ya fara fitowa daga front seat hannun shi ɗaya ruƙe da key din Motarshi, fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Motar zahra. "Sannu da dawowa Hajiya Zahra Surukar Kaka Obinna" Ya faɗa tare da buɗe Back Seat din Motar Shi Ya duƙar da kai Yana leƙan Baby Junaid dake zaune Hannayenshi rungume da Food basket dinshi, Ga school bag din shi a gefe, Sai faman ɗaure fuska Yake, Da alama rigimar tashi ce ta motsa. "Ranka Shi daɗe, Mun ƙaraso gidan, zaka iya takawa da kafarka ne mu shiga ciki ko kuwa ni kake so In goyaka"? Da zolaya mahboob yayi maganar yana dariya. Yamutsa mashi fuska baby junaid yayi "ni ka goyani" Ya fada A kule. Juya mashi baya Mahboob Yayi Ya ɗan zuƙunna Baby Junaid Ya Haye bayan nashi, Bayan Ya miƙe Ya ɗauko mashi Backpack dinsa tare da kwandonsa Adai dai Lokacin Zahra Ta fito daga motarta, tayi shiga cikin Lafaya, Hannunta ɗaya ruƙe da Ƴar purse dinta Fuskarta da fara'a take duban Baby Junaid Da Mahboob "yau wata rana mun dawo gida atare, baby junaid dina zo nan" ta faɗa tare da miƙa mashi hannu, babu musu Ya soma kiciniyar saukowa daga saman bayan mahboob, daukarshi tayi Mahboob yace"Wato ni kake gudu? Zamu hadune ɗan rainin wayau, tun da naje dauko shi Daga school Yake ta jin haushina saboda naje amakare shi kaɗai Ya rage ba'aje daukarsa ba, baisan nima bada son raina ba, Motarce ta samu matasala sai da nakaita gyara tukunna naje daukoshi da ita" Dariya zahra tayi"Gaskiya baka kyauta ba, taya zaka bar mana Baby Shi kadai Ga yunwa, meyasa baka kirani awaya naje daukosa ba" "Banyi dabarar yin Hakan ba, Yanzu dai tun da mun dawo gida, gashi nan ki kaima jatumarsa, nagaji da kallon kumburarran fuskarshi" "Mahboob baka da mutunci, zamu rama ne" ta faɗa tana dariya, baby junaid kuwa Ya ɗaure fuska, Kumatunshi sunyi jawur da su, da alama kuka Yake so yayi. Atare suka nufi cikin gidan, tana agaba mahboob Yana abayanta Bayan shigarsu Falo, Suka taras da mami da Ummi zaune suna kallo a plasma tv din falo, Cikin girmamawa suka gaishe da su. "Sannun ku da dawowa, Ya gajiyar aiki"? Cikin Kulawa mami tayi maganar, atare suka hada baki wurin cewa"yawwa mami" Ummi dake kallon Baby junaid tace"to fa, Me akayi masa ne naga yana ɗaure fuska" Mahboob Na dariya Yace"wallahi Ummi Rigimarshi ce ta motsa, Kinsan Halin shi. Zahra tace"bawani nan, shine Yaƙi zuwa ɗaukarshi da wuri, Yabar shi a school yana ta jira" "Gaskiya mahboob Baka kyauta mana ba, saboda Allah, Haka akeyi? Sai kabar mana Yaro ga Yunwa" Ummi ce ta faɗa tana satar kallon baby junaid duk don ta nuna mashi taji Haushi. "Ay mashi uziri mana, hakanan dai Mahboob bazaiƙi zuwa ɗaukar baby junaid ba sai dai idan wani uzirinne Ya ruƙe shi" mami na fadan hakan Mahboob Yace"ay har bayani nayi ma zahran, motana ne Ya samu matsala sai da nakaita gyara, in sha Allah Hakan ma bazata ƙara faruwa ba zan dinga zuwa ina dauko shi akan lokaci" Ummi tace"haka Yakamata" "Zonan babyn mommynsa" acewar Ummi ta fada tana miƙa mashi hannu, maƙe mata kafaɗa yayi alamar bazaije ba, Saima Ya ƙara ƙanƙame Zahra, mami na dariya tace"In banda abunki sai kace bakisan halinsa ba idan Yana fushi Yafi buƙatar jin ɗumin mommynsa," "Ina auntyn tawa take"? "Tana a kitchen" Maimaita kalmar kitchen Zahra tayi, aranta ta furta me kuma Aunty Aneelerh take yi a kicin"? Batayi Ƙasa a gwiwa ba, Ta nufi kitchen din Mahboob Har Ya zauna kan sofa, sai kuma Ya miƙe Yabi bayan zahra. Tunkafin su ƙarasa kitchen din suka hango Aneelerh ta haɗa uban gumi a kitchen tana girki, Ita kadai. Sam bata Ji alamar shigowarsu ba, ta zage damtse sai motsa miya take Yi "Aunty Aneelerh"? atare suka haɗa baki wurin kiran sunanta, da sauri Ta rufe soup pot din, Ta juyo tana fuskantarsu, kafin ta ɗaura idanunta akan Baby Junaid, Murmushi ta sakar masu "Sannunku da dawowa," "Yawww, Auntyna, Yau ke kike Aiki akitchen Ina Ana"? Zahra ce ta jefa mata tambayar, Mahboob Yace"Allah yasa dai lafiya" Girgiza kai tayi cikin sanyin murya ta soma magana"ba lafiya...." gaba ɗaya ta labarta masu abunda Ya faru zuwansu dakin Ana tare da su mami, Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yayi ba, Musamman Mahboob. "Bansan Ya zanyi ba, Taƙi faɗa mana abun da ke damunta, Ni tsorona kada wani abu Ya faru da ita" fuskarta da tsantsar damuwa ta furta maganar "Nima hankalin bai kwanta da ita ba, dafarko nayi tsammanin Damuwar halin da ƴan uwanta suke aciki ne ke damunta, ashe ba haka bane, daga gareta ne" Acewar Mahboob. Kafin Zahra ta furta magana baby Junaid Ya fashe da kuka, Dama ranshi a6ace Yake, da sauri Aneelerh Ta miƙa hannu ta kar6e shi cikin sigar lallashi take jijjiga shi tana fadin"Am sorry My baby boy, kayi hakuri nasan nice na 6ata maka rai,' muryarshi da shessheƙar kuka Yace"wayyo Allah mommy, Kuna ta surutu Kin ƙi kulani, baki missing ɗina ba" dariya zahra da mahboob su ka yi, hakan Ba ƙaramin 6ata mashi rai yai ba, Hada Jifar Su da harara Shafa sumar kanshi tayi"Na kar6i laifina, ay min afwa... " zumbura mata baki yayi, Zahra tace"aunty Aneelerh, Ki tafi dashi ɗaki Ni zan ƙarasa girkin, Inyaso da anjima Sai mu ƙarasa tattaunawa" "Keda kika dawo daga aiki a gajiye kuma kike neman in bar maki girki, a'a gaskiya Ki bari na ƙarasa ai ba ni kadai nake yi ba, Tare da Ummi muke Yi, bata jima da komawa falo ba.. " Kafin Ta ƙare maganar, Mahboob Yace"tun da tace zatayi kibar mata kawai, Nima saina tayata, baby junaid yana buƙatar kulawarki, Kije Ki lallashe shi" Murmushi tasaki Tana kallonsu, Har cikin ranta take jin tsantsar kaunar Yan uwanta, Haɗin kansu Na burgeta, fatanta Allah Ya dawwamar da farin ciki arayuwarsu, Hakika suna kyautata mata. "Nagode, zahra, Mahboob, Allah Ya barmu mun ku," Amsa mata su ka yi da ameen "Zan shiga ciki, pls zahra Ki dafa mashi indomie" amsa mata tayi da toh, Bayan fitar Aneeleeh daga kitchen din, Mahboob Ya ajiye food basket din Junaid, Yabi bayan aneelerh hannun shi ruke da backpack din Baby junaid, Bayan Ya ajiye mashi adaki, Ya fito Ya nufi nashi room din, shaf shaf Yayi wanka Ya sanya gajeran wando da ƴar singlet, Kafin Ya nufi kitchen don Ya taya zahra girki kamar wani mace, atare suka cigaba da kula da girkin, suna tattauna fira dangane da matsalar Ana. "Amma kai a tunaninka meke damunta"? "Sister Ni kaina nakasa gane wani tunani zanyi dangane da matsalar Ana, sai dai kawai mubita da addu'a, Allah ya yaye mata abunda ke damunta,' "Ni aganina, Mu kar6i Contact din Ƴan uwanta , mu tuntu6esu may be sunsan meke damunta, tunda sunfi kusa da ita" "Nima nayi tunanin hakan, Yanzu dai mu jira, zuwa lokacin da su Abie zasu dawo gidan, nasan zasu Kirata su tambayeta," "Hmm kana ganin zata Iya faɗa masu gaskiya? Bayan Aunty Aneeleeh tace tare da su mamie suka je dakin nata amma taƙi fada masu, ai ni aganina idanma akwai wanda Ya dace ta fadamawa baiwuci su mami dinba" Jinjina kai Mahboob Yayi"kin fadi gaskiya," "Ni abunma Ya fara bani tsoro, da naji aunty aneeleeh tace Ana ta dinga kwala masu ihu tana fadin su fita subar mata dakinta, Anya mahboob bata da matsalar kwalwa? Mahboob Yace"Bana tunanin hakan, wata'kil Aljanune suka shige ta, mu cigaba da tayata addu'a Allah Ya kawo mata saukin abunda ke damunta" "In sha Allah zamuyi mata" Daga haka basu ƙara magana ba, sun maida hankali akan Girkin da suke Yi. Fitowa Aneelerh tayi daga Bathroom, Bayanta goye da baby junaid, tayi mashi wanka, sai faman hade mata fuska Yake Yi, Riga da wando ta Dauko ta zura mashi ajikinshi, ta feshe shi da turare, zama tayi gefen gadonta,ta ɗaura shi saman laps dinta, hannunta ɗaya dafe ta shi,tarasa meke yi mata daɗi, Ita dai Hankalinta bai kwanta da halin da Ana take aciki ba, Ji take aranta kamar wani abunne Zai faru, zuciyarta batayi mata daɗi, sam ta manta da baby junaid Tayi zurfi a tunaninta, Har Ya fara lumshe ido zaiyi bacci, Muryar Zahra ta fargar da su, hannunta biyu ruƙe da plate din indomie, Sai tiriri Take Yi, daga saman indomie din ta shimfiɗa mashi Soyayyan kwai, Mahboob Yana abiye da bayanta, Hannun shi ruƙe da mugs biyu na kakkauran Tea. "Sannunku da kokari, nasanya ku aiki ko hutawa ba ku yi ba" "Pls ki daina fadin hakan, Mu yakamata mu Yi maki sannu, anbarki da girki a kitchen, Su mami suna a falo fira tai dadi" Mahboob Ne yai maganar Asaman Table zahra ta daura plate din, Mahboob Ma ya sauke nashi mugs din, atare suka fuce daga dakin. Baby junaid tunda yayi tozali da indomi Ya soma sakin murmushin murna, Har wani lashe le6ensa Yake Yi "Mommy da zafi, kuma ni Yunwa nake ji Allah" ashagwa6e Yayi maganar "calm down Your Mind my baby boy, Ni zan baka da hannuna, kasan dai mommy bazata bar baby junaid dinta Yaji zafi ba ko"? Ɗaga mata kai yai alamar" "Yawwa my boy" ta faɗa tare dakai hannu ta dauki fork, ta soma nannaɗo taliyar tana hura mashi da baki idan ta huce saita tura mashi abaki, kusan atare suka cinye indomie din dakwai, Kafin suka sha tea din su. "Kada kayi bacci, Yanzu za'a fara kiran sallar magrib," ɗaga mata kai yai alamar toh, Janshi ta soma yi da fira duk dan kada yayi bacci. Bayan Kammala sallar Magbrib, A lokacin Abie da Uncle ɗan Iya sun shigo gidan, babu wanda Ya tuntu6esu da maganar Ana, sun bari ne sai sun huce gajiyar da suka kwaso ,Har saida suka kammala cin abincinsu, Tukunna Ummi ta sanar da su Halin da ake ciki, babu 6ata lokaci, Abie Yasa suka hallara A falon gidan gaba ɗayansu, Ana ce kaɗai ke babu acikin su. Aneelerh da zahra da Mahboob suna zazzaune kan Carpet, A lokacin baby junaid Ya jima da yin bacci, Yana can kwance saman gado. Abie da Uncle ɗan Iya suna a zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Abie Yana sanye da farar jallabiya ya manna farin glass a idanunsa, Yayin da Uncle ɗan Iya yake asanye da Riga Yar shara ta farin Yadi, daga ciki ya sanya gajeran wando baƙi. Su Mamie da Ummi suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun biyu, dukansu Hijabai ne a jikin su. tamkar mutuwa ta gifta babu mai magana acikinsu, Har na tsawon mintuna kafin daga bisani Uncle ɗan Iya yayi masu gyaran murya, suka ɗago suna duban shi, da hannu Ya nuna Mahboob "Je ka kira ta" Amsawa mahboob Yayi da toh, ya miƙe ya nufi bedroom din Ana, abakin ƙofar Ya tsaya tare da kai hannu yayi knocking kofar kusan sau uku bata buɗe ba, Har ya fara tunanin ko bacci tayi ne sai kuma Yajiyo mutsu mutsunta ta cikin ɗakin. A hankali ta turo ƙofar ɗakin, tare da leƙo da kanta, Ko da mahboob yai tozali da fuskarta sai da gabanshi ya faɗi ganin yadda ta kumbura suntum, idanuwanta sun kaɗa jawur, daga gani kukan take cikin yi In a calm voice Ya furta"ina fata ban katse maki baccin ki ba" Muryarta adisashe tace"ban kaiga Yin baccin ba," Jinjina kai yayi"Uncle ne yace in kira ki, su na a falo shi da su mamie da abie" Shiru tayi jimmm kamar bazata motsa ba, har saida ya maimaita mata maganar tukunna tace Toh, ka jirani mu tafi atare" "Okey" Maida ƙofa tayi ta rufe ta, badajimawa ba sai gata ta fito sanye da doguwar riga, ta yafa mayafi akanta, Jin ta ruƙo hannun shi acikin nata ne yasa shi saurin kallonta, sam hankalinta ba akwance Yake ba, bai yi yunƙurin raba hannun shi daga nata ba, A haka suka nufi falon, sai da suka kusa isa yayi saurin zame hannun shi daga nata, Takun tafiyarsu ne Yaja hankalinsu mami ga dubansu Cikin girmamawa Ana ta gaishe da su, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana faman jan numfashi, bayan mahboob Ya zauna. Abie dake kallon Ana Ya soma Magana a tsanake "Inaso ki natsu ki saurare ni," jinjina mashi kai tai alamar toh "Ki ɗauka tamkar mahaifanki ne suke yi maki magana, kada ki ji shakkun faɗa mana abun da ke damunki, saboda mu kaɗai ne makusantanki a yanzu, Haƙƙinmu ne mu kula da rayuwarki, Idan wani abu ya same ki ba zamu ji daɗi ba" wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, haƙiƙa kalaman abie sun yi tasiri a zuciyarta. Uncle ɗan Iya ya ɗaura da cewa"banji daɗin abun da Ummi ta fada min ba, baki kyauta mana ba, ashe baki ɗauke mu yarda muka ɗauke ki ba, meyasa zaki zauna abu na damunki ki gaza gaya ma kowa? Meye amfanin 6oye mana eye"? Muryarshi da faɗa yake yi mata magana, alamar ranshi ya 6aci. Sunnar dakai ƙasa Ana tayi yayin da idanunta ke akan Yatsun hannayenta "Meke damun ki ne, inaso ki faɗi mini gaskiya"? Ya jefa mata tambayar, Su Aneelerh da su mami sun natsu suna kallon ta. Numfashi taja tare da sauke shi A hankali ta furta"Idan na 6ata maku rai, dan Allah ku yafe ni, Aunty Aneelerh, mami, ummi, Zahra, Mahboob, abie, uncle, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku, duk da kasancewata yar aiki agidan nan, Sannan ba musulma ba amma kun daukeni tamkar jinin ku, ko dan saboda nuna damuwar da ku ka yi akaina zan fada maku gaskiyar abun da ke damuna...." ta faɗa tana mai ƙanƙan da kanta, gaba ɗaya duk sun ƙagara da suji meke damunta, musamman Mahboob Ya kasa ɗauke idanunsa daga kan fuskarta, wani irin tsantsar sonta da ƙaunarta yake ji, ga matsanancin tausayinta dake addabar zuciyarsa. "Cikin kwanakin nan, Ina yawan yin mugayen mafarkai, waɗanda suke neman haukata ni, bansan meyasa hakan yake faruwa dani ba, idanuwana suna gane min abunda yafi ƙarfin gani na wanda silar hakan yasa nafara zaucewa, ni gani nake ma kamar mutuwa zanyi..... " muryarta na rawa ta ƙare maganar nan take ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, Jikin kowannansu yayi sanyi "Kiyi shiru, Kukan Ya isa haka, Ki faɗa mana me kike gani a cikin mafarkin naki"! Uncle ɗan Iya ne yai maganar Cikin shessheƙar kuka tace"wallahi duk yadda zanyi maku bayani ba lallai ku fahimce ni ba, ni kaɗai nasan halin da nake aciki, ni kaɗai nasan bala'en da nake gani, Ba tun yanzu ba, tun ina ƙaramata idan nayi mafarki mummuna yana zama dagaske, hatta rasuwar iyayenmu saida nafara yin mafarkin zasu yi hatsarin mota, sai gashi ya tabbata, uncle ɗina ma ni nayi mafarkin mutuwarsa kuma ya tabbata, da wuya inyi mafarki mummuna bai zamto gaske ba, ni damuwata mutanan da nake a tare da su bana son wani abu ya sami wani daga cikin ku...." tashin hankalin da ba'a saka mashi date, A matuƙar ruɗe Zahra take kallon Aneeleerh, Ummi ta kalli Mamie, Idanuwansu azare, mahboob kuwa kusan suman zaune yayi. Shiru tayi Tana faman yin shessheƙar kuka, Abie dake kallonta, nazarin maganarta yakeyi, yaso ace musulmace ita, kodan ya bata shawarar ta runƙa yawaita yin azhkar, da sauran addu'o'in neman tsari. Tsawon lokaci falon yayi tsit, babu mai magana acikinsu, sai kallon kallo da suke jefawa junansu. Muryar Uncle ɗan Iya ce ta katse Shirun nasu "Ki daina sanya damuwa aranki, Mafarki ba gaskiya bane, shaidan ne yake assasashi, Ki yawaita yin addu'a, muma kuma zamu tayaki, Allah shi yake tsare bawansa, in sha Allah babu abun da zai same ki, damu kanmu," Ajiyar zuciya ta sauke, Cikin sanyin murya tace"in sha Allah uncle, zanyi hakan" "Aneelerh, Idan zata kwanta bacci ki rakata dakinta, Ki yi mata addu'a," Ya fada yana duban Aneeleerh, Cikin girmamawa Ta amsa mashi da toh, Kwantar mata da hankali suka cigaba dayi, Kowa sai da ya sanya bakin shi wurin Lallashinta da bata baki, Har saida suka tabbatar Ta samu saukin damuwarta tukunna mamie tace"daga yau kada ki sake ware kanki a daki! Kina jina ko"? Daga mata kai tayi toh "Kidaina kuntata kanki adaki, ki dinga fitowa waje wurin su Aneelerh Kuna yin fira, hakan zai ɗebe maki kewa don na fahimci hada kaɗaici ke damun ki" jinjina kai ana tayi alamar toh. Gyaran murya abie yai tare da cewa"Idan kina buƙatar wani abu, Ki fadama Aneelerh ko zahra, su sanar dani in sha Allah zamuyi maki shi, kada kiji komai ki dauka tamkar Iyayenki ne" wannan maganar da abie Ya furta mata ba karamin ta6a zuciyarta yayi ba, nan take ta fashe masu da kuka mai tsuma zuciya, sautin muryarta dakyar yake fita wurin yi masu godiya. "Ku tashi ku rakata daki ta kwanta ta huta" Ummi ce tayi maganar tana nuna su zahra, ruƙo hannun Ana Aneeleerh tayi atare suka miƙe, Zahra tabi bayansu, Har cikin dakinta suka kaita, Bayan ta kwanta Aneelerh da zahra sukayi mata addu'o'i, Kafin daga bisani suka yi mata sallama, Kamar karsu barota haka suke ji, bayan sun fito daga dakin sun kulle mata kofar, zahra ta kalli Aneelerh "Nifa tsoro yakamani aunty na, tun da naji Ana tace mafarkinta yana zama gaskiya, wallahi bana so wani abu ya samu ɗaya daga cikin mu" Ita kanta Aneelerh hankalinta ba akwance yake ba, zuciyarta taki Aminta da kalaman ana, sai dai tayi kokarin danne damuwarta wurin kwantar ma zara da hankalin ta "Zahra kin riga kin sani, mafarki ba gaskiya bane, Ni ko kadan hankalina bai tashi ba, kema kuma inaso ki kwantar da hankalinki, In sha Allah babu abun zai faru, face alkhairi" Cikin sanyin murya zahra tace"Allah Yasa" Ta fada a yayin da suke shiga falon, komawa sukayi saman carpet suka zauna kowa zuciyarsa da fargaban maganar Ana. Idan muka koma 6angaren su Ummin america tun bayan kammala sallar magbrib, tayi wanka ta shirya cikin Baƙar jallabiya, tayi rolling veil akanta, ta bi ko'ina na jikinta ta feshe da turare, bakomai take jira ba face kiran Boss man, tun da ya fada mata yana son magana da ita gaba daya ta rasa sukuni ta kosa taji me ya ke son faɗa mata, tana cikin yin safa da marwa a room dinta, wayarta tayi ringing a hazarce tayi picking call din, muryar boss ce ta isar mata da sakon ta same shi a down, jiki na rawa ta fito daga dakin ta sauko down stairs babu kowa a falon, duk suna a dakunansu A falo ta same shi tsaye cikin shiga ta jallabiya, ya goya hannayensa akan kirjinsa, fuskarsa a sanye da face mask. Da fara'a ta nufe shi batare da 6ata lokaci ba, suka jera a tare suka nufi swimming area din gidan, ko'ina ka kalla hasken fitilun lantarki ne tamkar da rana. "ina sauraron ka Yalla6ai, tun da muka fito kayi shiru baka ce komai ba" ummi ce ta fada tana kallon Taj dake a gefenta. "ga dukkan alamu Kin ƙagara da kiji dalilin kiran da nayi maki" Jinjina mashi kai tayi alamar Eh, A yayin da suke zama saman kujerun dake a bakin pool din masu kyan gaske, suna fuskantar Junansu. "Nasan zakiyi mamaki idan nace maki chief ne Ya bada Sako A fada maki" A ruɗe tayi mashi farfari da idanunta cikin kagara ta furta"A message from the chief for me? Does he know about me? So what did he say? Calmly Boss Ya furta"Yeah Yasan da zaman ki fiye da tunaninki, chief da kike gani baya zama wuri ɗaya da mutumin da baisan tarihin rayuwarsa ba," Wani irin bugu kirjinta yayi mata cike da fargaba ta furta. "I don't understand what you mean! Chief ya san komai dangane da rayuwana! How is that possible?" Dariya boss yayi ganin yadda ta shiga ruɗani "Ki kwantar da hankalin ki Ummi, Amsarki tana atare dani, ki natsu ki saurari me zan fada maki" fuskarta a yamutse ta amsa mashi da toh. Numfasawa yayi kafin Yaci gaba da fadin"sakon da chief Yace A fada maki shi ne, Gobe Idan Allah ya kaimu, zamu fita tare da Yaran nan zuwa cikin estate din su, muna so su halarci Farewell dinner din Uncle ɗinsa Hateem, amma fa bama so kowa yasan da wannan zancen! Zuwan bazata zamuyi tare da su, ke kuma abun da muke so daga gare ki, ki yi kokarin shirya mana su.... " kafin Ya kare Maganar tace"wai kana nufin prime minister Hateem na canada ne za'ayiwa dinner din? ɗaga mata gira yai alamar eh, but amma meyasa naji kace zuwan bazata za'ayi da yaran"? Ta faɗa tana mai neman ƙarin bayani. Bai 6oye mata komai ba, dangane da budurin da aka sha lokacin da Danish ya rikiɗa, naƙin amincewa da zaman su a family din" Jikinta yai sanyi"Allah sarki, ashe abun da ya faru kenan, ko da yake dama zaiyi wuya su yarda da su, ni kaina lokacin daya rikiɗa ba ƙaramin firgita nayi ba, saboda abu ne da ban ta6a gani ba, toh su kansu abun da zai sa su ƙi yarda da zamansu kenan, bayan haka hukuncin da shi baba obie ya yanke na raba alaƙar prime minister hateem da danish yayi dai dai, a fahimta na yayi hakan saboda gudun kada ɗansa ya cutu.... " jinjina kai taj yai alamar gamsuwa da bayanin ta, kafin wani ya qara magana a cikin su, sai ga jami'in isod Ya fito daga ƙofar falo, hannun shi ruƙe da plate mai ɗauke da mugs biyu na coffee, akan table din dake a tsakatsakiyarsu ya ajiye plate din kafin yabar wurin Tura mata mug ɗaya taj yayi"kisha, ni nasa a kawo mana dan muji dadin tattaunawa' murmushi tayi har cikin ranta taji dadin karamcinsa, A hankali ta ɗauki mug din ta soma kur6ar coffee din, shima ya dauki nasa yana sha, bayan ta tsagaita da sha ne taci gaba da magana "kowani bawa da irin tashi jarabtar, Idan kaji na wani kai naka ba komai ba, shiyasa a koda yaushe akeson bawa ya zamanto mai hakuri dakai zuciya nesa, haƙiƙa ina tausayin wadannan bayin Allah, duk da ban kaiga jin tarihin rayuwarsu ba... ' murmushi taj ya ɗanyi tare da cewa"kada ki damu, nan badajimawa ba zaki ji tarihin rayuwarsu, In sha Allah" Gyaɗa kai tayi "A ina za'ayi dinner din sannan ƙarfe nawa ne zasu je can din"? "A cikin Estate din nan, Bayan sallar la'asar" Shiru tayi alamar tana nazarin wani abu, yayin da yake binta da kallo. "Menene dress code din da za'a sanya a wurin dinner din"? ta tambaya tana kallon fuskarsa. "abaya matan za su sanya, A cikin suturunsu mun sanya masu abaya na larabawa kala kala, A ciki za'a daukar masu masu kyau na mutunci, sannan bama son suyi shigar da zata baiyana sumar kansu, a rufe masu ko'ina na jikin su. Gyaɗa kai tayi"okey, in sha Allah amma baza'ay masu make up ba"? "Duk kyan da Allah yayi masu"? Ya faɗa da murmushi kan fuskanshi, Itama ummin murmushin takeyi"masu kyaun ma su na yin make up, ko da yake naji ka ce arufe masu ko'ina na jikin su, ba buƙatar yin make up, ɗaga mata gira yai alamar eh. "Tare da ni zaku tafi ne"? "Idan kina ra'ayin zuwa" Girgiza kai tayi alamar a'a "Meyasa"? "Nafi so kubarni a gida, nasan Su Unaisah zasu bani labari, har ma su daukar min video na dinner din in gani nima" "Ban yarda ba, yakamata kema ki shirya mu tafi tare dake, zaki ji dadin shiga cikin family ɗin Obinna," jim ta ɗanyi tana wani tunani aranta. "Kinyi shiru baki ce komai ba" Numfasawa tayi tare da cewa"ka yi hakuri amma zuwana ba lallai ya zama alkhairi agare ni da ku kan ku ba, bana so na 6ata maku shagalin ku, nasan ka fahimce ni" jim ya ɗanyi yana jujjuya mug din hannunsa, tabbas ya fahimci me take nufi,shi kanshi yasan ba lallai chief Ya amince su tafi da ita ba, yadai ɗan bugi cikinta ne don yaji idan tana son zuwa sai kuma akaci sa'a bata ra'ayi. "Alfarmar da nake nema a wurin ku, dan Allah ku barni in fita gobe, Inaso zan ziyarci gidan ƙawata dake aure anan abuja" "Bani da wannan hurumin, Amma in sha Allah zanyi kokarin nema maki alfarma wurin chief, but inaso kisan da sani duk inda zaki je jami'in mu ne zai kai ki," har cikin ranta taji dadin maganarsa. "Idan akwai abun da kike buƙata ki faɗa min" cikin kulawa yayi mata maganar yana dubanta. "Dan Allah ka fadamin shin dagaske ne chief Yasan komai dangane da rayuwana"? Ta fada cike da fargaba. Jim ya ɗanyi yana dubanta kafin Yace" "I'll give you an assignment. If you can find the answer, then I'll tell you what you want to hear," A ƙagare ta ke kallon shi, A hankali Ya sanya yatsun hannayen shi tare da zame mask din fuskarshi. Wani irin kallo ummi ta soma binshi da shi, Yau ne karo na farko da ta fara Yin tozali da fuskar Boss man, bata ta6a tsammanin Yana da kyawun fuska har haka ba. "Dama haka kake da kyau"? da alamun mamaki ta furta maganar, Murmushin gefen fuska Ya sakar mata har dimple dinsa ya lotsa, nan take ta soma kokarin tariyo inda tasan fuskarshi sai dai kash takasa tunawa amma tabbas tana ji aranta ta ta6a sanin shi ko kuma wani ne me kama da shi. "Ina da aure, Ki daina kallona, matana tana da kishi, zata iya yin komai akaina" da zolaya taj yayi maganar. Ummi tace"tasan tana da kishi meyasa ta auri namiji mai kyan sura? Ay kamata yayi ta auri mummuna, ni fa bazan 6oye maka ba, ka jima kana bani mamaki kai da abokin aikin ka big guy da chief din ku, tun da nataso rayuwata da wuya a samu namijin zan gifta awuri batare daya bi ni da kallo ba harma ya neme ni, amma ku sam babu wannan tunanin aranku, zuciyarki a tsarkake take, hakan ba karamin daure min kai yake yi ba, shi chief mace ko kallo ma bata ishe shi ba, wata irin dakakkar zuciya ce da shi. Ƙayataccen Murmushi Taj Ya sakar mata batare daya furta mata ƙala ba "Wallahi nasan ka, sai dai bazan Iya tuna a ina nasan ka ba, ni hatta muryarka na jima ina son tuna ina na son ta," still face dinsa da murmushi Yake dubanta. "Amma meyasa kake yi min kama da Unaisah? Ko dai idanuwana ne suke nuna min badai dai ba"? "Ba laifin idanuwanki bane, Unaisah Ƴata ce, Jini na ce, Ni mahaifinta ne, asalin sunana Tajuddeeen," "I can't believe it, Unaisa fara ce zan iya sanyata a jinsin larabawa, kai kuma daga ganin ka hausa fulani ne" "A salin sunana Zaheer Tajudeen, Zaheer sunan Mahaifina ne, Tajudden kuma sunana ne, Ki tambayi Unaisah menene full name dinta zata fada maki da bakinta, Ita kanta ayanzu haka batasan cewa Ni mahaifinta bane ƙaddara ce ta rabamu, sai gashi cikin ikon Allah mun sake haɗuwa," murmushi ummi tayi"Allah sarki, Na tayaka Murna, amma mahaifiyarta wani jinsi ce"? "Hausa Arab ce" Dariya Ummi tayi cikin raha ta furta"hausa arab! Bayan hausa fulani har Hausa rab ke da akwai, ban ta6a ji ba sai akanka" "Ina nufin Half cast ce, Mahaifinta hausa fulani ne, mahaifiyarta kuma Balarabi ce" gyaɗa kai tayi"masha Allah, shiyasa yarinyar taka takasance fara sol, Ga gashi tubarkalla amma tsakanin kai da mahaifiyarta halin wa ta ɗauko"? murmushi yasaki yana dubanta yace"meyasa kika tambaye ni"? "Unaisah tana da faɗa, daga ka kalli idanunta zaka shaidan hakan, ga wayau da kaifin basiri Allah Ya bata fiye da sauran ƴan uwanta" haƙiƙa Yaji daɗin Yabon da ummi tayi mata, "Haka mutane suke cewa, shiyasa nima nake alfahari da ita, Inason Unaisah, fiye da yadda nakeson kaina, A halin Yanzu bani da tamkarta a duniyarnan, Itace ta rage min wadda nake gani naji sanyi araina, silar unaisah nasamu alheri da dama wadanda idan na fada maki su zakiyi mamaki, ɗaya daga ciki Unaisah itace silar haɗuwana da Chief" da mamaki Ummi ta ɗan zaro mashi sexy idanunta haɗi da buɗe baki, Jinjina mata kai yayi" Murmushin gefen fuska tasaki"Ina ƙara tayaka murna, Yarinyarka Jarinka ce, Allah Ya albarkaci Rayuwarta" amsa mata yayi ameen, daga ita har shi sun ji daɗin zaman firar da su kayi, Haƙiƙa taj ya ɗebe mata kewar kaɗaicin dake damunta, ta ƙara ganin mutuncinsa da ƙimarsa a idanunta, Sai dai tarasa gane meyasa take jin kamar ta ta6a sanin shi? Musamman daya faɗa mata sunan shi sai yawo yake mata akai. Ni'imtacciyar Iskar dake kaɗawa ta ƙara masu ƙaimin firar ta su, kafin wani lokaci taj yace da ita"kada na cika ki da surutu, ko zaki koma ciki ne"? Fuskarta da fara'a tace"no ko kusa, ni baka takuramin ba, saima ɗebe min kewar da ka yi, naji dadi fiye da tunanin...... " bata ƙarasa maganarba sakamakon sautin dirar motar daya ratsa kunnuwanta, kusan atare suka juyo suna duban motar. Bayan sojan dake driving din motar yayi parking, Ya fito Ya zagaya ya buɗe mashi murfin back seat dinta, Ƙafarshi kaɗai ya zuro waje Gaban ummi ya faɗi rasss, jikinta ya soma kakarwa, A hankali ya ƙarasa fitowa daga cikin motar, kamar kullum cikin shiga ta malamai magadan annabawa, bai ɗaura idanunsa akan kowa ba sai akan Ummin america, a sukwane ta miƙe tana gyara mayafin da tayi rolling, taj kuwa fuskarshi dauke da murmushi ya nufi sheikh imam yana fadin"Ya sheikh Barka da zuwa tun ɗazu muke ta sa ran ganin ka" Martanin murmushin Shiekh Imam ya mayar masa a yayin da yake kokarin kau da idanunsa daga na ummi ya mayar da su akan fuskar taj, musabaha su ka yi shikeh imam yace"Ay min afwa, ban samu damar zuwa duba mara lafiya na ba, wallahi yana araina da shi na wuni, wani uziri ne ya ruƙe ni" Jiki na rawa Ummi ta juya ta nufi ƙofar shiga falo, Duk don kada su gaisa da sheikh imam, har ta kusa kaiwa ga ƙofar muryar taj ya ratsa kunnanta "Ummi, ki zo mana ku gaisa da sheikh imam" tamkar an dasa mata aya ta tsaya cak, tana mai mayar da numfashi, Har cikin ranta bata ji daɗin dakatar da itan da yayi ba, sai dai bata jin zata iya watsa mashi ƙasa a ido, musamman yau daya faranta mata rai. Tunkafin ta juya ta soma jin takun tafiyarsu bayanta, jiki asanyaye ta waiwayo tana dubansu, lokacin da suka ƙaraso da sauri ta sunnar da kanta ƙasa, muryarta na rawa ta furta"sannu da zuwa" Cikin sanyin murya ya amsa mata da yawwa Taj dake dubansu a fakaice yace"sheikh bari na gabatar maka da ummi,"jinjina mashi kai yai alamar toh "Ummi Tamkar uwa take a wurin yaran da muke raino, ita ce take kula da su" Fuskar sheikh babu annuri ya furta"anya kuwa sunyi dacen uwa"? Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aruɗe ya kalli fuskar shaikh imam *Daga alkalamin Boss Bature💋✊✍️* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 10 Complete by Novels Elite Admin May 25, 2024 _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القدر💋✊🔥 ~Takun Ƙarshe🔥~ قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aruɗe ya kalli fuskar shaikh imam. "Ya sheikh ko zan iya sanin dalilin da ya sa ka ce haka? Acewar Taj Sheikh imam yace "Tun da nake zuwa gidan nan ban ta6a ganin ta taka zuwa ɗakin yaron nan ba, domin duba lafiyarshi, bansani ba ko tana shiga bayan bana nan amma raina na bani tamkar bata zuwa, a matsayinta na maruƙiyarsu yakamata ace tafi kowa bashi kyakkyawar kulawa ko da kuwa addu'a ne take zuwa tana yi mashi akai akai" tun da sheikh imam ya fara kora jawabi hankalin ta ya kwanta jikinta yai sanyi laƙwas. "sheikh maganarka gaskiya ne, ummi baki kyautawa, kinga har sheikh imam ya fahimci baki zuwa duba lafiyarki ɗan ki" ya faɗa yana kallon ta, murmushin gefen fuska ta saki, cikin sanyayyar murta tace "nagode sheikh da tunasarwa, na gane kuskure na kuma in sha Allah daga yanzu zan dinga zuwa duba shi' "Masha Allah, yanzu naji magana, bismillah malama ummi mu shiga ciki, kiyi mashi addu'a in gani" ta fahimci sheikh imam kamar ya gano wayanta nason ta gudu, shiyasa yake kokarin ruke ta. Babu yadda ta iya adole ta amince suka nufi cikin gidan atare tana mai jin wani irin sanyi aranta. Bayan shigarsu ɗakin, kamar yarda suka barshi da asuba haka su ka taras da shi, babu abun da ya canza yana a kwance rabin jikin shi lullu6e da bargo, sumar kanshi an ɗaure mashi ita, ta kara tsayi har kusan mid back din sa, ga wani irin pure white da skin dinsa tayi har wani glowing ta ke yi, jikin ummi ba ƙaramin sanyi yayi ba, kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara shigowa dakin danish, bata ta6a tsammanin jikin yayi tsauri har haka ba, kamar matacce babu abun da ke motsi a jikin sa. Tsananin tasauyin shi ne ya kama ta aranta ta ayyana wato duk kyan mutun bai isa ya hana kanshi ciwo ko mutuwa ba, jiki asanyaye ta matsa bakin gadon, sheikh imam da taj suna daga tsaye suna kallon shi, yanayin fuskokinsu ya nuna damuwa. Girgiza kai sheikh yayi cikin jimami ya furta"Ya Allah ga bawan ka nan, kafi mu sanin a wani hali yake a ciki, ya Allah ka sauƙaƙa mashi abun da ke damun shi, Ya Allah ka raba shi da shaidanun dake azabtar da rayuwar sa... cikin harshen larabci yaci gaba da karanto addu'o'i yana tottofa mashi, rashin lafiyar danish ba ƙaramin ɗaga mashi hankali yai ba, damuwarshi kada yaƙi tashi, duk da yayi imanin addu'o'in da yayi mashi, da sallar daren da yake yi mashi basu tafi hakanan ba, sai dai idan lokacin shi ne yayi. Cikin rauni na murya ummi ta furta"baya iya tashi"? Taj da jikin shi ya gama mutuwa laƙwas, Muryarshi babu karsashi ya bata amsa da cewa "baya iya yin komai, sai dai ayi mashi, ta hanya daya muke gane ya farka daga bacci, yatsun hannayensa dana ƙafafuwansa suke kerma" Jinjina kai ummi tayi, tare da kau da idanunta daga kallon Taj ta dubi sheikh imam adai dai lokacin shima ya dawo da dubanshi gare ta, haɗa ido su ka yi da juna duk saita rasa sukuninta kamar wata mara gaskiya. "Addu'arki yake buƙata a matsayinki na mahaifiyarsa" har sai da taji gabanta ya faɗi jin sheikh imam ya furta a matsayinta na mahaifiyarsa. Ɗauke idanunta tayi daga kanshi, kafin ta dai daita nutsuwarta, ta ɗan ɗukar da kanta saitin inda Danish yake a kwance, cikin harshen larabci ta soma karanto addu'oi tana tottofa mashi, bayan ta gama ne ta ɗago tare da kallon fuskar sheikh imam, tayi mamakin murmushin da ta gani ɗauke akan fuskarshi, sunnar da kanta tayi ƙasa saboda kwarjinin da yayi mata "Chief yana nan ko ya fita ne"? ya tambaya yana kallon Taj. "Bayanan tun ɗazu da rana ya fita, yana a villa wurin daddynsa, Idan kana buƙatar yin magana zan iya kira maka shi" Girgiza kai sheikh imam yayi"a'a, dama na tambaya ne in ji ko yana nan" "yanzu me yakamata mu yi sheikh"? "Naga har yanzu bai farka daga bacci ba, nasan dole akwai yunwa atattare da shi sannan yana buƙatar wanka, amma kada a tada shi idan har bashi ya farka da kan shi ba" amsa mashi taj yai da toh. "Ina sauran yaran su ke ne? Sun yi mashi addu'o'in da suka sa6a yi"? ya tambaya yana kallon Man. "tun da asuba rabon su da dakin, bansani ba ko sun ƙara leƙowa" "Inason ganin su gaba ɗayan su yanzu" da sauri ummi ta ce"bari naje na kira su" dama neman hanyar da zata bar dakin take yi. Bayan fitarta daga ɗakin sheikh Imam ya ɗan haura saman gadon, tafin hannunsa ya ɗaura saman forehead din danish, ya fara jera addu'o'i na musamman yana tofe mashi jiki, tsawon lokacin kafin yacire tafin hannun ya maidashi kan saitin zuciyarshi, yaci gaba da yi mashi kira'ar alkur'ani mai girma, Taj dake kallon sheikh imam dake janyo kira'a ba karamin nutsuwa yaji ba a cikin zuciyarsa. Tun da ummi ta fito, a bakin kofar ɗakin ta la6e tana sauraron kira'ar sheikh imam mai ratsa zuciya, wasu irin zafafan hawayene suka cika mata idanunta, Jikinta har kerma yake yi, ga dukkan alamu akwai wani abu da yai silar jefa ta yanayin da take a ciki. Runtse idanunta tayi sosai, jin kukan na shirin kubce matane yasa tai saurin toshe bakinta da tafin hannunta, muryar ta na rawa ta furta "uhibuk kathiran ya 'abi har yanzu kai mahaifina ne ba abun da ya canza..." Duk waɗannan sambatun da take yi, A kunnan Unaisah, wadda fitowarta kenan daga dakin su ta kamo hanyar zuwa dakin Danish don ta duba jikin shi, karaf taci karo da ummi ta runtse idanunta tana matsar kwalla. Muryarta da ruɗani ta furta"Aunty Ummi!" Furgigit ummi tay saurin buɗe idanunta wadanda suke ajike sharkaf sun kaɗa jawur Ganin unaisah yasa tai saurin sanya tafukan hannayenta ta share hawayen dake karanyo mata "Aunty Ummi, yaushe kika shigo? Ina boss? Meyasa ki zubar da hawayen ki? Wani abu ya faru da danish dina ne..." hankalin ta atashe ta fada Muryar ummi adisashe ta furta"bamu jima da shigowa ba, ni da boss tare da sheikh imam... " ta fada muryarta na ɗan rawa "kada ki damu ba wani abu bane ya faru da ɗan uwanku, kawai naji tausayin shine ya kama ni, bansan ciwon nashi yakai har haka ba, naji haushin kaina da ban ta6a leƙowa domin duba lafiyar shi ba, yau da naganshi jikina yayi sanyi shiyasa kika ganni awaje ina sharar hawaye... ' wannan maganar da ummi ta furta tayi matuƙar karya ma Unaisah zuciya, idanunta tuni sun cicciko tab da kwalla, ganin hakan yasa ummi tayi saurin furta"dan Allah kada ki yi kuka, addu'armu yake buƙata A halin Yanzu" duƙar dakai ƙasa unaisah tayi, jiki asanyaye tace"bari na shiga in duba shi" ta faɗa tare da buɗe kofar tasa kai ta shige ciki, bayan shigarta Ummi ta sauko down stairs don ta kira su Haris kamar yadda sheikh Ya buƙata. Kafin wani lokaci gaba ɗayansu sun hallara a dakin danish, kowannansu ka kalla babu walwala, tsantsar damuwace akan fuskokin su. Ɗaya bayan ɗaya sheikh imam yake dubansu har sun yi shirin kwanciya bacci, kowannansu yana asanya da sleeping dress dinsa, kafin ya soma magana cikin sanyayyar muryarshi "Ku naso ɗan uwanku Ya samu lafiya"! har suna haɗa baki wurin furta eh "To ku dage da yi mashi addu'a, Ita yake buƙata daga gare ku, nasan kunayi to ku ƙara abisa wadda ku ke yi mashi, Kunga har yanzu mun rasa gane yanayin da yake aciki, yau jikin shi yayi tsauri fiye da kullum, tun safe babu alamun zai farka daga wannan dogon baccin da yake yi, shi kadai yasan me yake ji a jikin shi, addu'a da kuke gani takobin mumine ce da itane zamu yaƙi shaidanun dake sarrafa shi, kullum suna aiki akanshi, safe da dare, why mu bazamu iya tsayawa tsayin daka wurin ganin mun ruguza shirin su ba! Mu da ma mu kayi imani da Allah balle su da su ke mushirikai.... ' tun da sheikh imam ya fara yi masu magana suka nutsu suna sauraron shi, sun kewaye gadon da danish yake a kwance, kokari yakeyi ya tunzurasu donsu harzuƙa su kuma dage damtse wurin yi mashi addu'a, duk maganganun da sheikh imam keyi a kunan ummi da ke a la6e bakin ƙofar dakin tana sauraronsu. Sautin shessheƙar kukan unaisah ne ya soma karaɗe dakin, kamar jira sukeyi tafara kuka, Jemimah da azeeza suka fashe da kuka, suma sauran kowannansu kwalla ce a idanunsa. "Ba kuka yakamata kuyi mashi ba, kamar yarda na fada maku addu'arku yake buƙata, A cikin ku akwai wanda ke tashi yin sallar dare domin yi mashi addu'a akan Allah ya bashi lafiya"? Shiru su ka yi, saboda basu da amsar da zasu bashi, unaisah dake faman zubda kwalla muryarta a raunace ta furta"ina yi mashi, amma ba kullum ba, wani lokacin kona kwanta da niyar tashi inyi mashi bana farkawa, saboda bani da me tada ni" "Ni bansan yadda akeyi ba, da ace na sani har bacci zan iya hana kaina don inyi mashi addu'a, saboda danish yayi mana abin da bazamu ta6a mantawa ba, ya cancanci mu sadaukar da komai akanshi" cikin sanyin murya batool ta ƙare maganar, taj da sheikh iman sun nutsu suna sauraronsu haɗi da kallon la66an duk wanda yayi magana a cikin su. Cikin shessheƙar kuka jemimah tace"wallahi nima zanyi ma shi, saboda bana so Danish ɗin mu ya mutu kamar yadda na rasa Majnoon ɗina...." wannan maganar ta jemimah taja hankalin sheikh imam da taj sosai akanta, ta dage sai ku ka ta ke yi, kumatunta har sun yi ja, ruko hannunta sheikh imam yai tare da lallashin ta akan ta daina ku ka. Hanna dake matsar kwalla ta ce"In sha Allah babu abun da zai same shi, zamu yi iyakar bakin kokarin mu don ganin mun ceto rayuwar ɗan uwan mu da iznin Allah..." daƙyar ta ƙare maganar "In sha Allah daga daren yau zan fara yin mashi nafilfili, ni saima naji haushin kaina, bamu kyauta ba, har zamu iya dariya muyi bacci, bayan ɗan uwanmu yana akwance rai hannun Allah, komai sai anyi mashi, mutumin daya sadaukar da farin cikin shi akanmu? Ya hana idonshi bacci saboda ya bamu kariya, sai mune zamu gaza hana idanun mu bacci anya kuwa mun kyautawa kanmu"? gaba ɗaya suka fashe da kuka mai tsuma zuciya, haƙika maganar Haris Ta ta6a zukatansu, hatta ummi dake jingine da kofar dakin sai da ta zubda kwalla duk da batasan takan tarihin rayuwarsu ba, amma ta hasko wani abu. daga gefen gadon Danish sheikh Imam ya zauna jikinsa yayi sanyi lakwas, bai ta6a ƙaguwa da son jin labarin rayuwarsu ba irin yau. Cikin sanyin murya taj yace"kada ku ɗaurama kanku alhakin laifin da bana ku ba, hana ido bacci ba shi ke nuni da kun damu dashi ba, saboda ku kanku bazaku samu kwarin gwiwar yi mashi addu'a ba muddin baku da kwanciyar hankali da nutsuwa, abun da yakamata, tun da dare yayi in za ku yi bacci ku kwanta da wuri, wuraren ƙarfe uku na dare zan kira unaisah awaya in tunasar da ita, in yaso ita sai ta tashe ku daga bacci ku tashi kuyi nafilfili ku kai kukan ku wurin Allah akan halin da ɗan uwa ku yake a ciki, in sha Allah zamuyi nasara" Shawarar da boss man ya yanke masu tayi masu dadi. "Mungode sosai, Allah yasaka maku da mafificin alkhairinsa, Allah ne kadai zai iya biyanku, " godiya suka shiga yi ma shiekh imam da boss man...... "Yakamata kuje ku kwanta, ku yi bacci kada a makara" amsa mashi su ka yi da toh, bayan sunyi ma sheikh imam sallama, Suka nufi hanyar fita daga dakin jin takun tafiyar sune yasa ummi tayi saurin nufar bedroom dinta tana shiga ta fada saman gadonta taci gaba da yin kuka tamkar ranta zai fita... Unaisah taso ta samu damar ganin danish dakyau, amma saboda shiekh imam yasa takasa tsayawa, Idan har ba ita ta kashe mashi switch din dakinsa ba, ta kuma lullu6e shi da bargo ba, to kuwa hankalin ta bazai kwanta ba, tunani zatai tayi kamar ba'a lullu6e shi. Ɗaya bayan ɗaya kowannansu ya nufi room dinsa bayan sunyi sallama wa junansu, zuciyoyin su cike da zullumin halin da danish yake a ciki. Basu bar dakin shi ba, sai da Taj Ya lullu6e shi dukanshi da bargo, ya kuma kashe switch din kafin Suka fito tare da sheikh imam, har bakin motar da aka kawo shi ya raka shi, sun ɗan juma a jikin motar suna tattaunawa duk dai akan halin da danish yake a ciki ne, har ƙara jaddada mashi sheikh yayi akan su dinga dubawa akai akai ko Allah zaisa ya farka daga baccin, kafin daga bisani su ka yi sallama. _______________________Boss Bature✍️ 💋CHIEF OWAIS💪 Aso Villa. A yayin da yake a kwance saman katafaren gadon shi dake a Villa tsantsaran gaske, ya lullu6e half body dinsa da lallausan duvet dinsa, cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yake fitar da numfashin sa, ga wani irin sanyin A.c daya ƙarama dakin nashi ni'ima, babu haske dakin sai na bedside lap ɗaya da aka bari a kunne... sautin ringing ɗin wayarsa ne ya farkar shi, da wata irin kasala ya kai hannu ya lalubo wayar, A hankali yaɗan ware reddish eyes nasa masu dauke da bacci ya duba sunan mai kiran nashi, yayi mamakin ganin kiran prime minister Hateem, slowly ya dubi agogon bango ƙarfe wani abu na dare. Ya ilahi ya faɗa a zuciyarsa kafin ya miƙe zaune ya ɗaga kiran ya ƙara a kunnansa "Uncle... " iya abunda ya iya furtawa kenan. On the other hand muryar prime minister ta karade kunnuwansa. "I'm sorry na katse maka baccin ka, na tashi yin night prayers ne, shi ne na kiraka don inji awani hali yarona yake aciki, saboda mafarkinsa ne ya tada ni daga bacci" chief owais dake ta faman lumshe idanunsa, cikin yanayi na kasala ya furta"uncle saboda shi ka tada dani daga bacci"? "I'm so sorry my son, bansan ya zanyi maka bayani ba" Lumshe sexy eye dinsa yai kafin a hankali ya furta "Uncle, ka kwantar da hankalin ka, yanzu ni bana agidana, nazo Villa ne, amma in sha Allah gobe zan koma gidana da wuri saboda shi' Har cikin ran prime minister yaji dadin maganar Owais "Zullumi nakeyi, daga gobe shikenan bazan sanya shi a idanuwana ba, jibi da asuba jirginmu zai bar nigeria, gani nake kamar idan na tafi ba lallai na sake dawowa ba, balle har na sa ran ganawa da shi.... " dafe kai chief owais yayi da hannu ɗaya, Lamarin yafara kokarin rikata mashi lissafin kwalwarsa, aranshi ya ayyana anya kuwa Daddy Hateem bai fara zaucewa wa ba? ko dai ya samu matsalar kwalwa ne? Ko kuwa yafara ɗaga kwalba ne, Idan ba haka ba akan wani dalili zai ɗaga hankalin shi akan yaron da bai haɗa alaƙar komai da shi ba? Wannan wata irin ƙaunace? Jin shiru chief owais bai furta mashi magana bane yasa shi cewa"naji kayi shiru son, ko ka koma baccin ne... Slowly ya mayar da kanshi saman pillow,. "Uncle, I'm confused..." kafin ya ƙare maganar prime minister ya tari numfashin sa "I'm confused too, Owais....nasan me ka ke tunani aranka, may be ma kana yi min kallon kamar nafara zaucewa, owais na dauki soyayyar yaron nan amatsayin jarabta daga Allah, ni dai kawai fatana ya zama alkhairi agare ni, dan Allah ka tayani da addu'a Allah ya bashi lafiya... Lumshe ido chief owais yai, bakomai yake tariyowa ba face ranar da suka fara tozali da juna shi da danish suna a saman bene, suka jefa ma junansu kallon kallon, aranshi ya ayyana ba lallaima idan yaron ya dawo hayyacinsa ya kula prime minister ba saboda Yana da ilmin sanin halayyar ɗan adam, da ido kawai ya kalli danish ya fuskanci yana da wuyar sha'ani, yin mu'amala da shi ba abu ne mai sauƙi ba. "In sha Allah zan tayaka da addu'a, ni dai fatana ka daina sanya damuwa aranka, ka kwanta ka yi bacci, muna da liyafa a gobe" Yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar prime minister ta cikin wayarshi. "Nagode da kulawarka agareni my son, Allah yayi maka albarka" amsa mashi yayi da ameen Har zaiyi rejecting kiran muryarsa ta sake katse shi "Pls kada ka koma bacci, ka tashi ka shiga toilet ka dauro alwala, kayi mashi nafila ko da raka'a biyu ce, Allah ya bashi lafiya" Babu musu yace"In sha Allah zanyi" bayan sunyi sallama, chief owais yayi shiru yana tariyo kalaman Daddy hateem, shi kanshi yafara hasashen tabbas akwai wani 6oyayyan sirri dake a tattare da kaunar da uncle dinsa ke yima yaron Allah kadai yasan ko menene. Jefar da wayar yayi saman gadon, kafin ya miƙe ya zura ƙafafuwansa ƙasa inda ya ajiye gucci slippers din sa, yunƙurawa yayi ya miƙe ya nufi switch din dakin ya kunna a hankali haske ya gauraye ko'ina, wato wani hamshaƙin bedroom ne, komai na cikinsa launin royal blue and white colour ne. A gaban dressing mirror ya tsaya tare da ɗaura hannun shi ɗaya ya dafa mirror chair. Wasu hadaddun Cashmere pajama ne a jikinsa riga da wando masu tafshi launin sky blue, sumar kanshi tasha gyara sai daukar ido take yi ga wani kamshi dake fita daga cikin ta, chief karshe ne a fagen haɗuwa. Moving slowly ya nufi ƙofar toilet dinsa ya shiga daga ciki, alwala ya ɗauro ya fito fuskarsa da lemar ruwa ya nufi walk-in closet dinsa jim kadan ya fito sanye da jallabiya, ya hau kan darduma ya dai daita nutsuwarsa da kyakkyawar niya ya kabbara sallah. A kalla yayi kusan raka'a goma sha takwas batare da gajiyawa ba, har sai da yaji kafafuwanshi sun soma rurruƙewa tukunna ya dakata, ya zauna yana jero addu'o'i duk dai akan danish yayi su kamar yarda Uncle hateem ya nemi alfarmar yayi mashi. Bayan ya kammala komawa yayi saman bed nasa ya kwanta, tare da kai hannu ya ɗauki wayar shi, jim yayi yana mai mamakin ganin sakonta, a kalla sunfi wata biyar ko sallama basa yi ma juna, shiga cikin message din yayi, tare da karanta sakon da ya gani, ko kusa bai ji su a zuciyar shi ba, saboda kokwanton da yake yi, video din Ya kunna ya fara kallo, yana faman lumshe idanun shi, tayi mashi kyau yaji dadin kallon video din, almost 3 times yana maimaita kallon shi, kafin daga bisani ya fita daga chat din ya daura idanunshi kan hoton wallpaper din sa. A tsanake yake kallon baby face dinta, ta zare idanunta a hoton daga ganin hoton screenshot din shi aka dauka, kuma anyi hoton ne batare da sanin ta ba. Sam baya gajiya da kallon hoton, A hankali ya ɗaura soft pink lips dinsa saitin fuskar ya sumbace ta, kafin ya ɗaura hoton saman kirjinsa a haka bacci yai awon gaba da shi. ________________________✍️ Taƙi runtsawa ta addabi kowa ta hana su bacci saboda Jazz baizo ba, tace in har baizo ba to bazatayi bacci ba suma kuma bazasu yi ba, dakyar Salsabeel Ya shawo kanta Ya samu ya lalla6ata har ta ƙyale sauran ƴan uwanta suka kwanta a dakunansu, itama takwanta harfa ya kwanta da niyar ya runtsa can tsakar dare yajiyo bugun ƙofa, a firgice ya farka Yaje ya buɗe, Khadeeja ya gani tsaye ta ruƙe qugu tana faman kumbura mashi fuska tace Ina jazz din yazo? Agogo ya kalla sam yama kasa buɗe baki ya bata amsa, tace dama nasan baizo ba, ya manta dani, wlh Allah nima nayi fushi da shi. Cikin kwantar da murya salsabeel yace"dan Allah kiyi hakuri kije ki kwanta bacci, dare ne yanzu, gobe in Allah yakaimu da safe zan kira maki jazz" Maƙe mashi kafaɗa tayi alamar bazata kwanta ba, ganin zata 6ata mashi lokaci yasa shi ɗaure mata fuska ya daka mata tsawa tare da fadin"Zaki wuce kije ki kwanta ko saina yi ƙwallo dake" fashe wa tayi da kuka da gudu ta nufi falo ta zauna saman sofa tana kuka, ko tsoro bata ji ita kadai kamar aljanna" ko ta kanta baibi Yaja kofa Ya rufe Ya koma ya kwanta. Sai da tayi kukan mai isarta, kafin Ta miƙe tana shafa ciki Alamar yunwa take ji, kaitsaye ta nufi Kitchen ta shiga ta soma kiciniyar kunna gas, tsabar rigima. Mutsu mutsu tajiyo a kunnanta, hakan yasa ta dakata ta juya tana ƴan waige waige don ganin menene, Karaf idanunta suka sauka akan Ƙatoton 6eran dake tafiya saɗaf saɗaf Yana tunkarota baƙi wulik da shi, sam bata ji tsoron shi ba, Abun ka game ta6in hankali, Praying Fan ta ɗauko cikin sanɗa tabi bayan shi ta daddage ta kwaɗe shi da fan ɗin, ko shurawa baiyi ba ya sheƙa, Bindin shi ta ruƙo tana faman sakin nishi tace"Zaka ci ubanka, Kai ne 6arawon dake cinye mana sauran da muka rage a kitchen ko"? Ta faɗa tana leƙen idanun 6eran Yayi zuzuru dashi. "Ba zaka yi magana ba? Baka da gaskiya bakin munafuki, kai ne kake gwigwiyar mana bready, Bari na kai ka Gaban Alƙali Ya salsabeel Ya kashe min kai har lahira" Ta faɗa tare da fitowa da gudu ta nufi bedroom din salsabeel, Har Ya koma bacci, Yajiyo muryar khadeeja tana fadin"Ya salsabeel Ka buɗe min kofa na kama 6arawon dake cinye mana sauran abincin mu, gashi nan a hannuna, Ya salsabeel ka buɗe zai gudu' Afirgice Ya farka har yana tuntube garin sauri, koda Ya buɗe ƙofar Miƙa mashi 6eran tayi "Gashi ka kashe shi ko ka cire mashi hannayensa" Fuskarshi a yamutse ya kalli 6eran da idanunsa masu dauke da bacci, sun kaɗa jawur da su, yayi mamakin da har ta iya kamo 6era, tun da suka fara zama gidan bai ta6a ganin gifcin 6era ba sai yau. Muryarshi adisashe yace"khadeeja ba zaki barni inyi bacci ba? Ke baki runtsa ba nima kuma kin hana in runtsa, Meke damun ki ne"? Ta6e mashi lips dinta tayi alamar zata fashe mashi da kuka Da sauri yace"ya isa ni bance kimin kuka ba, Yanzu fada min ya kikeso ayi da 6eran nan da kika kama" "Ka cire mashi hannuwa" gyada kai yayi tare da sanya hannu ya kar6i 6eran"ki jira ni yanzu zan dawo amsa mashi tayi da toh, fita yai daga dakin tana atsaye tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannunsa babu 6eran "Yana ina"? "Na cire mashi hannuwa na yar" murmushi tasaki"mun hutu da masifa ko"? Ɗaga mata gira yai alamar eh "Muje na rakaki daki kiyi bacci" maƙe mashi kafada tayi"Ni yunwa nake ji, kaje kitchen ka dafa min abinci" Wahalallan kallo yabita dashi gaba ɗaya ta takurasa "Shikenan muje" Ya fada tare da yin gaba tabi bayan shi suka shiga falo, ta zauna saman sofa. Kitchen Ya shiga bawan Allah ga gajiyar bacci A haka Ya dafa mata indomie, Ya haɗo mata da water bottle, Ya shigo Da plate din Ya miƙa mata, gefen ta ya zauna don yasan koya koma daki indai batayi bacci ba to shima bazai runtsa ba. Yana kallonta Har ta cinye taliyar ta kora da ruwa, kwanciya tayi saman sofa din ta daura kafafuwanta saman laps dinshi bai tanka mata ba, yasan rigima take nema, Cikin sa'a bacci yai awon gaba da ita, A hankali Ya zame ƙafafuwanta ya miƙe tare da ɗaukarta ya nufi upstairs da ita, a kan gado ya kwantar da ita, yabi da bargo ya lullu6e mata jikinta, kafin ya fito ya datse kofar dakin nata, cikin sauri ya nufi dakinsa don ya kwanta ya karasa baccin dabai isheshi ba, bayan shigarshi daki har ya kwanta ya soma tunanin ko me ya hana jazz zuwa? Tun safe yake jaraba kiran layin shi baya picking, har ta 6angaren danish ba a kira shi ba wunin yau, fatan shi Allah yasa lafiya da wannan tunanin bacci 6arawo ya ɗauke shi. *💋BENAZIR❤* Kwance take a saman darduma, tun bayan data kammala sallar Isha bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, yayin da zeenatu take a can saman gado tana bacci. Tana a nannaɗe cikin dogon hijab dinta, tayi nisa acikin baccin ta, Ba zato ba tsammani hasken fitilar bedroom ɗinta ya ɗauke ɗuff, wani iko na Allah ba wutar gidan bace ta samu matsala, ɗakinta ne kadai hasken ya ɗauke, abun ka game bacci sam bata ji alamun hasken dakin ta ya ɗauke ba. Kwatsam! taji an damƙi wuyanta, tsabar zafin shaƙar da akayi mata ne yasa ta ware idanunta waje, bata iya ganin komai sai duhu baƙi wulik a idanunta Wani irin mahaukacin bugun fargaba zuciyarta keyi mata, Hankalinta a matuƙar tashe ta soma kokarin kwace wuyanta daga hannun mutumin daya shaƙeta, wuyanta tuni ya soma yi mata zogin azaba, zufa ta ko'ina ta wanke fuskarta, duk yadda benazir taso ta kwace kanta sai dai kash takasa, ga zeenatu kwance saman gado sai dai babu halin da zata iya buɗe baki ta nemi agajin ta, koma wanene yayi mata muguwar shaƙar da ko yatsanta takasa ɗagawa, bakinta tamkar an ɗaure mata shi takasa buɗe shi, hakan yasa tafara kukan zuci tana ambaton sunan Daddy, mommy, yaya shurem, Zeenatu, A karshe ta kamo kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un tacigaba da anbatonta acikin zuciyarta. Tana acikin wannan mawuyacin Halin har tafara fidda rai da rayuwa kwatsam wayar zeenatu da ta ajiye kan gado ta soma ringing, taken karatun al'ƙur'ani mai girma ne, Kamar Walkiya taji alamun an sakar mata wuyanta, kuma nan take hasken ɗakinta ya kawo, a gigice ta zabura ta miƙe zaune tana faman zazzare idanunta, bin ko'ina na dakin tayi da kallo bata ga kowa ba, Lamarin ya daure mata kai, tagaza gane meke shirin faruwa da ita? Don wannan yafi karfin a kirashi da mafarki, tabbas akwai me son rabata da rayuwarta, lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ƙaramar yarinya ita kadai tasan radaɗin da wuyan ta ke yi mata, zeenatu dake ta sharar baccin ta tuni ta soma mutsu mutsun farkawa saboda sautin kukan benazir daya fara addabar kunnuwanta, da sauri benazir ta tsagaita da yin kukan gudun kada zeenatu ta farka taga halin da take a ciki, cikin juriya ta miƙe ta zame hijab din jikinta, ta jefar da shi gefen gado, gaban madubi taje ta tsaya tana kallon wuyanta yayi jawur da shi hada sawun yatsun hannuwan mutun rudu rudu.. Hakika Ta gigita ta kuma tsorata a yanzu ta ƙara tabbatarwa kanta cewa akwai me son ganin bayan ta? Wanene? Laifin me ta aikata da har ake son kashe ta? Zuciyarta ce ta raya mata cewa zai iya yiwuwa jinnu ne, tafi yarda da abun da zuciyan nata ta raya mata saboda babu wanda take zargin zai iya yi mata haka acikin mutanan da take rayuwa da su,ta dai yanke shawarar zata sanarwa yaya shureim ko dan su nemi mafita a tare. Miryarta na rawa ta furta"Ya Allah ban cutar da kowa ba, Kada ka bada damar da wani zai cutar dani" ta jima atsaye gaban mirror, zuciyarta cike da rudani, ta nufi toilet, tsawon mintuna kafin ta fito jikinta da alamun lemar ruwan da ta watsa ma kanta. Tunawa da kiran wayar da akai mata ne yasa ta nufi bakin gado ta ɗauko phone din ta soma daddanawa call logs ta shiga nan take taga missed call na bakuwar number din nan Sai da ta fara kallon agogo, karfe wani abu na dare kafin ta danna call tana faman zazzare idanunta, jikinta nata kerma kamar wadda aka kada ma mazari Adai dai wannan lokacin Unaisah tana a zaune kan darduma ta zumbula hijabi a jikinta ta ɗaga hannayenta sama fuskarta sharkaf da hawaye bakomai take yi ba face yima danish addu'ar samun lafiya, Batul tana a kwance gefen ta, tun bayan da boss ya tashe su domin yin nafilfilin da za su yi kowannansu bai koma bacci ba, duk suna a dakunansu suna yin sallah, ita dama batul bata da jumurin yin sallah duka raka'a biyu ta samu tayi adaddafe kafin bacci yai awon gaba da ita, shigowar kiran wayar ta ne yasa takai hannu ta dauke ta, a inda ta ajiye ta gefen prayer mat din da suka akai Ko da tayi tozali da layin da take ta dannawa kira taga da shi aka kirata Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin yin picking din kiran, hadi da kara wayar a kunnanta. Tamkar kurame sunyi shiru suna sauraran sautin fitar numfashin juna. Jira take taji wanene mamallakin layin nan daya kira, Haka zalika itama benazir jira take tafara jin wanda ya ɗaga kiran yayi mata magana. Jin shirun yayi yawane yasa unaisah tace"Assalamu Alaikum" sautin daddaɗan muryarta ne ya daki kunnan Benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faɗuwar gaba ba. Muryarta babu nutsuwa ta amsa mata sallamar"Wa'alaikum Salam, barka da dare, dan Allah zan iya sanin dawa nake magana" ta fada cikin ƙagara. Shiru Unaisah tayi tana tunanin wacece wannan matar mai muryar ƴan gayu? Daga ji dai wayayyiya ce. Jin shiru ba'a ƙara magana ba yasa banezir furta"nayi magana anyi shiru b'a bani amsa ba, in ansan baza'a tanka min ba meyasa za'a takurani da kira da tsakar dare"? Har zata katse kiran Unaisah tayi saurin cewa"Aunty kiyi haƙuri, bakisan wacece ni ba, nima bansan ki ba" Ajiyar zuciya Benezir ta sauke kafin tace"okey, amma meyasa kika kira layina bayan baki sanni ba"! "Nayi kuskurene wurin rubuta number din da zan kira" "Okey" shiru su ka yi, babu mai magana na tsawon mintuna kafin benazir tayi karfin hali cewa"meye sunan ki? Shekarun ki nawa"? ta tambaya ne jin muryar kamar ta ƙaramar yarinya "sunana Unaisah, shekarata goma sha shida, ke fa"? Murmushine ya bayyana akan fuskar benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin farin ciki ba. "Sunana Aunty pretty, Amma fa ni ba yarinya bace, na girme ki, Shekarata talatin da wani abu" Murmushi unaisah tayi ita kanta dadi take ji, duk da halin damuwar da take aciki silar kiran nan ya haifar mata da kwanciyar hankali. "Kiyi hakuri na kiraki bisa kuskure, sannan na katse maki baccin ki" "Kada ki damu, Naji dadin haduwa dake" Shiru sukayi Kamar karsu Kashe kiran haka suke ji. "Baki so na sake kiranki"? Unaisah ce ta jefa mata tambayar . Murmushi benazir tayi don ta fahinci yarinyar batason su daina magana. "Ina so mana, tun da naji muryarki naji kin kwanta min araina, da ace babba ce ke da mun kulla kawance sai dai kin min ƙanƙanta" Cike da zumuɗi Unaisah tace"zan dinga kiranki muna gaisawa a matsayin aunty na, Idan kuma kina da ɗiya kamar ni, ko ƙanwa to ki hadani da ita sai mu dinga zumunci" "In sha Allah, yanzu ki kwanta ki yi bacci kada mommyn ki ta kama ki kina waya da dare, gobe zan kiraki mu ƙarasa gaisawa, Yanzu kinga dare yayi," Kamar karsu rabu, Haka sukayi sallama da junansu, fuskar kowannansu dauke da murmushi. Karatun kur'ani benazir ta kunna a wayar, saboda ta fahimci Kiran wayar da akayi mata sautin karatun kur'ani ya fita shine silar da Aljanin daya shaƙeta ya gudu, Gefenta ta ajiye wayar, ta kwanta tare da jan bargon da zeenatu ta lullu6a da shi, itama ta lullu6e kanta, zuciyarta acike fal da annurin farin ciki, Harta kosa gobe tayi, kodan ta kira Yarinyar su ƙara gaisawa, ita kadai take ta tufka da warwara har ta yanke shawarar zata haɗa yarinyar da zeenatu su dinga zumunci, in yaso ita sai ta kar6i layin maman yarinyar suna gaisawa da wannan tunanin wani baccin ya kuma daukarta. Bayan Unaisah ta kashe Kiran, wani irin daɗi take ji, aranta ta ayyana meyasa nake farin ciki akan matar da bansan wacece ita ba, wata'kil ma maman Sajeed ce, dole gobe in fada mashi munyi waya da matar dake a ruƙe da layin wayarsa, bata koma bacci ba sai da ta kara zuwa dakin danish cikin daren ta leƙa don ganin koya farka, kamar yarda suka barshi haka ta same shi, addu'o'i ta ƙara tofe shi da su ta ruƙo dogayen yatsun hannayensa ta sumbace su, tasha kuka a yayin da take agefen gadon shi ta roƙi Allah akan ya ba man dinta lafiya tamkar zatayi hauka ita kadai a dakin sa ko tsoro bata ji, raba dare tayi tana gadinsa har bacci yafara kokarin daukarta sai da aka fara kiran sallar Asubahi tukunna ta baro dakin tana sharar kwalla..............😥💋✍️ *FRIDAY MORNING* *Hajjaty the head maids* Sautin ringing ɗin wayar pravin ne ya katse mata baccin ta, A hankali ta buɗe idanunta masu dauke da bacci ta kalli ceilling na tsawon mintuna kamar mai nazarin wani abu, sam ta manta da abun da ya farkar da ita daga bacci har saida aka ƙara kira tukunna ta miƙa hannu saman mattress ta janyo wayar ta karata a kunnanta ba tare da ta duba sunan mai kira ba. Bankaɗo kofar toilet da akayine ya firgitar da ita kafin tayi wani yunkuri taji ya fisge wayar daga hannunta, har sai da gabanta ya faɗi ganin kumfar sabulu a jikin shi, Ko sutura babu haka ya fito daga bathroom zindir haihuwar uwarsa, duk dan kada taɗaga mashi waya' juyawa yayi da sauri ya koma toilet, hajjaty dake kallon shi da tsantsar mamaki ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin headboard tana jiran fitowarshi Badajimawa ba pravin ya fito daga toilet waist dinsa daure da towal, fuskarshi babu walwala tunkafin tayi mashi magana yai saurin tarar umfashinta da cewa"Karki kuskura kiƙara gigin ɗaga min waya idan an kira ni, babu ruwanki da wayata" lamarin ya ɗaure mata kai adabarbarce ta furta"laifine idan an kiraka na daga? Anya pravin kana da gaskiya kuwa saboda kawai na ɗaga wayarka shi ne ka fito tsirara daga toilet da ruwan kumfa a jikin ka"! Harara ya galla mata"wannan bai shafe ki ba, Nidai ina ƙara jan kunnanki babu ruwanki da wayata, ban yi maki iyaka da komai nawa ba, amma banda wayata," Kallon tuhuma take jefa mashi, ba tun yau ba ya tsani yaga ta ta6a wayarshi kamar ta tsunkuli ranshi ne. "Kallon Ya isa haka, ki tashi kije ki yi wanka" ta6e baki tayi kafin tace"ba yanzu ba, sai zuwa anjima idan zamu je dinner din Hateem" Ɗaure fuska yayi babu annuri ya furta"ay na faɗa maki, bazan bari ki halarcin dinner ɗin nan ba" "Amma dai dawasa kake min ko"? "Na ta6a yi maki wasa irin wannan"? "Amma meyasa zaka hanani zuwa bayan na riga dana kwallafa raina"? fuskarta a yamutse ta jefa mashi tambayar Shiru yai bai tanka mata ba, taci gaba da cewa"bazaiyiwu ba pravin, matan family din nan gaba ɗaya zasu halarci taron sai ni kadai zaka hana zuwa"? Gaban mirror ya tsaya yana gyara jikin shi, "Dakai fa nake magana"? Sai da ya mula yasha iska tukunna yace"abun da nakeso ki fahimta, zuwanki dinner din baida amfani! Saboda matan family din nan ba kaunarki su ke yi ba, iyakaci suci maki mutunci su zazzageki ni kuma abun da banaso kenan, sannan ni ina kishin kije wadannan dattawan masu gemu su kalle min ke" Kwantar da kanta tayi jikin pillow "Wannan ba hujja bace pravin, meya kawo maganar cin mutunci a taron bankwana da hateem kaima in banda abun ka, sannan kishi da kake ji ay bani kadai bace matar da zanje dinner din ba muna dayawa...." kafin takare magabar ya tari numfashinta da cewa"Amma ay ke kadai ce ba'asan da igiyar aure akanki ba, kowa kallon bazawara yake yi maki, uwa uba kuma surar jikin ki dake jan hankalin su" Saukowa tayi daga kan gadon ta nufe shi, ta tsaya daga bayanshi tare da ɗaura kanta saman bayanshi. "Hubbyna, dan Allah kada ka hanani zuwa, wallahi na ƙwallafa raina akan dinner din nan, ka taimaka min pls nayi maka alkawarin zan kare mutunci na, indai ka yarda dani pravin kabarni inje' da shagwa6a ta ƙare maganar tare da zagayo hannayenta kan waist dinsa tuni yafara jinshi a wata duniyar, ta san duk wata hanya da zata canza mashi ra'ayin shi. Lumshe idanunshi yayi, yayin da yake kallonta ta cikin mirror, tsantsar sonta da kaunarta yake ji, Ɗago dakanta tayi daga bayanshi ta daura kan kafadarsa ta hagu. Suka ci gaba da kallon juna. "Inaso ka faɗamin tsakanin ni da kai waya fi kama da ɗan mu" Shiru yayi tamkar baison furta maganar ya ce "kin fi kama da shi" Murmushi tasaki har dimple dinta ya lotsa "Allah ya ji ƙan shi" ya amsa mata da ameen. Sumbatar wuyanshi tayi, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba "Zaka barni inje babyna"? Baiyi niyar barinta taje ba, amma yanayin da tayi mashi maganar yasa shi amincewa batare daya shirya ba. Wani irin farin cikine ya lullu6eta shi kanshi ya shaida hakan "Atare dakai zamu je ne"? "No,ni ba lallai naje ba," "Amma yakamata kaje kaima zaiji daɗi, kaga daga yau shikenan gobe ba lallai ka samu danar ganawa dashi ba may be tashin asuba jirginsu zai lula" Janyo hannunta yayi ya dawo da ita ta gabanshi, yadda zaiji dadin kallonta dakyau "Nima zanje in sha Allah" "Bari na taimaka maka ka idasa shiryawa, nasan hajiya Saratu tana can tana dakonka, daga zuwa sallar asuba ka gudo dakina" "Matar da bata damu dani ba, ni fa banda amfani awurinta... " bata bari ya karasa maganarba ta rufemashi baki, don bata son yana aibata hajiya saratu awurinta. Shirye shiryen sun kankama, Don tun wuraren ƙarfe tara na safe Zungureriyar motar kamfanin su zahra mai ɗauke da tambarin Zahra World of beauty ta karaso estate din, kafin shigar motar sai da Security officers su ka yi mata wankan tsarki ciki da bai suka bincike komai da na'urorin tsaro, hatta Interior designers din dake a cikin ta ƴan matasa mata sai da Sojoji suka bincike su from head to toe, suka tabbatar ba su shigo da wani abun cutarwa ba, kafin suka bar motar ta shiga ciki, Hajiya saratu ce ta tsara lokacin da za'a fara aikin decoration din dakin taron saboda friday ne kurarran lokaci kwara ay komai da wuri acewar ta Masu aikin gidan kuwa tun asuba suka fara ɗaura girke girke, saboda uban aikin dake gare su, abinci ne za'a girka kala kala, Na ƙabilu daban daban, kafin kace me cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshi ya gauraye ko'ina na gidan baba obie, don anan ake aikin girkin.... Hajiya zahra kuwa yau tsabar murna kamar wadda akaiwa albishiri da gidan Aljana, tun jiya akayi mata saloon da kunshi na jan lalle kamar amarya, taci buri akan dinner din nan kamar ranar auranta, Saboda son ta dau gayu na kece raini motar Aneelerh ta ara da yake tafi tata motar tsada da kyau, Tuni taba mahboob motar ta hada shi da ƴan canji ya tafi kai ta wurin da za'a wanke ta don ta ƙara kyau, kowa na gidan sai da yasan da zancen zuwan Zahra Obie estate saboda ta addabi kowa duk bayan ƴan mintuna sai ta kalli agogo burinta lokaci kawai lokaci ya ci ka.... Ƙarfe 9 na safe, Zeenatu tana a zaune kan mirror chair, tana ƴan shafe shafen ta, bata jima da fitowa daga wanka ba, jikin ta sanye da bathrobe mai kyan gaske, ta ɗaure gashin kanta Fitowa benazir tayi daga toilet da alama itama wankan tayo, ta yi daurin gaba da towel, fuskarta babu walwala ta kumbura jawur da ita saboda kukan da tayi adaren jiya da abun nan ya faru Ganin zeenatu dake ta shafa powder yasa ta ɗan saki face din ta da zolaya tace"uhum su baby shuriem wa ake ma kwalliya" kunyar maganar Benazir yasa tayi kamar bata ji me tace ba Gyaran murya benazir tayi still bata ɗago ba, saima ta ɗauki jan baki tana shafawa "Wato kinyi imanin sai kin zautar min da yaya na"? Cak zeenatu ta tsaya da shafa jan baki, cike da jin kunyar benazir ta sunnar dakai ƙasa "Duk hasken da Allah yayi maki zeenatu har sai kin ƙara da powder in ban da asara, so kike ki koma zabayyana ne'? dariya ce ta kubce ma zeenatu har fararen hakoranta suka bayyana masu kyau da tsari Muryarta ƙasa ƙasa tamkar ta mai yin raɗa ta furta"aunty benazir mommy ma tana shafa powder in zata ma daddy kwalliya, shiyasa nima nake shafawa" dariya benazir tayi hadi da ɗan girgiza kanta.. Wucewa wurin closet din dakin tayi domin shirya kanta, within minutes benazir ta fito asanye da riga da skirt sun ɗan kama jikin ta Gaban madubin ta tsaya daga gefen zeenatu tana fadin"naga abun naki bamai karewa bane, ki tashi ki je ki sanya kaya, kafin darling din naki ya farka daga bacci" cike da jin kunyar maganarta, zeenatu ta miƙe tana faman sakin murmushi sai da tafara daukar hijab dinta dake ajiye bisa gado kafin ta nufi hanyar fita dakin don taje nata dakin ta sanya kaya Fitarta ke da wuya suka yi kici6us da dr shureim wanda ke kokarin doka sallama, tun da ya sauke idonshi akanta ya kasa janye su, cikin jin kunyarsa ta sunnar da kanta kasa tana faman noƙe kai ta furta"yaya shurem ɗina ina kwana, fatan ka ta shi lafiya.. ' ta faɗa la66anta na dan kerma without looking at him Gogan naka ya kasa magana saboda kyanta da ya dauke ma shi hankali Muryar ta da shagwa6a ta furta ya shureim ina magana ka share ni... Lumshe idanunsa yai yayin da yake shakar kamshin turaren dake fesowa daga jikin ta Muryarshi can ƙasa makoshi ya furta" nabd alqalb (نبض القلب) kin yi min kyau ban yi tsammanin idanuwana za suyi min tozali da kyakkyawar fuskar ki ba..." arude ta maimaita kalmar nabd alqalb ta dago tana zare mashi blue eyes din ta, muryarta na ɗan rawa ta furta"ya shureim bansan me kake nufi ba" Side smile ya sakar mata, tare da matsawa dab da ita, tamkar zaiyi mata raɗa a kunne ya furta"Bugun zuciyata" farfari tayi da idanunta wani irin farin ciki Ya lullu6eta Batai wanai aune ba taji ya manna mata sumbata saman soft cheek din ta' waro idanu tayi a ruɗe ta watsa da gudu ta nufi hanyar bedroom din ta Bin bayanta yayi da kallo tamkar yabi ta haka ya ke ji "Yaya Shureim kaine? Yaushe ka zo shine baka min sallama ba" kamar daga sama yaji muryar benazir firgigit yai tare da dubanta Yana kokarin bude baki yai mata magana karaf idanunsa suka sauka akan shatun yatsun hannun dake akan wuyanta ruɗu rudu fatar wurin tayi dabra dabra jawur, gabansa ne yayi wani irin mugun faɗuwa ji kake rass Benazir bata lura da abun da yake kallo ba, gaba ɗaya ta faɗa kirjinshi ta rungume shi haɗi da manna mashi peck kan kuncinsa, irin gaisuwarsu ta larabawa Idanunsa a zare yake kallon fatar wuyanta, kafin ya daddage ya ɗaura tafukan hannayensa kan kafaɗunta ya ɗago da ita "Benazir! " da karfi Ya ambaci sunanta "Me nake gani akan wuyan ki"? Ya jefa mata tambayar Farat ɗaya ta gane me yake magana akai, da sauri taja hannun shi suka shiga dakin gudun kada wani yajiyo su "Tambayarki nake yi kinyi shiru baki ce komai ba!" adan tsawace ya furta maganar Batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka ba, cikin shessheƙar murya ta labarta mashi abun da ke faruwa tun daga rana ta farko da aka fara kawo mata hari Ranshi yayi mugun 6aci na kin fada mashin da batayi ba, In a breaking voice ya furta"shi ne baki faɗa min ba"? "Yaya shureim bansan wanene yake son rabani da rayuwana ba, bansan meke shirin faruwa dani ba, na 6oye maku ne saboda ban dauki abun serious ba, da farko nayi tsammanin mafarki ne, ashe ba haka bane so ake akashe ni yaya shureim bansan zunubin dana aikata ba.... ' ta ƙarasa maganar tana faman shessheƙar kukan, Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, ya gaza yarda da abun da idanuwanshi suke gane mashi Ɗaura yatsun hannayenshi yai akan wuyan nata ya shafa shi a hankali, runtse idanunta tayi saboda raɗaɗin da taji, ganin hakan yasa shi janye yatsun sa Yama rasa tunanin da zanyi dangane da bakon al'amarin nan Ruko hannayensa tai acikin nashi tana cigaba da kuka take fadin"yaya shureim ka tayani da addu'a, bana son in mutu ban hadu da mijina da ƴata ba, yaya shureim ka taimaka min idan ba haka ba wata rana za'a iya farkawa ataras da gawata, jiya ba don kiran da akayi min ba har sautin karatun al'kurni ya fita da tuni na jima da mutuwa... Bai bari ta ƙare maganar ba, Ya toshe mata bakinta da tafin hannunsa Kwantar da kanta yayi kan chest dinsa muryarsa kasa kasa yake ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un yayin da zuciyarsa ke dakan uku uku!!! "Yaya shureim ko dai aljanune suke son kashe ni? Idan ba su ba to waye zaiyi min hakan a gidan nan? Babu wani bare a cikin mu, sai house maids da security officers, babu abun da ya ta6a haɗani da wani daga cikin su, bansan su ba, balle har ace na aikata wani abu ne da zaisa a nemi rabani da rayuwana...... ' cikin jin kunar rai ta furta maganar. "Yaya shureim dan Allah mubar gidan nan, dama saboda mu haɗu da aneeleerh ne yasa na ƙwallafa raina akan zuwa, tun da ban samu hanyar da zan hadu da ita ba, mu koma gida zai fi min kwanciyar hankali na...." Tuni idanun dr shureim sun cicciko da hawaye, yai matuƙar girgiza da jin abun da ke faruwa da yar uwarsa tabbas yana ji aranshi wani abu ne ke shirin faruwa da ita, dole ya miƙe tsaye don ganin ya ceci rayuwarta *(Mu haɗu Jibi Alhamis Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya, Don jin Yadda zata kaya)* *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 11 Complete by Novels Elite Admin May 26, 2024 Sponsored Link _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القدر💋✊ ~Takun Ƙarshe🔥~ قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘Best gifts for your loved ones An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘Best gifts for your loved ones Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Shafa sumar kanta ya soma yi cikin sigar lallashi ya furta"Allah yana atare dake, duk wani mai neman ki da sharri kanshi zai koma, bi'iznillahi bazan bari wani cutar min dake ba a karo na biyo, zan yi iyakar bakin kokarina don ganin na baki kariya da ayar Allah, zan iya hana idona bacci don inyi gadin ki a kowani dare kafin lokacin da zamu bar gidan, Inaso ki kwantar da hankalin ki, bana so ki sanya damuwa aranki, mu bi komai a hankali don ganin mun gano wanene ke yi maki hakan, bana son jin maganar nan abakin wani, kibarta kawai daga ni sai ke!!" kwantar mata da hankali yaci gaba dayi, tare da karfafa mata gwiwa har ya samu ya shawo kanta.... *💋CHIEF OWAIS💪* Kasancewar Jiya bai samu isasshen bacci ba, sakamakon nafilfilin da ya tsaya yi, hakan ya haifar mashi da jin matsanancin bacci mai nauyin gaske, tun wuraren ƙarfe bakwai na safe Daddy sharafudden yake ta faman zarya zuwa room din shi don ganin koya farka amma shiru har ya tafi office dinsa dake anan cikin Villa..... Wayarsa ce ta soma yin ringing, da zarar ta katse wani kiran ke shigowa, da wata irin kasalar bacci ya buɗe eyes dinsa wadanda suka canza launi, addu'ar ta shi daga bacci ya ambata aransa kafin ya maiƙa hannu ya dauko wayar dake kan nightstand, ba tare daya miƙe daga kwancen da yake ba ya soma duba me kiran nashi, missed calls ya gani har shida, Uku daga Prime minister, biyu daga boss man, lumshe idaninshi yayi kafin ya aje wayar ya sauko ya nufi bathroom, Ƴan mintuna ƙalilan Ya fito waist dinsa ɗaure da towel fari ƙyal, gaba ɗaya ƙirar Ƙarfinsa ta ƙara baiyana, ƙirjin nan nashi acike ya ke da albarkatu. A gaban mirror ya tsaya tamkar mai nazarin wani abu, A lokacin da baiyi tsammani ba kwatsam yaji An rungumo shi ta baya, A ruɗe Yakai idaninsa ga hannun wanda ya rungumo shi, nan take ya sauke ajiyar zuciya dama sai da ranshi ya bashi cewar shi ne. "Daddy ba sallama, har kasa gabana Ya faɗi" Tuntsirewa sharafudeen yayi da dariya ba tare daya raba jikin shi daga na chief ba Muryarsa da tsantsar farin ciki Ya furta"Nayi kewar ka ne sanyin idaniyata, da tunaninka na tafi office, nagaza ta6uka komai shiyasa na dawo don inga ko ka farka, Ina fata ka yi breakfast din ka" cikin kulawa yai maganar yana leken face din sa ba tare daya raba jikin sa daga na shi ba "Ban kaiga yin breakfast ba, saboda ban jima da tashi daga bacci ba" "Hakan na nufin baka samu isasshen bacci ba daren jiya, bana hana ka kaiwa dare kana aiki ba"? ya faɗa yana ɗaure mashi fuska' Chief owais dake kallon daddyn nashi wani irin sanyi ne ke ratsa heart dinsa "Ay min afwa dad, zan kiyaye hakan, nagode da kulawarka agare ni" "Good, yanzu faɗa min me kake son ci insa a haɗa maka" "Bazan samu damar yin breakfast ba, gida zan wuce" juyo da shi Dad sharafudeen yayi suka fuskanci juna "Yau ma kana nufin bazan samu damar cin abinci a tare da kai ba? Saboda kai na hana kaina yin breakfast duk don saboda muci atare, shi ne yanzu kake fada min tafiya za ka yi"? fuskarshi babu annuri Ya furta maganar, "Nayi jiran banza kenan, Bari na koma office, Allah ya kiyaye hanya" Juyawa yayi cikin takun sauri Ya nufi door room Kafin ya buɗe kofar, Chief owais yai hanzarin bin bayan shi, Gaba ɗaya yayi hugging dinshi ta baya "Am sorry dad, kasan bana son Bacin ranka, sannan bansan ni ka tsaya jira mu yi breakfast ba" Lumshe ido dad sharafuddeen yayi, yayin da yake sauraron shi "Lokaci na naka ne daddy, duk wani abu mai mahimmanci yabiyo bayan naka, Idan ma kace kada na fita, wlh ba inda zanje zan tsaya tare da kai ne" daɗaɗan kalamai chief owais yake furta mashi, cikin ƙankanin lokacin zuciyar sharafudeen ta sassauto daga fushin da yayi. Juyawa yai suka fuskanci juna ido cikin ido "Idan na tuna yadda Dan uwana hateem yake kukan rashin ɗa da Allah bai bashi ba, Ni kuma Allah Ya bani ɗan sai dai bamu da lokacin juna, abun ba ƙaramin karya min zuciya yake ba, bana so na bata maka lokaci, Ka tafi kawai, ay zamu hadu ne a wurin dinner da anjima" Girgiza kai chief owais yayi, calmy ya furta"ba zan iya fita ba daddy, idan har banyi breakfast tare dakai ba, ka yi hakuri, ka bari mu yi kawai, daga ni har kai zamu fi samun kwanciyar hankali" Dafa broad shoulder dinsa yai da hannu ɗaya"Ina alfahari dakai bugun zuciyata, kaga kuwa yadda ka kara girma da kyau? Ya fada yana duban jikin shi from head toe, "Da gaskiyar mutane da suke fadin na iya haihuwa" murmushin gefen fuska chief ya dan saki har dimple dinsa na chin ya lotsa wani irin madarar kyau. "Amma dai yau zanga Surukata ko"? ya tambaya yana ɗage mashi gira Jinjina mashi kai chief owais yayi alamar eh "Kasan ban ta6a ganin ta ba, saboda busy da nake shiga, amma tana araina, yau ka tabbatar tazo dinner din nan, Ina son ganin ta, ka kawo min ita gabana in sanya mata albarka" "In sha Allah dad" "Good, Ka shiga ka karasa shiryawa zan jira ka a dining room" amsa mashi yai da toh. Har Ya buɗe kofar zai fita ya ɗan dakata tare da waiwayowa baya ya kalli chief dake kallon shi "zan fada mata, tayi dacen miji," yana fada ya fuce daga dakin, qasaitaccen murmushi chief ya saki, fatan shi kamar yadda kowa ke fadin tayi dacen miji itama tayi alfahari dashi a matsayin a bokin rayuwarta. Da wannan tunanin ya nufi walk-in closet dinsa, within minutes Ya kamma shiryawa cikin Jalabiya launin ocean blue. A dining room ya taras da su gaba dayan su sun hallara, tun daga kan momynsa malikat tare da younger sis dinsa Hindu ƴar matashiya ce da bazata wuce 22 Years ba, Black beauty tana asanye cikin shiga ta jumpsuit Dark navy, kitson zanene akanta wutsiyar gashin har kan shoulders din ta, Allah yayi ta da ruwan kyau kamar ita ta zana kanta, Komai nata ƙaramine ɗan pink lips dinta da Asian eyes din ta, ga dogon hanci, Bata da ƙiba siririya ce, a haka structure din jikinta ba karamin kyau ne da shi ba, Kamannin ta sak dana Mommyn su Gimbiya Malikat Sarauta. ɗaya bayan ɗaya yayi hugging dinsu cikin mutunta juna suka gaisa, kafin ya zauna sukayi breakfast dinsu, daddy sharafudden yaji dadin cin abinci tare da ɗan nasa, har abaki yake bashi bayan sun kammala yayi masu sallama agurguje Ya nufo gidansa. _________________________✍️ A 6angaren su Unaisah kuwa bayan kammala sallar asuba, bacci mai nauyi yayi awon gaba da su kamar matattu, har wurin karfe tara babu alamun zasu farka, ummi sai faman yin zarya ta ke yi daga dakin ta zuwa nasu don ganin ko sun farka, saboda tana son ta fara gyara masu jikin su, ganin baccin nasu bamai ƙarewa bane yasa tabi su ɗaya bayan ɗaya ta farkar da su, wani abu da ya ɗaure mata kai, duk wanda ta tada daga cikin su sai taga ya watsa da gudu ya nufi upstairs second floor, da sauri tabi bayan su don ganin ina za su je, a dakin danish ta same su zuƙunne bakin gadon shi suna kuka kamar ran su zai fita, hankali a tashe ta tambaye su meya faru suke kuka? Cikin shessheƙar kuka suka ce mata meyasa danish din su bai farka ba? Sun hana idon su bacci jiya sun roƙi Allah akan ya bashi lafiya amma shine Allah bai kar6i addu'arsu ba bayan wahalar da su ka sha ko dan saboda danish baiyi imani da shi ba ne....." waro idanu waje ummi tayi tana kallon su, ita dai unaisah ko magana ma takasa furtawa lamarin yafi karfin ta ashe har yanzu akwai sauran rina akaba, abun ka ga masu ƙarancin ilmin addini Lallashin su ummi da unaisah suka dinga yi suna basu baki, akan su yi hakuri su daina fadin hakan babu kyau, gaggawa aikin shaidan ne, indai sunyi imani da Allah to su bi komai a sannu in sha Allah ɗan uwan su zai farka..." daƙyar su ka shawo kansu har suka samu komai ya lafa, ta sanya suka fito daga dakin ta rufe mashi ƙofa Ko da aka shirya masu breakfast kasa ci su ka yi saboda fargaba da zullumin kada su rasa ɗan uwan su, Hankalin ummi duk ya tashi saboda tausayin su da ya kamata, Kamar marasa lafiya haka suka koma, lalla6a su ta dinga yi har ta samu suka ci abincin kaɗan bayan sun gama ne ta tarasu a falo ta fada masu dangane da Farewell dinner din da zasu halarta na uncle din chief, sun ji dadi yau zasu shiga cikin family din chief koba komai zasu ɗebe kewar abun da ke damun su, duk cikin su mutun ɗayace batayi farin ciki da fitarsu ba, hakanan take jin gabanta na faduwa, babban abun da take jimawa ba lallai su samu kar6uwa a wurin family din chief ba, bugu da kari rashin wayewar ƴan uwanta, yafi komai ɗaga mata hankali, tana jin tsoron su shiga bainar jama'a su yi kauyacin da zaisa a gane jahilcin su harma a goranta masu ko a ƙyamace su. Hankalinta sam yaƙi kwanciya, har sai da taja aunty umminsu gefe ɗaya ta faɗa mata abunda take zullumi tace tana neman alfarmar abarsu su zauna a gida kada aje da su wurin dinner din nan. Ummin tace ta kwantar da hankalin ta, ba abun da zai faru saboda basu kadai zasu tafi ba, hada su boss man kuma tasan bazasu bari a wulakanta su ba awurin taron zasu basu kariya, sannan tasha jin labarin familyn obinna mutanene masu karamci da daraja ɗan adam don haka kada ta sanya damuwa aranta in sha Allah zasu samu kar6uwa a wurin su. Jin wannan maganar ya sa hankalin ta ya kwanta, Har ta fara zumuɗin lokaci ya cika don atafi da su. Ba tare da 6ata lokaci ba, Ummi ta tattara matan suka shiga Home beauty saloon din gidan, domin gyara masu jikin su, mazan kuma taj ne ya tafi da su 6angaren jami'an isod na gidan acan za'a gyara masu sumar kansu, ɗaya bayan ɗaya ta wanke ma kowan nan su sumar kanshi tagyarata tsaf tayi masu hair style kala kala, Unaisah da batool kalar nasu gyaran gashin all layers around ne yayi bala'en yi masu kyau sumar kan har kyalli take yi tana ɗaukar ido saboda mayukan da aka yi masu amfani da su, gashin ya ciza launin shi dark brown yayi washar washar da shi daga baya ya lullu6e wuyansu da tsakiyar bayansu kamar hijabi, Azeeza da jemimah kuwa kalar nasu styal din braided bun ne, wanda ake dunƙule gashin daga tsakiya sai kaga ya yi kamar donut, gyaran gashin su yayi kyau sai ya ƙara fito masu da beauty baby face din su, sun fito a jar fatar su ta turawa, Parveen da Hannah su nasu gyaran gashin Classy ponytails ne yara sun fito suffarsu ta kyawawan ƴan mata, Sai farin ciki sukeyi tamkar babu abunda ke damun su, bayan an gama gyaran gashin, ummi tafara gyara masu kafafuwansu da akaifinsu, Hakiƙa tayi kokarin yadda kasan ƴa'ƴan ta haka ta dinga tsaftace su ciki da bai, har hakoransu bata bari ba sai tayi masu amfani da tooth care product wurin wanke masu su, dalilin dayasa take yi masu gyara duk da boss yace kayan da za'a sanya masu ya zamanto sun lullu6e ko'ina na jikin su, ita tasan ba yadda za'ay a shiga da yaran nan wurin dinner ta prime minister ba tare da security din dake tsaron wurin su sanyasu cire mask din fuskarsu ba, shiyasa ta dage damtse wurin gyara su, don agansu da mutuncin su, saboda itama maganar unaisah ta sosa ranta, batason ayi masu kallon ƙasƙanci, harta fatarsu sai da ummi tagyare masu ita, Kamar Ƴa'ƴan Furanni saboda tsabar Kyan da su ka yi, ita kanta da take kallon su ba karamin tafiya da imanin ta suke yi ba, inaga idan suka shiga wurin dinner din tabbas zasu Ja hankalin jama'a, Bari dai in takaice maku zance, Ummi har yadda zasuyi magana ta ƴan gayu wayayyu da yadda zasu yi tafiya mai jan hankali sai da ta koya ma su, duk don kada suyi kauyacin da za'a tozarta su, sai wuraren sallar Juma'a ta sallame su tace suje su yi sallah after sun kammala su kwanta su huta kafin lokaci ya cika, A lokacin itama daki ta shiga don ta yi sallah ta kuma kwanta ta huta, fatanta Allah yasa taj ya nema mata alfarma a wurin chief ko ta samu ta fita yawo anjima Badajimawa ba, Su sajeed suka dawo atare da taj, Wa'iyazubilla yadda kasan mazan hurul aini a kyau, Musamman masu tarin sumar cikin su, Sajeed da Naufal sai Javed, wani hadadden gyaran suma akayi masu irin na gayun nan, yadda kasan ya'yan wani shege mai ji da naira, shi kan shi haris da bai kai su sumar kai ba, gyaran gashin da akayi mashi ya kara fiddo mashi da Inner beauty dinsa, bayan taj ya rako su sun dawo gidan basu taras da ƴan uwansu a falon ba duk suna a daki suna hutawa A falo suka zauna suna jiran lokaci ya ƙarasa cika, dadi suke ji za'aje da su wani wuri kamar su zuba ruwa ƙasa su sha tsabar murna. *DINNER HALL* Wuraren karfe huɗu da wanu abu. Katafaren Ɗakin taro ne dake a cikin Obie Estate, Aljannar duniya ce mai zaman kanta, saboda tsabar haduwar Hall din idan Ka shiga ciki gaba ɗaya zaka rude ka kasa tantance a ina kake ma, musamman a yanzu da yasha uban decoration an kawata shi da kayan ado masu ƙyalƙyali da ɗaukar ido, gaba ɗaya kewayen hall din Fusatattun sojoji ne majiya ƙarfi ke tsaron shi tare da Canadian polices ga kuma gwarazan jami'an Isod, bayan ga wadannan jami'an hada na'urorin cctv dake a kowace kusurwa har ta cikin fitilun lantarki da jikin kofafi, ciki da wajen ɗakin taron domin ba su tsaro daga dukkan wani abun cutarwa, yadda aka sanya tsaro a hall din bana tunanin ko sauro zai iya haura ƙafa Ya shiga batare da alburushin bindiga Ya tarwatsa kan shi ba, Entry way na shiga hall din tana a cikin Garden din gidan An kawata saman ta da gefenta da adon string lights mai walwali da daukar ido, ga wani shamfidaddan carpet da zai isar dakai cikin dakin taron lallausan gaske daga saman Entry door din anyi wani rubutu da adon furanni aka sanya *Welcome to the farewell dinner of Prime minister Hateem Obinna* Idan muka koma cikin hall ɗin kuwa sai dai muce masha Allah, Zahra world of beauty interior designers sun baje basirar su wurin ƙawata cikin ɗakin taron, wasu haddun dinner tables ne rukuni rukuni a kalla sun kai set hamsin kowani table yana a kewaye da rantsastsun kujeru masu nunfashi zubin bean bag chairs, daga kan kowani table an ƙawata shi da Centerpiece wanda ya kunshi Glass candle sticks An kunna wutar su gawanin ban sha'awa a kewaye da containers na furanni launuka daban daban, ga wasu jerin Crystal glasses ƴan uban su masu ɗaukar ido, bayan su kuma akwai Silverware and napkins with table ware a kowani dinner table hada menu card ajiye bisa tables din, komai fa ya tsaru ga wasu Crystal Sparkling chandiliers masu haskaka tsakiyar ɗakin taron da wani irin twinkling lights hakan baƙaramin ƙawata ɗakin taron yayi ba, ga wata ni'ima dake kurɗaɗowa ta cikin na'urorin A.c mai ratsa sassan jikin mutun, idan muka koma 6angaren abun da za'aci hohoho duniyar dadi wato daga can 6angare guda dinner buffet ne jerin nau'ikan abincine da aka killace su a cikin chafing dishes wato wani irin aroma ne ke tashi na daddaɗan kamshin abinci mai cika makoshi, ga jerin large glass bowls na kayan marmari da zungura zunguren glasses na Juice masu sanyi komai fa an tanada, babu ce kadai ke babu a dakin taron, anyi 6arin dollar, naira kuwa ta raina kanta a wurin, dukiyace aka narkar wurin ƙawata ko'ina, idan kuwa nace zan fayyace komai dake a hall din tabbas zamu ƙare takun karshe ne wurin kwatanta haduwarshi shiyasa na takaita da bayani don mu shiga kaitsaye cikin taron. Sannu a hankali danƙara danƙaran motocin su na alfarma zubin Mercedes benz S. Class suka soma shararowa izuwa cikin garden din a jere suke tafiya yayin da jami'an sojojin dake take masu baya suke bin motocin da kafafuwansu suke tafiya gefe da gefen su, hannayen su ruƙe da jibga jibgan bindigu ga wasu kuma soke a qugunansu sai faman mazurai su ke yi, tamkar a filin daga. Ƙarasowar motocin ke da wuya A hanzarce Sojojin suka buɗe back seat na motar farko, A hankali sheikha mujeedat ta zuro kafarta dake asanye cikin hadaddun takalman alfarma wadanda kudinsu kadai ya ishi wani talakan jari, kafin ta ƙarasa fitowa tabarakallahu ahsanun khalikin gaba ɗaya sojojin dake a wurin saida suka saki baki kamar lehen sakarai saboda tsabar kallon ta a fakaice. Embellished abaya ce a jikinta launin royal blue anyi mata adon stones work, fuskarta tana asanye da Gold chain mask, adon dake akan fuskarta kaɗai abun kallo ne, tayi masifar haduwa, daga ƙasa har sama ta ca6a ado nasu na sarauta tamkar ɗawisu a fagen haɗuwa, bata jima da fitowa ba, jami'an suka budewa Prime minister hateem other side din motar ya fito tamkar tauraro a cikin taurari yayi shiga na mutunci, hadaddiyar shadda ce a jikin shi gezna launin blue anyi amshi senator style abun ka ga dogon namiji ga kira kayan sun zauna mashi kamar a jikin shi aka dinka su, wata expensive watch ce a hannunsa sai kyalli take tana daukar ido, Yatsun hannunsa na sanye da zoben azurfa mai shegen kyau, sumar kannan tashi tasha gyara har ta gaji da haduwa, Bayan fitowarsu motar dake abayansu tasu Yazrin da Nazli ce, Lokacin da suka fito Kiris Ya rage zuciyoyin wasu su buga saboda tsabar haduwar wankan dasuka dauka na emirati abaya launin Silver, kowaccensu ta manna glasses a idanuwanta, ga adon gold knucles rings dake a yatsun hannayensu, sun yi rolling veils a kansu yadda kasan asace su saboda kyau. Bayan fitowar su Nazli, sojojin suka cigaba da buɗe ma sauran motocinsu, gaba ɗaya zaratan samarin family din maza da iyayensu ankon shadda gezna su ka yi, matasan ƴan matan kuwa arab abaya suka sanya masu kyau da tsada na alfarma na kuma kece raini da fita tsara, wasu sun sanya lace abaya, wasu embellished abaya wasu open front abaya, wasu kaftan abaya, wasu egyptian abaya kowa da kalar nashi wankan, kowaccen su tayi lagin gyale akanta, wasu ma babu gyalen zallar sumar kansu ce har gadon baya kamar indiyawa, duk wadda ka kalli wuyanta zaka ganshi manne da ziririyar sarka ta diamond wasu kuma ta zinari, gayu mutanan Allah, Hajiya saratu fa ta dauki kur adakanta rantsastsiyar dubai abaya ce a jikinta tsadaddar gaske launin maroon rigar harta gaji da haduwa abunka ga manyan mata masu dirin jiki kayan sun ladabtu a jikin su kamar donsu aka kera su, kwansu da kwarkwatansu suka jera izuwa cikin hall din, iyayen su maza kowannansu yana ruke da hannun matarshi, wani irin daddaɗan sautin kiɗe kiɗe da raye raye ne ya karaɗe ko'ina na ɗakin taron, Hada wani irin busa tamkar na sarewa Suna tafiya suna taka rawar dattako, cikin nishadi da raha, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki da annushuwa. Prime minister Hateem ne yafara shiga hannun shi ruƙe dana gimbiya mujeedat, daga bayan su Nazli da Yazrin ne, bayan su sai Mai girma sharafuddeen shima ya shiga hannun shi ruƙe dana gimbiya malikat, ɗayan hannun nashi ya ruƙo hannun uwargidansa Hajiya laurat daga bayan su Chief Owais ne wanda zan iya cewa shine farkon haduwa saboda kyawun surar shi, Shaddar jikin shi ta bayyana zazzafan kyanshi kamar shi ya ƙera kanshi, hannun shi yana a ruƙe dana kanwarshi Hindu itama ta dauki wankan abaya. Bayan wucewarsu Sir mubarak Ya shigo hannun shi ruke dana Mom turai, daga bayan su Zaki ne tare dr Jazz sai Ibad. Fuskar kowan nan su da fara'a, bayan shigarsu Senate lateef ya shigo shima tare da Mom madina hannun su ruƙe dana juna, Yayin da zulaihat da Ziyad suke abiye da bayan su. Abun gwanin ban sha'awa, bayan suma sun shiga His excellency abdul Razak ya shigo tare da her excellency Muhibbat, suma sun dauki nasu wankan, atare da ya'yan su suka shigo Captain Yaseer da Yusra. Daga su sai His excellency Deen Ya shigo fuskar nan awashe da annuri yayin da yake a ruƙe da hannun her excellency Hajiya Jameela, daga bayan su Dr nawaz ne da ɗan uwansa justice Nadeem sun dauki nasu adon. Basu jima da wucewa ba, Hajiya saratu tamu ta mutunci ta shigo hannunta ruƙe dana Pravin sunyi matuƙar haɗuwa abunka ga ba'indiye shaddar tayi mashi kyau. Daga bayan su Twins ne zayn da zayn wohoho wanka Yabi jiki, na madina masu kamshin zamzam tsayawa fasalta kawunsu a cikin shadda 6ata baki ne, Hannayensu na ruƙe dana kanwarsu Faryat, ta ca6a uban ado ciki riga red colour duk matasan wurin babu wadda tayi shigar fitsara irinta, abayar jikinta ta matse kirjinta, ko arziƙin ɗan kwalli babu akanta sai zallar kitson kalabarta, gaba dayan ƙamshin turaren su ya gauraya da na iskar A.c wata irin ni'ima ke tasowa. Har sun nufi inda aka tanadar masu kowa ya nannaɗe rigarsa zai zauna, kamar daga sama muryar Mc ta katse su da cewa"ban bada iznin a zauna ba"! Gaba ɗaya suka kai idanunsu gare shi don ganin wani isasshen ne mai walkin Sa, Ruke yake da mic can saman step fuskar nan ta shi a murtuke tsoro tukuf da shi, gashin kanshi duk hurhura hatta jagirarsa da gashin bakin shi hurhurar ce ga wani dogon gemu har kan cikin sa, daga ganinsa ɗan drama ne, ganin shi bakuwar fuska yasa suka soma tunanin wanene wannan? Hajiya saratu har ta fara karkata baki zata fara zabga mashi masifa muryarshi ta katse mata hanzarinta Kirari ya soma korowa yana nuna hanyar shigowa hall din da mic din hannun shi, gaba ɗaya suka kai idanunsu don ganin mai shigowa Obinna ne Ya shigo Cikin shiga ta alfarma tare da Babban amininsa Jan kunne. Lokaci ɗaya suka sauke ajiyar zuciya, tare da sakin murmushi, saboda jin yadda ake yabon mahaifinsu bayan mc din yagama da baba obie Ya koma kan prime minister ya soma koɗa shi yana fadin. _Tsakin tama gagara tauna Prime minister Hateem Obinna, Shugaba mai cikakken iko, na Mujeedat ba maza a gabanka. Kasar Canada taka ce, Namijin duniya Taka lafiya, hasken wata sha kallo, fari mai farar aniya, adalin shugaba namu na mutun ci_ sautin tafin hannayensu ne ya cika hall din. Mc din Yaci gaba da yi ma su kirari ɗaya bayan ɗaya "Ina kike 'yar sarki jikar sarki, basarakiya 'yar mun gada, uwar gida sarautar mata, sarauniya ɗaya tak dake mulkar zuciyar hateem, Damisa ki sabo, Sheikha Mujeedat Al Maktoum, Dubai da kewayenta ikonku ne. Damisa kike, kin ki kallo biyu. An gaishe ki uwar Nazli da Yazrin, ku ne yau ku ne gobe, har kullum ku ne. Sukari kuke ba ku yi farin banza ba.....' yayin da yake yi masu kirarin murmushine dauke akan fuskar Mujeedat, duk da kasancewar bata jin hausa prime minister hateem ne ke fassara mata abunda mc din Yake fadi hakan ba karamin dadi yayi mata ba Bayan ya gama koɗa Su gimbiya mujeedat Ya koma kan sauran Iyayen family din yaci gaba da cewa. _Ina ka ke, Sanata Lateef, fari mai farar aniyya, ina ka gane mini His excellency Abdul Razak, farin wata mai haske duniya. Ban manta da kai ba, His excellency Deen, na Hateem. Ku garafa ga manya nan, Soja birgimar hankaka, Sir Mubarak, Soja marmari daga nesa. Soja na gwamna ga rawa ga yaki_ gaba ɗaya filin taron Ya karaɗe da sowarsu, Sir mubarak dai murmushine dauke akan fuskarshi bashi ba hatta mom turai taji dadin yabon da akayiwa mijinta. _ina kake Sharafuddeen, Namijin duniya, An buga dakai an barka, Namijin uban maza, kaga adalin shugaba, nigeria taku ce ciki da wajen ta, Ban manta da ke ba, auta shalele, Hajiya Saratu. Auta ba kya laifi ko kin kashe dan masu gida. Bushiya kike kowa ya kwana da ke ya kwana salati._ Ƙasa ƙasa da murya hajiya saratu tace"lallaima dattijon nan! ya raina min wayau, wato ya rasa dame zai koɗa ni sai da bushiya"? Ta6e baki tayi babu yabo babu fallasa taja guntun tsoki, Ita da ba'ay mata gwanin ta. Cikin mutunta juna suke ƙara gaisawa da junansu ga sautin kiɗa na tashi, sun ɗan jima atsaitsaye suna ta fira cikin raha kafin daga bisani kowa ya samu wuri tare da Iyalansa, gaba ɗaya suka natsu suna sauraron mc Addu'ar buɗe taro ya fara karantowa Innalhamda lillahee, nahmaduhu wa nasta'eenuhu wa nastaghfiruhu, wa na'oodhu billaahi min shuroori anfusinaa wa min sayyiaati a'maalinaa. Mainyah dihillaahu falaa mudillilahu, wa mainyudlil falaa haadiya lah. "Alhumdulillah. Indeed, all praise is due to Allah. We praise Him and seek His Help and forgiveness. We seek refuge in Allah from our souls' evils and our wrong doings. He whom Allah guides, no one can misguide; and he whom He misguides, no one can guide." Wa ashhadu anlaa ilaaha illalaahu, wahdahu laashareeka lahu, wa ash hadu anna muhammadan 'abduhu wa rasooluh. "I bear witness that there is no god except Allah- alone without any partners. And I bear witness that Muhammad is His 'abd (servant) and Messenger." Allahumma salli 'alaa muhammadinwa 'alaa aali muhammadinwa 'alaa aali muhammadin kamaa sallayta 'alaa aali ibraaheema innaka hameedumajeed. Allahumma baarik 'alaa muhammadin wa 'alaa aali muhammadin kamaa baarakta 'alaa aali ibraaheema wa 'alaa aali ibraheema innaka hameedum majeed. Bayan ya kamalla ya soma gabatarwa cikin harshen turanci "We are gathered here today to hold a farewell party for Prime Minister Hateem Obinna, who is a wise and compassionate leader, and a beloved member of the Nigerian community. Though he is the Prime Minister of Canada, he has graced us with his presence and leadership here in Nigeria. Despite his many responsibilities as the leader of Canada, Prime Minister Hateem has shown great dedication and compassion to our community. Prime Minister Hateem, you have demonstrated the qualities of a great leader, and your kindness and wisdom have touched the lives of many. Though we will miss your presence in Nigeria, we know that your work will continue to make a positive impact on our world. Please accept our gratitude and well-wishes as you return to Canada. May Allah bless you and your family, and may you continue to be a beacon of compassion and strength to all those around you. Ya ɗan dakata da yin bayanin yana bin kowan nan su da kallo ɗaya bayan ɗaya, ga dukkan alamu kalaman shi sun tsuma zuciyoyinsu duba da yanayin da suka shiga, jikinsu duk yayi sanyi wani irin kewar prime minister da family dinsa suke ji, Cigaba da magana mc din yayi _Dear Prime Minister Hateem, We love you, and our love for you extends deep into our hearts. It is with heavy hearts that we say goodbye to you, but we must do so, as it is necessary for you to return to your home, May Allah guide you wit your family and protect you on your journey, and may you return in good health to your loved ones_Best gifts for your loved ones Jikin su gaba ɗaya yayi sanyi, musamman prime minister, Idanun shi har sun ciko da ruwan hawaye juriya ce ta hana shi fitar da su, bakomai yake tunawa ba face yaron daya kwallafa rai akanshi, mai girma sharafuddeen dake a gafenshi Ya lura da halin da ɗan uwan nasa yake a ciki, ruƙo hannun shi yayi acikin nasa ya ruƙe gam Yana lallashin shi haɗi da bashi baki. Daga bisani mc din ya gayyaci prime minister daya taso yayi jawabi, jiki ba kwari Ya miƙe Ya hau kan step, cikin sanyin murya yayi magana mai ratsa zuciya, bayan ya gama aka kira gimbiya mujeedat itama tayi nata, Harta su Senate lateef saida suka hau kan step suka bayyana yanayin da suke a ciki na kewar rabuwa da ɗan uwansu, baba obie ma yayi nashi speech din wanda Ya ta6a zukatansu sosai. Daga bisani komai Ya lafa, Sautin kiraɗa ya cigaba da wanzuwa a cikin hall din, Yayin da servers da ke jigilar raba abinci da kayan sha suka soma gudanar da aikin su. "Har Yanzu banga mutuniyarki ba, ko ina ta shiga? Watakil taji tsoron hada kanta da mu ne" Her excellency muhibbat ce tayi maganar tana karkaɗa kafarta, Hannunta ruƙe da glass na lemu tana sha. "Hauka takeyi da zata kawo kanta cikin mu? Ay rijiya ba wurin gaɗar makaho bane, ina nan ina jira inga ta inda zata 6ulo kinsan ba zuciya kare lashe ni nasan zatazo ne" acewar Hajiya saratu, ta fada tana faman tura dambun nama abakinta atsayice take taunsar shi. Ta6e baki Hajiya Laurat tayi tana fadin"ga ɗayar munafukar can, da yake yau tana a tare da me bata kari ko kallo bamu ishe ta ba, Ƴar kan uba, dalla jibi yadda ta ƙankame hannun shi kamar uban wani ya ce zai kwace mata shi" gaba ɗaya suka sanya dariya suna satar kallon 6angaren da su Hajiya turai suke, baiwar Allah sam hankalinta ba akansu yake ba, batasan ma sunayi ba. "Taci albarkacin Yaya mubarak, da wallahi yau saina sa ta raina kanta Allah," Acewar Hajiya saratu Mom madina dake sauraron su bata tanka masu ba, sai dai duk wanda yayi magana ta dube shi. "Mubar wannan maganar, shin ko kun lura prime minister baya fara'a? Ko dai baya farin ciki da dinner din nan ne wai"? Hajiya muhibbat ce ta fada tana faman yamutsa fuska Hajiya saratu tace"kinsan yayan nawa bai cika son surutu ba, duk da kasancewarshi ɗan siyasa abu kaɗan ke takura shi, may be baya jin dadin jikin shi ne" "Anya kuwa? Ni dai nafi tunanin wani abu ke damun shi," acewar Hajiya laurat , Hajiya jamila tace"may be yana kewar family dinsa ne, dole yaji ba dadi in fa suka tafi babu wanda yasan ranar dawowarsu, zamuyi missing din su sosai" Hajiya laurat jefi jefi take wurga idonta ta saci kallon Chief Owais wanda tun shigowarshi hall din yake a hamkimce kan kujera, tare da su Zaki da Justice Nadeem, hankalin shi na akan wayar hannun sa. Hajiya muhibbat ta lura da ita, hakan yasa tayi mata gyaran murya tare da cewa"Lafiya kuwa naga kin kurawa ɗan naki ido," Ta6e baki ta ɗanyi kafin tace"kawai ina mamakin halayansa ne, ni tun da nataso arayuwana ban ta6a ganin baudaddan mutun irin shi ba, mai wuyar sha'ani, kwata kwata owais baya kula ni a matsayina na matar daddyn sa, bansan meyasa ba, babu abun da ke shiga tsanina dashi in ba gaisuwa ba" Kwa6e fuska Muhibbat tayi"kin ban dariya, ay duk rashin sakarwa mutane fuska da baiyi, bai kai wannan yayan naki ba uban ƴan ji dakai, tun lokacin da yake akan mulkinsa har ya sauka ban ta6a ganin hoton shi da fara'a ba...." Hajiya Jamila tace"abun da zance kenan, wlh kamar kin shiga zuciyata, Allah najima ina mamakin Alhaji musa gashi dai namiji har namiji sai dai babu annuri a fuska, Har tambayar kaina na ke yi ko yaya matarshi take iya sarrafa shi? Don kuwa wannan mutumin zaiyi wuyar sha'ani" Hajiya saratu tace"ni kuma wallahi burgeni yakeyi, don bancika son namiji mara kamun kai ba, mai ɗan banzan surutu amma shi daga ganin shi namijin duniya ne, ni har kun tuna min da matar shi muna mutunci da ita sosai lokacin baya" Murmushin gefen fuska hajiya laurat tayi yayin da take sauraron su Babu alamun zata tanka masu, ay tun da suka soma zancen yayanta taja baki tayi shiru. Suna cikin yin fira wayar hajiya saratu tayi ringing daga cikin yar purse dinta, curo wayar tay ta duba me kiran. Miƙewa tayi har suna haɗa baki wurin tambayarta ina zuwa. "Surukata ce ta ƙaraso, tun ɗazu nake jiran ta, Yanzu haka jami'e ne suka hana ta shigowa ciki, Bari naje na taho da ita" Da tsantsar mamaki suka kalli juna, bata bi takansu ba, tayi saurin nufar hanyar fita daga hall din.......... Miƙewa pravin yayi daga mazauninsa Ya nufi area din da bakowa, Ya curo phone dinsa ya danna ma hajjaty kira har sai da ya kusa tsinkewa kafin tayi picking "Me ya tsayar dake ne har yanzu baki shigo ba, gaba ɗaya kinsa bana jin dadin dinner din" On the other hand muryar hajjaty tamkar zata fashe da kuka tace"waren ɗan kunnan da zan sanya ne bangani ba, shi na tsaya nema" Muryarshi da faɗa yace"saboda ibada ne sanya ɗan kunnan ko? "A'a" "Idan kika ƙara mintuna baki zo ba, kada kiyi tsammanin zan shigo da ke, kuma wlh Allah yasa inga kin ca6a wannan adon a jikin ki, Ni da ke ne...." ya faɗa tare da katse kiran ya koma mazaunin sa. Ganin yadda ta ƙanƙame mashi hannu ne yasa shi furta"matsoraci" sunnar dakai ƙasa hajiya turai tayi fuskarta dauke da murmushi Muryar shi tamkar zaiyi mata raɗa yace"Ki tashi kije wurin ƴan uwanki mata ku yi fira" girgiza mashi kai tayi alamar a'a, ɗaure mata fuska yayi"umarni nake bani" hankalinta ba karamin tashi yayi ba, muryarta na rawa ta furta"dan Allah kabarni anan bana sai naje wurin su," harara ya ɗan watsa mata"kada ki bari na maimaita maki" jinjina mashi kai tayi alamar toh, ba don taso ba, ta miƙe jikinta na kerma ta juya tana kallon 6angaren da su Hajiya laurat suke, sai fira sukeyi suna shan dariya, tunawa tayi da maganar da ta gaya mata jiya, ji tayi bazata iya zuwa wurinsu. Miƙewa Sir mubarak yayi a tsanake Ya nufi inda su Prime minister Hateem suke a zaune, ganin ƴan uwan shi maza sunyi mashi rumfa alamar wani abu na faruwa. yana isa ya shiga cikin su Yana tambayar lafiya, Daddy sharafudden dake a ruƙe da hannun prime minister ne yace"baya jin dadin jikin shi, amma da sauƙi, nasan bai wuci damuwar tafiyar da zaiyi bane," gimbiya mujeedat dake a gefen shi gaba ɗaya ta rasa sukuninta sai faman bin fuskarshi take yi da kallo Cikin kulawa senate lateef yace"dan Allah ka daure ka saki jikin ka, Idan baba ya fuskanci hankalin da kake a ciki bazai ji dadi ba, bama shi kadai ba, kalli kaga yarda mutanan ka suke raha cikin dangi" ya faɗa yana nuna mashi chief of staff din shi tare da national security advisor na canada sunyi shiga ta hausawa teburin da suke a zaune anan baba obie da abokinsa jan wuya suke, Sai fira sukeyi musamman da aka haɗo masu da High-end whiskey sun sha sunyi tatul in ka cire baba obie shi kadai ne baya shan giya a cikin su. Lumshe idanu prime minister yayi a hankali batare daya buɗe su ba, shi kanshi baiso yanayin damuwar da yake a ciki ya bayyana ba, ko dan saboda al'ummar da suka taru domin shi. "Idan akwai abun da kake buƙata ka faɗa mana muyi maka shi," acewar his excellency deen ya fada cikin nuna damuwarshi. Daƙyar ya bude idanunshi wadanda suka kaɗa jawur da su Muryar shi ƙasa ƙasa ya furta"lafiyata lou, dan Allah ku kwantar da hankalin ku, kada halin da nake a ciki Ya dame ku" "Taya zamu iya kwantar da hankalin mu bayan kana a cikin damuwa? pls kayi kokari ka danne zuciyarka ko mun samu a kammala taron nan lafiya, duba fa ka gani gaba ɗaya mun taru ne saboda kai" fuskar Abdul razak A yamutse yayi maganar. Sai lokacin Hajiya malikat dake a hakimce gefen su tayi ma Gimbiya mujeedat raɗa a kunnanta"ki ja shi ku ke6e ki ji meke damun shi, saboda ke kadaice zaki iya shawo kan shi" Gimbiya mujeedat taji dadin shawarar malikat. Duban ƴan uwan nashi tayi"idan ba damuwa inason zanyi magana da shi" Ta faɗa tare da miƙewa ta ruƙo hannun Prime minister, da sauri jami'an sirrin dake a cikin filin suna shawagi suka take masu baya don basu tsaro, wata corridor suka nufa an ƙawata ko'ina na wurin abakin ƙofar shiga ɗaya daga cikin resting rooms din dakin taron jami'an suka dakata abakin kofar su kuma suka shiga daga ciki. Duk abun da ke faruwa akan idon chief Owais, ya riga dayasan meke damun uncle din nashi, shi kanshi zuciyarshi ta karaya, "Babban mutum me kake tunanine"? Muryar Justice ce ta katse mashi zancen zucin nashi "Tun da muka zauna na lura baka fara'a meke damun ka ne"? Yamutsa fuska chief owais yayi"bakomai" "Ko ruwa baka sha ba, Kuma nasan kana Jin yunwa" Ya fada tare da janyo glass mai ɗauke da juice Ya tura mashi agabanshi, Ya haɗo mashi da suya, Ba dan yana jin yunwa ba, ya ɗauki glass din ya kur6i lemun wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar shi "Zaki gafa mutuniyar ka," ɗagowa zaki yayi tare da kallon direction din da justice ya ke nuna mashi, hajiya laurat ya hango. "ita kaɗai ce makullin da zata buɗe maka kofar haɗuwa da pretty ɗin ka" murmushin gefen fuska ya saki. "Kana ganin zatayi mana hanya? Ni fa ban ta6a kula ta ba, ko magana bata haɗani da ita" Cike da kwarin gwiwa Captain Yaseer dake a gefen shi yace"ay dolen ta ne tayi mana abun da muke so," "Kwara dai mubi ta lalama, don wlh matarcan da kake gani ba karamar kwaruwa bace, ƙanwar fa Alhaji musa wadata, hmmm baka san shi bane, wlh mutumin nan ba karamin jan wuya bane" acewar justice Ta6e baki Yaseer yayi"ni ina ruwana da wani alhaji musa, ina magana akan kanwarsa ne," "Da yaushe ne zaku yi magana da ita? In ba damuwa ku bani dama ni na tunkareta bayan an gama dinner din" acewar ziyad "Ni nasan ta yarda zanyi mata magana" Captain yace"ay dama kai zaka fi iyawa da ita, don wlh ta ce zatayi min ji dakai, tsaf zan dauke ƴar mutane da mari abainar jama'a" gaba ɗaya suka sanya dariya banda chief wanda hankalin shi ba akansu yake ba "Wlh da kuwa ka kare rayuwarka a gidan kurkukun ƙaddara, don kuwa ta6a matar can ba abune mai sauƙi ba, kai ko shi daddy sharafuddeen ba iyawa zaiyi da itaba, saboda mugun jin kaine dasu ga tarin dukiya da Allah yayi masu" justice ne ya faɗa Ta6e baki yaseer yayi ba tare daya ƙara furta kalma ba Idan muka koma 6angaren Hajiya turai, dake atsaye kamar wadda tarasa galihu fargaba Ya hana ta tunkari su Hajiya laurat, baiwar Allah tayi tsaye ita kadai, Sai faman yan waige waige take yi tana neman jazz tasan shi kadai ne zai share mata hawayen ta Kamar daga sama taji anyi hugging ɗinta ta baya, lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya jin sautin dariyar Hajjaty da sauri ta juyo suka fuskanci juna, tun shigowarta Alhazawan nan Na canada suke bin ta da kallo, musamman abokin baba obie dama yajima da dakon soyayyarta a zuciyarsa. Ita kaɗai ce a filin taron ta sanya Sari na indiyawa, launin red colour, masu ƙyalƙyali, fuskarnan tasha over make up, ga wasu highhills ƴan uban su dake a kafarta, hannunta ɗaya ruƙe da ƴar purse dinta Wani irin farin cikine ya lullu6e mom turai har batasan sa'adda ta kara huggin dinta ba, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"I'm glad to see you hajjaty, kinga yadda ki ka yi kyau?" ta faɗa tare da dago da kanta tana kallon ta Su hajiya muhibbat dake kallonsu ransu ya 6aci sai faman buga tsoki suke yi, sunji haushin zuwan hajjaty ɗakin taron saboda yadda taja hankulan dattawan dake awurin, har takaiga sun rasa sukunin su Ruƙo hannun juna sukayi sai faman sakin mirmushi takeyi kamar wadda akayiwa Albishir da gidan Aljanna "Me kike yi atsaye ke kadai? Sannan naga idanuwan ki sun ciko da kwalla fada min meya faru" cikin kulawa hajjaty keyi mata magana Cikin sanyin murya tace"bakomai, kawai banjin dadin zama nikadai," nan take hajjaty ta fahimci abunda ke damunta Bin ɗakin taron tayi da kallo karaf idanunta suka sauka kansu Her excellency muhibbat Wani irin mugun kallon harara suke jifarsu dashi. Ko ta kansu hajjaty bata bi ba, ta ruƙo hannun Mom turai suka samu wuri kan kujeru suka zauna suna ƙara gaisawa, pravin ne yayi magana da masu raba abinci suka kawo masu shaƙe da table, sai rawar kai yakeyi akan hajjaty don yaga hajiya saratu bata a hall din, ƙarfin hali hada zama wurin su. "Lallai mutumin can, wato don yaga hajiya saratu batanan shine ya zauna yana goga kafaɗa da waccan kilakin" rai a6ace laurat tayi maganar Muhibbat tace"zata ci ubanta ne wlh, ni dama tun fil azal na tsani matar can, ay tun farko kuskuran da hajiya saratu tayi na auran dangin masu bautar shanu ta kawo su cikin family dinta, wlh mutanan can basu da amana, sun iya munafunci da kisisina, ga kwaɗayin abun duniya, nidai fatana Allah yasa bada wata muguwar manufar suke zaune a family din nan ba" Guntun tsoki her excellency Jamila taja tace"takaici ma ya hana inyi magana, dalla jibi yadda ta ca6a ado ko kyau babu, mace kamar Aljanna, ita ala dole sai ta fi mu haɗuwa, kowa ya sanya abaya sai ita isassa mai walkin sa taje ta sanya sari, su kuma wadancan dattawan dake ta satar kallon ta bansan uban me suka gani a jikin ta ba. Hajiya madina na dariya tace"ba dole su kalle taba, mace tana tafiya mazaunai suna jujjuyawa kamar an jera marmarar sakwara" dariya suka saki gaba ɗayan su. Adai dai lokacin Hajiya saratu ta shigo hall din hannunta ruƙe dana zahra, nan fa hankali ya dawo kansu, zarah duk tasha jinin jikinta ganin zaratan samari da ƴan mata maƙil da hall din, duk da itama ba abaya ba, abaya din dake a jikinta irin na can ƙasan closet ne wadanda ake ji dasu ta dauko ta sanya launin skin pink, ta yi rolling veil akanta ga glass data manna, duk tabi ta ruɗe ganin yadda wasu ke kallonta, bakomai ne yasa suke kallon nata ba face ganin fuskar bare, koda shigowarsu pravin yayi saurin mikewa daga teburin su hajjaty gudun kada Hajiya saratu ta gan shi, lalla6awa yayi ya koma wurin su baba obie ya zauna. Sai da ta fara zuwa da zahra wurin su hajiya laurat ta gaishe su cikin girmamawa, da fara'a suka amsa mata taci albarkaci Hajiya saratu da kuwa ko kallo bata ishe su ba "Wacece wannan ko itace surukar taki"? Hajiya jamila ce ta tambaya Murmushi hajiya saratu tasaki hannunta ɗaya dafe da shoulder din zahra tace"kwarai kuwa, to Ya kuka gan ta"? "Masha Allah, kyakkyawa da ita son kowa kin wanda ya rasa, malama zahra sannu da zuwa" muryarta ƙasa ƙasa ta amsa masu. Jan hannunta hajiya saratu tayi"mu shiga ciki" tafiya su ka yi cikin hall din sai faman yan waige waige zahra ta ke yi, fargabanta bata san inda hajiya saratu zata kaita ba. Su twins ta hango kowan nan su ya ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya kan kujeru, tare da Dr Nawaz, wurin su hajiya saratu ta nufa da zahara wadda tuni gabanta ya soma dakan uku uku, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ganin suna tunkararsu "Barkan ku da hutawa" a tare suka dago suna kallon ta "Mom..." zaid ne ya kira sunanta bai karasa ba yai tozali da zahra, Kallo ɗaya zayn yai mata ya kau da idonshi yaci gaba da danna wayar hannun shi, har kwara dr nawaz da dan fara a face din shi "Yawwa ajiya na kawo maku, zahra ki zauna a wurin su, dan Allah ku kula mun da ita" amsa mata zaid yai da toh tare da nuna ma zahra kujera"have a seat," jikinta na kerma kerma ta zauna duk tasha jinin jikinta, sam ba ta so hajiya saratu ta kawota cikin maza ba, Ina laifin wurin ƴan matasan matan family din duk da tasan ba lallai ta samu shiga a wurin su ba. Cikin kulawa hajiya saratu tace"Idan kina buƙatar wani abu, ki faɗa masu zasu sa akawo maki, pls ki saki jikin ki, Idan aka kammala taron zanyi magana dake kafin ki tafi gida' amsa mata tayi da toh Bayan tafiyar hajiya saratu, zaid Ya soma jan ta da fira. "Kamar naso na gane ki" murmushi ta ɗanyi tare da cewa"ina ɗaya daga cikin interior designers din da suka yi aiki lokacin birthday din ku dana baba obie" "Oh yes, I remember now, What's your name"? "Zahra" "You look absolutely beautiful today" still face din ta da murnushi tace"thank u" Dr nawaz ya dube ta daga ƙasa har sama farat ɗaya ya gane ba ƴar masu kuɗi bace sai dai akwai kyau ko dan saboda wannan zai ɗan daraja ta. "Bimillah malama zahra" ya fada tare da miƙa mata glass na ruwa me sanyi ya haɗa mata da plate din chicken kebabs, godiya tayi mashi, harta kai hannu zata sauki glass din zayn ya ɗago da sexy eyes din nan nashi wani kallo ya jefa mata mai kama da harara, gaba ɗaya ta rikice ta fasa ɗaukar komai, ta duƙar da kanta ƙasa. "Are you okey? Ki ci mana" zaid ne ya fada yana ɗage mata gira. Dr nawaz yace"na lura kamar hankalin ta bai kwanta ba, Bari nayi magana da faryat inyaso sai ta koma wurin su ta zauna may be tafi sakewa' Har cikin ranta taji dadin maganar dr nawaz, wayar dake a hannun shi ya shiga dannawa ya kira layin faryat kusan sau uku batayi picking ba, a kira na huɗu ne ta ɗaga. "Ina son ganin ki yanzu ki zo ki same ni" ya fada yana bin hall din da kallo Can Ya hangota, Cikin su Hindu sun zaƙe sai fira sukeyi kowaccen su hannunta ruƙe da glass na lemu. Cikin takun yanga da kwarkwasa Faryat ta nufo wurinsu, tana karasowa ta ruƙe qugu tana fadin"Gani" da gira zaid Ya nuna mata zahra"bakuwar mommy ce, pls ki tafi da ita wurin ku" Wani kallon shaƙiyanci tabi Zahra da shi kafin Ta miƙa mata hannu"let's go" miƙewa zahra tayi faryat ta ruƙo hannun ta suka nufi wurin Ƴan uwanta. "Faryat ina kika kwaso mana wannan" Yusrace ta fada tana nuna zahra da hannu, baiwar Allah jikinta duk yayi sanyi duk zumudin da takeyi na son zuwa ya ragu "Bakuwar mommyne, Yaya zaid ne yace in kawota wurin mu" wani kallo suke bin ta dashi daga ƙasa har sama alamar ba'ajinsu bace, "Barka da zuwa ƴan mata, Zo ki zauna kusa dani," zulaihat ce tayi maganar fuskarta da fara'a, Hakan ba karamin sanyaya zuciyar zahra yayi ba, gefen zulaihat ta zauna, Hindu tace da ita"kina bukatar wani abu naci ko sha"? Ɗaga kai zahra tayi alamar eh, saboda yunwa take, bata ci komai ba kafin ta baro gida Magana tayi da server din dake a kusa da su tasa aka kawo ma zahra lafiyayyan abinci, tare da juices masu sanyi "Zaki iya ci kona baki abaki"? murmushine ya kubce mata jin abun da zulaiha tace Da sauri ta girgiza kai"a'a zan iya ci dakaina, nagode da kulawa" Hindu tace"kada kiji komai, ki saki jikinki, Ki ɗauka kamar kina a jirgi ne mai ya kare" dariya sukayi gaba dayansu cikin raha, zahra har ta fara sake wa "Meye sunanki ne"? Yusra ce ta tambaye ta "Zahra" "Masha Allah, family status fa"? Ras taji gabanta ya fadi aranta ta ayyana komai ya kawo maganar family status? Jin tayi shiru yasa yusra cewa"dake magana" Cikin sanyin murya tace"ɗan iya family" kallon juna su ka yi alamar basu ta6a jin sunan ba, hakan na nufin ba ƴar kowa bace, ta6e baki yusra tayi "Ni sunana yusra, ƴar gidan His excellency abdul razak, Jikar baba obinna, nayi karatu a U.S, na kammala degree dina a 6angaren medicine and surgery, ke fa"? Da izgilanci takeyiwa zahra magana ganin abun nata na neman wuce gona da iri ne yasa Zulaihat yin saurin tarar nunfashin ta da cewa"look Yusra, Ki ƙyale bakuwar tamu ta huta mana, ko ruwa bata sha ba, kin fara tsareta da tambayoyi kamar ƴar jarida" dariyar shakiyanci yusta tayi idonta acikin na Zahra tace"am sorry fa, kawai ina so ne musan juna, amma bakomai, nayi shiru" Kasa cin abincin zahra tayi, gabanta nata faduwa, sam jin kanta takeyi bare a cikin su saboda tarbar da wasu sukayi mata. "Companyn ku ne sukayi decoration din nan ko"? Zulaihat ce tayi mata tambayar jinjina kai zahra tay alamar eh "Masha Allah, gaskiya kuna da kwararrun interior designers, na jinjina maku, nima idan lokacin birthday dina yayi zan gayyace ku" Murmushi zahra tayi har cikin ranta taji dadin yadda zulaihat ta sakar mata fuska ita da hindu daga gani sun san darajar ɗan adam ba kamar Yusra da faryat ba. Sautin kiɗane Ya soma tashi, Mc yaci gaba da kiran Su daya bayan ɗaya suke shiga filin Taron suna taka rawa ta ko'ina sautin shewarsu ne da Dariya yake ya tashi, Bakomai ne Ya burge su ba face yadda mukarraban hateem na kasar canada suka hau kan dance floor suka dinga tiƙar rawa dama sun sha sun bugu har takai masu karo, ga abokin baba obie shima yana tangyal tangyal ya shiga tsakiyar filin Ya dinga tiƙar rawa, Nan fa ƴan mata suka dinga shiga suna yin rawa tare da su..... Tun da aka fara taron Nazli ke a zaune saman wata kujera ta alfarma, ta daura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, fuskarta babu annuri, a tsanake take danna wayar hannunta, lokaci ɗaya ta dakata tana kallon message din da aka tura ma chief owais ta layinta, nan take fuskarta ta canza zuwa tsantsar 6acin rai, tasan bakowane zaiyi mata haka ba face Yazrin, A hankali ta ɗago kyawawan idanunta tana bin hall din da kallo a kokarinta nata gano inda Yazrin ta shiga, Cikin rashin sa'a ta sauke idanunta akan chief owais dai dai lokacin ya ɗago suka haɗa ido da shi, kasa janye idanunta tayi daga kan shi, wani irin kyau taga ya ƙara mata musamman daya sanya shadda a jikin shi, kau da idanunsa yayi daga kan nata, itama ta janye nata, kamar wasu makiyan juna Text ta tura mashi _sakon da aka tura maka ta layi na bani na tura shi ba_ Reply yai mata da cewa"I don't know what message you're referring to_. Shiru tayi tana tunanin me yake nufi? Ko dai bai ga sakon ba. Wani sakon ne ya kuma shigowa wayarta _"Why did you send me a video of you on WhatsApp? Nace maki ina ra'ayi ne? Wani irin bugu kirjinta yayi, cikin sauri ta shiga whatsapp don ganin inda gaske an tura mashi video tana shiga ta taras da aika aikan da Yazrin tayi mata, Dafe kai tayi da hannu ɗaya, ji tayi tamkar ta fasa ihu tsabar takaicin zubda mata ajin da Yazrin tayi _"I didn't send you any video! You know I would never do such a thing. This must be Yazrin's doing!"_ _"I don't care about the excuses, I already understand that you're missing me. If you miss me so much, you know where to find me"_ ya rubuta text din tare da yi mata sending kafin ya ɗaura wayar kan table din gabanshi. Ta wutsiyar idanun shi yake hangota, runtse idanunta tayi tare da cije pink lips dinta, hakan ba karanin ƙayatar da shi yayi ba. Kifa kanta tayi kan laps dinta, yatsun hannunta har kerma sukeyi tsabar 6acin rai. Shin Ina Prime minister? Tun bayan shigarsu resting room, gimbiya mujeedat ta soma tarairayarshi tana kwantar mashi da hankalin shi, ganin yadda yake zubda gumi yasa ta taimaka mashi wurin cire rigar shi, Ya rage daga shi sai yar singlet, atsaye suke gaban mirror suna fuskantar juna. "Fada min meke damun ka"? Ta fada cikin kulawa tare da daura palm din hanunta kan wuyan shi. Har wani jiri yake gani a cikin idanun shi abu kamar jaraba ƙaunar Danish na neman zautar da shi, hatta tempereture din jikin shi ya ɗauki zafi rau kamar mai fama da zazza6i. Sam yakasa fada mata gaskiyar abun da ke damun shi saboda jin kunyar furtawa yake yi "hankalina bazai kwanta ba in har baka fada min ba, kasan tsakanina dakai babu 6oye 6oye, " Ɗaura head dinsa yai kan shoulder dinta, ya daddafe waist dinta da tafukan hannayensa Yana faman fitar da nunfashi da sauri sauri "Idan baka da lafiya zanyi magana a kira doctor ya duba min kai" da sauri ya furta"lafiyana lau," "Taya zan yadda da maganarka? Lokaci ɗaya ka canza kafin mu shigo dakin taron nan babu abun da ke damunka fuskarka da annurin farin ciki amma lokaci ɗaya ka canza mana meyasa? Hatta yanayin jikinka ya dauki zafi rau.... " fuskarta a yamutse tayi maganar Ɗago da fuskarshi yayi tare da kallon ta, ya sanya palms dinsa ya tallabi fuskarta dake asanye da gold chain "Ki kwantar da hankalin ki, kinsan dai bazan maki karya ba, kamar yadda na fada maki babu abun da ke damuna, zuciyata ne ke bata min dadi" Wani kallon kauna ta jefa mashi"ban yarda ba, Ko dai akan wannan Yaron ne na wurin owais"? Da mamaki ya kalle ta jin ta gano abun da ke damun shi "Ai ina lura da duk wani motsin ka, Jiya saboda shi baka runtsa ba ka zauna yi mashi nafila ko ba haka ba" ta fada tana binsa da kallon na kamaka Kamar wani mara gaskiya yayi shiru yana kallon ta "Har hotunan shi ka ajiye awayarka, lokacin da naje tada ka daga bacci naga hoton shi da kake kallo a wellpaper na wayar ka, mijina anya kuwa kana da lafiya? Ta faɗa fuskarta da tsantsar Al'ajabi Lumshe idanun shi yayi bai san amsar da zai bata ba "Akan yaron da bakasan ko wanene ba kake nema ka rasa sarrafa zuciyarka? What kind of crazy love is this? Na ruɗe please ka fahimtar dani' ta fada tana zare mashi kyawawan idanuwantaBest gifts for your loved ones "You don't know who he is, you have no connection to him, so why would you cause yourself so much pain for loving him" Cikin tausasa murya tayi maganar, bawan Allah yayi shiru yana sauraranta ya rasa abun fada.Best gifts for your loved ones "Hankalina ya tashi hubby, kwara mubar kasar nan tunkafin In rasa kanka, Maybe if we distance ourselves from him, you'll be able to forget about him.... " cikin karyayyar murya tai maganar, fuskarta duk ta yamutse. "Idan ma akan rashin haihur ɗa namiji da baka samu bane yasa kake son shi, nayi maka alkawarin zan dage da addu'a akan Allah ya bani ciki na ɗa namiji nima na haifa maka ko hankalin ka ya kwanta, zan kira mahaifina in fada mashi yasa ayi min addu'a...." tuni idanunta sun cicciko tab da kwalla, nan fa hankalin shi ya tashi don ko kadan baison 6acin ran gimbiya mujeedat gaba ɗaya yake rasa sukuninsa, da sauri ya janyota jikin shi. ya rungumeta sosai yana lallashinta, "Na gane kuskure na, ki yi hakuri gimbiyata, nima bayin kaina bane bansan ya akai na kamu da kaunarsa har haka ba, amma tun da baki so na daina, zanyi kokarin mantawa da shi arayuwana....' lallashinta yaci gaba da yi har sai da yaga ta dan saki jikinta kafin ya ɗago da ita. chain mask dinta Ya gyarata mata ganin ya karkace, bayan ya gama suka kalli juna lokaci ɗaya suka saki murmushi, yatsun hannun ta ya ruƙo ahankali ya daura mata soft lips dinsa hadi da sumbatar su, ya kuma dagowa ya sumbaci forehead dinta, sai da ya tabbatar ya faranta mata almost 15 mins, tukunna ya mayar da rigarsa, kafin Yaja hannun ta suka nufi kofar fitowa daga room din, Jami'an dake a bakin door suna jiran su, ganin sun fito yasa suka take masu baya. Suna gab da zasu ƙarasa ga mazaunin su, ba zato ba tsammani Hasken Hall ɗin Ya ɗauke gaba ɗaya duff ko'ina Yayi duhu sai hasken candles din dake a kunne, Hankalin jama'a ba karamin tashi yayi ba, Kowa Ya ruɗe sautin muryoyin su Ya cika hall din Kowa sai tambaya yake yi ya akai aka dauke wutar hall din ko an samu matsala ne "Jama'a wai meke faruwa ne? Meyasa za'a ɗauke mana hasken Hall? Ba'aji ina magana ba ne"! Hajiya saratu ce take ta faman surfa masifa Sautin muryarta yafi na kowa Faryat Har ta fara Fasa masu ihu saboda lalurar dake gare ta na rashin son duhu gaba ɗaya take firgicewa ta dinga kuka tana iface iface, Jazz na jin sautin ta jiki na bari ya shiga laluban ta cikin duhu cikin sa'a Ya cafko hannunta ta ƙanƙame shi tana kuka.... "Wannan wani irin rainin wayau ne za'abar mutane cikin duhu? Hajiya laurat ce ta faɗa atsiwace ran kowa Ya harzuƙa, Hankalin zahra ba karamin tashi yayi ba fargaban ta kada ace Aikin decoration dinsu ne Yajawo matsalar, tuni ƴan hanjin cikin ta suka kaɗa ido ya raina fata, harta fara tunanin zuwa prison. _Kwatsam ba zato ba tsammani, A lokacin da kowa Ya gama rikicewa wani Haske mai ƙyalƙyali daga saman ceilling Ya soma baiyana A hankali Ya ke haskaka bakin ƙofar shigowa Hall din, gently ya dira ƙafarsa kan Polished marble floor din wurin A matuƙar ruɗe suka kai idanunsu kan mai shigowa yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da ƙarfi ƙarfi_ (Mu hadu monday idan Allah ya kai mu da rai da lafiya in sha Allah) *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 12 Complete by Novels Elite Admin May 28, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ 12 سجن القدر💋✊🔥 ~Takun Ƙarshe🔥~ قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Gently ya dira ƙafarsa kan Polished marble floor din wurin A matuƙar ruɗe suka kai idanunsu kan mai shigowa yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da ƙarfi ƙarfi. Lokacin daya ƙarasa shigowa ciki, Gaba ɗaya Suke bin shi da kallo mai cike da tsantsar ruɗani, idanun kowa akan zazzafar surar jikin shi, kasancewar ya sanya face mask hakan ya 6oye ainihin suffar fuskarsa, wato wata hadaddiyar Emirati thobe ce a jikin shi yar ubansu launin Black gold, yadda kasan a jikin shi aka ɗinka ta saboda yadda ta bi shape nasa, ta baiyanar da surar shi mai matuƙar jan hankali, Musamman sick packs din kirjinsa ya fito 6aro 6aro, da murɗaɗɗan damtsensa, abun ka ga dogon namiji komai nashi is exraordinary, farar fatarsa kuwa har wani salƙi take tana walwali, yadda kasan namijin hurul aini tsabar kyau da daukar ido, wrist din hannun sa na asanye da agogo ƙirar Rolex sai ƙyalli take, face mask din dake lullu6e da fuskarshi dai dai ƙasan idanunsa ya rufe kyawawan sexy eyes dinsa waɗanda ke a kewaye da lallausan long eye lashes dark brown sun ƙara ƙawata kyawun idanunsa, yalwatacciyar sumar kanshi kuwa tasha gyara har ƙyalli take, gaba ɗaya gashin an tattare shi an ɗaure yasauka har kan gadon bayan sa, Wani irin sanyayyan ƙamshin turare ne ke fita daga jikin shi mai narkar da zuciya, Hankali fa gaba ɗaya ya tashi da ganin ɗan tahalikin nan, tun kafin ma ya buɗe fuskarshi sun gama girgiza da kyawun shi, kowannansu sake sake yake a zuciyarsa wanene wannan? Daga ina Yake? Zuciyoyinsu ba su gama kiɗima ba, sai da su ka yi tozali da kyakkyawar matashiyar dake shigowa hall ɗin ta bayan shi, wohoho zo ka ga yadda idanu suka koma kanta, from head to toe suke kallon ta, ta ɗauki wankan Embroidery Open front baya, launin black anyi mata adon gold stone works da zanan Red flowers, rigar tayi masifar yi mata kyau, ta yi rolling mayafi akanta, itama fuskarta asanye da face mask take, ƙafafuwanta kuwa Highhills ne jigunanu, Tsabar ruɗani Ya hana kowa na hall din furta magana sai dai su bi da idanu kamar kurame, ko da shigowarta daga gefen shi ta tsaya, Jim kadan suka cigaba da shugowa kowan nan su da face mask, matan cikin shiga ta abaya mazan kuma Emirati thobe ne a jikin su, sai da suka cika su goma sha ɗaya cuff tukunna suka dakata suna kallon kallo atsakanin su da mutanan hall din, ga dukkan alamu bakin su ya mutu, saboda babu alamun zasu furta magana, lamarin ya ruɗar da su, mamakin su ina aka samu wadannan matasan yan matan da samari? Daga gani dai ba yan nahiyar su bane saboda komai nasu is exraordinary, dai dai da yanayin tsayuwarsu abun kallo ne kamar a shirin drama. A ƙalla an shafe tsawon Mintuna ana jifar juna da kallon ƙurulla, daƙyar Hajiya saratu ta samu ƙwarin giwar buɗe baki ta furta"Su wanene ku"? Ta jefa masu tambayar tana mai zare idanu "Bayin Allah daga ina ku ke? Wanene Ya gayyace ku dinner din nan? Meyasa ku ka rufe fuskokin ku da face masks? Hajiya Madina ce tayi maganar a ƙagare da son jin amsarsu Gaba ɗaya mutanan hall din suka matso gab da su, kamar sunga sabbin halittu daga wata duniyar "To ko dai mutanan boye ne? Wai ba zakuyi mana magana ba, kuntsaya kuna kallon mu kun bar mu a cikin duhu"! Da tsiwa hajiya laurat ta faɗa tana tada jijiyoyin wuya. "Anya kuwa waɗannan ba mutanan 6oye bane? Nifa wlh hankali na bai kwanta da su ba, akan me zaku faɗowa mutane ɗakin taro babu sallama? mun tambaye ku su wanene ku kun yi shiru ba ku tanka mana ba, ko dai turo ku akayi ne don ku tarwatsa mana taron mu"! A faɗa ce Hajiya saratu ta kuma yin magana, Hankalin fa kowa Ya tashi wasu sun harzuƙa, su kan su tsabar fargaba ne ya hana su buɗe baki suyi masu sallama, duk sun sha jinin jikin su. Baba obie da Manyan mutanan canada sunyi kasaƙai Suna Kallon su tamkar a shirin drama, sam babu alamun sun tsorata da ganinsu saboda sun san akwai jami'an dake tsaron gurin dole akwai wanda ya gayyace su, sai dai zallar mamakin dake shimfiɗe a kan fuskokin su. Ƴan matasan family din maza da matansu sunyi cirko curko suna kallon su, cike da son sanin su wanene wadannan bakuwar fuskan da suka faɗo masu a hall!!! Mc da ke atsaye ya ruƙe mic sai mazurai yake yana fadin"ga dukkan alamu mun samu baƙi daga jinsin aljanu, suma sunzo taya mu jimamin tafiyar prime minister Hateem, wannan abun mamaki ne da al'ajabi, lallai prime minister ba karamin mai farin jini ba ne......." sai sambatu mc yake yi yana dubansu babu alamun wasa akan fuskarshi, bilhakki dagaske yake koro jawabi, su sir mubarak kuwa jira kawai suke suga iya gudun ruwan wadannan bayin Allahn da suka faɗo masu bagatantan babu sanarwa. Sannu A hankali sautin takalman prime minister ya karaɗe tsakar filin, babu fargaba ko kaɗan Ya nufi inda suke har ya ƙarasa gaban matashin nan daya fara shigowa kafin yaci burki yana bin shi da kallo tun daga sama har ƙasa, hakanan ranshi ya dinga bashi cewar yaron daya jima yana kwaɗayin sanyawa a idanun shi ne, zuciyarshi ce ta soma azalzalar shi da son tabbatar da abun da yake hasashe, a hankali Ya juyo baya ya dubi chief owais dake a can gefe ɗaya ya goya hannayensa bisa ga kirjinsa tamkar baisan meke wakana ba Haɗa ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...? *WAIWAYE A DON TAFIYA* Abun da ya faru, lokacin da Chief ya dawo gidan bai samu kowa a falon ba,, har su naufal da suka zauna sun koma daku nan su, direct Ya nufi bedroom dinsa bayan shigar shi, tsayawa yayi agaban mirror zuciyarsa a cike fal da tunanin ta wace hanya zai iya taimaka ma Uncle dinsa! Saboda yaji tsantsar tausayinsa ganin irin halin da ya shiga na kaunar yaron, bai da burin daya wuce danish ya farka ko dan Ya faranta Ma daddy hateem kafin yabar nigeria.... Yayin da ya ke wannan tunanin Yana safa da marwa a tsakar ɗakin sa Ya shafe kusan Mintuna ashirin, Batare daya samu mafita ba, Yanke shawarar kiran layin ɗaya cikin drs dinsu yayi don azo aduba lafiyarshi wata'kil adace, duk da shiekh Imam Ya ce basai sun kira likita ba saboda rashin lafiyar tasa bata asibiti bace, kawai a lokaci Ya ƙosane daya farkan shiyasa ya yi deciding kiran likita. A firgice ta farka daga gajeran baccin da yayi awon gaba da ita tun bayan kammala sallar azhar, Hannun ta dafe da saitin zuciyarta dake yi mata wani irin bugu tamkar ana dakan sakwara, wani irin faɗuwar gaba ta soma ji, Hankalin ta sam ba'a kwance yake ba, tarasa gane dalilin jin bugun da zuciyarta take yi mata da rana tsaka, kuma ita ba mafarki tayi ba, saukkowa tayi daga kan gadon su, batool dake a kwance babu alamun zata farka, Cikin sauri ta fito daga room dinsu zuciyarta na azalzalarta da taje ta ƙara duba danish dinsu don tana ji aranta wani abu ne ke faruwa da daya daga cikin su shiyasa taji wannan faduwar gaban, kuma bakowa ne ya fara fado mata aranta ba face shi din dama da tunanin shi ta wuni. Gudu gudu sauri sauri ta nufi second floor, ko da ta shiga falon babu kowa. Tana ƙarasawa bakin ƙofar ta sanya hannu biyu ta dafe ta da karfi har sai da ta buɗe kafin ta faɗa a fujajen shigarta keda wuya, idanun ta su kayi mata tozali da abun da Ya figitar da ita, da wani irin faduwar gaba take kallon shimfidar shi. Wata irin zuface take tsastsafo mashi tun daga cikin sumar kanshi take gangarowa har izuwa saman fatar wuyan shi, kyakkyawar fuskarshi ta jiƙe sharkaf da gumi, hatta jallabiyar jikin shi ta manne ma fatarshi saboda ruwan zufar daya jiƙe ta, muryart na kerma ta soma kokarin ambaton sunan shi. "Dad...da..nish" bata ƙare maganar ba, ganin yadda yatsun hannayensa dana ƙafafuwansa suka fara kerma tamkar na wanda sanyi ya kama. Kasa samun nutsuwa tayi, har batasan sa'adda ta haura saman gadon nashi da rarrafe ta ƙarasa saitin inda kanshi ya ke, ta zuba mashi ido tana kallon shi da tsananin firgi ci. Cikin lokaci ƙanƙani, Ilahirin Jikinsa Ya jiƙe sharkaf da gumin zufa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai. Tsabar Yadda Jikinsa ke kakarwa Har gadon kerma yake yi ita kanta jikinta ya kama kakarwa, tun zuciyarshi na bugawa a hankali har ta fara bugawa da matsanancin ƙarfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito waje, sautin numfashinsa mai haɗe da gurnani ya gauraye bedroom dinsa, da karfi Yake Jan shi tamkar babu wadatacciyar iskar da zai shaƙa. Ko wani sashe na jikin shi tuni ya soma motsawa, Unaisah dake kallon shi idanunta azazzare duk tabi ta rude ta firgice Lokaci ɗaya tsoro Ya cika ta, Zabura tayi da niyar ta watsa aguje gudun kada Ya cutar da ita don ta fahimci kamar baya hayyacin sa ... Sai dai kafin tayi wani yunkuri juyawa yayi wani kwakkwaran juyi tamkar mayunwacin zaki haka Ya damƙo sumar kan nan nata daya sha gyara gaba ɗaya ya dawo da ita jikin sa, Yana huci ya matseta kamar zai tsinkata biyu, Ji tayi tamkar an daureta da igiyoyin kaca, hucin zafin jikinsa har anata jikin take jin shi, Zuciyarta ce ta bata shawarar ta hankaɗe shi ta gudu, kafin yai yunƙurin cutar da ita, Cikin ƙarfin Hali ta daddage ta fusge kanta daga ruƙon da yayi mata, gaba ɗaya ta kundumo saman tiles kanta ya daku, Harta zabura zata mike da niyar ta watsa a guje taji ya damƙi ƙafarta ɗaya, ta ƙarfi ya janyota kamar ɗiyar roba ya dawo da ita saman gadon, runtse idanunta tayi da sauri tana ambaton La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. Dogayen yatsun hannayensa dake kerma ya ɗaura saman wuyanta, ya shaƙeta sosai tamkar zai tsinka wuyan, radadin azabane ya ziyarce ta, ta kware baki ta fasa wata irin ƙara mai sautin gaske, sai faman kiciniyar kwace kanta take yi amma ta kasa saboda ƙarfin dake gare shi tamkar zaki a haka ma don bai da koshin lafiya da tuni yajima da kashe ta cikin rashin sani. Radadin da tajine yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske Adai dai Lokacin Ummi ta fito daga room din ta, don taje ta fara shiryasu ganin lokacin dinner din Ya kusa Cika Har ta nufi stairs zata hau, kunnuwan ta suka soma jiyo mata Gunji gunjin kukan unaisah, Lokaci ɗaya taji gabanta yai mugun faɗuwa, tsabar rudanine akan fuskanta, fasa sauka tayi cikin takun sauri take bin hanyar da take jiyo sautin kukan cike da was wasin kodai kunnuwanta ne suke jiyo mata badai dai ba A hanzarce takarasa Bakin kofar, ta soma bubbugata tamkar zata 6alleta, muryarta da sauti mai karfi take ambaton sunanta"Unaisah!! Unaisa!! Unaisah" Kofar tamkar an datse ta da key taki buɗewa ta rufe gam, kware murya ummi tayi tana ambaton ba kowa ne akusa? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un unaisah idan kinaji na ki yi min magana! Meke faruwa dake ne'?_ Ta faɗa jiki na tsuma ta zura hannu ɗaya ta dauko wayarta daga cikin aljihun skirt dinta. Layin boss man ta danna ma kira bugu biyu yayi picking ko sallama babu tace"yalla6ai kazo gida an samu matsala, na fito daga daki na na ji yo sautin muryar unaisah a dakin danish tana kuka na tashin hankali, nayi kokarin buɗe kofar ta datse..." Muryarshi a ruɗe Ya furta"Chief bai dawo ba"? Yarfa hannu ummi tayi "bansani ba, yanzu na fito daga daki.... bai bari ta ƙare maganar Ba, Yayi rejecting kiran ranta ne ya 6ata cewar zai zo, tsayawa tayi abakin kofar Idanun ta sun kaɗa jawur ta tsorata dajin ihun unaisah, lokaci daya taji shuru babu ihun nata nan fa hankalinta ya kara tashi tadinga buga kofar da hannu da kafa Tana Ambaton"Unaisah dan Allah Kiyi min magana? Danish Ya farkane? Me yake yi maki? Meyasa kike kuka, Nashiga ukuna, Unaisah kada ki bari Ya cutar dake, Kiyi kokarin kare kanki! Unaisah kina jina? Naji kinyi shiru inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." hawaye har sun fara wanke fuskar ummi saboda ta gama gigita Zuciya da sake sake gani take kamar Danish Ya kashe ta ne shiyasa tajiyo shirunta. Kamar an jeho shi Ya faɗo falon A fujajen, wuyan jallabiyar shi ma akarkace take sam baya a hayyacinsa, da gudu Ya falfala Ya haye up inda ummi take atsaye tana faman buge bugen ƙofa, yana karasawa Ya daddage da iya karfin shi na karshe Ya bangaje ta da kafadarsa nan take kofar Ta zuge kanta da gudun gaske, Tsabar saurin su shiga suga meke wakana har suna bangaje juna shi da ummin america, duk wannan budurin da ake sauran yan uwan su basu san meke faruwa ba. Shigar su keda wuya, suka taras da abun da ya daure musu kai, Yana azaune bakin gadon Ya duƙar da kanshi kasa, Sumar kanshi Ta lullu6e fuskar Unaisah wadda kanta yake abisa cinyoyinsa' basa iya ganin fuskarta sai ƴan kafafuwanta, cike da fargaba da karyewar zuciya boss Ya furta Sunan shi"Danish! Unaisa meya faru ne? Ka yi mata wani abu ne? Haƙiƙa sun yi mamakin farkawarsa babu wanda yayi tsammanin zai tashi a cikin ƴan kwanakin nan. Adabarbarce ya kare maganar, tamkar yayi magana da bango babu alamun danish zai saurare su duk sun bi sun rude mutun kamar Ifritun aljani gashi ya damki yarinya a hannun shi Cikin shessheƙar kuka Ummi take rokonshi akan Ya saketa, kada ya kashe masu ita.....' Karfin Hali taj yayi da sauri Ya nufi gefen gadon inda su ke a zaune Ya miƙa hannayenshi biyu da niyar ya kawar da ita, Damƙar hannunsa Danish yayi tare da dagowa yana faman lumshe idanun shi tamkar na wanda yasha giya, muryar shi da kasala Ya furta"ina bukatar ruwan da zan yayyafa mata" kusan atare ummi da Taj suka sauke ajiyar zuciya, saboda sunyi tsammanin baya ahayyacinsa ne. juyawa ummi tayi da sauri ta fita daga dakin sai gata ta dawo hannunta ruƙe da robar ruwan da ta ɗauko a fridge ta miƙa ma taj, shi kuma Ya kar6a ya Miƙa ma danish, a hankali Ya sanya hannu ya kar6a bayan ya cire murfin ya tarfa hannunsa dake ɗan kerma Ya ɗebi ruwan ya watsa mata akan fuskarta, lokaci ɗaya ta zabura zata fara buge buge da sauri boss Ya damƙi hannunta, tare da dago da ita ya zaunar. Wani jiri jiri take gani a idanunta, hannu tasa ta dafe makoshinta tana fadin ruwa ruwa zan sha. Kwafa mata ruwan yayi abaki ta rurruke robar duka ta shanye shi, ta dago da luhu luhu idanunta wadanda suka kada jawur da su Sam ta manta a ina take zaune, gani take kamar amafarki lamarin Ya afku, Kwata kwata bata lura da danish ba, wanda ke a gefenta kuma shi ya bata ruwan da ta sha. "Unaisah, are you okey? Ina fata bai ta6a lafiyar jikin ki ba"! Cikin kulawa ummi keyi mata magana Kallon ummi tayi murya na ɗan rawa ta furta"nayi mafarki danish Ya farka, Har Ya shaƙe min wuyana" ta faɗa tana shafa wuyanta "Ba mafarki ki ka yi ba, dagaske ne Ya faru, danish Ya farka sai dai baya a hayyacinsa ne lokacin daya shaƙe ki" boss ne ya bata amsa, da wani irin Hanzari ta dubi danish da ke gefen ta, idanunsa suna a lumshe numfashin sa na fita a hankali. Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kukan farin ciki, ta kamo yatsun hannayensa acikin nata, Muryarta cikin shessheƙar kuka take fadin"My man...kana lafiya? jinjina mata kai ya danyi alamar eh. "Alhamdulillah Ya Allah, Alhamdulillah..." sakin hannunsa tayi ta sauko daga kan gadon ta zube saman gwiwowinta tare dakai goshi kasa tayi sujjada tana mai nuna godiyarta ga Allah. Murmushi taj ya soma saki yana kallon danish, Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e shi mara misaltuwa Yaji dadin farfadowar nan tashi, Har ya fara tunanin haduwar shi da Prime minister. Har yanzu Danish babu fara'a akan fuskar shi, jefi jefi Ya ke kallon su da lumsassun idanunsa, ganin lokaci na shirin kure masu yasa ummi ruko hannun unaisah tace su tafi su fara shiryawa, kamar karta baro dakin tana tafiya tana waiwayon danish gani ta ke kamar in ta fita zai koma yar gidan jiya, har sai da boss yace mata zai kira chief yanzu awaya tare da sheikh imam tukunna ta ɗan samu kwarin gwiwar barin dakin..... Batare da 6ata lokaci ba, Taj Ya kira chief awaya ya sanar da shi dangane da farfaɗowar danish, A lokacin chief Har Ya kira likitan da zai duba shi, yayi murnar jin zancen tashin danish, kafin ma karasowar su dakin sai da ya Kira Shiekh Imam suka jira Ya zo falon Kafin suka sauko shi da likitan dayazo duba dashi a tare suka nufi dakin shigar su keda wuya Chief owais ya nufi danish, tamkar dan uwansa na jini Ya miƙa mashi hannu ya taimaka mashi ya sauko daga kan gadon gaba ɗaya yayi hugging dinsa a jikin shi, ya ɗaura hannayensa abayansa yana dan bubbuga shi, har rada yai mashi a kunna ya furta"nayi farin ciki da samun lafiyar ka, Ina fata babu abun da ke yi maka ciwo ayanzu..." ya fada tare da dafe kafadun danish ya dago da shi. Babu wanda baiyi farin ciki acikin su ba, Musamman sheikh imam Ya ambaci kalmar alhamdulillah tafi sau a kirga, ya ɗaga hannayensa sama ya dinga zubawa Allah kirari Haɗi da nuna godiyarsa ga nasarar da suka samu, Bayan ya gama ya janyo danish din duk da bai sakar masu fuska ba wannan bai shafe su ba, dama su burinsu ya farfado kuma Alhamdulillah kwalliya tabiya kudin sabulu, Rungume shi shiekh imam yayi tamkar zai mayar dashi cikin sa, ya dinga shafa sumar sa yana karanto addu'o'i yana shafe mashi ko'ina na jikinsa. Ko da likitan ya duba danish baiga komai ba sai ma wani abun ban mamaki daya gano wato Lafiyar dake gare shi, har ta wuce wadda hankali zai dauka, babu ko ciwon kai a tare da shi. Bayan tafiyar likitan shawarwari suka tsaya sunayi atsakanin su, kafin daga bisani chief ya raka shi bathroom don yayi wanka, Kafin ya fito aka shirya mashi lafiyayyan abinci a daki aka shigo mashi da shi, atare da chief suka ci abinci, gwanin ban sha'awa kamar wasu yan uwan juna sai daya tabbatar danish Ya cika cikinsa tukunna ya samu kwarin gwiwar sanar da shi dangane da uncle dinsa dake son ganinsa, ya nemi alfarmar yana so su tafi atare, shiru danish yayi mashi dama yaƙi furta masu magana tun da ya farka kamar wani kurma sai dai yabi su da ido. Tarairayarsa suka dinga yi suna lalla6a shi, duk don ya amince, amma ɗan tahalikin nan yai shiru, dabara ce ta fadowa taj da sauri yace mashi a tare da su unaisah zamu tafi da sauran ƴan uwan ka, kuma duk sun amince zasu je. Jin ya ambaci zasu tafi da su unaisah ne yasa shi saurin amince masu ta hanyar jinjina masu kai, domin kuwa bazai bari su tafin masa da yan uwansa ba, Murmushi sukayi gaba dayansu ganin sunyi nasara akanshi... Nan fa suka fara shirya shi, kamar wani yarima. Lokacin da su sajeed suka ji labarin Farkawar danish, Aguje suka watsa da gudu suka nufi bedroom dinshi, Tsabar farin ciki maimakon suyi dariya saima suka fashe da kuka suka dinga rungumar shi, Dadi kamar zai kashe su, Shi kanshi yayi farin ciki da ganin su duk da yaki tanka masu sunyi sunyi dashi akan ya bude baki yayi masu magana amna yakiya sai dai fa kallo ko irin sakin fuskarnan babu Hakan bai wani dame su ba, tun da ya farka falillahil hamdu, duk wannan mai saukin ne, dama sun riga da sun san halin kayan su, bayan sun gama murnar samun lafiyan dan uwan nasu, Ummi ta tattarasu suka koma dakunansu, kowan na su yayi wanka, Suka soma shiryawa cikin kayan su cike da zumudi, bayan haka dangane da abun da ya faru a hall na kashe Hasken lantarki aikin chief owais ne shine ya tsara komai, tare da interior designers da sukayi decoration na hall din saboda yana son yaga reaction din family nasa, bayan ya gama tsara komai, Shi yafara halartar dinner din, ya riga su Unaisah tafiya kamar yadda ya tsara saboda yana son ya fara yi masu hanyar shiga batare da an samu matsala ba, tun da wurine mai tsaron gaske, su boss da big guy ne da wasu daga cikin jami'an isod sukayi jigilar daukar su Unaisah a cikin motocin su, suka kawo su bakin hall din, bayan tafiyar su tuni Ummi ta shirya saboda ta samu amincewar chief akan fitar da za ta yi, taje ne ya nema mata alfarma, Jami'in isod ne yayi driving dinta zuwa gidan da tace zata je na kawarta. (Wannan shine abunda ya faru kafin zuwansu dinner hall din) (CIGABAN LABARI) Haɗa ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...? Jinjina mashi kai chief owais yayi alamar eh, wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarshi dauke da wani irin annurin farin ciki mara misaltuwa da tafukansa ya tallabo fuskarshi yana bin shi da kallo mai nuni da tsantsar ƙaunarsa, kasa jurewa yayi baisan sa'adda Ya janyoshi zuwa ga faffadan kirjinsa yai huggin insa tightly kamar zai mayar da shi cikin cikinsa, hannayensa biyu dukansu ya tallabe bayan danish dasu, yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da bugu mai tsanani, wani irin yanayi mara misaltuwa.... Hakan ba karamin ɗaga hankulan mutanan dake a hall din yayi ba, gaba ɗaya sun ƙara rudewa da ganin rungumarshi da prime minister yayi. Muryar Hajiya saratu tamkar zata fashe da kuka ta furta"wai ba zakuyi mana bayanin su wanene ba? Kun barmu atsaitsaye cirko cirkon kamar sakarkaru" ta fada tana kallon chief owais don ta fahimci yasan da zamansu tun da taji Pm hateem ya tambaye shi shine.... "Owais su wanene wadannan Yaran! "? Baba obie ne ya furta maganar Sai lokacin chief Owais ya soma takowa yana tunkaro wurin da su ke atsaitsaye, cikin dakakkiyar muryarsa ya soma magana genlty "A gafarce ni, nayi laifi ban sanar da zuwan su ba....' ya faɗa awayance yana bin kowan nan su da kallo. "Idan ba zaku manta ba, na ta6a baku labarin Yaran da Sojin america suka tsinta a evil forest, suka damƙa case dinsu ga hukumar mu ta Isod, ga wadanda basu san da zaman su ba, to ga su nan, sune yaran da nake ruƙo a hannuna, na gayyace su ne don su gana da dangina saboda sun zama tamkar ƴan uwa agare ni" Lokacin da ya ƙarasa maganar, hajiya saratu ta zabga salati tana huci ta furta"wlh baka isa ba Owais! Ka haukace ne? da Zaka kwaso mana tsintattun Yaran da ba'asan asalin su ba, ka kawo mana acikin dangi? Anya kuwa kana a hayyacin ka? Rai amatuƙar 6ace tayi maganar, Hankalin su Unaisah ba karamin tashi yayi ba, Masu tsoro acikin su har sun fara Ja da baya jiki na kerma... A matuƙar firgice Senate Lateef Yace"kana nufin ƴan uwan yaron nan da ya rikiɗa ya koma maciji"? Wannan maganar da senate lateef Ya furtane Yaja hankulan mutanan Hall din, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, Muryoyinsu a kidime suke maimaita kalmar maciji ga wadanda basu san da zancen faruwar lamarin ba, nan take Pravin yayi wuf ya kwashe komai daya faru ya sanar da su, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un shine abunda suke furtawa a bakunansu.... Prime minister sam baya gane me su ke cewa saboda idanunsa sun makance, Ya kurmance baya ji baya gani tunda ya rungumi danish a jikin shi bai ƙara ɗago da kanshi ba, Kamar daga sama yaji an damƙi damtsen hannunsa da ƙarfi aka raba shi daga jikin danish wanda bakowa ne yayi hakan ba face Senate Lateef, ya janye shi gefe guda, Yana faman zazzaga masifa"wlh bazamu lamunta ba! Don Na fahimci bakasan ciwon kan ka ba, taya zaka kwaso mana mugun abu ka kawo mana a cikin dangi? Wannan wata iriyar masiface? So kake ka tarwatsa mana farin cikin mu? Ko kuwa so kake ka ƙarar mana da dangin mu ne!? Wai ma wanene ya baka shawarar ka kawo su wurin nan....."? Tunkafin Senate lafeef ya kare maganar, sautin shessheƙar kukansu Ya soma karaɗe hall din, sun girgiza da jin munanan kalamin da ake fada akansu, bayin Allah da farin cikin su da zumudi su ka zo ganin dangin chief owais sunyi tsammanin suma zasu sosu kamar yarda shima yake son su ashe ba haka bane......' "Wallahi sai dai ka za6a, ko dai ka tattara su ku koma can gidanka, ko kuma mu mu fita mubar maka hall din ka ƙare dinner din tare da su, don wlh baka isa ka jazamana masifa ba, wannan ay annobace ka kwaso mana" acewar hajiya saratu ta faɗa tana watsa hannayen ta. Chief owais dake sauraronsu ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo daman yasan za'a rina ba lallai su wanye lafiya ba, sai gashi ta tabbata, kowa da abun da yake tofawa, mutane ƙalilan ne basu tanka ba. Hankalin Hateem yafi na kowa tashi, ganin za'a raba shi da muradin ranshi, Ga samu ga rashi, Ji yake tamkar Ya fasa ihu, ƙiri ƙiri su Senate lateef sun rurruƙe hannayenshi gudun kada Ya ƙara tunkarar Danish. Security advisor din Hateem ne ya tambayi meke faruwa ne? Muryarsa a bubbuɗe yasha ya bugu baya gane komai sama sama yake jin kan shi, Kasancewar basa jin yaren hausa basu san takan zancen ba, da sauri pravin uban Ƴan zigi Ya buɗe baki da niyar Ya sanar dasu, wata irin tsawa mai kama da saukar aradu chief owais Ya sakar mashi, wadda tay matuƙar gigitasu a hanzar ce yaja baki ya yi shiru. Dalilin dayasa ya yi mashi hakan gudun kada ya sanar da su, don muddin sukaji da zancen Yaron daya rikida ya koma maciji to kuwa nan take zasu sa a dakatar da taron bayan haka zasu sanya jami'ansu su kori su unaisah don ba zasuyi ganganci da rayuwar hateem ba... Cikin sanyin murya prime minister yayi ma mutanansa bayani da yaren da zasu gane ya kwantar masu da hankalin su, da cewa family issue ne kuma in sha Allah zasu shawo kan matsalar yanzu, iya abun da ya fada masu kenan, dama kuma ba ahayyacin su suke ba, shiyasa abin yazo masa da sauki da tuni sunsa an tada taron gaba ɗaya. Da kakkausar murya chief owais Ya soma magana babu annuri akan fuskarshi. "ni ne silar dana kawo su wurin taron nan, bawani ya bani iznin in gayyace su ba, kuma basu suka nuna suna son zuwa ba, face don ni nake so su zo...." bai ƙare maganar ba, Hajiya saratu tayi yunkurin dakatar dashi aikuwa a fusace Ya ɗaga mata hannu alamar tayi shiru, Waro idanu waje tayi ba ita ba hatta sauran mutanan hall din sunyi mamakin rashin kunyar da owais yayi. "Suma ya'yane kamar kowa! Yaro kuma da bashi da lafiya, Bayin kanshi bane, Aljanu ne suka shafe shi, kuma ya samu lafiya bayan da shiekh Imam ya dau kwanaki Yana duba shi.....' bai ƙare maganar ba, muryar sheikh imam ta karaɗa kunnuwansu a yayin da yake shuowa dakin taron. "Tabbas maganar owais gaskiya ne, Yaran nan ba masu cutarwa bane, mutanene kamar kowa, kuma abin a tausayamawa ne....." a tsanake cikin hikma sheikh imam ya fayyace masu komai dangane da halin da danish yake a ciki, wasu sun fahimta yayin da wasu sam kamar kurame basa gane komai. Gaba ɗaya hall din Ya rikice da maganganunsu, wasu suna hura wutar akore su daga hall din yayin da wasu sukayi shiru basu tanka ba irin su mai girma sharafudden, sun natsu suna bin duk wani mai magana da kallo, ga dukkan alamu akwai abun da suke jira shiyasa suka yi shiru. Cikin sanyin murya prime minister yace"dan Allah kowa yakwantar da hankalin shi, Idan har saboda ni aka shirya dinner din nan, to ina rokon alfarmar ku bar su na yau kawai su zauna, in sha Allah ba abinda zai faru" idanunshi akan danish ya ƙare maganar, wanda tun shigowarshi hall din idanunsa suke alumshe tamkar ma baisan sunayi ba, su batool daine suka ruɗe jikinsu sai kerma yakeyi bayin Allah sun firgita. "Meye amfanin kawo su wurin nan? Inace an shirya dinner din nan ne saboda mu ƴan family ba bare ba! Don haka afitar mana da su idan ana son zaman lafiya, idan ba haka ba mu zamu tattara yanamu yanamu mubar masu hall din" rai a6ace hajiya laurat tayi maganar tana faman haɗe rai. Runtse ido chief owais ya yi, har cikin ranshi baiji dadin irin tarbar da akayi ma yaran ba, zuciyarshi ta raunana duk sai yaji dama bai sa anzo da su ba. _Cikin sanyin murya mai ratsa zuciya Unaisah ta soma magana"dan Allah ku yi hakuri idan mun 6ata maku rai, wlh ba mu zo da niyar mu cutar da kowa ba, hasalima ba da son ranmu mu zo ba, face don chief ya nuna yana son mu ziyarci danginsa, ba ku san mu ba, muma bamu san ku ba, bai kamata kuna munana mana zato ba, akan abun da baku da tabbas akanshi_ tun da ta fara magana hankula suka dawo kanta, Idanu zuru zuru cike da mamakin karfin halin ta. _A hankali ta sanya hannu ta cire facemask din fuskarta tare da jefar da shi gefe ɗaya, Tabarakallahu ahsanul khalikin, Hankalin maza ya tashi da ganin kyakkyawar fuskar unaisah wadda take a jike sharkaf da hawaye_ _Cikin murya kuka taci gaba da cewa"Idan bakusan ganin mu ba sai kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta sun sanyaya zuciyoyin wasu daga cikinsu, Hakika unaisah ta tafi da imanin wasu daga cikin su, Har mamaki sukeyi yarinya karama ga iya tsara kalami uwa uba gata kyakkyawa da ita_ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 13 Complete by Novels Elite Admin May 29, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القدر💋✊🔥 ~Takun Ƙarshe🔥~ قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Cikin muryar kuka taci gaba da cewa"Idan ba ku son ganin mu ba sai kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta sun sanyaya zuciyoyin wasu daga cikinsu, Hakika unaisah ta tafi da imanin wasu daga cikin su, Har mamakin ta su ke yi yarinya ƙarama ga iya tsara kalami uwa uba gata kyakkyawa da ita, ba karamin jan hankalin su Captain yasir tayi ba, sun kafe ta da idanun su kamar za su haɗiye ta. Fashewa da kuka Jemimah tayi muryarta da gunjun kuka ta ke fadin "wallahi babu inda zamu je, don baku san wahalar da mu ka sha ba mu ka yi gayu hada gyaran gashi saboda mu nuna maku, shi ne ma zaku kore mu, to wlh ba zamu tafi ba... " a faɗa ce ta faɗa tana nuna su da yatsan hannun ta, Hankulan su gaba ɗaya ya koma kanta, ƴar ƙarama da ita sai masifa, idanun ta sun yi jawur da su, ta harzuƙa, dama ya lafiyar giwa, tsana da tsangwama da zuluncin da akayi masu arayuwarsu ya ɗan ta6a lafiyar kwalwarsu, silar maganganun da ake fadi ayanzu ne ya fara motsa haukan kansu, da sauri Unaisah ta janyo jamimah ta ƙanƙameta a jikin ta cike da fargaban kada ta ja masu jaraba. Dafe goshi Azeeza tayi da hannun ta dake kerma kerma cikin wani irin yanayi na jin tsoro da fargaba ta soma magana muryarta da shessheƙar ku ka "Inna... lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ni dai mu koma gida, ku mai dani gida, ba su san mu, ba su son ganin mu, za su iya cutar da mu....' ba ta ƙare maganar ba, Sajeed yai hanzarin janyota tare da rufe mata fuskarta jikin laps dinsa. Sautin shessheƙar kukan su ya cika hall din, mazan cikin su ne kadai ba su karaya ba, sai dai hankulansu ba a kwance ya ke ba, Mom Turai sarkin tausayi zuciyarta ta karaya ita da Hajjaty har sun fara sharar kwalla saboda tausayi ne da su, ga kaunar yaran da ta ɗar su a zuciyoyin su, da ace suna da damar da zasu ja su a jiki su rungume su da kuwa sunyi hakan. A hankali unaisah ta ɗaura idanunta akan chief owais, mutumin da bata jima da sanin fuskarsa ba, duk da babu kwanciyar hankali atattare da ita sai da taji ya kwanta mata arai saboda jajircewarsa akan su. Kamar yarda take kallon shi haka shi ma yake kallon ta, har cikin zuciyarsa bai ji dadin zubar hawayen su ba. "ba laifin ka ba ne, abun da akayi mana, sai dai inaso ka sani bakowane zai fahimce mu ba ko ya kaunace mu kamar yadda ku kayi mana, zamu tafi kawai....." ta ƙarasa maganar ƙananun la66anta na kerma ta ruƙo hannun batool da na jemimah har zasu juya muryar Sir mubarak ta dakatar da su. "Duk da bansan su wanene ku ba, ni dai kun kwanta min araina, kun sace min zuciyata, don haka ban gaji da ganin ku ba, ina yi maku maraba da shigowa family din mu...." a ruɗe su hajiya saratu suke kallon Sir mubarak, wanda fuskarsa take ɗauke da murmushi yayin da yake kallon su. Pravin dake ta faman mazurai, jin maganar sir mubarak yasa shi jin bakin ciki da takaici tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, kwata kwata babu kwanciyar hankali a tare da shi, duk ya rasa sukuninsa kamar wanda yayi ma sarki ƙarya, burin shi a kore su daga hall din. Sheikh Imam dai lamarin nasu ba karamin mamaki yake ba shi ba, kallon su kawai ya ke yi, Sam baiji dadin halin da su ka jefa yaran ba. "Meye ribar ku idan kun 6ata ran wadannan bayin Allahn? Farin ciki ku ka yi ko bakin ciki da kuka sanya su zubar da hawayen su? Idan ya'yan ku ne a irin halin da ku ka jefa su za ku ji dadi ne? Daga ni har ku bamu da tabbaci akan abunda muke zargin su da shi, don haka yakamata mu kyautata masu zato, sannan shiekh imam yayi mana bayani, babu wanda baisan wanene sheikh imam ba, kuma mun yarda da maluntarka sa, bai kamata mu musa ma maganar shi ba, bayan haka owais jinin mune bazai ta6a kawo abun da zai cutar da ahlinsa ba, idan ma saboda kuna fargaban kada su cutar da ku ne to ku sha kuruminku owais shi ya ke da alhakin da duk wani abu da zai faru" cike da ƙwarin gwiwa Mai girma sharafuddeen yayi maganar babu wasa akan fuskar shi, tuni wasu sun fara shan jinin jikin su. Matsawa Chief owais yayi kusa da baba obie wanda tun ɗazu bai tanka ba, ruƙo hannunsa yayi acikin nashi, a hankali Ya ɗago suka haɗa ido da juna In a calm voice ya furta"banji kace komai ba baba, umarninka kadai nake jira, In har ka nuna bakason su zauna zan koma da su, Idan kuma ka amince babu wanda ya isa yasa subar wajen nan, sai dai mutun ya tafi" ran shi yakai maƙura awurin 6aci Lumshe idanu baba obie ya yi yana nazari, na ɗan lokaci yana yanke shawara da zuciyarsa kowa ya ƙagara yaji ta bakinsa domin kuwa shi kaɗai ne zai zartar da hukunci kuma dole ayi biyayya...... Komai dake faruwa akan idanun zahra, tsoro duk ya cika ta ganin rikicin dake shirin 6allewa, tun ɗazu ta 6oye kan ta a bayan su hindu dake a tsaitsaye, jikin ta sai kerma ya ke yi saboda batason tashin hankali arayuwarta... Pravin Allah Allah ya ke baba obie yaki amincewa da zaman su a hall din ji yake tamkar ya shiga zuciyarshi don ya samu damar tunzura shi akan kada ya bar su, jikin shi sai tsuma ya ke yi. Chief owais dake kallon shi amsar shi kawai yake jira, cike da fargaban kada Ya kunyata shi a bainar jama'a duk da yasan abune mai wuya baba obie yayi mashi hakan saboda baya son 6acin ransa. Gyaran murya yayi hankali gaba ɗaya ya dawo kan shi, kafin ya soma magana yana duban kowan nan su "Bana son abun da zai cutar da ahlina, sannan bana son duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a zuri'a na...." tunkafin ya kare maganar, munafuki pravin ya soma sakin shu'umin murmushin farin ciki don yasan karshen zancen zai ce ne a kore su. "Bawai don bana son yaran bane, ɗa na kowa ne, sai don ina son mu ƙare dinner din nan lafiya, zaman su acikin mu, ba lallai ya zama alkhairi ba, tun da wasu sun nuna basu buƙatar ganin su,......" da tsantsar mamaki chief owais ya ke kallon fuskar baba obie, hajiya saratu da su laura har sun fara sakin fuskokin su sai kace akan su za su zauna.... Chief bai tsaya jin karashen zancen ba, saboda zuciyarshi ta karaya, a raunace Ya sakin hannun baba obie, ya juya ya kalli prime minister wanda tuni ruwan hawaye sun kwanta luff a idanunsa... Cikin sanyin murya ya furta"am sorry uncle, banyi tsammanin abun zai kai haka ba, dana san ba za a kar6e su ba da banyi gigin zuwa da su dinner din nan ba, dama nayine saboda farin cikin ka" ya faɗa yayin da yake mayar da idanunsa kan baba obie "zan tafi tare da su....' yana ƙarasa maganar cikin takun sauri Ya nufi su unaisah, wani irin murmushi ne ya bayyana akan fuskar pravin da su hajiya saratu. "Owais"!! Har Ya kusa kaiwa bakin kofar muryar Baba obie ta katse shi, Cak ya tsaya da tafiya, dama da biyu yayi hakan don yasan baba obie bazai iya jurar 6acin ranshi ba. "Meyasa ba zaka tsaya kaji karashen maganata ba"? A hankali Ya juyo yana duban fuskarshi, Nan take murnar pravin ta koma ciki. Matsawo yayi kusa da shi, fuskarshi dauke da murmushi yace"kamar yarda kayi saboda farin cikin Uncle dinka, Ni kuma saboda farin cikin ka, na amince su shigo ayi shagalin dinner din nan tare dasu, sannan bana so na sake jin wani ya fadi abun da zai 6ata ransu, Umarni ne wannan!! Yana ƙarasa maganar shi, Chief owais ya nufeshi, gaba ɗaya yayi huggin dinshi. rai a6ace hajiya saratu ta nufi hanyar fita daga hall din. "Karki kuskura ki fita! Dawo ki zauna" muryar Sir mubarak Ce ta katse ta, tana faman haɗe rai ta dawo ta tsaya hannunta dafe da ƙugu. Damƙo hannun hajjaty pravin yayi, yana faman fitar da huci Yace mata ta biyo shi subar hall din, sam ya manta da hajiya saratu dake kallon shi, ga alama ya fita hayyacinsa, jikinshi duk yayi zufa sai kace babu a.c a hall din Muryar hajjaty da tsantsar tashin hankali ta furta"pravin meke damun ka ne? Agaban mutane kake ruƙe hannu na? ina zaka kaini ne? bayan ba agama dinner din ba, dan Allah ka kyale ni" ta fada tana kokarin cire hannunta daga mugun ruƙon da yayi mata. Da karfi hajiya saratu ta furta sunansa"pravin!!" ko kallo bata ishe shi ba, ƙoƙari kawai ya ke yi yaja hajjaty don su bar hall din, ita kuma ta dage akan bazata bi shi ba, gaba daya hankulan mutane ya dawo kan su. "Nashiga uku pravin, dan Allah ka kyaleni, nace maka bazan bika ba....." gigitacciyar tsawa hajiya saratu ta daka mashi da kakkausar murya mai haɗe da zafin kishi ta furta"ka fara haukane? Agabana kake ruƙe hannun ta? Anya kuwa kana acikin hayyacin ka" Ɗagowa ya yi da idanunsa waɗanda suka kaɗa jawur ya dubi hajiya saratu da masifa ya furta"Bai shafe ki ba!" har sai da taji gabanta ya fadi, Su hajiya laura sun saki baki da hanci suna kallon ikon Allah, hatta su Hajiya malikat da su sir mubatak mamakinne ya kamasu yadda ya rufe ido yana jan hajjaty da tsiya yake son fitar da ita daga hall din. Alhazawan canada suna ta kallon ikon Allah abu kamar a drama, anbarsu a duhu sun kasa gane meke faruwa... Tsawar da Sir mubarak Ya daka mashi ne yasa shi saurin shiga taitayinsa, A fadace yace"wannan wani irin shashanci ne? Baka da hankali ne? Ina ruwanka da ita? Tun da ta nuna batason tafiya ka ƙyale ta mana!" Kallon hajjaty pravin yayi idanunshi jawur yana huci ya furta"idan har baki bini mun koma gida ba ranki zaiyi mugun 6aci, wlh kada ki bari na riga ki fita daga hall din nan" yana fadar hakan Ya juya tamkar mayunwacin zaki Ya nufi kofar fita hall din cike da sa ran hajjaty zata bi bayan shi, sai dai har ya fuce babu alamun zata bishi, kamar an ruƙe ƙafafuwanta, hakanan taji ba ta son tabi shi, taji kunyar abun da yayi mata, agaban jama'a, tasan dole adasa masu ayar tambaya, ita kanta a ruɗe take batasan dalilin dayasa pravin ya rikice mata ba, Hajiya saratu yau taga abunda yafi karfinta, tamkar a mafarki take ganin komai, akan idonta pravin ya ruƙe hannun hajjaty bainar jama'a batare da ya ji tsoronta ba, lallai zai fuskanci horo mai tsanani daga gare ta, har ta ita kanta hajjatyn yaja mata bala'e domin kuwa bazata ƙyale ta ba, ransu twins su yayi mugun 6aci musamman zayn shi da yafi zuciya...... Bayan hatsaniyar ta lafa, senate lateef ya dubi su unaisah "tun da mahaifinmu ya yanke hukunci akan ku zauna, ba mu da ja, ya zamar mana wajibi mu tarbe ku, amma kafin nan ku sauke facemask dake akan fuskokin ku" ya fada yana nuna faces din su. Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyin su. "Kamar ka shiga zuciyata, nima abun da nakeso nace kenan, gaskiya ba zamu bari ku shiga da wannan face mask din ba, yakamata mu ga fuskokin ku," tun da aka fara rikicin nan sai yanzu his excellency abdul razak ya sanya baki, His excellency deen yace"to nima dai abuɗe min inga fuskokin nan, ko hankalina ya kwanta" ya fada da ɗan murmushin kan fuskarsa. A hankali Batool ta ɗaura yatsun hannunta da ke kerma ta ruƙo face mask din ta yaye shi daga kan fuskarta, Har saida gabansu ya fadi da ganin kyawun fuskarta, wato wani guntun murmushi da tayi ta sunnar da kanta kasa ba karamin tafiya yayi da imanin su ba, wasu tuni sun fara danasanin sanya su kuka da su ka yi. Bayan batool ta cire nata, Sajeed Ya zame face mask din fuskarshi, tsabar kiɗima da ganin fuskarshi yasa hajiya laura ɗan zaro idanunta ga dukkan alamu akwai wani abu da ya ruɗe ta da shi, kyawun sajeed ba ƙaramin tafiya yai da imanin su ba. "Saura ku, Ku cure naku mu gani" Zaki ne ya fada yana nuna sauran Sajeed ne ya taimaka wurin Cire ma Azeeza nata, Duk tabi ta ƙanƙame shi, fuskarta tayi sharkaf da hawaye har wani zazza6i ya lullu6e ta, ganin fuskar Azeeza ya yi matuƙar razana Sir mubarak har sai da ya kalli fuskar Mom turai, ba shi ba, hatta Dr jazz da su Ibad kusan a lokaci ɗaya suka jefa wa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar mamaki da al'ajabi. Jamimah dake a maƙale jikin angel, babu alamun zata motsa, ruƙo hannunta Angel tayi tare da cire mata mask dinta, fuskar ta 6aci da hawaye hada majina hakan yasa basu samu damar ganinta da kyau ba. Kusan atare Javed da Haris suka tu6e nasu face mask din, Kallon kallon aka komayi atsakanin Iyalan obinna kowa da abun da ya ɗaure ma shi kan shi. "Parveen ku cure naku" cikin sanyin murya Unaisah tayi masu magana Batare da 6ata lokaci ba, Parveen ta cire nata mask din, wani irin bugu zuciyar hajiya saratu tayi, haƙiƙa ta razana da ganin kamannin ta dana yarinyar, har sun 6aci kamar tayi kakin ta, banbancin su launin fata, ba ita ba harta sauran matasan family din da iyayan mamakine tsantsa akan fuskokin su... Lokacin da Naufal ya cire mask din fuskar shi, wata irin firgita hajjaty tayi, har sai da ta dafe saitin zuciyarta da ke yi mata wani irin mahaukacin bugu, tagaza yarda da abun da idanuwanta suke gane mata, gani take tamkar mafarki ne ba gaske ba, domin kuwa ita dai tasan wanda ya mutu baya dawowa, harta su Hajiya Muhibbat sai da suka saci kallon fuskar hajjaty da ta naufal saboda wani abu daya ja hankalin su.... Gaba ɗaya sun rikice Sun ruɗe, sun gaza gasgata abunda idanunsu ke nuna masu Tamkar an kulle masu baku nan su, Sun kasa magana, Lamarin ne yafi karfin tunanin mai tunani, mamakin su tayaya akai yaran suke bala'en kama da ƴan family din su? _Ba zata juri bugun da zuciyarta ke yi mata ba, da azalzalarta akan son ganin fuskar yaron da hateem ya kwallafa rai akanshi, tabbas tana son ganin shi, kowa na gurin burin shi Danish ya cire mask din fuskar shi, sunyi matuƙar ƙagara da son ganin sa, walking gently gimbiya mujeedat ta tako ta tsaya gab da inda danish yake atsaya kamar mai wani nazari abu akanshi, idanunshi na kallon kasa sam bayason hada ido da kowa_ Sanya hannu tayi ta cire mask din dake akan fuskar shi............ Kiris ya raga zuciyar gimbiya mujeeda ta daina bugawa saboda razanar da tayi, gaba ɗaya hankulan su ya dawo kan shi, Wani irin mugun bugu zukatan su suka soma yi, yadda kasan ana dakan sakwara, Gaba ɗaya suka zazzare idanunsu gami da buɗe bakunansu saboda tsabar kiɗima kamar sun ga wani mugun abu, wato Sun gigita sun razana da ganin wanan abin al'ajabi da yai matuƙar Ɗaga hankulan su, Afirgice Chief Of Staff Na canada Ya dubi fuskar Security Advisor da wani irin ruɗani akan fuskokin su, at same time su ka yi saurin kallon Prime minister Hateem, Baba obie kuwa kusan suman tsaye yayi da ganin wannan Kama ta ban al'jabi, Senate lafeef da su His excellency sai faman jinjina kan su suke yi sam sun gaza magana kamar kurame, sai yanzu suka gane dalilin dayasa hateem ya firgice ma su da kaunar yaron ashe shi yasan abun da ya gani, Kai kowama dake a wurin ya rasa lissafin kwalwarsa saboda ganin fuskar Danish, Wai shin Ina Nazli? Ay tun da tayi tozali da danish tsabar firgici da ruɗani yasa har batasan sa'adda ta saki wayar hannunta ba, gaba ɗaya ta kife kan flloor, Jikinta ya kama kerma kerma tana faman zazzare eyes din ta akan fuskar shi yadda kasan twin brother din ta. saboda ruɗu tunani su ka yi ko dai Nazli ce ta koma inda danish yake atsaye hakanne yasa sukayi Saurin kai idonsu inda take atsaye don suga idan tana nan, Ganinta yasa suka ƙara rikicewa. Security adivisor ya kasa samun nutsuwa saboda al'ajabin da ya kama shi, Muryar shi na rawa rawa yana tangyadi cikin harshen turan ci yace" dama prime minister yana da wani ɗane da ba mu san da shi ba, ko kuwa ƙaninsa ne? Ko dai giyar dana sha ce takai mun karo? Pls ku yi min bayani yadda zan fahimta. Senate lateef ne ya bashi amsa da cewa"ba su haɗa alaƙar komai ba, kama ce kawai" babu alamun za su gasgata maganar shi. "Abun da ɗaure kai, amma ya ya akai su ke bala'in kama har haka? Kamar an yi photo copy din fuskar Hateem, ko ma ince Nazli" his exellency Deen ne yayi maganar, Yazrin sam takasa samun nutsuwa Sai kallon shi take yi ko ƙyaftawa babu, wato danish ya girgiza su da kyawun shi, Hankulan su Faryat ya tashi haikam tsabar yadda su ke kallon shi kamar za su haɗiye shi, yadda kasan irin kura taga naman nan. Haƙiƙa sun rudu da prisoners, babu wanda bai yi mamakin sanyin kyan su ba, da al'ajabin kamanceceniyar su da ƴan uwan su yadda kasan ya'yan cikin wasu daga cikin su tsabar yadda kamannin su ya bayyana da juna... Ganin kallon nasu ba mai ƙarewa ba ne gashi sunbar yara atsaitsaye, da sauri Ziyad ya ce "Lokaci yana tafiya, yakamata acigaba da shagali" kafin Ya ƙare maganar sautin waƙa mai ratsa zuciya ya karaɗe cikin hall din, Ɗaya bayan ɗaya Suka juya suna nufar wurin zaman su kowa da abun da yake saƙawa a cikin zuciyar shi. Hateem kamar jira yake yi a samu maslaha, jiki na rawa ya nufi danish ya ruƙo hannun shi acikin nashi, burin shi su haɗa ido don su kalli juna dakyau amma yaƙi bashi damar hakan, murmushi ne dauke akan fuskar sharafudeen sai faman kallon su ya ke yi, yaji dadin ganin hateem a irin wannan yanayin. Da zolaya yace irin wannan kallo haka? Ka da fa ka lashe mana yaro" ƴar dariya hateem yayi, Chief owais da ke kallon su ba karamin kwanciyar hankali ya samu ba ganin ya faranta ran uncle din sa "Uncle ka tafi da shi, zaman shi anan bazai yiwu ba, saboda baya son hayaniya, kuma baya son ana kallon sa, From now until nightfall, I entrust him to your care" wani irin farin ciki ne ya ƙara lullu6e prime minister, kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna, cikin sanyin murya yake fadin"nagode owais, wlh ka gama min komai, bazan ta6a manta alkhairin ka a gare ni ba, Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta min" addu'o'i ya dinga zuba mashi, bai manta da sheikh imam ba wanda ke atsaye tun dazu murmushine akan fuskar shi. "shukran jazeelan Ya sheikh, Allah ne kadai zai iya biyan ka, saboda babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani da su wurin yi maka godiya" ya faɗa yana ruƙo hannun sheikh imam gaba ɗaya wani irin annurin farin ciki ne akan fuskokin su. Unaisah da ke ta sauraron su aranta Allah Allah take Danish ya amince da buƙatar chief yabi prime minister don tasan halin shi da kafiya ba kowa ke iya tankwara shi ba. Kafin ta ƙare zancen zucin nata ba, da mamaki taga danish yabi prime minister hannun su ruƙe cikin na juna suka nufi hanyar fita daga hall din ko irin ya waigo ya kalle su baiyi ba, ajiyar zuciya ta sauke, sarai ta fahimci masu satar kallon ta. gimbiya mujeedat sai bin su da kallo take yi, tarasa ma wani irin tunani zatayi game da bawon Allan nan mai tsantsar kama da Nazli, kasa jurewa tayi da sauri ta bi bayan su, ita ma Yazrin ta bi su, Nazli ce kaɗai ba tayi yunkurin bin su ba, kwata kwata babu annuri akan fuskarta, Ita bakomai ne damuwarta ba face abu biyu, na farko yaron da ke kama da ita! arayuwarta ta tsani ace wani yana kama da ita, saboda izzarta, tafi so mai nata ya kasance ita kadai ke da shi, bayan wannan sai Unaisah! Hankalin ta bai kwanta da ita ba, saboda wani kallo da taga sun jefa wa juna a tsakanin ta da chief owais nan take taji bata son ganin yarinyar, Nazli tana da zafin kishi, izzarta ce ke hanata bayyanawa. Fuskarta babu annuri ta kai hannu ta dauki wayarta dake kan floor, da wani irin takun qasaita ta juya tabar wurin su. Mom turai da ke ta kallon su tun ɗazu take son tunkararsu ganin babu dama ne yasa ta yi shiru tana kallon badaƙalar da ake yi, yanzu kuwa da ta samu dama, Da sauri ta nufi wurin Azeeza saboda sun bata tausayi da suna kuka, hanky ta zaro daga purse dinta, ta zuƙunna agaban ta tare da sanya shi kan fuskarta ta shiga share mata hawaye Cikin kulawa tace "Stop crying kin ji ko? everything is over now, we are welcoming you to our family" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyinsu har sun fara ɗan sakin jikin su. A hankali Sir mubarak Ya nufi Jemimah dake a maƙale da Angel ta cukuikuiye mata rigarta zukunna yayi agabanta, ya ruƙo hannayenta a cikin nashi yana rarrashinta ganin har yanzu tana shesshekar kuka. "Sorry baby girl, share hawayen ki...." muryarta na rawa ta furta"wlh baku son mu, shiyasa ku ke korar mu, ni dai gida zan koma Allah" a fadace ta faɗa tana faman zabga masu harara, ƴan kumatunta sunyi jawur da su. Ba zato ba tsammani Taji Sir mubarak Ya dauketa dungurum Ya daurata kan kirjin shi, wuƙi wuƙi tayi da idanunta. "Sai mu ga da wasu kafafun zaki koma gida, ay tun da ki ka shigo wurin nan sai mun ci abinci dake, idan kuma mutun yace zaiyi min rigima zan sanya bindiga ne in har be mashi tsakiyar kan shi" Ya fada Yana daura yatsan shi akanta, Murmushi kowan nan su ya dan saki. "Bismillah ku shiga daga ciki mu zauna, ko baku gaji da tsayuwa bane" Zaki ne yayi maganar Yana nuna masu cikin hall din, su kansu so suke su zauna kafafuwansu har sun fara ruƙewa kawai suna fargaban shiga ne. Ganin hakan yasa zaki matsawa ya ruƙo hannun Sajeed Dana Naufal Ya shiga da su cikin hall din, Da sauri Dr Jazz Ya matsa Cikin su ya ruƙo hannun javed dana haris yayi ciki da su. Bayan mom turai ta gama sharewa azeeza hawayenta, ruƙo hannun ta tayi suka nufi table din su. babu wanda yayi tsammanin Hajiya malikat zata tanka, don tunda aka fara rikicin bata sanya baki ba, sai yanzu data matso kusa da su ta ɗan saki fuskarta tana fadin"naga kowa dan uwansa yake dauka nima bari na dauki nawa" ta fada tare da ruƙo hannun Unaisah, ta haɗa dana batool dake a gefenta"mu shiga ciki Ƴan mata," wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da sauri suka bi bayan ta, chief owais dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa sai kallon su ya ke yi, hankalin ya kwanta babu sauran damuwa. "Toh, ni ma dai bari na dauki nawa ƴan matan" hajiya madina ce tayi maganar da fara'a akan fuskarta ta ruko hannun Parveen da na hannah, ta nufi wurin zaman su da su, gaba daya sun koma ciki, hatta su Hajiya saratu kowa Ya koma mazaunin su wasu suna daga tsaye har yanzu hankalin wasun su bai kwanta da yaran ba, Abunne ya daure masu kai sun gaza samun sukuni a fakaice su ke satar kallon su. Tuni Daddy sharafudden yayiwa sheikh Imam mazauni a wurin su, umarni aka bawa servers din dake awurin akan su kawo masu abin da zasu ci, nan fa suka fara aikin jera masu abinci kala kala da abin sha shaƙe da table... Wata irin nauyayyar zuciya jemimah take ta faman saukewa, mom turai da sir mubarak sun tasa su agaba sai faman tarairayarsu su ke yi, kamar ƴa'ƴan cikin su. "Me ku ke son ci"? Cikin kulawa tayi masu maganar. Jemimah ce tai kokarin bude baki tace"komai ma muna ci" murmushi mom turai tayi, ba karamin burgeta su ke yi ba, "Ko kin lura yaran nan suna kama da ke? Kamar ƙannan Jazz saboda sunyi kama da shi kan shi" murmushi tayi tana kallon Sir mubarak da yayi maganar. "Nima nayi mamakin kamannin mu" ta fada idanunta akan fuskar Jemimah da azeeza, wadan da tuni suka fara cin abincin da aka kawo masu. 6angaren Su Hajiya saratu kuwa, sun kasa sun tsare sai jifar Parvin take yi da wani kallo mai wuyar fassaruwa, dama su biyune hajiya madina takai su tebur din su, ita da hannah wadda jikin ta keta kerma "Baki da lafiya ne"? Hajiya laurane ta jefa mata tambayar fuskarta a yamutse, girgiza kai Hanna tayi, ta6e baki tayi"to meye kike ta kermar jiki! Tun da kun riga da kun samu wurin zama, ay sai ku saki jiki kuma ku kwashi arziki" ta fada tana hura hanci. "Please ni ban kawo su nan da agaya masu magana ba!" Hajiya madina ce ta fada tana mai nuna 6acin aranta, kafin ta mayar da dubanta ga su parveen "Ku ci abinci mana" da sakin fuska tayi masu magana, parvenn kamar jira takeyi aikuwa ta dauki glass of juice ta fara sha, tana shanyewa ta soma cin fruit salat, bayan ta gama ta koma tana cin spring rolls, ɗan zaro idanu hajiya saratu tayi tana kallon ikon Allah, yadda kasan irin kwancen yunwar nan, Hajiya laurat tace"ba banza ba naga tayi kama dake ashe itama din acici ce" ta fada da zolaya tana yar dariya, parveen dai ko kallo basu ishe ta ba, ta dage damtse komai ci take, har kwara hannah a hankali take dan cakura tana ci "Wai ni ka ɗai ce nake mamakin kamannin yaran nan da family din nan"? Hajiya madina ce tayi maganar, Hajiya saratu tace"hmmm, ay ni abun ya gama ɗaure min kai, har yanzu zuciyata ta gaza samun nutsuwa, na ruɗe musamman dana ga yaron nan mai kama da hateem" lumshe ido Hajiya laurat tayi tunawa da surar shi don ba karamin tafiya yayi da imaninta ba. Hajiya muhibbat tace"na girgiza da ganin shi, lokacin da mujeeda ta cire masa mask din fuskarshi araina sai da nace wannan kyau haka kamar ɗan sarkin aljanu? Dariya su kayi gaba dayan su "Ay tun da nayi mashi kallo ɗaya na kau da ido, saboda wannan kyan nashi kadai ya isa yasa mace fadawa ga halaka" acewar Hajiya laurat "Ina kananun Yaran nan ƴan mata masu kama da tagwaye, wlh yadda kukasan Hajja turai tayi kakin su, Ƙaramar fuskarta da komai kalar nasu ne, sai kuma wani mai kama da hajjaty kamar anyi photo copy din fuskarta acewar Hajiya mudeena. "Nima na lura da su, amma fa ni duk ba wannan ba, Yarinyar nan ta burge ni, kwarin gwiwarta ya tafi da imani na....".hajiya muhibbat ce ta yi maganar tana kallon can cikin hall din inda su unaisah su ke Duk wannan suratan da su ke yi, akan kunnan su Parveen sai dai sam basa ganewa hankalin ta na kan abinci ci, hajiya saratu sai faman satar kallon ta ta ke yi afakaice, tun parven bata lura ba har dai ta gano ta, da zarar ta ɗago suke haɗa ido da juna. _________________________💞 Gyaran murya Zaki yayi masu, a tare su ka dago suna kallon shi, "Kunyi shiru baku faɗa mana sunayen ku ba" Murmushi sajeed ya ɗanyi "Ni sunana sajeed, shi kuma ɗan uwana Sunansa Naufal" "Masha Allah, It's a pleasure to meet you both, I hope you will feel at ease with us, sannan ku dauka tamkar ƴan uwan ku ne mu" jinjina mashi kai su ka yi alamar eh. "Okey, Yanzu ina so ku bani mamaki, ku cinye wannan abincin da nasa aka kawo maku" dariya su ka yi gaba ɗayan su, har cikin ransu sunji dadin tarbar da zaki yayi masu. Nan fa suka saki jiki suka soma cin abinci. Ɗagowa zaki yayi tare da kallon Su captain, yayi mamakin ganin yadda suke dogon wuya suna leƙen table din su unaisah. Da zolaya yace"kun dai ji kunya wlh, ina ajin naku yake"? dariya ziyad yayi yana fadin"wlh yarinyar ce ta tafi da imanina, ni ka gane bawai sonta nake ba, wannan ay tafi karfin ɗan jarida, kawai dai kamar nasan fuskarta, sai dai narasa gane a ina nasanta, abun ya shige min akaina...." Daƙyar captain Yaseer Ya janye idonsa daga kan fuskar Unaisah. "Nifa ina ji zan canza sheƙa ne, wlh ko da dukiyata zata ƙare ne akan neman waccan yarinyar saina jaraba sa'ata..." justice na murmushi yace"karka soma wlh, domin kuwa iskace zata wahalar da mai karan kara, ay ni tun daga kan kallon dana ga chief yanayi mata raina ya bani cewar da akwai wata aƙasa" Kwa6e fuska captain yayi"kana nufin yana sonta"? Dage mashi gira Justice yai. Yatsina fuska yayi"again, bayan ya kwace nazli, ga kuma wata, mata biyu kenan zai aura!" "Ni duk ba wannan ba ma, ganin yaron nan mai suffar lu'u lu'u yaɗan girgiza ni, wai ku bakuyi mamaki ba? Ziyad ne ya fada. "Ay mamakinne yasa ka ji munyi shiru da zancen shi, domin kuwa kwakwalwa zata iya daina aiki" dariya su ka yi jin abun da Justice yake fadi. "Gaskiya nayi mamaki ace wai yaron nan a daji aka tsince shi, ay hankalima bazai dauka ba, kai daga ganin zubin halittarsa ɗan wani ne, shiyasa nifa gaba ɗaya na ruɗe da lamarinsu, kaina a duhu yake, kamanninsa sun 6aci da Uncle Hateem kamar yayi kakinsa kuma gaskiya ina kishi da shi Allah" captain ne ya fada. Sajeed dake sauraran su murmushi ne dauke akan fuskarshi, Naufal Kuwa gaba ɗaya ya rasa nutsuwarsa saboda kallon da hajjaty take mashi, Da zarar Ya ɗago da idanun shi karaf suke sauka acikin nata, saboda shi ta baro wurin da take ta dawo kusa da table din dake fuskantar nasu ta zauna tana ta kallon shi, ko kyaftawa babu. Cikin muryar raɗa yace da sajeed "waccan matar sai kallo na take yi kamar zata haɗiye ni, taƙi bari naci abinci cikin kwanciyar hankali, bansan me na tsare mata ba, ni fa duk na tsorata" da sauri sajeed ya saci kallon inda naufal ke nuna masa ganin hajjaty yasa shi yi ma naufal rada"ka kwantar da hankalin ka, saboda kana kama da ita ne shiyasa take kallon ka" ya fada yana ƴar dariya, shi dai naufal hankalin shi yaƙi kwanciya, kamar anyi mashi dole ya kalle ta. Hakanan take jin shi a zuciyarta, komai nashi sak kalar na yaron ta, bazata ta6a mantawa da suffar shi ba, abinne ya daga hankalinta, ya kuma tada mata tsohon Ciwon dake kwance a cikin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face yaronta da ta rasa tun farkon zuwan su nigeria wannan wani labari ne wanda sai nan gaba kaɗan zamu ji shi...🥺 Dr jazz sai Rawar kai yake yi da su Haris, kamar kannansa, Ya tasa su agaba shi da ibad sai fira suke jan su da shi. "A cikin ku wanene Haris"? yai tambayar yana duban su, da yake yana fuskantar su, da sauri Javed Ya nuna haris," ɗan zaro idanu Dr jazz yayi"masha Allah, kaine haris kenan"? Jinjina mashi kai haris yayi alamar eh, da biyu ya tambaye shi saboda yasha jin labarin shi awurin deeja, tana yawon yin sambatun sunan shi idan haukan ta ya motsa. Ruƙo hannun shi yayi a cikin nashi yana fadin"kun burgeni, ina kaunarku, ganin ku kawai da nayi kun kwanta min arai na" murmushi kowan nan su ya saki. "Wlh nima Na kamu da kaunarsu, dan Allah ku dawo gidan mu da zama, dama ni bani da abokai a nigeria" ibad ne yayi maganar da yar shagwa6ar shi. "Kun ƙi sakin jiki damu, ko dan baku san mu bane" kallon juna haris da javed su ka yi, sufa basu saba mu'amala cikin mutane ba. "Okey, yanzu bismillah mu fara cin abinci" Atare suka soma cin abincinsu, jefi jefi Dr jazz yake satar kallon Haris Aranshi ya ayyana duk ranar da khadeeja ta yi tozali da shi ba karamin hauka zatayi ba. "Yaya jazz, wadancan twins din sunyi kama da mommy da kai," ya faɗa yana nuna su azeeza. Murmushi jazz yasaki shi kanshi ya kamu da kaunsarsu, tun dazu yake ta faman satar kallon su, ji yake tamkar kannansa na jini. "Please Ya jazz mu yi wa daddy magana, akai mana su gidan mu, ni wlh bana so suna kuka, kaga mom saratu da waccen tsigai din ko ina ruwansu da rayuwarsu, ni fa shiyasa bana son zuwa nigeria saboda su, ko gajiya da masifa basayi, ina ruwan su da ƙaddarar rayuwarsu? Su ne suka tsara ma kan su ne? Ni fa kaganni ya jazz ba ruwana da shiga sabgar wani ko in wulakanta sa, wai don basu da asali, sai kace an gaya masu daga sama suka fado, mutun dai ay sai an haife sa yake xuwa duniya ba daga sama aka wurgo saba, balle ace da rashin asali aka haife su," Rai a6ace ibad yakeyin maganar da zallar shagwaba. Su haris sun saki baki suna kallon shi, komai nashi burge su ya ke yi, ganin suna kallon shi ne yasa shi dakatawa da maganar yana yar dariya yace"na cika ku da surutu ko"? Girgiza mashi kai su ka yi alamar a'a. Hankalin Zahra Yaƙi kanciya, bakomai ne yajawo hakan ba face Unaisah, ko kwanto takeyi kamar tasan ta, sai dai takasa gane a ina tasan fuskarta, sai yanzu ta samu damar kare mata kallo daga inda take azaune, duk wani motsin unaisah akan idon zahra, ta kwallafa rai akan son yin magana da ita dama kawai take jira.... Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin nauyin haɗa ido da chief ba, tun da suka zauna ta sunnar da kanta tana wasa da yatsun hannayenta, ƙamshin turarensa gaba ɗaya ya cika mata hanci, duk wannan abun da take yi chief owais na lura da ita, da yake suna fuskantar juna da shi, wayarsa ce ruƙe a hannunsa da yake daddanawa cikin nutsuwa. Ga jerin kayan abinci da aka shaƙe masu table da shi amma takasa ci, ga yunwa tana ji. Gyaran muryar da Hajiya Malikat tayi masu ne yasa suka dago a tare suka kalle ta, tana daga zaune gefen chief "Nasa an kawo maku abinci kun ƙi ci, meyasa?"cikin kulawa tayi ma su maganar. Murmushi suka dan saki suna faman noƙe kai. "Ko dai Kunyar Chief ku ke ji" kamar ta shiga zuciyar su, murmushi tayi ma su "Ku ci mana, hankalin shi ba akanku Yake ba" Batool ce ta fara cin abincin ganin zata sanya hannu yasa hajiya malikat cewa"ki ɗauki tsokali" muryarta na dan rawa tace"ban iya ci da shi ba" "Okey, nagane ki sanya hannun" Hannu tasa ta soma ci, unaisah kuma ta ɗauki glass na lemu tana ɗan kur6an shi sama sama take satar kallon fuskar chief owais da zarar taga zai ɗago da idanunsa take yin saurin kau da nata gefe ɗaya, bakomai ne yaja hankalin ta gare shi ba, face kamanninsu da Danish, kusan komai nasu iri ɗaya banbancin su kaɗan. Mai girma sharafudeen ne ya nufo wurin su, fuskarshi da fara'a Ya samu wuri ya zauna yana dubansu, da sauri suka gaishe shi cikin girmamawa ya amsa masu. Duban owais yayi"baka cika min alkawari na ba" ya faɗa yana ɗan haɗe fuskarshi. Dagowa chief yayi tare da kallon daddyn nasa, da alama bai fahimci me yake nufi ba "Maganar da mu kayi dakai ɗazu da safe" Sai yanzu ya fahinci inda zancen daddyn nasa ya dosa. A hankali ya ɗaura idanunsa kan Unaisah dake kur6ar lemu. Murmushi hajiya malikat tayi "tubarakallah Masha Allah, nagode ma Allah da ya nuna min wannan ranar da raina da lafiyana, gani ga second in-law ɗina, yarinya mai hankali da nutsuwa, ni dai surukan nawa duk kyawawa ne, ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa...." amsa mata yai da ameen. Ga dukkan alamu unaisah bata fahimci takan zancen ba, ta dai ji ana zancen suruka, Ruƙo hannunta daddy Sharafuddeen yai a cikin na shi fuskar shi dauke da murmushi yace"I'm so happy to meet you, my daughter-in-law, I don't even know how to describe the joy I feel just from seeing you today" murmushi tasakar masa har dimple din ta lotsa, duk da batasan wanene shi ba, ranta yana bata cewar Mahaifin Chief ne saboda kamannin su da ga gani. Muryarta cike da jin nauyin shi ta furta"nima naji daɗin haɗuwa da kai," "Shekarunki nawa ne"? ya jefa mata tambayar. "Sha shida amma na kusa shiga ta sha 17" A wayance Daddy sharafuddeen yace"Wonderful, Now, what about your studies? Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta amsa mashi tambayar da yayi mata ba. "Sorry kada daddy ya takura maki da tambaya ko"? Murmushi ta ɗanyi masa. "Inaso ne nasan me yakamata mu fara yi don tallafa ma rayuwar ki, ko ba haka ba" cike da rashin fahimtar kalamansa take duben shi, Hajiya malikat dake kallon ta murmushi ne dauke akan fuskarta, yarinyar ta kwanta mata aranta. Chief owais ya nutsu yana sauraron su. "Aure ko karatu wanne kika fi so a yanzu" waro mashi gray eyes dinta tayi da sauri ta sanya tafin hannu ta rufe fuskarta alamar taji kunya, hakan da tayi ba karamin dariya ya basu ba, hatta chief saida yayi murmushin gefen fuska. Hankalin batool gaba ɗaya baya akansu tun da ta samu abinci take ta aikin ci. "Kinyi shiru baki ban amsa ba" ya ƙara tambayarta, ƙasa ƙasa da murya chief ya furta"dad..." dakatar da shi daddy sharafudeen yayi"no kada ka shiga tsakanina da surukata, baby Angel ke nake sauraro," tayi mamakin jin ya ambaci nickname dinta, ba tare data buɗe fuskarta ba tace"Aure zanyi kafin na cigaba da karatu" Murmushin fuskarsa ne ya faɗaɗa da zolaya yace"ta kwana gidan sauƙi, yanzu faɗa min kina da saurayin da zaki aura ne ko babu" da sauri hajiya malika tace"haba dan Allah, kabarta mana, miji ay ta riga da ta samu ko ba haka unaisa"? Ɗaga mata kai tay alamarh. Duk wannan abun dake faruwa a tsakanin daddy sharafudeen da Unaisah akan idanun Nazli wadda tuni tagama cika ta batse ranta yayi mugun 6aci tamkar ta ɗaura hannu bisa kai tayi ihu, wani irin kishine Ya ziyarce ta ganin yadda chief owais yayi zaman shi a wurin yarinyar, tun zuwan su hall din bai tako yazo inda take ba, kamar ma baisan da zamanta ba..... Bazata juri kallon su ba, miƙewa tayi da niyar tabar hall din kamar daga sama muryar Faryat ta katse mata hanzarinta. "sister Nazli, Ina zaki je ne bayan ba'a kammala taron ba"! Ba tare da ta kalli faryat ba tace"bazan juri zama ba, sai nake ga kamar ba don mu aka shirya dinner din nan ba, because everyone's attention is focused on them. Daddy Ya tafi da wani wanda bamusan wanene shi ba and the chief is only paying attention to that girl." ta faɗa tana nuna saitin inda unaisah ta ke da hannun ta. Ruƙo hannunta faryat tayi a cikin nata" Sister, ba ke ya kamata ki bar hall din ba! They are the ones who should leaves" Girgiza kai Nazli tayi"no ni bana son hatsaniya, barina shi yafi min kwanciyar hankali" Ta faɗa tana kokarin kaucewa rukon da faryat tayi mata. Sai dai taki bata damar tafiya "Nasan menene ya 6ata maki rai sister, ba ke kaɗai ba, mu ma ran mu ya 6aci da zuwansu saboda babu alkhairi atattare dasu, gaba ɗaya hankali Ya koma kansu, Amma ni na maki alkawarin zan kawar da yarinyar can daga hall din nan, indai hakan zai kwantar maki da hankalin ki, amma bai kamata ki tafi ba, ba zamu ji dadi ba" shiru Nazli tayi na ɗan wani lokaci kafin ta ɗan sauke ajiyar zuciya. "What are you going to do to her I hope you won't hurt her."? Shu'umin murmushi faryat tasaki, "Don't worry sister, I won't hurt her. I'll just keep her out of sight until the dinner is over." "Bana so a samu matsala faryat!" 'kawai kibar komai a hannu na, abun da nake so dake da zarar kinga babu yarinyar kiyi kokarin jan hankalin Yaya owais" A hankali Ta furta Okey, fasa fita tayi da sauri ta juya ta koma wurin zaman ta. Faryat kuwa ba karamin dadi taji ba, dama ta tsani ganin unaisah, tun farkon shigowarsu taji bata yi mata ba, da sauri ta koma wurin su Yusra tana jiran ta samu damar da zata aiwatar da mummunan kudurin ta........ Bayan kammala cin abinci, Mc Ya Kira su ɗaya bayan ɗaya suke hawa saman step suna taka rawa, sautin kiɗa Ya karaɗe ko'ina na hall din, Ta ko'ina hasken camera ne ke Ƙyalli, sai daukar hotuna sukeyi, abun ba karamin burge prisoners yayi ba, Ay tuni Sajeed Ya miƙe dama ta samu tun da ya shiga filin Ya fara taka rawa hankalin kowa ya dawo kan shi, harta su baba obie da suke atsaitsaye hankalin su na akan shi, abun a jininsa yake da zarar yaji kiɗa bai iya jurewa kamar ana kada mashi mazari, In har baiyi rawa ba hankali sa bazai kwanta ba, wakar da aka sanya tana ƙarewa wakar calm down ta shiga, aiko jiki har rawa yake yi su Parveen suka shiga fili suka dinga tikar rawa, gaba ɗaya suka ja hankulan mutanan hall din, sunyi matuƙar burgesu in ka cire su Yusra dake jin haushin su badan komai ba, sai dai saboda sun hana su rawar gaban hantsi, Hankalin unaisah ba karamin tashi yayi ba, ganin yadda suke rawa da alama sun manta a ina su ke ne, daga ita sai batul ne ba su shiga filin ba, Manyan mutanan dake a wurin ne suka soma yi masu liƙin kuɗi, tamkar ana yayyafa masu ruwan sama. Hajiya turai da Hajjaty suma suka shiga filin suna tayasu yin rawar, kusan gaba ɗaya suka shiga cikin su, cikin raha da nishaɗi suka taka rawarsu. Jemimah ta dage duk wanda ya lika mata kuɗi sai ta kwashe su ta tura a aljihun rigarta, ta tarasu dayawa har a hammata take saƙe wasu, tayi zaton abun wasan yara ne. Mutanan dake harin Unaisah dama jira suke ta miƙe, a lokacin chief Owais Yabar wurin su, Ya tafi amsa kiran da akayi mashi awaya. Miƙewa ta yi tana tafiya a hankali yayin da idanunta ke akan dance floor din, da alama itama so takeyi tayi rawar ta ɗan gagije jikinta. "Baiwar Allah sannu" jin muryar mutun abayanta yasa tayi saurin dubanta, zahara ce fuskarta dauke da murmushi, Mayar mata da martanin murmushin unaisah tayi. "Yawwa" "Tun ɗazu nakeson yi maki magana ban samu damar yi ba, saboda mutanan da kike atare da su...." da ɗan mamaki take kallon bakuwar fuskar da tayi mata magana. Miƙa mata hannu zahra tayi don su gaisa, A hankali unaisah ta ɗaura hannunta a cikin nata. "Sunana zahra ke fa"? "Unaisah" "Banyi tunanin zakiyi saukin kai har haka ba," Murmushi unaisah tayi mata. "meyasa kikace haka"? "Raina ne ya bani haka" girgiza kai unaisah tayi "Kin burge ni, idan badamuwa inaso muyi hoto a tare" Bata kawo komai aranta ba, ta amince ma zahra. Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin curo wayarta daga cikin yar purse dinta, ta dinga daukar su hoto da unaisah, A kalla zahara ta dauki hoto sama ashirin, Tsabar iyayi na zahra harda rungumeta sukayi hoto amanne da juna kamar kanwarta.... "Kinga yanzu na samu wanda zan dinga kallo awayana," ta faɗa bayan sun gama "Ko zan iya samun layin wayarki? Ina so mu dinga gaisawa. "Ban haddace number dina ba, kuma wayar bata a hannuna" Shafa gefen fuskarta zahra tayi"ba damuwa, ay ina zuwa estate din nan zamu dinga haduwa...." wayar zahra ce ta soma ringing da ɗan sauri tace ma unaisah yanzu zan dawo ana kirana" amsa mata tayi da toh, har zahra tabar wajen Unaisah bata daina bin bayanta da kallo ba, hakanan taji ta burgeta, aranta ta ayyana wato duk yadda wani yaƙi ka, to wani zai so ka ne. Murmushi tayi, tare da juyawa da niyar tabar wurin cikin rashin sa'a ta bange ɗaya daga cikin servers din dake safa da marwa wurin raba abinci, Gaba ɗaya tray din lemun da matar ta ɗauko ya 6are a jikin abaya dinta, glass cups din suka rikito kan floor, hankalin ba karamin tashi yayi ba ganin ta 6ata mata wankanta don ma Allah yasa rigar baka ce Muryar matar na rawa ta soma bata hakuri. Shiru unaisah tayi tamkar bazata tanka mata ba tace"bakomai, ay ba laifin ki bane, Ni ce na bangaje ki, bansan da mutun abayana ba" A ruɗe matar tace"akwai rest room ki zo muje ki wanke rigarki please, idan ba haka ba za'a hukunta ni ne idan wani yaga ruwan lemun nan a jikin rigar ki" Girgiza kai unasah tayi"a'a bani buƙatar zuwa, Ki tafi kawai, ay rigar baka ce babu wanda zai gani" Magiya matar tadinga yi mata akan tazo su tafi ta wanke mata rigarta, ganin tasa naci ne yasa ta amince mata, da sauri matar ta zukunna ta kwashe glasses din ta mayar a tray, kafin ta juya Tayi gaba unaisah tabi bayanta, babu wanda ya lura da abun da ya faru saboda sautin kiɗan daya karaɗe hall din hankalin kowa na akan dance floor,. Wani corridor suka shiga a inda jerin rest rooms din suke ta nuna mata ɗaya daga cikin su, ki shiga zan jira ki anan" amsa mata tayi da toh. Unaisah kamar kada ta shiga haka take ji saboda hankalin ta bai kwanta da matar ba, buɗe kofar tayi shigarta ke da wuya taji alamun an datse ƙofar, sai dai ranta bai kawo mata komai ba, agaban sink ta tsaya ta kunna tap ruwa ya shiga karanyowa ta soma wanke inda lemun ya 6ata, bayan ta gama ta tsaya tana kallon fuskarta ta cikin mirror bakomai take tunawa ba face fuskar chief Owais hakika Yaja hankalin ta, musamman a lokacin da aka so aci mutunci su ya kare masu martaban su, Murmushi tasaki har dimple din ta ya lotsa, can kuma ta juya akalar tunanin nata ga garkuwarsu, tasan duk inda yake ayanzu yana cikin koshin lafiya don ta fahimci prime minister ba karamin kaunarsa yake yi ba, tabbas zataso taga yadda zai tarairaye shi..... _Sam ta manta a rest room take, tunawa da yan uwanta yasa tayi saurin juyawa zata fuce sai dai me? Tana jan ƙofar taji kamar ta damƙi dutse, bata kawo komai aranta ba, ta soma knocking tana fadin"pls kibuɗe min kofar na kasa" shiru taji mata bata amsa mata ba, kusan sau uku tana neman taimakonta amma shiru, bata amsa mata ba, gaba ɗaya taji ta takura hankalin ta ya fara tashi, bubbuga ƙofar tadinga yi tana cigaba da fadin pls bakowa ne akusa ku buɗe mun kofa, tun tana sa ran za a buɗe mata har ta fara fidda rai, zuciyartace ta soma raya mata gaya can za'a cutar da yan uwanta aikuwa da karfi ta soma bubbuga ƙofar kamar zata balle ta, har kafa take sanyawa tana harba jikin ta, babu alamun zata buɗe, tana nishi ta ja da baya ta watso da gudu ta bangaji kofar duk don ta samu ta buɗe amma duk abanza, Lokaci ɗaya tafara burkicewa dama brain ɗin su da rauni acikin ta, gaba ɗaga rayuwar kullan da su ka yi a gidan kurkukun ƙaddara ta fara dawo mata a cikin kanta, sautin dariya dariya ta soma ji da shessheƙar kuka yaran da muryoyin wadannan tsaffin da suka ta6a bata naman mutun ta ƙarfi suka sanyata dole ta ci, runtse idanuwanta tayi tare da sanya tafukan hannayenta ta daddafe kanta dake wani irin mahaukacin sarah mata, wani irin tsoro da firgici ne ya soma ziyartarta, rushewa tayi da kuka tana bugun kofar muryarta da shessheƙar kuka take fadin"Wayyo Allahna ku buɗe mun kofa! na shiga uku, zan mutu kaina, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in Boss ka buɗe min kofa zasu kashe ni, Danish kana ina kazo ka taimake ni, nasan bazaka bari a cutar dani ba, nashiga ukuna sajeed naufal Batool wai baku jina nane so kuka na mutu.... cikin fitar hayyaci take yin sambatun tuni mayafin dake akanta ya zame ƙasa, duk tabi ta yamutsa gyaran gashi da akayi mata tamkar mahaukaciya haka ta koma, jikinta duk ya raunata saboda bugun kofar da take yi tana faman ciccije la66anta, ga ƙarancin iskar dake a wurin ta fara affecting dinta, gwanin ban tausayi baiwar Allah, jan numfashi ta cigaba dayi tana ganin jiri jiri a idanunta kamar daga sama taji zubar wani abu a tsakankanin cinyoyinta da wani irin matsanancin ciwon mara na fitar hayyaci nan take wata juwa ta kwashe ta gaba ɗaya ta kife kan floor sumar kanta ta tarwatse har ta saman fuskarta, hannayenta daddafe da cikinta dake ta murɗamata yanayi mata zogin azaba, muryar ta adisashe take ambaton Allah.............._ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Mu haɗu jibi Alhamis Idan Allah yakaimu da rai da lafiya* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* S kukun Kaddara Takun Karshe Page 14 Complete by Novels Elite Admin May 31, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ _cikin fitar hayyaci take yin sambatun tuni mayafin dake akanta ya zame ƙasa, duk tabi ta yamutsa gyaran gashi da akayi mata tamkar mahaukaciya haka ta koma, jikinta duk ya raunata saboda bugun kofar da take yi tana faman ciccije la66anta, ga ƙarancin iskar dake a wurin ta fara affecting dinta, gwanin ban tausayi baiwar Allah, jan numfashi ta cigaba da yi tana ganin jiri jiri a idanunta kamar daga sama taji zubar wani abu a tsakankanin cinyoyinta da wani irin matsanancin ciwon mara na fitar hayyaci nan take wata juwa ta kwashe ta gaba ɗaya ta kife kan floor sumar kanta ta tarwatse har ta saman fuskarta, hannayenta daddafe da cikinta dake ta murɗamata yanayi mata zogin azaba, muryar ta adisashe take ambaton sunan Allah da daƙyar daƙyar, zufa ce ta soma tsastsafo mata ta ko'ina na jikin ta, kafin wani lokaci jikinta ya saki tamkar matacciya ko yatsanta bata iya ɗagawa ta gama fita hayyacin ta............_ *Shin Ina prime minister ya tafi da garkuwa?* Lokacin da suka fito daga Hall hannun su ruƙe cikin na juna, Yayin da gimbiya mujeedat da Yazrin suke a biye da bayan su, gaba ɗaya hankalin Jami'an da ke tsaron wurin Ya dawo kansu, da wani irin tsantsar mamaki da Al'ajabi suke kallon fuskar Danish da ta prime minister, Musamman jami'an Canada sun yi matuƙar girgiza da ganin shi, sun ruɗe sai faman Kallo ƙurulla suke bin su da shi. Wata danƙareriyar mota Suka nufa, irin motar da a mafarki kaɗai talaka ya ke iya ganin ta, da sauri Wani gabjejen Soja Ya buɗe masu murfinta, Cikin motar yadda kasan bedroom tsabar haɗuwarta ga wani sanyin A.c dake sanyaya zukata, a tare suka shiga ciki ba tare da sun raba hannun su daga cikin na juna ba, Gimbiya mujeedat da Yazrin motar dake a jere da tasu suka shiga, zuciyoyinsu cike fall da al'ajabin Danish.... Kusan a tare motocin suka soma tafiya A hankali, Yayin da sojoji ke take masu baya, da kafafuwansu suke tafiya ta gefe da gefen motocin nasu. Lumshe idanu gimbiya mujeedat tayi yayin da brain din ta ke tariyo mata fuskar Danish, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin tsantsar kaunarsa ba, farat ɗaya taji ta kamu da son shi ya kwanta mata aranta, batasan ma ya zata mistalta yadda take ji azuciyar ta ba. Ita kanta Yazrin zuciyarta ta tsunduma a kogon kaunar matashin da bata san wanene shi ba, jin shi take tamkar ɗan uwanta na jini...... "Mommy, fatana Allah yasa ba mafarki na ke yi ba" can cikin kunnanta ta tsinkayi maganar Yazrin da tayi magana cikin harshen larabci. Numfasawa ta ɗanyi muryarta da wani irin sanyi ta soma magana da yaren su na larabci "ban ga laifin mijina ba, yanzu nake danasanin maganar dana gaya mashi ɗazu da mu ka shiga restroom, ban ta6a tsammanin zanga yaron haka ba, ay dole ma ya nemi zaucewa, Ni ko a tarihi ban ta6a jin labarin kamanceceniya irin wannan ba" "Abun da yafi ɗaure mun kai shi ne, ba mu haɗa alakar komai da shi ba, bamu ta6a ganin ba, ba mu ta6a jin labarin shi ba, sai yau da Allah Ya haɗa mu..... Fuskokin kowan nan su da tsantsar al'ajab Slowly motor su ta ratsa katafaren entry way na shiga gidan hateem dake a tsare da security, basu nufi ko'ina ba sai cikin Ƙawataccen Lambun gidan. Bayan sunyi parking, da sassarfa sojojin dake safa da marwa su ka ƙaraso tare da buɗe ma su marfin motor. A hankali Prime minister Ya dira kafarsa Ya fito tare da ruƙo hannun Danish, Lokacin daya fito daga motar kusan suman tsaye jami'an dake tsaron gidan su ka yi, sai faman yin dogon wuya suke yi suna leƙen fuskar danish, Sun saki bakunansu kamar lehen sakarai, ƙasa ƙasa da murya sautin raɗar da sukewa junansu ta soma baiyana "Abun mamaki bai ƙarewa"! "Kodai idanuwana ne suke nuna min badai dai ba? "Dama prime minister Yana da ɗa Namiji ne? "To ko dai 6acewa yayi ne sai daga baya aka gano shi? In ba haka ba ni dai a iya sanina ya'yan sa biyu mata....." Murmushin gefen fuska prime minister ya ɗan saki jin tseguminsu, aranshi yana mai jin wani irin annushuwa. sai bayan da suka soma tafiya tukunna motarsu gimbiya mujeedat ta ƙaraso, sam bai son sun biyo su ba, saboda ya makance idanunsa danish kadai su ke iya gane masa, Fitowa su ka yi a tare suka bi bayan Su prime minister, wanda Ya miƙi hanyar shiga wurin shaƙatawarsa da ke a cikin garden. Yayin da suke tafiya wata irin ni'imtacciyar iska ce ke ratsa fatar su hakan bakaramin ƙaimi ya ƙarawa yanayin ba, danish Ya nutsu Yana bin furannin dake a garden din da kallo, dama can shi ma'abocin son furannine da alama dai Garden din ya burge shi... Hateem sai satar kallon shi ya ke yi kamar zai lashe shi, shi kuwa wanda akeyiwa kallon bai ma son anayi ba. Su Gimbiya Mujeedat da Yazrin suna a biye da su ba tare da sanin su ba. Sauke idanunsa yayi akan Peacocks da ke yawo a garden din sun bubbuɗe Tail feathers dinsa gwanin ban sha'awa, ba karamin burge shi su ka yi ba.. Wani ƙawataccen wuri suka nufa, inda akayi shimfiɗa ta alfarma irin ta sarakuna, a kewaye yake da furanni launuka daban daban, Ga wata lumbutsetsiyar Round mattress mai tudu lallausar gaske, an kewaye ta da matassan kai masu laushi. "Bismillah mu zauna" muryar Hateem ce ta dawo dashi daga kallon gardeen din da yake yi, A hankali suka zauna saman shimɗidar. Daga inda suke a zaune suna fuskantar swimming pool tamfatsetse, launin ruwan da ke a cikinsa blue sky ne pure, ga wasu fararen agwagi saman ruwan suna ta shawagin su. A ƙalla sun dauki tsawon mintuna babu alamun danish zai mayar da hankalinsa akan prime minister, ya nutsu sai kallon agwagin ya ke yi. Yayin da shi Hateem din gaba ɗaya ya tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan danish, wani irin kallon kurulla yake jifar shi da shi mai dauke da zallar kaunarsa, Jin shirun yayi yawa yasa shi yin gyaran murya, hakan Yaja hankalin Danish zuwa gare shi, slowly ya juyo tare da ɗaura fararen idanunsa akan fuskar minister, a karo na farko kenan daya fara kallon shi, nan fa suka fara jifawa juna kallon kallon, ko ƙyafta ido ba sa yi, sai da suka kusa shafe mintuna batare da sun kau da ido ga juna ba, su gimbya mujeedat dake a tsaye can gefen wata bishiya mai yalwar rassa da ganyayyaki sun kura ido suna kallon su, Ita da yazrin dake a gefen ta. Wani irin ƙwarjini Danish yayi mashi, da sauri ya katse kallon da suke jefawa juna ta hanyar yi mashi magana "Sorry ban gabatar maka da kaina ba, Ni sunana Prime minister Hateem Obinna, kai fa"? Ya faɗa yana duban shi har lokacin danish bai daina jefa mashi kallon ba, babu alamun zai tanka mashi kamar akwai wani abu daya ja hankalin da yasa shi kallon nasa. "Ka yi shiru baka ce komai ba," kamar kurma haka danish yayi mashi. Dafe kai Hateem yayi muryarshi da kasala ya furta"please ka yi min magana, ba ka son yadda na ƙagu da son ganin ka samu lafiya ba, na damu da kai kamar yunwar ciki na, dan Allah ka saki jiki dani, kada ka azabtar dani da kaunar ka...." fuskar shi a yamutse yake yi mashi magana. "Ina fata babu inda ke yi maka ciwo yanzu"? Ya jefa mashi tambayar, lumshe mashi idanu danish yayi alamar eh. "Ya Ilahi, ba zaka yi min magana ba, sai dai ka yi min nuni da ido, ni bana so ka daure ka yi min magana, Inason jin muryarka ko hankalina ya kwanta, namanta ban faɗa maka ba, gobe da asuba zan bar ƙasar ba lallai mu sake haɗuwa ba, shiyasa nakeso ka bani haɗin kai mu more lokacin nan da muka samu...." cikin sanyin murya ya ƙare maganar. Har lokacin kallonsa danish ya ke yi, abun ya ɗaure mashi kai, Ya rasa gane ma'anar kallon nan. "Ko dai kana mamakin kamannina dakai ne"? shiru yayi mashi. "Wayyo Allah na, to ko dai baka jin harshen hausa ne inyi maka da turanci ko larabci ko french wanne yare kafi ji a cikin wadannan"? A ƙagare da son jin amsar shi ya faɗa yana kallon la66ansa burin shi ya motsa su don yayi magana. Ƙiri ƙiri danish yana neman ya zautar da prime minister, zuciyarshi a jagule yace"nayi maka uziri tun da ba ka jima da farkawa ba, may be har yanzu baka gama dawowa normal ba, a hakan ma na samu kwanciyar hankali, ganin ka da nakeyi ba karamin faranta raina yayi ba" ya fada yana ɗan murmushi sama sama. "Nasan kana jin yunwa bari nayi magana akawo mana abinci" wayarsa ya zaro daga aljihunsa har time din yana lura da kallon da danish ke jefa mashi har ya fara jin shakkar ko dai ifritan dake jikinsa ne suka motsa, dauriya ce kawai irin ta Hateem "Namanta ban tambayeka ba, wani kalar abinci kake son ci"? Shiru yai masa, hakan yasa shi yamutsa fuska "Okey,Tun da baka iya yi min magana kar6i waya ka rubuta min ta text message sai in karanta" ya faɗa tare da miƙe ma danish wayar, baiyi tsammanin zai kar6a ba, sai gani yayi yasa hannu ya kar6a, Ya soma daddanata, Wani irin dadine ya lullu6e hateem, abun mamaki ya dauki lokaci yana yi mashi dogon typing har mamaki ya kama Hateem sai da ya mula yasha iska tukunna Ya miƙa ma Hateem wayar, Cike da zumuɗi ya kar6a don ganin me ya rubuta mashi Har saida gabanshi ya ɗan faɗi ganin jagwalgwalon da danish ya rubuta mashi, irin wanda yara sukeyi idan suka damƙi waya. da sauri ya dago suka haɗa ido da juna, baisan sa'adda dariya ta kubce mashi ba, ya dinga 6a66aka dariya har fararen hakoransa suka bayyana masu kyan gaske. Shi duk a tunaninshi dagangan Danish ya rubuta masa jagwalgwalo awaya, alhalin shi baisan amfanin wayar ba, Shi bai ma ta6a ganin waya ba sai da suka shigo duniyar mutane, sannan bata ta6a zuwa hannunsa ba, yadai san ana daddanata da yatsun hannu shiyasa ya kar6a ya yi mashi abun da zai iya. "Please meke damunka ne"? Bayan Ya tsagaita da yin dariyar ne yayi mashi maganar, shiru yayi bai tanka mashi ba. Yanke shawarar kiran Chief Owais yayi saboda ya tambaye shi dangane da Danish don kada a samu matsala tun da shi baisan ya rayuwarshi take ba, yana son yaji ko kurma ne. Bugu uku Chief yayi picking call din "Uncle yanzu nake shirin kiranka, Don inji ko lafiya"? "Owais baisan ya zanyi da shi ba, dama ka fada min yana da wuyar sha'ani, wallahi tun ɗazu yaƙi yi min magana sai dai kallona da yake ta yi, na rasa gane kanshi, har waya na bashi don ya rubuta min abunda yake son ci amma a karshe sai ma ya rubuta min jagwalgwalo, Ko dai kurma ne"? muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar. Da buɗar bakin chief sai cewa yayi"ina fata akwai sojoji a kewaye da ku"? ya fadi hakanne gudun kada lalurar Danish ta motsa musamman yanzu da yaji halin da suke a ciki. "Babu, Mu kaɗaine"! "Uncle ka sanya sojoji su yi maku ƙawanya saboda yaron ba shi ɗaya bane, bana so asamu matsala" "In sha Allah ba za'a samu matsala ba, kafin mu zauna nayi mana addu'a, kuma nayi imanin babu abun da zai cutar da ni ko shi bi'iznillahi" da kwarin gwiwa prime minister yayi maganar Yana iya jiyo sautin ajiyar zuciyar owais. "Uncle, ba kurma ba ne, abun da nake so da kai, ka ɗauka tamkar Jiriri ne sabon haihuwa, saboda bai son komai ba, wayar da ka bashi baisan amfanin ta ba, please ka bashi kulawa yadda ya dace sannan ka ƙara haƙuri da shi, A hankali zai fara sakewa" amsa mashi yai toh, kafin yai katse kiran. Danish nata kallon sa bayan ya gama, har zai kira don a kawo masu abinci, ya jiyo motsin tafiyar mutane da sauri yakai idanunshi kansu, Hadimai ne su biyu sanye da uniform na ma'aikatan gidan, kowaccensu hannayenta na a ruƙe da faffaɗan faranti, daga saman su anjera kayan abinci nau'i daban daban, wannan ba aikin kowa bane face Gimbiya mujeedat, itace tayi tunanin zasu buƙaci abinci shiyasa tayi saurin kiran landline na gidan ta isar da sakon a kawo masu abinci. Ya ɗanyi mamakin ganin su da abinci, bayan bashi ya bada umarnin su kawo ma su ba, kwata kwata baisan da zaman gimbiya mujeedat da yazrin ba, har yanzu bai gan su ba, saboda bai son sun biyo su ba. Cikin girmamawa hadiman suka russina har suna hada baki wurin furta"sannu da hutawa yalla6ai" suna magana suna satar kallon danish kamar kwayan idanunsu zasu faɗo ƙasa. "Wanene ya bada iznin a kawo mana abinci"? Da sauri sukace"umarni ne daga wurin gimbiya mujeedat"! nuna masu tsakiyar shimfiɗar yayi, anan suka ajiye masu kayan abincin kafin suka juya zasu bar garden din suna tafiya suna waiwayon Danish har da tuntu6en su tsabar gulma da kitsibibi. ta riga tasan halin hateem bai cika yarda ba, hakan yasa ta tura mashi tezt message. _I ordered them to bring you food because I was worried about you, tun da muka shiga dinner hall baka ci komai ba_ Murmushine dauke akan fuskarshi bayan ya gama karanta sakon nata, yai mata reply da cewa"Nagode Gimbiyata" Tuni ƙamshin soye soyen da aka kawo masu ya buɗe hancinansu, shi kanshi danish din yunwa yake ji, tamkar baici abinci ba. Farantin farko yana dauke da banƙararrun kaji anyi masu jar suya sai maiƙo sukeyi, ga tsiren nama daban kuma, yaji kayan lambu dana kamshi, ga wasu luxury warmers daga gani abinci ne a cikin su, ɗayan tray din Glasses ne da ke dauke da exotic sodas Fresh coconut water, premiun juices and coconut milk, sun haɗo masu da silverware and tissue box duk wani abu dai da zasu buƙata...... 'Bismilla me zamu fara ci ko in za6a mana"? Cikin kulawa yayi maganar yana duban danish dake ta faman haɗiyar yawu. Bai jira amsar shi ba, Ya zuba masu sakwara with egusi soup, taji uban naman ganda manyan yanka ta dahu tu6us. Ya lura bai da alamar ci, Hakan yasashi yanke shawarar bashi abaki,. Wanke hannunsa yayi a bowl kafin ya zura shi a plate din ya debo sakwarar da miya yakai mashi saitin bakin shi, bai yi tsammanin zai ci ba, ganin ya damtse bakinsa can kuma ya ɗan buɗe kananun la66ansa a hankali hateem ya sanya mashi abaki, yadda yake tauna tamkar baisan ci nan da nan ya haɗiye, cigaba da bashi yayi abaki yana ci, kamar wani karamin yaro, shi kuwa hateem dadi yake ji yana bashi abinci yana ci, Ba zato ba tsammani yaga danish ya sanya hannun shi ya ɗebo sakwarar ya miƙa mashi don yaci shi ma, yaga tun dazu yake ta bashi shi baici ba... Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Hateem, bakomai ne ya faɗo masa a ransa ba, face maganar Owais da yace yaci gaba da bashi kulawa a hankai zai saba da shi, tabbas kuwa hakane. Buɗe baki yayi danish ya sanya mashi ya soma ci, yayin da suke kallon juna, tuni yaji hawaye sun cika idanunshi sai dai bai bari sun zubar masa ba, da sauri yayi kokarin danne su... Cigaba da bama juna abinci su kayi, su gimbiya mujeedat dake kallon su ita da yazrin, murmushi ne ɗauke akan fuskokinsu, tsabar Jin dadin yanayi yasa suka samu wuri saman wasu kujerun shan iska suka zauna... Bayan sun gama da plate din sakwarar, Tsiran naman suka fara ci, Idan ya bashi shima sai ya bashi abaki, suna ci suna kallon juna. Saboda tsantsagwaran kauna da zarar abincin ya 6ata ma danish gefen bakinsa da sauri yake cirar tissue ya goge masa bakinsa, daga shi har danish din sun jima basu ji abinci mai yawan gaske ba irin nayau, kusan rabi da kwatar abincin saida suka cinye shi, bayan sun gama suka koma suna shan coconut milk da fresh juice. Sauke farantan hateem yayi can gefe ɗaya ƙasa, kafin ya mayar da hankalinsa akan danish, rungumo shi yayi ajikinshi, hannun shi ɗaya dafe da bayan shi, ɗayan hannun yana ruke da wayar shi, Camera ya shiga don ya yi masu hotuna ko ya samu waɗanda zai dinga gani yana ɗebe kewarsa, da sauri Danish ya runtse idanunsa alamar baya so, kokari yake ya buge wayar gaba ɗaya hakan ba karamin ɗaga hankalin hateem yayi ba, cikin sanyin murya ya furta"pls ka bari nayi mana hoto mana, inaso na samu wanda zan dinga kallo bayan na koma ƙasa ta," cikin sigar lallashi yake yi mashi magana akan ya buɗe idanunsa, dakyar ya samu ya ɗan buɗe su, maimakon ya kalli camera din sai ya dinga kallon fuskar hateem din, babu yadda baiyi dashi ba akan ya kalli camera amma yaƙiya kamar wani karamin yaro, A haka hateem yadinga daukarsu hotuna idanun danish akan fuskarshi, wasu hotunan ya rufe idanunsa, hada video yayi masu mai ɗan tsayi, ya kwantar masa da kanshi saman kafadarsa, da wanda ya sumbaci forehead dinsa, kamar wani ɗan cikinsa, A kalla ya dauki hotunansu sunkai Talatin, bayan video da yayi masu kusan goma. Kafin ya gama ɗauke ɗauken hotunan, kwatsam Yaji danish Ya ƙanƙame shi da hannayensa da farko ya ɗan ji fargaba amma daga bisani da yaga yana lumshe idanunsa sai yaji hankalin ya kwanta, wani baccine mai daɗi yayi awon gaba dashi, kanshi asaman shoulder din hateem, A hankali Ya gyara mashi kwanciyarshi, ya rungumo sa, kamar zai maidashi cikin shi, hannayen danish na abayan hateem ya ƙanƙamesa kamar wani yace zai ƙwace masa shi. Wani kallon so da kauna hateem yake binsa dashi yayin dayake yin baccin, A hankali ya soma shafa bayan shi da yatsun hannayensa kafin ya zura hannun cikin sumar kansa tamkar yanayi mashi susa, harta numfashin danish sai da ya canza saboda daɗin da yaji na abunda Hateem ke yi ma sa. Bakinsa yakai saitin kunnan danish, cikin muryar raɗa yayi mashi magana. "Do you feel what I feel about you?" Ya faɗi hakan batare daya sanya ran danish zai tanka masa ba, a tunaninsa yayi zurfi a baccin nasa. Kamar daga saman yajiyo daddaɗar muryarsa tamkar ana busa sarewa ta ratsa kunnansa da cewa "Yes, I do. I feel more than you might think" wayyo Allah dadi prime minister tamkar zai zauce tsabar murna da jin maganar danish, Cigaba da kallon fuskarsa yayi tamkar zai haɗiye sa. "Nakasa yarda cewa kaine kayi min magana da bakin ka, ko dai kunnuwana ne suke jiyo min ba dai dai ba"? da biyu ya fadi hakan saboda yana son ya ƙara jin muryar shi. "No, ni na maka magana" danish ya bashi amsa idanunsa a rufe, har time din basu raba jikin su daga na juna ba "Meyasa ka damu dani"? Danish ne ya jefa mashi tambayar Murmushi hateem yayi kafin ya furta"tun lokacin da nafara Yin tozali dakai, Naji na kamu da matsananciyar kaunarka, duk da bansan wanene kai ba, amma naji ka kwanta min araina, ka sace min zuciyata, babban abinda yafi jan hankalina gare ka shine kama da muke da juna, Ina jinka tamkar ni na haifeka, Allah ne kadai yasan son da nake maka Danish, wallahi bana son rabuwa dakai, bana son in tafi in barka, don bani da yarda zaniyi da natafi da kai" Kalaman da yake furtawa daga cikin zuciyarsa suke fitowa, abunda ke ransa ne yake bayyana masa ko ya rage radadin da yake ji na kaunarsa . A hankali danish ya ɗan buɗe idanunsa yana satar kallon fuskar hateem dake a dab da tashi, wani irin kallo yake jifar shi da shi mai wuyar fassaruwa batare da prime minister Ya ankara ba. "Bansan su wanene Iyayenka ba, bansan dalilin dayasa sukayi watsi da rayuwarka ba, amma bana tsammanin akwai wanda zai samu ɗa kamarka ya jefar sai dai idan da wani dalilin" Runtse ido danish yayi sam baya son anayi mashi maganar iyayen sa. Muryarshi na dan rawa ya furta"ka daina yi min magana akan iyayena, bana son su bana son duk wani abu daya shafe su, If I could see them, I would kill them." A ruɗe prime minister ya dubi fuskar danish da tsantsar mamakin yadda kalaman suka fito daga bakinsa, har kokwanto yayi anya shi yayi maganar? Ko da yai yunkurin tambayarshi meyasa yace haka, sai jinshi yayi shiru alamar wani baccin ya dauke shi.... Haƙiƙa furuncin da ya yi akan iyayen su sun tada masa hankali, sun tsaya masa a ƙahon zuciyarsa, duk da baisan dalili ba amma yaji fargaba aransa, musamman da ya ambaci Idan ya gansu zai kashe su ....... Lumshe idanunsa yayi, tare da ƙara janyo danish ajikinshi, yaci gaba da ɗan bubbuga bayansa kamar mai lallashin ƙaramin yaro a haka harshima baccin yayi awon gaba dashi, wata irin iskace mai ni'ima taci gaba da kaɗa wurin da suke....... gaba ɗaya abun da ke faruwa akan idanun Yazrin, sai dai basu samu damar jin komai da suke tattaunawa ba atsakanin su saboda akwai tazara. Nannauyar ajiyar zuciya Gimbiya mujeedat ta sauke tare da kallon Yazrin dake a gefenta"gwanin ban sha'awa, sun burgeni, a yadda suka kwanta kamar Uba da ɗansa, ban ta6a jin zafin rashin ɗa bamiji ba sai ayau dana kalli Hateem da yaron nan, wallahi sunyi min kyau sun tafi da imanina ......." Cikin sanyin murya Gimbiya mujeedat tayi maganar. Jikin Yazrin yayi sanyi lakwas tamkar wadda aka zarewa laka, idanunta sun ciko tab da kwalla ta soma magana ba tare data janye idanunta daga kan shimfiɗarsu Hateem ba. "Daddy ya bani tausayi, na tausaya masa mommy, daga shi har matashin nan, Ina kaunarsa Ina jinshi kamar ɗan uwana na jini... " da raunatacciyar murya tayi maganar. "Mommy abun da yafi ta6a zuciyana, yaran ba su da kowa a daji aka tsince su kamar yarda naji akhi owais Ya faɗa, wallahi banji dadin yadda Su oum saratu suke jifarsu da munana kalamai ba, ni abun da ya daure min kai Yaran sunyi kama da family din daddy sosai" Jinjina kai Gimbiya mujeedat tayi ba tare da ta iya furta komai ba, Ta yunƙura ta miƙe Cikin takun nutsuwa Ta nufi shimfidar su hateem, Yazrin na zaune bata bi bayanta ba, bakomai zuciyarta ke tariyo mata ba, face lokacin data haifi baby boy din su da suka rasa, haƙiƙa taji bakin cikin da bata samu damar ganin ko da gawarsa bane, taso ace ko da fuskarsa ne ta gani, tuna wannan yasa taji hawaye sun taru cikin idanuwanta Adai dai bakin shimfiɗar ta ɗan zuƙunna tana kallon danish from head to toe, yayin da zuciyarta ke azalzalarta da kaunarsa, sai kallon shi takeyi babu kyaftawa, ranta ne ya raya mata wani abu da bata da tabbaci akanshi, hakanan taji tana son ta jaraba gwadawa, Miƙewa tayi da sauri ta zagaya ta dayan bangaren da farantan abincin da aka kawo masu suke, ta zaro ƙaramar wuƙa ta yanka fruit, ta dawo bangaren inda danish Yake ta zuƙunna duk akan idon Yazrin da mamaki yagama cikata, zuciya da sake sake arude ta furta me mommy zatayi wuƙa"? hankalin ta yadan tashi tsoron ta kada ta aikata wani abu duk da tasan hasashenta bazai ta6a zama gaskiya ba... A hankali ta ɗaura ziraran yatsun hannunta kan sumar danish ta ruƙo ƙasanta, Cike da fargaban kada su farka, tana yi tana kallon fuskokinsu cikin kwanciyar hakali suke fitar da numfashinsu, bacci yayi dadi Yatsun hannunta na kerma ta yanki sumar kan danish da wuƙar, ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa ta mayar da wukar cikin kayan abincin kafin ta juya tana faman sauke ajiyar zuciya ta nufi Yazrin tunkafin ta ƙarasa yazrin ta miƙe tana tana fadin"mommy! Meyasa kika datsar mashi gashin kai"! Idanunta azare ta fada tana nuna ziraziran gashin danish da gimbiya mujeedat ta cira daga kanshi Fuskarta dauke da murmushi tace "Ki kwantar da hankalin ki, kinsan dai mom dinki ba matsafiya bace," dariya yazrin tayi"ina kyautata maki zato a koda yaushe Rabin raina" lumshe ido gimbiya mujeedat tayi"ki ajiye min gashin nan a wurinki, Idan muka koma gida zan tambaye ki shi" da sauri Yazrin ta kar6i gashin daga hannun mom mujeedat, ta cire cover din wayarta ta ɗaura gashin abayan wayan kafin ta mayar da cover din sosai ta matse shi ta yadda bazai ta6a faɗowa ƙasa ba. "Yanzu ki zo mu koma dinner hall, kada aji shiru babu ni babu hateem bayan saboda mu akayi taron" amsa mata yazrin tayi da toh" a jere suka nufi hanyar fita daga garden din, suna tafiya Yazrin na waiwayon shinfidar su danish, har saida ta 6ace ma ganinta tukunna ta dauke idanunta daga gare shi. *Dinner Hall* Bayan zahra ta kammala yin wayar, Jiki na rawa ta dawo Ciki tana nema unaisah, kamar zata zauce sai ƴan waige waige take yi babu ita babu alamarta, kusan sau uku tana zagaye tsakar hall din wurin neman unaisah amma babu ita, zuciyarta ba ƙaramar karaya tayi ba, Har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taso su sake ganawa da juna, Yarinyar ce ta kwanta mata aranta, musamman yadda ta sakar mata fuska har ta amince mata su kayi hutuna, dabara ce ta faɗo mata, ganin ɗaya daga cikin matasan ƴan matan a tsaye tana kallon masu yin rawa akan dance floor sai murmushi take saki, da sauri Zahra ta nufe ta, muryarta da sanyi ta furta"sannu baiwar Allah" firgigit batool ta dubeta da alama ta razana don bata tsammaci jin muryar wani a kusa da ita ba "Kiyi haƙuri na baki tsoro ko"? da fara'a zahra tayi mata maganar, batool kuwa sai kallon bakuwar fuskar takeyi taƙi tanka mata, gani take kamar zata cutar da ita ne tun da ta fahimci basa son su Miƙa mata hannu zahra tayi"ni suna zahra, ke fa"? Cike da rashin yarda ta furta"batool" muryarta da ɗan rawa tayi maganar, ba tare da ta ɗaura hannunta asaman na zahra ba, nan take zahra ta fahinci tsoron ta take ji hakan yasa tace"ki kwantar da hankali yar uwata, Bana ɗaya daga cikin waɗanda suka ci muku mutunci ɗazu...." still bata saki fuskarta ba "Shikenan, yanzu ki faɗa min ina ƴar uwarku Unaisah? Muna cikin magana da ita ɗazu aka kirani awaya sai naje amsa kiran kafin nadawo na taras bata nan, Ko kinsan inda take"!? Sai da ta ambaci sunan Unaisah batool tafara kyafkyafta idanunta tana bin dakin taron da kallo, sai yanzu ta tuna da tsawon lokacin da bata ga gifcin unaisah ba, kuma bata cikin masu yin rawa, nan fa hankalin Batool Ya fara tashi ta fara ƴan waige waige fuskarta a yamutse babu nutsuwa Ganin yadda ta ɗaga hankalinta ne yasa Zahra cewa"ko kema bakisan inda taje bane" ɗaga mata kai batool tayi muryarta adabarbace ta furta"ban..bansani ba, bamu jima da rabuwa da juna ba, atare muke zaune can mu da su chief kafin tashin ta" ta fada Tana nuna mata wurin.. Ruƙo hannun batool zahra tayi "zo muje mu nemo ta," da sauri batool tabi zahra suka soma bi sako da lungu na hall din suna neman Unaisah, ba tare da sun fada ma kowa ba ... ____________________________💋✍️ Jin ta ruƙo hannunshi yasa shi yin sauri fusgewa Yana bin ta da kallo mai cike da fargaba Jikinshi har kerma yake yi saboda matar bata kwanta mashi aran shi ba, Murmushi ta ɗan sakarmashi cike da fargabansa ta furta"kayi haƙuri dan Allah, bawani abu zanyi maka ba, Inaso mu yi hoto ne" ta fada tana nuna masa i phone din hannunta, maƙe mata kafaɗa naufal yayi muryarshi da yar tsiwa tamkar zai fashe da kuka yace"banso, Ni ki ƙyale ni, kuma wallahi ki daina kallona," Ranshi a6ace yayi maganar, arude hajjaty ta soma lallashin shi gudun kada ya janyo hankalin mutane gare su. "Dan Allah ka yi hakuri, Idan na bata maka rai, alfarma ɗaya nake nema a wurinka, Ka fada min sunanka"? Harara naufal ya wurga mata, Yana faman haɗe rai yace"sunana Sajeed" Tuni yanayin fuskarta ya canza, tayi zaton zataji irin sunan ɗanta, Gyaɗa kai tayi"masha Allah, Allah yayiwa rayuwarka albarka, amma baka ga muna kama da juna ba"? ta faɗa da fara'a akan fuskarta, Ta6e baki naufal yayi alamar ta takura masa hada ɗan bubbuga kafafunsa"Ni bani kama dake, bansanki ba, dan Allah ki ƙyale ni, In shaƙi iska" yanayin yadda yayi maganar yaso bata dariya, "Naji zan ƙyaleka, ka shaƙi iska but pls ka bari na dauki hoto dakai"! Juya mata ƙeya yayi atakure yace"sai dai ki ɗauki bayana" dariya tayi sosai tana kallon bayan shi. "Kaga dan Allah ka juyo na dauki fuskarka, Ita nakeson gani, Harma In nunawa Mijina shima yaga mai kama dani" maƙe mata kafaɗa naufal yayi alamar a'a. Magiya tadinga yi mashi amma yaƙi juyawa, ta rasa ya zatayi da shi. Sajeed da ke ta kallon su, baisan me suke tattaunawa ba, A hankali Ya nufo su, "Bro, meke faru ne"? Ya faɗa yana kalon fuskarshi dake a daure Da yatsan hannu ya nuna mashi hajjaty dake abayn shi"matar nan ce ta ɗazu da take ta kalllona, shine ta biyu ni wai dole sai ta dauke ni hoto ni kuma nace mata bana so" Ɗagowa naufal yayi su ka haɗa ido da Hajjaty, harta bude baki zatayi mashi magana sai kuma ta fasa, saboda ganin suffar Sajeed kamar zaifi naufal din taurin kai, a tunaninta amma ga mamakinta sai ji tayi yace mashi"to meye aciki? Ba hoto kawai ta buƙata ba"? Ɗaga mashi kai naufal yai, Ruƙo hannunshi sajeed yayi" dallah juya kaje ku ɗauki hoton, In ba haka ba bazan ƙara taimaka ba wurin koya maka karatu" ba don yaso ba, ya juya yana jifar hajjaty da harara kwayar idanunsa kamar zasu faɗo ƙasa, "Nagode sosai, Kai meye sunanka"? fuskarta dauke da murmushi ta tambayi Sajeed, Kafin yai yunkurin bata amsa naufal yai sautin cewa Sunan shi Naufal, Wani kallo Sajeed Yayi mashi da ruɗani akan fuskarsa jin Ya canza mshi suna, da ido yai mashi alamar da nan take ya gane me yake nufi wato Ya faɗa mata sunan sa amatsayin nashi, shine yace shi sunansa Naufal Jim ta ɗanyi har cikin zuciyarta sunan ya dake ta, Taso ace mai kama da itan ne yake da suna Naufal sai dai kash shi sunan shi Sajeed. "Kawo wayar nayi maku hoton" da sauri ta miƙa ma sajeed wayar ya kar6a, ya soma daukarsu hoto, Hada kokarin Jan naufal Ya matsar dashi jikin hajjaty gaba ɗaya ya takura mashi, duka hotunan sunyi bala'en kyau kamar ɗan ta, sai dai fa babu fara'a akan fuskar naufal har ya kammala daukar su, hajjaty ta kar6i wayar tana yi masu godiya. Suma su jamimah anyi masu hotuna tare da Sir mubarak da Mom turai, harta su Zaki sai da su kayi hotuna da su, kamar ƴan uwan juna. Haka zalika Su Haris da Javed suma hada su akayi hotunan, kowa ya yi kyau ana ta kwasar shagali. Hajiya saratu dake ta faman satar kallon parveen duk in da tayi akan idonta, ta sanya mata ido sosai, tsabar ji da kai ne ya hana ta nemi alfarmar ta su dauki hoto atare, sai ta koma tana daukarta a fakaice da wayar hannun ta ba tare da ta ankara ba. Hankalin Batool ba karamin tashi yayi ba, Ko'ina sun duba ita da zahra babu Unaisah, Jikin ta har Ya fara kerma tsabar tashin Hankali, sune har wajen hall din neman Unaisah, Dawowa ciki su kayi cike da fargaba, can zahra ta tuna da akwai restrooms a dakin taron, ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon batul tace su ɗan jirata, watakil ta shiga toilet ne, zama sukayi a table daya ita da batool suna jiran unaisah ta fito.. .. *Chief Owai* A tsaye yake a wani area dake a hall din, Ya juya bayansa, hannunsa ɗaya ruke da phone dinsa yayin da dayan hannun ya zuba sa a trouser pocket dinsa, bai jima da kammala yin wayar da ta yi silar tada sa daga wurin zaman sa ba. Layin boss Ya danna ma kira bugu ɗaya yayi picking. Muryarsa ƙasa ƙasa tamkar ta me yin raɗa ya furta" ina fata ka same su lafiya"? On the other hand muryar boss ta karade kunnansa"tun dazu na shigo gidan, suna nan cikin koshin lafiya yalla6ai, yanzu haka ina atare da salsabeel sai fada yake min wai jiya hankalinsa ba akwance yake ba, sun ji shiru Dr jazz bai leƙo su ba, sannan mu ma bamu kira ba kamar yadda muka sama" Daga can cikin wayar yajiyo muryar salsabeel yana fadin"ka fada masa jiya ko isasshen bacci ban samu ba, deeja ta hanamu sukuni daga ni har ƴan uwanta daƙyar na samu yarinyar nan tayi bacci". Lumshe ido yayi ahankali Ya furta" Please tell him I'm sorry. It won't happen again. We were busy with dinner preparations yesterday. in sha Allah, cikin kwanan nan zasu baro anguwar nan su dawo cikin ƴan uwan su" Taj yace"amma naji dadi Yalla6ai, saboda bani da burin daya wuce inga an haɗa kan yaran nan, su gana da ƴan uwansu, hankalin su sai yafi kwanciya" Sun ɗan jima suna yin wayar, kafin daga bisani su ka yi sallama, tunkafin ya sauke wayar daga kunnansa daddaɗan ƙamshin turarenta ya daki hancinsa har sai da lumshe idanunsa saboda yadda fragrance din Ya ratsa shi, tuni ranshi ya bashi cewar itace saboda haddar turarenta da yayi Shiru yayi batare daya juya sun fuskanci juna ba, sai ma ya ci gaba da danna wayarsa. Sautin tarin ta da yaji ne yasa shi saurin juyawa yakai idanunsa saitin inda take, hannunta ɗaya dafe da gefen cikin ta, ɗayan hannun kuma yana ruƙe da Mayafinta da ya zame, lallausar sumar kanta ta lullu6e bayanta baƙa wulik da ita, babu alamun tasan da zaman shi a wurin, yanayin ta kamar bata a hayyacin ta, ganin tana kokarin faɗuwa kan fillow yasa shi yin saurin nufarta, ya sanya hannu ya janyota gaba ɗaya ta fada kan broad chest dinsa, luf ta kwanta masa, ta daddafe waist dinsa da hannunta, yana iya juyo fitar numfashin ta da sauri da sauri, hankalinsa ba karamin tashi yayi ba. "Nazli! Are you okay? What's wrong? Are you alright?" a ɗan ruɗe ya yi maganar. Ƙara ƙanƙameshi tayi muryarta da wani irin sanyi da zaƙi ta furta"bana jin daɗi, kaina da ciki na ciwo su ke min, sannan bana son hayaniya, kwata kwata bana son zama awurin nan" yanayin yadda take yin maganar ba karamin narkar masa da zuciya yayi ba, ƙamshin turarenta ya kanainayesa. "Bana son zama anan, rikicewa nakeyi" cikin wani irin salo take maganar, Nazli karshe ce, babu namijin da zai haɗa jiki da ita batare dayaji sauyi atare da shi ba, koda kuwa zuciyarsa dutse ce. bakomai yasa shi yadda da kalamanta ba, face sanin lalurarta na rashin son hayaniya, tun da kuruciyarta, daga bayane ta samu sauƙi bayada likitoci suka tsaya tsayin daka don ganin ta dawo normal, tunaninsa abunne ya dawo mata yan zu shiyasa ya aminta da ita...... Yanke shawarar fita yayi da ita daga hall din kota samu lafiyar jikin ta, "It's okay, Let's go. I'll take you home and you can rest." maƙe mashi kafaɗa tayi tana fadin"I can't walk. My legs hurt." Kallon takalman kafarta yayi wasu matsiyatan high hills ne masu tsini na fitar shariya, irin takalman da tafi sha'awar sanyawa kenan, mafi yawan lokutta suna jaza mata ciwon ƙafa, sai da ya fara duddubawa ya tabbatar babu mai kallon su, kafin ya sanya hannu ya ɗauketa gaba ɗayanta Ya nufi second door da ake fita hall din bai bi ta ainihin kofar fita ba, don bayason wani yagansu. Bayan sun fita, yayiwa ɗaya daga cikin sojojin dake tsaron ƙofar magana akan ya kawo mashi motarsa, bayan ya miƙa masa key, jim kadai sai gashi ya kawo motar, ya fito tare da buɗe masu, a backseat ya shigar da Nazli, sai faman lumshe idanunta takeyi masu kama dana ɗawisu saboda kyau Cikin kulawa yace"Calm down, He will take you home." ya fada yana nuna mata sojan daya kawo masa motar, girgiza mashi kai tayi da wata irin kasalalliyar murya tace"I want you to take me. Don't you have time for me?" She bit her soft, pinkish lips. "Tomorrow, I will leave the country. I am not sure if we will meet again," her words touching his heart deeply sai yaji kamar bai kyauta mata ba, a matsayin ta na yar uwarsa rabin ransa kuma jinin jikinsa. Bai gama yanke shawara da zuciyarsa ba, Yaji ta ruƙo hannunsa baisan sa'adda Ya shige cikin motar ba, sojan da zaiyi driving dinsu Yai wa motar key, driving slowly suka miki hanyar zuwa gidan prime minister. A lokacin da baiyi tsammani ba, yaji ta ɗaura kanta saman broad shouder dinsa, ta ruƙo yatsun hannayenta a cikin nashi, wani irin sanyi sanyi ne ya ratsa zukatan su, Tsawon Lokaci basa kula juna till to day. Ranta ne ya bata cewar yana kallon ta, A hankali ta dago da sexy eyes dinta akan fuskarsa karaf suka shiga cikin nashi, cigaba da kallon juna su kayi babu alamun gajiya. _Unexpectedly, she planted a kiss on his chin. He closed his eyes for a moment, put one hand on her hair, and slowly put his smooth lips on her forehead, gently pecking it._ _Gaba ɗaya sun shiga yanayi, sai dai fa duk da haka babu fara'a akan fuskokin su kamar basa son kasancewa da juna, bayan motar ta isa gidan, bata bari chief ya kubce mata ba, don ta fahimci hankalinsa na akan dinner hall kuma tasan bai wuci saboda yarinyar nan ba, jan shi tayi da ƙaryar ciwo da kisisina har ta samu yabita Part din ta don taji dadin ruƙe sa kamar yadda faryat ta tsara mata.........👀_ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 15 Complete by Novels Elite Admin June 02, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ _Gaba ɗaya sun shiga yanayi, sai dai fa duk da haka babu fara'a akan fuskokin su kamar basa son kasancewa da juna, bayan motar ta isa gidan, bata bari chief ya kubce mata ba, don ta fahimci hankalinsa na akan dinner hall kuma tasan bai wuci saboda yarinyar nan ba, jan shi tayi da ƙaryar ciwo da kisisina har ta samu yabita Part din ta don taji dadin ruƙe sa kamar yadda faryat ta tsara mata.........👀_ (Back to Dinner Hall) Bayan tafiyar Nazli da Yan Mintuna, sai ga kiran ta ya shigo layin faryat, A lokacin harta koma wurin su Zulaihat bayan ta gama shirya makircin, A hanzarce tabar wajensu ta samu wurin da bakowa tayi picking ta kara wayar a kunnanta. Muryar Nazli tamkar tame jin bacci tace"faryat, nakira ne nayi maki godiya, yanzu haka muna a gida tare da chief" "Naji dadin jin hakan sisters, babu godiya tsakanina dake nayi ne saboda farin cikin ki" "Ina yarinyar nan take"? Rass taji gabanta Ya faɗi jin abun da Nazli tace, ita sam ta manta da zancen ƴar mutane da tasa aka kulle a restroom. "Naji kin yi shiru baki ce komai ba"? "Sister kulle ta nayi a restroom yanzu zanje na buɗe ta" "Okay, I don't want any problems tun da buƙata ta biya, kawai ki ƙyale ta tafi, i know her relatives will start looking for her as soon as they notice she is not there." "Okey, bari naje na buɗe ta" sallama su ka yi da juna, tsaye tayi tana bin Hall din da kallo, can Ta hango matar da suka hada baki da ita, Cikin sauri ta nufe ta. "Ke! Ina son Magana dake ki biyo ni yanzu" da sauri matar tabi bayanta suka ke6e a wani wuri. "Yarinyar dana sa kika kulle a restroom, ita nakeso kije ki buɗe ta yanzu" Hannu matar tasa tana laluban aljihun uniform din jikinta, can ta rabka salati tana fadin"Inna lillahi! Nashiga Uku..." idanu azare faryat tace"what"? Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Sister, I think I lost the key, ba tare da sani na ba" Waro idanu faryat tayi cike da masifa tace"amma Baki da hankali! So kike kija min bala'e, kin manta yadda mu ka yi dake ne? Sai da nace maki da zarar kinga kirana kije ki bude mata kofa, shi ne zaki ce wai key ya bata"? ta fada tana zare mata idanu taci gaba da cewa "to wallahi baki isa ba! Kisan yadda za'ay ki nemo shi da gaggawa ki buɗe ta" ta fada tana faman cije le6en ta, da yatsan hannu ta nuna ta"Don't you dare mention my name if anyone finds out what we've done, Idan ba haka ba hmmm kinsan sauran" rai a6ace ta faɗa tare da juyawa har ta fara tafiya ta dan dakata tunawa da CCTV dake a hall din, Hankali A tashe ta ta kuma juyowa ta kalli matar dake a tsaye ido ya raina fata, jikin ta sai kerma yake daga gani tana acikin matsanancin tashin hankali. Sassauta murya tayi "Kiyi kokari ki gano key din, ki je ki bude yar mutane, kinga akwai CCTV duk wani abu dake faru suna gani, kuma wallahi muddin baki bude ta ba har suka gano kece kika kulle ta, Na lahira sai yafi ki jin dadi" ta karasa tana sakin shu'umin murmushi ta kuma cewa"ni nasan yadda zan fidda kai na, ke ce a ruwa, dama kwadayin abun duniyane yasa kika amince min muka shirya komai, na riga dana biya ki kudinki, shawara ta rage wa mai shiga rijiya, ni kinga tafiya ta" cike da shakiyanci faryat ta juya ta nufi hanyar fita daga hall din don zaifi mata kwanciyar hankali akan ta tsaya ganin rikicin da za'ay na rashin ganin Yar Mutane Kafin ta fuce ta kira layin Jazz tace mashi ya same ta a bedroom dinta tana son ganin shi, tayi hakanne saboda ta samu damar ke6ewa dashi kafin gobe Subar Nigeria. Hankalin matar ba karamin tashi yayi ba, wata irin zuface ta soma wanko mata, har ta fara danasanin kudin da ta kar6a a hannun faryat, gaba daya tabi ta firgice sai faman lalube lalube take yi tana neman key din, Sako da lungu bata gan shi ba, ga shi lokacin ana gab da za'a rufe taron dinner din tasan dole a nemi yarinyar, a karshe da taga ba ta da wata manufa, sai ta yanke shawarar guduwa daga hall din..... ___________________________________✍️ "Ai ga irinta nan, Ni dama nasan za'a rina, yadda yake rawar kai akan yaron nan kamar ɗan cikinsa, hakan na nufin yafi kowa mahimmanci awurinsa shiyasa yaja su suka tafi wata uwa duniyar, Allah kadai yasan ina suka je..." senate lateef ne ya fada Yana huci yayin da suke atsaitsaye curko curko "Ni abunda nake ma fargaba, kada yaron nan ya cutar dashi, don ni wallah hankalina bai kwanta da shi ba, saboda ina zargin ba cikakken mutun bane" His excellency Deen yayi maganar Abdul Razak Yace"Laifin Owais ne, Ya cika daukar kasada, akan me zai hada shi da yaro, hada karfin halin cewa ya tafi da shi salon Yajaza mana bala'e" Kwa6e fuska Senate lateef yayi"ay tin farko ubansane ya daure masa wurin zama da duk hakan bata faru ba, Ina kallonsa dazu Ya hakikance akan cewa owais ba zai kawo abunda zai cutar da ahlinsa ba, Idan ma muna jin fargaban wani abu zai faro owais ne ke da alhakinsa, don haka bai kamata muna tada jijiyoyin wuyanmu akan sa ba, Mu zuba ido mu gani" "Wannan duk ba abun tada hankali bane, In sha Allah zai dawo cikin koshin lafiya, yakamata muna kyautata masu zato, ku kanku fa dazu ku ka gama tsegumin kamannin Yaron da hateem har kuna fadin baku ga laifinsa ba daya kusa zaucewa akan kaunarsa, shine kuma yanzu kuke korafi don kun ji shi shiru" ya fada yana ɗan jifar su da hararar zolaya. Dakuwa Senate lafeet yai masa"ungo nan, dani kake wannan maganar, ni banma ga wani kamanninsu ba, na dai fadi ne kawai" dariya suka sanya gaba dayansu. Sir mubarak yace"kaifa ɗan iskan mai raine, Lokaci ɗaya sai ka burkicewa mutane ka hakikance kan abu daga baya kuma ka dawo ka canza magana, daɗina da ɗan siyasa kenan, Haka halin ku yake, Shiyasa dazu na zuba maku ido kunata jaraba saboda an shigo da yara hall alhalin nan kuwa duk kun ƙyasa da ganinsu, musamman shi yaron da kuke magana akai" Harara suka watsa masa atare, Senate yace"ba ka girmamani mubarak" "Da dai ba lokaci ɗaya muka zo duniya ba," acewar Sir Mubarak. "Bari na fada maku gaskiya, wallahi da ace Hateem ya ta6a haihuwar Namiji tsab zan iya dafe alkur'ani ince dansa ne yaron nan sai dai kaffara ta hauni" his excellency abdul razak ne yai maganar. Deen yace"yadda kasan irin an tsaga kara, Har hancinsu da idanunsu, kai komai fa, ni fa da za'a bi ta shawarata zance ne muje asibiti ayi masu gwajin DNA" wani kallon harara Senate lateef yayi masa da zolaya yace"lallai siyasa tafara haukata ka, in ba haka ba kawai daga ganin yaro tsintacce daga daji sai ka ƙababa ma Hateem!" watsa hannu yayi"ni abunda ke raina na faɗa" Shiru suka danyi na wani lokaci kafin senate yayi yar dariya yana fadin Yau wani zaici ubansa a hannun shalelen baba obie" gaba ɗaya suka sanya dariya cikin raha don sun gane me Yake nufi Sir mubarak Yace"na tauyasa mashi, don wallahi nasan bazata ƙyale shi ba, sai ya yabawa aya zakinsa Hmm Allah dai ya kyauta. Senat yace"yayi banban kuskure na ruke hannun wata mace agabanta, Ni abun da bangane ba, meyasa yayi hakan ne? Ni fa nafara zargin mutumin nan, wallahi babu gaskiya acikin lamarinsa in ba haka ba akan me zai ja hannun baligar mace bazawara a bainar jama'a da sunan zai fitar da ita ta tsiya daga hall har yana ikirarin kada ta kuskura tabari ya riga ta fita......" His excellency Deen Yace"idan ma akwai wani 6oyayyan sirri atsakaninsa da ita, a sannu zamu gano koma menene ay mu ba'a shiga family dinmu da fuska biyu a zauna lafiya.... Fira suka cigaba da yi atsakaninsu, Abu kamar wasa har Bayan Magrib ana gab da za'a rufe taron babu prime minister babu Unaisah, Ga mutane sunataso suyi mashi bankwana saboda ba lallai gobe su haɗu da shi, asubar fari zasu bar nigeria, babu wanda bai jaraba kiran layin hateem acikin su ba, sai dai wayar tayi tayin ringing, ba'a picking, Shima owais sun kira layinsa wayar bata shiga, ransu yayi mugun 6aci, sauƙin su ɗaya zuwan gimbiya mujeedat itace ta sanar da su inda Hateem yake, ba tare da 6ata lokaci ba, suka yanke shawarar zuwa can su same shi, kusan gaba daya mutanan hall din suka nufi gidan prime minister don suyi mashi bankwana tun da shi yaki dawowa dakin taron, yana can tare da sanyin idaniyarsa., Idan muka koma bangaren zahra da batool lamarin Ya fara Tsoratar da su ganin Har mutane sun fara watse wa babu alamun Unaisah zata fito daga toilet, kwatsam wayar zahra tafara ringing, da sauri ta ɗaga ganin sunan hajiya saratu. "Meet me outside the hall right now, Zarah!" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh, bayan ta katse kiran, Ta kalli batool jikinta yayi sanyi lakwas sam bata so ta tafi tabar Hall din ba tare da an gano unaisah ba. "Ki yi hakuri sister batool, tafiya zanyi ba don naso ba, matar da ta gayyace ni dinner din nan itace take kirana, shawarar da zan baki, Ki sanar da sauran yan uwanki da kuma jami'an dake tsaron hall din su taimaka maki ku gano yar uwarku" ta fada tare da ruko hannayen batool a cikin nata kafin taci gaba da cewa"kada ki manta idan kun gano unaisah ki sanar da ita cewa na tafi da kewarta" batool ta amsa mata da toh, kamar kar su rabu da juna su ka yi sallama. Bayan tafiyar zahra, batool tabi yan uwan su daya bayan daya ta sanar da su zancen bacewar Unaisah, nan fa hankalin su yai mugun tashi, su sajeed suka bazama nemanta, tsantsar tashin hankaline da damuwa akan fuskokinsu, babban abunda suke ma zullumi kada ace wani mugun abunne ya faru da ita, dama sun lura bakowa ke son su ba, tsaf za'a iya cutar masu da yar uwarsu, bacci tuni yayi awon gaba da jamimah, Sai dai haris ya goyata abayan shi, itama Azeeza daukarta Naufal yayi abayanshi sbd lalurarta, Parveen da su Hanna idanu sunyi jawur ga bacci suna ji ga kuma tashin hankalin rashin yar uwarsu, babu wanda Ya lura da halin da su ke a ciki saboda babu mutane sai jefi jefi wasu suna bakin hall wasu kuma sun tafi gidan Hateem kusan su kadai ne suka rage a hall din sai servers din dake tattara kayan abincin da aka yi amfani da su, da kuma interior designers din da suka fara kwashe kayan decoration din dakin taron. A lokacin da ba su yi tsammani ba, Sai ga Boss tare da biy guy sun shigo hall din cikin takun sauri, sun zo ne domin tafiya da su ganin lokacin yayi, su parveen na ganin su suka fashe da kuka da gudunsu suka nufe su tare da fadawa jikin boss da big guy suna kuka suka fada masu basu ga unaisah ba, ta 6ace sun nemeta sun rasa. Da tsantsar tashin hankali Taj Ya furta"wai wata unaisah ne ta 6ace? Ko kuna nufin Angel dina"? Adabarbarce Yai maganar Yana dubansu, Sajeed Yace"ita muke nufi, tun dazu muke nemanta bamu ganta ba, mun duba ko'ina" Kallon juna boss da big guy su ka yi a lokaci daya, wani irin bugun fargabane Ya darsu a zuciyar taj, Jin Angel dinsa ta bata babu ita, Muryarshi na rawa yace"bata fada maku inda taje bane"? Hada baki sukayi wurin cewa Eh Dafa kafadarsa Big guy yai ganin Yana neman rikicewa. "In sha Allah babu abunda zai same ta, zamu nemo ta, sauƙin ma akwai cctv a dakin taron zamu ga inda ta shiga ne" Mayar da dubansa yayi kansu batool"sajeed, Ka tafi da su bakin hall din, akwai Jami'an mu dake jiran ku zasu tafi da ku gida" Muryar batool da shesshekar Kuka tace"ni dai bazan iya tafiya, in ba tare da unaisah ba, zan jira har agano ta ...." kafin ta rufe baki Sajeed Yace"nima bazan tafi ba, kamar yadda muka zo tare da yar uwarmu atare da ita zamu koma" ! "kwara kubarmu anan wlh ko mun koma gida, hankalin mu bazai kwanta ba, ko runtsawa bazamu iya yi ba, in har unaisah dinmu bata dawo ba...." Haris ne ya fada idanunsu sun ciko tab da kwalla, gaba ɗaya sun turje akan ba zasu tafi ba.... Cikin rauni na murya taj Yace"Ya isa haka! Ku daina zubar da hawayen ku, ku samu wuri ku zauna Yanzu zamu nemo ta," da sauri suka samu kujeru duk suka zauna suna jiran tsammani Ba su fara zuwa dakin cctv din ba, big guy ne ya bada shawarar su fara bincika restrooms din dake a hall din kafin su fara zuwa can, da sauri suka nufi hanyar da suke, daya bayan daya suka dinga dudduba cikin su ba su ga kowa ba, cikin rashin sani suka tsallake kofar wanda take a ciki ba tare da sun ankare ba, tsabar kidima yasa taj sulalewa jikin bango Ya zukunna, idanunsa sun kada jawur dasu, fuskarshi duk ta yamutse idan harfa ba ganin unaisa sukayi ba to kuwa bazai ta6a dawowa dai dai ba "Ni nafi tunanin ko dai tabi family din chief xuwa can gidan prime minister" big guy ne Ya fada Yana duban fuskar taj, wanda tuni ya hada gumi duk da sanyin A.c din dake a wurin babban tashin hankalin shi kada Ya rasa yarsa tilo da yake da ita, tabbas zuciyarsa zata iya bugawa. Ganin bai da alamun motsawa ne Yasa Big guy dafa kafadarsa Cikin kwantar da murya yace"dan Allah ka yi hakuri ka daure ka ta shi, mu shiga cctv room din zaifi sauki muga ina ta shiga" Zuciyarshi a hautsine Ya cire facemask dinsa tare da jefar da shi gefe daya. Cikin sanyin murya ta wanda Ya karaya yace"Wallahi tun ina agidan su salsabeel nake jin faduwar gaba, shiyasa nakasa samun nutsuwa na kamo hanya nazo hall din nan ashe abun da zan taras kenan" ya fada tare da kallon big guy"ka tafi ka duba, don bana jin zan iya matsawa daga wurin nan, jiri nake gani a idanuwana" Dan murmushin gefen fuska Big guy yayi mashi dazolaya yace"duk son nan da kake yi mata ahaka zaka damka ma wani kato ita yaci gaba da kula da ita" Kallon harara Boss Ya jefa mashi"kaga pls kada ka daura min wani hawan jinin, ka tafi kawai, Ina jiranka" Yar dariya yayi kafin ya juya ya bar wurin Dafe kansa yai da tafin hannunsa, wani irin ciwon kaine Ya farmasa, Yana cikin wannan Halin, kamar ance ya dago ya kalli Floor din wurin nan take eye balls dinsa suka sauka akan Stone din rigar unaisah, da alama daga jikin rigarta Ya fadi kasa, mika hannu yayi tare da daukar shi Ya kura ido Yana kokarin tariyo a ina ya ta6a ganinsa, sai da ya zurfafa tunaninsa kafin lokaci daya ya zabura ya mike yana bin kofofin toilet din dakallo saboda ya tuna itace ta sanya abaya me adon gold stones. Kofar da suka tsallake basu duba ta ba, ita Ya nemo, ganin ta adatse ya kara tabbatar mashi da tana a ciki. Muryarshi har rawa takeyi wurin ambaton sunanta"Unaisah!Unaisah!My Angel" shiru ba'a amsa mashi ba, nan fa hankalin shi ya kara tashi, Ga shi Ya duba babu key jikin kofar, Karfi yasa wurin bangaje ta da kafadunshi sai dai ko gizau kofar batayi ba, Ja baya yayi kafin Ya nufeta da iya karfin shi na karshe yayi mata wani irin bahagon bugu, nan take kofar ta saki, shi kanshi bai yi tsammanin Yana da karfin da zai Iya bude ta, batare da key ba Allah ne ya taimake sa. Karasa ture kofar Yayi, a fujajen ya fada cikin toilet din yana faman zubda gumi, shigar shi ke da wuya idanunsa suka sauka kan Unaisah dake kwance saman floor, baiwar Allah ita kaɗai tasan radadin azabar da ta fuskanta, taci bakar wahala ta jigata sosai, zufa ta gama wanke jikinta, Takalmanta ware da ware sun yi gefe guda, Ga mayafinta a kasa, hannunta daya dafe a saitin cikin ta, da wani irin rauni da murya ya furta"My Angel" A sukwane da sanyin gwiwa Ya zube gabanta saman gwiwowinsa, duk irin dauriyarsa baisan sa'adda hawaye masu dumi suka soma sintiri kan kuncinsa ba, yatsun hannayensa na kerma ya daura su kan kafadunta tare da janyota ya dawo da ita kan kirjinsa, ya rungume abunsa tare da runtse idanunsa yaci gaba da shesshekar kuka Yana ambaton sunan ta.... "Am.. sorry my Angel laifina ne da ban zauna a dakin taron ba, da duk hakan bai faru ba....." Baisan meke damunta ba da yai silar shigarta wannan Mawuyacin halin, baisan Ya akai aka kulle ta a restroom ba. Yana acikin wannan Yanayin big guy ya shigo da saurin shi, Yana ganin taj rungume da unaisah Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Daga bakin kofar ya tsaya don baisan me zai taras ba. Cikin sanyin murya yace"idonta biyu"? Muryar taj kasa kasa Yace"bansani ba, kamar ta sumane anan, amma daga gani taci bakar wahala" Big guy yace"mun gano wacece Ta kulle ta a restroom din, Kuma in sha Allah zamu bincikota sai ta dandani kudarta wallahi" Yana fuci Ya faɗa Babu alamun taj Ya fahimci me yake cewa hankaklinsa na akan Angel dinsa yace da shi"please Ka koma wajen yan uwanta kada su ji mu shiru, yanzu zan fito da ita" amsa mashi yayi da okey, a hanzarce Ya fice. Har ya yunƙura zai mike Yaji alamun lemar wani abu a hannun shi, da sauri Ya dago da tafin hannunsa Yana kallon jinin daya ta6o, sai lokacin Ya fara jin karninsa a hancinsa, Idanunsa azazzare yake kallon jinin Hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta dinga harbawa da karfi da karfi tamkar zata fasa kirjinshi,duk a zaton shi wani mugun abun akayi mata, zuciya da sake sake sai ta dinga ayyana mashi kodai raping dinta wani yayi ko kuma Wuka aka caka mata. Zuciyarshi na tashi, Yai hanzarin Sanya hannu Ya dage rigar jikinta, santala santalan cinyoyinta tsakankaninsu duk jinin ne daya gangaro mata. Sai da ya bincika ta sosai, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ganin ba abunda Yake zargi bane, A hanzarce ya fara wanke mata inda jinin Ya 6ata, kafin Ya lullu6a mata mayafinta ya daure mata qugunta da shi, asaman kafadarsa ya rungumo unaisah, yayin da ɗayan hannunsa ke a ruke da rigarta, tuni tajima da farkawa tun lokacin daya fara wanke mata jinin da ruwa sai dai bata iya komai, Jikinta ya sake ga wata irin kasala data mamayeta. Fitowa yayi da ita sabe a kafadarsa, tunkafin Ya karasa inda su Batool suke, da gudun gaske suka nufoshi, lokaci daya su ka ja burki idanunsa azazzare da tashin hankali suke kallon Taj Muryoyin su na kerma suke tambayar shi meya faru da unaisah? Bata da lafiya ne? Ko bacci take Yi ne"? Kokarin danne damuwarsa yayi kafin yace masu"Babu abunda ya sameta, lafiyarta kalou, Ku zo mu tafi gida" Da sauri Ya wuce gaba suka bi bayan shi, masu aikin dake zarya suna kwashe kayan da akayi amfani da su na hall din sai satar kallon taj suke Yi ganin shi dauke da yarinya kamar ba rai. Fitowa yayi daga Hall din su Batool suna abiye da shi, Jami'an dake tsaron dakin taron suna ganin shi suka fara tambayarshi meye faru da ita? Baibi takansu Ba, Ya nufi mota, da sauri jami'insu Ya bude mashi Ya shiga back seat tare da Unaisah, suma su batool suka shiga cikin sauran motocin da aka kawo su, kusan atare su ka bar garden din, da matsakaicin gudu suka nufi hanyar komawa gida Mutsu mutsun bude idanunta ta somayi wadanda suka kada jawur da su, da kyar ta dan ware su kadan ta kalli fuskar taj dake a rungume da ita, hannayensa duka biyu akan bayanta kamar wani yace zai ƙwace mashi ita. Idanunta na faman lumshewa dakyar dakyar take kallon fuskarshi ba tare da sanin shi ba, acikin zuciyarta ta dinga ambaton sunan shi daddyna daddyna dama kaine kake boye min fuskarka..." siraran hawayene suka wanke fuskarta, ganin yana kokarin juyowa yasa tai saurin lumshe idanunta, saukar hannun shi taji asaman kanta, A hankali Yake dan shafa mata shi, wata irin ni'ima taji ta saukar mata, jikin ta yayi sanyi ba kamar dazu da zazzabi Ya lullu6eta ba, bakomai take tunawa ba face lokacin da ya jefata cikin ruwa... Taj sam baisan cewa babu face mask a fuskarshi ba, gashi har unaisah taga fuskarshi, don ma babu kwarin jiki ai da ta tuhumesa nakin bayyanar mata da kanshi da baiyi ba, dama tuntuni ranta yana bata cewar daddynta ne duk da bata ta6a ganinsa ba, amma kulawar dayake bata fiye da ta sauran yan uwanta da yadda yake janta a jikin shi da kuma muryarshi su suka kara sanya ta hasashen ko shine. Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, tuni Kowa ya koma masaukinsa bayan da suka hallara a gidan prime minister inda suka karasa shagalin nasu acan, a 6angaren chief owais tun bayan da suka shiga Part din Nazli, ba tare da sanin shi ba, ta kashe mashi wayar shi don kada a kira shi, bayan haka ta hada baki da daya daga cikin hadiman gidan ta sanya mashi maganin bacci a coffee, duk don kada ya tafi yabarta, Sai wuraren karfe sha daya na dare tukunna chief Ya farka, a lokacin nazli har tafara bacci, bai bi ta kanta ba, da sauri ya fito daga part din ta ya sauko down, Kafin Ya kunna wayar shi, Layin prime minister Ya fara dannama kira don Yaji idan Yasa an mayar da danish gidansa. Bayan yai picking Hateem Ya fada masa suna atare da shi a bedroom dinsa, bai tsaya bata lokaci ba Ya nufi part din prime minister, dakyar ya raba shi da danish, kamar karsu rabu, na rana daya kawai sun shaku da juna har kyautar zobe ya ba shi mai tsadar gaske saboda ya dinga tunawa dashi, kuma yayi mashi alkawarin kullum xai dinga kiransa suna gaisawa, bayan chief Ya tafi da shi har kwalla saida Ya zubda daboda kewar rabuwa da danish....... Asubar Fari, Motoci suka dinga tururuwa wurin fita daga Estate din,da wata irin jiniya mai kuwar gaske tamkar zasu tashi sama, kaitsaye suka nufi shantalelen titin da zai sada su da Airport, gaba daya family din obinna ne dashi kanshi obinnan suka yi masu prime minister rakiya, Kamar karsu rabu da juna, musamman mahaifinsa da yan uwansa, duk irin juriyarsu saida suka share kwallar rabuwa da shi, Hajiya saratu tasha kuka kamar karamar Yarinya, shi kanshi hateem din saida Ya zubda kwallar rabuwa da yan uwanshi, Ji yake kamar idan ya tafi ba lallai Ya kara dawowa ba, hakika kowa yayi jimamin tafiyar prime minister da Iyalansa, ko bayan da suka baro Airport din suna akan hanyar komawa estate nasu lokacin da suka jiyo karar jirgin su Haka suka dinga leken jirgin ta windows din motocinsu, har Sai da ya bace ma ganinsu tukunna suka hakura kowa Ya sanyawa zuciyarsa salama, kusan duk aranar Su his excellency deeen suka bar abuja, harta su Justice kowa Ya koma inda Yake da zama wasu Nan cikin Nigeria wasu kasar suka bari, Zaki ne kadai bai tafi ba, yanzu estate din Ya rairaye ma zauna cikinsa ne kadai suka rage. *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 16 Complete by Novels Elite Admin June 06, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ A hankali ta buɗe idanunta wadanda suka kumbura suntum da su sakamakon kukan da tasha jiya, ƙurawa ceilling din dakin idanu tayi na ɗan wani lokaci zuciyarta cike fal da tunanin meya faru da ita a jiya? tamkar tayi loosing memory ɗinta, da sauri ta sanya hannu ta shafa kayan jikinta, lokaci ɗaya ta yunkura ta miƙe zaune tana faman sauke ajiyar zuciya, ko'ina na bedroom dinsu ta soma bi da kallo kafin ta sauke idanunta akan batool da ke kwance gefenta tana bacci, tayi mamakin ganin kayan bacci a jikinta, ƴar gown ce da bata wuce gwiwarta ba, launin purple colour, ta rude sai faman shasshafa jikinta take yi burin ta ta tunano ya akai aka canza mata kayan jikinta! kamar ma hada wanka akayi mata, hannu tasa ta ɗan bugi kanta a kokarinta nata farkar da kwakwalwarta ko taci gaba da yin aiki yadda ya dace. Buɗe ƙofar ɗakinsu akayi da sauri taja bargo ta lullu6e kanta, tunkafin ma taga wanene. Atare suka shigo dakin, boss tare da Ummi da ke abiye da shi cikin shiga ta kimono robe, ta yafa gyale a kafadarta, hannun kowannan su ruƙe da ɗan ƙaramin tray na kayan abincin. "Barka da safiya daughter" wani irin wurgi tayi da bargon gefe ɗaya ya faɗa kan Batool, ta ɗago tana faman zare mashi idanunta. Sunyi mamakin ganin yadda ta zabura, ummi tace"ko dai har yanzu jikin ne"? Ko kallo unaisah batai mata ba idanunta na akan taj, wanda ke sanye da facemask, A hankali take tariyo abun da ya faru jiya, lokaci daya ta rushe masu da matsanancin kuka wanda yayi silar farkawar batool. Hankalinsu atashe su ka soma ambaton sunanta, tare da tambayarta meke damunta! Ko ciwonta ya motsa. Sauko tayi daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja kofa ta rufe tana cigaba da yin kukan Kallon juna ummi da taj sukayi a lokaci ɗaya, fuskokin su dauke da matsanancin damuwa, atare suka daura trays din hannun su kan table suka nufi bakin kofar toilet Batool dake zaune kan gadon sai faman mutsustsuke idanu takeyi tana ambaton sunan unaisah... Magiya suka dinga yi mata akan ta buɗe ƙofar "Dan Allah unaisah Ki fada mana meke damunki? Ko cikin ki ke maki ciwo? Idan akwai inda ke maki radadi ki fadamin Yanzun nan zanje na karbo maki magani, wallahi mun damu dake jiya ko runtsawa bamuyi ba, har sai da muka ga kinyi bacci" cikin sigar lallashi ummi takeyi mata magana. "My daughter ki yi shiru ki saurare ni, nasan meke damunki, ni nasan dama dole kiji haushi, inaso ki kwantar da hankalin ki, saboda mun riga da mun gano wacece tayi maki aika aikarnan kuma in sha Allah zamu hukuntata, idan ma kinaso zamu kawo maki ita, ki rama abunda tayi maki" Maimakon unaisah ta sassauta kukanta, jin lallashinta da suke yi mata sai ma takara sautin kukan nata tamkar zata fasa kunnuwansu, da gudun gaske sajeed Ya fado dakin Yana haki daga shi sai gajeran wando bai jima da shigowa ba naufal Ya shigo shima yana tambayar meye faru da angel dinsu? Shigowa suka dinga yi, daga me hamma sai mai miƙa daga gani basu jima da farkawa daga bacci ba, dama da tunaninta suka kwanta bacci jiya shiyasa suka farka da ita aransu, atare Jemimah da Azeeza suka shigo kowannan su kayan bacci ne a jikin shi, ba su jima da shigowa ba, Parveen ta shigo hannun ta ruƙe da brush, sumar kan nan a haukace gyaran gashin da akayi masu duk ya tarwatse kowa fa hankalinsa Ya tashi matuƙa, Jemimah sai kuka takeyi masu hada tsallanta tana fadin dama tasani mutanan nan sai da suka cutar mata da Angel dinta, wallahi bazata ƙyale su ba dole ta rama mata... Gaba ɗayan su sunyi curko curko abakin kofar toilet din "Please ku kwantar da hankulan ku, ku bari muyi kokarin shawo kanta sai muji meke damunta" ummi ta fada tana duban su kafin ta mayar da dubanta ga boss man. "nifa ina tunanin watakil ko tayi zaton kai ne kayi mata wanka a daren jiya shiyasa take kuka" Dafe kanshi yai da hannu ɗaya saboda shi ma ya yarda da maganar ummi, cikin muryar lallashi Yace"Unaisah, bani ne nayi maki wanka ba, Aunty umminku ce, bayan na dawo dake jiya na kawo ki gida da taimakonta kika tsarkake jikinki har kikayi wanka.. " kafin Ya kare maganar, cikin muryar kuka tace"ni ba wannan bane damuwana ba, daddy meyasa za ka yi min haka? Hankali atashe taj ya ɗan zaro idanu Ya dubi ummi babu alamun ya fahimci abunda Unaisah take nufi sai ma cewa yayi"kinyi mafarki ne da daddynki"? A tsiwace tace"ba mafarki nayi dashi ba, a zahiri na ganshi jiya, saboda me zaka dinga 6oye min kanka daddy, ko ka daina sona ne" ta faɗa tana haki Dariya ce ta kubcewa ummi ganin yadda taj ya daura hannayensu biyu saman kanshi alamar Ya shiga Uku gaba daya yabi ya ruɗe Sai lokacin Ya tuna da abun da Ya faru Jiya, da kanshi Ya cire facemask dinsa Ya jefar da shi saboda baya ahayyacinsa ashe idonta biyu taga fuskarshi Muryarshi tamkar zai fashe da kuka Yace"am really sorry my Angel, nayi laifi ay min afwa, nasan ban kyauta maki ba, amma dan Allah ki fahimce ni, ki nutsu ki saurari me zan fada maki.." kafin ya kare maganar ta katse shi da cewa"ni bazan saurari komai ba daddy, kawai ka daina sona ne ba ka damu dani ba, kuma ba ka yi kewata ba shiyasa kake 6oye min fuskarka..." ta fada tana jan majina kafin taci gaba da cewa"Daddy, what did I do to deserve this punishment from you? Daddy kasan kuwa irin kalubalan rayuwar dana fuskan ta? Daddy duk halin da na shiga ban ta6a mantawa dakai ba, bana kwana batare da na sanya ka acikin addu'ata ba, kullum zullumina ya rayuwar daddyna ta ƙare? Meya faru da shi bayan Ya jefa ni cikin ruwa, Ya rayu ko ya mutu.... " Ba ta kare maganar ba saboda kukan daya ciyota, ta kuma fashewa da wani kuka tamkar ana zare ranta, abunne Ya tsaya mata aranta ya 6ata mata rai duk irin kewansa da tayi amma shine ya boye mata kansa. Gaba ɗaya hankulansu Sajeed Ya koma kan fuskar tajuddeen, kalaman Angel ne suka fahimtar da su wanene shi Muryar na rawa Azeeza tace"dama kai ne daddyn Angel wanda kullum take bamu labarin shi"? Da sauri Parveen tace"idan bazan manta ba, duk in muka zauna fira unaisah saita bamu labarinka, itace tafara sanya mana kwaɗayin ganin ka, da zumudin son muje gidan su don muyi rayuwar ƴan ci, har fada mana takeyi daddyn ta zai kar6emu kamar ya'yansa..... Kasa karasa maganar tayi nan take ta fashe da kuka. Cikin karyayyar murya Batool tace"ashe kai ne daddyn Angel, Ni burin da nake dashi idan Allah yasa na haɗuwa dakai shine inyi maka godiya saboda Angel ta faɗa min kaine ka ilmantar da ita, ka tsaya mata tsayin daka har ta samu ilmin addinin da take da shi, uwa uba kaine silar da Angel tazo duniya...." tana magana hawaye na wanke fuskarta. "Wallahi ba mu ta6a sanin wanene mahaliccin mu ba, sai a sanadin zuwan Angel GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, , In da mu ka yi rayuwar kulle, cikin duhun jahil ci, harta toilet atare muke shiga da ƴan uwanmu maza Angel itace ta tsawatar mana ta fada mana cewa babu kyau mu daina haramunne wani yaga tsiraicin wani......" kuka ne ya kubce ma batool, ummi dake sauraransu a matuƙar ruɗe take ɗan zare idanunta akan fuskokinsu, gaba ɗaya sun jefa ta a cikin ruɗani lamarin yayi muƙar girgiza ta, tayi matukar razana. Bata gama shan mamaki ba cikin sanyin murya haris Yace"Allah ne kadai zai iya biyanka daddy, zuwan Angel cikin rayuwarmu tamkar baiyanar haske ne a cikin duhu, wallahi baki bazai iya furta irin wahalar da unaisah tayi akanmu ba, duk da kasancewar ta ƙarama a cikin mu amma tana da kaifin basira kuma tana da hankali, Angel ta zama jigo na rayuwarmu, ta share mana hawayenmu a lokacin da muke kukan radadin kuncin rayuwar da muke aciki, Angel uwace agare mu, saboda ta kwatar mana ƴancin mu da aka tauye mana......" zu6ewa haris yayi kan gwiwowinsa hawaye naci gaba da sintiri kan fuskarsa, Gaba ɗaya sun gama kashe ma tajuddeen jikinsa, yayi sanyi laƙwas zuciyarsa ta karaya, wasu irin zafafan hawayene masu ɗumi suka soma wanko fuskarshi yayin da yake kallonsu ɗaya bayan daya, yana mai jin tsantsar tausayin su da kaunarsu azuciyarshi, Angel ta gama masa komai a duniyar nan baisan ma ina zai tsoma kanshi ba tsabar yadda Yake jin mahaukacin sonta na kara nunkuwa acikin zuciyarshi, ba zai iya misalta irin alfarin da ya ke da ita, burin kowani ubane ya sami ƴa kamar Angel wadda zata kare masa martabarsa da kimarsa a idon duniya, wadda zata daukaka darajarsa ta kuma yi silar shigar shi aljanna, hannu ɗaya ya daura akanshi Yana cigaba da kallon su jikin shi har kerna kerma ya ke yi. Duk wannan abun dake faru a kunnan chief owais da Big guy wadanda basu jima da zuwa bakin kofar dakin ba, sunzo zo ne don su duba jikin Unaisah sai kuma suka ji abunda ba suyi tsammani ba wannan dalilin ne yasa suka dakata suna sauraron su Cikin shessheƙar kuka Naufal Yace"daddy duk yadda zamuyi maka bayani ba lallai ka fahimce mu, amma wallahi muna kaunarka muna son ka daddyn Angel" wasu hawayen nan suka kuma wanke fuskar taj, idanunshi sunyi jawur da su gaba ɗaya ya rasa bakin magana sai dai kallonsu da yake tayi gwanin ban tausayi "Unaisah itace take ƙarfafa mana gwiwa, itace komai namu, itace muke gani muji dadi, unaisah ko mun 6ata mata rai bata yin fushi damu ba, sai ma taja mu ajikinta saboda tasan bayin kan mu bane, rayuwa mu ke a cikin duhun jahilci, ....." gaba ɗaya suka dubi batool da ta dauko maganar hawaye na sintiri kan kuncinta, dakatawa tayi da yin maganar na ɗan wani lokaci kafin taja numfashi taci gaba cewa"ɗaya daga cikin abun da unaisah tayi wanda har a bada bazai ta6a gogewa acikin zuciyata ba, shine musuluntar da yar uwar mu unaiza da tayi, unaisah bata bari unaizah ta mutu a matsayin arniya ba, sai da ta taimaka mata ta kar6i shahada duk don saboda ta tsira a lahira..." muryarta na rawa tayi maganar, kusan atare suka rushe da kuka tunawa da yar uwarsu unaizah, maganar batool ta fama masu raunin dake acikin zuciyoyin su. zu6ewa su ka yi gaba dayansu saman gwiwowinsu agaban tajuddeen, suna kuka yana kuka babu mai lallashin wani a cikin su, ummi da batasan kan zancen nasu ba tuni itama ta fara matsar ƙwalla cikin rauni na murya tace dan Allah ku fahimtar dani ku yi min bayani tun kafin zuciyata ta buga, saboda hankalina ya tashi na kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarku......." Lumshe ido chief owais yayi, zuciyarshi ta karaya, wankan suit ne ajikin shi, bai jima da dawowa daga Airport ba wurin rakiyar prime minister. A hankali Ya dubi Big guy dake a tsaye gefen sa, hawaye ya gani sun cika mashi idanunshi, Shi kanshi dauriya ce kawai, amma kalaman su sun ta6a ta6a zuciyarsa. Cikin sanyin murya ya furta"ka kira salsabeel a waya ka faɗa masa inji ni ya shirya sauran yaran, su zo nan gida su sameni, inaso suga yan uwansu" cikin girmamawa big guy yace"okey, sir." ya faɗa tare da zaro wayarshi ya danna ma salsabeel kira wayar na fara ringing, yayi picking, "barka da safiya yalla6ai" "Yawwa barka, Ina fata dai ban katse maka baccinka ba" muryarshi da yar dariya yace"ay bana yin baccin safe saboda khadeeja kasan halinta kamar mai fama da cutar yunwa, tun da safe take tashina, don in shiga kitchen in dafa mata indomie" "Allah sarki, ka cigaba da haƙuri da ita, Yanzu dai gani tare da chief, yace yana son ganin ka da sauran yaran yanzun nan ku same mu agidansa" Muryar salsaleen da dan rudani yace"yallabai badai wani abune ya faru ba? Naji kace nazo da yara da sassafen nan" "Ba wani abu kazo kawai, " amsa mashi yayi da toh, kafin su ka yi sallama Ya maida wayar cikin aljihu... Angel dake atsugunne bakin kofar toilet din, jikinta ya gama yin sanyi tamkar wadda aka zarewa laka, duk abunda su batool ke fadi akan kunnanta tuni tayi shiru ta dakata da yin kukan, ita kanta bata ta6a tsammanin sun ruƙe kyautatawar da take yi masu ba acikin zuciyoyin su, shiyasa ake son bawa ya kasance yana aikata abun alkhairi arayuwarsa saboda duniya tayi alfahari dashi, al'umma su yi koyi dashi ko bayan ba ranshi, unaisah dai ta bada gudummuwa ta bangarori da dama harta ta bangaren addinin musulunci ta musuluntar kuma ta fadakar Allah ne kaɗai zai iya biyan ta. Cikin shessher kuka suka soma yi mata magana, muryoyinsu duk sun disashe "Yar uwarmu rabin ranmu, amadadin abban mu, muna baki hakuri dan Allah ki taimaki daddynmu, Kiyi hakuri ki fito yana son ganinki, daddy ya gane kuskurenshi kuma ashirye yake daya baki hakurin laifin da yayi maki.... " magiya suka dinya yi mata duk don su samu ta buɗe masu kofa "Unaisah kin manta irin kyautatawar da daddynmu yayi maki tun kina karamarki, lokacin da mommynki ta gudu tabar ki a cikin kwamin wanka, ya daukeki yaci gaba da baki kulawa duk da kasancewar bakyajin magana ahaka yaci gaba da rainonki saboda irin son da ya ke yi maki shi bai tafi yabar ki ba, unaisah da bakin ki ki bamu labarin nan ko kin manta ne......" gaba ɗaya kowan nan su ya ƙosa ta fito saboda ta rungumi daddynta. Ba zato ba tsammani, suka ga taj Ya dafe saitin zuciyarshi yana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Muryarshi da wani irin sauti na tashin hankali, gaba ɗaya suka zabura da sauri suka rufe shi suna ambaton daddy meke damunka? Baka da lafiya ne...." Jin wannan maganar yasa unaisah yin saurin miƙewa, yatsun hannunta na kerma ta soma kiciniyar buɗe kofar, a fujajen ta fado dakin, ganinta yasa suka bata hanya, ta faɗa jikin tajuddeen ta ƙanƙame shi tana kuka take fadin daddy dan Allah kayi hakuri nasan nice na bata maka rai, ka tashi ka ji daddyna abun alfahari na, la66anta na kerma takeyin maganar, hawayen fuskarta tuni sun wanke fuskarshi, sumbatar goshin shi tayi, tare da manna masa wani kiss din kan kuncinsa ...." sai da taj ya bari ta gama firgita, tukunna ya buɗe idanunsa fuskarshi dauke da murmushi, fashe mashi tayi da kuka da sauri ya janyota jikinsa suka rungume juna tamkar zasu koma mutun ɗaya tsabar yadda suka matse junan su lallashinta yaci gaba dayi yana fadin"am sorry my angel, ki yafe ni, nasan bankyauta maki ba, wlh kina araina, kamar yadda kike fadin kin yi kewata nima haka nayi kewarki, angel rashinki ba karamin gi6i yayi min ba rayuwata sai da nakusa zaucewa saboda haukan rashin ki a kusa da ni, Angel bana iya bacci batare da nayi mafarkin ki ba, duk dare na Allah sai na tashi nayi salla saboda inyi maki addu'a Allah ya kare min ke duk da bani da tabbacin kina araye ko kin mutu......" dakatawa yai da yin maganar, idanunsa acikin na Angel dinsa, sai da ya fara tattara nutsuwarsa kafin cikin sanyin murya ya fara basu labarin abun da Ya faru dashi bayan ya jefa Angel cikin ruwa. _______________________________✍️ Abun da ya faru lokacin da wadannan migayun dattawan su ka ƙyasta lighter bayan sun zazzaga mashi fetur a jikin shi, idan ba zaku manta ba, ba su kaiga jefa mashi lighter din ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna suka cinna wutar, sannan ba su tsaya sunga wutar ta kone sa ba, suka shiga cikin motocinsu tare da fusgarsu suka bar dajin a guje, bayan tafiyarsu hucin wutar Ya daki fatar jikinsa wani irin radadin azaba ne ya ziyarci sassan jikinsa, nan take ya farfaɗo daga suman da yayi ko da yaga wutar dake ci, cikin matsanancin tashin hankali ya yi wani irin kwakkwaran juyi da dukkan karfinsa gaba ɗaya ya rubza cikin Kogon ruwan daya jefa Angel, tsulundun Ya rubza cikinsa ya nutse can kasan ruwan kuma nan take ya sake sumewa. Suna acikin ruwa ɗaya da Unaisah sai dai akwai tazara tsakaninshi da unaisah, wanda silar hakan yasa har danejo ta ceto rayuwar unaisah ba tare da tasan cewa akwai mutun acikin ruwan ba saboda ruwa daya ja shi... A kalla taj ya kwashe tsawon kwana uku acikin ruwan ba tare da ya samu taimako ba. Ana haka cikin ikon Allah, Wasu fulanin daji dake kiwo daga can wata ruga dake a cikin dajin, su biyu matasa suka koro shanayensu zuwa wurin da ruwan nan yake, Anan suka yaɗa zango, to ɗaya daga cikin su mai suna habu mayen ruwa ne duk in suka zo bakin ruwan sai ya shiga yin wanka, babu irin gargadin da ɗan uwansa garbati baiyi mashi ba akan yadaina shiga ruwa saboda hatsarin dake gare shi amma yai kunnan uwar shegu da shi saboda taurin kansa da kafiyarshi, Abun ne yabi jikin shi tun suna kanana Yake shiga ruwa yin wanka har izuwa girmansa, shi kuma garbati mugun tsoron ruwane da shi, ko kusa da ruwa baison zuwa jikin shi kerma yakeyi saboda Labaran da yake ji daga wurin mutane dangane da mugayen halittun ruwa dake cinye mutun shiyasa yake jin shakkar kusan ta kanshi da ruwa, aranar da suka je bakin ruwan, habu na kokarin cire kayan shi don yashiga yayi wanka, garbati yayi saurin damƙar rigarsa suka soma kokawa a tsakaninsu, cikin harshen fulatanci suke magana garbati yace wlh bazaka shiga ruwan nan ba, ka manta da gargadin da baffa yayi mana akan shiga ruwa? Ko so kake ka mutu ne kafin lokacin ka yayi? Habu da ya gama hasala Ranshi a6ace yace"Aradun Allah garbati baka isa ka hanani shiga yin wanka ba, ko da kuwa sama da kasa zasu hade saina shiga, idan ma wani abu ya same ni, ni naja ma kaina kai dai naka kallone kawai" duk yadda garbati yaso ya hanashi amma yaki ji, a karshe sai yasa hannu ya hankaɗe garbati gefe daya ya kife kan ciyayi da sauri habu ya bi ta hanyar da ya ke shiga ruwan ta cikin sauki yabi duwatsun dake kewayen da ruwan ya tsunbula cikinsa Ya cigaba da yin wanka yana raira waka cikin harshen fulatanci. Mikewa garbati yayi zuciyarshi a 6ace yaci gaba da kula da shanayensu yana jiyo muryar habu dake acikin ruwa yana raira mashi wakar habaici har yana kiran shi da ragon namiji, zaifi dacewa ya koma ɗaura zani maimakon wando, har ma ya dinga taya su Inno surfen Gero, ranshi ya 6ace jin wannan maganar, amma saboda hakurin dake gare shi sai ya share shi yaci gaba da kula da shanayensu Habu yana cikin yin nutso ya shige can kasan ruwan yana shawagi ba zato ba tsammani idanunsa suka sauka akan mutumin dake kwance kasan ruwa rai hannun Allah, kasancewar kasan ruwane idanunsa sunyi mashi biji biji sai ya dinga ganin kamar wata halittar ruwace me girman gaske, bakomaine ya fado mashi aranshi ba face gargadin da garbati keyi mashi akan ya daina shiga ruwa akwai mugayen halittun dake cinye naman mutun, nan fa hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta soma yi mashi dakan uku uku, Jiki na bari ya soma yin sama ya fiddo kanshi yana ihu na fitar hayyacin tamkar zai fasa makoshin sa, ko da garbati yajiyo ihun Habu abunka ga firgitacce bai tsaya tambayarshi menene ba, ya watsa aguje kamar karan farauta Ya nufi rigarsu.... Ya bar habu acikin ruwa Yana ta Zagba ihu tsabar rudu Ya hana ya fito daga ruwan gaba daya ya gama rikicewa. Da gudun gaske Fulanin Rigarsu suka nufo wurin ruwan wasu ko takalma babu a kafafuwansu, wasu kuwa hannayensu ruke da makamai saboda su ceto dan uwansu, bayan sun karaso gaban ruwa wasu dattijai daga cikin kakanninsu irin wadanda suka daɗe suna gwagwarmaya ne, basu da tsoro ko miskala zarratin, sun saba da duk wani abu daya shafi daji suna da kwarewa akansa Basu tsaya bata lokaci ba suka afka cikin ruwan don su ceto rayuwar dan su, ko da suka shiga, Habu Ya kankame kakansu Yana sambatu iri iri, ya dinga nuna masu saitin inda yaga halittar da hannun shi, da sauri ɗaya daga cikin kakannin nasa mai karfin Hali ya kutsa kai cikin don ya kashe halittar, aikuwa yana shiga yayi tozali da mutumin dake a kwance kasan ruwan, lamarin ya daure mashi kai, ganin ɗan mutun acikin ruwa, aranshi ya dinga tunanin mutunne ko aljan? Watakil aljanin ruwa ne" Wasi wasi yaci gaba dayi, har zai tafi sai kuma zuciyarsa ta dinga azalzalarshi akan ya dauko mutumin watakil tsautsayine ya afka da shi... Baiyi kasa a gwiwa ba yaje ya kinkimo tajuddeen abunka ga tsohon kashi na majiya karfi wadanda suke da shirinsu baiji nauyin taj ba akan kafadarshi ya sargafo shi, Ya fito masu da kawunansu daga cikin ruwa, ya ɗaga murya yana fadin"Ta mutunce ba aljani ba," Gaba ɗaya suka zaro idanu waje suna lekensu kowa da abunda yake sakawa aranshi, Bayan sun fito dashi daga ruwanne suka kewaye shi suna kallon shi, anan suka ga alamar bai mutu ba, da ranshi, wani abu daya basu tausayi game da shi, mummunan raunin da suka gani akan tafin kafarsa ta dama, fatar wurin ya rarake yayi rami, ba tare da sun 6ata lokaci ba suka tafi da tajudden can rigarsu, a inda suka cigaba da bashi kyakkyawar kulawa suka ɗaure masa raunin kafarsa bayan sunyi mashi ƴan dabarun su na mutanan daji, tsawon kwanaki baya acikin hayyacinshi, ko bacci yake yi ya dinga farkawa kenan yanayi masu sambatu akan yarsa da ya baro cikin ruwa, sun rasa gane me yake nufi saboda basa jin harshen hausa, wani lokacin kamar zautacce yai ta kuka yana ambaton sunan Angel, a kalla taj ya shafe tsawon watanni ba tare da ya iya taka kafarsa ba, wannan dalilin ne yasa bai samu damar zuwa neman Angel ba, bayan haka ya yi loosing memory dinshi, sunanta ne kadai ya tsaya mashi aran shiyasa yake yawan ambatonshi.... Lokacin da ya fara samun sauki yaci gaba da rayuwa da su yana ta kokarin ya tuna miya faru dashi amma ya kasa saboda lalurar data sameshi a haka ya rayu a rigar su na tsawon shekara biyu cikin ikon Allah a daren wata rana yana tsaka da baccinsa yayi wani mummunan mafarki dangane da Angel dinsa wanda ya yi silar dawowar memory din shi, tun a cikin daren ya fara kokarin barin rigar don yaje nemanta gaba daya ya tada masu hankali duk wani mai bacci sai da ya farka yai ta ambaton sunan ƴarsa da ya jefa cikin ruwa yana ta kokarin kwatanta masu sai dai sun kasa gane me yake nufi, lallashin shi suka cigaba dayi suna kwantar masa da hankali, a dole ya hakura bai fita a daren ranar ba, A Washe garin ranar da sassafe kakansu habu ya bashi kyautar sandar da zai yi amfani da ita wurin yin tafiya, saboda har time ɗin kafarsa bata dawo dai dai ba, lokacin da su habu zasu tafi kiwon shanu sai yabi bayan su don ya nemo Angel dinsa, sai dai kash ita kuma a lokaci har wannan tsautsayin ya fada da ita, tana acan gidan kurkukun kaddara, kuma bata jima da barin rigarsu Danejo ba, shi kuma yafara zuwa nemanta, tunda yaga kogon ruwan ya ƙafe babu ruwa acikinsa saboda damuna ta wuce, mutun na iya ganin komai dake a kasan ramin, yayi kuka na fitar hayyaci kamar ransa zai fita, har yunkurin fadawa yayi don ya kashe kanshi, da sauri su habu suka rirrike shi tare da jan shi suna lallashin shi, saidai sam baya fahimtar me suke cewa. Sai da takai ga abakin ramin ruwan yake kwana tun safe har dare ya ritsa da shi baya motsawa anan fulanin suke zuwa kawo mashi abincin da zai ci, tunda ya ƙi komawa rigarsu, yafi son zama bakin ruwa, hakika sunji tausayinshi duk da basu san meke damun shi ba, saboda son da kakansu habu keyi mashi, bukka ya haɗa mashi a wurin saboda yaji dadin cigaba da kwana abakin ruwan, hada bargon lullu6a suka mallaka mashi, da duk wani abu da zai buƙata...... Bayan wani lokaci, awata rana yana zaune abakin ruwan yayi zurfi a cikin tunaninsa, sai ga bafullatanar dajin da ta taimaki Angel, ta koro shanayenta zuwa kiwo, ita kanta bazata tuna rana ta karshe da ta zo bakin ruwan ba tun bayan da angel ta gudu tabar rigarsu bayan ta gama haukan jimamin rashinta gaba ɗaya danginta suka hanata fitowa kiwo, sai dai yan uwanta suka cigaba da yi, sai ranar ta samu suka barta, bata nufi ko'ina ba sai bakin ruwan da yabar tarihi a zuciyarta, tana cikin tafiya ta hango sabuwar bukkar da akayi abakin ruwan ga kuma mutun zaune ya zura kafafunsa cikin ramin, Kamar a mafarki haka take kallon shi, gaba ɗaya hankalinshi baya akanta.... Sautin kukan shanayenta ne suka dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga, firgigit yai tare dakai idanunsa gareta, duk a tunaninsa su habu ne suka zo yin kiwo, ko da idanunsa suka yi masa tozali da fuskar kyakkyawar matashiyar budurwa kamar aljana, da sauri taj ya mike yana kallon ta da tsantsar mamaki akan fuskarshi, babu wanda yayi ma wani magana acikinsu sai kallon kallo da suke jefawa junansu, ita dai danejo kallon sani take yima fuskarshi duk da tayi imanin wannan ne karo na farko data fara ganinshi, yayin da shi kuma tajuddeen baisan dalilin kallon da yakeyi mata ba, ya dai yi mamakin tsantsar kyawun dake gareta. Jin shirun yayi yawane yasa ta soma yi masa magana da yaren fulatanci"wanane kai? Daga ganin bakuwar fuskarka ba fulanin dajin mu bane" fuskar ta da murmushi tayi maganar tana nuna shi da sandar hannunta..... Bin ta da ido yayi don bai fahimci me tace masa ba. Tamkar bazai tanka mata ba yace"bana jin yaren da kikai min magana shi," waro mashi dara daran idanuwanta tayi, wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskarta, cike da mamaki yake kallon ta ganin tana ta murmushi, bakomai ne yasa ta farin ciki ba face jin yayi mata magana da yaren Angel dinta, yarinyar da ta kwallafa rai akan son ta. Bai yi tsammanin zatai mashi magana da hausa ba sai ji yai tace"Ya sunanka? Wanene kai? Me kake yi a rigar mu" dakyar hausar ke fita irin ta ƴan koyo. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bata amsa da cewa sunana tajudeen, bako ne a rigarku, ban jima da tsintar kaina a cikin ku ba," wani irin bugu taji kirjinta yayi mata, jin sunan daya ambata kamar ta ta6a jin sunan abakin angel, sai dai takasa tunawa Cigaba tayi da janshi da fira saboda Ya kwanta mata aranta, wunin ranar danejo tana atare da taj, ba laifi ta ɗebe mashi kewar dake damun shi, yawo suka dinga yi acikin dajin suna tafiya suna fira kaɗan kaɗan saboda rashin sabo, da kuma ƙarancin hausar dake gareta, bakomai ne take fahimta ba. Tun daga ranar daya haɗu da danejo, wata irin shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, kullum ne sai tazo kawo mashi abinci sau uku arana, wani lokacin gasassar masara zata kawo masu su zauna suna ci suna fira, har dai wata rana ta gayyace shi zuwa rigarsu, duk da ya nuna mata baisan zuwa, roƙansa ta dingayi hada sanya mashi kuka, a dole ya amince mata suka je rigarsu, tashin farko danginta suna ganin taj suka tada 6alli akan basa son ganin shi tare da ita, hankalin danejo ba karamin tashi yayi ba, jin zasu rabata da mutumin da take sa ran zai maye mata gurbin Angel, akan idonshi suka rufe ta da fada kamar zasu bugeta cikin harshen fulatanci inna wuro ke ta faman zazzaga masifa tana fadin ta manta gargadin da sukayi mata akan kada ta kuskura ta ƙara kawo masu wani a cikin rigarsu! So take ta kashe kanta saboda taimakon bare ne? Ko ta manta da irin wahalar da tasha bayan tafiyar yarinyar da ta ƙwalla rai akanta ne? Babban yayan su bawuro yace"tun wuri ta rabu dashi, idan ba so take su kashe shi ba" fashewa tayi da kuka hada bubbuga kafa tana fadin ita wallahi bazata rabu da shi ba, saboda zuciyarta ta kamu da kaunarshi," jin wannan maganar daga bakinta ba karamin fusata su yayi ba, Inna wuro tace"sai dai ta za6a ko su ko shi," abunka ga mai karancin hankali ga kuruciya dake damunta, da buɗar bakinta sai cewa tayi zata bishi, aikuwa a fusace bawuro ya kifa mata mari, da sauri taj ya dakatar da su ganin abun nasu na neman wuce gona da iri. Cikin kwantar da murya yace masu su yi hakuri, su daina bugunta indai saboda shi ne yanzu zai tafi yabar masu rigarsu" sam basu fahimci me yake cewa ba, sai ma wani irin kallon tsana da suke jifar shi da shi, har ya juya zai tafi danejo ta ruƙo hannunsa, a fusace gidado ya ruƙo hannunta, suka riketa don kada tabi shi. Sautin kukanta ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, shi kanshi baya son rabuwa da ita, ba don yaso ba sai don ba yadda zaiyi ne... Har yayi nisa da tafiya, ya ɗan dakata zuciyarshi na raya mashi ya juya ya kalle ta, watakil bazai sake haɗuwa da ita ba, har zuwa lokacin da zai bar dajin, Juyawar da zaiyi keda wuya, kwatsam idanunsa suka sauka akan rigar Angel dake shanye kan ɗaya daga cikin bukkokin su, daga gani wanke ta akayi aka shanya don ta bushe, da farko bai tantance abunda idanunsa ke nuna masa ba, sai da ya ɗan kara ƙura idanunsa tukunna Ya shaida itace rigar baccin da ke a jikin Angel aranar da ya gudo da ita, sune kayan jikin ta, was wasi yafara yi a cikin zuciyarsa tayaya akai rigar unaisah tazo dajin a hannun fulani? Ko dai suma suna da irin rigunan gayu ne"? Farat ɗaya zuciyarshi ta bashi amsa da cewa me zai kawo irin wannan suturar a hannun mutanan da ke rayuwa a daji? Sai dai idan tsintar ta su kayi...' muryarshi na rawa ya furta"idan har dagaske ne abunda nake hasashe tabbas Wani ya ceto rayuwar Angel ɗina bayan na jefata a cikin ruwa tun da gashi har rigarta ta bayyana... Ba zato ba tsammani, suka ga mutumin da suka kora ya watso da gudu ya dawo wurin rigarsu, har sun har zuƙa zasu fara dukanshi da sandunan su sai kuma suka fasa ganin Ya damƙo rigar da danejo ta shanya kan bukka, ruƙe rigar yayi a hannunshi zuciyarshi na bugawa da matsanancin karfi ya soma ambaton sunan Angel Angel, Lokaci ɗaya su bawuro da su hasiya suka kalli juna da mamaki jin yana ambaton sunan yarinyar da danejo ta tsinto a cikin ruwa, tambayar shi suka soma yi wanene shi? Ya akai yasan yarinyar? Hawaye na zuba daga idanunsa ya dago rigar yana nuna masu yace" wannan rigar ta ƴata ce Angel, da hannuna na jefa ta cikin ruwa, dan Allah ku fada min a ina kuka samu rigar? Ko dai kune kuka ceto rayuwarta....." kukane yaci karfinsa, gaba daya ya rikice masu, su kansu so suke son san me yake cewa don suji ko shine mutumin nan da yarinyar take nema don bazasu ta6a mantawa ba da irin kukan data dinga yi masu tana kaisu bakin ruwa donsu nemo mata daddynta tun basu fahimtar me take cewa har suka gane cewa wani nata ne take nema.. Danejo ce kaɗai ta fahimci me Yake cewa, nan take ta fashe da kuka Cikin harshen fulatanci ta sanar ma sauran ƴan uwanta abun da taj Ya ke faɗi nan suka gane cewa shine mahaifin Angel, yarinyar data tsaya masu aransu, har yau har gobe basu cireta aransu ba, hakika sunyi farin ciki mara misaltuwa da ganinsa. Tsabar farin ciki yasa danejo ta watsa da gudu ta fada kan kirjinsa ta rungume shi tana kuka, ta soma tambayarshi ina Angel? Ko ya ganta"? Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, a ruɗe ya tambaye ta me take nufi? Ba su suka taimake ta ba" cikin sanyin murya danejo ta labarta mashi komai daya faru tun daga lokacin da ta tsintota a cikin ruwa har zuwa time da ta gudu daga rigar su. Wani irin jiri yaji yana shirin kwasarshi saboda kuncin dayaji, bakomai ne ya jawo mashi jinkirin da yayi ba nazuwa daukarta face loosing memory din da yayi. Zubewa yai kan gwiwowinsa zuciyarsa a hautsine tamkar zata buga, gaba ɗaya suka kewaye shi, suna kallon shi gwanin ban tausayi, ganin yadda ya ke matsar kwalla. Saboda son da suke ma Angel yasa suka yi mashi kyakkyawar tarba, a kalla ya shafe wata a rigar su, kafin Yaji bazai iya cigaba da zama a dajin ba, kwara ya koma gida watakil idan yaje can ya sameta ta koma wurinsu Aneelerh. Ranar da taj ya shirya tafiya, zai bar rigar, ya yi masu bankwana kamar karsu rabu, yace masu zai fara zuwa wurin mutanan da suka taimake shi kafin ya wuce garin su, guzurin tafiya suka hada masa, kowa ya kawo abunda yake dashi, suka bashi sannan sukace mashi idan Allah yasa yaga yarsa angel ya fada mata sunyi kewarta, zuciyarshi cike fal da kewarsu ya kamo hanya zai bar rigarsu, harfa yayi nisa yajiyo takun gudunta sai faman kwala mashi kira takeyi, a hanzarce ya juya yana kallonta, danejo ce hannunta ruƙe da kullin kayanta, hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, ganin ta biyo shi. Karasowa tayi tana haki tace"dan Allah ka tafi dani inason ganin Angel" Girgiza mata kai yayi"kiyi hakuri bazan iya tafiya dake ba, meyasa kika yarda dani har haka? ki yi hakuri ki koma wurin ƴan uwanki" fashewa tayi da kuka. Ana cikin haka, yajiyo sautin takalman yan uwanta kusan gaba dayansu ne suka biyota. Fuskokinsu babu walwala, ruƙo hannunta kakansu yayi tare da mika ma taj, da mamaki yake kallonshi don bai fahimci me yake nufi ba, har saida yayi mashi da kurmanci Ya nuna mashi cewa ya tafi da ita, sun bar mashi ita, saboda tace in har basu bari tabi shi ba, to zata kashe kanta ne, shiyasa suka yanke shawarar kwara su bar mashi ita, don ko sun barta ba lallai su iya shawo kanta ba. Babu yadda taj baiyi da su ba akan subar yarsu, hankalinsu sai yafi kwanciya idan tana akusa da su amma suka sanya kafiya akan dole ya tafi da ita, ganin ya turje ne yasa suka fada mashi cewa marainiyace, tun kafin ta mallaki hankalin ta iyayenta suka rasu, bata ta6a neman wani abu daga gare su tarasa ba, don haka sun bashi amanarta, yaji tsoron Allah ya rike masu ita amana su je can su yi aure, hawaye ne suka wanke fuskarshi, jiki asanyaye yasa hannu ya ruƙo hannun danejo,yayi masu alkawarin bazai ta6a bari ta nemi wani abu ta rasa ba, zai dauki dukkan wani nauyi nata zai bata kulawa, sunji dadin abunda ya fada masu a karshe sukayi bankwana da junansu, yaja hannun danejo suka nufi rigarsu Habu. har sun fidda rai da sake ganin shi, tsawon kwanakin da yayi a rigarsu danejo kusan kullum sai sunzo neman shi a yar bukkarsa, sunyi mamakin ganin ya dawo masu tare da yar matashiyar budurwa, cikin harshen fulatanci danejo tayi masu bayanin komai dangane da taj...." labarin tajudden da Angel ya ta6a zuciyoyinsu, har hawaye suka zubda masa saboda tsananin tausayin shi da suka ji, bayan komai ya lafa ya sanar da su zancen tafiyar shi, ba don sunso ba sukayi mashi fatan alkhairi da addu'ar Allah yasa yaga yarinyarsa, kafin tafiyarsa saida suka hada mashi shatara na arziki, bayan haka suka yi masu rakiya har zuwa bakin titi, ba su tafi ba sai da sukaga ya samu motar hayar da zata shigar da shi cikin garin joss tukunna sukayi mashi bankwana. Tun da suka shiga motar, danejo ta kankameshi, kamar wani yace zai kwace mata shi, wani irin mugun tsoron mutane take ji, mutun ɗayane ta yarda dashi ta kuma damka amanarta agareshi saboda tasanyawa ranta cewa bazai ta6a cutar da ita ba. Kafin su karasa cikin garin, tuni bacci yayi awon gaba da ita, a yayin da kanta ke asaman kirjinsa, hankalin taj sam ba akwance yake ba, saboda fargaban kada miyagun da suka kai mashi farmaki su gansu, yasan muddin sukasan cewa bai mutuba, to kuwa zasu nemi hanyar da zasu kashe shi ne kamar yadda suka kashe dan uwansa uzair, mutuwar da tayi matuƙar girgiza shi, dabara ce ta fado mashi da sauri ya sanya hannu ya cire gyalen danejo da take daure qugunta da shi, ya lullu6e fuskarsa, Idanunsa ne kadai suke a bude. Bayan isarsu joss, motar ta sauke su a tasha, driver yace ina kudin mota, sai lokacin ya tuna da baida ko sisi, sai dai kayan da fulanin nan suka bashi, hakuri ya bashi ya hada shi da katon dawon fura, mai motar baiyi gardama ba ya kar6a, ruko hannun danejo yayi suka soma tafiya atare har ya sama masu abun hawan da zai kaisu unguwar da su ke, kafin isar su tuni dare ya ritsa da su. Da farin cikinsa Ya zo unguwar, amma lokacin dayaga gidajensu a kulle, nan take murnar ta koma ciki, tunkafin ma yaji abunda ya faru hankalinsa yai mugun tashi, baisan ina zai tsoma kanshi ba, ga yar mutane da yake ta yawo da ita, harta fara yi mashi kukan yunwa take ji, tausayinta ne ya kama shi, da ya san hakan zata faru dabai yi kuskuran tafowa da ita ba.. A bun hawa ya kuma tsaida masu, suka nufi gidan uncle abdalla da ita don ya ga ko sun dawo daga south korea, tunkafin me abun hawan da ya kawo su ya sauke shi ya hango gate din gidan a kulle alamar basa nan, tamkar ya daura hannu aka ya fasa ihu haka yaji. Tunawa da amininsa muhsin wanda Angel ta ta6a sace ma matarsa waren takalmi yasa shi yanke shawarar zuwa gidan shi tare da danejo, yasan acanne zai ji komai daya faru bayan 6acewarsu Basu sha wahala ba, cikin sa'a suka same shi agida, tare da matar shi, lokacin dayaji sallamar taj a firgi ce ya mike zaune yana kallon kofar shigowa falon, bai gane shi ba har saida ya cire mayafin danejo dake akan fuskarsa tukunna ya shaida shi, muryarshi na rawa yace taj! Dama kana araye? Tsawon lokaci muna ta neman ku babu kai ba uzair duka an nemi ku an rasa"? A rude yake jefa mashi tambayoyin, matarshi da sauri ta nufi danejo ta ruko hannunta suka zauna kan sofa, kafin ta mike ta shiga ciki ta kawo masu abinci da ruwan shi. "Dan Allah abban muhsin kabarshi Ya huta, bakasan daga ina yake ba, sannan bakasan meya faru dashi! Idan har bai samu nutsuwa ba tayaya zai iya fayyace mana abunda ya faru da su"? Fuskarta a yamutse tayi maganar, jinjina kai yayi fuskarsa da tsantsar al'ajabi yace da taj su shiga ciki yayi wanka ya canza kayan jikin shi, yaga duk sun jigata kamar na almajirai, Bayan sun huta, sunci sun koshi, har bacci yayi itama danejo ta dan runtsa, wuraren karfe shabiyu na dare yafarka ya taras da muhsin ya zabga uban tagumi yana kallon shi, mamakine yacika shi. "Ka yi hakuri taj, kada kaga na takura maka, wallahi na damu da rashin ku, hankalina bazai ta6a kwanciya ba har sai ka fadamin meya faru da ku da har kuka gudu aka neme ku aka rasa......" Mikewa zaune taj yayi, kafin a tsanake ya labarta masa komai daya faru, wani irin matsanancin kuka mai cin rai muhsin ya fashe dashi, bakomai ya firgita shi ba ya kuma bashi tsoro face mutuwar amininsu uzair ta yi matuƙar girgiza shi, cikin shesshekar kuka ya ke fadin"taj dama abunda ya faru daku kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan wata irin masiface, Uzair ya mutu, Angel ta 6ace, rana ɗaya an tarwatsa farin cikin zuri'arku, in sha Allah sai Allah ya saka maku wannan zaluncin da akayi maku....."muhsin ya yi kuka tamkar ransa zai fita, Lallashinshi taj ya somayi yana fadin yayi hakuri komai ya riga daya wuce, yanzu shi damuwarshi ina aneelerh take matar uzair"? Daƙyar muhsin Ya samu nutsuwa, ya fara mashi labarin abunda Ya faru bayan 6acewarsu, Yaji dadin jin cewa Aneelerh tana agidan iyayenta, abun da ya faranta ranshi, Yaron da yaji ta haifa masu, tunkafin ma yaganshi Yaji Ya kamu da kaunarsa, kaunar da yake yima uzair gaba daya ta koma akan yaron da bai ta6a ganinsa ba......' acikin labarin da muhsin ya fada masa abu ɗayane bai sanar da shi ba, rasuwar iyayensa gudun kada zuciyarsa ta buga, kwara idan ya samu nutsuwa ya sanar dashi daga bisani. A daren ranar kafin muhsin yabar dakin taj, Sai da taj ya gargaɗesa akan kada ya sanar ma wani cewa yagansa saboda rayuwarsa tana acikin hatsari, idan mutanan da suka kashe uzair suka san da zaman shi tabbas zasu cigaba da bibiyarsa har sai sunga bayan shi. Cikin sanyin murya muhsin yace in sha Allah babu wanda zaiji zancen dawowarshi, zai rufa masa asiri yaci gaba da zama a gidansa har zuwa lokacin da Allah zai kawo mashi mafita.... Tsawon wata guda suna agidan muhsin, a cikin kwanakin da yayi baya iya runtsawa saboda damuwar rashin angel, duk daren Allah Sai yayi nafilfili saboda angel dinsa, duk ya fita hayyacinsa sam baya da koshin lafiya ciwon kafarsa tamkar ana fama masa shi abu yaƙi ci ya ƙi cinyewa, muhsin yaso ya bi shi suje asibiti a duba lafiyarshi gudun kada ya rasa ranshi amma yaki yarda saboda bayason wani yaga fuskarshi, ya ƙwammace idan ma mutuwarce ta dauke shi agidan muhsin zaifi mashi sauƙi akan wadannan azzaluman mutanan su kona shi. A daren wata rana ne, Yana cikin Yin nafilfilin dare, Yajiyo dirar motoci a cikin gidan muhsin, A firgice Ya mike daga kan darduma Gabansa na faduwa, baisan su wanene sukazo gidan muhsin ba, a irin wannan lokacin karfe kusan sha biyu na dare, zuciyarsa na bugawa ya nufi falon gidan don ganin su wanene, Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, ganin matasan samari masu jini ajika suna shigowa kowannansu sanye cikin shiga ta bakake kaya sun rufe fuskokinsu da facemask. Bakomai ne ya tsoratar da shi ba face tunawa da wadannan body guards din da suka budewa alhazawannan motocinsu, nan take ranshi ya bashi cewar sune, hakan na nufin muhsin Yaci amanarshi, bayan yayi mashi alkawarin zai rufa masa asiri shine yabi ta bayan fage ya tona masa asiri, zuciyarshi ajagule ya furta meyasa zaiyi min haka! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, tashin hankalin shi danejo kada suce zasu haɗa da ita su kashe... A lokacin zuciyarshi ta riga ta gama hasala, Jininsa akan akaifarsa yake, tunkararsu yayi muryarshi a fadace yace"kun biyo ni nan dinma donku kashe ni? Laifin me nayi maku ne? Da ɗaci aransa ya furta maganar, kamar daga sama yaji muryar muhsin daga bayan shi yana fadin"taj, ka tsaya zanyi maka bayani" a sukwane ya juya ya kalle shi a fusace yace"wani irin bayani zakayi min muhsin? haka mukayi dakai? ka cuce ni muhsin, ba zan ta6a yafe maka ba, yanzu dakai za'a hada baki don akashe ni"? Hawaye cike tab da idanunsa yayi maganar, fitowa danejo da matar mushin sukayi daga dakin duk suka tsaya suna kallon su.... Matasan da suka tsaya abakin kofar falon sun harɗe hannayensu akan kirjinshi suna kallon shi, babu alamun zasuyi magana.. "Taj bazan ta6a cin amanarka ba, abun da ya faru da kai ba kai ka ɗai ya shafa ba, hada ni kaina saboda ina jinka tamkar ɗan uwana na, waɗannan matasan da kake gani, ba su zo da niyar su cutar dakai ba, sai don su taimaki rayuwarka, Idan ka basu hadin kai in sha Allah zakuyi nasarar nemo Angel dinka data 6ata, bayan haka zasu tayaka daukar fansa akan mutanan da suka kashe uzair" "Har yanzu ban fahimci inda zancenka ya dosa ba .." murmushi muhsin yayi kafin yaci gaba da cewa"su ɗin jami'an hukumar ISOD ne, nasan ba zaka rasa sanin CHIEF OWAIS ba, ɗan gidan Sharafudeen Obinna......" wani irin al'ajabi ne ya kama tajudden muryarshi na rawa ya maimaita sunan Chief Owais da tsantsar mamaki yace"muhsin dagaske kake min ko wasa? Tayaya akai ma su kasan da zamana" Kafin muhsin Ya bashi amsar tambayarshi, Chief owais Ya shigo bakin shi dauke da sallama cikin shiga ta kakin isod, da sauri matasan nan suka buga kafa tare da sara mashi, muhsin kamar zaiyi mashi sujjada tsabar yadda yake washe baki yana yi mashi sannu da zuwa yalla6ai, shi dai taj ya gaza yarda da abunda idanunsa suke gane mashi, kai ko a mafarki bai ta6a tsammanin zai haɗu da chief owais ba, mutumin da a tv kadai yake iya ganinsa, sai gashi yau a zahiri Allah Ya nuna masa shi. Cike da qasaita, Chief Ya nuna masa sofa alamar Ya zauna" jiki na 6ari taj yaje ya zauna yana ta faman bin shi da kallo a lokacin shima ya zauna kan sofa din dake fuskantar ta shi. Cikin harshen turanci yace"nasan zaiyi wuya ace baka sanni ba, amma duk da haka zan gabatar maka da kaina, da farko sunana owais sharafudeen Obinna, chief na hukumar Isod...." ya faɗa tare da ɗan dakatawa yana dubansa, tun anan taj ya fahimci ba karamin mutunne bane mai ji da kansa. "Malam taj, kamar yadda kake mamakin ganina nima haka nake mamakin kasantuwana acikin rayuwarka, ko a mafarki ban ta6a tsammanin akwai ranar da zan hana idona bacci saboda damuwa da mutumin da bansan wanene shi ba...." kalaman chief owais sun girgiza shi matuƙa, har dai ya gaza jure wa yace"dan Allah ka fadamin meyasa ka damu dani bayan baka sanni ba" da buɗar bakinsa sai cewa yai"ƴarka ce sila" waro idanu waje taj yayi da tsantsar mamaki yake binsa da kallo fuskarsa da rudani yace"meyasa kace haka"? Numfasawa yayi kafin ya soma magana muryarshi tamkar ana busa sarewa saboda dadin sauraranta.... A washe garin ranar dana dawo Nigeria daga U.S anyi min wani kira da ya tsaya min araina.... Fitowa yayi daga cikin bathroom waist dinsa daure da towel, yayin da dayan hannunsa ke a ruke da wani short towel yana tsane sumar kanshi, a gaban dressing mirror ya tsaya da niyar ya gyara jikin shi, wayarsa dake akan nightstand ta soma ringing, dakatawa yayi da tsane sumar kan da yakeyi a hankali ya nufi wayar ya dauko ta yana duba number din da aka kirasa da ita, yayi mamakin ganin bakuwar number, A matsayin shi na jami'in sirri komai nasu asirrince suke yin shi, harta phone number dinsa special ce, bakowa yasan shi da ita ba, sai mutun yakai yake samun damar mallakar ta, bai yi niyar picking call din ba saboda a ka'idarsa baya ɗaga bakuwar number, ko kiransa akayi indai ba family dinsa bane to baya picking sai anfara neman iznin yin magana da shi...... Amma a lokaci sai zuciyarsa ta kwallafa rai akan son sanin wanene ke kiransa... Baisan sa'adda Ya danna answer call ba, ko da yai picking ya kara phone din a kunnansa shiru yayi baice komai ba tsabar miskilancinsa jira yake yaji wani isasshen ne ya kira shi batare da iznin shi ba. Lamarin ya daure masa kai jin anyi shiru ba'ayi mashi magana ba, ko wanene wannan mai karfin halin? Har zaiyi rejecting call din sai kuma Ya fasa calmly ya furta "who is on the line"? Sautin muryar karamar yarinya yaji ta ratsa kunnansa "Angel ce," Yayi mamakin jin muryar karamar yarinya, aransa ya ayyana ko yar wacece ta kirasa, "kinsan dawa kike magana"? "a'a," ta bashi amsa atakaice "Ur age"? "7yrs" voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'? "Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya" Murmushin gefen fuska yadan saki har dimple dinsa ya lotsa, don ya fahimci ba'asan ta dauki wayar ba, tun daga kan muryarta ya gane irin yaran nan ne masu tsiwa "Can i call u video"? Da sauri tace eh, Nan take ya mayar da kiran Video call, da sauri ya sanya yatsan hannunsa ya rufe front camera din wayar saboda baison taga fuskarshi, baisan ko tarko aka ɗana masa da ita ba, lokacin da fuskar Angel ta bayyana akan faskeken screen din wayarsa wani irin bugu zuciyarsa tayi, bai yi tsammanin zai ganta kyakkyawa ba, fara sol ga manyan idanu launin gray dara dara da su, gaba ɗaya ya kasa kyafta idanunsa daka kallon fuskar ta, a sukwane ya koma gefen gadon shi ya zauna yana ci gaba da kallon ta... "I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale masa ido, murmushi yasaki yana kallon ƙananun la66anta tausasan gaske launin pink, chief Ya shagala da kallonta, tamkar a mafarki yake bin fuskarta da kallon ƙurulla kamar zai haɗiyeta, A can 6angaran Angel taji shiru ba'ayi mata magana ba, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, batasan cewa shine ya toshe front camera din wayarsa don kada tagansa, da sauri yayi screenshort din fuskarta ba tare da sanin ta ba... Zuciyarsa ba ƙaramin sosuwa tayi ba, ganin tayi rejecting call din, sam bai gaji da kallonta ba, da wata irin kasala ya kwantar da kansa bisa pillow, Ya bude hotonta yaci gaba da kallon fuskarta.... Baiyi tunanin kiran layin ba, haka ya wuni da tunaninta aranshi, tsawon kwana uku baya iya bacci batare daya kalli hoton fuskarta ba, sometimes a rungume da wayarsa yake kwana, sai da takaiga harta daddynsa da mommynsa sunsan da hoton yarinyar daya kwallafa rai akai, mahafinsa ne Ya bashi shawarar Ya nemo ta idan hakan zai kwantar masa da hankalinsa, Ya ji dadin shawarar daddynsa, maimakon ya tuntu6i layin tajuddeen kaitsaye su yi magana da shi, sai ya fara bincike ta hanyar amfani da phone number din da Angel ta kira da shi, anan ya sami bayanan taj hada shafukansa na social media da yake amfani da su wurin yaɗa aikinsu na ƴan jarida, cikin sa'a ya gano address din gidan radion da taj yake aiki, bai samu damar zuwa joss ba saboda kiran gaggawa da akayi masa tafiya ce ta kama shi zai bar kasar ba don yaso ba. Gaba ɗaya ya tattara komai ya damka a hannun Big guy, wanda ya kasance ɗaya daga cikin na hannun damansa, amintattunsa, Ya fada masa komai dangane da yarinyar data kirasa a wayar sannan yace mashi yana son yaje har can joss din Ya bincika mashi inda suke rayuwa, saboda yana son sanin komai dangane da ita........ Atakaice big guy shine mutumin da ya siya ma angel piano da kayan zane, a ranar da sukaje kasuwa da su taj ta sanya masu rigima sai ansiya mata su gashi basu da kudi, ashe shine ke bi biyarsu duk wani motsinsu akan idanunsa, chief shine ya bada umarnin komai suke bukata yayi masu shi sannan bayaso su san cewa shine yake bibiyarsu har zuwa lokacin da zai dawo kasar. Duk wani abu da unaisah tayi sai big guy ya turama Cheif ta wayarshi, hakan ba karamin dadi yake yi mashi ba .... Kafin chief ya dawo Nigeria wannan tsautsayin ya ritsa da su tajuddeen wanda yayi silar 6acewarsu, hankalin big guy ba karamin tashi yayi ba, lokacin da labarin ya riske shi, har sai da yaji fargaban sanar da chief saboda yasan yadda ya ƙwalla fa rai akan kaunar yarinyar, gashi saura kwanaki kalilan ya rage mashi ya shigo nigeria, Yaci burin haduwa da ita tare da mahaifinta, Allah bai nufa ba . ... Dakyar Big guy ya sanar da shi abunda ke faruwa na 6acewarsu, tsabar tashin hankalin daya fuskanta na jin mummunan labarin har zazza6i sai da yayi, duk da haka bai karaya ba, yabar komai nashi, ya dawo nigeria bai sauka a abuja ba, kaitsaye ya sauka a joss, big guy ne yaje tarbo su a airport, tare da jami'ansu dayazo da su... A katafaren gidan da big guy din yake da zama suka sauka, dama chief ne ya biya kudin gidan a lokacin daya tura shi neman gidan su Angel. Kwana uku da zaman su agidan kafin suka fara nasu binciken, basu tsaya bata lokaci ba suka nemi alfarmar Inspector General of CID da ya damka masu case din su tajudeen a hannun su, tuni suka amince masu saboda sunsan hukumarsu ta musammance, duk wasu bayanai nasu tajudeen saida suka tura ma chief hada makullan gidajensu da suka kar6a. Muhsin yana ɗaya daga cikin wadanda jami'an isod suka tuntu6a har gida suka kai mashi ziyara don jin cewa shi ɗayane daga cikin aminnan tajuddeen bayan sunyi mashi tambayoyi ya amsa masu wanda ya sani sai kuma sukace mashi ko bayan tafiyarsu idan yaji ɗuriyar tajudeen ko abokinsa uzair yayi gaggawar sanar da su, saboda sunsan zasu iya tuntubarsa tun da shi amininsu ne, contact dinsu suka bashi kafin sukayi mashi sallama kun ji yadda akai har muhsin ya samu damar sanar da jami'an isod zancen zuwan tajuddeen ba tare da shi taj din Ya sani ba, saboda ya fahimci baya son kowa yasan da zamansa, shiyasa bai sanar da shi dangane da jami'an isod dake nemansa ba... Bayan chief owais ya kammala bashi labarin, saukko yayi daga kan sofa din Ya zube saman gwiwowinsa hawaye nata sintiri akan fuskarshi cikin sanyin murya yace"dama angel itace silar da kasan da zamana"? Muryarsa na rawa ya furta maganar, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba, dama zuciyarsa a raunace take, "Allah sarki angel, ashe da rabon wata rana rashin jin ki ya yi min amfani...." kasa karasa maganar yayi, Da sauri chief ya ruko hannunsa acikin nashi, cikin sanyin murya yace"ka yi hakuri, ni banzo don na fama maka raunin dake acikin zuciyarka ba, nazo ne don na tallafi rayuwarka, idan har ka bani hadin kai nayi maka alkawarin zan yi iyakar bakin kokarina don ganin na baka kariya, na kuma tallafa maka da duk abunda nake da shi, Allah shine Ya hadani dakai ta silar yarka, Ina jinta tamkar kanwata, muhsin Ya sanar dani komai dangane da abun da ya faru dakai wanda yai silar bacewarku, in sha Allah mutanan da suka yi maku wannan aika aikar sai sunyi danasanin kasantuwarsu a doron duniyarnan......." kwantar masa da hankali chief ya cigaba da yi har saida yaga ya fara samun nutsuwa tukunna yace mashi zai jira ya yanke shawara...." ai tunkafin ya karasa maganar taj yace mashi ya amince, zai basu hadin kai, babu wata shawara da zaiyi, saboda shi bashi da mafita kwara su tallafa masa ya nemo yarsa..... Sunji dadin yadda taj ya amince masu batare da 6ata lokaci ba chief, Yace mashi su fara shiri zasu tafi abuja tare da shi, saboda Yana so ya sama masa muhallin da zai zauna akusa dashi sannan yace zai sama masa gurbi a hukumar su ta Isod bayan ya kar6i training dinsu, bayan tafiyarsu tajudeen abuja, rayuwarshi ta sauya, chief owais ya gatanta shi, a cikin gidansa ya ware masa part ɗaya, inda zai zauna tare da danejo bayan haka ya bashi kyautar mota, cin su da suturarsu gaba ɗaya shine yake daukar nauyin su, Kafin taj Ya fara kar6ar training din Isod sai da yafara auran danejo saboda yana son su ƙara kusanci da juna, bayason tayi kewar rashin wani nata. Big guy shi ne mutumin da ya shiga gidan Uzair, aranar da Aneelerh taje gidan har ya ɗauke mata baby junaid, bayan haka sune jami'an sirrin da suka kaita gidansu har su ka yi mata tambayoyi da suka shafi 6acewar su Angel. Sauke numfashi yayi bayan ya gama basu labarin cikin sanyin murya yace _"Kunji yadda akai na tsira daga hannun mutanan da suka so rabani da rayuwana, hakika cheif yayi min halaccin da bazan ta6a mantawa ba, ya kyautata min, ya faranta min a lokacin da gwiwata ta sage na fidda rai da rayuwar duniyar nan, badan Allah ya ƙaddarar haduwata dashi ba, da yanzu bansan awani hali zan tsinci kaina ba"_ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*Buy bestselling books online 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 17 Complete by Novels Elite Admin June 09, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋✊~*_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘Best gifts for your loved ones An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ Shessheƙar kukan su ta cika ɗakin, babu mai lallashin wani a cikin su, tsananin tausayin taj ne ya kamasu jin irin kalubalen da ya fuskanta, A hankali unaisah ta ɗaura tafukan hannayenta dake kerma kan fuskarshi ta share mashi hawayen shi, cikin sanyin murya tace"daddy, ka yi haƙuri, ka daina zubar da hawayenka, bana son ganin su, kallonta yai da rinannun idanunsa muryarsa na ɗan rawa yace"My Angel, ni nawa ƙaluban dana fuskanta bakomai bane akan naku! Ku ne kuka ga rayuwa, ku yakamata a jajanta mawa, a kuma tausayama rayuwarku....." gaba ɗaya hankulansu Sajeed na akanshi, da ruɗani unaisah tace"daddy, kasan abun da ya faru dani bayan na gudu daga rugar su danejo"? Lumshe idanunsa yai hawaye na sintiri ya ɗan jinjina kanshi kafin ya motsa la66ansa"na san abun da ya faru dangane da rayuwar kullan da ku ka yi a GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, da kuma irin baƙar izayar da suke yi maku, ranar da mu ka fara ji daga ni har chief duk irin juriyarmu sai da muka zubar da hawayen mu saboda abun ya ɗaga hankulanmu, ya razanar da mu, bazan iya misalta maku halin da muka shiga a lokacin da muka ji labarin abun da ake aikatawa a GIDAN KURKUKUN ƘADDARA. Kallon kallo Su Naufal suka soma jifar junansu da shi idanuwan kowannansu sunyi jawur da su, saboda kukan da suka sha, bakomaine yasa su kallon juna ba face mamakin yadda akai daddyn Angel Yasan abun da ake aikatawa agidan kurkukun ƙaddara, Unaisah ce kadai batai mamaki ba saboda tasan dama sun sani watakil abakin salsabeel suka ji komai. Murya na rawa Batool Tace"daddy dama kunsani? Meyasa baku kawo mana dauki ba? Kunsan kuwa irin ƙuntatar rayuwar kullan da mukayi a gidan kurkukun ƙaddara? Ta fada hawaye masu ɗumi suna sintiri akan kuncin ta, muryarsa a raunace ya furta"mu kan mu ba mu jima da sani ba, da ace tuntuni mun san da zaman ku da har rayukanmu zamu iya sadaukarwa don mu ceto rayuwarku" Ummin dake kallon batool jikin ta har tsuma yakeyi saboda tsabar ƙagara da son jin tarihin rayuwarsu babban burinta taji menene ma'anar gidan kurkukun ƙaddara da taji sunata ambato a bakunansu. Jan numfashi batool tayi kafin ta ɗaura da cewa"mun rayu tun kafin mu mallaki hankulanmu, bamu ta6a ganin hasken rana ba, babu shige babu fuce, a ɗaki ɗaya muke a kulle, kullum cikin uniform ɗaya, abinci sau ɗaya arana, bamusan dadin rayuwar duniyar nan ba, duk wani hakkinmu na rayuwa an tauye mana shi, mu bamu san dadin iyaye ba, sannan babu mai jin kukanmu, balle a kawo mana dauki, anjuye mana tunaninmu balle musan cewa muma mutane ne masu ƴan ci kamar kowa.... ..." bata ƙarasa maganarba saboda kukan daya tokare makoshinta, tamkar zatayi kakarin amai. Cikin karyayyar murya Unaisah tace"tsohuwa tamira ta ta6a fada min cewa na jininmu ne kadai zai Iya sadaukar damu, har yau nagaza yarda da maganar nan, Ina kokwanton tayaya za'ay iyayen da su ka yi silar zuwanka duniya ko wani naka ya sadaukar dakai inda za'a azabtar da rayuwarka? Daddy wanene ya sadaukar dani❓ A matuƙar ruɗe ta jefa mashi tambayar tana kallon shi. Cikin sanyin murya yace"unaisah ni kaina a rude nake, bansan wa zan zarga ba Allah shine yasan wanene mugun da yayi maki wannan aika aikar" Muryar ummi araunace tace"dan Allah ku fahintar dani, tun ɗazu inata magana kunki bani amsa! Inaso naji meya faru da ku? Sannan Ina ne GIDAN KURKUKUN ƘADDARA"!? Daƙyar Unaisah ta lallashi zuciyarta dake yi mata radadi, kafin ta ɗaura idanunta akan fuskar ummi"zan fada maki komai da kikeson ji aunty ummi" A hankali ummi ke kallon fuskar unaisah Lokacin da tafara bata labarin rayuwarsu wata irin zuface ta soma wanke fuskar ummi, jikinta ya hau yin kakarwa saboda razanar da tayi, ko a mafarki bata ta6a jin labari mai matuƙar firgitarwa irin wannan ba tuni hawaye sun soma yar tseral kan kuncinta. Abunda yafi tsaya mata arai cikin labarin da Unaisah ta bata shine mutuwar Unaizah yar gidan daddy, ba ita ba harta taj Jikin shi Ya gama mutuwa saboda bakomai suka sani ba dangane da rayuwarsu saida unaisah tafara basu labari, chief dake atsaye bakin door yana sauraron su kasa jurewa yayi, wani irin jiri jiri Yake gani acikin idanunsa, zuciyarsa har wani tafarfasa take yi tamkar zata kone kanta tsabar 6acin rai da fusata, jijiyoyin wuyansa tuni sun fito rudu rudu kan goshinsa, juyawa yai da sauri Yabar kofar dakin, A hanzarce big guy yabi bayansa gudun kada zuciya ta debe shi Ya je yai ma kanshi Illa. Zuciyar ummi dake hauhawa tana harbawa da wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali tama rasa ina zata jefa kanta taji dadi gaba ɗaya taji ta tsani rayuwar duniya, Hakika Labarin su Unaiza Ya karya mata zuciya, ya ƙara mata karfin imani sai yanzu ta gane babban kuskuran da tayi nagaza daukar ƙaddarar rayuwarta, cikin shesshekar kuka mai haɗe da gunjin kuka ta furta "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! Wannan wata irin musibace? Ku fadamin Tayaya akai har kuka Iya jure wannan ukubar da ƙananun shekarun ku batare da zuciyoyinku sun buga ba? La66anta na kerma ta fada tana dubansu kafin taci gaba da cewa "Zuciyata tagaza yarda da abun da kunnuwana suke jiye min! hankalina Ya tashi! Zuciyata ta karaya! Wannan wani irin zaluncine? Su wanene wadannan Fasikan mutanan mugaye azzulamai marasa imani da tausayi, wadanda basu ɗauki ran dan adam abakin komai ba, wai su wanene su dan uban su? Wasu irin dabbobine su jahilai, Masu matattar zuciya, Anya kuwa suna da zuciya a kirjinsu? Anya kuwa mutanene su kamar kowa? Ina kokwanto akansu..." gaba daya ummi ta burkice masu sambatu kawai takeyi kamar sabon kamu ahauka, da alama abun ya razana kwakwalwarta. Rashin imanin da akai ma yaran ya ɗaga hankalin ta, fashewa ta kuma yi da kuka kafin taci gaba da fadin"sun manta cewa zasu mutu su koma ga Allah? Wai su basa tunanin makomar su ne? Duniya kaɗai suka sa agaba, ko Sun manta cewa duk wani abu da suka mallaka aduniyar nan zasu barshi? Daga su sai halin su za'a binne su!?...." ɗaya bayan ɗaya take kallon su jemimah dake ta kuka aranta ta ayyana yanzu gaba dayansu nan an lalata rayuwarsu har da yan ƙananan cikin su wani irin yunkurin amai ne yazo mata da gudun gaske ta mike ta fuce daga dakin, Har batool ta yunkura zata bita taj yai saurin ruƙe hannunta, "ku barta tayi kuka ta hakanne zata samu saukin abunda take ji aranta" jiki asanyaye batool ta zauna. Shi kanshi bazai Iya misalta irin kunar da zuciyarshi take yi mashi ba Cikin muryar lallashi Yace da su"Idan na ce kuyi hakuri kamar na cuce ku ne, saidai ba yadda zakuyi hakurin nan dai shine yakamace ku, Allah Baya barin hakkin wani akan wani, wadanda suka azabtar da rayuwarku In sha Allah za su ga mummunar sakayyar da Allah zai masu tun agidan duniya zasu fara ɗanɗana kudarsu kafin su koma ga mahaliccinsu su fuskanci makomarsu......." daƙyar Ya samu ya shawo kansu, kafin ya bi su daya bayan daya yayi huggin dinsu duk don ya kwantar masu da hankalin su, sai da ya tabbatar ya share masu hawayensu tukunna yace "Dan Allah kada ku sanya damuwa aranku, ku kwantar da hankulanku in sha Allah komai yakusa zuwa karshe, yanzu ku koma dakunanku ku yi wanka ku kwanta ku huta, nasan baza a rasa masu fama da ciwon kai a cikin ku ba, zanyi magana akawo maku breakfast har bedroom dinku" muryoyin su adisashe suka amsa mashi da toh, kafin suka mike kamar wadanda aka zarewa laka haka suka nufi kofar dakin suka fuce. Bayan fitarsu Ya rage daga Unaisah sai batool sai kuma Taj, Mikewa batool tayi jikinta tamkar na wadda tayi zazza6i ganin ta nufi kofar dakinne Yasa taj yi mata magana"Ina zaki je ne"? "Ɗakin Aunty Ummi" amsa mata yai da okey, bayan ta fuce ya maida dubanshi ga unaisah, janyota yai tare da kwantar mata da kanta kan kirjinsa hannunsa akan kafadarta "Ina fata yanzu babu abunda ke maki ciwo"? muryarta kasa kasa tace"eh daddy," Da yar zolaya yace mata"ya rashin ji ko da yake naga kin daina Yanzu"? ƙara shige mashi tayi tana yar dariya, bubbuga bayanta yai da hannunshi, kafin ya janyeta, ya mike kan gwiwowinsa ya fuskanci alkibla yakai goshinsa kasa yai sujjada murmushi tasaki tana kallon shi, da sauri itama tayi sujjadar kamar yadda yayi, tsawon mintuna kafin suka dago da kansu fuskar kowan nan su dauke da annurin farin ciki "Daddy fada min me ka ce acikin sujjadarka" Numfasawa yai kafin yace"nayima Allah godiyane da ya bayyanar min da ke da ranki da lafiyarki" "Nima haka" murmushi suka kuma saki gaba dayansu, "Daddy Inaso na tambayeka, tayaya akai ku ka hadu da su salsabeel? Ko ya fada maku yadda akai suma suka ku6uta daga kurkukun ƙaddara"? Shiru ya ɗanyi kafin yace"ki bari idan yazo sai ki ji daga bakin shi, yanzu nafiso ki kara samun kwanciyar hankali" amsa mashi tayi da toh "ki tashi mu shiga toilet ki wanke fuskarki kizo mu ci abinci" Ya fada tare da ruko hannunta suka shiga toilet, bayan sun wanke fuskokin su suka fito atare A gefen gado suka zauna Ya bude masu abincin tray din da suka ajiye kan table Cikin kulawa yake bata abinci abaki tana ci, tsabar dadi kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, wai yau gata ga daddynta "Daddy, Ina aunty Aneelerh da babynta"? Murmushi Yasaki kafin Yace"suna nan cikin koshin lafiya, kwanakin baya nabibiyi layin wayarta amma ba'a ɗaga ba sai wata rana dana ci sa'a aka daga wayar kinsan wanene ya daga" girgiza mashi kai tay alamar a'a yana murmushi yace"ƙaninki baby junaid," waro idanu waje tayi da tsantsar farin ciki tace"daddy sunan shi junaid" daga mata kai yai alamar eh "baki ga yaron ba kyakkyawa dashi, ga wayau sai ma in yana surutu.." cike da zumudi tace"daddy inason ganin shi tare da aunty aneelerh, dan Allah ka kaini wurin su nayi missing dinta" "Zan kaiki in sha Allah, amma ba yanzu ba, ki ɗan ƙara hakuri" tur6une mashi fuska tayi, bakinta cunkushe da abincin daya tura mata, yar dariya yai tunawa da kuruciyarta. "Banji kin tambayeni danejo ba"! Sakin fuskarta tay, "tana araina daddy, bazan ta6a mantawa da halaccinta agareni ba, ni dai ba abun da zance sai dai inyiwa Allah godiya saboda Ya hadani da mutanan kirki masu sona tsakani da Allah' ta fada fukarta da ɗan murmushi, "Yaushe zaka kaini Wurinta in ganta"? "Ko zuwa anjima idan kika kara jin sauki sai muje ko"? Daga mashi kai tay alamar eh. Shiru suka dan yi kafin ta kuma cewa"daddy mommy adama fa? da uncle abdallah!! Suna nan suma"? Daga mata kai yai alamar eh, "Alhamdulillah Ya Allah" ta furta da matsanancin farin ciki, ashe da rabon in sake ganin yan uwana. "Ina granny ɗina da sauran mutanan buzaye" Jiki asanyaye ya ajiye cokalin dake a hannun shi, nan take ta fahimci babu lafiya, muryarta adan rude tace"daddy menene"? Cikin sanyin murya yace"unaisah sun riga mu gidan gaskiya, mahaifina da mahaifiyata, da kuma kakata kusan duk a lokaci ɗaya suka rasa rayukansu nima sai daga baya naji labari..." Cikin sanyin murya tace"ubangiji Allah Yajikansu ya gafarta masu, Allah ya jaddada rahama agare su..." amsa mata yayi da ameen Shiru suka danyi na wani lokaci batare da ya cigaba da bata abincin ba So take ta tambaye shi dangane da mahaifiyarta sai dai takasa saboda zuciyarta taki bata hadin kai, Har yanzu bata daina jin ɗacin radadin abun da tayi mata ba, ta tsani mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan, tana son ta haɗu da ita ba don komai ba sai don taji dalilin dayasa ta yi watsi da ita, idan ba ta son ta meyasa ta haife ta❓ *HAJJATY 💋* A zaune take gaban dressing mirror, fuskarta dauke da murmushi bakomai take tunawa ba face fuskar Naufal, ta kasa mantawa da shi, Yaron ya kwanta mata aranta, daren jiya data kwanta bacci har mafarkinsa tayi, da alama bata jima da fitowa daga wanka ba, duba da towel din dake daure a chest dinta Tun dazu takasa tabuka komai gaba daya ta shagala da tunanin naufal, ta ƙosa pravin ya shigo donta nuna mashi hoton naufal tasan zaiyi mamakin ganin me kama da ita. Wayar ta dake ajiye kan mirror din ta dauka ta budo hoton shi tana kallo har zooming din fuskarsa take yi Jin motsin shigowar mutun yasa tayi saurin juyawa don ganin wanene Pravin ne ya shigo sanye da farar jallabiya, fuskarshi babu annuri ko miskala zarratin kamar wanda aka fada ma sakon mutuwarsa Sam bata lura da yanayin shi ba, cike da zumudi ta mike ta nufe shi tana fadin"honey, ina ka shiga tun jiya bansaka a idanuna ba"? Fadawa tayi kan kirkinsa tai huggin nasa kafin ta ɗago da fara'arta tace"ka yi shiru baka ce min komai ba"? Wani kallo ya soma jefa mata mai kama da harara, da alama ta manta abunda tayi mashi jiya shiyasa ta zaƙe tana shige mashi Ganin baida alamun yi mata maganane yasa tace"fadamin baby, ko dai hajiya saratu ce ta 6ata maka rai"? Banza yai da ita baice uffan ba.. Murmushi tadan saki"nasan itace ta bata maka rai, bari na nuna maka wani abu nasan zakayi farin ciki idan ka ganshi" ta fada da sauri ta nufi mirror Goya hannayensa yai akan kirjinsa yana jiran karasowarta. "Baby, duba ka gani, jiya a wurin taro bayan tafiyarka naga wannan yaron mai kama da ɗan mu Naufal kyakkyawan gaske" cikin annushuwa ta mika mashi wayar don ya kar6a ya gani, rai amatuƙar 6ace yakai ma wayar bahagon naushi tayi sama ta ƙundumo kan tiles ta bada wani sauti mai karfi. idanunta azazzare ta dago tana kallon shi, Huci yake yi tamkar mayunwacin zaki Ya furta"kin manta abunda ki kai min jiya"? Dafe kai tayi da hannu daya idanunta tuni sun cuko tab da kwalla, ranta abace tace"pravin! Meyasa zaka jefar min da wayata? Laifin me nayi maka? Saboda kawai naki bin umarninka? Wai meke damunka ne pravin? Agaban mutane fa ka ruko hannuna kaja ni zaka fitar dani daga hall tayaya bazan ki binka ba? Ko so kake afara zargin mu ? Kafin ta ƙare maganar Ya daka mata tsawar data firgitar da ita, nuna ta yai da yatsan hannun shi"yi min shiru! Bana son jin komai daga gare ki, ashe harni ban isa in baki umarni ki bi ba! Hankalin ki ya kwanta Kin kunyata ni a idon jama'a..." hawayene suka soma sintiri akan fuskarta, muryarta na rawa tace"pravin ka fahimce ni mana, kasan bazan ta6a kin bin umarnin ka ba, hakanan batare da kwakkwarar hujja ba! Ni nayi hakanne saboda bana so wani ya tuhume mu..." yatsansa ya daura kan la66anta, shiru tayi tana kallon shi Can kuma ta fashe da kuka tasa hannu ta ture yatsan nasa tana fadin"baka kyauta min ba, Tun jiya nake zumudin in nuna maka hoton sajeed Yaron dake kama da danmu amma shine ka fasa min waya..."? Ta6e la66ansa yai kafin ya furta"ki yi hakuri rainane ya 6aci, " ya fada tare da zukunnawa ya dauki wayar yana fadin"zan siya maki wata" "bana so, ni dai ka gyaramin tawa, saboda bana son na rasa hoton sajeed" Harara ya watsa mata tareda cewa"meye alakarki da shi ne? Kawai daga ganin yaro yana kama dake? Mutun nawa kika sani suna da masu kama dasu a duniya? Kamar kanki farau" "Ni wannan bai dameni ba, Ina son shi saboda inajin shi kamar ɗana dana rasa" Rai a6ace ta fada kafin ta juya ta koma kan gado ta zauna, tana cigaba da matsar kwalla Murmushin gefen fuska pravin yasaki Yana dubanta, Komawa gefenta yai ya zauna bayan ya ajiye wayar ya ruko hannunta acikin nashi "Look, bana so ki sanya damuwa aranki, idan har rashin naufal ne ke damunki, nayi maki alkawarin nan bada jimawa ba zaki haifi wani babyn, sai ki sanya mashi sunan naufal din" Wani kallo ta jefa mashi batare da tace mashi ƙala ba, lallashinta Yacigaba dayi duk don ya samu yashawo kanta. HAJIYA SARATU _safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abunda Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanuƙarta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu ƙwarin gwiwar yi mata haka? ruƙe qugu tayi da hannu ɗaya fuskarta babu annuri_ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 18 Complete by Novels Elite Admin June 12, 2024 Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ __________________________✍️ 💫HAJIYA SARATU💫 _safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abun da Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanuƙarta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu ƙwarin gwiwar yi mata haka? ruƙe qugu tayi da hannu ɗaya fuskarta babu annuri_ Maganganun da suka Tattauna jiya ita da su Har excellency ta soma tariyo bayan fitowarsu daga hall kafin su nufi gidan prime minister. "Meyesa pravin zai ja hannunta abainar jama'a? Menene alakarsu? Wai ku ba ku zargin wani abu atsakanin su"? Hajiya laurace ta fada babu wasa akan fuskarta "Najima ina zargin matar nan, na dai yi shiru ne ban fada maki ba, saboda bana so in shiga tsakanin ki da mijin ki, amma ni kwata kwata hankalina bai kwanta da ita ba, tun daga kan yanayin yadda take daukar wanka zaki fahince akwai wata a kasa ba banza ba, ni ay ban ta6a ganin yar aikin da ta samun ƴanci kamar hajjaty ba"! Her excellency muhibbat ce tai maganar, Hajiya jamila tace"yanzu wani hukunci zaki yi masu"? ta fada tana kallon hajiya saratu. Da sauri Hajiya madina tace"please, ku daina tunzurata ku bar ta taji da abun da ke damunta, ni banga abun ɗaga hankali a maganar nan ba!" Hajiya saratu da ke sauraronsu ɗaya bayan ɗaya sai da ta cika ta batse kafin tace "Wallahi bazan ƙyalesu ba! Daga ita har shi sai sun fuskanci 6acin raina, sai tayi danasanin kasantuwarta yar aiki a gidan nan"! Ta fada a tsiwace tana huci "Ni shawarar da zan baki kawai ki kore ta daga gidan ta koma can kasarsu acigaba da bautar shanu, idan ba haka ba Allah kaɗai yasan munaƙisar da take shirya maki, ƙwara tun wuri ki yi maganinta kafin ta jaza maki matsala" Acewar hajiya Muhibbat Dafa kafaɗarta hajiya laurat tayi"idan da zaki bi shawarata kada ki tanka masu! Nasan yanzu hankulansu atashe yake saboda sun san dole ki tuhume su, abun da yakamata ki yi shine ki manta da zancen hukunta su, ki yi tamkar babu abun da ya faru, za su yi zaton kin kyale su ne, ki bari sai sun shagala tukunna ke kuma ki fara bincike akan su, ta haka ne kadai zakisan meke atsakanin su amma yanzu idan kikace zaki hukuntasu to ba za ki san menene alakarsu ba, kwara ki fara bin diddiginsu har zuwa lokacin da zakiyi nasarar kama su dumu dumu" Jinjina kai hajiya saratu tay alamar gamsuwa da shawarar Hajiya laurat.. Bayan ta dawo daga duniyar tunanin taja gauran Numfasawa haɗi da ɗan jinjina kanta, cikin takun sauri ta nufi wayarta dake ajiye kan pillow ta dauka ta kira landline na kitchen. Tana fara ringing akayi picking, kara wayar tai a kunnanta. "Inason ganin Marwa, ta same ni adaki bana son bata lokaci" ta fada tare da katse kiran ta ajiye wayar Cigaba da zagaye bedroom din tayi, yayin da take dunkule tafin hannunta na dama tana tura shi ana hagu kamar ƴar dambe. Knocking kofar da akayi mata ne yasa ta dakata. "Wanene"? "Aunty ni ce marwa" "Okey shigo ciki" Turo kofar tayi, Jikinta sanye da uniform na ma'aikatan gidan ta shigo, cikin girmamawa ta gaishe da hajiya saratu, bata amsa mata ba, sai tay tamkar ba ta ji me tace ba. Tuni marwa ta sha jinin jikin ta, tsoranta kada ace wani laifin ta aikata da yasa hajiya saratu ta kira ta don tasan halinta masifaffiya ce. Muryarta na rawa tace"Am.. Aunty gani, naji kina nemana" Wurga mata harara hajiya saratu tayi da sauri ta dukar da kanta kasa Tsawon lokaci bata tanka mata ba, gani ta ke kamar zubda ajine ta nemi taimakon yar aiki, sai dai ba yadda zata yi itace kadai hanya mafi sauki agareta. Zama tayi gefen gadonta, cike da isa ta dubi marwa"ke zonan"! da sauri marwa ta dawo ta zukunna agabanta. "Wani aiki nakeso kiyi min, bana so kowa ya sani daga ni sai ke! Na yaba da hankalin ki ne shiyasa na za6e ki saboda nasan zaki Iya......" Tun da tafara magana marwa ta soma zare idanunta cike da fargaba. "Kafin na faɗa maki, zan gindaya maki sharadi, Idan har na kuskura naji maganar nan abakin wani, ko kika bani matsala wallahi thumma tallahi na lahira sai yafi ki jin dadi...." Wani irin yawu marwa ta haɗiya jiki na bari tace"in sha Allah zan kiyaye." Ta6e baki tayi kafin ta ɗaura da cewa" me kika sani dangane da head maid din gidan nan? ya mu'amalarta daku take? Sannan Wacece aminiyarta acikin ku? Shin tana fada maku sirrinta"? Shiru marwa tayi aranta ta ayyana to fa! Ko me hajjaty ta aikata ma aunty masifatu da take neman karin bayani dangane da ita? Watakil watan cin ubanta ne ya tsaya A fili kuma tace "Abun da nasani dangane da ita, macace mai saukin kai, tana da mutunci kuma tana kyautata mana, ba ta shiga sabgarmu, sannan bata cika zama yin fira da mu ba, macece mai kamun kai bata da surutu, sannan bata da aminiya acikin mu balle har wani yasan sirrinta, wannan shine Iya abunda sani" Tur6une fuska hajiya saratu tayi, ita ba haka taso taji daga bakin Marwa ba. "Okey, ki nutsu ki saurareni," jinjina mata kai tai "Daga yau inaso ki fara shisshige mata, saboda ina zarginta, inason kisan duk wani sirrinta, ki zama aminiyarta, bayan haka duk wani motsinta ya kasance a tafin hannunki, idan har kikaga wani abu ba dai dai ba, to kiyi hanzarin sanar dani," amsa mata tayi da toh "Idan har na samu abun da nakeso nayi maki alkawarin zan baki mukamin da take da shi agidan nan, bayan haka zanyi maki kyauta ta musamman, kin dai san wacece ni, basai nayi maki bayani ba" Wani irin farin cikine Ya lullu6e marwa musamman da taji Hajiya saratu ta ambaci zata bata mukamin hajjaty ga kuma kyautar da zata samu, aranta ta ƙudiri aniyar saita yi ma hajjaty kutse koda kuwa bata kama ta da laifin komai ba, ita zata ƙala mata sharrin da za'a sauke ta daga kan mukaminta. Shu'umin murmushin gefen fuska tasaki. "Baki da matsala dani aunty, in sha Allah zaki samu abunda kikeso" "Zaki iya tafiya" mikewa marwa tayi zuciyarta cike fal da murna, dama ta jima tana jin haushin hajjaty saboda yadda tayi masu zarra agidan, komai itace akan gaba, gata head maid ga farin jini awurin mutanan gida, bayan ba wani aiki takeyi ba acikin gidan sune masu wahalar girka abinci, ita aikin ta tsara abunda za'a girka ne da kuma bada umarnin yadda abu zai kasance. Dole ta ɗana mata tarkon da bazata Iya fidda kanta ba, ko dan ta ƙwace mukamin ta, wannan alwashine ta daukarwa kanta! Ta fada aranta, yayin da take nufar hanyar komawa kitchen Bayan fitar marwa, hajiya saratu ta sauke ajiyar zuciya, yanzu ne ta samu kwarin gwiwar shiga toilet yin wanka Lokacin da fito, A zaune ta same shi gefen gadonta, sam bataji alamun shigowarshi ba. Tun da ya ɗago suka hada ido da ita yai saurin sunnar da kanshi kasa, wani irin nauyinta yaji, baisan ta ina zai fara shawo kanta ba, Yasan dole ta tuhume shi akan abun da Ya faru jiya. Kau da ido tai daga kan shi, Ta juya ta nufi closet, jim kaɗan Ta fito har ta sanya riga bubu ta atamfa, gaban mirror ta tsaya tare dakai hannu ta dauki turare ta soma feshe jikin ta da shi, yadda ta share shi kamar batasan da zaman shi a dakin ba. Shi kuwa gogan Ya kasa dauke idanunsa daga gareta. Kamshin turarenta ne yakai mashi karo har ya gaza jurewa duk da shakkarta da ya ke ji ƙarfin hali yai wurin furta"Har Yanzu fushi kike dani? Banza tayi da shi Mikewa yai tsaye ya nufeta, daga bayanta ya dan dakata Yana bin ta da kallo. Kafin cikin sanyin murya yace "Tun jiya nake ta so na baki hakuri, nasan ban kyauta maki ba, ni kaina ba'a hayyacina na aikata hakan ba, bansan meyasa na ruko hannunta ba, wallahi sharrin shaiɗanne" Murmushin gefen fuska tasaki, ba tare da ta bari ya gani ba, dama dagangan ta dauki wankar da zai zautar da shi "Na cancanci kowani irin hukunci daga gareki, a shirye nake dana kar6e shi, ni dai bana son 6acin ranki" ya faɗa tare da ɗaura kansa saman kafadarta saboda karfin hali irin nashi Lumshe idanunsa yai tare da shakar kamshin turarenta. "Kinyi shiru baki ce min komai ba" sai da ta mula tasha iska tukunna Tace"laifin me kayi min"? "Kin riga da kin sani" "In dai dangane da abunda ya faru jiya ne to ka manta kawai, bana son tada maganar, ko alokacin abunda yasa raina ya 6aci saboda ina kishin ka ne banji dadi ba, amma yanzu komai ya wuce" Tsabar mamakin kalamanta yasa shi saurin ɗagowa yana duban fuskarta ta cikin mirror. "Amma dai wasa kike min ko"? Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"na taba maka wasa irin wannan"? Girgiza kanshi yai"a'a, baki taba min ba, amma dai nayi mamaki, Allah yasa ba mafarki nake ba" juyowa tayi suka fuskanci juna, fuskar ta dauke da ƙayataccen murmushi ta ɗaura hannayen ta a kan kafadunsa. Lamarin ya ɗaure masa kai gaba daya ta canza mashi kamar ba hajiya saratun daya sani ba. Cikin sanyin murya tace"hubby, kada ka ƙara maimaita kuskuran da kayi, bana so, kasan inada kishi, akan ka zan iya komai daga ciki har da kisa" Zaro idanunsa yayi"in sha Allah hakan bazata faru ba, zanyi kokarin ganin na kiyaye duk wani abu da zai bata maki rai" Ba zato ba tsammani yaji tayi huggin ɗinsa tare da zagayo da hannayenta kan waist dinsa, tuni yafara jin shi awani yanayi. Sumbatar wuyansa tayi kafin ta dago da bakinta saitin kunnanshi cikin muryar raɗa mai hade da kwarkwasa tace"fadamin me ka ke so nayi maka wanda zai faranta ranka" "Nagaza yarda da abinda kike fada min, anya kuwa kece? Ko dai aljanune suka shige ki? Nifa ina kokwanto bana so saina shagala ki canza min ainihin kala dinki" dariya tayi cike da nishadi tace"ka daina kokwanto akaina, ni ce dai hajiya saratun daka sani, matarka uwar ya'yanka" Murmushi pravin yai cike da jin shaukinta "Ka yi breakfast ko insa a kawo mana mu yi a daki nima banci komai ba" "In ban da abunki ay kinsan bana iya cin abinci idan ba atare dake ba, don ma ke dince wani lokaci baki jira na" "I'm sorry Yanzu bari na kira akawo mana a daki, me kake son ci"? Yana faman washe baki yace "Duk abin da zaki ci, zabinki ay shine nawa" Shu'umin murmushin gefen fuska hajiya saratu tasaki tare dakai hannu ta dauki waya ta kira layin kitchen ta isar da sakon akawo masu abinci, bayan abla ta kawo masu atare suka zauna suna ci, kamar sabbin ma'aurata abaki ta fara bashi har sai da suka cinye kafin ta soma jan hankalin shi. Gaba ɗaya nema take ta zautar dashi da salonta, kasa jurewa yayi da sauri ya ƙara tighting nata a jikinsa. _________________________________❤✍️ Bayan shigar chief bedroom dinsa a zafafe Ya faɗa Bathroom dinsa don ya watsa ruwa ko ya samu zuciyarsa ta lafa daga radadin da ta ke yi masa. ganin ya shiga toilet yasa big guy sauke ajiyar zuciya, yayi tunanin zaiyi yadda ya saba ne idan ransa ya 6aci da wuya in bai yi ma kan shi illa ba, wani lokacin mirror yake kaima naushi ya tarwatsa shi har sai hannun shi ya faffashe saboda tsabar zuciyar dake gare shi. Kafin fitowarshi da sauri big guy ya fita na tsawon mintuna ya dawo hannun shi ruƙe da wooden tray mai dauke da breakfast din chief. Yayi mamakin ganin shi kwance kan gado, jikin shi sanye da bathrobe ya ɗaura hannunsa ɗaya kan lallausar sumar kanshi, ya lumshe wadannan kyawawan idanuwan nashi, bakomai yake tunawa ba acikin zuciyarsa face tarihin rayuwar prisoners, labarin yai matuƙar ta6a zuciyar shi. "Allah Ya huci zuciyarka Yalla6ai, ga breakfast dinka, nasan kana jin yunwa" cikin girmamawa yayi maganar Tamkar bazai tanka mashi ba, sai da ya dauki lokaci kafin Ya furta"ka koma da abincin bana jin zan iya ci" Cikin sanyin murya big guy yace"ka yi hakuri Sir, kasan ni mai biyayya ne agare ka, bana yi maka jayayya amma yau bazan iya bin umarnin ka ba, saboda na damu dakai, abun da ke damunka nima shike damuna..." ya fada yana cigaba da kallonsa. "Sir, ƙin cin abinci bashi bane mafita, kana buƙatar kwanciyar hankali da nutsuwa, wanda hakan bazai samu ba sai ka jajirce wurin ganin ka kauda damuwarka, sannan yanzu ne ya kamata mu dage damtse mu yi aiki tuƙuru don ganin mun gano su wanene azzaluman mutanan da suke aikata 6arna a kasarmu" Daɗaɗan kalamai Big guy ya cigaba da zayyano masa yana kara karfafa masa gwiwa da kwantar masa da hankali, A hankali Ya fara jin saukin radadin da zuciyarsa ke yi mashi. "Sir, har yanzu kana akan bakanka na bazaka ci abincin ba"? Ya faɗa yana duban cute face din Ogan nasa Slowly ya ɗan motsa tausasan pink lips dinsa in a low voice ya furta"zan kokarta" gyaɗa kai yai "Zan tafi yalla6ai, Ka huta lafiya" ya fada tare da sara mashi kafin Ya juya har ya kusa ficewa daga dakin muryar chief ta ratsa kunnansa"nagoda da kulawarka agare ni" Murmushi big guy yai"kada ka damu yalla6ai" Har zai fuce ya kuma dakatar da shi"please ka duba dakin Yaron nan, kaga Awani hali Yake a ciki, Idan ya farka a tabbatar Yayi breakfast dinsa, idan ya gama ka tambaye shi me yake bukata in ya fada maka ay gaggawar yi mashi, zuwa anjima sheikh Imam zai zo duba shi" "Okey, Sir" Ya fada tare da bude door room din Ya fito waje, dakatawa yayi da tafiya yana tunanin tawace hanya zai faranta ran chief? Don ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa aranshi, tunawa da Unaisah yasa shi saurin zaro wayarsa ya danna ma boss kira, tana fara ringing yai picking Call din Da zolaya yace"masu Ƴa, halan Har yanzu kana nan maƙale da ita" Sautin muryar boss da alamun dariya yace"To ɗan sa ido, ka fara tsokanar taka ko"? Dariya Big guy yayi" inatayaka murna abokina" "Nagode sosai mutumina, Ina chief ne ina fata yana lafiya" "Ba lafiya, Har yanzu akwai damuwa aranshi, Kuma kasan halinshi mutunne mai zuciya, yanzu haka ina a kofar dakinsa, na kai masa abinci yace min bazai iya ci ba" Muryar bos da jimami yace"amma banji dadi ba, pls ka yi kokarin kwantar masa da hankali kafin inzo" da sauri big guy yace"anya zan iya? Ko dai zaka turo unaisah ko da godiyane tayi mashi, watakil hakan Ya kwantar masa da hankalinsa" "Nima nayi tunanin hakan, yanzu zan turo ta in sha Allah" murmushi big guy yai kafin yai mashi sallama a hanzarce Ya nufi bedroom diny Danish. *❤GARKUWA💪* A kishingiɗe Yake kan gadon shi, Ya hakimce kamar wani basarake, wasu hadaddun sleeping dress ne a jikin sa launin red colour sunyi bala'en yi mashi kyau, hannunsa ɗaya rungume da pillow, lallausar sumar kanshi ta lullu6e gefen fuskarshi, yayin da kyawawan fararen idanunsa ke akan hadadden ceilling din dakin, tun da Ya farka daga bacci bai ta6uka komai ba, gaba ɗaya ya shagala da tunanin Hateem, wani irin kewarsa yake ji, mutumin ya kwanta masa aransa saboda yadda ya tarairayesa ya bashi kulawa kamar wani nashi, bai ta6a tsammanin zaiji tsantsar kaunarsa ba, sai gashi zuciyarsa takasa samun sukuni saboda tunaninsa, da zarar ya lumshe idanunsa fuskar Hateem yake gani dauke da murmushi......" Yana son ya sake sanya shi a idanunsa, kwata kwata bai fahimci cewa prime minister kasar ya bari ba. Har Yanzu kamshin turaren daddy hateem bai bar jikin shi ba, saboda rungumarsa da yadinga yi jiya kamar zai maida shi jikin shi, fragrance din Yana da karfi sosai shiyasa ya kama jikin sa. Kalaman hateem ne suka fara dawo mashi _zan tafi da kewarka, dan Allah kada ka manta dani, inaso ka ɗauke ni tamkar mahaifinka, aduk lokacin da wani abu ke damunka ka sanar da chief zai fada min, zamu dinga yin waya akai akai, daga yanzu inaso ka dinga kirana da sunan daddynka_ A hankali ya dago da yatsan hannunsa yana kallon zoben da ya sanya mashi ayatsa mai kyan gaske, wannan ne karo na farko daya fara sanya zobe, Daura yatsan yai kan kananun la66ansa Ya sumbace shi a hankali yanayin fuskarshi kamar zaiyi murmushi. Knocking din kofar dakin da akaine Ya sa shi daura idonsa kan kofar, bakomai Ya fado masa arani ba face Angel dinsa, yasan ita kaɗaice zata Iya zuwa duba shi awanan lokacin, Idan ba ita ba sai kuma yan uwansa, saukowa yai daga kan gadon bayan ya jefar da pillow hannunsa, da sauri Ya nufi kofar don Ya tarbe ta, saboda yayi kewarta jiya, idanunsa sunyi maraicin ganin ta,, shi kanshi baiyi tsammanin zai Iya mintuna batare da ita a gafen sa ba, sai gashi jiya daddy hateem Ya sace zuciyarsa. Ko da ƙofar ta bude yai arba da big guy tuni yanayin fuskarshi Ya canza, shi da ya taso da zumudinsa don Ya nuna ma Angel dinsa kyautar zoben da mutumin nan ya bashi, sannan Ya bata labarin abunda Ya faru atsakanin su ashe ba ita bace. "Barka da safiya danish" big guy ya fada da fara'a akan fuskarsa, ko kallo danish bai mashi ba, Hankalin shi na akan bayan shi, burin shi Yaga Angel don har yanzu bai fidda rai da ganin ta ba Da mamaki big guy ya waiga baya don yaga me yake kallo sai dai baiga komai ba. "Ina fata ka tashi lafiya" ya fada aranshi yana mai mamakin Girman Jikin Yaron ga tsawo tubarkalla uwa uba ga kyau kamar shi ya zana kan shi. "Magana na ke yi maka ka yi shiru ba ka ce komai ba, ko har yanzu ba ka jin daɗin jikin naka ne"? cikin sanyin murya ya furta"My Angel? Tana Ina"? Dafa kafadarsa big guy yai"kwantar da hankalinka tana nan cikin koshin lafiya, nasan zata zo dubaka..." kafin Ya kare maganar danish Yace"Ina son ganinta, " ya fada yana kokarin bi ta gefen shi Ya wuce, A hanzarce big guy yai saurin Shan gabanshi, gudun Kada Ya ruguza masa plan dinsa na zuwan angel part din chief. Wani kallo da danish Ya watsa mashi sai da yaɗan ji fargabansa, Karfin Hali Yai wurin furta"Ka yi hakuri bawai ina son dakatar dakai bane, daga gani yanzu ka farka daga bacci ko wanka ba ka yi ba, a haka zakaje wurinta? Itama bazata ji dadin ganin ba, kaje kayi wanka, kafin ka fito zan sa unaisah ta kawo maka breakfast dinka har daki" cikin sigar lallashi yakeyi mashi magana, badan Ya yarda da kalaman sa ba, ya amince mashi, juyawa yayi tamkar wanda ya rasa kuzarinsa, harta bugun zuciyarshi ya canza ji yake kamar wani abu na faruwa ko yana shirin faruwa Bayan ya shiga toilet Ya maida kofa ya rufa, ajiyar zuciya big guy ya sauke aranshi ya ayyana wai Allah daga ganin yaron nan zaiyi kafiya, dole saina mike tsaye idan ba haka ba zai iya zame min matsala. Ya fada tare da juyawa ya fuce daga dakin, Ya nufi sashen kitchen din su don Ya hada masa breakfast dinsa. *❤UNAISAH ANGEL💋* Bata jima da fitowa daga bathroom ba, sai rawar kai takeyi saboda daddynta Ya fada mata zancen zuwa dakin chief don tayi mashi godiya bisa ga irin kyautatawar da yayi mashi, ruwan ido Ya hana ta canki kayan da za ta sanya, tayi tsaye gaban faskeken closet dinsu, sai faman bin jerin kayan take yi da kallo, fuskarta dauke da murmushi tarasa gane meyasa take jin wani irin nishadi da annushuwa kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna. A ƙalla ta shafe mintuna kafin ta fito sanye cikin wasu riga da wando launin pearl pink masu kyan gaske, tsayawa zayyana kyawunta acikin kayan 6ata baki ne, abun sai wanda ya gani. Takalma ta ɗauko masu tsini launin kayan, ta zura su a kafarta, bayan ta dauko mayafi ta tsaya gaban mirror ta ta soma laga shi akanta. Ita kanta data kalli madubi sai da ta firgita da ganin wani sihirtaccen kyau daya bayyana akan fuskarta, murmushi tadan saki har dimples dinta suka lotsa. "Daughter I'm waiting For You, Kin bar daddy awaje Yana ta jiranki" Muryar taj tajiyo daga waje yana magana, da sauri ta nufi kofar ta fito, waro idanu waje taj yai arude Ya furta"Tabarakallahu ahsanun khalikin! My Angel? Kinga kuwa kyan da kikayi kamar hurul aini" sunnar da kanta kasa tay, fuskarta sauke da murmushi Ruko hannunta yai a cikin nashi suka nufi dakin chief. Abakin kofar dakin suka dakata suna kallon juna Lokaci daya suka sakar ma juna murmushi Raɗa yai mata a kunnanta"ba'ay mashi rashin jin magana ba kamar daddy bane da aka raina" dariya tayi jin abun da yace. Sakin hannunta yai"ki kula min da kanki," amsa mashi tayi da toh, kamar karsu rabu yana tafiya yana waiwayonta itama sai kallon shi take yi Ɗaga murya tayi tare da cewa"daddy kada ka tafi ka jirani in fito" "Ba nesa zanyi ba, Zanje gidane bazan jima ba zan dawo" ta6e mashi baki tayi kamar zatayi kuka, hakan ba karamin nishadi ya sanya shi ba. Zuciyarta Cike fal da fargaban haɗuwa dashi tay knocking kofar, Almost 3 times ba'a bude ba, harta fara tunanin ko dai bacci yakeyi ne ko baya a dakin har zata juya kofar ta soma zugewa a hankali ta buɗe, kamshin turarensa ne Ya fara dakar mata hanci har saida ta dan lumashe idanunta. Kasa shiga tay saboda zullumin hada ido da shi, da kuma jin nauyn magana da shi. Sai da ta shafe kusan mintuna biyar, tana saƙe saƙe a zuciyarta ba tare da ta motsa ba, kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta kwatsam kofar ta soma kokarin rufe kanta, da sauri ta ratsa ta tsakankanin door din da karfi ta faɗa dakin kamar wadda aka jeho, ƙiris Ya rage ƙofar ta datse da jikinta, wannan gangancin nata ba karamin mamaki ya bashi ba, sai faman nishi take yi hadi da sauke ajiyar zuciya, sai da tagama yan kame kamen ta, kafin a hankali kamar maijin tsoronsa ta soma bin dakin da kallon, Lokacin da ta daura idanunta akan shi har saida gabanta Ya fadi ganin surar jikin shi, Har yanzu bai motsa daga kan gadon shi ba, kamar yadda Big guy ya barshi haka ta taras da shi sanye da rigar wanka, ya daura Apple laptop dinsa kan waist insa, Yayin da kanshi ke akan pillow ya dan lumshe idanunsa, tuni kamshin turarenta yakai mashi karo Yawu ta haɗiya, a tunaninta baya ganin ta cikin sanda ta matsa daga gaban gadon tana faman zare gray eye dinta ta furta"ina kwana, ka tashi lafiya" magana takeyi hankalinta na akan kwantaccen sajen fuskarshi. "Lafiya" taji ya amsa mata da sanyin murya, tayi mamakin jin voice dinsa irin na danish. Shiru tayi tana faman wurwurga eye balls dinta, bata ta6a jin nauyin wani dan adam ba sai akan shi, kamar ma kunyar shi take ji Wasa takama yi da yatsun hannunta, batasan cewa yana kallonta ta cikin laptop dinsa ba. "Idan kingama tsayuwar zaki iya tafiya" sexy voice dinsa ce ta kuma ratsa kunnanta, muryarta da en ena tace"am.. um. wai Dama daddy ne yace inzo in yi maka godiya" Shiru yayi yana maimaita maganarta a zuciyarsa kafin ya furta"bake ki kayi niyar zuwa ba? Shiya tursasa maki kizo"? Dafe kai tay da hannu daya alamar ta kwafsa. "Mantawa nayi, ni nayi niyar zuwa inyi maka godiya". Ta6e pink lips dinsa yai na ɗan wani lokaci kafin yace"ba'ay min godiya, duk wani abu da nayi nayine don Allah, ina fata kin fahimce ni" amsa mashi tayi da toh, shiru suka kuma yi, Ganin yaki sake tanka matane yasa tai kafin halin cewa"tun da bakason ay maka godiya, to ka fadamin wani abu da zan dinga yi maka tunda kaima ka kyautata mana duk da nasan bazan iya biyan ka ba" ta faɗa tana cuke la66anta. A hankali ya dan ware reddish eyes dinsa, duk wani motsinta akan idonsa sai dai ita batasan Yana kallonta. "Will you do whatever I tell you?"da kwarin gwiwa ta amsa mashi Eh "Okey," ya furta tare da sauke Laptop dinsa gefe ɗaya, a hanzarce ta juya mashi ƙeya, Ganin zai mike kuma taga bathrobe ce a jikin shi, murmushin gefen fuska ya dan saki. Saukowa yai daga kan gadon Ya nufi walk-in closet dinsa, Jim kaɗan Ya fito sanye da thobe launin ruwan toka, tamkar a jikinsa aka dinka ta tsabar yadda ta bayyana surarsa. Kamar yadda yabarta haka ya same ta atsaye ta juya baya. Zama yai gefen gadon da alama bata san ya dawo ba. "Zaki Iya zuba min abinci"? ɗan zaro idanunta tayi kafin ta amsa mashi da toh, juyawa tayi a hankali ta saci kallonsa Idanunsa na akan wayar hannunsa, taji dadin ganin hankalinsa baya akanta Cikin takun sanda ta karasa daga gaban table din. "Me kakeso nafara zuba maka" "Duk abun da yai maki" farfari tayi da idonta hada ɗan gumtse baki alamar mamaki, sam batayi zaton zai kulata har haka ba, kallo ɗaya da tai masa ta fahimci mutunne mai ji da kansa Coffee ta mika masa yasa hannu ya kar6a A hankali Yake kurbarsa, Angel sai faman satar kallon la66ansa take Yi, ba karamin rudarta yakeyi ba, ga kamshin turarensa dake ta kai mata hari. Komai ta zuba masa cinye shi yake yi, mutumin da bai cika cin abinci ba, amma yau har saida yaso ya ƙwari cikin sa, ba tare daya ankare ba.. Bayan ta kammala serving nasa tace"ko akwai wani abun da zanyi maka? Ko in gyara maka bedroom din ka" "Idan kin ji zaki iya" ta6e baki tadanyi kafin tafara tunanin shiga toilet dinsa ta gyara masa shi, watakil kafin ta fito shi kuma Ya fita sai ta gyara dakin Juyawa tayi da sauri ta nufi toilet din, sai lokacin Ya dago Yana bin bayanta da kallo har sai da ta 6ace ma ganinsa tukunna ya kau da idonsa. *🤍ZAHRA🤍* A ƙudundune take kan darduma ta lullu6e jikinta da hijabi, tun bayan sallar asubahi bata farka daga bacci ba. Shigowa Dakin Aneelerh tayi, hannunta ruƙe dana baby junaid, sakin hannunta yai da gudu ya tunkari zahra Ya faɗa jikinta yana fadin"aunty zahra Ina tsarabar da kika ce zakiyi min jiya! Shine ma baki tada ni daga bacci ba" Janyo shi Aneelerh tayi tana fadin"meye haka? Ba ka ga bacci take yi ba"? Zahra dake sauraronsu tayi shiru batare da ta motsa ba ashe idonta biyu. Da shagwa6a baby junaid yace"mommy ay itane tace zata min tsaraba, Ni ta tashi ta bani abuna kamin taci gaba da baccin..." bai kare maganar ba, ta rufe bakinsa da tafin hannunta. "Yi shiru kada ta farka, mu tafi zuwa anjima sai mu dawo" maƙe mata kafaɗa yayi"nidai ba inda zani Allah, sai ta bani abuna" kwace hannunsa yai daga na Aneelerh Ya fada kan zahra yana kiciniyar tada ta daga bacci, duk yadda taso tayi pretending sai da takasa tana faman fitar da numfashi mai ɗan huci ta sanya hannu ta janye junaid kafin ta mike zaune ta tu6e hijab din jikinta ta jefar da shi gefe ɗaya Har saida gaban aneerlah Ya fadi ganin jirwayen hawaye akan fuskar zahra, idanunta sun kumbura suntum da su, da alama tasha kuka har ta gaji. Waro idanu waje baby junaid Yayi "mommy mun shiga uku, aunty zahra kuka tayi wani ya buge ta . " bai kare maganar ba, zahra tai saurin sanya hannu ta dan buge bakinsa"kada na kuskura nasake ji kayi magana," ta6e mata baki yai alamar zai yi kuka da sauri ta janyoshi tare da manna shi kan kirjinta, wani sabon kukan ne ta kuma fashewa da shi. Hankalin Aneelerh ba karamin tashi yayi ba, tuni yanayin fuskarta Ya canza, matsawo tayi kusa da zahra ta zauna, cikin sanyin murya tace"ni dama tun jiya da kika dawo gida hankalina bai kwanta da yanayin ki ba, saboda na lura da yadda kike kokarin danne damuwarki saboda kada mu gane! Meyasa zahra eyeh? Adan tsawace ta fada tana dubanta "Ki fadamin me ya faru dake ne? Waye ya ta6a min ke yanzun nan in ɗaura ɗamarar yin yaƙi da shi"! ta faɗa babu wasa akan fuskarta, Cikin shesshekar kuka zahra tace"a.. Aunty Aneeleerh zayn! Na shiga uku! Hajiya saratu ta haɗa ni da masifa, ashe lokacin da ta turamin sakon nan tace min in zabi daya daga cikinsu nayi kuskuran rubuta sunan zayn a maimakon zaid shine fa ta haɗa ni dashi, aunty aneelerh baki ji kalaman daya furta min ba.........' a tsanake tafara bata labarin abun da ya faru jiya bayan da hajiya saratu ta kira ta. Fitowa tai daga hall din tana ta faman yan kalle kalle can ta hango hajiya saratu tsaye abakin motarta, Cikin girmamawa ta ƙarasa daga gefen ta, bayan sun ƙara gaisawa zahra tace "mommy gani" murmushi hajiya saratu tasakar mata tare da ruko hannunta acikin nata"mu shiga ciki, inaga zaifi muyi magana a tsanake" ta fada tare da buɗe murfin backseat, bayan sun shiga taja kofa ta rufe, Zahra sai faman bin cikin motar take da kallo, saboda haduwarta ga sanyi a.c dake ratsa fatar mutun Shiru sukayi babu mai magana, Hankalin hajiya saratu na akan wayar hannunta da take ɗan daddanawa, "Zahra," ta ambaci sunanta, da sauri ta amsa da na'am "Ina fata kin nishadantu da dinner din nan," tana dan murmushi ta jinjina kanta tare da cewa"Eh mommy, Alhamdulillah, naji dadin gayyatana da kikayi, I can't thank you enough" Murmushin dattako hajiya saratu tayi"kada ki damu, kin cancanta ne, ni kaina najima ina mamakin yadda kika kwanta min araina, saboda ba kowa nake mu'amala da shi ba, ina da wuyar sha'ani zahra " ta faɗa ba tare da ta ɗago da idonta dake akan screen in wayarta ba. Zahra sai faman sakin murmushi takeyi taji dadin maganar da hajiya saratu ta furta mata. "Kinsan meyasa na kira ki"! "A'a" "Idan ba zaki manta ba, Kwanakin baya na tura maki hoton twins dina, har nace idan na baki za6i wanne kike so acikin su, ashe kin bani amsa ban samu damar duba sakon ba sai daga baya na gani" Dakatawa tayi da yin maganar, zahra nata kallon gefen fuskarta burinta ta karasa maganar nata, sai dai ta fahinci bata cika son magana ba. ba ta zaci zata dago ba, aikuwa karaf suka hada ido cikin na juna, wani irin kwar jini tayi ma zahra da sauri ta dukar dakanta kasa tana wasa da yatsun hannunta Daura wayar tayi akan laps dinta, ta ruko hannun zahra acikin nata, kafin ta soma magana "Zahra na yarda dake, Kamar yadda na fada maki kin kwanta min araina, kuma na yaba da hankalin ki, kyawawan ɗabi'unki da halayen ki sune suka sa har nafara kwadayin ki zama wani bangare na rayuwana, Ina nufin ina so ki zama surukata zahra" cikin kwantar da murya hajiya saratu take yi mata magana tamkar ba aunty masifatu ba Zahra jikinta yayi wani irin sanyi, ga wani annurin farin ciki daya lullu6eta duk da tana jin fargaban wanda za'a haɗa ta da shi Yaki amincewa... "Naji kinyi shiru bakice komai ba, Ni bazan maki dole ba, kada kiji nauyn fada min abunda ke aranki, saboda nima bazan bari ki auri wanda zuciyarki bata so ba" Numfasawa zahra tayi fuskarta da ɗan murmushi tace"mommy wa zai ki jinin ki? Ni ay abun farin cikine agare ni, saboda nima kin kwanta min araina, bazan 6oye maki ba, nayi mamakin tayin da kikayi min, saboda ni aganina ban kaiba mommy, ya'yanki sunfi karfi na, sannan inajin fargaban wanda zaki haɗani dashi yakini, tun da bamusan juna ba....." ta ƙarasa maganar idanunta cike tab da kwallar murna. Jinjina kai hajiya saratu tayi kafin ta furta"kada wannan ya dameki zahra, bana so na sake jin kin furta matsayin ki bai kai ba, ni na za6e ki don haka kada kiji komai, ƴa'ƴana kuma ni nake iko da su, abunda nakeso shi zasuyi don haka ki kwantar da hankalin ki, wadannan hawayen da nake gani ki share su" ta fada tare da zaro mata hanky ta mika mata, yatsun hannun zahra na kerma ta kar6a tafara shaye hawayen ta. Wayarta ta dauka tare da dannama zayn kira, bayan yai picking cike da bada umarni tace"ka sameni abakin hall yanzun nan Ina jiranka"! Bata jira amsar shi ba tai rejecting call din, tare da mayar da dubanta ga zahra "Nayi mashi magana yanzu zaizo sai ku fahimci juna" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh, sam bata kawo ma ranta zata ga akasin zaben da tayi ba. Kusan mintuna Kafin akayi knocking, murmushi hajiya saratu ta saki, tare da kallon zahra"ki gyara nutsuwarki, Yanzu zai shigo ku gana da juna" amsa mata tayi da toh, bayan fitar hajiya saratu, da sauri zahra ta bude purse dinta ta curo hanky ta goge fuskarta, ta zaro yar hodarta ta barbaɗa, hada jan baki ta murza ma la66anta, Jin motsin buɗe motar yasa tayi saurin maida kayan kwalliyar cikin purse din. tun daga kan kamshin turarensa daya daki hancinta tafara jin wani irin fargaba, a wani slow ya zauna kyakkyawar fuskar nan tashi a haɗe Yaci mur, ko kallon inda take baiyi ba balle ma ya nuna alamar yaga mutun a motar, da farko bata gane wanene ba acikin su, Dakyar ta furta"ina wuni" Banza yayi da ita, saima ya zaro wayarsa yaci gaba da dannata, nan take ranta ya bata cewar ZAYN ne, Hankalinta a matukar tashe take duban gefen fuskarshi, mutun har mutun ga kyau sai dai babu mutunci ko miskala zarratin, gaba ɗaya tarasa sukuninta tun kan aje ko'ina harta fara danasani, mamakinta tayaya akai zayn ya kasance wanda za'a hada ta dashi bayan zaid ne ta canka ba shi ba? Ko dai hajiya saratu tayi kuskure ne..." Tayi zurfi a tunaninta muryarshi ta ratsa kunnanta"wani tsautsayine yakai ki amincewa da zancen haɗani dake? Kinsan wanene ni"? Adabarbace tace a'a amma in ranka ya 6aci kayi hakuri ni ma bada son raina ba.." "Meyasa tun farko bakice mata baki sona ba"! A kausashe ya furta maganar, Muryarta na rawa tace"saboda bazan iyaba" "Wallahi idan kina son zaman lafiya ki janye zancen hadani dake da gaggawa idan ba haka ba ciwon zuciyane zaiyi silar mutuwarki, saboda ni nan da kike gani na ba mutumin kirki bane ɗan iska ne ni, sannan bani da mutunci .." Ras taji gabanta ya fadi, tunda yafara magana bai kalle ba, baima san wacece wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, amatukar rude take kallon shi jikinta na kerma "Nasan bazaki so ya'yanki su yi rashin dacen uba ba, shiyasa nake gargadinki, tun kafin kiyi danasani mara amfani, ke in banda ma haɗama da rashin sanin ciwon kai ina ke ina Zayn pravin obinna? Nayi maki kama da sa'ar auranki? Wai ke yar wacece ma"? Hawayen dake taruwa a cikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta Hankalin shi kwance yaci gaba da cewa"Ni nasan ba hakanan kika kyale mommy ba, Allah kadai Yasan me kika kulla da har ta amince zata hada ni da ke, idan ma kwaɗayin abun duniyane ya rufe maki ido to ki fadamin nawa kikeso tun daga miliyan biyar har abun da yai sama zan baki kije kija jari ki rufawa kanki asiri...." sautin shesshekar kukanta ne ya cika masa kunnansa, a zafafe ya juya da niyar ya dauke ta da mari kamar an ruke hannunsa ya dakata cak Yana huci idanunsa akan fuskar zahra da hawaye ya gama wanke ta, bakomai ne yaja hankalin shi ba face kyawun fuskarta ba laifi tana da sura dai dai wadaidai saidai baya jin zai iya kula macen da bata kai matsayinsa ba Sassauta muryarshi yayi"ke, yi min shiru in ba haka ba zan 6ata maki rai" yatsun hannunta na kerma ta toshe bakinta, sam takasa kallon cikin idanunshi gashi ya matso kusa da ita kamshin turarensa duk Ya gama kashe mata jikinta "Idan kinason zaman lafiyar, Kije ki fada mata, baki sona banyi maki ba"muryarya da shesshekar kuka tace"kayi hakuri amma ni bazan iyaba, saboda ina ganin girmanta, sai dai kai ka je ka faɗa mata" dakyar ta kare maganar tana faman jan numfashi "Tausayinki nake ji bana so kiyi danasani, wallahi bani da mutunci, ni banma shirya yin aure ba, saboda baya agabana, Ni nafi sha'awar inyi sharholiya ta son raina" ya fada yana shafa sajen fuskarsa" yanzu ke kin yarda ki auri dan iska mai mu'amala da matan banza"? Ya fada yana cizon lips dinsa da masifa Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ita kanta batasan tayi hakan ba, batasan ya akai zuciyarta take jin kaunarsa ba, a maimakon taji haushin kalamansa. Dafe kanshi yai da hannu ɗaya kafin ya furta"look, Idan burgeki nakeyi naji zan baki kaina, amma ki janye batun nan, saboda ni ban shirya ma aure ba, ko auran zanyi bazan auri wadda batakai aji na ba, bana so ki jefa rayuwarki cikin hatsari, kada kiga kamar ina lallashinki mommyn mu kaifi ɗayace idan ta furta magana babu wanda ya isa ya dakatar da ita, shiyasa nake lalla6aki saboda ke kadaice zaki canza ra'ayinta" zahra dake ta faman yin shesshekar kuka muryarta na rawa tace"har abada bazan iya tunkararta da maganar nan ba sai dai kai kaje ka fada mata..." bata ƙare maganar ba ya daka mata tsawar data firgitar da ita Nuna ta yayi da yatsan hannun shi"Share hawayen kan fuskarki, ki tashi muje ki fada mata baki sona banyi maki ba" muryarta kasa kasa tace"ay na fada maka bazan iyaba..." bata kare maganar ba, taji ya haɗe bakinsa acikin nata, wani irin bugu zuciyarta tayi mata, gaba ɗaya takasa tabuka komai, har sai da Ya gama abunda zaiyi kafin ya zame harshensa, Yai saurin zuge glass din motar Ya tofar da yawun bakinsa. tsabar wulakanci Ya zari hanky yana kara goge bakinsa kamar wanda ya ta6a najasa, rushewa tayi da matsanancin kuka ganin irin wulakancin da yai mata, abunda yafi ƙona mata rai sanya mata harshe da yai abakinta, arayuwarta ta tsani namijin da ba muharraminta ba ya ta6a ta, Tsawa yakuma daka mata tuni ta shiga taitayinta. "Kaɗan kika gani, wannan so mun ta6ine idan har baki janye kudirinki akaina ba, zan cigaba da amfani dake ne" ya faɗa yana mai kara jaddada mata "Ki share hawayen nan, Ki tashi muje ki faɗa mata kinjanye" muryarta na kerma ta amsa mashi da toh, shu'umin murmushin gefen fuska yasaki, dama yasan zata amince ko dan saboda abinda yai mata don ya fahinci ba yar hannu bace tana da kamun kai shiyasa ya tsorata ta. Hanky ta zaro ta share hawayen fuskarta, sannan ta daidaita nutsuwarta, kafin ta buɗe motar, ta fito shima ya fito ta ɗayan bangaren suka nufi hajiya saratu dake atsaye can nesa da su. Tunkafin su karaso ta nufosu, fuskarta da fara'a tace"Son, Ina fata kun sasanta kanku"! Nunata zayn yai"ki fada mata abun da kika gaya min acikin mota" amsa mashi tayi da toh kafin ta kalli hajiya saratu zuciyarta cike fal da tsoronsa ta ce"Mun gama magana dashi, Kuma mun fahimci juna" a gigice zayn yake kallon zahra jin abunda tace, zuciyarsa ba karamar hasala tayi ba, bai ta6a tsammanin yarinyar zatay taurin kai ba. "Zahra kin tabbata yayi maki? Amma meyasa naga idanunki sunyi ja"? Da sauri zahra tace"kaina ne keyi min ciwo, har fada masa nayi, shine yace yakamata na tafi gida na huta, zamuyi magana awaya..." da tsantsar mamaki zayn yake kallonta, gashi ba halin Ya karyatata, don ya fahimci ta kama zuciyar mommynsu. "Naji dadi my son, dama nasan bazaka ƙi tayin da nayi maka ba, da ace zaid ne ba lallai ya amince ba saboda shi na daddynsa ne kai kuma nawa ne, hakika yau ka faranta raina my son, Allah yayi maka albarka, zahra kema nagode maki sosai da kika aminta da tayina in sha Allah ba zakuyi danasani ba, Ina da tabbacin hakan, Ta fada tare da janyo zayn da zahra tayi huggin dinsu tana ɗan bubbuga bayansu, sai faman farin ciki takeyi yayin da su kuma zuciyoyin su suke a kuntacce da bakin ciki. "Zayn ko zaka kaita, Gida"? Ta fada bayan ta raba su daga jikinta, da sauri zahra tace"mommy kin manta nazo da mota dina" "Oh eh hakane, na shafa'a, Muje son mu rakata ta tafi gida" atare da zayn suka raka zahra bakin mota bayan ta shiga ta zauna, hajiya saratu tace"surukata, Anya zaki iya driving dinnan kuwa? Ko dai zayn yakai ki" wani irin mugun kallo zayn ya watsama zahra da sauri tace"a'a mommy, wallahi zan iya, ay ba sosai nake jin ciwon kan ba" "Toh zahra Ki kula min da kanki sannan ki gaishe min da mutanan gidan" "In sha Allah ngde ssae" Harara hajiya saratu ta watsa ma zayn"kai bazakai mata bankwanan ba, ahaka zakuyi auren" yana faman yamutsa fuska yace"bye, sai mun yi waya" aran shi ya furta "zakiyi danasani," Bayan ta baro estate din har ta hau kan titi tana driving, zuciyarta bata daina tariyo mata kalaman zayn ba. Uban tagumi aneelerh ta zabga da hannu ɗaya, tana kallon zahara data kammala bata labari "Zahra kinyi kuskure wlh, meyasa baki ɗauki shawararshi ba kin fada mata baki son shi? Zahra ina guje maki auran mutun mara kunya irin shi! Kowace uwa burinta ta sama ma ya'yanta uba nagari wanda zasu koyi da shi su kuma yi alfahari da shi ba irin zayn ba, sam bai dace dake ba" zuciyarta ajagule tafada, kwata kwata zayn bai kwanta mata aranta ba, tun kafin ma ta ganshi. Zahra Tana shesshekar kuka ta ruko hannunta"ki tayani da addu'a, ita nafi bukata, Aunty aneeleeh bawai nakasa fada mata bane, Ina son shi ne" Jinjina kai aneeleeh tayi"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Shikenan, zan tayaki da addu'a Idan alkhairi ne shi agare ki Allah Ya tabbatar mana dashi, idan kuma akasin hakan zan roki Allah Ya shiga tsakaninku, bayan haka dole su mami suji maganar nan" kwantar mata da hankali aneelerh tacigaba dayi saida komai ya lafa tukunna aneelerh tace"Ina alkwarina? Kince zaki ɗaukar min hotunan dinner in gani, Jiya da su na kwana araina, ganin kin kwaso gajiyane yasa ban takura maki ba" Murmushi zahra tasaki tunawa da Unaisah, yarinyar data kwanta mata aran ta. "Aunty aneeelerh, akwai labari, zaki sha kanun labarai, " ta fada tare da janye baby juanid dake langwa6e ajikinta, kamar maijin bacci Yai shiru Yanata sauraronsu. Gado Ta nufa ta dauko purse dinta ta curo wayarta donta nuna ma aneeleeh hotunan da ta dauka tare da unaisah Kwatsam wayar ta fara ringing, da sauri tayi picking ganin sunan abie Barka da safiya abie ina kwana"? "Lafiyou, zahra, Ina aneeleeh ne"? Da sauri tace gatanan adakina "Okey ki fada mata, ƙawarta ta turo min da sako ta layina, ta zo ta same ni a daki ina jiranta!" amsa mashi tayi da toh bayan ya kashe kiran ta dubu Aneelerh dake kallon ta, cike da son jin me abie Ya faɗa mata. "Abie ne ya kira, yace in faɗa maki Kawarki ta tura mashi da sako ta layin shi kije ki same shi adaki" Da alamun mamaki Aneeleerh ta furta"ƙawata kuma? Anya kuwa abie ya karanta sakon dai dai? In bahaka ba ni wata ƙawace gare ni da zan bata layin abie" "Aunty Aneelerh kije kawai ki gani, bamusan menene aka turo ba" amsawa tayi da toh a hanzarce ta mike ta bar junaid adakin. Ruko hannun shi zahra tayi"zonan In nuna maka hotunan dinner," Gefen gado ta zauna tare da daura shi kan laps dinta, ta buɗe gallery tana nuna mashi hotunansu, lokacin data buɗe hoton Unaisah, wuff Junaid Ya fusge wayar daga hannunta Yana fadin"Angel! angel! angel"! Har saida gaban zahra Ya fadi, a matukar rude take kallon shi ba tare data fahimci me yake nufi ba. *SALSABEEL💫* Zaune Yake kan sofa hannun shi ruke da wayar shi, Har ya kammala shiryawa, sai faman duba agogo Yake yi, Har ya fara gajiya da jiran su, ɗagowa yai tare da kallon su, suna a zaune tsakar falon suna cin abinci, mutun ɗaya ce ke babu acikin su, Khadeeja dake acan cikin toilet tana wanka, a kalla ta shafe kusan awa ɗaya da rabi har yanzu bata fito ba, gashi har yan uwan ta sun kammala shiyawa. "Dan Allah ku yi sauri ku ƙarasa, kun ga har karfe sha biyu ta buga" amsa mashi sukayi da toh "Yaya salsabeel, Khadeeja fa? Har yanzu bata fito ba, ko ban da ita zamu tafi" rubeena ce tayi maganar. "Bansan ya zanyi da ita ba, so take ta 6ata mana lokaci, bari naje na dubo ta" ya fada tare da miƙewa Ya nufi upstairs. "Wallahi Dama mu tafi mubar ta a gida, kada ta mana hauka, tun da ya salsabeel Yace wurin gasar kyau zamu je kuma in muka ci za'a bamu kyautar wani abu" acewar hibba. rubeena na murmushi tace"ni zan cinye ma gasar saboda nafi ku kyau" harara hawwa ta galla mata"a haka din? Dubi kumatunki, kuma ay cewa yai sun fi son mace doguwa mai gashi, mara jiki, me dogon hanci" daure fuska rubina tayi rai a6ace tace"wlh indai bani zanci ba sai dai kowa ya rasa" ta fada tare dakai hannu ta dauki robar zuma ta dinga watsa masu akan rigunansu, azabure suka mike suna faman zare idanunsu ganin ta 6ata wankan su. "Wallahi baki isa ba, Saina rama mana" sarah ce ta fada da sauri ta fisge zumar ta matsa mata a jikin rigarta, fashewa tayi da kuka tana fadin wayyo Allah ya salsabeel sun 6ata min kayana, shikenan ni bazanci gasar kyau ba, zuƙunnawa tayi gaban kayan abincin tana haki ta dauki coke da niygar ta watsa masu, damƙo hannunta Hawwa tayi nan fa faɗa ya kacame a tsakaninsu, daga wadda za'aja ja ma gashin kai sai wadda aka ca6e ma kwalliyar fuskarta, Mubeen dake a zaune yana kallon su sai faman tikar dariya yakeyi Duk wannan budurin da sukeyi salsabeel bai sani ba, Yana atsaye bakin kofar toilet din dakin su khadeeja, ba irin bugun kofar da baiyi mata ba akan ta fito, amma taƙi ko tanka mashi. Rai a6ace yace"wallahi idan kika bari nasa kafa nabar dakin nan sai dai ki zauna agida, Babu inda zaki je" muryarta da shesshekar kuka tace"wayyo Allah ya salsabeel ba kaine kace zamuje gasar kyau ba, shine fa nakeso in koma fara" waro ido waje yai jin soki burutsin ta, cike da takaici ya furta"Baki da hankali ne? Tayaya za'ai ki koma fara? Waya fada maki sai farare suke cin gasar kyau? to bari ki ji in fada maki bakake sune suka fi lashe gasar" muryarta da shagwa6a tace"ni dai Allah ba wani nan wayo kakeso kai min don kada inci" Dafe kanshi yai da hannu ɗaya"ke zaki fito ko ba zaki fito ba" shiru tayi bata tanka masa ba, Buga kofar yai da karfi"Khadeeja ranki zai 6ace in baki fito ba" still bata tanka mashi ba Banko kofar dakin akay, Mubeen ne ya fado ciki kamar an wurgo shi, Rigar shi duk ta 6ace da jan bakin su rubina A ruɗe salsabeel ke kallon shi Yama rasa ta ina zai fara "Yaya salsabeel, Kaga su rubina sun 6ata min kayana da jan bakinsu, kawai saboda nayi masu dariya suna fada" bai karasa sauraren shi ba yai saurin fucewa da sauri mubeen Yabi bayan shi tunkafin Ya sauko down Ya hango su manne da juna, sun kacame kamar irin kifin gwangwanin nan sai ihu suke Yi, Wata irin tsawa mai sauti Ya daka masu a firgice suka saki junansu, suna ganin shi suka fara kokarin bare baki zasuyi kuka Nuna su yai da yatsan hannun shi"kar wadda ta kuskura tayi min kuka" ya fada yana zare masu idanun shi da alama ranshi ya 6aci, Yaji haushin yadda suka 6ata kayan su, abu tun karfe kusan tara na safe ake ta fama yaki ci yaki cinyewa Sam yakasa yi masu fada, baisan meyasa yake jin nauyin ya furta masu kalma mara dadi ba. "Yanzu abun da ku kayi kun kyauta"? Sunnar dakai kasa sukai har suna hada baki wurin fadin"dan Allah ka yi hakuri ba zamu kara ba" ta6e baki yai" a haka zamu tafi,tun da kunfi son aganku a haukacen ku" "Ya salsabeel dan Allah kabari mu canza wasu kayan," harara ya watsa masu, rai a6ace Ya kama hanyar fuce wa daga falon Yana Fadin"ni na tafi sai kun taho" Watsawa su ka yi aguje suka nufi bedrooms dinsu, Jim kadan suka fito har sun canza kayan jikin su.. Salsabeel Yana atsaye gaban motocin da za su shiga,, Jami'in da zaiyi driving din su Har Ya hallara a mazaunin driver, da gudun gaske khadeeja ta fito hannun ta ruke da takalmanta, har tana bangaje Su Yasmin, kamar a filin Yaki, gaba daya hankalin Jami'an dake tsaron gidan sai da ya dawo kanta, wani burgujejen wando tasanya yadda kasan kafafuwan agwagwa, ga wata yar yaloluwar riga mai hannu daya, Ta dambara jan baki akan la66anta har saman kumatuntu, mascara din data sanyawa eye lashes dinta ya zazzago har kasan idanunta, babu wanda bai firgita da ganin ta ba, Jami'an sai faman kunshe dariya suke yi a bakunansu, ko mayafi babu akanta sai wannan guntun gashin kan nata mai ɗan yawa data fake shi da ribbom Ya karkarce gefe ɗaya. Ko ta kansu bata bi, Tana isa bakin motar, ta jefa takalmanta cikin car window, kafin ta daddage ta kama glass din Ta zura kanta aciki ta soma kiciniyar kutsawa ta karfi, dafe kai salsabeel yay da hannu ɗaya tamkar zai fashe da kuka, ya ma rasa me zaiyi, su rubina duk sun bude bakunansu asake suna kallon ta. A hanzarce Ya cafko kafafuwanta, Ya zarota daga tagar, tana ta faman haki ta dube shi idanuwan nan nata kamar na babie sai kyaf kyafta su takeyi _"Ya salsabeel baka ce nayi kyau ba" Cikin sanyi murya yace"kyawun ne ya ruɗe ni shiyasa nakasa magana" ya fada tare da bude mata murfin motar, ta shiga ciki ta zauna, Bayan kowan nan su Ya shiga, A jere suka fuce daga gidan kai tsaye suka haura kan titi_ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* Mu Haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Tags Kurkukun Kaddara YOU MAY LIKE THESE POSTS Previous Post Next Post GET IN TOUCH SUBSCRIBE USNovels Elite Home Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 19 Complete by Novels Elite Admin June 15, 2024 Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ ____________________________________✍️ ANEELERH Bakinta ɗauke da sallama ta shiga dakin abie, yana daga zaune gefen gadon shi sanye da farar jallabiya, idanunsa a manne da farin glass, yayin da hannun shi ke a ruƙe da kur'anin da yake karantawa, sai da yakai aya kafin ya ɗan ɗago yana dubanta tare da amsa mata sallamar da ta yi A tsanake ta shiga ta zauna daga kasan gadon kusa da kafafuwan shi, cikin girmamawa ta gaishe da shi Fuskar shi dauke da murnushi yace"oum junaid, kin tashi lafiya" sunnar da kanta kasa tayi fuskarta da murmushi tace"lafiyalou abie" "Ina jikallan nawa? Maimakon ki tafo min da shi? ko dai rowar ɗan za'ay min ne" cike da jin kunyarshi tace"a'a abie, ni na isa in hana ka jikanka" Murmushi yayi kafin ya Miƙa hannu ya ɗauko wayarsa dake ajiye kan side drawer ya miƙa mata "Kar6i nan, Ki duba sakon da aka turo miki" da sauri ta sanya hannu ta kar6a, kafin ta ɗaura idanunta kan screen ta soma karanta sakon _Assalamu Alaikum, barka da rana abie an wuni lafiya, ya iyali, ƙawar Aneelerh ce benazir matar tajudeen, Ina son yin magana da ita sai dai bani da contact dinta, dan Allah a hadani da ita, nagode sosai, ku huta lafiya__ Lokacin da ta kai ƙarshen Sakon Idanunta azare, baki a buɗe da tsantsar mamaki take kallon screen din wayar, sam takasa gasgata abun da aka rubuta mata, Muryarta ƙasa ƙasa take maimaita sunan Benazir Benazir! Abie dake ta kallon ta, ganin tayi kasaƙe babu alamun zata motsa ne yasa shi yin gyran murya, kamar wadda aka zungura da sanda a ɗan firgice ta dube shi tana faman zare idanu "Lafiya? Ko bakisan ta ba ne"? Muryarta a harmutse tace"abie, na kasa yarda ne da abun da gani, wannan sakon da aka turo min daga benazir ne aminiyar nan tawa, matar da yau tsawon shekara goma sha wani abu da 6atan ta...." kafin ta ƙare maganar abie yace"kina nufin Benazir yar gidan Alhaji ubaid? Wannan ƙawar taki ta ƙuruciya" jinjina mashi kai tai alamar eh. "To ki kira layinta mana sai ki ji idan itace da gaske" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta miƙe ta fuce daga ɗakin a falo ta tsaya kafin ta danna call, jikin ta har kerma yakeyi tsabar zumudin taji idan banezir ce take neman ta. ...... *DAULAR ALHAJI MUSA* Gaba ɗayan su sun Hallara a kan dining chairs, Tani da lami ne suke dawainiyar yin serving din su, an shake masu table da lafiyayyan abincin breakfast. Tun da suka zauna babu mai magana acikin su, zeenatu da benazir abayane a jikin su, sun daure kansu da head scarp, yayin da Hajiya sarah ta sanya fitted gown ta atampa, kayan sun bi shape din jikinta, sam babu ɗankwali akanta sai zallar gashin kanta da ya sauko har kan kafadarta, mom layla ma atampar ce ta sanya, Alhaji Ubaid da shureim jallabiya ne a jikin su, Alhaji musa ne kadai ya ɗauki wankan tsadaddiyar shadda launin blue sky, kayan sun zauna mashi abunka ga namijin duniya, yayi kyau sai dai babu annuri akan fuskarshi kamar kullum Ya haɗe rai kai kace bai ta6a murmushi ba, tsabar yadda ya ɗaure fuskarshi yana faman shan kamshi kamar wanda iska ke yi ma wari. Abinci yake ci kamar baisan tauna shi, hajiya layla dake kallon shi ji take kamar ta shaƙe shi saboda haushin shi da take ji. Dr shureim dake cin abinci a tsanake ranshi ne ya bashi cewar Ana kallon shi a hankali ya dago da idanunsa kai tsaye suka shiga cikin na zeenatu, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido ɗaya, da ɗan mamaki akan fuskarshi Ya zaro mata ido da sauri ta sunnar dakai kasa tana cigaba da sakin murmushi, girgiza kanshi yayi kafin ya maida hankalinsa akan abunda Yake yi. Gaba ɗaya Hankalin benazir baya atare da su, ta tasa plate din abinci agaba ta kasa ci saboda tunanin Yarinyar da ta kira ta a daren shekaran jira, tun washe garin jiya take ta kiran layin baya shiga hankalin ta yaƙi kwanciya. "Benazir Lafiyar ki kuwa? ko wani abu na damunki ne? Tun dazu na lura dake kin kasa cin komai" cikin kulawa mom sarah tayi mata magana. Sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace"ba abunda ke damuna mommy, lafiyana qalou" "Okey, ki fara cin abincin kada ya huce, ba lallai yai maki dadi ba" Amsa mata tayi da toh Spoon ta ɗauka ta soma cin abincin zuciyarta cike fal da tunanin Unaisah Wayar dr shureim ce ta soma ringing daga cikin aljihunsa, Hannu ya zura ya curo ta yana duban me kiran nasa. "Ka tsaya ka kammala cin abincin, Inya so daga baya sai ka yi picking call din" Muryar Alhaji ubaid ce ta katse masa hanzarinta. "Daddy, kira ne mai mahimmanci," "Shikenan je ka daga" mikewa yai a hanzarce yabar dining din Tafiyarsa keda wuya Hajiya layla ta dubi Alhaji Ubaida dake a zaune gefenta tace"ya maganar da mukayi dakai jiya"? Murmushi yadan saki Yana duban fuskar Alhaji musa Yace"ay na fada maki, Ki ƙara hakuri" girgiza kai tayi"bazai yiwu ba, ni bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba! Wannan ay abun kunyane ace muna zaune gidan kaninka....." maganar na dira kan kunnan Alhaji Musa Ya ajiye spoon din hannunsa, fuskarsa a murtuƙe Ya ke duban Hajiya layla, yasan tayi maganar ne don Yaji ta. Gaba daya hankulansu mom sarah ya dawo kanta. "dan Allah ki yi shiru ya isa haka! Muje ɗaki mu yi magana" galla masa harara tayi"wallahi babu inda zanje, ko na bika bai wuci ka bani hakuri ba, Ni nagaji da zama acikin gidan nan, gaba ɗaya a takure nake, Kai ko gudun surutun mutane ba ka yi? tsawon kwanaki kana zaune agidan kaninka tare da Iyalinka"? Hankali atashe mom sarah tace"dan Allah kiyi hakuri, mu kammala cin abincin sai muyi magana...." kafin ta ƙare maganar Alhaji musa Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tuni taja baki tayi shiru. Jikin zeenatu harya fara yin kerma saboda batason tashin hankali arayuwarta, abun kaɗan ke rikitata, ita dai benazir ba ta ce komai ba ta zuba ido tana kallom mommyn nasu dake ta faman tada jijiyoyin wuya. A gadarance Alhaji Musa Yace"Bana son haniya" Harara ta watsa mashi"ay idan baka fita harkar mijina ba, hayaniya yanzu ka fara jin ta, wallahi bakaso zaman lafiya ba, akan me zaka dinga juya mutane son ranka sai kace wasu bayin ka, komai sai dai ka bada umarni abi, to wlh bazan lamunta ba! Hakuri na Ya ƙare, idan shi ka rufe masa baki to ni baka isa kayi galaba akaina ba!" ta fada tare dakai hannu ta bugi gaban table da karfi, kafin ta yunkura ta mike tare da kallon Alhaji ubaid. "Ni zan tafi, tun da naga kai baka da niyar barin gidan," mayar da dubanta tayi ga benazir"tashi mu tafi" jiki asanyaye benazir ta miƙe, nan take zeenatu ta fashe da kuka tana fadin"Inna lillahi mom layla dan Allah kada ku tafi, wallahi banso, mommy kada ki bari su tafi, daddy kace masu su su yi haƙuri su zauna, ko kuma su tafi da ni" Hankalin Tani dana lami ba karamin tashi yayi ba, ganin rikicin dake shirin 6allewa. Wani irin tausayin ta ne ya kama benazir sam batason ta rabu da yarinyar sai dai ba yadda zatai dole tabi umarnin mahaifiyarta. Da sauri Alhaji Ubaid Ya mike muryarshi da 6acin rai Yace"haba layla menene haka? Yanzu abun ki kai kin kyauta? Mutane suna zaman su lafiya kin tarwatsa masu farin cikin su" Dakatar da shi Alhaji musa yai, Cike da isa Ya mike tare da kallon fuskar Hajiya layla dake huci. "Ga hanya nan ki tafi, Allah Ya raka taki gona" bayan ya furta hakan Ya juya azafafe Ya nufi bedroom dinsa Yana shiga ya dauki wayarsa, Call Ya danna tana fara ringing akayi picking Muryarsa akausashe Yace"kada ku bar kowa ya fita daga gidan nan Idan Har bani na baku umarni ba"! On the other hand Muryar wani basamuden mutun ta amsa mashi da cewa "Angama Yalla6ai" sauke wayar yayi "Haba dear, why ba zaka bari su tafi ba, na fa ji kiran wayar da kayi, meyasa zaka rike su? Tun da matar nan ta nuna bata son tafiya to ka ƙyale su su tafi mana," muryar mom sarah a kule tayi maganar tana duban bayan shi... Tamkar tayi magana da bango, babu alamun zai juyo ya fuskance ta balle harya amsa mata, Rai a6ace ta dawo ta gaban shi ta tsaya idanunta cike tab da kwalla ta furta"magana fa nake yi maka....." da buɗar bakinsa sai cewa yai"Toh Uwata Ina sauraron ki" ya fada yana ruƙe qugunsa, Idanunsa akan fuskarta, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin shakkarshi, sam takasa cigaba da yin maganar. Gefen wuyanta ya shafa da tafin hannun sa"sau nawa zan ja maki kunne akan ki daina shiga abun da ya shafi dangina!" cikin sanyin murya tace"bazan ƙara ba" Jinjina kanshi yai, kafin ya ƙara furta wata maganar, Muryar zeenatu ta karaɗe kunnan su. Shigowarta kenan dakin ko sallama babu, Muryarta da shesshekar Kuka take fadin"daddy dan Allah kada ka bari su tafi, ni ban gaji da ganin su ba, ko kuma ka bari na bi su mu tafi a tare" Juyawa yayi tare da daura idonsa akan ta, fuskarta tayi jawur hawaye na sintiri kan kuncinta. Miƙa mata hannu yai da sauri ta nufe shi, hugging dinta yai tare da ɗaura hannunsa kan bayanta yana dan bubbuga shi cikin sigar lallashi. "Ya isa, Ki daina kuka My daughter, ko dan saboda ke bazan bari su tafi ba, dolensu ne su zauna gidan nan ko suna so ko basa so" sauke ajiyar zuciya zeenatu tayi jin abunda yace, Hankalin ta ba karamin kwanciya yai ba, Hajiya Sarah ta kasa furta komai, Jikin ta yai mugun sanyi musamman yadda Taji Alhaji musa Yana magana da gadara babu ɗa'a a kalamansa.... A fusace Layla Ta nufi dakin ta, bayan tace da benazir taje ta haɗo kayanta su tafi, bin bayan ta Alhaji ubaid yayi kamar zai rufeta da bugu sai faɗa yake yi mata, Ko kallo bata isheshi ba, trolley din kayanta ta ɗauko Ta fara kwashe kayanta dake a cikin closet tana jerawa a akwatin. Dawowa dr shureim yayi aɗan rude yake kallon dining din ganin babu kowa, da sauri Ya nufi dakin Benazir Yana shiga ya sameta, zuƙunne gefen gadon ta tana kuka, ga trolley din kayanta da ta gama haɗawa. a ruɗe ya furta Benazir? Lafiya? Meya faru naga hawaye akan fuskarki"? Jiki asanyaye ta mike tare da kallon shi, fuskarta tayi jawur da ita. "Yaya shureim bayan kaje amsa kira, mommy ta fara faɗa akan ita bazata cigaba da zama gidan nan ba, shine tace min inzo in hada kayana mu tafi, ni kuma bana son tafiya saboda ban cimma burina ba, na ganin na haɗu da Aneelerh...." Share mata hawayen ta ya somayi da hannayensa cikin sigar lallashi Yace"kiyi hakuri ki daina zubar da hawayen ki, bana so kina sanya damuwa aranki, amma ni kaina na goyi bayan ku tafi benazir! Ko dan saboda abunda ke faruwa dake agidan nan, Ina jin tsoron na rasa ki, kwata kwata hankalina bai kwanta da zamanki ba' "Yaya shureim idan na tafi tayaya zan haɗu da Aneelerh"? Harya buɗe baki zaiyi magana, kwatsam Wayarsa ta fara ringing, a hanzarce Ya duba sunan mai kiran nashi, wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, arude benazir tace yaya shureim lafiya naga kana murmushi" "Alhamdulillah, Kiran da muke ta jira ne sai yau Allah Ya nufa zamu gana da su, kar6i kuyi magana, abban Aneelerh ne Yake Kiranki...." Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin picking call din kamar zata zauce tsabar murna Muryarta da zumuɗi ta furta"Assalamu alaikum Abie Ina kwana...." Kafin ta ƙare maganar unexpected Muryar Aneelerh ta ratsa kunnanta da wani sauti mai karfi ta furta"BENAZIR!! Mafarki nake ko gaske"? Fashewa da kuka benazir tayi jin muryar aminiyarta da kunnuwanta sukai maraicin ji na tsawon shekaru. Cikin shesshekar kuka tace"Wallahi nice Aneelerh, nice benazir din da kika sani..." Kafin ta ƙare maganar, Itama Aneelerh ta fashe da matsanancin kuka tana fadin"Benazir baki kyauta ma kanki ba! Meyasa? Meyasa? Meyasa kika gudu na tsawon shekaru? Idan wani abu ke damunki ba zaki faɗa mana ba? Kinsan irin kunci da radadin da muka ji bayan tafiyarki? Kin kama hanya kin gudu kin bar jinjira acikin kwamin wanka, Da ranki da lafiyarki baki ta6a kira kinji awani hali Yarki take a ciki ba, wai dan Allah meyasa kikayi haka benazir meyasa.....?" kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da ya sarƙe makoshin ta. Tsananin tausayin su ne Ya kama dr shureim, tun dazu yana atsaye yana kallon Banazir kuma yana sauraran komai da suke tattaunawa. "Dan Allah Aneleerh Ki nutsu inyi maki bayani..." Aneelerh bata bari tayi mata bayanin ba rai a6ace tace"me zaki faɗa min benazir? Ni meyasa ma kika kirani ne? lokacin da yakamata ki kira baki kira ba sai yanzu da lokaci ya kure...." hankali atashe benazir ta ke sauraron ta idanunta sun kaɗa jawur da su la66anta na kerma ta furta"meyasa kikace haka"? Ɗuff taji Aneelerh ta kashe kiran, hawaye na sintiri ta dago tana kallon shureim wanda tuni jikin shi ya gama yin sanyi. "Yaya shureim ta kashe kiran, dama nasani ba lallai ta kula ni ba..." tsananin tausayinta ne Ya kama shi, hannu yasa ya kar6i wayar, Ya sake Kiran Aneelerh taƙi ɗagowa. Text message Ya tura mata _Aneelerh ki ɗaga kiran, Ba benazir bace yayanta dr shureim ne Ina son Yin magana dake_ A 6angaren Aneelerh, Jiki amace ta sulale kan carpet ta zauna dirshan sai kuka takeyi, bakomai take tunawa ba face Angel da tajuddeen, Taji takaicin yadda Benazir tayi watsi da rayuwarsu gashi Yanzu ita benazir din ta dawo su kuma sun 6ata babu su a doron duniya Muryar Angel ta soma tariyowa kalaman da saba fada mata tuntana yar ƙanƙanuwarta _Aunty aneelerh wai meyasa Mommyna bataso na? gani yar kyakkyawa dani kowa rububina yakeyi amma ita, bata damu dani ba, shine ma ta haifeni ta bar ni acikin kwamin ka, idan bata sona to meyasa ta haife ni ay da ta sani ta kashe ni acikin ta_ Ƙarar shigowar sakon ne Ya fargar da ita daga zurfin tunanin da ta shiga, zuciyartace ta dinga tunzurata akan kada ta duba wayar ta ƙyale ta kawai, saboda ta bata haushi, Taji zafin abunda tayi. Wayar sai ringing takeyi taki dubawa, kasa jurewa tayi, saboda ita kanta tayi kewar aminiyartata, bazata taba mantawa da ƙawancensu ba, duk da taci wahalar banezir saboda rashin jin maganarta. Yatsun hannunta na kerma ta ruƙo wayar ta duba sakon, bayan ta gama karantawa, a kagare ta soma kokarin bin kiran don taji me dr shureim zai faɗa mata, aranta tana mai mamakin bayyanarsu lokaci ɗaya. Video Call ta kirasu don ta ƙara tabbar da cewa su dinne, bayan sunyi picking call din kallon kallon suka soma jefawa junansu, kowa yasha kuka, hakika sunyi mamakin canzawar da sukayi, duk sun fara manyanta... Cikin sanyin murya ta furta"ya shureim! Dama kana nan"! Jinjina mata kai yai alamar eh, kafin Ya soma magana cikin nutsastsiyar muryar shi. "Aneelerh, inaso ki nutsu ki saurari abun da zan fada maki" amsa mashi tayi da toh, saboda tana ganin girma dr shureim. "Abun da Ya faru da banezir bayin kanta bane, mu kanmu bamu san da hakan ba sai lokacin da ta dawo, bata a cikin hayyacinta gaba ɗaya alamomin da muka gani ajikinta ya tabbatar mana da cewa Kurciya akayi mata, shiyasa ta gudu tabar yarinyarta batare data tuntu6i kowa nata ba......" atsanake shureim ya fayyace mata komai, Ita kanta benazir din batasan da abun da suke zargin anyi mata ba sai yanzu da taji abakin dr shureim, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, aneelerh kuwa jikinta yagama mutuwa, cikin tashin hankali take ambaton inna lillahi wa'inna ilahirraji'un. Dr shureim Yace"hakuri zamuyi da abunda Ya riga ya faru, bana so muna tuna ba....." nasiha ya cigaba dayi masu har saida Yaga hankalin su Ya kwanta, kafin Ya bar wayar a hannun benazir Ya basu wuri don su gana da junansu Kamar yau ce rana ta farko da suka fara haɗuwa, sai bin kansu suke yi da kallon kurulla, Allah ne kaɗai Yasan irin kewar juna da su ka yi. "Benazir bansan yadda zan misalta maki farin cikin da nake a ciki ba, Allah shine shaidata, Naji dadin ganinki da ranki da lafiyarki" Cikin sanyin murya tace"nima haka Aneeleerh, ashe da rabon zamu gana bayan tsawon lokaci"? Ta fada tana matse kwallar da ta cike idununta. "Aneelerh, Ina Yarinyata dana bari? Ina mijina Yake? Mommy ta fada min basa kasar nan amma ni ban yarda da maganarta ba, dan Allah ki fada min gaskiya, saboda nasan ke kadaice zaki fada min" Fuskar Aneelerhh ɗauke da matsananciyar damuwa take kallon benazir dama sai da tayi fargaban tambayar da zatai mata, tuni taji zafafan hawaye sun cika mata idanunta. "Aneelerh kinyi shiru baki ce komai ba? Pls ki yi min magana wlh ji nake kamar zan zauce saboda ƙagarar da nayi na son ganin su ..." ta faɗa tana dubanta "Kada ki ji komai, Ki faɗamin kawai ko da ace sun mutune zan rungumi ƙaddara..." cikin karfin hali ta faɗa, tun da tafara maganar Aneeleeh ke kallonta gwanin ban tausayi. bata jin zata Iya sanar da ita a yanzu, ko dan gudun kada zuciyarta ta buga, ƙwara ta kwantar mata da hankalin ta. Ƙaƙaro murmushi tayi akan fuskarta "Abun da mami ta faɗa maki gaskiya ne, suna nan cikin koshin lafiya, sun yi tafiya zuwa south korea inda Uncle dinsa abdalla ke zaune, amma ina ji araina sun kusa dawowa" Tsabar farin ciki yasa banezir sakin dariya har fararen hakoranta suka bayyana, Aneelerh dake kallonta tsantsar tausayintane Ya ƙara kamata. "Dan Allah Aneelerh idan kina da hotonta ki turomin inason ganinta, Idan ma kina da number taj din ki bani sai muyi magana da shi, wlh naƙagara da son ganin su" Murmushi Aneelerh tayi"kada ki damu zan tura maki da hotonta har ma dana yaro na, sai dai bani da layin taj bansan da wanne yake amfani acan kasar ba" Da mamaki tace"Aneeleerh dagaske kin haihu? Ya'yan ki nawa yanzu"? "Shi kadai Allah Ya bani, baki ganshi ba, kyakkyawa kamar Angel dinki.." Muryarta na rawa tace"Allah sarki, Aneeleeh, na tayaki murna, Ina mijin ki ko shima hada shi suka tafi korean"? "Atare suka tafi" murmushi benazir tayi kafin ta kuma cewa"ki bani labarin Yarinyata, inason jin kuruciyarta, Ina fata dai bata dauko halina ba.." dariya aneelerh tayi da zolaya tace"like mother like daughter, Har tafi ki rashin ji magana," waro idanu banazir tayi hada sanye hannu ta dafe kanta ɗaya"indai kuwa hakane nasan ba lallai ta yi min da sauki ba, watakil ma ta tsane ni, bata son ganina" ta fada tamkar zata fashe da kuka "Ki ma daina wannan tunanin, taya ɗa zai ƙi jinin uwarsa, ay bata da abu mafi soyuwa da yawuce mahaifiyarta, ni nasan Angel bazata ta6a gudunki ba" kwantar mata da hankali taci gaba dayi, har ta bata labarin unaisah, taci dariya wani wurin kuma ta matse kwalla. "Allah sarki tajudden na barshi da dawainiyar yarinya, abunda yakamata ace ni nayi bansamu damar yi ba..." in a cool voice tayi maganar," shiru suka danyi na wani lokaci kafin Aneelerh tace"Har yau babu labarin Aisha! Baiwar Allah taga rayuwa, gaba daya ƙaddarace ke bibiyar rayuwarmu lokaci ɗaya ƙawancenmu ya tarwatse nayi takaicin rasa farin cikin amintarmu' hawayen dake taruwa acikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta.... Shiru banezir tayi zuciyarta cike fal da jimamin halin da suka tsinci rayuwarsu. "Inaso nazo gidanku Aneelerh, ki kirani da layinki, sai inyi saving contact naki" amsa mata tayi da toh, sunjima suna waya kafin sukayi sallama da junansu.. Meya faru bayan Ummi Ta fuce daga dakin su Unaisah? Da gudu ta nufi dakinta, tana shiga ta bude toilet ta tsaya agaban Sink tana kwarara amai, idanunta sun kada jawur da su, shatun jijiyoyin goshinta sun fito rudu rudu kamar zasu fasa fatarta, tayi kuka tamkar ranta zai bar gangar jikin ta, komai na duniyar nan ya sire mata, taji takaici da tsanar rayuwar da ta daukarwa kanta saboda takasa hakuri ta rungumi ƙaddarar ta, Sai gashi yau taji abunda Ya jefata adanasani, Yan kananun Yara da basu ji ba basu gani ba, wadannan ma tun suna jarirai suke fuskantar jarabawar rayuwa, Ita kuwa da ilminta da hankalin ta da tunaninta ta faɗa harkar karuwanci saboda ta kasa cinye jarabawarta lamarin yayi matukar gigita tunaninta... Faucet ta kunna ruwa ya soma shararowa ta tarfa hannu tana watsa shi akan fuskarta, kamar an zare mata karsashin jikinta, da wata irin kasala ta fito jiki babu ƙwari ta faɗa kan gadonta tare da kifa kanta jikin pillow, bakomai take tariyowa ba face rayuwarta ta baya... Sam ba taji motsin shigowar mutun ba, saboda ta lulu duniyar tunani A hankali batool take tafiya tana tunkarar gadonta, hayewa tayi kan gadon ta zauna kusa da ummi tana leƙen fuskarta "Aunty Ummi," kamar daga sama taji muryar batool, a hankali ta buɗe idanunta da suka kumbura ta daura su kan fuska batool. "Dan Allah ki daina kuka aunty ummi, bana son ganin hawayen ki, bana jin dadi" ta fada muryarta na rawa alamar zata fashe da kuka. Janyota ummi tayi tare da kwantar da ita kan kirjinta, sosai ta rungumeta ta daura hannunta akan bayanta batare data furta magana ba. Aranta tana mai mamakin tawakkalli irin Na Yaran, abunne da daure kai, da ace wani mai karancin imanin ne hakan ta faru da shi da tuni yajima da hadiyar zuciya ya mutu amma su a haka suka jure da dadi da ba dadi sukai ta rayuwar ƙunci a kulle tun kafin su mallaki hankalin su. Numfashi taja, wani irin kaunar yarance taji ta ƙara kama zuciyarta, har ta fara tunanin tawace hanya zata taimaka masu don ganin sun inganta rayuwarsu tun da basu san komai ba . Bakomai ne ya fado mata aranta ba face zagin da ta ta6a yima batool har ta kirata da sunan jahila wadda bata san komai ba sai ci da bacci... Runtse idanunta tayi sosai tana mai jin takaicin kalaman da ta furta mata, gashi yanzu yarinyar tafi kowa kaunarta Shafa sumar kan batool taci gaba dayi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba dasu arungume da juna kamar zasu dawwama ahaka.......💔 ___________________________________✍️ *❤Unaisah Angel💋💝* Fitowa tayi daga part dinsa bayan ta gama gyara masa shi, A hankali take saukowa down daga kan stairs zuciyarta cike fal da tunanin abubuwa da dama wadanda suka faranta mata rai a yau kamar wata zautacciya sai faman sakin murmushi take yi. "Daughter i'm back" miryar taj ce ta katse mata zancen zucin nata, kallon shi tayi fuskarta da fara'a, da sauri ta karasa sauko down, mayafin kanta har yana kwancewa daga kanta ya zame ya faɗo kan kafadarta, sumar kanta ta rufa mata bayanta. Tana ƙarasawa ta fada kan kirjinshi kamar wadanda suka dade basu ga juna ba. Murmushi yasaki yana fadin"sannu da kokari ina fata kin yi abun da Ya dace" ɗagowa tayi da kanta ta daura idanunta akan nashi"har gyara masa part din sa nayi, kafin ma na kammala har ya fita ban same shi ba" "May be ya tafi gidan kakansa ne" acewar chief, "Kinsan me naje yi agida" girgiza mashi kai tayi alamar a'a. "Auntynki na faɗa mawa ta hada maki wani abu mai dadin gaske zuwa anjima zatay baƙuwa, amma fa ban gaya mata wacece zata zo ba" "Naji dadi daddy, kana ji dani" Mayafin ta dake akan kafadarta ya ruko yana fadin"bari na gyara maki shi" A hankali Ya soma naɗa mata shi, bayan ya kammala ya manna mata sumbata kan kuncin ta kafin ya ɗago da kansa kwatsam! Ba zato ba tsammani Yaji saukar dundu akan bayanshi tamkar za'a rusa shi, tsabar zafin da yaji ne yasa shi saurin dafe bayan da hannu, tuni ya fara ganin jiri a cikin idanunsa. Hankalin ta amatuƙar tashi ta wurga idanunta don ganin wane yayi wannan aika aikar saboda itama taji sautin dundun da akayi mashi. Har saida gabanta Ya faɗi lokacin da tayi arba da shi atsaye yana huci tamkar mayunwacin zaki, tsabar fusata jikin shi har gumi yake fitarwa, magana yakeso yayi amma saboda zafin da zuciyarshi keyi mashi ya kasa sai la66ansa dake kerma. Harara ta watsa mashi saboda ya bata haushi, zuciyarta ajagule ta ruƙo hannun taj Tana fadin"Inna lillahi! daddy dan Allah kayi hakuri..."_ bata ƙare maganar ba, danish Ya fusgo ta tare da janyota jikin shi, yasa hannu biyu ya rungumeta kamar zai maida ta cikinsa Lamarin yayi matuƙar ɗaurewa taj kai, idanunsa jawur yake kallon danish Yama rasa me zaiyi, amma tabbas dundun da yayi masa ya kusa yi mashi illa saboda zogin da bayansa keyi mashi kamar an ɗoɗana masa wuta yadda kasan ba hannun mutun bane yayi dundun, yaji zafinsa sosai. Kiciniyar kwace kanta tafara yi hawaye tuni sun wanke fuskarta ganin baida alamun sakinta ne yasa ta daddage ta gartsa mashi cizo kan kirjinsa, ko gizau baiyi ba, saima ya kara hadeta da jikin shi, zuciyarta har tafarfasa take yi mata saboda 6acin rai. Kallon kallon suke jefawa junansu tsakanin shi da tajuddeen, kwata kwata bai yi yunƙurin Janye angel daga jikin danish ba, saboda ya fahinci Yaron ba shi kadai bane tun daga kan dundun da yayi mashi ya shaida hakan. Shigowo Falon big guy da ɗan saurinsa Yana ganinsu Ya nufe su da mamaki Yake kallon Danish daya rungume unaisah "Lafiya? Meke farune"? Taj ne yai karfin halin fada masa abun da danish yayi masa Zuciyarshi ta sosu Harara Ya watsa masa kafin Yace"Sakar ta, tun kafin na 6ata maka rai, kaida bawani koshin lafiya ba har ka fara neman rigima? Ko kunya baka ji ba ka rungume Yarinya gaban ubanta! Idan ma baka sani ba to bari na fada maka wannan da kake gani mahaifinta ne wanda Yai silar zuwanta duniya...." ko ajikinsa bai ma fahimci me Big guy yake nufi ba, sai ma haushin shi da yake ji, Jira yake big guy yakai hannu zai raba shi da ita anan ne zaiga ainihin true colour dinsa... Atsawace big guy yace"baka ji me nace ba, ka sake mana"! "Ka daina yi mashi tsawa, Ka kyale shi kawai, nayi mashi uziri saboda baisan komai ba, kuma Yaro ne sai muna lalla6a shi" Big guy bai tsaya sauraron Taj ba Ya kai hannu zai ja rigar unaisah, wata irin kururuwar tsawa danish Ya daka mashi tamkar saukar aradu, Gaba ɗaya saida suka firgita saboda Yadda sautinta Ya cika masu kunnuwan su, Unaisah dake manne ajikinshi tsabar kiɗima kiris Ya rage ta saki fitsari a wando, saboda firgitar da tayi. idanunsa sun kaɗa jawur Yana huci Ya furta"kada ka kuskura ka ta6aba, Ranka zai 6aci, zanyi maka abun da baka ta6a tsammani ba, Idan har kayi gigin shiga tsakanina da ita...." ya faɗa yana faman cije red lips dinsa, yadda kasan ba daga bakinsa kalaman suka fito ba saboda girman su. da gudun gaske Naufal da Sajeed suka fito daga dakunansu, kamar wadanda aka koro tun wannan tsawar da danish ya kwatsa kowan nan su Ya firgita har wadanda ke adaki, kai hatta Ummi da batool sai da suka farka daga bacci jiki na 6ari suka sauko down stairs, ɗaya bayan ɗaya suke fitowa ƙwansu da kwarkwatarsu, hankalinsu gaba daya yana akan Daninsh dake a rungume da unaisah, jikinta sai kerma yakeyi duk tabi ta ruɗe, numfashinta kanshi dakyar take fidda shi. Kusan atare suka hada baki suna tambayar meya faru? danish dan Allah kayi mana bayani meyasa ka ruke Unaisah ka sake mana ka matseta.. Sajeed ne yai maganar, Big guy daya gama harzuƙa Har Ya yunkura zai Ƙara kamo rigarta Taj yai saurin damƙar damtsen hannun shi, suka hada ido da juna girgiza mashi kai yai alamar a'a saboda shi yasan mai yaji dakyar in ba sai yayi jinyar bayansa ba. "Haka zamu zuba mashi ido muna kallon shi? Baka ga yadda Ya matse ta bane? Ko magana takasayi"! Cikin muryar lallashi Taj Ya dubi Danish dake ta faman zare idanunsa tsabar masifa har ƙanƙance su yakeyi "Dan Allah kayi hakuri ka sake ta, indai saboda ni ne bazan ƙara taba maka ita ba" Mamaki da al'ajabine Ya kama su Ummi dake kallon Ikon Allah "Meyasa zaka bashi hakuri? Kaida ƴarka? Tsoron shi kake ji ne"? A harzuke Big guy yai maganar Taj yace'ba tsoron shi nake ba, fitina ke bana so, idan mukace zamu bi ta karfi da yaji donmu kar6e ta wlh ba zamu iya ba sai dai muja yai mata wata illar kwara mu lalla6a shi' guntun tsoki Big guy yaja, gaba daya haushin danish Ya cika shi, duk da yana tausayin prisoners sai dai ayanzu lamarin danish Ya fara sanya shi kokwanto akansa, gani yake kamar yaron yana da wata muguwar manufa. Haduwa su Naufal sukayi suna ta yi mashi magiya don Ya sake ta, Amma Ya ƙi sakinta Suna acikin wannan Halin, a lokacin da basu yi tsammani ba, Sallamar Salsabeel Ta katse su, gaba ɗaya suka dago suna Kallon shi Ganin shi yasa danish sakin Unaisah tai taga taga zata faɗi da sauri batool ta ruƙota, sai faman haki takeyi tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu.... Sunyi tunanin shi kadaine Yazo, kusan atare muryoyinsu khadeeja Ya daki kunnuwansu, tunkafin su karasa shigowa suka fara kokarin tunano su wanene? Saboda sun haddace muryarsu ko tari sukayi za su iya sheda su. Ɗaya bayan ɗaya suka fara Shigowa bakunansu dauke da sallama, Lokaci ɗaya suka Ci burki suna Kallon su Unaisah dake kallon su, kusan atare zuciyoyinsu ke harbawa da matsanancin karfi, Tsabar rudani da al'ajabi Ya hana su gasgata abunda idanuwansu suke nuna masu, har abada ba zasu ta6a mantawa da muryoyin yan uwansu ba, balle kuma kamannin su da basu ta6a gogewa a idanunsu ba, Kokwanto sukeyi anya kuwa yan uwan sune da suka baro prison ba rai? Ko dai mafarki sukeyi ne? Ko kuwa idanunsu ne suke nuna masu badai dai ba? Tayaya ma haka zata yiwu? Murza idanunsu suka farayi don su kara tabbatarwa da kansu abun da suke gani dagaske ne ko akasin hakan! Kamar yadda suke al'jabin ganin su haka suma su Rubina suke kallon su da matuƙar ruɗani akan fuskokin su, babu mai magana acikinsu falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, har na tsawon mintuna kafin salsabeel Ya fara magana "Abun da kuke tunani dagaske ne, Ku daina kokwanto, wadannan da ku ke gani ƴan uwanku ne, da kuka baro agidan kurkukun ƙaddara, ni kuma sunana salsabeel ɗan tsohuwa tamira, nasan ba lallai ku shaida kamanni na ba, amma ita Unaisah ta gane ni...." fuskar shi dauke da murmushi ya yi maganar, har lokacin babu wanda ya motsa daga cikin su kamar gumaka, tsantsar tsabar rudani da mamaki ne Ya daure su har suka kasa magana, Hatta khadeeja da take da tabin hankali tayi kasaƙe tana bin su da kallo kamar tana so ta tuna su wanene su ...... . "Tayaya ma haka zata yiwu? Ni fa nagaza gasgata abun da idanuna suke nuna min, Kaina Ya ƙulle dan Allah ku fahimtar dani, ni dai a iya sanina kafin mu baro gidan kurkukun ƙaddarar amace muka barsu yanzu kuma sai mu gan su da ransu da lafiyar su? dama wanda Ya mutu Yana dawowa ne"? Sajeed ne Ya faɗa fuskarshi da alamun ruɗani Salsabeel Ya fahimci halin da kowan nan su Ya shiga, In har ba faɗa masu ainihin abunda ya faru yayi ba, toh zaiyi wuya su yarda da bunda suke gani, cikin sanyin murya ya fara ba su labarin abun da ya faru bayan barin su gidan kurkukun ƙaddara...... Waiwaye adon tafiya Tayaya akai Salsabeel tare da su khadeeja suka ku6uta daga gidan kurkukun ƙaddara!? Bayan a iya sanin mu su deeja sun mutu sakamakon zuciyarsu da ta buga❓❓❓ Bari mu koma baya don jin meya faru? Suna shiga Cikin Toilet ɗin, Danish Ya datse ƙofar da sihirin shi, ya Janye tukunyar fulawar daga kan ƙofar, nan ta ke ta bayyana duk irin wahalar da suka sha ta ƙi buɗewa shi Bugu ɗaya yayi mata gaba ɗaya ta 6alle murfin ƙarfen ya dare biyu, Sun yi mamaki da al’ajabi yace da su”Ba zai bi su ba, zai tafi da Akwatin kayan su tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ula idan sun ƙarasa” hankalin su bai kwanta da maganar shi ba, gani su ke yi kamar wani mummunan abun zai faru da su idan baya atare da su, ganin sun toge sunƙi tafiya yasa shi Kwantar masu da hankali, daƙyar ya samu su ka Zuƙunna ƙasa tare da kutsa kai ɗaya bayan ɗaya su ke shiga cikin ƙofar da rarrafe, Bayin Allah ga yunwa ga ƙishin ruwa, ga raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu, Ita kanta hanyar da suka biyo Wata uwar ƙura ga yanar girgizo da ƙwari sai hawan masu jiki su ke yi, Amma saboda rashin kwanciyar hankali yasa basu damu da su ba. Babu mai magana acikinsu saboda ƙunar da ran su ke yi masu, Angel ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan suci gaba da ambaton addu’o’in data koya masu ko sun samu sassaucin a wurin Allah, sun ɗau ki shawararta ahaka suka Dinga tafiya da rarrafe babu ƙaƙƙautawa, idan suka gaji su kan ɗan zauna su huta kafin su dasa da wata tafiyar, A ƙalla sun shafe tsawon awanni Takwas suna rarrafawa ba tare da sun kawo ƙarshen Ƙofar ba, a takure su ke Bayin Allah sun ga rayuwa gwiwowin ƙaffuwan su duk sun gurje sun sage, maƙoshinsu ya bushe ƙamas, tun suna ambaton ƙishir ruwa suke ji har sun gaji sun yi shiru.........”😭 A tsugunne yake gaban gawar tsohuwa tamira, yayin da hawaye ke sintiri kan fuskarsa, idanunsa sun kaɗa jawur da su, zuciyarshi ta gama karaya, tamkar baya a cikin hayyacin shi, gaba ɗaya rayuwar duniyar ta sire mashi, duk sai yaji ya tsani kanshi, bai da wani buri daya wuce shima Ya mutu, sai dai baya son ya mutu batare daya gyara rayuwarsa ba, yana da burin wata rana yayi rayuwar yanci, kamar ko wani ɗan adam, yana son yayi sallah ya gana da ubangijinsa, Tun kafin Ya mallakin hankalinsa Rayuwarsa take a cikin gidan kurkukun ƙaddara cikin kunci da takaici, idanunsa sun jima suna gane masa bakin zaluncin da ake aikawata agidan kurkukun ƙaddara, babban takaicinsa mutuwar mahaifinsa tamira batare da ta cimma burinta ba na ganin ta kawo karshen zaluncin shuwagaban nin gidan kurkukun ƙaddara, bai ta6a tsammanin zata riga shi mutuwa ba, yaso ace yacika mata burinta sai dai kash ƙaddara ta riga fata...... Babban burinshi Su Unaisah su tsira da ransu ko dan su kai labarin gidan kurkukun ƙaddara saboda al'umma su san da zaman shi, ko an samu wadanda zasu yi shahada su kawo karahen zaluncin da ake aikatawa..... Hawayen dake sauka kan kuncinsa a hankali suke ɗiɗɗiga saman gawar tsohuwa tamira.... Gaba ɗaya ya manta da lokacin shi da ke tafiya, sam ya shafa'a ya manta da zancen binne gawarsu da yace zaiyi saboda hankalinsa ya gushe. Kwatsam yayi zurfi acikin tunaninsa, ba zato ba tsammani kamar daga sama Yajiyo sautin dirar wani abu mai matuƙar razanarwa, harta ginin dakin sai da ya girgiza, lokaci ɗaya ya zabura ya miƙe zuciyarshi na harbawa da karfi da karfi, tunkafin ma yaga menene ranshi ya bashi cewar Giants ne na gidan kurkukun ƙaddara, mutanan da babu ɗigon imani aransu, zuciyarsu tamkar dutse take, kurame ne kuma makafi ne basa ji basa gani umarnin Elders din su kadai suke bi. Wani irin wahalallan Yawu salsabeel Ya hadiya mai ɗacin gaske, tuni zufa ta soma wanko mashi, gaba daya yabi ya zauce saboda bai da karfin da zai Iya ja da su, sunfi karfin shi nesa ba kusa ba. Tsabar kidimar da yayi ce ta shi yin zarya a dakin tsohuwa a kokarinsa naya nemo hanyar da zai kubutar da gawawwakinsu gudun kada su wulakantasu .. Kafin yayi wani yunkuri Ya soma jiyo takun tafiyarsu, A matuƙar firgice Yake kallon fadadan kafafuwansu. Kusan su uku ne, Wasu irin gabza gabzan samudawa masu kirar Zakuna, kamar fatalwu haka suka fado dakin, from head to toe sun rufe jikinsu da bakaken kaya baka Iya ganin komai nasu. _Yawu salsabeel Ya haɗiya, ta ko'ina zufa ce ke tsastsafo mashi ta cikin hudojin gashin fatarsa, muryarsa da tsantsar tashin hankali Ya furta"zanyi maku bayani...." bai ƙarasa maganar ba, Muryar wani basamude daga cikin su mai amon gaske Ya furta"Salsabeel ka yi kuskuren ƙetare iyakarka, ka riga da kasan hukuncin wanda Yaci amanar Elders! Sakamakon ka mutuwa ce, zakayi mummunar mutuwa salsabeel zamu kashe ka sannan mu watsa ma karnukan mu naman ka su cinye shi, bayan haka waɗannan ƙasƙantattun gawarwakin da ke a kwance zamu kwanta da su, idan muka gama biyan buƙatarmu da su, zamu cire sassan jikinsu muyi farfesu da su, Kasusuwan jikin su kuma zamu rataye su ne......_ 😳😳😳 *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* YOU MAY LIKE THESE POSTS Previous Post Next Post GET IN TOUCH SUBSCRIBE US[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 20 Complete by Novels Elite Admin June 20, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ _AUNTY XEE Thank you for being there for me. Your support has been a lifeline.💋💞_ __________________________E20✍️ Tashin hankalin da ba'a saka masa rana!, Idanunshi azazzare Yake duban su, jikinshi ya soma kakarwa, tsabar kiɗima zuciyarshi tamkar zata fasa ƙirjinshi saboda bugun da takeyi masa, bakomai ne yafi ɗaga masa hankali ya zautar dashi ba face kalmar zasu kwanta da gawawwakinsu, Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un wannan wace irin musiba ce? Cikin karyayyar murya yace"Ni yakamata ku hukunta saboda ni nayi maku laifi, na roƙe ku ko dan sanayyar dake a tsakanina daku....." Wata irin mahaukaciyar dariya suka tuntsire da ita jikinsu har jijjiga yakeyi kamar ana bugun ganguna, wani daga cikinsu ne ya kuma cewa"Ba sani, ba sabo a tsakanin mu, saboda ka tabka babban kuskure salsabeel ka yi ha'inci, don haka dole ka fuskanci hukunci mai tsanani daga gare mu" Sunan Allah Ya ci gaba da ambato acikin zuciyarshi, duk addu'ar da tazo mashi yinta yakeyi ba ƙaƙƙautawa, har jaraba Yin amfani da sihirin shi yayi don ya ku6utar da kanshi da kuma Gawawwakin amma abun yaci tura, ƙarfin sihirin shi bai kai na su ba, sun riga da sun yi mashi mugun ɗauri na sihiri ba zai iya ta6uka komai ba. Ja da baya ya soma yi ganin suna tunkaro shi, cikin matsanancin tashin hankali, kafin ya ƙurema bangon ɗakin tuni ɗaya daga cikinsu yai zazzafan taku ya damƙi wuyan salsabeel da kafcecen hannun shi, nan take numfashinsa ya soma ƙoƙarin ɗaukewa, ɗaga shi yai sama tun Yana kiciniyar ƙwace kanshi harya fara gazawa idanunsa sun kaɗa jawur sun fiffito waje, nan take ya soma bleeding ta baki ta hanci, wani irin raɗaɗin azaba ne Ya ziyarci salsabeel tamkar ana yi mashi ɗaskanan wuta a jikin shi, fuskarsa tayi jawur jini ya kwanta a fatarsa, hawaye da gudu suke kwararowa ta cikin idanunsa bakomai zuciyarshi ke tariyo mashi ba A lokacin face kalaman mahaifiyarsa Tamira, Idanunsa na akan gawarta.... Numfashinsa na kiciniyar ɗaukewa gaba ɗaya ya gama jigata har ya fidda rai da rayuwa, a lokacin da basuyi tsammani ba suka jiyo sautin dirar wani abu a bayansu, da sauri giant ɗin daya shaƙe wuyan salsabeel ya sake shi jiki ba ƙwari ya kife ƙasa kan shi Ya daki ƙasa daƙyar numfashin sa ke fita da hucin zafi, kusan atare Giants ɗin suka juya baya don ganin menene Ya faɗo cikin ɗakin da har Ya bada sautin mai kuwar gaske. Da wani irin tsantsar Al'ajabi suke kallon shi, yadda kasan saukar aradu Haka Ya faɗo masu Yana huci kamar Mayunwacin Zaki, kwata kwata babu riga a jikin shi sai dogon wandon kakin Giant, jikin shi sai tsuma ya ke yi tsabar fusata, ta ko'ina zufar 6acin rai ce ta ke tsastsafo masa, harta tsokokin jikinsa motsi su ke yi, da wani irin hucin zafi numfashin sa ke fita. Shin Wanene Wannan? To bakowa bane face GARKUWA, dalilin dayasa shi dawowa kurkukun saboda hankalin shi yaƙi kwanciya yasan mawuyacin abu ne Salsabeel ya samu fita daga cikin kurkukun tare da gawawwakin salin alin, ranshi na bashi cewar wani mugun abun zai iya faruwa da Salsabeel ɗin, shiyasa lokacin da su ka shiga cikin makewayin bayan ya buɗe ma su Angel kofa yaƙi bin su yace su fara yin gaba shi zai taho da Akwatin kayan su tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ulla idan sun ƙarasa, yayi hakanne don ya samu damar dawowa ya taimaki rayuwar salsabeel saboda baya son ya rasa shi ko dan saboda halaccin da ya yi mashi a rayuwa bazai ta6a mantawa ba, yaji mutuwar tsohuwa Tamira don haka bazai bari rayuwar salsabeel ta salwanta ba❗ Kallon kallo su ka soma jefawa junan su tsakanin Giants da Garkuwa, wato gaba da gabanta, Aljani Ya taka wuta, banbancin Danish da sauran Giants shi ƙarfin sa Na Evil giants ne masu Star Uku kai ko a cikin su Ya zarce su Power, babban kuskuran da Elders sukayi shine damƙa amanarsu gare shi saboda ya zama garkuwarsu a duk lokacin da za'a kawo masu hari, ba su ta6a tsammanin garkuwarsu zai Iya cin amanarsu ba, shiyasa suka bashi sihirin da ya fi na kowani giant na gidan kurkukun ƙaddara, a halin yanzu babu mai iya karawa da shi sai Elders wato Leaders ɗin su, Danish Yana da kwatankwacin ƙarfin giants ɗari a jikin shi, baƙaƙen shaiɗanun dake a jikin shi wani irin ƙarfi ne da su na fitar shari'a, kuma basa ji basa gani umarnin shi kaɗai suke bi, hatta su kansu elders ba su isa su hana shaiɗanun bin umarninsa ba, kuma su sukayi kuskuren ɗaurashi akan turbar da yake ashe da rabon su yi danasani mai girman gaske, Duk da Salsabeel baya acikin hayyacinshi Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, ganin Danish Ya dawo! Muryarshi na rawa ya furta "meyasa! Meyasa Danish? Meyasa ka dawo? Ina ka baro su Angel? Sautin muryarshi ko fita batayi shi kaɗai yake sambatun shi ba tare daya iya ɗagowa da kan shi ba, saboda raunatar da yayi. Ɗaya daga cikin giant dinne Ya ambaci sunan shi"Garkuwarmu"! Yana huci Yace"Ni ba garkuwarku bane! Garkuwar su ne! idan har kuna son zama lafiya to ku ƙyale salsabeel da gawawwakin nan, Idan ba haka ba, zanyi maku abun da baku ta6a tsammani ba"! da kakkausar murya ta majiyi ƙarfi ya faɗa yana nunasu da yatsan hannun shi. A lokacin kusan suman tsaye sukayi saboda mamakin kalaman shi! haƙiƙa yayi matuƙar ɗaure ma su kai sun firgita da jin furucin sa. "Amma dai wasa kake mana ko"? Girgiza kai yayi "na ta6a yi maku wasa makamancin wannan!? "Idan kuwa har dagaske ne, Elders sunyi kuskuren yarda dakai maci amana! Ka bamu mamaki! Ina ka samu ƙwarin gwiwar da har ka Iya gaya mana magana a gaban idon mu ba tare da jin shakkarmu ba?" Shiru yayi baice masu komai ba. "Tun wuri ka yi gaggawar Janye ƙudurinka, Saboda kai namune baka isa ka juya mana baya ba, har abada kai mallakin gidan kurkukun ƙaddara ne, kuma garkuwarmu, Idanma mafarki ka ke yi to ka farka tunkafin lokaci Ya ƙure maka, duk wani abu da zakai taƙama dashi anan ka same shi, kuma da zarar elders sunji maganar nan, kasan me zai biyo baya......" wanda yayi maganar Ya faɗa yana mai yi mashi kashedi. "Har abada ba zanyi danasanin bijiremaku ba, Shawarar da zan baku shine kuyi gaggawar barin wurin nan idan kunaso ku tsira da rayukanku saboda ni banzo da niyyar na cutar da wani ba, ɗan uwana kawai nakeso na ku6utar daga sharrin ku." Babu yadda Danish bai yi da su ba akan subar salsabeel amma suka sanya kafiya, dama su giants basu da tsoro kuma basa karaya sai dai komai zai faru ya faru, Kafin kace me faɗa ya kaure tsakaninsu tamkar a filin Yaƙi, tuni ƙura da kururuwa sun karaɗe cikin daƙin, bakajin komai sai gurnaninsu mai matuƙar firgitarwa, gaba ɗaya sun rikiɗa sun koma dodanni masu ban tsoro sai kaima juna farmaki su ke yi kamar abokan gaba, Kakin Giant ɗin dake jikinsu Ya faffasa saboda garkuwa ne agare su, idan har ba ciresu yayi ba to bazai iya yin galaba akan su ba balle har Ya yi nasarar kashe su, wani irin bahagon naushi ya soma sakar masu akan idanuwansu duk wanda ya nausa nan take ƙwayar idanuwansa ke zazzagowa cikin Jini Ta faɗo ƙasa, gaba ɗaya Ya zautar dasu Ya nakaɗa masu lugudan wahala, Har saida numfashinsu Yabar gangar jikinsu tukunna Ya zuƙunna Yana huci batare daya canza halittarsa ta mutane ba Yabi su ɗaya bayan ɗaya ya farke ƙirjin kowannan su ya 6an6aro zuciyoyin su Ya tura abaki Yana ci saboda Ya ƙara ƙarfin sihirin shi. Ɗakyar Salsabeel Ya samu ƙwarin gwiwar miƙewa numfashinshi na fita sama sama, muryarsa da rauni Yace "Danish meyasa ka baro su Unaisah Ka dawo don ka taimaki rayuwata, Idan wani abu ya same su fa"? Danish bai tanka mashi ba, har Sai da Ya gama abunda Yakeyi tukunna Ya girgiza jikinshi ya rikiɗa ya dawo ainihin suffarshi ta mutane. Ruko hannun salsabeel yayi acikin nashi yana faman fitar da huci Yace"Saboda rayuwarka tana da mahimmanci, bazan bari na rasa ka ba, nasan cewa zasu iya farmakar ka shiyasa na dawo don na ceci rayuwarka, Inaso na cika maka burinka na ganin ka binne gawarwakin su tsohuwa tamira sannan in ku6utar da kai. Girgiza kai Salsabeel yayi hawaye cike fal da idanunsa yace"Danish ka tafi kawai, Zasu Iya riskarka, wallahi ba zasu ƙyale ka ba, ni kuma bazanso ka ƙara shan wahala arayuwarka ba, Yanzu lokaci ne da yakamata kayi rayuwar yanci Danish, inaso kayi farin ciki kafin kabar duniya, Hakkin ka da aka tauye maka na rayuwa shi nakeso ka samu Danish dan Allah ka tafi, kabarni kawai, ka koma wurin su Unaisah ni basai na rayu ba, rayuwarku tafi mahimmanci agareni nasan zaku haɗa gwiwa don ganin kun kawo ƙarshen elders...." magiya ya dinga yi masa akan ya tafi ya ƙyale shi amma yaƙiya har saida ta kaiga Ya daka mashi tsawa a faɗace Yace"Ka tafi ka ƙyaleni!! nace maka ka tafi! ka tafi !kabarni kawai..." Cikin sanyin murya Danish yake faɗin "bazan tafi ba salsabeel, Idan kaga na bar wurin nan to na kubutar da kai ne..." Gaba ɗaya sun Harzuƙa, faɗa ne ya kaure atsakanin su kamar zasu bugi juna, kwatsam a lokacin da basuyi tsammani ba, sautin tarin Deeja Ya cika kunnuwansu, kamar an dasa masu aya suka dakata dayin sa'in sar da suke yi, kusan atare suka kai idanunsu ga duban inda take a kwance da tsantsar al'ajabi, babu wanda yayi zaton akwai me rai acikinsu, da sauri Danish Ya nufe ta Yana dubanta, idanunta a runtse take sambatu cikin fitar hayyaci take ambaton sunan haris da Angel tana faɗin "ku taimaki rayuwata kuna ganin za'a cutar dani........" kallon juna sukayi shida salsabeel, kafin Ya mayar da dubansa ga sauran gawawwakin dake baje ƙasa da sauri yakai hannu ya ɗan ta6a ƙafar Rubina wani iko na Allah nan take Taja Numfashi da ƙarfi ta fesoshi batare da ta bude idanunta ba, sai la66anta dake kerma, ɗaya bayan ɗaya yake farkar da su babu wanda yake a cikin hayyacin sa duk sun jigata sun galabaita, sai sambatu su ke yi suna ambaton ruwa ruwa za su sha, ƙi shi suke ji. Maimakon salsabeel yayi farin cikin farfaɗowar su, sai ya fashe da kuka yana faɗin "wallahi banso suka rayu ba, saboda bani da yadda zanyi da su, mutuwar ita ce hutunsu, ga shi babu yan uwansu sun riga sun tafi...." Cikin tashin hankali ya ruƙo hannun Danish yaci gaba da faɗin"ka taimakamin Mu binne su kawai, su ƙarasa mutuwa acikin ƙabarinsu, ni banga amfanin suci gaba da rayuwa a wannan duniyar ba, wahala zasu sha idan mutanan nan suka riske mu zasu kashe su ne bayan sun gama wulaƙanta rayuwarsu....", kafin Ya ƙare maganar Danish Yace"bazai yiwu ba, kamar yadda yan uwansu suka rayu suma haka zasu rayu, bazan ta6a bari su rasa ransu acikin gidan kurkukun kaddara ba, ko da kuwa zan jefa kaina cikin hatsari ne sai nayi musu hanyar da za su gudu" da ƙwarin gwiwa ya furta kalaman tare da fucewa daga dakin tsohuwa yaje ƙasan gadon Batool inda suke ajiye robobin ruwa ya dauko su ya wuce toilets din dakin su ya samo masu ruwan da zasu sha, bayan ya dawo yabi su daya bayan daya ya basu ruwan suka soma sha. Salsabeel dake kallon shi tsabar ƙululun bakin ciki baisan sa'adda ya fashe da kuka yana fadin "Danish ka tafi kawai, idan har bazaka taimaka min mu binnesu ba, dan Allah ka tafi zaifi min kwaciyar hankali, Ka rigada kasan bamu da wata hanya da zamu iya ceton su...." Cak Ya tsaya da yin maganar ganin babu danish Kamar walkiya Ya 6ace ma ganin shi, Shiru yayi yana faman haɗiyar yawu cike da zullumin ina Danish Yaje? Ko dai Ya tafin ne ...? Tuni ido Ya raina fata sai kace ba shi bane yake korarsa akan Ya tafi ba, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, hankali atashe yake kallon su Dija dake zazzaune a ƙasa cikin fitar hayyaci suke ambaton sunan ƴan uwan su musamman sunan Unaisah da na Danish, gaba ɗaya sun zauce, gawar mahaifiyarsa ya kalla tuni wani kukan ya kuma zuwa mashi cikin matsanancin tashin hankali Ya soma ƙwalawa Danish Kira don Ya dawo ya taimake shi ko ya samu ya binne su. Jin shiru babu alamun zai dawo ne ya sa shi zubewa kan gwiwowinsa Yana ta faman yin shesshekar kuka kamar ransa zai fita. Kamar daga sama Yaji motsi a ɗakin, A firgice Ya ɗago da idanunsa azazzare ya kai duban sa ga Bookshelve ɗin ɗakin tsohuwa tamira dake Ta motsi, Kafin yai wani yunkuri gaba ɗaya Ya rikito Ya rubza ƙasa, Jikinsa na 6ari Ya miƙe yana kallon ƙofar da ta 6ullo, da matuƙar mamaki akan fuskar shi. Ta cikin ƙofar Danish ya fito, fuskarshi sharkaf da gumi Ya dubi Salsabeel. "Zamu Iya tafiya" wani irin farin Cikine Ya lullu6e Salsabeel. A ruɗe ya furta"Danish tayaya akai ka gano ƙofar nan? Ban ta6a sanin akwai ta ba, kuma bana tsammanin ko ita tsohuwa tamira tasan da zaman ta" ya faɗa cike da son jin ƙarin bayani. Yana faman huci yace"Kada ka manta, ka riga ni tsintar kanka acikin kurkukun ƙaddara ni kuma nafi ka sanin komai na cikin sa, duk wata ƙofar sirri dake a kurkukun nan nasan da zamanta, tabbas tsohuwa bata san da wannan kofar ba, tsohuwar hanyace da aka jima da toshe ta, ni da kaina na sake haƙa ta da sihiri na, Idan muka bi ta cikin ta, zata 6ular da mu cikin wani kogon dutse dake wajen kurkukun nan, dalilin dayasa na za6i ku raba hanya da su Unaisah saboda nasan zasu iya farmakar mu idan har suka gano abunda ke wakana, inaso na raba masu hankali ne watakil in mukayi hakan wasu su rayu daga cikin mu" Bazai iya jure kallon Danish ba, Yaron Ya burge shi, Ya yi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba, ya taimake sa a lokacin da rayuwarsa take akan ga6ar salwanta, da sauri ya janyo shi ya rungume shi yana kuka, kafin ya raba jikin su cikin sanyin murya yace "Amma danish su Angel fa? Yakamata ka koma wurinsu suna buƙatar ka, bana so wani abu ya same su" Girgiza kai Danish yayi "kada ka damu, babu abunda zai cutar da su, saboda na rigada na ɗaure hanyar da suka bi da sihiri babu wani mahalukin da ya isa ya iya tsaga kofar ya shiga balle har ya cutar da su, kafin nazo nan sai da na kiyasta awannin da za su yi kafin su ƙarasa kofar da zata 6ular da su waje ni kuma zan riga su komawa bayan na taimake ku" Murmushin farin ciki salsabeel ya saki, Basu tsaya bata lokaci ba suka yi kokarin taimaka ma su Hibba don su miƙar da su tsaye, saidai mutun biyu daga ciki kafafunsu sun kasa ɗaukar su sakamakon abunda tsohuwa Zafreen ta yi ma su, bayin Allah sai ihun azaba suke saki, da sauri Danish Ya sungumi deeja ya goyata a bayan shi, ya sanya mayafin daya ɗauko a ƙasa ya ɗaureta tamau, kafin ya ɗauki Rubina ya ɗaurata a kafaɗar shi dama su biyune basu iya tafiya. shi kuma Salsabeel ya yi amfani da bargon tsohuwa tamira ya nannaɗe gawarta aciki ya ɗaurata a kafadarsa. A haka suka bi hanyar mai duhun gaske ga zafi tamkar ana rura garwashin wuta, sunci baƙar wahala su sarah kamar numfashinsu zai ɗauke. Cikin awanni takwas da su Angel sukayi suna rarrafawa akan hanyar su duk wannan abun Ya faru, baifi awa biyar ba su salsabeel sukayi nasarar fita daga cikin gidan kurkukun ƙaddara hakan na nufin sun riga su Angel ku6uta saboda tasu hanyar batai nisan wadda su Angel suka bi ba. Bayan su Salsabeel sun 6ula cikin kogon dutsen, Danish Ya sauke deeja da Rubina daya ɗauko, shima Salsabeel ya sauke gawar tsohuwa tamira, su hibba duk suka zube agajiye har lokacin bakunansu basu gushe da ambaton sunayen ƴan uwansu. Kallon juna sukayi kowan nan su na haki, da sauri salsabeel ya ruƙo hannun Danish, cikin sanyin murya yace "Danish, bazan ta6a mantawa da halaccin da ka yi min ba, kayi min abunda har abada bazan ta6a mantawa dakai ba, kaine silar ku6uta na daga Gidan kurkukun kaddara kuma kaine silar cikar burina na ganin na cika alƙawarin mahaifiyata dana ɗaukar mata akan in rufe gawarta kada in bari ta wulaƙan ta, Danish ko a mafarki ban ta6a tunanin akwai ranar da zan bar gidan kurkukun kaddara ba, nasha jaraba guduwa nida mahaifiyata amma mun kasa saboda karfin sihirin mu bai kai ba, sai gashi a sanadiyar ka nayi nasarar fita...." tuni hawaye sun wanke fuskarshi. "Danish, Koda ace ban rayu ba, ni ka gama min komai wallahi, koba komai na shaƙi iskar duniya bayan tsawon lokaci da na kasance a kulle" ya faɗa yana duban cikin idanunsa "ni dai burina ka yi rayuwar farin ciki tare da yan uwanka, ubangiji Allah Ya kare min ku ya tsareku a duk inda zaku kasance, bani da tabbacin zamu sake haduwa wataƙil ma ba lallai mu rayu ba....." bai ƙarasa maganarba ya fashe da kuka mai cin rai, da sauri Danish ya janyoshi suka rungume juna sosai suka kankame jikinsu. Bubbuga bayanshi Salsabeel yai da hannunshi "ɗan uwana, ka kula min da kanka, wallahi ina mutuwar sonka tun farkon ranar da aka kawo ka gidan kurkukun ƙaddara a cikin tsumman ka, naso ka Danish, zan tafi da kewarka, Allah ya rayamin kai Danish, Ina fata wata rana kaima ka zama cikakken musulmi, ka yi rayuwa kamar kowa kayi Aure ka hayayyafa....." Lumshe idanu Danish yayi cikin sanyin murya yace"ina sonka ɗan uwana, nima zanyi kewarka, ka kula min da kanka, ina fata mu sake haɗuwa" Yana faɗa Ya raba Jikin shi daga na Salsabeel, A hankali ya soma tafiya yana ja da baya yana duban Salsabeel da ƴan uwan shi waɗanda kwata kwata basa a hayyacin su, wasu irin zafafen hawaye ne suka cika idanuwan Danish bai daina kallon su ba har saida yayi nisa kafin Ya 6ace ma ganin su. Bai dira a ko'ina ba sai a bakin kogon bishiyar da su Angel zasu 6ula, adai dai lokacin su kuma har sun ƙaraso bakin kogon bishiyar suna ta faman ambaton sunan shi. Bayan tafiyar Danish A cikin Dajin salsabeel Ya samu wuri a gefen wata bishiya ya binne gawar tsohuwa tamira, ya zuƙunna gaban ƙabarinta yai mata addu'o'i yasha kuka kamar ba gobe, har shaida sai da yayi ma kabarin nata saboda yana da burin wata rana ya kawo masa ziyara tare da ƴan uwansa prisoners don su yi mata addu'a. (Masu karatu kunji yadda akai salsabeel da su Deeja suka ku6uta daga Gidan kurkukun ƙaddara, nasan wasu zasu ce tayaya har suka dau lokacin nan batare da an ritsa da su ba? To idan ba zaku manta ba, shuwagabannin kurkukun ƙaddara basa a ciki, bayan haka an samu tawayar tsaro, sannan babu wanda yasan meke faruwa a sashen su Angel saboda an rikita lissafin Allon tsafin su, su kan su waɗannan giants din da suka shigo sashen har suka ga salsabeel, bawai sun san me suke shiryawa bane, sun zo ne domin tafiya da su Deeja zuwa wani sashe na daban da suke tarasu don su basu ruwan sihiri wanda zai dawo masu da jinin al'adar su saboda su samu damar gudanar da black night ɗin da za'ayi a ƙarshen watan, amma saboda 6arnar da Danish yayi masu yasa duk wani shirinsu ya wargaje, haƙiƙa sunji zafin tafiyar garkuwa da kuma yaran daya tseratar daga tarkon su, wannan ne yasa lokacin da suka yi taron zaman tattaunawa ɗaya daga cikin Elders Yace _“Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu miƙe tsaye mun nema ma kanmu mafita ba, to tabbas za’ayi nasara akan mu, Ko a tarihi ba’a ta6a samun prisoners ɗin da suka tsira daga kurkukun ƙaddara ba, su ne na farko kuma sune na ƙarshe, da farko sunyi nasarar ƙetare kurkuku da taimakon Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani mahaluƙin da ya isa ya iya ƙetare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya ɗauke shi munyi nasarar yi mashi abunda zai dawo gare mu sai dai wani abun al’ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi_ Kamar yadda suka ce tun tarihin kafuwar kurkukun ƙaddara ba'a ta6a samun prisoners da suka tsira ba sai akan su, kuma ba kowa bace sila face ƙaddarar kurkuku, da ace unaisah ba ta kasance a gidan kurkukun ba, wallahi Danish bazai ta6a yunƙurin taimaka ma wani don ya gudu daga cikin sa ba shiyasa bai ta6a taimakon su Deeja ba bayan yana da hanyar da zai iya fitar da su. Salsabeel Ya ci baƙar wahala wurin ɗawainiya da su Hibba, babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, saboda yankin da su ka faɗo a dajin babu ko kayan marmari da mutun zai sha, yasha jaraba yin amfani da sihirinsa don ya sawwaƙa masu wahalar amma abun ya faska, Saida ta kai ga ciyawa su ke ci ko su ci ganye don suyi maganin yunwar cikinsu, ga Deeja ba hankali tun da tafarfaɗo sambatu takeyi shi kuma Mubeen wasu irin marurai ne masu masifar zafi suka mamaye fatar jikin shi, kullum sai yayi hauka kamar zai rasa ransa saboda raɗadin azaba, ga uwar rana dake ƙwalo masu ta ko'ina ba sauki, ga damuwar rashin yan uwansu sunyi kuka tamkar zasu kashe kawunansu, baƙin cikin da suka ƙunsa baya misaltuwa, hakika salsabeel yayi namijin kokari wurin ganin Ya basu kulawa duk da wani lokacin abun nema yake yafi ƙarfinsa, gaba ɗaya sun jigata sun sha wahala, babban tashin hankalinsu miyagun halittun daji dake kawo masu farmaki, kusan kullum ne sai Salsabeel Ya zubda jinin shi wurin faɗa da su. Satin su ɗaya acikin dajin suna shan baƙar azabar rayuwa, acikin rana ta takwas suna cikin tafiya agalabaice sunata yi ma Salsabeel kukan yunwa suke ji maƙoshinsu zafi yake yi masu ruwa zasu sha bawan Allah Ya rasa ya zaiyi da su, da gudu Ya nufi Cikin dajin yana neman inda zai samo musu ruwa tun yana tafiya da kuzarinsa har ƙafafuwan sa suka fara sagewa sai da yagama shan wahala bai samu ruwan ba yana kan hanyar komawa wurinsu kwatsam ya faɗa wani yanki na dajin ba zato ba tsammani ya hango gungun Sojojin ƙasar Ghana da suke yin atisayen horaswa a dajin, da gudu ya tunkare su kamar mahaukaci haka suka ganshi Ya faɗo masu, har sun saita shi da bindigu ya zube kan gwiwowinshi ya fara rokon su akan su taimaka mashi da ruwan sha, gaba ɗaya sojojin suka kewaye shi hannunsu ruƙe da bindigu saboda basu yarda da shi ba, sunyi tunanin wani mugunne shiyasa basu bashi taimakon daya buƙataba, tsawa suka fara daka mashi suna tambayar shi wanene shi? Meyake yi a cikin dajin, sam ya kasa ba su amsa, kwatsam ana haka sai ga su mubeen sun watso da gudu iya ƙarfinsu suna neman shi wata dabbar daji ce ta biyo su aguje, a gaggauce sojojin suka harbeta da bindiga tun kafin su ƙaraso nan take suka tarwatsa kan dabbar ta faɗi ƙasa tana birgima, ai koda sojojin suka ga prisoners sanye da jajayen kaya masu numbers a jikinsu sai suka fara zargin salsabeel ne Yayi garkuwa da su tun da shi ne babba acikin su kuma jikin shi akwai zanan tattoo, wanda alama ce ta tambarin wata ƙungiya, ba su tsaya bata lokaci ba suka ɗaure Salsabeel da igiya tamau, su Mubeen sunata kuka suna rokonsu su ƙyale masu ɗan uwansu amman ko ta kansu sojojin ba su bi ba, gaba ɗaya suka sanya su a bayan motarsu ta sojoji, ba su nufi ko'ina da su ba sai cikin ƙasar Ghana. Bayan isar su, A headquarter suka ruƙe salsabeel wurinsu, su kuma su Hibba Asibiti suka miƙa su ganin muggan raunin dake a jikin su, babu irin bugun da sojojin nan basuyi ma Salsabeel ba don ya faɗa masu me yakai shi daji tare da ƙananun yara amma yaƙi faɗa masu, sai ce masu yai bazai iya tuna komai daya faruwa da shi ba, ya faɗi hakanne saboda bai yarda da sojojin ba yasan ma koya faɗa masu gaskiya ba lallai su yarda ba, A ƙalla ya shafe kwana uku a hannun sojojin kafin ya faɗa masu cewa su ƴan nigeria ne, iya abunda zai iya tunawa kenan a rayuwarsa, ba su sake shi ba har sai da su rubina dake a Asibiti suka samu lafiya sunata tambayar ina ɗan uwansu Salsabeel tukunna sojojin suka gane cewa ba mugu ba ne, ba su tsaya 6ata lokaci ba don sun fahimci al'amarin su babba ne ba kamar rahoton da Asibiti suka bayar, hakan yasa suka tuntu6i hukumar sojin Nigeria don su sanar da su dangane da yaran inyaso sai su miƙa case ɗin wurin su. Lokacin da saƙon Ya riski su Sir Mubarak, bayan ya duba duka bayanan yaran, nan take ya yanke shawarar kiran chief owais don ya sanar da shi zancen case ɗin saboda yafi dace wa da hukumar Isod, su yakamata case din yaran ya kasance a hannun su saboda abune da ya shafi 6angaren bincike. Chief Owais yayi farin ciki lokacin da Sir Mubarak ya sanar da shi, dama a lokacin sunata faman bincike kan yadda zasu gano Unaisah, daga shi har taj sunyi tsammanin cikin yaran zasu ga Angel, sai dai ko da sukaje Ghana suka dubasu babu ita aciki, aranar da sukaje basu kwana ba, sai da suka haɗa yaran gaba ɗaya tare da Salsabeel suka tafi da su a privet jet din chief suka shigo Nigeria.... Bayan komai Ya lafa, Sun sama masu gidan da zasu zauna, basu fara bincikar su ba don sun lura da ba'a hayyacinsu suke ba, sai dai suna lura da duk wani motsin yaran sunyi matuƙar yin al'ajabi da irin rayuwarsu, ba su san komai ba, kamar ranar aka haifo su duniya, daga sunci abinci sai bacci, ba zancen yin sallah, ranar da boss ya kunna masu kallo a tv sunga tashin hankali, kuka suka dinga yi ganin baƙon abu da ba su ta6a gani ba, a ƙarshe deeja ce tayi silar mutuwar tv ɗin. Chief ne ya ɗaukar ma su Jazz a matsayin likitan da zai dinga duba lafiyar su, kafin ya bashi aikin sai da ya gargaɗe shi akan kada ya kuskura ya sanarma kowa ko da kuwa mommynsa ce, shiyasa dr jazz yaƙi sanar ma kowa nashi wanda silar hakan yaja har sir mubarak ya fara zargin shi akan wayar da yake yawan kama shi yanayi ta maganar gidan kaji, matsalar da aka samu shi Sir Mubarak baisan da zancen Aikin da Jazz ya ke yi ma chief owais ba, sannan baisan a gidan da chief owais ya killa ce su ba, amma Yana bibiyar case din yaran don jin wani hali ake ciki game da binciken su. Bayan wasu yan kwanaki, Su chief suka tuntu6i Salsabeel suka tsare shi da tambayoyi dangane da rayuwarsu, bai 6oye masu komai ba gaba ɗaya ya sanar da su, wa'iyazubillah kusan zaucewa sukayi saboda tsananin tashin da hankulansu suka yi, ba su ta6a jin labarin daya gigita su ba irin wanda Salsabeel ya ba su, abu kamar ashirin wasan kwaikwayo amman wai a zahiri yake faruwa zuciyoyin su sun karaya ainun. to a cikin labarinsa ne suka ji ya ambaci sunan Angel, sunyi matuƙar girgiza da jin cewa tana a cikin su, kuma sun raba hanya da su, hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, musamman taj kamar zai zauce jin cewa Angel dinsa tana a cikin su, ba dan zuciyar imani ba da tuni ya haɗiyi zuciya ya mutu, ganin yadda yake kuka kamar ƙaramin yaro yasa Salsabeel tambayar shi meya faru, Chief ne ya bashi amsa da cewa yarsa ce Angel ɗin da ya ke magana akai, wani irin farin cikine ya lullu6e Salsabeel ganin Mahaifin unaisah, jiki na rawa ya ruƙo hannun shi tamau ya fara jinjina mashi yana faɗin ya gode ma Allah saboda yarinyarsa tana da kaifin basira Allah yayi mata baiwar da zaiyi wuya asamu mai irin ta, bayan haka yace da shi ya kwantar da hankalin shi, in sha Allah babu abun da zai faru da su saboda suna atare da garkuwa yayi imanin in har ba lokacin mutuwarsu ne yayi ba to kuwa zasu ku6uta batare da sun cutu ba, abun da ya dace shine su tayasu da addu'a kuma a bibiyi dajin evil forest inda rabon agansu toh, shi kanshi Salsabeel ɗin yayi mamakin daɗewarsu a dajin, amma da yayi zurfin tunani sai ya tuna cewa Danish baisan inda zai kai su Unaisah ba, shi iya rayuwarshi daga gidan kurkukun ƙaddara sai cikin dajin evil forest, bai ma ta6a sanin akwai wasu mutane dake rayuwa a wajen dajin ba, kuma hada ƙarin ba su da taswirar dajin da komai zaifi zuwa masu da sauƙi, saboda dajin evil forest kurman dajine yana da wuyar sha'ani. Jami'an isod sun yi matuƙar ƙoƙari wurin ganin sun gano su a dajin, kusan kullum ne sai jiragensu sun kewaye shi suna shawagi Allah ne dai bai nufa za su haɗu da su ba. Babban abun da yaja ma su Angel daɗewa a dajin, Lokacin da Danish ya ke yin amfani da sihirinsa wurin jigilar ɗaukarsu idan dare yayi lokacin sun yi bacci yana yin tafiya mai nisa da su duk don su nisanta da gidan kurkukun ƙaddara silar hakan yaja har suka 6ace hanya suka bar yankin da ya kamata su faɗa, sukai can wani yankin daban. _Alhamdulillah, Kunji yadda akai Su salsabeel suka ku6uta daga gidan kurkukun ƙaddara, da kuma yadda akai suka haɗu da Chief Owais, kuma cikin ikon Allah daga baya sai gashi suma su unaisah an ceto rayuwarsu, a ranar da sojin america suka tuntu6i chief da case din samun yara yan Nigeria a daji, wani irin farin cikine ya lullu6e su, anci sa'a a lokacin yaje babban burnin america kuma sai ga labarin tsintar su unaisah, tunkafin suga su wanene ransu ya basu cewar sauran yaran ne kuma zaiyi wuya in babu ita acikin su, cikin ikon Allah sai ga hotunansu sun gani wayyo Allah tsabar murna lokacin da chief ya turama taj hotunansu da yake shi yana a Nigeria, ko runtsawa baiyi ba adaren ranar da suka shaida baiyanarta_ _A tsanake salsabeel ya ƙarasa ba su labarin yana duban fuskokin su_ *Mu haɗu Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya* Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 21 Complete by Novels Elite Admin June 25, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ _________________________________E21✍️ A tsanake salsabeel ya ƙarasa ba su labarin yana duban fuskokin su, waɗanda suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, sautin koke koken su ya cika falon, ta ko'ina shessheƙar kukan su ce, Ni kaina bazan Iya misalta zunzurutun farin cikin da ya mamaye zukatansu ba, saboda baya faɗuwa abun sai wanda ya gani da idanunsa, kamar an ruke kafafuwansu sun kasa motsawa su ƙarasa ga junansu, sai kallon ƴan uwansu suke yi kamar yarda suma suke kallon su, ashe rai kan rai? Ashe da rabon zasu gana da junansu? Muryar na rawa suka soma ambaton sunayensu Deeja Eve Yasmin, Rubina, Hibba, Sarah Mubeen, la66ansa na kerma suke ambaton sunayensu, gaba ɗaya rayuwar su ta prison ta dawo masu sabuwa fal acikin zukatansu wani irin tsantsar tausayin ƴan uwansu ne ya kama su jin irin azabtuwar da su ka yi a daji. "Ba kuka yakamata kuyi ba, Allah Ya kamata ku gode mawa, da ya sake haɗa ku da yan uwanku da ransu da lafiyarsu..." tun kafin Taj Ya ƙarasa maganar, cikin sagewar gwiwa gaba ɗaya suka zube kan gwiwowin su atare su ka yi Sujudash shukr, khadeeja ce ka ɗai ba tai sujjadar ba, hannayenta ruƙe da takalmanta da ta rungume a ƙirjinta sai faman zare idanunta ta ke yi tana ƙyafƙyafta su, hatta yanayin fuskanta ya canza ga dukkan alamu ƙwaƙwalwarta ce ke ƙoƙarin tariyo mata wani abu da ta yi loosing din shi sai dai kash ta ƙasa tunawa sai ma kanta da ya fara juya mata. Lokacin da suka ɗago daga sujjadar suna yiwa Allah kirari haɗi da yi mashi godiya, fuskokinsu sunyi jawur da su saboda kuka, da sauri suka fara rungumarsu a jikinsu kamar zasu mayar da su cikin su, ɗaya bayan ɗaya suke hugging dinsu hadi da sumbatar kuncinsu, sautin muryoyinsu masu dauke da tsantsar annurin farin ciki sun cika ko'ina na dakin, Haris sai faman tambayar deeja yakeyi wai fa bai gane ta ba, ba shi ba hatta Unaisah tambayar deeja takeyi suna ta fadin Ina deeja take bamu ganta ba .... salsabeel da ke sauraronsu dariya ce kumshe a bakinshi, Da hannu ya nuna masu ita tare da cewa"Gatanan tana kallon ku, sai kunyi hakuri da yar uwar taku, ba lallai ta gane ku ba..." tunkafin Salsabeel Ya karasa yi masu bayani haris ya nufe ta da gudu aikuwa ta watsa aguje kamar wadda taga wani mugun abu, bawan Allah kamar zai fashe da kuka saboda ƙagarar da yayi na son ganinta, Muryar shi da shesshekar kuka yace "Deeja na kin manta ni? Ni ne fa haris dinki na gidan kurkukun ƙaddara!..." fashewa tayi da kuka, hankali ya dawo kanta murya na rawa take fadin"wallahi ba kai bane Haris dina ba, ƙarya kake yi min ni bansan ka ba, Haris dina baƙi ne ba fari ba, kuma shi ba siriri bane' gaba ɗaya suka sanya dariya ga hawaye akan faces dinsu "Deeja ni fa baki gane ni ba"? Unaisah ce tai maganar, tana nuna mata kanta da yatsa, maƙe mata kafaɗa khadeeja tayi"wayyo Allah ni wallahi ban san su wa ne ne ku ba, Wai ya salsabeel ba cewa kai wurin gasar kyau zaka kaimu ba to su wadanda su wanene ni sun wani tsareni da idanunsu" tana kuka ta faɗa. "Khadeeja baki gane su ba? Ƴan uwanki ne fa" salsabeel ne ya fada yana kokarin fahimtar da ita watakil silar hakan ta dawo hayyacin ta. "Deeja haris dinki ne fa, abokin kukan ki me share maki hawayen ki, dan Allah ki tuna ni deeja, wallahi bakisan haukan rashinki da nayi ba, nayi kewarki deeja kamar zan zauce, har jinya nayi saboda ke" ta6e mashi baki tayi. "Wallahi bakai bane haris dina ba, ay shi ba haka yake ba" Dafe kan shi yai da hannu ɗaya zuciyar shi ajagule yace "Na fahimce ki, nasan na canza kema kin canza khadeeja, Ki kalle ni da kyau ni ne dai wannan haris din naki" harara ta watsa mashi tana faman zumbura bakin ta. magiya suka dinga yi mata a karshe da sukaga bata da niyar bari su ta6a ba, aiko da gudu suka nufeta gaba daya suka ɗauke ta suka ɗaga ta sama suna jujjuyata, tuntana kuka tana fadin su sauke ta ƙasa, Har dai ta fara tiƙar dariya ba don ta gane su ba, sai don jin dadin abun da sukeyi mata, sauke ta kasa sukai da sauri Haris ya rungumeta ajikinshi suka ƙanƙame juna, ta yi lamo tana faman sauke ajiyar zuciya kamar tana son ta tuna shi sai dai takasa. Ruƙo hannun Mubeen Angel tayi acikin nata, idanunsu cike tab da ƙwalla suke kallon juna, ta ji tausayin shi, ba zata ta6a manta abun da ya faru lokacin da zasu bar kurkuku ƙaddara ya yanke jiki ya faɗi haka suka haura kafa suka barshi, bawan Allah ashe har ciwo yayi, Huggin dinsa tayi a kirjin ta, hannayenta daddafe da bayan shi, shima ya dafe ta cike da kaunar junansu, Hankalin danish bai kai kansu ba, ya basu ya baya, hannayen sa suna acikin na salsabeel sai faman sakar ma juna murmushi sukeyi, wani irin dadi ne Ya lullu6e kowannan su "Kaine silar komai danish" salsabeel ne ya fada yana dan bubbuga shoulder din sa alamar jinjina Duk wannan abun dake faruwa akan idon sheikh imam babu wanda Ya lura da shi, Shigowar sa kenan falon Ya taras da abun farin cikin dake faruwa hakan yasa shi tsayawa abakin kofar yana kallon abunda yai matuƙar faranta ransa. Hatta Taj da big guy murmushi ne ɗauke akan fuskokinsu, kamar waɗanda akai wa albishir da gidan Aljanna babu wanda basu burge ba acikin su, sun tausayawa rayuwar su, ga wani irin son yaran da kaunar su da ya mamaye zuciyoyin su. Ummin america dake ta kallon su, idanunta sun yi jawur saboda kukan da tasha, dama ba ta jima da gama yin shi ba, gaba ɗaya idanunsu na akan prisoners dake ta tsalle tsallen farin ciki a tsakar falon suka rurruƙe hannayen junansu tare da kewaye kawunansu suka haɗasu guri guda gwanin ban sha'awa yadda kasan fararen furanni a garden tsabar kyan da sukayi..... Cikin Harshen Larabci sheikm Imam Ya fara karanto masu addu'o'i yayin da yake ƙarasa shiga cikin falon gaba ɗaya hankali ya dawo kan shi, da sauri suka raba kawunansu tare da ɗaga hannayensu sama suna amsa mashi da ameen ameen, mutun ɗayane baya amsa addu'ar sheikh imam wato Danish, har Yanzu bai matsa daga gefen Salsabeel ba. Bayan ya gama jera masu addu'o'in kowan nan su Ya shafa akan fuskarsa. Kafin su sauke hannayen su, sautin takalman mutanan da ke shigowa falon taja hankalin su ga duban su Chefs din dake girka abincin gidan ne suka shigo hannayen su ruƙe da ƙaton Cake stand mai hawa bakwai an ƙawata shi yayi matuƙar jan hankulan su. Bayan sun sauke masu cake din akan glass table, ba su tafi ba, tsayawa sukai don ayi shagalin da su. Cikin harshen turanci ɗaya daga cikin chef din yace"muna tayaku murnar haɗuwa da ƴan uwanku, kuma muna tayaku murnar samun ƴan ci arayuwar ku, sannan muna yi maku fatan Allah ya dawwamar da farin ciki arayuwarku" gaba ɗaya suka haɗa baki wurin yi masu godiya. "Bismillah, wannan na ku ne, chief ne Ya bada Umarnin A haɗa maku Cake, saboda ku ji daɗin yin shagalin murnar ganin yan uwanku" ɗaya daga cikin chefs dinne Ya faɗa, bayin Allah saboda farin ciki hawaye ne suka cicciko idanunsu waɗanda suka kumbura saboda kukan da suka sha. Hannayen su ruƙe cikin na juna suka kewaye Cake din, Lokaci ɗaya wani abu ya faɗo masu aransu wanda ba komai bane face farkon zuwan Sabbin prisoners gidan kurkukun ƙaddara, ba zasu ta6a mantawa da lokacin ba har abada, ranar da giants suka kawo masu cake sunata murnar yanka shi akarshe majnoon yayi ajalin shi. cikin shessheƙar kuka jemimah tace"Genie Ina majnoon ɗina? shi bai dawo ba? Yakamata shima Yazo tun da su deeja ma da suka mutu sun tashi" kumatunta jawur tayi maganar, gaba ɗaya ta karya masu zuciyoyin su. "Jemimah wanda ya mutu ba ya dawowa sai dai idan dama kwanansa ne ba su ƙare ba, Majnoob Ya mutu ba zai ta6a dawowa awannan duniyar ba, amma in sha Allah zamu haɗu da shi agidan aljanna" yayin da Unaisah take yin maganar bakomai take tunawa ba face fuskar majnoon da unaizah, hakika ba zasu ta6a mantawa da farkon zuwanta gidan kurkukun ƙaddara ba, lokacin da ta sauko kan stairs cikin shiga ta school uniform red colour, ƴar gayu da ita wayayya ta goya back dinta abayanta. muryarta ce ta soma yi ma unaisah gizo a kunnanta. _Hi, Am unaizah ƴar gidan daddy, can i know u_ _that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ɗin ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci_ Runtse ido unaisah tayi yayin da take jin wani irin kewarta a zuciyarta, tayi fatan ace gaba ɗayansu ne suka rayu sai dai kash Allah baya barin wani dan wani yaji dadi. Siraran hawaye ne suka wanke fuskar Sajeed tunawa da yar uwarsa Gabriella wadda a halin Yanzu ba shi da tabbacin tana araye kota mutu, lokaci ɗaya sautin muryarta ya soma cika kunnuwansa farkon kasancewarsu agidan kurkukun ƙaddara lokacin da za'a raba su da junansu tana kuka tace _ My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka_ Kowa da abun da yake tunawa aran shi, ganin jimamin nasu bame ƙarewa bane yasa sheikh Imam Yi masu nasiha mai ratsa zuciya, ya dinga jawo masu ayoyin kur'ani Yana fassara masu har saida yaga sun samun nutsuwa tukunna Ya dakata... "Waye zai fara Yanka mana cake din"? boss ne ya faɗa yana kallon su don jin za6in su, Har suna hada baki wurin furta"Unaisah" Idanunta amarairaice ta kalli faces din yan uwanta kafin ta sanya yatsun hannunta dake kerma ta dauki ƙaramar wuƙa, har taj ya yunkura zai ruƙo hannunta don ya taimaka mata ganin hannun ta na kerma, tunawa da danish yasa shi fasawa don har yanzu bayanshi bai daina yi mashi zogi ba. A hankali ta yanko cake din tare da ɗagowa tana kallon su idanunsu duk suna akanta, tama rasa wa zata fara bama cake din duk da akwai wanda zuciyarta ta aminta da cancantarsa, satar kallonsa tai nan take idanunsu suka shiga cikin na juna, "Angel ki ba danish, shi Ya cancanta ki bamawa," muryoyinsu sajeed ne suka cika kunnuwanta. kau da ido tayi daga kan danish ta kalli daddynta, Lumshe mata idanunsa yai alamar ya amince mata. Murmushi ta ɗan saki har dimples dinta suka lotsa, matsawa tayi kusa da danish, ta miƙa masa cake din ya buɗe ƙaramin bakinsa ta sanya masa, gaba daya suka soma tafa masu, Bayan ta ƙara cirar wani cake din ta miƙa ma daddyn ta Yaci. daga bisa ni ta miƙa ma Haris Wuƙar, Ya kar6a Ya datsi cake din ya sanya wa deeja abaki, wani irin farin cikine Ya lullu6e su Bayan ta gama taune na bakinta, ya bata wukar don ta bashi, abunka game tabin hankali, maimakon ta kar6i wuƙar sai ta sanya hannu ta 6allo ƙato ta duma masa abaki har cikin hancinsa ya shiga, gaba ɗaya suka sanya dariya, cike da nishadi. Kar6ar wukar batool tai, ta ballo cake din ta ba mubeen Abaki Yaci, Kafin Ta sake gutsuro wani ta miƙa ma Rubina itama taci, ɗaya bayan ɗaya duk sai da suka ciyar da junan su cake din. Tunawa da aunty umminsu dake ta kallon su, yasa batool ta sake kar6ar wukar daga hannun Sarah, ta yanko cake din taje gaban ummi ta miƙa mata, murmushi tasaki tare da ruƙo hannun batool ta tura shi abaki tana taunarsa ɗagowar da zatayi kwatsam suka haɗa ido da sheikh iman dake ta satar kallon ta, duk sai taji jikinta yayi mugun yin sanyi, tuni taji wasu hawayen sun cika idanunta, muryarta na rawa tace da batool"ba ki ba sheikh imam cake din ba" tana fadin hakan tai saurin juyawa ta nufi hanyar komawa bedroom dinta, sam yakasa janye idanunsa daga kallon ta hatta su taj sai da suka lura da kallon ummi da yakeyi sai dai basu kawo komai aran su ba. Jiki asanyaye Batool ta ƙara yanka wani cake din taje gaban sheikh Imam Ta miƙa mashi, sai da Ya fara ɗaura tafin hannunsa akanta ya ɗan shafa shi ya furta"Allah yayi maki albarka" kafin Ya buɗe baki ta saka mashi cake din' Murmushi kowan nan su Yasaki gwanin ban sha'awa. Da zolaya big guy yace"yau an nuna min wariyar launin fata, Ni babu mai bani cake din"? da sauri sajeed yace zan baka, girgiza kai yayi"I'm sorry Ni mace nakeso ta bani ba jin sina ba" dariya suka sanya gaba dayan su. Harara boss yadan jefa masa cikin muryar raɗa Yace"kai bana son iya shege fa, halan tazurancin naka ne Ya motsa" ƴar dariya yai har hakoransa suka bayyana. "Ni zan baka cake din" jemimah ce tayi maganar, da karfin hali fuskarta sharkaf da hawaye, gaba ɗaya suka sanya dariya, matsawa big guy yai tare da kai hannu ya dauki Jemimah, kafin Ya bata wukar Ta yanka ta bashi abaki, shima ya karbi wukar ya 6allo cake din Ya sanya mata abaki. Sautin tafin su Ya cika falon, wunin ranar shagali sukayi babu kakkautawa yadda kasan gidan biki. _______________________________✍️ Safa da marwa takeyi a tsakar dakin ta, fuskarta dauke da tsantsar farin ciki, gaba daya ta shagala da tunanin Yar ta Angel sam ta manta da zancen tafiyar su, zumuɗi Ya hana ta zauna jira take Aneelerh ta tura mata da hotunansu duk tabi ta kosa da son ganin fuskarta Jin ƙarar shigowar sakonni ta whatsapp din da ta buɗe ne, yasa tai saurin duba screen din wayar dake ruke a hannunta, wayyo Allah dadi, tsabar zumudin ta buɗe sakon Aneelerh yatsun hannunta har kerma sukeyi, lokacin da ta ɗaura idanunta akan hoton Unaisah ƙafafuwanta kasa ɗaukarta sukai, awani slow ta koma gefen gado ta zauna hannunta ɗaya dafe da bakinta take kallon hotunan Unaisah, yayin da zuciyarta ke harbawa da karfi da karfi tun da take a duniyar nan bata ta6a jin son wani ɗan adam fiye da yadda takeson ƴarta, duk da basu taba haduwa ba amma taji wani irin mahaukacin son yarinyar na ƙara shigar zuciyarta. Hotunan da Aneeleeh ta turo mata na unaisah tun tana jaririyarta nannaɗe cikin farin towel, hada hotunan Birthday dinta lokacin ta cika shekara goma aduniya, sunyi kyau hotunan kamar lu'u lu'u Wani irin sanyine Ya ratsa zuciyar benazir, a kalla ta shafe mintuna tana kallon hotunanta, kafin ta buɗe na baby junaid din Aneeleeh, Murmushi tasaki tana kallon kyakkyawan yaron kamar sabon fure ya kwanta mata aranta, Bakomaine Ya faɗo mata aranta ba face Fatimar yaya shureim ita kadaice babu acikin su A hankali ta furta"Allah sarki Aisha ke kadai ce babu jinin ki araye, mun yi babban rashi, Allah yajiƙan fatima Allah Yasa mai ceto ce....." idanunta cike tab da kwalla tayi maganar. "Benazir zaman me kike yi"? Rass taji gabanta ya fadi jin muryar hajiya layla, a hanzarce ta dago tana duban kofar shigowa dakin, Hannunta ruke da trolley din kayanta, fuskarta babu fara'a sai faman huci take yi, Shigowa dr shureim yayi da sauri yana kokarin shawo kanta"mommy dan Allah ki yi hakuri ki fasa tafiyar nan, kinga daddy bai amince maki ba, Yakamata kibi umarninsa ko dan gujewa fushin ubangiji...." harara ta watsa mashi tana fadin"shureim zan 6ata maka rai wallahi, Idan kai bazaka bi ni ba to ka ƙyale ni in kama gabana, har yaushe ne zan cigaba da zama ana raina min wayau agidan nan? nafa san me nake yi, ni ba shashasha bace..." mai da dubanta tayi ga benazir wadda tuni ta miƙe tsaye damuwa ce tsantsa akan fuskarta. "Wuce mu tafi, Idan kema ba zaki bi ni ba, to ki zauna tare da su" ta fada rai a6ace. Cikin sanyin murya Benazir tace"mommy ki yi hakuri dan Allah, kinsan bazan ƙi bi umarninki ba amma bazan iya tafiya ba...." baki asake Layla ke kallon ta. "Nima ba son zama gidan nakeyi ba, Aneeelerh ce ta kira ni awaya, kiran da muke ta jira, sai yau Allah Ya nufa, dan Allah mami kibarni in hadu da ita inyaso daga baya sai mu tafi" Girgiza kai hajiya layla tayi"kawai kizo mu tafi, in mun fita zamu fara biyawa gidan su Aneelerhn kafin mu tafi" da ƙarfin hali tai maganar, ita kanta tana jin fargaban zuwa gidansu aneelerh saboda bata so Benazir ta gane karyar da tayi mata nacewa su taj sun bar kasar amma a halin yanzu idanunta sun makance burinta su bar gidan duk abun da zai faru ya faru. Gyada kai Dr shureim yayi"ki bita ku tafi, Allah Ya kiyaye hanya, Ni zan jira daddy" Tsoki layla taja, tare da juyawa ta nufi kofar fita daga dakin, da sauri benazir ta dauko mayafi, dr shureim ne ya janyo mata trolley din kayanta, lokacin da suka fito falon gidan, yayi dai dai da fitowar su Hajiya sarah da gudu zeenatu ta nufi benazir tana kuka ta ruƙe mayafinta. "Aunty benazir kada ki tafi kibarni, dan Allah kada ki tafi, Mami Dan Allah ku yi hakuri ku zauna, Idan wani abu mukai muku badaidai ba zamu gyara, Ni dai banso ku tafi" "zeenatu zonan"! Muryar Alhaji musace ta katse mata koke koken nata, jiki ba kwari ta saki mayafin benazir ta koma wurin shi ta tsaya, ruƙe hannunta yai acikin nashi, Hajiya sarah kamar an rufe mata baki takasa ta6uka komai sai kallon su da take yi, dakatawa sukai da yin tafiya jin muryar Alhaji ubaid "Wallahi idan kika sa kafa kika bar gidan nan batare da yawuna ba, to ki sani abakin auran ki"!! hankulansu Dr shureim atashe suke kallon shi har suna hada baki wurin furta daddy meyasa? Dariyar takaici layla tasaki tana tafa hannu tace"sai me donka sake ni? Ni dama ay najima da gajiya dakai tun lokacin da na gane kai bakomai bane face rakumi da akala, Ina amfanin zama da namiji solo6iyo irin ka"? Rai a6ace ta faɗa tana kallon cikin idon shi, Kalamanta sun ƙona masa rai, daƙyar Ya iya hadiye yawu mai ɗaci ba tare da ya iya furta komai ba. Dauke idonta tayi daga kanshi ta kalli Alhaji musa, dake atsaye ya harɗe hannuwansa kan kirjinsa fuskarsa babu fara'a Harara ta watsa mashi kafin tace "Hankalinka Ya kwanta Ka shiga tsakanina da mijina, In sha Allah zaka ga sakayyar hakan" wani kallon ƙasan ido Ya watsa mata mai wuyar fassaruwa. "Shureim Benazir, kada ku bi ta idan har na isa daku, Kubarta ta tafi ita kadai tun da bata jin maganata" acewar Alhaji ubaid. Murmushin takaici layla tasaki, ba tare da ta ƙara furta kalma ba ta juya a fusace tabar falon "Ka bar su su tafi" Alhaji musa ne ya fada agadarance. Da sauri benazir taja trolley dinta tabi mommynta, shima shureim yabi bayanta A bakin motar shureim ta tsaya zuciyarta a kuntace, batai tsammanin zasu biyo bayanta ba Dr shureim na ƙarasowa Ya buɗe mata back seat din motar ta shiga ciki, sannan ya sanya masu trolley din kayan su a boot, daga bisani itama benazir ta shiga ciki. Bayan ya shiga ya zauna a driver's seat, yai ma motar key, zuciyarsa cike fal da damuwar abunda Ya faru, yaji takaicin yadda Alhaji musa ya nuna halin ko'in kula akan tafiyar mamin su, abun da Yafi bata masa rai furucin mahaifinsu yansu shikenan yana ji yana gani auran iyayensu zai rabu"? "Shureim! Ya akai naga ka dakata da yin driving din"? Cikin rauni na murya yace"mommy Kiyi hakuri mu koma, idan kika tafi ya kike so muyi da rayuwarmu? Ke kanki bazaki so abun da zai tarwatsa farin cikin mu ba...." Shiru tayi tana nazarin maganarshi, ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi lakwas "Mommy, kina atare damu Ya muka ƙare inaga idan baki nan? Duk wani mai nufin mu da sharri zaiji dadin cutar da rayuwarmu, bayan haka mommy tsawon shekara nawa kuna atare da daddy, auren soyayya kukayi kun tara zuri"a da dadi da ba da daɗi kunyi hakuri kun jure zama da juna sai akan wannan dalilin zaki kashe auranki? Mu kanmu bazamu ji dadi ba dan Allah ki tausaya mana mommy ku dubi girman Allah ki fasa tafiyar nan ko dan saboda mu" benazir ce tayi maganar tana duban fuskar mami kamar zata sanya mata kuka. Zancen zuci ta soma yi _wannan hanyar dana ɗaukarwa kaina ba me 6ullewa ba ce, ƙwara in tsaya in ƙwatar mana ƴancin mu, dole Inyi faɗa ko da kuwa zan rasa raina ne saina shiga tsakanin mu da shi_ Ba zato ba tsammani suka ga ta buɗe motar, wani irin farin ciki ne Ya lullu6e su, da sauri benazir ta fito shima shureim Ya fito suka dauko trolley dinsu dake a boot suka bi bayanta. Kamar yadda suka bar su hajiya sarah tsaye a falon haka suka taras da su, sunyi mamakin dawowar Hajiya layla, ko kallo ba su isheta ba, Kai tsaye ta wuce room dinta Da gudu zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna suna dariyar farin ciki, Fuskar hajiya sarah dauke da murmushi ta dubi dr shureim"ta fasa tafiyar ne"? "Eh mommy," ya bata amsa, Har cikin ranta taji dadin dawowarsu. Mutumin kuwa murmushin gefen fuska Ya ɗan saki, yayi tunanin security officers din gidanne suka hanata tafiya baisan cewa itace tai ra'ayin kanta ba, fucewa yai daga falon cikin takun isa. Alhaji ubaid dake kallonsu ajiyar zuciya ya sauke. "Daddy, dan Allah kuyi hakuri da abunda Ya faru atsakaninka da mommy, ku yi kokari ku sasanta junanku" Jinjina kanshi yai fuskarshi dauke da murmushi yace"kada ka damu shureim, ni dama ban dauka da zafi ba, itace ke da matsalar, in sha Allah zanje na lallashe ta" ya fada tare dakai hannu yadan bubbuga kafadarsa kafin Ya juya ya nufi dakin layla don su sasanta junan su. Koda ya shiga ɗakin, ya taras da ita zaune agefen gado, kamar mai jin shakkarta Ya raba ya zauna yana duban ta kafin yai magana tai saurin katse shi da cewa"basai ka bani hakuri ba, ni yakamata na nemi yafiyarka, ka yi haƙuri idan na 6ata maka rai, in sha Allah bazan ƙara ba, zan bi umarninka in zauna har zuwa lokacin da ka so mubar gidan" da wani irin mamaki yake duban fuskarta, kamar amafarki yake jin kalamanta, Wai yau layla ce da kanta take bashi hakuri har take fadin zata bi umarnin shi? "Allah yasa ba mafarki nakeyi ba" murmushi tayi tare da dubanshi tace"ba mafarki bane mijina, dagaske ne, abun nayi ban kyauta ba, su shureim sun yi min nasiha nima naga rashin kyautuwar hakan shiyasa na dawo. Ruko hannayenta yai acikin nashi hawaye tuni sun cika idanunsa Cikin sanyin murya yace"layla bazan iya misalta dadin da naji ba, kin faranta raina ayau, duk da nasan nine mai laifi amma kiyi hakuri ki yafe min, sannan inaso ki sanyani a addu'arki, Ni kaina bansan meyasa bana iya bijirema umarninsa ba, bana son bacin ran musa, saboda ya kyautatamin arayuwa shine silar duk wata nasara da na samu..." bai kare maganar ba tai saurin rufe bakinsa da tafin hannunta, saboda ta tsani taji Yana yabon musa, saboda ita tasan ba hakanan Ya kyale shi ba shiyasa baya iya ganin laifinsa, amma taci alwashin zata gano ainihin wanene Alhaji musa da duk wani abu dayake takama da shi. Abun da bai ta6a tsammani ba, Yaji layla ta kwanto da kanshi saman kafadarta, bawan Allah sai Ya kara lafe mata kamar wani karamin yaro. "Kada ka damu, ni bakai min laifin komai ba, In sha Allah zantayaka da addu'a kamar yadda ka bukata, kaima kuma inaso ka dage dayiwa kanka addu'a" amsa mata yai da toh, cigaba da kwantar masa da hankali tayi, har saida ta cika shi da farin ciki ta dinga zolayarsa tana tuna masa farkon haduwarsu kafin su yi aure. "Yanzu tun da komai Ya daidaita mu koma dining mu ƙarasa yin breakfast din" cikin kulawa mom sarah tayi maganar tana dubansu. "Aunty ki tayani murna" acewer benazir "Fada min meya faru"? "Aneelerh ta kirani awaya har mun yi magana da ita" Murmushi hajiya sarah tasaki"masha Allah, ina tayaki murna my daughter, wlh naji dadi yanzu yaushe zaki je can gidan na su"? Kallon dr shureim tayi wanda gaba daya hankalinsa na akan zeenatu dake a gefensa sai dadi take ji sun fasa tafiya. "Yaya shureim yaushe zamuje? Ni ko yanzu ma kace a shirye nake Allah" ta fada a kagare. "Gobe in sha Allah zan kai ki" da sauri zeenatu tace"yaya shureim nima zan bi ku, dan Allah ku tafi dani" ta faɗa a shagwa6e tana kallon shi. "Kada ki damu ƙafa ta kafarki, duk in da zani je a tare zamu tafi" cikin muryar raɗa yayi mata maganar, dariya murna tasaki. Benazar tace"kwantar da hankalinki rabin raina, gobe atare zamu je" "Nagode auntyna" "Ki daina murna, kin manta da daddyn ki halan, ba lallai ya amince ki fita ba" tur6une fuska tai. "Mommy pls ki roƙan mun shi yabar ni inje" ta fada tana bubbuga kafafuwanta "Zanyi mashi magana zuwa anjima nasan zai bari mu tafi da ita" acewar dr shureim Hajiya sarah na murmushi tace"kunfi kusa ay, nasan kana masa magana zai amince, tun da yana ji dakai na gaban goshinsa" dariya sukai gaba dayan su. ______________________Twins❣ A kwance yake kan katafaren gadonsu idanunsa na fuskantar ceilling, yanayin fuskarsa sam babu walwala ya haɗe rai kamar wanda aka aiko ma sakon mutuwarsa, bakomai ne yake damunsa ba face haɗin da mommynsa tayi masa, ya riga da ya san halinta ba lallai ta canza ra'ayin ta ba, shi fa arayuwarshi sam baida ra'ayin yin auren wuri, yafi sha'awar yai sharholiyarsa son ransa, a yadda ya tsara ma kansa sai yakai 45 years zaiyi aure, bugu da ƙari baya jin zai iya auran yarinyar saboda ba'ajinsa ba ce, jiya kafin ya kwanta bacci sai da yayi bincike akanta ta hanyar amfani da wayarsa har ya gano wanene mahaifinta wato karen ƴan siyasa, aransa ya ayyana tayaya shi da ya fito daga babban gida shahararren family da duniya tasan da zamansa, zai auri wannan yarinyar, Bayan haka mommyn sa minister ce daddynsa Ceo ne na babban companynsu Obi Tech, tayaya zai auri interior designer? Companyn ma da take aiki ba nata ba.... Abu ɗaya daya hana shi sukuni, kyawun fuskarta da surar jikin ta, daren jiya dakyar ya runtsa, ba halin Ya rufe idanunsa sai ya tuna lokacin da ta fashe mashi kuka la66anta na kerma, kissing ɗinta da yayi har cikin zuciyarsa yaji wani irin shauƙi da bai ta6a jin sa a wajen wata mace ba, kawai yayi ƙarfin halin tofar da yawu ne don Ya muzanta ta. Motsin buɗe toilet ne Ya katse masa zancen zucin nasa, A hankali yakai idanunsa ga duban mai fitowa Zaid ne ya fito waist dinsa daure da towel, suna haɗa ido da juna Ya sakar masa murmushi "Bro me kake tunani ne? kamar wani abu na damunka? Banza yayi dashi bai tanka mashi ba "Faɗamin meya faru jiya bayan mommy ta kira ka awaya" Yamutsa fuska yayi, tamkar baisan maganar ya furta"zaka iya tuna yarinyar nan da mommy ta kawo wurin mu"? Shiru zaid yayi yana kokarin tuna ta can yai murmushi tare da cewa"kana nufin Zahra"? Ta6e baki zayn yai kafin yace"oho na manta sunanta" "Itace zahra, yarinyar ta kwanta min araina saboda ina son mace mai kamun kai daga gani iyayen ta sun bata tarbiya" ya faɗa tare da samun wuri gefen gadon su Ya zauna yana kallon zayn "Mommy ce ta haɗa ni da ita...." bai 6oye masa komai daga abun da ya faru tsakaninsa da zahra. Har Ya ƙare maganarsa zaid bai ankara ba saboda zuciyarsa da ta karaya, har ga Allah bai ji dadin hukuncin da mommynsu ta yanke ba na hada zayn da zahra, saboda yasan halin ɗan uwan nasa bai jin magana fiye da shi, yarinya mai kamin kai an haɗa ta da ɗan iska, ina ma ace shi mommynsu ta hada da zahra da ba abun da zai hana ya gyara rayuwarsa saboda samun mace ta gari wadda zuciyarsa ke muradin mallaka... "Zaid? Naji kayi shiru bakace komai ba? Nasan kana tayani jimami ne" Jinjina kai zaid yai kafin yace"zayn banji dadin abun da kayi mata ba, saboda ba laifinta bane, mommy ce ta hada ta dakai, ni nasan ba itace ta shirya faruwar hakan ba..." ya fada cikin sanyin murya yana kallon zayn dake faman ya mutsa masa fuska "Me zai hana ka jaraba amincewa da buƙatar mommy, ni nayi imanin ba zaka ta6a danasanin auran zahra ba, watakil ta zama silar shiriyarka...." kafin ya ƙare maganar zayn ya wurga masa harara tare da katse sa da cewa"kana son ta ne? "Meya kawo maganar so? Kawai daga na baka shawara amatsayinka na dan uwana" guntun tsoki zayn yaja"bani buƙatar shawarar ka, nayi zaton zaka tayani jimamin abun takaicin daya same ni ashe ba haka bane dakai da mommy kanku ɗaya..." ya fada yana cije la66ansa"har abada bazan ta6a sonta ba, zan amince da ita ne saboda mommy, sannan zan aureta badan ina sonta ba sai don in mayar da ita abun biyan buƙata na amma babu maganar mutunci atsakaninmu muddin ta aure ni taga ma jin dadin zaman duniyar nan" muryarsa a kausashe ya furta maganar Runtse ido zaid yai har cikin ranshi baiji dadin kalaman zayn ba, baisan ya zaiyi ya shawo kan mommynsu akan ta janye maganar haɗa shi da zahra saboda zayn ba mutumin kirki bane, muddin ya auri zahra bakin cikinsa zaiyi silar mutuwarta, dole ya nema mata mafita tunkafin afkuwar lamarin, Indai daddyn su baisan da maganar ba zaiyi kokarin tunzurasa akan kada ya amince da maganar mommynsa....Saukowa zayn yai daga kan gado daga shi sai yar singlet da short Ya nufi toilet Yana huci Ya shige ciki, zaid dake zaune gaba daya kamar an zare lakarsa shi dai ya damu da zahra baya son mommynsu tayi silar jefa ta cikin wani hali wayar dake a kan side drawer din su, Yakai hannu ya dauka Ya danna wa landline din kitchen tana fara ringing maid ta ɗauka, ya bada umarnin akawo masu breakfast dinsu, Kafin Yai cutting kiran ya ajiye wayar kan drawer Badajimawa ba, Abla ta shigo dakin da tray mai dauke da kayan abinci, ta ajiye masu kan drawer bayan ta gaishe da zaid ta juya ta fuce.. ________________________Dattijon Arziƙi🤍 A zaune yake kan lallausar darduma, hannunsa ruƙe da cazbaha, a hankali Yake motsa la66ansa, kusan rabi da kwata na hankalinsa na akan chief owais dake kwance saman dardumar ya ɗaura head ɗinsa akan laps din baba obie, kyawawan idanunsa suna a lumshe tamkar na mai jin bacci, su duka biyun daga ka kalle su zaka shaida tsantsar nishadin da suke aciki, musamman baba obie, ransa fari fat tunda owais ya kawo mashi ziraya yau kusan wuni yayi awurinsa duk inda zasuje atare suke tafiya, ba su jima da dawo daga masallaci ba suka shigo garden don su sha iska, sai faman satar kallonsa yakeyi kamar ya haɗiyesa haka yake ji tsabar kaunarsa da ya ke ji. "Grandpa, wannan kallon na menene"? Idanunsa a lumshe Ya jefa mashi tambayar. Fuskar baba obie da fara'a Yace"Kallon so da kauna ne rabin raina, wallahi yau ka faranta min rai, gaba daya ka debe min kewar hateem dake damuna...." A hankali chief Ya ɗan bude idanunsa Ya saci kallon fuskar baba obie karaf suka hada ido cikin na juna "Baba...." Ya fada ba tare da ya ƙarasa maganar ba "Na'am sanyin idaniyata, Naji ka kira sunana kuma ka yi shiru" gyara kwanciyarsa yayi batare daya bashi amsar tambayar sa ba. "Duk cikin jikokina babu wanda Ya more ni kamar ka, kaga cinyar nan tawa tun kana ƙarami kake tumurmusarta, gashi har yanzu baka daina taushe min ita ba' murmushin gefen fuska Chief yai masa har chin dimple dinsa Ya dan lotsa. "Meya fi raina"? Ya fada Yana kallon fuskarsa. "Ni fa idan ina atare dakai, sai naii kamar an mallaka min komai na duniyar nan, ni dai Allah Ya jarabce ni da sonka kakana ina fata Allah ya dawwamar da farin ciki atsakanin mu zan cigaba da tayamu addu'a Allah Ya Ya ƙara mana tsawaicin kwana ko dan na cika maka burinka akaina......." tun da yafara magana baba obie ke kallon shi da wani irin matsanancin farin ciki akan fuskarsa, dakatawa yayi da jan cazbahar Ya ɗaura tafin hannunsa kan sumar Owais a tsanake Ya soma shafata kamar yana yi masa susa. "Kalamanka sun sanyaya min zuciyata, Owais kai na dabbanne, wallahi yadda nake jinka bana jin ko iyayanka, kai tamkar bugun zuciyana ne, wallahi bansan Yadda zan misalta maka kaunarka da nake yi ba....." kafin Ya ƙare maganar, ruwan hawayen da suka taru cikin idanunsa suka gangaro kan fuskar chief, lokacin da yaji saukar su a ruɗe Ya zabura ya mike daga kwancen da Yake, Idanunsa akan fuskar baba obie da alamun ruɗani Ya furta"baba meyasa ka zubar da hawayen ka? shiru yayi batare daya iya furta masa wani abu "Fadamin mana, ko dai maganar da muke yi ce ko kuma akwai wani abu dake damunka"? Girgiza kai yai"a'a owais kada ka damu babu abun da ke damuna, kawai bana son duk wani abu da zai shiga tsakanina dakai, Ina jin fargaban duk wani abu da zaisa ka juya min baya, ni dai bana son 6acin ranka......' ruƙo hannayen baba obie yai acikin nasa yatsun hannunsa har kerma sukeyi"baba bazaka iya boye min komai ba, idan har kana da damuwa kallo ɗaya nake yi maka na fahimta, Ina ji araina da akwai wani abu dake damunka dan Allah ka fadamin habibi na, nayi alkawarin zanyi iyakar bakin kokarina wurin kawar maka da damuwarka...." da ƙwarin gwiwa ya furta maganar Yana kallon idanun baba obie da suka kada jawur gray eyes dinsa sunyi ja tsufansa duk Ya ƙara fitowa. Wani murmushi yayi mai ta6a zuciya kafin yace"Idan na faɗa maka abun da ke damuna zaka 6oye min sirri na ba zaka fada ma kowa ba sannan zaka rufa min asiri" jinjina kai owais yai da alamun rudani akan fuskarsa kamar baison furta maganar Yace"najima inason sanar dakai, sai dai inajin fargaban yadda zaka dauki abun aranka, ka yi min alkawarin ba zaka fusata ba" ya fada la66ansa na kerma, ba karamin rikita tunanin chief owais Yayi ba, gwiwarsa harta sage In a low voice Ya furta"ni mai rufa maka asiri ne babana, bazan bari kowa Ya sani ba, tona maka asiri tamkar tonawa kaina asirine da zuri'armu" jinjina kai baba obie yai sai da yafara kallon garden Din Ya tabbatar babu mai kallon su kafin Ya matsa gab da chief owais Yayi masa raɗa a kunnansa. Lokaci ɗaya chief ya ɗan janye kunnansa da tsantsar mamaki Yake kallon baba obie wanda tuni yasha jinin jikinsa, ba zato ba tsammani a lokaci ɗaya suka tuntsire da dariya kamar wasu zautattu, Yaushe rabon da inga chief yayi dariya irin wannan ni kaina namanta, komai nasa mai jan hankali ne. dariyar tayi matuƙar tafiya da imanina, saboda gaba ɗaya ta bayyana zunzurutun kyan fuskarsa, dimpla dinsa duk sun lotsa, fararen hakoransa kamar auduga tsabar hasken su, sun ɗau lokaci suna tiƙar dariya kafin daga bisani chief ya kifa kansa bisa kafadar baba obie, hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba, da farkon yai tsammanin wani mugun abunne zai faɗa masa ashe ba haka bane Muryarsa tamkar tame jin bacci Ya furta"Grandpa are you kidding me"? Baba obie na murmushi yace"Wasa nake maka owais, Ni ina ni inayin aure, tsofe tsofe dani, ga tarin ya'ya da jikoki" "Wannan ba hujja bace, Indai Kana son Yin auren ka fadamin, in sha Allah I will try to find a righteous life partner for you." Da zolaya baba obie yai masa dundu akan bayansa tare da cewa"Owais wlh wasa nake maka, kawai don inga reaction dinka ne, kuma nagani tunda gayanan na sanya ka yin dariyar da ka dade baka yi taba" Sauke ajiyar zuciya chief yai kafin ya sake furta"please ko da nan gaba kaji kana bukatar abokiyar rayuwa ka sanar dani, zan goyi bayanka kuma zan nema maka dattijuwa dai dai da kai" dariya baba obie yayi "Allah ya kiyaye In auri tsohuwa, Haba owais Ina laifin Yar sha takwas mai jini a jika, wadda zata sangarta ni, kasan mu tsoffi munfison adinga tarairayarmu kamar irin new born baby, Yanzu ni owais idan na auri dattijuwa kamana me zata min"? da mamaki chief ya ɗago yana kallonsa kai kace ba daga bakinsa kalaman suke fitowa ba. Kafin Ya bashi amsar maganarsa, Wayar baba obie Ta fara ringing, da sauri ya zarota daga aljihu tare da picking call in ya kara a kunnansa. Chief owais sai kallonsa Yake yi har yau yana mamakin tsufan kakan nasa, kwata kwata babu rudin tsufa atare da shi, yana da karfi ga kaifin basira, idanunsa kuwa kona matashi albarka saboda yadda yake gani da su ko bai sanya glass ba, harta sandar da yake rukewa ta gayu ce ba dan ya gaza taka kafarsa ba. "Alhamdulillah Alhamdulillah, almost 3 time baba Obie Ya furta hakan, Hannunsa ɗaya dafe da saitin zuciyarsa alamar Yaji sanyi aransa. "Ina fata kun sauka lafiya, Ubangiji Allah Ya huta gajiya, Ina ƴan jikokin nawa da surukar arzikin Ina fata duk suna lafiya"? Ya tambaya yana sauraron muryar wanda suke magana da shi. "Madallah, naji dadin jin hakan, Hateem ka kula min da kanka, tun da ka haura kabar kasar nan nake ta zullumi duk bayan yan mintina saina duba Onn news inga ko kun sauka lafiya don nasan sune nafarkon da zasu fara buga labarin yadda jirginku yayi landing sai gashi cikin ikon Allah Ka kirani...' yai maganar fuskarsa dauke da murmushi "Muna atare da owais, watakil Ya manta wayarsa agidane, wuni yayi awurina yanzu haka muna a garden..." miƙa ma owais wayar yayi"uncle dinka ne ke son magana dakai, kar6i kuyi magana kai masa bangajia jirginsu Ya sauka lafiya...." da sauri chief Ya kar6i wayar tare da karata a kunnansa "My uncle, Ykk Ina fata kun sauka lafiya"? On the other hand muryar prime minister ta amsa da cewa Alhamdulillah Myson, tafiya tayi kyau yanzu haka Ina a bedroom dina dakyar na samu jama'a suka ƙyale ni" "Sunyi kewarka ne, Kai dinne badai farin jini ba, Yar dariya hateem yai kafin ya numfasa Yace"Ina yarona? tun ina a cikin jirgi nake ta tunaninsa, owais Yanzu haka da nake maka magana zazzabi nake ji a jikina saboda kewar sa, ina ta kiran layi ka donka bani shi mu gaisa bana samu" dagowa yai ya saci kallon baba obie Ganin sun haɗa iso yasa shi saurin canza yare zuwa larabci saboda baison Yaji me zai furta. "Uncle, zazza6i saboda shi"? "Hmm ba zaka gane ba, dan Allah Ka hadani da shi" Hankalinsa adan tashe Yace"pls uncle, ka daina sanya damuwa aranka, bana jin dadi, na manta wayana agida ne shiyasa baka same ni ba, amma in sha Allah idan na koma zan yi kokarin hada ka da shi ko hankalinka Ya kwanta amma kafin nan pls ka sha magani kada zaza6in yai yawa" "Owais babu wani magani da zai warkar da zazza6in nan kawai ka hadani da shi, saboda shi kadaine warakana" baba obie dake kallon owais ya kura masa ido ba tare da ya fahimci me suke cewa ba. "Okey uncle, zanyi abun da kake so" "Nagode owais, and pls abashi kulawa ta musamman, bana so ya nemi wani abu ya rasa, na yarda dakai kuma nasan zaka Iya min abun da nake so" cikin girmamawa ya amsa masa da toh uncle. Sun ɗan jima suna waya kafin sukai sallama Ya mika ma baba obie wayar, harara Ya galla masa"fadamin me kuke tattaunawa ne naji ka canza yare don kada naji ko" Girgiza kai owais yayi"ba haka bane....." bai ƙare maganar ba, sallamar Hajjaty ta katse su, ba karamin dadi owais yaji ba saboda bay da amsar da zai ba baba obie akan tuhumarsa da Yakeyi Tuni kamshin turarenta Ya gauraye hancinansu, Hannayenta ruke da tray ta shigo garden din, Tea set ne akan tray din tare da fresh fruit, bayan ta ajiye masu fuskarta da fara'a ta gaishe sa su,a mutunce suka amsa mata "Idan kin shiga ciki, Ki sanar da mutanan gidan su prime minister sun sauka lafiya yanzu ya kirani awaya ya fadamin nasan ba lallai suji ba" Murmushi tayi"in sha Allah zan sanar da su" ta fada tare da mikewa ta fuce daga garden "Kana sonta ne? Naga kana kallon ta" muryar chief ce Ta ratsa kunnansa da sauri ya kau da idonsa daga kallon bayan hajjaty ya wurga masa hararar zolaya"dan Allah ka daina wannan maganar, kawai daga na kalle ta? Ta6e baki owais yayi batare dayace komai ba, Ya dauki Tea pot Ya tsiyaya masu a cups, atare suka zauna suna sha gwanin ban sha'awa ___________________________________BossBature✍️ A6angaren Aneelerh wunin ranar da farin ciki tayi shi, babu wanda baisan da zancen bayyanar benazir ba, Harta su mami da abie sai da ta sanar da su, sunji dadi har addu'a sukai mata akan Allah ya ƙara tsareta daga sharrin wadanda sukai mata kurciya da kuma fatan Allah Yasa suma su Taj su bayyana kamar yadda benazir ta dawo. Tun bayan da ta kammala sallar la'asar ta duƙufa tana kallon hotunan benazir da ta tura mata awaya, kamar yau tafara ganin ta, gaba daya zumudin son ganinta takeyi, akwai abubuwa da dama da take son taji daga gare ta, tana son tasan meya faru da ita bayan guduwarta? Sannan A wani hannu ta faɗa? Murmushi tasaki yayin da take yin zooming fuskar benazir tayi haske jawur ta ƙara jiki ta zama big mama.. "Ya Allah kamar Yadda Ka nuna min benazir da ranta da lafiyarta Ya Allah ka nuna min su Uzair haka, har Yanzu ban fidda rai da su ba, saboda Inaji araina suna araye, Ya Allah ka tsare min mijina da dan uwansa da angel dina aduk inda suke, Ya Allah Idan sun riga mu gidan gaskiya kajiƙansu ka gafarta masu alfarmar annabi muhammd SAW......" muryarta na rawa ta ƙare maganar saboda kukan daya ciyota..... "Aunty Aneelerh" muryar zahrace ta katse mata kukan nata, da sauri ta sanya tafin hannu ta share hawayen don batason zahra taga kukan ta, hakan zai iya sanyata damuwa, murmushi ta kakaro akan fuskarta ta dago ta kalli zahra dake shigowa. "Na'am Sisterna" "Auntyna Ina ƙara tayaki Murna, Aunty benazir ta bayyana saura Angel dinmu in sha Allah itama zamu ganta, Ni nasan yau dakyar zaki iya runtsawa saboda zumudin haduwa da Aunty benazir" cike da nishadi zahra tayi maganar, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana dubanta. "Nagode zahra, ki cigaba da tayani addu'a Allah Ya bayyana su uzair, bana jin zan ma Iya bacci adaren yau, in sha Allah zanyi nafilfili akan su..." ta fada tana ɗan yamutsa fuskarta dake a kunshe da damuwa. "Lokacin da yayan benazir Ya fada min cewa kurciya akai mata har ta gudu tabar gida, wallahi bakomai ya fado min araina ba face 6acewar su taj, farat ɗaya aka neme su aka rasa, a tsakar dare, zahra baki tunanin suma kurciyar akayi ma su"? Idanunta Jawur ta jefa mata tambayar, shiru zahra tayi jimm alamar tana nazari kafin taɗan jinjina kai tace"nima nayi tunanin hakan, zai iya yiwuwa, amma kada mu dogara akan hakan tunda bamu da tabbaci" "Kin fadi gaskiya zahra" Shiru suka danyi na wani lokaci.. "Zahra, dazu muna cikin yin magana bamu ƙarasa ba abie Ya kira ni..." murmushi zahra tayi "Ni ma sham na shafa'a...." labari ta fara bata na dinner din hateem tun daga farko har karshe ta dire mata. Bakomai ne Ya tsaya ma Aneelerh arai ba face yarinyar da zahra ta bata labarin sun haɗu har sunyi hotuna. "Ki nuna min hoton in gani" zumbur zahra ta mike tana fadin inna lillahi na manta wayar a hannun baby junaid tun ɗazu tana a wurinsa, Allah Yasa bai yi min barna ba" da sauri ta fuce daga dakin ta shiga neman baby junaid itace har dakin ummi da mamie duk baya a ciki, har falo bata gan shi ba, da sauri ta nufi dakin abie nan ma babu shi ta dawo ta shiga dakin uncle still ba junaid Sai da ta gama shan wahalar nemansa har zata juya ta koma daki ta jiyo sautin muryarsa a kitchen shi da Ana suna magana. "Kinga wannan itace Angel dina aunty zahra ce ta dauko min hotonta" Adai dai lokacin zahra ta shiga kitchen din kafin Ana Ta kar6i wayar don taga hoton Angel din motsin shigowar zahra ya firgitar da junaid aruɗe Ya saki wayar ta kife kan floor, wani irin bugu zuciyar zahra tayi ba ita ba hatta Ana hankalin ta, sai da Ya tashi idanunsa azare suke kallon junaid wanda tuni yasha jinin jikin shi. Muryarsa na rawa ya furta"aunty zahra bani bane, Ana ne ta kada miki waya...' yana magana yana girgiza kansa duk yabi ya rude, Jikinta na tsuma Ta nufi wayar ta dauko ta tare da juyo da ita, gaba ɗaya screen dinta ya tsastsage fatsa fatsa baka Iya ganin komai..... Kamar ta fasa ihu haka Taji tsabar bacin rai, a fadace tace"junaid hankalinka Ya kwanta ko? Ka fasa min waya! daga abun arziki na baka ita don ka kalli hotuna" ta fada tana zare masa ido fuskarta adaure tuni Ya ƙara firgita. "Sister zahra kiyi hakuri shima bada son ransa hakan ta faru ba, kada ki tsorata shi" Ana ce ta fada cikin kwantar da murya. Bata tsaya sauraronta ba, Ta ruko wuyan rigar junaid"don kaga ina maka wasa da dariya ko? Shiyasa har ka samu kwarin gwiwar fasa min phone, muje daki yau saika yaba ma aya zakinta ɗan rainin wayau, dallah jibarka ko kunya babu" la66ansa ya fara ta6ewa alamar zaiyi kuka"kar na kuskura naga hawaye a idonka, wayar wuta zan sa maka" shiru yayi can kuma ya fara mata magiya"bazan ƙara ba aunty zahra, dan Allah kada ki buge ni, na tufa Allah" kiris Ya rage ta fashe da dariya ganin yadda Ya tsorata kamar ta ta6a bugunsa Alhalin tun da ya taso babu wanda Ya ta6a bugunsa Janshi tayi har zuwa bedroom dinta, Ta zaro wayar charger a jikin socket, kafin ta dawo gare shi da gudu ya fuce waje yana kuka, biyo shi tayi aguje tana kwala masa kira. Bai nufi ko'ina ba sai dakin mommynsa Yana shiga Ya faɗa kan laps dinta Ya ƙanƙameta yana fadin"mommy kice ma aunty zahra kada ta bugeni, bana so..." duk yabi ya dabarbace, a rude Aneelerh ke kallon bayansa Jikinsa sai kerma yakeyi"fadamin kaida wanene"? "Aunty kibarni da babyn nan, Allah Yau sai yaji ajikinsa, Har ni zai fasa ma screen din waya? daga abun arziki na bashi aronta don ya kalli hoton Unaisah shine zai fasa min phone" "Amma banji dadi ba junaid, meyasa zakai mata haka? Ka kyauta abun da kaima aunty zahra"? Ba tare daya dago dakansa ba yace"tayi hakuri bajan ƙara ba, mommy ki siya mata wata wayar cikin kudina da nake tarawa a wurin ki" dariya sukayi gaba dayansu jin abun da Yace. "Aunty aneelerh yanzu ya zanyi? Ni takaicina hotunan da baki gani ba" Mika mata hannu Aneelerh tayi muga wayar da sauri ta bata, duddubawa tayi kafin tace"zanyi magana da mahboob yakai maki ita wurin gyara, kada ki damu idan an dawo da ita sai ki nuna min hotunan" ajiyar zuciya zahra tadan sauke"shikenan amma duk da haka saina tsala masa wayar nan" ta fada tare da yunkurawa zata zane bayansa fashewa yayi da kuka yana fadin"aunty zahra kada ki bugeni, Allah Yana sama Yana kallon ki..." dariya zahra tayi"kasan da hakan shine ka fasa min wayar"? Muryarsa da shesshekar kuka Yace"ay mommy zata canza maki wata cikin kudina" tuntsirewa tayi da dariya cike da zolaya tace"ban ta6a sanin kai matsoraci bane sai yau, ay ko daga yanzu tun da na gano lagwonka, da zarar kamin rashin ji zan zane maka baya da wayar cazana" maƙe mata kafaɗa yai, ba tare daya tanka mata *HAJIYA ADAMA🤍* A hankali tai parking motarta, fitowa tai cikin shiga ta lace, ta yafa mayafi kan kafadarta, fuskarta manne da farin glass, Shopping bags ta ɗauko a back seat na motar, kafin ta Nufi cikin gidan tana gab da zata shiga bedroom din su ta tsinkayi Muryar Uncle abdallah yana waya "Kayi hakuri nasan ba haka mukai dakai ba, na saba alkawari amma ka dubi halin da nake aciki, lokaci ɗaya na rasa ɗana bayan haka na rasa ɗan yayana tare da yarsa, na rasa yayana da kakata kai kadaine zaka Iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kudin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su indai suna araye na ƙwammace na ƙare rayuwata a talauci akan inci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..." Muryarsa amarairaice yayi maganar kamar zaiyiwa mutun da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya Cak Ya tsaya da yin maganar ba tare daya ƙarasa ta ba, sakamakon kamshin turaren hajiya adama da hancinsa ya shaƙo masa, a hankali Yai rejecting call din yana kokarin dai daita nutsuwar shi "Ba halin ki bane Yi min la6e,"! Taji Ya faɗi fuskarshi ba fara'a Bata tanka mashi ba, har sai da ta ƙarasa gaban gado ta daura shopping bags din kafin ta juyo ta dube shi da alamun rudani akan fuskarta "Gaskiya ka faɗa ba halina bane, amma wannan wayar da kayi yanzu ta ɗan ɗaure min kaina, dear wani kudi ne naji kana fadin zaka mayar adawo maka dasu idan suna araye!? Har kake fadin ka ƙwammace ka ƙare rayuwarka a talauci akan ganin damuwana na rashin haihuwa? Su wanene kake yin magana akan su? da wani irin kallon tuhuma take duban shi. Hannu Yasa yaɗan shafa keyar shi, daga ganin fuskarsa babu kwanciyar Hankali, tsufansa Ya ƙara bayyana musamman fuskarsa duk tayi tamoji tamoji. Maimakon Ya bata amsar tambayarta sai cewa yai"Har Kin kammala siyayyar? Dame dame kika siyo mana ne" A waske Ya faɗa tare da nufar Shopping bags din da ta ajiye kan gado, Ya buɗe Yana dudduba kayan ciki. Kamar sakarya Haka Ya barta a tsaye Tana kallon Ikon Allah. "Hajiyata, Yunwa nake ji, pls Ki dafa min abunda zan dan ci" gyaɗa kai tay aranta ta ayyana koma menene zan bincika duk da ba halina bane amma da buƙatar nasan dawa kake waya akan su wa kake magana Cire mayafin tayi, ta daura sa kan gadon, Kafin Ta juya tana fadin"Sorry dear, nabarka da Yunwa, bansan lokaci Yaja har haka ba, bari naje kitchen na shirya mana abun da zamu ci" Bayan fitarta daga dakin ajiyar zuciya ya sauke, kamar wanda Ya ku6uta daga hannun dogarawan sarki, kwantar da kansa yai kan pillow idanunsa sun kaɗa jawur bakomai Yake tariyowa ba face nasihar yayansa Malam Zaheer haƙiƙa yayi babban rashin da har abada bazai ta6a samun makancinsa ba Agogon ɗakin Ya kalla kusan ƙarfe Biyar Na marece, lumshe idanunsa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin radadi daga gani yana acikin matsananciyar damuwa, Muryoyin su Uzair ne suka fara yi masa gezau acikin kan shi bazai ta6a manta ranar da suka shigo ɗakinsa da zumuɗin sanar dashi sun samu matayen da zasu aura. "Kunyi shiru bakuce min komai ba" "Taj ka fara fada masa" harara Taj Yai ma uzair ay kai yakamata ka faɗa masa ni kunyar shi nake ji Allah, acikin kunne sukeyin raɗar Murmushi Uncle abdallah yai sai yake ganin kamar komai A yanzu Yake faruwa. "Mijin mace ɗaya, abincin Ka Yana jiran ka" kamar daga sama ya tsinkayi muryar Hajiya adama, da sauri Ya mike Ya shiga toilet jim kadan Ya fito Ya nufi dinning din, A tsaye Ya same ta tana karasa jera masu abincin Murmushi suka sakarma Juna"Bismillah, babyn Hajiya adama" atare suka zauna suna fuskantar Juna. "Sannu da kokari matar mutun ɗaya, nagode da kulawarki agare ni, Naji dadin girkin nan" ya fada Yana kokarin tura jallop rice din daya debo a spoon"Shiyasa nake alfahari dake saboda kin Iya girki" Murmushi tasaki Jin Yabon da yai mata"nima ina alfahari dakai," shiru suka danyi kowa yana cin abincinsa can ya ƙara dagowa ya saci kallon fuskarta karaf suka hada ido duk saiya rasa sukuninsa "Wai lafiya naga kamar wani abu na damunka"? Girgiza kai yai"ba wani abu, kawai ina tunanin ranar da zamu rabu" ras taji gabanta Ya fadi arude tace"Abdallah? Meya kawo maganar rabuwa? Anya kuwa kasan me Harshen Ka ya furta"? Ya ɗan tsorata da ganin Yadda Ta ɗaga hankalin ta. "Kaga In baka lafiya muje nakaika asibiti bawai ka kama Yi min sambatu ba" babu wasa akan fuskarta tayi maganar. Cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri hajiyata, Nima zolayarki nakeyi, maganar rabuwa da nayi kinsan akwai mutuwa ko kuma wata kaddarar ta rayuwa da zata iya sanyawa mu juyawa juna baya! Harara ta galla masa, tuni idanunta sun ciko tab da ƙwalla mikewa tai da sauri tana fadin"banji dadin maganar nan ba, eh nasan mutuwa dole ce amma meye na kawo maganar rabuwa muna tsaka da cin abincin mu"? Ta jefa mashi tambayar hawaye nabin fuskarta shiru yayi sam ya rasa amsar da zai bata "Na rasa uzair da taj, na rasa unaisah, haba kabarni inji da wannan radadin mana, akan me zaka tada min maganar rabuwa...." rai a6ace Ta bar dining din ta nufi bedroom dinta Da sauri Ya miƙe yabi bayanta jiki na rawa saboda baisan bacin ranta, lallashin ta Ya dinga yi kamar zai mata sujjada dakyar Ya samu ya shawo kanta har ta daina fushin da shi *💘EX-PRISONERS❤* Wuraren ƙarfe takwas na dare Gaba ɗayansu sun hallara A main falo din gidan yadda kasan gidan biki ko suna, sai surutu sukeyi suna yin firar yaushe rabo abu Yaƙi ƙarewa kamar Yauce rana ta farko da suka fara sanin junan su, da alama dai gidan Chief Ya zama Gidan marayu kowa ka kalli fuskarsa annurin farin ciki ne, ummi tana azaune kan sofa tare da batool hannun ta ruke da waya video take daukar su ba tare da sun sani ba. Mutun ɗayace babu acikin su, Unaisah dake a daki Tana shiryawa, kamar yadda sukai da daddynta zai kaita Part dinsa dake agidan, wata hadaddiyar abaya ta sanya launin black and white ta ɗauko mayafi tayi rolling nasa akanta, tabi ko'ina na jikinta ta feshe shi da turare yarinya fa ta zama budurwa wani irin gayu take ji, Bayan ta sanya takalma, ta soma tunanin Ina ta jefa wayarta, sai yanzu ta fado mata aranta, farat daya tafara tunanin aunty pretty matar da sukai waya shekaran jira da dare gaba daya ta manta saboda lalurar da ta same ta ga kuma baiyanar daddynta da yan uwanta da suka ƙara mantar da ita zancen matar. _Neman wayar ta soma yi, tun daga kan mirror har cikin closet din su, tsabar ruɗu itace har karkashin gadon su neman wayar, zukunnawar da zatai keda wuya taci karo da kananun hotunan nan, tura hannu tayi tare da janyo su zuciyarta cike fal da tunanin hotunan wanene._ _Kamar a mafarki take kallon fuskokin mutanan dake akan hoton, wani babban mutun ne mai kyan sura ya ɗauki wankan tailored suit a jikinsa, ɗayan hoton baturiya ce fara sol itama suit ne a jikin ta._ _Ƙurawa hotunan ido tayi tana kallonsu ba tare data Iya gane daga ina suka fadowa ba, ko wanene Ya jefa su karkashin gado, to ko dai Aljanune suka ajiye su? ta fada acikin ranta, can kuma ta sake kallon hoton Alhaji sai taga kamar an daura mashi fuskar Sajeed banbancin su sajen dake a fuskar alhajin da kuma manyantakar sa shi kuma sajeed bai da saje a fuskarshi_ *Mu haɗu gobe idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE 1 COMMENTS Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Anonymous 27 June 2024 at 04:14 Dan Allah kurkukun kaddara takun karshe 22 Reply Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 22 Complete by Novels Elite Admin June 27, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ _________________________________E22✍️ Ta jima tana kallon hotunan kafin Ta miƙe ɗauke da su a hannunta, da sauri ta juya ta nufi mirror drawer ta buɗe gida na uku ta saka su a ciki. Tana ƙoƙarin mikewa sallamar Taj Ta katse mata hanzarin ta daga wajen dakin ta jiyo muryarsa. "Daddy gani nan zuwa na gama shiryawa, waya ta nake nema banganta ba" "Ina kika ajiyeta ne"? Watsa hannu tai kamar tana agabansa na manta daddy "Jiya naso na ganta a hannun ɗan uwan ku sajeed, bari na tambaye shi" amsa mashi tayi da toh aranta tana mai mamakin yadda sajeed yake da nacin son waya, sam baya gajiya da ita." Badajimawa ba, taj Ya turo kofar dakin Ya shigo hannunshi ruke da wayar. Face dinsa da murmushi Ya mika mata"Na lura baki son wayar nan taki, saboda ba ki damu da ita ba, me zai hana ki bar ma sajeed din tun da yafi ki sonta" Muryarta da yar shagwaba tace"wallahi inason abuna, sai dai asiya masa wata tunda Yana so, dr laura fa ta bani ita taya ma zan bada ita" ta yi maganar tare da kar6ar wayar daga hannun sa "Kin ta6a kiranta ne kunyi magana"? "Mantawa nakeyi wlh, amma in sha Allah zan kirata in na samu nutsuwa" "Baki kyautaba yakamata kiyi kokari ki kirata" amsa mashi tayi da toh "Daddy dani kadai zamu tafi"? "Eh, next time suma zan kai su gidan" Ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka fito daga dakin, babu wanda Ya lura da su fira taja hankulan su, tana kallon su Deeja dake ta faman sakin murmushi wani irin sanyi taji aranta, yanzu damuwarta akan sauran prisoners ne wadanda ke AGIDAN KURKUKUN ƘADDARA! Har sun kusa fita daga falon, Kamar ance ta wurga eye balls dinta kan second floor, kwatsam Ta hango Danish dake kallon ta, cikin shiga ta pajama launin blue sky, tayi tunanin ba ita Yake kallo ba, sai tai saurin kau da idon ta, gudun kada ya ga za su fita, tasan halin mutumin nata. Suna fita daga falon ta sauke ajiyar zuciya, kasancewar baida nisa part din nashi, A ƙafa suke tafiya suna fira hanyar da suka biyo ko'ina hasken electric bulbs ne tamkar ba dare ba ga wata iska mai ni'ima dake kaɗawa "Daugher, kina jin sautin da nake Jiyowa kuwa"? da mamaki Tace A'a daddy menene"? "Akwai mutun abayan mu, baki ji sautin tafiya ba" aɗan ruɗe ta furta mutum kuma? Wanene? bata jira ya bata amsa ba tayi saurin juyawa don ganin waye. Har saida gaban ta ya faɗi idanunta adan zare take kallon shi, Hannayensa harɗe akan kirjinsa, fuskarsa babu fara'a, kayan baccin da ta gan shi da su sune a jikinsa fararen ƙafafuwansa ko takalma babu. Juyowa taj yai tare da kallon shi, ashe tunda suka fito Yake biye da su, shi taj yasan da zaman shi itace bata lura ba. Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"daddy, mu tafi da shi kawai" ƴar dariya taj yai tare da cewa"ya zama dole ay, wa ya isa ya hana shi zuwa"? "mu tafi My man, nayi zaton kayi bacci, shiyasa ban neme ka ba, dama zamu je part din daddyna ne don in gaisa da Auntyna" kamar jira yake ta bashi damar yabi su, da sauri ya nufe su, a maimakon ya tsaya gefen ta sai ya shiga tsakaninta da taj, yasa hannu ya raba hannayensu dake ruke cikin na juna lamarin ya daurewa taj kai aranshi ya ayyana wannan wani irin namijin kishine? Uban nata ma bai ƙyale ba inaga idan wani ne daban ba? Tun yanzu ya fara jin fargaban yadda zata kaya tsakanin chief da danish tabbas akwai ƙura. A haka suka jera har suka ƙaraso ƙofar shiga Part din, Komai nasa shigen kalar na sashen da suke ne banbancin kaɗan ne amma fa Ya haɗu, Ita kanta Angel tayi mamakin katafaren Ginin gidan Chief gari guda An ƙawatashi kamar A dubai. Dafe kofar taj yai da hannunsa a hankali ta zuge masu, katafaren falo ne an kawatasa da furniture, ga wani sanyin A.c na mai sanyaya zukata Sai ƙara kallon ko'ina take tana ɗan jinjina kanta, har cikin ranta ta ƙara jin ƙaunar chief saboda kyautatawarsa ga daddyn ta. "Bismillah, Ku zauna bari naje nayi mata magana" ya fada tare da wuce ya nufi upstairs. A hankali suka zauna kan sofa, kallon sa tai suka hada ido cikin na juna. "Baki kewata ba? kin manta da dani jiya ko ki neme ni" yana magana tamkar baisan motsa lips dinsa "Ni da kai waye mai laifi? Jiya ko kallo ban ishe ka ba, ka kama hanya ka bi uncle din chief inata kallon ka ko waiwaye na bakai ba" ta faɗa tana kwa6e masa fuska Lumshe idanunsa yai batare daya furta mata komai ba "Har ciwon ciki nayi jiya kamar zan mutu, ni kadai a restroom na kasa bude kofa har na fadi kasa na suma duk kana ina"? "Ina atare dashi," atakaice Ya bata amsa Ruƙo hannunsa tai tana kalllon dogon yatsan hannunsa dake asanye da silver ring, yayi matukar yi mata kyau "Shi ne Ya baka wannan"? Ɗaga mata kai yai alamar eh, Da fara'a akan fuskarta tace"Bani labarin abun da ya faru tsakanin ku jiya"? Sai da ya fara kai soft lips dinsa saitin kunnanta kafin ya fara bata labari saboda bai iya ɗaga muryar shi. Sai faman sakin murmushi takeyi hakika taji dadin kyautatawar da prime minister yayi masa, kuma ta fahimce shima yaji dadi tun da gashi nan da bakinsa yake bata labari mutumin da be cika surutu irin haka ba. "My man, Ni dai fatana Allah yasa mutumin nan ya zama alkhairi agare ka, wlh tunda nagansa naji ya kwanta min araina saboda kamannin dake a tsakaninku..." kafin ta ƙare maganar Sautin takalman daddynta ne Yaja hankalin su ga dubansa, saukowa yai down a hanzarce Ya nufe su Yana fadin"daugher, bacci takeyi auntyn naki, ko zaki je ki same ta adaki, Inaso ki bata mamaki" murmushi tayi tare da mikewa da sauri Danish Ya miƙe zai bita, kallon shi tayi cikin sanyin murya tace"ka zauna ka jira ni, Yanzu zan fito ba daɗewa zanyi ba" Taj dake kallon su murmushi yai tare da ƙarasawa gefen Danish yace"Idan saboda ni ne, To mu zauna gani ka gaka ita sai ta shiga watakli hankalinka zaifi kwanciya,' Kamar kuwa yasan sbd shi Ya miƙe zai bita, komawa yayi ya zauna hankalinsa akan Angel dinsa Harta haura kan stairs. A hankali Ta zura kafarta cikin dakin, tana shiga ta soma bin ko'ina da kallo masha Allah, a hankali ta sauke idanunta kan Danejo dake a nannaɗe cikin bargo sai sharar baccin ta take yi. watsa wa tayi da gudu ta daddage ta haye kan gadon gaba ɗaya ta ƙanƙameta tana dariya, wata irin firgita danejo tayi cikin magagin bacci take fadin"daddyn Angel, wayyo Allahna kana ina wai wanene ke takura min! Nashiga ukuna" Yaye mata bargon Angel tayi, tana faman haki ta buɗe idanunta waɗanda suka kada jawur saboda bacci, A hankali ta sauke su kan fuskar Unaisah ta ƙura mata ido tana kallon ta, da tsantsar ruɗani take binta da kallo, Itama unaisah kallonta takeyi cike da kewarta, ba zata ta6a mantawa da fuskar denejo ba, ta ƙara haske fara jawur da ita kamar ba'indiya saboda kyau, ga gashin kan nan nata mai tsayi baki wulik har gadon bayanta.. Muryarta aɗan tsorace ta furta"wacece ke"? Mutun ko aljan"! Dariya unaisah tayi cike da nishadi tace mata"Baki gane ni na"? Waro idanu waje danejo tayi da ƙarfi ta furta"ANGEL" tuntsirewa unaisah tai da dariya tare da faɗa mata ta sake rungumeta, daura hannayenta biyu tayi akan bayanta tana fadin"Ni ce, Angel dinki, ashe da rabon zamu sake haduwa danejo na" mamaki Ya hana danejo magana, da sauri ta tallabo fuskar unaisah da tafukan hannayenta, ta kura mata ido tana kallon ta batare da ta kyafta idanunta ba, ko amafarki taga fuskar Angel sai ta shaida ta, duk da ta ƙara girma a yanzu ta zama yar matashiyar budurwa, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta, da sauri ta kwantar da unaisah kan kirjinta, itama kukanne Ya kubce mata, sautin shesshekar kukansu duk Ya cika dakin, a hankali take shafa sumar kanta tana faman sauke ajiyar zuciya, Allah ne kadai Yasan irin kaunar da take Yi mata, taso unaisah, tayi kukan rashinta kamar zata zauce, muryarta kasa kasa ta furta"Alhamdulillah Ya Allah, nagode maka wallahi bazan Iya misalta farin ciki da nake aciki ba, Ya Allah nagode maka daka bayyana min Angel ɗina, Ya Allah nagode maka...." cikin shessheƙar kuka ta faɗa, tama rasa inda zata tsoma ranta saboda murnar ganin Angel. ɗagowa unaisah tayi tasanya tafin hannu ta goge mata hawayen cikin sanyin murya tace"Aunty Danejo, naji dadi da Allah Ya sake haɗa ni dake a matsayin matar daddyna, I can't thank you enough saboda halaccin da kikai min arayuwa Allah ne kadai zai Iya biyan ki, kin so ni kin kuma kaunace ni tsakani da Allah, duk da bakisan koni wacece ba a lokacin amma kin taimaki rayuwa, kiyi hakuri ki yafe min laifin da nayi maki....' tana faɗa tana matsar kwalla. "Angel laifin me kikai min? Ni ay baki min laifin komai ba...." Girgiza kai tai hawaye nabin kuncin ta tace"nayi maki laifi, bayan mun shaƙu da juna, na gudu daga rugarku kina ji kina gani har biyo ni ki ka yi kina kiran sunana don in tsaya amma naki sauraronki, ashe da rabon in sha wahala" idanunta acikin na danejo takeyin maganar "duk da bana danasanin ƙaddarar rayuwar da ta riske ni saima farin ciki da nakeyi saboda a kowani rashi da nayi toh akwai nasara acikin sa" tun da tafara magana danejo ta nutsu tana sauraronta, har cikin ranta tana mai mamakin girman yarinyar da kaifin basirarta, komai nata na dabanne shiyasa take da saurin siye zuciyar mutune. "Aunty danejo, Kinga ikon Allah ko? Bayan na tafi sai gashi Allah Ya hada ki da daddy na har kun yi aure, amma baki takura kanki ba babu danginki a kusa, ki bani labari ya kikaji da kika fara shigowa cikin burni" yar dariya danejo tayi kafin ta fara bata labarin irin yadda ta tsinci kanta farkon shigowarta birni, ta tabka ƙauyanci taj ba karamin hakuri yayi da ita ba, saboda tsoro da rashin sabo da irin rayuwar birni. Gaba daya suka kama yin dariya kamar wasu zautattu, Yadda kasan wasu aminnan juna. "Amma dangin ki fa? Shikenan ba zaki sake haduwa da su ba"? "Ay Yayi min alƙawarin zai kaini rugarmu nan badajimawa ba" murmushi Angel tayi"amma naji dadi watakil nima in bi ki muje, in gano su hasiya da bawuro" "Baki manta da sunan su ba" jinjina mata kai unaisah tayi"ban manta ba, na haddace su akaina" "Dama kece bakuwar da zanyi"? ɗaga mata gira tai alamar eh. "Daddynki Ya faranta min raina, naji dadin ganin abun da banyi zato ba, amma lokacin da kika gudu ina kika je ne , tayaya akai aka gano ki? Ta fada cike da son jin karin bayani. "Ki manta kawai, nadai ci wahala amma komai Ya wuce, bana son tuna baya" jinjina kai tay alamar ta fahince ta. "Ina daddyn naki yake"? "Nabar shi a falo su biyu ne tare da ɗan uwana Danish" Ruƙo hannunta tayi"muje falon" saukowa sukayi daga kan gadon atare suka fito A lokacin Taj Yana zaune kan sofa tare da Danish, tun bayan tafiyar Unaisah hankalinsa Yaƙi kwanciya, musamman da yaji ta daɗe bata fito ba, taj Yaso Yaja shi da fira sai dai Yaƙi bashi hadin kai, Jin motsin saukowar su down, yasa shi saurin kai idonsa ga dubansu, lokaci daya ya sauke ajiyar zuciya ganin Angel dinsa. Fuskar taj ɗauke da murmushi yake kallon su, danejo kuwa tun da ta daura idonta kan fuskar danish gaban ta Ya fadi rass har sai da ta ɗan dakata da tafiya saboda taji fargaban ganin masifaffan kyan dake gare shi, ganin ta dakata da yin tafiyar ne yasa unaisah yi mata gyaran murya tare da cewa"Shi ne dan uwana danish, kada kiji komai atare da shi muka zo" jinjina kai tay kafin ta bi ta suka karasa saukowa down asaman sofa dake fuskantar su taj suka zauna, kowan nan su murmushine akan fuskarshi banda danish wanda hankalinsa ke akan unaisah. "daddyn Angel, inatayamu murna cikin ikon Allah sai gashi Allah ya bayyana mana ita, amma meyasa baka fada min anganta ba"? "Saboda inaso na baki mamaki" yar dariya tayi"wallahi ka bani mamaki kuma ka faranta min raina, ubangiji Allah Ya ƙara tsare mana ita daga sharrin makiya da mahassada dama duk wani abun cutarwa" har cikin ranshi yaji dadin kalamanta"ameen ameen, ga dan uwanta nan ku gaisa da shi" tun da tafara magana taki yarda ta kalli danish saboda tsoranshi da take ji, kallo ɗaya da ta masa kafin su sauko down ta gane ba shi kaɗai ba ne. Muryarta na dan rawa ta furta"eh ta fada min sunan sa danish, ya kake dan uwan angel, Ina fata kana lafiya" muryarsa kasa kasa Ya amsa mata da lafiya, ba tare da ya dube ta ba "Amma daddy Angel ya kuke da shi"? Taj yace"yanzu ba lokacin tambaya bane idan na samu time zan maki bayani, tashi muje kitchen mu dauko masu abunda kika shirya masu" mikewa tayi taj yabi bayanta suka nufi kitchen A hankali unaisah ta sanya idonta a cikin nashi, Murmushi tasakar mashi har dimple dinta Ya lotsa, sai yai tamkar baisan tana yi ba. "Ba dai fushi kake da ni ba? Fadamin ko na bata maka rai na"? Ta fada tana ɗage mashi gira wani kallon kasan ido mai kama da harara ya wurga mata "Na fahimce ka, nasan bai wuci saboda na tafi na barka bane, ni narasa gane kishin da kakeyi akaina, sau biyu kana dukan daddyna, na farko ka jefa masa pillow daga upstair saboda yayi hugging dina, na biyu kuma ka Naushe shi da wannan kafcecen hannun naka saboda ya gyara min mayafina, next time inaga hannayensa zaka karya idan Ya ƙara ta6ani..." ta faɗa tare da ɗaura kafa daya bisa ɗaya tana jifar shi da harara kallon kawai yakeyi bai tanka mata ba. "Ƙwara tun yanzu ka fara yi masa biyayya kana kyautata masa, saboda daddyna shi yake da ikon mallaka maka ni, Idan ba haka ba wallahi kana ji kana gani zai aura min...." kasa ƙarasa maganar tayi ganin yana nannaɗe hannun rigarshi, ay tuni tasha jinin jikinta, damtsen hannunsa Ya fito fari sol ga zanan tattoo na tambarin kurkukun kaddara, adan tsorace tace"my man yanzu saika buge ni akan wannan maganar" banza yayi da ita babu alamun zai tanka mata. Murmushi tayi tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake a jiye kan sofa inda tabar ta, a fakaice ta soma daukar shi video ba tare da sanin shi ba, saboda yayi mata kyau he looks so sexy cikin sleeping dress expecially da ya naɗe hannun rigarsa zanan tattoo dinsa ya bayyana. A tare Taj da danejo suka shigo falon hannayen su ruke da trays na kayan abinci, kafin su karaso tayi saurin ajiye wayar, ta yi ma danish alamar ya gyara hannun rigar sa, hannu yasa yaja hannun ya rufe damtsen nasa, bayan sun ƙaraso saman lallausan carpet din falon suka sauke masu farantan. "Bismillah My daugher, inaso ki ba auntynki mamaki, Ki zauna Ki cinye abincin nan ke da dan uwanki Danish" murmushi unaisah tayi kafin ta sauko ta zauna. "Malam Danish bismillah" ya faɗa Yana nuna masa carpet din, sam baiyi niyar ci ba, amma saboda unaisah Ya sauko Ya zauna, shima taj din da danejo suka zauna suna fuskantar su, tuni kamshin abincin Ya karaɗe hancin su, wani haɗaɗɗen dambun Shinkafa ne ta zuba masu a plate, Yaji kayan kamshi ga nama manyan yanka da ta jera masu asaman dambun, ta tsiyaya ma su juice mai sanyi a cups, tun da suka fara cin abincin, Ta lura da yadda danish yake ci kamar zai fasa ƙaramin bakinsa, da alama dambun yayi masa daɗi, hatta taj da danejo satar kallon sa suke yi su kansu ba suyi tsammanin zai iya cin abincin har haka ba, bayan sun kammala cin dambun ta sake zuba masu farfesun ƴan ciki, kamar masu fama da yunwa haka suka tasa shi gaba suka lamushe, ta kuma ƙara zuba masu gurasa haɗi na musamman taji kuli kuli da kayan lambu da aka yayyanka ga mai dake kyalli asamanta tare da tsiren nama, danish bai ta6a cin gurasa ba sai Yau, kai harta dambun shinkafar yaune karo na farko daya fara cinshi, yaji dadin abincin har ƙwarar cikinsa yayi, Angel dake kallonsa sai faman sakin murmushi takeyi ba tare da ya lura da ita ba, bayan sun kammala cin abincin kowa yayi kulu wash rabu hani'an danejo ta kwashe kayan abincin ta nufi kitchen da su "Daughter, dare yayi muje na raka ku gida, Kada chief Ya tuhume ni, kinsan yanzu bani da hurumin daukarki tun da a karkashin kulawarshi ku ke har zuwa time da zamu kammala bincike" "Bakomai daddy, na fahince ka," shafa gefen fuskarta yai, danish dake kallon su tuni ya hade ransa, shi fa har yanzu bai daina kishi da taj ba, saboda baisan alaƙar dake a tsakanin iyaye da dansu ba. Fitowa danejo tayi daga kitchen, ganin su tsaye yasa tace"ya akai nagan ku a tsaye ku zauna mana muyi firar yaushe rabo" Taj ya ce"Zasu tafi ne" ɗaure fuska tay"bangane me kake nufi ba, nayi zaton ta dawo gida kenan," girgiza kai yai"ay tana a gidan amma a part din chief suke da zama, zata dinga zuwa kuna gaisawa da juna...." dakyar ya samu ya fahimtar da ita, atare suka raka su unaisah har gida kafin sukayi masu sallama. Lokacin da suka shiga falon babu kowa har sun koma bedrooms dinsu alamar time din bacci yayi, kamar kar su rabu da danish har saida ta raka shi bedroom dinsa kafin ta dawo ta nufi nasu dakin, tana shiga ta samu deeja kwance kan gadon su sai jan minshari takeyi, murmushi tasaki tana kallon ta, har yanzu kwalliyar dazu ce akan fuskarta duk ta ca6e kamar ƴar mahaukaciya, ta jima tana kallon ta, kafin ta fara cire kayan jikin ta, ta musanya dana bacci, fuskarta dauke da annurin farin ciki, ta hayekan gadon, bata damu da rashin ganin batool ba, tasan bazata wuce dakin aunty ummin su ba, huggin pillow tai, Allah ne kadai yasan dadin da take ji sam ta manta da zancen kiran aunty pretty gaba daya tunaninta akan abun farin cikin daya faru yau ne ______________________________________✍️ Zaune ya ke kan sofa ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya, yayin da idanunsa ke akan laptop din gabansa da yake operating lokaci ɗaya ya ɗan dakata Ya jingina bayansa jikin Sofa haɗi da lumshe idanunsa zuciyarsa a cike take fal da tunanin prettynsa har yau jiran hajiya laurat yake yi don jin amsarta, tun jiya bayan kammaluwar dinner din hateem ziyad ya nemi alfarmar yin magana da ita bayan sun ke6e cikin girmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa daga bisani ya fara kora mata jawabi game da bukatarsu, lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya canza zuwa 6acin rai kamar bata son zancen Benazir da yake yi mata, acikin ranta tayi mamakin jin cewa a hannun Zaki ta faɗa ita sam ta manta da rayuwar benazir tamkar ma ba'a halicce ta adoron duniya ba, saboda tun fil azal hajiya laura basa ga maciji da hajiya layla wata irin gaba ce atsakaninsu shiyasa bata shiga shirgin abun da ya shafi layla, a lokaci shi kanshi ziyad ya lura da 6acin ran da take a ciki amma sai ta waske ta ƙaƙaro murmushi tana fadin Allah sarki benazir ashe dama zaki ne ya taimake ta? Alhamdulillah wlh nayi murna ziyad, sai dai abun da ya daure min kaina babu wanda Ya kirani daga gidan Ya fadamin cewa anganta amma in sha Allah zan fidda lokaci inje can gidan da kaina don in tabbatar ta dawo in yaso daga bisani zan tuntu6i shi zaki din...." akan haka suka ƙare magana ziyad yai mata godiya kafin suka rabu. A hankali Zaki ya buɗe idanunsa Yana kallon ceilling din falon, duk don saboda son haɗuwa da ita, ya ɗaga tafiyarsa canada. Yayi zurfi a zancen zucin nasa muryar turai ta ratsa kunnansa "First born barka da hutawa" ta faɗa tare da daura masa mug din coffee kan table, murmushi ya sakar mata, yana ɗaya daga cikin abun da yake burge shi da mommyn nasu in har zata ganshi zaune yana aiki akan laptop sai ta kawo mashi coffee . "Mom har yanzu baki yi bacci ba"? ya faɗa yana kallon ta. "Tayaya zan iya runtsawa Jazz bai dawo ba, daddynku bai dawo ba shima, su nake jira su dawo sai in kwanta" tayi maganar tare da ɗaura gwiwowin hannunta bisa ga hand sofa din da zaki yake zaune idanunta akan fuskarsa "Ko akwai wani abu dake damun ka ne"? Ta fada cikin kulawa "Babu komai" ya bata amsa atakaice tare da kai hannu ya dauki mug din Ya soma kurbar coffee "My son, tayaya zaka 6oye min damuwarka, bayan ni mahaifiyarka ce, ta ido kadai ina gane damuwarka, tun lokacin da ka shigo ƙasar nan na lura da damuwa aranka" Sauke mug din yai kan table kafin ya dubi hajiya turai"nagode da kulawarki agare ni, amma ki kwantar da hankalin ki ba abun da ke damuna" Gyaɗa kai tay"haka nakeson ji" ta faɗa ne ba dan ta yadda da maganarsa ba tasan baya son taji ne "Bari na shiga ciki, ka kula min da kanka" amsa mata yai da toh Bayan tafiyarta ajiyar zuciya ya sauke, bawai baya son fada mata bane yafi son ya fara jin halin da take a ciki in har ta isa gida lafiya, kuma iyayen ta sun kar6eta ba abun da zai hana shi sanar da nashi iyayen labarin ta. Ƙarfe goma da rabi, jazz da sir mubarak suka dawo gidan lokacin da suka shigo falon tuni Zaki Ya koma room dinsa ba su taras da shi ba, Hajiya turai na kwance kan gado tajiyo sautin sallamar sa, jikinta har rawa yakeyin wurin saukowa daga kan gadon da sauri ta nufe shi yana atsaye cikin shiga ta kakinsa "Sannu da dawowa, tun dazu nake ta jiranka nayi kewarka yau kayi dare " cikin nuna kulawa tayi maganar tare da ruko hannunsa suka shiga dakin "I'm sorry bansanar da ke zan kai dare ba, wani aiki ne mai muhimman ci Ya ruƙe ni" ya faɗa Yana kallon cikin idonta, "Ba nace ki daina jirana ba? daga kinga nayi dare to ki kwanta kiyi bacci" Maƙe masa kafaɗa tayi"kai ma kasan bazan iya jurewa ba...." murmushi ya ɗan saki"kinsan me na tuna"? Girgiza mashi kai tay alamar a'a" "Waɗannan twins din na wurin Owais, ko da yake yace min ba twins bane, ɗaya ta girmi ɗaya" da mamaki hajiya turai tace"ikon Allah, amma nayi mamakin jin hakan komai nasu fa iri ɗaya kamanninsu sun 6ace" "Zai iya yiwuwa yan gida ɗayane" jinjina kai tay alamar eh "Yaran sun kwanta min araina, kinsan ni da son ƴa'ƴa mata, duk family dinmu ni kadai ne nake da ya'ya maza ina alfahari da hakan amma inason ya'ya mata, ga hateem nan shi mazan yake so Allah bai bashi ba" shiru mom turai tayi kamar ta dan shiga damuwa, sam bai lura da halin da ta shiga ba, ya nufi toilet Ya shige jin ƙarar rufe kofar shi Yasa jiki asanyaye ta koma gefen gadonsu ta zauna idanunta sun ciko tab da kwalla.. Ceilling ta ƙurawa ido tana tunano wani abu da ya ta6a faruwa acan lokacin baya shakeru da suka gabata, ta ta6a haihuwa ya'yan suna mutuwa wanda silar hakan Yaja har sir mubarak Ya hanata haihuwar gaba ɗaya gudun kada itama tarasa ranta kamar yadda ya'yan da take haihuwa suke rasa ransu da zarar sun dira a duniya, Allah kadai yasan halin da ta shiga awannan lokacin saboda ta kwallafa rai akan son taga ta haihu da sir mubarak sai dai Allah bai bata ba shiyasa har su hajiya saratu suke yimata gorin sai dai taci ta kasayar Yunkurawa tayi jiki ba kwari ta mike ta futo daga ɗakin nasu ta nufi bedroom din jazz sai da ta matse kwallar da ta taru a idanunta kafin tayi mashi sallama shiru ba'a amsa mata ba, har ta fara tunanin ko yayi bacci ne, shigarta ke da wuya kwatsam taci karo da wayarsa dake yashe kan floor ga dukkan alamu wurgo da ita yayi, hatta lap coat dinsa anan ya jefar da ita, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, a razane ta kalli gadonsa a zaune ta same shi tsakiyar mattress, Ya kifa kansa bisa gwiwowin sa, lokaci ɗaya ta rasa sukuninta da sauri ta nufi kayan nashi ta kwashe su ta je ta ajiye masa kafin ta dauko wayar ta nufin gadon nashi ta hau sama ta zauna tana fuskantar shi "Jazz meke faruwa dakai ne"? ta fada fuskanta dauke da matsananciyar damuwa Shiru babu alamun zai tanka mata "Nasan kana ji na jazz, ka ɗago ka kalle ni sannan ka fadamin meke damunka" A hankali Ya ɗago da fuskarsa wadda ta jiƙe sharkaf da hawaye idanunsa sun kaɗa jawur, wani irin bugu taji zuciyarta tai muryarta na rawa ta furta"jazz kuka kake? Meke damunka ne? Ko bakada lafiya ne? Aruɗe ta fada tana shafa fuskarsa "Jazz dan Allah ka fadamin ko hankalina Ya kwanta" daƙyar Ya iya motsa la66ansa Ya furta sunan faryat, lokacin ɗaya annurin fuskar hajiya turai Ya ɗauke ɗuff, saboda ta fahimci silar shigarshi halin da yake aciki, batasan ya zatai da jazz ba, tayi fama da shi akan ya rabu da faryat amma yaƙiya saboda tasan bazata ta6a auran shi ba, hasalima ma yarinyar bata kwanta mata aranta ba, saboda fitsararta da rashin kunyarta.. "Jazz yaushe ne zaka daina yaudarar kanka akan yarinyar nan? sau nawa ina maka gargadi akan ka fita sabgarta? Na fada maka ba sonka takeyi ba yakamata ka hakura ka nemi wata ay ba ita kadai bace mace a duniya....." kafin ta ƙare maganar ya tarin numfashin ta da cewa"bazan iyaba mommy, Allah ne ya jarabce ni da sonta, wallahi nayi kokarin cireta araina amma na kasa ki tayani da addu'a Allah ya yaye min sonta in ba haka ba zatai silar da zan rasa raina..." har saida gaban turai Ya fadi jin abun da yace, ta fahimci mahaukacin son da yakema faryat ba lallai Ya fahimce ta ba "Me tayi maka ne"? labari Ya fara bata na abun da Ya faru tsakaninsu lokacin da ya je wurinta bai 6oye mata komai ba, har nemansa da tayi don ya bata hadin kai, "Mom kullum na kirata sai ta ci mutuncina, tace wai ni ba namiji bane tunda bazan iya biya mata bukatarta ba, sannan bazata ta6a auran mara asali dan tsohuwar mai aikin gidan su ba...." ya faɗa idanunsa cike tab da kwalla Ita kanta hajiya turai hawayen ne ke sintiri kan kuncinta, ta tsani taji ana yi mashi gorin asali kamar kanshi farau, ta rasa gane meke damun wasu mutanan sun manta cewa bawa bashi ke daurawa kansa ba? Allah ne Yake kaddara masa rayuwarsa? "Jazz ta yi kuskure A kalamanta, wallahi sai tayi danasani, saboda ka fi karfinta nesa ba kusa ba, kuma kaine cikakken mai asali tunda kana jin tsoron Allah kuma ka tsare mutuncinka, ni in banda kaddarar so ina kai ina Faryat"? ta faɗa ranta amatuƙar 6ace "Tafi ni komai tun da tana da asali" "Kaima kana da asali jazz" da sauri Ya kalle ta "Mom bangane me kike nufi ba, ke da kanki kika fada min baki da kowa a danginki mahaifina Ya rasu" girgiza kai tayi"na fada maka hakanne saboda ka fidda rai da kowa nawa, bana son maganar jazz ka cigaba da hakuri in sha Allah komai ya kusa zuwa karshe" tun da tafara magana jazz Yake kallonta har yau ya rasa gane dalilin dayasa bata son tayi maganar abun da Ya shafi danginsa, shi dama yasan dole tana da family dinta akwai dai wani abin da take 6oye masa, duk da yana neman ƙarin bayani daga gareta sai dai ya hakura yabarwa zuciyarsa zai cigaba da hakuri kamar yadda ta ce har zuwa lokacin da zata sanar da shi komai.... Shiru sukayi na wani lokaci babu mai magana a cikin su, "Ina ibad"? ya tambaya yana kallon ta "Tun bayan sallar Isha' Yai bacci, ya yi jiran dawowarka har fadamin yai ya kira layinka bakai picking ba" murmushi yayi"Allah sarki ɗan uwana, dama nasan dole ya neme ni, na sanya wayar a silent ne saboda aiki da nakeyi" "Bari na kawo maka dinner dinka nasan kana jin yunwa, but pls ka shiga toilet ka wanke fuskarka bana son ganin hawayen nan" ta fada tana nuna face dinsa da yatsa amsa mata yai da toh da sauri ya sauko daga kan gadon Ya nufi toilet. Tana ta bin bayansa da kallo har ya shige kafin Ta mike ta fito daga dakin Kitchen ta shiga ta shirya masu abinci ta fara kaima jazz a room dinsa kafin ta dauki na sir mubarak ta nufi dakin su Lokacin da ta shiga a tsaye ta same shi hannun shi ruƙe da wayarshi Yana daddanata har ya sanya kayan baccinsa "Ina kika je ne" ya fada ba tare daya kalle ta ba "Na shiga kitchen shirya maku abinci ne," ta fada tare da ajiye masa tray din bisa table, murmushin gefen fuska ya dan saki batare data ankara ba, abun da bata sani ba tun time da ta shiga dakin jazz Ya fito Yabi bayanta gaba daya ya ji maganganun da su ka tattauna har recording voices dinsu yayi a wayarsa, yayi mamaki abun da yaji suna tattaunawa, maganganun sun tsaya masa aransa, wani lokaci turai tana da zurfin ciki, in har ba la6e yayi mata ba ita da jazz bayajin damuwarsu sai in tura takai bango tukunna take sanar da shi. _______________________________✍️ Aneelerh har tayi shirin kwanciya bacci, sautin ringing din wayarta ya dakatar da ita, A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ganin sunan surukar arziƙi yasa tayi saurin picking call din idanunta na akan baby junaid dake kwance kan mattress Yana sharar baccin sa Cikin girmama suka gaisa da junansu "Aneelerh kwana biyu? Ya ki ke Ya su mamin"? "Alhamdulillah, muna nan lafiya lou" "Ina jikan nawa ko har anyi bacci" "Yayi bacci tun ɗazu" "Allah sarki nayi missing nashi, Ya maganar zuwan naku? "In sha Allah, cikin week din nan zamu zo" "Allah yakaimu lafiya" ta amsa mata da ameen daga bisani sukayi sallama taso ta fada ma hajiya adama zancen dawowar benazir amma ta bari sai benazir ɗin tazo gidansu sai ta kira ta awaya suyi magana don ta bata mamaki, murmushi tayi tare da ajiye wayar kan nightstand, ta janyo junaid on her chest ta rungume abun ta. _________________________________✍️ _Dare Mahutar bawa, sai dai bakowa ne ke samun kwanciyar hankalin runtsawa a cikin sa ba, saboda akwai wanda ya manta yaushe rabon da idanunsa su runtsa saboda rashin kwanciyar hankali_ *👹GIDAN KURKUKUN ƘADDARA👹* Daki ne madaidaici mai fadi da tsayin gaske, irin ginin dutsen nan ne dayai shekara aru aru, daga saman dakin fitilun kwai ne guda uku masu haske idan ka kalli bangon dakin ta ko'ina jirwayen jinine da ya daskare, kai harta iskar dakin ta gauraya da karnin jini da warin jikin mutanan dake rayuwa a cikin sa. Matasan Ƴan matane zazzaune kan gadajen ƙarfe, kowaccen su tana asanye da guntuwar riga launin ja wadda bata rufe gwiwar ƙafarsu ba sun rame sun ƙanjame fatar jikinsu duk sahun yakushi da kurajen fata kai gaba dayansu sun koɗe baka gane fari acikin su saboda duhun da fatarsu tayi wanda bakomai ne yajawo hakan ba face uƙubar da suke fuskanta, wadannan bayin Allahn babu irin tashin hankalin da ba su gani ba sunga bala'e da masifa tsirararsa, gaba daya an salwantar da rayuwarsu, tun lokacin da aka kaddara masu rayuwa agidan kurkukun ƙaddara amfani ake da su kamar injina, babu wani sassauci. gaba ɗayansu babu wacce ta haura shekara sha bakwai dukansu matasan Ƴan matane gwanin ban tausayi, dukkan gabban jikinsu sun raunata, ko tafiya ba su iyayi sai dai adauke su akai su inda za'a yi amfani da su in angama a dawo da su😭 zuciyarsu da fargaba take bugawa, numfashin su da tashin hankali suke buso shi, idanunsu sun kumbura suntum sun ƙafe saboda tsabar kukan da suke sha wanda tun sunayi hawaye na zuba har takaiga ruwan hawayen sun daina fitowa sai dai kukan zuciya mai ɗacin gaske, basu da wani burin dayawuce Allah Ya dauki ransu su huta. Biyo bayan da Garkuwa Ya gudu tare da wasu daga cikin prison haƙiƙa ran Elders yayi mugun 6aci matuƙa sun harzuƙa evil heart dinsu ta hasala, wanda silar hakan Yaja suka fara azabtar da sauran prisoners dake agidan kurkukun ƙaddara, babu imani ko miskala zarratin yanzu ko abinci mai dadi babu a gidan kurkukun ƙaddara babu wani jin dadi ko na daƙiƙa sai baƙar izayar rayuwa, Allah ne kadai Yasan adadin jinin da suka zubda na yaran da suke raino, da kuma Yaran da suka gur6ata ma rayuwa, wani shiri suka fara yiwa kansu saboda suna hasashen akowani lokaci za'a iya kawo masu farmakin bazata, kuma suna da tabbacin asirin su yana dab da tonuwa, basu ta6a fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba!! _Zaman tattaunawa sukayi a karo na biyu a dakin sirrinsu wanda a lokacin suka yanke shawarar za su ba ɗaya daga cikin Evil giant ɗin da suke da su horon zama prison shield saboda asamu wanda zai maye masu gurbin Garkuwar su da suka rasa saboda sun fahimci yayi masu nisan kiwon da ba zasu iya tanƙwara shi ba, da buƙatar su samu wanda zai zamanto abokin karawar Garkuwa, saboda a halin Yanzu Idan aka kawo masu farmaki tare da shi to kuwa tabbas za'a ci galaba a kansu tun da babu wani giant da zai Iya karawa da shi idan ba su elders din ba, amma Idan suka gurfanar da sabon Giant din su mai ruƙe da mukamin prison shield zai yi wuya a iya rusa su in ba wani iko na Allah ba, sannan shi wannan giant din zai iya aikata duk wani rashin imani da suke so, ba a halicci zuciyarsa da imani acikin ta ba, baƙin mugune kuma azzalumin mutun ne shu'umi mai hadarin gaske, baisan menene tausayi ba, kurma ne sannan makahone bayaji baya gani in ba umarnin ubayen gidansa ba wato Elders, Shi fa wannan giant din baida mararraba da bakin shaidanin Aljani saboda sune suka rinjayi halittarsa ta ɗan adam_ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions Our website uses cookies to improve your experience. Learn more Accept ! [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 23 Complete by Novels Elite Admin June 29, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ _________________________________E23✍️ Baiyanar sa tamkar bainar mutuwa ne, zaiyi wuya mutun ya hada ido da shi ba tare da zuciyarsa tayi yunkurin dakatawa da bugawa saboda firgitarwar dake gare sa, shin wanene Wannan Evil giant din? Asalin Sunan sa Jeremiah shi tun fil azal mugun mutunne tunkafin zamantowarsa Giant mugunta da zalunci kaɗai yasa a gaba, inaga yanzu da suka fara ba shi horon zama Garkuwar prison abun ba'a magana babban abun da zai baka mamaki ƙarancin shekarunsa dududu bai fi sa'an garkuwa ba amma a halitta basamude ne saboda girman jikinsa. A yanzu haka Yana a cikin Rijiyar sirihi, wato mataki na ƙarshe da suke ba mutun na horan zama evil giant, ita wannan rijiyar sihirin bata ruwa bace, mazauni ne na bakaken aljanu da shaiɗanu, kwanan watan da za su gurfanar da shi yayi dai dai da lokacin da suka ɗaga na yin black night, aranar za su fiddo da shi saboda rashin imani da zalunci, nayi imanin ko makiyina bazanyi mashi fatan yakai wannan ranar agidan kurkukun ƙaddara ba saboda musifar da zata afku na bayyanar Jeremiah, rayuka ne za'a salwantar bila adadin ba yara ba ba kanana ba ba tsoffi ba hatta jarirai ba zasu ƙyale ba wa'iyazubillah..... ________________________________✍️ Motsin buɗe ƙofar ɗakin ce ta karaɗe kunnuwansu kamar gumaka babu wanda ya motsa a cikin su sai faman zare idanunsu su ke yi, gaba daya sun sha jinin jikin su saboda sun san ba alkhairi ba ne ya ke tunkaro su. Dattijuwar macace tsohuwa tukuf, gata doguwa kamar Fatalwa, tun daga kasa har sama ta rufe jikinta da doguwar riga mai hula launin Ja, hannunta ɗaya ruƙe da sanda, kafafuwanta suna asanye cikin jajayen takalma, ta rufe fuskarta da mask launin Ja, tsoffin Idanunta ne kaɗai a buɗe, zuciyar mace da rauni aka santa amma ita wannan baiwar Allahn babu zuciyar imani a kirjinta, batasan menene tausayi ba, muguwar macace shaidaniya mai hali irin na kafuran farko, daga gaban rigarta akwai taurari uku masu kyalli daga gani tana ruke da babban muƙami na gidan kurkukun ƙaddara. A hankali ta zura kafarta sautin takun tafiyarta kamar na dawakai babu sassauci, daga bayanta akwai wasu gabza gabzan Giants dake take mata baya su biyu, ɗaya daga cikin su yana a ruƙe da madaidaiciyar tukunyar ƙasa an rufe samanta da jan ƙyalle, yayin da ɗayan kuma Yake ruke da faranti mai ɗauke da ganye sai ƙananun kofuna da alama ruwa ne a cikin su. A tsakar Dakin Ta dakata da yin tafiyar, wani kaskantaccen kallo ta soma jefa masu ɗaya bayan ɗaya kafin ta ba giants din umarnin su fara gudanar da abun da Ya kawo su. Mai ɗauke da tukunyar ne Ya sauke ta ƙasa yasa hannu ya buɗe jan ƙyallen da suka rufe ta da shi, cikin takun majiya ƙarfi Ya nufi gadajen ƴan matan, ɗaya bayan ɗaya ya ke damƙar su da karfi sannan ya cusa yatsun hannunsa tsakankanin cinyoyinsu, wata auduga ce naɗe cikin panties din su yake zaƙulowa jawur da ita, wani sabon salo suka 6ullo da shi idan yaran suka fara yin jinin al'ada sai su sanya masu audugar da suka tsaface ta a cikin panties dinsu, ita amfanin ta jinin al'adar da suke zubdawa ta ke tsanewa ta ruƙe sa a jikinta ko ɗiga baya yi, suna yin hakan ne saboda a buƙace suke da jinin na su wani mugun sihirine suke yi da shi. Tuni sautin koke koken su Ya cika dakin, Jikinsu sai kerma Yake yi saboda tashin hankali, duk audugar da ya curo a gabansu cikin tukunyar ya ke zuba su,, bayan Ya gama dattijuwar tai gyaran murya, da sauri ɗayan giant ɗin me ruke da faranti Yabi su ɗaya bayan ɗaya ya mika masu kofunan, wani ruwan sihirine a ciki mai kamar jini, ga ƙarni warinsa babu dadin shaƙa, bayin Allah kamar za su zauce a haka suke shan ruwan wasu har sun fara yunkurin amai amma saboda fargaban kada su zubda a azabtar da su yasa suka daure suna sha. Wani irin ɗaci ne Ya ratsa maƙogwaronsu tuni idanunsu sun kaɗa jawur tamkar garwashin wuta. "Zaku Iya ba su ganyen" dattijuwar ce ta furta maganar, watsa masu ganyen su ka yi a ƙasa, bayin Allah jiki ba kwari suka sauko kasa kamar dabbobi haka suka kama cin ganyen da aka watso masu ƙasa. Shu'umin murmushi dattijuwar ta saki ta cikin mask dinta, Har zata Juya kwatsam idanunta suka sauka akan Gado mai ɗauke da number 100, A hanzarce Ta wurga tsoffin idanunta kan Yaran dake cin ganyen rigunansu tabi da kallo masu dauke da numbers from 80 suka fara har izuwa 99 amma babu 100 nan take ta fahimci bata acikin su lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya canza zuwa 6acin rai. Da kakkausar Murya mai amo Ta furta sunanta "GABRIELA"! ta faɗa tana zare idanu cikin 6acin rai "Kada ki kuskura ki bari na sake maimaita kiran sunanki! Ki fito tun kafin ranki Ya 6aci"! Shiru babu alamun wadda aka kira da sunan Gabriela zata fito daga ma6uyarta, ran dattijuwar ya 6aci matuka ta fusata sai faman zazzare idanu takeyi tana bin ko'ina na dakin da kallo, Har yau tana mai mamakin karfin halin Yarinyar da rashin tsoranta, ga kafiyar tsiya abun a jinin ta ya ke.. Kallon sauran yaran tayi"Ina Yar uwarku gabriela take" da tsawa ta furta maganar, muryoyinsu na kerma suka amsa da cewa ba su san inda take ba.. Ɗaga murya ta kuma Yi a karo na biyu ta furta"nasan kina saurarona! Idan har baki fito ba, zakija ma sauran ƴan uwanki! Ina mai baki umarnin ki gurfanar da kanki agabana tunkafin In zaƙulo ki da hannu na" ta fada tana huci kamar zakanya, sarai tasan inda ta 6oya amma saboda karfin izza tafi son ta kawo kanta agabanta.. " Kallon giant din da ke a gefenta tay, kamar jira yake ta bashi Umarni, azafafe Ya Nufi gadon mai number ɗari, Ya zura hannu Ya damƙo ƙafarta Kamar yar dambe haka tadinga bubbuge shi da kafafunta hada karfin halin naushin sa da hannunta, wurgo da ita yai waje ta gangaro kan floor, yar guntuwar rigarta tuni ta tattare ta haura kan waist dinta da sauri ta sanya hannu ta kamo rigar ta lullu6e mazaunanta, gaba daya nannaɗadɗiyar sumar kanta ta rufe fuskarta. Yunƙurawa tayi da karfi ta miƙe tare da dunƙule yatsun hannayen ta alamar zatai faɗa sai faman haki take yi tana huci, daga ganin idanunta babu tsoro a cikin su, duk irin azabtarwar da ake yi masu baisa zuciyarta ta raunana ba, duk cikin yaran babu mai irin karfin halin ta. wani irin gumi ke tsastsafowa ta hancin ta da gefen kanta, Yarinyar ba karamin kyau ne da ita ba, ga dirin jiki tana shape irin na ƙarfafan mata, gaba ɗaya jikinta tabon raunuka ne, gefen goshin ta hada ɗinkin ciwo da aka ta6a yi mata agidan kurkukun sakamakon wani mugun rauni da ta ta6a ji akwanakin baya. Shu'umar dariya Dattijuwar ta saki tana tafa hannayenta kafin ta jinjina mata da babban yatsa ta ce"sannu da kokari Gabriella, da ace bakiyi min hakan ba da ban shaida ke jinin jatuminki bace, karfin halin ki yana burgeni ina son inga mace haka..." ta fada tana cigaba da sakin dariya mai sautin gaske. Gabriela dake kallonta tsantsar tsanarta take ji, ta tsani matar fiye da yadda ta tsani kowa a duniyar nan... Cike da karfin hali Ta furta"muguwa azzaluma.." kafin ta ƙare maganar dattijuwar ta daka mata tsawa mai razanarwa, a firgice sauran yan uwanta suka koma kan gadonsu jiki na kerma. Ita kuwa wadda akai ma tsawar babu alamun firgita atare da ita kamar ana tunzurata taci gaba da fadin"kin manta abunda na ta6a fada maki? Ni bana jin tsoronku har bada azabtarwar ku ba zata ta6a sanyani yi maku biyayya ba saboda ku din dabbobine dakikai kuma jahilai sai kun yi mummunan ƙarshe a wulakance zaku mutu...' ta faɗa tana cije la66anta da gumi ya jiƙa su. Idanu a matuƙar zazzare dattijuwar ke kallonta da wani irin fusata ta kalli ɗaya daga cikin giant din dake take mata baya da ido tayi masa magana, cikin takun majiya karfi Ya nufi gabriella gadan gadan, lokaci ɗaya ta soma ja da baya hankalinta a matuƙar tashe batasan me zai aikata mata ba, babban abun da take jima tsoro kada ta rasa ranta ba tare da ta cika burinta na ganin ta haɗu da ɗan uwanta gabriel, ba ta son ta mutu batare data gana da shi ba, daba don shi ba da tuni ta jima da kashe kanta. Watsa wa tayi da gudu ta nufi kofar shiga toilet dinsu ta buɗe kofar ta shige taja ta rufe, tana faman jan numfashi kamar daga sama taji dirar mutun a toilet din kamar aljani haka Ya faɗo mata tuni la66anta sun fara kakarwa muryarta na rawa ta soma faɗin karka kuskura ka ta6ani!! kada ka matso kusa da ni, ka ƙyaleni, Idan ka cutar dani dan uwana bazai kyale ka ba sai ya kashe ka..." sambatu tadinga yi cikin rawar murya mai haɗe da tsantsar tashin hankali da fargaba sam ta manta cewa giant basa ji basa gani, kallonsa take kamar dodo gaba ɗaya inuwarsa ta lullu6eta. Ƴan uwanta dake zazzaune kan gadajensu tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin su lokacin da suka fara jin sautin kururuwar gabriela ta cika dakinsu da wani irin azababben sautin kuka mai ƙaraji tamkar ana zare ranta nan take suka fahimci abun da giant din yake yi mata, haƙiƙa zuciyar su ta yi matuƙar karaya. Tsawa dattijuwar ta kwatsa masu babu digon imani aranta "kar in kuskura in ƙara jin sautin koke koken ku, ko da tari ne bana son ji idan ba haka ba, zansa ay maku abun da akai mata" jin wannan maganar yasa sukai shiru, kukan nasu ya koma na zuci. Tsawon mintuna goma cuf, Kafin giant din Ya fito daga makewayin sanye cikin kakinsa kamar bai aikata wani abu ba.. Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwar tayi idonta akan giant din ta jinjina masa da yatsan ta. Kafin ta juya cikin takun izza ta nufi kofar makewayin nasu ta buɗe kofar tasakai ta shiga. A kwance ta hango ta kamar matacciya babu sutura a jikinta sai faman sakin nishin azaba ta ke yi numfashinta na fita da hucin zafi, ga wani jini dake gangarowa ta tsakankanin cinyoyin ta, baiwar Allah ko ina na jikinta Ya raunata kwata kwata bata acikin hayyacin ta, ita kaɗai tasan tartsatsin azabar da ta sha, cikin fitar hayyaci take ambaton sunan ɗan uwanta gabriel, yayin da hawaye ke tsastsafowa kan kincinta masu ɗumin gaske, idanunta sun juye jawur kamar garwashin wuta, takasa tsaida gangar jikinta sai birgima takeyi saboda zogin azabar da gabanta yakeyi mata. Zuƙunnawa dattijuwar tayi saitin inda take, muryarta da gadara tace"bakin ki ne Yaja maki! Nayi mamaki da har kika Iya rayuwa, ay nayi zaton zanzo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba...." ta ƙare maganar tare da tofa mata yawu mai yauƙi kan fuskarta har cikin idanunta Ya shiga. "Faɗa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yunkurin yi min rashin ɗa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai' ta faɗa tare da kai hannu ta damƙi sarkar cross din wuyan gabriellah taja ta da karfi ta shaƙe mata wuya, birgima tadingayi cikin fitar hayyaci ta soma kokarin ceton kanta sai dai ta gaza, dattijuwar bata kyale ta ba har saida taga ta daina motsi jikinta Ya saki tukunna ta ƙarasa balle sarkar ta jefar da ita gefe ɗaya, fatar wuyanta tayi jawur saboda shakar da tai mata..... Mikewa dattijuwar tayi fuskarta babu fara'a ta sanya ƙafa ta naushi cikin gabriela tsabar rashin imani duk da ta sumar da ita hakan bai mata ba... Fucewa tayi daga toilet din, ta ba giant umarnin ya dauko gabriellah, yan uwanta na kallo ya fito da ita zindir babu kaya ya ratayata kan kafadarsa suka fice daga dakin, kamar jira suke su tafi gaba daya suka rushe da kuka mai cin rai, haƙiƙa sunji zafin abunda Ya faru da gabriela saboda suna sonta, tana taimakon rayuwarsu wurin kwantar masu da hankali idan damuwa ta addabe su sai gashi yau sun gaza taimakonta sunaji suna gani anci zarafinta an wulakanta rayuwarta. Allah kadai Yasan Ina zasu kaita? Zata rayu ko ta mutu? ________________________Gabriel💔 A firgice Ya farka daga bacci, hannunsa dafe da saitin zuciyarsa dake harbawa da karfi da karfi, fuskarsa ta jiƙe sharkaf da gumi. La66ansa na kerma ya soma ambaton inna lillahi wa inna ilaihirraji'un. zuciyarsa ce batay masa dadi, kuma yana ji aransa wani mugun abunne ya faru da yar uwarsa dake acan gidan kurkukun ƙaddara, saukowa yai daga kan gadon su, yakai hannu ya kunna switch din dakin haske ya gauraya ko'ina, idanunsa sun cika da kwalla, gaba daya ya rasa meke masa daɗi. A hankali yake yin tafiya kamar wanda aka zarewa laka sam babu karsashi a jikinsa, toilet ya shiga bayan ya fito ya nufi closet dinsu ya canza kayan jikinsa da jallabiya, kafin ya tsaya kan darduma ya fara jera nafilfili saboda yai mata addu'a. Bayan ya kammala jiki asanyaye ya ɗaga hannayensa sama ya fara addu'o'i hawaye na wanke fuskarsa Shesshekar kukansa ce ta farkar da naufal, tunkafin ya bude idanunsa kunnansa suka soma jiyo muryar sajeed Yana fadin"Ya Allah kada ka bari acutar min da ita, Ya Allah ka kare min ita daga sharrin duk wani abun cutarwa... Da wata irin kasala naufal ya sauko daga kan gadon yaje gefen prayer mat din Ya zuƙunna Yana dubansa. "Sajeed meke damunka ne naga kana kuka"? Idanunsa jawur ya kalle sa"Naufal bana jin dadin zuciyata, ina ji araina wani abu Yana faru da gabriela, kwata kwata banyi bacci mai dadi ba" Dafa kafadarsa naufal yai cikin kulawa da nuna tausayawa yace"meyasa baka ta da ni munyi sallar atare ba"? "Bana so na takura maka" girgiza kai naufal yayi"babu takura, nima yar uwata ce sajeed, zan iya hana idona bacci don muyi mata addu'a" Kallonsa kawai yai ba tare daya ce masa wani abu ba. "bro ba ka tunanin Danish zai Iya taimaka mana? Da alamun ruɗu sajeed ya furta"bangane me kake nufi ba" Naufal yace"ina nufin me zai hana mu nemi taimakonsa akan ya ɗauko mana yar uwarmu, tun da yana da ƙarfin da zai iya yin hakan" "tayaya zai iya zuwa gidan kurkukun ƙaddara Ya taimake ta? ni bazan Iya tunkararsa da maganar nan ba, saboda bana so ya sake shan wahala, Za su Iya cutar da shi idan Yaje......." Ya faɗa Yana faman matse kwalla, kafin wani Ya kuma furta kalma sautin motsin buɗe kofar dakin su Yaja hankulansu ga duban door room din, kusan a tare suka zabura suka mike tsaye suna kallon shi babu wanda Yayi zaton shi ne, saboda bai ta6a shigowa bedroom din su ba, watakil Yana ɗan zagaye gidanne Ya jiyo sautin muryoyin su shiyasa ya shigo dakin na su Har suna baki wurin gaishe da shi cikin girmamawa. Bai amsa masu gaisuwar ta su ba, gaba daya hankalinsa na akan fuskar sajeed, farar jallabiya ce a jikinsa ta kamasa. "Meke faru ne"? Ya jefa masu tambayar, da sauri naufal Ya nuna sajeed da yatsa"shi ne ke kuka" takawa yayi a hankali Ya karasa gaban sajeed yakai hannu ya dafa kafadarsa "I'm sorry nayi maku la6e, ba hali na ba ne, na fito ina zagaye gidanne sai najiyo voices ɗinku kuna magana, bakomaine Yaja hankalina ba, face sautin kukan ka, fadamin meke damun ka" da wata irin sanyayyar murya mai haɗe da kasalar bacci ya furta maganar Sajeed bai 6oye masa komai ba, dangane da Sister dinsa, ba zato ba tsammani yaji chief Yai huggin dinsa da hannu biyu kamar kaninsa, tuni yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarsa kamar an yaye mashi damuwar shi, a hankali chief ya daura hannu daya kan bayan sajeed Yana ɗan bubbuga masa bayan cikin sigar lallashi muryarsa kasa kasa kamar tameyin raɗa ya furta"ka cigaba da yi mata addu'a, Allah Yana atare da su, kuma Yana sane da duk wani hali da suke a ciki, in sha Allah komai yazo karshe, In har sister dinka nada tsawaicin kwana zata rayu ne kamar yadda kuma kuka rayu bayan wahalar da kuka fuskanta....." daɗaɗan kalamai chief ya cigaba da furta masa, ko a mafarki ba su ta6a tunanin chief zai shigo bedroom dinsu balle har ya rungumi ɗaya daga cikin su, sun kara ganin darajarsa da kimarsa a idanun su, sunyi mamakin hakan sosai, mutumin ya ƙara siye zuciyoyin su. Sai da ya tabbatar Ya kwantar masa da hankali kafin ya raba jikin su daga na juna. Fuskarsa da damuwa ya furta"time din sallar asuba yayi, ina jiranku a falo ku shirya mu tafi masallaci, ku sanar da sauran yan uwanku maza" amsa masa sukai da toh, gently ya juya har Ya kusa fita daga dakin muryar sajeed ta ratsa kunnansa. "Nagode chief, kamar yadda ka faranta min rai, kaima Allah Ya faranta maka naka" Ba tare daya juyo ya kallesa ba Ya furta"Ameen, but ku kira ni da sunana Owais, zanfi jin daɗi" Murmushi suka saki atare suka hada baki wurin furta"Yaya Owais" jinjina kansa yai kafin Yasakai Ya fuce daga dakin, wayyo Allah dadi kamar jira suke Ya fita, da sauri Sajeed Ya ruko gaban rigarsa ya soma shinshina kamshin turaren chief. "Naufal shinshina kaji" shinshinawa naufal yayi sai dadi suke ji "Wallahi baka ji dadi ba daya rungune ni, sai naji kamar an wanke min damuwana, mutumin Yana da mutunci sosai komai nasa yana burgeni....." santin chief suka cigaba dayi. Kafin daga bisani naufal yace"yana fa jiranmu zamu tafi masallaci, mu yi sauri mu shirya" 💘UNAISAH ANGEL💋 kiran sallar asubahin farko, wayarta ta fara ringing kamar zata fasa kunnuwan su, cikin duhu ta farka tare da laluba hannu ta damƙo wayar dake ajiye kan nightstand ta ɗago da ita ba tare da ta duba sunan mai kiranta ba tai picking "Unaisah! Ina kika shiga inata jaraba kiran layinki bana samu" wata irin zabura tayi aɗan ruɗe saboda bata gane wacece ba. "Nasan baki gane mai magana ba, Aunty pretty ce" Ajiyar zuciya ta sauke muryarta da kasalar bacci ta ce "Yanzu na gane, Ina kwana kin tashi lafiya" "Ki yi hakuri na katse maki baccin ki, na damu da son jin awani hali kike a ciki kwana biyu ba ki neme ni ba" Muryarta adidashe Tace"ba komai, nima kina araina" "Ban yarda ba, meyasa baki kara kirana ba? Ni ay fushi ma nake dake, kin manta dani" muryar benazir da alamun 6aci rai tay maganar. "Ba haka bane wallahi ban manta dake ba, nayi rashin lafiya ne amma yanzu naji sauƙi, wayar ma bata a hannu na sai jiya na kar6e ta" Tana jiyo sautin muryar aunty pretty tana zabga salati gaba daya ta ruɗe jin bata da lafiya "Inna lillahi! Yanzu ya jikin naki? da sauki? Murmushi unaisah tayi jin yadda ta ruɗe"ay na fada maki da sauƙi yanzu" Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar ta "Har naji sanyi araina, Allah ya ƙara maki lafiya, wallahi baki ji yadda naji ba saboda na damu dake, dan Allah Idan nan abuja kuke da zama, ki bani dama inzo gidan ku, dama yau nakeson fita anguwa" waro idanu unaisah tayi da sauri tace"a'a ni ban ma ta6a zuwa abuja ba, a kano mu ke" "Allah sarki, kinyi min nisa, in sha Allah wata rana zan kawo maku ziyara" "Nagode da kulawarki a gare ni" sun jima suna waya kafin daga bisani su ka yi sallama, ta ajiye wayar tana faman sauke ajiyar zuciya, ita kanta tana son haɗuwa da matar sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba, na farko batasan wacece ita ba? Idan har dagaske number da take amfani da ita ta sajeed ce me zai biyo baya? da wannan tunanin ta sauko daga kan gadon ta kunna hasken dakin nasu a hankali ta sauke idonta kan Deeja dake bacci tana jan minshari kwatsam taga ta fara mirginawa zata faɗo ƙasa daga kan gado, cikin zafin nama ta yi hanzarin tallabota a hankali ta wurga ta kan mattress din Murmushi ta dan saki kafin ta juya ta shiga toilet, har yau tana mamakin jinin daya dauke mata tun bayan da ta sha bakar wahala bai dawo ba, har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taji ance alamun girma ne ga mace, kuma idan tanayi boobies ɗin ta zasu kara cukowa sannan hips dinta zai ƙara faɗaɗa komai ma na jikinta zai canza ta zama cikakkiyar budurwa, a gaban sink ta tsaya tana lalubar wurin don taga idan za'a samu ko da alamunsa ne sai dai bata ga komai ba...." fuskarta ayamutse ta kalli mirror kamar zata fasa ihu haka take ji, ita da take son ta zama house wife idan har bata fara wadannan abubuwan ba ina ita ina iya zama matar aure? ta faɗa aranta, kafin ta sa hannu ta zame wuyan rigar baccin ta, ta soma leƙen kirjin ta, murmushi tayi ganin sun ƙara girma ba laifi, wani irin dadi ne Ya lullu6e ta, har yau bata bari danish ya gan su ba, saboda kullum in zata sanya kaya sai ta ɗaure su tamau don karsu fito. jujjuyawa ta yi agaban mirror din tana kallon qugunta, ni dai na rasa me angel take ma zumudi, da alama batasan meye ake azaman auran ba. Gaba ɗaya matasan gidan sun tafi masallaci, bayan sun kammala sallah shiekh imam ya zaunar da su don suyi karatun da yake biya masu kullum. Fitowa yai daga bathroom, waist dinsa daure da towel fari, gaban dressing mirror Ya tsaya zuciyarsa cike fal da tunanin halin da sajeed ke aciki, saboda Ya damu da yaran musamman wadanda ke acan gidan kurkukun ƙaddara sun tsaya masa a zuciyarsa, ayanzu baya da wani buri da ya wuce su kai masu ɗauki, shaf shaf Ya shirya kanshi cikin dark jeans tare da v neck shirt ta ɗame fatarsa. Hayewa yai kan gadonsa ya daura kansa bisa pillow, hannunsa ruke da wayarsa, layin Boss Ya danna ma kira bayan yai picking suka gaisa da juna "Inason ganinku, tare da salsabeel a room dina" amsa mashi boss yayi da toh" Bayan wasu ƴan mintuna, wayarsa tai alert, unclock Ya danna a hankali kofar ta buɗe suka shigo su uku, cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa masu "Have a seat" ya fada Yana nuna masu couch, zama sukai suna fuskantar sa... Ya ɗan dauki lokaci kafin ya dan bude idanunsa dake a lumshe ya dubesu daya bayan daya kafin ya tsayar da idanuna akan salsabeel "me yakamata mu yi? bana son abun yadau lokaci, ko dan saboda sauran yaran dake fuskantar barazana da buƙatar mu kai masu dauki....." babu wasa akan fuskarsa yai maganar Calmly Salsabeel Ya fara magana"yalla6ai, ni bani da hanyar da zan iya jagorantar mu zuwa gidan kurkukun ƙaddara, saboda garkuwar sihirina ta karye kuma ina da tabbacin daga wajen su ne suka yi min hakan, amma nasan ɗan uwana zai Iya taimaka maku, shi kadai ne yasan hanyar da zai shigar daku Gidan kurkukun ƙaddara amma fa dole mu bi komai asannu kada muyi gaggawa saboda gidane mai hatsarin gaske, wani irin kurman ginine idan har baka da ilmi akansa kai kuskuran shiga kwakwalwarka zata iya ta6uwa" Jin wannan maganar daga bakin salsabeel Yasa Taj da big guy suka kalli junansu da alamun rudani. "Amma idan har Garkuwa ne zaiyi maku jagora shi ya san ta yadda zai shigar daku ba tare da kun sha wahala ba, amma fa da wuya danish Ya bamu haɗin kai, mutum ne mai wuyar sha'ani yana da kafiya, kuma har yanzu shi garkuwar su ne zasu iya sarrafa shi daga can kurkukun, ni dai ashawarata tun yanzu ku fara jan shi a jiki kuna koya masa abubuwa masu mahimmanci kamar rubutu da karatu tun da baisan komai ba ta hakanne zai fara sakin jiki da ku har asamu abun da ake so" gaba ɗaya sun gamsu da bayanin salsabeel. Numfasawa chief yai kafin ya ce"in sha Allah zamu yi ƙoƙarin jan shi a jiki," Big guy yace"ni abunda ke ɗaure min kai da yaron kwata kwata baya son mutane su rabe shi in ba yan uwansa ba, kuma baya son wani ya rabi yan uwansa, meyasa"? ya tambaya yana kallon salsabeel "Rashin sabo ne, idan Ya saba da ku zai daina, amma fa da buƙatar ku guji bata masa rai, in har ya nuna baison abu to kada ayi masa in ba haka ba komai zai iya faruwa, idan ransa ya 6aci evil heart ɗinsa zata iya motsawa abun da bana fata" ta6e baki big guy shi dai har yanzu bai yarda da Danish ba. Shiru sukayi na wani lokaci "I understand that dealing with them won't be easy." gaba ɗaya suka maida duban su ga chief da yai maganar "in sha Allah, zamu yi zaman tattaunawa tare da chief of army, da kuma commender na america, bayan haka za mu tuntubi rassan jami’an ISOD da ke wasu kasashen, saboda taron ya shafi kowa da kowa. Dole ne mu hada kai kafin mu ci nasara a kansu. " "Haka Yakamata yalla6ai" suka fada atare Lumshe idanunsa yai gaba daya sun fahimci damuwar abunne ke addabar zuciyarsa A lokacin da basuyi tsammani ba suka ji ya furta"na rantse da wanda raina ya ke a hannunsa wallahi duk wanda na kama da sanya hannunsa a kungiyar matsafan kurkukun ƙaddara sai ya ɗanɗani kuɗarsa ko da kuwa mahaifina ne bazan raga masa ba, ..., " yayin da yake yin maganar idanunsa sun kaɗa jawur saboda tsantsar 6acin rai "In sha Allah sir mahaifinka ba zai ta6a zama ɗaya daga cikin su ba..." kafin taj ya ƙare maganar chief yai hanzarin katse sa yana huci yace"nima ina fatan hakan amma nasan mawuyacin abune, boss bana son na zurfafa bincike saboda fargaban kada inga wanda banyi tsammani ba, Ina jin tsoron ace akwai sanya hannun wani a family dina zuciyata zata karaya watakil ma hakan zaiyi silar da zuciyata zata buga...." ba su ta6a ganin tashin hankali tsantsa akan fuskar chief irin na yau ba, kwata kwata babu walwala atare da shi Hada baki sukai wurin kwantar masa da hankali suna bashi baki, dakyar suka samu ya lafa yana faman sauke ajiyar zuciya ya kifa kansa jikin pillow... Bai sake dagowa ba, kamar bacci ne yai awon gaba da shi. Miƙewa sukai atare suka bar dakin, zuciyoyin su cike fal da tashin hankali, su kansu tsoron ranar da asiri zai tonu suke yi saboda sun san dole akwai na jininsa, a kwanakin baya ya ta6a basu labarin kiran sirrin da wani bawan Allah yake yawan yi masa akan Ya binciki danginsa akwai bara gurbi acikin su wadanda suke sadaukar da yaran family ɗinsu har faɗa masa yai yaran da ake haihuwar su a mace ba mutuwa sukai ba suna nan da yaransu, bai ta6a maida hankali akan mutumin ba sai bayan da prisoners suka bayyana tukunna Ya fara gasgata maganar mutumin da har yau baisan wanene shi ba..." Abakin kofar dakin nasa suka dakata da yin tafiya suna kallon junansu damuwa ce ƙarara akan fuskokin su kowa da abun da yake saƙawa aran shi sam sun kasa magana daga bisani suka fuce. Chief Har ya fara nutsawa cikin baccinsa Wayarsa dake ajiye kan drawer ta fara ringing kaitsaye sautin ya daki kunnansa A hankali yadan bude idanunsa wadanda ke lullu6e da yalwar gashi ya kalli ceilling din dakin kafin miƙa hannu ya ɗauki wayar Motsa la66ansa yai tare da furta sunan Uncle hateem. Picking call din yai "Uncle am sorry, jiya na shiga bedroom dinsa na taras yana bacci shiyasa ban kira ka," On the other hand prime minister yace"Son ka hanani ganin maganin da zai warkar min da zazzabina....." "Sorry uncle nayi laifi ay min afwa" "It is okey, yanzu yana ina ya farka daga bacci"? "Yanzu zanje bedroom dinsa na duba sa" "Okey, akwai sako da za'a kawo masa daga company.." tun kafin ya ƙare maganar chief ya furta"uncle wani sako kenan"? "Idan an kawo zaka gani, nasan idan na fada maka ba zaka bari sakon ya iso ba, zaka hana ne" "Haba uncle, ni na isa in hanaka yin alkhairi..." "Hakane, amma bazan fada ba" ya faɗa da zolaya murmushi chief yai"andai hanani jin menene bakomai in an kawo zan gani, bari naje na basa ku yi magana" "Video call zamuyi zanfi jin dadin ganinsa" amsa masa yai da okey, janye wayar yai daga kunnansa Ya nufi desk ya dauko ƙaramar laptop dinsa Ya sauko down babu kowa sai masu aiki dake zaryar kai abinci kan dining, ta elevator ya hau ta sauke sa second floor........ Abakin ƙofar ya tsaya yai masa knocking, shiru ba abasa iznin shiga ciki ba, yanke shawarar shiga yai a hankali ya tura kofar a zaton sa bacci yake yi, yana shiga ciki yaji alamun motsinsa a toilet, har ya juya zai fita da niyar anjima zai dawo sai kuma yaji an bude ƙofar, fitowa yayi daga ci ki jikinsa asanye da kayan baccin sa Ganin mutum adakinsa Yasa shi cin burki ya tsaya yana kallon bayansa cike da mamakin wanene ya shigo masa bedroom dinsa... A hankali chief Ya juyo suka fuskanci juna, nan take danish ya ƙara daure fuskarsa tamau babu annuri. Takawa yai zuwa gabansa Ya miƙa masa hannu don su gaisa, maƙe hannunsa yai alamar bazai bayar ba, "Ba ay min haka" ya fada tare da sanya hannu ya janyo danish yayi huggin dinsa kamar zai maida sa cikin sa, kamar wani mugun abu ya rungumesa sai kankame jikinsa yake yi, bayan chief ya raba jikinsa daga nasa ya soma yi masa magana. "Barka da safiya, Ina fata ka tashi lafiya" shiru yayi bai tanka masa ba, wani kallon ƙasan ido yake jifa masa da ace chief baisan halinsa ba da sai yace ya tsane sa "Ba magana? Ko da ya ke nima dalili ne Ya kawo ni roon dinka, kar6i nan uncle dina ke son magana dakai" ƙin kar6a yayi, "Ina nufin uncle dina Hateem, mutumin dana hada ka da shi shekaran jiya, ina fata ka tuna sa" zare masa idanu danish yayi, sarai ya fahimci wa yake nufi abun da bai gane ba ta ina za suyi magana da uncle din nasa? In a low voice ya furta"yana ina"? Miƙa masa laptop din yai" anan zakuyi magana da shi ta video call" wani kallon rainin wayau danish yai masa arude ya furta"tayaya zanyi magana da shi ta wannan abun" ɗan zaro ido chief yayi, can kuma ya saki fuskarsa tunawa da wanene shi "Oh okey na fahimta lemme show you yadda zaku yi magana" bayan ya kira hateem video call fuskarsa ta cika laptop screen din, juyama danish ita yayi"look at him ku yi magana" har saida danish Yaso Ya firgita lokacin da ya sauke idonsa kan laptop screen din ganin fuskar hateem mai ɗauke da murmushi, muryarsa cike da nishadi Yace"my baby boy danish, ka tashi lafiya? Ya ka kwana jiya? Ka yi kewana kuwa ko kuwa ka manta dani" yatsun hannun sa na kerma Ya kar6i laptop din daga hannun chief Ya kura ma hateem ido yana kallonsa batare daya furta komai ba, shi mamakinsa tayaya har ya bayyana akan wannan abun? "Ka zauna ku yi magana" chief ne Ya fada tare da nuna masa gefen gado, jiki na bari yaje ya zauna yaci gaba da kallon hateem dake ta faman sakar masa murmushi "Ka yi shiru baka tanka min ba, ko dai kamanta dani ne? Fadamin sai in tuna maka" shiru yayi bai masa magana ba, mamakin duniya ya cikasa Chief dake atsaye ya harɗe hannayensa kan kirjinsa sai kallonsa yake yi zuciyarsa cike fal da tausayin rayuwarsa baiyi tunanin tsayawa ya kammala wayar ba sai ya juya ya fita daga dakin. "Bazan damu ba, kallon da kake yi min ya tabbatarmin da ka gane wanene ni, shekaran jiyama da muka fara haduwa sai da nasha wahala kafin Ka yi min magana" ya faɗa yana murmushi. "Nakasa jurewa ka tsareni da wadannan kyawawan idanun naka please ko da zagina ne kayi ni dai burina naji muryar nan taka mai kwantar min da hankali, chief bai fada maka nayi zazzabin rashin ka ba"? Ya fada yana marairaice masa fuska alamar zaiyi kuka... Yana faman furzar da numfashi Ya dan motsa la66ansa kamar baison furta maganar yace"ina son ganin ka" "Ba ga ni kana gani na ba" girgiza kai danish yai alamar a'a "Ka fito kazo nan dakina" "No bazai yiwu ba, ay bana kasar yanzu ina canada kai kuma kana nigeria, sai na hau jirgi tukunna zan iya zuwa wurin ka" hankali atashe danish Yace"a'a ni dai kawai kazo ka fito daga wannan abun ina son ganinka" waro idanu hateem yai da alamun ruɗani akan fuskarsa. "Ba yadda za'ae na fito, laptop ce fa, baka ga ƙarama bace taya ni da nake babban mutun zan fito ta cikin ta" kamar zai sanya masa kuka yace"ni dai kazo ina son ganinka" ya fada yana shafa laptop screen din a kokarinsa naya gano kofar da zai buɗe wa prime minister Ya fito waje..... Chief owais Na awaje Yajiyo sautin fashewar wani abu daga dakin danish.... *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions Our website uses cookies to improve your experience. Learn more Accept ![14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 24 Complete by Novels Elite Admin June 30, 2024 Novels Elite English _*~✊💋BOSSLADIESWRITERS💋*~_ سجن القد💋🔥💞 ~Takun Ƙarshe🔥~ Dedicated to Aunty Kubra💋💞 قصة حب رومانسية غير عادية بين السجناء مع تطورات معقدة💋💘😘 An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists ❤💋💘 Daga alƙalamin Boss Bature💋✊ Chief na waje ya ji yo sautin fashewar wani abu daga dakin danish, a hanzarce ya tura kofar ya shiga kwatsam ya taras da abun da banyi tsammani ba Gaba ɗaya ya fasa laptop din, ya raba ta gida huɗu, hakan bai masa ba sai da Ya zuƙunna a gaban pieces ɗin Ya sa hannu Yana tatta6a su kamar wani zararre komai ya kwance masa Chief Ya jinjina ma lamarin, abun ya ɗaure masa kai tamau, ta inda ya gode ma Allah laptop ba wadda ya ke aiki da ita ba ce, da kuwa yaja masa babbar asara. "Meyasa ka fasa ta? why pls ? Ko kallo bai ishe shi ba, damuwarsa akan Hateem ne da bai gani ba bayan yasha wahalar balla abun Girgiza kai chief yayi"da ita ne zaka iya amfani wurin yin magana da shi saboda baya a Nigeria" ɗagowa danish yayi fuskarsa a yamutse gaba ɗaya ya rasa sukuninsa, shi fa ya fasa ne da niyar ya buɗe ma prime minister hanyar da zai iso gare sa. "It is okey, koma ka zauna kan gadon ka, a hankali Ya koma kan gadon yana faman bin laptop din da kallo Ƙarasawa chief yai tare da kwashe pieces din ya fuce daga dakin Ya koma bedroom dinsa Yana shiga wayarsa ta fara ringing Da sauri Ya ɗaura laptop pieces din kan couch kafin Ya ɗauki wayar yai picking "Owais meya faru ne? Muna cikin yin magama da shi naji ɗuff ya katse kiran" "Uncle mai kuke tattaunawa ne da shi"? "Cewa yai yana son ganina in fito daga laptop din, nace masa bayadda za'ay amma ya matsamin shi ne fa naji shiru kiran ya katse" "Uncle Ya 6alla laptop ɗin, gaba ɗaya ta tashi aiki, Allah Yaso ma ba wadda nake amfani da ita bane ay dayaja min asara" Muryar Hateem da mamaki Ya furta"what? Ya fasata? Amma meyasa yayi haka"? "Saboda ka ƙi fitowa, may be yana nema maka hanyar da zaka fito daga cikin ta ne" Kusan atare suka fashe da dariya daga hateem din har chief din saboda abun Ya basu mamaki da al'ajabi...... Dakatawa sukai da yin dariyar, kowan nan su yayi shiru na ɗan wani lokaci, kwatsam sautin shessheƙar kukan prime minister hateem Ya karaɗe kunnansa lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga saboda jin abun da bai zata ba, aruɗe ya furta"uncle? Kuka kake yi? Ko dai kunne na ne suka ji min badai dai ba"? Muryarsa araunace Ya furta"Ina tausayin rayuwarsa owais, ya karya min zuciyata yau, mutum har mutun baisan komai ba, da ace ya taso cikin kulawar iyayensa koda ba dan masu hali bane zai samu ilmin addini dana zamani dai dai gwargwado....." yana magana sautin na fita da alamun kuka maitsuma zuciya. Lumshe ido chief yai kafin Ya furta"pls ka kwantar da hankalin ka uncle, zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ya samu ilmi akansa, kamar yadda nayi maka alƙawarin bashi kyakkyawar kulawa..." "Owais idan zai yiwu ku sanya shi makaranta, Ni zan ɗauki nauyin karatunsa because I want him to be like everyone else. ni wallahi da zaka bani dama zansa akawo min shi nan canada" Cikin kwantar da murya owais yace"Uncle zuwansa canada bazai yiwu ba, akwai abun da ban fada maka dangane da rayuwar su ba, amma dan Allah kayi min Uziri uncle nan badajimawa ba zan sanar da kai komai....." Yana jiyo sautin ajiyar zuciyarsa"Toh zan jira har zuwa lokacin, Allah yasa inji alkhairi, yanzu sai yaushe zan sake yin magana da shi saboda bangaji da ganin sa ba" "Ka bani lokaci uncle, zanyi kokarin fahimtar da shi yadda zaiyi amfani da laptop din" "Okey, nagode my son, sannan ina mai baka hakuri amadadinsa" "Kada ka damu uncle, ay ba yin kansa bane rashin sani ne" kwantar masa da hankali Yaci gaba da yi har ya samu ya shawo kanshi kafin daga bisani su ka yi sallama zama yai gefen gadonsa zuciyarsa cike fal da tunanin abun da ya faru. _________________________✍️ "Deeja! Deeja" kamar daga sama taji ana ƙwala mata kira, firgigit ta ware idanunta masu ɗauke da bacci ta sauke su kan ceilling da alama batasan daga ina ake kiran ta ba sai faman ƙyafta ƙyafta idanu ta ke Yi, fuskarta ta ca6e da jan bakin ta "gani anan tsaye ina kallon ki" wurga ido tai kan Unaisah da ke yi mata magana, tana a tsaye ta ruƙe qugu da hannu ɗaya, wata hadaddiyar riga doguwa ta sanya a jikin ta black colour tabi shape dinta ba karamin kyau tayi mata ba, hada light make up akan face dinta, tayi rolling veil ga wani daddaɗan fragrance dake tashi Zumbur khadeeja ta miƙe zaune fuskar a jagule take kallon ta "Sorry na katse maki baccin ki, safiya tayi tun ɗazu, ga shi ko sallar asuba bakiyi ba, yakamata kije kiyi sannan ki yi wanka ko kin ji dadin jikin ki" Yamutsa fuska Khadeeja tay"to ke din wacece ne? Kin cika ni da surutu Ina yaya salsabeel da su rubina"? Murmushi unaisah tayi"Yar uwarki ce unaisah baki gane ni ba"? Harara ta jefa mata"ni bansan ki ba Allah, ki fadamin ina yan uwana suke"? Zuba mata ido unaisah tayi da alama zatai kafiya, don ma tasan halin kayan ta. "Yan uwanki suna nan a cikin gidan nan, amma waye ya kawoki ɗakin mu jiya"? Sosa ƙeya tayi kafin tace"harisuna, shine Ya rakoni in kwanta" "Okey yanzu ki tashi ki shiga ga toilet can" ta fada tare da ɗan juyawa ta nuna mata kofar da hannu, saukowa tayi daga kan gadon tana miƙa tare da hamma ta nufi toilet ta shige, unaisah nata bin ta da kallo har ta shige. "kin canzamin kamar ba deejana ba, naso ace kina acikin hayyacinki komai Ya faru nasan zakiyi farin cikin saurayin rayuwar da muka samu, Allah Ya baki lafiya my sister" Bakomai take tunawa ba, face ranar da giant ya tafi da khadeeja da kuma lokacin da aka dawo masu da ita taje gaban gadon ta tana shessheƙar kuka ta tada ta daga bacci taja ta suka shiga toilet har take fada mata abun da akayi mata bayan an ɗauke ta Tuni taji jikinta yayi sanyi lakwas rayuwa kenan, babu wanda yayi tsammanin zasu kai wannan lokacin araye sai gashi Allah ya raya abun shi, dama ance wuya bata kisa sai in kwana sun kare. Faɗowa Dakin Haris Yayi, fuskarsa dauke da tsantsar farin ciki sai faman sakin murmushi Yake yi, ba don komai ba sai don zumudin ganin deejansa jiya da ita Ya kwana Aransa yanzu haka yazo ne don Ya ƙara ganinta ya kuma tabbatarwa kansa ba mafarki bane abun da Ya faru Jiya. Unaisah Na ganinsa Tace"ba sallama? Me ma Ya kawoka dakinmu da sassafe"? Shafa sumar kansa yai"ina deejana"? Aɗan ruɗe tay pretending"deeja kuma? Kayi mafarki da ita ne"! Hankali atashe Yace"bangane me kike nufi ba, wani irin mafarki bayan jiya sun zo gidan nan har mu ka yi shagali, da kaina ma na rakota dakin ku da tace min tana jin bacci. Fuska adaure tace"haris? Ko dai ka fara samun ta6in hankali ne? Meya kawo maganar deeja? Bayan ta riga da ta rasu tun a prison"? Yanayin yadda tayi magamar ba karamin kayar masa da gaba tayi ba jikin shi yai sanyi gwiwarsa ta sage "Kina nufin mafarki nayi jiya" ɗaga masa gira tay"zai iya yiwuwa" shiru yayi zuciyarsa ajagule yake kallon unaisah gaba daya so take ta rikita lissafin ƙwalwarsa .. "Lafiya ka tsaya kana kallona? Meke damunka ne"? Ƙwalla ce ta ciko idanunsa muryarsa na rawa ya furta"deeja na ta mutu? mafarki nayi jiya sunzo? har ta buɗe baki zata bashi amsa Kwatsam Deeja Ta banko kofar toilet din kamar an wurgo ta da karfi ta furta"Laahh! Haris kaine? Yana jin muryarta a ruɗe Yakai dubansa gareta lokaci ɗaya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da gudu Deeja Ta nufe sa ta ƙanƙame shi tana fadin"wallahi jiya har mafarkinka nayi harisuna" "Deejana Kin tashi lafiya"? Tana faman Washe Baki tace"lafiyalou wlh, nima muryarka najiyo ina ga daga Cikin toilet, Har na fara alwala na katse ta" Unaisah dake kallonsu tana dariya gaba daya mamakin ƙaunarsu ya gama cikata, wani abu daya ɗaure mata kai yadda deeja Ta yarda dashi bayan jiya sukai ta fama da ita akan ta tuna shi amma taƙiya sai gashi da yake kaunar tasu a jini take har sun shaƙu jiya izuwa yau "Sister kada ki sake yi min irin wannan wasan, zuciyata zata Iya bugawa Allah" Yai maganar idonsa akan Unasah "Naji romeo, bazan ƙaraba, Yanzu sai kabarta ta koma ta karasa alwalar ko fa salla batai ba" Harara deeja ta watsa mata"waike ina ruwanki dani in ma banyi sallar ba, ay ni ba kullum nakeyi ba sai na ga dama, Ko su hawwa basu min dole balle ma ke da bansan wacece ba' muryarta da shagwa6a take magana hakan bakaramin dariya ya basu ba Lalla6ata haris yayi"rabu da ita, kishi takeyi da take don taga kinfi ta kyau, " washe baki tayi jin Yana yabonta "Yanzu ki koma ki karasa alwalar in kin gama ki yi wanka sai ki fito muje muyi breakfast" amsa mashi tayi da toh da gudu ta juya tana fadin Kada ka tafi harisuna ka jira ni in fito Yana murmushi ya amsa mata da toh har ta shige bai daina kallon ta ba Da zolaya unaisah tace"Hankali Ya kwanta Haris, deeja Ta dawo, No more heartbreak " dariyar farin Ciki Ya saki" ba zaki gane ba, wlh daren jiya bayan na rakota dakin ku ta kwanta dana koma dakinmu har nafila nayi saboda in nuna godiya ga Allah daya sake hadani da ita, Ina son deeja Allah Yabar mun ita har abada, in ma mutuwa zata dauke ni ta dauke mu atare" idanu abude Unaisah ke kallon shi aranta tunani take tsakanin deeja da haris da kuma ita da danish suwaye sukafi son juna tsakani da Allah? anya idan danish Ya rasata zaiyi ciwon zuciya kamar yadda haris yayi akan deeja? Ko kuwa ita idan tarasa shi zatai hauka? tabbas A yanzu bata iya ganewa tun da wani bai ta6a rasa wani a cikin su ba, kuma bata fatan abun da zai raba ta da muradin ranta, her eternal lover "Haris Ina tayaka murna, Allah Ya nuna mana ranar auranku mu sha biki" da mamaki ya maimaita kalmar aure" yar dariya tay"cikar burin masoya kenan idan time yayi basai na maka bayani ba" murmushi kawai yayi duk da baisan me akeyi a auranba but maganarta tasa shi fara jin son ganin auran nasu. Ƙarfe tara daidai agogo ta buga, ɗaya bayan ɗaya suke fitowa daga dakunansu zuwa dining Room kowan nan su yayi wanka Ya shirya sunyi kyau daga ganin fuskokinsu zaka shaida Anyi kwanan farin ciki daren Jiya.... Da wani irin ɗaukin junansu suka fara ƴan rungume rungumen juna, gwanin ban sha'awa, ƙaunar su a jini ta ke, harta chefs din dake a dakin cin abincin kallon su sukeyi saboda sun siye zuciyoyin su. Mutun ukune ke babu acikin su, ummi da batool sai Danish, su kadai ne ba su kaiga ƙarasowa ba. Sun cika dining room din da surutu Ko zama sun kasa yai, Gyaran murya chef Yai masu Hankalinsu Ya dawo kan shi "Barkanku mu da safiya yan mata da samari, ina fata kun tashi Lafiya" a tare suka amsa mashi da lafiyalou "Yawwa, Yanzu ba lokacin surutu bane, lokacin bama ciki hakkinsa ne, nasan kunyi kewar Juna amma Ku ɗanyi hakuri ku zauna mana" murmushi Kowan nan su Ya saki, ɗayan Chef din Yace"Amma in ba damuwa zamu iya sanin sunayenku? Don gaskiya bansan sunanku ba unaisah kadai nasani' Ya faɗa Yana nuna ta da yatsa "Ba damuwa ni zan faɗa maku sunayen su," unaisah ce tayi maganar, kafin ta fara faɗa masu sunayen "wadannan biyun masu kama da twins sunayen su Jemimah sai Azeeza" ta faɗa tana nuna su da yatsa sai faman sakin murmushi sukeyi. Ɗaga masu hannu chefs din sukai alamar suna miko gaisuwa "Sajeed Naufal and Javed" ta nuna kowannansu da yatsa "Wannan Kuma sunan sa Haris ga deejarsa a gefe, kamar anta da jini suke" "Kina nufin masoya ne"? Ɗaga masu kai tay alamar eh" "Wow masha Allah, shiyasa suke bala'en kama da junansu ashe soyayyace atsakani, Muna miƙo maku gaisuwa" chefs din suka fada suna ɗaga masu hannu, washe baki deeja tayi shima haris din murmushi ne kan fuskarsa "Ita kuma wannan sunanta Hannah" ta nuna hannah dake tsaye gefen parven, ga kuma Parveen acici" dariya sukai don sunsan Halinta na cin abinci" Juyawa tayi kan su Rubina"rubina, eve and yasmin sai hibba" da sauri eve tace"kin manta jiya na fada maki yaya salsabeel Ya canza min suna hawwa" "Yeah Na tuna sunanta Hawwa, ga kuma sarah da mubeen" ta nuna su da hannu "thank You unaisah, kunga yanzu munsan sunan kowan nan ku saura mu saba da juna koba haka ba"? Atare suka hada baki wurin amsa masu da Yeah "Yanzu zamu fara shirya maku wurin zamanku tun da mun samu ƙaruwa" Ba tare da 6ata lokaci ba, mutun sha Biyu daga cikinsu suka zauna akan 12-seater dining table din da suka saba cin abinci akan shi, sauran suka samu gurbin akan 6-sitter dama ukune a dakin cin abincin. Har sun fara cikin abincin, sautin cokulansu Ya cika dining room din kamar a restaurant yanayin yadda suka zauna, chefs din suna daga tsaye suna kallon. Miƙewa unaisah tayi tare da kallon chefs din tace"zanje na kira aunty ummi da batool" bata jira amsar su ba tay saurin kama hanya don tasan zasu iya tsayar da ita.. Har takusa isa ga stairs, sai ga su sunfito daga daki, Hannunsu ruke cikin juna yadda kasan uwa da ɗiyarta, ummi na asanye da abaya maroon tayi rolling, batool tun kayan jiyane a jikin ta riga da wando na bacci Suna ganinta a tare suka sakarwa juna murmushi da sauri batool ta saki hannun ummi ta nufi unaisah suka rungume juna kamar sun jima ba su a tare "Barka da safiya My own sis, jiya ko ki neme ni, aunty ummi ta ƙwace min ke" ta faɗa tare da raba jikin su daga na juna. "Ni da ke waye mai laifi? jiya kamar zanyi hauka wurin nemanki, ina kika je baki fada min ba"? rai aɗan 6ace tayi maganar suna kallon juna "I'm sorry, nima bada son raina na tafi nabarki ba, naga kuna firar yaushe rabo kuma bana son in katse ku shiyasa na tafi...." "Ina kike je ne"? Ummi ce ta jefa mata tambayar "Part din daddyna dake acikin gidan nan, " da mamaki ummi tace"oh dama anan yake zaune? Ko da yake naga gidan ba karamin girma ne da shi ba, ay ko zan haɗu da shi maimakon ya gayyace mu muje baki ɗaya shine ya ware ki ko"? Ta fada da zolaya yar dariya unaisah tayi"wlh ba haka bane, yace min next time kuma zai gayyace ku kuje part dinsa wurin auntyna danejo" Murmushi ummi tayi"ai ko bai gayyace ni ba zanje da kaina, ko dan ingano danejo, inyi mata godiya saboda taimakon da tayi mana wurin ceto rayuwarki" Fuskarta dauke da murmushi tace"naji dadin maganarki aunty ummi, Allah yabarmu atare" amsa mata sukai da ameen "angama shirya mana breakfast a dining, naga baku futo ba shi ne nazo don in kira ku" "Yanzu haka da kika ganmu yunwar ce ta koro mu nida baby girl dina" ta faɗa tare da ruko hannun batool har zata ruko na unaisah donsu tafi a tare tayi saurin cewa" zanje na kira danish ne" amsa mata tai da okey, bayan sun tafi ta nufi bedroom dinsa tana gab da zata shiga taji motsin fitowarsa kusan atare idanunsu suka shiga cikin na juna kwata kwata fuskarsa babu annuri ganinta da yayi ne yasa shi ɗan sakin fuskarsa tun daga kan yatsan kafarta ya fara kallonta ba karamin kyau tayi mashi ba, rigar ta ƙara fito mata shape dinta. "My man, ina fata ka tashi lafiya," lumshe mata ido yai alamar eh "Oh ba zaka min magana ba, kasan kuwa yadda na ƙagu da inzo ganinka" ta faɗa tana jifar shi da kallo mai kama da harara irin kallon da ke jan hankalin shi gareta "Saboda kaga na damu kai ko" ta fada tana ruƙe qugunta Daƙyar Ya iya haɗiyar yawu Ya furta"kin tashi lafiya" Ɗaga mashi gira tayi"ina lafiya, pls ka shiga ka canza kayan baccin nan, sauran yan uwanmu suna jiranmu a dining muyi breakfast" "Mu shiga atare" maƙe masa kafada tai"a'a zanjiraka anan, ka shiga ka fito" batai aune ba taji yaja hannunta cikin dakin, ba yadda ta iya dole tabi shi ciki. Juya mashi baya tayi bayan ta cire hannunta daga nashi tace pls ka sanya kayan suna jiran..." kafin ta ƙare maganar ba zato ba tsammani taji Yai huggin din bayanta gaba daya ya kwanto da kanshi kan shoulder dinta tare da zagayo hannayensa kan waist dinta, a matuƙar ruɗe ta furta"meye haka"? Ta fada tana kokarin raba jikinta daga nashi, kamar ya ɗaureta da igiyoyi sam ta kasa ƙwatar kanta ƙara tighting nata yai tuni taji wani irin yanayi da bata ta6a fuskantar shi ba, rai a6ace ta fara zazzaga mashi masifa kamar baisan tanayi ba Muryarshi tamkar tame jin bacci Ya furta"ki taimaka min na sanya kayan" gaba ɗaya nema yake ya burkita mata lissafin kwalwa, muryarta na rawa ta furta"wai meke damunka ne? akan wani dalili zan taimaka maka ka sanya kaya"? A hasale Ta faɗa tare da kamo hannunsa dake akan cikinta tasoma kiciniyar banbare shi bakomai take jima fargaba ba face ɗan mayafin data ɗaure kirjinta da shi muddin ya warware danish zaiga abun da yajima yana jira kuma tasan sauran in har ya gani sai wani abu ya faru. Kamar zata fashe da kuka tace"danish ka sakeni banaso, Babu kyau! Ka matse min cikina! tsabar masifa idanunta arufe ta furta maganar Babu akamun zai saketa sai faman goga tsinin hancinsa Yakeyi akan fatar wuyanta wani irin Yanayi da bai ta6a jin makamancinsa ba. A lokacin da baiyi tsammani ba, Yaji ta gartsa masa cizo A hannunsa, ba don Yaji zafi ba Ya saketa, da wani irin kallo Yabita har ta fuce daga dakin da gudu..... Fitarta keda wuya Yaji kamar ancanza mashi tunaninshi, lokacin ɗaya yafara tunanin me yasa yayi mata hakan❓ Tun akan stairs jikinta ke kakarwa kamar wadda sanyi ya kama, Gaba ɗaya Ya jefata cikin Yanayi kamar bata a hayyacin ta Sam bataji takun tafiyar sa ba, har sai da muryarsa ta katse mata zancen zucin ta"Good morning daugher"! Wani irin firgita tayi don sai taji kamar muryar danish ne ganin daddyntane Yasa tayi saurin daidaita nutsuwarta gudun kada Ya fahimci wani abu Ya faru. Jiki asanyaye ta nufe shi ta fada kan kirjinsa tana faman sauke ajiyar zuciya ta furta"daddy Ina kwana, Ina auntyna danejo, Ina fata kun tashi lafiya" Dago da fuskarta yai suka hada ido cikin na juna, farat ɗaya yaɗan fahimci wani abu na damunta "Kamar wani abu na damunki? Ko baki da lafiyane" adan rude ta girgiza masa kai"bakomai daddy lafiyana lau" Ajiyar zuciya ya sauke "Auntynki tana gaisheki, Kamar zata sanyamin kuka tun jiya bayan mun yi maku rakiya mun koma gida ta dinga yi min surutu akanki, yau da safe har ce min tai zakizo nace mata aa sai tace min tana son tazo taganki dakyar fa na lallasheta ta hakura' Murmushi unaisah tayi"Allah sarki auntyna. Kada ta damu har sai ta gaji da ganina' Ruƙo hannunsa tai acikin nata"daddy muje muyi breakfast" "Am sorry daughter bana Jin yunwa, aunynki ta cika min cikina, but da anjima idan na shigo zamu ci dinner a tare yanzu zan tafi dama na shigo ne don inga sanyin idaniyata" farfari tayi masa da ido yakai hannu ya ɗan ja kumatunta huggin dinta Ya sake yi kamar karsu rabu "Ki kula min da kanki, Allah Yayi maki albarka," amsa mashi tayi da ameen daddyna kaima ka kula min da kanka Bayan sun raba jikinsu daga na juna. har ya juya zai fita sai kuma Ya ɗan dakata tare da waigowa Ya kalleta tana atsaye bata motsa ba itama shi din take kallo "Kin shiga wurin chief "? Girgiza masa kai tay alamar a'a,"pls ki dinga zuwa kina gaishe da shi, inaso kina kyautata masa dan Allah" "In sha Allah daddy, zanyi kamar yadda kace" "Ina wayarki ne" "Nabarta adaki" "Okey, zan tura maki sakon contact dinsa, ko da baki samu zuwa wurinsa ba, ki dunga tura masa sakon gaisuwa ko ki dinga kiransa awaya kuna gaisawa" cike da ladabi ta amsa mashi da toh, murmushi suka sakar ma juna kafin taj Ya fuce daga dakin Gaba daya abunda suka tattauna akan kun nan danish dake tsaye kan stairs Ya ɗaura gwiwar hannunsa na dama akan handrail, fuskarsa kamar jan gauta tsabar 6acin rai, ashe Yaji maganar Taj na cewa tadinga zuwa part din chief lallai kam akwai ƙura mai hayaƙi Saboda abunda danish Yai mata gaba daya taji breakfast din Ya fita aranta, kamar an dauke mata yunwar cikinta, wani irin fitsari Taji Ya ɗaure mata mara, ba arziki ta nufi dakinsu duk Yana kallonta, tana shiga ta faɗa toilet taja ƙofa. Tunda tafara sakin shi take ganin wani bakon abu da bata ta6a gani ba, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, bayan ta yi tsarki, gaban madubi ta tsaya zuciyarta na harbawa da wani irin sauri, In har fa bata gano menene ba hankalin ta bazai ta6a kwanciya ba... A 6angarensu ummi bayan sun zauna a dining chairs din, cikin girmamawa su rubina suka gaishe da ita, da fara'a ta amsa masu yayin da take kallonsu masha Allah, Gida Yayi albarka, dagowa tayi suka hada ido da chiefs din dake kallonta daga masu hannu tayi"hi sannunku da kokari" amsa mata sukai Da yawwa madam ba tare da sun daina kallon ta ba, ba tun yau ba indai zasu ganta sai sun bita da kallon mayuntaka wato sunga sura.. Gwanin ban sha'awa suke cin abinci, sam babu wanda Yayi tunanin Ina danish da Unaisah saboda firar da suke ɗan tabawa da su rubina taja hankulan su ... ___________________________Hajjaty✍️ Wuraren karfe 11 na safe ta fito daga kitchen hannunta ruke da madaidaicin faranti mai dauke da mug na green tea da kayan marmari Tuntana tafiya take jin motsin mutun abayanta alamar akwai wanda ke bibiyarta, da zarar ta juya sai taga wayam babu kowa, hakanan ta dinga jin tsoro da fargaba, gashi babu kowa main falo din gidan duk suna a part din su. Tana tafiya tana ƴan waige waige kamar zatayi tuntu6e, cikin takun sauri ta ƙaraso dakin baba obie, sallama ta fara yi masa daga ciki tajiyo muryarsa ya amsa mata sallamar tare da bata iznin ta shigo a kishingiɗe ta same shi kan gadon shi, Ya tada kansa a pillow, hannusa ɗaya ruke da cazbaha yayin da idanunsa ke a lumshe, tuni kamshin turarenta Ya karaɗe ilahirin dakin har saida Ya ɗan buɗe idanunsa.. A hankali Ta ɗaura masa tray din kan table "Barka da safiya baba, Ina kwana, kun tashi lafiya"? Murmushi ya sakar mata kafin yace"lafiylou Alhamdulillah, Ina fata kema haka" ta amsa masa da eh Mug din ta dauka ta mika masa yasa hannu ya kar6a tare da yi mata godiya' "Ko akwai wani abu da kake buƙata" ta faɗa cikin kulawa, bakomai ya fado masa aransa ba face maganarsu ta jiya shi da owais lokacin da yace masa ko yana son ta, shi kanshi yana yaba kulawarta da kyautatawarta agaresa matar tayi ta ko'ina, ga iya daukar wanka....jin yayi shiru bai amsa mata tambayarta ba yasa ta ɗan ɗago ta kallesa ganin kamar ya koma bacci yasa tace"baba ko ka koma bacci ne"? Girgiza kai yai alamar eh, "Idona biyu ke nake kallo" waro idanu tayi waje jin abun da yace da sauri ta sunnar da kanta ƙasa Ƴar dariya yayi ganin yadda ta ruɗe"kwantar da hankalin ki, ay ba laifi bane don na kalle ki, kinyi min kyau ne" gaba daya ta ƙara kame kanta, dakyar ta kakaro murmushi kan la66anta "Tashi ki tafi, nagode da kulawarki agare ni"nike da godiya" ta fada tare da mikewa ta nufi kofar fita kwatsam tajiyo sautin takun mutun, lokacin da ta fito bata ga kowa ba, tunani tayi anya ba wani ke bibiyarta ba? ga dukkan alamu anyi masu la6e, tuni tasha jinin jikin ta, da sauri ta miƙi hanya ta koma dakin ta, kamar yadda tabar pravin haka ta same shi kwance ya lullu6e rabin jikinsa da barko. Zama tayi gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya. Jin motsu motsin pravin yasa ta kalli bargonsa, murmushi tasaki ganin Ya fara buɗe idanunsa alamar zai farka, da sauri ta faɗa kan jikinsa muryarta da yar shagwa6a take fadin"babyn baby, tun ɗazu nake jira ka farka, ina fata ka tashi lafiya....." da wata irin kasala Ya ware manyan idanunsa da suka kada jawur saboda bacci ya sauke su kan fuskar hajjaty, manna masa sumbata tayi kan lips dinta kafin ta sumbaci karan hancin sa "Honey, ina alkawarin da kayi min jiya? ko har yanzu ba agyara wayar bane? ta fada kamar zata sanya masa kuka tsabar shagwa6a Har ya motsa la66ansa zai furta magana, unexpected sautin motsin ƙofarsu Ya daki kunnuwansu, lokaci ɗaya suka dakata tare da kallon ƙofar dake lilo alamar an ta6a ta... Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, aruɗe hajjaty ta furta"wanene ke ta6a min kofa" muryar marwa ce ta karade kun nan su"Ni ce marwa" kallon juna sukai ita da pravin cike da mamaki, saboda babu wanda ke shigowa dakinta, tsakaninta da sauran ma'aikatan gidan daga kitchen sai in sun haɗu a main falo ko wani part na gidan, kwata kwata bata sakar masu fuskar da zasu zo dakin ta, balle har suga sirrinta.. Muryar pravin kamar tame yin raɗa ya furta"wannan wani irin ganganci ne"? Hankalinta atashe tace"wlh ba laifi na bane, bansan meya kawota dakin nan ba, kaima ka sani bazan ta6a gangancin yin hakan ba" "Je kiji me zata ce maki, kada ki bari ta shigo" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta sauko ta nufi ƙofar ta buɗe ta leƙa karaf suka haɗa ido da marwa dake ta faman washe mata baki, da sauri ta ƙara babbake bakin ƙofar don kada ta samu damar ganin meke a dakin "Marwa! Ta fada da mamaki da sauri marwa tace"am...um..barka da safiya.." bata amsa mata gaisuwar ba, sai cewa tay"ina fata lafiya? Don banta6a ganinki a ɗakina ba..." washe baki marwa tayi muryarta da alamun rashin gaskiya ta furta"dama..um inaso zan fara aikin dinner ne da wuri to na shiga kitchen din sai naga store a kulle kuma babu makulli a bakin kofar, na tambayi abla ko ta dauka shine tace min yana a wurinki" wani kallon tuhuma hajjaty take jefa mata, abun yaso bata mamaki, Murmushin gefen fuska tayi"hmm marwa kenan, kina abu kamar wadda ta samu cutar mantau, in ba ni ba waye dama yake ruke makullin store? da har zaki tambayi abla ina Yake bayan haka wani girkine zaki fara a yanzu? Bayan breakfast da kuka kammala ko dai baki kalli agogo bane? Sosa ƙeya tayi"wai da afara dinner din da wuri" Kaitsaye tace mata"a'a babu bukata, kamar yadda kuka saba haka zakuyi dole sai lokaci Ya cika, sannan pls idan kinason Yin magana dani basai kinzo dakina ba! Ki kirani da landline din kitchen kamar yadda kuka saba kirana ku sanar da ni abu"! Ko amsar marwa bata jiraba, taja kofa Ta datse Rai a6ace marwa take kallon kofar, dakin wai har ita hajjaty zata ja ma kunne kan karta kara zuwa mata daki? Lallai buri ya yi kama da mutun da alama maganar hajiya saratu zata tabbata matarnan bata da gaskiya Allah kadai Yasan makircin da take kullawa da har batason wani Yazo dakinta, dani kike magana hajjaty saina zame maki karfen ƙafa agidan nan..." acikin ranta tafada Harta fara tafiya zata koma kitchen sai kuma ta dakata tana tariyo abunda Tajiyo adakin farkon dataje tafara yin la6e a kofar, tabbas taso tajiyo muryar hajjaty kamar tana magana da wani sai dai bata kaiga shaida hakan ba Murmushin mugunta marwa tasaki a fili ta furta"ni da ke ne" tayi maganar tare da kama hanya tabar wurin. Bayan komawar Hajjaty dakin, a zaune ta iske pravin yana jiran ta fuskarsa a yamutse saboda Ya tsani duk wani abu da zaija asirin shi Ya tonu "Ta fada maki abun da ya kawo ta"? Ya jefa mata tambayar, zama tayi gefen shi kafin ta sanar da shi maganar da sukai da marwa "Ni sai nake ga kamar leƙen asiri ta zo yi min saboda babu kwanciyar hanlali atare da ita" ta faɗa tana kallon fuskarsa Pravin yace bana tunanin haka, just ki bar komai a hannuna idan ta ƙara yi maki wani abu da hankalinki bai kwanta da shi ba ki sanar dani" ta amsa mashi da toh ___________________________ANEELERH✍️ Yau saboda da zumudin zuwan benazir ko breakfast batay ba saboda tafi son idan benazir tazo su ci abincin a tare, Su uku ne a kitchen suke aikin girka ma bakinsu abinci, gaba ɗaya kamshin abincin Ya cika ko'ina "Pls ku yi sauri mu kammala ta faɗa min da wuri zasu zo, dakyar ma in basu tafo ba" "Aunty Aneelerh wacece bakuwar tamu ne"? Ana ce ta faɗa tana kallon ta yayin da take tsaye gaban gass cooker tana aikin soye soye "Ki bari idan tazo zaki ga wacece, nafi so na baki mamaki" cikin raha ta faɗa "Allah ya kawo su lafiya, har nakosa na ganta" "Ameen," Kallon zahra tay, gaba ɗaya hankalin ta ba akan su yake ba, tana a tsaye gaban counter, inda ta ɗaura juicer ga kayan marmari shaƙe da bowl da alama ta tafi duniyar tunani, tafi karfi mintuna biyar bata ta6uka komai ba, gaba ɗaya tunaninta na akan zayn, zuciyarta sai azalzalarta ta ke yi akan son ganinsa tayi missing dinsa. "Zahra! Zahra!!" muryar aneelerh ce ta fargar da ita lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya tare da kallon ta "Me kike tunanine? Naga kamar wani abu na damunki"? Murmushin yake tayi"bakomai auntyna.." "Kedai faɗa min gaskiya ko dai damuwar rashin wayarki ne"? Da sauri tace a'a wlh ba haka bane "To menene tun ɗazu kin ƙi motsawa, Na fa faɗa miki da wuri zasu zo watakil ma sun kamo hanya," "I'm sorry bari na fara Yanzu zan kammala in sha Allah kafin ma su ƙaraso mun gama komai" Har sun kusa kammala girkin Mami ta shigo kitchen din tana fadin"wai wai irin wannan kamshi haka? Tun da ga ɗaki nake shaƙo shi, lallai Yau bakin mu zasu kwashi gyara" murmushi kowan nan su Ya saki "Mami sannu zuwa, me kikeso na zuba maki" zahra ce tay maganar "Ni iya juice din nan Ya ishe ni, sai dai bansan ko ummi zata bukaci wani abu ba" Zahra tace"to mami, bari na zuba maku hada snacks" "Yawwa zahra na, adan sanya min kankara aciki zaifi dadin sha" ta amsa mata da toh Kallon aneelerh tayi"har su nawa ne zasu zo naji dazu kamar kince hada Yayanta shureim" "Eh hada shi tare da ɗiyar Uncle din ta" Mami tace masha Allah, Allah Ya kawo su lafiya, bari na koma falon kada na cika ku da surutu...." har ta kusa fita ta kuma juyowa tana fadin"zahra ina jira" "Toh mami yanzun nan zaki ganni" Bata jima da fita ba, zahra taje ta kai masu a falo.... _____________________________✍️ ƙarfe sha biyu daidai benazir tana atsaye gaban mirror ta kammala shiryawa cikin atampha riga da skirt sun kama jikinta, ta tsara make up akan fuskarta wani irin kyawune ya ƙara bayyana ta fito ɗas balarabiyarta, ta kashe daurin dankwali bayan ta gama ta miƙe ta dauko mayafin ta dake a ninke kan mattress ta yafa shi a kafaɗa, jujjuyawa tayi gaban mirror din kafin ta sakarma kanta murmushi kyawawan dimples dinsa suka lotsa.. "Aunty benazir yaya shureim yace in baki fito ba zamu tafi mu barki agida" ta cikin mirror ta hango zeentu da tayi maganar, kamar aljanna ta ca6a uban adon lace launin blue sky mai walwali da daukar ido, ɗan ƙaramin bakinta ta shafe shi da jan baki, ga wani daurin dankwali da akayi mata mai kama da ture kaga tsiya ta sauko da gashin ta, ziririn wuyanta yana asanye da ziririyar sarƙar diamond A sukwane Benazir ta juyo fuska adaure ta kalle ta har saida tasha jinin jikin ta Da ƙarfi ta furta"zeenatu? meye haka? Wannan ado sai kace zamu je gidan surukan ki? Zazzare idanu tayi"ay ni ba su nayi ma kwalliya ba, ta yaya shureim ce amma idan baki son gani na da ita sai na canza wasu kayan in goge kwalliyar" Yamutsa fuska benazir tayi"da dai yafi saboda baki kyau ba, ko meye na shafa powder wai ke kinga fuskarki kuwa? Kamar wata fatalwa? Kina fara dole sai kin shafa powder? So kike ki zama zabayyana ne"? shiru tayi tuni annurin fuskarta ya fara daukewa muryarta da yar shagwa6a tace"Aunty benazir ay na fada maki mommy ma tana shafa powder in zatay ma daddy kwalliya, kuma kema ay fara ce sol amma kina shafa powder...." kafin ta ƙare maganar benazir tace"naji, amma ay ban kaiki haske ba, bana son jan magana kije ki canza kaya in har kinaso mu je dake" idanunta ne suka cicciko tab da kwalla benazir dake kallonta aranta ta ce kawai daga zan kara ki mu fita sai ki fini kyau hada wata sarƙar diamond...." Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi bazan canza kayan ba, ay yaya shureim yace nayi mashi kyau, kuma yace duk inda zaije ƙafarsa ƙafata don haka dole aje dani aunty benazir" ranta yakai makura 6aci juyawa tayi da gudu zata fuce daga dakin cikin rashin sa'a highhills din kafarda suka turguɗe gaba daya ta tafi zata kife ƙasa cikin zafin nama dr shureim Ya ruƙota ta dawo jikinsa babu wanda yasan da zuwansa a cikin su ashe yabiyo bayan zeenatu. Wankan shadda ne a jikin shi, zeenatu na jin dumin jikinshi ta ƙankameshi tana fada masa abun da benazir tace Murmushi yasaki yana kallon benazir dake kallon sa Da buɗar bakinsa sai cewa yai"ke baki gane ba? Kishi take yi dake saboda kinfi ta haɗuwa, itafa tun tana ƙarama in za'aje unguwa tafi so taga tafi kowa kyau don haka kada ki damu dabi'arta ce" jin wannan maganar yasa zeenatu fashewa da dariya har hakoranta suka bayyana. Ta6e baki benazir tayi fuskarta da dan murmushi tace"yaya shureim yanzu abun da kai ka kyauta? Agaban zeenatu kake fadin hakan? So kake ta raina ni"? Ɗaga mata gira yai alamar eh, jinjina kai tay"bakomai, na fahimci kafi son zeenatu akaina, soyayya ta rufe maka ido ya shureim ka rasa ma wa zaka so sai wannan ifritun sa'ar ƴar ciki na" ta fada da zolaya tana nuna zeenatu "Ahaka nakesonta" ya fada yana murmushi, zeenatu sai dadi takeji har wani ƙara maƙala hannunta acikin nasa take "Mu munyi gaba Ki iske mu a mota" yana ƙare maganar Yaja hannun zeenatu suka fuce, da sauri benazir ta dauko mayafi ta yafa a kafaɗa, hannun ta ruƙe da yar purse ta fito A falo suka iske su hajiya layla suna fira kamar wani abu bai ta6a faruwa ba, Yanzu ta kwantar da hankalinta tun bayan abun da Ya faru jiya "Zamu tafi mommy asanya mana albarkar iyaye" dr shurem ne yai maganar, atare suka dago da murmushi akan fuskokinsu Hajiya sara tace"masha Allah, tabarakallahu ahsanul khalikin kunyi kyau kamar dollars" dariya suka sanya gaba dayansu Fuskar hajiya layla da murmushi tace"nima naso aje unguwar nan dani amma zan bari zuwa nagaba" ta fada yayin da aranta take jin fargaban abun da benazir zata juyo awurin kawarta aneelerh tasan zaiyi wuya in bata fada mata ainihin abun da ya faru da mijinta da yar ta ba, daga nan zata gane tayi mata ƙaryane, tuna wannan yasa taji jikinta yayi sanyi ji take kamar ta hana au zuwa gidan saboda batason 6acin ran benazir ko kadan, fatanta Allah Yasa aneelerh tayi hankalin boye mata gaskiya. "Mommy layla ni da aunty benazir wayafi kyau"? Zeenatu ce tay maganar da sokana "Ay bama haɗi kin fita kyau nesa ba kusa ba" acewar layla da sauri hajiya sarah tace"a'a bana son sonkai Allah, aiko makaho ya shafa yasan wayafi kyau, auntynki tafi ki kyau nesa ba kusa ba, itafa jinin larabawa ce" kwa6e fuska zeenatu tayi jin abun da mommynta tace, da sauri ta kalli benazir dake yi mata dariya zumbura mata baki tayi "Shureim zata bata maku lokaci, Ku tafi ku kyaleta, dama daddynta dakyar ya amince ta biku," yana murmushi yace"toh mommy mu zamu wuce" atare suka hada baki wurin firta"Allah yakaiku lafiya, ku gaida mutanan gidan" "Zasuji in sha Allah" Har sun kusa fita falon hajiya layla ta ce"idan kun isa gidan Benazir ki kirani awaya inason yin magana da aneelerh" amsa mata tayi da toh kafin suka fuce, su zeenatu sai rawar kai akeyi za'aje unguwa... Abakin motar Dr shureim suka tsaya benazir ta fara daukar su hotuna da wayarta har kusan kala takwas bayan sunyi atare tayima zeenatu tare da dr shureim kafin taba zeenatu wayar tayi mata ita kadai sai kuma tayi atare da shureim...... Shiga motar sukai, Dr shureim yana a driver's seat zeenatu na zaune gefensa, benazir kadai suka bari a backseat. "yau ni za'a nunawa wariyar, wato zeenatu ce ta gaban mota, ni kuma ta baya babu komai nima idan mijina ya dawo zan koma ta gaban motarsa ne" dariya sukayi gaba dayansu, Bayan yai wa motar key ya fara driving a hankali Ya nufi gate din gidan babu wanda ya dakatar da su saboda an basu umarnin su barsu su fita. Bayan motarsu ta haura kan titi kowa Ya nutsu, zeenatu sai satar kallon benazir takeyi ta mirror din motar har gwalo take mata saboda ansanyata agaban mota Murmushi benazir tayi tare da ɗan girgiza kanta aranta ta ayyana bayan sangarta hada ƙuruciya ke damun ki "Aunty benazir masu number din nan ba su ƙara kiran layin ba"? "Namanta ban fada maki ba, me layin ta kirani awaya, yarinya ce kamar ki, ashe ta sanya wrong number ne, ko jiya na kirata awaya mun gaisa saboda ta kwanta min araina" *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Tags Kurkukun Kaddara YOU MAY LIKE THESE POSTS Previous Post Next Post GET IN TOUCH SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 25 Complete by Novels Elite Admin July 05, 2024 Sponsored Link Novels Elite English Gyaran Nono "Nima tunkafin naji muryarta har naji ta kwanta min araina, idan muka dawo gida ki kira min ita mu gaisa pls" a ƙagare tay maganar "Kamar kinsani, farko da muka fara waya da ita sai da tace min idan ina da ƙanwa kamarta in haɗata da ita, kinga shikenan sai ku ƙulla ƙawance" wani irin daɗi ne Ya lullu6e Zeenatu har ta fara imagining haɗuwarta da yarinyar tunkafin ma su fara magana a waya abunka ga me son ƙawaye, Gaba ɗaya firar da suke Yi akan kunnan Dr shureim, wanda Hankalinsa ke akan driving din da Yake yi, Basu sha wahalar gane gidan ba, ta hanyar amfani da address da Aneelerh ta basu har bakin gate din gidan suka iso, da sauri mai gadin gidan Ya buɗe masu gate motar su ta kunna kai ciki, Tunkafin Dr shureim Yayi parking Aneelerh ta fito da sauri ta nufi motar su tsabar son takai garesu har tuntube takusa yi, kafin ta ƙaraso Benazir tai saurin fitowa da gudun gaske ta nufi Aneelerh suka rungume juna kamar za su koma mutun ɗaya, Fuskar Dr shureim ɗauke da murmushi ya fito tare da zagayawa other side ɗin motar Ya buɗe ma Zeenatu, fitowa tay daga ciki ta soma bin ko'ina na gidan da kallo kafin ta sauke idanunta kan su Benazir dake a rungume da juna, "Yaya Shureim wannan itace ƙawar Aunty Benazir ɗin?" ɗaga mata kai yai alamar eh, Tsawon mintuna kafin suka raba jikin su daga na juna, fuskokin su sharkaf da hawaye saboda kukan da suka sha, Cikin shesshekar kuka Benazir tace"A.. Aneelerh! Ashe da rabon zamu ƙara ganawa da junan mu? Itama Aneelern da muryar kuka tace "Benazir kinga yadda kika koma? Nayi maraicin ganinki, nayi kewarki aminiyata sosae, wlh bakiji dadin da nake ji ba..." daƙyar suke magana saboda kukan da suke yi har lokacin, Zeenatu sarkin tausayi har ta fara matsar ƙwalla, shi kanshi Dr shureim dauriya ce kawai Yake Yi, amma ba ƙaramin tausayi suka bashi ba, bazai ta6a manta shaƙuwar da ke atsakaninsu ba, Fitowa Zahra tayi daga gidan karaf idanunta suka sauka akan su Dr shureim da Zeenatu Har saida taji gabanta Ya faɗi ganin irin kyawun mutumin da kamalarsa daƙyar ta janye idanunta daga kansu ta mayar da dubanta ga su Aneelerh, Murmushi Zarah ta saki saboda taji daɗin ganin aminnan atare, "Ki daina kuka bana son ganin hawayen ki," Aneelerh ce tai maganar idanunta jawur Benazir tace "Idan kinaso In daina kema ki daina, taya bazanyi kuka ba Aneelerh? Nayi babban rashin da har abada bazan Iya ta6a yafewa kaina ba, laifina ne gani nake kamar nice silar da zumuncinmu ya tarwatse..." da sauri Aneelerh ta sanya hannu ta toshe mata bakinta "ki daina ɗaurawa kanki laifi, saboda bayin kanki bane tafiyar da kikai, kema bada son ranki aka raba ki da danginki damu kanmu ba...." lallashinta taci gaba da yi Zeenatu har ta fara gajiya da tsayuwa dama ita bata saba da wahala ba, Tana faman jan ajiyar zuciya ta juya ta dubi su Shureim cikin sanyin murya tace"Aneelerh ga Yaya Shureim da Zeenatu ɗiyar Uncle ɗina" da sauri Aneelerh ta nufe su fuskarta da fara'a ta gaishe da Yaya shureim "sannunku da zuwa Yaya shureim ku shigo daga ciki" tay maganar tare da hugging ɗin Zeenatu tace "Yan mata sannunki kuyi haƙuri mun barku atsaye" Kamar bata son haɗa ido da shureim saboda girman shi da take gani, tun fil azal tana matuƙar jin nauyinshi kuma tana girmama shi, "Yawwa anaeelerh mun same ku lafiya", "Lafiyalou Yayanmu" tay maganar tare da ruƙo hannun Zeenatu suka yi gaba Shureim Yabi bayansu tare da Benazir da sauri Zahra ta koma falo tana jiran su shigo don su gaisa, Lokacin da suka shigo falon Mami da Ummi suna atsaye suna jiran shigowarsu don su tarbesu, koda Benazir tayi arba da Mami wani irin nauyinta da kunyarta ne suka kamata, Mami kuwa fara'a tasaki da sauri ta janyo Benazir ta rungumeta tana ɗan bubbuga bayanta "marhabun lale ƴata, tsawon lokaci munyi kewar rashin ki" lokaci ɗaya Benazir taji hawaye sun sake wanke mata fuska Muryarta da shessheka ta furta"Ma..mi " sam takasa ƙarasa maganar, "na fahimce ki basai kinyi min bayani ba, Aneelerh ta sanar dani komai, ki kwantar da hankalinki ba kuka yakamata kiyi ba, godiya yakamata mu yiwa Allah daya dawo mana dake cikin ƙoshin lafiya" Mamin ta faɗa tare da raba jikinsu ta sa tafin hannunta tana share mata hawaye Kafin ta ɗago ta dubi Dr shureim wanda tun da ya shigo ya sunnar da kanshi ƙasa saboda nauyin Mami da yaji gani yake kamar har yanzu tabon da yai ma kansa zaisa su guje shi, Daƙyar ya motsa labbansa zai gaishe da ita Mami tayi saurin katseshi da cewa "Allah sarki Shureim kaine ka koma haka? Gaba ɗaya kun canzamin, Shureim Ka yada zumunci ƙiri ƙiri Ka guje mu ka koma Egypt ban ta6a zaton zakai mana haka ba" Cikin sanyin murya yace"Mami ay min afuwa nima bada son raina ba nayi nesa daku, zaman ƙasar ne Ya gagareni saboda abun da Ya faru, amma wallahi ko bayan da na tafi kuna araina..." bai ƙare maganar ba Mami ta katse shi da cewa "bakomai Shureim, duk abun da Ya faru mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa Ya guje ma ƙaddararsa ba, naji dadin ganin ku cikin koshin lafiya sosae..." "Ku mu zauna" ta faɗa tare da nuna masu sofas, Bayan kowa Ya zauna Ummi da Zahra suka yi masu barka da zuwa "Muyiwa Annabi salati" acewar Mami gaba ɗaya suka yi atare kafin daga bisani Mami ta dubi Zeenatu dake ta faman zare blue eyes ɗinta, gaba daya tarasa sukuni saboda bata saba shiga mutane ba kamar tana jin tsoron su, "Tabarakallahu ahsanul khaliqin, Ƴata wacece wannan bakuyi min bayani ba, gata dai masha Allah daga gani ba jinsin ƙasar mu bane" murmushi Zeenatu tayi, Ummi tace"kin riga ni faɗa, tun da suka shigo ta tsole min ido, kamar in sace ta" dariya sukai cikin raha, "Sunanta Zeenatu, ɗiyar Uncle ɗina ce" waro idanu Mami tayi haɗi da jinjina kai, "Masha Allah, sannu Zeenatu" amsa mata tay da "yawwa" "Dan Allah ki saki jikinki, ki ɗauka kamar kina agidanku ne, don na fahimci kamar kin takura" Murmushi Zeenatu tayi har dimples dinta suka lotsa, "Ina su Maminku ina fata duk suna lafiya" cikin kulawa tayi Maganar tana kallon benazir" "Suna nan lafiya, sunce mu gaishe daku, taso mu zo tare amma tace sai zuwa na gaba", Murmushi Mami tayi "Allah Ya kawo ta Lafiya in ma batazo ba ni na fidda lokaci inje gidan naku" Shiru sukayi na wani lokaci, kowa da abunda Yake saƙawa aranshi, Benazir ta ƙosa su ke6e da Aneelerh don su ƙara jajantama junansu. Fitowa daga kitchen Ana tayi hannunta ɗauke da tray na kayan abincin da suka shirya masu har zata gifta ta ɗan dakata tare da kallon baƙin nasu karaf idanunta suka sauka akan fuskar benazir, tsabar kiɗima da ganin Benazir Ƙiris Ya rage ta saki kayan abincin hannunta Jikinta Ya hau bari da sauri takai abincin Dining ta nufo su, gaba ɗaya ta zube kan carpet tana ambaton sunan Benazir, Kusan atare suka ɗago suna kallonta duk tabi ta ruɗe muryarta na rawa take faɗin "Aunty Benazir! Kece? Ko dai makuwa nayi ne?" Hawaye ne suka ciko idon benazir bakomai Ya faɗo mata aranta ba face Irin azabtarwar da tayi ma yar'uwar Ana mai aikin gidanta Janet taci azaba a hannunta in tai mata laifi hada duka take haɗa mata, Cike da jin kunyar Ana tace"Ni ce Ana, ba makuwa kikai ba, fatan na same ki lafiya? Ina yar uwarki janet" Matse ƙwalla Ana tayi "Allah Sarki Aunty Benazir Ina nan lafiyalou, Janet tana a Jos tare da Esther ni kaɗai ce anan, Aunty Benazir Ina kika shiga tsawon lokaci bamu ji ɗuriyarki ba..." Kafin benazir ta bata amsa Aneelerh tayi saurin tarar numfashinta da cewa "Ana kije ki ƙarasa shirya masu abincin, zanyi maki bayanin komai" ta faɗi hakanne saboda bata son ana tayi maganar 6acewar su Angel gudun kada Benazir taji hankalinta Ya tashi, "Kada ki damu, zuwa anjima kafin mu tafi zan nemeki..." amsawa Ana tayi da toh, Jiki asanyaye ta miƙe tana tafiya tana waiwayon su Benazir tana mamakin Matashiyar da suka zo da ita, aranta ta ayyana watakil itace Yar uncle ɗinsu da taji ance zasu zo da ita...har sai da ta shige kitchen tukunna ta daina kallon su, Miƙewa Aneelerh tayi tare da kallon Benazir tace "mu shiga daga ciki", Mami tace "kuyi me? Ba zaki bari su ci abinci ba, salon ki cika ta da surutu" "Ba daɗewa zamu yi ba Yanzu zamu fito" Ummi tace"ke ko an daɗe ba'a haɗu ba, tana son su ɗan ke6e ne ay firar yaushe rabo", miƙewa Benazir tayi suka nufi bedroom ɗinta hannunsu cikin na juna, "Shureim ya'yanka nawa Yanzu" sunnar dakai ƙasa yai jin tambayar da Mami tayi masa, Dariya tayi "dan Allah kada kace min bakai aureba" Cike da jin kunyarta Yace "banyi ba Mami, amma nakusa in sha Allah" tayi mamakin jin maganarsa gashi har ya fara manyanta baiyi aureba koda Yake komai sai Allah Ya nufa, "Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" amsa mata su kai da ameen, Shigowa Ana tayi "Mami na gama shirya abincin" Mami tace"toh, ku tashi mu ƙarasa Ciki" Dr Shureim Yace"Alhamdulillah, bana Jin yunwa sai dai ko Zeenatu in zata ci" Maƙe kafaɗa Zeenatu tayi "nima bana jin yunwar ay naci abinci agida" yadda tai maganar yaso basu dariya har sun gane shagwa6a66iyace "Haƙuri zukuyi ku tashi muje, Nasan baza'a rasa space a cikin ku ba ko ruwan zumunci ne ku sha" lalla6a su Ummi tayi har dai suka miƙe suka bi su Mami zuwa dining.. A 6angarensu Benazir bayan sun shiga ɗaki da Aneelerh, cike da zumuɗi suka zauna daga gefen gado Sai faman bin juna da kallo suke yi kamar yau suka fada haɗuwa "Kinga yadda kika canza? Kin ƙara girma kinyi kyau abunki, bani labari bayan kin tafi ina kika faɗa"? Numfasawa tay kafin tace"Wani bawan Allah ne Ya taimaki Rayuwata, Mutumin kirki, ɗan family ɗin Obinna nasan ba zaki rasa saninsa ba, sunan shi Zaki Mubarak Obinna A ƙasar Canada Yake..." gaba ɗaya Benazir ta bata labarin Yadda suka haɗu da zaki a Abuja bayan ta gudu daga jos da yadda harya taimaketa suka bar kasar atare.. Jinjina kai Aneelerh tayi har cikin ranta taji dadi da rayuwar benazir bata wulaƙanta ba, "Koma wanene Yayi miki wannan aika aikar in sha Allah sai yaga sakayya, tun agidan duniya, anso a cutar da rayuwarki, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane cikin ikonsa kin faɗa hannu nagari", "Ni inda nagode ma Allah, ban tafi da tsohon ciki na ba, da bansan a Ina zan haife shi ba, ba rabon ƴata tasha wahala wlh banyi zaton zata rayu ba, inaji ina gani nabarta a kwamin wanka tana kuka tana kallona..." kuka ne Ya ci karfinta da sauri Aneelerh ta fara lallashinta "Ni damuwana wanene yake kokarin ganin ya rabani da dangina? Me na masa Aneelerh? Nasan bana jin magana tun a ƙuruciyata inada jan faɗa da masifa, mutane da dama na sanya su ciwon kai har da masuyi min mummunan fata amma wallahi ban ta6a zaton za'a samu wanda zaiyi min asiri, to waini me nayi masu haka??" idanunta jawur ta faɗa. Dafa kafadarta Aneelerh tayi"in sha Allah duk wani mai nemanki da sharri kanshi zai koma, ubangiji Allah Ya tona asirin su" "Ameen Aneelerh nagode sosai da kulawarki agareni, ni wlh banyi zaton zaku kar6e ni hannu biyu idan na dawo ba, ko gida da zan dawo nayi fargaban haɗuwa da su Daddy amma saina ga kowa Yana murnar gani na ba ƙaramin daɗi naji ba, yanzu damuwana ɗaya shine mijina da ƴata ina matuƙar jin shakkarsu saboda nasan da wuya su kar6eni hannu biyu kamar yadda kukai min..." "Meyasa zaki ce haka? ay su sai sun fi kowa murnar ganinki" Girgiza kai tay"ba zaki gane ba Aneelerh, bayan tafiyata lokacin ina agidan zaki, kwatsam wata rana saiga saƙon saki daga Taj hakan Ya tabbatarmin da yaji haushin abun da na masa" da mamaki Aneelerh tace"kina nufin bake kika nemi saki daga wurinsa ba?" Ɗaga mata kai tay alamar eh, shiru Aneelerh tayi jikinta Ya ƙara mutuwa lakwas saboda taj da kanshi Ya ta6a faɗa mata Benazir ta tura masa text message tana neman ya saketa, to kenan wanene Ya shirya wannan tuggun?" Ta jafe ma kanta tambayar da bata da amsarta, Ruƙo hannayenta Benazir tayi a cikin nata ta damƙe su sosai cikin sanyin murya tace "Dan Allah Aneelerh ki taimaka min Inason yin magana da tajuddeen, naji kince baki da layin da Yake amfani da shi, tun da suna a tare da mijinki dan Allah ki kira Uzair ɗin sai mu yi magana da shi..." Rass Aneelerh taji gabanta Ya faɗi, tuni ta nemi nutsuwarta ta rasa, batasan taya zata shawo kan Benazir ba sam ta manta da jiya ta faɗa mata hada mijinta suna a South Korea, "Kinyi shiru baki ce min komai" ta faɗa idanunta acikin na Aneelerh, farat ɗaya ta fahimci wani abu daga yanayin da ta nuna, Wani irin kwarjini Benazir tayi mata muryarta da inda inda ta shiga faɗin "am..umm..bani da layin shima uzair...au wayarshi ta lalace zan ce....." bata ƙare maganar ba ta katse ta da cewa "Kada kiyi min karya Aneelerh ba halinki bane, dan Allah ki faɗamin gaskiya ni dama najima ina kokwanton maganar mami, daga baya sai da raina ya bani akwai wani abu da take boyemin don itama lokacin dana tambayeta lambar Taj tunda nasan bata rasata ba kamar da suka bayyana man cewa suke kula da yarinyata lokacin dana dawo amman sai ta nuna man basu da lambarshi ta inda yake, tun nan na fara shakkun maganar ta tunda ko don saboda yarinyar tawa ai ya kamata ace suna da lambar tashi da suke magana, kawai ki faɗamin in da akwae wani abu nayi maki alkawarin bazan tada hankalina ba, boyemin bashi da amfani tunda duk min daren daɗewa zanji ne kuma bazan ji daɗin ƙin sanar man da kuka yi ba...." Jinjina kai Aneelerh tayi tuni taji ƙwalla ta cika idanunta don har yanzu zuciyarta da ciwon abun, Numfashi taja kafin ta fara bata labarin abun da Ya faru na 6acewar su Tajudeen, Tsabar tashin hankali Yasa Benazir saukowa daga zaunan da take a gefen gadon ta dawo kan floor dirshan ta ɗaura hannayenta biyu asaman kanta muryarta cike da tashin hankali take faɗin "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN! INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN......" Misalta tashin hankalin da zuciyarta ta fuskanta ba abune mai sauƙi ba, Idanunta sun kaɗa jawur facial muscle dinta har kerma take gaba ɗaya jikinta ya ɗau wani irin mahaukacin zafi kamar mai fama da zazza6i sai kerma take, Dafa kafaɗarta Aneelerh tayi muryarta a raunace ta furta "Innallaha ma'assabirin Iya abun da zan iya furta maki kenan, abun da Ya faru Ya riga daya faru Benazir, illa iyaka mu cigaba dayi masu addu'a ubangiji Allah Ya bayyanar mana da su tunda har Yanzu babu labarin suna araye ko sun mutu, Cikin shesshekar kuka Benazir take faɗin "nashiga uku Aneelerh! Meke faruwa da rayuwata ne? Da farko An rabani da dangina hakan bai isa ba sai da akayi silar da ƴata da mijina suka 6ace! Wai wanene ke bibiyar rayuwarmu ne? Uban me muka masa...." jin Yadda take ɗaga Murya Yasa Aneelerh saurin toshe mata baki da tafin hannunta gudun kada su Mami su jiyota.... A ƙarshe ma sai ta rungumeta saboda ta samu relief ɗin abunda ke damunta Allah kaɗai Yasan tafarfasar da zuciyarta keyi mata kamar numfashinta zai ɗauke bakomai take tunawa ba face fuskar Taj dana yarta Unaisah yanzu shikenan ta rasa su? Gunjin kuka taci gaba da yi, kwantar mata da hankali Aneelerh ta shiga yi, suna haka Mami ta shigo ganin halin da suke ciki yasa ta nufosu da sauri tana tambayar lafiya mike faruwa ne ta gan su haka da alamun tashin hankali, zama tayi a bakin gadon ta dafa kafaɗar Benazir tana faɗin "mike faruwa ne na gan ki cikin wannan halin??" Aneelerh ce dake ƙwalla ta faɗi mata dalilin shigarta halin, yanayin damuwa ne ya bayyana akan fuskar Mami tace ma Aneelerh tunda bata sani ba ai da bata sanar mata ba, shiru Aneelerh tayi cikin kuka Benazir tace "Mami nice na matsa mata ta sanar man, 6oye mani baida amfani don koda yaushe ina sa ran haɗuwa dasu ashe ba rabo, an raba ni da mijina da kuma ƴata, Mami suwaye waɗannan azzaluman da suka tarwatsa kan iyalin mu, mi mukai masu ne don Allah" gaba ɗaya ta gama karya masu da zukatansu itama Mami har idanunta sun ciko da ƙwallan, rarrashinta ta shiga yi tana karfafa mata gwuiwa kan inda rabo sai suga sun bayyana tunda har yanzu ba'a da tabbacin ko sun mutu har ta bata misali da ita yadda ta 6ace 6at ba'asan ina take ba tsawon lokaci gashi yanzu Allah ya bayyanar masu da ita don haka ba abunda zasu yi sai suci gaba da yin Addu'a, a tare suka cigaba da rarrashinta har saida suka ga ta ɗan samu nutsuwa Mami tace ta taso suje taci abinci dama shi ta shigo tayi mata magana, idanunta sunyi jawur ta girgiza mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace bazata iya cin wani abu ba a yanzu, dole Mami ta ƙyaleta Benazir ɗin ta buƙaci shiga toilet da sauri Aneelerh ta miƙe tana nuna mata toilet ɗin ta miƙe jiki ba ƙwari ta shiga, bayan shigarta Mami ta miƙe cike da tausayinsu ta fita, wanko fuskarta tayi bayan ta fito akan gadon aneelerh ta kwanta kamar ba laka a jikin ta, tsananin tausayinta duk Ya kama Aneelerh tana ta kallonta, bayan wani lokaci ta miƙe taje ta kawo mata abinci da juice don tasha tace mata bazata iya cin komai ba, lalla6ata tay dakyar ta samu tasha juice ɗin, shiru sukai can Benazir din tace "Ina yaronki? Naga bangan shi ba? Ina abie?" "Bayanan sun tafi unguwa tare da Mahboob ƙanin Zahra, su abie suma basa nan amma nasan zuwa anjima kaɗan zasu dawo gidan" "Allah Ya dawo da su lafiya" amsa mata tayi da Ameen daga haka bata ƙara magana ba har bacci Ya ɗan dauke ta a ɗakin. ____________________Chief Around 5 na marece Ya fito daga Gym room ɗinsa, daga shi sai short baƙi a jikinsa, Ya haɗa uban gumi zufa ta ko'ina take tsatstsafo masa, Hannunsa ɗaya ruƙe da short towel da yake goge gumin jikinsa, Bathroom Ya shiga, within 15 mins Ya fito daga wanka ya nufi walk-in closet dinsa cikin kankanin lokaci Ya kimtsa cikin suit navy blue sunyi bala'en Yi mashi kyau da alama zai fita wani wuri ne, hadaddiyar agogon hannunsa sai salki take, kafafunsa na sanye da hadaddun leather shoe ta ko'ina kamshin turarensa Ya karaɗe ɗakin, Wayarsa ce ta fara ruri ya ɗauko tare da duba sunan mai kiran sa, hidding number ce nan take Ya gane mutumin nan ne daya saba yi mashi kiran sirri, Picking call din Yayi tare da kara wayar a kunne, "Naji daɗi da ka fara yadda da maganata, Yanzu Ya rage naka Owais kai kokari wurin gano su wanene miyagun dake a family ɗinka tunkafin lokaci Ya ƙure maka" "Sai yaushe ne zaka bayyana min kanka? Ina son sanin Wanene kai?And how did you know everything that's happening with my fam? Sautin dariyar mutumince ta cika masa kunnansa "sanin wanene ni bai da amfani, idan kuma ka damu da son sanin wanene to ka fara kawo ƙarshen miyagun dake a cikin zuri'arku" runtse ido Chief Owais yai har cikin ranshi bai son jin Ya ambaci miyagu a family dinsa zuciyarsa karaya ta ke yi kalmar bata masa dadi, Rai a6ace yace "babu miyagu a family dina, ka kiyaye kalamanka," dariya mutumin yayi "shiyasa nake jin tausayin ka Owais saboda ka yarda da kowa na family ɗinka, me zai faru a ranar da ka gane gaskiyar da nake kokarin ganar da kai" a fusace Ya daka masa tsawa baima tsaya ya ƙarasa jin zancen mutumin ba Ya wurgar da wayar kan Gadonsa, Yana faman fitar da huci Ya furta "bazai ta6a yiwuwa ba, na yarda da family dina, babu bata gari a cikin su...." Yana a cikin wannan Halin Wayarsa ta sake Yin ringing, Ko kallonta baiyi ba a zaton shi mutuminne Ya ƙara Kiransa shiyasa bai kulata ba, Jiki amace Ya zauna kan couch gaba ɗaya Ya rasa sukuninsa zuciyarsa sam bata masa dadi, Wayarsa sai faman ringing take da zarar kiran Ya katse wani Yake shigowa, Runtse idanunsa yayi bakomai Yake hangowa ba face fuskar Daddynsa data Uncles dinsa kai harma da Kakansa mutanan kirki masu Daraja a idon duniya, abune mawuyaci ya gasgata maganar mutumin in har ba gani yayi a zahirance ba, to wai wa akeso Ya zarga a cikin su? hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wannan rashin imanin badai a family ɗinsa ba, sai dai wani baren dake a cikin su, Knocking kofarsa akai, nan take alert ya shigo masa, kamar bazai tashi ba, a kasalance Ya miƙe Ya nufi wayar Ya danna unclock slowly ƙofar ta buɗe, bai kai idonsa ga mai shigowa ba hankalinsa na akan missed calls din da akai masa daga delivery man na Companynsu, tunawa da saƙon Hateem yasa shi saurin dannawa mutumin kiran bayan yai picking suka gaisa ya sanar dashi saƙone Ya kawo masa tun ɗazu Ya shigo jami'ae sun hana shi ƙarasowa ciki, "Okey, Gani nan zuwa" ya furta, Sauke wayar yayi daga kunnansa Juyawar da zaiyi ke da wuya karaf idanunsa suka sauka akan ƙafafunta dake asanye cikin highhill, sam ya manta da izni daya bada na ashigo dakinsa, Tun daga ƙasa Ya fara kallonta har Ya sauke idanunsa kan fuskarta, ganin kallon da yake yi mata ne yasa tai saurin cewa "naga kana waya shiyasa ban yi magana ba" muryarta ba ƙaramin sanyaya masa zuciya tayi ba sai yaji kamar yasha pain reliever ne, Kallo ɗaya da unaisah tayi masa sai da ta fahimci wani abu na damunsa, "Ina wuni," Lumshe idanunsa yai muryarsa da sanyi ya furta "lafiyalou," "Idan akwai wani aiki da zan maka ka faɗa min" "Okey" ya faɗa tare da kallon bedroom dinsa "ki gyara min ɗakin but karki takura kanki" amsa mashi tayi da toh, Fucewa yai daga ɗakin Ya barta ita kadai wani irin dadi taji, sai da ta 6ata lokaci wurin shaƙar kamshin turarensa daya cika dakin kafin ta fara gyara mashi gadon shi, A sitting room dinshi Yasa aka shigo mashi da ɗan sakon, da sallama Ya shigo hannunsa ruƙe da wata katuwar shopping bag mai ɗauke da logo na Obie tech, "Barka da warhaka Yalla6ai, fatan na same ka lafiya" yana daga zaune kan sectional sofa Ya amsa mashi da barka da zuwa, "Yawwa Sir, ga saƙon" da hannu Ya nuna masa gaban sofa ɗin da Yake mutumin Ya ƙarasa Ya sauke jakar kayan Kafin sukai sallama Ya juya ya fuce, Ko minti biyar ba ayi ba wani senior agent Ya shigo sitting room ɗin hannunsa ruƙe da mug din coffee, cikin girmamawa ya gaishe da shi kafin Ya ɗaura masa cup din kan table din gabansa, Da hannu ya nuna masa shopping bag din "fito min da kayan dake a ciki" "Okey sir" zuƙunnawa yayi agaban Jakar Ya fara zaro Apple laptop sabuwa gal, tare da phone box na Iphone 15pro max, A hankali Ya ɗaura su kan rug din gaban sofa din kafin ya ƙarasa curo sauran kayan, Apple ipad da headphone tare da watch box and eyeglass case" bayan ya kammala curo su, chief Ya ɗan jinjina kansa kafin yace da shi ya maida su ciki ya amsa mashi da Okey Sir, mayar da su ciki yay sannan Ya miƙe Ya sarah mashi da hannu yay mashi alamar yaje ya juya ya fuce, Har cikin ranshi Yaji dadin kyautar da Hateem yayi ma yaron kaya masu kyau da tsada, aransa ya ayyana zaiyi amfani da wannan damar wurin ganin Yaja shi a jiki, Cup ɗin Ya dauka Ya fara kurbar coffee a halin Yanzu Baya buƙatar kowa a kusa da shi shiyasa Ya ke6e kansa don Ya samu damar Yin nazari, A 6angaren Unaisah dake gyara masa bedroom dinsa, har ta gama da gadon ta dawo gaban dressing mirror ɗinsa tana jera masa perfumes ɗin yayi amfani dasu, Tunkafin tagama take Jin kamar faɗuwar gaba, kamar ance ta ɗago ta kalli madubin kwatsam idanunta suka sauka akan shi, Rasss! taji gabanta ya faɗi, a matuƙar firgice ta juyo tana kallon shi ya harɗe hannayensa kan ƙirjinsa fuskarsa kamar wanda aka aiko ma saƙon mutuwa, ko tayaya akai ya shigo ɗakin bayan kofar tana da security? in badai Chief ɗin bai rufeta ba, anya kuwa shi ne? Ko dai iskokan dake ajikinsa ne? Taya akai ma Yasan tana a dakin Chief?, Yawu ta haɗiya daƙyar zuciyarta na harbawa da matsanancin bugu ta furta"..My man" Wani kallon tuhuma Ya wurga mata tare da ƙara haɗe girarsa, Muryarta da inda inda tace "um..ka gane, wai dama ina ɗan gyara masa dakinsa ne kaga ya taimaki rayuwarmu shiyasa nake son kyautata mashi....." kamar mara gaskiya haka ta fara kora masa jawabin da bai tambayeta ba, har wani gumi ta fara haɗawa akan fuskarta duk da sanyin A.c din dakin, "You don't want peace" da kakkausar murya taji Ya faɗa, "Me kake nufi?" "Abunda kunnanki Yajiye maki" Yai maganar tare da takawa yaje gabanta ya damƙo hannunta ya jata da karfi ya nufi ƙofar, kokarin ƙwacewa ta dinga yi tana fadin "dan Allah ka sake ni, ban kammala Yi masa gyaran ba, Daddyna ne yace na dinga kyautata masa...." ko ta kanta baibi ba har sai da Ya fito da ita daga ɗakin ya nufi bedroom dinsu da ita, A kan gado Ya wurgar da ita ta mirgina tana faman maida numfashi, "Kada ki kuskura ki ƙara zuwa ɗakin shi idan ba haka ba Kinsan zan iya komai akanki, har Daddyn naki bazan ƙyale sa ba saina ja masa kunne akanki in har yana son zaman lafiya dani" waro idanu waje tayi tare da ɗagowa tana kallon shi, Ya haɗe rai kai kace ba daga bakinsa maganar take fitowa ba, Harara ya watsa mata kafin ya juya zai bar ɗakin, durowa tayi daga kan gadon jiki na 6ari tayi saurin shan gaban shi Ya tsaya yana kallonta, Wani irin kwarjini yayi mata a ido, cikin sanyin murya tace"tunda bakaso bazan ƙara ba, amma dan Allah kada ka ta6a min Daddyna wallahi ina son shi bana son wani abu ya same shi, kuma ay shi baisan alaƙar dake a tsakanina dakai ba shiyasa yace haka..." marairaice masa fuska tayi kamar zata sanya mashi kuka wani irin kallo taga Yana bin ta da shi, tunawa da abunda Ya faru ɗazu ne Yasa tayi saurin matsawa ta bashi hanya don Ya wuce, Yana fita daga ɗakin ta sauke ajiyar zuciya, tsoki ta dan ja abun na shi ya fara bata takaici, Wannan wani irin kishi ne? "Jarababbe kawai" ta faɗa tare da samun wuri gefen gadonsu ta zauna tana faman haɗe rai, ta ƙudiri aniyar sai ta koma ɗakin chief yi masa aiki ko ba yau ba sai dai Ya haɗiyi zuciya ya mutu, saboda shi bazata ƙi bin umarnin Daddynta ba duk da tana jin tsoron yace zaiyi mashi wani abu don ta fahimci ba kaine da shi na, _______________Mahboob Shigowa gidan yayi bayansa a goye da Baby Junaid, tunda yayi sallama idanunsa suka sauka akansu Zeenatu dake a falon har kusan firgita yayi da ganinta saboda kyanta da yaja hankalinsa, Aneelerh na ganinsa ta miƙe tana faɗin "Oyoyo Baby junaid ɗina, mahboob Ina ka kai min shi tun safe sai Yanzu fisabilillah, halan koma abinci baici ba" ta faɗa tare da kar6ar Junaid ta rungume shi a jikinta, sam babu kuzari a jikinshi kamar bacci ma yakeyi ya farka Muryarsa tamkar zai fashe da kuka Yace"Mommy, Yaya mahboob bai da tausayi sai da nace masa ni ya dawo dani gida amma yaƙi ya dawo dani, kuma wallahi Allah bazan sake binsa unguwa ba" idanunsa aruntse yake masifa, gaba ɗaya mutanan falon Suka kwashe da dariya hada Benazir da bata jima da fitowa ba, Yaron ba ƙaramin burgesu Yayi ba musamman Zeenatu, duk rashin sakewarta jiki na rawa ta miƙe ta nufi su Aneeleeh tace "Aunty ki bani shi in dauke shi" Murmushi Benazir tayi "Allah yasa ya yarda rigima ne da shi" miƙa mata shi tayi, abun mamaki jikinshi har 6ari Yake wurin Miƙa ma Zeenatu hannu don ta ɗauke shi Ummi na dariya tace "ɗan ƙwal uba yaga farar fata, da mu mukace masa yazo yadda ransa ya 6aci ɗin nan wlh ba zuwa zaiyi ba" dariya sukai baki ɗaya, Rungumesa Zeenatu tayi har wani ƙara ƙanƙameta yakeyi, komawa tayi kan sofa ta zauna hannunta akan sumar kan shi daga bisani mahboob Ya gaishe da su Dr shureim fuskokinsu da fara'a suka amsa mashi, gabatar masu da shi Aneelerhtayi kamar yadda ta gabatar masu da Zahra a matsayin ya'yan uncle dinta, Sunji dadin karramasu da akayi, ko da lokacin salla yayi Mahboob ne Ya raka Dr shureim masallaci sukayi sallah atare, Har wuraren karfe shida na marece suna agidan, Dr shureim yaso su tafi Mami ce ta tsaida su saboda abie ya kira waya yace in sunzo su jira su dawo gidan don su gaisa, Bayan dawowar su Abie a falo suka zauna wata sabuwar firar suka soma yi cikin raha hada Uncle ɗan Iya Ya dinga basu labaran ban dariya gaba ɗaya suka cika su da farin ciki, baiwar Allah Benazir daurewa kawai takeyi duk don kada su gane halin da take a ciki, Aneelerh ce da Mami kadai suka san meke damunta, da zarar sun haɗa ido da Aneelerh take yi mata alamar tayi haƙuri, har bayan sallar magrib suna gidan Lokacin da zasu tafi har bakin motarsu suka rako su baki ɗaya Kamar kar su rabu da juna, musamman benazir da Aneelerh, haka itama Zeenatu da Junaid yaron Ya kwanta mata aranta, har hotuna tayi masu da wayar Dr shureim, ko time ɗin da zai ci abinci ita ta bashi abaki, bayan sunyi sallama da junansu suka tafi, su mami basu daina kallon motarsu ba har suka fuce daga gate din gidan kafin suka koma ciki. ______________ Tun cikin mota Zeenatu ta lura da Yanayin Benazir ta haɗe rai sosai fuskarta tayi jawur Ko magana bata son yi, Ita kaɗai tasan raɗadin da take ji ta ƙosa su koma gida saboda taji zafin 6oye mata gaskiya da Mami tayi, Motarsu na ƙarasa shiga gida Kamar jira take Dr shureim Yayi parking azafafe ta hankaɗe murfin motar ko yar purse dinta bata dauka ba ta nufi falo, Hankali a tashe Dr shureim Ya fito Yabi bayanta, Itama Zeenatu ta fito hannunta ɗauke da purse ɗin Benazir ta bi bayansu, Da karfi take ambaton sunan Mami kamar maƙoshinta zai 6allo, ko sallama batayi ba, Jiki na 6ari Hajiya layla da Hajiya Sarah suka fito daga dakunan su, Tunkafin ma tayi magana Hajiya layla ta fahimci meke damunta abun da take gudune Ya faru, dama tun ɗazu take zullumin dawowarsu har kiran Benazir ɗin tayi amma batay picking ba balle har ta samu damar Yin magana da Aneelerh don ta dakatar da ita akan kada ta faɗa mata gaskiyar abun da Ya faru, "Benazir ba saida nace maki idan kin isa gidan ki kira ni ba? Meyasa bakiyi hakan ba...." a rude Mami ta furta hakan, Cikin shesshekar kuka tace "Nagode ma Allah dana manta ban kira ba, abun da kike 6oye min shi aka faɗa min! Mami meyasa zakiyi min ƙarya akan 6atan mijina da ƴata?" rai a matukar 6ace tay maganar tana kallon cikin idonta, "Wallahi baku kyauta min ba, kinsan kuwa yadda na ƙwallafa raina akan son ganinsu? Mami why? Why kikai min haka..." "Dan Allah Kiyi haƙuri Benazir, tayi hakan ne saboda guje ma bacin ranki.." Hajiya Sarah ce ta fara kokarin shawo kanta, Zeenatu dake kuka da gudu ta nufi ɗaki ta shige saboda bata son tashin hankali, Idanunta jawur ta kalli Hajiya Saratu "miye amfanin boyemin da tayi? Bayan dole wata rana zanji awani wuri! Da ace ta faɗamin da yanzu komai ya wuce saboda ba yadda zanyi dole inyi haƙuri ....ni banji daɗi ba Mami wlh baki kyauta min ba...." Dr shureim Sam Ya kasa magana, tsananin tausayin benazir ne Ya cika sa, baisan Ya akai Aneelerh ta sanar da ita ba, Kallonshi Benazir tay"Yaya Shureim why? Kaima hada kai aka haɗa baki don 6oye mun gaskiya? Ban ta6a tunanin zakuyi min haka ba..." "Zanyi maki bayani ki nutsu ki saurare ni...." bai ƙare maganar ba da gudu Benazir ta bar falon ta shige ɗakinta, tana shiga ta maido ƙofa ta datse tabar su atsaye suna kallon kallo, "Shureim wai wanene Ya faɗa mata? Kuma kana agidan baka dakatar da hakan ba?" cike da damuwa Mami ta faɗa, "Wallahi Mami bansan komai dangane da wanda Ya faɗa mata ba nasan dai bai wuce Aneelerh, kawai yanzu tun da ta riga ta sani muje mu lallasheta har asamu ashawo kanta, Babu irin bugun da basuyi ma kofar dakin Benazir ba amma taƙi buɗe masu, tana jiyo sautin muryoyinsu daga waje sunata yi mata magiya akan ta buɗe masu ƙofa, Tana kuka tace masu dama sun daina wahala saboda bazata bude ba har sai lokacin da ranta yabar gangar jikinta" wannan maganar tay matuƙar ɗaga masu hankali, Mami tun tana lallashinta har takaiga hada mata da ashar amman tayi burus taki buɗewa, Wuraren ƙarfe tara na dare su Alhaji ubaid suka dawo gidan, nan fa suka tarar da abunda ke faruwa kowa Yayi tsaye kofar ɗakin Benazir in ka cire Alhaji musa wanda tun shigowarsu daya gama sauraran abunda ke faruwa yace su kyaleta in ta gaji zata buɗe kofar, Yana faɗan hakan Ya ƙara gaba abunsa, Babu wanda Yaji dadin maganarsa Hatta Alhaji ubaid yaji zafin Yadda Ya nuna halin ko'in kula akan halin da Benazir ɗin ke ciki, Har wurin ƙarfe 12 na dare ana abu ɗaya don dole suka hakura kowa Ya koma ɗakinshi ransu a jagule ahakan ma babu wanda Ya Iya runtsawa a cikin su.. Dr Shureim Yana Cikin Yin zarya a ɗakinsa kwatsam Ya tuna da shaƙar da ake ma Benazir idan dare Yayi Tabbas Yana ji aranshi za'a Iya kaimata hari duba da halin da take a ciki ba lallai ta iya ta6uka wani abu ba gashi ta datse kofa, Fitowa yai da sauri har Yana tuntu6e garin sauri Ya nufi kofar ɗakin Yay knocking shiru batai magana ba, Cikin sanyin murya yace "Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana ahaka, Yakamata kiyi hada nafila..." shiru bata tanka masa ba, jikinsa yai mugun sanyi baisan awani hali take a ciki ba, karshe zama yayi a ƙofar ɗakin don baya jin zai iya tafiya yabarta ya ƙwammace ya kwana anan. ____________________________ Sai dare Zahra ta kunna wayarta da Mahboob Ya kawo mata daga wurin gyara, Cike da zumuɗi ta shiga gallery dinta anan taga hotunan da suka ɗauka tare da Unaisah, da sauri ta fito daga ɗakinta ta nufi bedroom ɗin Aneelerh, tana shiga ta sameta a zaune kan prayer mat hannunta ruƙe da cazbaha tana ja yayin da acan ƙasan zuciyarta take tunanin ko ya su Benazir suka isa gida taji shiru bata kirata ba, har kira tay amma ba'ay picking ba, Jin sallamar Zahra yasa ta ɗago kai ta kalle ta, "Zahrah me kikeyi har yanzu baki kwanta ba"? "Taya zan Iya runtsawa bayan ban nuna maki hotunan dinner ba, sai Yanzu na samu damar kunna wayar ma" ta faɗa tare da miƙa mata, Kar6a Aneelerh tayi kafin ta soma bin hotunan da kallo, Zahra na atsaye tana kallonta, kwatsam taga Aneelerh ta zabura ta miƙe tsaye hannunta na kerma tuni cazbahar ta jima da barin yatsan ta, A ruɗe ta furta"Zahra wacece wannan Yarinyar da kukai hoto da ita??" Murmushi Zahra tayi "itace yarinyar da nake baki labari mun haɗu a wurin dinner ɗin, amma ya akai naga kamar hankalinki Ya tashi da ganinta?" Ta faɗa tana kallon fuskarta, "Zahra taya hankalina bazai tashi ba, ke baki ga fuskarta da kyau ba? wannan yarinyar kamanninta sun 6aci dana Angel ɗinmu...!" Saida Aneelerh tay wannan maganar Zahra tafara tariyo fuskar Yarinyar, haba shiyasa take tayi mata kallon sani, "Zahra bata fada maki sunanta ba"? "Tace min sunanta UNAISAH"! Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions Our website uses cookies to improve your experience. Learn more Accept ! [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 26 Complete by Novels Elite Admin July 07, 2024 Sponsored Link Novels Elite English Rass Taji gabanta Ya faɗi La66anta na kerma tace"Zahra itama ainihin sunanta Unaisah, Angel da muke kiranta nickname ne da daddynta Ya sanya mata, ɗiyar wacece ne a family din su"? Hankalin zahra ba karamin tashi yayi ba, ganin yadda aneelerh ta ruɗe ita kanta aruɗen take "Na manta ban faɗa maki labarin Yaran ba, Kamar Yadda naji daga bakin chief owais, kamar ba su da alaka da su, hasalima a daji suka tsinto su..." tiryan tiryan Zahra ta kwashe duk abunda Ya faru a wurin dinner din dangane da su Unaisah ta sanar da aneelerh Kusan zaucewa tayi hannunta dafe da kai, ganin tana tangyal tangyal kamar zata faɗi Yasa Zahra Yin saurin ruƙo Aneeelerh ta taimaka mata ta zauna gefen gado "Wallahi itace, Angel ce, Har abada bazan ta6a mantawa da fuskarta ba, ko shakku banayi wannan Yarinyar ANGEL ce tun da har kika ce tsintar su akai.... Gaba ɗaya rudanine akan fuskokin su, "Hakan na nufin Junaid Shi Ya fara gane itace? "Bangane me kike nufi ba yaga hoton ne"! Jinjina mata kai tay lokacin dana buɗe hoton don in nuna masa da karfi ya kwace wayar daga hannuna Yana fadin Angel Angel..." "Zai iya yiwuwa saboda Yawan nuna masa hotunanta da nake Yi shiyasa Ya gane ta, Ni dai Yanzu Ki taimaka min zahra! Inason na tabbatar da abun da nake hasashe! Taya zamu Iya ganin ta"❓❓❓ "Auntyna Ganinta ba abune mai sauƙi ba, dama ace bangaren su hajiya saratu suke da zama zaifi min sauki in nemi alfarmar ganinta, amma gaskiya tunkarar chief owais ba abune mai sauƙi ba! Kinsan Yanayin aikin su na jami'an sirri wallahi in ma suka ji maganar zasu Iya tuhumarmu" "Wallahi zahra In har ban samu ganin Yarinyar nan ba Hankalina bazai ta6a kwanciya ba, ke koda Zasu tuhume ni ne, gobe sai naje estate din nasu..." da kwarin gwiwa tayi maganar "Ƙwara mu bi komai a sannu, kada mu ce zamuyi gaggawa tun da bamu da tabbacin in itace dagaske...." kafin zahra ta ƙare maganar Aneelerh ta katse ta da cewa"zahra itace! Nifa ba makauniya bace, wallahi unaisah ce Yarinyar nan, tun fa tana jinjirarta muke kula da ita, shayar da ita ne kawai banyi na, tayaya bazan gane fuskarta ba"? Idanunta cike tab da kwalla ta furta maganar "Ki taimaka min zahra, dan Allah, ko dan saboda Halin da mahaifiyarta take a ciki, wallahi bakiga tashin hankalin data Shiga ba a lokacin dana sanar da ita zancen 6acewar su, ba dan zuciyar imani ba da tuni zuciyarta ta buga...." Ruƙo hannunta zahra tayi a cikin nata"ki kwantar da hankalinki aunty aneelerh, kada ki bari hawayen dake taruwa a cikin idanunki su zuba, muyi hakuri zuwa gobe inyaso sai muje can estate din nasu watakil adace su barmu mu ganta..." cikin kwantar da murya tayi maganar donta fahimci nema take ta zauce har lokaci bata daina kallon hoton ba "Mezai hana mu tuntu6i Ziyad? tun da shi yasan da zancen 6acewarsu kuma yana da hotunan Unaisah da na tura masa ko shi zai iya yi mana hanyar haɗuwa da ita" "Good Idea Auntyna, Yanzu Ki kwanta Ki huta, Gobe saimu ƙarasa maganar" Jinjina kai tayi"shikenan zahra, Allah yasa zan Iya runtsawa, Bakisan Yadda na ƙagu da son ganin Yarinyar nan ba, fatana Allah Yasa itace ɗin." "Amma kunyi waya da su aunty Benazir din? Sun isa gida Lafiya? "Na kira layinta bata ɗaga ba, sai zuwa gobe zan sake jaraba kiran ta.." Suna Cikin Yin magana Baby Junaid Ya fara mutsu mutsu zai farka daga bacci "Junaid zai farka, Ki koma gurinsa, ni zan wuce aunty aneelerh, Miƙa mata wayar tayi"mu kwana lafiya zahra" Fucewa tayi daga dakin, Aneelerh ta koma kan gado ta janyo junaid on her chest ta rungumesa Babu alamun zata Iya runtsawa saboda zumudin jiran gobe tayi, abu biyu ne suka tsaya mata aranta, na farko damuwar Benazir, na biyu yarinyar nan mai suna Unaisah... *HAJJATY* Can cikin bacci ta soma jin motsi a dakin ta wanda yayi silar farkar da ita, tayi zaton pravin ne Ya shigo shiyasa batai yunkurin tashi ba sai ma ta ƙara gyara kwanciyarta, kwatsam kamar daga sama tajiyo ƙarar faɗuwar wani abun firgigit ta zabura zaune tana faman zare idanunta jikinta Ya hau 6ari ta fara laluban fitila zata kunna hasken ɗakin, akan kunnanta taji takun tafiyar mutun adai dai lokacin ta samu damar kunna light din kamar walkiya taga gifcin mutun Ya lullu6e jikinshi da bargo, wata irin zufa ce ta keto mata numfashinta na hauhawa take kallon ƙofar cike da mamakin wanene Ya shigo? don kwata kwata baiyi kama da pravin ba... Wurga ido tai akan tsakar dakin bakhhoor burner din da take ajiyewa kan mirror shi ta gani kan floor daga gani kado shi akai Lamarin Ya ɗaure mata kai, saukowa tay daga kan gadon ta, gaba ɗaya tsoro Ya kamata, dama ƙwarin gwiwarta pravin ne gashi baya nan Yana can dakin Hajiya saratu. Tayi mamakin ganin bedside drawer dinta a buɗe, zukunna tayi gaban drawer din yatsun hannunta na kerma ta curo album din dake a ciki mai ɗauke da hotunan auransu, cike da tashin hankali take bubbuɗe su ganin ba'a ɗauki hoton Ba Yasa Hankalinta Ya ɗan kwanta, da sauri ta mike taje taja ƙofar ta datse, ta sanya key Komawa tayi gefe gado ta zauna har time din jikinta bai daina 6ari ba gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, tun da gashi har an fara kawo mata hari adakin ta, Allah Allah take gari ya waye pravin yazo don ta faɗa masa abun da ya faru ______________________BATOOL✍️ Tsakar dare ta farka sakamakon fitsari da ya matse ta, saukowa tayi daga kan gado Miƙa tayi kafin ta nufi toilet din tana dab da zata shiga, tajiyo sautin murya ƙasa ƙasa Ana magana har sai da taji gabanta Ya ɗan faɗi da sauri ta kalli gadon su duk a tsammanin ta ummi tana akwance ashe bata nan fululluka ta lullu6e da bargonta sai yai kamar mutun na akan gadon Kanga kunne tayi don ta ƙara tabbatarwa da kanta muryar waye take ji ƙasa ƙasa kamar ana raɗa "Kaima kasan bazan ta6a yin kuskuren da wani zaisan ina a tare da kai ba, yanzu haka da nake Yi maka magana ina a cikin toilet saboda bani kaɗai bace a ɗakin, akwai ɗaya daga cikin yaran da muke kula da su, Yarinyar tana sona, a tare muke kwana da ita........" Ɗagowa batool tayi da kanta, Idanunta aɗan zare babban abun da take jima tsoro da wa aunty ummi take magana a tsakar daren nan kuma acikin toilet? Wanene? Da har take faɗin bata son asan tana waya da shi? Gaba ɗaya tashiga ruɗani, Ƙara kanga kunnan tay jikin ƙofar "Bazai yiwu ba, Ni Bazan Iya yakice ta daga gare ni ba, na faɗa maka Yarinyar bata da matsala, she is innocent bayan haka bata da wayon da har za ta sanya min ido..." "Meyasa baka son kowa Yasan Ina atare dakai? kamar wani mara gaskiya kodai bakasan sunan ka Ya 6aci ne a idon jama'a"? Ta sake ji ummi ta faɗa, can kuma sai tajiyo tayi wani sauti mai kama da nishi nishi da jan numfashi Kwatsam tari Ya kubcewa batool waro idanu tayi kafin jiki na 6ari ta watsa aguje ta kashe light din dakin ta haye kan gado ta ja bargo ta lullu6e tana faman sauke ajiyar zuciya A fujajen Ummi ta fito daga toilet din, yar rigar bacci ce a jikinta shara shara, kai tsaye ta sauke idon ta kan gadon, ganin batool a kwance tana bacci Yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya, juyawa tayi ta koma cikin toilet din taja kofa ta datse Batool dake a kudundu ne cikin bargo jin alamun ta rufe kofarne Yasa ta ƙara jin hankalinta Ya kwanta, ta kudiri aniyar saita faɗa ma Unaisah maganar da aunty umminsu keyi a toilet, saboda ta tsorata gani take kamar akwai wani abu a ƙasa duk da bata zarginta. Ga fitsari cike da mararta amma saboda abun da Ya faru Ta hakura da yin shi, ta matse shi kuma cikin ikon Allah wani baccin Ya sake daukarta ____________________UNAISAH ANGEL Kiraye kirayen sallar asubahin da aka farayi ne Ya farkar da ita, addu'ar tashi daga bacci ta karanta sannan ta miƙe zaune ta ɗan jingina bayanta jikin headboad Kayan baccine a jikin ta, Milk colour riga da wando masu kyan gaske da alama baccin bai sake ta, sai faman lumshe idanu take Yi bakomai take tunani ba face Aunty pretty ɗinta, bata ta6a damuwa da ita irin na Yau ba, Wani irin marmarin son jin muryarta take Yi aranta ta ayyana ko awani hali take a yanzu? Canza akalar tunanin nata tayi akan danish, murmushi tayi tunawa da haukansa na jiya har yanzu inta tuna abun da yai mata sai taji wani irin yanayi atare da ita Ta ɗau lokaci tana ƴan tunane tunane, kafin ta ware gray eyes din ta, hannu takai ta ɗan bubbuga kafadar deeja dake bacci tana jan minshari "Sis ki tashi time din salla yayi" cikin magagin bacci deeja tace"Ni ki kyale ni, waike kullum sai munyi sallah ba a hutawa...." Murmushi unaisah tayi"Pls kada ki wahalar dani..." Daƙyar ta samu khadeeja ta farka daga bacci, bayan sunyi alwala suka sanya hijabi a jikinsu, Ko da suka kabbara sallar khaddeeja ba ibadar ce agabanta ba, da zarar unaisah tayi sujjada ko ruku'u sai ta daddage ta ɗuma mata dundu abaya Baiwar Allah, ahaka ta daure suka kammala sallar, bayanta har wani zogi Yake mata, Batasan Ya zatai da ita ba, Haris ne Yaja mata shi da ya fara kawota dakin su don ta kwana, Akan darduma bacci Yai awon gaba da khadeeja Miƙewa tay da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan mirror cike da zumuɗi ta danna ma aunty pretty call tasan i warhaka ta farka Yin sallar asuba Almost 3 times wayar tana ringing ba'ay picking ba, duk da haka bata hakuraba ta sake jaraba kira Cikin sa'a Akai picking batare da anyi mata magana ba Calmly unaisah tay mata sallama tare da cewa aunty pretty barka da asuba, kin tashi lafiya....." shiru ba alamar za'ay magana "Naji kinyi shiru bakice komai ba, dan Allah kiyi min magana jiya har mafarkin ki nayi ..." kafin unaisah ta ƙare maganar wata murya ta ratsa ta da cewa"Wacece Ke? Kuma wa kike nema"? Wani irin shock taji, Har saida gabanta Ya faɗi jin muryar Yarinyar sai taji kamar ta ta6a jinta awani wuri "I'll hang up if you don't talk!'" Da sauri tace"sunana unaisah, aunty pretty nake nema" "Oh ko ke ce kika kira wrong number rannan"? "Ni ce" "Okey, me wayar ba ta farka daga bacci ba..". "Wacece ke"? "Cousin dinta ce, sunana zeenatu" lokaci ɗaya taji yarinyar ta shiga ranta, ta rasa a ina ta ta6a jin muryarta tabbas akwai wadda ta sani mai irin voice din ta "Dan Allah, Idan ta farka daga bacci ki faɗa mata na kira," "Toh sai anjima" tana fadan hakan tay rejecting call din Ƙurawa screen din ido Unaisah tayi, yayin da kwakwalwarta ke cigaba da tariyo mata voice din zeenatu. A bangaren zeenatu bayan sun gama waya da unaisah, mikewa tay daga kan darduma jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ɗaya ruƙe da wayar cikin sauri ta fito ta nufi dakin Benazir Kamar yadda suka bar shi jiya haka ta same shi a garkame, dr shurem daya kwana awurin kiran sallar asuba ne Ya farkar da shi lokacin da zeenatun tazo baya awurin sun tafi masallaci Knocking kofar tayi"aunty benazir dan Allah ki buɗe min ƙofa, inason ganinki, jiya na damu da halin da kika shiga, ko baccin kirki bansamu nayi ba..." shiru babu alamun zata buɗe mata. "Zeenatu ki daina wahalar Yi mata magana ba buɗewa zatay ba, halin ta ne tun tana ƙarama in Ranta Ya 6aci sai munci wahala kafin mu shawo kanta..." hajiya layla ce tay maganar, baiwar Allah daga ganin idanunta ko bacci batay ba sunyi ja idon Ya ƙanƙance Muryar zeenat kamar zata fashe da kuka tace"tun jiyafa take a daki kulle! Bata magana, Idan wani abu Ya same ta fa..." Shigowar Su dr shureim ne Yaja hankulansu ga dubansu, Su ukune tare da Alhaji musa da Alhaji ubaid duk sun sanya jallabiya a jikin su. Zeenatu na ganin daddynta, da gudu ta nufe shi, ta faɗa kan kirjinshi tana kuka take fadin daddy aunty benazir taƙi buɗe ƙofa tun jiya, dan Allah kasa a balle ƙofar, bana so wani abu Ya same ta...' Fuskarsa babu annuri Yace"meyasa zaki damu kanki akanta? Ba ita ta kulle kan ta ba ne? Ko wani Ya rufe ta ne..." bai kare maganar ba hajiya layla ta katse shi cikin 6acin rai tace"wai kai wani irin bauɗaɗɗan mutun ne? Baka da tausayi ne kwata kwata arayuwarka? Jiya kana ganin halin da ta shiga har faɗa maka akai amma saboda rashin imani sai cewa kai a kyaleta in ta gaji zata buɗe kofar saboda ba yarka bace ko..."? bata ƙare maganar ba Alhaji ubaid Yai hanzarin katse ta da cewa"dan Allah kiyi hakuri ki daina ɗaga masa murya, jiya agajiye muka dawo gidan shiyasa Yace haka" harara ta wurga masa"kai ay saboda yarkace jiya ka hana idon ka bacci duk da agajiyen ka dawo gida, na tabbata da ace yarsace ke ahalin da benazir take aciki wallahi ba zaka iya runtsawa ba...." tun da tafara magana Alhaji musa Yake bin ta da kallo, arayuwarsa Ya tsani mutumin dake masa faɗa Yana ɗaga masa murya, babu wanda ya ta6a gigin yi masa hakan sai hajiya layla.... Dr shureim Bai tsaya kula su ba, ya juya ya nufi dakinsa zuciyarsa sam bata masa dadi, lamarin Family dinsa Ya fara gundurarsa kwata kwata ba zaman lafiya daga wannan sai wannan Jinjina kai Alhaji musa Yayi, ba tare daya tanka mata ba, har Ya ɗaga ƙafa zai wuce Hajiya layla ta dakatar da shi ta hanyar shan gaban shi Da mamaki Ya dago Yana kallon ta "Wallahi babu inda zakaje! In har bakasa an buɗe kofar dakin benazir ba ni kuma bazan ta6a bari kabar wurin nan ba..." tana huci ta faɗa haɗi da ruƙe qugun ta, wlh a lokaci niyar kwashe ta da mari yayi amma sai Ya fasa Yatsun hannunsa har kerma su ke tsabar 6acin rai, wai shi yau mace zata tari gabansa? Batare da jin shakkarsa ba? Wacece ita? Dame take taƙama ne"? "Layla ba haka mukai dake ba! Kin manta alkawarin da kikai mun na cewa ba zaki ƙara shiga huruminsa ba"? Azafafe ta kalli Alhaji ubaid"ban manta ba, amma wallahi Yau bazan raga masa ba, ay shi yasan ta yadda zaisa abude kofar, don haka bazan tsaya inaji ina gani in rasa ƴata ba dole yasa aballe kofar can" ta yi maganar tana watsa masa harara... Fashewa da kuka zeenatu tayi jikin ta har jijjiga yakeyi, cikin shesshekar kuka tace"daddy dan Allah kasa a bude kofar, ni bana son inga kuna samun sa6ani atsakaninku, dan Allah daddy ka taimaka mana..." kukan zeenatu ba karamin tafasa zuciyarsa yakeyi ba Gauran numfashi Yaja, tare da ɗan jinjina kansa Yana huci kamar mayunwacin zaki ya dubi hajiya layla da tai masa ƙerere kamar zata rufesa da bugu A fakaice taga Ya sakar mata wani shu'umin murmushi har saida taji gabanta Ya faɗi Sassauta fushin fuskarsa Yayi"naji zan buɗe ƙofar, ki bani hanya na wuce" matsawa tayi idanunta akan fuskarshi Ya nufi kofar dakin benazir Yana ƙarasawa bakin ƙofar, Ya ɗaura faffaɗan tafin hannunsa, turata yayi wani iko na Allah sai ga ƙofar ta buɗe Kallon Juna Alhaji ubaid da Hajiya layla sukai, abun da daure kai tun jiya suke gabzar kofar donta buɗe babu wanda bai jaraba karfinsa ba amma duk abanza ko motsi batayi amma shi daga turawa ta buɗe wani irin ƙarfi ne da shi? Basu tsaya dogon tunani ba, jiki na 6ari suka nufi ɗakin zeenatu da gudu ta rigasu faɗawa a ciki. Shugarsu keda wuya kowan nan su Yaci burki, Abun da suka gani Yayi matuƙar ɗaga hankulansu, kamar matatta haka suka hangota kwance kan floor rabin jikin ta a cikin toilet dake a buɗe, kamar irin tayi gudu ta kife awurin har kanta Ya daku goshin ta Ya fashe "Innalillahi wa'inna ilaihirraji!"un"! hajiya layla ce ta zagba salati tana tafa hannayenta, zeenatu da ta gama ruɗewa agaban benazir ta zube bisa gwiwowinta, takai hannu tana tatta6ata Aunty benazir! Meke damunki dan Allah ki tashi inna lillahi..mami daddy ku ce ta tashi dan Allah.... da sauri Alhaji Ubaid Yaje Ya ɗago da ita, jikinta duk Ya saki ya ɗauko ta da hannu biyu ya kwantar da ita akan gadon ta, sumar kanta duk Ta yamutse Fita hajiya layla tayi jim kaɗan ta dawo da robar ruwa ta buɗe murfin ta kur6i ruwan tare da furzar da shi kan fuskar benazir Ruwan na dura tayi wata irin zabura tana ambaton sunan taj ... adai dai lokacin shureim Ya shigo dakin ganin su tsaitsaye bakin gadon ta yasa shi saurin karasawa Tunkafin yayi magana Hajiya layla tace"shureim ka gani ko? Abun da nake gudu kenan! bansan ya akai ta faɗi kasa daga cikin toilet, kanta Ya bugu..." Hankalinsa atashe Yake kallon Benazir yatsun hannunta sai kerma suke, ta runtse ido tana sambatu kwata kwata bata acikin hayyacin ta Zeenatu duk ta damu, Hannunta ruke dana benazir sai faman shesshekar kuka take "Ya akai kofar ta buɗe"? "Uncle din ku ne Ya buɗe kofar," ta bashi amsa ataikaice, Alhaji ubaid Tuni Ya fuce Yabi Alhaji musa don Ya fada masa halin da benazir take ciki A lokacin Har Ya koma Part dinsa, sallamar Alhaji ubaid ce ta katse sa kamar bazai fito ba, don saida Ya ɗau lokaci har sai da hajiya sara tace da shi baiji ana sallama bane? Tukunna Ya mike cikin takun izza Ya fito daga dakin "Me kuma zanyi bayan na buɗe ƙofar"? A faɗace Ya faɗa Yana ƙanƙance idanunsa "Dan Allah ka yi hakuri da abun da layla tayi maka, bata jin maganata naja mata kunne taki bansan ya zanyi da ita ba..." ya mutsa fuska Alhaji musa yai"naji, Yanzu awani hali benazir din take a ciki? Kamar mai jin shakkarsa Alhaji ubaid Ya furta"mun sameta akwance kan floor, rabin jikin ta a toilet, kamar faɗuwa tayi don har kanta Ya daku sosai, ta farka sai dai kamar bata a hayyacin ta shiyasa nazo don na sanar dakai...." ta6e la66ansa yai kafin yace"zanyi magana da likita na, zaizo Ya duba ta" godiya ya yi masa kamar zai masa sujjada, komawa cikin dakin yai hajiya sarah dake a zaune kan darduma ta miƙe tana tambayarshi meya faru ne? Ko benazir ta buɗe kofar ne' amsa mata yai da eh jiki na rawa ta fuce daga dakin don taje dubota... Gaba ɗaya sun hallara a dakin Benazir kowan nan su Ya shiga hali na damuwa, bada jimawa ba Dr Mark Ya shigo gidan, wani basamuden Likita ne irin african american din nan, yadda kasan Jinin Alhaji musa, Fuskarsa babu fara'a, sumar kansa hada kitson zane, tun da Hajiya layla tayi arba da fuskar dr mark kuma taji cewa Alhaji musa ne Ya kira shi don Ya duba lafiyar benazir, tace wallahi bazai ta6a benazir ba, ai kwata kwata ita baiyi mata kama da likita ba, ta dinga surfa bala'e duk yadda alhaji ubaid Yaso Ya shawo kanta shi da su hajiya sarah akan ta bari aduba ta, amma abun Ya faskara a karshe sai dai Alhaji musa Ya sallami likitan Ya tafi ba tare da ya duba benazir din ba, ran Alhaji musa yai mugun 6aci yace tun da ta hana adubata bazai ƙara sanya hannu a zancen lafiyarta ba....ran kowa saida Ya 6aci da abun da layla tayi Alhaji ubaid har Ya gaji da yi mata faɗa, hajiya sarah ce ta basu shawarar su yi gaggawar kaita asibiti don abinciki laifiyarta, ba su tsaya bata lokaci ba, dr shureim Ya dauko benazir da hannu biyu ya tallabota, suka fito daga falon, A mazaunin baya na motarsa ya shigar da benazir, hajiya layla ta shiga ta rungume ta a jikinta, Alhaji ubaid Ya zauna a front seat tare da shureim, yayin da hajiya sarah ta shiga motarta tare da zeenatu kusan atare motocin suka nufi Gate din gidan, Waɗannan gabza gabzan security officers din suka tari gabansu har sai da suka kira Alhaji musa Ya basu iznin su barsu su fita kafin suka basu hanya Direct suka nufi Obie International Hospital. __________________ANEELERH Wuraren ƙarfe tara, Aneelerh ta kammala shiryawa cikin abaya tayi rolling, gaba ɗaya ta ƙagara su karasa estate din kamar tayi fiffike haka take ji, fitowa tayi daga bedroom dinta ta nufi dakin mami, bayan tayi sallama mami ta amsa mata ta shiga daga ciki ta gaishe da ita Kallo ɗaya mami tayi mata ta fahimci kamar bata jin dadi "Aneelerh baki da lafiyane naga idanunki sunyi ja? Kokarin danne damuwarta tayi"mami lafiyata lou, ban samu isasshen bacci jiya ba..." "Meyasa? Kar dai ace damuwar abun da Ya faru jiya ne"? Girgiza kai tay"a'a mami na tashi yin nafila ne shiyasa banyi bacci da wuri ba..." "Kunyi waya da su benazir din? Inataso inji ko sun isa gida lafiya"? "Tun jiya bayan sun tafi nake ta trying layinta baya shiga, har da safen nan saida na kira ba'a ɗaga ba "To Allah yasa dai Lafiya, Yanzu ina zakije ne naga kin shirya ko hakanan kikai gayu"? "Mami wani abun al'ajabi na gani jiya awayar zahra, wanda ya daure min kai shiyasa ma na shigo don in faɗa maki" "To fa, menene ? Zaro waya aneelerh tayi daga handbag dinta, ta lalubo layin zahra ta danna mata kira, Bugu ɗaya tay picking"zahra Kin gama shiryawa? "Eh yanzu zan fito" "Okey Ki same ni adakin mami dan Allah kada ki bata lokaci" Bayan ta katse wayar ta dubi mami"gata nan zuwa, abun da zan nuna maki yana awayarta" amsa mata mami tayi da toh cike da zullumin abun da zata gani Jim kaɗan zahra ta shigo dakin da sallama, Itama ta shiya cikin abaya maroon colour, ta yi rolling, hannun ta ruƙe da wayarta, a bakin gadon mami ta zukunna"ina kwana mami? Kun tashi lafiya"? "Lafiyalou zahrana, Ina abun da za'a nuna min"? danna wayar zahra tayi bayan ta buɗo hoton, ta miƙa ma mami wayar tasa hannu ta ƙarba. kura ma fuskar unaisah ido tayi kamar ta ɗan ruɗe can dai ta miƙe daga kishigiɗan da take ta ɗan kalli fuskar zahra da aneelerh kafin tace"wannan ay hoton Angel ne ko? Yaushe akai wannan hoton? Amma ya akai naga kamar ta ƙara girma anan..." at same time zahra da aneelerh suka saki murmushi saboda sunji dadin yadda mami itama ta gasgata abunda idanunta suka gane mata tunkafin ma su fada mata wa suke hasashen itace "Mami wannan yarinyar da kike gani sunanta Unaisah, a wurin dinner din prime minister zahra ta dauko hotonta a dakin taron..." da tsantsar mamaki Mami tace"oh wai da ba Angel din bace? Me kama da itace kenan"! "Mami itace, abunda muke hasashe kenan, zahra ki bata labarin abun da Ya faru a wurin dinner din...." gyara zama zahra tayi gaba daya ta kwashe abun da Ya faru ta sanar da mami Lamarin yayi mugun daurewa mami kai Aneelerh ta ƙara da cewa"yanzu haka can estate din zamuje, don mu tabbatar da abun da muke hasashe akan Yarinyar..." jinjina kai mami tayi ita kanta ta goyi bayan suje saboda kamannin Yarinyar dana Angel sun 6aci, bugu da ƙari da taji cewa Yaran tsintattune watakil su dace "Aneelerh zaiyi wuya ace yarinyar nan ba ita bace, amma dai kuje kawai, Allah Yasa adace" "Ameen mami, ki tayamu da addu'a Allah Yasa mu samu ganin ta cikin sauƙi, saboda estate din nasu ba karamin tsarone da shi ba, In har ba wani daga cikin Ahlin su Ya gayyace ka ba to basu bari bakuwar fuska ya shiga....." "Ita zahra ba suna mutunci da mutanan gidan ba"? Acewar mami Zahra tace"hajiya saratu ce, nasan indai na tuntu6eta zata taimaka mana, duk da nasan mawuyacin abune tun da yaran a hannun chief owais suke da zama, Ba lallai su bari mu gan su ba..... Shiru mami tayi kafin tace"to me zai hana ku kira ɗan jaridan nan shima badaga family dinsu Yake ba kuma ay yasan da zancen 6acewar yarinyar tun da har bayanan an tura masa....." "Har kiran layinsa nayi kwata kwata baya shiga, watakil ko Ya shiga wurin aiki ne..." Mami ta gyaɗa kai"shikenan Kuje kawai sai ku kira hajiya saratun, sannan dan Allah idan ba abaku damar shiga ba kada ku takura kanku ku dawo gida kawai inyaso sai ayiwa ɗan iya magana tun da shi ya saba hulda da yan siyasa watakil ku samu hanyar shiga ta wurinsa..... Amsa mata sukai da toh, Kafin su miƙe mami tay hanzarin dakatar da su"ku jira mahboob Ya shigo gidan, kwara kuje da namiji" Zama sukai har saida Mahboob Ya dawo Mami ta sanar da shi komai, ay tun da yaji zancen Unaisah ya gaza samun nutsuwarsa dama yajima da burin su gano yarinyar ba dan komai ba sai don jarin da Yake tunanin zai samu da ita shi uban son banza.... Lokacin da Motarsu ta shararo kan titin obie estate Aneelerh ta jinjinama haduwar wurin kasancewar yau ne na farko da suka fara zuwa, bata gama shan mamakin daular ba sai da Mahboob Yayi parking a gaban tankameman gate din estate din, hankalin su ba karamin tashi yai ba ganin Jami'an dake tsaron shi, sojoji da Jami'an Isod Babu wanda Yayi gigin fitowa daga cikin motar, Mahboob Yace"mun kawo kanmu, zahra ni fa tsoron tunkararsu nake Yi Allah, Sai dai wani daga cikin ku Ya ƙarasa driving din... Yar dariya zahra tayi"bansan Iya shege mahboob dalla ka ƙarasa mana sai kace ba namiji ba"? "Indai saina tunkari wadannan masu fuskar shanun zan zama namiji to wlh na kwammace ku kirani da sunan hajara...." dariya suka sanya gaba ɗayansu.... Mahboob Fa Ya dage akan bazai karasa da su ba...." Kwatsam biyu daga cikin sojojin suka tunkaro motarsu hannayensu ruke da bindigogi tuni zufa ta fara wanke fuskar mahboob ganin Yana kokarin tada motar Yasa zahra yin saurin cafke hannunsa"haba mahboob meye haka? Wai dama haka kake da shegen tsoro? Harara Ya galla mata"nifa ba tsoronsu nake ji ba, tashin hankali ne ke banso ..." daƙyar Ya ƙare maganar ganin har sojojin sun ƙaraso gare su Kwankwasa window glass din motar, ɗaya daga cikin su Yayi da kakkausar murya Ya furta"Put down the glass!" Aneelerh ce tayi karfin halin sauke glass din windown Ya zukunno da kansa Yana binsu da kallo idanunsa jawur "Su wanene ku kuma daga Ina? Murya na rawa zahra tace"wurin Hajiya saratu muka zo...." "Okey, Ku kirata awaya don ba'a sanar damu zuwanku ba" jiki na kerma ta amsa mashi da toh, da sauri zahra ta kira Layin hajiya saratu, kusan sau takwas baya shiga, Hankalinsu ba karamin tashi Yayi ba "Bari na ƙara kiran ziyad watakil shi Ya ɗaga" aneeelrh ta fada yatsun hannunta na kerma ta curo waya ta kira layin ziyad tana ringin baya picking, hankalinsu duk Ya tashi Ƙasa ƙasa da murya Aneelerh tace"mun shiga uku zahra shima bai ɗaga ba yanzu ya zamuyi"? Mahboob da ya gama tsorata Yace"mu koma gida kawai shine mafita in ba haka ba wlh wannan mai fuskar shanun tsaf zai Iya bombing motar mu... cikin muryar raɗa yai magana Zahra tace"wait bari na kira zayn duk da nasan mayucin abune yayi picking..." koda Ta kira layin zayn sau uku baiyi picking ba, A kira na huɗu ne Ya ɗaga muryarsa kamar ta mashayin giya ya furta "Waye"? Ko sallamarta bai amsa ba Cike da jin shakkarsa ta furta"zahra ce" "Wace zahra"? Sarai fa Ya gane muryarta har saving layinta Yana da shi awaya "Am..zahra wadda mommynka ta haɗa ka da ita, a wurin dinner din prime minister "Okey nagane, lafiya kika kira"? "Munzo estate dinkune an hana mu shiga, sojojin sunce dole sai an basu izni kafin su bari mu shiga Kafin ta kare maganar Zayn yace"kina hauka ne? Ki rasa wa zaki kira saini? Oh tun yanzu raini Ya fara shiga tsakanina dake! Uban me ma Ya kawo ku estate din? Hatta su Aneelerh sai da sukajiyo masifar da yake zazzaga mata "Dan Allah ka taimaka mana, bamu da wata mafita ne shiyasa na kira ka, wani abu ne mai mahimmanci Ya kawo mu...." kamar zata sanya kuka "Look, Ku koma inda ku ka fito tun da baku da wani alaƙa damu" Yana ƙare maganar Ya katse kiran, Tashin sense gasu dai agaban estate an hana su shigaa "Yanzu menene mafita? acewar Aneelerh "Aunty aneelerh mu hakura kawai tun da kowa yaki ɗaga kiranmu Inyaso ko zuwa gobe sai mu dawo in ba haka ba wahala zamu sha.." Gurgiza kai aneerlerh tayi"bana jin zan iya komawa gida, sai dai ku tafi kubarni, Ni kawai zanje na roke su su barmu mu shiga ta fada tare da bude car door din Ta fuce da sauri zahra da mahboob suka bi bayanta Babu irin magiyar da aneelerh batay masu ba, amma suka dage akan dole sai an basu izni, a karshe ma wani fusatacce daga cikin su Ya tsawatar masu akan su koma inda suka fito Rai a6ace Aneelerh ta dawo jikin motar ta tsaya fuskarta har ta fara zubda gumi, mahboob da zahra sai rokonta suke akan su hakura su tafi gida, amma ta kafe akan ba inda zataje, su kansu sunyi mamakin taurin kan aneelerh abun da bata ta6a yi ba...... Har mami zahra ta kira tayi mata bayanin halin da suke a ciki, tace su ba aneelerh waya su yi magana bayan ta kar6a mami tace tay hakuri su dawo gida kawai inyaso sai ayi ma uncle dan iya magana.." ta amsa mata da toh bayan sunyi sallama da mami, su zahra har sun fara sauke ajiyar zuciya a tunanin su zata koma akarshe sai cewa tayi"ita fa kawai ta amsa ma mami ne, amma fa ba inda zataje sai taga abun da ya turewa buzu naɗi..." kamar su daura hannu akai suyi ihu haka suka ji, sojojin dake zirga zirga sai kallonsu sukeyi su kansu sunyi mamakin taurin kan matar da basu san wacece ita ba, don ma Taci albarkacin Kyan dake gareta ay da tuni sunyi masu korar kare daga Layin. babban abun da Yafi damunta dayasa har ta kafe akan sai sun shiga halin Da benazir ta shiga jiya Ya ɗaga hankalinta da ciwon abun ta kwana jiya tasan mawucin abune in wani abu bai faru da ita ba, wanda yasa har bata neme ta ba kuma in ta kira bata samu Su zahra har sun gaji da tsayuwa tsawon awanni uku har karfe 1 na rana ta buga, kamar zasu sanya mata kuka fuskokin kowannansu sun Yi jawur Kiran wayane Ya shigo layin Aneelerh a hanzarce ta duba screen ganin sunan benazir ya bayyana ne Yasa tai gaggawar ɗaga kiran hadi da kara wayar a kunne Muryarta har rawa take wurin furta"benazir ina kika shiga inata kira baya shiga...." cak ta tsaya da maganar jin muryar Dr shureim "Aneelerh ba ita bace Shureim ne Ina fata kun tashi lafiya..." tun daga kan yanayin sautin muryarsa ta fuskanci babu lafiya Gabanta na faɗuwa tace"yaya shurem ina benazir din, tun Jiya bayan kun tafi nake ta jaraba kiran layin ta don inji ko kun isa gida lafiya amma ba'a ɗaga wa... "Aneeelerh! Kunyi magana jiya da benazir akan mijinta ..." Murya na rawa tace"eh.. munyi" "Meyasa kika faɗa mata abun da ya faru da su..." "Yaya shureim wallahi banyi niyar sanar da ita ba, itace ta matsamin..." gaba daya ta faɗa masa maganar da sukai da benazir har rikicewar da tayi "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..." shine abun da taji Ya furta... Su zahra dake kallon fuskar aneelerh Hankulansu duk sun tashi tunkafin ma suji me suke magana akai "yaya shureim wani abu Ya faru ne..." Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 27 Complete by Novels Elite Admin July 09, 2024 Sponsored Link Novels Elite English ___________________________________✍️ ❓ "Yaya shurem wani abu ya faru ne"? Tun daga farkon abun da ya faru bayan komawar su gida ya fara sanar da ita kafin ya ƙara da cewa"Yanzu haka da nakeyi maki magana muna a asibiti, an kwantar da ita, cos She is completely unconscious, sunan mijinta da ƴarta kadai take fadi, kuma dr ya tabbatar mana da cewa she is suffering from depression and panic attacks, sannan in har bata samu abun da take so ba zamu Iya rasa ta...." kusan suman tsaye Aneelerh tayi jiki asanyaye ta sulale daga jikin motar ta zuƙunna, idanunta cike tab da ƙwalla take ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! A kalla ta ambaci hakan yafi sau a kirga, zuciyarta da matsanancin karfi take bugawa kamar zata fasa kirjin ta... "Aneelerh ku ta yamu da addu'a, benazir taci wahala banaso narasa ƴar uwata.... " cikin rauni na murya yayi maganar Zuciyarta ce ta raya mata me zai hana ta sanar da shi zancen Yarinyar da suke hasashen unaisah ce ko dan hankalinsu Ya kwanta.. Da sauri tace yaya shurem akwai abunda nakeson sanar dakai, duk da bani da tabbaci...." Cikin rauni na murya ya furta menene? a tsanake Aneeelerh ta kwashe komai ta sanar da shi "Yanzu haka muna abakin estate din ba'a kaiga ba mu izinin shiga ciki ba, kaga idan Ya tabbata unaisah ce shikenan Zamu samu maslahar ciwon benazir...." Tana Iya jiyo Sautin ajiyar zuciyar dr shureim"Aneeelrh baki Ji yadda naji ba, Ubangiji Allah Yasa adace, Dan Allah Duk Yadda ake ciki Ki sanar dani....." "In sha Allah Yaya Shureim zaka ji daga gareni, awani asibiti ne aka kwantar da ita"? Yace"Obie International hospital" "Ubangiji Allah Ya tashi kafadunta, in sha Allah zamuzo dubata, Allah Ya bata lafiya" bayan sunyi sallama hawayene suka wanke fuskar Aneelerh "Aunty Aneelerh meya faru? Su zahrane suke tambayarta Cikin shessheƙar kuka ta kwashe komai ta sanar da su, gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi zuciyarsu ta karaya, musamman Aneeleerh wadda tuni ta sulele jikin motar ta zuƙunna tare da kifa kanta tsakanin cinyoyin ta... _______________________________✍️ Bayan dr shureim Yai sallama da Aneelerh, ɗagowa yayi da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur da su shi kadai ne tsaye a corner din da yai wayar, jiya izuwa yau gaba ɗaya ya fita hayyacinsa sam babu nutsuwa a tare da shi, Fatan shi Allah Yasa su Aneelerh suyi nasarar gano yarinyar nan kuma Allah Yasa ƴar benazir din ce da kuwa yafi kowa farin Ciki da hakan. Wani abu da ya ɗaure masa kai a binciken da likita yai ya bayyana masu cewa akwai wani abu da ya haifar mata da matsanancin tsoro lokaci ɗaya Ya fara tariyo maganar maminsu lokacin daya shiga dakin take fada masa halin da suka samu benazir ta faɗi ƙasa rabin jikin ta a cikin toilet har kanta Ya daku❗ Tuna wannan Ya shi Zare idanunsa, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi dama sai da yai fargaban faruwar hakan shiyasa ya kwana abakin ƙofar ɗakin ashe duk da haka sai da aka kai mata hari! Duk da bai da tabbacin abunda Yake zargi Ya yanke shawarar zai jira har zuwa lokacin da benazir zata dawo cikin hayyacinta don Yaji ainihin menene yayi silar faɗuwarta ƙasa❗❓ Cike da rashin kwarin Jiki Ya Nufi Medical room din da aka kwantar da benazir a Emergency depertment tun kafin Ya karasa Ya hango zeenatu abakin door room din tana sharar kwalla, baiwar Allah duk ta fita hayyacinta damuwa ta hanata sukuni Har ya ƙaraso Bata lura da da shi ba, saboda ta rufe fuskarta ta tafukan hannayenta. "Zeenat! Ba nace ki daina kuka ba?"? Sanyayyar muryarsa ce ta katse mata kukanta, Idanunta jawur ta dube shi"yaya shureim hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har aunty benazir bata dawo hayyacin ta ba..." ta faɗa tana jan numfashi "dan Allah Yaya shureim ku nemo mata babynta da mijin ta, ni bana so na rasa ta, ni kawai zan ma daddy magana yasa a nemo mata su nasan zai iya. ..." Ruƙo hannayenta yai acikin nashi"kiyi hakuri ki daina kukan Ya isa haka! Idan har dagaske kin damu da halin da take a ciki, to kiyi mata addu'a Allah Ya bata lafiya, hakan ne zai tabbatar da kaunar da kike mata.." la66anta na kerma ta fara karanto addu'o'i "Mu shiga daga ciki" ya faɗa tare da ruƙo hannunta suka shiga room din. Su Hajiya sarah suna zaune kan kujerun dake fuskantar gadon da benazir ke akwance, babu wani mai kwanciyar hankali a cikin, musamman hajiya layla, fuskarta tayi jawur tsufanta Ya fara bayyana duk ta yamutse kamar itama bata da lafiyan. Duk sun zuba ido suna kallon benazir wadda tun da likita yayi mata allurar bacci take ta yin shi, har wani firgita take yi kamar mai yin mafarki duk da karfin allurar cikin magagin bacci take ambaton sunan mijinta da yarta saboda sune aranta, baiwar Allah ba karamin jiki taji ba, la66anta sun bushe ƙamas tayi haske kamar ba jini a jikinta, kwarin idanunta sunyi ja da su... Agaban gadon dr shureim da zeenatu suka tsaya suna kallon ta gwanin ban tausayi, da ace suna da halin da zasu Iya cire mata ciwonta ya dawo jikin su da tuni sunyi hakan... Wayar hajiya sarah dake a cikin purse ce ta fara ruri da sauri ta curo wayar ta duba sunan mai kiranta My boss wato Alhaji musa. Picking call din tay ta kara wayar a kunne ko sallamarta bai amsa ba, da kakkausar murya ya ce "Kin manta Yau kina da aiki a office"? Bata bashi amsa ba, da sauri ta miƙe ta fito daga dakin Kafin tace"ban manta ba, I'll inform my secretary that I won't be going to work today na ɗauki hutu har sai benazir ta samu lafiya, ay nayi zaton ka kirane don kaji halin da ake ciki game da lafiyarta..." kafin ta ƙare maganar Ya katse da cewa"karki kuskura ki ƙara yi min magana kan benazir! Idan har ba so kike ranki Ya 6aci ba..." ranta Ya 6ace a hasale tace"wai meke damunka ne? Yarinyar nan fa yar yayanka ce, ɗiyarka ce, meyasa kake nuna halin ko'in kula akanta? Sai kace ba jinin ka ba..."? Daƙyar ta ƙare maganar jin wata tsawa da ya daka mata muryarsa da 6acin rai Ya furta"zaki dawo gida ki sameni! Har ni kike ma magana kina ɗaga min murya? Kina cikin hankalin ki kuwa"?yawu ta haɗiya Muryarta adabarbarce ta furta"i'm...so sorry" bata ƙare maganar ba Ya furta"ki faɗawa shurem ya dawo da zeenatu gida, ke kuma zaki zo ki same ni" Duff Yai rejecting call din. Ya Salam! hankalin ta idan yai dubu toh Ya tashi, bata ta6a hasala shi irin na yau ba, duk tabi tasha jinin jikinta, fargabanta kada taja ma kanta. _____________________________✍️ Prisoner's shield 👊❤ A hankali Ya ware idanunsa masu ɗauke da bacci da wata irin kasala ya yunkura ya miƙe haɗi da jingina bayan shi jikin pillow, wani irin lalaci yake ji tun karfe 12 bai leƙa ko kofar dakin sa ba, bacci kawai yakeyi, kamar baya jin dadi, short ne kaɗai a jikin shi launin ja, sumar kan shi ta rufe gefen fuskarshi kamar baccin bai ishe shi ba... Da wani irin kewar unaisah Ya farka, har mafarkinta sai da yayi, sai faman lumshe idanunsa yakeyi, kwatsam hasken ɗakinsa Ya ɗauke ɗuff kamar an kashe switch din dakin Sam bai lura ba ko'ina yayi duhu kamar dare "Garkuwa namu!...."! cikin kunnansa Yaji wata murya mai kama da ta dattijuwa ta ambaci sunan shi, yayi zaton gizau muryar ke yi masa shiyasa bai mayar da hankali akai ba "Shield! Shield!! Shield!!! Rass Yaji gabanshi Ya faɗi, A hanzarce Ya buɗe reddish eyes dinsa sosai, a matuƙar ruɗe, sam Ya gaza believing da abun da kunnuwansa suke Jiyo mashi Durowa yayi daga kan gadon Ya soma bin ceilling din dakin da kallo, a kokarinsa naya gano ta inda sautin muryar ke fitowa. A hankali Yake bin labulayen ɗakin da kallo farat ɗaya zuciyarsa ta raya masa hanya ɗaya ce zai Iya ganin me Yi masa magana... A hanzarce Ya juya Ya kalli inda madubin dakinsa Yake, wanda tun da jimawa Unaisah Ta rufe masa shi da towel saboda ta gane baison ganin mirror Walking slowly Ya nufi gaban madubin Yakai Yatsun Hannunsa dake kerma Ya Yakice Towel din Ya jefar da shi Kyawawan idanunsa Ya ɗaura akan mirror din duhu ne Ya mamaye cikin sa baka Iya ganin komai.... La66ansa na kerma Ya furta"KHALA❗❓..." sautin dariyarta ne Ya karaɗe ɗakin nashi daga ji tsohuwace tukuf "Garkuwarmu ko da Yake Yanzu Ka koma Garkuwarsu....' A hankali ta bayyana ta cikin duhun madubin kamar Yana kallon tv tsohuwa ce tukuf ta rufe ko'ina na jikinta da fararen kaya ko fuskarta baka iya gani sai dai idanunta da suka kasance farare ƙyal launin reddish irin nashi Muryarsa na rawa Ya sake maimaita sunanta Khala "Bani da isasshen lokaci yin magana!" ta faɗa tana kallon cikin idanunshi "Inaso nima na bada gudummuwata wurin ganin kunyi nasarar ruguza tarihin kurkukun ƙaddara ...." da tsantsar mamaki yake kallon dattijuwar Cikin harshensu na matsafa ta soma kora mashi jawabi...." a karshe ta furta"I'm waiting for your attack! Don't take time, the lives of the other prisoners are in danger!" (Ina Jiran farmakin ku! kada ku dauki lokaci, rayuwar sauran fursinonin tana a cikin hatsari)..." har Ya buɗe baki zaiyi magana ɗuff madubin Ya dawo suffarsa ta ainihi, da sauri Ya kawar da idanunsa daga kallon mirror din Ya ɗauko towel din daya jefar Ya lullu6e shi. Jikin shi har tsuma Yake Yi, numfashin shi da hucin zafi Yake fita, Sam Ya gaza matsawa daga gaban madubin, muryarsa da tsantsar al'ajabi Ya ke maimaita sunan JEREMIAH his childhood friend as the new prison shield gaba ɗaya He was extremely confused, Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana har wani tangyal tangyal yayi kamar zai faɗi dakyar ya iya tsayar da kansa bisa kafafunsa abunne Ya daki heart dinsa...❗ A cikin bayanan da dattijtuwar ta sanar da shi hada kwanan watan da za su yi black night ! Shin wacece Khala!?? Baku tunanin tarko ne za'a ɗana masu!? in ba haka ba tayaya matsafiya wadda take rayuwa acikin gidan kurkukun kaddara zata neme sa da sunan bashi gudummuwar tarwatsa kurkukun ƙaddara❓ Knocking kofar room dinsa akai da sauri Ya daidaita nutsuwarsa kamar wani abu bai ta6a faruwa ba... Yayi zaton unaisah ce sai da yaje gaban kofar ya buɗe karaf idanunsa suka sauka akan chief owais Ya ɗauki wanka cikin shiga ta kakinsa Yayi shirin zuwa Office, from head to toe Ya kalle sa kafin Ya haɗe fuskarsa bakomai Ya tuna ba face unaisah da ya gani adakinsa jiya shiyasa ya ƙarajin haushin mutumin Chief owais baibi takansa ba Ya nufi cikin dakin hannunsa ruƙe da shopping bag, Ya dire masa ita kan gadon shi A hankali Ya juyo suka fuskanci Juna "Ba ka Iya gaisuwa ba ne"? wani ɗan iskan kallo danish Yayi masa Murmushin gefen fuska chief Yai "Laifin me na maka kamar baka kaunar gani na"? Shiru yayi bai tanka masa ba Da ace chief yasan unaisah ce Silar dayasa danish Yake haɗe masa rai ay da tuni Yayi masa bayanin da zai kwantar masa da hankalinsa don shi A yanzu mace bata agabansa, burinsa ya gano miyagun gidan kurkukun ƙaddara da kuma kawo karshen su shi ne abunda Yasa agaba kallon shoppin bag din yai alamar yana neman ƙarin bayani yaga bakon abu adakin sa "It's a gift from Uncle Hateem. Please don't break them they're not toys," he said jokingly. tare da buɗe jakar ya soma fiddo da kayan cikin ta "suna da amfani, idan ka bani dama zan nuna maka yarda zakai amfani da su" cikin lallami yakeyi mashi magana Ganin Yayi tsaye Yaki matsowa Ya duba kayan, Yasa chief Tunkararsa Ya ruƙo hannunsa Ya janyo shi har bakin gadon "Zuwa anjima zan ware mana lokaci in fara koya maka Yadda zakai amfani da su ko baka so"? Yai maganar Yana dubansa sai wani shan mur Yake. Daurewa kawai cheif yakeyi amma fa ya fara hasala da halin danish kwata kwata baya sakar masa fuska kuma Yaƙi magana da shi, in banda ma Yana neman alfarma awurinsa ay da bai kai matsayin da chief zai kulasa ba Fucewa yai daga dakin Ya Bar danish a tsaye Ya kasa ta6uka komai, zuciyarsa har yanzu bata daina ambaton sunan jeremiah ba, kalaman tsohuwa Khala sun tsaya masa aransa sai yake ganin kamar amafarki ta bayyana.. zama yayi gefen gadon Ya zubawa kayan ido har cikin rashi Yaji dadin jin cewa Hateem ne Ya bashi kyautarsu, duk da baisan amfaninsu ba amma sunyi mashi kyau, bai ta6a ko ɗaya ba, ya yanke shawarar sai unaisah tazo zasu buɗe su atare ________________________________✍️ *ANEELERH* "Mu tafi asibitin kawai, bazan Iya jurewa ba...." gani take kamar zata rasa benazir, shiyasa ta hakura da shiga estate din Su mahoob daman hanyar da zasu tafi suke nema, jiki na 6ari Ya buɗe motar Ya zauna a driver's seat, Aneelerh ta shiga ciki, Zahra na kokarin shiga kwatsam ta hango dankareriyar motar dake tunkaro estate din dakatawa tayi saboda ranta na bata cewar Motar Hajiya saratu ce.... "zahra ke muke jira ki shigo mu tafi" acewar mahboob "Kaɗan jira, naga kamar motar Hajiya saratu ce ke tunkaro estate din..." jin wannan maganar yasa Aneelerh yin hanzarin fitowa daga motar shima mahboob Ya fito duk suka ƙurawa motar ido cike da sa ran ganin wanene a cikin ta Lokacin da motar ta kusa ƙarasowa dab da inda suke gudunta ya ragu slowly window glass dinta na back seat Ya zuge hakan Ya basu damar ganin na cikinta Wata irin nauyayyar ajiyar zuciya zahra ta sauke mai haɗe da annurin farin ciki Ita kanta Aneelarh ajiyar zuciyar ta sauke haka shima mahboob duk da basu ta6a ganinta ba Yau ne rana ta farko da suka fara ganinta ido da ido A hakimce take zaune cikin motar, ta ɗauki wankan lafaya, idanunsa na a manne da farin glass ba karamin kyau yayi mata ba Da alama su take kallo, Umarni ta ba security din dake driving dinta idan sun karasa kusa da motar su zahra yai parking, ya amsa mata da toh Daga bayan motarsu zahra yayi parking din motar, jiki na 6ari zahra ta nufe ta, a lokacin ta bude car door din ta zuro kafarta ɗaya waje Sallama tayi mata cikin girmamawa tace"sannu da zuwa mommy, ya gajiyar aiki...." Fuskarta da fara'a ta furta"lafiyalou daughter, zuwan bazata akai mana? Amma ya akai naganku a waje..." Zahra kamar zatai mata sujjada tsabar yadda take magana cikin ladabi da biyayya "Masu tsaron gate din ne suka hana mu shiga sunce dole sai an basu izni, har layinki na kira baya shiga nasan kin shiga busy ne..." "Eyyah! Na sanya wayar a silent lokacin da zan shiga meeting...' tai maganar tare da kai dubanta ga su aneelerh"su wanene? Ina fata dai lafiya? Ta fada cike da son jin karin bayani "Auntyna ne da ƙanina mahboob, wani abune mai mahimmanci Ya kawo mu .." da sauri Aneelerh da mahboob suka karaso bakin motar hajiya saratu cikin girmamawa suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu wato sunci albarkacin zahra shiyasa ta sakar masu fuska "Pls kuyi hakuri sun shanya ku arana, Yanzu ku shiga motar, mu tafi. " wani irin dadi Ya lullu6e su, da sauri suka nufi motarsu, bayan sun shiga a jere motocin suka nufi cikin estate din babu wanda yayi gigin dakatar da su cikin securities din sai ma gaisuwar da suke mika ma hajiya saratu wadda ko kallo basu ishe ta ba. Bayan sunyi parking, kowan nan su Ya fito, Aneelerh sai faman satar kallon katafaren estate din takeyi kamar a dubai, Inaga mahboob wanda Yake ta jinjina kai aranshi Yace"Wai dama haka daular obie estate take? Gari guda, Tabɗijan Daga gani anyi almubazzaranci wurin ginasa, Mutane kamar bazasu mutu subar duniya ba? Yo ni Allahna na tuna ko amafarki ban ta6a ganin katon gini irin wannan ba! Kai jama'a..sai faman santi yakeyi acikin ranshi Gaba hajiya saratu tayi da sauri suka bi bayanta, zahra hada kar6ar handbag dinta ta ruƙe mata ita, irin fadancin nan Ashe mahbbob baiga komai ba, suna shiga falon kiris Ya rage ya zabga salati saboda ganin makurar kayan alatun da aka baje ta ko'ina...har wani zazzabi yake ji ajikin shi Ga masu aiki dake kai komo cikin uniform "Bismillah ku zauna, Ku ɗan bani mintina kaɗan, Yanzu zan fito..' amsa mata sukai da toh, ta nufi daki zahra tabi bayanta don ta kai mata handbag dinta.. Ya rage saura mahboob da Aneelerh, zama sukai akan tamfatsa tamfatsan royal sofa din falon... "Karshen duniya yazo aunty aneelerh" ya faɗa yana kishingiɗa bayansa jikin sofa, duk da halin damuwar da Aneelerh take aciki sai da ɗan murmusa jin abunda Mahboob Yace, ita kanta ta girgiza da ganin katafaren ginin "Alhamdulillah Ya Allah.."ta furta aranta"Ya Allah kamar Yadda ka bamu ikon shiga gidan nan lafiya, Ya Allah ka bamu ikon ganin Yarinyar nan cikin sa'a ba tare da mun sha wahala ba" har cikin ranta wani irin sanyi takeji, fatanta Allah Yasa su dace Kallon mahbbob tayi wanda ke ta bin ko'ina da kallo baki asake kamar lehen sakarai "Mahboob! Pls kaja aji mana, kada kai mana kauyanci, duk fa abinda suke da shi mu ma muna shi agida...." tashin Farko Ya ce"muna da lifter..? murmushi aneelerh tayi"a'a amma ai akwai stairs ko"? Girgiza kai yai"ba irin wannan ba duba fa kiga ni har hawa uku, ga yan aiki ta ko'ina..." murmushi tayi tana kallon shi" nifa aunty aneelerh bawai kyawun gidanne Ya ruɗe ni ba, no kawai almubazzarancin da akai wurin ginasa shiyafi komai 6ata min rai, Allah ba karamin mai imani bane zai zauna agidan nan kuma yaci gaba da yin sallah..." yar dariya Aneelerh tayi Kafin wani Ya ƙara magana sofia ta nufo wurinsu hannunta ruƙe da tray na cool drinks tare da snack ta ajiye masu kan table "Inayi maku barka da zuwa" amsa mata sukai da yawwa "Hajiya saratu ce, ta bada umarnin akawo maku drinks, idan akwai abun da kuke bukata ku sanar dani..." har suna haɗa baki furta"a'a mungode, Bayan ta bar wurin Mahboob Yace"munci darajar Zahra wlh da ko kallo bamu ishi matar can ba, daga ganin ta zatai ji da kai..." Bayan wasu Ƴan mintuna, Hajiya saratu ta fito har ta canza kayan jikin ta, wata hadaddiyar abayace ta sanya, zahra na abiye da bayanta har suka karaso, zama tayi kan sofa tana fuskantarsu, itama zahra ta zauna. Ƙara gaisawa sukayi kafin ta ce"Zahra ta faɗa min abune mai mahimmanci Ya kawo ku! ina sauraronku..." cike da dattako tayi maganar. Gyara zama Aneelerh tayi cikin nutsastsiyar muryarta ta fara kora mata jawabin abun da Ya kawo su... bayan ta kammala hajiya saratu tayi jimm na ɗan wani lokaci kafin ta dubeta"kun tabbata Yarinyar ce? Shiru sukayi ta kuma cewa" Bana so asamu matsala! Ba ku tunanin ko mai kama da ita ce..."? Duk da ƙwarjinin da hajiya saratu tay wa aneelerh hakan bai hanata Yin karfin halin furta"muna sa ran itace, saboda ni tamkar uwa nake agareta, Yau shekara shida zuwa bakwai da 6atanta kamar Yadda na fada maki, kuma sunan yarinyar Unasah kamar yadda itama yarinyar da shi owais din yake ruƙo sunanta unaisah, amma muna kiran ta da Angel sunan da daddynta Ya sanya mata..." da kwarin gwiwa Aneelerh tayi maganar don ji take zata iya komai akan yarinyar nan Numfasawa hajiya saratu tayi abunka ga mace mai izza, bata son abunda zai jawo raini tsakaninta da chief gani take kamar zubda girmane ta nemi alfarma awurinsa shiyasa take jinjinawa lamarin da suka zo mata shi, duk da tana son taimaka masu. "Ina hoton Yarinyar, Ina son ganin shi" cikin sauri zahra ta buɗe mata hoton awaya ta muƙa mata. Bayan ta kar6a ta kurawa hoton ido nan take ta gane fuskar yarinyar cikin yaran da owais yazo da su wurin dinner..... "Ina hoton ita Yarinyar ta wurin ku"? Ta faɗa tana kallon Aneeelerh, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin saurin curo wayarta daga cikin handbag ta buɗe hoton Angel ta yunkura taje gaban hajiya saratu ta miƙe mata wayar Bayan ta kar6a ta jera wayar zahra da aneelerh akan table din gabanta, a tsanake take nazarta hotonan ita kanta ta gasgata abunda suke hasashe komai iri ɗaya, banbanci ita yarinyar da uwais Yake ruƙe ta fi angel dinsu girma amma duba da tazarar shekarun da yarinyar ta 6ace zai iya yiwuwa itace taƙara girma... Gaba daya hankulansu Aneelerh akan hajiya saratu duk sun kagara da son jin me zatace masu.. Bakomai take jinjina mawa ba face ta yadda zata zubda girmanta wurin yiwa owais magana, saboda basa jituwa tun time da ta fahimci bai kaunar mijinta, kuma tana jin haushin Yadda ake nuna wariya tsakanin Twins dinta da shi "Dan Allah ki taimaka mana kamar yadda Allah Ya taimake ki, wallahi baki ga halin da mahaifiyar yarinyar take a ciki ba, yanzu haka tana agadon asibiti kwata kwata bata a cikin hayyacinta, sunan mijin ta da yarta kadai ta ke Iya ambato..." muryar Aneelerh ce ta katse mata zancen zucin nata "Meya same ta ne? Ko kina nufin tsawon lokacin da yarinyar ta 6ace bata a cikin hayyacin ta..." ta jefa mata tambayar cike da sonjin karin bayani Labari aneelerh tafara bata tun guduwar benazir da kuma dawowarta har izuwa kan abun da Ya faru jiya Jinjina kai hajiya saratu tayi da alama abun Ya tsuma zuciyarta duk da bata nuna ba. "Allah ya bata lafiya" suka amsa mata da ameen. "Zan nema maku alfarmar ganinta, amma kafin nan ina bukatar ku bani zuwa gobe, kunsan yanayin aikinsu na jami'an sirri, kuma yaran kamar suna bincike kan case dinsu ne, ganinsu zaiyi wuya, dole sai na fara yin magana da shi....." Aneelerh taso ace ta kira chief din awaya sunyi maganar nan take amma dole ta hakura tunda su ne ke nema awurinta dole su yi biyayya A tare suka haɗa baki wurin yi mata godiya. har bakin motarsu hajiya saratu ta rakosu ta ƙara jaddada masu gobe zasuji daga gareta Lokacin da motarsu ta haura kan titi, shiru babu mai magana a cikinsu, "Wani jinkirin Alkhairi ne, muyi hakuri" zahra ce ta fada ganin damuwa na neman rikita auntynta "Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" suka amsa mata da ameen Dai dai motarsu ta kusa shiga tankameman gate din asibitin saiga motar dr shureim tana fitowa daga ciki, kasancewar window glass din abude Yake da sauri aneelerh ta kwala masa kira Ya shureim... Ya na ganinsu Ya samu wuri Yai parkin din motarsa, fitowa tayi da sauri ta nufi motar ta ɗan zukunna bakin glass din tana kallonsa Duk sai taji wani iri ba dadi ganin yadda fuskarsa tayi jawur idanunsa sun kumbura "Yaya shurem Ya jikin benazir din? "Da sauƙi, amma har Yanzu bata tashi daga bacci ba... "Allah Ya bata lafiya "Ameen..." shiru sukai kafin tace"naga ka fito ko gida zaka koma ne..." "Bani zan koma gida ba, zeenatu zan maida..." sai da yai maganar idonta Ya hango mata zeenatu dake zaune a backseat ta kifa kanta bisa gwiwowinta yatsun hannunta sai kerma suke daga gani babu nutsuwa atare da ita "Ina fata badai wani abu Ya same ta ba"! "Daddynta ne Yace amaida ta gida, shi ne take kuka" "Allah sarki baiwar Allah...." cikin nuna tausayawa tayi magnar, zeenatu duk tana jinsu saidai bata jin zata iya dagowa saboda gaba daya fuskarta ta ca6e da ruwan hawaye.. "Ya ake ciki game da Yarinyar kun samu ganin ta..."? Ya jafe mata tambayar saboda abun na aransa Nan Aneelerh ta sanar da shi Yadda sukai da hajiya saratu Jinjina kai yai"in sha Allah gobe idan ta kiraku awaya tare zamuje estate din....ko su mami ban sanar mawa ba saboda bana so su sanya rai har sai mun tabbatar in itace.... "Shikenan Yaya shureim Allah Ya kaimu lafiya amma zaka dawo ko"? "Ay dole na dawo aneelerh, Daga na kaita zan juyo..." Allah Ya dawo dakai lafiya Sallama sukai ma junansu, ta tsaya tana kallon motarshi har ta 6ace ma ganinsa Komawa tayi cikin motarsu, Mahboob Ya karasa shiga da su ciki tun kafin yayi parking yake ta faman jinjina kai Yana fadin anyi almubazzaranci wurin gina asibitin sai kace ba wurin jinyar marasa lafiya ba, komeye amfanin ƙawata asibiti ...." yana karasa yin parking suka fito da sauri suka nufi emergency ward sai da suka fara tsayawa wurin nurse's station bayan sun fada masu sunan marar lafiyar da suka zo dubawa, ɗaya daga ciki tayi masu jagora har dakin da aka kwantar da ita, kafin ma su isa suka hango Hajiya layla tare da Alhaji ubaid abakin kofar asitin suna magana atsakaninsu, fuskokin kowan nan su babu annuri sai tsantsar damuwa Takun tafiyarsu Aneelerh ne Yaja hankulansu ga dubansu "Aneelerh......" hajiya layla ta fada cike da mamakin ganin ta, ita kanta baza ta iya tuna rana ta karshe da tai tozali da ita ba. Aneelerh na karasawa ta rungume hajiya layla batasan sa'adda kuka Ya balle mata ba Shafa kanta hajiya layla tayi tana ɗan rarrashin ta, hakika tayi mamakin ganin yadda ta kara girma rayuwa kenan andade ba'a hadu ba, tun da zumuncin su Ya watse Tsawon mintuna hajiya layla tana lallashinta, kafin ta dago idanu jawur ta gaishe da Alhaji ubaid fuskarsa da fara'a ya amsa mata har yana ɗan zolayarta Aneelatu kece kika koma haka? Ƴayanki nawa? Cikin shesshekar kuka tace Yarona dayane Yana a school, "Allah shi raya shi, Tace"ameen" "Ya hakurin abun da ya faru da su Uzair"? "Mungode Allah" "Ubangiji Allah Ya bayyanar da su" ta amsa mashi da ameen Hajiya layla tace"ki shiga ciki," da sauri ta shiga dakin, Su zahra dake atsaye har suna haɗa baki wurin Gaishe da su ita da mahboob suka kuma yi masu ya mai jiki "Jikin da sauki bacci take, amma ku yan uwanta ne"? "Ƴaƴan uncle dinta ne mu" "Allahu akhbar kamar na ta6a ganinku da jimawa lokacin baku kai haka ba.." Zahra tace"eh ay muna yawan zuwa joss lokacin baya..." "Allah sarki ku shiga daga Ciki dan Allah kuyi mata addu'a' amsa mata sukai da toh Bayan sun shiga, agaban gadon suka iska Aneelerh ta zuƙunna kan gwiwowin ta, kanta akan gadon, hannunta acikin na Benazir, jikinsu duk sai yayi sanyi ganin yadda benazir ta faɗa daga jiya zuwa yau har ta canza... Har lokacin hajiya sarah na zaune kan kujera sallah kadai ke tada ta.. Gaishe da ita su zahra sukayi tare da yi mata ya mai jiki tace masu da sauki, "Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa kaffarane" ta amsa masu da aneen Gaban gadon suka tsaya kafin suka fara yi mata addu'o'i suna tofe mata jiki da su,..... Kamar masu zaman makoki haka suka tasa ta agaba suna kallon ta. Wureran karfe biyu da rabi ta farka kamar mai ta6in hankali haka ta dinga fusge fusge tana ambaton sunan taj da Angel, ta makance bata ji bata gani bata sauraren kowa hauka kawai takeyi masu, haka suka dinga rurruƙe ta don kokari ma take ta sauko daga kan gado, su Aneelerh sun sha kuka ba kamar da ta furta"kada su bari ta mutu bata sanya yarta a idon ta ba, bata son ta mutu bata ganta ba, su taimaka ma rayuwarta....." babu wanda bai zubar mata da kwalla ba, hatta mahboob Yaji tausayinta Likitan dake kula da ita ne Ya shiga dakin tare da wasu nurses Ya bukaci su hajiya sarah su fita daga waje Nan suka fito kowa Ya zauna kan waiting seat suna ta jiran tsammani Tsawon mintuna ɗuff suka daina jin sautin koke koken benazir, har sun fara fargaban meke faruwane sai ga dr adam Ya fito daga dakin tare da nurses din Suna ganin shi kowa Ya mike suka nufe shi suna tambayar awani hali take ciki"? Fuskarsa babu walwala Yace masu suci gaba da yi mata addu'a sannan su yi kokarin samo yarinyar da zata iya pretending amatsayin yarta daga yau zuwa gobe in ba haka ba sakamakon ba lallai Yayi masu dadi ba, don sunyi iyakar bakin kokarinsu amma abun yaci tura, Yanzu haka allurar bacci suka ƙara Yi mata....." Hankulansu ba karamin tashi Yayi ba, nan fa suka fara shawarar Yadda za su samo Yarinyar dake kama da Angel ƴar fara mai launin ido ruwan toka.. Aneelerh tayi saurin cewa akwai wata yarinya da ta sani mai kama da unaisah, amma ko za'a same ta sai ya kai zuwa gobe...." ta fadi hakanne saboda tana sa ran gobe hajiya saratu zata kirasu inyaso koda yarinyar ba unaisah bace sai su nemi alfarmar abasu ita aro har zuwa time ɗin da benazir zata ji sauki... Hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba, hajiya layla tsabar zumudi hada cewa me zai hana yarinyar tazo yanzu? In ma da bukatar suje gidan iyayenta neman alfarma sai suje..tace masu ay yarinyar ba'a kusa take ba, suyi hakuri zuwa gobe sai a sanar da iyayenta amsa mata sukai da toh .......... Bayan komai ya lafa, Aneelerh ta kira mami awaya don ta sanar da ita halin da ake ciki, a lokacin tana a falo zaune zuciyarta cike fal da tunanin kome Ya tsayar da su aneelerh har yanzu basu dawo ba? Ko dai sun samu shiga gidanne? Ita kadai take ta tufka da warwara, kiran na shigowa a hanzarce ta dau wayar dake akan sofa hand, ganin sunan aneelerh yasa tay saurin dagawa "Aneelerh! Ina fata kuna lafiya? Naji shiru baku dawo ba, ba sai da nace maku in baku samu shiga gidan ba kada ku takura kanku? On the other hand Aneelerh tace"mun samu shiga mami, amma bamu samu damar yarinyar ba...." a tsanake ta sanar da ita komai ta kara da cewa"tace zuwa gobe zata tuntu6e mu,..." Mami tace"to kuyi hakuri ku dawo gida, wani jinkirin alkhairi ne..." "Mami, Yanzu haka muna asibiti, benazir ba lafiya..." tunkafin ta kare maganar mami ta doka salati tana fadin wata benazir din? Meya same ta"? Gaba daya hankalin ta ya tashi Shigowa ummi tayi falon tana kallon mami dake ta zagba salati tana sauraron Aneelerh dake bata labarin abun da Ya faru bayan komawarsu dr shurem gida, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'i abu baiyi dadi ba, kai jama'a baiwar Allahn nan tana jin jiki, ubangiji Allah Ya tashi kafadunta, Anerlerh gani nan zuwa asibitin, kice wa mahboob kada ya manta da junaid karfe shida Yaje ya daukosa" amsa mata aneelerh tayi da toh Bayan ta katse kiran, fuska A yamutse ta kalli ummi dake tambayar ta lafiya meya faru taji ta ambaci sunan benzair Girgiza kai tayi kafin ta kwashe komai ta sanar da ita, hankalin ummi ba karamun tashi yayi ba. "Yanzu zanje asibitin, ki zauna ke inyaso gobe sai kije kada abar gidan ba kowa, duk da Ana tana nan ba lallai junaid Ya yarda da ita ba kinsan shi da rigima." Amsa mata ummi tayi da toh, cike da Alhinin abun da Ya faru, da sassarfa mami ta dauko hijabi ta zubla ta fito daga daki, ummi tayi mata adawo lafiy sanna tace agaishe mata da mai jiki, kafin taje goben Mami na fitowa daga gidan saiga motar abie ta shigo, hakan ba karamin dadi yayi mata ba, dama abun hawa zata tsayar akaita can, sai gashi Allah ya dawo da shi, Agabanta Yayi parking motar bata jira Ya fito ba, ta bude motar ta shige sai da ta zauna yake tambayarta ina zataje yaga kamar bata acikin nutsuwarta, nan ta sanar da shi abun da ya faru na rashin lafiyar benazir, har faɗa sai da yayi akan fada matan da aneelerh tayi mami tace bafa laifin ta bane, itace ta matsa mata, kuskure daine an riga anyi sai dai ayi fatan Allah Ya tashi kafadunta.... Karya kwana yayi da gudu motarsu ta fuce daga gidan kai tsaye suka nufi asibitin. _________________________________✍️ Slowly motar dr shureim ta kunna kai cikin gidan, bayan yai parking ya dago ya kalli zeenatu da ta kifa kai bisa gwiwa tana ta shesshekar kuka "Bazan gaji da lallashinki ba, dan Allah ki hakuri ki jure ya shurem bayason ganin hawayen babynsa, na fada maki addu'armu take bukata, kuka ba abunda zaiyi mata...." tun da yafara maganar bata dago dakai ba Fitowa yai daga motar ya zagaya dayan bangaren da take ya buɗe mata"fito mu shiga" still bata tanka mashi ba, dama dakyar ya rabata da asibitin. Ba karamar badakala suka sha da ita ba. Kuka tadinga yi akan bazata koma gidan ba, dakyar suka lalla6ata. Ganin zata bata lokaci Yasa shi kai hannayensa ya tuttu6eta kamar yar tsana Yai mata irin daukar da ake ma jariri Ya nufi cikin gidan da ita. Tana kuka tana fadin yaya shureim bazanje ba ni ka sauke ni, wurin aunty benazir zan koma...bai saurareta ba har ya karasa katafaren falon, Alhaji musa na azaune kan sofa ya daura kafa ɗaya bisa ɗaya, idanunsa na akan laptop dinsa, hada mug din coffee a gefe yana sha babu alamun damuwa akan fuskarsa hankalinsa kwance Shigowarsu ne Yasa shi dago da ido Ya kallesu Fuskar shureim a daure Ya dira zeenatu, ransa Ya baci da ganin uncle din nasa kamar baisan halin da suke aciki ba. "Shureim..." har ya kusa Fita ya dakatar da shi waiwayowa yayi babu walwala Ya ke kallonsa, shi kanshi alhaji musan Ya fahimci fushi Yake da shi "Ya jikin benazir din? Kamar bazai tanka masa ba ya furta"da sauki" "Menene sakamakon abunda ke damunta"? Sai da ya ɗanyi jim kafin yace"It's depression and panic attack...." bai kare maganar ba yai hanzarin fucewa daga falon don baya jin zai iya jurar kallon uncle musa tsaf zai Iya gaya masa magana Har ya kusa fita daga entry hall din kwatsam sautin muryar zeenatu Ya dakatar da shi Ya kasa kunne Yana sauraronta Cikin muryar kuka take fadin"Wallahi daddy baka da tausayi, kowa ya damu da halin da aunty benazir take aciki ban da kai! Jiya kana gani haka ta kwana akulle kaki taimakawa ka buɗe mata kofa, har sai da ta kwana, why daddy? Baka sonta ne? Ko tayi maka wani laifi ne da yaja har kake nuna halin ko'in kula akan ta, ni wlh ka 6ata min rai daddy tun da har baka damu da rashin lafiyar aunty benazir ba, hankalinka kwance kana agida sai kace ba ɗiyar yayanka ba,....." kamar daga sama dr shureim yaji saukar mari ji kake tasss A matuƙar furgice ya ware dara daran idanunsa, jikinsa na 6ari a sukwane Ya juya cikin takun sauri Ya nufi falon Har zai shiga wata zuciyar ta gargadesa akan kada Yaje Tsayawa yayi yana sauraron su daga inda yake yana iya hangen zeenatu wadda tunda daddynta ya kwasa mata mari gaba daya ta jirkice ta kife kan hannun sofa, jikinta yadinga bari kusan wannan ne karo na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ta....baiwar Allah gaba ɗaya ta furgice ta kasa dagowa ta dinga tsala kuka tana fadin na tsane ka daddy, da kanka ka sa hannu ka buge ni? Daddy ka makance ne? Wlh sai dai ka kashe ni daddy..." masifa ta dinga zazzaga mashi Zeenatu bata ta6a bashi mamaki ba irin na yau, duk irin shakkarshi da take ji hakan bai hanata fadan ta cikin ta ba, hakan ya tabbatar masa da taji haushin abunda yayi Yatsun Hannunsa Ya zubawa idanu cike da jin haushin marin ta da yayi, Duk da ita taja ma kanta, shi fa ba'ay masa fada ana ɗaga masa murya balle ita da take yar cikinsa... Walking slowly Ya nufi sofa din da take Ya zube kan gwiwowinsa agabanta. dr shureim dake la6e Yana kallon shi har saida Ya ɗan ware idanunsa cike da mamakin Yadda Alhaji musa Yai kneel down agaban zeentu mutumin da ko uwarsa baya tunanin Ya ta6a zukunna mata, wannan wani irin sone ya ke yi mata? Kamar zai mata sujjada haka Ya fara magana"i'm really sorry my daughter, kurkurene ba da son raina ba, kece kika fusata ni zeenatu, banso na mareki ba..." yadda yake yi mata magiya ba karamin ɗaure kan dr shureim yayi ba, har tafin hannu yasa ya shafa fuskarsa don Ya tabbatar in ba mafarki Yake Yi ba Cikin shesshekar kuka take fadin"Dad ..dy dama ka daina bani hakuri, don bayi zanyi ba, ni bana son ganin ka, tun da bakason Aunty benazir dina..." bata kare maganar ba, Yai hanzarin furta"waya fada maki bana sonta? benazir kamar ƴa take awurina..." To amma meyasa jiya kaki bude mata kofa "Saboda bani na kulleta ba, itace ta kulle kanta .." "Daddy ni ban yarda kana sonta ba, tun da kaki zuwa asibiti dubata..." Hannu yakai tare da janyo zeenatu ya kwantar da kanta saman broad chest dinsa Ya daura tafin hannunsa abayanta yana lallashinta..."ki daina kuka bana so, indai akan benazir ne zanje na dubata hope hakan yayi maki" Tana faman matse kwalla tace"daddy dr yace in har ba'a bemo mata yarta ba, zuciyarta zata buga ta mutu, dan Allah kasa a nemo mata yar babynta, daddy nasan zaka iya..." yamutsa fuskarsa yai kafin yace"naji zanyi kokarin sanyawa a nemo mata ita, Yanzu ki kwantar da hankalinki, Muje daki ki kwanta ki huta, zan sa tani ta kawo maki abinci nasan kina jin yunwa..." yai maganar tare da mikewa ya ruƙo hannun zeenatu acikin nashi, suka nufi bedroom dinsa gauran numfashi dr shureim Ya sauke aranshi yana mai al'ajabin irin son da Alhaji musa yake ma zeenatu Sai dai baiji dadin marin da yayi mata ba, yaji zafi aranshi, saboda yaga shatun yatsunsa sun fito ruɗu ruɗu kan kuncinta yasan dakyar in zazza6i bai kamata ba, saboda zafin hannu gare shi, ya ta6a marin zainab mai aikin gidansu lokacin dayaje joss kawai saboda ta haɗa hanya da shi har ta bangaje shi cikin rashin sani, tun da ya kwasa mata mari sai da tay 1 week tana jinyar fuskarta.... sai dai yasan ba lallai ya bari zeenatu taji jiki ba, tunda yana sonta zai mata maganin abunne Da wannan tunanin Ya fuce daga gidan Ya shiga mota Yaja Ya nufi asibiti. ______________________EX-PRISONERS A tsaye suke su biyu suna fuskantar junansu, tunda batool ta sanar da ita game da wayar da tajiyo aunty ummin su, tana yi a tsakar dare cikin toilet, taji hankalinta Ya tashi zuciyarta harta fara raya mata ko dai aunty umminsu da wata muguwar manufar take atare da su? "Taya za'ay insan dawa take magana"? Ta jefa wa kanta tambayar "Wai hada cewa ay bani da wayon da zan iya sanya mata ido..." acewar batool "Anya batool ba zaki daina kwana dakin ta ba? "Saboda me"? "Indai zaki cigaba dayi mata la6e duk ranar da ta gano ki, wlh zata Iya hukunta ki, tun da bamusan me take ƙullawa ba! Girgiza kai batool tayi"ni dai bana Yi mata mummunan zato, kuma bana so na daina kwana dakinta..." fuskarta ayamutse tayi maganar "Nima ina kyautata mata zato, amma meyasa take abu kamar mara gaskiya? Waya a toilet kuma a tsakar dare? Sannan har tana fadin baki da wayon da zaki iya sanya mata ido? Ruko hannun batool tayi"bazan hanaki kwana dakinta ba, amma kiyi takatsantsan, kada ki ƙara yi mata la6e kibarta kawai, In sha Allah ba abun da zai faru watakil ma bata son ki farka daga bacci ne shiyasa ta shiga toilet tanayin wayar don kada ta takura maki' jinjina kai batool tayi alamar gamsuwa da maganar unaisah Kafin wani ya ƙara yin magana a cikin su, suka ji an turo door room din, kusan atare suka dago suna kallon mai shigowa har saida gabansu Ya ɗan fadi ganin matar da suke gulmarta Tayi gayu abunda cikin riga da wando sun kama jikinta, head din data daura ba karamin kyau yayi mata ba, tuni kamshin turarenta Ya buɗe hancinansu Ganin yadda suka tsareta da ido ne Yasa tace"lafiya naganku atsaye? Ko dai gulma ta kukeyi ne"? Har suna hada baki wurin fadin"A'a" kashe masu ido tay tare da sakin murmushi tace"ku fadamin gaskiya ba abunda zanyi maku, meyasa da kuka ga nashigo kukayi shiru? Bayan kafin na shigo naji kuna magana cikin raɗa "Wlh ba gulmarki mukeyi ba..." ta6e baki tayi"shikenan tun da kunki fadamin gaskiya, Ku zo mu tafi dining, it's lunchtime. Yan uwanku suna jira..." Amsa mata sukayi da toh, a tare da ita suka fito daga dakin...tunkafin su Isa suka hango su Haris zazzaune kan dining chairs an cika masu table da lafiyyayan abinci Wuri suka samu kowa Ya zauna har sun fara cin abinci unaisah ta tuna da danish, har ta fara gajiya da halin shi, sam bayason zuwa dining cin abinci sai in taje tay masa magana tukunna Yake fitowa, Haka da safe lokacin da zasuyi breakfast sai dai Sajeed ne Ya kai masa adakinsa "Ina ɗan uwanku ne? Na lura baya son zama acikinmu Yaci abinci.." Ummi ce tayi maganar Naufal Yace"Bari naje na kira shi" yai maganar tare da mikewa, ajiyar zuciya unaisah ta sauke dama neman wanda zaije Ya kirasa Takeyi don batajin zata ƙara zuwa dakinsa gudun kada ya kara yi mata abunda yayi jiya Dawowa Naufal Yai"yace ki kai masa adakinsa" Ya fada idonsa akan unaisah, Yamitsa fuska tayi"batool ki kai masa pls" Ummi na murmushi tace"bake Yace kikai masa ba? Ki tashi mana ke Yake son gani" Maƙe kafaɗa tay alamar bazata je ba, Mikewa batool tayi"Bari naje na kai masa.." da sauri ummi tace"koma ki zauna ita zataje, tunda ita Yake son ta kai mashi, Ki kasan ko akwai abunda zai faɗa maki...." turbune fuska tayi ranta ajagule kamar an mata dole ta dauki plate da saving spoon ta zuba mashi fried rice ta haɗa mashi da juice, tasan bai cika son cin abinci dayawa ba... A bakin kofar dakin ta tsaya tare da kai hannu tay knocking, shiru ba'a buɗe ba, daga murya tayi"My man ni ce...." ta fada tana faman haɗe rai Buɗe kofar yayi, lokacin da ta daura idonta kanshi har saida gabanta Ya faɗi ganin babu riga a jikin shi, zanene kirjinsa Ya ɗan sanya ta jin fargaba Miƙa masa plate din tay"ga abincin..." Lumshe idon yai"ki shigo min da shi ciki" make kafaɗa tay"pls ka kar6a kawai ba saina shiga ciki ba,..." Ya fahimci rigime take ji"wani abu zan nuna maki..." Harara ta galla masa"salon in shiga ka kara yi min irin abun jiya ko. " sai da tay maganar Ya fahimci abun da take ma fargaba "Nayi maki alƙawarin bazan ta6a ki ba, tunda bakiso, pls ki shigo ki gani...." yanayin yadda yayi maganr ba karamin sanyaya mata zuciya yayi ba, cikin lallami Ya samu ta shigo Ya mai da kofa... Akan table ta daura masa plate din tare da juice Ganin Ya nufi gefen gadonsa yasa takai ido wurin har sai da taɗan ji gaban ta ya faɗi ganin acessories din dake zube kan mattaress dinsa masu kyau da tsada Da mamaki ta furta"My shield Waya baka wannan"? ta fada tana tunkarar kayan kamar mai jin tsoron su "Wannan mutumin ne Ya kawo min namanta sunanta, Yace min uncle dinsa hateem ne Yace abani su..." Waro idanu waje tayi tana Yarfa hannu Ta furta"wayyo Allah daɗi, my man yanzu duka wannan naka ne?amma natayaka murna.... Agaban gadon ta zauna yatsun hannunta har kerma suke Yi ta dauki Apple laptop din ta buɗe ta tana kallon ta. Ta aje laptop din gefe ɗaya takai hannu ta ɗauki iphone din sak kalar wayarta banbanci su colour ne.. bayan ta ajiyeta ta dauki apple ipad din tana jujuyata faskekiyar gaske... "Amma dai mutumin nan Yana ji da kai, Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi, kamar yadda yake kaunarka nima ina kaunarsa...." abun da bata sani na tun da tafara magana danish Ya nutsu yana kallon duk wani motsin ta, gaba daya ta tafi da imaninsa Yanayin yadda take yaba kayan tana murmushi tare da ɗan zare gray eyes din ta ba karamin kashe mashi jiki tayi ba.....idan ta motsa pink lips dinta kuwa har wani haɗiyar yawu Yake Yi Duk bata lura ba, Headset ta dauka tana dariya tace"amma dai atare zamu dinga amfani da su ko? Kaga ni bani da wannan.." tay maganar tare da kallon shi ta kashe mashi ido ɗaya tare da daura mashi headset din a kansa ta saita mashi a kunnansa. "Wow!...." wani Irin kyau yayi mata har bata san sa'adda ta manna masa kiss a cheeks din sa ba, mutumin fa gaba ɗaya ya fara zaucewa wani irin yanayi yake jin kanshi Cire mashi headset din tayi, ta aje kan mattress din ta janyo eye glss box din tana danna akwatin nan take ya bude jerin hadaddun glass ne na maza ta dauko wani mai walwali launin blue sky ta zura mashi a idanun shi Tabarakallahu ahsanul khaliqin shine abun da ta furta Da tafukan hannyenta biyu ta tallabo fuskarsa ta zuba mashi ido tana kallon Kamar yadda shima yake kallonta ta cikin glass din numfashin su har yana kokarin hadewa dana juna "Sai naga ka ƙara min kyau my man, bari na canza maka wani" da sauri ta cire na fuskarsa ta dauko wani glass din black colour ta sanya mashi "Wow kana kashe ni da kyanka...' ta fada tare da cire mashi glass din ta maida shi cikin ɗan akwatin Ta janyo watchbox ta buɗe shi jerin tsadaddun agogunane ƴan ubansu ta dauko ɗaya ta kamo hannun shi ta soma kiciniyar sanya mashi a wrist dinshi "Ka wani kura min ido kana kallona kamar yau ka fara gani na" tayi maganar da zolaya... Lumshe idonshi yayi ba tare daya furta mata komai ba.... "Wohoho Ina gwanin wani ga nawa..My man wlh kai na musamman ne, komai naka na kece raini ne...Kalli hannunka irin na ƴan gayu wadanda sukaji hutu..." sai faman santin hannunsa take agogon tayi bala'en yi mashi kyau ..... Sam ta manta da abun da ya faru jiya atsakaninsu ta zaƙe sai zuba take yi masa kamar aku "Kin fara period ne❓Kamar daga sama Taji Ya furta wani bugu zuciyarta tayi mata, a ruɗe ta dago tana kallon shi ido cikin ido suke kallon juna❗❓ *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️* *Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions Our website uses cookies to improve your experience. Learn more Accept ! [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: ____________________Boss Bature✍️ Sam ta manta da abun da ya faru jiya atsakanin su ta zaƙe sai zuba take yi masa kamar aku "Kin fara period ne❓Kamar daga sama Taji Ya furta, wani bugu zuciyarta tayi mata, a ruɗe ta dago tana kallon shi ido cikin ido suke kallon juna. har na tsawon mintuna ba tare da sun kyafta ba, gabanta ya soma faɗuwa, gaba ɗaya ta rasa sukuninta, la66anta sai kerma suke. Sexy voice dinsa ce ta sake ratsa kunnanta"tambayarki nakeyi, ko ba ki ji me nace ba"? Yawu ta haɗiya kutt kafin tayi ƙarfin halin furta"meyasa ka tambayeni"? Lumshe idanunshi yayi kafin ya ware su akan fuskarta"naga canji a tare da ke....." ɗan zaro ido tayi da tsantsar mamaki take kallon sa, girgiza mashi kai tay ba tare da ta iya furta wani abu ba "Tell me the truth, have you started menstruating? I want to know. It's something I've been waiting for a long time." rass Taji gabanta Ya ƙara faɗuwa muryarta na rawa ta furta"ni.. Ni ban..ma san kan me kake magana ba..." cikin dabara ta tafara zame jikin ta daga kan gadon, kwatsam Taji Ya damƙi hannunta, Idanu zare ta kalle sa. "Ki bani amsar tambayar da nayi maki" wani irin ƙwarjini yayi mata kamar ba man dinta ba, kamar mai jin tsoronsa ta furta"na fara, tun ranar da mukaje dinner din prime minister, amma ya ɗauke, a washe garin ranar.. " daƙyar ta ƙara maganar, ganin wani kayataccen murmushi gefen fuska daya bayyana akan kyakkyawar fuskarshi, hatta dimple dinsa sai da ya lotsa... "Amma tayaya akai kasan alamomin mace idan tafara period? Sannan meyasa naji kace abu ne da ka daɗe kana jira"! Aruɗe ta jefa masa tambayar saboda abun ya ɗaure mata kai. Matsawa yayi kusa da ita da sauri ta zame hannunta daga ruƙon da yayi mata, taja da baya kamar taga wani mugun abu. "Kamar yadda na faɗa maki, naga sauyi atare dake..." abun da ya sanyata aruɗani yanayi da tagani atattare da shi, ga wani annurin farin ciki daya wanke fuskarsa. "My man, Ya kamata na tafi tun da na kawo maka abincin, su aunty ummi suna jirana" adabarbarce tayi maganar jiki na 6ari ta sauko daga kan gadon daƙyar ta saci kallon shi suka haɗa ido"pls kada ka zauna da yunwa, idan ka kammala cin abincin ka yi wanka, ka sanya sutura a jikin ka, sannan pls ka daina kaɗaita kanka aɗaki ka dinga fitowa wurin su Haris...." tana magana tana ja da baya, tana kaiwa bakin kofar da sauri ta buɗe ta fuce daga gudu. Sai da ta 6ace ma ganin sa, kafin ya kau da idonsa daga kallon ta, kasa cin abincin yayi saboda bashi Yake buƙata ba, akwai wani abu da zuciyarsa take muradi, sai dai yasan ba abune mai sauƙi Ya same shi ba, wata irin kasala ce ta baibaiyeshi cikin sanyin jiki ya kwantar da bayansa kan mattress din, haɗi da lumshe idanunsa. Nannauyar Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke bayan ta sauka downstairs, Hannun ta ɗaya dafe da saifin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face kalamansa da suka tsaya mata arai, yayi matuƙar bata mamaki bata ta6a tsammanin Danish Yana da wayau har haka ba, ko tayaya akai yasan alamomin mace idan ta balaga"!? Ta jefa wa kanta tambayar da bata da amsarta..wucewa dinning tayi zuciyarta cike fal da tunanin sa... _____________________________✍️ Da marece Hajiya saratu tana a gym room na gidan, cikin shiga ta activewear black colour riga da short dai dai gwiwarta, A hankali take running kan threadmill, ta haɗa uban gumi kan fuskarta da jikin ta. Maganganun da suka tattauna da su zahra ne suka fara dawo mata akanta, Abun Ya tsaya mata aranta, tun bayan tafiyarsu take ta tufka da warwara, tana matuƙar son taimaka masu, but how? Tasan owais mai biyayyane agare ta, komai takeso zaiyi mata, sai dai bata jin girman kanta zai bari ta nemi alfarma agurinsa Kuma bata jin zata iya taka kafarta zuwa gidansa. "Me ya kamata nayi"? Ta jefa ma kanta tambayar, Farat ɗaya ta tuna da hajiya laurat! Ita kadai ce zata Iya bata shawarar daya dace. Fitowa tayi daga gym room din ta nufi part din su. Tana shiga daki, ta nufi toilet ta shiga, within 15 mins, ta fito sanye da bathrobe, ta zauna kan mirror chair, phone dinta ta dauka ta danna ma hajiya laura kira Sai da kiran ya kusa katsewa kafin hajiya laura tay picking "Matar yaya barka da marece?ya kike"? Ta faɗa da murmushi akan fuskarta On the other hand Hajiya laurat tace"Amarya kuma uwargida a wurin praving, lafiya lou, fatan kema haka..." jinjina kai ta ɗanyi kamar tana agabanta "naji kinyi shiru? Faɗamin meke damun ki? Don tunda naga kiranki a irin wannan lokacin raina Ya bani wani abu na damunki" "Shawara nakeso Ki bani...." ta faɗa kamar bata son furta maganar, A hankali ta zayyana mata komai dangane da zuwansu zahra... "Bansan Ya zanyi ba! Nayi masu alkawarin zuwa gobe zasu ji kirana, nasan sun kwallafa rai, ni kuma Allah bana son in nemi alfarma awurinsa, nasan owais yana da biyayya zaiyi min abun da nakeso amma ina jin nauyin zubda ma kaina mutunci..." Sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya cika kunnanta, nan take ta haɗe rai"bana son iya shege, Oh dariya ma na baki? tun da bazaki bani shawara ba, zan kashe kiran" Da sauri Hajiya laura tace"Am sorry hajiya, kin bani mamaki ne! Kamar kina jin shakkar tunkararsa, Ki aje wani jin kai gefe ɗaya, Yaron nan ɗan yayanki ne, kuma ɗanki, kina da iko da shi, ba alfarma zaki nema a gurin sa ba! abun da yakamata shine Ki bashi Umarni, kiransa zakiyi awaya kice mashi yazo inda kike Ya same ki, Idan Yazo ki zauna ki faɗa masa komai sannan kice mashi gobe zasu zo ganin yarinyar, baki bukatar wani abu da zai sa girmanki ya zube a idon su...." tiryan tiryan hajiya laura ta tsara mata komai, tunkafin ta karasa maganar, Hajiya saratu ta fara sakin murmushin gefen fuska, saboda shawarar tayi mata 100% shiyasa take ji da hajiya laurat, matar karshe ce wurin Iya bada shawara.. "I can't thank You enough, Hajiya ta, nagode da shawararki, shiyasa yayana Yake ji dake saboda kin Iya tsara kalami ga iya bada shawara...." sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya karade kunnanta Bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"nima naji dadi da kika dauki shawarata, Yanzu faɗa min Ya ake ciki game da hajjaty? Har yanzu baki gano komai ba"? Ta6e baki hajiya saratu tayi"Hmm Matar wayon tsiya gareta kamar dila, yarinyar dana sanya tana yi mata leƙen asiri, har yanzu bata gano komai ba, amma tace min tabbas akwai wani abu da take kullawa adakinta, saboda bata son kowa Ya shiga...." Hajiya laurat tace"munafuka, ay daga ganin ta zatai wayau, kuma wallahi ba wayanta bane akwai wanda ke ɗaurata akan hanya,..."! "Kamar ya bangane me kike nufi ba.."? "Ina nufin ba ita kadai take shirya plan ba, akwai wani dake taimaka mata..." da tsantsar mamaki hajiya saratu take sauraronta, tabbas Ta yarda da kalaman hajiya laurat saboda matar tana da kaifin basira... Sun jima suna tattaunawa akan hajjaty kafin daga bisani su ka yi sallama. ______________________________✍️ Kusan atare motocin su suka kunno kai cikin estate din, Bayan sunyi parking, Pravin Ya fito cikin shiga, ta suit, Ya jingina bayan shi jikin motar, Idanunsa akan motarsu twins dinsa, fitowa sukayi kowannansu Ya dauki wankan suit, sun kwaso gajiyar aiki sai faman lumshe idanu sukeyi Tunkarar shi sukayi da sauri shima Ya nufe su, gaba ɗaya ya hadesu Ya rungumesu, tare da daura hannayensa abayansu. "Yau mun dawo gida atare, ya gajiyar aiki" dagowa sukayi atare suka dube shi "Daddy Ba dadi, wallahi, na gaji, ni fa kasan bana son wahala.." zayn ne yayi maganar, Zaid Yace"Alhamdulillah daddy, kaima ya gajiyar naka aikin"? Murmushi yayi kafin yace"ay ni bana aiki, ina da masu yi min komai, illa Iyaka in karshen wata yayi in kwashi Albashina...." kallon juna sukayi da mamaki akan fuskokin su, Ko ajikinsa Yaci gaba da fadin"tuntuni naso In wayar maku da kai amma kuka ƙi yarda, Kunfi so ku yi ta wahala akan albashin da bai taka kara ya karya ba, har atm dina na baku don kuyi irin rayuwar da kukeso amma kuka ki kar6a saboda baku yarda dani ba ko.." Shiru sukayi suna kallonshi, kafin Zayn yai kafin halin cewa"daddy ta yaya zamu kar6i kudinka? Bayan ba halal dinka bane!! Baka aiki kuma kana kwasar albashi, hakan na nufin haramun kake ci, daddy kaji tsoron Allah, ka riga da kasan hukuncin wanda Ya gina kansa haram..." bai ƙare maganar ba, Pravin yayi saurin dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu, da kakkausar murya ya furta"Enough! Don't you dare repeat what you just said to me!! Gidan ubanwa nake cin haram? duk wani kuɗi da nake da su, Hakkina ne ina da goyan bayan waɗanda suka ɗaura ni akan muƙamin da nake da shi. ..." Yana faɗin hakan rai a6ace Ya nufi cikin gidan, da sauri zaid yabi bayanshi tare da shan gaban shi. "Daddy ka yi hakuri, naga ranka ya 6aci, Dan Allah ka yi hakuri da abun da zayn yace maka! ka yafe masa kada ka ruke sa a zuciyarka..." Murmushin gefen fuska pravin yayi"kada ka damu my son, komai Ya wuce" Ajiyar zuciya zaid Ya sauke, Tare da ruko hannun daddyn nasu suka shiga parlour. Zayn dake kallon su har sai da suka 6ace ma ganin shi, kafin ya jingina bayan shi jikin motarsu, kalaman zahra ya fara tariyowa, a lokacin da ta kira shi Yana a office, ya gama watsewarsa tare da abokiyar aikinsa yana akan network shiyasa Ya zazzaga mata masifa son ranshi aranshi ya ayyana ko sun samu shiga estate din? Ta6e la66ansa Yayi irin bai damu din nan ba, Ya wuce Ya nufi cikin gidan "CHIEF OWAIS💪💋* Yana a cikin Katafaren Office dinsa dake a isod Headquater, office ɗin Ya haɗu, an ƙawata shi da high-end supplies komai na cikinsa launin blue sky ne kalar da yafi so, office din Yana da mugun tsaro gaba daya na'urori ne ke sarrafa komai na cikin sa.." Daddaɗan ƙamshin turarensa Ya gauraya da ni'imtacciyar iskar dake ratsa saƙo da lungu na office din, a yayin da yake azaune kan wata tamfatsetsiyar Excutive chair Ƴar ubansu, Ya ɗaura kafarsa ɗaya bisa ɗaya, daga gaban shi luxury table ne mai ɗauke da High-end computer da sauran kayan amfaninsa dake a baje kan table din A hankali Ya buɗe idanunsa dake a lumshe, Ya cigaba da operating computer din gabansa, Adjusting webcam dinsa yayi, kafin ya danna video call Ya dan dakata Yana jira a amsa mashi. a hankali fuskar commender ta bayyana ta cikin screen din Murmushi suka sakar ma junansa, Cikin harshen turan ci suka fara magana "Commander, good to see you, sir," ya faɗa tare da sarah mashi da hannu "Chief, good to see you too," shima ya sarah mashi. "What can I do for you?" Numfasawa chief yai kafin yace"I'm calling to extend an invitation to a high-level meeting in Nigeria, dangane da yaran da kuka damƙa mana case din su" Ya ƙare maganar, Cike da sa ran zai amsa mashi Jinjina kai commender din Yayi na ɗan wani lokacin Kafin Ya furta" okey, What's the current situation?...bayani ya fara kora masa dangane da halin da ake ciki na binciken prisoners. Tun da ya fara commender Yake ɗan jinjina kanshi alamar gamsuwa, bayan ya ƙare maganar yace"yanzu wani mataki zaku fara ɗauka"? Chief yace"That's what we'll discuss during the meeting" "Tunani mai kyau, zanyi magana da na sama dani, idan har na samu goyan bayan su, zamu halaccin meeting din, yaushe ne kuma a ina za'ayi"? "Upper week, in Abuja. I'll send over the details. Thank you, Commander..." Ya fada tare da sara ma shi da hannu.. Shima commender din Ya sara mashi bayan sunyi sallama Ya kwantar da kansa jikin kujerar "DDG Is coming" Muryar na'ura ce ta ratsa kunnansa, A hankali Yakai idonsa ga duban Glass door ta office dinsa wadda ke kokarin zuge kanta Big guy ne Ya shigo sanye Cikin kakinsa, Cikin girmamawa Ya sara mashi. "Sannu da aiki Yalla6ai, Na ji shiru baka fito ba, ko baka lura da time ba ne"? Kallon agogon hannunsa yayi ƙarfe biyar na marece, har time din ta shin sa yayi bai lura ba. "Have a seat" Zama big guy yai kan kujerar dake fuskantar chief kamar yadda ya umarce shi "Munyi waya da commender..." a ƙagare big guy yace"ina fata Ya amsa buƙatarmu"! Calmly ya zayyana masa tattaunawar da su kai, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskar shi"Allah Yasa mu ji alkhairi" Ya amsa mashi da ameen Shiru sukayi na wani lokaci kowa da abunda Yake saƙawa aranshi "Ya kamata ka tashi muje in kaika gida, burina ka huta..." murmushi chief yayi"nagode da kulawarka agare ni, Ina boss ko har ya tashi aiki"? "Tun wuraren huɗu ya koma gida, kasan mutun mai Iyali, ba kamar mu da muke tazurai ba..." da zolaya yayi maganar, harara chief Ya dan watsa masa batare daya furta wata kalma ba Ya miƙe Ya nufi kofar fita, da sauri big guy yabi bayansa a tare suka fito daga office din. Tsayawa fasalta haduwar isod headquarter bata baki ne, abun sai wanda Ya gani, lifter suka hau ta sauke su down, ta ko'ina ka kalla Jami'an isod ne sanye cikin kakinsu tun daga senior agents dinsu har izuwa jenior agent, duk inda suka bi cikin girmamawa jami'an suke sara masu, Har suka fito daga headquater din, kaitsaye suka nufi katafaren parking space din su, dankara dankaran motocine makil tare da bikes dinsu killace a harabar. Da sauri wani agent Ya bude masu backseat na motar da zasu shiga, bayan sun shiga kowan nan su Ya zauna, agent din dake jigilar daukar su Ya yi wa motar key cikin ƙwarewa Ya fara driving dinsu zuwa gida..... Dai dai lokacin da motar su ta kunno kai cikin gidan, Wayarsa ta fara ringing, lokacin da ya duba sunan mai kiransa yayi mamakin ganin aunt saratu, Cos Ya manta when last Yar tahalikar nan ta kira da sunan tayi magana da shi. Picking call din yayi tare da kara phone din a kunne, Cikin ladabi Ya yi mata sallah tare da gaishe da ita Ko sallamar shi bata amsa ba ta furta"Owais, bayan sallar magbrib, Ka same ni a pool yard, Ina son yin magana dakai"! Cike da bada umarni ta furta, bata jira amsar shi ba, Ta katse kiran. Kurawa screen din wayar ido yayi ba tare da ƙyaftawa ba..." "Yalla6ai, Mun ƙaraso"! Big guy ne Ya fargar da shi, sam bai lura sun karaso ba, Fitowa yayi da sauri Ya nufi Cikin main falo din gidan Yana shiga bedroom dinsa, Ya rage kayan jikin shi, Ya shiga toilet domin Yin wanka, *HAJJATY* Safa da marwa Take Yi atsakar dakinta, tun safe take sa ran zuwan pravin shuru bai leko ba, Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, saboda abun da ya faru jiya yayi matuƙar daga mata hankali. Yanke shawarar fita neman shi tayi, da sauri ta dauko mayafi ta yafa akanta, Tana kokarin fita suka ci karo da juna har saida ta bangaji kirjin shi, da sauri taja da baya tare da dafe gefen kanta da hannu daya "I'm sorry wifey, Ina zaki je ne"? yayi maganar yayin da yake nufar cikin dakin idanunsa akan fuskarsa From head to toe Ya kalle ta, farat ɗaya ya gane akwai wani abu dake damunta, da alama ko wanka batayi ba. "Baki da lafiya ne" ya yi maganar tare da ruƙo hannunta suka zauna gefen gadon ta "Baki ji ina magana ba? Fashewa tayi da kuka tare da kifa kanta akan kafadarshi Hankalin shi yayi matuƙar tashi jin kukan hajjaty, yana daga cikin abunda Ya tsana arayuwarshi..... Cikin shesshekar kuka tace"pravin ina cikin tashin hankali, Saboda akwai mai bibiyar rayuwata, daren jiya bana acikin kwanciyar hankalina, a tsorace na kwana, ko baccin kirki banyi ba, ina ta jira ka dawo shiru baka zo ba..." Tuni yanayin fuskarshi Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, "Fada min meya faru dake a daren jiya? Wani ya shigo ne"?....ɗagowa tayi da kanta hawaye na sintiri kan kuncinta ta kwashe komai ta sanar da shi... Tafukan hannayensa ya daura kan fuskarta,A hankali Ya fara share mata hawayen ta "Ki yi hakuri, in sha Allah koma wanene ke naman ki da sharri kan shi zai koma, Allah Yana atare dake wani bai isa Ya cutar min dake ba! ...." bai kare maganar ba, tace"bansan ya zanyi ba, wallahi ina jin tsoron ranar da asirinmu zai tonu, pravin bana son abunda zaija mu rasa kimarmu da darajarmu a idon mutanan gidan nan, saboda ina ji araina akwai wanda ke son ya tona mana asiri shiyasa aka fara bibiyana.." ta faɗa tana jan numfashi kafin taci gaba da cewa"saboda fargaban abunda Ya faru daren jiya, ko abinci banci ba tun safe har yau kamar mai azumi, wanka ma nakasa yin shi...." Ta ƙare maganar, tana kallon cikin idanunshi "Tuntuni saida naso In siya maki gida daban inda zakiyi rayuwarki cikin kwanciyar hankali, amma sai kika nuna bakison rabuwa da su....abunda nake jiye mana kenan... "Duk laifinka ne, Abunda kayi min awurin dinner din hateem shine Yaja har wasu suka fara zarginmu, kuma ni gaskiya bazan bar gidan nan ba, kawai ka nema min mafita ..." Jinjina kanshi yayi tare da ruko hannayenta acikin nashi"zan tambaye ki wani abu" daga mashi kai tai alamar toh "Idan kika kama 6era adakin ki Yana yi maki 6arna, kuma kinsan zai iya haifar maki da gagarumar matsala wani hukunci zaki masa"? "Meyasa kayi min wannan tambayar"? "Kedai ki bani amsa"! Shiru tayi jim kafin tace"hannayen da yake yin amfani da su wurin yin 6arnar su zan naƙasa, sannan in murje bakin shi ta yadda bazai iya daukar komai da shi ba...." murmushi pravin ya sakar mata"kin kawo shawara mai kyau.." arude tace"bangane me kake nufi ba" Bai bata amsar tambayarta ba, sai cewa yai muje bathroom In taimaka maki kiyi wankan da kika kasa" Ajiyar zuciya ta sauke tare da mikewa suka nufi toilet atare almost 18 mins Ya fito dauke da ita a hannunshi, dukansu sun daura towel a waist dinsu, Taimaka mata yayi ta sanya kaya, shima ya maida nashi "Tashi ki je kitchen ki shirya mana abinci mu ci atare" amsa mashi tayi da toh, Bayan fitarta da yan mintuna ta dawo hannunta ruke da try na kayan abinci, ta ajiye masu kan rug, saukowa yayi daga kan gadon suka zauna atare suna ci..... ___________________________✍️ Bayan kammala sallar Magbrib, Owais Ya nufo pool yard din gidan baba obie, Jikin shi sanye da farar jallabiya, tunkafin Ya ƙarasa Ya hango Hajiya saratu zaune kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Hankalin ta na akan wayar hannunta da take dannawa Cikin kunnanta ta tsinkayi muryarsa"Assalamau alaikum" ba tare da ta kalle shi ba tace"wa'alaikum salam," Zukunnawa yayi daga gaban kujerar da take Cikin girmamawa Ya gaishe da ita, Har cikin ranta taji daɗin hakan da yayi mata sai dai bata nuna a fuska ba, wai don kada ya raina ta "Lafiyalou My son, ina fata Ka wuni lafiya? Ya aiki"? "Alhamdulillah.." "Bismilla ka zauna" ta fada tare da nuna masa chair din dake facing dinta, miƙewa yayi bayan ya zauna ya ɗago da ido ya kalle ta, babu alamun zata kalle shi "Mommy, kince kina son ganin na, zamu yi magana" sai da ta mula ta sha iska kafin tace"eh, magana ce mai mahimmanci, Ina fata zaka bani aron hankalin ka.." Amsa mata yayi da toh, tsawon mintuna biyar ta shanya shi, kafin ta fara kora mashi jawabi dangane da zuwan su Zahra, da alfarmar da suka nema a wurin ta...." tun da ta fara maganar, Yake dubanta da alamun rudani akan fuskarshi. "Ita zahran da ta kawo min maganar, tana ɗaya daga cikin interior designers din da suka yi mana aiki aranar dinner din hateem a hall dinne taga yarinyar, sunan yarinyar ta wurinsu Angel amma asalin sunan ta Unaisah, har hotonta sun nuna min, sunyi kama sosai da yarinyar wurin ka," Cike da son jin ƙarin bayani yace"ko ta fada maki sunan Baban Yarinyar da sunan mahaifiyar ta"? Shiru tayi tana kokarin tariyo sunan su ....can tace"na tuna, sunan mahaifin yarinyar zaheer tajudeen, mommynta kuma sunanta benazir" ." Bari na kira Daddyn nata, naji idan Ya san su" da mamaki hajiya saratu tace"oh dama mahaifin yarinyar yana atare da ku"? "Eh," ya bata amsa atakaice, har cikin ranta taji dadin jin hakan.... Phone dinsa Ya curo daga aljihu Ya danna ma Taj Kira, Tana fara ringing Ya saka wayar a handsfree don taji abunda zasu ce "Yalla6ai barka da marece, Na shigo gidan na taras baka nan.." "Ina agidan grandpa, zuwa anjima zan shigo" "Allah ya dawo kai lafiya" Am so nake na tambaye ka, Wa cece Aneelerh! Kamar na ta6a jin sunan abakin ka" "Yalla6ai ka kamanta ne halan, matar aminina ce uzair, kamar mahaifiya take awurin Angel ɗina..." murmushi hajiya saratu tasaki jin abun yazo mata cikin sauki "Zamuyi magana idan na shigo gidan" amsa mashi yayi da toh, bayan yayi rejecting call din Ya ɗago Ya kalli hajiya saratu dake kallon shi "Yarinyarsa ce..." "Alhamdulillah, Yanzu gobe da yaushe zasu zo ganin ta? ta tambaya tana kallon shi "Duk lokacin da yayi miki, su zo kawai" murmushin gefen fuska tasaki, Taji dadin yadda yake bata girma "Nagode my son, bari nasa akawo mana abun sha" da sauri yace"ina so zan shiga wurin baba" "Okey, mu tafi tare" mikewa sukayi atare suka jera suna tafiya, abun ba karamin dadi yayi mashi ba, tsawon lokaci basa jituwa da juna, sai gashi silar neman unaisah da yan uwanta sukazo yi Allah Ya haɗa kan su, Har fira ta fara jan shi da ita, a haka har suka karasa dakin baba obie... Idan muka koma 6angarensu Hajiya Layla dake a asibiti, wuraren ƙarfe 8 na dare, Hospital staff suka fara sallamar mutanan da ke zuwa dubiya, saboda a dokar asibitin karfe takwas na safe visitors suke zuwa da zarar takwas Na marece Yayi kowa zai tafi za'abar majinyaci karkashin kulawar nurses Hajiya layla tace ita fa ba inda zataje, dole ta kwana don ta kula da yar ta, dr shureim ma ya goyi bayanta, tunawa da barazanar kashe benazir da ake Yi, Idan suka tafi ba lallai nurses su san lokacin da za'a farmake ta ba, duk da akwai cctv camera a kowani daki na marasa lafiya, bayan hakan asibitin Yana da tsaro sosai, kawai dai bai yarda subar benazir ta kwana ba tare da wani nata akusa ba Hospital staff din basu Yi masu gardama ba, ganin sanannu ne a idon jama'a, kuma da ma ire irensu sunayi masu alfarma, kodan saboda matsayin dake gare su, musamman hajiya Saratu da takasance former firstlady ta kasar, tun da ta sanya baki a maganar suka amince hajiya layla ta kwana tare da ita. Gaba dayansu sun hallara a harabar ajiye motocin asibitin, Sun fito domin tafiya gidajen su, Mami da abie suna atsaye, Ga Aneelerh da Zahra da mahboob, Aneeleeh taso abarta tayi jinyar benazir, "Mu zamu wuce, Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah Ya tashi kafadunta, in sha Allah zamu cigaba da tayata addu"a" abie ne yai maganar tare da miƙa ma Alhaji ubaid hannu suka yi musabaha "Mungode sosai, Allah yakaiku gida lafiya," Mami tace"dan Allah duk halin da ake ciki game da rashin lafiyarta ayi kokarin sanar damu" Hajiya sarah tace"in sha Allah zamuyi kokarin hakan" bayan abie da mami sun shiga mota, Hajiya layla ta ruko Hannun Aneelerh acikin nata fuskarta dauke da matsananciyar damu tace "Dan Allah kiyi kokari Aneelerh, Zuwa gobe, Ku tuntu6i iyayen yarinyar da kikace tana kama da yarta, ku rokar mana alfarma awurinsu, su ara mana ita, idan ma suna bukatar mu biyasu kudi su faɗi nawa suke so, ko nawa ne zamu biya, wallahi bana so na rasa benazir, ina matuƙar jin tausayinta...." la66anta na kerma ta ƙare maganar, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta Wani irin tausayinta ne Ya kama Aneelerh, bata san sa'adda itama ta fara share kwallar ba, Yau dai sun sha kuka bayin Allah "Mommy in sha Allah zanyi kokarin ganin sun bamu yarinyar, Indai akan benazir ne wallahi sai inda karfi na ya ƙare...." "Pls kukan Ya isa haka, Ku yi hakuri, mu cigaba dayi mata addu'a Allah Ya bata lafiya..." acewar hajiya sarah Dakyar sukayi sallah da juna, bayan sun aneelerh sun shiga motarsu, A jere motocin suka fuce daga asibitin, "Zan tafi ba dan naso ba, amma In sha Allah, gobe da wuri zan shigo asibitin" Fuskar hajiya layla a yamutse tace"Sai Allah Ya kaimu.." "Duk halin da ake ciki, pls ki sanar dani" ta amsa mata da toh, "Allah Ya bata lafiya" ta amsa mata da ameen, dr shureim ne ya buɗe mata murfin motar, Ta shiga daga ciki, kafin Ya datse mata, akan idonsu motar hajiya sarah ta fuce daga asibitin Ya rage saura su uku dake atsaye suna kallon juna, "Shurem muje ko"? Alhaji ubaid ne yayi mashi maganar, Sam baya son tafiya, Gani Yake kamar in ya tafi wani abu zai faru da benazir, "Toh daddy" Yayi maganar, Tare da ruko hannun hajiya layla "Mommy, nasan ko ban fada maki ba, zaki kula da ita, amma inaso ki sanya ido sosai, dole sai kin hana idonki bacci in ba haka ba..." bai kare maganar Ba Alhaji ubaid Yace"meyasa kace haka"? "Daddy akwai wani abu da nake zargi akan benazir, zan sanar daku amma ba yanzu ba, saboda bana son ɗaga maku hankali, kawai abinda nakeso mommy kada kiyi gangancin kula da ita, in ba haka ba za'a iya samun matsala, duk da munsan Allah ke tsare bawansa amma da bukatar muma mu kula" Hankali atashe Hajiya Layla ke kallon shi, Muryarta na rawa tace"Shureim dan Allah ka fada min meke shirin faruwa da Benazir dina, ni dama najima ina zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta, so ake akashe min ita, ko faduwar da tayi a toilet sai da raina ya bani wani mugun abunne Ya faru da ita, in ba haka ba taya za'ace ta fita hayyacin ta? Bata gane kowa dake akanta?..." maganganunsu sunso rikita Alhaji ubaid Ya rasa gane inda zancen su Ya dosa "Dan Allah kuyi min bayani meke faru ne"? Da ido Hajiya layla tayi ma dr shureim Alamar yayi shiru saboda tana zargin ba hakanan Aka kyale Alhaji ubaid ba, kada su saki baki su sanar da shi zargin da suke Yi Yana iya zuwa ya sanar ma Alhaji musa, tunda Ya zama kamar ubansa komai zaiyi sai ya nemi shawarar shi Jinjina kai dr shureim yayi alamar Ya fahimce ta, "Daddy, Muje gida zan sanar da kai komai" Ya faɗa tare da ruko hannun shi, Hajiya layla tayi masu Allah Ya kiyaye hanya, tana atsaye tana kallon motarsu har suka fuce daga hospital din, Da sauri ta koma ɗakin benazir, tana shiga, ta iske Nurse agaban gadon ga benazir zaune jikin ta sai kerma Yake tana ta sambatu "Daddy, mommy, ku kira min taj, Ya kawo min babayna dana bar mashi, dan Allah ku bani ƴata, kada na mutu ban ganta ba...." lallashinta hajiya layla ta cigaba da yi sam bata fahimtar komai, sunan ƴarta da mijinta kadai take ambato, Har abinci nurse ta kawo mata, kwata kwata ta kasa cin shi, duk yadda mami takaiga lallashinta abun Ya faskara, Addu'oi ta koma tana tofa mata, har dare Ya tsala mami tana zaune kan kujera tana kallon ta, Har dr ya shigo ya kara duba jikinta, Ya bata magungunanta dakyar suka samu ta sha, daga bisani bacci Yayi awon gaba da ita, lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar ishai'a, mami ta shiga toilet cike da zullumin kada wani ya shigo dakin Ya cutar da benazir, saboda ta razana da jin kalaman dr shureim, jin motsin mutun adakin yasa tayi wuff ta bangaje kofar toilet din ta fito tana haki, Ko alwalar bata karasa ba.. *Daga alkalamin Boss Bature mu haɗu next page✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Y Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 29 Complete by Novels Elite Admin August 07, 2024 Sponsored Link Novels Elite English ✍️ Dafe kirji tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ganin likitan dake kula da benazir ne "Are you okey"? Daga mashi kai tayi alamar eh, Ganin tana mashi kallon kamar bata yarda da shi bane yasa shi cewa"zan tashi daga aikine, Na shigo na kara duba lafiyarta ne, kafin na tafi...." murmushin Yaƙe ta sakar mashi"mungode dr, Allah Ya saka da alkhairi, agaida gida" ya amsa mata da toh, harya fuce daga dakin Yana mai mamakin Hajiya layla, abun ya daure masa kai yadda ta fito daga toilet a haukace anya kuwa tana da lafiya"? Komawa cikin toilet din tayi, sam babu nutsuwa atare da ita, shaf shaf ta ƙarasa alwalar ta fito da sauri ta nufi closet din dakin ta dauko darduma ta shimfiɗa tare da kabbara sallah. Da zarar taji motsi adakin sai gabanta Ya faɗi, bayan ta ida sallar, ta zauna tayi addu'o'i ta kai kukanta wurin Allah, Kafin ta mike ta koma kan chair din dake fuskantar gadon benazir ta zauna tana kallon ta, patient gown din dake ajikinta launin light blue tayi mata kyau, A hankali ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta, tuni taji ƙwalla sun cika idanunta. Idan muka koma bangaren su Aneelerh, bayan komawarsu gida, A falo suka zauna kowa Yana jimamin halin da Benazir take a ciki, Ummi ta fito daga daki hannunta dauke da Baby junaid bawan Allah tunda Mahboob ya dauko shi daga makaranta, Ya dinga kuka Yana ambaton mommynsa, dakyar mami ta samu ta shawo kanshi Har yaci abinci tayi mashi wanka, har bacci Yayi, sauke shi ummi tayi da gudu Ya nufi Aneelerh ya faɗa jikinta Yana kuka, Ta rungune shi tana lallashin shi, dakyar ta shawo kanshi har suka sasanta junansu... Lokacin da hajiya sara ta shiga falon gidan, kasa yin sallama tayi saboda fargaban hukuncin da Alhaji musa zaiyi mata, Cikin sanɗa ta nufi bedroom din su ko sallama batayi ba, ta shiga ciki, A kwance ta same shi kan shimfiɗeɗan gadon shi, Ya tada kanshi bisa pillow, zeenatu na arungume da shi, ta daura kanta bisa kirjinsa, daga ita har shi kayan bacci ne a jikin su Tayi tsammani bacci suke Yi, ajiyar zuciya ta sauke, ta lalla6e ta nufi cikin dakin, ta daura key dinta akan mirror, ta nufi toilet ta shiga, alwala tayo tana kokarin fitowa daga toilet din suka ci karo da shi, wani irin bugu kirjin ta yayi, tuni gumi ya lullu6e fuskarta, la66anta na kerma tace"yanzu na shigo, nayi tunanin bacci kake Yi, fatan na same ka lafiya..." tsare ta da idanunsa yayi masu matukar gigitata, gaba daya yayi mata kwarjini "Ki faɗa min wani hukunci Ya dace Inyi maki"! Rass taji gabanta Ya fadi, marairaice mashi fuska tayi"am sorry bazan ƙara ba, wallahi bansan na ɗaga maka murya ba, dan Allah Ka yafe min.." Fuskarshi babu annuri Ya furta"cewa nayi ki fada min wani hukun ci Ya dace nayi maki"? Shiru tayi batare da ta furta kalma ba, duk tasha jinin jikinta....fargabanta kada Yace zai turata U.s Saboda bata son duk wani abu da zai rabata da shi, shiyasa take yi mashi biyayya sau da kafa, duk wani abu da tasan zai bata masa rai, tana kokarin ganin tayi takatsantsan da shi "Daddy kayi mata hakuri tun da ta gane kuskuranta," muryar zeenatu ce ta ratsa kunnuwansu, "Kinci sa'a, da yau sai kin yaba ma aya zakin ta" nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata wuce ya sake shan gabanta, a rude ta kalle shi "Ya jikin benazir din? "Jikin nata yayi tsauri, kwata kwata bata a hayyacin ta, baiwar Allah tana jin jiki" "Allah Ya bata lafiya, in sha Allah gobe da safe zanje dubata" har cikin ranta taji dadin jin zaije dubata, "Allah ya kaimu lafiya.." "Kije kiyi sallar, kafin kin kammala zan kira tani ta shirya maki dinner dinki, nasan kina jin yunwa, kin wuni baki ciki komai ba" ya fada tare dakai hannu Ya shafa flat tommy dinta, aruɗe hajiya sarah take kallon shi, kamar ba Alhaji musa ba,yadda kasan badaga bakinshi kalaman suke fitowa ba, Kamar sakarya haka ta kura mashi ido tana kallon shi, murmushin gefen fuska ya sakar mata, gaba daya ya nemi zautar da ita, dakyar ta samu nutsuwar sanya hijabi ta kabbara sallah,......" Sallamar su Alhanji ubaid ce ta karaɗe kunnuwansu, da gudu Zeenatu ta diro daga kan gado ta fuce kamar walkiya, tunkafin ta karaso dr shuriem Ya hangota, murmushi ya saki tare da bude mata hannayenshi ta faɗa kan kirjinshi tana dariya "Yaya shureim sannu da dawowa, naji dadin ganinka, dama ina ta zullumin kada kaki dawowa gida.." bata ƙare maganarba, Alhani ubaid Yayi mata gyaran murya, waro idanu tayi don gaba daya ta manta da shi awurin cike da jin kunyarshi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta Dariya Alhani ubaid Yayi"zeenatu, meya hanaki yin bacci..." muryarta da yar shagwa6a tace"yaya shureim nake jira ya dawo..." kafin ta kare maganar Alhaji musa Ya shigo falon Ya nufe su cikin takun nan nasa na isa "Sannunku da dawowa, ya mai jikin"? Alhaji ubaid Yace"da sauki, kafin mu dawo ta farka sai dai bata ahayyacin ta...." cikin nuna tausayawa ya furta"Allah Ya bata lafiya, gobe zanje asibitin, Ina Hajiya laylan ne"? Dr.shureim yace acan zata kwana" shiru yayi bai ce komai ba. wani abu daya daurewa dr shureim kai tun da ya dawo gidan zeenatu bata tambaye shi Ya jikin benazir ba, kwata kwata kamar irin ta manta da zancen ta, bayan tafi kowa nuna damuwa akanta, har magana yayi mata banji kin tambayin auntynki benazir ba, sai tayi shiru bata tanka mashi ba kamar bataji me yace ba, kusan sau uku yanayi mata maganar tana share shi, amma idan yayi mata wata maganar daban saita amsa mashi. Bayan shigar shi daki, kasa runtsawa yayi, har saida Ya kira mommynsu a waya ya tambayeta awani hali suke ciki? Ta tabbatar masa da komai lafiya kafin ya samu nutsuwar Yin bacci. *EX-PRISONERS* Around ƙarfe 10 na dare, ummi ta sauko down, har ta shirya cikin kayan baccin ta, Tunkafin Ta karasa Ta hango wasu daga cikin su kwance ka lallausar carpet din falon suna bacci, tun da zu tabarsu suna ta shan fira atsakaninsu tayi tunanin in sun gama zasuje su kwanta sai kuma ta taras da su kwance suna sharar bacci, wasu asaman sofas wasu akan carpet Murmushi tasaki haɗi da girgiza kanta, tama rasa tayaya zata fara tada su,duk sun sanya kayan baccin su..., ɗaya bayan ɗaya ta fara farkar da su "Batool My baby, wake up, Parveen! Hannah ku tashi dan Allah....! Ni bansan ya akai kuka bari bacci Ya dauke ku a falo ba, salon kawai ku wahalar da auntyn naku..." dakyar ta samu batool ta miƙe tana ƴan soshe soshe "Wuce kije daki" ta amsa mata da toh, "Praveen ku tashi..." cikin magagin bacci ta buɗe ido bakinta cunkushe da apple din da bata karasa cinyewa ba, bacci yayi awon gaba da ita, miƙa tayi tare da yin hamma ta nufi dakin su, ganin tana tangal tangal kamar zata fadi ne Yasa ummi yin saurin cafko hannunta, a lokacin ta samu hannah ta mike, ta ruko hannayensu a cikin nata har ɗaki takaisu, sai da taga sun kwanta kan gadonsu kafin ta dawo falon Taci gaba da tada su"sajeed! Naufal ku tashi dan Allah, Mubeen Haris! Javed! Wai baku ji ina magana ne"? da wata irin kasalar bacci kowan nan su Ya mike har kwara mazan da kwarin su, suka nufi bedrooms dinsu Wurinsu jemimah ta nufa, sun cunkushe kan sofa mai mazaunin mutun biyun yadda kasan kifin gwangwani, hannu biyu tasa ta dauki jemimah, ta daurata a kafadarta, kafin ta sa ɗayan hannun ta ɗago Azeeza, ta daurata a dayar kafadar ta, ahaka ta nufi dakin su, ta kwantar da su kan gadon su, sai da ta kashe masu switch din dakin kafin ta fito ta koma falon, "Sarah! Wake up, rubina! Hibba! Pls ku tashi! Mana, Yasmin"! Har ta fara gajiya da tada da su, mikewa sukayi kamar babu laka ajikinsu, raka su tayi bayan sun kwanta ta dawo tana kallon waɗanda suka rage, Eve ce kwance kan rug tare da Deeja..Sai unaisah dake a naɗe kan sofa, "Deejatun haris, Ta shi muje ki kwanta..." cikin magagin bacci ta fara sambatu tana fadin"wai meye haka ne? Ni ku kyaleni wallahi kada wanda Ya ƙara min magana..." Hannu ummi takai da niyar ta dago da ita, aikuwa ta daddage takai mata naushi a gefen bakin ta, tsabar zafin da ummi taji ne Yasa tayi saurin dafe bakin, ta lalla6a ta koma kan sofa ta zauna tana faman yarfa hannunta, ranta ya 6aci taji haushin naushin da khadeeja tayi mata, hakan yasa ta yanke shawarar barin ta a falon ta kwana, gudin kada ta lahantata garin tada ta daga bacci Mikewa tayi ta nufi hawwa ta dan bubbuga kafafunta, cikin sa'a ta farka "Ki je daki ki kwanta" amsa wa tayi da toh, bayan tafiyar hawwa ummi ta nufi unaisah Bata tada ta daga baccin ba, daukarta tayi akan kafadarta, ta nufi bedroom dinsu da ita, tana shiga ta kwantar da ita akan gadonsu, ta kashe mata switch dakin, Bayan ta fito falon, Ko kallon inda deeja take akwance batayi ba, don ranta Ya 6aci, kaitsaye ta nufi hanyar komawa dakinta, har ta kusa shiga taci karo da Batool kwance kan matattakar benan sai faman sharar baccinta take Yi da alama zamewa tayi awurin ta faɗi cikin magagin watakil tayi azan gadone shiyasa taci gaba da baccin ta Ɗaukarta ummi tayi da hannu biyu ta cucci6eta, ta haura da ita upstairs, bayan ta shiga dakin, ta kwantar da ita kan gadon su kafin itama ta haye ta kwanta tare da rungumota a jikin ta.... *❤‍🩹UNAISAH ANGEL💔* Around ƙarfe 1:30 na dare, ta farka da matsanancin ciwon mara mai azababben zafi, hannayenta dake kerma ta ɗaura su akan cikinta, sai faman murzarshi take yi, sai faman yin birgima take akan gadon, daƙyar ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur da su, cikin mawuyacin hali ta kai hannu jikin bedside lamp ta kunna fitilar haske ya gaure zagayen gadon da take, wani irin gumi ke tsastsafowa ta jikin ta, hatta pajama din dake a jikin ta sun manne ma fatarta, Yunƙurawa tayi daƙyar ta sauko daga kan gado ta shiga toilet, ta haye kan toilet seat, tayi fitsari anan taga jinin da ya dawo mata jawur yana gangarowa ta tsakantsakin cinyoyin ta, runtse idanunta tayi da karfi duk irin ɗaukin da take na son ya dawo mata sai da taji abun ya fita ranta saboda raɗaɗin da mararta ke yi mata Bayan tayi tsarki ta fito, babu wandon ajikin ta, can ta baro shi a toilet....a gaban drawer chest na wardrobe din kayan su ta zukuna ta buɗe tare da sura hannu ta ɗauko pad daya, ta haɗo da pant, akan mattress ta ɗaura su tana faman sakin nishi kamar mai naƙuda, "Can I give you a hand ."! kamar daga sama ta tsinkayi muryar mutun a kunnanta, sai tayi tsammanin gizo muryar shi keyi mata...kwatsam hasken ɗakin ya dauke ɗuff duhu ya gauraye ko'ina, a firgice take kallon duhun daya mamaye idanunta, gashi bata ƙarasa sanya pad din ba, cikin duhu tafara laluban gefen gadon don ta kunna fitar, ba zato ba tsammani taji saukar hannun mutun akan mararta, a matuƙar firgice ta zare gray eyes dinta, muryarta na kerma ta furta"de...deeja? deeja? Shiru ba'a amsa mata ba...tasan su biyu suke kwana dakin shiyasa ta ambaci sunanta, tunani tayi kadai batool ce "Batool ke ce? Shiru ba amsa,"dan Allah wanene? A tsananin tsorace tayi maganar. "Daddy...." bata kai ga ƙarasa maganar ba, Taji gaba ɗaya anjayota, ta faɗa kan kirjin shi, farat ɗaya ta gane koma wanene namiji ne kuma kakkarfa, Kware baki tayi zata fasa ihu yayi saurin haɗe bakinsu guri guda, jikinta ya fara kerma tafara kiciniyar kwace kanta, kamar yar dambe ta dinga ɗuma masa dundun da hannayenta waɗanda ke abayanshi, tayi kuka tayi haukan ko gizau baiyi ba har gartsa mashi cizo tayi wuri uku a kirjinshi amma babu alamun yaji zafinda zai sake ta Fashewa tayi da matsanancin kuka"wayyo Allah daddy na, Aunty ummi, my man kana ina? Kana gani za'a cutar dani, na shigo uku wayyo Allah..." da iya karfinta na karshe ta bangaje shi gaba ɗaya ta kife kan floor, bata iya ganin komai da rarrafe tana laluban hanyar fita daga ɗakin, ƙafafunta taji ya ruƙo da hannayensa biyu ya ɗago bai direta a ko'ina ba sai akan gadon ta Ta yunkura zata gudu Ya hambareta da gwiwar hannunsa, kanta ya daki pillow, kafin tayi yunkuri sake mikewa, mutumin ya toshe mata baki da tafin hannunsa gaba daya ya sakar mata karfi, ta yadda ko yatsan hannunta bazata iya motsawa ba, numfashinta dakyar yake fita, wani iri danshi danshi ta fara ji agabanta kamar ana zuƙe jinin dake fita ta farjin ta, runtse idanunta tay zufa ta fara tsastsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, ga wani azababen zafi da matsananciyar kasala da suka rufeta a lokaci ɗaya, ta fara jan numfashi tana nishi, hawaye masu ɗumi suka wanke fuskarta, gaba daya ta zauce ta rasa tunaninta, lamarin kamar a amafarki take jin afkurwarsa, ta kasa ta6uka komai, sunan danish dana daddynta da aunty ummi kadai take iya ambato cikin zuciyarta a karshe raci gaba da ambton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....... ❗ Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana! Shin wanene Yayi ma unaisah wannan aika aikar❓ _____________________________✍️ A zaune Yake kan darduma, Cikin shiga ta farar jallabiya, Hannunsa ruƙe da qur'ani Ya nutsu Yana karanta shi, "Assalamu alaikum"! Cikin kunnanshi Ya tsinkayi muryar abbansu, sai da yakai aya kafin daura kur'ani kan prayer mat din Ya dago da ita Ya dube shi, Yana asanye cikin kakin shi, zama yayi daga gefen gadon shi Yana duban fuskar dan nasa dakyau, "Ina kwana daddy, Kun tashi lafiya"! "Meke damunka"? Kai tsaye Ya jefa mashi tambayar, Sunnar dakai kasa yayi kafin ya furta me ka gani daddy"? "Abubuwa da dama! Na farko kwata kwata baka acikin nutsuwarka, tun zuwanka Nigeria na lura da akwai wani abu dake damun ka! Bayan haka me ya hana ka komawa bakin aikin ka!? Shiru yayi ba tare sa ya furta kalma ba, baiso daddynsu Ya fahimci halin da yake aciki ba, saboda baya son Ya ɗaga hankalin shi, "Kada ka 6oye min komai, duk duniya baka da kamata, kasan tsakanina dakai babu sirri, Idan wani abune ke damunka, ka sanar dani, in sha Allah zan taimaka maka mu sami mafita atare..." Ya faɗa cikin nuna kulawa Bayajin zai iya 6oye mashi damuwar shi,tun da harya riga daya gano da kan shi, kwara kawai ya fada mashi gaskiya, Cikin sanyin murya ya zayyana mashi komai, tun farkon haduwarsu da Benazir, da irin rayuwar da sukai har izuwa rabuwar su..." dagowa yayi idanunshi jawur cike tab da hawaye ya kalli daddyn nasu "Daddy ka tayani da addu'a, Allah Ya jarabceni da sonta, ko baccin kirki bana iya yi saboda rashin ta atare dani, bansan awani hali take a ciki ba, nayi jiran hajiya laurat shiru har yau bata neme ni ba..., bana jin zan iya barin kasar nan in har ban hadu da ita ba....." Tsananin tausayin shi ne Ya kama Daddyn nasa, "Meyasa baka fada min ba tun farkon zuwan ka"? "Banyi tunanin yin hakan ba, na bari sai in na hadu da ita sai in sanar dakai..." Murmushi sir mubarak yayi aranshi yana mai mamakin zaki, mutumin da bai ta6a ganin wata ƴa mace Ya nuna yana son ta ba, Aikinsa kadai Yasa agaba, al'amarin so da girma ya ke... A hankali Yasa hannu ya zaro wayar shi daga aljihu, ya ɗan daddanata, zaki dake kallon shi bai son me zaiyi ba. Kara wayar yayi a kunnansa, kafin Ya furta"Assalamu alaikum mutumina, Ina fata kana lafiya"? On the other hand muryar mutumin ta amsa masa da cewa"wa'alaikum salam! lafiyalou, Ina fata kaima haka"? "Alhamdulillah, naji muryarka kamar daga bacci ka tashi .." "No na jima da tashi, ya iyalin naka"? "Suna nan lafiya lou...Tambaya ce nake so inyi maka..." gaba daya zaki ya nutsu yana kallon sir mubarak, baisan dawa Yake magana "Ina sauraronka..." "Yar wurin Yayanka benazir da ta bace, ta dawo gida ko hanyar yanzu ba labarin ta .."? "Meyasa ka tambaye ni? "Ka fara bani amsar tambayar da nayi maka..." "Ta dawo gida..." azabure Zaki Ya miƙe tsaye da alamun rudani yake kallon daddyn nashi "Nagode mutumina, Idan muka hadu zamuyi magana" "Okey saina jika" katse kiran yayi, fuskarshi dauke da murmushi Ya kalli zaki, zubewa yayi agaban daddyn nashi, ya dafe gwiwowin kafafunsa da tafukan hanneyansa "Daddy wanene ka kira a waya.. "? "Uncle dinta ne Alhaji musa, baka san cewa shi mutumin mu bane, ay da tunfarko ni ka fara tuntu6a da maganar ta, da baka sha wahalar yi ma hajiya laura magana ba..." wani irin annurin farin cikine ya bayyana akan fuskar zaki, "Idan har kana so In haɗaka da ita, sai ka bani cin hanci" ya fada da zolaya "Daddy me kakeso na baka? Ka fada min koma menene...." dariya sir mubarak yayi "Farin cikin ka da kwanciyar hankalin ka nakeso .." dariya zaki yayi "Ka bani mamaki son, ji bi yadda soyayya ta jigata ka, kamar ba dan sir mubarak ba...." sunnar da kanshi kasa yayi cike da jin kunyar daddynsa "Ni kamarma na ta6a ganin yarinyar? Halan 6oye ta kake yi idan naje canada don kada na ganta ." girgiza kai yayi"a'a daddy, bana 6oyanta zaka iya saninta, duk wanda yaje gida sai yayi tsammanin yar aiki na ce, shiyasa baku ta6a lura da shakuwar dake atsakanin mu ba..." "Gaskiya zanso inji meya faru da ita? Meyasa ta gudu tabar Yarta? Amma kaima da laifinka, fisabilillah ina maka kallon uztaz ashe har mace kake 6oyo agidanka, almost 16years haba zakina! Kunyi ma kanku adalci kuwa? Da hankalin ka ka ajiye matar aure kuma kasan guduwa tayi daga gida bakayi yunkurin neman danginta ka fada masu ba!meyasa"? Ya faɗa fuskarsa adaure alamar baiji dadi ba "Daddy sonta ne Ya rufe min ido na, nasan na aikata babban kuskure amma nayi nadama, kuma ni harga Allah ban ta6a neman ta ba, abun dayasa ban nemi kowa nata ba saboda ta faɗamin ta tsani danginta, bata son ta dawo Nigeria, nayi kokarin shawo kanta donta amince in dawo da ita amma sai tace idan na matsa mata zata kashe kanta ne, shiyasa na kyale ta, daga baya mijinta ya turo mata sakon saki ta wayarta, daga ganin hakan saina kara samun kwarin gwiwar killace ta agidana saboda in mallake ta........." cikin sanyin murya ya kare maganar yana kallon daddyn nasa, "Kayi kuskure da baka sanar dani ba, ay da nayi maka hanyar auranta, yanzu koda ka hadu da ita zata iya bijire maka ta koma ma tsohon mijinta...." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya"daddy ka tayani da addu'a, Allah yasa rabona ce..." "In sha Allah zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ka samu abunda kakeso.." ajiyar zuciya ya sauke, kafin wani ya kara magana a cikin su, Sallamar hajiya turai ta katse su, atare suka amsa mata, ta shigo fuskarta dauke da murmushi"i'm sorry na katse maku firarku, my son barka dai, fatan ka tashi lafiya" da fara'a ya amsa mata"lafiyalou mommy, Kallon sir mubarak tayi"na kammala shirya mana breakfast, ka taso muje kaci kada ka makara" ruko hannun zaki yayi acikin nashi atare suka mike suka nufi dining din Adai dai lokacin, dr Jazz ya fito sanye cikin black trouser da shirt, Ya daura lapcoat akan kayansa, idanunsa manne da farin glass "Barka da safiya daddy..." "Yawwa Son, Harka shirya kenan" "Eh," Ya faɗa tare da samun wuri kan dining chairs suka zauna, turai ta fara yin serving nasu "Big bro Ina kwana.." murmushi ya sakar mashi kafin yace"lafiyalou, ina fata kaima haka" ya ɗaya masa kai alamar eh, Har sun fara cin abinci, Ibad Ya fito daga shi sai ɗan short, "Mommy ni an manta dani, shine ba a kirani inzo inci abincin ba . " ashagwa6e yayi maganar Turai tace"sorry babyn zaki, Ay nayi zaton zaka jira ne Ya kammala in ya rage sai ka ci.." murmushi sukayi "Oh wai har yanzu bai daina wannan ɗabi'ar ba"? Sir mubarak ya tambaya yana kallon zaki "Daddy bai daina, abun nasa kullum ƙara gaba yakeyi, bansan ya zanyi da shi ba, har friends dina sun gane halinsa, Na cin sauran abincin da na rage...."kallon shi sir mubarak yayi da sauri ya juya baya yana faman noke kai "Daddy pls kada kamin faɗa, ni wlh na saba, kuma nafi jin dadin cin ragowar abincinsa, daɗi Allah" dariya suka sanya gaba dayansu "Calm down Your mind, kai fa last born ne, shalelan mommy da daddy, ba wanda zaiyi maka faɗa, kayi abunda kakeso" yaji dadin maganar turai, "Zo ka zauna in zuba maka abinci.." da sauri ya samu guri ya zauna, Yana satar kallon daddyn su da jazz wanda tun ya zauna, hankalin shi baya atare da su, gangar jikinsa ce kadai atare da su ruhinsa yana wurin faryat daya kwallafa rai akai. "Jazz kaci abinci mana! Salon sai ka makara ko"? Cikin kulawa Sir mubarak yayi masa magana Kamar baisan cin abincin Ya dauki cuf of tea mai zafi Ya ɗan kur6a "Daddy dan Allah kace ma yaya zaki mu koma toronto, ko dan saboda karatuna, in ba haka ba zaija amaida ni baya..." da damuwa akan fuskarsa yayi maganar Harara zaki ya dan watsa mashi"kada na sake ji kayi magana!..." Sir mubarak ya katse shi da cewa"ba haka yakamata kace mashi ba.." ya faɗa tare da maida dubansa ga ibad wanda Ya haɗe rai. "Next month zaku tafi, in sha Allah" Murmushi ibad yayi"yawwa daddy thank you.." "Wato na lura gudunmu kake Yi ibad.. "No momy wlh saboda school, kuma na manta bibina a gida..." Yana nufi magensa, miƙewa jazz yayi"zan wuce" atare suka haɗa baki wurin yi mashi Allah kiyaye hanya, sai da yabi kowan nan su ya manna masu peck kafin ya tafi...... ________________________________✍️ Tun da garin Allah ya waya, Aneeleeh ta rasa kwanciyar hankalin ta, ta kasa tsaye taka zaune kamar mai fama da ta6in hankali, tayi matuƙar kagara ta kosa hajiya Saratu ta kira zahra, duk bayan yan mintuna sai ta leƙa dakin zahra don ta ji ko ta kirata shiru har yanzu babu wani labari, kamar yadda ta matsu haka hajiya layla ta matsu suzo da yarinyar, itace ta fara farkar da ita daga bacci da sanyin safiya ta kira ta awaya, tana kara jaddada mata akan kada ta manta tayi kokari su yi magana da iyayen yarinyar, ta rasa ya zatayi gaba daya ta daura ma kanta damuwa, daren jiya dakyar ta runtsa.. "Aunty Aneelerh"muryar zahrce ta ratsa kunnanta, Jiki na rawa ta juya da sauri ta nufi zahra dake shugowa dakin, tana sanye da hijab, hannunta ruko da wayarta... "Zahra ta kira? Ko har yanzu"? shiru zahra tayi fuskarta babu walwala.. Hakan ba karamin ɗaga hankalin Aneelerh yayi ba "Kinyi shiru baki ce komai ba"? fuskarta dauke da matsananciyar damuwa ta furta"muyi hakuri aunty Aneelerh, ta kira tace wai yarinyar ba unaisah ɗinmu bace....." "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Hankali atashe Aneelerh ta zabga salati tare da ɗaura hannayenta biyu akanta "Nashiga uku zahra! Ya zanyi? Ga shi nayi masu alkawarin yau zanzo da yarinyar, dan Allah ki taimaka min zahra, ki nema mana alfarma awurin hajiya saratun su bamu aronta...." gaba daya tabi ta ɗaga hankalin ta... "Aunty Aneelerh, ki kwantar da hankalin ki, tace muje gida mu same ta yanzu watakil ko zasu ba mu aronta ne.." nauyayyar ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, jiki na 6ari tace"bari na shirya sai mu tafi, mahboob Ya dawo ne"? "Bai kaiga dawo ba" amsawa tayi da toh, da sauri ta nufi toilet ta shige don tayi wanka Fitowa zahra tayi daga dakin, jikin ta duk yai sanyi, Bayan sun kammala shiryawa,sai da suka fara zuwa dakin mami suka sanar da ita kiran da hajiya saratu tayi masu, mami tace Allah Yasa muji alkhairi, idan kun isa komai ake ciki ku kira ku sanar dani,suka amsa mata da toh... Da matsakaicin gudu motarsu ta haura kan titi, Aneeleerh ce ke driving dinsu, zahara na zaune gefen ta.. "Auntyna ki bi a hankali mana, naga sai zura uban gudu kike kamar zamu tashi sama! "Ba zaki gane ba Zahra, wallahi ji nake kamar inyi fiffike in karasa estate din, gani nake kamar bana sauri, ni dai burina Allah yasa su taimaka su bamu yarinyar..." zahra ta amsa mata da ameen, Lokacin da motarsu ta karaso estate din, da sauri Aneelerh ta rage gudun motar, sunyi tsammanin security officers din zasu dakatar da su irin na jiya amma abin mamaki suna isa, da hannu sojojon suka yi masu alamar su wuce, gaba daya suka sauke ajiyar zuciya Bayan sunyi parking din motar, suka fito daga ciki, adai dai lokacin Hajiya saratu ta fito daga entry hall na gidan, ta dauki wankan leshi, idanunta sanye da farin glass Cike da zumudi suka nufeta, with respect suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu kafin tace"bismilla muje" ta nuna masu motarta da hannu, su biyu suka shiga back seat, security din da zai yi driving dinsu yana a mazaunin driver, Hajiya saratu na daga gefen shi... Kaitsaye motar ta nufi cikin estate din "Kamar yadda nake fada maku, munyi magana da shi jiya, nayi masa bayanin komai dangane da zuwan ku, to a gaskiya yarinyar bata wurin ku ba ce, amma yace zai iya baku ita har zuwa time da ita patient din naku zata ji sauƙi...." fuskarta babu fara'a tayi maganar. kallon juna zahra da Aneelerh su ka yi jikin su yayi sanyi lakwas... Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"hakan ma yayi mungode sosai..." ___________________________________✍️ Firgigit ta farka daga bacci tana faman zazzare gray eyes dinta tamkar kwayar idanunta zata faɗo kasa, hannun ta ɗaya dafe da goshin ta, numfashin ta na fita da sauri, kwata kwata babu kuzari a jikinta kamar wadda aka zarewa laka, ga wata kasala data baibaye sassan jikin ta, dakyar ta yunkura ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin pillow, fuskarta ta kumbura suntum, kumatun sunyi jawur, haka la66anta ma sun dan kumbura, idanunta sun ƙanƙance kwarmin idon yayi ja daga gani ta jigata ba kaɗan ba... Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata abunda Ya faru da ita adaren jiya, runtse idanunta tayi sosai kwallar da ta taru acikin su ta fara ƴar tseral kan kuncin ta, ta rasa gane meya faru? Shin mafarki ne ko gaske? Kokwanto ta soma yi saboda zuciyarta tagaza yarda da abun da ya faru, was wasi ta kama yi tana faman tariyo komai daya wakana adaren jiya, babu wata alama da zata tabbatar mata da abun ya faru dagaske, da sauri ta dubi yar rigar jikin ta, tayi uban squeezing kamar an ƙwatota daga bakin kura, da sauri taja rigar ta rufe santala santalan laps dinta, ta sauko daga kan gado tana faman bin dakin da kallo, mirror chair ta gani yashe ta jirkice kan floor "Ina wandona Yake"? Ta jefa ma kanta tambayar, Ringing din wayarta ne Ya doki dodon kunnanta, jiki na rawa ta nufi toilet saboda tana tunanin kamar anan ta cire wandon Tana shuga ciki ta iske shi akan hanger, tunawa tayi da jinin daya dawo mata gadan gadan adaren jira aranta ta ayyana shima dagaske ne ko duk cikin mafarkin ne"? Ta kare maganar tare da buɗe laps dinta ta laluba jikin ta, bata ga komai ba, sai dai wani farin ruwa mai yauƙi yauƙi dake gangarowa... Gaba ɗaya ta gama rikicewa, tunaninta ya kasu gida biyu, ta jima a toilet din kafin ta fara tunanin yin wankan Bada jimawa ba, ta fito sanye da rigar wanka, har ta kusa isa gaban mirror tajiyo bugun kofa, "Wanene"? ta fada tare da kallon ƙofar "Daddyn ki ne..." sanyi taji ya ratsa zuciyarta, da sauri ta nufi kofar ta buɗe mashi Tun daga kasa ta fara kallon shi, jallabiya ce a jikin shi maroon colour, sai kamshin turare ke tashi a jikin shi "Daddy, Ina kwana..." bata ƙare maganarba, ganin yadda yake binta da kallo mai tattare da ruɗani "Unaisah! Baki da lafiya ne? Meya faru naga fuskarki ta kumbura tayi ja, kamar kinyi kuka..." wani irin mugun bugu kirjinta yayi, babban tashin hankalinta kada ace abunda Ya faru jiya dagaske ne, ba mafarki ba Muryarta adabarbace ta furta"da.. ddy.. lafiyana lou, meka gani ne."? girgiza kai taj yayi"no ban yarda ba, fada min ko dai wani ya buge ki ne"? "Wallahi daddy ba komai, watakil ko dan saboda firar da muka tsaya yi jiyane ban samu isasshen bacci ba shiyasa fuskata ta kumbura..." kwata kwata hankalinsa bai kwanta da yanayin ta ba, janyota yayi tare huggin dinta, ya daura hanneyensa akan bayanta "Nayi missing dinki my daugher, ina fata kin tashi lafiya.." "Lafiyalou daddy ..." dago da kanta yayi"baki jin ciwon kai? Ko zazza6i haka" Ƙaƙaro murmushi tayi akan fuskarta duk don ta kwantar mashi da hankalin shi "Bana jin komai daddy, ni yau da karfina na tashi..." ajiyar zuciya ya sauke "Okey, ki shiga ciki ki karasa shiryawa, Chief Yana son ganin ki" waro idanu waje tayi alamar mamaki "Daddy ni kuma? ɗaga mata gira yai alamar eh "Ki sanya kaya masu kyau, zan jira ki awaje" cike da mamaki ta amsa mashi da toh, Bayan fitarshi cikin sauri ta nufi closet dinsu, ta dauko wasu hadaddun riga da wando ƴan pakistan, rigar fara wandon yellow, veil din kayan yellow, ita kanta data sanya kayan saida ta jinjina ma kyan da sukai mata, gaban mirror ta zauna ta fara gyara sumar kanta dakyar take sharce ta da comb, bayan ta kammala gyara gashin, ta shafa powder da lipstick, kafin tayi rolling veil din akanta, takalma ta dauko masu tsini ta zura su a kafafunta, Komawa tayi gaban mirror ta feshe jikin ta da turare Har lokacin bata daina tunanin abun da ya faru a daren jiya ba, was wasi take tayi aranta.., kwata kwata bata so ya zamana gaskiyane abun da ya faru da ita.... A hankali ta zura kafarta ta fito daga dakin, Walking slowly ta nufi daddyn ta dake atsaye yana jiran ta, babu kowa a falon da alama basu kaiga fitowa ba "Daddy yunwa nake ji, Ciki na babu komai.." ta fada yayin da ta ruko hannunsa acikin nashi "Kada ki damu, nima banyi breakfast ba, idan munje wurin chief din zamuyi atare da shi..." amsa mashi tayi da toh Kaitsaye suka nufi walkway bata san ina za su bula ba "Daddy ba part dinsa zamuje ba"? "Eh, yace mu same shi a backyard.. Zazzaune suke akan wasu jigunannun sofas ƴan ubansu, backyard din ya Haɗu an ƙawata shi sosai, chief da hajiya saratu suna a zaune kan sofa daya, Aneelerh da zahra suna fuskantar su, tun da suka zauna Aneelerh take ta jinjina ma haduwar gidan da shi kanshi mamallakin gidan wato chief, kallo ɗaya tayi mashi saida gabanta Ya faɗi, ya ɗauki wankan suit navy blue sunyi bala'en yi mashi kyau Zahra dake satar kallon shi, gani take kamar a mafarki yau gata ga director general na isod, crush ɗinta, mutumin da tayi haukan son shi a lokacin baya.. Round table din dake a tsakiyarsu, cool drinks ne da Snacks asaman hadadden wooden tray "Idan muka baku aron yarinyar sai yaushe ne zaku dawo mana da ita.."? Hajiya saratuce tayi masu tambayar "Idan da hali har zuwa lokacin da benazir din zata ji sauƙi, dan Allah ayi mana alfarmar nan..." gyaɗa kai hajiya saratu tayi"okey, amma fa zaku bani tukuici tun da ni nayi maku hanya a wurin chief..." ta faɗa da yar zolaya tana kallon su Murmushi suka saki zahra tace"bakomai mommy, ay duk abunda kikeso zamu baki.." yar dariya tayi"zolayarku nakeyi..." dariya sukai su kansu sun san tafi karfin tukuici, ta dai faɗi ne don ayi raha... Kwas kwas sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka dago tare da kallon inda sautin ke fitowa....❓ *Daga alkalamin Boss Bature mu haɗu next page on monday idan Allah yakaimu da rai da lafiya✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions Buy bestselling books online [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 30 by Novels Elite Admin August 11, 2024 Sponsored Link Novels Elite English Kwas! kwas !! sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka ɗago tare da kallon inda sautin ke fitowa... Ƙura idanu sukayi suna kallon su, kafin Aneelerh tayi wani irin yunkuri ta miƙe jikin ta na 6ari, zuciyarta na dakan uku uku, gaba ɗaya tabi ta rikice gani take kamar a mafarki take kallon su!! Kokwanto ta farayi anya kuwa sune? Tajudeen da Angel? Ko dai idanunta ne suke nuna mata badai dai ba? Tayaya mutanan da suka 6ace almost 16years yau kwatsam ta gansu, da ransu da lafiyar su, kanta ne ya wani irin sara mata da sauri ta dafe goshin ta, ganin hakan yasa Zahra ta miƙe a matuƙar ruɗe take kallon Aneelerh... Lokacin da unaisah ta ɗaura kwayar idanunta akan fuskar Aneelerh, Ras taji gabanta Ya faɗi, wani irin burki taci ta dakata da yin tafiyar, idanunta azare take kallon ta, wlh ko amafarki taga fuskar Aneelerh sai ta shaida ta balle kuma azahiri, La66anta na kerma ta furta"Aunty Aneelerh? Daddy! Auntyna ne? Ita ne nake gani azahiri ba mafarki ba? Daddy wallahi itace aunty Aneelerh ce...." kalamanta ne suka dira akan kunnan Aneelerh, baiwar Allah jiki na 6ari ta watso da gudu mayafin ta har yana ƙoƙarin zamewa, da gudu unaisah ta nufe ta, takalman kafarta suka kusa kayar da ita kasa, amma ahaka ta jure don bazata iya jira aunty Aneeleeh ta karaso gareta ba, zubewa Aneelerh tayi akan gwiwowinta tare da ware hannayenta biyu ta rungume unaisah, tayi hugging dinta tightly lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kukan farin ciki mai tsuma zuciya 😖 A hankali taj ya ƙaraso Ya tsaya daga bayansu, tare da goya hannayensa bisa kirjinsa. A sukwane hajiya saratu da chief suka miƙe tsaye suna kallon su, fuskokin kowan nan su ɗauke da murmushi su kansu da suka sake haɗa wannan zumunci ba karamin dadi suka ji ba, farin cikin da suka gani akan fuskar Aneelerh da unaisah ba zai misaltu ba. Yadda Aneelerh ta rungume unaisah, kamar zata mayar da ita cikin cikinta, a kalla sun shafe mintuna goma manne da juna, kafin Aneelerh ta raba jikin ta daga na Angel, a lokacin itama ta durƙusa kan gwiwowinta, Aneelerh ta sanya tafukan hannayenta biyu ta tallabo fuskar unaisah da su, itama unaisah ta tallabo fuskar Aneelerh da nata tafukan hannun, suka kurawa juna ido yayin da hawaye ke sintiri kan fuskokinsu, cikin shesshekar kuka Aneeleeh take fadin"Angel dina! Kece nake gani? Dan Allah ki fahimtar dani nagaza yarda da abun da idanuna suke gane min! Wayyo Allahana.." ta fada tana jan numfashi. "inna lillahi Ya Allah Idan Mafarki nake kada ku tada ni, kubarni kawai inci gaba da yin shi, Ya ilahi Angel dina ce..Ina kika shiga? Kika bar auntynki da ciwon rashin ki? Angel wayyo Allah...duk tabi ta susuce Cikin muryar kuka unaisah tace"Aunty Aneeleeh, ni ce Angel dinki, ƴarki, Aunty Aneeleehna, ba mafarki kike Yi ba, ni ce dagaske, Angel dinki abokiyar firarki, mai sanyaki nishadi..." ƙara rungumeta Aneeleerh tayi. Gyaran murya taj yayi cikin karayar zuciya ya firta"Aneelerh!.." kamar jira take yayi magana, a zabure ta mike ta tsaya agabanshi idanunta jawur ta furta"taj! kasan irin haukan rashin ku da nayi? Me nayi maka dana tsantsanci haka daga gareka?..." kwalar rigarshi ta damƙa da hannayenta biyu ta jijjiga shi kamar zata rufe shi da bugu taci gaba da fadin"taj meyasa kayi min haka? Meyasa ka gudu da unaisah kuka barni da kewarku? Taj kasan irin kunci da radadin dana naji a lokacin dana farka naga babu ku"? Kalamanta sun karya zuciyarshi baisan sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, Zahra dake kallon su tuni hawaye sun wanke fuskarta ga wani farin ciki da ya lullu6e ta na ganin Unaisah, Jikin chief owais yayi sanyi lakwas tsantsar tausayinsu ne ya kama shi, ba shi ba hatta Hajiya saratu sai da taji tausayinsu duk da bakomai ta sani ba dangane da rayuwar su ba. "Taj Ina mijina? Ina uzair! nasan Yana atare ku? Ka faɗa min taj meyasa kuka gudu daga gida? Tsawon shekara da shekaru baku ta6a waiwayena ba? Laifin me nayi maku taj? Idan wani abu ne yasa kuka gudu meyasa baku sanar dani ba? Harga Allah bakuyi min adalci ba taj! dai dai da rana ɗaya baku ta6a nema na ba ko da awaya ne...." Daƙyar ta ƙare maganar, Lokaci ɗaya ta yanke jiki zata faɗi da sauri taj ya tarota ta faɗo kan kirjinsa. Da sauri zahra ta karaso gabansu tana kuka, zuƙunnawa taj yayi a hankali ya kwantar da kanta bisa laps din sa, har lokacin Angel tana a durkushe kan gwiwowinta da karfi take furta"Aunty aneelerh ki tashi! Dan Allah ki tashi wayyo Allahna daddy ka ce mata ta tashi" duk tabi ta rude zahra ma kukan take tana ambaton sunanta, Hajiya saratu ta kasa furta komai, lamarin ne da ta6a zuciya.. robar ruwa mai sanyi chief ya dauko daga kan table, Ya nufo wurinsu Ya buɗe murfin tare da mika ma Taj, Hannunsa na kerma Ya kar6a Ya tarfa ruwan a tafin hannu Ya watsa mata kan fuskarta, nan take taja mumfashi tare da furzar da shi... Cikin karyayyar murya ya furta"Anila! dan Allah ki saurareni, wallahi bada son ranmu muka gudu ba, mummunar ƙaddara ce ta afka mana wadda tayi silar barinmu gida..., na rasa komai nawa Aneeleeh..." ya faɗa yana kallon cikin idanunta, dakyar take kallon shi, wani irin azababben ciwon kaine Ya far mata, ita kadai tasan halin da take a ciki. "Nasan zaki fahimce ni Aneeleerh, har abada kinsan bazan Iya gudunki hakanan ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, dukan mu babu wanda baiyi kewar rashinki ba, kuma ko bayan da muka gudu kina aranmu bamu manta dake ba....." "Taj ina mijina...."! Gabansa ba karamin faduwa yayi ba, kallon chief yayi da sauri ya girgiza mashi kai alamar kada Ya faɗa mata, saboda a halin da take ciki muddin suka sanar da ita tsaf zata iya zaucewa. "Aneelerh, bansan Ina uzair Yake ba! Idan ba zaki manta ba, ba atare muka bar gida ba, adaren ranar da abun ya faru kinzo har gida kin same ni kina kuka kika ce uzair bai dawo ba, har na kwantar maki da hankali, tun daga wannan lokacin ban ƙara sanya uzair a idona na, amma muna nan muna bincike akanshi, in sha Allah shima zamu gano shi. zuciyarta ba karamar karaya tayi ba, tuni ta sake fashewa da wani sabon kukan. Kafin wani ya sake magana a cikin su, wayar Hajiya saratu ta fara ringing, da sauri ta zaro wayar daga cikin handbag dinta, ta duba mai kiran ta, p.a din tace, picking call din tayi"Okey, Gani nan zuwa yanzu nan.." ta faɗa tare da katse kiran ta dago ta dubi chief. "My son yakamata na tafi, naso in tsaya amma kirane na gaggawa, duk halin da ake ciki pls ka sanar da ni..." ta fada cikin saurin murya, kafin ta dubi su Zahra. "Zahra, Ni zan wuce, in sha Allah idan na samu time zanzo asibitin in duba mara lafiyan..." tayi masu fatan Alkhairi, godiya suka dinga yi mata, Har bakin mota chief tare da zahra suka rakata, akan idonsu motar ta fice daga gidan. Dawowa sukai wurinsu Taj dake a durkushe ƙasa. "Taj baka fadamin meyasa kuka gudu ba..."? Cikin jin ƙunar rai ta jefa mashi tambayar. Atakaice ya labarta mata abun da ya faru da su, tun farkon da suka fara yi ma Alhazawan nan leƙen asiri da kuma farmakin da suka kawo mashi atsakar dare harya gudu da Angel....." sai dai bai sanar da ita wayar da uzair ya kira shi ba ya dai ce shi baisan meya faru da uzair ba, har yau suna neman shi ba su gan shi ba, hankalinta yayi mugun tashi jin wannan musifar data afka masu, hatta zahra tayi matuƙar firgita jikin ta sai tsuma yake abun ya bata tsoro... "Shiyasa bamu neme ki ba, saboda rayuwarmu tana a cikin hatsari, idan har miyagun suka san muna raye ba za su kyale mu ba, don dole muka killace ce kanmu kafin Allah ya tona asirin su" "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji! taj wannan wani irin tashin hankaline! Ni dama saida raina ya bani ba hakanan kuka gudu ba, Allah Yasa basu kashe uzair ba, nama san mawuyacin abune uzair ya rayu watakil sun kashe min shi...." bai bari ta ƙare maganar ba, Ya fara lallashin ta dakyar Ya shawo kan ta.... Zafafan hawayene suka cigaba da wanke kuncin ta, "Boss!" chief ne Ya kira sunan shi "Na'am yalla6ai" "Ina son magana daku, ban da unaisah" A hankali Ya ɗago da Aneeleeh, da sauri zahra ta zuƙunna tare da tallabo ta don gaba ɗaya jikin ta ba kwari dakyar ta samu ta miƙe. Unaisah dake kallon su ta shiga ruɗani tunda chief Yace Yana son ganin su ban da ita... Ruƙo hannunta taj yayi, suka nufi sofas din wuri ya zaunar da ita "Daddy meya faru"? "Kada ki damu, magana ce mai mahimmanci zamuyi, Idan muka gama zamu sanar dake, cike da gamsuwa tace toh "ɗazu Kin faɗa min kina jin yunwa, ga snacks nan da juice ki sha kafin mu gama magana" yatsun hannunta har kerma suke wurin daukar burger ta fara cin ta. idanunta akan su Aneelerh dake tafiya suna nufar can nesa da ita, zuciyarta cike fal da farin ciki, kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna, bakinta yaki rufuwa sai faman tariyo fuskar aunty aneeleeh takeyi, burinta su gama maganar don ta tambayeta ina ƙanin ta da daddynta ya bata labari ta haifa mata.... Bayan kowan nan su ya zauna kan kujeru suka nutsu suna jiran jin me chief zai sanar da su "Inaso ku faɗa masa abun da ya kawo ku neman ƴar sa"! Ya faɗa batare da ya ɗago ya kalli waninsu ba, aɗan ruɗe Taj Ya kalli su Aneeelerh. Baiwar Allah tama rasa ta ina zata fara, saboda tasan ba lallai Ya amince masu ba. "Aneelerh kinyi shiru! Faɗa min meyasa ku ka zo neman Angel? Tun jiya chief yayi min bayanin zuwan ku amma bansan cewa ku bane, nayi mamakin ganin ku! Tayaya har kuka gano inda mu ke!? Ya fada cike da son jin ƙarin bayani. Cike da fargaba Aneeleeh ta fara zayyana masa abun da ya faru na bayyanar benazir, bata 6oye mashi komai. tunkafin ta ƙarasa maganar yanayin fuskar taj ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, kwata kwata baiji dadin bayyanar benazir ba, saboda tafi ta aransa baya buƙatarta arayuwar shi, wani irin ɗaci yaji aran shi, Aneeelerh ta fama mashi tsohon raunin dake a zuciyar shi. ko sunan ta baison ji, aranshi ya arayyana da ranta da lafiyarta tsawon shekara da shekaru bata ta6a neman su ba? Idan har shi bata neme shi ba ay yakamata ko yarta ta nema baisan wata irin zuciya bace a kirjin benazir ya riga da yasan halinta domin kuwa ba zai ta6a manta irin rayuwar auran da sukai da ita ba, macace mara kunya batasan darajar aure ba, ta azabtar da shi da soyayyarta. gaba ɗaya sun lura da yanayin shi, kamar baya atare da su, Aneeleerh duk tasha jinin jikin ta, dafa kafadarsa chief yayi a hankali ya kallesa idanunshi sun kaɗa jawu"dan Allah kada kace inyi hakuri, saboda bana jin zan iya yafewa benazir, hasalima ban yarda cewa dagaske ta damu da mu har haka ba, Allah kadai kasan manufar da take da ita akan mu, ba zan ta6a yarda da benazir ba, matar da ta tafi tabar yarta a kwamin wanka, taje can tana yawon biɗiɗin ta tsawon shekaru bata ta6a neman mu sai yanzu"? Hawayen dake taruwa a cikin idanunsa tuni sun wanke fuskarshi hakan ba karamin ɗaga hankalin zahra da Aneeerh yayi ba.. Shi kadai yasan ƙunar da zuciyar shi take yi mashi Shiru chief yayi sam ya kasa furta magana, Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"dan Allah taj kayi hakuri mu manta da abun da ya wuce, Benazir tayi nadama, neman ku take ruwa ajallo don ta nemi yafiyarku, wallahi taj ta riga ta gane kuskurenta" tana magana tana marairaice mashi fuska don ya tausaya masu"ka dubi girman Allah ka kuma duba darajar yarinyar dake atsakaninku ko dan saboda ita yakamata ka sassauta mata, Allah ma muna yi mashi laifi ya yafe mana balle mu da muke ƴan adama, taj ita kanta bada son ranta ta gudu ba kamar yadda na faɗa maka asiri akayi mata, yakamata kayi nazari kada ka yanke hukunci cikin fushi, nasan Benazir bata kyauta maku ba, amma ka duba pls, tana fa sonku shiga akayi tsakaninku saboda babu yadda za'ay uwa ta haifi ɗan sunna tayi watsi da shi......" babu alamun taj zai fahimci maganar ta, idanunsa sun kaɗa jawur bakomai yake tunano ba face lokacin da ta ɗauki cikin unaisah hauka ne kadai batayi ba saboda ta tsani ciki, har fadi take zai bata mata shape din jikin ta, bayan haka tasha yin yunƙurin zubda shi Allah bai nufa ba. "Pls, koda bazaka yafe mata ba, dan Allah ka amince Unaisah ta gana da mahaifiyarta..." kafin ta ƙare maganar yace "Aneelerh kin riga da kinsan ƙiyayyar da unaisah take ma benazir, tunkafin ta mallaki hankalin ta, unaisah bata buƙatar mamanta, Nima kuma bana bukatarta...." hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Ga samu ga rashi, kallon chief Aneelerh tayi ya kasa kunne yana sauraron su. "Dan Allah ka taimaka mana ka sanya baki a maganar nan!...." ta fada hawaye na bin fuskarta. Duk yadda taj yaso hana chief magana sai da ya sanya baki "Taj, I won't come between you and your ex-wife, Unaisah ita ce damuwata! Bana so ta rasa gatan da uwa take ba ɗan ta! duk irin tsanar da tayi mata wlh tana bukatar soyayyar mahaifiyarta fiye da taka!" ya ɗan dakata da maganar yana kallon taj, wanda ya nutsu yana sauraron shi. "kai kanka ba zaka so unaisah ta rasa albarkar mahaifiyarta ba, shin zaka so unaisah tabar duniya ba tare data gana da mahaifiyarta ba? Ya jefa mashi tambayar cikin tausasa harshe shiru taj yayi "Zaka so ne ta mutu da bakin cikin mahaifiyarta? Taj Ka riga da kasan mahimmanci uwa a addinance, ko da kuwa ta banza ce, bana so mahaifiyar yarinyar nan ta mutu a sanadin rashin ganin yarta da batai ba, kuma bana so unaisah ta rasa soyayyar mahaifiyarta, ba zakai mata kwaɗayin ta samu ladar dake a cikin kyautatama iyaye ba? Ka gama da iyayen ka lafiya ita bakaso ta gama da nata iyayen lafiya ne"? cikin kwantar da murya chief ya cigaba dayi mashi nasiha, su Aneelerh duk sun nutsu sun kasa kunne suna sauraron shi, mutumin Ya kara shiga ransu, yadda yake magana cikin hikma da ilmi ba karamin sace mashi zuciya yai ba. Jikin shi yayi sanyi sosai, kalaman chief sun ratsa zuciyar shi, aranshi yana ji koda bazai yafewa Benazir ba, zai yi kokarin haɗa Unaisah da maman ta, Benazir taci albarkacin chief wlh da ko kallo bata ishe su ba. Koda kuwa zuciyarta zata buga ta mutu ne....." Gyaɗa kai yayi cikin sanyin murya yace"Na amince, wallahi taci albarkacinku, bazan iya watsa maku ƙasa a ido ba, Ina matuƙar ganin ƙimarku da darajarku, kuma bana fata Allah Ya nuna min ranar da zan bijire ma bukatarku..." ya faɗa yana kallon chief da Aneelerh, har cikin ran su sunji dadin maganar shi. Hanky chief Ya zaro daga pocket dinsa Ya miƙa ma taj don ya share hawayen shi, da sauri Ya kar6a yai masa godiya kafin ya share fuskarshi "Yanzu za'a iya bamu aronta muje da ita asibitin"? "Ban amince a fita da ita daga gidan nan ba, sai dai Idan mara lafiyar za'a kawo nan ta zauna"! Acewar chief, yarfa hannu Aneelerh tayi, tuni murnar da suke ta koma ciki, muryar ta kamar zata fashe da kuka tace"dan Allah ka taimaka mana! Ka dubi girman Allah ku bamu ita, mu kai ma mamanta, Benazir ba zata iya zuwa nan ba..." saukowa tayi daga kan kujerar ta zukunna kan gwiwowin ta, da sauri ta yace tashi ta zauna, jiki asanyaye ta koma ta zauna. "Aneelerh kina ganin unaisah zata yarda idan taji cewa wurin mahaifiyarta zaku kaita? kin riga da kinsan irin tsanar da tayi mata, tun kafin ta mallaki hankalin ta...." dafe kai Aneelerh tayi, sam ta manta da wannan zancen ita dai burinta kawai Angel taga mamanta "Ya zamuyi taj? Wallahi nasan mawuyacin abune Unaisah ta bamu hadin kai" Taj yace"ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba, Unaisah ba zata amince da ita ba don ta yanzu..." "Kana nufin ta san komai game da yadda mahaifiyarta ta gudu bayan ta haife ta?" "Ta sani yalla6ai"! "Ya salam, kunyi babban kuskure da kuka sanar da ita, saboda kun dasa mata ƙiyayyar mahaifiyarta, tun da kuruciyarta, kuma yaro yana da ruƙon abu a zuciya....." Shiru taj yayi shi kanshi yasan yayi kuskuren sanar da Angel, duk da ba a hayyacinsa ya faɗa mata ba, a lokacin da take cikin azabtar da shi da rashin jinta, har ya taushe mata fuska da pillow, aranar ne ya sanar da ita, don ta tausaya mashi tasan cewa shi kadai ne gatan da take da shi......." Shiru sukayi tsit na wani lokaci, Kowa da abunda Yake saƙawa aran shi Unaisah dake zaune tana shan lemu sai kallon su take Yi, ta rasa me suke tattaunawa, tsawon lokacin nan basu gama ba, gashi ta ƙosa ta sake huggin din auntyn ta. "Ko da zan baku unaisah! Zan gindaya maku sharudda, saboda a halin Yanzu bincike mukeyi kan case dinsu, Rayuwarsu tana a cikin hatsari, babu buƙatar kowa yasan suna araye, daga ita har taj din!" hankali atashe zahra da Aneelerh suka kalli fuskar chief da yayi maganar. "Dalilin dayasa tun farko na kira ku gefe ɗaya, don in gargaɗe ku akan kada ku kuskura kuyi gangancin da wani zaisan suna araye!!...." babu wasa akan fuskarshi yayi maganar. "Idan har kukai kuskuran da wani Ya sani, ku kuka da kanku! zaifi kuyi takatsantsan yadda mukai maganar anan to mu binne komai anan"! ya faɗa tare da kwankwasa table din gabansa. Zahra ba karamin tsorata tayi ba, Jikin ta har ya fara kerma, dama da biyu chief ya tsoratar da su don su dauki maganar serious kada su 6ata masu dokar aikin su. Murya na rawa Aneelerh tace"in sha Allah ba zamu bari wani ya sani ba,..." la66an zahra na kerma tace"wallahi nima bazan yi kuskuran sanarma wani ba, nayi maku alkawari..." Aneelerh tace"zahra bata da matsala, zata rufa mana asiri, ba zata bari wani ya sani ba, amma ni damuwana tayaya zamuje da unaisah asibitin"? "Unaisah ba zata bamu matsala ba, Zan ja mata kunne akan kada ta fadama kowa ina araye! Ita ma kuma kada ta bayyana kanta koda wani ya nuna ya santa! abun da yakamata shine zaku je da ita amatsayin yarinyar da kuka ce zaku kawo masu, kada abari kowa yasan itace yarta ta ainihi!" gaba ɗaya sunyi amanna da maganar Taj, "Itama unaisah za'a fada mata cewa zataje duba mara lafiyane wadda yarta ta 6ace mai kama da ita, ta hakane kadai zamu samu yardarta, inyaso daga baya idan suka shaƙu da juna ta yadda ba zata iya jurar rashinta ba, sai afaɗa mata gaskiya" sai da taj yakai Aya Aneelerh tace"amma anya ba za'a samu matsala ba? Benazir idan tana sambatu sunanka dana Angel take fadi saboda mun riga mun fada mata sunan yarta, bayan haka Alhaji ubaid yasan unaisah, itama tasan shi! Kana ganin idan ta ganshi bazata nuna ta sanshi ba? Ko ta tambayi meye alakarshi da mara lafiyar....." Calmly chief yace"wannan ba matsala bane, idan har zamu bada unaisah dole asibitin ya kasance a karkashin kulawar jami'an mu, zamuyi magana da likitocin dake kula da mommyn nata, zamu sa ahana kowa shiga dakinta, daga ita Unaisah din sai grandma dinta, ko itama tasan ta ne"? Girgiza kai tay yai"a'a hajiya layla bata san angel ba, bana tunanin ko a hoto ta ta6a sanin ta, saboda babu zumunci atsakanin ta da taj...." Taj yace"abun zaizo mana da sauki saboda kaf dangin Benazir ba wanda yasan Angel sai kakanta, bayan haka bana tunanin sambatun da maman nata takeyi zai tona asirin wacece ita, duk da Angel tana da kaifin basira but zata ruɗe ne saboda tasan ba ita kadai bace mai suna angel after that koda ta furta sunan taj ba lallai tai tunanin ni take nufi ba"! ajiyar zuciya Aneeelerh da zahra suka sauke a lokaci ɗaya. "Amma da zarar ta dawo hayyacin ta, Aneelerh ki sanar da ita cewa yarta ce, sannan kiyi kokarin jan kunnanta akan kada tace zata furta wata kalma da zaisa unaisah ta gane itace mahaifiyarta...." amsawa sukayi da toh Chief ya ɗaura da cewa"Ko da zamu baku ita, ba yanzu ba, sai zuwa dare zansa akawo ta asibitin, She will be under the care of our officers because we won't be careless with her life..." cike da gamsuwa suka amsa mashi da toh, sunjima suna tattaunawa, a karshe taj shi Ya ce zai yi magana da unaisah dangane da zancen zuwanta asibitin bayan haka sun yanke shawarar canza mata suna duk dan kada a gane itace. Godiya su Aneelerh suka dinga yiwa chief kamar zasuyi mashi sujjada, har saida taj yace su daina baison ana yi mashi godiya kafin suka dakata har cikin ransu sunji dadin hadin kan da suka samu a wurin shi........" Unaisah kamar jira take su kammala maganar, tana ganin sun nufo wurin ta, jiki na 6ari ta miƙe ta nufesu, murmushin farin ciki suka saki, da sauri Aneeelerh ta ɗauketa kamar karamar yarinya ta rungumeta a jikin ta, zahra sai jin dadi take yau gata ga yarinyar data kwallafa rai akai. Su uku suka zauna kan sofas din, taj da chief suna zaune can inda suka baro. Aneelerh ta kasa janye idanunta daga kan Angel, tayi mamakin girman ta, ga wata madarar kyau da tayi komai nata ya canza mata, sai faman sakar ma juna murmushi suke yi. "Aunty aneelerh, daddy Ya faɗa min kin haifa min baby boy, Yana Ina? "Angel, ƙanin ki junaid Yana a school, bawan Allah, Kullum burinshi yaga Angel, Yana matukar sonki Angel, tun yana jariri nake nuna mashi hotunanki, Yasan komai dangane dake ganinki ne kadai bai ta6a yi ba...." marairaice fuska tay kamar zata fashe da kuka "Ina son ganin shi..." da sauri zahra ta lalubo hoton junaid awayarta ta mika ma Unaisah, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin karbar wayar, ta kura mashi ido tana kallon ɗan kyakkyawan yaron aunty aneenerh, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskarta, hada videos dinsa ta kalla. "Aunty Aneelerh, fuskarshi kamar anyi photo copy din fuskarki, dake yake kama, Wallahi harna ƙosa mu haɗu da ɗan ƙanina, In rungume shi a jikina in ji ɗumin shi, Ya Allah nagode maka da ka nuna min wannan ranar, ga ni ga aunty na, ga ɗan kanina da zan gani wayyo dadi...." zahara dake kallon ta ji take kamar ta rungumeta, Yarinyar tajima da sace zuciyarta, tun ranar da suka hadu awurin dinner din hateem ashe da rabon su sake haduwa matsayin yar uwar mijin auntynta...... "Angel ga zahra, itace ta ɗauko min hotonki awurin dinner, ɗiyar uncle dina ce..." sai lokacin Angel ta dubi zahra dakyau, nan take ta gane fuskarta, da sauri taje ta rungume zahra, fuskar kowan nan su da murmushi.... "Angel ina tayaki murnar ganin auntynki, Nima nayi murnar ganinki, wallah ba zan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, naji dadi dana zama silar haduwarku...." ta ƙare maganr tare da raba jikinta daga na Unaisah, share mata hawaye tayi da tafukan hannayenta"ki daina kuka kinji, Allah yakamata muyiwa godiya daya sake hadaku, naga ma kamar baki da lafiya, fuskarki ta kumbura, Jikinki da zafi..." cikin kulawa da nuna tausayawa tayi mata maganr Cikin sanyin murya tace"lafiyana lou, babu abunda ke damuna, farin cikin ganin auntyna ne" ta fada tare da kallon Aneelerh dake kallon ta. Wayar Aneeleerh ce ta fara ringing, ta ɗauko bag din data bari kasan sofa ta zaro wayar "Tun bayan da chief ya kiraku wayarki take ta ringing, banaso na katse maku tattaunawarku shiyasa ban kawo maki ita ba..." murmushi aneelerh tayi aranta ta ayyana har yanzu tana nan da wayonta, ga hankali Ko da ta duba screen din wayar missed calls ta gani sunkai ashirin, daga wurin mutun uku hajiya layla da dr shurem dana mami din su.. Unaisah zan amsa kira" amsa wa tay da toh, mikewa aneelerh tayi ta nufi gefe ɗaya, tabar zahra zaune tare da Unaisah kamar wasu kawaye haka suka fara fira Hajiya layla ta fara danna wa kira, bayan sun gaisa hajiya layla tace"Aneelerh ya ake ciki? Naji shiru baki kirani ba, ko dai iyayen yarinyar basu bamu ita bane? Wallahi jiya ko baccin kirki Benazir batayi ba, tana ta sambatu tana ambaton sunan yarta .." "Ki cigaba da kwantar mata da hankali, nayi magana da iyayen yarinyar sun bamu ita, amma sai zuwa anjima zata zo asibitin" Muryar Hajiya layla da alamun farin ciki ta furta"Alhamdulillah!....wallahi naji dadi Aneenerh, dan Allah kuyi mana godiya wurin iyayanta..." Murmushi Aneelerh tayi"in sha Allah zanyi masu" sallama sukai da juna, ta sauke ajiyar zuciya, idanunta akan su unaisah, wani irin sonta ne ke kara baibaye zuciyarta, Layin mami ta kira, ko sallama Aneelerh bata kaiga yi ba, mami ta katse ta da cewe"Aneelerh sai yanzu zaki kirani? Baki ga missed call dina bane? Kunsa inata zullumi, na kasa tsaye na kasa zaune..." "Allah sarki mami, Yanzu na dauko wayar, banga call din ki ba" "Toh ya ake ciki ne"? "Mami, mun ga yarinyar, dagaske ba unaisah bace, zahra tayi kuskuren fada mata sunan ta, ashe ita wannan sunanta Azeezaty, suna bala'en kama da unaisah, amma iyayen yarinyar sun bamu aron ta har zuwa time da benazir zataji sauƙi" "Toh Aneelerh, har naji sanyi wlh, yanzu zakuje asibitin ne"? "Mu zamu tafi, ita kuma yarinyar sai zuwa anjima da dare za'a kaita" "Allah yakaimu lafiya" ameen mami, daga haka sukai sallama da juna, komawa tayi wurin su unaisah suka cigaba da yin firar yaushe rabo, chief tuni ya shige gidan saboda yana son ya fita office, zama taj yai a wurinsu suka dinga sanya juna nishadi, ana tuna rayuwar baya, har wuraren ƙarfe 9 na safe kafin su Aneelerh suka mike zasu tafi, Angel kamar tay masu kuka taso su shiga ciki suka ce a'a sai zuwa na gaba suna sauri ne, dakyar taj ya lallashe ta yace ta koma gida, zaije ya rakasu, tana ji tana gani ya tafi da su aneelerh, a motarshi yakaisu cikin estate din inda suka bar motarsu, sai da ya tabbatar sun tafi kafin ya dawo. ________________________________✍️ Fitowa dr shureim yayi daga bedroom dinsa, Ya kimtsa tsaf cikin shigar su ta larabawa, hannun sa ruke da wayarshi, har ya fara tafiya kiran Aneelerh ya katse mashi hanzarin shi, da sauri yai picking tare da kara wayar a kunnansa "Assalamu alaikum Aneelerh, barka da safiya, fatan kun wayi gari lafiya" On the other hand Aneelerh tace"lafiyalou Alhamdulillah, Ya shureim.." "Tun ɗazu nake ta kiran layin ki don inji Ya ake ciki game da yarinyar an dace ko kuwa"? "Yaya shureim, mu hadu asibitin zanyi maka bayanin komai" amsa mata yayi da toh, kafin sukai sallama, a tsanake Ya nufi falo, tunkafin Ya isa ya hango mutanan gidan a dining sun hallara sunayin breakfast, "Shureim har ka kammala shiryawa"? alhaji ubaid ne yai masa maganar "Eh daddy..." ya faɗa tare da gaishe da su, Alhaji musa yace"ba zakayi breakfast din bane"? "Idan naje can zanyi..." "Okey, Hajiya sarah tace"in sha Allah idan na taso daga office zanbiyo asibitin.." "Allah ya kawo ku lafiya..." satar kallon zeenatu yayi, hannunta ruke da cup tana shan tea, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido ɗaya...lamarinta ya fara bashi tsoro yarinya kamar mai iskokai? "Zeenatu ba zaki bini mu tafi ba"? "Ina zamuje"? "Asibiti wurin auntynki benazir.." maƙe mashi kafada tayi"bana jin dadi, bazan iya zuwa ba, ka tafi kawai..." da mamaki hajiya sarah take kallon ta "Zeenatu! Kin kuwa saurari abun da yace maki dakyau? Asibitinne ke bazaki je ba? Dallah tashi ki bi shi ku tafi, idan kika zauna gidan me zaki yi ke kadai? Daddynki ma fita zaiyi..." bata kare maganar ba, Alhaji musa ya katse ta da cewa"ba ki ji tace bata da lafiya ba? Rai a6ace hajiya sarah tace"amma ay lafiyarta qalou, ni banga wani alamun rashin lafiya atare da ita ba..." Alhaji ubaid yace"shureim ka tafi kawai, Kada ku takura mata, tun da ba koshin lafiya gare ta ba, ni bana so ma taje asibitin taita kuka kamar jiya da mukai ta fama da ita...." jiki asanyaye dr shureim Ya miƙe idanunsa akan fuskar zeenatu, itama kallon nashi take Yi, ji take kamar ta tashi tabi shi sai dai ta kasa kamar ana ruke kafafunta, a hankali Ya juya yana tafiya kamar babu kuzari a jikin shi, bakomai yake tariyowa ba face kalamanta! Meyasa zeenatu ta canza daga jiya zuwa yau? Ya jefawa kansa tambayar da baida amsarta!! *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 31 by Boss Bature by Novels Elite Admin August 27, 2024 Takun Ƙarshe Bayan komawar Unaisah cikin parlour, a dining room ta hango ƴan uwan ta, har sun fara yin breakfast sunyi neman ta har sun gaji ba su ganta ba, suna jin takun tafiyarta gaba ɗaya suka dago suna kallon ta..... "Sister! Ina kika shiga muna ta neman ki"? Batool ce tayi mata maganar, bata tanka masu ba, sai faman sakin murmushi takeyi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Allah, yau ranta fari fess, cike da zumudi taja kujera ta zauna tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, tasan in har ta sanar da su Azeeza game da zuwan auntyn ta aneelerh ba karamin dadi zasu ji ba saboda tasha basu labarinta agidan kurkukun ƙaddara, abunda bata sani ba tun da ta zauna suke ta kallon ta "Aunty ummi Ina kwana.. " wani kallo ummi tabi ta da shi, har saida tasha jinin jikin ta Kafin ummi ta furta kalma Sajeed Ya riga ta cewa"Sister baki da lafiya ne? ko kinyi kuka ne"? lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya canza! Kwata kwata ta manta da abun da ya faru daren jiya, saboda murnar zuwan Aunty Anila, maganar sajeed ce ta tuna mata, tuni murnar da take yi ta koma ciki. "Sister kinyi shiru baki ce komai ba? Meke damunki"? Cike da tashin hankali batool tayi maganar, su Parveen duk sun kura mata ido suna kallonta, jemimah tace"le6enki ma ya kumbura kamar yankan tumatur" "Unaisah! Lafiyarki kuwa"? Acewar ummi ta faɗa tana kare mata kallon ƙurulla Adabarbace ta furta"am.. Umm.." sam ta kasa ƙarasa maganar, idanunta azazzare take kallon su. gani take kamar sun san komai daya faru da ita adaren jiya, da sauri ta miƙe jikinta na kerma tace" aunty ummi babu komai, ba abunda ke damuna, lafiyana lou..." bata ƙare maganar ba, kamar mara gaskiya ta nufi hanyar fita daga dining room din zuciyarta cike fal da tashin hankali Gaba daya sun lura da tashin hankalin dake akan fuskarta Deeja na dariya tace"wallahi Allah kumatunta sun kumbura suntum kamar alkubus, wama ya sani ko bugun tsiya akai mata..." bata kare maganar ba, Haris ya toshe bakin ta.. Miƙewa ummi tayi sam hankalin ta bai kwanta da yanayin unaisah ba, miƙewa batool tayi da niyar tabi bayansu, da sauri ummi ta dakatar da ita"ki zauna ku karasa cin abincin, zanji da ita" jiki asanyaye ta amsa mata da toh.. Da sauri ummi ta nufi dakin su Unaisah, tana shiga tajiyo sautin kakarin amanta a toilet kamar zata fasa makoshin ta. Knocking ƙofar toilet din tay"unaisah ina son magana dake" Fitowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye, hannun ta ruke da ɗan pant din ta. "Meke damunki ne"? tana faman jan numfashi tace"bakomai aunty ummi..." katse ta ummi tayi"kada kiyi min karya, yanayinki ya riga ya nuna baki da koshin lafiya, kawai ki fadamin meke damunki! Idan ba haka ba hankalina ba zai kwanta ba..." cikin nuna damuwa tayi maganar, shiru tayi jim tana tunanin ko dai ta fada mata watakil ta taimaka mata.... Miƙa mata pant din hannunta tayi, waro ido ummi tayi"me zanyi da shi" matse shi tayi, tana faman noƙe kai tace"jiya da tsakar dare na tashi da matsanancin ciwon mara, kamar bazan rayu ba, bayan na shigo toilet na duba sai naga jini ne ya dawo min" cike da jin tausayinta ummi ta ruko hannunta suka zauna gefen gadon. "Sannu unaisah, wallahi daga gani kin ji jiki ba kaɗan ba, meyasa a daren baki neme ni ba? Ay da na taimaka maki, halan ko magani baki sha ba"? "Ban shaba ba aunty ummi, saboda naji saukin ciwon, kuma lokacin dana farka da safe banga jinin ba ya dauke! Aunty ummi dama Yana haka"? ɗaga mata kai ummi tay alamar eh"kada hakan ya dameki, nima sometimes yana yi min haka yaje ya dawo, in har bai wuce kwanaki goma shabiyar ba, to still jinin ne, amma da zarar kinji ya dauke duf babu shi sai kiyi wankan tsarki ki cigaba da sallah" ajiyar zuciya unaisah ta sauke, sam tagaza fada mata abun da ya faru jiya. "Me kike son nuna min a jikin pant din . " cike da jin kunyarta tace"wani abune da nake gani kamar kunu gayanan kyankyamin shi nake ji .." kiris Ya rage ummi ta fashe da dariya ganin yadda ta kwa6e fuska tana gwale la66anta. "Nuna min in gani .." buɗe mata pant din tayi. Shiru ummi tayi jim alamar tana nazartar abunda ta gani, tabbas sperm ne amma meya kawo shi? Cos Bata tunanin unaisah ta fara feelings...rayawa tayi aranta watakil ba abun da take tunani ba ne "Unaisah, dole fa sai kinyi takatsantsan, kamar yadda nayi maki bayani zan ƙara jan kunnanki, daga yanzu kada ki kuskura ki ƙara ba wani namiji damar da zai ta6a jikin ki, ko da ruƙe hannunki ne! In ba haka ba ke zakija ma kanki zunubi, saboda duk wasu hukunce hukunce na musulunci sun hauki, Idan kika aikata mai kyau za'a rubutaki, haka zalika idan kika aikata zunubi za'a rubuta maki. .."nan dai tayi mata takaitaccen bayanin dalilin dake kawo hakan dallah dallah yadda tasan zata fahimta, hankalin unaisah ba karamin tashi yayi ba. "Kuma idan kika bari Namiji yana wasa dake yana tattabaki, you can get pregnant, a yadda kike ƙaramar nan har ranki zaki iya rasa wa...." ummi bata kare maganar ba Unaisah ta daura hannayenta biyu akai la66anta na kerma ta furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un...." da biyu ummi ta fadi hakan saboda taja mata kunne. Tayi mamakin ganin Yadda jikinta ke kerma, da gudu ta fada toilet taja kofa ta datse.. " lamarin ya daurewa ummi kai, arude ta mike tana kwala mata kira"unaisah! Unaisah? Lafiyarki kuwa? Meya faru? ko dai maganar dana fada ce? To meye na damuwa"? Shiru bata amsa ba, bugun kofar ummi ta dinga yi kamar zata balle ta"ki bude min kofa, keda baki jira kin karasa jin me zance ba, meye na tada hankali kamar baki da gaskiya"? Ta faɗa tana kumshe dariya a bakinta saboda ta bata dariya. "Unaisah, ki fito muyi magana, watakil baki fahimci me nake nufi ba, zan yi maki bayani..." cikin disasshiyar murya ta furta"aunty ummi ki tafi dan Allah, cikina ne Ya katsa, idan na gama zan same ki a daki muyi magana" ajiyar zuciya ta sauke"shikenan zan jiraki" Sai da taji alamun ummi ta fita daga dakin, kafin ta fito fuskarta sharkaf da hawaye baiwar Allah, hankalinta yayi matuƙar tashi, ta raza da jin kalaman ummi, fargabanta kada ta samu ciki! Wani irin ciwon kaine Ya farmata, ga wani bacci da ta fara ji mai hade da kasala, Pant din da ta bari kan floor ta ɗauko ta koma toilet din, Wankan tsarki tayi tare da alwala, daga bisani ta fito sanye da towel, da wata irin kasala ta dauko wasu kayan tasa tare da hijab ta zura a jikin ta. Bayan ta kammala sallah ta zauna kan darduma ta ɗaga hannayenta tana addu'a hawaye na sintiri kan kuncinta, ko da ta gama bata motsa daga kan dardumar ba. Bakomai ne Ya faɗo mata aranta ba face Danish, ko ya ci abin ci? taga bata ganshi a dining ba, har cikin ranta ta damu da shi, bata son yana ke6e kan shi a ɗaki, batasan meke damunshi ba... "Sister dina!" muryar batool ce ta katse zancen zucinta, da sauri ta mike tare da juyawa ta kalle ta.., sam babu walwala atare da ita, duk ta damu da yar uwartata "Dan Allah ki fadamin meke damunki" ƙaƙaro murmushi tayi akan fuskarta "Calm down your mind! Ni Ba abunda ke damuna, lafiyana lou, ciwon ciki nayi jira da daddare naci wahala sister, amma yanzu da sauki jikin nawa..." huggin dinta Batool tayi sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta. "Ni kadai na kwana jiya adaki" tausayinta ne Ya kara kama Batool "Da na sani jiya na tayaki kwana, amma kodan saboda ke zan dawo kwana dakin nan" Murmushi unaisah tayi"kada ki damu, ay naji sauki ma" Kallon dakin Batool tayi"duk yayi datti bari na taimaka maki" "Nagode sister," ta fada tare da zama kan mirror chair tana jiran batool ta kammala gyaran. "Sister an kaiwa danish abinci a dakin sa"? "Eh, Haris Ya kai ma shi, ni bansan meke damun shi ba, kema kin lura da yanayin shi naƙin shiga cikin mu"? Ta faɗa a yayin da takai hannu tajanyo zanin gadon da yayi uban squeezing kamar an ƙwatoshi daga bakin kura. "Batool na lura, abun yana damu na, nayi masa faɗa yaƙi dainawa to ya zanyi da shi? ta faɗa da damuwa akan fuskarta"ko da yake halinsa ne ko a prison bai fiye shiga cikin mu ba, yafi son yaganshi kwance kan gado" daurewa kawai takeyi sam bata son batool ta fahimci halin da take a ciki. Adai dai lokacin Batool ta fara kakka6e zanin gadon, Kwatsam ba zato ba tsammani unaisah ta hango zoben da ya faɗo ta cikin bedsheet din..saukowa tayi daga kan kujerar, ta nufi inda Yake ta zuƙunna tana kallon shi, zoben azurfa ne sai kyalli yake a hankali tasa yatsanta daya ta ɗago da zoben, hankalin batool kwata kwata baya akanta, sai surutu takeyi mata.... Ƙura ido tayi sosai akan zoben, was wasi ta fara yi kamar wanda prime minister ya ba danish❗ Anya kuwa shi ne?❓ kokwanto ta shiga yi, tayaya akai zoben ya shigo dakin su idan na shi ne ...? yunkurawa tayi a sukwane ta mike, batare da sanin batool ba, ta fuce daga dakin. "Sister jiya kafin mu kwanta aunty ummi ta kunna min kallo a laptop din ta...." dakatawa tayi da yin maganar ganin babu kowa adakin. "Unaisah! Unaisah! "ranta ne Ya bata kodai ta shiga toilet, hakan yasa taci gaba da gyara mata dakin......." ________________________________✍️ Prisoners shield💔 Fitowa yai daga toilet, jikinshi a sanye da bathrobe, baijima da tashi daga bacci ba Ya shiga wanka, yayi wani fresh dashi, sumar kanshi ta lullu6e bayan shi. Walking slowly Ya nufi dressing mirror, zuciyarshi cike fal da tunanin Angel dinsa, yayi maraicin ganin ta idanunsa sun kwaɗaita da son ganin ta, tun safe baici komai ba, abincin da haris ya kawo mashi yana nan ajiye kan table ko buɗesa baiyi ba. Har ya yunkura zai zauna kan mirror chair, sautin knocking din kofar Ya dakatar da shi . .... Cike da zumudi Ya nufi kofar, fatan shi Allah Yasa Angel dinsa ce, Buɗe ƙofar yayi a hankali, tun daga kasa Ya fara kallon ta, ko takalma babu a kafarta kamar an korota, Gown din jikinta tayi mashi kyau sauke idanunsa yayi akan fuskarta har saida gaban shi Ya faɗi, ganin yadda ta kumbura gashi babu fara'a ko kaɗan ta haɗe rai, ido cikin ido suke kallon juna har na tsawon mintuna biyar kafin sanyayyar muryarshi ta katse mata shirun ta "Mu shiga ciki" yayi mamakin ganin batayi mashi musu ba, ta nufi ciki da sauri yabi bayanta, a tsakiyar dakin suka dakata "Meke damunki? Idanunki sun kumbura kamar kinyi kuka, faɗamin waya ta6a min ke" Lumshe idanunta tayi kafin ta buɗe su a hankali. Takawa tayi har zuwa gabanshi ta tsaya suka fuskanci juna "My man, Ina zoben da prime minister Ya baka"? Cike da fargaba Ta furta maganar ita kanta tsoron amsar da zai bata take ji saboda bata son zargin da take yi ya tabbata. da sauri Danish Ya ɗago da yatsun hannun shi Ya kallesu kwata kwata babu zobe aruɗe ya furta"ban gan shi ba, bansan a ina ya faɗi ba, bari na duba toilet watakil na manta shi a ciki" Juyawa yayi da sauri ya nufi toilet ya shige ciki. tana atsaye cikin jin kunar rai, take kallon shi har ya 6ace ma ganinta, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshinta, hankalin ta yayi mugun tashi, zuciyarta ta karaya jikinta yayi sanyi, ta gaza yarda da abunda take zargi!! dagaske danish ne ya aikata mata rashin imanin nan? babu tausayi babu imani Yana ganin tana fama da azabar radadin ciwo ahaka Yayi abun da yakeso yayi? Tunawa tayi da lokacin daya wurgar da ita kan gado, Ya sa hannu Ya hambareta har kanta Ya daki pillow, abun ya tsaya mata aranta. Fitowa yayi daga toilet din, ya ɗago suka hada ido, wani irin faduwa gaban shi yayi ganin kallon tuhuman da take jefa mashi, tuni yasha jinin jikin shi "My man, kaga zoben"? La66anta na kerma ta furta maganar Girgiza mata kai yayi"ban gan shi ba, bansan a ina Ya faɗi ba..." Murmushin takaici ta sakar mashi, kafin tace"Ni na ganshi"! da mamaki Ya kalle ta, hannu ta zura cikin aljihun gown din, ta zaro zoben ta miƙa mashi "A ina kika gan shi"? ya faɗa tare da matsowa kusa da ita, ya miƙa hannu zai karba, daddagewa tayi da iya karfinta na karshe ta ware yatsu biyar ta wanka mashi zazzafan mari kan kun cin shi, tashin hankalin da ba asaka mashi rana! lamarin ya gigita shi da sauri ya dafe kun shi, jikinsa na 6ari ya ɗago amatuƙar ruɗe ya kalli fuskarta...la66ansa na kerma ya furta"my.. Angel? Kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kika mara"? Harara ta watsa mashi da kakkausar murya ta furta"idan akwai abun da yafi mari zanyi maka shi! Mugu Azzalumi, fasiki ɗan iska... " waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata fado ƙasa He was completely confused "Danish me nayi maka dana cancanci haka daga gareka? Danish kaida kanka? Sai yanzu na gane dalilin dayasa ka tsareni jiya akan in faɗa maka idan na fara period, dama abunda kake jira kenan, Ina fata yanzu hankalin ka Ya kwanta, tunda ka samu abunda kakeso ...." rushewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai, bawan Allah Yama rasa bakin magana, har yanzu baisan kan me take magana ba, ko kaɗan baiji zafin marin da tayi mashi na, babban tashin hankalin shi miya faru da ita a daren jiya❓ "Kiyi min bayanin meya faru dake"? Tsawa ta daka mashi kamar zata rufe shi da bugu tace"kana nufin kamanta abunda kayi min? Saboda ba damuwarka bace in rayu ko in mutu ko"? Ta fada tana cije la66anta da hawaye suka jiƙa su. "Idan ka manta bari na tuna maka, jiya ka shiga dakinmu da daddare...." zayyana mashi komai tayi tunkafin ta karasa gabansa yayi wani irin mugun bugu na tashin hankali, miƙa mashi zoben tayi"a jikin zanin gadonmu na tsince shi, ina fata yanzu ka tuna komai....." Runtse idanunshi yayi, wani irin ƙunci yaji aran shi, jikin shi ya hau yin kakarwa kamar wanda Sanyi ya kama . shirun da yayi ne ya ƙara tabbatar mata da zarginta akanshi.....amsar shi kawai take jira.. Duk da bata bukatar wannan "Bani bane! Bazan Iya cutar dake ba Angel! bansan ya akai zobe na Yaje dakin ku ba..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wlh yafi ta jin radadin abunda akai mata, yaji zafi kamar ya fasa ihu! Wai Angel dinsa ce wani yayi ma wannan aika aikar? "Danish baka ta6a min karya ba sai yau, baka da wata hujja da zaka kare kanka awurina, zoben ka ba ƙafa gare shi ba, balle kace shi yakai kan shi dakina...Danish meyasa kayi min haka? Ko amafarki ban ta6a tunanin zakai min haka ba? A zato na kai garkuwane agareni mai bani kariya a duk lokacin da wani yayi yunkurin cutar dani sai gashi kai da kanka ka cutar dani, saboda idonka Ya makance burinka kawai ka samu abunda kake so ko"? Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya saboda wani irin sara masa da yai, ƙafafunsa sungaza daukarsa baisan sa'adda Ya zube kan gwiwowinsa ba. Ya rurruƙe ƙafafunta da hannayen shi, hawaye na fita ya furta"Unaish ki yarda dani! Ban ta6a maki karya ba, bani bane! Bansan wanene yayi maki aika aikar nan ba! Garkuwarki bazai ta6a cutar dake ba, ni aikina shine baki kariya kamar yadda kika faɗa" ya faɗa yana fitar da huci mai zafin gaske "ki tausayama rayuwata, kada ki yanke min hukunci akan laifin da bani na aikata ba! nayi maki alkawarin zan gano koma wanene yayi miki hakan ..." cikin rauni na murya ya ƙare maganar, yana kallon cikin idanunta. cike da jin tsanar shi ta sa kafa ta buge hannayenshi daya ruke kafarta da su, ta soma ja da baya tana fadin"wallahi bana son ganinka! Ka fita araina Danish! Na tsaneka! Ka 6ata komai, kullum burina in faranta maka rai ashe kai ba haka bane awurinka, abin da baka sani ba ni nema nake na nema mana hanyar da zamu mallaki juna na har iya tsawon rayuwarmu, sai dai kash gajen hakurin ka da son zuciyarka sun ja maka wurga mashi zoben tayi kan kirjin shi, da gudu ta juya ta fuce daga dakin. Jiki amace ya kwanta kan floor, hawaye suka cigaba da sintiri kan kuncinshi, ga wani azababben ciwon kai da yake ji, tuni zazza6i Ya lullu6e jikin shi, ɗaukar zoben yayi a hannunshi Ya kura mashi ido yana kallon shi, ya rasa ya akai zoben yaje dakin su?wa ya kai shi? Wanene Ya cutar mashi da Angel dinsa? sambatu ya fara yi"bani bane! Bazan iya cutar dake ba! Ni garkuwa ne agareki mai baki kariya, kada ki juya min baya, bana jin zan iya rayuwa batare dake ba, Angel kada ki fushi dani bani bane❗❗❗ Gaba ɗaya kalamansa acikin kunnanta, tana a durkushe bakin kofar dakinsa tana kuka kamar ranta zai fita, ganin lamarin take kamar a mafarki! wai Danish dinta ne yayi mata haka? Wlh ya karya mata zuciya! Ya kunsa mata kiyayyarshi, duk irin burin da taci na son ganin sun rayu a karkashin inuwa ɗaya ya ruguza komai.... Jin motsin mutun yasa tayi saurin share hawayen ta, jiki ba kwari ta miƙe daddynta ta hango yana shigowa, da alama Ita Yake nema... Sai da ta fara daidaita nutsuwarta kafin ta sauko down ta nufe shi, sam baiji takun tafiyarta ba, sai dai Yaji ta faɗa kan bayan shi ta rungumeshi, bata san sa'adda ta sake fashewa da wani kukan ba, duk yadda taso ta shanye shi takasa har saida Taj yaji, gaba daya yabi ya rikice, kafin yayi yunkurin ruko ta da gudu tabar jikin shi, ta nufi dakinsu ta shiga, a lokacin Batool ta jima da fita, kan gado ta haye ta kifa kanta jikin pillow ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita. da gudu Taj Ya faɗo dakin, Ya hau har saman gadon, jikin shi har kerma yakeyi tsabar rudu da tashin hankali, janyota yayi da karfi ya rungumeta sosai a kirjin shi, muryar shi na rawa ya furta "Unaisah! my Angel! Meya faru? Waya ta6a mun ke? baki da lafiya ne? fuskarta tayi sharkaf da hawaye, hatta temperature din jikinta ya dauki zafi rau. "My Angel meke damunki? Dan Allah kiyi min bayani? Ko baki da lafiyane?" sai da tayi kukan mai isarta kafin ta raba jikinta daga nashi ta sauko daga kan gadon, ta nufi toilet ta shige, jim kaɗan ta fito da alamun ruwa akan fuskarta...tsayawa tayi nesa da shi tana faman sauke ajiyar zuciya. "Zonan Unaisah" Ya kirata fuskarshi babu walwala, kamar babu laka a jikin ta ta karasa tare da zukunnawa ta zauna kasan gadon, saukowa yayi ya zauna suka fuskanci juna Ya ruko hannayenta a cikin nashi"fada min meke damunki? Meyasa kike kuka? Shiru tayi jimm har cikin ranta bata jin zata iya tona mashi asiri, koda zuciyarta zata buga saboda bakin cikinsa, ta ƙwammace tabar abun aranta. "daddy dan Allah kada ka tambayeni meke damuna, ka tayani da addu'a, in sha Allah zanji sauƙi.." ta faɗa tare kwantar da kanta saman kafadarshi, ɗaura hannun shi yayi akan bayanta yana dan shafa shi cikin sigar lallashi yace"kiyi hakuri duk da bansan meke damunki ba, tun da kin nuna bakison in tambayeki dole in hakura, amma dan Allah kada ki sanya damuwa aranki! Ki kai kukan ki wurin Allah, Nima zan tayaki da addu'a in sha Allah.." lumshe idanunta tayi har yanzu bata daina jin kukan ba... "Daddy, Inaso nayi nesa da gidan nan, na wani lokaci..." tun da yaji wannan maganar Ya fahimci akwai wanda Ya 6ata mata rai, a sannu zai gano koma wanene. dagowa tayi a hankali suka kalli juna, idanunta sun ƙanƙance sun kaɗa jawur saboda kukan da ta sha.. "Daddy, Ka kaini part dinka, in zauna gurin Aunty danejo, ko kuma ka kaini wurin aunty Aneelerh dan Allah" marairaice mashi fuska tayi kamar zata fashe da kuka, kallonta kawai yakeyi gwanin bantausayi, arayuwarshi yatsani duk wani abu da zai ta6a lafiyar yarsa, bai son damuwarta. "Daddy kayi shiru bakace komai ba"? Numfasawa yayi kafin Ya furta"magana nakeso nayi dake, shiyasa na shigo gidan nan, sai kuma na taras da abunda Ya 6ata min raina..." "Ka yi hakuri daddy, na daina kukan ay, ba zan kara sanya damuwa araina ba..." ta faɗa tare da ƙaƙaro murmushi akan fuskarta. Kwantar da ita ya kuma yi ajikin shi don ta samu relief din abunda ke damun ta.. Calmly ya fara zayyana mata maganar da suka tattauna da su chief "Ita mara lafiyan yar uwarsa ce, kuma kawar auntynki Aneelerh, tana a kwance gadon asibiti kwata kwata bata acikin hayyacinta tun lokacin data rasa yarta da mijin ta, likita yace idan har ba asamo yarinyar da zata iya acting kamar yartaba, to zata rasa ranta ne..." ɗagowa Unaisah tayi a hankali ta kalle shi da alama taji tausayin matar. "Muna so kije a matsayinta Unaisah, nasan zaki Iya!" "Daddy na amince muje asibitin, dama najima ina neman hanyar da zan kyautatama chief, na ji dadi data kasance yar uwar shi, Allah yasa in zama silar samun warakarta .." murmushi taj yayi "Ameen, amma akwai abunda nakeso in ja maki kunne akai! Idan har muka kaiki asibitin kada ki kuskura ki faɗa ma wani ina raye! Ko ki bayyana wacece ke! Saboda har yanzu rayuwarmu tana acikin hatsari akwai masu bibiyarmu unaisah! Waɗanda suka kashe uzair zasu iya kashe ni idan sukaji ina raye!" cikin matsananciyar damuwa yayi mata maganar donta dauki abun serious...girgiza kai tayi"daddy bazan bari kowa ya sani ba, saboda bana so na rasa ka" "Koda wani ya nuna ya sanki ki ce bake bace, kinji"? Ɗaga mashi kai tayi... "Ko kinsan mutun kika ganshi kada ki tanka mashi ko ki nuna kin sanshi, tun da haryanzu bamu san wanene ya sadaukar dake ba!" Gefen fuskarta yashafa da hannun shi, ki fara shiri zuwa anjima da daddare zamu tafi" ta amsa mashi da toh, jan ta da fira ya farayi duk don ya faranta mata rai ko ta manta damuwar da take a ciki....... ______________________________✍️ wuraren ƙarfe biyar, A jere motocin su Alhaji musa suka kunno kai cikin asibitin, A parking space suka dakata, da sauri body guard din dake driving din sa ya fito ya bude mashi mota, gently ya fito, ya ɗauki wankan shadda mai ɗaukar ido, fuskarsa na sanye da mask, Iya idanunsa ne kadai zaka Iya gani, fitowa Alhaji ubaid Yayi daga motar, a tare suka nufi ciki, wani irin farin jini ne da shi duk inda ya gifta satar kallon shi ake, daga nurses har drs din kai harma da visitors. Duk da ya 6oye fuskarsa hakan bai hana wasu gane shi ba, cikin girmamawa likitoci ke gaishe da shi wasu kamar zasu durkusa ƙasa, cikin isa Yake ɗaga masu hannu batare daya furta magana ba.... Kafin su karasa ga medical room din, suka hango dr shureim tare da Aneelerh da zahra atsaye suna tattaunawa.... "Shureim"! Alhaji ubaid ne Ya kira sunan shi, kusan atare zahra da Aneelerh suka dago tare da kallon su...Rass Aneeleeh taji gabanta ya faɗi ba ita ba hatta zahra saida taji wannan yanayin datayi tozali da Alhaji musa, Yayi matukar jan hankulansu... Ƙura mashi ido Anila tayi, a lokacin dr shureim Ya karasa wurin su, kamar taso ta gane wanene, sai ta ga kamar uncle din benazir, bazata ta6a mantawa da ɗan tahalikin nan ba, saboda kyautatawar da yayi masu tun da kuruciyarsu, kafin daga baya lokacin daya taka matsayi mai girma gaba ɗaya suka daina jin duriyarshi. "Aunty Aneelerh wanene wannan"? "Kamar uncle din benazir, banga fuskar dakyau ba amma inaji araina shi ne. ." bata ƙare maganar ba, su Alhaji ubaid suka karaso wurinsu, atare suka haɗa baki wurin gaishe da su Alhaji ubaid ne kadai Ya amsa masu, da fara'a Yace"Aneelerh sannunku da kokari, Ya mai jikin"? Ita yake yi ma magana amma hankalin ta na akan Alhaji musa ya wani kau da ido kamar bai gan su ba. "Alhamdulillah daddy, Jikin nata da sauki ba kamar jiya ba" "Aneelerh ga Uncle musa ku gaisa ko baki gane shi ba..." dr shureim ne ya faɗa Murmushin yake ta saki"ina wuni..." ƙasa ƙasa da murya ya furta"lafiya..." zahra na gaishe shi ko kallo bata ishe shi ba, Ya wuce Ya nufi dakin Alhaji ubaid yabi bayan shi. jinjina kai zahra tayi aranta ta ayyana wannan wani irin mutunne? daga gani Yana da girman kai da izza. "Shureim ko dai Ya manta dani ne? Naga kamar bai gane ni ba, duk sai naji ba dadi..." Shiru shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin halin ko'in kulan da alhaji musa Ya nuna ma Aneelerh ba bayan ya santa farin sani... Murmushi ya ɗanyi kafin Yace"bana tunanin ya ganeki" Ajiyar zuciya taɗan sauke kafin suka cigaba da magana game da yarinyar da suke jiran zuwanta anjima... Lokacin da su Alhaji musa suka shiga dakin, Hajiya layla tana azaune kan prayer mat, hannunta ruƙe da cazbaha, kamshin turaren Alhaji musa ne Ya fara dakar hancinta kafin sallamarsu ta ja hankalin ta ga duban su, kamar taga wani mugun abu haka ta zabura ta mike tana kallon shi cike da mamakin ganin shi, saboda bata tsammanci zaizo ba tun da bai damu da benazir ba.... Tunda ya shigo idonshi na akan Benazir wadda ke kwance ta lumshe idanunta sai sambatu takeyi ƙasa ƙasa, kai tsaye ya nufi gaban gadon Ya zauna kan chair din dake fuskantarta "Sannu daughter, Ya jikin naki"? Ya faɗa tare dakai hannu Ya shafa goshin ta, a firgice ta bude ido tana kallon shi, la66anta na kerma ta furta"Uncle! Daddy! ina babyna? Ina Angel dina, dan Allah ku nemo min taj ya kawo min babyna" Lumshe ido Alhaji musa yai kafin a hankali Ya furta"calm down your mind, zansa a nemo maki ita, but ki fara kwantar da hankalin ki" rurruke hannunshi tayi acikin nata"dan Allah ku kawo min ƴata da mijina, uncle ku taimaka min kada na mutu ban gansu ba...." tun shigowar shi bai dago Ya kalli hajiya layla ba, kamar babu ita adakin, wato yafi karfin yayi mata magana. Ita ko tayi tsaye tana kallon ikon Allah, sam batayi farin cikin zuwan shi ba, gani take kamar ba alkhairi ne Ya kawo shi ba... Gyaran murya Alhaji ubaid yayi mata "Layla ya jikin nata"? "Da sauki, mun samu taci abinci har wanka na taimaka mata tayi" "Ya ake ciki game da yarinyar da Aneelerh zata kawo"? "Sai zuwa dare zata zo asibitin" "Allah Ya kawota lafiya, amma iyayenta ba su nemi komai ba"? "Sai dai sunzo zamuji" ajiyar zuciya yadan sauke "Ba kiga musa ba ne? Naga baku gaisa ba" ya fada tare da nuna shi da hannu... Harara ta watsa mashi kafin tace"ay shi yakamata ya fara yi min magana bani ba, sai kace dai Nina tursasa mashi yazo asibitin"? gaba daya maganganun da suke tattaunawa akan kunnansa ko ajikinsa. Sun ɗan jima kafin ya miƙe Alhaji ubaid Yabi bayansa suka fito daga dakin Sai da suka fara zuwa office din likitan dake kula da ita don jin karin bayani dangane da lafiyarta, kafin suka fuce daga asibitin. _________________________________✍️ Wunin ranar Danish bai leƙo ko kofar dakin sa ba, babu wanda Yasan halin da yake a ciki, kamar yadda ita ma ta killace kanta adaki, wuni tayi kudundune cikin bargo lokacin sallah kaɗai ke tada ta, tuni zazza6i ya lullu6eta jikin ta har kerma yakeyi kamar zatai hauka saboda azabar raɗaɗin da zuciyarta keyi mata, tayi kukan har ta gaji ta gode ma Allah, danish ya dasa mata tsanar shi a zuciyarta, ko sunan shi bata son ambato, hauka tadinga tana bubbuga mattress da hannayenta kamar yar dambe duk ta hargitse dakin a karshe ta fashe da kuka tana fadin"ka karya min zuciya my man, na tsane ka! Bana son ka! Bana son ganin ka! Ban ta6a tsammanin zaka iya cutar da rayuwata ba! Meyasa kayi min haka? ..." tajima tana haukanta ita kadai kamar zata zauce. Wuraren ƙarfe takwas na dare, taj ya kirata awaya yace ta shirya ta same su a parking spot, jiki na rawa na shiga toilet, dama a kagare take data bar gidan kodan ta nisanta da shi, watakil ta samu relief din radadin da heart dinta keyi mata. Bayan ta fito shaf shaf ta shirya cikin abaya, ta dauko kaya kala uku ta cusa a backpack dinta, ta goya jakar abayanta, ta zura takalmanta kafin ta dauki wayarta, babu wanda Yasan da zancen tafiyarta, harta fuce daga gidan..... Cikin sauri take tafiya kamar zatayi tuntu6e, a parking space ta hango daddynta tsaye, ya sanya face mask a fuskarshi Kallo ɗaya yayi mata ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa atattare da ita Baisan ya zaiyi da ita ba, taki fada masa damuwarta, buɗe mata murfin motar yayi, wani sanyayyan kamshin turarene Ya daki hancinta, nan take ta gane kamshin wanene da sauri ta dago ta kalli daddyn nata Murmushi ya sakar mata kafin yace"ki shiga mana" "Wanene a ciki"? Ta jafe mashi tambayar "Chief ne, tare da shi zamu tafi" jim ta ɗanyi kafin ta kutsa kai ciki, har saida gabanta ya dan fadi lokacin da ta sauke idonta a kanshi, yana daga zaune ya ɗauki wankan shadda blue sky tayi bala'en yi mashi kyau, laptop dinsa ce akan laps dinsa, ya dan lumshe idanunshi.... Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin wani irin sanyi acikin zuciyarta. Sai da ta zauna gefen shi kafin ta samu kwarin gwiwar yi mashi sallama tare da gaishe da shi... Calmly ya amsa mata... Nutsuwa tayi idon akan glass din motar da bai karasa rufewa ba, tana iya hangen filin gidan.... "Zamu Iya tafiya" chief ne Ya faɗa, security din dake zaune a driver seat Ya tada motar, A hankali Ya fara driving dinsu, motarsu big guy tana abiye da bayansu su biyu aciki tare da daddynta, sai motar jami'ansu dake abiye da su.... Lokacin da motocin suka haura kan titi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta, ta lumshe idanunta, bakomai take tariyowa ba face abunda Ya faru tsakanin ta da danish, tayi fatan ace mafarkine ba gaske ba..........bata san sa'adda hawaye suka gangaro takan kuncin ta ba, kwata kwata ta manta da chief acikin motar, Ranta ne ya bata ana kallonta, a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur, karaf idanunsu suka shiga cikin na juna..... Daga ita har shi sun kasa sarrafa kansu, wani irin kallo suke bin juna da shi mai wuyar fassaruwa Ƙamshin turarenshi ba karamin kashe mata jiki yayi ba..." Tsananin tausayinta ne Ya kama shi, har yau yana mai mamakin kananun shekarunta da kuma irin wahalhalun rayuwar da ta fuskanta, shi tunda yataso rayuwarsa baisan menene wahala ko rashi ba. "I don't want to see your tears..." *✊DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️* *Mu haɗu Jibi, Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Tags Kurkukun Kaddara YOU MAY LIKE THESE POSTS Previous Post Next Post GET IN TOUCH SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 32 by Boss Bature by Novels Elite Admin August 28, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe lumshe ido tayi ya nutsu yana kallon eye lashes dinta da suka jiƙe da ruwan hawaye ita kaɗai ta san me take ji, zaro hanky yai daga pocket dinsa a hankali ya soma share mata tears ɗinta, jin saukar hannunsa akan fuskarta yasa ta yi saurin buɗe idanunta ƙiris ya rage karan hancinsu ya gogi na juna, hatta numfashin su kokawar haɗewa yake. Kasancewar chief na bala'en kama da Danish sai ta dinga ganin kamar shi ne a tare da ita, shima haka yake nuna damuwa akanta ya bata kulawa amma sai gashi rana ɗaya ya karya mata zuciya, duk irin burin da taci akan shi na son ganin sun mallaki juna. Tuna wannan yasa ta fashe da kuka duk yadda taso ta haɗiye kukan ta kasa, da sauri chief ya kwanto da ita kan kirjin shi, hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba, hatta agent din dake driving ɗinsu saida yaji sautin kukanta...." "Sir meke faruwa ne?" Ya faɗa tare da satar kallon su ta mirror, wani shock yaji cos bai ta6a ganin chief yayi hugging ɗin macen da ba muharramarsa ba. Bakomai ya jawo hakan ba face tausayinta daya rufe shi gani yake kamar kanwarsa ce Hindu take kuka... A hankali ya zagayo da hannayansa ta bayanta, cikin sigar lallashi yake ɗan shafa shi, wani irin relief taji tuni ta nemi kukan da ta ke yi ta rasa, nutsuwa tayi akan chest dinsa ta lumshe idanunta, tana jin wani irin yanayi da bata ta6a jinsa ba, at same time heart dinsu take beating rapidly, tsit kake ji babu mai magana a cikinsu, Cheif bai ta6a tsintar kanshi a irin wannan yanayin ba yana jin wani irin feelings a tare da shi, daƙyar ya samu ƙwarin gwiwar, raba jikin shi daga nata ya tallabo gefen fuskarta da hannun shi, sam ta kasa buɗe idanunta wani irin nauyin shi da kunyarshi take ji. Sexy voice dinsa ce ta ratsa kunnanta"Tell me, meke damun ki? Me yasa kike kuka" la66anta na kerma ta ce"ba abunda ke damuna, lafiyana lou" ta rasa ya akai take jin muryarshi kamar ta Danish hakan ba ƙaramin karya mata zuciya yake yi ba, "Ban yarda ba, kuka baya zuwa saida dalili! Faɗa min ko dai baki son zuwa asibitin ne? Daddynki ne Ya tursasa maki"? da sauri ta ce "ina son zuwa, ba shi ya tursasa min ba, kawai bana jin dadin jikina ne, bansan meke damuna ba...." gaba ɗaya idanunsa na akan pinkish lips ɗinta sun jiƙa da hawaye sunyi taushi... Ya fahimci akwai abunda ke damunta, bata son faɗa masa ne, kuma bai son ya takura mata hakan yasa shi furta "Okey, ki daina kuka, Idan muka isa asibitin, zanyi magana da likita ya duba min lafiyarki..." wani irin sanyi taji ya ratsa zuciyarta, still bata buɗe idanunta ba ta amsa mashi da toh, gyara zamanshi ya yi zuciyarshi cike fal da tausayinta ya maida hankalinsa akan laptop ɗinsa, yayin da Unaisah ta ƙurawa glass din motar ido tana kallon motocin dake zarya kan titi, ƙoƙari take ta kauda tunanin Danish a ranta amma abun ya faskara.....💔 _________________________✍️ Su Aneleerh suna zaune a hospital courtyard kan kujeru su uku ita da Zahra tare da Dr. Shureim sun ƙi tafiya gida kowan nansu ya ƙwallafa rai da son ganin haɗuwar Unaisah da mamanta, duk bayan ɗan lokaci sai a Anila ta duba agogon hannunta, Zahra harta fara gyangyaɗin bacci.. "Anila anya zasu zo? Naji shiru har yanzu.." Dr. Shureim ne ya yi maganar, fuskar shi ayamutse daga gani ya gaji ba kaɗan ba, "In sha Allah zasu so, mu ɗan ƙara hakuri, ina ji araina sun kusa ƙarasowa..." ta faɗa tare da kallon zahra dake gyangyaɗi Da zolaya ta ce, "Zahra kada fa kiyi mana bacci anan, kinsan dai ba iya ɗaukarki zanyi ba, sai dai ko Dr. Shureim ya taimaka mini" murmushi ya yi tare da kallon ta, idanunta sunyi ja muryarta da kasala tace "na gaji ne, ga yunwa ina ji, ga bacci..." "Ki zo na sauke ki a gida." girgiza kai tayi, "a'a Ya Shureim kaima nasan ka gaji, bana son ma na tafi, hankalina bazai kwanta ba, in har banga haɗuwar Aunty Benazir da Azeezaty ba.." har cikin ranshi yaji dadin yadda suke nuna damuwarsu akan yar uwarsa.... Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikin su, sautin horn Ya karaɗe kunnuwansu, kusan atare suka kai dubansu ga enterance gate din asibitin, a jere motocin suka kunno kai da matsakaicin gudu suka nufi parking space.... "Ina tunanin sune suka ƙaraso" a cewar Anila, miƙewa sukayi tsaye suna kallon su cike da sa ran ganin sune. Tun kafin motocin su ƙarasa yin parking, Md Dr.Jidenna ya fito daga cikin asitin babban mutunne ya fara manyanta, gashin kanshi duk hurhura, Dr. Jazz na abiye da shi, already sun san da zuwan Chief, shiyasa suka fito don su tarbe shi.... Da sauri Jami'an Isod suka fara durowo daga kan motarsu sanye cikin kakinsu, qugunansu na a soke da kananun bindigu, Cikin zafin nama suka buɗe masu murfin motar, A hankali chief ya fito kafin Unaisah ta fito idanunta akan katafaren asibitin, a ranta ta jinjina ma haɗuwar shi, su Aneleerh na ganinta farin ciki ya lullu6e su kasancewar akwai bulbs light daya mamaye ko'ina tamkar da rana.. "Yaya Shureim sune muje mu tarbo su" Anila ce ta faɗa da sauri suka nufi gurinsu, tunkan su ƙaraso Unaisah ta hango su wani irin farin ciki ne ya lullu6eta da sauri ta nufo su, kafin ta ƙaraso Anila ta buɗe mata hannu suka rungume juna, Dr Shureim tun da ya kafe ta da ido ya kasa ƙyaftawa wani irin faɗuwar gaba ne ya dirarsa masa, ya ƙura mata ido kamar zai lashe ta, ita ko ta ƙanƙame Aunty Anila kamar karta saketa, "Sannu da zuwa my Azeezaty, tun ɗazu muke sa ran ganin ku..." Anila ta faɗa tare da ɗago da fuskar unaisah, "Ga Yaya Shureim ku gaisa, ɗan uwan mara lafiyan ne" sai lokacin ta lura da shi ita kanta da ta kalle shi saida taji gabanta ya ɗan faɗi, cikin sanyin murya ta ce "ina wuni? Ya mai jiki?" Murmushi ya sakar mata, "Mai jiki Alhamdulillah, Malama Azeezaty, ina fata bamu takura maki ba, zamu ɗaura maki ɗawainiyar jinya," murmushi tayi "Babu takura, ni naji zan iya, kuma ni abun farin ciki na ne, fatana Allah ya bata lafiya" ba ƙaramin burge shi tayi ba, yarinyar ta shiga ran shi lokaci guda sai yaji inama ace yarinyar Benazir ɗinsu ce da sai yafi kowa farin ciki. "Aunty Zahra" miƙa mata hannu Unaisah tayi suka gaisa da juna, Zahra na murmushi ta ce "Na ji dadin sake ganinki, Azeezaty tamu, mai mutunci" murmushi kowan nans u yayi. Taj dake a zaune cikin motarsu Ya nutsu Yana kallonsu Aneelerh, fuskar shi kwata kwata babu walwala. "Pls ka tashi mu fita mana" girgiza kai ya yi ba tare da ya kalli Big guy ba yace "ba inda zanje, tunda na bada Unaisah babu buƙatar in shiga ciki, ka tafi zan jira ku anan", "Wai duk akan me kake fushin nan? Saboda baka son ganin ex-wife ɗin ka?" Banza yayi dashi bai tanka mashi ba, "Meye na damuwa? Matar da bata acikin hayyacinta, kuma in banda abunka wazai san kaine? Mu da zamu 6adda kama da face mask"? A takure ya ce"Don Allah ka kyale ni! Nace ba zan je ba, ka tafi mana..." gyaɗa kai Big guy ya yi, yasa hannu ya gyara mask din fuskarsa ya fito daga cikin motar, ya nufi wurin su Chief dake atsaitsaye suna gaisawa da su Dr Jidenna. Ɗaya bayan ɗaya ya miƙa masu hannu sukayi musabaha kafin ya ɗan russina saitin kunnan Chief cikin muryar raɗa yace"Sir taj yace bazai shiga ciki ba!" juyawa Chief yayi har zuwa bakin window glass din motar yayi kncoking din ta, "Taj, ka sauke glass" zuge shi yayi, Duƙowa chief yayi suka haɗa ido da shi "Haba mutumina, mun riga da munzo asibitin shiga ciki ne zai gagare ka uhuym?" Fuskarshi a yamutse ya ce "Sir pls, bana son shiga ne, nafiso kubarni anan..." "No taj, ban amince ba," ba don ya so ba, ya ɗauko backpack din Unaisah da ya kar6a a wurinta, ya sargafo hannun jakar a kafaɗarshi, kafin ya fito daga motar, Ruƙo hannun shi Chief ya yi suka nufi su Dr Jazz atare suka haɗu suka dunguma zuwa cikin asibitin, su Anila suna a biye da bayansu ta ruƙe hannun Unaisah a cikin nata, kamar wani yace zai ƙwace mata ita. Corridor din da zai sada su da emergency ward suka nufa, cikin girmamawa Nurses da Docs suke gaishe da Chief... Sau ɗaya Taj ya saci kallon Dr. shureim, ba su ta6a haɗuwa da juna ba, lokacin daya auri Benazir Dr shureim ɗin ba ya a ƙasar ya koma Egypt da zama, sau ɗaya suka ta6a gaisawa a waya lokacin da ya kira ya damƙa mashi amanar ƴar uwarshi..." Lokacin da suka ƙaraso gaban Medical room ɗin da Benazir take sai kowannansu Ya dakata da yin tafiya. Kasancewar kofar ta glass ce suna Iya hangen Benazir dake a kwance tana bacci, Dr Adam Yana a tsaye bakin gadon Yana ƙara duba ta, Knocking kofar Dr. Jazz ya yi, da sauri Dr Adam Ya juyo ya dube su, aiko da ganin su Chief jiki na 6ari ya fito cikin girmamawa ya miƙa masu hannu suka gaisa.. Fitowa hajiya Layla tayi daga dakin jikinta a sanye da hijabi bakinta washe ta fara gaishe da su, suka yi mata ya mai jiki ta amsa masu. tunda Taj Ya kalleta sau ɗaya ya kau da idon shi gefe, ba zai ta6a mantawa da irin wulaƙancin da Hajiya Layla tayi mashi ba, hakanan ta ɗaura mashi karan tsana saboda yana son yarta, har faɗi take in banda haɗama irin na ɗan talaka ina shi ina Benazir? waye ubansa a kasar? Da aikin Jarida zai ciyar da ita? "Wama ya sani ko asiri kayi mata shiyasa ta nace saita aureka .." murmushin takaici ya saki ta cikin face mask ɗinsa..., Dr Adam Ya ce, "ina yarinyar ne?" da yake basu lura da ita ba duk ta takure bayan Anila kamar tana jin tsoron wani abu, "Azeezaty, zo nan mana" Biy guy ne ya kira sunanta, fitowa tayi idanunta na kallon ƙasa ta tsaya a tsakiyar su, gaba ɗaya ta tsargu da kallon da su ke yi mata, Hajiya Layla ta kasa rufe bakin ta saboda mamakin ganin yarinyar, sai taga kamar sunyi kama da Benazir ɗinta, sai lokacin Dr Jazz ya lura da ita sun ɗan ruɗe da kyawunta, musamman Dr. Adam har dai ya gaza jurewa ya ce "Tabarakallahu ahsanul khalikin..." bai ƙare maganar ba, Dr jazz ya yi saurin yi mashi raɗa a kunne"kallon ya isa haka! Future wife ɗin babban yayanmu ce, wlh ka shiga taitayinka" da sauri Dr Adam ya rufe bakin shi da tafin hannu. "Azeezaty, ina fata anyi maki bayanin abunda ya kawo ki nan?" ɗaga mashi kai tayi alamar eh, "Okey, abunda muke so kaitsaye ki shiga ɗakin wurin patient ɗin, ki yi hugging ɗin ta sannan ki kirata da sunan Mommynki" amsa mashi tayi da toh, kafin slowly ta juya ta nufi ɗakin zuciyarta na dakan uku uku wani irin faɗuwar gaba take ji, gaba ɗaya sun nutsu suna kallon ta... Duk taku ɗaya idan tayi sai gaban ta ya faɗi rass, ta rasa gane dalilin shigarta yanayin da take a ciki. Tunda ta zura ƙafarta a ɗakin idanunta suka sauka akan mara lafiyan dake a kwance tana bacci, walking slowly ta ƙarasa ta tsaya daga bakin gadon tana kallon ta, tun daga kan fararen kafafuwanta har zuwa kan fuskarta, sumar kanta ta lullu6e gefen fuskarta daga gani ba ƙaramin hauka tayi ba kafin a samu ta runtsa. Wata irin kasala ce ta baibaye Unaisah gaba ɗaya ta kasa ta6uka komai sai kallonta takeyi kamar zata haɗiyeta..... "Ki rungumeta mana, ke muke jira" ƙasa ƙasa da murya Dr Adam ya furta maganar, Numfashi ta ja kafin ta daidaita nutsuwarta, a hankali ta zauna daga gefen gadon kafin ta faɗa kan ƙirjinta tare da lumshe idanunta lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka me sautin gaske ita kanta batasan kukan Ya kubce mata ba, hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba amma sai suka yi zaton tayi ne don abun ya tafi dai dai.. Sautin kukanta ne Ya daki kunnan Benazir, cikin magagin bacci ta fara sambatu tana faɗin "Babyna, wayyo Allah mami! ina babyna naji sautin kukan ta, don Allah ku kawo mini ita..." yatsun hannunta na kerma ta ɗaura su kan bayan Unaisah, da dukan hannayenta biyu ta fara shafa bayanta taji mutun akan cikin ta, hakan yasa ta fara kokarin buɗe idanunta, daƙyar ta buɗe su sun kaɗa jawur saboda bacci, Daga can waje Dr Adam ya ce "Nayi mamakin farkawarta, because bana tunanin allurar da nayi mata ta isa ta saketa..." Su Anila duk sun ƙagara Benazir ta karasa farkawa, gaba ɗaya jikinsu sai tsuma yake yi ga wani irin annurin farin ciki da ya wanke zukatansu, Mayafin kan Unaisah tuni ya jima da zamewa, hakan yaba Benazir damar cusa hannayenta acikin sumar kanta ta cigaba da sambatu tana faɗin "Babyna ne? Mami daddy kuna ina? Wanene Ya kawo min babyna? meyasa take kuka?" Sosai Unaisah ta ƙanƙameta, ta ƙara cusa kanta a kirjin Benazir babu alamun zata saketa, Allah sarki jini ɗaya ba wasa ba, wannan unconditional love ɗin dake atsakanin uwa da ɗanta shine yayi tasiri a zukatansu, a karo na farko da ta fara jin ɗumin mahaifiyarta ba tare da sanin itace ba, aruɗe Benazir ta zabura ta ɗago da fuskarta ta ƙura mata ido tana kallonta, baiwar Allah Angel fuskarta tayi jawur da ita ruwan hawaye ya wanketa tass, da ƙyar take buɗe idanu tana kallon cikin idon Benazir, kallon kallo suka fara jefawa junansu duk hawayen Unaisah sun wanke fuskar Benazir, la66anta na kerma ƙirjinta na bugawa ta furta "Mamana! Ni ce babyn ki, meyasa kika tafi kika barni? kin manta dani a rayuwarki? Nayi kukan rashin ki atare dani mamana!" Shigowa ɗakin Hajiya Layla tayi daga bakin gadon ta tsaya tana kallonsu, ƙwalla sun taru acikin idanunta, "Mommy ki faɗamin? Da gaske babyna ne nake gani ba mafarki nake ba? Angel ɗina ne?" Kwata-kwata Angel bata fahimci sambatun Benazir ba saboda ita kanta ta ɗan shiga ruɗanin halin da ta tsinci kanta game da matar, "Benazir, yarinyar ki ce Angel, ki rungume ta a jikin ki, " Hajiya layla ta faɗa da murmushi akan fuskarta, fashewa da kuka Benazir tayi, da sauri ta kwantar da Unaisah kan kirjinta ta rungumeta sosai kamar zata mayar da ita cikin cikin ta. Cikin shesshekar kuka take lallashin ta"kiyi shiru ki daina kuka, bana son ji, nasan nice na 6ata maki rai, kiyi hakuri ki yafe min bazan ƙara tafiya in barki ba, nayi maki alkawarin zan baki kulawa babyna, kinji my Angel"? Sambatu taci gaba da yi taƙi bari Unaisah ta ɗago da kanta ta ƙanƙame abun ta kamar wani yace zai kwace mata ita..... Jikin Taj ba ƙaramin sanyi yayi ba, da sauri ya duƙar da kan shi hawaye sun cika idanunshi, sai yaji inama ace zai iya zuwa ya haɗa su duka a kirjinshi ya rungumesu, Zahra sarkin tausayi tuni ta fara matse ƙwalla, ita kanta Aneleerh kukan ne ya kusa kubce mata, da hannu biyu ta toshe bakin ta don bata son ayi zargin ko yarta ce ta gaske, Lumshe ido Chief ya yi a yayin da yake kallon su, ya jima baiga abun farin cikin da ya sanyaya zuciyarshi ba irin na yau! abun ya ta6a zuciyar shi.... Hatta Docs ɗin dake a tare da su saida suka ji tsananin tausayinsu, A hankali Dr shureim Ya zaro hanky daga aljihu Ya share kwallar da suka tarar masa, yana ji aransa da wuya yarinyar in ba jinin su bace!! Dr Adam ne ya sauke yar ajiyar zuciya ya ce "in sha Allah zata samu sauƙi, naga alamun nasara tun kan aje ko'ina, Yarinyar ba ƙaramin wayau ne da ita ba, ta iya acting,..." kallon shi kawai Anila tayi su da suka san meke atsakanin su.. Dr jazz ma ya ce "Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa yarinyar nan ta zama silar warakarta" gaba ɗaya suka amsa mashi da ameen.... "Yalla6ai, muje office mu ƙarasa magana" Dr. Jidenna ne Yayi maganar, atare da Chief suka nufi katafaren office dinsa.Tattaunawa suka yi dangane da Unaisah, Chief ya ce masa baya son kowa ya sake shiga ɗakin mara lafiyan daga grandma ɗinta sai Unaisah, bayan haka Yana so a canza mata ɗaki su maida ta private room saboda Unaisah ta samu damar sakewa wurin yin jinyarta, ya ɗaura da faɗin "Bana buƙatar wani likita ya shiga dakin ta in ba Dr Jazz ba, shi nake so ya cigaba da kula da mara lafiyan" Dr Jidenna ya ce "Consider it done sir, in sha Allah a cikin daren nan zamu aiwatar da komai" sun jima suna tattaunawa a office din kafin daga bisani suka fito a tare, har lokacin su Shureim suna a tsaye bakin kofar dakin suna kallon su Benazir, Bayan sun dawo wurinsu chief Yaja hannun Dr Jazz suka ke6e wuri ɗaya dama shi mutuminsa ne, Yana jin dadin aiki da jazz yaron yana da hankali, "Jazz, nayi magana da Md, kaine zaka cigaba da kula da mara lafiyan! Pls bana so asamu matsala!" murmushi jazz yayi "In sha Allah babban yaya zanyi kokari sosai gurin basu kulawa," "Good, sannan inaso ka duba jikin yarinyar, ta faɗamun bata jin dadi, pls inaso ka bata kulawa ta musamman, bana so ta nemi wani abu ta rasa! Kayi kokarin kwantar mata da hankalinta kamar akwai abunda ke damunta" Jinjina kai jazz ya yi "In sha Allah My Boss, kasan bana wasa da duk wani abu da ya shafe ka" harara Chief ya ɗan watsa mashi, ya sunnar dakai ƙasa yana murmushi... Ruƙo hannunsa chief yayi suka koma wurinsu Taj, Duba agogo big guy ya yi "Yakamata mu tafi dare yayi, almost 12," Da sauri Anila ta ce "pls muna son muyi mata bankwana kafin mu tafi" Dr Adam ya furta "Okey, bari na kira maku ita" shiga dakin yayi, "Azeezaty yan uwanki suna son ganinki zasu tafi, ki fito kuyi sallama" shiru yaji bata amsa mashi ba, leƙa fuskokinsu yayi abun mamaki bacci ne ya ɗaukesu rungume da juna bayan sun gama shan kukan, gaba daya Unaisah tana kwance kan jikin Benazir shiyasa gadon ya dauke su.... Fitowa Dr Adam ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "sai dai kuyi hakuri bacci suke yi, ba zamu iya tada su ba" "Dr ga backpack ɗin kayanta, ka shigar mata da ita ciki" sauke jakar Taj ya yi tare da miƙa ma Dr Adam ya shiga da ita ciki ya ɗaurata kan kujerar gaban gadon. Kamar kar su tafi haka suka dinga kallon su ta cikin door glass ɗin, kafin daga bisani suka kama hanyar barin asibitin, har bakin parking space Hajiya Layla ta rakasu tana ta faman yi masu godiya kamar zata duƙa ƙasa, shima Dr. Shureim godiya sosai ya yi masu tare da fatan alkhairi, sallama sukayi wa junansu Zahra da Anila suka shiga motarsu, Taj da Big guy suka shiga tasu motar, kafin Chief ya shiga motarshi, saida Hajiya Layla ta ƙara yi masu Anila godiya saboda halaccin da su ka yi masu kafin motocin suka fuce a jere da matsakaicin gudu, ya rage saura Hajiya layla da Dr Shureim, su jazz tuni sun koma cikin asibitin.. "Shureim ka ga wani ikon Allah? Yarinyar nan tana kama da Benazir, bansani ba ko idanuna ne suke nuna min hakan" Murmushi shureim ya yi "ba idanunki bane, nima naga kamanceceniyarsu, wlh Mommy naji dadin ganin yadda Benazir ta rungumi yarinyar ajikinta, sai naji inama ace yarta ce, saboda ta kwanta mun araina..." Hajiya layla ta ce "ba kai kadai ba shureim, nima yarinyar ta burgeni, ga wayau daga gani tana da kaifin basira, iyayenta sunyi mana hallaci kuma basu nemi komai daga gurin mu ba, ko da yake naga yarinyar ma ƴar masu arziki ce...." Dr shureim ya ce "Mommy zan wuce gida dare yana ƙara yi, pls ki kula da yarinyar nan, kinga dai yadda yan'uwanta suka damƙa mana amanarta, bana so asamu matsala..." "In sha Allah Shureim, ay bazan yi sakaci da rayuwarta ba, dole inyi takatsantsan tun da naga ɗiyar manya ce, hada fa jami'ai cikin waɗanda suka kawo ta" Ƙara tattaunawa suka yi kafin ya yi mata sallama ya buɗe motar shi ya shiga ciki, akan idon ta motar ta fuce daga asibitin, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya ta nufi ciki cike da zumudin son ganin yarinyar.. ______________________________✍️ Bayan su taj sun rako chief part dinsa, saida suka ga shigarshi cikin bedroom dinsa kafin suka sauko falo, har sun kusa fita suka tsinkayi muryar ummi daga bayan su "Boss sannun ku da zuwa"! Atare suka juyo tare da kallonta, sleeping gown ce a jikinta, ta yafa mayafi akanta, da alama ta fara bacci ta farka "Yawwa Ummi, me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba"? Fuskarta ayamutsa tace"na kasa bacci saboda damuwar rashin unaisah, tun wuraren karfe takwas da rabi muke ta nemanta saboda muyi dinner shiru babu ita, ko'ina mun duba, ƴan uwanta ma dakyar na kwantar masu da hankali har su ka yi bacci, nayi zaton ko taje part din ka ne" Tay maganr tare da nuna taj Big guy dake kallon ta from head toe gaba daya ta jefa shi ayanayi, saboda kayan baccin jikinta sun bayyana surarta, "Ummi, unaisah ba agida zata kwana ba, taje asibiti" bai ƙare maganr ba, ummi ta zaro ido tare da dafe kirjin cike da tashin hankali tace"inna lillahi meke damunta? Bata da lafiya ne"? abun da yasa ta ruɗe saboda halin data ganta dazu a daki, abun ya tsaya mata arai, har jiran zuwanta tayi kamar yadda tace mata zata zo amma shiru bata neme ta ba... Kwantar mata da hankali taj yai"lafiyarta ƙalou ba ita ce ke bata da lafiya ba, yar uwar chief ce...." bayani yayi mata dalla dalla, lokaci daya ta sauke ajiyar zuciya, "Hankalina har ya kwanta, amma banji dadin tafiya da tayi batare data yi mana sallama ba, yanzu sai yaushe zata dawo gida"? "Bani da masaniya, amma bana tunanin zata dauki lokaci, pls ki kwantar ma yan uwanta da hankalli banaso su sanya damuwa aransu" "In sha Allah, mu kwana lafiya boss, agaida min da madam" ya amsa mata da toh, satar kallon big guy tay ya wani tsareta da ido, harara ta dan watsa mashi haɗi da yin murmushi ta juya ta nufi ciki, harta bace ma ganinsa bai kauda idonsa ba, sai da taj ya bugi kafadarsa kafin ya juya suka fuce kowa ya nufi part dinsa.. ______________________________✍️ Prisoners Shield💔 Bawan Allah, kwata kwata baya acikin hayyacinshi, Yasha bakar wahalar radadin da zuciyarshi keyi mashi, tun safe har kawo iyanzu da dare ya ratsa ko ruwa bai gifta makoshin shi ba, saboda tashin hankalin da yake a ciki, yayi haukan yayi kukan amma babu abunda Ya canza nadaga kuncin da yake ji, babu wanda yayi tunanin ya leko dakinsa yaga awani hali yake ciki, saboda su kansu yan uwan nashi yanzu mantawa su ke yi da shi tun da suka fahimci bayason shiga cikin su kuma baya son kowa ya ra6e shi, a fahimtarsu, unaisah ita kadaice ta damu da shi, bata iya wuni batare da ta leko dakinsa ba, ta damu da shi fiye da yadda ta damu da kanta, itace farin cikinsa kuma gatansa, baya jin zai iya rayuwa batare da ita ba, Unaisah kaddararsa ce! Bugun zuciyarsa ce. Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya ɗauke shi, hakan ba karamin relief ya sama mashi ba, yayi bacci sosai har na tsawon awanni, gab da za'a fara kiran sallar asuba, ya fara mutsu mutsu, yatsun hannayensa dana kafarsa suka fara kerma....." Farat ɗaya ya buɗe idanunsa waɗanda suka kaɗa jawur tamkar garwashin wuta, Gaba ɗaya rasa ƙwarin gwiwarshi, kamar matacce Sam ya kasa motsawa daga kan floor, ko yatsansa Ya gaza ɗagawa, wani irin gumi ne Ya wanke jikinshi kamar wanda aka tsamo daga cikin teku, ta ko'ina zufa ke tsatsafo mashi, ga wani azababben zafi da jikin shi ya ɗauka. shatun jijiyoyin goshinsa sun fito rudu rudu kan fatarsa,a kalla ya shafe mintuna yana kokarin sarrafa zuciyarsa gudun kada evil heart dinsa ta motsa, bakomai idanunse ka hango mashi ba face fuskar Unaisah. Dakyar ya samu kwarin gwiwar motsa gabban jikinsa, Ya lalla6a Ya miƙe tsaye kan ƙafafunsa, jansu ya dinga yi saboda wani nauyi da sukai mashi dakyar yakai kan shi toilet ya faɗa ciki yana jan numfashi, agaban sink ya tsaya yana faman sauke ajiyar zuciya. Sannu a hankali brain dinsa ta fara tariyo mashi abunda Ya faru daren jiya atsakaninsu, yaga komai a mafarkinsa. ɗago da hannayensa yayi tare da saita su saitin fuskarshi Ya ƙura ma tafukansa ido Yana kallon su ....da sauri ya girgiza la66ansa na kerma ya furta"bani bane! Bada son raina ba, bansan na akaita ba, bana a cikin hayyacina!...." dafe kansa yai da hannu ɗaya ya cusa yatsunsa acikin sumar kanshi, ya cigaba da cakuɗata gaba daya ya haukata gashin kanshi, duk ya rikice saboda ya gane shine da kafafuwansa Yaje dakinta adaren jiya har yayi mata aika aikar nan sai dai yayi imanin bayin kanshi bane❗ cije la66ansa yayi har saida suka fashe jini ya fara ɗiɗɗigowa, wani irin tsanar kanshi ne Ya kama shi, kamar ya kashe kanshi haka Yake ji, da karfi ya buga forehead dinsa jikin sink nan take fatar wurin tayi jawur kamar zata fashe, buga kanshi yacigaba dayi yana sambatu yana fadin Ni ne da kaina na cutar da Angel dina? tana kuka tana rokona dan in taimaka mata amma nagaza share mata hawayenta, bani da tausayi, ni mugune, na tsani kaina..." jinine ya fara gangarowa ta kofofin hancin shi, wani irin jiri ya fara kokarin kwasarshi, ya fara tangal tangal zai kife kasa kwatsam ba zato ba tsammani Yaji hannu mutun akan damtsensa, gaba daya ya janyo shi tare da rungume shi akan broad chest dinsa, ya zagayo da hannayensa akan bayan shi, bawan Allah baya gane komai, idanunsa sun makance, ji yake tamkar angel dinsa ce ta rungume shi, hakan ya shi ƙara ƙanƙame mutumin da ya rungumeshi duk ya 6ata mashi gaban Rigarshi da jininsa, hakan baidame shi ba, babban tashin hankalin shi halin da yaron yake aciki! Ya tsorata da ganin yadda yake kokarin kashe kan shi ❗lamarin yayi matukar gigita shi.. "Ki yafe min Angel, ba yin kaina bane, bazan iya cutar dake ba, sharri akaimin, ba halina bane, ki tausayama rayuwata, ke kadai ce farin cikin da nake da shi a duniyar nan, bani da gata daya wuce ke...." gaba ɗaya sambatunsa acikin kunnan sa, Ya nutsu Yana sauraron shi, har lokacin bai ɗago da kan shi ba, balle har yasan wanene Ya rungume shi. ___________________________________✍️ *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 33 Complete by Novels Elite Admin August 29, 2024 Takun Ƙarshe ✍️ EPISODE 33 Sai da yayi mai isarshi kafin A hankali chief ya raba jikinsu daga na juna ya tallabo fuskarshi da tafukansa, kwata kwata babu kuzari a jikin shi kamar lagwanin fitila, fuskarshi ta 6ace da blood dinsa, idanunsa sunyi nauyi dakyar ya iya buɗe su ya kalli chief yana faman jan numfashi, wani irin tausayin shi ne ya kama shi ga tsananin ƙaunar yaron da yake ji, duk da baisan meke damun shi ba, a sambatun da yayi, chief ya fahimci sun samu sa6ani ne tsakanin shi da Unaisah! Shiyasa jiya a mota ta dinga yi mashi kuka, har tayi mashi karyar bata jin dadin jikin ta, yanzu kuma ga ɗan uwanta yana sambatu akanta har yana yunkurin halaka kan shi, hakan na nufin akwai wani abu daya shiga tsakaninsu wanda yayi silar jefa su halin da suke ciki?! Abun ya daure mashi kai.! "Bansan meke damunka ba! banji dadin yadda kake kokarin illata kanka ba! Meyasa ba zaka nemi taimakon mu ba uhyum? Cikin kulawa yayi mashi maganar, shiru Danish bai tanka mashi ba saboda wani irin jiri jiri da yake gani a idanun shi Ruƙo hannun shi chief yayi da niyar su fita daga toilet din don Ya duba lafiyar shi, da sauri Danish Ya fuzge hannun shi, dakyar sautin voice dinsa ke fita "I don't want to see anyone! Just leave me alone! ka tafi kawai..." "No bazan iya ƙyale ka ba, Idan kai baka damu dakanka ba, Ni na damu dakai, Please, Danish, let's go treat your nosebleed." Girgiza kai Danish yayi"bana so, lafiyata qalou, zan kula da kaina, kawai ka tafi ni bana son ganin ka.. " "Ni kuma ina son ganinka, ba inda zan tafi, in kaga nabar dakin nan to ka samun sauƙin abun da ke damun ka ne" babu wasa a fuskarsa yayi maganar tare da harɗe hannayensa kan kirjin shi, kallon kallon suka fara jefawa junan su, chief ya rasa yanda zaiyi da shi, yaron yafiye taurin kai ga kafiya, da ƙiwuya kamar yaron goye ... Ƙwara ya lalla6a shi su wanye lafiya, idan ba haka ba zai iya illata kan shi.. Cikin sigar lallashi Yace"pls Danish, ka bani damar da zan baka kulawa, ba cutar dakai zanyi ba, bana jin dadin ganinka a halin da kake a ciki, na damu dakai Danish, ina jinka tamkar ɗan uwana, A shirye nake dana taimaka maka wurin ganin mun shawo kan abunda ke damun ka." tun da chief ya fara magana cikin sanyin murya, Danish ya nutsu yana sauraron shi kamar yana fahimtar shi. "Nayi maka alƙawarin ba zaka ta6a dana sanin yarda dani ba...." bai ƙare maganar ba, raunanniyar muryar danish ta katse mashi hanzarin shi"bazan ta6a yarda dakai ba, ƴan uwana kadai na yarda da su, amma ku ba abun yarda bane! duk halin ku ɗaya, kuna da son zuciya, ba ku da tausayi, Tun ina jariri na taso rayuwata a gidan kurkukun ƙaddara, bansan komai dangane da duniyarku ba, saboda an tauyemin hakkin rayuwata, ina da ciwon zuciyar abun da iyayena suka aikata min, bansan wani jin dadi na duniya ba, unaisah itace farin cikina......." wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskarshi, zuciyar chief ta karaya, baisan sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba, sambatun Danish sun ta6a zuciyar shi, shi kanshi baisan Yana furta kalaman ba, rashin Angel ya fara zautar da shi, dama kuma abun ya jima yana ci mashi tuwo a kwarya. Da sauri chief Ya ƙara huggin dinshi tighly a kirjin shi, kamar zasu koma mutun ɗaya, a hankali yake shafa bayanshi da tafukan hannayen shi cikin kwantar da murya ya soma yi mashi raɗa a kunanshi "Danish ba duka muka taru muka zama ɗaya ba, ina rokon alfarma a wurinka, ka jarabani nayi maka alkawarin zan sanya farin ciki acikin rayuwarka, inaso na samu kusanci dakai, saboda na share maka hawayenka in kuma baka kulawa, bayan haka zanyi kokarin sasanta tsakaninka da ƴar uwarka unaisah duk da bansan meya faru atsakaninku ba" Cikin sanyin murya ya furta"tayi fushi dani, ta daina sona, nasan ban kyauta mata ba, amma bayin kaina bane, ina so na bata hakuri koda ba zata cigaba da kula ni ba, ni burina ta yafe min kada ta ruke ni a zuciyarta, hukuncin yayi min tsauri bazan iya jure ba...ka taimaka min dan Allah..." a karo na farko da Danish Ya ambaci sunan Allah, ba tare da shi kanshi Ya lura da furucinsa ba, lumshe ido chief yayi, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar sa, har lokacin suna a rungume da juna, yaji dadin damar daya samu dama burinshi yaja shi a jikin don su samu abunda suke so, yanzu ya samu mafita, ya riga daya gane lagwonsa wato Unaisah, yayi imanin badan sun samu sa6ani atsakaninsu ba, da bazai ta6a samun damar da har Danish zai kula shi ba, murmushin gefen fuska ya saki aranshi ya furta yanzu wasan zai fara🔥 "Zan taimaka maka in sha Allah, zanyi iyakar bakin kokarina gurin ganin kun sasanta tsakaninku, amma fa sai ka yi hakuri ka cire damuwa aranka, yanzu muje ayi maka treatment na bleeding dinka" "Bani buƙata, zan iya gyara kaina" ya fada tare da raba jikin su daga na juna, ya sanya hannu ya matse hancin shi, nan take jinin ya daina ɗiga. "Inason zanyi wanka" fita chief yayi daga ɗakin, ya tsaya a bedroom dinsa Yana jiran shi, tufka da warwara ya fara dangane da yadda zai ja shi a jikin shi , yaso yaji meya faru atsakaninsu sai dai ya fahimci baya son sanar dashi, kamar yadda itama unaisan taki sanar da shi, bai damu da hakan ba, saboda shima baison yaji abun da zai hana shi runtsawa kwara atafi ahaka yana dai kyautata masu zato. Kafin fitowar Danish Ya kira landline na kitchen Ya isar da sakon Yana bukatar breakfast a kawo mashi a dakin Danish Within 10 mins chef Ya shigo hannun shi ruƙe da tray na kayan abinci har saida gabanshi ya faɗi ganin jinin dake agaban jallabiyar chief bai dai tanka ba, tun da ya gaishe shi Ya sauke masu akan table kafin Ya fice daga dakin. Harya fara gajiya da tsayuwa, jin motsin buɗe kofa Yasa shi saurin kai idon gare shi, Ya fito fess dashi kamar wani abu bai ta6a faruwa ba, towel ne ɗaure a waist dinshi, tun da ya fito chief yake kallon shi, bai ji dadi zanan tatttoo din da akai mashi ba, daga bayan shi har gaban kirjin shi da damtsen hannun shi zanan waɗannan halittunne masu zako zakon akaifu, launin ja da baƙi bawai don baiyi mashi kyau ba, hasalima kyau zanan yayi mashi sai dai abun da yake jimawa ranar daya musulunta dole yaji ba dadi saboda haramunne zanan tattoo kuma daga gani permanent ne nashi irin wanda bai gogewa, sauƙin shi ɗaya Idan ya musulunta bashi da zunubin komai. har saida ya nufi closet kafin chief ya kau da ido daga kallon shi, ƙarnin jinin ne Ya fara takura mashi fucewa yayi daga dakin Ya nufi dakin shi, ya canza kayan jikin shi ya sanya wata jallabiyar kafin ya dawo dakin danish. A zaune ya same shi akan mirror chair ya sanya short da singlet a jikin shi, ya zabga uban tagumi da hannun shi biyu, har yanzu ba yaji shi daidai. "Danish bismilla, taso muyi breakfast, nasan baka ci komai ba" cikin kulawa yai mashi maganar In a cool voice Ya furta"bana iya cin komai, Unaisah nakeson gani..." ya yi maganar tare da mikewa Ya nufi kofar fita daga dakin, da sauri chief yasha gabanshi... "Unaisah bata nan, ko kaje dakin su ba zaka ganta ba" Hankalin shi atashe ya furta"ta gudu saboda tana fushi dani ko"? Ya fada idanunsa cike tab da kwalla" Girgiza kai chief yayi"ba abunda kake tunani bane, muje mu zauna I'll explain everything to you.." Related Books: Abban Sojoji (Takun Karshe) hausa novels complete - Novels Elite Daudar Gora complete book 1 Document. Daudar Gora Book 2 Complete Document Jiddatul Khair book 1&2 complete ya ruko hannun shi suka zauna daga gefen gado suna fuskantar junansu.. Calmly chief ya zayyana mashi komai dangane da zuwanta asibiti, bai boye mashi komai ba ...." bawan Allah har cikin ranshi yaji dadi da unaisah ta haɗu da mamanta, sai dai yana jin tsoron ta juya mashi baya tun da ta samu iyayen ta..." "Angel dina taga mamanta"? Jinjina mashi kai chief yayi, "Kaima in sha Allah iyayenka zasu bayyana kuma zasu baka farin cikin daka rasa arayuwarka ..." yanayin fuskarshi ne Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai. "Bana son su, bani bukatarsu, bana son ganin su, na tsane su, ni bani da iyaye, unaisah ce gatana" murmushi chief yayi. "Baka tunanin kaima iyayenka suna kaunarka? Think about it. zai iya yiwuwa wani ne a danginka ya sadaukar dakai ba iyayenka ba, kai da kanka kace tun kana jinjiri aka sadaukar dakai, watakil iyayenka basu san an sace masu kai ba, don ni gaskiya bana tunanin a duniyar nan za'a samu iyayen da zasu haifi kyakkyawan yaro kamar kai su suyi watsi da shi...." shiru Danish yayi baice mashi komai ba, kamar yana nazarin maganar shi, sai dai babu alamun zai fahimce shi. Cikin dabara chief yacigaba da kwantar mashi da hankali, har ya samu suka ci abinci atare, bayan yayi mashi alkawarin zai kai shi wurin Unaisah amma ya bashi shawarar ya ɗan bata tazara watakil ta sauko daga kan dokin zuciyar da tahau...yace mashi bazai iya ba, baya jin dadi in bata atare da shi, yafi son yaganta akusa dashi ko da bazata kula shi ba.. Akarshe yace mashi da anjima zai kai shi wurinta suga juna in har hankalin shi zai kwanta.... Lokacin da su Batool suka farka har yar rige rigen zuwa dakin unaisah su kayi don suga kota dawo amma suna shiga suka iske babu kowa, Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba, wasu har sun fara kuka, saida Ummi ta sauko down ta same su zazzaune kan sofas kowannansu Ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki. Suna ganin ummi suka nufe ta"aunty ummi har yanzu yar uwarmu bata dawo ba, dan Allah ina taje ne bata fada mana ba"? Kwantar masu da hankali tayi kafin ta sanar da su inda taje, har suna hada baki wurin fadin aunty ummi dan Allah zamuje asibitin wurinta, harma muga yar uwar chief din muyi mata ya jiki" "Kuyi hakuri, ba za'a bari kuje ba, ku bari ta dawo kawai, in sha bazata jima ba" rigima suka sanya mata musamman jemaimah da azeeza dakyar ta samu ta shawo kansu har suka hakura. _______________________________✍️ *OIH* A hankali ta buɗe idanunta, ta ƙurawa ceilling ido na wani lokaci, kafin ta shafa jikinta da hannunta, jin babu mutun yasa ta yunƙura zata miƙe da sauri hajiya layla ta taimaka mata ta zauna, muryarta na rawa ta furta"wayyo Allah na, mami ina babyna? wa ya dauke min ita? Jiya fa na ganta da ido na, har na rungumeta a kirjina! Ko dai mafarki nayi ne..."? gaba ɗaya tabi ta ruɗe ta ɗaga hankalin ta, dafa kadarta hajiya layla tayi fuskarta da murmushi tace"kwantar da hankalin ki, babyn ki tana nan cikin koshin lafiya kuma tana a tare dake" girgiza kai tayi tana faman zare ido tace"to ay banganta ba! Babu ita ko'ina, wani ya dauke min Angel dina..." ta fada tana laluba bedmattress. tun da asuba aka canza masu room yanzu suna a privet room na asibiti, tamkar bedroom na gida haka Yake, har gado ɗaya aka ƙara masu saboda ya ishe su ita da unaisah. "Mommy wlh bata nan, ta 6ace, wani ya sace min ita, nama san taj ne Ya gudu da ita saboda yana jin haushina...." saukowa tayi daga kan gadon ta durkusa tana leƙen karkashin gadon sumar kanta duk ta rufe fuskarta da bayanta... "Benazir me kikeyi anan ki tashi mana, nace maki yarki tana atare dake yanzu zata fito, Ki zo ki sha maganin ki, ga breakfast an kawo mana..." ta faɗa tare da ruko hannunta, fashewa tayi kuka tana fadin"wayyo Allahna mami, wlh babu ita, na shiga uku na bani na lalace, baby ta 6ace..." duk yadda hajiya layla taso ta shawo kanta abun Ya faskara gaba daya nema take ta zauce... Motsin buɗe kofar toilet ne Ya katse mata kukan nata, a firgice ta juya tana kallon kofar tana faman zare dara daran idanunta, tundaga kasa ta fara kallon kafafuwanta dake asanye da slippers farare tas da su, da sauri benazir ta wurga idanunta kan fuskarta, harsaida ta lumshe su saboda wani sanyi daya ratsa zuciyarta, fitowarta kenan daga wanka, doguwar riga ce a jikin ta pink colour tayi wani fresh da ita kamar babu damuwa atare da ita. Ƙurawa juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, hajiya layla dake kallon su tsabar murna bakinta yaƙi rufuwa yadda kasan gonar auduga. Cikin sanyin murya unaisah ta furta"mamana! Kin tashi lafiya! Ya jikin naki? Kin farka baki ganni ba am sorry na shiga toilet yin wanka ne..." wani irin bugu zuciyar Benzar tayi yanayin fuskarta ya nuna kamar tana kokarin dawowa hayyacin ta ne. Murmushi Angel ta sakar mata har dimple dinta suka lotsa, kamar ta samu tv haka ta ƙura mata ido tana kallon ta. "Benazir baki gane ta ba? Babyn da kike nema ce, Kije wurin ta..." jikinta na 6ari kamar mazari ta mike ta nufi unaisah, tana karasawa ta zube kan gwiwowinta ta sanya hannu biyu tayi huggin dinta tightly akan kirjinta, wani irin yanayi suka tsinci kansu mara misaltuwa, kusan a tare heart dinsu ke bugu da karfi da karfi, tuni kwalla sun cika idanun kowan nan su. "Babyna ne"? Ta fada tare da tallabo fuskar unaisah ta ƙura mata ido tana faman zare mata idanunta har saida gaban angel ya fadi tarasa gane meyasa take jin ta kamar mahaifiyarta. "Kinyi shiru baki amsa min ba! Baby na ne? Ke ce? Ta fada tana ɗage mata eye brows dinta. Jinjina mata kai unaisah tayi"ni ce mamana" yawu benazir ta haɗiya kafin ta furta"taj ne Ya kawo min ke uhum? Yana ina"? Rass gaban Angel Ya faɗi ta zaro ido tare da kallon hajiya layla wadda ta kura masu ido tana kallon su gwanin ban sha'awa. Lamarin ya daure mata kai, meyasa take ambaton sunanta da sunan daddynta? To kodai itama sunan yarta ne da mijinta hakan? Abun da daure kai, tayaya akai sunan su yazo ɗaya"? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsar ta, ranta ne ya raya mata ay ba ita kadaice me irin nickname dinta ba suna dayawa, shima sunan taj din ba daddynta kadai ke da shi ba, hakan yasa ta saki jikin ta. Jinjina mata kai tayi"daddyna ne Ya kawo ni, shima yana nan zaizo wurinki amma sai kin kwantar da hankalinki..." cike da zumudi tace toh toh zan kwantar da hankalina..." Huggin dinta unaisah ta karayi wani irin dadi takeji, ta dade batayi bacci mai dadi irin na jiya ba, bata ta6a zaton zata iya runtsawa ba saboda halin damuwar datake a ciki na abun da ya faru tsakaninta da Danish amma cikin ikon Allah silar baiwar Allahn nan jiya tayi bacci mai nauyi kuma ta samu relief na radadin da zuciyarta keyi mata. "Mamana, Ki shiga toilet, kiyi wanka zaki ji dadin jikin ki, Idan kika fito dakaina zan baki abinci abaki .." wani irin dadine Ya lullu6e benazir, da sauri ta kalli hajiya layla idanunta cike tab da kwalla tace"mommy tana sona sosai, dama nasan bazata guje ni ba, saboda ita jinina nace, kuma tasan bada san raina na gudu nabarta ba..." rass gaban angel ya fadi maganar benazir ta jefata arudani, lokaci daya brain dinta tafara tariyo mata labarin mamanta data gudu tabarta a kwamin wanka, tuni yanayin fuskarta ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, gani take kamar yawancin iyaye mata basu da tausayin ya'yansu shiyasa suka watsar da su bayan sun haife su. "Benazir ki shiga kiyi wankan, babynki zata jiraki anan" jikin ta na rawa ta mike ta shiga toilet din, tun zuwansu hajiya layla ke taimaka mata tayi wanka saboda rashin nutsuwar da bata da ita, amma yau da kanta tayi wanka abun ba karamin dadi yayi ma hajiya layla ba, atare suka zauna da angel ta fara bata abinci abaki tana ci sai dadi take ji, ita ma ta dauki spoon ta debo ta sanya ma angel abaki hajiya layla nata kallon su gwanin ban sha'awa bayan sun kammala cin abinci, dr jazz ya shigo duba lafiyar benazir shi kanshi ya fahimci nasarar da suka fara samu don alamu sun nuna takusa regaining hankalin ta....yau ko allura ba'ayi mata ba, magungunanta kadai suka bata tasha. Kafin dr jazz yabar dakin saida Ya kira unaisah, suka ke6e a kofar dakin ya tambayeta meke damunta? Chief ya fada mashi bata da lafiya..." murmushi tayi masa kafin tace"ba abunda ke damuna, lafiyata qalou.." lallashinta ya dinga yi yana lalla6ata duk don ta fada mashi amma ta nace akan ita lafiyarta qalou, yace toh shikenan idan akwai wani abu da kike bukata ki sanar dani, chief ya bani amanarki bana son ganin damuwa atare dake, har cikin ranta taji dadin maganarshi, tace in sha Allah zan baka hadin kai dr, nagode da kulawarka agare ki, bayan tafiyar jazz ta juya zata shiga dakin har saida suka bangaji juna ita da benazir, taji shiru bata ganta ba shine tabiyota kada asace mata babynta, murmushi unaisah tayi tare da ruko hannunta suka koma cikin dakin, daga jiya zuwa yau wata irin shakuwace mai karfi ta shiga tsakaninsu, duk wani motsin unaisah akan idon benazir ta hanata sukuni tana a maƙale da ita ko toilet bata son ta shiga, tafi son taji dumin jikin ta anata, haka itama unaisah ko tari Benazir tayi saita nuna damuwarta akanta. Wuraren karfe 12 dr shureim da Alhaji ubaid suka zo asibitin, a bakin kofar dakin jami'an dake sanye da fararen kaya suka dakatar da su suka ce ba abada iznin shiga ciki ba, hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba saboda baisan da dokar za'a hanasu shiga room din ba, Alhaji ubaid yace bazai yiwuba babu yadda za'ay su hana shi ganin yar shi, tun da harya tako yazo dole ya shiga ya duba lafiyarta, ganin dagaske ba zasu bari su shiga bane yasa dr shureim kiran layin hajiya layla, bayan ta ɗaga ya sanar mata zuwansu, fitowa tayi daga dakin sanye da hijabi, wani irin annurin farin ciki suka gani akan fuskarta, bayan sun gaisa Alhaji ubaid Yace"ya mai jikin? Ina fata jikin nata da sauki. " murmushi hajiya layla tayi"mai jiki Alhamdulillah, benazir ta fara samun lafiya, shureim bai fada maka abun farin cikin daya faru jiya ba"? Murmushi alhaji ubaid yayi"ya fada min, wlh naji dadi nayi murna naso ace na gana da iyayen yarinyar don inyi masu godiya" labari ta fara basu na abunda ya faru da safen nan ta ƙara da cewa"yarinyar tana da wayou, baka ganta ba kamar benazir dince ta haifata sunyi kama, abunda yafi daure mun kai shakuwar su baka ga yadda suke tarairayar junansu ba. " wani irin dadine Ya lullu6e dr shurem da Alhaji ubaid "Alhamdulillah, ubangiji Allah Yasa yarinyar ta zama silar warakarta. " suka amsa mashi da ameen "Yanzu ba zamu samu ganin Benazir din ba"? Alhaji ubaid ne yayi maganar, Hajiya layla tace"ba zasu bari ku ganta ba, kuyi hakuri kawai har zuwa lokacin da zasu salleme mu" Dr shureim Yace"gaskiya ni bazan iya hakura ba, ina son ganin yar uwata..Alhaji ubaid yace ni bansan dalilin kafa dokar ba, in ma za'a hana wani ya shiga ay dai ba a hana ni ba, ni da nake mahaifinta.." kiri kiri jami'an suka hana su shiga ciki gashi sun kwallafa rai akan son ganin su, zuwan dr jazz ne Ya sama masu maslaha, da farko yayi kokarin fahimtar da su dangane da dalilin dayasa suka hana shiga, Yace iyayen yarinyar ne basa son wani abu ya samu yar su, shiyasa suka sanya tsaro a asibitin bayan haka basu san wani abu da zaisa ita benazir din ta gane ba mamanta bace" Alhaji ubaid yace su dai a taimaka abarsu su ganta.."_ ganin ya kafe ne yasa dr jazz ya kira chief a waya ya sanar da shi dangane da zuwansu Alhaji ubaid, shiru yayi jim yana nazari dama don saboda Alhaji ubaid suka kafa dokar amma daya tuna yadda taj ya fada masa ya yi ma unaisah bayani akan ko wani ya nuna ya santa kada ta nuna ta sanshi, ya dai san in suka hadu idan ta ganshi zata iya gane shi tun da yarinyar da wayon ta amma bai kamata su hana family din mara lafiyan ganin ta ba zasu iya zargin wani abu, hakan yasa chief furta"Jazz ku bar su su shiga, amma kada su ɗauki lokaci, sannan ka sanya ido akan su bana son fira mai tsayi ta shiga tsakanin su da yarinyar .." amsa mashi yayi da toh, bayan sun gama wayar ya sanar da su Alhaji ubaid sun samu iznin shiga amma kada su wuce mintuna biyar, lokacin da suka shiga unaisah ta shiga toilet, bata samu ganin su ba, ta dai jiyo muryoyinsu a dakin suna magana, sunyi jiran fitowarta amma har time ya cika ba ta fito ba, sai bayan da suka fita daga ɗakin kafin ta fito daga ciki. Around karfe 3 na rana su Anila suka zo tare da su mami hada abie, bayan sun gaisa sukayi ma hajiya layla ya mai jiki tace masu, ay tama fara samun sauƙi sosai, har labari taba anila na irin shakuwar da sukayi, ba karamin dadi taji ba, su kansu sun lura da cigaban da aka samu na lafiyarta, saboda tana gane kowa dayazo wurinta, har sunayensu take kira, Unaisah taji dadin zuwan aunty Anila, har tambayar baby junaid tayi anila tace mata ta yi hakuri school yake zuwa kuma sai marece yake dawowa cikin gida, bata ji dadi ba saboda ta kwallafa rai akan son ganin shi, lallashinta anila tayi tace kada ta damu zatayi kokari koda cikin weekend ne zata kawo mata shi, sun jima a asibitin kafin daga bisani suka tafi _________________________________✍️ Bayan sallar magrib, Unaisah tana zaune gefen gadon benazir dake akwance tana bacci ta ruƙe hannunta acikin nata don kada a sace mata babynta, Hajiya layla tana zaune kan darduma hannunta ruƙe da cazbaha tana ja,..." Baiwar Allah duk dauriyar da takeyi sai da tagaza jurewa duk bayan ƴan mintuna sai ta shiga toilet ta yi kuka, tayi kokarin cire shi aranta ta kasa, zuciyarta sai azalzalarta takeyi akan shi, bata bari hajiya layla ta gane halin da take a ciki ba .... A hankali ta cire hannunta daga na benazir, ta mike ta shiga toilet ta tsaya agaban sink, ta fashe da kuka da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta don kada su jiyota, fuskarta tayi jawur hatta idanunta sun kankance, damuwarta awani hali yake a ciki? Tasan halin shi yana da wuyar sha'ani ba lallai ya yarda da wani ba, zai cigaba da killace kanshi ne adaki watakil ma har zuciyarshi ta buga Ya rasa ranshi! Wa zai bashi kulawar da take bashi? Mutumin da baisan komai ba sai soyayyarta itama tasan da hakan, Itace jindadin shi na rayuwar duniyar nan...amma meyasa yayi mata hakan? ya rasa akan wa zai gwada rashin imaninshi sai akanta? Abunda yafi 6ata mata rai tana fama da radadin ciwon ciki ya nemi illata rayuwarta, duk in ta tuna yadda ya janyo kafafuwanta cikin rashin imani ya wurgar da ita kanta gado ya hambare kanta, abun Ya 6ata mata rai, sai dai har yanzu wani sashe na zuciyarta yaƙi aminta da zargin da takeyi mashi saboda bai ta6a yunkurin cutar da ita ba wannan ne karo na farko daya farayi mata hakan...." runtse idanunta tayi wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin cikin karyayyar murya ta furta"meyasa kayi min haka? Me nayi maka dana cancanci hakan daga gare ka? Ka rasa wa zaka cutar sai ni? Angel dinka? Mai son ganin farin cikinka me share maka hawayenki"? Ta jima acikin toilet, sai da ta gama sambatunta, kafin ta wanke fuskarta ta fito jiki asanyaye, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta nufi backpack din ta curo wayar tare da duba sunan mai kiranta, tayi mamakin ganin sunan chief Owais ya bayyana, tun time da daddynta ya bata layinsa bata ta6a kira ba ta daiyi saving dinta. Picking call din tayi tare da kara awayar a kunne cikin sanyin murya ta gaishe da shi ya amsa mata "Ya mai jikin"? Tace"alhamdulillah, da sauki sosai, bacci takeyi yanzu" "Okey, ina fata dr jazz Ya duba lafiyarki"? Ya fada tamkar baisan abun da ke damunta ba.. "Eh, naji sauki ma" "Okey, nazo asibitinne, amma ban shigo ciki ba, Ina parking a space, Yanzu zan turo ataho mun dake..." waro ido tayi jim kafin ta amsa mashi toh, Bayan ya katse kiran ta sanar da hajiya layla game da zuwan chief Ko minti biyar ba ay ba, sai ga agent sanye cikin kaki, da sauri ta dauko hijab ta zura a jikin ta, Allah yaso benazir bacci takeyi da kuwa ta hanata fita. Tana fitowa daga dakin agent din Ya miƙa mata face mask, ta sa hannu ta kar6a kafin ta sanya a fuskarta, tabi bayan shi suka fito... Tunkafin su karasa harabar ajiye motocin ta hango chief ya dauki wankan suit, yana daga tsaye ya jingina bayan shi jikin motarsa, fuskarsa na asanye da mask, gaba ɗaya hankalinsa na akan wayarsa da yake dannawa. ... "Assalamu alaikum..." sanyayyar muryarta ce ta ratsa kunnanshi, A hankali ya ɗago suka haɗa da juna da sauri ta sunnar da kanta kasa kamar wata munafuka, kunyar shi taji tunawa da huggin dinta da yayi a jiya. Lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta, jiya zuwa yau ba karamin jinta yake a cikin zuciyar shi ba. "Ya kuka ƙare da Sis din nawa"? Murmushi tayi kafin ta fara bashi labarin shakuwarsu.. " kallon ta kawai yakeyi daga yanayin ta ya fahimci taji dadin kasancewarta da mamanta hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba "Kinyi kuka ne"? da sauri ta girgiza kai alamar a'a "Kada kiyi min ƙarya, naga alamun hakan a idanunki" shiru tayi jikin ta ya fara kerma sam batason kowa yasan abunda ke damunta... "Ina daddy na da yan uwana"? tayi mashi tambayar ne don ta mantar da shi "Baki da layin shi"? "Ina da shi, amma wayar babu card da zan kira shi" "Ina wayar" da sauri ta fiddo da hannunta, ta miƙa mashi ita, bayan ya kar6a yace"ki shiga cikin motar, ki jirani" amsa mashi tayi da toh... Buɗe mata murfin motar yai, kwata kwata bata lura da mutun a ciki ba, ta kutsa kai ta shuga ta zauna, wani irin ni'imtaccen sanyin A.c ne Ya ratsa fatar jikin ta mai hade da kamshin turare Wurga idon da zatayi karaf ta sauke su akan fuskarshi, ta cikin mirror ta hango shi, kiris Ya rage ta fasa ƙara saboda ta tsorata batasan da mutun ba A firgice ta kalle shi, yana a gefenta farar jallabiya ce a jikin shi, fuskarshi sam babu walwala, zuciyarta ta hasala ranta ya 6aci da sauri tafara kokarin bude murfin motar taji shi a garƙame kamar taga wani mugun abu.. Hakan ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, wani irin shakkarta Yake ji "Angel... Pls ki tsaya inyi maki bayani nasan zaki fahimce ni..." banza tayi dashi kamar bata ji me yace ba "Nayi zaton kece mutun na farko da zaki fara yi min uziri ki fahimce ni idan na aikata badai dai ba sainaga ba haka ba, kamar bakisan wanene ni ba"? Muryarshi ba karamin kashe mata jiki tayi ba, ta haɗe fuskar kamar bata ta6a dariya ba duk don kada yayi tunanin zata raga mashi... Fashewa tayi da kuka tana fadin"bana son jin muryarka! Bana son ganin ka! Meyasa kazo"? Hawayene suka wanke fuskarshi. "Pls ka kyaleni in rayuwata, yanzu bana bukataka, na riga na gane ba dan Allah kake tare dani ba akwai wata manufa aranka..." ta faɗa tana zare mash gray eyes dinta wadanda suka kada jawur da su. "Bazan ta6a sauraronka ba, saboda kai makaryaci, kayi min karya danish meyasa baka yarda cewa kaine ka aikata min hakan ba lokacin da nazo dakin ka"? Ta jefa mashi tambayar tana kallon fuskarshi duk yabi ya dabarbace sai lokacin ta lura da yanayin shi har rama yayi ga wata matsananciyar damuwa data gani akan fuskarshi "Kiyi hakuri ki yafe min Angel, na aikata babban kuskure, amma ki fahimce ni bada son raina na aikata miki hakan ba, nima bana acikin hayyacina, lokacin da kikazo dakina na manta komai daya faru saboda bayin kaina bane sai daga baya nayi mafarkin abunda ya shiga tsakanin mu..." ya faɗa yana haɗiyar yawu mai ɗaci. "Angel kinsan bani kadai bane kuma har yanzu elders suna bibiyar rayuwata ko su zasu iya shiga tsakaninmu don su rabani dake saboda sun san cewa ke daice lagona, ta hanyar shiga tsakanina dake ne kadai zasu iya cin galaba akaina.." wani irin faduwar gaba take ji, ita kanta bata son tayi silar da zai koma kurkukun ƙaddara, maganar tashi taso tayi tasiri azuciyarta.... Jin tayi shiru yasa shi tunanin ko ta yafe mashi ne, matsawa yayi kusa da ita, ya ɗan kwantar da kanshi saman kafaɗarta da sauri ta sanya hannu ta ture shi da karfi ta wurga mashi harara da kakkausar murya tace"kada ka ƙara gigin ta6ani! Idan har ba so kake inyi maka abunda baka ta6a tsammani ba! Kabarni inji da abunda ke damuna Danish! Ka nisanta kanka dani zaifi maka kwanciyar hankali" Kamar karamin yaro haka ya fashe mata da kuka, bawan Allah Ya rasa meke yi mashi dadi a duniyar nan "Ki tausayama rayuwata angel, ki yafe min koda ba zaki cigaba da kula ni ba, bana so kina fushi dani, na yarda na amsa laifina, ki yanke min kowani irin hukunci ne a shirye nake dana kar6e shi...." Bata ta6a ganin tashin hankalin akan fuskarsa irin na yau ba, taji tausayin shi amma in ta tuna irin rashin imamin daya yi mata adaren shekaran jiya sai ta ji taƙara jin tsanar shi, akan me zataji tausayin shi bayan shi bai tausaya mata ba? kalaman auntyn ummi ne suka fara dawo mata cikin kanta, idan har tabari namiji yana ta6a ta zata samu ciki, wannan maganar ta ɗaga mata hankali, tabbas in har ta cigaba da bashi fuska zaicigaba da kokarin kusanta kanshi da itane, wannan dalilin ne yasa tace"Zan yafe maka, amma abisa sharaɗi ɗaya"? Jikinsa na kerma yace"wani irin sharaɗi ne"? "Kayi min alkawarin zaka yi komai nace"? ɗaga mata kai yayi alamar eh "Daga rana irin ta yau bana so ka kara kusanta kanka dani...." kafin ta kare maganar yace"bazan iyaba angel..." da sauri ta daura yatsanta kan la66ansa da ruwan hawaye suka jiƙa tsit yayi yana sauraronta "Idan har dagaske kai garkuwa ne agareni mai bani kariya daga dukkan abun cutarwa toh inaso kabani kariya daga sharrinka danish! Ka nisanta kanka dani, in har kana son farin cikina, saboda ganinka da nakeyi a yanzu raina yana 6aci..." wasu zafafan hawayene suka kara wanke fuskarshi "Baka da mafita data wuce wannan! In har kayi min hakan zan yafe maka.." runtse idanunshi yayi yana jin wani irin kunci da takaici kamar ya binne kanshi haka Yake ji, bakomai ya fado mashi aranshi ba face kalaman chief, dayace mashi ya bata tazara kada ya tursasa mata saboda ayanzu tana akan dokin zuciya! Numfashi Yaja kafin a hankali ya buɗe idanunshi a acikin nata, har saida gabanta ya fadi ganin yadda suka kaɗa jawur tamkar an watsa mashi barkono a cikin su, kyakkyawar fuskarshi ta 6aci da ruwan hawayen shi har cikin ranta tana jin kamar bata kyauta mashi ba. Cikin rauni na murya yace"na amince in har hakan zaisa ki yafe min, bazan ƙara takura maki ba" dakyar ya kare maganar, kafin ya kifa kanshi saman laps dinshi "Danish! Ta ambaci sunan shi bai amsa mata ba, "Bana so wani yaji abunda ya faru atsakaninmu! Koda chief ne! Duk da bansan ko ka riga da ka faɗa masa ba" muryarshi kasa kasa yace"ban fada masa ba" ajiyar zuciya ta ɗan sauke, da sauri ta share hawayen ta kafin ta kuma cewa"don na yanke alakar dake atsakaninmu hakan ba yana nufin bana sonka ba! Kawai bana son ka akusa dani ne, sannan bana son hukuncin da na yanke ya shafi rayuwarka! kada ka hana idon ka bacci saboda dani, kuma kada ka ƙi cin abinci, idan kayi hakan bazan ji dadi ba..." tana magana hawaye na kara wanke fuskarta, kasan hijab din jikinta ta sanya ta share hawayen kafin ta daidaita nutsuwarta. Kafin Takai hannu ta zuge window glass ɗin motar, tayi ma chief magana don ya buɗe mata car door ɗin da ta gaza buɗe wa, dagangan Ya datse kofar motar shiyasa ta gaza buɗe, yanzu daya tabbatar sun gama magana, da kanshi ya buɗe mata, ta fito idanunta cike tab da kwalla dakyar ta haɗiye kukan da take ji, haɗa ido sukayi cikin na juna, muryarta ƙasa ƙasa ta furta"mun gama magana inaso zan tafi" bata san hawayen da take 6oyewa sun fara sintiri kan fuskarta ba, hanky ya zaro mika mata"ki share hawayenki"! Kar6a tayi a hankali ta fara share kwallar Iphone dinta dake a hannun shi ya miƙa mata"na sa maki card, zan kira anjima zamu yi magana, ki koma ciki yanzu" amsa mashi tayi da toh nagode, kamar karta tafi haka take ji tana tafiya tana waiwayon motar zuciyarta cike fal da tunanin shi.... *AFTER SOME DAYS* (Bayan wasu kwanaki) tun daga ranar da chief Ya kawo danish asibitn bai ƙara matsa mashi akan ya kawo shi ba, daga shi har ita unaisah din sunji jiki ba kaɗan ba daurewa kawai sukeyi, sauƙin su ɗaya kowannansu Ya samu abunda Yake ɗebe mashi kewa, chief ya zama tamkar abokinshi baya barin shi acikin damuwa, sai da yasan ta yadda yai harya samu kar6uwa a wurin danish, kullum suna atare abinci ma atare suke cin shi, abu uku ke raba su lokacin sallah, lokacin zuwan chief wurin aiki da kuma lokacin bacci, wani lokaci har ƙarfe shabiyu na dare suna kaiwa adakin danish harya fara koya mashi yadda zaiyi rubutu da yadda zaiyi amfani da waya harma da laptop, saboda yana son su fara making phone call da prime minister hateem, su big guy har mamaki sukeyi idan suka ga chief da danish suna magana cos basu ta6a tsammanin yaron zai iya sakar ma wani jiki acikin su har haka ba, bawan Allah Danish dannewa kawai yakeyi ba dan chief yana kokarin lallashinsa da debe mashi kewa ba da tuni ya jima da zaucewa, saboda rashin ganin unaisah ba karamin illa yakeyi mashi ba, duk daren Allah sai ya farka da radadin rashin ta, shi kadai yake haukanshi kafin Allah ya kawo mashi sauƙi, bai ta6a bari chief yaga gazawarshi ba tun da ya fahimci mutumin baya son damuwarshi kuma yana bashi kyakkyawar kulawa... Idan muka koma 6angaren Benazir jikinta yayi sauƙi sosai, tana samun kulawa a wurin mutane ukun nan da suka tsaya mata, dr jzz, hajiya layla da kuma unaisah, cikin ƴan kwanakin nan ta dawo hayyacin ta sai dai babu wanda Ya lura da hakan kuma bata nunama kowa ba, ita kanta tasan dalilin ta nayin hakan, dagangan take yin pretending, kusan kullum ne sai su anila sunzo dubata, haka zalika Alhaji ubaid da shureim basa gajiya da zarya wurin zuwa asibitin, har ila yau Alhaji ubaid bai haɗu da unaisah ba, ba su ta6a cin karo ba, duk lokacin da zaizo tana a toilet, ko tana bacci, itama Hajiya sarah tana kokarin zuwa asibitin duk da ayyukan office da suke yi mata yawa, sau ɗaya suka ta6a haɗuwa da unaisah har suka gaisa da junan su wani abu daya daurema unaisah kai muryar matar tayi shige data cousin din aunty pretty da ta ta6a kira, aikuwa aranar har jaraba kiran layin aunty pretty tayi saboda ta tuna da ita, sai dai kash ba'a ɗaga kiran ba, saboda wayar ta koma hannun zeenatu dr shureim ne ya bata donsu dinga gaisawa, ita kuma dama bata cika ruke waya a hannunta ba, sai ta wuni bata dauketa ba sai in ta tashi kiran dr shureim tukunna take daukarta.. Alhaji musa tun zuwan da yayi sau ɗaya, bai ƙara zuwa asibitin ba, ko awaya baya kira balle har yasan wani hali suke a ciki, gashi har dr ya fara tunanin sallamar su saboda taji saukin jikin ta sosai.. *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Tags Kurkukun Kaddara YOU MAY LIKE THESE POSTS Previous Post Next Post GET IN TOUCH SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 34 Complete by Novels Elite Admin August 30, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe ✍️ EPISODE 33 Kwance take tana sharar bacci cikin kwanciyar hankali, cikin bacci ta yi kwakkwaran juyi zata gyara kwanciyarta kwatsam tayi arba da fuskar mutun wani irin firgita tayi a haukace ta zabura zata mike da sauri Benazir ta cafko hannun ta ta ruƙe shi gam, suka ƙurawa juna ido batare da ƙyaftawa ba, Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yayi ba, ta rasa gane meyasa cikin ƴan kwanakin nan matarke tsareta da ido kamar zata lashe ta, aranta ta ayyana kodai ta6in hankalin nata ne Ya motsa? Kada fa ta hau ta da bugu tun ba hankaline da ita ba..tuni tasha jinin jikin ta, tana faman haɗiyar yawu kutt murya na rawa ta furta"am..um.. mamana! Tun yaushe kika farka"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda Benazir tayi mata rumfa kamar zata danne ta, babu alamun zata tanka mata tayi shiru tanata kallon ta...babban tashin hankalin unaisah hajiya layla bacci takeyi balle ta kawo mata ɗauki, tuni ido ya raina fata. "Dan Allah na roƙe ki, ki daina kallona haka, babaynki ce fa, ki na bani tsoro. .." sai da tay wannan maganar, Benazir ta saki murmushin gefen fuska har dimple dinta ya lotsa... "Babyna ne"? La66an unaisah na kerma tace"ni ce, dan Allah kada kiyi min komai..." ƴar dariya benazir tayi, wani irin nishadi take ji.. Shafa sumar kanta tayi har wani kyafkyafta idanu take Yi kamar wata mara gaskiya Unexpected ta ji ta manna mata sumbata kan kuncinta, kafin tayi wani yunkuri ta kara mata wani kan la66anta, runtse idanu tayi kamar zata fasa ihu ta furta"na shiga uku, tawa ta same ni"! dariya benazir tayi kafin ta janye jikinta daga na unaisah ta koma kan gadonta ta kwanta idanunta na fuskantar ceilling..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarta da sauri ta cusa kanta jikin pillow, Satar kallon ta unaisah tayi, ta rasa gane meke damun matar, ta fara tsorata da lamarinta, kwanakin nan ta canza mata, ba kamar farkon da tafara jinyarta ba, ko meyasa❓ Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta sauko daga kan gadon, ta lalla6a cikin sanɗa take tafiya, backpack dinta ta buɗe ta curo wayarta ta nufi toilet ta shige ciki, Text message ta tura ma daddynta "Daddy, barka da dare, daddy ni dai nagaji da zaman asibiti, gida nakeso in dawo" tana tura mashi text din jim kaɗan saiga kiran shi, tayi mamaki saboda batasa rai zai bata amsa ba kusan karfe shabiyu na dare, tayi zaton yayi bacci. Picking call din tayi tare da kara wayar a kunne"My daughter! Me kike yi har yanzu baki kwanta bacci ba? Wani abu ya faru ne"? Cikin muryar raɗa ta furta"ba abun da ya faru, kawai bana jin dadin yawan kallona da matar takeyi, duk in na farka tsakar dare saina ganta akaina ta tsare ni da idanunta" Sautin dariyar shi ce ta ratsa kunnanta aiko ta haɗe fuska kamar tana agabanshi tace "Daddy dariya kake yi min? "Sorry daughter, maganarki ce ta bani dariya, but ki ƙara hakuri Anila ta fada min next tomorror za'a sallame ta" Shagwa6e fuska tayi, ko tsoro bata ji ita kadai a toilet "daddy ina yan uwana? Yau banji muryoyin su ba" "Suna nan cikin koshin lafiya, basu da wata damuwa" Shiru sukayi na wani lokaci, zuciyar ta sai azalzalarta takeyi akan ta tambaye shi ina Danish amma ina takasa furtawa... Kamar taj ya karanci abunda ke zuciyarta sai taji yace"Daughter, labari me dadi, dan uwanki Danish ya fara koyon rubutu da karatu a wurin chief, abun saiya baki mamaki yana da kaifin basira, kamar ke lokacin da kina ƙarama, kwakwalwarsa tana ja, abun burgewa sun shaku sosai da chief in kika gansu kamar ƴan uwan juna, tare sukeyin komai......." batasan ya akai ta tsinci kanta da sakin murmushin gefen fuska ba, har cikin ranta taji dadin jin labarin nan da daddynta ya bata.. "Daddy, na taya shi murna, kuma naji dadi wlh, Allah ne kadai zai iya biyan chief, yayi mana hallacci arayuwar mu, ina jin dadin kyautatawarshi agare mu, Allah yasaka mashi da mafificin Alkhairinsa....." addu'o'i ta cigaba da yi mashi daddynta yana amsa mata da ameen Kafin daga bisani yace"daughter, ki koma bacci, bana so ki makara sallar asuba, kiyi addu'a kafin ki kwanta sannan ki kula min da kanki" "Toh daddy, kaima ka kwanta kayi bacci, ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama da juna, kasa motsawa tayi daga cikin toilet din, wani irin yanayi take jin kanta mara misaltuwa, tanaji aranta kamar tayi missing din wani abu da zuciyarta take muradin son gani, ta wani bangaren taji dadin labarin cigaban da danish ya samu sosai har wani dan murmushi ta saki Lumshe idanu tayi tare da jingina bayanta jikin wall na tsawon mintuna kafin ta juya ta buɗe kofar, cikin sanda take tafiya tana satar kallon gadon benazir, ta lullu6e jikinta da bargo da alama ta koma bacci, hakan ba karamin dadi yayi ma unaisah ba.. Kan gado ta haye ta kwanta tare da jan duvet tayi covering jikin ta wani baccin ne ya kuma daukarta... _________________________________✍️ *Hajjaty* Tun da sanyin safiya bugun kofa Ya farkar da ita, tana tsaka da jin dadin baccin ta, da wata irin kasala ta miƙe ta sauko daga kan gadon tayi miƙa haɗi da yin hamma, Ƴar rigar bacci ce a jikin ta, sai da ta fara daukar hula ta lullu6e kanta kafin ta nufi kofar tana tambayar wanene"? Daga waje tajiyo muryar sofia cikin tashin hankali tace"Aunty ni ce sofia, ki buɗe min kofa" da sauri hajjaty ta buɗe kofar ta leƙa kai tana kallon sofia wadda gaba ɗaya babu kwanciyar hankali atare da ita ..tunkafin taji me zata faɗa mata gabanta ya fara faɗuwa. "Sofia! Meke faruwa ne? naganki kamar ba lafiya"? Yarfa hannu safiya tayi murya na rawa tace"marwa! Aunty mun shiga uku, kizo kiga abunda ke faru ! Marwa ta kuturce. .." aruɗe hajjaty ta ce"bangane me kike nufi ba? Meya faru da ita? Wata irin kuturta . "? Bata jira hajjaty ta kare maganar ba, taja hannunta da sauri suka nufi dakin marwa dake anan corridor din da ɗakunan house maids din gidan su ke.. Shigarsu ke da wuya hajjaty tayi arba da ƴan aikin gidan gaba dayansu, sun hallara, fuskar kowan nansu sharkaf da hawaye cikin tashin hankali suke sallallami idanunsu akan marwa. Suna ganin hajjaty suka buɗe mata hanya don taga abun tashin hankalin da suke kallo, Lokacin da ta sauke idonta kan marwa dake nannaɗe kan katifarta rass taji gabanta yayi mata wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali, ta waro idanu waje, agigice ta daura hannayenta biyu saman kanta, ta zabga salati tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'u!! la66anta na kerma ta furta"Mar..marwa! Meya faru dake? Ya akai kika koma haka? ta faɗa tana kallon yatsun marwa da suka dunkule irin na kutare ga wani ruwa mai yauƙi dake gangarowa ta tsakaninsu,, la66anta sun shafe babu hudar baki kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba, wani irin nishi take saki, idanunta sun kaɗa jawur ga zufa data wanke jikin ta baiwar Allah ita kadai tasan azabar da take ji, sai faman zare na mujiya takeyi jikin ta nata kerma. Fashewa hajjaty tayi da kuka, gaba daya sautin koke koken su Ya cika dakin "Wayyo Allah! Na shkga uku! Dan Allah ku fadamun meya faru da ita? kaina ya kulle nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Jiya jiyan nan mukayi aikin dinner tare da ita lafiya lou muka rabu da ita...taya akai ta samu wannan lalurar ta kuturta? Ina bakinta yake"? Cikin shesshekar kuka tayi maganar Abla tace"Aunty bamusan meya faru da ita ba, yau da safe mun tashi zamu fara aikin breakfast, mun ga bata fito daga daki ba, shine nace ma sofia taje tayi mata magana kada mu makara, bayan tafiyar sofia har mun fara aiki muka jiyo sautin ƙararta daga dakin marwa shine muka taho da gudu mu duka dan muga mike faruwa a nan muka tarar da marwa cikin wannan halin.. ." ta ƙare maganar tana kuka Sofia tace"wlh bansan meya faru da ita ba, Nima haka na sameta, ina shigowa dakin na isketa a nannaɗe kan kafita, har ina zolayarta nace mata bana son iya shege kina ji inata ƙwala maki kira kinyi shiru baki ce min komai, wlh aunty dana zo gaban katifar naga hawaye idonta gashi babu hudar baki, yatsun hannunta sun kuturce bansan sa'adda na fasa ihu ba, ni ban ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba, Allah daga gani Aljanune suka shafe ta . ..." gaba daya duk sunbi sun ruɗe, hankalin su Ya tashi, jikin hajjaty na 6ari tace"ba kallonta yakamata mu tsaya munayi ba, bari inje in sanar da mutanan gidan..." da sauri ta fuce daga dakin... . Kafin wani lokaci gaba ɗaya mutanan gidan suka hallara a dakin marwa, da sauri maids din suka basu hanya don su shuga ciki, baba obie ne kan gaba jikin shi sai 6ari yakeyi, Pravin da twins suna abiye da shi, har sunyi shirin zuwa office wannan abun tashin hankalin Ya risƙe su, hada Hajiya saratu ta shigo ta zumbula buba ajikinta, sai faman raba idanu takeyi tun kafin ma taga meya faru da marwan!! lokacin da sukayi arba da marwa gaba ɗaya hankulansu suka tashi, sunyi matuƙar razana da ganin yadda halittar marwa ta canza, kowa sai tambayar ba'asi yakeyi, Tafa hannu hajiya saratu tayi"La'haula walakuwata illa billahil azim! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni filmusibati.. Gaba ɗaya tabi ta rikice, "Ya akai Haka ta faru? Wata irin lalura ce wannan"? Ta faɗa tana zare na majuya Masu aikin suka hada bakin wurin fadin wlh bamu sani ba, haka muka same ta, Idan hankalin su twins yayi dubu toh ya tashi, wani irin ƙyanƙyami da ƙyamar marwa ne Ya kama su, babu wanda Ya lura suka sa6e daga dakin suka yi tafiyar su don bazasu juri ganin tashin hankalin nan ba. Tsabar tashin hankali da kiɗima Ya hana baba Obie furta kalma, dama da ƴar cazbahar shi a hannu sai faman jan ta yakeyi yana ambaton sunan Allah Pravin dake a ruƙe da kofa fuskar shi a hautsine Yana ta faman zazzare idanu kamar na kwarton muzuru har wani gumi Ya haɗa muryarsa na rawa yace"yarinyar nan ba ta rasa iskokai akanta, daga gani aikin aljanune, taya za'ace farat ɗaya mutun ya tashi ba baki? yatsu kuma sun kuturce"? Jin wannan maganar Ta pravin Yasa hankalin hajiya saratu yayi mugun tashi, nan fa ido ya raina fata, dama a tsorace take da lamarin, baban tashin hankalinta kada itama abun ya shafeta, tunda kwana nan suna mutunci da marwa saboda aikin leƙen asirin da take yi mata, batare da kowa Ya lura ba, ta lalla6a ta fuce daga dakin marwa, jiki na kerma ta koma bedroom dinta, ta yi shirin zuwa office don ta bar gidan, saboda rashin tausayi maimakon ta tsaya su nema mata mafita tunda dai ita takeyiwa aiki Baiwar Allah marwa ba halin Yin magana, kukan zuci take mai ɗacin gaske, ga abu tana so ta fada amma takasa sai kallon hajjaty da pravin takeyi hankalin ta yafi kakarta akansu Dakyar baba obie Ya haɗiye tashin hankalin shi, Ya dubi maids din dake kuka cikin sanyin murya yace"kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, ba kuka yakamata kuyi mata ba, addu'arku take buƙata..." ya fada tare da kallon Hajjaty"ku taimaka ku dauko ta, muje asibiti aduba lafiyarta. " da sauri hajjaty da Abla suka haɗa karfi wurin cuccu6ar marwa suka fito daga dakin sauran masu aikin suka bi bayansu, tunkafin su fito baba obie yayi waya da ɗaya daga cikin jami'an gidan, Aka fiddo da mota mai kama da bus, aciki suka shigar da ita, kowan nan su Ya samu wurin zama, motarsu baba obie da pravin tana abiye da tasu a jere motocin suka fuce kaitsaye suka nufi asibiti💔 tunkafin sukai asibitin marwa take ta kallon hajjaty kamar zata hadiyeta ita kanta hajjatyn dake aruke da ita tayi matuƙar tsorata da kallon da marwa keyi mata ga wani nishi da gurnani da takeyi😢 (Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana❓❗) __________________________________✍️ A zaune take kan dinning chair, ta sanya abaya dogo ajikinta, table din gabanta cike Yake da kayan breakfast ita kadai ta rage a dining, tana cikin shan tea a cup, ƙamshin turaren dr shureim Ya daki hancin ta, da sauri ta ɗago tare da kallon inda take jiyo sautin tafiyarshi, a tsanake Yake tafiya cikin kamala, Ya sanya shadda a jikin shi ta zauna mashi yayi wani fresh da shi hannun shi ruƙe da car key, Tunda ta kafe shi da ido sam ta kasa daina kallon shi, saboda yayi mata kyau Karasowa yayi gaban dining din, fuskarshi dauke da murmushi Ya furta"sanyin idaniya, ina fata kin tashi lafiya"? Farfari tayi mashi da ido hadi da sakar mashi murmushi kafin tace"hubbyna na tashi lafiya, ina fata kaima haka" Yace Alhamdulillah, "Yaya shurem, Ka zauna mu yi breakfast, ko ka riga da kaci ne? Yau ni kaɗai na rage a dining, ban iske kowa ba .." "Bana jin yunwa, Inason zan fita ne" yanayin fuskarta ne Ya canza, kamar zata fashe mashi da kuka tace"dan Allah ya shureim kada ka tafi kabarni agida ni kadai, kaga mommy ta tafi office, daddy da uncle sun je party meeting, kullum sai ni kadai kuke bari agida bana aikin kome" ta faɗa da shagwaba... Shiru yayi yana tunanin meya kamata yayi? Shi ma baison suna tafiya su barta agida ita kadai baisan ya zaiyi da ita bane tunda bata son zuwa asibiti wurin Benazir, gashi har benazir ta fara tambayar shi ina zeenatu, itama hajiya layla abun ya fara damunta duk in yaje sai tace wai meya hana zeenatu zuwa. Wata dabarace ta fado mashi aranshi, da sauri ya dubeta ta kura mashi blue eyes dinta masu walwali "Zaki rakani mu tafi atare inda zanje"? "Ina zamuje"? "Wani wuri ne..." shiru tayi jim kafin tace"ni dai saika fadamin ina ne" "Yawon buɗe Ido" waro ido tayi kafin tace"dagaske"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, da sauri ta mike tana fadin"yaya shureim bari naje na canza kaya" "Okey, ki same ni a mota, but karfa ki dade" amsa mashi tayi da toh, jikinta na rawa tsabar zumudi ta nufi part dinta Murmushin gefen fuska shureim ya saki aranshi ya furta"yau zanga meke akanki my zeenati"! Ya faɗa tare da juyawa ya fuce daga falon After some mins, Yana zaune a driver's seat, Ya dan jingina kanshi jikin headseat, har ya lumshe idanun shi Yaji motsin buɗe car door, A hankali Ya kalli zeenatu dake kokarin shigowa ciki, wani irin sanyayyan kamshin turarentane Ya ratsa hancin sa, kamar wadda zataje gasar miss world, wata hadaddiyar emirati abaya ce ta sanya launin yellow, abunka ga jinsin turai ta fito fara fess rigar tayi mata kyau, ga wani veil da tayo rolling, hannunta ruƙe da wayarta, kafarta kuwa wasu highhills ne masu tsini, harta zauna dr shurem bai daina kallon ta ba... Farfari tayi mashi da ido voice dinta da shagwa6a tace"yaya shureim wannan kallon fa" kayataccen murmushi ya sakar mata, tare da kai hannu ya shafa sajen shi, key yai wa motar, ya ɗanyi reverse kafin Ya fara driving slowly Ya nufi katafaren gate din gidan, tunkafin Ya karaso waɗannan Samudawan security office din suka yunkuro kamar zasu rufe motarshi da bugu ba don komai ba sai don saboda Ya dauko zeenatu... Ba arziki yayi parking motar, ya sauke glass din Yana kallon su da kakkausar murya daya daga cikin su Yace"da iznin wa zaka fita da ita.. " saboda karfin hali na dr shureim Ya wani hade fuska Yace"daddyn ta ne Ya bani izni" arude zeenatu ta kalle shi wato taji ya shureim yayi karya agabanta "Amma mu bai fada mana ba"! "Ku kira shi awaya sai kuji" ya fada yana ƙara tamke fuskar shi Kiran alhaji musa sukayi wayar tayi ta yin ringing ba'ayi picking ba, dr shureim Allah Allah Yake kada Alhaji musa ya ɗaga, kai hada addu'a yayi a zuciyar shi, cikin sa'a bai ɗaga ba.. Muryar zeenatu na kerma tace"ku kira mommy ku tambayeta, ay itama tasan da zancen fitarmu, daddyne ma yace ya tafi dani..." ba suyi ƙasa a gwiwa ba suka kira hajiya saratu bugu uku kafin suka samu ta ɗaga... "Ranki ya dade, da izninki dr shueim zai fita da zeenatu"? Kallon juna zeenatu da dr shureim sukayi duk suka sha jinin jikin su, fargabansu kada hajiya sarah ta kwafsa masu "To amma shi yalla6ai yasan da fitar su? Hajiya sarah tace"eh ya sani, kawai ku barsu su tafi"..kusan atare dr shueim da zeenatu suka sauke ajiyar zuciya.. munafukan gate officers din ba don sunso ba suka basu hanya, dr shurem Ya ƙara wa motar gudu Ya fuce daga gidan.... Lumshe idanu zeenatu tayi tana dariya tace"ya shureim kasan Allah da ace daddy ya ɗaga kiran nan da sukayi mashi wallahi bazai bari ka fita dani ba, ni narasa gane dalilin dayasa yake kullena kamar wata matar aure..." "Mommynki ta rufa mana asiri wlh, naji dadi my zeenatu, kinga yanzu zamu sakata mu wala..." yai maganar hankalinsa na akan driving din da yakeyi, A hankali ta daura hannunta saman dayan hannunshi gefe tare da lumshe idanunta, har satar kallon ta sai da yayi kamar wata jinjira komai nata burge shi yakeyi... ________________________________✍️ Gaba ɗayansu sun shirya tsaf, zasu ziyarci gidan uncle abdallah, tun daga kan mami, ummi, zahra, abi, da uncle ɗan iya, kowannansu ya ɗauki wanka na mutunci namu na hausawa, mutun biyu ke babu a cikin su, mahboob wanda tun safe ya tafi kai baby junaid school, har yanzu bai dawo ba.. A tare suka fito daga falon gidan, suka nufi harabar ajiye motocin su, Mami tace"yau dai Allah Ya nufa zamu cika mata alkawari, baiwar Allah mun saka mata rai, kullum ayta za'aje za'aja amma shiru.." ummi tace"nasan zatayi farin ciki idan taganmu kwanmu da kwarkwatarmu don ma babu junaid, ay da sai tafi jin dadi munzo mata da ɗan jikallan ta..." .murmushi kowannansu Yasaki, A bakin motocin suka dakata da yin tafiya, suna jiran Aneelerh da zahra su fito, Abie Yace"wai zaman me sukeyi agidan? Kwalliyar ce har yanzu ba'a gama ba? Uncle ɗan iya yace"da rabon mu tafi mu barsu agidan sun taho daga baya, dama tafiya indai da mata za'ayi ta to fa sai an 6ata lokaci, su komai nasu da nawa babu karsashi..." ya faɗa yana haɗe fuska.... Acan cikin gidan kuwa, fitowa zahra tayi ta dauki wankan atampa, an yafa veil a kafada, hannu ruke da jaka, ta ca6a uban ado, dakin aneelerh ta nufa, kafin takaiga kofar dakin sai ga Aneelerh fito cikin sauri, wata hadaddiyar lafaya ta laga a jikin ta,launin orange mai adon stones, ta fito ɗass abunta, itama ta ruko handbag din ta, zahra na ganinta taci burki tana fadin"Aunty aneeleeh! kinga yadda kikai kyau? Meyasa baki fadamin lafaya zaki sanya ba nima ay saina sanya nawa" ta fada tana hade fuska, murmushi Anila tayi"kai zahra ay kin ma fini kyau, kinga su abie suna jiranmu, mu tafi kada mu 6ata masu lokaci" ta fada tare da ruko hannun zahra suka fara tafiya, har sun kusa fita daga falon muryar Ana ta katse masu hanzarin su "Aunty Anila, Allah ya kiyaye hanya agaishe min da hajiya adama..." dakatawa sukayi da yin tafiyar, a wani irin yanayi Anila ta dubi fuskar Ana wadda ke acan tsaye kofar kitchen jikinta sanye da riga da mini skirt, ta ɗaure kanta da hula sai faman sakar mata murmushi takeyi . Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa, "Zahra kunyi kyau sosai, kun burgeni, sai naji dama hada ni zaku tafi" murmushi zahra ta sakar mata"mungode kada ki damu next time idan zamu ƙara zuwa hada ke zamuje, yanzu dai ki koma kitchen, pls kafin mu dawo ki gyara mana bedrooms dinmu sunyi datti..." amsawa tayi da toh, kafin ta sake kallon Anila wadda keta kallon ta ko kyaftawa bata yi murmushi Ana ta sake yi mata "Aunty anila, adawo lafiya.." Dakyar ta jinjina mata kai, cikin sanyin murya ta furta"Ana ba lallai mu dawo da wuri ba! Ki kula da gidan, sai anjima" awani slow ta kau da idonta daga na Ana, taja hannun Zahra suka fuce daga gidan... Ana tana a kitchen tana goge gogen floor da wiper ta jiyo tashin motocin su, *AGIDAN UNCLE ABDALLA" Hajiya Adama Yau ba zama, tunda Anila ta sanar da ita zancen zuwan su, ta fara yan gyare gyaren gida, ganin tana ta wahala ita kadai ga girkin da zata yi masu ko farawa batayi ba, hakan yasa Uncle abdalla Ya dauko mata hayar house help wata bayerabiya kakkarfa, atare da ita suka fara girkin cikin kankanin lokaci suka kammala shi, hajiya adama har mamakin matar takeyi kamar inji bata gajiya da aiki, tana da kwazo da ƙwarewa ta bangaren aikace aikacen gida, kafin wani lokaci sun kammala tsaftace gidan.. da sauri hajiya adama ta shiga toilet, tayo wanka, ta fara shirya kanta,wani tsadadden leshi ta sanya a jikinta, ta kashe daurin dankwali, ta zauna kan mirror chair tana ƙarasa yin make up ɗin ta... Sallamar uncle abdalla ce ta katse ta, "Har yanzu ba su iso ba"? ta cikin mirror ta kalle shi suit ne a jikin shi.. "Nima naji shiru, amma ina ji araina sun kusa karasowa, "Kodai basu gane gidan bane"? "Bana tunanin hakan, ay na tura mata address din gidan tun jiya, bari na kira Anila naji.." ta fada tare da miƙewa ta nufi wayarta dake ajiye kan mattress, kafin ta ɗauko kiran waya ya shigo da sauri ta duba sunan mai kiran nata, murmushi tayi tare da kallon uncle abdalla"Anila ce ke kira" picking call din tayi ta kara wayar a kunne "Anila kun taho ne"? On the other hand anila tace"Eh, dama na kirane in fada maki mun kusa shugowa unguwan naku" wani irin farin cikine ya lullu6eta"Allah ya kawo ku lafiya" bayan ta katse kiran ta kalli uncle abdallah"tace min sun kusa isowa, yakamata muje mu taro su" Murmushi uncle abdalla yayi"naga kina ta zumudin zuwan su, idan ma don saboda junaid ne kwara ki fidda rai, yau ranar school ne, ba lallai su zo da shi ba" daure mashi fuska tayi"ko baka fada ba, na sani, farin cikin dakaga inayi badan komai ba sai don saboda za'a kawo min ziyara gidana, kasan ba wani ke gareni a garin nan ba..." tay maganar tare da daukar mayafi ta yafa akanta, Tayi gaba yabi bayanta. daidai lokacin da suka fito daga entry hall, suka hango mai gadin gidan Ya buɗe gate, a jere motocin suka kunno kai cikin gidan, Bayan sunyi parking, hajiya adama ta nufi motocin da sauri kafin ta karaso anila ta rigata fitowa da sauri ta nufe ta suka rungume juna fuskar kowannansu dauke da annurin farin ciki. Abie da Uncle dan iya suka nufi uncle abdalla dake tunkaro su, suka fara yin gaisuwarsu ta manya” Sassannun ku, da zuwa, ku ƙaraso ciki”, Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su ɗauke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta miƙa mata hannu suka gaisa a mutunce,kafin ta janyo zahra tayi hugginta dinta, daga bisani suka haɗu gaba daya suka shiga falon gidan, yau ne karo na farko da su anila suka fara zuwa, zahra sai yan kalle kalle takeyi gidan ya burgeta ginine babba, ita kanta anila tayi mamakin haduwar gidan surukan nata, an wadata gidan da duk wani abu na biyan bukata. Bayan kowan nan su Ya zauna kan sofa, Uncle dan Iya yace"masha Allah, kunsan ni bani gani inyi shiru, abdalla kayi kokari wannan dankareran gida haka kamar dubai"? ya fada Yana bin falon da kallo, hakan ba karamin dariya ya basu ba, Mami tace"naso ace tuntuni mukazo ganin gida Allah bai nufa ba sai yau, gaskiya bamu kyauta ba.." hajiya adama tace"ay kun goge laifinku, tun da kuka zo yau gaba dayanku don ma babu jikalle na..." Mami tace"Allah sarki, Ya tafi school, abunda yasa ma bamu tsaya jiran shi ba, sai marece suke dawowa.." Fira ce ta barke tsakaninsu yadda kasan dangi ɗaya, daga bisani bayerabiyar dake a gidan ta shirya masu abinci akan dining, suka hallara gaba daya suka zauna suna ci, uncle dan iya sai santin abincin yakaye yi, ita dai anila hankalinta kamar ba akwance yake ba, ta kasa cin abincin, saboda wani irin faduwar gaba da take ji.. "Anila meke damunki ne? Naga kamar bakison cin abincin" cikin kulawa hajiya adama tay maganar, cikin sanyin jiki Anila tayi murmushi tace"babu komai mommy, abincin ne yayi min dadi shiyasa nake santin shi" dariya hajiya adama tay"karki damu idan ma baki koshi ba zansa akara maki ne nafi so ku ci ku koshi dama saboda ku akai girkin dayawa" murmushi kowan nan su yayi, zahra ba baka sai kunne Hankalin ta na akan plate din fatan doyan da take ci...... _______________________________✍️ A hankali motar dr shureim ta kunno kai cikin entrance gate din asibitin, bayan yayi parking din motar, Ya dan juya ya kalli zeenatu data langwa6e kanta kan shoulder dinshi, kwata kwata batasan inda suka zo ba, ta nutsu tana shakar kamshi turaren shi ta wani lumshe idanunta... Cikin sanyin murya ya furta"zeenatu mun ƙaraso" buɗe idanunta tayi tare da gyara zamanta, kwata kwata bata lura da inda suka zo ba, kusan atare suka fito daga motar, kamar ance ta kalli saman ginin karaf idanunta suka sauka akan sunan asibitin da aka rubuta da manyan haruffa masu daukar ido, wani irin bugu kirjinta yayi da sauri ta dafe saitin zuciyarta, "Yaya shureim! Ina ne nan? Kamar asibiti nake gani? Dama nan zaka kawo ni"? Cikin rawar murya tay maganar tana ja da baya "Zeenat ki kwantar da hankalin ki, kamar yadda kika gani asibiti ne, wurin auntynki benazir na kawo ki, kullum saita tamabayi kina ina meyasa baki zuwa dubata...." bai ƙare maganarba, zeenatu ta juya a firgice ta damƙi murfin motarsu ta kutsa kai zata koma ciki da sauri Ya cafki hannunta ya fiddo da ita yana fadin meya haka zeenatu? Meke damunki ne? Benazir din ke bakison gani" wani irin kakarwa jikinta ya farayi ta ɗaura hannu biyu akai ta fasa wata iri gigitacciyar ƙara wadda tajanyo hankulan visitors din dake zarya a harabar asibitin, gaba daya hankalin mutane ya dawo kansu wasu har sun fara tambayar meya faru? wasu kuwa sunyi tunanin wani mugun abun akai mata...." Cikin shesshekan kuka da murya mai ƙaraji take fadi "bazan shiga ba Yaya shureim ka maidani gida, wayyo Allahna na shiga uku, na bani ya shureim...." tsantsar tashin hankali ne akan fuskarshi gaba daya tabi ta rikitashi, ga jama'a da suka tasa shi gaba suna tambayar me akai mata...bai san sa'adda ya janyota kan kirjinshi ya rungumeta sosai kamar zai maida ita cikinshi, idanunshi sun kaɗa jawur yai saurin kai la66anshi saitin kunnanta, A hankali ya fara zuba mata kira'ar alqur'ni wohoho zokaga idanu mutane sun nutsu suna ba idonsu abinci, wasu sai santin karatun shi sukeyi, yayin da wasu kuma suka kokwanton watakil aljanu gare ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar zeenatu, gaba ɗaya ta narke mashi tana faman sauke ajiyar zuciya, tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa shi, tayi shiru sai ƙara nutsa kanta cikin kirjinshi takeyi, mutanan dake kallonsu sunyi masu ƙawanya hada masu daukarsu hotuna da video hakan yasa shi kare fuskarshi ya ƙara ƙanƙame zeenatun shi, ahaka yajata suka nufi cikin asibitin don bayajin zai iya juyawa da ita gida.💔 Duk ta kankame shi, mutane sai kallonsu sukeyi, nurses har tambayar shi suke yi patient ce? Yace masu a'a lafiyarta lou, hajiya layla dake tsaye tana waya bakin kofar privet room juyowar da zatayi keda wuya ta hango su, arude take binsu da kallon har suka karaso inda take "Shureim wacece wannan ka rungumo haka"? Ta fada tana kallonta sam bata gane wacece ba saboda ya rufe fuskarta. "Mami zeenatu ce, tazo duba jikin benazir ne" A ruɗe tace"meke damuntane? Ke zeenatu ya akai? Ko bakison zuwane aka matsa maki? Muryarta kasa kasa ta furta"bana jin dadin jikina..." "Haba shureim kasan bata da lafiya ka taso ta? Ko likita kukazo gani ne"? "A'a mami, lafiyarta qalou, zanyi maki bayanin abunda ke damun ta, mu shiga daga ciki....." ___________________________________✍️ A lokacin Unaisah tana zaune kan chair din gaban gadon Benazir, hannun ta ruke da glass na ruwa, magani take bata in ta sanya abaki saita bata ruwan ta sha, ta maida kanta kamar ƙaramar yarinya agaban unaisah, har yanzu bata daina binta da kallon kurullan ba... "Mommy ki maida hankali kan ruwan da kike sha, kada ki shake" murmushi taskar mata"bana gajiya da kallon ki ne, Kin sace min zuciyata" da mamaki unaisah take kallonta, kalaman matar suna sanyata kokwanton kamar ta dawo hayyacin ta Shigowarsu dr shureim dakinne Yaja hankulansu ga kallon kofar, "Benazir yau Allah yayi, zeenatu tazo dubaki, sai dai kamar bata jin dadin jikin ta,..." da wani irin yanayi benazir ke kallon zeenatu wadda ta 6oye fuskarta jikin shureim...cikin sanyin murya ta furta"Zeenatu...."! shiru bata amsa mata ba, Unaisah dai ta zuba ido tana kallon matashiyar dake kankame da shurem, jikinta sai kerma yakeyi kuma taƙi dago da fuskarta... "Zeenatu bakiga auntyn naki ba"? In a low voice ta furta"bana son ganinta" waro ido waje benazir tayi sam ta manta da pretending din da takeyi saboda ruɗewar da tayi, lamarin ya daure masu kai, arude hajiya layla ta kalli shureim suka hada ido, unaisah dake kallon su abun ya bata mamaki aranta ta ayyana kowacece wannan take ta wani boye fuskarta? Yanzu haka bawani kyan kirki gareta ba, in banda wulakanci hada wani cewa bata son ganin mamanta, yanzu haka yar kishiya ce... Acikin zuciyarta take wannan sambatu Banezir kuwa jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya da jin kalmar da zeenatu ta furta abun Ya girgizata sam takasa magana sai motsa la66anta take "Pls kada hakan Ya dame ku, bayin kanta bane, Ina tunanin iska ne suka shiga jikin ta..." calmly ya zayyana masu komai dangane da abun da ya faru ranar farko da ya koma gida har yayi mata maganar benazir ta share shi, har zuwa ga abunda ya faru yau, mami ta tafa hannu tana ambaton "inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in zeenatu Allah ya baki lafiya, Allah ya yaye maki abunda ke damunki, baiwar Allah ashe shiyasa tadaina zuwa asibitin, sannu zeenatu ta faɗa tana leƙen fuskarta, banza tayi da ita, benazir dai takasa magana kallon su kawai takeyi, ita dai unaisah ta baza kunne tana sauraron su bakomai ya bata haushi ba face Yarinyar da take ta boye fuska. "Yaya shureim ka maidani gida! Kada daddy ya dawo ya iske bana nan!..." Cikin kwantar da murya yace"ko ya dawo ba abunda zaiyi maki, ai ni na fito dake, da anjima zan maidaki, mu karasa ciki ki zauna..." yai maganar yana kokarin janyota cikin dakin, aikuwa ta turje tana yan fizge fuzge Hankali atashe mami tace"shureim abun da ban tsorofa kamar ba zeenatu ba, pls ka maida ita gida, tunda ta nuna bata son zama nan din.. Shi dai baison Ya maida ta gida saboda bai shirya komawa ba "Mami babu kowa gidan, ita da kanta ta nuna batason zama ita kadai shiyasa na taho da ita..." ya fada fuskarshi ayamutse... Saukowa Benazir tayi daga kan gadon ta tsaya agabansu cikin karyayyar murya ta furta"zeenatu! dagaske bakison gani na"? da wata irin tsiwa ta furta"Bana son ganin ki, ki daina yi min magana...." kafin ta ƙare maganar, Benazir takai hannu ta damƙi shoulder dinta dakyar ta rabata daga jikin dr shureim ta jijjigata da karfi har mayafin daya rufe fuskarta ya zame kan kafaɗarta.... Kamar daga sama sukaji Sautin fashewar glass kusan atare suka kai dubansu ga Unaisah wadda ta miƙe a sukwane tana faman zazzare idanun ta, tsantsar tashin hankali da rudani ne akan fuskarta "Azeezaty meya faru...." hada baki sukayi wurin tambayar ta, la66anta sai kerma sukeyi gaba ɗaya ta rikice ta kasa magana, gabanta na faduwa ta nufi zeenatu wadda ke ta kerma tana zare blue eyes dinta akan fuskar Unaisah Wani irin gumi ne ya wanke fuskar Angel duk da sanyin A.c din dake a dakin, ta sanya tafukanta ta murza idanunta saboda tana kokwanton ko dai gizau takeyi mata ne? In ba haka ba tayaya mutumin daya mutu zai dawo araye? Ta kasa yarda da abunda idanunta ke nuna mata, kusan sau uku tana murza su don su dawo dai dai, Hankulan su dr shureim na akanta, sun rasa gane meke damun ta! Ko dai tasan zeenatu ne? Meyasa ta razana da ganin zeenatu harta fasa water glass din hannun ta! Dukansu kansu ya daure Agaban zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai unaisah tayi da hannayenta biyu saboda wani irin sara mata da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta*"UNAIZA❗❓* *Daga Alkamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 35 Complete by Novels Elite Admin August 31, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️💋✊🔥 Agaban Zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai Unaisah ta yi da hannayenta biyu saboda wani irin sara matan da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta"UNAIZA❗❓ Arude Hajiya Layla ta maimaita sunan Unaisah Dr Shureim yace"wacece Unaizah"? Cike da fargaba Unaisah ta nuna Zeenatu da yatsan ta"ita ce, Yar uwarmu Unaizah...." gaba daya ta rikita lissafin ƙwaƙwalwarsu, Zeenatu da ta gama ruɗewa idanunta Azazzare ta furta"bani bace! Ni bansan ki ba, ban ta6a ganin ki ba. ..." Sautin muryar Zeenatu ya ƙara rikirkita ta, runtse idanunta tayi brain ɗinta ta fara tariyo mata muryar Unaizah idan tana magana! Tabbas wannan Unaiza ce ta dawo...." fashewa tayi da kuka ta cakumi hannayen zeenatu"wallahi ke ce, Unaizah din mu, yar uwarmu wadda ta rasu tayaya akai kika rayu bayan kin mutu ..."? Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana. Al'amarin yayi matuƙar ɗaure masu kai, Hankali atashe Benazir ta furta"babyna wacece Unaiza? Shiru Angel ta yi hawaye na sintiri kan fuskarta... Dr shureim yace"kodai tayi maki kama da yar uwarki ne? Ita wannan sunan ta Zeenatu ba Unaizah ba, bayan haka naji kin ambaci yar uwarku wadda ta mutu in banda abunki wanda ya mutu ay baya dawowa watakil sunyi maki kamane...." kalaman dr Shureim Sunyi tasiri a cikin zuciyarta, amma taya haka zai yiwu? Komai nasu iri ɗaya kamar mutun ɗaya! farar fatarsu, da launin idanunsu blue, hatta blonde hair dinsu iri ɗaya, bugu da ƙari surar jikin su, tun daga kan sirantakar su har big boobs din iri ɗaya. Gaba ɗaya ta jefa kanta aruɗani, su Benazir sun kafe ta ido suna kallonta, Kokwanto ta fara yi kodai gizau fuskar Unaizah takeyi mata akan fuskar yarinyar? Nan take tayi believing da abun da zuciyar ta ke fada mata saboda tasan ba mai yiwuwa bane, wanda ya mutu ya dawo, abu ɗayane zaisa ta yarda da abun da idanunta suka gane mata, wanda bakomai bane face Ƴan uwanta suga yarinyar nan! muddin suka ruɗe suka ambaci sunan ta da unaizah to anan ne zata gasgata abunda idanunta suka gane mata...." Lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya, sam takasa janye idanunta daga kallon fuskar Zeenatu, A hankali ta kau da idonta tare da kallon su shureim wata irin kunyarsu ce ta kama ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah, ku yi hakuri, na ruɗe ne, wallahi tayi min kama da wata dana sani, amma ita tama mutu tun da jimawa...." nannauyar ajiyar zuciya suka sauke, har suna hada baki wurin furta"Allah yajiƙanta da rahama.." Yawu Unaisah ta haɗiya mai zafi a makoshin ta, kafin ta sake kallon Zeenatu dake kallon ta"sister kiyi hakuri dan Allah, na tada maki hankalin ki, kuskuren fahimtane...." murmushi zeenatu ta sakar mata, su kansu saida sukayi mamakin murmushin da tayi ma Unaisah Cikin sanyin murya ta ce"Kada ki damu, babu komai...." miƙa mata hannu Angel tayi don su gaisa, da sauri zeenatu ta zira hannunta acikin nata sukayi musabaha, yau ne karo na farko da suka fara sanin junansu amma ga dukkan alamu sun kamu da kaunar juna, tabbas da ace lokacin da aka kawo masu Unaiza ta fada mata twins ne su wlh da ba abunda zai hana ta dafe alkur'ani tayi rantsuwar wannan Yarinyar Twin sister din Unaizah ce!! Ta dai bar abun aranta har zuwa lokacin da Allah zaisa ta hadu da su Batool sune zasu kara tabbatar mata da abunda take zargi na kamannin ZEENATU da UNAIZAH.........💔. Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikin su, wayar shureim ta fara ringing, a hanzarce ya curo wayar daga aljihu yai picking call ɗin "Shureim! Ka dawo da zeenatu gida, Ina jiran ka" rass yaji gaban shi ya faɗi, tun daga kan yanayin muryar Alhaji musa ya fahimci ba lafiya, ko jiran amsar shi baiyi ba ya katse kiran. "Wanene Ya kira"? Hajiya layla ta fada tana kallon fuskarshi "Uncle ne, Yace in maida zeenatu gida" Ta6e baki hajiya layla tayi ba tare da tace komai ba Har lokacin Zeenatu bata cire hannun ta daga na Unaisah ba, sun ƙurawa juna ido kowa da abun da yake saƙawa aranshi...... "Muje zeenatu" muryarshi ce ta katse shirun nasu, sallama yayi masu hajiya layla, ya ruƙo hannun zeenatu suka tafi, Unaisah bata daina kallon su ba, har leƙen su tayi abakin kofar dakin itama zeenatun suna tafiya tana waiwayon ta hada ɗaga mata hannu tayi mata bye bye...💔 *CHIEF OWAIS🔥✊* Slowly dankareriyar motar shi ta kunno kai cikin villa dinsa, yana daga zaune ya hakimce a backseat, su biyu ne a mazaunin baya big guy dake a gefen sa, kowan nansu kaki ne a jikin shi, da alama sun kwaso gajiyar aiki duba da yadda kowan nan su ya lumshe idanun shi kamar masu jin bacci.. .. bayan sun karasa parking space agent din dake driving nasu yayi parking A hanzarce Wani agent daga cikin jami'an dake kai komo a harabar ya karaso ya buɗe masu murfin motar. "Sir, mu shiga daga ciki" ya faɗa yana leƙen fuskar shi yayi shiru, soft lips dinsa sun bushe sun ɗan ciza kalarsu pink kamar bazai motsa ba, big guy yayi tsammanin bacci yakeyi hakan yasa shi kai hannu ya dafa shoulder din shi, da wata irin kasala ya buɗe reddish eye dinsa tare da kallon big guy "Mun ƙaraso gida, nayi tsammanin bacci kake yi.." yamutsa fuskar shi yayi, da zolaya big guy yace"ka bani dama in goya ka mana.." harara chief ya jefa mashi tare da zura kafar shi ya fito daga motar, da sauri jami'an dake a wurin suka buga kafa tare da sarah mashi, ko ta kansu baibi ba ya nufi cikin gidan, big guy yana abiye da bayan shi.... Har ya kusa shiga main falo, wayarsa ta fara ringing, gajiya ta hana ya dauki wayar, kaitsaye ya nufi upstairs Yana shiga daki, Ya rage kayan jikin shi ya fada toilet.... Ganin ya shiga ciki yasa big guy yin kwana ya fita daga dakin.. After some mins, ya fito daga wanka waist dinsa a ɗaure da towel ya nufi walk-in closet dinsa ya shirya kanshi cikin hanley shirt tare da black trouser na shan iska.. Bakomai yake son gani ba face Danish, Yau da tunanin shi ya wuni a office, Yaron ne ya tsaya mashi arai, baisan meyasa yake jin shi sosai acikin ranshi.... Yana ƙoƙarin zama gefen gadonsa, phone dinsa ta fara ringing sai time din ya tuna da kiran da akayi mashi dazu Ɗaukar wayar yayi daga kan pillow Ya duba sunan mai kiran nashi Yayi mamakin ganin kiran ta! saboda basu cika yin waya ba...daidaita nutsuwarshi yayi kafin yai picking ya kara wayar a kunne tare da yi mata sallama ya gaishe da ita cikin girmamawa. On the other hand muryar sheikha mujeedat ta amsa mashi sallamar shi cike da dattako ta fara yi mashi magana cikin harshen turanci tana hadawa da arabi "My in-law, did you see the message I sent you on WhatsApp"! "I just got back from work, ban kaiga dubawa ba..." "Okay, ka duba yanzu, ina so zamuyi magana dakai" amsa mata yai da toh ta katse kiran.. Zama yayi gefen gadon kafin ya shiga whatsapp dinsa, kaitsaye idanunsa suka sauka akan sakon gimbiya mujeedat, calmly ya fara karanta abun da ta turo ma shi _*DNA Paternity Test Report* _ A tsanake yake bin bayanan da result din ya kunsa har yakai karshen sakamakon _"DNA Profile Match: 99.99%. Paternity Index: 100,000,000:1 (extremely high probability). Conclusion: The DNA analysis conclusively confirms that Danish is the biological son of Sheikha Mujeedat bin khalid AlMaktoum._ Lokaci ɗaya chief ya zabura ya miƙe jikinshi na tsuma, tsantsar ruɗani da al'ajabine akan fuskarshi, A kalla ya maimaita karanta sakon yafi sau ashirin kamar irin bai fahimci me aka rubuta ba saboda tsabar kiɗima da mamaki! Tayaya haka zai yiwu? wai ma Wani Danish din ne? Na wurin shi da yake ruƙo ko wani ne daban"? Gaba ɗaya ya ruɗe tayaya ma akai gimbiya mujeedat tayi DNA test din? A yaushe? kuma daga ganin result din original ne daga babban asibitin toronto" Wahallan Yawu ya hadiya da sauri yai scrolling ya shiga contact ya buga mata call yana faman fitar da numfashi mai ɗumi. Kiran na shiga Gimbiya Mujeedat ta ɗaga..." la66ansa na kerma ya furta"mommy, ki yi min bayani, ki fahimtar dani! Na gaza yarda da abun da nagani I can't believe! I was confused, is this DNA test true? ya fada hankali atashe. Sanyayyar muryar gimbiya Mujeedat ce ta ratsa kunnanshi "Owais, kamar yarda hankalinka Ya tashi ka shiga rudani, nima haka na shiga, zanma iya cewa fiye da yadda ka shiga! Owais tun arana ta farko danayi tozali da yaron nan naji a jikina ɗana ne! Jini na ne shi, duk da bani da tabbaci But what strengthened my suspicions is the unconditional love Hateem has for him" Shiru ta ɗanyi kafin taci gaba da cewa" na san zakayi mamakin tayaya akai nayi gwajin!" bayani ta fara kora mashi dangane da yadda ta yanki gashin danish batare da sanin shi ba. jikin chief yayi mugin yin sanyi kamar wanda aka zarewa laka, gaba ɗaya yasha jinin jikin shi, ya girgiza bilhakki..." "My trusted doctor conducted the test. When the results came out, I was shocked, wlh har zazzabi nayi owais..." muryarta na rawa ta ƙare maganar cikin rauni na murya "Owais ka fadamin me kake tunani akan yaron? Kaima kana zargin jininmu ne"? Numfasawa chief owais yayi wata juwace ta nemi daukar shi da sauri ya koma ya zauna, yana faman jan numfashi sam ya kasa bata amsar tambayar ta, abunne ya rikirkita shi. "Owais naji kayi shiru bakace komai ba! Ni raina yana bani Omair dinmune, jinjirin dana haifa ba araye ba, amma in shine tayaya zamu iya gano gaskiyar lamarin? ni dama tun time din dana haifi yaron hankalina baikwanta da yadda aka hana mu ganin koda gawarsa ba, na dade da radadin abun a zuciya ta..."dakyar chief ya samu kwarin gwiwar furta"kin fadama uncle sakamakon DNA test din"? "Ban fada masa ba, saboda bana so in daga mashi hankalin.." jinjina kanshi yai kafin ya furta"bazan boye maki ba, tunaninmu yazo ɗaya, nima ina zargin babyn da kika haifa ne! Amma har yanzu bamu da ƙwaƙƙwaran hujjar da zamu tabbatar da hasashenmu in gaskiyane! Dole saimun fara yin bincike mun gano tayaya akai jinjirin daya mutu ya rayu! Sannan su wanene suka sace shi daga asibitin da abun ya faru❓ "yanzu muna da shaida ɗaya a hannu, ki ajiye result din dakyau, kibar komai a hannuna nayi maki alkawarin zan binciko komai, in har yaron nan ɗankune zai dawo gare ku in sha Allah, sannan pls mommy kada ki bari uncle yaga result din nan..." ta amsa mashi da toh, kwantar mata da hankali yaci gaba da yi, daga bisani su ka yi sallama. Shiru yayi jim yana tunani! idan har ya tabbata dan uncle dinsa ne to wanene ya sadaukar da shi? Yana jin fargaban ace hateem dinne ko wani daga cikin uncles dinsa tun da sadaukarwar na jininka ne kadai zai iya bada kai. ❗ Yana jin fargaban ranar da zai gano koma wanene! A sukwane ya fito ya nufi bedroom din Danish saboda ya yi maraicin ganin shi ya ƙara jin ƙaunar yaron a zuciyar shi fiye da kullum Baijima da fita ba, sai ga big guy ya hauro up hannun shi ruke da wooden tray na kayan abinci, knocking kofar yayi jin shiru ba'a bude ba yasa shi tunanin koya yi bacci ne ko yana toilet Yanke shawarar shiga ciki yayi, ya danna code din kofar ta bude kafin ya shiga da kayan abincin. A bakin door room din Danish ya tsaya tare dakai hannu yayi knocking almost 3 times ba'a buɗe mashi ba, baya jin zai iya juyawa batare daya sanya shi a cikin idanun shi ba. Tura kofar yayi tare da sakai ya shiga da sallama, yana zura ƙafar shi ya fara cin karo da papers din da ya kacaccala ya kekketasu akan floor, murmushi chief yayi aranshi ya furta hmm dakin ɗan koyo. Ya yi ma bedroom din nashi kaca kaca, kamar ance ya ɗago da idon shi karaf Ya hango zanen da yayi akan white board din da yake koya mashi rubutu da shi, wata halitta ya zana kamar jagwalgwalo daya ƙura ido saiya gane maca ce, yar diyar roba da marker yayi zanan, kafafuwanta kamar na cokula, ga gashin kanta a haukace ko wacece wannan? Murmushin gefen fuska chief ya saki kafin ya wurga eye balls dinsa kan bed dinsa a kwance ya hango shi, sai sharar bacci yakeyi kamar matacce, yar singlet ce a jikin shi fara kyal, tare da short ja, yayi wani fresh dashi. Gaba ɗaya ya barbaza papers din da yayi amfani da su, ga notebooks dinsa daya watsar, hannun shi yana aruke da pensil da alama yana cikin yin practicing na rubutu bacci yayi awon gaba da shi. Cikin takun sanɗa chief ya ƙasa daga gaban gadon ya zauna tare da sunkuyar da kanshi saitin fuskar danish ya ƙura mashi ido yana kallon shi, wani irin bugu zuciyarshi ta fara doka mashi, kamannin shi sun 6aci da yaron hatta dogon hancin su, da launun hair dinsu, da shape din bakinsu iri ɗaya sak, uwa uba reddish eyes dinsu masu kyan gaske da jan hankali, yadda yake yin baccin cikin kwanciyar hankali ba karamin kayatar da chief yayi ba, har baisan sa'dda ya manna masa peck a forehead dinsa, ya daura zira ziran yatsunsa saman tattausar farar fatar fuskar Danish mai kama data jinjiri saboda hasken ta da laushinta ya shafa ta a hankali.. In a low voice ya furta"I hope you will be my cousin, I will be proud of you. I will give you all my care. If it is confirmed that you are my blood cousin, I myself cannot describe the joy I will feel. I will hug you tightly, I will shed my tears on you, kuma nayi maka alkawarin zan ƙwatar maka duk wani hakkinka na rayuwa da aka tauye maka! Waɗanda sukayi silar sadaukar dakai zansa suyi danasani mara amfani....." cak ya tsaya da magana ganin ya fara motsi, da sauri chief ya dago da kanshi batare daya dauke ido daga kallon shi ba, gyara kwanciyar shi yayi. Ajiyar zuciya ya dan sauke ganin bai farka ba, hakanan yai sha'awar karanta rubutun da yayi a jikin papers din daya watsar kan mattress, paper din farko jagwalgwalone yayi bai iya gane komai ba, paper na biyune yaga ya rubuta I miss you, my Angel. Come back home..." yayi mamakin handwritting dinshi cos yayi kokari ba kadan ba, har kokwanto yayi anya shi ya rubuta? ɗayar paper din ya dauko ya duba rubutun dake akai. "I'm waiting for you, chief. Come back home..." murmushi chief yayi har dimple dinsa ya lotsa... Next paper daya duba sunan Daddy hateem ne ya rubuta duk da akwai kuskure amma yayi kokari..." bayan ya kammala reading dinsu, ya ajiye mashi abun shi gefe daya, har zai mike yaji ya damƙi hannun shi, ya ɗan furgita saboda bai tsammaci zai farka ba..a hankali ya buɗe idanunsa sunyi ja dakyar yake ware su akan fuskar chief, da wata irin kasala ya furta"You're back." jinjina mashi kai yai alamar eh.. Miƙewa zaune yayi tare da yin miƙa chief ya bi shi da kallo, ya jinjinama girman jikin shi, ba karamin kato bane ko'ina na jikin shi a murɗe yake irin na majiya karfi masu jini ajika. "Fadamin kayi missing dina"? Daga mashi gira yai"nayi missing dinka sosai, tun dazu nake jiranka don muyi karatu baka dawo ba..." cheif yace"ai naga ka fara" ya fada yana nuna zanen dake akan white board din. sunkuyar dakai danish yayi hadi da yin murmushi. Da zolaya yace"abunda na koya maka kenen"! Girgiza kai yay "a'a! "Wacece ka zana? Na kasa gane fuskar, Jemaima ce ko Azeeza"? Dagangan ya kira sunan su don ya bugi cikin shi... Kasa ƙasa da murya ya furta"Angel" dariya ce ta kubce ma chief, danish ya kura mashi ido yana kallon shi. "Haba my bro, Unaisah ce wannan Aljanar? Abu kamar agidan mahaukata, Ai ni dana ganta ƙarama nayi zaton jamaimah ne ." sunnar dakai kasa yayi batare dayace uffan ba... nan take chief ya fahimci halin damuwar da yake aciki harya ɗan rame ta wurin kwarin idanun shi sunyi ja. "Fadamin meke damunka.."? Shiru yayi jim kamar mai tunanin wani abu "Ina so Unaisah ta dawo gida, I miss her, I want to see her. She forgets me, Bata nema na..." kasa ƙarasa maganar yayi da sauri ya cusa kanshi cikin pillow. wani irin tausayin shine ya kama owais cikin sanyin murya ya furta"am sorry danish, unaisah zata dawo gobe in sha Allah, kuma ka daina tunanin ta manta dakai, kana aranta...." muryarshi da rauni ya furta"har yanzu fushi take dani, bata sona" har yau chief baisan soyayya ce atsakaninsu ba, yafi tunanin shakuwace mai karfi shiyasa ko kusa abun bai damun shi. "Ina wayarka"? "Tana akan mirror," ya faɗa batare daya dago da kan shi ba Miƙewa chief yai ya nufi mirror din ya dauko wayar, ya danna power ta kawo haske Wayarsa ya curo yayi copying contact din Unaisah ya saka awayar Danish... Kiran sunan shi yayi, dakyar ya amsa mashi na'am Na sanya maka contact din angel a phone inka, zaka iya kiranta ku gaisa, ko ka tura mata text message kamar yadda na koya maka..." dago da kanshi yayi wani irin dadine ya lullu6e shi, mika mashi wayar chief yayi yatsun hannun shi na kerma tsabar zumudi ya karba saida ya shiga wurin rubuta sakon ya kasa tabuka komai. Miƙa ma chief wayar yayi"ka rubuta min..." girgiza kai chief yayi"kai ya kamata ka rubuta...yamutsa fuska yayi kafin ya fara kokarin rubuta mata sakon saida ya kammala chief ya duba abunda ya rubuta dakyar ya gane meya ke nufi a sakon ya hade kalmomin babu space babu ƙa'idojin rubutu irin dai na yan koyo, "Kayi kokari" ya faɗa tare da mika mashi phone"ka danna send" ya amsa mashi da toh... "Zan shiga gym ko zaka bini? Daga mashi kai yai akamar eh, da sauri ya mike chief ya ruko hannun shi kamar wa da kani suka fita a tare.💞 _________________________________✍️ Meya faru bayan komar dr shureim gida? Tsaye yake gaban sofa ya goya hannayen shi kan kirjinshi, fuskar shi babu annuri idanunshi sun kaɗa jawur tsabar 6acin rai da fusata, abun da ya faru bayan fitar shureim da zeenatu kwatsam Motar su Alhaji musa ta kunno kai cikin gidan tunkafin bodyguard din dake driving dinsu yayi parking saiga kira daga likitan shi dr Mark, bayan yayi picking ko sallama baiyi ba muryar mark ta katse shi"yalla6ai! Da sanin ka dr shureim Ya fita da zeenatu...." lokaci ɗaya yanayin fuskar shi ya canza zuwa tsantsar bacin rai Saida ya mula yasha iska kafin ya furta"bada sani na ba"! Dr mark yace"yalla6ai, dole fa sai kayi takatsantsan idan ba haka ba zamu iya samun gagarumar matsala, saboda mutane sun ɗauki hotunan dr shureim tare da zeenatu rungume da juna, a bainar jama'a sai yaɗa shi sukeyi a social media..." a kiɗime Alhaji musa ya furta"what! Are you sure"? "Ƙwarai kuwa yalla6ai, ka duba whatsapp dinka, zan tura maka hotunan ka gani da idon ka..." katse kiran yayi, wani irin gumine Ya wanke fuskarshi saboda bacin rai! Har shi zai sanya doka agidan shi a karya"? Alhaji ubaid dake zaune gefen shi Ya lura da yanayin shi "Musa lafiya? Meya faru ne"? Ko kallo Alhaji ubaid bai ishe shi ba, Ya buɗe murfin motar Ya fito tamkar mayunwacin zaki Ya nufi gate security officers, suna ganinshi suka miƙe suna jiran tsammani Wata irin tsawa ya daka masu da ta gigita dodon kunnuwansu, yana huci ya furta"da iznin ubanwa kuka bari dr shureim Ya fita da zeenatu huh!? Kafin in fita basaida na gargadeku akan kada ku kuskura ku bari ko kofar falo ta leƙo ko ba....." ya ɗage sai masifa yake zazzaga masu ta inda yake shiga batanan yake fita ba. Alhaji ubaid Har ya fara kokarin lallashin shi aikuwa Ya daka mashi tsawa kamar ɗan cikin shi Ya nuna shi da yatsa yace"karka kuskura kasa baki, magana nake akan ƴata, ka wuce ka shiga ciki" jikin Alhaji ubaid na 6ari kamar mazari Ya juya ya nufi cikin gidan abisa umarnin Alhaji musa wato ƙanin shi 🤣 Hankulan gate officers din ba karamin tashi yayi ba, tsantsar tashin hankali da firgici ne akan fuskokinsu. Dakyar wani daga cikin su ya samu kwarin gwiwar fadin"yalla6ai har tambayar shi mukayi da iznin wa zai fita da ita yace mana da izninka, munyi kokarin tuntu6ar layinka amma baka ɗaga ba...." bai ƙare maganar ba sakamakon zazzafan marin da Alhaji musa ya wanka mashi wlh daga tsaye duk girman jikin mutumin saida Ya durƙushe kan gwiwowinsa. Kallon sauran gate officers din yayi waɗanda tuni sun sha jinin jikin su, babban tashin hankalinsu taya zasu fahimtar da shi cewa su ba laifin su bane? Alhaji musa bala'e ne, wani irin bauɗaɗɗan mutunne, bahago mai wuyar sha'ani. Wani mai rabon shan duka daga cikin su ne Yayi shahada wurin furta"yalla6ai, har kiran hajiya sarah mukayi awaya muka tambayeta da izininta zasu fita tace mana eh, ta kuma ce kaima da sanin ka...." bai kare maganar ba, Alhaji musa ya daddage Ya kwashe shi da mari da tafukan hannayenshi biyu nan take bakin officer din ya fashe jini ya fara bulbulowa. kallon sauran yayi yana jiran jin bayani daga gare su, sai tsuma suke yi suna ja da baya da alama sun razana.... "Ban ta6a sanin ku dakikai bane sai yau! Wallahi ku kuka da kanku! ....." zubewa sukayi akan gwiwowinsu suka dinga rokonshi sunayi mashi magiya don ya yafe masu, ko ta kansu bai bi ba, Ya nufi cikin gidan cikin takun nan nashi na izza, bawan Allah Alhaji ubaid Ashe yana la6e ta window yana leken abunda Alhaji musa yakeyi ma masu gadin gidan, Yaji haushi ranshi Ya 6aci sai.......💔 Adaidai lokacin da motar dr shureim Ta kunno kai sai ga motar hajiya sarah yau ta dawo da wuri, atare suka nufi parking space bayan sunyi parking, kusan atare shureim da zeenatu suka fito, kafin hajiya sarah ta fito da sauri zeenatu taje ta rungume ta "Sannu da dawowa mommy, ya aiki"? Shafa kanta hajiya sarah tayi"lafiyalou my baby,..." ta fada tare da kallon shureim murmushi suka sakar ma junansu, "Sannu da dawo Aunty, ya aiki? "Lafiyalou shureim ya mai jikin"? "Mai jiki Alhamdulillah, taji sauƙi sosai, gobe muke sa ran za'a sallame ta... da fara'a tace"Alhamdulillah, amma naji dadi, gobe in sha Allah tare dani zaku tafi..." atare suka jera suka nufi falon gidan, basu san bomb yana nan zaune yana jiran su ba. Lokacin da suka shiga falon kusan atare suka ci burki suna kallon shi, akace labarin zuciya atambayi fuska, tundaga kan yanayin shi suka sha jinin jikinsu, Yana zaune kan sofa ya haɗe fuska kai kace bai ta6a dariya ba, ya murtuke fuska ga wani gumi da ya jike gaban rigar shaddar jikin shi, tsabar fusata zufa ta ko'ina take tsastsafo shi." Kallon kallon suka fara jefa wa junansu, tsakanin dr shureim da hajiya sarah, kamar an dasa masu aya sun gaza ƙarasa shiga ciki.... "Daddy, yaushe ka dawo..."? Zeenatu ce ta ambaci sunan shi, da sauri ta nufe shi har takusa isa, Hajiya sarah tayi saurin cafko hannunta, shigowa ciki dr shureim yayi kamar jira yake su shigo ciki Ya miƙe agadarance ya nufi shureim Yana huci Ya furta"shureim da iznin ubanwa ka fita da zeenatu"? Har saida gaban shureim ya fadi saboda kalmar ubanwa da alhaji Musa ya furta. dakyar ya iya buɗe baki Yace"bada iznin kowa ba, ni na fita da ita saboda ta fada min tagaji da zama ita kadai agidan...." bai kare maganar ba Alhaji Musa ya damƙi gaban rigar shi ya jijjiga shi idanun shi jawur Ya kalli cikin idanun shureim. Hankalin su hajiya Sarah ba karamin tashi yayi ba, Allah kadai yasan mai yayi niyar yi mashi amma sai ya fasa ya saki kwalar rigar ya cije la66ansa a zafafe ya ce"shureim ni kayiwa karya? Ka ce da iznina ka fita da ita? Dama malamai suna karya? Kai ko kunya baka ji ba? Ina tsoron Allahn da addinin naka huh? Runtse ido dr shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin furucin Alhaji Musa ba, kuma bai ta6a tsammanin zai iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi hakan ba. "Ka bani mamaki shureim? A bainar jama'a ka rungume zeenatu a kirjinka, ƙato dakai baligi salon kaja min zagi a idon jama'a, so kake ka zubda min mutuncina da kimata..."? Fasa ƙara zeenatu tayi ta fashe da kuka tana fadin"Daddy ka daina yi mashi faɗa! banaso, Ka kyale shi! ba laifin Shi bane nice na rungume shi.." bata ƙare maganar ba, Ya dankara mata ashariya kamar bamaguje watsawa tayi da gudu ta nufi upstairs tana kuka tamkar ranta zai fita, tsautsayine Yaja Hajiya sarah ta buɗe baki furta"Yakamata kasan irin kalaman da zaka gaya mashi, wannan ba dacewa bane, shureim baiyi abun kunya ba kaine kayi abun kunya! Akan wani dalili zaka rufe shi da fada saboda kawai ya dauki yar uwarshi ya fita da ita! Shi ne laifi?...." kafin ta kare maganar Alhaji musa ya yai kukan kura ya ɗaga hannu zai ɗebe ta da mari da sauri Dr shureim ya shiga tsakaninsu, kai tsaye marin sauka akan fuskar shi, ji kake tasss! Waro ido waje hajiya Saratu tayi, zuciyarta ta hasala, Idanunta sun kaɗa jawur batasan sa'adda hawaye suka wanke fuskarta. Dr shureim dake atsaye hannunsa dafe da kuncinsa, tsabar radadin marin da yaji har wasu taurari masu wutsiya ya gani suna gilmawa a cikin idanun shi, zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshin shi, cikin karyayyar murya ya dubi Alhaji musa Ya furta"ni kadai yakamata ka hukunta saboda ni nayi maka laifi, saboda na ɗauki zeeenatu na fita da ita, kuma ni ne nayi karyar cewa da saninka, saboda ni a tunanina zeenatu yar uwatace ina da right din da zanyi iko da ita.." ya fada yana kallon cikin idon Uncle din nasa. "Duk akan Zeenatu kake tada jijiyoyin wuya? Meyasa? Kawai saboda na fita da ita munje asibiti duba yar uwarta! Wai duk kullan nan na menene? Ya jefa mashi tambayar, gaba ɗaya ya daure Alhaji musa da mamakin shi "Uncle yakamata ka sani, mu fa ba makafi bane, duk wani motsinka akan yadda kake tafiyar da rayuwar Zeenatu muna lura, Wallahi abinda ka aikata yau ya sa na fara kokwanto! sannan inaso ka sani don munayi maka biyayya ba hakan yana nufin muna jin tsoronka ba, ni bana tsoron kowa sai mahallici na......" waro idanu waje Alhaji Musa yayi jin furucin shureim, yayi mamakin yadda ya iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi magana batare da jin shakkar shi ba, Hajiya Sarah taji dadin martanin da Shureim ya mayar masa. gaba ɗaya kalaman dr Shureim a kunnan Alhaji Ubaid dake a la6e yana sauraron su, yaga komai daya faru akan idonshi, har hawaye saida ya zubar saboda yaji zafin kalaman da alhaji musa ya jefi shureim da su, sannan baiji dadin marin da yayi mashi ba, yaji takaici kamar ya binne kan shi. Yasan bazai iya yin komai ba shiyasa ya hana kan shi zuwa wurin su. "Idan ka cigaba da yanke hukunci cikin fushi, wallahi zakayi danasani"! Kamar sakarai haka Alhaji musa Yabi shureim da ido wato ta ko'ina ya daure shi da mamaki, Ya kasa furta kalma, ga wani gumi dake tsastsafo mashi... "Shureim ka yi hakuri dan Allah!.." hajiya sarah ta faɗa idanunta cike tab da kwalla,"kada ki damu Aunty", A fusace Ya haura kafa ya nufi room din shi, girgiza kai hajiya sarah tayi rai a6ace ta nufi dakin ta. Lokaci ɗaya Alhaji musa yaji jiri na niyar ɗibar shi, da sauri ya zauna kan sofa, ya dafe kanshi dake sarah mashi da hannu biyu" _________________________________💋✍️ Lokacin da motocin su Baba Obie suka ƙaraso asibitin, a gaggauce nurses suka fito da Stretcher, Hajjaty da Abla suka ɗauko marwa da taimakon nurses suka kwantar da ita kan Stretcher, kaitsaye suka nufi cikin asibitin da ita, da sauri su Hajjaty suka mara masu baya tare da su Baba Obie, mutane sai miko gaisuwa suke yi cike da girmamawa musamman da ya shiga ciki Nurses da Docs kamar zasu durƙusa ƙasa tsabar yadda suke gaishe da shi cikin girmamawa, tuni labarin zuwan shi asibitin ya isa kunnan Md Dr. Jidenna dama mutumin shine, yare ɗaya ƙabila ɗaya sai gashi ya fito da sassarfa ya nufi Baba Obie tare da wasu daga cikin docs na asibitin, barka da zuwa suka yi mashi daƙyar yake amsa masu duk sun fahimci baya acikin kwanciyar hankalin....., a Waiting Area su Hajjaty suka zauna kamar masu zaman makoki, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya suke yi na sakamakon ciwon marwa, babu wani mai kwanciyar hankali acikinsu, fuskokinsu sunyi jawur ruwan hawaye ya jiƙe su.Pravin kuwa Yana ruƙe da qugu ya haɗa uban gumi duk da sanyin A.c ɗin dake a wurin, ya kasa zaune ya kasa tsaye kamar mai fama da ɗan kanoma... Su kan su likitocin da sukayi arba da Marwa saida suka ruɗe saboda basu ta6a ganin patient mai irin lalurar ta ba, ba wai kuturtar ba toshewar bakin nata kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba!! Wasu ƙwararrun Medical team ne suka fara bincikarta, kafin su fara aikinsu sai da suka fara tambayar me ya jawo mata ciwon!! nan fa su Hajjaty da su Abla suka kora masu bayani dalla dalla dangane da yadda marwa ta tashi dare ɗaya da lalurar suka ce su kansu basu san menene makasudin ciwon nata ba...bayaninsu ya ƙara rikita Docs din, wannan wani irin ciwo ne farat ɗaya? A ƙalla Medical team din sun ɗauki tsawon awanni wurin duba lafiyar marwa, abun ya fara basu tsoro, saboda sunyi gwaje gwaje da aune aune but every result came back inconclusive. No trace of infection, no signs of trauma, lamarin Ya rikirkita su, sunyi iyakar bakin kokarinsu amma still babu wani sakamako daya nuna cewa Marwa tana da wani ciwo ko wata lalura, saima wani abun ɗaure kai lafiyarta qalou....'! Babu irin kokarin da likitocin basu yi ba akanta sun baje fasaharsu da kwarewarsu amma ba wani cigaba sakamakon dai ɗaya ne....❗ tun safe har wuraren karfe biyar na yamma babu wani abu da likitoci suka gano, Lokacin da likitocin suka fito, sun hada uban gumi akan fuskokinsu kai kace ba A.c a dakin, su kan su sun jigata basu ta6a cin karo da patient din da ya basu ɗan banzan wahala irin marwa ba, duk irin kwarewarsu da kwazon su basu iya gano komai ba.... Su Hajjaty suna a zaune bayin Allah, A asibitin sukayi sallah, ruwa ne kawai ya gifta ta makoshin su, tsabar tashin hankali Ya sa sun manta da yunwar cikin su, koda ganin Docs din sun fito jikinsu na 6ari suka miƙe suna kallon su, ganin sun nufi inda su Baba Obie suke yasa suka bi bayan su, kora mashi jawabi suka shiga yi cikin harshen turanci ɗaya daga cikin su ya fara bayani, "Duk da irin ƙoƙarin da muka yi, mun kasa samun nasara." ya fada yana ɗan girgiza kan shi, "munyi iyakar bakin kokarinmu, munyi duk wasu gwaje gwaje amma bamu ga komai ba, babu wata cuta da tayi silar kamuwarta da ciwon kuturtan da kuma toshewar bakin" tsantsar rudani da tashin hankali ne akan fuskokinsu.. Dr din dake a gefen wanda ya yi maganar ya ɗaura da cewa, "sakamakon binciken da muka yi ya nuna tana da koshin lafiya....." A ruɗe Baba Obie ya ce, "Bangane me kake nufi ba doc! ta yaya haka zai yiwu? Ga abun nan kuna gani da idonku zahiran! amma kuce baku gano komai ba"? Su Hajjaty dake sauraron su sai faman zare idanu suke yi duk sun bi sun ruɗe jin bayanan Docs. "Mun shiga uku! dan Allah docs ku taimaka mana, wallahi rana ɗaya ta kamu da cutar...." kallon su docs din sukai ɗaya daga cikin su softly ya furta, "We're sorry, but we cannot offer more help, ba abunda zamu iya yi mata......! su kan su Likitocin damuwace ƙarara akan fuskokinsu.. "Dama saida raina ya bani jinnu ne suka shafe ta, Baba abun da yakamata mu koma da ita gida a kira manyan malamai su taru akanta watakil a dace..." Hajjaty ce ta yi maganar tana matsar ƙwalla, idanunta akan Baba Obie wanda yayi jigum saboda damuwa....gaba ɗaya sun yi amanna da maganar Hajjaty dama tun kafin su zo asibitin babu wanda baiyi tunanin jinnu bane, saboda ciwo ne kwatsam Ya afka mata a dare ɗaya ba tare da dalili ba..... "Dr ba yadda za'ay ku buɗe mata bakin ta? Baba obie ya faɗa yana kallon docs ɗin, Girgiza kai ɗaya daga cikin su ya yi, "Sorry Sir, We cannot perform any surgery to open her mouth, because we don't know what is causing her illness. Without knowing the cause, we could potentially make things worse. Shawarar da zan baku shine a maida ita gida a nema mata magani." Sautin shesshekar su Abla Ya cika wurin bayin Allah duk sun bi sun ruɗe ga tashin hankali...... Dafa kafaɗar Baba Obie MD Doc Jidenna yayi cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ku sanya damuwa in sha Allah zata ji sauƙi, kamar yadda Docs din suka bada shawara kuyi kokarin nema mata magani, saboda rayuwarta tana a cikin hatsari zata iya rasa ranta..." cikin harshen igbo ya yi maganar, numfasawa Baba Obie ya yi kafin ya ce "To amman yanzu ni babbar damuwata ta ya zamu koma da ita a wannan halin, bamu san ta ya zata ci abinci ba hakan kuma ka ga babbar matsala ne ace mutum ya zauna ba cin abinci balle kuma ya sha ruwa, ina ganin kamar zai fi a barta a nan tun da likitocin baza su rasa dubarar da zasu yi ba su bata abincin, zamu san abun yi kafin gobe" jinjina kai MD ya yi kafin ya juya kan ɗaya daga cikin likitocin cikin harshen turanci ya yi mashi bayanin buƙatar Baba Obie in zai yuwu, amsa ya bashi da bazasu rasa hanyar da zasu yi hakan ba dama da suna bincikar lafiyarta sun saka mata ƙarin ruwa da wasu allurai da zasu ƙara mata karfin jiki ganin ta galabaita. Duk sun ji daɗin hakan, Baba Obie ya roƙesu kan su bata kulawar da ta dace kafin zuwa gobe, cike da girmamawa suka amsa mashi da zasu yi ƙoƙarin hakan. Su Hajjaty sunso su ƙara ganinta kafin su tafi, saidai basu son ƙara karya mata zuciya don sun san yanzu dole tana cikin matsananciyar damuwa ba kamar da aka kasa shawo kan matsalar tata, ba don sun so ba suka tafi kowannan su da tsananin tausayinta a zuciyarshi. Suna a kan hanyarsu ta komawa gida Baba Obie ya tuntu6i layin Sheikh Imam Malik ya sanar da shi cewa yana son ganin shi idan yana kusa, Sheikh Imam ɗin ya sanar da shi baya a gari, amma zuwa gobe da asuba zai shigo Abuja...lokacin da Baba Obie yake yin wayar Pravin yana zaune a gefen shi, tun da yaji Baba Obie ya ambaci yana son ganin Shiekh Imam cikin shi ya katsa, ƴan hanjinshi suka motsa, wata irin kiɗima yayi ga sanyin A.c a motar amma wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, sai faman zare na mujiya yake yi....! _______________________________✍️ A 6angaren su Aneelerh, tun Bayan sun gama kwasar girkin da akayi ma su, saida kowan nan su yayi kulu wash rabu hani'an kafin suka koma falon, firar yaushe rabo suka fara dama an kwan biyu ba ahadu ba. Wuni su kayi agidan, kiran sallar azahar ne ya tadasu, dakin baki hajiya adama ta kai Aneelah da Zarah su mami kuma dakinta ta kaisu don suyi sallah, wato su mami sun shagaltu da kallon dakin hajiya adama an zuba kayan alatu kamar dakin wata basarakiya.. yayin da mazan suka tafi masallaci bayan sun dawo a falo suka ƙara hallara, akaci gaba da hira ga launch an kawo masu ita dai aneelah tun zuwansu gidan hankalinta ba kwance yake ba, Ana sai faɗo mata arai take, ga wannan faduwar gaban data dameta hakanan dai take daurewa, zarah ta lura da ita duk wani motsin Anila akan idonta, ta fahimci babu kwanciyar hankali atare da ita, so take su ke6e taji ko lafiya, kiran sallar la'asar ne ya sake tadasu inda kowa ya nufi dakin da yayi sallah dazu Bayan sun gama sallah ta juyo da kallonta ga Aneelarh da dan yanayin damuwa tace "aunty aneelah miyake damunki tun zuwanmu gidan nan ina lura da ke kwata kwata kamar a takure kike ko duk tunanin Aunty benazir ne" yamutsa fuska tayi "A'ah zarah wlh Ana ce ta tsayamun a rai sannan tunda mukazo gidan nan gabana keta faduwa na rasa dalili raina ya bani kamar wani abu zai faru" cikin sanyin murya ta kare maganar, ruƙo hannunta zahra tayi a cikin mata suka kalli juna "In sha Allah auntyna babu abunda zai faru sai alkhairi, ki daina sanya damuwa aranki sannan kicigaba da yin addu'a" Numfasawa tayi kafin tace"nagode da shawararki zahra, bari na kira Ana in tuna mata ta dafa ma baby junaid indomie dan kinsan daya dawo ita yake fara tambaya" murmushi zarah tayi "ina ruwan sarkin rigima" yar dariya Aneelarh tayi, tare da ɗaukar phone ta danna ma Anah kira tashin farko aka sanar da ita layin akashe yake! kallon zarah tayi"na kira baya shiga!" Zahra tace"maybe tana a kitchen tana aiki shiyasa ta kashe wayar, ki bari ɗan anjima kadan saiki sake kira"ta fada tare da cewa muje kar a jimu shiru"ruko hannun Aneelah tayi suka fito daga dakin, addu'a anila ta dinga karantawa a zuciyarta amma kamar ana kara mata faduwar gaban. Wannan karan tamkar ana mata dakan sakwara a kirjin ta.. A falo suka tarar da su ummi jiki asanyaye Aneelerh ta zauna tana ambaton sunan Allah, sam hankalin ta baya atare da su mami dake ta fira ko gajiya basayi, can ta tsinkayi muryar mami a kunnanta "Anila ya kamata ki kira mahboob ki tuna mashi kar ya manta yaje da wuri ya dauko baby junaid, kinsan bayasan jira muma yanzu zamu tashi mu tafi yamma tayi"dariya sukayi su duka ummi tace"gaskia kam" tashi Anila tayi ta koma gefe ɗaya ta kira layin mahboob yana ɗauka tace" please karka manta kaje ka dauko baby junaid da wuri... Katse ta yai da cewa "ohhh Aunty Aneelah saikace karatu kusan kullum sai an tunamin inje dauko sa? to ki kwantar da hankalinki baby junaid tun ƙarfe 2 yana a gida, yau da wuri aka tado su, saboda za'ayi wani taro a school dinsu, nima abokina ne dake koyarwa a school din ya kira ya fada min an tada su shine naje na dauko shi, halan bakuyi waya da Ana bane"? Wani irin bugu zuciyar Anila tayi rass! Taji gabanta ya fadi zuciyarta ajagule ta furta"wai kana nufin tun karfe biyu junaid yana agida"? "Kwarai kuwa, naga kamar kin daga hankalin ki, idan ma don saboda shine kada ki damu kanki yana atare da Ana ita na damka ma amanar shi" Still hankalin ta bai kwanta ba tace"mahboob na kira layin Ana a kashe, pls ko zaka duba min su"? voice dinta kamar zatayi kuka ga wani faduwa da gabanta keyi "ki sake kira kiji ni yanzu bana agidan na tafi kallon match" sallama sukayi ta kashe wayar hannunta har kyarma yake wurin kiran layin Ana still dai a switch off, cikin sauri ta koma falo ta gayama su ummi yadda tayi da mahboob mikewa mami tayi tare da kallon su uncle abdallah "to mufa baki zasuyi halinsu" ta fada tare da yar dariya, hajiya adama tace"wlh kamar ku kwana banso ku tafi Allah, kun ɗebemin kewa yau, Anya bazan biku ba" da zolaya uncle dan iya yace"shi kuma abdallan ina zamu kai shi? aikuwa su duka suka sa dariya, Aneelarh kamar jira take ta yafa mayafinta zarah ma haka gaba ɗaya suka fito compound din gidan inda sukayi parking car dinsu... "Allah ya kiyaye hanya, mungode sosai, in sha Allah zanzo ganin jikana, agaida min shi..." Uncle abdalla yayi masu sallama akan idon su motocin suka fuce daga gidan hajiya adama hada kwallarta saboda bataji dadin tafiyar su ba, ruke hannunta uncle Abdalla yayi a cikin shi, suka koma cikin gidan su... Nima na ruƙe hannun alƙalamina✍️ (Mu haɗe Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya🔥) *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 36 complete by Novels Elite Admin August 31, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️ tun da motocinsu suka haura kan titi Aneelerh take ta tsuma ji take kamar ta ƙwace driving din daga hannun Abie don gani take kamar bai sauri, tsigar jikin ta sai tashi take, gaba daya ba ta da kwanciyar hankali.. Tsawon mintuna kafin suka ƙaraso anguwar su, baba mai gadi ya taso ya buɗe masu gate, motar abie ce farko ta uncle ɗan iya na abiye da bayan su, abie nayin parking hannunta na kerma ta buɗe motar ta fito ta nufi cikin gidan. Mami tace ohni Aneelerh ko irin alkunyar nan babu, baka lura da yadda ta ɗaga hankalin ta ba tun agidan hajiya adama..." mami ce tay maganar tare da buɗe motar ta fito abie na dariya yace"ya'yan zamani kenan, ay su ba ruwansu da wata kunya indai akan ya'yan su ne idon su rufewa yakeyi. Da sauri zahra ta fito tabi bayan Aneelerh, bayan ummi da uncle sun fito baba mai gadi ya karaso inda suke yayi masu barka da dawowa... Lokacin da Aneelerh ta shiga falon ko sallama batayi ba saboda idon ta ya rufe, yaronta kaɗai takason gani muryarta na rawa ta furta"Ana! Ana! Ana...! Shiru ba'a amsa mata ba, a kan sofa ta wurgar da handbag dinta, ta nufi bedroom dinta da sauri don taga ko baby junaid na anan tana shiga ta iske dakin wayan babu kowa, fitowa tayi a fujajen ta nufi kitchen"Ana! Ana! Wai ina kika shiga ne?...." tana shiga kitchen ta taras babu kowa ranta ne ya bata kodai yana adakin Ana suna bacci"? Hakan yasa ta juya da sauri ta nufi hanyar dakin Anah "Aunty Anila..." zahra ce ta kira sunanta, shigowarta kenan ta hango Aneelerh ta nufi dakin Ana da sauri tabi bayanta, kafin ta karaso Aneelah ta ture kofar dakin, cike dasa ran zata gansu kwance kan gado, zura kafarta keda wuya idanunta suka sauka akan gadon Ana babu kowa akai, dakin gaba ɗayanshi a haukace yake kamar anyi dambe a cikin shi, fululluka har biyu ta gani kan floor, ga zanin gado a yamutse yayi uban squeezing, wani abu da ya ƙara rikirkita Anila, dressing mirror din dakin data gani ya kife ƙasa, Wa'iyazubilla wani irin jiri jiri ta fara gani a cikin idanunta da wani irin azababban faduwar gaba ta ƙarasa shiga ciki kamar wadda aka zare wa laka, zahra tana abiye da bayanta sai faman zare idanu sukeyi cike da tashin hankali, tun daga kan yanayin dakin suka fahimci wani mugun abunne ya faru❗ "Mun shiga uku Aunty Anila! Meya faru da dakin Ana? Ta ina? Ina baby junaid..."? Aruɗe zahra take magana ita Anila gaba daya rudani Ya hana ta furta kalma, jikinta na kerma tasa hannu tayi knocking toilet door din dakin cike da sa ran Ana zata amsa mata, almost 3 times tana kwankwasa kofar toilet din babu alamun za'a tanka mata ko za'a buɗe kofar, da iya karfinta na karshe ta bangaje kofar da kafadarta nan take door din ta buɗe a slow ta bada wani sauti kiiiiiiiiii! Da wani irin faduwar gaba ta zura kafarta cikin toilet din, A hankali take bin ko'ina da kallo, bata ga kowa ba, sai shower da tagani a kunne ruwa yana ta kwararowa ya malale kan floor, ga faucet ma a kunne ruwan dake 6ul6ulowa ta cikin shi Ya cika sink din harya fara gangarowa ƙasa. Hankali atashe Anila da zahra suke karewa toilet din kallo.. Muryar Anila na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Zahra na shiga uku? Bangan su ba! Banga baby junaid ba! Ina Ana takai shi? Ina suka shiga!... Ruƙo hannunta Zahra tayi"Auntyna ki kwantar da hankalinki, muje mu duba sauran dakunan watakil taje gyara dakin wani a cikin mu, ko kuma sun fita backyard. Da sauri suka fito daga dakin, adai dai lokacin Su mami sun shigo suna zaune a falon suka hango zahra da Anila zasu gifta ta falon Muryar Mami ce ta katse su"Kai Ina zuwa haka? Kusan atare suka juyo muryar Anila na rawa ta ce"mami ba mu ga Ana da baby junaid ba, su muke nema..." jin wannan maganar Yasa ummi da su Abie suka mike tsaye Ummi tace"kun duba ko'ina"? Zahra tace"yanzu zamu karasa dubawa..." ta fada tare da ruƙo hannun Anila suka nufi hanyar dakunan su Abie... Abu kamar wasa sai da takaiga ko'ina na gidan sun duba saƙo da lungu amma ba su gan su ba, nan fa hankulan mutanan gidan Ya tashi, hatta su abie saida suka tayasu neman Ana, kowan nan su Ya hada uban gumi kan fuskarshi, sai da suka tabbatar babu su agidan sannan suka dawo falo suka tsaya cirko cirko. Fuskar mami A yamutse ta furta"to ina suka shiga ne? Ko dai sun fita daga gidan ne? Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, watakil ta fita da shi" Abie ne Yace"bari nayi magana da baba mai gadi, in ma fitar su kayi zamuji a wurin shi, A hanzarce Ya fuce daga falon Uncle dan Iya yabi bayan shi da sauri. Baiwar Allah Aneelarh, tafi kowa jin jiki, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita gaba ɗaya ta gama sarewa, tana zaune kan sofa, hannayenta biyu daddafe da kanta, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta. Zahra dake a gefenta itama damuwarce akan fuskarta, ta dafa kafaɗar Anila tana kokarin kwantar mata da hankali, ganin yadda ta canza fuskarta tayi jawur cheeks dinta har kerma suke, dama abunda take ta zullumi kenan, tunkafin barinsu gidan hankalinta bai kwanta da yanayin da taga Anah ba! shiyasa take ta jin faduwar gaba dama sau dayawa in wani abu zai faru da bawa Allah na bashi haske kan al'amarin. Mai gadi na zaune kan kujera Ya kure sautin radio dinshi, sam baiji Kiran da su Abie suke kwala mashi ba, har saida suka karaso gaban kujerar tukunna ya lura da su, da sauri Ya kashe radio din Ya miƙe yana kallon su "Bayan fitar mu daga gidan nan! Wani ya ƙara fita ne"? Abie ne ya jafa mashi tambayar, girgiza kai yayi"yalla6ai babu wanda Ya fita..." can kuma yace au na tuna Mahboob ya dawo tare da junaidu, bayan shigar shi ina zaune sai ga mahbob ya fito ya shiga mota ya fuce, bayan shi babu wanda Ya ƙara fita...." bai kare maganar ba Uncle ɗan iya ya tari numfashi shi da cewa"kana nufin baga ka lokacin da Ana ta fita da junaid ba..." girgiza kai baba mai gadi yayi yace"a'a gaskiya ni banga gifcinsu ba, Ina zaune na kasa na tsare ko sauro bai isa Ya haura gate din nan batare dana kama shi ba..." hankali atashe Abie da uncle dan iya suka kalli Juna. "Yalla6ai wani abu ya faru ne"? Baba mai gadi ne yayi tambayar ganin kamar damuwa akan fuskokinsu... Abie ne ya zayyana mashi abunda ke faru, baba mai gadi yace"ikon Allah! Amma yalla6ai kun duba ko'ina? Saboda wallahi ni banga fitarsu ba, Allah shine shaidata, ko gyangyadin bacci banyi ba, lokacin sallah kadai ke tada ni, kuma sallar ma abakin gate din nayita...." ba su tsaya jin karashen maganar shi ba, da sauri suka koma falon gidan, su mami na ganinsu suka mike har suna hada baki wurin tambayar abunda me ganin yace Abie ne ya kora masu jawabi. Kaf a kunnan Anila lokaci ɗaya ta rushe da kuka tana fadin"inna lillahi wa'inna ilahirraji"un..." daga kan sofa ta sauko kan floor ta zauna dirshan, taci gaba da kuka"wallahi saida raina ya bani wani abu zai faru da su, tun lokacin da muka bar gidan nan naketa jin faduwar gaba, ashe wani abu ne zai faru da junaid dina, na shiga uku mami ku taimaka mun! Ku nemo min Ana ta kawo junaid dina.."!! Da sauri Zahra ta rungumota a kirjinta, ta cigaba da lallashinta..ita kanta zahran kukan ne ke shirin kubce mata. "Haba Anila meye abun kuka? Kamar dai bakiyi tawakkali ba? Wayace maki wani abu ya faru da su? Uncle ɗan iyane ya fara mata magana cikin tausasa harshe. Ummi tace"ni abunda nake tunani kodai Mahboob ne Ya fita da su yakamata akira shi aji" da sauri Abie ya zaro waya ya danna ma mahboob kira yana dagawa ko sallamar shi abie bai amsa ba yace"mahboob kana ina"? On the other hand mahboob yace"ina akan hanyar dawowa gida..." "Ana tana atare dakai"? Da mamaki mahboob yace"ana kuma abie? Ba tana agida ba? Ko bata nan ne"? Katse kiran Abie yayi, tare da kallon su mami dake kallon shi "Baya atare da su..." sautin kukan Anila ne Ya ƙara karaɗe kunnuwansu... Mami tace"amma abun da daure kai! Ina Ana taje da shi? Ke zahra kira layin Ana muji..." sai yanzu dabarar kiranta yazo masu arai, cikin shesshekar kuka Anila tace"ko kun kira akashe zaku same ta, tun muna agidan hajiya adama inata kira baya shiga.." Zahra tace"bari dai a akara kira watakil ta kunna wayar" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Anah kira, nan take aka sanar da ita wayar akashe take, nan fa hankalinsu Ya ƙara tashi, Cire hula abie yayi zufa ta ko'ina ta fara tsastsafo mashi ta kan goshin shi, idanun mami tuni sun rune sun koma Ja, al'amarin yayi matuƙar ɗaga hankulan su fashewa zahra tayi da kuka tana fadin"Allah yasa Ana ba guduwa tayi da baby junaid ba! Raina yana bani itace ta gudu da shi..." cikin shesshekar kuka Anila tace"ni bana zargin Ana, bazata ta6a daukar min babay junaid ba, na yarda da ita sai dai idan wani abunne ya faru da su duka biyun." Ummi tace"Anila raba kanki da ɗan adam ba abun yarda bane, na jikinki ma zai iya cutar dakai balle ita da take yar aiki bare, Allah kadai yasan meya faru! Ina suka shiga"? Girgiza kai mami tayi hawaye nabin kuncinta tace"dan Allah ku daina waɗannan maganganun, dukkan mu babu wanda yasan meya faru da su? Ko ina suka shiga, bai kamata mu yanke mata hukunci batare da mun san ainihin abunda ya faru ba, dududu ba yanzu muka dawo ba, mu ɗanyi hakuri kafin dare yayi watakil ta dawo da shi, mu kyautata mata zato dan Allah..." dakyar ta kare maganar daurewa kawai takeyi Ita dai ummi hankalinta bai kwanta da Ana ba, tafi zargin itace ta gudu da junaid, dama tun lokacin da ta fada masu tana yin mummunan mafarki tafara zarginta, yanzu gashi ta 6ace babu ita ba junaid, wama yasani ko yar kungiyar asiri ce shiyasa ta sace shi har baba mai gadi baisan da fitar su ba. Ta dai bar abun a zuciyarta gudun kada ta daga masu hankali "Anya baba mai gadi gaskiya ya fadi? Taya za'ay su fita batare da sanin shi ba? Ga shi mun duba ko'ina babu su babu alamar su! In har bata kofar gate suka fita ba ay babu wata kofa da mutun zai iya fita daga gidan nan in ba dai 6acewa tayi da shi ba kamar yadda naga yan kungiyar asiri sunayi" Maganar ummi ba karamin firgitar da su tayi ba, cak Anila ta dakata da yin shesshekar kukan Idanunta jawur ta dubi ummi"bangane me kike nufi ba ummi! Dan Allah ki fahimtar dani!" kafin ummi ta buɗe baki, Uncle dan Iya ya wurga mata harara, Rai a6ace yace"baki da hankali ne? Ko so kike zuciyarta ta buga ne? meya kawo wannan maganar? Maimakon ki kwantar mata da hankali saima kara dagula mata tunani kike kokarinyi! Wallahi kar in kuskura in kara jin bakinki!!" faɗa sosai yakama yi mata kamar zai rufeta da bugu, har saida Abie ya dakatar da shi kafin suka samu yayi shiru. Miƙewa Anila tayi, zuciyarta ta karaya, jikinta yayi mugun sanyi, ga wani azababben zazza6i da ciwon kai mai raɗaɗi da tafara ji, gaba ɗaya suka bita da kallo ganin ta miƙi hanyar fita daga falo kamar bata a cikin hayyacin ta. da sauri Abie yabi bayanta ya damƙi hannunta fashe wa tayi da kuka tamkar ranta zai fita tadinga kokarin ƙwace kanta tana sambatu cikin fitar hayyaci ta furta"wayyo Allahna abie, dan Allah ka sake ni inje in nemo baby junaid dina, bana so na rasa shi, bana so acutar min da shi, kabarni abie, Junaid shi kadai ne jinin uzair da nake da shi, idan na rasa shi bansan inda zan tsoma raina ba..." Tana cikin yin magana ta sarƙe kwatsam ta yanke jiki zata faɗi da sauri abie ya kwanto da ita kan kirjin shi, sai lokaci mami ta fashe da kuka kalaman Anila sun karya mata zuciya, zahra ma kukan takeyi haka itama ummi gida ya zama kamar na masu zaman makoki, adai dai lokacin mahboob ya shigo falon ko sallama baiyi ba sautin koke kokensu Ya cika kunnuwanshi, hankali atashe ya karasa shiga ciki yana faman raba idanu akansu, arude yake fadin mami! Ummi! Zahra! Me..me ya faru? Daddy..bai kaiga kiran sunan abie ba yai arba da anila wadda ke rungume jikin abie, kamar ba numfashi atare da ita, tsabar kiɗima Yasa mahboob sakin key din hannun shi ya faɗi ƙasa. La66ansa na kerma ya furta"dan Allah kuyi min bayani meya faru kuke kuka? Meke damun Aunty Aneelerh? dakyar Zahra ta shanye kukanta muryarta a disashe ta kwashe komai ta sanar da maboob da buɗar bakinsa sai cewa yayi"ban yarda ba, wallahi bazai yiwu ba! Ni da kaina na ɗauko yaron nan daga school kafin ma mu iso gida bacci ya dauke shi, bayan nayi parking din motata na goyo shi abayana na shigo da shi cikin gidan banga kowa ba a falo, raina ya bani watakil kun tafin unguwar da naji kunce zaku je, sai na wuce da shi dakin Ana, bayan nayi knocking din kofar ta buɗe min naga idanunta jawur kamar daga bacci ta tashi, har na tambayeta ina mutanan gidan tace min ai kun tafi tun ɗazu, sai na miƙa mata junaid nace ta kwantar da shi idan ya tashi daga bacci ta yi mashi wanka ta bashi abinci, ta amsa min da toh, ta tambaye ni ni bazan ci abincin bane nace mata sauri nake zan tafi kallon match idan na fita zan tsaya agidan su abokina zanci acan, mukayi sallama da ita na juya cikin sauri har nakusa fita falon naji ta kwala min kira na jiyo na kalle ta, a lokacin ta rungume junaid dake bacci a kirjinta, ganin tana kallona da murmushi akan fuskarta yasa nace mata lafiya? Ko akwai wani abu da take son fadamin ne? Ta girgiza min kai tace a'a wai nayi mata kyau ne, bance mata komai ba, na dai ɗaga mata hannu na mayar mata da martanin murmushin da tayi min kafin nasakai na fuce daga gidan...." gaba ɗaya su mami sun kasa kunne suna sauraron mahboob dake basu labarin rabuwar shi da Ana har yakai karshe. "Tayaya za ku ce min ba ku gan su ba fisabilillahi? Idanunshi cike tab da kwalla yayi maganr, duk da bai tabbatar da abunda suka fada mashi ba, amma zuciyarshi ta karaya dama tunda ya damka ma Ana amanar junaid ya fita daga gidan yake ta jin wani iri, idanunshi suka dinga tariyo mashi murmushin da ta sakar mashi. Zahara tace"wallahi mahboob babu su, ko'ina mun duba, ba Ana ba baby junaid, ni abunda ya daure min kai, dakin Ana da muka gani a haukace babu gyara, duk an jefar da pillows ƙasa dressing mirror dinta ya kife ƙasa, daga gani wani abunne ya faru, maganar zahra ta ƙara jefasu a rudani...." Girgiza kai mahboob yayi cikin tashin hankali ya watsa da gudu ya nufi dakin Ana, don ya gane ma idon shi kafin fitowar shi Abie ya kwantar da aneelerh kan doguwar sofa, mami ta ɗauko robar ruwa a fridge mai sanyi ta buɗe murfin ta yayyafa mata akan fuskarta, dogon numfashi taja tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur ta dubi fuskokin su, biji biji take ganin su daƙyar ta iya motsa la66anta da suke bushe ƙamas ta furta"mami ina junaid ɗina? Ana ta dawo min da shi" shiru sukayi fargaban halin da zata shiga ya hana wani ya bata amsar tambayarta... Abie ne yai karfin halin furta"kiyi hakuri Anila, basu dawo ba, amma yanzu zamu tafi neman su, in sha Allah zamu dawo maki da yaronki..." runtse idanunta tayi wasu irin zafafan hawaye suka wanke fuskarta...fitowa mahboob yayi daga dakin Ana yana tafiya kafafun shi suna harɗewa saboda rashin kwanciyar hankali, dawowa cikin falon yayi ya tsaya yana kallon fuskokin su. "Zahra kun kira layin Ana ɗin"? ɗaga mashi kai tay"mun kira akashe" tsoki Ya buga tare da ruƙe qugun shi kafin wani ya kara magana a cikin su, sautin kiran sallar magrib Ya karaɗe kunnuwan su Uncle ɗan iya yace"dan Allah ku kwantar da hankalinku, in sha Allh zasu bayyana cikin koshin lafiya, yanzu ku je kuyi sallah kuyi masu addu'a duk inda suke Allah Ya kare mana su, in sha Allah idan muka fita zamu bi gidajen makwabta mu duba watakil adace ko sun shiga ciki" __________________________________✍️ *💋UNAISAH ANGEL💓* Wunin ranar Unaisah bata jin dadin jikin ta, kamar mai fama da zazzabi tun da idanunta sukayi tozali da zeenatu bata ƙara samun nutsuwa ba, Yarinyar ta tsaya mata aranta tunanin zeenatu yayi mata ƙatutu a cikin zuciyarta, ta rasa meyasa take ta faɗo mata aranta, har takai ga da zarar ta rufe idanunta fuskar Zeenatu take gani. Tana akwance kan darduma wani guntun baccine Ya ɗauketa bayan ta kammala sallar magrib, gaba daya ta kudundune kanta cikin hijab.... Benazir tana zaune gefen gadonta tana ta kallon ta, yayin da hajiya layla ke azaune kan sofa.. "Benazir..." dagowa tayi tare da kallon mami data ambaci sunan ta, kallon kallo suka shiga jefawa junansu, tuni benazir tasha jinin jikinta, dama tun dazu da abun nan ya faru na zuwan zeenatu ta lura da irin kallon da mami takeyi mata ga wani annurin farin ciki da take gani atare da ita... "Ya jikin naki? ɗazu naga kamar kin samu lafiya.." shiru tayi jim tana tunanin ta yadda zata 6ullowa mommyn nasu don bata shirya bayyana masu ta samu lafiya ba, tana da dalilinta nayin haka.. Jin tayi shiru yasa mami ta sake furta"dake fa nake magana? Hannu tasa ta ɗan sosa gashin kanta tare da kyafkyafta idanunta irin yadda masu tabin hankali sukeyi sam ta kasa buɗe baki tayi magana, hajiya layla ta kura mata ido tana kallon ta, ta ɗan rude da yanayin ta aranta ta ayyana ko dai har yanzu da sauranta"? "Mami ina baby na? Ban ganta ba? ta faɗa tare da saukowa daga kan gadon ta fara ɗaga pillow tana nemanta, hada kokarin yaye zanin gado duk don tayi pretending kada hajiya layla ta gane ta samu lafiya. Shesshekar kukan karya ta farayi hada yarfa hannu ta juyo ta kalli hajiya layla da ta saki baki sototo tana kallon ta. "Mami kodai wani ya sace min ita ne? na duba banganta ba.." abun ya ɗaurewa hajiya layla kai, yanzu fa take zaune tana kallon yarinyar amma farat ɗaya ta nuna bata ganta ba. Jinjina kai tayi aranta ta ayyana lallai haryanzu da sauranta, ganin yadda tabi ta ruɗe ne yasa mami yin saurin kiran sunan ta, a hautsine ta juyo tare da kallon ta "Gata nan a kwance kan darduma.." girgiza kai tayi"mami ba itace ba, wannan ƙatuwa ce, babyna karama ce" waro ido waje mami tayi can kuma tayi tunani kodai don taganta nannaɗe cikin hijabine, mikewa hajiya layla tayi taje gaban prayer mat din, a hankali ta cire ma Unaisah hijabin ta fiddo da fuskarta. "Kin ganta"? washe baki Benazir tayi tare da sanya tafukan hannunta, ta rufe fuskarta tana fadin"ashe itace ta lullu6e da hijabi, shiyasa bangane ta ba, mami gobe zamu koma gida da ita ko"? Shiru hajiya layla tayi gabanta na faduwa, jin abunda Benazir tace, yanzu ya zatayi gobe idan zasu tafi? Tasan dole Benazir ta sanya masu rigima muddin su ka ce zasu raba ta da yarinyar ba karamin daga za'ay ba. "Mami kinyi shiru..." murmushi yaƙe ta sakar mata"kinji ki da wata magana, in bamu tafi da ita ba, a asibitin zamu barta ta kwana ne"? Yar dariya benazir tayi tare da jujjuyawa tana fadin"wayyo Allahna naji dadi mami, nayi farin ciki, zamu tafi da babyna gida...." ita dai hajiya layla jikinta yayi sanyi, Da harta fara murnar Benazir ta dawo hayyacin ta ashe har yanzu bata gama wartsakewa ba. Ringing ɗin wayarta ne Ya farkar da ita, kaitsaye sautin ya daki kunnanta, a hanzarce ta tashi zaune ta cire hijab din jikin ta, idanunta har sun ɗan kumbura, ganin hajiya layla agabanta yasa ta ɗan firgita kaɗan. "Yanzu nake shirin tada ki daga bacci naga ko dinner baki ci ba, sai gashi kinma farka da kanki..." hajiya layla ta fada da murmushi akan fuskarta. "Babyna..." Benazir ce ta kira sunan ta, a hankali ta dube ta muryarta da kasalar bacci ta furta"na'am mommyna..." murmushi Benazir tayi"naji wayarki tana ringing, ki duba ki ga wanene ke kiran ki" amsa wa tayi da toh, ta mike ta nufi backpack dinta ta curo wayar a lokacin har kiran ya katse. kallon su hajiya layla tayi sam bata son yin waya agabansu, kamar mara gaskiya ta zura wayar a aljihun rigarta, ta juya ta nufi toilet ta shiga daga ciki taja kofa ta datse. Call ta danna mashi yana yin picking tace"daddy, barka da marece? Ka wuni lafiya"? On the other hand taj Yace"lafiyalou daughter, halan daga bacci kika tashi naji muryarki wani iri" "Eh, bayan na kammala sallah ne bacci yai awon gaba dani" Okey, dama na kirane don in kara kwantar maki da hankali, daga gobe ne in sha Allah za'a sallame ku da wuri, mun ma yi magana da chief ya fada min shi zaizo daukarki...." murmushi tayi har cikin ranta taji dadin jin hakan "Allah yakaimu lafiya daddy, amma zanyi kewar mommyna..." ta fada kamar zata sanya mashi kuka, dariya yayi"ke fa da kanki kikace kingaji da kallon ki da matar keyi..." "Wallahi daddy ina sonta sosai, bansan rabuwa da ita, jiyan ma dana fada maka ta bani tsorone ina fa bacci ta tsareni da ido amma ni ina kaunarta" "Kada ki damu, ko bayan kin dawo gida zan iya kaiki gidan su ki gidan ta" dadine Ya lullu6e ta, sun ɗan jima suna waya kafin sukayi sallama. Tana sauke wayar daga kunnanta, idonta ya sauka akan text message din da aka turo mata da bakuwar number, cike da mamaki ta danna sakon ya buɗe kura ido tayi tana kallon jagwalgwalon rubutun Daya bayan ɗaya ta fara karanta shi. _Deer swit angil, I mis yu soooo mutch Pleeease come hom to me, and I promis to met awl your condisions I wuv yu soooo mutch_ Dafe kai tayi da hannu daya zuciyarta cike fal da tunanin wanene yayi mata sakon? aranta ta ayyana daga gani ƙaramin yarone ya ɗauki wayar babarsa batare da sanin ta ba, ya danna wrong number shine aka tura mata sakon, tuntsirewa tayi da dariya da sauri ta toshe bakinta tunawa da su hajiya layla acikin dakinta... Murmushin gefen fuska tasaki cike da nishadi ta ƙara maimaita sakon saboda nata fahimci me aka rubuta ba, nutsuwa tayi sosai tana kallon rubutun tiryan tiryan lokaci ɗaya taji gabanta yaɗan faɗi ganin kamar nick name dinta wato Angel _My sweet Angel, i miss you so much, please come home to me, and i promise to meet all your conditions i love you_ Tabbas sakon ba kuskuren akayi ba, ita aka turo ma shi, ko wanene? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, a kalla ta maimaita karanta text din yafi sau ashirin batare data iya gano wanene ya turo mata shi ba, reply ta mayar masa"Please, may I know who you are? Bayan ta tura mashi sakon ta fito daga toilet din, a lokacin dr jazz ya shigo duba jikin Benazir yana ganin ta ya sakar mata murmushi da sauri ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'a, bayan ya kammala dubata, yayi masu sallama ya fuce daga dakin da sauri hajiya layla tabi bayan shi. "Dr. Jazz! Ina son yin magana dakai" tsayawa yayi tare da juyowa yana kallon ta, agaban shi ta tsaya suka fuskanci juna "Dr mungode sosai, kana kokari akan Benazir, ubangiji Allah Yasaka maka da alkhairi, Allah yabiya maka bukatunka..." addu'oi tadinga yi mashi yana amsa mata da ameen, da alama yaji dadin addu'arta Jin tayi shiru kamar akwai wani abu dake damuntane yasa shi furta"naji kinyi shiru ko akwai wani abu" yarfa hannu tayi fuskarta ayamutse tace"dr bansan ya zanyi da benazir ba! Ta ƙwallafa rai akan yarinyar nan, Ni damuwata halin da zata shiga idan aka raba ta da yarinyar kar akoma yar gidan jiya" ta faɗa tana marairaice mashi fuska, yama rasa amsar da zai bata don ya fahimci kamar so take abar masu yarinyar su tafi da ita abune da bazai yiwu ba" Calmly yace"na fahimce ki, amma gaskiya sai dai kuyi hakuri, iyayen yarinyar nan sunyi kokari da har suka iya baku ita na tsawon kwanakin nan, saboda ba karamin so sukeyi mata ba, itace kadai yar su tilo" dafe kai hajiya layla tayi da hannu ɗaya, sai yaji ta bashi tausayi. "Nasani dr, wlh sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, ni damuwata taya zamu rabata da yarinyar? Kana gani zata hakura"? "Kada ki damu, ni nasan ta yadda zan raba su batare da an samu matsala ba, in sha Allah komai zai tafi dai dai" gyaɗa kai tayi"mungode dr, agaida mutanan gidan," sallama yayi mata kafin ya juya da sauri ya nufi hanyar fita daga asibitin. ______________________________✍️ Bayan tafiyar su Abie masallaci, mami ta kalli Aneela dake kwance tana faman share kwalla"kiyi hakuri ki daure anila, bana son kukan nan da kike yi, ku tashi kuje kuyi sallah kuyi masu addu'a...." jiki asanyaye ta miƙe kwata kwata babu kuzari kamar zata faɗi kasa da sauri zahra ta taimaka mata suka nufi bedroom dinta... Cike da jimami ummi da mami suka nufi dakunansu domin yin sallah.... Bayan shigarsu dakin, Anila ta zame hannunta daga na zahra, ta zauna gefen gadon, wani iri gumi ne Ya wanke fuskarta, Numfashin ta da hucin zafi yake fita. tsananin tausayinta ne Ya kama zahra, cikin sanyin murya tace"Aunty Anila dan Allah ki daure ki tashi ki shiga toilet kiyi alwalar, idan muka kammala sallar sai muyi masu addu'a...." idanunta jawur ta kalli zahra, Cikin disasshiyar murya ta furta"Zahra ki barni kawai, Ni kadai nasan raɗaɗin da zuciya takeyi min! Zahra in har Ana bata dawomin da junaid ba, wallahi zaku iya rasa ni, saboda bazan iya rayuwa batare da yaron nan ba, zuciyata zata iya bugawa in mutu...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sarƙe makoshinta, fashewa da kuka zahra tayi"Aunty Anila ki daina wannan maganar! Bana jin dadi, Kina karya min zuciya ta! In sha Allah babu abunda zai faru dake, ba zaki mutu ba, kuma in sha Allah ba abunda zai faru da junaid, Zasu dawo cikin koshin lafiya..." lallashinta zahra ta ci gaba dayi dakyar ta samu ta shawo kan Anila, harta hakura ta mike ta shiga toilet yin alwala, bayan shigarta zahra ta nufi wardrobe din kayan Anila, don ta ɗauko mata hijabi, bayan ta bude murfin ta zura hannu cikin jerin hijaban Aneelarh dake a jere ta ruƙo ɗaya tana kokarin janyota kwatsam! ba zato ba tsammani idanunta suka sauka akan ɗan mutun dake kwance cikin shelve din wardrobe Ya kudundune kanshi atakure jikinshi duk ya sandare. Rass taji gaban ta ya faɗi nan take ta saki hijabin dake ruke a hannunta ya faɗi ƙasa ta runtse ido ta daddage ta fasa ƙara tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un jikinta ya fara kakarwa gaba daya tabi ta ruɗe takasa gane wanene ma ita dai kawai taga dan mutun kamar aljani, banko kofar toilet anila tayi da gudu ta fito jin sautin karar zahra, gabanta na faduwa ta furta"Zahra! Meye faru? Lafiya kike ihu? La66an zahra na kerma sam ta kasa magana sai nuna mata cikin wardrobe din takeyi da yatsan hannunta wanda ke ta kerma.. Adabarbarce ta furta"Aun...Aun... aunty Anila mutun! Ɗan mutun a ciki! ...." a matuƙar ruɗe Anila ta nufi wardrobe din ta kai idonta inda zahra ke nuna mata lokaci ɗaya ta waro idanunta waje da karfi ta furta"baby junaid..." sai lokaci zahra ta sake kallon shi dakyau taga fuskarshi sharkaf da gumi ya sandare kamar matacce duk ya takure kanshi a cikin shelve din da alama ya dade a ciki, wani abun daure kai towel ne ɗaure a jikin shi daga gani har wanka anyi mashi. Allah kadai yasan meya faru da har ya 6oye kan shi cikin wardobe.. " A hanzarce Anila ta ɗauko shi ta zauna kan floor tare da kwantar da kanshi saman kirjinta, ta shasshafa fuskarshi, muryarta na rawa tace ma zahra ta dauko mata ruwa, da sauri zahra ta fuce daga dakin jim kaɗan ta dawo hannun ta ruke da bottle water mai sanyi ta miƙa ma Anila, yatsun hannunta na kerma ta buɗe murfin ta gumtsi ruwan abaki ta watsa mashi saman fuskarshi, wata irin firgita yayi jikin shi ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama...nannauyar ajiyar zuciya anila da zahra suka sauke. Cikin sanyin murya anila ta ambaci sunan shi junaid! Firgigit ya ware idanun shi waɗanda suka kaɗa jawur har saida suka tsorata, Yana ganin fuskar mommynsa Ya ƙanƙameta ya cusa kanshi cikin kirjinta Ya fashe da kuka mai sautin gaske ya dinga sambatu na fitar hayyaci, hakan ba karamin ɗaga masu hankali yayi ba...lamarin yayi matuƙar daure masu kai? Meya faru da shi? Ya akai ya shiga cikin wardrobe ya boye kanshi❓hatta bugun zuciyarshi bana lafiya bane❗ *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 38 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 02, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe "Junaid Dan Allah ka daina kuka! Me ya faru dakai? Meyasa ka 6oye a cikin wardrobe? ina Anah? Kwata kwata baya fahimtar me take cewa, kuka yakeyi na fitar hayyaci hada kai hannu ya dunga bugun bayan ta, fashewa sukayi da kuka daga ita har zahra wani irin tausayin shine ya kama su, gashi sun rasa gane kan shi. banko kofar dakin ummi da mami su ka yi daga waje suka jiyo sautin kukan junaid hakan yasa suka watso aguje suka fado dakin, lokaci ɗaya suka ci burki suna kallon Anila dake a rungume da junaid, waro idanu sukayi hadi da buɗe baki tsabar mamaki da al'ajabi ne ya kama su! Sam sun kasa furta magana na dan wani lokaci kafin mami ta matsa kusa da su, muryarta da rudu ta furta"ikon Allah kamar junaid nake gani! a ina kuka gan shi ne"? Shuru ba wanda ya bata amsa har saida ta ɗan daka masu tsawa saboda akagareta"bakuji ina magana bane? A ina kuka gan shi"? Dakyar Zahra ta tsagaita da yin kukan tana faman jan numfashi ta labarta masu komai. Mami ta zagba salati tana tafa hannayenta, gaba daya sun shiga rudani, lamarin yayi matukar rikirkita tunaninsu sun rasa tunanin me zasuyi, kowa da abunda yake sakawa aranshi..." Mikewa Aneela tayi ɗauke da shi, ta nufi mami tana kuka Yana kuka an rasa me lallashin wani"mami ku taimaka ku lallashe shi yaƙi yin shiru na rasa gane meke damun shi, junaid baya a cikin hayyacin shi, idanunshi sun kaɗa jawur sai sambatu yakeyi mana" miƙa hannu mami tayi zata dauke shi aikuwa ya maƙe kafaɗa ya ƙara shigewa jikin mamanshi, sautin kukan shi ya cika kunnuwansu, sun rasa ya zasuyi da shi, gaba ɗaya suka yi mashi ƙawanya suna kokarin shawo kanshi ta hanyar lallashin shi kwata kwata baya sauraron su, adai dai lokaci su abie sun dawo daga masallaci kwatsam sukajiyo kukan junaid mai ƙaraji, wani irin faɗuwar gaba ne ya darsu a zukatan su, mahboob har yana tuntu6e garin saurin ya shiga ciki, gudu gudu sauri sauri uncle Ɗan iya da Abie Sukeyi suka nufi dakin Anila, suna shiga suka iske su mami tsaitsaye cirko cirko fuskokin su sharkaf da hawaye, kusan atare su abie suka kai dubansu ga junaid, arude mahboob Yace"Junaid! Aunty Anila a ina kuka gan shi? Ko Ana ce ta dawo da shi"? Abie ne yayi hamdala Yana fadin Alhamdulillah sun dawo kenan, dama saida raina ya bani wani wurin sukaje, Ina Anan take ne? Me kuma akayi mashi yake kuka.. "? Uncle ɗan iya yace"lafiya kuke kuka?Shima Yana kuka babu mai lallashin wani? Ina ita Anan"? cikin shesshekan kuka zahra ta sanar da su inda suka gano junaid "Abie, junaid baya sauraron kowa, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, kuka kawai yakeyi, mun rasa gane kan shi..." tsantsar tashin hankaline akan fuskokinsu har sun fara murnar ganin shi azatonsu Ana ce ta dawo da shi ashe ba haka bane. "Bani shi nan" abie Ya fada tare da miƙa ma Anila hannu, a firgice baby junaid Ya ƙankameta alamar bazai je gurin abie ba, cikin murya kuka tace"abie ya ki yarda da kowa, su mami sunyi kokarin lallashinshi amma Yaki sauraron su...." Girgiza kai abie yayi tare da ambaton Inna lillahi wa inna ilahirraji'un kafin daga basani ya kalli anila dake ta sharar kwalla, tana jijjiga junaid "Anila ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan, Kina kara ɗaga mashi hankali, je ki zauna ki lallashe shi, ke kadai ce zaki iya shawo kan shi, kiyi mashi addu'a ita yake bukata ayanzu..." amsa mashi tayi da toh, da sauri ta koma gefen gadon ta zauna, tare da sanya hannu ta talla6o kan shi, ta fara yi mashi kira'ar alkur'anin a cikin kunnanshi, su mami sunyi zungudum suna kallon su gwanin ban tausayi, cikin ikon Allah taji ya fara tsaitsayawa da yin kukan kafin a hankali taji yayi shiru ya nutsa kan shi a kirjin ta, fuskarshi tabi da kallo kumtunsa sunyi jawur, la66ansa sun kumbura suntum, hatta ƙwarin idanun shi sunyi jajir, siraran hawayene ke ta zarya kan kun cin shi, lokaci ɗaya taji ya fara sauke ajiyar zuciya a jere jere, nunfashin shi ya fara daidaita ba kamar ɗazu ba. bata dakata da yi mashi kira'ar ba har saida ta tabbatar ya daina shesshekar kukan kafin tayi shiru tana duban shi, ajiyar zuciya su mami suka sauke hankalin su ya dan kwanta jin yayi shiru Cikin sanyi murya ta furta sunan shi"junaid" motsa la66ansa yayi batare daya firta kalma ba... "Dan Allah ka daina kuka, kasan bana son 6acin ranka, nasan nice na bata maka rai na tafi anguwa nabarka, ka yi hakuri ka yafe min junaid, wallahi bansan za'a tada ku da wuri ba..." shiru yayi bai tanka mata ba... "Babyna, bazaka mun magna ba? Fadamin meke damunka? Kanka yanayi maka ciwo? Ko kana jin yunwa? Ina Ana? Meyasa ka yin kuka..." duk tabi ta rude sai surutu takeyi mashi, shidai yayi shiru bawan Allah shi kadai yasan bala'in da idanun shi suka gane mashi. "Kada ki takura mashi Aneelarh, tun da mun samu yayi shiru, ki kyale shi Ya huta, Allah kadai yasan meya faru da shi wanda yayi silar rikicewar shi"! Mami ce tayi maganar Ummi tace"ni ban ma san tunanin me zanyi ba wallahi, hankali na Ya tashi! abun da ya ɗaure min kai meya faru da su? Taya akai junaid yayi wayon 6oye kan shi a cikin wardrobe? To ko dai wani mugun abunne Ya faru da su bayan tafiyar mu, gaskiya ina ji araina Ana ce ta boye shi don kada a cutar da shi ko kuma shi ya boye kan shi sakamakon wani mugun abun daya gani, Allah daga ganin halin da junaid yake a ciki bana lafiya bane, Yaga wani abune daya razanar da shi" ta ƙare maganar tana kallon su Jinjina kai uncle dan iya yayi"nima abunda nake tunani kenan, amma taya za'ay mu san ainihin abunda ya faru bayan tafiyarmu? Cikin shesshekar kuka Anila tace"Junaid zai iya fada mana idan Allah yasa ya dawo hayyacin shi" Mahboob daya gama razana dakyar ya iya bude baki yace"ni damuwata yanzu ina Ana? Ga junaid ya bayyana saura ita baiwar Allah, bamusan meya faru da ita ba! Bamu san awani hali take a ciki ba..." bai kare maganar ba, Abie yace"in har wani abunne ya faru da su, zai iya yiwuwa itama ta boye awani wuri kamar yarda ta 6oye junaid..." jin wannan maganar yasa mahboob ruko hannun zahra yace mata tazo suje su kara nemo ta, da sauri suka fuce daga dakin bedroom dinta suka shiga, suka fara nemanta sako da lungu har karkashin gadon ta, da cikin wardrobe dinta amma basu ganta ba, sun duba ko'ina tun suna sa ran zasu ganta har suka fidda rai, kafin su fito daga dakin sai da mahbbob ya shiga toilet dinta Ya kashe shower din da aka bari a kunne da faucet, ruwa harya fara taruwa sosai har cikin dakin ta ya fara gangarowa, basu bar dakin ba sai da mahboob ya taimaka ma zahra suka gyara mata shi, kafin suka fito da sauri suka nufi sauran dakunan suna duddubawa, duk wani wurin sirri da mutun zai iya 6uya saida suka duba ko zasu ganta sai dai kash bata nan, ceilling ne kadai basu tsaga sun bincika ba don sunsan ba tayadda za'ay ta iya shiga ciki ta buya. Badan sunso ba dole suka hakura da nemanta, jikinsu yayi mugun yin sanyi, zuciyarsu ta karaya, gani suke kamar ba zasu kara ganin Ana ba. Anila taso takai baby junaid asibiti adaren saboda aduba mata lafiyar shi amma abie ya hanata yace mata ta cigaba da yi mashi addu'a in sha Allah zai samu lafiya, taruwa sukayi akan shi ɗaya bayan ɗaya kowannansu saida yayi mashi addu'a suka tottofa mashi a jikin shi, har indomie zahra ta dafa mashi ta kawo masu a plate amma yaƙi ci, ta koma kitchen ta haɗo mashi tea dakyar anila ta samu yasha tea din, jikin shi ya danyi sauki, zuciyar shi dai ce take bugawa da karfi, duk yadda taso ya bata hadin kai suyi magana don taji meke damunshi yaƙi mata magana kamar kurma sai dai yabi ta da ido, don dole ta hakura, gashi ya hanata sukuni ya manne mata kamar anta da jini, ko da zata shiga toilet ta karasa alwala sai dai ta shiga da shi, bayan ta fito ta goya shi abayanta ahaka tayi sallah 💔 ___________________________________✍️ *ALHAJI MUSA💪* Da sassafe ya shigo katafaren falon gidan, jallabiya ce a jikin shi grey colour, ta ɗanyi tighting arms dinsa, kamar kullum fuskarsa a daure ba fara'a, ya zuba hannayenshi cikin aljihun jallabiyar. Cikin takun izza yake tafiya yan aikin gidan dake kai komo suna yin aikace aikacen gyara falo dakai abinci dining suna ganin shi, suka fara gaishe da shi, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye ya nufi dining room ya tsaya bakin glass door din yana kallon zungureran table din dake a kewaye da kujeru ancika shi da kayan breakfast, wani abu da ya ɗaure mashi kai babu kowa a kan kujerun yayi mamaki sam ya manta da abunda ya faru jiya, saboda bayan ya gama balbalin bala'in shi gidan ya bari gaba daya bai ƙara dawowa ba, sai yanzu daya shigo da safen nan,baisan awani hali mutanan gidan suka kwana ba. Agogon hannunsa ya duba don yaga ko time na yin breakfast dinne baiyi ba sai kuma yaga lokaci yayi Ta6e baki yayi kafin ya dago ya kalli yan aikin, Tani ya hango da hannu yai mata alamar tazo, jikinta na bari ta nufe shi"yalla6ai gani" "ya akai banga mutanan gidan ba? Ko baku fada masu an shirya masu breakfast ba"? "Wallahi mun yi masu magana, ita zeenatu tace mun bazata ci ba, nayi nayi da ita taki kula ni, shi kuma shureim da naje dakin shi na iske shi kudundune cikin bargo kamar baida lafiya nayi mashi maganar breakfast yace min baijin yunwa in tafi kawai..." bata kare maganar ba, rai a6ace ya ɗaga mata hannu da sauri taja baki tayi shiru duk tabi tasha jinin jikin ta, wucewa yayi azafafe Ya nufi upstairs, ya ture kofar dakin zeenatu ya shiga daga ciki, tana a zaune kan prayer mat, hannunta ruke da al'kur'ani tana karantawa sam bata ji motsin shigowar shi ba. "Zeenatu"! Kakkausar muryarshi ce ta daki kunnanta, bata kula shi ba, tamkar bataji kiran da yayi mata ba, hakan ba karamun fusatashi yayi ba, kwatsam taji ya dauke kur'anin dake a hannunta, azabure ta mike idanunta sharkaf da hawaye ta furta"Daddy, give me my Qur'an..." ko kula ta baiyi ba ya rufe kur'anin ya nufi bookshelf din dakin ya daura shi asama kafin ya juyo ya kalle ta"fushi kike dani? Rai a6ace tace"daddy ba iya fushi nake da kai ba, haushin ka nake ji, dan Allah ka kyaleni in cigaba da karatuna ko na samun saukin abunda ke damuna..." fashewa tayi da kuka gaban hijab din jikin ta ya jike sharkaf da ruwan hawayen ta "You don't want my happiness, Daddy. You don't want peace kullum burinka ka 6ata min rai, a haka kake son inyi alfahari dakai amatsayin mahaifina!" ta faɗa tana zare mashi blue eyes dinta wadanda suka kaɗa jawur, ko kadan baiyi mamakin kalaman data furta mashi ba, ya riga da yasan meke damunta, wato saboda ya bata ma shureim rai jiya shiyasa take fushi da shi. Matsawa yayi kusa da ita da sauri taja da baya tana girgiza mashi kai, wani irin fargaba da tsoron shi ne suka kamata tayi zaton zaiyi mata wani abune. Batai aune ba taji ya damƙi arm dinta ya janyota kan broad chest dinsa yayi hugging dinta. softly yace"fadamin laifin me nayi maki? Meyasa kike fushi da daddynki? Cikin shesshekar kuka tace"ka 6ata ma ya shureim rai, jiya banji dadin kalaman daka gaya masa ba, daddy ya shureim baiyi maka laifin komai ba, amma ka rufe shi da fada harka shake wuyan rigar shi, baka dubi girman shi ba..." dakyar ta ƙare maganar, shafa bayanta yayi cikin sigar lallashi yace"yanzu me kike so nayi? Don in wanke laifina"? Ya faɗa tare da dago da fuskarta suka haɗa ido sai taji yayi mata kwarjini da sauri ta kau da idonta gefe murya na rawa tace"kaje ka bashi hakuri, idan yace ya yafe maka nima zan daina fushi dakai" ɗaure fuska alhaji Musa yayi jin abunda tace wai shi zaije yaba shureim hakuri, girman kanshi ba zai barshi ba, amma dayake shu'umun kanshi ne sai yace mata"okey, mu sauka down, muje kici abinci" maƙe mashi kafada tayi"bazan iya ci ba, in ba atare da ya shureim ba" "It's okey, muje sai in bashi hakurin" tace toh, ya ruko hannunta suka sauko downstairs. A dining room ta tsaya kamar yadda ya bata umarni, Shi kuma Ya nufi dakin shureim time din daya shiga da sallama abakin shi, bai taras da kowa ba adakin, sautin ƙarar zubar ruwa yajiyo daga bathroom, alamar yana aciki yana wanka, zama yayi gefen gadon shi yana jiran fitowarshi, Almost 15 mins yana jiran shi, har ya mike zai tafi don bayason jira arayuwarshi sai dai ajira shi, jin motsin buɗe toilet door dinne yasa shi dakatawa ya tsaya yana kallon shureim dake fitowa waist dinsa daure da towel, gefen fuskarshi yayi jawur kamar jini ya kwanta, hada sahun yatsun Alhaji musa shatunsu ya fito rudu rudu, sai yaji ba dadi aran shi, ganin irin illar daya yi mashi kuma yayi imanin zafin marin da yayi mashine ya haifar mashi da rashin lafiya a jikin shi kamar yadda yaji Tani tace bashi da lafiya. Kwata kwata shureim bai lura da Alhaji musa ba, cikin rashin kwarin jiki ya nufi dressing mirror. "Shureim"!Ya kira sunan shi, ɗaure fuska yayi batare daya kalli inda yake ba, duk da yayi mamakin jin Muryarshi a cikin kunnanshi aranshi ya ayyana kome yazo yi dakin shi?ya dai san ba hakuri yazo bashi ba abune mawuyaci. "Da kai fa nake magana"! ya faɗa fuskarshi adaure, da farko yaso ya shareshi don yaga iya gudun ruwan shi amma sai ya fasa saboda mutunne shi mai matukar ladabi da biyayya yana ganin girman nagaba da shi bayan haka akwai na annabawa wato hakuri. Juyowa yayi suka fuskanci juna Muryar shi kasa kasa ya furta"Uncle, barka da safiya? Ka tashi lafiya"? ya dan yi mamakin tarbar da shureim yayi masa, amma bai nuna a fuska ba, "ka zauna inason magana dakai" kasa kasa ya amsa da toh, kafin ya juya ya shiga wurin closet dinsa, jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya fara, a kan couch suka zauna shureim ya kau da idanun shi gefe ɗaya yana jiran jin dame yazo! "Shureim dangane da abun da ya faru jiya bana a cikin hayyacina, kasan inada bad temper idan raina ya 6aci bana iya controlling kaina..." yanayin yadda yayi maganar ya ɗaurewa shureim kai har saida Ya juyo dakai ya kalle shi don ya tabbatar idan dagaske uncle musa ne ke yi mashi magana ba wani daban ba. haɗa ido su kayi da juna da sauri dr. Shureim ya kau da idon shi gefe ɗaya, hakan bai dame shi ba yaci gaba da magana cikin tausasa harshe"inaso komai ya wuce shureim, ni bana son duk wani abu da zaisa mu samu sa6ani atsakanin mu..." sai da yai wannan maganar shureim ya dube shi dakyau yace"uncle ni wannan duk ba damuwata bace, bana ruƙe mutun a zuciyata, tabbas banji dadin kalaman daka jife ni da su ba, sun bata min rai, saboda ban ta6a tsammanin zaka iya furta min su ba, da ace wani na waje ne ya gaya min su bazan ji komai ba, amma kai da kanka uncle why? Saboda na fita da zeenatu yar uwata? Ko dan saboda rungumar da nayi mata wanda nikaina bada son raina nayi ba.." idanun shi cike tab da kwalla ya fada yana kallon cikin idon shi"saboda zafin kalaman daka furta min jiya ko bacci banyi ba, da bakin cikin su na kwana azuciyata" mood din fuskar Alhaji musa Ya canza sosai, kalaman shureim sun karya mashi zuciya sai yaji duk ba dadi. Ruƙo hannun shi yayi a cikin nashi ya ruƙe su gam na ɗan wani lokaci kafin ya fara magana a tsanake"Allah ya huci zuciyarka shureim, na gane kuskurena kuma in sha Allah zan gyara.."ya faɗa yana ɗan jinjina kan shi. "Da akwai wata tambaya da kayi min ajiya, dangane da kullan da ni ke yiwa zeenatu, kace ka fara kokwanto akaina! Shureim ina son jin dalilin dayasa kace haka? Wani irin kokwantone kake yi akaina..." ba tare da jin shakkar shi ba yace"ban yarda da kullan da kake yi mata ba, raina yana bani kamar akwai wani abu da kake 6oyewa shiyasa nake kokwanto akanka, ka hanata cigaba da karatu, ka hanata yin kawance da kowa, sannan ka hana ta fita, kamar baka son kowa ya ganta, ita kanta zeenatun ta fara korafi kan kullan da kake yi. Shiru Alhaji musa yayi tamkar bazai yi magana ba, can kuma ya saki Murmushin gefen fuska kafin yace"zan fada maka dalilin dayasa nake kullanta, in har hakan zai goge zargin da kakeyi akaina.." ya fada yana kallon shi. Kafin ya ɗaura da cewa"Dalilin dayasa nake kullan zeenatu, is that I'm a famous politician with many enemies who want to harm me. Zeenatu is my weakness, bayan haka itace ƴa ɗaya tak da nake da ita akusa dani, in har ban bata kariya ba, rayuwarta tana a cikin hatsari saboda akwai masu bin diddiginta, bana so inyi ganganci da rayuwarta, makiyana sun sha turo min sako akan zasu halaka zeenatu, shureim taya bazan killace ta agida ba"? Maganar Uncle musa tayi tasiri a cikin zuciyar shureim jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya, hankalin shi ya tashi da jin abunda ke faruwa da rayuwar zeenatu! "May be zeenatu ta manta bata fada maka ba, lokacin da tana zuwa high school, kusan kullum in zataje makaranta sai an samu wadanda suka kai mata farmaki, don ma Allah yasa akwai bodyguards da suke kula min da ita ay da tuni zeenatu babu ita araye" ya faɗa tare da dukar da kan shi ƙasa ya marairaice fuska kamar ba Alhaji musa ba. Cikin sanyin murya Dr shureim Ya furta"Uncle, hankalina ya tashi da jin maganar nan, yanzu na fahimci dalilin dayasa kake kullanta, ni kaina bazanso abun da zai cutar da ita ba, amma kullan yayi yawa tun da har ta fara takura, bai kamata saboda wasu ahanata jin dadin rayuwarta ba, bayan haka Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake, kuntata rayuwarta agida bashi bane mafita ba, wlh duk tsaron dake agidan nan bazai hana a cutar da ita ba, amma idan muka cigaba dayi mata addu'a, in sha Allah makiyanka ba zasu ta6a yin nasara akanta ba!" wasa wasa dr shureim ya 6uge dayi mashi nasiha har saida ya tabbatar Ya samu nutsuwa Kafin yayi shiru yana jiran jin me zaice.. "Shureim nagode da shawararka, zanyi tunani akai in sha Allah, sannan akwai magana da nakeson yi dakai idan na samu lokaci..." bai kare maganar ba, wayar shureim ta fara ringing, "Zan ɗaga kira" "Okey, pls ka sameni a dining, zeenatu tana jiranka, tace bazata iya cin abinci in ba atare dakai ba..." jinjina kai shureim yayi bayan fitar Alhaji musa ya nufi gaban mirror ya dauki phone dinsa Ya duba sunan mai kira, mommyn su ce da sauri yayi picking ya kara a kunnanshi Tunkafin yayi sallama muryar hajiya layla ta katse shi"shureim wai lafiya tun jiya inata kira bana samunka ko wani abu ya faru ne? Cikin sanyin murya yace"a'a mommy, kiyi hakuri, wayar tana a kashe ne ban jima da kunnata ba" Yanayin muryarshi ya sa ta tunanin kodai ba lafiya gidan? "Ya jikin Benazir din? Ko har dr Ya sallame ku" "Abun da yasa na kira ke nan, don in tuna maka, karfe 11 da rabi za'a sallame mu" Agogo Ya kalla karfe 9, ajiyar zuciya ya sauke"In sha Allah yanzu zan shigo asibitin" amsa mashi tayi da toh, da sauri ya karasa shiryawa cikin shigar larabawa, ya ɗauki facemask ya zura a aljihun shi da niyar in sun fita zai sanya ma fuskarshi, don baison mommyn su taga tabon marin da Alhaji musa yayi mashi yasan muddin tagani sai ta tada 6alli. Adai dai lokacin daya fito daga dakin, sai ga Hajiya sarah ta kimtsa cikin riga da skirt na atampa, ta kashe daurin kallabi mayafinta akan kafada ta daura shi, ta ruke purse dinta a hannu, kasa karasawa tayi gare shi ganin tabon dake akan fuskarshi cos tun jiya da abin ya faru kowa ya shiga dakin shi basu kara haduwa ba, taji nauyin hada ido da shi duk saitaji ba dadi. "Aunty, barka da safiya, kin tashi lafiya" fuskarshi dauke da murmushi ya nufe ta. Tuni taji idanunta sun ciko tab da kwalla cikin sanyin murya tace"shureim ka yi hakuri da abunda ya faru jiya, wlh bakin cikine Ya hana in leko dakin ka, banji dadin ganin yadda tabon marin ya bata gefen fuskarka..." Cikin sauri yace"pls komai ya riga daya wuce, kada ki damu kanki, lafiya kalou, ay uncle dinma yazo har daki ya bani hakuri harma mun sasanta kanmu" kallon shi kawai takeyi gwanin ban tausayi, ta dade bata ga mutumin mai saukin kai da hakuri irin dr shureim ba. Ganin tayi tsaye tana kallon shine yasa shi furta"nayi waya da mommy ta fadamin karfe goma za'a sallame su, yakamata muyi sauri muyi breakfast sai mu wuce..." girgiza kai tayi da sauri ta share kwallar data zubo mata, tabi bayan shureim suka nufi dining ___________________________________✍️ Around karfe 10 na safe, Unaisah tana a zaune kan kujerar gaban gadon Benazir, har ta kammala shirin ta cikin abaya maroon colour, tayi rolling veil akan ta, baiwar Allah jikinta yayi sanyi, zuciyarta batayi mata dadi, sam bata son rabuwa da Benazir ta kamu da kaunarta, duk yadda take zumudin son tafiya don taga yan uwanta, saida taji ba dadi, sabo kenan turken wawa... Gaba ɗaya ta shiga zurfin tunanin rabuwa da ita, benazir dake zaune gefen gadon ta ƙura mata ido tana kallon ta ko kyaftawa batayi, ta fahimci kamar wani abu yana damun yarinyar, ita kan ta faduwar gaba take ji kuma ranta yana bata kamar wani abu zai faru "Babyna me kike tunani"! Cikin kun nanta ta tsinkayi muryar Benazir, wadda tayi silar dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.. Numfasawa tayi a hankali take kallonta, tuni taji hawaye sun cika tab da idonta, hajiya layla tana a tsaye bakin kofar toilet tana kallon su fuskarta duk ayamutse, damuwarta halin da Benazir zata shiga idan aka raba ta da yarinyar, ita kanta ta shaku da yarinyar tana son ta, sai dai ba yadda suka iya dole su yi hakuri su rungumi kaddara. Tattausar murmushi Unaisah ta sakar mata, tare da miƙa mata kwayar maganin dake a hannun ta"mamana ki sha maganin ki," dakyar ta ƙare maganar tamkar zata fashe da kuka saboda tasan maganin bacci ne dr jazz ya bata don ta ba benazir tasha, duk don su samu tayi bacci ko sun tafi da unaisah.... Baiwar Allah Benazir kamar tasan me suke kokarin yi gabanta sai faduwa yakeyi, buɗe baki tayi unaisah ta sanya mata kwayar maganin, ta kanga mata glass din ruwan hannunta ta shanye shi, ƴan mintuna ƙalilan Benazir ta fara gyangyaɗi idanunta suka fara kokarin rurrufewa wani irin karfi maganin ke gare shi dr jazz ya iya aika aika...cikin karyayyar murya ta furta"babyna, kada ki tafi ki barni, inaji ajikina kamar tafiya zakiyi..." ɗan zaro ido unaisah tayi da sauri tace"ki daina wannan maganar mamana, ina atare dake babu inda zanje" dafe kai benazir tayi da hannu ɗaya, dakyar take buɗe idanun ta masu ɗauke da matsanancin bacci ta ƙurama unaisah ido cikin sanyin murya tace"dan Allah ki yafe min Angel, nasan ban kyauta maki ba, amma kada kice zakiyi fushi dani, kada ki tafi ki bar ni, wallahi ina sonki, Allah shine shaida ta bada son raina na tafi nabar ki ba, nayi maki alkawarin zan baki gatan da kika rasa na rashin uwa atare dake, zan tarairaye ki in baki kulawa Angel" a matuƙar ruɗe Unaisah ke kallon Benazir, kalamanta sun ta6a mata zuciya, sun fama mata ciwon dake a zuciyar ta, amma sai tayi tunanin watakil tana sambatune akan yarta da ta rasa. Kukane Ya kwacema Hajiya layla da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta saboda batason ta ɗaga masu hankali. Baccin ne Ya rinjayeta, jikinta ya saki a sukwane ta kwantar da kanta saman pillow, ta lumshe idanunta har lokacin bata daina yin sambatu tana ambaton sunan Angel. A hankali unaisah take binta da kallo zuciyarta na harbawa da karfi da karfi gani take kamar in ta tafi ba zasu ƙara haduwa ba, lokaci ɗaya taji tsantsar tausayin matar ya kamata, tayi fatan ace zata cigaba da kula da ita sai dai tasan daddynta bazai barta ba, after that yan uwanta suna bukatarta ita kanta bazataso tayi nesa da su ba, ruwan hawayen da suka taru acikin idanunta ne suka fara yar tseral kan kuncin ta. "Azeezaty! Ke nake jira muje ko"? Dr jazz ne yayi maganar yana daga tsaye bakin kofar ɗakin, miƙewa tayi daga kan kujerar, kamar wadda aka zarewa laka, ta sunkuyar dakanta saitin fuskar Benazir ta manna mata sumbata har sau biyu kafin ta juya taje ta ɗauko backpack dinta, ta kalli hajiya layla miƙa mata hannu tayi alamar tazo, da sauri unaisah ta ƙarasa gareta, hajiya layla ta rungumota a kirjinta. "Toh Azeezaty, mungode Allah yasaka maki da alkhairi, Allah ya baki ilimi mai amfani duniya da lahira, Allah ya baki miji nagari, zamuyi kewar rashinki, ɗan zaman da mukayi dake mun saba dake, benazir zatayi kukan rashin ki, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarki, Allah yasakama iyayenki da alkhairi..." amsa wa tadinga yi da ameen kamar kar su rabu da juna. "Ki gaida min da mutanan gidan, in sha Allah zamu zo wata rana har gidan naku" Murmushi Unaisah tayi"Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ƙara ma mamana lafiya, nima daddyna yace zai kawo ni gidan ku" murmushi hajiya layla tayi taji dadin maganar, sallama sukayi da juna, A hankali take tafiya tana waiwayon Benazir dake kwance tana ta sharar baccin ta.... Dr jazz harya fara gajiya da jiranta, sai faman duba wrist watch dinsa yake yi baya son chief ya karaso don yasan bai son jira. Har fa ta kusa fitowa daga dakin sai kuma ta juya da sauri ta koma gaban gadon Benazir ta manna mata peck a goshin ta. Ganin abun nata bame karewa bane yasa dr jazz shigowa dakin Ya tasa keyarta gaba suka fito, baiwar Allah tana tafiya tana waiwayon dakin hajiya layla tana tsaye bakin kofar room din, hawaye sun cika idanunta har saida suka bace ma ganin ta kafin ta juya ta koma ciki zuciyarta cike fal da kewar Azeezaty. A dai dai lokacin da suka fito, hamshakiyar motar chief ta kunno kai ta entrance gate din asibitin yar uban su launin ash colour har salƙi take da daukar ido, yanayin yadda motar take tafiya slowly yayi matuƙar jan hankalin visitors dake zarya a arean wurin, suka bi da ido har saida ta tsaya a parking sace. "Muje, Ina tunanin shi ne ya karaso" jaz ya fada tare da jan hannunta, tunkafin su ƙarasa take ta kallon hamshakiyar motar, tayi mata kyau, lokacin dayazo kawota ba irin wannan suka hau ba. Bayan sun ƙarasa gaban motar, ta ciki aka buɗe mata cardoor din wani daddaɗan fragrance ne Ya daki hancinta, mai haɗe da sanyi A.c. "Ki shiga ciki" jazz ya faɗa tare da nuna mata hanya, sunkuyar dakai tayi tare da shiga ta zauna, wurga ido tayi akan shi har saida taji gabanta ya fadi saboda wani kyau da taga yayi mata, ya kare gefen fuskarshi da phone dinsa, da alama waya yakeyi, fuskarsa tana asanye da mask. Hadadden yard din dake ajikin shi Senator cotton material ne light sky blue, rigar short sleeve ce ta bayyana strong arms dinsa, na karfafan maza masu ji da kan su, lallausar sumar kanshi ta sha gyara, ya sabunta military hair cut din sa Sunnar da kanta ƙasa tayi ganin yana ƙoƙarin juyawa, janye wayar yai daga kunnanshi, Ya ɗago suka haɗa ido da jazz sai faman sakar sakar mashi murmushi yakeyi "babban yaya, sannu da zuwa barka da safiya" Calmy ya furta"lafiyalou jazz, ina fata kaima haka" "Alhamdulillah" "Ya mai jikin? "Taji sauƙi sosai" "Naji dadin jin hakan, zamuyi magana anjima" amsa mashi yayi da toh, har time din bai kalli Unaisah ba, kamar baisan da zaman ta ba sai bayan da jazz ya rufe murfin motar, ta kamo belt zata daura taji ya ruko yana kokarin sanya mata ita wani irin shock taji, muryarta na ɗan rawa ta furta"ina kwana" "Ina lafiya" atakaice Ya amsa mata, agogon hannun shi tabi da kallo kirar rolex daytona tayi bala'en yi mashi kyau....bayan ya kammala sanya mata ya gyara zaman shi, A hankali ya dago ido ya kalli senior Agent din dake zaune a driver seat"zamu iya tafiya" cikin girmamawa ya amsa mashi okey Sir, Key yayi ma motar tare da yin reverse ya karya kwana motar ta fuce daga asibitin. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke idanun ta akan window glass din motar, asibitin take kallo cike da jin kewar Benazir matar ta kwanta mata aranta, amma idan ta tuna yar uwar chief ce sai taji hankalinta ya kwanta, ta wani bangaren ta kosa su koma gida ko dan taga yan uwanta almost one week tayi kewarsu" Fragrance din turaren chief Ya hana ta sukuni, ta wutsiyar ido take satar kallon shi, dogon hancin nan nashi ba karamin tafiya yake da ita ba. Hankalin shi na akan phone dinsa da yake scrolling Tayi tsammanin gida zasu wuce kaitsaye amma sai taga kamar sun canza hanya, ba wadda suka biyo ba aranar da zai kawo ta, aranta ta ayyana watakil wata hanyar ce da bata sani ba. Tana tsaka da yin zancen zucinta, suka karaso wani katafaren Obie mall luxury plaza Tayi mamakin haduwar wurin tunani ta farayi ko me zasuyi a mall din? Ta dai zubama sarautar Allah ido. bayan shigar su ciki agent din yai parking a katafaren parking space na mall din. Shiru tayi zuru tana jiran jin me zaice, sai da ya shafe 5 mins kafin taji ya furta"Let's go inside." fitowa sukayi atare, da sauri senior agent din ya fito ya take masu baya, Hankalin Ta ba karamin tashi yayi ba ganin wayayyun ƴan mata da samari yan gayu suna zarya a wurin duk sai taji ta raina kanta, wata irin kunyace ta kamata, takasa motsawa daga inda take ganin idon mutane ya dawo kansu, duk da facemask din dake akan fuskar chief hakan bai hana mutane kallon shi ba musamman yan matan dake gifta wa wasu kamar zasuyi tuntu6e tsabar yadda suke kallon shi, ga shi ba halin tunkarar shi saboda senior agent din dake atare da su, wani basamuden mutun ne ƙarƙarfa babu annuri kan fuskarshi, ga bindigu dake soke a qugun shi. Ganin bata da alamun motsawa ne yasa shi ruko hannunta a cikin nashi, rass taji gabanta Ya faɗi duk sai ta kama yan kame kame tana faman noke kai, duk da yadda taso ta daure kada tai kauyacin saida ta kasa a hankali take satar kallon mall din yayin da suka nufi main entrance, Security guard din dake tsaron wurin sun gane chief, sai miko gaisuwa sukeyi cikin girmamawa kamar zasu durkusa kasa, tun da taga haka sai ta fara jin kanta wata hajiya gata ga chief, murmushin gefen fuska ta dan saki tana wani tafiya taku dai daya tana hura hanci. Senior agent din ne ya ruke mata shopping cart, ganin taki daukar komai sai kalle kalle takeyi ne yasa agent din yi mata gyaran murya ta kalle shi"ki dauki abunda kikeso, sannan ki daukarwa yan uwanki" waro ido ta danyi tare da juya kai ta kalli chief, yana tsaye gefenta ya goya hannayen shi kan kirjin shi in a low voice ya furta"Do what he said" amsa mashi tayi da toh, nan fa tafara ruwan ido ta rasa me zata dauka ba sabon ba, ga mutane suna ta yin shopping dinsu hankali kwance ita ko kamar an daure mata hannayenta, Sun lura da yanayin ta ganin zata 6ata masu lokacine yasa chief kallan agent din ya bashi umarnin duk abunda yaga idanunta sun kalla ya daukar mata shi ko da mara amfani ne, ya amsa mashi da okey sir. juyawa chief yayi a hanzarce ya koma mota ya zauna saboda baison kallon da mutane sukeyi mashi. Bayan fitar chief, Unaisah ta miƙi hanya, agent ɗin yana abiye da ita jira yake yaga me idonta zai kalla, ita kuma taki yarda ta kalli komai tunda taji umarnin da chief ya bada, tafi son tayi ta kallon yan mata da samarin dake shopping a wurin. Adaidai wurin Confectionery, ta tsaya tana kallon chocolates din dake a jere ga cookies kala kala, da sauri agent din ya fara jidar mata su iri iri yana turawa a cart din duk abunda ta kalla saiya dauke shi, har saida ta kau da ido tukunna ya dakata. Tafiya ta cigaba dayi ta nufi gurin data ga an rubuta Female Fashion Floor, kayayyakine kala kala na mata da zarar ta kalli abu, cikin sauri agent din yake daukar mata shi koda kuwa mara amfanine kai har bras da pads saida ya kwasar mata saboda umarnin boss dinsa yake ki. Gabanta har faduwa yakeyi ganin cart din ya fara cika, ita fargabanta ba tasan kudin kayanba kada su yi almubazzaranci. Hakan baisa ta juya ba sai ta nufi Boys' Corner kayan mazane tundaga kan suturu masu kyau da tsada har izuwa takalma, shades, caps, watches komai fa babu ce kadai ke babu, da sauri agent ɗin yafara jidar kayan da yaga idanunta suna kallo, saida yaga ta kau da ido kafin ya dakata, cart din har ya cika yayi sauro, hakan yasa agent din yayi magana da wani sales assistant dake akusa da su yace mashi ya dauko masu wani cart din da sauri yaje ya dauko ya ruke mashi suka cigaba da take mata baya, aikin yi fa ya samu, ita fa hankalinta ma baya akan kayan, kawai gurin ne ya burge ta shiyasa taƙi tafiya, idonta take ba abinci, a wani Tech zone ta tsaya tana kallon kayan dake gurin da sauri ta juya duk suna abiye da ita kamar wata sarauniya, mutane sai kallon ta sukeyi suna mamakin kayan da ake kwasar mata, ko yar wacece? Har zata gifta gaban wani education hub ta dakata tana kallon writting material din dake a gurin, bakomai ta tunaba face yan uwanta bata da burin dayawuce su iya karatu da rubutu, yanzu ne taga abu mai amfani da zata iya nuna tana so..harta buɗe baki zatayi magana idonta ya sauka akan agent din da assistant din sun dage sai kwasar mata kayan sukeyi, tun daga kan notebooks, Dictionary, pens, pensil, markers, drawing book, duk wani abu da idonta ya kalla saida suka ɗaukar mata shi, gaba daya sun kashe mata baki, kamar sakarya haka ta saki baki tana kallonsu, ganin abun nasu bame karewa bane yasa tayi saurin furta"dan Allah ku dakata Ya isa haka! wadannan kayan sunyi mana yawa.." Agent din yace"banga alamun sun isa ba, Ni umarnin chief nake bi, in kina so mu dakata to ki kau da idonki daga kan kayan da sauri ta juya baya ta fara kokarin neman checkout counter dakyar ta gano gurin ta tsaya tana faman sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu, har cashier din sai da ta dan bashi mamaki, ganin yadda ta fado gaban counter din, bayan ya auna kayan da suka siya total 800k har saida taji yan hanjin cikinta sun kaɗa murya na rawa ta kalli agent din"dan Allah ku rage kayan su koma na dubu goma" maganarta taso ta basu dariya agent din yace"da alama bakisan wanene chief ba, idan duka kayan mall din kikeso zaisa a mallaka maki su, babu abunda zai ragu na daga tarin dukiyar da yake da shi.." jinjina kai cashier din yayi" amma dai yalla6ai, ita din bakuwa ce a family din su? Daga mashi gira agent din yai, murmushi cashier din yayi a lokacin har an kammala sanya masu kayan a cikin shopping bags har kusan huɗu, Agent din ya zaro master card din da chief ya bashi ya miƙa ma cashier din don ya ciri kudin, ƙin kar6a yayi fuskar shi dauke da murmushi yace "Grandpa dinsa Ya hana a kar6i kudinsa, ku tafi kawai" girgiza kai agent din yayi"ka kar6a ka ciri kudin, chief baya son siyan kaya batare da an kar6i kudinsa ba, gani yake kamar sadaka aka bashi" dariya sukayi cashier din yace"nasan halin shi ay, har yau bai canza ba kenan, kudin ay duk nasu ne ko an kar6a hannunsu yake komawa, pls ka bashi hakuri ni bazan iya cirar kudinsa ba, zaija min ne..." duk yadda agent din yaso ya kar6i card din yakiya dole suka hakura yace ma unaisah su tafi, ita dai hankalinta yaki kwanciya, ta ruɗe da alamarin, taya zasu sayi uban kayan nan kuma aki kar6ar kudinsu? Abunda bata sani ba, mall din mallakin famiy dinsu ne, juyawa tayi da sauri ta nufi hanyar fita agent din yabi bayanta, ma'aikatan mall din suka bi bayansu da shopping bags din.. Bayan sun sanya masu kayan a boot din motar, agent ya bude mata car door din ta shiga ta zauna tare da kallon chief ya nutsu yana daddana wayar hannunsa, shigowa ciki agent din yai ya zauna a driver's seat ta mirror ya kalli chief. "Sir, we've completed the purchase, and the goods are in the boot." Fuskarshi babu annuri Ya furta"Why didn't I receive a debit alert? "Sir, grandpa ɗinka Ya hana su kar6i kudinka, ba yadda banyi da cashier din ba amma yaƙi kar6a yace baya son yaja ma kan shi" ta6e baki chief yayi kafin a hankalli ya dan juya suka hada ido da unaisah dake ta kallon shi, da sauri ta sunnar da kanta ƙasa cikin sanyin murya tace"mungode Allah yasaka da alkhai..." bata kare maganarba ya toshe mata bakin ta da yatsan hannun shi..idanunsu acikin na juna ko kyaftawa basayi wani irin kallo suke jefawa junansu hatta agent din dake driving dinsu sai satar kallon su yakeyi ta cikin mirror fuskar shi dauke da murmushi yajima baiga macen data dace da chief irin yarinyar nan ba, sun burge shi. da sauri ta sauke idonta kasa ta kama yin yan kame kame kamar zata nutse kanta cikin cinyoyinta, zame yatsansa yai daga kan la66anta, laushinsu ba karamin fusgarshi sukayi ba, muryar shi tamkar tame jin bacci ya furta"kada ki ƙara yi min godiya bana so" daga mashi kai tay"bazan ƙara ba" Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 39 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 03, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️ "Good" ya furta tare da gyara zaman shi, babu wanda ya ƙara furta kalma a cikin su, shiru motar baka jin sautin komai sai sanyin A c dake ratsa fatar su, aranta Allah Allah take su karasa gida don ta nuna ma yan uwanta tsarabar da tayi masu tasan zasu ji dadi. Gaba ɗaya ƴan aikin gidan suna atsaitsaye gaban door room din marwa, fuskokinsu babu walwala idanunsu sun kumbura saboda rashin isasshen bacci da basu samu ba adaren jiya, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya sukeyi tun wuraren karfe shida sheikh imam ya karaso gidan, tunkafin karasowarshi bayan kammala sallar asubahi baba obie ya tura su hajjaty tare da security suka dauko marwa daga asibiti yanzu haka tana acikin dakinta tare da sheikh imam malik sautin ruƙiyar da yakeyi mata ya cika kunnuwansu bayin Allah sunyi zuru zuru, hankalinsu atashe tun safe ake abu ɗaya har yanzu ba wani labari mai dadi, a kalla sun shefe awanni abakin kofar dakin suna jiran sheikh imam malik. "Idan har ya tabbata aljanune suka ɗaura mata ciwon, ni dai inaga zan tattara kayana in koma kauyenmu da zamane, zaifi min kwanciyar hankali don bana jin zan iya cigaba da zama agidan nan...." cikin rawar murya safa tayi maganar. Abla tace"ni kaina na tsorata wallahi, jiya a zaune na kwana saboda fargaba da zullumin abunda ya faru da marwa, wlh ta bani tausayi baiwar Allah rana daya mutun ya tashi ba baki ga kuturta!" Sofia tace"nifa saboda tsoro jiya bayan mun dawo gida, dana shiga daki karatun kur'ani na kunna awayata sai da asuba na kashe" kowa yana tofa albarkacin bakinshi banda hajjaty dake tsaye ta goya hannayenta kan kirjinta, ita dai hankalinta bai kwanta da ciwon marwa ba! Jin motsin buɗe kofane yasa sukayi shiru suna jiran tsammani, A hankali sheikh Imam Ya fito daga dakin, farar jallabiya ce a jikinsa, ya ɗaure kanshi da rawani, hannun ɗaya ruƙe da cazbaha. cikin girmamawa suka fara yi mashi sannun da fitowa da fara'a ya amsa masu tambayoyi suka fara jere mashi kamar yan jarida "Malam ya ake ciki? Ya jikin marwan? Ta samu lafiya? Dagaske aljanune suka shafe ta? Sheikh zamu iya shiga ciki mu duba ta? Ɗaya bayan ɗaya sheikh Imam Yake kallonsu, Ya rasa wa zai fara amsa ma tambayar shi sun ƙi bari Yayi magana, ya fahimci sun matsu da su san awani hali take ciki. har ya buɗe baki zai yi magana Saiga baba obie tare da pravin sun nufo wurinsu. Miƙa mashi hannu baba Obie yayi suka yi musabaha"sannu da kokari sheikh, Ya mai jikin? An dace kuwa"? Fuskarshi da fara'a yace"mu shiga daga ciki ku gani da idonku.." da sauri suka nufi dakin su hajjaty suna abiye da bayansu, agaban katifar marwa suka tsaya cirko cirko, tana a kudundune cikin bargo jikinta sai makekketa yakeyi, tuni pravin Ya haɗe fuska tamkar bai ta6a dariya ba, ga wani gumi mai ɗumi daya wanke goshin shi, Hanky ya zaro ya fara goge zufar. An rasa wa zai fara cire bargon murmushi sheikh imam yayi don ya fahimci tsoro suke ji, da zolaya yace ma baba obie"baba kai yakamata ka fara cire bargon mu gani" waro ido baba obie yayi haɗi da girgiza kai yace"ya zakai min haka? dan Allah kadaina wannan maganar, kai dai daka fara aikin kai yakamata ka karasa ladarka.." yar dariya Sheikh Imam yayi tare dakai hannu ya ruƙo bargon ya fara jan shi ahankali, pravin kamar ya daura hannu akai ya fasa ihu haka yakeji duk ya rasa sukuninshi kamar wani munafiki sai cizon yatsa yakeyi.. Su hajjaty sun baza na mazurai suna jiran ganin marwa, gabansu sai faduwa yakeyi . Lokaci da sheikh Imam ya ƙarasa cire bargon, gaba ɗaya suka zabura suna kallonta idanunsu azazzare cike da mamakin ganin bakinta Ya buɗe sunyi matukar razana da lamarin, ta ko'ina zufa ce ke tsastsafowa ajikinta kamar wadda aka tsamo daga cikin tafki, kafafunta sun miƙe daga lauyewayar da sukayi, amma yatsun hannayenta basu dawo daidai ba har yanzu da kuturtar sai dai yatsun sun ɗan saki ba kamar farko da suka matse ba har suna fidda ruwa mai yauƙi yanzu babu ruwan. Kusan Atare su hajjaty suka ambaci sunanta da karfi Marwa. buɗe baki tayi zatayi magana sai dai ta kasa sautin muryar baya fita dakyau gura gura take magana kamar wadda harshenta ya ƙone kwata kwata ba'a iya gane me take cewa, har sun fara murna taji sauki ashe da sauranta, pravin har zai fita daga dakin jin takasa magana yasa shi dawowa ya tsaya yana kallon marwa afakaice yake sakin murmushin mugunta. Jikin su hajjaty yayi sanyi lakwas, har sun fara sharar kwalla Baba obie yace"Ikon Allah! sheikh dagaske dai jinnune suka shafe ta? Ya fada cike da son jin karin bayani, a tsanake sheikh imam ya ce "Eh, bakaken aljanune a jikin ta, sune suka haddasa mata ciwon..." waro idanu waje su hajjaty sukayi wani irin tsorone Ya kamasu murya na rawa abla tace"dama Aljanu suna iya canza ma mutun halittar shi" jinjina mata kai sheikh imam yayi"fiye da haka ma zasu iyayi.." kallon kallo suka jefawa junansu. Aruɗe baba obie ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Zuƙunnawa sheikh imam yayi daga gaban katifar marwa idanun shi akan fuskarta Ya soma magana"kada ki sanya damuwa aranki, Allah yana atare dakai, duk wani abu da kika ga ya faru dake mukaddarine daga Allah, bana so ki kuntata kanki, ko ki ƙyamaci kanki, balle kiyi tunanin illata kanki saboda wannan lalurar data same ki, kiyi kokarin cinye jarabawarki kada ki gaza, Aljanun da suka haddasa maki ciwon nan suma bayin Allah ne, babu abunda ya fi karfin mahaliccin mu...." tun da ya fara magana idanun marwa suka cicciko tab da kwalla ita kadai tasan me take kitsawa aranta. "nayi alƙawarin zan taimaka maki amma fa dole sai kema kin taimaki kanki, kiyi kokarin bin abun da Allah da Manzonsa sukace ayi domin samun kariya daga sharrin su, da zuciya ɗaya in sha Allah zaki ji sauƙi, jikinki zai dawo kamar yadda kike ada" jinjina mashi kai tayi alamar ta gamsu da maganar shi. "Ma.. malam muma ataimaka mana dan Allah, ka faɗa mana hanyoyin da zamu kare kan mu daga sharrin su" cikin shesshekar kuka abla tayi maganar. murmushi sheikh imam yayi tare da kallonsu ɗaya bayan daya sai yaji sun bashi tausayi ganin yadda jikinsu ke ta kerma kamar mazari "Ku samu wuri ku zauna zanyi maku bayani" da sauri suka kewaye sheikh imam suka zauna kan ƙasa suna jiran jin me zaice. Miƙewa yayi da sauri ya ɗauko kujerar mirror Ya ajiye agaban baba obie don ya zauna. "Nagode sheikh" ya fada tare da zama kan kujeran. Tun shugowar pravin dakin sheikh imam bai ɗaga ido Ya kalle shi ba, sarai ya san da zaman shi, dama tunfil azal basa jituwa tsakanin su ko gaisuwa bata ta6a haɗasu ba, Shiru yayi kamar akwai abunda Ya hana shi fara magana, wayar pravin ce ta fara ringing daga cikin aljihunsa da sauri ya fuce daga dakin don ya amsa kira. Fitar shi keda wuya sheikh Imam Ya fara magana yana duban marwa cikin tattausa harshe yace mata"kiji tsoron Allah! Rass gabanta Ya fadi, su hajjaty suka kalle shi da alamun rudani akan fuskokin su. "Idan akwai wani abu da kike aikatawa badai dai ba to ki daina! Sau dayawa mu muke ja ma kanmu shiga cikin masifa, Allah ya gatanta mu ya bamu hanyoyi da dama da zamu iya ba kanmu kariya amma muna wasa damar mu...." ga dukkan alamu Sheikh imam Ya canza maganar daya dauko da farko hannunka mai sanda yayi mata kuma ta fahimce shi hakan yasa ta duƙar da kanta ƙasa hawaye suna cigaba da wanke fuskarta. "Kina yin azkar? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a "Baki iya ba ne"? Ɗaga mashi kai tay alamar eh. "Ya salam! Wannan wani irin ganganci ne? Da ranki da lafiyarki? Wallahi da ace kina kokarin kiyayewa babu wani mahalukin daya isa ya cutar dake in ba Allah ne ya kaddara za'ayi galaba a kanki ba, azkar garkuwa ne agare mu, ita kuma addu'a da kike gani takobin mumuni ce kuma ita addu'a tana iya canza kaddarar mutun, daga mummuna zuwa mai kyau. Nasiha ya fara yi mata jikinta yayi sanyi lakwas, su abla tuni ido ya raina fata don su kansu bakowane keyi ba har kwara hajjaty itada ta musulta daga baya tana kokarin yi akai akai "Gaba ɗaya inaso ku bani aron hankulanku, ku saurari abunda zan fada maku..." amsa mashi sukayi da toh, Shiru yayi jim kafin ya fara magana"abunda ya kamata ku sani shine, Zikirin safe da yamma yana da matuƙar mahimmanci sosai, wanda inda Musulmi yasan mahimmancin sa da kuma kariya da yake bashi da bai barshi ba koda na kwana ɗaya ne, don haka ina ƙara jan hankulan ku da Ku yawaita Lazimtar Zikirin safe dana yamma.." atare suka hada baki wurin furta in sha Allah malam zamu kiyaye Shiekh imam ya ɗaura da cewa"abu na gaba Yin alwala, mutum ya kasance yana yawaita zama cikin tsarƙi domin hakan na bada kariya, bayan haka akwai Qiyamul laili, da kuma Neman tsari yayin shiga bayan gida (toilet) idan zaku yi bacci ku yi alwala, sannan ku karanta ayatul kursiyu bayan ita sai falaki da nasi suna da Muhimmanci sosai..." jinjina kai kowan nan su yayi sheikh imam ya numfasa yana dubansu kafin ya dasa da cewa "Sannan Faɗin La’ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa Ala kulli shai’in kadir sau ɗari safe da yamma Faɗin Bismillahillazi la ya durru Ma’asmihi shai’un fil ardi wala fissama wahuwa ssami’ul alim” sau uku safe da yamma, Faɗin “A’uzi bikalimatillahit-tammat min sharri ma khalaka” sau uku safe da yamma" baba obie ya nutsu yana sauraron sheikh imam har cikin ranshi yaji dadin yadda ya zaunar da yan aikin gidan yana koyar dasu yadda zasu kare kansu hakan ba karamin faranta ranshi ranshi yayi ba, shi kanshi ya karu da sheikh imam. "Malam, wallahi ni yawan mantuwa gare ni, kona yi kokarin yi sai wani abun yaja hankalina..." Sofia ce tay maganar, shiekh imam Yace"akwai islamic apps na waya, da zaki iya sauke wa.." da sauri hajjaty tace"ina da shi zan tura mata nima dashi nake amfani, shi yake tunasar dani lokacin yin ibadata da kuma lokacin yin azkhar" murmushi sheikh imam yayi idon shi akanta yace"kinyi masu wayau, zaman tare baice haka ba, meyasa tuntuni baki sanar da su ba"? Sunnar da kanta ƙasa tayi Calmy ta furta"ay ni bansan ba su amfani da shi ba" Gyaɗa kai yai"haka ya dace, In ka san abu na karuwa ne, to ka yi kokarin sanar da wasu suma su amfana, na tabbata da ace shirin labarina ne aka saki jiki na rawa zaki fada masu koba haka ba"? Gaba daya suka sanya dariya. Murmushi baba obie yayi, shima sheikh imam din murmushine akan fuskarshi. Baiwar Allah marwa duk da halin da take aciki saida tayi murmushi fuskarta sharkaf da hawaye... Nasiha ya cigaba dayi masu akan su daina shagala duk runtsi duk wuya kada su yi sakaci da ibadarsu da kuma neman tsari daga gurin Allah, cike da gamsuwa suke sauraran shi daga bisani yace Idan har ku ka kiyaye zikirorin dana faɗa maku, sannan ku ka kuma ƙaurace wa saɓon Allah toh haƙiƙa Allah zai kare ku daga kowani irin sharri, kuma zaku yi rayuwa cikin kwanciyar hankali domin da Ambaton Allah ne da yimasa biyayya ake samun natsuwa. Allah yasa mudace" atare suka amsa mashi da ameen haɗi dayi mashi godiya Baba obie yace"sheikh muna godiya sosai, jazakallahu khairan..." da fara'a ya amsa mashi da ameen... Kafin ya kalli Su abla"ina bukatar mutun ɗaya da zai dinga kula da marwa" shiru su ka yi kowa tsoron kusantarta ya ke yi, yanzu ma da suke adakin don sunga sheikah imam ne ga baba obie shiyasa suka saki jiki. "Kada ku bani kunya mana! Kun riga da kunsan lalurar nan ba ita ta daura ma kanta ba! idan har kuka ce zaku juya mata baya ko ku ƙyamace ta zaku sa ta tsani kanta ne harta aikata ma kanta abunda bama fata, ayanzu bata da wasu yan uwa na kusa da ya wuce ku, ku take gani amatsayin yan uwanta wadanda zasu share mata hawaye...." cikin sanyin murya hajjaty tace"wallahi bani ƙyamar marwa, kawai abune da bamu saba gani ba, muna jin tsoro amma in sha Allah zamuyi kokarin bata kulawa, ni nayi alkawarin zan dinga zuwa dubata...." Shiekh imam yace"Alhamdulillah, naji dadin jin hakan daga gare ki, zuwa anjima in sha Allah zan aiko maki da magunguna na musulunci, sannan kafin in tafi zan kar6i contact dinki saboda in tura maki addu'o'in da zaki dinga tofa mata aruwan wankanta dana shanta,.." "Toh malam, muna godiya Allah ya saka da alkhairi..." miƙewa yayi bayan yayi masu sallama baba obie ya ruko hannun shi suka fita daga dakin.... Kamar jira suke sheikh Ya fita daga dakin da sauri su abla suka gudu zuwa kitchen Ya rage saura Hajjaty adakin. Bata san sa'adda ta fashe da kuka ba, gashi ba halin Yin magana, da hannu ta dinga bugun katifa tana kuka, da sauri hajjaty ta rukota tana lallashin ta idanunta cike tab da kwallo, wani irin tausayintane Ya kamata. "Marwa ki daina kuka, In sha Allah zaki ji sauki ki dawo kamar yadda kike ada, nayi alkawarin zan taimaka maki muyi duk abunda sheikh imam yace" tunda hajjaty ta fara magana marwa tayi shiru tana kallonta wallahi tayi danasani yafi sau a ƙirga, kuma tayi mamakin yadda hajjaty ta amince zata kula da ita sa6anin sauran yan uwansu da suka gudu daga dakin. Bata ta6a tsammanin hajjaty tana da saukin kai, da tausayi ga mutunci irin na yau ba, sai taji ta tsani kanta, hakanan batai mata laifin komai ba mace mai kyakkyawar zuciya amma saboda abun duniya ta amince zata yi mata leƙen asiri don abata matsayinta akuma koreta daga gidan wa'iyazubullah, bakomai ta tuna ba face hajiya saratu, ita da tayi silar jefata halin da take aciki, amma kwata kwata bata nuna damuwarta akanta ba, ko kalmar sannu ay ya kamata ta furta mata, ayanzu ta gane wasu mutanan sai kana da amfani agurinsu suke kula ka da zarar sunga bazasu amfana dakai ba sai su watsar dakai, tayi danasani taso ace tana da baki da yau saita fallasa asirin wanda yayi silar jefata halin da take a ciki ko da zata rasa ranta ne❗ Amma duk da haka bata makaro ba, ta ɗauki alwashin saita tona asirin wanda ya cutar da ita! "Marwa"! Muryar hajjaty ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula "Kiyi hakuri Kinji yar uwata, bana son ganin hawayenki, nasan kina jin yunwa bari na kawo maki abinci in kika kammala ci sai in taimaka maki kiyi wanka..." kifa kai marwa tayi jikin pillow ta rushe da kuka mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita, zuciyarta ta karaya, a halin yanzu ba rayuwarta ta ke jima tausayi ba, rayuwar hajjaty itace abun tausayi....dakyar hajjaty ta shawo kanta har ta samu marwa ta daina kuka, da sauri ta mike taje kitchen donta haɗo mata abunda zata ci. ___________________________________✍️ *Hajiya Saratu* A zaune take kan mirror chair jikinta sanye da sleeping gown ta manyan mata, fuskarta sam babu walwala ta zabga tagumi da hannunta ɗaya bata jima da farkawa daga bacci ba, ko wanka ta gaza shiga tayi, saboda rashin kwanciyar hankali, duk bayan yan mintuna saita duba wrist watch din hannunta, lumshe idanunta tayi yayin da acan ƙasan zuciyarta take tariyo maganganun da suka tattauna ita da Hajiya laurat a jiya, bayan ta taso daga office tsoro da fargaba suka hana ta dawo gidan, tace ma driver dinta ya wuce da ita aso villa acan suka haɗu da hajiya laura tun daga kan yanayin fuskar Hajiya saratu ta fahimci babu lafiya akwai wani abu da yake damunta, bayan sun zauna a pool yard masu yi masu hidima suka kawo masu coffee da kayan marmari tace mata bismilla su fara sha, girgiza kai tayi alamar bazata sha ba, hajiya laura tace wai meke damunki ne? kiyi magana mana, a shirye nake da in taimaka maki don mu shawo kan matsalar, ajiyar zuciya hajiya saratu ta sauke tana faman yamutsa fuska ta kwashe komai daya faru dangane da ciwon marwa ta sanar da hajiya laura. "Wallahi ina cikin tashin hankali, zama gidan ma ya gagareni, yanzu haka da kika ganni daga office ko gida ban wuce ba nayo nan don in fada maki halin da nake ciki" Shiru hajiya laura tayi jim da alamun ruɗani akan fuskarta tace"ni abunda bangane ba, kina nufin dare ɗaya ta farka da lalurar"? ɗaga mata kai hajiya saratu tayi, al'amarin ya ɗaure mata kai "Kuma an kaita asibiti? "Bani da masaniya, amma bari na kira baba naji halin da ake ciki" tay maganar tare da curo waya ta danna ma baba obie bayan ya ɗaga, ta tambaye shi awani hali marwa take a ciki, ya sanar da ita abun da likitoci suka ce, tayi mashi sallama ta ɗago ta kalli hajiya laura da tayi zugudum tana kallonta, ta sanar da ita abun da baba obie ya faɗa mata, ga mamakinta sai taga hajiya laura ta saki murmushin gefen fuska takai hannu ta dauki cup of coffee ta kurba still da murmushi akan fuskarta, hakan ba karamin ɗaure ma hajiya Saratu kai yayi ba fuskarta a ɗaure tace"bana son iya shege meye abin murmushi aciki? Yar dariya laura tayi"kwantar da hankalinki mutuniyata, kinsan wani abu"? Girgiza kai tay alamar a'a "Wallahi ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba yarinyar nan marwa silar ciwonta yana da alaƙa da aikin leƙen asirin da kika sanya ta!! Hankali atashe Hajiya saratu ta zaro ido tana kallon laura aruɗe ta furta"ban..ban gane me kike nufi ba? "Ke yanzu har sai nayi maki bayani? Yakamata ki gane mana, kiyi amfani da brain dinki, ciwon yarinyar nan aikin asiri ne, wlh ture akayi mata, in ba haka ba taya za'a ce rana ɗaya mutun ya tashi da cutar kuturta sannan ba baki, ai ke daga ji kinsan ɗaura mata ciwon akayi, Ni abun da na fahimta watakil hajjaty ta kama marwa tanayi mata leƙen asiri, shiyasa ta kulle mata baki don kada ta iya furta magana, bayan haka ta ja mata cutar kuturta don kada ta samu damar da zata yi rubutu da hannayen ta balle harta tona mata asiri...." Dafe kai hajiya saratu tayi yayin da zuciyarta ke bugawa da karfi da karfi gaba ɗaya tabi ta ruɗe. Hajiya laura taci gaba da cewa"hmmm wallahi ɗan adam ba abun yarda bane! Dama na jima ina zargin hajjaty, indiyawan nan basu tsoro Allah, ko a fina finan su zakiga suna yawan zuwa wurin bokaye don ayi masu asiri, matar nan munafuka ce wlh, tana amfani da rauhanai shiyasa ta mallake mutanan gidanku har ta samu gindin zama take iya shegen data ga dama, yanzu gashi ta kassara rayuwar marwa....." Runtse idanu Hajiya saratu tayi, hankalinta Ya tashi har wani dishi dishi take gani a idanunta muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku"! hajiya laura tace"ay mun sha ja maki kunne akan ki kori hajjaty daga gidan kika ƙiya, ay ni banma san ya akai kika yi gangancin da pravin ya ɗauko maki bakauya yar kauyan india masu bautar shanu ya ajiye maku agida, to wallahi kwara tun wuni ku dauki mataki akanta in ba haka ba hmmmm nan gaba Allah kadai yasan me zata aiwatar.." maganganun hajiya laurat sun tsaya mata arai sun kuma ɗaga mata hankali, bata ta6a jin faɗuwar gaba da tashin hankali irin na jiya ba, ta jima a vila suna tattaunawa da hajiya laurat har shawarwari ta bata dangane da yadda zata kare kanta daga sharrin hajjaty da kuma hanyar da zata bi don ta gano ainihin wacece ita. Bayan sunyi sallama da juna, hatta shiga motarta tana zullumi da fargaban hajjaty, ta tsorata da ita ba kadan ba, ko bayan data dawo gida kasa shiga bedroom dinta tayi saboda tsoro, dakin baba obie ta fara shiga ta zauna wurin shi har saida aka fara kiran magrib ya tashi zai tafi masallaci kafin ta dawo dakinta sam ta kasa sukuni wani irin tsorone Ya kamata babban tashin hankalinta kada hajjaty tayi silar kassara rayuwarta kamar yadda ta kassara rayuwar marwa ya ilahi abin ya ɗaga hankalin ta, ba ita ta runtsa ba adaren jiya har saida pravin ya dawo ya fara mata faɗa akan rashin dawowarta da wuri, baiwar Allah saboda tsoro ta kasa mayar mashi da martani saima ta rungumeshi ta ƙanƙame shi hakan ba karamin daure mashi kai yayi ba, yaja hannunta suka zauna gefen gadon ya tambayeta meke damunta cikin sanyin murya tace mashi bata jin dadin zuciyarta tsoro take ji saboda abun da ya faru da marwa shiyasa taki dawowa gidan.. murmushi pravin yasaki har cikin ranshi yaji dadin tsoratar da tayi saboda shi agurinshi damace ya samu da zai dinga juyata son ranshi, tun da ya gano lagwon ta, a daren ranar sai da ya biya bukatar shi da ita, son ranshi ta sakar mashi jiki yayi abunda yakeso dama ya kwana biyu bata bashi hakkin shi ba. Bayan ta dawo daga duniyar tunanin ta miƙe tana zagaye ɗakin tana tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin dole ta ɗauki mataki! Ta tsani hajjaty fiye da yadda ta tsani mutuwarta❗ __________________________________✍️ Lokacin da Benazir ta farka daga bacci, da wata irin kasala ta buɗe idanunta wadanda suka kaɗa jawur muryarta na rawa ta fara ambaton sunan Angel mikewa zaune tayi kan gadon, hannunta ɗaya dafe dakanta, ga wata faduwar gaba da take ji "Babyna! Where are you? Mami Ina Angel dina? Bata nan ne? dakyar ta iya saukowa daga kan gadon tayi miƙa haɗi da yin hamma kafin ta fara baza ido tana neman Unaisah, ita kadai ce adakin, hajiya layla taje office din dr jazz domin amsa kiran da yayi mata. "Angel! Angel! Can't you hear me calling you? Where are you?" Da karfi tayi maganar tare da nufar kofar toilet ta kwankwasa"pls idan kina ciki, Ki amsa min babyna kinji..." ta fada tare da kanga kunnanta jikin kofar, shiru taji ba a amsa mata ba, da alama babu mutun aciki, hakan yasa tay pushing door din ta shiga ciki tana bin ko'ina da kallo kwata kwata bata ga kowa ba, ji tayi kamar ta daura hannu akai ta fasa ihu, gaba ɗaya tabi ta rude dama saida ranta ya bata cewar ba lallai ta ganta ba Fitowa tayi daga toilet din, ta nufi bed dinta, ta zukunna tana leƙen karkashin gadon don taga ko anan ta buya Adai dai lokaci hajiya layla ta shigo dakin hannun ta ruke da takardar sallama kaitsaye idonta suka sauka akan benazir. rass taji gabanta Ya faɗi ganin yadda tabi ta ruɗe tana ambaton sunan babynta, tuni taji hawaye sun ciko idonta sam takasa karasa shiga ciki saboda fargaban amsar da zata ba benazir idan ta tambayeta Ina babynta, batasan ya zatayi da ita ba, ga tsananin tausayinta da take ji. "Mommy"! Muryar dr shurieim ce ta katse mata zancen zucin ta, aɗan firgice ta juya baya tana kallonsu, a jere suka nufo ta su uku ne, Shureim da Alhaji ubaid tare da hajiya sarah fuskokinsu dauke da murmushi, dakyar ta haɗiye damuwarta ta nufe su tana fara'a suka rungume juna ita da hajiya sarah bayan sun raba jikinsu, shureim Ya matsa kusa da mommynsu Ya rungumeta tare da manna mata kiss gefen fuskarta. "Sannun ku da zuwa" hajiya sarah tace"ay min afwa wlh banji dadi ba, jiya banzo na duba jikin benazir ba, ban kuma kira naji ya kuke ba" murmushi hajiya layla tay"kai haba ba komai wlh, ay kinama kokarin zuwa dubata, wlh kada kiji komai benazir tana cikin koshin lafiya.." tai maganar tare da kallon Alhaji ubaid dake kallonta, harara ta ɗan watsa mashi afakaice saboda taji haushin rashin kiransu da baiyi ba jiya, cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri jiya bana jin dadin jikina ne shiyasa ban kira ba, naso ma inzo dubaku" ta6e baki tayi"ay kwara da kukazo gaba ɗayanku, ga Benazir can tana neman yarta, kuma yarinya masu ita sun dauki abunsu, dama likita ne ya bada maganin bacci aka bata tasha kafin aka rabata da yarinyar yanzu gata can ta hargitsa dakin tana neman yarta" Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Dr shureim yace"baiwar Allah, na tausaya mata, wlh dama saida naji fargaban zuwan ranar nan, gashi sun shaku da yarinyar" Alhaji ubaid yace"yanzu ya zamuyi jama'a? ay ni nayi zaton ma zamu taras da su ashe har sun tafi, gaskiya banji dadi ba, ban ta6a haduwa da yarinyar ba balle inmata godiya ita da iyayenta da sukai mana halacci.." Hajiya layla tace"wannan duk mai saukine tunda aneelah tasan gidan iyayenta, wata rana saimuje muyi masu godiya, yanzu dai muji da maganar benazir! Menene mafita"! Hajiya sarah tace"ni nama rasa ta cewa wlh, amma ni aganina, abun da yakamata shine mu lalla6ata mu fada mata cewa daddyn yarinyar yazo ya dauke ta sun tafi mall, da anjima zai dawo da ita, saboda mu samu mu bar hospital ɗin da ita, in ba haka ba dakyar zata amince ta bi mu" gaba daya sunyi amanna da maganar hajiya sarah, atare suka nufi dakin, suna shiga suka isketa zaune gefen gado duk ta yamutse gashin kanta kamar na mahaukaci, ga fuskarta sharkaf da ruwan hawaye. Atare suka hada baki gurin yi mata sallama, da sauri ta miƙe tana kallonsu, muryarta na rawa ta furta"mami! Ya shureim! Daddy! aunty Sarah! Ina babyna? Tana ina? Na duba ko'ina banganta ba! Dan Allah ku fadamin waya daukar min babyna? Wlh in har ba'a dawo min da itaba, zuciyata zata buga in mutu kowa ya huta"! kusan atare suka haɗiyi yawu kowa yasha jinin jikinshi, dakyar hajiya Sarah tayi karfin halin furta"haba Benazir? Meyasa zaki daga hankalinki akan yarki? Waya isa Ya rabaki da ita? Ki kwantar da hankalinki, Yarinyar nan takice halak malak.."bubbuga kafafunta tayi saika rantse da Allah batasan me take ba, bayan da hankalinta tsabar pretending ne "Ni kawai ku fadamin tana Ina? Meyasa banganta ba"? "Benazir, daddynta ne ya dauke ta, sunje mall zasuyi maki siyayya da anjima zai dawo da ita gida..." cike da fargaba hajiya layla tayi maganar, shiru tayi jimm na ɗan wani lokaci kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya fuskarta ayamutse tace"mami dagaske Taj yazo nan? Shi ya dauki Angel dina"? Murmushi suka sakar mata, dr shureim yace"kwarai kuwa dagaske shiyazo ya dauketa.." "Amma bai tambayeni ba? Ko ya daina sona? Ta fada tana zare masu eyes dinta Alhaji ubaid yace"ya tambayeki mana, ay saboda ke sukaje yin siyayyar, yana son ya faranta miki rai.." wani irin tsallan murna ta daka tana dariya. kallon kallo su hajiya layla suka jefawa junansu hankalinsu atashe, wato akwai gwarama idan suka koma gida taji shiru taj baizo mata da yarta ba. "Mommy zamu jiraku a mota" dr shureim ya fada tare da kallon daddynsu atare suka fuce, Badajimawa ba, saiga su sun fito tare da benazir har ta canza kayan jikinta ta maida kayan da aka kawota asibitin da su, a backseat na motar dr shureim ta zauna, yana agaba tare da alhaji ubaid, Hajiya layla kuma a motar hajiya sarah ta zauna, a jere motocin suka fuce daga asibitin. Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 40 Complete by Novels Elite Admin September 03, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe Ex-Prisoners💓 Gaba ɗayan su suna zaune kan sofas na falo. "Aunty ummi wai yaushe angel dinmu zata dawo gida ne? Jemimah ce ta faɗa tana faman haɗe fuska. Sajeed yace"ni ma na damu da rashin dawowarta gashi tun jiya ko awaya bata kira munji muryarta ba.." Batool tace"dan Allah aunty ummi ki kira mana ita mu gaisa, ko hankalinmu ya kwanta" tayi maganar tana kallon Ummi, gaba ɗaya hankalinta yana akan wayar hannunta da alama chatting takeyi batasan ma me suke cewa ba.. "Dama kun daina wahalar da kanku gurin yi mata magana, saboda hankalinta ba akanku yake ba.." acewar Parvin. ɗaga murya batool tayi"Aunty Ummi..." aɗan firgice ta ɗago da ido tana kallon ta"batool! Lafiya kike kwala min kira kamar baki san ina akusa ba"? Dariya su naufal sukayi Batool ta marairaice mata fuska"aunty ummi muna ta yi maki magana kin yi shiru baki amsa mana ba.." maida hankali tayi akansu "Okey, Ina sauraronku lafiya"? Kafin wani ya furta magana acikinsu ba zato ba tsammani, sallamar Unaisah Ta katse masu hanzarin su, kusan atare suka miƙe da gudun gaske suka nufeta hada masu tuntu6e garin sauri, Batool ce ta fara karasawa gareta ta faɗa jikinta suka rungume juna kamar zasu koma mutun ɗaya sai faman tikar dariyar murna sukeyi, gaba ɗaya sukayi mata rumfa kamar zasu lasheta yadda kasan sunyi shekara basu ganta ba, Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su ɗaya bayan daya tayi hugging din yan mata, sajeed Ya buɗe hannu zai rungumota tayi saurin ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi saboda gudun kada ta samu ciki. *_______________________________Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su ɗaya baya daya tayi hugging din yan mata, sajeed ya buɗe hannu zai rungumota tayi saurin ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi, gani take kamar ciki zai shiga, har naufal ya kai hannu zai yi hugging dinta again ta ƙara ja da baya hadi da girgiza kan ta, mamaki ne ya kama su Naufal ganin yadda ta hana su ta6a ta kamar taga wani mugun abu. "Meyasa mu bazaki rungume mu ba, ko bakiyi kewarmu ba"? murmushi ta sakar masu"kuyi hakuri ba haka bane, nayi missing dinku gaba ɗayanku.." girgiza kai sajeed yayi ni ban yarda ba Allah, naufal yace"kinfi son su batool shiyasa kika rungumesu ko"? Javed ma yace"ni banji dadi ba, wariya kike nunawa atsakanin mu.." gwalo parvin tayi masu, Sarah tace"nan fa ba prison bane, mun riga da mun gane jinsin mu, ku maza mu mata don haka kuyi hakuri no more hugs atsakanin mu ehe" dariya suka sanya. Batool tace"bayan haka aunty ummi ta fada mana babu kyau mace ta rungume namijin da ba muharramin ta ba, koda ruke hannunsa ne" wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Unaisah dake sauraronsu taji dadin yadda suka fara gane abunda ake koya masu. Gaba daya kalamansu akan kunnan chief dake abakin kofar shigowa falon maganar Batool ta faranta ranshi dama yajima yana son a fahimtar dasu game da mannewa juna da sukeyi amma yanzu alhamdulililah sun fara hankali Mubeen yace"amma ay a prison mu na yi kuma baku ta6a hana mu ba" Harara Parvin ta watsa mashi"ay lokacin muna a jahiliya period ne, yanzu kan mage ya waye..." maganarta ta basu dariya, fashewa ummi tayi da dariya ashe tana tsaye abayansu. Unaisah na ganinta tayi sauri nufarta suka rungume juna "Oyoyo my babe Unaisah, welcome back home munyi kewarki abar kaunarmu" "Nima nayi kewarku aunty ummi fatan na same ku lafiya..." ta fada tare da dago da kanta "Lafiyalou Unaisah, ya jikin patient din? Ko har an sallame ta"! "Yau za'a sallame shiyasa na taho gida, taji sauƙi sosai, tama ce in gaishe mata da ku" murmushi ummi tayi"Allah sarki muna amsawa, wlh naji dadin samun lafiyarta..." Kallon su Naufal tayi sun haɗe fuska babu annuri duk don saboda taƙi hugging dinsu, jemimah ta tuntsire da dariya tana fadin wai ma haushi suke ji don kinki rungumarsu jibar su ma kattai da su.."bata ƙare maganar ba, Sajeed Ya tallabi keyarta nan take ta fara ta6e baki zatayi kuka, Naufal Ya ɗaga hannu zai buge bakin da sauri ummi ta ruƙo hannun shi tana dariya tace"ya isa haka pls, wasa takeyi maku" "Pls Angel, To mu gaisa da hannu" Sajeed Ya fada tare da mika mata hannu shi, shiru tayi jimm har ta miƙa hannu zata ruko nashi ba zato ba tsammani chief ya shigo falon yayi hanzarin daura hannunshi akan na Sajeeed, gaba daya suka shiga nutsuwarsu sam basu san da zaman shi ba. cikin girmamawa suka fara gaishe da shi, ummi ma ta gaida shi ya amsa mata, Sajeed baki ya ki rufuwa saboda sunyi musabaha da chief, yaƙi sakar mashi hannu. "Pls chief can you hug me"? Ɗaga mashi gira chief yayi tare da yin huggin dinshi, wani irin dadi ya lullu6e shi. "Nima pls" acewar Naufa, miƙa mashi hannu yai da sauri naufal ya rungume chief harwani bude hanci yakeyi yana shakar kamshin turaren shi Kunya ta hana Haris yin magana, lura da hakan yasa chief mika mashi hannu da sauri ya matsa kusa da shi suka rungume juna, bayan ya saki haris Ya rungume javeed da mubeen wayyo dadi, tsabar murna kamar anyi masu albishir da gidan Aljanna, Ummi sai satar kallonshi takeyi saboda kyan da yayi mata, kai ko amafarki bata ta6a tsammanin zata haɗu da chief face to face ba sai gashi cikin ikon Allah ƙaddara ta haɗa ta zama da shi agida ɗaya, ta yaba da hankalinshi, nutsuwarshi, wayewarshi, saukin kanshi da ilminsa komai Allah Ya bashi uwa uba ga tarin Dukiya. Gaba ɗaya yan matan sun ɗaure fuska, ganin su naufal sun fara yi masu gwalo saboda chief ya rungumesu..." bubbuga ƙafa Jemimah tayi muryarta da shagwa6a tace"wayyo Allah, mu ma dan Allah yaya chief ka rungumemu..." dariya sajeed yayi tare da cewa"no bazai rungumeku ba, jinsin ku daban namu daban, kowa ya rungumi jinsinsa koba haka ba guys"? Ya fada cike da shakiyanci yana kallon su Javed, Naufal yace"haba kamar dai a jahiliya period? ay haramunne na mijin ya rungume mace, nan fa ba prison bane kan mage ya waye.. " gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Unaisah hada dafe ciki, chief dake atsaye ya goya hannayenshi kan kirjin shi, idanunshi na akan fuskarta wani irin kallo yake binta da tashi ta saki baki tana ta dariya fararen hakoranta tass da su bata ta6a jan hankalinshi irin na yau ba.. Babu wanda Ya lura da irin kallon da chief yakeyi mata gaba daya ya shagala A hankali ya kau da idon shi Ya juya Ya nufi part din shi. "Wallahi inason ku yan uwana, kuna faranta min raina, Allah yabarni daku, wallahi mai rabani daku sai Allah, shiyasa naketa zumudin in dawo gida saboda nasan anan ne kadai zan samu farin ciki da kwanciyar hankali...." cikin jin dadi tayi maganar, Ummi ta ruko hannun"mu shiga daga ciki, mun barki atsaye.." gaba ɗaya suka nufi Sofas din falon, kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, shi dai sajeed kalmar muharram ta tsaya mashi arai, so yake yaji wanene muharramin nan da shi kadai zai iya rungumar mace, abun da bai sani ba ita kanta Batool din batasan wanene muharram ba, tabbas ummi ta ta6a faɗa mata amma karatun bai zauna akanta ba. "Kinyi breakfast acan asibitin" cikin kulawa ummi tayi mata maganar, "Eh, nayi" labari ta fara basu na Benazir duk suka kasa kunne suna sauraranta "Matar tana sona nima ina sonta aunty ummi, mun shaku da juna, har grandma dinta muna mutunci da ita dayake adaki daya muke kwana kuma kinsan wani abu aunty ummi.." girgiza mata kai tay alamar a'a "bata gane cewa ni ba yarta bace, bansan wani hali zata shiga ba idan ta farka daga bacci taga bani akusa da ita..." cikin sanyin murya tayi maganar. Ummi tace"baiwar Allah, wallahi ta bani tausayi, ubangiji Allah Ya bata lafiya, inayi mata fatan Allah ya bata wata yar" suka amsa mata da ameen "Wani abu daya bani mamaki aunty ummi, matar tana kama da Batool yadda kikasan ita ta haifeta Allah..." murmushi ummi tayi, batool ta washe baki jin an ambaci me kama da ita"wallahi har naji ina son ganinta" murmushi unaisah tayi"hmmm ai ba ita kadai ke kama dake ba, ranar dana fara ganin yayanta dr shureim saida na ɗan razana, yadda kikasan yayi kakinki, ke gaba dayansu kamar family dinki ne..." wani irin faduwar gabane Ya darsu a zuciyar Ummi, sunan dr shureim da Unaisah ta faɗa ya tsaya mata aranta. "Dan Allah daske kike? Acewar batool, "Wallahi dagaske nake, Allah ya zuba masu ruwan kyau, grand ma dinta balarabiyace..." dafe kai ummi tayi da hannu ɗaya, gabanta na cigaba da faduwa.. Gaba daya sun lura da yanayinta, "Aunty ummi lafiya" da sauri ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace ba komai unaisah, can kuma tace. "Unaisah, kikace sunan yayanta dr shureim! Ita kuma Ya sunan ne"? Murmushi Unaisah tayi kafin tace"Aunty Benazir" ummi tayi jimm kamar mai nazarin wani abu. "Namanta ban fada maku, wani abun farin ciki daya faru ba.." har suna hada baki wurin furta"menene" dariya ta danyi kafin tace"kun tuna auntyna da nake yawan baku labarinta a prison" kallon juna sukayi batare da sun iya gano wacece ba. "Duk wanda ya tuna sunanta zan bashi kyauta ta musamman" ta fada cike da nishadi Nan fa suka fara canki canka, Hawwa tace"na tunata, sunanta Aunty adama" girza kai unaisah tayi"a'a ita wannan mommy adama take" "Kamar aunty bahijja ne" acewar hibba, dariya unaisah tayi"no ba haka sunan yake ba" Sajeed yace"Sunanta aunty laila" dariya unaisah tayi"no ba haka bane Allah indai baku fada ba, bazan baku tsarabar da nayi maku ba.." ta fada tana karkaɗa kafarta gaba ɗaya kamar ta manta da zancen Danish kamar an goge mata tunanin shi a brain dinta. "Sunanta Aunty Aneelerh, indai ba haka sunan yake ba to kuyi min dundu abayana" dariya Unaisah tayi tare da kallon batool"kin canka dai dai, aranar kafin in bar gida kunsan meya faru...."? Girgiza mata kai tayi, nan fa tafara basu labarin zuwan aunty Anila ko gajiya batayi, sai surutu takeyi kamar parrot, gaba daya hankalin ummi baya atare da su, kamar bata acikin nutsuwarta har saida kunnuwanta suka jiyo mata muryar Unaisah tana fadin"ashe ita aunty aneelerhn kawar aunty Benazir dince, atare mukaje asibitin abun da ya farantamin rai Aunty Aneelah ta haifa min dan kani sunan shi baby junaid, tama yi min alkawarin zata kawo min shi har gida..." wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Su Batool. "Wayyo Allah Angel maimakon ta shigo mu gaisa da ita, meyasa baki fada mata irin kaunar da muke yi mata ba.." parvin ce tay maganar, batool tace"Yaushe zata kawo mana ɗan kaninmu junaid mu gan shi, wlh munji dadin haduwar ki da aunty Aneelerh, saura muma mu hadu da ita amma dai zatazo nan ko"? Daga masu kai tayi"don ma namanta ban kar6i number dinta ba, amma zan ma daddyna magana nasan bazai rasa layinta ba" "Unaisah! da sauri Ta kalli ummi na'am "Wai ni kam dama can anan abuja kuke zaune keda daddynki"? Girgiza kai tayi"a'a a joss muke" gaban ummi ne ya ƙara faduwa, karfin hali tayi wurin furta"okey, amma ita auntyn naki Aneelerh, ya kike da ita ne? Ta fada cike da son jin karin bayani "Matar uncle dina ne Uzair" Shiru ummi tayi bata kara yin magana ba Motsin shigowar mutun a falon ne Yaja hankulansu ga kallon kofar, Senior agent din da ya kai su Unaisah mall ne ya shigo hannun shi ruƙe da shopping bags, ya goyo backpack dinta abayan shi, miƙewa tsaye sukayi suna jiran ya karaso A tsakiyar falon Ya ajiye mata shopping bags din kafin Ya sauke backpack din bayanshi ya ajiye ta"i'm sorry na tsaya amsa kira ne"_ murmushi tayi tare da cewa nagode sosai" Yace"Never mind" ya fada tare da juyawa ya fuce daga falon Gaba ɗaya suka zagaye bags din suna kallon su ummi tace"tsarabar mu ce wannan"? Unaisah tace"eh nakune, nima akwai nawa ciki" Zukunnawa ummi tayi agaban shopping bags din A hankali ta fara curo kayan tana ajiyesu kan rug, su Azeeza sai tsalle suke suna murna ganin cookies da chocolates kala kala dama mayinsu ne, kamar shazu mamu suke wurin shan zaki. Tun kan aje ko'ina suka fara kokarin kai hannu zasu ɗauka, ummi tace su tsaya ta raba su. "Unaisah wadannan uwayen kaya haka? Wanene ya siya maki su? da mamaki ta fada tana kallon fa.." "Atare da chief mukaje shopping mall, bakiga wurin ba ya hadu, ni fa bani na zabi kayan ba, shi yace mutumin daya kawo kayan komai yaga idanuna sun kalla ya daukar min shi ko da mara amfani ne" jinjina kai ummi tayi cike da mamakin maganar ta maida dubanta ga kayan, gasunan tili guda. ta fara ɗaga kayan tana ambaton sunayen su a fili, Fragrance set, hair accessories, gel nail kit, skincare set, jewelry box, lace robes, slippers, diary with a lock and key, throw blankets, shaving kit, smartwatches, earbuds, sports jersey, bluetooth speaker, da sauran su ga Writting material kala kala, can idon ta ya hango mata bras har kala uku da yan panties biyu, dagowa tayi tare da kallon unaisah baki asake tace"waɗannan fa"? Dariya Unaisah tayi tare da sunnar da kanta ƙasa wata irin kunyace ta kamata"wlh Aunty Ummi bansan hada bras acikin kayanba, sune suka daukarmun" dariya ummi tayi"ah toh ni dama nasan bada saninki ba, wannan ay sai dai Batool duk da bansan size dinta ba amma nasan zasuyi mata, ke kuma saiki bari in naki sun kara cukowa" gaba ɗaya su Naufal suka tsuntsire da dariya, daure fuska tayi rai a6ace take aika masu da harara, ummi tace"ku kuma meye nayi mata dariya kawai daga anyi abu cikin raha" kumshe dariyar sukayi "Sorry my babe, kada ranki ya 6aci, ni da wasa nayi maganar" ta6e baki tayi tana faman wurga masu naufal harara. Ummi tace"abun dai da yawa wlh, ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi.." ta fada tare dakai hannu tana kara dudduba kayan"suma dai waɗanda suka daukar maki kayan sun iya taya 6era barna.."ta fada tana yar dariya. "Hada phone, bayan kina da waya? Da sauri unaisah ta kalli phone box din" Da sauri batool tace"dan Allah sister ki bani dama bani da waya..." saejeed yace nima inaso dan Allah, haris yace wlh na riga ku dan Allah ni za'a ba, rigima suka sanya da sauri unaisah ta ɗauke phone box din, ta ruƙe a hannunta, ummi tace"kin raba gardama, ki ajiyeta agurin ki" ta amsa mata da toh, Kwashe kayan Unaisah da Ummi sukayi atare su ka maida su cikin bags din, ummi ta dibar masu chocolates da cookies ta rarrabamasu kowa ya buɗe nashi yana ci, sauran tace"za'a ajiye su adakin unaisah, duk rana zamu dibi kaɗan mu sha idan ba haka ba nasan ba zaku raga masu ba, duka zaku shanye su" amsa mata sukai da toh. "Unaisah ke da Batool, Ku kwashe kayan ku kai dakin ku, ku ajiye su dakyau" atare suka amsa mata da toh, kafin suka fara kwashe jakukku nan suka kai su dakin su. *UNAISAH ANGEL* Around karfe biyu na rana, tana a kwance kan bed dinsu ta ɗaura kanta bisa pillow, ta ɗan lumshe idanunta bakomai take tunani ba face Aunty Benazir, tun bayan data dawo gida hankalinta yaƙi kwanciya ta damu da son sanin awani hali take a ciki? Meya faru bayan ta farka daga bacci? "Ya Allah kasa kada aunty Benazir tayi kukan rashina, bana son tayi maraicina rashina akusa da ita! Zuciyarta ce ta raya mata me zai hana taje wurin chief ta tambaye shi awani hali Benazir din take a ciki tun da yar uwar shi. da sauri ta sauko daga kan gadon, ta dauko mayafi ta yafa akanta, taje gaban Shopping bags din da suka ajiye ta ɗauki ɗaya ta zazzage kayan cikinta a gidan drawer, ta ɗebi turare biyu ta hada da chocolates da cookies kala shida ta sanya a ciki tasan ma ba lallai ya kar6a ba, kawai tayi tunanin takai mashi ne. Miƙewa tayi hannunta ruƙe da ledar da sauri ta fuce daga dakin atsanake take tafiya.. Adaidai lokacin Danish Ya fito daga bedroom din shi yana daga tsaye a second floor, ya sanya singlet da boxer shorts a jikin shi, ya dafe handrail da hannayen shi, yana bin down stairs da kallo kwatsam idanun shi suka hango mashi ita, kamar a mafarki Yake kallonta, kwata kwata baisan ta dawo gidan ba, saboda bai fito waje ba, yana adakin shi yana karatu bacci ya ɗauke shi bayan ya farka ya shiga bathroom yai wanka hakanan yaji yana sha'awar fitowa waje yasha iska cikin ikon Allah yaci karo da ita... Yaji dadin ganinta sosai, har saida yaɗanyi murmushi dimples dinsa suka lotsa, ji yayi kamar yaje gurinta yayi hugging din ta ya faɗa mata irin kewarta da yai, sai dai yasan ba abune mai yiwuwa ba, saboda sharuddan data gindaya mashi, kuma yayi alkawarin bazai ta6a karyawa ba, in har ba ita da kanta ta janye kudurinta ba. Yanayin fuskarshi ne Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, zuciyar shi ta karaya ganin ta nufi upstairs kuma yasan bai wuci part din chief zataje ba, duk yadda ya kwallafa rai akan son ganinta amma ita bata damu da shi ba kamar ma ta manta da shi, da ace lokacin bayane kafin su samu sabani yasan shine mutun na farko da zata fara nema idan ta dawo daga wani guri. Kifa kan shi yai jikin handrail din yana jin wani irin ɗaci aran shi.... Lokacin da ta je part din chief bata iske shi ba, sau uku tana yin knocking bai buɗe ba, ranta ne ya bata ya fita hakan yasa ta juyo ta nufi stairs a hankali take taka matakalar, ranta ne ya bata kamar ana kallon ta, da sauri ta wurga eye balls dinta tana bin downstairs da kallon ganin ba kowa yasa ta maida dubanta ga second floor ganin zata ganshi yasa shi sauri juyawa ya buɗe room door dinsa zai shiga tsayawa tayi cak da yin tafiya tana kallon bayan shi har saida ya shige.. "Danish" acikin zuciyarta ta ambaci sunansa, sam takasa karasa cigaba da tafiya sam ta manta da shi sai taji wani irin a zuciyarta kamar bata kyauta ma shi ba. ganin shi da tayi yasa taji kewar shi ta mamaye ta sai dai bata jin zata iya zuwa gurin shi, ta san dalilin dayasa shima baizo gurin ta ba, saboda alkawarin da ya daukar mata, tun a prison tasan halin shi da ruƙe alkawari in har ba ita ta janye sharuddan ba, danish bazai ta6a kusanta kan shi da ita ba koda hakan zaiyi silar da zuciyarshi zata daina bugawa ne, shiyasa ta matsa mashi akan ya daukar mata alkawarin don tasan ta hakanne kadai zasu nisanta da juna. Ƙwallace ta cicciko idanunta jikinta yayi sanyi lakwas ji take kamar bazata iya jure rayuwa guri ɗaya da shi, batare data kusanta kanta da shi ba, har yanzu akawai kaunar shi a zuciyarta kuma har abada bata jin zata iya daina son shi, la66anta na kerma ta furta"I'm Sorry Danish, bani da mafita ne, nasan dagani har kai zamu cutu amma muyi hakuri da juna na ɗan wani lokaci..." karasa saukowa tayi daga kan stairs din ta nufi bedroom dinsu, tana shiga ta iske Batool zaune kan mirror chair, da alama ita take jira Jin motsin shigowarta yasa batool ta kalle ta "Sister ina kika je? Muna ta jiranki a adining, kizo mu yi lunch" In a low voice ta furta"pls basai kun jira ni ba, kuje ku ci abincin ku, zan zo" "Toh" Batool ta amsa tare da saukowa ta fuce daga dakin Zukunnawa tayi agaban drawer chest, ta buɗe ta karo chocolate da cookies masu yawa ta tura a jakar hannunta, ta dauko shaving set tana tunanin ko zai bukace su? mezaiyi da su, danish bashi da gashin da zai aske cos ta san shi tun a prison haka halittar shi take bai da underarm hair, hatta fuskarshi smooth take ba gashi, hakanan dai ta sanya mashi a jakar, ta ɗauki sport jersey ta sanya mashi, gani take kamar kayan sunyi mashi kaɗan, sai da ta kara mashi wasu akai, ta curo paper da pen ta rubuta mashi "I'm back, my man. I hope I find you safe. nayi kewarka, ga tsarabarka nan, Take care of yourself for me." acikin shopping bag din ta sanya mashi letter din, sam ta manta bai iya karatu ba, ita a tunaninta ya fara iyawa tunda daddynta ya fada mata chief ya fara koya ma shi, mikewa tayi da sauri ta fito ta nufi upstairs, a bakin kofar dakin shi ta ajiye mashi kayan, ta sanya hannu tayi knocking kafin ya fito ta watsa da gudu ta sauko down ta dawo bakin room door din su ta tsaya tana leken shi. Lokacin daya fito baiga kowa ba, har zai juya yai tuntu6e da shopping bag din da sauri ya dubi jakar, yayi mamakin ganin ta baisan wanene ya ajiye mashi ba. Zukunnawa yayi tare da buɗe jakar, ya fara zaro kayan yana kallon su, akan idon shi letter din ta fado ƙasa da sauri ya dauka ya buɗe yana kallon rubutun shiru yayi jim ya rasa gane me aka rubuta bawan Allah, Ya shafe mintuna yana harhada haruffan amma ya gaza karantawa, handwritting ɗin ta ya haɗu saika rantse da Allah babban mutunne Yayi rubutun saboda ƙwarewarta. Unaisah dake a la6e tana leƙen shi fuskarta ɗauke da murmushi sai dadi take ji amma data fahimci ya kasa karantawa sai taji wani iri aranta, daga inda take ta yi mashi gyaran murya kafin ya ɗago da ido ya kalleta tayi saurin juya mashi baya ta ruke qugu da hannu, ta yi mashi hakanne don yasan cewa itace ta kawo mashi kayan. Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, nutsuwa yayi yana kallon bayanta har saida ta shige daki kafin ya tattara kayan ya maida a cikin jakar ya mike da sauri ya shiga dakin shi bayan ya daura jakar kan gado, ya ɗauko paper da pen ya daura kan bedside drawer ya fara kokarin yin rubuta, bawan Allah idan yana so ya rubuta Ni sai ya fara daga Na ni no nu ne kafin ya canko wadda ta dace ya sanya.. Dakyar ya samu ya rubuta mata letter ɗin ya mike da sauri ya fito ya sauko down Yaje bakin kofar dakinsu Ya ajiye mata tare da yin knocking ɗin kofar, kafin ta fito yayi saurin komawa upstairs Ya tsaya yana jiran ganin ta Tana fitowa taci karo da letter din daya ajiye mata, zukunnawa tayi tare da daukar takardar ta buɗe ta... "Welkam bak hom, i miss yu so much, tanku" hawaye ne suka ciko idanunta wani irin tausayinshi ne Ya kamata da sauri ta dago ta kalle shi hannu ya ɗaga mata, a hankali itama ta ɗaga mashi hannu sai yanzu ta gane ashe shine ya tura mata text message awayarta lokacin da tana a hospital, hartana dariya tayi zaton karamin yarone ya dauki wayar babarsa.. Juyawa tayi da sauri ta koma cikin dakin su, ta dauki wayarta dake kan mirror, ta kwanta kan gado ta fara scrolling ta shiga messages dinta, murmushi tasaki tana kara karanta sakon shi bata san sa'adda kuka ya kubce mata ba...cusa kanta tayi jikin pillow tay kuka mai isarta kafin ta share hawayenta ta dago, ta kalli screen din wayar, yanke shawarar kiran shi video call tay, da number din daya tura mata sako ta danna mashi call yana shiga yai picking"Turn on your Wi-Fi, I'll call you on a video call." ta faɗa tare da katse kiran bata jira amsar shi ba, fatanta Allah yasa ya iya kunna wi-fi din, ta kunna na wayarta har zata danna mashi video call, Unexpectedly, taga kiran shi ya shigo via facetime. Picking tay tare da kanga wayar saitin fuskarta ta ƙura ido tana kallon doguwar fuskar shi abun da ya ɗaure mata kai ya lumshe idanun shi, da alama akwance yake kan gadon shi ya tada kai saman pillow kamar yadda tayi. Ta ɗan yi mamakin canzawarshi, kamar akwai rama ta wurin kwarin idanun shi fatar wurin tayi jajir ga zira ziran eye lashes dinshi da suka ƙawata kewayen idanun, la66an shi sun bushe ƙamas launinsu ya ƙara ciza wa, ga wani haske da yayi skin dinshi har salki take, gaba ɗaya ta shagala da kallon shi har saida taga ya fara kokarin buɗe idanun shi kafin tai saurin kau da nata gefe, kallo ɗaya da yayi mata saida yaji wani irin yanayi atare da shi, ta canza mishi ta ƙara yi ma shi kyau kamar yaune rana ta farko daya fara ganin ta haka ya nutsu yana kallon soft pink lips dinta, kafin ya maida duban shi ga grey eyes dinta, taƙi yarda su haɗa ido sai dai ta wutsiyar idonta take satar kallon sexy face dinsa ta screen din wayar.. "Tell me, have you forgotten me? Are you still angry with me? Or have you stopped loving me?" Sanyayyar muryar shi ce ta ratsa kunnanta, har saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ta furta"bana fushi da kaina, ban manta da kai ba, kana araina, kana tunanin daina sonka abune mai sauƙi agare ni"? Lumshe idanun shi yayi, yana jin nutsuwa tana shigar shi, kalamanta sun sanyaya zuciyar shi. "If you're even thinking about that, you should stop" ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"kamar yadda nayi maki alkawari bazan ta6a karyawa ba, amma inaso mu dinga yin magana ko da ta waya ne pls give me permission to call you every day" ya faɗa yana kallon fuskarta yadda kasan suna aguri ɗaya. "Okay, I give you permission, but you will call me only two times, and you can send me a message anytime, idan na gani I will reply to you immediately. After that, I don't want anyone to know what is going on between me and you, in har muka haɗu a falo ko hanya ta haɗamu indai ina atare da wani zan iya yi maka magana kaima haka..." tana magana idonta na kallon gefe ɗaya kwata kwata bata son su haɗa ido saboda yanayin da yake jefata kuma idon tana kallon shi, sai zuciyarta ta dinga tariyo mata abunda ya faru adaren ranar daya shugo dakin su. Shiru taji bai amsa mata ba, sai ma motsin buɗe leda da taji a kunnanta, aranta ta ayyana ko meyake ki? ko dai ya ajiye wayar ne? A hankali ta ɗan saci kallon screen din karaf idanunta suna shiga cikin nashi lokaci ɗaya taji faɗuwar gaba. Hankalinshi kwance yake kallon ta, Yana cin chocolate din data kawo mashi, yanayin yadda yake moving lips dinsa, sai taji wani iri zuciya da sake sake sai taga kamar da gangan yake don ya rikitar da ita cos he looks so sexy a yadda yake shan chocolate ɗin har wani lumshe idanun shi yakeyi alamar dadin yana kai mashi karo, sam takasa janye idanunta daga kallon lips dinsa, hatta yanayin fitar numfashin ta saida ya canza lokaci ɗaya ta nemi zaucewa da sauri ta kifa wayar jikin pillow tayi shiru tana jin wani irin abu mara misaltuwa ta rasa gane me yasa take jin hakan? chocolate kawai ya bude yana sha duk ta rasa sukununta har wani shauƙi take ji a jikin ta. "Hello, Angel? Are you there? Muryarshi ce ta fargar da ita Numfasawa tayi har ta fara motsa lips dinta zata bashi amsa muryar daddynta ta katse ta"daughter! Kina ina? Shi ne kin dawo ko ki neme ni ko"? Cutting din kiran tay, ba don ta gaji da kallon shi ba, ta miƙe da sauri ta sauko daga kan gadon, ta nufi door room din ta buɗe, yana atsaye bakin kofar fuskarshi dauke da murmushi yake kallonta"welcome back, my Angel" hugging dinshi tayi, fuskarta dauke da murmushi ta zagayo da hannayenta kan bayanshi"daddy ina wuni ya aiki, Ya aunty danejo na, wlh nayi missing dinka, kana araina tunda na dawo nake ta dakon zuwan ka.." dago da kanta yai daga kirjin shi ya dubi fuskarta dakyau"nima nayi kewarki, ay na yi zaton zaki kira ko awaya ne ki fadamin kin dawo gida, ni gaskiya ban yarda kinyi missing dina ba, kina can kin samu uwa kin manta dani ko"! Ya faɗa da zolaya Girgiza kai tay"a'a daddy, ba haka bane, ay bani da tamkarka a duniyar nan, mu shiga ciki kaga kayan da chief ya siya min..." Taja hannun shi suka shiga dakin, cike da zumudi ta dauko shopping bags din ta buɗe ta fara curo kayan daya bayan daya tana nuna mashi Waro ido ya ɗanyi alamar mamaki yace"Eyeh gayu mutanan Allah, duk ke kadai wannan? Amma naji dadi ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi Allah Ya ƙara mashi buɗi da daukaka" Fuskarta dauke da fara'a tace"ameen daddyna, wlh nima nayi mamakin kayan daya siya min amma fa bani kadai ba hada su Batool yace in daukarmawa inyi masu tsara..". "Kin nuna ma auntynku" "Eh, harma ta dibar mana chocolates da cookies sauran kayan tace mu ajiyesu adaki kafin lokacin da zata raba mana" Murmushi yayi har cikin ranshi yaji dadin jin chief ne ya je da ita mall da alama burin shi Ya kusa cika na ganin Ya kulla alaka mai karfi atsakanin su. "Daddy, na jima banga mutun mai mutunci irin chief ba, yana da saukin kai, ga shi wayayye ni dama can inason mutum irin haka..." ta saki baki tana surutu cikin rashin sani ta zazzago bras daga cikin shopping bag din dake ruke a hannun ta. Waro ido taj yai cike da zolaya ya furta"Subhanallah, daughter wannan fa na wanene"? da sauri ta dube su, wata irin kunyace ta kamata, da sauri ta sunkuyar da kanta kasa sam ta kasa kawar da su" Taj dake kallonta dariya ce kumshe abakin shi bai ta6a tsammanin Angel tana da kunya har haka ba. Tunawa yai lokacin da tana karama har fadi mashi take dan Allah ya siya mata ƴar bra irin na aunty anila idan ta girma boobies dinta suka fito itama ta dinga sakawa, ranar yaci dariyar maganarta, komi tagani anila tayi itama sai tace zata yi idan ta girma, anila itace silar da Angel ta fara kwadayin tayi aure ay gani take babu rayuwar da tafi dadi irin ta gidan aure. Tasha fada ma taj itafa house wife takeso ta zama, kuma bazata auri talaka ba, saboda ita matar manya ce, hamshakin mai kudi zata aura, inda zata sakata ta wataya bata aikin komai sai dai yan aiki suyi mata ita tana daga kwance, shiyasa taj yakeso yacika mata burinta, bawai don kwadayin abun duniya ba sai don baya son yakaita inda zata sha wahala, saboda ta cancanci tayi rayuwar farin ciki, ta auri miji nagari nagartacce. Jin yayi shiru bai ƙara tanka mata bane yasa ta dago da ido ta saci kallon shi, hankalin shi kwata kwata baya akanta, yayi zurfi cikin tunanin shi, da sauri ta kwashe bras din ta tura a cikin shogging bag din, kafin tace"daddy! " kallon ta yai"meye faru naga kamar kana tunanin wani abu" murmushi yayi mata. "Ke nake tunani" farfari tay mashi da ido"me kake tunani akaina" calmly ya furta"inaso ki faɗamin gaskiya kina son aure har yanzu"? Rass taji gabanta ya faɗi da sauri ta cusa kanta tsakankanin gwiwowinta, yar dariya yayi"wai ni waya koya maki jin kunya? Kamar ba Angel dina ba, ko dai anyi min musayarki ne"? Muryarta kasa kasa tace"a'a dadi ni din ce dai daka sani, Angel dinka," "Okey, fadamun amsar tambayar da nayi maki'! Miƙewa tayi da gudu ta shige toilet, taja kofa ta datse, murmushi yayi yana kallon kofar. Daga cikin toilet din yajiyo muryarta"daddy zan baka amsa ba yanzu ba, ka ɗibar ma aunty danejo tsarabar da nayi, kaima ka dauka..." dariya yayi haɗi da girgiza kan shi yana kallon kofar toilet din. Chocoletes da cookies ya dibar masu a dakin ya samu plastic bag, ya sanya a ciki, kafin ya mike yana fadin"ni zan wuce toh, ba zaki fito muyi sallama ba" Dakyar ya samu ta fito daga dakin, tana faman noƙe kai taje gaban shi ta tsaya"na manta ban tambayeki ba, ya mai jikin? "Taji sauƙi sosai, wlh kamar kar in barta, ina kaunarta sosai, lokacin ma da zan tafi, saida dr jazz ya bani sleeping pill na bata tasha saboda bazata bari atafi dani ba.." muryarta na rawa ta kare maganar kamar zata sanya mashi kuka"daddy dan Allah zuwa jibi ka kaini gidansu daga nan sai muje gidan su aunty anila inason inga babynta.." tun da tafara magana ya kafe ta ido yana kallonta, mood din fuskarsa ya canza sosai, tsantsar tausayin su ne ya kama shi, dama yasan dole su kaunaci juna, jini ɗaya ba wasa ba, tsakanin uwa da ɗa sai Allah. Cikin sanyin murya yace"ki kwantar da hankalinki, kada ki sanya damuwa aranki, zan yi kokarin kaiki gurin ta, amma ba yanzu ba, ki ƙara hakuri, ita kuma auntyn naki zan baki contact dinta, ki kira ta waya ku gaisa sai kiyi mata maganar junaid din nasan zata kawo maki shi" Nagode daddy,"da murna tay maganar, Taje ta dauko wayar ta bashi ya sanya mata layin aunty Anilah Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE KURKUKUN KADDARA Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 39 Complete by Boss Bature September 03, 2024 KURKUKUN KADDARA Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 38 Complete by Boss Bature September 02, 2024 KURKUKUN KADDARA Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 37 Complete by Boss Bature August 31, 2024 KURKUKUN KADDARA Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 36 complete August 31, 2024 KURKUKUN KADDARA Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 35 Complete August 31, 2024 KURKUKUN KADDARA Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 34 Complete August 30, 2024 POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION OPINION Opinion: A Beacon of Integrity and Leadership in Public Service by Novels Elite Admin August 21, 2024 YOU CAN ONLY GIVE WHAT YOU HAVE GOT June 12, 2024 Corruption:Legal forum Calls to investigate EFCC Boss over selective treatment November 17, 2022 FACEBOOK COMMENTS Anonymous Pls Ina naiman Hadamu mu Akayi Anonymous Matar so please Anonymous Don Girman Allah insamiki number na zaki turamini ... CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 40 Complete September 03, 2024 Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 39 Complete by Boss Bature September 03, 2024 Kuskure Ɗaya page 9 Complete by Jiddah S Mapi September 02, 2024 ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions[14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 41 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 04, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe Shigowa dakin hajjaty yayi bakin shi dauke da sallama, tsayawa yayi ganin bata a cikin ɗakin har ya juya zai fita ya jiyo saukar ruwa a toilet, ajiyar zuciya ya ɗan sauke ya nufi gefen gadon ta har ya yunkura zai zauna idanunsa suka hango mashi plastic bottles dake ajiye kan mirror drawer, miƙewa yayi tare da nifar mirror din ya tsaya yana kallon robobin kamar na ruwa haka suke, rubutun larabci ya gani a jikin su baisan me aka rubuta ba saboda baya jin harshen, zuciyar shi bata kwanta da su ba, ɗaya ya ɗauka ya buɗe murfin ta yakai hancin shi zai shinshina da sauri ya kawar da shi gefe ya yamutsa fuska haɗi da ta6e baki yana ɗan jan numfashi.. Motsin buɗe kofar toilet ne yaja hankalin shi ga kallon ta, fitowa tayi daga ciki, tayi ɗaurin gaba da towel, ta naɗe black hair din ta da wani towel ɗin Suna haɗa ido da juna ta sakar mashi murmushi. "mere pyaar, sai yanzu zan sanyaka a idanuna? Ina ka shiga ne ka barni da kewarka"? Lumshe idanun shi yayi a hankali ya buɗe su yana bin ta da kallo mai cike da jin shaukin ta. Ta baya tayi hugging din shi ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa, ta ɗaura hannayenta kan chest din shi. "Wifey, i'm sorry wani kira akai min mai mahimmanci shiyasa ban samu damar zuwa gurin ki ba, amma kina araina" kwanto da kanta tayi kan shoulder din shi, nuna mata robar hannun shi yayi"menene wannan? Fuskarta dauke da murmushi tace"maganin da sheikh imam Ya bada ne don adinga ba marwa tana sha, yace in sha Allah zataji sauƙi nan bada jimawa ba..." ta fada tare da manna mashi kiss kan cheek dinsa, gogan ya haɗe fuska sam bata kula da yanayin shi ba, taci gaba da cewa" "Nayi ma sheikh imam alkawarin zancigaba da kula da ita, har zuwa lokacin da zata ji sauƙi" ajiye robar yayi tare da janyota ta dawo ta gaban shi Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Meye alakarki da marwa ne"? Fuskar shi adaure yayi mata maganar "Yar uwata ce musulma, kuma tana bukatar taimakonmu saboda mune danginta ayanzu..." bata ƙare maganar ba ya rufe mata baki da yatsan shi Calmy yace "Kingane ni bazan hanaki yin aikin lada ba, kawai bana so kina shisshige mata ne, ke ko kyamarta ba ki ji? kuma baki gudun ta goga maki lalurarta"? Zame hannun shi tayi daga kan bakinta "Haba pravin, meya kawo wannan maganar? Ita ma fa ba ita ta daura ma kanta ba, bayan haka sheikah imam ya fada mana hanyoyin da zamu kare kanmu daga sharrin aljanu...." bata ƙare maganar ba yai saurin janyota kan kirjinshi yakai bakin shi saitin kunnanta, in a low voice ya furta"ni dai hankalina bai kwanta ba, kinsan bana son duk wani abu da zai cutar min dake, pls ki taimaka min ki aje aikin kula da marwa..." yanayin yadda yakeyi mata magana ba karamin kashe mata jiki yayi ba. cike da shagwa6a tace"dan Allah kabarni inyi aikin nan, indai kayi imani da cewa Allah shi yake tsare bawansa, nayi maka alkawarin zan kula da kaina, amincewarka kadai nake bukata..." Badan yaso ba ya amsa mata da toh. ƙara matseta yayi a jikin shi, a hankali ya fara manna mata hot kisses kan wuyanta har ya zuwa kan kirjin ta..tuni ta fara jan numfashi tana lumshe idanunta, daukarta yai gaba ɗaya ya kwantar kan mattress ya zame kayan jikin shi ya rage daga shi sai short, ya fada kanta yaja bargo ya lullu6e su...romancing dinta ya cigaba da yi, gaba ɗaya ya rikitata, tsawon mintuna shabiyar kacal, wani irin kasalallan bacci ya yi awon gaba da hajjaty. Fitowa pravin yayi daga cikin bargon ya sauko daga kan gadon Ya haɗa uban gumi a jikin shi, shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da kallon hajjaty dake bacci...A hankali Ya furta"I'm sorry, zan yi maki laifi, saboda bazan bari kiyi silar tona min asirina ba," ya faɗa tare da juyawa ya nufi robobin maganin ya kwashe su, Ya shige toilet da su, Allah kadai Yasan meya yi masu, jim kaɗan Ya fito da robobin a hannun shi yana faman sakin shu'umun murmushi ya ɗaura su kan mirror. Kafin ya fita daga dakin saida ya fara hawa gadon Ya sumbaci la66anta kafin ya sauko shaf shaf ya maida kayan jikin shi ya juya cikin takun tantirai Ya fuce daga dakin. Fitar shi keda wuya hajjaty ta fara mutsu mutsun farkawa daga bacci, wata irin kasalace ta mamaye jikinta dakyar ta lalla6a ta miƙe ganin babu sutura ajikinta yasa tayi saurin kai hannu ta janyo towel dinta ta lullu6e jikinta, muryarta adisashe ta fara ambaton sunan shi shiru taji bai amsa mata ba alamar baya adakin, lumshe idanu tayi tare da jingina kanta jikin headboard, A hankali take tariyo abunda ya shiga tsakaninta da pravin wani irin shaukin son shi take ji, dai dai da minti ɗaya bata ta6a gajiya da shi ba, saboda soyayyar gaskiyace a tsakaninsu, bata ta6a haɗa son shi da wani ba. Tunawa da marwa yasa tay saurin saukowa daga kan gadon ta shiga toilet, donta tsarkake jikin ta, bayan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta feshe jikinta da turare, ta yafa mayafi akanta, da sauri ta dauki robobin maganin ta tura su cikin ledar da aka kawo su, ta fito ta nufi dakin marwa, da sallama ta shiga dakin fuskarta dauke da murmushi take kallon marwa dake akwance kan mattress ta rufe idanunta. Zama hajjaty tay gefen katifar ta ajiye jakar agaban marwa. "Sannu marwa ya jikin naki? a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur ta dubi hajjaty, dakyar ta kakaro murmushi tana kallon ta tayi kyau abunta, ɗazu da safe hajjaty ta taimaka mata tay wanka har kaya ta canza yar doguwar rigace a jikin ta, jikinta sai kamshin turaren da hajjaty ta fesa mata yakeyi. "Sheikh imam ya aiko da maganin ki," ta fada tare da ruƙo kafadun marwa ta taimaka mata ta zauna tare da jingina bayanta jikin pillow "Kina jin yunwa" girgiza mata kai tay alamar a'a, "Dama nasan ba lallai kiji yunwa ba, saboda dazu kin cika cikin ki da abinci" ta fada yayin da take bude murfin robar farko mai ɗauke da sunan zam zam.. "Kiyi bismilla ki sha, kur6a ɗaya zakiyi" ɗaga mata kai tay alamar toh Lokacin data kurbi maganin kiris ya rage ta amayar da shi saboda zaurin da ya buso hancin ta. Lura da yanayin ta yasa hajjaty cewa"am sorry halan maganin bai da dadi? Ɗaga mata kai tay alamar eh Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Eyyah sai kin daure,kinsan yadda magungunan gargajiya suke akwai ɗaci, wani zakiji shi da bauri wani kuma tsami" ta faɗa tana yamutsa fuska, bayan ta kammala bata magungunan, tace"wannan ɗayan daya rage, a cikin ruwan wanka za'a ɗiga maki shi, zuwa anjima in sha Allah zan sake dawowa, sannan pls kada ki manta kiyi evening azhkar" tun da ta fara magana marwa keta kallonta so take ta faɗa mata wani abu tarasa taya zatai mata magana daga ta yunkuro zatai magana sai ta kasa saboda muryarta babu dadin ji Hajjaty sam bata lura da hakan ba, bayan ta maida robobin maganin a cikin ledar, ta ajiye gefen katifar marwa"ni zan tafi, da anjima zan shigo kawo maki dinner" ta fada tare da sakar mata murmushi ta mike ta tafara tafiya har ta kusa fita kunnuwanta suka jiyo mata marwa dake ta kokarin yi mata magana. Juyowa tay tare da kallonta da alamun rudani akan fuskarta, da hannu take yi mata alama, hajjaty ta kasa gane me taje nufi, ita dai taga marwa sai nuna mata dunkulallun yatsun hannunta takeyi "Marwa akwai wani abu da kike bukata ne"? Ɗaga mata kai tay alamar eh, komawa tayi gaban katifar ta zukunna tana kallonta, ruwan hawaye tagani kwance akan fuskarta"pls ki daina zubda hawayenki dan Allah, ki fadamun abunda kike so zanyi maki" da hannu marwa ta dinga goga floor tana kokarin kwatanta mata abunda take so ta dauko mata sai dai takasa fahimtarta Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Marwa kiyi hakuri, wallahi bansan me kike nufi ba" buɗe baki marwa tayi ta fara mata gura gura.. tsoron maganarta hajjaty take ji nan take ta tuna da maganar pravin dayace mata ita bata tsoron marwa ta goga mata lalurarta, tuna wannan yasa tay saurin mikewa gabanta na faduwa ta fara ambaton sunan Allah acikin zuciyarta. Cikin rawar murya tace"marwa sai anjima zan dawo in sha Allah" da sauri ta fuce daga dakin, marwa ta kifa kanta cikin pillow ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tamkar ranta zai fita 💔 ________________________________✍️ *(AFTER 3 DAYS BAYAN KWANA UKU)* A kalla yau kwana uku kenan da zuwansu Anila gidan hajiya adama, har ila yau ba su ƙara jin duriyar Ana ba, babu ita babu labarin ta, abun ya ɗaga hankulan mutanan gidan sun damu da rashin ta, kusan kullum sai anila da mahboob sun kira layinta a switched off suke samun shi, Lamarin ya ɗaure masu kai, basu da wata hanya da zasu Iya tuntu6ar wani nata, saboda ba su ta6a kar6ar layin yan uwanta dake a joss ba, abu biyu ya haɗe ma Aneelerh ga damuwar halin da junaid yake a ciki, kwata kwata baya sakin jiki da kowa ga ƙiwuya bai yarda da kowa na gidan ita kadai yake manne mawa, kuma har yau yaƙi buɗe baki ya tanka mata ya zama kamar kurma sai dai yabi ta da ido ko in yana jin yunwa sometimes yana bude baki ya furta kalmar yunwa, wani abu daya fi daure mata kai idan dare yayi zasuyi bacci ta rungume shi a jikin ta, sai ya dinga firgita yana sambatu kwata kwata bata gane me yake cewa. Har su mami ta sanar ma abunda yakeyi suka ce taci gaba dayi mashi addu'a in sha Allah zaiji sauki, ita dai hankalinta bai kwanta da yanayin shi ba, ranta yana bata wani abu ba dai dai ba agidan dole akwai wani abu daya faru wanda yayi silar guduwar Anah da kuma rikicewar baby junaid! Kwana biyu da baije school ba sai ga kira daga class master din su junaid, bayan sun gaisa da anila ta ta tambayeta meyasa kwana biyu junaid baizo school ba, tace mata baida lafiya ne amma idan yaji sauki zai cigaba da zuwa Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Cikin kwana uku anila duk ta fita hayyacinta har faɗawa tayi saboda damuwar rashin Ana da kuma halin da baby junaid yake a ciki, abie har kiranta yayi shi da uncle dan iya da su ummu suka taru akanta suka yi mata nasiha cikin lallami da lallashi donta kwantar da hankali saboda kowa ya fahimci bata acikin nutsuwarta, ko abinci sai zahra tayi dakyar take samu ta ci ta zama abun ban tausayi daga ita har junaid din harma kwara ita akan shi saboda ya takura kan shi ya kuma takura mata ya hanata sukuni ko toilet zata shiga sai ya sanya rigima zai bita, dakyar take samu ta lalla6a shi da wayarta don yayi game kafin ta samu ya kyale ta, idan salla zatayi sai dai ta goya shi abayanta, har yau babu abunda ya canza, yanzu girkin gidan ya dawo hannun mami da ummi saboda rashin Ana, zahra kuma ba azaune take ba, tana zuwa aiki, ita kuma anila kota nemi su bata ta tayasu aiki sai suce taje taji da junaid zasu kula da komai...💔 ________________________✍️ Shin Ya labarin Benazir? Ay tun ranar da suka dawo gida ta kasa ta tsare tana jiran taj da Angel su dawo daga kasuwa, shiru shiru taji basu dawo ba har marece ya nutsa hankali atashe tace ma hajiya layla ta kira mata layin taj awaya taji meya hana su dawo! Hajiya layla tana yan kame kame tace mata ta manta bata da layin taj, kuma dayazo asibitin daukar Angel bata kar6a ba, sai dai ko dr shureim watakil shi yana da layin shi, ko da ta yi ma dr shureim magana akan ya kira mata taj cikin rashin kwanciyar hankali ya kira wrong number da gangan saboda ta tsare shi da ido tana jiran shi ya kira mata mijin ta, a dole yayi pretending ya ci gaba da magana yana fadin pls taj marece yayi ga benazir tana jiran ku, dan Allah ku dawo hakanan okey toh sai anijima Allah ya dawo daku lafiya, bayan ya katse kiran yace mata tayi hakuri ta kara jira suna akan hanya, baiwar Allah jiki asanyaye ta zauna kan sofa tana jiran dawowarsu, hankalinta kwata kwata ba a kwance yake ba, gani take kamar bazata sake ganin angel din ta ba... Abu kamar wasa har dare yayi babu taj ba angel, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, lokacin da zasu yi dinner bayan su tani sun kammala shirya masu abinci a dining hajiya layla tace tazo su ci abinci, tace mata bazata iya ci ba, in har taj bai kawomata Angel din ta ba hankulansu ba karamin tashi yayi ba, gaba ɗaya suka taru akanta suka fara lallashinta suna bata baki duk don su samu su taci abincin amma taƙiya, babu wanda baiji tausayinta ba musamman da karfe goma sha ɗaya ta buga na dare, a lokacin ta gama gane karya sukeyi mata, zuciyarta ta karaya a karshe ta fashe da kuka tace su daina boye mata gaskiya, kawai su fada mata ina yarta Angel? Saboda tana ji aranta ba taj bane ya dauke ta, babu wani siyayyar da suka je yi mata duk plan ne .." gaba daya aka rasa wanda zai faɗa mata gaskiya saboda fargaban halin da zata shiga, ranta yayi mugun 6aci zuciyarta ta hasala ganin sun zuba mata ido an rasa me magana a cikin su, idanunta suka kaɗa jawur, zafafan hawaye suka wanke fuskarta, tsabar fusata jikinta har kerma yakeyi tana faman jan numfashi tace"mami! Ya shureim, aunty sarah ku fadamin gaskiya ina babyna take? Wanene Yake son rabani da ita? Yarinyar nan ƴata ce fa halak malak, akan me zaku yi min karyar taj ya dauke ta sunje shopping mall? Meyasa har yanzu basu dawo ba? Kusan karfe goma sha ɗaya na dare, wlh idan har baku dawo min da babyna ba, komai zai iya faruwa..." dakyar ta kare maganar tare da sanya tafukan hannayenta ta dafe kanta kamar yadda take yi idan zatay pretending ta fara yi masu kuka na fitar hayyaci kamar zata rotsa dodon kunnuwansu, gaba ɗaya tabi ta furgita su, zeenatu tsabar tsoro daki ta shige ta kulle dama tunda Benazir din ta dawo ko gaisuwa bata hada su ba, bayan ta shiga dakinne ta fara tariyo fuskar Unaisah yarinyar data kira sunanta da Unaizah, har cikin aranta tana son ta kara haduwa da ita kuma tana son tasan wacece Unaizar su data mutu? ya akai komai nasu yazo iri ɗaya? Tabbas tana son tasan komai dangane da ita bayan haka tana son su kulla kawance da Unaisah saboda ta kwanta mata aranta tun a kallo na farko da idanunsu suka shiga cikin na juna. Daga cikin falo ta dinga jiyo sautin muryoyinsu Hajiya layla suna ta kokarin lallashin Benazir, hada alhaji ubaid a lokaci baijima da shigowa gidan ba, gaba daya mutanan gidan suka taru akanta, in ka cire Alhaji musa saboda baya nan baisan budurin da sukeyi ba Adaren ranar dakyar suka samu bacci ya ɗauketa, jikinta hada zazza6i. har ila yau tana akwance ba lafiya, saboda rashin Angel dinta, tayi kukan harta gaji, kowa na gidan tausayinta yake ji, yau kwana uku kacal da rabuwarsu da unaisah tana jinyar zuciyarta bata son cin abinci ko wanka ta dainayi ta zama kamar mahaukaciya, kusan kullum sai hajiya layla ta matsa ma shureim akan ya kira anila yayi mata magana ta fada masu ina ne gidan iyayen yarinyar, dr shureim yace tayi su yi hakuri bazai iya ba, bayaso ya takura ma anila bayan haka babu amfanin suje gidan iyayen yarinyar tun da ko sunje yarinyar fa ba yar benazir bace ganinta bazai amfani benazir da komai ba saima ya ƙara ɗaga mata hankali tunda ba basu ita za'ae ba, adole hajiya layla ta hakura da yi mashi maganar Azeezaty _________________________✍️ Idan muka koma bangaren Marwa, jikinta ya ƙara tsauri babu wani cigaba a lafiyarta, yatsun hannunta sai ƙara matsewa sukeyi ga wasu kananun kuraje da suka fara feso mata akan fuskarta, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, wani lokaci idan hannunta suka fara mata radadi kamar zata zauce, duk da halin da take aciki kokari take ta fallasa asirin wanda yai silar ɗaura mata ciwon, sau uku hajjaty ke xuwa dubata kuma tana kokarin kiyaye duk wasu sharudda nayin amfani da maganin da sheikh imam ya bata sai dai takasa gane an canza ruwan maganin rashin sani ya fi dare duhu batasan tana ƙara wa marwa ciwon ta ba takasa lura da yanayin ta, gashi duk in ta shigo daki sai marwa tayi mata alama da hannu har yau takasa fahintar me take nufi, idan tayi yunkuri takura kanta akan tay magana wani irin radadi take ji a makoshin badan taso ba ta hakura, wani lokaci idan tayi ma hajjaty alama da hannu ta kasa ganewa saita buga kanta jikin pillow tayi ta kuka kamar ranta zai fita, dakyar hajjaty take samu ta lallasheta har ta shawo kanta. Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. A cikin yan kwanakin nan hajiya saratu bata bari hanya ta haɗata da hajjaty saboda tsoranta da take ji, hajjaty harta fara lura da ita, ranar da ta shiga kaima baba obie abinci hajiya saratu tana adakin, tun da taji sallamar hajjaty da sauri ta mike ko sallama batayi mashi ba ta fuce daga dakin, tun daga nan hajjaty ta fara lura da ita, abun ya ɗaga hankalin ta, tarasa gane laifin me tayi mata? Duk da dama tasan ba sonta take yi ba akwai tsanarta a zuciyarta amma yanzu abun ya karu fiye da lokacin baya Idan muka koma bangarensu twins tun ranar da suka ga iftila'in daya faɗawa marwa basu ƙara marmarin komawa gidan ba, saboda kyankyami da kyama suke ji, a hotel suka koma da kwana, daga bisani da hajiya saratu takira zayn awaya ta fara zazzaga mashi masifa akan rashin dawowarsu gida yace mata su fa bazasu dawo ba in har ba an fidda mai aikin nan daga gidan su ba, bata musa masu ba, saima cewa tayi su bata lokaci zatayi magana da baba obie akan a maida marwa garin su indai hakan zai kwantar masu da hankali, sunji dadin maganarta hada yi mata godiya ✊Boss Bature💋: ________________________✍️ A kishingiɗe yake saman lallausan rug din dakin baba obie ya ɗaura head dinsa kan pillow, jikinshi na sanye da jallabiya fara kyal, fragrance dinsa ya haɗe da sanyin A.c din dakin, ba su jima da dawowa daga sallar asuba ba yabiyo baba obie dakin shi...A hankali yake danna phone dinsa Kira ne ya shigo ganin sunan commender james yasa shi picking call din tare da kara wayar a kunne, cikin girmamawa suka gaishe da junansu kafin daga bisani commender james ya sanar da shi sun samu izni daga manyan su, za su shigo Nigeria da shi da sauran sojojin da suka tsinci su Angel a dajin evil forest Chief yace"I'm very happy to hear that, I can't wait to see you" Commender james yace"I'm also very happy, this is the first time I'll be coming to Nigeria because of the children we found in the forest. Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions Our website uses cookies to improve your experience. Learn more Accept ! [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 42 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 05, 2024 Takun Ƙarshe Boss Bature A kishingiɗe yake saman lallausan rug din dakin baba obie ya ɗaura head dinsa kan pillow, jikinshi na sanye da jallabiya fara kyal, fragrance dinsa ya haɗe da sanyin A.c din dakin, ba su jima da dawowa daga sallar asuba ba yabiyo baba obie dakin shi...A hankali yake danna phone dinsa Kira ne ya shigo ganin sunan commender james yasa shi picking call din tare da kara wayar a kunne, cikin girmamawa suka gaishe da junansu kafin daga bisani commender james ya sanar da shi sun samu izni daga manyan su, za su shigo Nigeria da shi da sauran sojojin da suka tsinci su Angel a dajin evil forest Chief yace"I'm very happy to hear that, I can't wait to see you" Commender james yace"I'm also very happy, this is the first time I'll be coming to Nigeria because of the children we found in the forest, naji dadi saboda abun alfahari ni agare ni" sun ɗan jima suna tattaunawa kafin daga bisani su ka yi sallama da juna. Fitowa baba obie yayi daga toilet, jikinshi sanye da jallabiya fara, ya dago da ido ya dubi owais fuskarshi da fara'a yace"jikallena, nabarka zaune kana jira na, uziri ne ya ruƙe ni a ciki" dagowa chief yai tare da kallon shi suka haɗa ido da juna"barka da fitowa," "Yawwa owaisu na, fadamin me kakeson ci insa akawo mana, yau atare zamu yi breakfast.." ya faɗa yayin da yake nufar bedside drawer chief yace"duk abunda kakeson ci nima shi zan ci " Landline din kitchen baba obie ya kira, bayan an daga kiran ya isar da sakon abunda za'a kawo masu na breakfast bayan ya ajiye wayar Ya samu guri kan lallausar rug din ya zauna haɗi da daura kan shi saman laps din chief yadda kasan uba da ɗansa. ya ɗago ya kalli fuskar Owais dake kokarin saita shi da phone camera"me zaka min haka"? "Hoto zan ɗauke ka, naga ka yi min kyau" murmushi baba obie ya sakar mashi"duk kyau na nakai ka"? "Eh mana, mu da mukai gado agurin ka, gaba ɗaya kamanninka muka ɗauko" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Na tsufa owais, yanzu babu wannan kyan da kake faɗin ina da shi" "Kai kake ganin haka, ni tun da na taso rayuwata ban ta6a ganin mutumin daya tsufa da kyan shi irinka ba" ƙayataccen murmushi baba obie ya saki yana kallon fuskar chief, yaji dadin kalaman shi sun faranta ran shi. "Baba, ɗazu kace zamuyi magana, ya fada bayan ya kammala daukar shi hoton. shigowar hajjaty dakin ne ya katse firar su, ta ɗauki wankan material, hannunta ruƙe da tray na kayan breakfast dinsu agabansu ta ajiye tray din cikin girmamawa ta gaishe da su suka amsa mata har ta juya zata fuce daga dakin muryar baba obie ta dakatar da ita. "Ya jikin marwa"? "Da sauƙi baba," "Okey, ubangiji Allah ya bata lafiya" ta amsa mashi da ameen bayan ta fuce daga dakin chief ya dubi baba obie"wacece marwa"? Ba halinsa bane tambayar abunda bai shafe shi ba, just saboda yaji ya ambaci ya jikin ta. "Ɗaya daga cikin masu aikin gidan nan ce, bata da lafiya" iya abunda ya fada masa kenan saboda baison ya ɗaga mashi hankali, kamar yadda su twins sukai hijra saboda kyamar marwa. "Allah ya bata lafiya" ya amsa mashi da ameen Tea pot baba obie ya dauka ya tsiyaya masu shayi a kananun kofuna suka dauka suna sha "Ka tambaye ni dangane da maganar da nace maka inaso muyi ko" ɗaga mashi kai yai alamar eh "Nasan bazaka ji dadi ba, amma kada ka hanani tafiya" janye cup din hannunsa yai daga kan lips dinsa"tafiya zakayi"! Jinjina mashi kai yayi"lagos nakeson zuwa gurin aminina, kasan na daɗe ban ziyarce shi ba, kuma shi yana kokarin zuwa akai akai ya dubani har gida" jinjina kai chief yai"yaushe ne zaka tafi"? "Karshen watan nan, 3 weeks zanyi in dawo" ɗaure fuska chief yayi"har sati uku baba, ina laifin one week" murmushi yayi"dama sai da nayi fargaban fada maka nasan da wuya ka kyale ni, indai bazaka barni ba to saidai muje atare" girgiza kai chief yayi"ba zan iya binka ba, naso muje atare amma ayyuka sunyi min yawa, amma fa bazan bari ka tafi kai kadai ba,"! Yamutsa fuska baba obie yai"to ni da wa zan tafi owais? Kowa yana da aikin yi, bana son in takura masu" Shiru yayi jim kafin yace"zanyi magana da pravin, ya ɗauki hutun aiki Ya bika ku tafi, don gaskiya ni bazan bari ka tafi kai kadai ba" "Haba owais kamar wani karamin yaro, sai kace bakasan wanene kakan naka ba, waɗannan kafafuwan nawa ba inda basu taka ba, har birnin sin sunje, nafa yi yawan duniya fiye da tunaninka, tun ina matashina nake fita kasashen waje ni kadai abuna." Murmushi chief yayi"da da yanzu ba ɗaya ba, ka manyanta sosai ga tsufa, shiyasa nake tattalinka bana son wani abu ya same ka, duk da nasan Allah ke tsare bawansa." kalaman chief sun kara faranta ranshi murmushi yayi yana kallon fuskar shi"anya akwai wanda yakaini dacen jika a duniyar nan"? chief yace"ni yakamata nayi wannan tunanin, cos bana tunanin akwai wanda yayi dacen kaka irina, ina alfahari dakai," dariyar farin ciki baba obie yasaki idan owais na yabon shi dadi yake ji kamar ya zuba ruwa kasa ya sha. "Owais Mu fara cin abincin nan kada ya huce.." Chief ne yayi serving dinsu atsanake suke cin abinci ya lura duk dagowar da zaiyi sai sun haɗa ido da baba obie wani kallon so da kauna yakeyi mashi. "Naga kana kallona, ba zan canza maganata ba, zanyi magana da pravin din atare zaku je nasan zai baka kulawa ta musamman kuma zai dinga sanar dani duk wani motsinka" dariya baba obie yayi"oh ɗan leken asiri zaka hada ni da shi kenan" ɗaga mashi gira chief yayi"bakomai nasan saboda kaunar da kake yi min ne, naji na amince muje atare da shi din" ya fada yayin da yake tura abinci abakin shi. Knocking room door din akay daga waje, baba obie yace shigo ciki" muryar hajiya saratu ce ta katse masu cin abincin nasu, atare suka dago suna kallonta, shugowa tayi jikinta sanye da swiss code lace, idanunta sanye da farin glass, ta aza veil a kafadarta, ta kashe daurin ture kaga tsiya, hannunta na aruke da handbag dinta. Kwata kwata babu annuri akan fuskarta saida taga chief ta ɗan saki fuskarta. "Shalelena barka da safiya, har anyi shirin xuwa office.. " murmushi ta sakar mashi"barka da safiya babana, ina fata ka tashi lafiya" tay maganar tare da samun guri ta zauna tana fuskantar su.. "Lafiyalou auta," "Barka da safiya auntyna, kin tashi lafiya? murmushi tasakar ma chief da fara'a tace"lafiyalou my son, ina fata kaima haka ya aiki"? Yace"Alhamdulillah" "I'm sorry na shiga busy, kwanaki nace zan shiga asibiti in duba patient din nan banje ba, Ya jikin nata? Ya kuma babynta Unaisah ina fata suna lafiya"? cikin kulawa tayi maganar tana duban shi. "She's feeling better, almost 3 days da sallamarta, unaisah tana lafiya" "Masha Allah, naji dadin jin hakan" tun da suka fara magana baba obie ke kallonsu cike da mamakin taya akai suka sasanta tsakaninsu, shi dai yasan tsakanin jikallan nasa da autarsa ba sa jituwa. gaba ɗaya sun fahimci kallon da yakeyi masu, murmushin gefen fuska ya saki har cikin ranshi yaji dadin shiryawarsu"tun yaushe kuka sulhunta tsakaninku bansani ba"? Ya faɗa yana kallon su Murmushin dattako hajiya saratu tayi batare data furta kalma ba, chief ne ya bashi amsa da cewa"me ka gani baba? Nuna su yayi da yatsan shi"ga abunan azahiri, ku fadamin wani ɗan arzikin ne ya hadamin kanku? Ni dai nasan baku jituwa" tattausan murmushi sukayi Hajiya saratu tace"Allah ne ya hada kanmu, dama can shaidan ne ya shiga tsakaninmu amma muna kaunar juna, ko ba haka ba my son" ta faɗa tana kallon shi "Hakane baba, kuma in sha Allah ba za'a kara jin kanmu ba" har cikin ranshi yaji dadin maganarsu, dama baya son sabanin da suke samu atsakaninsu. "Alhamdulillah, naji dadi ubangiji Allah ya cigaba da hada mun kanku, Allah ya kara dankon zumunci atsakaninku, shi kuma shaidanin daya shiga tsakaninku Allah Ya kare mu daga sharrinsa" A tare suka amsa mashi da ameen, kwata kwata baiyi masu maganar mara lafiyan dayaji sun ambata ba, hankalin shi ya karkata akan jituwar da suka samu. Miƙewa chief yayi da sauri baba obie yace"Grandson ina zuwa bamu gama yin breakfast ba"? "I'm sorry, Grandpa. I'll come back later" ya faɗa tare da russinawa ya sumbaci forehead dinshi hajiya saratu dake kallonsu ba karamin burgeta sukayi ba, sabanin da da take jin haushi intaga baba obie da owais suna bama junansu kulawa kamar uba da da, abun yana 6ata mata rai saboda ita aganinta baya son twins saboda ubansu ba jinsinsu bane shiyasa yake nuna wariya tsakaninsu, abun da ta fahimta ayanzu owais yana matukar girmama baba obie biyayya yakeyi mashi sau da kafa dama ita zuciya tana son mai kyautata mata. Tayi zurfi a tunaninta, muryar baba obie ta katseta, firgigit tayi tare da kallon shi, har chief ya fita daga dakin bata lura ba. "Fada min meke damunki? Tun shigowarki na lura da yanayinki kamar bakya jindadi ko"? Gyara zama tayi, kafin ta fara kora mashi jawabi. "Baba akan marwa ne! Naga ciwon nata yayi tsauri shine nace me zai hana amaida ita garinsu gaban iyayenta? Ita kanta zataso ta kasance a karkashin kulawarsu hankalinta sai yafi kwanciya, ba kamar nan ba, ba dangi iya bana baba, kuma kaga ciwon nan nata bana lafiya bane, zata iya goga ma wani...." fuskarta ayamutse tayi maganar, kamar irin ta damu da ita din nan. Shiru baba obie yayi jim kafin yace"Auta, kin taba zuwa duba lafiyarta ne"? ɗaure fuska tayi Murmushi yai"nayi mamakin jin maganarki, inace tin ranar farkon da ta fara lalurar baki kara leƙawa ba, aranar ma guduwa kikayi daga dakin ko"? Ya faɗa da zolaya, sunnar da kanta kasa tayi batare da tace komai ba. "Meyasa zaki ce amaida marwa garinsu? Ko dan saboda lalurarta? Da can da take mana hidima bamu guje ta ba sai yanzu da Allah ya jarabce ta? Munyi mata adalci kuwa? Yamutsa fuska tayi"baba ka fahimce ni, nasani ba ita ta daura ma kanta ba, babu wanda yafi karfin Allah ya jarabce shi, amma ni dai aduba mana, saboda lalurarta su twins suka daina kwana gida, kasan su da kyankyami kuma abune da basu saba gani ba, shiyasa duk suka firgice, ni kaina hankalina ba akwance yake ba, wlh dakyar nake iya bacci agidan nan gani nake kamar nima abun zai shafe ni..." da mamaki baba obie ke kallonta, ta haɗe rai ba annuri akan fuskarta, duk zaman nan da ake baisan cewa su twins sun bar gidan ba sai yanzu da yaji a bakinta ay da tuni yasa an dawo da su. "Indai akansu twins ne zansa su dawo gida, amma marwa bazata koma gurin iyayenta ba, har sai ta samu lafiya, saboda anan ta samu lalurar, kuma anan zata samu warakarta in sha Allah, Ni ba zan bari mutuncina ya zube a idon jama'a ba, yarinya da lafiyarta ta fara aiki agidan nan sai kuma in maida ma iyayenta don amfaninta ya kare uhyum? Kiyi tunani mana, su kansu iyayenta ba za su ji dadi ba, su ga mun maida masu yarinyar su da nakasa a jikin ta.. " Ran hajiya saratu ya 6aci muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"baba ban taba neman abu agurinka kaki yi min ba, sai yau saboda kawai na nuna bana son zaman marwa agidan nan! Yakamta ka duba lamarin nan baba fisabilillahi saboda ita su twins sun kasa zama gidan nan, nima na rasa kwanciyar hankali, baba kafison farin cikin marwa akan namu kenan..." yunkurawa tayi zata miƙe da sauri ya dakatar ta ita"saratu koma ki zauna" zama tayi fuskarta ba fara'a... Bottle water ya dauka me sanyi ya tsiyaya mata ruwa a cup ya mika mata, tana faman haɗe rai ta kar6a ta kurbi ruwan sau uku kafin ta ajiye tana kallon shi. Yayi shiru yana nazarin maganar ta, arayuwarshi baya son bacin ran ya'yan shi, sannan baya son duk wani abu da zai haifar da rashin kwanciyar hankali atsakaninsu, sai dai bayajin zai iya mayar da marwa garinsu ahaka batare da taji sauki ba, yanajin tausayin ta, bayan haka bazaiso mutuncin shi ya zube agurin iyayenta ba. "Baba nasan me kake tunani, indai akan iyayenta ne, wlh daga mun basu kudi zasu ja baki suyi shiru, kaga sai suci gaba da yin jinyarta, ni nayi alkwarin zan dauki nauyin duk wani abu da za'a kashe gurin nema mata lafiya, ni kawai gidan ke banaso ta zauna" gauran numfashi yaja kafin ya dubeta"auta" tace"naam baba" "Kada ki makara, ki tashi ki tafi aiki, zanyi tunani, in sha Allah idan na yanke shawara zan sanar dake" amsa mashi tayi da toh, kafin ta mike tayi mashi sallama ta fuce daga dakin. __________________________________✍️ Lokaci ɗaya Zuciyarta ta fara bugawa da matsanancin ƙarfi tamkar ana buga ganga, numfashinta ya fara fita cikin sauri, yayin da kirjinta ke harbawa yana sama da ƙasa da kokarin jawo iska a cikin hunhunta, wani irin gumine ya fara tsasstsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, zufa ta soma gangarowa ta cikin nannaɗaɗdiyar sumar kanta tamkar yayyafin ruwan sama jikinta ne ya fara kakkarwa, Yatsun kafafunta dana hannunta suka kama kerma, idanunta suna arufe gam ta matsesu, fatar kwarin idanunta sai kerma take sakamakon kwayar idanunta dake jujjuyawa, kokari take ta buɗe idanunta takasa saboda raunin da sukayi, jikinta tamkar babu jini saboda rashin kuzari, ga wata matsiyaciyar kasala data daskarar da ita daga yunkurin da take yi na son farkawa, Allah kadai Yasan tsawon makonnin da ta dauka bata acikin hayyacin ta sakamakon duguwar sumar da tayi. A kalla ta shafe awa cikin mayuwacin hali tana kokarin ƙarfafa kanta donta samu damar buɗe idanunta, ta ko'ina ba sauƙi, jikinta tamkar an daddaure shi da igiyar kaca, sai faman jijjiga jikin takeyi donta samu kwarin gwiwar tada kanta. La66anta dake a bushe ƙamas fatarsu ta faffashe hada busasshan ɗigon jini, da ƙyar ta iya moving dinsu ta furta"GABRIEL" kwata kwata sautin muryarta baya fita, cigaba da ambaton sunan tayi duk da radadin da makoshinta keyi mata mai azabar zafi, meyasa ta ambaci sunanshi? A karo na farko data dawo hayyacinta? Saboda shi ne aranta. Lokaci ɗaya ba zato ba tsammani kwatsam tayi wani yunkuri da iya karfin ta na karshe ta daddage ta banbare kanta daga jikin abunda take a kwance tayi wata irin zabura ta miƙe zaune tana faman jan numfashi, sannu A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhune bakikkirin ya mamaye ganinta, bata ganin komai tamkar ta makance, batasan a ina take ba? Meya faruwa da ita? ta manta komai, kamar tayi loosing memory din ta, tayi matuƙar rudewa ta rikirkice tunaninta ya gushe, daddafe kanta tayi da tafukan hannayenta cikin rawar murya ta furta"A ina nake? wa ya kawo ni nan? Meya faru dani? Babu mai jina ne? Kuyi min magana bana ganin komai, ko dai na makance ne...." sautin muryarta baya fita dakyau. Kamar ta fasa ihu haka take ji, saboda takasa gane meke faru da ita? A ina take. A lokacin da batay tsammani ba, kwatsam ba zato ba tsammani, wani siririn haske ya kurdado ta saman gurin da take, Waro idanu waje tayi cikin tashin hankali da tsantsar rudani take kallon hasken, A hankali hasken ya fara mamaye ɗakin har saida ya karaɗe cikin sa tamkar da rana. Idanunta suka washe, amatuƙar ruɗe take kallon inda hasken ya fito ashe fitilune na saman ceilling din dakin, da sauri ta dubi inda take a zaune, Metal bed ne (gadon ƙarfe) irin kirar zamanin da na kaka da kakanni, Gadon Yana da girma da tsayi, ga wata lumbutsetsiyar katifa tattausar gaske mai dadin zama hada matassan kai guda biyu, daga saman gadon Yana da rumfa hada labulaye a kewaye da shi, kamar irin gadon sarakuna Gaba ɗaya ta ruɗe ta rasa gane waya kawo ta dakin? Da sauri ta kalli kayan jikinta, farar riga ce shara shara kamar matacin kwakko, komai na jikinta ana gani, rigar tana da dogon hannu, tsayin ta bai wuci Iya gwiwar ta ba. Sumar kanta kamar an kifa mata yayi, ta bushe ba gyara duk gashin ya yamutse, ƙoƙarin saukowa tayi daga kan gadon sai dai ta kasa saboda tsayinsa bata san ya zatay ba, matsawa tayi daga bakin gadon ta leƙa ƙasa cikin sa'a ta ga matakala irin ta bene mai hawa shida, numfashi ta ɗan ja tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ɗaura ramammun kafafuwanta kan matalar farko ta yunwa zata miƙe aikuwa wani irin jiri ya kwashe ta saboda rashin kwarin jikinta gaba ɗaya ta kundumo ƙasa timmm! ba karamin dakuwa tayi ba, amma saboda karfin hali da kwarin gwiwa irin nata ta daddage ta miƙe tana faman fitar da numfashi mai haki kamar wadda tasha uban gudu miƙewa tay tsaye tana kallon katafaren ɗakin mai girman gaske, gado ɗaya ne aciki sai book shelve ma'ajiyar littattafai, da tsoffin akwatinan karfe daga gani tsohuwar ajiya ce, ga wardrobe mai girma ta jikin bango, wurga idanu tayi kan tukwanan kasa da ta gani girke a kasa, ɗaya saman ɗaya an jera su daurin ɗaurin sunyi sauro a jikin bangon da suke, hada kwaryaye rufe da faifan su, hada tukwanan furanni masu ban sha'awa daga gani koma wanene mamallakin ɗakin ma'abocin son kayan laka ne ko kuma makerin su ne. A hankali ta ɗauke idanunta daga kan tukwanan ta bi bangon dakin da kallo, zanunnuka ta gani masu ban sha'awa, a hankali take tafiya tana nufar tsakar dakin tana cigaba da kallon abun mamaki da al'ajabi gami da rudani ita dai batasan waya kawota cikin shi ba! Ta manta komai. tana cikin jujjuya idanu karaf ta hango Madubi zagayayye yana da mariƙi dake ajiye kasa...takawa tayi cike da fargaba ta nufi madubin yayin da zuciyarta ke cigaba da harbawa da karfi da karfi..tsayawa tayi agaban madubin tana kallon fuskarta, ta tsorata da ganin ramar da tayi, kashin wuyanta ya kwambare kamar zai fasa fatarta, ziraran yatsun hannunta ta daura akan wuyan tana shafa kashin kafin ta motsa yatsun a hankali ta shafa fuskarta, manyan idanunta dara dara launin brown ta zare su tana bin kanta da kallo, tana iya hangen dukiyar fulaninta sun rame sun kanjame bayan ada ba haka take ba, tana da kira irin ta karfafan mata masu jini ajika amma yanzu ta rame ta bushe ta faɗa kamar ba ita ba. da zata iya tuna mummunan abunda ya faru da ita har zuciya zata iya hadiya ta mutu saboda tana da fusatacciyar zuciya, idan ta rikice babu mai iya sarrafa ta. ta jima tana kallon kanta a cikin madubin, jiri jiri ta fara gani a idanunta da sauri ta dafe cikinta dake yi mata kukan yunwa ga wani kishin ruwa na fitar shari'a, makoshinta ya bushe ƙamas ko yawun da zata hadiya ta samu relief din kishin babu shi abakinta. juwa ce ta kwashe ta gaba ɗaya jikinta ya rinjayeta ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume.. Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Cikin abunda baifi minti ashirin ba kacal, taji safkar ruwa mai sanyi kan fuskarta, dogon numfashi taja haɗi da sauke ajiyar zuciya sam takasa ta6uka komai, ko yatsan hannunta bata iya motsawa saboda rashin kwarin jiki. cikin mawuyacin hali ta ɗan yi karfin halin buɗe idanunta biji biji take kallon mutumin dake tsaye akanta batasan wanene ba. Cikin disasshiyar murya ta furta"ruwa!ruwa!ruwan, zan sha! Kishi nake ji..." dakyar sautin muryarta ke fita tana tsaka da sambatu taji an kanga mata wani abu kamar bakin gorar ruwa saitin bakin ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokacin da ruwan ya jiƙe makoshinta nan da nan ta fara kwankwaɗarshi makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat...!! "Ki sha A hankali kada ki shaƙe" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar dattijuwar dake mata magana. Sai dai kwata kwata bata fahimtarta, tafi buƙatar ruwan fiye da komai ayanzu kamar rayuwarta ta dogara akan shi. saida tasha mai isarta kafin ta fara numfarfasawa tana haki, wata irin nutsuwace ta shige ta, hatta bugun zuciyarta da fitar numfashinta sun daidaita, ganinta dawo daidai sannu a hankali take kallon fuskar tsohuwar da ta tallabe kanta akan kirjinta, hannunta yana ruƙe da gorar ruwa, tana asanye da alkyabba fara sol mai hula, tsohuwace tukuf fuskarta duk tamoji tamoji, gashin kanta fari fat hurhura ta mamaye ko'ina na gashin, hatta gashin jagirarta fari ne fat, daga ganin tsohuwar tayi gwagwarmaya a duniya, tsufanta bai boye kyawunta ba, bakowa bace wannan face Tsohuwa *KHALA* dattijuwar arziƙi, fara mai farar aniya, tsohuwa mai zuciyar imani, macace mai tausayi da jinkan mutane, abun da zai baka mamaki tana ɗaya daga cikin Elders na kurkukun ƙaddara sune masu fada aji, tana da ƙarfin iko, amma meyasa ta fita daban acikin su⁉️ Gabriella ta tsareta da idanu tana binta da kallon kurulla, fuskarta da alamun ruɗani kamar yadda take kallonta haka itama tsohuwa khala take kallon ta. la66anta na kerma ta furta"wacece ke? Wa ya kawo ni nan? Meya faru da ni? Ki fadamin ina son sani" shiru tsohuwar tayi nata ce mata komai ba. "Kinyi shiru baki ce mun komai ba, meyasa kike kallona? Wacece ke?....." ta faɗa arude tana tararraba idanu. Tattausan murmushi ne ya bayyana akan fuskar dattijuwar, cikin sanyin murya ta furta"Sunana Khala, nasan baki sanni ba, kuma baki ta6a jin labari na ba, yau ne karo na farko da kika fara ganin fuska ta..." cike da dattako tayi maganar. Ta ɗan dakata tana kallon gabriella. "Yau tsawon makonni Ina jinyarki, Due to the traumatic brain injury that put you in a coma, I know you can't remember what happened to you because you've lost your memory..." tun da ta fara magana Gabriella ta nutsu tana kallonta. "naji dadin samun lafiyarki, inatayaki murna" Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. ta fad'a fuskarta ɗauke da annurin farin ciki, ita dai gabriella takasa gane komai, gaba daya arude take da tsohuwar, bata fahimtarta "Naji kin ambaci nayi jinya tsawon makonni bana acikin hayyacina, meya faru dani"? Girgiza kai khala tayi"I won't tell you because I don't want you to remember what happened to you, ko dan saboda lafiyarki, a yanzu nafi bukatar kwanciyar hankalinki, saboda ina da buri akanki"! Aruɗe Gabriel take kallonta, harta buɗe baki zata tambayeta wata irin yunwa ta murɗa cikin ta, da sauri ta dafe cikin da hannu tana faman yamitsa fuska ta kalli khala"ki taimaka min da abinci, yunwa nake ji..." Ajiye gorar ruwan hannunta tayi, tare da taimaka mata ta zauna dakyar, Sandar ta dake ajiye kasa ta ɗauka, ta mike tare da juyawa ta nufi wani teburi dake a dakin hada kujeru biyu a kewaye da shi, daga saman teburin kwanukan abinci ne. Ta ɗauko bowl ɗaya ta juyo tare da kallon Gabriella "Bansani ba ko kin iya cin zogale da kuli..." tunkan ta ƙare maganar gabriella tace"Ina ci, koma menene zanci.." murmushi khala tasaki ta nufo gurinta ta miƙa mata kwanon, Hannunta na kerma ta cire murfin ta fara dibar zogalen tana ci, duk da babu ɗanɗano abakinta, kunnuwanta har motsi sukeyi tsabar dadi, hannu baka hannu kwarya take duma loma tana turawa a karamun bakin ta kamar zata shake, kamar kyaftawar ido ta lamushe shi tass hada sanya harshe tana lasar kwanan..dariya khala tayi"kin koshi ko kina bukatar kari" da sauri ta ɗaga mata kai, juyawa khala tayi cikin takun dattako ta koma gaban table din ta buɗe wani kwano mai ɗauke da tsokokin nama taje ta mika mata kwanon"kalacina ne na safe, da naci na rage, bansan yau zaki farfadowa ba, shiyasa ban tanadar maki abinci ba, amma kiyi hakuri da wannan, idan aka kawo min lunch dina zan baki kici ki koshi" kar6e kwanon gabriel tayi hannunta na kerma ta fara daukar tsokar tana ci, sai da tacinye tass khala ta ɗauki gorar ruwan ta miƙa mata, ta kar6a ta sha. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wani irin relief taji a jikin ta, duk da bata koshi ba, taji ɗan dama dama a cikinta. Kokarin mikewa tayi da sauri khala ta taimaka mata ta mike tsaye kan kafafunta, cikin sanyi murya tace"har yanzu baki bani amsar tambayoyin da nayi maki ba, na ruɗe na kasa tuna komai, wanene ya kawo ni nan? Ko kece? Sannan meya faru dani? A ina nake? "Ki manta da komai, sai ki zauna lafiya, tunawar baida amfani, idan kika bani hadin kai, kuma kika bi sharuddan da zan fada maki zaki tsira da rayuwarki, idan kuma kikayi min gaddama zaki dawwama awahala..." kalamanta sun rikita gabriela cikin rawar murya tace"meyasa zaki hanani tambayarki? Ina son nasan wacece ni! Meya faru dani, ina ji araina kamar na manta wani abu arayuwata, dan Allah ki tuna min..." dafa kafadarta tsohuwa khala tayi"nayi maki alƙawarin zan baki amsar tambayoyinki amma ba yanzu ba, har sai zuwa lokacin da tunaninki ya dawo dai dai..." shiru gabriella tayi gaba daya jin kanta take kamar ba ita ba, kamar ma ba aduniyar mutane take ba. Tafiya khala ta soma yi tana nufar cikin dakin calmly ta cigaba da magana tana kallon fuskar gabriel "Sharuddan da zan gindaya maki, na farko koda gigin wasa kada ki ƙetare iyakarki! Ma'ana kada kiyi yunkurin nema ma kanki hanyar da zaki fita daga dakin nan! Babu ruwanki da komai da zaki gani adakin nan! Ki zama tamkar makauniya, bana son mutum mai karanbani da kafiya..." ta faɗa tana jinjina mata kai, ita dai gabriela tayi zuru tana binta dana mujiya saboda batasan komai ba sai yadda akai da ita. "Idan kika bani hadin kai, zaki tsira da ranki, kuma zan gatantaki, babu abunda zaki nema ki rasa adakin nan.." fuskarta da murmushi tayi maganar, kafin ta juya ta ɗaga sandar hannunta tayi mata nuni da wata ƙofa Sannan tace"wannan kofar, makewayina ne, idan uziri ya kamaki zaki iya shiga, harma wanka zaki iyayi don kiji dadin jikin ki, arana zaki ci abinci sau uku, idan kadaici ya dame ki, zan baki story books da zaki dinga karantawa, suna da dadi zasu debe maki kewa, ga kuma furanni abun sha'awa zasu faranta maki rai" ta faɗa still da murmushi akan fuskarta. Gabriella tayi sototo tana kallonta kamar sakarya, wuce wa tsohuwa khala tayi agaban bookshelve ɗin ta tsaya tare da kai hannu cikin shelve tana neman storybooks din da zata bata guda uku ta curo ta juyo ta nufi Gabriel ta nuna mata su. "su kadai na baki iznin ki karanta, bayansu ban laminta ki ta6a sauran littattafan dake a cikin shelve din ba" jinjina mata kai tay alamar toh, bayan ta kar6i books din khala tace"ki samu guri ki zauna, har yanzu jikinki ba kwari," cike da ladabi ta amsa mata da toh, don yanzu ganinta take kamar mamanta saboda itace mutun na farko data fara gani a idanunta bayan tsawon lokaci data ɗauka a coma.. Ruƙe hannunta khala tayi, taja ta har zuwa gaban table din ta zaunar da ita kan kujera"idan kika gaji da karatun, ki koma kan gado ki kwanta kiyi bacci ki huta" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh. "Akwai inda ke yi maki ciwo a jikin ki"? Girgiza kai tay alamar a'a "Okey, ko bayan na fita daga dakin, kika ji wani guri nayi maki ciwo a jikin ki, ki kira sunana sau uku, zan ji ki" "Toh," "Good girl" ta faɗa tare da shafa fuskar Gabriella da yatsun hannunta. "Ki kula min da kanki" lumshe ido gabriela tayi kafin ta buɗe su tuni tsohuwa khala ta bace ma ganinta, har saida taji gabanta ya fadi ganin babu ita, akan table din ta ajiye books din data bata. ta mike tsaye jikinta na kerma take bin ko'ina da kallo a kokarinta nata gano ina ta shiga, ganin babu ita adakin, yasa ta hakura da nemanta, ta juya ta nufi kofar makewayin da ta nuna mata, ta buɗe ta shiga, makewayine irin na zamani ya hadu komai cikinsa fari kyal, a tsaftace ba kazanta, a hankali take kallon cikinsa, bathtub ta gani ga shower, ga toilet seat, da cabinet, bata tsaya bata lokaci ba, ta cire rigar jikinta ta rataya a hanger, ta zukunna zatay fitsari taji gabanta amatse dakyar fitsarin ke fita nishi ta dinga yi a wahalce ta samu ta kammala. ta miƙe tana faman sauke ajiyar zuciya, Takura kanta tayi da tunani har saida kwakwalwarta ta fara neman rikicewa tukunna ta hakura tana faman jan numfashi, ta nufi kwamin wankan ta shiga ta kwanta tare da kai hannu ta kunna bathtub faucet ta cika kwamun da ruwa mai ɗumi wata irin ni'ima taji mai dadin gaske. Ta daɗe acikin ruwan tana ɗumama jikinta kafin tayi wanka ta maida rigarta, ta fito ta zauna kan kujerar, ta dauki storybook ta fara karantawa. Murmushine ya bayyana akan fuskarta, da alama labarin da take karantawa ya faranta ranta, babi huɗu ta karanta, ta fara jin kasalar bacci, miƙewa tayi tare da kwashe books din ta nufi book shelves din dakin inda taga khala ta dauko mata su, tana kokarin ajiyesu ta hankaɗe wasu jerin littattafai dake a shelves tana kokarin tallabe su biyu suka rikito ƙasa, wani irin faduwar gaba ta ji, tsoro ya kamata tunawa da gargadin da tsohuwar tayi mata akan kada ta ta6a komai na dakin, jikinta na kerma ta zuƙunna tana kokarin tattara books din kamar diary suka an kulle su da makulli tayadda baza'a iya buɗe su ba. Akan laps dinta ta daura books din kamar ance ta kalli covers dinsu karaf tayi tozali da hoton abunda ke akan diary na farko, zanan kananun yara ne su uku sanye da jajaye kaya, mata biyu sun sanya namiji a tsakiyar su, kayan matan rigace dai dai gwiwa launin ja, shi kuma namijin riga da wandone jajaye, abun da ya ɗaure mata kai da hoton cover din, duka yaran an daure masu hannayensu da igiya, an toshe bakinsu da jan kyalle, ga hawayen jini kwance kan fuskokinsu, da rubutun larabci aka rubuta sunan books din kokarin karantawa tayi A hankali ta furta sunan shi *sijill al-sujnā* bata san menene ma'anar sunan shi ba, janye na farkon tayi ta dubi sunan ɗayan diary din *tārīkh sijnil qadar* miƙewa tayi da sauri ta maida su gidan da suka fadowa, ta gyara su dakyau ta yadda ba azagane dun faɗo ba, da sauri ta nufi matakalar gadon ta haye ta kwanta tare da lumshe idanunta. ___________________________✍️ *HAJJATY* Safa da marwa takeyi atsakar dakinta, Hannun ta ruƙe da wayarta, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita, saboda fargaba da tashin hankalin ciwon marwa jiya taga abunda ya rikitar da ita, kusan kwana tayi adakin marwa tana kokarin shawo kanta saboda kukan da takeyi abun yayi yawa kamar zata kashe kanta, hajjaty ga tsoronta da take ji amma ahaka ta daure ta zauna adakinta har saida ta shawo kanta ta hanyar kunna mata karatun kur'ani kafin ta samu jikin marwa yayi sauƙi har bacci ya ɗauke sannan ta dawo daki, yau tun da safe ta buga ma sheikah imam kira awaya ta sanar da shi halin da marwa take aciki, tace mashi ta kasa gane meke damunta, sheikh imam ɗin yace zai shigo in sha Allah. A yanzu haka shi take jira, ta kasa shiga dakin marwa saboda bata jin dadin ganin ta a mawucin hali, yarinyar ba karamun tausayi take bata ba. Kira ne ya shigo wayar da sauri ta duba screen din wayar ganin sunan sheikh imam ne yasa ta daga da hanzari ta daidata nutsuwarta gurin yi mashi sallama bayan ya amsa mata yace"na iso gidan" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta dauki mayafi ta rufawa kanta, ta zura flat shoes a kafarta, ta fito ta nufi main falo din gidan tasan anan yake tsayawa idan ya shigo. Tunkafin ta karasa ta hango shi zaune kan sofa as usual cikin shiga ta magadan annabawa.. masu aikin gidan dake ta kai komo cikin girmamawa suke gaishe da shi, har abunsha sun kawo mashi da snack, har ya fara shan lemun ya hango hajjaty, mikewa yayi tare da tunkararta, da fara'a tace"barka da safiya malam, ya gida ya iyali" murmushi yayi jin ta tambaye shi ya iyali. bayan sun kammala gaisawa tayi gaba yabi bayanta har zuwa dakin Marwa saida ta fara shiga kafin tayi mashi iso ya shiga daga ciki, a lokacin marwa tana kwance kan katifarta, bacci mai nauyine ya dauke ta sai faman jan numfashi take yi, daga gani awahalce takeyin baccin. "Malam, ni dai narasa gane kanta cikin kwanakin nan, in ta fara kuka kamar ranta zai fita, kuma wlh ina kiyayewa gurin bata maganin kamar yadda ka ce.." tay maganar tana kallon shi. Matsawa yayi daga gaban mattress din Ya zuƙunna Yana kallon yatsun hannayen marwa da fatar fuskarta, farat ɗaya ya gane babu lafiya, ciwon nata ma ƙara ha66aka yakeyi babu alamun sauƙi, lamarin ya ɗaure mashi kai, a kalla ya shafe mintuna yana kallonta yana nazari akan yanayin ta. Hajjaty dake kallon fuskarshi sheikh imam tuni tasha jinin jikinta ganin yanayin shi ba walwala. mikewa yayi tare da kallon hajjaty"anya kuwa kinbi sharuddan bata maganin dana fada maki dai dai? Ko dai kinyi kuskure ne" arude ta girgiza kai"wallahi ban ta6a kuskureba, ina kokarin kiyayewa kamar yadda na fada maka..." bayani tayi mashi yadda take bata maganin, dalla dalla kamar yanda ya fada mata, tabbas ya yarda da maganarta, abunda bai gane ba ta ina matsalar take! Shiru yayi jim yana kara bin marwa da kallo Muryar hajjaty na rawa tace"malam akwai matsala ne"? Ya fahimci hajjaty bata lura da habbakuwar ciwon marwa ba .. Numsafawa yayi kafin ya furta"ina maganin nata yake"? Jikinta na 6ari tace"ga su can akan mirror, bari in dauko maka" dakatar da ita yayi da hannu tsayawa tayi, tana faman zare idanunta, juyar da kai sheikah imam yayi tare da kallon gaban mirror din marwa A hankali Ya nufi gaban madubin Ya tsaya tare da kallon robobin maganin, ɗaya ya ɗauko ya buɗe ya kalli ruwan dake a ciki, yakai hancin shi ya shinshina da sauri ya kawar da kanshi gefe saboda zaurin daya buso hancin nashi. Hankalin hajjaty ba karamin tashi yayi ba ganin yadda ya haɗe rai sosai, ɗaya bayan ɗaya ya buɗe murfin robobin cikin matsanancin tashin hankali ya juyo a sukwane ya kalli hajjaty dake ta zare idanunta "Ya akai haka"? Ya faɗa yana dubanta Muryarta na rawa tace"meya faru shiekh? Ban gane me kake nufi ba" haɗe rai yai tamkar ba sheikh imam ba, da kakkausar murya yace"wanene ya canza ruwan maganun dana baki"! Rass taji gabanta Ya faɗi ta fara zare na mujiya, jikinta ya hau yin kerma abunka ga matsoraciya kamar wata mara gaskiya sam takasa bashi amsar tambayar da yayi mata. Hakan ba karamin bata mashi rai yai ba"baki ji ina magana bane! Wanene Ya canza ruwan maganin? Saboda ni ba haka na baki shi ba, gaba ɗaya an canza ruwan cikin shi, bayan ni a iya sanina launin ruwan maganin baya canzawa..." A fusace ya fada yana binta da kallon tuhuma Hankalin ta idan yai dubu toh ya tashi, Gabanta ya dinga faduwa gaba daya tabi ta rude, ta rasa amsar da zata bashi, wlh kwata kwata bata lura da hakan ba, sai da yayi maganar ta tuna da lokacin da ɗan aiken shi ya kawo mata maganin tabbas da ta buɗe tana dubawa taga launin ruwan ya banbanta. Wahalallan yawu ta haɗiya cikin rawar murya ta furta"wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa bani na canza ruwan maganin ba! Wlh bani bace, bansan wanene ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un..." gaba ɗaya tabi ta ruɗe wata irin zufar tashin hankali ce ta wanke fuskarta, gani take kamar shiekh imam yana zargin ta. Girgiza kai shiekh imam yayi"kin bani mamaki! Meyasa zakiyi mata haka? Ko dan kin gaji da jinyarta ne? Ni fa ban tursasa maki ba, aikin lada ne tun lokacin dana bukaci wanda zai kula da ita da kin fadamin bakiso ay da ba haka ba" Runtse idanunta tayi, wasu zafafan hawaye suka wanke fuskarta, kalaman sheikh imam sunyi mata tsauri, taji ɗacin su azuciyarta. "ka yarda dani, wlh ni ba muguwa bace, bazan iya cutar da marwa ba, ina da zuciyar imani, ko kiyashi bazan iya cutarwa ba, balle ɗan adam, wlh bani na canza ruwan maganin ba, na shiga ukuna" ta fada tare da dafe goshinta da hannu daya. tunda sheikh imam yaga yadda ta rikice nan take ya fahimci ba ita bace, dama da biyu ya furta "Ya Isa haka, Na yarda bake bace, amma wanene toh? Dole akwai yarda akai aka canza ruwan, kuma koma wanene mutunne, lokacin da dan aikena ya kawo maki maganin a ina kika ajiye shi"? Waro ido waje tayi murya na rawa tace"a dakina" Sheikh imam yace"hakan na nufin anan aka canza ruwan maganin kenan? To wanene? Akwai wanda ke shiga dakin ki ne"? Shiru tayi jim gabanta na faduwa da matsanancin karfi, hankalinta ya tashi, kwata kwata bata kawo ma ranta pravin ba, tasan bazai ta6a yi mata hakan ba, me ma zai kaishi canza maganin marwa? Har abada ba za ta bari wani yasan akwai alaka tsakaninta da pravin ba. Tayi zurfi cikin tunaninta muryar sheikh imam ta katse ta"kinyi shiru baki bani amsa ba? Wakike tunanin ya canza ruwan maganin? In har baki fadamin gaskiya ba, zanje in fada ma baba obie abunda ke faruwa" a firgice ta zare mashi dara daran idanunta, wani irin faduwar gaba ta ji daram kamar ana mata lugude a kirjin ta, arude ta girgiza mashi kai"kayi hakuri sheikh, wlh bani da masaniya, amma nayi maka alkawarin zan binciko koma wanene" jinjina kanshi yayi"kinyi alkawari? Ɗaga mashi kai tay"in har kika sa6a hmm kinsan sauran, keda baba obie ne" matse kwalla tayi, cikin sanyin murya tace"in sha Allah ba zan saba ba, amma sheikh meyasa kake tunanin wani ne ya canza ruwan? Baka tunanin bakaken aljanun jikinta ne sukayi mata hakan don kada ta samu sauki? In ba haka ba taya za'ay wani ya canza ruwan? Akan wani dalili"? Ta faɗa tana kallon fuskar shi. Murmushi shiekh imam yayi tare da dan girgiza kanshi kafin yace"ba al'janu bane suka canza ruwan, mutunne, dole akwai yadda akayi, ki zauna kiyi tunani dakyau..." Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh, "Sannan sheikh, akwai wani abu da marwa takeyi min, ni dai nagaza fahimta, duk in na shugo dakin zan bata magani, sai ta dinga goga hannunta a kasa, taita yunkurin yi min magana idan taga na kasa gane me take nufi saita kifa kanta jikin pillow...." bata ƙare maganar ba sautin tarin marwa ya katse hanzarin su, sam sun manta da ita dakin, maganganunsu su ne suka farkar da ita Atare suka kalle ta, tana a zaune kan mattress din, ta jingina kanta jikin bango, idanunta suna rufe ga siraran hawaye dake zarya kan kuncinta, gwanin ban tausayi "Marwa"! Jin muryar sheikh iman yasa tay saurin bude idanunta. tana ganin shi ta fara kokarin yin magana donta gaishe da shi sai dai takasa. "Basai kinyi min magana ba, na fahimce ki," ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun kaɗa jawur da su Zukunnawa yai agaban katifar yana dubanta yace"Hajjaty ta faɗa min da akwai wani abu da kike yi mata nuni da hannu ta kasa gane menene ko zaki nuna min in gani"? da sauri ta ɗaga mashi kai, jikinta na kerma ta matso bakin kafitar, ta daura hannunta akan floor ta dinga goga su tana kallon sheikh imam cike da sa ran zai fahimce ta, ita dai hajjaty sai faman zare ido takeyi fatanta Allah yasa shikeh imam ya gane menene marwa ke son fada mata abun yana damunta. A kalla marwa ta kwatanta mashi yafi sau biyar ganin kamar baigane ba yasa ta fara matsar kwalla. zurfin tunani ya shiga can yace"wani yana zuwa dakin nan? Girgiza mashi kai tay alamar a'a" "Ko ana tsoratar dake ne"? Still ta girgiza mashi kai, shiru yayi yana kara hasasowa can yakuma cewa"kodai kina son kiyi rubutu ne.. "Ga mamakin sa sai yaga ta daga mashi kai alamar eh hada ɗan murmushin ta. Hajjaty tayi mamakin jin hakan sosai, da sauri ta nufi drawer din marwa ta fara neman littafi dakyar ta zakulo wata jotter tare da pen, ta dawo bakin katifar ta buɗe mata jotter din ta ajiye agabanta, ta zira mata pen din dakyar ta matse biron da hannayenta, ta soma kokarin gogawa paper din, lamarin ya daure masu kai, daga hajjaty har sheikh imam din, sun kagara da suga me ta ke son rubutawa. Duk yadda taso ta rubuta sunan wanda yayi mata aika aikar takasa, biron yaki zama a hannunta duk ta cakalkala paper din akarshe ma ta yayyage, jefar da pen din tayi kasa ta fashe da kuka tare da kifa kanta jikin pillow, gaba daya jikinsu yayi sanyi, zuciyarsu ta raunata da tausayinta. Cikin sanyin murya shiekh imam ya ce"kiyi hakuri, na fahimce ki, akwai wani abu da kike son fada mana, amma kin kasa, abunda nakeso dake ki kwantar da hankalinki, in sha Allah nan badajimawa ba ciwonki zai zama labari, zamu tayaki da addu'a sannan zan canza maki wasu magungunan. tun tana shesshekar kuka hartayi shiru ta hakura musamman da taji maganar sheikh imam hankalinta ya ɗan kwanta, har taji zata iya hakura har zuwa time da zataji sauki tunda bata da mafita. Mikewa yayi tare da kallon hajjaty, "ki zubda ruwan maganin dake a cikin robobin, zan kawo maki wani amma fa dole kiyi takatsantsan, kada ki kuskura ki bari wani yasan inda kika boye su ko kuma wani yasan na canza mata maganin nan daga ni sake wannan maganar, In kuwa kikai gangancin da wani ya sani har aka sake samun matsala to ki kuka da kanki domun kuwa bazan kyale ki ba...." a kausashe yayi mata maganar saboda ta ɗauki maganar shi serious, baiwar Allah duk tabi ta rude jikinta har kerma yakeyi sai taji dama bata kar6i aikin ba saboda bata son abunda zai hana ta kwanciyar hankali. Sallama shiekh imam yayi mata, ya fuce yabarta da jimami ________________________✍️ Zaune yake a gefen gadon shi, jikinshi sanye da voile fari, tafukan hannayenshi tallabe da qur'ni, Ya tattara dukkan nutsuwarsa akan kira'ar da yake yi, acan kasan zuciyar shi damuwa ce cunkushe baya jin dadin zuciyarshi saboda halin da Benazir take a ciki ya damu ita, yana matukar jin tausayin ta. Yana tsaka da yin kira'ar, sautin knocking Ya katse shi Ɗaga murya yayi"wanene"? "Ya shureim ni ce, Ina son yin magana dakai" jin muryar Benazir yasa shi saurin miƙewa ya ajiye kur'anin Ya nufi kofar ya buɗe mata, A hankali ta shigo ciki, jikinta sanye da abaya, tayi rolling veil akanta, hannun ta ruƙe da yar purse dinta, ga wasu highhill da ta saka a kafarta, aruɗe yake kallon ta ganin hada make up akan fuskarta. "Ina kwana ya shureim ka tashi lafiya..." "Lafiyalou sister, Ya jikin naki"? "Naji sauki sosai" shiru sukayi fargaban shi kada tace yakaita gurin azeezaty ya san halinta in rigimarta ta motsa. "Lafiya? Naga kamar kinyi shirin zuwa anguwa,"? Murmushi ta sakar mashi "Eh, gidan su anila nake son zuwa, jiya munyi waya da ita, ta fadamun yaronta baida lafiya, ashe shiyasa bata kira ta yi min ya jiki ba.." tun da tafara magana shureim ke kallonta gani yake kamar karya ta shirga mashi don ta samu yakaita gidan. Ganin irin kallon da ya ke yi mata ne yasa tai saurin furta"wallahi dagaske nakeyi maka, bari in kira maka anilan ku yi magana" tay maganar tare da kai hannu ta buɗe purse dinta, ta curo wayar ta kira layin anila tana fara ringing, ta miƙa mashi fuskarta dauke da murmushi. "Assalamu alaikum, Anila barka da safiya"! On the other hand tace"ya shureim ina kwana ka tashi lafiya? Ya jikin benazir din? Wlh junaid ba lafiya shiyasa ban samu na kira naji ya ku ke ba ashe ma har an sallame ta" ajiyar zuciya ya dan sauke. "Lafiyalou anila, Benazir taji sauki, itace ma ta kira min ke, tace tana so tazo duba junaid, ubangiji Allah ya bashi lafiya, in sha Allah yanzu zamu zo" "Allah Ya kawo ku lafiya, ngde" sallama sukayi ya mika ma Benazir wayar "Ki bari sai anjima muje, yayi wuri yanzu" girgiza kai tay haɗi da ɗaure fuskarta"ya shureim itafa ta nuna tana son inje yanzu" "Naji, amma dan Allah idan mu ka je gidan, kada ki yi mata maganar yarinyar nan Azeezaty, nasan hada hakan yasa kike zumudin zuwa gidansu, kiyi hakuri Benazir yarinyar nan ba yarki bace idan kika sa hakuri in sha Allah kema zaki ga taki yar.." dukar dakai kasa tay, idanunta suka ciko da kwalla. "Kiyi hakuri idan maganata batayi maki dadi ba" girgiza kai tay'na fahimce ka, in sha Allah bazanyi mata maganarta ba, ay na hakura tuntuni" ajiyar zuciya ya sauke "haka nakeson ji, Kin fada masu mommy zaki fita" girgiza kai tay"a'a yanzu in zamu tafi sai mu gaya masu" amsa mata yai da toh Kafin ya juya ya shiga ciki ya ɗauko carkey dinsa Ya fito suka jera atare suka nufi dining room, mutanan gidan duk suna azaune suna yin breakfast, mutumin ya haɗe fuska sai shan kamshi yake kamar iska tana mashi wari, abincin ma da aji da izza yake cin shi tamkar baya son tauna shi.. A fakaice hajiya layla take aika mashi harara kamar zata rufe shi da bugu, shi dai Alhaji ubaid ya nutsu Yana cin abin cin shi, yayin da zeenatu take fuskantar mommyn ta, sam takasa cin abincin ruwan lemu kawai take ta aikin durawa cikin ta, hankalinta da tunaninta suna akan Azeezaty, jiya har mafarkinta tayi, bata da burin daya wuce su haɗu da ita, don ta tambayeta wacece Unaizah mai kama da ita❓ Takun tafiyar su shureim ne yaja hankulansu ga duban su, Bayan sun karaso cikin girmamawa suka gaishe da su kowa ya amsa masu banda Alhaji musa hakan bai dame su ba, sun riga sun dan halinshi mami ta dube su"ina zuwa haka shureim"? "Zamuje gidansu anila ne, yaronta baya jin dadi" hajiya sarah tace"Allah sarki, itace kawar benazir wadda suke zuwa asibiti dubata ko"? Benazir ta amsa mata da eh"Allah ya bashi lafiya" mami tace"ay da kun fada min tun dazu dana shirya mun tafi atare, amma idan kun isa gidan ku kirani dan Allah" suka amsa mata da toh, Alhaji ubaid yace"ku gaishe min da mutanan gidan, ace ma anila inayi mata yamai jiki, Allah ya bashi lafiya, idan na samu lokaci zan shigo gidan" ya amsa mashi toh. "Ya shureim zan biku dan Allah" zeenatu ce tayi maganar, har zata miƙe Alhaji musa ya jefa ta da wani kallo tuni tasha jinin jikin ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah daddy ka bari su tafi dani, mommy kice ya shureim ya tafi dani inaso in bi su" atsawace Alhaji musa ya furta"karki kuskura ki ƙara magana! " a tsorace taja baki tayi shiru, idanunta akan fuskar shureim dake kallon ta, wani irin tausayinta ne ya kama shi, yana so su tafi da ita sai dai yasan daddynta bazai barta ba. "Musa ka barsu su tafi da ita tunda tana son zuwa..." Alhaji ubaid ne yai maganar, Banza yayi da shi tamkar baiji abunda yace ba, hakan ya sosa zuciyar Alhaji ubaid musamman layla ranta ya 6aci, harara ta galla mashi akan idonshi, ita day hajiya sarah tayi shiru batace komai ba. "Shureim ku tafi, Allah ya tsare hanya.." ta fada tare da yi masu alamar su je, ruko hannun Benazir yayi suka kama hanyar fita daga falon yana jiyo sautin shesshekar kukan zeenatu, har waiwayowa yayi sai kallon shi takeyi duk sai yaji ba dadi amma idan ya tuna abunda alhaji musa ya fada mashi sai yaji kwara zamanta agidan duk da shi baiga amfanin hakan ba saboda yayi imanin cewa Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake. Har suka shiga mota, bai daina tunanin zeenatu ba, ta tsaya mashi aranshi yana jin tausayin rayuwarta Tsawon mintina kafin suka karaso anguwarsu anila, motarsu ta na shigowa layin gidan suka hango anila atsaye cikin shiga ta abaya fara ta goya baby junaid abayanta, hannunta ruƙe da wayarta.. Tunkafin su karaso ta ɗaga masu hannu alamar su tsayar da motar, agabanta yayi parking, ta nufi backseat ta buɗe ta shiga ta zauna kafin ta warware goyan junaid ta kwantar da shi kan kirjin ta. Dr shureum yayi zaton gidan zasu shiga har zai tada mota benazir ta ruƙe hannun shi ya dubeta da mamaki"ba ciki zamu shiga ba, Anila ki faɗa masa inda zamuje" Cikin sanyin murya tace"ya shureim obie estate zaka kaimu" aruɗe yake kallonsu da mamaki yace "Bangane ba, me zakuyi acan? Anila fada mun ina fata dai ba gidan iyayen yarinyar nan zakuje ba"? "Ya shureim muje kawai, zamuyi maka bayani daga baya, wani abune mai mahimmanci zai kai mu can" bai musa masu ba, yayi reverse ya miƙi hanyar fita daga unguwar "Anila ya jikin junaid din! Ko dai shima duk plan dinku ne"? Murmushi suka saki, Anila tace"a'a ba plan bane, dagaske baida lafiya, amma jikin nashi da sauƙi.." "Meke damun shi ne"? Kafin ta bashi amsa junaid ya fara mutsu mutsu kamar zai farka hakan yasa tay shiru tana kokarin lalla6a shi don ya koma baccin. Cikin kulawa dr shureim yace"Allah ya bashi lafiya" ta amsa mashi da ameen. Tags Kurkukun Kaddara YOU MAY LIKE THESE POSTS [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 43 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 05, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE Bayan ta samu ta lalla6a junaid ya koma bacci, tun da motarsu ta haura kan titi suke ta satar kallon juna tsakaninta da Benazir ta cikin mirror din motar kamar wasu munafukai, kwata kwata hankalin dr shureim baya akansu ya tattara nutsuwarsa akan driving din da yakeyi, hakanan ranshi ya raya mashi ya dubi fuskar Benazir, ta wutsiyar idanun shi ya ke kallon ta adaidai lokaci sun kura ma juna ido ita da Anila da alamun rashin gaskiya atattare da su, duk dagowar da zaiyi sai ya kama su suna kallon juna ta mirror, gyaran murya yayi masu da sauri suka dube shi. "Ban yarda daku ba! Ku faɗamin gaskiya meke faruwa ne? Meyasa kuke satar kallon juna ta mirror? Ina fa lura da duk wani motsinku acikin motar nan, kamar baku da gaskiya, ku ji tsoron Allah ku sanar dani abun da kuke boye min"! Shiru su ka yi suna ta ƴan kame kame an rasa me bude baki ya bashi amsa duk sun sha jinin jikin su. "Da ku nake magana? Me zamuje yi a obie estate? In har baku fadamin ba zan dakata da yin driving din..." fuskar shi adaure yayi maganar batare daya kalle su ba, kallon juna suka sake yi ta mirror, kafin su yanke shawara da junan su dr shureim ya yi parking din motar a gefen titi Ya kashe ta tare da jingina kanshi jikin headrest. "In har ba zaku fadamin abunda kuke boye min ba, to kuwa zamu kwana anan ne.." yawu Anila ta hadiya tare da kallon benazir da hankalinta ya gama tashi, Cike da fargaba benazir tace"yaya shureim..dama ummm gidan su Azeezaty zamu je..." Dakyar ta ƙare maganar ganin ya juyo dakai ya kalle ta tuni ya hade rai, annurin fuskarshi ya gushe rai a6ace yace"meyasa baki jin magana ta? Har nasiha nayi maki nace ki yi hakuri tun da yar nan ba taki bace ki hakura mana, ni dama tun da naga take takenku raina ya bani gidan su yarinyar nan zaku je, to wlh bada ni ba, da nasan gidan su azeezaty zamuje da ban biye maku ba." kallon juna sukayi hankalin su atashe damuwa ce ƙarara akan fuskokin su. Juyawa yai tare da kallon Anila cikin sanyin murya yace"haba anila! Meyasa zaki biye mata? Ni nasan bada son ranki ba, itace ta matsa maki, Benazir bata da hakuri ta fiye kafiya da naci, ba irin lallashin da ban yi mata ba akan ta hakura da yarinyar nan amma taƙi jin maganata" kifa kai Benazir tayi jikin seat din da take azaune ta fashe da kuka tana fadin"yaya shureim na hakura da ita, nasan ba yata bace na yarda da hakan, Anila tayi min bayanin komai dangane da ita kuma na fahimce ta...." ta ƙare maganar tana shesshekar kuka, kafin yayi magana Aneelerh ta riga shi cewa"ka yi hakuri yaya shureim ban nemi shawararku ba nayi gamon kaina, saboda ina tausayin halin da Benazir take a ciki" ta fada tana kallon fuskar shi"shekaran jiya ta kirani awaya take faɗa min ita fa tun a asibiti ta fahimci yarinyar nan ba yarta bace kun ce mata taj ya dauketa sunje mall shiru basu dawo ba kun hana tasan gaskiya kun boye mata saboda baku san 6acin ranta, ni kuma abunda nayi tunani duk daran dadewa dole Benazir tasan gaskiya tun da gashi harta kirani awaya ta fadamin tagane ba yarta bace shiyasa kawai na faɗa mata gaskiyar zance, sannan na kwantar mata da hankali nayi mata nasiha nace tayi hakuri da boyen matan da akai munyi hakanne saboda gudun kada mu rasa ta"! tun da ta fara magana dr shureim yayi shiru yana sauraronta, jikinshi yayi mugun yin sanyi zuciyar shi ta karaya. Benazir ta ɗaura da cewa"Yaya shureim bayan Anila ta fadamin gaskiya, nayi kokarin cire azeezaty araina saboda a lokacin na hakura da ita, nasan inda rabo wata rana nima Allah zai bayyanar min da ƴata Angel, amma wallahi nakasa ya shureim Inason Azeezaty, Allah Ya jarabce ni da kaunarta, kai shaida ne akan irin Son da nake mata, ko bayan dana gane ba ƴata bace, ina sane nake yi maku pretending saboda kada ku rabani da ita, shiyasa ko bayan da muka dawo gida na ɗaga hankalina sosai saboda na fahimci kun rabani da Azeezaty" ta ɗan dakata da yin maganar tana kallon dr shureim dake kallon ta, Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. numfasawa tayi kafin taci gaba da cewa"jiya batare da sanin kowa ba, na kira Aneelarh awaya na fada mata halin da nake a ciki na rashin azeezaty, na roƙe ta akan ta taimaka min ko sau daya ne in ganta, saboda na kasa cire ta araina, shine tace min in jira zata yi magana da iyayen yarinyar idan sun amince muje gidan zata sanar dani, sai yau da safe ta kira ni ta fadamin tayi waya da daddyn azeezaty yace muzo gidan mu ganta, har ce mata yai ita ma yarinyar tana son ganina tun bayan data koma gida kullum sai ta yi maganata kaga itama kenan tana jin abun da nake ji agame da ita, ko da bamuje gidan ba, zata sa daddynta ya kawota gurina ne saboda itama ta damu dani" Muryarta adisashe tayi maganar tana kallon dr shureim, ajiyar zuciya ya sauke har cikin ranshi yaji dadi da Benazir ta hakura abunda ya kara kwantar mashi da hankali jin cewa da sanin iyayen yarinyar zasuje gidan dama shi abun da yake jima fargaba kada su kwasa su je gidan ba tare da sanin iyayen yarinyar ba, benazir ta sanya masu rigima akan su bata ƴarta, tun da ba hankali gareta ba, yanzu kuma yaji daga bakinta tasan me takeyi ashe dagangan takeyi masu pretending don kada su raba ta da yarinyar, baiyi mamakin jin hakan ba, cos ya riga da ya san halin Benazir tun tana ƙaramarta idan ta kwallafa rai akan abu har aljanun karya take yi masu don ta ɗaga masu hankali kan abun. yayi zurfi acikin tunanin shi, Benazir ta katse shi cikin rauni na murya tace"ya shureim dan Allah ka taimaka ka kai mu gidan, nasan me kake tunani, in sha Allah bazan bamu matsala ba, nayi maka alkawarin hakan, Ni kawai burina inga Azeezaty, kona samu kwanciyar hankali" nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanun shi yayi shiru jimmm yana nazari kafin ya buɗe su akan fuskar Anila"ba ki yi laifi ba Anila, kinyi abunda ya dace ne, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani gurin yi maki godiya ba saboda naji dadin yadda kika damu da Benazir, wlh kin faranta min rai, saboda kwanakin nan dakyar nake bacci saboda damuwar halin da Benazir take a ciki, amma yanzu kin sama mana maslaha atsakanin mu da ita, ubangiji Allah yasaka maki da mafificin alkhairinsa." Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke, fuskarta dauke da murmushi tace"ameen ya shureim, ay ba godiya atsakaninmu, mun riga mun zama ɗaya, zan iya yin komai saboda farin cikin ku" har cikin ransu sunji dadin maganar Aneelerh. Kallon Benazir yayi suka haɗa ido da juna, fuskarta tayi jawur saboda kukan da tayi"kiyi hakuri kinji, ki share hawayenki, yanzu na fahimce ku, kuma naji dadin yadda kika ɗauki dangana, in sha Allah kema zaki gana da yarki wata rana, zamu ci gaba da yi masu addu'a ubangiji Allah ya bayyanar mana da su" suka masa mashi da ameen Daga bisani ya tada motar ya cigaba da yin driving dinsu, Hankalinsu Ya kwanta sosai, Yanzu basu da sauran damuwa, har yanzu junaid bai farka daga bacci ba, maganganun da sukayi baisa ya farka ba, wani irin bacci yake yi mai nauyin gaske. _________________________________✍️ *UNAISAH ANGEL💓* Tana a zaune tsakiyar Bedmattress dinsu, kayan baccin jiya ne a jikinta riga da wando da alama ko wanka batayi ba, gaba daya hankalinta na akan notebooks din da ta jera kan katifar, ta sanya farin glass a idanunta kamar wata malaman makaranta, ta ruƙe red pen a hannunta, ta nutsu tana dudduba notebooks din data kar6a a hannun su Parveen, Assignment ɗin da ta basu jiya shine yau take dubawa, ta rasa gane me suka rubuta, duk jagwalgwalo ne, wani rubutun kamar na ƴan china wani shigen na thailand, tun da tafara checking note books din fuskarta ɗauke da murmushi wani lokacin saita kwashe da dariya hada kifawa kan katifa ba karamin nishadi suka sanyata ba, ta fahimci kwata kwata basu gane abunda take koya masu, kwakwalwarsu bata daukar karatu, bayin Allah sai taji ta karajin tausayinsu da kaunar su. Motsin buɗe toilet door ne Yasa ta ɗago dakai ta dubi kofar, Batool ce ta fito daga ciki, ta sanya bathrobe kafafuwanta sanye da slippers, ta nannaɗe sumar kanta da farin towel, dakatawa tayi da yin tafiya ganin irin kallon da Unaisah ke yi mata duk saita sha jinin jikinta, da sauri ta bi kanta da kallo don ta ga ko tayi wani abu badai dabai ba, ganin lafiyalou babu wani aibu yasa tace"Sister, meyasa kike kallona? Akwai wani abu ne"? Murmushi ta ɗanyi tare da girgiza mata kai"bakomai wlh, You look so gorgeous, like a pearl" kayataccen murmushi Batool ta saki har dimples dinta suka lotsa, taji dadin yabon da unaisah tayi mata. "tun dazu nake jira ki fito nima in shiga inyi wankan," ta faɗa tare da saukowa daga kan gadon ta fara tattara notebooks din ta ɗaurasu kan bedside drawer. "ki zauna ki jira ni, idan na fito zan za6a mana kayan da zamu sanya, har make up zamuyi" dadine ya lullubeta"amma pls kada ki daɗe" "Toh" da sauri ta nufi mirror chair ta zauna tana jiran fitowar ta. Tsawon mintuna kafin ta fito daga toilet din, tayi ɗaurin gaba da towel fari, ta naɗe sumar kanta da towel kamar yadda Batool tayi...tsayawa tayi tana kallon batool ganin ta daura kanta gaban mirror idanunta arufe alamar bacci takeyi da alama taji dadin wankan da tayi shiyasa ta 6uge da bacci Karasawa tayi gaban mirror din ta ɗauko hairdryer ta jona ta a socket, takai hannu ta tum6uke towel din da batool ta ɗaure kai da shi, ta saita hairdryer din akanta iska ta fara busowa buuuuu a firgice Batool ta farka tana kokarin buge dryer din hannunta. Dariya Unaisah tayi"Sorry na katse maki baccin ki, inaso na gyara maki gashin ne naga kin wanke shi, ajiyar zuciya ta sauke tare da jingina bayanta jikin kujerar ta dafe saitin zuciyarta da hannu"kin bani tsoro sister, wallahi nayi azan wani mugun abunne" Still fuskar Unaisah da murmushi ta cigaba da cakuɗa sumar kanta tana busar mata da ita "Duk in na tuna farkon haduwar mu a prison, sai inji na kara kaunarki a zuciyata, saboda kin so ni a lokacin da kowa ke guduna, bakisan wacece ni ba, amma ki ka kirani da sunan sister dinki, duk da irin ƙyarar da nake maki hakan baisa kin juya min baya ba, har saida kika dasa min kaunarki a cikin zuciyata" Murmushi Batool tayi"nima har yau idan na tuna farkon haduwarmu sai inji na kara kaunarki, abun da ya daure min kai a lokacin ya kuma bani mamaki, irin masifar son da nake yi maki, wallahi ko yan uwana da muka taso atare da su tun kafin mu mallaki hankalin mu ban yi masu irin son da nake maki ba, Allah ya jarabce ni da kaunarki a zuciyata..." ta fada tare da runtse idanunta. Unaisah dake kallonta ta cikin mirror, tuni taji kwalla ta cika idanunta wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta.. Shiru sukayi na wani lokaci kafin batool ta ce"sister akwai wani abu dake damuna"! "Menene"? ta tambaya tana kallon fuskarta Cikin sanyin murya ta furta"Danish, wallahi na damu da shi, bansan meyasa ya canza mana ba, ba kamar lokacin da muna a prison ba, gaba ɗaya, baya son kowa yaje kusa dashi, ko magana nayi mashi dakyar yake amsa mini, har tambayar shi nayi meke damun shi yace min bakomai..." yanayin yadda tayi maganar tamkar zata fashe da kuka.. "Hatta su Haris sun fahimci baya son suna zuwa dakin shi, shiyasa suka janye jikin su, ni so nake naji idan wani abu muka yi mashi sai mu bashi hakuri ya yafe mana" shiru unaisah tayi batare data iya furta komai ba, Dama tasan dole su damu da halin ko in kulan da yake nuna masu, batasan meyasa yake takura rayuwarshi ba, kwata kwata baya son kowa ya ra6e shi in ba ita ba, yanzu da suka samu sa6ani atsakanin su abun Ya ƙara ta6ar6arewa, har cikin ranta bata jin dadin hakan Kokarin kwantar mata da hankali tayi"pls kada hakan Ya dameki, sai kace bakisan halin shi ba tun a prison, dama can shi ba mai san shiga mutane bane, kinfi kowa sanin halin danish, baya son hayaniya, shi indai zai samu gado ya kwanta yayi bacci toh bashi da wata damuwa, ki daina tunanin ko kunyi masa laifi ne, wlh babu abunda kukayi masa abun a jininsa yake, kuma bawai ya daina damuwa daku bane, kuna aran shi" ajiyar zuciya Batool ta sauke, kalaman unaisah sun kwantar mata da hankalin ta. Bayan ta gama gyara ma Batool gashin, ta zauna itama ta gyara mata nata daga bisani Unaisah tayi masu make up, powder suka shafa da lip gloss mai kyalli launin pink. Bayan sun gama suka koma gaban closet ɗin su, inners suka fara sanyawa, Unaisah ta ɗauko mata sabuwar bra ta miƙa mata don ta sanya ta kar6a tafara kiciniyar sakata kamar zatai dambe saboda bata saba ba, batasan ya zata sakata ba, dariya unaisah tayi"bari na taimaka maki" ta faɗa tare da ruƙo hannun bra ɗin ta saƙala mata shi, ajiyar zuciya ta sauke da sauri ta koma gaban mirror tana kallon kirjinta, Yau ne karo na farko data fara sanya bra, tayi mata cuf cuf yadda kasan wadanda suka ɗauko bras din sun san size din ta. Unaisah dake kallonta ji tayi dama ita, yamutsa fuska tayi"idan kin kammala kallon madubin ga kayan da zaki saka nan na zabo maki" ta faɗa tare da daura mata su kan gado. Batare da bata lokaci ba, kowan nan su ya sanya kayan shi, tsayawa sukayi agaban mirror suna kallon tsantsar kyan sukayi gaba ɗayansu Long sleeved gown ce a jikinsu launin Ice blue sai kyalli take da ɗaukar ido, ga wata hadaddiyar Silver necklace da suka saka a wuyan su, yayin da wrists din hannunsu ke asanye da Beaded Bracelets, sun saki curly hair dinsu ya lullu6e gadon bayan su, yadda kasan wadanda zasu halacci gasar miss word su kansu sun jinjina ma haɗuwarsu, sun tasa madubi gaba sai jujjuya jikinsu sukeyi. Saida suka gama kallace kansu kafin unaisah ta dauko masu fragrance set suka fara barin ruwan turare ajikinsu saida kamshin ya gauraye dakin su tukunna su ka dakata da shafa shi. "Wlh munyi kyau, Allah Ya zuba mana ruwan kyau sister" batool ce ta fada tana yarfa hannayen ta, murmushi unaisah tayi tana kallon kanta ta cikin mirror "Sai yau na kara ganin kamanninmu Allah, dukanmu tubarkalla dogaye ga dogon hanci, ɗan bakin mu heart shaped, gaskiya mungode ma Allah..." proudly ta faɗa "Bari na dauke mu hoto" da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan pillow, ta dawo kusa da batool suka hada kai ta fara daukar su pics har kusan kala ashirin.. "Bari inje in nuna ma aunty ummi wankan dana dauka nasan zata ruɗe da kyawuna" da gudu ta fuce daga ɗakin hannayenta ruke da bazar rigarta kamar wata amarya, har ta fuce daga dakin unaisah bata daina kallonta ba har saida phone dinta ta fara ringing kafin ta kau da idonta, screen din wayar ta duba ganin sunan My man yasa ta ɗan yi murmushin gefen fuska kamar yasan jiran kiran shi takeyi girman kai ne ya hana ta fara neman shi, zama tayi daga gefen gadon ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta Tayi shiru bata ce komai ba, tana jiran jin me zaice mata. "My Angel..." bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa"ɗazu na tura maka message, nace ka sauko down muyi breakfast why didn't you come?" Ta faɗa tana haɗe fuska kamar tana agaban shi. Softly ya furta"Naga sakon da kika tura min, amma ban fahimci me kika rubuta ba, shiyasa ban zo ba" jikinta ne yayi sanyi lakwas duk sai taji ba dadi "Meyasa baka kira ka tambayeni me na rubuta maka ba? Shiru yayi bai bai tanka mata ba. "I have no answer,"? Still baice mata komai ba. "Okey, kayi breakfast dinka"? Sai lokaci taji ya ɗan sauke ajiyar zuciya"nayi, Haris ne ya kawo min adaki" Lumshe idanunta tay, wani irin yanayi take jin kanta, Sautin muryarshi ba karamin rikita ta ya ke yi ba, A hankali ta kwantar da bayanta jikin pillow, dadin muryar shi take ji, idan suna yin waya har bata son suyi sallama da juna ______________________________✍️ Lokacin da motar dr shureim Ta biyo kan titin Obie Estate tun kafin su karasa Benazir take bin ganin da kallo yau ne karo na farko da ta fara zuwa, ta ruɗu da ganin haɗuwar katafaren entrance gate din dake abuɗe ga wasu fusatattun sojoji dake tsaron ƙofar cikin taku na majiya karfi suke kai komo abakin gate din sun kasa sun tsare babu mahalukin daya isa ya ƙetare kofar batare da an basu izni ba. Hatta dr shureim bai ta6a zuwa ba, ya dai san estate din amma bai ta6a shiga ciki ba. rage gudun motar yayi slowly yayi parking dinta gefe guda, don yasan ba lallai su barsu su shiga ciki ba. ."Anila kina ganin zasu barmu mu shiga"? Benazir ce tay mata maganar tare da dubanta "Eh, amma dole saida iznin wani daga cikin mutanan gidan," ta fada tare da daukar wayarta daga cikin handbag, A hankali ta kwantar da baby junaid kan seat ta dubi dr shureim"bari na kira daddyn azeezaty din" amsa mata yai da toh, ta bude murfin motar ta fito daga waje ta danna ma shi kira, bayan ya ɗaga ta kara wayar a kunne. "Taj, munzo yanzu haka muna a bakin entrance gate na estate din" On the other hand taj yace"tare da wa kike zo"? Lokaci daya taji gabanta Ya fadi, tunawa da gargadin da sukayi mata sam ta manta. Dakyar tay karfin halin ce mashi"tare da Benazir, sai yayanta dr shureim shine ya kawo mu..." bata kare maganar ba taj ya furta"why Anila? Why? Kin manta kashedin da chief yayi maki? Akan me zaki zo da su gidan nan? Ke kadai fa nace kizo saboda Angel tana son ganin junaid" Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba duk tabi ta rude, ta fahimci ranshi ya 6aci "Kina atare da su ne"? "A'a na fito daga cikin motar ni kadai ce, Zanyi maka bayani, nasan zaka fahimce ni"! Shiru yayi yana sauraron ta cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri idan na bata maka rai, nasan ban kyauta ba, amma ba yadda zanyi ne, bazan iya jure ganin Benazir cikin mawuyacin hali ba, wlh baka ga yadda ta koma ba, saboda rashin Unaisah bata da kwanciyar hankali, ko abincin kirki bata iya ci duk ta rame, Kai kace min da zarar ta dawo hayyacin ta, in sanar da ita cewa yarta ce, yanzu tasan komai..." bata kare maganar ba, Taj yace"kina nufin kin fada mata har abunda ya faru da mu"? Yamutsa fuska tay tamkar zata saka mashi kuka tace"na faɗa mata, amma na gargadeta akan kada ta bari kowa yasan kuna araye, sannan nace mata kada ta bari unaisah ta gane itace mamanta kamar dai yadda kukayi mana bayani haka itama na sanar da ita, kuma tayi min alkawarin ba zata sanar da kowa ba" "yayanta fa kin fada mashi? Shiru tayi gabanta na faduwa Har saida ya sake maimaita tambayar da yayi mata kafin tace"A'a bai sani ba, mun dai fada mashi zamu zo gurin Azeezaty ne, kuma kasan dr shureim bai son ka ba, bazai iya gane komai ba, balle shi da bai cika shiga sabgar da bata shi ba wlh baida matsala, mutunne mai kamun kai" saida takai aya kafin yace"Anila na fahimce ki, amma Bana so Benazir ta yi wani abu da zaisa unaisah ta gane cewa mahaifiyarta ce, pls komai ya tafi yadda muka tsara shi, idan kika bari aka samu matsala ke da chief ne" "In sha Allah baza asamu matsala ba, zamu kiyaye" Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar shi"okay, zanyi magana da chief, ku ƙara hakuri," amsa mashi tay da toh, bayan sunyi sallama ta buɗe murfin backseat ta shiga daga ciki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, atare dr shureim da anila suka kalle ta "Ya ake ciki"? Murmushi ta danyi tare da kallon benazir tace"yace mu jira, za'a bamu iznin shiga" ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke. Dr shureim yace"junaid har yanzu bai farka ba, ko dai kin bashi sleeping pill ne" yar dariya tayi"a'a wlh, nima nayi mamakin baccin shi kamar wanda yasha ƙwaya, may be ko dan jiya bai samu isasshen bacci bane..." ta faɗa tare dakai hannu ta shafa gefen fuskarshi. Benazir tace"Allah nafara gajiya da jira, Allah yasa kada su shanya mu awaje, nifa naƙosa naga babyna" cike da zolaya dr shureim yace"bari maman babyn taji kina kiran sunan ƴarta da sunan taki, kotu ce zata rabaku" dariya sukayi gaba dayan su. Kafin wani daga cikinsu Ya ƙara furta kalma, Suka ji anyi knocking window glass din motar da sauri dr shureum ya sauke glass din Wani soja ne tsaye fuskar shi a murtuke ba annuri ya furta"Who is Anila?" Yawu ta hadiya muryar ta na dan rawa tace"I am sir" "Okay, ku shiga daga ciki, an baku izni" kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, dr shureim ya tada motar ya nufi drive way din da zai sada su da cikin estate ɗin, Anila ce ta dinga nuna mashi hanyar da zai bi har suka karaso gidan chief, basu sha wahala ba, motarsu na karasowa bakin gate din jami'an dake tsaron shi suka basu iznin shiga ciki bisa umarnin mammallakin gidan hakan na nufin an san da zuwan su, tun da motarsu ta shiga benazir ta ke ta jinjina kai wato sunyi mamakin haduwar katafaren villa din, daga gefen wani stunning fountain dr shureim ya tsayar da motar. Rungume baby junaid anila tayi akan kirjinta, ta buɗe murfin motar ta fito, kafin dr shureim da Benazir suka fito daga ciki, A hankali suke karewa tamfatsetsen ginin kallo, ba su ta6a zaton za'a samun daular data kai ta Alhaji musa haduwa a birnin abuja ba, sai gashi yau Allah ya haɗasu da gidan director general Of Isod. Jikin motar suka jingina bayan su, kowa da abun da yake sakawa aran shi, musamman Benazir ta kosa ta ga taj da Angel dinta murmushi kawai take saki ita kadai tasan dadin da take ji "Bani junaid din in ruke maki shi" miƙa mata shi anila tayi bayan Benazir ta kar6e shi ta rungume a kirjin ta, Jami'an dake kai komo sai kallon su suke yi. "Ina zamu nufa"? Benazir ta fada tana kallon Anila, tayi shiru saboda batasan ina zasu dosa ba, har ta yanke shawarar kiran Taj, kwatsam Horn din mota Ya karaɗe kunnuwan su, kusan atare suka dubi hadaddiyar motar dake tunkaro kirar black Mercedes Agaban su motar tayi parking, sun ƙura ido suna jiran ganin wanene mamallakin ta. Ta ciki aka buɗe car door din, gently ya fito daga ciki gaba daya suka bi shi da ido, yana sanye da kayan kakinsu na isod ya rufe fuskan shi da mask, zagayawa yai ta other side ɗin motar ya buɗe murfin, slowly chief ya fito daga cikin, hannun shi ruƙe da wayar shi, fuskarshi sanye da face mask, gaba daya dr shureim Ya kasa dauke ido daga kallon su, musamman Benazir gabanta har faduwa yakeyi gani take kamar taj ne sai dai takasa gasgata hasashenta saboda face mask din dake akan fuskar shi yasa ta kokwanton anya shi ne? sai kallonshi take yi shi kuwa ya haɗe fuska yama ki yarda su haɗa ido da juna don kada ta samu sararin da zata gane shi ne, Hankalin Anila ba karamin kwanciya yayi ba, aranta ta ayyana ashe ma suna atare da chief din tasan already ya fada mashi kwa6ar da tayi masu, fatanta Allah yasa kada ya tuhumeta. Cikin girmamawa Anila ta gashe da su, chief ya amsa mata, dr shureim Ya mika masu hannu sukayi musaba a mutunce suka gaisa da juna. Anila ta lura da taj, dama tasan za'a rina, ita ta gane shine kuma tasan saboda Benazir ya sanya face mask, sannan yaki tanka masu don kada taji muryar shi. "Ya jikin naki" muryar chief ce ta katse mata zancen zucin nata, da sauri ta kalle shi har saida taji gabanta ya fadi, kwata kwata bata kalli fuskar shi ba, sai da yayi mata magana, ta so ta ruɗe sai taji kamar muryar Zaki. jin tay shiru bata amsa ba yasa Aneelerh tayi saurin ce mashi"jikinta da sauki, Alhamdulillah" A hankali ya dubi taj sarai ya fahimci dagangan yaƙi magana saboda ex-wife dinsa, ita kuma baiwar Allah ta tsareshi da ido saboda ta gane shi ne.." "Bismilla..." ya fada tare da nuna masu walkway din da zasu bi Gaba yai tare da taj su Aneelerh suka bi bayansu, baiwar Allah Benazir ta zama kamar mutun mutumi, jikinta duk yai sanyi laƙwas cikin muryar raɗa tace ma anila"taj ne ko"? Jinjina mata kai anila tayi" shine amma kiyi hakuri dan Allah, kada ki sanya damuwa aranki, har yanzu yana akan dokin zuciya ki bashi lokaci nasan zai kula ki." hawaye ne suka cicciko idanunta, ganin shi da tayi ya fama mata ciwon son shi dake a cikin zuciyarta. Gaba ɗaya ya canza mata, ba kamar taj din da ta sani bane ada, Ya zama babban mutun dashi, ga kyawun sura da cikar kamala, har wani ƙwarjini yayi mata, lallai da da yanzu ba ɗaya ba, cos ba zata taba manta yadda ta azabtar da shi da soyayyarta ba, ta gasa mashi aya hannu, ta raina shi kamar bawanta haka take sarrafa shi sai abunda taga dama akeyi agidan su, yanzu kuwa taj yafi karfinta, ita kanta ta shaida hakan, dr shureim dake abiye da su kwata kwata bai lura da halin da Benazir take a ciki ba, hankalin shi baya akan su abakin wata glass door suka dakata da yin tafiyar, Chief ya buɗe masu kofar, Sanyin a c ne ya fara busowa ta cikin ɗakin mai dadin gaske, atare chief da taj suka shiga, Benazir da Aneelarh suka shiga daga bayansu kafin dr shureim ya shigo, sitting room ne Ya gaji da haduwa, a saman sofas suka zauna, anila da benazir da dr shureim suna akan sofa mai mazaunin mutun uku, yayin da chief da taj suke a zaune kan 2 seater dake fuskantar su. Miƙewa taj yai ya nufi benazir, tayi azan zaiyi mata magana ne harta fara dan sakin murmushi bai ko kula ta ba, ya sanya hannu ya kar6i junaid daga hannunta, Ya koma ya zauna tare da kwantar da shi kan kirjin shi. Da ido Aneelah tayi mata alamar tayi hakuri ta kwantar da hankalin ta, dukar da kanta kasa tay tamkar zata sanya kuka ba dan bata so dr shureim ya gane gaskiya ba ai da tuni ta cakumi rigar taj ta rungune shi. Takun tafiya ne Yaja hankulan su ga duban mai shigowa, wani jenior agent ne Ya shigo hannun shi ruƙe da wooden tray mai ɗauke da softdrinks and snacks ya ajiye masu akan table kafin ya juya ya fuce "Bismillah, zaku iya sha" Taj ne ya fada tare da yi masu nuna da table din, Anila ta ɗauki juice ta zuba masu a cups ta miƙa ma dr shureim ya kar6a, koda ta mika ma Benazir girgiza mata kai tay alamar a'a, jiki asanyaye Anila ta fara shan wanda ta zuba mata. falon yayi tsit baka jin sautin komai sai sanyin a.c din dake ratsa fatar jikin su. Gaba daya hankalin benazir na akan taj, Ta kasa janye idanunta daga kallon fuskar shi, so take ya ɗago su hada ido yaƙi yarda, sai ma Ya maida hankalin shi akan junaid dake rungume a kirjin shi, a hankali yake shafa sumar kan shi da hannun shi, son yaron yake kamar yadda yake son Angel dinsa. "Dan Allah kuyi min bayani wanene daddyn Azeezaty a cikin ku? ina son nasan shi" dr shureim ne ya katse masu shirun nasu. Da hannu chief ya nuna mashi taj, murmushi dr shureim yayi"Allah sarki, dama inaso ne in ƙara yi maku godiya, wallahi munji dadin taimakon da kukayi mana, Allah ya saka maku da alkhairi..." atare suka amsa mashi da ameen. "Daddyn Azeezaty, Ina tayaka murna, ka ƙara gode ma Allah daya baka yarinya mai hankali irin na manya, ga kaifin basira gata da saurin shiga rai" murmushi taj yai har cikin ranshi yaji dadin yabon da shureim yayi ma angel dinsa"thank you so much," ya faɗa yana mai nuna jin dadin shi. "You should call her" chief ne ya faɗa tare da mikewa Ya nufi hanyar fita daga dakin. Curo waya yai daga aljihun kakinsa Ya kira layin Unaisah Bayan ta ɗaga yace"daughter kina ina ne"? On the other hand tace"ina adakin mu" ɗagowa yai tare da kallon su anila, gaba daya hankalinsu na akanshi. Kwantar da baby junaid yai kan sofa, yai ma anila nuna da hannu da sauri ta mike taje ta dauki baby junaid ta rungume a jikinta. Miƙewa taj yayi ya nufi bakin kofar dakin ya tsaya saboda baison su ji abun da zasu tattauna, muryar shi kasa kasa ya ci gaba da yi mata magana "Auntynki tazo tana son ganinki" yana juyo sautin ihun farin cikin data saki "Daddy, atare da baby junaid tazo"? "Eh, harma da aunty Benazir dinki," "Wayyo Allahna, gani nan zuwa daddy" da sauri yace"ban gama magana ba" nutsuwa tayi tana sauraron shi "Ina yan uwanki suke"? "Suna a falo" "Okay, bana son kizo da kowa, ke kaɗai zaki zo..." "Amma daddy suna son ganin baby junaid, na riga na fada masu mun hadu da aunty anila kuma sun kwallafa rai da son ganin ta" "Look, kija baki kiyi shiru, kada ki fada masu game da zuwanta, kin riga da kinsan komai ba sai nayi maki bayani ba, idan har yaran nan suka zo zasu iya furta wata kalma da zaisa agane wani abu game daku, kuma hakan ya sa6ama dokar aikin mu, shiyasa nace kizo ke kadai, ke ma din dakyar na samu chief ya amince su ganki, Ina fata kin fahimce ni"? Shiru tayi da alama bata ji dadi ba Fahimtar yanayin ta yasa shi sassauta muryar shi"Idan ki ka kwantar da hankalin ki, next time zasu sake dawowa ne in yaso sai su hadu da su" ajiyar zuciya ta sauke"toh daddy, na fahimce ka, amma ya zanyi da batool? Ta riga da taji komai, namanta tana adakin, dan Allah daddy kabari in zo da ita" shiru yayi baice mata komai ba "Daddy, naji kayi shiru, pls ita kadai, batool ba zata bamu matsala ba, tana da hankali, zan ja mata kunne akan kada ta furta komai da zaisa su san wani abu dangane da rayuwar mu, nasan zata fahince ni" Numfasawa yai kafin yace"ya zanyi dake tunda kin matsa akan son zuwa da ita, kuzo amma kinsan Allah idan aka samu matsala ki kuka da kanki" ya fada da zolaya, dariya tayi"ba abunda zai faru in sha Alah" "Okay," ya fada tare da yi mata kwatancen inda sitting room din yake. "Pls kada ku dauki lokaci, suna jiranku" cike da zumudi ta amsa mashi da toh, katse kiran yai tare da juyawa ya dubi su dr shureim sunyi shiru suna jiran tsammani, kallon benazir yayi ta kifa kanta kan sofa hand, idan yace baiyi kewarta ba yayi karya, almost 17yrs rabon shi da ita, ta canza mashi ba kaɗan ba, ya danyi mamakin girmanta, ta zama babbar mace ba kamar lokacin daya aureta ba, yar siririya da ita sai rashin kunya cike da kai, daurewa kawai ya ke yi ba ya san ta gane ya yi kewarta yafi so ta ɗanɗani irin ɗacin da ya ji aran shi na irin bakin cikin da ta kunsa mashi, Abun Ya ta6a zuciyar shi ba kaɗan ba, ƙwara itama taji ajikinta kamar yadda yaji, batare da sanin su ba, Ya fuce daga sitting room din Ya koma waje Ya tsaya zuciyar shi cike fal da tunaninta, Allah sarki tsohuwar zuma, yajima yana tambayar kanshi meyasa zatay mashi haka? Laifin me yayi mata? bai ta6a tsammanin tsanar da tayi mashi takai harta haifa mashi jinjira ta ajiye acikin kwamin wanka ta gudu tabar su, kusan shekara goma sha bakwai, bata ta6a waiwayarsu ba, taya zai iya yafe mata cikin sauƙi? Idanunshi ne suka ciko tab da kwalla, da sauri ya jingina kanshi jikin bango, Allah kadai yasan radadin da yake ji acan kasan zuciyar shi, Maganar anila ya fara tariyowa inda take ce mashi bafa yin kanta bane, shiga akayi tsakaninsu, bada son ranta ta gudu ba, har yanzu tana son su, girgiza kai yai cikin karyayyar murya ya furta"ban yarda ba, nasan wacece Benazir, zata iya aikata fiye da haka ma, dama ba sona takeyi ba..." shi kadai yake sambatun shi abunne ya dame shi. "Har yanzu shiru basu ƙaraso ba, ko dai Azeezatyn tana a school ne"? Dr shureim ne yayi maganar Anila tace"nima nayi tunanin hakan, watakil sai an daukota daga school, mu dan kara hakuri" ta fada tare da kallon Benazir da ta langwa6e kai jikin sofa, ta lumshe idanunta... Tsantsar tausayinta ne ya kamata, dr shureim yayi tunanin saboda azeezaty ta shiga halin damuwa hakan yasa shi yi mata gyaran murya ta buɗe ido ta kalle shi"meke damunki ne? Tun da muka shigo na lura da yanayinki! Nasan bai wuci saboda azeezaty bane ko"! Murmushin yaƙe ta sakar mashi cikin sanyin murya tace"kamar ka sani ya shureim, wlh na ƙagara da in ganta, kamar zan zauce" yar dariya yayi tare da miƙa hannu kan table din gaban sofa din, Ya dauki juice Ya zuba a cup, yana kokarin kaiwa bakinsa Ya ɗan dakata Yana sauraron muryoyin da kunnuwanshi suke jiyo mashi "Mu je ciki mana" "Dan Allah ki fara shiga, ni wallahi kunya nake ji," "Meye abun kunya a ciki, Aunty Anila ce fa, tare da aunty Benazir, ni ki wuce mu shiga..." Kusan atare Anila da Benazir suka dubi ƙofar sitting room din, su biyu ne ɗaya ta rurruƙe ɗayar da ta turje akan ba zata shiga ba, Kamar zasu yi dambe, kwata kwata basu ga fuskokin su ba, Ita Batool mayafin da ta yi rolling akanta ne ya warware ya rufe fuskarta, sakamakon ingizatan da unaisah takeyi, Yayin da ita kuma Unaisah take abayanta tana kokarin tursasa mata akan ta shiga, murmushi Anila da benazir suka saki suna kallon ikon Allah Cikin sanyin murya dr shureim Ya furta"Ki bi ta a hankali pls, kada ki ja ta fadi taji ciwo" Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (300) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 44 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 06, 2024 Sponsored Link BOSS BATURE✊ Jin maganar dr shureim yasa ta saki Batool da ke ta faman yin haki, tana ta ƙoƙarin Gyara veil ɗinta daya rufe fuskarta Unaisah taja hannun ta suka nufi Ciki, Gaba ɗaya idanun su Benazir na akan su, Yadda suke tafiya a tsanake cikin nutsuwa yayi matuƙar burge su, Tamkar tagwaye komai na jikinsu kala ɗaya, gwanin ban sha'awa suke kallon su, Batool sai kiciniyar gyara mayafin takeyi takasa ga ɗan kunnanta da ya maƙale gashinta kwata kwata Unaisah bata lura da halin da take a ciki ba, sai janta ta ke yi. "Babyna" Benazir ce ta kira ta da sauri ta dubi inda take atsaye lokaci ɗaya ta saki murmushin farin ciki, ta saki hannun Batool cike da zumudi ta nu fe ta Benazir ta rugumota a kirjinta kamar zasu koma mutun ɗaya, wani irin sanyi ne Ya ratsa zukatan su, kamar sun yi shekara ba su haɗu ba sunyi kewar juna. Fuskar Aneelerh ɗauke da murmushi take kallon su har cikin ranta taji dadin faranta ransu da ta yi... "Babyna, nayi kewarki, shi ne kika tafi kika barni, fushi nake dake baki damu dani ba" ta fada tare da ɗago kanta ta haɗe fuska alamar bata ji dadi ba' rufe fuska unaisah tay da tafukan hannayenta cike da jin nauyinta ta furta"i'm really sorry mommy na, wallahi na damu dake, ban manta dake ba kina araina" Murmushi Benazir tay, tare da manna mata peck a forehead ɗinta, ta tallabo fuskarta da tafukan hannayenta, wani irin kallon so da kauna take bin ta da shi kamar zata maida ita cikin cikinta, tuni Unaisah tasha jinin jikin ta da ganin irin kallon ƙurullan da take yi mata.  Bakomai take tunawa ba face lokacin data barta a kwamin wanka yar jinjira da ita cikin jini, sai gashi Allah ya raya abun shi, ta girma ta zama ƴar budurwa da ita, tsakaninta da taj sai godiya yayi namijin ƙoƙari gurin rainon Angel, har abada bazata ta6a rabuwa da shi ba, ko da bazai kula ta ba sai ta san yadda tay ta maida auran su ko dan saboda Unaisah, ganin bata da alamun daina kallonta ne yasa ta ƙara rudewa muryarta adabarbace ta furta"Ya jikin naki? Kin ji sauƙi"? Yar dariya Benazir tay don ta fahimce unaisah ta gano ta Ɗaga mata gira tay"Alhamdulillah my baby, naji sauƙi sosai..." "Yanzu kin gane ni wacece" dariya suka yi gaba ɗayan su, Hakan Yasa ta fahimci taji sauƙi yanzu tasan ita ba ƴarta bace. . "Ki ɗauka har yanzu ban dawo cikin hayyacina ba, saboda bana so ki daina kira na da sunan mamanki, kuma bana so na rasa kulawar da kike bani" tattausan murmushi unaisah tay"in dai wannan ne baki da matsala dani, zan cigaba da kiranki mamana, babu abunda zai canza" Gaba ɗaya Sun maida Hankali akan Unaisah, In ka cire dr shureim wanda gaba ɗaya ya tattara Hankalin shi akan Batool dake ta ƙoƙarin gyara mayafinta ga raɗaɗin da kunnanta ke yi mata duk tabi ta burkice, ajiye cup din hannun shi ya yi kan table tare da miƙewa ya je gabanta ya tsaya ya ruƙo Veil ɗin Zai gyara mata jin hannun mutun yasa muryarta na rawa ta furta"Earring ɗina Ya maƙale gashina za fi nake ji"  'Okay, calm down, I'll help you."  jinjina mashi kai tay, ruƙo mayafin yai tare da zame shi Ya sauko kan kafaɗarta bai kalli fuskarta ba sai da Ya Cire mata earring ɗin da ya sarƙe gashin, kafin ya ɗago da idanunshi slowly ya dubi fuskarta adai dai lokacin ta buɗe idanunta kaitsaye suka shiga cikin nashi bai san ya akai ya tsinci kan shi da jin matsanancin faduwar gaba hatta yanayin bugun zuciyarshi saida ya canza tamkar ana buga ganga. wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarce shi, kamar yadda yake kallon ta haka itama ta ƙura mashi kyawawan idanunta sai faman kyafkyafta su takeyi kamar Yaji ya shiga cikin su, gaba daya ta razana da kallon da ya ke yi mata ga wani yanayi da ta tsinci kanta mai wuyar fassaruwa,  hankalin ta ya ɗan tashi, duk tasha jinin jikin ta aranta ta ayyana wanene wannan? Meyasa ya ke kallona? Ko dai jira yake in yi mashi godiya ne"? Muryarta adabarbarce ta furta"Um... thank you.'   sam Ya kasa tanka mata sai kallon ta ya ke yi, yau ne karo na farko da suka fara ganin juna,  amma dukansu sun ji wani baƙon al'amari a zukatansu Hankalin su Unaisah kwata kwata baya akan su.. Abunda yaɗan ɗaure mashi kai kaman nin shi da yarinyar, tun da Allah ya halicce shi bai ta6a ganin ɗan adam din da yake bala'en kama da shi irin Yarinyar nan ba! Ko Benazir da take kama da shi kamannin su bai kai haka ba, ita wannan kamar anyi photocopy din fuskar sa ne don ma ya ɗan manyanta. "Baby na Who is she? Is she your sister?'  muryar Benazir ce ta katse Kallon kallon da suke jefa ma juna su, ajiyar zuciya dr shureim ya sauke tare da juyawa ya koma kan Sofa Ya zauna yana mai mamakin kaman nin shi da yarinyar yau yaga abun al'ajabin daya rikita shi. "Sunan ta Batool Sister dina ce" da alamun rudani Benazir take kallon fuskar Batool Ta ɗan razana da ganin kaman nin su, aruɗe ta dubi Dr Shureim ta kuma juya ta kalli Aneelerh hankalinsu gaba ɗaya ya koma kan fuskar Batool, itama Aneelerh tayi mamakin ganin fuskar yarinyar kamanninta sun 6aci dana dr shureim. Sun yi matuƙar ruɗewa da ganinta, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin irin kallon da su ke yi mata Jikinta har Ya fara kakarwa, Unaisah ta ɗan rude da ganin kallon da su ke yi ma Batool amma sai tay tunanin ko dan sunga kamanninta da dr shureim ne hakan yasa ta ɗan yi murmushi tare da ruƙo hannun Batool dake kerma tace"Sister, kinga aunty Benazir, ga yayanta Dr Shureim da nake baki labarin kamannin ki da shi, dama nasan za ku yi mamaki idan kuka haɗu" dakyar Batool ta ƙaƙaro murmushi akan fuskarta hankalinta sam ba'a kwance yake ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. ' Miƙa mata hannu Benazir tay jiki asanyaye ta matsa kusa da ita, ta yi hugging dinta tightly a kirjinta lokaci ɗaya ta fara jin bugun zuciyarta na ƙarfafa haɗe da faduwar gaba, nan take fatimar dr shureim ta faɗo mata aranta Ƴar jinjirar da ta rasu bayan haihuwar ta da watanni ita kanta batasan ya akai ta tsinci kanta da tunanin yarinyar ba, sam ta kasa raba Batool daga jikinta kamar zata maida ita cikin ta a hankali take shafa bayanta da  tafukan hannayen ta, Batool ta yi shiru tana jin wani irin sanyi da kwanciyar hankali Yana ratsa zuciyarta. Gyaran murya dr shureim yayi masu, A hankali Benazir ta raba jikinta daga na Batool "Kun barsu a tsaye ku zauna mana" ya fada tare da nuna masu Sofa, ruƙe hannun Batool Benazir tay acikin nata suka zauna suna fuskantar dr shureim. Unaisah ta nufi Aneelerh tun shigowarsu take ta ɗaukin son taga baby junaid, ta ɗanyi jinkiri ne don kada ta 6ata plan din su.. "Aunty Anila ina wuni? Ya su Mami da zahra" Magana takeyi ma anila amma hankalinta na akan baby junaid da anila ta rungume a kirjin ta, wani irin kaunar shi take ji kamar ta ƙwace shi daga hannun Aneelerh, ta yi kokari kame kanta ne kada ta cika zaƙewa agane sun san juna da jimawa  fuskar Aneelarh da fara'a tace"lafiyalou, Zahra tana gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.."  "Lafiyalou Aunty Aneelerh" Dr shureim Yace"Babyn Benazir, Ni baki ganni bane, tun da kika ga mamanki kin manta da mu ko" ɗan murmushi tay"ba haka bane ya shureim, kana araina, ina wuni, ya su mami? ina zeenatu"? "lafiyalou Azeezaty, su mami suna gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.." "Lafiya lou, naga jikin mamana yayi sauƙi, ubangiji Allah ya ƙara mata lafiya"  "Ameen babyn mamanta" yar dariya sukai, kafin wani ya kara magana wayar hannun shi tay ringing daga cikin aljihunsa, a hanzarce Ya curota Ya duba sunan me kiransa, mikewa yai tare da kallon Benazir dake kallon shi"Mami ce"? "A'a bakuwar number ce, bari na ɗaga naji" cikin sauri Ya nufi hanyar fita daga sitting room din, zuciyar shi cike fal da tunanin yarinyar daya tsaya ma shi aran shi, baiso kiran ya katse mashi kallonta da yake yi ba, bai kula ba tun da ya miƙe Batool tabi bayan shi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, harya kusa fucewa ya ɗan juya don ya saci kallonta karaf suka haɗa ido da juna, sanyayyar murmushi ya sakar mata tare da ɗaga mata hannu, kunyar shi ce ta kama ta da sauri ta juyar da kan ta gefe ɗaya, mutumin ya kwanta mata aranta tun da Unaisah ta bata labarin kamannin su, yau da ta gan shi face to face sai taji ta kamu da ƙaunar shi. Da ido Unaisah tay ma Batool nuni da data gaida su Aunty Aneelerh muryarta na dan rawa ta furta"Aunty Anila Ina wuni" da fara'a Anila ta ce"lafiyalou sister fatan mun same ku lafiya"  "Muna lafiya"  Bata kau da ido daga kallon fuskar Batool ba, tana so tasan wacece ita? Ko itama ɗaya ce daga cikin yaran da zahra ta bata labarin badakalar da aka sha akan su ranar dinner din prime minister, ko kuwa dai yar uwar chief ce? Ta ayyana acikin zuciyarta, Ta dai bar abun aranta har zuwa time da za su yi magana da unaisah, tayi zurfin acikin tunanin ta taji hannun unaisah akan nata a hankali ta kau da ido daga kallon batool ta dubi unaisah, kar6ar junaid tay daga hannunta ta kwantar da shi kan laps ɗinta, ta ƙura ma shi ido tana kallon shi kamar zata lashe shi.. "Yau dai na kawo maki babynki, da kike ta zumudin son ganin shi, Ina fata na wanke laifi na" ta faɗa tana leƙen fuskarta, jinjina kai Unaisah tay"da har nayi fushi, da ace baki kawo min shi ba, zansa daddyna ne ya kawo ni har gida don inga ɗan ƙanina, amma yanzu kin wanke kanki agurina" ta faɗa da murmushi akan fuskarta Anila tace"Tun acikin mota yake ta sharar bacci, Kamar wanda Yasha ƙwaya" "ay ko dai yanzu zan tada shi, saboda ba karamin missing din shi nayi ba...." kafin ta ƙare maganar Baby junaid Ya fara mutsu mutsu alamar zai farka lura da hakan ya ɗaga hankalin Aneelerh, fargabanta kada junaid ya kwafsa masu, tasan muddin ya farka zai yi wuya in bai gane Angel  ba kamar yadda kwanaki ya shaidata a hoto sauƙin ta ma dr shureim ya fita daga ɗakin dama shine damuwarta bata da matsala Benazir tasan komai already sunyi plan. burinta Ya farka su haɗa ido da juna matsawa tay da fuskarta saitin ta shi ta kurama shi idanunta, miƙewa batool tayi ta dawo gefen Unaisah ta zauna tana kallon junaid ba ta son ta nuna zumudinta akan shi saboda unaisah ta kwa6eta, shiyasa taƙi sakin jiki kada tay wani abu ba dai dai ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Da wata irin kasala Ya karasa buɗe idanunshi, sun kaɗa jawur da su, biji biji yake ganin fuskar mutun a saitin tashi, red lips dinsa na kerma ya furta"mommy," shiru yaji ba'a tanka mashi ba, a hankali ya ɗaura yatsun hannayen shi akan fuskar Angel ya shafata har zuwa saitin la66anta ya ɗan matsa su kamar ya samu abun wasa, sam bai gane wacece ba saboda idanunsa sun disashe "Mommy" ya sake ambaton sunan yana faman yamutsa fuskar shi. Jin shiru taki amsa mashi ne yasa shi murza idanunshi da yatsunsa suka washe ya sake duban fuskar Unaisah dake yi mashi murmushi, shiru yayi yana kallonta yanayin fuskarshi ya nuna kamar ya ruɗe da ganin ta, tsawon mintuna bai tanka mata ba, kowa yayi shiru suna jiran ganin me zai yi  Tsinin hancinta Yaja da hannun shi, ta lumshe ido tana dariya, shima sai ya kama dariya kamar sun san juna, lamarin ya daure ma su anila kai, da alama junaid yayi azan mafarki yakeyi Cikin sanyin murya ta furta"My little bro" Lokaci ɗaya yanayin fuskarshi Ya canza Ya kura mata ido Yana kallonta ba tare da ƙyaftawa ba,  Unexpectedly taji ya furta"ANGEL"? Waro idanu waje tay tare da buɗe baki ta dubi Batool itama mamakinne Ya kamata saboda ta faɗa mata basu ta6a haɗuwa da juna ba wannan ne karo na farko Sam Ta ƙasa furta kalma har sai da taji Ya ce"Angel uhm? Angel ɗina ne? Yayata" Sautin muryarshi baya fita dakyau ta fahimci kamar baya jin dadi, ruwan hawaye ne suka taru akan fuskarta, cike da jin dadi ta jinjina mashi kai  la66anta na kerma ta furta"ni ce" Aneelerh sai faman sakin murmushi ta ke yi dama tasan zai yi wuya in bai gane ta ba. Still da ruɗu akan fuskar shi, kokwanto yake, kamar bai yarda ba, Lumshe idanun shi yai tare da buɗe su. ɗago da kan shi tay tare da kwantar da shi saman kirjinta, ta tallabe shi tare da manna mashi sumbata har sau uku kan cheeks dinsa Gyaran muryar da Aneelerh tay mata ne yasa ta ɗago adabarbarce ta dube su sam ta manta da Benazir duk saita kama kanta tana faman rarraba idanu  akan su, Basarwa Benazir tayi tamkar bata ji me Junaid yace ba sarai ta fahimci ruɗewar da Angel tayi tasan don saboda ita ne kada ta gane wani abu. Tun da Aneelerh tay gyaran murya junaid ya kalle ta tayi azan zai sanya rigima akan ta ɗauke shi kamar yadda ya sa6a yi ma kowa ƙiwuya amma wani iko na Allah sai ta ga bai yi ba, aranta ta ayyana watakil ya ga ne Angel dince shiyasa ya yarda da ita, miƙa hannu Batool tay da niyar ta dauke shi Ya maƙe kafaɗa alamar ba zai je ba. Anila tace"sai kunyi hakuri da shi, baya da koshin lafiya" atare suka haɗa baki gurin furta"Allah ya bashi lafiya" ta amsa masu da ameen "Kana buƙatar wani abu"? Cikin kulawa unaisah tay maganar tana kalon fuskar shi Ya nutsu Yana ta kallonta "Batool zubo mashi juice a cup" unaisah ta fada tare da kallon ta da sauri batool ta ɗauko juice din da dr shureim Ya aje a cup bai sha ba ta miƙa wa Angel ta kar6a ta kanga mashi abaki A hankali ya fara sha. "Naji shiru yaya shureim bai dawo ba" ta faɗa tare da kallon Anila "May be bai kammala Yin wayar ba" acewar Anila Sauke ajiyar zuciya ta ɗanyi har yanzu da sauran damuwa akan fuskarta. Wrist watch din hannunta ta duba karfe ɗaya da rabi "Bansan lokaci yaja har haka ba," Anila tace"nasan mami zata neme ni" "Batasan kin fito bane"? Ta sani amma ce mata nayi gidan ku zanje" Da zolaya Benazir tace"Mai karya dan wuta dai," dariya Anila tay.. "Naji shirun yayi yawa, bari naje na duba Ya shureim" ta faɗa tare da miƙewa ta fuce daga dakin Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke tare da kallon su Unaisah, Hankalinta Ya kwanta da ganin yadda junaid Ya saki jiki da ita. "Aunty Anila ki bani wayarki mu dauki hoto, Na bar nawa a daki.'  Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Okay" ta faɗa tare da zaro wayar tace"bari nayi maku pics din da kaina, ku gyara" hotuna ta fara ɗaukar su kala kala wani daga zaune wani daga tsaye wani kuma sukayi atare su uku junaid dai yana a maƙale da Unaisah Batool tay kwakwar ta ɗauke shi Yaƙi yarda da ita, bayan sun gama ɗaukar hotunan Anila ta ɗibi snacks a dan plate ta ba unaisah" ki bashi yaci, da safe baici abincin kirki ba" kar6ar plate din tay ta fara bashi abaki Yana ci. Lokacin da Benazir ta fito waje neman Dr shureim A tsaye ta hango shi jikin Motar shi yana yin waya, da sauri ta nufe shi adai dai time din ya kammala yin wayar"ya shureim lafiya naga ka dade baka dawo ba" fuskar shi babu walwala Ya ce"Zeenatu ce ta kira ni da layin tani, tana kuka bata jin dadin jikin ta tace inzo gida tana son gani na" "Baiwar Allah, dole taji ba daɗi ya shureim, Banji dadin yadda Uncle yake takura rayuwarta, ni nasan hada damuwar hakan" ta fada cikin sanyin murya tana kallon shi "Ka tafi ya shureim, Inyaso sai mu tsaida me abun hawa Ya kai mu gida" girgiza kai yai"a'a bazan iya tafiya nabarku ba, zan bata hakuri ta jira zuwa lokacin da zamu koma gida" ya fada yana kokarin danna mata kira da sauri Benazir ta ruƙe hannun shi amarairaice ta furta"a'a ya shureim kada ay haka, tunda kaga ta kira ka da akwai wani abu dake damunta, tana son ganinka, kuma kaima nasan hankalin ka bazai kwanta ba in har ba zuwa kai gurin ta ba..."  shiru ya yi jimm yana nazarin maganarta, aranta Allah Allah take Ya tafi duk don saboda ta samu taj yace zai kaisu a motar shi ɗagowa yai da ido Ya dube ta"zan tafi amma zan dawo zuwa anjima in ɗauke ku" Amsa mashi tay da toh ka kula min da kanka" murmushi ya ɗanyi mata harga Allah baiso tafiyar shi ba, saboda yarinyar nan mai kama da shi ta tsaya mashi aranshi. Akan idon Benazir motar dr shureim ta fuce daga gidan, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da duƙar da kanta ƙasa, damuwa ce cunkushe a cikin zuciyarta, ga dai yarta Allah ya nuna mata da ranta da lafiyarta kuma tayi farin ciki mara misaltuwa sai dai bata jin zata samun sukuni da kwanciyar hankali in har taj bai yafe mata ba,  har yanzu tana son mijinta kuma bata jin zata iya rayuwa da wani ɗa namiji a duniyar nan in ba shi ba, zurfin tunani ta shiga da ace tun farko da ya aureta sunyi zaman lafiya zai iya yi mata uziri amma Yanzu koda yaji cewa Asiri akai mata ta gudu tasan bazai ta6a yarda ba saboda yasan wacece ita Cikin karyayyar murya ta furta"Halina ne Yaja min, Ni na ja ma kaina..." batai aune ba taji safkar hawaye kan kuncin ta, da sauri ta sanya tafin hannu ta share ƙwallar, kafin ta juya ta nufi hanyar koma wa sitting room din tana ta ƴan waige waige cike da sa ran zata ga 6ullowar taj sai dai har ta shiga babu shi babu alamar shi... __________Ummin America Futowa tay daga bedroom din ta jikinta sanye da bubu gown ta material, tay rolling akanta, flat shoes ne a kafarta, matsawa tay gaban handrail ta dafa tana kallon downstairs, A falo ta hango su gaba ɗayan su banda mutun uku, kowan nan su yana azaune kan rug sun haɗa kai suna rubutu a cikin notebooks din su, Sajeed ne kadai ya zauna kan sofa da alama shi ke koya masu rubutun. Zura hannayenta tay acikin aljihun rigarta, ta nufi stairs cikin nutsuwa take taka matakalar ta sauko down ta nufe su babu wanda Ya lura da ita a cikin su har sai da tay masu gyaran murya tukunna suka dago da kai suka kalle ta har suna haɗa baki gurin furta"Aunty Ummi zo ki ga Rubutun mu, Ki za6i nawa yafi kyau" kusan atare suke mike tare da kewayeta kowa Ya miƙa mata notebook din shi. ƙin kar6a tay gudun kada ta haɗa rigima kallo ɗaya da tai ma rubutun su sai da taji gaban ta ya faɗi ganin wani jagwalgwalo, a fakaice ta kalli sajeed karaf suka haɗa ido da juna da sauri Ya kumshe dariya yai mata alamar ta duba mana. "Aunty ummi nawa zaki fara dubawa, nafi su abun kirki" Jemimah ce ke rokon ta, kar6ar book din tay tare da duba rubutunta itace ke yin rubutu shigen na thailand ka rasa ta yadda take jagwalgwala shi "Aunty ummi in kin gama duba nata saura nawa" acewar Azeeza, Deeja tace"wlh na riga ki nawa zata duba" kamar zasu sanya mata rigima. Jinjina kai ta yi"Jemimah Kinyi ƙoƙari ki dage kin ji, idan kika maida hankali har kyauta zanyi maki" uban tsalle ta daka na murna hada yi ma Azeeza gwalo ta kar6i notebook dinta tana ta murna "Muga naki azeeza' mika mata tay aranta ta ayyana tab lallai wlh da a school suka rubuta Iya shegen nan, jakkin duka zasu ci' amma a fili sai ta ɗan murmusa tace"kema kinyi kokari, Ki ƙara himma" dadine Ya lullu6e azeeza ta kar6i book dinta ta juya ta nufi jemimah. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Ɗaya bayan ɗaya saida ummi ta duba notebooks din Har ƙwara Naufal Ya iya rubuta ba laifi tayi mamaki har saida ta tambaye shi ya akai yafi su iyawa, Da hannu ya nuna mata Sajeed"kullum A ɗaki kafin mu kwanta bacci, Shi yake koya min rubutu da karatu..." jinjina kai tay"Sajeed sannu da kokari, amma yakamata suma sauran ka dage da koya masu kamar yadda kake koya ma naufal" amsa mata yai da toh. Deeja sai haɗe rai take don ba'a yabi nata ba, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"rubutun ma bazan ƙara yi ba" ta faɗa tana kokarin keta littafin da sauri Haris Ya ruƙe hannunta"wayace maki rubutun baiyi kyau ba, ay naki yafi na kowa" kwa6e fuska tay tare da kallon Aunty Ummi tana faman zum6ura baki tace"amma ayni baki yabi nawa ba ko" yar dariya ummi tay"oh wai saboda ni zaki keta littafin, toh kiyi hakuri mantawa nayi amma naki yafi na kowa" washe baki tay har taji dadi.. "Ni rubutun ma yai kyau ko kar yayi ba damuwa ta bace, indai ba za'a hanani cin abinci ba" ta faɗa tana hura hanci, gaba ɗaya suka sanya dariya, girgiza kai Ummi tay"Allah ya shiryeki foodie, ke dai indai zaki samu abinci baki da sauran damuwa" ɗaga mata gira tay. Sarah da ta gama haɗe rai wurga notebook dinta tay kan sofa ta juya zata tafi  "Hey! Where are you going?' muryar ummi ce ta katse mata hanzarin ta, yamutsa fuska tay"nagaji da rubutunne zanje na kwanta" murmushi ummi tay"nasan me kike ma fushi don ban yabi rubutunki ba ko" girgiza kai tay"a'a kawai nagaji ne" daga yanayinta ummi ta fahimci zatai rawar kawai dama tana lura da ita, ta iya raina abu in baiyi mata ba. "Okey, kije ki kwanta ki huta, da anjima, da kaina zan koya maku rubutun" "Okay, thanks" ta faɗa tare da juyawa  ta nufi dakin su tana tafiya kamar zata balle tsabar tsawon ta har yanzu bata da ƙiba. "Kuma idan kun gaji ku aje karatun, kwakwalwa tana buƙatar hutu, amma fa dole ku dage ilmi yana da matuƙar amfani, you have to endure and persist before you succeed." ta6e baki parvin tay"Allah aunty ummi da kin daina wahalar da kanki gurin yi mana bayani, bamu gane komai.." sakin baki tay sototo tana kallon parvin abun ban haushi abun dariya Rubina tace"nima Allah bani ganewa, Nifa nafison in kwanta inyi bacci ko inci abinci" kallon ta ummi tay Hibba tace"dama girki kika koya mana, da yafi, kin ga sai mu dinga girka abun da ran mu yake so" Harara ta ɗan watsa mata"hauka nake in kai ku kitchen da sunan zan koya maku girki? A haka? Ku fara samun ilmin kafin in yi tunanin koya maku girkin" Hannah tace"wai komai saida ilmi, to a jika abamu musha sai mu haddace" tuntsirewa ummi tay da dariya, Sajeed dake sauraron su baisan sa'adda ya fashe da dariya ba "Aunty ummi dama kin daina wahalar da kanki gurin yi masu bayani, ba zasu fahince ki ba, har yanzu da sauran su" acewar Sajeed, tsagaitawa tay da yin dariya cike da nishadi tace"wani lokacin kamar masu hankali, wani lokacin kuma wlh kamar in hada ku da tsumagiya inta jibga" dariya sukayi gaba dayan su "Ina Unaisah da Batool? Banga gifcinsu ba, ko suna adaki ne"?  Hawwa tace"basa nan tun dazu muka je neman Unaisah don ta bamu notebooks dinmu mu yi karatu bamu ganta ba kuma bata a toilet sai dai muka ɗauko books din"  "Kun duba ko'ina baku gan su ba? Ko dai sun je dakin Danish ne"? Haris Yace danish Yana atare da chief suna karatu bana tunanin sun je dakinsa" "To Ina suka je ne"? Ta fada tana kallon su Yasmin tace"kila sun fita waje ko dai muje mu nemo su"! Shiru ummi tay bata amsa ba tunani tay ko dai sun shiga bangaren daddyn unaisah ne"? Da sauri ta zaro wayarta daga aljihu ta lalubo contact din unaisah ta kira layinta tana ta kira ba'a picking har ta katse almost 3 times Yanke shawarar kiran taj tay har wayar ta ƙare ringing ba'a ɗaga ba "Nafi tunanin suna acikin gidan nan, ku tayani neman su" amsa mata su kai toh, da gudu wasu suka nufi bangaren hagu wasu dama Suka fara bin sako da lungu suna neman su.  _________________________✍️ Bayan dr shureim ya isa gidan, a hanzarce Ya fito daga motar Ya nufi Cikin main falo Yana ta sauri saboda Hankalinsa Ya tashi Da halin da Zeenatu take a ciki Ya kosa Ya ganta ko hankalinsa ya kwanta har ya kusa fita daga falon muryar Tani  ta katse mashi hanzarin shi. "Shureim har an dawo" dakatawa yai tare da kallonta"Tani na same ku lafiya" da fara'a tace"lafiyalou, " "Ina mutanan gidan"? "Hajiya layla tana aɗaki, zeenatu kuma bata jin dadi amma na kira daddynta awaya na faɗa mashi, Yanzu haka ya turo family doc din su Yana aɗakin Yana duba lafiyarta..." tun kafin Ta ƙare maganar dr shureim Ya furta"Ya Salam! Mami tasan bata da lafiya"? Girgiza kai Tani tay"dana je faɗa mata na iske tana bacci shiyasa ban tadata ba" Hankalin shi atashe Yayi saurin nufar upstairs, azafafe Yake taka stairs din harya haura second floor, Yana isa gaban ƙofar ɗakin yajiyo wata Murya irin ta giggan tantira daga cikin ɗakin "Don't waste My time, idan baki bani haɗin kai ba, zan kira daddyn naki awaya in fada mashi,"  shesshekar kukan zeenatu yajiyo tana fadin"ni wlh banso, ka kyaleni, ka kyaleni nace banaso" zuciya da sake sake ta raya mashi wani mugun abunne ke shirin faruwa, gabanshi na faduwa Ya ture ƙofar ɗakin da hannu kai tsaye idanun shi suka sauka akan jibgegen katon nan Ya haye kan gadonta yayi mata rumfa da gabjejen kirjin shi ta maƙure kanta jikin headboard, jikinta sai kakarwa yake yatsun hannunta dana kafafuwanta sai kerma suke, ta rufe kirjinta da tafukanta, Yar rigar wanka ce a jikinta da bata wuci gwiwar kafarta ba, sumar kanta duk ta rufe fukarta....wani irin kishi ne Ya rufe dr shureim baisan sa'adda yai kukan kura daga inda yake yai wani ƙwaƙƙwaran taku Ya damƙi kafar dr mark A firgice Zeenatu ta ware idanunta akan fuskarshi la66anta sai kerma suke. Dr mark ko ajikin shi, Fuskarshi a murtuke ba annuri Ya dubi Dr shureim da ya ruke kafar shi. A gadarance yace"malam Lafiya ka ruƙe min ƙafa" ya faɗa yana bin shi da wani kaskantaccen kallo Rai a6ace dr shureim yace"uban me kake yi akan gadon ta"? ta6e baki dr mark yai tare da nuna mashi Syringe ɗin hannun shi"Ubanta ne Ya kira ni don in duba lafiyar yar sa, ko kana da Ja ne" ya faɗa tare da ɗage mashi gira, ƙarfin halin mutum ya ɗaure mashi kai ko kunya bai ji ba Ya kure karamar yarinya kan gadon ta. "Amma dai baka da hankali, Don ubanta Ya kiraka ka duba kafiyarta sai yace maka ka shigo har dakinta saman gadon ta? meyasa ba zaka tura me aiki ta kira maka ita ka dubata a falo ba? Hakan da kai ka kyauta?  Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Ganin dr shureim zai raina mashi wayau yasa shi saukowa daga kan gadon Yana wani buɗe kafadunshi Ya tsaya agaban shi"meye naka aciki huh? Yakamata kasan irin kalaman da zaka furta min, Ni ba sa'an yin ka bane, kada kace zaka shiga hurumin aikina, ba yau na fara ba!  kuma umarnin mahaifinta nake bi" A harzuke dr Shureim yace"oh shi uban natane Yace ka shigo dakinta har kan gadon ta don kayi mata allura kuma haka ake allura abi a danne mutum"? Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallon tuhuma. "Malam ka tsaya a iya matsayinka, nima in tsaya a nawa, tun wuri ka fuce daga dakin nan tun kafin na 6ata maka rai"! A kausashe Ya faɗa Yana Huci saboda baya ɗaukar raini, daga gani yana ji da karfi, juyawa yai da niyar ya koma kan gado saboda kunya bata ishe shi ba, a zafafe dr shureim Ya damƙi Strong Arm dinsa, a sukwane dr mark yai mashi wani kallo mai nuni da kashedi "Sakar min hannuna! Karka kuskura ka bari na maimaita abunda nace"! Girgiza kai dr shureim yai duk da ya ɗan sha jinin jikin shi amma baya jin zai iya bari dr mark Ya koma kan gadon zeenatu da sunan zai mata Allura, ko ba dan kishinta da yake ba hakan bai dace ba kwata kwata Hankalin Zeenatu ba karamin tashi yayi ba jikinta sai kerma ya ke yi kamar wadda sanyi ya kama cikin shesshekar kuka tace"yaya shureim ka ƙyale shi dan Allah, wlh idan daddy ya ji ka hana ya dubani ranshi zai 6aci, ni allurar ce bana so tun da akwai magani ya kyale ni in sha" idanunta sun kaɗa jawur Wata irin zufar 6acin rai ce ta wanke fuskar dr shureim  Ido cikin ido suke kallon kallo tsakanin su, Taurin kan dr shureim da kafiyarsa sunyi matuƙar daure mashi kay,  mutane da dama suna jin shakkar shi sai gashi yau Allah Ya hada shi da shureim  "Yaya shureim na roƙe ka, ka sake shi, bana son tashin hankali"  "Wallahi ba zaka dubata ba! Muddin ina numfashi, wannan wani irin yahudanci ne? Daga kai sai yarinya adaki saboda rashin ta ido har kan gadonta"?  Dr mark ya gama hasala Har yayi wani yunkuri Zai kai mashi naushi Zeenatu tay saurin saukowa daga kan gadonta, ta faɗa tsakanin ta riqe dr shureim tana kuka.   Da ace Zeenatu bata yi gaggawar raba tsakanin su ba, da Allah kadai yasan me dr mark zai yi mashi saboda ya fusata shi. Sassauta fushin fuskarshi yayi, tare da kallon zeenatu da ta kankame shi, hankalin shi ya ɗan tashi da jin zafin jikin ta Ganin mayen kallon da mark ke binta da shine yasa shi juyawa da zeenatu suka bashi baya. Shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da zaro wayar shi ya danna ma Alhaji musa Kira bugu uku Ya ɗaga. "Sir, Wannan balaraben na gidan ka ya hana in duba lafiyarta saboda kawai Ya iske ni akan gadon ta ina kokarin yi mata allura shine ya rufe ni da faɗa yana gaya min magana mara daɗi" ya faɗa yana kallon bayan dr shureim, sarai yasan sunan shi amma saboda girman kai Ya kira shi da sunan balarabe on the other hand Alhaji musa yace"Dr shureim Ya dawo gidan ne"? "Yeah, shi nake magana akai, Yanzu haka muna adakinta" "Okay, mark ka tafi kawai, i will call you later" ba don yaso ba ya amsa mashi da Okay" duk suna sauraron shi abun da ya ƙara bata ma dr shureim rai jin ya fada ma alhaji musa yadda ya iske shi adakin batare da jin nauyin hakan ba, hakan na nufin dama ya saba zuwa dakin zeenatun ya hau gadon kuma da sanin Alhaji Musan. Harara dr Mark Ya watsa ma bayan shi, tare da jan Tsoki ya fuce daga ɗakin. Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, tallabo fuskarta yai da tafukan hannayen shi, idanunta amarairai ce ta kalle shi wani irin tausayinta ne ya kama shi, kumatunta sunyi ja, pink lips dinta sun kumbura daga gani ta jigata taji jiki ba kaɗan ba "Me ke damunki"? Muryarta da shagwa6a tace"ciwon ciki, daga fitowana daga wanka, na fara jin ciwon ciki yaya shureim nasha wahala kamar zan mutu har fadowa nayi daga kan gado, sai da Tani ta shigo ta iske ni kwance kasa ina murza cikina.. Shine ta kira daddyna awaya ta fada mashi shi kuma ya kira mark don ya dubani ni, ni kuma bana son allura" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Calmy yace"amma zeenatu why baki ce ya jira ki fito falo ba? Hakan ya dace ya shigo har dakin ki kan gado zai duba ki"? La66anta na kerma tace"yaya shureim ni banma san lokacin daya shigoba, ina kwance kawai na gan shi akaina, dama haka yake yi min in dai zaizo dubani baya tsayawa falo ɗaki yake shugowa, kuma daddy da mommy sun sani..."  Girgiza kai yai sha'anin rayuwar gidan uncle nasa sai du'a i, yafi jin haushin Tani da ta kira Alhaji musa, sai kace mami bata agidan ay da ta sani ta tada ta daga baccin da duk hakan bata faru ba. Ganin kamar damuwa akan fuskarshi yasa tace"ya shureim ranka ya 6aci ko"? Dakyar take magana saboda cikinta dake mata radadi, Girgixa mata kai yai"bakomai, ina maganin naki" da hannu ta nuna mashi kan mirror Juyawa yai ya nufi closet dinta ya dauko mata abaya ya miƙa mata, hannunta na kerma ta kar6a tasaka a jikin ta. "Kin ci abinci"  "Bana jin yunwa ɗazu da safe na cika kina"  "Okey, ki zauna ki jira ni" make mashi kafada tay"dan Allah kada ka tafi kabarni ni kadai" "Ba tafiya zanyi ba, ruwa zan dauko" amsa mashi tay da toh ta zauna gefen gadon tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannun shi ruke da Cup din ruwa ya zauna ya taimaka mata tasha maganin ganin yadda hannunta ke kerma bayan ta kammala sha, yasa Yace ta kwanta ta huta, marairaice mashi fuska tay da shawaga6a tace"so kake inyi bacci donka tafi kabarni ko"  Yanayin yadda takeyi mashi magana ba karamin kashe mashi jiki ya ke yi ba, ba zai juri kallon ta ba. "Ba tafiya zanyi ba, zan koma falo," miƙewa tay"nima zanje falon" "Pls ki kwanta ki huta, babu lafiya a jikinki" Kuka ta saka mashi"haba ya shureim nagaji da zama ni kadai, ya kake so nayi da raina? nasan tafiya zakai kabarni..." lallashinta ya farayi"ya isa haka ki daina zubda hawayenki bana so, Idan saboda ni ne muje falon tare saiki kwanta kan sofa, in har hakan zai kwantar maki da hankali" ajiyar zuciya ta sauke ya zaro hanky daga aljihu ya share mata tears din fuskarta, ya ruƙo hannunta suka fito daga dakin ________________________________✍️  A bangren su Aneeleerh har wuraren biyu na rana suna agidan, Sun Mori lokacin su tare da su Unaisah sallah kadai ta tadasu, sun sha fira da su kamar ƙawayansu, sun ɗebe masu kewa ba kadan ba, musamman Aneelerh taji dadi tayi farin cikin ganin yadda Junaid Ya saki Jiki da Unaisah in a short time su ka shaku da junan su, wasan doki suka dinga yi mashi ita da Batool, akan bayanta ta ɗaura shi ta dinga rarrafe tana zagaye sitting room din batare da gajiyawa ba, Sai murna yake yana fadin doki sukuta sukuta. Aneelerh tasha ruwan mamaki Ganin Yadda Yake tiƙar dariyar, yaushe rabon da ta ga dariyar Junaid tun ranar da Ana ta 6ace ko murmushi bayayi ga ƙiwuya amma yau ya sake kamar bashi ba, har ta fara tunanin in suka koma gida zata lalla6a shi cikin lallami ta tambaye shi meya faru da ana  aranar watakil ya fada mata tun da taga bakin shi ya buɗe. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. har video Benazir ta ɗauke su da wayarta saboda sun burgeta taji daɗin walwalwar da su ke yi cikin nishaɗi bayan sun gama yi mashi wasan dokin, Unaisah ta daure idanunta da mayafinta ta dinga zagaye dakin tana neman su, Batool taja hannun junaid suka dinga garata sai da suka wahalar da ita dakyar ta cafko baby junaid ya dinga ihu Yana tsalle yace mata shima ta ɗaure mashi ido yayi wasan, ta cire mayafin ta ɗaure mashi idanunshi yadda bazai ji zafi ba, kamar makaho haka ya rinƙa miƙa hannu ya na laluban su da gangan Unaisah ta je gaban shi ta tsaya don kada su wahalar da shi, cafko rigarta yai da hannayen shi ya ƙankameta yana fadin ya kama ya kama. Duba agoga Aneelerh tayi kafin ta kalli Benazir"yakamata mu tafi, kada mami taji na dade" sai lokacin Benazir tace"yanzu abun hawa zamu hau mu koma? nasan ko na kira dr shureim ba lallai yazo ba saboda rashin lafiyar zeenatu..." ta fada tare da ta6e baki Murmushi Aneelerh tay saboda ta gano me take mawa "Pls ki kira mijina ya maida mu gidajen mu" cike da zolaya tace"ki dai iya bakinki, Kada babyn naki taji kina kiran sunan ubanta da sunan mijinki, Yanzu ki tada mana 6alli" murmushi Benazir tay tare da kallon su Unaisah dake a zaune kan rug sun gaji da wasan hutawa suke. Waya ta curo ta danna ma Taj kira tana fara ringing yai picking,  Tunkafin tay magana Yace"Aneelerh ykk ya su Unaisah, Ina fata kunji dadin kasancewa da su"  "Alhamdulillah, gasu nan zaune sun gama shan wasa da baby junaid, shima yau yaji dadin ganin yar uwarsa"  ta fada tana kallon su  "Masha Allah, Naji dadin jin hakan, Yanzu nake kokarin, kiranki,yakamata su koma yan uwansu sun fara neman su" "Allah sarki, Nima abun da yasa na kiraka kenan, mun shirya tafiya kuma dr shureim bayanan Ya tafi ɗasu aka kira shi daga gida har yanzu bai dawo ba, mun kira layin shi baya shiga" ta faɗa tana kallon Benazir data tsare ta da ido fatanta Allah yasa ya amince yazo ya dauke su. Shiru yayi jimm na ɗan wani lokacin kafin yace"Okay, Naso na maida ku gida amma bana a kusa, zansa jami'en mu ya kai ku" haɗe fuska Benazir tay tuni idanunta suka ciko tab da kwalla, gani take kamar ya ɗago su ne shiyasa yace zai turo jami'en su ya kaisu amaimakon shi "Shikenan, Mun gode ssai," tay mashi sallama,  Kallon juna su ka yi ita da Benazir "Nasan saboda ni ne yace bazai maida mu ba" ruko hannun ta Aneelerh tay"pls ki yi hakuri kamar yadda na fada maki, bana so yaran nan su fahimci wani abu kwara mu rabu lafiya, ki daure idan muka shiga mota zamuyi magana, nayi maki alkawarin zan taimaka maki mu shawo kan shi"  A hankali Benazir ta share hawayen ta, har ga Allah bata son tafiya tabar gidan ji take kamar su kwana anan sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba. Suna azaune jami'en da taj ya turo yayi masu sallama Yace su fito Yana jiran su. Hankalin Unaisah ba karamin tashi yayi ba ganin za'a rabata da baby junaid, bawan Allah sai ƙara kankameta ya ke yi duk don kada su raba shi da ita,  bayan sun fito abakin motar suka tsaya, Aneeleeh ta kar6i junaid yana kukan rabuwa da Angel tace mashi yai hakuri za ta zo har gida ta same shi, dakyar tayi mashi wayau ya hakura. "Toh Mu zamu wuce, zamu tafi mu bar ku da kewar mu" Anila ta fada tana kallon su, duk sun ɗaure fuska saboda basu son su tafi Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Dan Allah yaushe zaku dawo"? Cikin sanyin murya batool ta yi maganar, Benazir tace"in dai mune kusha kuruminku, har sai kun gaji da ganinmu" dadine ya lullu6e su, miƙa masu hannu tay da sauri suka matsa kusa da ita ta haɗa su duka ta rungume su, Cikin kunne ta yi ma Unaisah raɗa"zan kar6i contact dinki a gurin Aneelerh, Ki kula min da kanki, Ina kaunarki sosai" murmushi unaisah tasaki"nima zanyi kewarki mommyna" Bayan sun raba jikin su daga na juna ta dubi Batool ta shafa gefen fuskarta da tafin hannun ta "zanyi kewarki, Yau na fara ganinki amma kin kwanta min araina, kamar yadda Babyna ta sace zuciyata, Ina kaunarki, Ki kula min da kanki" dariyar farin ciki batool tayi"in sha Allah, nagode sosai aunty Benazir, nima ina sonki, " taso ta tambaye su dr shureim amma saita kasa saboda kunyarta da take ji. Miƙa masu hannu Aneelerh tay, itama tay hugging dinsu baby junaid ya haɗe rai Idanunshi sun ciko tab da kwalla. Sumbatar kumatun shi Unaisah tay, cikin sigar lallashi tace"I'm sorry my little bro,  Zanzo har gidan ku, Aunty aneelerh pls ki kwantar masa da hankali bana so yayi kukan rashi na" ta fada tana kallon fuskar junaid "Kada ki damu bazan bari yai kuka ba, ku gaida mana mutanan gidan" atare suka amsa masu da toh Akan idonsu Motar su ta fuce daga gidan, fitar su keda wuya Ummi ta fito daga kofar falon har bayan motar saida ta gani yayin da take karasa fucewa daga gate din Sun yi tsaye cike da jimamin tafiyar su, baby junaid Ya tsaya masu aransu. Kwata kwata basu lura da ummi ba har saida ta ambaci sunayen su da sauri suka dube ta  "Daga ina kuke? Motar waye naga ta fita yanzu? Kallon ta su ka yi ba tare da sun furta kalma ba "Ba ku ji Ina magana bane"? Ajiyar zuciya suka sauke atare Unaisah tace"bamu san motar wanane ba,  muma yanzu muka fito" "Daga ina"? Kallon juna su ka yi "Kamar baku da gaskiya, ku fada min mana daga ina kuke" ta fada tana jifansu da kallon tuhuma. "Mun je part din daddyna ne, daga can muke" ba dan ta yarda da su ba tace"shine ko ku fadamin ay dana shirya mun je tare, gaskiya baku kyauta min ba" ta fada tana jifar su da harara dariya sukai atare..  "Ku wuce mu shiga ciki," gaba tay suka bi bayan ta hannun su ruke cikin na juna  *💋BOSS BATURE✊* Da marece tana a zaune gaban mirror chair tana yin wani makeup ɗin akan fuskarta, saboda kwalliyar da ta yi ɗazu ta goge.  gown ɗin ɗazu ce a jikinta da alama bata gama gayun ba, ko kuma wanda akayi dominsa bai gani ba, ita kaɗai ce a ɗakin, sai ƴan shafe shafe take ma fuskarta, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tayi matuƙar yin kyau, ta nutsu tana kallon fuskarta ta cikin mirror, pink lips dinta sun jiƙu da lip gloss sai shinning su ke. Knocking ɗin kofar da akai ne Yasa ta ɗan juya ta kalli room door ɗin su. Jemimah ce ta shigo jikinta sanye da Overall, ta ɗaure  blonde hair ɗinta da ribbon ta fito ɗass Farar fatar ta gwanin sha'awa. "Little Sis halan dalili ne Ya shigo dake dakin mu"? Ta faɗi hakanne don tasan bai wuci chocolate tazo roƙo a gurin ta ba. murmushi tayi"Aunty ummi ce tace In kiraki, kizo mu yi dinner, in ba zaki ci ba sai mu cinye naki" dariya Unaisah tay"su acici mala'ikun tauna, Ku da baku gajiya da Cin abinci, Har wani fadi kike zaku cinye abinci na ai ko dana karanta maku Charman dudu cikin kowa ya kumbure" waro idanu Jemaimah tay"Wlh wasa nake maki fa" miƙewa Unaisha tay daga kan chair din"oho in ma dagaske ne bismillah, ku ci ku ga abun da zai biyo baya" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Veil ɗinta dake ajiye kan bed ta dauka ta yafa akan kafadarta, ta koma gaban mirror  ta dauki turare ta fashe jikin ta da shi. "Sis Unaisah Kin yi kyau wallahi"  "Thank you, ki tafi ki ce masu su jirani Yanzu zan fito" Maƙe kafada Jemimah tay"wlh ba inda zanje, so kike muje muyi ta jiran ki kiqi fitowa yawun mu yai ta tsinkewa ko"? Girgiza kai Unaisah ta yi ba tare da ta tanka mata ba "Kamar dole saida ni zaku ci, kullum sai anzo kirana" Kafin ta ankare Jemimah ta buɗe drawer chest, Ta Saci Chocotes biyu ta tura a aljihun rigarta. "Sis Unaisah mu tafi pls, suna jiran mu"  "Kada ki takura min pls" ta faɗa tare da juyawa ta nufi shoe rack ta ɗauko wasu hadaddun cone heel ta zura a ƙafafunta. "Aunty Ummi tace Ki ɗauko mata wannan abun jin kiɗan zata kunna  mana music" Girgiza kay tay"Aunty ummi ta iya Taya beraye 6anna" ta faɗa tare da nufar inda ta ajiye bluetooth speaker din ta ɗaukota a hannu tace ma jemaimah mu tafi  Adaidai lokacin da suka fito daga dakin Danish yana atsaye gaban handrail din bene jikinshi sanye da kaftan maroon colour, muryar jemimah ce taja hankalin shi ga kallon su bai sauke idanunshi akan kowa ba sai kan Unaisah, wankan data ɗauka yayi matuƙar ƙayatar da shi, musamman data ju ya baya tana ta fi ya, kwata kwata basu lura da mutun ba, kuma ba su ji ajikin su ana kallon su ba. Tun kafin su karasa Dining din, Ta hango Su gaba ɗayan su sun hallara A zazzaune kan dining chairs, an cika masu table din da lafiyayyan abinci. Tana shigowa sautin takalmanta Ya karaɗe kunnuwansu, kusan atare suka ɗago suna kallonta kamar sun samu tv, kwalliyarta tayi masu kyau Nan fa suka fara Santi suna yaba kyan da tayi.  Ummi tace"lallai yau ƴan matanci ake ji, faɗa min wa kikayi ma kwalliyar nan" farfari tay mata da idanu"Someone special" ta fada da zolaya sajeed yace"Zan Iya cankan wanene"? Ɗaga mashi gira tay murmushi yayi kafin Ya firta  "Chief" waro idanu waje su ka yi gaba dayan su, Praveen tace"baka da hankali Sajeed, chief dinne zata ma kwalliya, Mutumin da ko kallon mutane ma bayayi. Ummi tace"ba abun mamaki bane, Ni dama na fara tunanin akwai wani abu tsakanin su, shiyasa ran nan yaje dake shopping mall ya yi maki siyayya..." ɗaure fuska Unaisah tay"kai aunty ummi, saboda inyi tsaraba yayi min siyayyan ba dan wani abu ba" ta faɗa tare da miƙa mata speaker ɗin hannunta, kar6a ummi tayi ta kunna ta kafin ta ajiye ta under chair ɗin da take a zaune, ta zaro wayarta daga aljuhun rigarta, tayi connecting ɗinta da speaker din. sai daɗi suke ji za'a kunna masu music, kallon su Unaisah tay sun cika dogon table din ba space, Shima ɗayan mai mazaunin mutun shida babu space, sai ɗayan dining table ɗin daya rage mai mazaunin mutun Uku Javed yana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun dake a kewaye da shi, anan ta samu guri ta zauna. "Ku fara Cin abincin mana" ummi ce tay maganar. Sajeed yace'wai da jira muke ki fara kunna mana music ɗin, zaifi armashi muna ci muna sauraro" ummi tace"na lura dakai mayen kiɗa da rawa ne, wa ya koya maka ne, cos ka fita daban ko acikin yan uwanka"  Murmushi yayi batare daya ce mata komai ba, don bazai Iya tuna komai ba dangane da yadda Ya iya rawa ya dai san abun a jinin shi yake. "Wata waƙa zan sanya mana"? Ta tambaya tana kallon su,  Har suna haɗa baki gurin faɗin baby calm down, dama itace wakar da suka fi sani. bayan Ta kunna masu wakar suka fara cin abincin suna gyaɗa kawunansu, wasu daga cikin su har wakar suke bi kamar su suka rairata saboda yadda suka Iya bin baitikan tiryan tiryan ba kuskure. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. babu wanda Ya lura da shigowar shi, abakin kofar dining room ɗin ya tsaya yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, ba zai iya tuna rana ta karshe daya shigo dining ɗin da sunan zaici abinci ba, Sai yau da dalili ya kawo shi. "Danish"! da ƙarfi Haris Ya ambaci sunan shi, bai tsammaci wani zai gan shi ba, adaidai lokacin da wakar da suke sauraro ta ƙare hakan Yasan duk suka ji Kiran da Haris yayi mashi, da sauri suka kalli Inda yake atsaye da alamun mamaki akan fuskokin su. Kusan kowan nan su saida Ya ambaci sunan shi, In ka cire Unaisah da tay shiru tana kallon shi Ummi tace"Sannu da shigowa, ina fata kazo kaci abinci tare da mu ne" shiru yai bai tanka mata ba,  "Pls danish kazo muci dinner atare, Munyi missing ɗinka" Batool ce tay maganar, Naufal Yace"Yau kawai dan Allah, baka ga dadin da muka ji ba na ganinka"!  gaba daya suka haɗa baki suna yi mashi magiya don ya shigo su ci abincin atare.  "Dama kun daina wahalar da bakunan ku, Idan so kuke Yaci cikin sauƙi, Unaisah zaku roƙa ba shi ba"   Sajeed ne yai maganar fuskar shi da murmushi, gaba ɗaya suka maida dubansu Ga Unaisah"pls Kiyi mashi magana, ya shigo muci atare" kau da ido tay gefe ɗaya tay shiru bata tanka ma su ba tayi mamakin maganar sajeed ko taya akai ya gane baya  jin maganar kowa in ba nata ba. "Aunty Ummi ki sa baki, Ta yi mashi magana" duƙar dakai ƙasa Unaisah ta yi, girman kanta Ya hana ta yi masu abunda suke so, ita kanta so take ya shigo ya zauna suci abincin atare amma bata jin zata iya yi mashi magana. Calmly ummi tace"Unaisah, pls ki masa magana mana, Ƴan uwansa suna son suci abinci da shi.."   sai da ta mula ta sha iska, kafin ta wurga eye balls dinta kan Danish kamar me jin shakkarta, tasan saboda ita ne yaki shigowa gudun kada ya sabama sharuddan ta, ba ta yi niyar yi masa magana ba amma saboda batasan su fahimci sun samu sabani atsakaninsu yasa ta canza ra'ayin ta. Har Ya juya zai fuce, sanyayyar muryarta ta dakatar da shi "Big bro, ka zo mu ci abinci atare" a wayance ta faɗa tana kallon shi har saida ya maimaita sunan data kira shi acikin zuciyarsa "Ga wuri Na tanadar maka" ta faɗa tana nuna Kujerar dake facing ɗin ta. baiyi niyar zama ba, amma saboda muradin ransa tayi mashi magana, Ya fasa tafiya Ya jiyo ya shiga cikin dining room ɗin, yan uwansu sai murmushi su ke yi saboda sunji dadin shigowar shi. Ummi dai ta yi mamakin shakuwar dake atsakanin shi da Unaisah, aranta ta ayyana ko meyasa yake jin maganarta fiye da kowa! Yafi fifita ta akan yan uwansa tana lura da shi, abun da ta fahimta itama Unaisah din tafi ji da shi akan yan uwan shi, don tana lura da ita lokacin da ta ke ji da shi, duk in zasu ci abinci sai tace ma Haris ya kaima Danish nashi aɗaki bayan haka wasu lokuttan tana ganin Unaisah tana satar hanya ta shiga dakin shi, tabbas tana son tasan meke atsakanin su amma tasan ko da ta tambayi Unaisah zaiyi wuya ta faɗa mata gaskiya, aranta ta ayyana yanzun nan zan gano da kaina. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Zama yai kan chair din dake fuskantar Unaisah, ya jingina bayan shi jikin kujerar, ya ɗan lumshe idanunshi ba tare daya kalle ta ba, don baya son abin da zai ja ya karya alkawarin daya ɗaukar mata. Sun yi shiru babu mai magana a cikin su. Har saida ummi tace"me kuke Jira Unaisah? Ku fara cin abincin mana" A hankali ta ɗan saci kallon fuskar shi Har saida ta ɗanji faɗuwar gaba saboda kyan da yayi mata, tayi missing din ganin shi a kusa da ita. a hankali take cigaba da kallon shi ganin ya lumshe idanun shi tasan ba lallai ya buɗe su ba, aranta ta ayyana wani irin kyau ne wannan kullum kamar ana ƙara mashi..." gudun kada wani ya zargi wani abu tsakanin su yasa ta ɗauki glass of milkshake ta tura mashi agaban shi, ta haɗa mashi da plate of grilled steak with roasted vegetables ta aje agaban shi. Cikin sanyin murya tamkar tame yin raɗa ta firta sunan shi, A tsanake ya buɗe reddish eyes dinsa dake lumshewa tamkar na mai jin bacci ya kalle ta da su, gaba ɗaya suka tsinci kansu da kallon juna ba tare da kyaftawa ba ya rasa a ina zai tsayar da eye balls dinsa, lip gloss din data shafa ma soft lips ɗinta ba karamin rikitan shi yake ba. makeup din fuskarta ya tafi da imaninsa, kamar yadda yake kallonta haka itama take bin shi da kallo, tun daga kan dogan wuyansa ta fara har iya zuwa soft lips din sa a hankali tay moving eye balls dinta zuwa ga dogon han cin shi wani irin yanayi take ji ajikin ta mara misaltuwa, sam takasa ta6uka komai, Javed dake akusa da su baisan wainar da suke toya ba hankalin shi na akan abincin da yake ci. Babu wanda Ya lura da su sai ummi da ta sanya masu ido duk wani motsinsu akan idanunta   Yawu ta haɗiya tana ƙoƙarin kau da ido daga kallon shi, ba zato ba tsammani sautin daddadan kiɗa Ya karaɗe kunnuwan su taken waƙar Ko wuya ko dadi adai dai inda baifin Ya fara da  Ko wuya ko dadi Ni dake ba zamu rabe ba Ka zamo ni na zama kai Ba ranar rabuwa Ko wuya ko dadi Ni dake ba zamu rabe ba Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Ka zamo ni na zama kai Ba ranar rabuwa.. gaba ɗaya jikinsu Ya mutu, wata irin kasalace ta mamaye sassan jikinsu, hatta yanayin bugun zuciyar su saida Ya canza. Kasa ƙarasa cin abincin ta yi A hankali Ta jingina bayanta jikin kujerar batare da ta daina kallon shi ba, waƙar ba karamin shagalar da su tayi ba, sun shagala da kallon juna, sun kasa ta6uka komai, kowa na cin abinci ban da su..." Cigaba waka tay sun nutsu suna sauraran baitin Dani dake soyayya ta ginu A zuciya ta ke na saka kin sanu Kice dani kin barni na banu Shine kadai zai sanya ayi mini duren kunu Kiji ni dai zama dake daram dam-dam Na rike ki ta kam kam-kam Makiyan mu suje chan Banda son ki bansan komai ba... Lumshe idanunta ta yi a hankali ta dan numfasa ba tare da buɗe idanun ba, wani irin bakon abu take ji a jikin ta, mara misaltuwa, sai taji tamkar saboda su aka yi waƙar saboda yadda wakar take shigarta. yatsun hannunta sai kerma suke, gaba ɗaya ta shiga yanayi ba zata iya jurar cigaba da kallon shi ba. Danish dake kallonta wata irin nutsuwa ce ke shigar shi, musamman data rufe idanunta hakan ya bashi damar kallon ta son ran shi, farar fatar dogon wuyanta yabi da kallo Silver necklace ɗin data sanya tayi matuƙar ƙawata wuyanta, moving eyes dinsa yai slowly izuwa kan kirjin ta sam ta manta bata ɗaure boobs ɗinta ta ciki ba kamar yadda ta sa6a, yau yaga abun da take boye mashi, duk da ƙarantar su nipples dinta ba karamin girma ne da su ba. hannun shi na dan kerma ya dauki milkshake din data ajiye mashi ya fara shan shi ba dan yana jin dadin shi ba, saboda kallonta da ya ke yi yafi mashi komai. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. baitin Wakar ne Ya ƙara rikirkita tunanin shi ya ɗan runtse idanun shi yana sauraron daddadar muryar da kunnuwan shi ke jiyo mashi sai yaji kamar Angel dinsa ce ke raira mashi ita. Na rike ka hannu biyu baby na Kai kazam fitila annuri na Ko ana fizgemin nama na Zan yabe ka da karfin harshe na Sai da kai Ba ya kai Ka sarkafe mini a zuciya ta Ba ya kai Ummi tasan takan tsiya, dagangan take maimaita wakar saboda ta ƙara rikitar da su, yau taga abun da Ya ɗaure mata kai, tun daga kan yanayinsu ta fahimci irin tsantsar kaunar da suke ma junan su, don ita abun da tagani ma ya wuce A kira shi da so hada shaukin junansu da suke ji, yar wakar da ta kunna masu kadai ta jefa su awani hali dama da biyu ta kunna ta Kasa jurewa yayi da wata irin kasala Ya miƙe zai bar dining din gudun kada yayi wani abu ba dai dai ba da zaisa su sake samun sabani da ita, da sauri ummi ta dakatar da wakar ta dube shi. "Danish Ina zakaje? Naga ko abincin baka fara ci ba" tamkar baisan furta magana yace"bana jin yunwa" marairaice mashi fuska su Haris sukayi"pls danish, kada ka tafi ka zauna ka ci abinci" girgiza kai yai, Shi kadai yasan me yake ji ajikin shi, In har ya cigaba da zama Yana kallon Unaisah komai zai iya faruwa a yanzu haka jikin shi sharkaf Yake Ga gumi da ya wanke shi duk da sanyin a.c din dake a dining room din, su basu lura ba amma ita Ummi tasan me yake ji a wayance tace"ko dai kana da uziri ne"? ya ɗaga mata kai alamar eh. Shu'umun murmushi Tasaki Okay, Muna jiranka idan ka gama uzirin naka, ka dawo kaci abincin" bai kula ta ba Ya fuce daga dinning din ba don ya gaji da zaman shi ba, sai don bayason yaja ma kan shi bala'e.    Fitarshi keda wuya Unaisah ta buɗe idanunta da suka kaɗa jawur da su, ga wani zafi da temperature din jikinta ya dauka kamar mai fama da zazzabi. ta rasa gane meke mata dadi, fitar Danish daga ɗakin yasa taji batasan cin komai, mineral water kadai ta sha ta miƙe jikinta na tsuma ta nufi hanyar fita daga dakin muryar aunty Ummi ta katse ta"Wai lafiya? Shi ya fita baici komai ba, kema kin miƙe zaki fita? Meke damunku ne"? Ta tambaya kamar batasan meke wakana ba. Yamutsa fuska Unaisah tay tare da kallon Ummi datay maganar "Wayata zan dauko adaki, yanzu zan dawo" ta fadi hakanne don kada su zargi wani abu. kumshe dariya ummi ta yi abakinta, tana lura da yadda jikinta ke tsuma. "Okay, muna jiranki" fucewa tayi daga dining din tana tafiya da nawa kamar wadda kwai ya fashe mawa, tana shiga dakin su ta faɗa toilet taja ƙofa ta datse, zama tay akan toilet seat tayi shiru tana tariyo abunda ya faru a dining room. Ta rasa gane dalilin dayasa take tsintar kanta awani yanayi duk idan tagan shi ko taji muryarshi! Batasan menene ba, ta kasa ganewa. bata gama zancen zucin ba, zatayi tsarkin fitsarin da tayi taga wannan farin ruwan mai yauƙi wani irin kyankyami da kyamane suka kamata, da sauri tayi tsarkin ta fito ta tsaya abakin kofar toilet tana faman sauke ajiyar zuciya, bayanin aunty Umminsu ta fara tariyowa a lokacin da take faɗa mata dalilin dake kawo shi, abun da ya daure mata kai kallon juna kawai sukayi ba wani abu ba amma sai gashi ta gan shi, dole ta nemi ƙarin bayani agurin Aunty ummin su. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. ga yunwa tana ji sai dai bata jin zata iya komawa dining room din, faɗawa tayi kan bedmattress ta janyo pillow ta rungume shi a kirjinta, wani sanyine ke ratsa zuciyarta, ga wani dadi da take ji a jikin ta. ta shafe tsawon mintuna shabiyar a kwance ba tare data motsa ba. "Sister, Aunty Ummi tace kizo wai" muryar hawwa ce ta katse mata zancen zucin ta, ba tare da ta bude idanunta ba tace"okay, gani nan zuwa" bayan fitar hawwa daga dakin ta sauko daga kan gadon ta, ta gyara mayafinta, tana ƙokarin fitowa daga dakin kamar daga sama taji Sallamar Salsabeel da sauri ta juya ta dubi kofar falon, a tsaye yake ya ɗauki wankan shadda kamar ba shi ba, hannun shi ruƙe da trolley, kwata kwata bai lura da ita ba. "Yaya salsabeel," muryar ta ce ta fargar da shi, murmushi yayi tare da nufarta yana jan trolley ɗin. "Unaisah ykk" da fara'a tace"lafiyalou, ya salsabeel kwana biyu baka leko mu ba, munyi fushi"  ta fada tana haɗe fuska yar dariya yayi"i'm really sorry, wlh kuna araina, yanzu hakama da kika ganni saboda ku nazo"  Miƙa mashi hannu tayi"kawo na ruƙe maka trolly din" miƙa mata yai tasa hannu ta ruƙe handle din"Menene aciki? Ko kayanka ne"? Girgiza kai yai" mu karasa ciki, zan nuna maki abunda ke a cikin shi" amsa mashi tayi da toh suka nufi cikin falon akan sofa Ya zauna, Ta aje trolley din agaban shi Yace mata ta kira sauran yan uwanta ya faɗa yana hangen su a dining room suna cin abinci sam basu lura da shi ba, da sauri ta juya ta nufi dining room din ta shiga ta kira su, tun da suka ji ta ambaci ya salsabeel ya zo kowa ya ajiye spoon din hannun shi, Cike da zumudin son ganin shi suka fito daga dakin su dukan su hada Ummi. Kafin su karaso ya mike fuskanshi dauke da fara'a ya gaishe da ummi ta amsa mashi da fara'arta,  kallon su Haris yayi daya bayan ɗaya aranshi yana tariyo lokacin da suke a prison, rayuwa ta canza sun wadatu da kwanciyar hankali Hannu ya miƙa ma mazan sukayi musaba, Ya dubi Yan matan dake ta faman hade rai Dariya yayi"fushi kuke dani"? Khadeeja tace"eh mana, tun yaushe rabon da kazo gurin mu, ka manta damu.." Mubeen Yace"kullum sai munsa ran zuwanka amma saika ki zuwa" gaba daya suka rufe shi da korafe korafen su dakyar Ya samu ya shawo kan su, har suka hakura da fushin da sukeyi da shi bayan sun gama gaisawa da junansu yace su zauna zasuyi magana mai muhimman ci. Bayan Kowan nan su Ya samu guri Ya zauna kan Sofas suka nutsu suna jiran jin me zaice masu. "Ya salsabeel, Wannan akwatin fa? Ko tsaraba ne ka kawo mana" parveen ce tay maganar tare da nuna akwatin da hannu "Eh tsaraba ce amma bata abun ci ba, Kayan sawa ne" kallon juna su kayi da mamaki akan fuskokin su. "Ina Danish"? Ya tambaya yana kallon su "Yana a daki" suka haɗa baki gurin bashi amsa" Yace"okay, wani ya kira min shi" Haris ne Ya mike da sauri Ya je kiran shi. falon yayi tsit baka jin hayaniyar komai, duk sun ƙagara da son ganin menene acikin trolly din me kuma ya Salsabeel zai fada masu mai mahimman ci'?  Jim kaɗan saiga Haris Ya dawo tare da Danish, Har ya canza kayan jikin shi yanzu silk pyjama ne a jikin shi na bacci. Tun shigowarsu Falon, Unaisah take satar kallon shi, bayan sun rungume juna da salsabeel a amutunce suka gaisa da junan su kafin daga bisani kowan nan su Ya zauna suka nutsu suna kallon salsabeel Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Mu farayiwa Annabi salati" suka amsa mashi da toh, bayan sun gama yayi shiru yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu, Azeeza da Jemimah sai faman kumshe dariya su ke yi kamar wasu zautattu. Ɗaya bayan ɗaya ya fara kiran sunayen su, duk wanda ya kira sunan shi sai ya amsa mashi da Na'am, ummi dai tayi shiru tana jiran jin me zaice ma su Numfasawa yayi kafin ya fara magana cikin nutsuwa "Gobe Idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya, za'a tafi daku Isod headquarter...."  Kallon juna su ka yi arude suka maimaita sunan Headquarter, Sajeed Yace"me za mu yi acan ɗin"? Da alama sun ruɗe, murmushi Salsabeel yayi kafin yace"zaku gana da manyan jami'an Isod" Hankali tashe Unaisah tace"mu ɗin"? Jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, Lokaci yayi da zasu gana da ku, don suji daga bakin ku, Suna bukatar bayani game da rayuwarku a gidan kurkukun ƙaddara, zasuyi maku tambayoyi da suka shafi rayuwar da kukai agidan kurkukun ƙaddara da kuma shi kanshi gidan kurkukun"  Ya fada yana duban fuskokin su sunyi shiru suna sauraronshi kowa da abunda yaƙe sakawa aranshi. "Nazo ne don in ƙarfafa maku gwiwa, nasan akwai masu jin tsoro har yanzu acikin ku, to inaso ku aje tsoron nan gefe ɗaya da duk wani shakku da zakuji, yanzu lokaci ne da zaku bada gudummuwa ku taimaka masu gurin kawo karshen kurkukun kaddara, bayanan da zaku basu da su zasuyi amfani wurin yin binciken waɗanda suka azabtar da rayuwar ku, kada ku 6oye masu komai, duk mun ƙanƙantar abu da kuka sani ku faɗa masu zai iya zama mai amfani agare su"  tun da salsabeel ya fara magana Danish Ya rufe idanunshi gam kamar baya atare da su, sarai salsabeel Ya lura da yanayin shi. "Ku faɗa masu irin kuncin rayuwar da kukayi, Ku faɗamasu azabtarwar da sukayi maku da kuma wulakanta rayuwarku da su ka yi, ku kaɗai kuka san meya faru arayuwarku, tunkafin ku mallaki hankalinku kuke a kulle ba shige ba fuce, idan har kuka 6oye wani abu baku fada ma su ba, kanku zaku cuta, kwara ku tona masu asiri don uban su kowa yasan me suke aikatawa" ya faɗa tare da bugun sofa din da yake zaune akai da hannun shi. "ku daina ganin ayanzu kun tsira kun samu rayuwar ƴanci wallahi har yanzu rayuwar ku tana acikin haɗari saboda ba zasu ƙyale ku ba, suna nan suna bibiyar rayuwarku don su salwantar daku saboda kune prisoners na farko da suka fara karya dokar kurkukun kaddara, tayaya ku ke tunanin zasu ƙyale ku? Ay ko dan kada ku tona masu asiri dole su nemi hanyar da zasu shafe babin ku"  Maganar salsabeel ta ɗaga hankulansu, Tuni ido ya raina fata, wasu daga cikinsu har sun fara sharar kwalla, ya faɗa masu hakanne don Ya tsoratar da su ya kuma tunzura su don su fusata su samu kwarin giwar tona masu asiri idan jami'an sirrin suka tambaye su. "Ko ba don saboda ku ba, Ku tuna ƴan uwanku da kuka bari agidan kurkukun ƙaddara! Waɗanda basu ji ba basu gani ba kamar ku dai, suna can ana azabtar da rayuwarsu, Sun maida su kamar dabbobi sai azabtar da su sukeyi, meye ribarku idan ku kun samu jin dadin rayuwa su kuma suna awahala? Baku da burin ku dauki fansar abunda akayi maku? Sannan ku cecei rayuwar yan uwanku? Za ku ja baki ne kuyi shiru acigaba da salwantar da rayuwar kananun yara da basu ji ba basu gani ba"? Ranshi a6ace yayi maganar yana kallon su, Jiki asanyaye sajeed Ya sauko daga kan sofa, Ya dawo ƙasa ya zauna hannayen shi biyu tallabe da kan shi, Idanunshi sun ciko tab da kwalla. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Shesshekar kukan su ne Ya cika falon, kalaman salsabeel sun fama raunin dake acikin zuciyar su..."  Salsabeel bai dakata ba saida ya tabbatar sun fusata sun harzuka kafin ya tsagaita da yin maganar Yana jiran jin me zasu ce. Cikin shesshekar kuka sajeed yace"wallahi ko ba ka fada mana ba, ba zamu raga masu ba, ni ashirya nake da duk wata tambaya da za'ayi min, nayi alkawarin zan fadi iya abunda nasani saboda nima twin sister dina tana can, bana so su kashe min yar uwata duk da bani da tabbacin tana araye kota mutu...." kuka ne Yaci karfinshi, Ya kifa kanshi saman  sofa. Wani irin tausayin su ne Ya kama Ummi, Tuni taji hawaye sun cika idanunta, lamarin rayuwar yaran tana matuƙar tada mata hankali, har yau tana jin labarin su tamkar a mafarki saboda abun yafi karfin tunaninta. Fashewa jemimah tayi da kuka tana fadin "nima wlh saina tona masu asiri, mugaye azzalumai kawai, hadama wannan tsohuwar data kusa kashe mu nida su Azeeza, Inaji ina gani majnoon dina ya mutu, wlh saina daukar mashi fansa, koda zan rasa raina ne..." rai a6ace tay maganar, idanunta sunyi jawur ga ruwan hawaye dake zarya kan kuncin ta, dafe kai Deeja tayi da hannunta tamkar zata fasa masu ihu, idanunta sun rune zuwa ja, kwata kwata bata son jin maganganun da su ke yi, miƙewa tayi da sauri ta fuce daga falon, duk suka bi bayanta da kallo babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita. "Bazan ta6a manta irin azabtarwar da sukayi mana ba, wallahi rantsuwar ɗan musulmi ba gudu ba ja da baya sai mun fallasa su kwara duniya tasan me suke aikatawa, ay yaya Salsabeel ba sai ka sha wahalar yi mana bayani ba, dama mu lokaci kawai muke jira in ma takama har prison din aje damu ayi faɗan da mu, wallahi zamu bada goyan baya ɗari bisa ɗari ko da silar hakan zai ja mu rasa ran mu wlh sai inda karfin mu Ya ƙare, Kome suke son ji zamu faɗa masu...."  tun da Unaisah ta fara zazzaga masifa, suke kallonta jikinta har jijjiga ya ke yi tsabar fusata da 6acin rai, an ta6o inda keyi mata ƙaiƙayi.." bata ƙare maganar ba, Danish Ya miƙe daga zaunan da yake kan Sofa, gaba ɗaya suka bi shi da kallo Salsabeel Yace"Danish Ina zakaje ban gama magana ba"? Ko kallo bai ishe shi ba,  Ya fuce daga falon, sam unaisah takasa karasa maganar, Da tsantsar mamaki suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko  Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Haris Yace"ka gani ko ya salsabeel? Danish Ya canza kamar bashi ba, Yanzu ji muna magana mai mahimmanci Ya tashi Ya tafi kamar abun bai shafe shi ba, haka muke fama da shi baya son shiga cikin mu kuma baya son muje gurin shi..." cikin jin kunar rai Haris yayi maganar yana kallon Salsabeel. Korafe korafe suka dinga fada mashi akan danish, Unaisah tace"nasan ma zai yi wuya ya bamu hadin kai, kuma yafi mu sanin komai dangane da gidan kurkukun ƙaddara"  a marairaice tay maganar, Shiru salsabeel yayi jim yana ɗan jinjina kan shi kafin cikin sanyin murya yace"sai kun yi hakuri da shi, saboda ba yin kan shi bane,  sau dayawa wasu abubuwan da za ku ga yanayi wallahi ba shi bane"! A matuƙar ruɗe suka kalli Salsabeel, Musamman Unaisah Maganarsa Ta jefata a ruɗani, Har dai tagaza jure tace"Ya salsabeel ban fahimci me kake nufi ba! Naji kace wani lokaci ba shi bane"! Kallon ta salsabeel yayi"ina nufin wani abun da ya ke yi bayin kan shi bane, shaidanun  dake a jikin shi ne, su ne suke Controlling din shi, zai iya wuni ba acikin hayyacin shi ba, nasan baku taba lura da hakan ba, shiyasa baya son shiga cikin ku, kuma baya son wani yaje gurin shi, idan ba wanda yake son gani ba, amma abun da yakamata ku cigaba da taya shi addu'a, In sha Allah idan mukayi nasarar raba shi da evils din jikin shi, zaku sha mamaki, zai dawo ainihin wanene shi...."   "Yaya salsabeel amma dai bazai manta damu ba ko"? Batool ce tay mashi maganar, "Taya zai manta daku? Abokan kuruciyar shi, sai dai wasu abubuwan da yake yi zai daina su, zai canza sosai fiye da yadda baku ta6a zata ba.."  Hankalin Unaisah Ya tashi ba kaɗan ba, Aranta ta ayyana idan har maganar Salsabeel ta tabbata tabbas akwai damuwa ba kadan ba, sai dai ta hana zuciyarta gasgata maganar shi. Buɗe trolley din gaban shi yayi duk suka kura ido [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 45 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 06, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe Zama ya yi daga gefen gadon tare da kallonta Ya kashe mata ido ɗaya ya ɗage gira cike da izza yace"me kike tunani ne? Kinyi mamakin ganina ne"? Shiru tayi bata tanka mashi ba, saboda ita har yanzu bata yarda cewa dagaske shine take gani ba, kokwanto take anya bata samu ta6in hankali ba Sarai ya fahimci Halin da take aciki, Ko ajikin shi, saima kwantar da kanshi da yai saman pillow "Ummi!, Haƙuri na ya ƙare, bazan iya jurewa ba, sha'awar son kasance wa dake tana neman tayi min illa, kin san ke kadai ce macen da ke iya gamsar dani, shiyasa na tako da kaina nazo don in kar6i hakkina agurin ki!" ya faɗa yana bin ta da wani shu'umin kallo "Tun zuwan karshe da ki kai gidana ban ƙara ganin ki ba, in har ba zaki dinga zuwa kina bani hakkina ba, toh ni zan dinga zuwa ina kar6a, kin riga da kin san wanene ni indai akan bukatar kaina ne bana ji bana gani" gaba ɗaya ta ruɗe, La66anta na kerma ta furta"dagaske kai nake gani? Ɗaga mata gira yai. "Tayaya akai ka shigo gidan nan"? "Kin san bana son tambaya, Last time, I warned you to stop asking me questions. If you believe me, babu bukatar ki tuhumeni akan duk wani abu da zan yi" dafe kai tayi da hannu ɗaya, lamarin shi ya fara bata tsoro ba kaɗan ba. "I'm waiting for you, come and satisfy me." ya faɗa yana shafa sajen fuskar shi. Girgiza kai ta yi"kayi hakuri bazan iya ba, ina jin fargaban wani yagan mu zan iya samun matsala, ko kamanta a gidan wa muke? Ta faɗa atsorace tana kallon shi. A gadarance ya furta"gidan director general of Isod, Sai me"? Idan naga dama har gidan ubansa sai in shiga inyi abun da naga dama, bawai iya gidan sa ba, ina da ƙarfin ikon yin hakan" ya faɗa tare da ɗago kan shi daga jikin pillown ya miƙe zaune, ya fara cire front buttons ɗin jallabiyar shi, kafin ya miƙe ya zame rigar gaba dayanta ya rage daga shi sai short black colour.. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Gabanta ba karamin faduwa yayi ba, har ila yau ta gaza sabawa da Zanan dake akan fatar shi, daurewa kawai takeyi saboda Allah ya jarabceta da kaunar shi ya riga daya mallake zuciyarta, ya zama wani bangare na rayuwarta, shi din kaddararta ne. "Inaso ki zautar dani har in manta wanene ni..." ya faɗa yana sakin wani ɗan iskan murmushi irin na fasikan tantirai da suka kai matakin degree a tashanci. ba yau suka saba yi ba amma duk lokacin da zai kusance ta, ba karamar azaba take ci ba saboda yanayin halittar shi bakowace mace zata iya jurarta ba. Adabarbace ta furta"nayi maka alkawarin zanzo har gidanka da anjima dan Allah ka tafi yanzu bana jin dadi ne, kuma bana so yaran nan su dawo su iske ni awani yanayi da zai sa su zargi wani abu" ta faɗa tana zare mashi idanunta dake kara rikita shi. "After that, it's risky to have sex in this house." Dakyar ta ƙare maganar ganin yadda ya tunkarota gadan gadan, juyawa tayi da niyar ta buɗe kofa ta fuce, sai dai ina tuni ya cimmata, wata irin damƙa yayi ma waist dinta da faffadan tafin hannunshi, Ya matseta jikin ƙofar yana fitar da numfashi mai hucin zafi, jarabar tashi ta motsa zai iyayin komai awannan lokacin. Tun da taji jikin shi anata gaba daya ta shiga yanayi na bukatarshi dama tayi kewarshi kawai tana tsoron wani ya gansu shiyasa ta nemi bijire mashi, batasan meyasa bata iya yakice shi daga gare ta ba, ya riga da ya saba mata da kanshi, Ya 6ata ta ba kaɗan ba, Ya zamar mata karfen kafa. can ƙasan makoshi Ya furta sunan ta Ummi..." kamar shi ya raɗa mata sunan saboda yadda yake furta shi da wata irin siga ta jan hankali. Sam takasa motsawa sun manna ma kofar kamar zasu shiga cikin ta "Mahaifin ki Yaja min bala'e, Yayi min baki Ummi, na gaza mallakar ki amatsayin mata na, Ya hana ni jin dadin rayuwana na har abada, yayi min illa ba kaɗan ba har yanzu ina jin ciwon abun a zuciyata duk yadda nayi kokarin ganin na mallakeki abun yaci tura..." ya faɗa yana ƙara cusa kanshi tsakanin wuyanta yayin da tafukansa ke adaddafe da kirjinta. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. zuciyoyin su atare suke bugawa, numfashin su na fita da sauri da sauri, kwata kwata ta fara fita hayyacin ta sam bata ji kalaman shi ba, batai aune ba taji ya ɗauketa ɗungururum gaba ɗayanta ya nufi shimfideden gadonta ya kwantar da ita akai yabi ya rufa mata ƙirjin shi 😳 _______________________________✍️ Lokacin da motocin su ka ƙaraso Head quarter A parking space su ka tsaya, kusan atare jami'an dake driving ɗin su suka fito daga ciki tare da buɗe masu cardoors ɗin. Big guy da Taj ne Suka fara fitowa A hanzarce Jami'an Dake a harabar gurin suka buga ƙafa tare da sara ma su cikin girmamawa suka gaishe da su. Ɗayan bayan ɗaya Prisoners suka soma fitowa daga cikin motocin, gaba ɗaya sun rufe rabin fuskokin su da Cotton Scarfs ɗin su, umarnin chief ne tun suna acikin mota, ya ce A sanar su rufe fuskokin su. tun da suka fara fitowa Matasan Isod soldiers dake kai komo a filin harabar suka fara satar kallon su kamar za su yi tuntu6e, kura taga nama sai dai ba halin tunkarar shi, hankalin maza ya tashi da ganin zankaɗa zankaɗan matasan ƴan mata masu jini a jika, rainon mai girma Chief Owais. sun ruɗu da ganin kyawun Unaisah saboda launin idanunta sun ƙara ƙawata kyawun ta, gaba ɗaya hankali ya dawo kan su, su kuwa duk sun sha jinin jikin su ganin yadda gwarazan Jami'an ke bin su da kwallo, Jami'an Isod da mata basa agaban su yau dai alkadarinsu ya karye ganin prisoners. Lura da yanayin yadda jikin wasu daga cikin su ke kerma alamun rashin nutsuwa da kallon jami'an yasa big big yai masu dakuwa da hannu da sauri suka kau da idanun su, abakin motocin suka tsaya, Batool tana ruke da hannun Unaisah, Azeeza ta ruƙe hannun Jemimah, Hawwa ta ruƙe hannun Yasmin, Parveen da Hanna sun ruƙe hannun juna, Sarah da Hibba sun ruƙe nasu hannun, itama Rubina ta ruƙe hannun Deeja gam a cikin nata, haka suma mazan Haris ya ruƙe hannun Javed, Naufal yana ruƙe da hannun Sajeed. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Taj ne ya buɗe backseat na Cardoor din Chief, Gently ya fito daga ciki, ya ruƙo hannun Danish, wato tun kafin suga hannun wanene chief Ya ruko Jami'an dake sintiri suka ƙura idanu suna jiran ganin hannun wani hamshakin ne tsabar kyawun yatsunsa kamar na mace aran su suka ayyana koma wanene ba karamin jan wuya ba ne tun da har chief ya ruƙo hannunsa, lokacin ɗaya ya ƙarasa fitowa kusan suman tsaye jami'an su kai bakomai ne ya ruɗar da su ba face ƙirar jikin shi, ba su ta6a ganin saurayin daya ja hankalin su irin Danish ba, saboda sun haɗa komai suna ji da kan su amma yau sun ga wanda ya take su akan komai in ka cire Chief ɗin su wai ahakan ma da suka ganshi Ya rufe fuskar shi da Hanky, tun a cikin mota chief ya rufe mashi fuskar, kyawawan idanun shi ne kaɗai a bude ya ɗan lumshe su saboda bai cika son kallon da mutane suke yi ma shi ba hatta chief da su big guy sun lura da kallon da jami'an ke yi mashi har sun manta basu sara ma chief ba balle aje ga batun yi mashi sannu da zuwa. "Zamu iya tafiya" big guy ne ya faɗa tare da nuna masu hanya, cikin takun nutsuwa suka soma tafiya suna ta ƴan waige waige suna ƙarewa head quarter din kallo don ba ƙaramin burge su ginin ya yi ba kamar ba'a 9ja ba wasu tankama tankaman floor to ceilling glass windows ne ta ko'ina launin sky blue daga waje kana iya ganin cikin Secure Operation Center ɗin su kamar reception, Gaban su sai faɗuwa ya ke yi saboda kakin jami'an isod ya yi shige dana Giant din kurkukun ƙaddara, gani suke kamar Prison suka koma, duk sun sha Jinin jikin su kamar marasa gaskiya, sai ƙara ƙankame hannun junan su suke yi, zuciya da sake sake wasu har sun raya aransu in wani mugun abun ya faru zasu arce da gudu. Lokacin da suka shiga SOC ɗin, Muryar Na'ura ta karaɗe kunnuwan su, bayani take bayawar dangane da zuwan Chief, tsayawa sukayi kamar an dakatar da su, A tsorace suke bin tsakar gurin da kallo, matasan Isod agents ne bila adadin sanye da kakin su, hankalin su kwance suke gudanar da ayyukan su agaban Computers yan bala'e Na'urori ne kala kala har ta jikin Glass din gurin. "Wallahi tsoro nake ji, ganin su nake kamar giant din kurkukun ƙaddara" murya na rawa Batool tayi magana tana faman rarraba idanu akan jami'an, Cikin muryar raɗa unaisah tace"ki kwantar da hankalinki pls, kakin su ne irin na giant nima na ɗan tsorata kaɗan" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. ta faɗa tare da satar kallon fuskar Danish, kamar baisan da zaman su ba, kwata kwata yaƙi sakewa ya ƙi yarda ya haɗa ido da kowa. Suna atsayen nan jami'an suka dinga miƙo gaisuwa gurin su chief kamar zasu durƙusa mashi ƙasa tsabar yadda suke girmama shi. "Meyasa kuka dakata da tafiya? Akwai wani abu ne"? Big guy ne ya tambaya yana kallon faces din. su, hankalin chief na akan Phone dinsa da ya ke daddanawa. Kafin wani ya ba shi amsa daga cikin su, Hankulansu suka karkata akan Lift dake saukowa down ta glass dinta suka hango wasu gungun ƙarfafan Jami'an Isod abin da da ya firgitar su, zubin siffar jami'an dake a cikin lift din sak irin ta Giants na gidan kurkukun ƙaddara, Aikuwa suka fara kokarin tarwatse wa hankulan kowa ya dawo kan su, ganin yadda jikinsu ke kerma yasa Taj yi masu magana cikin kwantar da murya yace"pls ku kwantar da hankulan ku, Ku nutsu nasan me kuke tunani, duk wanda kuka gani anan jami'en Isod ne ba masu cutarwa bane" ajiyar zuciya suka sauke still wasu daga cikin su hankalin su bai kwanta ba, a tsorace suke da jami'an. Lokacin da suka ƙarasa saukowa down, Lift din ta buɗe kusan su shida ne, cikin takun majiya karfi suka tunkaro su, fuskokin su rufe da face mask, suna karasowa agaban su suka tsaya azafafe suka buga ƙafa tare da sarah ma Chief, kafin suka hada baki gurin gaishe da shi ya amsa masu daga gani na hannun damar shi ne. Kamar sun lura da yanayin yaran dake ta kallon su atsorace hakan yasa suka fara cire face mask din dake akan fuskokin su. Su Unaisah sun nutsu suna jiran ganin su wanene, sun ɗan yi mamakin haduwar su matasan samari majiya karfi masu ji da karfin ikon su, Allah ya zuba masu baiwa da fasaha ga wayewa, wasu daga cikin su farar fata ne yayin da wasun su kuma suka kasance bakar fata. "Introduce yourselves to them" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. chief ne ya faɗa tare da nuna masu prisoners, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskokin su, wani black american ne daga cikin su ya fara magana cikin harshen turanci idanun shi akan fuskar Unaisah. "Greetings, I'm Ahmed Hassan, Chief of Operations. I oversee all field operations and tactical decisions. Welcome!" he said cheerfully. Na gefen shi wani fari fat hatta sumar kan shi yayi Dyeing ɗinta ta koma fara daga gani ɗan yankin asia ne awayan ce yace"I'm Commander Haroon, Chief of Intelligence. I gather and analyze intelligence and advise the DG and COO" ya faɗa tare da nuna Chief Owais da Big guy kafin yace"We've been expecting you" da fara'a ya nuna su Unaisah Gaba ɗaya sun nutsu suna sauraron su duk wanda yayi magana idanunsu na akan la66ansa. 'I'm Dr. Zara Saeed, head of Counter-Terrorism Division and leader of high-risk missions." "Agent Ethan Kim, Tactical Expert, your go-to guy for high-risk missions." "Agent Jabeer Osman, mid-level operative specializing in infiltration and surveillance." Bayan sun gama gabatar da kan su, atare suka hada baki wurin yi masi barka da zuwa. Murmushi kowan nan su ya saki, Har sun ji hankalin su ya kwanta. "Mu karasa daga Ciki" big guy ne ya faɗa tare da nuna masu hanyar da zata sada su da inda zasu je. Taj da big guy ne agaba prisoners suna abayan su, Chief da Danish suna abiye da su, yayin da Manyan jami'an ke take masu baya Har suka ƙara so wani katafaren guri kamar falo Ya haɗu ba kaɗan ba, jami'an da suka iske aciki girmamawa suke gaida su chief. A saman hadaddun sofas din da ke agurin Taj yace su zauna, dama agajiye suke da tsayuwa da sauri suka zauna, daga gefen Danish ta zauna saboda ta lura da mood dinshi kamar baijin dadin shi, tana so ta ɗan kwantar mashi da hankali gudun kada Yaƙi basu hadin kai. tuni ƙamshin turaren junansu ya shiga hancinan su sosai su ke shakar shi, ga ni'imar sanyin A.c din da ke ratsa jikin su. Idanunsu na akan su Big guy dake atsaye tare da manyan jami'an nan sun haɗa kai suna tattaunawa atsakanin su daga inda suke basa iya jin me suke cewa. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. A lokacin da bai yi tsammani ba, Yaji ta ruƙe yatsun hannun shi a cikin nata, aruɗe ya dube fuskarta tamkar batasan tayi ba, ta wani Basar ta kalli gefe ɗaya. "Meke damunka"? Ta fada batare data kalli fuskar shi ba "Na lura tun da mu ka zo kamar babu walwala atare da kai, ka ki sakin fuskarka kamar wani abu na damunka ko baka jin daɗi ne? Ta tambaya ba tare data kalli fuskar shi ba, Saboda ƙwarjinin da yayi mata. lumshe idanun shi yayi tare da jan numfashi har saman fuskarta taji saukar iskar numfashin sa wani irin yanayi taji atare da ita. "Nayi maka magana kayi shiru baka tanka min ba, ko dan na damu da kaine"? nutsuwa yayi yana kallon kyawawan idanunta kwata kwata taƙi yarda su haɗa ido saboda sunyi kusa da juna kuma bata son ta jefa kanta cikin irin halin da suke tsintar kan su duk in su ka haɗu da juna. Ba zato ba tsammani taji ya shigar da yatsunsa a cikin nata ya yi tighting din su wani irin shock taji har tay kokarin zame hannunta daga nashi amma ya ƙara ƙanƙame su ta yadda bazata iya kwatsar kanta ba. Arude ta furta"pls ka sakar min hannuna! Kada wani gan mu," can ƙasan makoshi ya furta"Ke kika fara ruƙe min hannu, don haka bazan saki ba" ya faɗa yana kallon idanun ta so yake ta juyo su fuskanci juna ko ya samu nutsuwar da yake samu agurinta amma taki bashi haɗin kai. Babu wanda ya lura da halin da suke a ciki, Hankalin yan uwan su na kan su Taj da mutanan su. Bayan wasu ƴan mintuna, taj Ya nufo su gurin su suna ganin shi suka fara sauke ajiyar zuciya dama duk sun takura da zama su kadai "Batool, Unaisah da ku zamu fara, Bismillah ku taso ku shiga daga ciki" ya fada tare da nuna masu ƙofar Questioning Room din. Batool harta fara jin faduwar gaba amma da taji tare da Unaisah ne sai taji hankalinta ya kwanta. Ƙoƙari take ta miƙe Danish Yaƙi sakin hannunta, fargabanta kada daddynta ya gani dakyar ta samu ta ƙwace hannunta daga nashi ta ta ruko hannun Batool suka bi bayan daddyn ta. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. bayan sun shiga ɗakin suka tsaya suna ƙare mashi kallo, wasu hadaddun kujeru ne biyu suna fuskantar ɗaya daga tsakiyar su madaidaicin table ne. ga wani two-way mirror a jikin bangon dakin, wanda anyi shine saboda masu duba wanda ake tambaya su samu damar kallon shi daga Observation Room, tsabar tsaron ɗakin hada Surveillance Cameras (Kyamarorin sa ido) Nau'o'in ɓoyayyun kyamarori masu daukar video recording, ta kowace kusurwar dakin har ta cikin fitilun kwai da jikin kofa duk sune a makale ba zaka ta6a ganin su ba in ba an fada maka akwai ba, gaba daya sun shagala da kallon ɗakin har saida taj yayi masu gyaran murya kafin suka yi saurin kallon shi Murmushi yayi masu"ku zauna mana" muryar Unaisah da yar shagwa6a tace"daddy zamu iya cire mayafin daga kan fuskar mu? Wlh ya takura mana" da kan shi ya cire mata mayafin, Ya yi mata rolling akanta, Ya matsa gaban Batool ya warware mata na kan fuskarta itama ya naɗa mata akan ta, sai dadi takeji ganin yayi mata yadda yayi ma Unaisah. Bayan sun zauna ya ɗan dafe table din gabansu da tafukansa Ya dubesu da kyau "Pls kada ku bamu kunya, ku natsu ku kwantar da hankulan ku gurin amsa mashi tambayoyin da zai yi maku, Mutun ɗaya ne zaiyi maku tambayoyin dan haka ku kwantar da hankalinku" kallon juna su ka yi atare kafin suka dube shi. Murmushi ya sakar masu "ina fatan zakuyi min haka" atare suka haɗa baki gurin first"Eh" yar dariya yayi"lokaci yayi zan tafi, ku kula mun dakan ku" amsa mashi su kayi da "toh" Bayan fitar shi daga dakin kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, kowa da abun da yake sakawa aran shi, damuwar Unaisah akan Danish tana ji aranta zaiyi wuya ya basu hadin kai. "Sis Wai wanene Zai yi mana tambayoyin"? Batool ce tayi mata tambayar kafin ta bata amsa suka ji motsin shigowar mutun atare suka kalli kofar ɗakin. har sai da gaban su ya fadi saboda ba su tsammaci ganin chief owais ba, ta wani bangaren sunji dadi saboda sun san wanene shi sun kuma yarda da shi ɗari bisa ɗari. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Walking Slowly yabi ta bayan kujerun su Ya nufi frigde ya buɗe ya dauko juice mai sanyi ya haɗo da cups biyu ya daura akan table din gaban su, duk wani motsin shi akan idanun su yanayin yadda yake tsiyaya masu ruwan lemun a cup ba ƙaramin tafiya ya yi da imanin su ba, komai nashi cikin aji, ƙasaita da nutsuwa yake yin shi" kwata kwata bai ɗago Ya dube su ba, har sai da ya gama zuba masu juice din mai sanyi a cups Ya tura ma su agabansu kafin a hankali Ya zauna tare da ɗaura kafarshi ɗaya kan ɗaya, ganin sunƙi daukar cups din yasa shi tunanin ko basu san su ya zubawa ma ba, kamar ya sani kuwa ai gani suke basu kai matsayin da chief zai zuba masu lemu a cup ba. Da index finger din shi ya nuna masu Cups din, Hakan yasa suka fahimci nasu ne, a tsanake suka ɗauka suka fara sha a hankali don kada yaga sun yi ƙauyanci musamman Unaisah da aji take shan juice din yayi mata dadi ga sanyi. A gayun ce ta rage kaɗan a cup din ta ajiye kan table, Batool kuwa duka ta shanye shi har tana shaƙe wa cikin raɗa unaisah ta yi mata magana don kada ya ji su "shashasha, Ki yi irin na yan gayu ki rage kaɗan, kada yaga hadamarki" baiwar Allah idanunta amarairaice ta kalli cup din ta shanye kaf tsoronta kada Unaisah tayi mata faɗa sunnar dakai ƙasa Unaisah ta yi ganin chief na kallonta wata irin kunyarshi da nauyinshi ne suka kamata. mayar da idanun shi yayi kan Batool in a cool voice ya furta"kin koshi ko in ƙara maki"? Maimakon ta bashi amsa sai ta kama kallon unaisah, nan take ya fahimci tana jin tsoron tayi mata fada. bai jira amsarta ba, ya ƙara mata juice ɗin a cup"ki dauka" jikinta asanyaye ta kar6i cup din takai baki saida ta shanye kafin ta ce"thank you" "Neva mind," ya faɗa tare da gyara zaman shi "Can we start?" ya fada yana kallon su Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Atare suka amsa mashi da Eh, tun kafin su zo head quarter din an sanar da su da harshen turanci za su yi magana saboda duniya ce zata saurari tattaunawar su. Shiru ya yi yana duban su da alama nazarin wani abu yake yi tsawon mintuna kafin kasaitacciyar muryarshi ta katse shirun na su "Da farko Inaso ku gabatar da min da kan ku" Unaisah ce ta fara gabatar da kanta kafin batool ta yi nata introduction din. "Tayaya akai kuka tsinci kan ku agidan kurkukun ƙaddara"? Kallon juna su ka yi, kafin Unaisah ta fara bashi labarin lokacin da ta gudu daga rigar fulani da yadda Bakar mota tayi parking agabanta aka zuro hannu daga ciki suka dauketa. "Daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba.." tiryan tiryan ta labarta mashi, bayan ta kammala nata cikin kuka saboda duk lokacin da ta tuna rayuwar da sukayi a kurkukun kaddara sai taji zuciyarta ta kare musamman mutuwar unaizah da majnoon dinsu, Ya mai da duban shi ga Batool jikinta sai kerma yake duk ta rasa nutsuwarta gaba daya sun fahimci halin da take a ciki. Jin tayi shiru yasa Unaisah ingiza kafadarta, Muryarta na rawa ta fara magana. "Ni bansan lokacin dana tsinci kaina agidan kurkukun kaddara ba, tsohuwar da ta raine mu wadda muke kira tsohuwa Tamira ta ta6a faɗa mana tun muna jarirai aka kawo mu gidan kurkukun, itace ma ta shayar da mu ta kuma raine mu har muka mallaki hankalin mu" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. dakyar ta ƙare maganar duk tabi ta ruɗe saboda kwarjinin da chief ke yi mata duk in ya ɗago da ido ya kalleta tun bai fahimta ba har ya fara ɗago ta, shi dinne akwai jan hankali dole mace ta ruɗe agaban shi kamshin turaren shi kadai ya isa ya susutar da su balle kuma shi din gaba ɗayansa. Kamar ɗan jarida haka ya tsare su da tambayoyi tun suna amsa mashi cikin dadin rai har suka fara galabaita tuni Gumi ya fara wanke goshin su duk da sanyin A.c din dake dakar fatar su, numfashin su har sauri sauri yake gurin fita musamman Batool kirjinta sai sama da kasa ya ke yi ta fara rikicewa, wata tambayar ma da kunya suke amsa mata saboda nauyin amsa mashi da suke ji. "Bayan sun ɗauke ki na tsawon watanni me su ka yi maki" ya fada tare da nuna batool da girarsa, sunnar da kanta ƙasa ta yi gaban ta na faɗuwa. "Ina sauraron ki" ya fada cikin aji yana duban Batool "Can I help her"? Unaisah ce tay maganar, tana faman jujjuya eye balls dinta "Rasa kunya 6eran tanka, nasan zata aika" big guy ne ya faɗa da zolaya yana kallon Taj, ashe suna atsaye gaban Mirror suna kallon su tare da su COO, CI, and Senior agents daga observation Room. harara Taj Ya jefa mashi"bana son Iya shege wlh" Big guy yace"gaskiya ke bakaso jarin ka bata da kunya, ita sister dinta tana jin kunya shine ita rasa kunya take fadin zata taimaka mata..." murmushi Taj yai batare daya ƙara tanka mashi ba. Girgiza kai chief yayi "No, I prefer her to tell me herself, kinsan ance waƙa bakin mai ita tafi dadin sauraro ko ba haka fa"? Ya faɗa tare da daga mata gira, cike da jin kunyar shi ta sunnar da kanta kasa tana dan sakin murmushi. Kayataccen murmushin gefen fuska ya dan saki tare da kallon Batool da ta tsare shi da idanunta. Yawu ta haɗiya kutt sautin Ya fita, cikin rawar murya ta fara en ena hakan yasa shi dakatar da ita"ki fara daidaita nutsuwarki" tuni tasha jinin jikinta muryarta na rawa ta amsa mashi da toh, shiru su ka yi na tsawon mintuna kalilan kafin yace da ita kin shirya amsa min"? Yanayin yadda yayi mata magana yasa taji wani bakon abu ya ziyarceta wanda batasan menene shi ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Jinjina mashi kai tay alamar eh kafin atsanake ta fara bashi labarin abin da ya faru da ita bayan giants sun dauketa na tsawon watanni. runtse idanun shi yayi tare da dafe forehead din shi da hannu ɗaya, wani irin tsantsar bacin rai ne ya ziyarci zuciyar shi, hatta su taj dake kallon su jikin su yayi mugun yin sanyi, sauran jami'an dake kallon su babu wanda ran shi bai 6aci ba, jikin su har tsuma yake yi tsabar fusata. Lokacin da ta karasa bashi labarin, dakyar ya iya buɗe idanun shi ya dube fuskarta suka hada ido cikin na juna "Iya abunda su ka yi maki kenan? cikin sanyin murya da yar sheshshekar kuka tace Eh Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kafin ya furta"idan kunayin jinin al'ada ne kadai suke daukar ku"? Tace eh Mayar da duban shi yayi kan Unaisah"ke fa"? da gira yai nuna da ita. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Cikin sanyin murya ta fara bashi labarin abun da ya faru lokacin da ta saci hanya ta fita daga dakin su na gidan kurkukun ƙaddara ta tafi neman Neman Danish har tsautsayi ya rutsa da ita ta haɗu da tsohuwa zafreeen. Bata boye mashi komai ba, sai da ta sanar dashi, abun da yafi kona mashi rai wankan jinin da matsafan su ka yi mata bayan sun tu6e mata kayanta, ga kuma azabtarwar da suka yi mata cikin shesshekar kuka tace"ta karfi ta tsiya suka sa ni na farke mace mai tsohon ciki da wuka har jaririnta saida wukar ta yanka, bayan haka suka tursasa min saida suka bani naman mutun tafasasshe suka sa karfi gurin banbare bakina kafin suka tura min naman, har ciwo saida naji gurin ya dinga bleeding...." wani irin tsantsar tausayin su ne ya kama shi da sauran jami'an da ke kallon su, chief baisan sa'adda Ya ruko yatsun hannunta a cikin nashi ba, saboda ta bashi tausayi sai yaji kamar ya yi huggin din ta da alama ya manta da jami'an dake kallon su. *DAGA ALƘAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*_______________________________________✍️💋✊ Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (302) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions[14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 46 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 07, 2024 Takun Ƙarshe Calmly yace"share hawayen bana son ganin su" jinjina mashi kai tay alamar toh Ya zuba mata juice A cup Ya miƙa mata, Yatsun hannunta na kerma ta dauka takai baki ta yi kur6a ɗaya ta aje, ta nutsu tana jiran tambaya ta gaba "Sun ta6a yin raping ɗin ki"? Dakyar yai mata tambayar saboda fargaban amsar da zata ba shi. Shiru tayi jimm tana tunanin meye ma raping din? Ko yana nufin irin abun da matsafan su ka yi ma su Deeja kamar yadda ta bata labari. Shirun da ta yi ba karamin kayar mashi da gaba tayi ba, hankalin shi ya tashi matuƙa. "Ko baki gane me nake nufi ba" da sauri tace"na gane, ni ba su ta6a yi min ba, saboda sai wanda ya fara jinin al'ada suke yi mawa" Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanunshi wani irin sanyine ya ratsa zuciyar shi ita kanta ta lura da yanayin shi tayi mamakin hakan. Sun ɗauki tsawon lokaci Yana jera masu tambayoyi Cikin ikon Allah suka amsa mashi duk wata tambaya da yayi masu babu abun da suka boye mashi saida suka faɗa mashi komai da suka sani dangane da rayuwarsu agidan kurkukun kaddara daga farko har zuwa lokacin da suka tsira daga kurkukun. gaba ɗaya jami'an dake kallonsu saida zuciyarsu ta karaya da tausayin rayuwar yaran musamman wadanda basu san labarinsu ba, abun ya girgiza su ya yi matukar ɗaure masu kai da al'ajabi, suna sauraran abun kamar amafarki saboda al'ajabin da ya rufe su, abin da yafi karya masu zuciya labarin Unaizah, wlh hankalinsu yayi mugun tashi sun girgiza da jin rashin imanin da matsafan suka yi mata, duk irin dauriyar jami'an isod sai da idanunsu suka kaɗa jawur tsabar fusata sunji zafin mutuwar yarinyar da yadda uban ta ya yaudareta ya salwantar da rayuwar ta tsabar mugunta da zalunci. "Menene Sunan mahaifinta"? Ya jefa ma Unaisah tambayar. Wani ikona Na Allah gaba daya ta manta da sunan kamar an shafe mata shi a kwakwalwarta. Girgiza kai tay"na manta sunan shi, amma idan na tuna zan sanar dakai, ta dai ta6a fadamin babban mutun ne a Nigeria" jinjina kai chief yayi"A cikin backpack din dinta da sojojin america suka ba mu, munga textbooks, jotter da diary kun ta6a buɗe su"? Shiru ta yi jimm kafin ta girgiza kai"bazan iya tunawa ba, amma yan zu backpack din tana adakin mu tun lokacin da na kar6a agurin daddyna" "Okey, Idan muka koma gida zan kar6a" amsa mashi tayi da toh Sara ma su yayi da hannun shi kafin ya jinjina masu da babban yatsan shi, gaba ɗaya suka saki murmushi "Thank you for your cooperation, Unaisah and Batool, The information you provided will help us find the oppressors and put an end to them In sha Allah" ya fada yana kallon su, at same time suka sauke ajiyar zuciya, dama aƙagare suke da ya kammala yi masu tambayoyin don ba karamar gajiya su ka yi ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Miƙewa ya yi ya nufi room door suka bi bayan shi, suna fitowa daga dakin da sauri Yan uwan su suka nufo su suna tambayar su me aka tambaye su. "Ku bari idan ku ka shiga zaku ji abunda muka ji amma fa akwai juice me sanyi zaku sha dadi" unaisah ce tayi maganar. Tun fitowarsu Chief Ya Bar wajen Ya nufi Observation room saboda ba shi ne zaiyi ma sauran tambayoyi ba. Tayi mamakin ganin Danish yana bacci ya langwa6e kan shi saman kujera da alama yaji dadin sanyin a.c din dake ra6ar shi, hakan ba karamin tada mata hankali yayi ba, gani take kamar baccin nashi bana lafiya bane da sauri ta nufi Sofa din ta zauna daga gefensa ta ƙura ma shi ido tana fuskar shi. Taj ne ya fito daga dakin da suke Ya nufo gurin su, Mutum uku Ya kira Parveen, Jemimah da Azeeza su uku aka shiga da su dakin tambayar, ahaka aka dinga dibar su ɗaya dayan duk wanda ya fito daga ɗakin jikin shi ba kuzari ga zufa saboda galabaita da tambayoyin da akeyi masu saukin su akwai Juice da ruwa me sanyi ita jemimah uwar son banza daga anyi mata tambaya daya sai tace ta gaji abata lemu ta jiƙa makoshin ta, ahaka aka samu ta amsa tambayoyin, haka itama parvin Jami'en da yayi mata tambayoyi yasha bakar wahala saboda shiririta da ta saka ga rashin nutsuwa kafin agama yi mata tambayoyin saida tasha juice yayi cup goma, Deeja kuwa dama basu sanya ran zasu samu wani abu daga gareta ba saboda ta6in hankalin ta, kamar ma bata jin dadin jikinta ko irin haukan da takeyi masu agida batayi a headquarter din ba tana zaune kan sofa ta yi shiru tana kallon duk wani mai giftawa. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Ɗaya bayan daya saida suka amsa tambayoyin da akayi masu, mutun huɗu da jami'an suka ji dadin tattaunawar su da yaba kokarin su Unaisah da Batool sai mazan cikin su duk da bakomai suka iya tunawa ba kamar abun da ya faru da su lokacin da aka ɗauke su na tsawon watanni sun kasa tuna abun da akayi masu sun dai san sunci baƙar azaba kuma duk wanda yaji alamomin da suka dawo hayyacin su da su a jikinsu zai fahimci hada homo su ke yi da su. Jami'an Sun firgita da jin irin rashin Imanin da matsafan suke yi ma su, sunji abun da Ya gigita tunanin su ba dan juriya irin tasu ba da kuwa sun fashe da kuka saboda bakin ciki da takaicin abunda akayiwa yaran da ba su ji ba basu gani ba, suna ji aransu idan ya'yansu ne hakan ta faru da su ya zasuyi? Wlh har zuciya zasu iya hadiya su mutu. Bayin Allah gaba ɗaya sun dawo kan kujerun sun zauna, fuskokin su sharkaf da ruwan hawaye saboda an fama masu raunin dake a cikin zuciyar su, idanunsu sun kaɗa jawur kamar jan gauta, sun yi shiru suna tuna rayuwarsu ta prison babu mai magana a cikin su, yanzu saura mutun ɗaya ya rage a shiga dashi dakin tambayar, sun ma rasa taya zasu farkar da shi daga bacci, ya hakimce kan sofa Hankalin shi kwance yake fitar da numfashi shi baisan meke wakana ba. Agaban kujerar da ya ke zaune jami'an suka tsaya suna kallon shi daga cikin su hada chief da taj da big guy. "Sir, Mu tada shi daga baccin"? taj ne ya faɗa tare da kallon chief "Bana so mu takura mashi, Mu jira zuwa lokacin da zai farka inaga zaifi" girgiza kai big guy yai"Sir ni anawa shawarar mu tada shi, saboda yaron yana da nauyin bacci, bamu san lokacin da zai farka ba ga baƙin mu na america da muke jiran ƙarasowar su, bayan haka yan uwanshi akagare suke da su koma gida, saboda sun gaji suna bukatar hutu" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. cikin tausasa harshe ya ƙare maganar yana duban chief, maganar big guy ta tuna mashi da nauyin baccin Danish, zai iya kai magrib bai farka ba, wrist watch din hannun shi ya duba kusan karfe ɗaya da rabi. "Sir, Nima anawa shawarar Atada shi daga baccin" acewar COO, Ci yace"nima na goyi bayan a tada shi daga baccin duba da lokaci" gaba daya jami'an sun goyi bayan a farkar da shi daga bacci. Duk abun da ke faruwa akan idanun su Unaisah suna kallon ko me ke faruwa. Kamar za su tada jariri daga bacci cikin muryar raɗa Taj ya furta sunan shi"Danish! Danish"! Kamar ya yi magana da bango, babu alamun zai farka A hankali ya dan bubbuga kafadar"pls danish ka tashi" still bai farka ba CI yace"amma dai yaro ne da jikin manya ko? Cos ni lokacin da aka turo mana hoton fuskar shi banyi tsammanin yakai haka girma ba" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Yar dariya Big guy yai"adinga hadawa da tubarkalla, dama nasan sai ka tanka, kai da baka iya gani ka yi shiru, to yaro ne shekaran shi 20" da zolaya yai maganar, murmushi Su ka yi tare da maida hankalin su akan Taj dake kokarin tada Danish. Big guy yace"Dama na faɗa ma ku Nauyin bacci ne da shi, a samu ruwa me sanyi a yayyafa masa a fuska watakil Ya farka" girgiza kai chief yayi"ban amince asanya mashi ruwa ba, bari na jaraba tada shi" mikewa taj yayi don ya bashi damar zama kusa da Danish. Bayan ya zauna ya kai hannu ya ɗan bubbuga kafadar shi"Danish? Ka tashi ina so zamu yi magana!.." a kalla ya ambaci sunan shi yakai sau biyar har Senior agents din sun fara jin fargaban anya lafiyar shi kalau. Ba zato ba tsammani, suka ga ya fara motsa yatsun hannayen shi alamar zai farka, kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, A hankali ya ɗan bude idanun shi waɗanda suka kaɗa jawur ya dubi fuskar chief. "Sannun da bacci, ka barmu muna ta jiranka" yamutsa fuskar shi yayi ba tare da ya furta kalma ba. Ruko hannun shi chief yayi"ta shi mu shiga ciki, mun gama yi ma yan uwanka tambayoyi saura kai kadai ka rage, Ina fata zaka bamu hadin kai kamar yarda suka bamu" Cikin kulawa ya yi maganar yana duban shi. Da wata irin kalasa Yake kallon chief dake masa magana, hanky din da ya rufe rabin fuskar shi tuni ya jima da warwarewa. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Tun daga kan yanayin shi Jami'an suka fahimci zaiyi ji dakai, Aransu suka ayyana kamar kanin chief saboda kamannin su da suka gani. Sunyi mamakin ganin yadda chief ke lalla6a shi kamar zai durkusa mashi mutumin da suke ma biyayya sau da kafa suke tarairayarshi yau shi ne dakan shi yake tarairayar wani, ba komai ne yasa shi yin hakan ba face don ya samu ya shawo kanshi ya amsa masu tambayoyin su baya son Danish ya bashi kunya. Dakyar Ya samu Danish Ya miƙe chief ya ruke hannun shi Yaja shi suka nufi Questioning Room ɗin yasan yadda yake da wuyar sha'ani shiyasa ya zabi kan shi a matsayin wanda zaiyi mashi tambayoyin yasan da wuya in wani ne Ya saki jikin shi. Gaba ɗaya burin jami'an Suga tattaunawar chief da Danish, sun ƙwallafa rai akan son jin bayanan da zai bayar, Suna atsaye gaban mirror din suna kallon su ta cikin Observation room din. Bayan sun zauna kan Chairs dake fuskantar junan su, Chief Ya zuba masu juice a cup ya miƙa mashi. kin dauka yayi har saida chief yace"na ka ne kadauka" kafin ya cira hannu ya dauki cup din Ya kur6i juice ɗin wani irin sanyi ne ya ratsa throat dinsa. bayan ya kammala sha ya aje cup din ya mayar da hankalin sa akan chief dake kallon shi, bai ta6a jin fargaban tambayar wani dan adam a duniyar nan ba irin yadda yaji fargaban tambayar Danish sun kurama juna ido an rasa me magana a cikin su. Jami'an dake kallonsu sunyi matukar ƙagara, Yayin da taj da Big guy hankalunsu ke atashe saboda zullumin kada Ya basu kunya. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Idan muka koma 6angarensu Unaisah, tun da suka shiga da Danish ta rasa nutsuwarta, Hankalinta atashe Yake saboda ita tasan mawuyacin abune Danish ya basu hadin kai, idan ta tuna rayuwarsu ta baya yadda kwata kwata bai ta6a fada mata wani abu daya shafi kurkukun kaddara ba duk irin mutuwar son da ya ke yi mata, haka ya dinga boye mata ko ta tambaye shi baya fada mata ita da take kaddararsa balle su da har yanzu bai yarda da su ba kallon su kawai ya ke yi saboda ba yadda zaiyi da su. Tun tana daga zaune har dai ta miƙe ta fara zarya a tsakar gurin da suke, hatta su Sajeed sai da suka lura da yanayin ta, ko da suka tambaye ta meke damunta sai tace masu ba komai ta kosa su koma gida ne. "Zamu iya farawa"? Ya tambaya yana kallon sa, tamkar baisan furta maganar Yace"yeah..." ajiyar zuciya chief ya ɗan sauke kafin ya fara magana "Ka fara gabatar mana da kanka, muna son muji sunan ka da takaitaccen tarihin rayuwarka" kalma ɗaya tak ya furta"Danish" daga nan bai ƙara magana ba, kuma baida niyar yin ta. Hakan bai damu chief ba, yayi mashi uziri saboda yasan ba lallai yasan me ake nufi da gabatar da kai ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Tun kana jariri ka tsinci kanka agidan kurkukun kaddara hakan na nufin kai rainon su ne, tun da a hannun su ka mallaki hankalin ka, kasan komai dangane da elders kuma kasan duk wani abu da suke aikatawa agidan kurkukun kaddara a matsayinka na prison shield dinsu..." ya faɗa yana kallon fuskarshi, yadda kasan yana fahimtar shi ya nutsu yana sauraron shi. Numfasawa chief ya yi kafin ya ɗaura da cewa"ɗan uwanka Salsabeel ya fada min kafi shi sanin su wanene shuwagabannin kurkukun kaddara ka kuma san komai dangane da su, bayan haka kaima kana ɗaya daga cikin Giants masu babban muƙami agidan kurkukun kaddara, saboda suna ji dakai kuma sun yarda da kai shiyasa har suka baka mukamin garkuwar su hakane"? Ya tambaya yana bin shi da kallo, ɗaga mashi gira Danish yai alamar eh ba tare da ya furta ba. "Bayan haka munji bayani daga bakin yan uwanka, kaine kayi masu hanyar da suka fita daga gidan kurkukun kaddara shima hakane"! Again ya ɗaga mashi gira. Ran Big guy yayi mugun 6aci saboda a gurinsu disrespecting ne Chief Yana magana Ka amsa mashi da gira ji yake kamar ya fada dakin Ya kifa mashi mari dama shi akwai zuciya. Chief kuwa bai kawo komai aran shi ba dangane da yadda Danish Yake amsa mashi. "Who are the Elders? Do you know their faces? cike da sa ran zai amsa mashi yayi tambayar. Girgiza mashi kai yai alamar a'a, Sai a lokacin Ya lura da yadda yake amsa mashi ba ɗa'a kwata kwata ranshi ya sosu. Muryarshi da sanyi ya furta"ba zaka iya yi min magana ba"? ɗaga mashi gira yai alamar eh, runtse idanun shi ya yi ranshi ya ɗan baci amma sai yayi kokarin sarrafa temper dinshi saboda bayason ya bi shi ta karfi yafi son ya lalla6a shi su rabu lafiya. "Kana nufin tsawon lokacin daka dauka agidan kurkukun kaddara bakasan su wanene elders ba? Ko fuskokin su baka sani ba"? Yamutsa fuska ya yi dakyar ya furta"nasan su amma ban san fuskokin su ba" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Don't lie to me, Nasan ba halin ka bane" "Why should I lie? If I don't want to tell the truth, I'll just shut my mouth." fuskarshi adaure yayi maganar. Jinjina kai chief yayi"sunayen su fa? Ka sani" Shiru yayi bai tanka mashi ba, hakan na nufin yasani baison fada mashi. Bai matsa mashi ba Har cikin ran shi baiji dadi ba, daurewa yayi ya canza mashi wata tambayar. "Ina so ka fadamin komai dangane da gidan kurkukun ƙaddara, da kuma abunda ake aikatawa a cikin sa"! Wani kallo Danish Ya jefa mashi mai wuyar fassaruwa, A kalla sun shafe mintuna Danish bai amsa mashi tambayarba, kuma bai da niyar amsa mashi. Jikinshi yayi mugun yin sanyi, bai ta6a zaton zaiyi mashi haka ba, duk irin yadda ya aje girman shi Ya kaskantar da kai agurinshi duk don ya samu ya basu hadin akai ashe shi ba ayi mashi gwanin ta. Cikin karyayyar murya ya furta"Ka yi shiru ba ka amsa min ba ko baka ji me nace ba"? Kawar da kan shi gefe yayi alamar bazai amsa mashi ba Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Softy chief yace"kada kayi min haka, idan ka fadamin ba iya mu zamu amfana ba, ku ma zaku amfana, Danish baka da burin daukar fansa akansu? Meyasa zaka rufa masu asiri? Mutanan da suka raba ka da iyayenka tun kana jariri suka sace ka, bayan haka suka tauye maka hakkinka na rayuwa tun baka mallaki hankalin ka ba, idan ma kana yi masu kallon iyayen ka masu kaunar ka toh ka dauna, Yakamata ka farka Danish! Mutanan da kake gani amatsayin wani naka basu ta6a sonka ba, sun raine ka ne saboda biyan bukatar kan su, duk ranar da ka mutu zasu manta da kai ne, tsawon shekara ishirin suka kuntata rayuwarka sun cutar dakai sun kuma raba ka da iyayenka saboda tsabar zalunci, kai baka tunanin ina nasu ya'yan suke? Nasan ba lallai kayi wannan tunanin ba amma inaso ka sani wallahi suna da ya'ya suna acikin mu suna rayuwar yanci cikin kulawa da gatantawar su, kai kuma sun wulakanta ka da sauran yan uwanka" a faɗace ya faɗa yana duban shi. "Rayuwata ba ta ta6a burge ka ba? Lokacin da ka shigo cikin mutane amatsayin wanda baison komai ba, shin baka yi tunanin sun yaudare ka ba? Ya tambaya rai abace yana kallon shi, Maimakon yaga rauni atare da shi saima yaga ko ajikin shi, maganganun chief basu karya mashi zuciya ba, su Taj dake kallonsu duk sun fahimci hada jahilci ke damun Danish, Elders sun kashe mashi rayuwa sun yaudareshi ta yadda bazai iya gane cutar da shi sukayi ba. Sun riga da sun yi mashi hudubar su, sun gatanta shi sun nuna mashi cewa su kadaine gatan shi a duniya. "ba gaskiya kake faɗi ba, they've never hurt me. Suna sona kuma sune iyayena, bayan su bani da wasu iyaye a duniyar nan" bai ƙare maganar ba chief owais daya gama harzuka rai a6ace ya ɗaki gaban table din ko gizau Danish bai yi ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Muryarshi a kausashe Ya furta"kai wani irin bauɗaɗɗan mutunne? Baka da tunanine? Ko bakasan ciwon kanka bane? Tayaya ina kokarin in fahimtar dakai kana kauce hanya? Meyasa kake yaudarar kanka? duk abunda mu ke yi munayi ne saboda mu daukar maku fansar cin zalunku da akayi mu kuma ceto rayuwar sauran yaran da ke a hannunsu sannan mu kawo karshen miyagun da suka kafa kurkukun ƙaddarar! Kai kadai zaka iya taimaka maka Danish! Don haka dole ka bamu hadin kai..." Ran shi yakai makura agurin 6aci baima san yayi mashi tsawa ba. idanunshi sun kaɗa jawur saboda bai ta6a neman abu agurin wani ya rasa ba Danish shi ne mutun na farko da yayi rejecting din bukatarsa. Jami'an dake kallonsu sun harzuƙa Musamman big guy Yafi fusata ganin yadda Danish ke wahalar da chief duk basu ji dadi ba Ga mamakinsu murmushin gefen fuska Danish yayi tare da furta"I'm respecting you, so please don't pressure me. If you want peace with me, stop asking about the prison of destiny and stop insulting the elders, bayan haka inaso ku sani bazan ta6a baku hadin kai ba indai akan su ne, saboda ku ba kowa bane agurina, ban hada alakar komai daku ba, duk da bani da ilmi amma nasan me na ke yi, Ina da hankali baku isa kuyi min wayau ba yan uwana kadai na sani su kadai zan bawa kariya kuma ina tare dasu babu wani wayau da za ku yi min" Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. maganar Danish ta yi matuƙar daure masu kai, Hankulansu yayi mugun tashi, gaba ɗaya chief ya rasa bakin magana saboda Danish Ya sagar mashi da gwiwa, yanayin fuskarshi ya nuna tsantsar mamaki da al'ajabi gaba daya ya fara sare da lamarin shi. "Zan iya tafiya" ya fada yana kallon fuskar chief dake kallon shi kamar gunki haka Ya kame sam ya kasa magana, idan har ya biyewa zafin zuciyarshi ba karamin faɗa zasuyi da junan su ba, sai dai bazai ta6a biye ma shi ba saboda shi ba ajin yin shi ba ne, bayan haka yana yi mashi Uziri duba da irin rayuwar daya taso still akwai tsantsar tausayin Danish a cikin zuciyar shi. bai jira Amsar da chief zai ba shi ba, Ya miƙe Ya nufi hanyar fita daga room ɗin, yana ruƙe handle din kofar yaji ta adatse. juyowa yayi tare da kallon chief, bawan Allah Ya dafe kan shi da tafukan hannayen shi, tsabar bacin rai da takaici ne ya addabe shi, wata irin zufar 6acin raice ta fara tsastsafo mashi, la66ansa har kerma suke shima sam bai iya fushi ba, zuciya ce da shi. "Ka buɗe min kofar zan fita" babu wasa akan fuskarshi yayi maganar A fusace chief yace"I'm not done talking to you! Come back and sit down. If you don't answer my questions, we'll spend the whole day here." kwatsam Yaji alamun buɗe kofar, aruɗe ya ɗago yana kallon shi yayi mamakin yadda ya iya bude kofar bayan computer ce ke controlling din ta, dole saida izninsu kofar zata buɗe. har ya ɗaga kafa zai fita kenan chief ya yi hanzarin mikewa ya bi bayanshi yana isa gaba daya ya faɗa kan bayanshi yayi hugging dinshi tighly kamar zasu koma mutun ɗaya. Cikin rauni na murya ya furta"Danish, I'm really disappointed in you.You embarrassed me, I never thought you'd do this to me you're hurting the heart that's trying to save your life. ban ta6a zaton za ka yi min haka ba" ya faɗa yana jan numfashi haɗi da ƙara cusa jikin shi ana Danish, wlh tsabar bacin rai ne yasa shi yin hakan saboda gaba ɗaya ya fara sarewa da lamarin shi, kafin su baro gida adakin Danish sai da ya roƙe shi akan ya ba su hadin kai yace mashi ya amince amma sai gashi yanzu ya bijire ma su, Bai ta6a zaton zai kunyata shi ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Rungumar da chief yayi mashi ba karamin kashe mashi karfin jikin yayi ba, Zuciyar shi taso ta karaya sai dai baya jin zai iya amincewa da su, kalaman chief sun tsaya mashi aranshi sun kuma sanya mashi kokwanto a tunanin shi, ga wani irin yanayi da yake ji mara misaltuwa atare da shi yana ji kamar suna da connection da chief, sam ya kasa ta6u ka komai yanayin fitar numfashin shi sam babu kwanciyar hankali. Lumsassun idanunshi ya ɗaura akan hannayen chief daya dafe flat tommy din sa, Har cikin ran shi baiji dadin bijire ma shin da yayi ba, baisan ya akai yake jin mutumin aran shi ba, Yana matuƙar ƙaunar Chief baya son bacin ran shi. Komai dake faruwa akan idonsu big guy, sun yi shiru suna jira suka ga martanin da zai mayar wa chief. A hankali Danish ya daura tafukan hannayen shi akan na chief ya damƙe su sosai yana mai jin wani irin yanayi mara misaltuwa, In a weak voice Ya furta"Ka yi hakuri, bazan iya ba ku hadin kai ba, pls kada ku tursasa min akan abun da banyi niya ba.." yana faɗan hakan ya 6an6are hannun chief daga ruƙon da yayi mashi ya fuce daga dakin, wani irin jiri ne ya kusa ɗibar shi da sauri ya dafe ƙofar da tafin hannun shi. Da ƙarfi Big guy ya ture kofar Observation room Ya futo Yana huci Ya nufi Danish dake kokarin komawa gurin su Sajeed, da sauri sauran Jami'an dake a tare da shi suka biyo bayan shi ganin yadda ya fusata, sun san halin shi yana da bad temper. Taj dake abiye da su hankali atashe Ya ke danna wayar sa layin Salsabeel ya kira cikin sa'a ya ɗaga ko sallama baiyi ma shi ba ya faɗa mashi abunda ke faruwa, salsabeel ya zabga salati dama sai da yai fargaban faruwar hakan, saboda shi yasan wanene Danish, mutum ne mai kafiyar tsiya ga girman kai da rashin yarda. "Yanzu haka ina acikin head quarter din, wallahi nasan za'a rina shiyasa na yanke shawarar zuwa saboda shi" acewar salsabeel bayan sunyi sallama taj ya mayar da dubanshi ga big guy wanda tuni Ya cimma Danish wani irin kukan kura yayi tare da kai hannu Ya damƙi kwalar rigar shi, Jami'an dake a kewaye da su suka rurruƙe hannun big guy suna kokarin su raba tsakanin su. Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana, Kusan atare su Unaisah suka miƙe idanunsu azazzare suke kallon su cike da faduwar gaba. Da wata irin kakkausar murya ya furta"Who the hell are you? ɗan uban wanene kai a kasar nan? Me kake taƙama da shi ne huh? Kana da wani gata ne daya wuce Allah da shi chief din ne? Saboda tsabar rainin wayau yana magana kana amsa mashi da gira tsaran wasan ka ne shi"? Ya faɗa yana bin shi da wani ƙasƙantaccen kallo, big guy irin bauɗadɗun mutanan nan ne masu saurin fushi, wani lokaci sai daga baya su yi dana sani, shiru Danish ya yi batare daya tanka ma shi ba. Big guy yaci gaba da fadin"Da kasan wanene chief da ba ka yi mashi haka ba, in ba dan aikin shi ba kai ka kai matsayin da zai kula ka ne? Ka rasa wa zaka yi disrespecting sai mutun mai kima da daraja a idon mutane, mutumin da ya ke hana idon shi bacci don ya taimaki rayuwar al'umma, mutun mai tausayin da jin ƙan na ƙasa da shi..." ya faɗa A harzuke Yana kallon cikin idanun Danish wanda yayi kasaƙe yana kallon shi, karfin halin mutumin ya bashi mamaki yadda ya damƙi kwalar rigarshi batare da jin shakkar yin hakan ba. "Sir, ka yi hakuri ka daina yi mashi faɗa, me zai hana mu lallashe shi ni inaga idan muka bi shi ta lallama zai bamu hadin kai kodan abunda muka ji wurin yan uwanshi dole muyi mashi uzuri" CI ne yai maganar cikin kwantar da murya Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Agent zahra Yace"sir Please, ka kyale shi, He's still young, it's not your place to argue with him, He doesn't know anything, We need to persuade him gently." cikin tausasa murya ya faɗa yana kallon fuskar Big guy tamkar baisan suna magana ba Ya haɗe rai ba annuri ko kaɗan akan fuskar shi. Dafa kafaɗar shi COO yai"Allah Ya huci zuciyar ka Yalla6ai, mu kan mu bamu ji dadin abun da yayi ba amma yakamata muyi mashi Uziri saboda baisan komai ba..." bai kare maganar ba Unaisah ta fashe da matsanancin kuka, kamar jira su Batool su ke ta fara kuka suma suka fashe da kukan gaba daya sautin shesshekar kukan su Ya karade kunnuwan jami'an dake agurin, tsabar tashin hankaline Yasa suka fashe da kuka dama tun da suka fito daga dakin tambayar zuciyarsu araunace take saboda raunin da aka fama masu ga kuma wani tashin hankalin da suke kallo duk da basu san meya faru ba amma sun fahimci Danish ne yayi wani abu badai dai ba. "OMAR, pls ya isa haka! Ka sake shi, nayi magana da Salsabeel awaya ya faɗa min yana acikin head quarter din yanzu zai shigo" idanun shi jawur Ya dubi Taj a fusace Yace"Taj I won't let him go. He must return and answer the chief's questions, ya 6ata min rai ya rasa wazai disga sai chief din mu? Tsaran wasan shi ne? duk kokarin da ya ke yi akan su shi baya gani ne? Ni bana son mutun mara ɗa'a irin shi ..." Ya fada tare da cije le6en shi ya maida dubanshi ga Danish wanda tuni Jikin shi Ya fara kakarwa wata irin zufar 6acin rai ce ta fara tsatstsafo mashi, Numfashin shi ya fara hauhawa yana fita cikin sauri, lokaci daya temperature din jikin shi ya ɗau wani irin zafi, idanun shi suka rune zuwa Ja. "Yaya Omar dan Allah Ka sake shi, nayi maka alkawarin zan shawo kan shi" cikin shesshekar kuka Unaisah tayi maganar Haris yace"dan Allah Ya Omar ka ƙyale Danish, Idan laifi yayi maku ku yi hakuri zamu fahimtar da shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya yi hakuri Ya saki Danish Adaidai Lokacin da Salsabeel Ya faɗo arean da suke yana faman wurga idanu don ya gano inda suke kwatsam idanun shi suka sauka akan gungun jami'an da su ka kewaye su. Gaban shi ne yayi wani irin faduwa aguje ya nufe shi har yana bangaje jami'an dake sintiri kamar mahaukaci haka suke kallon shi Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Yana ƙarasawa ya sanya karfi ya raba tsakanin big guy da Danish Yana faman haki ya dubi Danish wani irin faduwar gaba yaji ganin sa6ar majici akan wuyan shi babu wanda Ya lura da sabar sai shi da Allah ƙaddara zai ganta, wahalallan Yawu ya haɗiya la66anshi na rawa ya furta"Danish, please...don't. Please, Danish, try to control your anger.." gaba ɗaya jami'an sun ruɗe da ganin yadda Salsabeel ke lallashin shi, Musamman Big guy ranshi ya ƙara 6aci a faɗa ce yace"meya sa ka ke bashi hakuri"? Salsabeel bai tanka mashi ba saboda tashin hankalin da yake tunkaro su batare da su sun sani ba, In har evil heart dinshi ta motsa zai rikiɗa ne ya canza halitta, ya tarwatsa head quarter din gaba ɗayanta ba ƙamar 6arna zai yi ma su ba. Da hannu ya dafe saitin zuciyar Danish, Ya marairaice mashi fuska tare da girgiza mashi kai alamar A'a... gaba daya jami'an sun kasa fahimtar me Salsabeel Ya ke nufi! Wani irin dogon numfashi Danish Yaja cikin zafin nama Ya bangaje hannun Salsabeel daga kan kirjin shi yana faman fitar da huci mai zafi ya miƙi hanya, aguje su Unaisah suka bi bayan shi suna kwala mashi kira ko kallo ba su ishe shi ba, bai sha wahalar gano kofar da suka shigo Soc din ba Ya fu ce daga ciki Ya nufi main enterance gate na head quarter din. Kafin karasawar shi big guy ya kira layin ɗaya daga cikin jami'an dake tsaron gate din Ya basu Umarni karsu kuskura su bar shi Ya fita. Lokacin daya karaso Yana tafiya kamar baya acikin hayyacin shi, hankulan jami'an dake sintiri gaba daya ya dawo kan shi, fisatattun jami'an dake tsaron gate din suna ganin shi suka gane shi ne matashin da aka basu umarni karsu bari ya fita, aikuwa azafafe suka yi mashi ƙawanya kamar zasu rufe shi da bugu. Yan uwanshi sai kuka suke suna ambaton sunan shi hadi da yi mashi magiya akan ka da ya tafi ya bar su, babban abunda suke ma fargaba in ya fita ina zai dosa? Dakyar chief ya iya lallashin zuciyarshi cike da rashin ƙwarin jiki ya fito daga ɗakin Ya nufi su big guy dake atsaitsaye curko curko sun kasa kunne suna sauraron Bayanin da Salsabeel ya ke yi masu dangane da Danish "Ga chief nan" taj ne Ya fada kusan atare suka kai duban su gare shi, damuwa ce karara akan fuskar shi. Bawan Allah da buɗar bakinsa sai cewa"Ina Danish? Ina sauran yaran"? Kafin wani daga cikin su Ya bashi amsa sautin ringing wayar big guy ya katse hanzarin su Da sauri Ya kara wayar a kunnan shi. Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. "Sir, Yaron nan fa Ya fita! Mun yi kokarin mu dakatar da shi amma mun kasa, gaba ɗaya ya watsar da jami'an da sukai kokarin hana shi fita..." a kidime Big guy ya furta"what? Ya fita! Garin yaya hakan ta fadu"? Wani irin faduwar gabane Ya ɗarsu a zuciyoyin su, sunyi matukar mamakin jin hakan shin tayaya akaima har ya iya fin karfin jami'ansu Ya fuce daga head quarter din? "Yaran suna nan, amma ɗaya daga cikin ƴan matan mai launin ido ruwan toka ta kubce mana, yanzu haka wasu daga cikin jami'an mu sun bi bayan su" Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, Salsabeel bai tsaya yaji karashen zancen ba, Ya watsa aguje Ya fuce, Agaggauce Senior agents din suka rufa mashi baya, ya rage saura big guy da chief atsaye suna fuskantar juna "Meya faru Omar? Meyasa Ya tafi? Wani ya 6ata masa rai ne ko abunda ya faru tsakanin mu ne"? Dakyar big guy yai karfin halin zayyana mashi abunda ya faru bayan fitowar Danish Girgiza kai yayi cikin sanyin murya yace"meyasa Omar? Meyasa zaka yi mashi haka? Kamanta wanene shi? Yaron da bai san komai ba yanzu daka bata mi shi rai ina kake tunanin zai dosa? Wa ya sani agarin nan"? Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora. Yanayin yadda chief ke yi mashi magana araunace ba karamin karya mashi zuciya yayi ba. "Duk abun da nayi nayi ne saboda kai, kasan irin kaunar da nake maka, zan iya jure komai amma wlh muddin wani yayi kokarin bata maka rai bazan kyale shi ba, koma wanene.." "Nasani Umar, amma ni baka kyauta min ba, yakamata kayi amfani da hankalin ka, rayuwar shi abun tausayi ce, tabbas raina ya 6aci da abun da yayi min amma wlh ko kusa ban ji haushin shi ba, saima son shi da ya ƙara ninkuwa acikin zuciyata, yakamata mu yi mashi Uziri bai kamata mu ga laifin shi ba yaron da har yanzu suna iya control dinshi..." bai ƙare maganar ba ya juya cikin takun sauri Ya nufi hanyar fita daga Soc din da sauri big guy yabi bayan shi *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* YOU MAY LIKE THESE POSTS Previous Post Next Post GET IN TOUCH SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (23) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (302) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (3) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: _________________________________✍️ Sautin ringing ɗin wayarta ne ya farkar da ita daga dogon baccin daya ɗauke ta, tana a kudundune cikin lallausan duvet dinta. da wata irin malalaciyar kasala ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da su kai mata nauyi saboda baccin da tasha ga wani irin tsami da jikin ta yayi mata, lalube ta fara yi tana shasshafa bedmattress din don taji idan yana nan har ta ƙare lalubawa bata ji mutum akan gadon ba, hakan na nufin ya jima da tafiya. Tunawa da yanayin da take a ciki yasa tay saurin ware idanunta cike da fargaba ta dubi jikin ta zir take ba sutura, lumshe idanunta tayi cike da jin shaukin shi take ɗan jan numfashi, yayin da ƙwaƙwalwarta ke tariyo mata abun da ya faru tsakanin ta da shi a lokacin da suke tsaka da jin daɗin su. A hankali ta miƙe zaune ta ja duvet din ta lullu6a kirjin ta da shi, kafin ta jingina bayan ta jikin headboard, sumar kanta ta yamutse saboda damƙar da tasha a hannun big boss, ko ina na jikin ta zafi ya ke mata. idanunta sun kumbura sun kaɗa jajawur, haka la66anta ma sun kumbura don ba karamin tsotsa suka sha ba, ta galabaita sosai har wani jirin kasala take ji a jikin ta. Kifa kanta tayi kan gwiwowinta tunawa da nasihar da mahaifinta ke yawan yi mata. "Ke kadai Allah Ya bani mamana, tun kina ƙaramarki bani da burin daya wuce in inganta rayuwarki ki zama hafizar alkur'ani mai ilimin addini da zamani saboda inyi alfahari dake sannan ki zama abun kwatantace, Alhamdulillah cikin ikon Allah sai gashi kin cika min burina ko'ina zancenki ake duk in na shiga cikin jama'a sun dinga yabonki suna fadin ƴata malama ce hafiza mai cikar kamala da kamun kai ga kyautatama al'umma da son taimako, kowa yabon ki yakeyi, burin kowace mace tayi koyi da Aishatu bintu imam malik mace ɗaya tamkar da dubu, Ummi nasihar da zan maki ko bayan ba raina kiji tsoron Allah, kada ki canza daga yadda nasanki, abun da zaki min wanda zaki biyani shi ne Ki karemun martabana da kimata a idon duniya, kada kiyi abun da zai zubda min mutuncina Aishana" Rushewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, a duk lokacin da ta tuna nasihar mahaifinta zuciyarta ba ƙaramar karaya ta ke yi ba, tana jin tsanar rayuwar data ɗaukarwa kanta, tana mai danasanin abun da yayi silar rabuwarta da mahaifinta, saboda bata da abu mafi soyuwa da ya wuce shi a duniyar nan, kai duk wani gata da ya zata samu agurin ubanta ta samu ninkin baninkin sa. tana jin raɗaɗin karya alƙawarin mahaifinta da ta yi na kare mashi martabarsa. kifa kanta tayi jikin pillow, ita kadai baiwar Allah babu mai lallashin ta. Ba halin ta bane, ba laifin ta ba ne, tana da ilmi tasan zina ba kyau ta kuma san hukuncin wanda ke aikatata amma meyasa takasa dainawa ko da tayi nufin ta tuba ta koma ga Allah? Tasha yunƙurin yin hakan amma aduk lokacin da big boss ya buƙace ta bata iya bijire ma shi. Ta yi kuka tamkar ranta zai fita kamar ƴar dambe ta dunƙule hannayenta ta dinga bugun mattress kamar zatai hauka ta tsani abunda take aikatawa bata so ta mutu batare da yafiyar mahaifinta ba, kuma batason ta mutu tana aikata sabon Allah tana matukar jin tsoron makomarta. Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita hayyacin ta, fuskarta sharkaf da hawaye ta janyo wayar daga kan drawer ta duba sunan me kiranta. Maji daɗina shine sunan daya bayyana akan screen din, kasa picking call din tayi saboda fushin da zuciyarta ke yi. Text message ne ya shigo on the top of the screen din wayar, cikin zuciya ta soma karanta abunda ya rubuta mata _"ummi, na tafi ba tare da nayi maki sallama ba, ki yi hakuri da hakan nasan zaki tashi da kewana, anyi min kiran gaggawane, ba dan nagaji da jin ɗumin jikin ki ba, bazan iya misalta daɗin da kika jiyar dani ba, kin bani cikakkiyar gamsuwa da zan iya ɗaukar kwanaki ban nemi matana ba, bazan iya biyanki ba Ummi, ki fadamin me zanyi maki don in faranta maki"_ Runtse idanunta tayi gam, siraran hawaye suka dinga shararowa kan kuncin ta.. "Ya Allah Ka cire min jarabar son bawan nan naka, Ina neman tsari da shi...." bata kare maganar ba kwatsam taji dirar motoci acikin gidan, a firgice ta jefar da wayar ta faɗa kan mattress ta duro daga kan gadon, tafin hannunta a tallabe da bargon ta faɗa toilet taja ƙofa ta datse, tana faman zare idanunta, sam ta manta da su Batool tasan bai wuci sune suka dawo gidan ba, abunda take jima fargaba kada wani ya shigo ɗakinta tasan in har suka ga gadonta sai sun zargi wani abu saboda ya 6aci ba kaɗan ba. Cikin Takun sauri Chief Ya faɗo Falon Ya nufi upstairs, agurguje taj da big guy suka biyo bayan shi, kwata kwata babu kwanciyar hankali akan fuskokin su damuwace ƙarara saboda jami'an da suka tura su nemo Danish kusan awanni har yanzu ba wani labari, har tracking layin sa sukai a karshe suka gano location din da wayar take agida yabar ta baije da ita head quarter din ba, wannan dalilin ne yasa suka yanke shawarar su dawo gidan, watakil su gan shi. bai nufi ko'ina ba sai bedroom din Danish Yana isa bakin kofar yayi knocking ɗin ta cike da fargaban kada su ki ganin shi. Jin shiru ba'a buɗe kofar bane yasa shi tureta da hannun shi ya faɗa ciki Yana haki saboda gudun daya sha, bazai iya tuna when last yayi irin shi ba. da matsanancin faduwar gaba yake bin dakin da kallo wayam babu kowa adakin dafe kan shi yayi da hannu ɗaya idanunshi sun kaɗa jawur babban tashin hankalin shi Ina Danish yaje? ya zai yi da yan uwan shi? Me zai fada ma Uncle hateem idan ya kira yana son yin magana da shi"? "baya aciki ko"? muryar boss ce ta katse mashi zancen zucin shi Big guy duk ya rasa kuzarin shi Ya daura ma kanshi alhakin 6atan Danish saboda shi ne silar daya ja har ya yi zuciya Ya tafi, sai yanzu ya ke danasanin bata mashi rai da yayi ganin yadda ya ɗaga hankalin chief Owais. "Taj bansan ya zanyi ba, baya nan, ya tafi, ya zanyi da raina, bana so na rasa yaron nan wallahi danasan abun da zai faru zuwan mu headquarter da ban tursasa mashi akan yabi mu ba..." dakyar yake magana saboda damuwar data cika zuciyar shi. jikinsu yayi mugun yin sanyi. Cikin raunin jiki ya dubi big guy"Omar, kaga abunda kaja min ko? Idan har yaron nan bai dawo gida nan ba, bazan yafe maka ba..." gaba ɗaya ya rikice masu. "Sir kayi hakuri, na kar6i laifina, kuma nayi danasanin 6ata mashi rai da nayi, bada son raina ba ya 6ata min rai ne amma nayi maka alkawarin zanje in nemo shi duk in da ya shiga agarin nan..." yana faɗan hakan ya juya azafafe ya haura kan stairs ranshi ya 6aci da furucin Chief, kalmar daya furta mashi ɗazu daya ce Son danish na kara ninkuwa azuciyar shi yaji haushinta bayan irin cin mutuncin da yaron yayi mashi amma ko kadan ransa bai 6aci ba, shi arayuwarshi bayason wanda zai shiga tsakaninsa da chief, yana matuƙar jin kishin yaga chief yana nunama wani so fiye da shi hakan na kona masa rai yafi so koda yaushe ya zamana na hannun daman shi. Dafa kafadar chief yai da hannun shi"dan Allah ka kwantar da hankalin ka, bana so kana sanya damuwa aranka, in sha Allah Danish zai dawo ..." lallashin shi ya cigaba da yi, bawan Allah gaba ɗaya ya rasa ƙwarin gwiwar shi. "Nima Zan bi Omar, Zamuje mu binciko shi" Numsafawa yai kafin ya dubi Taj da rinannun idanun shi "Ina sauran Yaran? Sun shigo?" bai ƙare maganar ba, suka jiyo sautin tafiyar su da sauri taj ya dubi kofar shigowa falon, ɗaya bayan ɗaya suke shigowa kamar yan gudun hijra saboda jigatar da su ka yi, fuskokin su sharkaf da hawaye sun sha kuka bayin Allah har sun gaji sun gode ma Allah, Unaisah tafi su jin jiki har wani jiri take gani acikin idanunta, sun ruke hannun Juna ita da Batool suma sauran sun rurruka hannayen junan su. "Sun shigo," "Pls, Calm them down, I don't want them to worry about losing their brother, ka cigaba da lallashin su, Sannan ashirya masu lunch dinsu" "Sir kaima kana bukatar hutu, ka koma daki ka kwanta ka huta zanyi magana akawo maka lunch din ka" girgiza kai yai"wallahi bazan iya cin komai ba in har Danish bai dawo gidan nan ba" Taj yayi mamakin kalaman shi, bai ta6a zaton son da chief yake ma Danish yakai har haka ba, aranshi ya ayyana watakil ko dan saboda sabon da sukai da junan su cikin kwanakin nan. "Da ka daure.."bai kare maganar ba ya katse shi"Boss ka tafi kawai, Ka kula da sauran yaran, Ka kira auntynsu ka fada mata halin da suke a ciki" Cike da jin tausayin shi ya amsa mashi da toh. Lokacin da ya sauko down, A kan sofas Ya hango su zazzaune sun yi shiru kamar masu zaman makoki, tsayar da idanun shi yayi akan Unaisah da ta kwantar da kanta saman kafadar Batool, tayi matukar bashi tausayi, bakomai yake tunawa ba face lokacin data bi bayan Danish ta haura kan titi mota takusa hankadeta ba dan Allah yasa Jami'an su sun yi gaggawar Kai mata agaji ba da tuni rai yai halinsa saboda ta furgice idanunta sun makance bata ji bata gani danish kawai take nema ido rufe, har wani zazza6i take ji ajikin ta mai azabar zafi, ga ciwon kai daya fara takura mata, ta rasa meke mata dadi duniyar nan, ita damuwarta ina Danish ya shiga? Baisan kowa ba agarin abuja, abun da take jima fargaba kada yace zai koma Gidan kurkukun kaddara duk in zuciyarta ta raya mata hakan sai taji matsanancin faduwar gaba ga tashin hankali da firgici. kwata kwata babu wanda Ya lura da Taj a cikin su saboda damuwar data rufe idanun su. Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka kalle shi in ka cire Unaisah wadda ta rufe idanunta hawaye sai suntiri suke yi kan kuncin ta. Jiki asanyaye ya zauna yana dubansu "Unaisah! " dakyar ta buɗe idanunta da suka rune zuwa ja ta kalle shi "Meyasa baki jin maganata? Bana hanaki yin kukan nan ba? Ko shi zaisa ya dawo ne"? Yawu mai ɗaci ta hadiya tamkar bata son yin maganar tace"daddy, bana jin dadin jikina ne" "Ba dole jikinki yaki dadi ba, duk kinbi kin daga hankalinki uhyum! Sai kace ba kisan tawakkali ba Unaisah! Ce maki akai Ya bace ba zaki kara ganin shi ba ne? ya fada yana kallon fuskarta, shiru tayi tana sauraron shi tasan ba lallai ya fahimce ta ba tun da shi a zaton shi sabo ne kadai atsakanin su. Sassauta muryar shi yayi cikin sigar lallashi yace"kuyi hakuri nima na damu da rashin shi, amma bai kamata ku zauna kuyita kuka ba, ba zai yi maku maganin komai ba saima ya kara jaza maku wani ciwon, ku tayashi da addu'a in sha Allah zai dawo ko dan saboda ku..." sun yi shiru suna sauraron shi. "Allah Ya kare mana shi aduk inda yake, Allah Ya karkato mana da tunanin shi ya dawo gida .." cikin sanyin murya suka amsa mashi da Ameen Miƙewa Parveen Tayi boss yace"ina zuwa"? hannunta dafe da cikinta tace"fitsari ne Ya matse ni" ta fada tare da kama hanyar ta nufi dakin su, "Nima fitsarin nake ji, tun ɗazu ya matse ni" murya na rawa jamimah tayi maganar tare da mikewa daga kan sofa ta watsa da gudu ta nufi dakin su. "Time din sallah azhar har ya wuce, Ku tashi ku tafi ɗaki, ku yi wanka ku yi sallah kafin ku fito zanyi magana a shirya maku lunch din ku nasan kuna jin yunwa" cikin kulawa ya faɗa yana duban su. Bata jin zata iya cin abinci in har Danish bai dawo ba, cike da rashin kuzari ta miƙe idanun ta akan daddynta dake kallon ta bakomai ne ke daure mashi kai da ita ba face haukan da tayi ɗazu ya rasa gane meke a tsakaninta da Danish!. Ta ɗan tsargu da kallon da yake yi mata, in a weak voice tace"Zan shiga daki, bansan ko zan dawo na iske ka ba, ka gaida min aunty Danejo" bata tsaya taji amsar shi ba, ta juya ta nufi dakin su tana tafiya a harharɗe kamar zata kife ƙasa har sai da ta shige dakin tukunna ya ɗauke ido daga kallon ta. Knocking door room dinta da akayi ne yasa tayi sauri fitowa waist ɗinta daure da towel, hannun ta ruƙe da wani short towel da take tsane sumar kanta da shi. Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Batool daga waje tana fadin "Aunty Ummi ni ce, Mun dawo, ki buɗe min ƙofa..." wani irin sanyi ne taji ya ratsa zuciyarta, taji dadin jin muryar Batool saboda a halin da take a ciki tana bukatar wanda zai kwantar mata da hankalin ta. "Batool, ki jira ni, Ina shiryawa ne" "Toh" Cikin kankanin lokaci ta kammawa shiryaw cikin abaya baƙa mai kyan gaske, ta yi rolling headscarf, ta nufi door room din tana buɗewa Batool tayi sauri faɗawa kan kirjinta, tayi mata wata irin runguma kamar zata koma cikin ta wani irin faduwar gaba taji saboda kunnnata sun jiyo mata shesshekar kukan batool, dama tun da ta rungume ta taji aranta ba lafiya ba. Aruɗe ta furta"My Babe, meya faru? Baki da lafiya ne"? Ta faɗa tare da tallabo fuskar Batool da hannunta, hankalinta ya ƙara tashi da ganin yadda fuskarta ta yi jawur ta jike da ruwan hawaye Jijjiga kafaɗarta tayi"meke damunki ne? Wani abu ya faru ne? Fadamin mana waya ta6a min ke"? Ta fada akagare da son jin amsarta. La66anta na rawa ta labarta mata abunda ya faru a head quarter dangane da batan Danish. Hankalinta Ya tashi matuƙa muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa inna ilaihirraji"un Amma banji dadin abun da big guy yayi mashi ba, bai kyauta ba Allah, da hankalinshi da komai sai kace baisan wanene Danish din ba..." rai a6ace tay maganar. "Yanzu Ina su Unaisah din"? "Duk suna adakin su, gaba ɗaya basa jin dadin jikin su saboda abunda ya faru, munyi kuka har mun gaji" tsantsar tausayinsu ne Ya kamata ga damuwar bacewar Danish tana jin shi kamar kaninta saboda kaunar da takeyi ma su Da tafukan hannayenta ta share ma batool hawayen dake sintiri kan fuskarta. "Ki daina zubda hawayenki, bana so pls, ni nasan zai dawo ne in sha Allah, mu tayashi da addu"a" ta fadi hakanne saboda tasan bazai iya jure rashin Unaisah ba, tun shekaran jiya data ga abunda ke tsakaninsu tasan ba karamin abu ne zai iya raba su ba. "Aunty Ummi ko sallah banyi ba.." "Okay, ki shiga ciki ki yi, bari naje gurin yan uwan naki, nasan zasu neme ni" a hanzarce ta fuce daga dakin, sam ta manta bata gyara gadon ba, saukin ma ta bar bargon a toilet. _________________________________✍️ *ANEELERH💓* a Zaune take kan gadonta jikinta sanye da riga bubu, ta yi shiru tana kallon baby junaid dake zaune gefen ta hannun shi ruƙe da plate din wainar fulawa wanda zahra ta soya mashi ita, sai tsantsani yake saboda dadin da tayi mashi dama ya iya kwaɗayi, kadan yake balla ya ɗan dangwala yaji saiya tura a cikin karamin bakin shi Shekaran jiya izuwa yau ya ƙara samun lafiya walwalar shi ta dawo tun da yaga Angel dinsa ta cika shi da farin ciki, ko bacci yake yana ambaton sunanta, tun da suka dawo gida ya addabeta akan ta kira Angel awaya tace mata tazo yana son ganin ta, dakyar take samu ta shawo kan shi, sai dai har yanzu bakowa yake yarda ya ɗauke shi ba, daga momynsa sai zahra da mami amma su abie kam ƙiwuya yake yi masu abun yana daure mata kai, har mahboob bai cika yarda ya dauke shi ba. Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar shi ta katse ta "Mommy, wannan sauran wainar dana rage na Angel ne, wa zai kai mata? ko ni zakisa mahboob yakaini a mota in kai mata..."ya faɗa yana nuna mata rabin wainar da ya rage a plate din Murmushi tasakar mashi"na fada maka ba Angel bace, bana so wani yaji kana kiran sunan Angel, ita yarinyar da ka gani sunan ta Azeezaty suna kama ne da Angel din mu" yamutsa fuska yai tare da maƙe mata kafada"wallahi wayo zaki min, Angel dina ne ita ay har tambayarta nayi tace mun eh itane ko" ya faɗa da shagwa6a yana hade fuska. Ƙura ma juna ido sukayi batasan ya zatay da shi ba tana son ta tambaye shi meya faru amma tana jin fargaban kada akoma yar gidan jiya, zai iya birkice mata tun da ta fahimci baison maganar kwata kwata. "Mommy kina kallona ko zaki ci wainar ne in ɗan maki" ya fada yana kokarin 6allo mata da sauri ta furta"a koshe nake my baby boy, na fiso ka ci ka koshi..." farfari yayi mata da idanun shi "Yaushe zaka koma school"? Maƙe mata kafaɗa yai"shaina ƙara samun lafiya" yar dariya tayi "junaid na ganoka gudun school kake, Allah next week zan maida ka, ay naga kaji sauki jikin ka ya murmure" yamutsa mata fuska yai tare da zumbura mata baki "Allah in kinasho in koma ki sani makarantar su Azeezaty, sai mu runka yin wasa da ita" ya faɗa tare da 6allo wainar da ya rage ma Angel ya tura abaki yana ci, murmushi tayi tare yin kasa da muryar ta"babyna" ya amsa mata naam Takai hannu ta shafa sumar kan shi. "Zaka iya tuna abun da ya faru ranar da muka je gidan Hajiya adama"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda ya ware idanun shi da karfi, Jikin shi ya fara kerma kamar mazari. da sauri ta janya plate din wainar ta daura kan table, ta saukowa daga kan gadon ta zukunna agaban kafafuwan shi kamar mai neman gafara. "Dan Allah junaid ka fada min, kaga ni mommynka ne, duk duniya baka da tamkar ni, idan ma kana jin tsoron ka fadi ne wasu suji nayi maka alkawarin bazan bari kowa yaji ba daga ni sai kai...." tatta6e fuskarshi yayi ruwan hawaye suka taru acikin idanun shi labbanshi suka kama kerma taji faduwar gaba da ganin yanayin shi sai dai bata jin zata iya hakura a wannan karan, saboda tayi matukar ƙagara da son jin meya faru da su aranar!. Ruko hannun shi tayi cikin sigar lallashi da wayau da dabara ta karya murya tare da marairaice mashi fuska duk don ya tausaya mata ya fada mata, magiya ta dinga yi mashi yayi shiru yana kallonta da tsantsar tashin hankali akan fuskarshi. can dai ta ɗan bugu cikin shi da wayau tace"Ni dama na sani Ana guduwa tayi junaid, sai da nace mata kada ta tafi tabarmu amma shine ta tafi, ni bansan laifin da nayi mata...." bata ƙare maganar ba, sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata daga bakin junaid Cikin shesshekar kuka yace"mommy bafa guduwa tayi ba, Allah dodone Ya kashe ta a cikin gidan nan, ni na ganshi da idona kuma itane tace in gudu in 6oye" kamar an dasa mata aya ta tsaya cak tana kokarin tariyo maganar shi acikin zuciyarta lokaci ɗaya ta saki dariya tana fadin"haba junaid, abun naka hada zolaya, karya fa babu kyau, In ba zaka fadamin gaskiya ba ay basai ka shirga min karya ba..." girgiza mata kai yai babu alamun wasa akan fuskarshi ya furta"wallahi mommy dagaske nake faɗe maki, dodone Ya cinye ana adakinta, tana ta kuka hada jini a jikin ta..." yadda kasan kanzon kurege haka take sauraron shi sai tikar dariya takeyi irin ya raina mata wayon nan shi kuwa ya haƙiƙance yana faɗa mata iya gaskiyar shi sai ma ta maida maganar tashi abun nishadi. "Mommy ki daina dariya, ba abun dariya bane wlh dagaske nake maki" wani kallon rainin wayau ta wurga mashi kafin tace"junaid bana hanaka yin rantsuwa akan karya ba..." kuka ne Ya ci karfin shi wannan karan ta ɗan ji faduwar gaba duk da bata yarda da maganar ba ta dauki abun shiririta arude ta ke lallashin shi cikin shesshekar kuka yace"mom.. my ba karya bane, ki daina min dariya, ni banaso dodon daya kashe ana ya kashe mu mommy, dan Allah mu gudu mubar gidan nan ni wlh tsoro nake ji..." bata san sa'adda ta rungume shi a kirjinta ba, hankalinta yayi mugun tashi saboda kukan da junaid yake yi mata tasan halin kayanta ba karamin abune zaisa junaid yin kuka ba irin haka, tabbas wani mummunan abu ya faru da ya yi silar zaucewarshi sai dai zuciyarta taki yarda da maganar shi, gani take bame yiyuwa bane. _______________________________✍️ A ƙalla ta fi karfin mintuna a tsaye tana kallon Unaisah dake a kwance kan darduma ta nannaɗe kafafunta cikin hijab, idanunta suna a rufe gam sai yan siraran hawayen da ke sintiri kan fuskarta tayi kukan tayi addu'ar amma har yanzu zuciyarta taki sarara mata daga radadin da take mata, gani take kamar ta rasa Danish. aranta tana ji in har kurkukun ya koma tabbas zata bishi ne ko da hakan zaiyi silar rasa ranta don ji take bazata iya rayuwa batare da shi ba. "Unaisah!" ummi ce ta kira sunan ta, tayi shiru tamkar bata ji ta ba "Nasan kina ji na, ni bansan ya zanyi dake ba, duk irin kokarin da nayi gurin kwantar maki da hankali kinki daina kukan nan, ga abincin ki dana sa akawo maki shima kinki ci, to wai kukan da kike shi zaisa ya dawo ne? Tun da kinyi addu'ar sai kibar ma Allah komai In sha Allah zai dawo...." cikin sigar lallashi ta faɗa tare da zukunnawa gaban prayer mat din "Dan Allah ki tashi ki ci abincin ki..." da wata irin karyayyar murya ta furta"aunty Ummi, ba zaki gane ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, zuciyata bata min dadi ji nake kamar zan rasa raina ne, yaya Omar ya 6ata min rai, shine silar komai, wallahi Aunty ummi naji zafin kalaman daya gaya ma Danish, duk da baida ilmi ko jahili akayi ma gori sai yaji ba dadi" jikin Ummi ba karamin sanyi yayi ba, ga wani irin tsantsar tausayin Unaisah daya kamata, tasan bai wuci hada soyayyarshi ke azabtar da ita ba. "Kiyi hakuri Unaisah, In sha Allah Danish zai dawo, Allah shi zai tsare sa aduk inda yake, mu taya shi da addu'a ni inaji araina ko dan saboda kaunar da yake yi maki zai dawo" dakyar ta buɗe idanunta wadanda suka kada jajawur ta dubi ummi duk da halin da take a ciki tayi mamakin kalmar kaunar data furta. fahimtar hakan yasa ummi tay saurin furta"naga kamar yafi kaunarki a cikin yan uwanki, kema haka shiyasa nace haka, kada ki ɗauka ko ina sanya maku ido ne" shiru tayi bata tanka mata ba. "ni abun da nake tunani watakil ya ke6e kanshine awani guri don ya gusar da bacin ranshi in ba haka ba Danish ay ba za ace ya 6ace ba, mutumin da ba shi kadai bane tsaf zai iya kawo kan shi gidan nan..." bata kare maganar ba ta dakata tana kallon Unaisah ganin yadda ta zabura ta miƙe tsaya kamar zata fadi saboda rashin kwarin jikin ta "Ina zuwa"? "Yanzu zan dawo aunty ummi, wani abu zan duba" tana fadan hakan tasa kai ta fuce daga dakin cike da sa ran hasashen ta zai zama gaskiya, maganar da ummi tayi ta tuna mata da wani abu daya ta6a faruwa. ________________💋Chief Owais💪 Kwance yake akan gadon shi, yar singlet da short ne ajikin shi, damuwa ta hana shi ta6uka komai, ya dade bai shiga tashin hankalin daya shiga a yau ba, wayarsa dake akan bedside drawers sai ringing ta ke yi daga kiran ya katse wani ke shigowa sautin ya cika kunnuwan shi, amma baya jin zai iya picking din su yasan bai wuci Na hannun damansa bane suke kira don suji ko an ga Danish. Shaf ya manta da bakin da za su yi, saida tunanin Ya faɗo mashi aran shi kafin ya mike ya janyo wayar shi tare da duba screen din My dad shine sunan daya gani saida ya fara daidaita nutsuwarsa kafin yai picking call din "My Son, Ya kake Ya aiki, ka manta da daddyn ka ko"? Duk da halin da yake aciki sai da yaji nutsuwa ta shige shi jin muryar daddynsa lumshe idanun shi yayi cikin sanyin murya ya furta"lafiyalou daddyna, ni na isa in manta da bugun zuciyata? Mutumin da nake kwana in wuni da tunanin shi araina saboda kaunar da nake masa" Sautin dariyar mai girma sharafuddeen ce ta ratsa kunnan shi cike da nishadi yace"My Son kasan duk wata hanya da zaka kare kanka agurina, ka faranta raina, but meke damunka ne? Naji muryarka kamar baka jin dadi..." Shiru yayi jim dama yasan zai yi wuya in daddyn nasa bai gane wani abu ba, dayawan lokutta ta muryar shi kadai yake gane halin da yake a ciki. "Babu komai, yanzu na tashi daga bacci ne, shiyasa kaji voice dina wani iri" "Hmm owais kenan, har ni zaka boye ma damuwarka"? "Daddy, ka yi hakuri zan iya kiranka anjima mu yi magana"? "Okay, in ba baka kira ba, Ni zan kiraka, ko inzo gidan naka da kaina kasan bana wasa da lafiyarka" yar dariya chief yayi saboda yaji dadin maganar shi ba wani jimawa sukayi ba sukai sallama layin Omar ya danna ma kira kusan sau uku tana ringin bai ɗaga ba sai a kira na hudu yayi picking. Kara wayar yayi a kunnan shi"Omar, kana Ina"? On the other hand big guy yace"na tafi neman bugun zuciyarka saboda bana so in rasa ka" shiru yayi jimm yana maimaita maganar big guy harya fahimci ranshi ya 6aci saboda yayi mashi karya, location dinshi ya nuna yana agidan kamar ko ya sani yana akwance kan gadon bai jima da tashi daga bacci ba. "Omar zamuyi magana, nasan meke damunka, pls don't forget to get the soldiers ready and go to the airport, jirgin su commender yakusa yin landing nan da minti talatin " "Consider it done, sir, amma ya yakamata kaima ka shirya mu tafi airport din atare, zasu fi jin dadin tarbar da zamuyi ma su" "Just do what I say" ya umarta, bai bari big guy ya kara magana ba yayi rejecting call din don baya jin zai iya fita daga gidan a halin da yake a ciki. *Unaisah Angel* Bayan fitowarta daga dakinsu bata nufi ko'ina ba sai upstairs tana tafiya jiki duk ba kwari ta tura kofar ɗakin ta shiga daga ciki bata ga kowa ba. Gadon shi tabi da kallo sai ta dinga ganin kamar zata gan shi kwance yana bacci, kau da idanunta tayi ta juya ta nufi toilet dinsa. A hankali ta daura tafukan hannayen ta, ta tura ƙofar ta buɗe ta, dira ƙafarta ke da wuya taci karo da abunda yayi silar razanar da ita ta daddage ta fasa kara tana ambaton sunan Allah ta dafe kanta da tafukan hannayenta, hadi da runtse idanunta jikinta ya fara kakarwa, wani irin faduwar gaba taji tamkar ana dakan sakwara a kirjin ta. dukkan ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tayi matuƙar firgita da abunda idanunta suka gane mata, tayi matukar razana, yatsun hannunta na kerma ta bude kofar ɗakin garin saurin ta fita cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da ƙasan hijab dinta dake ja da kasa gaba ɗaya ta wuntsila ta yi kundunbale ta kife ƙasa hankalinta yayi mugin tashi jikinta yadau zafi rau wata irin zufar tashin hankali ce ta fara tsastsafo mata. Tana ta kokarin mikewa donta gudu taji motsin buɗe ƙofar tuni tasha jinin jikin ta, ta ƙame a durkushe ta kasa ɗagowa yayin da ƙwaƙwalwarta ke tariyo mata Halittar da tagani a cikin toilet dinsa kamar Wolf (kerkeci) jibgegen gaske. Ƙamshin turaren Chief ne Ya ziyar ci kofofin hancin ta, Kafin Daddaɗar muryarsa ta katse zancen zucin ta "Unaisah? Are you Okay"? Ay tana jin muryarshi ta yi wani irin yunkuri da iya karfinta na karshe ta zabura ta miƙe, gaba ɗaya ta faɗa kan broad chest dinsa ta ƙanƙame shi, cikin shesshekar murya take faɗa mashi abunda ta gani a cikin toilet din tare da yi mashi nuni da yatsan ta. Sam ya kasa fahimtar me take nufi, sai kallonta yake yadda ta kankame jikinshi ta hanashi motsawa daga gani ta tsorata ba kadan ba. "Unaisah, what's wrong? Who's in the toilet?" Batare data ɗago ba ta furta"dodo ne a toilet din sa," "Okay, zanje na duba, ki jira anan" ya fada tare da ruko hannayenta a hankali ya banbare su daga kan waist dinsa. yayi mamakin uwar zufar daya gani akan fuskarta kamar an yayyafa mata ruwa ga zafin da jikinta ya ɗauka yaji shi har jikin shi da ta rungume shi sai faman jan numfashi take tafin hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta. "Ki kwantar da hankalin ki, Ina atare dake, ba abun zai faru..." yawu ta haɗiya tana faman zare idanunta acikin nashi ta amsa mashi da toh. har ya ɗaga ƙafa zai nufi toilet din Yaji ta damƙo upper arm dinsa, slowly yakai duban shi gare ta. Girgiza mashi kai tay a tsorace tace"Don't go alone, I don't want anything to harm you" murmushin gefen fuska ya sakar mata har cikin ranshi yaji dadin nuna damuwa da ta yi akan shi hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba. "Kada ki damu, ba abun da zai faru dani in sha Allah" ya fada yana kallon Heart shaped lips dinta da suka jiƙu da ruwan hawayen ta. Taƙi sakin rigar shi saboda ta tsorata da abunda tagani tana jin fargaban wani abu ya same shi, shi da bai saba da wahala ba. Maƙe mashi kafada tay kamar ƙaramar yarinya cikin sanyi murya tace"hankalina bai kwanta daka shiga ba, pls kada kaje, ka kira salsabeel awaya yazo ya gani ko ka kira sheikh imam malik" A hankali ya cire hannun ta daga kan arm dinsa Kamar ta sanya mashi kuka, bai jira ya kara jin me zatace ba, Ya nufi toilet din sai da ya fara karanta addu'ar shiga kafin ya sa tafin hannunsa ya ture ƙofar A hankali ta buɗe. Without feeling nervous ya fada cikin toilet din, Yana shiga idanunshi sukayi mashi kyakkyawan gani yayi matuƙar mamakin ganin shi kwance cikin kwamin wanka Ya cika shi da ruwa, ko kayan jikin sa bai cire ba ahaka ya kwanta a ruwan Kamar ma bacci yake yi. _Tsantsar mamaki da al'ajabi ne suka bayyana karara akan fuskar shi, Ikon Allah mutumin da suke ta wahalar nema kamar zasu tada garin abuja, ba irin neman da jami'an su basuyi mashi ba sako da lungu na garin saida suka bincika basu gan shi ba ashe yana acikin toilet dinsa kamar al'jani, ko taya akai ya shigo gidan? Bayan har gate officers ɗin gidan sai da ya tambaye su koya dawo gidan suka ce mashi bai dawo ba, gani yake kamar amafarki yake kallon shi saboda zuciyarsa taki aminta da abun da idanunsa ke nuna mashi_ Da tsantsar ruɗani ya furta"Danish! Is that you?" *DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE✍️* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: __________________________________✍️ "Danish is that you"! Ya faɗa yana bin fuskar shi da kallo, babu alamun yaji maganar shi, babu inda ke motsi a jikin shi in ka cire numfashin shi dake fita cikin nutsuwa. Walking slowly chief ya isa bakin bathtub ɗin ya zuƙunna kan kafafunsa ba tare daya kau da ido daga kallon fuskar Danish ba. Allah kadai yasan farin cikin da ya mammaye zuciyar sa wanda misalta shi ma bazai yiwu ba, Yau da ya rasa ɗan tahalikin nan Allah kadai yasan halin da zai shiga. Abun da ya faranta ranshi da baije ko'ina na, ko da suka bata mashi rai bai yi fushi ba, bawan Allah sai ya dawo gida yayi kwanciyar shi cikin ruwa hakan na nufin bazai iya rayuwa ba tare da yan uwansa ba, duk runtsi duk wuya yana atare da su. Cikin sanyin murya ya sake ambaton sunan shi"Danish" Shiru bai motsa ba, cike da fargaban kada ace wani abun ne ya faru da shi chief ya daura tafin hannunsa na dama saman forahead dinsa ya shafa shi har zuwa kan karan hancin sa. Ba zato ba tsammani yaji Danish Ya damƙi wuyan Hannun sa, eye lids dinsa na kerma dakyar ya buɗe idanun shi da su kai mashi nauyi ya dubi chief. Da wata irin kakkausar murya yace"saboda yan uwana na dawo nan" Wani irin faduwar gaba Unaisah taji, yayin da take kokarin shigowa toilet din cike da fargaban me zata taras jin shiru chief bai fito ba shiyasa ta yanke shawarar bin bayan shi. Lokaci ɗaya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata muryarshi, tayi matuƙar yin mamaki saboda ita lokacin data shiga toilet din jibgegen wolf tagani zaune cikin bathtub ɗin shiyasa ta raza, yanzu ta gane shi ne ya rikiɗa ya dawo mutun. wani irin tsantsar farin ciki ne mara misaltuwa ya wanke zuciyarta, dama saida ranta ya bata zai dawo, hasashen da tayi ya tabbata maganar da ummi tayi ce ta tuna mata da ranar daya rikiɗa kafin ya zama maciji da jikin shi ya dauki zafi rau cikin kwami ya shiga ya tsuma kanshi da ruwan sanyi. yanzu ta gane idan ranshi ya 6aci yana son yayi cooling temper dinsa ruwan sanyi yake shiga, taji tausayin shi, shi dai rayuwarshi wani sa'i kamar bata mutane ba. "Danish, ka tada min hankalina, daga ni har yan uwanka da abokan aikina, babu irin neman da ba ayi maka ba a garin nan, saboda kai ko abinci na gaza ci, ban ta6a tsammanin damuwar da nayi dakai takai har haka ba..." ya faɗa yana kallon cikin idonshi. "Da na san ranka zai 6aci da ban matsa maka mun tafi head quarter ba, banji dadin abunda big guy yayi maka ba, na tsawatar mashi kuma ya gane kuskuren shi, bazai ƙara gigin bata maka rai ba" yanayin yadda chief ke yi mashi magana da sigar lallashi ba karamin kwantar mashi da hankali yayi ba, zuciyarshi taso ta karaya da jin irin kaunar da yake yi mashi, tun daga kan facial expression dinsa yaji ya yarda da duk wani abu daya faɗa masa. "Kayi hakuri idan na bata maka rai, sannan inaso Ka faɗa min duk wasu sharrudda da zamu bi don mu zauna dakai lafiya batare da mun 6ata maka rai ba saboda naji jiki ba kaɗan ba lokacin da aka sanar dani ka fita nayi zaton bazan ƙada ganinka arayuwata ba" softy ya fada tare da tsamo hannun Danish daga cikin ruwan ya haɗe yatsun hannun su cikin na juna, yayi shiru yana sauraron shi. "Sannan Alfarmar da zan roko a gurinka, nasan baka yarda da ni ba, amma dan Allah ko dan saboda yan uwanka kada wata rana kayi fushi ka koma inda ka fito.." ya ɗan dakata yana kallon yanayin fuskar Danish. "nasan za ka yi tunanin kodan saboda ina son ka bamu hadin kai shiyasa nake lallashin ka, ba haka bane, Kamar Yadda Allah ya jarabci Uncle dina da kaunarka nima haka nake jinka a zuciyata" Unaisah dake atsaye bakin toilet door din gaba daya tana sauraran maganar chief, zuciyarta ta karaya da tausayin su, aranta ta ayyana wannan wata irin zazzafar kaunace suke yi ma shi? Anya Danish bai da alaƙa ta jini da su? Lumshe idanun shi yayi tare da numfasawa slowly ya ware eyes dinsa akan fuskar Chief Baiyi tsammanin zai tanka ma shi ba, in weak Voice Danish Yace"ban ruƙe ka a zuciyana ba, amma ku daina bata min rai in na nuna bana son abu kada ku tursasa min, ni bana so na cutar da kowa, shiyasa na ke6e kaina saboda in sanyaya zuciyata, kamar yadda kake jina a zuciyarka nima haka nake jinka, haɗin kaine kawai bazan baku ba, sannan ka yi hakuri da bata maka rai da nayi, I didn't realize I was rude to you and disrespected you until he told me." runtse idanu chief yayi gam na dan wani lokaci bai furta komai ba, har cikin ranshi yaji dadin maganar da Danish Ya furta mashi na cewa shima yana jin shi kamar yadda yake jin shi, yasan sannu a hankali wata rana zai samu amincewar shi. Phone ringing dinsa ne Ya sa shi hanzarin buɗe idanun shi tunawa da bakin su, wrist watch din hannun shi ya duba. "Danish, Ka fito daga cikin ruwan nan haka, Inaso Ka shirya, nasan kana jin yunwa, zan sa ashirya mana dinner" Amsa mashi yayi da Okay Fitowa Chief yayi daga toilet din, Ya zaro wayar daga trouser pocket dinsa, misscalled ya gani da layin big guy. Kira ya danna masa bayan yayi picking, big guy ya sanar da shi cewa yanzu haka suna akan hanya sun dauko su commender daga airpot. fuskar shi da fara'a ya furta Alhamdulillah Allah Ya kawo ku lafiya, bai sanar dashi game da ganin Danish ba, ya bari sai in ya zo gidan ya ganshi. Bayan sun yi sallama, Ya kira layin Ci ya sanar da shi game da ganin Danish yace ya sanarma sauran abokan aikin su, Ci yayi farin ciki sosai harya shawarce shi akan su lalla6a shi kada su yi duk wani abu da zai 6ata ma shi rai. Sai da ya kammala yin wayar ya lura babu Unaisah a dakin, ranshi ya bashi may be ta fita ne don ta sanar da uwanta. bayan fitar Chief da yan mintuna, A hankali Danish Ya futo daga ciki, har ya cire kayan jikin shi, short kadai Ya bari, sumar kanshi dake a jike ta manne ma fatar bayan shi da gefen fuskar shi, tamkar babu kuzari a jikinshi da wata irin kasala yake taka kafafun shi, a duk lokaci daya rikiɗa ya dawo suffar shi ta mutane ba karamin jiki yake ji ba. Gaban dressing mirror ya dakata da tafiya ya dafe gaban mirror ɗin da tafin hannun shi ɗaya. Kunnuwan shi ne suka soma jiyo ma shi motsin mutun a dakin shi, yayi zaton chief ne hakan yasa bai damu daya ɗago da ido ya kalle wanene ba. "Meyasa ka tafi batare da ka fada min inda zaka je ba? Kasan irin tashin hankalin dana shiga na rashin ganin ka"? Da sauri ya kalle ta ta cikin madubin Tana tsaye abayan shi ta goya hannayenta kan kirjin ta, abayan labulen dakin shi ta la6e saida taga chief ya fita tukunna ta fito don ta samu damar zazzaga mashi masifa. Har sai da gabanshi ya ɗan fadi ganin yadda idanunta suka kumbura sun kaɗa jawur ko ba afada masa ba yasan tasha kuka tamkar ranta zai fata. tuni yasha jinin jikin shi yasan ba zai tsira daga fushinta ba dole ta hukunta shi. Bai aune ba, yaji ta faɗa kan faffaɗan bayanshi ta zagayo da hannayenta kan broad chest din shi ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rufe idanunta da ke tsiyayar da ruwan hawaye ta dunkule yatsunta kamar yar dambe ta dinga bugun kirjin shi da karfi, duk da hakan bata huce ba sai da ta gartsa mashi ciwo har sau uku akan fatar bayan sh Ko kaɗan baiji zafin abun da tayi mashi ba, ya fahimci irin radadin da taji na rashin shi yasan tayi tunanin Ya koma kurkuku ne. Cikin shesshekar kuka take fada mashi abunda ya faru bayan tafiyar shi. Zuciyar shi ta karaya ya kara jin tsantsar kaunarta da sonta acikin zuciyar shi, yadda takusa salwantar da rayuwarta saboda shi! Duk da fushin da take da shi na abunda ya faru tsakaninsu hakan baisa ta daina damuwa da shi ba, kamar ma ana kara mata zazzafar kaunar shi. yayin da yake wannan tunanin idanunshi sun cicciko tab da kwalla a hankali yake kallon hannuwanta dake akan kirjin shi ta gama naushin nashi yanzu tsunkulin kirjin shi ta ke yi duk fa don ta huce radadin daya kunsa mata, zuciyar shi tayi matuƙar karaya saboda tausayin rayuwarsu daya kama shi, yana jin tsoron ranar da mutuwa zatayi masu yankan kauna, yasan dole wata rana ɗaya ya riga ɗaya mutuwa acikin su, fatanshi Allah yasa in ma mutuwarce ta fara daukar shi saboda baisan yaga mutuwar Unaisah, ko ma ta ɗauke su atare saboda yasan ba lallai ta iya surviving batare da shi ba, yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa yaki yarda ya bada hadin kai saboda shi ya san me zai biyo baya. Lumshe idanun shi yayi yayin da siraran hawaye suka fara yar tseral kan kuncinsa, shesshekar kukan ta da yake ji a kunnansa ba karamin karya masa zuciya ta ke yi ba. Sai da tayi mai isarta, tayi shiru tana kara makalkale jikin shi yana jin duk wani motsinta a jikinshi harta bugun zuciyarta da dumin jikinta duk yanaji anasa jikin.. In a weak voice ta fara magana taja jan numfashi "Ban hana ka tafi duk inda zaka je ba, amma ka fara tunanin wani hali zan shiga kafin ka yanke shawarar tafiyar, sannan in ma zaka tafi toh ka tafi dani, idan ba haka ba zan hadiyi zuciya na mutu ne" bata kare maganar ba, yai saurin ruko hannunta acikin nashi ya janyota ta dawo ta gabanshi yayi saurin rungumeta tightly a kirjin shi kamar zasu koma mutun daya. hijab din jikinta ta jiƙe sharkaf da gumi kamar babu a.c adakin tsabar hucin da jikinta keyi mata ba, da alama Unaisah ta manta da hudubar aunty umminsu ta kuma manta da sharuddan data gindaya mashi na kusantar inda take sai gashi yau saboda halin data shiga na gudun kada ta rasa shi yasa ta kunsata kanta da shi ta kuma rungume shi saboda tana bukatar jin dumin shi a jikinta, tausayinshi da kaunarshine suka rufe mata ido har tagaza gane abunda take badai dai bane ta manta. Sunyi shiru babu mai magana acikinsu, ko motsi basa sonyi saboda yanayin da suka tsinsu kan su mai wuyar fassaruwa ji suka inama zasu dawwama ahaka sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi ko ba mutuwa akwai kaddara da zata iya raba su 🥺 Da wata irin kasala Yasa hannu yaja hijab din jikinta ta zame ta dawo kan kafadarta. ya cusa hannunshi cikin lallausar sumar kanta ya nannaɗeta gefe guda ya fiddo da kunnnata na dama. Saitin kunnan ya daura tausasa red lips dinsa cikin sanyin murya mai dadin sauraro ya furta"kamar baki yarda da kaunar da nake maki ba? Meyasa zaki ɗaga hankalinki bayan kinsan cewa bazan iya rayuwa batare da ke ba, idan ma kina tunanin hakan toh ki daina...." ya faɗa cike da bata tabbaci har cikin kunnnata take jin iskar numfashinsa.. "mutun yana rayuwane tare da ƙaddararsa sannan bai isa ya guje mata ba, nima haka take agurina, bazan taba tafiya nabarki ba in har bake kika bani iznin in tafi ba, ke kadaice zaki bani umarni in bi, gaba ɗaya burin rayuwana akanki ne da yan uwana, bazan ta6a rabuwa babu ku ba, duk runtsi duk wuya zan kasance atare daku" bai ƙare maganar ba ta tari mumfashin shi da cewa"ka yi hakuri da abun da ya Omar yayi maka, nasan shine ya bata maka rai, nima raina ya 6aci zanyi mashi magana yadaina bata maka rai" ta fada ba tare da ta dago kanta ba. Murmushi ya danyi har cikin zuciyarshi yaji dadin maganarta shiyasa yake kara kaunarta saboda kaunar da take masa, zata iya bata mashi rai amma wani bai isa ya daga masa yatsa ta kyale shi ba. "Ki kyale shi, ba laifinsa bane, ni ne na 6ata masa rai, komai ya faru ni naja ma kaina.." Hankalin shi Yayi mugun tashi da abunda idanunsa suka gane mashi, tsabar kidima da tashin hankali har wani jiri jiri yake gani acikin idanunshi, da sauri ya dafe kofar dakin gudun kada jiri ya kwashe shi ya kife ƙasa, Yayi danasanin zuwa dakin Danish dayasan zaiga abunda zai jijjiga kwakwalwarsa da tashi hankali da baiyi gigin zuwa ganin Danish ba!. Ya gaza yarda da abunda idanun shi ke nuna mashi da kuma abunda kunnuwanshi suke jiyo mashi. Angel dinsa ce kwance ajikin namiji sun kankame juna kamar anta da jini? Wlh bai ta6a zaton zatay mashi haka ba, ta karya zuciyarshi ba kadan ba. bazai juri kallon su ba, adaddafe Ya juya yabar kofar dakin dama yazo ne donya ga Danish Chief ne Ya bashi labarin sun ganshi, bawan Allah da farin cikinshi ya zo don ya bashi hakurin abunda big guy yayi mashi ashe da rabon yaga abun da zai hana shi runtsawa adaren yau. shi mamakin shi tayaya Unaisah har tasan dadin ta rungumi namiji? A tunanin shi batai wayon da za ta yi hakan ba, bayan haka yana yi mata kallon mai hankali bai ta6a zaton zatay abunda tasan haramun ne ba. yana tafiya kamar zai kife kasa saboda jirin dake shirin kwasar shi, babban tashin hankalinshi ya zaiyi ya raba alaƙar su? Saboda ya fahimci azababbiyar kaunace atsakaninsu ko romeo da juliet albarka, kai wannan har layla da majnoon sun shallake sai yanzu ya gane dalilin dayasa ɗazu ta haukace tabi bayan Danish har mota takusa hankadeta ashe sone Ya makantar da ita. shi azaton shi shakuwace atsakaninsu ashe shine bai fahimta ba, bakomai yake tunawa ba face alkawarin daya daukarwa kanshi na mallaka ma chief Unaisah, tun kafin ma ta bayyana ya bashi ita, sadakine kadai bai biya, ba yadda za'ay ma ya amince ma soyayyar Unaisah da Danish! Ko ta halin ƙaƙa sai ya raba su, bama zai ta6a yiwuwa ba, ay bata isa tasa shi zubda girman shi ba, bare aje ga batun bashi kunya. Acikin zuciyarshi yake ta sambatu kamar wani zautattace. Peck ya manna mata akan forehead dinta ta lumshe idanunta tana jin wani irin abu yana ratsa tsigar jikin ta. numfashi ta ɗanja tare da sauke shi kan kirjin shi iskar ta daki fatar shi. tana kokarin ɗago da kanta kamar daga sama tajiyo muryoyinsu Batool daga waje suna ambaton sunan Danish a ruɗe ta raba jikin ta daga nashi tayi saurin komawa bayan curtain ta 6oye tana faman sauke ajiyar zuciya. Bin labulan yayi da kallo baiso suka katse masu hanzarin su ba, murmushi yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba, daga gani yaji dadin faranta masa rai da tayi. Kamar an korosu suka fado dakin ko sallama babu, da karfin suka hada baki gurin furta"Danish"! Juyowa yayi tare da kallonsu, gaba ɗayan su ne babu wanda babu acikin su. Wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskokinsu, bayin Allah tun da suka dawo daga headquarter tashin hankalin bacewar shi Ya hana su canza uniform din jikinsu ko wanka ba su yi ba. harya motsa lips dinsa zai yi magana bai yi aune ba gaba daya suka nife shi suka fada kan jikinshi kamar zasu kayar da shi kasa, saboda yadda suka baibaye shi kamar ƙudajen zuma, gaba daya sautin kukan su ya cika dakin nashi. dayasan halin da zai jefa su da bai tafi yabarsu ba, a zaton shi sun daina damuwa da shi ashe har yanzu ba abun da ya sauya na daga kaunar da su ke yi ma shi. Dakyar ya samu suka kyale shi cikin shesshekar kuka suka fara korefe korafe akan tafiyar da yayi yabar su. Haris daya fara zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu kowa yana fada masa irin tashin hankalin daya shiga, murmushi yadinga sakar masu kamar zaiyi dariya saboda sun bashi nishadi sun kuma faranta ranshi, ita Batool da tafi su jin jiki pillow ta dauko ta fara buga mashi kan kirjin shi aikuwa kamar jira suke gaba daya suka fara wasa da pillows suka dinga kwala mashi ta ko'ina. tun yana murmushi yana kokarin kare kanshi harya fara tiƙar dariya kamar sakarkaru haka suka saki baki suna kallon shi cike da mamakin ganin Dariyar shi. Duk abun da ke faruwa akan idon Unaisah gaba daya ta shagala da kallon fararen hakoranshi masu kyau da tsari sai dariya yakeyi kamar zai shaƙe. ba su kyale shi ba har saida ya faɗa kan gadon shi yana fadin ya isa haka na kar6i laifi na bazan kara tafiya nabarku ba.." jefar da pillows din su ka yi kan mattress din sai haki suke suna kallon shi sun kewaye gadon shi. "Waya faɗa maku na dawo" ya tambaya yana kallon su, Atare suka hada baki gurin furta"daddy Taj" "Banyi zaton kun damu dani har haka ba..." bai kare maganar ba suka fara naɗe hannayen shirts dinsu alamar zasuyi bugu dabi'arsu ce tun a prison.. "Ku kyale shi ya gane kuskuranshi" muryar Unaisah ce ta dakatar da su, atare suka jiyo tare da kallon ta, tana tsaye atsakiyar dakin duk a tunaninsu daga waje ta shigo ba su san cewa tana la6e jikin labule ba. Haduwa sukayi gaba suka zauna gefen gadon shi, ba zasu iya tuna when last suka nishadantu da Danish irin na yau ba, ya sakar masu fuska sun yi fira cikin raha sunyi nishadi kamar lokacin da suke a prison. Jin shiru Unaisah bata dawo ba, tun da tace ta jira har yanzu bata ji duriyar ta ba, gajiya tayi da zaman dakin shiyasa ta fito don ta neme ta, sai kuma ta taras babu su a falon har zata juya idanunta suka sauka akan taj dake zaune kan sofa ya zabga uban tagumi kamar wanda ya rasa mafaɗi a duniya, tun daga kan yanayin fuskarshi ta fahimci babu lafiya atare da shi, kamar akwai wani abu na damun shi. Karasawa tayi gaban sofa din da yake ta ambaci sunan shi shiru bai tanka mata ba, har saida ta maimaita kusan sau uku na karshen ne ta ɗaga murya a ɗan firgice ya dago da ido ya kalle ta, murmushi tasakar mashi, da sauri ya fara kokarin danne damuwar shi ya ɗan saki murmushin yake yace"Ummi ya kike, kin wuni lafiya" bata amsa mashi tambayarba sai cewa tay"yalla6ai meke damunka ne? Kusan sau uku ina kiran sunanka baka amsa min ba, anya lafiya" still da murmushi akan fuskarshi ya furta"ummi ba komai lafiyana lou, ba abun da ke damuna" Tunani tayi kodai rashin Danish ne yasa shi shiga halin damuwa hakan yasa tace"Ya mukaji da abun da ya faru na 6atan Danish? Wlh nima ɗazu Batool ke fadamin, Hankalina ya tashi ba kaɗan ba.." bata kare maganar ba taj yace"oh bakisan An gan shi ba..." waro idanu waje tayi"dagaske"? "Eh, ay yanzu haka su Unaisah suna acan dakin shi" wani irin ihun farin ciki ta saki tare da firta Alhamdulillah kusan sau uku tace"wlh naji dadin ganin shi da akayi, saboda hankalina ya tashi musamman ganin yadda yan uwanshi suka gaza cin abinci saboda rashin shi. "bari naje naganshi" har zata jiya taj ya kira sunan ta tajiyo ta dube shi. "Idan kin shiga dakin, pls ki kirasu, su zo su shirya akwai baki da zasu zo bayan sallar magbrib" amsa mashi tay da toh, zumudin son ganin Danish Ya hana ta tambayi su wanene bakin da sauri ta juya ta nufi upstairs. Bin ta da kallo taj yayi har ta 6ace ma ganin shi, sunkuyar da kan shi ƙasa yai kamar bawan dake neman gafara, abun duniya ya ishe shi tun dazu bakin cikin abunda yagani yake ta nanukarsa, idanunshi sunki daina tariyo mashi abun takaicin daya gani.... Lokacin da takarasa bakin kofar dakin tunkan ta shiga ta fara jin hayaniyarsu yadda kasan gidan biki ko suna sun cika ko'ina da surutun su. knocking kofar tayi almost 3 times ba wanda ya buɗe mata, zafin dumi Ya hana su ji bugun kofar, murmushi tasaki tare da tura ƙofaf ta shiga ciki Tsayawa tayi tare da goya hannayenta kan kirjinta tana kallon ikon Allah sun cike dakin shi, wasu akan couch wasu gefe gadon shi har saman gadon. ta fahimci yau ba karamin nishadi suke ji ba. Kokari take ta hango Danish din duk sun rufe shi dakyar idanun ta suka hango mata bayan shi ya kifa kanshi jikin pillow, Unaisah tana kishingiɗe gefen shi sun shagala da kallon juna, sun bar su Batool sai ɗumin surutu suke . Yanayin fuskartane Ya canza zuwa tsantsar mamaki da rudani, tun da take rayuwa agidan bata ta6a lura da zanan tottoo din shi ba, tasan yana da shi amma bata ta6a ganin dukanshi ba, sai yau datayi arba dashi babu riga a jikin shi, abunka ga farar fata zanan ya fito 6aro 6aro bakomai ne ya rudar da ita face ganin zanan tattoo dinsa sak irin na big boss kamar anyi copying tattoo din big boss an manna mashi abayan shi. wannan abu ya bata mamaki har ta gaza yi masu magana saboda kallon Abun al'ajabin daya ruke ta.. __________________________💓✍️ Safa da marwa take yi atsakar dakin ta, fuskarta babu walwala ga dukkan alamu akwai wani abu dake damunta wanda yayi silar shigarta halin da take a jiki... Sallamar dr shureim ce ta katse zancen zucinta, kamar dama jiran shi takeyi da sauri ta nufe fuskarta ayamutse tace"shureim fita zaka yi ne"? Girgiza mata kai yai"a'a, wurinki nazo inaso muyi magana ne" ya fada tare da wuce ta ya zauna gefen gadonta, itama ta zauna tana kallon shi cike da son jin wata magana ne zasuyi.... "Meke damunki ne? Yanayin fuskarki ya nuna kamar bakya jin dadi"? "Shureim lamarin Benazir yana ɗaga min hankali, kai baka lura ba har yanzu da yanayin ta ba? Wani lokaci tana abu kamar mai ta6in hankali ni tsorona kada ta haukace..." ta faɗa sukuku babu walwala, maimakon taga tashin hankali akan fuskarshi sai taga ya saki tausasan murmushi arude tace"lafiyarka kuwa? Ko bakaji abun da nake magana akai bane" ruko hannayenta yayi acikin nashi, fuskarshi da fara'a tace"mommy zan fada maki gaskiya amma kada ki fadamawa kowa..." cike da mamaki tace"toh, Ina sauraronka" ta fada tana kallon cikin idanun shi "Benazir taji saukin abinda ke damunta, haukan da kika ga tanayi pretending ne, har tambayarta nayi meyasa take yin hakan? Sai ta nuna min bata son asan ta samu lafiya... Baki asake hajiya layla take sauraron shi tayi mamakin jin hakan aranta ta ayyaba lallai benazir ashe haryanzu tana nan da dabi'arta nayin karyar ciwo. "Amma shureim baka tunanin akwai wani dalili dayasa benazir take pretending? In ba haka ba taya mutun da lafiyarshi zai za6i zama mai ta6in hankali" ta jefa mashi tambayar Shiru yayi jimm shi kanshi yayi wannan tunanin amma koda ya tambayeta sai tace mashi bakomai. "Gaskiya bana tunanin akwai dalilin dayasa yakeyin hakan cos na tambayeta tace min bada wata manufa ba saina rashin son a rabata da azeezaty" Girgiza kai hajiya hajiya layla tayi"ni nasan kayana shureim, Benazir bata ta6a yin abu batare da dalili ba, dole akwai dalili, ni fa najima ina zargin da akwai wani abu da Benazir ta sani ko ta aikata wanda har yaja akayi mata asiri..." maganar hajiya layla ta ɗan ɗaga hankalin shi tunawa da bibiyar rayuwar Benazir da akeyi acikin gidan dama kuma yana zargin wanda yayi mata asiri ne yake son karasa kasheta bayan haka itama Benazir din zai iya yiwuwa maganar hajiya layla ta zama gaskiya. amma saboda bayason ɗaga mata hankali shiyasa yaki sanar da ita zancen bibiyar rayuwar Benazir da akeyi sai dai ya yanke shawarar zai je dakin Benazir don ya tambayeta meya faru da ita aranar data kulle dakin ta. Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar Hajiya layla ta katse shi"kaima kana tunanin abunda nake tunani ne ko kuwa" murmushin yaƙe ya sakar mata"mami bana so ki sanya damuwa aranki, hasashen da kike ba lallai ya zama gaskiya ba, zai iya yiwuwa wani tayi ma rashin kunya kinsan wasu mutanan da bakar zuciya ga mugunta arai watakil ita ta manta da ta bata masu rai shine su kuma da babu Allah aransu suka yi mata asiri don su kuntata rayuwarta, ko kuma wanda ya aikata mata hakan yayi ne da niyar ya ɗauki fansar wani abu da ku ka ta6a yi masa..." dafe kirji hajiya layla tayi da tafin hannunta alamar ta shiga uku itama fa tayi rashin mutunci lokacin da Alhaji ubaid Yake akan mulki tunma kafin ya hau kujerar gomna ba mutunci ne da ita ba, yanzu ne tayi hankali ta gane Allah ɗaya ne. "Ni fa ban fada maki donki tashi hankalinki ba, inaso ne na kwatanta maki ba lallai hasashen ki ya zama gaskiya ba, banaso ki matsa ma benazir kan ta ta fada maki meyasa take pretending, mu kyaleta kawai iyakacinmu da ita addu'ane kawai ubangiji Allah Ya kare mana ita daga sharrin duk wani abin cutarwa..." amsa mashi tayi da Ameen ita dai hankalinta bai kwanta da lamarin benazir ba. sun jima suna fira adakin harya bata labarin zuwansu gidan su Azeezaty duk don ya kara kwantar mata da hankali taji dadi kamar ta zuba ruwa akasa tasha tsabar farin ciki. __________________________💓✍️ akwance take kan gadonta, jikinta sanye da night dress, ta ruƙe wayar ta a hannunta, ta nutsu tana kallon hoton fuskar Unaisah dake akan wallpaper din ta... bata gajiya da kallon fuskar ƴarta, takan wuni tana kallon hotunan su Unaisah ba tare da gajiya ba. kwantar da wayar tayi kan kirjinta ta ɗage kai sama tana kallon ceilling. bakomai take tunawa ba face shawarwarin da Aneelerh ta bata akan yadda zata shawo kan Taj ta hanyar kyautata mashi tun shekaran jiya take tura mashi love messages har yau yaki mata reply kamar tay hauka, ta rasa ya za ta yi ta shawo kanshi har jaraba kiran shi tayi tun da ya ɗaga sau ɗaya yaji muryarta bai kara picking call din ta ba. ɗago wayar tayi ta shiga cikin whatsapp dinta, a chat dinsu da Anila tayi copying contact din Unaisah data turo mata.. Cike da marmarin son Jin muryarta ta sanya number din tana kokarin yin saving kwatsam ba zato ba tsammani taga number din already akwai ta a contact list dinta da sunan God gift, Yarinyar da ta kira wrong number a matukar rude ta kurawa contact din ido batare da kyaftawa. lamarin ya daure mata kai tunani tayi ko dai Aneeleerh wrong number ta tura mata? zuciyarta ce ta raya mata bakya tunanin duk itace? Dama kuma sunansu iri ɗaya Unaisah hakan na nufin yartace yarinyar da suke waya? Ta jefa ma kanta tambayar, kokwanto ta farayi anya kuwa itace? Yarinyar fa ta fadamata ba abuja suke ba. "Bari dai na jaraba kira inji" call ta danna almost 20 times ba'ay picking ba, damuwace karara akan fuskarta, jin knocking ɗin room door dinta yasa ta yin saurin aje wayar kan side drawer ta fara haɗe rai zatay pretending... A hankali ta shigo dakin, Jikinta sanye da dogon hijabi, a tsakar dakin ta tsaya tana kallon Benazir kamar tana jin shakkar tunkararta, tayi mamakin Ganin zeenatu adakinta yau wata rana tun lokacin da aka sallameta ba ta kara kusanta kanta da ita ba. aranta ta ayyana watakil iskokan dake akanta ne suka saketa shiyasa ta fara neman su shirya da juna Kurama juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, har na tsawon mituna kafin zeenatu tay karfin halin firta"Aunty Benazir, zan iya shigowa ciki"? Ɗaga mata gira Benazir tay ba tare data furta mata kalma ba, wucewa tayi kan gadon ta haye tare da juya mata baya sunyi shiru kamar basu ta6a sabawa da junan su ba "Aunty benazir ina Azeezaty? Nasan kuna waya da ita, ba ta6a tambayarki ni ba"? Kallon bayanta Benazir tayi kafin tace"kina nufin babyna"? Tace Eh "Tana tambayarki, duk in mu ka yi waya sai tace in gaida mata ke.." dadine ya lullu6e zeenatu har batasan sa'adda ta aje kunyar gefe guda ta juya suka fuskanci juna ita da benazir "Itama ta damu dani, kamar yadda na damu da ita kuma tana so na" ta tambaya tana kallon benazir dake kallon ta.. Ɗaga mata gira tay alamar eh Murmushi tasaki"yaushe zaki kiramin ita mu gaisa"? "Gobe in sha Allah" washe baki tayi tana faman kyafkyafta blue eyes din ta... Ita yanzu tausayi zeenatu ke bata, shiyasa kwata kwata bata ruƙe ta aranta ba. Ganin kallon da Benazir ke yi mata yasa tay saurin rufe idanunta, cike da jin nauyinta tace"Aunty benazir dan Allah ki yi hakuri da abun da na maki" murmushi Benazir tayi"zeenat laifin me kika min"? "Banje asibiti na duba lafiyarki ba, bayan kin dawo ban kula ki ba" yar dariya Benazir tayi"haba karki wani damu wlh, nayi maki uziri ya shureim ya fada min bakyajin dadi .." ajiyar zuciya ta sauke har taji sanyi aranta, ta ɗan buɗe idanunta akan fuskar Benazir miƙa mata hannu tayi"nayi missing dinki ba kaɗan ba sisterna rabin raina, da naganki adakina naji dadi, dariyar farin ciki zeenatu tasaki tare da kama hannun Benazir ta ruƙe shi gam a cikin nata. _________________________________✍️ Bayan sallar Mabrib, gaba dayan su sunyi wanka sun shirya cikin shiga ta mutunci yan matan sun sanya abaya sunyi rolling kamar larabawa, mazan kuma sun sanya jallabiya kusan kalar shigar da su kayi aranar dinner din Hateem sun yi kyau sosai. a falo suka hallara mutun ɗaya ke babu acikin su Danish da har yanzu bai karasa shiryawa ba, Ummi ma tana atare da su ta dage sai daukar su pics take yi saboda sunyi mata kyau "Wai su wanene bakin da zasu zo ne"? Sajeed ne yai tambayar idonshi akan Unaisah, yasan dakyar in batasan su wanene ba, "Nima bansani ba, na kosa naga su wanene mu kara hakuri su karaso Allah yasa muga alkhairi" su ka amsa mata da ameen, su jemimah sai yan guje guje suke atsakar falon ita da azeeza da parvin kamar wasu tsararrakin juna har saida ummi ta tsawatar masu kafin suka daina wasan.. "Ku nutsu pls, manyan bakine su zasu zo.." "Aunty ummi su wanene wai"? Akagare Hanna ta tambaya tana kallonta Ummi tace"nima bansan su wanene ba, amma boss ya fadamin bakin chief ne, tun da naji hakan nasan ba kananun mutane bane, shiyasa nace ku nutsu kada ay abun da za'aji kunya..." kallon juna su ka yi, duk sun kagara da su ga su wanene... Shigowa falon Taj yayi hannayen shi zube cikin aljihun jallabiyar shi, kwata kwata babu annuri akan fuskarshi kamar wanda aka fada ma sakon mutuwar shi. Kwata kwata basu lura da shi ba har saida Javed Ya ambaci sunan shi kafin hankalinsu yakai gare shi, Unaisah na ganin shi ta nufe shi da sauri donta fada mashi abun farin cikin daya faru na bayyanar Danish azatonta bai sani ba. tana karasowa Taj yayi saurin kauce mata kamar bai ganta ba, fuskarshi a haɗe ya nufi su Naufal Ya mika masu hannu daya bayan daya ya yi musabaha da mazan kafin Ya maida hankali kan su sarah da fara'a yake amsa masu gaisuwar da su ke yi mashi. gaba ɗaya ta gaza ɗaga kafafunta saboda faduwar gaban da taji, hankalin ta ya tashi da ganin abun da daddynta yayi mata, kokwanto tayi anya ya ganta? Ko dai bai lura da ita bane? In ba haka meyasa zai shareta ya nufi yan uwanta? ta sanyawa ranta cewa bai ganta bane saboda bai ta6a mata hakan ba, cike da kwarin gwiwa ta nufe shi a lokacin yana tsaye, ta fada bayan shi ta rungume shi tana fadin"daddy ni baka ganni ba ne..." rai aɗan bace ya furta"unaisah ki sake ni, tun kafin na bata maki rai" ya fada tare da janye hannunta Ya jefar da shi gefe ɗaya. aruɗe ta kalli fuskar shi, ya haɗe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne. Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su Duk da haka bata kawo komai aranta ba, ta kuma cewa"daddy, chief ya fada maka an ga danish a cikin toilet dinsa..." banza yayi da ita tamkar baiji maganar ba, hakan ba karamin ɗaga mata hankali yai ba. komawa tayi cikin yan uwanta ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba. [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: ________________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️😈😳👹 ..." bai kare maganar ba General Noah Ya katse shi da cewa"Dole saida shi zamu iya farmakarsu? Shi ɗan uwan nashi salsabeel bazai iya yi ma sojojinmu jagora ba" girgiza kai big guy yai"saboda laifin daya aikata masu, sun ɗauke garkuwar sihirin shi, Salsabeel bai da karfin ikon da zai iya jagorantarmu, dole sai dai shi Danish din"! A kalla sun shafe tsawon awa da rabi suna tattaunawa a karshe dai ba su tsayar da ranar kai farmakin ba, har sai zuwa lokacin da Danish zai basu haɗin kai.... A yammacin ranar Su uku ne zaune saman kujerun backyard din gidan, sunyi shiru babu mai magana acikin su, yanayin fuskokinsu kadai zai tabbatar maka da akwai wani abu dake damunsu, kowan nan su da abunda yake sakawa cikin ran shi.. Muryar chief ce ta katse shirun nasu"Ina salsabeel din? Ka kira shi? Naji shiru baizo ba" Cikin nutsuwa big guy yace"yace min yanzu zai shigo, mu kara hakuri nasan yana akan hanya" jinjina kai chief ya yi tare da kallon Taj, wanda gaba ɗaya hankalin shi baya akan su, Ya langwa6e kai jikin sofa, har yanzu damuwar Unaisah ta hanashi sukuni baida wata walwala. "Taj"! A hankali Ya dubi Chief daya kira sunan shi Na'am.. "What's wrong with you? tun zaman mu anan banji kayi magana"! murmushin karfin hali yayi in a cool voice yace"Sir bakomai, idan ma akwai abunda ke damuna bai wuci tunanin yadda zamu kawo karshen kurkukun kaddara ba" murmushi chief yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba. "In sha Allah komai ya kusa zuwa karshe, bi'iznillah mu ne da nasara" da kwarin gwiwa ya furta maganar, suka hada baki gurin faɗin"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" kafin wani yakuma magana, sallamar Salsabeel ta katse su atare suka dago tare da kallon shi, cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa amsa mashi "Ay min afwa, Uziri ne Ya ruke ni, nabarku kuna ta zaman jira na" big guy yace"kada ka damu bismilla zauna mana" zama yayi kan kujerar dake a gefen Taj, ya maida duban shi ga chief ya nutsu yana jiran jin me zai ce. Big guy ne ya zayyana ma shi komai da suka tattauna agurin meeting, ya ƙara da cewa"ko yau muka samu wanda zaiyi mana jagora zuwa gidan kurkukun, a shirye muke da mukai farmaki, yanzu haka da nake maka magana mun riga da mun tadani rundunar dakarun Sojoji, da kuma makaman yaƙi, ku kadai muke jira Salsabeel! We don't need to waste time!. Chief ya ɗaura da cewa"nayi alkawarin bazan ƙara takura ma Danish game da zancen kurkukun ƙaddara! Salsabeel kai kadai ne kasan ta wace hanya zamu iya samun haɗin kanshi, saboda kafi mu sanin wanene shi, pls ka taimaka mana Salsabeel, muna so muje mu gane ma idon mu abunda suke aikawata mu kuma kawo karshen su...." yanayin yadda chief ke yi mashi magana da raunin murya ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, ji yake inama ace zai iya yi masu jagora da kan shi basai sun bukaci Danish ba wlh da babu abunda zai hana koda hakan zai yi silar rasa rayuwarshi..yayin zurfi cikin tunanin shi muryar Taj ta dawo da shi hayyacin shi "Kayi shiru baka ce komai ba, gaba dayanmu mun ƙagara da muji daga gareka, Salsabeel mun yi imanin zaka sama mana mafita in sha Allah, pls kada ku sagar mana da kwarin gwiwar mu, hatta commender james shima ya shirya bada gudummuwarshi gurin kai farmaki, haka zalika Rundunar Sojojin Nigeria suma sun shirya tsaf lokaci kadai suke jira mu faɗa masu" ya faɗa yana duban Salsabeel"saura kai Salsabeel ka bamu gudummuwarka mun san ka yi kokari amma muna bukatar ƙari" Dukar da kanshi ƙasa yayi lamarin na nema yafi karfin shi baisan ya zaiyi da Danish ba, shi kadai zai kawo masu cikas, baisan yadda zaiyi ya tankwara shi ba, amma tabbas yana da tabbacin mutun ɗayane duk duniyar nan zai sa shi abu yayi, Cikin karyayyar murya. yace"Yalla6ai, Ku bani mintuna shabiyar In ba damuwa, inaso zanyi magana da Danish din" big guy yace"muna jiranka" miƙewa yayi cikin takun sauri Ya nufi cikin gidan. Yana shiga falon Ya hango Unaisah tare da Danish su biyu zaune kan rug, sun tasa notebooks agaba tana koya mashi karatu, tsakanin jiya izuwa yau, ta janye sharuddan data gindaya mashi duk da bata sakar mashi fuska. Sam basu lura da shi ba, har saida yayi masu gyaran murya kafin suka dago tare da kallon shi, suna ganin shi suka mike tare da gaishe da shi ya amsa masu sam ba walwala ya dubi Danish. "Inason yin magana dakai" ya faɗa tare da juyawa ya nufi upstairs sai da ya fara kallon Unaisah tace"yana jiranka, ka tafi, ni zan tsaya anan idan kun gama maganar sai mu ci gaba da karatun" amsa mata yai da toh kafin Ya bi bayan Salsabeel, a dakinsa Ya same shi tsaye, cikin lalama Salsabeel Ya fara magana. "Danish ka bani mamaki! Ina hankalinka da tunaninka suke? Kamar baka da zuciya a kirjinka ka rasa su wa zaka rufa ma asirin sai waɗanda suka cutar da rayuwarka? Danish baka da burin daukar fansa akansu? Ko dan saboda mu kawo karshen zaluncin su mu kuma ceto rayuwar sauran yaran dake a hannunsu yakamata ka basu hadinkai, mutanan nan sun shirya tsaf don sukai farmaki a mutu ko ay rai kai kadai suke jira pls Danish kada ka bani kunya mana, a yadda nasanka kai mutunne mai tausayi da son taimako kuma da kake cewa sune iyayenka masu sonka karyane elders baxasu taba zama masoyanka ba iyayenka daka kullata a ranka zai iya yiyuwa basu suka sadaukar da kai ba suma suna cen suna kewarka ka wani ne a danginka kayi tunani mana. .." tunda ya fara maganar facial expression din Danish bai nuna ya karaya da kalaman Salsabeel ba. Bai ma bari Ya karasa maganar ba, Ya katse shi da cewa'I can't, please don't pressure me i don't want anything to disturb my peace of mind, Salsabeel you know who the elders are! basai nayi maka bayani ba, ka kuma san su wanene Evil giants, sannan ka san kurkukun kaddara gaba da baya, tayaya kake tunanin zasu iya kai masu farmaki su yi nasara akansu? Inajiye masu tsoron su rasa rayukansu saboda basu da karfin da zasu Iya cin galaba akan su" bai kare maganar ba Salsabeel Ya katse shi cikin marairaice fuska yace"Danish! Wannan ba hujja bace! Allahn daya halicci elders din shi ne zai basu nasara, saboda sun dogara da shi kuma sunyi imanin zasu iya cin galaba akansu, kawai ka yi abun da suke so" "Bazan ta6a fahimtar abunda kake fadi ba, ka daina wahalar da kanka salsabeel, banaso mu samu sabani atsakaninmu pls na roke ka ka kyaleni, kaima kuma ka fita sabgarsu in har ba so kake rayuwarka ta salwanta ba..." duk yadda Salsabeel yaso ya shawon kanshi Yaki fahimtarshi ya kangare ya sanya taurin kai da kafiya, tun yana lallaba shi ta lallama har takaiga Ya cakumi Gaban rigarshi da hannayenshi cikin jin kunar rai ya dinga zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a karashe yace tunda na bika ta lallama ka ki bani hadinkai, zan bi dakai ta tsiya ne, hanyar da baka isa ka guje mata ba, dole kaje ko kana so koba so.." bayan ya fita daga dakin akan stairs ya tsaya yana faman fitar da hucin bacin rai, yaji haushi da takaicin hali irin na Danish, duk da yanayi mashi Uziri saboda sanin cewa bashi kadai bane har yanzu elders suna iya sarrafa shi amma A halin Yanzu daga zuciyarshi ne bawai Evils din jikinshi bane. Abunda ya fahimta dangane da Danish baya son rabuwa da Unaisah shiyasa yaki basu hadin kai, gani yake kamar in yabisu suka je kai farmakin rayuwarshi zata Iya salwanta batare daya cika burin shi akan Unaisah ba gyaɗa kai yai da alama ya kamo bakin zaren saukowa down yayi bai ganta a falon ba, kaitsaye ya wuce bedroom din su, yayi knocking almost 3 times kafin ta buɗe mashi kofar yaci sa'a ita kadai ce a ciki. "Ya salsabeel yau kai ne adakin mu" dakyar ya kakaro murmushi kan fuskarshi yace"ni ne Unaisah, tun da kika ganni kinsan abune mai mahimmanci ya kawo ni gurin ki" cike da mamaki tace mashi toh, daga gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna, ta tsare shi da idanunta cike da ƙagarar son jin wata magana zai mata "Unaisah Kin san meya faru lokacin da chief ya shiga da Danish Questioning room a headquarter wanda yayi silar fusata Omar har suka samu sabani..." aɗan ruɗe ta girgiza mashi kai"ba komai na sani ba, kaɗan na fahimta daga furucin ya omar" Nan take Salsabeel Ya labarta mata abun da Ya faru tsakanin Danish da Chief,shi ma abakin big guy yaji komai. ranta ya sosu da jin abunda Danish yayi ma chief, babban abunda ya fi bata takaici daya ce ma chief ba gaskiya ya ke faɗi ba, they've never hurt him Suna sona shi kuma sune iyayen shi, bayan su bashi da wasu iyaye a duniyar ranta yayi mugun 6aci ba kaɗan ba, sam ta kasa magana sai jinjina kai take. "Unaisah babu irin magiyar da banyi ma Danish ba, akan ya amince ya basu hadin kai yakiya, nayi lallashin nayi roƙon duk abanza wlh da raina ya baci kamar in rufe shi da bugu saboda ya bata min rai..." ya faɗa rai a6ace ya ɗan dakata Yana kallon unaisah dake kallon fuskarshi "Wallahi da ace zan iya jagorantarsu zuwa gidan kurkukun kaddarar da tuni nayi hakan Unaisah, sai dai ni yanzu bani da wani karfin ikon da zan iya yin hakan, bayin Allahn nan sun shirya tsaf sun tanadi rundunar sojoji da makaman yaƙin da zasu farmake su abu ɗaya ne zaiyi masu cikas wanda zai yi masu rakiya zuwa gidan kurkukun kaddarar, Unaisah basu san hanyar da zasu bi ba, ba su san a daidai ina ginin yake ba! Shin akan ƙasa Yake ko karkashin kasa Yake? Bayan haka ke kinsan yadda ginin yake wani irin kurman ginine mai rikitarwa da tsoratarwa in har mutun baida ilmi akan shi wlh tuni zai zauce, Danish shine makamin da zamu iya tunkararsu da shi ..." da yai wanann maganar bakomai ta tuna ba face lokacin data saci hanya ta fita matakalar bene ta dinga mayar da ita baya, ga wannan rudin mai rikita kwakwalwar mutun ya dinga ganin abun da babu azahiri. "Kinyi shiru baki ce komai ba, yakamata Mu ne mi mafita Unaisah, In ba haka ba elders zasu cigaba da aikata zalunci, kwara muyi amfani da wannan damar kada muyi gangancin da zata kubce mata..' tsantsar damuwace akan fuskarta cikin sanyin murya tace"Yaya Salsabeel menene mafita? Kafi kowa sanin halin Danish, Yana da taurin kai da kafiya, Idan ya fadi abu babu wanda Ya isa Ya canza ra'ayin shi...." bata ƙare maganar ba, Salsabeel yai saurin furta"akwai mafita Unaisah" a kagare tace"menene mafita" shiru yayi jim yana jin shakkar yadda zata dauki abun amma daya tuna irin burin da take dashi na son ruguza kurkukun kaddara sai ya samu kwarin gwiwar ce mata"Unaisah, duk duniyar nan mutun ɗaya ne kacal zai iya tursasa mashi Ya bashi umarni kuma Ya bi shi sau da ƙafa..." da ruɗu akan fuskarta tace"wa kenan"? Nuna ta yai da index finger din shi waro idanu waje tayi kamar wadda taji wani mugun abu "Ke Unaisah! Basai nayi maki dogon bayani ba, kin riga da kinsan irin tsantsar kaunar da Danish ya ke yi maki, wanda ko sauran yan uwanshi da suka taso atare bai ta6a yima kwatankwacin shi ba, wlh nayi imanin in har kika bashi umarni yaje zai je..." da matukar tashin hankali ta girgiza mashi kai labbanta na rawa tace"I can't... I can't change his mind Danish won't listen to me ya Salsabeel kai fa ka fadamin wasu lokuttan ba shi bane zai iya wuni baya a hayyacinsa taya kake tunanin zan iya bashi umarni ya bi"? Ta fada idanunta azare take kallon shi, ita babban tashin hankalinta a haɗa ta dashi don ta shawo kanshi bataso su sake samun sabani bayan haka tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar masoyinta cikin haɗari, da alama soyayyarshi na nema ta rufe mata idanunta.. "Unaisah Zaki Iya, Ko ba don saboda son da yake yi maki ba, idan ba zaki manta ba na ta6a fada maki dalilin dayasa suke kiranki da kaddarar kurkuku" kura mashi ido tayi batare da kyaftawa ba. "Ma'anar hakan shine ke kaɗaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara! Kamar yadda yazo a allon tsafin su, duk da bamu da tabbaci Allah kadai yasan gaibu amma In Allah Yasa hakan ya zamana gaskiya ne kinga kenan wannan wata hanyace da zaki yi amfani wurin kawo karshen su, Ki zamar masu mummunar ƙaddarar da zatayi silar tarwatsa su. maganar salsabeel ta farfado da tunaninta na son kawo karshen kurkukun ƙaddara amma bataji zata iya tursasa danish don ya yi masu jagora. Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"ya Salsabeel na fahimce ka, amma bana jin zan iya tursasa ma Danish, Ina matuƙar jin tsoron in jefa rayuwar shi cikin hadari, in har wani abu ya faru dashi bazan ta6a yafe ma kaina ba, idan ma zuwan ya zama dole sai da shi to ku haɗa da ni. kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya tokare makogwaronta nan hawaye suka dinga zarya kan kuncinta. Zuciyarshi taso ta karaya da maganarta, Shesshekar kukan tane Ya fargar da shi, Cikin sigar lallashi yace"in har kin yi imanin cewa Allah shi ke tsare bawansa bai kamata kina tunanin Zai rasa ransa a gurin Yaki ba, ay bashi kadai zaije ba Unaisah baga mu ba ko mu baki damu mu mutu ko muyi rai ba? Wlh Unaisah jininmu akan akaifa yake babu gudu ba ja da baya ko da zamu rasa ranmune sai mun yi yaƙi da dukkan karfin mu, mun dogara da Allah kuma munyi imanin shine zai bamu nasara akan kyakkyawar niyar da muke da ita na ganin mun kawo karshen zaluncin kurkukun kaddara...." Kwata kwata bata gane me yake cewa ba, ita fa damuwarta akan Danish ne cikin karyayyar murya tace"ni abun da nafi jimawa har yanzu shi ba musulmi bane, I don't want him to lose his life as an unbeliever! ya makomarsa zata kasance?..." ta faɗa tana kallon fuskarshi da idanunta wadanda suka kaɗa jawur da su shi kanshi abun na damun shi, baida burin daya wuce Danish ya musulunta ko dan ya tsira da imaninsa, amma yasan bamai yiwuwa bane in ba wani iko na Allah ba, saboda wadannan evils din na jikin shi. "Mu cigaba da taya shi addu'a in sha Allah zai musulunta, ni dai yanzu damuwana ki yi kokari kisa ya amince mana..." kifa kanta tayi jikin pillow, sam bata son maganar gani take kamar tursasa mata yakeyi don ta ingiza danish ga fadawa halaka.. Sarai ya fahimci daga ita har Danish din Giyar soyayyace ke dibarsu, shiyasa har suke neman su bijire.. Gwiwar shi ta sage, cike da rashin kwarin jiki Ya miƙe ba tare daya kauda idanun shi daga kallon ta ba Yace"banzo nan donna bata maki rai ba, kodan na tursasa maki nazo ne don mu hada hannu gurin cimma burin da muka dade muna jiran ranar da zamu aiwatar da shi, kada ki manta nayi ma mahaifiyata alkawarin zan kawo karshen zaluncin Elders bayan haka kema kin min alkawari watakil Yanzu kin manta nasani..." wani irin radadi take ji acikin zuciyarta tana maijin bakin cikin gaza amsa mashi bukatar shi "Zan tafi Unaisah, ki zauna kiyi nazari da hankalin ki, Zan jira har zuwa lokacin da zaki aiwatar da abun da na sanyaki, bana so kiyi danasani mara amfani..." ya fada tare da juyawa ya nufi kofar fita daga dakin Harya ruke handle din Ya dan dakata tare da juyawa ya dube ta, still bata dago da kanta ba sai kuka take yi "Kina tunanin zaman Danish agidan nan shi zaisa Ya tsira da ranshi? Abunda baki sani ba dokar elders ce duk wanda ya san sirrinsu dole su kashe shi, in har baije Ya farmakesu ba, to su zasu farkama ke shi ne akowani lokaci" ya na fadan hakan yasa kai ya fuce Fitar shi keda wuya ta kuma fashewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, maganar salsabeel ta fara tariyowa farkon haduwarsu agidan kurkukun ƙaddara _inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka_ _"NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi'iznillahi_ Tuna wannan yasa ta ƙara sautin kukan nata. A bangaren Salsabeel bayan ya koma backyard din kamar yadda yabarsu Chief haka ya taras da su zaune suna jiran shi. Bawan Allah duk Ya rasa kuzarin shi, su Unaisah sun bata mashi rai ba kaɗan ba.. Hankalin su baya akan shi har saida yai masu sallama kafin su ka dube shi, zama yai kan kujera ya sunkuyar da kan shi ƙasa tun daga yanayin shi suka fahimci akwai damuwa.. "Salsabeel ka yi shiru baka ce mana komai ba! Ya kuka ƙare da shi"? Cikin kulawa Taj yai maganar.. Cike da jin nauyin su ya girgiza kai, "Danish ya bani kunya, ban ta6a zaton zai bijire min ba..." tun da suka ji hakan damuwa ta bayyana akan fuskokin su don sun riga sun hasaso karashen zancen na shi.. Rai a6ace Omar yace"meyasa zamu wahalar da kanmu akan shi? Yaron nan fa ɗan rainin wayau ne, idan muka ce zamu bishi ta lalama bazai ta6a bamu haɗin kai ba, kwara mu bi shi ta ƙarfi da yaji mu ci ubanshi har sai ya miƙa wuya..."yana huci ya faɗa kamar zai haɗiyi zuciyarsa saboda bacin rai.. Chief ya ɗaga mashi hannu badan Ya ƙarasa maganar ba yaja baki yayi shiru fuskar shi a murtuke.. "In har bashi yayi niya ba, ko da zamu rasa damar da muke da ita na zuwa gidan kurkukun bazan bari a tursasa masa ba, itama Unaisah ban amince ayi amfani da ita gurin shawo kan shi ba, cos zai ga kamar ni na sanya ta ne" Salsabeel ya ɗan kalle sa cos shi harya riga daya tuntu6i Unaisah. Cike da takaici Big guy ke kallon chief da yai maganar "Haba Owais, Saboda shi kawai zamu fasa niyar mu"? "Omar, ba ina nufin zan fasa aikin mu bane, sai dai mu nemi wata hanyar..." bai ƙare maganar ba, Big guy ya mike yana huci ya kama hanya zai bar backyard din.. Damuwa ta hana Taj furta kalma baima san me suke cewa ba. Miƙewa chief yayi da sauri yabi bayan Omar, don bazai bari su sabamu sabani tsakaninsu ba dama kwanakin nan yana jin haushin fifita Danish da yake yi. Bayan tafiyar su, ya rage saura Taj da Salsabeel sunyi shiru babu mai magana acikin su. Ganin yadda Taj ya zabga uban tagumi ne yasa Salsabeel furta"Sir are you Okay"? Yamutsa fuska yai"kada ka damu, i'm okay, just banji dadin yadda ɗan uwanka yaƙi bamu haɗin kai ba" ya fada yana kallon Salsabeel "Amma Salsabeel babu dabara da zamu iya yi don mu shawo kan shi"? Shiru Salsabeel yayi yana nazarin maganar shi, wata dabara ce ta faɗo mashi arai da sauri Ya dubi Taj "Akwai hanya ɗaya" akagare Taj yace"Ina sauraronka" "Ƴarka Unaisah, Ita kaɗai ce zata Iya sa shi dole yayi..." lokaci ɗaya Taj ya haɗe rai, annurin fuskar shi ya ɗauke, saboda zafin maganar Salsabeel daya ji. "Meyasa kace haka"? Murmushi Salsabeel ya ɗanyi kafin ya fara zayyana masa dalilinsa nacewa haka! "in har ta umarce daya je zai je, saboda ya mutu akan Sonta, ba irin magiyar da banyi mata ba akan taje ta rokar mana shi amma taƙiya saboda gudun kada ta yi silar da zai rasa ranshi, amma ina da tabbacin in har ka yi mata magana zamu iya cin galaba akan ta saboda kai mahafinta ne, bazata ki bin umarninka ba"... Tun da ya fara magana Taj ya tsare shi da ido batare da kyaftawa ba, bakomai yake tunawa ba face abunda idanun shi suka gane mashi, ɗari bisa ɗari ya yadda da maganar Salsabeel saboda shi shaidane akan mahaukacin son da suke ma junan su, duk da ya ɗauke ƙafa akanta amma yana jin zai iya zuwa gurinta don ya jarabata" Har salsabeel ya ƙare maganar Taj bai sani ba, gyaran muryar da yayi mashi ne ya fargar da shi "Pls, ka taimaka koda sau ɗaya ne ka jaraba yi mata magana.." fuskar shi amarairaice ya fada.. Wayar Taj ce tay ringing, kallon Salsabeel yayi"it is Okay, zan jaraba" ya faɗa tare da miƙewa Yai picking call din "Sir, ina fata lafiya, naji shiru baku dawo ba" "Boss, Ka sallami Salsabeel ya tafi, kaima zaka iya tafiya..." amsa mashi yai da toh.. "Chief yace ka tafi, zai neme ka" mikewa yayi"pls sir, sai naji daga gare ka" jinjina mashi kai yai batare daya fur ta kalma ba. _________________________________✍️ Su Batool na zaune a falo suna fira kusan su dukkansu in ka cire Unaisah da Danish sai ummi su kadai ke babu a cikin su... Sam basu lura da shugowarshi ba fira taja hankalin su, ganin babu Unaisah yasa shi juyawa ya nufi bedroom din... Adai dai lokacin ta fito daga bathroom, sanye da yar rigar wanka, zuciyarta cike fal da tunanin abunda suka tattauna da Salsabeel Wayar ce ta fara ringing, har zata dauka taji anyi knocking din kofar "Wanene"? "Ki buɗe kofar ki gani" ras ta ɗan ji gabanta ya fadi jin muryar daddynta, tana jin shakkar shi yanzu ba kadan ba saboda canzawar da yayi mata. "Unaisah ba zaki buɗe min ƙofar bane"! Jikinta na 6ari ta je ta buɗe ƙofar, shigowa ciki yai tare da aza idanun shi kan fuskarta wani irin tausayinta ne ya kama shi. Cikin rawar murya tace"daddy Ina wuni" ta fada tana kallon shi Shiru yayi bai tanka mata ba hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.. Kasa jurewa tayi batasan sa'adda ta faɗa kan kirjin shi ta kankame shi tana tana kuka tace laifin me na maka daddy? Meyasa ka canza min? Ka daina sakar min fuska, idan na gaishe ka dakyar kake amsa min idan na kira wayarka baka ɗagawa, daddy don soyayyarka da manzon Allah ka fadamin laifin me nayi maka sai in nemi yafiyarka, wlh bana so kana fushi dani Daddy, kaifa mahaifina ne kasan hukuncin wanda iyayensa ke fushi da shi ...."sambatu taci gaba dayi batare data raba jikinta daga nashi ba.. Zuciyarshi ta karaya da jin furucinta, ta bashi tausayi ba kadan ba, ga kaunarta dake kara ninkuwa cikin zuciyarshi, jiya dakyar ya runtsa hatta Danejo saida ta lura da yanayin shi ba irin magiyar da batai mashi ba akan ya fada mata gaskiyar abunda ke damunshi amma yakiyi saboda bazai iya tona ma yarsa asiri ba, kamar tona ma kansa ne.. Baiwar Allah muryarta harta disashe, Unxpectedly taji ya ɗaura tafukan hannyenshi akan sumar kanta ya ɗan shafa bayanta cikin sigar lallashi Kafin ya fara magana "Unaisah, kin bani mamamki, kinyi min abunda ban ta6a zato ba..." a firguce ta dago tana kallon fuskar shi "Ina yi maki kallon mai hankali, kuma mai jin tsoron sabawa Allah ashe nayi kuskure Unaisah, na yaudari kaina.." cike da tashin hankali ta furta"daddy ni din? Me nayi maka"? girgiza kai ya danyi cike da takaici ya zayyana mata abunda Ya taras sunayi adakin Danish... Dafe kai ta yi da tafin hannunta, wani irin faduwar gaba da tashin hankali taji "Idan shi jahili ne baida addini, ke ay ba irinsa bace, Kinsan babu kyau unaisah, ina tarbiyar dana baki? Baki ji komai ba kika biye mashi kuka rungume juna, haba Unaisah baki kyauta ma kanki ba, nima kuma baki kyauta min ba, wlh kin karya min zuciyata, kin samin fargaba saboda zullumin kada ya lallata min rayuwar yata...." kusan suman tsaye tayi, jikinta ya fara kakarwa kamar mazari ga kunyar shi data lullu6e ta, tasan bata da gaskiya shiyasa ta sunnar da kanta ƙasa cikin sanyin murya ta furta"daddy, na kar6i laifina, amma dan Allah kada ka zarge mu, wlh bamu ta6a aikata wani abu daya sabama Allah ba, duk da Danish baida addini ba ɗan iska bane daddy, bazaiyi abunda zai cutar dani ba, idan yayi ba daidai ba ina faɗa masa babu kyau a addinina kuma baya musa min, abun da ya faru ranar bana a cikin hayyacina daddy, hankalina ya tashine naji matuƙar tausayin shi kuma naji tsoron kada na rasa shi shiyasa na rungume shi, amma wlh ba shine ya fara rungumata ba, ni ce daddy...." yanayin yadda take yi mashi magana jikinta na kerma ba karamin rauni ta sanya mashi ba, yayi niyar yayi mata fada sosai amma sai yaji bazai iya ba, ya yarda da maganarta yasan Unaisah bazatai mashi karya ba. "Meke atsakaninki da shi"? Ya tambaya yana kallon ta Kamar mai in ina ta fara yan kame kame tana fadin"amm..umm..dama.."ta ɗan kau da idonta gefe kamar bazata karasa maganar ba tace"bazan boye maka ba, dama najima inason in faɗa maka, nasan zaka goya min baya akan abunda nakeso...." tashin hankali idanun shi aware yake kallon ta. "Daddy Allah ya jarabce mu da son juna ni da danish, soyayyar dake tsakaninmu bazata misaltu ba, har rayukan mu zamu iya sadaukarwa akan junanmu, daddy wlh ina son danish, shi kadai ne namijin da nake da burin in aura..." bata ƙare maganar ba, sakamakon tsawar da Taj Ya daka mata wadda tay silar rikicewarta arazane Ta zazzare grey eyes dinta akan fuskar shi Yana faman fitar da huci yace"Impossible Unaisah! Wlh bazan lamunta ba, ba zaki sa nayi karamar magana ba, baki isa ki kunyata ni ba, kina hauka ne unaisah? Meye abunso atare da shi? Yaron da baida adinini arne ne, ga jahilci cike da kai, sannan bashi da wani galihu, bayan haka ina yake da halin da zai iya ruke min ke!? wani irin jiri jirin tashin hankali ta gani acikin idanunta kalaman daddynta sunyi matuƙar ɗaga hankalin ta, tayi mamakin furucin da yayi akan danish kamar dai ya manta cewa komai ya faru arayuwar shi bayin kan shi ba ne... "Unaisah Ina burin da kike shi na son auran attajirin me kuɗi? Mai ilmin addini dana zamani mai cikakken asali wanda zai gatantaki Ya tarairayeki ya baki kyakkyawar kulawa? "Daddy, na jima da soke wannan burin, ba dole sai na auri miji mai kudi zan samu farin ciki ba, sau dayawa wasu masu ilmin basu aiki da shi daddy, ni kawai miji na gari nake nema kuma na samu daddy, duk abunda ka lissafa Danish zai iya bani fin su, saboda yanayi min soyayyar da bazai iya cutar dani ba, yana yi min son da zai iya hana kanshi farin ciki saboda farin ciki" Ta ɗan numfasa kafin taci gaba da cewa" ka kira shi jahili daddy banji dadi ba, bayan kasan ba shi yaja ma kanshi hakan ba, idan ka amince min, zanyi amfani da son da yakeyi min in musuluntar da shi..." bata ƙare maganar ba, Ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu! wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makogwaronsa, Ya ma rasa me zaiyi ya huce haushin sa, Yayi mamaki wai har Unaisah ta iya gaya mashi da bakinta bata ji kunyar shi ba lallai ba karamin so take ma shi ba, zata iya komai akan shi.. Kafadunta Ya dafa da tafukansa Ya jijjigata har saida Sumar kanta ta yarfo ta gaban fuskarta fashewa tayi da kuka don ta gane bai fahimce ta ba.. Da kakkausar murya ya furta"Bazan ta6a amince ma soyayyarku ba, ba son shi kike ba, tausayin shi kike ji, tun wuri ki cire zancen zaki aure shi, saboda na riga da nayi maki miji sadakinki ne kadai bai biya ba, kuma yana sonki, shine za6ina unaisah in har ba bijiremin zakiyi ba, bana so ki bani kunya kada kisa na karya alkawarin da nayi masa, ki cika min burina Unaisah, danish ba dole saida ke zai iya rayuwa ba, ga sauran yan uwanki nan sai ya zabi daya acikin su, Unaisah burin kowace uwa ta sama ma ya'yanta uba nagari ba jihili ba. abun da Taj bai sani ba tuni tajima da sumewa, idanunta daya gani a kakkafe shi yasa shi gane hakan..cikin jin faduwar gaba ya hadiye sauran maganarshi da bai amayar ba, saboda tashin hankali, Ashe nashi wasane bai ta6a ganin true love ba sai yau, ay yayi zaton daga layla da majnoon andaina samun irin soyayyar nan, sungumarta yayi kan fadar shi ya kwantar da ita kan gadon su, Ya fito daga dakin jiki na kerma Ya tafi dauko ruwa kafin dawowar shi, Batool ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi ta zauna gefen gadon tana kallon wani sabon salon kwanciya agurin Unaisah, tayi zaton dadin baccine yasa ta dauki tsawon lokaci bata leko waje ba. "Sister Ya kamata ki tashi, Aunty Ummi ta hanamu baccin marece.." ta fada tare dakai hannu ta ɗan bubbuga ƙafar Unaish shiru bata farka ba, "Unaisah wani irin bacci ne wannan kamar mai fama da cutar bacci" ta fada tana kara bubbuga legs din ta. Adaidai lokacin Taj ya fado dakin hannun shi ruke da robar ruwa me sanyi, Yana ganin Batool yaci burki gaban shi na faduwa yasan muddin tasan Unaisah suma tayi sai ta yi kukan da zai jawo hankalin sauran yan uwanta. Jin motsin adakin yasa Batool ta juyo ganin daddyn Unaisah yasa ta miƙe da fara'a tace"ina wuni daddy, i'm sorry watakil ka yi sallama banji shigowarka ba..." yawu ya haɗiya dakyar ya tattara nutsuwarsa yana kokarin danne damuwar shi yace"lafiya lou daughter.." da alamun rudu kan fuskarta tace"daddy naga water bottle a hannunka.." washe baki yayi"eh ni zan sha ne, kishi nake ji" murmushi tayi"ko kazo ganin Unaisah ne" a kagare ya daga mata gira"bacci take, yanzu nake kokarin tadata" da sauri yace"kinga bari ni in tashe ta, kije gurin ummi naji kamar tana nemanki..." kamar taso ta ɗago shi, ta lura kamar wani abu badaidai ba, amma sai batayi mashi gaddama ba, ta fuce daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya datse ƙofar dakin, ya zauna gefen gadon da sauri ya cire murfin robar ya yayyayafa mata ruwan kan fuskarta. dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya.. "Unaisah, Pls ki yi hakuri ki tashi, kinji! I won't hurt you anymore..." dakyar ta iya buɗe idanunta wadanda suka kada jawur ta dube shi Wani irin ciwon kaine Ya far mata... Cikin disasshiyar murya tace"daddy, kada ka raba ni da Danish, zan iya rasa raina.." Kwata kawata baya son tana fadin zata rasa ranta akan Danish, Ranshi baci yake kamar ya hadiyi zuciya, kuma yana akan bakanshi bazai janye ba. "I'll think about it, Yanzu bana son duk wani abu da zai ɗaga hankalinki, kwanciyar hankalinki nakeso..." hankalin ta ya ɗan kwanta, gani take kamar daddynta zai duba mata ne. "Amma daddy, baka son Danish ko"? Girgiza mata kai yai"Ina son shi Unaisah, Kuma ina jin tausayin rayuwar shi, maganganun da kikaji nayi ɗazu rainane Ya 6aci bawai don ina nufin hakan ba, ni kawai banaso kina sakar mashi jikin ki ne" cikin kwantar da murya ya faɗa. Ruko hannun shi tayi a cikin nata"daddy pls ka min alkawarin ba zaka raba ni da shi ba"! Dafe kai yai da tafin hannun shi, ji yake kamar ya kifa mata mari saboda haushin da yake ji in ta ambaci sunan Danish "Kina so In amince ma Soyayyarku?In kuma ba shi damar Auren ki"? jin wannan maganar daga bakin daddyn nata yasa ta miƙe zaune cike da zumudi tace"Eh daddy..." Numfasawa yayi kafin yace"Zan baki Umarni, If you do what I say, I promise to fulfill your dream of marrying your choice". gabanta ne ya ɗan faɗi duk da batasan umarni da zai bata ba, taji fargaba sosai.. "Daddy, wani irin Umarni ne? Ka faɗa min in sha Allah zan yi maka biyayya" ta faɗa cike da jin fargaban amsar da zai bata.. Ido cikin ido su ke kallon jun. "ki bashi Umarnin, ya yi mana jagora zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara..." wata irin razananniyar faduwar gaba taji, kamar zata zauce ta daddafe kanta da tafukanta dama saida ranta ya ayyana mata abun da zai umarce ta da tay... "Inaso in tabbatar da kaunar da ya ke yi maki, ta hakanne zan gane shin jarumtakarsa takai in mallaka mashi lu'u lu'u na? ya faɗa yana kallon idanunta da suka rune zuwa Jajawur kamar Jan gauta. Cikin shesshekar kuka tace"daddy, pls ka bani wani umarnin daban, wannan is too hard for me! I can't force him I don't wanna put his life in danger" Kwata kwata babu annuri akan fuskarshi, ya haɗe rai sosai saboda yana son ta ɗauki maganar shi serious "Unaisah, karna kuskura na ƙara ji kin furta kalmar kada ki jefa rayuwarsa cikin hadari! Ke ba musulma bace? Ba kiyi imani da Allah ba? Ko baki yarda da ƙaddara ba? Ko kuwa ƙarancin tawakkali ne ke damunki"? Runtse idanunta tayi tana jin wani iri yanayi a zuciyarta mara dadi "Ba haka nasanki ba Unaisah! Kin canza min! Ina zuciyar imaninki take? na fahimci so ne ke nema ya rufe maki ido, Unaisah kin manta mummunar ƙaddarar data rabamu? Kin ta6a tunanin zaki ku6uta daga kurkukun ƙaddara? Kin ta6a tunanin zamu sake haɗuwa? Ikon wanene yin hakan"? In a weak voice tace"Allah" "Toh inaso ki sanya ma ranki, duk wani abu da zai faru da shi muƙaddari ne daga Allah, tun zuwan shi kurkukun kaddara bazai hana Allah ya jarabce shi da wata ƙaddarar ba, har kwarama yaje can yayi jahadi gurin ceton rayuka...." nasiha ya cigaba dayi mata tun bata fahimtar shi har ta fara yin amanna da maganar shi... "Daddy, ni damuwana he's not a muslim, banson ya mutu batare daya kar6i kalmatusshada ba" ta faɗa hawaye na bin fuskarta... Ruko hannayenta yayi acikin nashi ya ruƙe su gam kafin yace"In sha Allah zai musulunta Unaisah, idan sheikh imam yazo zamu nemi taimakon sa" "Amma daddy, nima ina neman alfarma agurinka"! "Wace alfarma"? "Ku tafi dani, Nima ina son in bada gudummuwata..." waro idanu waje yayi aranshi ya ayyana bazai yiwu ba, amma a fili sai yace"Zan yi magana da chief, kinsan dokar aikinsu babu mace, amma in har ya amince zamu tafi dake" ajiyar zuciya ta ɗan sauke, fatanta Allah yasa Chief ya amince mata, dalilin dayasa ta za6i tabisu saboda abu biyu, na farko don ta kashe Jan wuya, duk da batasan wanene shi ba, kuma batasan ko yana ɗaya daga cikin members na kurkukun ƙaddara ba, sai dai taji aranta dakyar in ba ya cikin Elders, abu na biyu donta ba Danish kariya, koda Ajali zai riske shi, toh su mutu atare zaifi mata kwanciyar hankali. Kiraye kirayen Sallar isha'i da aka fara yi ne, yasa Taj miƙewa ya dube ta"zan tafi, kiyi kokarin aiwatar da umarnina, in sha Allah silar biyayyar da zakiyi min, ba zaki ta6a danasani ba, saima ya zama silar farin cikin ki na har abada" cikin sanyin murya tace "in sha Allah daddy, zanyi masa magana, duk yadda mukai zan sanar dakai" "Gobe da safe, in tashi da labari mai dadi" jinjina mashi kai tay Miƙa mata hannu yayi da sauri ta sauko daga kan gadon ya rungumota, yana ƙara lallashinta da bata baki har saida ya tabbatar taji hudubarshi kafin su ka yi sallama da juna kamar karsu rabu.. _________________________________✍️ Idan muka koma bangaren Benazir sam ta kasa walwala, maganganun Zaki sun tsaya mata arai, sun hana ta sukuni gani take kamar batayi masa adalci ba, tayi kuka sosai har zazza6i saida ya lullu6eta, Wlh Yabata tausayi bata ta6a ganin rauninsa ba sai awannan lokacin, yayi mata taimakon da har abada bazata ta6a mantawa da shi ba, ya bata lokacin shi! Ya bata kulawarshi! Ya bata ci da sha Da suturu harma da aikin yi, ya kuma ruketa agidan sa na tsawon shekara goma sha bakwai bai ta6a goranta mata ba, sun shaku da juna, ya zama tamkar uba agare ta! babu wanda yasan wani abu dangane da zuwan Zaki, daga Ita sai Alhaji musa suka san da maganar, fatanta Allah yasa kada Uncle musa yayi ma Daddynta maganar don batason duk wani abu da zai daƙile maganar komawarta dakin Mijin ta, taso taji daga bakin uncle me Zaki ya fada masu sai dai takasa ma tunkarar shi saboda bata son taji abunda zai hana runtsawa. Har kiran Layin Zaki tayi don ta kara bashi hakuri amma kwata kwata kiran baya shiga.. Tunani ta somayi me zatayi don ta saka mashi? Zuciyarta ta bata amsa da cewa me zai hana ta hada shi da Aneelerh! aranta kuma ta ayyana zaiyi wuya su sasanta cos zaki bazai kara gangancin fadawa tarkon son macen da kaddara ta rabata da mijinta, kamar dai ita 💔 _________________________________✍️ Har wuraren ƙarfe shaɗaya na dare bata runtsa ba, saboda matsananciyar damuwar data addabi zuciyarta, sai faman juyi takeyi kan matress kamar me fama da ciwon ciki, maganganun daddynta dana Salsabeel ne suka dinga dawo mata cikin kwalwar kanta, bata san ya zatayi ba, bata da wata mafita daya wuce ta amsa bukatarsu sai dai tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar man dinta a cikin haɗari amma idan ta tuna burin da take da shi na kashe jan wuya, da kuma nasihar daddynta sai taji kamar ana kara mata kwarin gwiwarta. *CHIEF OWAIS* Bacci ya ƙauracewa Idanun shi, Ina zai sa ran shi yaji dadi? chief irin mutanan nan ne waɗanda idan suka kwallafa rai ga abu suka saka buri da naci da komai in har ba su ga sun Cimma nasara ba to fa hankalin su bazai ta6a kwanciya ba.. Ya ƙuntata kanshi Ya hana zuciyar shi sukuni, baisan taya zai 6ullowa lamarin ba, Danish Yana nema Ya zamar ma shi ciwon kai... Yayin da yake wannan tunanin safa da marwa yake a tsakar bedroom ɗinsa, boxer short ne kaɗai a jikin shi, fuskarshi a yamitse ba annuri.. Jefi jefi in damuwar ta addabe shi tafin hannunsa yake cusa cikin sumar kanshi ya yamutse ta kamar ɗan mahaukaci wani lokaci da karfi ya ke bugun iska da hannayen shi. Phone ringing dinsa ne ya katse hanzarin shi, kamar bazai duba mai kira ba, zuciyarshi ta takura mashi akan ya duba, juyawa yayi a sukwane cikin rashin kuzari ya dauko wayar dake aje kan mirror chair, yayi mamakin ganin almost 16 missed calls, picking call din yayi tare da kare wayar a kunnan shi yai shiru yana jiran jin me zaice "Owais, ya ake ciki game da kai farmakin?..." "Only a few days remain" "Ko zaka Iya faɗamin menene shirin ku a yanzu ni kuma zan ƙarfafa maku gwiwa" Har yanzu bai yarda da mutumin ba, shi mugu bashi da kama, zai iya bayyana ta suffar mutanan kirki don ya shiga jikin mutun... "I'm sorry to say, bazan iya faɗa maka ba, in har dagaske kana son taimakona ba dole sai kaji me muke shiryawa ba" "Hakane, Ka faɗi gaskiya, Owais, shawarar da zan baku shi ne, Ku sanya malaman addini su tayaku addu'a, sannan ku ma iyayenku magana su tayaku da addu'a, ku kuma yawaita sadaka ga marayu da mabuƙata suma su tayaku da addu'a, ku nemi kariya daga wurin Allah, in sha Allah badai mutun da Aljan ba sai Allah...." bai ta6a jin 6oyayyan mutumin ya burge shi irin na yau ba yaji dadin shawarwarinsa Har ya buɗe baki zai yi mashi godiya yaji ɗuff yai rejecting call din.. Hakanan Yaji Yana ra'ayin ganin Unaisah, wall clock Ya kalla ƙarfe 11 na dare, yasan i war haka tayi bacci Jaraba kiran layinta yayi, tana fara ringing ta yi picking yayi mamaki bai zata zata ɗaga ba .. Kara wayar yayi a kunnan shi yama rasa me zai ce mata. Sanyayyar muryartace ta ratsa kunnanta "Barka da dare chief, ka wuni lafiya"? "Why are you still not sleeping" "I woke up for the night prayer" yaji dadin jin hakan "Okay, if you dont mind I want you to bring me the girl's backpack" "Toh" rejecting call ɗin yayi, sai da yayi unclocking ɗin kofarsa don ta samu damar shigowa, kafin ya shiga bathroom don yayi wanka. Saukowa tayi daga kan gadon ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta ta cikin madubin. Silk Pyjama ne a jikinta, riga da wando launin blue sky, rigar tana da dogon hannu sun yi matuƙar yi mata kyau. Lallausar Curly hair dinta tabi da kallo, duk Ya har gitse saboda rashin kwanciyar hankali ta manta when last tayi fixing dinsa. Fragrance set ta ɗauko ta feshe ko'ina na jikinta da shi, cikin kankanin lokaci daddadan kamshin turarenta ya buɗe ɗakin ta ɗauko veil ta yafa ma kanta kafin ta saka flat shoe a kafarta. Back pack din ta dauko, ta daurata kan mattress, ta curo wasiyar da Unaizah ta bata guda biyu ta boye su cikin diary ɗinta, don bata jin zata iya rabuwa da su tunda kamar amana ta bata, tafison ta damƙa ma iyayenta da hannunta. Goya jakar tayi abayanta, ta fito daga ɗakin, gidan shiru babu kowa a falon alamar duk sunyi bacci adakunansu.. Bata nufi ko'ina ba sai ɗakin Chief, tana ƙarasa bakin kofar takai hannu zatayi knocking sai taji ƙofar ta fara kokarin buɗe kanta ta ɗanyi mamaki Almost 3 times tana yin sallama ba'a amsa mata ba, ta kutsa kai ta shiga ciki, bata ga kowa ba, sai dai taji sautin safkar ruwa daga toilet dinsa, wurga ido tayi tare da kallon glass wall din toilet nasa yayi duhu sama ka dai take iya gani.. Gajiya tayi da tsayuwa, ga wata kasala da take ji, wasa wasa ta fara gyangyaɗin bacci, har ta saki backpack din hannunta ta fadi kan floor ba tare data lura ba.. Lokacin daya fito waist dinshi ɗaure da towel fari kyal, fatar shi tayi freshi danshin ruwa ya jiƙata...yana kokarin ɗaga kafa ya nufi dressing mirror ba zato ba tsammani ya hango mutun kwance kan rug kamar an jefar da ita a gurin ta baje sai sharar bacci take yi, ga backpack ɗinta yashe gefe ɗaya... Yayi mamaki cos bai tsammaci zai iske ta adakin ba, ya daisan ya cire security din kofar, abun da ya fi daure mashi kai ta yadda bacci yayi awon gaba da ita akan rug dinsa, kamar wadda tasha kwaya.. Walking slowly ya nufi rug din Ya zuƙunna daga gabanta, ya nutsu yana kallonta, yanayin yadda take fitar da numfashi cikin nutsu kirjinta na sama da kasa ba karamin tafiya tayi da imaninsa ba, kamar jinjira la66anta sai kerma suke. Sai yanzu yayi tunani me ya hanata bacci da wuri? tabbas akwai damuwa aranta wanda silar hakan ta kuntata kanta ta hana idanunta bacci shiyasa da tazo dakinshi baccin yaci karfinta har yai awon gaba da ita batare da sanin ta ba.. Baya jin zai iya tada ta daga baccin, bai shirya katse mata jin dadin ta ba, baccin da takeyi sauki ne agare ta. Yanke shawarar canza mata gurin kwanciya yayi, A hankali ya sanya hannayen shi biyu ya tallabota ya dago da ita tare da miƙewa Ya nufi katafaren gadon shi da ita, kusan itace mace ta farko da zata kwanta akan shi, A tsakiyar mattress din Ya shimfidar da ita, duk da baccin da takeyi hakan bai hanata jin dadin sauyin gurin kwanciyar da akayi mata ba, numfashinta har canzawa yayi, lallausan duvet ɗinsa ya janyo ya lullu6e ta shi har zuwa kan kirjinta, kasa janye idanun shi yayi daga kallon ta gaba ɗaya ya shagala da kallon kyakkyawar sexy face dinta wani irin yanayi ya fara ji a jikin shi hakan yasa shi saurin miƙewa Yabar gaban gadon, badan bai yarda da tsoron Allahn shi ba sai don gujewa sharrin shaidan... Can cikin bacci kunnuwanta suka soma jiyo mata daddaɗar kira'ar karatul qur'anin shi, kamar amafarki take sauraron karatun a lokaci yana zaune kan darduma jikinshi sanye da farar jallabiya, raba dare yayi yana kai kukansa gurin Allah, bayan ya kammala ya buɗe kur'ani yacigaba da karantawa. Yana tsaka da karatun, tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci ta dinga mirgino kiris Ya rage ta kundumo ƙasa, yana gani yai hanzarin miƙewa yai saurin tallabota da hannayen shi biyu.. Zuƙunnawa yayi gaban gadon ya bi ta da kallo, ganin kamar tana kokarin buɗe idanunta, biji biji ta fara ganin kamar mutun a kusa da ita aranta ta ayyana anya ba mafarki take ba"? Murya na rawa ta furta"Batool" shiru ba'a amsa mata ba "Aunty ummi" still ba amsa mata ba "Sajeed" nan ma shiru ba'a amsamata ba Murza idanunta tayi da yatsunta, don ta samu damar ganin wanene...wani irin faduwar gaba taji lokacin da idanunta suka washe ganinta ya dawo normal, kokwanto ta farayi anya Chief ne? Ko dai mafarki ta ke ba? Taya za'ai chief ya shigo dakin su"? Kwata kwata ta manta abun da ya faru. Tunani tayi ko Danish ne ya koma mata Chief, Cikin disasshiyar murya ta furta"Danish" Jin shiru bai amsa mata ba, yasa ta fara kokarin miƙewa da wata irin kasala a jikin ta, zama tayi tare da jingina bayanta jikin headboard. "Kin tashi lafiya"? sexy voice dinsa ce ta ratsa kunnanta, firgigit ta ware idanunta sosai akan fuskar shi wani irin faduwar gaba taji, a rude ta kalli bedroom din sai yanzu ta gane adakin wa take..nan take ta tariyo abunda ya faru daren jiya bayan ta zo dakin shi bacci yaci karfinta adakin shi...tsabar rudu jikinta na kakarwa ta zabura zata sauko daga kan gadon ai kuwa gaba ɗaya jiri ya kwasheta kiris ya rage ta kifa kasa da sauri Chief Ya janyota ta fado kan laps dinsa, wata irin kunyace ta kamata, ta runtse idanunta la66anta na kerma tace"i'm really sorry, I didn't know I fell asleep in your room dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini" Ƙamshin turarenshi ya hana ta ƙarasa maganar saboda ratsa makoshinta da yayi. Batai aune ba taji numfashin shi na kokawa da nata numfashin Jin shiru bata ji move dinsa ba yasa ta ɗan kyalla ido ɗaya don ta ga wani hali yake ciki Unexpectedly suka haɗa ido cikin na juna, sam ta kasa runtse idanunta.. gani take kamar amafarki wai yau gata ga chief, ya ɗauketa kamar yar jinjira..bakomai take tunawa ba face maganganun daddynta, duk da bai fito fili ya faɗa mata wanene mijin da yayi mata ba, taji aranta Chief ne, kuma tabbas taga abunda yake kokarin ankarar da ita, Chief ya haɗa komai da zaisa mace ta so shi. Matsawo yayi da fuskarshi saitin tata, har tsinin hancinsu ya gogi na juna anata wautar tayi azaton kiss zai mata abaki, gaba ɗaya tabi ta dabarbarce kamar wadda electric shock ya kama, ƙayataccen murmushi ya sakar mata har dimples dinsa ya lotsa aransa ya yi mamakin kamun kanta cos yadda mata ke hauka a kanshi da wata ce ta samu kusancin nan da shi tuni zata ƙwaye masa. Ya riga da ya fahimci me zuciyarta ke raya mata.. A hankali ya sauke ta kan floor din. da sauri ta miƙe tare da sunnar dakanta kasa. Veil dinta dake ajiye kan gadon shi ya dauko ya yafa mata akai tare da naɗe mata shi. "Thank you.." tafiya tasoma yi zata bar dakin ya dakatar da ita"ban gama magana da ke ba" tsayawa tayi tare da juyowa ta dube shi Zama yayi gefen gadonshi, da yatsan shi Ya nuna mata backpack din data kawo ma shi "Buɗe min jakar" da sauri ta dawo ta zukunna ta bude backpack din.. "Ki curo komai dake aciki" ta amsa mashi da toh, bayan ta kammala curo kayan dake a cikin jakar ta jerasu kan floor. "Ki buɗe min textbooks din, Inason ganin meke a cikin su.."zama tayi dirshan kafin ta fara bude shafukansu harta kammala Ya rage saura Diary din Unaizah.. "Zaki iya karanta min" ɗaga mashi kai tayi alamar eh a gogo ya kalla saura rabin awa afara kiran sallah asubahi. Kasa kunne yayi yana sauraronta, yayin da idanunshi ke akan tausasan pinkish lips dinta ta zaƙe sai karanta mishi takeyi da zazzaƙar muryarta. Kafin ta kammala karantawa tuni idanunta sun cicciko tab da kwalla, saboda akwai chapters na rayuwar Unaizah da suka ta6a zuciyarta, duk wani abu daya faru da ita mai dadi ko mara dadi sai da ta rubutashi. shi kanshi chief dake sauraronta zuciyarshi ta karaya da jin irin rayuwar sharholiyar da yarinyar tayi tare da iyayenta batare da sun tsawatar mata ba, saima suka bada gudummuwar gur6ata rayuwarta, hakan na nufin dama cen mahaifinta ya sadaukar da ita shiyasa ya wulakanta rayuwarta ya hana tasan addinin shi don kada Allah ya tuhumeshi aranar gobe kiyama saboda shi jaki ne. Cikin shesshekar kuka tace"na gama karantawa" Mika mata hannu yayi ta bashi diary ɗinta, shafin farko ya duba shi anan yaci karo da corners na hotuna guda uku babu biyu sai ɗaya daya rage na Unaizah. A cikin zuciya ya karanta sunayen dake akasan gidan hoton _My lovely dad, Red Neck, and my first love, my momma, and me, Unaizah, Yar gidan daddy_ ya shafe mintuna Yana kallon hoton Unaizah ya rasa a ina ya ta6a ganin fuskar nan! "Red neck, sunan wanene"? Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar shi Sai lokacin ta tuna da sunan mahaifin Unaizah, da sauri tace"Nickname din daddynta ne, Jan wuya" jinjina kanshi yayi "Kin ta6a buɗe diary din nan"? "Eh, amma ban ta6a karanta rubutun ciki ba sai yau" Ya juyo mata shafin farko da yatsa ya nuna mata wurin da ya kamata hotuna su kasance. "Ina waɗannan hotunan suke, ko lokacin da kika fara buɗe diary din haka kika gan shi da hoto ɗaya"? Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa, shiru tayi tana kokarin tunanowa sai dai ta kasa, ganin kamar ta rudene yasa chief aje diary din, Ya janyo drawer chest din gadon shi, Ya curo diary dinshi hadadden gaske, mai gidan key a jikin shi ya buɗe tare da nuna mata shafin farko, Hoton daddynsa ne mai girma sharafuddeen tare da Mommynsa Malikat sarauta, Ga hoton shi a tsakiyar nasu lokacin baifi shekara shabiyar ba. "Kinga yadda nawa ɗiary din Yake! Kuma naga kamar kusan iri ɗayane da nata, zai iya yiwuwa akwai hutanan a jiki cos ga shaidanan alamar an ta6a manna hotuna a jikin corners din, watakil cikin rashin sani kin ta6a buɗe diary din hotunan suka faɗi without your knowlegde" ❓❗❔❕ *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: __________________________________💋✍️💋🌹🔥🫀💘 a ruɗe ta kalli fuskar shi, ya haɗe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne. Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su Duk da haka bata kawo komai a ranta ba, ta kuma cewa, "Daddy, Chief ya fada maka an ga Danish a cikin toilet ɗinsa...." banza yayi da ita tamkar bai ji maganar ba, hakan ba karamin ɗaga mata hankali ya yi ba. komawa tayi cikin yan uwanta jiki a mace ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba. Walking slowly yake taka stairs, da karfi Jemimah ta furta sunan Danish hakan yaja hankulansu gaba daya suka kalli stairs din bakunansu a buɗe saboda tsantsar kyan da yayi, wata hadaddiyar light grey thobe ce a jikinsa ta bi surar jikin shi, ya ɗaure sumar kan shi with hair ties, gaba daya sun shagala da kallon shi, ƙasa-ƙasa da murya ummi ta furta Tabarakallahu ahsanil khalikin, Allah yayi halitta..." A second to the last step na stairs ɗin ya ɗan dakata da yin tafiyar jin alamun kamar ana kallon shi kafin ya ɗago da ido ya dube su, motsin buɗe kofar falo yaja hankulan su. Gaba ɗaya hankalinsu ya koma kan masu shigowa, Big guy ne ya shigo da sallama a bakin shi, kafin U.s armies din suka shigo kowannansu suit ne a jikin shi...zuba masu idanu su ka yi kamar ba su gane su ba, sun yi shiru suna kokwanton anya su ne? Saboda basu tsammaci zasu gan su ba. Dakatawa su ka yi da yin tafiyar suna kallon su kusan su shida suna jira suga reaction din su, Wani irin ihun farin Ciki Gabriel Ya saki, da gudu Ya nufi Lieutenant thompson Sojan daya taimake shi a dajin evil forest saboda sarkar cross din shi, kafin Ya ƙaraso thompson Ya bude mashi hannayen shi ya fada jikin shi yayi hugging din shi gaba daya suka fashe da dariya. Wayyo Allah daɗi da wani irin farin ciki sauran ex-prisoners suka nufe su kafin su ƙaraso suka miƙa masu hannuwansu don su yi hugging din su, aiko suna ƙarasawa ƴan matan suka ƙi bari su yi hugging ɗinsu sai dai suka yi shaking hands, in ka cire jemimah da ta maƙalƙale Commender har saida ya ɗauke ta, mazan cikin su suka yi hugging dinsu ɗaya bayan ɗaya, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, sunyi mamakin zuwan bazatan da suka yi ma su. Da tsantsar mamaki Unaisah ta furta"Commander James! Captain Lewis! Major Smith! Jackson Lee! Canal Harry! Lieutenant Thompson! What an astonishing reunion! Is this really a chance encounter?" Dariya suka saki gaba dayan su, da fara'a commender james ya ce, "Indeed, it's us! We hope you're overjoyed to see us. We've come specifically because of you, and we hope you'll welcome us with open arms." (Yeah mu ne, muna fata kunyi farin cikin ganin mu, munzo ne saboda ku, fatan zaku kar6e mu hannu biyu..." ) bai ƙare maganar ba suka haɗa baki gurin furta, "We welcome you, most warmly! We're truly elated to see you!" Daɗi ne Ya lullu6e sojojin, sai kallonsu sukeyi gwanin ban sha'awa sunji dadin sauyin da sauka samu sun kuma jinjina ma Chief, su Hibba da basu san su wanene ba sai faman baza masu na mujiya su ke yi cike da son sanin su wanene su ɗin. Captain lewis ne ya nuna su da hannunshi cikin harshen turanci ya ce, "waɗannan sune sauran yan uwan naku"? A tare suka haɗa baki gurin furta Eh, Tambayar sunayen su yayi Sajeed ne ya gabatar masu da su.. Yana zuwa daidai kan Deeja Commender Ya dubi Haris, "Is she your sister cos you look alike" Yana murmushi yace Eh sister ɗinsa ce. "She's the cause of his heartbreak" Unaisah ta faɗa da zolaya, dariya sojojin su ka yi. Major smith Ya ce,"Dear Angel, where is that handsome young man, mai nauyin bacci ban gan shi ba ko baya nan .." bai ƙare maganar ba Thampson Ya ce, "nima abunda nake so na tambaya kenan, Ina Danish"? da yatsa Unaisah ta nuna ma su shi, yayi tsaye kan stairs, idanunsa na akan su, gaba ɗaya suka kai duban su gare shi Commender ya ce, "Har yanzu yana nan da ƙyuiyarsa?" ganin kamar baida alamun zuwa gurinsu ne yasa Unaisah yin saurin cewa,"may be bai gane ku ba ne," major ya sake cewa, "Mun riga da munsan halin shi ai, Ya bacci har yanzu yana yi ko ya daina? Dariya suka saka gaba ɗayan su, da ido Unaisah tayi mashi alamar ya zo gurinsu ganin kamar sun damu da son ganin shi. Saukowa down ya yi ya nufe su, commender ya miƙa mashi hannu, "Danish, come here, I'm thrilled to see you! I hope you're safe and sound," ya faɗa tare da yin hugging ɗin shi, In low voice ya furta, "I'm fine, ina yi maku barka da zuwa" ya faɗa tare da raba jikinshi daga na commender ya bi sauran yayi hugging ɗinsu tare da yi masu barka da zuwa hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ma su ba. Big guy ne yace da su, "Mu shiga ciki, ku zauna ku huta." Hannayen su ruƙe dana prisoners suka nufi falon, kafin su ƙarasa Taj dake tsaye yana kallon su, Ya matso kusa da su suka gaisa da junansu, big guy ya gabatar masu da Taj a matsayin mahaifin Unaisah sun yi murnar jin hakan sosai, duk budurin da ake Ummi tana can gefe ɗaya tana yin waya har sai da commender ya hangota yana ganin bayanta ya gane itace, nufar ta yayi yana isa ya rungume bayanta, a ɗan firgice ta juya don ta ga wanene ta haɗe rai amma koda ganin commender James sai ta waro idanu cike da mamaki ta ambaci sunan shi, "Sir James, is that you? I'm surprised," ta faɗa tana yar dariya Sir james ya ce, "It's me, dear. Yesterday when we called, I hid the point of my coming because I wanted you to be surprised." Murmushi ta sakar mashi, "I welcome you wholeheartedly I'm at a loss for words to express my happiness and how much I've missed you." "I've missed you too, dear one. I'm overjoyed to see you." Ya bata amsa. Ya yi zaton za ta yi hugging na shi amma sai ya ga akasin hakan, Taj da Big guy kuwa tun rungumar farko da commender yayi mata suka kalli juna, dama sun san za'a rina tun da su dabi'ar su ce yin hakan, a kan sofas suka zauna gaba dayan su, nan fa ex-prisoners suka fara cika su da surutu suna basu labarin abubuwan da suka faru bayan dawowar su Nigeria, suna tsaka da yin fira Chief Ya sauko down shima ya kimtsa tsaf cikin suit nasa, suna ganin shi suka miƙe da sauri commender ya nufe shi suka rungume juna a mutunce suka gaisa ya yi mashi barka da zuwa, kafin ya nufi sauran sojojin ya miƙa masu hannu suka gaggaisa. Kowa na gidan tun daga kan Gate security Officers har Chefs na kitchen saida suka shigo falon domin yi ma baƙin Chief barka da zuwa, hakan ba ƙaramin faranta ransu yayi ba ganin yadda kowa ke ɗokinsu sai girmama su ake. Batare da bata lokaci ba, Chefs suka shirya masu dinner a dining, duk girman table ɗin saida suka cika shi da kayan abinci kala kala. Yau gaba ɗayansu su ka yi dinner a tare da baƙin su, gwanin ban sha'awa su commender sun ji daɗin karramawar da akai ma su, abun da yafi burge su yadda prisonsers suka saki jiki da su kamar irin sun haɗa alaƙa ta jini da su, hakan yasa suma suka samu walwala kamar suna a gidajen su na America, ga jemimah da ta yi ta basu nishaɗi da surutunta, ta maida commender kamar kakanta, har abinci take bashi a baki, ta yi kane-kane akan laps din shi, Danish kuwa hankalinshi na akan Unaisah ya lura kamar akwai wani abu dake damunta saboda yadda take cin abinci kaɗan kaɗan kuma hankalin ta yafi karkata akan daddynta saboda shine damuwarta. Bayan sun kammala cin dinner ɗin, wata sabuwar firar ce ta 6arke a tsakanin sojojin da su Chief har kusan ƙarfe goma kafin Big guy ya raka su masaukin da za su zauna, duk yadda Unaisah taso ta gana da daddynta a daren ranar abun yaci tura tana ta jiran zuwan shi tasan ya saba duk in yana gidan dare yayi sai ya zo dakinsu yayi mata sallama kafin ya tafi amma yau taji shiru, koda ta fito bata iske kowa a falon ba, shima yayi tafiyar shi, da damuwa ta kwana a ranta. Gidan Kurkukun Ƙaddara🔥 _____________________________✍️ Meke faruwa a gidan kurkukun ƙaddara? Saboda gabatowar gagarumin shagalin da zasuyi na black Night, sun fara shirye-shiryen tarbar wannan dare mai daraja a gurin su, Yanzu sun dakata da yin duk wani mugun abu da suke yi a gidan kurkukun, hatta fursinonin su sun yi mamakin sauyin da suka gani, lafiyayyan abinci suke basu mai rai da lafiya har sau uku a rana, bayan haka sun tsaftace ɗakunan prisoners din da makewayin su sun kuma canza masu sabbin Uniform. Duk da sauyin da suka samu, hakan bai saka su yin murna ba, saboda sun san da wata manufa a ƙasa, wata wutar bala'en ce zata kunno kai, kamar ko sun sani dalilin dayasa suka sauya masu cimarsu daga ganye zuwa lafiyayyan abinci mai gina jiki, saboda albarkatun jikinsu su cicciko suyi ƙiba fatarsu tayi kyau don su ji daɗin aikata fasiƙanci da su, a cikin abincin da ake kawo masu hada wata kwayar sihirin da suke saka masu a cikin dafaffen kwai, kamar sha ka fashe take aiki a jikin ɗan adam walau mace ko namiji, cikin kankanin lokaci Yake ciko da duk wata ramar jikin su ya ha66aka jinin jikin su. Lallai Elders Sun shirya ma Black Night..💔 Yau gaba ɗaya Sun fiddo da Prisoners din dake a kurkukun zuwa tsakar prison din, ko ina ka kalla sune birjik, sun jera layi, as usual jajayen uniform ne a jikin su, a yanzu babu masu black Uniform na ƴan baiwa tun daga kan su Unaisah. A ƙalla fursinonin da suka rage agidan kurkukun ƙaddara zasu kai kimanin ɗari uku da hamsin, daga ciki harda jariran da suke raino. Yan matan suna asanye da short gown wadda bata wuci gwuiwarsu ba, mazan kuma riga da wando ne ajikin su, babu mai magana a cikinsu kamar gumaka sun ƙame a tsaye ko motsi basa yi, Iya ƙwayar idanun su ce kadai take kyakkyaftawa sai numfashinsu dake fita. Bakomai ne yasa suka nutsu ba, fa ce Giants ɗin dake a kewaye da su, Wasu irin gabza-gabza masu jini a jika. sun kasa sun tsare sai suntiri suke umarni kawai suke Jira su aiwatar. Cikin takun Izza Tsohuwa Inno ta nufo gurinsu hannun ta ruƙe da sanda, kamar kullum a cikin shiga ta red gown take, daga bayanta Giants ɗin dake take mata baya ne, kan matakalar benan dake fuskantar prisoners ɗin suka dakata da yin tafiya, ta tsaya tana bin su da ƙasƙantaccen kallo. har na tsawon mintuna batare data furta kalma ba, sai da ta mula ta sha iska kafin ta fara magana a a gadaran ce "Duk wanda na kira lamba ɗin shi a cikin ku, Ya koma gefe ɗaya" ta faɗa tare da nuna masu inda zasu tsaya da sandar hannun ta.. "Prisoner no twelve, Thirteen, Fourteen...' duk wanda ta kira sunansa, Jikinsa na kerma yake fitowa daga cikin layi ya tsaya gefe ɗaya, daga gani masu kyawun surar cikin su take zaƙulowa waɗanda suka zama matured. Kusan fursinoni arba'in da takwas ta kira, mata sunfi yawa acikin su, saida ta kammala kiran lambobin waɗanda ta zaba kafin ta furta prisoner no 100 shiru ba'a amsa mata ba, da alama ta manta aika aikar dasa giant yayi mata, tsawa ta daka masu, "baku ji ina magana bane? Where is she?" Murya na rawa wata young adult daga cikin su ta yi ƙarfin halin furta, "tun lokacin da kika sa Giant Ya tafi da ita, bamu ƙara ganin ta ba"! Shiru tayi jim sai da yarinyar tayi magana kana ta tuna abun da tasa aka yi mata. Giant ɗin dake a gefenta ta kalla, "Tana raye ko ta mutu?" Cikin girmamawa da wata irin buɗaɗɗiyar murya ya ce, "Bani da masaniya, bayan na kaita ɗakin fiɗa kamar yadda kika bani umarni, ban ƙara bi ta kanta ba" Murmushin gefen fuska ta saki, "If she dies, I will be sad because I want her to witness the black night, Even though I know even if she is alive, she will not be useful anymore." Cike da shaƙiyanci ta faɗa kafin ta sake ce ma giant ɗin, "Ina ji a raina bata mutu ba, amma bayan da ka kaita ɗakin fiɗa ka tabbatar sun feɗe sassan jikin ta? Ta jefa mashi tambayar. "Bayan na kaita ɗakin fiɗar, ban ƙara komawa ba, saboda ba hurumina bane" Bata tsaya taji ƙarshen zancen nashi ba, ta juya cikin takun sauri giants din suka rufa mata baya. bata nufi ko'ina ba sai dakin fiɗa, koda ta shiga ta tambayi Gigantes Medici ɗin dake a gurin game da Gabriella, basu iya tuna meya faru bayan an kawo ta ba, ta nemi su bata records na fursinonin da su ka cire sassan jikin su, kwata kwata babu sunan ta. Babu inda bata duba ba, kamar zata yi hauka, har records ta kar6a na dead prisoners nan ma bata ga sunan Gabriella ba, nan take zuciyarta ta raya mata cewa wani ya ceci rayuwarta. Wani irin ƙululun baƙin ciki da takaici ne suka mamaye zuciyar tsohuwa Inno, tsabar fusata har wani hayaƙin huci take fitarwa ta kofofin hancin ta, rai a 6ace ta furta, "duk inda kika shiga zan gano ki ne, koma wanene ya ceci rayuwarki yayi babban kuskuren da bazai iya kubcema azabata ba! " da karfi ta buga sandar hannunta tare da furta sunan Gabriellah da wani irin amon murya mai amsakuwa.. A matuƙar firgice Gabriella ta farka daga dogon baccin da ya ɗauke ta, kanta ne ya fara sara mata da ciwo. da tafukan hannayenta ta daddafe kan, wani irin gumin zufa ne ya fara tsattsafo mata, Kakkausar muryar dattijuwarne ya fara dawo mata a cikin kanta. _"Faɗa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yunƙurin yi min rashin ɗa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai_ waro idanunta waje tayi, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, ta fara jan numfashi da karfi da karfi _bakin ki ne ya ja maki! Nayi mamaki da har kika iya rayuwa, ai nayi zaton zan zo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba_ Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, cos she recovered her memory, ta tuna komai, abun ka game zuciya ta dinga buga kanta jigin karfen gadon har saida goshinta ya fara barazanar fashewa, wani tafarfasa zuciyarta ke yi mata saboda bakin cikin abunda dattijuwa inno tasa aka yi mata. Ba dan Allah yasa tsohuwa khala ta faɗo dakin ba, da tuni Gabriella ta jima da kashe kanta, tana shigowa sautin kukan da take saki ya tari hanzarinta, ta waro ido waje tana kallon yadda Gabriella ke buga kanta, Cike da tashin hankali ta yi kukan kura tayi dirar mikiya kan gadon ta damƙi wuyan rigarta, ta jijjigata da hannayenta ta fara kokarin rarrashinta amma saboda bad temper dinta ta makance bata iya fahimtar komai da khala ke faɗa mata, sai kuka take tana fadin, "Let go of me! Let go of me! Why am I still alive? why didn't you kill me? You wicked oppressors, Jesus will never forgive you, you will all go to hell! cikin fitar hayyaci take zazzaga masifa tana kokarin kwace kanta daga hannun tsohuwa khala don ta ƙarasa kashe kanta, tausayinta ne ya kama tsohuwa Khala duk da tayi mamakin zuciyar dake gare ta, in wani ne ya ga ya tsira zai zauna cikin salama ne amma ita so take ta kashe kanta ta karfi da yaji, da tasan zata dawo cikin hayyacinta da bata bar dakin ba, yanzu gashi tana neman ta dawo da hannun agogo baya, don bazata manta lokacin da ta ɗauka gurin yin jinyarta ba, har ɗinki sai da tayi mata a gabanta saboda raunin da taji. Allah ne ma ya nufa zata rayu don da wuya giant su kwanta da mace ta tashi da lafiya batare da ta haukace ba ko ta mutu. Kamar zasu yi dambe ita da Khala, saboda ta sanya karfi dama Allah yayi ta da ƙarfi kamar doki, da ƙyar khala tayi nasarar buga kanta jikin pillow ta tamurshe ta, ta yadda numfashinta bazai rasa hanyar fita ba, kasa ɗagowa ta yi da kanta saboda khala ta tokare kanta da tafin hannunta, zafafan hawayene suka fara yar tseral kan kuncin ta, cikin disasshiyar murya ta furta, "Bana so na mutu, kada ki kashe ni, Ina son ganin ɗan uwana Gabriel," Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa khala ta kwashe da ita tuni jikin Gabriella yayi sanyi lakwas. Da kakkausar Murya khala ta ce, "Kinsan baki son ki mutu me yasa kike kokarin kashe kanki? Yar ƙarama dake sai baƙar zuciya kamar ta kafuran farko! Dame kike taƙama ne? Ina karfin naki yake uhm!"? Nishi ta dinga yi tana huci kamar zata iya ta6uka wani abu. Sassauta murya Khala tayi, "Ba duka muka taru muka zama ɗaya ba, kasancewata a gidan kurkukun ƙaddara, ba hakan yana nufin nima muguwa bace, kamar yadda kika zata, kinyi min mummunar fahimta, amma nayi maki uziri saboda bakisan komai dangane dani ba..." ta faɗa tana kallon idanun Gabriella da suka kaɗa jawur. Numfasawa tayi kafin ta ɗaura da cewa, "Da ace ni muguwa ce da ban taimaki rayuwarki ba, nasan yanzu tunaninki ya dawo, dama abunda na ke gudu kenan saboda nasan za'a rina, yanzu da ban zo ɗakin nan ba da tuni kin jima da kashe kanki saboda ɗamsil basira, idan kina tunanin mutuwa mafita ce a gareki toh ki daina, shi jarumi ba'a san shi da karaya ba, kada ki zama raguwa ki zama jaruma mai iya tankwara zuciyarta me kuma burin ɗaukar fansar zaluncin da aka yi mata. Tana jan nishi da ƙyar ta furta, "Who are you? Where did you find me? and Why did you help me?" "Sanin wacece ni baida amfani, iya abunda zan iya sanar dake shi ne ba a haife ni a gidan kurkukun ƙaddara ba, bada son raina na kasance a cikin shi ba, ta karfi da yaji aka kawo ni nan, bazan iya misalta maki ƙunci da raɗaɗin da na ji a lokacin dana buɗe idanuna na tsinci kaina a gidan kurkukun nan ba, na ga musiba da bala'e da idanuna, abunda ban ta6a zaton ko a mafarki zanga makamancin shi ba, zuciyata a karye take saboda anci amanata an yaudare ni, bayan haka an nuna min fin karfi ba yadda na iya,...." idanunta ne suka ciko tab da kwalla. "Kamar yadda kika so kashe kan ki, nima nasha yin yunkurin yin hakan amma idan na tuna menene makomata? Sai inji na gaza! Mutuwa bazata hana su cigaba da aikata fasadi ba, saboda su ɗin 6atattu ne in har bamu haɗa hannu mun kawo ƙarshen su ba, babu abunda zai canza na daga zaluncin da suke aiwatarwa, bayan haka babban abunda yasa nake so na rayu shi ne ya'yana inason na sake ganin su ko da da numfashina na ƙarshe ne". muryarta na rawa ta ƙare maganar, hawaye suka cigaba da sintiri kan fuskarta, Gabriella dake sauraran khala, itama hawayene kan fuskarta, tana da wuyar sha'ani a rayuwarta bata yarda da mutane amma karo na farko ta yarda da tsohuwa Khala, maganarta ta karya mata zuciya. A hankali ta zame tafinta daga kan Gabriella, hakan ya bata damar miƙewa ta zauna da ƙyar tana duban fuskar khala da tausayawa "Ke ɗan uwan ki ɗaya ne, ni kuma jikokina da suka salwanta agidan kurkukun ƙaddara yawa ne da su, inaji ina gani ban iya tsinana masu komai ba saboda an nuna min fin ƙarfi...." fashewa ta yi da kuka kamar ƙaramar yarinya. Itama Gabriella din kukan ta fashe da shi saboda tausayin khala da ya mamaye zuciyarta ashe ita bata ga komai ba tayi mamakin haƙuri da juriyar tsohuwar da har ta iya kai tsawon lokacin nan bata haɗiyi zuciya ta mutu ba. "Yau kimanin shekara ashirin cuf, rabon da in shaƙi iskar duniya saita gidan kurkukun ƙaddara, bani da burin da ya wace in tona masu asiri, kullum ne sai na roƙi Allah dare da rana ba fashi, duk da har yanzu ba wani sauyi, ban ta6a gajiyawa ba, saboda nasan Allah ne kadai zai iya cika min burina kuma yana sane dani, wani jinkirin Alkhairi ne kuma ina ji araina ƙarshen kurkukun nan ya zo" ta faɗa tana jan magina. "Kin tambayeni Ina na tsinto ki?" A ranar bayan na fito daga fadar Elder naji ina sha'awar in kewaya kurkukun duk da bana so nayi tozali da abunda zai hanani kwanciyar hankali, har zan gifta na hango tsohuwa inno tare da giant din da ya ɗauko ki babu sutura a jikin ki raina ya 6aci ba kaɗan ba, nayi zaton ma kin mutu ne, kwatsam idanuna suka hango min yatsun ƙafarki na motsi, wani iko na Allah ni da bana shiga huruminsu bansan ya akai zuciyata ta azalzala min akan in taimaka maki ba, cikin sanɗa na bi bayan su, har suka aje ki a ɗakin fiɗa, tafiyar su ke da wuya, nayi 6adda kama ta hanyar amfani da sihiri na, na shiga cikin Gigantes Medici din batare da sanin su ba saboda hankalinsu ya karkata akan aikin fidar da sukeyi, kafin su zo kanki cikin abunda bai fi daƙiƙa talatin ba, na sace ki na kawoki ɗakina, na fara kokarin tsayar da bleeding din da kike yi kafin na dinke raunukan jikin ki...." tiryan tiryan khala ta zayyana mata komai, wani irin son tsohuwar ne ya kamata har batasan sa'ar da ta faɗa kan kirjinta ba, ta rungumeta cikin shesshekar ta furta, "Ki yi haƙuri nayi maki mummunar fahimta, ki yafe min" Ɗan murmushi khala tayi kafin ta daura da cewa, "Tun kafin ki dawo hayyacinki na ji kina ambaton sunan ɗan uwanki Gabriel, na kwallafa rai a kan son sanin wanene shi? a cikin bookshelve ɗina ina da littafin register na fursinoni (Sijil al-sujna) a cikin littafin na buɗo ina bincikawa don inga wanene me suna Gabriel, ban sha wahala ba, saboda nayi nazari na gane cewa ku ɗin ba tsoffin prisoners bane cikin waɗanda aka kawo ne a ƙarshen shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, cikin sa'a na ga sunayen ku, a fahimtana ɗan uwanki ne ko?..." cikin sanyin murya tace, "twin brother ɗina ne." "Zaki iya tuna tayaya akai kuka tsinci kanku a gidan kurkukun ƙaddara?" Girgiza kai ta yi har lokacin bata raba jikinta daga na khala ba. "Bazan iya tuna komai ba, ɗan uwana kadai na sani, pls ki taimaka min in gan shi..." Shiru tsohuwa khala ta yi saboda tasan me zai biyo baya in har ta faɗa mata cewa baya a cikin kurkukun, cos ta ga sunan shi cikin list na escaped prisoners, ta lura da yadda take mugun son shi in har ta faɗa mata, zuciyarta zata karaya ne kuma zata ga kamar ya manta da ita ne shiyasa ya tafi ya barta batare da ya taimaki rayuwarta ba" Ɗagowa tayi da kanta, "kinyi shiru baki bani amsa ba, bana so na rasa ɗan uwana, nasan yana cikin wahala kuma yana nemana, pls ki ɗauko shi ya dawo nan mu rayu atare" Dafa kafadarta khala tayi, "Zan iya jefa rayuwarmu da tashi cikin haɗari, abunda yasa nake 6oyenki saboda a yanzu haka dattijuwar da ta kusa kashe ki, nemanki take ruwa ajallo, amma in har Allah yayi mana tsawancin kwana gaba na yi maki alƙawarin zan hadaki da ɗan uwanki..." cikin karyayyar murya ta ce, "ya mutu ko"? Girgiza kai tsohuwa khala ta yi, "A'a yana raye, " "Ta ya kika san yana a raye"? "Zan nuna maki" Ɗaga mata kai ta yi alamar toh, saukowa suka yi daga kan gadon, ta ɗauki sandar ta, ta nufi gurin furannin dake a ɗakin, Gabriella tana a biye da bayanta, da sandar ta nuna mata fure kore shar da shi a cikin wata tukunyar shi mai kyan gaske. "Ɗan uwanki yana a cikin ƙoshin lafiya, kin gan shi nan" aruɗe ta dubi khala, "tayaya hakan zai yiwu! Mutun ya zama fure??" Dariya khala tayi, "It's a magic trick kema idan naso sai in mayar dake fure, Ko kina da ja ne?" Ta faɗa da zolaya, da sauri ta girgiza kai, Zuƙunnawa tayi a gaban furen ta ƙura ido tana kallon shi, cikin sanyin murya ta furta sunan shi abun mamaki sai ta ga furen ya motsa ganyayyakinsa kamar iska ta kaɗa shi. Murmushi ta saki,"Da gaske kaine?" again ya ƙara motsa ganyen shi, wani daɗine ya lullu6eta har ta buɗe baki zata ƙara magana kwatsam ba zato ba tsammani taji kamar an jeho mata wuƙa a kirjin ta, dafe shi ta yi da hannun ta, radadi ya hana ta motsa, nan take ta fara yin aman jini, Hankalin Khala kwata kwata baya akanta batasan meke faruwa da ita ba, saboda tayi zurfi acikin tunanin ta, sai kokari Gabriella take ta ruƙo rigarta amman ta kasa saboda kermar da yatsunta ke yi....🥺 __________________________________✍️ *BENAZIR💔* Suna a zaune kan darduma su biyu ita da Zeenatu, sun haɗa baki suna karatun kur'ani da suka buɗe akan qur'an stand Wayar tace ta fara ringing, bayan takai aya ta dakata da yin karatun ta miƙe da sauri ta nufi wayar dake ajiye saman gadonta "Aunty Benazir, Azeezaty ne?" Zeenat ta tambaya tana kallon ta Bata ba ta amsa ba, har saida ta dauki wayar, ta dubi sunan me kiranta, tayi mamakin ganin sunan Uncle ya bayyana yau wata rana Alhaji musa ya kira ta, a ranta ta furta Allah yasa alkhairi ne. Ɗaga kiran ta yi ta kara wayar a kunnanta, tana kokarin yi mashi sallama ya katse ta da cewa, "Ki same ni a garden yanzu" amsa mashi ta yi da toh. Aje wayar tayi gaban mirror, ta juya suka haɗa ido da Zeenatu ta ƙura mata ido tana kallon ta. "Daddynki ne ya kira ni, ki cigaba da yin karatun yanzu zan dawo" tace toh" Bayan fitar Benazir, cike da zumuɗi ta miƙe, ta ɗauko wayar Benazir ta fara laluban layin Azeezaty, sam ta kasa ganowa saboda batasan sunan da Benazir tay mata serving ba, amma da ta tuna Benazir ta fada mata jiya ta kira layinta bata samu ba, hakan yasa ta shiga call logs, lambar farko da akai ma saving da God Gift ta danna Call almost 3 times tana kira baya shiga, ba dan ta so ba ta hakura. Lokacin da Benazir ta ƙaraso Garden ɗin tunkan ta ƙarasa idanunta suka hango mata mutun uku zaune kan lallausar darduma kowannan su shadda ce a jikin shi. bata iya tantance su wanene ba, saida ta isa wani irin burki ta ci ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya da tsantsar mamaki ta furta, "ZAKI!" Yana Jin muryarta da sauri ya ɗago ya kalle ta, zumbur ya miƙe tare da ambaton sunan ta "Benazir!" Hawaye ne suka ciko idanunta, tayi mamakin ganin shi, kuma tayi farin cikin ganin bawan Allahn nan ba zata ta6a manta halaccin da yayi mata ba.. Gaba ɗaya hankalin Sir mubarak, da na Alhaji musa ya dawo kan su, Sir mubarak na ganin Benazir a ranshi ya ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa Zaki ya ruɗe akanta, da alama dai Sir Mubarak ya yaba da kyanta. Jinjina mashi kai tayi, "Yayana ni ce," Cikin sanyin murya ya ce, "Benazir baki kyauta min ba, kinsan irin tashin hankalin dana fuskanta saboda rashinki a kusa da ni.. " bai kare maganar ba, Sir Mubarak ya yi mashi gyaran murya atare suka kalle shi. Cikin sauri Zaki Ya gabatar mata da Daddynsa, Cike da jin kunyarshi ta gaishe da shi, fuskarshi a sake ya amsa mata, tare da yi mata fatan alkhairi. "Benazir, ki shiga da shi ciki." Alhaji Musa ne ya faɗa fuskarsa a sake kamar ba shi ba, amsa mashi ta yi da toh, bata yi aune ba ta ji ya ruƙo hannunta a cikin nashi kamar yadda ya saba yi lokacin da suna tare. Fita su ka yi daga garden din, yace mata ba zai shiga gidan ba, yafi so suyi magana a cikin motarsa, ya buɗe back seat na motar shi yace ta shiga, ji ta yi bazata iya yi mashi musu ba hakan yasa ta shiga ta zauna bayan shima ya shiga ya datse car door din, suka Ƙurama juna ido kamar yau suka fara haɗuwa, sunyi kewar junan su sosai. "Da ranki da lafiyarki Benazir, baki neme ni ba, kamar kin manta dani a rayuwarki, baki yi tunanin damuwar da zan shiga ba, kin tafi kin barni da kewarki kullum zullumina kina ina? Kin isa gidan iyayenki lafiya ko kuwa?" Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, bata ji dadin halin da ta jefa shi ba, tasan shaƙuwar dake tsakaninsu dole ya damu da ita.. "Ka yi hakuri Yayana na kaina, wlh kana a raina, ban manta da kai ba, kamar yadda ka damu da ni nima haka na damu da kai..." katse ta ya yi, "Amma meyasa ba ki neme ni ba? "Ka manta wayata tana a hannunka?" "Ba hujja bace Benazir, kin riga da kinsan wanene mahaifina a ƙasar nan, kinsan family estate dinmu, why baki je can kin neme ni ba in har dagaske kin damu dani?" Fuskarshi a yamutse ya yi maganar, kwarjini ya yi mata ta sunnar da kanta ƙasa, tasan bata kyauta mashi ba.. "Me nayi maki dana cancanci hakan daga gare ki? Ko kin daina ƙaunar yayan naki ne?" Yanayin yadda yake magana ba ƙaramin karya mata zuciya yake yi ba, ga kamshin turarenshi da ya kanainaye hancin ta. Da ƙyar ta furta, "Na kar6i laifina, ban kyauta maka ba, amma ka yafe min, bazan ƙara maimaita kuskuren da nayi ba." Lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta, matsawa yayi dab da ita da sauri ta ja da baya, har saida ya ƙureta jikin murfin motar . Shafa fuskarta ya yi da tafin hannun shi, yana kokarin haɗe bakinsu ta yi saurin kauce mashi, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin shi yayi ba, saboda ta sauya mashi. "Kin canza min, meyasa?" Muryarta na kerma ta ce, "Yayana ka yi haƙuri, ba halina bane, ko a lokacin da nake amince ma hakan bada son raina bane, sai don bani da mafita ne, kewar mijina ne yasa nake biye maka saboda in samu relief..." wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyar shi, idanunshi suka kaɗa nan da nan suka fara yin ja... "Kin haɗu da mijin naki?" Ɗaga mashi kai ta yi alamar eh, Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, damuwa ce ƙarara kan fuskarshi, ita kanta ta sha jinin jikinta da ganin yadda numfashin shi ke fita.. "Tayaya akai ka gano inda nake?" Da ƙyar ya furta, "Uncle ɗinki, abokin Daddyna ne,..." ta yi mamakin jin hakan. A takaice ya bata labarin tun farkon dawowarshi abunda Ya faru har zuwa lokacin da Sir Mubarak ya kira Alhaji musa ya fada mashi lokacin da zasu zo ganin ta ..." ƙiris Ya rage ta fashe da kuka saboda tausayinshi da ya kamata, bata ta6a sanin yana sonta ba sai yanzu da ya ke faɗi mata, tayi mamakin zurfin cikin shi... Ruƙo hannayenta ya yi acikin nashi. "Ki taimaki rayuwana, ban saba da wahala ba, bansan menene so ba, sai akan ki, ke shaida ce, mata basa a gabana, aikina kawai nasa a gaba, wlh bazan 6oye maki ba tun rana ta farko da na fara ganin ki naji na kamu da ƙaunarki, shiyasa koda kika faɗamin kina so ki yi nesa da kowa naki ban yi maki faɗa ba, saima nayi maki hanyar da zamu bar ƙasar atare saboda idanuna sun makance akan sonki, a ranar da kika faɗamin kina da aure, ban runtsa ba saboda hankalina ya tashi kuma duk da sanin hakan ban ji son ki ya ragu ba saima ƙaruwa...." dafe kanta ta yi da tafukan hannayenta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kalaman Zaki sun tsuma zuciyarta da tausayin shi, ba dan Taj ba da ba abunda zai hana ta amince mashi saboda gayen ya haɗa komai da mace zata buƙata a gurin namiji, sai dai kash bata jin zata iya rabuwa da Uban ƴarta. Muryarta na rawa ta ce,"kai ne ka tura ma mijina saƙon ya sake ni?" Girgiza kai ya yi, "Ba ni bane, bazan iya aikata hakan ba." numfashi ta ɗan ja, kafin ta runtse idanun ta, ya zuba mata ido yana kallonta kamar zai hadiyeta saboda tsantsar son da yake yi mata... "Daddyna ya bani goyon bayan in nemi soyayyarki, In har kika amince min zai yi magana da iyayenki, on friday za'a ɗaura mana aure, Next week zan koma dake Canada, na yi maki alƙawarin ba zaki ta6a danasanin aure na ba, kin riga da kinsan wanene ni kin san halina, kuma ko bayan auren bazan hana yarinyarki ta zo inda kike ba, har shi kanshi ex-husband din naki bazan raba zumuncin dake tsakanin ku ba..." Kuka ne ya kubce mata, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinshi ya yi ba, bazai juri kallon hawayen ta ba, da sauri yayi hugging dinta, halin da take a ciki ya hana ta kwace kanta daga gare shi. Cikin shesshekar kuka ta ce,"In har da gaske kana so na kuma kana son farin cikina, to ka barni in rayu da mijina, wallahi bazan iya rayuwa da wani ɗa namiji in ba shi ba, ba dan ƙaddara ta raba ni da shi ba, babu abunda zaisa na juya mashi baya, ko dan darajar ƴar dake tsakaninmu bazan Iya rabuwa da shi ba..." kusan suman zaune yayi jin maganar ta, raba jikinta ta yi daga nashi, fuskarta ta jiƙe sharkaf da hawaye taci gaba da cewa, "Ka taimaki rayuwana, ka rufa min asiri, in har taimakon da kayi min kayi ne don Allah, toh ka haƙura da ni, mu cigaba da zumunci har ƙarshen rayuwarmu, amma maganar aure babu ita tsakanin mu..." Maganganunta sun karya mashi zuciya, wani irin zafi ne ya mamaye jikinshi, duk da sanyin A.c din motar hakan bai hana shi fitar da gumi ba. kifa kanshi ya yi kan kafaɗarta yana ambaton Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan min ha..." sambatu ya ci gaba da yi kamar ya fara zaucewa.. Tasan irin radadin karya zuciya ba kowa ke iya jurar shi ba, fargabanta kada tayi silar da Zaki zai rasa rayuwarsa amma ya zata yi? Bata da mafita da ya wuce ta lallashe shi taci gaba da bashi hakuri... "Yayana nakaina, matsayinka bazai ta6a canzawa agurina ba, bazan ta6a juya maka baya ba, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, ina mai takaici ƙin amsa bukatarka, bawai don baka kai in aureka ba, wlh kowace mace zata yi burin ta auri namiji jajirtacce nagari irinka, saboda ka haɗa duk wasu kyawawan dabi'u da halaye wanda zaisa mace ta so ka, sai dai kash Allah bai kaddara kaine mijina ba, muyi haƙuri mu rungumi kaddara, zan tayaka da addu'a Allah ya baka mace tagari, wadda zata maye maka gurbina...." cikin karyayyar murya ya furta, "Benazir bazan Iya rayuwa batare dake ba, zan roƙi Allah ya dauki raina in huta da radadin rasa ki da nayi" da sauri ta ce,"In sha Allah bazan zama silar da zaka mutu ba, sai dai in zama silar farin cikin ka na har abada, zan tayaka da addu'a Allah ya baka ikon cinye jarabawar soyayyata, Allah ya cire maka sona acikin zuciyarka..." cikin rawar murya ta ƙarashe maganar. shiru yayi bai ƙara magana ba, sai bugun zuciyarsa da take ji a jikinta. "Alfarmar da zan roƙa a gurinka, don darajar manzon Allah SAW, ka rufa min asiri yayana nakaina, kada ka faɗama Daddynka komai da ya faru tsakanin mu, saboda zai iya sanar da Uncle ɗina shi kuma zaiyi min dole ne, nasan bazaka so abunda zai 6ata raina ba..." wani irin zazza6i ne ya lullu6e jikin shi, kamar ya fasa ihu haka yake ji, So bala'ene, duk maganganunta akan kunnanshi sai dai ya kasa furta kalma. Shafa sumar kanshi tayi da tafin hannunta cikin sigar lallashi ta ci gaba da kwantar mashi da hankali maimakon yaji sauƙi a ranshi saima yaji kamar tana ƙara rura wutar sonta a zuciyar shi.. Tayi fatan ace zata iya share mashi hawayenshi ta aminta da auren shi sai dai kash bazata Iya ba, kamar yadda yake jin azabar sonta itama haka take jin azababbiyar soyayyar Taj, duk namijin da zai aure ta sai dai ya auri gangar jikinta amma ruhinta yana agurin Taj. Bayan wani lokaci, ta fito daga cikin Motar, da gudu ta nufi cikin gidan tana shiga daki bata iske Zeenatu ba, saman gado ta faɗa ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai ita. Hanky ya zaro daga front pocket dinsa ya share fuskar shi, saboda baisan daddynsa ya gano abinda ya faru da shi, saboda yayi mata alkawarin zai rufa mata asiri, ka ji masoyi na gari samun irinsu zaiyi wuya aduniyar nan. Zaki mutum ne mai haƙuri ga tawakkali. Bayan ya goge fuskar shi, Ya rufe murfin motar, ya zaro shades ya sanya ma idanunsa. Bayan tafiyar Benazir da yan mintuna Sai ga Sir Mubarak da Alhaji Musa sun fito daga garden din gidan, fuskokinsu ɗauke da fara'a da alama sun ji daɗin firar da suka yi. "Naji daɗin karramawar da aka yi mana, yanzu sai yaushe mahaifin nata zaizo Abujan ko mu zamu je can Jos dinne? cos ina son ganawa da shi game da zancen auransu" Alhaji Musa ya ce, "kada ka damu, basai kunje can ɗin ba, tun da har ni na amince da aurensu, shima zai amince ne." murmushi Sir Mubarak yayi, "Mutumina ka faranta raina, Allah ya ƙara dankon zumunci a tsakaninmu," Ya amsa mashi da ameen. "Ba zaka shiga ciki ka gaisa da madam ɗina ba" "Ban shirya haɗuwa da surukata ba, sai zuwa na gaba in sha Allah." Ya faɗa yana bin compound din da kallo yana ci gaba da yin murmushi. Fitowa Zaki ya yi daga motar, fuskar shi da fara'a ya ce, "Daddy, mun riga da mun gama magana da ita, harma ta koma ciki." Farin ciki ne ya lullu6e Sir Mubarak, "Uncle, ina godiya da damar da ka bani, Allah ya ƙara girma da ɗaukaka" ya faɗa yana kallon Alhaji musa, Murmushin gefen fuska ya sakar ma shi, "Kada ka damu, na dauke ka kamar ɗana, komai zan iya yi saboda farin cikin ka." Bayan sunyi sallama da juna, Alhaji Musa Ya koma gidan, su kuma suka shiga motar su. Kwata kwata Sir Mubarak bai lura da yanayin fusakarshi ba saboda shades din da ya sanya ya rufe idanun shi ya hana yaga eye balls dinsa waɗanda suka kada jawur tamkar garwashin wuta. "Bani labari mana my son, ya kuka yi da ita?" Shiru yayi jim kafin ya cije ya ce, "ta amince Daddy, " "Alhamdulillah, yanzu da yaushe zamu zo nema maka auren ta?" Tamkar baison furta maganar ya ce, "Ba yanzu ba daddy, mun yi da ita sai bayan na sake samun hutun aiki zan zo Nigeria sai a ɗaura mana auren" farin cikine ya cika Sir Mubarak. "Ina tayaka murna my son, ni dama nasan da wuya a samu macen da zata yi rejecting dinka, saboda kai din na musamman ne." Murmushin takaici ya ƙaƙalo kan fuskar shi ba tare da ya iya furta kalma ba, a ranshi ya riga da ya yanke shawarar barin ƙasar gobe, kwara ya nisanta kanshi da ita in ba haka ba zai iya zaucewa. *MEETING ROOM* Around ƙarfe 11 na safe hamshaƙan motoci suka fara kurɗaɗowa ta entrance gate din Isod headquarter, jigunannun gaske da matsakaicin gudu suke tururuwar shigowa a jere har kusan guda shida, kowace mota tana da tinted. A parking space motocin su ka yi parking, a hanzarce Jami'an dake sintiri su ka yi saurin ƙarasawa bakin car doors ɗin suka bubbuɗe masu kofar.... Chief Owais ne ya fito tare da Big guy, motar bayan tasu Senior agents ɗin su ne. Bayan su sai Commender james Ya fito shima tare da sauran sojojin da suka zo, kowannansu yana asanye da kakinsa.. Motar ƙarshe General ɗin sojoji ne. A gaggauce Jami'an dake kewaye da su sukayi hanzarin buga kafa tare da sara ma su cikin girmamawa suka gaishe da su kamar zasu zuƙunna masu tsabar ladabi. Basu tsaya 6ata lokaci ba, Cikin takun dattako suka nufi Secure operation center duk inda suka gifta sai ƙamshin turarensu ya gauraye da iskar gurin daddaɗan gaske, kuma duk hanyar da suka bi jiki na 6ari jami'an dake a gurin ke sara masu, sai dai kawai su ɗaga masu hannu alamar sun kar6i gaisuwar tasu. Bayan sun hau lift ta sauke su a third floor, A bakin awani Katafaren Meeting room (ɗakin taro na sirri) wanda gaba ɗayan shi a kewaye yake da zallar glass launin blue sky, wanda ke a waje bazai iya ganin na ciki ba, bayan haka bangon gilashin ɗakin soundproof ne irin wanda ke hana sauti fitowa waje, duk wani abu da za'a tattauna iya cikin ɗakin sautin ke tsayawa na waje bazai ta6a iya ji ba.. Gaba ɗaya sun nutsu suna jiran kofar ta buɗe ma su, biometric authentication ce sai ta tantance mutun kafin ta bashi iznin shiga.. Tafin hannu Chief ya ɗaura kan saitin na'urar ta yi screening din shi ta haska kwayar idanun shi kafin ƙofar ta fara sliding slowly har ta ƙarasa zuge kanta.. Walking majestically suka fara shiga ɗaya bayan ɗaya cikin katafaren Meeting room din, U.s armies din dake a tare da su sai faman jinjina kai suke saboda ƙawatuwar dakin taron yayi matuƙar burge su, cos ba su tsammaci zai kai haɗuwar meeting room ɗin su na America ba, wata irin ni'imtacciyar iskar A.c ce mai fita da ɗumi ta fara ratsa hudojin gashin jikin su irin mai sanyaya zuciyar mutun ta kwantar masa da hankali yaji shi a wata duniyar daban. Wani katafaren zunguraren table ne a tsakiyar ɗakin shape ɗinsa kamar rectangle ya ke iya jikinshi abun burgewa ne sai salƙi da daukar ido yake, ga wasu high-end Chairs kewaye da shi ga wasu haɗaɗɗun Microphones da Laptops a gaban kowace kujera, bangon dake fuskantar table ɗin wani tafkeken large screen ne. Komai na yin meeting an tanade shi a ɗakin. A tsanake kowannan su ya ja kujera ya zauna, suka fuskanci junan su, bayan sun daidaita nutsuwarsu ɗakin yayi tsit na ɗan wani lokaci, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyar shi... Abu na farko da suka tsara yi ma junansu barka da zuwa da kuma gabatarwa.. Dakin taron ya yi tsit a daidai lokacin da Chief Owais ya miƙe daga kan kujerarsa tare da tawagarsa, domin fara gabatar da kan shi cikin dattako ya fara magana yana duban kowannansu.... "Good morning everyone, i'm director Owais Sharafudeen Obinna, the Chief of Isod, With me are my team members," ya faɗa tare da yin nuni da su, "Deputy Director General Omar Musa Wadata, Chief of Operations Ahmad Hassan, Chief of Intelligence Commander Haroon, and Senior Agents Dr. Zarah Saeed, Agents Ethan Kim and Jabeer Osman." yanayin yadda yake gabatar da su ba ƙaramin burge su yayi ba komai nashi cikin aji yake yin shi, duk wanda ya ambaci sunanshi zakaga ya saki ƙayataccen murmushi kan fuskar shi.. "Muna yiwa kowa barka da zuwa" ya fada tare da komawa kan kujerarsa ya zauna suma duk suka zauna. The next person General Noah ne wani bayerabe baƙi mai jiki ya miƙe yana gyara necktie ɗinsa, "Hello everyone, nice to meet you all, I am General Noah the General Officer Commanding the Nigerian Army, It's an honor to be here today." ya faɗa fuskar shi da murmushi kafin ya koma ya zauna. Cike da kwarin gwuiwa Commender James Ya miƙe tare da tawagarsa su shidda, "Hello everyone, I am Colonel James, the U.S. Commander of the Joint Task Force. I am joined by my team.." ya faɗa tare da nuna U.s armies din dake gefen shi, Ya fara zayyana sunayen su, "Major Smith, Captain Lewis, Canal herry and Lieutenant Thompson tare da Jackson lee, munayi ma kowa barka da zuwa, mun ji daɗin gayyatar mu da ku ka yi" gaba daya sunji dadin gabatarwar da yayi bayan sun zauna ɗakin yayi shiru na ɗan wani lokaci. Kafin Chief ya numfasa calmly ya cigaba da kora jawabi, "Thank you, everyone, Let us proceed with the agenda, we are gathered here today to discuss a grave and urgent matter, already mun riga da mun san abun da ya tara mu, dangane da yaran da sojojin America suka tsinta a dajin Evil forest suka damƙa case dinsu a hannun hukumar mu ta Isode..." gaba ɗaya sun nutsu suna sauraron shi hadi da kallon fuskar shi, Ɗan dakatawa yayi kafin ya daura da cewa, "...bayan bincike da hukumarmu tayi mun samu bayanai daga gurin yaran, wato wasu miyagun matsafa ne suka ƙirƙiri wani gini a karkashin ƙasa wanda suke kira da Gidan Kurkukun kaddara! Inda suke kulle mutanan da basu ji ba basu gani ba ta ƙarfi da yaji suke killace su, anan suke aikata duk wani fasadin su.." gaba ɗaya hankalin Jami'an ya karkata akan shi cos ba komai suka sani dangane da yaran. "But that's not all, bayan ƙuntata rayuwar yaran, suna azabtar da su azaba mai raɗaɗi, ta hanyar yin amfani da karfin sihirin su gurin sarrafa su, su yi amfani da su ta ƙarfi da yaji..." "But that's still not the worst of it. They use these innocent children as sacrifices for their dark magic rituals, draining their blood and exploiting their suffering for their own gain. And, tragically, they have been known to target young girls during their period, subjecting them to... unspeakable atrocities..." kasa ƙarasa maganar yayi saboda takaici da baƙin ciki da ya mamaye zuciyar shi, tuni gumi ya fara tsartsafo mashi akan fuskar shi, haɗa ido su ka yi da commender kasancewar suna fuskantar juna, tun daga kan yanayin yadda ya ƙura mashi ido ya fahimci maganar da yayi tayi matuƙar girgiza shi, a ƙagare yake da son jin karin bayani, hatta sojojin sun yi matuƙar girgiza da jin maganar kurkukun ƙaddara. Mamakinsu wai har za'a samu yan adam da zasu iya shirya mugunta da zalunci a ƙarƙashin ƙasa na tsawon lokaci batare da asirin su ya tonu ba? "Owais, kai muke sauraro, Muna bukatar ƙarin bayani daga gurin ka." General Noah ne ya yi maganar... Cikin sanyin murya ya amsa mashi da Okay, kafin ya kunna laptop din gabanshi ya fara operating ɗinta nan take large screen ɗin dake a jikin bangon dake fuskantar su ya kawo haske kamar tv nan take ya yi displying video ɗin su Unaisah a Questioning room wato ɗakin tambayoyi, lokacin da suke bada bayani dangane da rayuwarsu agidan kurkukun ƙaddara komai da suka tattauna camera ta naɗe shi. Yayin da suka nutsu suna sauraron tattaunawar su, wata irin zufar bacin rai da tashin hankali ce ta wanke goshin su kamar ba A .c a dakin, wlh sun yi matuƙar kiɗima da jin labarin kurkukun ƙaddara da kuma irin mugunyar azabar da ake yi ma matasan yaran da basu ji ba basu gani ba... tsabar fusata da baƙin ciki da takaici yasa jikin commender ya fara tsuma yana zubda gumi. Bakomai yafi Karya masu zuciya ba face Labarin Unaizah da Majnoon duk irin dauriyar Soja saida ruwan hawaye suka cika idanuwansu kamar zasu fashe da kuka, Dunƙule hannu General Noah yayi ya dinga bugun gaban table din yana cizon lower lips dinshi, saboda tsabar fusata. Commender James kuwa da shi da tawagar shi tsantsar mamaki da al'ajabi Ya hana su ko motsa, sai faman jinjina kawunansu suke yi al'amarin ya girmi tunaninsu, su mamakinsu yadda har matsafan suka share tsawon lokaci suna aikata 6arna a ƙasa batare da an iya kama su ba, a ganinsu sakacin shuwagabannin ƙasarne da kuma waɗanda keda alhakin kula da tsaron ƙasar" Jikin kowannansu yayi mugun yin sanyi lakwas, ɗakin taron yayi tsit baka jin sautin komai saina muryoyin su Unaisah. Murya na rawa General Noah Ya furta"Owais, I can't believe what I'm hearing. Am I not dreaming? What cruelty and evil? I have never heard of such a thing before! a kasar nan wannan tashin hankalin ke faruwa batare da saninmu ba? Toh meye amfaninmu? Nayi danasanin mukamin da nake dashi tun da har ban iya kawo karshen ta'addanci a kasar nan ba, bamu ba al'umma tsaron da ya dace ba..."bai ƙare maganar ba saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare maƙoshin shi. da sauri Canal dake gefen shi ya dafa kafaɗarshi cikin sigar lallashi ya fara ƙoƙarin kwantar mashi da hankali. Cikin sanyin jiki chief Owais Ya zaro hanky daga front pocket ɗinsa Ya miƙa ma general Noah ganin yadda yake zubda gumi yatsun hannunsa na kerma Ya kar6a ya fara share hawayen dake sintiri kan kuncin sa..." "Owais lamarin Ya ɗaga hankali na! Wai dagaske ne Yana faruwa?" Commender James ne ya yi maganar tsabar ruɗin tashin hankali yasa shi jin al'amarin kamar almara. Jinjina mashi kai ya yi alamar eh ba tare da ya iya furta kalma ba.." Gaba ɗaya saida ya kunna masu videos ɗin prisoners lokacin da aka zo kan nasu Jemimah kifa kai general Noah yayi kan table ɗin kamar zai fasa ihu saboda tsananin tausayin yaran, kukan zuci yake mai azabar radadi. Babban abun takaicin da ya haddasa matsananciyar damuwa a zuciyarsu yadda matsafan suke lalata rayuwar ƙananun yaran saboda rashin imani a lokacin da suke tsaka da raɗaɗin ciwon cikin jinin al'ada. Bayan haka sun karaya da jin irin kullan da suke yi masu tun suna jarirai babu shige babu fuce, abinci sau ɗaya a rana, kaya kala ɗaya, sun ƙasƙantar da rayuwarsu sun tauye masu hakkinsu na rayuwar duniya sun maida su kamar dabbobi. "Wlh, na rantse da wanda raina yake a hannun shi, mutanan da suka ƙirƙiri gidan kurkukun ƙaddara ba zasu ƙara shaƙar numfashi cikin kwanciyar hankali ba, ɗaya daga cikin su bazai sha ba, idan har suka kuskura suka zo hannu wlh sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwayensu suka yi a duniyar nan, sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sun manta da duk wani jin daɗi da suka ta6a ji a duniyar nan..." a harzuƙe Noah ya faɗa kamar ana tunzarashi da ƙyar suka lalla6a shi ya koma ya zauna yana faman yin haki kamar wanda yasha gudu... Shiru suka yi na ɗan wani lokaci, batare da wani ya ƙara furta uffan ba, ƙoƙari suke su kwantar da hankalunsu don su samu nutsuwar faɗin ta cikin su, tashin hankali ya hana ko ruwan sanyi su kora ma maƙoshin su. Muryar Big guy ce ta katse shirun nasu "Abunda muka gano dangane da kungiyar matsafan, sadaukarwa da su ke yi, dole sai danginka, mutun ba zai iya sadaukar da wanda bai haɗa alaƙar jini da shi ba". Girgiza kai Dr. zahra ya yi, "Banma san me zance ba, mutanan nan sun san me suka taka, kuma daga ji manyan mutane ne a ƙasar nan, shiyasa suka daɗe suna aikata ta'addanci batare da asirin su ya tonu ba..." Maganar Dr. Zahra ta ɗaga hankalin Chief Owais da Big guy saboda sunsan su wanene ke ruƙe da ƙasar wato family ɗin su. "Mutane ne masu hatsarin gaske, tunkarar su ba abune mai sauƙi ba, ta ya za'ae ma mu san su wanene su balle har mu iya kawo ƙarshen su? Babban abun da ya ɗaure mana kai yaran gaba ɗaya ba su ta6a ganin fuskokinsu ba, hatta shi babban cikin su Salsabeel da ya fi su daɗewa a gidan kurkukun, kai hatta yaron da ke ruƙe da muƙamin garkuwarsu, ya rayu tsawon shekaru baisan fuskokinsu ba amma yasan Nicknames ɗin su, saidai yaƙi faɗa mana komai dangane da su, yana da taurin kai, mutunne mai wuyar sha'ani, ɗan uwansa Salsabeel ya faɗa mana cewa yafi shi sanin su wanene elders..." Big guy ya ƙare maganar yana dubansu. Ci ya ɗaura da cewa, "Har yanzu suna sarrafa shi, mawuyacin abune ya bamu haɗin kai, ɗan uwansa yace in har muka tursasa mashi zai iya ja mana gagarumar matsalar da bazamu iya magance ta ba..." Agent Jabeer Osman ya ɗaura da nashi bayanin, "Matsafan suna da kaifin basira da wayau, sun san cewa wata rana asirin su zai iya tonuwa shiyasa basu ta6a yin kuskuran da wani zai san fuskarsu a cikin yaran da suke raino ba, sun iya takun su..." ya faɗa yana jinjina kan shi. "Garkuwar nasu Yaro ne mai kafiyar tsiya, bai yarda da bare ba, yan uwansa kaɗai ya sani, amma abun ɗaure kai shine silar ɗaukar yarinyar da suka ruƙa matsayin ƙaddararsu suka kaita gidan kurkukun wanda silar kasantuwarta a gidan ya ja har suka samu shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninta da shi garkuwar nasu ta yadda su kan su suka gaza raba shi da ita, silar hakan yaja har ya ku6utar da su daga kurkukun. Big guy ne ya kora jawabin, bayan ya kai karshe Commender James Ya ce"That means Unaisah is his weak point, she can be used to control him, right?" Jinjina mashi kai chief yayi murmushin gefen fuska James ya saki, "Everything will be easy for us if we can use her to control him" "Da buƙatar mu san ya ƙarfin ikon su Yake? Menene rauninsu? da kuma Location ɗin da gidan kurkukun kaddarar Yake kafin mu fara shirye-shiryen kai masu farmaki" A cewar Captain lewis... Chief Owais yace, "Karfin ikon su, suna iya 6acewa, bayan haka harsashin bindiga baya iya fasa fatarsu, makami ko wuta basa tasiri akan su, In har ba an ta6a lafiyar idanunsu ba, wanda kuma yin hakan ba abu ne mai sauƙi ba, saboda kakin Gaints ɗin dake a jikin su garkuwa ne, makami irin namu bazai iya yi masu illa ba..." gaba ɗaya hankalinsu ya tashi da jin bayanin Chief! Tunaninsu ta ya za'ai su farmaki mutanan da basa jin bullet, ko wuta balle wani makamin irin nasu. Big guy ya ɗaura da cewa, "Bayan haka, su basa faɗa da makami sannan da bugu ɗaya suke kashe mutun." Waro idanu waje su commender suka yi gaba ɗaya sun kiɗima da jin zancen nan, "Sanin inda gidan kurkukun ƙaddara yake mutun ɗaya ne zai iya yi mana jagora kuma shi kaɗaine zai iya taimaka mana gurin sanin ta yadda zamu iya kashe su cikin sauƙi" *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440*[14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: _____________________________✍️🔥☠️🌹💋💔☠️💘😈❓❗ Ya faɗa yana ƙoƙarin taimaka mata don ta tuna. Shiru tayi fuskar ta da alamun ruɗu sam takasa tunawa, Girgiza kai ta ɗanyi"bazan iya tunawa ba, dama hoto ɗaya ne akai..." bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"zan baki lokaci, ki nutsu kiyi tunani a ina hotunan suke, cos inaji araina akwai hotunan nan biyu da babu jikin diary din, pls ki kokarta ba karamin taimako zaiyi mana ba gurin gudanar da binciken mu" jinjina mashi kai tayi"in sha Allah zanyi kokarin in tuna" rufe Diary dinsa yai tare da maida shi cikin drawer. Kiran Sallar asubahin farkone Ya karaɗe kunnuwansu, mikewa tayi da sauri tace"zan iya tafiya" ɗaga mata gira yai alamar eh.. Juyawa tayi da sauri ta nufi kofar fita, bai daina kallonta ba, har saida ta 6ace ma ganin shi. Cikin tafiyar sanɗa take taka matalar benan gudun kada wani ya ganta ta fito daga ɗakin Chief a irin wannan lokacin, kamar wata munafuka. Kwata kwata bata lura da mutun agabanta ba, sai yan waige waige takeyi kamar wuyanta zai balle Unexpectedly tayi tuntu6e da faffaɗan kirjin shi. tsabar tashin hankali kusan suman tsaye tayi tunkafin ma ta kalli fuskarshi ta riga da ta gane wanene! Ja da baya ta ɗanyi tare da sa tafin hannu ta dafe handrail ta ɗago tare da kallon shi from head to toe tayi mamakin ganin sleeping dress dinsa kalar na jikinta launi ɗaya, idanun shi manne da shade fari ya ɗaure sumar kan shi ta baya, ba karamin kyau yayi mata ba sai dai ta ji shakkar yanayin shi, ya haɗe rai kamar bai ta6a murmushi ba, Allah kadai yasan tun yaushe yake tsaye. Ido cikin ido suke kallon juna batare da kyaftawa ba tayi mamakin ganin fuskarshi a yamutse idanunshi sun dan kumbura da alamun rashin bacci atattare da su, ko me ya fito da shi a wannan lokacin? Ko dai damuwar maganarsu Salsabeel ce ta hana shi runtsawa ne"? Aranta ta ayyana hakan. Shiru babu wanda yayi magana sai sautin numfashinsu dake fita har na tsawon mintuna biyar kafin ta katse shirun nashi da faɗin"My man, me kake haryan zu ba ka yi bacci ba"? Shiru bai tanka mata ba "How long have you been here"? "Tun lokacin da kika shiga bedroom ɗinsa" waro idanu waje tayi sam ta kasa magana sai yan kame kame ta ke yi. "Me kike yi adakinsa? Har na tsawon awanni hudu"? He asked throwing her a suspicious look She could see the jealousy on his face Muryarta da inda inda tace"am..um..dama ɗazu ne da dare naje kai mashi backpack ɗin Unaizah daya bukaci yana son ganin ta saboda binciken da suke yi, shi ne da na shiga dakin na iske ya shiga toilet wanka, bansan bacci ya dauke ni ba, sai yanzu na farka..." kasa karasa maganar tayi ganin yadda ya matso kusa da ita kamar zai rufe ta da bugu tuni tasha jinin jikin ta, bakomai yake kallo ba face kayan baccin jikinta sunyi uban squeezing kamar an kwatosu daga bakin kura, zuciya da saƙe saƙe saita dinga hasaso mashi abinda ya shiga tsakaninta da chief har wani jirin 6acin rai yake gani a cikin idaninsa. Da wata irin kasalalliyar murya tamkar tame jin bacci ya furta"na yarda dake nasan ba zaki iya cin amana ta ba, amma meyasa zaki je dakinsa ki ɗauki lokaci har haka? Ki rasa inda zaki bacci sai dakinsa"? Dafe kai tayi da hannu ɗaya harta fara tunanin lallashin shi ta bashi hakuri amma da ta tuna maganar daddynta sai ta samu kwarim gwiwar cewa"Sai me Danish in nayi bacci dakinsa? Fiye da haka ma zan iyayi!" gabansa ne ya fadi cike da mamaki yake kallon ta "Ka bani kunya my man, ka rasa wa zaka butulce mawa sai Chief? Da ya Salsabeel? i heard everything daya faru tsakaninka da Chief" ta fada tana galla masa harara "Wai har elders kake ikirarin basu ta6a cutar da rayuwarka ba, kuma sune kake kallo amatsayin iyayenka! Are you crazy? Ko ka fara shaye shaye ne"? Ta fada tana kallon cikin idanunshi, babu alamun zai tanka mata, kamar ana tunzurata ta cigaba da cewa "Saboda me zaka ƙi ba su haɗin kai? Meyasa zaka rufawa Elders asiri? Ko dai kun haɗa baki da su? In ba haka ba, tayaya zaka rufa asirin miyagun da suka kaskantar da rayuwarka saboda muguwar manufarsu akanka"! Runtse idanun shi yayi gam maganarta ta daki zuciyarshi bai ta6a zaton zaiji kalaman nan daga bakin ta ba. "Hmmm, dama nasan ba zaka ce komai ba, saboda baka da gaskiya Danish! I have been suspecting you for a long time since we were in prison baka ta6a faɗamin komai dangane da kurkukun ƙaddara ba, ni ban ma ta6a sanin me ake aikatawa a cikin kurkukun ba sai da karanbani na yakaini na gani da ido, meyasa ka boye min a lokacin uhyum"? Bata jira amsar shi ba ta daura da cewa"Bayan haka ranar da Giants suka zo daukar Batool da hannunka ka miƙata, ta rayu ko ta mutu, baka damu ba, hakan na nufin kaima da sa hannunka ake akaita komai, watakil ma ɗan leƙen asirin su ne halan...." kasa karasa maganar tayi sakamakon bugun handrail da yayi da tafin hannun shi, saboda zafin maganarta dayaji, buɗe idanunshi yayi sun kada jawur ita kanta sai da taji gabanta Ya faɗi amma ta dake ta jajirce don ta harzuƙa shi tayi karfin hali cigaba da magana "Ka sha faɗamin kai garkuwane agareni, mai bani kariya, zaka iya komai dan farin cikina, Danish Ina son na tabbatar da son da kake min, shin zaka Iya sadaukar da farin cikin ka saboda nawa" ta fada batare da ta kau da ido daga kallon shi ba.. Jinjina mata kai yai alamar eh, murmushin gefen fuska ta dan saki kafin ta haɗe fuskarta tamkar bata ta6a dariya ba. "Danish, Inaso ka yi masu jagora zuwa gidan Kurkukun ƙaddara..." bata kare maganar ba Yai hanzarin furta"bazan Iya ba, pls kada ki tursasamin inyi abunda banyi niya ba..." a rude yake maganar da kakkausar murya tace"nasan zaka Iya ne shiyasa na umarce ka da kaje, saboda ni nasan wanene Man dina, kada ka bani kunya, bansan ka da tsoro ba.." "Bazan je ba, bana son duk wani abu da zaiyi silar raba mu, suma ina jiye masu haɗarin da zasu jefa rayuwarsu, Ja da Elders ba abune mai sauƙi ba, basu da karfin da zasu iya farmakarsu please understand me..." fuskarsa ayamutse yayi maganar "Danish Idan har bazaka je ba, to inaso ka sani zan yanke duk wata alaƙa dake a tsakanin mu! Saboda bazan ta6a auran ragwon namiji ba, matsoraci wanda bazai iya jefa rayuwarshi cikin hadari don ya ceci rayukan Al'umma ba ya kuma kawar da masu aikata zalunci a doron ƙasa.." waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata faɗo ƙasa. "Chief yafika jarumtaka, yana da zuciyar imani da tausayi, baisan mu ba, bai hada alakar komai damu ba, amma saboda kyakkyawar zuciyarshi burinshi Ya taimaki rayuwarmu data sauran yaran dake agidan kurkukun kaddara sannan ya kawar da miyagu a cikin al'umma bai damu daya rasa ranshi ba! a shirye yake da ya sadaukar da ranshi saboda ya ceci rayuka kaifa? Ta jefa mashi tambayar shiru yayi bai tanka mata ba "Saboda kai na hakura da burina na ganin na auri attajirin mai kuɗi mai asali ɗan babban gida, mai ilmin addini dana zamani, naji zan iya rayuwa dakai ahaka saboda kaunar da nake maka, amma meyasa kai ba zaka iya hakura da ra'ayinka akan nawa ba"?...dakyar ta ƙare maganar saboda hawayen da suka kubce mata tana mai jin takaicin tilasta masan da take kokarin yi. "Danish baka da komai, in banda kyan da Allah yayi maka, If I marry you, how will I be proud of you"? Cikin shesshekar kuka ta faɗa "Ace na auri ragon namiji mai tsoron zuwa yaki? Ko arne mara addini? Ko kuwa jahili dabaisan komai ba? Ko matsafi mai goyon bayan matsafa wurin aikata zalunci"! Kiris Ya rage Ya yanke jiki ya fadi saboda wutar bacin rai data ziyarci zuciyar sa Maganganunta sun ta6a zuciyarshi ba ƙadan ba, Yaji zafin su sosai, ita kanta ta tsorata da ganin yadda gumi ke tsastsafo ma shi, duk da tana jin tsoron kada Evil's heart dinsa ta motsa, amma dayake idanunta sun rufe burinta kawai ya amsa bukatarta. Da wata irin karyayyar murya mai cike da 6acin rai ya furta"Angel, mafarki nake ko gaske? Da kanki kike jifana da waɗannan munanan kalaman? ni Angel? Your Shield"? numfashi ya ɗan ja kamar bazai iya karasa maganar ba yace"meyasa zaki min haka? Lafin me nayi maki da cancani cin mutunci daga gareki? Angel kema Kina min kallon jahili? Mara asali? Kuma kika kira ni da matsafi"? ɗaga mashi gira tai"Hell fucking yeah, ko nayi ƙarya ne"? Kasa magana yayi, "abu ɗaya ne zakayi wanda zai wanke ka daga gareni, shine Ka cire tsoro, Ka basu haɗin kai akai farmaki gidan kurkukun kaddara, ta hakanne kaɗai zan yarda dakai in kuma har ka bijire min kaki bin Umarnina, wlh na rantse da wanda raina yake a hannunsa muddin baka bada goyon baya ba, na kwammace in mutu da ciwon sonka, akan in aure ka"! Da sauti mai karfi tayi maganar tare dakai hannu ta daki handrail.. duk abunda ke faru tsakanin su babu wanda ya sani "In kuwa har ka bari Chief yayi nasarar ruguza kurkukun ƙaddara batare da taimakonka ba, zan mallaka mashi kaina..." bata kare maganar ba sakamakon zazzafan marin daya kwasa mata wanda shi kanshi bada sanin shi ba, a karo na farko data fara jin tafin hannunsa akan fuskarta da sunan mari, wa'iyazubillah wani azababben radadi taji ya ratsa sassan jikin ta kamar an watsa mata wuta jirine Ya kwashe ta, ta tafi zata kife ƙasa cikin zafin nama Ya taro ta da hannunshi ya dawo da ita kan kirjin shi, yayi hanzarin daukarta kan kafadarshi Ya nufi bedroom dinshi da ita gudun kada wani ya riskesu a halin da suke a ciki. Yana shiga ɗakin Ya kwantar da kan gadon shi, kamar matatta, da alama suma tayi saboda azabar da taji. Hankalin shi idan yai dubu toh ya tashi, Jikinshi sai kerma yake kamar wanda sanyi Ya kama, zafin Kishi Yaja mishi bala'e.. Duk da sanyin A.c din dakin hakan bai hana gumi tsastsafo mashi kan fuskarshi ba, zukunnawa yayi daga bakin gadon yana kallon gefen fuskarta, shi kanshi Ya tsorata da ganin yadda fatar gurin tayi ja sosai, shatun fingers in shi ya fito ruɗu ruɗu. Yatsun hannayen shi Ya zuba ma Idanun shi Yana kallon su cike da danasanin marin da yayi mata, ya san yadda marin Evil giant yake da zafi, zata Iya kai Sati da radadin dafin marin a jikin ta. cike da takaici ya dinga bugun kanshi da hannayen shi kamar zai zauce saboda zafin abun da ya yi mata Tuni hawayen da suka taru cikin idanunshi suka fara Yar tseral kan kuncin shi, abu biyu ya haɗe mashi ga zafin munanan kalaman data jefe shi da su ga takaicin marin da yayi mata. Cikin karyayyar murya ya furta"ba laifina bane, ke ce kika bata min rai, gashi kinja na mareki bada son raina ba" ya faɗa tare da daura tafin hannunsa saitin inda Ya mare ta, dabara ce ta fado mashi da sauri ya saita fuskar shi saitin tata, sihiri gaskiyar mai shi, ruwan hawayensa dake ɗiɗɗiga kan fuskarta sune suka goge tabon marin da ya yi mata cikin kankanin lokaci fatar ta dawo fara sol kamar ta jinjira, numfashi Yaja tare da sauke ajiyar zuciya a hankali launin idanunsa suka dawo yadda suke. kallonta da yake yi ahaka yafi masa kwanciyar hankali akan Ya farfaɗo da ita saboda fargaban masifarta. Daga gefenta Ya raba jikin shi, Ya kwanta tare da lumshe idanun shi, bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na yau ba, tayaya zai iya shawo kan Unaisah ta fahimci abunda yake nufi"? Kwatsam yana a cikin mawuyacin halin nan ba zato ba tsammani ya tsinkayi Muryar Khala a cikin kunnanshi.. "Uhum Garkuwa Namu" A rude Ya mike zaune yana bin dakin da kallo, cikin sauri Ya share hawayen fuskarsa, jikinshi har 6ari yake garin zumudin ya sauko daga kan gadon, Hasken ɗakin shi ne Ya dauke ɗuff Duhu Ya mamaye ko'ina, bai nufi ko'ina ba sai gaban mirror Ya yaye madubin idanunshi su ka yi mashi tozali da tsohuwa Khala zaune kan armchair, Cikin shigarta ta gado fuskarta a yamutse ba annuri. Zama yayi kan Mirror chair din with respect ya gaishe da ita, da fara'a ta amsa mashi Kafin Ya nutsu Yana jiran jin me zata ce ma shi "Ina fata kun fara shirye shiryen kawo farmaki"? shiru ya yi baice mata uffan ba. Yanayin dake a kan fuskarshi ta nazarta nan take ta fahimci baida matsaya Yar dariya tayi"jikana, faɗamin ba, me ake Ciki ne"? dakyar Ya labarta mata abinda ke faruwa bai boye mata komai ba Girgiza kai tay"yaro man kaza, Har yanzu Jinin Elders ne a jikin ka, amma Alhamdulillah naji dadi da Allah Ya bani ikon ganawa dakai a karo na biyu, saboda na fahimci ka na bukatar in wayar maka dakai, in kuma yi maka karatun ta nutsu ta yadda zaka fahimci su wanene Elders da kuma dalilin dayasa suka raine ka..." aruɗe Yake kallon fuskarta... "Kasan wacece ni, ka kuma san matsayina agidan kurkukun kaddara, nafi ka sanin komai Danish, duk wani abu da suke aikatawa a tafin hannuna yake" ta faɗa tana nuna mashi tafin hannun ta. "Abu na farko da baka sani ba, Elders Mayaudara ne, Maha'inta, maciya amana, bansan ko ka san da labarin nan ba, amma inaso ka sani tun kana jinjirinka cikin tsummanka suka sace ka daga wurin iyayenka, suka rabaka da su batare da saninka ba, sannan suka sadaukar da kai zuwa gidan kurkukun ƙaddara, Ni nasan su wanene Iyayen ka, wallahi basu san kana araye ba, an yaudare su ne da sunan ka mutu...." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya zuciyarshi cike fal da ruɗanin maganarta, bazai ce tayi karya ba sai dai kokwanton da zuciyarshi keyi bazai bari ya aminta da ita ta cikin sauƙi. "Bani da isasshen lokacin da zan yi maka bayani, amma atakaice ka zauna kayi nazari Danish, kai ganau ne ba jiyau ba, kasan komai, har yau zubda jinin mutane suke yi kamar kwari, Laifin me suka yi masu? Ahaka zaka rufa masu asiri uhyum? Ita kanta yarinyar da kake gudun rabuwa da ita ba zasu kyale ta ba, wallahi in har baka bada goyon baya an kawo karshen su ba, da kai da ita sai kun salwanta, saboda suna nan suna shirin yadda zasu kashe ku.." waro idanun shi waje yayi jin abinda tace. Murmushin gefen fuska ta saki tare da jinjina mashi kai"hmm wai kana tunanin Suna kaunarka? To wallahi ko ɗaya basu ta6a kaunarka ba, sun raineka ne don biyan bukatar kansu, idan kai me hankali ne ga misali nan, Yanzu da suke ganin sunci moriyarka amfaninka ya kare kana neman tona masu asiri ba ga shi har sun ɗauke mukamin da suka baka na garkuwarsu ba, sun ba Jeremiah, kai kuma nema suke su salwantar da rayuwarka saboda kai kadaine kasan sirrinsu dakai kadai za'a iya farmakarsu...." wani irin gumin tashin hankaline Ya wanke fuskarshi, Maganar tsohuwa khala tayi matuƙar yin tasiri a zuciyar shi. Kusan sau uku Tana ambaton sunan shi bai amsa mata ba, saboda zuciyarshi ta lula duniyar tunani Har saida tayi mashi gyaran murya kafin ya dawo hayyacin sa "Ina Gabriel? Ya rayu ko ya mutu"? ya ɗanyi mamakin jin ta tambayi gabriel ko a ina ta san shi"? "Yana adakinsa, bacci yakeyi" "Masha Allah, Naji dadin jin hakan, sai dai, Yar Uwarsa daya bari agidan kurkuku tana acikin mawuyacin hali..." "Who's she? ya tambaya don sam ya manta da cewa Gabriel Yana da sister. "His twin sister Gabriella...." a takaice ta labarta mashi rashin imanin da tsohuwa inno tasa giant yayi mata, tsabar 6acin rai jikinshi har tsuma yakeyi "ta rokeni akan Tana son ganin ɗan uwanta, nayi mata alkawarin ko zan rasa raina ne in dai muna da tsawaicin kwana zan haɗa ta da ɗan uwanta" cikin rauni na murya tayi maganr tare da mikewa daga kan kujerar da take, ta haske mashi Gadon da Gabriella take akwance kamar babu rai a jikinta, sai jan numfashi take dakyar dakyar "Nayi zaton ta samu lafiya, amma wani abu ya faru jiya wanda Ya ɗaga hankalina, tana daga zuƙunna tayi aman Jini, ta dafe ciki tana faɗin Yan hanjinta suna konewa, Inaji araina Inno ce tayi mata asiri, nadai yi kokarin yi mata yan dabaruna ahaka Jikin da sauƙi amma tana bukatar taimakon gaggawa daga gare ku idan ba haka ba da wuya ta rayu.." Jikin shi yayi sanyi saboda tsantsanin tausayin yarinyar daya kama shi, yanzu ya tuna ranar farko da aka kawo su har tsohuwa Zafreen tasa aka raba su. "Danish Ahaka zaka rufa masu asiri? Shikenan babu wani wanda zai kawoma bayin Allah dauki! Haka zamu barsu su cigaba da azabtar da rayuka? Ba zamu ɗauki mataki ba"? Sam ya kasa magana saboda raunin da zuciyar shi tayi *Da wata irin kakkausar murya ta firta"YA RAGE NAKA GARKUWA, DOLE ƊAYA CIKIN BIYUN NAN YA FARU! KO DAI KA BADA GOYAN BAYA AKAWO MASU FARMAKI, KO KUMA SU SU KAWO MAKU FARMAKI SU GA BAYAN KU..."* Sau Uku ta maimaita Hakan, kafin ta cigaba da ƙarfafa mashi gwiwa daga bisani bayan ta ƙara jaddada mashi kwanan watan da zasu yi black night, ta bashi wasu muhimman bayanan da zasu amfane su, daga nan ta 6ace ma ganin shi, kifa kanshi yayi gaban mirror ɗin Zuciyar shi cike fal da damuwa, anan wani wahalallan bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi. Lokacin da Batool ta farka daga bacci taga babu Unaisah adakin, bata damu ba, bayan tayi sallar asuba, taji shiru bata dawo ba, hakan yasa ta miƙe ta fito daga dakin tafara neman ta, sai da tabi ɗakunan Yan uwansu duka ta duba taga babu Unaisah, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba,. Da sauri ta nufi ɗakin Aunty Ummunsu, tayi knocking almost 3 times, kafin ta samu Ummi ta buɗe kofar, tana miƙa hadi da yin hamma ko kayan baccin jikinta bata kaiga cire wa. "Babe, Har kin tashi"? Daga mata tayi"Aunty Ummi sister tazo nan? Na farka banganta ba" Girgiza kai Ummi tayi"Bata zo ba, kin duba ko'ina"? "Eh," ta fada da damuwa "Kada ki damu, nasan duk inda taje tana acikin gidan nan" ta faɗa tare da ruko hannunta"mu shiga daga ciki, Ki jira ni in shirya sai mu fito tare" amsa mata tayi da toh. Bayan shigar su ɗakin, Ummi ta kunna mata kallo a laplop ɗinta, kafin ta shiga bathroom don tay wanka. Nutsuwa tayi kan gadon tana kallon drama, ta shagala da kallon wayar Ummi ta fara ruri. Ɗauko wayar tayi daga kan pillow, ta duba screen ɗin bata gane me aka rubuta ba saboda bata iya karatu ba.. Da karan banin ta tayi picking call ɗin kamar yadda taga Unaisah nayi, ashe video call ne, yanayin yadda ta ruke wayar yatsan hannunta yayi hiding front camera, wanda Ya kira bazai Iya ganin ta ba, kura idanu tayi aka fuskar mutumin dake kwance cikin bathtub, ruwan kumfa ya rufe Jikin shi fuskar shi kaɗai take Iya gani yayi shiru yaki magana itama tayi shiru taƙi furta kalma zuciyarta cike fal da tunanin wanene Wannan ƙaton. "Ummi meyasa kike boye fuskarki? jira kike saina maki magana"? Muryar shi ce ta katse shirun ta.. Jin motsin buɗe kofar toilet, yasa ta danna end Call, da sauri ta mayar da wayar kan pillow ta aje. Ta yi hakanne saboda Ummi ta ta6a gargaɗinta, akan in ankira wayarta bata akusa kada tayi picking dama bata ta6a kuskuren daukar mata waya ba saboda ta fahimci bataso. Koda Ummi ta fito bata faɗa mata an kira wayar ba, bayan ta kammala shiryawa atare suka fito daga dakin. Har wuraren ƙarfe tara, basu ga Unaisah ba, gashi Har time ɗin Yin breakfast dinsu ya yi gaba ɗaya yan uwansu sun hallara a dining ita kaɗai su ke jira sun yi neman har sun gaji kuma babu wanda yai tunanin tana adakin Danish. Can cikin kunnuwanshi suka soma jiyo mashi sautin tarin ta, firgigit Ya farka da kasala Ya miƙe zaune Yana kallon ta da idanunsa waɗanda suka kumbura. A hankali ta miƙe zaune tana Hamma Wata Irin Yunwa take ji, kwata kwata bata iya tuna abun da ya faru ba, fitsari ne Ya matse, saukowa tayi daga kan gadon da sassarfa ta shige toilet ɗinshi sai da ta gama tana kokarin fitowa idanunta suka sauka akan shi, Ya zafga Uban tagumi da tafukansa kamar wanda Ya rasa gata a duniya. Nan take komai daya faru tsakanin su Ya dawo mata acikin tunaninta, gefen fuskarta daya mara ta shafa da tafin hannun ta, harara ta watsa mashi taja tsoki, kafin ta juya zata bar ɗakin. takun tafiyarne Ya fargar da shi, da sauri Ya miƙe ya shagabanta kiris Ya rage kirjinta Ya bangaji na shi "Bani bukatar Jin komai daga gare ka, bani hanya na wuce"! tana huci ta faɗa tana neman rabawa ta gefen shi don ta wuce Cikin sauri ya ruƙo Arm ɗin ta, hakan yasa ta dakata da tafiyar "I want to ask you one question." shirun da tayi ne yasa shi fahimtar jiran shi takeyi "baki tsoron ki rasa ni"? "Danish, ko da Ina jin tsoron In rasa ka, Ka tuna ranka ɗaya ne tak! da shi kadai zaka Iya taimakon dubban rayuka, ka kuma yi silar tarwatsa gang din azzalumai" "Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"? jinjina mashi kai ta yi"nafi maka kwaɗayin ka mutu a filin yaƙi, kwara mu hakura da duk wani buri da muke da shi, mu bada rayukanmu donmu taimaki bayin Allah, in sha Allah ko bamu ji dadi anan ba, zamuji acan, in ba haka ba mutanan nan bazasu ƙyalemu muyi rayuwar farin ciki ba, saboda mun san sirrin su kuma mune na farko da muka gudu daga gidan kurkukun ƙaddara, mun tona asirin su, zasu nemi hanyar kashe mu ne, ka fada min taya zamuji dadin rayuwa da fargaba a zukatan mu? Kaima fa har yanzu suna atare kai, Ka tuna abunda kayi min rannan, wata rana har kashe ni zaka iya yi ba acikin hayyacin ka ba, dan Allah ka fahimce ni, rayuwa bazata yiwu ahaka ba, kana bukatar ka zama cikakken mutun"❗ duk yadda taso ta jure saida idanunta suka cika tab da kwalla kwata kwata bataso Yaga rauninta, tafi son yasan da gaske take don ta samu ya amince. Batai aune ba, Taji Ya zube kan gwiwowinsa, A hankali ya jinginar da kanshi jikin laps dinta, ya zagayo hannayen shi kan waist ɗinta ya ruƙe ta gam, da wani irin hucin zafi numfashin shi ke fita ya riga daya sadaƙas Angel had already won him over, dole Ya mika wuya, abu ɗaya da bazai ta6a mantawa ba, munanan kalaman da ta furta mashi, tabbas Yana son wata rana ya bata mamakin da zaisa tayi danasanin abunda tayi masa. Cikin karyayyar murya tamkar ta majinyaci Ya furta"Na amince, zan basu haɗin kai, all because of you, Whatever happens to me, blame yourself .." kasa ƙarasa maganar yayi saboda raunin da zuciyar shi tayi.. Angel dake tsaye kamar gunki tana kallon sumar kanshi, ruwan hawayen ta dake gangarowa kaitsaye suka ɗiɗɗiga saman sumar kan shi, baiwar Allah duk sai taji ba daɗi, Zuciyarta ta karaya da kalaman shi,. Ta rasa farin ciki zatay da amincewarshi ko bakin ciki? ita dai tasan Ita da kwanciyar Hankali sunyi bankwana. Yatsun Hannunta na kerma Ta shafa sumar kan shi, dakyar ta banbare hannayenshi daya ruke waist ɗinta da su, ta fuce daga ɗakin, akan flooe Ya kwanta tamkar babu jini ajikin shi. maganganun mutun biyu ne sukayi tasiri akanshi, Tsohuwa Khala and his Destiny, yaci alwashin duk runtsi duk wuya sai yaga bayan Elders sannan Yana son yaje kurkukun kodan Ya haɗu da tsohuwa khala saboda yana son ta faɗa mashi su wanene iyayen shi saboda ya fahimci su kadai ne zasu iya bashi abun da akeyi mashi gori akai❓ ___________________________________________✍️ Idan muka koma Gidan baba Obie, tun da Owais Ya faɗa ma Pravin zancen tafiyar da yake so suyi tare da baba Obie, Hankalin Shi ya tashi haiƙam, gaba daya ya rasa nutsuwar shi saboda bakin ciki Ya tafi batare da ya ƙarasa aiwatar da mummunar kudirinsa ba, wunin ranar a daki yayi saboda damuwa har hajiya saratu saida ta lura da yanayin shi har tambayar shi tayi meke damun shi yace mata bai da lafiya zazza6i ke damun shi ga owais ya nemi alfarmar ya raka baba Obie lagos, baisan ya zaiyi ba yana jin nauyin yace bazai je ba Hajiya saratu tace bazaima yiwuwa ba, zatayi ma baban magana anemi wanda zai bi sa suje tunda shi ba koshin lafiya gare shi ba. kafin hajiya saratu tayi ma baba Obie magana Pravin yaji labari awurin hajjaty, a jiya daya shiga ɗakinta ya iske ta zaune tsakiyar gado tana ta kuka ya tambayeta meke damunta, nan take labarta masa baba obie ya kira ta adakinsa ya sanar da ita gobe kafin ya tafi zaisa jami'ai su maida marwa garin su gurin iyayenta, zata fi samun kulawa agurin su su kuma zasu cigaba da bata tallafi. Da jin wannan maganar, pravin ya washe baki, bai ma tsaya ya karasa jin karashen zancen ba, Ya fuce daga dakin Ya koma dakin hajiya saratu ya tambayeta shin dagaske ne za'a maida marwa garin su tace mashi eh, ay itace ma tayi ma baba obie magana amayar da ita saboda su twins tana son su dawo gidan da zama. farin cikine ya lullu6e parvin harya manta da karyar ciwon da yakeyi yace mata ay yama ji saukin zazza6in zaibi baba obie suje lagos din, tace mashi a'a gaskiya tafi son ya wartsake in yaso daga baya sai ya bishi, yasa naci akan shi dai zaije tace meyasa zai takura kansa bayan ba koshin lafiya gare shi ba, ya marairaice mata fuska da dadin baki ya shawo kanta harta amince bazata fada ma baba Obie ba. Washe gari da sassafe, jami'an da za su tafi da marwa, suka doko sallama, a lokacin hajjaty tana adakinta tare da sauran yan aikin gidan sun hadu suna shirya mata kayanta, Baiwar Allah sai kuka take yi su kansu kukan sukeyi na rabuwa da ita, bayan sun kammala shiryata Hajjaty da Abla suka daukota sauran masu aikin na abiye dasu A harabar ajiye motoci su ka iske mutanan gidan sun hallara domin yi mata bankwana. A lokacin bakowa marwa ke kallo ba face pravin dake ta kashe mata ido yana sakin wani dan iskan shu'umin murmushi duk idan ya fakaici idon mutane, marwa tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda bakin cikin zata tafi batare da ta tona asirin wanda yai mata aika aika ba.. har suka shigar da ita cikin mota bata daina gunjin kuka ba, haka ta dinga bugun window glass din motar da hannayenta kamar zata fasa shi. babu wanda ya fahimci mai marwa take nufi, gaba daya sunyi tunanin zafin rabuwa dasune yasa take yin haka, har alkawari hajjaty tayi mata akan kullum zata dinga kiranta awaya sosai ta kwantar mata da hankali, bayan sunyi mata bankwana Akan idonsu Motar ta fuce daga gidan bayin Allah sunyi kukan Rabuwa da marwa. Pravin kau ranshi fari tass Kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha Hankalin shi ya kwanta baida sauran damuwa, Ya kira zaid awaya yayi masu albishiri na tafiyar marwa, Ya kuma labarta masu maganar tafiyar da zai yi tare da baba obie, sannan Yace su dawo gida Yana son ganinsu kafin su tafi. Bayan dawowar su twins, murna awurin hajiya saratu kamar ta shekera bata gan su ba, cos tayi kewarsu ko kaɗan batai masu fadan zaman su a hotel ba, haka shima Uban saima tarairayarsu da ya ke yi. Wuraren ƙarfe shabiyu na yau, gaba daya Yan family din dake a estate din suka yi ma baba Obie rakiya zuwa Airport kamar wanda zai bar kasar, hada Owais da su Senate Lateef kowa da kowa, kamar karsu rabu da shi saboda kaunar da suke ma mahaifin su. ________________________✍️ (After One Day, Bayan kwana ɗaya) Yana tsaye gaban Dressing Mirror, har ya kammala shirin xuwa Office, jikin shi sanye da kakin shi, fuskarshi kwata kwata babu walwala tamkar bai ta6a dariya ba, saboda matsananciyar damuwar data yi mashi ƙatutu a zuciyarshi, Ga rashin isasshen baccin da baiyi ba jiya idanun shi sunyi ja sun ɗan kumbura. Har ya miƙa hannu zai ɗauki watch daya daura gaban mirror kamar ance ya ɗago da idanun shi ya kalli mirror Unexpected ba Ya hango shi tsaye ta cikin madubin Ya goya hannayen shi akan kirjin shi, Jean da t.shirt ne a jikin shi. wani irin faduwar gaba yaji saboda bai tsammaci zaiga mutun adakin shi ba! Taya akai ma ya shugo bayan kofar tana da security? Zuciyarshi ce ta bashi amsa da cewa ka manta sihirin dake ajikin shi? A sukwane ya juyo tare da kallon shi.. Yadda kasan wanda Ya ku6uto daga gidan mahaukata, Sumar kanshi ta yamutse, Fuskarsa ba annuri kamar bai ta6a dariya ba. hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, ganin yanayin da Danish Ya faɗo ɗakinsa, ya rasa meke damun shi? Yayi rashin lafiya ne? Kai daga ganinsa ba lafiya ba. muryar shi da ruɗani Ya furta"Danish? Meke damunka? Baka da lafiya ne"? Ya faɗa akagare da son jin amsar shi. Cikin sanyin murya yace"zan baku haɗin kai, and I will lead you to the Prison of Destiny, I will help you fight them" kamar amafarki yaji kalaman Danish saboda mamakin daya mammaye shi, hannu yasa ya ɗan murza kunnan shi don ya tabbatar ba makuwa yayi ba yace"dagaske kake ko wasa"? "I'm serious..." tsabar farin Ciki yasa chief zubewa kan gwiwowinsa yayi sujjada domin nuna godiyarsa ga Allah. a daren jiya ya raba dare yana yin Nafilfili akan Allah ya shiga lamarinsu ya kawo masu hanya mafi sauki da zasu farmaki Elders sai gashi cikin ikon Allah yau da safe Allah ya kar6i addu'arsa. Lokacin daya ɗago daga sujjadar tsantsar farin cikine akan fuskarshi, miƙewa yayi tare da nufar Danish yayi hugging ɗinsa tighly kamar zai maida shi cikin shi saboda faranta masa da yayi bai ta6a jin masifar kaunarsa ba irin na yau. Dagowa yayi tare da dafa kafadunsa suka fuskanci juna. "Danish, bazan Iya misalta maka farin ciki da nake a ciki ba, Ka faranta min raina, amma kai da kanka kayi ra'ayin ka bamu hadin kai ko wani ya tilasta maka? Saboda yanayin ka ya nuna kamar bada son ranka ba" Girgiza mashi kai yayi ba tare daya furta kalma ba. "Kamar baka da lafiya"? Ya kuma tambayarsa "Lafiyana lou, just ask me anything you want to hear from me, and I'll tell you." abun nema ya samu da sauri chief ya ruko hannun shi ya zaunar da shi gefen gadon shi. Kafin ya dauki wayarsa Ya kira landline din kitchen Ya isar da sakon akawo mashi breakfast ɗinsa da baiyi niyar ci ba, amma saboda suji dadin tattaunawa da danish shiyasa ya umarci akawo mashi. Ba'afi mintuna biyar ba, kuku ya shigo hannayenshi ruke da wooden tray shaƙe da kayan abinci ya aje masu kan table kafin ya fuce daga ɗakin. "Nasan kana jin yunwa, mu fara yin breakfast, kafin mu fara tattaunawar tamu" girgiza mashi kai yayi"bazan iya cin komai ba.." bai ƙare maganar ba chief ya katse shi"pls kada muyi haka dakai, ko kaɗan ne ka ci" matsa mashi yayi dakyar chief ya shawo kanshi, bayan sun kammala yin breakfast ɗin, Chief ya cire Coat dinsa Ya rage daga shi sai vest, babu zancen zuwa Office, zuwan Danish Yafi komai mahimmanci a halin yanzu. A tsakiyar gadonshi suka zauna suna fuskantar juna kamar malami da dalibinsa, sai da ya fara kunna audio recording din wayarsa, kafin ya tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan Danish *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: ________________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘 "duk da ɗan uwanka Salsabeel da sauran Yan uwanka sun fada mana komai dangane da gidan kurkukun kaddara, Ina neman ƙarin bayani daga gare ka, saboda kafi su sanin komai" A tsanake Danish ya fara kora mashi jawabi tiryan tiryan bai 6oye mashi komai ba. "Inaso Naji tayaya su ke mayar da mutun ya zama Giant ɗin su"? Ya tambaya yana kallon cikin idanun shi" Wa'iyazubillah, Tunkan Ya karasa labarta mashi, chief Ya runtse idanun shi saboda fusatar da zuciyarshi tayi tamkar zata tarwatse tsabar bacin rai, bakomai yafi karya mashi zuciya ba face irin azabtarwar da suke yi masu kafin su mayar da su Giant, matasan yaran da basu ji ba basu gani ba, abu mafi muni rashin imanin da suke sanyawa su aikata abun ya munana sosai. wani irin tsantsar tausayin Danish Ne ya ƙara ninkuwa cikin zuciyarshi, abun ya ɗaga hankalinshi matuƙa. la66anshi na rawa ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"! Ya ambaci hakan Yafi sau talatin.. Danish dake kallon shi Ya fahimci matsanancin tashin hankalin da ya ke a ciki. Numfashi ya ɗanja yayin da siraran hawaye suka fara zarya kan kuncin shi.. Cikin raunanniyar murya ya furta"I can't describe the pain I felt in my heart, it saddened me hakika sun cutar da rayuwarku, yanzu da kananun shekarun ka, ahaka suka sanyaka ka aikata duk wadannan abubuwan, Wa'iyazubillah, what kind of disaster is that?" Jinjina kai ya yi "Allah baya barin hakkin wani akan wani, akwai sakayya, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara gir6ar abun da suka shuka kafin su fuskanci mutuwar su.." Danish yayi shiru yana sauraron shi, bawan Allah Ya zama kamar saƙago jikinshi duk babu karsashi shi kadai yasan damuwar dake adabbarsa.. "ka faɗamin gaskiya dagaskene bakasan fuskokin su ba? Abun ya tsaya min araina tsawon shekara 20 tun kana jariri harka mallaki hankalinka amma baka ta6a ganin fuskar su ba"? Ya faɗa fuskarsa ayamutse yana mai dubashi. "ba sanin su ke banyi ba, nasan fuskokin su amma bazan ta6a iya shaida su ba acikin mutane, saboda suna amfani da karfin sihirinsu gurin canza kamanninsu dama halittar jikinsu shiyasa nace maka bansan fuskokin su ba" gyaɗa kai chief yayi na yarda dakai amma miye sunayen su daka san suna amfani da shi"? "Elder, shine shugaban kurkukun ƙaddara, Da iznin sa komai ke faruwa, bayan shi sai mataimakinsa Jan harshe shine mai zartawarwa, na ukun su Jan Wuya shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon Giant, na hudun su Jan Ido shike kula da bangaren safarar yaran da ake kaiwa gidan kurkukun ƙaddara.........." Tun daya fara magana Chief Ya nutsu yana sauraron shi har sai da yakai aya kafin yace mashi"Alfarmar da zan nema agurinka, kafin mu kai farmakin Inaso ka dinga bin mu zuwa headquarter donka taimaka ma Isod soldiers din mu da horon yadda zasu yi faɗa da Giants.." Amsa mashi yayi da toh sannan ya faɗa masa date din daya kamata su je, kamar yadda tsohuwa Khala ta shawarce shi da su kai farmaki adaren ranar, amma bai sanar da shi daren menene ba. Da tsantsar farin ciki Chief Ya ruƙo hannayen Danish a cikin nashi ya ruke su gam. "Bansan taya zanyi maka godiya ba, kalmomi sunyi kadan Danish, Ka faɗamin duk wani buri da kake son cimmawa, Ni kuma na maka alƙawarin In har baifi karfina ba zan cika maka shi" ya faɗa da ɗan murmushi kan fuskarshi, Danish bai furta komai ba, sai faman lumshe idanun shi yakeyi kamar gyangyaɗin bacci ya ke yi. Lura da hakan yasa Chief ya ruƙo hannayen shi Ya taimaka mashi Ya kwanta kan gadon, wani irin bacci ne mai nauyin gaske yayi awon gaba da shi. (Lallai Gadon Chief Yayi albarka, Unaisah ta kwanta, Ga Danish ma Yayi bacci akan shi😂 saura ni ma zan ɗana) _________________________________✍️ Da yammacin Ranar, Chief Ya kira Meeting din gaggawa wanda su kayi A headquarter din su tare da Manyan jami'an Isod dana Sojoji, da kuma U.s army, gaba ɗayan su suka hallara a meeting room ɗinsu, bayan Chief ya kunna masu audio ɗin daya dauka na tattaunawar shi da Danish, sunyi matuƙar yin mamakin amincewar shi, musamman big guy, sun kuma ji dadin yadda ya basu hadin kai cikin sauki batare da sun sha wahala ba, ba tare da 6ata lokaci ba, kowa Ya fara kawo shawarar shi dangane da yadda zasu kai farmakin, babu wanda bai tofa albarkacin bakin shi ba, basu suka tashi meeting din ba, har saida suka tsayar da kwanan watan da Danish Ya faɗa ma chief amatsayin Ranar da zasu kai farmaki. Tun daga ranar su ka fara shirye shiryen tafiya Yaƙi babu kama hannun yaro, basu da wani hutu, gagarimin shiri suke na musamman kuma komai nasu cikin sirri suke yin shi saboda tsaro ba don tsoro ba, sun tanadi Miyagun Makamai da zasu yi amfani da su agurun gabzawar. Tawagar Dakarun sojoji Uku ne zasu je kai farmakin, tawaga ta farko Isod Soldiers ne, bayan su sai Tawagar Sojojin Nigeria, Tawaga ta uku ta U.s Soldiers ce. a bangaren Unaisah Da Danish tun ranar da ta tursasa mashi akan ya amsa zai basu hadin kai, basu ƙara haɗuwa da juna ba, walwalarsu ta ragu, rayuwarsu ta ƙuntata saboda tsantsar damuwar da suka shiga na fargaban kada su rasa junan su, bayin Allah ta ko'ina ba sauƙi, kokari sukeyi su saba ma kansu rayuwa batare da juna ba don su saukaka ma kansu radadin son juna da suke ji a zukatansu, sai dai abun yaci tura, abun sai ya zamana kamar suna kara rura wutar son da suke ma junansu ne. Ba karamin maraicin shi takeyi ba, saboda shirya shiryen da sukeyi na tafiya yaƙi yasa baya zama gidan, atare da chief suke zuwa headquater saboda taimakon da yakeyi masu gurin ƙara wayar masu da kai game da kurkukun ƙaddara, Saida takaiga idan Chief yaje da shi headquarter din su jami'ansu ji suke da shi suna masa biyayya kamar dai chief din, wani irin farin jini gare shi, abunda yafi burge su da shi karfin da Allah yayi mashi, ga kaifin basira da Allah ya bashi, har jaraba shi sukayi ta hanyar haɗa shi da ƙarfafan Isod soldiers don suyi wrestling da shi, saboda su tabbatar idan giant basa jin bugu aikuwa sun sha ruwan mamaki, Isod Soldiers din da suka hada shi da su gurin damben su kusan hamsin saida Ya sumar da su, a hakan ma baiyi masu bugun da zasu raunata ba saboda baison yai masu illa shiko ko kwarzane ba su yi ma shi. Idan suka tafi Basu tashi dawowo gida, sai marece idan ya dawo agajiye daya samu yayi wanka ko abinci bai nema bacci yake yin awon gaba da shi, baya tashi farkawa sai lokacin da dare ya tsala kowa yayi bacci tukunna ya ke tashi yaci Dinner din shi. dauriya kawai yakeyi amma kewarta na neman tayi mashi illa, haka itama ko abincin kirki bata ci, ta rame tayi haske sosai kamar babu jini a jikinta, kullum a bedroom ɗinsu take killace kanta bata son kowa ya ra6e ta, tafi son kadaici duk da ba karamin azabtuwa takeyi ba na rashin ganin shi, tun tana 6oye abun da ke damunta idan yan uwansu suka matsa mata musamman auntyn umminsu har takaiga sun gano da kansu saboda kauracewa junan da sukayi ita da Danish, nema take ta zauce kullum ciwo ba koshin lafiya, abinci sai aunty ummi tayi mata dole take cin shi akarshe ma ta amayar da shi a toilet ba tare da sanin su ba, bacci Ya kaurace ma idanunta idan dare yayi haka zatay ta juyi kan gado rungume da pillow a kirjinta, idan abun ya isheta nafilfili take tashi tayi kuma duk akansu takeyin sallar, wani lokacin akan prayer mat baccin ya ke yin Awon gaba da ita. wannan wani irin Azababben So ne❓ Gaba daya abunda ke faruwa Taj baisani ba, saboda shima ba zaune ya ke ba, ummi har yunkurin kiranshi tayi don ta fada mashi halin da Unaisah take a ciki na rashin Lafiya amma Unaisah ta dinga rokonta akan kada ta sanar da shi saboda gudun faɗan da zaiyi mata, dakyar ta samu Ummi ta fasa kiranshi bayan ta gindaya mata sharadi akan bazata ƙara fashin cin abinci ba, tace mata eh ta amince ahaka ummi ta samu ta ɗan shawo kanta. Kamar yadda boyayyan mutumin nan Ya ba Chief shawarar su sanya manyan Malaman addini suyi masu addu'a, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tuntu6i shiekh Imam malik awaya, Ya nemi alfarmar yana son su haɗu anan gidan shi. Shiekh imam yace mashi in sha Allah zai shigo gidan. After Magbrib Bayan sun kammala yin dinner din su, ba suje sun kwanta ba, gaba ɗayan su suna zaune a falo, sunyi shiru babu mai magana acikinsu, kwata kwata babu annuri akan fuskokin su, gashi dai sun sanya kayan baccin sai dai baccin Ya kauracewa idanunsu saboda damuwar da zuciyoyin su suka shiga, babban tashin hankalinsu jin za'a tafi da Garkuwarsu, babu irin magiyar da basuyi ba akan suma atafi da su amma Salsabeel yace bazai yiwu ba, suyi hakuri su biyu sun isa suyi ma Sojojin jagora. Unaisah ta ƙwallafa rai akan son aje da ita kuma har yanzu tana akan bakanta don bazata bari su tafi da Danish batare da ita ba, abun daya daure masu kai har yau babu wanda ya faɗa masu date din da zasu je kai farmakin, duk in suka tambayi Taj ko big guy sai suce masu basu fidda lokaci ba, haka shima Danish yake fada masu, gaba daya sun yarda da maganarsu, Unaisah ce kadai hankalinta bai kwanta da zancen ƙin bayyana masu kwanan watan ba, ta fahimci sun haɗa baki ne, ranta yana bata tafiyar bazata zasuyi batare da sanin su ba shiyasa suka shirya hakan, tun da ta fahimci hakan kusan kullum sai ta addabi daddynta da Salsabeel akan su faɗa mata date ɗin amma suka ƙiya, tayi magiyar tayi rigimar duk abanza, harta hakura tadaina tambayar su, ta dai zuba ma sarautar Allah ido. Fitowa Ummi tayi daga Bedroom dinta, jikinta sanye da doguwar rigar bacci, ta zuba hannayenta cikin aljihun rigar, Daga inda take ta hango su zazzaune kan sofas na falo, sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki. Girgiza kai tayi tare da zaro waya daga aljihu ta kira Layin Boss. Bayan yayi picking suka gaisa cikin girmamawa kafin tace"yalla6ai akwai matsala fa, Yaran nan sunƙi zuwa su kwanta ga su can zaune falo sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, Ni nasan bai wuci zancen tafiyarku bane Ya ɗaga hankalin su..." ta fada fuskarta ayamutse. Muryarshi da damuwa ya furta"Ya sallam, Ummi pls ki yi koƙarin kwantar masu da hankalin su" "Wallahi ba irin lallashin da banyi masu ba, amma duk abanza" "Ummi, ki zauna dasu, yanzu zamu shigo gidan In sha Allah" "Okay, Allah ya dawo daku lafiya" "Ameen" da ga haka Su ka yi sallama. Saukowa down tayi, har ta shigo falon ba su ankara ba. Sau uku tanayi masu sallama babu wanda Ya amsa mata saboda Hankalinsu baya atare da su. Binsu da kallo ta yi, daga wanda ya ɗage kai sama, Sai wanda Ya langwa6ar da kan shi jikin Sofa, kowa dai da alkibilarsa da ya kalla Bakowane Yafi bata tausayi ba, face Unaisah, baiwar Allah ita kadai ce kwance Kan rug, yadda kasan tsumma, ta nannaɗe guri guda kamar kifin gwangwani ko motsi batasan yi. Kware murya tayi da karfi ta furta"wai bakwa ji nane"? A firgice suka zabura kowannan su Ya gyara zaman shi, kusan atare suka dube ta, In ka cire Unaisah wanda ko gizau batay ba, tana nan yadda take a kwance.. "Aunty ummi har kin bamu tsoro," hanna ce tay maganar. Haris Yace"wai har yanzu basu dawo ba"? "Aunty ummi, ko zaki kira mana su? Mun yi ma Unaisah magana tace wai batasan inda ta jefa wayar ta ba, kuma mun duba bamu ganta ba" acewar Batool.. Naufal yace"pls Aunty Ummi, nasan ba zaki rasa sanin ranar da zasu tafi ba, dan Allah ki faɗa mana wlh munyi maki alkawarin ba zamu faɗa masu mun sani ba" Bata tanka masu ba, wuri ta samu kan Sofa ta zauna, batare data kauda ido daga kallon su ba. Calmly tace"yanzu nayi waya da boss, Yace min suna akan hanyar su ta dawowa gida.." "Aunty ummi duk ba wannan ba, kawai ki fada mana ranar da zasu tafi, in ba haka ba hankalin mu bazai kwanta ba" acewar Naufal. "ku yarda dani, wlh nima bansan date din da zasu tafi ba, har tambayar boss nayi yace min basu fidda rana ba, kunsan yanayin aikinsu na jami'in sirri, kuskure kadai zai iya lalalata shirin su, yakamata mu fahimce su ko" ta fada cikin kulawa tana kallon su. Sarah tace"amma ay ba laifi bane in mun sani, zamu tayasu da addu'a ne kawai," Murmushi ummi ta ɗanyi"in zaku tayasu da addu'a ay ba dole sai kun san ranar da zasu tafi ba, wannan baya daga cikin sharuddan yin addu'a" "Look aunty ummi, kin san komai, kawai kina boye mana ne" fuska a daure Sajeed Ya faɗa. Yar dariya tayi"dama nasan zaiyi wuya ku yarda dani, in ma baku yarda ba toh kada Allah yasa ku yarda" ta fada tare da yi masu dakuwa da hannunta, tuntsirewa su Ka yi da dariya itama dariyar tayi "Kun fiye taurin kai Allah, haba mana, kusan karfe tara, Yakamata kuje ku kwanta, ga little sisters dinku nan sai gyangyadin bacci sukeyi nasan saboda ku yasa suka ki zuwa su kwanta bacci" ta fada tana nuna Azeeza da jemimah da hannunta sun manne ma juna sai gyangyadi su ke yi.. "Hmm aunty ummi kenan, Salon muje mu kwanta bacci, lokacin da zamu farka ace mana sun tafi ko? Da fa wayon mu" dariya tayi sosai maganar javed ta sanyata nishadi. Mikewa tayi ta nufi sofa din da su jemimah suke a zaune, ta dauki jemimah ta goya abayanta, kafin ta tada Azeeza tana layi ta mike kamar wadda tasha kwaya.. Ruko hannunta tayi, ta nufo bedroom dinsu dasu, sai da ta tabbatar sun kwanta bacci ta kashe masu switch din dakin tana kokarin fitowa unexpectedly Jiniyar motocin dake shigowa gidan ta karaɗe kunnuwan su. Kusan atare suka mimmiƙe tsaye suna jiran shugowar su, Unaisah ce kaɗai bata motsa ba tana nan inda take akwance.. Cikin takun sauri suka fara shigowa falon, Chief ne agaba hannun shi ruƙe dana Danish daga bayan su Shiekah Imam Malik ne, Yayin da Boss da big guy hada ma Salsabeel su ke abiye dasu, mutun biyune babu kaki a jikin su, Danish da Salsabeel, black jean da white shirts ne a jikin su kala ɗaya. Tun da Ummi taji Sallamar shiekh Imam malik, ta kasa fitowa daga dakin su Jemimah.. Kusan atare suka ci burki suna kallon su, sun yi mamakin ganin su a tsaitsaye curko curko suna ganin Danish jikinsu har 6ari yake garin saurin su karasa gare shi, daya bayan daya saida yayi huggin din su duk da agajiye yake har wani jiri jiri yake gani acikin idanun shi.. Atare suka hada baki gurin yi masu sannu da dawowa, kafin suka gaishe da shikeh imam malik cikin girmamawa.. "Sheikh, mun jima bamu ganka ba, kamanta damu" sajeed ne yai magana Tattausan murmushi shiekh imam Ya sakar masu"masha Allah na ji dadin ganinku cikin koshin lafiya, Yan jikokina, ban manta daku ba, kuna araina, duk in zanyi addu'a saina sanyaku a ciki" murmushin farin ciki suka saki.. Gaba daya hankalin Taj baya akansu, Yar shi Yake nema Yaga babu ita a cikin su, baisan awani hali take ciki ba, ya yi kewarta ba kadan ba.. "Bismillah, mu shiga ciki" big guy ne ya fada tare da nuna masu hanya Kafin su karaso, da sauri Unaisah ta mike cike da rashin kwarin jiki ta zauna. Bayan sun karaso cikin falon Prisoners gaba daya suka zauna kan rug, su Chief suka zauna kan sofas din. Kwata kwata basu lura da ita ba, ganin daddynta ya miƙe yana kokarin nufar dakinsu yasa tay karfin halin furta"sannu ku da dawowa, ya gajiyar aiki" atare suka dago suna kallon ta, haduwar idanunsu Cikin na jina yasa Danish yin saurin kawar da fuskarshi gefe daya saboda kallonta da yakeyi ba karamin karya mashi zuciya yakeyi ba, hakan da yayi ya sanyata jin wani iri a azuciyarta, gani take kamar fushi yake da ita.. "Unaisah Lafiyarki kuwa? Meke damunki"? Taj ne ya tambaya yana kallon ta.. Murmushi ta kakaro kan fuskarta"bakomai daddy, idan ma akwai abinda ke damuna, bai wuci zullumi da fargaban tafiyar ku bane" Jiki asanyaye Taj ya zauna gefenta, tare da ruko hannayenta acikin nashi. Hankalin Chief gaba daya yana akansu, shi kanshi Ta bashi tausayi ya lura da ramawar da tayi. "Pls ku bamu aron hankalin ku nan" big guy ne yai maganar, gaba daga suka dube shi, a lokacin Unaisah ta kwantar da kanta saman kafadar daddynta.. "Ina Auntyn naku take"? "Taje ta kwantarsu da su jemimah dakin su, har yanzu bata fito ba" "Okay, wani ya kira mana ita" Har mubeen Ya miƙe zaije kiranta, sai gata ta fito komawa yai ya zauna.. Tana karasowa, cikin sanyin murya tayi masu bangajiyar aiki, kafin ta dubi sheikah Imam malik kallon juna sukayi ido cikin ido daga gani sunyi kewar ganin junansu Muryarta na dan rawa ta furta"ina wuni sheikh ya fama da jama'a.." tamkar bazai amsa mata ba, ya furta Lafiya..daga haka Ya kau da idanun shi gefe ɗaya. "Bismillah, Ki zauna" big guy ne ya fada tare da nuna mata sofa, bayan ta zauna falon yayi tsit baka jin motsin komai kamar mutuwa ta gifta. Gyaran murya sheikh Imam Yayi tare da duban Chief yace"Owais, meke faru ne? naga kamar wani abu na damunku, daga ku har yaran babu mai walwala, ince dai ko lafiya"? Jinjina mashi kai chief yayi"kada ka damu, babu wani abu." ya fada tare da kallon Omar batare daya furta mashi komai ba, da ido ya fahimci me chief yake nu fi.. A tsanake ya fara labarta ma Sheikh Imam, dangane da shirye shiryen da suke yi nakai farmaki, sai dai ba komai ya faɗa masa ba, ya dai ce mashi miyagun yan'ta'addane kuma matsafa ne masu hadarin gaske zasu je kaima farmakin a kurmin daji.. Sheikh Imam Malik Ya jinjina lamarin, tun da big guy ya fara zayyana mashi, Yake ta dan jinjina kan shi alamar ya girgiza da jin zancen. Chief Owais Ya daura da cewa"baba, alfarmar da muke nema agurinku, munaso ku haɗa kai da manyan malamanmu na addini don ku yi mana addu'o'i, sannan zamu bada abun sadaka abawa mabukata da marayu suma su taya mu da addu'a." Numfasawa sheikh Imam yayi fuskar shi dauke da matsananciyar damuwa yace"Owais, Kunyi tunani mai kyau, tabbas tunkarar miyagun matsafa ba abune mai sauki ba, mutanene masu haɗarin gaske, amma ta inda kuka fi su ku kun dogarane ga Allah ne, kuma kun yi imanin shi ne zai baku nasara akan su..." ya fada yana ɗan jinjina kanshi "In sha Allah Owais, tun da har kuka nemi mu taya ku da addu'a zamuyi aiki tukuru, bi'iznillahi ba zasu ta6a cin galaba akan ku ba, saboda kyakkyawar niyar da kuke da ita na ganin kun kawar da masu aikata fasadi adoron kasa.." gaba daya sunji dadin furucin sheikh Imam malik "Zan iya sanin yaushe ne zakuyi tafiyar"? prisoners duk sun baza kunne suna jiran jin amsar da chief zai ba shi. "bamu fidda rana ba, amma a kowani lokaci zamu iya tafiya" "Okay, in sha Allah zuwa gobe da safe zan sanarwa yan uwana malamai yan team dinmu wadanda nayi imanin in har muka hada kai da su gurin yi maku addu'a babu wani mahalukin daya Isa Ya ci galaba akan ku, Sihirinsu bazai ta6a tasihiri a kanku ba, in ba wani iko na Allah ba....." Gaba ɗaya sunji dadi maganar shiekh Malik, "Amma, malam, Danish har yanzu bai musulunta ba" gaba daya suka maida hankali akanta, sunnar da kanta kasa tay, ganin irin kallon da daddynta yayi mata. A hankali suka maida duban su ga Danish, wanda ya dafe goshinsa da tafin hannun shi Salsabeel Yace"kamar kin shiga zuciyata Unaisah, wlh tun dazu nake ta zucci zuccin inyi mashi maganar shi, gaba daya mun damu da rashin addininsa" Chief yace"nima abun na damuna, ataimaka mana sheikh, a karkato mana da hankalin shi Ya kar6i shahada, kafin lokacin da zamu tafi" Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, babu wanda baiyi magana ba, akan damuwar su na rashin addinin Danish In ka cire Big guy ko kadan bai sanya baki a maganar ba. "Danish, Har yanzu baka da ra'ayin kar6ar addinin musulunci"? Shiekh imam ne ya tambaya yana kallon shi.. Gaba daya sun kagara da su ji me zai ce Sai da ya mula ya sha iska kafin ya firta"bani da ra'ayi," "Meyasa"? Shiru yayi bai tanka ma shi ba. Hakan ba karamin karya zuciyoyin su yayi ba.. "Inason Yin magana dakai, a ɗakin ka" bai yi mashi musu ba, Ya mike sheikh Imam Yabi bayan shi suka nufi second floor har dakin danish bayan sun shiga Shiekh Imam Ya kulle Kofar. Gaba daya sun kagara da su fito, fatan su Allah yasa Ya kar6i musulunci. Kasa kasa da murya Taj yace ma Unaisah"kun ci abincin daren ku"? "Eh daddy," "Pls ki daina sanya damuwa aranki, banason ganin ki a rame haka babu walwala, in har saboda tafiyar da zamuyi ne addu'arki muke bukata ba damuwarki ba.." "Toh daddy, zan daina, amma pls ka fadamin date da zaku tafi na maka alkawarin bazan sanar da kowa ba" Aranshi ya ayyana ay ko da zan fada ma kowa Unaisah bazan fada maki ba, ni nasan me zai biyo baya in kikaji, rigima zaki sa sai mun tafi da ke .. "Daddy ka yi shiru" "Unaisah, Chief Yana kallon mu, kuma shi Ya hana asanar da kowa, kuma mun yi mashi alƙawarin zamu ruke amana, kinga bai kamata in zama mutun na farko da zanci amanar shi ba, amma ki ƙara hakuri zan nemi izni daga gurin shi In har Ya amince zan sanar da ke" yamutsa fuska tayi tamkar zata sanya kuka tace"ran nan ma haka ka ce min zaka yi mi shi magana akan in biku amma baka yi masa ba" Shiru yayi bai tanka mata ba, ta fahimci wayou ya ke yi mata gashi takasa tunkarar Chief din da maganar wani irin nauyinsa ta ke ji. Agogon Hannunsa ya duba karfe goma na dare, ɗagowa yayi tare da kallon Chief, Wanda Hankalinsa ke akan Phone dinsa da yake daddanawa.. Har saida suka fara gajiya da jiran sheikah Imam, A kalla sun shafe mintuna talatin Cuf, Wasu daga cikin Prisoners har sun fara bacci. A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga sheikh Imam Ya fito daga dakin batare da Danish ba, tunkafin ya karaso su ka lura da yanayin damuwar dake akan fuskarshi, nan take suka fahimci ba ay nasara ba... Har ya zauna ba su daina kallon shi ba, yayi shiru babu walwala akan fuskarsa "Baba an dace kuwa"? Kallon chief yayi tare da girgiza mashi kai yace"ban ta6a yi ma wani ɗan adam da'awa irin wadda nayi mashi ba, kuma da wuya inyi har in gama mutun baiji imani ya shige shi koda bai musuluntan ba, amma banaso hakan Ya dame ku, kowa ni dan adam da irin tashi Jarabawar, wani har ya mutu baiyi imani da Allah ba, amma fa kada ku yanke kauna da shi, idan Allah yaso shi da rahama koda da numfashi na karshe ne in Allah ya nufa sai kuga ya furta kalmatusshahada..." bai ƙare maganar ba, Unaisah ta mike da gudu ta bar falon, gaba daya suka bita da kallo har ta 6ace ma ganin su. Suma sauran yan uwan nata, kuka suka kamayi, shiekh imam ne yayi masu nasiha mai tsuma zuciya harya samu ya shawo kan su, Kafin tafiyarshi, sai da Ya ƙarfafa masu Chief gwiwa, Ya jima agidan har wuraren karfe sha daya kafin yayi masu sallama ya tafi. Bayan tafiyar shi, Taj Yace suje su kwanta, jikin kowan nan su asanyaye suka mike ko sallama ba su yi ma su ba, kowa ya nufi ɗakin shi Ummi ma ta yi ma su sallama ta nufi nata ɗakin. (After two days da zuwan Sheikh imam, Bayan kwana biyu) Yau tunda sanyin safiya, kiran Taj ya farkar da Ummi tana tsaka da yin baccin ta, bayan ta daga sun gaisa Yace Ta shirya su Unaisah, tare da ita kanta, yana son su kawo ziyara part dinsa gurin Danejo, Ummi taji dadi dama Ta gaji da zama guri daya tafi son tana ɗan yawata. Batare da 6ata Lokaci ba, taje dakunansu ta tada su daga bacci ta isar masu da sakon Boss, duk da halin da damuwar da suke a ciki hakan bai hanasu jin dadin zasu je part din daddy taj ba, Unaisace kadai Hankalinta bai kwanta da zancen zuwansu part din daddynta, saboda ranta yana bata yau ne kwanan watan da zasu je kai farmaki, shiyasa akayi masu wayau don a kawar masu da tunanin su, aikuwa ko brush batayi ba, wankan ma ta kasa yi, A karkashin gado ta boye kanta duk don kada tabisu. "Sister! sis! Where are You, Mun fa shirya, ke kadai muke jira" muryoyin su Batool tajiyo a cikin kunnanta, shiru tayi bata amsa masu ba. Can tajiyo muryar Ummi tana fadin"Unaisah Ina kika shiga ne? Kun duba toilet ɗinta kuwa"? Ta fada tana kokarin tura kofar toilet dinta, koda Ummi ta buɗe kofar ta shiga ciki bata ga kowa ba, tayi mamakin ganin babu ita a ciki, rufe kofar tayi, tare da kallon su, sunyi tsaitsaye. "Aunty ummi ki kira daddyn nata, Muji idan taje can ɗin" acewar Sajeed Waya ta zaro daga Cikin Yar purse ɗinta, ta danna ma Taj kira almost 3 times tana kira baya shiga har ta gaji ta hakura da kiran nashi.. "Mu tafi, may be tana can din" fitowarsu keda wuya daga dakin sai ga big guy ya shigo part din su Kaitsaye idanun shi suka sauka akan Ummi, from head to toe Yabi ta da kallo, fitted gown ce a jikinta ta material launin ash colour kamar ajikinta aka dinka kayan, ta kashe daurin dankwalinta sai ɗan gyalen data yarfa a kafadarta, ko makeup batayi ba amma tayi matukar jan hankalin shi. Gaba daya sunyi mamakin kallon da big guy keyi ma Auntyn ummin nasu, ita sam bata lura ba da fara'a tace"Gm Sir, ya gajiyar aiki? dakyar ya haɗiye abunda ke ransa Yace"lafiyalou Ummi, Ina zuwa haka"? Ya tambaya kamar baisan da plan din su ba "Zamuje kai ziyara a Part din Daddyn Unaisah" murmushin gefen fuska Ya sakar ta, kafin Ya dubi prisoners. "Guys, Kunyi kyau, Muje na raka ku part din nasa" ya fada tare da nuna masu hanya, su ka yi gaba shi kuma Yajera da Ummi cikin nutsuwa suke yin tafiya. "Kinyi mini kyau, badan Ina busy ba, da na daukeki mun fita yawan buɗe ido" "Banyi zaton kana Kula mata ba.." ta fada tare da kallon shi.. Murmushin gefen fuska yayi"nima fa banajin magana, tubabbe ne, daga baya na shiryu silar Owais.." "Allah sarki Chief, Mutumin kirki, har kasa na kara jin kaunar shi saboda shi din na dabanne samun irin shi da wahala" still fuskarshi da murmushi yace"That's why I'm proud of him..." "Kasan wani abu"? Girgiza mata kai yai saikin faɗa "najima ina yi maka kallon sani, hatta muryarka tayi min kama data wani mutumina Allah, kuma kun ɗanyi kama da shi" "Zan iya sanin sunanshi"? "A'a, bana faɗi, amma ka fadamin sunan Family dinka" Yar dariya yayi yana binta da wani shu'umin kallo, kamshin turarenta duk ya kashe mashi kuzarin shi musamam Yadda qugunta ke gogar nashi ba karamin tsuma shi take ba.. "Wayau zaki min Ummi, Ke kin ki faɗamin sunan mutumin naki sai ni zan fada maki sunan family ina, bazai yiwuwa ba Allah" Murmushi tayi"na yarda kowa ya ruke nashi, amma kai ba hausa bane zalla ko? Cos kayi kama da ruwa biyu" ɗaga mata gira yayi. "Meye Full name ɗinka"? har ya buɗe baki zaiyi magana Muryar Sarah Ta katse su"Aunty Ummi, ke muke jira fa" Gaba daya sun shagala sunata fira sam sun manta da su, har sun karasa bakin kofar part din... Karasowa sukayi, big guy ya kwankwasa kofar, almost 3 times kafin suka ji motsin bude kofar ta ciki Taj Ne Ya fito Jikin shi sanye da kakinsa Yana ganinsu ya saki fuskar shi da fara'a suka gaisa da juna cikin girmamawa. "Bismillah Ku shiga, madam Tana a ciki tana jiran ku..." murmushi suka saki gaba dayan su, har sun fara shiga ciki Taj ya lura babu Angel acikin su.. Da sauri Yace"Ina ita Unaisah din"? Ummi tace"wlh bamu ganta ba, mun duba ko'ina har cikin toilet dinsu, mun yi zaton ta riga mu karasowa ne" Big guy yace"ni banma lura babu ita a cikin su ba, sai yanzu da kayi maganar nan.." fuskar Taj A yamutse Yace"ku shiga daga ciki, Bari naje na dubota" ya fada tare da kallon Big guy"muje" sai da ya fara kallon ummi Yai mata waving kafin Yabi bayan Taj, suna fitowa daga falon,yayi locking door din dama da biyu suka turo su nan. Bin falon su ka yi da kallo, jin shiru matar gidan bata fito ba, ummi tace mu zauna mu jira ta.." da sauri kowannansu ya samu guri kan Sofas suka zauna. Badajimawa ba, sautin takalamanta Ya karade kunnuwansu, kusan atare suka kalleta yayin da take saukowa down, ta dauki wankan abaya baƙa, tayi rolling akanta. jinjina kai ummi tayi aranta ta furta masha Allah. Sallama tayi masu, kamar tana jin shakkarsu, har yanzu bata saba da mutane ba.. A wayance Ummi ta mike tare da ruko hannayen Danejo Acikin nata, ta sakar mata murmushi"sannu madam, fatan mun same ku lafiya.." sai faman rarraba idanu takeyi akansu Rubina Dakyar ta firta"lafiyalou" Ummi tace"kamar baki gane su wanene ba, Ko dai Mijin naki bai fada maki zuwan mu bane" sai lokaci tayi murmushi"wlh ya fadamin, na shafa'a ne, da yake banganku tare da ƴartawa ba shiyasa na ɗan ruɗe amma yanzu nagane ku" Hugging ɗinta Ummi tayi, Kafin suka zauna kusa da juna. Da sauri Prisoners suka gaishe da ita. Da fara'a tace"tabarakallahu ahsanul khalikin, Kune Yan uwan Angel ɗin? Atare suka amsa mata da eh "Masha Allah Jinsin kyawawa Naji dadin haɗuwa daku, amma Ina Unaisah ɗin take"? Ummi tace"bata karasa shiryawa bane, shiyasa muka tafo, amma dadynta Yaje ya taho da ita" "Ke ce mommynsu ne"? Yar dariya ummi tayi"kina nufin wadda ta haife su? Daga mata kai tay, dariya ta kumayi kafin tace"kin iya zolaya, ni ina zan iya haifan wadannan har su goma sha, ko nayi maki kama da matar aure ne"? Ta tambaya tana kallonta, murmushi Danejo tayi"A'a amma dagaske baki ta6a yin aure ba"? ɗaga mata gira ummi tay, waro idanu waje Danejo tayi da mamaki tace"tab lallai, aradun Allah da a rigarmu kike da tuni Kin aje tatta6a kunne, Ko kina so ko bakisho dole ay maki aure" tuntsirewa sukayi da dariya gaba dayansu, hausarta ba karamin nishadi ta basu ba, kana jin maganarta zaka gane bafullatanar daji ce. Sai dadi takeji ganin yadda ta sanya su nishadi Maimakon ta dauko masu abunsha, sai ta kama basu labarin haɗuwar ta da Taj, har zuwanta birni da irin wautar da tadinga yi mashi, sunci dariya kamar zasuyi kuka. Ta zaƙe sai zuba takeyi masu kamar aku, Har saida Parveen ta gaji da zuba na mazurai taji shiru bata kawo masu abinci ba, gashi ko breakfast basuyi ba suka taho Hannunta dafe da cikinta tace"Aunty Danejo, mufa Yunwa muke ji, bamu ci komai ba muka taho" dan zaro ido ummi tayi tana kallonta, sarai parveen taga kallon da ummi tayi mata amma saita kawar da idonta gefe. Mikewa Danejo tayi"i'm really sorry, na cika ku da surutu, kunsan mutumin dake zama cikin kadaici in ya samu abokin fira komai ma mantawa yakeyi, kuma fa tun dazu Nayi maku girki tunda daddyn angel ya sanar dani zuwanku..." har ta fara tafiya ta juyo tare da kallon su"wa zai bini kitchen din mu dauko kayan abincin"? Da sauri Parveen da Yasmeen suka mike atare suka nufi kitchen. Ajiyar zuciya sajeed Ya sauke tare da kallon aunty umminsu yace"da farko dana ganta kyakkyawa nayi zaton miskila ce ashe ta iya dan banzan surutu" dariya ummi tayi tana fadin"Pls kadaina maganar nan kada taji ka, amma fa kamar ka shiga zuciyata, Nima nayi zaton hakan" Jemimah tace"gulma haramun, Allah In tadawo saina fada mata abunda kuka ce" Harara sajeed Ya galla mata"dako Kin ci na jaki Allah, Yar sa ido kawai" gatsina mashi hanci tayi tare da hararar shi, Ya janyo throw pillow Ya ɗan buga mata akanta. Azeeza tace"Aunty Ummi, wai itace maman angel ne? Wadda Ta gudu tabarta acikin kwamin wanka" waro idanu waje sukayi Batool tace"ke fa baki gane komai, Kin manta bafullatar dajin da Angel ta bamu labarinta? Wadda ta tsinceta acikin ruwa.." ta faɗa tana kokarin fahimtar da ita can tace"Yanzu na gane ta" ummi dake kallonsu a hankali ta sauke idanunta kan Deeja, data daura kanta saman kafadar Haris, hannunsu ruke cikin na juna tun zuwansu basuyi magana ba, aranta ta ayyana"Mun baro romeo da juliet agida, ga kuma layla da majnoon" Fitowar su Danejo daga kitchen ne Ya katse firarsu, kowan nan su ruke da farantai shake da kayan abinci , akan rug suka ajiyesu, kowannansu ya sauko kan rug din suka kewaye farantan,tun da kamshin abincin ya daki hancinsu suka fara hadiyar yawu Har sun fara Cin abincin, Batool tace"ba zamu jira Unaisah ba"? Ummi tace"nima dai naji shiru bata karaso ba"danejo tace"kada ku damu, itama na ajiye mata abincin ta, duk lokacin data karaso sai taci" daga haka ba su kara magana ba, Kowa ya maida hankali kan abincin da yake ci da alama yayi masu dadi, su parveen ba baka sai kunne, Hannu baka hannu kurya, kwata kwata bata Iya bakunta ba. Ummi har alama tayi mata da ido donta daina loma amma ta wani basar kamar bata ganta ba Danejo ko sai fadi take kuci ku koshi in ma bai isheku ba, akwai saura abincin dana aje mana.. _________________________________💔 Around ƙarfe 2 na rana da matsakaicin gudu motocin su suka kunno kai Cikin Villa din.. Su biyune zaune a back seat din Motar Chief, babu mai magana a cikin su, sunyi shiru daga gani ba karamar gajiya suka kwaso ba .. Gently yake daddana wayar hannun sa, yana kokarin kiran daddy dinsa sai ga kiran shi ya shigo, yayi mamaki kamar yasan shi yake shirin kira.. Picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnansa yana niyar yi mashi sallama miryar Mai girma sharafudden Ta katse masa hanzarinsa"Owais Inason ganinka Yanzun nan..." har saida gabansa yadan fadi da jin yanayin muryar daddyn nasa. "Am...daddy, Ina fata lafiya" bai kare maganar ba Yace"idan kazo zaka ji koma menene" daga haka Ya katse Kiran Lamarin Ya daure mashi kai! Bai ta6a jin muryar daddynsa cikin fushi irin Na yau ba, fatan shi Allah Yasa ba wani abun bane ya taso. A hankali Ya dubi Danish dake a hakimce kan seat, Ya langwa6e kan shi, Idanun shi suna a lumshe kamar ma bacci ne yayi awon gaba da shi. "My Boy, Bacci kake Yi"? Cikin kunnanshi ya tsinkayi muryar chief a wahalce ya buɗe rinannun idanun shi batare daya iya furta kalma ba. Adaidai Lokacin Motocin suka yi parking, agent Ya buɗe masu cardoors ɗin. . Atare suka fito, adai dai lokacin Taj da big guy sun fito daga motarsu.. Gaba daya suka maida Hankali akan Chief da Danish.. "Daddy Ya kira ni yanzu a mota, Yace Yana son gani na, zan tafi.." ya fada yana kallon su "Pls take care of my baby boy, he's very tired and needs your care. Ensure he bathes, eats, and then goes to bed and rests before the time is full..." yamutsa fuska Omar yayi kasa kasa da murya ya furta"sai kace wani jinjiri, kowa ma agajiye yake ay" "Magana kake yi ne"? Chief ne ya fada yana kallon shi, Girgiza kai yayi"a'a," ya fada tare da kallon Danish baima san yanayi ba, hankalin shi baya atare da su.. "Sir, Allah ya dawo mana dakai lafiya, agaishe mana da mutanan gidan" amsa masu yai da ameen Kafin Ya koma cikin motar, basu bar gurinba, har saida motar chief ta 6ace na ganin su. "Guy ina zuwa, Ka manta amanar da Chief Ya bamu"? Da zolaya ya fada yana kallon shi, a lokacin Danish Har yayi gaba abun shi.. Harara Ya galla mashi"Ya 6ata min rai, tarairayar da yakeyi masa tayi yawa sai kace wani jinjiri? Bai da magana sai ta Danish..." Yar dariya Taj yayi"wlh Omar Ka fara bani tsoro! Bana tunanin ko matar da zaka aura zaka yi kishinta makamancin wanda kakeyi ma Chief, kai dai bakaso kowa ya ra6e shi, bazan manta farkon zamana agidan nan ba, kiri kiri Ka fara jin haushina saboda kyautatamin da chief Yakeyi, naci wuyarka kafin muka saba da juna.." kayataccen murmushi Big guy yayi"ba zaka gane ba Taj, duk yadda zanyi maka bayani ba lallai ka fahimce ni ba, wlh ina tsananin kaunar chief son shi nake, fiye da yadda nakeson kowa nawa, nifa ji nake dama mu Twins ne ni da shi..." ɗan zaro idanun yayi maganar Omar ta bashi mamaki"nifa wlh ban ta6a zaton kai mataimakinsa bane saida na fara kar6ar training na isod, nayi mamki cos kamar ɗan aikinsa baka gajiya dayi masa hidima" yar dariya Big guy yai"kauna ce kawai, shima yayi fama dani akan indaina amma nakiya sbd banaso wani ya samu kusanci da shi." Murmushi Taj yayi" Allah yabar kauna tsakaninka Da Chief, Allah yasa mutuwace kadai zata rabaku" ya kar6e da cewa"ita ma mutuwar bana fata ta rabamu, nafison ta dauke mu atare ni da shi" murmushi Taj yayi bakomai ya fado mashi arai ba face ɗan uwansa kuma amininsa Ozair, har abada bazai samu abokin da zai maye masa gurbinsa ba. tuni Yaji Kwalla ta cike idanunsa a fakaice Ya share Hawayen don kada Omar Ya gani raba hanya su ka yi da Omar, Ya nufi part din chief don Ya cika Umarnin sa na ba Danish Kulawa. A lokacin Danish Har Ya shiga bathroom, Koda ya shigo bedroom dinsa bai iske shi ba, landline din kitchen ya kira ya isar da sakon su kawo ma Danish lunch dinsa. Yana katse kiran saiga kiran Ummi Ya shigo Layinsa, Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnansa. "Boss, Har yanzu Unaisah batazo ba, har jaraba kiran layinta nayi amma akashe, kuma naga kofar falon anyi locking ɗinta already.." dafe kai yayi da hannu ɗaya sam Ya sha'fa'a da batun Unaisah.. "Ummi, i'm really sorry, dazu mantawa nayi wlh, amma yanzu zan dubota" "Okay, sai naji daga gare ka" Rejecting call din yayi, Cikin sauri ya fito daga dakin Danish, Ya nufi Bedroom dinsu shigarshi Keda wuya adai dai lokacin Tana kokarin fitowa daga karkashin gado ashe tun bata fito ba, anan bacci yayi awon gaba da ita sai yanzu ta farka. Wani irin burki Yaci Yana kallonta cike da mamaki, Yarinya ta zama kamar aljana, kwata kwata bata lura da shi ba, dakyar take jan numfashi saboda zazza6in dake nema yafi karfin ta, ga wata matsiyaciyar Yunwa da take ji, Sleeping Gown ɗin jikinta tayi squeezing, Kamar yadda sumar kanta ta yamutse. Gyaran Muryar da yayi mata ne, Yasa tay firgigit Ta juyo ta fuskance shi da idanunta wadanda suka ƙankance... Wani irin faduwar gaba taji, girgiza kai taj yayi"Unaisah, Irin Rayuwar da kika zaba ma kanki kenan? Bakya jin maganata Unaisah, soyayya ta rufe maki Ido kinbi duk kin hana kanki kwnaciyar hankali" jikinta na kerma ta girgiza mashi kai batare data Iya furta kalma ba A faɗace Yace"Zoki wuce Kibi Yan uwanki, tun safe suke ta jiranki" Make mashi kafaɗa tayi cikin disasshiyar murya ta furta"daddy, ni bazan bi su ba, anan zan zauna, kuma ko wanka ma banyi ba" Ɗaure mata fuska yayi"Uban me Ya hana Kiyi wankan tun dazu? Ai kina sane kika boye karkashin gado, kega mai wayau ko"? Marairaice mashi fuska tayi"Dan Allah daddy, Ka ƙyaleni bana son zuwa, nafison na zauna nan, Ni bazan bi su ba..." Ganin Yana tunkarota gadan gadan Yasa Ta fara kokarin gudu, yana kokarin Cafkota, ta kufce mashi ta watsa da gudu Ta fuce daga dakin, Aguje yabi bayanta sai dai koda ya fito baiga gifcin ta ba, kamar walkiya ta 6ace ma ganinsa, Ranshi Ya 6aci ba kaɗan ba. ________________________________✍️💔 Fitowa yayi daga Cikin toilet, waist ɗinsa ɗaure da white towel, motsin mutun yadinga ji acikin kunnanshi, hakan yasa shi dakatawa da tafiya, slowly yake bin bedroom ɗin nasa da kallo Unexpectedly eye balls dinsa suka sauka akan Curtain dakin dake motsi, alamar akwai mutun a ciki.. Yatsun kafafunta Ya hango ta ƙasan labulen daya ɗage sai kerma suke ...farat ɗaya Ya gane itace..yayi mamakin ganinta adakinsa bayan kwanakin da suka shafe batare da sun nemi junan su ba, kome ya kawota bedroom dinsa? Aransa ya ayyana hakan. Yi yayi tamkar baisan da zamanta adakin ba, shaf shaf Ya shirya kan shi, Cikin Singlet fara da short.. kafin Ya koma gefen gadonsa Ya zauna tare da maida hankalinsa kan breakfast din da Taj yasa aka kawo mashi.. A tsanake Yake Cin abincin ta wutsiyar idanunshi Yake satar kallonta yayin da take buɗe labulen Tana leƙensa ji take kamar taje garesa tayi hugging dinsa sai dai ina wani irin shakkar tunkararshi takeji, saboda maganganun data gaggaya masa marasa dadi ita kanta bata tsammaci zai dyauki tsawon kwanaki bai kula ta ba ko kiranta awaya bayayi.. Gajiya tayi da tsayuwar, ta fito daga bayan curtain din tayi tsaye tana kallon shi. Tayi zaton baiganta ba, cikin sanyin murya tace"My man, fushi kake dani? Banza yayi da ita hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba. "Baka ga halin damuwar dana shigaba, saboda kai ko bacci bana iyayi,nasan komai ya faru laifina ne, nina ja ma kaina amma ka yi hakuri ka yafe mim, I don't know if we'll meet again, maybe this will be our last meet, duk da bansan date da zaku tafi ba, amma inaji araina yau ne, shiyasa daddyna yace mu tafi part dinsa mu zauna, ni kuma na boye saboda inason muyi bankwana kafin mu rabu..." ta faɗa idanunta cike tab da kwalla, So hana ganin laifi, duk yadda yaso Yaki jin tausayinta hakan ya gagare shi, kalamanta sun ta6a zuciyar shi. slowly ya dubeta daga kasa Ya fara kallonta, Hankalinshi ya tashi da ganin irin ramar da tayi, daga gani bata samun isasshen bacci ko bata cin abinci yadda ya kamata ga shi babu gyara a jikinta, kamar zai zubda mata kwalla saboda matsanancin tausayinta dayaji yasan duk akan shine ta shiga halin Damuwa... Da spoon din hannun shi ya nuna mata gefen shi, cike da rashin kwarin jiki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya batare da ta kauda ido daga kallon shi ba.. Cup din tea Ya dauko Ya kanga mata abakinta, ganin taki buɗe baki yasa shi furta"kisha" la66anta har kerma suke da sauri take kur6ar shi, nutsuwa yayi yana kallon throat dinta dake moving slowly. sai da ta shanye shi kaf kafin ya dauki fork duk tana kallon shi Ya nannaɗo noodles ya tura mata abaki, kamar yasan yunwa take ji, sakin jiki tayi ya dinga bata tana ci saida ya tabbatar taci ta koshi kafin ya aje spoon ɗin. Ya ruko yatsun hannayenta a cikin nashi, bata ta6a jin kunyar hada ido da shi irin na yau ba, saboda rashin mutuncin data zazzaga mashi, sunnar da kanta kasa tayi Cikin nutsastsiyar muryarsa ya ce"Ni ban ruƙe ki a zuciyata ba, baki min komai ba, amma yanzu kin min abunda banji dadin shi ba..." a rude ta kalle shi "Meyasa zaki takura kanki akaina"? Cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, nasan nina tursasa maka akan kaje aman wallahi ni kadai nasan radadin da zuciyata keyi min saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya idan ka tafi, wallahi bana so na rasaka, kuma wallahi bada son raina na gaggaya maka magana ba, nayi ne kawai don in fahimtar dakai amma kaima kasan irin son da nake maka zan iya rayu wa dakai ahaka yadda kake, koda kuwa zaka makance ne ka kuturce, ka gurguce wlh zan rayu dakai bazan ta6a canza maka ba" bata kare maganarba, ya rufe la66anta da yatsan shi, hakan yasa ta haɗiye sauran maganar da bata amayar ba.. Nutsuwa yayi yana kallon siraran hawayen dake sintiri kan kuncin ta.. "Basai kin yi min bayani ba, na fahimce ki, ina jin abun da kike ji..." lumshe idanunta tayi tana jin wani iri aranta... "Listen to me carefully, now I need your peace of mind because that way, I'll have the confidence to do everything, maganganun da kika gaya min tabbas banji dadinsu ba, amma ta wani bangaren sun taimakamin gurin Farfado da tunanina..." Ya ɗan dakata Yana duban fuskarta, sill bata bude idanunta ba. "Abu ɗaya da nakeso Kiyi min alƙawari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, and even if I don't come back, be patient, Endure a life without me" (sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba) bai ƙare maganar ba, ta katse shi cikin shesshekar kuka tace"Bazan iya daukar maka alkawarin nan ba, saboda bazan iya jurewa ba, bazan ma iya rayuwa batare dakai ba.." fuskarta ya tallabo da tafukan hannayensa"meyasa zaki karaya Unaisah? Kin manta abunda kike ce? ...girgiza kai tayi"ka manta da abunda ya wuce, ba acikin hayyacina na fada ba.." murmushi takaici yayi "Ki sama ranki zan dawo da raina da kuma Lafiya na, Nayi maki alkawarin hakan, zan kare kaina bazan bari na mutu ba.." bai kare maganarba tay saurin furta"baka ce In sha Allah ba"? Shiru yayi bai amsa mata ba. Gyada kai tayi"tunda ba zakace ba, ni zanyi maka addu'a, Allah ya kare mun kai, Allah ya dawomin dakai da ranka da lafiyarka, in sha Allah, ko bayan kun tafi zan raba dare na biyu, rabi inyi baccin awanni kadan rabin In tashi tsakar dare inyi maku addu'a...." har cikin ranshi yaji dadin maganarta, kuma, Har time din bata buɗe idanunta ba. Batai aune ba, Taji safkar Yatsunsa agaban rigarta, a firgice ta bude idanunta, wata irin kunyace ta kamata ganin Yana maida mata front buttons ɗin rigarta, sakamakon gudun da tayi ɗazu gaban rigar ya buɗe batare da ta ankara ba, tun da yafara bata abinci yake ta kokarin gyara mata rigar saidai ya kasa saboda gudun masifarta. Sunkunyar da kanta kasa tay, tasan yaga abun da take 6oye masa.. "Ranar dana dawo, what will you do when you see me?" Ya fada tare da zame yatsunsa daga gaban rigarta ya maida tafukansa kan shoulders din ta kamar kanwarsa. "I can't imagine how happy I'll be, I'll cry for joy and hug you tightly" ha6arta Ya ɗago da hannun shi"shi kadaine abunda zaki min"? Jinjina mashi kai tay, "That won't be enough for me.." "Faɗa min me kake so"? Kunnanta ya ruko tare da yi mata raɗa bai ƙare maganar ba, tay sauri toshe bakin shi da tafin hannunta, kamar wadda taji wani mugun abu, jikinta har rawa yake, His shyness enveloped her, and his sexy words made her burn with desire he also set his soul on fire, lumshe idanun shi yayi tare da ware su cikin nata, harara ta ɗan watsa mashi tare da murguɗa mashi small lips din ta.., kashe mata ido ɗaya yai tare da ɗage mata gira batasan sa'adda ta saki murmushin gefen fuska ba, wato son da takema Danish irin unconditional love ne, idan tana tare da shi takan manta da komai, kamar dai yanzu da suke atare ta manta ma da hudubar da daddyn ta yayi mata kan hada jiki da sukeyi indai tana tare dashi mantawa take da komai shi kadai take gani kuma takeso ta kasance dashi. Yana kokarin janye hannunta daga bakinshi, ba zato ba tsammani suka ji anyi knocking ɗin kofar, kallon juna sukayi wani irin faduwar gaba taji, sam ta sha'fa'a ta manta da daddynta da ke neman ta. Muryarta nawa tace"nasan baiwuci daddyna bane, ni bana so naje part dinsa nafiso Inga tafiyarku tukunna, pls kada ka fada masa ina aciki, Ni zan boye..." wani irin kallo yake binta da shi, jikinta na kerma ta mike da sauri ta boye bayan curtain Daga waje sukajiyo muryar Taj Yana fadin"Danish, Ka bude min ƙofa" mikewa yayi yaje gaban room door din Ya bude mashi. shigowa yayi fuskarshi babu walwala Yace"Unaisah tazo nan"? Danish dabai Iya karya ba, Ya nuna mashi Curtain din da hannun shi"tana ciki" cike da takaici Taj Ya nufi labulen Ya ɗage shi, wata irin gigitacciyar ƙara ta fasa kamar zata zauce, ta dinga ihu tana fadin daddy bazanje ba, Ka kyale ni, kabarni inga tafiyar ku"! ga tausayinta yanaji amma ji yake kamar ya rufeta da bugu. bai bata lokaci ba, Ya sungumeta kan kafadar shi, Ya juya ya nufi kofar dakin kuka ta dinga Yi tana mika ma Danish Hannu don Ya kawo mata dauki bawan Allah Yana ji Yana gani Taj Ya fuce da ita, baisan ko wannan zai kasance rabuwarsu Ta karshe ba, yana jiyo sautin muryarta daga waje cikin shesshekar take sambatu _"I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_ Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor..... Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin jikinta duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa.. *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘 Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor..... Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa.. Agaban kofar shiga falon part dinsa, Ya danna Password din ƙofar, ta bude kafin Ya shiga da ita ciki, adai dai Lokacin Yan uwanta sun kabbara sallar La'asar da ake ta kira, anan falo Danejo ta shimfiɗa masu prayer mat sun daidaita sahun su. Kwatsam su ka jiyo kukan Unaisah hakan Ya ɗaga hankulansu a rude suka katse sallar, gaba daya suka kai dubansu ga Taj, sun firgita da ganin yadda Ya daukota a saman kafadarshi, sai hauka ta ke yi mashi, har suna hada baki gurin tambayar Taj meya faru da Unaisah. bai bi takansu ba, Ya nufi bedroom dinshi da ita, adai dai lokacin Ummi da danejo sun sallame sallamarsu kusan atare suka mike tare da bin bayan shi. Sai dai kafin su ƙaraso Taj ya datse ƙofar ɗakin. A saman gadon shi Ya wurgar da ita gaba ɗaya ta kife kan mattress din gashin kanta ya tarwatse Yana huci Yace"shashasha, wlh kin bani kunya, wlh badan kaunar da nakeyi maki ba da yau saikin yabawa aya Zakin ta, bugun tsiya zanyi maki, wawuya kawai, ban ta6a zaton za ki min haka ba, har yanzu kina nan da kafiyarki ta kuruciya, saboda soyayya bakya ganin kowa da gashi, shi kadai kike tsoron ki rasa, na fahimci ma kinfi damuwa dashi akaina, nima fa hadani za'aje kurkukun, amma kwata kwata bata ni kike ba..."! Daƙyar ya ƙarasa maganar saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare makoshin sa. A hankali Hawaye masu ɗumi suka wanke fuskarsa. Dagowa tayi agalabaice tana kuka ta girgiza mashi kai muryarta ashake ta furta"daddy ba haka bane, ka fahimce ni, kaifa mahaifina ne, wallahi na damu dakai, har abada bazan ta6a samun madadinka ba..." bata kare maganar ba, Ya juya zai bar dakin yana huci, durowa tayi daga kan gadon da gudu ta nufe shi harya ruke handle din ƙofar, tay saurin rungumeshi ta baya ta zagayo da hannayenta kan stomach dinsa, ta maƙyalƙyleshi cikin shesshekar kuka take lallashin shi tare da bashi hakuri.. su ummi sai bugun kofar sukeyi don ya bude masu. Hakan da tayi masa ba karamin sanyaya zuciyar shi tayi ba, tuni ya sauko daga kan dokin zuciyar da ya hau, A hankali Ya ruko hannunta tare da janyo ta ya dawo da ita ta gaban shi, Yayi hugging dinta tightly, a hankali yake shafa sumar kanta, duk da halin damuwar da take a ciki sai da taji sauƙin radadin da take ji a cikin zuciyarta. cikin sanyin murya yace"komai ya wuce Unaisah, na daina fushi dake, raina ne ya 6aci amma yanzu na fahimce ki, kiyi haƙuri dukkanmu addu'arki muke bukata, amma kukan nan da kike yi da sanya damu aranki bazai ta6a canza mana kaddararmu ba, saboda addu'a ce kadai take canza kaddarar bawa, Ki yi mana addu'a Unaisah In sha Allah, zamu dawo cikin koshin lafiya.." cikin kwantar da murya yakeyi mata nasiha, su Ummi dake tsaye bakin kofar dakin sunyi shiru suna jiran ya bude masu ƙofa.. daga bisani ya ruƙo hannunta suka shiga toilet, Ya wanke mata fuskarta, suka fito daga toilet din still hannun shi ruke cikin nata suka zauna kan gadon shi.. "Daddy, bazan kara kuka ba, zanyi maku addu'a, Allah ya kare min ku ya dawo min daku lafiya" tsananin tausayinta ya kama shi damuwar shi a haka zai tafi yabarta gashi yaji alamun zazza6i a jikin ta. "Yawwa my daughter, yanzu kin share min kokwantona akanki, ni dama nasani, ƴata mai biyayya ce, zatayi abunda daddyn ta yake so.." ya faɗa tare da shafa gefen fuskarta data kumbura jawur, wlh shi kadai yasan irin yadda yakeji azuciyarshi duk in ya tuna inda zasuje da kuma yarsa tilo da yake da ita, bayason wani abu ya faru kawai dai yayi imanin komai zai faru da su mai kyau ko mara kyau mukaddari ne daga Allah, Bawa bai isa ya guje ma kaddararsa ba. "Banaso sauran Yan uwanki, su gane wani abu, pls kija baki kiyi shiru, ko da sun tambayeki me yasa kike kuka, ki fada masu wani abun daban, nasan kina da wayau basai na maki bayani ba " jinjina mashi kai tay, Rungumota yayi akan kirjinshi, ya fara janta da fira Yana tariyo mata kuruciyarta duk da halin damuwar da take aciki saida taji sanyi aranta. "Nan dakina ne, Zaki Iya zama aciki kafin mu dawo, ga toilet ki shiga kiyi wanka.." amsa mashi tayi da toh.. Sumar kanta yaci gaba da shafawa, yadda ya sabayi mata tuntana yar kankanuwarta, ahaka yake samu tayi bacci, aiko cikin sa'a yaji alamun bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke a hankali Ya kwantar da ita kan gadon, sai da yayi mata addu'o'i kafin Ya mike da baya da baya yake tafiya yana kallon ta idanunsa cike tab da kwalla. Jiki asanyaye yajuya tare da buɗe room door ɗin Ya fito su ummi na ganin shi suka kewaye shi kamar yan jarida suka tsare shi da tambayar meya faru da Unaisah... "bata Jin dadin jikinta ne, zanyi magana da dr, zai zo ya duba ta, yanzu bacci takeyi pls idan ta farka ummi ki taimaka mata tayi wanka taci abinci sannan ki sanya mata ido sosai.." basu kawo komai aransu ba, Ummi tace in sha Allah zanyi duk abunda kace. Kallon Danejo yayi"My wife, Pls ki taimaka ma Ummi, Ku kula da su, " fuskarta dauke da murmushi tace"toh, daddyn Angel, kaima ka kulamin da kanka" sallama yayi masu, kafin fitarshi daga part din a ƙalla ya shafe mintuna biyar yana tunani kafin Ya fuce..💔 _______________________________✍️ *CHIEF OWAIS* A Hankali Motar shi ta kunno kai cikin wani katafaren Resting Home na mai girma sharafudeen, tun kafin SA din dake driving dinsa yayi parking ta window glass din motar Ya hango Jami'an DSS kewaye da Courtyard din gidan dama kafin su shigo yaga sojoji tsare da gate din gidan hakanna ya dinga jin faduwar gaba. Motarsu nayin parking bai jira an bude mashi car door ba saboda sauri da kanshi ya bude ya fito, with respect Dss din dake tsaye suka sara mashi, ko kallo basu ishe shi ba Ya nufi main door din falo. Walking quickly ya haura Uptairs a gaban ƙofar katafaren Master suite na mai girma sharafudden ya ɗan dakata da yin tafiyar. "Come In" daga cikin ɗakin Ya juyo muryar daddynsa Da sallama ya shiga ciki a seating area ya hango shi A zaune kan wata katafariyar Sofa, ya dauki wankan tailored suit a jikin shi, yayin da idanun shi ke a manne da farin glasses, Hankalin sa na akan Apple Ipad din da yake pressing. Madaidaicin table din gabansa na ɗauke da cups na cofee ...Ya daura kafa daya bisa daya. Tun daga kan yanayin fuskar daddynsa Ya fahinci akwai damuwa, Karasa shigowa yayi tare da zukunnawa kan kafafuwansa agaban daddynsa Cikin girmama Ya gaishe da shi, sam babu walwala atare da shi Ya amsa mashi tare da nuna mashi sofa din dake facing dinsa "have a seat," ya fada batare daya dago ya kallesa ba. Jiki asanyaye Chief ya mike ya zauna kan sofa din, Kafin ya maida hankalinsa kan daddyn nasa yana jiran jin me zaice ma shi.. Da ipad din hannunsa ya nuna cup of coffee yace"ka ɗauka kasha naka ne" yana cikin shan coffeen Muryar daddynsa ta katse shi"Owais, dagaske ne zakuje kai Farmaki.." Ƙiris Ya rage ya saki cup din hannun shi, A matukar ruɗe yake kallon daddynsa, kwata kwata bai dago ya kalle shi ba, Still Hankalin shi na akan Ipad dinsa. "Kayi shiru baka ce komai ba, Inaso naji daga bakin ka ne"! Dakyar Ya iya furta Eh daddy, dagaske ne, amma tayaya akai ka sani? Bayan asirrince muka shirya komai ban sanar da kowa nawa ba..." Sai da yai wannan maganar mai girma sharafudden ya dago da idanunsa ya dubi cikin idanun shi. "hmm owais kenan, kada ka manta, tun kafin ka mallaki hankalinka nake sanya jami'ai su bibiyi rayuwarka, sai yanzu da ka girma ka ke tunanin zan daina sanya ido akanka"? ya tambaya yana kallon shi, lamarin ya daurewa chief kai kuma hankalinsa ya dan tashi. "Owais, meye hadinka da zuwa kai farmaki? dama shugaba Yana zuwa Yaƙi ne? "Daddy, Ni na za6i da naje..." bai kare maganarba, ya katse mashi hanzarin shi "Owais, bazan ta6a yin gangancin da zan rasaka ba, ka riga da kasan irin kaunar da nake maka, kai kadaine ɗa namiji tilo da nake da shi, taya zan zuba maka ido ka dinga yi min wasa da ranka"? A fadace ya fada. Hankalin chief ba karamin tashi yayi ba, ganin dad dinsa na nema Ya jaza mashi matsala. "Daddy, pls wanene Ya fada maka zancen zuwa kai farmakin nan! Inaso na sani.." fuskarshi ayamutse ya faɗa Girgiza kai Sharafudeen yayi"ba bu bukatar ka sani, kuma kada kayi tsammanin cikin jami'an ku ne, a'a ko ɗaya, dan leken asiri nane ya fada min" "why pls? Daddy kasan banaso!, a matsayina na jami'in sirri bai kamata ka sanya dan leken asiri yadinga bibiyar rayuwana ba, hakan ya sa6ama dokar aikina"! Ya fada rai abace "Naji Ubana Obinna, zan dakatar da ɗan leken asirin, amma ka sani, babu kai babu zuwa Kai farmaki, bada yawuna ba wlh..." saukowa yayi daga kan kujerar dayake azaune, Ya zukuna gaban daddyn nasa tare da ruƙe hannayensa acikin nashi. "Daddy, dan Allah kada ka sage min kwarin gwiwar da nake da shi, daddy kamanta ne? Kaine fa kake karfafamin gwiwa akan aikina, tun da muke zuwa kai farmaki baka ta6a dakatar dani ba sai yanzu daddy"? Ya fada fuskar shi amarairaice. "pls Kada ka hanani Yin aikin da zan taimaki rayuwar bayin Allah, in kuma kawar da mugun iri a cikin al'umma, daddy, Kasan ni mai biyayya ne agareka, ban ta6a maka gardama ba, amma dan Allah daddy, ka barni inje, na kwallafa rai akan son zuwa, Inaso naje daddy...." Tamkar zai saka mashi kuka, Ya jima baiga damuwar dayagani yanzu akan fuskar shalelensa ba, idanunshi sun kada jawur kamar jan gauta. Saidai bayajin zai yarje masa yaje don shi bai shirya rasa shi ba. "Owais, Ni bawai zan hanaku yin aikin ku ba, kawai hankalina Ya tashi da jin inda zaku je kai farmakin, saboda ɗan leƙen asirin nawa ya fadamin inda zakuje gurin matsafa ne masu hadarin gaske, inajin tsoron Su cutarmin dakai, gaskiya ban amince kaje ba, saboda kai yanzu director General ne, babu zuwa Yaƙi a aikinka, ba dole saida kai zasuyi nasara ba, kawai ka tura Yaranka suje mana"_ ya faɗa babu wasa akan fuskar shi, harya buɗe baki zai kara furta kalma ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"na gama magana Owais," ya faɗa tare Ya duba agogon hannunsa "I have a meeting, I don't want you to go anywhere, you'll spend the whole day here" yana fadan hakan yasa kai ya fuce. Dafe kanshi Yayi da tafukan hannayen shi, kamar zai fasa ihu saboda tashin hankalin da zuciyarshi ta shiga! Mamakinsa taya akai daddynsa yasan da zancen farmakin da zasu ƙaddamar? Wai har yasan gurin matsafa zasuje? Bayan haka meyasa tunda Yake zuwa Yaki bai ta6a dakatar da shi ba sai wannan karan❓ Sun riga da sun gama tsara komai, tafiya kadai ta rage masu amma daddynsa na neman Ya kwafsa mashi. Wayarsa dake acikin Trouser pocket dinsa sai ringing takeyi, yasan bai wuci na hannun damansa ne ke nemansa ba. Kifa kan shi yayi, jikin Sofa wani irin sarawan Ciwon kai Yake Ji, Ji yayi bazai Iya bari damar nan ta wuce shi ba, Shi kadai ne zai bada Umarni su tafi kai farmakin nan In har basu ji daga gare shi ba, gaba daya plan dinsu zai lalace. Yana tsaka da tunanin nan kwatsam lokaci ɗaya ya fara Jin wani irin matsanancin bacci na neman yaci karfin shi lokaci daya ya zare idanun shi cike da tashin hankali Ya ke duban Cup din da daddynsa Ya bashi Yasha cofee yunkurawa yayi da wata irin kasala Ya nufi kofar dakin Yaja handle din Yana kokarin bude ta sai dai ga mamakin shi Ya datse kofar ta waje, Kuma dole saida fingerprint ɗin daddynsa ko na mommynsa za'a iya unlocking ɗinta, tashin hankalin da ba asaka masa Rana. Gwiwowin ƙafafunsa ne suka sage, wata irin juwa ta ɗebe shi gaba ɗaya Ya kife kan floor kamar wanda yasha giya takai mashi karo bai ta6a zaton daddynsa zaiyi masa haka ba, dama saida boyayyan mutumin nan yace mashi kada ya yarda da kowa saboda kowa zai Iya cutar da shi a halin Yanzu da alamun kamshin gaskiya amaganar shi. Still bai daina kokarin mikewa ba, dakyar Ya zaro wayar shi daga trouser pocket dinsa, yanata faman kiciniyar bude idanunshi dake lumshewa, dakyar Ya lalubo layin Mommynsa Ya danna mata Call, cikin sa'a tayi picking. "My baby boy, how are you"? Kokari yake ya buɗe labbansa sai dai yayi masa nauyi, kamar harshen shi ya karye, dakyar ya iya furta"mom... myyy ... in.. Ina a resting home din dad... he locked me in his master suite...I can't open the door...I need your help...come quickly, Mommy." yana faɗan hakan wayar ta sulbe daga hannun shi. Yana jiyo muryarta da karfi take ambaton"hello Hello, Owais! Kana ji na? Me ka yi masa ne? Kalmar karshe da kunnansa su ka ji ta furta kafin kiran Ya katse, bai ƙara sanin inda kan shi Ya ke ba.. (TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASHI RANA🤔❓) __________________________________✍️ Yayin Da Chief Owais ke a garƙame Cikin ɗakin Mai girma sharafuddeen, acan Gidansa kuwa Ƙarfe biyar na maraice dai dai ba ƙari, Dankara dankaran Motocin suka fara shararowa Cikin gidan, kamar a filin daga, Wasu irin Dakarun Sojojine Majiya karfi, masu kirar samudawa, sunyi tsayuwar jarumtaka kan motocin, gaba dayansu Army Combat Uniform ne a jikin su, baka iya ganin fatar su saboda ta ko'ina sun rufe jikin su with protective gear, kowan nansu yana sanye da helmet(hular kwano) Bayan motocin sun yi Parking, cikin zafin nama sojojin dake akan motocin suka diddiro tare da bubbbuɗe Cardoors din, U.s Armies ne su ka fito kowan nan su yana a sanye da kayan yaƙi sun shirya tsaf. Ta glass door din Falo, Big guy ya hango su, shima harya kammala shirinsa cikin Isod Combat Uniform. Wata irin damuwace ta bayyana akan fuskarshi Ganin har su commender james sun karaso amma chief bai dawo daga Villa ba, Ya riga daya san halin turawa basu wasa da lokaci, kuma basa sa6a alƙawari, In har suka ji Chief bai nan Bazasu ji dadi ba, zasu ga kamar ba'a ɗauki abun da mahimmanci ba ne. Kusan sau Hamsin Yana danna mashi Call baiyi picking ba, Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, cike da takaici ya furta"Ya salam,! Chief Ina ka shiga! Pls kada ka 6ata mana shirin mu, dan Allah ka ɗaga kirana, bana so mutanan nan suga gazawar mu" ya faɗa idanun shi akan screen ɗin wayar shi dake ruƙe a hannun shi.. Layin Boss Ya danna ma Kira, bayan yayi picking Ya ce"boss, akwai matsala fa" on the other hand Taj Ya furta"meya faru Omar"? "Chief Har yanzu bai dawo ba, Ina ta kira wayarsa baya picking, gashi har tawagar su commender sun karaso..." Hankali atashe Boss Yace"Ya salam, Yanzu ya zamuyi Omar? Ko dai zaka jaraba kiran daddynsa" "Har layin daddyn nasa na kira baya shiga" "To ka jaraba kiran layin mommynsa watakil aci sa'a ta ɗaga" "Okay, zan jaraba, but pls kuma Ya kamata ku fito Yanzu" ya amsa mashi da toh kafin Ya katse kiran Yana kokarin kiran Gimbiya malikat Sai ga sako Ya shigo wayar shi da bakuwar number.. Buɗe sakon yayi tare da karantawa _Omar, I won't be able to come; inform every team of fighters. I have canceled the attack_ (Omar, bazan samu damar zuwa ba, Ka sanar da kowace tawaga ta mayaƙan, Na soke kai farmakin) Tsabar bacin rai, tuni idanun big guy sun kaɗa jajur, kamar zai fashe da kuka baima san sa'adda Ya jefar da wayar Ta fada kan sofa. jiri Yaji Yana niyar dibar shi adaddafe ya zauna kan sofa, adai dai Lokacin, yaji Motsin Buɗe kofar main Falon, zumbur Ya miƙe Yai saurin daidaita nutsuwar shi don kada su gane wani abu... ɗaya bayan ɗaya suka soma shugowa falon, dakyar Ya kakaro murmushi kan fuskarshi ya nufe su da sauri suka sara ma junansu, a mutunce suka gaisa da juna.. Cikin harshen turanci Commender James yace"Omar me kuke Jira ne? Naga banga sauran ba, Ina Chief Yake"? Fuskarshi da matsananciyar damuwa kamar mara gaskiya sam Ya kasa bude baki Ya basu amsa saboda nauyin maganar da zai furta masu gaba daya sun fahimci kamar akwai wani abu dake damun shi "Omar kayi shiru bakace komai ba, Ina Chief dinne"? Yawu mai ɗaci Ya haɗiya, adabarbarce Ya furta"Am..sir.. dama dazu ne daddynsa Ya kira awaya yana son ganin shi, Har yanzu dai bai dawo ba, shi muke jira" Yamutsa fuska Commender James Yayi da alama ranshi Ya 6aci bai dai ce komai ba. "Pls mu shuga daga ciki" ya fada tare da nuna masu Cikin falon.. Girgiza kai Commender Yayi"ba zama ya kawo mu ba, bamu da lokacin da zamu 6ata, ka kira Chief kace mashi Yazo Mu tafi" "Na kira layin shi baya shiga" "Me hakan ke nufi"? Ya tambaya yana kallon Big guy. Kafin Ya furta Kalma sai ga Boss Ya na saukowa Down daga second floor, jikinshi sanye da kakin yakinsa karasowa yayi tare da sarah masu commender suma suka sara mashi. kallon big guy yayi "Har yanzu baka same shi ba"? Jinjina mashi kai yai alamar eh.. Cike da damuwa Taj Ya dubi su commender"sir, pls ku ƙara hakuri, watakil wani Uzirinne Ya ruke shi, idan ba damuwa mu shiga daga ciki" "Taj kuyi kokari ku nemo Chief, idan ba haka ba zamu rasa damar da muke da ita" ya fada tare da kallon yan tawagarsa"mu je" bin bayan shi su ka yi a kan sofas suka zauna. ya rage saura Taj da big guy atsaye suna fuskantan juna sam sun kasa magana duk basu ji dadi ba. "chief bai kyauta mana ba, Ni dama saida raina ya bani da wuya mukai farmakin nan lafiya batare da an samu matsala ba" rai aɗan bace Yai maganar. Kafin Taj Ya furta kalma, wayar Big guy Ta fara ruri, da sauri Ya duba screen din tamkar zai fashe da kuka Ya dubi Taj"mun shiga Uku, General ne ke kira, may be Suma sun shirya tawagar su" "Omar, ka kwantar da hankalinka, In sha Allah, komai zaifi daidai, Yanzu ka ɗaga kaji me zaice maka"! Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi bayan sun gaisa General Noah Yace"Ya ake ciki ne? Na kira layin chief baiyi picking ba, Already mun shirya tawagar Sojojin mu, Umarnin shi kadai suke jira" yamutsa fuska big guy yayi, da ido Taj yake karfafa mashi gwiwa dakyar Ya furta"Sir, nan badajimawa ba, zakuji daga gare mu" daga haka su ka yi sallama. Dagowa yayi tare da kallon Taj" hmm kasan meya faru"? Girgiza kai Taj yayi "Chief ya turo min message, na boye ne saboda inajin nauyin in furta, amma chief Ya soke kai farmakin ayau" wani irin faduwa gaban Taj yaji arude Ya firta"tayaya hakan zai yiwu Omar? Anya kuwa ka karanta sakon da kyau" Mika mashi wayar yayi don ya karanta da kanshi bayan ya kammala karantawa Ya kalli Omar"ka yarda Chief ne ya rubuta sakon nan? Girgiza kai Omar yayi"ina kokwanto wlh, saboda Chief kaifi ɗayane baya sa6a alkawari in ba wani kakkauran dalilinne zai hana shi zuwa ba, bayan haka meyasa bai turo min sakon da layin shi ba"? Boss yace"uhum ni nasani ay, Allah kadai yasan meke faruwa, gaskiya ƙwara muje villa din.." Da sauri Omar Yaje ya sanar da su commender cewa zasuje Villa donsu ga meya tsayar da Chief, commender Yace suyi kokari kada a bata lokaci. gudu gudu sauri sauri suka fito daga Falon da karfi Big guy Ya kwaɗawa Jami'an dake akusa da parking space Kira Yace su buɗe masu mota, agaggauce jami'an suka bude, Taj ne ya fara shiga big guy na kokarin shiga, ba zato ba tsammani, saiga Motar Chief ta kunno kai cikin gidan da gudun gaske kamar zata tashi sama. wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Big guy ya sauke. "Boss Ga chief din nan" da sauri boss Ya fito daga motar suka nufi motar Chief, motar Na tsayawa Big guy ya buɗe mashi car door din, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, Ya jigata ba kadan ba. Huggin dinsa Yayi kamar zasu koma mutun ɗaya a kalla big guy ya sauke ajiyar zuciya yafi sau uku.. "Ka tada min hankali Owais, meyasa ka dade? Ina ta kiran layinka baya shiga" ya fada tare da dago da kan shi har saida yadanji gabanshi ya fadi ganin yanayin fuskar Chief sam babu walwala kamar wanda yayi jinya. Hatta boss Yasha jinin jikinshi da ganin yanayin nasa. "Wani abu ya faru ne? arude Ya fada Yana kallon shi Baya Jin zai iya sanar dasu abun da daddynsa yayi mashi. dakyar ya iya shanye damuwarshi Ya kakaro walwala kan fuskarshi kafin Yace"bakomai, lafiyana lou, bacci ne ya dauke ni acan, kuma na sanya wayar a silent batare da sanina ba" badan sun yarda da maganar ba suka amince. boss Yace"Sir mu shiga daga Ciki, tawagar su commender sun karaso, Suna a falo suna jiranka, bayan haka tawagar sojojin nigeria suma sun shirya, gaba dayanmu Umarninka muke jira..." numfasawa yayi kafin ya furta"okay Danish da salsabeel fa? Suma sun shirya"? "Eh, duk sun shirya" ajiyar zuciya ya sauke. Bayan sun shiga Gidan, atsaitsaye Ya gaisa da su Commender kafin Ya nufi bedroom dinsa, don Ya shirya... (Tayaya akai Chief Ya ku6uta daga tarkon da Mahaifinsa Ya ɗana masa"?) Bayan da ya kira Mommynsa awaya, ba'a fi minti biyar ba, sai ga hamshakiyar motarsu ta shigo a parking space security din dake driving dinsu yayi parking, A hanzarce Gimbiya Malikat ta fito daga mazaunin baya na motar, Jikinta sanye da tsadaddiyar Lafaya lace, hadadden shade din data sanyawa idanunta ba karamin kawatasu yayi ba, takalman kafarta kadai abun kallo ne, tana tafiya p.a ɗinta na take mata baya, wata katuwar mace karkarfa, Jikinta sanye da Suit, tasha kitson zane akanta. Cikin takun qasaita take tafiya, yanayin fuskarta sam babu walwala, saboda Hankalin ta ya tashi da jin abunda Owais Ya fada mata. Kaitsaye suka Nufi master suite din Mai girma sharafudden. Abakin kofar Room ɗin suka dakata da yin tafiya, Gently ta ɗaura Thumb ɗinta akan Biometric scanner ɗin dake jikin handle din kofar, nan take kofar tayi Unclocking ɗin kanta... Juyawa tayi tare da kallon P.a ɗinta, abunka ga masu Izza a jini, da ido tayi mata alamar ta tsaya anan, with respect ta amsa mata da okay ma'am.. shigarta keda wuya kofar tayi locking kanta.. Ɗakin tabi da kallo, kwatsam idanunta suka hango mata shi kwance kan floor kamar matacce kwata kwata baya motsi. Numfashin shi ne kadai ke fita.. Hankalinta yayi mugun tashi, a sukwane ta zare shade din dake akan fuskarta..cikin sauri ta nufe shi ta zukunna agabanshi ta sanya hannayenta biyu ta dago da kanshi ta kwantar saman laps ɗinta. shasshafa fuskarshi tayi muryarta na rawa ta furta"My son! Lafiya ka kwanta kan floor kamar wani mara gata? Meke damunka ne? Owais kana Ji na kuwa? tariyo maganar da sukayi awaya tayi lokaci ɗaya zuciyarta, ta raya mata ba baccin lafiya yakeyi ba, saboda yanayinsa yafi kama da na wanda yasha kwayar maye. a hankali ta kwantar da kan nashi kan floor, ta mike tare da kai idonta kan coffee table din dake a seating area. Cups ta gani biyu akai, matsawa tayi gaban table din, ta dudduba cups ɗin, ita dai bata ga komai ba har ta juya zata koma wurinshi kwatsam idonta ya hango mata packet na pills daga gefen table din kiris ya rage ya shige karkashin sa. Yatsun hannunta na kerma ta dauki packet din ta soma karanta rubutun dake a jikin shi zaro ido tayi saboda ta gane sleeping pills ne. Hankalinta ya tashi ba kadan ba! tamkar zata fashe da kuka ta furta"why Owais! Why! Me ya hadaka da maganin bacci mai hadarin gaske.." juyawa tayi tare da kallon shi bawan Allah baimasan inda kanshi yake ba.. fitowa tayi daga dakin hannunta ruke da fakitin, P.a na ganinta tay saurin russina mata.. "Duba min maganin nan" ta fada tare da mika mata roban "Inaso akawo min antidote dinsa Yanzun nan.." Jinjina mata kai p.a tay, tare da juyowa ta bar gurin, tana atsaye tana jiran ta, badajimawa ba saigata ta dawo hannunta ruke da Injection ta miƙa mata. Tasa hannu ta kar6a, tare da juyowa ta koma ɗakin, kasancewar tana da ilmin abun bata sha wahala ba, bayan ta kamma yi mashi allurar. Zama tayi gefen shi, tana kallon shi, zuciyarta cike fal da tunin meya faru tsakanin shi da mahaifin shi.. Tsawon mintuna ashirin, Ya fara zubda gumi a jikin shi, kamar an yayyafa mashi ruwa, yatsun hannunsa dana kafafunsa suka fara kerma kamar wanda sanyi ya kama, ajiyar zuciya ta fara saki ganin ya fara dawowa hayyacin shi...a hankali ya bude idanunshi wadanda suka kaɗa jawur ya kurawa ceilling din dakin ido kamar ya manta da abunda ya faru. "Owais," jin muryar Mommynasa yasa shi saurin kai idonshi gare ta..wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya tattara karfin jikinshi Ya samu ya mike tare da matsawa kusa da ita, cikin sauri ta rungumoshi kan kirjinta, hannunta daya acikin sumar kan shi.. "My son, are you Okay? ta fada cikin kulawa. Jinjina mata kai yai alamar eh, bata kara tanka mashi ba, yayi shiru yana faman jan numfashi har saida Ya ƙarasa wartsakewa Ya dawo hayyacin shi kafin ta tambayeshi dangane da kwayar maganin baccin daya sha! "Kai nake sauraro Owais, ka daga min hankalina, kuma meya hadaka da daddynka, dayaja harya kulle ka adakin sa"? ta fada tana kallon fuskarshi, still bai dago daga jikinta ba. Cikin disasshiyar murya ya furta"mommy, zanyi maki bayani, amma ba yanzu ba, pls ki kwantar da hankalinki, ba abunda ya faru tsakanina da shi..." fuskarta ayamutse tace"meyasa bazaka fadamin yanzu ba"? A gajiye ya girgiza kanshi"mommy, tafiya zanyi, abokan aikina suna jira na, I don't want to lose the opportunity I have, In har banje ba, all our plan will be ruined" gefen fuskarshi ta shafa da hannunta"shikenan, Na fahimce ka, bazan matsa maka ba, nasan yanayin aikinku, amma pls, ka kula mun da kanka Owais..." lumshe idanunshi yayi tare da jinjina mata kai, ya ruko hannayenta biyu acikin nashi"mommy, Ina barar addu'arki, nasan kinayi min, amma kwanakin nan ina bukatar ƙari akan wadda kike yi min, bama ni kadai ba, hada abokan aikina .." cikin sanyin murya tace"in sha Allah Owais, zanyi maka addu'a, ay bana mantawa dakai, amma kayi ma daddynka magana akan yayi maka addu'a ? girgiza kai yayi"a'a mommy, nafi bukatar taki, in har kikayi min kamar yayi minne, and pls, bana so daddy yasan kin bude min dakin nan, kiyi min hanyar da zan fita daga gidan nan batare da wani ya ganni ba..." ta ɗan rude da jin abunda Yace amma sai bata kawo komai aranta ba, saboda ta yarda da ɗan nata da kanta tayi mashi hanyar barin gidan batare da security officers din da mahaifinsa yasa tsaron gidan sun tuhume su ba. Kunji yadda akai Chief Ya ku6uta daga tarkon daddynsa ✍️ Fitowar Chief daga Part dinsa tayi daidai da fitowar Danish Da Salsabeel. Gaba ɗaya Hankulan U.s Army din Ya dawo kan shi, yayi matuƙar jan hankalinsu yadda kasan Diamond a sararin samaniya saboda kyan da yayi Cikin shigar Isod Combat Uniform, Ya rufe fuskar shi da Mask, hadaddiyar sumar kan shi ya daure ta da head ties jelar gashin ta sauka agadon bayansa. Ƙafafuwansa suna asanye da wasu hadaddun Combat boots ko a kakin yakin bakomai ya sanya ba babu protective gear saboda baya bukatar su. har ya sauko down basu daina bin shi da kallo ba, tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin Matashin sarauyin da kakin Yaki su kayi ma kyau irin Danish ba ya fita daban acikin su, ya fito a suffar jarumtakarsa, sadaukin namiji mai ji da karfin sa.. Kallo ɗaya big guy yai masa ya kau da kai gefe, taj kuwa sai da yadan sha jinin jikin shi aranshi ya ayyana ba mace ba ko namiji ya kallesa sai ya burge shi, ina ma amfanin kyau irin nashi ba ilmi wannan ay masifa ne bakaramar 6arna zaiyi ba, a ganinsa kyawun shi ne ke ruɗar Unaisah da kuma tausayinsa shiyasa ta ke nema ta zauce akan son shi. A hankalin Salsabeel Ya ruko hannun Danish acikin nashi. Bayan sun karasa saukowa down U.s Armies suka fara zuzuta kyawun da kakin su ka yi mashi hatta chief sai da ya yaba, gaba daya suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan. abun daya 6ata ma big guy rai Yana niyar ya shiga Motar da chief zai hau Chief ya ja hannun Danish suka shiga motar, Yaji zafin hakan sai dai Ya hakura Ya shiga Motarsu Taj. bayan us armies din sun shisshiga motocinsu, da gudun gaske suka fuce daga Estate din saboda Lokaci. A cikin Mota Chief Ya kira Sheikha Mujeeda, Aransa yana Allah Allah ta ɗaga Yasan ba ta daga kira in ba an fara tura mata sakon neman izni ba amma cikin ikon Allah tayi picking yadan yi mamaki amma da ya tuna maganar da sukai akan Danish sai ya gane dalilin dayasa ta daga kiransa bayan sun gaisa yace mata ɗanta na barar addu'arta zasu yi wani aiki mai hadarin gaske. yanayin muryarta da damuwa tace In sha Allah zanyi mashi addu'a, In yana kusa ka bashi wayar" mika ma danish wayar yayi baisan wanene ba Ya kar6a ya kara a kunne yayi shiru baice komai ba har saida gimbiya Mujeedat ta furta"My Son kana lafiya"? arude Ya kalli Chief tare da tambayar who is She? Murmushi Chief yai tare da cewa"matar daddy minister" nan take ya tariyo lokacin farko daya fara ganinta, bazai ta6a manta yadda ta cire mask din fuskarshi ba ta zuba mashi kyawawan idanunta. Cikin sanyin murya ya gaishe da ita with respect, ta amsa mashi kafin tace"chief ya fada min zakuyi wani aiki mai hadarin gaske, In sha Allah zan tayaku addu'a..." yace mata ya gode, har tana zolayar shi da cewa tasan da daddy minister ne suke waya sai yafi sakin jiki saboda sun saba amma ita kamar baison yi mata magana.. Ko gama wayar basuyi ba ya mika ma Chief saboda wani yanayi dayake ji atare da shi, Zuciyarshi Ta kasa samun sukuni tun kafin su bar garin Ya fara jin matsananciyar kewar Unaisah. Tafiya yankin azaba sun ɗauki tsawon awanni akan hanya, da misalin sha biyun dare, suka qaraso cikin Dajin da suka haɗa katafaren sansaninsu, dajin yana a kusa da evil forest, katafaren Military base ne mai girman gaske ga wasu Irin Dakarun Sojaji masu ƙira irin ta zakuna kowan nan su yana asanye da army combat uniform dinsa, Cikin takun majiya karfi suke sintiri a cikin sansanin tamkar da rana saboda hasken electricity din dake a ko'ina na sansanin. Bayan sun fito daga cikin motocin su, duk inda suka gifta cikin girmamawa sojojin ke sara masu tare da yi masu maraba da zuwa, a haka har suka shiga inda masaukinsu yake domin su dan hutu na wucen gadi. THE DAY👹👺 Asubahin fari suka farka daga bacci, musulman dake acikin sukayi sallah awani ke6a66en wuri dake a cikin sansanin, bayan sun yi kalacin su, gaba ɗaya sojojin suka hallara a filin dambe, suka fara motsa jikin su har dambe sai da su ka yi a tsakaninsu wanda ya kasance kamar gasa ce su ke yi, Danish ya zama zakaran gwajin dafi a wurin an kasa samun wanda zai kayar dashi dayawa sun kara samun kwarin gwuiwa da ganin irin kwazon shi, bayan sun gama damben suka ɗan huta har wuraren ƙarfe shida na marece kafin daga bisani suka fara shirin shiga evil forest. A helipad din dake a wani sashe na cikin Sansanin Wasu dankara dankaran Jiragen yaƙi ne a jere masu saukar ungulu da aka tanadar masu, ko da ido ka kalle su sai gabanka ya fadi, already fighter Pilots ɗin da zasu Yi jigilar daukarsu tuni sun shige cikin helicopters din. Bayan komai ya daidaita, har dakarun sojojin sun gama shiga cikin jiragen, Kafin wani Lokaci jiragen suka lula sama, yayin da trucks ɗin makamai dake tafiya akasa suke bin su. *FATAN NASARA* ____________________________________✍️ *🔥GIDAN KURKUKUN ƘADDARA🔥☠️* Farkawarta kenan daga bacci, A hankali ta buɗe idanunta tare da kallon rufin gadon, Har na tsawon mintuna, har rama ta qara saboda azabar rashin lafiyar da tayi. ta wutsiyarta idanunta ta hangi mutun kwance gefenta, da sauri ta wurga idanunta akanta, ajiyar zuciya ta sauke ganin tsohuwa khala, da alama tayi nisa acikin baccin ta, ta ɗan yi mamaki don tunda ta tsinci kanta a dakin khala bata ta6a kwana kan gadon ba, a saman kujera take yin baccin ta a zaune kamar dogari. Kasa kauda ido tayi daga kallonta, wani irin kaunar dattijuwar take ji acikin zuciyarta, batasan sa'adda ta matsa kusa da ita ba takai hannu ta shafa gefen fuskarta mai tarin tamoji tamoji, ta manna mata sumbata kan goshin ta ta danyi murmushi har chin dimple dinta Ya motsa. "Bayan ɗan uwana gabriella, bani da abu mafi soyuwa daya wuce ke, Inasonki Khalana.." kamar daga sama ta tsinkayi muryar Khala acikin kunnanta"Nima Ina sonki Jikata" zare brown eyes dinta tayi fuskarta dauke da annurin farin ciki ta furta"Khala, Idonki biyu"? Ta fada akagare da son jin amsarta.. A hankali Khala ta buɗe idanunta akan fuskar Gabriellah. "Ya jikin naki Jikata"? still da murmushi kan fuskarta tace"Naji sauki, yanzu babu inda keyi mani ciwo" Tattausan murmushi khala ta sakar mata"haka nake sonji, Na lura kamar Kina farin ciki Yau, saboda tunda nake dake banta6a ganin murmushin ki ba..." yar dariya Gabriel tayi "khala, kece silar farin cikina, da na yanke kauna da rayuwar duniyar nan, amma silar haduwana dake da kuma alkawarin da kika daukarmin na haɗani da ɗan uwana Yasa naji Ina son na rayu, Ina son na zama jajirtacciya jaruma kamar ke, kuma ina son na ɗauki fansar abunda akayi mana" tunda tafara magana khala ke binta da kallo, arayuwarta tana Son ya'ya musamman idan tagan su cikin nishadi da walwala shiyasa aduk lokacin data ga ana azabtar da rayuwar su take jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin da takaici. "Amma khalana, Idan muka yi nasarar ku6uta daga kurkukun nan, atare zamu rayu ko"? Murmushi khala tayi"Idan na fita bansan inda zanje ba, bani da kowa, ko kina da inda zaki ajiye ni"? Shiru gabriella tayi tare da ta6e bakinta kamar zatay shagwa6a tace"nima bani da kowa, amma dani da ɗan uwana Gabriel, zamuyi aiki tukuru, donmu gina gidan da zamu zauna, nayi maki alkawarin zamu baki kyakkyawar kulawai..." cike da nishadi khala ke sauraronta.. Kwatsam suna tsaka da yin fira, ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka jiyo masu wani irin sautin Bugun ganguna dumdum kamar dodon kunnan su zai fashe, tsabar sautin bugun gangar Ginin Har girgiza yakeyi, hatta gadon da suke kwance akai ya kama girgiza. gaba daya Gabriella tabi ta ruɗe, baiwar Allah dama ba lafiyar kwalwa gare ta ba, da sauri ta toshe kunnuwanta da tafukan hannayenta. Tsohuwa Khala kuwa tashin Hankali da farga Ya hana ta motsa sai faman zare idanunta takeyi. Lokaci ɗaya suka daina Jin bugun gangar, sai kuma suka fara jiyo ɗaddaɗar Busar sarewa tana tashi lokaci ɗaya yanayin fuskar Khala Ya sauya, aruɗe ta furta"ELDERS" Cikin ruɗu Gabriellah ta kalle ta cike da rashin fahimtar me take nufi.. Damƙo hannunta tayi acikin nata"akwai abunda na manta ban fada maki ba, daren yau dare ne mai hadarin gaske, bugun gangar da kika ji alama ce dake nuna ƙarasowar ELDERS. "abunda nakeso dake ki 6oye karkashin gadon nan, kada ki kuskura ko tari kiyi idan ba haka ba zaki jefa rayuwar ki cikin haɗari ne.." Hankalin Gabriella ba karamin tayi yayi ba, muryarta na rawa ta furta"Dan uwana fa? kada su kashe min shi..." katse ta khala tayi"babu abunda zai same shi, kiyi abunda nace maki kawai" saukowa sukayi daga kan gadon da sauri Gabriella ta shige karkashin gadon, ba laifi Yana da faɗi da tsawo, kamar ƙaramin ɗaki, tayi mamakin ganin buhun huna kusan Biyar a karkashin gadon ga wasu akwatinan ƙarfe, jikinta na kerma amma saboda karanbani saida ta yi kokarin kwance buhun don ta ga menena aciki, Sai dai takasa saboda mugun ɗaurine akayi masu, tatta6a jikin buhun tayi sai taji kamar Makamai ne a cikin su... Komawa tsohuwa khala tayi kan gadon ta kwanta tare da lumshe idanunta, zuciyarta cike fal da fargaban abun da zai biyo baya don tasan muddin Elder ya ƙaraso adakinta zai huce gajiyar shi. bakomai yafi damunta ba face zuwan Garkuwa, Allah Allah take su karaso saboda batason Elders suyi nasarar Salwantar da rayuka a wannan daren, In har daren yau ya wuce Bata cimma burinta ba, bata jin zata Iya jure rayuwa adoron duniyar nan, saboda in har ta kuskura asirin ta Ya tonu na abunda take kullawa Allah kadai Yasan Mummunan hukuncin da zasuyi mata, donma saukinta daya Elder Yana Ji da ita. Bata kare zancen zucinta ba, Kamar daga sama Taji dirar wani abu adakinta, Sautin shu'umar dariyar shi ce ta karaɗe kunnuwanta, Tuni tasha jinin jikin ta. "Da wata irin Murya irin ta tantiran ƴan'duniya Ya furta"Idan ma bacci kike, toh ki farka..." yunkurawa tayi ta miƙe zaune, tare da kai dubanta gare shi, Yana atsaye cikin wata rantsattsiyar alkebba launin Ja mai adon duwatsu irinta sarakuna..ya lullu6e kanshi da hular alkyabbar, rabin fuskarshi arufe yake da takuntumi, kafafunshi suna asanye da wasu hadaddun takalma na alfarma, yayin da hannunsa ke aruke da sanda ta zallar Zinari. ba'a Iya ganin fatar jikin shi saboda ya lullu6e ko'ina hatta yatsun hannunsa safa ya sanya masu. Gabriella dake labe ta kasa kunne tana sauraronsu, da ga inda take tana Iya hangen kafafuwan Elder.. "Taya zan Iya bacci batare dana sanyaka acikin idanuna ba, tun bayan daka tafi kabarni da kewarka, idanuna sunyi maraicin ganin ka, sanyin idaniyata, mijina uban ya'yana, sarki ɗaya tak da ke mulkar zuciyata..." cike da qasaita yake sakin dariya yayin da yake tinkarar gadonta cike da dattako yake taka matakalar gadon. "Meyasa soyayyar mu bata tsufa ne? Aduk lokacin dana ganki sai inji kamar ana rura wutar sonki a cikin zuciyana, bazan Iya misalta kewarki da nayi ba. yayin da yakeyin maganar, wani irin kallo khala take binsa da shi mai wuyar fassaruwar, ta tsane shi fiye da yadda ta tsani mutuwarta, shine silar komai 💔 gaba daya tayi zurfi a tunaninta sam ta manta da shi akusa daita, batai aune ba taji ya janyota jikin shi, wani ɗaci taji aranta, sai taji kamar ta hada jikinta da wuta saboda tsanar da tayi mashi.. Sumbatar kuncinta yayi, cikin wani irin salo ya fara sarrafa ta. Gabriella dake la6e a karkashin gadon, gabanta sai faduwa yakeyi ganin yadda gadon ke girgiza kamar zai rubzo mata, gani take kamar mutumin dayazo ne ke cutar da Khala. kasa jurewa tayi duk tabi ta rude jikinta sai kakarwa yakeyi bata san sa'adda ta saki ƙara ba, da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta. Lokaci ɗaya Elder Ya raba jikin shi daga na Khala, ido cikin ido suke kallon juna..tun daga yanayinta ya fahimci akwai wani abu da take boye masa. Kamar daga sama taji Ya furta"kamshin mutum nake ji adakin nan..." arazane ta ware idanunta akan fuskar shi, jinjina mata kai yayi "Ke da wanene Kuke rayuwa adakin nan? Kuma Yana ina"? Ji tayi kamar ta fasa ihu saboda tashin hankali, batasan ya akai ya gane akwai mutun ba.. . "Kinyi shiru baki bani amsa ba, Ko kin bani za6i In gano da kaina"? Yawu mai daci ta hadiya muryarta na rawa tace"bakowa, Ni kadai ce, nayi mamaki da naji kace kaji kamshin mutun bayan ni kadai ce mutum da ke rayuwa a cikin dakin nan.." "baki saba min karya ba, Amma yau kinyi min, kinsan na tsani makaryaci, saboda alamace dake nuna mutun zai Iya cin amanarka wata rana" idanunta ne suka ciko tab da kwallo, cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, na gane kuskurena, kasan ba halina bane, dama yarince daga cikin prisoners, inason yarinyar ne shiyasa na taimake ta..." tun kafin ta kare maganar Ya daka mata tsawa a faɗace Ya furta"meke damunkine? Kina cikin hayyacinki kuwa? Kin manta gargadin da nayi maki? Kamar ƙaramar yarinya ya rufe ta da faɗa. "Ki rasa wa zaki kawo cikin dakina sai ƙasƙantacciya Prisoner? Ɗakin Elder? kefa sirrina ce, sai da na fada maki banaso kowa ya rabeki in bani ba" kokarin bashi hakuri tayi, ko kallo bata ishe shi ba, saukowa yayi daga kan gadon da kakkausar murya ya furta"Tana ina"! Jiki na rawa tsohuwa Khala ta sauko daga kan gadon. "Pls kada ka rabani da ita, Inasonta, wallahi bada wata manufa na ajiyeta adakin nan ba.." magiya ta dinga yi mashi amma dayake zuciyar irin ta fir'auna ce ko kadan bai saurare ta ba. Tsoro Ya hana Gabriella fitowa, kirjinta kamar ana luguden ta6are.. "Zaki fito da kafafuwanki, ko kuwa Ni kikeso In fito dake..." cikin karyayyar murya khala ta kira sunanta.. Jiki asanyaye ta fito daga karkashin gadon, wani dan iskan kallo Elder yabita da shi, farat ɗaya Ya gane ƴar wacece. Dariyar shaƙiyanci Ya saka kafin Yace"wannan Ay yar gurin Jan wuya ce, sadaukarwar Jini ce, bazan Iya barmaki ita ba, dama wata ce daban, Ko ubanta Yaji kin dauke ta sai yazo ya kar6eta ya mayar da ita cikin prisoners, kinga kuwa babu amfanin boyeta agurin ki...." Gabriel ta ruɗe da jin maganar shi, ta fashe da kuka, idanunta akan fuskar Khala dake kallon ta. cikin shesshekar kuka tace"kada ki bari arabani dake, kashe ni zasuyi, bana so na koma gurin su, kada ki manta da alkawarin da kikayi min pls...." Da kallon tuhuma Elder Ya dubi Khala"wani alkawari ne kikayi mata" "Zan hada ta da ɗan uwanta" ta fada rai a6ace.. "Ku shigo ku dauke ta" suka ji ya fada, kafin wani Ya furta kalma sai ga Giants biyu karfafa sun fado cikin ɗakin, wani irin faduwar gaba Gabriella taji, jikinta na bari kamar mazari ta la6e bayan Khala, ta rurruke hannunta tanayi mata magiya kan kada ta bari su tafi da ita. shiru khala tayi jikinta yayi sanyi lakwas, Zuciyarta ta karaya. "Ku maida ta, Cikin Ƴan uwanta," Duk yadda Gabriella taso ta kubce masu abun yaci tura, tana ji tana gani suka nuna mata fin karfi akan idonta Giants suka fuce da Gabriella... Jiki asanyaye ta koma kan kujera ta zauna, idanunta suka cicciko tab da kwalla... Matsawa yayi kusa da ita tare da sunkuyar da kanshi gab da fuskarta"fushi kike dani"? Ya faɗa tare da ɗage mata gira.. *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘 Yar dariyar takaici ta yi, "Elder kenan, ka jima kana nuna min fin ƙarfi, wlh tun ranar dana gane asalin wa nene kai, na ji ka fita araina, wlh na tsaneka kamar mutuwa, babu abunda nake kwaɗayi da ya wuce inga bayanka, dan Allah ka mutu mana, na gaji ! na gaji !! da irin baƙincin da kake ƙunsa mini, wai kai wani irin mutunne? ko sau ɗaya baka ta6a jin nadamar irin zunubban da kake aikatawa ba? Na jima ina kokwanton anya kai mutunne? Saboda babu zuciyar imani a ƙirjinka... " Bata ƙare maganar ba, ya daka mata tsawar da tayi silar rikicewarta tuni tasha jinin jikinta, nuna ta yayi da yatsan shi, "Bansan a ina kika samu ƙwarin gwiwar gaya min magana cikin idona ba, koda yake dama haka kike da kafiyar tsiya, ke kin sani bada son raina na jefa ki cikin kurkukun nan ba, kece sila, shisshiginki da bin kwakkwafinki ne suka ja maki, naso mu dawwama acikin farin ciki amma kin 6ata komai, wallahi ba don son da nake maki ba da tuni najima da kashe ki, amma saboda ƙaunar da nake maki shiyasa na killaceki anan saboda kada ki tona min asirina..." Cike da taikaici ta yi murmushi haɗi da ɗan girgiza kai ta ce, "Ai ni tuni kajima da kashe ni, me kuma ya rage? Tsawon shekaru ashirin rabona da inga hasken rana, tsawon shekara ashirin rabona da inga wani dangina, dan Allah ka kashe ni in huta, na roƙe ka Ka kashe ni mana...!" cikin jin kunar rai ta faɗa. Lumshe idanunshi yayi akan fuskarta tare da buɗe su, da wata irin siga ta jan hankali yace, "Idan na kashe ki, kamar na kashe kaina ne, nafison in ma mutuwar zakiyi mu mutu atare." "Elder kenan, makomarmu ba zata ta6a zama ɗaya ba, ni da nake so In mutu Cikin rahamar ubangiji, taya za kai min fatan mu mutu atare?" Tuntsirewa ya yi da dariya, cike da tsana take kallon shi.... "Bazan bari ki 6ata min ranata ba, yau ina cikin farin cikin zagayowar ranar da muka kafa gidan kurkukun ƙaddara, ko murna baki tayani ba..." Wani kallon rainin wayau ta jefa ma shi a cikin ranta ta furta, "In Sha Allah yau ce rana ta ƙarshe da zaku yi black night a duniya, Ubangiji Allah Yasa su kawo maku farmaki su tarwatsa tawagar azzalumai..." "Me kika ce?" Firgigit ta kalle shi cike da fargaban kada ace Yaji ta, duk da ta dai san a zuciya tayi maganar amma tasan yana iya karantar abunda take saƙawa acikin zuciyarta. "Kaji nayi magana ne?" Girgiza mata kai yayi. "Ni zan Shiga fadata, ko zaki raka ni?" Banza tayi da shi, "Ki kula min da kanki." Bai tsaya yaji amsarta ba, Ya 6ace ma ganin ta.. Me ya faru bayan Giants sun tafi da Gabriella? Tana ta kuka tana tirjewa, a haka suka miƙi hanyar komawa cikin Kurkukun da ita, adaidai zasu karya wata kwana kwatsam saiga Tsohuwa Inno ta fito daga fadar elders karaf idanunta suka hango mata Gabriella... A sukwane ta dakata da yin tafiya ta zuba mata idanu, yarinyar da take nema ruwa ajallo sai gata yau Allah Ya haɗasu.. Dariyar mugunta ta saki mara daɗin ji kamar haniniyar jaki, A firgice Gabriella ta kai dubanta ga tsohuwa Inno jin sautin dariyarta, Lokaci ɗaya yanayin fuskarta Ya canza ganin matar da ta tsana fiye da mutuwarta. Ƙarasowa Inno tayi gaban su da sandarta ta tsaya cike da shaƙiyanci ta ce, "Wanake gani kamar Gabriella? Yarinya mai ran ƙarfe, ashe rai kanga rai? dama saida raina ya bani baki mutu ba, Kina nan da ranki, kai! amma fa nayi mamakin tayaya akai kika rayu bayan tiyatar dana sa giant yayi maki? Wani mai imanin ne yayi jinyarki? Banza tayi da ita, ta6e baki Inno tayi tare da kallon giants din dake a ruƙe da ita, "A wace Bola kuka tsunto sharar nan"? Wannan kalma ta ƙona ran Gabriella, ta ƙulu sosai. Ɗaya daga Cikin Giant ɗinne Ya ce, "Daga ɗakin Khala, Elder ne ya bada Umarnin mu dawo da ita cikin yan uwanta." Ta6e baki Inno tayi, "Dama nasani, duk cikin kurkukun nan babu mai zuciyar imanin da zai iya jinyarki in ba ita khala ɗin ba, amma fa na tayaki baƙin ciki, da kin mutu da kin huta." Ta faɗa tana leƙen fuskarta, warin bakinta duk Ya cika hancin Gabriella, wani irin yunƙurin amai ta fara Ji.. Bin ta da kallo tayi daga ƙasa har sama, saboda tsabar fitsara hada sanya hannu ta ɗage rigarta ta tura kai tana leƙen gabanta don taga aikin da akai ma wurin, duk tayi shiru bata hanata ba... Ɗagowa tayi fuskarta dauke da shu'umin murmushi ta ce, "Kin ɗinku da kyau, wuri fa yayi kyau, naji dadi kinga yau Manyan Baƙin mu zasuyi badago a kanki..." ta faɗa tana sakin dariya. Ƙululun baƙin cikine Ya tokare makoshin Gabriella sai huci take kamar zakanya, kashe mata ido tsohuwa Inno ta yi kafin ta kalli giants din dake a ruƙe da Gabriella ta basu Umarnin su tafi. Kamar jira take Giants ɗin subar wurin dama zuciyarta ta kawo wuya, aikuwa tayi wani irin kukan kura da iya ƙarfinta na karshe ta daka uban tsalle tayi zaman yan bori akan Tsohuwa Inno, kamar Allah ya aikota ta dinga gartsa mata cizo da yakushi tsohuwa inno ta dinga kokarin Kayar da ita ƙasa amma takasa, sai da ta kekketa fatar ƙwalƙwalin kanta, duk ta ciccisge mata yar hurhurar dake a kan, tayi ma kwallan kan rantali da akaifarta duk ya yi jaga jaga da jini... Wa'iyazubillah! Wata irin kururuwa tsohuwa inno ta saki tare da jijjige jikinta silar hakan yasa Gabriella ta kundumo ƙasa timm! nan take Inno ta rikiɗa ta zama wata mummunar halitta mai razanarwa, gurnaninta kaɗai Ya isa ya rikita kwakwalwar mutun. Da mugunta ta durfafi Gabriellah, a lokacin so tayi ta kasheta ta hanyar handameta, aikuwa ta watsa aguje ta nufi wata doguwar hanya mai duhun gaske, bin ta Halittar ta yi aguje duk inda ta taka sai floor ɗin gurin ya girgiza saboda girman halittar, gaba ɗaya Gabriella ta rude ta razana ta rasa ina zata boye kanta, don tasan muddin Tsohuwa Inno ta kamata Sai dai buzunta... Saƙo da lungu ta dinga bi, tana tsaka da yin gudun ta faɗo cikin wani ke6a66en wuri mai tarin komatsai ga shi babu wadataccen haske, Gurnanin dabbar da ta jiyo ne yasa ta furgice ta soma ja da baya, cikin rashin sani tana ƙara ɗaga kafarta ta taka wani wuri gaba ɗaya ƙasan gurin ya rubza da ita ta zurma cikin wani rami wanda bakomai ne a cikinsa ba face zallar jini mai ƙarnin gaske ga ɗoyi, shi wannan tafkin asalin samuwar shi daga ɗakin fiɗa ne na gidan kurkukun ƙaddara, jinin mutanan da suke feɗewane idan ya gangaro ta cikin pipe kai tsaye yake shiga cikin tafkin anan ya ke taruwa in suka tashi amfani da jinin zuwa suke su dibe shi a cikin tuluna. Wa'iyazubillahi! kamar zata haɗiye zuciya saboda azabar ƙarnin da ya toshe ƙofofin hancinta, jinin ya mamaye jikinta Iya wuyanta ne awaje sai ihu take tana kokawar fitar da numfashin ta. Ko da tsohuwa Inno ta faɗo wurin ta hango Gabriella tana ihu cikin jini, nan take ta Rikiɗa ta dawo ainihin suffarta ta mutane, wata irin mahaukaciyar dariya ta saki, ganin haƙarta ta cimma ruwa, Saboda zalunci maimakon tabarta haka sai da tayi mata sihiri ta ƙarasa nutsar da ita cikin jinin kanta ya shige gaba ɗaya, tasan bazata rayu ba, sai dai a fito da ƙasusuwanta in namanta ya gama zagwanyewa. A bangaren Tsohuwa Khala Hankalinta Yaƙi kwanciya, saboda fargaba da zullumin abun da zai biyo baya in har su Garkuwa basu kawo farmaki ba, baiwar Allah ta kwallafa rai akan zuwansu, ta kasa tsaye ta kasa zaune har gaban madubin ɗakinta ta je ta zauna kan kujerar gabansa, tayi siddabarun da ta saba yi donta samu damar yin magana da shi amma bata ga komai ba a cikin madubin, nan fa hankalinta ya ƙara tashi ganin har dare yayi❗ _______☠️👹☠️BLACK NIGHT💀👹☠️_______ Ƙarfe Goma daidai agogon Gidan kurkukun ƙaddara ta buga, adai dai wannan Lokacin, Dubban shahararrun matsafa suka fara tururuwar fitowa daga masaukin su na gidan kurkukun ƙaddara, adaren ranar duk wata halitta dake bacci a cikin dajin Evil forest da kurkukun saida ta farka saboda sautin bugun ganguna da busar sarewa daya karaɗe ko'ina tamkar za'a fasa ginin saboda Yadda kiɗan ke tashi.. takaitaccen tarihin Daren Black Night, shidai wannan dare, ya samo asaline aranar da Elder Ya Ƙaddamar da gidan kurkukun ƙaddara, Dare ne mai daraja a gurin su, suna alfahari dashi, kuma suna ɗokinshi saboda dare ne na sharholiya, kowa zaiyi bushasha suci karensu babu babbaka sannan a daren suna ƙara ƙarfin tsafinsu, agurinsu kenan, amma agurin Prisoners Daren black night kamar guguwar annobace saboda tashin hankalin da suke fuskanta adaren, kada na cika ku da surutu bari mu leƙa muga meke wakana adaren Black Night❗❓ Ɗaya bayan ɗaya matsafan ke fitowa daga masaukinsu, Wasu a hawa na ukun bene, wasu suna a hawa na biyu yayin da wasu suke a hawa na farko, kowani matsafi Ya ƙure kuri adakansa, ƙarshen wanka na kece raini, matsafan ma jinsi jinsi ne. Tawagar matsafan yankin Asia ne a hawa na farko, sunyi anko shigar su kamar irinta kayan gargajiya launin jajaye na ƙasar China, ga wani dogon gemu har kan tulun tumbinsu, uban goshin su kamar jirgi ya yi asubanci, ga wani uban sanƙo dake gare su, idanuwan nan nasu mitsi mitsi kamar na kifaye. A hawa na biyu kuwa tawagar Matsafan India ne, Sun buga adon su kamar malaman majami'u, wasu irin mutane ne masu ƙaton tumbi da manyan mazaunai burguza burguza ga wani uban rantali akawunan su, Munanan gaske, duk sun yi fentin ja da baƙi a jikin su, kwata kwata babu sutura a jikin su, zir suke haihuwar uwar su sai jan fentin da suka shafe jikinsu da shi, ga mutum mai ƙyanƙyami in ya kallesu sau ɗaya bazai sake marmarin kallon su ba. Tawagar matsafan kurkukun ƙaddara, Su kuma nasu wankan wasu dogayen rigunane a jikinsu baƙaƙe har ƙasa suke ja, sun lullu6e kawunansu da hulunan rigunansu, sun rufe fuskokinsu da mask mai suffar ƙwarangwal. Tawagar matsafan yankin Europe da America suma ba'a barsu baya ba, suma sunyi ankon su na kece raini. Gaba ɗayansu sun hallara a tsakar kurkukun, ƙwansu da ƙwarƙwatar su ko'ina ka kalla sune birjik. Babu masaka tsinke, saboda shagalin yau, ko'ina na kurkukun saƙo da lungu wasu irin dakarun Giants ne majiya ƙarfi ke sintiri sai mazurai suke, Jira suke kawai suga badaidai ba su aiwatar da aikin su. Ko sauro bai isa Ya ratsa kurkukun ba batare da sun gan shi ba, hatta dakin maduban tsafinsu makil yake da giants sun kasa sun tsare suna kallon komai dake wakana a kowace kusurwa ta kurkukun da dajin Evil forest don tabbatar da tsaro, duk da basu sama ransu wani zai kawo masu farmaki ba, saboda ba'a ta6a gigin yi masu kutse ba, shiyasa suka daɗe suna sheƙe ayar su. Surutunsu Ya karaɗe ko'ina, da wani irin Yare mara daɗin Ji suke magana cikin harshen su na matsafa, sai raha suke suna hira cikin nishaɗi. Daga kan ground floor ɗin gurin wani haɗaɗɗen red carpet ne aka shimfiɗa tun daga fadar mai girma Elder har zuwa ƙarshen bango inda aka ƙawata wurin kamar karagar sarakuna, ga wasu jigunannun Armchairs guda shida an ƙawatasu da kayan ado. Daga can gefe ɗaya a tsakiyar Ground floor din wani zungureran Table ne ɗauke da tsadaddun kayan shaye-shaye masu haɗarin gaske ga tulunan Jini da aka girke kan table ɗin, ga farfesun nama cike da farantai nau'ika daban daban irinsu, farfesun naman ɗawisu, na naman shanu kai hada farfesun yan cikin mutun, soye soye kala kala da kayan maƙwalashe. Yayin da makaɗan suke ta yan kiɗe-kiɗe da raye rayen su, wasu gungun yan rawa manyan mata masu dirin jiki suka fara fitowa Kwata kwata babu sutura a jikinsu zir suke haihuwar uwarsu, wata irin rawar qugu sukeyi mai jan hankali, nan fa matsafan suka fara washe haƙora suna kallon su.. Gaba ɗaya sun ƙagara a fara shagalin, fitowar Elders kaɗai suke Jira.. Idan muka koma cikin fadar Elders kuwa, tattaunawa su ke yi a tsakanin su, Elder yana a zaune kan kujerar mulkinsa yayin da sauran Elders din suka kewaye shi suna a zaune kan carpet din fadar, Gaba ɗayansu sunyi shiga ta alfarma irin ta mai girma Elder, sun rufe ko'ina na jikin su baka iya ganin koda akaifar su ce, su shida ne cuf ba ƙari. Cike da nishadi Ya soma magana Yana dubansu, "Me ya rage mana"? Ya faɗa yana bin su da kallo.. "Babu komai Elder, Mun riga da mun toshe kowace Hanya da za'a Iya kawo mana farmaki, dama duk burga ce, wane yaro! rijiya ay ba wurin gaɗar makaho bace, ƙananun kwarine su, in banda ma hauka ina su ina ja da mu? sunyi tunanin sauƙi ne Ja da mu, ko Dajin Evil forest basu isa su ƙetare ba, mune masu ƙarfin iko, da izinin mu komai ke wakana, in muka so Da kalma ɗaya zamu shafe babinsu mu mayar da su tur6aya!" Gaba ɗaya suka tuntsire da dariyar shaƙiyanci, bayan sun tsagaita da yin dariyar Elder Ya dubi wanda yayi maganar Jan Le6e, "Na ji daɗin bayanin ka.." Ya faɗa tare da maida dubanshi kan Elder din dake zaune gefen Jan Le6e ya ce, "Mutumina Jan wuya, Ko akwai labari? Ko kuwa sai mun sha mun bugu don nasan halinka da miskilanci kafi sakin baki idan ka hau kan network..." Cike da shaƙiyanci ya furta, "Musamman in akwai mata da giya anan linzamina yake kwancewa..." Dariya suka saka gaba ɗaya.... "Baka da matsala mutumina, yau ranarmu ce, saika za6a ka darje," Ƙasaitacciyar dariya jan wuyan ya saki. "Jan kunne na ji ka yi shiru baka ce komai ba"? Ya faɗa Yana duban shi. Muskutawa ya yi ya gyara zaman shi, "Elder, Ni bani da abun cewa, Hankalina Ba a kwance Yake ba, ban ta6a tsintar kaina a yanayi na jin faɗuwar gaba irin na yau ba..." gaba ɗaya suka maida hankali kan shi. Da kakkausar Murya wani mai zafin rai a cikinsu wanda suke kira jan harshe Ya ce, "Wannan wani irin zancen banza ne? Ka kuwa san me hakan Yake nufi? Faɗuwar Gaban Elder yana nufin mummunar ƙaddara zata Iya afka mana, tun wuri Ka dakatar da zuciyarka, ba'asan Elder da raunin zuciya ba..." Yana ƙare maganar Jan Wuya Ya ce, "Ka gafarce ni, kaima kayi kuskure a maganarka Jan harshe, Elders sunfi ƙarfin mummunar ƙaddara, ita kanta ƙaddarar tsoron mu take ji, shiyasa bata ta6a gigin afka mana ba..." Da gadara suke magana. (Duniya budurwar wawa, Wanda Ya 6ace Ya 6ace.....) "Jan wuya, kai ɗin na dabanne, namijin duniya, wanda bai ta6a karaya ba, ina son ƙwarin gwiwarka mutumina..." Ya faɗa tare da yi masa alamar jinjina da babban yatsansa, kafin Ya dubi Jan Kunne "Kai kuma, kada na kuskura na ƙara jin ka ambaci faɗuwar gaba, nasan me ke damunka, da zarar kaga mata masu manyan mazaunai zaka wartsake..." Dariya suka saka gaba ɗayan su. Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikinsu, Evil Giants masu ƙirar samudawa har su Goma suka kewaye kofar shiga Fadar...ɗaya cikinsu mai wata irin ƙatuwar murya ne Ya ce, "Elders baƙi sun hallara, lokacin shagali ya yi, zamu iya tafiya..." jinjina kai Elder yayi tare da miƙewa suma sauran Elders din suka Miƙe cikin takun dattako suke tafiya akan jan carpet din da aka shimfiɗa masu, hannuwan su ruƙe da sandunan su na alfarma. Lokacin da suka 6ullo ta ground floor ɗin makaɗan dake kiɗa suka ƙara kaimi gurin buga gangunan kamar zasu fasa su, ga wata daddaɗar busar sarewa dake tashi, wani irin kirari suka fara yi masu suna kurantasu da hura masu kai har wani rausayawa suke yi alamar kirarin yana kai masu karo. Gaba ɗaya Hankulan matsafan Ya dawo kan Elders, Taurari masu haskaka duniyar matsafa, kowa burinsa ya ga Elders, musamman sababbin matsafan da basu jima da shiga harkar ba, saboda wani irin farin jini ne da su, sun shahara a fadin duniya. Cikin girmamawa matsafan suke miƙo gaisuwa kamar zasu durƙusa masu saboda biyayya....bayan Sun ƙarasa gurin da aka ƙawata masu, kowan nan su ya zauna kan armchairs ɗin da aka tanadar masu. Ɗaga hannu Elder ya yi cikin sauri masu buga gangar da masu raye rayen suka dakata ... Duk faɗin girman gurin idan ya yi magana sai kowa Yaji shi kuma a hankali yake yin ta cikin nutsuwa. "Ina yi ma kowa barka da zuwa, haƙiƙa bazan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba na ganin kowannanku, abun alfahari ne a gareni, ace waɗannan dubban mutanan saboda ni suka baro muhallinsu suka zo don su taya ni murnar zagayowar ranar dana Kafa GIDAN KURKUKUN ƘADDARA....." Ya ɗan dakata Yana bin matsafan da kallo tun daga kan hawa na Uku har izuwa na farko, sun kasa kunne suna sauraron shi.. "A daren yau, muna taya juna murnar nasarorin da muka samu, bamu ta6a faɗuwa ba, dukkan abunda muka sa gaba sai mun cimma shi, ina fata abokan harkar mu zaku tayamu murna." Sowa suka sanya da ƙarfi suke amsa mashi da, "Yeho! Yeho!! yehoo!! Gyaɗa kai ya yi kafin ya ɗaura da cewa, "Kamar yadda kuka zo domin mu kuka faranta mana, muma zamu faranta maku, wannan yasa muka tanadar maku shirye shiryen da muka saba yi A kowane black night..." Bayan Elder Ya gama kora jawabin shi, Jan Harshe Ya ɗaura da nashi... "Gasar da zamu gabatar, faɗan gwada karfin iko ne, team da suka zo na ɗaya suka yi nasarar lashe gasar, zamu basu santala santalan yan mata har guda goma sha biyar, waɗanda suke tsaka da Yin jinin al'adarsu, don su biya buƙatarsu da su, bayan haka zamu basu matasan maza goma sha biyar suma su biya buƙatarsu da su..." Wani irin ihu matsafan suka sanya har sun fara saƙa buri akan suyi nasara saboda tsananin kwaɗayin mace mai jinin al'ada su ke yi.. Dakatawa yayi da yin bayanin, kafin ya ɗaura da cewa, "Tawagar da ta zo a mataki na biyu, mun tanadar masu jarirai goma sha biyar, tare da Tulunan jinin al'ada da muka tsuma, bayan haka zamu basu mata masu ɗauke da juna biyu su yi amfani da su sannan su sha jinin abunda ke acikin su..." Tunkan Ya ƙare maganar matsafan suka sake sheƙewa da shewar Murna. "Tawagar matsafan da suka zo na uku, mun tanadar masu sabbin gawawwakin da muka tsuma, sannan zamu basu sassan jikin fursinonin mu." Wani irin ihun farin Ciki matsafan suka saki, su fa yau shar kakarsu ta yanke saƙa... "Saura waɗanda basu yi nasara ba, suma ba zamu barsu hakanan ba, kamar yadda muka yi alkawari zamu faranta ma kowan nan Ku...." Yana ƙare maganar Ya ɗaga hannu nan take masu buga gangunan suka ci gaba da gashi. ________________________________________✍️ Shigowa ta yi cikin katafaren Hall din da suka tara za6a66un prisoners da suka tanada saboda faranta ma baƙin nasu. Hall ne mai faɗi da tsawon gaske ta cikin shi akwai ƙofofin ɗakunan dake a jere jikin bangonshi, Yana da dogayen benaye, a wani sashe na hall ɗin akwai wasu tsoffin rijiyoyi da suke a garƙame da murafen ƙarafuna, ga wasu kaskwayen wuta dake ci, hall ɗin ya kasance inda suke bada horon zama Giants zanunnukan dake a jikin bangon hall ɗin kadai ya isa ya razanar da mutun..Anan suke killace duk wani abu da suka tanada saboda baƙin su. Tana ƙarasa shiga ta iske female giants ɗin dake shiryasu su ukku cikin kakinsu. Sun tu6e masu uniform dinsu, saboda basu buƙatar su shiga da su gurin taron da sutura, jikinsu sai kerma da kakarwa yake yi, daga ka kalli idanunsu zaka ga tsantsar tashin hankali, a ƙalla prisoners ɗin sun kai su arba'in da wani abu. Female giants din na ganinta suka russina tare da gaishe da ita, ko kallo ba su ishe ta ba.. Zama tayi kan kujerar dake fuskantar su tana ƙare masu kallo, bayan ɗan lokaci ta kai hannu ta kware ƙasan rigar ta, tsamurarrun cinyoyinta ne suka bayyana,wani ƙyalle dake naɗe da ɗaya daga cikin cinyoyin nata ta fara warwarewa, Ya ilahi! wani irin uban wari ne ya buso yadda kasan gunyar ƙwai ta fashe lokacin data ƙarasa kwance wurin, wani irin ciwo ne ya mamaye wurin har wurin can ƙasanta kamar dai gyambo, da ƙyar in baza'a rasa yan ƙananun tsutsotsi a wurin ba, gyara wurin ta shiga ƙoƙarin yi, Hankulan Prisoners din ba ƙaramin tashi ya yi ba, yunƙurin amai suka soma yi sakamakon ɗoyin ciwon da ya bugi hancinan su, aikuwa da kakkausar murya tace, "Duk ɗan iskan da ya kuskura ya yi amai a gurin nan sai na sa ya lashe shi da harshen shi...!" Waro idanu waje suka yi da sauri suka toshe bakunan su da tafukan hannayen su... Tsautsayi ne Ya ritsa da wasu ƴan biyu maza dogaye sirara da su, irin masu ƙyanƙyamin nanne, duk yadda suka so su hana aman fitowa daga bakinsu saida ya kubce masu aikuwa suka fara amayar da abunda ke cikin su. Murmushin mugunta tsohuwa Inno ta saki, "Ku ko wani tsautsayin ne Yaja maku yin amai?" Hankali a tashe suka fara yi mata magiya akan tayi haƙuri, Tsawa ta daka masu tuni suka sha jinin jikin su, da yatsa ta nuna masu wurin, "Ku zo ku sha daɗi.." Fashewa suka yi da kuka suna kallon sauran yan uwan su, wani irin tausayin sune Ya kamasu. "Kada kubari in maimaita abunda nace!!" Ba yadda suka Iya, sun riga da sun san bala'en da zai biyo baya idan suka bijire mata.. Cike da jin shakkarta suka nufe ta, zuciyoyin su na tashi haiƙam suka durkusa kan gwiwowin su agabanta, Idanun su na kallon tashin hankali! Da yatsa ta nuna na tsakiyarsu, "Kai zaka fara, Kafin na buɗe idanuna kayi hanzarin kafa bakinka..." Tana faɗa ta kulle idanunta. Yawu Ya haɗiya, cike da kyankyami yake kallon wurin ga azababben warin yafi yawa da suka matso gab da ita gaba ɗaya ya kanainaye hancinsu.. Tsohuwa Inno har wani murmushin mugunta take saki jin hucin Numfashin su a jikinta. Kwatsam! ba zato ba tsammani, kamar daga sama taji an buga mata wani abu mai azabar zafi a wurin, bugun har agaban ta. Wata irin zabura ta yi ta miƙe tsaye, cikin ruɗu ta zare tsoffin idanunta akan Giant din dake tsaye a gabanta, hannun shi ruƙe da Ƙatuwar guduma ta ƙarfe.. tuni Jini Ya 6alle mata kamar pipe din ruwa ya fashe... A tsananin ruɗe take kallon shi kafin ta dubi yan ukun dake tsaye bayan shi..da sauri ta dubi female giants din dake a wurin, wata irin razana ta yi ganin gawarwakinsu baje a ƙasa, Cike da al'ajabi ta furta, "Kai! wanene kai??" *"GARKUWAR FURSINONI"* Ya faɗa tare da sanya hannu ya zare Mask ɗin fuskar shi, Tsabar mamaki da al'ajabi hadi da razana ya hana ta furta kalma, kusan suman tsaye tayi ganin Garkuwar Kurkuku, Zance ya 6aci! daƙyar ta haɗiye al'ajabinta, Muryarta na rawa ta furta, "Garkuwarmu! Kai nake gani dagaske ba mafarki nake ba?tayaya ka shigo kurkukun nan eye? Ka dawo gurinmu ne? Ni dama nasan bazaka Iya rayuwa batare damu ba...." Sai sambatu take yi mashi kamar wata zararra, abu biyu ya haɗe mata ga azabar zafin da gabanta keyi mata. Wani ƙasƙantaccen Kallo Ya wurga mata mai tattare da ƙyama, cike da ƙwarin gwiwa ya furta, "Na dawo, amma ba a matsayin Garkuwarku ba, a matsayin garkuwar fursinoni." jikinta na kerma kamar mazari kafin ta furta wani abu ta jiyo sautin takalmansu ɗaya bayan ɗaya suke shigowa cikin Hall ɗin, ba zaka ta6a gane ba giants din kurkuku bane saboda kayan jikinsu sak irin Na giants ne. Ɗaya bayan ɗaya suka soma cire mask din fuskarsu, waro idanu waje tsohuwa Inno tayi Ganin baƙin Fuskoki a gidan Kurkukun Ƙaddara. Kallo ɗaya Chief Owais ya yi ma Prisoners din dake a gurin ya yi saurin kawar da idanun shi, Haka shima Big guy kasa jurewa yayi ganin babu sutura a jikin su, Taj da zuciyarshi ta gama karaya da tausayinsu ji yayi kamar ya fashe da kuka, a ranshi ya ayyana wai anan yarsa Angel tayi rayuwa har na tsawon shekaru, Ya salam!!!. Salsabeel kuwa tun shigowarshi idanun shi na akan Inno wani irin kallo mai cike da tsana yake jefa mata.... "Su wanene ku!.." bata ƙare maganar ba, sakamakon wani zazzafan Mari da Chief Owais Ya kwasa mata har saida wuyanta ya nemi jirkicewa, Kafin ta ɗago Ya daddage ya sakar mata mahangulba kan mummuƙenta...gaba ɗaya ta kife ƙasa a susuce ta furta,"kai, kai, kai, kai....." Prisoners din dake a gurin gaba ɗaya sun ruɗe sun rasa gane su wanene wadannan baƙuwar fuskar? shin sun zo ne da niyyar taimakonsu? ko kuwa suma mugaye ne..? "Kai ku maida Kayan ku" Big guy ne ya faɗa ba tare da ya kai idonshi kan su ba, jikinsu na kerma suka ɗauki uniforms dinsu dake yashe kasa suka shiga zirasu a jikin su. Ƙululun baƙin ciki ne Ya tokare makoshin tsohuwa inno, tun da take wani ɗan adam bai ta6a gigin ta6ata ba da sunan bugu sai yau da Allah Ya haɗata da Chief, yunƙurawa tayi ta miƙe tana layi ta soma rarraba idanunta akan Salsabeel da Danish. Tana huci ta ce, "Maciya amana! saina tona maku asiri gurin Elders" Ta faɗa tana kokarin Yin sihiri don ta 6ace sai dai wani iko na Allah kamar an ɗauke mata sihirinta, A ruɗe take kallon hannayenta ganin sun ƙi tasiri. "Kina mamaki ne?" Danish ne ya faɗa tare da ɗaga mata gira, takaici ya ishe ta.. "Wai dama haka matsafan suke, munana, gasu ƙazamai, gwanin ban ƙyama." Fuska a yamutse Big Guy ya faɗa tare da watsa mata yawu kan fuskarta ya ce, "Daƙiƙiya, dama karfin naki na sihiri ne, yanzu da babu shi taya zaki faɗa ma Elders dangane da zuwan mu? Bayan mun riga da mun mamaye gidan kurkukun da dakarun sojojinmu, munyi basaja mun saje da Giants ɗinku, Yanzu haka ɗaya bayan daya sojojinmu suke bi suna yi masu kisan mummuke batare da sanin ku ba." Dafe kai tsohuwa inno tayi da hannayenta ta fara jijjiga jikinta tana kokarin ta rikiɗa nan ma dai abun ya ci tura. Batai aune ba Sai dai taji safkar wuƙa a makoshinta, Big guy ne ya farke ta har saida ya dire ƙasa, Jini ya dinga tartsatsi kamar pipe din ruwa ya fashe, gaba ɗaya gangar jikinta ta zube ƙasa tana bullayi ta dinga sakin wata irin kururuwar azaba har rai ya yi halin sa.... "Har yanzu nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Ina jin abun kamar a mafarki ashe dagaske komai ke faruwa!" cikin jin ƙunar rai Chief Ya faɗa kafin Ya dubi Sojojin dake a bayansu ya ce, "Ku tafi da yaran!" Cike da bada Umarni Chief Ya faɗa. Kuka suka fara Yi masu jikinsu sai kakarwa yake yi, sun yi zaton cutar da su zasu yi, fahimtar hakan yasa Taj yi masu bayani ya ce sun zo ne don su taimakesu su ba masu cutarwa bane. Waro idanu waje suka yi, wlh alƙalamina bazai Iya mistalta irin yadda suka yi mamaki da al'ajabin jin za'a taimaki rayuwarsu ba, batare da 6ata lokaci ba, huɗu daga cikin Isod soldiers dinsu suka tafi da yaran.. Duk wannan abun dake faruwa Babu wanda Ya san da zuwan su cikin kurkukun, sai mutun ɗaya wato tsohuwa Khala. Saboda sautin bugun gangunan da makaɗa suke yi Ya hana Matsafan su jiyo sautin abun da ke faruwa.. Ajiyar zuciya suka sauke batare da jin fargaba ba, suka fito daga Hall din cikin tafiyar sanɗa suka nufi wata doguwar hanya mai kwana-kwana.. Duk Giant din da ya ankara dasu kafin yayi wani yunƙuri tuni suke fille kanshi da adda, Kisan Gilla su ke yi masu... (SHIN TAYAYA AKAI SUKA SHIGO GIDAN KURKUKUN ƘADDARA?) Bata nufi ko'ina ba sai hall ɗin da madubban tsafinsu suke, tana shiga ta iske giants din dake kan duty, tasan muddin Su garkuwa suka ƙaraso sune na farko da zasu fara kawo masu cikas saboda suna kallon komai dake wakana a cikin kurkukun ƙaddara da kuma dajin evil forest, gyaran murya tayi masu, cikin girmamawa suka gaishe da ita, tace meya hanasu shiga filin taro? Bayan yau rana ce mai mahimmanci da buƙatar kowa dake a kurkukun ya halacci wurin shagalin, Giants din su ka bata amsa da ba'a basu umarnin subar aikin su ba, tsohuwa khala tace a matsayinta na matar Elder tana mai umartarsu da su aje aikinsu, suje suma ayi shagalin da su, ba suyi mata musu ba, saboda sun san wacece ita, kuma Elder ya gargaɗesu akan suyi mata biyayya sau da ƙafa, in har ta buƙaci wani abu kada suyi mata jayayya su dauka kamar shi ne ya basu umarni, tuna wannan yasa Giants din suka bar bakin aikin nasu. Murmushi Tsohuwa khala tayi, tana ganin fitarsu, ta bi madubban tsafin ɗaya bayan daya ta jefar da su gaba ɗaya suka faffashe. Fitowa tayi daga hall din tana cikin tafiya cike da fargaba, kwatsam ta hango wasu gungun matsafa a cikin baƙinsu kusan su takwas sun nufo wurin kamar dai suna ƙarewa ginin kallo ne, gyaran murya ta yi masu da sauri suka dubeta, fuskarta da fara'a ta nufe su bayan sun gaisa ta gabatar masu da kanta a matsayin Matar Elder, sai faman washe baki suke yi suna ƙara gaishe da ita tace masu in ba damuwa su biyota zata nuna masu wasu bangarori na kurkukun tasan zasu so su gani. Basu kawo komai a ransu ba, suka bi bayanta ta nufi wani ɗaki da su, suna shiga ta datse ƙofar a ruɗe suka kalle ta ganin ta rufe ƙofa, kamar sun fara zargin wani abu, sai dai kafin su gano hakan Tsohuwa Khala ta yi hanzarin zare ƙaramar wuƙarta gaba ɗaya ta kashesu, ta zuƙunna ta cire kayan dake a jikinsu dama shine abun da take so.. 6acewa tayi, bata dira a ko'ina ba sai a cikin ɗakinta, ta jefar da kayan saman gadonta kafin ta kuma 6acewa ta bayyana a wani ke6a66an guri inda Danish ya faɗa mata ta nan zasu biyo idan suka ƙaraso. Tana tsaye hannunta ruƙe da sandar ta, zuciyarta cike fal da zullumi, Allah Allah take su ƙaraso kamar ta fashe da kuka saboda bugun barazanar da zuciyarta ke yi mata, ta aikata 6arna ba kaɗan ba, har ta fidda rai da zuwansu zuciyarta ta fara raya mata ta kashe kanta kawai tun kafin Elders su ankara da 6arnar da tayi masu. A lokacin da bata yi tsammani ba, ta fara jin motsi ta saman ceilling din da take, A hanzarce ta kalli silin din ta sauke idanunta kan wasu tsofaffin tagogine dake a kulle jikin shi. Cike da sa rai take kallonsu, Unexpectedly taga Murfin windows din na motsi wlh tsabar farin ciki bata san sa'adda takai goshinta ƙasa tay sujjada domin nuna godiyarta ga Allah, tunkafin ma ta tabbatar in su ɗinne, Kafin ta ɗago daga sujjadar kunnuwanta suka jiyo mata ƙarar 6allewar murfunan tagogin, a zabure ta miƙe tana kallon kafafuwansu, ɗaya bayan ɗaya suka fara dirowa ƙasa, kamar ana jeho su. Dariyar farin ciki ta saki duk da mask din dake akan fuskar Danish hakan bai hana ta gane shi ba, shima yana ganinta ya nufeta gaba ɗaya ta rungumeshi kamar zata maida shi cikinta, kai ƙarshe ma sai ta fashe mashi da kuka, cikin shesshekar murya ta ce,"Alhamdulillah, nagode ma Allah da ya nuna min wannan ranar da raina, har na fidda rai da zuwanku.." Ta faɗa tare da raba jikinta daga na Danish ta dubi sauran sojojin dake atsaitsaye ga wasu dake ta durowa ƙasa. "Khala" Salsabeel ne ya ambaci sunanta, bata gane shi ba saboda mask din da ya rufe fuskarshi, cikin sauri ya matsa kusa da ita, ta rungumeshi nan ma ta kuma fashewa da wani kukan farin ciki, Allah abun godiya.. Bayan ta raba jikinta daga na Salsabeel, Danish ya gabatar mata da Chief Owais, wanda tun da ya duro hankalinsa ke akan ginin yana mai jinjina girmansa, amma lokacin da kunnuwansa suka jiyo mashi muryar Khala da ruɗu ya tsayar da idanunsa akanta, kamar yadda take kallon shi haka shima yake kallonta, muryarta na rawa ta furta, "Owais, kaine ka girma haka?" Tayi zaton a cikin zuciya ta yi maganar, gaba ɗaya sojojin sun ɗan ruɗe da jin yadda tayi maganar kamar tasan shi, shi kanshi Chief din ya ruɗe da jin muryarta kamar yasanta, sai dai ya kasa gane wacece saboda ta rufe fuskarta da tukunkumi. Idanunta kaɗai suke iya gani... Bai aune ba, yaji ta cakume shi da hannayenta biyu ta rungume shi sosai fiye da yadda ta rungume su Salsabeel...Allah kaɗai yasan me take ji acikin zuciyarta.. Idanunta cike tab da kwalla, ta ɗago tare da kallon su, "Ku kaɗai ne"? Ta faɗa ganin kamar sun gama shigowa kuma duka basu fi su hamsin ba, Salsabeel ya ce, "Ba mu kaɗai bane, akwai sauran sojoji sama da ɗari biyar, suna akan hanyar shigowa." Ajiyar zuciya ta sauke, still idanunta akan Chief Owais, duk yasha jinin jikinshi da ganin irin kallon da tsohuwar take yi mashi, "Ina yi maku barka da zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara, a yanzu haka sun fara gudanar da shagalin Black Night basu san komai dake faruwa ba, saboda na toshe duk wata hanya da zasu iya ganinku ta madubin tsafin su, sannan akwai tanadi da nayi maku, ku biyo ni." Ta fada tare da juyawa suka bi bayanta, har suka isa ɗakinta basu ci karo da kowa ba. Bayan sun shiga, Ta umarce Salsabeel da Danish da su fiddo kayan dake a karkashin gadon ta.. Bayan sun fiddo Buhunhunan da akwatinan ta ce, "Makamai ne acikinsu, a gidan kurkukun nan ake ƙera su, na daɗe ina tara su a 6oye saboda burin da nake dashi na ganin na kawo ƙarshen zaluncin su." Ta ɗan dakata tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa, "Makaman dake a hannunku ba za su yi tasiri akan su ba, amma in har kukayi amfani da makaman nan cikin sauƙi zaku kashe su" Farin Ciki ne Ya cika su, a hanzarce Salsabeel da Danish suka kwance buhunhunan, sun yi mamakin ganin yawan makaman, Wuƙaƙe ne da adduna, harda takubba da kibiyoyi, ga gatari da manyan gudumomi, nan kowan nansu ya ɗauki makamin da ya kwanta masa arai, bayan sun kammala ɗauka, ta ce, "Ku fara kokarin ceto rayukan fursinoni dake a ciki kafin su ankara da shigowarku, Danish da Salsabeel kuyi masu jagora zuwa daƙunan da fursinoni suke." suka amsa mata da toh. Ta ƙara da cewa, "Duk yaran da kuka taimaka, ku kawosu nan, zan taimaka masu su fita daga kurkukun..." With respect suka amsa mata da toh. Akwatinan ƙarfen ta nuna masu, "Kakin giants ne a ciki, na tanadar maku sune saboda kuyi 6adda kama ku saje da su, duk da naga kakin ku sunyi shige da nasu." Ta kuma nuna masu kayan Matsafan da ta kashe, "Ga wasu kayan nan ma." Big guy yace, "Ba dukkanmu keda irin kakin ba, akwai sauran tawagar sojojin da zasu ƙaraso, in yaso sai wasu daga cikinsu suyi amfani da kayan." Jinjina kai ta yi, "Hakan yayi, zaku iya tafiya, Ina yi maku fatan nasara" Har cikin ran su sunji dadin taimakon da tsohuwar tayi masu, yaune karo na farko da suka fara ganinta amma ta kwanta masu a rai. (Kunji yadda akai suka ƙaraso Cikin gidan kurkukun ƙaddara) Suna cikin tafiya suka ci karo da wani bene mai kanannaɗa, Kwata kwata babu fargaba a tare da su, suka hau benen ya 6ula da su cikin wata hanya mai tarin kofofi, har zasu gifta ta wani ɗakin kwatsam wani gabjejen Giant ya fito sanye da lab coat fara a jikin shi gaba ɗaya suka sha jinin jikin su.. Da farko da ya kallesu yaso ya ruɗe amma sai ya ji a jikin shi ba Giants din su bane. "Su wanene Ku?" Da wata irin ƙatuwar murya ya yi maganar, Yan hanjin cikinsu ne suka kaɗa aka rasa wanda zaiyi mashi magana acikin su.. kamar yaso ya ɗago su amma sai yayi azan daga cikin baƙinsu ne da suka zo. Ƙarfin Hali Chief ya yi wurin furta, "Daga cikin baƙin kune, muna ƙarewa ginin kallo ne" Maraba ya yi masu tare da nuna masu ƙofar dakin da ya fito ya ce, "Ɗakin fiɗa ne, zamu iya shiga ciki idan kuna neman ƙarin bayani dangane da yadda muke gudanar da aikin mu." Ya faɗa tare da buɗe kofar dakin ya shiga suka bi bayanshi, sun yi matuƙar girgiza da ganin fursinonin dake a kwance kan gadajen ɗakin, Hada mata masu ciki, jikinsu sanye da fararen kaya, Ga wasu gungun Gigantes medici dake tsaka da yin aikin fiɗa a gaban gadon fursunan da suka farke cikin shi, har sannu da aiki suka yi masu, giant doctor din da ya shigo dasu ya gabatar dasu ga sauran yan uwansa likitoci kafin yace masu su ƙarasa ciki, Ya nufi gaban wasu manya-manyan furizozi Ya bubbuɗe su, sun razana sosai da ganin sassan jikin mutanan da suka feɗe masu yawan gaske.. Hankulansu sun tashi matuƙa sai dai basu yi gangancin da zai sa a gano su ba, bayani ya fara kora masu game da yadda suke feɗe mutun su cire sassan jikin shi da yadda suke amfani da shi har safarar sassan suke yi zuwa wasu ƙasashen su siyar da su. Chief da Big Guy sun harzuƙa matuƙa, jikinsu sai tsuma yake yi saboda tsabar fusata kamar su rufe shege da bugu. Kwatsam yana tsaka da kora masu bayani Taj ya yi su6ul da baka gurin furta, "Amma dai baku da imani" kaitsaye maganarshi da dira cikin kunnan Giant doctor din. Nan take ya dakata da kora masu bayanin da tsantsar ruɗani Ya furta,"Who are you?" Shiru suka yi, hakan ya ƙara ƙarfafa zarginsa akan su. Wata irin gigitacciyar tsawa ya daka masu tamkar zai fasa dodon kunnansu da karfi ya ce,"baku ji ina tambayarku bane? Su wanene ku huh?" Maganar da yake yi ce ta janyo hankulan sauran Giant doctors din dake aikin fiɗa, suka ajiye tiyatar da suke yi gaba ɗaya suka zagayesu kamar zasu rufe su da bugu, safunan hannayensu jaga jaga da jini.. Jin sunyi shiru sun ƙi basu amsa ne yasa ɗaya daga cikinsu ya kai hannu zai cire Mask din dake akan fuskar Chief, bai kaiga ƙarasa cirewa ba, Danish Ya zaro addarsa azafafe Ya datse hannunsa ya 6alle biyu jini ya dinga tartsatsi, koda ganin hakan sauran giants ɗin suka harzuƙa matuƙa, suka afka masu faɗa ya kaure atsakanin su, sun ci wahala kafin suka yi nasarar kashe su gaba daya suka zubar da gawarwakinsu akan floor. Sai haki suke suna nishi, Big guy ya dubi Taj da ya dafe cikin shi, "Next time kada ka ƙara maimaita kuskuren da ka yi, yanzu da ka ja mun rasa rayukanmu." daƙuwa Taj ya yi masa batare da ya furta kalma ba. Fursinonin dake a kwance kan gadajen suna ganin abunda ke faruwa saidai sun kasa tashi zaune saboda alluran da suka banka masu sun kashe kuzarinsu, kwayar idanunsu ce kadai ke motsi.. "Ya zamuyi dasu"? Big guy ne ya tambaya. Salsabeel Ya dubi Danish, "ka yi wani abu pls" duk suka maida hankali kanshi, shi kadai yasan me ya yi masu sai gasu sun miƙe kan ƙafafunsu. Basu tsaya 6ata lokaci ba, wasu daga cikinsu suka tafi da fursinonin... Fitowa sukayi daga ɗakin fiɗar, Suka faɗa dakin dake akusa dashi, nan fa suka ga abun da ya ƙara ɗaga hankulansu, jarirai suka gani a cikin containers, kamar bakwaini gwanin ban tausayi...Taj har ƙwalla saida ya zubda masu, Big guy ya ce, "ya zamu yi da su?" "Dan Allah mu taimaka masu, kada mu barsu anan" Taj ne ya faɗa. Salsabeel ya bashi amsa da, "Bazai yiwu ba, don ta yanzu, mu barsu kawai Allah yana atare da su." Fucewa suka yi daga ɗakin suka shiga ɗakin dake a gaba, rasss! gabansu ya hau faɗuwa ganin ɗarurrukan kwarangwal na mutane sagale jikin igiyoyi ga wasu nan zube a ƙasa har jikin bangon ɗakin ko'ina su ne na mutanan da suka kashe, wa'iyazubilla zuciyoyin su sun karaya ba kadan ba. Wata shari'ar dai sai A lahira wallahi. Kusan zagaye kurkukun suka yi saƙo da lungu suka dinga shiga, sune har cikin treatment rooms din kurkukun, anan suka ga majinyatan fursinonin da suka kwantar, sun ci baƙar azaba a hannun masu jinyar su wurin yin faɗa dasu, da ƙyar suka kashe su kafin suka ceci majinyatan suma. Saida suka gama kwashe fursinonin, kafin suka dawo baya, har sun kusa 6ula ground floor din da ake shagalin Chief Ya dakata da yin tafiya, kallon shi su ka yi, duk da basu san me ya hana shi cigaba da yin tafiyar ba, sun fahimci kamar Yana jin fargaban yaga wani dangin shi a cikin matsafan, dama da zargin mahaifinsa aransa ga kuma abun da ya faru tsakaninshi da tsohuwa Khala na furucin da ta yi akanshi. Idan muka koma bangaren Elders, sun shagala suna kallon karawar da matsafan su ke yi a tsakar fili, kowani matsafi ya zage damtse gurin nuna ƙarfin sihirin shi, dambe ne na fitar shari'a suke yi kamar zasu kashe juna, idan bala'e yayi bala'i har rikiɗa suke yi su koma dodanni su cigaba da dambatawa a tsakanin su. Saida aka zo zagaye na ƙarshe a wasan, Elders suka ji shiru ba'a zo da prisoners ba babu su babu alamar su... Da yatsa Elder Ya yi ma ɗaya daga cikin Evil giant din dake bayan shi alamar Ya matso kusa, sunkuyar da kanshi yayi saitin fuskar Elder... Cike da bada Umarni Ya ce, "Ka yi ma Giantesses magana, suzo da yaran da sauran kayan da aka tanada Yanzun nan...!" da buɗaɗɗiyar murya Giant din Ya amsa mashi da angama sir, daga Inda Yake bai matsa ba ya 6ace ma ganin shi. Bai dira a ko'ina ba sai a hall din da suka tara prisoners, Nan Ya ga abunda Ya tada hankalinsa, gawarwarkin da ya gani baje ƙasa na female giants dinsu, Ga Gawar tsohuwa Inno...aruɗe da yana yi na mamaki Evil Giant din Yake bin ɗakin da kallo kamar a mafarki, Fitowa yayi daga Hall din saboda dakakkiyar zuciya irin nasu, neman waɗanda suka kawo masu hari ya shiga yi, don Ya aika su lahira. Yana Cikin tafiya suka bangaji juna shi da wani giant, tun daga yanayin yadda yayi tangal tangal zai faɗi Evil giant din Ya gane ba nasu bane saboda giant basa bangazar juna. Da kakkausar murya ya furta"Wanene kai?" Rasss ya ji gabanshi ya faɗi, yan hanjin cikin shi suka kaɗa, baima san ubanda ya janyo shi wurin ba shi kaɗai batare da kowa ba gashi sam ya kasa yin wani yunkuri don ya ce ci kan shi, ware faffaɗan tafukansa evil giants ɗin ya yi da niyar Ya tarwatsa ƙoƙan kanshi sai dai kafin ya yi hakan baiyi aune ba Yaji dirar Zarto saman kan shi, kwatsa kwatsa Ya faffasa kan nashi Kafin Ya ƙwalƙwalo idanunshi yabar gangar jikin shi yashe a ƙasa, ajiyar zuciya Taj ya sauke wlh har ya fidda rai da rayuwa badan Allah Ya hankaɗo Danish ba da tuni evil giant ɗinnan Ya aikasa Barzahu. Duk da bawani sabawa suka yi da juna ba saida yaji kaunarsa ta shiga ranshi, cikin sanyin murya ya furta, "Thanks" Jinjina mashi kai ya yi tare da nuna mashi hanya, "Zamu iya tafiya." Bin bayanshi Taj yayi suka nufi sauran jami'ansu da sukai Basaja.. Jin shiru Evil giant din da suka aika bai dawo bane yasa Elder Sake tura wani, a karo na biyu yaji shiru bai dawo ba, wasa wasa har giant biyar suka aika basu dawo ba, lamarin ya ɗaure masu kai, Miƙewa elder ya yi Jan Wuya ya ce, "Ina zaka je?" "Ina so naje na duba Hall din, tayaya zamu aika mutun biyar shiru basu dawo ba, kada a yi abin kunya!" Girgiza kai Jan Wuya ya yi, "Ba kai yakamata ka je ba, bari na je na duba.." ya faɗa tare da miƙewa cikin takun ƙasaita ya fuce daga filin taron, bayan tafiyarshi, Elders suka Ji shiru shima bai dawo ba, hakan yasa Jan Harshe ya miƙe Ya tafi neman shi, shiru shima bai dawo ba, har saida ta kaiga gaba ɗaya Elders sun bar filin shagalin, Fitarsu keda wuya kwatsam! ba zato ba tsammani wata irin kururuwar Fashewar bamabamai ta karaɗe gidan kurkukun, Gaba ɗaya taron matsafan da ke a gurin shagalin babu wanda Ya tsira da ranshi, saboda mamayarsu aka yi sihirinsu bai amfane su da komai ba, Haka wuta ta dinga balbali tana Cin naman jikinsu, suka runƙa sakin wata irin kururuwar radadin azaba mai amon gaske. Har Cikin Kunnan Elders yayin da suka je hall din don su ga meya hana giants din da ake aika dawowa. Kowa ya shiga ciki wani irin burki yake ci sakamakon abun al'ajabin da idanunshi ya gani, a haka har suka haɗu su duka, Cak duk suka yi sun kasa yin wani ƙwaƙƙwaran motsi, da wani irin matsanancin mamaki da al'ajabi gami da ruɗanin tashin hankali suke duban junansu....ganin abunda basu ta6a zaton ga ni ba, ga kuma sautin da kunnuwansu suka jiyo masu. Wannan shi ake kira bazata!!! *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘 Kowa ya shiga ciki wani irin burki yake ci sakamakon abun al'ajabin da idanunshi ya gani, a haka har suka haɗu su duka, Cak duk suka yi sun kasa yin wani ƙwaƙƙwaran motsi, da wani irin matsanancin mamaki da al'ajabi gami da ruɗanin tashin hankali suke duban junansu....ganin abunda basu ta6a zaton ga ni ba, ga kuma sautin da kunnuwansu suka jiyo masu. Wannan shi ake kira bazata!!! Sun sha ruwan mamaki! Elder da ya gama ruɗewa ya ce, "Ni kaɗai nake ganin abun da idanuna ke nuna min? What the hell is happening? Who killed them? Where are our prisoners?" A tsawace ya ƙarashe maganar. Jan kunne Ya ce, "Abun da ɗaure kai! Anya ba farmaki aka kawo mana ba??" Jan wuya yana huci ya furta, "This can't be happening, it's not true. Ƙarya ne, I can't believe it! how is this possible?" "Zance Ya 6aci! Tabbas an kawo mana farmaki! Wasu sun shigo kurkukun nan, Kuma Ni na jiyo ƙara wadda ba tantama ta fashewar Bomb ce." Cike da tabbaci Jan le6e ya yi maganar.. "Kai! Ina ba zata ta6a sa6uwa ba, Ta ya ma har wani zai iya ƙetare dajin Evil forest ya shigo kurkukunmu bayan tsaron da muka sanya? Wannan zancen bazai ta6a zama gaskiya ba!" Jan harshe ne ya furta cikin ruɗanin zuciya. Gaba ɗaya sun ruɗe sosai ganin abun suke kamar a mafarki, bama su gasgata abunda idanunsu suka gani ba, da abun da kunnuwansu suka jiye masu ba. "Ina! bazai yiwu ba, wannan ba gaskiya bane, Muje Mu duba..." A cewar Jan Ido. Suna ƙoƙarin Juyawa katsam suka yi arba da Dakarun sojojin da ke shigowa cikin hall ɗin runduna guda suka yi masu ƙawanya, Hannuwan su ruƙe da muggan makaman da Khala ta rarraba masu. Wlh an shammace su, sun girgiza matuƙa, Ko a mafarki Elders basu ta6a tsammanin wannan ranar zata zo ba, Al'ajabi da rudani Ya hana su Iya furta kalma, sai jinjina kai sukeyi kamar wasu ƙadangaru. Mamakinsu tayaya akai har aka yi nasarar kawo masu farmakin bazata a gidan Kurkukunsu! Abunda ba'a ta6a gigin yi masu ba, Lallai yau alkadarin su Ya Karye, gaba ɗaya sun ruɗe da lamarin. Ɗaya bayan ɗaya suke kallon Dakarun Sojojin, Hankalinsu fa Ya ɗugunzuma ainin, amma saboda dakakkiyar zuciya da ƙarfin hali irin na Elders kawai sai suka fashe da wata irin mahaukaciyar dariya mai razanarwa, kai daga gani sun san me suka taka.. "Kun aikata babban kuskure!! Da har kuka shigo gonar mu! Wani tsautsayinne Yasa kuka kawo mana farmaki huh?" Jan Harshe ne ya faɗa yana huci. Jan Le6e ya amshe, "Rabon ajaline Ya kawo ku..." Bai ƙare maganar ba, dakarun sojojin suka dare tare da buɗe hanya, Ɗaya bayan ɗaya suka fara shigowa, ba su iya tantance fuskokinsu ba saboda masks da suka saka. Kallon kallon suka fara jefawa juna tsakanin su da Elders, tsabar yadda zuciyar Chief Owais ke bugawa kamar zata fasa ƙirjinshi saboda zullumin wanda zai gani a cikin danginsa tun kafinma ya ga fuskokinsu, haka shima Big guy hankalinsa ba a kwance yake ba. "Kune na farko da kuka fara kawo mana farmaki, amman hakan ba yana nufin kun ci galaba akanmu bane, ba zamu ta6a ƙyale ku ba, sai kun yi danasanin kuskuren da kuka tabka!!!" Da kakkausar Murya Jan Ido ya yi maganar. Tun da suka fara magana basu tanka masu ba, wani abu da suka lura da shi, Wasu daga cikin Elders ɗin sun ƙi yin magana, wannan yasa su zargin sanannu ne shiyasa suka ƙi magana don kada aji muryoyin su.. Big guy ne ya yi ƙarfin halin furta, "ELDERS, nayi farin Cikin ganinku, ashe dama ana iya ganin ku cikin sauƙi haka?" Ransu Ya 6aci da jin maganar shi, "Dalla dubeku, wasu bajimaye daku, ko kunya baku ji ba! Mutane marasa imani, wlh da ace tuntuni munsan da zamanku a doron duniyar nan wallahi da tuni mun jima da shafe babinku, mugaye, azzalumai marasa imani, yau dai dubunku ta Cika, wlh saikun ɗanɗani kuɗarku...!" Kalaman Big Guy sun yi matuƙar fusata zuciyoyinsu, tun da uwayensu suka haife su a duniyar nan wani ɗan adam bai ta6a tunkararsu gaba da gaba Ya faɗa masu kalaman 6atanci ba sai akan Big Guy. "Ni bansan ma da wani jinsi zan misalta ku ba, saboda ku ɗin Jakkunane, dabbama tafi ku kyan kai, gaku dai ƙazamai, saboda shafewar basiri da ruɗin duniya da son kai da zalunci kun manta cewa wata rana dole ku mutu kubar duniya ku koma ga mahaliccin ku, Wai ku anya kuna da zuciya a ƙirjinan ku? Wasu irin mugaye ne ku.......!" Taj da ya ɗauko maganar bai ƙare ta ba, sakamakon wata irin razananniyar tsawa da Jan wuya Ya daka mashi, tuni Ya haɗiye sauran maganar da bai idasa amayarwa ba.. Girgiza kai Chief ya yi, wlh takaici da baƙin cikin ganin Elders Ya hana zuciyarshi salama, Rai a matuƙar 6ace ya ce, "Mai kuke jira ne!" Ya faɗa tare da kallon dakarun sojojin su. "Ku kama su! Da ransu muke son su, dole su fuskanci hukunci mai tsanani!!!" Kamar Jira Sojojin su ke yi ya basu umarni suka fara ƙoƙarin kama Elders aikuwa kwatsam! Ba zato ba tsammani suka fara ganin wasu irin samudawan Evil Giants suna faɗowa cikin Hall ɗin masu yawan gaske, Kai da ganinsu sai gaban mutun Ya faɗi saboda ƙirar karfin su, gaba ɗaya su ka cika Hall ɗin, Sai gurnani su ke yi tamkar mayunwatan zakuna.. Sai lokacin Elder Ya buɗe baki ya ce, "Garkuwa, kayi tunanin bazan gane ka bane?" Sautin muryarshi ta canza kamar ta matashin saurayi, A hankali Danish ya cire Mask ɗin fuskarshi, Ya fuskance su da ainihin suffarsa ta jarumta, gaba ɗaya sun girgiza sun kuma kiɗima da ganin shi.... Cikin karyayyar murya Elder Ya kuma cewa, "Ni nasan ba yin kanka bane, tursamaka suka yi, kada ka manta baka da gata da ya wuce mu a duniyar nan, mune rufin asirinka, mu muka raineka muka gatanta ka, mu ka inganta rayuwarka. Ka manta irin gatanci da muka yi maka ne? Kada ka ce zaka Ci amanarmu.." Elder bai kai ga ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Chief Owais ya daka masa yana huci, bai kaiga furta kalma ba Jan Harshe Ya ɗaga masa hannu, "Karka kuskura ka ƙara maimaita kuskuren da kayi!! Ba a yiwa Elder tsawa! Idan Yana magana ba'a katse shi!" Wlh ƙarfin halinsu ya yi matuƙar ɗaurewa Chief kai. Cike da takaici Garkuwa ya ce, "Babu wanda ya tursasa mini, Ni nasa kaina, maƙaryatan banza, you've been deceiving me for a long time under the guise of privilege" ( ka daɗe kana yaudarata da sunan kune gata na!") Tuni idanun shi sun cicciko tab da ƙwalla, ga wani ɗaci da yake ji a ranshi. "Yanzu na riga da na gane cin zalun da kukayi mini, tsawon shekara ashirin tun ina jinjiri na kuka raba ni da iyayena, batare da sanin su ba, kun yi masu ƙaryar na mutu bayan ina raye, laifin me na yi maku??" Ya faɗa a tsawace kamar zai rufe su da bugu, wlh sun razana da jin abun da ya ce, basu yi zaton zai gano gaskiya ba. He was extremely angry, maganarsa ma daƙyar take fita saboda 6acin rai, "You never loved me, you hurt me and violated my right to live. Kun raine ni saboda biyan buƙatar kanku, da ace nasan gaskiya tuntuni, hmmm, da yanzu babu ku a doron duniyar nan, na tsaneku Elders...." Bai ƙare maganar ba, Jan le6e Ya tari numfashin shi da cewa, "Kai har ka kai matsayin da zaka Ci amanarmu? Ka manta duk wani abu da kake taƙama dashi agurinmu ka same shi! Ba don mu ɗin ba ina zaka samu ƙarfin halin tunkararmu har ka rako wasu don ku farmake mu? Dube ka dallah! Sun maida ka sauna, shashasha, sakarai sai yadda suka yi da kai..." Murmushin takaici ya yi batare da ya furta kalma ba, su Taj da ke sauraronsu kamar su rufe shaggu da bugu suke ji saboda zafin maganarsu, Salsabeel da ya gama fusata rai a 6ace ya zame mask ɗin fuskar shi don su ganshi da kyau. Nuna shi Elder ya yi da yatsan shi batare da ya iya furta kalma ba saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare maƙogwaron sa... Cikin zafin rai Jan Harshe Ya furta, "Maci Amana, dama nasan kana acikin su, bakasan cewa nemanka muke yi ruwa a jallo ba? Hmmm, na ji daɗin ganinka ɗan maciya amana, tun da har kayi kuskuren kawo kanka cikin kurkukun nan, to ka sani mun tanadanar maka azaba mai raɗaɗiii..." "Ta Allah ba taku ba, dama nasan kun ƙullace ni, naji daɗi dana dasa baƙin ciki a cikin zukatanku, ko ba komai mahaifiyata ta yi nasara akanku saboda itace silar komai...." tiryan-tiryan Salsabeel ya labarta masu shirin da suka daɗe suna yi akan ɗaukar fansar mahaifinsu Habibullah da suka kashe har izuwa taimakon da suka yi ma prisoners gurin tseratar da su, Haƙiƙa Elders sunji zafin cin amanar da suka yi masu, sai dai basu nuna hakan ba. Yar dariya Big Guy ya yi tare da cewa, "Na fahimci haushin su kuke ji saboda sun tona maku asiri, idan ku masu hankaline kuyi nazari mana, gaba ɗaya duk wani shirinku lalacewa yake yi...." "Ga misali nan kun gani, Danish yanzu namu ne, kun raine shi mu kuma zamu ci moriyar shi, garkuwar ku Ya juya maku baya yanzu mu yake goyon baya, kuma dashi zamu yi amfani gurin kawo karshen zaluncin ku" Ya faɗa tare da yi masu gwalo, aiko ransu Ya 6aci, zuciyarsu ta harzuƙa, Big Guy da ƙarfin hali Ya kuma cewa, "Wai ashe Elders ɗinma matsorata ne, naga kun rufe fuskokinku, In ba tsoro ba, ku buɗe mu ganku mana, Ko kuna jin tsoron kada mu gane su wanene ku?" Shiru suka yi basu tanka mashi ba. Sai da ransu ya kai maƙura a 6aci, suka harzuƙa ainun kawai Elder ya ba Evil Giants umarnin su farmake su, Kafin kace me faɗa Ya kaure tsakanin Sojojinsu da Evil Giants, wata irin ƙura da kururuwa ta karaɗe tsakar Hall ɗin, Bugun mutuwa suke yi ma junansu, Abu fa ya ture don ginin wurin har girgiza ya ke yi saboda bala'e, baka jin komai sai sautin naushi da ƙarar buge buge da sukar kibiyoyi. Lokaci ɗaya Hankulansu Chief ya fara tashi ganin yadda Evil Giants suke kashe sojojinsu, Jini sai ambaliya yake yi, Wani irin kisan rashin imani suke yi masu, cikin ƙanƙanin lokaci sun kashe sojojin sama da hamsin. Yayin da su kuma ko ƙwarzane babu wanda ya yi masu saboda Garkuwar kakin dake a jikinsu, bayan haka suna amfani da sihiri gurin 6acewa, sai dai mutun ya ji sun dira a bayanshi kafin ya ankare tuni suke farke cikin shi da akaifun su, Evil Giants Bala'e ne...! Shu'umin murmushi Elders suka fara saki, dama sun san bazasu iya karawa da Evil Gaints ɗinsu ba. Ganin suna neman su rasa Sojojinsu yasa Danish yin wata irin suka ya dira a tsakiyarsu, Da gudumar hannunsa Ya dinga tarwatsa kawunan su, da bugu ɗaya yake kashe su, kamar Allah Ya aiko shi, ganin haka yasa su Omar fara sakin kabbara da ƙarfin gaske suma suka afka cikin filin dagar, Cikin Ikon Allah sai gashi sun Ci ƙarfin Evil Giants ɗin, sun bada ƙaimi haiƙan a filin dagar, wani zungureran mashi ne a hannun Chief Idan ya saita shi ya jefa shi kaitsaye mashin yake soƙe kawunan Giants, a lokaci ɗaya sai mashin ya kashe giants sama da goma, da Evils din suka ga haka sai suka rikiɗa suka koma wasu irin mugayen dodanni masu zaƙo zaƙon akaifu suka fara farka cikin Sojojin da ƙwalƙwale idanuwansu. Duk fa abunda ke faruwa akan idanun Elders suna a tsaye suna kallon su, Abun da ya ɗaure masu kai, ganin makaman da suke faɗa da su yana tasiri akan Evil Giants ɗinsu, kuma abun mamakin da ya sha masu kai sun lura makaman kamar irin wanda maƙeran kurkukun ƙaddara suke ƙerawa ne, har sun fara 6ata rai ganin ana kashe nasu amma da suka ga Evil Giants din sun cigaba da kashe sojojin sai suka fara sakin dariyar mugunta. Bayin Allah sun ci baƙar wahala, kusan sau biyar Evil Giants suna kokarin kashe Taj sai dai Danish ya hana, duk yadda zaiyi ya kare shi ko ya kawar da shi sai ya yi don baison Unaisah ta rasa mahaifinta, Ya gwammace shi su dake shi akan su ta6a Taj, ba don shi ba da tuni Taj ya sheƙa barzahu. Big Guy kuwa da yake Allah ya zuba mashi ƙarfi shi da Chief Owais kuma sun ƙware wurin sanin dubarun yaƙi sosai hakan yasa ko ƙwarzane basu yi masu ba, kamar ana ƙaro masu Giants ɗin don daga sun kashe su wasu ke ƙara kurɗaɗowa ta jikin bango suke shigowa, Kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, Kwatsam! Suna tsaka da yin artabun nan wani shaiɗanin Evil Giant ya damƙi Big guy Ya daddage ya ɗaga shi sama kafin ya buga da ƙasa nan take Kan shi Ya fashe jini Ya fara bulbulowa.. Karaf akan idanun Chief, wani irin Ihu Chief Ya fasa ganin zai rasa amininsa, ya yi kukan kura Ya dira agaban Giant ɗin ƙazamin faɗa ya kaure tsakanin su, gaba ɗaya hankalin Sojojinsu baya akansu saboda kowan nan su hankalinshi ba a kwance Yake ba ganin abun na neman fin ƙarfin su koma a ce yafi ƙarfinsu, Giants sun mamaye su ba kaɗan ba.... Duk yadda Chief ya so ya kashe shi abun ya faskara, saboda wani kafirin ƙarfine da shi, da mugunta Giant ɗin ya sakar mashi naushi a tsakiyar cikin shi, nan take ya fara aman jini, duk da haka bai ƙyale Chief ba, Ya daddage ya buga kan shi jikin wani ƙarfe nan take goshinshi ya faffashe jini ya fara bleeding ta hancin shi. Hakan bai yi mashi ba, saida ya kai shi ƙasa ya damƙi wuyan shi ya fara jan shi a ƙasa ya tunkari wani kaskon wuta da niyyar ya tura kan shi ciki, gaba ɗaya Chief ya fita hayyacin shi ya kasa taimakon kan shi, a dai dai lokacin Danish ya ankara da abun da ke faruwa, ai baisan sa'adda Ya fasa ihu ya saki gudumar dake a hannunshi, sai dai me, kafin Ya kai mashi taimakon gaggawa wasu gungun Evil Giants suka rufe shi da bugun mutuwa suka hanashi motsawa, dama raunin shi suke jira, kamar zaiyi hauka. A can bangare guda kuwa Taj shima Ya gamu da nashi bala'en, wani ƙasurgumin shaiɗanine ya take cinyar shi da basamudiyar ƙafarshi, nan take kafar ta bada wani sauti rukukus kamar zata cizge, har fashewa saida tayi jini ya fara bulbulowa, Azaba goma da tara Ihun ma ya kasa yi sai juyi yake yi a ƙasa..... Salsabeel yana tsaka da yin faɗa ya zage damtse sai kashe su yake yi, bai aune ba yaji an damƙi damtsen hannun shi, da sauri ya juyo don ya ga wanene, rass! ya ji gabanshi ya yanke ya faɗi ganin ɗaya daga cikin Elders dama haushin shi suke ji.. Kafin ya yi wani yunƙuri Elder din da ya damƙesa ya murɗe hannun shi, azabar raɗaɗi ya hana ko ihu ya yi, naushi ya sakar mashi a gefen fuskar shi nan take jini ya wanke bakin shi, duk da haka bai ƙyale shi ba, sai da ya damƙi kanshi ya ja a ƙasa ya nufi matakalar bene ya buga kan a ƙasa, bawan Allah Salsabeel radadi ta ko'ina yake ji, saboda rashin Imani hakan bai masa ba, ya ɗaga ƙatuwar ƙafarsa da niyyar ya take kan nasa sai kuma ya fasa sakamakon wani abu da ya ja hankalin shi wanda ya ja har ya bar gurin salsabeel..... Evil Giant ɗin da ya damƙi wuyan Chief yana ƙoƙarin tura kanshi cikin kaskon wutar, Unexpected ya ji an damƙi hannun shi, Yana huci ya juyo karaf suka haɗa ido da elder, kafin ya furta wani abu Elder ɗin ya murɗe kanshi nan take ya kife ƙasa matacce, ba tare da sun ankara ba ya janye Chief daga filin dagar ya nufi ƙofofin dake a cikin hall ɗin ya wurga shi a cikin wani daki kafin ya ja ƙofar ya datse ta, babu wanda ya lura da hakan. Daƙyar Danish yafi ƙarfin Evil Giants ɗin da suka rurruƙe shi ya yi kukan kura ya watsar da su, jikinshi ya yi rauni sosai, sun faffasa kakinsa da ƙumbunansu har sun ta6a fatar shi, fuskar shi duk ta 6aci da jinin raunukan da suka ji ma shi. Wata irin jijjiga ya yi ya rikiɗa ya zama jibgegen Zaki.. Ya afkawa Giants, cikin zafin nama ya dinga kakkashe su ta hanyar farke Idanunsu, cikin ƙanƙanin lokaci ya kashe Giants sama da ɗari, gaba ɗaya ya zubar da gawarwakinsu ƙasa. Koda ganin haka nan fa Elders suka fara shan jinin jikin su.. ganin yadda Danish Ya salwantar da rayukan Giants ɗin su, ta ko'ina jininsu ne ke tartsatsi yana sauka ƙasan wurin kamar ƙoramar jini...ga yan hanjin cikin su waje sun zazzago, ransu ya 6aci matuƙa har ƙoƙarin sarrafa shi suka yi da sihirinsu don ya koma yana kashe sojojin don mugunta, sai dai wani iko na Allah Evils ɗin Danish sunƙi responding umarnin da suke basu, lamarin ya girgiza su ba kaɗan ba, sun rasa gane tayaya zasu shawo kan shi. Basu gama kaɗuwa ba sai ga tawagar U.s Army sun faɗo Hall din, Sun gama da matsafan da sukai saura sun dawo nan don su tayasu yaƙi, ashe duk wani bomb da ya fashe a filin shagalin U.s Armies ne suka dasa su. Bayan sun yi 6adda kama sun saka kayan matsafan da Khala ta basu, suka shige cikin matsafan dake a filin shagalin, Cikin hikima da ƙwarewa suka dasa bombs a saƙo da lungu na ground floor ɗin kurkukun, bayan sun tabbatar da Elders sun fita daga cikin filin dama haka suka tsara saboda basa son Elders su mutu a raye suke son su, da ganin fitarsu a hanzarce suma suka nisanta kansu da filin taron kafin suka danna remote din dake a hannuwan su nan take bama baman suka faffashe. Hankulansu ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin yadda aka kashe Sojojinsu, koda Elders suka ga sun ƙaru kuma zasu iya yi masu 6arna ba kaɗan ba ga Danish ya zamar masu masifa sai zubda jinin Giants yake yi, hakan yasa suka fara tunanin buɗe rijiyar da Jeremiah yake a ciki, saboda shi kaɗai ne zai iya ƙarar da su kaf cikin mintuna ƙalilan. Bawai don su basu da ƙarfin yin faɗa dasu bane, kawai rainine a gurinsu su yi gogayyar kafaɗa dasu gurin yin faɗa, sun fi so su nuna masu ƙarfin ikon su. Kafin su aiwatar da mummunan ƙudurinsu, tuni U.s armies sun haɗa hannu da Danish duk da ba a suffarshi yake ba sun fahimci shine sanin yana iya canza suffa kamar yadda aka sanar masu kuma gashi sun ga yana farmakar Giants, nan fa suka ci gaba da bada ƙaimi suka ci gaba da kashe Giants ɗin. Kafin ka ce me, tuni sun wanke Hall ɗin da jinin Giants ya malale ƙasa kamar ambaliyar ruwa...hakan ba ƙaramin tada hankalin Elders ya yi ba, ransu ya kai maƙura a gurin 6aci, Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar fusata, ga wani gurnani da suke saki kamar mayunwatan zakuna. Saida suka ƙarar da Giants ɗin, hankalin Danish ya karkarta akan su Taj, gaba ɗaya sun razana da ganin su cikin jini kamar babu rai, Cikin sauri ya nufi Big guy dake yashe ƙasa, ya taimaka mashi gurin ɗaure mashi kan shi da wani jan ƙyalle da ya tsinta a nan, sai nishi yake yi bawan Allah, Shi kaɗai yasan irin azabar da yake ji, daƙyar ma ya rayu. Jini duk ya wanke fuskarshi, cikin fitar hayyaci Ya furta,"Danish.... Chief, help him! I don't want him to die, go find him, I want to see him before I die...." Tsantsar tausayinshi ne ya kama su, duk da halin da yake a ciki damuwar shi akan Chief ne, wannan wata irin ƙauna ce 💔 "Danish ! Ina Chief?" Commender ne ya tambaye shi, Girgiza kanshi ya yi yana huci ya furta, "Bansan ina ya shiga ba, amma zan binciko shi." Ya faɗa tare da miƙewa, juyawar da zai yi keda wuya yaci karo da Taj wanda ke kwance cikin gawarwaki kamar ba numfashi a jikin shi, Hankalin shi ya tashi matuƙa, cikin sauri ya nufe shi ya taimaka mashi ya miƙar da shi zaune tare da jinginar da shi gefen Big guy, bawan Allah sai sambatu yake yi yana faɗin yar shi, ya bar masa amanarta, ya ruƙe mashi ita, baya so ta yi maraicin rashin shi, kalaman Taj sun karya zuciyar Danish, bai san sa'adda ya ji hawaye sun wanke fuskar shi ba. In a weak voice ya furta, "Ba zaka mutu ba, zaka rayu, Angel tana buƙatarka, bana so ta rasa ka...." Ƙafar Taj da ta lanƙwashe ya jata da ƙarfi ta bada wani irin sauti, tsabar raɗaɗin da Taj ya ji ne yasa shi sakin ihun azaba, nan take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme, duk Danish ya bi ya ruɗe, ya kasa gane yana raye ko ya mutu ne? Ya dai samu ya tsayar da bleeding ɗin cinyarsa. Miƙewa ya yi tare da kallon su Commender da sauran sojojin da suka rayu, gaba ɗayansu babu wanda bai raunata ba, sun jigata sosai, gaba ɗaya sun sare da lamarin. "Salsabeel!" Hankali a tashe Ya furta lokacin da idanunsa suka hango mashi Salsabeel kwance rai hannun Allah, da gudun gaske ya bi takan gawarwakin dake zube a ƙasa ya nufi gaban benen, yana isa ya zube kan ƙafafuwansa tare da tallabo kan Salsabeel, wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarshi ganin hannun shi dake a karye ƙiris ya rage ya 6alle biyu, ƙashi har ya 6ullo ta fatar, da ƙarfi ya fasa ƙara mai sautin gaske shatun jijiyoyin goshinshi suka fito ruɗu ruɗu kan fatarsa, Su Commender dake kallon shi jikinsu ya yi sanyi sosai kamar su zubda mashi ƙwalla saboda tausayi. Unexpectedly Ginin kurkukun Ya fara Jijjiga kamar zai 6a66ako, lokaci ɗaya kunnuwansu suka fara jiyo masu sautin wata shu'umar dariya ta tantirin shaiɗani mara daɗin saurare. Tunkafin ma su ga wanene suka sha jinin jikin su, saboda tashin hankali gaba ɗaya sun shafa'a sam sun manta da zaman Elders a hall ɗin waɗanda tuni sun jima da 6acewa, 6at babu su babu alamarsu, sun riga da sun san tsiyar da suka shuka, sun tafi sun bar su da masifa. Cikin hanzari Danish ya miƙe tsaye, zuciyarsa na dakan uku uku, yayin da rinannun idanunsa ke akan rijiyoyin dake a hall ɗin saboda yasan yana ciki. "Ina Elders suke? Sautin dariyar da muke ji ta wanene?" Canal Herry ne ya yi tambayar a ruɗe. "The Elders have disappeared, the only way to escape is to run away before the evil giant emerges from the wall, He's the most dangerous evil giant in the prison of Destiny, and their new prison shield, ba zaku iya ja da shi ba, Ku barni da shi, In ba haka ba, zaku rasa rayukan ku ne!" Wani irin faɗuwar gaba suka ji, kafin wani daga cikin su ya motsa, Unexpectedly murfin ɗaya daga cikin rijiyoyin ya 6alle da karfi tattare da iska ya yi sama kafin ya ƙundumo ƙasa, gaba ɗaya suka zare ido suna jiran ganin menene zai biyo baya. A firgice Danish Ya dinga yi masu tsawa yana faɗin su tafi! su barshi da shi, amma suka ƙi tafiya saboda bazasu Iya barinshi shi kaɗai ba. Lokaci ɗaya wani irin hayaƙi mai haɗe da tartsatsin wuta ya fara fitowa daga cikin rijiyar tuni suka sha jinin jikin su, ashe basu ga komai ba, lokacin da basamudan shaiɗanin ya duro daga cikin rijiyar kusan suman tsaye suka yi tsabar razana da kiɗima. Wani irin zabgegen mutun, kwata kwata babu sutura a jikin shi, zir yake haihuwar uwarsa, gaba ɗaya jikinshi zanen tattoo ne da zanan aka yi mashi sutura, Ga wasu zaƙo-zaƙon akaifu masu kama da tsinin mashi, lokacin da ya buɗe idanun shi ƙiris ya rage su commender su arce a guje saboda wani irin jajayen idanu gare shi, Idan ka kalleshi sau ɗaya ba zaka ƙara marmarin haɗa idanu da shi ba saboda tsoratarwar da gare shi. Bakowa bane wannan face sabon Garkuwar kurkukun ƙaddara wato JEREMIAH. Da ƙarfi commender ya ba sojojin da suka rage umarnin su fara harbin shi, saita shi suka yi da bindigu suka dinga sakar mashi wuta ta ko'ina sai dai ko gizau baiyi ba, har bomb suka wurga mashi ya gangara agaban shi, ya ɗaga faffaɗan tafin ƙafarsa ya murje bomb ɗin, koda ganin haka ai saifa jikin taƙaura ya yi La'asar! Tun fitowar shi daga rijiyar idanun shi na akan Garkuwa shi kaɗai yake hari, dama da niyyar ɗaukar fansa suka ƙirƙire shi, girgiza jikin shi yayi tare da sakin tsawa mai kuwar gaske, tamkar zai fasa dodon kunnuwansu, duk saida suka girgiza. Tsautsayi ne ya kai wani soja gaban shi ya ɗaga wuƙa zai caka mashi aikuwa ya damƙi wuyanshi, nan take ya tsinka shi biyu, jini ya dinga tartsatsi ya jefar da gangar jikinsa gefe ɗaya, ai koda ganin hakan nan fa suka fara Ja da baya In ka cire Danish shi kaɗai ne bai motsa daga inda yake ba, ƙarasowar shi kawai yake jira. Da gudu wasu sojojin suka nufe shi, tunkafin su karasa ya matse yatsun hannayenshi nan take jikinsu ya faffashe kamar anyi jajjagen kayan miya... Waro idanu waje su Commender suka yi, lamarin ya gigita tunanin su, basu ta6a ganin bala'e da musiba ido da ido ba sai yau da Allah Ya haɗa su da Jeremiah. Gaba ɗaya gurnanin Jeremiah ya addabi kunnuwan su, Danish dake atsaye ya rasa abun yi, yasan muddin Jeremiah ya baro bakin rijiyar wlh sai ya kashe su kaf ɗinsu da ido kadai zai iya salwantar da su. Shiru ya yi yana yanke shawara da zuciyar shi lokaci ɗaya ya fara tariyo kalaman Unaisah sai ya ji kamar a lokacin take furta mashi su, _I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_ Yana so ya gana da tsohuwa khala saboda yaci burin ta faɗa mashi su wanene iyayensa yana matuƙar son ya gansu fiye da komai na duniyar nan, yana kuma son ya rayu saboda Unaisah, amma ya zai yi? Baida wata mafita da ya wuce ya aiwatar da abun da yake ganin dai dai ne. Su Commender sai kiran sunanshi suke yi don su ji me yakamata su yi kafin Evil din ya farmakesu, Hankalin shi baya atare da su, gangan jikinsa kaɗai suke gani amma ruhinsa yana atare da Unaisah... Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira ƙafarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana ɗaga ƙafarsa kafin Ya dire ta ƙasa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana ƙarasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya ƙarfin shi na ƙarshe ya ingizasu gaba ɗaya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kanshi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!😭😭😭 Da ƙarfi suka dinga ambaton sunan Danish kamar zasu fasa ihu saboda tashin hankalin kada su rasa shi, da gudun gaske su Commender suka nufi rijiyar, suka haɗa hannu duka Sojojin suka fara kiciniyar 6alle murfin, saida ina, abun ya ci tura saboda murfin rijiyar mugun ƙarfene da aka tsaface shi, haka suka dinga zubda gumi suna ta haki tare da jan murfin don ya buɗe amma duk a banza. Duk irin jarumtakarsu ta sojoji saida suka fashe da kuka tamkar ransu zai fita, babu irin makamin da basuyi amfani da shi ba don su buɗe murfin rijiyar abun yaci tura, har bomb suka ɗaura saman murfin don ya buɗe suka ja da baya tare da duƙewa ƙasa, sai dai koda bomb ɗin ya fashe babu abunda murfin rijiyar ya yi. A gaban rijiyar suka zuzzuƙunna cike da takaicin rasa Danish da suka yi, Suna tsaka da tashin hankalin nan, saiga Chief ya duro ta tagar ɗakin da Elder Ya garƙame shi, daƙyar yake jan ƙafar shi, jini duk ya wanke fuskarshi da gaban kakinsa, babu inda bai raunata ba ajikin shi, hankalin shi ya tashi da ganin gawawwakin rayukan da aka salwantar, nan take ya fara jin matsanancin faɗuwar gaba da tashin zuciya gami da ruɗani... Kalmar farko da ta fara fitowa a bakinsa shine Ina Danish? Ina Omar? Ina Taj da Salsabeel?" Shiru sojojin suka yi an rasa wa zai bashi amsa saboda fargaban halin da zai shiga, cikin rauni na murya ya furta, "Wai baku ji ina magana ba? Ina Danish ne?" Cikin karyayyar murya Commender James ya ce, "Omar, da Taj da Salsabeel, sun raunata sosai, bamu da tabbacin suna a raye ko sun mutu," Ya faɗa tare da nuna mashi inda suke, daƙyar ya iya hangosu, Cikin sanyin murya ya ce, "Shi fa Danish yana ina?" Kallon juna su ka yi batare da sun furta kalma ba.. "Kada kuce min ya mutu! Meyasa nake ganin hawaye akan fuskokinku?" A wahalce yake yin magana, daƙyar Major ya bashi amsa da cewa, "Kayi haƙuri Sir, bamu da tabbacin yana araye ko ya mutu...." "Yana Ina ne??" Ya faɗa kamar zai saka masu kuka, da hannu lieutanant Jackson ya nuna mashi rijiyar. Kafin ya labarta mashi abunda ya faru na baiyanar Jeremiah ya ƙara da cewa, "Mun yi iyakar bakin ƙoƙarinmu, sai dai mun kasa buɗe murfin rijiyar, gaba ɗaya bamu ji daɗin abunda ya faru ba, saboda mu rayu, ya sadaukar da kan shi...." Ya faɗa hawaye cike tab da idanun shi. Cikin rauni na murya Thompson ya ce, "I've never seen a braver person than him, He's the real hero" Captain ya ɗaura, "Ni kaina na jima banga mutun mai jarumta irin nashi ba, Ya cancanta ya rayu amma tayaya zamu iya taimakon shi..."? Idanunshi cike tab da ƙwalla ya ƙare Maganar, jiri Chief ya fara gani a cikin idanun shi, duk irin juriyarshi saida ya fashe da kuka mai sauti kamar ƙaramin yaro, a sukwane ya zube kan gwiwowinsa ya kifa kanshi ƙasa kamar zai haƙa ƙasa ya binne kanshi saboda wutar baƙin cikin da ke ruruwa acikin zuciyar shi, da sauri su commender suka kewaye shi don su lallashe shi amma ina zuciyarshi ta kai maƙura, Yunƙurawa yayi ya miƙe da sauri suka rurruƙe shi, idanun shi a rufe yake tambayar Ina Elders? Suna a raye ko sun mutu?" Commender Haroon Yace, "Sun 6ace ma ganin mu, ina da tabbacin sun gudu daga gidan kurkukun nan." Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya, ji yake kamar ya kurma ihu ko ya samu ya fitar da abunda ke ranshi, bakowa ya faɗo mashi a rai ba face tsohuwa Khala yasan zata iya taimakon su. Sai da ya fara umurtar wasu daga cikin sojojin yace su ɗauki su Taj su tafi da su, a kafaɗa suka rataya su, basu tsaya 6ata lokaci ba, cikin sauri suka nufi hanyar da zata sada su da ɗakin tsohuwa khala, sai dai me, kwatsam! suna tsaka da yin tafiya gaba ɗaya hasken gidan kurkukun ya ɗauke ɗuff, wani irin duhu baƙiƙƙirin Ya mamaye idanun su, Cikin sauri suka zaro Torchlight ɗin su tare da kunna su haske ya ɗan wadata kaɗan. Dakatawa Chief yayi da yin tafiya, gaba ɗaya suka kalle shi, tsantsar tashin hankali suka gani akan fuskarshi, a ruɗe ya furta, "Kun kira pilots ɗinmu dake a waje" Gabansu ne ya faɗi, wlh sham sun shafa'a basu tuntu6e su ba, balle su ji meke faruwa a can, sun san tabbas za'a iya farmakarsu tun da Elders sun 6ace. Cikin sauri Commender ya zaro tactical radio ya kanga a bakinsa, kusan sau uku yana kiran sunayen matuƙan nasu shiru ba'a amsa mashi ba.. A hanzarce Chief ya ciro wayarsa ya kanga a baki da ƙarfi ya dinga furta sunayensu nan ma shiru, wa'iyazubillah! Tamkar zai fashe da kuka ya furta, "Taya zamu san meke faruwa da sauran sojojinmu da muka bari a waje!" Dafa kafaɗarsa James ya yi, "Ku kwantar da hankalinku, ba lallai abunda kuke hasashe ya zamana gaskiya ba, zai iya yuwuwa matsalar network ne, saboda na fahimci network da suke amfani da shi iya cikin kurkukun ne yake aiki, wanda ke a ciki bazai iya kiran na waje ba, haka shima wanda ke a waje bazai iya kiran wanda ke a cikin kurkukun ba..." Commender da ya yi maganar ya faɗane don ya kwantar masu da hankali amma shi kanshi yasha jinin jikin shi. Cike da takaici chief ya ja tsoki kafin suka cigaba da tafiya, a ƙalla sun karya kwana ya kai takwas kafin suka kawo kan dogayen benayen nan, aikuwa suna hawa benayen suka fara maidosu baya, idanunsu suka fara yi masu gizon yan uwansu da suka bari a gida suka dinga ganin su a kan hawa na uku Giants sun rurruƙe su suna kokarin wurgo da su ƙasa. "Daddy, don't let them kill me! Help me, Daddy" Dafe kai commender Jemes ya yi jin muryar yarsa tilo, saboda ruɗu da tashin hankali ya fara kokarin komawa hawa na ukun don ya taimaketa, damƙar hannunsa Chief ya yi, sai hauka hauka yake yi yana faɗin ya sake shi zai je ya ceci ƴarsa... Chief yana fitar da huci ya ce, "Ka manta abunda Danish Ya faɗa mana, kafin zuwanmu gidan kurkukun nan? Abun da kake gani ba gaskiya bane, sun yi hakanne don su razanar da mu..." Yana ƙoƙarin shawo kan Commender James batare da sanin shi ba, Major smith ya watsa da gudu ya haura hawa na uku, ganin giants ruƙe da matarshi mai tsohon ciki sai kuka take yi tana miƙo mashi hannu don ya taimake ta. Yana ƙarasawa gaban benan Giants ɗin suka jefo da ita, aikuwa cikin fitar hayyaci ya daka suka ya bi bayanta don ya ceto ta, kafin su ankara tuni Major Smith ya kife ƙasa nan take kanshi ya fashe ko shurawa bai yi ba ya mutu, matar da yabi dama babu ita gizaune kawai Giants ɗin ma duk sun 6ace babu su. Zuciyar Chief ta karaya sosai, commanders da sauran sojojin jikinsu yayi mugun yin sanyi, wlh sun ji baƙin ciki da takaicin rasa sojan su, Kamar su ɗaura hannu akai su fasa ihu, don ma jarumta irin na sojoji ba yau suka fara ganin irin tashin hankalin nan ba.. Dafa kafaɗar Commender Chief ya yi in a cool voice ya furta,"I'm really sorry..." Girgiza kai Commender ya yi, "Kada ka damu, ajalinshi ne ya yi, ba mu isa mu hana shi mutuwa ba, balle muda muke sojoji dama saida muka bayar da rayukanmu kafin muka kar6i aikin, sannan duk rashi da muka yi bai kai naku ba..." Da ƙyar suka shallake benan suka ci gaba da tafiya suna haska hanya da torchlight ɗin hannunsu, wani abun tashin hankalin duk in suka haska bango sai sunga inuwar Evils. Wani sa'in har gifcin shaiɗanun suke gani...amma da yake zuciyar su ta kangare sun ma daina jin fargaban komai...gaba ɗaya ginin nema yake ya juye masu lissafin ƙwaƙwalwar su sun kasa gano hanyar da ɗakin tsohuwa khala yake lalube kawai suke a duhu, suna tsaka da tafiya kwatsam saiga wata tsohuwa kamar mahaukaciya ta faɗo ta gabansu hannunta tallabe da tsohon cikinta, sai kuka take yi tana roƙonsu su taimaka mata naƙuda take yi, abunka da me tausayi Chief har ya yi niyyar taimaka mata zuciyarshi ta raya mashi, "karka kuskura! kai baka ga ta yadda ta faɗo gaban ku ba..." Kafin ya yanke shawara da zuciyar shi tsohuwar ta daka suka ta haye kan Thompson ta dinga yakushin shi da cizon fuskar shi, cikin xafin nama Chief Owais ya damƙi ƙeyarta ya 6am6areta daga jikin Captain ya daddage ya buga kanta da ƙasa, kafin ta ɗago Commender James ya sakar mata harsashi a tsakiyar kanta, nan take ta sheƙa... Kallon Thampson suka yi, fuskarshi ta yi jaga jaga da jini gwanin ban tausayi, haka suka dinga cin karo da tsoffin mata matsafa sai hari suke kawo masu, ɗaya bayan ɗaya suke kashe su. Sai da suka gama shan baƙar wahala duk sun jikkata daƙyar suka gano ɗakin tsohuwa Khala, tun kafin su shiga gabansu ke faɗuwa ganin ɗiɗɗige-ɗiɗɗigen jini kan benan da zai kai su ɗakin nata. Kallon kallo suka jefawa junansu, an rasa wanda zai fara shiga ɗakin saboda zullumi da fargaban abunda zasu taras.. Sun shafe mintuna biyar a bakin ƙofar ɗakin batare da sun iya ta6uka komai ba. Daƙyar Chief ya yi ƙarfin halin tura ƙofar da sunan Allah a bakin shi ya zura ƙafarshi, su Commender suka bi bayan shi. Wani irin burki suka ci, ganin babu khala aɗakin ta, abun da ya jefa su a matuƙar ruɗani gaba ɗaya ɗakin nata a hargitse yake, hatta gadonta ya jirkice, tukwanan furannin dake a ɗakin duk an faffasasu, Ga jinin da ya malale kasa... YA ILAHI❗❗ *INA TSOHUWA KHALA❓* INA PRISONERS DIN DA SUKA KU6UTAR❓*IN BAKU MANTA BA ITA TA CE SU KAWO YARAN DA SUKA KU6UTAR WURIN TA GASHI BABU ITA❓* *MEKE SHIRIN FARUWA NE❓* *MEKE FARUWA TSAKANIN JEREMIAH DA DANISH BAYAN SUN FAƊA RIJIYA❓KUNA TUNANIN ZAI RAYU❓*SHIN YA BATUN BIG GUY, TAJ DA SALSABEEL WADANDA A HALIN YANZU BAMU SAN TAƘAIMAIMAI SUNA A RAYE KO SUN MUTU❓😭* *SU CHIEF ZASU FITA LAMI LAFIYA DAGA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA❓* *INA ELDERS*❓ *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*[14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: ______________________________🔥💫 Wani irin burki suka ci, ganin babu khala adakin ta, abun daya jefa su arudani gaba ɗaya dakin nata a hargitse yake, harta gadonta Ya jirkice, tukwanan furannin dake a dakin duk an faffasasu, Ga jinin dayake malale kasa.. YA ILAHI❗❗ Alkalamina bazai Iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba. Sun rasa gane meya faru da tsohuwa khala? Jinin wanene suka gani a kasa? babban abun da suke ma zullumi Fursinonin da suka turo akawo gurin ta, basu san awani hali suke ciki ba, fargabansu kada ace jinin fursinonin ne! badan zuciyar Imani ba da tuni Chief Ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin da Elders suka kunsa masu. La66ansa na kerma ya furta"La'haula walaqu wata Illah Billa, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un....." wani irin zafi jikinshi ya dauka rau... Cike da ruɗu Commender James Ya furta"ni fa bangane ba, meke faruwa ne? Ina prisoners din da muka kubutar? Ina tsohuwar take? Jinin menene wannan"? ya faɗa yana nuna jinin dake malale kasa... Yawu mai ɗaci thompson Ya hadiya ga radadi daya addabe shi, cikin sanyin murya yace"bana fata abunda nake hasashe ya zamana gaskiya, Zai iya yiwuwa Matsafan ne suka kawo mata farmaki watakil sun gano hada sa hannunta gurin kawo masu farmaki..." bai ƙare maganar ba, Chief yai hanzarin katse shi ta hanyar girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya furta"in kuwa hakane Elders sun kashe ni, sun gama dani..." kamar zautacce ya dinga nanatawa Kanshine ya fara juya mashi wata irin juwace ta fara kokarin daukar shi da sauri Ya dafe bangon dake abayan shi, Yana huci hadi da jan numfashi kamar mayunwacin zaki.. "Ba zamu bar Nigeria ba, har sainaga bayan Elders, dole su fuskanci mummunan hukunci mai tsanani" rai a6ace commender James ya fada... "Me yakamata muyi yanzu? Bana bukatar mu 6ata lokaci gurin nemo su"! Commender haroon ne ya fada... Captain lewis Yace"Where should we begin searching for them? Do you think they're still in this prison?" Dukansu fa arauna ce suke, gabban jikinsu duk sun raunata ga yunwa da bacci dole su jigata tun dare ake gabzawa har gari ya waye batare da sanin su ba, amma saboda karfin hali irin na soja, burinsu su karasa aikin da suka dauko bata kansu suke ba, dare guda ba bacci sai zallar tashin hankali...." "I don't think they're here, We should return to Nigeria and devise a new plan, we've lost our soldiers, and we're too weak to fight them now. We need to know what's happening with the soldiers we left outside" (bana tunani suna nan, ni dai shawarar da zan bamu shine mu koma Nigeria, In yaso saimu sake sabon shiri, tunda yanzu duk mun rasa sojojin mu, Mu kanmu a raunace muke bamu da karfin da zamu iya yin faɗa da su a halin yanzu" acewar lieutanant Jackson) Numfasawa Chief yayi"in sha Allah, karshensu ne yazo tun da har mu ka yi nasarar shugowa kurkukun nan, kuma mun yi masu barnar da ba zasu iya gyarata ba, nasan sun tsoratane shiyasa suka gudu, hakan ma wata nasarace...." ya faɗa yana jan numfashi kafin Ya ɗaura da cewa"Zaku Iya tafiya amma ni bazan Iya barin kurkukun nan ba, saboda ɗan uwana Danish, zan jira har zuwa lokacin da Allah zai fiddo dashi daga cikin rijiyar zamu dawo tare da shi..." ya faɗa idanun shi cike tab da kwalla, tsananin tausayin shi ne Ya kamasu, commender james Ya dafa kafadarshi Cikin kwantar da murya yace"ka yi hakuri Chief, bana tunanin zai rayu acikin rijiyar nan, ka daure kayi hakuri ka lallashi zuciyar ka, Mu tafi kawai..." Zafafan hawayene suka wanke fuskar sa, wlh kallonsu kawai yakeyi yasan bazasu ta6a jin irin kunar da zuciyarshi keyi mashi ba. cikin karyayyar murya ya furta"Bazan Iya tafiya ba, tayama zan tafi in bar Danish acikin rijiya tare da wannan Shaidanin? What if he kills him?" Girgiza kai yai"Idan Nayi haka banyi mashi adalci ba, saboda mu rayu ya jefa kanshi cikin haɗari, sai kuma mu tafi mu barshi? Dakyar ya kare maganar, daurewa kawai yakeyi, cike da tausayinshi su ke kallon shi, su kansu hawayen ne cike tab da idanunsu. "Abun da nakeso ka fahimta, Danish Ya sadaukar da kan shine don mu rayu! Idan har muka bari muka rasa ranmu hakan na nufin burin shi bai cika ba, pls ka jure ka rungumi kaddara" acewar Commender Haroon. Girgiza kai yai"ba zaku fahimce ni ba! But Danish deserves to live, wai shi mema Ya mora a rayuwarsa ta duniyar nan? Ya zo awahalce yanzu kuma kuna nufin in barshi Ya mutu? Shikenan fa ya mutu baisan iyayen shi ba, Bai ta6a jin dumin mahaifiyarshi ba, Baisan menene dadin iyaye ba, idan Uncle hateem Ya kirani ya tambayi ina yaronsa wata amsa zan bashi? kai Ina, wlh bazai yiwu ba dole naje na ceto rayuwar sa koda zan rasa rainane..." da alama chief owais Ya fara zaucewa sai sambatu yakeyi masu marasa kan gado, kafin su gama yanke shawara da zuciyarsu chief yai hanzari juyawa da gudu Ya fuce daga dakin da niyar ya koma gurin rijiyar, da gudun gaske suka bi bayan shi cike da tashin hankali suke ƙwala mashi kira haɗi dayi mashi magiya akan ya tsaya kada yaje amma ko waiwayen su baiyi ba, saboda Idanun shi sun makance Danish kawai ya ke son gani, bawan Allah kusan sau hudu yanayin tuntu6e Ya fadi kasa ahaka zai mike Ya cigaba da gudu, Yana kokarin shan wata kwana kwatsam ba zato ba tsammani ginin Kurkukun Ya fara Jijjiga kafin kace me tuni ginin ya fara tsastsagewa, hankalin Su commender ba karamin tashi yayi ba, akan idon su komai ke faruwa yayin da Chief kwata kwata bai lura ba saboda baya acikin hayyacin sa. wannan shi ake kira da tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, wasu irin marmarar duwatsun da akayi ginin ne suka fara 6a66akowa daga sama Kaitsaye suke rubzowa ƙasa da wani sauti suka tartwasewa, duk wanda kuwa tsautsayi yasa suka afkwa kanshi tofa Ya tashi aiki. Chief daya rikice bai kaiga isa hall din ba, Wani Gingirimeman dutse Ya yanko mai girman gaske Gaba daya ya zube ƙasa, ya shiga tsakanin chief da hall din, ras gaban shi ya faɗi ya zare reddish eyes dinsa sam ya kasa motsawa, Wlh zuciyarshi ta gama karaya ya riga daya fidda rai da Danish. Saboda ya rude kokari yake ya nemi hanyar da zai bi ya karasa ga hall din, wani ginin ne ya zazzago daga saman ceilling din dayake batare daya ankara ba, Cikin zafin nama commender james Ya damƙi damtsen hannun shi ya jefar da shi gurin Su captain da sauri Suka rurruke shi Yana kuka Yana kokarin fisge kan shi daga hannunsu ahaka suka sanya karfi gurin ingiza shi. bawan Allah sai waiwayon ginin hall din daya rushe yakeyi..Yana ji Yana gani ahaka suka tafi da shi kamar yayi hauka sai sambatu yakeyi _tun da na fara aiki ban ta6a faduwa ba sai yau da nagaza taimakon ka, Naji kunya Danish, i'm a looser, ka sani ba kai kadai bane danish, Kana da Allah kuma kana da dani, Danish bazan bari ka mutu ba, zan dawo Danish, zan dawo dole na ɗaukar maka fansa..........😭😭😭_ (Finally Su Chief Sun yi nasarar fita daga kurkukun kaddara bayan kalubalen da suka fuskanta) *__________________________ELDERS 🔥* A zazzaune suke kan Sofas cikin wani Daki mai duhu, saika kura ido zaka Iya ganin su da taimakon wutar Candles dake Ci, round table din dake agaban su shake Yake da kwalaben Giya sun sha sun bugu har ta kai masu karo. Idanunsu sun kaɗa jawur kamar jan gauta, fuskokinsu babu annuri ko miskala zarratin basu taba fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba, sunyi babbar asara ba kaɗan ba.....❗ "Sune na farko da suka fara kawo mana farmaki! sun latata ginin da nayi wahalar kafawa tsawon shekaru! Sun san komai da muke aikawata, sun san sirrin mu, sun gani da idanunsu, sun kuma kashe rabi da kwata na Giants din mu, bayan irin 6arnar da sukayi mana na, sun 6ata shagalin black Night, sun kashe dubban matsafan da basu ji ba basu gani ba..." ya faɗa yana jan numfashi cikin fushi, kafin ya daura da cewa"hakan bai ishe su ba, sai da suka kwashe Fursinoni da muka raina tsawon shekaru don mu amfana da su, sun tarwatsa duk wani shirin mu" "Yaron da muka raina da hannun mu don ya zama garkuwar mu yaci amanar mu ya koma garkuwar su, tsohuwa Tamira da Salsabeel haka suma suka ci amanarmu, abunda yafi karya min zuciyata, wadda na damƙa ma yarda ta da amanata, hada ita cikin waɗanda suka bada gudummuwar kawo mana farmaki! meke shirin faruwa da mu ne? Meyasa waɗanda muka yarda da su suke cin dunduniyar mu"? bai karasa maganar ba Yana huci Ya ɗaga kwalbar giyar dake a hannun shi Ya rotsa ta kan table din gaban shi nan take ta tarwatse. Ran Elder yayi mugun 6aci, a wannan gabar komai zai iya faruwa. Hankulan sauran Elders din ba ƙaramin tashi yayi ba, wata irin kururuwar ihu Ya fasa tare da tallabe kan shi da tafukan sa. Lallashin shi suka fara yi cikin kankan dakai da girmamawa dakyar suka shawo kan shi. Gyaran Murya Jan harshe yai kafin ya furta"Karaya ba tamu bace, Ba'a san elders da rauni ba, har yanzu muna da damar da zamu Iya dawo da ran kurkukun ƙaddara...." bai ƙare maganar ba, Elder Yana huci Ya tari numfashin shi da cewa"tayaya zamu iya yin hakan? Bayan sun riga da sunsan komai, sanin ka ne muddin wani yasan sirrin inda muke yin tsafinmu abu na farko da zai faru lalacewar ginin kuma ya riga daya faru, abu na gaba shine karyewar sihirinmu In har hakan ta faru cikin sauki zasu shafen tarihin da muka daɗe muna kafa shi...."gaba daya sukayi shiru suna sauraranshi, da alama sun kadu sosai. dakatawa yayi da yin maganar wani irin kululun bakin ciki da takaici ne ya tokare makoshin shi"a matsayin mu na mashahuran da duniya tasan da zamammu, abun kunyane asan me muke aikatawa, Ina jin tsoron mu rasa kimarmu da darajarmu fiye da yadda nake jin tsoron mutuwata, mutuncinmu zai zube a idon duniya, girmamamu da mutane suke yi suna ganin martabarmu zai tashi abanza, daga nan basai nayi maku bayanin abun zai faruwa ba, kun riga da kunsan sakamakon bazai ta6a yin kyau ba..." ya fada yana binsu da kallo daya bayan daya. bakowane daga cikin su ya karaya ba, shi dama Elder mutunne mai wata aƙida tun fil azal baya son duk wani abu da zaisa mutuncin shi ya zube yana girmama ƙimarsa. muzkutawa Jan le6e yayi kafin da wata irin muryar mai tattare da zafin fusata Yace"garkuwar kurkuku Ya zama garkuwar Fursinoni, ƙaddarar kurkuku ta zama mummunar ƙaddara agare mu, babban kuskuren da muka tabka shine barin tsohuwa Tamira da ranta, a lokacin da muka kashe Habibulllah, da mun sani mun haɗasu duka mun kashe su, shima garkuwarmu da ace bamu kawo ƙaddara gidan kurkukun mu ba, nayi imanin bazai ta6a cin amanar mu ba" ya ɗan dakata da yin maganar yana mayar da numfashi kafin yaci gaba da cewa"ita kuma Khala Elder Kayi hakuri da abunda zan faɗa, tunkafin zuwan wannan lokacin saida muka baka shawarar ka kasheta saboda ita din tana da kyakkyawar zuciya kuma tana ƙyamatar abunda muke aikatawa amma saboda kaunar da kake mata, shi yaja har ka gaza Yanke mata hukuncin daya dace" Cike da danasani Elder ya sunkuyar da kan shi ƙasa, tunda suka fara magana, Jan wuya Yana a kishingide Yana binsu da kallo babu alamun kaɗuwa atare da shi, shi kuwa Jan kunne kamar yafi su shiga damuwa dama duk cikinsu shine mai raunin zuciya. Jan Ido Yace"kada ku bani Kunya, duk wani abu daya faru ya riga daya faru, Mu fa Elders ne, babu wani mahalukin daya isa yaga bayan mu, abun nawa muka aikata bamu ta6a karaya ba sai wannan lokaci don kawai wasu kananun kwari sun kai mana farmaki? Rai nawa muka salwantar? Ya fada cike da gadara. "sai wadannan zasu gagaremu! In har muna so mu dawo da karfin ikonmu dole mu bi abun da allon tsafinmu ya nuna mana, dole mu aiwatar saboda itace dama takarshe da ta rage mana wadda zamuyi amfani da ita gurin dawo da ran kurkukun ƙaddara" Ya faɗa tare da dan dakatawa yana dubansu"a wannan karon dole mu cire sonkai atsakaninmu, bi'amana mu kashe duk wanda Yasan sirrinmu koda mafi soyuwa ne agaremu..." sarai Elder Ya fahimci da shi yake magana. "ita kuma dama ɗayan nan data rage mana itace mu cire Zuciyar Yarinyar nan, Mu ba dodon tsafin mu Ya handame ta, sannan mu kashe ƙaddarar kurkuku, ta hakane kaɗai gidan kurkukun ƙaddara zai farfaɗo...." wata irin mahaukaciyar dariya suka kwashe da ita, ganin har yanzu suna da saura damar da zasu cigaba da aiwatar da shaidancin su. Cike da izza Jan wuya yace"abun farin ciki, Garkuwar da suke taƙama da shi, Ya rasa ranshi saboda shi wawane shashasha, Ya sadaukar da kanshi saboda ya basu kariya, duk da muma munyi babban rashi amma wannan duk ba wata matsala bace da zamu daga hankalinmu akai, Ni ta inda najiye mana dadi gaba dayansu wadanda suka san sirrinmu basu san fuskokin mu ba, tayaya suke tunanin zasu iya yin nasara akanmu? In banda ma sudin dakikai ne iya fa sunayen mu suka sani, sai kuma sirrinmu amma azahirin rayu basu san su wanene Elders Ba...." Maganar Jan Wuya ta faranta masu rai, ganin sun samu mafita... "Yanzu wanene Zai kawo mana Yaran?" Jan harshe ne yayi tambayar, Cike da isa Jan wuya yace"kubar komai a hannuna" tuntsirewa suka kuma yi dariya hahaha _________________________________✍️ Shin Ya Labarin Tsohuwa Khala❓ *Bayan wani lokaci* Farfaɗowa tayi daga dogon suman da ta yi na tsawon awanni, A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhu ne ya mamaye ganin ta, tana ƙoƙarin motsa jikinta taji kamar an daddaureta. gumin zufa ne Ya wanke fuskarta, bata gama wartsakewa ba sai nishi take yi tana jan numfashi.. takun tafiyar mutun taji a cikin kunnanta yana tunkaro ta, cikin disasshiyar murya ta furta"wanene"? Kakkausar murya Elder ce ta razanar da ita yayin daya furta"me nayi maki dana cancani cin amana daga gare ki" Shiru tayi bata furta kalma ba, Hankalinta dai idan yai dubu toh ya tashi, zuciyarta sai dakan uku uku take tasan yau sai buzunta, mai kwatarta a hannun Elder sai Allah. A hankali Hasken fitilun dake saman ceilling din ɗakin ya haskaka ko'ina tana a zaune kan Kujerar ƙarfe, a rude take kallon igiyar kacar da suka ɗaɗɗaure jikinta da ita, ko yatsanta bazata Iya ɗaga wa ba, Da sauri takai dubanta gare shi yana a tsaye Ya juya mata baya, tun da taganta adakin da suke hukunta wanda yaci amanarsu na gidan kurkukun kaddara Ta tsinci kanta da jin matsanancin faduwar gaba, ga wasu karfafan Evil giants data hango tsaye abakin kofar dakin.. "Tun da naga irin makaman da sukai amfani da su gurin kashe giants nasan cewa koma wanene ya basu makamin acikin mu yake, saboda mu kadai keda irinsu acikin gidan kurkukun nan ake ƙera su, bakowa yazo min araina ba face ke dama kin jima kina gaya min zaki dauki fansa akaina" Cike da karfin Hali tace"banyi mamakin abun da kayi min ba Elder, Ni angaya maka bani da zuciya a kirjina ne? Taya kake tunanin bazan ci amanarka ba? Dama akwai amana tsakaninmu? Kaida ka rabani da kowa nawa, har kana da bakin furta naci amanarka? Akwai maci amanar daya wuce kai mugu, Hakanan kawai saboda nasan sirrinka bisa kuskure ka rabani da dangina, ya'yana, Jikokina, ka kafe ni da asirinka cikin kurkukun nan." idanunta jawur ta faɗa yayin da hawaye ke shararowa kan kuncin ta..ta daura da cewa "tun lokacin dana nasan sirrinku, a ranar na daukar wa kaina alwashin saina yi silar Tonuwar asirinka, kowa yasan wanene kai, da miyagun ayyukan da kake aikatawa, shiyasa na dinga satar makamanku ina boye su saboda tanadin zuwan wannan ranar" bata ƙare maganar ba, Taji Ya sheƙe da dariya, cike da izza Ya juyo ya fuskance ta, batare daya furta kalma ba, gently yake jujjuya sandar hannun shi. "Dariyarka ta bazance Elder, Ni nasan Ayanzu haka Ƴan hanjin cikinka kaɗawa sukeyi saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya, Na kunsa maka bakin cikin da har abada ba zaka manta ba, naja maku babbar asara, koba komai Yau kaga wadanda suka fi karfinka" ta fada da murmushi akan fuskarta. Wata Yar iskar dariya Ya saki, Kafin Ya furta"dame kike takama ne? Da ido Ta nuna mashi sama tace"Allah, shine abun tinƙahona, koken dana daɗe ina kai mashi akanka Yau ya amsa addu'ata, daga Yanzu ka kasance cikin shiri akowani yanayi mutuwa zata Iya riskarka, zaka wukalanta ka zama kaskantacce, kimarka da darajarka zasu zube a idon duniya....." bata ƙare maganar ba Elder Ya buga sandar hannunsa ta daki ƙasa har saida ƙura ta tashi, wani irin radadi taji acikin kanta hakan yasa ta dakata da yin maganar. Yana Huci Yace"kina tunanin kinyi nasara akaina ne? Bayan Duk wani shirinki Ya tashi Abanza, wadanda kike takamar zasu ga bayan mu a yanzu haka babu ko daya acikin su, duk sun mutu a hannun giants din mu, suma fursinonin da kika ku6utar basu tsira ba zamu kashe su ne" Wani irin faduwar gaba taji arazane Ta furta"kana nufin Danish da Owais sun mutu su ma" jinjina mata kai yayi" gaba daya sun mutu...Don haka kidaina farin ciki, saboda haryanzu baki kamo hanyar da zaki ga bayana ba, kashe Elder ba abune mai sauki ba, Ita kanta mutuwar tsorona take ji..." a gadarance yai maganar. ta kiɗima da jin maganar shi, idanunta cike tab da kwalla ta furta"saboda shafewar basira da jahilci kamanta kafin kai anyi wasu azzaluman da suka gabata yanzu duk suna ina ? Ta jefa mashi tambayar bai furta kalma ba. "mutuwa bata tsoronka Elder Lokacin ka ne baiyi ba, Allah yana sane da duk wani abu da kake aikatawa dama ce ta dan wani lokaci kuma kajira ka gani wlh karshenka bazai kyau ba" ta faɗa tana sharar kwalla "kuma karya kake min, Danish dina bai mutu ba, owais dina ma bai mutu ba ina ji araina suna araye..." Fashewa yayi da dariya"ki yarda ko karki yarda matsalarki, Kina kurarin kin tona asirina, bayan Har yanzu asirina arufe yake saboda babu wanda yasan ainihin Elder, ko fuskata basu sani ba, taya zasu iya tona min asirina? Bayan Ko tuhumata basu isa suyi ba saboda basu da wata shaida...." ya fada yana sakin dariyar shakiyanki. ranta a 6ace ta furta"ni zan tona maka asiri..." ta faɗa tana huci. Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"kin ta6a ganin gawa tayi magana"? Cike da tashin hankali ta zare ido tana kallon shi, matso da fuskarshi yayi saitin tata"Oh wai kina tunanin zan barki araye? Bayan kece kika san su wanene Elders, Ko da can da kika san sirrina nabarki araye nayi danasani da ban kasheki ba, da nasan zaki zamarmin masifa da tuni najima da fille kanki...." gaba daya tabi ta rude da jin maganar shi muryarta nawa ta furta"kada ka kasheni, Kabarni da raina, Ina son naga ya'yana da jikokina, Ina so na koma gurin dangina, ko dan son da kake min da zaman amanar damukayi da juna ka kyaleni da raina.." Girgiza kanshi yayi"ke da ganin su, Sai a lahira, nasoki tamkar raina amma tunda kika nunamun tsantsar kiyayyar da kike min naji nima kin fita araina, Inasonki amma nafi son mutuwarki ayanzu idan nabarki zaki zamarmun annoba" Ya faɗa tare da dafe saitin zuciyarshi, batay mamakin ganin hawaye da suka cika idanun shi ba.. "bazan ta6a son wata halitta kamar yadda nasoki ba, nasan zanyi bakin ciki da takaicin rasaki arayuwata, zanyi maraicin rashin ki, zan dawwama da radadin kashe ki da zanyi, Bazan ta6a yafe maki abunda kikai min ba, kece silar komai, Kin Ci amanar kaunar dake atsakaninmu, meyasa tun farko kika tsananta bincike akaina? Meyasa Kika san sirrina? Kinyi silar lalata Farin cikin rayuwarmu, kema kin sani nasoki fiye da yadda nakeson kaina...." zubewa yayi agabanta kan gwiwowinshi...sosai ta fashe da kuka cikin karyayyar murya ta furta"komai ya faru mukaddarine daga Allah, sirrinka dana sani Allah ne Ya kaddara zan sanin, shiyasa har nasan komai, da ace kai musulmine kayi imani da Allah da ka gane abunda nake faɗa maka.. "duk yadda na karya maka zuciya bai kaiga yadda ni ka karya min tawa ba, ina farin ciki na auri miji nagari mai sona da bani kulawa ashe mugun mutum na aura, da kanka ka musuluntar dani ashe kai din kasungumin arnene matsafi da baiyi imani da Allah ba, sannan ka ciyar damu haram, wlh ko bayan ba raina sai Allah ya tona asirinka, in sha Allah Elder saika yi kaskantacciyar mutuwa, duniya gaba daya zata juya maka baya, komai daka mallaka zai lalace.." bata kare maganar ba, Ya zabura Ya mike tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki...tuni ta hadiye maganarta, Hankalinta atashe take kallon shi. Giants ɗin dake abayanshi Yaba Umarnin su ɗaure mashi ƙafafuwanta da igiya jikin fankar dake liƙe saman ceilling din dakin, fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita ita ba mutuwar take tsoro ba, abu biyu take ma bakinci zata mutu bata tona asirin Elder ba, abu na biyu zata mutu bata gana da ya'yanta ba bayan tsawon shekaru ashirin da Ya garkameta akurkukun basu san tana raye ba. tana ji tana Gani, giants din suka kwance igiyoyin da suka daureta a jikin kujerar, daya ya ruketa sai kuka take tana kallon Elder Ya saddar da kanshi kasa don baya son raunin zuciyar shi ya hana shi kashe ta. a jikin fankar Suka ɗaure kafafuwanta gangar jikinta da kanta suna kallon ƙasa, Da ido yayi sihiri Nan take Kasan inda kanta ke kallo ya wawake ya zama katon rami wata irin wuta mai balbali ta kama ci...lokacin da hucin wutar Ya fara ta6a kanta, wani irin azababben kuka ta fashe da shi kamar ana zare ranta, wani irin radadin azabane ke rabar kowani sashe na jikin ta, cikin shesshekar kuka Ta dinga yi mashi magiya akan ya kwance ta, Kada ya kasheta ko dan darajar ya'yan dake tsakaninsu amma saboda rashin imani irin na Elder cikin sauri Ya juya Gints suka rufa take mashi baya basu kai ga isa kofar dakin ba suka 6ace ma ganin ta. Ita kadai baiwar Allah ga wutar sai kokarin kama jikinta ta ke yi, bata da wani sauran sihiri ajikinta balle tace zata kwance kanta, saboda elder ya riga daya karya garkuwar sihirin dake a jikin ta. sambatu tadinga yi cikin fitar hayyaci take ambaton duk wata addu'a da tazo bakinta ahaka har numfashinta Ya fara kokawar daukewa zufar jikinta ta dinga tsastsafowa kamar yayyafin ruwan sama kafin wani lokaci bugun zuciyarta Ya tsaya cak, numfashinta Ya dauke da alama dai Khala rai yayi halinsa, wutar harta rufe ta....Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un 😭😭😭 ____________________________________✍️ After One week (bayan sati ɗaya dakai farmaki Gidan Kurkukun ƙaddara❓ *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋🌹 ~__________________________~✍️ After One week (bayan sati ɗaya dakai farmaki Gidan Kurkukun ƙaddara❓ Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yayi ba, Jin shiru har tsawo sati ɗaya basu dawo ba, lamarin Ya ɗaga hankalin ta ba kadan ba, dauriya kawai takeyi kamar yadda tayi ma su alkawarin zata daina kuka, kuma bazata sanya damuwa aranta ba, sannan ba zata hana idanunta bacci da kuma cin abinci. Abu ɗaya ne bata wasa da shi, Tashi Yin nafilfili takai kukanta gurin Allah, idan dare yayi, biyu take raba lokacin ta, rabi tayi bacci rabi ta tashi tayi nafila, wani sa'in in ta fara tsayuwar daren Har sai kafafunta sun fara raɗaɗi tukunna take dakatawa. mafi yawan lokutta akan prayer mat bacci ya ke yin awon gaba da ita, Unaisah da Aunty Umminsu sai batool ne kadai sukasan da tafiyarsu kai farmaki sauran yan uwanta babu wanda ya sani abu daya da suka sani shine har yanzu suna shirye shiryen tafiya amma basu tafi ba, kamar yadda Unaisah ta sanar da su, tayi masu hakanne don kada su daga hankulansu yayin da ita kuma hankalin nata ba akwance yake ba, sai dai suna yawan tambayar meyasa Danish baya leƙo su? kuma su an bar su anan ko nan zasu ci gaba da zama ne kuma yaushe ne zasu je kai farmakin, dakyar suke samu su shawo kansu ita da ummi, harta Danejo batasan komai ba dangane da kai farmaki ta dai san zasu je yin wani aiki kamar yadda Taj ya faɗa mata, abunda yafi damunsu babu wanda ya kira su awaya balle su san awani hali suke a ciki....💔 A daren jiya ne ta farka tsakar dare da matsanancin faduwar gaba sakamakon wani mummunan mafarki da tayi, Hankalin ta ya tashi matuka jin yadda tsigar jikinta da zuciyarta ke tashi, gaba daya tarasa samun nutsuwarta saboda tana ji aranta wani mummunan abu ya faru da su, a lokacin idanunta sun makance burin ta kawai ta ganta a part din Chief don taga idan sun dawo ko basu dawo ba, hijab ta zura a jikin ta, batare da sanin kowa ba ta fito daga dakin daddyta dama anan suke kwana ita da Batool bayan tafiyar su. Ta sauko down ta nufi main door ta falo, ta dinga ƙoƙarin buɗe ƙofar ta kasa saboda security din dake a jiki, batasan menene password din kofar ba, har jaraba sanya numbers tayi sau biyu ana nuna mata wrong code tare da warning message. zukunnawa tayi bakin kofar tafukan hannayenta toshe da bakinta don kada yan uwanta sujiyo ta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sai da ta gama hasala can zuciyarta ta ayyana mata me zai hana ta jaraba sanya kwanan watan da aka haife ta, cos ta sani tuntana karama mahaifinta baida password da ya wuce date of birth inta, cikin hanzari ta miƙe ta danna numbers din fortunately ƙofar ta buɗe batai wata wata ba ta fuce aguje ta nufi part din Chief, ko tsoro bata ji dare ne fa sosai donma akwai hasken Electricity tamkar rana. Fitarta keda Wuya Batool ta farka sakamakon fitsari daya matseta Bayan ta fito daga toilet din ta dawo dakin Sai lokacin ta lura babu Unaisah, hankalin ta ya tashi tana fitowa ta hango Ƙofar Falon abude kasancewar Unaisah bata datse ƙofar ba, nan take ranta ya bata fita tayi cikin sauri ta nufi kofar harta kusa Isa kwatsam Ta tsinkayi muryar Ummi cikin Kunnanta. "Babe Ina zuwa" cak ta tsaya da tafiya, Ummi ta nufo ta cike da mamaki take duban kofar falo data gani abuɗe. "Ina zaki haka da tsakar dare ko mayafi babu akanki? Wanene kuma Ya buɗe kofar nan? Ko wani ya shigo ne? cikin rawar murya ta fada mata babu Unaisah adaki, Da jin haka Ummi ta ruko hannunta suka bi bayan Unaisah, fitarsu keda wuya kofar falon ta datse silar bangazar da sukai mata.. Suna fitowa suka hango Unaisah tsaye agaban Security officers din gidan ta ruƙe qugu, ashe sun ganta lokacin da take gudu tana kokarin karasawa ga kofar shiga bangaren Chief. a hanzarce suka kewata suna tambayarta ina zataje da tsakar daren nan? Gaba daya sun fahimci bata acikin hayyacinta sai haki take muryarta na rawa ta furta wurin Chief zataje. Officers din sukace mata ay basu dawo ba, don haka ta koma inda ta fito, ta fashe da kuka tana fadin ba inda zataje, ita ta gaji da zama cikn fargaba kawai su kaita inda suke. rigima ta saka masu duk yadda suka kaiga zare mata ido da yi mata tsawa akan ta koma takiya har takaiga wani Soja yai kokarin kai hannu da niyar ya ɗauke ta aikuwa ta gartsa mashi cizo har saida ta fasa mashi fata, ranshi ya 6aci matuƙa harya daga hannu zai kwasa mata mari cikin zafin nama officer din dake a gefen shi Ya damƙi hannunsa da kakkausar murya yace"karka kuskura, In har ba so kake ka rasa aikin ka ba" Yana huci Ya fusge hannun shi ya juya yabar wurin, lallashin ta suka cigaba dayi don su samu ta koma tace masu in har suna so ta koma su bude mata kofa ta shiga ta dauko wayarta data bari, Officer din yace ta fada masu inda ta ajiye wayar zasu kawo mata zuwa gobe yanzu dare yayi taje ta kwanta, kin fada masu tayi tace itama batasan inda ta ajiye wayar ba sai ta shiga zata duba, kuma a yanzu take son wayar" Ba yadda suka iya da ita adole suka kira Layin Agent zahra saeed daya daga cikin na hannun Chief amintattunsa, saboda ba wanda zai iya bude kofar idan ba su din ba. Saboda rigimar Unaisah yana bacci tare da iyalinsa yayi recieving call din su, bayan sun sanar da shi abunda ke faruwa yace su dauke ta su mayar part din, Officern yace mashi yalla6ai ba fa yadda zamuyi da ita, abokin aikinmu da yai gigin ta6a ta cixo ta gartsa mashi har saida ta fasa Fatar shi, yana can yana jinyar kan shi" da jin hakan agent zahra yace"tafi karfin ku ne? wai ma wacece acikin yaran" kallon ta officern yayi meye sunanki" muryarta ashake tace Unaisah.. "Sir sunan ta Unaisah, tana launin ido ruwan toka" da jin hakan okay yace su jira shi. Adai dai lokacin su ummi suka karaso tayi mamakin ganin Unaisah tsaye gaban Security Officers, Hijab din jikinta ta jike sharkaf da gumi ta hade rai kamar bata ta6a dariya ba, tambayarsu tayi meke faruwa ne, anan officers din suka sanar dasu komai daya faru, batai mamaki ba ta riga tasan halin kayanta in taso abu kamar zawo take bata da uziri ko kaɗan. Batool ta tausaya mata sosai, ganin yadda ta fita hayyacin ta, jikinta sai kerma yake, rungumota tayi a jikinta, officers din suna ta kallon su kamar zasu hadiye su... Bayan yan mintu, Sai ga kiran agent zahra ya shigo wayar officer din daya kira shi, bayan yai picking yace suje bakin kofar ya buɗe ta. Unaisah ta danyi mamaki jin hakan amma da ta tuna kofar tana da security sai taga ai bakomai bane may be yai amfani da computer ne gurin buɗe kofar daga can inda yake. Suna zuwa bakin kofar ta zuge da kanta, ajiyar zuciya kowannnasu ya sauke kafin suka shiga ciki baiwar Allah idanunta na akan Second floor ta dinga kallon door room dinsa dake a datse, har gizau ya dinga yi mata ta hango shi tsaye ya dafe handrail fuskarsa ɗauke da murmushi, jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya, gaba ɗaya ta shagala da kallon shi, har saida ummi tace tayi sauri ta dauki wayar suna jiran ta kafin ta nufi Bedroom dinsu Batool tabi bayanta, ummi tana a falo tana jiran su. Suna shiga ɗakin suka bazama neman wayarta, Batool tace sis ki yi kokari ki tuna inda kika ajiye ta, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace wlh na manta inda na saka ta, har zanin gado suka yaye tare da kakka6e shi duk basu ganta ba, Har closet dinsu suka duba basu ga wayar ba, suka duba under bed nan ma basu gani ba, cikin hanzari Batool ta zazzago da mirror drawer chest tana lalubawa unexpectedly hotuna suka faɗo kan floor, cikin sauri ta dauƙi hotunan ta kura masu ido tana kallon su farat daya ta gano inda ta ta6a ganin Faces din mutanan dake akan pics din, cike da zumudi ta furta kai Ina kika samu hoton mutumin aunty Ummi da kawarta" Kaitsaye maganar ta daki dodon kunnan Unaisah a lokacin ta gaji da neman wayar har zata zauna gefen gado ta tsinkayi maganar Batool, mikewa Batool tay da sauri ta nufe ta tare da mika mata hotunan tace ina kika same su"? Da ruɗu ta kar6i hotunan ta soma duba su tana kokarin tunano inda ta gan su sai da ta zurfafa tunanin dakyar ta iya tuna ranar da ta gansu a karkashin gado a lokacin tana cikin neman wayarta. Numfasawa tayi kafin ta furta" ran nan ne nagansu a karkashin gadon mu shine saina boye su a cikin drawer" "To ay mutumin aunty Ummi ne wannan" ta fada tana nuna mata hotonsa" Ita kuma wannan kin tuna ƙawarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue"? Da mamaki Unaisah ta ƙara duba hotunan dakyau tabbas ta gane fuskar baturiyar kawar aunty Ummin su, farko data fara ganin hotunan sai da tay mata kallon sani sai dai bata iya gano a ina ta ta6a ganin ta ba. "Amma taya akai kikasan Mutumin aunty ummi ne wannan"? Ta jefa mata tambayar.. "Zan faɗa maki, amma dan Allah kada ki fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a buga min warning, akan kar in daukar mata waya in an kira..." Unaisah tace taji ba zata fada ma Aunty ummin ba.. Nan Batool ta labarta mata ranar da ya kira video call tayi picking, abun daya ɗaure ma Unaisah kai ta yadda har Batool ta iya ruƙe fuskarshi a karo na farko data fara ganin shi a video call. "Kin tabbata shine"? "Wlh shine, watakil kuma mai kama da shi ne, amma gaskiya kamanninsu ya 6aci sosai.." lamarin ya ɗaure mata kai taya akai hoton kawar aunty ummi da saurayinta yazo dakinsu? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, Ta dai san aunty ummi baza ta yi gangancin kawo hoton saurayinta adakin su ba tunda har ta gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bataso asan komai dangane da abun da ya shafi phone dinta. Kafin wani ya ƙara furta kalma daga cikinsu suka jiyo muryar Ummi daga waje tana fadin Wai har yanzu baku ga wayar ba ne. Cikin sauri Unaisah tace ma Batool kada ki fada mata komai dangane da hotunan, nima bazan faɗa mata ba, inaji araina hotunan nan akwai wani abu atattare da su, zanyi kokari insan daga inda suke" kafin Ummi ta shigo ɗakin su ka yi hanzarin mayar da kayan cikin drawer din, hotunan ma cen cikin wasu notebook dinta dake qasan drawer din ta boyesu. Adaren ranar basu koma part din daddynta ba, bayan da taga wayar officers suka ce su fito su koma part din daddynta, aikuwa ta sanya masu rigima akan bazata koma ba anan takeson kwana, ganin dare ya nutsa sosai yasa suka kyale ta, taso ta kwana adakin Danish sai dai takasa bude room door dinsa saboda an kulle kuma bata san code din kofar ba, adole ta hakura suka kwana adakinsu ita da Batool, Ummi kuma ta kwana adakinta. Morning🌄 Zaune suke su Uku akan dining Chairs, sun tasa Abincin breakfast din da aka jere masu kan table agaba sai dai sun kasa ci, saboda rashin kwanciyar hankali tun kayan baccin jiya ne a jikin su babu wanda Ya cire nashi. "Unaisah, ku ci abinci mana" ummi ce ta faɗa tana kallon su, kamar wadanda sukayi amai da gudawa duk sun faɗa, sai uban kasusuwan wuya.. In a cool voice Unaisah tace "Aunty Ummi, wlh abincin ma bayayi min dadi, turawa kawai nake yi.." Batool tace"kamar kin shiga zuciyana wlh nima dai babu dadi..." shiru ummi tayi cike da damuwa take kallon su to ita ma dindai ba dadin abincin take ji ba, turawa kawai takeyi.. "Yau tsawon sati guda Aunty Ummi, babu labarinsu, kullum da zullumi muke kwana, tunanin mu meya faru da su? Sunyi nasara ko kuwa? Tayaya zamu sani Aunty Ummi? Ko awaya babu wanda Ya tuntu6e mu...." dakyar ta ƙare maganar saboda kukan dake kokarin 6alle mata, dakyar ta haɗiye shi. "Jiya har mafarkin Danish nayi, da daddyna, Amma mafarkin baiyi min daɗi ba, shiyasa ban ma baku labari ba..." ta faɗa arauna ce, dafa kafadarta Ummi tayi"mu kara hakuri Unaisah, tun da bamusan meya tsayar da su ba, amma wani jinkirin Alkhairi ne In sha Allah zasu dawo cikin koshi lafiya..." yamutsa fuska tayi batare data furta kalma ba, Wayar Ummi ce tayi Ringing daga cikin aljihun wandonta, zaro wayar tayi tare da duba sunan me kiranta, kamar mara gaskiya ta dago suka hada ido da su Unaisah har suna hada baki gurin furta"Daddy ne"? Girgiza kai tay"ba shi bane, Friend dina ne" kafin tay picking call din ya katse mayar da wayar tayi cikin aljihu kafin ta maida dubanta gare su. A fakaice Unaisah ta kalli Batool suka hada ido batare da ta lura ba, gaba ɗaya sun fahimci bata son yin waya agabansu in har ba daddyn Unaisah ne ya kira ba ko big guy. "Guys yanzu dai mu daure mu ci ko rabin abincin ne kada ay almubazzaranci"..." matsa masu tayi dakyar ta samu Suka ci kaɗan. mikewa Unaisah tayi daga kan dining din ta nufi dakin su. Bayan tafiyarta Batool ta dubi aunty Ummi"yaushe zamu koma part din daddy, kada suji mu shiru" Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, Bari na kira Danejo awaya in fada mata don ta kwantar masu da hankali" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Danejo kira. zama tayi gefen gadon Su hannunta ruke da iphone dinta data dauko, messages ta shiga ta buɗo Sakonnin daya ta6a tura mata, nutsuwa tayi tana karanta su fuskarta ɗauke da murmushi, bayan ta gama karanta sakonnin ta shiga gallery ta bude hotunan da ta ta6a yi mashi batare da sanin shi ba, yayi mata kyau a pics din har wani lumshe idanu takeyi idan tana kallon su, ta kosa ya dawo ko dan ta cika mashi burin shi, idan ta tuna alkawarin daddynta dayace in har ta bi umarninsa zai bari ta auri zabin ranta sai taji wani dadi ya lullu6e zuciyarta, fatanta Allah yasa suyi nasarar ruguza kurkukun kaddara su dawo cikin koshin lafiya. Kira ne Ya shigo wayarta, murmushi ta dan saki ganin sunan mommyna ya bayyana akan screen din wayar, picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta.. "Haba my baby, kin daga min hankali kullum saina kira bana samun ki, Almost a week?! Meke damun ki ne? sautin muryarta da damuwa ta tambaya. "I'm sorry mommy, school ne ya boye ni, bayan haka wayar ma ta samu matsala sai jiya aka gyara min ita" On the other hand, Benazir kiris Ya raga ta sanya dariya, ta rasa gane meyasa Unaisah take son yi mata karya, bayan ba halin ta bane, since last week ta riga da ta gane itace Unaisah yarinyar da ta kira wrong number tay mata karyar a kano suke yanzu kuma tace tana school bayan a labarin da Aneelerh ta bata Unaisah bata zuwa School. basarwa tayi tare da cewa"Okay, kada ki damu, nima bazanso na takura maki ba, am babyna Ina daddynki ne? Almost a week bana ganin shi a online.." su6ul da baka tay What's your connection with him?" yar dariya benazir tayi"son shi nakeyi, tun ranar dana fara yin tozali da shi, don ma yaƙi kulani ay da tuni mun yi maki ƙani..." waro idanu Unaisah tayi can kuma tadan saki dariya, har cikin ranta taji dadin maganar Benazir don kuwa time da ta fara ganin ta saida tayi ma daddynta sha'awar auranta, tadaiyi shiru ne saboda tana kokwanton ko tana da aure bayan haka bata son yayi ma Danejo kishiya ga kuma aunty Aneelerh da take burin ya aura saboda kaninta junaid ya samu Uba nagari. tayi zurfi a tunaninta muryar Benazir ta katse ta"kinyi shiru babyna, kin san nima na rasa mijina da yata, ina maraicinsu, Aneelerh ta fadamin baya tare da mommynki, shiyasa nakeso nazo na maye gurbinta, ko bakya son in auri daddynki" murmushin yaƙe tayi kamar tana agabanta tace"inaso, amma bata faɗa maki yana da au..." bata ƙare maganar ba, sakamakon dirar motocin data jiyo acikin kunnanta, rejecting call ɗin tayi tare da jefar da wayar Kan gado, ta fito da gudu ko Mayafi bata ɗauka ba ta nufi hanyar fita daga falon jikinta sai kerma yake tsabar zumuɗi, kafin ta ƙarasa Ummi da Batool suka bi bayanta da ɗan gudun su. At same time motocin su ka yi parking, a gaggauce Officers dake tsaron gidan suka Yi masu kawanya tare da yin hanzarin buɗe cardoors, Adai dai lokacin Unaisah ta zuro kofarta waje wani burki Taci idanunta azare take Kallon motocin Cike da fargaban wa zata fari gani. CO ne Ya fara fitowa cikin hanzari ya zagaya bayan motarsu ya buɗe boot ya cure folding wheelChair ya ajiye ta kasa ya fara kwancewa sai da ya daidaita wheelchair din kafin Ya furta"zaku iya fitowa da shi" Wani irin faduwar gaba taji gaba daya tabi ta rude jin ya furta za'a iya fitowa da shi ko wanene? sai faman rarraba idanu takeyi akan motocin, lokacin da idanunta su kayi mata tozali da mutumin da SA suka rurruko daga backseat na ɗaya daga cikin motocin, jikin shi sanye da patient uniform blue yar riga ce mai tsayi, Cinyar kafarsa ɗaya gaba dayanta a nannaɗe take da bandage daga gani aiki akayi masa a tsakiyar cinyarsa, A hankali suka zaunan dashi kan wheelChair din sai nishi yake yana fitar da numfashi mai huci daga gani babu lafiya atattare da shi. Cike da tashin hankali ta zare idanunta, la66anta na kerma ta furta"inna lillahi wa'inna Ilaihirraji'in! Daddy"! Da karfi ta furta sunan shi, bawan Allah a firgice Ya dubi inda take har rama yayi saboda azabar ciwo, suma Jami'an suka maida hankali akan ta.. watsawa tayi da gudu tana karasawa gaban shi a slow ta zube kan gwiwowinta, ta fashe da matsanancin Kuka tamkar ranta zai fita Cikin shesshekar kuka ta furta nashiga ukuna! daddy Meya faru dakai? Meya faru da kafarka? tsantsar tausayinta ne Ya kama shi, Ummi da Batool sun kasa motsawa saboda tashin hankalin da idanunsu suka gane masu, daya bayan daya sauran dake acikin motocin suke fitowa, Chief owais ne jikin shi sanye da Singlet fara sai short, gaba ɗaya goshinshi bandage ne, fuskokin su duk sun 6aci da tabonnin raunukan da suka ji, Wa'iya zubilla, dafe kirji ummi tayi cike da tashin hankali ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool kuwa Fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita musamman data lura babu Danish a cikin su, daga cikin sauran da suka fito daga cikin motocin U.s armies din da suka rage ne su Biyar, babu cikon ɗayansu, sai wasu daga cikin na hannun daman Chief wadanda ba'aje Kai farmakin da su ba. Akace labarin zuciya atambayi fuska, tunkafin suyi masu bayani suka karanci komai daga yanayin su, Dakyar Taj yai karfin halin janyo Unaisah Ya rungumeta akan kirjin shi, tare da shafa sumar kanta yana faman sauke ajiyar zuciya, har cikin ranshi yaji dadi da Allah yasa ya rayu ashe da rabon zai sake ganawa da yarsa? sai dai abu daya da yake ma fargaba. hannun Ummi ruke dana Batool suka karaso Gurin su Chief, Fuskokinsu sharkaf da hawaye Murya Na rawa Batool ta furta"Ina Danish din mu"? Shiru sukayi don basu shirya komawa asibiti da wanin su ba.."dan Allah ku faɗa min Ina danish? Meyasa bangan shi ba..." cikin shesshekar kuka tayi maganar, Sunyi shiru suna kallon ta, Chief ma Hankalinsa baya akan su, saboda matsananciyar damuwar data mamaye zuciyarsa. Unaisah data kwantar da kanta a kirjin daddynta, Hankalinta Idan yai dubu toh ya tashi, tin da taji muryar Batool tana tambayar Danish ta fahimci babu shi su ka dawo! Babu!!babu!! Hasbunallahu wa'ni imal wakeel, acikin zuciyarta ta dinga maimaita duk wata addu'a datazo cikin bakin ta. Ummi kuwa Jikinta yagama mutuwa Cikin sanyin murya ta wanda Ya kara tayi masu Chief barka da dawowa da tambayar ya jikin su, fuskokin su kwata kwata babu walwala suka amsa mata, Kafin Commender james ya nemi su shiga ciki saboda majinyatan jikinsu da suka jigata, dakyar Chief yake Tafiya saboda rashin kuzari, bawan Allah shi kadai yasan me yake ji a cikin zuciyarshi bazai ta6a mantawa da Danish ba Har abada ya kafa tarihi acikin zuciyar shi, gaba daya abun da suke jima fargaba yadda yan uwan shi zasu kar6i abunda zasu fada masu saboda su sunsan irin kaunar da suke ma Junansu komai zai iya faruwa idan suka ji cewa Danish ya mutu. "Commender pls, meya faru ne? Hankalina Ya tashi, Ina son nasan Ina Danish ne? Ina Omar? Ina Major"? Suna Ina"? Girgiza kai commender yayi cikin rauni murya da harshensa na turanci ya furta"Ummi, muje ciki zamuyi maku bayani" yana fadan hakan yabi bayan Su Chief suka nufi ciki. mutun uku ya rage a harabar, gaba daya suka zukunna Agaban Taj, Cikin rauni na murya Unaisah ta furta"daddy, Ina Danish"?cike da fargaban amsar da zai bata tayi maganar, tare da dago kanta daga kirjinshi, fuskarta ta 6aci da hawayenta, gwanin ban tausayi ya ke kallon ta. "Dan Allah Daddy Ka fada mana, Ina Dan uwanmu Danish"? batool ce ta fada still bata daina kukan ba... Ummi ma tace"tun da kuka tafi, Hankalinmu ba akwance yake ba, saboda zullumi da fargaban awani hali kuke ci, gashi kun dawo ba yadda muka zata ba, babu wasu daga cikin ku, sannan ku kanku araunace kuke, that means something bad happened."? Ta fada idanunta cike tab da kwalla, yayi shiru yana binsu da kallo... "Daddy, pls ka fada min, yana raye koya mutu, kada kace zaka boyemin, saboda duk mun daren dadewa dole naji, kwara ka fadamin ayanzu inyi jinyar zuciyata idan ina da rabon cigaba da rayuwa, ay ma nayi imani da kaddara, in ma ya mutun Zanyi hakuri in rungumi ƙaddara..." wani kallo Taj yayi mata bakomai yake tunawa ba face abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu irin haukan da tadinga yi na zai raba ta shi, shine yanzu take kokarin yi mashi burga salon Ya fada mata Ya rasata na har abada. ganin kallon da ya ke yi mata yasa ta kama in-ina hawaye na cigaba da tsastsafowa kan fuskarta tace"wlh daddy bazan damu ba, ka fadamin kawai.." tana kuka tana dariya tayi maganar kamar zautacciya. hmmm baiwar Allah bashi ba, hatta ummi ta karaya da ganin yanayinta, kodan saboda Unaisah zataso ace Danish Yana raye. Da ido tayi mata Taj alamar karya kuskura ya fada mata, don ita tasan me ta gani wlh, Shafa fuskarta yayi da tafukansa Ya kakalo murmushi kan fuskarshi"meye naga kun wani daga hankulanku"? "Daddy taya hankalinmu bazai tashi ba, kun dawo gaba dayanku ba lafiya, kuma babu Danish da ya Omar" jinjina kanshi yayi"hakane daugher, amma inaso ki sani dan uwanku yana nan cikin koshin lafiya.." ba dan sun yarda da maganar ba, Tace"yana ina"? kafin ya bata amsa Ummi ta katse su da cewa"Haba Unaisah, dudufa Yanzu suka dawo, baki ga halin da yake a ciki ba, ki bari Ya shiga Ciki Ya huta mana, inyaso sai muji komai daga bakinsu," dakyar Ummi ta lallashe su suka hakura da yi mashi tambayoyin. Unaisah da Batool ne suka gungura Wheelchair din Taj ganin ya raunata sunsan ba lallai ya iya gungura kan shi ba, suka nufi main falo din ummi na abiye da bayan su, anan suka iske su commender zazzaune kan Sofas, gaba dayansune da suka shigo, a tsakiyar sofas din Su batool suka dakata da gungura shi, kan floor suka zauna kamar masu zaman makoki, ummin ma ta zauna gefen su. saida suka huta nutsuwa ta shige su sosai, kafin chefs din gidan suka shiga jera masu Abinci, kamar sarki haka suka dinga lallashin chief donyaci abinci yace masu bazai iya ba, ko yaci bazai ji dadin shi ba, subar shi kawai shi kadai yasan halin da yake aciki, cikin kwantar da murya commender yace"in har bakaci abincin ba, taya zaka samu karfi ajikinka balle harka Iya Karasa aikin ka"! "What you need now is peace of mind because your brain needs rest to function, Chief worry won't solve anything, it will just lead to loss and regret, just Forget about every bad thing that happened in the prison of destiny, Strengthen your heart and face what lies ahead, that's how you'll achieve success ka fuskanci abunda kasa agaba, ta hakane zaka cimma nasara..." kalamai masu karfafa zuciya Commender james Yaci gaba da furta mashi sauran na hannun damanshi duk suka saka baki gurin kwantar masa da hankali har saida suka samu Ya ɗan lafa, cikin sanyin murya ya furta"nagode da shawarwarinku, in sha Allah zanyi abunda kuka ce, amma Yanzu nafi bukatar wanka, zan shiga ciki, idan na fito zanci abincin.." yana faɗan hakan Ya miƙe cike da rashin kuzari Ya nufi part dinsa. Yana shiga Ya faɗa kan gado Idanunsa na fuskartar ceilling, komai daya faru a gurin Yaƙin Ya fara tariyowa Hannunsa daya dafe da saitin Zuciyarshi, Yafi jin Danish Fiye da kowa sai kuma amininsa Omar wanda a halin yanzu yana agadon asibiti rai hannun Allah As a result of his brain injury, ya shiga coma ba lallai ma ya dawo da cikakkiyar lafiyarsa ba, a bayanin da docs su ka yi ma shi kenan. abu na biyu da ya kwallafa rai akai Shine Elders, Alwashi ne ya daukarwa kanshi Elders ba zasu kai karshen watan nan ba batare daya gano su ba, abun da Yafi tada mashi hankali tsohuwa Khala matar ta tsaya mashi aranshi! Kalmar data fara furta mashi "owais kaine ka girma haka"? Meyasa yake jin kamar ya san muryarta? Meya faru da ita? Hakika tsohuwa Khala tayi masu kokari, ba wai iya makamai ta taimaka masu da shi ba, ta taimaki fursinonin da suka ku6utar, shi Kanshi ya jinjinama jarumtakarsu Ita da Danish sun cancani a yaba masu, don shi ji yake da ace Danish yana raye ba abun da zai hana Ya sauke mukamin shi na director general Ya damƙa mashi saboda ya cancan ta. A hankali siraran hawaye suka wanke fuskar shi ya ɗan numfasa tare da lumshe idanun shi yana jin wani irin yanayi mara dadi a tattare da shi aranar da suka kwana a sansani kasancewar a masauki daya suka zauna kafin suyi bacci sun dan ta6a fira da shi har ya dan bugun cikin shi yace ya fada mashi meke a tsakanin shi da Unaisah kar yai tsammanin yana sanya masu ido ne, kawai Ya lura da yadda suke kaunar junansu, a lokacin har saida yai murmushi kafin yace ma shi ya dauka Unaisah bugun zuciyar shi ce, yana tunanin mutun zai iya rayuwa batare da zuciyarshi tana bugawa ba? Dariya chief yai ya girgiza kai yace a'a bama zai ta6a yiwuwa ba, yace mashi toh haka Yake jin Unaisah, a lokacin Chief ya sake tambayarsa ya fada masa wani buri yake so ya cika masa idan suka dawo bayan sunyi nasara, ya danyi jim kamar yana nazari kafin yace baya bukatar komai, kawai shi abunda yake so yai masa alkawarin koda bai rayu ba idan sukaje kai farmakin Ya ruke Unaisah da mahaifinta da sauran Yan uwan shi yabar mashi amanar su ita kadaice alfarmar da zai nema agurinsa. Bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya lula A hankali ya Kife kanshi jikin pillow, fuskarsa ta 6aci da hawayensa.. _______________________________✍️ "Dan Allah ku faɗa mana ina dan uwanmu Danish meya faru daku"? Batool ce ta kuma tambaya... Cikin sanyin murya Commender Haroon yace"ku kwantar da hankalin ku, Danish bai mutu ba, saboda bamu shaida mutuwarsa ba" A takaice Ya labarta masu abunda Ya faru a ranar da suka kai farmakin bai boye masu komai ba" Canal herry yace"munyi babban rashin na har abada ba zamu ta6a warkewa daga radadin da muka ji ba na rashin Danish, zai yi wuya asamu jarumi irin shi a duniyar nan" Ya fada tare da saddar da kan shi ƙasa. mikewa Unaisah tayi kamar bata acikin hayyacinta kafafunta sai kerma sukeyi ruko hannun ta Taj Yayi"My angel, zauna muyi magana, bafa mutuwa yayi ba, ni nasan zai dawo ne da kanshi In ma bai dawo ba zamu koma ne" gaba daya hankalinsu Commender na akanta, ta runtse idanunta sosai, jikinta kakarwa yakeyi kamar wadda sanyi ya kama, dakyar ta furta"daddy, Danish Yana acikin rijiya ta gidan kurkukun kaddara tare da evil giant me hadarin gaske? ku ka tafo ku ka baro shi!, sannan Elders basu mutu ba sun yi nasara kenan? ta faɗa tare da dafe goshinta tana huci tace"shiyasa nace ku tafi dani, ni dama saida raina ya bani wani mummunan abu ya faru ashe mafarkin da nayi gaskiya ne" "Unaisah, Ki fahimta bamu da yadda zamuyi ne, Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, bamu isa mu canza mashi kaddarar shi ba, yakamata ki godema Allah Unaisah baki yi farin ciki ba? Saboda sadaukarwar da Danish yayi Mun ceto rayukan Yan uwanku dake a kurkukun kaddara yanzu haka suna a asibiti a karkashin kulawar likitoci, bayan haka mun ku6uta da ranmu da ba don shi ba da tuni mu kanmu mun rasa rayukanmu" Bata jira karashen zancen shi ba, ta zame hannunta daga Nashi Cikin sauri ta nufi dakinsu ta shiga ta fada toilet, ta kunna shower da faucet don kada sauti Ya fita, da hannu biyu ta daddafe kanta dake sara mata, Ta daddaga ta fashe da wani irin kuka mai cin rai kamar ranta zai fita, ihu tadinga Yi tana hauka hauka gaba daya shatun jijiyoyin goshinta Ya fito rudu rudu kan fatarta, hatta wuyanta shatun jijiyoyinne, wani irin mahaukacin zafi temperature din jikinta Ya dauka, Idanunta suka kaɗa jawur kamar garwashin wuta, kamar ana rura wuta Cikin zuciyarta saboda bala'en radadin da takeyi mata, sau uku tana buga kanta Jikin sink, har saida fatar goshinta ta faffashe jini ya wanke kyakkyawar fuskarta, nan take Hancin ta ya fara bleeding, lokaci daya tafara jin wani irin azababben ciwon kai mai azabar radadi, juwace ta kwasheta gaba daya ta yanke jiki ta faɗa kan floor, wani irin duhune Ya mamaye ganinta, Ji take kamar ta tsaga kirjinta ta ciro zuciyarta ta jefar saboda tafarfasar da ta ke yi. Maganganunshi ne suka fara dawo mata acikin kanta .. _"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"?_ _"Abu ɗaya da nakeso Kiyi min alƙawari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba..."_ "Meyasa zaka yi min haka? Ta fada acikin ranta "Don nace ka bada ranka ba ina nufin ka mutu ba, taya kake tunanin zan iya rayuwa batare dakai ba? Na rasa farin cikin rayuwata, me rage min? ya Allah Ka dauki raina in huta" Lokaci ɗaya ta fara tariyo farkon haduwarsu agidan kurukukun kaddara, at sight da sukayi tozali da juna sai da ta razana da ganin kyawun shi...In har Danish bai dawo ba, to kuwa tabbas zata dawwama da bakin ciki arayuwarta.....💔 Tana jiyo sautin bugun kofar da suke yi mata, sama sama muryoyinsu ke yi mata yawo akai Unaisah ki bude kofa, pls ki bude, wai baki ji Ina magana! Ba zaki bude ba"? ko yatsanta bata iya dagawa, saboda halin da ta shiga... Lokaci ɗaya ta fara jin matsanancin ciwon kirji, hudojin fatar jikinta suka fara fitar da gumi ta ko'ina zuface Ke tsatsafo mata kamar an yayyafa mata ruwa, numfashinta yayi karanci dakyar take Jan shi bata kara sanin inda kanta yake ba💔 *Bayan Wani Lokaci* *OIH* Da matsakaicin Gudu Motar su ta shigo asibitin tunkafin suyi parking, Nurses suka fito a gaggauce hannayensu ruke da Stretcher agaban motar suka aje, Jikinshi na rawa ya fito daga backseat na motar, Ya zura hannu Ya dauko Unaisah dake a rungume Jikin Ummi, kwata kwata babu Numfashi a jikinta, Batool sai kuka takeyi kamar ranta zai fita, da kanshi Ya kwantar da ita kan Stretcher din, Nurses suka gungura ta zuwa Emergency ward yayin da Su ummi ke abiye da bayan su. A waiting Area Ummi da batool suka tsaya Suna jiran tsammani, Chief yana a zaune kan seat Ya dafe forehead dinsa da tafin hannunsa, idanunsa sun kaɗa jajur saboda tashin hankalin da yake fuskanta. Bayan yan mintuna, Motar Us armies da ta Senior agents ta karaso asibitin, visitor din dake kai komo a harabar asibitin sai kallonsu sukeyi, gaba daya suka fito daga Cikin Motocin hada Taj wanda gaba daya fuskarsa ta jike da hawaye kamar karamin yaro yayi kuka sosai, ga shi ba koshin lafiya gare shi ba, dama ko sallamar shi ba ay ba Ya matsa lamba akan a sallame shi saboda yar shi, dakyar ya samu Chief ya sanya hannu suka sallame shi acan inda aka kwantar da su a (Combat support hospital) gaba dayansu babu wani mai kwanciyar Hankali, Sun rasa ina zasu sa ransu suji dadi a duniyar nan, Na hannun daman Chief suka kewaya batool da Ummi suka fara lallashinsu da kwantar masu da Hankali, Shima Taj haka suka dinga tausarshi yana azaune kan wheelchair dinsa ya sadda kan shi kasa, Kasa jurewa yayi a karshe ya gungura kujerarsa Ya koma bakin Kofar dakin da aka kwantar da ita, Kasancewar Kofar ta glass ce yana iya hangen Docs din da suka kewaye gadon ta, sun dage damtse suna ta kokarin ceto rayuwarta, leken ta ya dinga yi tana a kwance kan medical bed Sai jan numfashi take duk da sun sanya mata Oxygen mask akan fuskarta. Addu'o'i Ya dinga yi mata acikin zuciyarsa akan Allah ya bata lafiya..💔 Wunin ranar suna asibiti Har lokacin likitoci suna aiki akanta, Kafin marece docs din suka kammala bincike sakamakon ya nuna tana fama da severe depression and Heartbreak Syndrome, She's in a critical situation, dealing with two major issues simultaneously, docs din ma sunce in har ba'ay kokarin shawo kanta ba, Zuciyarta zata bugawa ne, amma zasuyi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya. Hankalin su Ya tashi matuƙa sun shiga matsananciyar damuwar abunda ke damun Unaisah, duk wannan abun dake faruwa Danejo da sauran Yan uwansu dake agida basu sani ba. (Get well Soon Unaisah Angel) *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞💓💔💞🫀🌹 ~<><><><><><><><><><><><><><><>✍️~ ~__________________________________~ gajiya tafari yi da tsayuwa charging kwata kwata baya sauri, zama tayi gefen gadon su ta dan fara gyangyadi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba da ita. A hankali ya ke saukowa down ya zuba hannayensa Cikin aljihun wondon baccin sa, sam ya kasa runtsawa saboda tunanin a wani hali Unaisah take a ciki? Ta yi bacci ko idonta biyu? Ya damu sosai akan ciwonta, direct ya nufi bedroom dinsu Yana gab da zai shiga ya jiyo shesshekan kukan ta kasa kasa. Almost 3 times yana kwaɗa sallama shiru tare da knocking door din, ba'a amsa mashi ba Har zai juya sai kuma ya kasa jurewa saboda baya son damuwarta ga kuma kukan da ya ji ta na yi. A hankali ya tura kofar ɗakin Ya shiga da sallama abakin shi, babu wadataccen haske a dakin sai na bedside lamp da suka bari a kunne, Batool ya hango a kwance kan gadonsu tana ta sharar baccin ta ita kadai abun ta. Wurga eye balls dinsa yai saitin inda yake jiyo shesshekar kukanta, wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi ganinta a cikin prayer corner tana a zaune kan prayer mat, jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ruke da prayer beads tana lazami, yayin da idanunta ke akan qur'anic stand din data buɗe. tabbas tajiyo kamshin turaren Chief sai dai bata kawo aranta cewa shine ba kuma kwata kwata ba ta ji motsin shigowar mutum ba saboda tayi nisa a cikin ibadarta. Unaisah ta yi Namijin kokari ba lafiya gare ta ba, amma saboda ta nema masa rahama gurin Allah yasa ta hana idonta bacci ta tsaya tsayin daka don ganin tayi masa addu'a dama alkawari ta daukar masa zata raba daren ta biyu rabi ta yi bacci rabi ta yi addu'a, samun masoyi mai sonka tsakani da Allah da zai iya yi maka addu'a batare da sanin ka ba zaiyi wuya a duniyar nan. Hakika ta burge shi sosai, Har ya zagayo ta gabanta bata lura da shi ba, saboda ta ɗan lumshe idanunta, dogayen eye lashes din ta sun jiƙu da ruwan hawayenta. Kyakkyawar fuskarta ta 6aci da hawayen ta, ɗaga hannayenta tayi sama Cikin harshen larabci ta fara karanta addu'o'i duk akan Danish dinta. Lumshe idanun shi yai a hankali ya sake bude su kan fuskarta, ya jinjinama irin kaunar da take ma Danish yayi fatan ace shi ya samu soyayyarta, saboda samun mace tagari irin ta zaiyi wuya a fadin duniyar nan, yarinyar da zata iya tashi in the middle of the Night tayi nafilfili don ta yi maka addu'a Omg😘 A hankali Ya zukunna ta gefen ta, Ya zuba mata lumsassun idanun shi masu ɗauke da bacci. Bakomai yake kallo ba fa ce eye lashes dinta da soft lips dinta dake kerma sun jiku da hawayen ta sometime har tongue take zurowa ta lashe su baisan ya akai ya tsinci kan shi da kallon ta ba. A hankali ya mayar da eye balls dinsa kan kwantaccen gashin forehead dinta dark brown ya nannade gwanin ban sha'awa kai komai nata abun ban sha'awa ne. Kasa yi mata magana yai cos yai tunanin she may feel uncomfortable if she sees him in front of her. Slowly ya miƙe tare da juyawa ya nufi hanyar fucewa daga dakin Kamar daga sama yajiyo muryarta a cikin kunnan shi"Wanene" dan dakatawa yai ba tare da ya juya ba, Zumbur ta mike gabanta na faduwa cos tajiyo motsin tafiyar shi. waro idanu waje tay lokacin da tay arba da faffadan bayan shi, wlh sai taga kamar Danish ne yanayin tsayuwarsa banbancin Danish yafi sa tsayi da kuma doguwar sumar kai, uwa uba launin fatarsu ba daya ba. "Wanene"? Ta ƙara faɗa cike da fargaba, gudun kada ya tsoratar da ita yasa shi juyowa a hankali suka fuskanci juna tana ganin chief tay saurin share hawayen ta saboda ya hanata kuka, tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin a cikin dakinsu, arude ta furta"barka da dare" ya fahimci rudani dake akan fuskarta hakan yasa shi cewa"I'm sorry na shigo dakin ku batare da izninku ba, na fito ina zagayawane najiyo shesshekar kukanki, Hankali ya tashi sau uku ina yin sallama ba'a amsa min ba, har knocking nayi shiru shiyasa na yanke shawarar shigowa ciki amma ba halina bane" Cikin sanyin murya ta furta"na fahimce ka, kuma nagode da kulawarka agare ni, ka damu dani sosai" Sam taki bari su hada ido tun kallon farko da tay mashi ta kawar da idanun ta. "Kin manta sharaddun da dr ya gindaya maki? I thought I would find you sleeping, although you are doing good thing, but you should continue resting until you've fully recovered, ban hana ki masa addu'a ba, zaki iya yi masa addu'a aduk lokacin da kikai sallah, amma yanzu dare ne Unaisah" with respect ta amsa mashi da toh. Shiru suka ɗanyi na wani lokaci, takun tafiyarsa taji da sauri ta dago matsowa yai dab da ita.. Ta sadda kanta kasa tana dan jin faduwar gaba. In a cool voice yace"a ranar da mu ka kwana a sansanin mu, Danish ya nemi in yi masa alkawarin ko bayan ransa In kula da rayuwarki data mahaifinki da yan uwanki, and I vowed to fulfill his request" jin wannan maganar yasata kusa fashewa da kuka jikinta ya kama kerma. "Ban fada maki don in fama maki raunin dake a cikin zuciyarki ba, sai don inaso ki taimakamin Unaisah, Ki bani hadinkai gurin ganin na cika masa alkawarinsa, in har kika bani dama duk da ina shiga busy saboda aiki zan yi kokarin ware mana lokacin da zamu dinga ganawa da juna, in sha Allah I'll support you in overcoming the pain that's troubling you." dakyar ya ƙare maganin ganin yadda hawaye ke yar tseral kan kuncinta aranta ta ayyana wata irin kauna Danish yakeyi mata? Ya Ilahi, Shi damuwar shi wanda zai kula da rayuwarsu in baya nan wayyo Allah hakika tayi babban rashi arayuwar ta. batai aune ba taji safkar yatsun chief kan fuskarta gently ya soma share mata hawayen ta. Muryarsa tamkar ta me yin raɗa ya furta"If you give me a chance, I will replace him, despite knowing I may never fully replace him in your heart" ya ɗan dakata yana mayar da numfashi, ta nutsu tana sauraron shi. "Na riga shi sanin ki amma ya riga ni haduwa dake, nasan da ace tun lokacin na bayyana kaina agurinki da nima na samu gurbi acikin zuciyarki, sai dai kash na makaro amma har yanzu ina da sauran dama Unaisah, nasan kun shaku da juna ke da shi, kun sha wahala a tare, kun yi rayuwa a guri ɗaya, kun san sirrin juna, nikuma bansan komai dangane dake ba, amma idan kika bani dama nayi maki alkawarin zan canza maki rayuwarki...." da wata irin siga ta jan hankali yai mata maganar, har saida taji wani irin yanayi atare da ita, kalamansa sun ta6a zuciyarta. Ɗagowar da zatay keda wuya karan hancinsu ya gogi na juna razanar da ta ɗanyi ne yasa ta ɗaga ƙafa zatay baya aikuwa gaba daya ta tafi zata kife kasa saboda rashin kwarin jikinta. Cikin zafin nama yai hanzarin damko waist dinta Ya janyota gaba daya ta fada kan broad chest din shi, wani irin faduwar gaba taji, She could feel his heart beating rapidly, lumshe idanunta ta danyi sam ta kasa motsawa daga jikin shi, ta rasa gane me take ji? Amma tabbas taji wani irin sanyi da kwanciya hankali yana ratsa zuciyarta. har ga Allah bai janyota da wata manufa ba, gudun kada ta fadi yasa shi rukota sai kuma abun ya nemi ya jefasa a wani yanayi mara misaltuwa, nutsuwa yai yana kallon fuskarta tay lamo a jikin shi kamar jinjira. Damuwar rashin Danish ta fara affecting brain din ta, komai ya faru Danish take gani a yanzu haka ji take kamar a jikin Danish ta faɗa shiyasa ta kara narke masa. abunka ga mabukacin dake bukatar duk wani abu da zai sanyaya mashi zuciya. "Unaisah" shiru bata amsa mashi ba. "are you sleepy? Ya tambaya yana leken fuskarsa. Still bata motsa ba, Batool ce ta fara mutsu mutsu kamar zata farka, hakan yasa shi raba ta daga jikin shi ya ɗan jijjigata dakyar ya samu ta buɗe idanunta wadanda suka kaɗa jawur kamar an watsa masu barkono. "Muje ki kwanta" kamar gunki tay shiru babu alamun zata ɗaga ƙafarta, kamar bata jin me yake cewa. Sungumarta yai kan Shoulder inshi Ya nufi bed da ita, Cikin kulawa ya kwantar da ita.. "Kada Ki kwana Da hijab a jikin ki, Ki cire sannan ki yi addu'a" sai lokacin ta dan jinjina ma shi kai. Ajiyar zuciya ya sauke kafin Yai hanzarin juyawa ya fuce daga dakin. Sai bayan daya fitane ta samu kanta, maganganunsa ne suka dinga yi mata yawo akai a haka har bacci mai dadi yai awon gaba da ita. "ANEELEERH🌹* ba ita ta tashi farkawa ba sai wuraren ƙarfe huɗu na dare dayake tasa abun aranta har mafarki saida tayi, idanunta biji biji ta buɗe su ta dubi agogo, kafin ta curo wayar daga chargy harta cika, Kunna wayar tayi Haskenta na kawowa taga abunda ya karya zuciyarta hoton Ana ne da baby junaid akan wallpaper dinta sunyi murmushi a hoton. Bata samu wayar da password ba, lalube ta cigaba dayi mata ta shiga whatsapp dinta, tana tsaka dayin scrolling ta fada Archived anan taga wani Group da Ana ta bude ita da sisters dinta,, Shiga ciki tayi ta soma karanta firarsu. _sister, ke da kike zaune cikin rufin asirin Allah, meyasa kika ce kin gaji da zama gidan? Bayan irin sabon da kikayi da Aneelerh, gashi muma ta silarki mun samu taimako a gurin ta_ _ba zaku gane ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, bawai don son raina nakeso In bar gidan ba, kawai hankalina ba akwance Yake ba, ni dai kawai inaso nabar gidan ne_ _kinga in wani abu ke damunki, ki fada mana, mu nemi mafita a tare_ _kada ku ɗaga hankulanku, babu komai, kawai inaso nadinga ganinku kullum akusa dani, saboda kuka dai ne dangin da kuka rage min a duniya_ _idan kina so mu dawo kusa dake, toh ki sama mana aiki anan abujan mana, sai mu dawo, muma munfiso mu zauna kusa da ke_ _bazan bari ku dawo nan ba, sai ni kusa ma min aiki in dawo nan_ _meyasa_ _nafison zama a Jos din fiye da nan_ Dakatawa Aneelerh tayi da karanta sakon, aranta ta ayyana meyasa Ana take gudun zama abuja? Bayan kafin zuwansu tafi kowa daukin zasu dawo nan"! Girgiza kai ta danyi kafin ta yanko wata firar tasu ta ci gaba da karantawa.. _janet tace"Ana! Kina cikin hayyacinki kuwa? Meyasa kike magana kamar wata musulma"? esther tace"Na fara zarginta, cikin kwanakin nan kullum in zakiyi magana a group chat dinmu sai kin sanya mana abun addinin musulunci bayan mu ba musulmai bane_ _Voice note ta tura masu"nagaji da 6oye maku da nake yi, ku yan uwana ne babu wani sirri atsakanin mu, nasan zaku goyi bayana" su kace muna sauraronki"Na musulunta, Yau wata biyu kenan, amma babu wanda ya sani, ko Aneelerh ban fada mata ba, A boye nake yin sallah ta"_ _"Dagaske kike ko wasa" janet ce ta fada_ _"Na ta6a maki wasa irin wannan"? Janet tace"a'a"_ _Ana Tace"toh, Dagaske nake Ana ɗinku Yanzu musulmace ni, na yi imani da Allah kuma nayi imanin cewa Jesus da muke bautamawa bawan Allah ne kuma manzon sa ne"_ Esther tace"nagaza yarda Ana, kamar dai kin haukace, taya zaki bar addinin iyayen mu da kakannin mu"? _Dogon voice note ta tura masu mai dauke da bayanin abunda Yaja hankalinta harta musunta tace ita kawai ta kaɗaitu da son addinin musulunci saboda kyawawan dabi'un Aunty Anila, tana burgeta tana sonta tana son yadda take janta ajiki, da yadda take kyautata mata, bata ta6a nuna wariya tsakaninsu ba, tana son tayi koyi da komai nata, yanayin mu'amalarta, kyawawan halayanta, da yadda take karatun al'qur'ani, hatta shigarta ta musulunci burgeta takeyi dama kuma ta ta6a yi mata tayin addinin tun farko farkon fara aikinta gidan Uzair ta nuna bataso, tun daga nan bata kara takura mata ba, tadaice mata tayi bincike sosai akan addinin musulunci zata gane abunda take son fahimtar da ita, kunji abunda yasa na musulunta kuma sai nagane shine addinin gaskiya, kuma Inaso ku musulunta don mu gudu tare mu tsira a tare_ wani chat nasu da Anila ta duba, yan uwan Ana ne su ka yi mata voices da murnarsu suka fada mata sun musulunta, tayi murna kamar kamar me sukace ta za6a masu suna tace ita sunan data canza ma kanta sunan nana Aisha, Ita kuma janet ta sanya mata sunan Khadija, sai Esther Zainab, bayan ta raɗa masu sunan janet tace sufa ko alwala basu iya ba, bayan haka basu san komai ba, tace kada su damu zata dinga koya masu kur'ani da hadissai acikin group din nasu itama da apps na musulunci take amfani da kuma sauraran karatun malamai da wa'azinsu ta haka ta ke samun Ilmi. Lokacin da Aneelerh ke karanta Chat din, hawayene Cike tab da idanunta, wani irin murmushin farin ciki tadinga saki kamar wata zautatta, aranta ta ayyana ashe ana ta musulunta bata sani ba? Allahu akhbar, Abunda yafi faranta ranta, hada Yan uwanta ta musuluntar. taji dadi da Ana ta musulunta ta silar ta, A hankali ta furta"Alhamdulillah Ya Allah na gode maka..." har sujjada saida tayi. yanzu A ina zan samu ana? Ta jefa ma kanta tambayar? yanke shawarar kiran layin Yan uwanta tayi sam ta manta dare ne ta shiga danna masu kira babu wanda yayi picking, Zuciyarta cike fal da farin ciki ta jingina bayanta Jikin gadon su, kiraye kirayen sallar asubahi da aka fara ne yasa ta aje wayar, ta mike ta shiga toilet don tayi alwala. Bayan ta sallame sallar, ta zauna tayi addu'o'in da ta saba yi daga cikin harda Ana tayi ma addu'a sosai, kafin ta mike ta dauko wayar Ana ta koma kan gadonta, Gallery ta shiga ta dinga budo hotunan Ana dana yan uwanta. Ta shagala tana kallon su Unexpected yatsan ta ya danno video ba tare da sanin ta ba, shesshekar kukan da tajine Yasa Ta mayar da hankali akan videon.. wani irin faɗuwar gaba taji, Lokaci daya ta zazzare idanunta wadanda bakomai ne acikinsu ba face tsantsar tashin hankali da rudani gami da al'jabi, ta yi matukar razana da jin abun da kunnuwan ta suke jiye mata, gaba daya ta rude, gumin tashin hankaline Ya fara tsastsafo mata ta ko'ina a jikin ta, kafin kace me Tsigar jikinta ta fara tashi haikam, La66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati... tsabar kiɗimar da ta yi ne Yasa tadinga sambatu kowace addu'a tazo bakinta furta ta kawai takeyi, har saida takaiga junaid dake bacci ya farka a firgice sakamakon sallallamin dayaji Mommynsa nayi. Yana buɗe idanunshi suka sauka akan fuskar Aneelerh wadda ta jike sharkaf da gumi, Idanunta sun kaɗa jawur har wani zazza6i zazza6i take ji a jkin ta..." Kusan sau uku Junaid yana ambaton sunanta bata ji shi ba, saboda kwakwalwarta ta tafi hutun wacin gadi, abune da bata ta6a zata ba. "Aunty Aneelerh? Kina ina ne nake jin kukan baby junaid" muryar zahra ce ta fargar da ita, a firgice ta zabura ta sauko daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja ta rufe. lokacin da zahra ta shigo junaid kadai ta gani zaune sai kuka yakeyi idanunshi akan kofar toilet din dakin. da sauri ta nufe shi ta zauna gefen gadon tare da daukar shi ta rungume a kirjinta"junaid lafiya kake kuka? Ina mommyn naka kota shiga wanka ne"? Da yatsa Ya nuna mata toilet door din"nan ta shiga da gudu, inata kiran shunanta bata amsa ba..." da ɗan mamaki ta dubi kofar toilet din kafin ta maida dubanta ga junaid"i'm sorry, Yi shiru, mu jira ta fito" kwa6e fuska yayi "to ai jiya nace ta hada min tea bata kawo ba, har bacci ya ɗoke ni" kallon cup din dake ajiye kan Table tayi"Ko shi ne wannan ta ajiye maka" sai da tay maganar ya lura da cup of tea din da Aneeleeh ta ajiye. Zahra tace"shine ma, amma naga Ya huce, Bari naje na hado maka wani hada noodles zan dafa maka" Aneelerh dake acikin toilet tafukan hannayenta biyu toshe da bakinta gudun kada kukan ya kubce mata, tana cikin halin ha'ula in nan tajiyo muryar junaid daga waje yana kwankwasa kofar toilet din"mommyn ki fito" gaban faucet taje ta wanko fuskarta ta buɗe kofar ta fito, a tsaye ta same shi ya ruƙe qugun shi fuskar shi a daure kamar wani babban mutum. "Junaid, i'm sorry, jiya na kawo maka tea din sai na iske kana bacci" da shagwa6a yace"tea dinma ya huce, aunty zahra zata haɗo min wani kuma ma zata dafa min noodles..." "Yawwa, Yanzu mu shiga toilet inyi maka brush, kafin ta dawo" amsa mata yai da toh, cikin sauri taje ta ajiye Wayar Ana Cikin rigar pillownta ta zuge ta, kafin ta dawo ta ɗauki junaid ta shiga toilet da shi. da shigarsu ba'afi minti talatin ba, sai ga zahra ta shigo hannunta ruke da madaidaicin tray mai dauƙe da plate biyu na noodles da zafinta tare da cups of tea ta ajiye kan table din gaban gadon, ta zauna tana jiran fitowar su don taji motsin ruwa a toilet. Wayar hannunta ta cigaba da dannawa, Har zuwa lokacin da Aneelerh ta fito bayanta a goye da baby junaid, har wanka tayi mashi ta lullu6e shi da towel dinsa. Yana ganin abunda zahra ta kawo masa ya fara Washe baki, tun da ta fito take ta kokarin kaukauce ma zahra don kada su hada ido.. "Auntyna Barka da safiya kun tashi lafiya? "Lafiyalou zahra, Hope kina lafiya" da fara'a tace"lafiyalou" "Sannun da kokari zahra, baki gajiya dayi mana dawainiya" ta fada tare da daura junaid kan gadon. "Haba Aunty Aneelerh, wata irin dawainiya"? Ta faɗa tare da mikewa ta nufi closet din kayan junaid"Yaushe zai koma school ne? Ta fada yayin da take dauko mashi kayan da zai sanya "In sha Allah next week zai koma" Riga da wando ta dauko mashi, da kanta ta sanya mashi, Aneeleeh dake a zaune ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa mafaɗi a duniya Zama zahra tayi kusa da ita, ta daura junaid kan laps dinta, tea ta fara bashi Ya shanye duka kafin ta dauki fork ta soma nannado noodles tana tura mashi abaki yana ci. sam bata lura da Halin da Aneelerh take aciki ba, sai surutu takeyi tana fadin"Aunty Aneelerh ba zaki ci bane,? Shiru taji bata amsa bata ba, juyowa ta danyi tare da leƙa fuskar ta, gabanta ne ya faɗi ganin tsantsar damuwa akan fuskarta, idanunta sun kaɗa jawur. Da karfi zahra ta furta"Aunty Aneelerh"! Firgigit tayi tare da kallonta razanar da tayi yasa Zahra jin fargaba. Adabarbarce ta furta"am...um...zahra.. Har kin sa mashi kayan..." a ruɗe zahra ke kallon ta duk tabi tasha jinin jikinta.. "Aunty Aneelerh, Lafiyarki kuwa? Kinga yadda idanunki suka kumbura, kumatunki sun yi ja, kamar kinyi kuka, gaba daya ma kin sauya min kwata kwata babu nutsuwa atare dake" dakyar ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace"bakomai wlh, lafiyana lou, kawai tunanin duniya ne..." girgiza kai zahra tayi"wlh kallo daya mutun zaiyi maki ya fahimci baki cikin nutsuwarki, auntyna in akwai abunda ke damunki, ki fadamin dan Allah sai mu nemi mafita a tare..." murmushi ta danyi"Zahra ki yarda kawai babu komai" gyaɗa kai tayi"shikenan, ga noodles din nan ki ci pls, kada ki zauna da yunwa ni zan tafi gurin aiki har na kusa yin late" "Nagode da kulawarki zahra, ki kula min da kanki" tana murmushi tace"kema haka" kar6ar junaid anila tay don taci gaba da ba shi abincin. Zahra Harta kusa ficewa daga dakin ta tsinkayi muryar Aneelerh"Uncle na nan ne"? Zahra bata kawo komai aranta ba tace"Eh, yana nan dakinsa" "Okay, " fuce wa zahra tayi daga dakin.. Bayan tafiyar zahra, da rabin awa ta fito Hannunta dauke da baby junaid ta nufi dining area, tunkafin ta karasa ta hango mutanan gidan gaba daya sun hallara akan dining chairs zahra ce kadai babu atare da su. tsayar da idanunta tayi akan Uncle dan iya daya hakimce kan kujera Ya ƙwama wani uban glases akan idanunsa, Ya tasa farfesun yan ciki shake da plate sai sharbar romo ya ke yi kamar ƙaramin yaro, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa matuƙar bacin rai, fusata, da tsantsar tsana Aranta ta furta Mugu bashi da kama, Cike da rashin kuzari ta karasa cikin girmamawa ta gaishe da su da fara'a suka amsa mata, mami ta mika hannu ta kar6i junaid ta zaunar da shi kan laps dinta nan fa ya fara zuba mata shagwa6a. Tun da ta zauna mami ta yi serving dinta duk cokali daya idan tay sai ta dago ta kalle shi gabanta sai faduwa yakeyi, hakanan yaji kamar Ana kallonsa yana kokarin dagowa tay saurin kawar da idanunta, a dabarbarce ta shiga tura chips abakinta, Mayar da kansa yai ganin ba abunda ya zata bane. "Aunty Anila ya maganar komawar Junaid School ne? Tun da yaji sauƙi ya kamata amaida shi, karatu yana ta wuce shi" "Zahrama ta tambayeni dazu, in sha Allah sati mai zuwa zai koma" Mahboob Yace"Allah Yakaimu lafiya" ta amsa da ameen Junaid dake zaune saman Laps din mami tana bashi abinci tuni ya haɗe fuskar shi muryarshi da shawaga6a yace"Allah ni bazan koma ba, dodo zai ɗauke ni in naje.." dariya su ka yi Abie yace"jikana mai abun ban mamaki! Wani irin dodo ana zaman lafiya"? Yana faman zumbura baki yace"wanda Ya kashe..." a firgice Anila tay sauri katse shi da karfi ta furta"junaid! Ya isa haka, kamanta abunda na fada maka" da sauri ya rufe bakinsa da tafin hannunsa, dariya su ka yi inka cire Uncle ɗaya wanda hankalinsa kwata kwata baya akan su, Anila kam Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba su ɗago komai ba sun maida abun wasa, agogon hannunsa ya duba kafin ya mike Abie yace"har za'a fita"? Uncle yace" Yau hutu nake har gobe ina gida" Ya fada tare da juyawa ya nufi bedroom dinsa. Mami tace"wai nikam Ina zahra ne? Ko har an tafi aikin"? Ummi tace"eh tun dazu ta wuce, tazo tayi min magana cikin bacci naji ta" ummi tace"nima kam naso naji ta tana knocking yau fitar wuri akayi kenan, Abie Yace"zahra badai hankali ba, bata iya tafiya aiki batare dabi kowannan mu tayi mashi sallama ba" Mahboon yace"dama tayine don afada" dariya sukayi, Ummi tace"na fahimci kana kishi kaji an yabi zahra" ta6e baki yayi Anila dake kallonsu daya bayan daya wani irin tausayin su ne Ya kamata. A Obie Estate kuwa, Yau shirye shiryen Tarbar baba Obie su ke yi, kasantuwar yau ne ranar da zasu dawo daga Lagos, maids din gidan tun safe suka fara gudanar da aikinsu. Tsaye take a gaban dressing mirror tana ɗan jujjuya jikin ta, wani hadadden Saree ta sanya launin ja mai adon duwatsu sai sheki suke, yayi bala'en yi mata kyau kamar amarya, ta zuba adon Zabba da awarwaro a hannayen ta, ga wasu jerin gemstone necklaces a wuyanta masu daukar ido, ta saki doguwar sumar kanta a abayanta baka wulik sai sheki take, A hankali take kokarin gyara Earrings din dake a kunnanta, yayin da idanunta ke kallon cikin madubin, Ita kanta ta yaba da haɗuwarta, Sareen jikinta ya nadu sosai ya zauna mata, ɗan light makeup tay akan fuskarta tayi kyau, daddaɗan ƙamshin turarenta dana bakhhoor burner din data Kunna Ya gauraye iskar ɗakin da wani irin kamshi mai dadin shaka. Murmushi ta dan saki har dimple dinta Ya lotsa, ta fito sak ba'indiyarta ta usili, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, bakomaine yasa ta farin ciki ba face murnar dawowar Pravin Jiya sunsha waya da shi yana fada mata irin kewarta da yai yace mata ta shirya mashi kanta don idan ya dawo sai ya fanshe kwanakin da baya nan. Cikin harshen indianci ta furta"Ina jiran ƙarasowarka my lovely husbad" ta faɗa tana yar dariya. High heels ta ɗauko ta zura a kafafunta ta fito ta nufi kitchen don ta duba masu aikin gidan. *HAJIYA SARATU* Tana a kwance kan katafariyar bedmatress dinta tayi nisa a baccin ta, Ta wawware kafafuwanta daya tay dama daya tay hagu sai jan minshari takeyi, Sleeping gown ce a jikin ta, zanen kitson da ke akanta ya kara fiddo da kyawun fuskarta duk da babu annuri akanta. Iphone dinta dake ajiye saitin kunnanta ce ta fara ruri da karfi sautin ya addabi kunnanta, har saida ta fara kokarin farka cikin magagin bacci da bacin rai ta dinga katse kiran almost 4 times a na hudu ne ta fusgo wayar ta kara kunne rai a6ace ta furta"wai wanene ke son takura mini ne"? "Jatuminki ne" ras taji gabanta Ya fadi jin muryar baba Obie, a rude ta zabura ta miƙe fuskarta ya amutse cike da jin nauyin furucin da tay sam takasa magana saboda kunya. Murya na rawa ta furta"baba i'm sorry, wlh bansan na furta ba, Kiran wayarka ne ma ya tashe ni daga bacci bansan kai bane ka kira..." bata kare maganar ba ya katse ta"Auta Ko da bani bane abun da kikai ya dace? Idan abokan aikin ki ne fa"? "Baba ka gane mana, daga bacci na tashi, ban gama wartsakewa ba" "Pravin bai fada maki yau zamu dawo bane"? Yamutsa fuska tay"ya fada min"? "Shi ne kuma kike ta baccin asara, ba zaki tashi kije ki gyara kanki ba"? Haɗe rai ta yi "baba wani irin gyara kuma"? sautin dariyar shi tajiyo"its Okay, yanzu haka muna akan hanyar zuwa airport" "Okay, zan zo in tarbe ku, Yanzu zan shirya Allah ya kawo ku lafiya" ya amsa mata da Ameen kafin sukai sallama. Saukowa tay daga gadon tana ƙuƙuni kan maganar gyara da baba obie yai mata. "Haba Akan me zan takura kaina, Gyara ya wuce mutun Ya dawo ya iske iyalinsa daya bari cikin koshi lafiya, Nifa ba baiwar Namiji bace ehe.." ta ƙarashe kukunin tare da bude toilet door ta shige. Lokacin da ta ƙaraso Kitchen din kamshin abinci ne ya daki hancin ta har can cikin makoshinta kamshin ya ratsa. Sam basu lura da zuwanta ba, gaba daya Hankulansu na akan girke girken da sukeyi. Gyaran muryar da tay masu"Aikinku na kyau" atare suka dube ta, kamar yau suka fara ganinta tayi masu kyau, murmushi suka saki tare da gaishe da ita cikin girmamawa, da fara ta amsa masu. "Ya kamata kuyi sauri ku kammala, sun kusa karasowa" Sofia tace"in sha Allah kafin su karaso zamuyi kokari mu gama" Hajjaty tace"yanzu dame dame ku ka kammala"? Safa ce ta lissafa mata. "Okay, naji kince hada dambun Nama, pls Ki dan zuba min shi tare da juice, wlh yunwa nake ji" ta fada tana shafa cikin ta, dariya sukai cikin raha tana lura da satar kallonta da sukeyi tasan da wuya in basuyi gulmarta ba kamar ko ta sani gulmace ke cin su. Bayan Safa ta zuba mata dambun naman a plate ta haɗo mata da glass na juice a kan madaidaicin tray ta daura mata tare da muka mata tasa hannu ta kar6a tare da yi mata godiya ta juya ta fuce. fitarta keda wuya Abla tace"wannan gayu haka hajjaty, Kamar wadda zataje gasar kyau"? Ta fada baki asake, sofia tace"ni dai wlh tana burgeni, inason mace mai tsafta da iya daukar wanka, amma abunda bangane ba Wa takeyi ma kwalliya ne? Naga dai ba wani guri take zuwa ba kullum tana a gida" "Kun cika sa ido, Nifa bansan gulma wlh, naga dai ba yau ta fara yin kwalliya ba" safa ta fada tana jifarta da harara. "Ba yau ta saba ba amma na yau yasha banban, yau fa baba Obie da pravin zasu dawo meyasa zata ca6a adon nan sai kace wadda zata tarbi Mijinta, ko dai hajiya saratu batay gayun nan ba bana tunanin ma ta tashi daga bacci, sai ita zakakka abun nata na nema ya wuce gona da iri ya kamata ta tsaya a matsayinta na yar aiki" Ta kare maganar tana hura hanci Fashewa sukayi da dariya.. "Pls Ya isa haka Sofia, nasan meke damunki, Bakin cikine da hassada, Saboda kinga hajjaty Allah ya zuba mata ruwan kyau gashi tafi ki matsayi shiyasa kike kishin ta" tsoki Sofia taja"Allah ya kiyaye inyi mata hassada Ni kawai na fara zargin akwai wanda takeso ta mallaka agidan nan shiyasa take caba ado nan don taja hankalin sa, In kuwa hakan ta faru mu zamu zama bayinta, kuna gani dai haka Harriet ta aure Sir mubarak to wai mu ko bamu da farin jini ne a gurin mazan family din nan" ..fashewa sukayi da dariya. "Duniya tayi maku dadi, wato Na lura gaba daya kun manta da marwa" acewar Abla, Atare suka hada baki gurin furta Alah sarki marwa ko awani hali take? Safa tace"jiya nayi waya da innarsu ta fada min jikin nata da sauki har ta fara kokarin yin magana" Sofia tace"baiwar Allah tadaiji jiki sosai, Alah ya bata lafiya, ko ta samu ta dawo bakin aikin ta, In sha Allah nima da anjima zan kira inji ya jikin nata" _____________________________________✍️ A hankali take tafiya cikin takun dattako, wata hadaddiyar egyptian abaya ce a jikinta mai tsadar gaske, tay rolling head scarf, yayin da Idanunta ke amanne da farin glases, Ko hoda bata shafa ba amma ba ƙaramin kyau ta yi ba, hannunta daya na a ruke da purse dinta, ga wani daddadan fragrance dinta dake tashi. Har zata gifta idanunta suka hango mata hajjaty, wani uban burki ta ci ganin yadda ta caba ado kamar wata amarya. "Ke zonan" ta fada da ɗaga murya, hajjaty bata san da zamanta ba, har takusa shiga part dinsu na maids ta tsinkayi muryar Hajiya saratu rass taji gabanta Ya fadi arude ta juya tana kallon ta, da hannu tay mata alamar tazo. Hankalinta ya tashi don tasan kiran hajiya saratu ba alkhairi bane. Jiki asanyaye Ta nufe ta aranta tana ta ambaton la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. Koda ta karasa nesa da ita ta tsaya cikin sanyin murya tace"gani aunty saratu" harara ta galla mata har saida tasha jinin jikinta. "Uban wa kikai ma wannan adon"? sunkuyar da kanta kasa tay, aranta ta furta"mijinki nayi mawa, a fili kuma tace"Aunty, kamar dai yau kika fara ganin nayi kwalliya"? Ji tay kamar ta kwasa mata mari saboda fusata"karki kuskura ki kara kirana da sunan aunty, in banda munafurci sai da kika saisaici ranar da kikasan mijina da baba zasu dawo tukunna kika caba adon nan ko? A cikin su wa kikai mawa"? Ta fada tana cije lips dinta hadi da matsowa kusa da hajjaty, jikinta sai kerma yake tray din hannunta kamar zai kife kasa, Cikin rawar murya tace"Allah shine shaidata, Ni banyi kwalliyar nan don daya daga cikinsu ba, nayi ne saboda in burge kaina" idanunta cike tab da kwalla ta kare maganar. Da hannu hajiya saratu ta cafko pallu din sareen data laga kan kafadarta.. Ta soma goge mata kwalliyar fuskarta ran hajjaty ya 6aci sosai duk ta cabe mata kwalliyarta. Murmushin mugunta hajiya saratu ta saki da alama ta manta da abunda hajiya laura ta fada mata"Idan kin koma ɗaki, Ki cire sareen nan, Yau nafi son naganki cikin uniform na ma'aikatan gidan nan fatan kin fahimce ni" jinjina mata kai tay"Toh" "Yawwa zaki iya tafiya" har zata juya ta kuma kiranta Da yatsa ta nuna tray din hannunta"meye a ciki"? Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"dambun nama ne" "Samun wuri, Wato ke har kin riga masu gidan dandana girki ko? Ta fada tare da kai hannu ta buɗe plate din Ta duma hannu ta dibi dambun naman ta tura abaki tana tauna, bakinta a cunkushe tace"kafin in dawo kisa a shirya min Lunch dina, komai da aka dafa za'a zuba min.." ta fada tare da kara dumbuzar dambun naman ta tura abaki, kafin ta dauki Juice ta kur6a, duk hajjaty tana atsaye tana kallonta. Tsoki taja"duk na bata hannuna da maiko ni da zanje airport tarbo mijina" cikin sanyin murya hajjaty tace"yakamata ki wanke" ta fada tare da nuna mata Sink din dake a kusa da in da suke. harara ta galla mata"nifa komi zakiyi ba zaki taba burgeni ba.." Ta fada tare da zaro hanky daga purse dinta ta mutsustsuke hannun dashi duk don kada hajjaty taji dadin ta bi shawarar ta, juyawa tayi ta nufi hanyar fita daga falon. Binta da kallo Hajjaty tayi har ta bace ma ganinta, murmushi ta saki ta danyi mamaki da ta ci abun hannunta musamman a kwanakin nan data lura kamar batason ko hanya su hada, tabbas ta bata mata rai amma har yau Allah bai sanya mata tsanarta ba, Ita dai tana so su dinga mutunci da juna. Juyawa tayi jiki asanyaye ta nufi dakinta. kaitsaye hajiya saratu ta nufi hamshakiyar motarta, a hanzarce Officern da zaiyi driving dinta yai hanzarin bude mata cardoor har ta zura kai zata shiga muryar Twins ta katse mata hanzarin ta"Mommy" gently ta juyo tare da kallonsu, yayin da suke fitowa daga Entry hall sun dauki wankan suit kamar a turai. Murmushi ta sakar masu, Suna karasowa ta haɗa su duka tayi hugging dinsu gwanin ban sha'awa.. Bayan sun gaishe da ita ta amsa masu tare da cewa"my twins Ina zuwa haka? Yau dai ba aiki na sani ko za'a fita yawon bude ido ne" zaid yace"No, daddy ya fada mata time da jirginsu zai karaso shiyasa muka shirya don muje tarbo su" "Kunyi tunani mai kyau, Nima yanzu haka airport din zanje, me zai hana mu shiga mota dina" Bayan sun shiga suka sanyata tsakiya suna zaune a gefe da gefenta. Sai da motarsu ta haura kan titi kafin ta dubi zayn"ya zahra? Two days ban tuntube ta ba, amma nasan kai kana waya da ita" yamutsa fuska yai a dakile ya furta"may be tana lafiya" wani kallo ta wurga mashi"oh baka da tabbaci ma? Thats mean baka kiranta awaya"! "No ba haka bane mommy, Kinsan yanayin aikina bakasafai nake samun lokacin yin waya ba" girgiza kai tay"banji dadi ba, yakamata kana bata kulawa zayn, nan bada jimawa ba zata zama matarka" daure fuska yai, zaid sai faman kunshe dariya yakeyi.. "Mommy hannunki kamshin nama yakeyi ko hancina ne" Ya fada tare da ruko hannunta Yakai saitin hancin shi yana shinshinawa. "Kai Zayn Allah ya wadaran naka ya lalace, ka cika sa ido" ta fada tare da dago purse din hannunta, ta kwala mashi akai" dariya suka sanya gaba dayansu da alama dai suna acikin farin ciki. __________Hajjaty___________ Bayan da ta dawo daki, zama tayi daga gefen gadonta, ta ajiye din akan table din gabanta, A tsanake ta fara cin dambun naman fuskarta dauke da murmushi wato abunda hajiya saratu tay yabata dariya, aranta ta ayyana in da ni muguwace kamar yadda kike fadi wlh da abinci kadai zan iya kashe ki saratu. Wayarta ce ta soma ringing, tayi azan Pravin ne cike da zumudi ta janyo wayar daga kan pillow ganin ba pravin bane yasa murnar ta koma ciki amma taji dadi data ga kiran daga kayin marwa ne. Picking call din tay tare da kara wayar a kunnnata. "Ina wuni inna, ya jikin marwan"? Bata kare maganar ba, Muryar Marwa ta katse ta da cewa"Aunty Hajjaty Nice marwa dakai na" Da mamaki ta furta"Wai dagaske Marwa kece? Allahu akhbar amma natayaki murna naji dadi da bakinki Ya bude Marwa Ya jikin naki" "Da sauki, yatsun hannayena ma sun warke har abinci Ina ci dakaina" tsantsar farin ciki ne Ya cika hajjaty"Alhamdulillah Ya Allah mungode maka, Allah ya kara maki Lafiya marwa, Allah ya kara tsare ki daga sharrin Aljanu". "Ameen aunty, nagode da kulawarki agare ni" shiru sukayi na dan wani lokaci kafin hajjaty tace"kinji kwana biyu ban kira na tambayi lafiyarki ba, wlh na shiga busy ne amma kina araina, bari na hada ki da su Abla ku gaisa" har ta yunkura zata mike Marwa tay saurin katse mata hanzarinta"Aunty akwai wani abu da nake son fada maki sirri ne" jin wannan maganar yasa hajjaty ta koma ta zauna ta nutsu tana sauraronta. "Kiyi hakuri ki yafe min, Abunda ya faru dani hakkinki ne ke bibiyana, baki min komai ba, amma saboda kwadayin abun duniya na rufe ido na kar6i tayin aikin leken asiri da aka sani akanki" wani irin faduwar gaba hajjaty taji gaba daya tabi ta rude murya na rawa tace"ban.. bangane me kike nufi ba!" Marwa bata boye mata komai ba ta sanar da ita zargin da hajiya saratu takeyi akanta da kuma aikin data bata don tayi mata leƙen asiri don ta gano me take kullawa. "Marwa Dama kece kike tsoratar dani"? Cikin shesshekar kuka marwa tace"wallahi nice, nayi danasani hajjaty, baki min laifin komai ba hasalima kin kaunace a lokacin da wasu ke kyamatata, da zuciya daya kikai jinyata, na dade banga mace mai kyakkyawar zuciya irinki ba, kina da hakuri ga son taimako...." kasa karasa maganar tay saboda kukan daya kwace mata. Zafafan hawayene suka wanke fuskar hajjaty tabbas hankalinta ya tashi da jin abun da hajiya saratu tasa ay mata ashe tsanar da tay mata har takai ta sa adinga bibiyarta? Laifin me tay mata? Numfasawa tay kafin ta furta"marwa ki daina kuka, wlh na yafe maki, har ita hajiya saratun, Allah ya yafe mana baki daya, kuma naji dadi da kika gane kuskurenki" Bayan Marwa ta tsagaitawa da yin kukan tace"bawai iya wannan ne abun da na kira in fada maki ba..." A kagare hajjaty tace Ina sauraron ki marwa. "Bansan ya zaki ɗauki abun ba, amma kiyi hakuri ban fada maki don in tada maki hankali ba face sai don In ceto rayuwarki saboda Kyautatamin da kika yi, Da farko nayi danasanin aikin da hajiya saratu ta sakani amma daga baya Naji dadi saboda silar aikin Allah ya nuna min wani mugun abu dake rayuwa agidan nan" Yawu hajjaty ta hadiya kutt zuciyarta cike fal da fargaba ta furta"marwa menene? Fada min dan Allah! Numfasawa marwa tay kafin ta daura da cewa"Aunty PRAVIN shine silar ciwo na, Saboda Ya gano nice nake yi maku leken asiri shine Ya daura mini cutar kuturta Ya toshe min bakina" bata kare maganar ba sakamakon tsawar da hajjaty ta daka mata"Ya isa marwa! Bana son karya ki rasa wa zaki wa kazafi sai pravin? Taya pravin zai iya daura maki ciwo? Sai kace dai Aljani"! "Saboda shi din mugun matsafine, kece bakisan wanene Pravin ba, tun farkon fara aikina gidan nasan munanan dabi'unsa, Ya saba Bibiyar mu yana laluban jikinmu dayi mana barazana akan in muka tona masa asiri zaisa a koremu daga aiki....." wani irin faduwar gaba hajjaty taji daram dararam kamar ana mata luguden ta6are a kirjinta, Jikinta sai kerma yake kaf kaf idanunta azazzare cike da tashin hankali wlh ji take kamar a farmaki sam takasa yarda da maganar marwa taya ma wai pravin dinta zay aikata hakan? "Naji kin shiru, dama nasan ba lallai ki fahimce ni ba, amma ki sani wlh rantsuwar dan musulmi ba kazafi nayi masa ba, Halinsa ne, a daren ranar dana tashi da ciwon kuturta shine mutun na karshe daya shigo dakina, bayan na fito daga wanka naje gaban madubi kwatsam na hango mutun abayana ya goya hannayensa akan kirjinsa a razane na zabga salati na jiyo na dube shi nace pravin taya akai ka shigo dakina bayan na kulle kofa? Yana dariya yace min Nice na kira shi, daban shiga gonar shi ba da abunda zai kawo shi dakin, Hankalina ya tashi nayi azan yazo ya yi min abunda ya saba yi mana ne amma sainaga akasin haka yana matsowa kusa dani naja da baya har saida ya kure ni jikin bango, Ina zare ido nace in har bai fita ba, zan yi ihu in tona ma shi asiri kowa yasan ya shigo dakina still yana dariya yace ko nayi ihu abanza babu wanda zaiji, da naga bani da wata mafita yasa na fara rokon shi akan kada ya ta6a ni yace shi ba wannan ya kawo shi ba, yana so in fada masa wanene ya sanyani aikin yi maki leken asiri? Nayi mamaki jin yai magana akanki saboda ni a iya sanina farko daya kawo ki gidan nan ya kira ki da sunan yar uwarsa marainiya wadda ta rasa mijinta bai ma nuna kina da mahimmanci agare shi ba, A lokacin sai nace mashi Meye alakarka da ita? Kuma taya kasan Ina yi mata leken asiri? Yace saboda ke matarsa ce, maganar taya akai yasan ina yi maki leken asiri bata shafeni ba kawai yana son yaji waya sanya ni, na watsa mashi harara nace Munafukin banza wlh saina tona maka asiri agurin hajiya saratu, maciya amana, yace taya za'ay in tona mashi asiri Ina tunanin zai kyale ni ne bayan nasan sirrin shi, injira inga abunda zai faru dani, yana fadan hakan Ya juya ya fuce yana huci, bayan fitarsa na fara zumudin gari ya waye saboda na kudiri aniyar da sassafe zanyi sammako inje in fadawa hajiya saratu alakar dake atsakaninku dama abunda nake nema kenan" Ta dan dakata da bata labarin tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa"Aunty kwatsam tsakar dare ina tsaka da bacci na fara jin yatsun hannayena sunayi min kaikayi, a furgice na farka ina kikarin motsa labbana naji sunki budewa aunty adaren ranar naga bala'e ban kara komawa bacci ba....." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota..." Tunda tafara labarta mata abunda ya faru gaba daya Ta rude tabi ta rikice ta rasa tunaninta, ta razana matuka idanunta azare take jujjuya eye balls dinta, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata akan goshin ta..wa'iyazubilla bata san sa'adda wayar ta zame daga hannunta ta fada kan floor. fadawa tay kan mattress Ta lumshe idanunta da suka kaɗa jawur, Hakika hankalin ya tashi Ahakama bata gasgata maganar Marwa ba, saboda ta yarda da pravin ta cikin sauki bazata yarda don afada mata wani mugun abu daya shafe shi ba, Ita tasan wanene Mijinta, In har bashi ya bude baki ya fada mata da kanshi cewa ya aikata ba to ba lallai ta yarda ta cikin sauki ba, kawai tayi believing marwa karya takeyi mata sai dai abu daya dayasa ta jin farga harya haifar mata da kokwanto shine taya akai Marwa tasan akwai aure a tsakaninta da pravin❓ Fashewa tayi kuka tana fadin wallahi karyane, Ni nasan wanene Mijina, pravin ba matsafi bane, kuma baya bin mata, sharri ne kawai akeso ayi masa wlh marwa dana san zaki fadamin wannan maganar da banyi jinyarki ba saboda ke din ba mutuniyar kirki bace, Makira algunguma kawai kinaso ki shiga tsakanina da mijina ne..." kamar mahaukaciya ta dinga sambatu tana bubbuga mattress da hannayenta gashin kanta duk ya hargitse..." _________________________________✍️ *Chief Owais🔥🌹* Time da motarshi ta kunna kai cikin gidan baba Obie, tunkafin SA din dake driving dinsa yayi parking Idanunsa suka sauka akan Security details din daddynsa ta window glass din motar yake hango su, sunyi tsayuwar dakaru agaban dankara dankaran motocin su. Tuni yanayin fuskarsa Ya canza zuwa tsantsar bacin rai, yanzu baida abu mafi tsana a duniyar nan daya wuce mahaifinsa! Baya son ganin shi, ko sunan shi baya son ji, yanzu har takaiga ba zarginsa yakeyi ba tabbaci yake da shi akan cewa yana ɗaya daga cikin Elders na gidan kurkukun ƙaddara shiyasa kwata kwata yanzu baya jinsa amatsayin Uba, Ya toshe duk wata hanya da zata hada su, yanzun ma daya san yana agidan da baizo ba. Fitowa Yayi daga Cikin Motar, Farar jallabiyace a jikin shi ya naɗe kanshi da arab turban saboda baya son wani yaga raunin dake akan goshinsa, saboda baya son ya daga masu hankali, Walking slowly Ya nufi main palour, with respect maids din dake sintiri suke gaishe da shi bai ko kula su ba ya nufi part din baba Obie tunkan Ya karasa Ya dinga jiyo muryoyin Uncles dinsa suna fira cikin raha .. Knocking door din yayi,"wanene"? Hajiya saratu ce ta tambaya daga cikin dakin. "Owais ne" "Okay, Come In" tura kofar yayi tare da sa kai Ya shiga da sallama abakin shi, kusan a lokaci daya suka dube shi. baba obie yana daga kishindige kan Tattausan Rug Ya tada kansa saman Pillow, daga gaban shi wooden tray ne na fresh fruits da aka kawo ma sa, Hajiya saratu ce ka bashi Kayan marmarin a baki Yana sha. yayin da Senate Lateef da Sir Mubarak suke a zaune kan Sofa, Mai girma sharafudeen Yana a zaune kan arm Chair, Ya dauki wankan suit... "Zauna mana," Hajiya saratu ce tay maganar ganin yayi tsaye kamar mai nazarin wani abu. A hankali Ya zauna cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa mashi, kafin ya matsa kusa da baba Obie ya sumbaci forehead dinsa. "Sannu da dawowa baba, Ya gajiyar tafiya"? fuskar baba Obie da murmushi Yace"Yawwa shalelena, gajiya tabi jiki musamman da na ga rabin raina" dan murmushi yayi"nayi kewarka, bayan haka Naji dadi da Allah ya dawo min dakai cikin koshin lafiya" still fuskar baba obie da murmushi yake kallon shi, Har cikin ran shi yaji dadin maganarshi. Tun shigowarshi bai bari sun hada ido da daddynsa ba, shi ko Ya kura masa ido fuskarsa ba walwala ganin yanda Owais yaba banza ajiyar shi, Ko irin gaisuwar nan da suka saba yi in suka hadu da juna baiyi mashi ba, hakan ya jefa shi a yanayi na damuwa. Hajiya saratu tace"owais ina ka shiga ne? Kusan two weeks bama ganin gifcinka, ko an kira ba'a samunka"! Senate yace"abunda zance kenan, Kwata kwata baya leƙo mu, ko dan kaga kakan naka baya nan ne? Dama albarkacinsa muke ci halan" "Ba haka bane, wlh kuna araina, aikine ya boye ni" Sir mubarak yace"kufa haka kuke dakai da dan uwanka baku da magana sai ta aiki kamar agogo bakwa gajiya" dan murmushi yayi Baba Obie yace"karfa ku takura ma shi tom, in ba haka ba yanzu zan kora ku waje, kowa Ya kama gabansa kubarni da abun kaunata" dariya suka sanya banda mahaifinsa wanda ya zabga ubam tagumi. "Baba Ya aminin naka, na lura kaji dadin zama agurinsa, kai da kace zakai 3 weeks sai ga shi har ka kara kwanaki akai" yar dariya yayi Owais"ba zaka gane ba, wlh kamar kar mu rabu, dakyar fa escords dinshi suka rabamu a airport, wlh har kwalla saida na zubda saboda tausayinshi daya kamani" dakyar ya kare maganar, kwalla cike tab da idanunshi. Jikinsu duk yayi sanyi, tausayin baban nasu Ya kamasu Sir mubarak yace"har yau har gobe ina mamakin amintakarku baba, na dade banga abokai masu rukon amana da kaunar juna, da suka taso tunkuruciya batare da wani abu ya raba su ba irinku, Ina alfahari da ku, Allah ya ƙara dankon zumunci atsakaninmu da shi" kalaman Sir Mubarak sun faranta ranshi da fara'a yace ameen Senate Lateef Yace"baba mezai hana ya dawo nan mana, tunda shi ba iyali gare shi ba, a legos dinma ba wani dangine da shi ba, kai kadaine dai danginsa" numfasawa baba Obie yai kafin yace"ba yadda banyi da shi ba akan ya dawo nan mu zauna, amma yaƙiya shi dai yafi sha'awar zaman legos, hada sabo ke dawainiya da shi amma in sha Allah idan ya halarci family meeting din da zamuyi zanyi kokarin jan hankalinshi akan Ya dawo nan din.." "Ina pravin dinne? Ina so inyi mashi bangajiya" chief ne ya fada, hajiya saratu tace"Yana adaki" "Okay, ya fada tare da kallon Sir mubarak"Uncle, Ina zaki? Tsawon kwanaki banji duriyarsa ba, ko na kira bana samun layin sa" "Ay Zaki tun satin daya wuce suka koma canada.." hajiya saratu tace"ba sallama"? Ta fada ranta adan bace. Senate Yace"gaskiya ba a kyauta mana ba" Sir mubarak yace"kuyi hakuri, ai ba jimawa zaiyi ba, Idan za'ayi family meeting zai halarta ne" gaba daya hankalin sharafuddeen baya atare da su, bawan Allah Hankalinsa na akan dansa dake ta kakkauce masa.. "Baba Ina neman alfarma, agurin kowannanku" acewar Chief, gaba daya hankalinsu ya dawo kanshi.. Baba Obie Yace"ina sauraronka fadi kaitsaye" Shiru ya ɗanyi jimm kafin ya ce"inaso a yi family meeting a ranar birthday dina" da dan mamaki suke kallon shi, basu ta6a canza date na family meeting din su ba. "Alfarma nake nema, Idan kowa Ya amince min, amma idan bazai yiwu ba, ba damuwa" Numfasawa baba obie yayi tare da cewa"owais, wannan ai ba wani abu bane, canza date bazai zama matsala ba, nidai bani da damuwa na amince maka, sai dai bansan ra'ayin iyayen naka ba" ya fada tare da nunasu da hannun shi. Hajiya saratu tace"haba bakomai wlh, nidai na amince masa" "Nagode Auntyana" murmushi tasakar mashi Senate lataeef Yace"ka yi tunani mai kyau owais, kaga kowa zai halarci birthday dinka har ma wadanda basa kasar saboda family meeting, Nima ta bangarena na amince" fuskarshi asake Yace"nagode Uncle senator" ya maida dubansa kan sir mubarak wanda ya hade rai "Thats impossible, akan me za'a canza date da aka saba yin family meeting saboda kai? Gaskiya ni ban amince ba," hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, hatta sauran Uncles din nasa sunyi mamakin maganarshi haka baba Obie ma baki asake yake kallon shi, cikin sanyin murya chief yace"Shikenan, tun da baka amince ba, na hakura nima abarshi a kwanan watan da akeyi" dariya Sir mubarak yayi"zolayarka kawai nakeyi, kasan ni bani da matsala Owais, tun da har baba ya amince nima na amince maka, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya" sanyine ya ratsa zuciyar chief cike da jin dadi Yace"ameen Uncle dina thank you" "Sharafuddeen Me ke damunka ne"? Muryar Baba Obie ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula, murmushi ya kakaro kan fuskarsa babu komai baba," "Ina fata kaji alfarmar da ɗan naka yake nema agurinmu"? Jinjina kanshi yayi"naji baba, Allah ya nuna mana lokacin" iya abunda ya furta kenan. Wayar Chief ce tayi ringing, mikewa yayi da sauri Yayi masu sallama Ya fuce daga dakin don Ya daga kiran da aka yi mashi.. Bayan ya kammala yin wayar juyawar da zaiyi keda wuya yayi arba da daddynsa bawan Allah fuskarsa A yamutse yake duban shi. "Owais, Laifi me nayi maka? Meyasa kake guduna ko kallona baka son yi? Why Owais kayi blocking duk wata hanya da zan iya magana dakai" ya fada amarairaice. kallon tuhuma Owais Ya doka masa da kakkausar murya yace" ka daina boye true colour din ka, yanzu na riga da nasan ainihin wanene kai! kuma wlh alwashi na dauka saina tona maka asiri kowa yasan abunda kake aikatawa..." waro idanu waje mai girma sharafuddeen yayi da tsantsar rudani akan fuskarshi yace"owais wannan wani irin zancan banza ne? wani irin asirine kake ikirarin zaka tona min"? Banza yayi dashi bai tanka ma shi ba, matsawa Yayi kusa da shi"owais Ka fadamin dan Allah, me na aikata? Idan ma saboda Sleeping pill din dana bakane yasa kake zargina wlh banyi da wata manufa, nayi ne saboda naji tsoron in rasa ka" harara Chief Ya galla masa, ji ya ke kamar ya shaƙe wuyan uban nasa saboda tsanar da yayi masa. Hannu yakai yana kokarin ta6a turban din dake akansa da sauri Owais Ya cafke wrist dinsa a tsawace ya furta"Don't even think about touching me, or you'll face unforeseen consequences"! Hankalin Sharafudeen ba karamin tashi yayi ba, He couldn't believe that wai owais ne ke yi masa magana kamar zai doke sa? Babu tausasa harshe? Anya bai fara shaye shaye ba? Ko dai har yanzu ƙwayar maganin bancin daya bashi ce ke aiki ajikin shi❗❓ *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~<><><><><><><><><><><><><><><><>✍️~ ~______________________________________~ Cikin sanyin murya ya furta"Owais, bayan dana hana ka zuwa kai farmakin sai da kaje ko? Ka daina jin magana ta Owais! " ya faɗa idanunsa akan ciwon goshinsa daya ɗan leƙo batare da saninsa ba. "Lafiyata bata shafeka ba! Kuma Daga Rana Irin ta yau babu ni babu kai! Ni ba dan ka bane, kakane shine mahaifina mutumin kirki ba irinka ba, Kuma na rantse ka jira ka gani..." yana ƙarasa maganar Ya jefar da hannun sa daya ruƙe, Ya juya azafafe Yabar Part din Ko sallama bai je yayi ma baba Obie ba. Ya tafi Yabar Sharafudeen cikin rudani, bai taba zaton owais zaiyi masa haka ba, Kai ko a mafarki, Ji yayi bazai Iya jurewa ba, Cikin sauri Yabi bayanshi Yana fitowa Ya hango Motar Owais dake fita, da sauri ya nufi Security Details dinsa tunkafin ya karaso suka bude mashi cardoor din motarsa Ya shiga ciki, ya basu Umarnin su kai shi Gidan owais. Chief yana zaune seat din baya na motar, ya rufe gefen fuskarsa da hanky, Idanunsa sun kaɗa jawur, bai ta6a karaya da rayuwar duniya ba irin wannan karan yayi fatan ace ba'a halitto shi acikin ta ba, wai mahaifinsa matsafi ne! fasiki mai shan jini da cin naman mutun, Ya Ilahi! "Sir, motocin mahaifinka suna abiye da bayan mu" SA din dake driving dinsa ne yayi maganar, aransa ya furta wato mutumin nan saida ya biyo ni! Motarsu na shiga main gate na villa dinsa Ya ba Security officers Umarnin karsu kuskura su bar kowa ya shigo gidan. Bayan ya fito daga Motar, Cikin sauri Ya Part dinsa Yana kokarin Haura wa kan stairs Unexpectedly muryar Shi ta katse hanzarinsa"Owais? Lalacewar taka har takaiga ni kake bada Umarnin a hana shugowa gidan ka"? Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin shi Ya tsani jin koda muryarsa. a cikin kunnansa yake jiyo takun tafiyar shi bai motsa ba har ya karaso ya zagayo ta gaban shi suka fuskanci juna. Gabansa ya dan fadi ganin hawaye na sintiri kan kuncin mahaifinsa. Cikin raunanniyar murya yace"owais, Dan Allah ka fadamin Laifin me namaka? Wlh Hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har baka fadamin ba..." Zuciyarshi taso ta karaya, amma In ya tuna wanene Mahaifinsa nasa sai yaji kamar ana kara rura wutar ƙiyayyarsa a zuciyarshi. Bai ko kula shi ba, Ya nemi ra6awa ta gefen shi zai wuce, cikin sauri Sharafudeen Ya damƙi Arm dinsa. Cikin karyayyar murya yace"Owais, in har ba so kake zuciyata ta buga in mutu ba, ka fadamin laifin me nayi maka da yaja har kake zargina! wai ni owais, mahaifinka"! Kallo mai cike da tsana Chief Ya watsa mashi kafin yace"kafi kowa sanin laifin da ka aikata min, zaifi ka fita sabgata, don bazan taba fahimtarka ba, kawai ka jira lokacin da zan fallasa asirinka a bainar jama'a.." ya faɗa tare da bangaje hannun sharafudeen Ya kara gaba Ya shige part dinsa Yayi locking room door dinsa rai a6ace. A bangaren Mai girma sharafudeen Kasa motsawa yayi, al'ajabi da bakin Cikin maganganun da Owais ya gaggaya masa sun ruƙe zuciyarshi tamau sun hana kafafunsa motsawa, Ya rasa ya zaiyi bai ta6a sanin Owais yana da kafiya da taurin kai ba Sai yau da Allah ya nuna masa, tunani ya soma yi waya kamata Ya kira ya fada masa halin da yake a ciki!. Tsadaddar Wayarsa Ya zaro Ya daga aljihu ya shiga call logs Ya danna ma Number din da yayi saving da jini ɗaya kira, Tana fara ringin yayi picking.. A mutunce suka gaisa da junansu kafin Yace"pls ko zaka kira Owais, kuyi magana, akwai wani abu da ke damunsa yaƙi fadamin may be kai ya sanar dakai" tun daga yanayin muryarsa prime minister Hateem Ya fahimci dan uwan nasa yana acikin damuwa. Othe other hand prime minister yace"Okay, Don't worry, I'll call him Just calm down and take care of yourself for me" "Okay, Nagode kaima ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama ya juya ya tafi zuciyarsa a hautsine.. *ANEELERH* Ta fi karfin rabin awa tana safa da marwa a tsakar dakin ta, tana ta tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin, tun da ta saurari maganganun Ana gabanta keta faduwa, Hankalinta yaƙi kwanciya, damuwarta Ina Ana? Tana raye ko ya kashe ta? batajin zata Iya hakura taja baki tayi shiru batare da tayi gaggawar daukar mataki ba ko dan ta kwatarwa Ana hakkinta, ta kuma ku6utar da family dinta, zuciyarta ce ta dinga azalzalarta da tunzurata akan taje ta tunkare shi kaitsaye ta fada masa ta san komai sannan tayi masa barazana in har bai fada mata ina take ba zata tona masa a asiri uban kowa yasan me ya ke aikatawa sannan ta kaishi kara gurin hukuma. Kwakkwaran Numfashi taja, fuskarta babu annuri ta fito daga dakin bata iske kowa a falo ba, Mami da ummi suna a kitchen suna aikin lunch. Bata nufi ko'ina ba sai ɗakin Uncle dan Iya, da kwarin gwiwa take tafiya yayin da bugun zuciyarta ke ƙaruwa Ga tsoro tanaji amma ahaka ta dage ta durfafi dakin nasa har takusa kutsa kai Cikin ɗakin taji kamar an ruke kafafunta dakatawa tayi da yin tafiyar, nan take brain dinta ta fara tariyo mata maganar Ana. _watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda yace bazai kyaleni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kunga ni kadaice agidan, yanzun nan naga shigowar shi shiyasa na gudo daki don in samu damar yi maku video, dan Allah don sonku da manzon Allah saw Aduk lokacin da kuka kalli videon nan kuyi gaggawar kaishi ƙara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku bata lokaci, saboda shi din mutum ne mai hadarin gaske, ya sha yi min barazana akan In har na kuskura na fada ma wani abun da ya ke min wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na fadamawa shiyasa nakasa sanar daku_ Tuna wannan maganar yasa Aneelerh taji tsoro ya mamaye zuciyarta, tayi shiru tana sauraron gargadin da zuciyarta ke yi mata. _Kada ki kuskura Anila! Ba zaki Iya ja da shi ba, in har yasan kin san sirrin shi kashe ki zaiyi, mutane irinsa basu da imani zasu iya aikata komai donsu rufawa kansu asiri, Kwara ki nemi wata mafitar...." tayi zurfi cikin tunaninta kwatsam Ta tsinkayi muryar mutum abayanta "ANEELERH"! Ras gabanta Ya fadi jin muryar mutumin datazo nema, tuni taji tsigar jikinta na tashi, Yan hanjin cikin ta suka hau kadawa. "Ko ba ita bace"? Zazzare Idanu tayi, Cikin sauri Ta daidaita nutsuwarta, A hankali ta juyo ta fuskance shi, Yana atsaye Cikin riga yar shara da gajeran wando, Junaid Ya jima Yana fada mata Uncle dinta mummuna ne ba ta6a ganin muninsa ba sai yau data gano mugun halinsa. zuba mata jajayen idanun shi yayi, Cikin rawar murya ta furta"am.. um..un uncle barka da rana, dad..dama kai nake nema, um.. inaso ne dama in tuna maka maganar...." cike da rudani yake kallonta Jin yadda take yin magana a dabarbarce kamar mara gaskiya amma bai kawo komai aransa ba yasan Anila da kunya may be tana jin nauyin yi masa magana ne shiyasa ta ruɗe. Murmushi yayi tare da cewa"Anila kenan, to meye abun rudewa aciki? Kawai don zakiyi min magana? Waini sai yaushe zaki daina jin kunyata? Sai kace ba Uncle dinki ba"? kakaro murmushin yaƙe tayi kan fuskarta batare da ta tanka masa ba. Dafe kai yai"kash Kiyi hakuri kinji shiru tun da kika tura min credentials ɗin ki, har yanzu ba'a neme ki ba, kema ce baki tuna min, kinsan uncle din naki da mantuwa abubuwane sunyi yawa akaina bakasai nake tunawa ba, In sha Allah zan tuntubi Md din asibitin mutuminane ai..." washe baki tayi tace"bana so na takura maka ne, nasan uzirurrukane sukai maka yawa, shiyasa bana yi maka magana, yau ma don naji kace kana gida shine nace bari na tuna maka" "Allah sarki, nasa maki rai kina ta faman jirana, ki kara hakuri In sha Allah yanzun nan dana shiga daki zan kira shi awaya in tuna ma shi, Ki ma fara shirye shiryen fara zuwa aiki" ya fada tare da tafa hannayen sa. Washe baki ta kumayi alamar taji dadi tace"nagode uncle, Allah yasa ka da alkhairi Saina Ji daga gare ka, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" "Ameen Anila, ai baki da wata damuwa, ke da kike dani? Asibitin Obie ai namune ke sai ma kin zabi albashin da kike so a yankar maki Allah wallahi" fashewa tayi da dariya tana fadin"kai uncle, Ina kara gdy da kulawarka agare ni" batai gangancin da zai gano ta ba, lokacin da ta baro gurinsa wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tafin hannunta dafe da saitin Zuciyarta. Tana shigowa falo taja tunga ta tsaya tana tunanin meya kamata tayi? dafe kai tay kamar mai fama da ciwon kai. Aranta ta ayyana Ko dai ta sanarma Mami? Can kuma ta girgiza kai ba lallai su yarda ba, ko da ta nuna masu video din tun da bayani ne Ana tayi bawai videon abun da ya ke yi mata ne ba, Bakowane zai gasgata maganarta ba kai koda zasu yarda hadari ne Ta gaya ma wani acikin gidan hankalinsu zai tashi a karshe ma garin nukunuku Ya gano su. Gaba daya Aneelerh ta ruɗe, kwakwalwata na neman rikicewa.. Juyawar da za ta yi ke da wuya tayi arba da mami dake ta kallon ta. Washe baki tayi adabarbarce ta furta"ma.. mi dama yanzu nake niyar shigowa kitchen din don in tayaku aiki"! Wani kallo mami ta yi mata. "Aneelerh lafiyarki kuwa? Tun dazu Ina tsaye abayanki baki lura dani ba har kiran sunanki nayi kusan sau uku baki amsa min ba, meke damunki ne!" yawu ta haɗiya ƙut jikinta na tsuma tace"mami ki yarda dani babu komai, ba abunda ke damuna" "Anya Anila? Ko dai baki da lafiya? Ta fada tana karewa fuskarta. girgiza kai tay"lafiyana lou mami" Ba don ta yarda da maganarta ba tace"toh," har zata juya ta dan dakata"Kunyi waya da mahboob ne"? "A'a," "Kinsan ba kai gare shi ba, kada yabar mana yaro da yunwa, Ki kira shi ya dawo da junaid gida" amsa wa tay da toh. "Naji kince zaki ta ya mu girki, mun kammala ay, ga gidan nan ki kara gyara shi" ta amsa mata da toh. Mami na barin gurin ta sauke ajiyar zuciya. ________________________________________✍️ *PRAVIN* Cike da zumudin son ganin ta, ya shigo dakin tashin farko yai arba da awarwaron ta akan floor inda ta watsar da su, Hankalinsa ba ƙaramin ta shi yai ba, a yadda yasan Hajjaty da tsafta ba karamin abu zaisa tabar dakinta a yamutse ba gyara ba, hakan yasa shi fahimtar babu lafiya. Sam bai lura da ita ba, har saida ya karasa tsakiyar dakin, Idanunsa suka sauka akanta tana a kwance kan gadonta bayan data gama koke koken bacci ne yai awon gaba da ita, from head to toe yabi ta da kallo kamar mahaukaciya, naɗin sarin jikinta duk ya warware, har inners din ta sun fito, ga gashin kanta a hargitse kamar bata gyara shi ba, aransa ya ayyana meya faru da ita? Meke damunta"? damuwace karara akan fuskarta, hawa yai kan gadon ya matsa kusa da ita, da ya dubi fuskarta sai da yaji gabansa ya fadi, Gaba daya kwalliyar da tayi ma fuskarta ta baci da jan bakin data shafa ma lips dinta. Lumshe idanun shi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta A hankali ya Shafa fuskar da yatsun sa har izuwa kan wuyanta ya dire su kan kirjin ta. Numfashi ta ɗan ja tare da sauke shi da hucin zafi. Baya so ya katse mata baccin ta, amma yana son yaji meke damun ta. Can kasan makoshi ya furta"My lovely wife, am back, nayi kewarki sosai" ya faɗa tare da manna mata sumbata kan lips dinta. ya saba duk in ya dawo daga aiki ko ya dawo daga tafiya ya shigo dakinta zai taras da ita tayi gayu ta gyara ko'ina na dakin don ta faranta masa kuma zata watso da gudu ta rungume shi sannan ta yi kissing din shi amma yau sai yaga akasin hakan taya ba zai damu ba? Hannunshi ya zura ta bayanta yana kokarin kwance igiyoyin rigarta bai aune ba yaji ta damƙi hannunsa, da sauri ya kalle ta, A hankali ta buɗe idanunta wadanda suka kada jawur ta sauke su a cikin nashi, gaban sa ne ya ƙara faɗuwa ganin yadda idanunta suka yi ja kamar an watsa barkono acikin su. Arude ya furta"kin tada min hankalina, meke damunki ne? Gaba daya dakin a hargitse babu gyara, ke kanki ba acikin nutsuwarki kike ba, wai meke faruwa ne"? Maganganun marwa ne suka soma dawo mata a cikin zuciyarta, Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, hakan ba karamin daga hankalinsa yai ba, duk yabi ya rude cikin rawar murya yake yi mata magiya akan ta fada masa damuwarta.. Lumshe idanunta ta danyi kafin ta kuma bude su akan fuskarta. Zuciyarta naci gaba da tariyo mata abun da marwa ta faɗa mata akansa. Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar Pravin ta katse ta ransa adan bace ya furta"wai ba zaki fada min abun da ke damunki ba ne? Kina ji ina magana kin share ni"! Numfashi taja tare da sauke shi da karfi. Ta yi saurin daidaita nutsuwarta cikin disasshiyar murya tace"sannu da dawowa. "Ba wannan na tambayeki ba, ki fada min meke damunki" "Kada ka damu, babu komai" "Karya kike yi, Dole akwai abunda ke damunki" "Hakane, bana so na tada maka hankali ne, wlh Cikina ke ciwo, kasan halin da nake shiga idan na fara ciwon ciki" girgiza kai yai"ban yarda ba, kawai ki fada min abunda ke damunki"? Ya fada fuskarsa a daure. Tunani ta soma yi ya zatay da shi? Don bata jin zata iya fada masa abunda marawa tace akan shi, tasan bazaiji dadi ba in yaji anyi masa kazafi kwara ta bar abun acikin zuciyar ta. Kurama juna idanu sukayi har na tsawon mintuna goma, sai da ransa ya gama baci jin tayi shiru taki tanka masa, yana huci yace"yau ni kike boye ma abunda ke damunki? kina da wanda yafi ni ne? Okay, kada Allah yasa ki fada" Saukowa yai daga kan gadon Har ya kusa fucewa daga dakin tayi saurin mikewa ta duro daga kan gadon ta nufe shi da gudu ta faɗa bayanshi tare da zagayo hannayenta kan kirjin shi Dakatawa yai da yin tafiyar da kakkausar murya ya furta"kin shirya fadamin"? "eh" batare daya juyaba yai shiru yana sauraronta. "Hajiya saratu ce ta bata min rai, taci mutuncina pravin, ni bansan wata irin tsana tayi min ba..." karya ta shiga shirga mashi abun da ba halin ta ba, duk don ta samu ta kawar masa da tunanin abunda ke damun ta. Ransa ya baci da jin abunda hajiya saratu tayi mata. Cikin shesshekar kuka ta kara da cewa"ita ce ma ta cabemin kwalliyar da nayi maka" ta fada tare da ruko sareen dai dai Inda hajiya saratu ta goge mata kwalliyar da shi ta nuna mashi da yar shagawaba tace"ka gani ko"? Runtse idanun yai ji yake kamar yaje ya shake wuyan hajiya saratu. Yana huci yace "bazan ƙyale ta ba, dole In rama maki cin zalun da takeyi maki, mara mutunci kawai.." still da shagwa6a ta tallabo fuskarsa da tafukanta"babe, Ni ban fada maka don ka rama min ba, wlh na yafe mata, kawai banji dadi bane, amma komai ya wuce, mu kyale ta kawai" Jinjina mata kai yai tace"ina fata kun dawo lafiya? Ya baba Obie? Ya kuka baro aminin nasa"? "Mun baro shi lafiya, Baba Obie Yana a part dinsa, da anjima ki shiga kiyi ma shi barka da dawowa" "Okay, fada min me kake son in kawo maka"? "Bana jin yunwa, Naci abinci agurin hajiya saratu, A yanzu nafi bukartar ki" ya fada tare da daukarta kamar Yar baby, Dariya ta saki tana kallon shi.. Jujjuyata yai kafin ya nufi gadon su da ita, ya jefa ta a hankali, tana daga kwance tana kallon shi yayin da yake a tsaye yana Unbuttoning din rigarsa. "Ba zan raga maki ba, almost one month, dakyar nake Iya bacci saboda rashin ki" Tace"nima haka, ba raga maka zanyi ba, ka tafi ka barni da kewarka" _________________________________✍️ Shigowa dakin ta yi, tana kokarin Yaye veil din da tay rolling, taga wayam babu pravin data bari yana cin abinci adakin. "Ina ya shiga ne? Ko ya shiga toilet"! Ta fada aranta, tare da nufar toilet door ta danyi knocking shiru ba'a amsa mata ba, sai dai taji sautin safkar ruwa alamar ana amfani da shi. Watsa hannayenta tayi, ta koma ta zauna daga gefen gadon, Ta curo waya daga cikin yar purse dinta ta danna na Hajiya laura Kira. "Mara mutunci, Sai yau kika tuna dani? "Banson iya shege matar Yaya, don kar in tuhume ki shine kika rigani magana ko"? Fashewa hajiya laura tayi da dariya"Sorry aminiyar arziki, bana fada maki zanje dubai ba? Sai jiya na dawo agajiye wlh" hajiya saratu tace"kai haba, Ashe kun dawo, Ya gajiyar tafiya" "Alhamdulillah, gajiya tabi jiki, akwai fa kaya, munyi sabuwar ɗauka, Na tura maki videos ta whatsapp yakamata ki hanzarta zabar wanda kikeso tunkafin akwashe kizo kina cizon yatsa" Hajiya saratu tace"Amma naji dadi wlh, dama ga hidima muna da ita, dazu Owais ya nemi alfarmar ayi family meeting a birthday dinsa, kuma kinsan In Owais zaiyi birthday, ko biki albarka saboda yarda baba Obie ke ji da shi ina mai tabbatar maki za'ai harka ta arziki" dariya suka sanya gaba dayansu Laura tace"amma da mamaki Owais daya saba yin birthday a canada inda aka haife sa kice wannan karan A Nigeria za'ae, Amma fa naji dadi wlh, Allah ya nuna mana lokacin lafiya" Sun dan jima sunayin waya da hajiya laura kafin su ka yi sallama. Gallery ta shiga ta buɗe hotunan da tayi ma Parveen aranar dinner din Hateem batare da sanin ta ba. Kamar ibada kullum saita kalli hotunanta, ta6e baki ta ɗanyi. _____________UNAISAH ANGEL Tana a kwance kan gadonsu, Ta lumshe idanunta yayin da brain dinta ke tariyo mata memories dinsu da Danish, wani sa'in ta yi murmushi wani sa'in ta zubda kwalla, Amma yau tunanin nata ya kasu gida biyu, saboda kalaman da Chief ya furta mata adaren Jiya da su ta wuni aranta, bata ta6a zaton mutun me matsayi irinsa zai iya aje girmansa da komai donya ja ta a jiki ba. "Unaisah" muryar Ummi ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula Su biyu suka shigo dakin, Hannun Batool ruke da wooden tray mai dauke da dinner dinta akan table ta daura mata shi. "Su daddy sun dawo" Ummi tace"a'a may be sun tsaya yin sallar isha'i ne naji an fara kira, yanzu dai ki daure ki tashi kije ki yi wanka" Maƙe kafaɗa tayi"Pls aunty Ummi, dan Allah kibarni, Bana son maganar wankan nan nafi jin dadin jikina a haka, Ni wlh tsoron ma taba ruwan nake"? Baki asake ummi ke kallon ta. Batool tace"pls Ki daure kiyi wankan zaki ji dadin jikin ki, baki ga yarda kika koma ma ba? Kamar yar mahaukaciya" Ummi tace"fada mata dai, Gashin kanki ko kyan gani babu, Pls ki tashi kiyi amfani da ruwan zafi zaki fi jin dadin jikinki" girgiza kai tay Ummi ta dubi Batool"in muka bita ta lalama bayi zatay ba, Abun da za'ay ki kama hannunta ni in kama kafafuwan mu shiga da ita ciki muyi mata wanka" kafin ummi ta karashe maganar suka ga ta zabura ta mike tsaye tana girgiza dariya suka kwashe da ita. "Dan Allah ku kyaleni, tun da nace bana son wankan, Ba jikina bane wai" Basu tsaya sauraronta ba, Ummi ta haye ta cafko ta tare da daukarta saman kafadarta, tana ta zabga mata masifa akan ta kyaleta hada ambaton sunan daddy. Shigewa Ummi tayi da ita cikin toilet. Jim kadan ummi ta fito bayan ta wanke mata gashin kanta, ta barota a cikin toilet din, kafin ta fito Batool ta dauko mata kayan da zata sanya. Bayan ta shafe mintuna, sai gata ta fito tana ta faman daure fuska, Jikinta a sanye da bathrobe.. Kallo daya tay masu ta wuce ta nufi gaban dressing mirror ta zauna, ummi ta fara gyara mata gashin kanta cikin kankanin lokaci ya fara sheƙi. "Zaki iya shafa lotion din ko in shafa maki" yamitsa fuska tay"zan iya" murmushi suka saki, kamar babu laka a jikin ta kwata kwata bata da kuzari, dakyar ta shafe jikinta da body lotion bayan ta kammala tace su fita zata saka kaya ummi tace"wani dare ne je mage bai gani ba Unaisah? Time da baki a hayyacin ki kin san sau nawa inayi maki wanka"? Ras gabanta ya fadi waro idanu waje tay har zata fasa zazzaga masifa Batool tace"zolayarki takeyi" cije le6e ta yi, dakyar ta mike ta nufi kayan da Batool ta aje mata kan bedmattress ta dauka ta nufi wurin closet dinsu can cikin dakin ta shige don kada su ganta. Jim kadan suka jiyo takun tafiyarta a tare suka dube ta, oversized shirt ce tare da wando plazzo Green colour, ta daura veil din kayan a saman shoulder dinta. Ummi tace"ku dai Allah yayi maku ruwan kyau, dama kika rame sai kika kara kyau, musamman Collarbone dinki ya kara kawata kyawun kirjin ki" yamutsa fuska tayi cikin sanyayyar voice dinta tace"Anya aunty Ummi ba sharri kike min ba? Kashin wuya ne abun kyau"? Batool tace"wlh dagaske yayi maki kyau" tabe baki tayi "Kizo ki zauna ki ci abincin ki" ta fada tana nuna mata tray din. Jiki asanyaye ta nufi gafen gadon ta zauna, Batool tayi serving dinta, sam takasa Cin abinci, ko kamshin shi bata son Ji. "Pls ki daure ki ci ko kin samu karfi a jikin ki" girgiza kai tay"bana jin dadin shi, Ko naci amayar da shi" Duk yadda sukaso taci abinci takiya, Suna tsaka da rarrashinta su ka ji yo dirar motoci a cikin gidan. Jikinta na kerma ta mike tsaye ummi na tambayarta ina zataje tace"Su daddy sun dawo zataje gurin su" "Batool taimaka mata ku tafi, kwarama da suka dawo watakil idan shi ya yi maki magana asamu ki ci abincin" Fitowar su daga dakin yayi daidai da shugowar su falon. Taj ne Agaba kan wheelChair dinsa Sai faman gungurata yakeyi, Chief da sheikh Imam suna abiye da bayansa A masallaci suka hadu da shi bayan sun kammala sallah Anan harya yai mamakin ganinsu yace ashe sun dawo sau uku yana zuwa gidan neman sa saidai ace mashi baya nan ya kuma tambayi meya faru da su? Ganin rauni a kafar Taj, Chief yace in ba damuwa yazo su tafi gida sai su karasa magana acan. Takun tafiyarsu ne Yaja hankulan su Chief ga kallon direction din da suke, kaitsaye idanunsa suka sauka a cikin nata, kayan jikin ta sunyi mashi kyau. Karasowa sukayi Cikin girmamawa suka gaishe da sheikh Imam Kasa amsawa yayi saboda hankalinsa daya tashi ganin goshinta a nade da bandage, ta rame ba kamar yadda yasanta ba ita. "Subhanallah, Unaisah meke damunki"? Murmushi tay, "Bani da lafiya, amma naji sauki" Chief yace"mu karasa ciki" gaba daya suka nufi falon kowa ya samu guri ya zauna, Ummi tana a labe bakin kofar dakin su.. "Chief, Hankalina ba akwance yake ba, Inaso nasan meya faru daku? Farmakin da kuka je kaiwa anyi nasara ko kuwa? Naga Taj da rauni a kafa, ga Unaisah ma ba lafiya, kaima haka naga ciwo a goshinka, Sannan Ina sauran yaran suke ne"? aruɗe ya tambaya yana dubansu. Gyaran murya Chief yai kafin ya soma magana calmly. "Ba zamuce bamuyi nasara ba, Alhamdulillah munci rabin yakin munga tasirin addu'a, abubuwa da dama sun faru masu dadi da marasa dadi..."dan dakatawa yai yana kallon Unaisah dake a zaune gefen daddynta ta daura kanta saman kafadarsa lumshe idanun ta tayi don batason jin karashen zancen na shi. "We lost Danish, Salsabeel ya samu karaya a hannunsa, Umar has a brain injury, gaba daya an kwantar da su a asibiti, su Commender ma Sunyi rashin daya daga cikin sojijin su, sauran yaran suna a part din Taj..." Muryarsa na rawa ya furta"danish Ya mutu ne"? "Bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, saboda bamu ga gawarsa ba" tashin hankalin da damuwane tsantsa akan fuskar Sheikh Imam, Ya girgiza da jin basu dawo Danish ba, wlh yaji zafi acikin zuciyar shi.. Girgiza kai yai idanunsa cike tab da ƙwalla. Ya dan jima batare daya furta kalma ba, Can ya numfasa cikin karyayyar murya yai masu nasiha akan suyi hakuri da rashin da sukayi Su mika lamuransu gurin kada su sare, Danish kuma zasu tayashi da addu'a in ya mutu Allah yajikan shi In kuma yana araye Allah ya bayyanar da shi. Sannan Ya bukaci yana son yaje ya duba su Salsabeel chief yace idan suka tashi zuwa zai kirashi sai suje atare su duba jikin su saboda asibitin ba a kusa yake ba. Shiru sukayi falon yai tsit kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyar shi. "Ina auntynku? Ko itama tana a dayan bangaren ne"? Kaitsaye maganar shi ta dira a kunnan Ummi tayi mamakin Jin sheikh Imam ya tambayeta. "Tana anan tare da mu" Batool ce ta bashi amsa.. Batay niyar fitowa ba amma saboda maganar sheikh Imam yasa ta fito jikinta sanye da dogon hijabin data dauko a cikin closet din su Unaisah. Har kasa ta zukunna ta gaishe da shi fuskarsa da fara'a ya amsa mata, ta danyi mamaki mutumin da ko kallonta baisonyi amma yau haryake tambayar tana ina. "Hateem Yasan da maganar"! Girgiza kai chief yai"ban sanar da shi ba ko da zaiji ba yanzu ba," Sheikh yace"Allahu akhbar, Allah baya barin wani don wani yaji dadi, Hateem yaso yaron nan kamar dan cikinsa, nasan in yaji hankalinsa ba karamin tashi zaiyi ba" ya fada fuskarsa da damuwa jikinshi duk yai sanyi, Zuciyarsa ta karaya, saboda shi kan shi yaso yaron kuma bakomai yafi daga masa hankali ba face kin kar6ar shahadar da baiyi ba. "Sheikh ga Unaisah nan, Har yau bata daina sanya damuwa aranta ba, dakyar muke samu tayi bacci, dan Allah ay mata nasiha.." Taj ne yai maganar. Ya tambayi meye silar ciwonta, Taj ya fada masa komai. Tsananin tausayin su ne Ya kama shi, Cikin sanyin murya ya farayi masu Nasiha har na tsawon mintuna talatin kafin Ya gama gaba daya jikinsu yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu sosai. Har wurare karfe 9 Shiekh Imam yana agidan daga bisani yai masu sallama Chief Ya rakasa Har cikin motarsa sai da yaga tafiyarsa kafin ya juyo. Time daya shigo falon ya tsinkayi muryar Ummi tana fada ma Taj Unaisah taki cin abinci. Da damuwa akan fuskarsa yace"Why Unaisah? Baki so ki samu lafiya ne? Ai ta fama dake akan kici abinci" Muryarta kasa kasa ta furta"Zuciyata ke tashi,duka abincin da naci da safe dana rana saida na amayar da su a toilet, ban fadi maku bane saboda bana son in tada maku hankali, abincin ma bana jin dadin shi ..." Kafin wani ya furta kalma muryar Chief ta katse su. "Gobe idan dr yazo duba ki ki fada masa aman da kike yi, amma bazan bari ki kwana da yunwa ba, Fada min me kike son Ci" ya fada tare da dafe Sofa da hannayensa Yayin da idanunsa ke akan fuskarta. Saboda nauyin shi da take jine yasa ta ce"zan daure naci wanda aka kawo min" "Ina abincin nata yake" Batool tace"yana a daki" "Je ki ɗauko min" mikewa ta yi da sauri ta nufi dakinsu. Jim kaɗan sai gata ta dawo hannayen ta ruke da tray ta ajiye shi kan rug. Zagayowa yayi tare da samun wuri Ya zauna a gaban tray din, mamakin chief ya rukesu Musamman daya Kira Unaisa Ya nuna mata gaban tray din Yace tazo taci abinci" Ta dan zaro idanu tare da kallon Taj fuskarsa ɗauke da murmushi yai mata alamar taje mikewa tay jiki ba kwari ta zauna tana fuskantarsa, yayin da tray din ya raba tsakanin su. Coconut water ya dauka da sauri ta mika yatsun hannunta dake kerma da niyar ta kar6i Glass din Batai aune ba taji ya kanga mata strawa din a baki, wata irin kunyace ta kamata, adan rude ta saci kallon su ummi da Taj fuskokinsu dauke da murmushi.. Ganin ta ki motsa lips dinta yasa shi furta"ki sha" yawu ta hadiya ƙutt kafin a hankali ta fara zukar shi, abunda tagaza sha dazu sai gashi ta kwankwade shi duka batare da ta ankara ba har saida ya janye straw din daga bakinta. Spoon ya dauka Murya na rawa ta furta"zan iya ci da kaina" ta fada tana kyafkyafta gray eyes din ta Hakan ba karamin Jan hankalin shi yai ba. "Ki bari ya baki mana Unaisah, Baki ga yadda hannunki ke kerma ba taya zaki iya ruke spoon" Ummi ce ta yi maganar aranta ta ayyana Samun wuri. Batool sai faman hadiyar yawu take yi, ba yunwa take ji ba, Amma yadda taga Chief na ciyar da Unaisah yasa taji dama ya bata itama. Taj kuwa Ransa fari fat da farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, Burinsa yana daf da cika, abun da ya daɗe yana jira abunda yafi burgesa yadda Chief ya nuna kulawa agare ta agaban shi inaga idan sukai aure? Allah kadai yasan gatancin da zata samu a gurin sa, Shi yasan Unaisah ta gama morewa. Tun tana jin kunyar ya bata abaki har ta dan saji jiki ganin daddynta bai nuna wani abu ba.. duk in ya bata one spoon sai sun haɗa ido da juna launin idanunsa da take kallo bakomai yake tariyo mata ba face kyawawan idanuwan Danish kasancewar launin idanunsu daya hatta shape dinsu kamar an zana saboda kyau. "My Angel" muryarsa ce tay mata gizau a cikin kunnanta... Lumshe idanunta ta danyi wasu zafafan hawayene suka taru a cikin su sam bata son kowa ya gani. Nutsuwa ya yi yana kallon fuskarta, tuni Ya dakata da bata abincin ganin halin da ta shiga. "Unaisah" muryarta na rawa tace"Naam" "Pls don't shed your tears"! jinjina mashi kai ta yi. "Na koshi da abincin, Ina so zan shiga toilet" bata jira amsar shi ba, Ta mike har zata fara tafiya taj yace"har kin kammala cin abincin ne"? danne damuwarta tayi"Eh, Inaso zan shiga toilet" Da sauri ta nufi dakin su, Tana shiga toilet taja kofa ta datse, tare da jingina kanta jikin bango wani jiri jiri take gani kamar zata kife kasa, sai faman jan numfashi takeyi tare da zare gray eyes dinta. Har yanzu ta gaza yarda cewa man dinta baya atare da ita, bata taba zaton zata iya rayuwa batare da shi ba. Duk irin burin da ta ci akan shi in sunyi aure zata kyautata mashi saboda halaccin da yai mata yanzu gaba daya plan dinta Ya lalace. Saitin Zuciyarta ta dafe da tafin hannunta"My man, na gaza yarda cewa ka mutu, Ina ji araina kana raye, shiyasa har yanzu zuciyata take harbawa, don da ace baka raye babu makawa saina bika nima" *Mr President* Around ƙarfe shabiyu na dare bai runtsa ba, ya wuni da bakin cikin da owais ya kunsa masa, har ciwon kai saida yai, kayan bacci ne a jikin shi ya zuba hannayensa a cikin aljihunsa wandonsa, Sai sintiri ya ke yi a tsakar katafaren bedroom din Hajiya laura, ya rasa meke masa dadi? Komawa yai window Ya dafe glass din da tafin hannunsa Ya zuba ma sararin samaniya idanunsa da suka kaɗa jawur.. "Why Owais? why? girgiza kai ya danyi"Ni nasan bayin kanka bane Owais, akwai wanda ke son Ya shiga tsakanina dakai, amma meyasa zaka zargeni kamar bakasan wanene mahaifinka ba"? Bai aune ba Yaji tayi hugging dinsa ta baya tare zagayo hannayenta kan flat tommy insa. "My big boss, pls ka fada min meke damunka? gaba daya yau nakasa gane maka, kwata kwata babu walwala a tare dakai. "Ina da damuwa amma bazan iya fada maki ba kawai ki tayani da addu'a Allah ya kawo min mafita" Kwantar da kanta tayi kan shoulder dinsa"in sha Allah zanyi maka addu'a, amma pls muje mu kwanta, dare yayi sosai kana bukatar hutu" "No kije ki kwanta bana jin bacci yanzu" zagayowa tayi tagan shi tare da jinginar da bayanta jikin window glass din a hankali yake dubanta, Nightgown ce a jikinta shara shara rigar. Kashe murya tayi"ko dai kazo muje mukwanta ko kuma In kira Sarauta In fada mata abun da ke faruwa tunda ni kaki sanar dani" tana fada ta juya zata nufi cikin dakin donta dauko waya da sauri yakai hannu Ya damƙi waist dinta Ya janyo ta ta dawo Jikin shi. "Ba sai kin kirata ba, naji zan kwanta" kashe mashi ido daya ta yi"ai da ka bari na kirata, kai kasan me zai biyo baya" Baisan ya zaiyi da laura ba, sometimes indai yana tare da ita koma mashi take yarinya duk da yana jin dadin hakan sosai. Lallaba shi tayi harta samu yabita suka kwanta. ______________________________bayan wani lokaci A kwana A tashi ba wuya wurin Allah, yau Wata daya Cuf dakai farmaki gidan kurkukun Kaddara. meya faru a yan kwanakin nan a kowani Family? A bangaren Aneelerh cikin kwanakin da suka gabata, ta kasance cikin tsananin damuwa abun duniya ya ishe ta, ta rasa ya za ta yi, kullum tunanin ta wa yakamata ta tunkara da maganar? Ga shaida tana da ita a hannu sai dai tasan mawuyacin abune a yarda da ita, bayan haka tana jin tsoron ta sanarma wani maganar ta koma masa, akarshe ta jefa rayuwarsu cikin hadari. tuntana 6oyewa har sai da ta kai ga kowa na gidan Ya fahimci Akwai abunda Ke damunta saboda yawan razanar da takeyi da zarar ankira sunan ta, In tana cin abincin Yatsun hannunta kerma suke kaf kaf, bayan haka takan raba dare bata runtsa ba. Babu irin magiyar da basu yi mata ba akan ta fadi abunda ke damunta tace itafa ba bakomai lafiyarta qalou, Har abie Yasa aka kirata a falo suka zauna duka mutanan gidan Ya matsa mata akan ta fadi meke damunta a karshe tayi masu karya tace dama a kwanakin nan tana yawon yin mafarkin Uzair da Taj shiyasa ta shiga damuwa, har kuka ta yi masu, duk don su ɗauki maganarta Serious, tausayin ne ya kama su, gaba daya suka haɗu suna lallashinta hada uncle dan iya shine kan gaba, har ila yau bata ta6a yin kuskuren da zai gane tasan wani abu game da shi ba. ___________________________________✍️ Idan muka koma bangaren Unaisah, sai dai muce Alhamdulillah, jikinta ya fara murmurewa, damuwarta ta ragu saboda gatancin da take samu agurin mutan dake bata kulawa, Aunty Ummi, Batool, Taj uwa uba Chief, cikin kankanin Lokaci Shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, baya gajiya da bata lokacin shi, kulawar shi, soyayyar shi. kullum ne sai sun haɗu da juna, mafi yawan lokutta atare su ke yin breakfast da dinner agaban kowa yake bata abinci abaki tun tana jin kunyarsa yanzu har ta saba da wayewar shi ganin Taj bai taba nuna ya damu da hakan ba saima dadi da ya ke ji. Haƙiƙa Chief yayi namijin kokari gurin samun lafiyarta, kullum cikin faranta mata rai ya ke yi, Yanzu atare suke motsa jiki a gym room dinsa, bayan haka atare suke yin Kallo a tv room dinsa, har garden din gidan suke zuwa atare su yawata ba karamin nishadi take samu ba, komai ta ke so shi ya ke yi mata, saboda tsantsar kulawar da yake bata ko tari tayi wanda bai kwanta masa arai ba sai ya kira dr don yazo ya duba ta, saboda baya wasa da lafiyarta. duk wani abu da daddynta Ya fada masa wanda tafi so tuntana Yarinya sai da Chief yasa aka kawo mata shi agidan. Saboda kyautatawar da yake yi mata ne yasa ta fara Jin shi sosai a cikin ranta, da tunanin shi take kwana da shi take ta shi, In ta farka daga bacci shine mutun na farko da take kwaɗayin ta hada ido da shi. Har yanzu Danish Yana aranta sai dai ta rage damuwa da rashin shi, ta dauki dangana tama fidda rai da shi, saboda ya taba fada mata bazai iya tafiya yabarsu ba, tabbas da ace yana a raye da tuni ya dawo gare su amma yau har one month shiru babu alamun shi. Abu daya da bata fashi shine yi mashi addu'a har yau bata fasa tashi tsakar dare tayi nafilfili saboda shi ba 💔 A bangaren yan uwanta dake a part din Taj Har yau basu san meke wakana ba, abu biyu ne ke damun su, Kulle su da akayi a part din taj da kuma rashin dawowar su Unaisah Part din, amma saboda yawan kiransu video call da sukeyi Yasa hankalinsu Ya dan kwanta In suka bukaci suna son yin magana da Danish ita keyi masu wayau ta gyara muryarta ta koma irin tashi da yake ta kware gurin iya kwaikwayon muryar Danish Ba zaka taba gane ba shi bane, Ta hake take shawo kan su, ko da sun nuna suna son suyi video call da shi sai tace masu sun manta Danish baya kallon camera? In ta fadi hakan sai suce eh sun tuna fa. wani sa'in kamar zasu saka mata kuka su dinga mata magiya akan su dai suna so su dawo nan su zauna atare da su, tace su kara hakuri suma suna jirane sai su Danish sun tafi sai su dawo nan. Alhamdulillah duk da suna a kulle part din Taj suna samun kulawa chief bai barsu hakanan ba, ya sanya masu duk wani abu na more rayuwa da zai shagalar da su ya kawar masu da damuwarsu, Basu da matsalar komai, Hutu kawai suke sha, rana ta farko da Unaisah tayi video call da su saida ta yi mamakin ganin yadda Kumatun parveen suka cuccuko, sunyi kiba sunyi haske kamar ya'yan turawa, Duk in zasu yi waya sai sajeed Ya tuna mata akan ta fada ma Danish Yar uwarsa dake a prison dan Allah kada su manta da ita su taimaka su ɗauko ma shi ita...💔 __________________________________ ✍️ Idan Muka Koma Obie Estate tuni sun fara shirye shiryen Bithday din Owais da family meeting kasantuwar saura kwanaki kalilin ya rage, prime minister harya kira baba Obie awaya ya fada masa ranar da zai shugo Nigeria yakuma ce su fara shirin tarbarsa. saboda gabatowar ranar Baba Obie Yasa aka fara gyara Estate Din tare da ƙawatasa yadda kasan Masarauta saboda kayan alatun da aka wadatasa da su. A bangaren Hajjaty tuni tayi watsi da maganar Marwa, kuma tayi blocking contact dinta saboda bata bukatar ta karajin koda muryarta, tun da tayi ma Praveen kazafi taji ta fita aranta. BENAZIR💔 A Zaune take kan Mirror chair, Hannunta ruƙe Da wayarta, hotunan Unaisah take kallo Idanunta sun cuccuko tab da kwalla, Baiwar Allah Hankalin ba akwance yake ba, ta damu da rashin samun su awaya, In ta kira Unaisah kiran baya shiga, shi kuma, Taj ko ta kira baya picking sometimes rejecting call din yakeyi har sako ta tura ma sa tace dan Allah idan ma bazai kula ta ba, ya hada ta da Unaisah tana son yin magana da ita, shiru bai kirata ba kuma bai mayar mata da reply ba, ta rasa ina zata tsoma ranta taji dadi! Gashi since last da sukai waya da Unaisah Bata kara bacci Cikin kwanciyar hankali ba, saboda munanan mafarke mafarken da ta ke yi akan ta da kuma tana ji aranta wani abu na faruwa da su, Har tunanin zuwa estate din ta yi sai dai tasan Ba lallai ta samu hanyar shiga ba ko da taje, tunda ba wani gareta ba, Taj da take takama da shi baya kula ta amma tasan indai ta nemi Anila da maganar zata taimaka mata suje tunda dama ita ta hadata da su kuma ta san Taj yana ganin girman Aneela. Kifa kanta ta yi gaban mirror tana shesshekar Kuka. "Aunty Benazir" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Zeenatu, Kasa dagowa tayi saboda bata son yanayinta ya jefa zeenatu a hali na damuwa Shigowa dakin zeenatu tay, jikinta sanye da jallabiya fara. Ganin Benazir zaune ta kife kai gaban mirror yasa ta nufe ta. "Aunty Benazir, lunch is ready, we're waiting for you" ta fada tare da karasawa gaban ta. Jin shiru bata dago ba yasa zeenatu tayi tunanin ko bacci ta ke yi. Dafa bayanta tayi"aunty Benazir, Wake up pls, " taji tayi shiru bata tanka mata ba. tasan in har ba magana ta yi mata ba, ba tafiya za ta yi ba, a yanzu bata son kowa a kusa da ita tafi son kadaici. "Zeenatu! Pls ki kyale ni, basai kun jira ni ba, Ki tafi kawai ku ci abincinku," ras gabanta ya dan fadi jin yadda Benazir take magana cikin shesshekar kuka arude ta furta"Aunty Benazir! Meke damunki? Baki da lafiya"? Bata san sa'adda ta daka mata tsawa ba"bansani ba, Zeenatu! Nace ki kyaleni, Ki rabu dani, bana son ganin kowa akusa dani..." zazzare blue eyes dinta tayi, abunka ga shagwababba ta fashe da kuka ta juya ta fuce da gudu ta nufi dining area. A lokacin Mami da Hajiya sarah tare da Dr shureim da Alhaji Ubaida suna azaune kan dining Chairs har sun fara cin abincin, Kukan zeenatu ne yaja hankulansu ga dubanta, azabure suke mike suna kallonta, Ta na karasawa ta fada jikin mommynta tana ci gaba da kuka, Hankali atashe suka dubi juna kafin suka maida idanunsu akanta. " Zeenatu meya faru? Ina Benazir din? Wa ya tabaki"? Alhaji ubaid ne ya tambaya. Mami tace"ki bude baki kiyi magana mana! Wani abunne Ya hadaki da Benazir dinne"? Dago da ita Hajiya sarah tayi"Daughter, Daina kuka, Fada min meya faru"! Cikin kula tayi maganar tana share mata hawayen fuskarta Cikin shesshekar kuka tace"Ah.. an.. aunty Benazir ce take kuka, Nace tazo muci abinci shine ta daka min tsawa tace in tafi bata son ganin kowa a tare da ita" Dr shureim bai tsaya ya karasa sauraron maganar Zeenatu ba, Ya zame jiki Ya nufi dakin Benazir tunkafin Ya karasa shiga Ciki yajiyo sautin kukanta, gabansa na faduwa ya afka ciki Ta cikin madubi Ya hango fuskarsa sharkaf da hawaye ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa gata a duniya, da sauri ya nufe arude ya furta Benazir! Lafiya kike kuka? Meke damunkin ki ne? mikewa tayi ta nufe shi ta kwantar da kanta saman kafadar shi tana kuka, bubbuga bayanta ya somayi da hannunsa cikin sigar lallashi yace"pls ki fadamin damuwarki, Zan taimaka maki mu nemi mafita, amma kukan nan bazai amfane ki da komai ba, saima yajaza maki ciwon kai" dakyar ta hadiye kukan tace"yaya shureim ina ma mutuwa zata zama hutu agareni wlh dana mutu na huta, nagaji nagaji da azabtarwar da zuciya keyi min akan rashin mijina da yata, yaya shureim bana jin dadin komai, hankalina ba akwance yake ba, Ina so nagan su..." dakyar ta karashe maganar.. Gaba daya a kunnan su Mami da basu dade da shugowa dakin ba, Gaba dayansu sunyi tsaitsaye cirko cirko suna sauraron maganar Benazir, tausayinta ne ya kamasu mami tuni idanunta sun ciko tab da kwalla, batasan ya zatay ba, ita kanta zataso Benazir ta hadu da bayin Allahn nan ko ta samu nutsuwar hankali.. Zeenatu dake kuka kalaman benazir sun karya mata zuciya, wani kukan takuma fashewa da shi. "Benazir, Kiyi hakuri, Ki kara jurewa dan Allah, Na roke ki, sanya damu arai bazai haifar maki da komai ba, saima ta fama maki raunin dake a cikin zuciyarki, bana so a koma yar gidan jiya, dan Allah Benazir kiyi hakuri zamu tayaki da addu'a kema ki dage in sha Allah zasu bayyana" Hajiya sarah ce ta yimaganar cikin sanyin murya. Girgiza kai Alhaji ubaid yai shi kanshi abun na damun shi. "Kinga kukan Ya isa haka, Kiyi shiru, in sha Allah Idan Uncle dinku ya dawo zanyi magana da shi ya taimaka yasa a yi cigiyar su agidan jaridu watakil adace..." gaba daya tunaninsu har yanzu babu labarinsu ita kadai tasan Da zaman su.. A hankali ta dago daga kan kafadar dr shureim Idanunta sun kada jawur ta dube su ji take kamar ta fada masu Taj da Unaisah suna nan kuma tasan inda suke, ko dan ta samu su tayata neman yafiyarsa. Girgiza kai tayi"nagode da kulawarku agareni, Amma basai an yi cigiyarsu a gidan jaridu ba, Aneelerh ta fada min sunyi iyakar bakin kokarinsu gurin yada hotunansu a social media da Gidan jaridu amma har yau babu labarinsu...." ta dan dakata kafin ta daura da cewa"dan Allah kada ku damu da halin da nake a ciki, bawai don banyi imani da kaddara ba, wlh nayi kokarin In manta da su a cikin zuciyata amma abun Ya faskara..." ta faɗa tana matse kwalla. Kallonsu Dr shureim yayi"pls Ku barni da ita, ku je ku ci abincinku, Zan yi mata nasiha" Alhaji ubaid yace"yawwa shureim pls kayi kokarin shawo kanta, bana so ciwonta ya tashi" amsa mashi yai da toh, fita su ka yi ya rage saura su uku Kallon zeenatu yayi, Tana atsaye bakin kofar sai shesshekar kuka take. "Calm down your mind, Ki kawo min lunch din ta a daki" ta amsa da toh ta juya ta fuce.. Ruko hannunta yai suka zauna kan gadon ta. Nasiha ya farayi mata cikin kwantar da murya har saida taji zuciyarta ta dan lafa da radadin da takeyi mata. Sai da yaga ta samu nutsuwa sosai kafin yace"akwai inda ke maki ciwo" girgiza ma shi kai tay"a'a ya shureim, lafiyana lou" "Okay, " ya fada tare da sauke ajiyar zuciya. Shigowa zeenatu ta yi cikin dakin, hannayenta ruƙe da tray mai dauke da lunch ta mika ma dr shureim Yasa hannu ya kar6a yadago ya dube ta"thanks, yanzu sai hankalin ki ya kwanta, tunda auntyn naki ta daina kuka" murmushi tadan saki. "Ki je ki ci abincin ki" Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh. Bayan fitar Zeenatu daga dakin Ya maida hankalinsa akan Benazir, A baki ya soma bata abincin tana ci, sai kallon shi takeyi har saida Ya tsargu da kallon Yace"Akwai wani abu ne"? "Yaya shureim dan Allah ka taimaka ka kaini gidansu Anila Inason ganinta." "Da yaushe"? "Ko yanzu kace sai in shirya mu tafi" "Kin fada mata ne"? Shiru tayi jim don rabon da suyi waya da Aneelerh kusan two weeks babu wanda ya tuntubi wani amma saboda tana son Taje din yasa tay mashi karyar sunyi waya harma ta fada mata zasu zo Yace toh idan sun kammala Cin abincin zai kai ta. Dadine Ya lullubeta bayan sun gama cin abincin, Ya fita don yaje ya shirya. Jikinta na rawa ta dauki waya ta danna ma Anila kira, don ta sanar da ita batun zuwansu, almost 3 times tana doka mata kira ba'a picking a karshe ta hakura da kiran nata ta fada toilet don tayi wanka. *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Health College Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 61 Complete by Boss Bature by Novels Elite Admin September 29, 2024 Sponsored Link Takun Ƙarshe Zaune yake a mazaunin driver na motarsa, ita kaɗai ya ke jira su tafi, har ya fara gajiya da jiran ta, wayarsa ya zaro daga front pocket din rigarsa ya danna mata Call. "Idan kika ƙara minti ɗaya baki fito ba zan koma ciki ne." Yana fada yayi rejecting call ɗin, jingina kanshi jikin headrest ya yi tare da lumshe idanun shi. Sam bai ji tahowarta ba, sai dai ya ji motsin buɗe cardoor din, buɗe idanunsa yai tare da kallon ta baki a buɗe ganin yadda ta ca6a ado kamar wadda zata je gidan surukanta, Wani hadadden Code lace ta saka orange riga da skirt sun ɗan kama jikinta, mayafin kayan a kafaɗa ta daura shi, ga wani hadadden daurin dan kwali da ta yi, baƙar sumar kanta ta sauko har mid back dinta, fuskarta ta sha make up....,sunkuyar da kai ƙasa ta yi ganin kallon da Dr Shureim ɗin ke yi mata. "Benazir, wa ki kai ma kwalliyar nan? sai ka ce wadda zata je bikon mijinta?" Tuntsirewa ta yi da dariya, ta yi mamakin jin ya canki abunda ta shirya, don wannan kwalliyar da ta yi saboda Taj ta yi ta, yau ta ɗaura ɗamarar janyo hankalin shi gare ta. "Zai iya yiwuwa." ta faɗa tana sakin murmushi, ta6e baki ya yi tare da ɗan girgiza kan shi ba tare da ya kawo komai a ransa ba, Kafin ya yi wa motar key a hankali ya yi reverse, a tsanake Ya ke yin driving ɗin su... "Zeenatu ta ganki da zaki fito daga gidan?" Ya tambaya yayin da yake juya sitiyari. "Eh, amma bata nuna zata bini ba, naji tace zata bi Aunty Sarah Office, may be shiyasa bata damu da ta biyo mu ba." Tafiyar mintuna ƙalilan Suka ƙaraso layin su Aneelerh, Bayan Baba mai Gadi Ya buɗe masu gate Dr Shureim ya shigar da motar ciki, a parking space ya dakata. "Mu shiga ciki" Girgiza kai ya yi, "ki fara shiga zan shigo daga baya" amsa mashi tayi da toh, Fitowa ta yi ta nufi cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama ta shiga... "Muryar wa nake ji kamar Benazir?" Murmushi ta saki tare da sauke idanunta akan Mami da Ummi dake zaune a falo suna kallo a tv, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta bayan sun amsa sallamar da ta yi... "Wlh ni ce Mami, na yi maku zuwan bazata ban kira na faɗa ba" ta fada tare da karasawa ta dan duƙa gaban sofa ɗin da suke a zaune ta gaishe da su. "Ina wuninku, fatan na same ku lafiya" A tare suka haɗa baki "lafiya lou, ya mutanan gidan naku?" "Suna nan lafiya, Sun ce agaishe masu da ku." "Ina Zeenatu da Shureim namu"? A cewar Mami, "Yaya Shureim shi ya kawo ni, yana a waje, shi ya ce in fara shugowa zai biyo ni, mun baro Zeenatu a gida za su je office tare da Mommynta." Mami tace"Allah Sarki, na ji kin ce kin yi zuwan bazata baki kira kin fada ba, nan ay kamar gidan ku ne Benazir, naji dadin zuwanki..." Still fuskarta dauke da murmushi.. Ummi ta ce"Ga mutuniyar taki can, ta ɗaura aure da zaman ɗaki, dan Allah Benazir in kin shiga ki yi kokarin kwantar mata da hankali, kwanakin nan mun rasa gane kanta," "Bata da lafiyane?" Mami ta ce, "Hmmm, ta sanya damuwa a ranta ne, wai kwanakin nan tana yawan yin mafarkin su Uzair shine fa duk tabi ta hana kanta sukuni..." "Subhanallah!" Fuskarta da damuwa ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dakin Aneelerh.. A bakin kofar dakin ta tsaya, kusan sau uku tana doka mata sallama shiru ba'a amsa mata ba, har saida ta fara gajiya da tsayuwa, a ƙarshe ta yanke shawarar shiga ciki. Tana Shiga idanunta suka sauka akan Aneelerh dake a kwance kan gado, ta ƙurawa Ceiling idanunta ko kyaftawa bata yi, lamarin ya daurewa Benazir kai, a ranta ta ayyana wannan wata irin damuwace da zata sa aita maka sallama baka ji? Ta karashe zancen zucin tare da kai hannu saman kafar Anila ta 6aka mata bugu, wata irin zabura ta yi, a firgice ta miƙe zaune tana zare idanunta muryarta na rawa ta furta,"Na shiga ukuna!" hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta. Hankalin Benazir ba karamin tashi ya yi ba, ganin yadda Aneelerh ta rame kwata kwata bata a cikin nutsuwarta. "Ni ce fa..." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta sauke Idanunta akan Benazir don sam bata lura da ita ba. Numfashi ta dan ja tare da sauke ajiyar Zuciya ta ƙaƙaro murmushi kan fuskarta.. "Benazir ke ce? Meyasa baki fada min zaki zo ba?" Bata tanka mata ba har saida ta samu guri ta zauna daga gefen gadon kafin ta maida hankalinta kan Aneelerh. Duk tabi ta dabarbarce ganin irin kallon da Benazir ke yi mata, washe baki ta shiga yi tana kokarin danne damuwarta ta ce, "Sannu da zuwa Benazir, ya ki ke? Ya su Mami? Ina ya Shureim da zeenatu?" Cike da damuwa Benazir ta furta, "Don Allah meke damunki haka Aneelerh? sau uku ina doka sallama baki amsa ba, nama yi zaton kin shiga toilet ne ko bacci kike yi, ashe idonki biyu kina a kwance kin takura kan ki, why pls dubi yadda kika rame? Fuskarki duk ta yamutse kamar wata tsohuwa" Ta fada tana ƙare mata kallo.. A rude Anila ta girgiza kai muryarta da in-ina ta ce,"Lafiyana lou ba abun da ke damuna..." Kaitsaye Benazir ta ce, "ƙarya ne wallahi, Dole akwai abunda ke damunki sai dai idan baki son fadamin ne." Murmushi ta dan yi,"Bafa wani abu bane, kawai ina yawon yin mafarki akan Uzair...." tunkan ta kare maganar Benazir ta tari hanzarinta, "Mami ta faɗa min hakan, amma ban yarda ba Anila, Look, nifa nasan wacece ke, mafarkin Uzair bazaisa ki shiga damuwa har haka ba, bayan kinsan mafarki ba gaskiya bane, in ma hakanne a yadda nasanki da tawakkali Addu'a zaki dage kina cigaba da yi masa bawai ki tsananta damuwa ba, kawai ni yanzu ki fadamin meke damunki kinsan tsakanina dake babu 6oye-6oye, Kinsan sirrina nasan naki, kuma dai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, pls In har kin yarda da ni...." Shiru Anila ta yi jim tana tunanin kodai ta fadawa Benazir watakil ta taimaka mata su nemi mafita, ruƙo hannayen Benazir ta yi acikin nata, suka ƙurawa juna ido.. A hankali hawaye suka fara zarya kan kuncin Anila, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Benazir ya yi ba. "Zan fada maki saboda na yarda dake, amma dan Allah ki rufa mini asiri Benazir, bana so kowa ya sani mu barshi a matsayin sirri tsakanina da ke.." A ƙagare Benazir ta jinjina mata kai. Nan take Anila ta fayyace mata komai, tun daga ranar da suka je gidansu Hajiya Adama da abunda ya faru bayan dawowarsu game da 6atan Ana, da inda suka ga Baby Junaid a sume cikin drawer shelve da yadda Junaid ya burkice masu suka rasa gane kanshi, komai saida ta sanar da ita, har wayar Ana ta curo daga cikin pillow case ta kunna mata videon ta mika mata don ta gani da idanunta. tunkan ta Ƙarasa kallo yatsun hannunta keta kerma kamar wayar zata kife kasa, idanunta azazzare cike da tashin hankali ga wani irin faduwar gaba da take ji, labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha..., bata ƙare sallallamin ba Anila ta yi saurin toshe mata bakinta da tafin hannunta gudun kada wani ya ji yo su. Tuni hawaye sun wanke fuskar Benazir, Sai faman girgiza kai ta ke yi. Cikin muryar rada Anila ta ce,"Allah abun tsoro dan adam abun tsoro, muna nan sake da baki ashe muna a tare da mugun iri acikin mu! Benazir ki fada min taya hankalina zai kwanta? Wai Uncle dina shi ne yake aikata wannan fasikancin a cikin gidan nan? Babban tashin hankalina Ina Ana? Yau kusan wata uku babu ita Benazir, ina jin tsoron ace ya kashe ta...." Ta fada tana kuka ƙasa kasa. A hankali Benazir ta zame hannun Anila data toshe mata baki da shi. Hawaye wasu na bin wasu akan kuncinta ta ce, "Anila dama Ana ta 6ace shine baki fadamin ba tun lokacin da abun ya faru?" "Na yi zaton da son ranta ta gudu shiyasa ban fadamaki ba saboda na saka ran zata dawo." Jinjina kai Benazir ta shiga yi. "Mugu bashi da kama Anila, munafuki kamar na Allah, wlh bazamu kyale shi ba, dole mu ƙwatarwa Ana hakkinta sannan mu maka dan iska gurin hukuma...." bata kare maganar ba Anila ta yi saurin katse ta, "Pls ki daina ɗaga murna bana so wani ya ji, yanzu me yakamata mu yi? Kin dai ji ta ce mutunne mai hadarin gaske in har muka yi kuskuren da maganar ta koma masa zai iya salwantar da rayuwarmu tunda ba imanine da shi ba, Allah kaɗai ma yasan munanan ayyukan da yake aikawata bayan wannan da Ana ta fada." Jinjina kai Benazir ta yi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abubuwan dake faruwa da ita a gidan Uncle Musa, yunƙurin kashetan da ake yi ga kuma kurciya da aka yi mata, tun rana ta farko da aka fara yi mata take zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta. Anila da ta zuba mata ido ganin ta yi shiru bata da niyar yin magana yasa ta dafa kafadarta, "Benazir kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Numfasawa Benazir ta yi kafin ta ce, "Aneelerh, akwai damuwa, nima fa akwai wanda ke bibiyar rayuwata a gidan Uncle Musa, kusan sau hudu ana yunkurin kashe ni....." Waro idanu waje Anila ta yi, cike da ruɗani take kallon Benazir ya yin da gabanta ke faduwa rass rass!!! Nan Benazir ta labarta mata komai da ya faru da ita tun farkon zuwanta gidan.. "Aneelerh wallahi ba don Allah yana kawo min ɗauki ba, da tuni an jima da kashe ni, don ma yanzu babu tabon yatsun hannun mutumin a wuyana ya goge dana nuna maki kin gani" Hankalin Anila fa ya tashi sosai, duk tabi ta rude, "Benazir! anya ba iska bane? In ba haka ba wanane zai yi maki hakan agidan Uncle Musa? Gidan dake a tsare da Security Officers taya wani bare zai iya shigowa har dakin ki ya yi yunƙurin kashe ki??" ta fada tana zare idanunta... Girgiza kai Benazir tayi, "Wlh Anila ba iska bane, mutunne! Abunda yasa na kara karfafa zargina saboda abu biyu, na farko kurciyar da aka yi mini! Aka rabani da dangina, Na biyu labarin da Ana ta bada, Shine ma ya farfaɗo da tunanina, koma wanene mutunne kuma yana amfani da sihiri kamar yadda Ana tace Uncle ɗan-iya yana amfani da sihiri gurin sarrafa ta" Da ƙwarin gwiwa ta yi maganar tana duban Anila wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari. "Ina zargin mutumin da yayi min kurciya shine yake son kashe ni.." Cikin shesshekar kuka Anila tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'iun! Banazir mun shiga Uku! Wanene wannan? Laifin me ki ka yi masa da ya ja har ya ke son raba ki da rayuwarki? Wai dan Allah meyasa hakan ke faruwa da rayuwarmu? Daga wannan sai wannan?" Maganar Anila ta sake tuna mata abunda ta faɗa mata game da Taj, cikin saurin ta ce, "Anila! Kinsan tunanin da nake kuwa??" Girgiza kai tayi da sauri, "A'a." Gyara zama Benazir ta yi, A labarin da kika bani na abunda ya faru da su Uzair, kin tuna Alhazawan da suka yi ma leƙen asiri? Har suka rikiɗa suka handame uba da ƴa'yansa saboda yayi masu leƙen asiri...?" Cikin sauri Anila ta jinjina kai,"Kwarai kuwa haka ne!" "To baki tunanin ko halin da nike ciki nada alaƙa da hakan, sai nike ganin kamar idan muka fada ma Taj komai zai taimaka masu gurin yin binciken da su ke yi akan Alhazawan nan da kuma 6atan Uzair? Kuma kinga Taj yanzu jami'e ne shi, sannan yana a gidan Director General In har muka je masu da maganar wallahi ina mai tabbatar maki zasu dauki mataki akan Uncle dan-iyan, tunda su jami'ai ne sun fi mu sanin ta yadda zasu bullowa lamarin, ko ya kika gani?" wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anila ta sauke, Wlh sham ta shafa'a ta manta da cewa Taj jami'in bincike ne ai da tuni ta sanar da shi komai. "Ban ta6a sanin ni shashasha bace sai yau da kika ankarar dani, Mu da muke da jami'i a hannu, Wlh gaba ɗaya kaina ya kwance tsawon kwanakin nan inata neman mafita, kwata kwata tunanina bai bani in tuntubi taj ba, nama manta da cewa shi jami'i ne sai yanzu da kika tuna min." Murmushi suka sakar ma Juna. "Yanzu ya za a yi? Babu buƙatar 6ata lokaci, da zafi zafi ake bugun ƙarfe, ƙwara muyi amfani da damar da muke da ita tunkafin lokaci ya kure mana" A cewar Anila. Benazir ta ce, "Ay daga nan sai gidan DG, Nifa dama da shirina nazo wlh, na ma manta ban fada maki abunda ya kawoni ba saboda halin dana riskeki..." "Anila kusan One month bana samun Unaisah a waya! Shima Taj kona kira baya picking? Baki ga na rame ba nima? Damuwa ce wllh, Gashi kwanakin nan sai munanan mafarke-mafarke na ke yi akanta da ni kaina, Ina ji araina kamar wani abu na faruwa da su..." Fuskarta a marairaice ta faɗa, Anila ta ce, "Ai bake kadai ba, Ni kaina Idan na kira bana samun su a waya, wlh hankalina ba a kwance yake ba, don ma tashin hankalin videon nan da na gani ya dauke mun hankalina almost 2 weeks ban neme su ba." "Ba surutu yakamata mu tsaya muna yi ba, na baro Dr Shureim a waje yana jirana, ki tashi ki shirya mu tafi." _________________________________✍️ "Shiru Har yanzu basu fito ba," A cewar Ummi, Mami ta ce, "Kinsan ƙawaye In aka haɗu ba'a gajiya da fira," Ummi ta kuma cewa,"Kuma na ji ta ce ita da yayanta ne, shi ba zai shigo bane? An bar shi a waje yanata jira." "Nima abunda na gani kenan, bari na je na yi masu magana su je suce ya shigo." tana kokarin mikewa sai ga Benazir da Anila sun nufo falon hannunsu ruƙe cikin na juna. Ba zaka ta6a gane sun yi kuka ba, kowaccensu ta gyara fuskarta ko alamun hawaye babu, dubai abaya Anila ta saka ta yi rolling veil akanta ko makeup bata tsaya yi ba. "To fa Ina zuwa kuma? Ai da yanzu nake niyyar shigowa inji me ake kitsawa ne, Kun yi zamanku shiru a ɗaki." Murmushi suka saki, Mami ta kuma cewa, "Yakamata kuyi wa Shureim magana ya shigo ciki mana." Sai lokacin Anila ta ce, "Dama zamu fita unguwa ne." "Ina zaku je ne?" Kallon juna suka dan yi kafin Benazir tayi saurin cewa, "Gidan Hajiya Adama, tuntuni ni ke ta so inje Allah bai nufa ba, sai yau na yanke shawarar zan zo Anila ta rakani, dama itace ta fadamin sun dawo nan da zama...." Fara'a Mami tasaki, "Kai Amma kinyi tunani mai kyau, nima nayi kauron baki ne amma wlh abun na araina, tuntuni nike ta so in shawarci Anila ta raka ki ku je su gan ki, ni nasan zasu yi murnar dawowarki." Ummi ta ce, "Nifa wlh na yi zaton ma sun san da dawowarta, ashe ba'a fada masu ba, gaskiya ba'a kyauta masu ba" "Ai yau zamu wanke laifinmu, zan basu mamaki, har gida zan kai masu Benazir" A cewar Anila, dariya su ka yi, Mami ta ce, "Ku tafi yana ta jiranku gashi ko ruwa ba a kai mashi bama, in kun isa ku gaishe mana da su, sannan kada ku daɗe dan Allah, zan ma kira Abie dinku in faɗa masa" "Zasu ji, in sha Allah bazamu dade ba." A bangaren Dr Shureim, har ya gaji da jiran Benazir jin shiru bata fito ba, buɗe motar ya yi tare da fitowa da niyyar ya bisu, ƙarar horn din motar da ya ji ne yasa shi ɗan dakatawa ya juya yana kallon motar dake kunno kai cikin gidan. Ta gaban shi motar ta wuce ta yi parking a gaban entry hall, bayan ta kashe motar ta fito tare da zagayawa other side din motar ta buɗe backseat, ta ɗauko baby Junaid dake ta sharar bacci jikin shi sanye da uniform dinshi, dayan hannunta ruke da food basket dinsa, Two weeks kenan da komawarsa School. "Yaya Shureim ina wuni?" Ta faɗa da fara'a akan fuskarta, Fuskarshi dauke da murmushi yace, "lafiya lou Zahra, ya kike? Ya gajiyar aiki?" "Alhamdulillah, Kai kadai ka zo ne"? "Benazir na kawo tana ciki." ya fada tare da kallon Junaid, "Junaid bacci ake yi, ankwaso gajiyar school." Murmushi Zahra ta yi tare da cewa, "Mu shiga daga ciki" Ta faɗa tare da yin gaba yabi bayanta, har sun kusa shiga falon sai ga Benazir da Anila sun fito suka yi kacibus da juna. Da fara'a Zahra ta gaishe da Benazir ta amsa mata da fara'a itama akan fuskarta. "Aunty Benazir why zaki bar ya Shureim a waje fisabilillah?" Yar dariya Benazir tayi, "Bafa ni na hana shi shigowa ba, shine ya ce in fara shiga zai biyoni daga baya." Bayan Anila ta gaisa da Dr Shureim ta ce ma Zahra unguwa zasu fita, ta kula da Junaid, sai zuwa anjima zasu dawo." Bata nemi sanin inda zasu je ba ta ce, "Allah ya dawo daku lafiya." Suka amsa da ameen, bayan Zahra ta shige ciki Dr Shureim ya dubesu da dan mamaki yace"Bangane ba! ina zaku je ne?" "Yaya Shureim mu je zamu faɗa maka." Bai yi musu ba suka nufi motar, bayan duk sun shiga ya tasheta suka tafi. _____________________Obie Estate🔥 Koda suka ƙaraso main gate na estate din basu sha wahalar shiga ba, Security Officers basu dakatar da su ba, Saboda sun gane fuskar Anila kuma tayi masu bayanin cewa gurin Hajiya Saratu suka zo, suna jin hakan suka basu permission din shiga. Bayan Motar su ta shiga cikin estate din kaitsaye suka nufi villa ɗin Owais, Tunkan su ƙarasa Security Officers din dake tsaron gate din suka nufo motar hakan yasa Dr Shureim yin packing din ta. Officers shidda ne suka yiwa motar tasu ƙawanya, Knocking window glass din aka yi, "Get out of the car!" ɗaya daga cikin su ne ya umarta. Bayan sun fito suka fuskance su. "Su wanene ku? Daga Ina kuke? Wa kuka zo nema?" Da hannu Dr Shureim ya nuna Benazir da Anila, "Ai sai ku yi masu bayani, Ni dama ban so zuwa ba, don nasan ba lallai mu samu shiga ba, amma kuka matsamin, yanzu ba ga irinta nan ba." ya faɗa fuskarsa a haɗe don shi baya son abunda zai haɗa shi da masu kaki... "Ki kira Taj din a waya, Ni nasan kona kira ba lallai ya ɗaga ba." Benazir ce ta faɗa idanunta akan Officers din da suka zuba mata ido har saida Dr Shureim ya ankara da mayataccen kallon da suke binta da shi, ransa ya 6aci cikin harshen larabci yace ta lullu6e jikinta da mayafinta. Da sauri ta gyara mayafin ta lullu6e kirjinta da kanta sa6anin da da yake akan kafadarta, duk da haka basu daina kallonta ba, ta ji haushi ita da ta yi kwalliya don Taj ya gani sai gashi wasu na nema su riga shi gani. Almost 3 times Anila tana doka masa kira baya picking, hankalin su ba ƙaramin tashi ya yi ba.. "Ya zamu yi Benazir! Ya ƙi ɗagawa wlh" "Keep trying, idan ba haka ba wadannan masu fuskar shanun ba bari zasu yi mu shiga ba." Cikin harshen larabci ta yi maganar.. Murmushi Dr Shureim ya yi tare da ɗan girgiza kanshi jin abunda yar'uwarsa ta fada, jami'an kuwa sun baza kunne da yake ba arabi da ace da hausa ko da turanci ta fada da taci na jaki. Taj na ƙoƙarin fitowa daga toilet yana ta gungura wheelchair dinsa ya jiyo muryar Batool tana kwaɗa masa kira,"Daddy, wayarka tana ringing, wani ne ke kiranka" Har ya nufi ƙofar dakin sai gata ta faɗo ko sallama babu, tana ta haki ta miƙa masa wayar tana fadin, "A falo ka barta saman hannun kujera." Bai kar6i wayar ba sai cewa ya yi ta karanta mashi sunan me kiran, ɗan zare ido ta yi kafin ta dubi sunan da ya bayyana akan screen din wayar. "An..An..Antin Yu.. nai..sah.." daƙyar ta ƙare karatun a lokacin har kiran ya katse, Murmushi Taj ya sakar mata, "Auntyn Unaisah ne, kin yi kokari daughter, Allah ya yi maki albarka." Ya faɗa tare da kar6ar wayar, sai faman sakin murmushi ta ke yi, tana son taji an yabeta in ta yi abu. "Ina ƴar uwar taki ne?" "A ɗaki na barota kudundune cikin bargo." "Bacci ta ke yi ne?" Girgiza kai ta yi, "Waya ta ke yi da Chief, Daddy baka ji yadda take kashe mishi murya ba hada shagwa6a fa," fashewa yayi da dariya har fararen hakoransa suka bayyana. "Shaƙa mini in ji me take ce masa?" Da biyu ya yi maganar saboda yana son yadda Batool take kwaikwayon maganar Angel dinsa, aiko da yar shagwa6a ta ce, "Shine ka tafi baka jira na tashi daga bacci ba, pls kada ka daɗe ka dawo gida bazan jure zama batare dana sanyaka a idanuna ba" Tuntsirewa Taj ya yi da dariya, Itama dariyar ta kama yi yadda kasan uba da ƴarsa. "Daddy, ka ji daɗi?" Ɗaga mata kai ya yi, "Sosaima, kema da kika bani labarin ga wannan" Ya fada tare nuna mata robar peanut din da ya aje kan drawer bai kaiga fara ci ba, da sauri taje ta dauka tare da yi ma shi godiya. Fitowa ta yi daga ɗakin jikinta a sanyaye, kwata kwata babu walwala, a saman stairs ta zauna hawaye cike tab da idanunta take kallon Peanut din da daddy Taj ya bata, A hankali ta soma ɗebowa tana afkawa a baki tana ci, hawaye na sintiri kan kuncin ta, Allah kaɗai yasan me ke damun ta. Fitar Batool ke da wuya, wani kiran na Anila ya sake shigowa wayar tasa, picking ya yi tare da kara wayar a kunne. Bayan sun gaisa ne Anila ta fada masa gasu a bakin gate na gidan security sun hana su shiga ya taimaka ya yi masu hanya su shigo. Shiru ya yi yana tunanin hanyar da zai dakile shigowarsu saboda baya son suga halin da yake a ciki, ga Chief ma baya nan, bayan haka ba'a son ma kowa yasan wani abu dangane da farmakin da suka kai, in har su Anila suka gan shi zaune kan wheelchair dole hankalinsu zai tashi harma su nemi jin me ya faru da shi.. "Taj na ji ka yi shiru baka ce komai ba?" Muryar Anila ce ta katse tunanin da ya ke..... Muryarsa a dabarbarce ya furta, "Anila meyasa baki kira kin fadamin zaku zo ba?" "Banyi tunanin yin hakan ba, saboda na ga Almost weeks kona kira bana samunka." "Anila, sai dai ku yi hakuri ku koma gida, yanzu bama nan mun je yin meeting a headquarter ɗin mu." On the Other Hand Anila ta zabga salati tana fadin, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, dan Allah Taj ka taimaka ka bada iznin a barmu mu shiga ciki, wlh zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo gidan, Don Allah Taj, wlh wani abune mai mahimmanci ya kawo mu, It's urgent, please help." Ta fada tana kallon Benazir data yamutsa fuska kamar zata sanya kuka. Shiru Taj ya yi yana nazarin maganarta, tun daga kan yanayin muryarta ya fahimci da akwai wani abu da ya kawota gidan, "Okay, ku ɗan jira" Ta amsa mashi da toh, rejecting call din ya yi, ya shiga tuntu6ar layin Chief, almost 5 times tana ringing bai yi picking ba, ana shidda ne ya ci sa'a Chief ya ɗaga kiran.. "Yalla6ai mun yi baƙi, Anila ce tare da Benazir, Wlh bansan da zuwansu ba saboda basu faɗamin ba, sai dai kawai ta kira a waya ta fadamin suna a bakin gate an hanasu shigowa, wlh da nasan da zuwan da bazan bari suzo ba, amma na ji Anila tace matsalace ta kawo su." Koda jin wannan maganar Chief ɗin ya ce zai yi magana a basu iznin shigowa ciki. Godiya Taj ya yi masa bayan sun yi sallama, ya zura wayar Cikin aljihun jallabiyar sa. A hankali Motar Dr Shureim ta karaso cikin parking space, bayan ya tsayar da ita. suka fito daga ciki, kallon kallo Benazir da Anila suka jefawa junan su. "Yaya Shureim ko zaka jira mu anan?" Benazir ce ta yi maganar saboda basa son su shiga dashi ba don komai ba sai don kada su ƙetare iyakarsu ga kuma gargadin da aka yi masu. "Ba damuwa, ku shiga zan jira ku, but pls kada ku daɗe." Amsa mashi su ka yi da toh kafin suka nufi main door na falo, suna ƙarasawa ƙofar ta zuge suka shiga bakinsu ɗauke da sallama, wani sanyayyan sanyin Ac ne na daban ya ratsa fatar jikinsu har wani lumshe idanu suka yi. Time da suka buɗe idanun nasu kaitsaye suka sauka akan Taj dake a zaune kan Sofa ya nutsu yana jiran ƙarasowarsu, Ba zaka ta6a gane yaji rauni a cinyarsa ba saboda ya lullu6eta da jallabiyar jikinshi, Sofa ɗin ma daƙyar ya samu ya yi dubarar da ya zauna akanta, da ɗayar ƙafarsa me lafiyan ya tura wheelchair din ta koma tsakankanin sofas saboda baya son su ganta. Ta wutsiyar idanunshi ya ke hangosu yayin da suke nufo shi. Anila ta yi mamakin ganinsa bayan ya ce mata basa nan ashe yana nan, komi yasa ya boye mata da farko? Ta ayyana a cikin ranta. Har saida suka ƙaraso kafin ya ɗan ɗago da niyyar ya kallesu karaf idanun shi suka shiga cikin na Benazir, har saida ya ɗan ji gaban shi ya faɗi saboda kyan da ta yi ma shi, amma da yake namijin duniya ne sai ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi. Murmushi Anila ta yi kafin ta gaishe shi ya amsa mata fuskar shi asake. Cikin sanyin murya Benazir ta gaishe da shi a daƙile ya amsa mata.. "Ku zauna." A kan Sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna suna fuskantar shi.... Gaza jurewa Benazir tayi idanunta cike tab da ƙwalla ta ambaci sunan shi"Taj!" Shiru bai tanka mata ba.. "Nasan har yanzu fushi kake dani, amma meyasa idan na kira baka picking? Har saƙo na tura maka akan ka taimaka ka haɗani da Unaisah saboda idan na kira bana samun layinta amma kwata kwata ba response..." Hannu ya ɗaga mata tuni ta haɗiye maganarta, "Dama wannan ne abun da ya kawo ku?" Ƙasa-ƙasa da murya Anila ta raɗa mata "pls ki aje wannan maganar gefe, ki yi haƙuri mu yi abinda ya kawo mu, kinga daƙyar muka samu aka bamu damar shigowa ciki." Jinjina mata kai ta yi alamar ta gamsu. Mayar da dubanta ta yi akan Taj, "Dama issue ne akan yar aikin gidan mu Ana data 6ace yau wata Uku kenan." Jin wannan maganar Yasa Taj ya maida hankali akan Aneelerh. Dakatawa ta ɗan yi ganin kuku ya nufo su hannun shi ruƙe da wooden tray na fruit da cool drinks ya ajiye masu kan table, bayan ya tafi Aneelerh ta cigaba da zayyana masa komai da ya faru har izuwa kan videon da ta gani...." tunkafin ta kai ƙarshen zancen yanayin fuskar Taj ya sauya zuwa tsantsar mamaki, tashin hankali da kuma ruɗani... "Zan iya ganin Videon??" Da sauri tace "Eh," Ta faɗa tare da zaro wayar daga cikin handbag dinta ta shiga pressing dinta, bayan ta kunna masa video ta miƙe taje gaban shi ta miƙa ma shi. Bayan ya kar6a, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi matuƙa, saboda tsabar girgiza da kidima duk da sanyin A.c din falon saida ya fara zubda gumin zufa lamarin ya ɗaure masa kai, Lallai sun zo da case mai girma, abun da ya ɗan jefa shi a rudani a bayanin Ana ya fahimci shi Uncle ɗin Anila matsafine kuma abun da yake yi ma Ana yayi kamanceceniya da cin zarafin da Elders su ke yi wa prisoners a lokacin da suke yin jinin al'ada. A dabarbarce ya furta, "Anila dama Ana tana nan?" Idanunta cike tab da ƙwalla tace, "Eh, atare da ita muka dawo gidan Uncle din" Jinjina kanshi ya yi Idanunshi sun kaɗa sun ɗan yi ja, "Ku sha lemun" Ya faɗa yana nuna masu drinks din.. Miƙa hannu Anila tayi ta dauki Juice ta tsiyaya masu a glass cups, saboda dadin da ya yi masu kusan duka suka shanye.. "Tanimu Ja'afar Falgore, inkiya Ɗan-iya shine full name na uncle dinki ko?" Ya tambaya yana kallon Anila, Jinjina mashi kai ta yi alamar eh, a ransa ya furta karen yan siyasa zai aikata fiye da hakan, ya ƙarashe zancen zucin nashi tare da aje wayar Ana a gefen sa. Har ya zaro waya zai dannawa Chief kira maganar Anila ta dakatar da shi..., "Benazir na ji kin yi shiru baki ce komai ba? ba zaki fada masa abunda ke faruwa dake ba?" Cikin karyayyar murya ta wanda ke shirin saka kuka tace,"Ba ki ga ko kallona bai son yi ba, Even if I tell him, he won't take me seriously." A hankali Taj ya dubi Benazir da tayi maganar, idanuwansu suka shiga cikin na juna, da sauri ta kawar da nata idanun gefe ɗaya. "Ina sauraronki! Faɗamin me ke damunki?" Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta jin ya kula ta, aikuwa ta gyara zama ta fara labarta masa abun da ke faruwa da ita, nutsuwa ya yi yana sauraronta, dan dakatawa ta ɗan yi tana haki kamar wadda tasha gudu. Da hannu ya nuna mata Mineral water,"Ki sha" da sauri ta dauka ta ɗan kur6a. Bayan ta ajiye taci gaba da bashi labari.. *bari mu koma baya don jin meya faru a ranar da Benazir ta dawo daga gidansu Anila bayan ta fada mata komai dangane da batansu Angel harta kulle kanta a daki, a ƙarshe da aka bude dakin aka iske ta kwance a ƙasa rabin jikinta a cikin toilet👇* Bayan da ta gama shan kukanta tamkar ranta zai fita, lokaci ɗaya ta fara Jin azababben ciwon kirji, tana jiyo bugun kofar da suke yi mata haɗi da yi mata magiya akan ta bude amma taƙi saboda bata son ganin kowa a kusa da ita, a kan floor ta kwanta tana cigaba da sharar ƙwalla. "Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana a haka, yakamata ki yi hada nafila..." Muryar Dr Shureim ta jiyo acikin kunnanta. Daƙyar ta iya tattara ƙarfin da ya yi saura a jikinta ta mike ta nufi toilet don tayi alwala kamar yadda Dr Shureim ya shawarce ta. A gaban sink ta tsaya tare da kunna faucet, ta soma yin alwalar sai dai gaba ɗaya hankalinta baya a tare da ita, ta lula duniyar tunanin ina zata ga Taj da ƴarta? Tana tsaka da yin alwalar hasken electric bulb din dake a saman ceilling ya fara wasa ya kawo ya dauke, bata kawo komai aranta ba ta yi tsammanin electricity din gidan ne ya samu matsala, hakan yasa taci gaba da yin alwalarta. Bata yi aune ba, unexpectedly glass din madubin da take fuskanta ya fara tsattsagewa, a razane ta ƙura ido tana kallon abun mamakin gani take kamar idanunta ne ke nuna mata ba dai dai ba, dama bata a cikin hayyacinta damuwa ta fara zautar da ita, miƙa hannu ta yi da niyar ta shafa madubin don ta tabbatarwa kanta abunda take gani gaske ne ko ƙarya kwatsam! madubin ya tarwatse da kan shi glass din ya zubo kan floor, har ta kware baki zata fasa ƙara ta ji an fusgo hannuwanta izuwa cikin madubin, ta ƙarfi da yaji ake kokarin janta cikin shi, fashewa ta yi da matsanancin kuka na tashin hankali ta dinga yan buge-buge tana ƙoƙarin kufcewa yayin da hannayen da suka rurruke nata suka ja kusan rabin jikinta cikin madubin, daddagewa tayi da iya ƙarfinta na ƙarshe ta shiga karanta ayatul kursiyu bata kaiga direta ba ta ji an wurgo da ita gaba ɗaya gangar jikinta ta dawo cikin toilet ɗin kanta ya daki floor, A zabure ta miƙe ta watsa a guje ta nufi ƙofa sai dai me? Kafin ta ƙarasa ƙiiiii taji kofar ta datse kanta, fasa ƙara ta yi da ƙarfi take ambaton sunan Yaya shyureim dana Mommyn su don su kawo mata a gaji, bugun kofar ta dinga yi kamar zata 6alle ta, gurnanin mutun ta jiyo a bayanta jiyowar da zata yi keda wuya tayi arba da wani gabjejejn mutun ƙaƙƙarfa jikinshi sanye da baƙaƙen kaya ya rufe ko'ina na jikin shi, zazzare mashi idanu ta yi kamar mai fama da farfaɗiya ta dinga farfari zuciyarta na bugawa da tsananin fargaba ta dinga sambatu tana fadin, "Na shiga Uku!!! Wanene kai? Wallahi kada ka ta6a ni, kada ka matso kusa dani, zan ƙona ka da ayar Allah..., bata ƙare maganar ba ya ɗaura gabjejen tafin hannunsa kan wuyanta ya damƙe shi ya jata tana kuka da yan buge-buge ya nufi bathtube da ita, wani irin ruwan zafi ne ya kwararo ta cikin faucet har tiriri yake yi kamar za'a zabka kaza haka ya soma ƙoƙarin tura kanta cikin ruwan, wanda hucinsa kaɗai bala'e ne tsaf zai ƙona fatar mutun, fashewa tayi da kuka tana ihu ga bleeding da hancinta ya fara yi, Sai yakushin hannunshi take yi don ya saketa, yana gab da zai tsumbula kanta cikin ruwan, ta furta wata addu'ar neman tsari da Dr Shureim ya koya mata, wallahi ko second ba a ƙara ba mutumin ya 6ace 6aat hasken toilet din ya daidaita, madubin ma ya maida kansa yadda yake, hannunta dafe da wuyanta dake mata raɗaɗi take kallon Ikon Allah, Wato addu'a tayi a rayuwa musamman in kayi imani ba tare da kokwanto ba, ganin ya 6ace yasa ta zabura aguje ta nufi kofar toilet ɗin ta dinga bugunta daƙyar ta samu ƙofar ta buɗe sai dai kafin ta fuce wani irin jiri ya ɗebeta gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗi yaraf har goshinta ya fashe sakamakon dakar floor da kanta ya yi. Hankalin Anila dana Taj ba ƙaramin tashi ya yi ba, Sun yi matuƙar girgiza da jin abunda ke faruwa da Benazir. "Kin taba faɗa ma wani?" Ɗaga kai ta yi,"Eh, Yaya Shureim ne kadai ya sani, amma ban faɗa masa na ranar dana shiga toilet ba saboda ban farfado cikin hayyacina ba. Cike da al'ajabi yake ɗan jinjina kanshi yayin da zuciyarshi ta cika fam da tashin hankali, Komai da suka faɗa yayi shige da case din da suke aiki akai, yanzu ya fara yarda da abunda Anila ta faɗa masa akan Benazir. Chief ya kira bayan ya yi picking gaba daya ya fayyace masa abun da su Aneelarh suka sanar da shi, tashin farko ya ce wannan babban al'amari ne, kuma ya ji dadin zuwan su, in ba damuwa su jira shi ya dawo yana son yin magana da su. Ɗagowa ya yi tare da kallon su Aneelerh, "Ya buƙaci yana son magana daku, zaku iya jira har lokacin da zai dawo?" Aneeleerh ta ce, "Ba damuwa zamu jira shi" Faɗa mashi ya yi kafin su ka yi sallama ya aje wayar gefen ta Ana... "Naga baku sha fruit din ba," Ya ɗan tambaya idanunsa akan Benazir dake ta kallon shi.. "Ni wlh hankalina kwata kwata ba a kwance yake ba, bana jin cin komai" "Look Aneelerh, Ki kwantar da hankalin ki, tun da har ku ka yi dubarar tuntu6armu in sha Allah komai zai tafi dai dai" jinjina kai ta yi .. "Ina su Unaisah ne?" Benazir ce ta tambaya "Suna a daki" ya bata amsa batare da ya dubeta ba... "Zan iya ganin ta" girgiza mata kai ya yi"A'a!" "Meyasa? pls Taj, almost one month ban ji muryar ƴata ba? Dan Allah meyasa ka ke yi min haka? Laifin da na yi maka tsakanina da kai ne, banga dalilin da zaisa ka shiga tsakanina da ƴata ba, saboda ni na yi wahalar naƙudarta na kuma haifa maka ita..." ranta a 6ace ta yi maganar tana aika masa da harara. "Sau nawa kina yunƙurin zubar da cikin nata don kada ya 6ata maki shape?" Bai ƙare maganar ba Anila ta yi saurin furta, "Dan Allah Taj ku daina, ba girman ku bane, bai kamata aji maganar nan daga bakin ka ba, Benazir koda da son ranta ta gudu tabar Unaisah amma ai tayi nadama ko? Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana yakamata kaima ka yafe mata." Murmushin gefen fuska ya ɗan saki, "Ni zolayarta nake yi, amma komai ya wuce awurina, sannan ni ba hanata Unaisah na ke yi ba, tayi rashin lafiyane har kwantar da ita asibiti saida aka yi, bana so na ɗaga maki hankali ne shiyasa ko kin kira bana ɗagawa ....." Bai ƙare maganar ba sakamakon kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un da Benazir ta furta tare da miƙewa tana yarfa hannu ta furta "Meke damunta ne? Wani irin ciwo ne ta yi? Don Allah ka haɗa ni da ita! Dama saida na ji a raina wani abu na faruwa da ita, har mafarkinta nake yi ashe bata da lafiya...." Ta faɗa har hawaye sun zubo kan fuskarta, Da damuwa akan fuskar Anila ta ce, "Taj, meke damun Unaisah ne? Meyasa baka sanar dani ba?" "Calm down your mind, Unaisah ta ji sauƙi yanzu, bari na kirata ku gaisa." Ya faɗa tare da ɗaukar wayarsa yana ƙoƙarin danna mata kira Unexpectedly suka jiyo shesshekar kukanta! Kusan a tare suka kai duban su gare ta, tana a tsaye jikinta sanye da Satin fitted gown black colour tabi shape dinta, bata ɗaure sumar kanta ba,ta sake ta har mid back dinta, ƙafafunta na sanye da highhill masu ɗan banzan tsini.... Jikinta sai kerma yake yi kamar mazari, yayin da idanunta dake fitar da hawaye ta tsayar da su akan Benazir, ashe tunda Taj da Benazir suka fara sa'insa ta fito daga daki kaitsaye maganganunsu suka sauka acikin kunnanta. "Daughter meyasa kike kuka? Ko jikin ne?" Da damuwa akan fuskar Taj ya tambaya..... Da index finger ɗinta ta nuna Benazir, "Dama kece mahaifiyata wadda ta haifeni a wulakance! ta barni a cikin kwamin wanka sannan ta gudu ta tafi ta barni! Dagaske kece Aunty Benazir?" Rai a matuƙar 6ace ta faɗa da tsiwa tana fitar da numfashi mai huci. "Ki amsa min tambayata??" Ta faɗa tana zare mata gray eyes dinta... Tsabar ruɗu da tashin hankali ya hana Benazir furta kalma, wani irin shakkarta take ji.... "Shirun da kika yi ya tabbatarmin da abunda kunnuwana suka jiye min." Ta faɗa tare da maida kallonta akan Aunty Aneelerh cikin jin ƙunar rai ta ce,"Aunty Aneelerh, I know you won't lie to me tell me, who is she?" Yawu Aneelerh ta haɗiya ƙutt, cikin sanyin murya ta ce,"Pls Unaisah, zo ki zauna za mu yi maki bayanin komai..." Fashewa tayi da kuka tare da girgiza kanta, "Daddy, Aunty Aneelerh meyasa kuka 6oyemin cewa itace matar nan data gudu ta barni? Kuka sani na je nayi jinyarta a asibiti, bayan kunsan irin tsanar da tayi mini, bata taba sona ba, wallahi dana san kece bazan taba yin jinyarki ba koda zaki rasa ranki ne" with a burning heart ta faɗa tana aika mata harara. "Why didn't you kill me at birth if you couldn't care for me? You left me in the bathtub and abandoned me for years, You never thought to return and check on the child you left behind!, wlh hakkina kaɗai bazai bari ki gama da duniya lafiya ba...." Bata ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Aunty Aneelerh ta doka mata, "Unaisah ya isa! Ya isa haka!! Har yanzu ita mahaifiyar kice, karna kuskura na ƙara jin kin gaya mata maganganu marasa daɗi" Fashewa da kuka Benazir tayi, baiwar Allah tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi. "This woman will never be my mother! I don't like her, I hate her, I don't want to see her, You're heartless and don't deserve to be called a mother! Dan Allah na roƙe ki ki fuce daga gidan nan in har ba so kike ni in bar maki gidan ba" Cike da takaici Taj ya dafe forehead ɗinsa da tafinsa, dama saida yayi fargaban zuwan ranar nan, shi yasan za'a rina saboda Unaisah ta ƙullaci Benazir aranta, haushinta take ji sosai, tsanar ta samo asali ne tun daga kuruciyarta. Bata saurari kowannan su ba ta juya a zafafe ta nufi kofar dakinsu, da gudu Benazir tabi bayanta ta kai hannu tare da ruƙo hannun rigarta, aikuwa cikin fushi Unaisah ɗin ta bangajeta har saida ta yi taga taga zata faɗi, cikin sauri Aneelerh da ta biyo bayanta tayi saurin tallabota. Rushewa ta yi da matsanancin kuka tana fadin wai ƴar da ta haifa ce ta ke gaya mata magana kamar zata doke ta? "My own daughter calls me heartless! Na shiga Uku Aneelerh ta tsaneni bata son ganina! Wayyo Aneelerh zuciyata zafi ta ke yi min..." Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi da abunda Unaisah ta yi, abun da ya ƙara ƙona ma Benazir rai yadda Taj ya yi banza da su ko motsawa baiyi ba daga kan kujerar da yake balle ma harta sa ran zai taimaka mata su shawo kan Unaisah, tayi masa mummunar fahimta, batasan lalurace ta hana shi miƙewa ba, dama da haushin shi aranta saboda tasan shine ya cusa ma Unaisah tsanarta acikin zuciyarta shiyasa harta ƙullaceta arai in bashi ɗin da ya fada mata ba, Uzair da Aneelerh ba zasu ta6a tona mata asiri a gurin Unaisah ba dole sai in a wurin Taj ta ji. Bawan Allah Taj damuwa ce ƙarara akan fuskarshi, kwata kwata bai ji daɗin abun da Unaisah ta yi mata ba. "Aneelerh, Ku dawo ku zauna, ku barni da Unaisah, zanyi magana da ita." Rai a6ace Benazir ta nufe shi kamar zata doke shi ta damƙi gaban jallabiyar shi da hannyenta biyu tana huci ta ce, "You caused everything Taj, I hope you're happy now, kaine ka cusawa Unaisah tsanata a cikin zuciyarta, saboda kaine ka faɗa mata cewa na haifeta nabarta acikin kwamin wanka, wai laifin me na yi maka ne? Wace irin tsana ka yi minne???" Runtse idanun shi ya yi batare daya iya furta kalma ba, cikin sauri Aneelerh ta damƙi hannun Benazir ta soma kiciniyar 6am6are shi daga wuyan Taj, "Wai miye hakane Benazir? Idan rai ya 6aci ai hankali bai kamata ya gushe ba, Taj bazai ta6a faɗa ma Unaisah abun da ki ka yi don yasa ta tsane ki ba..." "Ki barni Aneelerh, wlh bazan ƙyale shi ba, yadda ya saka mata ƙiyayyata acikin zuciyarta dole ya je ya saka mata soyayyata a cikin zuciyarta, saboda shine ummul aba'isin komai, wlh he must fix what he ruined." Ta ƙarashe maganar tare da bangaje Aneelerh, ta ƙara kakkama gaban rigarshi, ɗaurin kallabin kanta tuni ya jima da zamewa, doguwar sumar kanta duk ta hargitse kamar mahaukaciya, yana jan numfashi da ƙarfi ya furta, "Benazir ki sakar min rigata, mara kunya, har yanzu bazaki ta6a canzawa ba, tsakanin ni da ke wanene mai laifi? Da har zaki ce ni ne silar komai? Bayan kece ummul aba'isin duk wani abu da ya faru..." Ya faɗa yana buɗe idanunsa da suka kaɗa jawur ransa ya 6aci ganin Benazir na neman ta ɗaura masa laifi. "Tabbas, Ni na faɗa ma Unaisah, kuma Allah shine shaidata ni ban faɗama Unaisah don ta tsaneki ba, fa ce sai don ta tausayamin ta daina azabtar da ni, saboda a lokacin da tana ƙarama mugun halinta sak irin naki ne, bata jin maganata kusan kashe ni ta yi da baƙin cikinta, kin tashi kin tafi kin barni da jinjira ke baki yi tunanin taya zan iya rainonta ba ne? Benazir in bazaki iya godemun ba bai kamata kiji haushina ba!" Yana huci ya ƙare maganar, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, Still taƙi sakin gaban rigarshi. Hankalin Aneelerh ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin takasa shawo kan Benazir ne yasa ta watsa da gudu ta nufi hanyar fucewa daga falon don ta je ta gaya ma Dr Shureim, tasan shi kaɗaine zai iya dakatar da Benazir saboda bad temper dinta in takai maƙura a 6acin rai ko mai iskokai bazai nuna mata yadda ake bori ba. *UMMIN AMERICA🔥* Su biyu ne a zaune kan rug din dakinta, ita da Batool sun ƙurawa laptop screen idanunsu, wani korean drama ne su ke kallo ita da Batool, Ummi ta toshe kunnuwanta da Headset kwata kwata bata jin wani sauti daga waje saina abunda take kallo. Batool ce ta fara jin hayaniyar mutane a cikin gidan, tun tana jin maganganun nasu ƙasa-ƙasa har ta fara ji da ɗan karfi. "Aunty Ummi" Shiru bata amsa mata ba, bubbuga kafaɗarta ta yi, a ɗan firgice ta dube ta, "Babe lafiya?" "Kina jin hayaniyar mutane acikin gidan nan?" "Banji me kika ce ba," Ta faɗa tare da zame headset din ta maida hankalinta akan Batool, "Kamar wasu ne ke faɗa acikin gidan nan, naji hayaniyarsu a cikin kunnena, ki saurara ki ji" Ɗan zare ido Ummi ta yi tare da yin shiru ta kasa kunne a hankali ta fara jiyo maganganunsu... "Su wanane? Ko munyi baƙi a gidan ne?" Girgiza kai Batool ta yi, "Wallahi nima bansani ba, kawai yanzu na jiyo hayaniyar su kamar faɗa su ke yi...." Da sauri Ummi ta miƙe, mayafinta data bari akan gado ta ɗauka tare da yafa shi kan kafaɗarta... "Ki ci gaba da yin kallon, bari na je na gano mana meke faruwa." Ta amsa mata da toh da sauri Ummi ta fuce daga ɗakin......✍️ Dira ƙafarta keda wuya unexpectedly ta tsinkayi muryar Dr Shureim a cikin kunnuwanta.. "Benazir baki da hankali ne? Meye haɗin ki da shi? Mutum da girmansa zaki shaƙe gaban rigarsa!" Ya faɗa yayin da yake shigowa falon cikin sauri idanunsa akan Benazir da har lokacin bata saki kwalar Taj ba, Anila tana abiye da bayan Dr. Shureim gaba ɗaya hankalinsu ya tashi sosai, batai aune ba Dr shureim Ya damƙi hannunta ya fusgeta gefe ɗaya har saida tayi taga-taga kamar zata faɗi. Rai a matuƙar 6ace ya dubeta kamar zai kife ta da mari. "Uban meya haɗa ki da shi? Dama dalilin da yasa kika matsamin in kawo ki gidan kenan? Saboda kawai ki tada husuma?" Tana shessheka ta ce,"Yaya Shureim Taj ne fa, My Ex-husband, Uban ƴata dana haifa, Azeezaty itace yarinyata Unaisah....." A ruɗe Dr shureim yake kallon Benazir sam ya kasa furta kalma saboda yadda maganar ta dira a cikin kunnansa ta rikita lissafin kwakwalwarsa. Juyawa ya ɗan yi tare da kallon Anila wadda jikinta keta kerma saboda fargaban kato6arar da Benazir ta yi masu, bayan irin gargadin da aka yi masu akan kada su fallasa asirin Taj yana a raye. "Inna lillahi! Benazir meyasa kika faɗa masa? Meke damunki ne? Kin manta amana na faɗa maki, kuma kika yi alƙawarin ba zaki faɗa ma kowa ba!" Ta faɗa a faɗace kamar zata doke ta. Taj dai tun da ya sunnar da kan shi ƙasa bai ƙara ɗagowa ba saboda halin damuwar da zuciyar shi ta shiga. Tana kuka ta ce, "Ai wallahi ƙwara kowa ma ya san yana a raye, in ba haka ba baƙin cikin shi zai kashe ni ne! " Gaba ɗaya Dr Shureim ya gama ruɗewa, sai faman rarraba idanunsa yake yi akan Taj da Benazir da Anila. Dakyar ya shanye mamakinsa da wata irin raunanniyar murya ya furta, "Dan Allah ku fahimtar dani! Na kasa ganewa, shin dagaske shine Taj mijinki! Azeezaty kuma itace ƴarki Angel?" Ya tambaya yana kallon su... Cikin sanyin murya Anila ta ce, "Hakane Yaya Shureim." Ɗan zare idanunshi ya yi tare da maida idanunshi kan Taj da tsantsar mamaki yake kallon shi. "Bawan Allah, ka ji tsoron Allah ka faɗamun gaskiya, da gaske kaine Taj mijin Benazir?" Jinjina mashi kai Taj ya yi alamar Eh. Baki asake ya kuma mayar da duban shi akan su Anila kamar waɗanda suka yi ma sarki ƙarya sunyi zuru zuru... Gaba ɗaya sun kasa furta kalma sai kallon kallo suke jefawa junansu... "Yaya Shureim! Benazir!! Aneelerh!!! Muryarta na rawa ta furta sunayen su, Kaitsaye sautin muryarta ya daki dodon Kunnuwansu, wata zabura suka yi a firgice suka kai dubansu inda take a tsaye saman stairs fuskarta sharkaf da hawaye idanunta sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono acikin su, yanayin fuskarta ya nuna tsantsar ruɗani da tashin hankali gami da al'ajabin ganin bayin Allahn nan, Tayaya zata manta fuskokin su? Bayan irin haddar da ta yi masu... "Is that really you? Or am I dreaming? I can't believe my eyes!" Tashin hankalin da ba'a saka mashi date! Al'ajabine ya ɗaure zukatansu ya hana la66ansu motsawa sai dai idanu da suka bita da su batare da ƙyaftawa, Yau tsawon shekara goma sha takwas da ɗauriya rabon su da yar tahalikar nan tun da ƙaddara ta raba su da ita, ba zasu ta6a mantawa da Aishatu bint Sheikh Imam Malik ba! Ba zasu ta6a manta raɗaɗin da suka ɗanɗana na abun da ya rabasu da ita ba. "Dama Kunsan Juna ne?" Daƙyar Taj ya furta maganar yana dubansu, yayi mamakin ganin yadda suka ƙame atsaye idanunsu azazzare kamar waɗanda suka ga wani mugun abu. Benazir ce ta yi ƙarfin halin furta, "ƘAWATACE AMINIYATACE, ITA ƊIN TAMKAR YAR UWA TA JINI TAKE A WURINMU! YAU SHEKARA GOMA SHA TAKWAS RABON MU DA ITA, TUNDA ƘADDARA TA RABA MU❗❓ *(WAIWAYE ADON TAFIYA)* *WACECE AISHATU BINT IMAM MALIK? MENENE DANGANTAR AISHA DA ANEELERH DA BENAZIR DA KUMA DR SHUREIM? WACE ƘADDARA CE TA RABA SU❗❓👇* *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE 1 COMMENTS Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Anonymous 30 September 2024 at 10:52 Thank you and jaxakillahu Khairan Reply Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa (1) Al'adu (1) Alkamawa (3) Article (3) Blogger Tips (1) Economy (5) Education (2) Entertainment Gist (1) Gyaran-Jiki (5) Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya (1) Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci (5) Kwalliya (4) Labaru (25) Lifestyle (1) Ma'aurata (1) News (304) Nigeria (5) Noma (1) Opinion (4) Picture (3) Politics (15) Profile (2) Q&A (1) Ramadan (9) Ramadan Tafsair (1) Siyasa (1) Sports (72) Tarihi (5) Technology (1) Tips (3) Video (3) YouTube (5) Zain Abeed (1) Zamantakewa (1) Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions Our website uses cookies to improve your experience. Learn more Accept ![14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~<><><><><><><><><><><><><><><✍️~ ~___________________________________~ Sheikh Imam Malik Shahararren malamin addinin musulunci ne, kuma babban alkalin Kotun Musulunci, Haifaffen jihar jos ne, wayayyen malamin addinin musulun ci ne kuma dan boko maiji da kanshi, ga wadatar arziki da Allah ya yi mashi, sheikh Imam ya yi suna wajen yin adalci, rukon amana tausayi da jinƙai, yana da ƙwarewa ta fannin shari'ar musulunci, mutunne shi mai tsastsauran ra'ayi akan addininsa, kuma kaifi ɗaya ne In ya furta magana baya canza ta, da dama mutane masu aikata mugayen laifuka suna jin tsoron shari'ar sheikh Imam Malik saboda sun san Halinsa baya kar6ar Cin hanci, dole mutun Ya kar6i hukunci dai dai da abunda ya shuka ko ɗan uban wanene, sannan yana da zuciya idan ranshi ya 6aci, sai dai duk da hakan Yana da sauƙin kai ga wanda ya iya zama da shi. Matarsa Ta farko Malama Fatima Batool wadda ta kasance Yar uwarsa diyar wan mahaifinsa mazaunin Sudan, Auren zumunci iyayensu suka haɗa su, Kuma cikin Ikon Allah jininsu ya haɗu soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu har takai su ga yin aure, Sunyi zama Na amana saboda Ra'ayinsu yazo ɗaya, Yaji dadin zama da ita saboda kyawawan halayenta, tanayi mashi biyayya sau da kafa, A lokacin data samu ciki yayi murnar da bazata misaltu ba, baya gajiya dayi mata addu'a akan Allah ya sauke ta Lafiya, bayan data haihu ne ta koma ga Mahaliccinta yayin da tabar masa Yar jinjiran da ta haifa masa, Shiekh Imam Yaji rasuwar ta, duk irin juriyarshi da tawakkalinsa sai da ya zubda ƙwalla saboda babban rashin da yayi. Rainon yarsa ya koma hannun gwaggwansa kanwar Mahaifiyarsa, A lokacin iyayensa duk basa araye, itace ta kula masa da Yarsa Har ta dan fara tasawa. daga bisani Kawunsa na sudan ya bashi auren kanwar Matarsa Aunty Laura, a wani zuwa da yai sudan kai masu ziraya, A lokacin sheikh imam baida niyar ƙara aure saboda bai warke daga radadin rasa matarsa da yayi ba, amma saboda aunty laura ta kasance Jinin Malama Batool yasa shi amincewa da aurenta. Bayan auransu da wata daya Rainon Aisha ya dawo hannun Aunty laura, ta rike ta da amana kamar yar cikinta, tana bala'en Son Aisha, saboda jininta ce ita uwa uba kamanninta sak dana Yayarta Malama Batool, saboda yadda take bata kulawa ba zaka taba gane ba yarta bace sai an fada maka. hakika sheikh imam malik yayi namijin kokarin gurin tarbiyantar da rayuwar yarsa, ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, gaba daya halayanta da dabi'unta irin nashi ne, abu daya da bata ɗauko na shi ba shine Zuciya, tana da tsantsar hakuri kamar Mahaifiyarta Malama Batool, hausawa sukace kyan ɗa ya gaji ubansa itama hakan ta ke Aisha tagaji mahaifinta da kuma mahaifiyarta malama Batool. Sheikh Imam ya ɗaura mata burin duniya, Bai taba son wata aba kamar yarda yaso Aisha ba, ita kadai ce ƴa daya tilo da Allah ya albarkace shi da ita, Babu irin gatan da sheikh Imam bai yi mata ba. Aishatu macace mai cikar kamala, mai tsantsar kamun kai, samun matashiya mai irin baiwar ilmin da Allah ya bata zaiyi wuya a fadin duniyar nan, ta haddace alkur'ani mai girma tun tana da shekara goma sha uku a duniya, mutane dayawa suna yabonta saboda kyautatawarta a gare su, kyawawan dabi'unta da halayanta abin koyi ne ga duk wata ya mace, kuma burin kowani namiji ne ya mallaki mace kamarta. duk wani abu da zai sabama Mahaliccinta gudun shi takeyi, tana da jinƙai da son taimako bata gajiya da hidimtawa addininta. Abun burgewa iyaye mata da matan aure suna karuwa da ita, also she's a role model for young women. tun tana yar matashiyarta take koyawa a islamiyar Mahaifinta mai suna madarasatul Fatima Batool dake a kusa da gidan su, tana yin wa'azi ta kuma yi da'awa ga waɗanda basuyi imani ga Allah ba, ta dalilin Aisha, Sheikh imam malik Ya samu daukaka fiye da zaton shi, ta kare mashi martabarshi da kirmarshi ta kuma daukaka darajar shi a idon duniya, sau dayawan lokutta baya sanin tayi wani abun, sai dai akira shi awaya ko azo har gida ayi mashi godiya akan alkhairin da Aisha tayi, yai ta mamaki farin ciki ya cika shi, sai ya kirata ya tambayeta me tayi tukunna take fada masa Alherin da take samu a gurin Gasar karatul al'qur'ani da wadanda mutane suke bata kyauta saboda dadin wa'azinta da suke ji, dama A duk lokacin da ta kawo mashi kudin don ya dauki wani abu baya kar6a, kudinne take tarawa in suka taru dayawa da su take amfani gurin tallafawa marasa karfi, tana yawan ziyartar asibitoci, gidajen yari, da gidajen marayu ta basu tallafin kayan abinci da suturu in kuma bata da kudin da zata basu zatayi masu wa'azine da nasiha mai ratsa zuciya, shiyasa sheikh imam ya ke bala'en ji da Aisha, yana matukar son Yar shi, itama bata da abu mafi soyuwa dayawuce Mahaifinta, tana yi mashi biyayya sau da kafa, batason bacin ran mahaifinta, tana kokarin yin duk wani abu da zai faranta ran shi. Dangantar da ke a tsakanin Benazir da Ayshah da Dr shureim ta samo asali ne tun daga kan Iyayen su Maza, Sheikh Imam malik baida amini daya wuce Alhaji ubaid Wadata sun kasance makwabtan junane, Gidansu Yana a jikin na juna, Akwai zumunci mai karfi a tsakanin Iyalansu, atare suka taso tun kuruciya, kasantuwar Alhaji ubaid Dalibin Mahaifin sheikh Imam ne agurinsa yake ɗaukar karatun addini kafin Allah yayi masa rasuwa, Alhaji Ubaid dan babban Gidane, Family dinsu yayi shura A jihar, saboda Arzikin Mahaifin su marigayi Alhaji mu'azzam wanda akeyiwa lakabi da wadata babban dan kasuwane a zamaninsa. Benazir da Aisha Ƙawayen junane kuma aminnai tun kuruciya, atare suka taso kuma atare su ka yi primary da secondry a makarantar Sheikh Imam Malik wadda Har Islamiya ake koyawa a cikin ta, abun da zai ɗaure ma kai, kwata kwata halin Aisha dana Benazir baizo daya ba, sun sha banban, Benazir tana da girman kai, rashin kunya kuma bata iya shigar mutunci ba, duk suturar da zata sanya sai ta matse jikin ta. Sarai Sheikh Imam yasan da Halin Benazir Ya kuma san Gado tayi agurin Hajiya layla, mutane suna yawan kawo mashi tsegumi akan ya raba yar shi da Benazir In ba haka ba zata bata masa tarbiyar ƴa, Bai ta6a ɗaukar maganarsu ba, saboda Shi ya yarda da tarbiyar daya ba Aisha yasan bazata ta6a bari Benazir ta rinjaye ta ba, sai dai ita ta rinjayi Benazir gurin karkato da hankalin ta don ta shiryu, bayan hakan Yayi Wa Benazir farin sani, Yasan Bata Jin magana kuma bata da kunya sai dai ita din ba Yar iska bace, bata shaye shaye, bata bin maza, Rashin ɗa'arta abaki ne da kuma yanayin Shigarta, sai kuma yawon gantali da take fita a kowani dare ne sai taje Night club, gata yar hana biki maraici, kuma zabaya ce a fagen rawa, amma Sheikh bai ta6a gigin raba ƙawancen su ba, saboda yana son duk wani abu da Aisha ke so. bayan haka baya son abunda zai raba zumuncinsu da makwabtan shi. Wadannan dalilan ne suka sa Shiekh imam Ya amince ma ƙawancen Aisha da Benazir, Amma sai da ya gindaya mata sharudda akan bai lamunta tadinga fita yawo ba, kulle ya ke mata daga makaranta sai gida, In har zasu hadu da Benazir sai dai tazo gidan su, Ko kuma In Aunty laura zataje gidan gurin Hajiya layla ta tafi da ita, sai kuma in sun haɗu a school, amma sam bai yarda ta dinga bin Benazir suna fita yawon gantali ba bayan haka ya hanata kula kowani saurayi saboda akwai wanda yake burin ta aura har sa'insa su ke yi da Aunty laura akan ya hana Aisha kula samari ita ta rasa gane ma manufarsa akan Aisha kamar ba yar cikinsa ba, maganganu marasa dadi take fada masa bai ta6a biye mata ba. Aunty laura wayayyiyar macace Yar boko kwararriya ta fannin business, ta inda suka sha banban da Imam ita tana da karancin addini akai, kwata kwata halinta ba irin na yayarta mariganya Batool bane, shiyasa basu jituwa da sheikh imam malik, sa'insa suke da junansu saboda ta tsani yadda yake zafafawa akan addini kuma A ganinta kullan da ya ke yi ma Aisha takura ce. shi kuma yanayi ne saboda Farin jinin da Allah yayi mata, Babban abunda Ke ci mashi tuwo a ƙwarya yadda wasu mazan basa iya kau da maitarsu akan Aisha, saboda Dirin da Allah yayi mata, tun tana ƙanƙanuwarta wani irin dirin jiki ne da ita mai jan hankali, duk taku daya idan tayi sai jikin ya girgiza koda kuwa ta sanya dogon hijabi ajikinta ne sai shatun dirinta Ya bayyana wani irin farin jinin samari gare ta kuma mafi akasarinsu ba don Allah suke son ta ba sai don kwaɗayin Surar ta. wannan dalilinne yasa shi tsananta mata tsaro ko fita za ta yi dole ta sanya dogon hijab da niƙab, daga makaranta sai gida makarantar ma shi ke kai su da kanshi In an tashi ya dauko su ita da Benazir, wani sa'in In aikin yayi mashi yawa ko zaiyi zaman shari'a Aunty Laura ce ke dawainiyar kaisu wani lokaci in ta samu damar dauko su daga school in an tashe su sai ta saci hanya takai su Shopping mall tayi masu siyayyar kayan amfanin su na mata. Awata rana ne Aisha tana a zaune kan darduma sai ga Benazir ta shigo gidan da rawar jiki ta shigo har dakinta ta ruko hannunta da farin ciki take fada mata tazo taga Uncle musa da Yaya shureim sun dawo Nigeria, kasantuwar su dukansu A lokaci ba mazauna Nigera bane, Shi Alhaji musa harkar kasuwancin shi yakeyi a kasashen ketare yayin da Shureim ke karatu a kasar egypt can gurin ammin su ya ke da zama. da fara'a Aisha tace meyasa bata fata mata ba, Benazir tace kawai tana son tayi suprising dinta ne, cike da farin ciki tace ta jira ta a falo zata shirya, Benazir na fita daga dakin Aisha ta soma shirya kanta cikin abaya, sai ga Aunty laura ta fito daga daki ta iske Benazir zaune kan sofa, da fara'a suka gaisa da juna har ta tambaye ta meya sanyata farin ciki nan take fada mata yaya shureim da Uncle musa ne suka dawo Nigeria shine ta zo don ta fada ma Aisha, washe baki aunty laura tayi tana fadin Ah lallai manya manyan baki, shine ba'a fada min ba? tana cikin magana sai ga Aisha ta fito sanye da dogon hijab hada nikab akan fuskarta. fuska adaure Aunty laura tace kefa matsalata dake kenan, kamar kinfi kowa tsoron Allah, kullum cikin nikab, yanzu nan da gidan makwabtan namu sai kin saka hijab da nika..." a karshe ta korata daki tace taje ta sako Mayafi..da damuwa tace ita bazata iya ba, saboda hijab mutuncin ya mace ne, bayan haka baba ya hanata fita ba hijabi har ta soma janyo mata aya, aunty Laura ta mike rai a6ace taja hannunta suka koma daki, adole saida ta tursasa ma Aisha ta saka Wani guntun veil a kafadarta, baiwar Allah duk sai taji ba dadi ganin yadda abaya din ta ɗame jikinta, dirinta nan nata mai jan hankali ya bayyana muraran musamman ta gurin mazaunanta sun fito rudu rudu.. ahaka Banezir taja hannunta suka tafi gidansu, shigarsu keda wuya ta gate din adai dai Lokacin Alhaji musa Yana atsaye gaban dankareriyar motarsa ya dauki wankan shadda hannunsa ruke da waya, kallo daya da Aisha tayi mashi saida gabanta ya fadi saboda ƙwarjinin dake gare shi, wata irin kirar jiki gare shi irin ta yan dambe. Benazir ce ta gabatar mata da Uncle dinta, duk irin izzar Alhaji musa da yayi tozali da Aisha saida Ya rasa nutsuwarsa saboda shi irin mazan nan ne masu kwadayin mace mai kyawun sura, sanin da yayi mata tuntana karamarta yanzu kuma ta girma, wani irin kallo yadinga binta da shi harya kasa amsa gaisuwar da ta ke yi mashi, A lokacin rudewa Aisha tayi saboda bai kwanta mata arai ba, musamman da ta ga hakoransa ya sanya masu Gold-plated teeth.. ita kanta Benazir ta lura da yanayin da ya shiga. Hakan yasa taja hannun Aysha suka nufi cikin gidan, Uncle musa yabi bayanta ta da kallo yanayin yadda take tafiya jikinta na girgiza ba karamin tayar masa da maitar sha'awarsa tayi ba, kuma tun daga lokacin ya kudiri aniyar saiya mallake ta. Bayan sun shiga babban falon gidan, anan suka iske Hajiya layla tare da Alhaji ubaid suna zantawa tsakaninsu, bayan sun gaishe dasu hajiya layla tace su shiga ciki su gaida shureim.. Tun da Allah Ya Halicci Aishatu Bintu Imam bata ta6a ganin mutumin daya kwanta mata aranta ba, da kallo ɗaya ta fada tarkon son shi sai akan dr shureim yanayin da suka same shi adakin shi yana zaune kan darduma Ya buɗe al'kurni yana karatu cikin nutsastsiyar Muryarsa ba karamin jan hankalin ta yayi ba, tayi mamakin girman daya ƙara tsawon shekaru a lokacin rabon shi da Nigeria. Sai da yakai aya, cikin sanyin murya yace masu su shigo yaga sun yi tsaye bakin kofar dakinsa, Jan hannunta Benazir tayi suka zukunna agaban dardumarsa ta gabatar masa da aminiyarta yar makwabtansu diyar sheikh Imam, ganin kamar bai gane ba don tun suna kanana Yabar Nigeria, Aisha ta gaishe da shi tare da yi mashi bangajiyar tafiya, da murmushi akan fuskarshi ya amsa mata, abunda bata sani ba Dr shureim yasan da zamanta, Yana yawan sauraron kira'arta da take yawanyi a taron musabaka, wanda mutane ke yaɗa videon a social media amma saboda miskilancinshi sai ya nuna kamar bai gane ta ba. sun ɗan jima Yana jan su da fira, lokacin da ta tashi tafiya dr shureim ne ya yi mata rakiya tare da Benazir har kofar gidansu, saida suka ga shigarta kafin suka koma gidan su. a daren ranar Alhaji musa Ya kira Benazir ya soma tambayarta dangane da Aisha, ko tana da tsayayyan da zata aura"? Benazir tayi mamakin tambayoyinsa saboda tasan Uncle din nata mugun miskiline bai cika shiga sabgar da bata shi ba, In fact mata basa agaban shi bata kawo komai aranta ba ta fada masa komai dangane da Aisha, Hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba jin cewa bata kula samari, fargabansa daya Sheikh Imam malik saboda basa ga maciji. A bangaren Aisha tun bayan data koma gida tunanin dr shureim Ya hana zuciyarta sukuni, Kwana take da shi aranta, haka zalika in tana koyama dalibanta karatu wasu lokuttan shagala take da tunaninsa har sai daliban su ankarar da ita. ta bayan fage Uncle musa ya fara ba Banezir makudan kudi masu auki don suje yin siyayya da Aisha, kuma yace mata baya son Aishar ta sani, Benazir bata ta6a fada mata Uncle musa ne ke bata kudi ba, Sai ma in ta tambayeta ina take samun kudi sai tace dr shureim ne ya bata, hakan ya sa ta saki jiki duk da bata da kwadayin abun duniya tayi azan yaya shureim yana son ta ne shiyasa yake ba Benazir kudi don suyi siyayya. kusan kullum sai Aunty laura tayi masu hanyar fita daga gidan batare da sanin Shiekh Imam ba, don suje Mall suyi siyayya harma da yawon buɗe ido koda Aisha ta nuna bata son fita Aunty laurace ka tursasa mata in ta turje sai ta fashe mata da kuka tana fadin bata mata biyayya saboda ba ta ɗauketa uwa, don taga ita bata haihuwa, in ta fadi hakan jiki na rawa Aisha take bin Umarninta. Tun bata sake ma Uncle musa in suka haɗu harta fara sabawa da shi, tana matukar girmama shi tanayi mashi kallon Uncle dinta. Haka zalika shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da dr shureim, Benazir tayi mamaki saboda sanin da tayi ma Aisha bata Kula maza sai gashi dr shureim ya ciri tuta, sun saba da juna, Benazir ta sanya masu ido sosai, Ta fahimci dukansu suna son juna, ita Aisha Kunya ce ta hana ta furta mashi Kalmar so, yayin da shi kuma miskilanci ne Ya hana shi bayyana mata, bayan haka Yana jin nauyin yayi soyayya da Aisha saboda yanayi mata kallon Kanwarsa. A duk lokacin da Benazir taso Ta bugi cikin shureim don ya fada mata In yana son Aisha sai yace mata shi babu soyayya atsakaninsu kallon kanwa ya ke yi mata, haka In ta bugi cikin Aisha don taji in tana son ya shureim sai tace mata ita fa ba son shi ta ke yi ba, kawai tana yi mashi kallon yayanta ne saboda zumuncin dake a tsakaninsu, In Benazir zata shekara tana tambayarsu amsa daya suke bata. Bayan da suka kammala Secondry School, Alhaji Ubaid ya sama masu admission a wata Jami'a dake a birnin hagen na kasar Jamus batare da sanin sheikh Imam Malik ba sai daga bisani ya same shi har gida ya sanar da shi. shiekah Imam bai nuna amincewarshi ba, Yace shi bazai bari yarsa ta tafi uwa duniya karatu ba, duk Universities din dake a Kasar har sai an fita waje neman ilmi? Alhaji ubaid ya ce yayi hakuri da bai nemi shawarar shi ba ya tashi ya yanke hukunci dama yaga Benazir ta kwallafa rai ne akan son zuwa can tayi karatu kuma ta nuna tana son suje tare da Aisha shi kuma yayi la'akari da shakuwar dake a tsakaninsu In aka rabasu ba zasu ji dadi ba shiyasa ma har ya nemi Benazir data kar6o ma shi Academic record din Aishah. A ranar da su ka yi maganar, bayan Alhaji ubaid yayi mashi sallama ya tafi, ranshi a bace Ya kira Aisha ya fara mata fada akan takardun karatunta data kai ma Alhaji ubaid don ya sama mata admission, tace mashi wallahi ba ita ta bashi takardun ba, hasalima ita batasan da maganar ba, ko da jin hakan nan take ranshi ya bashi da sa hannun Aunty Laura, Har daki Yaje ya same ta da maganar, maimakon ta kar6i laifin ta saima ta dinga masifa tana fadin taje ta bada kuma wallahi bai isa Ya hana Aisha taje karatu kasar waje ba, shi ko dan zumuncin dake a tsakanin shi da Alhaji Ubaid bazaisa Ya amince be? Idan Ma yana jin tsoron wani abu ya same ta acan din Ba Allah ke tsare bawansa ba, bayan haka tun da Ba ita kadai zataje ba hada Benazir ya bar ta mana, shiekh imam yace mata ya gama magana bata isa tasa shi canza ra'ayin shi ba. Ganin da gaske Shiekh Imam zaiyi mata bukulun kudin da take samu agurin Alhaji musa yasa ta kwashi kafa taje gidan kakarsu ta bangaren Uba da ta rage masu mai Suna Hajjo, ta tsara mata karya da gaskiya akan kullan da Sheikh imam ya ke yi ma yarsa, ta ce ita bakin cikinta gorin da ya ke yi mata akan Aisha sai kace ba diyar yayarta ba, In da kara aisha ai yar ta ce tana da ikon juyata son ranta, bayan haka ta fada mata Alhaji Ubaid Ya sama ma Aisha gurbin karatu a kasar germany ita da Benazir amma Ya hana bai dubi zumuncin dake a tsakanin su ba, Hajjo da ranta ya 6aci ta sa Aunty laura ta kira mata imam a waya tace yazo tana son ganin shi, koda yazo ta balbaleshi da fada kamar zata rufe shi da bugu kasancewar shi mai biyayya yadinga bata hakuri kamar zai durkusa mata kasa tace mashi in har yana son farin cikin ta yabar Aisha ta tafi karatu kasar germany, Shiekah imam yayi kokarin ankarar da ita illar dake akwai na tura ɗa karatu kasar waje balle ita da take mace amma Hajjo ta rufe ido tace itafa ta gama magana, kawai yabi abunda tace mashi, ta ko'ina ta matsa mashi lamba ba dan yaso ba ya amince zai barta, don yasan halin Hajjo rikicin tsufa ne ke damunta. bayan komawarsu gida baibi takan Aunty Laura ba Ya kira Aisha ya tambayeta da son ranta zataje kasar waje karatu? Aisha tace aa bata so saboda batason tayi nesa da shi, amma benazir ta nuna tana so suje suyi karatun atare acan tun da ba wasu shekaru ne masu yawa ba" a maganarta shiekh ya fahimci bada son ranta ba amma tana son ta bi aminiyarta ba yadda ya iya hakanan ya amince. Bayan Alhaji Ubaid Ya kammala yi masu travel arrangement, ana i gobe zasu tafiya sheikh imam bai iya runtsawa ba, saboda zazza6in tafiyar da Aisha za ta yi, wannan ne karo na farko da zatayi nesa da shi, bawan Allah akan dardumarsa Ya raba dare yana yin nightprayers duk akanta, washe garin ranar aunty laura ta shirya ta tsaf, a motar sheikh imam suka tafi, acan airport suka hadu da Benazir tare da family dinta da su ka yi mata rakiya, Aisha tasha kuka na rabuwa da Baba imam, har nasiha yayi mata akan ta ji tsoron Allah, kada ta canza a yadda yasan ta, sannan ta kare mutuncin kanta, karatu yakaita daga shi bai amince tayi wani abu da zai sa6awa mahaliccinta ba. Baba imam bai ƙyale Aisha hakanan ba saida Ya hadasu da Benazir ya karayi masu nasiha mai tsuma zuciya sannan ya damƙa ma Benazir amanar Aisha yace ya yarda da ita bai ta6a barin Aisha ta kula wata kawa in ba ita ba don haka ya bata amanar yar shi, ta kula mashi da ita. Benazir jikin ta ba karamin sanyi yayi ba, har kuka saida tayi saboda tausayin baba Imam, Alhaji ubaid ma yayi masu nasiha, bayan ya gama dr shureim Ya kirasu agaban shi Yayi masu addu'o'i tare da yar nasiha A lokacin Aisha ta dinga kallon shi, tayi fatan Ya furta yana sonta kafin su tafi amma sai baiyi ba saboda shi kallon kanwa ya ke yi mata, bawai don baya sonta ba sai don kasancewarsa miskili da zurfin ciki ko kallonta bai cika yi ba, bayan Aunty laura da hajiya layla sun sanya masu albarka tare da fatan alkhairi a karatun su, daga nan suka yi masu bankwana. Silar hawan su jirgi Allah Ya ƙaddara haduwarsu Da Aneelerh Muhammad falgore itama a lokacin za ta je yin karatu kasar germany, ta zauna a seat daya da Benazir taga ta burgeta ta ɗan fara janta da fira har Benazir ta dan saki jiki da ita, A lokacin Aneelerh batasan da zaman Aisha a cikin jirgin ba tana a seat din bayansu ta rufe fuskarta da mayafinta zuciyarta cike fal da tunanin mahaifinta data bari da kuma muradin ranta. Bayan jirginsu yayi Landing a airport na birnin hagen, Alhaji Musa Ya turo wani escord ɗinsa Yazo daukarsu a hadaddiyar mota, sukayi sallama da Aneelerh suka shiga mota, a zaton su kaitsaye escord din zai wuce da su Jami'ar da zasuyi karatu acan, amma sai suka ga akasin hakan, a wani katafaren gida da Alhaji musa Ya kama masu haya a kusa da Jami'ar, Anan Escord din yakai su a matsayin gidan da zasu zauna, Aisha tayi mamakin haduwar katafaren Gidan, tayi azan a hostel zasu zauna amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci hada masu aiki Ya aje masu agidan, kamar ba karatu suka je yi ba Aisha ta ɗanji shakkun ta zauna agidan saboda gudun kada ta shagala ta kasa ta6uka abunda ya kawota amma saboda Benazir yasa ta amince ta zauna, rana ta farko da suka fara shiga jami'ar, ba zato ba tsammani sukayi arba da Aneelerh ashe itama a nan zatayi karatu, Sunyi farin ciki da ganinta duk da ba'a department ɗaya suke da ita ba, rayuwarsu a jami'ar gwanin ban sha'awa shiga class kadai ke rabasu amma da zarar sunfito zasu hadu da Aneelerh a karshe ma da kawancensu yayi karfi da Aneelerh sai suka yi mata tayin ta baro hostel ta dawo gidansu da zama, Aneelerh bata musa ba ta amince masu toh ita kanta data ga inda suke rayuwa saida ta girgiza da mamaki saboda haduwar Gidan. Uncle musa ba karamin gatanci yayi masu ba, shi ke daukar dawainiyar komai nasu, tun daga cinsu shansu suturarsu masu kyau da tsada har account ya sanya yaronsa ya bude masu na kasar germany, baya gajiya da tura masu dollars kamar baison zafin neman su ba, lamarin shi ya fara daurewa Aneelerh da Aisha kai ganin yadda ya ke ji dasu yana tarairayarsu, wani abun daure kai Duk weekend sai yazo kasar germany daga America, kuma agidansu Yake sauka anan zai kwana su yi breakfast lunch dinner duk tare da shi, har yawon buɗe ido Yake zagayawa dasu a motar shi, da abun ya fara damun aisha ta dai gaza hakuri ta fada ma Benazir itafa zata koma hostel da zama saboda tana jin tsoron baba Imam Yaji labarin ba a jam'ar take zaune ba zai iya yi mata fada bayan haka bata son yadda Alhaji musa ke kashe masu kudi abun yayi yawa, sannan meyasa yake zarya duk week end sai yazo ya kwana agidansu? A ganinta hakan bai dace ba, a matsayinsu na musulmai kuma mata su dinga barin Namiji yana kwana a gidan su, Benazir ta nuna kin amincewarta da komawar Aisha Hostel, ta dinga lallashinta akan tayi hakuri ta zauna, na dan wani lokaci ne, kada ta damu da Alhaji musa halinsa ne shi mutum ne mai son yin alheri yana da wayewa don haka kada ta dauka da wata manufa ya ke zuwa kawo masu ziyara, sannan kuma kada ta damu sheikh Imam bazai ta6a sani ba. dakyar Benazir ta shawo kanta har ta hakura da komawa hostel ɗin, kusan kullum ne saita kira babanta a waya hakan ba karamin kwantar masa da hankalinsa ya ke yi ba, kuma duk in ya kira sai yayi mata nasihar daya saba yi mata, haka aunty laura ma suna yawan yin waya da ita, wasu lokuttan da dama tana son ta kira Yaya shureim amma idan ta tuna bai ta6a nemanta ba sai ta fasa saboda bata son ta zubda ajinta Sai dai taji labarinsa awurin Benazir idan tayi waya da shi wani lokacin Benazir tana bata wayar don ta gaisa da shi hakan ba karamin dadi yakeyi mata, haka itama Aneelerh silar Benazir ta san Yaya shureim har suka saba da shi, itama Aneelerh duk in zatayi waya da mami da Abie sai ta hadasu da aminnanta donsu gaisa ta haka suka ƙarfafa zumuncin su. har whatsapp group suka buɗe na sada zumunci da family dinsu harta baba Imam saida Aisha ta sanya shi aciki, Aneelerh ta saka abie da mami, itama Benazir ta sanya Alhaji ubaid da hajiya layla tare da dr shureim Wani irin zumunci mai karfi ne ya shiga tsakanin family din su duk time da suka hadu online fira suke sha ba kadan ba, har hotunansu suke tuttura masu. Duk idan suka samu hutun School Nigeria suke dawowa tun a airport family dinsu zasu harhadu domin tarbarsu har party Uncle musa Yake hada masu, idan hutu ya kare zasu koma germany har kuka sukeyi saboda basu son rabuwa da family din su. Akwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin sa'a suka kammala degree dinsu, duk da Benazir da Ummi sun riga Aneelerh kammalawa saboda ita nata course din almost 6 years ne medicine and surgery su kuma Business Administration ne shekaru uku ne, Amma saboda shakuwar da tayi da su yasa ta matsa lamba akan zata ajiye karatun saboda bata jin zata iya cigaba da zama a germany batare da su ba, tasan in suka gama tafiya zasuyi su barta, suma sun damu da hakan, a wani zuwa da Uncle musa yayi gidansu, Benazir ta same shi da maganar Aneeleerh, Sai cewa ya yi karsu damu, zai sa arage mata shekarun karatun ta ya koma daidai da nasu, sunyi matukar yin mamakin hakan, aikuwa sai gashi Ya yi mata hanyar da zasu kammala a shekara daya da ita, Amma duk da haka In ta dawo Nigeria sai ta kara karatu akan wanda tayi. Uncle musa yayi masu halaccin da bazasu taba mantawa da shi ba, Kyautatawarshi agare su bata misaltuwa, da Ayshah tana kokwanton dukiyar shi ganin yadda yake masu barin kudi kamar baisan wahalar nemansu ba, Benazir ce tayi brainwashing dinta, ta fayyace mata cewa kudinsa na Halal ne, babban Dan kasuwane kamar dai mahaifinta Alhaji Ubaid. ranar da zasu yi graduation celebration (bikin yaye dalibar) wanda shuwagabannin jami'ar ne suke daukar nauyin yin shi a cikin makarantar, gaba daya family din kowan nan su saida Ya hallara hatta sheikh Imam saida Yaje masu aiko Aisha tayi murnar ganin baba Imam, Ranar sunyi farin cikin da basu ta6a yin makamancinsa ba saboda Yadda yan uwa da abokan arziki suka dinga basu kyaututtuka da yi masu fatan Alkhairi arayuwa, aranar ne sukayi hotuna sosai, abunda yafi basu sha'awa Yadda Family dinsu suka hada kai kamar yan uwan juna, musamman Aisha tayi murna da ganin yadda ya yadda Shikeh Imam ya yarda da Abie din Aneelerh sun zama abokai, haka iyayen su mata sun hada kai sai zumunci suke sadawa a tsakanin su. (Bayan dawowarsu Nigeria, da sati biyu kacal) A yammacin wata rana Sheikh Imam Yana zaune akan Sofa dake a cikin katafaren Sitting room din gidansa, yana tsaka da karanta Jarida, daya daga Cikin security Officer na gidansa yayi masa sallama bayan ya amsa Ya isar da sakon Ana sallama da shi, bai motsa daga Inda yake ba ya tambaye sa wanene ke nemansa? Officer din yace Kanin makwabcin su ne Alhaji Musa, Shiru ya danyi jim aransa yana mai mamakin karfin Halin Alhaji musa da har ya iya takowa yazo gidansa neman shi, daga bisani yace ma Officer din ya shigo da shi. sallamar Alhaji musa ce ta katse zancen zucin nashi, dakyar ya sakar mashi fuska suka gaisa har ya taya shi murnar kammala karatun su Aisha, bayan sun yi shiru na dan lokaci kowa da abunda yake sakawa aranshi, daga bisani Alhaji musa yai gyaran murya ya ce"dama nazo ne don in nemi alfarma agurinka" bai jira jin ta bakin sheikh imam ba ya cigaba da cewa"Ina son ka bani auren Aisha, saboda ta kwanta min araina" wani kallo shiekh Imam ya watsa masa mai kama da harara. Tashin farko Yace"sai yau na tabbatar da baka da Hankali Musa, kai baka ji kunyar tunkarata ido da ido ka fadamin wannan maganar ba? an gaya maka ni mahaukacine da zan dauki ƴata mai daraja in hada ta da fasiƙin mutun, irin ka"? Maganar imam Ta sosa zuciyar Alhaji musa amma dayake shike nema agurinsa sai ya shanye bacin ransa, yace"bai kamata ka gaya min maganganun nan ba, wanda yace yana son naka ai masoyinka ne, saboda nasan mutuncinta shiyasa na tako nazo da kaina don in nemi aurenta agurin ka..." murmushin takaici Sheikh Imam yayi"Haba Musa, ko kayi zaton namanta wanene kai"? Ya fada tare da miƙewa daga kan kujerar da yake ya juya ya nufi bookshelves din dakin mai ɗauke da kundin dokoki dana tarihi, da sauransu. A cikin kundaddakin Ya curo Criminal record Na Alhaji Musa, Ya wurga masa akan kirjinsa, Kafin Ya dafe table din gabansa da tafukansa Ya soma magana Yana kallon Cikin idanunsa.. "Mara Kunya fitsararre, Sau nawa Muna yanke maka hukunci a kotu akan mugayen laifukan ka, amma da zarar kaje prison sai dai muji labarin ka fita, saboda kasan me ka taka kana da manyan mutanen da suke daure maka gindi, sune suke sama maka mafaka a kasar waje, shiyasa kake sheke ayarka" ya faɗa yana kallon Cikin idanun shi. "Tayaya har kake tunanin Ni Imam malik zan iya baka auren yata aisha bayan nasan Halinka ciki da bai? Musa kaine Dealer mai fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan, kai ne Cin zarafin mata masu rauni gurin tilasta masu don suyi karuwanci a kasashen waje, baka gajiya da keta haddin mata, last shari'ar da nayi akanka, yara masu talla kayi ma fyade sannan ka binne su da ransu don kada asirinka Ya tonu, cikin rashin sa'a aka samu wani bawan Allah dayaga lokacin da kake aikatan hakan harya kaika kara police station bayan sun gama bincike akanka suka mika ka kotu abun takaici bayan mun yanke maka hukuncin daya dace dakai mun tura ka prison sai dai muka ji labarin babu kai a kurkuku harma Ka gudu ka koma America da zama, saboda bakin zalincin ku, kai da ubayen gidan ka kuna amfani da haramtacciyar dukiyar da ku ka tara gurin toshe bakin shaidu da bawa jami'ae cin hanci...." Ya karashen maganar yana huci tamkar zai doke sa. Alhaji Musa ya sunkuyar da kansa kasa, ya dunkule yatsunsa, ransa ya baci matuka da jin maganganun da Sheikh Imam ke gaya masa saboda kawai ya nemi auren yarsa. "ka yi haƙuri ka nemi wata, amma sam ba ka cancanci ka mallaki aisha ba, nafi sha'awar ta auri mutun mai tsantsar ilmin addini musulunci, mai jin tsoron Allah, mai kuma kyawawan halaye da dabi'u wanda zai ruke min ita amana, Wallahi idan har na aura ma Aisha kai banyi mata adalci ba, Allah ma bazai barni ba saboda ita din amana ce agare ni"! yanayin fuskar Alhaji musane Ya canza ganin wahalar shi na niyar ta tashi abanza. Cikin kankai dakai yace"kada kayi min haka, wallahi inason Aisha itace mace ta farko da nayi burin in mallaka don mu raya sunnah, idan har don saboda halayena ne, nayi maka alkawarin zan shiryu in har zaka bani auren ta" cike da takaici Sheikh imam Yace"Oh har saina baka aurenta zaka shiryu! Ba zaka shiru don Tsoron mahaliccinka ba"? "Naji zan shiru saboda Allah, Kawai ni ka amince min in aure ta, komi ka ke so zan baka ina da tarin dukiya wanda zai ishemu muyi rayuwar mu" Da gadara yakeyi masa magana, Dariya sheikh imam yayi"Musa kenan, Kai abun duniya ya dama, ni dukiya bata agaba na, ban damu da kyalekyalen duniyar nan ba, wanda wata rana zaka mutu kabarsu ne, daga kai sai halinka za'a binne ka, sannan ka duba kaga gidan da nake rayuwa cikin rufin asirin Allah, babu abunda na nema na rasa don haka kadaina yi min bagu da dukiyar daka tara ta hanyar Haram.."! hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, abunka ga mutumin da bai ta6a neman abu ya rasa ba, babban takaicin shi yadda ya aje girman kansa da komai yazo don ya nemi auren ta amma Sheikh imam Ya watsa mashi kasa a ido. "Amma ai ka bari ita yar taka ta furta bata sona ko"? Ya fada tare da ɗage masa gira... Shiekh Imam Yace"Wallahi koda Aisha tana sonka ba zata aure ka ba! Balle ma nasan Jinina bazai ta6a kaunar fasiki irin ka ba, in sha Allah kaida Aisha sai dai hange daga nesa amma aure har abada, nayi fatan ma ace shureim ne yazo min da maganar auren ta, wallahi jiki na 6ari zan aura mata shi, saboda Ya cika duk wasu sharuddan da zan Iya mallaka masa Aisha..." cikin rauni na murya Uncle musa yace"da me shureim yafi ni? wasu sharuddane ya cika wanda ni ban cika su ba" Sheikh Imam Yace"ko ban fada maka ba, kai ka sani, shureim hafizi ne mai dumbin tarin ilmin addini, mutum mai tsoron Allah, mai koyi da sunnar manzon Allah SAW, ba kamar kai ba, daka sa duniya agaba...." wani irin zafin kishine Ya rufe idon Uncle musa, Yaji zafin maganar Shiekh Imam Ko sallama bai yi mashi ba Ya mike azafafe Ya fuce daga sitting room din. Bayan Uncle musa Ya koma gidan yayansa damuwa ta hana shi sukuni, Yana ji aransa in har bai mallaki aishaba har ransa zai iya rasawa, bakomai yake hadama ba face surar jikin ta.. Dayaga bashi da wata manufa sai ya yanke shawarar tunkarar Aisha don ya nemi soyayyarta, yasan in har ta amince mashi Shiekh imam bai isa Ya raba su ba, Har court zai iya kai shi ƙara. Da taimakon Aunty laura ta shirya mashi ranar da zaizo gidan donsu gana da aisha aranar shiekh Ya tafi gurin aikinsa. . Agarden suka zauna, tana asanye cikin dogon hijab dinta cikin girmamawa ta gaishe da Alhaji musa ta kara yi mashi godiya bisa ga kokarin da yayi akan karatunsu, yaji dadin tarbar da tayi masa har yaji aransa ba zata ta6a ƙin amsa bukatarsa ba. Cikin nutsuwa Uncle musa ya fayyace mata irin kaunar da yakeyi mata, tashin farko Aisha tace"kayi hakuri da amsar da zan baka, wallahi bawai bana sonka bane, kawai ban ta6a yi maka so daya shafi aure ba, Ina jinka kamar Uncle dina saboda zumuncin dake atsakanina da Benazir, amma ni inada wanda nakeso..." bata kare maganar ba Yai saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga nata hannu har saida tadan sha jinin jikin ta. "Karya kike kice bakisona, babu macen dana ta6a nuna inaso tayi rejecting dina, don haka kema akwai soyayyata acikin zuciyarki, idan ma kina jin kunyata ne to ki daina, ni ba Uncle dinki bane, ashirye nake da in aure ki, Aisha kiyi tunani akaina kafin ki yanke shawara, zan jira naji daga gare ki" yana fadan hakan yayi tafiyarsa, gaba daya tashiga halin damuwa kuma ta kasa sanarma kowa, hatta Benazir da Aneelerh basu san da maganar ba, kusan sau biyar Alhaji musa yana tuntubarta a waya don yaji in ta canza ra'ayi amma ta nace akan ita bazata iya auren shi ba, tana da wanda takeso, daya matsa mata akan ta fada masa wanene takeso sai tace mashi yaya shureim ne, a lokacin ji yayi kamar ya binne ta da ranta saboda bakin kishine da shi, ya ji zafin furta sunan shureim da tayi, zuciyarshi ta raya mashi cewar ba ra'ayinta bane Shiekh imam ne ya cusa mata nasa ra'ayin dama ya nuna yafi sha'awar ta auri shureim daga nan ne ya kuduri aniyar saiya shiga tsakanin su. Har gida yaje ya samu shureim Ya tambayesa meke a tsakaninsa da Aisha, dr shureim yace babu komai face mutunci, shi ya dauke ta kamar kanwarsa. Uncle musa yace bai yarda ba, in har yana son ta ya fada mashi zaiyi mashi hanyar auren ta, daya matsa mashi da tambaya kawai sai yace mishi eh yana sonta amma bai ta6a sanar da ita ba. Hankalin Uncle musa ba karamin tashi yayi ba, saboda ya fahimci dukan su suna son juna, kuma In har Shureim Ya furta yana son Aisha tofa babu makawa sai Sheikh imam Ya bashi ita. hakan yasa shi yanke shawarar komawa gurin imam malik don ya kara rokonsa akan ya bashi ita, kusan sau biyar yana zuwa gurin imam amma ya rufe ido akan bazai ta6a aura masa aisha ba, ta ko'ina babu sauki, har aunty laura yaba cin hanci na makudan kudi donta karkato da hankalin sheikh imam akansa amma duk abanza, itama aishar ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta amince da soyayyar shi akarshe sai tayi blocking duk wata hanya da zata haɗa ta da shi, hatta gidansu Benazir ta daina zuwa sai dai Benazir tazo gidansu ta same ta, ranshi ba karamin baci yayi ba, shi a ganin shi bata yi mashi halacci ba, kodan saboda dawainiyar da yayi dasu yaci ace ta saka mashi amma saita butulce dama shi baya abu dan Allah sai idan yasan zai samu riba. bayan wasu kwanaki Uncle musa ya ɗauke ƙafa da zuwa Gidan yayansa kwata kwata suka daina jin duriyarshi, da Benazir ta sanar da Aisha baya kasar Ba karamin dadi taji ba, kuma ta saki jiki ta cigaba da zuwa gidan, wani lokaci atare suke zuwa gidansu Aneelerh wani sa'in kuma Anila ce ke zuwa gidajen su ta kawo masu ziyara, har takaiga iyayen su na ziyartar junan su. Daga baya da soyayyar Aisha ta fara addabar Dr shureim har takaiga dakyar yake runtsawa saboda tunaninta, baya da burin daya wuce ya aureta, aranar daya shirya tunkararta don Ya fada mata irin kaunar da yake yi mata, A lokacin Aysha da Aneelerh sunzo Gidan su suna a dakin Benazir Suna fira, A bakin kofar dakin ya tsaya yana tunanin taya zai tunkareta da maganar? Zata kar6i tayin soyayyar shi ko kuwa? yana jin fargaban Aisha taki amincewa da shi shiyasama tuntuni yaki sanar da ita saboda fargaban amsar da zata ba shi. Har ya zaro waya daga Aljihu da niyar Ya kirata don ta fito su ke6e, kwatsam kunnuwansu suka jiyo mashi firar da su ke yi.. "Yanzu tun da mun kammala karatu me ya rage mana"? Benazir ce tayi tambayar. Aneelerh tace"Aiki da kuma Aure, amma Abie yace bazai bari in fara aiki a private hospital din daya buɗe min ba har sai na tsayar da miji" Benazir tace"Why not Ki ba Uzair damar ya turo da magabatansa? Tun da naga Jininku Ya haɗu da shi" Murmushi Anila tayi"Wai da Ke nake Jira, Idan Kinba Taj damar Ya tura da nasa magatan Gidan ku nima sai in ba Uzair Damar Ya tura gidan mu..." wani kallo mai kama da harara Benazir tayi mata.. "Pls mana ki amince masa nasan fa Kin mutu akan kaunarsa amma sai ki ta wani Ja mashi Aji" "hmmm nifa ba aji nake ja masa ba, Ina tunanin ta yadda zan tunkari mommy da wannan maganar, daddy baida matsala nasan zai amince min, amma mommy bansan ya zata dauki abunba kinsan Mommy bata son dan jarida sannan shi ba dan wani Hamshakin mai kudi bane..." Tun da suka fara magana Aisha bata tsoma baki ba, tayi shiru kamar hankalin ta baya akansu, har saida Benazir ta ɗan dafa kafadarta tukunna ta mai da hankali akansu. "Meke damunkine? Tun dazu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko baki ji abunda muke magana akai bane" Murmushi tayi"Naji mana, mamakine ya kamani, Naji kuna maganar Taj da Uzair su wanene su din? Yanzu duk kawancen mu daku ashe har akwai wani sirri naku da bansani ba"? Dariya su ka yi, Anila tace"Ay mana afwa Ustatha, ba haka bane, wlh mu ma bamu dade da sanin su ba, kin tuna ranar da muka fada maki zamuje shopping mall? One week da dawowarmu"? "Hakane na tuna, Ay ranar na fadamaku Uzirin daya hana ni fita" Benazir tace"toh A ranar muka hadu da su, kyawawan Samari kuma sun kwanta mana arai" Taya su murna tayi Allah ya sa su zama Alkhairi agare ku Suka amsa mata da ameen. Anila tace"pls muna so muji ra'ayinki, Donni bana so mu riga ki yin aure, nafi so yadda muke aminnan juna, Muyi aure atare ya'yan mu su taso a tare" Benazir tace"Aisha fa bata da matsala, Kinsan Allah yayi ta da farin jinin samari iri iri, attajiran masu kudi, Manyan Malamai sai ta zaba ta darje, Ko yau ta fidda miji baba Imam aurar da ita zaiyi Allah" ta fada tana dariya, Murmushin takaici malama Aisha tayi Cikin raunanniyar murya tace"Bazan boye maku ba, dani daku mun riga da mun zama daya, Munsan sirrin Juna, Wallahi bana alfahari da farin jinin da nake da shi, saboda mafi akasarin mazan da suke sona ba dan Allah bane sai don Surar Jikina, Wlh Benazir da wuya namiji yazo gurina da sunan soyayya batare daya neme ni ba, Ina jin bakin ciki da taikacin hakan, ni nasan zaiyi wuya asamu wanda zai soni dan Allah..." dakyar ta kare maganar saboda kukan daya ciyota, Kalamanta sun karya masu zuciya. Cikin shesshekar kuka tace"Inason Aure fiye da tunaninku, inaso in raya sunnar manzon Allah SAW amma taya zan samu wanda zai soni dan Allah"? Gaba daya tausayinta ne ya kamasu. Lallashinta suka somayi tare da kwantar mata da Hankali, su ka ce In sha Allah zasu tayata da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zaiso ta tsakani da Allah. Dr shureim dake a labe yana sauraronsu tun dayaji maganganun Aisha sai jikinsa yayi sanyi zuciyar shi ta karaya, Har Yaji shakkar furta Yana sonta saboda gudun kada tayi tunanin shima surar jikinta ya ke so. Bayan wani Lokaci, Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa kuma cikin sa'a ya shiga da kafar Dama, Arziƙin shi ya habbaka sosai, Rawar kai a wurin Hajiya layla har ba'a fada, dama ta jima tana cusa mashi ra'ayin ta akan ya shiga siyasa saboda taga yadda Alhaji musa ke fantama da dukiya abunda take ma kwadayi kenan, dama arayuwarta ta tsani taga Alhaji musa yafi Alhaji Ubaid Arziƙi tana jin haushin hakan sosai. Dr shureim ya so ya kalubalanci siyasar da mahaifinsa ya shiga, Amma Hajiya layla ta take mashi burki ta hana shi magana adole yaja baki yayi shiru. Alhaji musane yayi mashi hanyar da ya shiga Jam'iyarsu, a Karon farkon da Jam'iyar JDP ta tsayar da shi a matsayin Dan takararsu Na Gomna sunyi murnar da bazata Misaltu ba. Saboda Farin Cikin hakan yasa Hajiya Layla ta shirya masu gagarumin Party don taya Alhaji Ubaid murnar takarar da aka tsayar da shi da kumayi mashi fatan Alkhairi. Kafin Shigarshi siyasa saida ya fara tuntubar Shiekh Imam don ya bashi shawara, Sheikh yace shi bazai hana shi yin siyasa ba amma da zai bashi shawara yacigaba da kasuwancinshi sai yafi zama alkhairi a gare shi, saboda yawancin yan siyasa sai sun kauce hanya suke samun mulki, Nasiha sosai yayi mashi har yace ya dauki shawarar shi amma daga baya sheikh imam sai dai yaji labari agurin mutane cewa Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa yayi mamaki sosai saboda bai ta6a bashi shawara bai dauka ba sai a wannan karan, abun daya kara ɗaure mashi kai, ɗauke kafa da Alhaji Ubaid yai kwata kwata ya daina shigowa donsu gaisa sai in sun hadu a masallaci, daya fahimci kaukaucewar da yakeyi masa sai ya kyale shi don ya gano baya son ya hana shi yin siyasa shiyasa ya janye jiki da shi. Lokacin da Celebration din Ya matso, Hajiya Layla ta gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayasu Murna, daga cikin wadanda ta gayyata hada Aunty Laura, Benazir kuma ta gayyaci Anila da malama Aisha, koda Aisha ta nemi izni agurin baba Imam yace bai amince taje party ba saboda yahudancine babu shi a addinance, bata ta6a musa masa ba sai akan maganar Party din nan, ta dinga rokonshi akan yabarta taje saboda ta yi ma Benazir alkawarin za ta je, In har ba ta je ba Benazir ba za ta ji dadi ba, Shiekh imam Yace tayi hakuri kawai, don bazai ta6a bari taje ba, wunin ranar kwata kwata babu walwala akan fuskarta, Har Aunty laura ta roka akan ta nema mata alfarma agurinsa aunty laura tace ita bazata sanya masu baki ba, saboda an nuna mata iyakarta don haka suje can su karata ita da uban nata, abunda yasa tace haka saboda taji haushin bukulun da shiekh imam yayi mata akan kudin da Alhaji musa yayi mata alkawarin zai bata intaja hankalin imam da Aisha suka amince da auranshi amma gaba daya suka watsa mata ƙasa a ido abun ya kona ranta. Ana i gobe za'ayi partyn, Tafiya ta kama sheikh Imam malik, manyan abokansa wadanda suka kasance shahararrun malaman addinin Islam yan kasar sudan dayake acan yayi karatu lokacin daya zauna gurin Kawunsa, abokanne suka gayyace shi wani taron karrama malamai da za'a gabatar a kasar sudan, kafin tafiyarshi saida ya kira Aisha ya kara gargadinta akan bai lamunta taje partyn nan ba, tace mashi toh in sha Allah bazata je ba, bayan tafiyarsa Aunty laura tace ma Aisha ay yanzu tunda mai gadin nata bayanan, sai ta shirya ta tafi tace ta fasa zuwa saboda batason ta sa6ama mahaifinta, bata matsa mata ba amma da Alhaji musa Ya kira ta waya yace mata yana son Aisha ta halarci Partyn in har tasa tazo zai bata Dala dubu goma sha biyar, Jiki na 6ari Aunty laura taje har dakin Aisha ta tunzurata akan ta shirya su tafi, baiwar Allah duk yadda taso ta hana zuciyarta bijirema mahaifinta saida takasa saboda tana son zuwa itama. Wuraren ƙarfe biyar na marece dai dai, suka shigo gidan Alhaji Ubaid, Aunty Laura ta dauki wankan shadda, Ta coge daurin dan kwalin ture kaga tsira, Ita dai Aisha Abayane a jikin ta doguwa har kasa, sai nikab din da ta sanya. Anan suka iske manyan bakin su Hajiya layla, babu masaka tsinke, Yan uwa da abokan arziki duk sun hallara a katafaren garden din gidan da aka kawata shi da kayan ado da kujerun da baki zasu zauna an tanadi duk wani abu da baki zasu bukata don jin dadin su, Ga mawaka da Maroka sun Cika gidan sai kaɗe kaɗe sukeyi da yan raye raye. Tunda suka shigo gidan gaban Aisha keta faduwa rass rass, kwata kwata hankalinta ba akwance yake ba, duk sai taji ba dadi saboda ta sabawa mahaifinta. Lokacin da ta lula duniyar tunani Yayin da Aunty laura ta shige Cikin mutane tabarta. Sam bata ji takun mutun ba, sai dai taji an rungumeta, har firgita saida tayi amma da taga Benazir ce sai ta sauke ajiyar zuciya, cike da farin Ciki suke kallon juna, Banezir ta ɗauki wankan tsadadden leshi ko arzikin dan kwali babu akanta.. "Amma wallahi naji dadin zuwanki Aminiyar, har na fara fidda rai, ashe zakizo, ya ki ke ya baba imam? Cikin sanyin murya tace"baba bayanan ya tafi sudan, atare da aunty laura mukazo" ruko hannun ta Benazir tayi "mu shiga ciki, ki gaishe da Uncle Musa, tun Shekaran Jiya ya dawo Nigeria, tare da matar daya aura baturiya, amma baizo da ita nan ba, acan gidansa na Abuja yabarta, bai sanar da kowa game da auransa ba sai dai muka ji abakinsa jiya daya zo" tun da Benazir ta fara surutu Hankalinta ba akwance yake ba, wani irin faduwar gaba taji jin ta ambaci sunan Uncle musa fuskarta babu walwala tace"kina nufin Uncle musa yana acikin gidan nan"? Jinjina mata kai tay"eh," tace toh tabari da anjima in an gama partyn sai suje su gaida shi, Benazir ta amsa da toh, damuwace karara Akan fuskarta, Benazir bata lura da halin da take a ciki ba. bayan sun shiga falo ta iska kawayen Benazir Hada Anila kowaccen su ta dauki wanka na mutunci Aneelerh na ganinta cikin sauri taje ta rungumota, Sauran kawayan Benazir sai murna suke yi Aisha bintu imam tazo, har rige rigen daukar hotuna sukeyi da ita, baiwar Allah tadinga kakkauce masu saboda gudun kada baba Imam yaga hotanta agurin partyn daya hana ta zuwa, Aneelerh ce ta lura da yanayinta hakan yasa taja ta gefe daya ta tambayeta meke damunta? Bata boye mata komai ba ta sanar da ita, ta kara da cewa ita kawai hankalinta bai kwanta ba, tana ji aranta kamar wani abu zai faru, cikin sigar lallashi Aneelerh ta soma kwantar mata da hankalinta har saida taga ta saki jiki... tun da aka fara gabatar da shagalin hankalin Aisha ba kwance Yake ba, ga kawayen Benazir sai cashewa suke yi suna tikar rawa ga abinci kala kala ko kadan batay sha'awar ci ba. Tana zaune kan kujera Wayarta ta fara ringing, tayi picking tare da karawa kan kunnanta Muryar shureim Taji yana fadin ta same shi a upstairs yana son yin magana da ita" Bata kawo komai aranta ba, ta yi azan zai bayyana mata soyayyar shi ne Hakan yasa ta mike batare da sanin kowaba Ta nufi upstairs, abakin kofar dakin dataga takalmansa tayi knocking ana bude kofar dakin aka janyota ta fado ciki, a firgice ta dago don taga wanene rass taji gabanta Ya fadi ganin Alhaji musa atsaye fuskarsa babu annuri daga shi sai short a jikin shi, wani irin faduwar gaba taji, da tsantsar mamaki ta furta"uncle kaine"? Daga mata gira yayi"nine Aisha.."arude tace"amma yaya shureim ne Ya kira ni, yana ina" "Ni ne nayi muryarsa, saboda nasan idan kikaji ni ke kiranki ba zuwa zaki yi ba" matsawa yayi dab da ita tayi saurin ja da baya cikin sanyin murya yace"aisha, inaso ki dubeni daga kasa har sama ki fadamin me Allah ya rageni da shi"? Kawar da kanta gefe tayi muryarta na rawa tace"bakomai" "In har hakane meyasa baki sona?.. "Saboda bakai nake so ba,"runtse idanun shi yayi saboda jin zafin maganar shi "Aisha idan kikai min hakan baki min adalci ba, kin hana zuciyata sukuni saboda ke na kashe makudan kudi donki samu rayuwa mai kyau, Harta karatun da kukayi a germany nine na dauki nauyin shi ba Alhaji Ubaid ba, kawai nayi amfani da shi ne saboda nasan Halin mahaifinki da tsautsauran ra'ayi ba lallai in yaji nine nayi hakan Ya amince kije ba, kuma nayi hakanne saboda in dinga samun ganinki akai akai, saboda Imam bazai bari ina zuwa zance gurin ki ba, amma da kuna karatu a germany ba karamin morewa nayi ba saboda ina ganinki a duk lokacin dana so" Hankali atashe tace"Dama duk dawainiyar da kayi mana a germany ba dan Allah kayi ba? saboda son da kake min ne" jinjina mata kai yayi... "Wallahi da ace nasan kaine ka dauki nauyin karatunmu a kasar germany, da ba abunda zaisa inje" tana fada ta juya zata fuce yayi saurin ruƙo qugunta da tafin hannun shi ya janyota da karfi ta faɗo kan kirjin shi, ya soma matsa mazaunanta yana sakin nishi, For the first da ta fara hada jikinta da namijin daba muharramin ta ba, rai a6ace ta banbare jikinta daga nashi ta daddage ta wanka mashi zazzafan mari ji kake fasss!. dafe kuncinsa yayi da tafinsa, idanunsa suka kada jawur cike da bacin rai yace"ni kika mara"? Tana haki tace kadan ka gani, Nan gaba idan ka kara gigin ta6a jikina wallahi saina yi maka abunda har abada ba zaka manta ba, dama ba don Allah kakeso na ba, sai don wata mummunar manufa taka" tana fada ta buɗe kofa ta fuce... Tun da yake wani dan adam bai ta6a daga hannu ya maresa ba sai akan Aisha, yaji zafin marin nan adaddafe Ya fada kan gadon shi yana juyi, ransa ya baci matuƙa jikin shi har gumi yake zubdawa. abangaren malama Aisha bayan fitarta daga dakin a jikin bango ta Jingina bayanta, fuskarta sharkaf da hawaye taji takaicin rungumar da Uncle musa yayi mata, kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta ke ji, Ya dasa mata kiyayyarsa a cikin zuciyarta. Tana cikin tafiya wani irin ciwon mara Ya turnuke ta, da sauri ta dafe cikinta da tafin hannunta, sam takasa cigaba da tafiya a nan ta durkushe tana faman fitar da huci... Adai dai lokacin dr shureim Ya hauro Upstairs din domin amsa kiran da Uncle Musa yayi ma shi, Yana ganinta Jikinshi na rawa ya karaso gurinta Yana tambayarta meke damunta? muryarta na rawa ta furta"cikina yaya shureim ciwo yake min, ka taimaka ka maida ni gida" ganin halin da take a ciki yasa shi ruko hannunta, ya taimaka mata ta miƙe suka sauko down, A lokacin babu kowa a falon gaba daya sun Koma garden can inda akeyin shagalin. Har suka fito harabar gidan basu ci karo da kowa ba. Sai nishi takeyi tana jan numfashi, dr shureim sai sannu yakeyi mata har suka karaso Cikin Gidan Imam, Ya tambayeta tana da maganin ciwon cikinne ko yaje ya siyo mata ne? Dakyar ta bude baki tace mashi bata da shi ya kare" Cikin sauri Dr shureim Ya fita Ya nufi chemist din dake a kusa da su don ya siyo mata maganin, tausayinta duk ya kama shi.. Lokacin daya dawo gidan hannun shi ruke da leda ta maganin daya siyo mata, a bakin kofar falo yai ta ƙwala sallama shiru bata amsa mashi ba, Kuma Yan aikin gidan duk basa a kusa, wayar sa ya zaro ya danna mata call tana fara ringing, tayi picking yanayin yadda yaji Muryarta ba karamin ɗaga masa hankali tayi ba. Cikin shesshekar kuka take fadin"ya shureim mutuwa zanyi, ka taimaka min, " adabarbarce ya furta"Aisha kina ina ne? Ga maganin na kawo maki" shiru yaji bata amsa mashi ba, a rude Ya mike Ya soma neman bedroom dinta saboda bai taba shiga dakinta ba, duk zuwan da zaiyi gidan A falo ya ke tsayawa. Dakyar ya gano bedroom dinta, saboda tsabar rudu ya afka Ciki, a kwance ya taras da ita tsakiyar gadonta, sai juyi takeyi tana murkususu, tafukan hannayenta adaddafe da mararta, sam babu abaya ajikinta zafin daya taso matane yasa ta cireta cikin fitar hayyaci batare da saninta ba, sai Camisole data rage a jikinta shara shara gaba daya surar jikinta ta bayyana muraran. Bai kula ba saboda hankalinsa ba akwance yake ba burinsa kawai ya taimake ta, Aje maganin yai akan bedside drawer Ya fito da sauri jim kadan ya dawo hannun shi ruke da bottle water Ya zauna daga gefen gadon.. Sai da Ya ballo kwayar maganin Ya juyo don ya taimaka mata tasha, kwatsam Idanun shi suka sauka akan Santala santalan Cinyoyinta lokaci ɗaya tunanin shi ya gushe, ya fara jin wata irin matsananciyar sha'awa na taso mashi kamar ransa zai fita, Zuciyarshi ta dinga azalzalarshi kanshi ya fara juya mashi kamar hankalinshi na barin jikinshi, Bawan Allah a lokacin yaita kokari kaucewa sharrin shaidan amma abun Yaci tura saboda yadda surar ummi ke fusgarsa har baisan sa'adda Ya afka mata ba, ga zafin ciwo tana fama da shi a haka dr shureim ya keta mata haddi, taji radadin da bazai misaltu ba, cikin fitar hayyaci ta dinga Sakin kukan azaba, tana yi masa magiya akan ya kyale ta, kada ya kashe ta, kada ya rabata da mutuncinta, amma duk abanza saboda a lokacin shureim yayi nisan da baya jin kira. Ya Ilahi! *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~<><><><><><><><><><><><><><>✍️~ ~___________________________________~ Bata tashi farkawa ba, sai Bayan sallar Magrib, bakinta dauke da sunan Allah, tana kokarin motsawa don ta miƙe taji wani azababben zafi agabanta, ga wata kasala data baibaye sassan jikinta, tunani to soma yi meya faru da ita? A ina take"? jin iska na ratsa jikinta yasa tay saurin shafa jikin nata, lokaci daya gabanta Ya soma faduwa jin babu sutura a jikinta cikin sauri ta yunkura ta miƙe zaune, tana kallon kanta kafin ta yi saurin kallon gefenta, shureim ta gani a kwance kan gadon batare da sutura a jikin shi ba, sai dan bargon daya lullu6e ass dinsa, sam ta kasa tuna komai amma tabbas taji a jikinta raping ɗinta yayi Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ana zare ranta, Koken da ta ke yi ne ya farkar da shi, a firgice ya bude idanun shi da suka kada jawur ya dube ta da su, baiyi aune ba yaji saukar zazzafan mari kan kuncinsa ta shaƙe wuyanshi tana kuka ta furta"nashiga uku! yaya shureim ka kashe min rayuwata, ka gama dani! Ka wulakanta martabar jikina ka goga min ƙazantar Zina, Allah Ya isa tsakanina da kai, bazan ta6a yafe maka ba..." zafafan hawayene suka wanke fuskarshi kwata kwata baiji zafin marin da tayi mashi ba saboda ruɗun da kwakwalwarsa ta shiga gaba daya yabi ya rikice yana kokarin tariyo abunda ya aikata mata, saboda baya a cikin hayyacinsa komai ya faru, wlh ko a mafarki bai ta6a sha'awar ya kusanci macen da ba muharramarsa ta aure ba, balle Aisha da yake yi mata kallon kanwarsa, tana kuka Yana kuka Yace"Aisha bayin kaina bane, ba halina bane aisha, ke shaidace akaina, wlh ni ba mazinaci bane..." bai ƙare maganarba ta Fasa tsawa tana huci tace "babu abunda zaka fada min ya shureim, wlh sai Allah yayi min sakayya, da kasan irin burin da nake dashi akanka da ba kai yi min haka ba, da tunfarko ka fadamin kana son Jikina, Ni mai iya aurenka ce don in dinga biya maka bukatarka saboda son da nake maka, amma ka rasa ta hanyar da zaka neme ni sai ta hanyar Zina"? Tana magana Jikinta na kerma, Idanunta sun kada jawur kamar an watsa mata barkono. Cikin disasshiyar murya tace "ka karyamin zuciyata yaya shureim, ka cuceni, ka zalunce ni, Inayi maka kallon mutun mai tsoron Allah, ashe kaima fasiki ne, kana daya daga cikin mazan da basa son mace don Allah sai don surar jikin ta, kaja mun aikata zunubi, Yanzu da wani ido kakeso In kalli Babana, da mutanan da sukeyi min kallon mutuniyar kirki! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." duk yadda yaso ya shawo kanta ya kasa, taki ta saurareshi balle ta fahimce shi, saukowa tayi daga kan gadon jikinta duk ba kwari dakyar ta mayar da rigarta da gudu ta shuge toilet tana kuka ta kulle kofar, tabar shureim a zaune kan gadonta yana ta kuka kamar karamin yaro, sau uku yana marin kanshi saboda bakin ciki da takaicin abunda ya aikata ma Aisha, Matar da yayi burin ya aura. "Ya Allah ba halina bane, Kafi kowa sanin bawan nan naka, Ni maijin tsoronka ne mai gudun saba maka ne, kullum ina rokonka akan ka kareni daga sharrin zuciya da sharrin shedan amma meyasa Hakan ta faru dani? Meyasa na aikata ma Aisha haka"?... Cikin shesshekar kuka yajiyo muryarta daga cikin toilet tana fadin"Yaya shureim ka tashi ka tafi tunkafin Aunty laura ta dawo".. Jiki asanyaye Ya sauko daga kan gadon Cike da danasani Ya mayar da suturarsa, Wlh Yaji kunya mara misaltuwa, Yaji radadin da har yau In ya tuna sai yaji ɗaci aran shi. ______________________________________✍️ Lokacin da su Benazir suka lura babu malama Aysha a gurin partyn nanfa hankalinsu ya tashi suka dinga nemanta sako da lungu na gidan, har layin wayarta suka kira akashe. Hankalin su atashe suka tuntu6i Aunty Laura da maganar, tace kada su damu, ta koma gida dama bada son ranta tazo ba, bayan Kammala partyn suka biyo Aunty Laura gidan don suga idan ta dawo, bayan sun shigo gidan suka Nufi dakinta, adatse suka iske kofar, Knocking su ka yi tare da ambaton sunanta, Tana jinsu tayi shiru bata amsa masu ba, har saida suka fara gajiya da bubbuga kofar su ka fara tunanin ko bata nan ne. A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga kiran ta ya shigo layin Benazir, cikin sauri Benazir tayi picking up tana tambayar ina ta shiga ne? Suna ta neman ta. Cikin raunanniyar murya Aysha tace kada su damu, tana acikin dakin, ta kwanta ne saboda bata jin dadin jikinta amma da sauki. Cike da tausayinta Benazir tayi mata sannu da jiki kafin ta mika ma Anila itama tayi mata sannu. Daga bisani su ka yi wa Aunty Laura sallama suka tafi, zuciyoyinsu cike fal da tunanin yanayin da sukaji Muryar Aisha. Tun daga Ranar Aisha ta ɗauke Kafa da zuwa gidan aminnanta, Babu wanda yasan abunda ya faru tsakaninta da dr shureim, ita kadai tayi ta nukunuku ta ki yarda Aunty laura ta gane halin da take a ciki, saboda bata son kowa ya sani ta fiso ta rufawa kanta asiri. Tsawon kwana uku bata bude wayarta ba, baci ba sha, ba bacci, ta killace kanta adaki, wani irin depression ne Ya kamata ga ciwon rabin kai da take fama da shi, In ta fara kuka har sai hawayenta sun kafe tukunna take dakatawa, kusan kwana ta ke yi tana yin istigfari tare da kai kukanta gurin Allah. Saboda tayi imanin shi kadai ne zai kawo mata mafita, Hankalin Aunty laura ba karamin tashi yayi ba, ganin Aisha na neman ta halaka kanta, Ta rasa gane meke damunta gaba daya ta hana kanta sukuni, ta rame tayi duhu, idanunta kullum a kumbure suke saboda kukan da take sha, ba irin magiyar da batayi mata ba akan ta faɗa mata meke damunta amma taki sanar da ita, sai dai tace ta tayata da addu'a Allah ya yaye mata abunda ke damunta, tace toh In sha Allah zatayi mata addu'a. Idan muka koma bangaren Dr shureim tun washe garin ranar da abun Ya faru, Yabar Kasar, Ya tafi Egypt saboda bazai Iya cigaba da jurar zama yana ganin Aisha da abun kunyar daya aikata mata ba. Bayan makonni da afkuwar Lamarin, Sheikh Imam Ya dawo Nigeria, Bayan ya huce Gajiya a dakinsa, Aunty laura ta jera mashi abincin shi akan rug din dakinsa, Kasa cin abincin yayi saboda faduwar da gaban shi keyi, kuma yaji shiru Aisha bata leko ta yi mashi sannu da zuwa ba, kamar yadda ta saba yi mashi. "Ina mamana? Ko taje islamiya ne, Aunty laura tace aa tana adaki Yace ta kira ma shi ita. Fitowa tayi daga dakin ta shiga dakin Aisha, tayi mamakin ganinta a kudundune cikin bargo jikinta sai kerma yakeyi kamar wadda sanyi ya kama. Hankali atashe Aunty Laura ta haye kan gadon tare da yaye bargon, gabanta ne ya fadi rass, ganin yadda idanun Aisha suka juye, tsabar zafin da jikinta ya dauka tamkar naman da aka gasa da wuta, arude Aunty laura ta zabga salati Ta watso aguje ta nufi dakin sheikh Imam Ta sanar da shi halin da Aisha take aciki, abincin da bai ci ba kenan, jikinshi na 6ari yabiyo bayan Aunty laura suka nufi dakin Aisha, Suna shiga suka taras da Amai na fita daga bakinta. "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" arude Sheikh Imam Ya furta, baiyi wata wata ba, Ya sungumi Aisha Ya fuce da ita da gudu Laura tabi bayanshi, Suka shiga mota. Kaitsaye Suka Nufi Asibiti da ita, aranar saida aka kwantar da ita saboda jikinta yayi tsauri. A asibitin suka kwana, Sheikh Imam bai runtsa ba, Yadda Ya ga rana haka yaga dare, har fada saida yayi ma Aunty Laura akan sakacinta na rashin kula da Aisha, gaya nan har ciwo yakamata batare da ita ta sani ba, Aunty laura dai sai hakuri take bashi tace ba laifin ta bane, nan ta fayyace masa halin da Aisha ta shiga bayan tafiyarsa, ta kara da cewa ba irin magiyar da banyi mata ba akan ta fadamin meke damunta amma takiya sai dai tace Intaya da addu'a, Sheikh Imam ya damu sosai, Babban abunda ya kara daga masa hankali ramewar da tayi, kamar ba Aisharsa ba. Basu sanar da kowa game da ciwonta ba, a duk lokacin da su Benazir suka kira Aunty Laura su kai mata korafin sun kira layin Aisha basa samu sai tace masu su yi hakuri ayyuka ne su ka yi mata yawa, kwanansu ɗaya a asibitin baci ba sha saboda damuwar Halin da Aisha take a ciki, Bayan dr din dake kula da Aisha ta gama bincikenta akan lafiyarta, ta kira Sheikh imam don suyi magana acikin Office din ta. Bayan sun shigane Dr din Ta dube shi dakyau fuskarta da damuwa tace"Sheikh, naji dadi da Ya kasance Ni Ce amintacciyar Likitar dake duba Iyalanka, Saboda kai malamina ne, ni kuma dalibarka ce, ni me rufa maka asiri ce don kare martabarka" Cike da gamsuwa sheikh Imam Ya jinjina mata kai da alamun rudu akan fuskarsa. Takardar dake a hannunta ta miƙa masa jiki asanyaye ya kar6a har zai buɗe muryar Dr din ta katse shi. "Sakamakon gwajin da mukayi ma Aisha ne" A hankali Ya soma karanta sakamakon, abun mamaki sai taga yana dariya maimakon taga tashin hankali akan Fuskarshi don ta san muddin Ya karanta sai Hankalinsa ya tashi ba kadan ba. "Sheikh Lafiya naga kana dariya" mika mata takardar yayi"Ki duba dakyau, wannan sakamakon bana Aisha bane, watakil kunyi mistake ne, Aisha da bata da aure, Ina ita Ina ciki"? Ya fada da murmushi akan fuskarta, Idanun Dr dinne suka cicciko tab da kwalla saboda tsananin tausayin shi daya kamata. "Dan Allah, Ki bani na Aishana inaso in san meke damunta, wannan kuma ku nemo mai shi ku bata, kada asamu matsala..." girgiza kai Dr din tayi cikin rauni na murya tace"Kayi hakuri Sheikh, kai malamine nasan kayi imani da Allah ka kuma yi imani da kaddara, wlh result din Aisha ne, Tana dauke da juna biyu, Nima dana ga sakamakon saida na karyata kaina saboda nasan Aisha bata da aure, sannan Aisha kamilar macace, amma dana zurfafa bincike na sai na gano dagaske Cikine a jikin ta...." bata ƙare maganarba sakamakon Tsawar da Sheikh Imam Ya doka mata tamkar zai fasa dodon kunnanta, Tuni tasha jinin jikin ta. Yana Huci Ya furta"Kin bani mamaki dr Husaina, kin kuma ji kunya wlh, baki taba yi min karya ba sai yau, wannan sakamakon da kika nuna min bana Aishana bane, mamana bazata taba aikata zina Ba, Ƴata kamila ce, mai jin tsoron Allah bazata taba aikata abunda zai sabawa Mahaliccin ta ba, Na yarda da ƴata Aisha bazata ta6a ruke koda hannun Namijin daba muharraminta bane, don haka ki gaggauta janye kazafin da kike kokarin yi mata, watakil biyanki akayi don kiyi mata ƙazafi, dama akwai masu jin haushin daukakar da Allah yayi mata watakil kema kina daga cikin su...' kwata kwata Dr husaina bataji haushin kalaman Shiekh Imam ba, sai ma tausayin shi daya ƙara kamata. Kekketa Takardar yayi, Tare da watsa pieces din saman table din gabanta, Ya juya afusa ce Yabar Office. Yana tafiya Visitors dake zarya acikin asibitin sai kallon shi sukeyi ganin Sheikh Imam wasu har gaishe da shi sukeyi amma bai kula su ba, Yana shiga dakin da aka kwantar da Aisha Ya iske Aunty laura zaune kan kujerar dake a gefen gadon ta zabga uban tagumi.. Tana jin motsin shigowarshi ta mike tana tambayarshi me dr tace. Rai a6ace yace"ba zamu cigaba da zama acikin asibitin nan ba, Gida zamu tafi inyaso sai muyi jinyarta acan" "Amma ba'a sallame mu ba, kuma jikin nata har yanzu da sauranshi..." bata ƙare maganar ba, Ya daka Mata tsawa"Ki ruko Aisha mu tafi" jikinta na bari ta taimaka ma Aisha ta mike baiwar Allah ko tafiya bata iyayi sai layi take kamar zata kife ƙasa a haka suka shiga mota da ita. Bayan sun dawo gida Aunty Laura Ta matsa mashi akan ya faɗa mata me doc Husaina tace akan ciwon Aisha Nan ya kwashe komai da suka tattauna ya sanar da ita, itama a lokacin biye mashi tayi suka karyata maganar Dr husaina. Cikin da laulayi ya zo ma Aisha, bakar wahala take sha, wani sa'in tana a kwance kan gado take fara kwarara amai ta sauko da gudu ta fada toilet ta karasa shi acan. Gashi kullum Cikin yin zazzabi takeyi, daga bayane Aunty Laura ta gano Ciki ne da ita, Bazan Iya misalta tashin hankalin da Aunty Laura ta shiga ba, a daki ta same ta kwance kan gado tace taji tsoron Allah ta fada mata gaskiya! Akwai ciki jikinta ko babu? saboda ta fara kokwanto akan yanayin ta, Kafin ta sanar da ita saida ta fara rokonta akan karta fada ma baba Imam tabarshi a matsayin sirri atsakaninsu duk da tasan watarana dole ne Yaji, Aunty laura tace tayi mata alkawarin bazai taba ji abakinta ba. Anan ta labarta mata komai daya faru tsakaninta da shureim, a lokacin Aunty Laura ta zabga salati tana sallallami, Jikinta Ya kama bari Saboda razanar da tayi, ta girgiza ba kadan ba, musamman dataji cewa Shureim ne yayi mata aika aikar, Babban tashin hankalinta Idan Sheikh Imam Ya gano Cikin ne dagaske, to fa itace mutun tafarko da zai fara tuhuma saboda ita ta matsa ma Aisha akan suje Partyn. Aunty Laura tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda tausayin Aisha daya kamata, Yarinya Kamila da ita an zubar mata da mutuncin ta, dr shureim Yasha tsinuwa agurin Aunty laura, tace dan iska munafuki mai fuska biyu, kamar Na Allah, In sha Allahu sai yaga sakayyar abunda yayi mata, daga bisani ta lallashi Aisha taja ta ajiki sosai, ta dinga bata hakuri hadi dayi mata nasiha har hakuri ta bata akan Tursasa matan da tayi akan taje, gani take ma kamar itace Silar komai daya faru da Aisha. A haka aka cigaba da rayuwa, Har Ila Yau sheikh Imam yaki yarda cewa Aisha ciki gare ta, wani'sa'in agaban shi zatayi amai amma ko kadan bai yarda ya zargeta da ciki ba, Iya bakin gwargwado tana samun kyakkyawar kulawa agurin Baba Imam, baya barinta cikin damuwa, Ya hana a kaita asibiti kuma Ya hana dr Husaina zuwa agidan, Ko tazo da niyar duba Aisha tun daga bakin gate security Officers ke korarta. lamarin ya daure mata kai, ita burinta kawai ta taimaka ma sheikh Imam su nemi mafita gudun kada kimarshi ta zube sai dai Yaki bata damar ganawa da shi, Har court taje ta same shi a office dinshi Amma Yaki sauraronta, badan taso ba tahakura da bibiyar shi. Saboda zullumi da fargaban abunda zai biyo baya In sheikh Ya san Aisha tana da ciki, yasa Aunty Laura ta rame, kamar mai fama da zazzabi har saida sheikh Imam Ya lura da canjin da tayi, ko da ya tambayeta meke damunta sai tace mashi Ciwon aisha shine silar damuwarta, hakuri kawai yake ba. Dubarace ta fado mata arai, ta sami Aisha da zancen su zubda Cikin kawai, Aisha tace bazata iya ba, bata son ta kuma aikata wani zunubin na kisan kai bayan wanda suka aikata, ita bazata iya kashe rai ba, laifin da shureim ya aikata mata bazai shafi abun dake a Cikin ta ba. Aunty laura taita kokarin tunzurata don ta amince asamu arufawa kai asiri amma Aisha ta yi kunnan Uwar shegu da maganarta, ganin tasa kafiya yasa Aunty laura ta dinga zuba mata maganin zubar da ciki aboye take barbada mata shi cikin abinci ko cikin abun sha, sai dai wani Iko Na Allah tun da tasoma yunkurin 6arar mata da ciki Allah bai nufa ba, saima kara lafiya da ta ke yi. Lokacin Da Cikin Yakai wata Biyar, Ya fara bayyana a jikinta, daga ka kalle ta zaka gane tana da ciki Amma sheikh Imam Ya kasa Yarda Ciki ne saima yace ture akai mata, Ajiyar Aljanu ce, haka ya dinga banka mata ruwan addu'o'i tana sha, In zataci abinci sai ya tofe shi da addu'a in zata kwanta bacci sai ya shigo har daki gaban gadonta yayi mata addu'a, Zuciyar Aisha ta karaya da ganin irin Yardar da mahaifinta yayi da ita, shiyasa ta kasa buɗe baki ta furta mashi Ciki ne a jikin ta, sai dai in suna atare yanayi mata addu'a ko yana bata abinci abaki, tayi ta zubar da hawaye tana kallon shi, ya dinga lallashinta yana fadin mamana kiyi hakuri Allah yana tare da bayinsa masu Hakuri, ki jure ki cinye jarabawar nan, In sha Allah koma wanene yake nemanki da sharri kanshi zai koma, mutanene ba Allah aransu bakin ciki da hassada sunyi yawa azukatan mutane. Wani sa'in in yanayi mata maganar sai ta dinga Yunkurin buɗe baki don ta fada mashi gaskiya amma sai ta kasa, In Aunty laura na akusa taga tana kokarin fada masa sai tayi saurin janye hankalin shi da tunanin wani abun. Saboda Lalurar Aisha Yasa Sheikh Imam Ya hana ta fita ko kofar falo bata leƙawa, saboda baison wani yaga Aljiyar da aljanu sukayi mata a zargi ciki ne, duk wanda yazo nemanta gida sai dai suce mashi bata nan tayi Tafiya Sudan gidan Kawunta, babu wanda yasan Aisha tana agida har su Benazir. Daliban Aisha na islamiya, Da abokananta malamai da duk wani mai sauraren wa'azinta sai da ya damu da rashin ganin Aisha, saboda Allah yayi ta da farin jinin mutane suna son Aisha. A kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin Aisha Ya Cika wata tara Cuf, tashi dakyar zama dakyar haka ta ke fama, a daren wata ranar Juma'a ne nakuda ta kamata, Aunty Laura ta matsa akai ta Asibiti ganin yadda take shan wahala, amma Sheikh Imam Ya hana yace ciwonta bana asibiti bane, sai dai ya bata ruwan addu'a tasha, a lokacin Aunty Laura, har yunkurin fada mashi gaskiya tayi amma saboda tsoron Kada ya saketa Yasa taja baki tayi shiru, ta bar shi ya gani da idon shi. A falo ya zauna yana jan cazbaha, Ya baro Aunty laura adakin Aisha. Bayan wani Lokaci, Kukan Jariri Ya cika kunnen shi, Wani irin Bugu Zuciyar shi tayi tamkar zata fasa kirjin shi, Tsantsar tashin hankali da rudanine Ya bayyana akan fuskarshi, cikin sauri Ya miƙe Ya shiga dakin Aisha, dira kafarshi keda wuya ba zato ba tsammani idanun shi suka sauka akan Jinjirin da Aunty Laura ta ruƙe a hannunta. Lokaci daya yanayin fuskarshi ya sauya, A lokacin Ayshah tana a kudundune Cikin bargo Aunty laurace ta taimaka mata tayi wanka bayan ta kar6i haihuwarta. Jikinshi na kakkarwa ya karasa shiga dakin a gaban Laura ya tsaya yana ƙarewa Jinjirar kallo idanunshi azazzare. Babyn Fara Sol da ita, Idanunta dara dara farare kamar an diga zaiba, ga wata yalwatacciyar sumar kai har gaban goshinta gashin ne a nannaɗe, kallo daya zakai mata kagane Ba jinsin bakar fata bace. A lokacin Jikin Aunty Laura kerma yake kamar mazari, Ga wani bugu da kirjinta keyi mata saboda tsoron Hukuncin da Shiekh Imam zai yanke mata. Numfashi yaja tare da miƙa hannu Ya kar6i jinjirar daga Hannun Laura, Ya kura mata idanu Yana kallon ta. Ya kasa yarda da abun da Zuciyarshi ke raya mashi, ya yi fatan ace mafarki ya ke yi ba gaskiya ba, wani kululun bakin cikine da takaici Ya tokare makoshin shi.. Muryarshi na rawa ya furta"Shegiya agidana? Gidan Alkali sheikh Imam? Sanannan malamin addinin islama! Me yi ma wasu fada da nasiha akan aikata Barna"? Yau agidana aka aikata barna? Ni sheikh? yata Aisha ce ta haifi Shegiya acikin gidana? Batare da Aure ba? inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." wani makokon bakin cikine ya mamaye zuciyarshi, hannayenshi na kerma Ya mika ma Laura yarinyar da sauri tasa hannu ta kar6a, jikinshi na kerma ya zauna Gefen gadon Aisha Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya ya furta"mamana, tayaya kika samu Ciki? Wanene yayi maki aika aikar nan"? Kunya da bakin cikine suka sa Aisha tagaza furta kalma, taki fitowa daga cikin bargon jikinta sai kerma ya ke yi. Shurun da tayi ne ya bata masa rai, Ya doka mata tsawar data firgitar da su, Har Jaririyar saida ta fashe da kuka Yana Huci Yace"Ba zaki bani amsar tambayar da nayi maki ba"? Aunty laura tana kuka tace"Abien Aisha tsautsayine da kaddara..." Bata kare maganar ba, Ya zabura ya miƙe ya nufe ta gadan gadan, batai aune ba Taji safkar maruka zafafa kan kuncinta, Har saida shatun hannayensa suka fito rudu rudu akan kuncin ta, gefen bakinta ya fashe jini ya fara ɗiɗɗiga. "Allah Ya isa tsakanina dake Laura, Kin cuce ni kin cuci kanki kin kuma Cuci Aisha, sannan kin Cuci malama Batool! Kin ci amanata, nasan komai ya faru da Aisha kece Sila, kece kika ja komai, shashasha mara hankali" Fashewa tayi da kuka Jinjirar hannunta sai kuka takeyi. "Kunyi tunanin bansan komai bane? Duk abunda ke faru agidan nan an fada min, Kece Kika matsa ma Aisha kuka tafi partyn dana hanata zuwa, kina amfani da biyayyar da takeyi maki gurin Cutar da rayuwarta.." Cikin shesshekar kuka tace"wallahi Allah shine shaidana, Ni ban ta6a Cutar da Aishaba, na ruke amanar da ka bani, Kai ka sani in ba ni ba wa kake tunanin zata kula maka da yarka kamar yadda na kula maka da ita"? Bai kula ta ba, Ya koma ga Aisha Ya sanya Hannu Ya yaye bargon data lulluba da shi wata irin zabura tayi ta mike zaune jikinta na kerma ta dinga girgiza kai batare data iya furta kalma ba. "Ki gaya min wani fasikin ne yayi maki ciki"? Cikin rawar murya ta zayyana mashi komai daya faru. "Dan Allah ka yafe min baba, Ba laifina bane, bayin kaina bane, Na rantse maka da wanda raina yake a hannunsa Bada son raina komai ya faru ba, dr shureim shine Ya yi min fyaɗe, baba kayi hakuri kayi hakuri, nasan nakarya maka zuciya, Naji kunya baba, nayi abun kunya, har rokon Allah nayi ya dauki raina in huta saboda bakin cikin abunda yaya shureim yayi min..." sambatu tadinyi yi mashi... Bai san sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba. Cikin raunanniyar Murya yace"Aishana, meyasa lokacin dana hanaki fita partyn bakiji maganata ba? Meyasa? Har ni zansa maki doka ki karya saboda Wannan shashashar ta tursasa maki" ya fada yana nuna Aunty laura da yatsa. "Aishana baki taba yi min gardama ba, ban taba hanaki abu kika ƙiyi ba sai akan Paryn nan! Kika bijiremin, Ni dama saida raina ya bani wani abu zai iya faruwa shiyasa Na hanaki zuwa, da ace kinbi maganata da duk hakan bata faru ba, Kinga illar Kin bin Umarnin Iyaye ko"? jinjina mashi kai ta yi Jikinta nata kerma. "Aisha, Kinbiyewa Son zuciyarki, Kin cuce ni Kin Cuci kanki, Kin kuma Cuci mutanan da suka yarda da mu, sannan Kin zubarmin da mutucina kema kuma Kin zubar da naki mutunci, kinja mana abun kunyar da shiga cikin mutane zai gagaremu, Kin karya alkawarin da kikayi min na kare mun mutuncina da kimata a idon duniya, masuyi maki kallon mutuniyar kirki da zarar sunsan abun kunyar da kika aikata zasu fara yi maki kallon fasika mai fuska biyu, da Ina alfahari dake amma A yanzu babu wannan Aishana, Kin lalata komai, farin Cikin da kika sama min tun ranar haihuwarki a yau kin bata shi, Kin dasa min bakin cikin da har abada bazan ta6a warkewa daga radadin da naji ba, Aisha Ina da makiya wadanda suke son ganin bayana, Idan har sukaji abun kunyar da kika aikata zasuyi min dariya, kuma zasu yi amfani da hakan gurin ganin raunina..." fashewa tayi da kuka tana fadin"baba kadaina fadin maganganun nan bana jin dadi baba, Kaifa malamine, kafi ni sani baba, Abunda ya faru dani Kaddara ce, wata irin addu'ar neman tsari ce bakai min ba? Nima haka inayi ma kaina amma hakan bai hana kaddara ta afkamin ba, saboda Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, babu wanda Allah baya jarabta baba, Annabawan Allah sun fuskanci jarabobin rayuwa basu taba gazawa ba, ya kamata kaima kayi koyi da su, baba wannan ne karo na farko daka fara fuskantar jarabawa mafi muni arayuwarka sau ɗaya tak yarka tayi ciki batare da aure ba, Dan Allah baba Mu dauki Hakan amatsayin Kaddararmu, muyi hakuri mu jure, baba Kafi jin kunyar duniya akan ta lahira? Mutane bazasu amfane mu da komai ba saboda basune zasuyi mana hisabi ba"! Maganganun Aisha sun karya Zuciyarshi, har ya gaza yanke mata hukuncin da yayi niyar yi mata. Mikewa yayi da sauri Ya fuce daga dakin, Yana fita Aunty laura ta mika mata Jinjirar dake ta kuka"ki bata nono Tasha yunwa take ji" Kar6ar jinjirar Aisha tayi, ta fara shayar da ita idanunta akan fuskar Jinjirar yayin da take tsotsar nono sai kallon fuskar mamanta takeyi, hawayen Aisha dake gangarowa ta cikin idanunta kaitsaye yake sauka saman fuskarta, tayi azan In ta haifi yarinyar zataji tsanar ta saboda bata sameta ta hanyar aure ba, amma sai ta ji tsantsar kaunar yarinyar fiye da komai na duniyar nan. Aunty laura ta kara lallashin Aisha har saida ta kwantar mata da hankali. "Aisha nayi danasani da nayita kokarin zubda maki Ciki saboda inajiye maki bakin mutane da kuma abunda zai biyo baya idan mahaifinki Yaji, wlh yanzu da kika tunasar damu sai naji jikina yayi sanyi, da na kashe yarinyar nan da nayi danasani na har abada, baiwar Allah gata kyakkyawa kamanninta sak dana Ubanta, Allah ya raya mana ke bisa tafarkin addinin islam, Allah yasa ki gaji Kyawawan halayan Mamanki" aisha na murmushi ta amsa mata da ameen. "Bari naje na shirya maki Abinci nasan kina jin yunwa" "Aunty Laura, Baki gaji ba? Naga kin raunata" murmushi tayi kada ki damu Aisha, duk raunin da zan ji bai kai wanda kika ji ba. Ta fada tare da fucewa ta shiga kitchen da kanta Ta hada mata farfesu bayan ta gama ta kawo mata adaki. A bangaren Sheikh Imam bayan daya Koma dakinsa safa da marwa ya cigaba dayi, Zuciyarshi cike fal da tunanin ta yadda zai bullowa lamarin saboda bayason asirin abun da ya faru da yarshi aisha ya tonu a idon duniya, yana jiye masu tsoron tozarcin da zasu fuskanta agurin mutane.. A bangaren Dr shureim tun bayan daya Koma Egypt gurin aminsa, Bai kara samun kwanciyar hankali ba, saboda damuwar abunda yayi ma Aisha, Sai da ya shafe sati daya cur bai runtsa ba, abinci sai anyi dakyar ake samu yaci, ya yi duhu ya rame saboda tunanin A wani hali aisha take aciki, ga wani irin azababben sonta daya kara nunkuwa acikin Zuciyar shi, har takaiga baya iya bacci batare da yayi mafarkinta ba, Sometimes sai yayi tunaninta ya ke samun nutsuwa a cikin zuciyar shi, kusan kwana yakeyi akan darduma yana istigfar tare dayi ma Aisha addu'ar Allah yaye mata damuwarta ya kawo mata sauki acikin rayuwarta, saboda yasan zunubin daya aikata mata bazai barta ta zauna lafiya ba, dole su fuskanci kalubale ita da Mahaifinta. tun yana boye abunda ke damunshi har amminsu ta lura da rashin walwalar shi ta dinga tambayarshi meke damunshi yaki fada mata, ta kasa jurewa ta kira iyayen shi ta sanar da su halin da Dan su ke a ciki, da jin hakan Hajiya layla ta bashi Umarnin ya dawo Nigeria, saboda ammi tace ta rasa gane kanshi, baya bacci baya son cin abinci, wanka ma saita matsa mashi ya ke yi kamar karamin yaro. Bayan ya dawo Nigeria, Iyayenshi suka tasa shi agaba da tambayar meke damunshi? yaƙi ya sanar dasu, Ba irin lallashin da basuyi mashi ba amma duk abanza. Saida Ya samu nutsuwa ya kira Benazir a dakinsa ta same shi ya tambayeta Ina Aisha? Tace mashi rabon ta da Aisha kusan wata tara da kwanaki, Aunty Laura tace masu ta tafi sudan gurin kawunta, Ko sun kira layinta basa samu kuma koda zata tafi ba ta yi masu sallama ba" Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, Zuciyarshi ta karaya sosai. Ana haka saiga kiran Sheikh Imam Ya shigo wayar shi, wata irin kunyace ta kama shi kamar bazai daga kiran ba sai kuma Ya daga, Ko sallamar shi sheikh Imam bai amsa ba Yace shureim Inason ganinka, Ka same ni agidana, Ya amsa mashi da toh. Bai bata Lokaci ba, Ya shirya kanshi cikin shadda Ya nufi gidan Sheikh Imam A garden Ya taras da shi zaune kan kujera fuskarshi babu walwala kamar bai taba dariya ba, tuni Shureim Yasha Jinin jikin shi. Bayan daya zauna kan kujerar dake fuskantar sheikh Imam Malik Ya yi shiru Yana sauraron shi.. Kallo ɗaya sheikh Imam yayi mashi Ya lura da irin ramar da yayi daga gani yana acikin damuwa. "Akwai wata rana, dana farka tsakar dare, na fito daga daki Ina zagaye Gidana, dama Ina yawan yin hakan sometimes bana iya bacci batare dana tofe ko'ina da addu'a ba, ina gab da zan gifta dakin aisha Najiyo shesshekar kukan ta, Kasan me naji tana fadi"? ya tambaya da tsantsar bacin rai Yana kallon fuskar Shureim daya gama rudewa, Girgiza kai yayi"aa baba' "Addu'a takeyi Allah ya cika mata burinta na ganin ta auri yaron makwabtana data mutu akan kaunarsa batare da sanin shi ba.." wata irin karaya Zuciyar dr shureim tayi. "Nayi mamaki a wannan lokacin, saboda Aisha bata taba bude baki ta fadamin ga wanda takeso ba, amma a lokacin danaji tayi addu'ar nan ni kuma sai nayi alkawarin zan aura mata yaron nan da take so saboda in cika mata burin ta.." zafafan hawayene suka wanke fuskar Dr shureim. "Yarinyar da tayi dakon soyayyarka acikin zuciyarta na tsawon shekaru, ta hana idonta bacci don ta roki Allah ya mallaka mata kai ita ka wulakanta rayuwarta Shureim? Ya faɗa rai abace. "Inayi maka kallon mutumin kirki kamili, mai jin tsoron Allah, ashe na yaudari kaina! shureim ka sani ka take sani? Da yata ka aikata zina? Sannan baka taba waiwayonta ba, Ka haura kafa kabar kasar, Sai jiya na samu labarin ka dawo! Baka damu da halin da ka jefata ba shureim! Har yabonka nakeyi saboda na yaba da kyawawan halayenka amma ka tashi ka watsa min kasa a ido" Fashewa da kuka dr shureim yayi kamar karamun yaro, shima sheikh Imam din hawaye ne ke zarya kan kuncinsa. Cikin karyayyar murya mai tattare da danasani dr shureim Shureim Ya soma bashi hakuri Yace ya amsa laifinsa amma wlh baisan Ya akaita ba, Allah shine shaidarshi bai ta6a kusantar zina ba, bai ta6a sha'awar Ya kusanci Aisha batare da aure ba, Amma ya karbi laifinsa kuma Yana neman alfarmar ya bashi aurenta saboda su rufawa kansu asiri. Sheikh Imam yace yaji amma yana so yaje gida Ya fada ma iyayensa abunda Ya aikata sannan Ya sanar da su zai auri Aisha, Duk abunda su ka ce Yazo ya sanar da shi, Jikinshi na 6ari ya mike har tambayar sheikh yai Aisha tana nan cikin gidan? Yace mashi eh, ya sake cewa zai iya ganinta? Imam Yace aa bai amince Yaganta ba, har sai bayan an daura auransu. Bayan komawar Dr shureim gida ya kira Alhaji ubaid da Hajiya layla a falo Benazir ce kadai ke babu a cikinsu. Bayan sun nutsu, Dr shureim Ya fayyace masu komai daya faru tsakanin shi da Aisha Sannan Yace Ya yanke shawarar zai aureta.. Tunkan Ya kare maganar Hajiya layla ta fara zazzaga masifa tana fadin wallahi bada yawunta ba, bai isa Ya bata masu suna agari ba, sai dayaga zabe ya kusa zai zo masu da wannan maganar mara dadin ji? Salon yaja masu zagi agurin Jama'a? ta inda take shiga bata nan take shiga ba. Da farko Alhaji Ubaid yaso Ya fahimci dr shureim Har fada yayi masa akan abunda yayi ma Aisha, sannan yace ya amince masa zaije suyi maganar aurensu da sheikh Imam din, Shureim Yaji dadin maganar Mahaifinsa hajiya layla sai banbamin bala'i takeyi, Ita damuwarta ba akan abun kunyar da shureim yayi ma aisha bane, face Takarar da Alhaji ubaid Ya tsaya ga zabe ya kusa In har abokan adawarsu suka Ji abun nan zasu nemi bata masu sunane, a karshe su rasa kujerar da suke nema. Bayan kwana daya da afkuwar Lamarin, Alhaji Ubaid Ya canza magana, ya kira shureim Ya fada masa yayi hakuri amma gaskiya bazai bari ya auri Aisha ba, saboda yayi bincike ya gano aisha ba mutuniyar kirki bace, dama can ta saba bin maza, har videos dinta na batsa wanda tayi tare da maza an tura masa awaya, sannan abun da ya faru tsakanin shi da ita ya yarda bayin kanshi bane, laifin Aishar ne itace shaidaniyar dataja Hankalin shi donta biya bukatar kanta. Hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba, ya dinga salati Yana karanto duk wata addu'a da zata sanyaya zuciyarshi, ranshi ya 6aci matuka da jin kazafin da mahaifinsa yayi ma Aisha, Yace wlh daddy karyane, wannan maganar ba gaskiya bace, kaji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da zaka koma gare shi, Aisha ba fasika bace, mutuniyar kirkice ita, abunda aka fada maka akanta karyane, kai kasan wacece aisha tuntana karamarta kamilar macace mai kamun kai, daddy kada ka biyewa son zuciyarka! Nasan siyasa ce ke nema ta rufe maku ido shiyasa kuke gudun in auri Aisha kuma maganar nan har yanzu ma ba Wanda yasan da ita daga gidansu sai nan, dan Allah kubarni in aureta in rufa mata asiri, Nine fa nayi silar jefasu a halin da suke aciki ita da mahaifinta, meyasa ni ba za ku ga laifina ba sai laifinta ta? Ita da nayiwa fyade"? hajiya layla Ta balbale shi da masifa tace"ko yaki ko yaso aisha ba mutuniyar kirki bace, abunda mahaifinsa ya fada akanta gaskiya ne, dama ita can bata yarda da ita ba, munafukar kullum tana yawo cikin hijabi kamar ta Allah, ashe maza take bi, gashinan zata bata mata tarbiyar ɗa, don haka ta yanke duk wata alakarsu da sheikh Imam malik, zumuncinsu Ya kare. Gaba daya suka juya ma Dr shureim baya, duk wannan abun dake faruwa Benazir bata sani ba, Saboda bata agidan ta tafi Abuja gidan Uncle Musa. Shiekh Imam malik ya yi ta Jiran zuwan Alhaji Ubaid Ko shureim don Yaji daga garesu amma Yaji shiru wai malam yaci shirwa. Har dai ya yanke shawarar zuwa gidan da kanshi don yaji ya ake ciki. Bayan ya isa Security Officer din dake tsaron Gidan Ya shiga yayi mashi sallama da Alhaji Ubaid. Sai ga Jam'in ya dawo yace mashi Ya shiga daga ciki. A falon gidan Shiekh Imam Ya zauna kan Sofa Yana Jiran fitowarsu, Tsawon mintuna Sai ga Alhaji ubaid da Hajiya layla sun fito daga part dinsu, akan sofa suka zauna suna fuskarshi, tun daga yanayin fuskarsu Ya fahimci babu lafiya, kamar basu taba yin dariya ba, Koma arzikin gaisuwa bai samu ba. ya yi tsammanin zasu bashi hakuri kan abun kunyar da dansu yayi ma yarsa, amma sai yaga akasin hakan, bayan da ya kora masu jawabin abunda ya kawo shi Alhaji Ubaid Yace Yayi hakuri ya rungumi kaddara, Amma shureim bazai auri Aisha ba, saboda sun yi bincike akanta sun gano ba mutuniyar kirki bace ta saba bin maza.." bai dire maganar ba Sheikh Imam Ya doka masa tsawa Rai amatukar bace Yace"amma baka da Mutunci Alhaji Ubaid, ka bani mamaki, mutumin banza mutumin wofi, yau da kanka kake yiwa aishana kazafi? Yarinyar data taso agabanka tuntana karama kasanta farin sani, har alfahari kakeyi da ita saboda kyawawan halayanta, ba kamar yarka Benazir ba da kowa yasan bakin halinta data gada awurin jatumarta, Ni ban ta6a aibata yayanka ba saini zaka aibata nawa Ubaid? Akwai dan iskan dayawuce danka daya keta mata haddi? Nayi zaton in masifa ta same ni kaine mutun na farko da zaka fara rufa min asiri ka sharemin hawayena ashe na yaudari kaina!!...." Dakyar ya ƙare maganar hawaye wasu nabin wasu akan kuncinsa Yaji zafin maganar Alhaji Ubaid. Hajiya layla ranta Ya 6aci matuka da jin yadda sheikh Imam Ke gaya magana akan ya'yanta, dama ba mutunci gareta ba, tana da sonkai, nata kadai ta sani, ko da take zumunci da su Albarkacin Alhaji ubaid suke Ci. Nan ta shiga surfa mashi ruwan masifa zagi ta uwa ta uba kamar zata dokesa, saboda rashin kunya, kwata kwata sheikh Imam bai damu da maganganunta ba saboda yasan halinta, Bata da kunya fitsararriya ce, kuma dama ita tabarmar kunya da bori ake naɗeta. Alhaji Ubaid kasa magana yayi, saboda Zuciyarshi da tayi rauni saboda maganar Sheikh Imam malik ta karya Zuciyar shi, Ya danji tausayin shi amma da ya tonu hudubar da shaidan yayi mashi saiya canza ra'ayin shi. Ya mike Ya fara gaya ma sheikh Imam magana Yace"ya jira ya ga abunda aka tura masa, zaisan ba kazafi yayi ma Aisha ba" Ya juya ya nufi dakinsa sheikh Imam Yana atsaye jikinshi na kerma zuciyarshi cike fal da tunanin menene Alhaji Ubaid zai nuna masa"? Bai karashe zancen zucin ba, sai Ga Alhaji Ubaid Ya fito hannun shi ruke da wayarsa Ya miƙa ma Sheikh Imam"gayanan ka gani da idonka" Yatsun hannunsa na kerma Ya kar6i wayar lokacin daya daura idanunsa akan Screen din wayar saida Zuciyar shi takusa dakatawa da bugawa saboda tsabar firgitar da yayi, a lokacin Jikin shi yadinga tsuma idanunshi suka kada jawur, baisan sa'adda Ya saki wayar Ta fadi kasa Ya juya cikin fitar hayyaci ya fuce daga gidan Yana tafiya kafafuwanshi na hardewa kamar zai kife kasa. Bayan fitarshi Zainab mai aikinsu Taje ta fada na Dr shureum abunda Iyayensa sukayi na sheikh Imam Malik, Ransa ya 6aci a zuciye yaje ya same su ya dinga yi masu fada kamar zai doke su, Yace basu kyauta ba, meyasa zasuyi ma sheikh Imam haka? Shifa makwabcinsu bayan haka sunyi zama na amana, amma saboda rashin adalci da son zuciya sun rufe ido akan rashin gaskiya suka ci mutuncin shi, babban abunda yafi kona mashi rai abunda suka nuna ma Sheikh Imam ya gani, yaji zafi sosai, amma su ko a jikinsu. Aisha tana zaune cikin dakinta a kan gado, tana tsaka da shayar da babynta, Baba Imam ya fado dakin Afujajan ko sallama baiyi mata ba, Jikin shi na zubda Gumi Yakai hannu Ya damƙi ƙeyar Aisha da ita da yar duka Ya wurgo su tsakar falo Ta kife kasa Yarinyar ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Da gudu masu aikin gidan suka fito sakamakon Kukan Aisha da suka jiyo, Aunty Laura dake a cikin dakinta tana tsaka dayin waya tajiyo kukan Aisha dana jinjirarta, batasan sa'adda ta jefar da wayar kasa ta watsa da gudu Ta shigo falon tana haki, Gabantane ya yanke ya fadi ganin Sheikh Imam tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki ga Aisha da jinjirarta yashe a kasa suna kuka. Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ta faɗa tare da nufar Aisha donta taimaka mata ta mike sai dai kafin Ta karasa Sheikh Imam Ya doka mata tsawa Yace"karki kuskura ki taba ta! Idan ba haka ba, abakin aurenki" cak ta tsaya jikinta na kerma. "Allah Ya isa tsakanina dake Aisha, Allah Tsine maki Albarka, In sha Allah sai kinga sakayyar abunda kikai min" waro idanu waje Aunty laura tayi, Hankalinta amatukar tashe, gashi ba halin tayi magana balle ta dakatar da shi, maids din suka daura hannayensu asaman kansu cike da tashin hankalin jin furucin sheikh Imam ga yarsa, ba su taba zaton zai yi mata haka ba, su din amintattunsu ne, koda asiri Ya tonu agidan suka gane Aisha tana da ciki basu ta6a nuna sun sani ba saboda basa son abunda zai zubar da martabar sheikh Imam da ita Aisha. "Kin cutar da rayuwata kin yaudareni Aisha, Idan aure Kikeso Meyasa ba zaki fada min ba inyi maki!? Sai kika zabi ki zubarmin da mutunci na, inayi maki kallon mutuniyar kirki ashe ke din fasika ce, mara tsoron Allah, Dama tun farko banso Kika je Germany karatu ba saboda hankalina bai kwanta ba, ashe bayan da kika je karuwanci ki ke yi acan, naga komai Aisha an nuna min videos dinki da hotunanki tare da kato, Yau silarki An zageni anci mutuncina Aisha wlh nayi danasanin haihuwarki da akayi"❗ *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~___________________________________~ A bakin door room dinta suka tsaya, fuskokinsu ɗauke da damuwa. "Aisha meyasa baki tuntube ni ba a lokacin da abun ya faru? saboda laifin ya shureim ya shafe ni? mun yi zaton kina a Sudan ashe kina a gida, da ace kin sanar dani ke kinsani ni me iya tsaya maki ce, wlh zan tayaki faɗa ne don ganin na kwatar maki hakkin ki, amma bansan komai ba, sai dai na ji labari bayan na dawo gida, abun da yafi ƙona min rai tafiyar da ki ka yi batare da kin neme ni ba, kuma baki yi tunanin kije gidan su Anila ba......" daƙyar Benazir ta ƙare maganar tana jan numfashi saboda Zuciyarta dake tafarfasa. Idanunta na akan door room din Aisha, suna jiyo shesshekar kukan ta daga cikin dakin. "Lokacin da naji abun da ya faru tsakanin ki da ya shureim da kuma kazafin da akayi maki, Har jinya nayi gadon asibiti saboda baƙin cikin da na ji, wallahi Allah shine shaida ta, nayi bakin cikin da bazai misaltu ba, Na ji zafin hukuncin da baba Imam ya yanke maki cikin fushi batare da ya yi bincike ba, mu shaida ne akan ki Aisha sannan mu shaida ne akan Yaya Shureim abun da ya faru a tsakanin ku sharrin shaidan" Aneelerh ta ɗaura da cewa,"Ni kaina sai dai naga sakon ki, har kiran ki na yi ba ki yi picking ba, har messages na tura maki akan ki faɗa min ina kike ko ki zo gidanmu amma babu amsa, Aisha meyasa ki ka zabi ki tafi ki bar mu? Bayan kinsan irin kaunar da muke yi maki, ko bayan tafiyarki bamu manta dake ba, a Kullum muna cikin damuwar rashin ki, tunanin mu ina kike? Kina raye ko kin mutu? Meke faruwa a cikin rayuwar ki.... " Aneelerh bata ƙarasa maganarta ba, Dr Shureim ya katse ta, cikin sanyayyar muryarsa mai tattare da rauni ya ce,"Pls Aisha, mu manta da abunda ya wuce, ki yafe mini, Ki yi hakuri Aisha, dan Allah ki fito mu yi magana, gaba ɗaya ɗokin ganinki mu ke yi" Babu alamun zata tanka masu. "Pls Ku dawo ku zauna mana, indai Ummi ce tana a gidan nan, duk da bansan meya faru a tsakaninku ba amma na tausaya maku, in har kuka bamu hadin kai in sha Allah zamu yi kokarin sasanta ku da ita" Taj ne ya yi maganar daga inda yake a zaune, Jikin su asanyaye suka baro kofar dakin Ummi ba don sun so ba, suka koma falo kowannan su ya zauna kan Sofa, kwata kwata babu walwala akan fuskokinsu, Idanunsu sun kaɗa jawur saboda kukan da suka sha, babu mai magana a cikinsu kowa da abunda yake saƙawa a cikin Zuciyar shi. Taj dake fuskantarsu, A tsanake ya ke nazarin yanayin su sam ya kasa dauke ido daga kallon su. "Pls ina son insan meye alaƙarku da Aisha ne? A nan take zaune?" Murmushi Taj ya ɗan yi tare da kallon Dr Shureim da ya yi maganar. A tsanake Taj ya zayyana masu alakar dake a tsakanin su da Aisha, tun daga kan aikin da U.s armies suka saka ta, ya ƙara da cewa,"Tamkar uwa take a gurinsu, tana kula da su sosai..." Ajiyar zuciya suka sauke gaba daya hankalin su ya kwanta da jin a nan take da zama don basu son su kara rabuwa da ita. A bangaren Ummi bayan data shige daki ta yi locking door din, tana kuka ta fada kan gadon ta, Batool dake a cikin toilet tana jiyo shesshekar kukanta ta fito hankalinta atashe ta haye kan gadon tana tattaba bayanta, "Aunty Ummina! Meke damunki? Meyasa ki ke kuka? Waya 6ata maki rai!" Kwata kwata Ummi bata saurare ta ba, hakan yasa ta fashe da kuka itama tana fadin, "Dan Allah aunty Ummi ki daina kuka, bana so! Ki faɗa min meke damun ki?" dakyar ta iya furta,"Bana jin dadin Zuciyata, zafi take yi mini! Babe na rasa Fatima na, I've lost my Batool ta mutu, na yi babban rashi! Baki ji radadin da nake ji ba..." sambatu ta dinga yi mata, Batool data gama ruɗewa ta kasa gane inda maganganun ta suka dosa. "Aunty Ummi, ban mutu ba, Ina a raye, ba ga ni a kusa dake ba?" ta faɗi hakanne saboda ta yi zaton ita Batool din take nufi. Tana kokarin tallabo fuskar Ummi da tafukanta don ta miƙar da ita zaune saboda karfin hali irin nata.. Ba ta yi aune ba, Ummi ta janyota kan chest ɗinta ta rungumeta sosai, duk don ta samu relief na radadin da take ji, damuwace ta mamaye zuciyar Batool lokacin da fatar jikinta ta haɗu data Aunty Umminsu, saboda zafin da jikinta ya ɗauka har a jikinta tana jin shi. Ruɗewa ta yi cike da tashin hankali take fadin,"Baki da lafiya Aunty Ummi, you're burning up, in wani abu ke damunki ki fada min zan taimaka maki har ki samu sauki.. " ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga rukon da Ummi ta yi mata don ta samu damar zuwa ta faɗa ma daddy Taj da Unaisah halin da take aciki sai dai sam Ummi taƙi bari ta motsa. Tunawa tayi da addu'a, cikin sauri ta fara karanta yan addu'o'in da ta iya a cikin zuciyarta ta tottafa mata saman wuyanta. Kafin Ta ɗaura hannayenta biyu akan bayanta cikin sigar lallashi ta ke ɗan bubbuga bayanta kamar ta samu karamar yarinya. Ji ta yi inama ace Batool ce ɗiyarta, Murnar da za ta yi ba zata misaltu ba, tana son Batool sai dai ita bata fito daga mahaifarta ba, tasan duk mun daran daɗewa, wata rana Batool zata ga iyayenta ne. Cusa yatsun hannayen ta ta yi acikin sumar kan Batool, yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar babynta, bazata taba mantawa da suffarta ba, tana ji aranta tabbas da ace tana a raye kuma ta girma, ba abun da zai hana su yi kama da Batool saboda kamanninta da Dr Shureim, ta dade tana ganin kamanceceniyar su sai yau ta ƙara tabbatar da hasashen ta. "Aunty Ummi da sauki?" Cikin disasshiyar murya ta furta,"Ki cigaba da yi min addu'a, Allah yaye min abunda ke damuna" Da sauri ta amsa mata da toh . Time da aka fara kiran sallar la'asar, Taj yace ma su Anila su shiga daki su yi sallah, bayan ya nuna masu ɗaya daga cikin bedroom dinsu Sajeed suka tashi suka shiga, Dr Shureim ya ce ya tashi su tafi masallaci, sam ya ma manta da ƙafarsa dake ciwo har ya yunkura zai mike kafar ta fara yi masa zogi ba arziƙi ya koma yana nishi, anan Dr shureim ya fahimci baida lafiyar ƙafa har ya tambayi meke damunshi ne? ya ce mashi ya samu rauni ne a cinyar sa ta dama amma da sauƙi, cikin nuna tausayawa Dr shureim ya yi masa sannu da jiki, har ya ce in bazai iya zuwa masallacin ba ya yi zaman shi tun da lalurace, Taj yace ma shi kar ya damu, zai iya zuwa ai yana da wheelchair, ya faɗa tare da kai hannu Ya janyo kan kujerar sa da ya 6oye tsakankanin Sofas, ya janyota ta dawo ta gaban shi, ya yi ta ƙoƙarin miƙewa yana kasawa har saida Dr. Shureim Ya taimaka mashi ya zauna a akanta, tukunna suka tafi. __________________________________✍️ Tana a kwance tsakiyar gadonsu, ta ƙurawa ceilling idanunta da suka kaɗa jawur, hawayen da suka cika idanunta a hankali suke gangarowa kan kuncinta, bakomai take tariyowa ba face fuskar Benazir, wai dama itace mahaifiyarta da ta yi watsi da ita? Tana yi mata kallon mutuniyar kirki ashe ba haka bane ta yaudari kanta, abin da yafi ƙona mata rai, jinyar ta da ta yi, ta bata abinci a baki, ta yi hugging dinta har ma ta sumbace ta saboda kaunar da ta ke yi mata bisa rashin sanin wacece ita, but now that she knew the truth, she hated her more than anything in the world, abun da yafi tsaya mata a rai meyasa ta gudu tabarta bayan ta jefar da ita cikin kwamin wanka? In bata sonta meyasa bata kashe ta ba tun lokacin da ta haife ta, Laifin me ta yi mata da yaja har ta tsane ta? Tabbas tana son ta tunkareta gaba da gaba don taji amsar tambayoyin ta.. ranta yakai maƙura a gurin 6aci, sai faman yin juyi ta ke yi akan gadon kamar mai fama da ciwon mara. _______________________________🌹✍️ Around ƙarfe biyar na marece, motar Chief ta kunno kai cikin main gate, bayan driver dinsa ya tsayar da motar a parking space cikin hanzari ɗaya daga cikin security Officers din da ke sintiri yai hanzarin zuwa gaban car door ya bude masa motar, fitowa ya yi daga ciki jikinshi sanye da Suit. With respect Security Officers din suka sara mashi, har zai juya muryar driver dinsa ya katse shi "Sir, should I bring in the suitcases?" He nodded, then turned away, ya nufi falo. Cikin sauri SA ɗin ya buɗe tanƙameman boot din motar Chief, ya soma fiddo wasu hadaddun akwatina, guda biyu bayan ya gama ya rufe boot din, ya ruƙo handles dinsu ya bi bayan Chief da su. Chief bai taras da kowa a falon ba, Kaitsaye Ya nufi Upstairs saboda a gajiye ya dawo he needs some rest, duk da yafi bukatar ya gana da su. Bayan shigar shi dakin, SA din Ya shigo mashi da akwatinnan ya ajiye su kafin ya fuce. Shaf shaf ya rage kayan jikin shi Ya shiga bathroom don ya yi wanka. Bayan wani Lokaci ya fito daga part dinsa ya dauki wankan blue sky voile, sai kamshi ke tashi a jikin shi, walking magestically ya nufo down. tun kafin ya ƙaraso takun tafiyarsa yaja hankulansu ga duban shi, a lokacin sun dawo falo suna jiran shi. A hanzarce suka mimmiƙe tsaye, kaitsaye ya nufi Dr Shureim, side hug ya yi masa tare da ruko hannunsa sukayi musabaha, Dr shurem ya ɗan yi mamakin saukin kan Chief yadda ya tarbe shi kamar sun saba da juna. With respect Aneelerh da Benazir suka gaishe da shi tare da yi mashi sannu da dawowa, fuskarsa da fara'a ya amsa masu. Gaba ɗaya Ya lura da yanayin fuskokin su kamar ba walwala akai. Sarah mashi Taj ya yi daga zaunen da ya ke bai motsa ba ya yi mashi sannu da dawowa, mayar masa da martanin sarawar ya yi kafin ya amsa gaisuwar da ya yi masa tare da miƙa masa hannu suka gaisa da juna. Daga bisani ya zauna gefen Taj, ya kasance suna fuskantar su Dr shureim.. "A yi mini afwa, na barku kunata jirana." Ɗan murmushi suka yi gaba dayansu. Dr shureim ya ce, "bakomai wlh, Allah yasa dai bamu katse maka aiki ba" Fuskarshi a sake ya ɗan jinjina kan shi, Tunkafin ya tambayi wani abu Taj ya yi hanzarin daukar wayar Ana dake ajiye gefensa ya kunna masa videon tare da miƙa masa ya sa hannu ya kar6a tare da daura idanunsa akan Screen din wayar ya nutsu yana kallon videon, bayan ya gama kallo shiru ya yi yana ɗan jinjina kan shi. Lamarin ya ɗaure mashi kai tamau, kuma tunanin su ya zo ɗaya dana Taj. Gyaran murya ya yi masu a hankali suka mayar da dubansu gare shi. Tambayoyi ya fara yi ma Anila dangane da Ana da kuma Uncle din ta, bata boye masa komai ba duk abunda ya tambaya sai ta bashi amsa. Bayan Ya kammala yi mata tambayoyin, Taj ya ce, "Benazir, ki yi masa bayanin abun da ke damun ki" cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh, A tsanake ta kwashe komai da ya faru da ita a gidan Uncle musa ta sanar da Chief, ta ƙara da cewa, "Ban sanar ma kowa ba, Yaya Shureim ne kaɗai ya sani, bayan haka yanzu an ɗaga ƙafa da kawo min harin." Yanayin fuskar Chief ya nuna tsantsar ruɗani da al'ajabi, kallon Dr Shureim ya yi wanda gaba daya hankalin sa baya akan su, duba da yadda ya sadda kan shi ƙasa. "Za ki iya suffanta mini mutumin da ya kawo maki hari a cikin toilet?" Ta amsa da eh, kafin ta fara siffanta mashi mutumin. Kallon kallo suka jefawa juna tsakanin shi da Taj, lamarin ya daure masu kai, saboda gaba ɗaya yadda Benazir ta suffanta mutumin, baida bambanci da giant ɗin kurkukun Ƙaddara, amma abun tambayar anan meyasa ake son kashe ta? Zurfin tunani Chief ya shiga har na tsawon yan mintuna, kafin ya ɗago ya dubi Benazir suka haɗa ido cikin na juna. "A lokacin baya, kafin ƙaddara ta rabaki da gidan mijin ki, babu wanda ki ka ta6a yi ma laifi kuka samu sa6ani a tsakanin ku har ta kai ya ci wani alwashi a kan ki?" Girgiza kai ta yi,"Gaskiya ni ba wanda wani abu ya taba haɗa ni da shi..." Bata ƙare maganar ba, ganin irin kallon da Taj ya yi mata, nan take ta fahimci me yake nufi wato yasan halinta ciki da bai. Gyaran murya ta dan yi, "A lokacin baya nasan bana jin magana, idan nace ban taba samun sabani da wani ba to na yi ƙarya, amma bana tunanin na yi laifin da har za'ayi yunƙurin kashe ni" "Bakya tunanin wanda ya yi maki kurciya shine yake nema ya kashe ki saboda ya ga kin dawo a raye, may be akwai wani abu da ya haɗa ku ko sanin sirrin wani wanda baya son asirin shi ya tonu ta silar bayyanar ki shiyasa yake nema ya halaka ki..." Maganar Chief tasa ta jin faduwar gaba, zurfin tunani ta shiga yayin da ƙwaƙwalwarta ke kokarin tariyo mata abubuwan da suka faru a lokacin baya kafin ta gudu daga gidanta, sai dai ta kasa tuna komai kamar an wanke mata brain dinta. "Ki yi kokari ki tuna Benazir, ba ƙaramin taimako zaiyi mana ba" Taj ne ya yi mata maganar cikin kwantar da murya, har kallon shi saida tayi kamar wani abu bai shiga tsakaninsu ba, Chief yana lura da duk wani motsin su haɗi da karantar yanayinsu ta fuskarsu. Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Aneelerh dake yi mata magana cikin raɗa, "Please ki tuna Benazir, ni nasan baza a rasa wadanda kuka taba samun sabani da su ba, ko ya ya ne ki yi tunani pls" Wani abu da Chief ya lura da shi shine satar kallon Dr shureim da take yi, hakan yasa shi zargin akwai abun da ta sani, kuma tana so ta fada sai dai bata son Dr Shureim ya ji shiyasa take satar kallon shi a fakaice. Fahimtar hakan yasa shi cewa, "Kada ki damu, zan baki lokaci, bayan kin koma gida kiyi kokari ki tuna in ya so sai ki kira Taj a waya ki sanar da shi" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da ɗin murmushi ta ce, "In sha Allah idan na tuna zan kira in sanar da ku" Shiru suka dan yi na wani lokaci. "Meke damun shi ne?" Chief ne ya fada idanunsa akan fuskar Dr Shureim ƴan hawayen da suka cika idanun shi sai kokarin sauka kan kuncinsa suke yi. Taj ya ce, "Yawwa Sir, namanta ban fada maka ba...." A hankali Chief ya mayar da hankalinsa akan Taj, komai da ya faru bayan fitowar Ummi Ya sanar da shi, jinjina kai ya yi tare da kallon su Anila, "Zan iya sanin menene alaƙar ku da ita?"? Har suna haɗa baki gurin furta eh saboda suna son ya taimaka masu tunda agidanshi take da zama. "Yaya Shureim," Benazir ce ta kira sunan shi, cike da damuwa ya ɗago ya kalle ta, a kunne ta yi masa raɗa, "Suna son sanin menene alakar mu da Aisha, zan iya faɗa masu komai da ya faru? tun da ka ga agurinsu take da zama may be idan su ka ji su taimaka mana" Ya ɗan ji nauyin maganar, amma a halin yanzu baida za6i, Cikin sanyin murya ya ce, "Idan kina ganin zasu sama mana mafita, ki fada masu komai," Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta maida dubanta akan Taj da Chief. Nan ta fara basu labarin rayuwarsu, da alakar su da Aisha, da kaddarar data raba su da juna, bata 6oye masu komai ba, da yake ta iya bada labari ko mistake bata yi. Lokacin data ƙarasa basu labarin idanunta cike tab da ƙwalla, yayin da su kuma tsantsar mamaki da al'jabine ya kamasu, A sanin su da Ummi tantiriyar Karuwace da ta yi ƙaurin suna a America, ashe kaddara ce ta canza mata rayuwa, sun ji tausayinta sosai, har ta kai ga sun yi shiru jimm suna ɗan jinjina heads din su, shi dama Taj ya daɗe yana yi mata kallon sani, sai yanzu da Benazir ta bada labarinsu, Ya tabbatar ma kansa Bintu Imam ce. "Dan Allah ku taimaka mana, kada ku bari Aisha ta koma America, ku ruke mana ita har sai mun sansanta tsakaninta da mahaifinta da kuma mu, muna so ta koma kamar yadda take a da, sauyin da muka gani atare da ita ya tada mana hankali, wlh kallo ɗaya da nayi mata na fahimci ta canza rayuwarta" Chief ne ya ce,"Na yi maku alkawari In sha Allah, Aisha ba zata koma America ba, zan cigaba da ruke ta anan har sai na cika maku burukan ku, saboda nima na damu da ita na tausayama rayuwarta sosai, na ji zafin abun da ya yi silar rabata da mahaifinta da kuma halin da ta jefa rayuwarta, wanda nayi imanin tsinuwar da mahaifinta ya yi mata ce ke bibiyarta, bayan haka Dr Shureim..." Ya amsa mashi da na'am idanunsu acikin na juna. "Kaima na tausaya maka sosai, labarinku ya ta6a zuciyata, kun bani tausayi, please ka cigaba da hakurin da ka saba yi, in sha Allah ni Chief na yi maka alƙawarin Ummi won't leave this house until everything is settled" Maganar Chief ta kwantar masa da hankalinsa, wani dadine ya ji ya lullu6e zuciyar shi, Anila Da Benazir basu san sa'adda suka saki murmushin jin dadi ba, har suna hada baki gurin yi mashi godiya. "Ina fata mun gama magana, ko akwai sauran wani abu?" Cikin kulawa Chief Ya faɗa yana duban su, "Unaisah, ta ƙi kula ni...." gaba daya ta fada mashi abunda ya faru tsakaninta da Unaisah, har cikin ranshi bai ji dadi ba, amma ya fahimci Unaisah, baiga laifinta ba, dole ne dama ta ƙi accepting din ta saboda ta ƙullace ta aranta. "Kada Ki damu, Ni zan yi mata bayanin da zata fahimta, In sha Allah" Ita dai Anila tunaninta ya fara komawa gida fargabanta kada Junaid ya saki baki ya furta dodon da ya kashe Anah a gaban Uncle. "Akwai gargadin da nake so na yi maku gaba dayanku, daga rana irin ta yau inaso ku dauki kanku a matsayin jami'an sirri, kada ku kuskura ku faɗa ma wani damuwarku, sannan kada ku bari yanayin ku ya nuna! Duk wani abu da muka tattauna anan to mu binne shi anan!" Ya faɗa yana nuna floor da index finger ɗinsa. "Sirrinku a cikin zuciyarku, In zai yiwu ma, ku daina tunanin abun cos kuskure kaɗan zai iya jefa rayuwar ku cikin hadari. Tun da har kun fada mana komai, from now on Case din yabar hannun ku, yanzu yana a hannunmu, kuma in sha Allah zamu cigaba da yin bincike akai" Gaba ɗaya sun yi amanna da maganar shi, kuma sun daukar mashi alƙawari zasu kiyaye. "Yakamata mu tafi, na ga an kusa fara kiran Magrib" Aneelerh ce ta faɗa tana duba wrist watch din hannunta. Taj ya ce, "Zamu ruƙe wayar Ana a hannun mu, har zuwa time da zamu kammala bincike. Mungode sosai, Allah ya maida ku gida Lafiya" Atare suka hada baki gurin furta Ameen muna godiya muma da aka kar6e mu hannu bibbiyu tare da fatan nasara. Dakyar Dr shureim ya mike fuskarsa sam ba walwala, ya so ace zai iya ganin Aisha kafin su tafi. Daƙyar ya iya furta,"Please zan iya samun phone number din Aisha?" Taj ya ce, "Mi zai hana." ya ɗauko wayarsa ya lalubo layin Ummi ya mika masa, yatsun hannunsa har kerma suke saboda zumudin ya kar6a, shaf shaf yayi copying dinta bayan ya gama ya mika ma Taj tare da yi mashi godiya. Benazir dake kallon shi ta kasa gane me ya hana shi mikewa? A ganinta ko rakiya ne yakamata ya yi masu. "Muje nayi maku rakiya" Chief ne ya fada tare da mikewa, ya ruko hannun Dr shureim a cikin nashi suka yi gaba, Aneelerh da Benazir suna a biye da bayan su. Bin su da kallo ya yi har saida suka 6ace ma ganinsa, lumshe idanun shi yayi a hankali yake tariyo komai da ya faru tun farkon zuwan su Benazir. Unexpectedly ya ji an sumbaci forehead dinsa, a firgice ya buɗe idanun shi, har saida gaban shi ya fadi da ya yi tozali da Benazir ta sunkuyo da kanta saitin fuskarshi, nan da nan ya haɗe rai, "Baki tafi ba?" "Taya zan tafi kana fushi dani" Ɗaure mata fuska ya yi. "Pls abunda ya faru ɗazu ka yafe mini, raina ne ya 6aci," Ta fada tana kashe mashi murya. "Na ji, ya wuce." "Yaushe zaka maida ni ne? Na gaji da jira." Wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce, "Toh rasa kunya 6eran tanka, ke baki ji kunyar furta in maida ki ba? Hauka nake da zan dauki macen da take ruƙe kwalar rigana kamar zata doke ni!" Ya fada babu wasa akan fuskarsa. Marairaice fuska ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce, "Pls ay na baka hakuri, wlh na gane kuskure na, don Allah ka daina wahalar da ni mana, nafa san kana sona har yanzu." ta faɗa tana yi mashi farfari da idanunta. Hakan da tayi ba ƙaramin sace zuciyar shi ta yi ba. "Ka yi shiru bakace komai ba," Ta fada da yar shagwa6arta. Ɗagowa ya yi suka hada ido cikin na juna wani kallon so da kauna suke jefawa junan su, bakomai take tuna mashi ba face Unaisah. "Wallahi wannan karon idan ka mayar dani, zan yi maka biyayya sau da ƙafa, zan tarairayeka kamar jinjiri, yanzu fa na canza ba Benazir din da ka sani ada bace, ka ga yanzu na iya girki, na iya gyara gado, na iya wanki, wlh har wanka zan dinga yi maka...." Duk yadda ya kai ga hana kanshi sakar mata fuska baisan sa'adda ya tuntsire da dariya ba, saboda kalamanta sun bashi dariya, kuma dagaske take fada masa babu wasa akan fuskarta. "Oh, kina nufin yanzu kin gane an halicci hannayenki don ki girka ma ƙato abinci?" Ya fada tare da ɗage mata gira, dariya ta saki har dimples dinta ya lotsa. "Bama iya girki ba, komai zanyi masa." Tabe bakinsa ya dan yi. "Yakamata ki tafi suna jiranki." Ɗan bubbuga kafafunta ta yi kan floor, "Taya zan tafi baka bani amsa na ba?" "Zamu yi magana a waya" Ba don ta so ba tace, "ka yi mini alƙawari?" Jinjina mata kai ya yi. "Okay, ka rama min kiss da na yi maka." Zare idon shi ya ɗan yi bata jira amsar shi ba ta manna mashi peck ta juya tana dariya ta nufi Kofa, bin bayanta ya yi da kallo har ta bace ma ganin shi. ________________________________________✍️ Around ƙarfe tara na dare, Benazir ta fito daga bedroom dinsu, hannunta a ruƙe da wayarta, har ta sanya kayan bacci a jikin ta, sai dai baccin ya ƙauracewa idanunta, a hankali take tafiya yayin da zuciyarta ke ta azalzalarta akan ta kira Taj ta faɗa masa abunda ta kasa sanar da su ɗazu, sai dai tana matuƙar jin shakkar ta fitar da sirrin gani take kamar zai koma masa ne, amma in ta tuna halin da Aisha ta shiga, da irin uƙubar da Dr Shureim Ya sha akan yarinyar sai kawai ta ji ƙwara ta fada kawai ko da hakan zai yi silar rasa rayuwarta ne, ta ma san ko bata fada ba, hakan bazai hana a cigaba da yunƙurin kashe ta ba. Tana Ƙoƙarin juyawa ta koma ɗaki ta ji motsin shigowar mutun Falon, da sauri ta kai idanunta ga duban shi, Alhaji Musa ne ya shigo cikin takun nan nasa na izza yake tafiya fuskarsa ba annuri, ya zuba hannayensa cikin aljihun wandon shaddar Jikin shi, hakanan ta tsinci kanta da jin faduwar gaba, cikin sauri ta juya da sauri ta faɗa bedroom din ta, kamar munafuka ta dinga leƙen shi, waro ido ta yi ganin ya dan dakata da yin tafiyar, alamun ya ji ajikin shi ana kallon shi, jikinta na kerma ta datse kofar ɗakin. A hankali yake bin ko'ina da kallo, ganin ba abunda ya yi zata bane yasa shi gyaɗa kai ya cigaba da tafiya Ya nufi part dinsa. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hadiyar yawu, tunani ta soma yi a ina yakamata tayi wayar cos bata so wani ya ji koda kalma ɗaya da zata furta ne. Ɗaura idanunta ta yi akan Zeenatu da ke a kwance kan bedmatress tayi nisa acikin baccin ta, Cikin tafiyar sanɗa ta nufi gadon ta janyo duvet ta lullu6e mata jikinta gaba daya. har ta nufi toilet zata shiga sai kuma ta fasa, tunawa da babu kyau yin magana acikin toilet. Gaba daya kanta ya ɗaure, tsoro take ji, ga shi abun ya dameta so take kawai ta fallasa sirrin da ta daɗe da shi a cikin zuciyarta, ba zata iya jira gobe ta yi ba. Akan Mirror Chair ta zauna, ta fara danna wayar ta kira layin Taj ta kurawa screen din wayar idanunta tana jiran ya yi picking. Lokacin da kiran ya shigo layin Taj, yana a kwance kan gadonsa har ya fara bacci kiran ya katse shi. Kasantuwar ya aje wayar a kusa da kunnansa, ransa a ɗan 6aci ya janyo wayar ko da ganin kiran Benazir cikin sauri ya daidaita nutsuwar shi. Bayan yayi picking ya kara wayar a kunnansa. Ko sallama bata yi mashi ba ta ce, "shine ko ka kira ka tambayi mun isa lafiya ko?" Cikin disasshiyar muryarshi ta wanda bacci bai ishe shi ba yace, "I'm sorry Ummu Unaisah, wlh kuna araina, tun dazu nake ta zucci zuccin in kira ku.." Da shagwa6a ta ce, "Hankalinka kwance ma bacci kake yi, Ni gani nan damuwar rashin ka a kusa dani ta hanani runtsawa sai faman tunanin ka nake yi" Har cikin ranshi ya ji dadin kalamanta, murmushi ya yi, "Waya fada maki ni ban damu dake ba? Nima kin tafi kin barni da tunanin ki, da zarar na rufe idanuna ke nake gani," Sautin dariyarta ne ya cika kunnan shi. ( Allah sarki tsohuwar Zuma😂 har wani ƙara kankame pillow yake yi a kirjin shi, da alama Benazir tayi winning heart din Taj.) "Ina babynmu?" "Tana a bedroom din su, may be ta yi bacci" "Okay," shiru su ka dan yi jimm har saida ya furta, "Akwai wani abu da kike son fada mini ne?" Cikin sauri ta ce, "Eh dama dazu akwai tambayar da ku ka yi mini ban samu na amsa maku ba, saboda Yaya Shureim yana a wurin bana so yaji..." Cike da zumudi Taj ya ce,"Okay, Ina sauraron ki Ummu Unaisah" Calmly Ta soma ba shi labari. "Kafin dawowar mu Jos, A lokacin ina a gidan Uncle Musa, ban kai ga sanin komai da ya faru tsakanin Yaya Shureim da Aisha ba, na ta6a kama Uncle yana yin wata waya ta sirri, wuraren karfe ɗaya na dare ban runtsa ba, dama dabi'atace idan ina yin Chatting bana yin bacci da wuri, to adaren ranar na fito daga ɗakina dake a cikin gidan sa, hannuna ruke da wayata ina tafiya ina yin chat da niyyar daukko ruwa, gaba daya na shagala har na sauko down batare dana ankara ba, Na shiga zagaye falon gidan kafin na nufi walkway din da zai sadani da backyard din gidan na tsaya, kwatsam kunnuwana suka soma jiyo mun muryar mutum yanayin waya ƙasa kasa kamar baya son wani ya ji shi, a firgice na kalli saitin inda nake jin maganar sa a hankali cikin sanda na karsa bakin kopar da zata 6ula da kai bayan gidan, a zaune na hango shi kan ɗaya daga cikin kujerun shaƙatawar dake a wurin, a lokacin na dan ji tsoro saboda ban tsammaci zanga mutun a irin wannan lokacin ba, amma sai na dake saboda ina son in san wanene kuma ina son jin wayar mecece ya ke yi a tsakar dare! Ni abunda yafi daure mun kai duk rooms din dake acikin gidan da falo ya rasa inda zaiyi waya sai a backyard, hakan yasa na dasa masa alamar tambaya, aikuwa cikin sanɗa na matsa gaban tukwanan furannin da ke a bayanshi na zukunna tare da kasa kunnena ina sauraron shi. "Kada ku bari ta yi 30 Mins a cikin ramin, zamu iya rasata ne, ku kasance a ankare, da zarar kun ga jami'an sun tafi da shi, kuyi hanzarin haƙa ramin ku ɗauko Jinjirar, Sannan bayan kun cire ta daga ciki, Ku kashe daya daga cikin karnukan ku, Ku je ku zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin" Lokacin da naji wannan maganar wani irin faduwar gaba na ji duk da ban fahimci inda zancen nashi ya dosa ba, gaba daya nabi na rude amma a haka na toshe bakina na cigaba da sauraron shi saboda ina son inji karashen zancen na shi. "Bana so a samu matsala, dole sai kun yi taka tsantsan! ka da ku yi gangancin da wani zai gan ku, idan ba haka ba kun sauran sauran," Ya faɗa tare da yin rejecting call din ganin ya miƙe yasa na yi saurin zuƙunnawa ƙasa da rarrafe na dinga tafiya cikin sanɗa sai da na ga nayi nisa da backyard din, tukunna na mike da sauri na koma dakina na ja kofa na datse. Aranar na kwana da tunanin wacece naji Uncle Musa yana bada umarnin a haƙa ramin da take a ciki a curo ta? Kuma yace a kashe kare a zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin? Menene manufarsa ta yin hakan?" A lokacin gaba daya na ruɗe, na kasa gane komai, dakyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ni, tun daga ranar ban kara samun kwanciyar hankali ba, saboda tunanin wayar dana kama Uncle musa yanayi atsakar dare, zuciyata ta dinga azalzalata akan in tunkare shi in tambaye shi game da wayar da na ji yanayi, sai dai tsoro da fargaba sun hanani yin hakan, bayan haka bansawa raina wani mugun abun ya ke yi ba saboda na yarda da Uncle Musa, daga baya ma sai na watsar da zancen na cigaba da yin harkokin gabana. Taj da ya kasa kunne yana sauraronta, tuni ya mike zaune saboda mamakin daya daure zuciyar shi. Benazir ta ɗaura da cewa, "Lokacin da na kudiri Aniyar saina gano koma wanene ya shiga tsakanin Ya shurem da Aisha, da kuma munafukin da ya ƙulla mata makirci a ƙasar Germany, Lokacin da na saci hanya na shiga dakin Aunty Zainab na tambaye ta meya faru a tsakanin Dr Shureim da iyayen mu saboda ina zargin bakomai suka faɗa mana ba, bayan zainab ta fayyace mini komai, Hankalina atashe na koma ɗaki na, inata wasi wasi akan wayar nan dana ta6a kama Uncle Musa yana yi a bayan gidan sa, sai da na zurfafa tunanina nayi dogon nazari kafin na gano wayar nan fa da Uncle musa yake yi akan babyn Ya Shureim ce. Amma abun da ya ɗaure min kai shine Meyasa Uncle Musa zai yi haka? A raina na ayyana ko dai yana son ya yi mashi hankaline saboda rashin hankalin da ya yi na binne ƴarsa, amma kuma dana kara yin tunani sai na gano wannan fa yafi karfin abunda nake hasashe, ganin an dauki kwanaki Uncle Musa baida niyar fallasa shi ya dauki yarinyar, bayan da kunnanshi ya ji irin bakar wahalar da Ya Shureim yasha bayan ya binneta kuma ya yi danasani, to amma meyasa da farko Uncle Musa ya nuna baisan komai ba? Bayan mun yi waya da Ya Shureim har ya fada mini yasha jaraba kiran layin wayar Uncle don ya nemi taimakon sa, amma baya samun shi, tun daga nan ne na fara zargin da akwai wata mummunar manufa atare da shi. Ban tunkare shi da maganar ba, saboda a lokacin ka zo mini da maganar zaka turo magabatan ka ayi maganar auren mu, shiyasa na watsar da maganar na bar komai araina. Bayan mun yi aure da kai, A lokacin Daddyna har ya samu nasarar lashe zabe ya zama gwamnan jihar wanda tun da ya hau mulkin bai ƙara lafiya ba, saboda ciwon ƙafa da ya matsa mashi, ba irin maganin da ba'ayi mashi ba amma ciwon yaki ci yaƙi cinye wa. Wani iko na Allah da zarar an fita da shi kasar waje don a nema masa lafiya sai ciwon nashi ya warke, amma da zarar an dawo da shi Nigeria ciwon na shi yake komawa sabo, a karshe da yan jam"iyarsu suka fahimci ciwon nashi bame ƙarewa bane, sai suka shawarce shi da ya aje mulkin yaje ya nemi lafiyarsa, Shekara daya yayi kafin ya sauka, zaman Jahar ya gagare shi silar hakan iyayenmu suka koma Dubai da zama, Ni kuma saboda auren da na yi ne yasa suka barni a Jos. A lokacin Uncle Musa ya zama Shahararran dan siyasa, ganin sa yayi mini wuya saboda bai cika zuwa Jos ba tun da iyayen mu suka koma Dubai, ya ɗaga ƙafa da zuwa Jos daga Abuja sai ƙasashen waje, Kuma duk in na kira phone numbers dinsa bana samu. A ƙarshe na yanke shawarar tura mashi text message, na rubuta mashi komai dana ji ya fadi a cikin wayarsa, sannan na yi mashi barazanar ko dai ya dawo da babyn Shureim, Ko kuma in tona masa asiri a gurin Daddy da Mommy har da ma Ya Shureim din. Da tura mashi saƙon ko minti biyar ba'ayi ba, sai ga kiran Uncle Musa ya shigo wayata, na yi mamaki sosai saboda tunda nake kira ba'a picking. Bayan na ɗaga ko sallamata bai amsa ba ya ce, "Benazir! Ni za ki yi ma kazafi? Yaushe kika ji ina yin wannan maganar? Bayan haka ni miye haɗina da yarinyar Shureim da har zansa a binno ta daga rami? Me zanyi da gawa..."? Bai ƙare maganar ba na ce, "Haba Uncle, wlh baka isa ka raina mini hankali ba! Da kunnena na ji ba gaya min a ka yi ba, Wlh babyn Shureim tana araye kuma ta na a gurin ka, Kai kasan inda ka kaita, kuma na rantse idan har baka dawo masa da ƴar sa ba, saina tona maka asiri.." Ina ƙarashe maganar na kashe wayar, cike da saran zai neme ni. Aikuwa ba zato ba tsammani a yammacin ranar da na yi waya da shi sai ga kiran shi ya shigo waya ta, a lokacin baka a gida, bayan na ɗaga kiran na ji yace in fito wajen gidana ya turo da escort dinsa yana jirana a cikin Mota. Na ɗan ji fargaba amma da ya ke lokacin ina jin tashen rashin ji, bana jin fargaba kuma bana jin tsoron tunkarar koma uban wanene. Batare da saninka ba, na bi Escort dinsa acikin mota ya kawo ni guest house din Uncle Musa dake anan Joss. Bayan na fito daga motar, escort din ya rakani har cikin falon gidan, Ina shiga na taras da shi a zaune saman Sofa ya ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, fuskarsa kwata kwata babu annuri kamar bai taba dariya ba, Nima na haɗe rai fiye da yadda ya haɗe ta shi fuskar, tunkafin ya bani iznin in zauna na samu guri kan sofa din dake fuskantar shi, na zauna tare da ɗaura ƙafata ɗaya kan ɗaya hakan ba karamin daure mashi kai ya yi ba. Tambayar farko da ya yi min shine in fada masa gurin wa na ji maganar dana fada masa?" Na ce in har yana so in fada masa to ya fara kawo min Babyn Shureim. Lallashina ya fara yi duk dan in faɗa masa, na sanya kaifi nace wallahi ya daina wahalar da kanshi saboda bazan faɗa ba, dole sai ya fara kawo mini yarinyar. Shu'umin murmushi ya saki tare da cewa bai damu ba in je in fada ma duk wanda zan fadamawa, saboda bani da hujjar da zan iya tuhumar shi, balle har in tona masa asiri, kuma in bi a hankali in ban iya kama barawo ba sai barawon ya kama ni.." na yi dariya hada shewata na ce, "Ka bani mamaki Uncle, ina yi maka kallon mutumin kirki ashe kai din mutumin banza ne! Ka yi zaton bansan komai ba?" Na faɗa ina zare mashi idanuna, a lokacin yanayin fuskarsa ya sauya zuwa tsantsar al'ajabi da rudani. "Benazir Ni kike kira mutumin banza? Ido cikin ido batare da jin shakkata ba? Kin manta matsayina agurin ki?" Harara na galla masa, "Na je na fada Uncle, Wallahi Hakkin Aisha bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba, Ka cuce ta Ka cuci Yaya shureim ka kuma cuci Babyn da suka haifa"! Ina magana hawaye na shararowa kan kuncina. "Ashe dama duk kyautatawar da ka yi mana ba don Allah bane, sai don saboda wata mummunar manufa taka, baiwar Allah Aisha saida ta nuna batason zama agidan da ka kama mana haya a kasar germany saboda hankalinta bai kwanta da shi ba, sannan ta nuna rashin jin dadin ta akan zaryar da kake yi cikin gidan duk weekend sai ka zo ka kwana ga kudi da kake kashe mana, ni da kaina na kare ka agurinta na nuna mata cewa kada ta damu Uncle dina mutunne mai son yin alheri kuma dukiyar ka ta halal ce kasuwanci kake yi, sai daga baya na gano komai, arzikin da kake taƙama da shi ba ta hanyar halal ka tara shi ba, mu ka raina ma wayau da sunan kasuwanci kake yi, bayan haka ina zargin kana a ƙungiyar asiri ta yan shan jini, kuma kaine ka haɗa Aisha da mahaifinta, wato ka yi amfani da damar da kake da ita, a lokacin da kake zuwa ka kwana a gidanmu, sai ka bari dare ya yi sai ka saci hanya batare da sanin mu ba ka ke shiga ɗakin Aisha, ka dauketa video da hotuna, wama ya sani ko asiri kake yi mata shiyasa har batasan kana yi mata hakan ba, wallahi ka ci amanar yardar da na yi maka! kuma na rantse da wanda raina yake a hannunshi in har baka dawo mana da babynmu ba saina fallasa asirin ka...." Tun kafin in ƙarasa maganar, Uncle Musa ya doka min tsawa yana huci kamar mayunwacin zaki, saboda tsabar fusata da bacin rai jikin shi ya dinga fitar da gumi, abun da ya daure mashi kai ya kuma ɗaga hankalinsa shine ta yaya akai duk nasan abunda yake ƙullawa?" Sam ya kasa magana sai huci yake fitarwa, Idanunsa sun kaɗa jawur. Ganin baida niyar yin magana yasa naci gaba da cewa, "Kuma kaine ka shiga tsakanin Yaya Shureim da Aisha, ka yi masa asiri kasa yayi mata fyaɗe ba'a cikin hayyacin sa ba, komai dake faruwa kana bin diddiginsu kana samun information a gurin yan leƙen asirin ka, Hatta Mahaifinmu baka ƙyalesa ba, kana amfani da sihiri gurin juya shi don yabi ra'ayin ka, bayan haka kaine ka turama Daddy videos din Aisha daka dauka tare da kai sai ka 6oye fuskarka don karsu gane kaine kabar fuskar Aisha saboda tsabar mugunta da zalunci irin naka! kuma kai ne shaidanin da ya tunzura mahaifinmu akan karya kuskura ya yarda Shureim ya auri Aisha in ba haka ba zai rasa kujerar da yake nema kuma mutane zasu juya mashi baya saboda abun kunyar da Shureim ya akaita, munafukin Allah kaita faɗa masa kauli da ba'adi har saida ka shiga tsakanin daddy da Ya Shureim...". Ban kai ga ƙarasa maganar ba ya katse ni ta hanyar bugun table din gabansa da hannunsa, Jikinshi har wani jijjiga yake yi saboda bacin rai. "Benazir! Bana so ki jefa rayuwarki a cikin hadari! Ina mai gargadin ki, Tun wuri ki yi gaggawar janye zargin da kike yi mini, tun kafin ki yi danasani" Na yi tsalle na dire na ce, "Wlh Uncle bazan janye ba, saboda ni akan gaskiyata nake, ba zargin ka ni ke yi ba, tabbaci gare ni, kai baka yi mamakin tayaya akai nasan sirrinka ba uhum? Na faɗa ina kallon cikin idanunshi, wlh a lokacin ya razana dani ba kadan ba, amma da yake shu'umin mutunne sai ya dake ya tirje akan cewa ba gaskiya nake fada ba, ƙazafi nake yi masa. raina a 6ace na juya zan bar falon ban ma jira ya karasa maganar shi ba, har na kusa fucewa Ya dakatar dani ta hanyar kiran sunana na tsaya ina jiran jin me zai ce. "Ki fada mini komai kike so a duniyar nan zan yi maki shi, amma maganar zaki tona min asiri bata taso ba, Ki yi watsi da maganar nan, nifa Uncle dinki ne, In kika tona mini asiri kamar kin tona ma family din mu ne, ki dawo mu sasanta tsakanin mu" A hankali na juyo na fuskance shi. "Baka so zaman lafiya ba Uncle, ai wlh in har kana son sasanci to ka dawo mana da babynmu, ni kuma nayi maka alkawarin babu wanda zaiji maganar nan! Ni ita kadai nake so bandamu da abunda kake aikatawa ba, wannan tsakanin ka da Allah ne, duk wanda ya yi da kyau ya sani, kuma dai akwai mutuwa akwai hisabi kowa zai girbi abunda ya shuka ne..." Dafe kanshi ya yi da tafin hannunsa kamar mai fama da ciwon kai, "Meyasa kin fiye taurin kai da kafiya ne? Yakamata ki iya bakinki Benazir! Har yanzu bakisan wanene ni ba! Sabo da kaza bai hana in yankata! Wlh zan iya salwantar da rayuwarki, kuma idan na kashe ki na kashe banza." A lokacin gabana ya faɗi na kuma sha jinin jikina amma ban bari ya gane hakan ba, saima na yi dariya na ce, "Idan ma kana tunanin kashe ni shine mafita agare ka, to ka daina, saboda hujjojin dana fada maka ina da su, bani kadai ke da su ba, Nima ina da mutanene da nake yin aiki tare da su, idan yau ka kashe ni, wlh zasu fallasa asirin ka ne duniya tasan me ka ke aikata, ka ga kuwa baka da wata mafita da ya wuce ka bini ta lalama" Maganar da na yi ta ɗaga hankalinsa matuƙa, Zuciyarshi ta hasala kamar ya rufe ni da bugu haka yake ji. Har na ɗaga kafa zan fuce na sake tsinkayar muryarsa a cikin kunne na, "Ko don saboda abun da ke a cikin ki, Yakamata ki yi takatsantsan idan ba haka ba, zaki jefa rayuwarsa a cikin haɗari ne..." Wani irin faduwar gaba na ji, saboda a lokacin bansan ina ɗauke da juna biyu ba, cikin sauri na dafe cikina tare da zare idanuna akan fuskar shi, gaba daya na bi na ruɗe, Murmushin mugunta ya sakar mun saboda ya gano lago na.. "Benazir, nafi karfin ki nesa ba kusa ba, wlh baki isa ki ja dani ba, ƙaramar yar iska mai kwana da wando, saboda baki da hankali ki rasa wa zaki tuhuma sai ni? Kinsan wanene ni kuwa?? Ki fara sanin wanene ni kafin ki yi ja in ja dani, Sannan zan ƙara tuna maki, kina da miji, kina da juna biyu, kina da iyaye, kuma kina da ya ya mafi soyuwa a gare ki, Ina fata Kin fahimci abunda nake nufi???" Yana karasa maganar ya juya ya nufi up batare da ya sake waiwaye na ba, har saida ya 6ace ma ganina kafin na kawar da idanuna daga barin kallon sa. Har na dawo gida ban daina tariyo maganarsa a cikin kunnena ba, Saboda hankalina ya tashi sosai, Lamarin Uncle Musa ya fara bani tsoro, na riga da na gane mugun mutunne shi, mara imani, kuma tantirin shaidani nasan zai iya aiwatar da komai don ya rufawa kansa asiri.. Bayan sati biyu na je ganin likita batare da saninka ba, bayan doc yayi mini gwaje-gwaje sakamakon ya nuna ina dauke da ciki na sati biyu, nan fa hankalina ya ƙara tashi kwata kwata ban yi farin ciki da cikin ba a lokacin saboda zai zama rauni na, kuma ina jin tsoron in haife shi saboda fargaban kada Uncle Musa ya salwantar da rayuwarsa, Ko ya ɗauke sa kamar yadda ya dauke ɗiyar Ya Shureim, wannan dalilinne yasa nayita yunkurin in zubar da cikin Angel, wlh Allah shine shaidata badan bana son shi ba, Kawai a lokacin muna yawan samun sabani da kai saboda bani da kwanciyar hankali, Damuwa tayi mini katutu, kullum cikin zullumi da fargaba nake yi saboda nasan Uncle Musa bazai ƙyale ni ba, kamar yadda ya fada dole ya dauki mataki akaina, kuskuren da na yi shine ƙin sanar da kai, Na ƙi faɗama kowa nabar abun a matsayin sirri, saboda gudun kada na faɗa ya koma mashi karshe inja ma kaina da kuma dangina don har lokacin ban saduda na kyaleshi kan fito da yarinyar Yaya Shureim ba, ka ji dalilin da yasa a duk lokacin daka kamani ina yunkurin zubar da cikinta ka tuhume ni dalili, sai ince maka bana son ya'ya, kuma bana son cikin saboda zai bata mini shape ɗin jikina, Amma a zahirin gaskiya bada son raina ni ke yin hakan ba, gaba daya rayuwar aurena da kai wani abun sai daga baya na gane bayin kaina bane, nasan bana jin magana, amma wlh Taj na so mu yi zaman lafiya sai dai na kasa faranta maka, saima cuzguna makan da nake yi hakanan bakai mini komai ba, kawai sai inji haushin ka, da tsanarka acikin Zuciyata, hatta mai aikin gidanmu Janet na ji na tsane ta, laifin da bai kai ya kawo ba idan ta yi mini bana ƙyale ta, saina azabtar da ita...." Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan da ya ƙwace mata, Haƙiƙa Zuciyar Taj ta karaya, tsantsar mamaki da al'jabi sun ruke zuciyar shi tamau, duk da sanyin A.c din dake a dakin hakan bai hana shi fitar da zufa ba, jikin shi har tsuma yake yi, wani irin tausayin Benazir ne ya kama shi ya yi danasanin zarginta da ya dinga yi, ashe bayin kanta bane, makircine aka shirya mata. Numfasawa ta yi, cikin shesshekar kuka ta ci gaba da cewa, "Bayan wani lokaci, ban ƙara jin ɗuriyar Uncle musa ba, har lokacin da cikin Unaisah Ya cika wata tara cuf, nima kuma ban ƙara tuntubarsa ba ko in yi tunanin sanar da wani game da sirrin, a tunanina saboda bana son in jefa rayuwar ahalina Cikin hadari ne, a daren ranar da naƙuda ta kama ni, da ni da kai muna a kwance kan gadonmu mun yi nisa a cikin baccinmu, kwatsam ba zato ba tsammani, na fara jin naƙuda na taso mun, a firgice na farka daga baccin hannayena daddafe da cikina, ina ta faman cizon le6e saboda radadin da nake ji a jikina. Zufa duk ta wanke jikina, naita kokarin kai hannu don in tashe ka daga bacci amma nakasa, na yi kokarin in yi koda addu'a ne nan ma abun ya ci tura saboda haƙorana sun game gam, Taj ban ƙara sanin me ya faru dani ba, nadaisan bana a cikin hayyacina na sauko daga kan gado ina jan ƙafa na tura ƙofar toilet na shiga. Wlh Taj haihuwar Unaisah ikon Allah ne, kwata kwata bana a cikin hayyacina a haka na kar6i haihuwana da kaina amma bansan na yi ba, bansan dame na yi amfani gurin yanke cibin ba, a lokacin dana haifeta saida na kalleta cikin jini, na rungume abuna ina kuka tana kuka, abun da nake ta gudun in haifa sai gashi na haifeta, kuma sai na ji na kamu da ƙaunarta fiye da komai na duniyar nan, ina tsaka da kallonta, Kwatsam na fara jin ana ambaton sunana da wata iriyar murya mai matuƙar tsoratarwa, kuma nan take na dinga jin bakin ciki a cikin zuciyata, na ji na tsani komai in har ban je na amsa kiran da bakuwar muryar ke yi mini ba zan iya rasa raina ne, saboda yadda tsigar jikina ke tashi kamar ana tunzurani, yadda kasan ana zare raina ban ma san sa'adda na kwantar da Unaisah cikin bathtube ba, cikin hanzari duk da rashin ƙwarin jiki na fuce daga cikin toilet din, ko waiwaye ban yi ba na nufi gate, baba mai gadi yana adakinsa yana bacci baisan na fita ba, saboda wani ƙarfine ya zo mini bangaza ɗaya na yi wa kofar jikin gate din mu dake a kulle nan take ta buɗe nasa kai na fuce da gudu na bi santar mu. Ban ƙara sanin meya faru ba, sai dai na wayi gari na ganni a kwance kan gadon asibiti magashiyan rai a hannun Allah, bayan dana dawo hayyacina na tambayi nurses din dake kula dani akan meya faru da ni? anan suke faɗamin wani matashi ne ya bankaɗe ni da motarsa akan titi shine ya kawo ni asibitin, abun da ya ɗaure mini kai, ni da na ke a Jos meya kawo ni Abuja? Ban sanya damuwa araina ba saboda lokacin burina kawai in yi nesa da dangina saboda bana son su a kusa da ni.💔 Tun kan ta ƙarasa bashi labarin ya soma ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! cikin karyayyar Murya ya ce, "Benazir! Dama haka komai ya faru baki ta6a sanar da ni ba? Kika sa nayi ta zargin ki, Ya Salam!! Pls ki yafe mini"! In a cool voice ta ce, "Ba laifin ka bane, rashin sanine ya jawo hakan, Nima ka yafe mini 6ata maka rai da na yi a zaman mu na aure.." "Ki manta da komai ya wuce, saboda ke ma bayin kanki bane, Ina tunanin Uncle dinki shine Ummul aba'isin komai da ya faru, yanzu ina so ki faɗa mini kece kika tura min sakon In sake ki!" "Bani bace Taj, saboda ni ban tafi da waya ba, ni bansan wanene yayi mini hakan ba amma ina zargin Uncle Musa, saboda bayan na dawo gida Daddy da Mami sun faɗa min ana tura masu sakonni ta layin wayata, wai hada sakon da nace ni na gudu da son raina kuma na shiga duniya kada suyi tunanin zan dawo gare su kuma kada su sha wahalar nema na..." Dafe kai Taj ya yi da tafin hannunsa, Idanunsa sun kaɗa jawur da su. "Benazir, Ni kuma saƙon da aka tura mini da bakuwar number ne, Idan bazan manta ba, abun da aka rubuta a cikin sakon shi ne ka sake ni Taj, kuma kada ka yi tunanin zan dawo na tafi kenan har abada, har kiran layin na yi amma saina ji shi a kashe kuma daga ranar ba'a ƙara tura min saƙo ba, tun ina sa ran dawowarki har dai na fidda rai" Fashewa ta yi da kuka tana fadin, "Shiyasa kowa ya ƙullace ni aranshi saboda ana zargin da son raina na tafi, Koma wanene ya yi min hakan bazan ta6a yafe masa ba, Allah ya isa wlh sai Allah ya yi min sakayya, lallashinta ya shiga ya har ya samu ta yi shiru, shima ya yi shiru na ɗan wani lokaci, sai sautin Numfashin junan su da suke ji ta cikin wayar, so yake ya bata labarin rayuwar Unaisah a gidan Kurkukun ƙaddara saboda Yana zargin dasa hannun Uncle dinta sai dai ya kasa saboda baya son ya ƙara ɗaga hankalinta, ganin halin damuwar da ta shiga, gaba daya ya fahimci bibiyar rayuwar su ake yi, tun daga kan Benazir, da Aisha da Dr Shureim, da kuma Iyayensu suma ba'a ƙyale su hakanan ba. Jin shirun ya yi yawa ne yasa shi tunanin ko ta yi bacci ne . "Benazir?" In a low voice ta ce, "Na'am' "Pls, Ki kwantar da hankalinki, nasan ba zaki rasa ciwon kai ba saboda kukan da kika sha, dan Allah kada ki sanya damuwa a ranki, maganar Uncle din ki zan faɗa ma Chief in sha Allah, duk yadda mu ka yi da shi zamu tuntu6e ku, yanzu ki kwanta ki yi bacci..." Bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa, "Don Allah Taj, ku taimaka mana, har yanzu ina ji araina Babyn Shureim tana a raye, kuma tana a gurin Uncle, shi kadai yasan inda ya aje ta, amma nasan in har kuka yi bincike akan shi zaku gano komai..." Kwantar mata da hankali ya cigaba da yi saida suka raba dare suna yin waya kafin suka yi sallama, A daren ranar Taj bai iya runtsawa ba, saboda maganganun da suka tattauna da Benazir sun hana shi sukuni, har dai ya gaza jurewa ya kira layin Chief saboda yasan ba lallai bane idan ya yi bacci ba saboda a irin lokacin yana yawan tashi yin nafila, Cikin sa'a Chief ya yi picking call dinsa, a nan ya sanar da shi sun yi waya da Benazir, ya ce ya duba whatsapp dinsa ya tura mashi recording din da ya ɗauka na tattaunawar da suka yi, Chief ya amsa mashi da toh. Bayan Chief ya kammala sauraron audio din da Taj ya tura masa, har sujjada saida yayi saboda nuna godiyarsa ga Allah da ya fara kawo masa sauƙi a cikin lamuransa ya kuma ƙara yin addu'ar neman nasara akan abun da suka sa a gaba. After Two days, ana gobe za'a yi family meeting, kiran sallar asubahin farko Private jet din Prime minister ya yi landing a Airport, Mai girma Sharafuddeen tare da Security details dinsa ne suka je dauko su acikin dankara dankaran motocin su, wannan karon daga shi sai Escorts dinsa suka zo Nigeria batare da iyalinsa ba, kuma bakowa ne yasan da zuwan nashi ba sai family dinsa, ko yan jarida ba a bari sun san da zancen zuwan na shi ba. Kaitsaye suka wuce Vila da shi, Sai da ya fara huce gajiyar da ya kwaso, Har bacci ya yi a dakin ɗan uwansa Sharafudden kafin zuwa marece suka shigo Estate. Gaba daya yan'uwansa suka hallara a main falo din baba Obie don su tarbe shi, Yana shigowa falon suka nufe shi cike da tsantsar farin cikin ganin shi, ɗaya bayan daya suka dinga yin hugging dinsa, burinsa ya ƙarasa ga mahaifinsa sun hana shi motsawa kowa ɗokin ganinsa yake yi. Daƙyar ya samu suka kyale shi ya nufi Baba Obie dake ta sakar mashi murmushi ya rungume shi kamar zai maida shi cikin jikin shi, su Hajiya Saratu baki yaƙi rufuwa saboda murnar ganin Yaya Hateem, kowa ya buɗe baki sai ya tambaye shi ina iyalinsa? Meyasa bai zo da su ba? Ya ce masu su kwantar da hankalinsu suma zasu zo ne, amma a halin yanzu gimbiya da su Yazrin sun tafi Dubai gurin danginta hidima ce gare su, ita kuma Faryat bata samu hutun makaranta ba, shiyasa bata samu damar zuwa ba. Lokacin da marece ya nutsa, sai ga kiran his excellency Abdul razak ya shigo wayar Baba Obie ya sanar da shi sun ƙaraso Abuja yana a aiport, Batare da 6ata lokaci ba Baba Obie ya tura da motocin Escorts suka dauko shi, bai jima da ƙarasowa ba sai ga motocin His excellency Deen na Kaduna sun iso cikin Estate din. Sun yi farin cikin sake haduwa da yan uwansu saboda sun yi kewar juna, Baba Obie sai haba haba yake da su, saboda murna bakinsa ya ƙi rufuwa. A daren ranar saida suka raba dare suna hira da mahaifinsu kamar ba zasu yi bacci ba har saida Baba Obie ya ce suje su kwanta su huta tukunna suka yi sallama da shi, Hateem dai ruƙe shi ya yi a ɗakinsa yace tare zasu kwana saboda ya yi kewarsa, hakan ba ƙaramin dadi ya yi ma Prime minister ba, a kan gadon Baba Obie suka kwanta, zai kwana da tunanin mutumin da ya kwallafa rai da son ganinshi, ɗazu da Chief ya zo gaishe da shi har tambayar shi ya yi ina baby boy dinsa? Yana lafiya? A lokacin hankalin Chief ba karamin tashi ya yi ba, amma saboda baya son ya ɗaga masa hankali yasa shi cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya, amma baya a gidansa yanzu, yana a camp din su na isod, yana kar6ar training. Dakyar ya samu ya shawo kan Hateem har ya haƙura da maganar Danish amma fa yace duk yadda za'a yi kafin ya koma yana son ganin sa. ~________________________________🍁~ *_🔥🔥🔥The Chief Owais Birthday Celebration and Family Gathering🔥🔥🔥_* *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~___________________________________~ fashewa tayi da matsanancin kuka sam ta kasa buɗe baki ta yi magana saboda bakin cikin tsinuwar da mahaifinta yayi mata, bata taba zaton zaiyi mata haka ba ko da kuwa ta aikata abunda ya ke zargin ta da shi, ta rasa gane wanene yayi mata kazafi? Laifin me tayi masa"? A lokacin Aunty Laura kasa jurewa tayi, tana jin koda zai sake ta ne sai tayi magana, Cikin fushi da nuna bacin rai tace"wallahi ka bani mamaki baban Aisha! Idan rai ya baci ai hankali bai kamata ya gushe ba, shin Ina ilminka ya ke da har zaka bari shaidan da zuciya su rinjaye ka! Kai fa ba mahaukaci bane, Da hankalin ka amma tayaya za'ay wa yarka kazafi ka yarda harka dauki mummunan mataki akanta...." bata kare maganar ba, sakamakon Marin daya kifa mata akan kuncinta, tuni hawaye sun cuccuko tab da idanunta, taji zafin marin da yai mata. Ganin hakan Yasa Maids din gidan suka sha jinin jikinsu, daya bayan daya suka bar falon zuciyarsu cike fal da tausayin Aisha da babynta. Murmushi Aunty laura tayi tana kallon cikin idanunshi da suka kada jawur sai tsuma yakeyi yana huci.. "Bazan fasa magana ba wlh, ko da zaka kashe ni ne! Wlh ka bani kunya kuma ka bani mamaki, sannan kaji kunya wlh, Tun wuri kayi gaggawar janye hukuncin da kayi ma Aisha tunkafin kayi danasani! Abune da ka sani na sani, kai da Aisha kuna da makiya masu jin haushin daukakar da Allah yayi maku kai baka tunanin sune suke kokarin 6ata maku suna? Bayan haka videos din da kake ikirarin an nuna maka ka ganta da ƙato Ka duba dakyau ba fuskarta aka dauka akayi editing ba"? Ta jefa mashi tambayar tana akai masa harara sam baya fahimtarta, ya riga daya hau kan dokin zuciya.. Sassauta muryarta tayi"yakamata ka dinga amfani da kwakwalwarka da kuma saninka, idan Aisha batayi abun kunya ba, to kai ne zakayi babban abun kunya, haba Imam ko da ace Aisha ta aikata laifin da kake zargin ta, kai ba maiyi mata uziri bane kaja ta ajiki don ta shiryu, korarta da za ki yi shi ne mafita? Hmm duk dai inda Aisha zataje Yarka ce, Kuma kowa yaganta zai ce diyar imam malik ce, Kaga kuwa babu ribar korarta! bana so kayi danasani mara amfani ...." Kalaman Aunty Laura sunso suyi tasiri acikin Zuciyarshi, Amma duk idan Ya tuna abun da idanunsa suka gane masa sai yaji wani irin kunci a cikin zuciyar shi, saboda shi yasan wacece Aisha, yana da tabbacin videos din da aka nuna mashi ba editing bane itace da kanta" Sheikh Imam bai dauki hudubar Aunty laura ba, ya ce ma Aisha ta tashi Tabar mashi gidan shi! baya bukatar ganinta, yana karashe maganar ya fuce yabar gidan. Maids din da Aunty Laura suka kewata sunata aikin lallashinta da bata hakuri, bata taba ganin bakar rana irin ta yau ba, har addu'a tayi Allah ya dauki ranta ta huta amma dayake Lokacin mutuwar nata baiyi ba sai bata mutun ba. Kasa tafiya tayi saboda bata son ta tafi, mahaifinta Yana fushi da ita, ga tsinuwar da yayi mata, tafi son Ta roki yafiyarsa inyaso saita tafi. Tsawon kwana uku tana zuwa dakinsa donta bashi hakuri bai ta6a sauraronta ba, Ko gaisuwarta baya amsawa, gaba daya ya ɗauke ƙafa da yi mata magana, ko kallon ta bai son yi. Aunty laura ta yi kokarin ta tunbi Hajjonsu don ta sanar da ita abunda ke faruwa don tasan ita kadaice zata iya take mashi burki A lokacin da take kokarin kiran layin Hajjo batasan sheikh Imam Ya shigo dakin nata ba, aiko batai aune ba, taji ya fusge wayar ya Maka ta da kasa ya take ta da kafarsa, yana huci ya gargadeta akan in ta kuskura ta fada ma wani wlh abakin auren ta, ba arziki taja bakinta tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido. Aisha ta shiga tsaka mai wuya, damuwa takusa tayi mata illa ko ma ince tayi mata illa, da abun ya ishe ta, ta kunna wayarta sakonni sukai ta tururuwar shigowa, ko ɗaya batayi sha'awar budewa ba ta lulubo layin Anila ta danna mata kira, don bata jin zata iya fadama Benazir saboda sun fita aranta batason komai daya shafe su. Lokacin da Anila taga kiran malama Aisha tayi mamaki bayan tsawon watannin data dauka bata neme su ba. Bayan ta daga kiran tayi ta tambayarta meyasa ta yada su? In sun kira basu samun layinta, kuma tayi tafiya ko sallama ba ta yi masu ba. Cikin shesshekar Kuka Aisha ta kwashe komai daya faru ta sanar da Aneelerh, Aneelerh Tayi kuka taji bakin ciki da takaicin abunda dr shureim yayi mata, Duk da tasan ba halinsa bane, kuma taji zafin Hukuncin da baba Imam yayi ma Aisha, sannan taji tausayinta sosai, Aisha tace mata tayi danasanin zuwanta germany karatu saboda anyi mata kazafi an daura mata laifin da bata aikata ba, Hankalin Aneelerh ya tashi sosai har tace mata zatazo gidan tare da Abie da Mami donsu tayata bashi hakuri ya yafe mata. Cikin sauri Aisha tace karta kuskura ta fada masu halin da take a ciki, Baba Imam yana da bad temper idan ransa ya 6aci baya ji baya gani sai daga baya ya ke yin danasani, Idan har yasan ta fada mata abunda ke faruwa da ita, to kuwa zai kara hukuntata ne, amma ta roke ta akan ta tayata da addu'a in sha Allah komai zai tafi daidai. badan Aneelerh taso ba tace mata toh amma dan Allah kar ta tafi ta zauna agidan, idan ma ya matsa mata akan ta bar masa gidan toh toh tazo gidan su ta zauna, Aisha tace mata toh. Bayan sun kammala waya Aneelerh bata ƙara samun kwanciya hankali ba, saboda zullumi da fargaban kada Aisha ta tafi, gashi ta hana ta faɗa ma Benazir halin da take a ciki ta kuma hana itama tazo gidan saboda gudun kada laifinta ya shafe su. Tayi azan Baba Imam zai sassauta hukuncin daya yanke mata, Ganin har anyi kwana biyu bai kara yi mata maganar ba, haka Aunty Laura ma tayi tunanin yaji nasihar ta ne shiyasa ya ƙyale Aisha, Hankalin su har ya dan kwanta. a daren wata ranar Alhamis, tana tsaka da yin bacci, ta rungume babynta da ke bacci akan kirjinta, Sai ga sheikh Imam Ya fado dakin Yana huci Ya tashe ta daga bacci Yace ta tashi tabar gidan bai son ganinta, Ta yi nesa da shi idan ba haka ba zai kashe yarta, Ya tsaneta baya son ganinta kuma wlh in har ta bari wani yasan tayi cikin shege ta haihu Sai Ya lahantata, tace mashi baba kada kayi min haka! Idan ka kore ni a cikin daren nan ina kake tunanin zan tafi? Bayan ka hana in nemi taimakon dangin mu, nifa yarka ce baba, amana ce agare ka, nasan da mahaifiya ta, tana araye wlh koda ace ni karuwace ba zata kore ni ba, saima taja ni a jikin ta don in shiryu, balle kai da ka taso tare dani ka sanni ciki da bai, ka tarbiyantar dani, kuma ka yarda dani amma a yau kaine kake korata? Saboda kaddara ta afka min? Bai Saurareta ba, Tana kuka ta sauko daga kan gadon, ko Aunty laura bata sani ba adaren ranar shekh imam Ya kori aisha daga gidan Har bakin gate Ya rakata Bata dauki komai nata ba sai yar wayar data tsira da ita. a bakin gate din gidan Alhaji Ubaid ta tsaya hannayenta rungume da jinjirarta dake ta sharar baccinta. Tana kuka Ta kalli sararin samaniya taga hadari ya hadu bakikkirin Babban tashin hankalinta kada a barke da ruwa sama batasan Ina zata sanya yarta ba. Anan ta yanke shawarar kiran dr shureim duk da bata da tabbacin yana nan ko bai nan don tunda abun nan ya faru bata kara jin duriyarshi ba tun da ba fita ta ke yi ba, wayarta kuma akashe take, ko ya kira ba sani zatayi ba. sau uku tana Kira baya Picking, sai ana hudune taci sa'a yai picking tace"shureim ina a kofar gidanku, Baba Imam ya kore ni daga gida, Ka zo ka kar6i yarka, idan ba haka ba zaka rasata ne"! Tana karasa maganar, ta kashe kiran. Ko mintuna biyar ba ayi ba sai ga dr shureim Ya fito jikin shi sanye da jallabiya, kallo daya da yayi ma Aisha saida gaban shi ya fadi ganin yadda ta rame idanunta sun kaɗa jawur sun kumbura, A lokacin yaji kunyar hada ido da ita kamar ya haƙa ƙasa ya binne kanshi, tsantsar tausayintane ya kama shi sam bai ma lura da babyn hannunta ba. Karasawa yayi kusa da ita, harya bude baki zaiyi mata magana ta dakatar da shi"ban kiraka don muyi magana ba, Yaya shureim nagode da abunda ka saka min da shi," ta fada tare da manna mashi yarinyar da ke a nannaɗe cikin towel dinta a kirjin shi yai sauri rungumeta wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyar shi. "Gatanan Itace abunda muka samu, nabar maka ita amana, badan bana sonta ba na baka ita, sai don bana so tasha wahala tunda ni yanzu bani da kowa banma san inda zan tafi ba, wata rana zan dawo in kar6i abuna, Inaso kayi mata huɗuba da sunan mahaifiyata FATIMA BATOOL, Idan har kabari rayuwarta ta cutu ka sani Allah yana sama yana Kallonka, Nima kuma bazan yafe maka ba, akwai ranar hisabi" maganganun Aisha sun karya mashi zuciya, baisan sa'adda ya fashe mata da kuka ya dinga yi mata magiya akan kada ta tafi tabarshi wlh yana sonta ashirye yake da ya aureta yayi mata alkawarin zai wanke laifinsa zai share mata hawayenta, zai kula da rayuwarta, tace mashi ya makaro, Lokacin daya kamata ya furta mata hakan ya riga daya wuce, sai bayan daya 6ata komai, sannan ita bazata taba auren namijin daya santa ba. Ba yadda baiyi da ita ba amma ta kafe, har cewa yayi ta shigo ta kwana agidansu amma takiya, ta juya zata tafi yabi bayanta yace sai dai su tafi atare saboda bazai iya rayuwa batare da ita ba, sannan Yar da tabar masa, shi baida abunda zai shayar da ita ta taimaka ta dawo suyi aure su rufawa kansu asiri da kuma yarsu. Aisha bata saurare shi ba, da taga dagaske Dr shureim binta zaiyi sai ta watsa da gudu Shima yabita aguje a karshe ta bace ma ganin shi... 😭 Tun daga wannan Lokacin dr shureim bai kara ganin Aisha ba, babu wanda yasan Ina ta dosa, Anila saidai taga sakon data tura mata. _Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu."_ A daren ranar bayan Dr shureim Ya koma da baby cikin gidan, batare da sanin kowa ba, Ya nufi daki da ita Ya kwanta kan gadonshi yayin daya rungume Yarshi a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da bakin cikin abunda yayi ma Aisha shine silar komai, yaji takaicin tafiyarta, yaji kunci da radadin rasata da yayi. Dakyar ya samu nutsuwa, ya buɗe fuskar babyn ya zuba mata idanunshi da suka kada jawur yadinga kallonta kamar zai hadiyeta, A hankali ya sumbace ta a saman forehead dinta da cheeks dinta, wani irin tsantsar sonta ne ya lullu6eshi kamar ya mayar da ita cikin shi, a kalla ya shafe rabin awa yana kallonta, aranshi ya ayyana inama ace ta hanyar aure suka same ta da sai yafi kowa farin cikin zuwanta duniya, amma ahakanma Ya gode ma Allah daya bashi ita, addu'o'i sosai yayi mata har yai mata huduba da sunan*FATIMA BATOOL* Bai tashi sanin yana a cikin musibaba, Saida Ta farka tsakar dare ta fara tsala kukan Yunwa, A firgice ya farka ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi duk yabi ya Ruɗe, ya sungumeta akan kafadarshi ya sauko daga kan gadon ya dinga zarya da ita a tsakar dakin yana lallashinta haɗi da jijjigata. Sakamakon kukan data dinga tsalawane Yaja har mutanan gidan suka farka daga bacci, Cike da mamakin jin kukan jinjira a cikin gidansu. Da gudu Suka nufo Dakin Dr shureim Alhaji ubaid da hajiya layla sai Mai aikinsu zainab, suna shigowa suka iske shureim ya rungume baby a kirjin shi. Cike da mamaki suka tambaye shi yar wacece? Donsu kwata kwata basu san Aisha ta haihu ba, sun dai san abunda ya faru tsakaninta da shureim. Jin yayi shiru bai basu amsa ba yasa hajiya Layla ta doka mashi tsawa tace shureim ba kaji ina magana ba? Yar uban wacece wannan"? Cikin sanyin murya yace"ƴata ce, babyn da Aisha ta haifa mince, Baba Imam ya koreta daga gidansa, shine ta kawo min ita jiya da daddare" Bai ƙare maganar ba Hajiya layla tayi tsalle ta dire tace"Wlh bazata sa6u ba! Shegiyar zaka kawo mana acikin gida? So kake kaja mana surutu agurin mutane? Wato shi uban nata ya koreta saboda gudun abun kunya sai mu zaka jajubo mana annoba ka kawo mana agida? Saboda baka da hankali"? Ta inda take shiga bata nan take fita ba, Kamar zata rufesa da bugu, Kalamanta sun Kona ransa, musamman data kira yarsa da sunan shegiya, bai kula ta ba hankalinsa na akan fatima dake ta kuka surutunsu Ya kara hargitsa kwakwalwarta duk tabi ta rude ga yunwa tana ji. Alhaji Ubaid Yace"shureim, kayi hakuri da abunda zance, badan bana son jininka ba, sai don gudun abun kunya, kuma kaga an kusa fara zabe in har maganar nan ta fita wlh za ka ja min asara ne, don Allah ka dauki yarinyar nan ka kaita gidan marayu su kula maka da ita, Inyaso sai ka dinga zuwa kana dubata..." sai a lokaci Ya fuskance su da wata irin fusatacciyar murya yace"ɗan ku ne shegen da yayi wa uwarta ciki ta haifeta, wallahi ba inda zan kaita! Ban taba sanin baku da imani ba sai yau da kuka nuna min, Yarinyar nan koba dan kasancewarta jinina ba Yakamata ku tausayamata, Jaririya ce fa? Ta rasa mahaifiyarta, ni kadai na rage mata, ya kuke so tayi da rayuwarta ne"? Idanunsa cike tab da kwalla yai maganar. Aunty Zainab tayi kokarin tayashi fadan amma Hajiya layla ta koreta daga dakin ta fuce tana kuka saboda sun bata tausayi. Kusan dare suka raba ana abu daya, kowa yana akan bakanshi. Hakika dr shureim Yaci wahalar Iyayenshi, kullum sai sunyi barazanar kashe mashi ƴa in har bai fitar masu da ita daga gidan ba amma Yakiya. wulakancin yau daban na gobe daban Sun daura mata karan tsana ba gyaira ba dalili, Aunty zainab ce ke shayar mashi da ita a boye batare da sanin su ba. Hajiya layla har ɗaukar babyn tayi batare da sanin shi ba, ta fuce da ita daga cikin gidan, a lokacin yaje masallaci yin sallah sai da ya dawo ya duba dakin shi bai ganta akan gado ba, ya fito arude yana nemanta, Aunty zainab ce ta fada mashi taga hajiya layla ta shiga dakin shi, tana da tabbacin itace ta ɗauke ta, hankalinsa ya tashi, ya dinga kiran layinta bata picking, time data dawo cikin motarta ta shigo gidan ya nufeta yana huci yace ina yarshi tace tabada ita sadaka. Ji yayi kamar ya dauketa da mari, ya dinga rokonta akan ta dawo mashi da yarshi tayi banza ta kyale shi, yai hakuri Ya jira time da Alhaji ubaid ya shigo gidan, ya tuntube shi da maganar ya dinga rokonsa akan ya yi ma mommynsu magana ta dawo masa da yarsa, Alhaji ubaid bai kulasa ba saima yace tayi abunda ya dace. rai a6ace Ya nufi Kitchen Zainab tana a ciki tana yin girki taga yashigo ya dauki wuka Ya fita da ita aguje tabi bayanshi. A lokacin Hajiya layla tana a zaune kan kujera tana danna waya batai aune ba, taji ya ɗaura mata wuka a akan wuyanta, ta zare ido gabanta na faduwa, shureim yana huci yace"kodai ta fada mashi inda takai mashi baby, ko kuma ya kasheta" adabarbarce tace"nashiga uku shureim ni zaka kashe? Mahaifiyarka? Saboda kawai na kawar da ƙazantar zina daga cikin gidan mu"? Ihunta da Alhaji Ubaid ya ji yo ne yasa shi watso wa da gudu Yafito daga dakin shi ganin abun da Shureim ke kokarin yi ne Ya tada hankalinsa kafin Ya karaso Shureim Yace"kana karasowa zan hada dakai in kashe!" ba arziki Alhaji ubaid Yaci burki yana lallashin shi akan ya aje wukar zasu dawo mashi da yar shi, Zainab tana kallon komai dake faruwa, ko kadan bata sa baki ba, saboda taji dadin barazanar da Shureim yayi masu, tun da su ba Allah aran su. Hajiya layla data gama tsorata cikin shakakkar murya ta fada mashi sunan gidan marayun data kai Batool. Sakin wukar yayi da gudu Ya fuce daga gidan Cikin motar shi Ya tafi. Kafin marecen ranar sai gashi ya dawo da babynsa, ya rungume abunsa a kirjin shi, baiwar Allah tayi kuka har ta gaji idanunta sun kada jawur dakyarma ya samu Caregivers din dake rainon yaran suka bashi ita, saida ya basu cin hanci harna Dubu dari shidda kafin suka damka mashi ita. Abun da ya ɗaurewa shureim kai, Mugayen halayan da iyayensa suka sauya wanda ada ba haka suke ba, har kwara hajiya layla yasan tunfil azal bata da mutunci, batason talaka, ta tsani talauci, ga girman kai, amma mahaifinsu Alhaji ubaid ba halinsa bane, Shi shaidane babansu mutumin kirkine amma tunda ya faɗa harkar siyasa ya canza shima, Ya rasa gane meke faruwa ne? Duk wannan badakalar da aka sha Benazir bata sani ba, ko awaya inta kira su don su gaisa ko suka kira donsu gaisa da ita babu wanda ya taba gigin faɗa mata. don wlh da ace ta sani zasu sha ruwan mamaki saboda masifarta, har hajiya layla data gado shakkarta take ji, zata tsayama shureim ne kuma babu wanda ya isa ya ɗaga ma yarsa yatsa agidan. Shureim harya fara tunanin sun hakura, ganin kwana biyu basu bi takanshi ba, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba, ashe wata wutar bala'en ce zasu kunna mashi. Alhaji Ubaid yasa aka kulle mashi bank account dinsa, Ya hana shi abincin gidan shi, duk wani abu da yayi mashi a matsayin uba saida ya kwace shi, hada key din motarsa ya kwace ya kasance baida ko sisi, ita kuma zainab da hajiya layla ta gano tana shayar da yarsa kuma tana satar abinci aboye takai ma shureim aikuwa tayi mata shegen duka da girmanta da komai ta kuma koreta daga gidan gashi bata da kowa a nigeria danginta da komai suna a egypt haka tayi ta gagari cikin gari. Dr shureim ya shiga matsananciyar damuwa, da shi da yarshi suna a tsaka mai wuya, Ya rame yayi duhu, Itama jinjirar ba lafiya, ga yunwa da rashin bacci, kwana su ke yi idon su biyu har rokon su yayi kan su taimake shi kada ya rasa yarshi suka kiya saima su ka ce In har yana so su mayar masa da komai nashi da suka kar6a to ya mayar da Batool gidan marayu, kusan kullum sai ya jaraba kiran layin Uncle musa don ya fada masa halin da ya ke a ciki saboda yasan shi kadai ne zai goyi bayansa sannan ya taimaka masa amma ko ya kira layin a kashe ya ke samun shi, baisan ya zaiyi ba, ga Hajiya layla tace in har ya kuskura ya kira wani nata don ya taimaka mashi Allah ya isa bata yafe ba shiyasa ya kasa kiran Ammin su. Baida wata mafita daya wuce ya gaya ma Allah, A karshe ya dauki yarsa yabar masu gidan. Ko a jikinsu damuwarsu daya kada su rasa dan su amma donta yarinyar basu damu ta mutu ko tayi rai ba. Baisan Ina zai nufa da ita ba, a wannan zamanin bakowane zai kula maka da dan ka tsakani da Allah ba, gashi bakowa ya sani a joss ba, saboda rabi da kwata na rayuwarsa a gurin amminsu yayita can Kasar egypt. Tafiya ya ke yi Jikin shi ba kuzari, ya rungume babynsa a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da tunanin makomar rayuwar yarsa. Tuntana kuka har ta gaji tayi shiru bacci ya ɗauketa, kwatsam aka fara ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ya rasa ina zai sama masu mafakar da zasu zauna, Baiwar Allah tana tsaka da baccinta ruwa ya farkar da ita, Ta dinga tsala kuka ya rasa ina zai kaita don kada ruwan yai mata illa. a karshe dai ruwan gaba daya akansu ya ƙare, Har dare ba adaina ruwan ba, saida daren Ya tsala ruwan Ya dauke a lokacin Ya ma fidda rai da ita saboda Zuciyarta ta daina bugawa Jikinta ya saki. Anan ne ya yanke shawarar binneta, Saboda yaga baida wata mafita, in har ya barta wahala zata cigaba da sha, mutane ma ba zasu kyale ta ba za'acigaba da tsangwamarta ne tunda har iyayensa sun shegantata sun kirata da kazanta inaga mutanan waje? Kowa ma zai samu kwarin gwiwar cuzguna mata ne idan ta girma, kwara ya saukaka mata ta huta itama, yasan in ta mutu Allah zaiji kanta. A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacin shi kamar ya fara zaucewa, Da hannayenshi Ya haƙa rami, Ya sakata a ciki ya kwantar da ita yayi mata addu'a, Yana kallon yatsun kafafunta dake motsi alamar bata mutuba, amma Ya rufe ido saboda bayason taci gaba da shan wahala Ya rufe mata kasa a jikinta ya daddale gurin da kafafuwan shi, anan ya zauna kamar mahaukaci yaci gaba da sambatu shi ka ɗai daga bisani ya suma akan kabarin ta. Bayan sati Biyu da afkuwar lamarin, Dr shureim Ya farka a gadon asibiti, ya fara lalubar Yarsa Yaji shiru babu ita a jikin shi, Yabi ya rude hankalin shi Ya tashi, ya sauko daga kan gadon Yana fadin Ina yarsa! Ina fatimarsa! Ina batool dinsa! Tana Ina"? Likitan dake dubashi Ya rurruke shi Yana kokarin kwantar masa da hankali, aikuwa ya bangaje shi da karfi har saida doc din Ya kife kasa. Hajiya layla Da Alhaji Ubaid da ke a waje suna jiran tsammani, muryarsa da suka jiyo daga cikin dakin yana kwala ma batool kira yasa suka yi saurin shigo cikin dakin, yana ganin su ya nufe su yana tambayar su Ina yarsa take? Ta na ina? Hajiya Layla tace suma basu san Inda ya kai ta ba, abun da ya faru bayan ya bar gida suka baza jami'ae don su nemo shi, cikin sa'a jami'an suka tsintoshi a sume a gaban wata bishiya, amma basu ga yar shi ba, shine suka garzaya da shi asibiti, Yau sati biyu kenan baya a cikin hayyacin shi.." sai da tayi wannan maganar ya tuna da abunda ya aikata ma Batool, wani irin jiri jirin tashin hankali Ya gani acikin idanun shi, ya dinga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un kamar maganarsa zata kare! wai mike faruwa da rayuwarshi kamar wanda akayima jifa? bala'i daga wannan sai wannan. Bai karasa jin zancen ba, Ya watsa da gudu Ya fito daga asibitin, suka biyoshi a cikin motar su, Ya dinga gudu kamar zai fadi kasa, har titi Ya hau mota ta kusa bankade shi Allah ne dai Ya tsare shi dakyar Ya gano gurin da ya binne ta, Ya zube kan gwiwowinsa, Jikinshi na kerma Ya haƙa ramin wani irin faduwar gaba Yaji ganin kasusuwanta, Harta mutu ta rube kashinta kadai ya rage, daddafe kanshi yai da tafukan hannayen shi saboda matsanancin ciwon kan da yaji, nan Take Ya yanke jiki ya fadi a sume. A lokacin motorsu Alhaji Ubaid ta karaso gurin da yake, bayan sun fito suka taras da shureim rai hannun Allah, ga ramin daya haƙa abude sai kasusuwa birjik a cikin sa. Basu tsaya bata lokaci ba, Alhaji ubaid Ya dauke shi ya shigarshi da shi cikin motar, suka koma asibiti da shi. Tun daga wannan Lokacin shureim bai kara hankali ba, ya zama mahaukacin karfi da yaji, bayagajiya da sambatu yana fadin wayyo Allahana, na kashe Batool, da hannuna na binne ta acikin rami, Batool ta mutu ta zama kashi, Naci amanar da aisha ta bani, Allah bazai barni ba" sai da takai ga ko sallah shureim bai iyayinta cikin nutsuwa, A lokacin Hajiya layla da Alhaji Ubaid sun ji tausayin shi sun kumayi danasanin tilasta mashin da sukayi akan yarinyar gayanan sun ja ya binneta ta mutu, shi kuma Ya haukace. saida ya shafe wata daya bai dawo daidaiba, A lokacin Hajiya layla ta dawo da zainab mai aikinsu gidan tana daya daga cikin masu bashi kulawa duk da baya acikin hayyacin shi tayi kokarin tambayarshi meya faru? A haukan nashi Ya fayyace mata komai, tayi bakinci sosai sai dai bata ga laifin shi ba, saboda tasan me yaja mashi ya aikata hakan, haka ta dinga kokarin kwantar mashi da Hankali. Ganin za6e ya kusa ga mutane sun fara yi masu surutu akan Halin da shureim ya shiga duk da kullan da sukeyi mashi amma an asamu wasu daga cikin ma'aikatan gidan sun fitar da sirrin su a boye, Hakan Yasa suka yanke shawarar tura shi Egypt, to a lokacin ya ɗan fara dawowa hayyacin shi tunkafin ma suje mashi da maganar ya tattara yanashi yanashi batare da saninsu ba ya tafi egypt saboda bayason zama tare da su sun fita aranshi, bayan ya isa ne ammin su ta kira hajiya layla ta sanar da su shureim yazo sai dai bata gane meke damun shi ba, ko magana ba ya iya yi mata. Hajiya layla tace ta taimaka ta lallashe shi sannan ta bashi kulawa, ya samu tabin hankali ne sakamakon buguwar da kanshi yayi garin tukin mota ya yi accident har jinya yayi a asibiti. Karya da gaskiya ta dinga fada mata har ammi ta yarda da maganarta tace in sha Allah zatayi kokarin bashi kulawa, hakan ba karamin dadi yayiwa hajiya layla ba. Bayan komawarsa egypt ya gaza jure radadin da zuciyarshi keyi mashi kullumne sai yayi mafarkin Batool a cikin rami tana kuka, Hakan ya ƙara dagula mashi lissafi har takaishi ga fadawa harkar shaye shaye ya zama cikakken dan kwaya. _(Kunji alakar dake atsakanin Ummi da su Benazir da kuma shiekh Imam malik, da kuma kaddarar datayi silar rabuwar su da ita, Bayan haka duk wata sa'insa da dr shureim yakeyi da iyayenshi bayan dawowarshi daga egypt a lokacin dayaji sauƙi ya dawo hayyacin shi ya kuma daina shaye shaye, wannan rashin jituwar ta samo asaline daga abunda sukayi mashi, yana yawan furtawa hajiya layla sune silar masifar daya shiga, ita kuma tace basu bane saboda lokacin da zai aikata bai yi shawara da su ba, bayan haka Hotunan da yake yawan kallo acikin wayarshi hoton mutun biyune! Hoton Aisha da kuma hoton Yarsa Batool daya ta6a dauka a wayarsa, ko bayan dawowarsa Nigeria bai yarda yarsa batool ta mutu ba, saboda a lokacin duk in zaiyi mafarki da ita araye yake ganinta ba amace ba, sannan kasusuwan daya gani a cikin kabarinta yana kokwanton bana mutun bane kamar na kare ne, bayan haka yana mamakin yarda tayi saurin zama kashi in two week da binne ta❗ shiyasa yake zargin akwai wata makarkashiya, amma daga baya ya hakura da tuhumar iyayensa Ya dauki dangana, Benazir bata tashi sanin abunda Ya faruwa ba saida ta baro gidan Uncle musa aranar ma tare da shi suka zo joss din da iyalinsa Sara da kanwarsa Hajiya laura dake zaune agidansa, anan sukaji komai daya faru abakin Alhaji ubaid sai dai bai bayyana masu ukubar da su ka yiwa shureim da yarsa ba, sun dai fadi laifin shureim na binne Batool da yayi, Uncle musa ya nuna rashin jin dadin shi har fada saida yayi masu akan sakacin da sukayi har suka bari shureim ya binne yarsa, Benazir kuwa saboda bakin cikin abunda shureim yayi ma Aisha da kuma yar daya binne saida tayi jinya gadon asibiti saboda tana da fusatacciyar Zuciya, bayan da aka sallame ta daga asibitin ne, ta taka taje har gidansu anila ta rufe ta da fada akan boye matan da tayi, anila tay ta kokarin fahimtar da ita cewa ba laifinta bane, Aisha ce ta hana ta sanar da ita saboda gudun abun da zai biyo baya in mahaifinta yaji ta fitar da sirrin, aranar saboda fadan daya kaure tsakanin Benazir da anila saida mami da abie suka rabasu dakyar bayan sunci uban juna, abie ya tambayi meya hadasu faɗa, anan Anila ta fayyace masu komai, hankalinsu ya tashi matuka basuji dadin abunda ya faruwa ba, Ita kuma Benazir acikin labarin da Anila tabada nan taji wani abu daya ɗaure mata kai tamau har ta kudiri aniyar saita gano koma wanene ya shiryama Aisha da yaya shurem makirci, saboda ta gane ba laifinsu bane, tuggune aka shirya masu, musamman ita Aisha da aka yi mata kullalliya tun a kasar germany, bayan Benazir ta dawo gida, batare da sanin kowa ba, ta shiga dakin zainab mai aikin su ta tsare ta da tambayoyi akan ta fada mata meye faru tsakanin shureim da iyayen su saboda taji aranta bakomai suka sanar da su ba, anan zainab ta fayyace mata komai, bayan ta baro dakin zainab din ta koma nata dajin ta dauki waya ta kira dr shureim a lokacin duk yana a egypt, cikin sa'a ya daga kiran bayan tayi ma shi ta'aziyar babaynsu da suka rasa ta bashi hakuri tare da lallashin shi, har ya tambaye ta agurin wa taji nan ta labarta ma shi komai, har tace yaya shureim meyasa baka sanar dani ba? bayan haka meyasa da suka matsa maka baka dauki yarinyar ka kaima Aneelerh don ta ruke maka ita ba? Yace mata baiyi tunanin hakan ba, saboda a lokacin baya acikin hayyacin shi komai ya faru, ta kuma tambayar shi meyasa me kira uncle musa ya nemi taimakonsa ba, yace mata ya kira amma baya samun shi, a karshe tace mashi kada ya damu, in sha Allah zata dawo mashi da farin cikin shi, a lokacin bai gane maganar ta ba, har dai su ka yi sallama da juna Sauran bayani game da abun da ya faru zamu ji ne abakin wanda ya dace muji👍)_ Gaba ɗaya suka bita da kallo yayin da take ƙarasa saukowa daga kan stairs ɗin ta nufe su Jikinta na 6ari yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta. cikin raunanniyar murya dr shureim ya furta"Aisha dama Kina nan"! Muryar mutumin da yai silar tarwatsa rayuwarta, tun kallo daya da tayi ma shi tayi saurin kawar da idanunta akan su Benazir. Anila data gama rudewa tace"Aisha kece dagaske Nake Gani? Aisha dama Kina nan da ranki da lafiyarki baki ta6a tunanin ki waiwaye mu ba? ko awaya baki taba kiran mu ba, ko mun kira bama samunki! kullum layinki a kashe! aisha Kinsan Irin radadin danaji saboda tafiyarki? Laifin me mukayi maki Aisha dayaja har Kika manta damu arayuwarki, kika zabi kiyi nesa damu bayan alkawarin da mukayi ma juna duk runtsi duk wuya zamu kasance atare, Why Aisha? Kinbar mu da zullumin ina kika tafi? Kina araye ko kin mutu? Awani hali kike Ciki...."? Kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata kamar ranta zai fita. Idanunta akan na Aisha wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa ya ke yi kamar mazari, ga hawayen dake yar tseral kan kuncin ta. Cikin shesshekar Kuka Benazir tace"baki kyauta mana ba Aisha! Kinci amanar amintakar mu, a zatona In matsala ta same ki nice mutun ta farko daya kamata ki fara tuntuba sai bakiyi hakan ba, tsawon shekara goma sha takwas baki waiwaye mu ba, ban ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zatazo ki juya mana baya ba, sai gashi tazo Aisha.."! Kasa karasa maganar tayi saboda zafin da zuciyarta tayi mata ta fashe da kuka, Taj dake ta kallon su duk da baisan me ya faru da su ba, jikin shi yayi sanyi kawas, zuciyarshi ta kwaɗaita da son jin labarin Alakar dake a tsakanin su, Ummi tana ƙarasowa gaban su Benazir da Anila suka rungumeta kamar zasu mayar da ita cikin su, Jikinta ne yayi sanyi lakwas tausayin junansu ya kamata, they had deeply missed each other, more than words could express cike da sanyin jiki a hankali ta daura hannayenta akan bayansu, suka haɗa kawunansu Jikin na juna suna ta kuka babu mai lallashin wani, idanunsu arurrufe sai ruwan hawayen da ke shararowa ta cikin su. "Aisha, ashe da rabon zan sake ganin ki a rayuwata"? Ya faɗa yana kallonta har time din bata raba jikinta daga nasu Benazir ba, tsawon mintuna kafin a hankali suka raba jikinsu daga na Juna. Komai daya faru arayuwarta take tunawa, gani take kamar a yanzu komai ke faruwa, Kallon kallo suke jefawa Junansu tsakaninta da Anila da Benazir, sunyi mamakin haduwar bazatan da sukayi. Taj dai Ya rasa gane takan maganganunsu, duk yabi ya rude sai binsu da kallo yakeyi .. Dr shureim duk ya Sha jinin jikin shi ganin kamar bata son kallon shi, fargabansa kada ace har yanzu bata yafe masa ba. Lokacin da Idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassaruwa, tayi mamakin manyantakarsa, ba kamar yadda ta tafi ta barshi ba, Ya ƙara girma ya kuma ƙara kyau, su ma sunyi mamakin Sauyawar da Aisha tayi, ta zama babbar mace, dirin jikin nan nata yana nan ya ma kara ninka na da. Dakyar ya iya furta"Aisha, na gaza yarda cewa kece nake gani, dan Allah ki yi min magana ko na gasgata kaina" Ya faɗa idanunsa cike tab da kwalla. "Nice ya Shureim..." bai jira ta karasa maganar ba, ya furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! ya ambaci hakan Yafi sau a kirga kafin ya zube kan gwiwowinsa tare da daura goshinsa kasa yayi sujudusshukur cikin harshen larabci yake yiwa Allah kirari tare da hamdala saboda bayyana masa Aisha da yayi,.Lamarinsu Ya daurewa Taj kai Ya rasa gane meke faruwa, sun bar shi a duhu. Mikewa yayi ya mayar da duban sa agare ta, Cikin karyayyar murya dr shureim Yace"ba irin neman da banyi maki ba, Allah bai nufa zan ganki ba, har yau bandaina kallon hutunanki ba, kuma har yau bandaina jaraba kiran layin wayarki ba don inji ko zai shiga amma ban ta6a samun ki ba Aisha, Kin manta damu, amma ni ban manta dake ba, You're always in my nightly prayers" Lumshe Idanunta tayi tare da bude su A hankali kan fuskar shi, Ji yake kamar yayi hugging din ta ko ya samun sassauci nadaga abunda Zuciyarshi ke ji a game da ita, Sam sun kasa Daina kallon juna, ita kadai tasan me take ji "Dan Allah Aisha ki bude baki kiyi magana ko munji sanyi a cikin ranmu" Aneelarh ce ta fada tana share kwalla. Numfasawa tayi kafin ta furta"Ya shureim Where's my baby, ina Fatima Batool dina? Has she grown up? Is she attending school? Have you told her about me? Does she know about me?" Gabansu ne Ya faɗi rass! gaba daya suka sha jinin jikinsu, Da jin abunda tace sun fahimci bata su take ba, Yar da ta bari itace aranta. Sunkuyar da kanshi yai kasa sam Ya kasa bude baki Ya furta kalma saboda fargaban halin da zata shiga! Hankalinta ne Ya tashi jin yayi shiru bai furta mata kalma ba. "Ya shureim kayi shiru bakace komai ba? Inason ganin ta fiye da komai na duniyar nan! Nasan yanzu ta girma, a lissafina zata kai shekara goma sha takwas...." bata ƙare maganar ba, ganin hawaye na shararowa kan kuncinsa, aruɗe ta dubi su Benazir daga yanayin fuskarsu ta fahimci wani abu ya faru. "Benazir, Ina fatima na? Nasan kin kula min da ita, saboda na yarda dake, nasan ba zaki taba bari jinina ya wulakanta ba, dan Allah ki fada min ina take? Inason naganta! Ku kai ni gurin ta! Sunkuyar dakai kasa Benazir tayi, idanunta cike tab da kwalla. Hankalin Ummi ba karamun tashi yai ba, hannayen Anila ta ruko a cikin nata.. "Anila, nasan ba zakiyi min karya ba, pls ina babyna dana barma ya shureim? Keda Benazir wanene Ya shayar min da ita uhm? Waye ya raine ta har ta girma? Na yarda daku nasan ƴata tana samun kulawa a gurin ku, Dan Allah ku fada min tana ina"? Kamar mai faman da tabin hankali, sam babu nutsuwa atare da ita, Yar ta kawai take son gani. Gaba daya maganganun Aisha sun ruɗa Taj, sai binsu yakeyi da kallo daya bayan ɗaya, ya rasa gane inda suka dosa. Dakyar ya iya furta"pls ku zauna, sai kuyi magana atsanake! Kukan Ya isa Haka, bana so inganku a cikin damuwa, duk da bansan meya hada ku ba" "Daddyn Angel, kace suyi min magana Ina babyna take? Sunyi banza sun kyale ni suna ji ina magana"! Tausayin ta ne ya kama Taj, yace"dan Allah ku fada mata Ina babynta ta ke"! In a cool voice shureim yace"kiyi hakuri Aisha, fatima ta koma ga mahaliccinta tun bayan da kika bani ita, badajimawa ba ta rasu....." kasa ƙarasa maganar yayi ganin yadda ta dafe kanta da tafukan hannayenta labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un.. "Kiyi hakuri Aisha, wlh Yaya shureim yayi iyakar bakin kokarinsa gurin ganin ya ruke amanar da kika bashi, amma Allah bai nufa Batool zatai zawaicin kwana ba..." Benazir bata ƙarasa maganar ba, Aisha ta soma ja da baya tana girgiza kanta, wani irin kuncine Ya mamaye zuciyarta, Taji zafin mutuwar yarinyar data kwalla fa rai akai, tayi azan ta girma har ta zama budurwa ashe ma ta rasu. "Pls Aisha, Ki tsaya zamuyi maki bayani, pls, kiyi hakuri ki jure, mu ma munji zafin mutuwar ta, ba yadda zamuyi ne Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan.." Aneelerh da ta dauko maganar, bata kaiga dire ta ba, Aisha ta juya da gudu tana kuka kamar zatayi tuntube yayin da take taka stairs, cikin sauri suka bi bayanta sai dai kafin su karasa tuni ta shige daki ta kuma datse ƙofar. *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* [14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 _*~....................................................................~*_ ~___________________________________🌹✍️~ Around Ƙarfe 10 na safe, Kiran Chief Ya shigo wayar ta, a lokacin tana a zaune kan prayer mat ta nutsu tana yin karatun alkur'anin da ta buɗe akan qur'anic stand, bayan da ta kai aya miƙewa tayi daga kan Prayer mat din, ta ɗauko wayarta da ɗaura kan Pillow ta yi picking Call din tare da kara wayar a kunnanta. "My babe, how're you? i hope you slept well "? Sa'ilin da muryarsa ta ratsa kunnanta wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta. "I'm doing well, thanks hubby, "Okay, Idan baki komai ki same Ni a part ɗina" "Okay Sir" rejecting call din ta yi. da sauri taje gaban prayer mat din ta rufe qur'anin, Bayan ta saka High heels dinta ta fuce ta nufi part dinsa. yana a kishingiɗe kan bedmattress dinsa, single da short ne a jikin shi Ya mike kafafunsa yayin da idanunsa ke a lumshe kamar na mai jin bacci, yau tun da ya farka daga bacci Omar ke ta faɗo masa arai, saboda a duk ranar birthday dinsa Omar ne mutun na farko da ya ke fara turo ma shi happy Birthday greetings tare da Birthday gift, Omar baya so wani ya riga shi taya Chief murnar birthday dinsa, wannan karan Allah bai nufa za'ayi da shi ba. Lokacin da ta karaso bakin Door room din, sau ɗaya tayi knocking kofar ta buɗe, sallama tayi mashi daga ciki tajiyo voice dinsa ya furta"Come In babe" Walking slowly ta nufe shi ta dan tsaya daga gaban Gadon, idanunta akan fuskar shi still bai buɗe eyes dinsa ba suna a lumshe. sumar kan shi tabi da kallo ganin hadadden ducktail haircut din da akayi masa, ya ƙara ƙawata kyawun fuskar shi, ya yi mata kyau daga gani yau akayi masa shi. Sau uku tana gaida shi bai amsa mata ba, tayi azan bacci yakeyi amma sai ta tuna before ta shigo saida ya bata izni. "My Chief, ko ka yi bacci ne? Nayi magana naji ka yi shiru, pls kayi min magana" bata ƙarashe maganar ba, taji ya furta"kin bata min rai Unaisah, fushi nake da ke" Ya faɗa tare da buɗe idanunsa akan fuskarta. Gabanta ne ya fadi adabarbace tace"I'm sorry ban fahimce ka ba, Meyasa ka ke fushi da ni? Laifin me nayi maka"? Saukowa yayi daga kan gadon, hannun sa ruke da wayar sa, ya juya ya nufi tattausan rug din dakin sa, a ruɗe tabi bayan shi da kallo, gently ya zauna akan rug din tare da nuna mata gabansa da yatsan shi"sit here Babe" jiki asanyaye ta zauna tana fuskantar shi, jikinta duk yayi sanyi ganin mood dinsa ba walwala. Kasa jure kallon da ya ke yi mata tayi, slowly ta kawar da idanun ta gefe daya.. "Meyasa kika tsani mahaifiyar ki? Laifin me ta yi maki? nan take bacin rai ya wanzu akan fuskar ta, her voice barely above a whisper tace"Because she doesn't love me, she hates me, That's why lokacin da ta haife ni ta jefa ni a cikin bathtub, sannan ta gudu ta tafi batare da ta sake waiwaye na ba...." tun da ta fara magana ya nutsu yana kallon smooth pinkin lips dinta har saida ta kai aya tayi shiru tana jiran amsar shi.. "You were rude to her, banji dadin maganganun da kika gaggayawa mahaifiyar ki ba!" ya fada yana mai nuna bacin ran shi "uwa uwa ce koda ta banza ce It's not acceptable to disrespect her!" "Amma bata sona meyasa tayi watsi da ni"? "Ki daina cewa bata sonki Unaisah"! Da yar tsawa ya fada, har saida ta zare mashi gray eyes dinta hakan yasa shi sassauta muryarsa saboda baison ya daga mata hankali "I know you're intelligent and thoughtful, Don't you think there's a reason your mother ran away from you? pls kiyi tunani ta haife ki a tsakar dare a cikin toilet ta kar6i haihuwarta da kanta, ta saka ki a cikin bathtub ta gudu daga gidan ba tare da sanin mahaifin ki ba..." arude ta dube shi gabanta na faɗuwa "Nasan bakomai kika sani dangane da tafiyarta ba, kamar yadda shima mahaifinki bakomai ya sani ba, rashin sani ne yasa kuke fushi da ita saboda kunyi tunani ta gudu ne saboda bata son zama da ku bayan ba haka bane....." gaba daya Unaisah ta rude da jin maganar shi. Audio Recording din da ya ɗauka na Labarin Ummi da Benazir ya kunna mata a wayarsa, ashe ya yi recording batare da sanin su ba. Tun da ta fara sauraran shi yanayin fuskarta ya canza zuwa rudani da tashin hankali, aranta ta ayyana dama Aunty Ummin su Malama ce? Bata taba jin mace mai tausayi da kamun kai da tsantsar ilmin addinin islama irin ta ba, baiwar Allah ashe kaddara ce ta yi silar canza rayuwar ta. Hawaye ne suka cika idanunta tab, tsananin tausayin Aunty ummin su ya kamata, ga wani kaunarta daya shiga zuciyarta, abun daya yafi ta6a zuciyarta a cikin labarin Hukuncin da sheikh Imam ya yanke ma ta, da kuma binne yarinyar da wan mahaifiyar yayi, Abun ya ta6a Zuciyarta sosai, muryarta na rawa tace"ban ta6a jin labarin daya taba zuciyata ba, irin wannan, kuma banyi zaton sheikh Imam zai iya yin hakan ba, a matsayin shi na malami, Aunty ummi ta bani tausayi ita da ya ya shureim, amma banji dadin binne yarinyar da yayi ba" muryarta na rawa ta ƙarashe maganar. "Yanzu inaso ki fadamin, Kafin ki saurari wannan labarin Wani irin kallo ki ke yi ma Aunty Ummin ku"? tamkar zata fashe da kuka tace"tun kafin na santa, Dr. Laura ta america ce ta fara bani labarin ta, tace min karuwace ita, bata da kamun kai, kuma tayi kaurin suna a america, kawai dai ba mutuniyar kirki bace, amma da zama ya hada mu da ita sai na gane tana da sauƙin kai, ba kamar yadda na zata ba, a ranar da ta fara yin karatun al'qur'ani agabana, na razana sosai, har nayi tunanin meya sa bata amfani da saninta take aikata sabon Allah ashe ba halin ta bane, kaddara ce ta afka mata...." ta karasa maganar cikin sanyin murya. "Yanzu fada min meyasa ki ke yi mata kallon mutuniyar banza"! "Rashin sani ne," Gyaɗa kai Chief yayi"haka zalika, itama mahaifiyarki rashin sanine yasa ki ke tunanin ta gudu ta bar ki saboda bata sonki, bayan ba haka bane, itama bada son ranta ba" waro idanu waje tayi, jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, ni na hana mahaifinki yayi maki magana, saboda na daukarwa mommynki alkawarin zan sasanta tsakanin ki da ita, tun shekaran jiya da su ka zo bayan sun tafi, a daren ranar mommyn ki ta kira dad din ki, ta fada masa komai da ya faru da ita, har ma sunsasanta tsakanin su saboda ya gane ba laifin ta bane, may be bai fada maki ba, saboda nace yabar komai a hannu na" ya ƙarasa maganar tare da kunna mata audio din da Taj ya tura masa ya mika mata wayar "Calm down and listen, zaki samu amsoshin tambayoyin da kike nema a gurin mommyn ki..." yatsun hannunta na kerma ta kar6i wayar daga hannunsa tare da kangata saitin kunnanta don ta samu damar ji da kyau. A hankali Chief ke kallon fuskarta yadda take zazzare gray eye balls dinta tare da moving lips dinta ba ƙaramin tafiya yake da shi ba. Bai aune ba Yaga ta zabura ta miƙe, Jikinta na kerma yadda kasan wadda Electric shock Ya kama, wayarsa dake a hannunta sai kerma take saboda jikinta dake kakarwa, Dafe kanta tayi da tafin hannunta, Labbanta na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"! Ganin ta juya arude yasa shi sauri kiran sunanta"Unaisah Ina zaki je ne"? Yarfa hannun ta ɗaya tayi, ta kamo gaban hijab din jikinta ta soma fifita da shi saboda zafin daya taso mata gaba daya ta rude. "Calm down babe, dawo ki zauna muyi magana mana" Calmly ya faɗa idanunsa akan fuskarta dake fitar da gumi kamar babu A.c a dakin. Lokaci daya ta fashe da kuka tana fadin wayyo Allah na, na shiga uku, ina son naga momnyna, Ina son in nemi ya fiyarta, Inaso na bata hakuri! i love her, i really wanna see her..." ganin yadda ta daga hankalinta yasa Chief Ya miƙe tare da kar6ar phone din gudun kada ta kayar da ita kasa, Cikin boxer pocket dinsa Ya zura phone din, kafin ya tallabo fuskarta da tafukansa. "Kalli cikin idanuna Unaisah" dakyar ta iya buɗe idanunta da suka cika da hawaye, cheeks dinta sunyi jawur da su. "Ki daina kuka, Ba laifin ki bane Unaisah, rashin sanine yajawo hakan, nasan yanzu kinyi danasani, saboda kin gane gaskiya" Jinjina mashi kai tayi alamar Eh. "Ki gode ma Allah Unaisah, mommyn ki jaruma ce, I've wondered who gave birth to this remarkable child, cos you're different, with a sharp mind and loving, Ina alfahari da mommynki, saboda tayi bajinta, tayi abunda ya cancanta a jinjina mata..." tun daya fara magana ta ɗan sassauta da kukan sai shessheka da ta ke yi, Kalaman Chief Sun ƙara sa ta jin wani irin masifaffan son mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan. "Uncle din mommynki Shine silar komai daya faru, shine munafukin dake ƙulla makirci atsakanin su, bayan haka muna zargin yana da sa hannu a kungiyar matsafan kurkukun kaddara, yanzu haka mun fara bin diddiginsa nan bada jimawa ba zai shigo Hannu" In a low voice tace" I think he's the one who sacrificed me, kuma ina zargin yarinyar Aunty Ummi daya dauka in dai basu kashe ta ba, zai iya yiwuwa tana a cikin fursinonin kurkukun kaddara, watakil ma tana atare da mu" "Tunanin mu yazo ɗaya Unaisah ..." "Amma, Ina jin fargaban mommy na taƙi kula ni" "Zata kula ki Unaisah, a yanzu haka jiran ki ta ke yi, na fada mata zaki neme ta da kanki, ki kira ta awaya ki bata hakuri sannan ki nemi yafiyarta hakan zaisa taji dadi acikin zuciyarta" cike da zumudi ta juya zata tafi yai saurin dakatar da ita"ina zaki je" Fuskarta a yamutse tace"i wanna call her" kayataccen murmushi Chief ya dan saki"Okay, ga kayanan ki tafi da su" ya fada tare da nuna mata suitcases din dake ajiye gaban Couch, arude take kallon su a lokacin harya juya ya nufi ƙofar da zata kai shi gym room dinsa Ya shige ciki. Kasancewar akagare take da ta kira mommynta, bata tsaya yin wani dogon tunani akan akwatinan ba, cikin sauri ta nufe su, taja handle din daya ta fuce da shi. ______________________________🍁✍️ Tana shiga Bedroom dinsu, ta ɗaura akwatin saman gadon su, Ta dauko wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta danna ma layin da tayi saving da Aunty Benazir kira, saboda zumuɗi sam ta kasa zama sai zarya ta ke yi a tsakar dakin, almost 3 times tana kira ba'a picking, jikinta ne yayi sanyi saboda ta yi zaton fushi take yi da ita shiyasa bata daga ba. _Message ta tura mata mommy, dan Allah ki daga kirana akwai abun da nakeso In fada maki_ Ba'afi minti biyu data tura sakon ba, sai ga kiran Aunty Pretty ya shigo wayar ta, kwata kwata batayi farin ciki da ganin kiran ba, saboda a halin yanzu bata son ganin kiran kowa in ba na Aunty Benazir ba, har ya katse batayi picking ba, sai da aka ƙara kira, ta haɗe rai ba annuri ta ɗaga kiran tayi shiru batayi mata sallama ba. On the Other hand jin tayi Shiru yasa Benazir tace"daughter, kin bukaci kina son yin magana dani, kuma na kira kinyi shiru"? Waro idanu waje ta yi saboda rudanin da ta shiga, sai da ta fara janye wayar daga kunnanta ta duba number ɗin da kyau taga ta aunty pretty ce da sauri ta shiga messages ta duba number ɗin data tura ma saƙon, taga ba kuskure tayi ba Aunty Benazir ne ta turamawa amma ya akai Aunty Pretty ta kira ta sannan tace taga sakon ta? Nan take zuciyarta ta bata amsa da cewa zai iya yiwuwa mutun ɗayane ke amfani da layi biyu, Ras taji gabanta Ya dan faɗi, labban na kerma ta furta"Aun.. Aunty pretty, dama kece Mommyna Aunty Benazir"? Sautin Dariyar Benazir ce ta ratsa kunnanta, cike da nishadi tace"ni ce mana, layin da kika turama sako na Uncle din ki ne da nake amfani da shi, bayan na kar6i contact dinki agurin Aneelerh, ina saka number din Unexpected naga sunan da nayi maki saving ya bayyana akan screen din wayata nayita mamaki nace ashe da daughter dina nake waya batare da sanina ba, daga nan na yanke shawarar kiran ki da layin ya shureim saboda bana so ki gane ni ce...." wata irin kunyace ta kama Unaisah, tayi shiru tana zare idanun ta. "Kin daina fushi dani..."? Benazir ce ta tambaya akagare da son jin amsar ta. Kwatsam taji ta fashe mata da kuka kamar ranta zai fita, Hankalin ta ba karamin ta shi yayi ba, muryarta na rawa tace"Unaisah lafiya kike kuka? Meke damunki ne? Waya taba min ke"? Cikin shesshekar Kuka tace"Forgive me, Mommy I realize my mistake I apologize for hurting you, I love you more than anything in this world, I want Daddy to remarry you and bring you back to me, cos I need you in my life...." tana jiyo muryar Benazir dake ambaton Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya nuna mini ranar da nake ta jiran zuwanta Unaisah dagaske Kina sona yanzu? Kina son mommynki ta dawo kusa dake"? Jinjina kai tayi kamar tana agabanta tace"seriously, I love you so much, i want you to take care of me, I thought since Daddy had done everything for me, bazan bukace ki ba amma ayanzu na gane ke ce cika makon farin cikin rayuwata, bani da tamkar ki har abada..." Bata karasa maganar ba sautin kukan Benazir ya cika kunnan ta, hankalinta ne ya tashi da rawar murya tace"dan Allah ki daina kuka, bana son ji, pls, Allah zaiyi fushi dani idan kina kuka akaina..." cikin shesshekar murya Benazir tace"ba kukan bakin ciki bane Unaisah, kukan Farin Ciki ne, kin faranta raina, Kin sani jin kamar nafi kowa farin ciki a duniyar nan, yanzu bani da sauran damuwa, Mijina ya daina fushi dani, yata ma ta daina guduna, Alhamdulillah..." "Ba ki ce kin yafe min ba"? Benazir bata bata amsar tambayarta ba, sai taga ta canza call din zuwa Video Call, picking tayi lokacin da idanunta suka sauka akan fuskar Benazir wata irin kunyace ta lullube ta, fadawa tayi kan gado wayar na a hannunta tayi saurin janyo pillow da dayan hannun ta lullu6e fuskarta tana dariya, itama Benazir din dariya take ma yi. Cike da zolaya tace"rasa kunyan 6eran taka, Lemme see your face, kin tuna karyar da kikai min, Kina zuwa school sannan a kano kike da zama uhum"? Ƙyalƙyalewa tayi da dariya ba tare data furta kalma ba. "Oh ni Benazir, mamaki nake wai ni ce na haifi zankaɗeɗiyar balarabiyar nan tubarkalla kamar hurul ain" fashewa ta kumayi da dariya, Hakan ba karamin faranta ran Benazir ya yi ba, dama tayi ne donta saka ta farin ciki ganin ta damu sosai. "Aneelerh ta bani labarin kuruciyarki, yadda kasan ni agari, nima haka nayi kuruciyata amma fa ban kaiki rashin ji ba, gaskiya ni ban taba sa an kai daddyna cell ba" ta fada tana kallon Unaisah data kare fuskarta da pillow sai dariya ta ke yi. "Taya zamuyi magana bayan kinki bari inga fuskarki uhm? Pls let me see your face, " A hankali ta zame pillow din, ta matso da screen din wayar saitin fuskarta suka zubawa juna ido gwanin ban sha'awa. "Wow, ƴata tafi ta kowa kyau, launin idanunki irin na Ammin mu ne ta eygpt, kinsan me har yanzu tana araye ta tsufa tukuf..."murmushi Unaisah ta yi tana faman sauke ajiyar Zuciya. "Fadamin waya sa ki kirani awaya"? "Chief ne, shine ya fada min komai daya faru da ke" "Mutumin kirki, ya taimake ni, Allah ya saka sa masa da mafificin Alkhairin sa" Ta amsa mata da ameen.. "Kina da saurayi" cike da jin kunyarta tace"shine ai" "Wa"? "Zan fada maki ba yanzu ba" "Okay, abun da nakeso dake, Ki manta da komai daya faru, na yafe maki Unaisah, kuma ba laifin ki bane, rashin sanina yasa kika ƙulla ce ni aranki, amma ni ban ruke ki a cikin zuciyana ba, in ma akwai mai laifi to ni ce Unaisah, duk da nima bada son raina na tafi nabarki ba, amma naji dadi da ban tafi dake ba, watakil da yanzu baki araye tunda bana acikin hayyacina zan iya jefar dake akan titi...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan dake kokarin balle mata, cikin karyayyar murya Unaisah tace"pls kada kiyi kuka mommy, bana son ganin hawayen ki,..." jinjina mata kai tayi"bazan yi ba tun da bakya so....." sun dade sunayin waya akalla sun shafe awa daya da rabi a hakan ma basu gaji da yin wayarba, sai da Benazir tayi mata alkawarin zata zo gidan tukunna ta hakura su ka yi sallama da junansu. miƙewa tayi tsaye kan gadon, ta dinga tsalle kan matress din fuskarta dauke da murmushin Farin ciki. Shigowa dakin Batool tayi, jikinta asanye da kayan bacci riga da wando ko mayafi babu akanta. burki ta ci ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda Unaisah ke daka Tsalle tana dariya kamar karamar yarinya. Baki asake da mamaki tace"Sis Meke damunki ne? Meyasa kike yin tsalle akan katifa sai kace karamar yarinya"? Bata amsa mata ba, ta duro daga kan gadon ta nufe ta, tare da rungume sosai, Batool duk ta rude ta rasa gane kanta fatanta Allah yasa ba tabin hankali ta samu ba. "Sis meyasa ki farin ciki ne uhm"? Ta fada tare da raba jikinta daga na Unaisah Fuskarta dauke da annurin farin ciki tace"Batool ki tayani farin ciki, na gano wacece mommyna wadda ta haife ni" waro idanu Batool tayi"are you serious? Ta ina? Wacece"? Murmushi tayi"Aunty Benazir, mai kama dake, Itace Mommyna, kuma itace Aunty pretty da mukeyin waya da ita.." farin ciki ne ya lullu6e Batool"ina tayaki murna sis, Kinji dadin rayuwarki, Mommynki da daddynki suna nan, Baki rasa kowa naki ba..." maganar Batool ta taba zuciyarta, jikin ta ne ya yi sanyi sosai, tsananin tausayinta ne ya kama ta, su da basu taba sanin dangin su ba. "Sis amma kin yafe mata laifin da tayi maki ne? Kuma taya akai kika gane itace mommynki uhum"? Ta fada akagare da son amsar ta. "Shekaran jiya bana baki labarin Aunty Benazir da Aunty Aneeleeh sunzo ba"? "Eh na tuna, ay time din na fada maki aunty ummi bata jin dadi, atare ma bacci ya dauke mu adakin ta.." ɗan girgiza kai Unaisah tayi"baiwar Allah, Aunty Ummi, ta bani tausayi, naji labarin rayuwarta ashe kawaye ne su, da ita da mommyna da Aunty Anila, kaddara ce tayi silar raba su, nima mommyna bada son ranta ta gudu tabar ni ba" ta fada fuskarta. amarairaice. "Waya fada miki pls, nima ina son ji"? "Zan baki labarin komai daya faru amma ba yanzu ba, saboda nasha kuka wlh har zazzabi nake ji a jikina, amma da nayi waya da mommyna sai naji sauki acikin zuciyana.." badan taso ba tace"Toh sis zan jira ki, wlh har na kagara naji, kuma ina ƙara tayaki murna Unaisah" "Nagode my own sis," "Lah! Akwatin wanene wannan"? Ta faɗa tana nuna suitcase din da Unaisah ta aje, bata jira amsarta ba ta nufi akwatin dake ajiye, ta zauna daga gefen gadon ta soma kokarin bude shi tana fadin"wallahi yayi kyau sosai..." sai da tayi maganar Unaisah ta tuna da akwatin, da sauri ta dawo gaba gadon ta zauna, suka saka akwatin a tsakiyar su.. Kasa bude akwatin tayi, dakyar Unaisah ta buɗe shi waro Idanu waje su kayi ganin jigunanun Laces dinkakku tare da Materials da atampopi hada shaddoji, ɗaɗɗaga kayan suka somayi bakunansu sun ki rufuwa saboda mamaki. "Dan Allah waya baki su" "Ɗazu da chief ya kirani naje dakinsa shine yace min in dauka, dama ya kar6i awona ran nan, amma naji dadi wlh dama bamu da kayan hausawa acikin kayan mu..." sai murna ta ke yi tana yaba kayan, Batool dai jikinta yayi sanyi ganin kamar kayan na Unaisah ne kadai banda nata a ciki. "Bai ce hadani ba"? Da budar bakin Unaisah sai cewa tayi"Anya, kamar nawa ne ni kadai, amma kada ki damu zamu dinga sanyawa atare, ai abuna naki ne" mood din fuskarta kamar bataji dadi ba, in a cool voice tace"a'a ni bazanyi amfani da su ba, naki ne saboda ke ya siye su, kada ki damu..." ta fada tare da saukowa daga kan gadon, ruko hannun ta Unaisah tayi"meya faru ne naga kamar bakya farin ciki"? Murmushi ta kakalo kan fuskarta"don't mind your self, Am ok, inaso zan je dakin Aunty Ummi" tana ƙarasa maganar ta juya ta fuce daga ɗakin, Unaisah bata kawo komai aranta ba, ta maida kayan cikin akwatin kafin ta datse shi tare da ruko handle dinsa, ta sauko ta fito daga dakin ta nufi dakin Aunty Ummi. _💘UMMIN AMERICA💘_ Fitowa tayi daga Toilet jikinta sanye da bathrobe, wayar ta dake akan gado sai ringing takeyi, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa. Hararar wayar tayi bata da niyar daukarta. Sai da ta gama shirya kanta cikin Jallabiya, kafin ta dauki wayar tare da yin picking ta kara a kunne. Kakkausar muryarsa ce ta ratsa kunnanta " Ummi, why haven't you been answering my calls for two days? I've even sent you messages, but you didn't respond." Batasan ya akai ta tsanci kanta da jin haushin shi ba. "Bana jin dadi ne, wayar ma ban san inda na jefa ta ba, sai yau na dauko ta" "Okay, ya jikin naki" "Da sauki" "Inason ganin ki, zanzo da anjima.." bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa"Sorry, basai ka zo ba, ka bari idan na samu time zanzo gidan ka" muryarsa da mamaki yace"Ummi kin canza min, wani abu ya faru ne"? "A'a ba abunda ya faru, kawai bana so kazo nan dinne," "Okay.." ya na faɗa yai rejecting call ɗin. nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata aje wayar saiga kiran dr shureim ya shigo wayar, tun shekaran jiya da suka zo yake ta kiran ta, sau daya ta taba picking tana jin muryar shi ta katse kiran amma tayi saving contact dinsa. A kalla tana da missed calls dinsa kusan dari da hamsin, daga shekaran jiya izuwa yau, ga messages da ya ta turo mata na ban hakuri da rarrashin ta akan rashin da su ka yi na yar su. Wi-pi din wayar ta kunna kafin ta shiga whatsapp, ta bude chat din shi, A hankali ta zauna daga gefen gadon ta soma karanta last message da ya tura mata. _Aisha ba zaki yafe ma yayanki ba? Pls bani baki tausayi, tsawon shekara sha takwas ina dakon soyayyarki a cikin zuciyata, dan Allah ki taimaki bawan Allahn nan, gani da ƙoƙon barata agare ki, ko bacci bana iyayi saboda tunanin ki, nasan da babynmu tana araye watakil inci albarkacin ta, saboda kina son ta, amma baki son mu sake samun wata atare? Kiyi tunani Aisha ni kadai ne zan iya baki irin ta_ A hankali ta furta"nasani ya shureim, kai kadai ne zaka iya bani irin ta, tabbas ina so na sake haihuwar mai kama da ita, but I can't marry you! I've already told you I won't marry the man who raped me, I can forgive you, but I can't marry you, even though I still love you amma meyasa kayi mini haka? jefar da wayar tayi kan gado kafin ta kifa kanta jikin pillow, kuka take ji sai dai hawayen sunƙi zubowa, sai dai takama yin kukan zuci. "Aunty Ummi" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah, Da sauri ta shanye damuwarta ta mike zaune tana kallon Unaisah dake shigowa ciki hannunta ruke da akwatin ta. "Ina Batool din? Tace min zatazo gurin ki, " "Batool bata shigo nan ba, akwatin wanene wannan"? Ta fada tana nuna akwatin hannun ta "Kayan da Chief ya siya minne" ta fada tana murmushi, Ummi tace"Masha Allah, amma na taya ki murna, gaskiya Chief yana ji dake.." ta fada yayin da take buɗe akwatin data kar6a a hannun ta, tayi mamakin kayan masu kyau da tsada. ______________________________✍️ bayan ya kammala motsa jikin shi, ya fito daga Gym room din ya nufo dakin sa, hannun shi ruke da bottle water me sanyi, ya rataya farin towal akan shoulder dinsa, kwata kwata babu riga a jikin shi sai Boxer short dinsa, gaba daya jikin shi gumi yake fitarwa.. Harya bude murfin robar zai kai baki da niyar yasha ruwan, wayarsa ta doka alert, dan dakatawa yayi ya nufi wayar dake akan couch, ya danna unclock button, bai jira yaga wanene zai shigo ba ya juya baya ya kanga bottle din abakinsa ya fara shan ruwa. can cikin kunnansa yajiyo takun tafiyar mutun, abun ya daure kansa aransa ya ayyana wanene ya shigo masa daki batare da sallama ba? A sukwane ya juyo don yaga wani isasshen ne, da dan mamaki akan face din sa ya ke kallon ta, tayi tsaye idanunta na kallon floor, kamar mara gaskiya sai wasa takeyi da yatsun hannunta.. *~_____________________________////////////////////🔥🌹~* *Daga Alkalamin Boss Bature🔥🫰* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*[14/10, 6:06 PM] ‎Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 _ *The Unexpected Guest *_ ~___________________________________🌹✍️~ Da ace wani ne ya shigo masa daki haka zai tuhumesa ne amma da yake yasan wacece ita, da irin rayuwar da tayi sai bai damu ba. "Me ke damun ki"? Ya fada ganin kayan baccin jikinta sunyi squeezing, ga sumar kan nan nata a haukace ba gyara. Sam ta kasa bashi amsa, wani irin shakkarshi take ji, batasan ma ta shigo dakin ba, saboda bata a hayyacin ta, Nufo ta yayi jikinta na bari ta juya zata fuce, tana ruke handle din kofar taji ta adatse, wani irin faduwar gaba taji, ta dinga jan handle din amma taki buɗewa kamar zata saka kuka. Mamakine ya kama shi, ya rasa gane kan ta, aransa ya ayyana ko dai tana da tabin hankali? If not why zata shigo dakinsa ba sallama kuma yayi magana tayi shiru, sannan ya nufo ta tana kokarin guduwa"? Daga bayanta ya tsaya yana kallon yalwatacciyar suman kanta data cika bayanta. "Fada min meke damun ki? Baki da lafiya ne? Ai ko ki akayi guri na? Ko kinzo ne don ki gaishe dani'? Cikin rawar murya tace"am sorry, bansan na shigo ba, ba wanda ya aiko ni, " "Look, ni nasan ba hakanan ki ka zo ba, dole akwai abunda ya kawo ki daki na, just Calm down and tell me " Batare data juyo ta dube shi ba tace"ka ba Unaisah akwati, ni baka bani ba kuma inaso" Murmushin gefen fuska ya saki"Akwati biyu nace ta dauka, daya nata daya naki" "Ai daya ne tazo da shi, kuma tace nata, ita kadai ka ba mawa" juyawa yayi tare da kallon inda ya ajiye akwatinan daya ya gani. "Oh, ina tunanin ta manta bata ji ni dakyau ba..." ya juya ya nufi akwatin ya janyo handle dinshi ya mika mata"ga naki kema" maimakon ta juyo ta kar6a sai ta mika mashi hannun ta ta baya don ya bata. "It's improper ki juya mun baya ina magana, if you wanna me to give it to you, Turn around and face me" sarai ya fahimci shakkar shi take ji, kuma tana da kunya. Dakyar ta juyo ta fuskance shi idanunta na kallon floor. dayasan haka zai ganta inya matso kusa dabai ce ta juyowa ba, saboda gaba daya shatun nipples dinsa sun fito sosai ta jikin rigar baccin ta, bata saka bra ba, da sauri ya kawar da idanunsa gefe ɗaya, Ya mika mata akwatin hannunta na kerma ta ruƙe handle dinta cike da zumudi ta juya zata fuce ya dakatar da ita. "Kar in kuskura in ƙara ganin kina yawo babu mayafi akanki! Ki dinga suturta jikinki dakyau" gabanta na faduwa ta amsa mashi da toh, Ya raba ta gefenta Ya danna code din kofar ta buɗe da sauri ta fuce, tsayawa ya yi yana kallonta yayin da take jan akwatin ta nufi stairs, sai dadi take ji har zukunnawa tayi kan stairs ta shasshafa jikin akwatin batasan yana kallonta ba, sai da tagama kalle shi ta mike cike da zumudi ta karasa sauka down ta nufi dakinsu don taje ta gwado ma Unaisah itama ya bata suitcase. Sakin kofar yayi ta yi locking kanta, har zai juya idanun shi suka sauka akan siraran gashin kanta da ya kakkaba a kan floor, wasu irin dogaye masu kanannaɗa. juyawa yayi ya nufi tissu box dinsa dake ajiye gaban mirror ya yago tissue ɗin ya dawo ya zukunna gaban gashin Ya daura tissue din Ya nannaɗo su aciki, Kafin ya mike ya nufi drawer, ya bude Ya sanya Tissue din a ciki. ______________________________🔥🔥🔥 Bayan Kammala Sallar Juma'a around ƙarfe biyu da yan mintuna, Hamshakan Motoci Suka fara tururuwar shigowa Obie Estate, bakowane a cikin su ba face yan uwa da Abokanan Chief Owais yan team dinsa na isod tare da U.s Armies. Raba hanya motocin su kayi wasu suka nufi Gidan Baba Obie yayin da wasu suka nufi Gidan Chief Owais.. *CHIEF OWAIS🔥💪* Yana atsaye Cikin Lift, ya dauki wankan tuxedo suit, anyi masu adon Gold Gem stone dark blue, sai kyalli su ke yi, kayan sunyi fitting dinsa, ga wannan hadadden ducktail hair style din da yayi ma sumarsa. idanunsa na akan wrist watch dinsa kirar patek philippe wanda sai dan wane da wane suke sanyata. Time yake kallo, Yana karasa saukowa down Lift din ta buɗe Ya fito Ya nufi Dining area Tun kan ya karasa fragrance dinsa Ya daki kofofin Hanci nan su kusan atare suka dago suna kallon shi, ya yin da su ke a zaune kan Dining Chairs suna cin lunch din su. kasa haɗiye kingin abincin dake a bakunan su sukayi saboda rudewar da sukayi na ganinsa, Ya tafi da imanin su, Ba ummi ba ba taj ba har Unaisah da Batool sun shagala da kallon shi.. Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka gyara nutsuwar su.. Cikin girmamawa Ummi da Taj suka gaishe da shi, fuskar shi asake ya amsa masu kafin ya mayar da dubansa akan Unaisah dake ta kallon shi a fakaice Ya kashe mata ido ɗaya, gaba daya ya ƙara dagula mata lissafi, sai ta dinga ganin kamar Danish ne. "Happy birthday Chief namu, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka, Allah ya kara girma da daukaka, Allah ya kare mana kai daga sharrin makiya da mahassada" "Ameen, Thanks, Allah yabar zumunci atsakanin mu" "Bangane ba, Yau ne birthday din Chief, shine ba'a fada mana ba"? Ummi ce ta faɗa tana duban Taj "Am sorry, Laifi na ne da ban fada maku ba, yau ne Birthday dinsa, ya ƙara shekara daya, saura kaɗan ya cike 40yrs" ya fada da zolaya yana murmushi. "Amma dai banji dadi ba, da an fada mana da wuri ay da mun shirya muma anyi celebration din da mu"! ta faɗa tana kallon Chief, tattausar murmushi ya sakar mata. "ay min afwa, Idan na dawo da anjima zamuyi wani celebration din agida.." "Allah yakaimu anjima lafiya, sannan nima ina tayaka murnar birthday dinka, Allah ya cika maka burikanka na rayuwa, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya mara yankewa arayuwarka, Allah ya ƙara maka lafiya, Allah kuma ya baka mata tagari wadda zata zama cika makon jin dadin rayuwar ka..." a hankali yake amsa mata da ameen ameen, Unaisah tun da taji an ambaci mata tagari kuma taga ya kalle, ta dan saki murmushin gefen fuska tare da kawar da idanun ta gefe ɗaya. "Happy Birthday Chief, Allah ya faranta maka rai kamar yadda kake faranta mana" Batool ce ta faɗa da murmushi akan fuskarta, kallonta yayi ganin ta yi rolling mayafi akanta hakan ya tabbatar masa da taji warning din da ya yi mata. "Thank You," Wani kallo Taj yai ma Unaisah hakan yasa tace"happy birthday My husband to be, Allah ya baka nasara akan abunda kake nema, Allah kuma ya cika maka burikan ka" Waro idanu Ummi tayi"What"? cike da jin kunya ta sunnar da kanta ƙasa, Batool ce kadai bata fahimci me tace ba, shi kuwa Chief ƙayataccen murmushi Ya saki idanun shi akan fuskarta, Taj sai faman sakin murmushi yakeyi Yaji dadin abun nan. "Amen, shukran laki wife to be, Allah ya cika mana burin mu" cike da jin kunyar daddynta ta amsa mashi da ameen. "Zan kai karfe shida, pls kafin na dawo Ku shirya kanku, zan ma Chefs magana su hada maku Cake..." haɗa ba ki su ka yi gurin yi mashi godiya, tare da fatan Alkhairi. har ya juya baya basu daina kallon shi ba, yadda yake tafiya cike da aji ba karamin kayatar da su yayi ba, kafin taj ya dawo da duban shi gare su tuni Unaisah ta gudu zuwa daki saboda kunyar kada ta hada ido da shi. Yana fitowa Falo Yayi Arba da motocin da ke shigowa Villa Dinsa, a jere suka tsaya a parking Space. Ɗaya bayan ɗaya suka soma fitowa daga Cikin motocin, Kowan nan su Ya ɗauki wankan expensive Suits na kece raini, tun daga kan CO, CI, Agent zahra and Osman, tare da U.s Armies, fuskokinsu dauke da farin ciki suka nufe shi, aransu sai yaba kyawun shi su ke yi su kansu wankan shi ya tafi da imanin su, Gaba daya sai yaji bakin Ciki Ya mamaye zuciyar shi saboda rashin Ganin Omar atare da su, Farin cikin shi ragagge ne, suna karasowa suka sara mashi, shima Ya sara masu, tare da mika masu hannu daya bayan daya sai da ya yi Musabaha da su, a mutunce suka gaisa da junansu, bayan sun yi mashi happy birthday, Saida suka fara shigowa Cikin gidan suka duba jikin Taj kafin suka fito, ahanzarce security officers suka bude masu Cardoor suka shiga cikin motocin a jere suka nufi Cikin Obie Estate. Daidai Lokacin da za'a fara gudanar da Shagalin, gaba daya Hall din a kewaye yake Da sojoji harma da Isod Soldiers, baka jin komai sai sautin kidan Isod Anthem dake ta shi. A gaban Hall din motoci suka dinga yin parking. Ahanzarce Jami'an suka soma bude masu cardoors... Yana ƙoƙarin fitowa daga Cikin motar, Idanunsa suka sauka akan Daddynsa dake fitowa daga cikin motar shi, Karaf idanunsu suka shiga cikin na juna, nan da nan Ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi gefe ɗaya. Girgiza kai sharafuddeen yayi duk sai yaji ba dadi, badan ya damu da shi ba, da ba abunda zai sa shi zuwa birthday dinsa sai dai shi bazai biye mashi ba. gaba ɗaya Uncle dinsa sun fito daga cikin motocin su hada Baba Obie, jikokin family din bakowane Ya samu damar halarta ba, wasu uzuri ne ya ruke su, kowan nan su Ya dauki wankan shadda geztner blue sky, sai ya zamana kamar sunyi anko da Chief ne. Akan Idon shi Chief Ya nufi Baba Obie yayi hugging dinsa tighly tare da manna masa peck a cheeks dinsa, bayan sun gama gaisawa ya nufi Hateem Yayi hugging dinsa kafin Yabi sauran Uncle dinsa da Yan uwansa duk yayi hugging dinsu, amma shi ko arzkin gaisuwa bai samu ba, hakan ba karamin taba zuciyarshi yayi ba. babu wanda ya lura da hakan sai Hateem dama tunda yazo ya fahimci akwai wani abu dake damun Dan uwansa, bai dai tambaye shi ba, sai yanzu yaga amsar tambayar shi lamarin ya daure mashi kai sosai. Gaba ɗaya suka dunguma izuwa Cikin Hall din da aka kawata shi da decoration, makada da mawaka da akayi inviting Sun hada kai sai kirari suke yi ma Chief. basu dade da shiga Ciki ba, Saiga Mommynsa gimbiya malik tare da hajiya laura da kanwarsa hindu sun shigo, gaba dayansu Laces ne a jikin su, yana ganinsu ya nufe su, tun kafin Ya karaso hindu ta riga shi isa tayi hugging dinsa tighty tana fadin"happy birthday Big bro, we're so proud of you" fuskarshi dauke da murmushi Ya dan bubbuga bayanta da tafin sa. Kafin ya dago ya rungume mommynsa, shafa sumar kan shi tayi"happy birthday, my beloved son, You're the light of our family, and I'm so grateful for your kindness, compassion, and leadership, May this year bring you happiness and success." "Ameen mommy, I can't thank you enought, kin gama min komai, kece silar daukakana" ya fada tare da raba jikin shi daga nata, murmushi suka sakar ma Juna. Kafin ya dubi Hajiya laura, suka gaisa a mutunce itama ta yi mashi fatan Alkhari. Shigowa Hall din Hajiya Saratu tayi, jikinta sanye da pakistan na manyan mata riga da wando, tayi rolling veil akanta, ga wani hadadden shade fari data saka, ta wanku iya wankuwa, pravin Yana a gefen ta, yayin da su twins ke abiye da bayansu, gaba dayansu Indian outfits ne a jikinsu, sunyi bala'en kyau, sun fito da ainihin suffar su ta indiyawa. Hajiya laura na ganinta ta nufe ta da fara'a suka yi hugging din Juna sai yaba kyanta Hajiya laura take yi, bayan su twins suna gaishe da ita suka wuce Gurin Chief, suna karasowa Ya yi hugging dinsu atare sukayi mashi happy birthday. Pravin ma Yaje yayi mashi, kafin Hajiya saratu itama ta matso kusa tayi hugging dinsa tare da yi mashi fatan Alkhairi, Kafin kace me tuni Hall din ya cika da yan uwa da abokan arziki, Sai yan gaishe gaishe suke yi atsakanin su, Hatta U.s Armies da Senior agents saida Chief ya kai su gurin baba Obie suka gaishe da shi, ya kuma kaisu gurin Mommynsa suka gaishe da ita cikin girmamawa, haka sauran Uncles dinsa duk saida su ka gaisa da abokan aikin sa mahaifinsa ne kadai bai kai su wurin shi ba. daga bisani Mc ya hau kan Stage, hannun shi ruke da mic, ya farayi ma Baki maraba da zuwa, tare da gabatar masu da kan shi, dayawa sun gane fuskarshi shine yayi mc A farewell dinner na hateem, Baba Obie ne ya yi inviting dinsa a wannan karo ma. Bayani ya soma korawa, Hankulan Kowa Ya dawo kan shi. _"Ladies and gentlemen, esteemed guests, family, and friends, welcome to Chief Owais's birthday celebration!"_ _Today, we gather to honor a remarkable leader and an extraordinary individual"_ ya fada yana nuna Chief Owais. gaba daya suka fara tafa mashi, bayan ya kammala Speech dinsa Yayi inving Iyayen Chief don suyi speech dinsu, bayan Gimbiya Malikat Ta kammala nata mutane sunata tafa mata, Mai girma sharafuddeen ma yayi nashi Speech din mai ratsa zuciya, sai dai ko kadan Chief bai nuna Yaji dadin yabon da yayi mashi ba, saima yaki dagowa su hada idanun su, hakan ba karamin bata ran Mai girma shafuden ya yi ba_ Time da Mc yayi inviting Chief don yayi speach dinsa, Hankalin Kowa na hall din ya dawo kan shi... Cikin nutsastsiyar muryar shi mai Jan hankali Ya kora jawabi mai matuƙar taba zuciya, abun da ya kara daurewa Uncles dinsa Kai Jin ya yabi mahaifiyarsa tare da su, amma bai sanya sunan mahaifinsa ba, basu kawo komai aran su ba, saboda sun yi tunanin ba dagangan ya yi ba. Bayan Ya kammala speech dinsa Mc yace"I'm inviting his wife to give a speech on stage" Tunkan Ya kare maganar Hajiya saratu ta ɗaga murya tace"ai har yanzu bashi da aure, tazuru ne" gaba daya hall din suka kama dariya cikin nishadi, sun sa shi jin kunya. Cike da zolaya Mc Yace"Chief what are you waiting for? Me ka nema ka rasa? Zankadedan saurayi kamar ka, burin kowace ya mace uhm? Ya faɗa yana kallon sa, kamar baisan yanayi ba, idanunsa na akan wayarsa da yake dannawa.. "Cikin yan matan nan da suke hauka akanka ya kamata aba daya dama mana" dariya suka sanya, Hajiya saratu tace"He has a fiancee, Insha'Allah, we will soon invite you to his wedding celebration" Gaba daya jama'ar dake acikin Hall din suka sanya shewar murna. Daga Bisani Labulan daya Lullube ke6ataccen gurin da aka tanada saboda Chief ya soma ɗagewa sama a hankali gaba daya hankulan mutane ya koma kan shi Wata katafariyar throne Chair ce da aka kawatata saboda shi, daga gaban kujerar wani hadadden table ne anan aka daura katon cake din da akayi domin sa, mai hawa 10 hada sunan shi a jikin Cake din da wani salon rubutu me jan hankali akayi shi, daga saman silin din gurin an kawata shi da navy blue balloons da steamers, wurin Ya burge mutane, friends dinsa ne suka yi mashi rakiya Ya hau kan kujerar Ya zauna tare da daura kafarsa ɗaya kan ɗaya like a King on his Throne. Minti 30 aka ware saboda baki su samu damar Cin abinci, bayan kowa yaci yasha anyi kullu wash rabu hani'an Mc Ya sa Mawaka suka fara wake Cheif Owais, wakar tayi mashi dadi hatta yan uwansa sunji dadin wakar birthday din da akayi masa. Lokacin da Mc Yayi inviting Yan uwa da abokan arziki donsu fito tsakiyar filin su taka rawa, nan fa suka fara hawa kan dancer floor din cike da nishadi suke taka rawar girma, kowa saida Ya taka In ka cire Mutun daya Mai girma sharafudden da ransa yagama 6aci, Jira yake kawai agama shagalin su shiga family meeting don Ya fallasa abun da ke faruwa tsakaninsa da owais, saboda hakurinsa ya ƙare ya ƙwammace kowa ya ji. Lokacin da aka kusa kammala shagalin, Yan uwa da abokansa suka taya shi Yanka cake, ya 6allo cake din Yaba momynsa abaki, bayan taci itama ta debo ta saka mashi abaki yaci. ya bi Uncle ɗin sa daya bayan daya ya gutsuro cake ɗin ya sanya masu abaki suka ci, ko da yazo kan sharafudeen Saida Ya fara aika masa da harara kafin Ya bashi cake din, badan idon mutane ba da ba abun da zaisa ya ci cake din nan, hakanan ya jure ya bude baki Ya sanya mashi cake din kamar anyi masa dole. Bayan ya gama basu Hindu ta debo cake din ta bashi abaki, shima ya bata abaki, Baba Obie Ya ballo Ya tura masa abaki, kowa ka kalla fuskarsa dauke da farin Ciki banda mahaifinsa. Mintuna talatin da suka rage kafin A kammala Birthday din, photographers suka fara daukar su Hotuna da videos, sai da Chief Ya dauki hoto da kowa daya halarta amma banda mahaifin sa, Ko kusa da shi Yaƙi bari Yazo, balle yasa ran zai yi hoto da shi. Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, Yan uwa da abokan arziƙi sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, bayan kammala addu'ar tashi daga taro da Mc ya gabatar tare da yi ma Baki fatan sauka gida lafiya. *HAJJATY🍁* Tana akwance kan gadonta, Ta lullube kanta cikin bargo, Jikinta sai makekketa yakeyi saboda zazzabin daya lullu6eta, duk yadda taci burin ta halarci birthday din Owais, Allah bai nufa ba, Tun safe take fama da zazzabin har magani tasha amma yaƙi sauka, har kiran layin Pravin ta yi don ta fada mashi halin da take aciki amma bai yi picking call din ba, rabon ta da shi tun bayan kammala sallar asubahi daya leko dakin ta bata ƙara ganin ƙeyarsa ba. Yan aikin gidanne kadai suka san bata da lafiya, Har abinci suka kawo mata amma takasa cin shi, burin ta kawai taga pravin saboda shi kadai ne zai iya kwantar mata da hankali. ________________FAMILY MEETING🔥 "Owais meya haɗa ka da Mahaifinka? Meyasa kake zarginsa? wani laifine kake tuhumarsa da shi Ya fada min ba yadda bai yi dakai ba akan ka fada masa amma ka ƙi sanar da shi why pls"? Hateem ne Ya faɗa Idanunsa a kan Chief owais dake a tsaye yana fuskantarsa, Suna a cikin dakin Baba Obie. Fuskarsa babu walwala ya furta"zanyi maka bayani anjima" girgiza kai Hateem yayi ransa abace yace"No, Yanzu nake son ji Owais, Dole ka amsa min tambayata idan har ba so kake raina Ya baci ba"! Shiru yayi saboda ya rasa ta ina zai fara kora masa jawabi. "Hateem meke faruwa ne? Har an fara shirin Family meeting bangan ku ba, yanzu nake tambayar kuna ina, auta take fadamin taga shigowarku dakin baba " Sir mubarak ne ya yi maganar yayin da ya ke shigowa dakin idanun shi akan su. Kafin wani daga cikin su Ya furta Kalma suka ji an banko kofar dakin gaba daya suka kai dubansu ga mai shigowa. Mai girma sharafuddeen ne Ya shigo dakin fuskarsa kwata kwata babu annuri, sai huci Yake yi kamar mayunwacin zaki, kaitsaye ya nufi Owais yana karasawa gaban shi, Ya damƙo Arm dinsa da ƙarfi Ya fusgoshi Ya nufi kofar dakin da shi... Hankali atashe Hateem da Sir Mubarak suka bi bayanshi suna kokarin dakatar da shi. Bai nufi ko'ina ba sai falon, A lokacin Baba Obie tare da sauran Uncles dinsa da Hajiya saratu duk suna a Falon kowan nan su yana azaune kan sofa, shigowar Shafudden ne Ya ɗaga hankulan su a razane suka mimmike tsaye , cike da rudu suke kallon su.. "Dad.. let go of arm" yana huci ya fada sharufudeen Yace"bazan saki ba Owais, kayi duk abun da za ka yi..." "meke faru ne? Yaya sharafuddeen? Owais! Me ya hada ku ne"? Hajiya saratu ce ta yi maganar, bai ko kula ta ba, ya nufi baba Obie da ya gaza miƙewa agaban shi Ya wurgar da chief owais, gaba daya ya tafi zai kife ƙasa baba Obie yayi hanzarin ruko kafadunshi Ya janyo shi ya dawo kan laps dinsa. Yana haki Yace"gayanan baba, ka tambayesa Uban me nayi masa! watakil kai ya iya faɗa maka" ya faɗa yana nuna Owais da yatsan sa, Kafin Ya dubi yan uwansa cikin bacin rai yaci gaba da cewa"Owais Ya ɗaura min karan tsana, yau wata ɗaya kenan, rabon da in yi bacci cikin kwanciyar hankali saboda shi, gaba ya ke yi da ni! ya juya min baya, yana zargina akan laifin da ban aikata ba, ba yadda banyi da shi ba akan ya fadamin me nayi masa amma yaki ya faɗa...." Daura hannu biyu hajiya saratu tayi akanta.. Uncles dinsa gaba daya sun rude da jin abunda ke faruwa tsakanin Owais da mahaifin sa. Cikin sanyin murya Baba Yace"meyasa baka fadamin ba tun lokacin daya juya maka baya"? "Saboda bana so na daga maku hankali, shiyasa nabar abun araina, yau ma dana fada maku naga abun nashi ya fara wuce gona da iri, nema yake ya daura min hawan jini, Baba Hakurina ya kare, Owais Ya kona min rai" ya fada idanunsa cike tab da kwalla. Gaba daya basu ji dadin abun da Owais ya yi masa ba. Senate lateef Yace'baka kyauta ba, owais, ka bani mamaki, ina hankalin ka ya ke? Da har ka bari mahaifinka Yana kwana da fushinka acikin zuciyar shi"? Ya faɗa yana kallon chief wanda har lokacin bai ɗago ba, tunda Baba Obie ya daura kanshi asaman laps dinsa. "Owais, ka tashi kayi mana bayani, wani laifi ne kake tuhumar mahaifin ka da shi? " His excellency abdul razak ne yayi maganar.. His excellency deen daya gama fusata da kakkausar murya yace"ba kaji ana magana bane? Ka tashi ka fada mana meya hada ka da shi"! Cikin sanyin murya Hateem Yace"pls, Kubi shi a hankali, " ya fada tare da kallon Owais"My son, pls, ka tashi kayi mana bayani, in sha Allah zamu fahimce ka," Pravin da ke ƙoƙarin shigowa falon har zai saci hanya ya nufi dakin hajjaty ganin abunda ke faruwa yasa shi cin burki Ya karya kwana ya nufi gurin su ya tsaya tare da ruke qugun shi da hannu daya ya kasa kunne Yana sauraron maganganun su. A fusace Owais Ya miƙe tare da juyawa ya nufi daddynsa gadan gadan Kamar zai dokesa, lamarin ya daure masu kai owais bai taba basu mamaki irin na yau ba, har sun fara kokwanton anya ba Aljanu ba ne a jikin shi. Hannu yasa Ya daki kirjin shi yana faman fitar da hucin bacin rai idanunsa sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono a cikin su, wlh a lokacin Sharafuddeen Yasha jinin jikin shi saboda bai taba ganin owais acikin bacin rai irin na yau ba, Batare da jin shakkarshi ba ya fuskance shi gaba da gaba. Da farko yayi zaton Dukanshi zaiyi, ganin yadda Ya tsaya a gabansa Yana huci. Gaba daya kawunnansa sun zubawa sarautar Allah ido, suna jira su ga iya gudun ruwan shi. Dakyar ya haɗiyi ƙululun bakin cikin daya tokare Zuciyar shi.. Sautin muryarsa dakyar yake fita"ka za6i in tona maka asiri agaban su"? Ya jefa mashi tambayar, muryar sharafuddeen tamkar zai fashe da kuka Yace"Sai me owais? Ka fada masu suji, wlh da Allah na dogara, ni nasan ban aikata komai ba..." Gyaɗa kai Chief Owais yayi tare da cewa"kana ɗaya daga Cikin Elders na gidan KURKUKUN ƘADDARA❗...." Aruɗe Sharafuddeen yace"bangane me kake nufi ba Owais, su wanene Elders? What Prison of Destiny are you talking about"? Kallon kallo Uncles dinsa suka fara jefawa Junansu gaba daya sun rude da jin abunda Owais Ya faɗa! Su kansu sun kosa suji su wanene Elders? Kuma wani gidan kurkukun kaddara ne ya ke magana akansa? Hateem har ya buɗe baki zaiyi magana baba obie ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"kabarsu suyi magana atsakanin su, kada wanda ya sa masu baki"! ya umarta, batare daya motsa daga kan kujerar da ya ke ba. Wani makirin murmushi Pravin ya saki tare da cizon leben shi saboda dadin da yaji. "ka riga da kasan me nake magana akai, ina da tarin hujjoji akanka, kawai ka amsa min tambayata, Idan har baso kake In fallasa asirinka agaban su ba..." bawan Allah Sharafudden Ya rasa Ina zai tsoma ranshi yaji dadi, murmushin takaici ya saki, tare da kai hannu Ya damƙi kwalar Chief yana huci yace"ka dade baka tona min asirin ba dan ubanka! ka fada kowa yaji Owais..." "Haba yaya Sharafudeen pls Owais.." Hajiya saratu da ta ɗauko maganar, bata kaiga dire ta ba, baba obie Ya daka mata tsawa tuni taja baki tayi shiru, da rudu take duban baban nasu ta razana ba kadan ba. Kasa hakuri Hateem yayi don bazai juri kallon Dan uwansa Da dansa a yanayi irin wannan ba, Nufarsu yayi da niyar ya raba su, bai kai ga isa ba Baba Obie Ya ambaci sunan shi da kakkausar murya"Hateem!" fuskarshi dauke da damuwa yace"baba pls kada ka hana ni! Bazan iya jure kallon dan uwana ahali irin wannan ba, ɗan sa fa ne, wannan ba abune da zamuja baki muyi shiru ba muna kallon uba da ɗa suna faɗa atsakanin su.." fuskar baba Obie adaure Ya nuna masa sofa"ka koma ka zauna, Umarni nake baka"! Badan yaso ba ya nufi sofa din daya nuna masa ya zauna ransa abace. Hajiya saratu data gama hasala juyawa tayi rai abace ta nufi part dinta don bazata juri kallon abunda ke faruwa ba. "Ba zaka fada ba"? ya fada batare daya saki kwallar rigar shi ba.. Yaso Ya rufa mashi asiri saboda koba komai mahaifinsa ne shi, amma ganin yadda ya matsa ma shi akan ya fada ne yasa shi ya zuciya har baisan sa'adda Ya fara gaya masu irin miyagun ayyukan da Elders suke aikatawa.. Lokaci ɗaya yanayin fuskokinsu Ya canza zuwa tsantsar tashin hankali da rudani mara maisaltuwa hadi da tsantsar al'ajabi. bai karasa maganar ba, Sakamakon Tsawar Da Hateem Ya doka masa, tamkar zai fasa dodon kunnansa. wannan karon bai saurari baba Obie ba ya mike cikin fushi Ya nufi Owais yana fadin "zaka tabka kuskuren da zakayi danasani arayuwarka! Idan ma zarginsa kakeyi to ka daina, Ka sake bincike akan wadanda kake zargi, amma mahaifinka baya daya daga cikinsu, sai dai idan kazafi aka yi masa...." girgiza kai Chief yayi hawayen da suka taru acikin idanunsa tuni sun fara sauka kan kuncinsa. "Uncle Ba zarginsa nakeyi ba, tabbaci nake da shi, Yana daya daga cikin Elders, saboda shine mutumin da ya janye ni daga fagen fama, Ya jefani acikin daki don kada a cutar dani, bayan haka aranar da zamuje kai farmaki, saida ya kira ni a resting home dinsa, Ya gargadeni akan kada inje kai farmakin, ashe ya saka min maganin bacci mai hadarin gaske acikin coffee din da ya bani nasha...." a takaice ya fayyace masu dalilan da sukasa ya ke zarginsa. Maganganun Owais sun so suyi tasiri a cikin zuciyoyin su, har sun fara jifar sharafudeen da kallon tuhuma. Dafe kai sharafuddeen yayi da tafin hannunsa, wani irin kululun bakin cikine ya tokare makoshinsa, sam ya kasa magana, dakyar yake iya furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.. "Baba dan Allah kasa baki a maganar nan! Kai kadaine zaka iya tsawatar masa..." His excellency deen ne ya fada yana kallon Baba Obie, wani abun daure kai, kwata kwata fuskarsa babu alamun damuwa. "Me ku keso ince? Sharafuddeen shi yakamata ya kare kansa agurin Owais, Ni banga laifin Owais ba, kubar yaro yayi aikinsa, ko kun manta cewa shi jami'en bincike ne"? Cike da rudani suke kallon baba Obie, jin abunda yace, sun fahimci shi ko ajikin shi bai damu ba, "Ba ku kai shi son mahaifin shi ba, Hakanan dai owais bazai tuhumi mahaifinsa batare da yana da kwakkwarar hujja akan shi ba, kunsan dai ba zai yi maku karya ba....." Bai kare maganar ba, sharafudeen Ya katse shi, Cikin raunanniyar murya yace"baba, da bakin ka kake fadan hakan? Ka yarda da maganar owais, kaima kana zargina? Baba kaifa mahaifina ne kafi kowa sanin halina, kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, wlh banji zafin kazafin da owais yayi min ba, kamar yadda naji zafin maganar ka..." dakatar dashi baba Obie yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu"Ni bance ina goyon bayan Owais ba, kuma bana goyon bayanka saboda bansan wanene mai gaskiya acikin ku ba, amma in har zaka iya kare kanka agaban yan uwanka nayi alkawarin zan dauki mataki akan Owais, In kuma ka gaza yin hakan hukuma zatayi aiki akanka, donni bazan bari ka zubarmin da mutuncina ba...." juwace ta kusa dibar Hateem da sauri Ya nemi sofa ya zauna tare da dafe kanshi dake sarah mashi. Sir mubarak sam Ya kasa magana, saboda yana da fusatacciyar zuciya in har ya bude baki ran kowa zai 6aci ne. Sun rasa wa zasu goyama baya a cikin su? owais da baba Obie sun haifar masu da kokwanto akan sharafuddeen, aganinsu son owais ne ya rufe mashi idanun shi shiyasa ya goyi bayan shi. Munafuki Pravin sai ya fakaici idon mutane yake sakin makirin murmushin nan nashi, Ji yake kamar ya zuba ruwa kasa Yasha saboda farin cikin sabanin da owais ya samu da mahaifinsa dama yajima yana jin haushin Owais.. Fuskar Sharafudeen amarairaice ya dubi Yan uwansa.. "Kuma Kuna zargina akan abunda owais ke tuhuma ta"? Shirun da su ka yi ne yasa shi tunanin suma sun goyi bayan Owais da baba Obie, zubewa yayi kasa kan gwiwowin sa, hawaye suka wanke fuskarsa, ga wani matsanancin ciwon kai da yake ji, zuciyarshi ta karaya. "ba mu zargin ka, saboda mu shaida ne akan ka, mun san wanene dan uwan mu, amma abun da muke so da kai shi ne ka fada mana, meyasa ka sanya mashi sleeping pill a cikin coffee? After that! Why ka hana sa zuwa kai farmaki bayan baka taba hana shi ba! sai wannan karon? Sannan Yace ka yi fitar sirri a daren ranar da suka je kai farmaki, Sharafuddeen Ina kaje"? his Excellency abdul razak ne ya jefa mashi tambayar. Shiru yayi batare daya iya kare kanshi daga abunda suke tuhumar shi ba. A hankali Chief owais Ya sadda kanshi Kasa ko kallonsa baison yi saboda baison tausayin shi ya kama shi, gaba daya komai dake faruwa akan idanun Hajiya saratu dake atsaye bakin kofar shiga part dinta, taji komai daya faru saboda bata kaiga shiga ciki ba.. Hannayen shi dake kerma ya ɗaga sama cikin karyayyar murya ya ce _"Ya Allah, bani da mafita daya wuce kai! Kaine shaida ta, kafi kowa sanin wanene bawan nan naka...." bai kaiga ƙarasa maganar ba, sakamakon muryar dattijuwar data karaɗe kunnuwan su *_"NI INA DA JA AKAN MAGANAR KA OWAIS, JINI NA BAZAI TABA AIKATA MIYAGUN LAIFUKAN DA KAKE TUHUMARSA DA SU BA"!*_ ~*_________________________________*~ *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* [14/10, 8:15 PM] Amina Musa Mustapha💕💕: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 _ * *_ ~___________________________________🌹✍️~ A matuƙar ruɗe suka juya tare da kallon mai shigowa... Sandar hannunta ce ta fara zurowa cikin falon, Kafin ta kunno kai, farar jallabiya ce a jikinta ta lullu6e kanta da head scarf ta rufe fuskarta da takunkumi, haka zalika idanunta suna asanye da shade fari, daƙyar ta ke dogara sandar hakan ya bayyana rashin kuzari a tattare da jikin ta, daga gani bata da koshin lafiya duba da yadda jikinta ke kerma. Cike da tsantsar ruɗani suke kallon ta daga ƙasa har sama, basu san wacece ba, amma maganar da ta furta ta tsaya masu a ƙahon zuciya. A sukwane Sharafudeen Ya miƙe yana duban ta, Muryarta ta yi masu kama da ta mahaifiyarsu da suka rasa tsawon shekaru wanda basu mance da yanayin sautin muryar tata ba. Pravin sai faman zazzare Idanunsa ya ke yi burinsa kawai ya ga wacece ita duk da fargabar da ta shige shi saboda muryarta ta yi masa kama da ta wata da ya ta6a sani.. Baba Obie sam ya kasa motsawa, zuciyar shi ta ƙi aminta da abunda kunnuwanshi suke juyo mashi, haka kuma ya kasa yarda da abunda idanunsa ke nuna mashi, kokwanto ya ke aransa ya ayyana hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wanda ya mutu ba ya ta6a dawowa, duk da yanayin fuskarsa ya nuna tsantsar ruɗani, sai dai babu alamun fargaba atare da shi saboda ya yi imanin hakan bazai taba yiwuwa ba, sai dai idan fatalwarta ce ta dawo... "Wace ce ita? Da izinin wa ta shigo estate din nan?" Tambayar da ta cika zuciyoyinsu kenan, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji dame ta zo musu. "Baiwar Allah daga ina ki ke? Wa kike nema ne? Kuma tayaya akai kika shigo estate ɗin?" His excellency Deen ne ya tambaya fuskarsa a murtuke. Hajiya saratu dake a tsaye bakin kofar shiga part dinta tayi sototo tana kallon Ikon Allah.. Kusan atare Sir Mubarak Da Hateem suka miƙe daga zaunan da suke akan Sofas suka bi ta da kallo... "Wacece wannan dattijuwar ne? Me ya kawo ta nan? Da iznin wa ta shigo Estate din nan uhum"! Acewar His excellency Abdul Razaq... "Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya faɗa yana zare idanun sa.. "Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..." Senate Lateef ne ya ɗauko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ƙoƙari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari ya hanata yin saurin. Tana gab da zata ƙarasa gaban Sofas ta ɗan dakata tana mayar da numfashi. Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka ƙaraso tsakiyar Sofas ɗin, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...." Bai ƙarasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma. Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate ɗinsu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!' Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzuƙa za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta. Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike taƙama ne?" Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!" Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hankaɗo mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..." Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ruɗu yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?" "Ba zaku ɗauki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da baƙaƙen aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..." Pravin ne Ya faɗa Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru. Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana ƙarasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta damƙi mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya zaƙinta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.." Balbaleta da faɗa Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Sai da suka gama harzuƙa kowa zuciyarshi ta zo a wuya. Pravin yana ƙoƙarin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya faɗo ƙasa ta bi tasa ƙafarta ta take shi ya faffashe. Ɗagowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta ɗaga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba ɗaya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya ɗarsu acikin zukatansu, Sun ruɗe da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita. Sai lokacin ta yi ƙarfin halin buɗe baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!" Ta faɗa tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya miƙe tsaye a kiɗime yana zazzare idanunsa! lokaci ɗaya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matuƙar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ruƙe shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa.. Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike taƙama ne, wace ce ke wai..."! Bata ƙare maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ruɗe ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafaɗunta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana ƙoƙarin gano wacece ita.. Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!" Ta faɗa tana ƙoƙarin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak! Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da ƙwalla. Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ba laifinku bane, laifin ubanku ne, Mugu azzalumi, Kun ganshi nan..., Shine ya ɗauke ni tsawon shekara ashirin ya raba ni da ku, ya yi maku ƙaryar na mutu bayan ina a raye...." Waro idanunsu waje su ka yi suna kallon fuskarta yayin da ƙwaƙwalwarsu ke ƙoƙarin tariyo masu wacece ita saboda ta canza musu sosai, tayi tsufan da bazasu iya gane ta ba cikin sauki. Saboda tsabar tashin hankali, duk da sanyin A.c din dake a falon hakan bai hana baba Obie fitar da gumi ba, jikinshi Ya jiƙe sharkaf kamar wanda aka tsamo daga teku, Firgici da tsoro sun mamaye zuciyar shi, duk yabi yasha jinin jikin shi. Pretending ya yi duk don ya ƙara dagula masu lissafin ƙwaƙwalwar su ya ce, "This can't be Aurora Edward, bazai ta6a yiwuwa ba, matata ta mutu kuma mun shaida mutuwarta, wanda ya mutu baya dawowa sai dai idan Aljana ce ke!" Ya faɗa a tsawace kamar zai doke ta, bata ko kula shi ba ta mayar da dubanta akan ya'yan ta burinta su gane ta saboda hankalinta ya tashi ganin sun kasa yarda cewa ita ce. "Hateem, Sharafudden nasan ko kowa bai gane ni ba, Ku zaku gane ni..." Ta faɗa tare da tallabo fuskar Hateem da tafukan ta, wata matsananciyar damuwa ce mai tattare da ruɗani ta mamaye zuciyar Hateem da Sharufudeen, kokwanto su ke yi akanta, abu ɗaya da ya yi masu kama dana mahaifiyarsu ajikin ta, shine launin ƙwayar idanun ta. In a broken voice, Hateem yace "Momma... Is that really you I'm seeing? But how is that possible after you died? Ni dai a iya sanina wanda ya mutu baya dawowa ..." Ya faɗa yana girgiza kansa. Bai ƙare maganar ba Sharafuddeen ya ce, "Don Allah ki fahimtar damu, kin jefa mu a ruɗani! gaba daya mun ruɗe, tabbas ba zamu manta da mahaifiyarmu ba, amma taya kika rayu bayan kin mutu? Dan Allah ki fada mana! Mafarkine wannan ko gaske..." Ya faɗa fuskarsa sharkaf da hawaye. Murmushin takaici ta saki tare da juyawa ta dubi baba Obie da ya yi tsaye sototo kamar mutun mutumi. "Ku tambayesa ina ya kai maku mahaifiyarku tsawon shekaru ashirin bayan ya yi maku ƙaryar na mutu, shine ummul aba'isin komai, shine ya azabtar da mahaifiyarku, wuya ce ta sa na yi tsufan da basu kai na shekaru na ba..." La66ansa na kerma ya ce, "Kada ku yarda da ita! Ƙarya take gaya maku, Fatalwa ce ba mutun ba ce, dan Allah ku kawar da ita daga cikin gidan nan, ku kira Security officers su fitar da ita, Ku kore ta bana son ganinta" Ya faɗa yana nunata da yatsansa dake kerma.. "Don't believe her! I don't want to see her, Crazy ghost, hypocrite, get her out ba mutun bace Aljana ce ku kira sheikh Imam ya yi mata ruƙiya zaku tabbatar da abunda nake faɗa maku..." Kamar zararre sai sambatu ya ke yi, duk yabi ya dabarbarce ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Murmushin takaici ta sakar mashi, ga wani ƙululun bakin ciki da ya tokare maƙogwaronta, "Haba Obinna, idan har ni aljana ce to kai kuma bakin shaiɗani ne, wannan bawan Allah da kuke gani ba mutumin kirki bane, fasiƙi ne mara imani, daga shaidan sai shi, daga shi kuma sai fir'auna a wurin aikata zalunci...." bata ƙare maganar ba suka daka mata tsawar da ta razanar da ita, gaba daya sun ruɗar dasu, da ita da baba Obie sun rasa maganar wa zasu ɗauka sai dai sun yarda da mahaifinsu fiye da yadda suka yarda da kansu. Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da ya ƙame a tsaye kamar gunki sam ya kasa motsawa, tsantsar rudanine da fargaba akan fuskarsa. Damƙar hannunta baba Obie ya yi ya dinga janta yana faɗin, "Zo ki fice ki bar mana Estate, wuce ki tafi, mahaukaciya, makira annamimiya mai son haɗa uba da yayansa, ni nasan maƙiya ne suka turo ki don ki yi mini ƙazafi..." Fashewa ta yi da kuka tana kiran sunan Hateem dana Sharafudeen don su kawo mata ɗauki. "A'uzu billahi minasshaiɗanir rajim tuf tuf, wa innahu min sulaimanu wa'innahu bismillah! Aniyarki ta biki makira algunguma baƙar munahika" Ya faɗa yana tottofa mata yawu akan ta, sam sun kasa tsayar da shi, al'amarin ya rikita zukatansu. Tana kuka haɗi da waiwayonsu cikin shesshekar murya tana magana tana miƙa masu hannu, "Hateem kada ku bari ya fitar dani, Sharafudeen ka taimaka mini, kada ku bari ya ƙara raba ni daku! Na yi kewarku, Wlh ni ce mahaifiyarku Aurora Edward! Your momma, ban mutu ba, ba fatalwa bace ni, Owais Kada ka bari ya kore ni, Ni kaɗai ce zan iya fayyace maku komai akan shi, Owais kaima ba ka tuna ni ba kakarka momma? ...." Ta faɗa idanunta cike tab da ƙwalla, tana ta ƙoƙarin ƙwace hannunta daga mugun ruƙon da baba Obie ya yi mata sai dai ta kasa saboda babu karfi atare da ita. Hankalin Pravin Idan yayi dubu toh ya tashi, murnar da yake yi tuni ta koma ciki, ya murtuke fuska, hannayenshi biyu ya ɗaura a saman kanshi alamar ya shiga uku, ƙirjin shi kamar ana luguden ta6are, kafin ka ce me tuni ya haɗa uban gumi, jikinshi ya kama makyarkyata kamar wanda farfaɗiya ta kama. Har ya kusa fucewa da ita daga falon Sharafudeen ya yi kukan kura ya watsa da gudu ya nufe su, yana ƙarasowa ya bangaje baba Obie gaba daya ya kife ƙasa kafin ya ɗago Sharafudeen ya damƙo hannun Khala ya juyo da ita suka dawo Falon. Da sauri Hateem ya nufe su ya kar6e hannun Khala dake acikin na Sharafuddeen ya yi hugging ɗin ta akan broad chest dinsa, ya ƙanƙameta sosai kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta kamar yadda shima ya ji sanyi a ranshi, rungumar da ya yi mata tasa ya ƙara yarda mahaifiyarsu ce saboda wani yanayi da ya tsinci kan shi wanda uwa da ɗa kadai ke jin irin shi idan jikinsu ya haɗu da na juna. "Yaya kun yarda da ita? Kun yarda cewa momma ce?" Hajiya saratu ce ta faɗa a ruɗe "Ta yaya bazamu yarda da ita ba, koda kowa bazai yarda ba mu mun yarda mahaifiyarmu ce, ni tun lokacin da idanuna suka shiga cikin nata, raina ya bani momma ce..." A cewar Sharafuddeen. "In hakane taya akai ta rayu bayan ta mutu? kuma mun ga gawarta da idanunmu?" Ta jefa ma su tambayar . Sharafuddeen ya ce, "Shi yakamata ku tuhuma.." Ya faɗa tare da nuna baba Obie "Saboda na fara kokwanto akan shi! kuma dama shi borin kunya da hauka ake naɗe shi, in ba haka ba meyasa zai ɗaga hankalinshi don kawai ya ganta? Bayan haka a gabanku baba ya juyamin baya ya hana kowa ya yi magana akan tuhumar da Owais ke yi mi ni, wai har ni zai ce in kare kaina agurin Owais!....." Ya faɗa yana jifar shi da kallon tuhuma. Bai ƙarasa maganar ba Baba Obie Ya nufo su cike da rashin kuzari, yana fitar da huci kamar mayunwacin zaki ya nufi Khala da Hateem ya rungume, har ya miƙa hannu da niyyar ya damƙo ta, Sharafuddeen ya yi saurin damƙo hannunsa ya jefar da shi gefe ɗaya baima san sa'adda ya daka mashi tsawa ba, dama da haushinshi a cikin zuciyar shi. Gabansa ne ya yanke ya faɗi jin yadda Sharafudeen ɗan cikinsa ya daka masa tsawa kuma ya jefar da hannunsa, hankali a tashe ya furta, "Na shiga uku..!!!" "Baba, don't dare touch our momma! Don't touch her! Let her talk, Idan har kana da gaskiya meyasa zaka ɗaga hankali akanta huh? Ka barta ta yi magana mana!" rai abace Sharaudeen ya faɗa yana kallon cikin idanun shi. Zare idanu baba Obie ya yi with pure confusion on his face, Tsantsar mamaki ya hana su Sir mubarak furta magana sai binsu da idanu su ke yi. nuna kanshi ya yi da yatsan shi, "Sharafuddeen ni kake yi ma tsawa? Ka na cikin hayyacinka kuwa? Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.." ya faɗa yana dafe kanshi da tafukan hannayensa.. "Baka ga komai ba Obinna...." Tsohuwar ce ta faɗa tare da raba jikinta daga na Hateem ta dubi baba Obie da wani ƙasƙantaccen kallo mai cike da tsana.. "Dama bana faɗa maka ba akwai ranar ƙin dillanci? Shin ban fada maka duk min daran daɗewa asirinka zai tonu ba? Dama hausawa sun ce rana dubu ta 6arawo rana ɗaya ta me kaya, yau dubun taka zata cika...." Girgiza mata kai ya dinga yi idanunsa sun kaɗa jawur tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, ya rasa ya zai yi ya dakatar da ita.." Cikin raunanniyar murya ya furta, "Kada ki yi min haka! Na roƙe ki, kada ki tona mini asiri, Kada ki raba ni da ƴaƴa na, kada ki raba ni da mutuncina, Ki rufe mini asiri ki agazama rayuwata, ki taimake ni kodan saboda darajar ya'yan mu, In kika fallasa asirina kamar kin fallasa asirin ahalinmu ne, zaki ja mana tozarci a idon duniya...." Zubewa ya yi akan gwiwowinsa yana ci gaba da girgiza mata kai hadi da marairaice mata fuska don ta tausaya mashi. Kallo Ya koma sama, kalaman Baba Obie sun ɗaga hankulansu, sun jefa zuciyoyinsu acikin rudani tunma kafin su ji wani asiri ne nashi da baya son ta tona. "Lokacin da na dinga roƙonka akan kada ka kashe ni ka barni da raina baka yi hakan ba saboda zuciyarka ta ƙeƙashe babu ɗigon imani a ranka, zalunci kadai kasa a gaba, ba irin magiyar da ban yi maka ba amma ka toshe kunnuwanka kuma ahaka kake tunanin ni zan rufa maka asiri bayan Allah ya tseratar da ni uhm?" Ta faɗa tana kallonshi da raunatattun idanunta. Ruƙe ƙafafunta ya yi da hannayenshi ,"Dan Allah ki rufa mun asiri, kiyi min rai, kada ki kashe min rayuwata, na yi maki alƙawarin zan shiryu..." cikin jin ƙunar rai ta haɗiyi yawu mai ɗaci tare da kawar da idanunta daga barin kallon shi ta dubi sama hawaye na cigaba da zarya kan kuncinta, ranar da ta daɗe tana gargadinsa akan zuwanta, ba irin jan hankalin da bata yi mashi ba amma yaƙi ji yanzu wa gari ya waya? "Dan Allah ki faɗa mana dagaske momma ce ke? Dama baki mutu ba kina a raye? Kuma me ya faru dake? Me babanmu ya akaita? Dan Allah ki faɗa mana, kun ɗaga mana hankali, Kun ruɗar damu..." Hajiya Saratu ce ta fada fuskarta a yamutse, Sir Mubarak ya ce,"Momma ki faɗa mana gaskiya, muna son mu ji taya akai kika rayu bayan kin mutu? Kuma me mahaifinmu ya akaita maki? Sannan wani asiri ne nashi da baya son ki faɗa?" Tsantsar tausayinsu ne ya kamata, saboda tasan in ta faɗa su da farin ciki har abada, watakil ma baƙin cikin mahaifin nasu zai yi silar rasa ran wasu daga cikin su. Amma ya zata yi bata da mafita da ya wuce wannan, saboda alwashine ta daukarwa kanta, Allah ne ya amsa addu'arta shiyasa har ta rayu don ta tona masa asiri don haka bazata butulce ba, mutun azzalumi irin sa bai cancanci a rufa masa asiri ba. Cikin karyayyar murya tana kuka ta ce, "Ku yi haƙuri! ku yi haƙuri!! ku yi hakuri!!! da abun da zan faɗa, nasan abun da ciwo amma ya zaku yi ubanku ne ya ja maku, shine silar komai...." Ta faɗa da tsawa tana kuka jikinta har jijjiga ya ke yi, Chief Owais ya kasa furta kalma, sai rarraba idanunsa ya ke yi akan fuskar Obie da Khala haƙika sun jefa shi a ruɗani. "MAHAIFINKU OBINNA SHINE ELDER NA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, SHI DIN MUGUN MATSAFI NE, BAIDA IMANI, MUGUNTA DA ZALUNCI YASA A GABA, TUN FIL AZAL, DUKIYARSA BATA HALAL BACE, KUMA SHI BA MUSULMI BANE, ARNE NE, IDAN BAKU SAN KURKUKUN KADDARA BA, ZAN FAYYACE MAKU KOMAI, GIDAN KURKUKUN KADDARA GIDAN MATSAFA NE, YA KAFA SHI TSAWON SHEKARU TALATIN DA DAURIYA, ME AKE AIKATAWA A GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? ƘANANUN YARAN DA BASU JI BA BASU GANI BA SUKE KULLEWA A CIKINSHI, BA FUCE BA SHIGE, TUN SUNA JARIRAI SUKE RAINONSU HAR SU GIRMA, ZASU TASO BATARE da addini ba, ba salla ba sallati, sai tsantsagwaran jahilci cike da kansu, basu san wanene mahaliccinsu ba, gaba daya sun tauye masu hakkinsu na rayuwa, abu mafi muni suna azabtar dasu azaba mai radadi, su yi lalata da su, su sha jininsu, su kwanta da gawa, su cire sassan jikin su, kai har jarirai basu bari ba da mata masu ciki suna kwanciya dasu, matasan yan mata da suke tsaka da shan azabar Jinin al'ada a haka suke saduwa dasu duk watan Allah idan ya kama, Ni kaina bazan iya misalta rayukan da suka salwantar ba, Nima ina ɗaya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, saboda tsautsayi yasa na yi masu leƙen asiri nasan sirrinsu shiyasa ya shirya makirci ya dauke ni daga gare ku,....." Bata ƙarasa maganar ba Sir mubarak ya doka mata tsawar da ta yi silar firgicewarta, Yana huci ya ce, "Ƙaryane! Bazai ta6a zama gaskiya ba, kazafi ki ke yi masa, mahaifinmu bazai ta6a iya aikata munanan zunubban nan ba, mahaifinmu mutumin kirki ne, Mai jin tsoron Allah, mutun ne mai zuciyar imani da tausayi, bazai taba aikata abunda kike zarginsa da shi ba...." Bai ƙare maganar ba senate Lateef da ya gama harzuka zuciyarshi a wuya yai kukan kura zai shaƙe wuyanta, Sharafuddeen ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar damƙe wuyan hannunsa, yana huci ya ce, "Ka sake ni Sharafudeen!! Wannan mahaukaciyar matar ta rasa wa zata yi ma ƙazafi sai mahaifinmu? Baka ji munanan kalaman da ta jefe shi da su ba? Wai mahaifinmu ne matsafi? Ɗan kungiyar asiri???" Ya faɗa yana zare idanunsa da suka kaɗa jawur. Cikin jin ƙunar rai His excellency Abdul Razak ya girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya ce, "Wlh kodai ku fitar da tsohuwar nan ko kuma in kashe ta a gurin nan, ta ya zaku bar mahaukaciya tana cin zarafin mahaifinmu a gaban idanunmu, wannan ai zancen banza ne, wlh sai munyi shari'a dake dole ki fuskanci hukunci mai tsanani...." Deen ya amshe, "Ai ga irinta nan! tun farkon shugowarta yakamata a kore ta, ni bansan uban waye ya bata iznin shigowa ciki ba! Ku kuma kun yi tsaye kamar wasu sakarkaru a gabanku ake yi wa mahaifinmu ƙazafi, daga gani abokan adawarmu ne suka turota don ta tarwatsa zaman lafiyar mu...." Ya faɗa yana nuna su Hateem. Kalamansu sun cika kunnan baba Obie, wata irin karaya mai haɗe da faɗuwar gaba ce ta ɗarsu acikin zuciyarshi dake yi mashi wani irin mahaukacin bugun barazana, wani kallo yake binsu da shi mai wuyar fassaruwa ganin yadda suka haƙikance akan kazafi ne ake yi masa saboda yardar da su ka yi da shi. Cikin raunanniyar murya Khala ta ce, "Koda zaku kashe ni bazan fasa faɗar gaskiya ba, na yi maku uzuri saboda nasan irin yardar da ku ka yi wa mahaifinku, hakika ya cutar da rayuwarku, ya zalunce ku, tsawon shekaru kuna tare da mugun iri acikin ku batare da kun sani ba, Ya daɗe yana munafurtarku...." Ta ɗan dakata tana jan numfashi, sai ƙoƙarin kai mata bugu suke yi amma Hateem da Sharafudeen sun hana, sai ma suka katangeta ta yadda bazasu iya ta6ata ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, tana a tsakiyar su taci gaba da magana. "Dukiyarsa bata halal bace, Haramun ce tsantsa, ya ciyar daku da haram! Ya tufatar daku da haram!! Ya gina ku da haram!!! Mahaifinku mutunne mai neman duniya ido rufe, baidamu da lahirarsa ba, koda ya ke baiyi imani da Allah ba, burinshi ya shahara, darajarsa ta ɗaukaka duniya tasan da zaman shi, shiyasa ya jefa kanshi cikin halaka da ku kanku saboda kuma bai barku hakanan ba, duk wata nasara da kuka samu, da duk wata ɗaukaka da kuka samu, sun samo asali ne daga abunda mahaifinku ya ke yi maku, shiyasa baku ta6a faɗuwa ba a rayuwarku, ya sanya maku farin jinin da in har kuka shiga mutane sai kun shahara acikin su, haka zalika in kuka ta6a abu zai yi albarka......" Wannan karon bakinsu ya mutu bawai don sun yarda da maganar ba, sun dai fara wasiwasi acikin zuciyoyin su. Yanayin fuskokinsu ya nuna tsantsar tashin hankali da damuwa haɗi da rudanin al'ajabin maganarta. Baba Obie dake a zuƙunne kan gwiwowinsa ya kasa motsawa ji yake kamar an rufa masa bargon azaba a bayanshi saboda tashin hankalin da ya shiga, da wani ido zai dubesu a wannan baƙar ranar, gaba daya ya ɗimauce ji yake kamar ya haƙa rami ya binne kansa, babban abun takaicin sihirinsa ya ƙi tasiri a kanta, ya so tun farko ya dakatar da ita sai dai Allah bai yarda ba, this time around jikinta akwai kariyar ubangiji. Tsohuwa Khala bata dakata da yin magana ba taci gaba da cewa, "Sau nawa matayenku suna haihuwar ya'ya su zo babu rai a jikinsu ko bayan sun haihu jariran su mutu?" Ta faɗa tamkar tana yi masu tambaya, Ta ɗaura da cewa, "To waɗannan yaran ba mutuwa su ka yi ba, ku tambayi ubanku Obinna ina yaran ku suke! Ta faɗa a tsawace tare da nuna shi da yatsan ta. Tashin hankalin da ba'a saka mashi date!, Wlh alƙalamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyarsu ta karaya da ganin yadda ya yi shiru ya kasa kare kanshi daga abunda tsohuwar ke tuhumarsa." Cikin shesshekar kuka Hajiya Saratu take fadin, "Nashiga Uku! Na bani na lalace! Baba dan Allah ka yi magana! Baba ka ƙaryata tsohuwar nan! Baba ka agazamana zuciyarmu ta raunata! al'amarin nan ya fi karfin zukatanmu! Baba mu mun yarda da kai munsan bazaka iya aikata abunda take jefanka da shi ba, wlh kazafi ta ke yi maka, Mahaifinmu ba fasiƙi bane, mahaifinmu ba matsafi bane, mahaifinmu bazai taba iya aikata rashin imanin da kike tuhumarsa da shi ba, dan Allah baba ka tashi ka ƙaryata tsohuwar nan....!" Tana cigaba da kuka ta nufe shi ta dafa kafaɗunsa tana kokarin mikar da shi tsaye don ya yi magana sai dai ya ƙi bata haɗin kai, wasu irin narka narkan shatun jijiyoyine suka fito saman fatar goshinsa.. "Baba ka taimaka min, Ka agazama rayuwarmu, baba ka yi magana, na roƙe ka, dan Allah dan soyayyarka da manzon Allah SAW......" Murmushin takaici khala ta yi, "Hmmmm Saratu dama kin daina wahalar da yawun bakin ki, saboda a halin yanzu mahaifinku baida bakin magana, wannan kaɗai ya isa yasa ku gasgata magana ta..." Ta faɗa tana kallon fuskar baba Obie dake fitar da gumin zufa, shatun jijiyoyin wuyansa sun fito ruɗu ruɗu, jikinshi ya ɗauki wani irin mahaukacin zafi. "Duk wani jariri da matayenku suka haifa ya zo ba a raye ba sune suke ɗauke shi daga gare ku, da haɗin bakin munafukan likitocin asibitinsa, Ku tambayi munafuki MD Dr Jidanna, da Dr Adam da kuma Dr chisom, da sa hannunsu ake yi maku wannan aika aikar...." "Zaku haifi ɗa ku ganshi a mace alhalin ba shi bane rufa ido su ke yi maku su yi musayar shi da aljani su ɗauke na gaskiyar su tafi da shi gidan kurkukun kaddara, ku kuma ku dauki aljanin ku yi jana'izarsa ku rufe a ƙabari da sunan jinjirinku ku ka rufe...." ta faɗa cike da takaici, "Haƙiƙa Obie ya zalunce ku wlh wata shari'ar sai dai a lahira, amma fasiƙin mutumin nan ya daɗe yana aikata luwaɗi da zina da jikokinsa da ya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, ya sha jininsu, ya kashe su saboda neman duniya, bashi kaɗai ba harda sauran fasiƙan da suke aikata fasadi a bayan ƙasa, Elders din suna da yawa sune miyagun dake sadaukar da jininsu matsayin fursinoni, da yawa ma ƴa'ƴan naku azaba ce ke kashe su, cikin ka so ɗari baifi ka so goma ne ya rage daga cikin su ba...." Numfashinta ne ya fara tsaitsayawa, jini ya fara bleeding daga cikin hancinta hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Sharafudeen da Hateem ya yi ba.. Daurewa ta yi duk da azabar da ta ke ji a jikinta a haka ta cije ta ci gaba da cewa, "Na rantse da wanda raina ya ke a hannunshi duk abunda na faɗa maku ba ƙarya bane, idan baku yarda ba, gayanan agabanku ku turkeshi ya fada maku gaskiya...." Tsayawa ta yi tana haki fuskarta ta jiƙe sharkaf da gumi, ta dafe saitin zuciyarta da tafin hannunta... "Kamar yadda na faɗa maku, bashi kaɗai bane Elder, akwai muƙarrabansa da suke take masa baya, Amininsa Ifeanyichukwu inkiya Jan kunne amma a gidan kurkukun kaddara jan harshe shine nickname dinsa, shine Mataimakinsa a tare suke aikata fasadi, abun takaici sun auri junansu tun da daɗewa saboda tsantsagwaran jahilci da tumasanci...." Kutumar U! Zaro idanu suka yi kamar ƙwayar zasu faɗo ƙasa, sun shiga matsanancin tashin hankali, maganarta ta ƙara dagula masu lissafi, jin abun suke kamar wasan kwaikwayo. "Bayan haka, surukinku mijin Saratu, shine Jan kunne na gidan kurkukun ƙaddara..." Tunkan ta ƙarasa maganar hajiya Saratu ta daddafe kanta da tafukan hannayenta, ta dinga girgiza kanta, tsabar kiɗimar da ta yi ne yasa ta dinga sambatu kowace addu'a ta zo bakinta furta ta kawai ta ke yi.. Runtse idanunta ta yi ruɗu yama hana ta iya tantance me Khala take nufi, buɗe idanunta keda wuya Unexpected ta hango Pravin da ya arta a guje ya nufi sashen yan aikin gidan, aikuwa jikinta na 6ari tabi bayan shi... Khala bata dakata ba, ta ci gaba da cewa, "Sir Benjamin baturen amuruka, abokin mahaifinku wanda suka yi tashen yawon duniyarsu atare da obie da amininsa, shine jan le6e na gidan kurkukun ƙaddara, mugun fasiƙi ne....." "Bayan shi sai baƙin shaidanin da taƙadarancin sa yafi na fir'auna, zan iya cewa tun da Allah ya halicce ni ban ta6a ganin mugun bawa irinsa ba, bazan iya misalta mugayen zunubban da yake aikatawa ba, shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon giants ɗin kurkukun ƙaddara, baida imani ko misƙala zarratin, asalin shi bawan Obie ne daga baya da likafa ta ci gaba sai ya bashi muƙamin Elder...shish.. Shish..... Kasa ƙarasawa ta yi saboda abun da ya sarƙe maƙoshinta, dama ba koshin lafiya ne da ita ba, jiri ne ya kwasheta a galabaice ta yanke jiki zata faɗi, cikin sauri Sharafudden ya sungumeta ya kwantar da ita akan doguwar kujera, sai kokarin ƙarasa maganar take yi amma ta kasa... Wai shin Ina Chief Owais? bawan Allah Komai dake faruwa akan idanunsa kuma kunnuwansa na sauraro, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, zufar dake tsastsafowa ta saman fatarsa ta jiƙe jikin shi sharkaf, kwata kwata ya gaza yarda da abunda Khala ta faɗa, Gani yake kamar mafarki yake yi ba gaske bane, duk da ya gama raunana zuciyarshi ta karaya da ganin yadda baba Obie ya yi shiru bai tanka ba! Hakan na nufin da gaske ne ba kazafi aka yi masa ba tun da ya kasa kare kan shi, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! La'haula wala quwata illa billah, da wannan ranar ƙwara mutuwarsa, addu'o'i yake ta nanatawa acikin zuciyar shi.. Jiki a mace Sir mubarak ya zauna kan Sofa, zafi ne ya taso mashi har ta kai ga ya tu6e rigar shi ya jefar da ita ƙasa, ya ɗaura gwiwar hannunsa akan hand sofa ya zagba uban tagumi, kamar wanda ya rasa gata a duniya. "Deen! kana jin abun da nake ji kuwa? Deen Ka tsunƙule ni dan Allah inaso na tabbatar in ba mafarki nake yi ba..." Cikin raunanniyar murya His excellency Abdul Razak ya faɗa yana kallon His excellency Deen da ya haɗa uban gumi a jikin shi, girgiza kai ya yi cikin karyayyar murya ya ce, "Ba mafarki bane, kada mu yaudari kanmu! Da gaske ne komai ke faruwa, baba da muke sa ran zai kare kansa daga ƙazafin da tsohuwar nan ta yi masa ya kasa, gashi nan yana ji ya yi shiru..." Ya faɗa yana nuna Obie.. Muryar Sharafuddeen ce ta katse shi da cewa, "Abun da momma ta faɗa akansa ba ƙarya bane, ya aikata ne shiyasa ya kasa kare kansa....." "In kuwa hakan ya tabbata gaskiya ne, Baba ka kashe mana rayuwa, ka gama da mu, mun mutu, mun bani mun shiga Uku! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un......" Senate Lateef da ya ɗauko maganar bai kaita karshe ba Ya yanke jiki ya faɗi a sume, a firgice Deen da Abdul Razak suka rufa akan shi suna ambaton sunan shi haɗi da bubbuga jikin shi don ya tashi.. "Ruwa, tana buƙatar ruwa..." Hateem ne ya yi maganar, cikin sauri Sharafuddeen ya je ya dauko bottle water me sanyi yana gab da zai ƙaraso Ya lura da Owais dake a tsaye baya motsi da alama suman tsaye ya yi, wuce shi yayi ya nufi Hateem ya miƙa masa robar ruwan Ya kar6a yatsun hannunsa na kerma ya kanga ma tsohuwa Khala a baki, kusan rabin ruwan ta shanye sam ta kasa magana idanunta ma sun rufe gam bata iya buɗe su. Kar6ar robar Sharafuden ya yi daga hannun Hateem cike da rashin kuzari ya nufi su Deen Ya mika masu bayan sun yayyafa ma Senate Lateef ya farfado yana sambatu kamar mai tabin hankali har yana fadin Allah yasa mafarkine abunda ya ji. Kar6ar robar ruwan ya yi daga hannun Deen ya je gaban Owais ya daddage ya watsa mashi ruwan a saman fuskar shi, lokaci ɗaya yaja dogon numfashi ya furzar da shi da wani irin zafi. Kamar mahaukaci haka ya damƙi gaban rigar Sharafudeen hawaye na zarya akan kuncinsa da wata irin karyayyar murya ya ce,"Ka faɗa min kaima kana ɗaya daga cikinsu?" Ya fahimci ba ya acikin hayyacinshi, tsigar jikinshi duk ta tashi haiƙam zuciya ta riga da ta tsinke. Tsananin tausayin shine ya kama shi, Cikin sanyin murya ya ce, "Bana ɗaya daga cikin su Owais..." "Meyasa ka kasa kare kanka lokacin dana tambayeka?" Girgiza kanshi ya yi, "Saboda na daukarwa baba alƙawarin bazan faɗa ma kowa ba..." Katse shi ya yi, "Wani alƙawari ne ka daukar masa?" "Shine ya kira ni a waya ya faɗamin zaku je kai farmaki gurin matsafa masu haɗarin gaske, ya gargade ni akan kada in kuskura in barka ka je, nace mashi ai yafi kusa da kai kafi jin ma maganarshi, me zai hana ya yi maka magana, sai ya ce min ba ya son bacin ranka ne yasan idan ya hana ka zuwa baza ka ji daɗi ba, shiyasa ya kasa amma yasan ni idan na yi maka magana bazaka ji komai ba, kawai in baka umarnin kada ka je, nace mashi baba ban ta6a hana Owais ya je kai farmaki ba, hasalima ni nake ƙarfafa masa gwiwa akan aikinsa idan na hana sa wannan karan dole zai ji ba daɗi ne, sai ya fara min faɗa yana fadin har shi zai bani umarni in ƙi bi! Yana magana ina magana, da ni da owais din duka ba a ƙarƙashin ikon shi muke ba? Na dinga bashi haƙuri har saida na amince zan yi maka magana tukunna ya haƙura, Sannan ya ce zai turo da ɗan saƙo da maganin bacci in saka maka a cikin Coffee, saboda in kasa kafiya ka turje akan ba zaka bi umarnina ba, sai in baka kasha coffee din, kuma baya son kasan shi ya sakani, nayi masa alkawarin bazan bari ka sani ba, kaji dalilin da yasa lokacin da na kira ka a resting home dina ka ƙi bani hadin kai ni kuma na baka coffeen dana zuba maganin baccin ka sha...." Gaba ɗaya maganganun Sharafudden a cikin kunnuwansu sun ji komai, hankulansu sun ƙara tashi, cikin rawar murya Owais ya ce, "Kana nufin baba shine ya hanani kai farmaki, kuma shine ya sa ka bani maganin bacci, amma a daren ranar ina ka je saboda an faɗa min ba a gan ka ba?" Ya fada a ƙagare da son jin amsar shi.. "Owais ni ban je ko'ina ba, ina a villa, adakin mommynka na kwana zaka iya tambayarta ka ji, bayan haka sanin kowannanku ne Villa tana da tsaro, ba yadda za'a yi shugaban ƙasa ya yi fitar sirri in the midst of the night batare da wani daga cikin security ya bi shi ba, Allah shine shaida ta..." Ya fada fuskarsa a yamutse. "Hakan na nufin Baba shine ya ƙulla maka makirci saboda ya ɗaura maka laifin sa? Ko don ya shiga tsakanina da kai?" Jinjina kai Sharafudden ya yi,"Babu tantama Owais, baba shine Master planner ɗin da ke shirya maƙarƙashiya atsakaninmu, bansan meyasa ya yi hakan ba..." Cikin shesshekar kuka ya ƙarashe maganar, wata irin juwa ce ta ɗibi Chief ya yi taga taga zai kife ƙasa cikin zafin nama Sharafudeen ya janyoshi ya rungume abunsa akan kirjinshi, atare suka fashe da matsanancin kuka tamkar ransu zai fita. Haƙiƙa baba Obie ya muzanta, kunyar duniya ta kama shi, ya shiga matsananciyar damuwa, bai ta6a zaton wannan ranar zata zo ba, Wani irin azababben ƙunci da bakin ciki da takaici ne suka turnuke zuciyar shi, jin kanshi yake kamar ba mutun ba saboda tashin hankali. A zabure ya miƙe kamar mahaukaci ya juya jikinsa na 6ari zai bar wurin sai dai kafin ya kai ga tafiya Owais ya hango shi, a zuciye ya 6an6are jikinsa daga na daddynsa ya nufi baba Obie cikin zafin nama ya damƙi damtsen hannunsa ya juyo da shi suka fuskanci juna gaba da gaba, kunya ta hana baba Obie ya haɗa ido da Owais saidai ya sadda kanshi ƙasa. Cikin raunanniyar murya ya ce, "Baba kai kaɗai ne zaka share min shakku na, Ina so na ji daga bakin ka, da gaske kaine Elder na gidan kurkukun ƙaddara? Kuma kaine mutumin da ya fitar da ni daga fagen yaƙi ya jefa ni a daki uhum??" Ya faɗa cike da fargaban amsar da zai bashi, wlh ya yi fatan ace zai iya kare kansa sai dai ya kasa saboda asirinsa ya riga da ya tonu. Gaba ɗaya idanunsu na a kan fuskarshi amsar shi kawai suke jira su ji, batare da ya ɗago da idanunshi ya dube shi ba ya jinjina mashi kai alamar Eh, a lokaci ji ya yi kamar ya haƙa ƙasa ya binne kansa saboda baƙin cikin da ya ziyarci zuciyarshi, raɗaɗin da suka ji yafi na ƙunar wuta zafi..Ya Ilahi! Zuciya ce ta ɗibi Owais baisan sa'adda ya ci kwalar rigarshi ba, da hannu biyu ya damƙe shi sosai jikinshi na 6ari. Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, duk irin jarumtakar namiji hakan bai hana sun fashe da kuka ba kamar ƙananun yara, gaba ɗaya sautin koke kokensu ya cika falon, wasu suka dafe kawunansu da tafukan hannayensu saboda azabar radadin da zuciyarsu ke yi musu, wlh sun yi danasanin zuwansu duniya a lokacin, sun ji ɗaci a ransu, ranar ta zame masu mafi muni a rayuwarsu. Gaba daya suka kewaye shi suna tambayar shi don me zai yi musu haka? Meyasa ya ci amanarsu ya ha'ince su? Wannan wani irin neman duniya ne? Me yasa ya aikata musu hakan? Wlh Hankalinsu ya tashi matuƙa, duk sun fita hayyacin su, kuka kawai suke yi kamar ransu zai fita.. Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, bai ta6a danasanin irin rayuwar da ya daukarwa kansa ba irin yau, saboda Allah ya jarabce shi da masifar son ya'yan shi, Koda ya ke sadaukar da jikokin shi bai ta6a sadaukar da ya'yan shi ba. daƙyar ya iya haɗiye baƙin cikin shi, da wata irin karyayyar murya ya furta, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN!!! Na shiga Uku! wlh na daɗe ina fargaban zuwan wannan ranar, dama nasan duk mun daran daɗewa asirina zai tonu ne sai dai ban ta6a zaton zai tonu ta wannan hanyar ba! Ranar da nake jin zullumi da fargaban zuwanta, ranar da nake jiye ma kaina tsoron zuwanta, ya zan yi da rayuwana? ya zan yi da rayuwarku? Nasan na cutar da rayuwarku cuta mafi muni, na zalunce ku, na kuma zalunci kaina, Amma koma dai menene bakin alƙalami ya riga da ya bushe, na riga dana tabka babban kuskure, ban kuma san da wasu kalmomi zan roƙe ku gafara ba, banma cancanci in nemi yafiya agurinku ba, wlh na muzanta, na tozarta, na ji kunyar haɗa idanuna da ku, kaicona!...." Bai ƙarasa maganar ba ya fashe da kuka, hawaye suka wanke fuskar shi, mutumin da sun manta when last suka ga hawaye ya zuba daga cikin idanunsa saboda jarumtakarsa ashe tsantsagwaran matsafine, Yana kuka suna kuka an rasa me lallashin wani, daƙyar yake kallon fuskokinsu cike da jin nauyin abun kunyar da ya aikata musu. "Nasan na biyewa son zuciya, amma wallahi ba laifina bane, Nima gado na yi, tun kakanninmu da iyayenmu na taso acikin matsafa, shine hanyar samunmu, na yaudare ku da musulunci amma ni ba musulmi bane, arne ne ni kamar yadda ta faɗa muku, tun da na taso rayuwata bansan mai kyau da mara kyau ba haka iyayena suka tarbiyantar da ni, duk abubuwan da suka faru son zuciya ne da son ɗaukaka, buri na in tara dukiya, in ɗaukaka in zama shahararre a duniya, ƴa'ƴana ma su ɗaukaka a idon duniya, wannan dalilinne yasa gaba ɗaya kuka ɗaukaka kowannanku na nema masa duniya kuma ya same ta..." Bai ƙare maganar ba HATEEM ya katse shi ta hanyar cakumar shi cikin tsananin tashin hankali ya furta, "Baba! Baba!! baba!!!...." Idanuwansu cikin na juna a marairaice yake kallon shi.. "Meyasa ka za6i ka ciyar da mu haram? Baba duk irin ƙaunar da muke yi maka, kullum burinmu mu kare maka mutuncinka sai gashi kai ka zubar mana da namu mutuncin, ɗaukakar daka sama mana ta tashi a banza wlh! Saboda da zarar mutane sun ji abunda kake aikatawa wlh mun zama abun gudu, za'a juya mana baya ne a tsangwamemu zamu zama abun ƙyama, makiya zasu samu damar cuzguna mana, Baba ka bar mana mummunan tabon da mutane zasu dinga cin zarafin mu da shi! Haba baba! Wlh ka bamu mamaki baba, wai mahaifinmu ne yake aikata munanan zunubban nan?" Ya faɗa yana haɗiyar yawu mai tsananin ɗaci cikin mutuwar jiki ya sake shi.. Sharafudeen ya ɗaura da cewa, "Baba yanzu ina amfanin irin wannan? Wace riba ka samu baba? Ina hankalinka yake? Tayaya ka bari shaidan da zuciya suka rinjaye ka? Kamanta da wata rana zaka mutu ka koma ga Allah, baba Idan ka nema mana duniya lahirarmu fa? Ya kake so mu yi baba? Muna alfahari da kai, kaine abun tunƙahon mu, kaine silar ɗaukakarmu ashe mun yaudari kanmu baba, A yau mutuncinka ya zube acikin idanunmu baka da sauran daraja baba, wlh da wannan bakin cikin daka ƙunsa mana da kashe mu ka yi kamar yadda ka saba kashe ya'yan mutane...!" Kuka ne ya ci ƙarfinsa har ya kasa karasa maganar.. Baba Obie sai kuka yake yi babu ƙaƙƙautawa.. Senate Lateef ya ce, "Baba wace shafewar basira ce ta same ka? Ni abun da ya dauremin kai yadda har ka iya kashe mutun ka sha jinin shi, ka kuma lalata rayuwar yaran da basu ji ba basu gani ba, baba wa ya koya maka zaluncin nan? Har yanzu na gaza yarda kaine kake aikata hakan Baba, Tsawon shekara nawa kana aikata fasadi a doron ƙasa! Wallah baba da ace ka yi hakuri tun fil azal ka yi rayuwarka cikin talaucinka da sai ya fiye mana kwanciyar hankali, shi arziki da daukaka na Allah ne, sai wanda ya so yake bawa, watakil ma kana ɗaya daga cikin wadanda Allah ya tsaga da rabonsu kaine baka sani ba, ka biyewa son zuciyar ka baba, gayanan ka jefa rayuwarmu a halaka, bayan haka jin dadin duniya ƙalilan ne baba, gaba dayanmu mutuwa zamu yi, komai muka mallaka anan gidan duniya zamu barshi, lahiri itace dawwamammiya, wlh da wannan masifar daka jefa mu a ciki wlh gara ace mun taso rayuwarmu a matsayin musakai marasa gata a duniya da dai irin wannan rayuwar, baba yanzu da ka ɗaukakamu ya zaka yi da mu? sai da ka bari duniyar tasan da zamanmu ana yi mana kallon mutane masu daraja da ƙima, masu martaba a idon duniya, yanzu idan suka ji miyagun laifukan da kake aikatawa me kake tunanin zai biyo baya?" Ya jefa mashi tambayar yana kuka yana girgiza kai. kafafunsa ne suka gaza ɗaukarsa ya zube kan gwiwowinsa, idanunsa sun rune jawur, kumatunsa sun yi jajir, duk ya faffasa labbansa da haƙoransa, gemunsa ya jiƙe sharkaf da ruwan hawayensa, Ko'ina na jikinsa zufa ce take tsattsafo masa kamar babu A.c a falon. Wlh ya sadaƙas bai ta6a zaton zai ji kunyar zunubban da yake aikatawa ba sai yau da Khala ta fallasa asirin sa a gaban ya'yansa mafi soyuwa a gare shi. Dukkan ilahirin jikinsa kerma ya ke yi, ga wani irin azababben zazzabi da ya lulllu6esa, mutumin da sai ya yi shekara da shekaru bai yi ciwo ba saboda ƙoshin lafiyar dake gare shi to yau dai hada matsanancin ciwon kai, bazama a raza ciwon zuciya na farat daya ba saboda depression din da ya kama shi, gaba ɗaya suka zauna kewaye da shi kamar malami da almajiransa kuka hada majina, sun kasa tsayar da kan su. 😭 Daƙyar ya iya furta, "Idan na ce ku yi hakuri ban yi maku adalci ba, iya cutarwa na cutar da rayuwarku, ban cancanta na ci gaba da rayuwa ba, nasan a halin yanzu da kuka gano wanene ni kun tsane ni fiye da komai na duniyar nan, don haka na miƙa wuyana a gare ku, nasan na aikata maku ba dai dai ba, Ku yanke mini duk wani hukunci da kuka ga ya dace dani, ku azabtar da ni, sannan ku kashe ni, idan ba haka ba, Ni zan kashe kaina, saboda bazan iya cigaba da rayuwa da abun kunyar da na aikata muku ba..." Yana faɗa yana kuka haɗi da tari. Sama sama khala dake a kwance kan Sofa take jiyo maganganunsu, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, ta tona masa asiri burinta ya cika sai dai bata yi farin ciki ba, saboda halin da ya'yan shi suka shiga shiyasa kafin ka fara aikata wani abu mara kyau ka fara tunanin makomarka da kuma halin da zaka jefa wanda ya yarda da kai abun yana da ciwo. "Ku kashe ni, in har baku kashe ni ba mutane bazasu ƙyale ni ba, ku kashe ni kawai nafi so na mutu a hannunku, ko dan saboda ku dauki fansar abun dana aikata maku, ku kashe ni na ce, in ba haka ba zan kashe kaina..." Zumbur ya miƙe jikinshi na kerma, Lokaci daya gabansu ya fadi ganin jinin da ya wanke gaban wandon shi. Har suna haɗa baki gurin ambaton sunanshi, Allah sarki duk da abun da ya aikata hakan bai hana su ɗaga hankalinsu a kanshi ba, "Mu kai shi asibiti kada ya rasa ranshi!" Sharafuddeen ne ya yi maganar a ruɗe. Har sai da baba Obie ya dube shi da raunatattun idanunsa, ƙasa ƙasa da murya ya ce, "Duk abunda na yi maka baisa ka daina damuwa da ni ba Sharafuddeen....?" Girgiza kai ya yi, "Ku yi hakuri bazan je asibiti ba, ku barni a gida, in ma mutuwace ta riske ni a cikin ku...." Yana ƙarasa maganar ya shallake su ya juya a hanzarce ya nufi part ɗinsa, da gudu suka bi bayanshi kafin su ƙaraso tuni ya shige ɗakin ya ja ƙofa ya datseta ta yadda ba zasu iya buɗeta ba. 😭 Yanke jiki ya yi ya faɗi kan floor ya dinga birgima yana bubbuga goshinsa kan floor har saida ya fashe jini ya 6alle masa, daga waje suna juyo kururuwar azabar da yake fitarwa mai kuwar gaske kamar zai fasa dodon kunnuwansu. Da iya ƙarfinsu na karshe suka dinga bubbuga ƙofar hadi da ambaton sunan shi da karfi. Chief kamar zai 6alle ƙofar da kafaɗarsa ya dinga bangazarta duk da raɗadin da ya ke ji. "Baba ka buɗe mana ƙofa, bamu gama magana da kai ba, baba kada ka mutu kabar mu, baba dan Allah ka buɗe bamu gaji da ganin ka ba, akwai tambayoyin da baka bamu amsoshinsu ba, baba! baba!!, zamu iya yafe maka amma ka buɗe mana kofar, baba pls, baba pls, idan ka tafi ka barmu a cikin wannan mawuyacin halin daka jefa mu ya kake so mu yi da rayuwarmu! Ka taimaka mana baba, ka fitar damu baba.. " Ba irin bugun da ba su yi ma kofar ba amma ta ƙi 6allewa, a karshe da suka galabaita a gaban kofar ɗakin nashi suka zazzauna suna cigaba da yin kuka kamar masu zaman makoki. Gaba ɗaya abun da ke faruwa ƴan aikin gidan basu sani ba, saboda anyi masu iyaka da shiga falon dama ƙa'ida idan za'ayi family meeting ba'a buƙatar bare agurin shiyasa kwata kwata basu leƙo ba kuma basu ji sautin koke koken da ake yi ba, saboda akwai tazara tsakanin sashen su da main falo. _____________________PRAVIN 🥵 Tun lokacin da khala ta fara fallasa asirin su, cikin rawar jiki ya bar falon batare da sanin kowan nan su ba, bai nufi ko'ina ba sai sashen yan aikin gidan. A lokacin Hajjaty tana a ƙudundune cikin bargo har ta samu bacci ya ɗan dauke ta, kwatsam ba zato ba tsammani kamar daga sama ta ji an cakumeta, ta fasa ƙara tana kokarin kwache kanta cikin ruɗu da tashin hankali, kwata kwata batasan wanene ba saboda bargon da ya lullu6e fuskarta, a saman kafaɗarshi ya sa6e ta, tana kuka tana ihu tare da ambaton sunan pravin don ya kawo mata ɗauki, juyawar da zai yi keda wuya ya yi arba da hajiya Saratu dake shugowa ɗakin afujajan nan take gabanshi ya yanke ya faɗi ya zazzare idanunshi yana kallon ta kamar yadda take kallonshi da tsantsar tashin hankali akan fuskarta.. Numfashinta na fita da hucin bacin rai ta ce,"Munafiki, Gidan ubanwa zaka kai ta eye? Yan iska maciya amana, wato Kun daɗe kuna cin amanata, yanzu da ka ga asirinka ya tonu shine ka lalla6o ka saci jiki ka shugo don ka dauki kwartuwarka don ku gudu ko?" Ta faɗa tana zare idanunta. Tsawa ya daka mata har saida ta razana, muryarsa na rawa ya ce, "Ki matsa ki bani wuri in wuce tunkafin in yi maki illah!" Cikin fusatacciyar murya ta ce, "Illah kuma ta nawa? Ka bani mamaki pravin, Ka karya min zuciyata, munafuki dama na daɗe ina zargin Hajjaty ashe tare kuke aikata fasiƙanci, wai a haka na aure ka na haifa maka ƴa'ƴa, Ka cutar da rayuwata pravin, hakkina da na ya'yanka bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba wlh, kuma na rantse babu gidan ubanda zaku je, mayaudaran banza, dole ku gurbi abun da kuka shuka..." Bata ƙarasa maganar ba, sakamakon naushin da ya sakar mata akan kuncinta, nan take gefen bakinta ya fashe ta fara bleeding, azabar zafin da ta ji ne yasa ta dafe gefen bakin, da mamaki ta furta,"Pravin! yau da hannunka ka dake ni? Inna lillahi..! " Rai a 6ace ta yi kukan kura ta haɗa su duka biyun da shi da Hajjaty ta hankaɗa su gaba ɗaya suka kife ƙasa, bargon jikin Hajjaty ya warware baiwar Allah tuni ta jima da sumewa sakamakon buguwar da kanta yayi dama ya lafiyar gwiwa. Ransa ya 6aci matuƙa, a harzuƙe ya yunƙura ya mike Ya nufi hajiya Saratu batai aune ba, ya damƙi ƙeyarta da hannunshi ya jata ta karfi ya nufi mirror tana ta kokarin ta kwace kanta sai dai ta kasa saboda raunin da zuciyarta ta yi yasa ta kasa ta6uka komai. Yana isa gaban madubin ya buga kanta jikin shi nan take madubin ya fashe, duk ya sossoke fuskarta, tuni ta fara bleeding, kukan ma ta kasa yi saboda zogin azabar da ya ratsa sassan jikin ta, ya ɗago da kan nata ya wurgar da da ita a galabaice ta kife kan floor ta mirgina numfashinta yana ta kokawar ɗaukewa. Hakan bai masa ba sai da ya take yatsun hannayen ta da tafin ƙafarsa duk ya murjesu suka faffashe jini ya soma tsastsafowa. kwata kwata babu imani a zuciyarsa, ga idanun nan nasa sun kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin su, Ya na huci ya furta, "Allah ya isa tsakanina da ku, Dangin matsafa masu arziƙin jini, Duk ubanku ne ya ja min shiga halin da nake a ciki, shine mugun da ya sa na jefa rayuwata cikin halaka ina zaman zamana lafiya, dama ni ban ta6a son ki ba, dukiyarki ce tasa na aureki da kuma kwaɗayin surar jikin ki, Kin daɗe kina baƙanta min rai ke ga mai arziki ɗiyar ƙaruna, ki yi ta min gorin arziƙi don ina zaune a gidan ku, to ai ga irinta nan, yanzu ai kin gane arzikin naku bana halal bane ko? Ya faɗa yana tottafa mata yawu a kan fuskarta. "Kuɗin jini ne kuke tunƙaho da su, wlh badan ƴa'yan dake tsakanina dake ba da ba abun da zai hana in huce haushina a kanki, zan bar ki da ranki ne ba don na so ba.." Ya faɗa yana kallon fuskarta da ta jiƙe sharkaf da jini kamanninta har sun sauya saboda azaba ta gama fita hayyacinta, juyawa ya yi da sauri ya nufi bargon Hajjaty ya janyo shi ya rufa mata a jikinta tare da nannaɗeta a cikin bargon ya mayar da ita kan kafaɗarsa, Ya tsallake hajiya Saratu dake a kwance rai hannun Allah cikin sauri ya fuce daga ɗakin, batare da sanin kowa ba ya gudu daga Estate ɗin......💔 ___________________________________✍️ *_(SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN AHLIN FAMILYN SUKA KARASO SUKA JI ABUN DA KE FARUWA❓GA HAJIYA SARATU AKWANCE RAI HANNUN ALLAH! WA ZAI KAI MATA DAUKI❓ YA RAYUWAR BABA OBIE ZATA KAYA ZAI KASHE KANSHI NE KO KUWA❓ ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN ELDERS SUKA JI LABARIN ASIRIN ELDER YA TONU❓YA LABARIN PRAVIN DAYA GUDU DA HAJJATY GIDAN UBAN WA ZAIJE❓ DA WANI IDO YA'YAN BABA OBIE ZASU FUSKANCI DUNIYA? KUNA TUNANIN BA ZASU FUSKANCI KALUBALE BA AKAN MUKAMAN SU❓ TAYA ZA'A HADA KOWANI PRISONERS DA IYAYENSA❓ TAYA ZA'A KAMA SAURAN ELDER❓ TO WAINI TAYAYA MA AKAI TSOHUWA KHALA TA RAYU?😳 YANZU NE LOKACIN DA ZAKU ƊAURA ƊAMARARKU TAMAU DON JIN YADDA ZATA KAYA🔥💪_* *Gani ga wane Ya ishi wane Jin tsoron Allah😭 page din nan ya taba zuciyata)* *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥🔥😭* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*