Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 *Dedicated this page to you my one and only friends Mom muwadda and Pink darling Ina sonku sosai Allah ya bar mu tare🥰😍🥰* *Maman ihsan da sauran members na Jajirtattu ina mika gaisuwata gare ku. Na gode da haɗin kai da kuma gudunmawar da ku ka bani Allah ya ƙara haɗa kawunan mu sannan ya bamu zaman lafiya mai ɗore wa🙏* بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! Aminci ya tabbata ga shugaban fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW. Da sahabbansa da matayensa baki ɗaya. Yau ma kamar kullum gani tafe da sabon littafi na mai suna. *KUNDIN CINIKAYYA* wanda yake ɗauke da ilimantar wa,wa'azantar wa, kayatar wa, da kuma nishadantar wa* Daji Magarƙama da kuma Birni. Three siblings from different part of the world 🌎 *Ban yarda a chanza min littafi ta ko wace tsiga ba Koh kuma s sayar min da littafi na tare da sani na bah Koh kuma s ɗora min littafi a internet bah tareda izins bah toh idan kuwa mutum ya kuskure ya chanza min littafi, yaje na bar shi wa Allah*. *Kuma ba zan yafe masa bah* Ban yi wannan littafin dan cin zarafin wani koh wata bah, nayi shi ne domin mutanen al'umma su amfana da darusukan dake cikin ta. Idan wannan littafin yayi dai-dai da rayuwar ka toh arashi nee *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣▶️2️⃣* *________________________* *JIGAWA STATE* *DUTSE 🪨* *FEDERAL HIGH COURT* *DUTSE* *SHEKARA TA DUBU BIYU DA BIYAR * __fitowa ta yi daga cikin Motar 'yan sanda yayin da hannayenta ke sanye da handcuf. Nan ƴan sanda suka kalle ta tare da yi mata nuni da ta yi gaba. Tafiya ta fara yi cikin kasala da fauwala wa Allah lamuranta. Ta ke mutanen wajan suka fara tofa albarkacin bakinsu a kanta yayin da suke Allah wadai da halinta. Kare ta police ɗin wajan suka shiga yi gudun kar wani a cikin jama'ar wajan ya yi ƙoƙarin illatata. shigar da ita cikin kotu suka yi mai matukar girman gaske. Cikin kotun ya kasance mai matuƙar faɗi gaske benci da wajan tsayawar shaida kake gani tare da kujeru, tebura, kofofi, lectern sai ƙaramin tebur don wakilin kotu kusa da benci na alkali an rufe da magatakarda kotu, sai kuma katako shinge mai raba shari'a daga gallery. gefe guda jama'a ne da ƴan sanda yayin da lauyoyi suke tsaye tare da alkali. Kallon su alkalin ya yi tare da basu damar zama. Zama kowanen su ya yi yayin da kotun ta yi shiru tamkar babu wani ɗan adam dake cikin ta. Mai da kallon sa alkali ya yi kan wanda hake tuhuma yayin da ya bata umarnin da ta fito gaban kotu domin jin hukuncin da haka yanke. Jiki a sanyaye ta miƙe tsaye tare da nufar gaban kotu tana mai fuskantar jama'an dake cikin wajan. Magana Alkalin ya fara yi kamar haka, "A bisa hujjoji da muka yi la'akari da su, bisa dogaro da abubuwan da haka bayyana tare da ƙwaƙwarar bincike cewar Mrs Laila Abdullahi tana amfani da kamfanin ta da sunan tana taimakon talakawa bayan kuma safaran yara ta ke tare da aika mata ƙasashen waje domin yin karuwanci suna samar mata da kuɗaɗe sannan tare da miyagun ƙwayoyi da kayan maye wanda duk mun sani cewa doka ta haramta yin hakan". " Don haka wannan kotun mai albarka ta yanke nan da sati ɗaya za'a mata hukuncin kisa ta hanyar rataya. Yana kaiwa nan. Kwamitin alkali ne suka miƙe tsaye tare faɗin. "Court". Jin hakan ya sa kowa fita daga cikin kotun yayin da kowa ke farin ciki tare da murnan hukuncin da kotu ta yanke mata. Fitowa Mrs Laila Abdullahi ta yi hawaye na bin kan ƙuncinta. Gefe guda kuma mutane ne a tsatsaye suna mata tofin Allah tsine. Shigar da ita jami'ai suka yi cikin motan ƴan sanda yayin da haka nufi can prison da ita. Bayan wasu kwanaki warders suka fito da ita jikinta sanye da kayan magarƙama tare da nufar inda za'a rataye ta. Kuka sosai ta ke tamkar ranta zai fita yayin da ta ke ji ina ma ta samu koda mutum ɗaya wanda zai yarda cewa bata aikata miyagun laifukan da haka tuhume ta dasu bah. Sai da haka kaita har inda za'a rataye ta. Nan ta ke mai zartarwa ya fito da igiya yayin da haka ɗaure igiyar a sama. Sannan haka ɗauki abin rufe fuska haka rufe mata fuska da baki. Sannan haka saka kanta saitin igiyar tana ihuu tana kururuwa. A firgice ta farka daga mummunar mafarkin da ta ke, yayin da zufa suka fara ƙeto mata ta ko wane sashi na jikinta yayin da damuwa da tashin hankali suka bi suka tunkushe guri guda a zuciyarta na halin da ta ke ciki na rashin mai taimakon ta. Nan da nan zuciyarta ya shiga bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Dafe cikinta ta yi wanda ya kumburo sosai alamun cewa tana da juna biyu. Sosai taji gaba ɗaya jikinta sunyi mata nauyi yayin da ta kasa motsa koda ɗan yatsarta saboda tsananin azaba da raɗaɗi na ciwon dake tattare da ita. Jin alamun motsin mutum daga bayanta ya sa ta sauriin waigawa. Nan ta haɗa idanu da gandirebas ɗin da ke tsaye ƙe ƙam a kanta. Ta ke zuciyarta ta ƙara faɗuwa a karo na biyu!. Don ta tabbatar cewa sun zo ne domin tafiya da ita kotu. Kallon su ta yi hawaye na bin ƙuncinta ta ce. "Dan Allah kuyi min wata alfarma, ina son kafin ku kaini kotu a yanke min hukunci ɗaya daga cikin ku ya hara min waya na kira ƴan uwana dan Allah". Kallon juna gandirebas ɗin suka yi yayinda ɗaya daga cikin su ya kalle ta ya ce. "Kotu bata bamu damar yin hakan bah. dan haka kada ki ce zaki yi wani yinƙuri a nan wajan idan ba haka bah zamu samu bindiga mu harbe miki kai dan haka obey the law". Jiki a sanyaye ta miƙe. Jikinta sanye da tufafin ƴan magarƙama. Yayin da ta miƙa hannunta gaba ɗaya a cikin su ya sanya mata handcuf a hannun sannan suka fice daga cikin wajan. Bangare guda kuma sauran matan cikin Magarƙamar suka bita da kallo. Cikin police van wato motar ƴan sanda ta shiga yayin da suka nufi kotu da ita. Tun da suka fara tafiya ta ke ta istigifari tare da salati har suka isa kotun. Parking police suka yi. Duk idanuwan jama'a a kansu yayin da suke jiran fitowar Mrs Laila Abdullahi. Fitowa ta yi daga cikin motar. Ba zato taji saukar dutse a kanta. Dafe kanta ta yi cikin raɗaɗi hawaye na zarya bisa fuskarta. Nan da nan mutane suka fara jifar ta da duwatsu tare da fara Allah wadai da halinta. Ganin hakan ya sa jami'ai suka shiga kare ta. Har haka shigar da ita cikin kotun. Ƴan jarida da jama'a ne gaba ɗaya suka ƙaraɗe gaban kotun high court yayin da koh ina ƴan sanda da sojoji kake gani hannunsu riƙe da bindigogi don rike mutane a kan madafun iko. *"Muna buƙatar adalci!muna buƙatar adalci!. Kalmomin da jama'ar wajan ke ta nanata wa kenen. Daff da wani dattijo wasu ƴan jarida suka nufa, tare da seta mike saitin bakinsa sannan suka ce. "Bawan Allah mene ne sunanka?". Amsa dattijon ya basu da cewa. "Sunana Namadi". Tambayar sa ƴan jaridan suka yi a karo na biyu da cewa. "Bisa wane laifi ne ku ke tuhumar wannan matar dashi, kuma me yasa kuke jifanta?". Amsa dattijon ya fara bata kamar haka. "Muna tuhumar ta da ƙwamushe yaran mu tana safarar su. Dukkanmu muna buƙatar wannan kotu ta yi mana adalci hakan zalunta da yaudarar mu da ta yi. Ta ɓata rayukan ƴaƴan mu mata, ta kashe mana yaran mu yayin da ta ke saka wasu yaranmu suna mata safaran miyagun ƙwayoyi. Muna tunanin ce mun samu walihiya mai share kuka da baƙin cikin mu. ashe muguwa ce shigo-shigo bah zurfi ta yi mana.Ta yi mana alƙawarin cewar zata horar da ƴaƴanmu kuma za ta ba su aiki a kamfaninta ashe ta riƙe ƴaƴan mu ne domin ta kai su wasu kasashen don samar mata da kuɗaɗe ta hanyar karuwanci.Dan haka muna son a bi mana hakkin mu a kan abin da haka aikata mana". Ya faɗa yana mai fashe wa da kuka. Sannan ya ƙara da cewa. "Ta cuce mu ta zalunce mu, mu ɗora mata yardar mu ta hanyar bata amanar ƴaƴan mu. Indai har kotu bata yanke mata hukunci bah toh tabbas sai mum kashe ta". Mai da kallon ta ɗaya daga cikin ƴan jaridar ta yi kan camera sannan ta ce. "Jama'a fatan kunji abin da wannan dattijon ya faɗa kan cewar suna zargin Mrs Laila Abdullahi da aikata laifin safaran yara da safaran miyagun ƙwayoyi. Neman gaskiya da amfanin jama'a, Bayyana zalunci, yi rahoto da gaskiya da daidaito. Kare yancin jama'a da mutuncin dan Adam duk a wannan kotu mai alfarma muke samunsa. Dan haka mu jira hukunci". *Shigar su cikin kotu keda wuya Alkali shigo shi ma ciki Ma'aikacin ma'aikacin kotu yana sanar da lokacin da alkali ya bada umarnin da kowa ya zauna. Umarni Alkali ya bada da Mrs Abdullahi Muhammad ta fito gaban kotu. Fitowa ta yi har inda masu laifi ke tsayuwa. Yayin da police suka tsaya daga bayanta. Buɗe littafi Alkali ya yi tare yin rubuce rubucen shi a ciki tare da bawa mgatakadda damar ya tashi. Miƙe wa magatakadda ya yi tsaye sannan ya ce. "Assalamu alaikum Barka da safiya fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya". Ɗaukar takarda da alƙali ya miƙa mai ya yi sannan ya ce. "A wannan rana ta Litinin ɗaya ga watan february, a wannan kotun tamu mai dumbin albarka zamu ci gaba da sauraran ƙaran da wasu suka kawo bisa zargin aikata wannan laifi. Kuma a wannan rana za'a yi zama na ƙarshe na sauraron shari'ar Mrs Laila Abdullahi wanda hake tuhuma da safarar yara da salwantar dasu". "Shin koh lawyer Mrs Lailah Abdullahi yana nan? da kuma lauya da ke kare wanda suke tuhumar Mrs Lailah Abdullahi yana nan? Idan gaba ɗaya kuna kusa muna bukatar ku Miƙe tsaye. Miƙe wa lawyer dake kare Mrs Lailah Abdullahi ya yi tare da bashi amsa da cewa, "Eh ina nan". Yayin da ɗaya tsagin shima ya miƙe tsaye. Magana magatakadda ya fara yi kamar haka. "Bayan hujjoji da haka gabatar a gaban kotu cikin zama da ya gabata na ɗaya na biyu dana uku kotu zata bayyana matsayinta hakan wannan shari'ar". Yana kaiwa nan ya zauna. Kallon lauyoyin dake kare kowane ɓari yayi sannan ya ce. "Shin akwai wata hujja da zaku gabatar koh A'a?". Amsa wa suka yi da "babu". Ɗaukar littafin dake kan tebur ɗinsa alƙali ya yi sannan ya ce. "Bisa la'akari da hujjoji da suka bayyana a gaban kotu waɗan da hujjojin duk suna nuna cewa abin da hake tuhuman Mrs Lailah Abdullahi, laifin ta ruga ta aikata kuma ba bu wata da lauyarta ya bayar ƙwaƙwara da zata gamsar da kotu cewa bah ita ta aikata wannan laifin bah. Don haka wannan kotun mai alfarma ta zata yanke mata hukunci kamar haka". "Bisa dogaro da duba da haka yi da halin yana yin da ki ke ciki na juna biyu. Wannan kotun ta bada umarnin cewa ba za'a rataye ta ba har sai ta haifa abin ke cikinta, sannan wannan kotu mai alfarma ta bada umarnin cewa Mrs Lailah Abdullahi ta samu kulawa daga likitoci da kuma cikin magarƙama tare da bata abinci masu kyau har lokacin da za ta haifi abin da ke cikin ta, sannan nan da shekaru biyar masu zuwa za'a rataye ta. Wannan shi ne". Kwamitin alkali ne suka tashi tare da cewa. "COURT". Miƙe wa jama'a suka yi. Yayin da babu wanda yaji daɗin hukuncin da Alkali ya yanke sunso nan ta ke zai bada order da a rataye ta sai kuma suka ji hakasarin hakan sakamakon cikin dake cikinta. Fita jama'a suka yi daga cikin kotun, yayin da jami'ai suka fito da Mrs Lailah Abdullahi tare da nufar inda motar police ke a fa ke. Bah zato ta ji saukar mari kan fuskarta. Saurin dafa ƙuncinta Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta kalli matar hawaye ni bin kan ƙuncin ta. "Allah ya tsine miki albarka, muna fuka maciya amanar ƙasa, dole ki gurbi abin da kika shuka". Cewar wata dattijuwa. Ganin suna tunkaran inda Mrs Lailah Abdullahi ta ke ya sa jami'ai suka fara kare ta yayin da suka shigar da ita cikin mota. Nan ta ke suka ji saukar talkalma kan jikinsu yayin da suka fara bubbuga jikin motar da Mrs Lailah Abdullahi ke ciki. Ruff da ciki Mrs Lailah ta yi tare da fara rusa kuka. Kukan da ta ke yi ba saboda cin mutuncin da jama'a suka yi mata bah. Tana kuka ne bisa ga nadama da kuma takaicin abin da ya sa ta yarda da mutum. Haƙika yardar da ta baiwa mutane shi ne ya yi silar tarwatse war rayuwarta, shi ne mafarin kuma ƙarshe na rugujewar rayuwarta, tabbas ta aikata babbar dana sani a rayuwarta. Tun da suka fara tafiya ba abin da ta ke sai kuka har suka isa harabar magarƙamar da ita. Parking daya daga cikin police ɗin ya yi kafin daga bisani gaba daya suka fito daga cikin motar yayin da warders mata suka nufo motar tare da buɗe wa suka fito da Mrs Lailah Abdullahi waje tare da shigar da ita cikin magarƙamar mata wato ɓangaren mata sannan suka shigar da ita cikin kurkuku tare da ƙulle ƙofar wajan. Guri Mrs Lailah Abdullahi ta samu ta zauna yayin da ta shiga yin tunanin koh a wane hali ƴan uwa ta suke ciki a yanzu. Motsi tajiyo daga bayanta. Saurin waigawa ta yi tareda zuba idanuwanta hakan matar da ba za ta wuce shekaru arba'in zuwa sama bah a duniya. Murmushi matar dake gefenta ta yi sannan ta ce. "Kada ki ji tsoro sunana Hajiya Binta nima kamar ke haka lokacin da haka kawo ni magarƙama na dinga kuka bah tare da aika ta wani laifi bah sa'anan ina ji ina gani na kasa aiwatar da komai saboda fito da gaskiya lamari. Kuma abin takaicin ma kina da juna biyu. Karki damu zan kula da ke tamkar ƴar uwa har ki sauka lafiya kinji?". Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta ce. "Nagode sosai ƴar uwa". Ta faɗa tare da zaro wani babban littafi a cikin jakarda haka kama ta dashi. Sannan ta miƙa ma hajiya Binta littafin ta ce. "A gaba ɗaya magarƙamar nan ke kaɗai ce wacce na gani naji hankalina ya kwanta da ita, dan haka Ina son ki hadana min wannan littafin saboda yardar da miki domin na san duk abin da ya yi ƙarshe akwai mafarin faruwar sa, ina son ki hadana min shi". Miƙa hannun Hajiya Binta ta yi tare da karɓar littafin wanda ya ke da matukar girman gaske. Juya littafin Hajiya Binta ta yi a hannunta sannan ta ce. "Wannan littafin fah mene ne a ciki?". Murmushi Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta bata amsa da cewa. "Tarihi na da mafarin lamarin duk abin da ya shafi rayuwata da kuma abubuwa da dama wanda baki ba zai gama faɗar su bah duk sune a ciki. Ina son ki hadana min shi koh bayan raina idan ina da rabon haihuwa a duniya ki bawa ɗan da na haifa wannan littafin domin ya san wane ne shi, idan ma mace ce ki bata domin sanin wace ce mahafiyarta da kuma ita kanta". "Kai maza ku taso kuyi aiki". Cewar wata warder a cikin magarƙamar. Miƙe wa suka yi yayin da Hajiya Binta ta ɓoye littafin a ƙarƙashin pillow ɗinta. Tana saka wa suka fice daga cikin ɗakin da suke. *BAYAN WATANNI UKU* kwance ta ke yayin da ta ke jin bayan ta nayi mata ciwo ga wata iriyar azababbiyar ciwon mara da ta bi ta addabe ta. Yayin da cikin wanda ya yi tartsotso a gaba yake ta faman motsi. Nan ta ke ta saki wata iriyar razananniyar ƙara!. A firgice matan dake cikin magarƙamar suka nufi inda ta ke yayin da suka shiga bata taimakon gaggawa. ta ke suka haɗa rufi da tsumma tare da zagaye wajan. Nan da nan mutane suka cunkushe guri ɗaya. Cikin tsananin azaba na naƙuda take nishi tare da furzar da iska mai zafi yayin da numfashinta ya ke ƙoƙarin sarƙewa. Ganin hakan ya sa Hajiya binta ta fara danna mata cikin tana ihuu yayin da saura matan suka shiga yi mata addu'ar sauka lafiya. Ganin tana ƙoƙarin rufe idanuwanta ya sa hajiya binta ta yayyafa mata ruwa tare da tattaɓa fuskarta. Gani ta yi gaba ɗaya ƙarfin ta ya ƙare yayin da ɗan dake cikin ya kasa fitowa. Ba zato suka ji kukan jaririya ta fito. Nan ta ke farin ciki ya lulluɓe fuskokin su yayin da suka shiga yi wa Allah godiya. Ɗaukar jaririyar Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Masha Allah, ubangiji ya albarkaci rayuwarki". Ta faɗa tare da miƙa wa ɗaya daga cikin matan magarkama suka sanya jaririyar a cikin tsumma tare da rufe ta. Sannan hajiya Binta ta ɗauki placentar yarinyar wanda haka yanke ta haƙa rami a can bayan magarƙamar ta bunne. Mai da kallon ta kan Mrs Lailah Hajiya Binta ta yi. Nan ta ke Lailah ta kuma fashe wa da wani irin azababbiyar ƙara mai matuƙar razanarwa. Cikin kiɗima da firgici kowanennsu ya mai da kallon sa kanta. Yayin da suka ga Lailah ta ci-gaba da naƙuɗa. Zaro idanuwa waje Hajiya Binta ta yi cikin farin ciki ta ce. "Kenen ba guda ɗaya bace bah akwai wata a ciki. Allah mun gode maka da ka albarkaci wannan baiwar taka da ƴaƴa waɗan da sune za su zamo gata da kuma abun alfaharin ta. Ganin ɗan dake cikin ta kasa yin nishin da zai fito ya sa ta shiga cikin tunani. Wani dabara ne ya faɗo mata. Miƙe wa ta yi yayin da sauran mata da warders suka bita da kallo. Wani babban bokiti ta ɗauka mai matuƙar faɗi da girma yayin da ta cika she bokitin tsaff da ruwa. Tare da ƙoƙarin jan bokitin ta nufi inda Laila ta ke. Ganin ta kasa ya sa warders suka taimaka mata ta ɗauki ruwan yayin da suka kai har gaban lailah. Ajiye wa suka yi yayin da suka cinciɓe ta tare da saka ta cikin ruwan. Nan ta ci gaba da naƙuɗa yayin da jariri ya ƙi fitowa. Sai da ta ɗau hawanni biyu tana abi ɗaya bah tare da anji labari mai daɗi bah. Zama hajiya Binta ta yi tare da girgiza kanta ta ce. "Ba za ta iya haihuwa da kanta bah saboda bata samu kulawar da ta ke buƙata bah, wannan aikin ba mune zamu yi bah dole likitoci ne zasu yi kuma wannan bah maganar kawo likitoci magarƙama bane tana buƙatar a kaita asibiti yanzu nan kafin lokaci ya ƙure. Ɗaya daga cikin warders ɗin ne ta kalli Hajiya Binta ta ce. "Asibiti kuma? Ta ya ya zamu fita da ita cikin magarƙama bayan ita ɗin babbar mai laifi ce kuma kotu bata bamu damar aiwatar da hakan bah.kafin hakan ta faru dole sai da sa hannun kotu tukun nan". Cikin ɓacin rai Hajiya Binta ta kalleta ta ce. "Wato ta mutu a gaban idanuwan mu kenen koh? kotun banza kotun wofi na bi kotu da gudu ba wando. Idan ta rasa rayuwarta ba tare da haifar abin da ke cikin ta bah shin kun san da cewa babban laifi ne? Saboda kuna ji kuna gani tana buƙatar agaji ku ka ƙi agaza mata sannan kuma wallahi idan ta mutu sai kin fuskanci mummunar uƙuba tare da hukunci dan haka kuje a haɗa jami'ai a tafi da ita asibiti. Maza-maza yanzun nan". Cikin ƙanƙanin lokaci warders suka tara jami'ai yayin da haka ɗauki Mrs Lailah Abdullahi haka shigar da ita cikin mota. Riƙe hannun Hajiya Binta Lailah ta yi sannan ta ce. "Ga amanar ƴata na baki ki kularmin da ita tamkar ƴar cikin ki sannan kada ki taɓa faɗa mata cewar ke ɗin bah mahafiyarta bace, har sai ta kai munzalin sanin hakan. ina son ki nemi ta gano inda mahaifinta ta ke. Tana kaiwa nan ta saki hannunta alamun ta suma. Jikin Hajiya Binta ne ya yi sanyi yayin da ta kalli jaririyar dake hannunta cikin tausayawa. Tada mota jami'ai suka yi yayin da suka fita da ita daga cikin magarƙamar tare da nufa da ita babban asibiti. Tun da suka shiga cikin asibitin mutane ke binsu da kallo yayin da suke ganin kamar Mrs Lailah ce a cikin motar. Nan da nan labari ya zagaye gari cewar Mrs Lailah Abdullahi tana cikin international hospital zata haihu yayin da ƴan jarida suka cika wajan domin ɗaukar rahoto da bayanai. Bangare guda kuma Jami'ai sun zagaye asibitin hannunsu riƙe da bindigogi. Fitowa Nurse's suka yi da gadon ɗaukar mara lafiya sannan suka ɗora ta a kai tare da shigar da ita labour room tare da shirya ƙwararrun likitoci domin karɓar haihuwa. Nan likitoci suka shiga cikin labour room ɗin da haka ajiye ta sannan suka fara gudanar da aikinsu. Yayin da suka canza mata kayan dake jikinta suka saka mata na marasa lafiya. Sannan suka saka mata ƙarin ruwa. Su kuma suka saka hand glove da facemark tare da wular kai. Ganin sai naƙuda ta ke ta kasa haihuwa ya sa suka yi scanning ɗin cikin ta. Nan suka gano cewar ba guda ɗaya bane ke cikin ta yara biyu ne. Ganin hakan ya sa ɗaya daga cikin doctor's ɗin faɗin ba za ta iya haihuwa da kanta bah dole ne a yi mata operation idan har muna son ceton ranta da kuma ƴaƴan dake cikin cikinta. a halin yanzu jininta ya zuba sosai dole muna buƙatar wanda zai yi donating ɗin jini domin a ƙara mata don kada ta rasa rayuwarta. Dan haka dole mu muyi mata operation to save her life. Cewar wannan likitan. Jin hakan ya sa suka kwaso kayan aiki yayin da haka canza mata position tare da direction na haihuwan. Sannan suka yi mata allurar kashe zafi da raɗaɗi. Sannan daga bisani suka yi mata allurar bacci. Ganin bacci ya ɗebe ta ya sa suka fara gudanar da aikinsu. cikin ƙware wa suka tsaga cikin ta tare da fiddo yaran ciki. 🌎🪐🌎🌎🪐🌎🪐🪐 *mafarin kenen. Koh ya zata kasance gaba? Ta ya ya kowanen suka kasance a ɓangare daban-daban? Shin kuma da gaske Mrs Lailah Abdullahi safaran yara ta ke tare da miyagun laifuka? Domin jin amsoshin tambayoyin ku, ku kasance tare da ni domin jin yadda zata kaya*💃💃💃 *Yawan comments yawan post ina son na ga ruwan comments*🥳👌 🥳 *kuma wannan littafin zai dinga zuwar muku ne da zarar ina ganin comments 💃🥳da likes* DON'T FORGET TO COMMENT AND SHARE PLEASE 🙏 🙏 🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣➡️4️⃣ *___________________________________________* kukan jariran ne ya kauraye gaba ki ɗaya cikin room ɗin. Hamdala likitocin suka yi ganin sun yi nasaran ceton yaran da kuma mahaifiyar su. Nan ta ke daya daga cikin likitocin ya ɗauki ɗaya daga cikin jariran, yayin da bayan hannunsa ya kasance a kan bangon mahaifa wato ji ga gefen mahaifa. Sa'an nan kuma tare da yatsun hannunsa sannan ya miƙa hannunsa baya da gaba don raba mahaifa ya fara yi a hankali daga bangon mahaifa kadan-kadan, bai dakata bah har sai da ya ga mahaifar ta cire. Ajiye jaririyar ya yi sannan ya ɗauki ɗayar jaririyar ya cire mata mahaifa kamar yacce ya yi wa ta farko. Ɗaukar towel suka yi sannan suka saka su a ciki yayin da suka ajiye su a kusa da Mrs Lailah. Kallon jariran likitocin suka shiga yi ganin yadda Ubangiji ya yi musu baiwa ta halitta, juyawa suka yi tare da ficewa daga cikin room ɗin suka bar iya Mrs Lailah Abdullahi da jariran. A hankali ta fara buɗe idanuwanta tana lumshe su yayin da ta ji dukkan gaɓoɓin jikinta nayi mata ciwo. Miƙe wa ta yi zaune tare da maida kallonta kan jariran. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta yi tare da rintse idanuwanta jin yadda maranta ke yi mata mugun ciwo. Ɗaukar jariran ta yi tareda ƙura musu ido. Zaro idanuwa waje ta yi ganin kowacce da kalar idanuwanta ɗaya blue eyes, sannan kuma ɗaya green eyes. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bata bah. Rungume su ta yi a kirjinta ganin yadda suke ta faman kuka. Waige-waige ta fara yi ganin ba bu kowa a ɗakin ya sa ta ajiye jariran sannan ta miƙe tsaye a hankali. Tafiya ta fara yi a daddafe harta isa gaban ƙofar ɗakin. Leƙawa waje ta yi ta jikin ƙofar. Nan ta ga jami'ai a tsatsaye tare da warders gaba ɗaya sun zagaye wajan. Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara zarya bisa ƙuncin ta. Koma wa ta yi ta zauna tare da ci-gaba da rusa kuka cikin shesheƙar kuka ta ce. "Mene ne na aikata dana cancanci irin wannan sakayyar? shin wane zunubi ne na aikata? me ya sa haka zata kasance dani?". "Mutanen da na taimaka da hannuna na ciyar da su sannan na basu abubuwa na more rayuwa. Ina tunanin koda na shiga wata matsala nsn gaba zasu tsaya mun saboda abubuwam alkhairy dana dinga aikata musu. Sai kuma gashi yau da kansu suka juya min baya saboda abin duniya suka butulce yayin da idanuwansu ya rufe suka kasa gane gaskiya. Wannan wace iriyar zamani ce wanda ba bu yarda kwata-kwata s cikinta saima cin amana da yaudara". "Ban yi tunanin zasu iya cin amana ta har haka bah, amma ba komai Allah shi ne abun dogaro sannan shi ne mai warware kowace matsala, ina da yaƙinin cewa nan gaba sai gaskiya ta yi halinta". Ta faɗa tare da maida kallonta jikinta ta ga faba ɗaya ta ɓata gadon saboda ba ƙaramin bleeding take yi bah. *"Yauwa Nurse Nadiya ina son ki ɗauki ruwan zafi ki kai room 8 akwai patient ɗin mu a ciki sannan kuma kiyi wa yaran wanka. Ga tea nan mai zafi a flask wanda haka kawo mata ki kai mata tasha, sannan kuma ki bata maganin relief tasha". Cewar Doctor ɗin. "Shi kenen sir in sha Allahu zan yi kamar yadda ka faɗa". Ta faɗa tare da kwashe kayan ta zuba su a troley sannan ta ɗauki towel mai kyau tare da tissue da allura sai maternity pad da kuma bedsheet. Tana gama haɗa wa waje ɗaya ta nufi room ɗin da su. Sai da taje har gaban room ɗin zata shiga. Nan ta ke ɗaya daga cikin jami'an mata ta dakatar da ita yayin da ta yi amfani da portable scanner ta fara scanning ɗin jikin nurse ɗin gudun kada ta kasance tana tare da abun cutarwa. Ganin dai ba bu komai ya sa ta bata hanya nurse Nadiya ta shiga cikin room ɗin. Ajiye troley ɗin ta yi a gefe sannan ta shiga toilet tare da haɗa ruwan zafi a cikin babban baff. Fitowa ta yi tare da nufa wajan mrs Laila wanda ke zaune kan patient bed. kallon Mrs Lailah nurse Nadiya ta yi ta ce. "Na gama haɗa ruwan ki zo ki ɗan gasa jikin ki sannan ki saka maternity pad don naga kina bleeding so sai, sannan kuma zan baki magani wanda bleeding ɗin zai tsagaita amma sai kin fara cin abinci tukun". Ta faɗa tare da cire zanin gadon dake kai wanda ya yi chaɓa-chaɓa da jini sannan ta ɗauki zanin gadon dake kan troley ta shimfiɗa a kai. Maida kallonta ta yi kan jariran sannan ta chanza musu position na kwanciya. Shiru Mrs Lailah ta yi ma nurse ɗin tare da sakin murmushi wanda ya fi kuka ciwo. Maida kallonta nurse Nadiya ta yi kan Mrs Lailah sannan ta ce. "Madam kiyi haƙuri ki daure ki tashi kiyi wanka. Hana hakan ne duk saboda lafiyar ki sannan kuma gashi kina ta yin bleeding ya ƙi tsaya wa. Ya kamata ki tashi na taimaka miki ki shiga toilet ki gasa jikin ki. Ga jariran ki suna ta kuka da alama yunwa suke ji kuma kin ƙi ki shayar da su ga ruwan nono ya nata zuba a jikin ki. Nurse Nadiya ta faɗa tana mai zuba ma Mrs Laila idanuwanta. Shiru Mrs Lailah ta yi mata a karo na biyu. Ajiyan zuciya ta sauke cikin dashashiyar murya ta ce. "Shin za ki iya yi min wani taimako?". Cikin rashim fahimta nurse Nadiya ta ce. "Taimako kuma? wace iriyar taimako zan yi muku?". Amsa Mrs Lailah ta bata da cewa, "Ina son ki taimaka min na fita daga cikin wannan asibitin". Zaro idanuwa waje nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Na taimaka miki ki futa kuma, ke ɗin fah babban mai laifi ce, ta ya ya zan taimaka miki ki gudu bayan kuma kina gama samun lafiya za'a mayar dake cikin prison. Gaskiya ba zan taɓa iya taimakawa makashiya bah". Saurin share ƙwallan dake shirin zubo mata Mrs Laila ta yi tare da miƙe wa tsaye daka kan gadon sannan ta durƙusa kan gwiwowinta tare da haɗe hannayenta guri ɗaya tana mai fuskantar nurse ɗin ta ce. "Na roƙe ki da girman fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) ki taimake na fita daga wajan nan na samu na tseratar da rayukan yarana sannan na ceci tawa rayuwar. Bana son na mutu ba tare da gaskiya ta yi halinta bah, ina so koda nan gaba yarana na su kasance sune waɗan da za su bayyana gaskiya sannan jama'a suyi alfahari da su, su kasance ababen faɗa na alkhairy a wajan jama'a. Ki tamaika min dan Allah". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka. Tausayin ta ne ya kama nurse Nadiya. Saurin ɗaga Mrs Laila ta yi tsaye sannan ta ce, "Na dahimce ki kuma na tausaya miki matuƙa amma matsalar ba daga nan take bah, matsalar ita ce yanzu koda na barki ta ina za ki fita bayan ko ina a asibitin nan karaɗe yake da jami'ai tare da CCTV camera. Ya kamata kiyi ƙara nazari a kai saboda kin san yin hakan babban hatsari ne dole sai mutum ya shirya don koh a ƙofar gate ma akwai jami'ai Da ƴan jarida jira kawai suke ki fito su fara karɓar bayanai. Kuma sannan jariran ta ya ya za ki fita da su?". Kallon nurse Nadiya Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Guda ɗaya zan ɗauka na bar ɗaya". What!" Nurse Nadiya ta furta. Cike da da mamaki ta ce, "saboda me za ki ɗauki ɗaya ki bar ɗaya bayan kuma duka yaran ki ne? baya sannan ma naji an ce kin haifi guda ɗaya a cikin magarƙama ga kuma biyu a nan. Idan ki ka tafi da guda ɗaya sauran biyun ya zaki yi da su? saboda me za ki aikata hakan?". Haka nurse Nadiya ta shiga jera mata tambayoyi. Murmushi Mrs Laila ta yi tare da nufar inda jariran suke tana mai shafa fuskarsu ta ce. "Ina so ne gaba ki ɗayansu su taso a gurare daban-daban a cikin wannan duniyar. Bawai zan raba su bane saboda wani kuduri nawa. Zan yi hakan ne kawai saboda tseratar da rayukan su sannan kuma su san mahimmanci da rayuwa take dashi. Ina da dukiya wanda yawanta ba zai misaltu bah kuma wannan dukiyan tun kafin na haife su na mallaka musu. Kuma hakan wannan property ɗin makiya na za su iya kashe koh nawa ne domin yarana su saka hannu hakan wannan property ɗin daga baya kuma su kashe su domin shi ne burinsu. Ni kuma ba zan bar hakan ta faru bah. Shi ya sa zan raba su, su rayu a gurare daban-daban yayin da kowaccen su za su kasance da uwa daban-daban. Daga baya idan sun girma su binciki tarihin su, tohh dole ne a dawo da shari'a sannan a bayyana gaskiya ta hanyar bayar da gamsassun bayanai". Nannauyan ajiyan zuciya nurse Nadiya ta sauke sa'anan ta ce. "Shi kenen baki da wata matsala. Na miki alƙawari idan ki ka ɗauki ɗaya zan riƙe ɗaya koh kuma ba bawa duk wanda ya zo yana neman haihuwa zan bashi, idan kuma bansamu bah zan damƙa ta gidan marayu. Kuma sannan na miki alƙawarin ba zan taɓa cin amanar ki koh na yaudare ki bah. Amma kuma ina da wata tambaya, shin ta ya ya yaran gaba ki ɗaya za su haɗu bayan kuma duk a gurare daban-daban suke? kuma sannan ta ya ya za su san koh su ɗin su wane ne bayan kuma ba bu wani hujja da za'a fahimtar da su cewar iyayen da suke tare da su ba iyayensu ba asalin iyayensu ba ne? kuma wane ne zai basu property ɗin su?". Murmushi Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Wannan ba abun damuwa bane gaba ɗaya bayanai da hujjoji suna tare da hajiya Binta a magarƙama. Ban faɗa mata komai ba saboda gudun cin amana, amma na san ba zata ci amana ta ba kamar yadda na saka ran cewa kema ba za ki ci amana ta bah. Kuma sannan haɗuwa da sanin asalin su za su fahimta domin Hajiya Binta zata sanar dasu ko mai". Kallon ta nurse Nadiya ta yi ta ce. "Wace ce kuma hajiya Binta?". Amsa Mrs Laila ta bata da cewa, "hajiya Binta ita ce na zauna da ita a magarƙama kuma komai yana wajan ta hatta ta ukun su tana wajan ta". "Shi kenen toh na fahimta yanzu dai abin da zamu yi domin fita daga cikin wajan nan shi ne dole na baki kayan nursing scrubs wato kayan mu na Nurse's ƙi saka saboda kada a gane ki sannan na baki face mark. Ita kuma jaririyar da za ki ɗauka ki saka ta a cikin troley na ƙasa amma dole sai na bata maganin bacci gudun kada ta yi kuka a gane. Bauan kin fita ni sai nayi ihuu na ce kin fasa min habu sannan kin gudu". "Eh hakan ya yi shi kenen sai mu fara koh". Cewar mrs Laila. Nan da nan suka shirya kamar yadda suka tsara yayin da Mrs Laila ta saka kayan Nurse's ɗin wanda suka kwanta suka ƙarɓi jikinta sannan kuma ta bawa nurse ɗin kayan patient ta saka a toilet. Sai da suka gama shiryawa tsaff. Sannan mrs Laila ta saka facemark tare da nufar inda jariran suke wanda gaba ɗaya sun lulaya duniyar bacci saboda wanka da gasa musu cibi da nurse ta yi tare da maganin bacci. Kallon su ta yi hawaye na bi bisa ƙuncinta ta ce. "Kuyi haƙuri ku yafe min, banso haka ta kasance ba, banida niyar raba ku amma dole ce ta sani zan raba ku. Kaddarar mu ce a haka kuma wannan jarabawar da zaku shiga, in sha Allahu sai kun tsallake ta". Ta faɗa tare da ɗaukar ɗaya daga cikin jariran mai green eyes sannan ta yi rolling ɗinta a cikin towel daga bisani ta saka ta a ƙasan troley ɗin wanda samansa ke rufe da kaya magunguna a kai. Maida kallonta ta yi kan nurse Nadiya sannan ta nufe ta tare da rungume ta ta ce. "Insha Allahu ba zan taɓa manta irin wannan habun alkhairin da ki ka aikata a gare ni bah na gode sosai Nurse". Tausayinta da kuma yaran ne ya ƙara shiga zuciyar Nurse Nadiya ta ce. "Kada ki damu da wannan ɗan ƙaramin taimakon, idan da ina da halin yin fiye da haka ma zan yi. Kuma karki ƙara ce min Nurse suna na Nadiya ki ɗauke ni tamkar ƴar uwa kamar yadda ki ka ɗauki Hajiya Binta. Dan haka yanzu ki hanzarta ki fita kafin wani yazo ya ganki". Ta faɗa tare da cire ID card ɗin ta sannan ta sawa Mrs Laila a wuya. "Kinga yadda ki ka yi kyau kuwa a cikin uniform ɗin nan, yacce ki ka san real Nurse, ba but wanda zai gane ki kinyi ɓadda kama sosai. Murmushi wanda bata yi tsamani shi ba ne ya suɓuce wa Mrs Laila sannan ta ce. "Na gode sosai Nadiya, Allah ubangiji ya baki damar sauke nauyin da ki ka ɗauka". "Ameen". Nurse Nadiya ta furta. Mrs Laila na kaiwa nan ta riƙe troley ɗin sannan ta fara ja harta isa bakin ƙofa. Tsayawa ta yi tare da maida kallonta kan jaririyar dake kan gado sannan ta ce. "Nadiya duk wanda ya yi adopting ɗin ƴata kice mai ya kula min da ita sosai saboda ba dan banason ta na ajiye ta bah". Tana kaiwa nan ta murɗa hannun handle ɗin ƙofar tare da ƙoƙarin fita daga cikin ɗakin. "Dakata!". Ta ji nurse Nadiya ta furta. Tsaya wa ta yi chakk ba tare da ta motsa koda ɗan ƴatsarta ba. Ta kowa nurse Nadiya ta fara yi tana nufo inda Mrs Laila take. Nan ta ke gaban Mrs Laila ya shiga faɗuwa! Saida tazo kusada ita sannan ta miƙa hannunta tare da riƙe na Mrs Laila sannan ta saka mata kuɗaɗe. Nan ta ke Mrs Laila ta sauke nannauyan ajiyan zuciya. Murmushi Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Na baki tsoro ne? ga kuɗi nan ba bu yawa na san zaki buƙaci kuɗin hawan mota da kuma kuɗin da za ki ɗan ci wani habu idan kina jin yunwa kuma sannan number na yana jikin Id card ɗina idan kina da buƙatar wani taimako ki kirani kinji". Nan ta ke Mrs Laila ta ji ina ma a ce dukiyoyin ta na kusa da ta mallaka wa nurse Nadiya ɗaya daga ciki. Share hawayen da ke zarya kan ƙuncinta ta yi sannan ta ce. "Nagode sosai Nadiya haƙiƙa ke ɗin mace ce ta ƙwarai kuma in sha Allahu saina saka miki da alkhairy". Girgiza kai nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Ni banyi miki hakan ba domin ki saka min nayi ne domin Allah dan haka ki hanzarta ki tafi kada su shigo su tarar damu". "Shi kenen". Mrs Laila ta furta Daga bisani ta fice daga cikin ɗakin. Kallon ta jami'an suka yi yayin da suka ga kamar yanayin nurse da ta shiga da kuma wacce ta fito ya bambanta domin tafiyar da take yi tamkar mara lafiya. Fargaba da tsoro ne ya cunkushe guri ɗaya a zuciyar Mrs Laila. Tafiya ta ci-gaba da yi a karkace da troley yayin da hannayenta da ƙafafuwanta ke kakkarwa saboda tsoro, gashi maranta bai daina yi mata ciwo bah duda cewar ta sha maganin relief. Saida taje har gaban gate zata fita taga an dakatar da ita. Tsayawa ta yi tana mai kallon masu gadi. Daga gefe kuma police ne da sojoji sai ƴan jarida zagaye a wajan. Ɗaya daga cikin police ɗin ne ya kalle ta ya ce. "Nurse ina kuma za ki je da troley bayan kuma ba'a fita da shi?". Wani irin zufa ne ya fara ƙeto daga kowane sashe na jikin ta. Cikin ƙasa da murya ta ce, "Eh dama zan zubar da magunguna ne a shara zan dawo da troley ɗin". Kare mata kallo police ɗin ya yi sannan ya ce. "Shara kuma? bayan dustbin ɗin asibiti ina kuma za ki je da wannan. Kuma yana ga kina magana kamar wata mara gaskiya, hanya ke nurse ce kuwa?". Rass! Gaban Mrs Laila ya faɗi. Cike da tsoro ta kalle shi ta ce, "ni nurse ce kuma Doctor ne ya umarce ni dana zubar da waɗan nan dattin a waje. Saboda wari yana affecting ɗin patient ɗin mu na asibiti kuma yana iya tada musu da rashin lafiyar su". Jinjina kai police ɗin ya yi sannan ya saka a ɗauko masa portable scanner domin ayi scanning ɗin troley dake hannunta. Ganin hakan ya sa gaban Mrs Laila ya tsananta faɗuwa. Karɓar scanner police ɗin ya yi wajan ɗaya daga cikin jami'an sannan ya fara scanning troley ɗin. Rintse idanuwanta Mrs Laila ta yi yayin da take karanto duk wani addu'oin da ya zo cikin zuciyarta. Saida ya zo daff da inda jaririyar take sannan ya ɗauke scanner ɗin tare da bata damar fita. Hamdala Mrs Laila ta yi sannan ta fara jan troley ɗin harta je daff da bakin ƙofa. Daga sama ta ji muryar police ɗin ya ce. "Dakata". Chak Mrs Laila ta tsaya Tare Dmda jiran furucin da zai ƙara fitowa daga bakinsa. Zuwa police ɗin ya yi daff da ita sannan ya ce. "Ina son kafin ki fita ki cire facemark ɗin fuskarki na ganki". Ta ke zuciyar Mrs Laila ya buga da mugun ƙarfi. Cikin zuciyarta kuwa ta ce. "Na shiga uku yanzu na san shi kenan asirina zai tonu. Ya zama dole na ƙara yi masa wata ƙaryar domin fita daga wajan nan". Juyawa ta yi tana mai fuskantar sa sannan ta ce. "Kayi haƙuri ni ɗin matar aure ce miji na ne ya bani umarnin yin hakan, kuma ya ce kada na kuskure na buɗe fuskana saboda baya son haga matarsa. Kuma kaga dole na bi umarnin sa saboda igiya uku ce a kaina ba zan so na rasa su ba kuma aljannata tana ƙarƙashin kafar mijina dole nayi masa biyayya. Ko kaima ba zaka so matar ka ta bijire maka bah". Ta faɗa tana mai kauda kai gefe. "Shi kenen na fahimce ki. Tabbas ke ɗin mata ce ta gari har ki iya jure zafin rufe fuskarki saboda kiyi wa mijinki biyayya toh tabbas ba bu makawa ke ɗin ta gari ce, ba bu komai za ki iya tafiya". Godiya Mrs Laila ta yi masa daga bisani ta fice daga cikin asibitin. Bayan ficewar Mrs Laila daga cikin room 8 nurse Nadiya ta ɗauki ɗayar jaririyar sannan ta ɓoye ta a ƙarƙashin gado. Maida kallonta kan CCTV camera dake cikin ɗakin ta yi sannan ta ɗauki ƙarfe tare da fasa cameran. Yayin da ta samu kanta ta dinga bugawa a jikin gini har saida taga yafara jini. Nan ta ke ta faɗi ƙasa sannan ta ƙwalla wani irin razananniyar ƙara!. Nan ta ke ƴan sanda da warders suka fara nufo hanyar ɗakin yayin da likitoci suka nufo wajan. Buɗe ƙofar suka yi yayin da suka tarar da nurse Nadiya a kwance rai a hannun Allah. Ɗaya daga cikin jami'an ne ya isa gare ta tare da tambayar ta me ya faru?. Cikin ciwo ta ce. "Ta gudu mai laifin ta gudu ita ce ta ji min rauni saboda kada na tona mata asiri". Shitttttt! Ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa yayin da ya ɗauki field telephone na ƴan sanda tare da sanar da sauran jami'ai. Nan ta ke labari ya karaɗe cikin asibitin cewar Mrs Laila ta gudu. Ta ke ƴan sanda da warders suka shiga zagaye cikin asibitin suna neman Mrs Laila. Police ɗin da ya bar Mrs Laila ta fita ne ya yi nazari yayin da yaga cewar tabbas shi ɗin babban maloho ne har bai iya gane cewar ita ta fita bah. Nan ta ke suka fita tare da fito da police dog's da makamai na tsaro. Nan ta ke ƴan jarida suka fara ɗaukar rahoto na labarai cewar Mrs Laila ta gudu daga asibiti. Fita jami'an suka yi daga cikin asibiti sannan suka saki karnuƙa suka fara bin ƙarnin jinin dake jikin Mrs Laila. TOH FANS KOYA ZATA KASANCE DA MRS LAILA DA KUMA JAMI'AI? SHIN ZA SUYI NASARAN KAMA TA KO KUWA TA TAFI KENEN? SHIN NURSE NADIYA MAI AMANA CE KOH KUWA MAI BUTULCI CE? SHIN YARANTA ZA SU TASO SU GURARE DABAN DABAN SU SAN JUNA DAGA BAYA? WAI WACE CE MA MRS LAILA? DOMIN JIN AMSOSHIN TAMBAYOYINKU KU CI-GABA DA BIBIYA DON JIN YACCE ZATA KAYA. *KADA KU MANTA INA SON NAGA RUWAN COMMENTS. YAWAN COMMENTS YAWAN POST😍😘💕💕😍. COMMENTS ƊIN KU SHI NE ZAI NUNA KUNA MARABA DA WANNAN LITTAFIN SANNAN KUNA JIN DAƊIN SA*. COMMENTS & SHARE PLEASE 🙏 🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B (Zinariyar Jajirtattu) [7/24, 11:15] Ayeesher M.B🥰🥰: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g Ku shiga channel ɗina domin samun sauran littatafai na👆👆👆👆👆 *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣▶️6️⃣ *__________________________________________* "Sir Mrs Lailah Abdullahi fah ta gudu daga asibiti amma yanzu mun bazama nemanta". "What! Kamar ya ta gudu? ina ku ke da harta samu damar fita daga cikin wannan asibitin? wannan wane irin shashanci ne?". Cewar DPO "Kayi haƙuri sir ɓadda kama ta yi hakan ya sa bamu gane ta ba. Amma yanzu zamu je mu binciki ccctv camera domin ganin komai". Cewar police officer ɗin "Shi kenen ba bu damuwa. Amma yanzu me zamu ce wa mutanen gari da kotu kenen? wai waya ce muku ma ku fito da ita daga magarƙama?. Yanzu dai shi kenen best solution shi ne kuje gidan radio da gidajen jarida ku buga news paper da photon ta ku saka wanted duk wanda ya ganta yana da kyauta mai tsoka. Kuma baya sannan ku sanar da masu motoci da adaidaita cewar yau ba bu aiki kada wanda ya fito hatta masu motar tasha karsu fito domin banason ta fita daga cikin garin nan kajini Koh?". "Shi kenen sir yadda kace haka za'a yi". Yana kaiwa nan ya kashe wayar yayin da suka nufi cikin inda ccctv cameran yake. Miƙarda Nurse Nadiya ɗaya daga cikin police ɗin ta yi. Yayin da Doctor ya saka mata bandage tare da bata magani rage zafi tasha. "Wai mene ne ya faru?". Ɗaya daga cikin warders ɗin ta tambayi Nurse Nadiya. Share hawayen ta Nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Na shigo zan bata magani sai ta ce min na taimaka mata na fitar da ita ni kuma naƙi amince mata harna yi iƙirarin cewar zan tona mata asiri, kawai sai ji nayi ta buga min ƙarfe a kaina sannan ta cire min kayan Nurse's ta saka. Bayan ta buga min ban sake sanin inda kaina yake bah sai yanzu". Ajiyan zuciya police ɗin suka sauke sannan suka ce. "Amma shin ina yaran da ta haifa suke?". Nan ta ke zufa ya fara ƙeto ma nurse Nadiya ta kowane sashi na jikinta. Cikin daƙewa ta ce. "Iya jaririya ɗaya na gani a wajan ta kuma ta fita da ita". "Shi kenen Kada ki damu zaki bamu number ki da address ɗin ki domin mu ci-gaba da investigation hakan wannan lamarin because this is an criminal offense ba zai yu a rufe bah. Kuma sannan zamu bincika gaba ki ɗaya ccctv camera dake cikin asibitin nan". Yana kaiwa nan ya yi musu alamun da su fita. Fice wa suka yi gaba ki ɗaya yayin da suka bar iya nurse Nadiya da doctor a ciki. Gaban nurse Nadiya ne ya tsananta faɗuwa jin cewar za'a je a duba ccctv camera. Ta ke kukan jaririyar dake ƙasan gado ya karade ɗakin. Rass! gabanta ya faɗi. ____ Yauwa Doctor ina ccctv csmersn cikin room 8 naga kowane ɗaki ccctv camera yana yi amma banda na room 8. Muna so ne mu ɗau recording duk abin da ya faru a ɗakin". Cewar ɗaya daga cikin ƴan sandan. "Kuyi haƙuri na manta ban faɗa muku bah ccctv cameran ɗakin nan ya daɗe da de nayi kuma mun kira mai fixing ɗinshi ya ce zai zo ya gyara". Cewar likitan. Miƙe wa ɗan sandan ya yi a fusa ce sannan ya ce. "Wannan wane irin shashanci ne? ya za'a ce ccctv camera na room 8 bayayi bayan kuma duk sauran suna yi? kin san mahimmanci cctv camera kuwa?". Cctv hana sanyawa a cikin ɗakunan majiyyata, da sassan kulawa masu mahimmanci. Wannan na iya taimakawa wajen lura da yanayin marasa lafiya da faɗakar da ma'aikatan kiwon lafiya idan akwai gaggawa. Cctv kuma na iya taimakawa wajen lura da hulɗar marasa lafiya tare da masu ba da lafiya don saka idanu hakan ingancin kulawa da bin ka'idoji. Amma shi ne zaku je wannan room 8 ɗin ba bu, a shi ma ya kamata a bar cctv domin babban makashiya ce a ciki dole a dinga ganin take-taken ta. Yanzu da a ce cctv na ɗakin nan nayi da binciken sai ya fi mana sauƙi. Rubbish kawai". Police ɗin ya faɗa tare da ficewa daga wajan. Ganin hakan ya sa sauran jami'an suka mara masa baya. Haka jami'an suka bazu cokin gari wajan neman mrs Laila Abdullahi. Yayin da bangare guda kuma Jami'ai waɗan da ke tare da police dog's wajan bin ƙarnin jinin Mrs Laila sun gaza samo ta. Ba yacce suka iya haka suka koma police station. Ɓangare guda kuma ƴan sandan sun buga photon Mrs Laila a jarida wanda haka saka wanted a jiki. Sannan suka fara kafawa a titinuwa. Yayin da gefe guda kuma suka je gidan radio tare da sanar da jama'ar garin. Nan da nan garin ya karaɗe da maganar Mrs Laila Abdullahi babbar yar ta adda mai safaran miyagun ƙwayoyi wanda gaba ki ɗaya garin ya amsa da hakan. **Ɓangaren Mrs Lailah Abdullahi kuwa tun da ta fara tafiya gabanta ke tsananta faɗuwa. Gefe guda kuma jaririyar dake hannunta sai kuka take. Hawayenta mrs Laila ta share yayin da ta fara waige-waige koh Allah zai sa ta ga mai napep ya kaita tasha. Cikin sa'a kuwa ta hango tawowar mai napep. Ganin hakan ya sa ta yi saurin gyara zaman face mark ɗin da ke kwance kan fuskarta. saida ta rufe fuskarta gaba ɗaya ba'a ganin komai banda idanuwanta. Tare shi ta soma yi. Ganinta ya sa mai napep ɗin ya tsagaita da tafiya. Tsayawa mai napep ɗin ya yi daff da ita sannan ya ce mata. "Madam ina zaki je?". Amsa ta bashi da cewa, "Ina son ka kaini sabon tasha zan hau mitar kano". Girgiza kai mai napep ɗin ya yi sannan ya ce. "Amma naji jami'ai suna cewa wai wata criminal ta gudu daga asibiti kuma ance kada masu motocin tafiya su yi aiki yau saboda yau za'a rufe kowace hanya ta shige da fice domin kama wannan criminal ɗin. Na faɗi hakan ne badan ina zargin ki ba na faɗi hakan ne kawai saboda kada ki je ki ɓata kuɗin motar ki kiga yau basu yi aiki bah. Kuma ba iya su kaɗai ba harda masu napep nima na fito ne kawai saboda zan siyi abin da zanci". Ɗan jimm Mrs Laila ta yi yayin da ta gyara kwanciyar jaririyar dake hannunta. Maida kallonta ta yi kan mai napep ɗin sannan ta ce. "Naji dukkanin abin da ka ce amma ina son nayi wannsn tafiyar ne ba dan komai ba saboda wani abu wanda ke da mahimmanci a rayuwata, dan Allah ka kaini koh nawa ne zan biya ka mundin zaka kaini sabon tasha kuma nayi maka alƙawari ba bi wanda zai tuhume ka da cewar me ya sa ka fito aiki. Kayi wa Allah da annabi ka kaini kaji?". Ajiyan zuciya mai napep ɗin ya sauke tare da maida kallonsa kanta ya ce. "Ni wallahi har kin fara ban tsoro ma karna je ma ko ke ce wanda ƴan sanda suke nema ni nazo na shiga uku. Amma ba bu matsala zan kaiki kamar yadda ki ka buƙata saboda duba da nayi cewa kina tare da jaririya kuma keda ita kuna matuƙar buƙatar kulawa. Ba bu damuwa kiyi sauri ki shigo cikin motan kada wani ya ganmu zan bi one way ne inda na san ƴan sanda da ƴan road safety da karota basua wajan". "Shi kenen na gode sosai". Mrs Laila ta faɗa hawaye na ƙoƙari zubo wa kan ƙuncinta sannan daga bisani ta shiga cikin motan. Tada napep ɗin mai sahu ya yi sannan ya fara tafiya. Kamar yadda mai sahun ya faɗa one way ya bi inda ba bu jami'ai ko ɗaya a wajan. Tun da suka fara tafiya ƙarnin jinin jikin Mrs Laila ya karaɗe cikin adaidaitar. Tunani mai sahun ya fara na kodai ya shigo da wani abu ne wanda ke ƙarnin shi bai sani bah. Kawar da kai ya yi sannan ya ci-gaba da tafiya. Mintuna ashirin ne ya yi musu suka isa tashar. Parking mai napep ɗin ya yi tare da fara dube-dube. "Dama na faɗa miki ba bu wanda zai yi aiki yau domin ƴan sanda sun yi annoucing kada wanda ya fito aiki yau duba ki gani". Waigawa Mrs Laila ta yi yayin da taga ba bu koda ƙuda a wajan gaba ɗaya sun rufe motocin da kayan mota wajan gaba ki ɗaya ya ɗauki shiru. Kuka mai ƙarfi ne ya kufce mata sosai Mrs Laila ke kuka tamkar za'a zari ranta. "Wannan wace iriyar ƙaddarar rayuwa ce? shin mena aikata haka? ni da nake ƙoƙari wajan faranta wa mutane marasa shi harda waɗan da suka da hali sai kuma yau ni ce na ƙare ina yawon kan titi domin tseratar da kaina. Ya hayyu ya ƙayyun Allah ka kawo min agaji". Shiru mai napep ɗin ya yi yayin da ya zuba ido ya kallonta. Bai san dalilin ta nayin kuka ba kuma bai san wace ce ba saidai yaji tausayinta ya shiga cikin ranshi. Tantama ya soma yi cikin zuciyarshi. "Ko dai ita ce Mrs Laila Abdullahi wanda ya gudu daga asibiti?". Tambayar da ya yi wa kansa kenen. Maida kallonsa ya yi kanta sannan ya ce. "Shin na tambaye ki wani abu?". Girgiza kai Mrs Laila ta yi alamun eh. Juyowa ya yi gaba ɗaya yana mai fuskantar ta sannan ya ce. "Shin kece Mrs Laila Abdullahi wanda ta gudu daga asibiti har ƴan sanda suka ce duk wanda ya yi ƙoƙarin gano ta yana da kyauta mai tsoka?". Saurin kauda kanta Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "A'a bani bace ba ni ban ma san wace ce Mrs Laila bah". Ta faɗa bakin ta na rawa yayin da ta kasa nutsuwa. Murmushi mai napep ɗin ya yi sannan ya ce. "Alamu ya nuna cewa kina jin tsoro a san wani abu game da ke dan gashi ma muryar ki rawa yake. Kada kiji tsoro ni ɗin mutum ne mai tausayi kuma mai fahimta. A wannan duniyar yana da wuya ka yarda da mutum bai ci amanar ka bah, shi yasa ma ba zan ga laifin ki ba koda baki gaya min ba saboda mutanen yanzu ba abin yarda ba ne. Dan haka ki yarda dani 100% ba zan ci amanar ki ba. Ki faɗa min wace ce ke?". Shiru Mrs Laila ta yi masa daga bisani kuma ta cire face mark ɗin kan fuskarta. Zaro idanuwa waje mai napep ɗin ya yi sannan ya ce. "Tabbas ke ce Mrs Laila wannan fuskar ta yi kama sakk da wanda na gani a jikin jarida". Murmsh Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Ƙwarai kuwa nice Mrs Laila Abdullahi kuma ni ban aikata wani laifi ba haka kaini magarƙama hakasari ma ni ɗin mai taimakon wanda haka zalunta ce sai kuma yau ya kasance ni hake zalunta yayin da na kasa aiwatar da komai domin wanke kaina. Tabbas mutane sun raunata rayuwata gaba ɗaya sun yi amfani da rauni na wajan cin galaba a kaina sai dai kuma wannan ba ƙarshe bane wannan mafari ne domin kuwa ba zaka taɓa koma wa ga ubangijinka ba tare da ka gurbi abin da ka shuka tun a nan duniya bah. Ƴan uwa na iyaye na, ƙawaye na da kuma mijina ba bu wanda ya taɓa zuwa magarƙama duba lafiya ta bah. Dai-dai da rana ɗaya kacal ba bu wanda ya zo koh ya tambaye ni mai na aikata bah kowa dai abin da yake gani ni ɗin makashiya ce mai safaran yara yin karuwanci tare da safarar miyagun ƙwayoyi. Kuma wai duk ni ce ke aikata waɗan nan munanan ayyukan. Wallahi ba zan taɓa yafe ma abin da suka aikata a gare ni bah". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka. Shiru mai napep ɗin ya mata yayin da yaji tausayinta ya kama shi sosai. Cikin jimami da tunanin rashin kyautata wa da haka yi mata ya ce. "Shin idan na faɗa miki wani abu zaki yarda?". Share hawayenta ta yi sannan ta ce. "Eh zan yarda". "Ni ɗin jami'in ɗan sanda ne wanda haka bawa aiki nayi ɓadda kama kamar yadda ki ka yi na kama ki". Mai napep ɗin ya faɗa tare da nuna mata police warrant ID card. Zaro idanuwa waje Mrs Laila ta yi ta ce. "Shi kenen yanzu komai ya ƙare. *ASIBITI* "Wannan ba kukan jariri nake ji ba a ƙarƙashin gado?". Cewar Doctor. Miƙe wa tsaye nurse Nadiya ta yi tare da ɗauko jaririyar dake kwance a ƙasa ta ce. "Ƙwarai kuwa kukan jaririya ce kuma jaririyar ma yarinyar Mrs Laila ce". "What! Doctor ya furta sannan ya ce. Kin san abin da ki ke faɗa kuwa? dama akwai jaririya a ɗakin nan kuma ki ka ce da su jami'ai ba bu". Shiru nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Nayi ma mahaifiyarta alƙawarin cewa ba zan taɓa bari wani abu ya samu ƴarta ba kuma nayi mata alƙawarin zan damƙa ta a hannun mutanen ƙwarai koh kuma ni na riƙe ta, shi ya sa ban fito na faɗa cewar akwai yarinya a nan ba dan Allah ka rufa min asiri banason wani abu ya samu wannan yarinya saboda mundin maƙiyan Mrs Laila suka gano tana da ƴa a nan sai sun san yadda suka yi suka ɗauke ta domin cimma wani kudirin nasu". Ɗan jimm Doctor ɗin ya yi sannan ya ce. "Shi kenen ba bu damuwa zan rufa miki asiri kuma sannan zan taimaka miki. Yanzu dai ki kai yarinyar gida kada ki bawa kowa ke ki riƙe ta s matsayin ƴarki idan mijinki ya aminta da hakan idan kuma bai amince ba sai a kaita gidan marayu Koh kuma duk wanda suka zo suna son adopting ɗin ƴa sai a basu". Godiya sosai Nurse Nadiya ta yi mishi sannan daga bisani ta fice daga cikin ɗakin. Ɓangaren magarƙama kuwa bayan binciken da ƴan sanda suka yi sun gano inda asalin mahaifan Mrs Laila ke zaune hakan ya sa suka yanke shawarar cewa su kai musu yarinyar dake hannun Hajiya Binta tun da ita ma jaririyar ƴar gidan ce. Ba bu yacce Hajiya Binta bata yi dasu ba wajan ganin basu tafi da jaririyar ba amma koh sauraranta basu yi ba. Ba yacce ta iya haka ta haƙura ta barsu suka ɗauki jaririyar. Kamar yadda suka shawarta a tsakaninsu haka suka ɗibi jami'ai da lauyoyi tare da warders suka nufi gidan ahalin Mrs Laila Abdullahi da jaririyar. Mintuna talatin ya yi musu a cikin estate ɗin Wanda ke kusads Abubakar rimi houses estate. Wani katafaren gida na hango wanda koh ina zagaye yake da jami'ai kallo ɗaya zaka yi kasan gidan babban mutane ne masu jini a jiƙa. Tsayawa faɗa muku yadda gidan nan ya tsaru ɓata lokaci ne domin sai mu gaba page ɗin ba'a gama ba saboda irin kyau na gidan tabbas kuɗaɗe ba ƙaramin kuka suka yi ba wajan gina wannan gidan. Horn jami'an suka yi. Nan ta ke masu gadi na gidan suka fara buɗe gidan. Shiga cikin gidan suka fara yi ɗaya bayan ɗaya har na daina ganin motocin nasu. Kai tsaye wajan parking space suka nufa tare da yin parking daga bisani kuma suka fara fitowa daga cikin motan. Ganin hakan ya sa ahali gaba ɗaya fitowa daga cikin gida. Wani dattijo na hango a zaune kan wheel chair da alamu shi ne mai gidan sai kuma wata mata kusa da shi alamu sun nuna cewar ita ce matar gidan gefe guda kuma mature guy's ne tsatsaye a gefensu su biyu ɗayan barin kuma mata ne kyawawa guda biyu. Magana dattijon ya fara yi kamar haka. "Me kuke nema kuma bayan Kun kama mai laifin da ku ke buƙata mai ya rage?". Ɗaya daga cikin police ɗin ne ya nuna warrant ID card ɗin da sannan ya fara magana da cewa. "Mun zo gidan nan ne ba dan komai ba sai dan mu baku jaririyar da ƴarku ta haifa a magarƙama sannan kuma zamu yi bincike a cikin gidan ku da nata don sanin koh nan ta zo bayan ta gudu daga asibiti". "What! Kamar ya ban fahimta ba? shin an gaya muku cewar bayan ta gudu nan ta tawo? koda nan ta tawo ba zamu taɓa karɓar ta ba domin ta zubar mana da mutunci da kimar mu. Mun daɗe muna rwyuwa cikin farin ciki ba tare da wani tseko ba amma Laila haka taja mutuncin mu ya zube a kan titi. Wannan wheel chair ɗin da nake zaune a kai yanzu ita ce sanadiyar hakan. Kuma yanzu ku kawo min ƴarta ku ce na karɓa ai ba'a wannan gidan ba don ba zan taɓa karɓar wannan yarinyar bah. Ni kimar gidana ta fiye mun komai a rayuwa. Ba zan karɓi wannan jaririyar ba domin yanzu mahaifiyarta bata da halaƙa da wannan ahalin dan haka ku fice min daga gida". Ɗaya daga cikin lauyoyin ne ya yi magana cikin girmama wa. "We due respect sir, yarinyar nan jikar ka ce kuma ba ta yadda za'a yi ka ƙi karɓar gudan jininka koda kuwa laifin da Laila ta aikata ya kai girman ruwan ƙorama. Idan kace ba zaka karɓe ta ba yarinyar zata sha wahala ne sannan zata tashi bata da kowa, bai kamata laifin uwa ya shafi ƴa bah. Dan Allah kayi nazari kayi haƙuri ka karɓe ta koba komai dai jikarka ce". Dafa shi matar dake kusa da shi ta yi sannan ta ce. "Mai gida ya kamata mu yafe ma Laila. Ina da tabbacin cewar abin da haka ce Laila na aikatawa ƙarya ne bai kamata laifin ta kuma ya shafi yarinyar ta ba dan Allah kaji". Shiru dattijon ya yi sannan ya ce. Shi mijin Laila Yana ina? me ya sa baku kai masa yarinyar ba sai ni zaku kawo wa. Kafin na irga uku idan har baku fita daga gidan nan ba sai na lahira ya fiku jin daɗi, zan sa jami'ai na su zo su yi waje daku saidai muyi shari'a a kotu wallahi. Maza ku fice". Jin hakan ya sa manyan yaransa maza suma suka fara nasu zuben suna koran jami'an. Ganin hakan ya sa jami'an suka shiga cikin motocin su tare da barin gidan. LOW BATTERY🪫 🪫 NASO NAYI MUKU WANDA YAFI HAKA YAWA AMMA BA BU CHARJI KUYI MANAGE. TOH FAH MRS LAILA DS YARANTA SUNA GANIN RAYUWA KOYA MRS LAILA ZATA YI DA RAYUWARTA? GASHI MSI NAPEP YA BAYYANA MATA CEWAR SHI ƊIN JAMI'I NE. GA KUMA MAHAIFINTA YAƘI KARƁAR ƳARTA SO SAD 😢 😭 😢💔. ALLAH YA KUƁUTAR DAKE MRS LAILA ALLAH YA BAKI NASARAN CINYE WANNAN LARABAWAN🙏🙏 COMMENT & SHARE FISABILULLAH🙏🙏🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) [7/28, 14:43] Ayeesher M.B🥰🥰: Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g Ku shiga channel ɗina domin samun sauran littatafai na👆👆👆👆👆 *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 7️⃣▶️8️⃣ *__________________________________________* "Kenen dama kai ɗin ɗan sanda ne ba mai napep ba?, me ya sa saida na gama faɗa maka dukkanin sirri na tukun zaka fito ka gaya min cewar kai ɗin ɗan sanda ne?". Ajiyan zuciya ɗan sandan ya sauke sannan ya ce. "Ki kwantar da hankalin ki Mrs Laila ni ɗin bana ɗaya daga cikin ƴan sandan da haka ce su ɓadda kama wajan kama ki. Ƙwarai da gaske ni ɗin jami'i ne amma banzo nan dan na kama ki ba, hasali ma nazo ne don na taimaka miki". "Ƙarya ka ke yi, duk bakin ku ɗaya. Wato so ka ke na ƙara yarda da kai a karo na biyu domin cutar da rayuwata ko?, to ni bana buƙatar taimakon naka, idan kamani zaka yi ka kamani ka daina kwane-kwane". Mrs Laila ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka saboda baƙin ciki. "Mijin ki ne ya ce nazo na taimaka miki ba wani ba, ni ɗin ɗaya daga cikin jami'an mijin ki ne, shi ya aiko ni gare ki. Dan haka ki kwantar da hankalin ki, ni zan taimaka miki". Cewar ɗan sandan. Cikin rashin fahimta Mrs Laila ta ce. "Mijina?, mijina shi ne wanda ya aiko ka?, me ya sa zai yi hakan bayan lokacin da nake buƙatar taimakon sa bai taimake ni ba, ba bu ɗaya daga cikin ahalina ko mijina da yazo ya tsaya min a kotu, haka na zama tamkar marainiya. Dai-dai da rana ɗaya mijina bai zo ya duba ni a magarƙama ba. Sai yanzu kuma da nake shirin samun ƴanci zai wani turo min da kai. To bana buƙata, lokacin da nake buƙatar tsimakonsa bai taimake ni ba sai yanzu da nake shirin samun ƴancin kaina na gudo daga asibiti domin gaskiya ta wanzu a gaban idanuwa na. Ni ba zan bi ka ba". Mrs Laila ta faɗa tare da fito wa daga cikin napep ɗin. Gyara kwanciyar jaririyar dake hannunta ta yi hawaye na sauka kan ƙuncinta ta ce. "A gaban idanuwan mijina ƴan sanda suka zo suka kama ni ba tare da ya dakatar da su ba. Ba bu abin da yafi bani mamaki kamar yadda naga mijina ya haɗa hannu da maƙiya na, koda zan iya yafe wa kowa a duniyar nan to banda mijina". Mrs Laila ta faɗa tana mai barin wajan. Saurin fitowa ɗan sandan ya yi yana mai binta a baya. Ɓangaren Nurse Nadiya kuwa, kamar yadda Doctor ya faɗa mata, haka ta ɗauki jaririyar dake hannunta ta nufi gidan ta da ita. Cikin sa'a kuwa ta tadda mijinta na gida. Sai da ta yi addu'ar shiga gida kafin daga bisani ta shige cikin gidan. Kwance ta ganshi kan wani makeken kujera 3seater, yayin da remote ke riƙe a hannun shi da alama kallo yake yi a tv. Sallama nurse Nadiya ta yi. Juyowa ya yi ya kalle ta sannan ya ci gaba da kallon shirin da hake haskowa a tv. Nannauyan ajiyan zuciya nurse Nadiya ta sauke, sanin yadda halinshi yake ya sa bata ko tanka masa ba ta ƙara riƙe jaririyar dake hannunta ƙamm tare da nufar ƙofar ɗakin ta. Daga sama taji muryar shi na faɗin. "Daga ina ki ke?". Juyowa ta yi, ciki rashin fahimta ta ce. "Ban gane daga ina nake ba?, ina zanje in banda gurin aikina?". Ta faɗa tana mai haɗe rai. Murmushi ya sakar mata sannan ya dubi jaririyar dake hannunta ya ce. "Wannan jaririyar fa daga ina ki ka ɗauko ta?". Jin hakan ya sa nurse Nadiya ta saki ranta tare da sakin murmushi, ta fara nufar inda yake a zaune. Saida ta ƙarasa har inda yake tare da zama kusa da shi ta ce. "Ba ka san wace ce ba ko?, kayi haƙuri na karɓi yarinya ba tare da na nemi izinin yin hakan daga gare ka ba. Maganar gaskiya dama wannan yarinyar ita ɗin ƴar babbar mai laifin da ƴan sanda suke nema ce, wato Mrs Laila Abdullahi, kuma nayi mata alƙawarin cewar zan kula mata da ƴarta har izuwa girmanta, sannan kuma nice na taimaka mata wajan guduwa daga asibiti. Ina fatan dai ba zaka ƙi yarinyar nan ba mai gida". Ta faɗa kanta a sunkuye. Zaro idanuwa waje mijin nata ya yi tare da miƙe wa tsaye, cikin fusata ya ce da ita. "Shin kin yi hauka ne?, ta ya ya zaki kawo min ƴar babbar mai laifi gidana sannan kuma kiyi tunanin zan barta a ciki?, wato so ki ke kija wo min bala'i nima ƴan sanda su fara nema na ko?. Lallai wuyanki ya isa yanka. Toh bara kiji, ki ɗan yadda zaki yi ki fitar da yarinyar nan daga gidan nan, mundin baki fitar da ita daga gidan nan ba kin kaita wani gurin daban toh wallahi a bakin auren ki, don ba zan zauna ina zaman zamana ki jawo min masifa har gida ba". Ya faɗa ranshi a matuƙar ɓace. Baki sake nurse Nadiya ta bishi da kallo yayin da hawaye suka fara zarya kan fuskarta. Maida kallonta ta yi kan jaririyar. Nan take taji tausayin jaririyar ya kamata.a yayin da ba bu abin da jaririyar keyi in banda kuka domin ba ƙaramin yunwa take ji na, gashi kuma bata da ruwan nonon da zata bata. Cikin tausayawa ta ce. "Allah sarki yara, daga zuwan ku duniya har kun fara fuskantar ƙalubale, wannan wace iriyar rayuwa ce, a ce ba bu wanda ya dube ku da idon rahama ya taimaka muku. Ya Allah na roƙe ka, ka sa wannan wahalar ta tsaya a iya yarintar su kaɗai kada ya kasance har izuwa lokacin girmansu". Maida kallonta ta yi kan mijinta sannan ta ce. "Kada ka ce haka mai gida, nayi wa Mrs Laila alƙawarin cewa zan yi iya bakin ƙoƙarina wajan ganin na taimaka wa yarinyar ta sannan na riƙe ta a matsayin ƴar da na haifa. Ita ɗin da yarinya ce kaɗai, bai kamata a ce laifim uwa ya shafi ƴa ba, yanzi idan ka ce na fitar da ita ina ka ke son na kaita?, rayuwarta zai kasance tana shan wahala ne, a yayin da kuma ba bu wanda zai share mata kuka ko ya sata farin ciki domin bata da uwa a kusa da ita. Ba ita kaɗai bace ba su uku ne matan kuma kaga tun basu san kan su ba haka raba su domin tseratar da rayukansu dana mahaifiyar su, sannan kuma domin su san mahimmanci da rayuwa take dashi. Dan Allah kada ka ce A'a kaji na roƙe ka". Ta ƙaradhe maganar tare da fashe wa da kuka. **"Yanzu mene ne abin yi kenan?, mun bi diddigin mijin nata sannan munje gidan ance ya daɗe da barin ƙasar baki ɗaya, yanzu kenen dole dai a kai yarinyar nan gidan marayu". Cewar DPO wanda ke zaune kan bencin dake cikin magarƙamar a yayin da sauran ƴan prison ɗin suka zagaye jami'an suna kallon jaririya mai brown eyes ɗin da ke kwance kan cinyar ƴar sanda mace, a sa inda ba bu abinda jaririyar keyi sai kuka. "Haka ne sir, nima abin da nayi tunani kenen, ina ga kawai best solution shi ne a kaita gidan marayu, dan ba lallai a samu wanda zai iya riƙe ta ba a nan dole dai chan za'a kaita domin sai ya fi mata alkhairy". Cewar ɗaya daga cikin warders ɗin. "Shi kenen tom ku shiyar jami'ai, domin zamu kaita gidan marayun". Daga sama suka ji an ce. "Ni ce nan nafi cancanta dana riƙe ta". Waigawa gaba ɗaya suka yi rareda zuba wa Hajiya Binta idanuwa. Cikin rashin fahimta DPO ya ce. "Kamar ya ke ki ka fi cancanta da ki karɓi yarinyar nan?, kenen a tunanin ki mu baki ita ki lalata yarinyar mutane, so ki ke a barta cikin magarƙama ta zama irin ku?, ta ina ma ki ke da halaƙa da ita da har zaki buɗi wannan ƙazamin bakin naki kice ke zaki riƙe ta?". Ta kowa Hajiya Binta ta fara yi, bata tsagaita da tafiyar ba har sai da ta tabbatar da isa gaban shi sannan ta jefa idanun ta cikin nasa ta ce. "A matsayina ta mai riƙo, kuma sannan nayi wa mahaifiyar ta alƙawarin cewa zan kula mata da ita sannan na bata ingantacciyar rayuwa. Kada kuyi tunanin ko saboda ni mai laifi ce ku gna bi yarinyar, samm abin da ku ke tunani ba haka bane ba. Na riga dana ɗaukar mata alƙawarin cewar ba zan taɓa barin hannun yarinyar ba har izuwa numfashina na ƙarshe sannan ba zan bari ta san mene ne hake nufi da kalmar hawaye ba, domin ba zan taɓa bari ruwa ya fita daga idanuwanta ba saidai idan bana raye, ba zan bari tasha wahala kamar yadda tasha a rayuwarta na yanzu ba. Kunji dan Allah ku bani ita ". Ta faɗa kanta a ɗuƙe. Kallon juna jami'ai Da DPO suka shiga yi. Gyaran murya DPO ya yi sannan ya ce. "Zamu baki ita ne mundin kotu ta aminta da hakan, amma in har kotu taƙi amincewa to sai dai kiyi haƙuri dan ba bu abin da zamu iya yi a kai". Miƙe wa tsaye ya yi sannan ya mika wa hajiya Binta jaririyar. Hannu Hajiya Binta ta sa tare da karɓar yarinyar. Kallonta DPO ya yi sannan ya ce. "Ni zan ɗauki nauyin kula da yarinyar nan, kama daga abinci, tufafi, da dai sauran abubuwan da ba za'a rasa ba. Yanzu dai zan saka wasu daga cikin jami'ai suje su suyo baby food domin ga dukkanin alamu jaririyar nan yunwa take ji, kuma ya kamata a ce shayar da ita a kayi bawai a bata abinci ba, don haka yanzu ki riƙe ta, zanje na samu alƙali da sauran jami'ai indai har yarinyar ta dace ta zauna a nan to za'a barta, idan kuma suka ƙi amincewa ko wani nata yazo to zamu damƙa masa ita ne. Kin amince da hakan?". Girgiza kai Hajiya Binta ta yi ta ce. "Na amince". Ta faɗa tare da rungume jaririyar kan kirjinta. *"Mrs Laila ki dakata, jami'ai za su iya ganinki sannan su maida ki magarkama, kuma hukunci da za'a yi miki zai ninka na da ne domin guduwa ki ka yi". Tsayawa Mrs Laila ta yi tana mai fuskantar sa ta ce. "Dama bayan rataya akwai hukuncin da ya ninka shi?, rataye ni da za'a yi, to faɗa min wane hukunci ne ya ninka rataya?, ni na gwammace su kamani su yi min abin da yafi rataya dana bi ka. Da a ce kasan irin ƙuncin da mutane suka dasa mun a cikin rayuwata da ba zaka faɗi hakan ba. Dan haka ni ko kuma ƴata bamua da buƙatar taimakon ku". Ta faɗa tare da ci-gaba da tafiya. Ƙaran motocin ƴan sanda be ya karaɗe ilahirin wajan. Jin hakan ya sa ɗan sandan ya fara ƙwalla kiran Mrs Laila tare da cewa. "Ga sunan sun zo kama ki, ki tawo mu gudu kada suyi nasarar ɗauke ki, don idan suka kama ki za su raba ki da ƴarki kuma rabuwa ta har abada". Jin hakan ya sa Mrs Laila waigawa tana mai fuskantar ɗan sandan. Kafin ta yi wani yinƙuri. Ƴan sandan suka zagaye su da motocin su. "Sir gata nan mun ganta tare da wani, yanzu haka ƙoƙarin kama su muke". Cewar ɗaya daga cikin jami'an wanda waya ke riƙe a hannun shi. Murmushi ya saki ta cikin waya sannan ya ce. "Very good, aikin ku na kyau kuyi maza-maza kumata domin muna da bukatar fingerprint ɗin ta yanzu". Mutumin dake kan waya ya faɗa. Ganin suna ƙoƙarin kama su ya sanya ɗan sandan ya yi hanzarin jan hannun Mrs Laila tare da bangaje wasu daga cikin jami'an suka fara gudu. Ganin hakan ya sa jami'ai suka gyara zaman bindigogin su sannan suka fara shooting ɗin bullet. Da gudu suka tafiya ba bu gaggautawa yayin da jaririyar dake hannun Mrs Laila keta faman kuka. Cikin rashin sa'a ɗaya daga cikin bullet ɗin da jami'an suke harba wa ya samu wajan ƙafar ɗan sandan dake tare da mrs Laila. Nan take ya faɗi ƙasa yayin da jini ya fara fita daga ƙafar. Ƙara mai sauti ya saki!, da sauri Mrs Laila ta koma kan shi tare da ƙoƙarin ɗaga shi. maida kallonsa kan mrs Laila ya yi sannan ya ce mata. "Maza ki tafi ki tseratar da rayuwarki da kuma ta ƴarki, kada ki tsaya, maza kije". Cikin kuka Mrs Laila ta ce. "Ba zan iya tafiya na barka a cikin wannan mawuyacin halin ba, idan nayi hakan ban kyauta ba, karka damu kafin su iso zaka tashi". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka. "Ki tafi ki barni, ni ba zan iya tafiya ba daga nan. Dan haka ki tafi!". Ya faɗa cikin ɗaga tsawa. Miƙe wa tsaye Mrs Laila ta yi yayin da taga jami'an sun kusan ƙaradowa inda suke. Da sauri ta bar wajan sannan ta ci gaba da gudu. Ƙarasowa wajan jami'an suka yi yayin da wasu suka tsaya tare da kama ɗan sandan sannan wasu suka bi Mrs Laila a baya. Tun da ta fara gudu bata san inda take nufa ba, yayin da ƙafafuwanta suka ji rauni saboda bata sanye da takalma. Haka ta ci gaba da gudu ba tare da ta dakata ba. Yayin da zufa suka bi suka lulluɓe jikinta baki ɗaya. Cikin rashin sa'a kafarta ya bugu wani dutse. Nan take ta faɗi tare da fara gangarawa cikin daji mai cike da bishiyu da namun daji. Haka ta ci gaba da gangarawa a ƙasa harta faɗa a cikin wani kogi mai wanda ya cika da ruwa. Nutse wa ta yi cikin ruwan yayin da kukan jaririyar ya karaɗe gaba ki ɗaya ilahirin dajin. Wani itaciya ta hango daga chan nesa da sauri ta fara swimming harta isa ga wannan itaciyar sannan ta saka hannu tare da riƙe itaciyar ƙamm a hannunta sannan ta fara yinƙurin fitowa. A hankali ta fara jan itaciyar yayin da ta fara sama daga cikin ruwan. Cikin rashin sa'a itaciyar ta tsinƙe yayin da mrs Laila ta faɗa a ciki ruwan. Nan take ruwa ya shige mata baki da hanci, yayin da hakan ya jawo ta kasa numfashi sosai. Nan da nan namomin daji suka fara fitowa. Birririka ne gaba ɗaya suka zagaye kogin. Da sauri Mrs Laila taja da baya tana mai ambatar sunan Allah. Fuskanta suka yi da cewar tana da buƙatar taimako, hakan ya sa suka fara tsalle kan bishiyu suna ciccire itacuwan dake jikin bishiyoyin sannan suka fara haɗa igiya dashi tamkar mutane. Nan da nan suka ɗaure igiyar jikin wata ƙatotuwar bishiya sannan suka jefa wa Mrs Laila dake jikin ruwa igiyar a yayin da su kuma suka ja da baya. Riƙe igiyar Mrs Laila ta yi ƙamm a hannunta sannan ta fara jan igiyar tana yin sama. Saida taje sama daga ciki kogin sannan ta ajiye yarinyar tare da yi wa Allah godiya da ceton su da su birrirukan suka yi. Cikin farin ciki ta kalli yarinyar sannan ta ce. "Bayan wuya sai dad'i, Allah ya yi wa rayuwarki albarka. Daga yau sunanki zai kasance Amrah". Ta faɗa tare da rubuta sunan da jinin dake fita daga hannunta a jikin ƙaramin dutsen dake kusa da ita a kogin. Bayan ta gama rubutawa ta fara ƙoƙarin fitowa daga cikin kogin da igiyar dake hannunta. Nan take taji saukar bindiga a saitin zuciyarta, yayin da jininta ya fesu jikin jaririyar da dutsen. Nan take ta saki igiyar yayin da ruwa ya yi hawon gaba da gangan jikinta. Nan take birrirukan suka hau jami'ai tare da fara yayyaƙushi su da cizo. Ihuuuuu! Jami'an suka yi yayin da suka fara guduwa tare da barin ilahirin dajin baki ɗaya. Komawa kan jaririyar suka yi jin yadda take ta faman kuka ya sanya sauran namun jejin fitiwa baki ɗaya. *"Wallahi Nadiya ba zan bari ki ajiye jaririyar nan a cikin wannan gidan ba, shin kin yi hauka ne da har zaki kawo min wata baren yarinya cikin gidana?, Nadiya ki fita daga idona na rufe, kada ki bari na chanza daga yadda ki ka sanni a da. Idan har kina son zaman lafiya to ki san yadda zaki yi ki fitar da yarinyar nan daga cikin gidan nan". Hawaye nurse Nadiya taji suna ƙoƙarin sauko mata, saurin share su ta yi sannan ta ce. Shi kenen zan yi kamar yadda ka ce amma ka bari na bata abinci ko cerelak ne saboda na san tana jin yunwa sosai gashi ko shayar da ita ma ba'a yi ba". "Shi kenen". Mijin ya faɗa tare da shige wa ɗaki. Maida kallonta nurse Nadiya ta yi kan jaririyar ganin yadda take ta faman kuka ya sa ta miƙe tsaye tare da nufar cikin kitchen domin haɗa mata cerelak. Cikin ƙanƙanuwar lokaci ta gama haɗa wa yayin da ta fito da cerelak ɗin cikin ɗan ƙaramin fida da alamu ita ma tana da ƴa ko ɗa. Ajiye fidar ta yi kan table sannan ta ɗauki jaririyar daga kan kujera ita kuma ta zauna, yayin da ta ɗora jaririyar ksn cinyarta sannan ta fara bata cerelak ɗin tana sha. Saida ta gama tsaff sannan ta kuma yi wa yarinyar wanka a karo na biyu. Yayin da ta shigar da ita ɗaki tare da saka mata kayan jariran da mijinta ya siyo domin yaranta. Sakawa yarinyar su ta yi yayin da kayan suka yi wa yarinyar kyau tare da karɓar jikinta. Nan da nan bacci suka kwashi yarinyar. Ganin hakan ya sa ta ɗaukar towel tare da goya yarinyar a bayanta sannan ta shiga toilet tare da ɗauro alwala. Bayan ta gama ne ta fito daga toilet ɗin yayin da ta ɗauki dadduma tare da hijabi sannan daga bisani ta tada sallah. Bayan ta idar da sallan ya sa ta fara azkhar tare da lazumi yayin da ta fara kaiwa Allah kukan ta. Bayan ta gama ta miƙe tsaye tare da nufar hanyar palour. Zuwanta keda wuya ta tarar da mijinta riƙe da akwati yayin da yake s tsugunne yana ƙoƙarin buɗe akwatin. Da mamaki ta bishi da kallo sannan ta ce. "Mai gida me kuma zaka yi da akwati a wannan tsakar daren?". Murmushi ya sakar mata sannan ya ce. "Wannan akwatin ina zuge shi ne domin mu saka yarinyar a ciki sannan mu jefar da ita kan titi kinga duk wanda ya tsince ta ya yi sa'a sai ya riƙe ta". Saurin ja da baya nurse Nadiya ta yi sannan ta ce. "Wannan ai rashin adalci ne, ta ya ya muna ji muna gani zamu saka marainiyar Allah cikin wannan akwatin, zafi ma kaɗai ya ishe ta. Kuma mu rasa inda zamu ajiye ta sai bakin titi. Mundin ina nan to ba zan taɓa barin hakan ta faru ba". Miƙe wa mijin nata ya yi sannan ya fara tunkaran inda take. Bai yi wata-wata ba, ya zuba mata lafiyayyun maruka har guda biyu. Dafe ƙuncin ta nurse Nadiya ta yi yayin da jaririyar dake kwance s bayanta ta yi matuƙar razana da jin sautin. Nan take ta fara kuka. Ɗago idanuwanta Nurse Nadiya ta yi wanda suka ciko da hawaye. Nuna ta mijinta ya yi da ɗan yatsarta sannan ta ce. Mundin baki bi umarni na kinyi abin da nace ba, wallahi sai kin gane cewar Allah ɗaya ne. Domin ni ba zan lamunci naje magarƙama saboda wannan yarinyar da dangi uwa ba ba dangin uba ba. Don haka kiyi min shiru ki miƙo min yarinyar naje na jefa ta a chan bakin titi". Girgiza kai nurse Nadiya ta yi tare da fara ja da baya ta ce. "Ba zan taɓa miƙa maka wannan yarinyar ba sai dai ka kashe ni idan zaka iya amma ba zan bari ka jefar da yarinyar nan ba, domin ba alƙawarin dana ɗaukar wa mahaifiyar ta ba kenen". A fusa ce ya yi kanta tare da fuzge zanin da ta goya yarinyar dashi. Nan take jaririyar ta faɗi ƙasa yayin da kanta ya bugu da jikin table dake tsakiyar falon. Nan take yarinyar ta fashe da matsanancin kuka mai sauti. Ture nurse Nadiya mijin ya yi yayin da ta faɗi ƙasa. Maida kallonsa ya yi kan jaririyar tare da miƙa hannu ya ɗauke ta sannan ya nufi inda akwatin yake da jaririyar. Saurin riƙe ƙafar sa nurse Nadiya ta yi hawaye na zarya kan ƙuncinta ta ce. "Na roƙe da girman fiyayyen halitta, kada ka jefar da yarinyar nan, kayi tunanin idan da ƴar kace a kayi mata haka zaka ji dad'i, dan Allah ba dan ni ba kodan duban halin maraicin da take ciki na rasa kowa nata ka kyale ta. Dan Allah na roƙe ka, idan kace zaka yi haka, zaka shiga hakkin marainiya, ka taimaka ka ƙyale ta". Ta faɗa tare da fashe wa da kuka. S hassale ya wafce ƙafarshi daga hannunta ya yi ya sa ƙafarsa ta dama tare da naushin cikin ta. Take nurse Nadiya ta saki wata iriyar razananniyar ƙara, nan take idanuwanta suka fara lumshe wa. Kallon jaririyar dake hannunsa ta yi sannan ta ce. "Allah ga baiwar ka nan, ka kare ta a duk inda take sannan ka shiga cikin alamuranta, ka sanya maƙiyanta suyi danasanin abubuwan da suka aikata mata tare da sauran ƴan uwan ta mata. Ya Allah ka saka yarinyar nan tare da sauran ƴan uwanta sune za su zamo jagororin wannan garin, yayin da maƙiyansu waɗan da suka yi sanadiyar faɗawarsu cikin wannan mummunan yanayin su zo suna duƙa musu". Tana kaiwa nan ta yi shiru alamun ta suma. Saka yarinyar mijin nurse Nadiya ya yi cikin akwatin yayin da ya nufi hanyar waje da ita. Saka akwatin ya yi a bayan mota yayin da kukan jaririyar kawai ka ke ji domin ta kasa shaƙar iska daga cikin akwatin yayin da idanuwanta waɗan da suke blue suka ƙara rinewa sosai saboda kuka. Buɗe gate ya yi yayin da ya koma jiki motan tare da shiga ciki. Tada motar ya yi daga bisani ya fita daga cikin gidan. Saida ya yi tafiya mai nisan gaske yayin da gaba ɗaya mutane sun rurrufe shagunan su saboda dare ya ratsa sosai. Chan ya samu guri a tsakiyar titin da ba bu kowa ko mai wuce wa balle a samu mai ganinsa ya yi parking ɗin motar. Sannan ya fito daga cikin motan tare da buɗe bayan boot. Fito da akwatin ya yi daga cikin motan. Saida ya tabbatar da ba bu mai ganinsa sannan ya ajiye akwatin a tsakiyar hanya inda mutane ke wucewa sannan daga bisani ya bar wajan da sauri tare da shige wa cikin mota ya bar harabar wajan baki daya. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 *Ohh waɗan nan ƴan ukun suna ganin rayuwa tun kafin sun san mene ne ciwon kansu, ko yaya zata kasance da jaririya mai blue eyes?, yanzu ɗaya na daji tare da namun jeji, ga kuma ɗaya a magarƙama, yanzu kuma ɗaya na bakin hanya sannan yaya girman su ukun zai kasance?, ko ta ya ya za su hadu da juna nan gaba sannan su san su ɗin su uku ne. Muje dai zuwa domin jin yadda zata kasance*. COMMENTS & SHARE FISABILULLAHI 🙏🙏🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g Ku shiga channel ɗina domin samun sauran littatafai na👆👆👆👆👆 *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 9️⃣▶️🔟 *_________________________________________________* Ba bu abin da jaririyar ke ta faman yi sai kuka, yayin da namun jejin suka bita da kallo. Nan take wasu daga birrirukan suka fara arewa kan bishiya yayin da suka nufi gidan zuma tare da ɗaukar kashin zuma suka nufi inda jaririyar take. Suna isa suka saka mata a baki, nan take ta fara tsotsan zuman tana yi tana kuka. Ɗaukar ta gwagon biri ya yi tare da ɗora ta kan cinyarsa, a yayin da ya yi mata lulluɓi da ganye sannan ya fara bata zuman da kansa. Nan da nan gaba ɗaya namun daji suka tsaya tare da zagaye su. Nan take jaririyar ta kalle su tare da sakin murmushi. **Saka shi suka yi a cikin cell yayin da suka fara jibgarsa ta ko ina, saida suka tabbatar ya jigata sannan suka ƙyalesa. Zama DPO ya yi yana kallonsa ya ce. "Shin wane ne ya tura ka don ka taimaki Mrs Laila?, ba za ka faɗa ba ko sai an ƙara maka duka?". Ɗago da rinannu isanuwansa ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ni ɗin jami'i ne, kuma doka bata yarda jami'i ya daki jami'i ba tare da wani ƙwaƙwaran hujja hakan abin da ya aikata ba, sannan kotu bata baka damar yin hakan ba, mundin kotu ta gano to tabbas sai an cika tarar maƙudan kuɗaɗe sannan kuma a dakatar da kai daga aiki". Baki sake DPO ke kallon ɗan sandan sannan ya ce. "Ni tun da nake ban taɓa ganinka a cikin rukunin ƴan sanda ba, ƙarya ka ke kai ɗin ba ɗan sanda bane, so dai ka ke ka faɗi abin da za ka kare kanka da shi, to ni kuma ba zan bar hakan ta faru ba, mundin ina nan saina tabbatar da cewa kotu ta hukunta ka bisa ƙwaƙwaran hujjoji da nake dasu a kanka. Don haka ka faɗa min gaskiya domin a sassauta maka hukunci da za'a yanke maka". Murmushi ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ko za ka kai gobe kana duka na tare da tambaya na ba zan taɓa faɗa maka ba, sai dai kayi duk abin da ka e ganin za ka yi". Tashi tsaye DPO ya yi sannan ya ce. "Ohh haka kace?, nayi duk abin da nake ganin zan yi ko?, shi kenen za ka ga aiki da cikawa". Yana kaiwa nan ya ƙwallah jami'ai kira. Nan da nan jami'ai suka hallara a ciki cell ɗin, yayin da ya ce da ɗaya daga cikin jami'ai da ya ɗauko masa iron. Nan da nan jami'in ya ɗauko masa dutsen guga kamar yadda ya buƙata. Saka iron ɗin ya yi a jikin socket wanda ke kunne, yayin da ya saka suka tuɓe masa kaya. Ɗaukar iron ɗin ya yi wanda ke fitar da tiriri saboda zafi sannan ya kalli jami'in ya ce. "Zan ƙara tambayar ka a karo na ƙarshe, idan har baka bani amsar da nake buƙata ba, zan ɗora maka wannan iron ɗin a jikin ka". Cikin rashin tsoro ko fargaba ɗan sandan ya kalle shi sanann ya ce. "Me ka ke jira?, maza ka aiwatar da abin da ka ke niyar yi, kada kayi tunanin za ka tsorota ni da wannan dutsen guga, idan wahala ne jiki na ya saba da wahala, dana faɗa maka gaskiya na gwammace na fuskanci kowace tsanani ko duka da zata fito daga gare ku. Don haka maza ka fara". Kallon jami'an DPO ya yi, yayin da ya sa suka kwantar da ɗan sandan. DPO bai yi wata-wata ba ya ɗora iron mai zafi a jikin ɗan sandan. **"Haba Zainab, kina magana kamar wacce bata san ƙaddara ba, haihuwa fa na Allah ne, na san mundin lokacin mu ya yi za'a ƙwanƙwaso mana ƙofar alkhairy ne. Don haka dan Allah ki daina kuka, likita ya ce idan kina shan maganin ki a kan lokaci za'a samu sauƙi". Dattijon ya faɗa yana mai ci-gaba da tuƙi. Matar dake kusa da shi ce ta ɗago da jajayen idanuwanta tare da ɗora wa a kansa sannan ta ce. "Mai gida me ka ke so nayi to?, yanzu kimanin shekaru goma kenen muna ta fafutuka wajan neman haihuwa, ta ya ya ka ke tunanin ba zan yi kuka ba?, ƴan uwanka da mahaifiyar ka gaba ɗaya sun sa min ido. Kuma nima ban taɓa ganin laifin su ba, saboda ba bu wata uwa da zata so ta bar duniya ba tare da ta ga jikanta ba?, ni kawai ka barni na ci-gaba da kuka na ko zan ɗan samu sassauci a cikin zuciyata" Girgiza kai mutumin ya yi sannan ya ce. "Karki damu Zainab, Allah yana sane damu, in sha Allahu next week zamu je America domin a duba ki kinji. Kuma da yardar Allah komai zai yi dai...... Da wani irin sauri yaja wani mugun birki. Saurin ɗago da kai Zainab ta yi ta ce. "Me ya faru mai gida?". Fita daga cikin motan mutumin ya yi, yayin da ita ma matar ta fito waje. Kallon akwatin mutumin ya yi sannan ya ce. "Kinga wani akwati ina tunanin mutum ne ya manta shi s wajan". Kasa kunne matar ta yi jikin akwatin. Zaro ido waje ta yi sannan ta ce. "Kamar fa naji motsin wani abu a ciki, dan Allah ka zo mu tafi kada wani abu ya cutar damu, yanzu fa dare ya yi sosai ya kamata mu bar nan wajan". "Ki tsaya Zainab, zanje na ɗauki akwatin kedai ki zuba ido ki gani". Ya faɗa tare da nufar inda akwatin take. Addu'a ya yi yayin da ya yi bissmillahi sannan ya ɗauki akwatin. Jin da nauyi ya sa ya kuma tabbatar da cewa akwai wani abu s ciki. Zuwa ya yi har gaban motar sa sannan ya ajiye akwatin. Dafa kafaɗar shi matar ta yi cikin tsoro, sannan ta ce. "Dan Allah kada ka buɗe inajin tsoro". "Dan Allah Zainab kiyi haƙuri ki barni na buɗe akwatin nan in ba haka ba hankalina ba zai kwanta ba". Ya faɗa yana mai zuge akwatin. Saidai ya zuge akwatin gaba ki ɗaya sannan ya yi bissmillahi tare da buɗe murfin akwatin. Zaro idanuwa waje gaba ki dayansu suka yi. A yayin da zuciyoyinsu ya fara dukan uku-uku. Baki na rawa matar ta ce. "Me nake gani haka?, jaririya ce da suka saka ta a akwati, wane mara imanin ne ya aikata miki haka?". Fiddo jaririyar mutumin ya yi sannan ya ce. "Yanzu ba lokacin magana bane, mu fara kaita gida in yaso gobe mu kaita police station ko gidan radio domin bincikar inda iyayenta suke". Karɓe jaririyar matar ta yi sannan ta ce. "A'a, ba bu inda za'a kaita, zata zauna tare da mu har tsawon ƙarshen rayuwar ta, me ya sa iyayenta zasu watsar da ita su barta a cikin wannan mawuyacin hali. Yanzu da a ce bamu zo ba da wuri da tuni ta rasa rayuwarta saboda rashin iska. Tun da har waɗan da suka haife ta basua sonta ni ina sonta kuma zan riƙe ta tamkar ƴar cikina, ina sonta kuma ina ƙaunar ta. Don haka kamar yadda ka faɗa next week zamu bar ƙasar nan baki ɗaya domin muje mu gina sabuwar rayuwa tare da yarinyar mu". Ta faɗa tana mai rungume jaririyar kan kirjinta. *BAYAN SHEKARU*. *GOMA* Kwance take kan bench na ajin, yayin da ayaniyar yara ya cika ajin baki ɗaya. Ɗago da rinannun brown eyes ɗinta ta yi, tare da ɗora wa kan yaran dake ta faman wasa a cikin ajin. A hankali ta ɗago da fuskarta gaba ɗaya. Masha Allah baki na ya iya furta wa lokacin da nayi gamo da cute and pretty face ɗin ta mai matuƙar kyau. Lumshe idanuwanta ta yi wanda suka kunkumbura saboda kuka sannan ta buɗe su baki ɗaya. Miƙe wa tsaye ta yi tare da nufar inda sauran ɗalibai na ajin suke. Suna ganin ta iso wajan su, gaba ɗaya suka yi saurin barin wajan. Kallonsu ta yi cikin shesheƙar kuka ta ce. "Wai me ya sa a koda yaushe ku ke gudu na idan ba tunkari inda ku ke?, ban san mena yi muku ba, nima ina son kasancewa tare da ku, ina son na yi wasa sannan muyi karatu tare, bana jin daɗin zama ni kaɗai a cikin wannan makarantar". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka. Kallonta ɗaya daga cikin yaran ya yi sannan ya ce. "Kinga Zahra Mu ba zamu iya zama da ƴar magarƙama ba, an ce Mamanki sheɗaniya ce tana kashe yara, kuma kema a cikin magarƙama ki ka taso, yayin da ita kanta wacce ta riƙe ki ƴar magarƙama ce. An ce gaba ɗaya ahalin ki rabuwa suka yi dake saboda ba zasu iya riƙe ki ba. muma kuma ba zamu iya zama ko muyi tarayya dake ba, saboda muma kada muje ki kashe mu". Wata a cikin ɗaliban ce ta ce. "Nima mahaifiyata ta faɗa min cewa kada na kuskure na haɗa ƙawance dake ko na zauna dake. In ba haka ba zata dake ni. Don haka dan Allah ki rabu damu, mu ba zamu zauna da ƴar makashiya ba". Kallonsu Zahra ta yi sannan ta ce. "Ƙarya ku ke, Mamata ba muguwa bace ba, Idan ku ka ƙara cewa Mamata wai muguwa ce, saina kai ƙarar ku wajan shugaban makaranta. Ɗaukar jakarta ɗaliban suka yi tare da jefa mata a jiki. Hana haka malami ya shigo cikin ajin. Nan take kowanensu ya koma wajen zamansa. Banda Zahra wanda ke a tsaye sai faman kuka take. Kallonta malamin ya yi sannan ya ce. "Zahra me haka yi miki ki ke kuka?". Kallonsa ta yi cikin shesheƙar kuka ta ce. "Malam zagin Mama ta suke yi, kuma wai suna ce min ƴar magarƙama". Taɓe baki malamin ya yi sannan ya ce. "To ai da gaskiyar su, in da mahafiyar ki mutumiyar kirki ce bata damfari al'umma ba da ba za'a dinga yi miki wannan kallon banzan ba, don haka duk abin da haka yi miki to ki ƙaddara cewa Mamar ki ce ta jawo miki. Dani ne ma shugaban makarantar nan da ba zan karɓe ki a makarantar nan ba wallahi". Durƙusawa Zahra ta yi kan gwiwowinta tana mai fashe wa da kuka. Nan take ɗaliban ajin suka fara mata dariya, tare da fara tsokanarta, yayin da suka fara jifarta da littafi. Miƙe wa ta yi da sauri sannan ta fice daga cikin ajin. Nufar inda warders wanda ke mata rakiya izuwa makarantar ta yi, yayin da ta kalle su sannan ta ce. "Ina son ku maida ni gida yanzu nan". Ta faɗa tare da shige wa cikin mota. Kamar yadda ta faɗa haka suka ja mota suka bar harabar wajan. Bai fi lokaci ƙalilan ba, suka isa cikin magarƙama. Fitowa ta yi daga cikin mota tare da rugawa a guje ta nufo inda Hajiya Binta ke da zama. Binta da kallo mutanen dake cikin magarƙamar suka yi, ganin yadda idanuwanta suka kunkumbura ya sa hankalin kowanensu ya tashi, Da sauri sauran mutanen dake cikin magarƙamar suka nufi inda take. Shiga cikin ɗakin da Hajiya Binta take ta yi. Tana mai fuskantarta ta ce. "Shin laifi ne dan na kasance ƴar magarƙama?, kowane yaro farin ciki yake, amma ni a koda yaushe ba bu abin da nake fuskanta sai baƙin ciki da ƙyama. Kuma na san duk abubuwan nan na faruwa ne saboda Mamata, da a ce bata tafi ta barni ba, da hakan ba zata faru ba. Na tsane ta, bana sonta, me ya sa da zata tafi bata kashe ni ba?, amma ta barni cikin kaɗai ci". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka. Da sauri Hajiya Binta ta isa gare ta tare da rungume ta . "A'a ƴata, mahafiyar ki ba muguwa bace, bada son ranta ta tafi ta barki ba. Mamanki tana sonki sosai, kuma karki damu, nan gaba mutane za su daina tsokanarki kuma su daina gudunki kunji". "Shi kenen Aunty, kiyi min alƙawarin cewa za su daina tsokana ta". Murmushi Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Nayi miki alƙawarin cewa ba bu wanda zai ƙara tsokanarki Zahra". Murmushi jin daɗi Zahra ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da fice wa waje domin yin wasa. *BAYAN WASU SHEKARU GOMA* *AMERICA* Ba bu abin da ke tashi a cikin mashayar nan in banda haka. Yayin da ba bu abin da ka ke gani sai mata da maza, yayin da matan ke sanye da ɗingilallen skirt da shi gwanda ba bu. Chan na hangi wata matashiyar budurwa wacce ba zata wuce shekaru ashirin ba a duniya sai tiƙan rawa take yi. Yayin da gaba ɗaya turawan wajan idanuwansu a kanta. Ɗaya daga cikin mutanen wajan ne naji ya ce. "Diana". Juyowa ta yi tare da baje gashin ta, masha Allah na furta lokacin da nayi kicibus da haɗaddiyar fuskantar wanda ke ɗauke da light makeup. Kallonsa ta yi cikin cool voice ɗinta ta ce da shi. "How are you John?". Ta faɗa da yaren turanci na ƴan ƙasar America. Amsa wa John ya yi da cewa. "Am good baby". Ya faɗa yana mai ƙoƙarin shafa jikinta. Nan take budurwar ta ɗago da blue eyes ɗin ta tare da ɗaga hannunta ta kwashe shi da mari. Nan take mai Dj ya kashe waƙar dake tashi, yayin da gaba ɗaya idanuwan jama'ar wajan ya karkata izuwa kansu. Nuna shi ta yi da ɗan yatsarta cikin ɓacin rai ta ce. "How dare you John?, are you mad or something?. Idan har ka ƙara yi min wannan shashanci saina yi maka abin da yafi hakan". Diana ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar car key ɗin ta sannan ta fita daga cikin club ɗin. Da sauri ƙawayenta suka bi bayanta. Nausar iska John ya yi yayin da ɗayan hannunshi ke dafe da ƙuncin shi. "Diana! Diana! Diana". Haka ƙawayenta suka shiga ƙwalla kiran sunanta, amma ko juyowa bata yi ba ta saurare su, haka ta shige cikin mota tare da jan motan ta bar harabar wajan. Girgiza kai ƙawayenta suka yi yayin da suka koma cikin club ɗin. Tafiya mai nisa ta yi kafin daga bisani ta isa gida. Parking ta yi tare da fitowa daga cikin mota. Ta fara takawa da takalmin ta mai tsini ji ka ke ƙwass! Ƙwas! Ƙwass. Shiga cikin faɗeɗen palourn su ta yi a tsorace. Cire takalman ƙafarta ta yi sannan ta fara sanɗa tana tafiya. Saida taje daff da zata hau kan upstairs ta ji muryar mahaifiyarta. Da gudu ta haye kan upstairs tare da shige wa cikin ɗakin ta. *NIGEIRA*. "Wannan wane irin shirme ne Aliyu?, sama da yara amsin nasa haka yi safaransu izuwa kasashen waje, amma yanzu sai kace min wai wani ɓoyayyen jami'i ya sake su sun tafi, ta ya ya hakan zata faru?. Nafi sama da shekaru talatin ina wannan aikin nawa a ɓoye, kuma yanzu rana tsaka kace min wai yaran da na aika duk jami'ai sun karɓe su sannan suka mai da su gidajen su. Kasan dai wannan abun zai iya taɓa siyasa ta ko? Gashi zaɓe ya kusa, idan har mutane suka gane abin da nake aikata wa ta ya ya za su yarda su zaɓe ni a matsayin govnor. Ya zama dole kasa a rufe wannan abun, in ba haka ba saina sa an ɓatar min da kai daga cikin wannan duniya. Ɗago da fararen isanuwansa masu kyau da ɗaukar ido ya yi yayin da ya furzar da iska mai zafi waje cikin jin haushi da takaicin abin da ɗan majalisan yake aikata wa ya dube shi ya ce. "Kada ka damu yallaɓai, ko ta halin ƙaƙa ba zan bari komai ya fita ba, nayi maka alƙawarin hakan. Yanzu zanje na samu Mk ne a magarƙama. Na san yana da cikakken bayani game da wanda ya kunce yaran. Mundin ya faɗa min, in sha Allahu zan zo na sanar da kai". Yana kaiwa nan ya fice daga cikin office ɗin ƴan majalisa yayin da ya nufi inda motarsa take kai tsaye. Shiga cikin motan ya yi tare da jan motan ya nufi hanyar magarƙama. Isarsa magarƙama keda wuya, ya tarar da wasu mata suna buga ƙwallon ƙafa. Tafiya ya soma yi yayin da jami'ai suka tare shi. Nan take ya nuna musu ID card ɗin sa. Ganin shima jami'i ne ya sa suka barsa ya shiga. Sanye matashiyar take da kayan magarƙama yayin da take sarrafa ƙwallon cikin ƙware wa, a yayin da fuskarta ke ɗauke da farin ciki da annashuwa. Buga ball ɗin ta yi da ƙafarta na dama. Cikin rashin sa'a kuwa ball ɗin ya bugi Aliyu. Zaro idanuwa gaba ɗaya mutanen wajan suka yi tare da bin budurwar da Aliyu da kallo. Cike da ɓacin rai Aliyu ya ɗaga dara-daran idanuwansa tare da ɗora wa a kan ball ɗin. Cikin ɓacin rai ya ce. "Wace banzar ce ta cilla min ball a jiki?". Amsa wa budurwar ta yi da cewa. "Nice nan na wurgo ball ɗin". Ta faɗa tana mai juyo da kyakkyawar fuskarta. 💃💃💃💃💃💃💃💃💃 MANAGE PAGE COMMENTS & SHARE FISABILULLAHI 🥰🙏🥰 ALƘALAMIN ✍️ AISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣ *_________________________________________________* Sakar baki Aliyu ya yi yana kallonta, yayin da ya rasa me ke mai daɗi. Ganin kamar ma baya cikin hankalinsa ya sa Zahra faɗin. "Kai malam miƙo min ball ɗin nan". Kallon kanshi Aliyu ya yi sannan ya mai da kallonsa kan Zahra ya ce. "Kina da hankali kuwa?, kin wurgo min ball maimakon ki bani haƙuri shi ne za ki ce na wani miƙo miki ball. Kin san kuwa ko ni wane ne". Murmushi Zahra ta yi tare da nufar inda yake a tsaye. Kallon shi ta yi ido cikin ido ba bu tsoro balle fargaba sannan ta ce. "Ba bu ruwa na da ko kai wane ne, nan yanki na ne kuma gida na, kuma cikin ta ka shigo, sai abin da nace hake yi. Don haka ka ajiye duk izzan da ka ke takama da shi ka watsar a gefe, don ba za ta amfane ka da komai ba a nan wajan". Ɗaukar ball ɗin Aliyu ya yi sannan ya ce. "Dame ki ke takama?, waya tsaya miki a cikin magarƙamar nan da har ki ka samu ƙwarin gwiwar faɗa wa ɗan sanda maganganun nan?". Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce. "Dan sanda?, wai kai nan ɗan sanda ne ko?, kuma ka ke tunanin naji tsoron ka?, a kan me ma zan ji tsoron ɗan sanda?. To ka saurare ni kaji ni ƴan sanda su suke min ma bauta ƙarewanta". Haɗe ransa Aliyu ya yi sannan ya ce. "Kada kiyi tunanin zaki ci mutuncin aiki da kuma kaki na, ƙarya ne ƴan sanda su yi wa mai laifi wacce ke zaune cikin magarƙama bauta. In kuma da gaske ki ke nuna min evidence". Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta ce. "To shi shi ke nen yanzu za ka ga aiki da cikawa". Ta faɗa tare da juya bayanta sannan ta fara ƙwalla kiran jami'an dake cikin magarƙama. Kafin ƙiftawan ido gaba ɗaya suka hallara a wajan. Maida kallonta Zahra ta yi kan Aliyu sannan ta ce. "Wane evidence ka ke buƙata kuma bayan wannan?. Ka sani cewa waɗan nan da ka ke gani sune suke kaini makaranta, su kaini siyayya, su suturta ni sannan su bani abinci a baki, kuma duk abin da na umarce su suyi nan take za su aiwatar. Domin DPO ɗin ku shi ne ya ɗauki gaba ki ɗaya nauyin karatu na har da ma waɗan nan jami'an. To faɗa min a kan me zanji tsoron ka bayan ni a cikin jami'an ma na taso?". Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Perfect, amma sai dai ni hakan samm bata yi min daɗi ba, domin bai kamata a ce jami'ai suna yiwa mai laifi bauta ba, nayi Allah wadai da ku jami'ai. Irin kune ɓata gari a dinga tunanin cewar haka gaba ɗaya jami'ai suka taru suka zama ɗaya. Sai dai ni nawa aikin ya bambanta domin bana ɗaukar shashanci". Ya faɗa tare da ajiye ball ɗin a ƙasa sannan ya sa ƙafarsa ta dama ya taka ta. Nan take ball ɗin ta fashe. Ganin ta fashe ya sa shi sakin murmushi sannan ya ce. "Na fasa ball ɗin kiyi duk abin da ki ke ganin za ki iya, maza kije ki kira koma wane, ko uwarki bata isa ta yi min komai ba". Nan take ran Zahra ya ɓaci yayin da brown eyes ɗin ta suka ƙara rinewa sosai. "Ni zaka fasawa ball?, har kai waye da za ka faɗi magana hakan mahaifiyata?". Ta faɗa yayin da ta juya tare da mai da kallon ta kan jami'an wajan sannan ta yi musu nuni da su rufe ƙofar magarƙamar. Kamar yadda ta buƙata haka suka rufe ƙofar magarƙamar tare da datse wa da kwaɗo. Juya wa ta yi tare da kallon sa cikin hassala ta ce. "Me ya sa zaka sako uwata a cikin maganar ka?, shin kai baka martaba iyaye ne?, tun ds har ka kuskura kayi magana a kan mahaifiyata sai na yi maka abin da ko da so ɗaya ba zaka kuma ƙoƙarin zuwa magarƙamar nan yin investigation ba". Maida kallonta ta yi kan matan cikin magarƙamar. Nan take suka fuskanci abin da take nufi. Nan da nan gaba ki ɗaya suka zagaye Aliyu yayinda suka ririƙe hannayensu tare da yin circle. *. DAJI🌲🌳* (🦍🦧🐅🐘🐒🐈‍⬛🐂) *_______________________* Gudu take tamkar barewa tana mai aye wa kan manya-manyan bishiyun dake cikin jejin tamkar ƴar biri, yayin da take tsalle gashin kanta na tashi sama, hakan bai bani damar ganin fuskarta sosai ba. Riƙe hannunta yake da wani ɗan ƙaramin biri. Yayin da gefe guda namun jeji ke mara mata baya. Nan take ta dira a ƙasa tare da baza gashin ta. Masha Allah na iya furta wa lokacin da nayi kicibus da kyakyawar fuskarta wanda ke lulluɓe da farin ciki da annashuwa. Sanye take ciki kaya wanda alamun birrurukan ne suka yi mata, domin gaba ɗaya kayan anyi amfani da ganyayyaki wajan sa ƙashi ne.lumshe green eyes ɗinta ta yi tana mai mai da kallonta kan namun jejin sannan ta musu ciki yaren ko ni kaina ban sani ba". Nan da nan suka girgiza kai gaba ɗaya tare da watse wa . Yayin da birrurukan suka fara aye wa kan bishiyu suna ɗiban fruits ɗin da ke kai wato kayan marmari. Ganin gaba ɗaya sun watse ya sata sakin murmushi, sannan ta yi wani irin tsalle. Nan take ta dira a kusa da wani jibgegen dutse wanda ke zaman kansa a cikin dajin. Ajiyan zuciya ta sauke Tare da nufar katoton ruwan dake cikin dajin. Sannan ta shige ciki. Nan take ta fara wanka. Ganin hakan ya sanya birrirukan suka fara saukowa daga kan bishiyu, sannan suka ɗauki ganyayyaki suka tunkari inda take. Nan take suka zagaye ta da ganyayyakin tare da kare ta dasu. Sai da ta gama wankan sannan ta fito daga cikin ruwan. Fitowa ta yi ta ga sun zagaye ta da ganyayyaki sannan sun shirya mata kaya na ganyayyaki wanda zata saka. Murmushi ta sakar musu wanda ya sanya dimple ɗin ta ƙara lotsawa. Cikin yaren su na birirruka ta ce. "Na gode sosai ƴan uwana, ina matuƙar alfahari da ku, ina sonku sosai soyayya mara misaltuwa". Ta faɗa tare da janyi kayan ganyen da suka ajiye sannan ta saka. Fitowa ta yi daga cikin ruwan. Ganin ta sanya kaya ya saka suka ajiye ganyen da suka zagaye ta da shi. Tafiya ta fara yi tare da nufar inda dutse dake gabanta yake. Sai da ta ƙarasa wajan sannan ta zauna tare da jingina a jikin dutsen. Shafa jikin dutsen ta fara yi tana mai shafa sunan Amrah dake rubuce a jiki. Nan take fuskanta ya chanza daga walwalah izuwa damuwa. ganin kamar tana ƙoƙarin shiga cikin damuwa ya sa su birrirukan suka tunkaro inda take yayin da suma sauran namun jejin suka nufo inda take. Nan da nan gwagon biri ya ɗauke ta chakk tare da cilla ta sama. Nan take farin ciki ya lulluɓe fuskar Amrah. Nan da nan suka shiga yin wasa abun gwanin burgewa. Ajiye ta gwagon birin ya yi tare da ajiye Amrah a kan wata ƙaramar giwa, nan take giwar ta fara tafiya da ita tare da yawa ta da ita yayin da sauran namun jejin ke mara musu baya. *AMERICA* "What is wrong with you Safeera?, wannan ba tarbiyyar da na baki bane ba, me ya sa za ki dinga zuwa club for God sake?, sunanki Safeera amma kin mai da sunanki Diana saboda bakya jin tsoron duk abin da zai je ya dawo ko?". Matar ta ƙarashe maganar ranta a matuƙar ɓace. Miƙe wa zaune wacce haka kira Safeera ta yi sannan ta dubi mahaifiyartata cikin shagwaɓa ta ce. "Am sorry Mom, wallahi zan daina zuwa club sannan na daina saka waɗan nan matsatsun kayan kinji. Banason ina gani kina shiga damuwa saboda ni , i promise you that I will change, kuma sunan Diana ƙawaye na ne suka saka min a makaranta, amma zan ce kar su ƙara kira na da sunan kinji". Cewar Safeera. Murmushi Mom ta sakar mata sannan ta ce. "Don't forget that promise is a debt". Miƙe wa tsaye ta yi tare da nufar inda take sannan ta zaunar da Mom ɗin tata ta ce. "Yes Mom, I promise I will never hurt you again because I love you so much Mom". Rungume ta matar ta yi sannan ta ce. "That's my baby I love you more than you do". Jin shigowar mutum ya sa su miƙe wa tsaye tare da maida kallonsu inda suke jin takun mutum. Washe baki Safeera ta yi yayin da ta tafi da gudu tare da rungume shi. "Welcome back daddy, I really missed you". Ɓanɓare ta daga jikinsa mutumin ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Oh my cute baby, wai yaushe za ki girma ne?, so ki ke ki ɓalla ni, ji fa yadda ki ka tawo ki ka rungume ni". Murguɗa baki Safeera ta yi sannan ta ce. "idan ka karye ai sai na fi kowa shiga damuwa". Ta faɗa tana mai kwashe wa da dariya. "Shi ke nen tom naji, wai ina Mom ɗin ki take ne?, ta zo fa na dawo mata da good news". Cewar Daddy. Daga bayansa yaji ta ce. "Ai gani nan my one, ba saika neme ni ba". Cewar Mom. Da sauri yaje tare da rungume matar ta shi sanann ya ce. "Na tawo miki da good news, maza ku zauna". Zama suka yi suna mai fuskantarsa. Kallon su ya yi sannan ya ce. "Akwai ɗan yahya na yau ko gobe zai zo neman auren Safeera, kunga idan haka yi engagement a nan sai mu koma Nigeria da zama tun da anyi min transfer ɗin wajan aiki na koma Nigeria, kuma wanda zai zo neman auren ki shi ɗin police officer ne, kinga zaki kasance koda yaushe kina da tsaro". Miƙe wa tsaye Safeera ta yi sannan ta ce. "NI banason nayi aure yanzu, kuma ba zan je Nigeria ba. Ni a nan zan ci gaba da zama. Ko da karatu ban gama ba, amma shi ne za'a kawo min maganar aure. Ni dai gaskiya ba zan taɓa auran wanda zaku kawo min ba domin ni banason aure yanzu karatu nake so na ci gaba". Miƙe wa Daddy ya yi ranshi a matuƙar ɓace ya ce. "Kina nufin ba za ki bi umarni na ba kenan?, ɗan yahya na ne fa zai zo neman auren ki, shi ne za ki ce bakya so, to ki kina so ko bakya so sai anyi engagement ɗin nan, kuma karatu daga yau na dakatar da shi,bake ba ba karatu". Fashe wa da kuka Safeera ta yi sannan ta ce. "Wallahi ba za'a min aure a wannan shekarun nawa ba". Tana kaiwa nan ta shige ɗakin ta tare da rufe ƙofar ɗakin. Maida kallonta Mom ta yi kan Daddy sannan ta ce. "Daddyn Safeera ina ganin kamar kada mu tilasta mata, tun da bata so kawai mu rabu da ita ta yi karatun tun da shi take so". Kallon Mom Daddy ya yi sanann ya ce. "Kiyi min shiru Zainab, dama kece ki ka sangalta yarinyar nan ta zama haka. To ki jini da kyau ko tana so ko bata so wannan engagement ɗin kamar anyi an gama ne, sai dai ba bu numfashi a tattare da ni". *LONDON*. Kwance yake a kan faɗeɗen gadonsa mai matuƙar girma, yayin da ya rufu da bargo mai matukar laushin gaske. Ba bu abin da ke tashi a ɗakin sai ƙamshi da ƙaran Ac. a hankali ya ta shi zaune. Tabbas dukkan yabo da jinjina za su ci gaba da tabbata ga Allah SWA wanda ya yi wannan kyakyawan halittar. Lumshe fararen idanuwansa ya yi masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Wayarshi yaji tana ruri. A hankali ya duba kan table ɗin da ke kusa da shi yayin da ya ga sunan Abba bayyane kan screen ɗin shi. Ɗaukar wayar ya yi yayin da ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnensa sallama riƙe a bakin sa. Daga ɗayan ɓangaren haka amsa sallamar. Sannan naji an ce. "Umar yaushe za ka dawo Nigeria?, na faɗa maka cewar ina so a fara aiki a wannan dajin domin a fara gina wannan company, nayi magana da engineers ɗin da za su je suga yadda girman dajin yake, amma an ce akwai namun jeji a wajan dole sai an kore su. Ya kamata ka dawo Nigeria domin a san abun yi". Ajiyan zuciya Umar ya sauke, sannan ya ce. "Shi ke ne Abba, in sha Allahu zan dawo nan da next week. Ya maganar zaɓe ko har yanzu ba'a fara ba. Ni a tawa shawarar Abba ya kamata ka ajiye govnor wallahi, kamata ai a ce kana hutawa a gida, ka bari wani ya hau kawai". Murmushi Abbban na shi ya yi sannan ya ce. "Ai kuma kaga ba zai yiwu ba domin ni buri na shi ne na idimtawa al'umma da ƙasar baki ɗaya. So kaga aikin lada kawai nake bawai saboda kuɗi ba ko mulki". "Shi ke nen Abba ba bu damuwa, zan dawo ko cikin week ɗin nan ne". "Okay son Allah ya dawo mana da kai lafiya". Amsa wa Umar ya yi da Amin daga bisani ya kashe wayar. Miƙe wa tsaye ya yi tare da ɗaukar towel ya shiga toilet. Sai da ya ɗau lokaci sosai kafin ya fito daga cikin toilet ɗin ƙugunsa sanye da towel, sannan ya nufi wajan dressing mirror. Ɗaukar mai ya yi ya fara shafa wa. Sannan ya ɗauki wani oil tare da shafa wa a sumar ƙanshi wanda suka kwanta suka yi luff. Ɗaukar turarruruka ya yi tare da feffeshe jikinsa da su. Nufar wardrobe ɗin shi ya yi tare da zaƙulo ƙananun kaya brown colour sannan ya sanya su. Nufar inda takalman sa suke ya yi, tare da ɗaukar canvas brown sannan ya sanya su. Bayan ya gama ya nufi inda yake ajiyan hulinanshi sannan ya ɗauki Pcap brown ya sanya. Sannan ya nufi inda yake ajiyan eye glasses ɗin shi sannan ya ɗauki daya daga cikin glasses ɗin shi wanda ke photochronic ya manna a fuskarsa. Nufar inda wrist watch ɗin sa suke ya yi tare da ɗaukar wrist watch rolex ya sanya a hannunshi. Gaba ɗaya abubuwan da sanya diamond 💎 ne. Masha Allah kawai baki na ya furta lokacin da naga irin haɗaɗɗiyar shigar da ya yi wanda suka yi masa mugun kyau. Ɗaukar wayarsa ya yi yayin da kai tsaye ya shiga contact list. Nan take naga ya danna kiran sunan officer. Ringing biyu haka ɗauka. Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Peace be unto you Sir, hope everything is going we'll?". Amsa ya bashi da cewa. "in sha Allah". Sannan ya ƙara da cewa. "Ina son ku haɗa mun motoci yau zan dawo Nigeria, kuma kada ka sake mahaifina ya san da cewar na dawo, wannan ya zama secret a tsakanin mu, banason maganar da muka yi da kai ya fita". "In sha Allahu Sir ba bu wanda zai sani, baki na ƙanin ƙafata". Cewar officer ɗin. Jin hakan ya sa Umar kashe wayar. Sannan ya nufi inda box ɗin sa yake tare da ɗaukar troley ɗinsa sannan ya fice daga cikin ɗakin. *NIGERIA* *. INSIDE PRISON* "Kana tunanin zaka shigo inda nake zaune ka zagar min mahaifiya kuma na barka ka tafi?, a duniyar nan zan iya yin wasa da komai amma banda mahaifyata, tun da har ka riga da kuskura ka ambaci mahafiyata a maganar ka dole yau ka fuskanci uƙuba ta". Zahra na kaiwa nan ta nufi inda yake. "Zahra!". Ta ji an ambata da ƙarfi. Tsayawa chakk zahra ta yi. Nan take kowa ya watse. Juyawa Zahra ta yi tana mai fuskantar ta. Rass! gabanta ya faɗi. "Zahra me ki ke shirin aikata wa?, kina shirin dukan ɗan sanda ne?, karki yi tunanin kina zaune cikin magarƙama a matsayin mara laifi kuma kiyi tunanin idan ki ka aikata ba dai-dai ba, ba za'a hukunta ki ba. Maza ki bar wajan nan kafin na ɓata miki rai". Cewar Hajiya Binta. Ɓata rai Zahra ta yi tare da galla wa Aliyu harara sannan ta bar wajan. Ganin hakan ya sa Aliyu ɗaukar alwashin sai ya koya wa Zahra hankali. Juyawa ya yi tare da fice wa daga cikin magarƙamar baki ɗaya. Yana fita bai zarce ko ina ba sai gida, yayin da fuskarta kawai yake masa gizo a idanuwansa. Yayin da ya ji tsanarta ya ɗarsu cikin zuciyarsa. Wanka ya yi tare da chanza kaya sannan ya saka kayan shi cikin box. Sai da ya ɗauke shi hour biyu yana shirya wa, kafin ya gama. Fitowa ya yi sanann ya ɗauki car key ɗin shi ya nufi parking space. Shiga cikin motan ya yi tare da tada mota sanann ya bar gidan. Bai zarce ko ina ba sai airport, yayin da ya karɓi passport ɗin sa tare da visa sannan ya shiga cikin jirgi. Ɗaukar wayarsa ya yi tare da dialing number wanda ke rubuce da uncle. Ringing biyu zuwa uku uncle nasa ya ɗaga kiran sannan ya ce. "Hello Aliyu, ka tawo?". Amsa Aliyu ya ba shi da cewa. "A'a yanzu dai ina cikin jirgi, kuma yanzu zata ta shi. Nan da two to three hour's zamu isa America. Don haka ka kwantar da hankalin ka ina nan zuwa, yanzu dai jirgin zata ta shi zan kashe waya na sai anjima". Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Ajiyan zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce. "Zainab kije ki shirya Safeera Aliyu yana nan zuwa nan bada jima wa ba, yanzu haka zanje na jira shi a filin jirgi". Girgiza kai kawai Mom ta yi sannan ta nufi ɗakin Safeera. Aliyu na ajiye wayar ya kashe wayar sannan ya saka seat belt. Maida kallonsa ya yi waje. Nan take idanuwansa ya sauka a kan Umar. Zaro ido ya yi waje. Da sauri ya lalubo wayar shi. Nan take haka sanar da jirgi zai ta shi. Wata daga cikin hottest na jirgi ce ta dube shi sanan ta ce ya kashe wayar. Ba yadda ya iya haka ya kashe wayar tare da ajiye ta. Yayin da ya ci gaba da kallon Umar wanda officer's suka zagaye shi. Nan da nan jirgi ya tashi. Sai da ya ɗauke su lokaci kafin su isa America. Fitowa ya yi daga cikin jirgi yayin da suma sauran passengers ɗin suka fito. Daga nesa ya hangi Uncle ɗin sa. Da sauri ya isa gare shi. Rungume Aliyu Daddy ya yi sannan ya ce. "Welcome my son in law". Kunya ce ta kama Aliyu sanann ya gaishe da shi. Shiga cikin motan gaba dayansu suka yi sanann suka nufi hanyar gida. ******************** Shigar Mom cikin ɗakin Safeera keda wuya, ta tarar da Safeera ta yi kaca-kaca da ɗakin tare da fasa glasses design ɗin da haka ƙawata ɗakin da shi. Gani Mom ta yi Safeera ta chanza shiga ta shirya tsaff. Sakar baki Mom ta yi tana kallonta. Murmushi Safeera ta yi sannan ta ce. "Na san za kiyi mamaki Mom, na zauna nayi tunani ne, koba komai shi ɗin mahaifina ne dole nayi masa biyayya. Murmushi Mom ta yi sannan ta ce. "Shi ya sa nake matuƙar sonki my dear". Horn suka jiyo daga waje. Ta shi tsake Safeera ta yi ta ce. "kije Mom zan ƙarasa shirya wa, na san sune suka ƙaraso". Ta faɗa tare da nufar inda wardrobe ɗin ta yake. Fice wa Mom ta yi daga ɗakin. Ganin Mom ta fita daga ɗakin ya sa fuskar Safeera ya sauya daga walwalah zuwa damuwa. Nan take ta haɗe rai sannan ta ce. "Ba zan taɓa auransa ba, domin ni ba aure nake so ba". Shigowa su biyun suka yi ciki, yayin da ya umarci Aliyu da ya zauna. Zama Aliyu ya yi kan kujeran 1seater yayin da ya fara kallon cikin parlourn kamar wani baƙauye. Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce. "Bara na kira Safeera ta kawo maka abinci". Fitowa Mom ta yi daga cikin kitchen hannunta riƙe da plate da lemo. Zuwa ta yi har gaban Aliyu tare da ajiye wa. Gaishe ta Aliyu ta yi yayin da Mom ta amsa sama-sama. Guri ta samu ita ma ta zauna. Zama Daddy ya yi kan kujera tare da ƙwalla kiran sunan Safeera. Jin Daddy na kiranta ya sata saurin saka veil a fuskarta tare da rufe gaba ki ɗaya fuskarta, sai iya ƙwayan idanuwanta kawai. Fitowa ta yi daga cikin ɗakin tare da nufar parlour ta tarar da su a zaune. Binta gaba ki ɗaya suka yi da kallo. Cikin ɓacin rai Daddy ya kalle ta ya ce. "What's the meaning of this?, maza cire mayafin kafin ranki ya ɓace". Girgiza kai Safeera ta yi ta ce. "Am sorry Daddy i can't". "What! Daddy ya furta. Ganin kamar ran Daddy ya soma ɓaci ya sata fara cire mayafin a hankali daga ƙarshe ta cire bako ɗaya. Zaro idanuwa waje Aliyu ya yi tare da miƙe wa tsaye. Cikin kiɗima ya nuna ta da yatsa hannusa da jikinsa gaba ɗaya na kakkarwa ya ce. "Kece, ta ya ya ki ka ƙaraso nan?, meya kawo ki?". Cikin rashin fahimta gaba ɗaya suke kallonsa yayin da Daddy ya kalle shi ya ce. "Bangane ba Aliyu kayi min bayani, wannan fa ƴata ce ba wata ba". Maida kallonsa Daddy ya yi kan Safeera sannan ya ce. "Shin kin san shi ne?". Girgiza kai Safeera ta yi baki na rawa ta ce. "ni samm ban ma taɓa ganin shi ba". Maida kallonsa Daddy ya yi kan Aliyu sannan ya ce. "Ƴata bata taɓa zuwa Nigeria ba koda sau ɗaya, kuma ba aikin jarida take ba ko siyasa balle ka ganta a cikin tv. To a ina kuma ka santa?". Jiri ne ya fara ɗiban Aliyu ya ce. "Ita ce muka haɗu a magarƙa..... Kafin ya idda maganar ya tafi luuu tare da faɗuwa ƙasa sumamme. 💃💃💃💃💃💃💃💃 *TOH FAH AKWAI RIKICI GABA, KOYA ZATA KAYA A GABA? MUJE DAI ZUWA. KU DAI KU CI-GABA BINA TARE DA SAMBAƊO MIN COMMENTS TA YADDA ZAN DINGA JIN DAƊIN YI MUKU SHI*💃💃💃 *KOYA HAƊUWAR ZAHRA, AMRAH DA SAFEERA ZAI KASANCE?*MUJE DAI ZUWA* *KADA KU MANTA DA COMMENTS LIKES, AND SHARE FISABILULLAHI 🙏🙏🙏* *_______________________* *KUYI HAƘURI DA RASHIN UPDATE KWANA BIYU WALLAHI INA FAMA DA CIWON HANNU NE SHI YA SA*🥺🥹😢. @@@@@@@@@@@@ ALKALAMIN ✍️ @A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣ *_________________________________________________* Zaro idanuwa waje su Mom suka yi. Nan take suka nufi inda Aliyu ke a yashe. Ɗaukar wayarsa Dad ya yi tare da dialing number ɗan uwansa domin labarta masa abin da ke faruwa. Ringing biyu haka ɗauki wayar. Kara wayar Dad ya yi a kannensa sannan ya ce. "Hello Yahya, akwai matsala fa, Aliyu ya zo yana ganin ƴata Safeera ya suma, kuma ban san dalilin hakan ba". Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Kada ka tashi hankalin ka, haka yake da zarar ya ga wani abu ya firgita shi to suma yake kai tsaye. Don haka kada ka tashi hankalinka, zai farfaɗo. Idan ya farfaɗo ka tambaye shi me ya firgitar da shi, za ka ga ya manta domin yana da cutar mantau". "What!", Dad ya faɗa hankali tashe. Sannan ya ƙara da cewa. "Yahya kana nufin Aliyu yana da cutar mantau?, ta ya ya hakan ta faru?, ni dai na san a yadda na san Aliyu bashi da wata cuta". Daga dayan ɓangaren haka ce. "Ƙwarai da gaske, cutar tashi bai taɓa tashi bane a gaban ka, amma tabbas Aliyu yana da cuta tun yana yaro. Shi ya sa ma na masa yawo na turo shi domin su gana da ƴarka a ɗaura masa aure ko Allah zai sa cutar ta kau". Girgiza kai Dad ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen Yahya zan kira ka". Yana kaiwa nan ya katse wayan. Kallon Aliyu ya yi tare da maida kallonsa kan Safeera wacce ta yi zuru-zuru tana kallon Aliyu wanda ke a yashe a ƙasa. Shiga kitchen Mom ta yi tare da nufar inda fridge yake. Buɗe fridge ɗin ta yi tare da ɗaukar ruwan roba mai sanyi sannan ta rufe fridge ɗin ta wuce parlour. Tana zuwa ta buɗe murfin roban sannan ta watsa wa Aliyu ruwan a jiki. Nan take Aliyu ya buɗe idanuwansa tare da dafa kujera domin ya miƙe tsaye. Taimaka masa Dad ya yo ya miƙe sannan ya zauna a kan kujerar three seater. Kallon shi Dad ya yo sannan ya ce. "Aliyu me ya tsorata ka game da Safeera?, shin blue eyes ɗin ta ne ya tsoratar da kai ko kuwa?". Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya fara kalle-kalle. Zumbur ya miƙe tsaye yana mai fuskantar su. "Ta ya ya na zo nan wajan?, wace ce kuma Safeera". Sakin baki gaba ɗaya suka yi suna kallonsa. Cike da mamaki Dad ya kalle sa ya ce. "Kana nufin baka san yadda ka zo nan ƙasar ba?". Amsa Aliyu ya ba shi da cewa. "Ƙwarai ban sani ba, ni dai na san zan shiga cikin magarƙama ne amma ban san ta yadda na zo nan wajan ba, ya kamata na tafi domin ina da hayyuka a gaba na". Jikin Dad ne ya yi sanyi. Ji ya yi kamar ya kurma ihuu saboda takaici. Cikin ransa ya ce. "Tabbas akwai matsala babba, ta ya ya zan aura wa ƴata wanda yake da cutar mantau?, tun da yanzu ya ce bai san ta ba, wata ran idan sun yi aure ma haka zai ce ba matarsa bace. Shi ke nen tun da ya manta ba zan aura masa ita ba, zan barta kawai ta ci gaba da karatun ta a Nigeria". Dawo wa ya yi daga duniyar zancen zucin da ya shiga, sannan ya dubi Safeera ya ce. "Kada ki damu ƴata, ba zan yi miki aure yanzu ba kunji". Murmushi Safeera ta yi tare da gyaɗa kai sannan ta shige cikin ɗakin ta. Maida kallonsa Dad ya yi kan Aliyu sannan ya ce ya shi ke nen Aliyu za ka iya tafiya. Amma me zai hana ka bari zuwa next week muma zamu koma Nigeria da zama saboda anyi min transfer ɗin wajan aiki. Kaga sai mu koma tare, koya ka gani?". "Shi ke nen". Kawai Aliyu ya furta. Ɗaukar jakar Aliyu Mom ta yi sannan ta yi masa rakiya izuwa ɗakin baƙi. Safeera na shiga ɗaki kuwa, ta buga tsalle yayin da ta fara murna cewa Daddyn ta ba zai yi mata aure ba. "Shi ke nen yanzu ba bu ni ba bu auren wancan mutumin. Wayyo daɗi kashe ni, zan ci gaba da zuwa makaranta, daga ƙarshe na zama babban Barrister ko lawyer. Sai dai a ji a cikin kotu hana cewa. "Barrister Safeera can you come forward please. Nima daga nan na tashi domin kare wanda haka cuta sannan na tsaya tsayi daka domin ƙwatar wa mutane haƙƙinsu. Wow abin ya burgeni, daga ƙarshe dai zan zama Barrister". Safeera ta faɗa tana mai tiƙan rawa a cikin ɗakin. *NIGERIA CIKIN MAGARƘAMA* Zama Zahra ta yi a ɗakin tana mai fuskantar Hajiya Binta. Girgiza kai Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Wai me ya sa ki ke da zafin zuciya ne Zahra?, ba daman mutum ya yi miki wasa shi ke nen za ki ɗauki zafi". Turo baki gaba Zahra ta yi sannan ta ce. "Zan iya wasa da komai amma banda mahaifiyata, a kan me ya sa zai zage ta?, dan yana matsayin ɗan sanda shi ne haka ce ba zai san bambancin dai-dai da kuma ba dai-dai ba?, wallahi da a ce baki zo ba ɗazun nan Allah da saina koya masa hankali. Ni da so samu ne Allah na bar cikin magarƙamar nan domin na gaji da zaman cikin ta, ba bu wani freedom sosai, daga aiki sai wasa sai a zo a bawa mutum abinci wanda ko akuya ta ci ba lallai ta ji daɗinsa ba". Ta ƙarashe maganar tana mai ɗora idonta a kan wani babban littafi. Ajiyan zuciya hajiya Binta ta sauke sannan ta ce. "Ai idan har na sake na barki ki ka fita daga cikin magarƙamar nan to sai dai ba bu rai a jiki na, domin kuwa rayuwar ki yana cikin hatsari. Ba bu wanda ya san da cewa kina raye, da a ce sun san da cewa kina raye da tunan an sace ki domin ki je ki dangwala hannu a kan wasu dukiyoyi wanda yawan su ba zai misaltu ba. Yanzu dai ba lokacin wannan magana bane, ki tashi ki fita wata warder ta ce tana nemanki". Tashi tsaye Zahra ta yi sannan ta ce. "Shi ke nen Aunty bara naje". Ta faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin. ****************** "Hello yallaɓai, yanzu nan nake jin labarin cewa ɗan ka Umar ya sauka a Nigeria". Zumbur mutumin ya miƙe daga kan kujeran da yake, sannan ya ce. What!, kana nufin Umar ya shigo Nigeria?, me ya sa ku ka bari ya sauka a Nigeria bayan na faɗa muku cewa rayuwarsa tana cikin hatsari. Ɗazun nan muka gama waya da shi ya ce min wai sai next week zsi dawo Nigeria. Ta ya ya kuma yanzu za'a ce min wai ya shigo Nigeria?. Yanzu haka gurɓatattun ƴan sanda da ƴan daba neman sa suke ruwa a jallo. Saboda ya kama ɗaya daga cikin babban mai laifi wanda gaba ki ɗaya ƙasa ke nema, kuma sannan ya ƙwace ƴan mata wanda hake ƙoƙarin yin safaransu a ƙasashen waje, sannan ya yi siezing ɗin miyagun ƙwayoyin da hake shigo da su shi da abokin sa wanda yake aikin custom. Yanzu dai abin da nake so da kai shi ne, na san da cewa yana da jami'ai securities wanda ke ba shi kariya. Ina son ka tara jamiai ku dinga binsu a baya har sai sun iso gidan nan lafiya". "Shi ke ne". Jami'in ya faɗa, daga bisani ya kashe wayar. Tafiya motar su Umar suke a kan titin layin ɗan masara. Chan na hangi wani katafaren gida mai matuƙar kyau da tsaruwa. Tabbas kuɗaɗen sun yi kuka wajan gina wannan katafaren gidan. horn jami'an suka yi. A take masu gadi suka fara buɗe gate . wayyo Allah wanan gidan shi hake kira aljannar duniya . inda hake parking motoci suka nufa tare da yin parking. Kashe motocin suka yi, gba ɗaya motoci ne ya zagaye gidan kai kace wajan saida motoci ne saboda yawa. gaba ɗaya gidan zagaye yake da sojoji, inda gefe ɗaya kuma flag of nigeria ne a sama. dakuma flag na jami'ai. gaba ɗaya jami'an gidan riƙe suke da bidigogi chan nesa kuma baban gida ne da alama ɗakin karnuka ne wato police dogs daga gefe kuma swimming pool ne babba mai matuƙar faɗi da girma. chan gefe kuma ɗakin lantarki ne da kuma ɗakin gana wa masu laifi azaba. cctv cameras ne kewaye a gaba ki ɗaya gidan. gidan babba ne yadda ka san gidan shugaban kasa saboda yadda ya zagaye da sojoji. Idan na ce zan tsaya gaya muku yadda gidan nan ya haɗu sai na gama page ɗin nan ina bayyana irin kyau da gidan yake da shi. Kai tsaye cikin labari. wasu maza uku ne sanye da kakin soja suka nufo inda suke, ɗaya daga cikin su ne ya bude side ɗin Umar tare da buɗe masa ƙofar mota sannan ya sara masa. Ɗaga mai hannu Umar ya yi da ya dakatar da sarawan. Fitowa ya yi daga cikin motan tare da shige wa cikin gidan. Masha Allah baki na ya iya furta wa lokacin da nayi gamo da parlourn gidan. Gaba ɗaya kayan furnitures ɗin gold ne. Biyo shi securities suka yi da box ɗin shi. Juyawa ya yi tare da kallonsu sannan ya ce. "Ku ajiye ƴan aiki za su zo su ɗauka". Ajiye wa suka yi tare da fice wa daga parlourn. Fitowa gaba ki ɗaya family gidan suka yi tare da yi mishi barka da zuwa. Ɗaga musu hannu kawai ya yi daga bisani ya shige part ɗin shi. Baki sake suke binshi da kallo. Wata budurwa ce sanye da atamfa riga da siket ce ta dubi sauran ƴan uwan nata sannan ta ce. "Wai me ya sa yahya Umar yake haka ne?, kwata-kwata shi bashi da wata farha?, ya kamata a ce Abba ya yi masa magana, mu fa ƙannensa ne ba maƙiya ba". Ta ƙarashe maganar damuwa bayyane a kan fuskarta. Ɗaya daga cikin su huɗun ne ya dube ta ya ce. "Khairiya kin san dai ba yau ne ya fara ba, tun da mahaifiyarsa ta yi hatsarin mota ts rasu shi ke nen ya chanza a gidan nan, walwala da kuma dariya shi ya guje. Abba ma bai ƙyale shi ba balle mu. Kunga ku tawo mu bar nan kafin ya fito ya tarar da mu". Kallonsa khairiya ta yi sannan ta ce. "Allah ya bayyana wanda zata sauya Yahya Umar ya dawo yadda yake a da". "Ameen thumma Ameen". Gaba ɗaya suka furta. Bayan Umar ya shiga ɗakin ya shiga toilet tare da watsa ruwa. Fitowa ya yi tare da nufar ɗakin Abba, sallama riƙe a bakin shi ya shiga cikin ɗakin. ************************** *HOSPITAL*. Zaune take a kan kujera yayin da ta zurfafa cikin tunani, ta rasa me ke mata daɗi. Dafa ta ɗaya daga cikin nurse's ɗin ta yi ta ce. "Nurse Nadiya wai me yake damunki?, tun a kwanakin baya na fahimci cewa kina cikin damuwa, kuma a wasu lokutan idan naga kin idar sallah ina yawan ganin kina kuka kina haɗa hannayen ki guri ɗaya, kuma ni hakan ba ƙaramin kasalar min da jiki yake ba. Ya kamata a ce ki fauwala wa Allah komai Allah shi ne mai jiƙan bayinsa". Cewar nurse ɗin. Share hawayen dake gangaro mata nurse Nadiya ta yi sannan ta dubi nurse ɗin ta ce. "Ba za ki taɓa fahimta ta ba nurse, koda a ce zan faɗa miki abin da ke ci min tuwo a ƙwarya ba za ki gane ba. Ina cikin halin tsaka mai wuya, na ɗauki alƙawari kuma ban cika ba. Ban san me zan yi ba, gaba ɗaya na ji duniyar ma ta ishe ni, ji nake kamar na mutu na huta". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka. Ajiyan zuciya nurse ɗin ta sauke sannan ta ce. "Komai da ki ke gani a duniyar nan muƙaddari ne, ki ci-gaba da kai kukan ki ga ubangiji ko za ki ji sassaucin abin da ke damun ki". "Shi ke ne". Kawai nurse Nadiya ta faɗa sannan ta ya miƙe tsaye tare da koma wa baki aikin ta. ************************** *DAJI* Kwance Amrah take kan jibgegen bishiya, yayin da iska mai ni'ima ke kaɗawa yana shiga kowane sashi na jikinta. Lumshe green eyes ɗinta tare da buɗe su gaba ɗaya. Kallon aku wato parrot dake kusa da ita ta yi sannan ta ce. "Shin bayan wannan duniya tawa akwai wata duniyar da ta kai wannan kyau?". Girgiza mata kai akun ya yi. Jinjina kai Amrah ta yi sannan ta ce. "Toh indai haka ne zan so in ga ya birni yake, ni dai na san ba za ta kai duniyata kyau ba. Kuma sannan su ya halittar su take?". Ta faɗa tana mai ɗora hannunta kan haɓar ta. Jin kururuwan dabbobi ya sa ta saurin miƙe wa daga kan bishiyar. Yayin da ta yi tsalle ɗaya ta dira daga kan bishiyan. Gudu ta fara yi tamkar wata zakanya, yayin da ta fara bin hanyar inda take jiyo kururuwan dabbobin. Daga chan nesa ta hango kura da dila suna faɗa a tsakaninsu yayin da suke kaiwa juna hari. Ganin hakan da Amrah ta yi ya sa ta ƙara saurin gudun nata. Ganin kura tana ƙoƙarin kaiwa dila cizo ya sa Amrah buga tsalle ɗaya tare da shiga tsakiyar su sannan ta yi musu alamu da hannu da su dakata. Chakk suka tsaya yayin da sauran. A fusa ce ta dubi su biyun ta ce. "Mene ne yake damun ku?, shin kun rasa tunanin ku ne?, me ya sa a koda yaushe ku ke yawan faɗa ne?, shin ba zai yu ku zauna lafiya bane?. To daga yau ku saurare ni muddin na ƙara ganin kun ƙara faɗa saina yi muku hukuncin da baku taɓa tsanmani ba sannan daga ranar ba zan ƙara kula ku ba". Maida kallonta ta yi kan dila sannan ta ce. "Ke kuma kin san da cewa kura ya fi ƙarfin ki amma ki ke ƙoƙarin faɗa da shi, yanzu idan ku ka je ku ka illatar da kanku fa?. to ku sani cews gaba ɗaya zan ɓata muku rai idan baku daina faɗa ba". Tana kaiwa nan ta juya musu baya alamun ta yi fushi da su. Nan take gaba ɗaya suka sunkuyar da kawunansu tare da nufar inda take. Shafa jikin ta suka fara yi yayin da suka je gaban ta tare da ɗurƙusawa, sannan suka sunkuyar da kai ƙasa alamun suna bata haƙuri. Ganin sun sunkuyar da kai ƙasa ya sa ta nufar inda suke tare da ɗurƙusawa kan gwiwowinta sannan ta janyo su jikinta ta ce. "Ku sani cewa kune komai nawa, kune dangi da kuma iyaye na, ba zan juri naga kuna faɗa a tsakanin ku ba, ku daina kunji ko". Maida kallonta ta yi kan sauran namun jejin sannan ta ce. "Maza gaba ɗaya ku zo mu yi wasan tsere ko. Idan na riga ku zaku ɗauke ni gaba ɗaya kunji ko. Dan haka ku tawo muje mu yi wasa". Duk abin da take faɗa da yaren dabbobi take yi. Da gudu ta bar wajan fuskarta ɗauke da annashuwa. ganin hakan ya sa suma namun jejin suka bita da gudu. ************************ "Mai gida ya kamata a ce ka yafe wa ƴarka, ita ɗin fa ƴar mu ce. Yanzu haka ta riga da ta rasu, bai kamata a ce har yanzu kana fushi da ita ba". Cewar wata dattijuwar mata. Ɗago da kansa mutumin dake kan wheel chair ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Yafiya?, kina nufin na yafe wa Laila cin mutunci da zubar mana da kima da ta yi a shekarun baya?. Abun da ta yi ya daɗe da faruwa amma ina jin shi sabo ne a cikin zuciyata, kin san dai ba bu abin da na fi tsana sama da na ga mutunci na da na ahalina ya zube. Ta ci amanata, samm bata cancanci na yafe mata ba, ni na tsani ma jin sunanta a inda nake, kada ki ƙara kawo min irin wannan maganar na faɗa miki. Kuma abin da ta yi wanda ya sa a yanzu jika na Aliyu yake fama da cutar mantau, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ba zan taɓa yafe mata ba, dan haka ki ƙyale ni". Girgiza kai matar ta yi sannan ta ce. "Shi ke nen, amma ka sani cewa cutar mantau na Aliyu ba laifin Laila bane, tsautsayi ne kawai bada gangan ba, dan Allah a matsayina na uwa nake roƙan ka, dan Allah ka yafe wa Laila ko ruhinta sai samu salama". Ta ƙarashe maganar hawaye na gangaro kan fuskarta. Nuna ta dattijon dake kan wheel chair ya yi sannan ya ce. "Amina kada ki kuskure ki fusa ta ni nayi miki abin da ba za ki ji daɗin sa ba. Ta ya ya za ki ce ba ita ce silar cutar mantau ɗin Aliyu ba, shi kanshi mijin ta tun da haka kaita magarƙama bai taɓa zuwa ya duba ta, saboda ya san ba mutumiyar kirki bace. Laila ta karya min duk wani yarda ta a kanta, ita ce dalilin zama na a kan wannan wheel chair ɗin. Laila ta ci amanar yardar da nayi mata, ta zalince ni, duk dukiya da companies da take dasu basu ishe ta ba, sai ta haɗa da miyagun laifuka, eh?, na ce duk basu ishe ta ba sai ta haɗa da safaran yaran mutane. ta saka bana iya fita saboda abin kunyar da ta janyo wa wannan ahalin. Har abada ba zan yafe mata abin da ta yi ba". "Aba mai gida, Allah ma muna yi masa laifi yana yafe mana balle mutum ɗan adam. Ni ina da yaƙinin cewa Laila bata aikata kowane laifi ba, ita ɗin fa mai gaskiya ce da riƙon amana. Amma ba bu damuwa na san dai wata rana gaskiya zata yi halinta, kuma ramin ƙarya ƙurarre ne dole dai wata ran gaskiya zata fito". *********************** "What!, Umar ka san abin da ka ke faɗa kuwa?, kana nufin a yau zamu je wannan dajin?, yau ɗin nan da ka dawo ku hutawa baka yi ba, ka bari zuwa next week mana, ka ga kafin nan gaba ɗaya engineers da architecture da kayan aiki za su kasance a shirye. Wannan wajan naka ne amma akwai namun jejin dake zaune a cikin dajin, waje ne mai matuƙar hatsarin gaske, ba zai yiwu kaje ba. Kawai kayi zaman ka a gida in ya so idan haka kori namun jejin wajan sai ka zafi filin da ka ke so a wajan". Ɗago kai Umar ya yi ya kalli mahaifin nasa sannan ya ce. "Saboda me za'a kari dabbobin dake zama a cikin dajin?, su kenen basu da ƴanci na rayuwa ne ko me?, kana ji ba za'a taɓa ɓangaren su ba, za'a gina company ne a wani guri a cikin dajin amma banda ban yarda a taɓa ɓangaren inda dabbobin suke zama ba, kuma a yau nake so na je na ga wajan". "Amma Umar wajan nan fa gaba ki ɗaya mallakin ka ne, kuma gaba ɗaya wajan ne namun jeji ke zama, ko dai za ka sauya wani jejin da ban muje na Kano?". Amsa Umar ya ba shi da cewa. "A'a, ni wannan dajin nake so, kuma yanzu nake so na je". "Shi ke nen Umar, tun da haka ka ke so zan yi wa engineers magana za'a tafi da kayan aiki domin a fara gudanar da aikin company". Cewar mahaifin na shi. Bayan hawanin biyu da misalin ƙarfen biyar na yamma gaba ɗaya suka shirya tsaff yayin da haka haɗa rukuni na jami'ai da bindigogi suka nufi hanyar dajin. Tun da suka fara tafiya Umar ke jin gabansa na tsananta faɗuwa, ya rasa me ke masa daɗi, gaba ɗaya ya shiga wani irin yanayi. Lokaci ƙalilan ya yi musu a cikin dajin su Amrah. Shiga suka fara yi da motoci cikin dajin yayin da suke tattaka itacuwa da ganyayyaki saboda ba bu wata hanya ta mota a wannan jejin. Suna cikin tafiya ƙwatsam suka buge ɗaya daga cikin dabbobin dake bin Amrah a baya. Tsayawa motocin suka yi a tare. Sannan gaba ɗayansu suka fito daga cikin motan banda Umar wanda ke zaune a bayan mota securities sun zagaye motar da yake ciki da bindigogi. Juyawa Amrah ta yi sakamakon jin ƙaran ɗaya daga cikin namun jejin da ta yi. Zaro idanuwa ta yi waje tare da sakin wani irin ƙara! mai razanarwa. *TOH FAH YANZU HAKE YINTA, KOYA ZATA KASANCE TSAKANIN AMRAH DA UMAR?. MUJE DAI ZUWA* KADA KU MANTA DA COMMENTS DA KUMA SHARING PLEASE 🙏 🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣5️⃣▶️1️⃣6️⃣ *_________________________________________________* Da mugun gudu Amrah ta isa inda dabban yake, sannan ta fara duba shi, ganin cewa ba bu alamun rai a tattare da shi, ya sa ta ɗago da green eyes ɗin ta wanda suka ƙara rinewa saboda ɓacin rai sannan ta ɗora a kansu. Gurnani Amrah ta fara yi. Da sauri ta miƙe tare da nufar inda suke. Ganin tana nufo inda suke ya sa jami'an suka yi saurin zagaye motar Umar yayin da suka saita bindigun su kanta. Tsalle ɗaya Amrah ta yi tare da dira kan motan da Umar ke ciki. Zabura gaba ɗayansu suka yi. Nan take suka janyo ta ƙasa ta faɗi, sannan suka fara ririƙe ta. Ɓangaren Umar kuwa ba abin da yake yi sai aikin kallonta, yayin da ya ji kanshi cikin sabon yanayi da shi kanshi bai san dalilin faruwar akan ba. Fitowa ya yi daga cikin motar tare da ƙura mata idanuwansa. "She is so pretty and cute". Ya faɗa cikin zuciyarsa. Ɗago da idanuwanta Amrah ta yi tare da sauke su a kan na Umar. A matuƙar fusa ce ta ƙwace kanta daga riƙon da jami'an suka mata, yayin da ta fara dukansu tana ɗaga su sama tare da wurga dasu ƙasa. Saida ta gama da su sannan ta fara yowa inda Umar yake. Saida ta je har gabansa da zimmar dukansa. Tsayawa ta yi chakk saboda ganin irin ƙwar jinin da ya yi mata. Gurnani ta fara yi tana mai nuna dabba da suka buge. nan take ta fara hawaye tana dukan motan da ya bude dabban. Jikin Umar ne ya yi sanyi yayin da ya ji jikinsa ya mutu. Kallon tufafin da ke jikinta ya yi. Ganin gaba ɗaya ganye ne sanye a jikinta akan ya ƙara tabbatar masa da cewa Amrah ƴar daji ce. Jin kukan Amrah ya sa sauran namun jejin fitowa izuwa harabar wajan. Ganin Amrah durƙushe tana kuka, ya sa suka fara gurnani yayin da suka fara nufar inda Umar yake da zafin nama. Ganin suna nufo inda yake ya sa Umar ya fara ja da baya-baya. Ɗago da rinannun green eyes ɗin ta Amrah ta yi tare da sauke su akan namun jejin. ganin suna nufar inda Umar yake da zimmar illata shi ya sa ta sauri miƙe wa, yayin da ta tafi da gudu tare da shan gabansu. Da sauri jami'an suka miƙe tsaye. Yayin da a dai-dai lokacin yan hukuman row suka ƙaraso wajan. Dakatar da dabbobin Amrah ta yi da hannunta sannan ta ce da su. "Maza ku ja da baya, kada ku ce zaku cutar da shi, bada sane suka buge ɗaya daga cikin ƴan uwan mu ba, dan aka maza ku koma. In ba aka ba gaba ɗaya rayuwar mu tana cikin hatsari". Gani suka yi tana yin magana ba tare da fahimtar abin da take cewa ba. "Sir Umar ka bamu dama domin mu kashe dukanin dabban dake cikin dajin nan, domin nan mallakin ka ne ba ta su ba". Dakatar da shi Umar ya yi da hannunsa sannan ya ce. "Kada kuyi komai ba tare da izini na ba, gaba ɗaya kuna under control ne don aka be careful. Maza ku tawo mu bar nan sannan yarinyar nan ku saka ta a mota ku tawo da ita". "Yes Sir". gaba ɗaya suka faɗa, yayin da suka nufi inda Amrah take tsaye tana faɗa wa dabbobi da su koma. Juyawa dabbobin suka yi tareda barin wajan. Ba zato ta ji sun rirriƙe ta. Da sauri ta dube, sannan ta fara ƙoƙarin ƙwace kanta. A matuƙar hassale ta gantsara wa ɗaya daga cikin su cizo. Nan take ya saki wata iriyar azababbiyar ƙara. Buga tsalle Amrah ta yi tare da ƙwace kanta daga gare su. Faɗuwa gaba ɗaya jami'an suka yi. Ganin haka ya sa Amrah ta fara gudu yayin da ta fara aye wa kan manya-manyan bishiyun dake cikin dajin tsalle suka ga ta fara yi tamkar ƴar biri, tana aye wa kan bishiyu ɗaya bayan ɗaya. Da sauri jami'an suka bi bayan ta. Sannan suka fara sakin harbi. Ganin sun fara harbi ya sa Umar dube su yana mai cewa. "Don't shoot". Ko saurarensa basu yi ba aka suka ci gaba da harbin bishiyun domin su samu Amrah. ********************* *Magarƙama* "Gani nan naji ance wai kuna nema na". Zahra ta faɗa ba bu alamun tsoro a tattare da ita. Tsayawa ƴan sandan da warders suka yi suna kallonta. Ɗaya daga cikin su ne ya ce. "Zahra wai me ya sa ki ke da wannan jiji da kai ne?". Kallon wacce ta yi maganar Zahra ta yi sannan ta ce. "Ki tambayi wacce ta haife ni zata baki amsa". Da kallon mamaki suka fara binta da shi. Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya ce da ita. "Ta ya ya zata tambayi mamarki bayan bata raye?, koda yake dole ai a tambaye ta tun da uwa ƴar daba ita ma ɗiya ƴar daba. Wannan dai gadon hali ku ka yi". Danne fusho dake ƙoƙarin ta so mata Zahra ya yi sannan ta ce. "Ɗan sanda ka iya bakin ka, mahaifyata ba abar wasa bace, kada ka tunzurani na aikata abin da raina bai so ba". Sakin baki ɗan sandan ya yi yana kallonta. "Idan ban iya bakin nawa ba duka na za ki yi?. To ki sani cewa mahafiyar ki babbar sheɗaniya ce, ba bu wanda ya kaita sheɗanci kuma sannan ita ce sanadin mutuwan rayukan mutane a lokacin baya. Don haka ko kina so ko bakya so da kallon ƴar sheɗaniya zamu dinga kallon ki. Ni a duniyar nan akwai wacce ta kai Mrs Laila arha kuwa?, domin ko a gidan karuwai albarka". Nan take idanuwan Zahra suka kaɗa suka yi jajir. Take ta sak wata iriyar ƙara mai matuƙar razanarwa!. Shaƙe wuyar ɗan sandan ta yi da dukkanin ƙarfin ta. Tare da ɗaukar hannunta ta ƙwaɗa masa mari. Tare da fara naushin bakin sa da mugun ƙarfi. Ganin abin da ke faruwa ya sanya sauran jami'an suka ƙaraso wajan, yayin da suka fara ririƙe ta tare da ƙoƙarin ƙwace ɗan sandan daga hannun Zahra. Da sauri suma ƴan magarƙamar suka ƙarasa wajan. Hajiya Binta dake cutting grass ce ta hango taruwa mutane. Da sauri ta saki gatari da take cutting da shi tare da nufa wajan. Riƙe shi Zahra ta yi ƙamm a hannunta yayin da ta ci gaba da nausar bakin sa. Cikin huci ta dube shi sannan ta ce. "Mahaifiyata ce take da arha?, wato mahaifiyata ce ko a gidan karuwai albarka ko?, yau za ka gane kuranka. Ka sani cewa zagin mahaifiyata da kay shi ne kuskuren da baka taɓa aikatawa ba a rayuwarka domin saina yi maka dukan kawu wuka, saina yi maka dukan da ko ƙauyen ku ka koma da ƙyar yaran ka su gane cewa kai babansu ne". Tana kaiwa nan ta ci gaba da sambaɗansa saida ta yi masa sambaɗe baɗe, sannan ta ci ka shi. Isa wajan Hajiya Binta ta yi tare da janyo Zahra sannan ta kwashe ta da mari. Dafe ƙuncin ta Zahra ta yi, karo na farko a rayuwarta da hajiya Binta ta taɓa lafiya jikinta. A matuƙar fusa ce Hajiya Binta ta kalleta sannan ta ce. "Me yake damunki Zahra?, shin kinyi hauka ne?, ɗan sanda da ki ka daka kin san abin da akan zata haifar?, dole ne na ɗau mataki a kan ki in ba aka ba za ki jawo min abin kunya ne". Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya ce. "Ba saikin ɗau mataki ba, mu da kanmu zamu ɗauki mataki a kanta. Don haka tun da harta sake ta ɗora hannunta a kan ɗan sanda dole ta fuskanci mummunan hukunci. Jami'ai maza ku kama ta ku wuce da ita offishi sannan ku saka ta a cell yau saita gane cewar Allah ɗaya ne". Jin haka ya sa Hajiya Binta ta fara basu haƙuri. Ko kallonta basu yi ba haka suka kama Zahra tare da nufar inda motocin ƴan sanda suke. Ba tare da turjiya ba Zahra ta shiga cikin motan. Shige wa suma suka yi cikin motan yayin da suka cinciɓi ɗan sandan da Zahra ta yi wa duka sannan suka saka shi cikin mota. Fice wa suka yi daga cikin magarƙamar. A sa'in da motar da aka saka ɗan sandan da Zahra ta yi wa duka ta wuce asibiti. Yayin da kuma sauram motocin suka wuce police station. Suna isa chan suka fito daga cikin motocin yayin da suka kama Zahra sannan suka shigar da ita cikin police station tare da jefa ta cikin cell. ***************** Ɓangaren Amrah kuwa neman ta suka yi suka rasa a cikin jejin. Alama Umar ya yi musu da su koma cikin mota. Koma wa suka yi cikin mota gaba ɗaya yayin da suka tada mota tare da barin harabar dajin. Kai tsaye gida suka koma yayin da suka zayyane wa mahaifin Umar duk abubuwan da suka faru. ************************ *AMERICA* Cikin harshen turanci ya dubi abokin nasa ya ce. "John ya kamata ka manta da abin da ya faru, Diana bata yi akan da son ranta ba, ya kamata ka manta da komai". Cewar abokin nasa. Kallonsa John ya yi sannan ya ce. "A kan mene ne zai sa na rabi ita?, a gaban jama'a ta ɗauki hannu sannan ta kwashe ni da mari, ko zan yafe komai ba zan taɓa yafe wannan abin da ta yi min ba. Ya zama dole na ɗauki fansar abin da ta aikata, saina shayar da ita azabar da har abada ba zata manta da ni ba. Ya zama dole na aure ta domin ita ɗin tawa ce ta ni kaɗai, bayan na aure ta zan gana mata azaba, ba dai tana ji da kanta ba, ni nan zan sauke mata jiji da kanta". Yana kaiwa nan ya fice daga cikin ɗakin wanda ya gauraye da hayakin shisha. ****** Gaba ɗaya Aliyu ya rasa me kai masa dad'i. A duk sa'in da Safeera ta zo ta wuce ta gefen sa sai ya ga tamkar ya santa. Wayarsa ya ji tana ringing. Ɗaukar wayar ya yi ya ga numbern Nigeria ke kiran shi. sunan yallaɓai ne bayyane kan screen ɗin wayar. Ɗaga kiran ya yi tare da karawa a kunnensa. "Hello yallaɓai". Daga ɗayan ɓangaren ya ce. "Ya batun maganar da muka yi da kai Aliyu?, kace za ka je ka ga MK a magarƙama har yanzu baka dawo bane?". Cikin rashin fahimtar maganarsa Aliyu ya ce. "Ni kuma?, ni yaushe na ce zan je magarƙama?. Ni fa a halin yanzu ina America kwata-kwata bana ƙasar Nigeria, don aka ka bari idan na dawo Nigeria zamu yi magana". Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Sakin baki mutumin ya yi yana mai kallon wayar dake hannunsa. "Lallai Aliyu ka cika ɗan rainin wayo, za ka gane kuranka ne". ******* Fitowa Safeera ta yi cikin ƙananun kaya wanda suka karɓi jikin ta tare da fara takawa tana nufar parlour. Tsayawa Aliyu ya yi da danna waya tare da maida hankalinsa gaba ki ɗaya kan Safeera. Dogon tsaki Safeera ta ja ganin irin mayen kallon da Aliyu ke binta da shi. Guri ta samu tare da zama. Cikin ɓacin rai Aliyu ya kalle ta sannan ya ce. "ke baki iya gaisuwa bane?". Kallon shi Safeera ta yi tare da sakin miskilin murmushi sannan ta ce. "Ban iya ba saboda banga mutum a zaune ba". Mamaki ne ya kama Aliyu ya ce. "Kin san wane ne ni kuwa?, kada ki fusata ni nayi abin da raina bai so ba". Miƙe wa tsaye Safeera ta yi cike da ɓacin rai ta dube shi ta ce. "Me za ka yi?, kana nufin duka na za ka yi kome?". Shigowa Daddy ya yi dai-dai lokacin da Safeera ta faɗi kalman "Duka na za ka yi?". Kallon su biyun Daddy ya yi sannan ya ce. "Me yake faruwa ne?". ********* *NIGERIA*. Gaba ɗaya Umar ya rasa me ke masa daɗi. Tun da ya ga Amrah ya kasa zaune ya kasa tsaye. Zama ya yi kan faɗeɗen gadonsa sannan ya ce. "Who is she?, me ya sa take zaune a ciki wannan dajin?, shin bata da iyaye ne?, me ya sa take rayuwa cikin dabbobi?. Dole ita kaɗai ce zata iya bani amsar tambaya ta. Ya zama dole gobe na koma wannan dajin domin yin bincike. Samm ban yarda da wannan yarinyar ba". Ya faɗa yanaai ɗaukar wayarsa tare da shiga contact list sannan ya lalubo numbern ɗaya daga cikin jami'an sa. Ringing biyu aka ɗaga kiran. "Hello ranka shi daɗe". Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya ce. "Su waye a kan duty gobe?". Amsa jami'in ya bashi da cewa. "Mune, shin da wata matsala ne?". Jami'in ya tambaya. Amsa Umar ya bashi da cewa. "A'a ba bu wata matsala, dama ina so ne ka sanar da sauran jami'an da ke tare da kai cewa gobe zamu koma wannan dajin". "What!". Jami'in ya faɗa sannan ya ƙara da cewa. "Sir dajin nan yana da matuƙar hatsari, baka ga abin da ya faru bane ɗa zu?, mahaifinka ya sanar da ni cewa kada mu sake mu ƙara zuwa wannan dajin koda ka buƙaci muje, an sorry sir amma ba zan iya bujire wa umarnin mahaifinka ba". Yana kaiwa nan ya kashe wayar. A matuƙar fusa ce Umar ya wurgar da wayar ta faɗi ƙasa. Dafe kanshi ya yi jin yana mugun sara masa. "What is wrong with me?, me ya sa gaba ɗaya ina neman in fita daga cikin hayyaci na saboda wannan yarinyar ƴar daji, why am I worrying myself because of that forest girl?, what am I suppose to do now?, ya zama dole na koma wannan dajin domin fitar da ita daga cikin wannan jejin, because her life is in risk and i need to rescue her life, if not ba zan yafe wa kaina ba". ********** Washe gari da safe ƴan sanda suka nufi hanyar kotu da Zahra. Suna isa suka tarar da ƴan jarida cike a bakin kotu. Ganin motar su Zahra ta ƙaraso ya sa ƴan jarida suka nufi inda motar take da sauri yayin da suka saura cameras ɗin su da speaker. Fitowa Zahra ta yi ba bu wani alamun tsoro a tattare da ita. Da sauri ɗaya daga cikin ƴan jaridan ta saita Mic saitin bakin Zahra sannan ta ce. "Shin za ki iya faɗa mana dalilin me ya sa ki ka daki ɗan sanda?". Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Ku saita cameran ku da kyau ta yadda kowa zai ganni". Saura kamerorin ƴan jaridan suka yi da kyau. Gyara tsayuwar ta Zahra ta yi hannayenta sanye da handcuf sannan ta ce. "Na dake sa ne domin ya zagar min mahaifiya, kuma ni mahaifiyata tamkar zinariya ce a gare ni, bana wasa da ita. Duk wanda ya yi ƙoƙarin zagar min mahaifiya to saina koya masa hankali, gudun karya je ya aikata wa wani bayan ni ya saka nayi masa mugun duka. Ba mahaifiyata ba ko mahaifiyar wani na ga an zaga ba zan ƙyale mutum ba, domin iyaye ba abin wasa bane". Tana kaiwa nan ta shige cikin kotun. Nan take ƴan jarida suka fara sakawa a news ɗin su yayin da ko ina a garin ya ɗauka. Ba bu abin da ka ke ji da gani a gari sai maganar da Zahra ta yi. *********** Kunna tv Mom ta yi nan taje ta fara ganin news na yawo a tv. Rass! rass! gaban ta ya faɗi!. Wasu irin zufa ne suka fara ƙeto mata ta ko wane sashe na jikin ta. Ɗaukar medical glass ɗinta ta yi tare da sanya wa a idonta sannan ta maida kallonta kan tv. "Wannan kamar Safeera". Miƙe wa ta yi tare da ƙwalla wa duka ƴan gidan kira. Da sauri su Daddy da ke parlour suka nufi ɗakin Mom. "Shiga cikin ɗakin su Safeera suka yi. Yayin da Daddy ya tambaye ta ."meya faru?". Nuna tv Mom ta yi. Nan take idanuwan Safeera dasu Daddy ya sauka a kan tv. "Rasss gaban kowanensu ya faɗi! sakamakon ganin abin da basu yi tsammanin gani ba. @@@@@@@@@@@@ *AM SORRY FOR THE LATE UPDATE PLEASE 🥺 🥺* ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g 🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣7️⃣▶️1️⃣8️⃣ *_________________________________________________* Abin da ya firgita su ba komai bane illa ganin film na horror wanda ke bayyane kan tv ɗin. Kallon Mom Daddy ya yi sannan ya ce. "Ke kin san za ki dinga tsorata ki ke kallon film ɗin horror?, wallahi ki ka sake yi mana irin aka sai na ɓata miki rai". "Film ɗin horror kuma?". A cewar Mom. Maida kallonta ta yi kan tv ɗin. Da mamakin ta ta ga an chanza tashar da ta ga Zahra. Girgiza kai ta yi sannan ta ce. "A'a ba wannan tashar nake kallo ba, ina kallon news ne, kuma abin da ya tsoratar da ni ba komai bane fa ce ganin mai kama da Safeera da nayi. Babu banbanci tsakanin ita da Safeera. Sai dai wancan eyes ɗin ta ba blue bane brown ne". "What! gaba ɗaya suka furta. A sa'inda suka kalli juna tare da kwashe wa da dariya. Maida kallonta Safeera ta yi kan Mom sannan ta ce. "Ni kuma Mom?, how can that be possible?, ta ya ya kuma za'a ga mai kama da ni, hanya Mom kin goge medical glass ɗin ki kafin ki saka?". "What nonsense are you saying?, I am not blind I can see clearly without even my glasses, not wearing my glasses doesn't mean I can't see clearly, I know what am talking about, you guy's should believe me". Ajiyan zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce. "Ko za ki kai gobe kina faɗin abu ɗaya babu wanda zai yarda da ke. Bana son ki sake cewa kinga mai kama da Safeera na dai gaya miki". Yana kaiwa nan ya fice daga cikin ɗakin. Zuwa daff da ita Safeera ta yi sannan ta ce. "Mom please take a rest, yanzu lokacin shan maganin ki ya yi, ya kamata ki sha maganin ki kinji, yanzu zan je nayi karatu ne gobe muna da exam a makaranta and i have to prepare well to pass this exam. For now am leaving okay Mom have your rest". Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da fice wa daga ɗakin. Dafe kanta Mom ta yi a sa'inda ta fara magana ita kaɗai. "Ko dai da gaske gizau idona yake min ba mai kama da Safeera bace?, amma kuma fa na ganta sosai fa sanye da kayan magarƙama, tabbas babu tantama akwai mai kama da Safeera kuma saina tabbatar musu da hakan". Tsayawa Aliyu ya yi yana mai nazarin kalamanta. Ƙarasawa in da take ya yi tare da ɗurƙusawa kan gwiwowinsa sannan ya dube ta ya ce. "Da gaske ne kinga mai kama da Safeera Mom?". Kallonsa Mom ta yi sannan ta ce. "Au kenen kaima baka yarda da cewar na ga mai kama da Safeera ba a tv?". Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Me zai ana?, na yarda mana ɗari bisa ɗari, amma kuma ba kowa ne zai yarda da hakan ba. Domin nima kaina har yanzu ina tantamar cewa ba mai kama da Safeera ki ka gani ba. Amma shi ke nen babu komai na san abin da zan yi, domin sanin gaskiya dangane da abin da ki ka faɗa. Zan ɗauki photon Safeera sannan na tura wa jami'an da ke Nigeria muddin akwai mai kama da ita da gaske za su binciko ta. Don aka ki shafa wa zuciyarki ruwan sanyi". Sai a lokacin Mom ta ji wani nutsuwa ya ziyarce ta. Kallon Aliyu ta yi sannan ta ce. "Na gode sosai Aliyu, tabbas babu wanda ya da ce ya auri Safeera sama da kai. Don aka zan faɗa wa Daddyn Safeera cewa mu koma Nigeria da zama, daga nan sai ayi auran ka da Safeera a chan". Murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen, duda cewar ban iya tuna mai ya kawo ni nan ba amma gaskiya yarinyar ku ta burge ni sosai kuma ahalina za su yi farin cikin samu sirika irin Safeera". *NIGERIA🇳🇬* Government House. Kunsan mutane goma na hango kan kujera a cikin parlourn wanda ke ƙunshe da kayan al'atu da kayan more rayuwa. Zaune mahafin Umar wato Gov. Musa Muhammad yake kan kujerar three seater wanda aka yi amfani da royal furnitures wajan ƙera wa. Kallon engineers da architectures ɗin da ke zaune ya yi sannan ya ce. "Me da me ake buƙata domin fara wannan aikin na company da za'a gina?, ka lissafo duk abin da ya kamata za'a yi". Ɗaya daga cikin engineers ɗin ne ya dube shi ya ce. "Farko dai za'a bawa surveyors engineers domin duba kwalitin ƙasa ko fili ta yadda za'a san ginin zai zauna ko A'a, sannan za'a ɗebo ƙasar wajan a je a duba a laboratory domin sanin ginin zai zauna ko A'a". "Bayan aka zamu fara auna tsare-tsaren gefen ta gine-gine ta ƙasa ko ta fili. Sannan architecture ya riga ya yi zanen yadda ginin company zai kasance. Yanzu dai zamu ɗebo laburori su fara tonan tushen ginin, sannan a zo s fara tsarin ƙirar injiniya da tsarin lantarki. Sai ƙirƙirar sandar ƙarfe da ginshiƙai. Bayan nan sai mu zo muyi order na yashi mai kaifi, yashi mai laushi, yashin tsaƙuwa da siminti. Sannan ayi amfani da kankare ko rodi a cikin tushe. Bayan order wannan sai a zo a fitar da kewaye bango na gine-gine da rushewar sassan. bayan aka idan ya kai matakin doc za'a jefa dukkanin gishinƙai tare da kankare". "Bayan nan zamu koma baya mu cika da latarite. Don za'a yi compactor don ƙaddamar da latarite. Bayan shi dpm ne ledder sa'an nan mu shirya hardcore saboda ya kwanta da wayar raga. Na ƙarshe kuma shi ne jefa gadon kankaren 6inch (dpc). Bayan hakan shi ke nen". Ajiyan zuciya Gov. Musa Muhammad ya sauke!, sannan ya dube su ya ce. "Wannan bayanin sai ku engineers don ban fahimta ba sosai. Yanzu dai duka kuɗin da kuka yi calculating zaku faɗa min zan saka a ciki cashbook ɗina ko kuma ku faɗa nayi muku transfer, saboda ina so ne a fara aikin yau. Sannan kuma bana son Umar ya san da wannan batun. Wannan maganar ta tsaya a iya tsakanin mu kawai. Muddin na ji labarin cewa Umar ya san da za'a je dajin nan domin fara aiki saina ɓata muku rai, saboda gaba ɗaya mun san da cewa ba zai taɓa bari a je wannan dajin domin fara wannan aikin na company ba. Don aka You guy's should keep this as secret. Apart from you guy's I don't want you here that somebody heard our conversation". Amsa wa gaba ɗaya suka yi da cewa. "Yes Sir. In sha Allahu wannan maganar ba zai fita ba. Bakin mu ƙanin ƙarfar mu. Yanzu dai ka sako mana jami'ai mu tafi tare domin koran waɗan nan namun jejin, ko a ɗebe su gaba ɗaya a wuce da su gidan zoo ko kuma idan ka bamu dama mu saka su kashe kowacce dabba ta cikin jejin kawai". "Shi ke ne, kuyi dai abin da ku ka ga zai da ce. Kuje ku fara aune-aunen yau, idan ya so gobe zan saka a kawo yashi da blocks sannan zan tura laburori wajan ko kuma nayi muku transfer ɗin kuɗin komai da komai idan ya so sai kuyi aikin. Yanzu dai idan kun tafi ɗaya daga cikin ku ya yi calculating kuɗin everything da ake buƙata na aikin wannan company, in ya so saina yi muku transfer. Yau dai zan sama jami'ai su kori namun jejin gaba ɗaya. Idan ya so gobe kawai sai ku fara aikin". Cewar Gov.Musa Muhammad. Miƙe wa gaba ɗaya engineers ɗin suka yi tare da yiwa Gov. Musa Muhammad godiya daga bisani suka fice daga cikin parlourn. ************************** Ɓangaren Zahra kuwa tana shiga cikin kotun ta tarar da ƴan sanda tare da alkali a zazzau ne. Chan ta hango dan sandan da ya yi wa sambaɗe-baɗe daga nesa. Taɓe baki ta yi tare da bin kotun da kallo sannan ta ce. "Su ashe na harda shi a zuwa kotun, da an barni da kai da jikin ka ya faɗa maka". Maida kallonta ta yi cikin kotun ta ce. Dama aka kotun take?, ji fuskar alƙalin ma kamar tsohon biri, fuska tamkar kashi". Tsayawa ta yi in da masu laifi ke tsaya wa. Tashi lawyer da ke kare ɗan sandan ya yi sannan ya ce. "Ina miƙo gaisuwata ga alƙali tare da mutanen da ke cikin kotun baki ɗaya. Muna nan ne gaba ɗaya domin maganar case na wannan budurwar da ta ɗauki hannu ta daki ɗan sanda wanda hakan a dokance bai kamata ba. A cewar sashe na 356 na dokar aikata laifuka, kai hari ga ɗan sanda babban laifi ne, kuma duk abubuwan da za'a bayyana domin kare ta zai ci-gaba da zama babban laifi ne. Don aka ina neman wannan kotu mai alfarma ta dubi halin da dan sandan nan ya shiga, ta hukunta wannan budurwar ta hanyar hukunta ta dai-dai da laifin da ta aikata". Yana kaiwa nan lawyer ya zauna. Maida kallonsa alƙalin kotun ya yi kan Zahra sannan ya ce. "A kan wane dalili ne ki ka ɗaga hannu ki ka daki ɗan sanda?". Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Na dake shi ne domin ya zagar min mahaifiya, abin da kuma bana taɓa bari kenen". Kallonta alƙalin ya yi sannan ya ce. "saboda ya zagar miki mahafiya shi ya sa za ki yi masa irin wannan dukan?". Murmushi Zahra ta yi tana mai kallon ɗan sandan wanda ya cunkushe guri ɗaya yayin da fuskar sa ke zagaye da bandage. Maida kallonta ta yi kan alƙalin sannan ta ce. "Ƙwarai da gaske da a ce ma ba su zo sun kawo masa agaji ba a dai-dai wannan lokacin da saina yi masa dukan da har ya mutu sai ya dinga tuna wa dani". "Wannan kuskure ne ki ka aikata, dukan ɗan sanda yayin da yake sanye cikin kayansa na ƴan sanda kuskure ne, ɗan sanda yana da damar dukan koma waye muddin ya yi masa laifi amma ke baki da damar yin akan, don aka abin da ki ka aikata kuskure ne". Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta saki sannan ta ce. "Kuskure?, kenen kuskure ne don na tsaya domin kada a ci zarafin mahafiyata?, kuskure ne dukan ɗan sandan da bai san daraja da kima uwa ba?, kuskure ne dukan ɗan sandan da bai san aikin shi ba?. Wai shin tukun nan ma ka san wace ce uwa kuwa?, uwa ita ce ɗaukar ciki wata tara, shayar da yaro, ita ce malamar mu ta fark a duniya, sannan cinyarta shi ne wajan ɓatawan mu idan muka yi fitsri ko kashi. Ta raine mu, ta tarbiyartar damu, ta bamu kulawa wanda babu wanda zai iya mana. To a kan me zai sa ba zamu daraja ta ba?, idan abin da na aikata wa wannan ɗan sandan kuskure ne to shi ma abin da ya aikata kuskure ne. Don aka ni da shi masu laifi ne gaba ɗaya dole a hukunta mu ni da shi". "Don ya kasance ɗan sanda akan bai bashi damar ya ci zarafin mace ba, ba uwa ta kaɗai ba, koda wata uwar ya sake zaga to saina tabbatar da na fasa masa baki". Buɗe littafi Alƙali ya yi tare da yin rubuce rubucen sa a ciki. Ɗago da kansa alƙalin ya yi sannan ya ce. "Duba da yanayin abin da ki ka aikata sannan duba da kotu ta yi na cewa ke mace ce. Kotu za ta sassauta miki hukunci. Hukunci da wannan kotun ta yanke ita ce. Za'a kai wannan budurwar izuwa gidan gyaran hali da ke garin Kano zata zauna a chan na kimanin tsawon shekara guda tare da aiki babu sassauta. Wannan shi ne". Zaro idanuwa waje Zahra ta yi sannan ta ce. "Shi kuma ɗan sandan fa?, ba za'a masa hukuncin ba kenan?". Kamata jami'ai mata suka yi tare da fitar da ita daga cikin kotun sannan suka sanya ta a cikin motan ƴan sanda tare da rufe motan. Shiga cikin motan DPO ya yi tare da kare wa Zahra kallo sannan ya ja dogon tsaki. Tayar da mota jami'ai suka yi tare da barin harabar kotun. Yayin da ƴan jarida da mutanen wajan suka bi motocin ƴan sandan da kallo. Kai tsaye hanyar garin Kano suka nufa. ************************** *Ɓangaren Daji kuwa*. Bayan da jami'an Gov. Musa Muhammad sun shiga cikin jejin suka fara harbe duk wani dabban da suka yi kicibus da shi. Suna saka wa a cikin mota. Sosai suka fara kashe dabbobin cikin jejin yayin da babu abin da ke tashi a ciki daji sai ƙarar bindig. A sa'inda ɓangare guda dabbobin suka fara yi ta kansu. Amrah da ke kwance kusa da dutsen da sunanta ke rubuce ta jiyo ƙaran bindiga da sauri ta miƙe tsaye, sannan ta fara gudu tana nufar in da suke jiyo ƙarar bindigu. Zuwanta keda wuya ta ga an kashe gaba ki ɗaya namun jejin da ke cikin wannan dajin. Chakk ta tsaya yayin da hawaye suka fara zarya kan ƙuncin ta. Wani irin razananniyar ƙara ta saki! tare da buga tsalle ɗaya ta dira kan ɗaya daga cikin jami'an. Nan take ta fara kokawa da su . Yayin da ta sa hannayenta wanda ke ɗauke da zara-zaran farcina ta fara yagar su da shi. Aka ta cigaba da yagar fatar jikin su babu gaggauta. Kururuwa ta yi tare da yin yin tsalle ta aye kan bishiya. Nan take ta janyo sandan dake jikin bishiyar mangwaron dake tsakiyar wajan. Ɗaukar sandan ta yi wanda da matuƙar girma sannan ta dira ƙasa. A zafafe ta fara buga musu wannan sandan ɗaya bayan ɗaya tare da dukan su da shi. Nan take wasu daga cikin jami'an suka ja da baya ganin cewar tabbas idan suka ci gaba da tsayuwa zata hallakar da su. Ɗaukar bindiga ɗaya daga cikin jami'an ya yi tare da saita saitin kafarta sannan ya harbe ta. Nan take ta faɗi ƙasa tare da sakin wata iriyar azababbiyar ƙara!. ************************* "Hhhhhhh!, suka ji Zahra ta kurma wata iriyar ƙara mai matuƙar firgitarwa a cikin motan. Jikinta ne ya soma kakkarwa yayin da haƙoranta na sama ya fara dukan na ƙasa. Nan take zazzaɓi ya rufe ta yayin da jikinta ya soma rawan ɗari. Nan take ta faɗi a cikin motan sumammiya. Mamaki ne ya kama jami'ai da DPO da ke cikin motan ganin lokaci ɗaya ta kurma ihuu tamkar mai aljanu. ******* Ɓangaren Safeera kuwa suna zaune a parlour suka ga ta faɗi tare da sakin azababbiyar ƙara!. Zumbur gaba ɗaya suka miƙe tare da nufar kanta da sauri. Nan take suka ga ta dafa kanta yayin da zazzaɓi ya rufe ta shure-shure ta fara yi hannunta dafe da cikin ta. Nan take suka ga ta daina yin shure-shuren. Zuwa kusa da ita Aliyu ya yi tare da saka hannunsa saitin hancin ta. Ganin bata numfashi ya da shi saurin ɗago da kansa sannan ya ce. "Safeera fa ta suma". "Suma kuma?". Cewar Mom. Sannan ta ƙara da cewa. "Wai me yake faruwa ne?". *TOH FAN'S 💃💃NI MA DAI ZANCE ME YAKE FARUWA NE🤔?, DAGA HARBIN AMRAH GABA ƊAYA SAURAN BIYUN SUN FITA A HAYYACIN SU, KODAI AKWAI ABIN DA KE FARUWA NE🤔?, MUJE DAI ZUWA*. *KUYI MANAGE NA PAGE ƊIN NAN BANI DA CHARGE NE SANNAN KUMA BANA JIN DAƊI SOSAI. NA SO NAYI MUKU FIYE DA AKA AMMA KUYI MANAGE* LIKE, SHARE, AND COMMENTS PLEASE 🙏🙏🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) 🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣ *_________________________________________________* Mom ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta yayin da ta riƙe Safeera ƙamm jikinta. "Wallahi Allah masani, hanya yarinyar nan ba ta da aljanu kuwa?". Aliyu ya faɗa. Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Gaskiya bana tunanin tana da aljanu saboda a wannan ƙasar babu aljanu balle maye, kuma ba ta taɓa zuwa Nigeria ba balle na ce a chan ta ɗebo aljanu". Kallon baka da hankali Aliyu ya bishi da shi sannan ya ce. "Okay wato a iya Nigeria ne kaɗai ake samun aljanu ko?, gaskiya Daddy ya kamata ka koma islamiyya ko ka dinga shiga YouTube ko chrome kana koyan abubuwan da ya daganci addinin musulunci, don naga kamar har yanzu da sauran ka". Kallonsa Daddy ya yi sannan ya ce. "Na je islamiyya mana kuma har ma nayi sauka sai dai ba'a ƙasar Nigeria na ta so ba a wannan ƙasar America na ta so". Kallonsu gaba ɗaya Mom ta yi ta ce. "Yanzu ba irin wannan magana ya kamata kuyi ba yanzu, ya kamata a ce ku san abin yi domin ta farfaɗo, tun ɗazu nake jijjigata har yanzu ba ta numfashi. Dan Allah ku taimaka bana son na rasa ƴata ɗaya tilo". Kallonta Aliyu ya yi cikin tausayawa ya ce. "Na fahimci yadda ki ke ji Mom, yanzu mafita ɗaya muke da shi, dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin gargajiya. Idan muka ce zamu yi a nan sanadin hakan ƴan sanda za su iya kama mu, domin za su ɗauka cutar da ita zamu yi hakan na iya sawa su kai mu magarƙama ma. Yanzu mafita ɗaya ce shi ne muje Nigeria domin wannan maganin gargajiya ne kawai zai yi aiki. Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "maganin gargajiya kuma?, gaskiya ba za'a bawa ƴata irin wannan ƙazaman maganin ba, saboda ni duk ban yarda da ire-iren waɗan nan magungunan ba". Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Ko ka yarda ko karka yarda dole ne muje Nigeria domin yi mata maganin, in ba aka ba za ku rasa ta". Jin an ambato batun za'a rasa ta, ya sanya Mom ta miƙe zumbur tare da nufa part ɗin ta. Saida ta ɗau lokaci kafin ta fito daga cikin ɗakin ta. Fitowa ta yi sanye da hijabi yayin da hijabi ɗaya na hannunta. Ƙarasowa wajan ta yi tare da ɗurƙusawa ta sanya wa Safeera hijabin a jikin ta". Miƙe wa ta yi tsaye sannan ta ce. "Yanzu me ya rage, maza ku shirya mu tafi". Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Ai kuma bamu haɗa kayayyakin da zamu tafi Nigeria da su ba". Kallonsa Daddy ya yi ya ce. "Kada ka damu da wannan zan saka ƴan aiki na su aiko mana su". "Amma ka san da cewa bamu da visa, kuma kuɗaɗe basua aiki a wannan ƙasar domin idan ka ce za ka basu kuɗi za su kama mutum ne, sannan kuma ta ya ya zamu je filin jirgi da ita a haka?, domin fa kwata-kwata ba ta numfashi, ba kayi tunanin cewa ƴan sanda za su yi zargin cewa ko sace ta muka yi. Yanzu dai dole ne muna iya ba da shaida takardun aure, takaddun Haihuwar Ma'aurata da masu dogara, hotunan da ke nuna kyakkyawar alaƙa da dangi da abokai". Cewar Aliyu. Kallon Daddy Mom ta yi sannan ta ce. "Yanzu mene ne abin yi?". Ta tambayi Daddy. Amsa Daddy ya ba ta da cewa. "Ina da aboki ɗan sanda a chan airport sannan kuma ina da wani ma wanda na san idan na roƙe shi zai bamu visa tun da gaba ɗaya muna da password. Yanzu kawai abin da zamu yi muje chan ɗin, na san da cewa idan suka ganta za su gane ta domin sun san ta sosai ko a cikin office ɗina suna zuwa su ga photon ta a ajiye kan table, so za su gane cewar ƴata ce". "Tom shi ke nen, yanzu waye zai ɗauke ta?". Mom ta tambaya. Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Kada ki damu, ni zan ɗauke ta". Yana kaiwa nan ya shiga cikin room ɗin sa. Saida ya ɗau kusan rabin hour bai fito ba, sannan daga bisani ya fito cikin ƙananun kaya wanda suka yi matuƙar karɓar jikin sa. Nufar in da suke ya yi sannan ya sa hannu tare da ɗaukar Safeera sannan ya yi hanyar waje da ita. Ganin hakan ya sa su Daddy suka mara masa baya bayan sun ɗauki muƙulli. Kai tsaye in da motocin gidan suke Aliyu ya nufa. Danna muƙullin motan Daddy ya yi. Nan take motar ta buɗe da kanta. Ganin hakan ya sa Aliyu saka Safeera cikin motan yayin da gaba ɗaya su Daddy suma suka shiga cikin motar. Tada motar Aliyu ya yi. Yayin da gate man ya buɗe musi ƙofa daga bisani suka fice daga cikin gidan baki ɗaya. Basu nufi ko ina ba sai hanyar airport. ************************ *Nigeria* "Mene ne ka aikata haka officer?, me ya sa za ka harbi yarinyar nan bayan da cewa Gov. Musa Muhammad ya ce baya son ɗansa ya san da cewa munzo mun kori dabbobin da ke cikin daji nan". Officer da haka faɗa wa hakan ya ce. "To baka ga yadda take tsalle kan bishiyoyi ba kamar biri, na san ba zamu iya kamata ba idan muka ce zamu kamata za ta illatar da mu ne. Bani da wani zaɓin ne shi ya sa na harbe ta a ƙafa". "Wannan laifin ka ne, yanzu idan Sir Umar ya sani na san tamu ta ƙare". Wayarsa ya ji tana ringing. Ɗauko wayar ya yi daga cikin aljihun sa sannan ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnen sa ya ce. "Hello". Daga ɗayan ɓangaren haka ce. "Maza-maza ka ce da sauran jami'an wajan nan su bar wajan, domin kuwa Sir Umar ya nufo hanyar wajan yanzu". Zari ido jami'in ya yi tare da katse wayar sannan ya kalli sauran jami'an ya ce. "An kira yanzu an ce mu bar nan domin sir Umar yana tawo wa nan". Da sauri suka matsar da Amrah wanda ke yashe kafarta sai fidda jini yake gefe. Sannan cikin ƙware wa suka fara shiga cikin motocin. Tare da tada mota suka bar harabar wajan. Bai ɗauki Umar lokaci ba ya ƙaraso wajan. Guri ya samu a cikin dajin sannan ya yi parking. Fitowa ya yi ciki cikin izza. Sannan ya rufe ƙofar motan. Dafe zuciyarsa ya yi ciki ranshi ya ce. "ban san dalilin da ya sa zuciyata take ta buga wa da ƙarfi-ƙarfi ba, amma yanzu tun da na zo , na san hankali na zai kwanta". Ya faɗa tare da fara tafiya. Sai da ya yi tafiya mai nisan gaske kafin ya isa wajan kogin dake cikin dajin. Tsayawa ya yi jin yadda dajin ya ɗauki shiru. Mamaki ne ya kama shi jin babu ko da kururwan wani dabba a cikin dajin sai dai tsuntsaye wanda suke ta kai kawo a sama. Ƙatasawa in da kogin yake ya yi. Take idanuwansa ya sauka a kan dutsen da ke kusa da kogin. Daff da dutsen ya je ganin kamar abi rubuce a jiki. Durƙusawa ya yi tare da shafa sunan dake jikin dutsen ya yi. Murmushi ya yi sannan ya ce. "Kenen sunanta Amrah, nice name". Miƙe wa ya yi tsaye sannan ya bar wajan. Tafiya ya soma yi yayin da ya fara arangama da dabbobin da ke yashe a ƙasa. Mamaki ne ya kama shi ganin dabbobin da ke daji yashe a ƙasa cikin jini. Daga nesa ya hangi Amrah dake kwance kusa da jikin bishiya. Zaro idanuwa ya yi waje yayin da ya tafi da gudu tare isa in da take. Yana zuwa ya durƙusawa tare da aza kanta a kan cinyarsa. Tattaɓa fuskar ta ya soma yi. "Amrah me ya sa me ki?, wane ne ya yi miki haka?". Ɗaukar ta ya yi chakk tare da nufar in da motar shi yake da ita. Saka ta ya yi cikin mota sannan shima ya shiga tare da tuƙa motan sannan ya bar harabar wajan. Kai tsaye asibiti ya nufa da Amrah. **************** Ɓangaren su Zahra kuwa suna isa Kano basu nufi ko ina ba sai asibiti suka nufa. Nan take nurse's suka saka ta a gadon marasa lafiya tare da shigar da ita cikin ɗaki. Nan take suka fara mata aiki ta yadda numfashinta zai dawo. Saka mata oxygen suka yi tare da bata allura. Cikin ƙanƙanin lokaci numfashinta ya dawo. Allurar bacci suka bata tasha ta yi bacci. Fita likitocin suka yi suka bar Zahra kaɗai a ɗakin. Miƙe wa DPO ya yi sannan ya dubi ɗaya daga cikin likitocin ya ce. "Me yake faruwa ne?, ya jikin nata?". Amsa likitan ya ba shi da cewa. "Lafiya ƙalau munyi nasaran cetan ta domin kuwa yanzu harta samu bacci. Hamdala DPO ya yi sannan ya ce. "Yanzu zamu iya shiga mu ganta?". "Eh za ku iya, amma dan Allah banda hayaniya". Yana kaiwa nan ya bar wajan. Shiga ciki gaba ki ɗaya suka yi, yayin da suka tarar ba ta kan gadon. Zaro ido gaba ɗaya suka yi ganin ba ta kan gadon. Kallon jami'an DPO ya yi ya ce. "Me ya sa muka yi sakaci har ta fece daga nan". Daga sana suka ji muryarta na cewa. "Yallaɓai DPO gani fa a ta nan". Zahra ta faɗa tana mai sakin murmushi. Kallon ko ina suka yi basu ganta ba. Nan take suka maida kansu kan gado. Kallonta DPO ya yi ya ce. "Ta ya ya kuma ki ka dawo kan gado bayan bakya nan?". Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ta ya kuma, kune dai baku duba ba da kyau amma ni dai ina nan banje ko ina ba". Ajiyan zuciya DPO ya sauke sannan ya ce. "Shi ke nen ta so mu ta fi tun da kin samu lafiya". Murguɗa baki Zahra ta yi sannan ta ce. "Ku fita to zan yi wani abu". Duk abin da za ki yi kiyi babu in da zamu je, wato so ki ke ki gudu ko?". Haɗe rai Zahra ta yi ta ce. "Idan na gudu ina zanje?, wa na sani a wannan garin?, zan yi turoso ne shi ya sa". "Shashasha kawai". DPO ya faɗa tare da fita daga cikin ɗakin. Fice wa sauran ƴan sandan suma suka yi daga cikin ɗakin. Tsaki Zahra ta ja ta ce. "tsohon banza kawai, idan an girma a san an girma. Ya tsaya yana biye wa sa'anin ƴaƴan sa. Guduwa ce kuma ya zama dole, domin tabbas saina gudu, haka kurun za'a kaini wani gidan gyaran hali sai ka ce wacce take rashin ɗa'a". Ta faɗa tana mai waige-waige. Nan take wani dabara ya faɗo mata. Tashi ta yi tsaye tare da nufar ƙofar window sannan ta buɗe tare da fita ta wajan. "Yess". Ta faɗa cike da farin ciki". Sauri-sauri take domin ta fice daga cikin asibitin. Babu zato ta ji an rungumeta ta baya. Zaro ido waje ta yi tare da juyawa. Nan take gabanta ya yi mummunar faɗuwa?, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku. Take ta tsinci kanta cikin baƙon yanayi. Sakinta matar wacce ta yi burzuzu da gashin kanta tamkar mahaukaciya ta yi. Kallonta matar ta yi ta ce. "Ki fitar da ni daga nan ni ba mahaukaciya ba ce kinji, ina so na koma ga ahali na, ina son na ga yarana". Nan take jikin Zahra ya yi sanyi dubar matar ta yi ta ce. "Kiyi haƙuri ki koma, magani suke miki fa". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin barin wajan. Da sauri likitoci suka ƙaraso wajan suna mai rirriƙe matar. Kallon Zahra suka yi sannan suka ce kiyi tafiyar ki yarinya, ita ɗin mara lafiya ce, kada ki damu da duk abin da za ta faɗa miki". Girgiza kai Zahra ta yi tare da fice wa daga cikin asibitin. Ta rasa me ya sa tun da ta ga wannan matar hankalinta ya kasa kwanciya. Zama ta yi a bakin titi tana mai hasko matar a cikin idanuwanta. "To wannan matar wace ce?". Ta tambayi kanta. Basar wa ta yi sannan ta ce. "To koma wace ce ina ruwanki zahra, kiyi abin da zai finshe ki kawai". Dafe cikinta ta yi jin yadda yake murɗawa saboda yunwa. Daga nesa ta hangi shopping mall. Da sauri ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Dole na je na ci wani abun don ba zan zauna da yunwa ba". Ta faɗa tare da nufar wajan. Nan take ta ga fadawa da securities na fito wa daga cikin wajan. Yayin da ta ga mutanen wajan gaba ɗaya sun ɗuƙa ƙasa. Shiga cikin wajan ta yi yayin da ta ga kowa gwiwar sa a ƙasa. Sakin baki ta yi tana kallonsu. "To me ya mi waɗan nan mutanen kuma na ga kowa a durƙushe. Koda yake wannan ba damuwar ki ba ce ba". Ta faɗa tana mai ƙara shige wa cikin wajan. Chan ta hangi ma'aikacin wajan a durƙushe a ƙasa. Ƙarasawa ta yi wajan sannan ta ce. "Ina son a bani snacks ko lemo duk abin da ku ke da shi wanda zai ƙosar da ni". Alamu mutumin ya yi mata da ta yi shiru. Hangame baki Zahra ta yi ta ce. "Bangane ba, na ce ka zo ka saida min da abu ka ce nay shiru, saboda me?, ko kyauta ku ke bayar da kayan naku ne?". Ta faɗa cikin ɗaga murya. Daga sama ta ji an ce. "Wane ne yake mana wannan tsawan?". Nan take mutanen wajan suka sha jinin jikin su. Juyawa ta yi da zimmar zuwa ta ɗauki abin da ranta yake so. Nan take idanuwanta ya sauka kan wani handsome mature guy mai jini a jiƙa. Kallonta ya yi da idanuwansa masu matuƙar rikitarwa sannan ya ce. "Me ya sa ke baki tsungunna ba bayan kowa dake cikin nan ya durƙusa min, kin san wane ne ni?". Sakin baki Zahra ta yi tana mai bin shi da kallon rainin wayo. Kallon sama da ƙasa ta yi mishi sannan ta ce. "First of all matsa min daga hanya". Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace. Ƙara tunkaro in da take ya yi sannan ya ce. "Idan na ƙi fa?, kin san waye ni? , ni ɗin yarima ne understood?". Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce"au haba da gaske?, amma sam baka yi zubin ƴan sarauta ba, ka san da irin su wa ka ke kama a jigawa?, kana kama ne da ƴan daƙo, domin kuwa wannan kayan da ke sanye a jikin ka su ƴan daƙon jigawa suke sawa". Ta faɗa tana mai kuma fashe wa da dariya a karo na biyu. A fusa ce. "Yariman ya ce. "Za ki san ni ki ka gaya wa wannan maganar". Nan take yanayin Zahra suka sauya izuwa ɓacin rai sannan ta dube su baki ɗaya ta ce. "Idan kun isa ku tunkaro in da nake". ************************** Umar na isa asibiti, likitoci suka saka Amrah kan gado yayin da suka shiga yi mata aiki domin cire bullet ɗin da ke ƙafarta. Fita ya yi tare da koma wa cikin mota sannan ya nufi hanyar gida. Da mugun gudu yake tuƙa motan yayin da yake ji kamar ya tashi sama domin zuwa in da mahaifinsa yake. Mintuna ƙalilan ya yi masa a gida. Ko gama parking bai yi ba ya fito daga cikin motan tare da nufar hanyar gida. Ƙafar sa na dama ya sa tare da ɓalla ƙofar parlourn. Nan take mahaifinsa tare da jami'an dake cikin wajan suka miƙe tsaye. Kallonsu gaba ɗaya Umar ya yi sannan ya ce. "Me ya sa ku ka je ku ka kashe kowane halitta a cikin wannan dajin?, ba na ce bana buƙatar wajan nan ba?, to me ya sa za ku kuma koma wa wajan?, why Abba?". Ajiyan zuciya Gov. Musa Muhammad ya sauke sannan ya ce. "Nayi hakan ne saboda farin cikin ka son". Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Farin ciki na?, kayi hakan ne saboda farin cikin ɗanka, baka ji kunyar abin da ya fito daga bakin ka ba, ka tsayar da fari cikin wasu domin samar min da gurɓatacciyar fari ciki mara ɗore wa, kuma a hakan ka ke kiran kanka ɗan siyasa?, shin dama haka shugabanni suke wa waɗan da basu ji ba basu gani ba?". "To gaba ɗaya ku saurare ni kuji, muddin wannan yarinyar ta mutu ba zan ƙyale kowane mutum daga cikin ku ba hatta kai Abba, kuma sannan wannan farin cikin da ka ke faɗa to za ka rasa shi na har abada ne, domin kuwa ba za ka sake sanya idanuwanka a kaina ba". "A'a Umar, kada ka yi haka, in sha Allahu babu abin da zai same ta kaji, kada ka nesanta kanka da ni Please". Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Umar ya yi sannan ya ce. "Saboda gudun abin da zai bata min rai hakan ya sa na koma london da zama, kuma duk saboda kai, me ya sa ka ke ƙoƙarin cusa min tsanar ka a cikin zuciyata Abba?. To zan faɗa zan ƙara maimaita wa muddin yarinyar chan ta mutu saikun gane kuranku baki ɗaya. Kuma sannan shi companin ma bana da buƙata, domin bana son koda naira goma daga cikin dukiyar ka, bana so". Yana kaiwa nan ya fice daga cikin ɗakin. Kallon jami'an Gov. Musa Muhammad ya yi sannan ya ce. "Shashashan banza ku sani cewa muddin ɗana ya yi nesa da ni saina ga bayan ku, maza ku ɓace min daga gani". Fita jami'an gaba ɗaya suka yi. Wayarsa ya ji tana ringing. Ɗaukar wayar ya yi yayin da ya ga private number bayyane kan screen ɗin. Ɗaga kiran ya yi tare da karawa a kunnensa. Daga ɗayan ɓangare haka ce. "Barkan ka dai govnor Musa Muhammad. Na san za ka yi mamaki to ni ne, ban mutu ba ina raye. Na kira ka ne domin sanar maka da bad news a gare ka, mrs Laila wacce kayi sanadin rugujewar rayuwarta har izuwa yanzu tana raye". Zumbur gov. Musa Muhammad ya miƙe tsaye. Yayin da zufa ya fara ƙeto masa ta kowane sashi na jikinsa. Duda iskan AC da ke kaɗawa a cikin parlourn hakan bai hana shi yin zufa ba. Cikin rawar jiki Gov. Musa Muhammad ya ce. "Waye kai?". Amsa mutumin ya ba shi da cewa. "Ni ne ɗan sanda wanda ku ka saka haka rufe tsawon shekaru, ni ne MK wato Mubarak. Ka ɗauka ban san duk wani shirin ka ba?, na san da cewa ka aiki ɗaya daga cikin masu ta ya ka aikata miyagun laifuka domin ya yi magana da ni a cikin magarƙama domin neman in da yarinyar Mrs Laila take. Amma sai dai kafin ya zo waje na wata ta dakatar da shi. Ka san wace ce?, to ƴar Mrs Laila ce". Jiki na rawa Gov. Musa Muhammad ya ce. "Tana ina?, ina da buƙatar thumbprint ɗin ta domin buɗe wannan ma'ajiyarta, ka gaya min in da ƴar tata take". Murmushi MK ya yi sannan ya ce. "Idan na gaya maka, saka wa za ka yi a kamata?, daga nan kuma fa?, ka saka yaranka su kashe ta?, ko da yake safara mata ita ce aikin ka ko?. To ka sani cewa ƙarshen ka ya kusan zuwa, domin kuwa ba yarinya ɗaya Laila Abdullahi ta haifa ba, su uku ne, blue, green and brown, ƴan uku daga gurare da ban- da ban . Su ne za su yi nasarar kawo ƙarshen ka sannan su wanke mahaifiyarsu daga zargin da kotu da jama'ar gari keyi mata. Sannan kuma su ja ka a kan titi, kamar yadda ka sanya ta gudu a kan titi, haka suma yaranta za su saka ka kayi gudu a titi yayin da jama'a za su yi ta jifar ka da duwatsuna, kana ihuuu kana neman taimako, amma babu wanda zai zo domin ya agaza maka. Ka jira ka gani, domin kuwa ranar tana nan zuwa. Saina tabbatar da ka gurbi abin da ka shuka. Ƴar daji, ƴar magarƙama, da kuma ƴar birni. Gaba ɗaya suna nan zuwa domin ɗaukar fansar abin da ka aikata wa mahaifiyarsu, ka jira ka ga sakamakon abin da ka aikata". 💃💃💃💃💃💃💃💃 *HANA WATA GA WAYA*. *WAI SHIN DAMA MRS LAILA BA TA MUTU BA TANA RAYE?, KENEN ƊAN SANDAN DA YA CECI MRS LAILA NA RAYE?, MENE NE HAƊIN MAHAIFIN UMAR DA MRS LAILA?, MUJE DAI ZUWA DOMIN JIN YACCE ZATA KAYA* *KADA KU MANTA DA LIKING, COMMENTS, DA KUMA SHARING*💃💃🥰🥰🥰😍. ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (ZINARIYA JAJIRTATTU) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣1️⃣▶️2️⃣2️⃣ *_________________________________________________* Nan take cikin Gov. Musa Muhammad ya ɗuri ruwa. Katse wayar ya yi yana mai faɗin. "Tabbas in dai da gaske tana a raye ba za ta barni na cika ƙudiri na ba, ga shi zaɓe ya kusan gaba to wa, ya zama dole nayi wani abu". Nan take wani dabara ya faɗo masa. Ɗaukar wayar sa ya yi tare da shiga cikin contact list, nan ya lalubo wata number wanda aka rubuta Aliyu a jiki. Kiran wayar ya fara yi amma tana ba shi switch off. Wurgar da wayar Gov. Musa Muhammad ya yi ya ce. "Pick up Aliyu! Pick up. I need your help urgently please". Aka yake ta faman magana shi ɗaya. ******** Ɓangaren su Aliyu kuwa, har an shirya musu visa sun shiga jirgi sannan suka kashe wayoyin su. Kowa na cikin jirgin su suke kallo ganin Safeera a goye bayan Mom kamar ƙaramar yarinya. Ganin cewa kowanen mutum a jirgin su yake kallo ya sa Aliyu faɗin. "We should all concentrate on something necessary please". Ya faɗa tare da ɗaura seat belt. Jin hakan ya sa kowa ya kawar da kansa. Nan take aka sannan cewa kowa ya kasance a shirye sannan kowa ya saka seat belt tare da kashe wayoyi domin jirgi zai tashi. Saida kowa ya kammala sannan jirgin su ya tashi. ************* "Wai ke ƴar gidan wace ce?, daga gani ma daga magarƙama ki ka fito domin kuwa wannan kayan ƴan magarƙama ne sanye a jikin ki". Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Wannan ba abin da ya shafe ka ba ne, idan ma hakan ne mene ne naka a ciki, kada ka ce za ka faɗa min magana wanda raina baya so". Kallonta yariman ya yi ya ce. "Kada ki manta fa Kano ki ka shigo, kano ko da me ka zo an fika. Don aka ki ajiye wannan jiji da kan naki domin kuwa ba za ta yi miki amfani a nan Kano ba". Kallonsa Zahra ta yi tare da sakin wani miskilin murmushi sannan ta ce. "Au aba da gaske?, kenen dai ko da hauka na zo an fini ko?. Ka sani cewa ni Zahra ce, kuma ba'a haifi wanda zanji tsoron sa ba, bayan ma'halicci na sai fiyayyen halitta. Don aka ka matsa domin bani da lokacin ɓata wa". Zuwa ya yi daff da ita sannan ya ce. "Idan na ƙi fa?, me za ki yi?". Kallon cikin idanuwansa Zahra ta yi sannan ta mayar masa da martani da cewa. "zan yi maka sambaɗe-baɗe, zan yi maka dukan da gaba ɗaya masarautar ku sai an gagara gane ka". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin wuce wa ta gefen shi. Babu zato ta ji ya janyo hannunta tare da janyo ta jikinsa. Zaro idanuwa Zahra ta yi waje, nan take ta kurma ihuuu! tana mai faɗin. "Kai ɗan iska ne?, wato dama kai dan iska ne ko?, ni ƙanwar ka ce da za ka jawo ni jikin ka?, maza ka sake ni kafin nayi maka abin da ba za ka ji dad'i sa ba". Matse hannunta yarima ya sake yi a karo na biyu sanann ya ce. "Ba zan saki ba". Duk abin da ke faruwa a gaban idanuwan jama'an da ke wajan. Nan take fadawa suka shigo tare da ƙwace Zahra daga hannun yarima sannan ɗaya daga cikin su ya ce. "Ranka shi daɗe, mai maryaba ya umarci da mu dawo da kai gida yanzu, ya kamata ka tawo mu bar nan wajan". Ɗaga musu hannu ya yi ya ce. "Naji shi ke nen". Maida kallonsa ya yi kan Zahra ya ce. "Ke kuma, muddin ki ka bari muka sake haɗuwa saina hukunta ki bisa raina ni da ki ka yi". Gwalo Zahra ta yi masa ta ce. "Kaje ka ji da abin da ke damun ka malam yarima mai ɗagaggen wando". Ta faɗa tana mai kwashe wa da dariya. Kare shi fadawan suka dinga yi har suka isa bakin mota. Shiga ciki gaba ɗaya suka yi tare da barin harabar wajan. Murmushi Zahra ta yi ganin cewar ta yi nasaran zaran wasu kuɗaɗe a aljihun yarima tare da wani ɗan ƙaramin maƙulli. Saka maƙullin ta yi a cikin aljihun ta. Maida kallonta zahra ta yi kan ma'aikata tare da jama'ar wajan sannan ta ce. "To ku ta shi mana, kun wani durƙusa ƙasa kamar masu bara. Shi da mutum ne kamar kowa amma shi ne ku ke ba shi wani girmama wa har kuna durƙusawa ƙasa saboda mutum ɗan adam irin ku, tirr gaskiya kun bani kunya". Miƙe wa gaba ɗaya suka yi yayin da ɗaya daga cikin ma'aikatan wajan ya kalle ta ya ce. "Yarima Junaid kenen, mutum ne mara tausayi, mara imani. Baya tausayin talakawa sannan baya da mutunta wa, duk in da ya samu ƙusa kai yake ba tare da yana jin tsoron kowa ba, an sha kai ƙarar sa gidan mai martaba sarki. Kuma sarki yana ɗaukar mataki hakan abin da yake yi sai dai kuma muddin ya fito sai ya je har gidan wanda ya kawo ƙararsa sannan ya tozarta shi ya sa shi ya bar gari gaba ɗaya. Sai dai yana da yahya wanda yake matuƙar tsoro, tun da yahyansa ya bar ƙasar nan ya je ƙasar waje aiki shi ke nen ya ƙara iskancin sa a kan na da. Amma da a ce yana nan ba za ka taɓa ganin koda inuwar sa ba". Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Ni dai karya sake ya gwada min wanann shashanci don ba zan rabu da shi ba.". Ta faɗa tana mai ɗaukar lemo da biscuit sannan ta miƙa wa ma'aikacin kuɗin da ta zara a aljihun Yarima Junaid. Karɓa ma'aikacin ya yi tare da yi mata godiya. Fice wa ta yi daga cikin wajan yayin da ta samu bakin hanya ta fara kurɓan lemo. Nan take mutane suka fara binta da kallo. Ɓangaren asibiti kuwa su DPO na shiga ɗaki suka tarar Zahra ba ta ciki. Nan take suka bazama neman Zahra yayin da suka fara patrol a cikin wajan fita suka yi daga cikin asibitin sannan suka fara bibiyar Zahra. ********************** *JIGAWA* Yallaɓai tun ɗazu muke ce mata ta sauko amma ta ƙi sauko wa. Ajiyan zuciya Umar ya sauke!, sannan ya ce. "Yanzu tana ina?". Amsa Nurse ɗin ta ba shi da cewa tana cikin room 6. Jin hakan ya sa shi nufar in da ɗakin take. Baiyi wata-wata ba ya shiga cikin ɗakin. Duba ko ina ya yi ya ga babu Amrah a cikin ɗakin. Hankalin sa ba ƙaramin tashi ya yi ba. Duban nurse ɗin da ke tare da shi ya yi ya ce. "Ina mara lafiyar da na kawo?". Amsa nurse ɗin ta bashi da cewa. "Ka duba saman silin yallaɓai. Jin hakan ya sa Umar ya maida kallonsa sama. Abin da ya gani ba ƙaramin firgita shi ya yi ba. Saurin ja da baya ya yi ganin Amrah zaune kan fankan ɗakin ta rirriƙe shi gamm tamkar bishiya. Maida kallonsa ya yi kan nurse ya ce. "Garin ya ya ku ka bari ta au kan fanka?, ita ɗin fa mara lafiya ce, ya kamata a ce kuna kusa da ita domin ku dinga kula da lafiyar ta". Kallonsa Nurse ɗin ta yi ta ce. "Munyi hakan yallaɓai, amma kwatsam sai mu ka ga ta firgita ta miƙe tsaye, bamu yi aune ba kawai muka ga ta buga tsalle tare da aye wa saman fanka tamkar buri, Allah ma ya sa babu wuta a jikin fankan da shi ke nen mun rasa ta". Ajiyan zuciya Umar ya sauke jin abin da nurse ɗin ta ce. Sannan ya dube ta ya ce. "Wace ce special nurse ɗin da aka aje a nan domin ta dinga kula da ita?". Amsa nurse ɗin ta bashi da cewa. "Nurse Nadiya ce, ita ce take kula da ita kafin ka zo". "To ki je ki ce mata ta zo ina da buƙatar ganinta". Cewar Umar. "Shi ke nen". Nurse ɗin ta faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin. ******* Ɓangaren su Aliyu kuwa, hawanni ƙalilan ya yi musu suka iso Nigeria. Yayin da suka sauka a airport. Fito wa suka yi tare da neman taxi suka hau kai tsaye suka nufi hanyar asibiti. ****** Mitin ƙalilan nurse Nadiya ta isa ɗakin da su Umar suke. Da sallama ta shiga ɗakin Umar ya amsa. Dubansa ta yi ta ce. "Naji an ce kana kira na lafiya dai ko?". Amsa Umar ya bata da cewa. "Lafiya ƙalau, ina neman taimakon ki ne, yanzu zanje gida ne na ɗauki abun da zai sa ta sauko ƙasa. Ina so ne ki jire min ita dan Allah kinji?, bana son ta fita ko ina please". Murmushi Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Aiki na ne yin hakan, don aka kada ka samu damuwa za ka iya tafiya ni zan zauna na kular maka da ita". Godiya Umar ya yi mata sannan ya fice daga cikin ɗakin. Zama nurse Nadiya ta yi tana mai maida kallonta sama sannan ta girgiza kai ta ce. "Allah mai iko, ko ta ya ya na aka yi ta ɗane kan fanka oho. Kina jina ƴar lele, maza sauko ƙasa kinji kyakyawa, zan siya miki alewa". Ganin Amrah ba ta kula ta ba saima ƙara zama da ta yi kan fankan. Furzar da iska nurse Nadiya ta yi sanann ta ce. "Shi ke nen tun da ba za ki sauko ba". Ta faɗa tare da ɗaukar lemon ɓawo da ke cikin plate ta fara ƙoƙarin kai bakin ta. Hango lemon ɓawo da Amrah ta yi ya sa ta dira ƙasa tare da wafce lemon, sannan ta fara haɗa wa da bawon jikin sa tana sha. Zaro idanuwa Nurse Nadiya ta yi ganin irin launin idanuwanta. Cikin ranta ta ce. "Wannan green eyes ne da ita, sakk kalar idanun ɗaya daga cikin yaran Mrs Laila. Allah sarki". Ta faɗa yayin da hawaye suka fara bin kan ƙuncin ta. ************* Bayan isar Yarima Junaid fada ya shiga cikin part ɗin sa ba tare da ya kula kowa ba. Shiga wani ɓangare ya yi a gidan sannan ta duba aljihun shi domin ya ɗauki maƙulli. Zaro idanuwa ya yi waje gani cewar babu muƙullin ɗakin sa a aljihun shi. "Ta ya ya hakan za ta faru?, ina maƙullin ya shiga kuma?, na shiga uku!, muddin banga maƙullin nan ba sai Yahya ya hukunta ni, yanzu me zan yi kenen?". Nan take ya tuna da cewar ɗazu ya riƙe Zahra. "Kodai ita ce ta ɗauka?". Ya tambayi kanshi. Da sauri ya fita daga cikin part ɗin sa. Tare da fita hanyar waje. nan take ya ci karo da mai martaba. Sunkuyar da kansa Junaid ya yi sannan ya ce. "Allah ya ƙara maka nisan kwana ranka shi daɗe". Dubansa mai martaba sarki ya yi sannan ya ce. "Junaid me ya sa ka fita daga cikin masarautar nan bayan na hana ka fita?". Nan take cikin Junaid ya ɗuri ruwa. *************** Ɓangaren su Safeera kuwa, shigar da Safeera aka yi cikin room 8, yayin da likitoci suka rufa a kanta. Babu abin da Mom ke yi in banda addu'a yayin da take ta kai kawo a cikin reception ɗin. Saida suka ɗau lokaci sosai a kanta kafin daga bisani suka samu numfashin ta ya dawo. Nan take suka yi mata allurar bacci. Fito wa likitocin suka yi suna sharfe zufa. Ganin sun fito ya sa su Mom suka nufi in da suke tare da tambayar ya lafiyar Safeera. Ɗaya daga cikin doctor's ɗin ne ya dube su ya ce. "Alhamdulillah, mun samu numfashin ta ya dawo yanzu kuma ta samu bacci. Zamu saka ɗaya daga cikin nurse ɗin mu ta je ta duba ta. "Shi ke nen". Daddy ya furta. Shiga cikin room ɗin da nurse Nadiya take likitan ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Nurse ina son ki je ki dinga kula da wata mara lafiya tana room 8". Kallonsa Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Am sorry to say sir, but ba zan iya rabu wa da wannan mara lafiyar sannan na koma kan wata ba, wannan an bani amanar ta ne. Kuma nayi alƙawarin zan kula da ita, kuma yana da kyau idan mutum ya ɗau alƙawari ya yi ƙoƙarin cika wa. Ka saka wata nurse ɗin ta je ta kula da ita Please sir ". Ta faɗa cikin ƙasa da murya. Kallonta doctor ɗin ya yi sannan ya ce. "Ina mara lafiyar da ki ke kula da ita take?". Amsa nurse Nadiya ta bashi da cewa. "gata chan a sama". Maida kallonsa Doctor ɗin ya yi sama. Zaro idanuwa waje ya yi domin abin da ya gani ya yi matuƙar bashi mamaki. "I can't believe this, how can this be possible". Ya faɗa. Maida kallonsa ya yi kan nurse Nadiya sannan ya ce. "Ina so yanzu kiyi maza-maza kije ki duba patient ɗin ke cikin room 8 yanzu". Ya faɗa hankalin shi a matuƙar tashe. Kallonsa nurse Nadiya ta yi ta ce. "Lafiya dai Doctor, naga kamar hankalin ka a tashe". Doctor ɗin ya dube ta ya ce. "Dole hankali na ya kasance a tashe domin naga abin da ya firgita ni, kije ki duba ɗakin ko mara lafiyar mu tana wajan, ni zan wuce office". "As you wish sir". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye tsreda fice wa daga ɗakin. Zama Doctor ɗin ya yi yana mai kallon Du'a wanda ke a kan fanka. "Abin mamaki baya ƙare wa, yanzun nan da na fito daga ɗakin ɗayar yarinyar amma kuma yanzu na zo nan, na tarar da mai kama da ita sakk. Wai ko dai na sha maye ne yau?". Ya tambayi kansa. ****** "Shi ya san abin da ya gani hankalin sa ya tashi, koma dai mene ne zan je ɗakin na gani". Cewar nurse Nadiya. Tana isa ƙofar ɗakin ta murɗa handle ɗin ƙofan. Chan ta hango Safeera a kwance. Riƙe haɓar ta nurse Nadiya ta yi ta ce. "Lahaula, Amrah wato har kin riga ni zuwa nan ɗin ma. Ta ina ki ka bi har ki ka riga ni zuwa?". Dube-dube ta fara yi. "To wai ina mara lafiyar take ne?, wato dai wannan likitan so yake kawai ya bani wahala shi ya sa ya ce min wai akwai mara lafiya a nan". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan safeera wacce ke kwance kan gado idanuwanta a lumshe. Mamaki ne ya kama nurse Nadiya ganin cewar tufafin da ke jikin Safeera ba irin shi ne a jikin Amrah ba. "Ta ya ya Amrah ta iya sauya kaya cikin ƙanƙanin lokaci aka?". Nurse Nadiya ta tambayi kanta. Furzar da iska ta yi sannan ta ce. "Mybe ni ce ban duba ba sosai . Amrah ina zuwa bara naje na faɗa wa Doctor ɗin cewa banga mara lafiyar da ya faɗa ba". Ta faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin. Nufar ɗakin da Amrah take ta yi. Tana isa ƙofar ɗakin ta buɗe tare da shiga cik. Yayin da idanuwanta suka sauka a kan Amrah. Nan take gabanta ya yi mummunar faɗuwa!, yayin da gabanta ya shiga dukan uku-uku. Babu zato ta ji kanta ya yi mugun sara mata. baki na rawa ta ce. " Amrah!, kenen ba Amrah na gani a wan can ɗakin ba?, to in dai da gaske ba Amrah bace a wannan ɗakin ita kuma ta cikin ɗakin wace ce?". 💃💃💃🌹🌹💃💃💃 *TASHIN KAI, NURSE NADIYA FA TA SHIGA RUƊANI KOMAI ZAI FARU IDAN TA GANO CEWAR SU BIYU NE A ASIBITIN, SANNAN KUMA YARAN LAILAH ABDULLAHI NE?. MUJE DAI ZUWA* *WAYYO LOW BATTERY 🔅 🔋, MUNA FAMA DA RASHIN WUTA BANI DA CHARJI🥺, JIYA MA NASO NAYI MUKU AMMA RASHIN WUTA YA HANA. KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE PLEASE 🙏*. KARKU MANTA DA SHARING, COMMENTS, AND LIKES FISABILULLAH 🙏🙏🙏🙏. ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣3️⃣▶️2️⃣4️⃣ *_________________________________________________* Nurse Nadiya ta faɗa cikin ruɗu da gigicewa. Kuma maida kallonta ta yi kan Amra sannan ta ce. "Amrah green eyes ne da ita, ita kuma wan can fa?, to in har wan can ta ɗakin blue eyes ce da ita hakan yana nufin ƴaƴan Mrs Laila ne". Ta faɗa tana kuma koma wa ɗakin da ta ga Safeera. Tana ƙarasawa ƙofar ɗakin ta shiga ciki. Da mamakin ta kuwa sai ta ga babu kowa a ɗakin. Hakan ba ƙaramin mamaki da tsoro ya sanya ta ba. "Kodai na fara gane-gane ne?, ba'a nan ɗakin ba ɗa zu naga wata mai kama da Amrah?, where is she?". Ta tambayi kanta. Tuna wa da cewar Umar ya ce kada ta bar Amrah ita kaɗai ya sanya ta saurin barin wajan tare da nufar in da ɗakin da Amrah take. Safeera kuwa bata je ko ina ba sai bandaƙi domin ɗaura alwala. Bayan ta gama ta fito daga cikin toilet ɗin yayin da ta duba ko ina amma babu hijab sai iya ɗingilallen mayafin ta. Zama ta yi a bakin gado sannan ta duba arabar wajan. Sai a lokacin ta lura cewar ba'a gida take ba. Zumbur ta miƙe tsaye tana mai waige-waige. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin cewa tabbas nan ba ɗakin ta ba ne. Kwalla kiran sunan Mom ta fara yi cikin tsoro da fargaba. Su Mom da ke reception jin muryar Safeera hakan ya sa su yin saurin nufar ɗakin da take. Da sauri suka shiga ɗakin suka tadda ta tsaye gaba ɗaya duk ta bi ta rikice. Kallonta Mom ta yi ta ce. "Ƴata Safeera kin farka?, Alhamdulillah Allah na gode maka". Duban Mom Safeera ta yi ta ce. "Mom where am I?, which place is this?, Mom what's going on because I don't understand am confuse, this place doesn't look similar". Ajiyan zuciya Mom ta sauke sannan ta ce. "Safeera calm yourself down okay?, nan wajan da ki ke gani ba America ba ne, yanzu haka muna Nigeria ne". Zaro idanuwa waje Safeera ta yi. "What!". Ta furta cikin tashin hankali ta ce. "Why mom why?, me ya sa muka zo Nigeria bayan na faɗa muku cewa bamu kammala second semester ɗin mu ba?, and you know tomorrow am having a paper, so now what do you expect me to do now?". Ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta. Kallonta Aliyu ya yi baki ya ce. "Sannu Mommy's pet, ke hana ta rai wa yake ta karatu?, idan babu rai za ki iya zuwa ki rubuta paper ɗin?, abin da ya sa muka kawo ki ƙasar nan mun ɗauka kina da aljanu ne shi ya sa kuma cinciɓo ki muka tawo da ke". Kallonsa ta yi cikin rashin fahimta ta ce. "Aljanu!, mene ne kuma aljanu?". Kallon baki da hankali Aliyu ya bita da shi ya ce. "Kije kiyi searching a google zai baki amsa. Aikin banza wai mene ne aljanu". Ran Safeera ne ya ɓaci ta dube shi ta ce. "Kai mind your word's, I can't tolerate any stinking shit from you okay, apart from that ma, i dislike Nigeria, the country it so disgusting I prefer America, Mom please let's go back, there is too much heat here and dirty environment". Sakin baki Aliyu ya yi yana kallonta sannan ya ce. "Sannu ƴar America, to iyayen ki ƴan Nigeria ne, kuma nan ƙasar mu ce ta gado, ko kina so ko bakya so sai kin zauna, sannan tun da kakannin ki da iyayen ki suka zauna wajibi ne kema saikin zauna". Kallon Aliyu Daddy ya yi ya ce. "Ka ga ka rabu da ƴata, idan ta ce bata so fine sai mu koma, ba wani abun tayar da hankali ba ne. Yanzu dai bara naje na samu Doctor ya zo ya duba ki, idan ya ce kun samun sauƙi zamu iya tafiya da ke sai mu wuce gidan mu, na san Baba zai yi farin ciki sosai". Yana kaiwa nan ya fita daga cikin ɗakin. Ɓangaren Nurse Nadiya kuwa tana zuwa ta tarar Amrah bata ciki ɗakin. Bincika ko ina ta yi na ɗakin ta ga ba ta ciki. "Innalilahi wa innahilahir rajihun!". Kalmar da ta fito daga bakin ta kenen. Cikin tashin hankali ta ce. "Na shiga uku ni Nadiya!, ina kuma Amrah ta shiga?, yanzu me zan faɗa wa mijin ta idan ya zo". Tana cikin magana taji sallamar Umar. Amsa sallamar sa ta yi tana mai maida kallonta kansa. Dubanta Umar ya yi ya ce. "Nurse lafiya naga kamar hankalin ki a tashe?". Ajiyan zuciya Nurse Nadiya ta sauke!, sannan ta ce. "Ina da lafiya, naje domin duba wata a wan can ɗakin, kafin naje na dawo sai naga matar ka Amrah ba ta cikin wannan ɗakin. "What!". Umar ya furta. "Kamar ya ba ta cikin ɗakin?, saida na faɗa miki fa cewa kada ki barta kije ko ina saboda ita ɗin ba kamar mu take ba daga daji take. And besides Amrah ba matata ba ce ba, nayi helping ɗinta ne kawai. Ni yanzu ina ki ke so naje na nemo ta fisabilullah?". Ya faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin. Fita ya yi daga harabar wajan baki ɗaya. yayin da ya saka securities suka bincika masa asibitin baki ɗaya. Duba ko ina na harabar asibitin suka yi amma babu alamun Amrah. Gaba ɗaya hankalin Omar ba ƙaramin tashi ya yi ba. Da sauri ya shiga cikin mota tare da tada motan sannan ya bar harabar wajan. Tuƙi ya fara yi yayin da yake buga styring motan da ƙarfi. Cije leɓensa wanda suke jajir ya yi. Tare da shafa sumar kansa. Kamar an ce masa ya juya. Juya wa ya yi ɗayan ɓangaren. Zaro idanuwa ya yi waje ganin Amrah daga ɗayan side ɗin titi kan bishiyar mangwaro. "Alhamdulillah". ya furta tare da samun guri a hanyar titin ya yi parking. Fitowa ya yi tare da tsallaka wa izuwa ɗayan ɓangaren da Amrah take. ****************** Su DPO kuwa sunyi neman duniya basu ga Zahra ba hakan ya sa ba yacce suka iya suka kama hanyar Jigawa. ****** Zahra kuwa da ta ga zaman bakin titi ba zai finshe ta hakan ya sa ta miƙe wa tsaye sannan ta fara tafiya. A matuƙar gajiye take tafiya ba tare da ta san in da take nufa ba. Tafiya ta yi mai nisan gaske kafi daga bisani ta tsagaita da tafiya. Tsayawa ta yi ta kalli gabas da arewa ta ce. "To wai nan ina ne?, yanzu ta ya ya zan koma Jigawa?, idan na ci gaba da tsaya wa aka yunwa ce za ta kashe ni. Ya zama dole na nemi mafita". Chan ta hango wani shago na kayan cosmetics. Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta ƙarasa cikin shagon. Sallama ta yi mai shagon ya amsa yana mai kallon kayan dake sanye a jikinta. Ganin yana binta da kallo hakan ya sa ran Zahra ya soma ɓaci dubansa ta yi ta ce. "Malam ya dai ka ke kallo na?, kona yi maka kama da wacce ta yi gudun hijira ne?". Kawar da kansa mutumin ya yi yana mai ci-gaba da karkaɗe kayansa sannan ya ce. "Ai naga kina sanye da kayan ƴan magarƙama ne dole naji tsoro kuma na kalle ki, haka kurin hana zaune ƙalau ki ƙundume min kaya". Hangame baki Zahra ta yi ta ce. "Ni nayi maka kala da ɓarauniya?, to idan baka sani ba ni ce ƴar gatan magarƙama, wanda a kaff magarƙaman jigawa babu wacce ake ji da ita sama da ni. Karka sake ce min ɓarauniya". Ta faɗa tana mai gyara tsayuwar ta sannan ta ce. "Dama na zo nan ne na tambaye ka cewa nan wajan ina ne?". Dubanta mai shagon ya yi ya ce. "Nan zoo road ne kin gane". Jinjina kai Zahra ta yi ta ce. "Tom naji idan babu damuwa dan Allah ka ɗauke ni aiki saboda na tara kuɗi na koma jigawa". Girgiza kai mutumin ya yi ya ce. "Ni?, chab ɗi jam, A'a kam kiyi haƙuri amma ba zan iya ɗaukar ƴar magarƙama aiki ba gaskiya, ba zan ɗauki wannan kasadar ba". Kallon shi Zahra ta yi ta ce. "To su ƴan magarƙamar ba mutane ba ne?, kenen basu da damar neman aiki?, ni zan yi aiki ne kawai saboda na tara kuɗaɗe na koma in da na fito, domin ni naga alamun ma zaman magarƙama ya fi nan wajan ƴanci". Kallonta mai shagon ya yi ya ce. "Yafi nan ƴanci me ya sa to ki ka gudo daga cikin magarƙamar?, kamata ai a ce ki zauna a chan tun da yafi nan ɗin ƴanci. Ni dai ba zan baki aiki ba sai dai zan baku shawara guda ɗaya wacce za ta yi miki amfani. Shawarar ita ce. Ki samu kwano ki zauna a bakin titi kiyi bara na san za'a taimaka miki. Ina ganin kamar hakan zai fi". Murmushin takaici Zahra ta yi ta ce. "Naje bakin titi inda kowa ke wuce wa nayi bara ko?, kuma kai ɗin mutum ne da gaske mai zuciyar imani?, ta ya ya za ka ce naje nayi bara?, da a ce ni ƙanwar ka ce ko ƴarka haka za ka ce naje nayi bara?, tirr da halinka. Ni dai da nayi bara na gwammace na dauwama a wannan garin banje ko ina ba, haramunne yin roƙo idan baka sani ba yau ka sani. Shashashan banza kawai alade". Tana kaiwa nan ta ja tsaki tare da barin shagon. Jikin mutumin ne ya yi sanyi. basar wa ya yi ya ci-gaba da aikin da ke gabansa. ***************** *MASARAUTA* "Kayi haƙuri mai martaba hakan ba zata sake faruwa ba". Prince Junaid ya faɗa yana mai duƙar da kai. Kallonsa mai martaba ya yi ya ce. "Na san iya Sooraj ne kaɗai zai yi maganin ka". Barin wajan mai martaba ya yi ya bar Junaid a tsaye. Ajiyan zuciya Junaid ya sauke tare da faɗin. "Allah na gode maka da bai ce zai faɗa wa yahya Sooraj ba da na shiga uku". Yana kaiwa nan ya fita harabar fadan. Masha Allah baki na ya iya furta wa ganin yadda masarautar take da matuƙar girma da kyau. Grand entrance na hango daga nesa ƙofa mai matuƙar ban sha'awa yayinda bangare guda ƙofofi ne masu ado na gida je cikin masarautar. Yayin da katangar wajen masarautar anyi sa ne da dutse mai sheƙi tamkar lu'ulu'u tare da sassakaƙƙun sassaƙa na tagogi mai ƙyalli. Chan gefe kuma baranda ce wacce tsayin ta baki ba zai gama faɗi ba. Chan gefe turret ne da husumiya spiers mai tafiya da imanin mutum. Ɓangare ɗaya kuma manyan fadoji ne tare da kyawawan kayan ado wanda aka haɗa da chandeliers na kristal masu kyau gaba ɗaya kayan kwalliya ne ya cikashe su tare da kayan al'atu da kayan more rayuwa. An ƙawata fadojijin da sassakaƙƙun sassaƙa wanda ke nuna fasaha na musamman. Bangare ɗaya kuma manyan zaure ne da ɗakunan karaga masu kyau an tsara su don dalilai na biki dana hukuma. tare da ɗakunan ma'aikata da na fadawa harda na bayin masarautar. Chan ɓangaren kuma kyawawan lambuna ne wanda ya ƙawata masarautar ta kuma bada wata iriyar kyau mara misaltuwa. Ɓangare ɗaya kuma ɗakunan kayan tarihi ne da kayan al'adun mu na gargajiya sai gwala-gwalai da lu'ulu'u masu matuƙar sheƙi da kyau. Tsayawa misalta yadda masarautar nan take da kyau ɓata lokaci ne ku dai kawai ku fasalta a ranku. Kai tsaye cikin labari. Direct garden Junaid ya nufa yayin da ya samu karƙashi bishiya ya zauna. Ganin fitowar sa ya sa ma'aikata da fada wa suka ƙaraso wajan sa suka fara kwasar gaisuwa suna mai yi masa ƙirari. Dakatar da su Junaid ya yi ya ce. "Ku tafi ya isa". Jin hakan ya sa suka bar wajan suka ci gaba da harkar gabansu. Dafe kansa Junaid ya yi ya ce. "Ni yanzu a ina zan samo maƙullin nan, kuma ina da tabbacin cewa yana wajan wannan ƴar dabar nan ta ɗazu, to a ina ma zan ganta?, kuma muƙullin nan yana da mahimmanci sosai, gashi mai martaba ba zai barni na fita daga masarautar nan ba. Yanzu ya zan yi kenen?". Ya tambayi kansa. ******** Ɓangaren Umar kuwa yana tsallaka wa ya sauko da Amrah daga kan bishiya yayin da ya ga fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye babu abin da take yi sai kuka. Damuwa ne ya lulluɓe fuskar Umar. Kallonta ya yi ya ce. "Amrah me ya faru?, kina son ki koma wajan ƴan uwan kine?". Babu tsanmani ya ga ta girgiza masa kai. Mamaki ne ya kama shi. Cike da farin ciki ya ce. "Kina iya fahimtar abin da nake cewa?". Gyaɗa kai ta kuma yi a karo na biyu. Hamdala Umar ya yi ya ce. "Shi ke nen naji dad'i tun da kina iya fahimtar abin da nake cewa. Yanzu dai kina so ne na kaiki wajan ƴan uwan ki ko". Gyaɗa masa kai ta yi. Tare da fara kalle-kalle. Nan ta hango ruwa wanda ya zuba a ƙasa. Murmushi ta yi tare da wafce hannunta ta nufi in da ruwan yake. Ganin hakan ya sa Umar bai yi ƙasa a gwiwa wajan bin bayanta ba. Tana isa bakin ruwan datti da ya zuba a ƙasa ta tsugunna kan gwiwowinta tare da kokarin kai hannunta kan ruwan domin ta sha. Ganin hakan ya sa Umar saurin dakatar da ita. Mikar da ita ya yi ya ce. "A'a Amrah karki damu in dai ƙishin ruwa ki ke ji zan siya miki ruwa ba saiki sha na datti ba, maza tawo mu je". Ya faɗa tare da jan hannunta. Ba musu Amrah ta bi bayanshi yayin da babu abin da take ta faman yi illa kallon jama'ar da ke wajan tare da tufafin da ke sanye jikin su. Kallon jikinta ta yi ta ga dai ita nata tufafin da nasu da iri ɗaya ba ne domin naya na ganye ne. Binta jama'ar wajan kawai suke da kallo. Wani ƙaramin super market Umar ya samu ya shiga da Amrah yayin da ya yi order ruwa. Cikin lokaci ƙalilan aka kawo masa ruwan roba. Karɓan ruwan Umar ya yi tare da buɗe murfin roban ruwan sannan ya miƙa wa Amrah. Bin roban da kallo kawai Amrah ta yi tare da kawar da kanta. Sauke ajiyan zuciya Umar ya yi sannan ya ce. "Ki karɓa ki sha ruwa ne fa, maza karɓi ki sha idan ya so muje na kaiki gidan mu ina da ƙanne za su kula da ke kinji". Karɓar roban ruwan Amrah ta yi tana mai jujjuyawa a hannunta. Taɓe baki ta yi sannan ta fara kwararar da ruwan a ƙasa. "Ya Salam". Umar ya furta yana mai dafe kansa. Karɓar ruwan ya yi sannan ya fara bata da kansa. Take ta shanye ruwan tasss. Mamaki ne ya kama Umar ganin lokaci ƙalilan ta shanye ruwan roba ɗaya. Girgiza kai Umar ya yi sannan ya ce. Tashi mu tafi ko. Gaba ɗaya mutanen super market ɗin sai binsu Umar suke da kallo most especially Amrah wanda suka ga shigar ta sakk irin na ƴan jeji. Lura da Umar ya yi cewa mutanen wajan su suke kallo hakan ya sa shi miƙe wa tsaye sannan ya je ya bada kuɗin ruwan roban da ya siya. Tare da jan hannun Amrah suka fice daga wajan. Tafiya suka fara yi yayin da Umar yake ta faman kallon Amrah. Wai shi ne yau tare da mace yana lallaɓa ta kamar ƙwai. Abun ba ƙaramin mamaki yake ba shi ba. Ba zato ya ga Amrah ta ƙwace hannunta daga nasa ta fara gudu. Zaro ido Umar ya yi tare da saurin bin bayan ta. "Amrah ina za ki je?, ki dakata, oh my God hanya ban ɗaura ruwan dafa kaina ba kuwa ni Umar?". Abin da ya sa Amrah gudu kuwa bakomai ba ne fa ce gani da ta yi wata mai ciki za ta tsallaka titi ga mota ya tawo sai faman sharara gudu yake. Hakan ya ja hankulan mutane yayin da suka fara ihuuu taimako. Kaɗan ya rage mota ya buge matar da sauri Amrah ta sha gaban matan tare da matsar da ita gefe. Nan take motan ya buge Amrah. Zaro ido jama'ar wajan da Umar suka yi. Ga mamakin su kuwa sai gani suka yi ta tashi sama tare da sauka ƙasa ta tsaya chakk tamkar ba ita mota ya buge ba. Sakin baki mutane suka yi ganin abun mamaki da ya faru a dai-dai lokacin. Ɓangaren Umar kuwa abin ba ƙaramin mamaki ya bashi ba ganin yadda mota ta kaɗe ta amma bata faɗi ba. Saurin zuwa bakin titin Umar ya yi tare da jan hannun Amrah. Janyo ta ya yi har izuwa in da motar sa yake sannan ya tsaya ya dube ta ya ce. "Kina da hankali kuwa?, chan fa tsakiyar titi ne ba kamar dajin ku ba ne wanda za ki dinga tsalle kina shiga da fice yadda ranki yake so, yanzu da a ce wani abu ya same ki fa, kin san wane hali zan shiga". Ya ƙarasa maganar yana mai kallonta. Lura da ya yi cewar gaba ɗaya hankalin ta ba'a kansa yake ba yana wani wajan da ban ya sa shi faɗin. "To wai wannan ina take kallo?". Ya faɗa yana mai bin in da take kallo da kallo. Mai mangwaro ya hango zaune a bakin junction. Kallonta ya yi ya ce. "Shima mangwaron sha za ki yi?". Gyaɗa masa kai ta yi. Takaici ne ya kama shi ya ce. "Ke yanzu komai ki ka gani za ki sha?, to ai yanzu dai bamua kusa da wajan saiki tawo mu tafi". Ya faɗa tare da juyawa sannan ya buɗe mata ƙofar ƴan zaman banza. "Zo ki shiga". Ya faɗa hin shiru bata shiga ba ya sa shi juyawa. Zaro idanuwa ya yi waje ya ce. "Ina kuma ta shiga?". Daga chan tsallake ya hango ta wajan mai mangwaro babu abin da take ta faman yi sai gwawuyan mangwaro kamar ta samu goruba. Ɗora hannunsa biyu Umar ya yi a kai ya ce. "Ya Allah!". Tafiya ya fara yi tare da tsallaka wa bakin titin ganin ta sha mangwaro sun kai biyar hakan ya sa ya ciri kuɗi a aljihun shi ya biya mai mangwaron. Maida kallonsa ya yi kanta tareda fara janta. janta ya fara yi ya ga dai taƙi jawuwa. Ganin hakan ba zai finshe shi ba ya sa shi ɗaukarta chakk sannan ya nufi in da motar sa take. Tafiya ya yi sosai kafin daga baya ya isa in da motar sa take sannan ya saka ta a cikin motan tare da saka wa ƙofar lock. Koma wa ya yi mazaunin driver sannan ya tada motar suka bar harabar wajan. A takure ta zauna a cikin motan yayin da iskan AC ya addabe ta. Hannu ta saka tana mai ƙoƙarin fasa glass ɗin motan domin ta shaƙi iskar waje. Ganin tana ƙoƙarin fasa glass ya sa Umar saurin kashe Ac ɗin. ********** "Yanzu dai munyi magana da Doctor ya ce kin samu sauƙi sosai zamu iya tafiya da ke". Murmushi Safeera ta yi ta ce. "Na gode Daddy amma yanzu Airport zamu wuce ko?". Amsa Daddy ya bata da cewa. "A'a dole sai mun je mun fara ganin su grandma da grandpa ɗin ki tukun". Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Shi ke nen, amma muna zuwa zamu koma America, saboda i can't stay here". Fita suka yi gaba ɗaya tare da shiga cikin motan taxin da ya ɗauko su daga airport sannan suka fice daga harabar asibitin. Kai tsaye hanyar gidan Grandpa suka nufa. Dai-dai junction suka tsaya sakamakon goslow da ya cike wajan. Daga nesa Safeera ta hango mai mangwaro. Murmushi ta yi ta ce. "Laa Mom dama akwai Mango a Nigeria?, ina so zan sha please Mom". Kallonta Mom ta yi ta ce. "A'a Safeera nan titi ne ki bari Aliyu zai zo ya siya miki daga baya". "No Mom gaskiya ni ba zan iya jira ba". Tana kaiwa nan ta fice daga cikin motan tare da tsallaka wa ɗayan ɓangaren. Ganin hakan ya sa Mom fita daga cikin motan sannan ta bita a baya. Safeera na zuwa ta kalli mai mangwaron ta ce. "Hey you, I need one mango how much dollar is it?". Ƙura mata idanu mai mangwaron ya yi yayin da mamaki ya bayyana kan fuskar shi. Kallonta ya yi ya ce. "Bake ba ce yanzu ki ka sha mangwaro guda biyar da tufafin ƴan daji?". Ƙarasawa wajan Mom ta yi ta kalli Safeera ta ce. "Ki tawo mu tafi babu Nigeria money yanzu a waje na, they don't deal with dollar okay let's go". Miƙa mai dollar ɗaya Safeera ta yi ta ce. "Take it I need one mango". Kallon kuɗin mai mangwaro ya yi ya ce. "Ni za ki kawo wa kuɗi bogi. yanzu-yanzu da ki ka sha mangwaro kusan biyar amma a ce har kin dawo za ki ƙara". Kallon mai mangwaron Mom ta yi cikin rashin fahimta ta ce. "Ƴata kuma?, hanya kuwa?, yanzu fa ta zo nan wajan". Girgiza kai mai mangwaron ya yi ya ce. "A'a Hajiya, ɗa zu ƴarki ta zo sai dai ba wannan shigar ba ne a jikinta, ita ne da wani ya zo ya ɗauke ta a nan suka tafi. Nayi mamaki ne ganin lokaci ƙalilan harta chanza kaya ta kuma dawo wa sannan kuma idanuwanta naga ba kalar da ɗa su ba ne na ɗazu kamar kore ne idanuwanta". Sai a lokacin Mom ta tuna da mai kama da Safeera da ta gani a Tv. Kallon Safeera Mom ta yi ta ce. "Babu shakka magana ta gaskiya ce, kenen da gaske ne akwai mai kama da Safeera?, to wai ta ya ya hakan ta kasance?, kodai Safeera ƴan biyu ne, kenen hakan yana nufin ajiya biyu ne su ɗin?". 💃💃💃💃💃💃💃💃 *LIKE SHARE & COMMENTS FISABILULLAH 🤌🙏* *YANZU WASAN YA SOMA. MOM BA AJIYA BIYU BA NE, AJIYA UKU NE😂, KI SHAFA WA ZUCIYAR KI RUWAN SANYI. KAI KAM UMAR KAGA TA KANKA DOLE KA SHIRYA DOMIN ZAMA DA AMRAH BA WASA BA NE🤣* ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣5️⃣▶️2️⃣6️⃣ *_________________________________________________* Kallon Mom Safeera ta yi ta ce. "Aba Mom kema kin yarda da wannan tatsuniyar, ta ya ya ma za'a ce akwai wata mai kama da ni, ai abin da ba zai taɓa yiwu wa ba kenan. Ya kamata mu tafi daga nan nama fasa siyan mango ɗin duk ƙudade sai bi suke its looks disgusting". Jan hannun Mom Safeera ta yi suka koma cikin taxi ɗin. Nan goslow ɗin ya ragu har suka samu hanya suka wuce. ******* Umar kuwa bai zarce ko ina ba sai gidansu. Horn ya yi jami'ai suka buɗe masa ƙofa. Direct parking space ya nufa tare da yin parking. Ajiyan zuciya ya sauke tare da maida kallonsa kan Amrah wacce ta takure guri guda. Fitowa ya yi tare da zuwa side ɗin Amrah ya buɗe mata ƙofa. Fito da ita ya yi. Kallon fuskarta ya yi nan yake ya ga hawaye kan kwance a kai. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba . "Mene ne ya sa ki ke kuka Amrah?, ko gidan namu baiyi miki ba ne?, kina son na maida ki wajan ƴan uwanki". Da sauri ya ga ta girgiza masa kai. Murmushi ya yi ya ce. "Karki damu zan maida ki chan wajan su yanzu haka na saka jami'ai suyi treating ɗinsu wasu sun mutu wasu kuma suna raye don haka kiyi murmushi kinji, domin zan maida ki bayan komai da komai ya kammalu". Yana kaiwa nan ya ja hannunta tare da shigar da ita cikin gidan. ******* A matuƙar gajiye take takawa yayin da mutane ke binta da kallo. Daga nesa ta hangi wata mai ƙosai a baki jection. Da sauri ta nufi in da mai kosan take sallama riƙe a bakin ta. Amsa sallamar mai ƙosan ta yi ta ce. "Na nawa za'a baki?". Sosa ƙeya Zahra ta yi ta ce. "A gaskiya bani da kuɗi sai dai idan za ki taimaka min da shi ina matuƙar jin yunwa ne". Kallon sama da ƙasa mai ƙosan ta bita da shi sannan ta ce. "Ke a wa zan baki kyauta?, ke baki ga kowa garin ya yi masa zafi ba ne?, kin san yadda wake yake tsada kuwa, to ko na goma wanda na san ma babu sai dai ashirin ba zan iya baki ba. Maza ki bar nan wajan. Ke ana ganin ki ma an ga wacce ta gudo daga magarƙama, to ki bar nan kafin nayi miki ihuun ɓarauniya". Nan take ran Zahra ya ɓaci ta dubi matar ta ce. "ke wace iriyar gajarabul asaratun donkey ce?, shin na ce miki ki bani ƙosai ne ko an gaya miki cewa ni mabaraciya ce?, na zo na taimaka miki shi ne za ki wani yaɓa min magana da wannan hangamammen bakin naki". Tashi mai ƙosan ta yi daga kan kujerar da take sannan ta ce. "Ni ce mai hangamammen bakin?, ke dama kallo ɗaya za'a miki a san ƴar fashi da makami ne domin kuwa shi ne gadon ahalin ku. Gaskiya uwar ki bata iya haihuwa ba". Ba zato ta ji saukar mari kan fuskarta. Nan take hankulan jama'a ya garzayo wajan yayin da mutane suka taru. Nuna mai ƙosan Zahra ta yi ta ce. "Zan iya tolerating komai amma banda zagin mahaifiyata, idan har bakya son ki ganki kwance a gadon asibiti to ki kiyaye harshen ki. Wannan marin da nayi miki ba mari ba ne shafa miki fuska kawai nayi wanda zanyi miki next sai dai aga tiririn hayaki yana fita daga kunnuwanki. Shashashan banza ƴar kutumur kitabi dangin gajeru kawai". Tana kaiwa nan ta bar wajan. Yayin da mutane suka bita da kallo. Ganin yadda mutane suke binta da kallo ya sa ta dube su ta ce. "ku kuma ya aka yi ne?, sa'idinawa kawai". Ta faɗa tana mai barin wajan baki ɗaya. Barin wajan mutane suka yi . Dafa kumatun ta mai ƙosai ta yi yayin da take jin fuskanta nayi mata zugi dan ba ƙaramin shigar ta marin ya yi ba. Simi-simi ta koma kan aikin ta. Ci-gaba da tafiya Zahra ta yi. Nan take hadari ya taso yayin da aka fara iska mai ƙarfi. "Wayyo Allah kodai ruwa za'a yi ne?, ni yanzu ina zanje na zauna". Bata yi aune ba ta ga an fara yayyafi. Ganin hakan ya sa ta ƙara sauri chan ta hango wani kango ba ta yi wani tunani ba ta yi saurin nufar in da kangon yake sannan ta shige ciki. Tana shiga aka zuge da ruwa. Hamdala ta yi tana mai juya wa. Nan take gabanta ya faɗi!, ganin rukunin ƴan daba a cikin wajan babu abin da suka yi sai shaye-shaye. Yayin da gefe guda kuma mata biyu ne zaune sai sharɓan kuka suke. "Barka da ƙarasowa kyakkyawar budurwa. Kaga wata tsuleliyar budurwa wannan kam ta yi". Cewar ɗaya daga cikin ƴan shaye-shayen. Tashi suka yi gaba ɗaya suka fara tunkarar in da Zahra take. ****** Taxi ɗin su bai tsaya ko ina ba sai gaban family House ɗin su Aliyu. Sauko wa suka yi daga cikin motan yayin da suka biya mai taxi ɗin. Kallon ƙofar gidan Daddy ya yi cike da kewa ya ce. "Gaskiya nayi kewan wannan gidan, yanzu shekaru ashirin kenen rabon da na ɗora ƙafata kan wannan gidan". Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Daddy this place is so annoying let's just go back to America please". Maida kallonsa Daddy ya yi kanta ya ce. "Nan shi ne asalin gidan mu Safeera ba America ba, ya kamata ki gane hakan". Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Rabu da ita kawu, idan ta ci tuwo za ta san cewar ba rayuwa take yi ba a America nan shi ne in da jin daɗi yake". Yana kaiwa nan ya fara ƙwanƙwasa ƙofa. Nan take mai gadi ya buɗe. Ganin wanda ke bakin ƙofar ya sa shi wangale musu gate tare da yi musu barka da zuwa. Washe baki Daddy ya yi ganin har izuwa yanzu Baba Sule ne yake yi musu aiki. "Baba sule har yanzu kana nan dama?". Amsa Baba Sule ya bashi da cewa. "Ina nan ɗana ya ka ke?, kaje ƙasar ƴan gayu ka ƙi ka dawo ko?, wannan ita ce ƴarka?". Amsa Daddy ya bashi da cewa ƙwarai kuwa ita ce ƴa ɗaya tilo da Allah ya bani". "Masha Allah gata kuma kyakkyawa tabarakalla. Ku shigo na san su Alhaji za su yi fari cikin ganin ku". Shiga ciki suka yayin da suka tarar babu kowa a compound ɗin. Sai yara wanda ke wasa, babu abin da ka ke ji sai ayaniyar yara. Tsayawa yaran suka yi suna mai kallonsu. Da gudun su suka tawo tare da zuwa suka rungume Aliyu. "Welcome back, brother Aliyu where have you been?, we missed very much". Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Yanzu dai ai na dawo kuma na tawo muku da chocolate masu dad'i. Ina su grandma da grandpa suke?". "Suna cikin gida". Yaran suka faɗa Jin yara suna ta ihuu na farin ciki ya sa mutanen gidan fitowa baki ɗaya. Mamaki ne ya kama kowanensu ganin su Daddy a wannan lokaci. Kallon Daddy Grandpa ya yi cikin ɓacin rai ya ce. "Lallai sannu Ibrahim, wato tun bayan shekaru ashirin da ka saka ƙafa kaida matar ka ku ka fice daga gidan nan baka sake garzayo wa ba sai yanzu ko, me ka zo yi to maza ka koma domin kuwa bamua da buƙatar ku". Kallon Grandpa Grandma ta yi ta ce. "Aba mai gida, bai kamata ka faɗi haka ba, koba koma shi ɗin ɗan ka ne kuma ya zo ne tare da matarsa da kuma ƴarsa". "Yi min shiru Amina, ɗana ne kuma ni nafi ki iko a kansa. In dai har yana son zama a cikin wannan gidan to ya zama dole ya tattara ina shi ina shi ya dawo nan da zama na har abada ba tare da ya koma chan ƙasar kafirai ba, sannan kuma dole ƴarsa ta auri Aliyu ko tana so ko bata so". Zaro idanuwa waje Safeera ta yi jin cewar ba za su koma America ba. Murmushi Daddy ya yi ya ce. "Shi ke nen Abba in dai abin da ka ke so kenen na amince zan zauna tare da matata da kuma ƴata, sannan kuma batun auren Safeera wannan a zaune take dole Aliyu ya aure ta tun da abin da ka ke so kenan". A zabure Safeera ta ce. "No Daddy, ta ya ya zamu dawo nan da zama na har abada, how do you expect me to marry this guy that has a mental issues?. No it can never be possible I can't". "Will you keep that your dirty mouth shut. Are you out of your senses?, what's wrong with you Safeera?, he is your grandpa, he knows what is bad and good for you okay". Mom ta faɗa cike da ɓacin rai. Fashe wa da kuka Safeera ta yi ta ce. "Wallahi ba zan zauna a nan ba, i rither die than to stay in this environment". Tasss ta ji saukar mari kan fuskarta. Dafe ƙuncinta ta yi cike da mamaki yau karo na farko da a aka taɓa sanya hannu kan fuskarta. Ɗago da rinannun idanuwanta Mom ta yi ta ce. "Waɗan nan families ɗin ki ne karki kuskure ki faɗi magana mara daɗi a kansu". Murmushi Grandma ta yi tare da janyo Safeera jikinta ta ce. "Aba Zainab me ya sa za ki mare ta?, yi haƙuri jinki jikata, zamu yi maganin ta. Maza ku tawo mu shiga daga ciki. Shiga ciki suka yi yayin da suka samu guri a parlour kowa ya zauna. Nan suka shiga yin labarai na yaushe rabo. Suna yi suna dariya abun gwanin burgewa. Dubansu mahaifin Aliyu ya yi ya ce. "Me ku ke so a kawo muku?, zansa su Zuwaira su kawo muku". Nan take wasu kyawawan ƴan mata guda uku suka fito daga cikin kitchen hannun kowannensu riƙe da abinci. Nan take suka ajiye abincin da lemukan hannayensu tare da fara serving ɗin su Daddy. "Zuwaira ki miƙa wa Safeera nata ta ci". Cewar Abba wato mahaifin Aliyu. "Tom Abba bara na zuba mata". Zuwaira ta faɗa tana mai ƙoƙarin zuba abinci a plate. Kawar da kai gefe Safeera ta yi ta ce. "Bana son, ba zanci wannan ƙazamin abincin naku ba". Kallon ta kowa ya yi cike da mamaki ganin irin hali na Safeera. Abba ne ya ce. "Ke kuwa ki ɗanɗana ki ci za ki ji daɗin sa fa, shi iyayen ki suke ci kafin su tafi ƙasar America, tuwo da miyan taushe gashi ya ji kayan haɗi maza ki sauko m muci". "Bana so kuci kayan ku". Ta faɗa tare da kwanta kan kafaɗar grandma ta ce. "Grandma ɗita ce kawai mai mutunci a cikin ku gaba ɗaya baku da mutunci, ita ce kawai ta yi min maraba da zuwa. Ku kuma kamar baku san da halitta ba , karo na farko kunga yarinyar ɗan ahalin nan maimakon kuyi farin ciki da hakan sai ku wani yi kamar baku ga mutum ba, hakan me zanci abinci". Dafe kansa Abba da sauran mutanen parlourn suka yi sannan Grandpa ya ce. "Kiyi haƙuri shalele mun san mun aikata kuskure a gafarce mu ko". Ƙura mata ido Abba ya yi ya ga suna matuƙar kama da ƙanwar sa Laila. "Laaa Baba ka ga abin mamaki, ƴar Ibrahim tana matuƙar kama da Laila sosai ku duba ku gani". Nan take gaba ɗaya suka maida idanuwansu kan Safeera yayin da Safeera ta yi baki tana kallonsu a ranta tana cewa. "Wace ce kuma Laila?". Zumbur Grandpa ya ɗago idanuwansa tare da gyara zamansa a kan wheel chair ɗin sa sannan ya ce. "Kada ku sake kawo min maganar Laila a in da nake na ga muku, ita ce silar faɗa wa ta cikin wannan yanayin, na tsane ta" . Shiru Grandma ta yi damuwa ɗauke kan fuskarta ta ce. "Allah muna yi masa laifi ya yafe mana ballantana mu ƴan adam, ya kamata a ce komai ya riga ya wuce mai gida". ****** Da gudu su Khairiya suka fito tare da su Ramlat da Usman. Tsayawa suka yi chakk ganin Umar da yarinyar jeji. Kallon Amrah Khairiya ta yi ta ce. "Yahya wannan fa daga ina?". Kallonsu Umar ya yi gaba ɗaya ya ce. "She is your new sister, ina son ku ɗauke ta matsayin ƴar uwarku, bana son naji abu wanda ya saɓa wa hakan ba. Ku kaita part ɗinku ku chanza mata kaya sannan kusa ta yi wanka tare da yi mata kwalliya kunji ni ko. Ita ma daga yanzu a nan zata dinga zama". "Wow yahya she is so amazing she looks pretty and cute, oh m God green even ne da ita". Ramlat ta faɗa tana mai jan hannun Amrah suka shigar da ita part ɗin ta. ************** "Kai ku dakata me ku ke shirin aikata wa?". Zahra ta faɗa tana mai ja da baya. Dariya ƴan daban suka kwashe da shi sannan ɗaya daga cikin su ya ce. "Za ki iya dakatar da mu ne?, muna so ne mu haɗa da ke, ƴar cika kamar ki kice ba zamu yi miki komai ba". Ya faɗa yana mai babbakewa da dariya. Cikin ɓacin rai Zahra ta ce. "Kuna da hankali kuwa?, ku samm bakua daraja mace ne?, idan baku saki ƴan matan nan kun basu haƙuri ba saina yi maganin ku baki ɗaya". Dubanta ƴan daban suka yi suka ce. "Sarkin yawa yafi ƙarfin sarki, ta kanki zamu fara". Suna kaiwa nan suka sa hannu tare da jan Zahra. Nan take Zahra ta kurma ihuu!, yayin da ta yi nasarar ƙwace kanta. Daga nesa ta hangi wata ajajjiyar bulala. Da sauri ta nufi in da bulalar take tareda ɗauka sannan ta nufi in da suke. Bata yi wata-wata ba ta fara zuba musu bulala a jiki. Ihuuu ƴan shaye-shayen suka fara yi suna mai ƙoƙarin guduwa. "Ina za ku je?, baku tsageru ba, nafi ku tsageranci, shashashu ƴan iska kawai marasa ɗa'a. Saina yi maganin ku, idan gomnati bata ɗauki mataki a kan mutane ire-iren ku ba mu zamu ɗauka". Da sauri ta yi wa matan alama da su fita daga cikin wajan. Da sauri matan suka tashi tsaye tare da fita daga cikin kangon suka bar Zahra da ƴan shaye-shayen. Cikin rashin sa'a ta ji saukar naushi kan cikin ta. Nan take ta kurma wani azababbiyar ƙara!. Su Daddy da ke zaune babu zato suka ji Safeera ta kurma wani irin razananniyar ƙara! Mai matuƙar firgitarwa. Ɓangaren Amrah ma haka ƙara ta saki tare da fusge hannunta daga na Ramlat. Nan take jami'an gidan suka nufo in da suka jiyo ƙaran yayin da shima Umar ya sauko daga kan upstairs da sauri. "Me ku ka yi mata?". Girgiza kai kowanensu ya yi ya ce. "Wallahi babu abin da muka yi mata kawai muna cikin tafiya muka ga ta kurma ihuu". ***** Safeera what's going on?, me ya faru?". Daddy ya tambaye ta. Kuka Safeera ta fara yi hannunta dafe da cikinta ta ce. "My stomach, ciki na wayyo ciki na!". 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 *NI FA ƳAN UKUN NAN LAMARIN KU SAI AN HANKALI🧐😏😏. DA ZARAR ABU YA SAMI ƊAYA SAI SAURAN SUNJI A JIKIN SU🧐. MUJE DAI ZUWA*. KADA KU MANTA DA LIKING DA KUMA SHARE TARE DA COMMENTS PLEASE DOMIN ALLAH 🙏🙏🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣7️⃣▶️2️⃣8️⃣ *_________________________________________________* Hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Safeera ke birgima s ƙasa tana ihuun cikin ta. Da sauri Aliyu ya ɗauki waya tare da kiran family Doctor ɗin su. Ɗaukar Safeera Aliyu ya yi tsreda shigar da ita cikin ɗaki sannan ya kwantar da ita a kan gado. Cikin lokaci ƙalilan likitan su ya zo tare da fara duba Safeera. Yayin da gaba ɗaya family ɗin suka kasa zaune sai kai kawo suke a cikin gidan. ***** Ɓangaren Amrah kuwa. Ɗaukarta Umar ya yi sannan ya nufi part ɗin sa da ita yayin da su Khairiya da Usman suka bi bayan shi. Yana zuwa ɗakin shi ya kwantar da ita kan gado yayin da ya sa su Khairiya suje su haɗa mata shayi mai kauri. Fita suka yi suka bar Umar da Amrah a cikin ɗakin. Tashi Umar ya yi tare da fita domi ya je pharmacy domin siyo maganin ciwon ciki. **** Kwashe wa da dariya ƴan shaye-shayen suka yi yayin da suka dubi Zahra wacce ke kwance cikin mawuyacin hali sannan suka ce. "Ke ba ƴar ranin wayo ba, yanzu zamu yi duk abin da muke sonyi da ke ba tare da wani ya dakatar da mu ba". Suna kaiwa nan suka nufi kanta. Nan take suka ji karan motocin ƴan sanda. Da mugun gudu suka fice daga cikin kangon yayin da suka bar Zahra ita m ɗaya a cikin wajan. Shiga cikin kangon suka yi tare da matan da suka fita daga cikin kangon ɗazu. Nan suka tarar da Zahra kwance cikin mawuyacin hali. Kallon ƴan sandan matan suka yi sannan suka ce. "Yauwa ita ce ta cece mu daga wajan ƴan daban dan Allah ku taimaka ku kaita asibiti". "Shi ke nen". Ɗaya daga cikin ƴan sandan ya faɗa. Kana ya saka mata ƴan sanda suka cinciɓi Zahra, basu zarce ko ina ba sai asibiti. Shigar da ita ciki asibitin suka yi. Nan take nurse's suka fito da gado tare da karɓar ta sannan suka shige da ita cikin asibitin. Nan take suka fara ba ta taimakon gaggawa. ********* Bayan su DPO sun isa garin Jigawa ya sa suka wuce magarƙama kai tsaye. Suna zuwa ya fito yayin ya tarar da Hajiya Binta ta yi tagumi. Zuwa ya yi daff da ita. Ganin su ya sa Hajiya Binta saurin miƙe wa sannan ta ce. "DPO ina Zahra take?". Kallonta DPO ya yi tare da ba ta amsa da cewa. "Ƴarki ta gudu daga sjaan mu, yanzu haka tana Kano bamu san in da take". Gaban Hajiya Binta ne ya yanke ya faɗi!, cikin tashin hankali ta dubi DPO ta ce. "Kamar ya baku ganta ba?, aba DPO kaima fa ka san Zahra amanarta aka damƙa min, mene ya sa baku nemo ta, na dai san aikin ku ne yin hakan. Kuma kai da kanka ka san babu in da ta sani a wannan garin balle a ce garin Kano wanda ba ta ma taɓa zuwa ba sai a wannan karan. Ni dai gaskiya ka sa a nemo ta in ba haka ba zan sa a kai ƙarar ku wajan shugaban ƴan sanda". Ajiyan zuciya Dpo ya sauke!, sannan ya ce. "Ki kwantar da hankalinki Binta, ina da tabbacin cewa Zahra za ta iya kula da kanta domin kuwa ba shiru-shiru bace, kai kanki kin san fitinanniya ce ba ta jin magana, ita ce ta gudu daga hannun mu. Karki damu zan saka a nemo ta duk in da take kuma za ta dawo da izinin Allah". ************* *ƘASAR CHINA* "Hello MK, da gaske ne cewar matata tana raye tare da ƴaƴanta?". Daga ɗayan ɓangaren Mk ya bashi amsa da cewa. "ƙwarai da gaske yaranka tare da matarka Laila gaba ɗaya suna raye". Ajiyan zuciya dattijon ya sauke!, tare da yin hamdala sannan ya ce. "Alhamdulillah Allah na gode da ya kasance matata tare da yarana suna raye. Dan Allah ka tabbatar da kana kula da shige da ficen su, bana son su kasance cikin kaɗaici kowanen ka shiga cikin rayuwarta domin kare ta, kai ɗin jami'i na ne kuma na yarda da kai ɗari bisa ɗari, ina so kayi min wannan alfarman dan Allah". Daga ɗayan ɓangaren Mk ya ce. "Kai ɗin kamar walihi ka ke a gare ni Sir Bashir, a kan me ya sa ba zan yi abin da zai faranta maka ba, bayan kuma kai ka faranta mu tare da iyalaina, ka fito da ni daga cikin magarƙama kuma ka sa an maida ni kan aiki na, dole nayi maka duk abin da ka ke so. In sha Allah zan shiga rayuwar kowacce a cikin su domin kare su. Ba zan taɓa barin Gov.Musa Muhammad ya ci galaba ba". Yana kaiwa nan ya katse wayar. Ajiyan zuciya Sir Bashir ya sauke!, sannan ya kwanta kan lallausar gadon sa ya ce. "Tabbas na aikata babban kuskure, na san ba za ki yafe min ba Laila, duk abin da ya faru ba laifi na ba ne, ban zo nan ba domin na sa a cutar da ke, na zo ne kawai saboda mahaifin ki ya bani umarnin yin hakan. Ina matuƙar ƙaunar ki matata". ********************** *NIGERIA* Safeera kuwa, bayan likita ya duba ta ya ba ta magani ta sha. Cikin ƙankanin lokaci bacci ya yi hawon gaba da ita. Yayinda Grandma ta saka su Zuwaira da Salma su yi mata farfesun kaji". Fita suka yi suka bar iya Aliyu da kuma Safeera a ciki ɗakin. Tsaya wa Aliyu ya yi yana kallon kyakkyawar fuskar Safeera. Tagumi ya yi cikin ransa ya ce. "Yarinyar nan ba dai kyau ba, duk wanda ya same ki gaskiya ya yi sa'ar mata". Ya faɗa cikin ransa yayin da ya ci gaba da kallo yadda take fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali. ****** Bayan Umar ya dawo ya tarar da su Khairiya su haɗa wa Amrah shayin. Shiga cikin ɗakin suka yi a tare. Cikin mamaki kuwa suka tarar ba ta cikin ɗakin. Zaro idanuwa waje gaba ɗaya suka yi yayin da Ramlat ta ce. "Ina kuma ta je?". Dafe kansa Umar ya yi sannan ya ce da su. "Maza ku bincika cikin gidan nan gaba ɗaya, na san ba za ta wuce cikin nan ba". Haka gaba ɗaya suka bazu cikin gidan suna nemanta, yayin da Umar ya saka jami'ai suma suka shiga bincika wa. Neman duniya sunyi amma basu ganta ba. Nan take wani tunani ya faɗo wa Umar. Da sauri ya nufi garden yayin da suma su Usman suka bishi a baya. Dube-dube suka fara yi. Tsayawa Umar ya yi chakk jin musharin mutum. Ganin ya tsaya ya sa suma suka tsaya. Shiru kowanensu ya yi. Kasa kunne Umar ya yi domin jin ta ina musharin yake fitowa. Babu zato ya ji Khairiya da Ramlat sun fasa ihuu!. Da sauri ya dube su sannan ya ce. "Mene ne ya faru?". Baki na rawa suka haɗa baki wajan faɗin. "Ka duba sama kan bishiya". Kamar yadda suka ce babu musu Umar ya duba sama. Abin da ya gani ne ya bashi mamaki. Ganin Amrah ya yi kwance kan bishiya sai sharɓan baccin ta take. Dafe kansa Umar ya yi ya ce. "Ya salam!, wannan yarinyar ta riga da ta saba da zaman jeji, idan ba nan na maida da ta ba ba za ta taɓa iya zama damu ba". "Ko ta ya ya ma ta iya hawa kan bishiyar nan". Usman ya faɗa. Duban jami'an gidan Umar ya yi sannan ya saka su su ɗauko masa igiya. Kamar yadda ya umarta haka suka je suka ɗauko igiya mai matuƙar kauri sannan suka ɗaure cikin bishiya da shi tare da riƙe shi gamm a hannun su. Kama igiyar Umar ya yi tare da fara hawa kan bishiyar. Yayin da jami'an suka ƙara riƙe igiyar sosai a hannunsu. Jan igiyar Umar ya fara yi yana mai hawa kan bishiyar har ya isa in da Amrah take sannan ya janyo ta. Zumbur ta miƙe tsaye. Nan take Umar ya ja da baya. Cikin rashin sa'a kuwa igiyar ta tsinƙe. Nan take su Ramlat suka saki ihuu domin kuwa Umar yana shirin faɗo wa ne daga saman bishiyan. Ganin yana ƙoƙarin faɗi ƙasa ya sa Amrah saurin riƙe masa hannu yayin da ta fara jan shi kan bishiyar. Hawa da shi ta yi kan bishiyar yayin da Umar ya shiga sauke ajiyan zuciya. Kallonta ya yi sannan ta ce. "Maza zo mu sauka ƙasa, bana son wani abu ya same ki, za ki iya faɗo wa ki karye". Girgiza kai Amrah ta yi. Babu zato ya ga ta dira ƙasa ba tare da tsoro ba. Zaro idanuwa waje gaba ɗaya suka yi ganin yadda ta dira ba tare da wani tsoro ba. Furzar da iska mai zafi Umar ya yi ciki ransa ta ce. "To ta ina zan fara sauka daga kan bishiyar nan?, hanya ban jawo ka kaina ba kuwa?". Kallon saman bishiyar Amrah ta yi sannan ta yi mai nuni da ya sauko. Ba tare da wani tsoro ba Umar ya fara bi ta jikin bishiyar yana sauko wa a hankali. Kai hannunsa Umar ya yi domin riƙe bishiyar sosai. Cikin rashin sa'a hannun sa ya suɓuce ya tafi ƙasa daga kan bishiyar. "Yahya Umar!". Gaba ɗaya suka furta. Ganin ya kusan faɗo wa ya sa Amrah ta buga tsalle tamkar ƴar biri tare da chafko Umar sannan ta ajiye shi ƙasa". Sauke ajiyan zuciya suka shiga yi tare da yin hamdala. Kallon Amrah su Khairiya suka tsaya yi sannan suka ce. "Wannan ita ce ma mace mai kamar maza, irin wannan ƙarfi haka, daga gani ƴar daji ce". ************ "Ta ya ya hakan za ta kasance?, farko na shiga room 8 na ga Amrah q ciki, bayan na kuma koma wa cikin room ɗin da na baro Amrah na kuma ganinta a ciki. Tabbas babu ta yacce hakan zai yiwu dole dai mutum biyu na gani. Amrah green eyes ne da ita, sannan kuma ƴaƴan Mrs Laila da na sani mai green eyes ne sai blue eyes, dole dai ta room 8 blue eyes ne da ita. Idan kuwa har da gaske ne blue eyes ne da ita to babu tantama ƴaƴan Mrs Laila ne". Aka Nurse Nadiya ta shiga yin magana ita ɗaya kamar zautacciya. ********** *Daji*. Babu abin da ka ke gani a wajan sai mata wanda aka ɗaɗɗaure musu hannu da baki. Kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar da cewa ba ƙaramin jigata suka yi ba. Yayinda ɓangare guda allurori ne a ƙasa wanda aka yi musu domin a kawar musu da tunani. Kuka sosai suke yi. Ɓangare daya kuma maza ne hannunsu riƙe da bindigogi yayin da fuskokinsu gaba ɗaya yake a rufe. Baka iya ganin komai na fuskarsu sai iya ƙwayar idanuwansu. "Your excellence, matan da muka yi kidnapping yanzu za su kai kumanin 250. Yanzu muna jiran cewar ka ne domin a je a siyar da su a kasuwa, za'a mu yi safarar su ne zuwa ƙasashen waje yayin da kai kuma kuɗaɗe ne kawai za su dinga shigo maka". Murmushi mahaifin Umar ya yi sannan ya ce. "Well done guy's, aikin ku na kyau yadda ya kamata. Maza ku sa su a Bus, zan saka a ƙaro muku bus domin Bus ɗaya ba zai isa ba. Sannan kuma kamar yadda muke yi abun nan cikin sirri bana son ɗana da kuma ƴan sanda su sani, domin idan suka sani abun ba zai yi min daɗi ba". "Yes Sir". Mutumi ya faɗa. Ɗaya daga cikin matan wajan ne ta yi nasarar kunce kanta da kuma kunce bakin ta. Zumbur ta miƙe tsaye tare da kallon Gov. Musa Muhammad sannan ya ce. "Kai mugu azzalumi, ka sani cewa ƙarshen ka ba zai yi kyau ba, kana ɗaukar mu da ƴaƴan mu wanda muka damƙa maka su a matsayin amana kana safarar su izuwa ƙasashen waje". Duban kanta dattijuwar ta yi tare da tsugunna kan gwiwowinta ta ce. "Da wannan hannun nawa na ɗauki dutse na bugi Mrs Laila da shi. Tabbas na aikata kuskure, nayi zaton Mrs Laila ita ce muguwa ashe kaine asalin tantiri, ka ɓata mata suna a idanun duniya, ka sani cewa koda mun barka Allah ba zai barka ba. Kuma ka sani cewa Allah saiya tona maka asiri". Kallonta Gov. Musa Muhammad ya yi tare da kwashe wa da dariya. *********** Ɓangaren Zahra kuwa bayan anyi mata treatment ta samu bacci ya ɗebe ta. Saida ta ɗau hawanni biyu tana bacci kana daga bisani ta buɗe idanuwanta. Nan take idanuwanta suka sauka a kan mahaukaciyar da ta gani kwanaki. Miƙe wa ta yi zaune tana mai kallon matar da ke zaune kusa da ita. Shafa fuskarta mahaukaciyar ta yi murmushi ɗauke kan fuskar ta. Lokaci ɗaya Zahra ta ji ƙaunar matar ya shiga ranta ba tare da sani dalilin hakan ba. Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Wace ce ke?, me ya sa a koda yaushe ki ka ƙoƙarin zuwa in da nake?, shin kin san ni ne?". Girgiza kai kawai mahaukaciyar ta yi. Shigowa likitoci suka yi yayin da suka kama hannun mahaukaciyar domi fitar da ita. Fuffuzgewa mahaukaciyar ta fara yi. Kallonsu Zahra ta yi sannan ta ce. "ku ƙyale ta mana ya za ku wani kamata kamar yarinya za ku fita da ita, wannan sam ba adalci ba ne". Kallonta ɗaya daga cikin likitocin ya yi sannan ya ce. "Ita ɗin fa mahaukaciya ce, yanzu shekaru ashirin kenen tana cikin wannan asibitin. Kuma yanzu aka ma magani zamu je mu ba ta bawai cutar da ita zamu yi ba". Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "To kuyi mata mana a hankali bawai sai kun dinga janta ba, yanzu da wannan mahaifiyar wani a cikin ku ne za ku ji dad'i ku ga wani yana janta a ƙasa kamar kayan wanki?. Maza ku cika ta kafin na ɓata muku rai". Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace. 💃💃💃💃💃💃💃💃 COMMENTS, LIKE, AND SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏 🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B (Zinariyar Jajirtattu) https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣9️⃣▶️3️⃣0️⃣ *_________________________________________________* "Kinga malama muna kan aikin mu ne, ita ɗin mara lafiya ce kuma nauyin kula da lafiyarta yana rataye a wayar mu ne , don aka Please ki bar mu muyi aikin mu. Ke mene ne ma naki a cikin tun da ita ɗin ba ɗaya daga cikin dangin ki ba ce ko ko kuma ince ita ɗin ba mahaifiyar ki bace don aka ki ƙyale mu". Ɗaya daga cikin su ya faɗa yayin da suka fitar da ita daga ɗakin. Ajiyan zuciya Zahra ta sauke!, sannan ta ce. "Kuma fa maganar sa aka ne, me ya sa nake nuna damuwa ta sosai a kan matar?, sa'anan kuma me ya sa naji ta shiga raina sosai?". Basar wa ta yi sannan ta ce. "Ki basar kawai, naji ta shiga raina ne kawai". Aka ta cigaba da magana ita ɗaya. Miƙe wa tsaye ta yi tare da fizge drip ɗin da aka saka mata. Ya mutse fuska ta yi ganin yadda jini ke fita a saitin in da ta fizge drip ɗin. Sannan ta ɗauki cotton wool da ke ajiye kan table ta saka a wajan. Kallon taga ta yi ta waje ta ga mutane na fice da shige. "Ya kamata na tafi daga nan". Ta faɗa tana mai dafa cikin ta da sauri jin yadda yake murɗa mata. "Wayyo ni Fatima Zahra, yanzu me zan ci?, gashi ko biyar bana magani, ya kamata na tafi daga nan wajan". Ta faɗa tana mai fice wa daga cikin ɗakin. *************** Cikin masarauta kuwa, ko ina ka kalla tarin jama'a ne, tare da fadawa a tsatsaye. Yayin da kowa ke riƙe da kwanon abincin. Junaid ne zaune gefe ɗaya yayin da gefensa kuwa tarin buhun shinkafa. Babu abin da yake sai faman miƙa wa jama'a kayan abinci. Al'adar masarautar kenen a duk wata ana sadakar avinci tare da kuɗaɗe ga talakawa marasa ƙarfi. Fitowa mai martaba ya yi. Nan take mutane suka fara kwasar gaisuwa tare da yi masa kirari. Zama ya yi kan kujera kusa da Junaid yayin da ya cigaba da zuba ido ga abin da Junaid yake yi don ya sanshi da albazaranci. *********** Kallonta Gov. Musa Muhammad ya yi sannan ya ce. "Au aba da gaske?, sune za su kawo ƙarshen nawa?, gaskiya kina da abin dariya. To ki sani kafin ma su san cewa ni ne na wargaza su nayi sanadin rabuwarsu izuwa gurare daban-daban zan gama da su. Don aka ba zan kashe ku ba yanzu, domin idanuwan ku ya gane muku abin da zan aikata, zan sa ne a fitar min da ku daga wannan ƙasar gaba ɗaya". Ya ƙarashe maganar yana mai kallon ɗaya daga cikin yaran nasa sannan ya ce. "Maza ku saka su a mota ku tafi da su, ni yanzu zan wuce gida". "Done". Suka furta gaba ɗaya. Shiga cikin motarsa Gov. Musa Muhammad ya yi yayin da jami'an sa suka ja mota tare da barin cikin dajin baki ɗaya. ******** "Habib wai me yake damun yarinyar ka Safeera ne?". Cewar Grandpa. Amsa Daddy ya ba shi da cewa. "Wallahi Abba nima ban sani ba, na rasa me yake damunta, aka ma lokacin da muke a America ta faɗi kasa saida muka zo nan Nigeria sannan ta buɗe idanuwanta. Aliyu ya ce min ko Aljanu ne da ita, amma ni samm ban yarda ƴata tana da aljanu ba, ban san mene ne abin yi ba". Sauke ajiyan zuciya gaba ki ɗaya suka yi sannan suka ce. "Dole dai akwai wani abu a ƙasa, babu ta yadda za ta dinga faɗuwa aka kurun ba tare da wani ya yi mata abu ba". Cewar Grandma. Gyara zamansa Grandpa ya yi kan wheel chair sannan ya ce. "Maza ku zo muje wajan wani tsohon aboki na a chan wani ƙauye, shi ɗin babban malamin ruƙiya ne, aljanu, mayu da sheɗanu tsoronsa suke dole muje mu kawo sa da kannu domin ya duba ta. na san shi zai san koma mene ne yake damunta". Grandpa ya faɗa tare da ƙwalla wa Aliyu kira. Nan Aliyu ya fito daga ɗakin. Kallon Aliyu Grandpa ya yi sannan ya ce. "Aliyu zamu fita yanzu, zamu je mu ɗauko maganin ruƙiya mu kawo domin sanin meke damun Safeera. Don aka ka zauna ka kula da Safeera mu zamu je mu dawo, su Zuwaira basua nan sun tafi makaranta don aka na baka amanar Safeera idan ka ɓata mata rai sai nayi maganinka". Girgiza kai Aliyu kawai ya yi sannan ya ce. "Tom shi ke nen Kaka sai kun dawo". Ya faɗa yana mai koma wa ɗaki da Safeera take. Fita su grandma suka yi tare da shirya wa suka shiga cikin motocin gidan sannan suka fice daga gidan. Kai tsaye suka nufi hanyar Gujingu. ******** Koma wa Aliyu ya yi kan kujerar da ke fuskantar Safeera sannan ya cigaba da zuba mata idanuwansa. A hankali Safeera ta fara buɗe idanuwanta a yayin da a ƙarshe ta yi nasarar buɗe su bako ɗaya tare da sauke su kan Aliyu wanda ya zuba mata idanuwa sai kallonta yake kamar wani maye. Zumbur ta miƙe zaune sannan ta ce. "Ya dai mene ne ka ke yi tare da ni?, where is my Mom?". Furzar da iska Aliyu ya yi ya ce. "Sun tafi wajan malamin ruƙiya domin a kawo shi ya yi miki ruƙiya aljanun da ke jikin ki su fita". Nan take ran Safeera ya ɓaci ta ce. "Kamar ya Aljanu?, ni ce mai aljanu?, koda yake ba laifin ku ba ne ba". Taɓe baki Aliyu ya yi ya ce. "Ke Safra ki ke da suna ko me, ki dinga sarrafa harshen ki domin ni hannu na rawa yake zan iya bugar bakin ki da shi". Cikin jin haushi Safeera ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Ka ga malam sunana Safeera ne ba Safra ba idan ba za ka iya cewa Safeera ba ka kira ni da nickname ɗina wato Diana. Sannan kuma da ka ke cewa za ka buge baki na kai a waye za ka ce za ka buge baki na?, wallahi ka fita daga cikin harka ta na gaya maka. Kuma wallahi su Mom na dawo wa zamu tattara komai namu mu bar gidan nan, dan ni gaskiya ba zan iya rayuwar wannan ƙasar ba". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin fita daga cikin. Da sauri Aliyu ya fizgo ta jikinsa tare da matse ta ya ce. "Kada ki manta ni da ke ne kaɗai a gidan nan, idan ki ka yi min rashin kunya zan zane ki kuma na zane banzam sannan shi wannan ƙasar da ki ka ce bakya so na ga dai iyayen ki ƴan nan ne ba'a ƴan chan ƙasar ba, don aka makntain your word's okay". Cire jikinta ta yi daga na shi sannan ta ce. "Kada ka sake ɗora hannun ka a jiki na, domin kai ɗin ba miji na ba ne okay, you don't have the right to touch a responsible lady like me okay, please don't add to my anger this afternoon". Murmushi Aliyu ya yi tare da janyo ta sannan ya samu bakinta tare da kama wa ya fara murɗawa. Nan take ta saki ɗan ƙaramin ƙara na raɗaɗi!. "Leave me alone". Ta faɗa hawaye na bin ƙuncinta. Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "In fa ki ka ce za ki yi jayayya da ni sai dai kici wuya, kuma da ki ke wani ikirarin cewa ni ba mijin ki ba ne, na san da hakan ai amma kuma an your future husband so ya kamata tun yanzu na fara saita ki kafin ki shiga gida na". Ya faɗa tare da sakin leɓenta wanda suka ƙara rinewa suka yi jajir saboda jan da Aliyu ya yi musu. Riƙe leɓenta Safeera ta yi sannan ta ce. "Wallahi Allah ya kiyaye na zamo matar ka, kuma in dai suka dawo saina faɗa wa Grandma abin da kayo min kuma wallahi bashi ka ɗauka domi saina rama". Ta faɗa tare da fice wa daga ciki ɗakin. Chan ta samu guri a parlour ta zauna tare da kunna tashar Bollywood ta fara kallo. Saida ta ɗau lokaci sosai tana kallonta cikin nishaɗi hankalinta kwance take kallon abinta. Fitowa Aliyu ya yi tare da samun guri ya zauna a parlourn sannan ya ɗauki remote tare da chanza tashar izuwa tashar Ball. Nan take ran Safeera ya ɓaci dubansa ta yi ta ce. "A kan mene ne za ka zo ka wani chanza min channel ɗin da nake kallo?, maza ka maida min abuna. Kai na fahimci cewa baka son zaman lafiya kuma ni ma zan nuna maka cewa nafi ka rashin son zaman lafiya, maza ka mayar min". Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "To Mama ɗanki zai yi kamar yadda ki ka ce". Ya faɗa tare da sakin wani killer smile sannan ya ce. "Nan ɗin ba gidan ku ba ne balle ki saka wani doka ko order okay, nan ɗin gidan mu ne, don aka be careful". ************** Jan kumatun Amrah Khairiya ta yi sannan ta ja hannunta suka shigar da su part ɗin su. Nan suka cire mata grasses ɗin jikin ta tare da ɗaura mata towel sannan suka nufi toilet da ita. Nan suka shiga wanke mata gashin kanta wanda suka kwanta har gadon bayanta. da hair oils masu ƙamshi. Bayan sun gama wanke mata tass ya fita sai sheƙi yake. Ne suka fara nunnu na mata yadda za ta yi amfani da toilet ɗin ɗakin. Ita ko Amrah kawai kallonsu take domin kuwa ita ba ta san ta ian za ta fara amfani da irin wannan toilet ɗin ba. Fita suka yi suka barta tsaye a cikin toilet ɗin. Bin ko ina ta yi da kallo. Sannan ta fara tattaɓa socket ɗin toilet. Nan hannunta ya kaiga water heater ɗin toilet ɗin. Ba tare ta san mene ne ba ta danna. Nan ruwa ya fara zubo wa kanta. Zaro idanuwa ta yi waje jin ruwa mai matuƙar zafin gaske. Da sauri ta fita daga cikin bandaƙi tana mai sauke ajiyan zuciya. Zumbur su Khairiya da Ramlat suka miƙe ganin yadda ta fito daga cikin toilet a guje. "Mene ne ya faru kuma Amrah?". Ramlat ta tambaya. Kawar da kai gefe Amrah ta yi sannan ta nuna toilet. Maida kallonsu suka yi cikin toilet sannan suka ce "Shin baki gane bayanin da muka yi miki ba ne?". Girgiza musu kai ta yi da alamun "Eh". Nan suka koma toilet ɗin tare da sake nunnuna mata yadda za ta yi amfani da shi. Bayan sun gama suka fita suka barta cikin toilet ɗin. Nan dai wuya da ƙyar Amrah ta yi wanka. Ko 1minute ba ta yi ba ta fito daga cikin toilet ɗin. Mamaki ne ya kama su ganin cikin ƙanƙanin lokaci har ta gama wankan. Nan Khairiya ta ɗauko mata ɗaya daga cikin abayoyinta wanda ke dark blue gaba ɗayansa storn ne. Saka mata su suka yi tare da yi mata kwalliya ta fito ta yi kyau kamar ba ita ba. Kallon ta suka yi yayin da su biyun suka haɗa baki wajan faɗin. "Wow you look awesome and gorgeous, you are so beautiful. Kin ganki kuwa kamar ƴar Arab". Jinsu kawai take yi domin kuwa ba su ne a gabanta ba so take ta ga ƴan uwanta namun jeji. *********** Zahra na fita daga cikin asibitin ta fara tafiya ba tare da ta san in da take cilla ƙafafunta ba. "Ni wallahi rayuwar magarƙamar ma yafi dad'i, ya zama dole na tara kuɗi na koma Jigawa, mutum ai sai yunwa ta kashe shi ma bai sani ba". Ta ƙarashe maganar tare da tsaya wa. Nan ta tuna da abin da ya faru ɗazu tsakaninta da ƴan daba. "Da a ce zan sake haɗuwa da ku ko da sai kun shinshina takashin ku". Ta faɗa tana mai waige-waige kan titi. Chan ta hangi wata dattijuwa. Tana ƙoƙarin saka kaya cikin mota amma hakan ya cutura. Tausayin matar ne ya kamata hakan ya sa ta nufi in da matar take da sauri sannan ta taimaka wa matar ta saka kayan nata a cikin boot ɗin motar. Kallonta matar ta yi sannan ta ce. "Gaskiya naji dad'i da irin wannan taimakon da ki ka yi min, don aka bara na baki kuɗi". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ni bana taimaka miki ba ne domin ki biyan, nayi ne saboda Allah don aka kawai ki riƙe kuɗin ki". Ta ƙarashe maganar tana mai dafa cikin ta wanda har izuwa wannan lokacin bai daina murɗa mata ba. Kallonta matar ta yi sannan ta ce. "Amma na ga kamar kuɗin zai yi miki amfani, ya kamata ki karɓa". Kuma girgiza mata kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ki barshi wallahi, ni kawai abin da za ki bani ki burge ni a halin yanzu dai shi ne abinci, domin tun ɗazu ƴaƴan ciki na suke ta faman kuka, ina son na saka su dariya ta hanyar cin abinci". Dariya dattijuwar ta yi sannan ta ce. "Gaskiya ne, karki damu wannan ba mataala ba ne, muje fada akwai abinci kala-kala iri-iri da ban da ban duk wanda ki ke so shi za'a baki, kuma in dai kina buƙatar aiki ma ni zan baki". Washe baki Zahra ta yi sannan ta ce. "Wallahi kamar kin san ina neman kuɗin da zan koma garin mu. Kin ga saina dinga yi mini aiki ki dinga biya na har na tara ƙuɗaɗe na koma". Murmushi matar ta yi sannan ta ce. "Mene ne sunanki?". Amsa Zahra ta ba ya da cewa. "Sunana Fatima amma ana kira na da Zahra". Kuma kallonta matar ta yi ta ce. "Nice name, faɗa min nawa ki ke buƙata ni zan baki sai ki koma gida da shi". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a wallahi, nafi son nayi aiki da gumi na na samu kuɗi na tafi saina fi jin daɗi domin kuwa nima zan dinga tuna wa cewa nayi abun kirki". Murmushi matar ta yi ta ce. "To shiga mota muje ko". Ba tare da jayayya ba Zahra ta shiga mota. Nan matar ta shiga motar tare da jan motan suka bar harabar wajan. Kallon matar Zahra ta yi ta ce. "Shin baki da ɗana ne wanda zai dinga tuƙa ki?, naga kamar girma ya kama ki, idan ma babu ya kamata ki nemi driver". Kallonta matar ta yi ta ce. "Ina da ɗa kuma ina da driver, shi drivern nawa bashi da lafiya ne ya koma ƙauyen su. Shi kuma ɗana ƙwalli ɗaya baya ƙasar nan yana ƙasar India shi ɗin babban likita ne sunansa Sooraj ina matuƙar alfahari da shi". "Sooraj!". Zahra ta maimaita sunan cikin ranta. Taɓe baki ta yi sannan ta ce. "Shin ba zai dawo ba ne a chan zai zauna?". Amsa matar ta ba ta da cewa. "Zai dawo ƙarshen month ɗin nan in sha Allahu". Sosai suka dinga hira da Zahra kamar sun san juna a baya. Nan matar ta ji Zahra ta shiga ranta sosai. Saida suka ɗau lokaci kafin daga bisani suka isa cikin masarauta. Parking matar ta yi tare da fita daga cikin motan. Nan take fadawa da jama'a suka fara kwasar gaisuwa. Mamaki ne ya kama Zahra ganin tarin jama'a a wajan. Zololo ta yi tana kallon masarautar. "Wayyo ai wannan shi ake kira aljannar duniya, shi kuma nan ɗin ina ne?". Zahra ta tambayi kanta tare da fita daga cikin motan. Junaid kuwa tashi ya yi ya bar fadawan su xigaba da sadakan sannan ya nufi hanyar parking space. Nufo in da su Zahra suke ya yi. Nan take suka haɗa ido a tare. Take gaban Junaid ya faɗi!, ganin Zahra a wnanan lokacin. Da sauri ya nufi in da su Zahra suke sannan ya gaidar da dattijuwar. Amsa wa ta yi ta ce. "Junaid ga sabuwar ƴar aikin da muka samu a masarautar mu, fatan dai ta yi maka ko". Kallon sani Zahra ta yi masa sannan ta cem "Ba kaine wannan yariman ba mai jiji da kai?, tabbas dai kaine, wai dama Aunty wannan ɗanki ne?". Murmushi natar ta yi ta ce. "A'a step son ɗina ne amma shima kamar ɗa yake a guri na". Kallonta Junaid ya yi ciki ɓacin rai sannan ya maida kallonsa kan matar ya ce. "Mami bamua da buƙatar ƴar aiki, wanda muke da su sun isa. Ke kuma". Ya faɗa yana mai maida kallonsa kan Zahra ya ce. "Bani maƙullin da ki ka ɗauka a aljihu na, sam ba za ki yi mana aiki a wannan masarautar ba". Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Dama kun san juna ne Junaid?, me ya sa ba za ta yi mana aiki ba?". Amsa Junaid ya ba ta da cewa. "saboda ita ɗin ɓarauniya ce, ta sace min maƙullin ɗaki tare da kuɗaɗen aljihu na, dama kana ganin ta ka san gadon sata ta yi, ɓarauniyar banza kawai maza ki dawo min da maƙulli na ni na bar miki kuɗaɗen". Nan take fuskar Zahra ya chanza daga walwalah izuwa ɓacin rai yayin da idanuwanta suka kaɗa suka yi ja. Matsar da Mami ta yi gefe sannan ta fara tunkarar Junaid a matuƙar fusa ce ta ce. "Wace ce ɓarauniyar?, ni ɗin?, wallahi kayi sa'ar cewa nan ɗin gidan ku ne, da ba dan aka ba uhmmm, da yau saika san da cewa Allah ɗaya ne, kuma maƙullin ƙarfi ya cinye idan za ka iya ƙwata ka zo ka ƙwata, kuma gidan nan na shigo ta kenen ba zan fita ba har saina gadamar fita don aka ka shirya zama da tantiriya domin kuwa zama da ni sai wanda ya shirya". Nan hankulan jama'a da na sarki ya karkata izuwa kansu Zahra. *JUNAID KA BI A HANKALI FA, ZAHRA BA KANWALLASA BACE BA😂. BA TA ƊAUKAR RAINI, IDAN BA KIYAYE BA ZA TA YI MAGANIN KA*.💃💃💃 MANAGE PAGE PLEASE. COMMENTS, LIKE & SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏 🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu). Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣1️⃣▶️3️⃣2️⃣ *_________________________________________________* Ƙaraso wa mai martaba sarki ya yi wajan su kana ya dube su ya ce. "Me ya ke faruwa ne nake jiyo hayaniyar ku?". Amsa Junaid ya ba shi da cewa. "Mai martaba babu komai". Kallon mai martaba zahra ta yi kana ta ce. "Mai martaba ƙarya yake da akwai komai, aka ya ce min wai ɓarauniya, ranka shi daɗe ɗan nan naka yana da matsala ya kamata a kai shi asibitin dawanau domin duba ƙwaƙwalwar sa". Murmushi mai martaba ya yi kana ya ce. "Gaskiya ki ka faɗa ƴar nan dole ne ma na saka a kai shi chan ɗin. Ku shiga daga ciki ko. Kai kuma ka zo ka same ni ni a fada yanzu". Ya faɗa yana mai kallon Junaid kana daga bisani ya bar wajan. Sallamar mutanen wajan dogarai da fada wa suka yi suka fita daga cikin masarautar". Bin bayan mai martaba Junaid ya yi yayin da Mami ta yi murmushi kana ta ja hannun Zahra suka shiga cikin fada. Kai tsaye cikin parlour suka shiga. Yayin da Zahra ta saki baki tana kallon yadda cikin fadan da parlourn ya yi matuƙar tsaruwa. "Wayyo Allah na, wannan gida aka ko a mafarki ban taɓa ganin irin wannan gida ba". Zahra ta faɗa cikin ranta. Suna tsaka da tafiya kawai suka ga an sha gabansu. Dakata wa suka yi da tafiya kana suka dubi matan da suka tsaya a gaban su. Motsa leɓenta Mami ta yi ta ce. "Saratu, Talatu mene ne kuma?". Kallon juna waɗan da Mami ta kira Saratu da Talatu suka kana suka kwashe da dariya. Dungure wa Mami Kai Talatu ta yi kana ta ja dogon tsaki ta ce. "wato har kin samu damar ɗauko ƴar aiki ki kawo cikin fadan nan?, uban waye ya baki izinin yin hakan?". "Rabu da ita Talatu, ai naji duk abin da ya faru a waje, har ƴar talakawan nan ta samu bakin da za ta iya furta wa ta faɗa wa ɗana Junaid magana, lallai dole na koya miki hankali A'isha. Dama yanzu ɗanki Sooraj baya nan balle ya ƙi barin kowa cikin sukuni a gidan nan, saimun ta galla za wa rayuwar ki. Idan ɗan naki ya dawo daga ƙasar da yaje sai ki faɗa masa. Ke kuma". Gimbiya Saratu ta faɗa tana mai maida kallonta kan Zahra ta ce. "Ke kuma ƴar talakawa, wato kenen kina tunanin kin zo gidan masu arziki ko za ki iya shoshale kuɗin mu ko, to maza ki fice daga cikin masarautar nan kafin na saka yara mata su zo suyi min waje da ke". Murmushi Zahra ta yi kana ta fara ƙoƙarin gaya wa Gimbiya Saratu maganar da za ta tsufa tana jimamin shi. Ji ta yi Mami ta riƙe mata hannu tare da girigza mata kai . Nan hawaye ya fara sauka kan ƙuncin Mami ta ce. "A'a Zahra kada ki furta komai ke ɗin ƴar aiki na ce, kada kiyi magana dan Allah". Wafce hannunta Zahra ta yi kana ta ce. "A kan me ya sa ba zan yi magana ba?, baki ji yadda suke gaya miki maganganu marasa dad'i ba ne. Chabb Gaskiya wannan masarautar tana da buƙatar gyara sosai. Kuma ni nan zan gyara mutanen cikin ta". Da sauri Mami ta ja hannun Zahra kana ta nufi part ɗin ta da ita. *********** "Wow Amrah wallahi kinyi kyau sosai. Maza muje ki nuna wa yaya Umar kwalliyar ki". Ramlat ta faɗa tare da jan hannun Amrah wacce ta yi zuru zuru da idanuwa tana kallon su. Kai tsaye parlour suka nufa da ita yayin da suka nufi in da Umar yake wanda ke zaune kan kujera. Kamar an ce ya ɗago kansa. Ɗaga kansa ya yi tare da ɗora wa kan Amrah. Bai sanda bakinsa ya furta kalmar masha Allah tabarakalla ba. Ajiye system ɗin da yake yin aiki ya yi kana ya miƙe tsaye ya ce. "Muje yanzu nayi muku siyayya tare gaba ɗaya". "Laa yau yaya da kanka za ka kai mu shopping, wannan abu kamar a mafarki". Khairiya ta furta suna mai haɗa ido da Ramlat. Dubansu Umar ya yi ya ce. "Mene ne a ciki dan na kaiku shopping da kaina?, na ga dai ba wani abu ba ne". Sosa ƙeya Ramlat ta yi ta ce. "A'a yaya ba saika wahalar da kanka ba, mun riga mun faɗa wa yaya Usman ya ce zai kai mu da kansa, kuma sannan koda ma bai kaimu na ga dai akwai jami'ai a gidan nan za su kai mu, amma a ce da kanka ka kaimu ai abun ya yi wani iri". Kallonsu ya yi kana ya ce. "Ni nayi ra'ayi bawai ku ka sani ba kun fahimta, don haka ni zan kai ku , karku ɗauka wa saboda ku ne kun gane". Girgiza kai Ramlat da khairat suka yayin da suka girgiza kai suka haɗa baki wajan faɗin. "Mun fahimta". Dai-dai lokacin Usman ke sauko wa daga kan bene. Ƙaraso wa in da suke ya yi ya ce. "Muje ko". Cewar Usman. "A'a Usman ke kayi hayyukan ka, ni zan kai su, saboda bana son wani abu ya same su domin idan wani abu ya same su ba zan ji daɗin hakan ba, ana neman rayukan mu ruwa a jallo. Bayan kariyar Allah muma ya kamata mu kare kanmu. Don haka ni zan kai su kai ka koma kawai". Girgiza kai Usman ya yi kana ya ce. "Tom yaya nima kuma akwai in da zan je Ramlat ta na ce wai saina kai su shopping. Yanzu kuma tun da ka ce za ka kai su shi ke nen, ni zan tafi in da zanje". Ya faɗa tareda fita daga cikin parlourn. Nan ya ci karo da Gov. Musa Muhammad wato Abban su. Gaishe shi Usman ya yi, yayin da Abba ya amsa kana ya shiga ciki. Nan take idanuwan Gov. Musa Muhammad ya sauka a kan idanuwan Amrah. Nan take gaban shi ya faɗi!, yayin da ya ji kamar an buga masa ƙararrawa a kai. Salati ya saka sannan ya ce. "Who is this fine beb?". Ya tambaya. Kawar da kai Umar ya yi kana ya ce. "Am sorry to say Sir, but this is none of your business, please mind your self, banzan ji dad'i nayi maka rashin kunya ba. Wannan da ka ke gani rayuwata ce kuma a kanta babu wanda ba zan iya faɗa da shi ba muddin wani ya ce zai yi ƙoƙarin taɓa ta to lallai ya janyo wa kansa bala'in da babu wanda zai iya cetar sa daga ciki". Ya faɗa tare da jan hannun Amrah kana suka bi ta gefen Abba suka wuce. Baki sake gaba ɗaya suka bisu da kallo. Maida kallonsa Gov. Musa Muhammad ya yi kan su Ramlat kana ya ce. "Ita ɗin wace ce?". Amsa Khairiya ta ba shi da cewa. "Ita ɗin ƴar daji ce yaya ne ya kawo ta ya ce mana a nan za ta dinga zama har sai ya gano in da ainiyin iyayen ta suke. Bayan nan bamu san komai ba". Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Shi ke nen kuna iya tafiya". Kamar jira suke ya ce su tafi m nan suka ruga a guje tare da fice wa daga cikin parlourn. Samun waje Gov. Musa ya yi ya zauna kan kujera tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya furzar da iska mai zafi tare da sakin murmushi ya ce. "Umar kenen mai zuciyar ƙarfe. Amma fa ba laifi yarinyar nan ba dai kyau ba, ga green eyes masu tafiya da hankali. Tabbas idan nayi safarar wannan ba ƙaramin kuɗaɗe ƴan ƙasar waje za su bayar ba, za su bada fiye da millions ma, ya zama dole na san yadda zan yi na sace ta. The girl is so beautiful and sexy". Haka Gov. Musa ya shiga yin magana shi ɗaya kamar wani zautacce. Bayan su Umar sun shiga cikin mota ne Umar ya tada mota yayin da Amrah ta zauna a mazaunin gaba. Nan Umar ya tuƙa motar suka bar harabar gidan baki ɗaya. Kai tsaye hanyar shopping mall suka nufa ********************** *KAUYEN GUJINGU* "Malam wallahi abin da ke faruwa da ƴata ya wuce s kaita asibiti sai dai wajan malamai shi ya sa muka zo gare ka. A da chan ba ta yin hakan. Amma kwanan nan kawai sai mu ga tana faɗi ƙasa ita ɗaya ba tare da anyi mata wani abu ba". Daddy ya ƙarashe maganar damuwa ɗauke kan fuskarsa. "Ƙwarai da gaske Malam, saboda wannan abun da ke damunta ne ya sa muka baro America mu ka zo Nigeria domin neman mafita. Dan Allah ka taimaka mana". Cewar Mom. Murmushi dattijon ya yi wanda ke zaune kan wata katifa wanda aka zagaye shi da kara. Yayin da ɗakin gaba ɗaya rubutun Qur'ani ka ke gani tare da magunguna kala-kala na cututtuka da na aljanu. Kallonsu malamin ya yi kana ya ce. "Shin ku kuka haife ta?". Nan take gaban Mom da Daddy ya faɗi!, kallon juna suka yi yayin da suka haɗa baki wajan faɗin "Eh mu muka haife ta". Sauke ajiyan zuciya Malamin ya yi kana ya ce. "kuma kuna da tabbacin cewa ita ɗaya ce ba ta da wasu ƴan uwan wanda basua tare da ita?". Amsa Daddy ya ba shi da cewa. "Eh babu ita kaɗai kawai muka mallaka a duniyar nan". Girgiza kai Malamin ya yi kana ya ce. "To ƴar ku ba ta da wani aljanu, samm babu aljanu ko sihiri ko kuma maita a tattare da ita. Wannan abun da ke faruwa da ita ba wai haka kawai ba ne dole dai akwai dalilin faruwar hakan. Amma batun cewa ko aljanu ke damunta, samm ba gaskiya ba ne". "To Malam idan ba aljanu ba ne mene ne?, Sannan kuma mene ne abin da zamu yi ya daina?". Cewar Grandpa. Amsa Malamin ya ba shi da cewa. "Babu abin da zamu iya yi ya daina domin da wannan abun haka haife ta, sannan alamu ya nuna cewa wannan ahali naku sun aikata wani babban kuskure a baya wanda a yanzu ba za ku iya gyara wann kuskuren ba domin kuwa lokaci ya riga ya ƙure. Dole a chan baya kun cutar da wata wanda ba ta ji ba, bata gani ba, sannan kuma kunyi shedar zurr hakan abin da ba ta aikata ba, to ku sani cewa ƴaƴanta su ne za su ɗaukar mata fansar abin da haka aikata mata". Cikin rashin fahimta gaba ɗaya suka dubi malamin kana suka haɗa baki wajan faɗin. "Bamu fahimci abin da ka ke magana a kai ba". Murmushi Malamin ya yi kana ya ce. "Baku da wata ƴa a ahalinku ku ka kore ta ba tare da tabbatar bincike da kuma ƙwaƙwarar hujja hakan abin da ba ta aikata ba". Nan take jikin kowanensu ya yi sanyi. Ajiyan zuciya Grandpa ya sauke!, kana ya ce. "Babu wacce muka kora sai Laila, kuma ita ma ɗin na kore ta saboda zubar min da mutunci da ta yi a idanun duniya kana kuma ta lalata sunan ahalin mu, ita ce dalilin kasance wa ta kan wheel chair yanzu. Ta chanza sunan ahalin mu daga masu mutunci izuwa marasa mutunci. Ita ce kawai nake tunanin na kore ta na damka ta a hannun ƴan sanda. Sannan har yau har gobe ba zan manta irin cin mutunci da jama'a suka yi mana ba duk ta dalilin ta. Kuma bayan nan ma ta dalilin ta ne jikana yanzu haka yake da cutar mantau. Don haka ba zan taɓa yafe mata ba, koda zan yafe wa kowa a duniyar nan to banda Lailah". Share hawayen da ke shirin zubo mata Grandma ta yi kana ta ce. "Kuma ita ɗin a halin yanzu ba ta raye ta riga da ta je gidanta na gaskiya, kuma ina fatan tana cikin rahamar Ubangiji". Sauke ajiyan zuciya Malamin ya yi kana ya ce. "Tabbas kun aikata babban kuskure a rayuwar ku, ya zama dole ku nemi gafarar wannan ƴar taku idan kuwa ba haka ba, rayuwar ku za ta taɓe. Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya. Baku gani ba sannan baku sheda ba ku ka yanke wannan mummunar hukuncin a kanta, idan ma baku samu kun nemi gafarta ba to ku nemi gafarar ƴaƴan ta domin kada fushin Ubangiji ya dauwama a kanku. Ni na gama magana ta za ku iya tafiya". Ya ƙarashe maganar yana mai kwanciya kan katifar sa. Kallonsa Mom ta yi ta ce. "Malam batun maganar ƴata fa?". Jin shiru babu amsa ya sa gaba ɗayansu miƙe wa sannan suka fice daga ɗakin Malamin. Kai tsaye wajan motocin su suka nufa sannan suka shiga ciki yayin da drivers da ke tsaye suka shiga cikin motan tare da tada motocin sannan suka bar harabar wajan. Kai tsaye suka nufo hanyar Dutse. Tun da suka fara tafiya kowanensu ke ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa yayin da gaba ɗayansu suka kasa samun sukuni. *********************** Zumbur Safeera ta miƙe tsaye tqreda nuna Aliyu da yatsarta sannan ta fara kokarin magana. Nan wata zuciyar ta ce da ita ta rabi da shi kawai. Waje ta samu ta zauna sannan ta kawar da kai gefe ta ce. "Ina neman wata alfarma". Murmushi Aliyu ya yi kana ya ce. "To fa, alfarma a waje na kuma, me ya sa sai a waje na?". Amsa Safeera ta bashi da cewa. "Saboda na ga kafi cancanta na nema a wajan ka ne. Ina da buƙatar sabulu da man shafa wa sannan da kayan sawa. Duka kaya na suna chan America. Ina da wasu ƴan kuɗaɗe a acc ɗina, shi ne na ce idan babu damuwa ka taimaka ka kaini in da ake shopping domin na yi siyayya". Kallon baki da hankali Aliyu ya bita da shi kana ya ce. "Wato ma ke ɗin nan kin cika ƴar rainin hankali, yanzu-yanzun nan ki ka gama yi min rashin kunya, and you are expectimg me to take you to shoppin mall, hope dai kina lafiya ba wai giyan wake ki ka sha ba". Turnuƙe fuska Safeera ta yi ta ce. "Tun da na zo fa banyi wanka ba, am irritating myself, I feel so disgusted I can't take it anymore shi ya sa na nemi alfarma, amma idan ka ga ba za ka kaini ba it fine, i know what to do". Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi kana ya ce. "Shi ke nen je ki saka hijabi na kaiki". Murmushin jin daɗi Safeera ta yi kana ta ce. "Amma ba zan iya zuwa haka ba ne, na ga dai akwai sutura a jiki na ga kuma veil na yafa". Binta Aliyu ya yi da kallo tare da kallon matsatsun kayan da ke jikin ta. Kawar da kai ya yi gefe sannan ya ce. "In dai da wannan kayan za ki bini to babu in da zan je wallahi kinji na faɗa miki". Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Shi ke nen bari na ɗauko hijabi. Ta faɗa tareda shiga cikin ɗakin su Zuwaira ta ɗauko maroon hijab ta sanya. Sosai hijabin ya yi mata kyau. Fitowa ta yi kana ta ce. "Muje ko". Kallonta Aliyu ya yi cikin zuciyarsa ya furta kalmar. "Masha Allah Alhamdulillah, tabbas su Mom sun zaɓa min mace kyakyawa, gaskiya nayi dace". Taɓe baki ya yi a fili ya ce. "Ko kyau, abu kamar a hura ta faɗi". Taɓe baki Safeera ta yi ta ce. "Koma dai mene ne kai ka sani". Fita suka yi a tare da shiga cikin mota a tare. Tada mota Aliyu ya yi kana suka fice daga cikin gidan yayin da ma'aikatan gidan suka bisu da kallo. Saida suka yi tafiya mai nisan gaske kafin su isa ga shopping mall ɗin. Ɓangaren su Amrah kuwa sosai su khairiya ke yi wa Amrah siyayya, kama daga abayoyi atamfa, Arabian gowns, hijabbai da mayafai tare da set na kayan makeup da dai sauransu. Jan hannun Amrah Umar ya yi kana ya fara zagaya da ita cikin mall ɗin domin ya zaɓo mata wasu abubuwan. Bayan shigar su Aliyu ne suka nufi ɓangare da za su samu abin da Safeera ke buƙata. Sakin hannun Amrah Umar ya yi kana ya fara dube-duben wasu abubuwan. Safeera ganin hankalin Aliyu ya tafi wani wajan ya sa ta yi saurin barin wajan tareda nufar wani part na ciki wajan Amrah kuwa barin in da Umar yake ta yi tare da nufa ɗayan sashin da ba ta san ko ina ba ne. Juyawar Umar keda wuya kawai ya ga Amrah ba ta nan. Waige-waige ya fara yi ya ga dai still bai ganta ba. Hankalin sa ba ƙaramin tashi ya yi ba domin kuwa a tunanin sa waɗan da suke bibiyar rayuwarsa sune suka sace Amrah nan take ya kira jami'ansa. A ɓangaren Aliyu dai shima haka domin ya yi neman duniya bai ga Safeera ba. Chan Aliyu ya hango Amrah a tsaye. Mamaki ne a ya kama shi domin duk a tunanin shi Safeera ce. "To ikon Allah wato Safeera harta chanza shiga izuwa pink abaya". Ƙarasa wa in da Amrah yake ya yi kana ya ja hannunta ya ce. "Ke safeera ina ki ka je ki ka sa nake ta neman ki?". Juyo wa Amrah ta yi. Nan take idanuwan kowannensu ya sauka a juna. Take gaban Aliyu ya yi mummunar faɗuwa!, sauri sakin hannunta ya yi tare da ja da baya. Baki na rawa ya ce. "Safeera garin ya ya idanuwanki suka chanxa kala?". Ɓangaren Umar kuwa ganin Safeera ya yi tana ta tsince abubuwan da take so. Murmushi ya yi ba tare da sanin ba Amrah ba ce ba ya ja hannun ta ya ce. "Ke Amrah kin fiye yqwo maza mu tafi. Mamaki ne karara ya bayyana kan fuskar Safeera. Saurin wafce hannunta Safeera ta yi ta ce. "Hey wane ne kai kuma?, wace ce kuma Amrah?". Juyo wa Umar ya yi domin kuwa ya yi matuƙar mamki a karo na farko Amrah ta yi magana. Juyawar sa keda wuya idanuwansa ya sauka a na idanuwan Safeera. Gabansa ne ya bada wani irin ƙara tare da wani irin bugu. Da sauri ya saki hannunta yayin da ya nuna ta cikin zallar mamaki ya ce. "Gari ya ya idanuwan ki suka sauya izuwa blue kuma?, dama kin iya magana ne?". ************************ "Wai Mami su wane ne waɗan chan matan ne?, na san a girma za ki girme su amma shi ne suke miki rashin kunya, ni fa idan da abin da nafi tsana bai wuce zagar min uwa da raini ba. Shin ke ƴar aiki ce a gidan nan ne suke yi miki irin wannan cin fuskar?". Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "A'a ni ɗin ba ƴar aiki bace ba, su ɗin kishiyoyi na ne ni kuma ni ce Uwar gidan su". Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce. "Kuttmelesin chan dumadu, chabb ɗi jamm kenen dama wai kishiyoyin ki ne?, kai Mami, gaskiya kinyi sanyi da yawa, chabb na yarda da kaina. Wayyo ni Zahra, dama ni ce nake zaune da waɗan nan kishiyoyin guda biyu da tuni na saita wa kowanensu zama duk gaba ɗaya na ga ɗuwawunsu rawa yake duk da saina saita musu shi. Gaskiya Mami kinyi sanyi da yawa. Ai kuwa dole ne na gyara wa kowa zama a gidan nan kafin na bar wannan masarautar. Domin samm ba zan juri ire-iren waɗan nan abubuwan ba, me yafi wannan raini. Na ga ma kamar sun raina ki, wata a cikin su mai haƙora kamar na akuya mai gatso ɗin nan Talatu na ji kin ce ɗazu ko, ita harda wani dungure miki kai tsabagen ta raina ki". Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "To ya zanyi Zahra?, ni sam bana san tashin hankali da hayaniya, shi ya sa kawai nake zaune da su a hakan banason rigima. Shiru- ba tsoro ba ne gudun magana ne, a lokacin da ɗana Sooraj yana nan babu wanda ya isa ya yi min abin da suke yanzu. Domin kuwa kowa tsoronsa yake a gidan nan. In dai baya nan ne suke mim waɗan nan abubuwa, idan kuma ya dawo kowa shan jinin jikinsa yake. Ni kuma ban taɓa buɗar baki na faɗa wa mai martaba ko ɗana Sooraj ba. Saboda bana son tashin hankali". Girgiza kai Zahra ta yi kana ta ce. "Tabbas ni ce zan kawo sauyi cikin wannan masarautar saina tabbatar da na saita musu zama kafin na bar gidan nan, ba zan iya zuba ido na ga ire-iren waɗan nan abubuwan na faruwa ba, ya zama dole na koya musu hankali". Babu zato suka ji an banko ƙofar cikin ɗakin. A zabure gaba ɗaya suka juya tareds sauke idanuwansu a kan matan da ke tsaye bakin ƙofa babu abin da suke ta faman yi sai tauna chewgum yayin da suka ɗora hannuwansu kan ƙugu. Sanye kansu yake da gashin ƙari wanda ya sauko musu har gadon baya yayinda ko ina na jikin su ke sanye da azurfa masu kyau da sheƙi. Kallo ɗaya za ka musu ka tabbatar da cewa su ma ƴaƴan wannan masarauta ne. Ƙaraso wa ciki mata ukun suka yi sannan suka buga tsaki. Daya daga cikin su ce ta ce. "Ke Mami me ya sa har yanzu baki je kin wanke min panties ɗina ba?". Kallon Mami Zahra ta yi kana ta ce. "Mami su waye kuma waɗan nan almajiran?". Kallonta Mami ta yi kana ta ce. "Su ɗin ba almajirai ba ne, ƴaƴan kishiyoyi na ne, Samira, Yusra, da Fasma". A matuƙar fusa ce ƙaramar cikin su ta dubi Zahra ta ce. "Su wane ne almajiran, nan ɗin gidan ubanki ne. Tsaya ma tukun nan ke ɗin wace ce daga wane duniyar ki ka zo nan". Cewar Fasma. Yusra ce ta dubi Fasma ta ce. "Dalla ƙyale ta Fasma zamu ji da ita daga baya. Yanzu wajan wannan banzar matar muka zo, ta zo ta wanke mana kayan mu, domin ni yau bana sha'awar saka kaya a cikin washin machine da hannu nake so a wanke mu". Idan ran Zahra ya kai dubu to ya ɓaci. Cikin ɓacin rai ta ce. "Kuna da hankali kuwa?, ku san da cewa wannan matar ba sa'ar iyayen ku mata ba ce, amma shi ne ku ke cewa ta zo ta wanke muku panties da kaya, lallai kamm banga ta zama ba a gidan nan domin daga yanzu ya kamata na soma aiki na". Rai a ɓace su ukun suka tunkari in da Zahra take kana suka ce. "Eh mun aike ta ɗin wace ce ke da za ki dakatar da mu?". Nuna su gaba ɗaya Zahra ta yi kana ta ce. "Zai iya kasance wa kun daɗe kuna yi mata abin da ranku ya gada ma, like mothers like daughters ko, to tun da na riga da sanya ƙafafu na cikin wannan masarautar komai ya zo ƙarshe domin kuwa ba zan bar koda iyayen ku mata su ƙara ci mata mutunci ba balle ku ƙananun ƙwari". Nan take Samira ta saka ƙafarta wanda ke sanye da takalmi mai tsini ta taka ƙafar Mami da shi. Nan take Mami ta saki wani irin azababbiyar ƙara!. Nan take ran Zahra ya ɓaci yayin da ta kai hannu tare da fizge gashin dokin da ke kan Samira sannan ta kama ƙwaƙwidon kan Samira kana ta kwashe ta da lafiyayyun maruka har guda biyu. Nan take su Yusra suka ja da baya. Shafa kan Samira Zahra ta yi ta ce. "Wai dama ba gashin ku ba ne, ashe gashin doki ne, ji gashi kamar ammatar ɗan iska". Ta faɗa tana mai kwashe wa da dariya sannan ta maida kallon ta kan Mami ta ce. "Mami kada ki damu za ki riɓanya hakan abinda ta yi miki kiyi mata times 2". Girgiza kai Mami ta yi kana ta ce. "Ki rabu da ita Zahra, bana son matsala". "A'a Mami ba zai yu ba, me ya sa koda yaushe waɗan da suke da shiru-shiru su haka fi raina wa ne?, ke sa'ar su ce da za su wai ki wani wanke musu kaya da panties, idan ba rashin tarbiya ba wa ye zai faɗi hakan?". Cewar Zahra. Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra umarni nake baki ba shawara ba maza ki sake ta". Jin hakan ya sa Zahra sakin gashin Samira tare da shinshina hannunta. Nan take ta ji wani mugun wari ya bugi hancin ta. "Ya subha'anallahi!". Zahra ta furta kana ta ce. "Wannan kai ne ko kashin akuya?, ji wani wari da ke fita daga kan wannan Samira kamar mutacce alade. Chabb ashe duk gayun da iyayin na banza ne tun da ba'a iya tsaftace jiki". Node Kai su ukun suka yi kana suka ce. "Za ki san mu ki ka taɓa wallahi yau kin taɓo wa kanki bala'i, kuma za ki gani". Suka faɗa tare da fita daga cikin ɗakin. Duban su Zahra ta yi ta ce. "Zan ga alkhairy ba tsiyar ku ba, shegun yara kawai". Su Samira na fita kuwa suka je suka sanar da su Gimbiya Saratu da Talatu duk abubuwan da Zahra ta yi musu. Nan take gaba ɗaya suka miƙe tsaye yayin da suka nufi kitchen daga mai ɗaukar wuƙa saime ɗaukar chokali. Yayin da su Yusrah kuma suka ɗauki wayar chaza suka nufi ɗakin Mami. "Ke Zahra, nan fa ba kamar gidan ku ba ne, za su ya cutar da lafiyar ki ni kuma ba zan bari hakan ta faru ba, tun da ki ka ji sun ce za ki gani to sun tafi ne su haɗa dabar su za su iya cutar da ke, ya kamata ki bar masarautar nan yanzu". Cewar Mami. Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Mami ki barsu su zo dai-dai nake da kowaccen su, nayi da wanda yafi su ma balle su ƙananun tantirai. Jira nake su ƙaraso a nan za su tabbatar da cewa Allah ɗaya ne, domin duk saina koya musu hankali". Ta faɗa tana mai hango dorina a ajiye kan table. Da sauri ta nufi in da dorinan take tare da ɗauka ta riƙe a hannunta tana mai jiran shigowar su Samira. ******************** 💃💃💃💃💃💃💃💃 *KAI ZAHRA KINA ƘAMSHI MUNA BINKI DA UMRAH, INA YINKI OVER😂, MA ZA KIYI MANA MAGANIN SU. SU SAMIRA JIKIN KU ZAI FAƊA MUKU DOMIN ZAHRA BA ABAR RAINA WA BACE. ALIYU DA KUMA UMAR FA SUN RIKICE, SUN KASA GANE SAFEERA DA AMRAH. KOYA ZA TA KASANCE MUJE DAI ZUWA💃💃💃.* *KADA KU MANTA DA LIKING, SHARING DA KUMA COMMENTS FISABILILLAH🌹🫠🫠🥰💞* ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣3️⃣▶️3️⃣4️⃣ *_________________________________________________* Saida su Gimbiya Saratu suka zo dai-dai lokacin da za su shiga part ɗin Mami ne suka ci karo da Junaid. Shan gabansu Junaid ya yi sannan ya dube su ya ce. "Mene ne ku ke shirin yi haka?". Maida kallonsa ya yi kan Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Ammi what's going on?, kar dai wajan Mami za ku je?". Kallonsa Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Koma wajan ta zamu je ina ruwan ka?, maza ka bamu hanya mu shiga. Har ma ta kai da har za ta kawo wata ƴar aiki cikin fadan nan kuma ta saka ƴar aikinta ta ɗaga hannu ta mari Samira saboda ta cika tangararriyar ƴar iska". Fashe wa da kuka Samira ta yi ta ce. "Wallahi yahya kome za ka yi ba zan rabu da ita ba, ɗaga hannu da ta yi ta mare ni kawai ka bamu hanya mu shiga don wallahi saina yi mata tsinannen duka". Sauke ajiyan zuciya Junaid ya yi sannan ya ce. "Kun san dai mai martaba yana nan. Kuma idan har ya ji abin da ku ke shirin aikata wa to ran mu ne gaba ɗaya zai ɓaci. Hanyar zaman lafiya a bita da shekara. Yanzu me ku ke so ita ƴar aikin ta yi muku?". Amsa Gimbiya Talatu ta bashi da cewa. "In dai tana so mu rabu da ita to dole ne ta zo ta durƙusawa har ƙasan gwiwowinta ta bawa Samira haƙuri kuma bayan nan za ta wanke musu kayan su. Wannan shi ne". Ta ƙarashe maganar hannunta riƙe da ƙugunta Furzar da iska Junaid ya yi waje, sannan ya dube su ya ce. "Shi ke nen kuje ku zauna a parlour zan kira ta za ta zo ta baku haƙuri gaba ɗaya har da ma ita Samiran". Ya faɗa yana mai shige wa part ɗin Mami sallama riƙe a bakin sa. Su Gimbiya Saratu kuwa jin abin da Junaid ya faɗa ya sanya suka koma parlour tare da zaman jiran fitowar Zahra. Ƙarasawa ciki Junaid ya yo yayin da Zahra ta bishi da kallo. Murmushi Mami ta yi ta ce. "Junaid kaine a wannan lokacin". Cikin jim kunya ya ce. "Eh Mami ni ne". Ya faɗa yana mai maida kallonsa kan Zahra. Mamaki ne ya kama shi ganin dorina kan hannun Zahra. Baki sake ya bita da kallo sannan ya ce. "ke kuma me ki ke da dorina?, me za ki yi da shi?". Kallonsa Zahra ta yi sannan ta bashi amsa da cewa. "Zan daki ƙannen ka da shi ne, ko za ka rama musu?". Kawar da kai Junaid ya yi gefe cikin jin haushin furucinta ya ce. "Ki fito babban parlour yanzu nan ko kuma ranki ya ɓaci". Yana kaiwa nan ya fice ya bar musu ɗakin. Dogon tsaki Zahra ta ja sannan ta ce. "Aikin banza, ni gaba ɗaya ma zaman magarƙamar ma ya fi ƴanci a kan nan wajan". Binta da kallo Mami ta yi ta ce. "Kije Zahra zai iya yiwu wa sun kai ƙarar ki wajan mai martaba". Zama Zahra ta yi kan kujera ta ce. "Ni babu in da zani ina nan tare da ke". Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi haƙuri ki tashi ki je ko kuma mu je tare kinji ni". "Shi ke nen Mami zanje ne kawai saboda ke, amma da ba dan haka ba babu abin da zai sa na ɗau ƴan matan ƙafafuwa na naje wajan su". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye sannan ta fita daga cikin ɗakin. Ganin hakan ya sa ita ma Mami ta bin bayan Zahra. *********************** Cikin rashin fahimta Safeera ta dubi Umar ta ce. "I don't understand what you are talking about, wace ce kuma mai green eyes?, ni a ina na sanka ma da za ka ce wai ni mai green eyes?. Kodai kana imagination ne?, ya kamata ka je asibiti a duba ka". Ta faɗa tare da juya wa ta yi tafiyar ta. Baki sake Umar ya bita da kallo sannan ya ji zuciyar shi nayi masa zugi. Baiyi aune ba ya ga Safeera ta ɓa ce masa daga gani. Ɓangaren Aliyu kuwa gaba ɗaya ya rasa me ke masa daɗi yayin da ya rasa me zai yi domin tabbatar da cewa wannan Safeera ce ko ba ita ba ce. Yana tsaka da tunani ne kwatsam ya ji wayarsa ta fara ringing. Nan hankalin sa ya ɗauke daga kan Amrah izuwa wayarsa. Ɗaukar wayar sa ya yi ganin sunan wanda ke bayyane kan screen ɗin wayar ya sa shi saurin ɗaga wayar. Juya wa Amrah ta yi tare da barin wajan sannan ta nufi ɗayan sashen da Umar yake. Dai-dai lokacin da Safeera ke yowa wajan. Kai tsaye in da Aliyu yake ta nufa ba tare da sun haɗu da Amrah ba. "Hello your excellence fatan komai lafiya". Cewar Aliyu wanda waya ke maƙale kan kunnensa alamun yana waya. Daga ɗayan ɓangaren Gov. Musa Muhammad ya ce. "Aliyu ina so kayi min wani aiki". "Okay". Aliyu ya ce yana mai jiran mai Gov. Musa zai fada masa. Magana Gov. Musa ya fara yi kamar haka. "Ina son ka bincika min wane ne ya kuɓutar da Lailah harta gudu daga asibiti a wannan lokacin". Cikin rashin fahimta Aliyu ya ce. "Ban fahimci me ka ke faɗa ba yallaɓai, kamar ya na bincika waye ya taimaka mata. Ita ɗin fa ta riga da ta bar wannan duniya, kuma ko ba komai ita ɗin kamar ƴar uwa take a waje na ko kuma na ce tamkar uwa take a waje na a kan me ya sa za ka ce na bincika waye ya taimaka mata. Gaskiya ba zan iya yin wannan aikin ba sai dai ka saka wani ya yi maka". Yana kaiwa nan ya katse wayar. Ɓangaren Gov. Musa Muhammad kuwa idan ranshi ya kai dubu to ya ɓaci!, cikin hassala ya ce. "Lallai ma aliyu, mun daɗe cikin harkar nan tare da kai shi ne kuma yanzu ka ke ƙoƙarin juya min baya na san ta yadda zan ɓullo maka". Kiran wasu daga cikin body guards ɗinsa ya yi tare da faɗa musu cewa su binciko wacce ta taimaka wa Laila ta gudu a asibiti. Kamar yadda ya umarce su haka suka fice suka fara yawo a gari domin neman wace ce ta taimaka wa mrs Laila Abdullahi. *************** Bayan Aliyu ya sauke wayan ne ya ci karo da Safeera a tsaye sai binshi da idanuwa take. Binta ya yi da kallo sannan ya ce. "Wato yanzu ma kin kuma sauya shiga kenen kuma ƙwayar idanunki kin mayar da su yadda duke da sannu da ƙokari kinji". Cikin rashin fahimta Safira ta dube shi ta ce. "Ni fa ban gane abin da ka ke magana a kai ba". "Koma dai mene ne ke ki ka sani, maza tawo mu tafi idan kuma baki gama ba ni na tafi na barki a nan". Ya ƙarashe maganar yana mai fice wa daga wajan. Ganin yana ƙoƙarin ya tafi ya barta ne ya sa ta yi saurin bin bayansa. Suna isa waje suka tadda jami'ai zagaye ta ko ina. Mamaki ne ya kama su. Simi-simi Aliyu ya nufi in da ya ajiye motar sa tare da shiga ciki nan ita ma Safeera ta shiga cikin mota. Tada mota Aliyu ya yi sannan suka bar harabar wajan. Ɓangaren Amrah kuwa kai tsaye wajan Umar ta nufa. Nan Umar ya shiga binta da kallo yayin da ya rasa a mafarki yake ko zahiri. Ya shiga cikin ruɗani. Su Khairiya kuwa bayan sun gama siyayya ne suka nufi wajan su Umar. Kallon Umar suka yi ganin gaba ki ɗaya yanayin shi ya chanza ya sa Ramlat faɗin. "Yahya meya faru?". Ta faɗa da alamar tambaya. Girgiza kai kawai Umar ya yi sannan ya ce. "Babu komai mu tafi". Ya faɗa yana mai jan hannun Amrah suka fice daga cikin wajan. Nan ya ga jami'an da ya kira har sun iso harabar wajan. Sara masa jami'an suka shiga yi a sa'inda suka buɗe musu kofofin mota suka shiga. Gaba ɗaya yanayin Umar ya sauya ba kamar yadda suka sanshi ba. Binsa da kallo kawai Amrah ke yi ganin dan murmushin nan da yake mata baya yi hakan ya sa ta cikin wani irin yanayi na damuwa. Tada mota jami'ai suka yi tare da barin wajan baji ɗaya. ***************** Zahra da Mami na fita kuwa suka tarar da ƴan aiki tare da su Gimbiya Saratu da Talatu tare da su Samira a zazzau ne gaba ɗaya sun ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Ƙarasawa wajan su Zahra ta yi sannan ta ce. "Gani na zo me ya faru?". Ta faɗa idanunta a kan Junaid. Sauke ajiyan zuciya Junaid ya sauke!, kana ya ce. "Maza ki durƙusa ki bawa Samira haƙuri tare da sauran domin yin hakan ne kaɗai zai sa ki zauna lafiya a cikin masarautar nan". Jin maganar Zahra ta yi tamkar saukar aradu. Ƙasa da kai ta yi yayin da ta ji wani zuciyan ya ce mata kawai ta bawa Gimbiya Saratu da Talatu haƙuri domin a haifa sun haife ta. Dubansu ta yi kana ta ce. "Shi ke nen tun da abin da ku ke buƙata kenen zan yi. Amma Gimbiya Saratu da Talatu kawai zan bawa haƙuri Samira kuwa laifi ta yi don haka ba zan iya ba ta haƙuri ba". Miƙe wa tsaye Gimbiya Talatu ta yi sannan ta ce. "To idan ba za ki iya ba ta haƙuri ba muma bamua da buƙatar haƙurin ki, in dai kina son mu yafe miki kuma keda wannan matsiyaciyar Mamin ku zauna lafiya cikin fadan nan to dole sai Mami ta durƙusa har ƙasa ta bawa Samira haƙuri". Nan take jinin Zahra ya fara tafarfasa yayin da ta ji wani irin ɓacin rai ya ziyarce ta. Nan take ta dubi Gimbiya Talatu ta ce. "A kan me ya sa za ta ba ta haƙuri?, ni ce da laifi ba ita ba, kuma ita ta kawo ni masarauta nan ba ku ba, ya kamata ku san irin furucin da za ku dinga furta wa domin ita ɗin ba sa'ar ku ba ce ba". Duban Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Aba ke kuwa Zahra wannan ba shi ba ne karo na farko da zan fara basu haƙuri ba wannan abu mai sauki ne. Ki bari kawai na ba ta haƙuri ". Ta faɗa hawaye na gangaro wa kan fuskarta yayin da ta fara yinƙurin durƙusa wa kan gwiwowinta. Da sauri Zahra ta riƙe ta sannan ta ce. "Aba Mami, sai dai idan bani da rai shi ne kawai zan barki ki durƙusa a wajan nan amma muddin da numfashi na to babu abin da zai sa ki durƙusa mata". Maida kallonta ta yi kansu sannan ta ce. "Na san Mai martaba bai san duk abin da ku ke yiwa Mami ba to a yau duk zan tona muku asiri domin saina faɗa masa komai". Ta faɗa tana mai yinƙurin fita. Take suka ci karo da mai martaba a hanyar ta na fita. Hamdala Zahra ta yi kana ta ce. "Mai martaba dama ina so na faɗa maka abu ne sai kuma gashi Allah ya kawo ka, dama....... Zahra ba ya kai ga ta idda maganarta ba suka ji Gimbiya Saratu da Talatu sun fashe da kuka. Maida kallonsa Mai martaba ya yi kansu Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Me ya faru?". Cikin kuka Gimbiya Talatu ta ce. "Mai martaba uwar gidan ka ce ta kawo sabuwar ƴar aiki take yi mana rashin kunya harda zagin uwata. Sannan kuma uwar gidan ka ta saka ƴar aiki ta mari Samira sannan kuma ta zage mu". Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai faɗin. "Innalilahi wa innahilahir rajihun, wannan wane irin sharri ne, ku sani cewa ramin ƙarya ƙurarre ne". Kallon Mami Kai martaba ya yi sannan ya ce. "A'isha maganar su Talatu gaskiya ne?". Sunkuyar da kai Mami ta yi hawaye na sauka kan fuskar ta. Kallonta mai martaba ya sake yi a karo na biyu sannan ya ce. "A'isha da ke nake fa, na ce maganar su Talatu gaskiya ne ko ƙarya?". Girgiza kai Mami ta yi tare da share hawayenta sannan ta ce. "Eh gaskiya ne". Kallon juna Gimbiya Saratu da Talatu suka yi tare da sakin murmushin mugunta. Kallon Mami Zahra ta yi kana ta ce. "Aba Mami me ya sa za ki ɗora laifin da ba naki ba a kanki?, me ya sa za ki amsa abin da ki ka san baki yi ba? ta ya ya za ki ce da gaske ne bayan kuma sam ba haka ba ne ba". "Yi min shiru!!". Mai martaba ya faɗa a matuƙar tsawa ce. Shiru Zahra ta yi tana mai maida kanta gefe tare da dunƙule hannunta na dama kana ta cije leɓenta cikin tsananin ɓacin rai da zafin zuciya. Kallon kowanensu mai martaba ya yi sannan ya maida kallonsa kan Mami ya ce. "Na yarda da ke A'isha na san ba za ki iya aikata abin da suka faɗa ba, don haka ki koma part ɗin ki". Nan take farin ciki ya ziyarci zuciyar Zahra. Jiki a sanyaye Mami ta koma part ɗin ta. Maida kallonsa mai martaba ya yi kan Zahra sannan ya ce. "Ke kuma, tun da ki ka iya ɗora hannunki kan Samira kuma ki ka iya zagin gimbiyoyi dole ki fuskanci hukunci. Don haka hukuncin shi ne dole ki dinga share gaba ki ɗaya masarautar nan har na tsawon sati ɗaya". Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin abin da Mai martaba ya faɗa. Nan take Zahra ta durƙusa kan gwiwowinta sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce. "Ranka shi daɗe ka gafarce ni, dan Allah na yarda ayi min wani hukuncin amma banda wannan, na san kai ɗin mai tausayi ne kuma mai fahimta. Don Allah a sassauta min". Jin hakan ya sa Mai martaba kallonta sannan ya ce. "Shi ke nen zan sassauta miki. Sassaucin kuwa shi ne dole idan ɗana na fari wato Sooraj ya dawo daga ƙasar da ya je to ya zama wajibi ki dinga masa aiki, kama da share-share, aiki da dai sauransu duk ke ce za ki dinga yi masa har na tsawon lokacin da ki ka ga za ki bar wannan masarauta". Jin hakan ya sa Zahra ta yi wa mai martaba godiya da irin wannan hukuncin da ya yanke. Kallonta mai martaba ya kuma yi a karo na biyu sannan ya ce. "Akwai wani ajiyayyen ɗakin sa daga yau nake so ki fara aikin maƙullin yana hannun Junaid shi zai baki". Yana kaiwa nan ya fice daga wajan. Tashi tsaye Zahra ta yi tare da karkaɗe jikinta sannan ta ce. "To me kuma ya rage ko duka na za ku yi?". Ta faɗa tana mai kallon su Gimbiya Saratu. Idan ransu Gimbiya Saratu ya kai dubu to ya ɓaci. Miƙe wa tsaye suka yi sannan suka bar cikin babban parlourn. Kallon Junaid Zahra ta yi sannan ta ce. "Malam Junaidu ina muƙullin yake?". Galla mata harara Junaid ya yi sannan ya ba ta amsa da cewa. "Muƙullin ba yana hannun ki ba, shi ne ai ki ka ɗauke a cikin aljihu na". "Ohh to ai ban sani ba, shi ke nen sai a nuna min ɗakin ko, na je na fara aiki na tun yanzu". Nuna mata hanyar ɗakin Junaid ya yi sannan ya ce. "Wan can shi ne ɗakin". Ya faɗa yana mai wuce wa part ɗin sa. Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Duk saina koya muku hankali, ƴan iskan yara kawai, gaba ɗaya yaran gidan nan an lalata su da sangarci". Ta faɗa tana mai nufar in da Junaid ya nuna mata. Tana zuwa ƙofar ɗakin ta ɗauki muƙullin sannan ta saka a bakin ƙofan. Nan take ta ga ƙofar ya fara ƙoƙarin buɗe wa. Ba ta yi aune ba ta ga ƙofar ya fito da thumbprint wanda dole mamallakin shi ne kawai zai iya saka hannu ya buɗe wajan. Sauke ajiyan zuciya Zahra ta yi sannan ta ce. "Ikon Allah sai ka ce ɗakin sirri da har za'a saka masa password, to ni kam mene ne password ɗin ƙofar nan?, ko na ce hannun waye za'a saka kuma ya buɗe". Haka ta shiga yin magana ita ɗaya ba tare da ta san mene ne abun yi ba. Nan take tunanin mahaifiyarta ya faɗo mata. "Allah sarki Allah ya jiƙan ki Mamata duda ban taɓa ganinki ba amma ina jin sonki a cikin zuciyata Mrs Laila". Ta faɗa tana mai rubuta Mrs Laila a jikin in da haka saka enter password. Da mamakin ta kuwa ta ga ƙofar ya buɗe. Zaro idanuwa waje Zahra ta yi ta ce. "Laaaa!, lallai na yarda babu in da Allah baya ikon sa. Daga rubuta sunan uwata gaskiya nayi farin ciki sosai ashe soyayyar da nake wa uwata na gaskiya ne ba ƙarya ba". Nan take ta ƙarajin son mahaifiyar ta yana ƙara ninkuwa cikin zuciyarta. Ba tare da dogon tunani ba ta ƙusa kai cikin ɗakin. Gaba ki ɗaya ɗakin cike yake da ƙura tare da datti, sai ajiyayyun takaddu tare da akwatina tare da hotuna. Sakin baki kawai Zahra ta yi tana mai cigaba da bin ɗakin da kallo. Ɗaya daga cikin ajiyayyun hotunan Zahra ta ɗauka tare da goge wa da mayafin jikin ta. Rass! gabanta ya faɗi!, nan take ta saki hoton ya faɗi ƙasa yayin da glass da ke jikinshi suka tarwatse suka fashe. Saurin ja da baya Zahra ta yi tareda nuna hoton ta ce. "Wannan ba ita ce wannan mahaukaciyar da na gani a asibiti ba?, me kuma hoton ta yake yi a cikin wajan nan?, shin ita ɗin wace ce?. Kodai ita ma tana da halaƙa da wannan masarautar?". Haka ta cigaba da magana ita ɗaya kamar wata zautacciya. Ba ta yi aune ba ta ji an banko ƙofar ɗakin da take. Zumbur Zahra ta miƙe tana mai maida kallonta kan ƙofa don ganin wane ne. ************************** Su Aliyu kuwa suna isa gida suka shiga parlour nan suka tarar da su Grandpa tare da su Daddy a zazzau ne. Gaishe su suka yi a yayin da Safeera ta samu guri ta zauna kusa da Mom. Kallonsu Aliyu ya yi sannan ya ce. "Grandpa ya hanya?, me haka ce yake damun Safeera?". Amsa Grandpa ya bawa Aliyu da cewa. "Babu abin da ke damun Safeera lafiyarta ƙalau bawai shafar aljanu ba ne". Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi sannan ya ce. "To alhamdulillah haka ake so". Maida kallonsa Grandpa ya yi kan Safeera sannan ya ce. "Jikata ki kwantar da hankalin ki komai lafiya, baki da wani aljanu kinji ko". Girgiza kai kawai Safeera ta yi tare da miƙe wa tsaye ta shigar da kayan da suka siyo cikin ɗaki. ************************* Ganin babu kowa a wajan ƙofa ya sa Zahra sauke ajiyan zuciya. Nan take ta miƙe tsaye tareda ɗaukar mayafinta ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya, sannan ta ɗauki tsintsiya da ta gani a ƙasa ta fara share ɗakin. Saida ta kwashe fiye da awa biyu tana abu ɗaya. Ganin ɗakin ya fara dawo wa yadda yake ya sanya ya kwanciya tana sauke ajiyan zuciya!, Ganin ba ta ga ta kwanciya ba ya sanya ta miƙe wa sannan ta ɗora daga in da ta tsaya. Saida ta gama tsaff tare da jera hotunan cikin ɗakin kan bango sannan ya fito daga ɗakin kana ta rufe ɗakin. Nan suka ci karo da Junaid a tsaye sai faman kallonta yake. Turnuƙe fuska Zahra ta yi ta ce. "kai ya dai na ga kana kallo na kamar wani tsohon maye?". Girgiza kai Junaid ya yi sannan ya ce. "Ni ba ke nake kallo ba, mamaki nake ta yadda ki ka iya buɗe ɗakin nan ba tare da taimakon kowa ba. Mutum ɗaya ne kacal a gidan nan ya san sirrin buɗe wannan ɗakin kuma shi ne yahya Sooraj bayan shi babu wani. Muƙullin nan ma ba buɗe shi duka yake yi ba dole sai yahya Sooraj ne kawai yake buɗe ɗakin nan, amma nayi mamaki ta yadda ki ka iya sanin sirrin buɗe wannan ɗakin". Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Kai ba ka san ni ɗin ƴar baiwa bace ba?, lallai mutumin nan kana wasa, to in faɗa maka ni ɗin ƴar baiwa ce shi ya sa na iya buɗe wa. Kuma Ni fa kun dame Ni da maganar wani yahya Sooraj, wai shi ɗin wane ne haka?, na ga gaba ki ɗaya masarautar nan suna matuƙar ji da shi hatta mai martaba da Mami, yaushe ne zai zo na ganshi. Ina son na ganshi kafin na bar fadar nan". Murmushi Junaid ya yi sannan ya ce. "nan ba da daɗe wa ba zai dawo. Amma fa me iya zama da shi saita shirya, duk wannan rawan kai da jiji da kai da ki ke takama da shi duk saiya sauke su. Na san baki san ko shi ɗin wane ne ba amma lokaci zai yi da za ki ga ko wane ne shi". Yana kaiwa nan ya bar wajan. Tsaki Zahra ta ja sannan ta ce. "Aikin banza to ya zo ɗin mana, wa yake tsoronsa, ai ba haifi wanda Zahra za ta ji tsoronsa ba. Kuma ni dai-dai nake da koma wane ne". Ta faɗa tana mai wuce wa part ɗin Mami. ******************** "Hello sir, mun samo wacce ta taimaka wa Mrs Laila Abdullahi ta gudu daga asibiti, sunan matar Nadiya ita ɗin nurse ce a cikin asibitin da haka kai mrs Laila". Murmushi gov. Musa ya yi sannan ya ce. "Maza ku sace ta ku kaita gidan gona ta. Zuwa gobe zan sa a sace Amrah a wajan birthday ɗin Umar. idan Nurse Nadiya ba ta faɗi gaskiya ba sai a haɗa da ita da Amrah muyi safarar su izuwa ƙasar waje. Ku kasance a hankare saboda shima Umar jami'i ne idan ya gane gaskiya gaba ɗaya ba zamu tsira ba". "Shi ke nen yallaɓai". Mutumin ya faɗa yana mai kashe waya. Nan ya ɗauki wani perfume tare da fesa wa Nurse Nadiya. Nan take jiri ya fara ɗiban Mrs Laila faɗuwa ta yi a ƙasa sumammiya. Nan take suka rufe fuskokinsu da mask. Tare da cinciɓar Nurse Nadiya sannan suka saka ta a mota. Tada mota suka yi tare da barin harabar gidan nurse Nadiya. Su Umar kuwa na isa gida. Kai tsaye ɗakin sa Umar ya nufa tare da shiga toilet sannan ya kunna wa kansa shawa. Rintse idanuwansa ya yi a sa'inda ruwan ke zuba jikinsa. Tunanin abin da ya wakana ɗazu a shopping mall ne ya faɗo masa. Nan take ya buɗe idanuwansa. Ɓangaren su Amrah kuwa guri suka samu a parlour suka zauna. Yayin da Ramlat da Khairiya suka shiga kitchen domin su ɗora abincin dinner. Amrah kuwa kwanciya ta yi kan kujera idanuwanta a kan silin. Fitowa Gov. Musa ya yi nan take idanunsa suka sauka a kan Amrah. Murmushi ya saki kana ya nufi in da take. Tare da tsayawa a kanta. Ganin mutum zololo a kanta ya sa Amrah saurin miƙe wa tsaye tare da ja da baya. Murmushi Abba ya yi sannan ya ce. "Ke kuwa ya da firgita sai ka ce kinga wani dodo, ina so na faɗa miki gobe ne zagoyowar haihuwar ɗana Umar don haka gobe akwai babban shagali kinji ko, don haka ina so ki shirya kema kike. Ba zan faɗa masa ba sai dai muyi masa ba za ta". Ya faɗa yana mai shige wa ɗakinsa. Fitowa Umar ya yi ya tarar da Amrah tsaye gaba ɗaya ta yi wani iri. Kallonta ya yi sannan ya ce. "Amrah me ya faru?". Girgiza kai Amrah ta yi alamun babu komai. Bayan su Khairiya sun gama shirya dinner me suka fito da abinci tare da jera wa kan dining. Nan suka kira Abba tare da jami'ai sannan suka basu nasu abincin. Bayan sun gama cin abinci ne kowa ya wuce part ɗin sa. Yayin da ita ma Amrah ta nufi garden tare da awa kan bishiya ta yi kwanciyar ta ba tare da ta bar su Umar sun lura da fitar ta ba. Washe gari da sassafe Abba ya sa aka ƙawata gidan da kayan al'atu tare da flowers masu kyau. Nan ya sa haka kawo masa cake ɗin da ya kashe makuɗan kuɗaɗe domin a yi shi. Gaba ɗaya ƴan majalisa tare da govnors daga kowane gari sun cika gidan babu abin da ka ke gani sai shige da ficen mutane. Yayin da harabar gidan ya zagaye da sojoji tare da police men. Motoci kawai ka ke harba da su marasa iyaka. Bayan su Khairiya sun gama shirya wa ne. Suka tarar da cewa Amrah ba ta ɗakin su. Nan suka fuskanci cewa tana garden ne. Nan suka nufi garden yayin da suka sa ta sauka a kan bishiya nan suka nufi part ɗin su da ita yayin da suka sa ta yi wanka sannan suka shirya tsaff tsaff cikin Arabian gown wanda ya yi matuƙar fito da kyawunta. Fitowa suka yi gaba ɗaya yayin da Dj ya zo sannan ya fara playing ɗin waka. Ba'ayi aune ba mutane suka cika gidan gaba ɗaya. Umar kuwa bayan ya tashi daga bacci ne ya nufi toilet tare da taking bath ɗin shi sannan ya shirya domi zuwa wajan aiki. Bayan ya gama shirya wa ne ya nufi hanyar waje. Yana buɗe ƙofa ya ga mutane a tsatsaye. Nan take Dj ya saki sauti yayin da suka fara yi masa wakar happy birthday. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Umar ya saki tare da yi musu godiya sannan ya nufi hanyar waje domin ya tafi wajan aiki. Ganin hakan ya sa Abba ya sha gabansa sannan ya ce. "Umar ina kuma za ka je?". Amsa Umar ya ba shi da cewa. "Zan je wajan aiki ne mana". "Aba Umar kai baka ga party ɗin da na haɗa maka ba?, duk wannan fa nayi shi ne saboda kai. Ya kamata ka nuna kayi farin ciki ". Sauke ajiyan zuciya Umar ya yi tare da nufar wajan cake ɗin sannan ya ɗauki ƙaramin wuƙa sannan ya fara yanyanka cake ɗin. Nan take su ministers da sauran govnors tare da jama'ar cikin gidan suka bishi da kallo. Da sauri Amrah ta nufi in da yake tare da riƙe hannun Umar sannan ta girgiza masa kai. Ƙwace wuƙar ta yi daga hannunsa tare da dungure masa kai. Shafa in da ta dungure masa Umar ya yi tare da sakin murmushi sannan ya ce. "Mene ne kuma?, kema bakya so na tafi wajan aiki ne?". Gyaɗa kai ta yi alamun "Eh". "Shi ke nen tom ba zan je ko ina ba kinji". Nan take fari ciki ya lulluɓe fuskokin gaba ɗayansu. Nan haka cigaba da shagali yayin da haka yanka cake kowa ya ci ya sha. Har ƙarfe takwas da rabi na dare suka kai ana shagali a cikin gidan. Harabar gidan suka cigaba da shagali wanda haka ƙawata shi da kayan more rayuwa. Awa kan hall ɗin da Gov. Musa ya sa haka haɗa musamman saboda Umar. Umar ya hau kana ya gaida kowa na wajan. Sannan ya fara magana kamar haka. "Hello ladies and gentlemen, ina mai godiya da irin wannan ba za ta sa ku ka yi min, naji dad'i sosai Allah ya saka da alheri. Sannan shima mahaifina wato Gov. Musa Muhammad ina mao godiya da irin wannan babban shagalin da ya haɗa musamman saboda ni. Don haka ina godiya. Kuma sannan ina so na gabatar muku da wacce nake so muka nake muradi na aura wato Amrah". Ya faɗa yana mai waige-waige. Da sauri su Khairiya suka au kan hall ɗin sannan suka sanar da Umar cewa Amrah ba ta cikin gidan. Nan take Umar ya rikice da sauri ya sauka daga wajan yayin da shiga bin lungu da saƙo na gidan domin neman Amrah. "Yahya Umarrrrr!!!". Gaba ɗaya suka ji an furta. Juyowa Umar ya yi yana mai sauke idanunsa kan nata nan take ya yi mutuwar tsaye ganin cewar tabbas Amrah ita ce wacce ta kira sunansa ba wani ba. Da mugun gudu ta nufo in da Umar yake domin kuwa babban ringlight da ke tsakiyar wajan na shirin faɗo masa. Da mugun sauri ta nufi wajan sa tare da ture sa. Nan take ringlight na wajan ya faɗo mata a jiki. Zaro idanuwa waje gaba ki ɗayansu suka yi take gaban Umar ya faɗi. Faɗuwa Amrah ta yi tare da gangarawa ta faɗa cikin swimming pool ɗin harabar gidan. Umar bai yi wani tunani ba ya faɗa cikin swimming pool ɗin domin ceto Amrah. 💖💖💖❤‍🔥❤‍🔥💖💗💗 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (ZINARIYAR JAJIRTATTU) Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣5️⃣▶️3️⃣6️⃣ *_________________________________________________* Mintuna ƙalilan ya ɗauki Umar a cikin ruwan ya fito da Amrah. Sauke ajiyan zuciya ya shiga yi babu gaggauta wa tare da maida kallonsa kan Amrah. Da mamakin sa kuwa ya ga ta sakar masa murmushi kamar ba ita ce wacce ya shiga ruwa domin ceta ba. Miƙe wa tsaye Umar ya yi a fusa ce tare da duban Amrah ya ce. "A kan me ya sa za ki salwantar da rayuwarki saboda ni?, kin san wane irin hali zan shiga idan wani abu ya same ki?, na ga alamun so ki ke sonki ya kashe ni ko?". Ƙasa da kai Amrah ta yi ta ce. "Kayi haƙuri, ba zan sake ba". Tsaki Umar ya ja. "Aikin banza kawai". Ya furta tare da barin wajan party ɗin baki ɗaya. Gaba ɗaya mutanen wajan suka bishi da kallo. Zuwa in da Amrah take su Khairiya suka yi tare da kamo hannun Amrah domin su shiga ciki da ita. Wafce hannunta Amrah ta yi daga na Khairiya kana ta nufi garden da gudu tare da hawa kan bishiya sannan ta kwanta. Ganin Amrah ta nufi garden ya sa su Khairiya suka mara mata baya. Kallon gaba ki ɗaya baƙin nasu Gov. Musa ya yi tare da basu haƙuri sannan ya sa haka rufe party ɗin. Nan take kowa ya watse. Umar kuwa yana shiga cikin gida bai nufi ko ina ba sai ɗakin sa. Faɗa wa ya yi kan lallausar gadonsa tare da sakin ajiyan zuciya. Lumshe idanuwansa ya yi. Gaba ki ɗaya Amrah ce kawai ke yi masa gizo a cikin idanunsa. Nan take abin da ya faru ya faɗo masa. Zumbur ya miƙe zaune. Kana ya ce. "Ta ya ya ƙwayar idanunta suka iya sauya wa lokaci ɗaya?, am really confused!, ko dai mutum biyu ne". Girgiza kai ya yi ya ce. "No it can't be possible, ba zai yu su kasance su biyu ba, mybe ni ne ban gani ba sosai green ne ba blue ba". ************************* Shiga cikin ɗakin Safeera Mom ta yi ta tarar da Safeera zaune kan kujera ta yi tagumi kamar wacce haka yi wa mutuwa. Ƙarasawa in da take Mom ta yi tare da zama kusa da ita. Sannan ta dubeta ta ce. "Safira tunanin me ki ke?". Ajiyan zuciya Safeera ta sauke sannan ta ce. "Babu komai Mom, kawai dai ni ina son na koma America ne, ina so na ci gaba da karatun lawyer please Mom. Am tired of this country I just want to go back". Murmushin yaƙe Mom ta yi ta ce. "Ke kuwa Safira ba ana karatun law a Nigeria ba, sai kiyi abunki kawai a nan. Idan ya so ma kafin lokacin anyi engagement ɗin ku keda Aliyu. Kawar da kanta Safeera ta yi gefe ta ce. "Ni fa ba zan yi aure yanzu ba, ni so nake na yi karatu bana son aure". Girgiza kai Mom ta yi kana ta ce. "Ki sani cewa shi aure sunnar manzo Allah (SAW) ne. Kamar ta bakin mahaifin ki ko kina so ko bakya so sai an ɗaura miki aure da Aliyu kuma sai kin zauna. Duda cewar auren dole haramun ne amma na san kafin ma lokacin da za'a miki auren za ki fara son Aliyu kuma za ki ce na faɗa miki". "Allah ya kiyaye, wallahi nafi ƙarfin shi". Safira ta furta tana mai yamutse fuska. Miƙe wa tsaye Mom ta yi ta ce. "Lokaci zai zo da za ki yarda da maganar da na faɗa miki". Tana kaiwa nan ta fice ta bar mata ɗakin. Ajiyan zuciya Safira ta sauke!, kana ta ce. "Koma dai mene ne saina koma ƙasar America wallahi". Ta faɗa tana mai shige wa toilet tare da ɗauro alwala sannan ta gabatar da sallah. ************************** Zahra na fita kai tsaye part ɗin Mami ta nufa. Tana shiga ta tarar da Jakadiya tana yi wa Mami massaging ɗin ƙafarta. Da sallama ta shige cikin ɗakin kana ta samu guri a ƙasa ta zauna. Kallon Zahra Mami ta yi cikin farha ta ce. "Zahra kin gama aikin kenen". Girgiza kai Zahra ta yi kana ta ce. "Eh Mami na gama sai kuma na gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya". Kallonta jakadiya ta yi ta ce. "Masha Allah gaskiya kin burge ni, kuma da alama ba za ki ɗauki raini ba. Ni sai nake ganin kina min kama da wata wallahi". Yaƙe Zahra ta yi ta ce. "Su aba gaskiya ne, masha Allah hakan yy dama an ce kowane ɗan adam yana da mai kama da shi, ina ga mai kama da ni ɗin ne ki ka gani". "Uhmmm!". Jakadiya ta yi kana ta maida kallonta ƙasa. "Kash". Ta furta sannan ta ce. "Gaba ɗaya na manta ban tawo da nail cutter daga part ɗin su Samira ba. Kuma sabo ne, bara naje na ɗauko". Kaɗa kai Zahra ta yi ta ce. "Aba dai me ya sa za ki je ki ɗauko bayan ina zaune a nan wajan?, kada ki damu kiyi zaman ki kawai a nan zan je na ɗauko". "Shi ke nen". Jakadiya ta furta. Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tare da nufae hanyar waje. Saida ta je daff da za ta fita ta ji muryar Mami na faɗin. "Zahra dakata". Tsayawa chakk Zahra ta yi tare da maida kallonta kan Mami ta ce. "Mene ne Mami?". Amsa Mami ta ba ta da cewa. "Babu komai, ina so in faɗa miki cewa idan ki ka je chan duk abin da za su yi miki kada ki tanka su dan Allah, bana son a kuma samun wani matsalar please and please". Girgiza kai zahra ta yi kana ta ce. "In sha Allahu ba zan kula su ba". Ta faɗa tana mai fice wa daga ɗakin. Kai tsaye in da ta ga su Samira sun nufa ɗazu ta nufa domin ɗauko nail cutter ɗin Mami. Saida ta zo dai-dai ƙofar part ɗin su kana ta buɗe handle ɗin ƙofan ba ta yi wata-wata ba ta ƙusa kai ciki. Take ta shaƙi hayakin da ya gauraye ilharin parlourn part ɗin su Samira. Tari Zahra ta fara yi tare da toshe hancin ta. Domin kuwa warin shisha ne kawai ke tashi a ɗakin. Waige-waige Zahra ta fara yi. Nan take idanuwanta suka sauka a kansu Samira wanda ke faman zuƙan shisha. Dubanta suka yi tare da cewa. "Ya haka yi ne?, me kuma ya kawo ki ɗakin mu?". Ƙasa da kai Zahra ta yi cikin jin takaicin abin da suke aikata wa. Ɗaga kanta Zahra ta yi ta dube su ta ce. "Tirr da wannan rayuwa irin taku. Gaba ki ɗaya kun taso babu tsoron Allah a zuƙatan ku, wannan wace iriyar rayuwa ce?, kuna mata kuna shan hayaƙi wanda babu abin da take haifar wa sai cutarwa, Allah ya shirye ku. Ni duk ba wannan ba na zo ne duba nail cutter ɗin Mami yana ina?". Dariya gaba ɗaya suka kwashe da shi. Yayin da Yusrah ta miƙe tare da zuwa daff da in da Zahra take sannan ta busa mata hayaƙin bakin ta. Kawar da kanta Zahra ta yi gefe tare da ɗaga hannun da zimmar dirza bakin Yusrah a bango. Nan kawai furucin Mami suka faɗo mata da cewa duk abin da za su mata kada ta kuskure ta tanka musu. Furzar da iska Zahra ta yi waje sannan ta ce. "Ni banzo wajan nan domin na takale ku ba, na zo ne saboda na nail cutter ɗin Mami". Ɗaukar nail cutter ɗin da ke kan table Samira ta yi kana ta ce. "Gashi nan ba za'a bayar ba me za ki yi?". Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Ni babu abi da zan yi kawai ki bani nayi tafiya ta salin alin". Miƙe wa tsaye Samira ta yi ta ce. "Na ce ba za'a bayar ba, kina ƴar aiki kina yi mana magana yadda ki ke so, to ki sani cewa ko uwark.......... Maganar Samira ce ta dakata sakamakon tsawar da Zahra ta daƙa mata wanda saida ya ratsa ilahirin ɗakin baki ɗaya. Take tsoro ya cikashe zuciyoyin su baki ɗaya. Cikin huci Zahra ta nuna Samira da ɗan yatsarta kana ta ce. "Duk abin da za ki yi to ya tsaya a kaina banda mahaifiyata. Idan kuwa ki ka kuskure ki ka yi sakin baki wajan furta magana mara daɗi kan uwata a ranar za ki san bambancin ƴar sarauta da kuma ƴar magarƙama. Maza miƙo min nail cutter ɗin kafin na ɓa ta muku rai". Jiki na rawa Samira ta cilla wa Zahra nail cutter ɗin. Chafke wa Zahra ta yi sannan ta bi gaba dayansu da kallo tare da girgiza kai ta ce. "Na fuskanci cewa ba za ku iya zama da mutum cikin lafiya ba tare da wani hayaniya ba. Amma tun da haka ku ke so faɗuwa ta zo dai-dai da zama. Domin ni gyatumar ku ce a fannin rashin son zaman lafiya. Mu zuba mu gani, sai kun ɗanɗana wa aya zaƙin ta". Tana kaiwa nan ta fice ta bar musu ɗakin. Suna ganin ta fita suka sauke ajiyan zuciya. Kallon Samira Fasma da Yusrah suka yi sannan suka ce. "Me ya sa za ki ba ta nail cutter ɗin?". Amsa Samira ta basu da cewa. "Ta ya ya ba zan ba ta ba, kuna gani lokaci ɗaya yadda fuskarta ya canza kuma ku ce kada na ba ta nail cutter, wannan idan haka bar mu da ita tsaff za ta zane mu, don wallahi yadda nake ganin yanayin ta kamar ƴar daba ko in ce ƴar jagaliya". Tsaki Fasma ta buga kana ta ce. "An dai ji kunya wallahi, wai a ce wannan ƴar talakawan ta zo har masarautar mu tana razana mu, gaba ɗaya ta ana mutane saƙat dole muyi wani abu domin yin maganin ta. Idan ba haka ba to ba za ta daina ba, dole mu koya mata hankali". "Ƙwarai kuwa Fasma, maganar ki gaskiya ce dole mu koya mata hankali". ************************* "Amrah maza ki sauko mu shiga ciki kinji". Cewar Ramlat. Girgiza kai Amrah ta yi kana ta ce. "Babu in da zani, ni kawai ku maida ni wajan ƴan uwa na, su nake son gani". Dafe kanta Khairiya ta yi ta ce. "Shi ke nen zamu kaiki kinji. To sauko". Girgiza kai Amrah ta yi alamun A'a. Babu yadda suka iya haka suka koma ciki suka bar Amrah a kan bishiya. ********** "Hello yallaɓai, mun samo matar da ka ce mu samu wannan malamar asibitin yanzu haka tana wajan mu a dajin da muka saba haɗuwa wajan yin harƙalla". Murmushi Gov. Musa ya saki sannan ya ce. "That's great wannan good news ne ku bani nan da mintuna ashirin zan zo". Yana kaiwa nan ya katse wayar. Yana sauke wayar ya ga kira ta kuma shigowa sai dai na wannan karan da private number haka kira. Kallon screen ɗin wayar Gov. Musa ya yi cike da mamani yake bin wayar da kallo. Ɗaga wayar ya yi tareda saka wa a handsfree sannan ya ce. "Who's on the line?". Ji ya yi an saki murmushi sannan ya ce. "Wato baka gane ni ba kenen, to MK ne, naji labarin cewa ka sa an sace nurse Nadiya saboda ta faɗa maka in da Mrs Laila take, sai dai kuma hakan ba zai yi aiki ba domin ita kanta ba ta san Laila na raye ba. Maza ka sa yaranka su sake ta idan kuma ba haka ba zan tona asirinka a wajan ɗanka, na san da cewa babu abin da kafi so a duniyar nan sama da ɗanka bayan ɗanka sai kuɗi ko, to ka sani cewa ni ɗin zan je na tona maka asiri na faɗa masa irin mahaifin da yake da shi". Ɗan jimm gov. Musa ya yi daga bisani kuma ya babbake da wata mahaukaciyar dariya. Nan take ya haɗe ransa tamkar bai taɓa dariya ba ya ce. "Ta ina za ka faɗa masa ko ni ɗin wane ne?, wane hujja ka ke da shi a kan hakan?, ka sani cewa ɗana ba zai taɓa yarda da kai ba muddin ba hujja ka nuna masa ba". Daga ɗayan ɓangaren Mk ya saki murmushi sannan ya ce. "Tabbas kayi gaskiya bani da hujja amma ka sani cewa ina da hujja ta yadda kayi amfani da makircin ka wajan kashe mahaifiyarsa. Ka san dai babu wanda ya fi ƙauna a duniyar nan sama da mahaifiyar sa kuma kai ɗin nan ka kashe ta saboda abun duniya". Take gaban Gov. Musa ya faɗi!, yayin da zufa ya fara ƙeto wa ta kowane sashe na jikin sa. Duk iskan AC da ke kaɗa wa a ɗakin sa bai ana shi yin gumi da tamkar wanda haka watsa wa ruwan zafi haka gov. Musa ya rikice. Tattaro nutsuwar sa ya yi kana ya ce. "Ta ya ya ka sani?, wane ne ya faɗa maka?". Dariya Mk ya kwashe da shi ya ce. "Wato har ka manta da tsohon abokin ka kenen wato Abdullahi mijin Mrs Laila?, Kai da kanka ka sa his Excellency Abdullahi ya gudu daga Nigeria izuwa ƙasar China saboda sharrin da ka maƙala wa matar sa da kuma shi. Kada ka damu gaskiya ta kusan bayyana domin kuwa kundin littafin da ka ke nema na duk asalin abubuwan da ya faru yana nan cikin tsararren guri. Zan ƙara tunatar da kai idan ba ka sa yaranka sun saki Nurse Nadiya ba zan tona maka asiri. Sannan bara na faɗa maka wani abu, ƴar mrs Laila guda ɗaya tana Kano idan ka isa ka gano in da take kuma ka sace ta". Yana kaiwa nan ya katse wayar. Gaba ɗaya gov. Musa ya rikice da jin furucin Mk hakan ya sa ya yi gaggawan kiran yaran sa masu taya shi aikata miyagun laifuka sannan ya ce dasu su saki nurse Nadiya. Kamar yadda ya buƙata haka suka saki nurse Nadiya yayin da suka maida ta gidan ta. *AFTER ONE WEEK* Ko ina a cikin masarauta ya cika yayin da haka ƙawata ko ina da kayan al'atu tare da na al'adu. Yayin da dakarai suka jeru sai kai kawo suke a masarautar. Babu abin da ke tashi sai ƙamshi abinci da ƙamshi abubuwan laƙumashe. Yayin da ƴan aiki suka bazama sai girke-girke da share-share suke. Jin hayaniya ya sa Zahra miƙe wa daga kan gadon ta tare da yin miƙa sannan ta ce. "Wai yau me ke faruwa a masarautar nan ne?, kodai baƙo za su yi ne?". Ta tambayi kanta. Takawa ta fara yi tare da nufar hanyar waje sannan ta fice daga ɗakin. Nan taci karo da Mami wacce ta ci kwalliya cikin shigarta na alfarma. Sakin baki Zahra ta yi tana mai bin Mami da kallo. "Mami irin wannan kyau haka, meke faruwa a ne?". Murmushi Mami ta yi kana ta ce. "Magajin wannan masarautar ne zai dawo wato gawurtaccen ɗana Sooraj, duk waɗan nan kwalliya da yadda haka ƙawata masarautar nan duk saboda shi ne, s duk sanda zai dawo daga ƙasar waje to ana taruwa ne ayi masa tarba mai kyau". Jinjina kai Zahra ta yi ta ce. "Gaskiya ne sai kace ɗan gold. Ni har na matsu ma na ga Sooraj ɗin". Kallonta Mami ta yi ta ce. "Kada ki damu a yau za ki ganshi. Yauwa na ma tuna na ce zan aike ki da wasu daga cikin ƴan aikin masarautar nan zaku je ne kasuwa siyo mai special kayan girki wanda nake yi masa special domin baya cin abinci kowa in ba nawa ba. Sannan kuma yana matuƙar son black tea gashi kuma babu, shi ne nake so ku ɗan je driver ya kaiku ku siyo dan Allah". "Aba Mami sai kin ma haɗa ni da Allah, kada ki damu in sha Allahu yanzu ma zamu je bara na ɗauko mayafi na". Ta faɗa tana mai shige wa ɗakin ta, lokaci ƙalilan ya ɗauke ta a ɗaki ta fito kanta sanye da mayafi blue colour. Zuwa inda Mami take ta yi ta ce. "Shi ke nen bani kuɗin muje". Miƙa mata kuɗaɗe Mami ta yi kusan dubu dari biyu. Zaro idanuwa waje Zahra ta yi baki na rawa ta ce. "Mami irin wannan kuɗi haka sai kace za'a biya kuɗin sadakin wata. Ina laifin dubu dubu ɗaya ƙarƙari ma mun kashe kuɗi da yawa 1500 amma shi ne za'a zuba uban kuɗi haka. Ni tunda nake ma ban taɓa ganin kuɗaɗe masu yawa haka ba sai yau". Dariya zahra ta bawa Mami. Girgiza kai kawai Mami ta yi ta ce. "Zahra kenen, kina da abin dariya ke za ki ga kamar sun yi yawa ne amma kuwa babu yawa". Saka hannu Zahra ta yi ta karɓi kuɗi salati riƙe a bakin ta. Maida kallonta ta yi kan Mami ta ce. "Amma ni bana so naje da su ƴan aiki". "To da wa ki ke son ki je?". Mami ta tambayi Zahra. Amsa Zahra ta ba ta da cewa. "Da su Samira nake son muje". Zaro ido Mami ta yi waje. "Zahra ki rufa min asiri, ke kin san ba za su je ba wahalar da kai ne kawai". Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Tabbas ni nan zan sa su suje, bakin ce suna matuƙar tsoron ɗanki ba, to ki jira ki gani". Ta faɗa tana mai fice wa daga part ɗin Mami. Chan ta hangi su Samira sai sha'anin su suke hankali kwance. Hamdala Zahra ta yi tare da nufar in da suke. Binta suka yi da kallo ganin yadda ta yi cirko-cirko a kansu. "Ke mene ne ki ka wani zo ki ka tsaya a kanmu?". Amsa Zahra ta basu da cewa. "Yahya Sooraj ne ya bamu umarni da muje kasuwa yin siyayya tare". Jin Zahra ta ambaci sunan Sooraj ya suka miƙe tsaye jiki na rawa suka ce. "To ai sai ki faɗa mana tuntuni bawai ki tsaya a kanmu ba". Nan suka nufi wajan parking space tare da shiga cikin mota. Yayin da driver ya tashi mota suka bar harabar masarautar. Kai tsaye kasuwa ya nufa. Yana zuwa ya yi parking yayin da suka fita. Nan Zahra ta shiga cikin kasuwa tareda fara siyayyar abubuwan da Mami ta gaya mata. A sa'inda su Samira suka samu guri suka zauna a bunsu. Saida Zahra ta gama siyayya tsaff sannan ta saka hannu domin ciro kuɗi a jikin ta. Wayam ta ga babu kuɗi ba alamar su. Zaro idanuwa waje ta yi tare da sakin salati. "Yau akwai tashin balagan tsuntsaye. Wane ɓarawon ne ya sace min kuɗi, tabbas yau babi wanda zai fita daga kasuwan nan muddin ba'a fito da kuɗin nan ba". ******* Jere fararen motoci ke tafiya kan titin wanbai. Tare da dokuna wanda suka mara musu baya da kuma fadawa wanda suka zagaye motocin yayin da jama'a suka shiga miƙa gaisuwa. Cikin motan kuwa wani mature guy ne zaune cikin mota a ƙalla zai kai kimanin shekaru 35 zuwa 38 ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayin da news paper ke riƙe a hannunsa. Dukkan yabo da jinjina su tabbata ga ubangiji wanda ya yi wannan kyakyawar halittar. Sanye idanuwansa suke da broline glass yayin da hannayensa suke sanye da rolex wrist watch. Lumshe idanuwansa ya yi masu kama da madara. Yayin da suman kansa suka kwanta suka yi luff. Sajen fuskarsa masu taushi da laushi suka ƙara masa kyau. Sanye yake cikin labcoart duban driver ya yi cikin cool voice ɗin sa ya ce. "Ka wuce da ni kasuwa zan siya black tea". Murmushi Driver ɗin ya yi ya ce. "Aba ranka shi daɗe, mene ne amfanin mu?, yau ɗin nan ka dawi Nigeria bai kamata ka shiga kasuwa ba idan muka isa fada ƴan aiki za su zo su siya". Girgiza kai mutumin ya yi ya ce. "Kaine shugaba ko ni ne shugaba?, maza kayi yadda na ce". "A gafarce ni ranka shi daɗe in sha Allahu zamu je. Amma me ya sa ba zamu wuce shopping mall ba sai cikin kasuwa?, ina ganin kamar hayaniya ta yi yawa a chan". Shiru Yarima ya yi sannan ya ce. "Shi na gadaman zuwa kai mene naka?". "Bakomai ranka shi daɗe ". Driver ɗin ya faɗa. Kai tsaye kasuwa ya nufa da su. Yayin da ya tarar da taru jama'a sun yi zagaye da alama wani abu ne ke faruwa. Ɓangaren Zahra kuwa babu abin da take sai surfa bala'i yayin da ta rikita kasuwar a lallai sai an fito da wannan kuɗi. Babu abin da mutane ke yi sai kallo. Fitowa Yarima Sooraj ya yi daga cikin mota. Daga nesa su Samira suka hango shi. Nan take cikin su ya ɗuri ruwa. A hankali suka silale daga wajan. Ƙarasawa wajan Sooraj ya yi. Nan idanuwan shi ya sauka a kan Zahra wanda sai faman masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Takaici ne ya kama Sooraj, dubanta ya yi ya ce. "Ke baki da hankali ne za ki zo ki tada wa mutane hayaniya a wajan nan". Ya faɗa cikin ɓacin rai. Dubansa Zahra ta yi nan suka haɗa ido a tare. take gaban kowanensu ya faɗi!, yayin da suka fara jin wani irin yanayi na da ban. Galla masa harara Zahra ta yi ta ce. "Kai malam waya gayyace ka nan?, shin ka zo ka biya kuɗin da haka sace ne?, to maza ware daga nan". Nan take ran Yarima Sooraj ya ƙara ɓaci. Take ya ji tsanarta ya shiga cikin ransa ya tsani mace mara kamun kai da rashin sanin darajar kai. Juya wa Yarima Sooraj ya yi tare da barin wajan. Shiga cikin mota ya yi yayin da driver suka tada mota suka bar wajan. Kai tsaye masarauta suka nufa. Bayan tafiyar Sooraj ne Zahra ta ga kuɗin a dunƙule s ƙasa. Hamdala ta yi tare da bawa mutanen gurin haƙuri. Miƙa wa mai kayan kuɗin ta yi tare da karɓar abubuwan da ta siya. Waige-waige ta fara yi domin gani su Samira amma ba ta gansu. Haka ta ci gaba da cigiyar tmds ta ga ba zata iya ba ta shiga cikin mota yayin da driver ya ja ta suka bar kasuwan. Shiga ciki motocin su Sooraj ya yi cikin masarauta. Nan take dakarai da fadawa suka shiga durƙusawa suna kwasar gaisuwa tare da yi masa ƙirari. Fitowa Yarima Sooraj ya yi tare da amsa gaisuwar tasu. Yayin da su Gimbiya Talatu suka sha jinin jikinsu. Gaishe da mai martaba Yarima Sooraj ya yi cikin girmama wa tare da gaidar da su Gimbiya Saratu. Sama-sama su Gimbiya Saratu suka amsa. Part ɗin sa ya nufa tare da nufar ɗakin ajiyar sa sannan ya saka thumbprint ɗin sa. Nan take ƙofar ta wangale gani ya yi an tsaftace ɗakin an gyara shi ba kamar yadda yake ba. Mamaki ne ya bayyana kan fuskarsa. Da sauri ya fita daga cikin ɗakin tare da fitowa harabar fada yana mai ƙwalla kiran kowa na wannan masarautar. Kan ka ce me mutane sun taru a fada. Kallon kowanensu ya yi sannan ya ce. "Wane ne wanda ya shiga ɗakin ajiya ta?". Shiru gaba ɗaya suka yi babu mai bakin magana. Dai-dai lokacin da Mami da su Samira ke ƙarasowa wajan. Daka musu tsawa ya yi yana mai faɗin. "Na ce wane ne ya shiga ɗakin ajiya ta?". Ya faɗa rai a matuƙar ɓace. Sannan ya ce. "Tabbas ko wace ce wannan ƴar leƙen asiri ce kuma ba zan rabi da koma wane ne ba. babu wanda ya san password ɗin wannan ɗakin sai ni kaɗai, ta ya ya haka iya buɗe wa bayan ni kaɗai ne na san password ɗin?". Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Eh wata sabuwar ƴar aikin mu ce sunanta Zahra. Laifi ta yi shi ne mai martaba ya ce za ta dinga share wannan ɗakin kuma babu ranar da za ta tashi ta faɗi ba ta share ba". "Where is she?". Yarima Sooraj ya tambaya cikin tsananin ɓacin rai. Dai-dai lokacin da motar su Zahra ke shigowa. Parking motan ya yi yayin da ta fito tare da kayayyakin da ta je siya. Maida kallonsu suka yi baki ɗaya kanta. "Yauwa ka ga ƴar halak ita ce wannan". Mami ta faɗa tana mai nuna Zahra. Take rab Yarima Sooraj ya ƙara ɓaci ganin yarinyar da ya gani a kasuwa. Ƙarasawa wajan Zahra ta yi ganin yadda gaba ɗaya suke binta da ido ya sa ta kawar da kanta gefe. Nan take ta haɗa ido da Sooraj. Take gabanta ya faɗi!. Sakin kayan da ta riƙo ta yi gaba ɗaya suka faɗi ƙasa. Sannan ya fara tafa hannunta tare da riƙe haɓarta ta ce. "Iyyeeh!, wato har gida ka biyo ni kenen, ƙara ta ka kawo ko me?, dama ina ganin fuskar ka na san kai ba na Allah ba ne. To maza zo ka fice daga cikin masarautar nan kada ka bari Yarima Sooraj ya shigo ya tarar da kai a nan domin ba za ka ji da dad'i ba". Murmushi Yarima Sooraj ya yi ya ce. "Au aba da da gaske?". Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Ƙwarai da gaske nake ko zaci ƙarya nake?. Idan ka bari Yarima Sooraj ya zo ya ganka a nan ba za ka ji da dad'i ba". Kallonta Mami ta yi ta ce. "Wane Yarima Sooraj kuma bayan gashi nan a gaban ki". Nan take gaban Zahra ya bada wani irin sauti. "Kambala'i, da gaske shi ne?". Amsa Mami ta ba ta da cewa. "Ƙwarai da gaske shi ne". Haɗiye tsoron da ke ƙoƙarin bayyana Zahra ta yi ta ce. "Shi ke nen tawa ta ƙare!". *KUYI HAƘURI DA RASHIN UPDATE DA WURI DAN ALLAH*. LIKE, COMMENT AND SHARE FISABILILLAHI 🙏 🥺 🥺 🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (ZINARIYAR JAJIRTATTU) *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Thre siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣7️⃣▶️3️⃣8️⃣ *___________________________________________* Jiki a muce Zahra ta ɗauki kayan da ta zube a ƙasa sannan ta fara ƙoƙarin wuce wa ta gefen Sooraj, a sa'inda zuciyarta ke dukan uku-uku!. Daga sama ta ji muryarsa. "Dakata!". Ta ji Sooraj ya furta. Tsaya wa chak Zahra ta yi yayin da ta kasa motsa ko da ɗan yatsarta ne saboda tsananin tsoron da ta shiga. Zagayowa Yarima Sooraj ya yi har gabanta sannan ya tsaya yana mai fuskantar ta. Yayin da ɓangaren guda idanuwan jama'a a kansu. Ƙura mata idanuwansa ya yi masu matuƙar ɗaukar hankali sannan ya ce. "wace ce ke?". Jin tambayar da ya yi mata, hakan ya sa Zahra ta bashi amsa da cewa. "Ni mutum ce mana". Kallonta ya yi cike da mamaki ganin yadda babu wata alama na nuna jin tsoronsa a tattare da ita, hakan ya ƙara bashi aushi. "Ke haka na ce wace ce ke, me ya kawo ki wannan masarautar?, sannan daga ina ki ka fito?, da me ki ke takama?, sannan tambaya ta ƙarshen ta ya ya ki ka iya buɗe ɗakin ajiyana bayan ni kaɗai ne na san maƙullin sirrin buɗe wannan ɗakin?". Zololo Zahra ta yi tana kallon shi. "Kai kuwa Yarima irin wannan tambayoyi haka sai ka ce google ake tambaya, ai sai kayi min tambayar ɗaya bayan ɗaya. To farko dai ni sunana Fatima ana kira na da Zahra, na rasa mahaifiya ta ne tun kafin na san ciwon kaina, yanzu haka bani da kowa sai iya Aunty Binta wacce ke kula da ni. Sannan batun me ya kawo ni masarautar nan babu ita domin ba ni ce na kawo kaina ba Mami ce ta buƙaci na zo nayi aiki domin tara kuɗin motan da zan koma garin mu Jigawa. Sannan ka ce da me nake takama, to ni dai babu wanda nake takama da shi sai mahallici na bayan shi kuma babu, sannan sanin ta yadda na iya buɗe wannan ɗakin abu mai sauƙi ne domin wani suna kawai na danna ya buɗe, shi ke nen". Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, sannan ya ce. "Har yanzu baki bani amsa gamsashiya ba. zan ƙara tambayar ki a karo na uku ko. Wace ce ke?". Furzar da iska mai zafi Zahra ta yi kana ta ce. "Kamar yadda na faɗa maka tun fari, sunana Zahra, ni ɗin na taso ni cikin magarƙama tsakiyar masu laifi, hatta daga yin wayo na har izuwa girma na a magarƙama nayi". Zaro idanuwa waje gaba ki ɗaya al'ummar masarautar suka yi. Murmushi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kenen dai ke ɗin babbar mai laifi ce ko?". Sauke ajiyan zuciya Zahra ta yi!, sannan ta ce. "A'a, mahaifiyata ce haka yi mata sharri shi ne aka kaita magarƙama bayan ta haife ni ne ta rasu, kuma ƴan uwanta suka ƙi ƙarɓa ta shi ne Hajiya Binta ta raine ni". Ta ƙarashe maganar zuciyarta nayi mata zafi da ƙuna. Murmushin mugunta Sooraj ya saki kana ya ce. "Kenen dai mamarki ita ce muguwa ko?, ita ce babbar mai laifi har aka kaita magarƙama. Ai dole ma ƴan uwanta su yi rejecting ɗin ki saboda kar su zo suna dana sanin karɓar ki, sai kuma gashi kema kin yo halin uwar taki". Danne fushin da ke ƙoƙarin bayyana kan fuskar ta Zahra ta yi tare da kawar da kanta gefe sannan ta ce. "Yarima ka san me za ka faɗa dan Allah, ka iya sarrafa harshen ka". "Ba zan sarrafa harshen nawa ba". Sooraj ya faɗa a matuƙar tsawa ce. Nuna Zahra ta yi da yatsarsa sannan ya ce. "Na tabbatar da cewa ke ƴar leƙen asiri ce, kuma idan ki ka kuskure na gano ko asalin wace ce ke to ba za ki sha ba". Yana kaiwa nan ya shige cikin fada sannan ya nufi part ɗin ta. Sallamar kowa Junaid ya yi, yayin da jama'a suka watse saura mutanen cikin masarautar. Kallon Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Zahra tawo mu shiga daga ciki". Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Wallahi Mami nayi duba da irin mutunci da kuma kima da ki ke da shi ne a waje na. Hakan ya sa na rabu da yarima Sooraj, amma da ba dan haka ba wallahi sai ya san cewa Allah ɗaya ne, ba zan ji daɗin a zagar wa wani mahaifiyarsa ba, haka zalika nima ba zan ji daɗin a zagar min tawa mahaifiyar ba, da ka zagin uwa ta na gwammace ka kwana kana zagi na". Tana kaiwa nan ta shige cikin fadan sannan ta shiga ɗakin kwanan ta wanda haka ware mata a matsayin ƴar aiki. Kallon Juna Gimbiya Saratu da Talatu suka yi tare da bushe wa da dariya yayin da suka riƙe hannun juna sannan suka shige part ɗin su. Girgiza kai kawai Mami ta yi sannan ta ce. "Allah ya ganar da ku gaskiya". Ta faɗa tare da shige wa part ɗin ta. Rakiya Junaid ya yi wa mai martaba izuwa fadar sa. Gaba ɗaya gidan ya koma kaman gidan makoki. Babu wani hayaniya ko surutu. Abincin ma da aka jera kan dining babu wanda ya bi ta kansu. Zahra na shiga ɗaki kuwa ta kwanta kan gado. Yayin da fuskar Sooraj ya fara yi mata gizo. Lokaci ɗaya ta ji tsanar sa ya mamaye zuciyar ta. "Aikin banza kawai, dan kawai yana matsayin ɗan gidan sarauta shi ne zai zo ya dinga raina wa mutane hankali, ni Allah ya bani kuɗi ma ni na haɗa kuɗin mota na tafi, na san kuɗin motan ba za ta wuce dubu biyu zuwa dubu uku ba". Dafa cikinta ta yi jin yadda yake murɗa mata alamun yunwa take ji. "Kambala'i, ashe fa ban ci abincin safe ba na fita, chab Zahra me ki ke jira maza-maza tashi kije ki cika cikin ki". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye sannan ta nufo hanyar ƙofar ɗakinta ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita. _________________________ "Dan Allah Amrah ki nutsu, ko daina kuka kinji, munyi miki alƙawarin duk in da ƴan uwanki suke zamu kai ki wajan su". Ramlat ta faɗa damuwa bayyane kan fuskarta. Girgiza kai Amrah ta yi cikin ƙaramin muryarta ta ce. "Ni A'a, ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, ina son ganin ƴan uwana". Ta ƙarashe maganar tana mai rushe wa da kuka. Dai-dai lokacin Umar ke ƙaraso wa wajan. Su Khairiya kuwa, ganin Umar ya ƙaraso ya sa su sakin ajiyan zuciya sannan suka ce. "Yauwa yahya barka da dawo wa, ka ga Amrah tun ɗazu take kuka wai ita a mayar da ita in da aka ɗauko ta". Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya nufi in da Amrah take zaune karƙashin bishiya ta yi ruff da ciki. Ƙarasawa ya yi wajan da take sannan ya dube ta ya ce. "Amrah, me ki ke so?". Ɗago da rinannun idanuwanta Amrah ta yi ta ce. "Ina son ganin ƴan uwa na". Kallonta Umar ya yi a karo na biyu ya ce. "Shi ke nen, idan ki ka ga ƴan uwan naki komai zai dawo dai-dai?". Girgiza kai Amrah ta yi alamun eh. Miƙe wa tsaye Umar ya yi ya ce. "Shi ke nen, zamu kaiki wajan na su". Kallon Umar Usman ya yi ya ce. "Yahya me ka ke cewa haka?, ta ina zamu samo su?, basun riga sun mut...... "Shshiiiiiii!". Umar ya yi alama da hannu da ya yi shiru. Shiru Usman ya yi yana mai jiran furucin da zai fito da baki yayan nasa. Kallon Umar Khairiya ta yi ta ce. "To yahya a ina za'a samo su?". Amsa Umar ya ba ta da cewa. "Wallahi nima ban sani ba, lokacin da Abba ya je ya saka mutanen sa suka je suna kashe dabbobin dajin ban sani ba sai daga baya naje na tarar da sun kashe duk dabbobin dajin. Ni yanzu ban san ya zan yi ba". Kallon su Ramlat ta yi ta ce. "Yahya ina da shawara". "Mene ne?". Suka furta a tare. "Ku matso ku ji". Ramlat ta faɗa. Matso wa suka yi kusa da ita tare da kasa kunnen su in da take. Shiru ta yi kana daga bisani ta ce. "Me zai ana muje gidan Zoo na san dai akwai dabbobi a chan, mybe idan muka kaita ta ga dabbobin cikin wajan za ta yi farin ciki. Amma ya ku ka gani?". Murmushi Khairiya ta yi ta ce. "Wow wannan shawara ce mai matuƙar kyau". Shiru Umar ya yi na ɗan wasu lokaci sannan ya ce. "Kuma ganin wannan shawarar za ta yi aiki kuwa?". "Me zai ana?, zai yi aiki mana, suma ai dabbobi ne a chan na san idan ta gansu za ta yi farin ciki". Cewar Usman. Sannan ya ƙara da cewa. "Amma kamar babu gidan zoo a nan dutse ko?, ni dai ban sani ba ko akwai ko babu". Kallonsa Umar ya yi ya ce. "Ko akwai ma, ba na wannan zamu je ba, ina son muje Kano daga nan zan yi bincike na a kan wanda nake nema mai safaran miyagun hayyuka". "Shi ke nen bara muje mu haɗa wasu kayan mu da wanda Amrah za ta saka". Khairiya ta faɗa suna mai shige wa ciki. Lokaci ƙalilan ya ɗauke su suka gama shirya wa sannan Umar ya kalli Amrah ya ce . "Tashi muje zamu kaiki in da ƴan uwanki suke". Jin abin da Umar ya faɗa, hakan ya sa Amrah saurin miƙe wa tare da sakin murmushi. Juyawa suka yi gaba ɗaya suka nufi wajan parking space, ganin hakan ya sa Amrah ta yi saurin bin bayansu. Shiga cikin motan ɗaya Usman da su Khairiya yayin da Usman ya tada mota, tare da fice wa daga gidan. Buɗe wa Amrah ƙofa Umar ya yi ta shiga sannan ya sauke mata glass ɗin motan ƙasa. Sannan ya tada motan tare da barin harabar gidan. Daga bisani suka nufi hanyar garin Kano. *To kafin mu cigaba dai muna son sani wane ne asalin Umar? sanann wane ne asalin gov. Musa Muhammad*. Alhaji Muhammad shi ne asalin mahaifin Musa Muhammad. Alhaji Muhammad ya kasance mutum tawakali da kuma sanin ya kamata, ya kasance mutum bai bin ƙa'ida. Matar sa Halima ta rasu ne a lokacin da take naƙudan ƴar su ta biyu wacce ta ci suna A'isha. Musa ya kasance ɗa na fari a wajan mahaifin sa sai kuma A'isha. Musa ya taso tun yana ƙarami da burin zama ɗan siyasa domin shi gaba ɗaya a tunanin shi babu komai a cikin yin harkar siyasa sai kuɗi. Hakan ya sa ya ƙudiri niyar zama ɗan siyasa. Alhaji Muhammad ya tura musa karatu domin ya yi karatun Engineering, sai dai kuma abin da bai sani ba shi ne Musa ya chanza course ɗin da mahaifin nasa ya zaɓa masa izuwa Political science. Musa ya gama diploma sa ne yana da shekaru talatin shif. A wannan lokacin A'isha ta kammala HND ɗin ta. yayin da ta fito da wanda take so wato ɗan sarkin garin Kano. Bayan an ɗaura musu aure shima Musa ya auri matarsa Khadija wanda suka haɗu da ita a University ɗin da ya yi. Haka ya cigaba da sha'awar zama ɗan siyasa ba tare da mahaifin ko matar sa ta sani ba. Khadija ta kasance mace mai riƙo da addini, tana ƙoƙarin gujewa duk abin da zai ɓata wa mijin ta rai. Bayan shekara ɗaya ta haifo santalelen ɗanta wanda ya ci suna Umar. Farin ciki wajan waɗan nan ma'auratan ba zai misaltu ba. Ana tsaka da aka, Musa ya je ya bayyana wa mahaifin sa abin da ya karanta a jami'a. Hakan ya sa ran mahaifin sa ya yi matuƙar ɓaci. Yayin da mahaifin sa ya ƙudiri niyar cewa muddin yana da rai ba zai bari ya zama ɗan siyasa ba. Jin furucin da ya fito daga bakin mahaifin nasa ya sa Musa ya tunzura sannan ya yi tafiyarsa sai bayan wasu lokaci ya dawo wajan mahaifin sa, sai dai a wannan karan bai dawo domin neman yafiyar mahaifin sa ba, ya dawi ne domin ya ɗauki ran mahaifin sa. Bayan isarsa chan ne ya tara ƴan daba suka zagaye gidan a yayin da ya sa a ɗaukar masa video ta yadda zai kashe mahaifin na shi. Alhaji Muhammad na kwance cikin jinya da tsananin ciwo Musa ya shiga ɗakin nasa. Ganin yana kwance ya sa shi sakin murmushi ba tare da imani ko tausayawa ba ya samu pillow ya danne fuskar mahaifin nasa da shi. Haka Alhaji Muhammad ya dinga kuruwa har rai ya fita daga jikin shi. Musa bai sake shi ba saida ya tabbatar da baya da sauran numfashi. Hakan ya sa shi farin ciki a sa'inda ya dinga ganin kansa matsayin govnor domin kuwa tunda mahaifin nasa ya mutu babu wanda zai ana shi zama govnor. Jama'a sun yi kuka na rashin Alhaji Muhammad da suka yi, yayin da ita ma Khadija ta ci kukan ta har ta gode wa Allah. Musa ya fara neman takara shida babban Abokin sa wato Abdullahi wanda suka taso tun suna ƙanana har izuwa girmansu tare suke. Hakan ya sa kowanensu yake da burin zama ɗan siyasa. amma sai dai shi musa bai yi nasara ba domin babu wanda ya karɓe sa hannu biyu. A yayin da Abdullahi ya zama babban ɗan siyasa ya yi alƙawarin gyara ƙasar sa da mutanen cikin ta. Musa ya ji aushi sosai ganin abokin saya samu takara shi bai samu ba, hakan ya sa ya ɗora tsanar duniya a kan abokin nasa, a yayin da yake zuwa wajan Abdullahi da fuska biyu na kirki da kuma na mugunta. Umar yana da shekaru biyar a duniya Khadija ta kuma haifo santalelen ɗanta saidai yaron bai zo da rai ba. Bayan wasu shekaru Khadija ta sake haifo namiji wanda ya ci suna Usman, Sannan Ramlat sai kuma ta ƙarshe Khairiya wanda su ukun gaba ɗaya shekara ɗaɗɗaya ne a tsakani. Haka rayuwa ta cigaba wataran da dad'i wataran kuma godiyar Allah. Ana tsaka da haka wata rana Khadija na gyara ɗakin Mijin ta, nan ta tarar da wani caset. Ɗaukar caset ɗin ta yi sannan zuciyar ta tace da ita ta saka caset ɗin a tv ta ga ko film ne. Bayan ta saka caset ɗin ne a tv ta ga abin da ya yi matuƙar firgita tunaninta. Mijinta ta gani ya kashe mahaifin sa da hannunsa . Hakan ya sa ta ji dana sanin auran sa. A dai-dai wannan lokacin kuma Musa ya shigo ya tarar da ita a ɗakin tana kuka. Nan dai ya gano cewa ta gano shi ne wanda ya kashe mahaifin sa. Ganin hakan ya sa Musa ya fara roƙon matar sa da ta rufa masa asiri. Amma ita kuma Khadija taƙi amincewa sannan ta ce dole ta sanar da ƴan sanda ko wane ne mijinta domin ba za ta iya take gaskiya ba. Ganin dai taƙi bashi haɗin kai ne ya sa ya ɗauki glass cup sannan ya rotsa wa kanta. Nan take kanta ya fara fidda jini yayin da ta faɗi ƙasa mutacciya. A dai-dai wannan lokacin Umar ya dawo daga makaranta sannan ya shiga cikin ɗakin nan ya tarar da gawar mahaifiyarsa a kwance. Hakan ya sashi sakin ƙara yayin da ya faɗi ƙasa sumamme. Ganin hakan ya sa Musa ya goge kowane sheda da ƴan sanda za su bi domin gano makashin. Bayan nan ne ƴan sanda suka zo suka yi ƙaraci binciken su basu samu komai ba. Hakan ya sa haka rufe case ɗin. Bayan wasu kwanaki ne Umar ya dawo cikin hayyacinsa a yayin da yake mafarkin mahaifiyar sa sannan ya ƙudiri niyar dole ya zamo jami'i, domin ya san wanda ya kashe mahaifiyar sa sannan kuma ya kare ƙasar sa daga sheɗanun mutane irin mahaifinsa. Umar ya fara jin tsanar mahaifinsa ne tun lokacin ya ga mahaifin sa da wasu karuwai a gidan su. Daga wannan rana Umar ya tsani mahaifin sa. Bayan Umar ya yi karatun sa na boko da na addini ne ya shiga training school na jami'ai. Hakan ya sa ya fara gudanar da al'amuran sa shi ɗaya. A sa'inda duk abin da ƙanensa suke da buƙata shi yake musu. Kan kace me Umar ya zama babban jami'i wanda gaba ɗaya ƙasa ke magana kan ƙwarewarsa domin kuwa duk wani mai laifi idan ya yi musu wahalan kama wa Umar shi ne wanda ake bawa wannan aikin kuma duk in da wannan mai laifi yake zai nemo shi sannan ya tabbatar da an hukunta shi. Aka ya cigaba da bincike domin gano makashin mahaifiyar sa, sai dai har izuwa wannan lokacin bai gano ko wane ne ba kuma bai san irin aikin mahaifin sa ba. A ɓangare guda kuma shima Musa ya zama ɗan siyasa ba tare da an san ta wace hanya ya bi ya samu wannan takara ba. *Amma idan ta yi tsami zamu ji ta yadda ya samu takara shiga siyasa* Haka su Khairiya suma suka taso cike da ƙaunar juna. Yanzu dai Usman ya gama karatun sa yana aiki a office. Sai kuma Ramlat wacce ke University level 300 tana karatun Optometrist. Da kuma Khairiya wacce ke 100 level tana karatun biology. *Wannan dai shi ne takamaiman tarihin Umar* ___________________ Shigowa da motoci masu tsaron govnor Musa suka yi. Fitowa Gov. Musa ya yi daga cikin mota ganin babu motoci guda biyu a gidan hakan ya nuna masa alamun cewa tabbas Umar ya fita. Kallon masu tsaron gidan ya yi ya ce. "Where's Umar?". Amsa ɗaya daga cikin masu gadin ya bashi da cewa. "Yanzu suka fita". Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Kun san in da suka je?". Amsa suka ba shi da cewa. "A'a, amma mun ji kamar suna zancen za su je Kano". "Kano!". Gov. Musa ya maimaita sunan. "Shi ke nen". Kawai ya ce sannan ya shiga part ɗin shi. Yana shiga ya yi saurin ɗaukar wayarsa sannan ya lalubo number Aliyu tare da danna mai kira. ______ Aliyu da ke zaune sai faman kallon Safira yake yana murmushi ne ya ji wayar sa na ruri. Maida kallonsa ya yi kan wayar. Ganin sunan wanda ke bayyane kan screen ɗin ne ya sa shi miƙe wa sannan ya bar cikin parlour ɗin daba bisani ya ɗaga kiran. Ya ce. "Salamu alaikum". Daga ɗayan ɓangaren Gov. Musa ya amsa sallamar sannan ya ce. "Aliyu ina da buƙatar taimakon ka yanzu dan Allah, ɗa na da ƙannensa su tafi hanyar Kano, yanzu haka na san sun kusa isa chan, ina son ka bibiyar mun su bana son ya gano gaskiyar ko ni wane ne, sannan kuma bayan nan akwai yarinyar Mrs Laila a Kano ina son ka bincika min duk in da take ka sa a sace ta. Dan Allah ba dan ni ba Please, zan tura maka duk kuɗin da ka ke da buƙata". Ɗan jimm Aliyu ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen naji, million goma shi ne kuɗin aiki na, kuma cash nake so ba transfer ba". "Shi ke nen Aliyu, ni zan ma ƙara maka ya zama twenty ni dai kawai buri na shi ne ka dakatar da su sannan ka nemo in da yarinyar Lailah take". "Kada ka samu damuwa wannan abu ne mai sauƙi, nan da sati ɗaya zan nemo duk in da take, kai dai kawai ka shirya min kuɗaɗe na". Cewar Aliyu. "Angama". Gov. Musa ya faɗa tare da katse wayar yana mai maida numfashi. Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi sannan ya shiga ɗakin sa tare da haɗa kayan sa cikin travel box. Bayan ya gama saka kayansa ne ya nufi ɗakin su Grandpa sannan ya sanar da su yana son yin tafiya sainan da sati zai dawo. Addu'a suka yi mai. Daga bisani ya saka kayansa cikin mota. Babu abin da Safira kai ta faman yi sai satar kallonsa. Babu zato suka haɗa ido da Safira, saurin kawar da kanta Safira ta yi gefe. Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Kodai za ki je ne?". Taɓe baki Safira ta y ta ce. "Nop, ni kam babu in da zani". Ta faɗa tare da shige wa ciki gidan. Girgiza kai kawai Aliyu ya yi tare da tada mota sannan suka yi sallama da mutanen gidan gaba ɗaya daga bisani ya fice daga gidan. Bai zarce ko ina ba sai hanyar Kano. _________________________ Zahra na fita ta hangi kuloli a jere kan dining hakan ya sa ta haɗiye yawu. Da sauri ta je ta zauna kan table ganin zaman kujera ba zai finshe ta ba, ya sa ta kwashe gaba daya kulolin ta jera a ƙasa sannan ta zauna a ƙasa ta fara buɗe kulolin. Take wani irin ƙamshi ya bugi hancin ta hakan ya sa lumshe idanuwanta sannan ta sake buɗe su. Tuwon shinkafa ne miyan taushe ya ji naman turkey yayin da bangare ɗaya kuma fried rice ne ya ji coslow da naman kaza. Sai ɓangare ɗaya kuma kunun aya cikin jug da kuma lemo mai sanyi tare da Fruit salad. Ganin ba za ta iya ɗauke ido kan wannan abinci ba, ya sa ta cire duka chokulan kan trey ɗin abincin ta zubar a ƙasa. Hakan ya sa ƙaran chokulan suka bada wani irin ƙara. Jin ƙara daga parlour ya sa su Gimbiya Saratu da Talatu tare da ƴaƴanta fitowa. Yayin da ita ma a dai-dai lokacin Mami ta fito daga cikin ɗakin ta domin ganin meke faruwa. Dai-dai lokacin kuma Junaid ke dawo wa daga fadan mai martaba. Fitowa Sooraj ya yi daga cikin ɗakin sa. Tare da nufar hanyar parlour. Tsaya wa chakk gaba ɗaya suka yi ganin yadda Zahra ke ɗura wa ciki ta abinci. Cin abinci ta take hankali kwance ba tare da tsoro ko wani tunani ba. Sai loma take ta kwara abincin da lemo tare da kunjn aya. Haka ta cigaba da cin abinta ba tare da ta kula da zuwansu Sooraj wajan ba. Baki sake gaba ɗaya suke kallonta. Zahra kuwa sai da ta cinye Tuwon shinkafan tass sannan ta koma kan fried rice. Haka ta na ci tana sumbatu. "Wayyo dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni, dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni" Sannan ta ƙara da cewa. "Gaskiya kuɗi duniya ne, Allah kayi mu yadda muke so. Yoo ƴan banza ba dole su dinga tumbi ba suna cin abinci mai daɗi da gina jiki. Daɗin ta ma ba za su ci ba, kinga kenen zanci sosai na ƙoshi, naci na ci na bar na bari. Shi ya sa wannan Gimbiya Talatun bakinta yake wangalele kamar na akuya tunda tana cin abinci mai daɗi dole, sai kuma waɗan nan ƙwalaye ukun nan su Samira ko, dole su dinga yadda suka gadama tun da suna cin kayan dad'i. Yanzu ni duk ba wannan ba hanyar da zanbi na koya wa wannan mai ƙaton kai hankali nake Sooraj yake ko, saina koya mai hankali, ba an ce ni ce zan dinga kula da shi ba, kawai idan Mami ta bani abinci shi na cinye sai in kai mai ragowa ya ci". Ta ƙarashe tana mai bushe wa da dariya. Duk abin da take a gaban idanunsa. A sa'inda ɓangare ɗaya Gimbiya Talatu ta yi mugun ƙulu wa. Jin abin da Zahra ta faɗa game da halittar bakinta. Sooraj kuwa mamaki kawai ya shiga yi ganin yadda take ta sumbatu tana cin abinci duk ba ga san suna tsaye a wajan ba. Saida ta gama da komai da cikin kulan tass sannan ta kora da kunun aya da fruit salad. Ji ta yi cikin ta ya yi mugum cika. Gatsa ta yi ta ce. "Ya kamata ki kwanta Zahra domin abincin da ki ka ci su zazzage". Ta faɗa tana mai kwanciya a ƙasan wajan tana mai fuskantar saman silin. Gabanta ne ya bada wani rass!, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku ganin gaba ki ɗaya ƴan gidan tsaye a kanta. Zumbur ta miƙe tsaye tare da karkaɗe jikin ta. Kallonta Sooraj ya yi tare da kallon kulolin da ta cinye abincin ciki sannan ya girgiza kai ya ce. "Sannunki da aiki, yanzu mutum in banda dabba waye zai iya cinye uban abincin nan, to ki sani cewa baki ci a banza ba domin kuwa sai kin koma kasuwa kim siyo duk abin da ki ka ci sannan kin sake dafa irin shi komai da komai". Rai a ɓace Gimbiya Talatu ta ce. "In banda iskanci ƴar talakawa har ta samu matsayin da za ta ci abinci a kulan da muke cin abinci. Sannan kuma har ta samu damar ta ce wai ni mai wangalellen baki. Lallai kam wuyarki ya isa yanka". "Madam za ki iya mana shiru a nan". Cewar Sooraj. Tsaki Gimbiya Talatu ta ja tare da wuce wa part ɗin ta ganin hakan ya sa Saratu ta bi bayanta. Sannan sauran ma suka watse ya rage Sooraj, Mami, da kuma Zahra. Kallonsa Zahra ta yi bakin ta duk maiƙon kaza ta ce. "Yarima wallahi ban iya girki ba, ban taɓa yi ba, ta ya zan iya yin mai daɗin wannan?, kayi haƙuri dan Allah". Gyara tsayuwar sa Sooraj ya yi ya ce. "My wish is my command, dole ki sake girka irin wannan kuma taste ɗin dole ya zama iri ɗaya. Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin kalmarsa ta ƙarshe. "Ni na san ma sai dai nayi muku jagwab ɗin abinci don ban iya ba". Bai ƙara cewa komai ba ya koma part ɗin sa. Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi abin da ya ce karki damu da wajan nan da ki ka ɓata zan sa ƴan aiki su gyara, maza kije ki siyo ingredient ɗin, domin ya ce ba za'a taɓa na gida ba". "Shi ke nen". Zahra ta faɗa tare da shiga ɗaki ta saka saka hijabi. Fitowa ta yi yayin da Mami ta ba ta isashun kuɗaɗe domin siyan kayan abincin da ta ci. Bayan ta ba ta kuɗin ne fita daga cikin harabar masarautar tare da tarar mai napep ya kaita kasuwa. Bayan Aliyu ya isa Kano ne ya samu wani guri kusa da kasuwar kwari ya yi parking. Sannan ya fara waige-waige. Chan ya hango mai tallan tsire. Hakan ya sa ya tare shi tare da siyan na dubu ɗaya domin rage yunwar da take damun shi. Zahra kuwa saida mai napep ɗin ya yi tafiya mai nisa sosai kafin nan ya isa kasuwar kwari. Chan ta hango tsayuwar Aliyu jikin motarsa. Tunani ta shiga yi kamar ta san wannan mutumin. "Wannan kamar wannan ɗan sandan da ya so raina min hankali a magarƙama ne ko?". Ƙara kura masa idanu ta yi. "Laa babu tantama kuwa shi ne". Dakatar da mai napep ɗin ta yi da ya tsaya. Ba tare da ta tsaya biyan mai napep kuɗin sa ba ta tsallaka titi da gudu tare da nufar in da Aliyu yake tana mai faɗin. "Malam ɗan sanda mai ɗagaggen wando kaine a garin Kano?". Juyawa Aliyu ya yi ganin waye wannan mai furta wannan kalma. Nan take ya haɗa ido da Zahra. Take gabansa ya yi mummunar faɗuwa!. Nuna ta ya yi ya ce. "Safira!". Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Wace ce kuma haka?, wai Safira, kai ni ce fa baka gane ni ba a magarƙama da ka zagar min uwa na so nayi maka duka ka tuna?. Ba kai ne wannan ɗan sandan mai ɗagaggen wando ba?". Dafe kansa Aliyu ya yi jin yadda kansa ke ƙoƙarin sara masa. Riƙe kansa sosai ya yi domin yin tunanin a ina ya santa. Ɗaga kansa ya yi ya kalle ta ya ce. "Kenen ba ke ba ce Safira ba?". Haɗe giran ta Zahra ta yi tare da turnuƙe fuska ta ce. "Wace ce kuma Safira?, ni fa malam sunana Zahra ba Safira ba". "I am totally confused, what's going on?". Aliyu ya tambayi kansa. Nan take ya fara tuna wan can ta magarƙamar. Rass gabansa ya faɗi. Cikin ransa ya ce. "Tabbas wannan ita ce wanda na gani a magarƙama kwanaki mai brown eyes, sannan Safira ma tana kama da ita, ga kuma ranar nan na ga wata mai kama da Safira mai grey eyes. Kenen hakan yana nufin su uku ne?, idan kuwa hakan ta kasance to tabbas hasashen Mom gaskiya ne, kenen hakan yana nufin yaran Mrs Laila ne?!". COMMENTS & SHARE FISABILILLAHI 🙏 🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 3️⃣9️⃣▶️4️⃣0️⃣ *___________________________________________* "Wai tunani me ka ke yi ne malam ɗan sanda?". Cewar Zahra. Murmushi Aliyu ya saki sannan ya ce. "Babu komai kawai dai ina mamaki ne, masha Allah gaskiya naji daɗin haɗuwa da ke. Idan babu damuwa shin zamu iya zama abokai?". Harara Zahra ta galla mai sannan ta ce. "Ta ina ka taɓa jin ana aboki tsakani mace da namiji?, ni bana son wanda zamu fara abota ya kawo min zancen soyayya, atohh dai, dan na san yawancin ku daga abota za ku fara sai a zarce soyayya". Dariya Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai karki damu ni ina da ma wacce zan aura, sunanta Safira". Taɓe baki Zahra ta yi sannan ta ce. "To Allah ya bar soyayya". Amsa wa Aliyu ya yi da "Ameen". "Shi ke nen, ni zan tafi, zanje in siyo abu ne a wannan kasuwan kada na daɗe kuma wan can yariman ya zo ya fara balbale ni da masifa, ni bai san ma ɗaga mai ƙafa kawai nake ba". Zahra ta faɗa tana mai ƙoƙarin tafiya. Saurin dakatar da ita Aliyu ya yi sannan ya ce. "A'a karki tafi bari nayi miki rakiya, ai yanzu mum zama abokai ko, don haka duk abin da ki ka siya ni nan zan riƙe". Dariya Zahra ta yi ta ce. "Kai kuwa ka san me zan siyo?, ba za ka iya riƙe wa ba, idan na ce zan baka duk abin da zan siya sai dai ma na saka kuka domin ba za ka iya ba, kawai dai kayi tafiyarka". Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai, ni fa ba ragon namiji ba ne, ni jarumin jarumai ne, kedai kawai ki bari muje tare zan baki mamaki". Murmushin mugunta Zahra ta yi ta ce. "Tom shi ke nen malam ɗan sanda muje, ni ba zan ana ka ba". Ta faɗa tana mai tafiya. Saurin bin bayanta Aliyu ya yi tare da farin cikin ya samu shiga jikin Zahra saura kuma yadda zai yi ya sace ta. _________________________ Su Umar ba su suka iso Kano ba sai wajan la'asar. Yayin da kai tsaye suka wuce gidan zoo. Bai ɗauke su lokaci ba suka isa gidan zoo dai-dai lokacin da ake kiran sallah. Parking gaba ɗaya suka yi yayin da suka fito daga cikin motocin. Kallonsu Ramlat da Usman Umar ya yi ganin hankalin Amrah yana wani wajan da ban, ya sashi faɗin. "Na san ba za'a rasa wasu namun jeji a nan ba, kuje ku kaita ta gansu na san koba komai dai za ta ɗauka ƴan uwanta ne. Kai kuma". Ya faɗa yana mai kallon Usman, "maza biyo ni muje muyi Sallah a masallaci". Ya ƙarashe maganar yana mai yin gaba. Bin bayansa Usman ya yi suka wuce masjid domin gabatar da Sallah. Maida kallonsu su Khairiya suka yi kan Amrah sannan suka riƙe hannayenta suka fara shiga ɓangaren dabbobi da ita. Gani suka yi gaba ɗaya dabbobin sun ragu babu wasu dabbobi chan sosai. Daga nesa Amrah ta hango wasu birurruka cikin zagaye. Da sauri ta wafce hannunta tare da nufar wajan da mugun gudu, a sa'inda jama'ar wajan gaba ɗaya suka bita da kallo. Da sauri su Khairiya suka bi bayanta a matuƙar tsorace. Ƙarasa wa wajan Amrah ta yi tana mai aye wa kan ragar birurrukan. Da sauri su Khairiya suka je tare da kokarin saukar da ita. Saukar da ita suka yi. Sannan suka fara kwantar mata da hankali. Shiru Amrah ta yi sannan ta ƙura wa birurrukan idanuwa. Girgiza kai ta fara yi tana mai ja da baya, tana mai faɗin. "A'a, waɗan nan samm ba su ba ne". Saurin maida kanta ta yi kansu ta ce. "Ina ku ka kai su?, kun kashe su ko?, me ya sa ku ka yi min ƙarya?". Ta faɗa tana mai fashe wa da kuka. Kallon juna Ramlat da Khairiya suka yi yayin da bakinsu ya kasa furta komai. Share hawayenta Amrah ta yi jin kukan yaro ƙarami wanda ya karaɗe wajan. Saurin waiga wa ta yi domin jiyo ta idda wannan kukan ke fitowa. Nan take idanuwanta ya sauka kan wani yaro a ƙasa sai faman kuka yake. Da sauri Amrah ta isa idda yaron yake sannan ta ɗauke shi tare da sakin murmushi ta ce. "Daina kuka yaro za ka yi wasa?, bara muyi wasa ko". Ta faɗa tana mai cilla yaron sama. Take mutane suka saki ihuu ganin yadda ta jefa yaro chan sama sosai. Da sauri su Khairiya suka dube ta suka ce. "Ke Amrah kinyi hauka ne?, maza ki sauke wannan yaron". Ko kula su Amrah ba ta yi ba, saima cigaba wa da ta yi. Nan ta ci gaba da jefa yaron sama yana ihuu yana kururuwa. A sa'inda jiri ya ɗebi yaron ya suma. Bayan ya dawo hannunta ne ta ga yaron ya yi shiru. Murmushi ta yi ta ce. "Kun gani ko, yaron ma har ya yi bacci abunsa hankali kwance". Dafe kanta Ramlat ta yi ta ce. "Mun shiga uku, Amrah me ki ka aikata aka?, kin fa sumar da shi". Dai-dai lokacin da wata mata take ƙaraso wa wajan hannunta riƙe da leda alamun ita ce mahaifiyar wannan yaron. "Me yake faruwa ne na ga mutane sun taru a nan wajan?, ina ɗana yake?". Ta faɗa a yayin da idanuwanta suka sauka kan yaronta da ke hannun Amrah. Ɗora hannayenta ta yi a kai tana mai fasa ihuu!. "Innalilahi wa innahilahir rajihun!, me ku ka aikata wa ɗana, me ya faru da shi. Wallahi idan wani abu ya samu ɗana ba zan ƙyale kowa ba". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin wafce ɗanta a hannun Amrah. Nan take Amrah ta riƙe hannun matar ta ce. "Ba zan baki shi ba har sai ya farfaɗo". Wafce hannunta matar ta yi daga na Amrah sannan ta ce. "To maza farfaɗo da shi". Kwantar da shi Amrah ta yi sannan ta hura mai iskar bakinta kan fuskarsa. Cikin ƙanƙanin lokaci yaron ya farfaɗo. Nan take mutane suka fara mamaki. "Dama iskar baki na iya farfaɗo da wanda ya suma?, kodai ita ɗin ba mutum ba ce, don yadda ƙwayar idanunta suke green ma za ka tabbatar da cewa wannan ba mutum bace?". Abin da suka shiga furta wa kenen. Ɗaukar ɗanta matar ta yi cikin farin ciki sannan ta juya tare da barin wajan ba tare da ta yi wa Amrah godiya ba. MK da ke zaune cikin mota duk abin da ya faru a gaban idanuwansa. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ya yi ya ce. "Da a ce a wajan iyayenku ku uku ku ka taso da rayuwarku ba ta kasance haka ba, amma haka Allah ya riga ya kaddara cewar ba za ku taso da mahaifiyar ku ba. Ina fatan duk in da mrs Laila take ya kasance tana ƙoshin lafiya, har izuwa yanzu ban sani ba ko tana raye ko kuma ta riga mu zuwa gidan gaskiya. Amma ina fatan duk in da take ya kasance tana cikin rahamar ubangiji". Ya faɗa yana mai tada mota sannan ya bar harabar wajan. ___________ "Hello your Excellency yanzu haka muna cikin gidan zoo ɗin, umarnin ka kawai muke jira". Daga ɗayan ɓangaren gov. Musa ya ce. "Perfect, ni na san Aliyu ba zai iya wannan aikin shi ɗaya ba shi ya sa na tura ku chan. Ina son ku sace Amrah kai tsaye ku wuce da ita hanyar Airport ku wuce ƙasar waje domin a sata a kasuwa. Amma fa ku tabbata Umar bai ganku ba sannan ku rufe fuskokin ku kada ku kuskure ku buɗe". "Shi ke nen yallaɓai kamar yadda ka ce". Mutumin ya faɗa yana mai kashe wayar. Nan take su biyar da ke cikin mota suka kalli juna a yayin da lokaci ɗaya gaba ɗaya suka rufe fuskokinsu da mask. Sannan suka fito daga cikin mota. Kai tsaye in da Amrah ke tsaye suka nufa wacce ke ta faman kallon dabbobin cikin wajan. Suna isa wajan suka rirriƙe hannunta tare da ƙoƙarin tafiya da ita. Nan take hankulan mutane da nasu Ramlat ya karkata izuwa kansu. Dai-dai lokacin da su Umar ke ƙarasowa wajan. Ganin abin da ke faruwa ya sa Umar ya yi saurin nufar wajan tare da ƙoƙarin ƙwace Amrah daga gare su. Gani Umar na shirin dakatar da su ya sa ɗaya daga cikin su ya kai mishi naushi a ciki. Faɗuwa Umar ya yi a matuƙar zafafe ya miƙe tare da yin kansu sannan ya fara kokawa da su. Nan take mutane suka fara ɗaukar video ganin yadda ɗan gidan govnor musa yake faɗa da ƴan ta'adda. Cikin rashin sa'a ɗaya daga cikin su ya kai masa naushi cikin sa a karo na biyu. Faɗuwa Umar ya yi yana mai sakin ƙara. Zaro idanuwa waje su Ramlat suka yi a matuƙar tsora ce suka nufo kan ɗan uwansu. Ganin abin da suka aikata Umar hakan ya sanya ran Amrah ya fara tafarfasa yayin da ta saki wata iriyar razananniyar ƙara mai matukar firgitarwa. Ba ta yi wata-wata ba ta shaƙe wuyan mutane biyu daga cikin su tare da ɗaga su sama sannan ta naka su da ƙasa. Ganin hakan ya sa sauran ukun suka yi saurin ja da baya. Da sauri ɗaya daga cikin ya ɗauki sanda sannan ya buga wa Amrah. _________________ "Mom!!!!!". Safira ta faɗa da mugun ƙarfi tana mai dafe kanta. Da sauri su Mom da ke zaune a parlour suka fito garden in da Safira ke zaune. Dubanta Mom ta yi ta ce. "Mene ne ya fara ki ka saki uban wann ƙarar haka?"., Rintse idanuwanta Safira ta yi ta ce. "Mom ina ji wani iri a jiki na, gaba ɗaya bana jin daɗin jiki na, ina ji kamar wani abu mara kyau na shirin faruwa da ni". Zama kusada ita Grandma ta yi ta ce. "Kiyi addu'a kinji ƴata, in sha Allahu komai zai zo miki da sauƙi, babu abin da zai faru sai alkhairy". Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "A'a Grandma gaba ɗaya jiki na ciwo yake yi, ba zan iya jure wa ba, jiki na yana min ciwo kamar wacce ta yi dambe da mutane". "Tashi zo mu shiga ciki na ɗora miki ruwan zafi ki gasa jikin ki". Cewar Grandma. Tashi tsaye Safira ta yi cikin jin ciwo sannan ta bi su Grandma suka shiga cikin gida". Nan dai Grandma ta ɗora mata ruwan zafi sannan ta fara gasa mata jikin ta. Cikin mamakin su kuwa abun sai ƙara tsamari yake, a maimakon ya ragu saima ƙaruwa da ya yi. Gani hakan ya sa hankulan gaba ɗayansu ya tashi. "Wai Safira me yake faruwa da ke ne haka?". Cewar Daddy. Hawaye ne ya fara gangaro wa kan ƙuncin Safira sannan ta bawa Daddy amsa da cewa. "Wallahi ban sani ba, dan Allah kuyi wani abu ina jin raɗaɗi sosai, ina tunanin mutuwa zanyi. Kunga ni na kasa motsa hannayena, na shiga uku, Mom mutuwa zanyi". Nan take hankalinsu ya sake tashi gani gaba ɗaya Safira ta kasa motsa koda ɗan yatsarta. _________________________ Rintse idanuwanta Zahra ta yi jin yadda jikin gaba ɗaya ke mata ciwo. "Wayyo Allah, ya naji lokaci ɗaya jiki na namin ciwo, gaba ɗaya jiki na ya mutu. Ya kamata na samu guri na zauna". Ta faɗa tana mai hango rumfar mai saida kayan miya. Da sauri ta nufi wajan a matuƙar jigata ta isa wajan tare da zama. Saurin isa wajan Aliyu ya yi ya ce. "Ya ki ka zauna kuma bayan baki siyi abin da za ki siya ba". Girgiza kai Zahra ta yi a matuƙar jigace ta ce. "Ba zan iya tafiya ba, jiki na ya mutu. Ji nake tamkar nayi dambe saboda a halin yanzu gaba ɗaya gaɓobin jiki na ciwo yake. Tun da yanzu kai aboki na ne ka taimaka min ka siya min duk abin da nake da buƙata". Mamaki ne ya kama Aliyu ganin yadda gaba ɗaya ta bi ta galabaita. Tamkar wacce aka yi wa duka. "Me ke faruwa?, ba yanzu na ga mum tawo jikin garau ba?, amma a ce yanzu kuma wai jikin ki yana ciwo. Dama dai tun asali baki da lafiya shi ne ki ka tako ki ka zo kasuwa, maimakon kije kina huta wa". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ni samm ba haka ba, lafiya ta ƙalau babu abin da ya same ni. Ni kaina mamaki nake sannan na shiga cikin ruɗu ta yadda lokaci ɗaya na tsinci kaina da ciwon jiki. Amma na san zuwa wani lokaci zai daina, ina ga saboda abincin da na dinga ɗurƙa wa ciki na ne ya sa jiki na ya mutu". _______________________ Faɗuwa ƙasa Amrah ta yi yayin da ta saki wata ƙara sannan ta buga tsalle ɗaya ta dira kan ɗaya daga cikin su ukun. Nan take ta fara buga mai hannu a kai tare da gantsara masa cizo a kunne. Nan take ya saki ihuu. Sauka ta yi kansa tare da yin kan sauran. Ganin ta nufo in da suka ya sa suka saka gudu domin tsere wa. Ganin suna ƙoƙarin tserewa ya sa Amrah ita ma ta bi su da gudu. Miƙe wa tsaye Umar ya yi a ɗingishe sannan ya fara ƙwallah kiran sunan Amrah. Amma ina Amrah ta yi nisan da ba za ta jiyo kira ba. *😨😨😨😨😨😨😨* *MANAGE PAGE 📄 📃 PLEASE 🥺* ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (ZINARIYAR JAJIRTATTU) Follow the 🌺🌎A'ISHA M.B🌹 HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣1️⃣▶️4️⃣2️⃣ *___________________________________________* Da mugun gudu suka nufi wajan motocin su domin tsere wa daga wajan Amrah, kafin suyi aune suka ji an chafko rigar su tare da ɗaga su sama sannan ta fara ajijiya da su kamar dabba. Ganin hakan ya sa mutane zaro ido waje a sa'inda suke cewa Amrah ba murum bace. Da sauri Umar da su Ramlat suka isa wajan tare da fara ƙoƙarin dakatar da Amrah, amma ina samm hakan ya cutura. Chakk Amrah ta dakatar da abinda take yi sakamakon tsawar da Umar ya daƙa mata. Sauke su ta yi yayin da mutanen Gov. Musa suka shiga mota tare da barin wajan. Zuwa daff da ita Umar ya yi ya ce. "Mene ne hakan?, me ya sa ki ke so ki zubar mana da mutunci?, ko dan kinga ina sonki ne?. Ba dai wajan ƴan uwanki ki ka ce na maida ki ba, shi ke nen zan maida ki". Ya faɗa yana mai juya wa sannan ya bar wajan. Ƙasa da kai Amrah ta yi. Jiki a muce su Khairiya suka riƙe hannunta tare da ƙoƙarin tafiya. Cire hannunta Amrah ta yi daga na su sannan ta girgiza kanta ta ce. "Ku tafi kawai ku barni a nan". Kallonta Usman ya yi ya ce. "Aba Amrah kiyi haƙuri, kada ki damu da maganar yaya Umar wasa yake miki". Girgiza kai Amrah ta yi s karo na biyu tana mai faɗin. "Ai ni abin da ya faɗa shi nake so, shi ne ya maida ni wajan ƴan uwa na, ni samm ban san yadda zan iya irin taku ba, kuma idan na cigaba da zama da ku zan dinga jawo muku abun kunya ne gwara ku neman mu ƴan uwana". "Tom shi ke nen karki damu za mu neme su kinji". Cewar Umar. Jin hakan ya sa ta bi su suka tafi. Shiga motan gaba ɗaya suka yi, a sa'inda Umar kuwa ko ɗaga kai bai yi ya kalli Amrah ba saboda har izuwa wannan lokacin ranshi a ɓace yake. Tada motocin nasu suka yi yayin da suka wuce babban gidan Umar wanda ke a layin Darmanawa. ______________________ Girgiza kai Aliyu ya yi jin furucinta ya sa shi kwashe wa da dariya sannan ya ce. "Ikon Allah, wato kina da ci kenen irin kune masu ci amma ba'a ƙiba". Miƙe wa tsaye Zahra ta yi rai a ɓace ta ce. "Malam karfa ka raina mim hankali, ban san shashanci, ka iya bakin ka banƙi yanzu na kutuntuma maka ashariya ba, India ka san wannan ne abota to zamu yanke ta gaskiya". Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Ayi haƙuri hajiya babba, na tuba. Ni kin ma tuna min har yanzu da ban san sunanki ba, ina son ki faɗa min mene sunanki?". Kallon rainin wayo Zahra ta yi masa sannan ta ce. "Kana nufin baka san sunana ba kuma kace za ka yi abota da ni?, to ni sunana suna da yawa, ba lallai ka iya riƙe su ba". Murmushi kawai Aliyu ya yi ya ce. "Ina jinki faɗa min su, ni kuma na miki alƙawari duk zan riƙe". Murmushin mugunta Zahra ta yi sannan ta ce. Sunana oho". Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Allah ya shirye ki, dan Allah ki faɗa min". Taɓe baki Zahra ta yi. "Toh me ya sa ka damu lallai saika san sunana?, kodai akwai abin da ka ke ƙulla min ne?, haka aka ce ka karɓo sunana ka kaiwa boka ya yi maka magani?". Dariya Aliyu ya kwashe da shi sannan ya ce. "Aba dai Allah ma ya tsare, ina ni ina wajan boka, rufa min asiri". Jinjina kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Tom shi ke nen ni dai sunana Fatima kai kuma fa mene naka sunan?". "Wow! nice name". Aliyu ya faɗa sannan ya ce. "Ni dai sunana Aliyu". "Masha Allah". Zahra ta furta. Karɓar kuɗin da ta ba shi ta yi sannan ta fara siyayyar abin da ya kawo ta. Saida ta gama tass sannan Aliyu ya ɗauke ta ya kaita har gaban masarauta. Fitowa Zahra ta yi daga cikin motan yayin da Aliyu ya bita da kallo. "Zahra". Ya faɗa cikin maƙe murya. Hangame baki Zahra ta yi ta ce. "Mene haka kuma sai kace kana kiran budurwar ka, idan za ka fa Zahra ka faɗa da muryar ka ta garda wa ba saika maƙe ta ba. Don haka ina jin ka me ya faru?". Murmushi kawai Aliyu ya yi sannan ya ce. "Babu komai, dama ina mamaki ne da na ganki a nan masarautar, dama ke ƴar sarauta ce?". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a ko ɗaya, ni ɗin ƴar aiki ce". Ta faɗa tana mai shige wa ciki. Ganin ta shiga ciki ne ya sa shi sakin murmushin mugunta kana ya ce. "My mission will soon be complete, ya zama dole na yi taka tsantsan idan ba haka ba za ta iya gano shiri na". Ya faɗa yana mai tada motan sannan ya bar harabar masarautar. Ɓangaren Zahra kuwa ta shiga cikin masarautar ta ci karo da Sooraj a tsaye ya rungume hannuwansa a ƙriji. Ƙasa da kai Zahra ta yi cikin ranta ta ce. "Na ga alamun wannan mutumin da gaske yake na cewa dole sai ya azabtar da ni, ni kuma wallahi dai-dai nake da kai". "Ke!". Zahra ta ji ya faɗa a matuƙar tsawa ce. Ko kallonsa ba ta yi ba ta ci gaba da tafiya. Ganin ta share shi ne ya sa ran shi ya ƙara ɓaci ya ce. "Ke ba da ke nake ba?". Sai a lokacin Zahra ta tsaya tare da juya wa tana mai fuskantar shi. Binsa ta yi da kallo sannan ta ce. "Kayi haƙuri ranka shi daɗe, ni sunana ba ke ba, naji kana ta ke, ni kuma ba da ke aka yanka min ragon suna ba, Zahra ne sunana". Girgiza kai Yairma Sooraj ya yi rai a ɓace ya ce. "Kenen bani da hankali kenen ko?, kenen ba a kan dai-dai nake ba?". Kawar da kai Zahra ta yi ta ce. "Na sani, abu a duhu a baƙar leda". Furzar da iska mai zafi ya yi waje sannan ya ce. "Wane ne wanda ya kawo ki a mota yanzu?, wane ɗan wahalan ne?". Riƙe aɓar ta Zahra ta yi ta ce. "Toh!, ikon Allah mutum da duniyarsa, kenen ban isa a kawo ni gida a mota ba ne ko me?, to saurayi na ne kuma shi zan aura sai kuma me ya faru?". Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Wato kenen mai saurayi ko?, wane ɗan wahalan ne ma ya ce yana sonki, ya rasa wacce zai so zai ballagaza mara kamun kai irin ki". Murmushin takaici Zahra ta yi sannan ya ce. "A hakan ya ganni ya ce yana so, sannan kuma kada ka manta so babu ruwanshi da ballagazanci ko rashin kamun kai ko kuma kuɗi ko iko, ka gane Yarima, sannan kuma koma dai mene ne ina ruwan ka?, meya shafe ka da hakan?, wallahi karka kaini bango na faɗa maka maganar da za ka kwana ka tashi ba za ka manta ba, kada ka sa na faɗa maka maganar da za ta sanya ka rashin lafiya harta kai ga an kaila ƙasar waje operation ɗin zuciya, na gaya maka domin kuwa idan na gaya maka magana sai zuciyar ka ta fito ta bugi ƙasa sannan ta koma". Jinjina kai Sooraj ta yi sannan ta ce. "Kin san kuwa da wa ki ke magana?, ni Sooraj ki ke gaya wa aka?. Shi ke nen kije ki girka duk abin da ki ka ci yanzu nan kuma za ki yi". Harara Zahra ta galla masa ba tare da ya sani ba sannan ta ce. "Naji". Ta faɗa tana mai shige wa ciki. Girgiza kai Sooraj ya yi yana mai ayyana irin ƙuntata wa Zahra da zai yi, zai nuna mata banbamcin ɗan sarauta da kuma ƴar aiki". Haka ya cigaba da ayyana maganganu sa kana daga bisani ya shiga ciki. Zahra kuwa ba ta zarce ko ina ba sai cikin kitchen ajiye kayayyakin ta yi kan table sannan ta yi jugum tare da bin kayan da kallo. "Zahra kin taro wa kanki match, yanzu ta ina za ki iya girka abin da ki ka ci". Su Samrah suka faɗa suna mai kwashe wa da dariya. Binsu da kallo Zahra ta yi rai ɓace ta ce. "Zan yi kuma za ku gani, an gaya muku ban iya girki ba ne, to zan yi ma wanda yafi wannan dad'i, maza ku ɓace min daga gani". Ta ƙarashe maganar tana mai maida kallonta kan ingredients ɗin. Fice wa su Samrah suka yi suka barta a kitchen ɗin. Zama Zahra ta yi tana mai ɗora hannayenta guda biyu a kai sannan ta ce. "Na shiga uku!, yanzu ta ina zan fara?, ni da ko girki ban taɓa yi ba ta ina zan iya wannan abincin, gashi ba'a taɓa girki a gaba na ba balle na iya, yanzu ya zan yi. Kuma idan ban yi ba hukunci wannan Sooraj ɗin zai yanke min, ya kamata nayi abu. To me ma zan yi?". Ta tambayi kanta. Ɗaukar babban tukunya ta yi tare da ɗora wa kan gas cooker. Dafe kanta ta yi tana mai nazarin mene ne abu na gaba da za ta yi. Nan ta ɗauki man gyaɗa tare da zuba wa cikin tukunyar sannan ta zuba kayan haɗi da wanda ta san mene ne da wanda ba ta san mene ne ba duk ta zuba tare da zuba yaji mai matuƙar yawan gaske, sannan ta yanka albasa ta zuba a ciki tare da kwara wa man gyaɗa ɗin ruwa. Take tukunyar ta kama ci da wuta mai matuƙar ƙarfi. Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai ƙoƙarin rage gas ɗin amma ina wutan ba zai ba ta damar kai hannunta wajan gas cooker domin ta rage ba. "Yanzu ya zan yi na rage wutan nan?, ko na zuba masa ruwa ne?". Ta tambayi kanta. Girgiza kai kawai ta yi tare da cewa. "Kawai bara na rage da kai na". Ta faɗa tana mai kai hannunta wajan gas ɗin. Haka ta naji tana gani ta ƙusa hannunta wajan wutan tare da rage gas ɗin. Da mamakin ta kuwa ta ga samm wutan bai yi mata komai ba. Basar wa ta yi kana ta cigaba da yin hayyukan. Ta fara shirye-shiryen kunun aya da coslow saidai duk ba ta iya ba. Gashi kitchen ɗin duk ya yi kaca-kaca ruwan da ta ɗora ya tafasa har ya fara zuba a ƙasa. Zama ta yi cikin gajiya ta ce. "Gaskiya ba zan iya ba, ina ga guduwa kawai zan yi, shi ne zai fi min sauƙi. Haka kurum za'a bunne ni da raina, chabb ina naga ta zama". Ta faɗa tana mai waige-waige. Leƙo da kanta ta yi wajen kitchen ɗin ganin ƴan aiki da su Samrah basua nan ya sa ta sakin ajiyan zuciya sannan ta cire takalman ƙafarta ta riƙe su a hannu kana ta fara tafiya cikin sanɗa tare da saurin bin hanyar backyard. Saida ta tabbatar da ta fita daga ciki sannan hankalinta ya kwanta. Nan ta fara nufar wajan garden domin kada wani ya ganta. Haka ta cigaba da tafiya da tafiya ba tare da kowa ya lura da ita ba. Ganin babu kowa a wajan ya sa ta fara gudu saida ta je daff da za ta fita daga garden ɗin taci karo da Sooraj tare da Junaid. Nan take ta yi saurin jan burki. Ba ta yi aune ba ta ji zufa ya fara ƙeto mata ta kowane sashe na jikinta. "Ina kuma za ki je?, ko dai ba za ki iya ba ne shi ne ki ka yi tunanin guduwa?". Cewar Sooraj. Nuna kanta Zahra ta yi ta ce. "Ni!, nayi maka kala da wacce za ta gudu?, ka san kuwa wace ce Zahra?, zahra ba ta taɓa guduwa sai dai a gudan mata, ba guduwa zan yi ba naga baku da albasa ne a kitchen shi ne na fito tsinka". Ta faɗa tare da kawar da kanta gefe sannan zuciyarta ya shiga dukan uku-uku!. "Junaid dama muna da shukar albasa a masarautar nan?". Cewar Sooraj. Dariya Junaid ya yo ya ce. "A'a yaya, ina ga ita ce ta shuka shi ne ta zo tsinka. Don mu dai bamu da wani shukan albasa a nan wajan". Maida kallonsa Sooraj ya yi kanta sannan ya ce. "Kinji dai ko, babu albasa nan gwara ki lallaɓa ki koma ki cigaba da abin da ki ke yi". Sunkuyar da kai Zahra ta yi sannan ta girgiza kai ta ce. "Shi ke nen". Ta faɗa tana mai koma wa ciki. _______________________ "Safira yanzu kin ji dai-dai?". Cewar Mom. Girgiza kai ta yi ta ce. "Eh Mom naji dai-dai, Mom dan Allah ku barni na koma America, mun kusan fara exam ɗin mu na Law, kuma shi ne exam na tantance wa, ya kamata ku barni na tafi". Murmushi Mom ta yi sannan ta ce. "Amma na tambaye ki wani abu?". Girgiza kai Safira ta yi alamun eh. Kallonta Mom ta yi ta ce. "Me ya sa ki ke son zama lawyer bayan akwai wasu courses ɗin da yawa bayan shi?, sannan so ki ke kiyi ne don kuɗi ko don kare al'ummar da aka zalunta?". Murmushi Safira ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da juya wa mahaifiyartata baya ta ce. "Ina son na zama lawyer ne domin kare haƙƙin al'umma sannan duk wanda aka zalunta nayi ƙoƙarin tsaya masa har saina ga an ƙwatar masa haƙƙin sa, ina son nayi law ne domi bayar da adalci tare da gaskiya, ban taɓa jin ina son yin aikin Law saboda kuɗi ba, ina son ne nayi domin tsaya wa tsayin daka domin kare haƙƙin ɗan adam. Idan tsanani ya kai maƙurar tsananta to adalci ne kaɗai yake iya maganinta. Sannan ina ji a jiki na kamar an taɓa zalunta ta a baya, shi ya sa nake son nayi wannan aikin. Dan Allah Mom karki ce A'a". Ɗan jimm Mom ta yi sannan ta ce. "yanzu misali na tambaye ki, idan wani talaka ya zo domin ki tsaya masa a shari'a saboda na cuce shi, sai wanda ya cuce shi ɗin ya kawo miki maƙudan kuɗaɗe da kiyi shari'ar ƙarya kan wanda ya nemi taimakon ki idan ba haka ba zai kashe ki. To a wannan lokacin mene ne za ki yi?". Murmushi Safira ta yi sannan ta ce. "Farko zan amince masa sannan na karɓi kuɗin, a yayin da muka je kotu zan tsaya wa wanda aka cuta naga an ba shi gaskiya sannan kuma shi wancan a yanke masa hukuncin kuma baya sannan a gaban idanuwan shi zan ɗauki ƙuɗaɗen da ya bani sannan na bawa wannan talakan, yayin da shi kuma kotu ta yanke masa hukunci". Girgiza kai Mom ta yi sannan ta ce. "Kinga kenan maganganun da aka faɗa kan lauyoyi na cewa suna da baki biyu gaskiya ce. Farko kin gaya wa mugun cewa kin amince sannan bayan kinje kotu kuma ki ka faɗi wani abun da ban ba wanda ku ka shirya da shi ba, kinga hakan yana nufin kinci amanarsa kenen. Ke za ki iya gani cewa ta hanya mara kyau hakan iya samar da gaskiya da adalci. Amma asalin hanya ita ce ka bi ta hanya madaidaiciya domin samar da adalci wannan shi ne. Kinga kenen ba za ki iya aikin Law ba". Saukar da ajiyan zuciya Safira ta yi sannan ta ce. "No Mom, I can do it. Ina da tabbacin cewa zan iya wannan aikin kuma ki zuba ido ki gani. Nan gaba za ki yi alfahari da ni". ________________________ "Wannan wane irin shashanci ne?, ta ya ya za ku ce Amrah ta gagare ku kun kasa kamata?, yanzu kenen duk plans ɗina za su tafi a banza?. To wallahi na baku 24hours ku sace ta, idan kuma ba haka ba zan sa a gama mun da ku". Ya ƙarashe maganar tare da jan tsaki sannan ya kashe wayar. Wurgar da wayar ya yi sannan ya ce. "I have to make another plan, in ba haka ba, duk wahala na za su tafi a banza". ******** Zama Nurse Nadiya ta yi kan gadon kwanciyar ta sannan ta ce. "Na kasa gane me yake faruwa, me ya sa waɗan can mutane suka sace ni?, me ya sa suke tambaya ta mrs Laila, ko dai Mrs Laila har yanzu tana raye ne?, ya kamata na fara bincike kan wannan lamarin, idan ina son sanin gaskiya dole naje prison ɗin da take domin sanin asalin labari". ********* "Hajiya Binta ki daina kuka, Zahra fa ba yarinya bace, ba za ta ɓata ba, ita ɗin ma ƴar iskar kanta ce, kin ga za ta iya kare kanta ba tare da taimakon kowa ba". Share hawayenta Hajiya Binta ta yi tana mak maida kallonta kan Dpo sannan ta ce. "Ai don saboda ba ƴar ka bace shi ya sa ka ke faɗin hakan, akwai kundin littafin da mrs Laila ta bani kafin ta tafi, ta ce idan Zahra ta kai lokacin da ta mallaki hankalin kanta na ba ta wannan littafin. Kuma gashi Zahra ta kai minzalin da zan ba ta wannan littafin gashi kuma an rasa in da ta shiga. Banason wani abu ya faru da ita saboda idan wani abu ya same ta ba zan yafe wa kaina ba". Ta faɗa tare da miƙe wa tsaye ta shige ciki. Shiru Dpo ya yi a sa'inda gaba ɗaya jikinsa suka yi sanyi. ______________________ Ganin Zahra ta shiga ciki ya sanya Sooraj maida kallonsa kan Junaid sannan ya ce. "Junaid ka sa ido kan wannan yarinyar ni sam ban yarda da ita ba, ina son zan fita naje wani wuri ne". Girgiza kai Junaid ya yi ya ce. "Tom yaya in sha Allah, amma dai dakarai ne za su kai ka ko?". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a ni kaɗai nake son zuwa bana son kowa ya bini". Ya faɗa yana mai wuce wa wajan parking space, nan take ƴan aiki suka fara kwasar gaisuwa, yayin da dakarai suka nufo in da yake. Dakatar da su ya yi da hannunsa sannan ya ce. "Kuyi zaman ku bana da buƙatar ku". Ya faɗa yana mai buɗe mota ƙirar ferari tare da shiga. Nan take ya zura maƙulli sannan ya tada motar yana mai barin harabar masarautar sannan ya fice daga masarautar baki ɗaya. Bai zarce ko ina ba sai asibiti. Lokaci ƙalilan ya ɗauke shi ya isa asibiti. Ganin motar wanda ya yi parking ya sa likitoci suka fara nufar in da yake. Suna mai gaida shi. Fito wa ya yi daga motan yana mai amsa gaisuwar sannan ya dube su ya ce. "Where is she?". Nuni ɗaya daga likitocin ya yi masa da cewa tana cikin room. Nufar wajan ya yi bai tsaya ba har saida ya isa bakin ɗakin sannan ya kai hannunsa kan handle tare da murɗa handle ɗin ƙofan sannan ya ƙusa kai ciki. Yana shiga ya tarar da ita kan kujerar mara sa lafiya ta yi ruff da ciki sai kuka take. Nan take idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, zuwa ya yi daff da ita sannan ya zauna kusada ita ya ce. "Me ya sa ki ke kuka eh mrs Laila?". Ɗago da rinannun idanuwanta Mrs Laila ta yi tare da ɗora wa kan Sooraj. cikin dashashiyar muryar ta tace. "Me ya sa ba zan yi kuka ba Sooraj?, yarana duk na rasa su ban sani ba ko suna raye ko Allah ya amshe kayansa. Na rabu da ƴaƴa na tun kafin su san ciwon kansu, yanzu ban sani ba ko suna raye ko A'a, sannan miji na bai damu ta nemi in da suke ba, ƴan uwana basu neme su ba, ni haka tawa kaddarar take". Ta ƙarashe maganar tare da fashe wa da kuka. Furzar da iska mai zafi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kada ki damu na dawo Nigeria ne duk saboda na nemo in da suke, kuma naje chan ne domin neman maganin ki. Zan ƙoƙarta wajan ganin kin samu lafiya sannan anbi miki haƙƙin ki da na yaranki". ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B (ZINARIYAR JAJIRTATTU) *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣ 3️⃣➡️4️⃣4️⃣ *___________________________________________* Sooraj ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye. Sannan ya juya da zimmar tafiya. Saurin riƙe hannunsa Mrs Laila ta yi sannan ta ce. "Na gode sosai Sooraj, ban san da mai zan iya saka maka ba, da a ce ƴaƴana suna nan da na aura maka ɗaya daga cikin su tunda baka da aure". Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Aba ke kuwa suma ai kamar ƴan uwa na suke, sannan na sha gaya miki cewa ki daina min wannan godiyar kinji. Ni yanzu zan tafi, zan sa likitocin su cigaba da kula da ke, sannan kuma na manta ban faɗa miki ba, akwai wani abun mamaki da ta faru a dawowar nan nawa. Na dawo na ga an shiga wannan ɗakin ajiyar sannan kuma sunanki ne password ɗin wannan ɗakin, amma abin da ya bani mamaki wata ƴar aiki a cikin masarautar mu ta iya gano password ɗin sannan kuma ta buɗe bayan kuma babu wanda ya san wannan password ɗin daga ni sai mahallici na". Girgiza kai kawau Mrs Laila ta yi ta ce. "Zai iya kasancewa kawai canka ta yi bawai ta sani ba, ko kuma wani ne ya faɗa mata. Yanzu dai ya kamata ka tafi, saboda bana son maƙiyana su san cewa ina raye ". Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen, zan tafi yanzu kamar yadda ki ka buƙata". Ya faɗa yana mai kiran likitoci. Cikin mintuna ƙalilan suka bayyana a wajan. Nan ya faɗa musu cewa su cigaba da kula da ita sannan duk abin da take da buƙata su bata ba tare da sun tambayi umarnin sa ba. Bayan ya gama yi musu bayani, ya miƙe tsaye tare da barin room ɗin sannan ya nufi wajan parking space. Bai yi aune ba ya ga ya taka ƙafar mutum. Da sauri ya ɗago da idanuwansa tare da ɗora wa kan wanda ya taka. ******* Ɓangaren su Amrah kuwa, basu zarce ko ina ba sai wani babban gida wanda ke cikin layin darmanawa, fitowa Usman ya yi daga cikin mota sannan ya buɗe gate ɗin domin kuwa babu kowa a cikin wannan gida. Shiga ciki gaba ɗaya suka yi yayin da Usman ya koma tare da rufe gate ɗin. Fitowa Amrah ta yi daga cikin mota, kallo ɗaya za ka mata kasan cewa samm ba ta farin ciki. Maida kallonta ta yi kan Umar wanda ko inda take bai kalla ba saima fitowa da ya yi daga cikin mota sannan ya shiga cikin gidan. Jan hannun Amrah su Khairiya suka yi tare da shigar da ita ciki gidan. Suna shiga suka tadda ƙawataccen parlour mai matuƙar kyau. Zama suka yi a matuƙar gajiye. Yayin da suka miƙe suka bar Amrah a zaune tare da shiga ɗaki suka ɗauro alwala domin gabatar da sallah da ake binsu. Bayan su gama alwalan ne suka fito daga cikin ɗakin tare da nufar inda Amrah take suka ce ta tashi ta yi alwala. Binsu kawai take sannan daga bisani ta kawar da kai daga kallonsu. Kallon juna Khairiya da Ramlat suka yi mamaki bayyane kan fuskokin su sannan suka ƙara cewa. "Amrah ki tashi kiyi alwala mu haɗa jam'i tare. Jin shiru kamar ma bata san suna magana ba ya sanya su jan hannun ta tare da yi yi mata alwala ba dan tana so ba ta tsaya suka fara nuna mata yadda za ta yi alwala bayan sun gama ne, suka sanya mata hijabi sannan suka ɗauko sallaya daga cikin wardrobe suka shimfiɗa a ƙasa. Sannan suka tada sallah. Kamar yadda ta ga suna yi haka ita ma Amrah ta yi. Sannan ta bi bakinsu da kallo ganin bakin nasu na motsi ba tare da sanin me suke cewa ba. Haka dai suka yi har suka idar da sallah. Azkhar suka yi sannan Ramlat ta miƙe tsaye nufi hanyar kitchen domin dafa indomie da ƙwai. Mintuna ƙalilan ya ɗauketa ta gama girka indomie sannan ta soya ƙwai tare da zuba su a kan indomie. Chan kan dining ta nufa da abincin a sa'inda ta ƙwalla wa su Umar da su Khairiya kira. Cikin ƙanƙanuwar lokaci gaba ɗaya suka bayyana a wajan. Zama Umar ya yi kan kujera dining table sannan ya ɗibi abinci sannan ya yi bissmillah ya fara ci. Daidai wannan lokacin su Amrah da Khairiya ke fitowa. Zaunar da Amrah Khairiya ta yi kan kujera dining sannan ta zuba mata indomie ɗin tare da saka mata chokali a ciki. Maida kallonta Khairiya ta yi kan Amrah sannan ta ce. "Amrah kici wannan indomie, tunda ki ka zo gidan mu kayan marmari kawai kike sha. Bakya cin abinci, kuma ya kamata ki dinga cin abinci wanda za su ƙara miki lafiya". Kallon abincin Amrah ta yi sannan ta kawar da idanuwanta tare da cewa. "Ni bana ci wannan ƙazamin abun" Maida kallonsu gaba ɗaya suka yi kanta. A sa'inda Ramlat ta ce. "ke kuwa Amrah ki ɗauka kici mana". Kallon indomie ɗin Amrah ta yi tare da buge shi gefe harta kai ga ya zube a ƙasa. Yayin da kwanon da aka zuba indomie a ciki ya fashe. A matuƙar fusa ce Umar ya miƙe tsaye sannan ya ɗaga hannu tare da wanka mata mari. Dafe ƙuncinta Amrah ta yi da zallar mamaki. Mamaki ne ya kama kowanne a cikin su. "Kinyi hauka ne?, tayaya za ki zubar da abinci bayan wasu suna chan basu samu ba?, ke naga alamun idan mutum ya biki ta lallami kike yi masa iskanci. To ki tsaya ki saurare ni ba zaki yi wannan shashanci da ni ba. Idan nace ina sonki bawai hakan yana nufin kiyi abinda kika gadama ba, dan kawai kinga ana rarrashin ki shi ne za ki dinga yi wa mutane hauka tsewwn!" ya faɗa yana mai jan tsaki sannan ya bar dining ɗin gaba ɗaya. Ja da baya Amrah ta yi yayin da jikinta suka fara kakkarwa. Kallonta su Ramlat suka yi sannan suka shiga bata haƙuri. Da sauri Amrah ta nufi hanyar waje tare da ƙoƙarin fita daga gidan. Ganin hakan ya sa suka bi bayanta nan suka shiga dakatar da ita, amma ko sauraransu ba ta yi ba. Da sauri Usman ya koma ciki domin sanar da Umar halin da ake ciki. ****** "Grandma wai wace ce wannan matar da nake gani a photon da Grandpa ya ce a ƙona?". Ajiyan zuciya Grandma ta sauke sannan ta ce. "Wane hoto kenen?". Amsa Safira ta ba ta da cewa. "Wani photo kwanaki da na taɓa gani a parlour". Sauke ajiyan zuciya Grandma ta yi a karo na biyu. Sannan ta ce. "Kina nufin ƴata Lailah?"., Girgiza kai Safira ta yi alamun eh sannan ta ƙara da cewa. "Tana ina ne?, ita ɗin bata da ƴaƴane ko kuwa bata nan ne?". Amsa Grandma ta ba ta da cewa. "Lailah ko ta na raye ko ta mutu Allah ne masani, sannan maganar ƴa tabbas a shekarun baya an kawo ƴar da ta haifa a gidan yari aka kawo ta mahaifin Lailah ya yi rejecting ɗin yarinyar. A yanzu haka bamu sani ba ko tana raye ko kuma ta mutu, amma fatana shi ne idan suna raye gaba ɗaya Allah ya cigaba da kare su sannan kuma Allah ya dawo da su wannan family ɗin mu koma yadda muke a da, mu cigaba da rayuwa cikin farin ciki, shi ne kawai fatana". Girgiza kai Safira ta yi ta ce. "Amma mene ne ta yi da har Grandpa yaƙi karɓar yarinyar ta sannan kuma ita mene ne ta aikata da har aka kaita gidan yari?". Murmushi Grandma ta yi sannan ta ce. "Labari ne mai dogon zango ko ni kaina ban san tushen labari ba, amma ni na san da cewa Lailah ba zata taɓa aikata abinda haka ce tana yi ba domin na yarda da ita ɗari bisa ɗari, Lailah tana da kyakyawar zuciya. Tana gudanar da aikin Company tana taimaka wa talakawa marasa ƙarfi, sannan ta saka yaransu a makaranta yayin da ta buɗe gidan marayu na marasa iyaye. Duk don ta taimaka wa al'umma amma shi ne haka ƙaƙala mata sharri haka ce duk tana hakan ne saboda kuɗi". Ta ƙarasge maganar tana mai fashe wa da kuka. Tausayin Lailah ne ya kama Safira hakan ya sa ta ƙudiri aniyar cewa duk sanda ta zama lawyer saita wanke Lailah. ******* "Ya ƙuri na taka ka bada sani na ba". Cewar Sooraj. Murmushi MK ya yi sannan ya ce. "Ƙwarai na san ba da sanin ka kayi hakan ba domin hakasari ma ni ne nan wanda na sa ƙafata a wajan da zaka wuce". Nan take fuskar Sooraj ya sauya daga walwalah zuwa ɓacin rai. "A kan me ya sa za ka saka min ƙafa a wajan tafiyata?, so ka ke na faɗi ko me?". Cewar Sooraj Girgiza kai MK ya yi ya ce. "A'a ko ɗaya, nayi hakan ne domin janyo hankalin ka izuwa gare ni. Shin mene ne alaƙar ka da Mrs Laila Abdullahi?". Shiru Sooraj ya yi jin tambayar da bai san amsarta ba. Kallon mk ya yi ya ce. "Me ya sa ka ke son sanin alaqa ta da Mrs Laila, tukunan ma wane ne kai?, me ya sa ka ke bibiyar rayuwar mrs Laila da tawa?, ka faɗa min waya turo ka?". Tashi tsaye mk ya yi daga kan kujerar da yake kai sannan ya ce. "Ni ne wannan ɗan sandan da ya taimaka wa Mrs Laila Abdullahi a shekarun baya. Na ɗauka Laila ta mutu, sai kuma daga baya na gane cewar taba raye bata mutu ba, hakan ya sani yin farin ciki, yanzu dai ina da good news da zan baka. A cikin yaran mrs Laila akwai guda ɗaya a cikin masarautar ku". Zaro ido waje Sooraj ya yi ya ce. "Da gaske ka ke?, wace ce?". Murmushi MK ya yi ya ce. "Ba zan faɗa maka ba kai ka gano ta da kanka, ita ma ɗaya daga cikin ma'aikatan masarautar ce. Abinda kawai zan faɗa maka kenan, na barka lafiya". Ya faɗa yana mai barin wajan. Ruɗani Sooraj ya shiga tare da ƙoƙarin gano ko wace ce amma hakan ya cutura. Shiga cikin matarsa ya yi tare da tada wa yana mai barin harabar wajan. ***** "Yahya Amrah na ƙoƙarin fita daga gida". Cewar Usman. "What!". Cewar Umar, sannan ya ƙara da cewa . "Amrah kuwa, saboda me, muje na gani". Ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye sannan suka fita suna zuwa suka tarar ta fice daga gidan. Tarar da su Ramlat suka yi a zaune a jugun, ganin Umar ya fito ya sanya su faɗin. "Yahya Amrah ta tafi, mun bi bayanta amma bamu ganta ba". Jin hakan ya sa hankalin Umar ya tashi, "Kamar ya baku ganta ba, muje mu nemo ta domin ba zan yafe wa kaina ba idan wani abu ya same ta". Ya faɗa suna mai shiga mota tare da barin gidan domin neman Amrah. ****** Zama Zahra ta yi tana mai bin komai na kitchen ɗin da ido nan ta shiga tunanin ta ya ya zata fara girkin. Tunani ta yi ta duba google sai kuma ta yi duba da cewa ita ɗin bata da waya. Jungum ta yi tana mai cigaba da bin kitchen da kallo. Daidai lokacin Gimbiya Saratu da Talatu suka shigo cikin kitchen ɗin tare da kwashe wa da dariya. Riƙe ƙugu Gimbiya Saratu ta yi sannan ta ce. "Ya dai?, kin kasa girkin ne?, an dai ji kunya". Kallonta Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ke Zahra ko mene sunanki, kin san ba za ki iya girka ba me ya sa ki ka cinye abincin?, gashi kuma shi Sooraj ba zai barki abinda ki ka yi ya tafi a banza ba dole ne ki yi girkin nan ko kin iya ko baki iya ba". Murmushin takaici kawai Zahra ta yi tare da girigza kai ta ce. "Ban san me ya sa mutane suke shiga abin da babu ruwansu ba, sai kutsen jaraba kamar tinkiyoyi, mutane baka shiga harkar su ba amma dole su shiga harkar ka, sun shigo da wasu ƴan matan ƙafafuwansu sun zo suna min aushi". Kallon ta Gimbiya Saratu ta yi rai ɓace ta ce. "Da wa ki ke?, abaici ki ke ko me?, wallahi ki shiga taitayinki domin ni ba sa'ar uwar....... Maganarta ce ta tsaya chakk sakamakon tsawar da Zahra ta daka mata. Nan take suka sha jinin jikinsu. Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Kada ki kuskure ki ƙarasa wannan kalmar, da a ce kin ƙara da yau za ki san bambancin jinin sarauta da kuma jinin talaka. Ban tanka muku ba dan haka ku barni, ni zan yi kayana da kai na". Ba tare da sun so ba haka suka fice daga cikin kitchen ɗin. Shigowa ƴan aiki suka yi domin su taya Zahra girka abincin, amma Zahra taƙi amincewa da su tayata. Ba yacce suka iya haka suka fice suka bar mata kitchen ɗin. Ganin zama ba zai finshe ta ba, ya sanya ta miƙe wa tsaye sannan ta fara shirye-shiryen girkin. Haka ta cigaba da girki cikin tunani, yayin da duk abin da ta gani zuba wa kawai take ba tare da sanin mene ne shi ba. Bayan nan ta yi blending ɗin kunun aya a blender sannan ta tace garin nan ta saka mai su flavour da dai sauran kayan da ba za'a rasa ba. Haka ta cigaba da yin girkin ba tare da ta huta ba. Ba ita ta gama girkin ba sai bayan insha'i. Zama ta yi tana mai yarfe zufan da ke ƙeto mata. "Tunda nake ban taɓa shan wahala irin ta yau ba, ba gaira ba dalili wan can banzan mutumin ya sani girkin dole, na san ma ba zai yi dad'i ba". Ta faɗa tana mai jera abinci sannan ta fita daga cikin kitchen ɗin. Tare da nufar hanyar dining sannan ta ajiye abincin tare da fara ƙwalla wa gaba ɗayansu kira. Cikin kankanin lokaci gaba ɗaya suka hallara daidai lokacin shima Sooraj ke fitowa daga part ɗin shi Zama suka yi a kan dining ɗin sannan Zahra ta zuba wa Sooraj abinci domin ya ji ɗanɗanon. Ɗaukar spoon Sooraj ya yi sannan ya ci chokali ɗaya, ji ya yi abincin ya yi daɗi, amma dan kada ya nuna cewa yayi dad'i hakan ya sa ya haɗe rai. "Wannan wane irin abinci ne haka mara daɗi?, ko taste babu. Maza ku kwashe abincin nan ku kaiwa karnuka su ci". "Ƙwarai kuwa domin mu ba zamu ci wannan ƙazamin abincin ba". Cewar su Gimbiya Saratu da su Samira. Murmushin gefen baki Zahra ta yi, sannan ta cire ɗan kwalin kanta tare da ɗaura wa a ƙugu sannan ta rungume hannayenta a ƙirji, ta maida kallonta kan Sooraj ta ce. "Me ma kace?, a kaiwa karnuka abincin da na ɓata lokaci na wajan yinsa, kunsan hawanni nawa nayi ina girka abincin nan tare da haɗa su fruit salad da kuma kunun aya shi ne za ku ce ba za ku ci ba. Ai wallahi tallahi baku isa ba, na rantse da Allah sai kunci wannan abincin tass". Ta faɗa tana mai nufar hanyar ƙofar parlour tare da saka wa ƙofar parlourn maƙulli sannan ta saka maƙullin a cikin aljihunta. "Mene ne ki ke ƙoƙarin aikata wa?, wato muci wannan abincin, to ba za mu ci ba, kiyi abin da ki ka ga za ki iya". Cewar su Fasma. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Ashe yau za'ayi tashin balagan tsuntsaye a masarautar nan, chabb wallahi yau akwai tashin hankali a masarautar nan muddin baku zauna kun cinye abincin nan ba. Wato na gama shan ɓakar wahala shi ne za ku ce za ku kaiwa karnuka dan ma kun raina wa mutane wayo, to ku sani idan kuna yiwa kowa iskancin ku ba zaku yi min ba. Maza-maza ku fara ci dama ai kuna da hannu maza ku zuba da kanku kuci salin ali abunku ɗanoinoi". "Ba za mu ci ba me za ki yi?". Cewar Sooraj. Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Ohh nufin ku ba za ku ci wannan abincin ba?, haka ku ka ce ba za ku ci ba ko?, uhmm shi ke nen. Idan baku ci ta lallami ba za ku ci da ƙarfi da yaji". Ta faɗa tana mai shiga ɗakinta. Tsayawa gaba ɗaya suka yi domin ganin me ta shiga ɗauko wa. Gani suka yi ta fito hannunta riƙe da igiya tare da turare. Bata yi wata-wata ba ta fesa musu turaren a fuska tana mai rufe hancin ta. Nan da nan jiri ya fara ɗiban kowanensu, ganin sunyi laushi ya sa Zahra ta fara ɗaɗaure kowanensu da igiya tana mai faɗin. "Ƴan kutumur kitabi dangin gajeru kawai, wai nayi girki suce ba za su ci ba, kun ma isa, chabb da Zahra ku ke zancen wallahi da kaina zan ɗurka muku abincin har sai kun cinye tass". Haka ta cigaba da ɗaɗɗaure su ba tare da gajiya ba. Duk abinda ake yi Mami ba ta sani ba domin kuwa tana chan part ɗin sarki. Zahra kuwa ɗauri ta yi musu kamar ta samu akuyoyi. Bayan ta gama ta miƙe tare da ɗaukar abincin ta sauko da su ƙasa. Zuba mai mugun yawa ta yi cikin plate sannan ta kai dubanta kan gaba ɗayansu ta ce. "Ni kuma ta kanwa zan fara ɗura wa wannan abincin?, yauwa Samiran nan zan fara tura wa dan naga tafi dogon baki a cikin su". Ta faɗa tana mai zuwa inda Samira take sannan ta lanƙwasar da kan Samira tamkar za ta ɗura wa yaro magani haka Zahra ta shiga ɗura wa Samira abincin nan ba tare da gaggauta wa ba. Dariya Zahra ta fashe da shi ganin yadda gaba ɗayansu suka ƙwalalo da idanuwa waje. "Shashanci banza kawai, aka ce bakua ji ashe gani ne bakua yi. Wallahi duk saina saita muku zama a gidan nan, marasa mutunci kawai. Su Sooraj kuwa suna ganin komai saidai jikinsu ba zai yi motsi ba balle su dakatar da ita domin kuwa turaren da Zahra ta ɗauko ba normal turare ba ne. Haka ta shiga ɗura musu abincin da shi da su kunun aya tare da tuwon shinkafa. Tana ɗura musu abincin tana raira waƙa. "Hayya ra'iye alagidibo, yara sai dai kallo amma ba'a isa aiwatar da komai ba". Ɓangaren Sooraj kuwa hayyana wa yake irin rashin mutuncin da zai yi wa Zahra idan ya dawo cikin hankalinsa. ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar Jajirtattu) . *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣5️⃣▶️4️⃣6️⃣ *___________________________________________* Haka Zahra ta shiga ɗura wa kowanensu abinci har saita da ta kai kan Sooraj. Tsayawa ta yi tare da zuba masa idanuwa sannan ta ce. "Kaine babba ko?, harda wani cewa, kiyi maza-maza ki kije ki girka abincin nan, sannan na gama ka ce wani a kaiwa karnuka saboda ka raina min hankali, to kai ma saikaci domin naka ma yafi yawa ka ganshi ko, ta faɗa tana mai nuna ƙaton kula wanda ya cika da abinci. Maida kallonta ta yi kansa ta ce. "To sai ka cinye abincin nan tass in faɗa maka gaskiya". Ta faɗa tana mai ɗaukar chokali sannan ta ɗibi abincin ta kai bakin sa. Ganin ya matse bakinsa yaƙi buɗe wa ya sanya ta kama fuskarsa tare da buɗe bakin nasa da ƙarfi sannan ta cusa chokalin ciki. Haka ta shiga ɗura mai abinci har na kulan ya ƙare. Tashi tsaye Zahra ta yi tare da karkaɗe jikinta ta ce. "Ƴan banza kawai wato ku nan ƴan sarauta ko?, ko banza dai kunci abincin". Ta faɗa daidai lokacin da Mami ke fitowa daga ɗakin ta. "Ya subha'anallahi!". Kalmar da ta fara zuwa bakin Mami kenen. Kallon Zahra Mami ta yi ta ce. "Zahra wane ne ya yi musu haka?, ji fa yadda aka ɗaɗɗaure su kamar wasu akuyoyi, mene ne abin da ya faru?". Kallon Mami Zahra ta yi ta ce. "Yauwa Mami barka da ƙarasowa". Ta faɗa tana mai zuwa kusa da Mami sannan ta kalleta ta ce. "Kin san mene ne suka aikata?". Girgiza kai Mami ta yi alamun A'a. Maida kallonta Zahra ta yi kan su sannan ta ce. "Kina ji ba, Yarima Sooraj ba ya ce saina ƙara girka wannan abincin da na cinye ba, to wai bayan na gama ɓata lokaci na nasha wahala sannan na kawo musu, wai da suka zo wai yarima Sooraj ya ce wai a kaiwa karnuka su cinye. Ni kuma na ce idan na yarda mai tatsine ya dawo duniya, na ce suci suka ce ba za su ci ba. Ni kuma da naga aka na je na ɗauko wani turare na kashe jiki a ɗaki nima ban san turaren na mene ne ba, na fesa musu sannan na ɗaɗɗaure su kana na basu abincin da kaina, shi ke nen fa". Salati Mami ta rafta tana mai faɗin. "Zahra kin kashe ni, Sooraj fa yana da cutar Asma kuma chronic ne, bai kamata a ce kinyi musu haka ba, domin kuwa ke ƴar aiki ce kawai, ya kamata a ce kina iya sarrafa fushin ki a wasu lokuta". Ƙunce su Mami ta fara yi yayin da ita ma Zahra ta saka hannu suka kunce su tare. Saida suka shafe kusan hawa guda ba tare da wani a cikin su ya dawo cikin hayyacin sa ba. Bayan wasu mintuna suka fara dawo wa cikin hayyacin su , yayin da suka shiga amai. Gaba ɗaya babu wanda bai farfaɗo ba sai dai Sooraj wanda har izuwa wannan lokacin bai farfaɗo ba. Hankalin Mami ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin Sooraj bai farfaɗo ba. Ɓangaren Zahra ma gaba ɗaya hankalinta ya tashi yayin da take tsoron kada ta je ta kashe ɗan mutane. ****** Bayan Umar yaji labarin cewa Amrah ta tafi ya sa hankalin shi ya tashi. Yayin da suka bazama nemanta amma hakan ya cutura. A sa'inda Umar ya kira jami'ansa domin su zagaye gaba ɗaya garin Kano dan a nemo ta. Ɓangaren Amrah kuwa, bayan fitar ta daga ciki gidan ta fara tafiya ba tare da ta san inda take sanya kafafuwanta ba. Babu zato ta ga wasu motoci sun zagaye ta. Nan wasu mutane suka fito fuskokin su rufe da mask. Ba ta yi aune ba ta ji sun shaƙa mata wani abu. Take jiri ya ɗibe ta yayin da bacci mai nauyi ya kwashe ta. Shigar da ita suka yi cikin motan sannan suka bar harabar wajan da ita. ******* Tun ana ɓoye wa har labari ya garzayo kunnen sarki. Nan haka wuce da Sooraj asibiti yayin da aka shiga bashi taimakon gaggawa. Gaba ki ɗaya hankalin Sarki da na Mami ya tashi. Yayin da ɓangaren Zahra take ta faman addu'a Allah ya sa bai mutu ba. Nan dai likitoci suka yi nasarar dawo da numfashin sa, saida Sooraj ya kwashe kwana biyu a asibiti ana duban lafiyar sa. Kafin daga bisani aka sallamo shi daga asibiti. Gaba ki ɗaya jikin ƴan gidan ya mutu yayin da suka kasa furta komai, tare da ganin duk laifin Zahra ne da a ce ba ta yi abin da ta yi ba da hakan ba ta faru da shi ba. Zama gaba ɗaya suka yi a parlour, yayin da Zahra durƙushe gwiwowinta a ƙasa ta duƙar da kai ƙasa. Kallonta Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Kinga abin da ki ka aikata ko?, yanzu da a ce daga nan ya mutu mene ne za ki ce?, kin san da a ce ya mutu kema rataye ki za'a yi?, wannan wane irin shashanci ne da almubazarancu". Kallon Sooraj Zahra ta yi nan take taji nadamar abinda ta aikata. Duƙar da kai ƙasa ta yi ta ce. "Ina mai baku haƙuri gaba ɗaya, banyi hakan ba dan wata manufa a zuciyata ba, nayi hakan ne dan kawai na saku kuci wannan abincin amma bawai nayi hakan ba da nufi cutarwa. Idan duk na ɓata muku rai kuyi haƙuri ba zan sake ba". "Babu wani ba za ki sake ba, kawai mafita shi ne ki tattara komai naki ki bar wannan masarautar". Cewar Gimbiya Saratu. Ɗaga musu hannu Sooraj ya yi ya ce. "A'a, ba zata je ko ina ba, bazan bari ta tafi haka nan ba, dole ita ma ta ɗanɗana kuɗarta, tunda harta iys ɗora hannayenta a kanmu to ba zata tafi kuma a ƙyale ta ba". Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Amma Sooraj ya kamata kayi nazari, ta riga ta baku haƙuri, ni kawai zan sallame ta tafi". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "A'a Mami, da a ce na mutu haka za ki ce a rabu da ita?, bazan bar abinda ta aikata ba, wallahi saina gana mata azaba a masarautar nan, saina sa ta gwammaci mutuwa da rayuwa". Ya ƙarashe maganar tare miƙe wa tsaye sannan ya nufi part ɗin sa. Maida kallonta Mami ta yi kan Zahra ta ce. "Zahra tashi ki shiga ɗaki kinji". Girgiza kai kawai Zahra ta yi sannan ta miƙe tsaye tare da nufar ɗakinta. Binta kawai su Samira suka yi da kallo, yayin da suke hayyana irin muguntar da za su yi mata. Zahra na shiga ɗaki kuwa ta faɗa kan gadonta tana mai sauke ajiyan zuciya sannan ta miƙe zaune ta ce. "Wai me yake nufi?, yana nufin zai azabtar da ni?, dan ma ya samu na bashi haƙuri shi ne zai dinga fadar waɗan nan maganganun, to wallahi daidai da kai aikin banza kawai". Ta faɗa tana mai buga tsaki. ***** "Hello Please am I talking to Safira Ibrahim?". Girgiza kai Safira ta yi kamar tana gaban mai maganar a waya sannan ta ce. "Yes of course, please how may I help you?". Daga ɗayan ɓangaren aka ce."The law school you applied to has accepted you, now you just need to start, but before that, today we need you to come in for signing so that we can verify your details. They will come to pick you up at home, and don't worry about receiving a visa or passport because everything has been completed. We are just waiting for you." Miƙe wa zumbur Safira ta yi cike da farin ciki ta ce". Wow!, thank you so much, I can't even describe how happy I am. Very soon, I'll be heading to America." Ta faɗa tana mai katse wayar. Da sauri ta fita parlour ciki sa'a ta tarar da su Mom a parlour, nan ta sanar musu abin da ya faru. Babu wanda bai yi farin ciki ba amma Mom samm ba ta so hakan ba domin ba ta som ta yi nisa da ƴarta. A gurguje Safira ta koma ɗaki kana ta shirya kanta da kayanta. Bayan ta gama shirya kayanta a travelling box. Ta saka kaya masu kyau riga da wando sannan ta saka ɗan ƙaramin veil sannan ta ɗora kimono a kan riga da wandon. Fitowa ta yi da box ɗin sannan ta nufi hanyar waje. Bakwana suka yi da kowa na gidan yayin da Daddy ya shiga saka mata albarka. Mom kuwa shiru ta yi domin gaba ɗaya hankalinta ba'a kwance yake ba, ji take kamar wani abu na shirin faruwa da ƴarta. Kallon Safira ta yi ta ce. "Safira, ni da za ki ji ta baki na kiyi zamanki kawai, idan ya so idan za mu koma America sai kiyi komai, wallahi hankali na ya kasa kwanciya, tsoro na shi ne kada wani abu ya same ki". Murmushi Safira ta yi ta ce. "Kada ki damu Mom babu abin da zai same ni da izinin Allah". Daidai lokacin suka jiyo horn ɗin mota a waje. Bye-bye tayi musu kana daga bisani ta fice daga gidan. Fitowa driver ɗin motan ya yi sannan ya karɓi box ɗin kayanta tare da saka su a bayan mota. Shiga cikin motan ta yi kana daga bisani driver ya ja mota suka bar wajan. Sosai Safira ke farin ciki yayin da take gani kamar cewa ta riga ta zama lawyer. Kallon driver ɗin ta yi ta ce. "Yanzu hanyar airport zamu wuce ko?". Shiru driver ɗin ya yi mata bai ko tanka mata ba. Mamaki ne ya kamata ganin bai amsa ba, hakan ya sa ta yi tunanin ko bai ji ba ne. Hankalinta bai tashi ba sai sanda ta ga anyi wani kwana da ita ana shiga cikin dajin. Nan take gabanta ya tsananta faɗuwa. Kallon driver ɗin ta yi ta ce. "Kai driver ina ka ke ƙoƙarin kai ni?, ba airport ka ce zamu je ba, ni ka ga just take me back home please". Ganin ko kulata bai yi ba ya sa hankalinta ya ƙara tashi. Addu'a ta shiga yi tana mai neman kariyar Ubangiji. Yayin da hawaye ya fara sauka kan ƙuncinta tana mai nadama kan me ya sa ta biyo wanda ba ta sani ba, kuma saida Mom ta faɗa mata cewa kada taje ta bari idan za su koma America. Saida suka je chan cikin tsakiyar daji. Sannan driver ɗin ya tsagaita da tafiya. Parking ya yi kusa da sauran kidnapper's ɗin sannan ya fito daga mota. Buɗe mata ƙofa ya yi kana ya dube ta ya ce. "Duk abinda haka faɗa miki a waya to ƙarya ne. A halin yanzu dai kina ƙarƙashin mu ne, kuma idan muka gadama za mu kashe ki har lahira, ina son ki bamu haɗin kai idan ba haka ba ki mutu". Faɗuwa gaban Safira ta yi sannan ta ce. "Dan Allah ku faɗa min mene ne na aikata muku?, sannan wane ne ya turo ku sace ni?". Murmushi mutumin ya saki sannan ya ce. "Kina son sanin wane ne?". Girgiza kai Safira ta yi alamun eh. Amsa mutumin ya bata da cewa. "To Aliyu ne". Rass! gabanta ya buga da mugun ƙarfi. Kallon mutumin ta yi ta ce. Wane Aliyu?, Aliyu wanda zan aura?". Amsa suka bata da cewa. "Ƙwarai kuwa da gaske". Kallon su Safira ta yi cikin rashin yarda ta ce. "Ƙarya ku ke, samm Aliyu ba zai sa a sace ni ba, saboda me zai yi hakan?, ni ce fa wacce zai aura. Kunga ku faɗa min gaskiyar cewa ba Aliyu ba ne, domin na yarda da shi ba zai taɓa sace ni ba, kuma mene ne ribarsa ma idan ya sace ni?, me zai samu?". Dariya gaba ɗaya suka kwashe da shi sannan suka ce. "Kina son sanin me zai samu?. To ki baza kunnuwanki kiji, zai samu kuɗaɗe ne, dubbunan kuɗaɗe, Aliyu samm ba sanki yake ba illa dukiyar ki, kuma dai Aliyu shi ne ba wani ba. Idan baki yarda ba duba nan ki gani". Mutumin ya faɗa yana mai nuna mata wayarsa. Nan ta ga Aliyu tare da mutanen wajan suna raba kuɗi a tsakanin su, yayin da suke maganar yadda suka sace Amrah, gashi za su sace Safira. Jikin Safira ne ya mutu, yayin da takaici ya ana ta kasa cewa ƙala. Hawaye ne ya fara gangaro wa bisa ƙuncinta. Ta ce. "Ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba Aliyu, me ya sa zai aikata min haka?, da na yanke cewa zan amince na aure sa domin ya nuna min cewa yana so na sannan kuma yana da nutsuwa da sanin ya kamata, ashe duk ƙarya ne". Ta ƙarashe maganar tana mai fashe wa da kuka. ********** Zahra na zaune ta ga ƴar aiki ta shigo sallama riƙe a bakin ta. Amsa sallamar Zahra ta yi ta ce. "Mene ne ya faru?". Amsa ƴar aiki ta bata da cewa. "Yarima Sooraj ne ya ce na kira wo masa ke, kuma ya ce ki zo cikin gaggawa". Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Allah ko?". Sannan ya ƙara da cewa. "To ki koma ki gaya masa cewa ba zan zo ɗin ba, idan zai iya zuwa ya tafi da ni chan ya zo ya ɗauke ni, sannan kice mai tunda shi ne yake buƙata ya zo da ƙafarsa amma ba dai ni na je ba, ni Mami kawai nake yi wa aiki bawai shi ba, ita kaɗai ce za ta sani aiki nayi ki gaya masa hakan". Ta faɗa tana mai koma wa tare da kwanciya. Fita ƴar aikin ta yi sannan ta nufi part ɗin Sooraj ta zayyane masa duk abin da Zahra ta faɗa. Nan take ran Sooraj ya ƙara ɓaci. "Ni ce zan kira ta tace wai ba zata zo ba sai dai ni da kaina naje?, za ta gane kuranta". Maida kallonsa ya yi kan ƴar aikin ya ce. "Jeki na san yadda zan yi da ita". Jin hakan ya sa ƴar aikin ta bar masa part ɗin sa. ****** Zahra na kwance taji an banƙo mata ƙofa. A matuƙar razane ta miƙe tsaye. Su Gimbiya Saratu ne tare da su Fasma. Rufe ɗakin suka yi sannan suka saka maƙulli suka rufe. Murɗa hannayensu suka yi a ƙirji sannan Gimbiya Talatu da su Samira suka fara karkaɗa ɗuwawu. Kallonta Yusra ta yi ta ce. "Wati ke kin cika ƴar iska da har za ki iya sa mu ci wannan ƙazamin abincin naki". Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Naji ƙazami ne, amma dai koba komai kunci abincin. Tukun na ma me ya kawo ku ɗaki na?". Amsa Gimbiya Saratu ta bata da cewa. "Munzo mu nakaɗa miki na jaki ne, duka zamu yi miki". Babu zato Zahra ta kwashe da dariya. Kallon juna su Gimbiya Saratu suka yi ganin tana dariya ya sa abin ya basu mamaki. Saida Zahra ta yi mai isarta sannan ta ce. "Wai da gaske duka na ku ka zo yi?. To masha Allah maraba da zuwa, me ku ke so na kawo muku, tuwo ko shinkafa?, kun san ana son mutun kafin ya fara dambe ya fara cin abinci mai lafiya ta yadda zai samu ƙarfin yin duka sosai". Kallon juna suka yi gaba ɗaya suka yi ganin tana neman shashantar da su ya sasu cewa. "Da gaske fa muke ba wasa ba". Jin hakan ya sa Zahra ta haɗe ranta sannan ta ce. "Zan baku shawara kyauta ba tare da ko sisin ku ba, kuyi wa kanku faɗa ku koma, domin idan na fara dukan ku karku zo kuna bani haƙuri naƙi hakura, ku yanke shawara a tsakanin ku tun kafin a fara". Kallonta Samira ta yi ta ce. "Kin ɗauka za ki iya dukan mu ne?, ko kin manta cewa sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi?, to ba za mu fita ɗin ba kiyi abin da ki ke ganin za ki yi" . Jin hakan ya sa Zahra miƙe wa sannan ta nufi hanyar waje ta ƙara rufe ƙofar sosai sannan ta cire ki ɗin tare da saka wa a ciki kayanta wanda yake doguwar riga atamfa mai aljihu. Koma wa ta yi ta zauna kan gado ta ce. "Ta kan wa za'a fara?, ku gimbiyoyi ku koma ku zauna ku ga idan yaranku suna da ƙarfi ko basu da shi". Kamar yadda ta faɗa aka gimbiya Saratu da Talatu suka koma suka zauna, yayin da suke jiran kawai suka yaran nasu sun fara jibgar Zahra. Take Samira ta kaiwa Zahra naushi a fuska. Da sauri Zahra ta kawar da kai sannan ta kama kan Samira da Fasma ta gwara su guri ɗaya. Nan take suka saki wata iriyar azababbiyar ƙara!. Ƙaran da suka saki ya janyo hankulan su Junaid da na so Sooraj ɗakin. Da sauri suka nufi hanyar ɗakin Zahra tare da bubbuga ƙofan. Ɓangare Zahra kuwa ɗaukar dorina ta yi ta fata shauɗa musu babu gaggauta wa. Ihuu suke suna neman a kawo musu agaji . Ganin ba za su iya cigaba da jure wa ganin Zahra na dukan musu yara ba ya sa su miƙe wa suka fara rirriƙe hannun Zahra. Ɗaga hannu Zahra ta yi zata zuba wa wanda ya riƙe ta dorina. Chak da dakata ganin su Gimbiya Saratu ne. Wafce jikinta ta yi daga nasu ta ce. "Ba zan iya dukan ku ba, domin kuwa kuma a matsayin iyaye na ku ke, dan haka ba zan taɓa iya ɗora hannu na a kanku ba". Ta faɗa tare da koma wa ta zauna. Miƙe wa su Samira suka yi suna hawaye, yayin da su Gimbiya Saratu suka shiga rarrashin su gani yadda jikinsu ya yi jajir yayin da satin bulalan Zahra duk ya fito jikinsu. Kallon Zahra Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ki bamu maƙulli mu fita". Kallonsu Zahra ta yi mamaki bayyane kan fuskarta ta ce. "Ku fa ku ka ce ba za ku taɓa fita daga ɗakin nan ba har sai kun dake ni, to a kan me ya sa za ku fita bayan baku dake ni ba?, to ku sani cewa muddin baku dake ni ba bazan baku maƙullin ɗakin nan domin ku fita ba". Roƙan Zahra gaba ɗaya suka fara yi. Yayin da suka ce ba za su sake irin wannan gangancin ba. Saidai Zahra ko sauraren su ba ta yi ba illa ca da ta yi cewa. "Wallahi ba zan bari ku fita ba muddin baku dake ni, maza-maza ku tawo ɗaya bayan ɗaya ku dake ni kunji ko, kunce za ku dake ni kafin ku fita kuma baku dake ni ba. To ku sani cewa ko wane ne zai zo bai isa ya sani na baku maƙulli domin ku fita ba har sai kun dake ni kamar yadda ku ka furta, ba saida na faɗa muku kuyi wa kanku faɗa ba?, na baku shawara na ce ku tafi amma ku ka yi kunnen ƙashi, kuma na riga na faɗa muku idan na fara jibgar mutum idan wani ya roƙe ni na buɗe ƙofa ba zan buɗe ba, dan aka a yanzu mun sa ƙafar wando ɗaya da ku, sai dai ku dauwama a cikin ɗakin nan muddin baku zo kun taɓa ni ba". *KAI ZAHRA AKWAI ƘARFIN HALI😹😹😹, KI ƘYALE SU AJEBUTTERS SU FITA😂🤣* ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (ZINARIYAR JAJIRTATTU). https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g *🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part of the world)*🪐🌎🪐. Daji 🌲 Magarƙama🏢 da kuma Birni🏙️ WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣7️⃣▶️4️⃣8️⃣ *___________________________________________* Shiru gaba ɗaya suka yi jin furucin Zahra. Takaici ne ya kama kowanne a cikin su. A matuƙar fusa ce Gimbiya Saratu ta ce. "Karki manta kefa ƴar aiki ce kawai a masarautar nan, kinga kenen muna da iko a kanki, dan haka a matsayina na Gimbiya mai faɗa a ji, ina mai baki umarmin ki buɗe wannan ƙofan yanzu". Dariya Zahra ta kwashe da shi sannan ta ce. "Sannu Gimbiya mai faɗa a ji, wato kina mai bani umarni na buɗe ƙofa ko, tun farko mena faɗa muku muddin na fara ba zan buɗe muku ba, amma ku ka yi kunne uwar shegu ku ka ƙi tafiya, shi ne yanzu kuma za ku ce na buɗe muku ƙofa, chab kuna ruwa wallahi". Shiru gaba ɗaya suka yi, yayin da suka ji cewa dama tun farko basu shiga ɗakin ba. Ƙarasa wa inda Zahra take Gimbiya Talatu ta yi tare da zama kusa da ita ta ce. "Zahra na san ke yarinyar kirki ce, kuma na san kina daraja manya sai dai idan manyan basu kama girman su ba kamar dai yadda muma bamu kama ta mu girman ba, a madadin kowa da ke nen, ni zan bada haƙuri bisa ga abinda muka aikata. Dan Allah kiyi haƙuri". Shiru Zahra ta yi tana mai sauke ajiyan zuciya ta ce. "Shi ke nen zan barku ku fita amma da sharaɗi". Washe baki gaba ɗaya suka yi jin cewa zata barsu su fita. Nan suka haɗa baki wajan faɗin. "Mene ne sharaɗin?". Murmushi Zahra ta yi kana ta gyara zamanta a kan gado sannan ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ce. "Na san da zarar na barku kun tafi za ku je ku sake wani ƙulla-ƙullan, hakan ya sa na ce da sharaɗi kafi ku tafi, sharaɗin shi ne". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan Fasma ta ce. "Ku biyun nan za ku wanke min banɗaki na wato toilet, ku gyara shi tsaff saiya fita. Sannan ke kuma". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan Samira ta ce. "Za ki gyara min ɗaki na har saiya fita fess. Bayan nan Samira da ke da Yusra za ku wanke min kayana gasu chan basu da yawa. Ku kuma su Gimbiyoyi masu faɗa a ji, za ku yi musu jagora kusa ido a kan abin da za su yi, bayan nan ku zo kuyi min tausa a ƙafafuwana naji suna min ciwo, yanzu kuje ku fara kafin nan ni zan ɗanyi baccin rabin lokaci ". Jin maganganunta suka yi tamkar saukar aradu, mamaki ma ya sa kowanensu ya kasa buɗe baki ya yi mata magana. A take ɓaccin rai da baƙin ciki ya ziyarci kowanensu. Dubanta Samira ta yi ta ce. "Har ke wace ce za ki saka mu muyi miki wanki, sharan ɗaki da kuma wankin toilet?". Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Dan ma kunci sa'a ban haɗa muku da panties ɗina ba, wato kenen har ni wace ce ko?, ita Mami da ku ke sata ta yi muku wanki shara ta wanke muku panties ba ta isa haifar ku ba?, har kuna da ma bakin magana?, to wallahi idan baku yi abinda na ce ba, ba zaku fita ba". "Wallahi ba za mu yi ba sai dai karki buɗe mana ƙofa". Cewar Gimbiya Saratu sannan ta ƙara da cewa. "Kina matsayin ƴar aiki za ki ce muyi miki wanki da shara, mu kuma mu zo muyi miki tausa ko?, ina tunanin kin sha giyan wake, wallahi sai dai mu dauwama a nan ɗin da na zuba ido naga yara na suna yiwa ƴar aiki shara da wanki". Murmushi Zahra ta yi sannan ta ce. "Toh shi ke nen mu zuba mu gani, kun san dai nafi ku taurin kai ko, to karku yi, ni kuma ban baku mamaki". Ta faɗa tare da kwanciya cikin ƙankanin lokaci baccin ɓarawo ya yi hawon gaba da ita. Takaici ne ya kama kowanensu ganin yadda Zahra ke bacci harda minshari hankalinta kwance. Baƙin ciki ne ya bi ya cunkushe guri ɗaya a zuciyoyin su yayin da suka ji kamar su sa pillow su danne ta har lahira. Aka suka cigaba da zama ba tare da wani a cikin su ya yi abin da Zahra ta ce ba. Ganin dai an fi hour ɗaya ana zaune gashi kuma Zahra ba ta da niyar buɗe musu ƙofa ya sa suka fara shawara a tsakanin su. Kallonsu Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Kun san me?". Amsa suka bata da cewa. "A'a. Gyara muryarta ta yi ta ce. "Kawai ku zo muje muyi abin da ta ce, ina ga hakan zai fi mana sauƙi ko". Yamutse fuska kowanensu ya yi a sa'inda Samira ta ce. "Aba Ammi wallahi ni gaskiya ba zan yi ba, ita ɗin fa ƴar aiki ce, kuma shi ne za ta zo ta saka mu wai muyi mata wanki shara da gyaran toilet, lallai ma". Girgiza kai Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Kunga ku zo mu rufa wa kanmu asiri muje muyi kafin ta tashi, kinga idan ta tashi bamu yi ba kuma ta ganmu a zaune za ta iya zuwa ta faɗa wa ƴan cikin masarautar nan cewa mun shigo ɗakinta". "Kunga ni ku tashi". Cewar Gimbiya Saratu. Miƙe wa kowanensu ya yi yayin da Fasma da Yusrah suka nufi toilet, Kai tsaye ba ɓata lokaci suka fara wanke wa. suna yi suna hawayen baƙin ciki, wai yau gasu suna wanke banɗakin ƴar aiki. Ɓangaren Samira ma kuwa, haka ta ɗauki tsintsiya ta fara share ɗakin yayin da baƙim ciki ya bi ya cunkushe guri guda a zuciyarta. Kukan da take haɗiye wa ne ya suɓuce mata. Take ta fashe da kuka, tana mai yi wa Zahra Allah ya isa. Haka ta cigaba da share wa ba tare da taso hakan ba. Su kuwa gimbiyoyi kamar yadda Zahra ta faɗa haka suka fara yi wa Zahra Tausa. Yayin da suke ji kamar su hallaka ta saboda takaici. Bayan sun gama ne Samira da Yusrah suka kwashe kayan Zahra wanda basu da wani yawa, suka shiga da shi toilet suka sa a bokiti tare da balbala omo suka fara wanke wa. Haka su cigaba wanke wa suna kuka da hawaye. Karo na farko a rayuwarsu da suka fara yin wanki. Bayan sun gama ne suka shanya su a igiyar toilet ɗin. Zama suka yi suna mai sauke ajiyan zuciya dan gaba ɗaya su ba ƙaramin gajiya suka yi ba. Dai-dai lokacin Zahra ta farka daga bacci. Ganin ta farka ya sa gaba ɗaya suka washe baki suna mai faɗin. "Mun gama komai da komai Hajiya Zahra, yanzu dai a bamu maƙullin mu fita". Sosa ƙeyar ta Zahra ta yi tare da miƙe wa tsaye ta ce. "Saina ga aikin ku sosai, in dai na ga akwai wani kuskure to sai kun sake shi daga farko". Ta faɗa tana mai girgiza kai duban ɗakin gaba ɗaya ta yi sannan ta ce. "Wai ke Samira sharar ma baki iya ba?, ya za ki yi to idan ki ka je gidan mijin ki?. To ni fa sharar nan ba ta yi ba dole ki sake wata gaskiya". Samira ji ta yi kamar ta shaƙe Zahra ta mutu kowa ma ya huta. Shiga banɗakin Zahra ta yi ta girgiza kai sannan ta maida kallonta kan wankin da su Samira suka yi ta ce. "Ya salam!, wannan wane irin wanki ne?, sai ka ce wasan yara?, idan ku ka sa Mami wanki haka take wanke muku kaya a jagwalgwale?, to fa baku isa ba sai kun sake wanke kayan nan". Fashe wa gaba ɗaya suka yi da kuka suna mai nadamar shigowa ɗakin Zahra. Kuka suka cigaba da rusa wa kamar yara suna mai faɗin. "Wannan wace iriyar masifa da bala'i ce?, dama mun sani bamu shigo wannan ɗakin ba, dan Allah kiyi haƙuri ki rabu da mu haka, wallahi ba zamu sake ba, mun tuba mun koma ga Allah, a iya hakan ma ai kin koya mana hankali, dan Allah ki buɗe". Duk abin da ke faruwa a kunnen Sooraj wanda ke tsaye a bakin ƙofa har izuwa wannan lokaci. Furzar da iska Zahra ta yi waje ta ce. "Zan barku ku tafi ne kawai saboda kun haɗa ni da Allah, amma da ba dan haka ba da saikun sake duk abinda ku ka yi". Kallonta suka yi a gajiye suka ce. "Mun gode Aunty Zahra". Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Tohh!, yau an kira ni da sunaye kala-kala, wai yau ni na zama Aunty Zahra, harda su Hajiya Zahra, kwa ji da shi chan ta matse muku". Ta faɗa tana mai nufar hanyar waje domin ta buɗe ƙofan. Ganin hakan ya sa suka tawo a guje. Tsayawa Zahra ta yi tana mai kallonsu ta ce. "Kada ku fusata ni fa na fasa buɗe ɗakin". Da sauri kowanensu ya ja da baya. Ƙarasawa bakin ƙofan ta yi kana ta saka maƙullin a jiki sannan ta buɗe musu ƙofan. Take suka haɗa ido da Sooraj wanda ke tsaye ƙeƙam ya harɗe hannuwansa a ƙirji. Da sauri su Gimbiya Saratu suka zo fita. Nan suka ci karo da Sooraj. Kallonsu Sooraj ya yi yana mai yi musu kallon ƙurilla. Ya ce. "Mene ne wannan yarinyar ta aikata muku?". Shiru kowanensu ya yi yayin da suka ji kunyar furta cewa Zahra ta sa su aiki. Washe haƙora Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Bakomai kawai dai muna ciki muna hira ne, gaskiya Zahra yarinyar kirki ce, domin ta yi mana tarba mai kyau". Ta faɗa suna mai kallon junansu. Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ya naga jikin kowannenku ya yi datti?". Murmushi Samira ta yi ta ce. "Yahya fa bakomai wasa kawai fa muka yi, kasan muɗin ne har yanzu muna ji da yarinta". Ganin hankalin shi ya karkata izuwa kan Zahra ya sa su saurin barin wajan. Ƙarasawa inda Zahra ke tsaye Sooraj ya yi, yayin da yaje daff da ita har numfashin kowanensu na bugan na wani. Take ta ga fuskarsa ta chanza izuwa maƙurar ɓaccin rai. Da sauri Zahra ta ja da baya, ganin cewa zai iya aikata mata komai ya sa ta juya da zimmar shige wa ciki. Da sauri ya janyo hannunta. Take ta faɗa kan ƙirjinsa. Saurin ɗaga ta yi daga jikinsa sannan ya kwashe ta da lafiyayyun maruka har guda biyu. Dafe ƙuncinta Zahra ta yi yayin da idanunta suka kaɗa suka yi ja. Shigar da ita yayi ɗakin nata sannan ya shaƙe mata wuya cikin lion voice ɗin sa ya ce. "Wato abinda ki ka yi mana na abinci ma bai ishe ki ba, sai kin ja su ɗakin ki kin sa su abin da basu yi niya ba ko, to wallahi a yau zan koya miki hankali, harma na sa a kira ki, kice min ba za ki zo ba, lallai na yarda wuyanki ya isa yanka, na niyar rabuwa da ke amma ganin abin da ki ka aikata wa ƴan uwana da gimbiyoyi ya sa saina huƙunta ki". Ya faɗa yana mai ƙara shaƙe wa Zahra wuya. Kakari Zahra ta fara yi, da sauri ta cire hannunsa daga wuyanta. Tari ta fara yi. Kallonsa ta yi ta ce. "Me ya sa za ka tambaye ni?, kafin ka tambaye ni kaje ka fara tambayar su mene ne suka zo aikata min, zuwa suka yi suka ce za su dake ni, kenen ni naje na same su na jawo su nan?, nayi ƙoƙarin ganar da su cewa suyi wa kansu faɗa su koma amma suka yi kunnen uwar shegu suka ƙi tafiya, kenen sai kace laifi na ne?". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Me ya sa to za ki saka su wanki shara harda wankin toilet sannan ki sa su Gimbiya Saratu suyi miki tausa bayan kuma ke ƴar aiki ce. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Su da ma ba iyayenka ba kaji haushin abinda nayi musu, kai ka san abinda su biyar ɗin nan suke aikata wa Mami da baka nan?, haka za su saka ta shara da aiki susa ta wanki". Ɗago da idanuwansa Sooraj ya yi wanda suka kaɗa suka yi jajir ya ce. "Mahaifiyar tawa suke yi wa hakan?, me ya sa ki ka barsu suka fita?". Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Saboda sun roƙe ni ne shi ya sa". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Tabbas yau sai sun ɗanɗana kuɗarsu". Ya faɗa yana mai fice wa daga cikin ɗakin Zahra. Ganin hakan ya sa Zahra ta yi saurin bin bayansa". ********************* Amrah kuwa kidnapper's ɗin da suka sace ta basu nufi ko ina da ita ba sai wani ƙatoton gidan kango wanda ke tsakiyar jeji. Chan na hango ta an ɗaɗɗaure ta da igiya. Ƙoƙarin kunce kanta take amma hakan ya cutura. Kallonsu ta yi da rinannun idanuwanta cikin ƙaramin muryarta ta ce. "Ku kunce ni". Ta faɗa cikin jin raɗaɗi. Ɗaya daga cikin su ne ya kira gov. Musa yana mai zayyane masa cewa aiki ya kammala. Murmushi gov. Musa ya yi ya ce. "Ku wuce da ita Lagos idan ya so daga nan sai a wuce da ita ƙasar waje". Godiya ɗaya daga cikin kidnapper's ɗin ya yi. Sannan ya kashe wayar. Sakawa ya yi haka kunce. Miƙe wa tsaye Amrah ta yi tana mai kalle-kalle ta ce. "Ina ne nan wajan?, me ya sa ku ka kawo ni nan?, su waye ku?". Tambayoyin da ta shiga yi musu kenan. Shiru kowanensu ya yi mata ba tare da ya sanar da ita komai ba. Basu yi aune ba suka ji tsayuwar mota a wajan. Da sauri gaba ɗaya suka juya. Umar ne tare da su Ramlat suna mai nufo wa wajan. Murmushi su kidnapper's ɗin suka yi. Take gaba ɗaya suka sara masa. Ƙarasowa wajan Umar ya yi yana mai sakin murmushi ya ce. "Nice job guy's". Ya faɗa yana mai maida kallonsa kan Amrah. Su Ramlat kuwa da sauri suka nufi kan Amrah tare da rungume ta suna mai fashe wa da kuka. Kallon jami'an nasa Umar ya yi ya ce. "Kun gano wane ne ya sa aka sace Amrah?". Shiru jami'an suka yi yayin da ɗaya daga cikin su ya ce. "A'a yallaɓai". Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Ƙarya ne, kada ku ji tsoro, kawai ku gaya min gaskiya". Cire jikinta Amrah ta yi daga na su Ramlat sannan ta nufi inda Umar yake ta ce. "Me ya sa ka zo nan?, me ya sa ka saka aka sace ni?". Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya ce. "Amrah zan yi miki bayani daga baya, yanzu bamu da wannan lokacin". Girgiza kai Amrah ta yi ta ce. "A'a ni yanzu za ka faɗa min". Shiru Umar ya yi na ɗan wasu lokaci sannan daga bisani ya ce. "Na sa an sace ki ne saboda na gano cewar akwai wani wanda ke ƙoƙarin ya sace ki, tun a gidan zoo na fahimci hakan, hakan ya sa na sa jami'ai na suka bibiyi bayan wanda suka zo gidan zoo, a nan muka kama ɗaya daga cikin su ya faɗa mana cewa wani ne ya ce su sace ki amma kuma basu faɗa mana ko wane ne ba, jin hakan ya sa a ranar da kika zubar da abinci na mare ki saboda kiji aushi ki fita idan ya so su kuma jami'ai na su sace ki domin ki kasance cikin tsaro. Amma ina mai baki haƙuri bisa ga marin da nayi miki kinji". Shiru Amrah ta yi dan ita ba ta wani fahimce shi ba sosai. Waige-waige ta fara yi. Chan ta hango manya manyan bishiyu masu ɗaukar ido. Washe baki ta yi tare da sakin murmushi da sauri ta nufi inda bishiyun suke ta fara ɗane su tamkar ƴar biri, aka ta fara aye wa kan bishiyu ɗaya bayan ɗaya tana mai yin tsalle a kansu. Gaba ɗaya babu abin da suke faman yi in banda binta da idanuwa. Juyawa Umar ya yi ya maida kallonsa kan ɗaya daga cikin jami'ansa ya ce. "Ku gaya min wane ne wanda ya sa a sace Amrah, kada ka damu kawai faɗa min". Kallonsa jami'in ya yi ya ce. "Maganar gaskiya ainiyin wanda ya sa a sace Amrah shi ne mahaifin ka wato Gov. Musa Muhammad, mun gano shi ɗin yana aikata miyagun laifuka, yana safaran mata tare da shigo da ƙwayoyi ba tare da izinin kowa ba, am sorry to say sir but your Father is a big terrorist kuma bai cancanci zama Govnor ba". Jin maganganun jami'in Umar ya yi tamkar saukar aradu. "Mahaifi na, safaran miyagun kwayoyi da kuma mata!". ya faɗa yana mai cigaba da nanata maganar. "I can't believe this, ni fa jami'i ne, ban yarda Baba na zai aikata hakan ba". "Gaskiya nake faɗa maka yallaɓai, amma idan baka yarda ba shi ke nen". Cewar jami'in. Nan take ran Umar ya ɓaci yayin da yaji tsanar mahaifin na shi ya shiga cikin ranshi. Duban kowanensu ya yi ya ce. "Ku kulan mun da su zanje Kano yanzu wajan mahaifi na, sannan na kama da na damƙa sa wajan ƴan sanda". Ya faɗa yana mai barin wajan kai tsaye inda motar sa take ya nufa tare da tada motan sannan ya bar harabar wajan. ******************* *JIGAWA* Shiga cikin dajin Aliyu ya yi yana mai faka motarsa. Fitowa ya yi daga cikin motan. Chan ya hango Safira zaune kan dutse gaba ɗaya idanuwanta sun kumbura saboda kuka. Ƙarasa wa inda take ya yi. Ganin Aliyu ya sa Safira saurin miƙe wa tsaye tana mai ja da baya ta ce. "Don't you dare!, karka kuskure ka zo inda nake. Nayi maka kallon mutumin kirki, ashe kai ɗin mugu ne, mena yi maka da zaka sa a sace ni?, wai kuma a hakan ni za ka aura?, i have never knew that you are a criminal until now. Na tsane ka Aliyu, wallahi ba zan yafe maka ba, idan kashe ni zaku yi kada ku mata lokaci wajan zaryar da hakan kawai ku aiwatar da abinda ku ke da niyar yi". Shiru kawai Aliyu ya yi ba tare da ya ce da ita ƙala ba. ******** *KANO* "Wallahi Gimbiya ba zamu rabu da ita haka ba, dole mu koya mata hankali har ita ta kai ta saka mu wanki muyi". Cewar Gimbiya Saratu. Shiru kawai Gimbiya Talatu ta yi ta ce. "Ni dai ina ganin kamar mu rabu da wannan yarinyar, dan gaskiya idan muka ce zamu biye mata mune zamu cigaba da jin kunya sannan mu cigaba da shan wahala, yarinyar tamkar mai aljanu duk abinda muke yi mata gaba ɗaya yana tashi a banza ne. Ni dai gaskiya na zubar da makamai na". Tashi tsaye Samira ta yi ta ce. "Wallahi ba zamu zubda makaman mu ba, kenen mu barta taci banza?, sai na ganar da ita cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne, idan ta san wata ba ta san wata ba". Suna cikin haka suka ji an banƙo ƙofar part ɗin su. Da sauri gaba ɗaya suka miƙe tsaye. Sooraj da Zahra suka gani a tsaye a yayin da hannun Sooraj ke riƙe da ballet. Dubansu ya yi ya ce. "Idan kin san kin taɓa sa Mami na aiki ki matso nan wajan kafin na ƙaraso da kaina". Nan take cikin kowanensu ya ɗuri ruwa, kallon juna suka yi cikin tashin hankali. Da sauri gaba ɗaya suka ja da baya. Saurin shan gabansa Zahra ta yi sannan ta saki murmushi ta ce. "Kai baka san wasa ba, babu abinda suka yi wa Mami kaji, kawai dai na faɗi hakan ne saboda na kare kaina, ka tafi kawai". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Wato raina min hankali ki ke so kiyi ko?, za ki gane kuranki". Ya faɗa yana mai damƙe hannun Zahra sannan ya fitar da ita daga cikin wajan. Suna fita gaba ɗaya suka shiga sauke ajiyan zuciya. Yayin da suka yi mamakin yadda Zahra ta rufa musu asiri. Sooraj bai nufi ko ina da Zahra ba sai part ɗin sa. Wani irin daddaɗar ƙamshi ne ya bugi hancin ta. "Wow!". Zahra ta furta ganin yadda part ɗin Sooraj ya yi maƙurar haɗuwa, gaba ɗaya ko ina a tsaftace gaba ɗaya abubuwan da ke ciki Royals ne. Wurgar da ita ya yi ta faɗi a ƙasa. Miƙe wa tsaye Zahra ta yi ta ce. "Malam ya dai?, mena yi maka, ka kiyaye ni fa, ka san dai ni ba sa'ar ka bace ba, ka san ni ɗin ƴar ina ce?, to ni ɗin ƴar gidan yari ce, kuma wallahi kayi min wani shirme, zan danne ka nayi maka tsinannen duka". Ta faɗa a tsorace dan ita kanta ta san ba zata iya ba, domin tana matuƙar tsoron Sooraj sai dai bata taɓa nuna masa hakan. Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Wato ni za ki yi wa tsinannen duka ba?" .ya faɗa yana mai ɗaukar ballet ɗin sa. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce tare da ja da baya ta ce. "Lahaula!, ni asuwa kare da gudun layya, aba yahya Sooraj kana ƙamshi muna binka da umrah, afuwa ɗan sarki mai jiran gado, ka san ba zamu yi hakan da kai ba". Sooraj bai san sanda murmushi ya suɓuce masa ba. Da sauri ya haɗe ransa sannan ya dube ta ya ce. "Dama ina son kiyi min wani ɗan ƙaramin taimako ne". Kallonsa Zahra ta yi cike da mamaki ta ce. "Taimako kuma daga wajen nawa?". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Ke dalla bana son shirme, shadda nake son na siya kuma an tura min hotunan su, to bana son naje na zaɓi ishirinka ne saboda ban san yadda yake ba, genzna nake so. Kuma bana gane yanayin su, dan ni ban cika siya ba gaskiya, shi ne za ki zaɓar min genzna ba ishirinka ba, na san ku talakawa za ku gane bambancin sosai. Saboda ina son naje wani guri mai mahimmanci ne". Girgiza kai Zahra ta yi. "Lallai ma wannan Sooraj ɗin, wato talakawa ko, za ka gane kuranka, harda cewa wai wani guri zai je ina ga ma wajan budurwa zai je". Ta faɗa cikin ranta sannan daga bisani ta ce. "Kai yanzu kana namiji baka san yadin ishirinka ba da na genzna, an dai ji kunya, to shi ke nen nuna min hotunan shaddodin". Ɗaukar system ɗin sa Sooraj ya yi yana mai nuna mata shaddodin. Duba wa Zahra ta fara yi ɗaya bayan ɗaya. Take idanuwanta ya sauka a kan yadin ishirinka murmushin ta saki sannan ta ce. "Yauwa ga genzna nan gata blue sai sheƙi take za ka yi kyau a ciki sosai". Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Kin tabbata dai ba ishirinka ba ne ba ko?". Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Zan yi maka ƙarya ne, gashi nan kana gani genzna ce fa". "Tom shi ke nen naji". Ya faɗa tare da tura hoton yadin izuwa ga toilor ɗin sa sannan ya ce ya nemo masa irin wannan yadin. Sosai mamaki ya kama toilor ganin Yarima guda zai saka ishirinka. Kamar yadda Sooraj ya faɗa haka toilor ɗin sa ya sa aka nemo irinsa sannan ya ɗinka masa a ranar. Zahra kuwa tashi ta yi ta bar masa part ɗin sa tana mai dariya. Yayin da ta ƙosa ta ga yarima cikin ishirinka ta yadda za ta tsokane shi. *********** "Safira zan yi miki bayani daga baya, koda na gaya miki gaskiya ba za ki fahimta ba". Ya faɗa yana mai barin wajan. ************* "Tun jiya fa nake kiran number Safira baya shiga, gaskiya ina cikin damuwa, ina tunanin wani abu na shirin faruwa da ƴata". Cewar Mom. Kallonta Grandpa ya yi ya ce. "Babu abin da zai faru da Safira sai alkhairy, kada ki damu zamu je office ɗin ƴan sanda tunda shima Aliyu ɗan sanda ne zai taimaka mana wajan neman inda Safira take, in sha Allahu ma tana cikin ƙoshin lafiya". Da tunanin Safira gaba ɗaya suka kwanta. ***************** *Sooraj pov*. Da sassafe ya shirya tsaff cikin ishirinkan sa ba tare da ya san cewa ba genzna Zahra ta zaɓar masa ba. Fesa turare ya yi tare da kallon kansa cikin madubi. Sannan ya taje summar kansa. Bayan ya kammala ya ɗauki maƙullin motarsa ya fita. Tun daga takunsa har izuwa suturar jikinsa abun kallo ne. Gaba ɗaya ƴan aiki tare da fadawa suka bisa da kallo ganin karo na farko Yarima ya saka yadi, kuma yadin ma na ishirinka. Ganin suna binsa da kallo ya sa shi ya yi tunanin cewa ko genznar sace ta yi musu kyau. Shiga cikin mota ya yi tare da tada mota sannan ya bar harabar gidan. Tun yana kan hanyar tafiyar sa Sooraj yake ta tantama a kan kayan da ya sa. Amma hakan bai sa ya chanza ƙudirin sa na zuwa inda yake son zuwa ba. Wata zuciyar ce ta ce masa ya tsaya da tafiya ya gwada fita. Hakan ya yi, parking ya yi sannan ya fito daga cikin motan. Nan take ya fara jin jama'a na cewa "Dama Yarima yana saka ishirinka?". Nan take ransa ya yi mugun ɓaci. "Kenen dai wannan banzar yarinyar ishirinka ta je ta zaɓar min ba genzna ba, lallai yau saina koya mata hankali". Ya faɗa yana mai shiga cikin mota sannan ya tada motan ya juya ya koma gida. Da mugun gudu yake jan motan a kan titi har ya isa izuwa fada. Ko parking bai yi ba sosai ya fito ya nufi cikin gida. Chan ya hango Zahra zaune kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Daga nesa ta hango Sooraj, da sauri ta miƙe tsaye, ganin yadda yadin yake ƙyalle ido sai maiƙo yake ya sa ta nufar in da yake sannan ta saka hannu ta taɓa ishirinkan. Nan take ta bushe da dariya. Tana mai faɗin. "Daga nesa kamar genzna, saina matso na ga shadda ce, da na taɓa naji shegen ne, ashe ishirinka maraya ne". Ta ƙarashe maganar tana mai kwashe wa da wata dariyar. Baƙin ciki da takaici ne suka bi suka cunkushe cikin zuciyar Sooraj. Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Kenen kina sane ki ka zaɓar min yadin ishirinka a maimakon genzna?". Sosa ƙeya Zahra ta yi ta ce. "Kaine fa kace mu talakawa ne dama muke iya gane ishirinka kuma kace genzna ka ke so, kuma ni duk na duba genzna babu wacce ta fi kyau sai wannan ishirinkan, shi ya sa na zaɓar maka ita, kai baka ga yadda kayi kyau a cikin wannan yadin ba, yadda ka san wani basarake". Baƙin ciki ya ana Sooraj ya furta komai, illa girgiza kai da ya yi sannan ya aura sama domin chanzo wani kayan. Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Yaran masu kuɗin nan basu san komai ba, uhmm ai ishirinka maraya duniya ne. Na san zuwa zai yi ya saka wani kayan, ai wallahi ba zan bari ya fita daga gidan nan ba, duk kayan da zai je ya saka saina kushe su gaba ɗaya". Ɓangaren Sooraj kuwa, shiga ɗakin sa ya yi ya cire yadin ishirinkan ya watsar da su gefe. Sannan ya saka ƙananun kaya t-shirt da trouser white colour tare da facing cap sannan ya fito daga cikin ɗakin. Kai tsaye downstairs ya nufa. Zahra na hango shi ta miƙe tsaye tana mai hangame baki ta ce. "To wannan kuma wane irin shiga ce kamar ɗan gudun hijira, ka wani ɗamɓara hula sai kace ɗan vigilante. Ko kyau ma baka yi ba, yadda ka san kamar wani ɗan almajiri". Ta faɗa tana mai bushe wa da dariya. Baƙin ciki Sooraj yaji ya cika zuciyarsa. Koma ya yi cikin ɗakinsa. Haka yana ji yana gani, ba yacce ya iya sai illa ya ɗauki jallabiya ya zumbula". Fitowa ya yi inda Zahra take domin yaji ko zata sake kushe kayan. Sai ya ji ta ce. "Yauwa ko kaifa, yanzu ka fito a musulmi, amma ka wani saka matsantsun kaya sai kace wanda zai je ya burge mata". LIKE, COMMENTS AND SHARE FISABILILLAHI 🙏🌹🌺💗 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (ZINARIYAR JAJIRTATTU) [11/30, 12:58] null: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 4️⃣9️⃣▶️5️⃣0️⃣ *___________________________________________* Girgiza kai Sooraj ya yi tare da zama kan Three seater yana mai fuskantar Zahra ya ce. "Me ya sa bakya jin tsoro na Zahra?". Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Hakan me zan dinga jin tsoron ka kaida ba maye ba, aini babu wanda nake tsoro sai Ubangiji na". Shiru Sooraj ya yi ya ce. "Kin san ina zanje ne kika zaɓar min Ishirinka a maimakon genzna?". Taɓe baki Zahra ta yi ta ce. "Ina za ka je kuwa in banda wajan ƴan matan ka, dan yadda na ga ranka ya yi mugun ɓacin nan nasan cewa akwai wata a ƙasa. Koma dai mene ne, ni ban ana ka zuwa wajanta ba zaka iya tashi ka tafi". Girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Samm ni bana da ƴan mata balle budurwa, zanje wajan mahaifiyata ne". Jin maganar sa ya sa Zahra shiga cikin ruɗani. Dubansa ta yi ta ce. "Wace mahaifiyar kuma bayan Mami?". Amsa ya bata da cewa. "Ƙwarai Mami ita ce asalin mahaifiyata, kuma ita ma waccan tamkar mahaifiyata na ɗauke ta, yanzu haka na san tana asibiti tana jira na". Shiru Zahra ta yi ta ce. "To ita bata ɗa ko ƴa ne?". Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "Zomu je chan zan baki amsa". Ya faɗa yana mai miƙe wa tsaye tare da fice wa daga gidan. Babu gardama ta bisa a baya. Motar da ta ga ya shiga ta shiga, a sa'inda ya tada mota tare da fita da su daga cikin masarautar, kai tsaye asibitin da Mrs Laila take suka nufa. ************ Umar kuwa hawanni ƙalilan ne ya ɗauke shi ya isa Jigawa kai tsaye gidan su ya nufa, bai gama parking ba ya fito daga cikin mota tare da shiga cikin babban parlour. Nan ya tarar da mahaifin shi zaune kan kujera yana shan juice. Furzar da iska mai zafi Umar ya yi waje sannan ya dubi mahaifin na shi ya ce. "Abba". Sai a lokacin Gov. Musa ya lura da zuwan Umar wajan. Saurin miƙe wa tsaye ya yi sannan ya ce. "Son yaushe ka shigo?, ina su Khairiya suke?". "Abba ban taɓa tunanin zaka iya aikata abinda aka faɗa min saboda kuɗi ba". Umar ya faɗa a yayin da idanuwansa suka yi ja tamkar an zuba garwashi. Rass! Gaban Gov. Musa ya faɗi. Cikin ransa ya ce. "Kodai Umar ya gano munanan hayyukana ne?". Kallon Umar ya yi ya ce masa. "Umar ban fahimci inda ka dosa ba, me kake nufi da hakan?, ka fahimtar da ni". Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Really?, wato baka san me nake nufi ba, wai tukun nama shin kai mahaifi na ne ko maƙiyi na?, me ya sa za ka sa a sace Amrah?, wato kenen aikin ka shi ne safaran mata ko. Karka manta ni jami'i ne mai gaskiya, kuma duk wanda yake yin laifi burina shi ne a hukunta shi, koda kuwa ƙanne na ne balle kuma kai. Ba zan yi duba da cewa ko kai mahaifi na ba ne, dole na miƙa ka domin a hukunta ka". Koma wa gov. Musa ya yi kan kujerar da ya tashi tare da zama yana mai fuskantar Umar ya ce . "Wato harma wani zai zo ya faɗa maka mummunar magana a kaina kuma ka yarda?, banyi tunanin hakan daga gare ka ba, kai ɗin ɗana ne mafi soyuwa s gare ni, ni ne nan na ɗora ka a matsayin da ka ke a halin yanzu". "A'a, samm ba kai ba ne ba, jajircewa ta da kuma ƙwazo na ne ya kaini wannan matsayin ba kai ba, ka faɗa min gaskiya shin kana aikata abinda ake tuhumar ka da shi?". Cewar Umar. Shiru Gov. Musa ya yi na ɗan wasu lokaci kana daga bisani ya ce. "Kenen dai baka yarda da ni ba?, well shi ke nen, tunda yanzu babu yarda tsakanin mahaifi da ɗa me ya rage, kawai ka zo ka saka min handcuf ka kaini kotu a yanke min hukunci. Ba aka ka ke so kaji na ce ba. So ka ke na faɗi abinda banyi ba na ce nayi". Girgiza kai Umar ya yi sannan ya ce. "Shi ke nan Abba, bama sai ka faɗa min ba, ni da kaina zan gano. Kuma ka sani cewa muddin da gaske ne abinda aka faɗa a kanka ba zan bari ka tsira ba, domin saina sa an yanke maka hukuncin da zaka gwammace baka haife ni ba, dole a bi wa mtane haƙƙin su domin suma mutane ne kamar kowa, kuma suma suna da madu sonsu bawai babu. Kuma ka sani cewa muddin wani abu ya sami Amrah, ba zan rabu da kai ba". Ya ƙarashe maganar tare da fice wa daga cikin parlourn. Murmushin mugunta Gov. Musa ya yi ya ce. "Umar kenen, ba zaka taɓa samu wata hujja a kaina ba". ********************* "Safira ina son ki bani haɗin kai, bana son kiyi min gardama, maza yanzu ki biyo ni". Aliyu ya faɗa yana mai kallon Safira. Banzan kallo Safira ta watsa masa sannan ta ce. "Idan kai ka isa da ni to ka sa na bika" Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke ya ce. "Okay tom idan baki je ta lallami ba za ki je ta dole". Ya faɗa tare da jan hannunta. Wafce hannunta daga nasa Safira ke shirin yi amman akan ya cutura. Nan take ta fashe da kuka tana mai dukan bayansa tare da cizon hannunsa, amma hakan bai sa ya sake ta ba. Jefa ta ya yi a cikin mota sannan ya ɗaure ta a jikin mota kana ya tada mota ya bar wajan. ***************** Parking Sooraj ya yi tare da fitowa daga cikin mota. Nan ita ma Zahra ta fito daga cikin motan. Yayin da ta fara bin asibitin da kallo. "Kamar na taɓa zama a asibitin nan". Zahra ta faɗa cikin ranta. Zaro idanuwa waje Zahra ta yi sakamakon riƙe mata hannu da Sooraj ya yi. Nan take ta ji gabanta ya tsananta faɗuwa. Murmushi Sooraj ya saki kana suka shiga daga ciki. Nan likitocin asibitin suka shiga kwasar gaisuwa. Kai tsaye inda ɗakin Mrs Laila yake suka je. Tare da shiga ciki. Nan take Zahra ta haɗa ido da Mrs Laila. Take gabanta ya ƙara faduwa ƙarasa wa ciki ta yi tare da bin Mrs Laila da kallo. Gaishe ta Zahra ta yi ta amsa yayin da suka shiga kallon juna. Zahra kuwa tunani take a ina ta taɓa ganin matar nan. Sai a wannan lokaci ta tuna cewa tabbas a wannan asibitin ta taɓa ganin ta. Kallon Zahra Sooraj ya yi ganin yadda ta nutsu ya sa shi sakin murmushi sannan ya ce. "Zahra kenen, to wannan ita ce mahaifiyar tawa da nake baki labari". Shiru Zahra ta yi sannan daga baya ta ce. "Ina asali ƴarki ko ɗanki yake?". Ta faɗa tana mai kallon mrs Laila . Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Ni ba wai ƴa ɗaya gare ni ba, yara uku ne, amma sai dai na rabu da su saboda na ceci rayuwarsu da tawa. A halin yanzu dai ban san ko suna raye ko sun mutu ba, amma ni yanzu fata na shi ne na gansu ko a karo na biyu ne kafin na bar duniyar nan ". "Amma shin baki bawa kowa riƙo ba?". Cewar Zahra. Amsa mrs Laila ta bata da cewa. "Mutane biyu na bawa riko, ɗaya kuma na ajiye ta a daji sakamakon lokacin ƴan sanda suna ta bibiyata, ban samu na tafi da ita ba, amma na saka mata suna Amrah, sannan ɗuk ƴaƴan nawa uku suna matuƙar kama da juna, sai dai kowanne da irin kalar ƙwayar idanuwansa. Amma kinga maƙiya na duk sun sa na rabu da su, duk dan saboda abin duniya ". Ta ƙarashe maganar hawaye na sauka kan ƙuncinta. Tausayin matar ne ya kama Zahra. Sai a lokacin ita ma ta tuna da cewa bata da uwa. Share wa Mrs Laila hawayenta ta yi sannan ta ce. "Kinga kamar yadda kika rasa ƴaƴan ki, aka nima bani da uwa, ban sani ba ko ta mutu ko kuma tafiya ta yi ta barni, amma a kullum a jikina sai ina jin cewa wata rana zan ganta. Ina son ki ɗauke ni a matsayin ƴar da ki ka haifa dan Allah". Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Shi ke nen ƴata". Ta faɗa tana mai rungume Zahra jikinta. Lokaci ɗaya zuciyar ta ya buga da ƙarfi. Kallon su Sooraj ya yi tare da taɓe baki sannan ya ce. "Ni kuma shi ne aka ware ni a gefe ko?, yanzu Mama shi ne kika share ni ko?". Murmushi Mrs Laila ta yi ta ce. "Aba my son, to kaima tawo nan kaji ɗan Mommy". Murmushi Sooraj ya yi ya ce. "A'a ba saina zo ba". Saida suka taɓa hira kafin daga nan suka shirya domin su tafi. Tashi tsaye Zahra ta yi sannan ta dubi Mrs Laila ta ce. "Tunda yanzu ke mamata ce, zan taimaka miki wajan neman sauran ƴaƴanki saboda nima yanzu ƴan uwa na ne". Ta faɗa tana mai fice wa daga ɗakin. Kallon Mrs Laila Sooraj ya yi ya ce. "To mu dai zamu tafi, karki damu an kusan sallamar ki daga cikin wannan asibitin, sannan kuma zan cigaba da neman yaranki har sai inda ƙarfi na ya ƙare". Yana kaiwa nan ya fita daga cikin ɗakin. Nan ya tarar da Zahra a gefen motarsa ta tsaya tana share hawaye". Mamaki ne ya kama Sooraj ganin karo na farko ya ga Zahra na hawaye. Dubanta ya yi ya ce. "Dama akwai abinda zai iya saki kuka ban sani ba?". Share hawayenta Zahra ta yi ta ce. "Yahya Sooraj ka yafe min, na san na ɗan wahalar da kai kaɗan a gidan ku, amma yanzu na chanza in sha Allahu zan daina tsiwa sannan zan kasance mai haƙuri a kome za'a yi min, kaji idan ma hukunta ni za ka yi a kan rashin kunyar da na dinga yi maka zaka iya ɗauka". Harara Sooraj ya yi mata ya ce. "Na yafe miki, amma ni na san ba za ki chanza ba, ko duka jikina ƙunne ne ba zan yarda za ki iya chanza wa ba". "Ka yarda da ni yanzu na chanza, baka gani ba ina kuka ɗazu, ina dana sani ne, idan muka koma gida ma zan je na bawa su Gimbiya Saratu haƙuri, ni yanzu na chanza kuma chanza wa na har aba........ Maganarta ya tsaya chak sakamakon taka ta da wata matashiyar budurwa ta yi. Nan take Zahra ta zaro idanuwa waje tare da fara kutuntuma ashar. "Kutumeli chan, idan na yarda shegiya nake, har ni zata wuce ta taka kuma taƙi bani haƙuri saboda shegiya ce, zata gane kuranta ". Ta faɗa tare da ƙoƙarin bin bayan budurwar. Da sauri Sooraj ya dakatar da ita sannan ya ce. "Yanzu fa ki ka ce min za ki chanza, amma kuma kinga abinda ki ke yi". Girgiza kai Zahra ta yi jikinta na tsuma ta ce. "Na san na faɗi akan. Amma ka bari na fara koya mata hankali kafin nan saina chanza". Ta faɗa tare da nufar hanyar da budurwar ta yi. Dafe kansa Sooraj ya yi ya ce. "Wallahi Wannan yarinyar duk wanda ya aure ta zaiga bala'i, domin wannan annoba ce". Ya faɗa tare da bin bayanta. Ƙara sauri Zahra ta yi yayin da kafafuwanta na harɗe wa dana juna saboda tsananin sauri da kuma bala'in da take. Ganin budurwar na ƙoƙarin shiga mota ya sanya ta fara gudu harta isa inda budurwar take. "Ke!". Zahra ta daka mata tsawa. A razane budurwar ta ɗago idanunta tare da duban Zahra ta ce. "Who are you?, me ki ke nema, kinga kiyi tafiyar ki bani da chanjin da zan baki, dan haka ku baratan nan ku ke da zarar kun ga mai kuɗi ku ke kiɗime wa". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Yau akwai ƙura, wato ni ce mabaraciya ko?, kin taka ni kin wuce shi ne ko ki iya bani haƙuri". Kallon sama da ƙasa budurwar ta bi Zahra da shi sannan ta ce. "Ai na san na taka ki, kuma ina sane nayi hakan, dan aka ki ɓace min daga gani". Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Idan kinga kin bar wajan nan to bani bace. Kalle ni nan wallahi ni bana ɗaukar raini, kina wani tafiya kamar wata lanƙwasashiyar sanda. Ke daɗin abun ma baki da wani kyau balle kiyi wa mutane iyayi, kalli fa fuskarki yadda ka san wata akuya wacce ta yi shekara ta jin yunwa, ga kunnuwa fala-fala, kamar gwargwaron amarya, kin buɗe ƙwaƙwidon kanki a waje ko gashin ma babu yadda ka san gashin hammatar ɗan iska, kina wani fallewa kamar injin markaɗe. To wallahi ki sani cewa muddin baki bani haƙuri ba saina ci ubanda ya yi tattalin goron auren bikin uwar... Da sauri Sooraj ya rufe mata baki. Wafce jikinta Zahra ta yi daga nasa sannan ta ce. "Me ya sa za ka dakatar da ni". Maida kallonsa Sooraj ya yi kan budurwar ya ce. "Zubaida kada ki damu da abinda ta faɗa miki kiyi haƙuri kiyi tafiyarki ". Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Daman ka san wannan mahaukaciyar?". Amsa Sooraj ya ba ta da cewa. "Ba mahaukaciya ba ce ita ɗin wacce zan aura ce". Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai cewa. "Akwai ƙura kuma a akwai kallo. Gaskiya babu mai mummunar sa'a a duniyar nan kamar kai, duk rashin sa'an wasu ya biyo bayanka. Kai yanzu me ka gani a jikin wannan mai kama da jaɓar?". "Ki iya kalaman ki Zahra, auren haɗi za'a yi mana, kuma bana son ki ƙusa baki ciki". Cewar Sooraj. Kallonsa Zubaida ta yi ta ce. "Abun qauna, me ya sa ka ke yawo da wannan ballagazar, kodai budurwar ka ce?, yanzu kenen cin amana ta ka ke ban sani ba". A fusa ce Zahra ta ce. "Yaci amanar taki ɗin me za ki yi?, ke zanci bala-balan banki bariki....... Bata ƙarasa ba taji an kwashe ta da mari. Dafe ƙuncinta Zahra ta yi ta ce. "Yahya Sooraj, mari na kayi, ni ka mara?". Girgiza kai Zahra ta yi cikin jin aushi ta fita daga asibitin. Da sauri Sooraj ya koma inda motarsa take tare da tada motan sannan ya fice da sauri daga cikin asibitin tare da bin bayan Zahra. ********************* Ɓangaren Aliyu kuwa Kano ya nufa da Safira tare da kaita kangon dake cikin daji. Sannan ya yi parking tare da fito da Safira yana mai shigar da ita cikin kangon tare da ɗaure ta. Tana kuka haka ya kammala ɗaure ta sannan ya dube ta ya ce. "Ba za ki san dalilin da ya sa nake miki hakan ba, amma nan bada jimawa ba zaki fahimta". ***************** Umar kuwa yana cikin tuƙi wasu ƴan daba suka tsayar da motarsa. Nan suka buɗe motar tare da fesa mai hoda wanda ya sanya shi fita daga cikin hayyacin shi. Nan take ya suma. Shiga motan suka yi da shi tare da tada motan suka bar wajan. Cikin motan kuwa Amrah ce kwance bata cikin hayyacin ta. Chan kangon da Aliyu ya nufa da Amrah aka nufa. Yayin da aka jefa su a ciki. *********** "Zahra kiyi haƙuri ki shigo mu tafi". Cewar Sooraj yana mai cigaba da bin bayan Zahra. Harara Zahra ta galla mai ta ce. "Ba zan shigo ɗin ba, yanzu ka gama mari na kuma kace na shigo, to ba zan shiga ba. Kaje chan da riɓaɓɓiyar motar ka". Ganin Zahra ba zata bashi haɗin kai ba ya sashi tsaida mota tare da fito wa daga ciki sannan ya nufi inda take, bai bata lokaci wajan ɗaukar chakk ya ɗora a ƙafaɗa. Fusge-fusge Zahra ta fara yi amma samm Sooraj bai ajiye ta ba har saida ya isa motarsa sannan ya direta tare da sakawa motan key. Sannan ya zagaya ya shiga yana mai tada motan suka bar wajan. Kai tsaye Masarauta suka nufa a sa'inda babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka isa. Mamaki ne ya kama Zahra da Sooraj ganin yadda fadawa da dogarai tare da ƴan aiki da mai martaba tare da su Gimbiyoyi suka taru guri ɗaya. Fitowa Zahra da Sooraj suka yi daga cikin motan. Fashe wa da kuka Gimbiya Saratu da Samira suka yi. Kallon su Sooraj ya yi ya ce. "Me ke faruwa ne naga mutane sun taru?". Share hawayenta Samira ta yi ta ce. "An nemi sarƙar zinaren Ammi an rasa, shi ne aka ce kowa ya fito, wasu fadawa ne da dogarai ne suke searching kowane saƙo da lungu na gidan kuma duk wanda aka ganshi a ɗakinsa shi ne ɓarawon". Mami kuwa babu abinda take in banda addu'ar ganin gold ɗin. Zahra taɓe baki ta yi dan ta san bata ɗauki wani gold ba. Saida suka shafe kusan awa guda a tsaye kana daga bisani suka jiyo muryoyin fadawa na faɗin an ganshi. Ƙarasawa wajan fadawa guda biyar suka yi tare da miƙa wa mai martaba gold. Kallonsu Sooraj ya yi ya ce. "A ɗakin wa ku ka ga sarƙar gold ɗin?". Amsa ɗaya daga cikin fadawan ya bada da cewa. "A ɗakin ɗaya daga cikin ma'aikatan masarautar nan wato Zahra". Zaro idanuwa waje gaba ki ɗaya jama'ar da ke wajan suka yi. "Zahra kuma!". Mami ta faɗa cikin shiga ruɗani. Kallonsu Zahra ta yi ta ce. "Wannan ƙarya ne, ni ta ya ya zan ɗauki gold bayan ban san ma da shi s fadar nan ba, wallahi bani bace". "Ƙarya ki ke, dama ba yau ki ka fara yi mana sata ba, kin daɗe kina yi shi ne yau Allah ya tona asirinki, dama an ce rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya". Cewar Gimbiya Saratu. Maida kallonsa Sooraj ya yi kan Zahra ya ce. "Zahra da gaske ke ki ka saci wannan gold ɗin?, me ya sa za ki aikata hakan". Hawayen da Zahra ke ƙoƙarin riƙe wa ne suka suɓuce mata. Dubansu ta yi ta ce. "Wallahi bani bace ba, sharri kawai suke suyi min saboda a kore ni daga masarautar nan saboda ina muzguna wa rayuwarsu. Amma wallahi sata ba hali na ba ne". Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra babu sharri ko ƙarya a nan an ga sarƙa a ɗakin ki, ta ya ya to sarƙar ta shiga ɗakin naki?, ko ita sarƙar ce zata kai kanta ɗakin?". "Kenen kema Mami baki yarda dani ba?". Cewar Zahra wacce duk ta bi ta rikiɗe. "Waye ma zai yarda da ke, ɓarauniya, dama aka ku talakawan nan ku ke da zaran kun samu guri, ku ke iskanci yadda ranku ke so". Cewar Gimbiya Talatu. "Maza zo ki fice daga cikin masarautar nan bamua son sake ganin fuskarki". Cewar Sooraj wanda ranshi ya yi matuƙar ɓaci. "Dakata!". Suka ji an furta. Juyawa gaba ɗaya suka yi domin ganin wane ne, MK ne tsayem ƙarasowa wajan su ya yi sannan ya dubi kowanne daga cikin su ya ce. "Zahra tafi ƙarfin ta saci gold. Kun san wace ce mahaifiyar ta. Idan da a ce kun san wace ce Zahra da kun dinga yi mata hidima. Mahaifiyar ta na ɗaya daga cikin masu kuɗi na duniya wanda kowa ya san da hakan". Mamaki ne ya kama kowanensu. Mamaki ne ya kama Zahra dan ita ta san dai ba ƴar masu kuɗi bace. Kallon Mk ta yi ta ce. "Bana son kayi min ƙarya ni mahaifiya ta ma ban taɓa ganinta ba, kuma ni ɗin ba ƴar masu kuɗi bace asali ma ni ɗin a kurkuku na taso, dan haka karka yi min ƙarya dan ka kare ni". Murmushi Mk ya yi sannan ya ce. "A wajan ki ke ƴar talakawa ce, amma a zahiri ke ɗin ƴar gidan masu arziƙi ce. Idan da a ce ana siyan masarauta, to tabbas babu tantama a cikin dukiyar ki ƙarami daga ciki zai siyi Masarautar nan har sau biyar". Jin hakan ya sa kowanensu ya zaro idanuwa waje. MANAGE PAGE PLEASE 🙏 🙏 🌹. KUN JINI SHIRU KWANA BIYU, WAYATA CE TA LALACE, AMMA YANZU NA GYARA DA YARDA ALLAH ZAN DINGA MUKU UPDATE A KAI A KAI. ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (ZINARIYAR JAJIRTATTU) [12/2, 19:56] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣1️⃣▶️5️⃣2️⃣ *___________________________________________* "kamar ya ya? mufa ba mu fahimta ba ya kamata ka fahimtar da mu. Kowa a nan wajen kai yake jira kuma sannan bamu san me yake faruwa ba ya kamata ka sanar da mu ko wacece Zahra". cewar mami wacce ta tsaya ta zubawa zahra idanuwa. ajiyan zuciya mk ya sauke sannan yace. "ko ku yarda ko karku yarda wannan ba damuwa ta bace ba amma tabbas Zahra shahararriyar yar masu kuɗi ce, ba lallai yanzu ku fahimta ba amma nan gaba tabbas zaku sani yanzu dai ku maida ta ciki dan Allah". girgiza kai Sooraj ya yi sannan ya ce. "Tabbas zamu maida ta ciki amma kuma ina so ka faɗa mana ainihin gaskiya, kazo ne ka tsayar da mu, kuma kana so ka faɗi gaskiya amma ka yi shiru ya kamata ka fito ka bayyana mana duk abinda ke faruwa. Mu yanzu ka saka mu a cikin duhu ya kamata ka fito damu cikin haske, kada ka manta nan cikin masarauta ka shigo ba wai waje ba, ya kamata ka san inda ka ke a halin yanzu". murmushi Mk ya saki sannan ya ce. "Ya kamata ka saurare ni yarima, na riga na gaya muku cewa nan ba da jimawa ba zaku san ainihin zance yanzu lokacin bayyanar ta bai yi ba shi ya sa ban faɗa muku ba amma insha Allah nan ba da jimawa ba za ku san gaskiya". Ajiyan zuciya kowa ya sauke jin furucin mk na karshe furzar da iska kowa ya yi waje sannan kowa ya shige cikin fada yayin da bakin ciki da takaici suka bi suka cinkushe guri guda cikin gimbiyoyi da yaransu. kowa ya shiga ciki yayin da ya rage iya Mk da Zahra kallonsa zara tai sannan ta ce. "Ni fa ban san ka ba, kuma ta yaya za'a ce mahaifiya ta wata ce bayan kuma ni tunda nake ma ban taba ganin mahaifiyar tawa ba, ko da kamshin jikinta ban taba ji ba. Kasan mene ne nifa ba 'yar masu kudi bace ba ka zo nan ka dan bara musu ƙaryar ka, yanzu sai ka san ai yadda zaka wanke kanka dan ni yanzu bansan me zanyi maka ba. Wallahi idan ka saka aka kore ni daga masarautar nan, ba zaka ji da daɗi ba. Ina zaman zama na zaka zo ka tayar min da hankali eh, ni yanzu kawai ka je ka gaya musu cewar duk abinda ka faɗa musu karya ce don wallahi idan gaskiya ta fito duk abinda yazo ya biyo baya babu ruwana kar ma ka nuna ka san ni ko kuma ka taɓa gani na dan ni dai ba abinda ya shafe ni, tunda kaine kazo kayi musu karya ba ni ba '. Dan haka dan Allah dan Annabi ka tawo ka je ka gaya musu gaskiya. Ya kamata ka san da haka wallahi ni ban san kowa ba ma ni a garin nan in banda magarkama ". "A'a Zahra ba zan iya aikata akan ba domin duk abinda na faɗa babu ƙarya a cikin ta gaskiya nake faɗa miki na san ba lallai ki yarda dani ba amma tabbas wata rana za ki tuna da cewa nazo har gabanki na faɗa miki asalin wace ce ke, sai a lokacin zaki tuna abinda na faɗa miki. Kada kiyi tunanin ko nazo ne saboda wani abu ne domin na taimaka miki amma tunda kin riga kin nuna cewar ba kya son haka ni zanyi tafiya ta nagode". Mk ya faɗa yana Mai ƙoƙarin tafiya. Da sauri Zahra ta dakatar da shi sannan ta ce da shi. "Tsaya!". tsayawa mk ya yi yana mai fuskantar Zahra. Karasawa inda yake Zahra ta yi sannan ta ce. "Ya kamata ka faɗa min toh inda mahaifiyar tawa take tunda kace kasan ta kuma kasan ita ɗin me kuɗi ce nima kuma yar ta ce kuma in yi ma ina da dukiya, to ya kamata ka kaini wajen ta ina so na ganta domin na tabbatar da abinda ka ke faɗa amma idan baka kaini ba ba zan taɓa yarda da maganar ba. Ya kamata ka san da cewa ni ba komai ne za'a kawo min na yarda ba, ina yarda da wasu abubuwan amma wani abun idan ka faɗa mun ba zan yarda da shi ba. Dan haka ka gaya mun inda mahaifiyata take idan kuwa ƙarya ka ke ba zan ƙyale ka ba dan wallahi sai na muzanta ka a gaban mutane". Murmushi kawai Mk ya yi dan bai iya ce mata ƙala ba, sannan ya ce. "Hmm Zahra kenan, duk a cikin 'yan uwanki halinki ne kawai ya bambanta da na sauran, bansan ta yadda zan fara fahimtar da ke ainihin gaskiya ba amma ina son daga yau har izuwa sati mai zuwa kada ki kuskure ki fita daga cikin wannan masarautar saboda ana neman rayuwar ke ruwa a jallu sannan kuma da zarar kin fita za'a sace ki ina fada miki hakan ne ba dan wai banason ki fita bane da komai na rayuwarku gaba daya yake akaina dan haka ya kamata ki saurare ni sannan ki fahimci abunda nake fada miki wannan ba wasa nake fada ba gaskiya nake fada miki Zahra duk da cewa nasan ki ba mai daukar komai ba amma ya kamata kyau wannan muna tawa". kallon sama da ƙasa Zara ta bishi da shi sannan ta ce. "Kamar yaya 'yan uwana? ni fa bani da wasu 'yan uwa sannan da ka ke cewa kada na fita daga cikin masaurartan nan har kai waye da zaka cemin karna fitar ko ina?, ni nake da kaina kuma duk inda nake so zanje da inda bana so bazan je ba ya kamata ka fahimci cewa ni ba kanwanlasa bace babu wanda ya isa taɓa ni ko ya yi yunkurin cutar da rayuwa ta ballantana ma a sace ni. Kana ji na ko, kaje ka koma duk inda ka fito dan ni ba za'a taɓa rinjayata ba, ya kamata ka san wace ce Zara, ni ba kamar sauran mutane bace da za su zo a gaya musu magana su zo su dauka ka gane, idan ba zaka iya ba ka ja baki kan shiru. Sannan ya kamata ka je ka gaya musu cewar ni ba 'yar kowa bace ba ka zo ne kayi mun sharri ban ji ba ban gani ba zaka je ka saka ni a inda Allah bai kaini ba". Tana kaiwa nan, ta juya masa ƙeya tare da barin inda yake kai tsaye falo ta nufa wato babban falon sarki. Nan ta tarar da su gimbiya talatu da saratu tare da 'ya'yannan su cikin ranta ta ce. "Ba dai ni ku ka je ku ka yi wa sharrin cewar na saci gold ba, to wallahi zaku ga bala'i a gidan nan, dan duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, ba zan taɓa ƙyale duk abinda ku ka yi mun ba sai na fanshe duk abinda ku ka aikata mun, kuma wallahi, wallahi ba za ku ci bulus ba tunda har ku kasa nayi kuka da idona, dole kuma sai nasa ku kuka ba zan ƙyale ku ba domin kuma sai kun ɗanɗana kuɗarku". Tana kaiwa na ta isa inda suke. Ganin tana iso inda suke ya sa ga baki ɗayansu miƙe wa tsaye tare da kwashewa da dariyar mugunta. girgiza kai Zara ta yi tare da sakin murmushi sannan ta fara yin waƙa da cewa. "kaga ƴan bura'uba, da ni suke bura'uba, ƴan buhum bura'uba, kai ka ga 'yan bura'uba ga wata yar bura'uba, so take in bata bura'uba". Nan take ran kowa a cikin su ya ɓaci. Dai-dai lokacin Sooraj ya shigo parlourn tare da zama domin ganin Zahra a wajan. Nan ya shiga kallonta kamar zai cinye ta. Ganin Sooraj yana ta kallonta ya sa Zara faɗin. "Ni dai na shiga uku wannan wani irin kallo ne haka kamar maye". Da sauri Zara ta rufe bakinta jin furucinta na ƙarshe tare da saurin jan baya zaro idanuwa ga baki dayansu suka yi jin furucin Zahra na ƙarshe. mike wa tsaye Suraj ya yi a fusa ce sannan ya dube ta ya ce. "Ni ki ke kira maye?, ni ne maye ɗin?, wato lallai yarinyar nan sai yau na ƙara tabbatar da cewa kin gama raina ni, idan har ban koya miki hankali ba, ba za ki daina min duk abinda ki ke min ba. Ai kuwa yanzu za ki gane kuren ki, a yau zan nuna miki halin maitar". Yana kaiwa nan ya ce yi saurin nufar inda take tare da fisgo ta sannan ya kwashe ta da marika har guda biyu. Ihu Zara ta kwalla tare da fara neman taimako, ganin su gimbiya sun ja baya suna ta yi mata dariya ya sa ta fara ƙoƙarin ƙwace kanta daga wajen Suraj, amma ina hakan ya ci tura. Fusgota suraj ya ƙara yi tare da nufar hanyar past ɗin sa da ita. Yana isa part ɗin sa ya wurga ta ciki tare da nufara kan waydrop dansa sannan ya dauko bulala tare da igiya. Ganin hakan ya sa Zara ta fara kuka wiwi tare da fara bashi hakuri ta ce mai. "Kayi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba, na tuba, dan Allah kayi haƙuri, dan Allah kada ka dake ni na roke ka kada ka ɗaure ni". Tana faɗa hawaye na bin ƙuncinta, amma ina Suraj ya kada sauraran ta. Aka ya janyo ta ya daure ta a jikin gado sannan ya ɗauki bulala bai yi wata wata ba ya ɗaga domin zabga mata sai wani tunanin ya sa ya dakata. Furzar da iska ya yi waje tare da ƙura mata ido ganin gaba ɗaya hankalinta a tashe duk jikinta ya ji ƙe da zufa ya sa shi kwashe wa da dariya tare da zama a kan gadon yana mai fuskantarta sannan ya ce. "Dama haka ki ke da tsor ai ni ban sani ba sai yau kenan ma dama duk waɗan nan rashin kunyar da ki ke yi kenan duk baki ki ke da shi ba karfi gare ki ba?, ai na dauka ke irin jarumar nan cee ashe- ashe raguwa ce. To ni dai an dai ji kunya". Ya ƙara faɗa yana mai kwashe wa da dariya. Kallon Suraj ta yi ta ce. "wallahi ƙarya ka ke yi, ni ba raguwa bace ba, ni da ka ke gani na nan sai da na taɓa dukan ɗan sanda kuma na sha ba tare da anyi min komai ba. Kaga tunda ma na iya dukan ɗan sanda ba tare da anyi min komai ba ka ga ni jaruma ce kenan. dan haka ya kamata kayi hakuri ka manta da komai na riga na gaya ma cewar na tuba na koma ga Allah. Na riga dana canza". Kallon ta Suraj ya yi sannan ya ce. "A hakan ne ki ka canza?, yanzu- yanzun nan naga kina yiwa gimbiyoyi rashin kunya sannan kuma kice min kin canza ba wani canza wanda ki ka yi". Yana kaiwa nan ya kunce ta, sannan ya ce ta miƙe ta zauna. Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tare da galla masa harara sannan ta ce. "Na gode Yahya Sooraj". *************** *Umar pov.* Buɗe idanuwansu Umar da Amra suka yi, yayin da suka gansu cikin wani kango da sauri suka miƙe tsaye sannan suka fara wage-wage can suka hango wasu matasan mata cikin ƙunci da bakin ciki suna a ɗaɗɗaure. Da mamaki Umar ya kalle su sannan ya ce. "Me ku ke yi a nan wajen?, ta ya ya haka ta faru?, me ya same ku haka?, wane ne wannan mutumin ne wai da yake addabar mutane?, mene ne yake nema ga mutane?, me yake so?, me yake da buƙata?, waye shi?". Tambayoyin da ya shiga yi kenan yayin da babu wanda ya ɗago idanuwan sa. Nan suka ji watan budurwa ta kallesu ta ce. "Wani ne governor Musa Muhammad". Nan take gaban umar ya yanke ya faɗi. Kallonsu ya yi ya ce. "Govnor Musa Muhammad kuma?, kin san wane ne gwamna musa muhammad?, shi ne fa mahaifina, kuma shi din babban mutum ne wanda gaba ɗaya duniya ta san shi, ya za ki zo kiyi mai ƙarya. Sam -sam bashi ba ne ba". kallon sa budurwar ta yi a karo na biyu sannan ta ce. "Kwarai da gaske mahaifinka shine wannan wanda yake yi mana barazana, yake mana duk abinda yake da bukata yake mana tozarci, ya samu cikin baƙin ciki, da wulakanci duk ya saka mu a cikin ƙunci. Kuma shi ne wanda yake safaran mata, yake safaran miyagun ƙwayoyi yake safarar miyagun laifuka sannan har izuwa halin yanzu babu wanda ya taɓa sanin shi din babban mai laifi bane in ba mu ba. Ya kamata ka fahimce mu ya kamata ka saurare ni sannan kuma ya kamata ka yarda dani bansan wane hujja zan iya baka dangane da hakan ba amma tabbas mahaifinka masheki ne babba kuma criminal ne". saurin dafe kansa wanda ke ƙoƙarin sara masa Umar ya yi dannan ya ce. " I can't believe this, mahaifi na shi yake duk waɗan nan lefukan kuma ina matsayin ɗanshi jami'in kuma shine ban san da hakan ba, tabbas na aikata babban kuskure, dama na daɗe ina zargin shi da hakan, amma zuciya ta ta kasa aminta da haka sai kuma yanzu na zo na kara ji daga bakin ku, ban taɓa tsammanin cewar mahaifina shi yake aikata duk laifukan da nake kokarin gano wane ne ainihin criminal ɗin ba ashe ma asalin criminal ɗin yana zaune a gida na ban sani ba. To wallahi ba zan bar shi ba ba zan duba ko shi ɗin mahaifina bane dole sai na kama shi na damka shi wa hukuma sannan an bi muku hakkin ku kum........ Maganarsa ce ta tsaya sakamakon ƙarar da Amrah ta ƙwalla wanda ya cikashe ilahirin gidan kangon baki ɗaya. Nan take suka ga ta fara laulayi tana mai dafe kanta. Ɓangaren su Aliyu, bai yi aune ba ya ga Safira ta buɗe ƙofar mota tare da faɗa wa cikin jeji. Nan take ta fara gangara wa cikin daji ba tare da ta tsaya ba. Da sauri Aliyu ya bi bayanta yayin da suka haɗu su biyu suna gangarawa cikin daji. ********* Ɓangaren Sooraj kuwa, da mamakin sa ya ga jikin Zahra ya fara ƙaƙƙarwa. A matuƙar tsora ce Sooraj ya miƙe tsaye tare da karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa. Bai yi aune ba yaga Zahra ta tafi zata faɗi da sauri ya isa gare ta tare da kare ta daga faɗuwa. Nan ta faɗa a jikinsa. MANAGE PAGE PLS. SHARE FISABILILLAH 🙏 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 ZINARIYAR JAJIRTATTU [12/7, 16:26] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣3️⃣▶️5️⃣4️⃣ _______________________ a tsora ce Suraj ya dube ta ya ce. "Zara me ke faruwa dake haka? me ya sa me ki haka?, ya kamata ki sanar dani me yake faruwa dan Allah ". Ya faɗa a matuƙar razane. A hankali Zahra ta buɗe idanuwanta sannan ta cire jikinta daga na shi tare da ƙwalolo idanuwa waje tana mai yin gurnani. Ganin hakan ya sa Sooraj razana sannan ya ja da baya, yana mai karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa. "Zahra lafiyar ki ƙalau kuwa?, ya kamata ki dawo yadda ki ke". Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta zauna a ƙasa tare da sunkuyar da kanta. Kallonta ya yi yana mai ƙura mata ido. Nan take ya ga ta ɗago idanunta tare da kwashe da dariya. Firgita Sooraj ya yi ganin yadda Zahra ta ƙyalƙyale da dariya. Takawa ya fara yi tare da isa inda take ya ce. "Zahra kina lafiya kuwa?". Fashe wa da dariya Zahra ta ƙara yi a karo na biyu tana mai faɗin. "Dama kana da tsoro aka?, ai ban san aka ka ke da tsoro ba sai yau. Dama nayi hakan ne saboda na tsoratar da kai kamar yadda nima ka tsoratar dani". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kenen kina sane ki ka kurma ihuun nan?, tare da kakkarwar nan?". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a, wannan bana sane naji kamar an buga min guduma a kaina shi ya sa na kurma ihuu, amma ka yarda dani iya wannan ne ba da sane nayi ba". Shiru kawai Sooraj ya yi ya ce. "Fitar min daga ɗaki". Taɓe baki Zahra ta yi tare da shagwaɓa fuska sannan ta ce. "Saboda za ka kore ni?". Tashi tsaye Sooraj ya yi ya ce. "Idan baki fita ba zan miki dukan babban bargo yanzu nan". Ba musu Zahra ta miƙe tsaye tare da fice wa daga ɗakin. Ganin ta fita ya sa shi jan dogon tsaki, kana ya koma kan gado. ******************* Chan cikin jeji Safira da Aliyu suka tsinci kansu. Ganin kan Safira na fidda jini ya sa hankalin Aliyu ya tashi. Da sauri ya miƙe a hankali saboda shima yaji rauni sannan ya yi saurin isa gare ta. Saurin ɗaga masa hannu ta yi ta ce. "Kada ka kuskure ka matso kusa da ni, bana ƙaunar wani abu da zai haɗa ni da kai, dan Allah kayi tafiyar ka". Aliyu bai ko saurare ta ba ya ƙarasa inda take, sannan ya samu ya yagi ɗan ƙarami daga jikin mayafin ta, tare ɗaure mata inda jinin yake fita. Kana ya shafa kan fuskarta. Saurin ture shi ta yi daga inda take sannan ta ce . "Wai bana ce ka rabu da ni ba, me ne ne na ƙulle min ciwo?, dama ba so ka ke ka kashe ni ba, to ka barni na mutu ɗin mana. Wai kai jami'i ne ko?, kai sam baka cancanci zama jami'i ba ko kaɗan, tunda har ka iya tauye haƙƙin wasu saboda son abin duniya, sannan ka iya manta da irin halin da iyayenka za su shiga samm baka cancanci kasance wa jami'i ba, Allah wadaran mutum irin k......... Maganarta ne ya tsaya sakamakon tsawar da Aliyu ya daka mata. ****** Ɓangaren su Umar kuwa, waɗan da suka yi kidnapping ɗin su ne suka jiyo ƙara da Aliyu ya daka. Da sauri suka fita daga wajan tare da bindigogin su domin ganin wane ne. Umar kuwa da sauri ya nufi inda Amrah take yana mai rungume ta a kirji tare da shafan lallausan gashin kanta. A hankali Amrah ta buɗe idanuwanta tana mai rungume Umar sannan ta ce. "Ina son zan faɗa maka wani abu". Ɗaga ta Umar ya yi daga jikinta ya ce. "Mene ne?". Furzar da iska waje Amrah ta yi ta ce. "Shin idan na faɗa maka wani abu za ka yarda da ni?". Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "In sha Allah, ai na san bakya ƙarya, ki faɗa min ko mene ne zan yarda". Shiru Amrah ta yi na ɗan wasu lokaci, murya a raunace ta ce. "Mahaifin ka shi ne wanda ya kashe mahaifiyar ka". Rass gaban Umar ya faɗi!, yayin da mutanen wajan gaba ɗaya suka zaro idanuwa waje. "Ban fahimta ba, ki fahimtar da ni, ta ya ya ki ka san da cewar mahaifi na ne ya kashe mahaifiyata?, samm hakan ba zai yu ba, duk rashin imani mahaifina ba zai iya kashe rai ba". "Tabbas idan mahaifinka ne abinda ya fi hakan ma zai aikata". Umar ya ji wata ta faɗa. Da sauri ya juya domin ganin wace ce. Chan ya hango Nurse Nadiya a ɗaure kusada wani benching wanda mutanen gov. Musa ke zama a kai. Mamaki ne ya kama Umar ganin nurse ɗin kwanaki da ya taɓa kai Amrah wajanta lokacin da ta suma. "Kamar ke ce wannan Nurse ɗin ko wanda na baki amanar Amrah a asibiti lokacin muna Jigawa?". Umar ya tambaya. Amsa nurse Nadiya ta bashi da cewa. "Ƙwarai da gaske ni ce nan ba wata ba, Mahaifin ka ya yi sanadiyar tarwatsa rayukan mutane babu adadi, shi ya yi sanadiyar rabuwar uwa da yaranta duk dan saboda abin duniya. Mahaifin ka ya kasance ya na aikata laifuka ne tun kafin ya zama Govnor, shi ɗin babban mara imani ne, ya ƙala wa baiwar Allah sharri wacce bata ji ba bata gani ba, ya sa kuma iyayen ta sun tsane ta dangint mijinta duk sun ƙi ta, sannan kuma duk da hakan bai rabu da ita ba, yana neman dukiyarta wanda ke a ɓoyayyen, wanda babu mai zuwa sai ita ko yaranta, gashi ya kashe ta, yaran ma bamu san inda suke ba. Shin mahaifinka baya tunanin shima wata rana zai koma ga ubangijin sa?, baya tunanin ta yadda zai fara sauke nauyin haƙƙin mutane da ya ci bayan ya mutu?". Shiru Umar ya yi yayin da ya rasa ta cewa. Ji yake dama ba ta hanyar mahaifin shi ya zo duniya ba, nan take ya ji tsanar mahaifin na shi ya cikashe zuciyarsa baki ɗaya. ********* "Safira ya ishe ki aka, kina ta tsawatar min ina yin shiru, na riga na gaya miki cewa zan faɗa miki komai daga baya amma kin ƙi saurare na, me ki ke so nayi miki. Kin san dai ina sonki kuma ina ƙaunar ki, ta ya ya zan iya cutar da wanda nake so har cikin raina?, ya kamata ki fahimce ni, duk abinda ki ka ga ina yi, to ina yi ne ba dan komai ba sai dan saboda ke, ina san na bayyana miki wata gaskiya, kuma bana don na bayyana miki wannan gaskiyar ta baki na fison na bayyana miki ki gani da kanki". Tashi tsaye Safira ta yi ta ce. "Bana da buƙata, ni kawai ka mayar da ni gida. Kai ɗin macuci ne, da a ganka a ga maciji, gwanda a fara kashe ka kafin a kashe wannan macijin, domin kai kafi maciji cutarwa". Jin takum takalman mutane ya sanya Aliyu saurin riƙe hannun Safira sannan ya fara gudu da ita. Ƙoƙarin wafce hannunta take amma hakan ya cutura. Kuka Safira ta fara yi ganin yadda Aliyu ya matse mata hannu yana gudu da ita. Aliyu bai tsaya ba saida ya isa bayan kangon babban gidan da su Umar suke sannan ya dakata yayin da ya ja hannunta tare da shigar da su domin su ɓuya. **** Mutanen Gov. Musa kuwa suna zuwa wajan, suka tarar ba kowa, hakan ya sanya su koma wa inda suke. Ajiyan zuciya Safira ta shiga jera wa tana mai kallon hannunta da Aliyu ya riƙe. Gani ta yi guri ya kaɗa ya yi jajir. Nan da nan hawaye suka fara bin ƙuncinta. "Yi haƙuri Safira duk abinda ki ka ga ina yi duk saboda ke ne". Aliyu ya faɗa murya a ƙasa. ************* Ɗaki mai num105 na hango hajiya Binta ta yi tagumi idanuwanta a kan littafin da mrs Lailah ta bata, yayin da take tunano maganar da Mrs Lailah ta faɗa mata kafin su rabu. "Ga amanar ƴata na baki ki kularmin da ita tamkar ƴar cikin ki sannan kada ki taɓa faɗa mata cewar ke ɗin bah mahafiyarta bace, har sai ta kai munzalin sanin hakan. ina son ki nemi ta gano inda mahaifinta ya ke". Share hawayen da ke shirin zubo mata Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Yanzu Zahra ta kai minzalin sanin wace ce ita tare da sanin inda mahaifinta yake, na san dai ba iya ita ɗaya Lailah ta haifa ba. Ina son na bawa Zahra wannan littafin amma ban san ta ya ya zan bata ba". Daga nesa ta hango wata warder. Nan ta miƙe tsaye kana ta fara takawa izuwa inda wannan warder ɗin take. Kallonta warder ɗin ta yi ta ce. "Ya aka yi?, me ya sa baki ke kinyi cutting grass ɗin da aka sanya ki ba". Shiru Hajiya Binta ta yi ta ce. "Taimako nake so kiyi min, maganar cutting grass, zanyi shi, dan Allah wannan littafin nake son ki bawa DPO, kice idan ya ga MK ya ba shi wannan littafin, na san Mk zai iya sanin inda Zahra take. Ya bata littafin, gaba ɗaya tarihin mahaifiyar su yana ciki". Turnuƙe fuska warder ɗin ta yi ta ce. "Ba zan kaiba maxa kije kiyi aikin ki". "Dan Allah kiyi haƙuri ki karɓa, dan Allah". Ta faɗa hawaye kan fuskarta. Ganin hakan ya sa warder ɗin karɓar littafin sannan ta jaddada mata cewa zata bawa DPO. Jin hakan ya sanya Hajiya Binta yin farin ciki sannan ta koma inda take. *********************** Bayan fitar Zahra ne ta saki murmushi yayin da ta fara jin son Sooraj ya fara shiga zuciyarta. Chan ta hango Mami zaune tana shan lemo a parlour. Da sauri Zahra ta yi fuska tare da ƙoƙarin wuce wa dan kada Mami ta ganta. Cikin rashin sa'a ta ji Mami ta ce. "Zahra zo nan". A kunya ce Zahra ta ƙarasa inda take tare da gaishe ta. Amsa wa Mami ta yi murmushi kan fuskarta ta ce. "Zahra kenen, da fuska za ki yi ki wuce ko?". Sosa kai Zahra ta yi ta ce. "A'a Mami, ai ban isa ba". Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Wai me ke tsakanin ki keda Sooraj, naga yanzu kuna shiri ba kamar da ba, sannan naga har fita kunyi tare, yanzu ma naga kin fito daga ɗakin sa, faɗa min meke faruwa, kodai akwai wata a ƙasa" . A kunya ce Zahra ta sa hijabin ta tana mai rufe fuska sannan ta girgiza. Murmushi Mami ta yi ta ce. "Mene kuma na jin kunya, ki faɗa min gaskiya, nimai sa sarki ne ya je a neman miki auren ki wajan iyayen ki". Ɗago kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Ni bani uwa ko uba, amma ina da Hajiya Binta wacce ta maye min gurbin uwa". "Ohh Allah sarki, ban san baki da iyaye ba, Allah y a jiƙan su ya yi musu rahama". Amsa wa Zahra ta yi da "Ameen". Sannan ta ƙara da cewa. "Ni bani nake nani ƙewa yahya Sooraj ba, shi yake naniƙe min kinga kuwa shine yake sona, kuma nima na san yana sona kawai ɓoye min yake, bai san na sani ba". Ta faɗa tana mai yin dariya. Girgiza kai Mami ta yi tare da miƙe wa sannan ta ce. "Na manta ban baki kyautar da na siyo miki ba, bara naje na dauko min, ki jire min lemo na". Gyaɗa kai Zahra ta yi ta ce. "Tom zan jire miki". Jin hakan ya sa Mami barin parlourn tare da shiga part ɗin ta. Duk abinda suke yi a gaban idanuwansu Gimbiya saratu da yaransu. Tashi Zahra ta yi jin wani ƙishin ruwa ya dame ta ya sata nufar hanyar kitchen domin samo ruwa. Miƙa wa Samira ƙullin magani Gimbiya saratu ta yi ta ce. "Kije ki zuba wannan garin maganin a cikin lemon nan kafin wan can sheɗaniyar yarinyar ta dawo daga kitchen, maza-maza, ina son A'isha ta mutu idan ta sha maganin nan. Da sauri Samira ta karɓa tare da zuwa inda lemon Mami yake sannan ta fara zazzaga maganin a ciki. Dai-dai lokacin Junaid ya shigo da sauri ya ɓuya sakamakon harba da ya yi da Samira. Bai yi dogon tunani ba, ya fara yin video sannan ya yi saurin juyawa. Dai-dai lokacin Zahra ta shigo cikin parlourn yayin da idanuwanta ya sauka kan abinda Samira ke aikata wa. "Kuttmelesi!, me nake gani haka, guba za ki saka wa Mami a lemo". A razane Samira ta dube ta kana ta karkaɗe hannunta ta ce. "Toh ina ruwan ki?, waya gaya miki guba nake saka mata, na ɗanɗana lemon ne naji ba zagi shi ne na saka mata siga saboda ya yi daɗi". "Ƙarya ki ke munafuka". Cewar Zahra sannan ta ƙara da cewa. "Lemon haɗi ne da zai buqaci siga?, wannan lemon roba ne, ki faɗa min gaskiya me ki ka saka a ciki, ko na danne ki a nan wajan nayi miki duka". Dai-dai lokacin Mami ta shigo parlourn. Ganin Mami na zuwa ya sa Samira ta yi saurin wurga wa Zahra ƙullin maganin tare da fasa ihuu. Nan da nan mutane suka cika cikin parlourn. Kallonta Mami ta yi ta ce. "Samira me ya sa za ki kurma ihu aka?". Amsa Samira ta bata da cewa. "Zahra na gani tana saka miki guba a cikin lemo". Take gaban Zahra ya faɗi. "Ni kuma?, hakan me ya sa za ki yi min sharri?, ba ke na kama ba kina saka mata guba". Dai-dai lokacin Sooraj ke fitowa daga part ɗin shi. Nan ya yi kicubus da su Mami tare da su Gimbiya saratu a tsatsaye. Mamaki ne ya kama shi. Ƙarasa wa inda suke ya yi ya ce. "Me yake faruwa?". Amsa Samira ta bashi da cewa. "Zahra muka gani tana zuba wa Mami guba a cikin lemo". "What!, no wannan ƙarya ne, saboda me za ta aikata hakan". Maida kallonta Mami ta yi kan Zahra ta ce. "Zahra da gaske ne abinda Samira ta faɗa?". Girgiza kai Zahra ta yi ƙwallah fal idanuwanta ta ce. "Wallahi bani bace ba, ita na gani tana saka wa Mami guba shi ne ita kuma ta ƙala min sharri". "Ƙarya kike muma mun ganki lokacin da ki ke saka wa". Cewar Gimbiya Talatu. Zuciya a rauna ce Mami ta ce. "Zahra ki rasa da me za ki saka min da shi sai sanya min guba cikin abin sha na?, Why Zahra why?, ga kyautar sarƙar da na siya miki nake shirin baki amma ki ka ɓata wayon ki ta hanyar wannan hanyar da ki ka biyo". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Wallahi Mami bani bace. Yahya Sooraj tunda Mami bata yarda da ni ba kai ka yarda da ni, samm ba zan iya aikata hakan ba". "Tunda kin ce ƙarya muke miki ki ɗauki lemon ki sha, a nan ne zamu tabbatar baki saka guba ba". Cewar Gimbiya Saratu. Furzar da iska waje Sooraj ya yi. Take idanuwansa ya sauka kan hannun Zahra wanda ke riƙe da ƙullin magani. Da sauri ya ƙarasa inda take tare da sa hannu ya karɓi ƙullin maganin ya shinshina. Da sauri ya kauda kai jin cewar tabbas wannan poison ne. Ɗago da idanuwansa ya yi tare da ɗora su kan Zahra ya ce. "Tabbas Zahra kece nen ki ka zuba wa mahaifiyata guba a lemo, idan ba ke bace ta ya ya ƙullin magani ya zo hannunki?". Nan su Gimbiya Talatu da yaransu suka saki murmushin mugunta. Hawaye ne suka fara bin ƙuncij Zahra ta ce. "Ban san ta ya ya zan fara yi muku bayani ba, ni bani da sheda sai Allah. Allah shi ne sheda na, shi ne ya san wanda ya sa wannan guban. Wallahi bani ni ce..... Bata ƙarasa maganar ba Sooraj ya kwashe da marika har guda biyu wanda ya yi sanadiyar faɗuwa Zahra ƙasa. "Mahaifiyar tawa za ki kashe?, wacce ta ɗauki ki tamkar ƴar cikinta?, a da ina tunanin ke ɗin mutuniyar kirki ce ashe ke ɗin mutuniyar banza ce. Na tsane ki, na tsani duk wanda yake ƙoƙarin cutar da lafiyar mahaifiyata. Wallahi da a ce mahaifiyata ta sha wannan poison ɗin, da saina tabbatar da kinsha baƙat azaba a rayuwarki, zan sa a kama ki a zartar miki hukunci. Yanzu aka ma baki tsira ba, domin yanzu zan kira ƴan sanda su kama ki". Babu abinda Zahra ke yi sai kuka. take ta ji kewar iyayen ta da na danginta. Da a ce suna raye ba za'a dinga yi mata hakan ba. Dakatar da Sooraj Mami ta yi ta ce. "A'a kada ka kira ƴan sanda, bana son wannan abun ya isa kunnen mai martaba domin hukuncin zai fi haka, kawai ta tashi ta fice daga masarautar nan kuma kada mi sake ganin koda inuwarta a nan fadan". Miƙe wa tsaye Zahra ta yi tana mai share hawayenta. Kallonta Sooraj ya yi ya ce. "Maza zo ki fice, bana son na sake ganin wannan fuskar taki" Ya faɗa yana mai yi mata nuni ga hanyar ƙofa". Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Zan tafi amma kafin nan, zan sha wannan lemon idan ya so ni zan mutu a maimakon Mami". Ta ƙarashe maganar tana mai nufar inda lemon yake. Da sauri Sooraj ya tafi domin dakatar da ita. Amma ina kafin ya isa, Zahra ta ɗauki kofin lemon tare da shanye lemon ciki kana ta wurgar da glass cup ɗin". Zaro idanuwa gaba ki ɗayansu suka yi. Take gaban kowanensu ya faɗi!. Nan take Zahra ta faɗi a ƙasa. ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (ZINARIYAR JAJIRTATTU) [12/14, 18:40] Ayeesher MB🥰🥰: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣ _______________________ A matuƙar tsora ce Sooraj ya nufi inda Zahra ta faɗi da mugun sauri tare da ɗago ta ya fara jijjiga ta a razane da firgici yana mai faɗin Zahra me kika aikata haka? ya za ki sha wannan abunda kika san guba ce a ciki kina da hankali kuwa". Hankalin Mami da sauran ƴan cikin falon ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Zahra ta fara fita daga cikin hayyacin ta. fusge jikin ta zahra ta yi daga jikin na Sooraj sannan ta miƙe tsaye a hankali nan take jiri ya ɗebe ta, ta faɗi a ƙasa . Da sauri Sooraj ya nufi inda take sannan ya dauke ta ya nufi waje da ita da mugun gudu saboda sauri ko ganin gabansa ba ya yi. Kai tsaye inda motarsa yake ya nufa tare da nufar side ɗin ƴan zaman banza tare da buɗe ƙofar motar sannan ya saka Zahra a cikin mota sannan ya rufe ya juya tare da shiga mazaunin driver ya sa car key ya ta da motar tare da jan motan da gudu ya fita daga cikin masarautar. tafiya yake yi ba gaggautawa tare da wani irin gudun tuki tamkar ana tseren mota. Maida kallonsa ya yi kan Zahra hankali a tashe ya ce. "Kada ki damu Zahra babu abinda zai same ki zan ceci rayuwar ki duk rantsi duku ya bazan taba bar ki ba, saboda dalilin mu bazan so a ce kin rasa rayuwar ki ba, ban sani ba ko gaskiya ne abunda su Samira suka faɗa amma tabbas na san da cewar ba zaki iya aikata abinda suka ce kin yi ba, amma ke ma me ya sa za ki sha wannan guba tunda kin san da cewa cutar dake zai yi bai kamata a ce kin sha ba, ya kamata ace anyi bincike kafin nan a gano gaskiyar lamari amma kuma kika ɗauki gubar ki ka sha gashi nan za ki mutu a banza. Ya kamata a ce kin fahimce ni ban so a ce kin sha wannan guban ba, idan kika mutu ban san wani hali zan iya shiga ba". Zahra dake kwance ta yi luff jin maganganun Sooraj ya sa ta sakin murmushi cikin zuciyarta ta ce. "Dama haka ya damu da ni shi ne kuma zai mare ni wato dai ya san ba nice na saka wannan guban ba amma kuma shi ne yake yi kamar bai sani ba, lallai dole in koya masa hankali". Buɗe idon ta guda ɗaya ta yi tare da kallon sa da gefen ido da sauri. A hankali ta buɗe idonta gaba ɗaya tare da kallon sa. A matukar tsora ce Sooraj ya dube ta sannan ya ce. "Kina lafiya?, babu abinda ya same ki?". Harara Zahra ta galla masa sannan ta saukar da glass ɗin motan tare da tofar da poison din bakinta. Mamaki ne ya kama Suraj ganin cewar bata haɗiye poison din ba. "Wai dama ashe ba haɗiye poison din nan kika yi ba ki kai kamar kin haɗiye?". Kallon baka da hankali Zahra ta bishi da shi sannan ta ce. "jaka ce ta mun gula da zan haɗiye guba?, an gaya maka bana son rayuwata ne eh?, na ce an gaya maka bana son rayuwata ne?. To in faɗa maka kawai na sha ne saboda na kawar da tunanin ku a kaina amma me zai kaini shan guba bayan ba gajiya nayi da rayuwar ba". girgiza kai Suraj ya yi sannan ya ce. "lallai yarinyar nan kin cika tantiriya kuma a hatsabibiya, wato dama baki sha wannan gubar ba shi ne kuma kika tayar mana da hankali lallai yarinyar nan sai na koya miki hankali wannan wani irin shashanci da akuyanci ne wannan ai ba daidai ba ne, me kike tunanin zai faru by mistake kika haɗiye guban?". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Eh ba matsala Allah ya yi lokaci na ne ya yi. Sannan ma da ka ke wani min magana ina ruwanka da ni?, ɗazun nan ka gama mari na yanzu kuma kana nuna wa kamar ka damu da ni. Ni ka bani ruwa na kuskure bakina guban yana min wani iri a baki". "Bani da ruwa, ko kinga frigde ne a cikin motan?". Cewar Sooraj wanda ya tsaya faman kallonta yayin da yake driving. Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Na sani abu a duhu a bak'ar leda, na sani ko Kanada fridge a motarka?, ni ka kalli gaban ka kada kasa muyi hatsari, idan kaga mai shagon saida ruwa saika tsaya kaje ka siyo min". Kallon baki da hankali Sooraj ya bita da shi ya ce. "Karki samu damuwa shi kanshi mai shagon da shagon gaba ɗaya zan haɗa na kawo miki". ****************** Shiru kawai Safira ta yi yayin da taji cikin ta nayi mata ciwo alamun tana jin yunwa. Kallon Aliyu ta yi da rinannin idanuwanta cikin raunatacciyar murya ta ce. "Ina jin yunwa, ciki na yana min ciwo dan Allah ka kaini gida Please". Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Karki damu zan nemo mana abinci, yanzu idan na fita za su ganmu kuma su kashe mu". Cikin rashin fahimtar maganarsa Safira ta dube sa ta ce. "Su waye kuma za su ganmu kuma su kashe mu?". Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mutanen da suke neman rayuwar mahaifiyar ki da kuma taki rayuwar tare da na ƴan uwanki, sannan duk wanda ya yi nasaran kashe ki ko mahaifiyar ki da ƴan uwanki, za su samu dubbannin kuɗaɗen da ba za su misaltu ba". "What!". Safira ta faɗa cikin rashin maganarsa ta ce. "I don't understand, me Mom ta yi musu za su kashe ta?, sannan kuma wane ƴan uwa ka ke magana a kai?". Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Bawai ina nufin Mom ba, domin Mom ba ita ce mahaifiyar ki ba". Rass! Zuciyar Safira ta buga yayin da ta zaro idanuwa waje. Rai a ɓace ta ce. "Kamar ya Mom ba ita ce mahaifiyata ba?, wannan wane irin shirme ka ke faɗa aka?, idan Mom ba ita bace ta haife ni wace ts haife ni to?". Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mrs Lailah Abdullahi, tana ɗaya daga cikin richest women in the world, ita ɗin Aunty ta ce, kamar uwa take a waje na". "Hanya ba wani abun ka sha ba kuwa?, ni bani da wata uwa in ba Mom ba, ka daina faɗa min waɗan nan tatsuniyoyin domin ba yarda zanyi ba". ************* "Gashi yallaɓai Hajiya Binta ce ta ce na baka wannan littafin, ka bawa Zahra shi idan ka ganta". Cewar warder. Kallon littafin hannunta DPO ya yi ya ce. "Littafin mene ne kuma wannan?. Shikenen naji labarin cewar Zahra na Kano har yanzu sannan tana masarautar chan, zan je na tabbatar idan tana chan sannan na dawo da ita". Ya faɗa tare da miƙa hannu ya karɓi littafin sannan ya ajiye a gefe. ******* Sooraj kuwa chan ya hango mai saida ruwa. Parking ya yi tare da sauka sannan ya je ya siyo ruwa guda ɗaya. Saida ya ɗau lokaci Sosai Kana ya dawo cikin motan. Zuwan shi keda wuya ya ga bata cikin motan. Mamaki ne ya kama Sooraj . "Lallai ma yarinyar nan, yanzu kuma ina ta shiga". Waige-waige ya soma yi, chan idanuwansa ya sauka a kanta. Tsaye take da wasu samari guda uku suna sanye da baƙaken suit. Yayin da Zahra ke surfa musu bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba. Dafa kansa Sooraj ya yi. "Wayyo Allah, wannan wace iriyar masifa ce, wai ko ina taje saita nuna halin ta". Ya faɗa yana mai ƙarasa wa inda take. Zuwa wajan keda wuya Zahra ta ganshi. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce . "Yauwa masha Allah kazo a dai-dai, zo ka jini da wata masifa, ina zaman-zama na waɗan nan kajin dake sanye cikin wannan abun da suka kira suit suka zo inda nake, na tambaye su me suke so suka ce wai ai zuwa suka yi su sace ni, shi ne na ce idan za su iya su sace ni". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kema in banda abunki ai wasa suke miki". "A'a wallahi waɗan nan ba wasa suke ba, kana ganinsu yadda ka san wasu ƙasurguman masheƙa, ni kuma dai-dai nake da su". Cewar Zahra wacce ta faɗa hannunta riƙe a ƙugu tana karkaɗa su tare da karka ƙafarta yadda kasan wacce zata yi dambe. "Shi ke nen to mu tafi ko". Sooraj ya faɗa yana mai kama hannun Zahra. Nan take maza ukun da ke sanye cikin suit suka kalli juna, nan suka fito da wani abu kamar perfume tare da fesa musu. Duk abinda ke faruwa a gaban idanuwan Mk. Nan take jiri ya ɗebe su suka faɗi a ƙasa. Kwashe su mutanen suka yi tare da saka su a mota. Ganin hakan ya sa jama'a suka saki ihuu yayin da suka jifar motan kidnappers ɗin da dutsina. Da sauri kidnappers ɗin suka tada mota tare da fara ƙoƙarin barin wajan. Nan jama'a suka dinga binsu a baya har suka ɓace wa ganinsu. Da sauri Mk ya nufi inda motar Sooraj yake domin ganin idan akwai inhaler a motar domin ya san perfume da aka fesa musu zai iya affecting ɗin shi, domin kuwa ya san Sooraj yana da asma. Nan ya fara dube-dube a motar. Cikin sa'a kuwa ya ga inhaler ɗin saman kujera. Da sauri ya ɗauka sannan ya nufi motarsa da sauri tare da tada wa ya bi bayansu Zahra. Gudu suke falfalawa kamar za su tashi sama. Buɗe idanuwanta Zahra ta yi ta gansu cikin mota. Ihuuu ta buga yayin da ta fara dukan wanda ke bayan seat ɗin kusa da Sooraj. Nan take ɗaya a cikin su ya kwaɗe ta da mari. Jin marin Zahra ta yi har cikin ƙwaƙwalwarta. Nan take ta fusa ta yayin da ta kama kunnen wanda ke kusa da ita tare da fara gantsara masa cizo. Ihuuu saurayin ya buga yayin da ya fara ƙoƙarin ƙwace kanshi amma hakan ya cutura. Kuma hakan bai sa sun dakatar da tuƙin ba. Nan saurayin ya taki sa'a ta sake shi. Ganin ta saki kunnensa ya sa shi dafa kunnensa wanda ya yi jajir. Gurnani ya fara yi. Nan ya shaƙe mata wuya tare da ƙoƙarin yi mata allura kan jijiyar wuyanta. Duk abinda ke faruwa Sooraj bai sani ba, domin har izuwa wannan lokaci bai farfaɗo ba. Babu zato suka fara jiyo Sooraj yana nishi sama-sama alamun asma ɗinsa ya tashi. Ganin hakan ya sa Zahra ta sa dukannin ƙarfinta ta ture wannan saurayin. Hankali tashe ta ɗaga Sooraj tare da girgiza shi. "Yahya Sooraj me ya sa me ka?, dan Allah kada ka mutu ka barni". Cikin fitar hayyaci Sooraj ya dube ta ya ce. "Asma ɗina ya tashi kuma inhaler ɗina yana cikin motata". Zaro idanuwa waje Zahra ta yi nan take tausayin Sooraj ya kama ta. Kallon kidnappers ɗin ta yi ta ce . "Dan Allah ku mayar da mu, idan ba haka ba zai mutu, ko baku ga yana cikin mawuyacin hali ba ne". Ko kallon Zahra basu yi ba saima ƙara wa motar gudu da suka yi. Rungume Sooraj Zahra ta yi tare da ɗaukar ruwan da ya siyo ta bashi yasha. Chan cikin dajin suka isa. Tsayar da motar suka yi tare da fitowa. Sannan suka fito da Zahra da Sooraj kana suka ɗaɗɗaure su jikin bishiya sannan suka nufi inda su Amrah suke domin fito da su. Dai-dai lokacin shima Mk ya ƙaraso wajan. Da sauri ya nufi inda su Sooraj suke sannan ya bashi inhaler ya shaƙa. Dubansa Zahra ta yi ta ce. "Dan Allah ka kunce mu". "Shiiiiii!". Mk ya yi mata alama da hannu da ta yi shiru. A hankali Mk ya fara kunce su yana mai waige-waige. ****************** "Wai ni kamm Yahya Usman ina su Amrah da Yahya Umar suke?, har yanzu shiru basu dawo gida ba, ni fa ina tsoron kada wani abu na cutarwa ya cutar ds su. Cewar Khairiya. Kallonta Usman wanda ke zaune kan 3seater ya yi ya ce. "Babu abinda zai same su, insha Allah suna cikin ƙoshin lafiya, ni na matsu su dawo mu koma jigawa". Kallon su Ramlat ta yi ta ce. Ni fa ina ganin kamar akwai abinda ke tafiya ba dai-dai ba, tabbas akwai wani abu da Yahya ke ɓoye mana, kuma baya son mu sani". Kallonta Usman ya yi ya ce. "Mene ne to Yahya zai ɓoye mana?". Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Jiya na kira Abbah, munyi waya to a lokaci da muka gama wayar ya manta bai kashe wayar ba, naji yana yin magana da wani bansani ba ko mace ce ko namiji, naji yana cewa ya tabbatar su Yahya basu tsira daga gare shi ba, sannan a tabbatar an tafi da Amrah Lagos daga nan a wuce da ita ƙasar waje. Na kasa gane me ke faruwa". Kallonta Usman ya yi ya ce. "Kina nufin Abba ya sace su Amrah?". Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Ƙwarai kuwa tabbas ya sace su. Kenen dama Abba ba mutumin kirki bane?" ********* Ɓangaren su Umar kuwa su kidnappers ɗin na zuwa suka ga babu kowa a wajan in banda Amrah da kuma Umar. Ɗaga bindigar su suka yi kan Umar sannan suka ce. "Ina sauran mutanen suke". Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Mun kunce su, sun gudu". "Zaku ga abinda za mu yi muku maza ku fita". Cewar ɗaya daga cikin kidnappers ɗin. Da sauri Umar ya riƙe hannun Amrah sa'anan suka fita waje. Bayan Mk ya gama kunce su Zahra. Sooraj ya riƙe hannun Zahra suka fara gudu suna nufar inda kangon yake. Dai-dai lokacin da su Amrah ke fitowa daga wajan. Take Amrah ta buge Zahra cikin rashin sani. Da sauri Zahra ta juya domin ganin waye. Dai-dai lokacin suka haɗa ido da Amrah. Chakkk Zahra ta dakata yayin da gaban kowanensu ya buga da mugun ƙarfi. Zaro idanuwa waje Umar da Sooraj suka yi. Sakin baki Zahra ta yi tare da shafa fuskantar. Kallonta Amrah ta yi domin ganin mai kama da ita sakkk. "Me nake gani haka?, wayyo Allah babu maraba dani da ita". Cewar Zahra wacce ta ƙura wa Amrah kallo. Yayin da itama Amrah abinda take yi kenen. "I can't believe this". Cewar Sooraj. "Wayyo Allah shin gamo nayi ko kuwa". Amrah ta faɗa cikin zuciyarta. "Babu maraba tsakaninsu, abinda ya bambanta su shi ne ƙwayar idanuwa". Cewar Umar wanda ya saki baki yana kallo. ****** Riƙe hannun Safira Aliyu ya yi sannan ya fita da ita. Zagayawa suka yi daidai inda su Zahra suke. Cikin rashin sa'a ƙafar Safira ya buge itace. Hakan ya sa ta sakin ƙara!. Waigawa gaba ɗaya suka yi nan take idanuwansu ya sauka kan Safira. Yayin da ita ma Safira nats idanuwa suka sauka kan su Zahra. Nan take gabanta ya faɗi!, yayin da wata iriyar razananniyar ƙara! . Ɗora hannu Zahra ta yi a kai ya ce. "Na shiga uku wai masu kama dani ɗin har guda nawa ne?, shin mafarki nake yi ko kuwa". Nan Zahra, Safira da Amrah suka haɗa baki wajan faɗin. "muɗin su waye?". Jiri ne ya fara ɗiban su ukun. Nan take kowacce a cikin su ta faɗi ƙasa sumammiya. Ba tsammani su Umar suka ga an fara wani irin iska mai haɗe da guguwa wacce karaɗe ilahirin dajin baki ɗaya. WASA FARIN GIRKI🤸‍♀️💃💃💃🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️ ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 ZINARIYAR JAJIRTATTUhttps://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *DIAMOND 💎 STAR⭐* *LADIES 🧝‍♀️🧝🏼‍♀️🧝‍♀️* (We stand together) 🤝🤝🤝 بسم الله الرحمن الرحيم *BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM* Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai! *🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 5️⃣5️⃣▶️5️⃣6️⃣ _______________________ A matuƙar tsora ce Sooraj ya nufi inda Zahra ta faɗi da mugun sauri tare da ɗago ta ya fara jijjiga ta a razane da firgici yana mai faɗin Zahra me kika aikata haka? ya za ki sha wannan abunda kika san guba ce a ciki kina da hankali kuwa". Hankalin Mami da sauran ƴan cikin falon ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin yadda Zahra ta fara fita daga cikin hayyacin ta. fusge jikin ta zahra ta yi daga jikin na Sooraj sannan ta miƙe tsaye a hankali nan take jiri ya ɗebe ta, ta faɗi a ƙasa . Da sauri Sooraj ya nufi inda take sannan ya dauke ta ya nufi waje da ita da mugun gudu saboda sauri ko ganin gabansa ba ya yi. Kai tsaye inda motarsa yake ya nufa tare da nufar side ɗin ƴan zaman banza tare da buɗe ƙofar motar sannan ya saka Zahra a cikin mota sannan ya rufe ya juya tare da shiga mazaunin driver ya sa car key ya ta da motar tare da jan motan da gudu ya fita daga cikin masarautar. tafiya yake yi ba gaggautawa tare da wani irin gudun tuki tamkar ana tseren mota. Maida kallonsa ya yi kan Zahra hankali a tashe ya ce. "Kada ki damu Zahra babu abinda zai same ki zan ceci rayuwar ki duk rantsi duku ya bazan taba bar ki ba, saboda dalilin mu bazan so a ce kin rasa rayuwar ki ba, ban sani ba ko gaskiya ne abunda su Samira suka faɗa amma tabbas na san da cewar ba zaki iya aikata abinda suka ce kin yi ba, amma ke ma me ya sa za ki sha wannan guba tunda kin san da cewa cutar dake zai yi bai kamata a ce kin sha ba, ya kamata ace anyi bincike kafin nan a gano gaskiyar lamari amma kuma kika ɗauki gubar ki ka sha gashi nan za ki mutu a banza. Ya kamata a ce kin fahimce ni ban so a ce kin sha wannan guban ba, idan kika mutu ban san wani hali zan iya shiga ba". Zahra dake kwance ta yi luff jin maganganun Sooraj ya sa ta sakin murmushi cikin zuciyarta ta ce. "Dama haka ya damu da ni shi ne kuma zai mare ni wato dai ya san ba nice na saka wannan guban ba amma kuma shi ne yake yi kamar bai sani ba, lallai dole in koya masa hankali". Buɗe idon ta guda ɗaya ta yi tare da kallon sa da gefen ido da sauri. A hankali ta buɗe idonta gaba ɗaya tare da kallon sa. A matukar tsora ce Sooraj ya dube ta sannan ya ce. "Kina lafiya?, babu abinda ya same ki?". Harara Zahra ta galla masa sannan ta saukar da glass ɗin motan tare da tofar da poison din bakinta. Mamaki ne ya kama Suraj ganin cewar bata haɗiye poison din ba. "Wai dama ashe ba haɗiye poison din nan kika yi ba ki kai kamar kin haɗiye?". Kallon baka da hankali Zahra ta bishi da shi sannan ta ce. "jaka ce ta mun gula da zan haɗiye guba?, an gaya maka bana son rayuwata ne eh?, na ce an gaya maka bana son rayuwata ne?. To in faɗa maka kawai na sha ne saboda na kawar da tunanin ku a kaina amma me zai kaini shan guba bayan ba gajiya nayi da rayuwar ba". girgiza kai Suraj ya yi sannan ya ce. "lallai yarinyar nan kin cika tantiriya kuma a hatsabibiya, wato dama baki sha wannan gubar ba shi ne kuma kika tayar mana da hankali lallai yarinyar nan sai na koya miki hankali wannan wani irin shashanci da akuyanci ne wannan ai ba daidai ba ne, me kike tunanin zai faru by mistake kika haɗiye guban?". Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "Eh ba matsala Allah ya yi lokaci na ne ya yi. Sannan ma da ka ke wani min magana ina ruwanka da ni?, ɗazun nan ka gama mari na yanzu kuma kana nuna wa kamar ka damu da ni. Ni ka bani ruwa na kuskure bakina guban yana min wani iri a baki". "Bani da ruwa, ko kinga frigde ne a cikin motan?". Cewar Sooraj wanda ya tsaya faman kallonta yayin da yake driving. Amsa Zahra ta bashi da cewa. "Na sani abu a duhu a bak'ar leda, na sani ko Kanada fridge a motarka?, ni ka kalli gaban ka kada kasa muyi hatsari, idan kaga mai shagon saida ruwa saika tsaya kaje ka siyo min". Kallon baki da hankali Sooraj ya bita da shi ya ce. "Karki samu damuwa shi kanshi mai shagon da shagon gaba ɗaya zan haɗa na kawo miki". ****************** Shiru kawai Safira ta yi yayin da taji cikin ta nayi mata ciwo alamun tana jin yunwa. Kallon Aliyu ta yi da rinannin idanuwanta cikin raunatacciyar murya ta ce. "Ina jin yunwa, ciki na yana min ciwo dan Allah ka kaini gida Please". Kallonta Aliyu ya yi ya ce. "Karki damu zan nemo mana abinci, yanzu idan na fita za su ganmu kuma su kashe mu". Cikin rashin fahimtar maganarsa Safira ta dube sa ta ce. "Su waye kuma za su ganmu kuma su kashe mu?". Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mutanen da suke neman rayuwar mahaifiyar ki da kuma taki rayuwar tare da na ƴan uwanki, sannan duk wanda ya yi nasaran kashe ki ko mahaifiyar ki da ƴan uwanki, za su samu dubbannin kuɗaɗen da ba za su misaltu ba". "What!". Safira ta faɗa cikin rashin maganarsa ta ce. "I don't understand, me Mom ta yi musu za su kashe ta?, sannan kuma wane ƴan uwa ka ke magana a kai?". Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Bawai ina nufin Mom ba, domin Mom ba ita ce mahaifiyar ki ba". Rass! Zuciyar Safira ta buga yayin da ta zaro idanuwa waje. Rai a ɓace ta ce. "Kamar ya Mom ba ita ce mahaifiyata ba?, wannan wane irin shirme ka ke faɗa aka?, idan Mom ba ita bace ta haife ni wace ts haife ni to?". Amsa Aliyu ya bata da cewa. "Mrs Lailah Abdullahi, tana ɗaya daga cikin richest women in the world, ita ɗin Aunty ta ce, kamar uwa take a waje na". "Hanya ba wani abun ka sha ba kuwa?, ni bani da wata uwa in ba Mom ba, ka daina faɗa min waɗan nan tatsuniyoyin domin ba yarda zanyi ba". ************* "Gashi yallaɓai Hajiya Binta ce ta ce na baka wannan littafin, ka bawa Zahra shi idan ka ganta". Cewar warder. Kallon littafin hannunta DPO ya yi ya ce. "Littafin mene ne kuma wannan?. Shikenen naji labarin cewar Zahra na Kano har yanzu sannan tana masarautar chan, zan je na tabbatar idan tana chan sannan na dawo da ita". Ya faɗa tare da miƙa hannu ya karɓi littafin sannan ya ajiye a gefe. ******* Sooraj kuwa chan ya hango mai saida ruwa. Parking ya yi tare da sauka sannan ya je ya siyo ruwa guda ɗaya. Saida ya ɗau lokaci Sosai Kana ya dawo cikin motan. Zuwan shi keda wuya ya ga bata cikin motan. Mamaki ne ya kama Sooraj . "Lallai ma yarinyar nan, yanzu kuma ina ta shiga". Waige-waige ya soma yi, chan idanuwansa ya sauka a kanta. Tsaye take da wasu samari guda uku suna sanye da baƙaken suit. Yayin da Zahra ke surfa musu bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba. Dafa kansa Sooraj ya yi. "Wayyo Allah, wannan wace iriyar masifa ce, wai ko ina taje saita nuna halin ta". Ya faɗa yana mai ƙarasa wa inda take. Zuwa wajan keda wuya Zahra ta ganshi. Girgiza kai Zahra ta yi ta ce . "Yauwa masha Allah kazo a dai-dai, zo ka jini da wata masifa, ina zaman-zama na waɗan nan kajin dake sanye cikin wannan abun da suka kira suit suka zo inda nake, na tambaye su me suke so suka ce wai ai zuwa suka yi su sace ni, shi ne na ce idan za su iya su sace ni". Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kema in banda abunki ai wasa suke miki". "A'a wallahi waɗan nan ba wasa suke ba, kana ganinsu yadda ka san wasu ƙasurguman masheƙa, ni kuma dai-dai nake da su". Cewar Zahra wacce ta faɗa hannunta riƙe a ƙugu tana karkaɗa su tare da karka ƙafarta yadda kasan wacce zata yi dambe. "Shi ke nen to mu tafi ko". Sooraj ya faɗa yana mai kama hannun Zahra. Nan take maza ukun da ke sanye cikin suit suka kalli juna, nan suka fito da wani abu kamar perfume tare da fesa musu. Duk abinda ke faruwa a gaban idanuwan Mk. Nan take jiri ya ɗebe su suka faɗi a ƙasa. Kwashe su mutanen suka yi tare da saka su a mota. Ganin hakan ya sa jama'a suka saki ihuu yayin da suka jifar motan kidnappers ɗin da dutsina. Da sauri kidnappers ɗin suka tada mota tare da fara ƙoƙarin barin wajan. Nan jama'a suka dinga binsu a baya har suka ɓace wa ganinsu. Da sauri Mk ya nufi inda motar Sooraj yake domin ganin idan akwai inhaler a motar domin ya san perfume da aka fesa musu zai iya affecting ɗin shi, domin kuwa ya san Sooraj yana da asma. Nan ya fara dube-dube a motar. Cikin sa'a kuwa ya ga inhaler ɗin saman kujera. Da sauri ya ɗauka sannan ya nufi motarsa da sauri tare da tada wa ya bi bayansu Zahra. Gudu suke falfalawa kamar za su tashi sama. Buɗe idanuwanta Zahra ta yi ta gansu cikin mota. Ihuuu ta buga yayin da ta fara dukan wanda ke bayan seat ɗin kusa da Sooraj. Nan take ɗaya a cikin su ya kwaɗe ta da mari. Jin marin Zahra ta yi har cikin ƙwaƙwalwarta. Nan take ta fusa ta yayin da ta kama kunnen wanda ke kusa da ita tare da fara gantsara masa cizo. Ihuuu saurayin ya buga yayin da ya fara ƙoƙarin ƙwace kanshi amma hakan ya cutura. Kuma hakan bai sa sun dakatar da tuƙin ba. Nan saurayin ya taki sa'a ta sake shi. Ganin ta saki kunnensa ya sa shi dafa kunnensa wanda ya yi jajir. Gurnani ya fara yi. Nan ya shaƙe mata wuya tare da ƙoƙarin yi mata allura kan jijiyar wuyanta. Duk abinda ke faruwa Sooraj bai sani ba, domin har izuwa wannan lokaci bai farfaɗo ba. Babu zato suka fara jiyo Sooraj yana nishi sama-sama alamun asma ɗinsa ya tashi. Ganin hakan ya sa Zahra ta sa dukannin ƙarfinta ta ture wannan saurayin. Hankali tashe ta ɗaga Sooraj tare da girgiza shi. "Yahya Sooraj me ya sa me ka?, dan Allah kada ka mutu ka barni". Cikin fitar hayyaci Sooraj ya dube ta ya ce. "Asma ɗina ya tashi kuma inhaler ɗina yana cikin motata". Zaro idanuwa waje Zahra ta yi nan take tausayin Sooraj ya kama ta. Kallon kidnappers ɗin ta yi ta ce . "Dan Allah ku mayar da mu, idan ba haka ba zai mutu, ko baku ga yana cikin mawuyacin hali ba ne". Ko kallon Zahra basu yi ba saima ƙara wa motar gudu da suka yi. Rungume Sooraj Zahra ta yi tare da ɗaukar ruwan da ya siyo ta bashi yasha. Chan cikin dajin suka isa. Tsayar da motar suka yi tare da fitowa. Sannan suka fito da Zahra da Sooraj kana suka ɗaɗɗaure su jikin bishiya sannan suka nufi inda su Amrah suke domin fito da su. Dai-dai lokacin shima Mk ya ƙaraso wajan. Da sauri ya nufi inda su Sooraj suke sannan ya bashi inhaler ya shaƙa. Dubansa Zahra ta yi ta ce. "Dan Allah ka kunce mu". "Shiiiiii!". Mk ya yi mata alama da hannu da ta yi shiru. A hankali Mk ya fara kunce su yana mai waige-waige. ****************** "Wai ni kamm Yahya Usman ina su Amrah da Yahya Umar suke?, har yanzu shiru basu dawo gida ba, ni fa ina tsoron kada wani abu na cutarwa ya cutar ds su. Cewar Khairiya. Kallonta Usman wanda ke zaune kan 3seater ya yi ya ce. "Babu abinda zai same su, insha Allah suna cikin ƙoshin lafiya, ni na matsu su dawo mu koma jigawa". Kallon su Ramlat ta yi ta ce. Ni fa ina ganin kamar akwai abinda ke tafiya ba dai-dai ba, tabbas akwai wani abu da Yahya ke ɓoye mana, kuma baya son mu sani". Kallonta Usman ya yi ya ce. "Mene ne to Yahya zai ɓoye mana?". Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Jiya na kira Abbah, munyi waya to a lokaci da muka gama wayar ya manta bai kashe wayar ba, naji yana yin magana da wani bansani ba ko mace ce ko namiji, naji yana cewa ya tabbatar su Yahya basu tsira daga gare shi ba, sannan a tabbatar an tafi da Amrah Lagos daga nan a wuce da ita ƙasar waje. Na kasa gane me ke faruwa". Kallonta Usman ya yi ya ce. "Kina nufin Abba ya sace su Amrah?". Amsa Ramlat ta bashi da cewa. "Ƙwarai kuwa tabbas ya sace su. Kenen dama Abba ba mutumin kirki bane?" ********* Ɓangaren su Umar kuwa su kidnappers ɗin na zuwa suka ga babu kowa a wajan in banda Amrah da kuma Umar. Ɗaga bindigar su suka yi kan Umar sannan suka ce. "Ina sauran mutanen suke". Kallon su Amrah ta yi ta ce. "Mun kunce su, sun gudu". "Zaku ga abinda za mu yi muku maza ku fita". Cewar ɗaya daga cikin kidnappers ɗin. Da sauri Umar ya riƙe hannun Amrah sa'anan suka fita waje. Bayan Mk ya gama kunce su Zahra. Sooraj ya riƙe hannun Zahra suka fara gudu suna nufar inda kangon yake. Dai-dai lokacin da su Amrah ke fitowa daga wajan. Take Amrah ta buge Zahra cikin rashin sani. Da sauri Zahra ta juya domin ganin waye. Dai-dai lokacin suka haɗa ido da Amrah. Chakkk Zahra ta dakata yayin da gaban kowanensu ya buga da mugun ƙarfi. Zaro idanuwa waje Umar da Sooraj suka yi. Sakin baki Zahra ta yi tare da shafa fuskantar. Kallonta Amrah ta yi domin ganin mai kama da ita sakkk. "Me nake gani haka?, wayyo Allah babu maraba dani da ita". Cewar Zahra wacce ta ƙura wa Amrah kallo. Yayin da itama Amrah abinda take yi kenen. "I can't believe this". Cewar Sooraj. "Wayyo Allah shin gamo nayi ko kuwa". Amrah ta faɗa cikin zuciyarta. "Babu maraba tsakaninsu, abinda ya bambanta su shi ne ƙwayar idanuwa". Cewar Umar wanda ya saki baki yana kallo. ****** Riƙe hannun Safira Aliyu ya yi sannan ya fita da ita. Zagayawa suka yi daidai inda su Zahra suke. Cikin rashin sa'a ƙafar Safira ya buge itace. Hakan ya sa ta sakin ƙara!. Waigawa gaba ɗaya suka yi nan take idanuwansu ya sauka kan Safira. Yayin da ita ma Safira nats idanuwa suka sauka kan su Zahra. Nan take gabanta ya faɗi!, yayin da wata iriyar razananniyar ƙara! . Ɗora hannu Zahra ta yi a kai ya ce. "Na shiga uku wai masu kama dani ɗin har guda nawa ne?, shin mafarki nake yi ko kuwa". Nan Zahra, Safira da Amrah suka haɗa baki wajan faɗin. "muɗin su waye?". Jiri ne ya fara ɗiban su ukun. Nan take kowacce a cikin su ta faɗi ƙasa sumammiya. Ba tsammani su Umar suka ga an fara wani irin iska mai haɗe da guguwa wacce karaɗe ilahirin dajin baki ɗaya. WASA FARIN GIRKI🤸‍♀️💃💃💃🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️ END OF BOOK 📚 1 ALƘALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 ZINARIYAR JAJIRTATTU