[5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: KUDIRAR ALLAH BOOK 2. (Don Allah ku zamo masu rik’on amana, idan kin san kin siyi littafina ne don ki watsa shi a duniya don Allah tun ban yi nisa ba ki gaya min na dawo miki da ku’dinki. Ina yin littafi kyauta Amma wannan dai ban yi niyya ba. Don haka pls ku kiyaye kada mu zo muna samun rashin fahimta da mutum kuma ya k’ulla ce ni, Allah yasa ku ji kuma ku bi, idan kun bani ha’din kai zaku ji da’din harka da ni In sha Allah.🤗) 08033748387. . Da yawa daga cikinsu k’wak’walwar su da tunaninsu ya daina aiki na wuncin gadi. Tsoro da fargaba ya ziyarcesu suka rasa sukuni a zuciyarsu. Harta Sarki wani irin gumi yake yarfarwa. Bai tab’a tunanin abubuwan da suke ji a tatsuniya za su iya kasancewa a gaske ba, wato Fatalwa! Shin dama wanda ya mutu yana dawowa ne? Shine tambayar da ya yiwa kansa a zatonsa a zucuayrsa ya yi tambayar sai dai kallon da fadawa suka masa ya saka shi sanin cewa lallai a zahiri ya yi maganar. Don suma da alama tambayar da suke son yi kenan sai dai zuciyar kowa da bakin kowa ya kasa bari ya yi furucin tsoro ne sosai a ransu, ji suke kamar su dare su bar wajen. Wani abu ne da kai tsaye za’a iya kira ALMARA ko irin mafarkin nan mai wuyar sha’ani. Su kansu matan Sarki sun girgiza da ganin wannan baiwar Allahn idanunsu duk a waje suke suna cigaba da kallon Fatalwar matar a tsaye a gabansu tana sakin murmushi cikin isa da ginshira kamar dai yarda take kasancewa a lokutan da suka gabata. Fulani Saddik’a kanta a firgicen take, balle Fulani Raheena da take jin kamar ta saki fitsari a wando. Ta runtse ido ta bu’de ya fi a k’irga duk don ta tabbatar ba wancan rud’anin mafarkin da ta saba ba ne. Nene ma da k’arfin gaske take yafito yawun bakinta take ha’diya don yawun bakin gaba d’aya ya k’afe k’af, jin mak’ogoronta take a bushe kamar baa tab’a halittar yawu a wajen ba. Suna yara sanda abubuwan suka faru har ta rasa ranta amma sam hakan ba zai saka ta manta da fuskar matar ba. Ta girmesu a shekaru amma alherinta ga al’umma kamar ba jinin sarauta ba yasa ta samu soyayyar jama’a kowa yake rububinta da gasken gaske. Abubuwan suka dinga dawo mata kamar majigi a kwanyarta ta dinga kallonsu kamar wancan lokacin da abubuwan suke faruwa a zahiri. Hannun Najee ta kama ta damk’e da k’arfin gaske tana sake runtse idonta zuciyarta na bugu saboda razanar da take ciki. Idan har ya tabbata ba mutuwa ta yi ba tabbas akwai gagarumar k’ura a masarautar gabas! Najee ta juyo tana kallon yarda hannayenta suke kakkarwa a tsorace ta ce “Nene lafiya menene?” Yatsanta ta saka a baki alamar ta yi shiru tana girgiza mata kai idanunta cikin na Najwan itama Najwan ita take kallo tana mamakin yarda idanun Nene suka jirkita zuwa jajaye sosai da alama tashin hankalin da take ciki ba shi da ma’auni balle a taskance mizanin sa. Sai itama ta ji tata zuciyar ta firgita bata san sanda ta koma jikin Nenen ta lafe ba tana danne k’irjinta da yake bugawa da k’arfin gaske. Sarki Mukhtar ya cigaba da kallonta ita d’in ma shi take kallo kafin ta saki murmushi tana fisgar leb’enta. Sannan ta sauke idanunta akan Hadiman da cikinsu har da me rawar d’ari. “Kuna mamakin dawowata ne bayan kun binne ni a kushewa.” Sai ta lumshe ido hawaye suna bin k’uncinta. “Allah ya nufi dawowata cikin Amincinsa bayan dawowartawa kuma sai yasa na dawo har da y’ay’ana na halak malak. Bayan Murad da kuke gani akwai k’aninsa Jaheed, wanda ya yi aure yana da matansa biyu, a yanzu ne zaku fuskanci duk abinda Allah ya so ko ana muzuru ana shawo sai Allah ya k’addara nufarsa.” Ta fa’da tana sakin murmushi ta cigaba da takun isarta zuwa inda sarki yake a zaune ta zauna a gefensa kujerar da ba wanda ya isa ya hau sai shi ba wanda ya tab’a kwatanta hawanta har ta da Fulani Raheena da ake ganin ta cika ta tumbatsa. Wannan karan Nene kanta a cikin firgici take jin ashe matar wai ta san Jaheed to ta ina? Ta ina kuma suka zama y’ay’anta da har take bibiyar rayuwarsu har ta san sun yi aure? Kada dai da gaske su Jaheed y’ay’anta ne, to ta yaya ta ina kuma? Ji ta yi kanta yana wani irin sarawa ta kama hannun Najee ta sake damk’e wa da kyau kamar dai Najeen ce zata tsareta daga dukkan abin cutarwa. “Ina raye mai martaba ban mutu ba, ka daina min kallon fatalwa am still alive and am still your’s favorite person…..” ta fa’da tana saka idanunta cikin na Sarkin da ya gama ru’dewa sai dai izza da isa ta mulki ta hana shi bayyana hakan ya daure ya jure ya d’aga mata kai alamar ya gamsu, duk da har a zuciyarsa bai gama gamsuwar ba. “A tashi taron nan mai martaba bana buk’atarsa don ni na yiwa yaro na mata zarka’ded’iya ba wacce kuke so ku Aura masa ba, tuni an d’aura masa aure… don haka yanzu nake son a sallamesu.” Ba wani Ja Sarki ya kalli Bafadensa d’aya ya masa alamar da ya sallami jama’ar wajen. Take kuwa aka sanar da mutane an fasa wannan aure don haka kowa ya tafi. Aka rufe sarki don ya mik’e ya shiga cikin zabgegiyar motarsa matar tana gefensa kamar ta shige jikinsa ta bi bayansa suka shiga motar mutane sam ba su yi mamaki ba, don sun san duk wanda sarki zai so a rayuwa to bayan Tauraruwa ne sunan da yake gaya mata kenan a zamanin da take raye. Murad ta yafito da hannu ta masa alamar da ya shiga da sauri ya girgiza kai yana kallon Mamma da ta kafa masa ido don haka kai tsaye ya bi bayan Mamma. Tauraruwa ta saki murmushi kawai tana girgiza kai. Aka ja motar Sarki zuwa fadarsa ta cikin gida. Fulani Raheena kasa jiran motar ta yi sabida yarda zuciyarta take a hautsine da sauri ta bi ta wata siririyar hanya don isa sashenta tana jin duk duniya ba wanda ya kai ya tashin hankali, duk da ba ita ta aikata komai ba amma ta san komai ta san kuma wa’danda suka aikata. Sauri take kamar zata tashi sama bata bari kowa ya ganta ba balle a bita ta shige sashenta, ta mayar da k’ofar ta rufe da k’arfin gaske, rufewarta ta ya yi daidai da bugun zuciyarta kamar zata b’alle k’irjin ta fito. Ta fige mayafin kanta da alkyabbar da ta jik’e da gumi kamar ta shiga ruwan sama. Har ta suman kanta d’igar gumin take, zaman dirshan ta yi a k’asa tana tura yatsun hannunta cikin sumar kanta da ta tashi kamar ta mahaukata a firgicen ta ce “Na shiga uku ni Raheena? Komai ya lalace min dama wannan matar ba ta mutu ba, suka min k’arya ta mutu suka saka na sakankance da cikar dukka burikana, wayyo Allah na ni Raheena tabbas b’aragurbin k’wan gab yake da fashewa warinsa kuma zai iya kashe al’umma da dama a cikin Garin Gabas. Bata san hawaye take ba sai da ta ji d’igar su a saman harshenta ta lumshe ido tana sake datse leb’enta. A fili ta furta “Kun cuceni! Kun jefa ni a Ramin da ba mai iya fitar da ni sai Allah, sai dai ina tabbatar muku wannan abin har ku zai shafa Ba Raheenatu ita ka’dai ba.” Ta fa’da tana sake hargutse sumar kanta. Bugun k’ofar da ake ne a sassanta ya saka cikinta sake hautsinawa da sauri ta fa’da toilet gudawa ta yi sosai kafin ta fito ta nufi parlourn ba tare da ta rufe kan nata ba ta ce “Waye ne?” “Wanda kika san zai zo.” Aka furta daga can. Raheena ta ware ido tana mamakin jin Muryar yau a zahiri duk da da sai dai ta ji ta a cikin waya ko a cikin duhu. Da sauri ta saka hannu ta zare mukullin tana murnar ganin ko wane shege ne mai bata umarnin da sam bata iya ja da shi a zahiri. Idanunsu ne suka sark’afe cikin na Juna hanjin cikin ta ya sake hautsinawa ta bu’de idonta a razane ta ce “What? Dama kai ne?” Murmushi ya sakar mata yana tureta gefe ya shiga cikin parlourn bayan ya mayar da k’ofar ya rufe ta ruf. Ya k’are wa d’akin kallo kafin ya mayar da kallonsa kan Raheenan da idanunta still suke a waje gashin kanta da yanayinta ya nuna ta a matsayin mahaukaciya sabon kamu. Murmushi ya saki ya ce “Tun yanzu Raheena? Tun komai ma bai faru ba na gan ki a haka? Ina ga idan wad’ancan sirrikan suka bankad’a. Kin ga zauna magana nazo mu yi ta nutsuwa. Idan kika sake kika bayyana sirrin da ya da’de lullub’e a cikin k’asa wallahil azeem sai na sanar da sarki wacece ke? Bana son jin sunana a maganar kisan Tauraruwa don na san kin san komai duk da ba hannun ki a ciki, wallahi kika sake kika tona mana asiri sunan naki sirrin banka’dadde.” Ya fa’da yana sakin dariya sannan ya juya ya fice da sauri duk da a firgicin yake shima hakan bai hana shi nuna jarumta ba da nuna bai san komai ba. Raheena ta bi bayansa da kallo tana jin tashin hankalinta na sake hauhawa me yake nufi? Ta b’oye laifinsa da kai tsaye za’a jingina mata laifin ko me? Shikkenan ita Raheena ta zama mai laifi kashi kashi kenan? Idan kuma bata b’oye laifin ba haka na nufin fashewar b’aragurbin k’wan kenan? Cabd’ijam! Tabbas Ni Raheena ina cikin matsala. Ta furta a fili. Fulani Saddik’a kuwa jikinta a salub’e yake sosai, duk wani karsashinta ya gudu sai tsoro da jin kamar shikkanan za’a rabata da Murad da take jin sa kamar gudan jininta. Ta shiga sashenta hannunta cikin na Murad da sam ya kasa sukuni da walwala shima zuciyarsa a cikin ru’danin take, neman wanda zai sanar da shi wacece waccan matar yake? Yana jin nauyi da kunyar tambayar Mamma duk da itace Tambayar da son amsarta ya fi kowace tambaya a wajensa. Maganar matar da take ikirarin aura masa ba matsalar sa ba ce muddin matar bata masa ba sakin ta zai yi, ba ruwansa da wai itace mahaifiyarsa me yasa tana son sa ta wullar da shi kuma wanene Jaheed da har take kiransa d’an uwansa? Fulani Saddik’a cikin d’akinta ta shigar da shi. Kafin ta koma kitchen ta ha’da masa tea mai lipton zalla don dai ta san cikinsa yau kam bai ga abinci ba, kamar yarda nata itama bai gani ba. Kanta a d’aure yake da tarin tambayoyi sai dai bata bari hakan ya bayyana akan fuskarta ba. Ta d’ebo tea d’in bayan ta soya masa scramble egg ta fito da su zuwa d’akin nata. A zube yake a k’asan carpet ya yi pillowa da hannayensa yana kallon ceiling. Ta saki ajiyar zuciya tana furta “Murad me ye haka? Sarki guda mai jiran gado a zube a k’asa, tashi maza ka sha tea idan ba so kake ka sake d’aga min hankali ba.” Ya mik’e kamar yarda take so ya kuma karb’i cup d’in a hannunta bai yi la’akari da zafin sa ba ya kafa A bakinsa. Da sauri ta kalleshi sai dai kafin ta yi magana ya zuk’eshi tas yana mayar da numfashi. A tsorace ta kalleshi “Me ye haka Murad? Kana cikin hankalinka kuwa?” Da k’arfin gaske ya runtse idonsa ya furta “Bana ciki Mamma, ina son sanin wacece waccan matar?” Da sauri Fulani Saddik’a ta kafa masa ido, tana son karantar yanayin da yake ciki. Tsoro ne ya kamata ganin kamar Murad cikin zakwa’din son sanin mahaifiyarsa yake, idan kuwa hakane ya zama na ita zata tashi a tutar babu. Da sauri ta dakatar da zuciyar ta ta kuma ha’de rai tana kallonsa ta ce “Me kake son sani game da ita? Kana son ka san ko itace mahaifiyarka a zahiri? Me hakan yake nufi akwai inda na tauyeka ne?” Ta fa’da cikin yanayi mai nuna zallar b’acin ranta. Wannan karan abin da ta yi bai da Murad ya ji zuciyarsa ta canja daga zakwa’din son sanin ainahin mahaifiyarsa ba da ma d’an uwansa guda da zai kira tilo, sai dai gudun b’acin ranta sai ya danne damuwarsa ya koma ya kwanta kamar yarda yake a da, sai dai yanzu ya lumshe ido ne yana cigaba da saurarar sak’a da warwara da zuciyarsa take masa. Fulani Saddik’a ta saki ajiyar zuciya tana mik’ewa ganin kamar barci ya d’aukeshi ta fice daga d’akin da sauri don isa wajen su Nene da take tunanin acan duk amsoshin tambayoyinta su ke. Yanayin da ta bu’de k’ofar zai tabbatar maka da ta na cikin rashin nutsuwa. Nene da suma suke cikin rashin nutsuwar suka d’ago da sauri suna kallonta. Fuska ba walwala ta isa wajen su, ba tare da ta rufe k’ofar ba. Ta zauna idanunta cikin na Nene ta ce “Ki sanar da ni wacece ke? Sannan kuma ina son sanin shin abinda kika fa’da min da gaske ne ke kika haifi Murad ko kuwa?” Nene ta saukar da idanunta k’asa kafin ta jijjiga kai ta ce “K’warai har a yanzu bana manta rad’ad’i da zafin naku’dar haihuwar Murad da na yi nice mahaifiyarsa abinda yake bani tsoro waccen matar da ta bayyana kanta a matsayin mahaifiyarsu tabbas shine irin turaren da nake ji a jikin matar da ta taimakeni a wancan lokacin….” Da sauri Fulani Saddik’a ta bu’de manyan idanunta ta ce “Da gaske?” Nene ta ce k’warai kuwa ban mance ba, sanda ta ke taimakona ina nak’udar Murad ita kuma ta bani mak’udan ku’dad’e da gwalagwalai ta ce na nesanta kai na daga masarautar gabas kada na sake dawowa don akwai mutanen da suke jiran rayuwata abinda yasa kenan na yi nisa da garin nan, amma tabbas ni na yi nak’udar haihuwar Murad na kuma d’aukeshi a cikin tsawon watanni tar……. Yawun bakinta ne ya k’afe ganin Murad yana tsaye idanunsa cikin na Nene da ta ha’diye sauran maganar a cikinta. Yana nuna ta da yatsa ya ce “Ke ce magaifiyata? Me yasa kika b’oye min?” Ya fa’da yana zubewa a gabanta…. JIKAR NASHE✍🏽🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: (*** Da dai ba zan yi magana ba, amma fisabilillah an min abinda ban ji da’di ba, sai da na rok’eku akan kada a Fidda min littafi sai gashi har ya fara galantoyi a gari saboda son zuciya akan 500 ki ja min asara da yawa. Ina littafin kyauta amma wannan tunda kuka ji na ce na ku’dine me yasa ba zaku bar ni na ci gajiyarsa ba nima, ko ban ce komai ba na tabbata Rabbi yana ji kuma yana gani. 😟😭 littafi nawa na yi kyauta?***) Tauraruwa itace mace mafi soyuwa a gareni fiye da kowa da komai a duniya, ciki kuwa har da ku dama duka mata na gaba d’aya. Ina son Tauraruwa irin son da ba zan iya kwatantashi da komai ba, sanda labarin rasuwar ta ya iskeni sai da na yi jinyar zuciyata sosai kafin na koma yarda nake da, duk da dai duk wanda ya san ni da yasa ba Mukhtar bane na canja zuwa wani mutum mai yawan shiru da tunani ba don komai ba sai don ji nake kamar na rasa wani b’angare na zuciyata. Dukkan wani farin ciki na yana tattare da rayuwa da Tauraruwa ne, don haka yanzu nake jin zuciyata ta dawo sabuwa dal irin zuciyar da tauraruwa ta tafi ta barta da kewarta da tunaninta. Na yi kewar hirar Tauraruwa murmushinta rigimarta da saurin fushinta, don haka Murad ina umartarka ka so Tauraruwa ka bi kuma dukkan abinda tace in dai kana son farin ciki na, watarana da kanta zata zaunar da kai ta baka labarin yarda aka yi kazo duniya, na tabbata banda taimakon tauraruwa da har yanzu banda Magaji… tauraruwa ce silar samuwarku a duniyar nan…” Sarki Mukhtar ya fa’da yana d’auke k’wallar idanunsa abinda bai tab’a yi a gaban Murad ba. Shi kansa Murad nasa jikin ne ya yi sanyi ya tabbata soyayyar Sarki ga tauraruwa girmanta ya zarce kwatance… Yana share k’wallar ya cigaba da fa’din “Bana fatan Allah ya sake maimaita min ranar da labarin mutuwar Tauraruwa ya riskeni, ba zaka santa ba ko a hoto dalili ni na yi umarni a kawar da duk wani abu da zai dinga tuna min da ita ciki kuwa har da hotunanta na kuma yi umarnin idan ba ni na amince ba ban yarda wani ko wata a cikin masarautar nan ya sake tuna min da ita ba, don na tabbata a duk sanda aka sake ambata min ita ko hotonta zan sake shiga tashin hankali duk da hoton nata sam bai b’ace min a zuciya da ruhina ba, ina sanar maka zan iya rasa komai da kowa idan har Zan samu tauraruwa a raye kuma tana tare da ni muna cikin walwala da nisha’di kamar lokutan baya, Murad ka so Tauraruwa in dai kana buk’atar soyayya ta……” Shiru Murad ya yi yana mayar da numfashi a hankali ga tambayoyi fal a cikinsa amma mamakin furucin sarki yasa ya kasa magana sai lumshe idanunsa kawai da ya yi,zuciyarsa na bashi shawarar ya tsaya ya yi bincike da nutsuwa har ya gano komai a hankali. Don haka ya mik’e a hankali zai fice daidai lokacin da tauraruwa ta fito daga d’aki tana zabga k’amshin turare murmushi ta sakarwa Murad d’in tana neman wajen zama. Fuskarsa a ha’de ya d’an dubeta kafin ya d’auke kai yana mamakin kamanceceniyar da suka yi mai taken kwabo da kwabo. Bata masa magana ba har ya fice daga d’akin. Baya buk’atar magana don haka kai tsaye d’akinsa ya wuce. Mai martaba kuwa kallon Tauraruwa yake fara’a fal fuskarsa kafin ya ce “Ta yaya kika samu cika min buri na bayan fitar da raina akan haihuwa ina son sani?” Dariya ta yi mai ha’de da shashshek’a kafin ta ce “Ka k’addara faruwar hakan a matsayin KUDIRAR ALLAH ni kai na ba wayo na ko dabarata ba ce Suka ba ni haka, duk abinda na aikata d’in na aikata ne Saboda kai da kuma ni, Alhamdulillah a yanzu dukka burikana sun cika, zan bayyana maka komai ba amma ba yau ba sai rana ita yau ranar da Amaryar Murad zata tare a cikin taron mutanen zan sanar da kowa yarda duk abubuwan da suka faru, na yi alk’awarin bayyana gaskiyar lamari a ranar, ba zan b’oye komai ba samuwar cikinsu haihuwarsu da kuma ko su waye suke da hannu a cikin kisa na, da hanaka samun zuri’a.” Sarki ya jijjiga kai ya tabbata Tunda ta ce zata fa’di gaskiya ta kafe kuma sai ranar ya san zata fa’da d’in ba zai takurata ba zai jira lokaci ya san ko zai mutu yana rok’arta ba zata janye k’udirinta ba, Tauraruwa na da kafiya da naci ha’de da tsayawa akan abinda take so daidai ko akasin sa. “Allah ya kai mu” ya furta murya a tausashe yana sakin murmushi. Itama murmushin ta saki ta cikin idonsa ta hango yarda ya k’agu da son sanin labarin sai dai ya danne ne gudun b’acin ranta, haka yake dama tuntuni yana sadaukar da nasa farin cikin da wanzuwar nata farin cikin koda baya so. **Najwa kuwa zubawa Nene ido ta yi tana mamakin yanayin da ta shiga na dogon tunani. Murya a raunane ta dafata tana furta “Kada ki sawa kan ki damuwa fa Nene.” Girgiza kai ta yi “Ba damuwa na yi ba Najee, ina tunanin yarda k’addara ke watangaririya da rayuwata ne yau fari gobe tsumma, babban takaici na rashin sanin takaimaimai inda Iyayena suke suna raye ko sun mutu.” Najee ta d’aga kai ta ce “Dole za ki damu na sani amma ki saka a ranki duk wani bawa baya wuce k’addararsa mai kyau ko akasinta, ta ki jarrabwarce ta zo a haka In sha Allah kuma kin kusa amsata daidai nasara na tafe In sha Allah.” Nene ta zuba mata ido cike da k’aunarta ta ce “Allah yasa Najee, idan kuma k’addara ta sa Sarki ya min mummunan hukunci ina rok’on Ubangiji ya baku wuyan d’auka.” Ta fa’da tana share zufar da take kwaranyo mata har saman wuyanta. “Kira min Umma d’azu kin ce ta kira bana cikin yanayin da zan iya amsa waya, yanzu kuwa na samu nutsuwa kad’an da na sanar da Murad nice mahaifiyarsa.” Najee ta ciro wayar a jakarta tana danna kiran layin Umma tana sake maimaita sunan Murad a ranta zuciyarta cike da tsanarsa da jin haushin kallon wulak’ancin da yake mata “Matarka ta shiga uku!” Ta furta a zuciyarta ba tare da sanin cewa maganar tata ta fito fili ba. Nene ta bita da kallo tana murmushi ta ce “Wa kenan?” Da sauri Najee ta jijjiga kai sai kuma kunya ta kamata ganin kamar Nene ta gano wanda take nufi ba zata so ace ta zagi d’an a gaban Uwarsa ba don haka ta bagarar da zancen tana kara wayar a kunnen Nene ta ce “Ga Umman.” Nene ta amsa tana sakin murmushi zuciyarta na sak’a mata abinda kai tsaye zata kira almara auren Murad da Najee gwara ma dai a tsaya a Jaheed d’in shine mai sanyin hali, ba Murad mai zafin zuciya ga k’arfin izzar mulki da na Soja a tare da shi, ya yiwa Najee girma halayensa bana rik’on k’aramar yarinya mai k’ananun shekaru irin Najee ba ne. “Nene ba kya ji ne?” Umma ta fa’da daga d’ayan b’angaren jin Nenen ta yi shiru bata ce komai ba. Ajiyar zuciya mai k’arfi ta sauke kafin ta ce “Ina ji Umman yara, an yi sallah lafiya? Kin ji ba mu kira ba ko wani al’amarine mai girma ya hana mu kira.” Nan ta shiga bawa Umman labari. Cikin mamaki da al’ajabi Umman ta ce “Ikon rabbi! Yanzu ya kenan? Ga shi Baffa gobe zai dawo bana son ya dawo bai tarar da ku ba, ko Najee zan saka a d’auko min idan yaso ke sai ince kina wajen Hajja Kaka bana son ya gane kuna masarauta.” Nene ta d’an yi Jim don sam bata son Najeen ta tafi, sai dai Umma ta fita gaskiya tabbas idan Baffa ya koma ba su koma ba akwai matsala don haka murya a raunane ta ce “Ko dai mu taho gaba d’aya?” Umma ta girgiza kai kamar Nenen na ganinta ta ce “A’a Ai ke bai kamata ki taho ba ki yi zamanki mu ga abinda hali ya yi, idan da yiwuwar mu taho taya murna sai mu rankayo gaba d’aya…” Nene dai ta saki murmushi kawai ba tare da zuciyarta ta amince za’a zo tayata murnar ba, ba mamaki ma a mata d’aurin talala. “Faruk zai zo yau komai dare ya taho da ita, don Allah Nene ki kula kada a samu matsala.” Muryarta cike da rauni ta ce “To” ta zare wayar a kunnenta tana jin duk gangar jikinta na sanyi saboda rashin sanin madafa. Najee idanunta tsura mata tana mamakin canjawarta “Nene me ya faru?” Nenen ta d’ago tana kallonta sai ta ke ji a ranta kamar ta rabu da Najeen kenan idan suka tafi ba zasu sake waiwayarta ba, wani babban al’amarin zai faru. A sanyaye ta ce “Umma ta ce ki shirya yau Faruk zai zo ya tafi da ke gobe Baffa zai dawo kada ya dawo bai samemu ba.” Najee wani irin dum ta ji kanta ya yi, sai ta ji zuciyarta bata son rabuwa da Nenen wasu tarin k’walla suka fara karakaina akan k’uncinta. Murya a raunane ta ce “Bana son na bar ki Nene.” “Nima bana so Najee amma haka dole zamu hak’ura kada mu jawowa Umma matsala.” Najee ta yi shiru tun daga wannan maganar sai jikinsu ya yi sanyi suka zauna a d’akin ba mai cewa komai. Fulani Saddik’a kuwa tun da lamarin ya faru ta kasa gasgata abinda idanunta suka gani, Tauraruwa a raye? Kada dai fa duk wa’dancan Umarnin da ake bata Tauraruwar ce take bata, idan haka ne me yasa ta nunawa jama’a cewa ta mutu alhali tana raye. Ta janyo wayarta tana kallon numberr da kai tsaye ake kiranta zuciyarta na sake tsinke wa idan har ta tabbata tauraruwa ce take bata umarnin tabbas akwai lauje cikin na’di. Ta kai gwauro ta kai mari cikin d’akin tana sake kiran wayar da har a lokacin ake sanar da ita a kashe take wayar, kamar lokutan baya da take yawan kiran layin baya shiga in dai ba su suka kira ta ba. Bata san sanda ta yi cilli da wayar ba cikin takaici tana bin wayar da harara kamar ita ta mata laifi. ** K’arfe hu’du Faruk ya isa Fadar suka gaisa da Bafaden nan mutuminsa mai karb’ar cin hanci. Sannan ya kira Nene ya sanar da shi zuwansa cikin masarautar. Nene hankali tashe ta dubi Najee da take zaune tsuru fuskarta a ha’de alamu sun nuna sam bata son tafiya. Dafata ta yi tana furta mu je ki yiwa Fulani sallama. A k’aramin parlourn Fulanin suka tarar da ita. Ta zuba musu ido kawai har suka gama bayani bata dakatar da su ba, sai da ta tabbatar sun gama sannan ta ja ajiyar zuciya ta mik’e ta isa d’aki wata sark’a mai kyau ta d’auko ta gold ta mik’awa Najee tana furta “Ki gaida Mamanki kafin mu zo har gida yi musu godiya.” Najee ta amsa tana d’aga kai. Suka fice daga d’akin. Tun daga nesa Faruk yake kallonsu dariya yake sosai ganin yarda kamannin Najee suka sauya gaba d’aya. Baki ta turo gaba ta ce “Ya Faruk bana so fa!” Ya gaisa da Nene sannan suka mata sallama tana d’aga musu hannu suka fice da motar. Hawaye ta ji yana bin k’uncinta. Baffa ya dawo cikin k’oshin lafiya bai lura da rashin Nene ba don ko tambayar ta bai yi ba. Yana zaune yana cin alkubus da miyar taushe. Umma ta ce “Baffan Yara Najma fa ciki ne da ita” Da sauri ya d’ago kai yana kallonta kafin ya furta “Da gaske?” Umma ta d’aga masa kai “Allah ya nufa dole sai ta samu d’a da Jaheed sai dai ayi fatan Allah ya raba lafiya… sai kuma ka sanar da Jaheed d’in” Baffa ya d’aga kai yana furta “Shima yana daf da zuwa, haka ya ce min In sha Allah.” Ya wanke hannunsa yana dawowa ya d’au cup d’in zob’on yana sha kafin ya kalli cikin idon Umma ya ce “Ina Nene kira min ita…..” JIKAR NASHE.✍🏽🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Jikin Nene ne ya fara rawa ganin yarda Murad ya gigije hannunsa na rawa ya damk’i nata hannun, cikin rashin nutsuwa ya fara furta gaya min mana, gaya min ta yarda nazo duniya ina son sani please!” Nene damk’e nata hannun ta yi cikin nasa zuciyarsu na bugawa lokaci guda kamar yau suka fara ganin juna haka suka zubawa junansu ido, kafin Murad ya kai mata wata irin runguma yana sakin numfashi a hankali wata irin nutsuwa da sanyi na shiga zuciyarsa daga jin yarda jikinsa yake amsar sak’on bugun zuciyarta ya tabbata da gaske itace mahaifiyarsa, yarda ya lura tun fara ganin matar ya ji duk duniya ba abu mafi soyuwa a wajensa kamar ita, baya gajiya da kallonta kamar yarda kunnuwansa basa gajiya wajen saurarar tausasan lafazinta. Shiru Nene ta yi itama wani farin ciki na ratsa zuciya da gangar jikinta sai yau ta tabbatar da mafarki yana iya zama gaske ashe, ta sha yin irin wannan mafarkin tana ganin Murad kwance a jikinta yana kuka da farin cikin ganinta. Fulani Saddik’a har ma da Najee hawaye suke sharewa ba na komai ba sai na zallar tausayinsu da gaske duk wanda ya raba uwa da mahaifiya akwai cutarwa mai girman gaske zai kuma gamu da Allah. Tunda take ba ta tab’a ganin raunin Murad ba kamar yarda ta gani a idanunsa yanzun. Tsawon lokaci yana kukan da ba wanda ya hana shi ya da’de a rayuwarsa zuciyarsa cikin k’unci da rashin walwala sai dai yana b’oye hakan gudun b’acin ran Mamma da take ba shi duk wata kulawa da d’a yake buk’ata ga mahaifiyarsa, amma yau ya gaza ya kasa danne abinda yake ransa har sai da rauninsa ya bayyana akan idanunsa da fuskarsa bai ji kunyar Mamma ba ya rungume Uwar da ya da’de yana mafarkin jin d’umin jikinta cikin nasa jikin. Tsawon lokaci yana haka kafin ya zame jikinsa yana mayar da ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa a hankali yana furta “Ina son sanin yarda nazo duniya, ina kuma jin tsoron a furta ni shege ne tunda Maimartaba ya tabbatar bai aureki ba, ta yaya kika samu cikin mai martaba a jikin ki ba tare da aure ba?” Ya fa’da idanunsa akan Najee data zuba masa ido ya zabga mata harara kafin ya d’auke kai yana furta “Bar nan wajen kafin na saka k’afa na doke shegen dogon bakin ki.” Bakin ta sake turowa gaba ta mik’e ta fice daga d’akin. Murad ya bita da kallo yana tsaki k’asa k’asa baya fatan Najee ta zama k’anwarsa ta jini. Mamma kafa masa ido ta yi tana hango irin yarda fuskarsa ta washe daga wancan duhun da take gani a lokutan baya, wannan Murad d’in wani ne daban mai matsananciyar fara’a da walwala, fuskarsa ta nuna d’okin son sanin asalinsa, itama tana da burin sanin hakan don haka bata togaceshi daga tambayar ba suka taru suka zubawa Nene ido suna jiran k’arin bayani, duk da ta san Nenen ba ta da ta cewa kamar yarda ta sanar da ita bata san komai ba, ta dai wayi gari taga ciki a jikinta aka kuma tabbatar mata da cikin d’an sarki ne na halak a jikinta. Murya cikin rashin karsashi Nene ta ce “Ban sani ba Murad, ban san duk yarda abubuwan nan suka kasance ba, abu guda na sani ni na yi nak’udarka na haifeka da kai na Wallahi har a yanzu ban mance ra’dad’in nak’udarka ba.” Murad shiru ya yi yana murza hab’arsa yana nazarin maganar Nene zuciyarsa na sake gasgata masa abinda yake tunani DASHEN CIKIN aka mata amma wanene kuma menene dalili? Idan har dashe ne zai zama daga matan sarki tunda ance shi d’in DAN HALAK NE BA SHEGE BA. Wacece waccan matar? Da sauri ya mik’e ya fara nufar tafiya burinsa ya je wajen mai martaba ya sanar da shi wacece tauraruwa? ____________ Tun bayan isar su turakar mai martaba ta mayar da k’ofa ta rufe tana nazarin d’akin da k’amshinsa yasa ta fara tuna duk wata rayuwarta ta baya komai a d’akin bak’o ne a wajenta idan banda Maimartaba da bai sake mata daga mutumin da ta sani ba, barin ma yanzu da take zaune daf da shi yana sanye cikin jamfa da wando kansa ko hula babu. Ya zuba mata ido yana mamakin yarda aka yi ta rayu tsawon shekaru talatin ba tare da ya ji a jikinsa cewa tana raye ba, me yasa ta b’oye masa sai yanzu taga damar bayyana kanta bagatatan, shin bata san irin yanayin da ya shiga ba tun bayan rasuwarta bata san da k’yar walwalar sa ta dawo ba. Haushi take ba shi ta yarda ta bagarar da lamarinsa tsawon wad’annan shekarun don haka ya kasa ce mata komai illa zuba mata manyan maganansa da ya yi, yana mata kallo da ta tabbatar na tuhuma ne da neman ba’asi. Sai dai ta k’i furta komai kamar yarda yake so illa juya cup d’in futar hannunta da take cikin nisha’di tana sakin walwala ta kai cup d’in furar bakinsa kamar yarda ta saba a Zamanin baya in dai tana kusa ita take ciyar da shi ta shayar da shi bata amince wani ya ba shi komai ba sai ita da kanta. Kamar zai bu’de bakin ya sha sai kuma ya doke hannunta furar ta zube musu a jiki gaba d’aya. Murmushi ta saki tana furta “Haba mai martaba Tauraruwarka ce fa, Sadauki baya fushi da tauraruwarsa ina neman afuwa ka sha furar nan zan sanar da kai yarda duk abubuwan Suka faru a haka da kuma dalilina na aikata hakan.” Haka kawai ya ji zuciyarsa na rawa ya ji kuma yana son k’aryatata sai ta ga ya mik’a da sauri ya fisge d’ankwalin da yake kanta da mayafin da yake kanta. Gashinta ya ja sosai ya duba tsakiyar kanta sai ga abinda yake nema a bayan wuyanta wata babbar tawadar Allah ce a gefen wuyanta, ya mayar da gashin nata da ya kwanta har gadon bayanta yana sakin ajiyar zuciya. Kallonsa take tana sakin murmushi ta ce “So that yanzu ka yarda nice dai Tauraruwarka ba fuska na saka ba ko?” Ya d’aga kai a hankali kawai ba tare da ya ce komai ba ya koma ya zauna yana kallon zoben hannunta da nasa ne ya bata shi tun kafin ta mutu nan ya sake tabbatar da dai tauraruwa ce a gabansa ba wata ba sai ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa murya a cunkushe ya ce mata “Ina saurararki gaya min dalilin da yasa kika yi k’aryar mutuwa alhali kina raye?” “Saboda ka samu magaji, na san idan ba haka na yi ba har abada ba za su barka ka samu magaji ba. Yanzu kuwa da na aikata haka ba gashi komai ya zama sai labari ba, bayan Murad kana da d’a Jaheed yana nan kuma cikin k’oshin lafiya har da matansa biyu……” wani irin kallo ya mata ya ce “Ta yaya aka yi aka aurar min da d’a ba tare da sani na ba? Tauraruwa wani irin abu ki aikata haka? Kuma da gaske kin tabbata yaran nan y’ay’a nane na halak, za kuma ki bada shaida a duk inda aka buk’aci hakan?” “Nima ban san an aurar da shi ba, don ban bayyana kaina ba a wajen iyayen rik’on sa sai dai yanzu nake son sanar da su komai…. Jaheed da Murad kamarsu d’aya don ba zaka iya banbance kamaninsu ba sai dai ta banbancin halayya. Kuma ko Kur’ani za’a bani na dafa zan tabbatarwa da duniya d’iyoyinka ne halak.”Maimartaba shiru ya yi ransa yana sake dugunzuma yana b’aci ace d’ansa na cikinsa bai san da shi ba har ya yi aure? Sabida kawai tsoron sharrin magauta ashe kuwa lokaci yazo da ya kamata ya fuskanci magautansa idan ta kama ko yak’i ne zai yi da su Wallahi don sun zalunceshi. Farin ciki guda da yake da ya zama tabbas Murad da Jaheed yaransa ne na halak, ba kamar yarda al’umma ke zargi ba, sai ya samu zuciyarsa da samun nutsuwa fiye da fargabar da yake ciki a da. “Ka yi hak’uri duk na aikata haka ne a bisa son cetoka da ni kai na daga b’aragurbin mutanen da suke cikin Fada burinsu na kashe ni bai cika ba duk da k’ok’arin su na aikata haka.” Ya d’ago yana kallonta sai kuma ya jinjina kai ya kasa furta abinda yake ransa, gani kawai ta yi ya mik’e ya shige toilet hakane ya bata damar mik’ewa itama don fita daga d’akin zuwa nata d’akin da yake gaba da parlournsa ka’dan. Tun asali anan b’angarenta yake bata tab’a yarda ta yi nisa da mai martaba. Tana tura k’ofar Murad na kai hannu da niyyar kwankwasawa. Turus ya tsaya yana kallonta idanunsa cikin nata zuciyarsu na bugawa lokaci guda. Tsawon mintuna biyu suna kallon juna kafin ta janye nata idon ta kama hannunsa tana furta “Haba farin cikin rayuwata baka yi murna da gani na bane d’an Mamansa…” Hannunsa ya janye a hankali yana furta “Ba ke ce Mamana ba ina son sanar da ke haka don ko a yanzu ina tare da Mamana….” Ta d’ago tana masa wani kallo sai kuma ta saki murmushi ta zare hannunta cikin nasa ta yi hanyar tafiya murya a k’asa ta furta “Har abada ni Uwarka ce Murad! Duk da ban yi nak’udarka ba amma kai d’ana ne halak malak, duk duniya ba wanda ya isa ya canjawa tuwo suna, Albishir guda da zan maka ka shirya nan da sati guda zaka tare a gidanka da matar da na aura maka!” Ta shige sashenta ta bar shi a tsaye yana cizar leb’e da mamakin wacece ita da take magana murya cike da confidence. Ya yi kwafa yana cigaba da nocking d’akin Maimartaban. Fitowarsa daga wankan gumin da ya sha saboda firgici kenan ya ji bugun k’ofar kamar za’a b’alle k’ofar mamaki ya kama shi, sai kuma ya saki murmushi sanin cewa Tauraruwa Uwar rigima ta sake bayyana wato halinta na nan na rashin uziri ga kowa a duk sanda ta so wani abu. Bai damu da jallabiyar da ke jikinsa ba ya yar da towel d’in hannunsa kafin ya saka hannu ya mur’da handle d’in, sab’anin tauraruwa Murad ya gani a tsaye yana mayar da numfashi kamar wanda ya ci tseren gudu. Kamar Uwa kamar d’anta, sau tari ya sha kwatanta d’abi’u da halayyar Murad da na tauraruwa ashe dai tabbas jininta ne. Murmushi ya sakar masa yana furta “Ran Sarki ya da’de lafiya ake min wannan bugu haka?” Mamaki fal fuskar Murad ya zubawa Sarkin ido yana mamakin fara’ar da yake gani da walwala a fuskarsa alamar yau a cikin farin ciki yake, zai iya cewa tun tashinsa bai tab’a ganin Sarkin a yanayin farin ciki irin wannan ba. “Shigo Murad, don na san abinda ya kawo ka.” Maimartaba ya fa’da yana saka tarin hannunsa cikin na Murad d’in da yake tsaye kamar mutum mutumi. Bai bar shi ba sai da ya zaunar da shi a bakin tattausan gadonsa ya koma ya cigaba da shafa kansa har yana yin y’an wak’a mamaki ya dinga neman kashe Murad a zaune. Sai da y fesa turarukansa sannan y taje sumar kansa kamar wani sabon ango sai ya dawo gurin Murad ya zauna daf da shi yana furta “Da gaske itace Mama ta?” Na san shine tambayar da kake son yi min. Amsar itace “Eeh da gaske Tauraruwa itace Babarka duk duniya baka da wata Babar da ta zarce ita……… JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: KUDIRAR ALLAH BOOK 2. (Don Allah ku zamo masu rik’on amana, idan kin san kin siyi littafina ne don ki watsa shi a duniya don Allah tun ban yi nisa ba ki gaya min na dawo miki da ku’dinki. Ina yin littafi kyauta Amma wannan dai ban yi niyya ba. Don haka pls ku kiyaye kada mu zo muna samun rashin fahimta da mutum kuma ya k’ulla ce ni, Allah yasa ku ji kuma ku bi, idan kun bani ha’din kai zaku ji da’din harka da ni In sha Allah.🤗) 08033748387. . Da yawa daga cikinsu k’wak’walwar su da tunaninsu ya daina aiki na wuncin gadi. Tsoro da fargaba ya ziyarcesu suka rasa sukuni a zuciyarsu. Harta Sarki wani irin gumi yake yarfarwa. Bai tab’a tunanin abubuwan da suke ji a tatsuniya za su iya kasancewa a gaske ba, wato Fatalwa! Shin dama wanda ya mutu yana dawowa ne? Shine tambayar da ya yiwa kansa a zatonsa a zucuayrsa ya yi tambayar sai dai kallon da fadawa suka masa ya saka shi sanin cewa lallai a zahiri ya yi maganar. Don suma da alama tambayar da suke son yi kenan sai dai zuciyar kowa da bakin kowa ya kasa bari ya yi furucin tsoro ne sosai a ransu, ji suke kamar su dare su bar wajen. Wani abu ne da kai tsaye za’a iya kira ALMARA ko irin mafarkin nan mai wuyar sha’ani. Su kansu matan Sarki sun girgiza da ganin wannan baiwar Allahn idanunsu duk a waje suke suna cigaba da kallon Fatalwar matar a tsaye a gabansu tana sakin murmushi cikin isa da ginshira kamar dai yarda take kasancewa a lokutan da suka gabata. Fulani Saddik’a kanta a firgicen take, balle Fulani Raheena da take jin kamar ta saki fitsari a wando. Ta runtse ido ta bu’de ya fi a k’irga duk don ta tabbatar ba wancan rud’anin mafarkin da ta saba ba ne. Nene ma da k’arfin gaske take yafito yawun bakinta take ha’diya don yawun bakin gaba d’aya ya k’afe k’af, jin mak’ogoronta take a bushe kamar baa tab’a halittar yawu a wajen ba. Suna yara sanda abubuwan suka faru har ta rasa ranta amma sam hakan ba zai saka ta manta da fuskar matar ba. Ta girmesu a shekaru amma alherinta ga al’umma kamar ba jinin sarauta ba yasa ta samu soyayyar jama’a kowa yake rububinta da gasken gaske. Abubuwan suka dinga dawo mata kamar majigi a kwanyarta ta dinga kallonsu kamar wancan lokacin da abubuwan suke faruwa a zahiri. Hannun Najee ta kama ta damk’e da k’arfin gaske tana sake runtse idonta zuciyarta na bugu saboda razanar da take ciki. Idan har ya tabbata ba mutuwa ta yi ba tabbas akwai gagarumar k’ura a masarautar gabas! Najee ta juyo tana kallon yarda hannayenta suke kakkarwa a tsorace ta ce “Nene lafiya menene?” Yatsanta ta saka a baki alamar ta yi shiru tana girgiza mata kai idanunta cikin na Najwan itama Najwan ita take kallo tana mamakin yarda idanun Nene suka jirkita zuwa jajaye sosai da alama tashin hankalin da take ciki ba shi da ma’auni balle a taskance mizanin sa. Sai itama ta ji tata zuciyar ta firgita bata san sanda ta koma jikin Nenen ta lafe ba tana danne k’irjinta da yake bugawa da k’arfin gaske. Sarki Mukhtar ya cigaba da kallonta ita d’in ma shi take kallo kafin ta saki murmushi tana fisgar leb’enta. Sannan ta sauke idanunta akan Hadiman da cikinsu har da me rawar d’ari. “Kuna mamakin dawowata ne bayan kun binne ni a kushewa.” Sai ta lumshe ido hawaye suna bin k’uncinta. “Allah ya nufi dawowata cikin Amincinsa bayan dawowartawa kuma sai yasa na dawo har da y’ay’ana na halak malak. Bayan Murad da kuke gani akwai k’aninsa Jaheed, wanda ya yi aure yana da matansa biyu, a yanzu ne zaku fuskanci duk abinda Allah ya so ko ana muzuru ana shawo sai Allah ya k’addara nufarsa.” Ta fa’da tana sakin murmushi ta cigaba da takun isarta zuwa inda sarki yake a zaune ta zauna a gefensa kujerar da ba wanda ya isa ya hau sai shi ba wanda ya tab’a kwatanta hawanta har ta da Fulani Raheena da ake ganin ta cika ta tumbatsa. Wannan karan Nene kanta a cikin firgici take jin ashe matar wai ta san Jaheed to ta ina? Ta ina kuma suka zama y’ay’anta da har take bibiyar rayuwarsu har ta san sun yi aure? Kada dai da gaske su Jaheed y’ay’anta ne, to ta yaya ta ina kuma? Ji ta yi kanta yana wani irin sarawa ta kama hannun Najee ta sake damk’e wa da kyau kamar dai Najeen ce zata tsareta daga dukkan abin cutarwa. “Ina raye mai martaba ban mutu ba, ka daina min kallon fatalwa am still alive and am still your’s favorite person…..” ta fa’da tana saka idanunta cikin na Sarkin da ya gama ru’dewa sai dai izza da isa ta mulki ta hana shi bayyana hakan ya daure ya jure ya d’aga mata kai alamar ya gamsu, duk da har a zuciyarsa bai gama gamsuwar ba. “A tashi taron nan mai martaba bana buk’atarsa don ni na yiwa yaro na mata zarka’ded’iya ba wacce kuke so ku Aura masa ba, tuni an d’aura masa aure… don haka yanzu nake son a sallamesu.” Ba wani Ja Sarki ya kalli Bafadensa d’aya ya masa alamar da ya sallami jama’ar wajen. Take kuwa aka sanar da mutane an fasa wannan aure don haka kowa ya tafi. Aka rufe sarki don ya mik’e ya shiga cikin zabgegiyar motarsa matar tana gefensa kamar ta shige jikinsa ta bi bayansa suka shiga motar mutane sam ba su yi mamaki ba, don sun san duk wanda sarki zai so a rayuwa to bayan Tauraruwa ne sunan da yake gaya mata kenan a zamanin da take raye. Murad ta yafito da hannu ta masa alamar da ya shiga da sauri ya girgiza kai yana kallon Mamma da ta kafa masa ido don haka kai tsaye ya bi bayan Mamma. Tauraruwa ta saki murmushi kawai tana girgiza kai. Aka ja motar Sarki zuwa fadarsa ta cikin gida. Fulani Raheena kasa jiran motar ta yi sabida yarda zuciyarta take a hautsine da sauri ta bi ta wata siririyar hanya don isa sashenta tana jin duk duniya ba wanda ya kai ya tashin hankali, duk da ba ita ta aikata komai ba amma ta san komai ta san kuma wa’danda suka aikata. Sauri take kamar zata tashi sama bata bari kowa ya ganta ba balle a bita ta shige sashenta, ta mayar da k’ofar ta rufe da k’arfin gaske, rufewarta ta ya yi daidai da bugun zuciyarta kamar zata b’alle k’irjin ta fito. Ta fige mayafin kanta da alkyabbar da ta jik’e da gumi kamar ta shiga ruwan sama. Har ta suman kanta d’igar gumin take, zaman dirshan ta yi a k’asa tana tura yatsun hannunta cikin sumar kanta da ta tashi kamar ta mahaukata a firgicen ta ce “Na shiga uku ni Raheena? Komai ya lalace min dama wannan matar ba ta mutu ba, suka min k’arya ta mutu suka saka na sakankance da cikar dukka burikana, wayyo Allah na ni Raheena tabbas b’aragurbin k’wan gab yake da fashewa warinsa kuma zai iya kashe al’umma da dama a cikin Garin Gabas. Bata san hawaye take ba sai da ta ji d’igar su a saman harshenta ta lumshe ido tana sake datse leb’enta. A fili ta furta “Kun cuceni! Kun jefa ni a Ramin da ba mai iya fitar da ni sai Allah, sai dai ina tabbatar muku wannan abin har ku zai shafa Ba Raheenatu ita ka’dai ba.” Ta fa’da tana sake hargutse sumar kanta. Bugun k’ofar da ake ne a sassanta ya saka cikinta sake hautsinawa da sauri ta fa’da toilet gudawa ta yi sosai kafin ta fito ta nufi parlourn ba tare da ta rufe kan nata ba ta ce “Waye ne?” “Wanda kika san zai zo.” Aka furta daga can. Raheena ta ware ido tana mamakin jin Muryar yau a zahiri duk da da sai dai ta ji ta a cikin waya ko a cikin duhu. Da sauri ta saka hannu ta zare mukullin tana murnar ganin ko wane shege ne mai bata umarnin da sam bata iya ja da shi a zahiri. Idanunsu ne suka sark’afe cikin na Juna hanjin cikin ta ya sake hautsinawa ta bu’de idonta a razane ta ce “What? Dama kai ne?” Murmushi ya sakar mata yana tureta gefe ya shiga cikin parlourn bayan ya mayar da k’ofar ya rufe ta ruf. Ya k’are wa d’akin kallo kafin ya mayar da kallonsa kan Raheenan da idanunta still suke a waje gashin kanta da yanayinta ya nuna ta a matsayin mahaukaciya sabon kamu. Murmushi ya saki ya ce “Tun yanzu Raheena? Tun komai ma bai faru ba na gan ki a haka? Ina ga idan wad’ancan sirrikan suka bankad’a. Kin ga zauna magana nazo mu yi ta nutsuwa. Idan kika sake kika bayyana sirrin da ya da’de lullub’e a cikin k’asa wallahil azeem sai na sanar da sarki wacece ke? Bana son jin sunana a maganar kisan Tauraruwa don na san kin san komai duk da ba hannun ki a ciki, wallahi kika sake kika tona mana asiri sunan naki sirrin banka’dadde.” Ya fa’da yana sakin dariya sannan ya juya ya fice da sauri duk da a firgicin yake shima hakan bai hana shi nuna jarumta ba da nuna bai san komai ba. Raheena ta bi bayansa da kallo tana jin tashin hankalinta na sake hauhawa me yake nufi? Ta b’oye laifinsa da kai tsaye za’a jingina mata laifin ko me? Shikkenan ita Raheena ta zama mai laifi kashi kashi kenan? Idan kuma bata b’oye laifin ba haka na nufin fashewar b’aragurbin k’wan kenan? Cabd’ijam! Tabbas Ni Raheena ina cikin matsala. Ta furta a fili. Fulani Saddik’a kuwa jikinta a salub’e yake sosai, duk wani karsashinta ya gudu sai tsoro da jin kamar shikkanan za’a rabata da Murad da take jin sa kamar gudan jininta. Ta shiga sashenta hannunta cikin na Murad da sam ya kasa sukuni da walwala shima zuciyarsa a cikin ru’danin take, neman wanda zai sanar da shi wacece waccan matar yake? Yana jin nauyi da kunyar tambayar Mamma duk da itace Tambayar da son amsarta ya fi kowace tambaya a wajensa. Maganar matar da take ikirarin aura masa ba matsalar sa ba ce muddin matar bata masa ba sakin ta zai yi, ba ruwansa da wai itace mahaifiyarsa me yasa tana son sa ta wullar da shi kuma wanene Jaheed da har take kiransa d’an uwansa? Fulani Saddik’a cikin d’akinta ta shigar da shi. Kafin ta koma kitchen ta ha’da masa tea mai lipton zalla don dai ta san cikinsa yau kam bai ga abinci ba, kamar yarda nata itama bai gani ba. Kanta a d’aure yake da tarin tambayoyi sai dai bata bari hakan ya bayyana akan fuskarta ba. Ta d’ebo tea d’in bayan ta soya masa scramble egg ta fito da su zuwa d’akin nata. A zube yake a k’asan carpet ya yi pillowa da hannayensa yana kallon ceiling. Ta saki ajiyar zuciya tana furta “Murad me ye haka? Sarki guda mai jiran gado a zube a k’asa, tashi maza ka sha tea idan ba so kake ka sake d’aga min hankali ba.” Ya mik’e kamar yarda take so ya kuma karb’i cup d’in a hannunta bai yi la’akari da zafin sa ba ya kafa A bakinsa. Da sauri ta kalleshi sai dai kafin ta yi magana ya zuk’eshi tas yana mayar da numfashi. A tsorace ta kalleshi “Me ye haka Murad? Kana cikin hankalinka kuwa?” Da k’arfin gaske ya runtse idonsa ya furta “Bana ciki Mamma, ina son sanin wacece waccan matar?” Da sauri Fulani Saddik’a ta kafa masa ido, tana son karantar yanayin da yake ciki. Tsoro ne ya kamata ganin kamar Murad cikin zakwa’din son sanin mahaifiyarsa yake, idan kuwa hakane ya zama na ita zata tashi a tutar babu. Da sauri ta dakatar da zuciyar ta ta kuma ha’de rai tana kallonsa ta ce “Me kake son sani game da ita? Kana son ka san ko itace mahaifiyarka a zahiri? Me hakan yake nufi akwai inda na tauyeka ne?” Ta fa’da cikin yanayi mai nuna zallar b’acin ranta. Wannan karan abin da ta yi bai da Murad ya ji zuciyarsa ta canja daga zakwa’din son sanin ainahin mahaifiyarsa ba da ma d’an uwansa guda da zai kira tilo, sai dai gudun b’acin ranta sai ya danne damuwarsa ya koma ya kwanta kamar yarda yake a da, sai dai yanzu ya lumshe ido ne yana cigaba da saurarar sak’a da warwara da zuciyarsa take masa. Fulani Saddik’a ta saki ajiyar zuciya tana mik’ewa ganin kamar barci ya d’aukeshi ta fice daga d’akin da sauri don isa wajen su Nene da take tunanin acan duk amsoshin tambayoyinta su ke. Yanayin da ta bu’de k’ofar zai tabbatar maka da ta na cikin rashin nutsuwa. Nene da suma suke cikin rashin nutsuwar suka d’ago da sauri suna kallonta. Fuska ba walwala ta isa wajen su, ba tare da ta rufe k’ofar ba. Ta zauna idanunta cikin na Nene ta ce “Ki sanar da ni wacece ke? Sannan kuma ina son sanin shin abinda kika fa’da min da gaske ne ke kika haifi Murad ko kuwa?” Nene ta saukar da idanunta k’asa kafin ta jijjiga kai ta ce “K’warai har a yanzu bana manta rad’ad’i da zafin naku’dar haihuwar Murad da na yi nice mahaifiyarsa abinda yake bani tsoro waccen matar da ta bayyana kanta a matsayin mahaifiyarsu tabbas shine irin turaren da nake ji a jikin matar da ta taimakeni a wancan lokacin….” Da sauri Fulani Saddik’a ta bu’de manyan idanunta ta ce “Da gaske?” Nene ta ce k’warai kuwa ban mance ba, sanda ta ke taimakona ina nak’udar Murad ita kuma ta bani mak’udan ku’dad’e da gwalagwalai ta ce na nesanta kai na daga masarautar gabas kada na sake dawowa don akwai mutanen da suke jiran rayuwata abinda yasa kenan na yi nisa da garin nan, amma tabbas ni na yi nak’udar haihuwar Murad na kuma d’aukeshi a cikin tsawon watanni tar……. Yawun bakinta ne ya k’afe ganin Murad yana tsaye idanunsa cikin na Nene da ta ha’diye sauran maganar a cikinta. Yana nuna ta da yatsa ya ce “Ke ce magaifiyata? Me yasa kika b’oye min?” Ya fa’da yana zubewa a gabanta…. JIKAR NASHE✍🏽🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: “Au Hassan d’inka.” Nene ta fa’da tana kallon idon Murad da Yake mata nuni da alamar shine babba. Murmushi ya saki jin gyaran da Nenen ta yi ya amshi wayar yana gyara muryarsa da kyau don ta sake kaurara ya yiwa Jaheed barazana da ita. “Hello Yayanka Murad ke magana.” Jaheed daga can ya runtse idanunsa yana tunanin shin da gaske ne abinda kunnuwansa suke gaya masa ko kuwa k’ailular mafarkin da ya saba ce. “Murad da gaske kai ne?” “Point of correction Malam, Yaya Murad dai ko?” Jaheed ya saki dariya sosai daga jin muryar Murad ya san za’a yi rigimammen gaske sai ya dinga imagining d’insa a k’wayar idanunsa “Mhmn girman kwana nawa ka bani? Har na matsu nazo na ganka wallahi.” Kamar yarda nima na matsu na ga stubborn brother na da zan saka aiki ya yi kuma ko yana so ko baya so, dama ka shirya maza maza ka taho, ya kamata mu fuskanci mahaifinmu da wannan lamarin.” Jaheed ya saki ajiyar zuciya mai tafiyar da duk wani hucin bak’in ciki da yake cin ransa na shekara da shekaru ya furta “Wannan shine zance, zan zo Murad jibi ka saka ido In sha Allah.” Murad ya furta “Rabbi ya sha.” Kai tsaye yana kashe wayar idanunsa cikin na Nene da take kallonsa tana jifansa da murmushi mai bayyana tsananin soyayyar da take tsakanin uwa da yaranta. Wani irin Farin ciki ne yake sake kwaranya a zuciyarta wanda ba shi da misali. Murad ya kama hannayenta “Da zarar Jaheed ya zo ina so duk wani tsoro da shakka ya kauce daga wajenki Mah, Ina son ki jajirce komai ma zai faru ya faru amma ba zai yiwu kura da shan bugu….” Ya fa’da yana kallon tsakiyar idanunta sai kuma ya matsa yatsunta “Ki saka a ranki Sojan d’an ki na tare da ke, zan tsaye miki har sai naga an yi miki adalci a cikin duk wani hukunci da za’a zartar okay?” Idanu ta lumshe bayan ta d’aga masa kai kwanyarta na sake maimaita sunan Mah da ya kirata da ita, sunan ya yi da’di akan harshensa wato shi ba zai kirata da Nene ba sai Mah. Sai ta ji a ranta ta samu k’arfin zuciyar fuskantar duk abinda zai ma faru a gaba, ta shanye ma abubuwan fargaba da suka gabata balle yanzu. “Promise Mah?” Ya fa’da yana sanya mata hannunsa mai nuni da d’aura alk’awari nata yatsun k’arami ta saka ta sark’afe cikin nasa tana furta “In sha Allah Murad.” Ji kawai ta yi ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya a hankali ji yake ruwa da iska ba mai raba shi da mahaifiyarsa yarda yake jin son ta a dukkan sassan jikinta tun kafin ma ya san itace ta haifeshi balle yanzu da ya san itace ta d’au cikinsa ta kuma yi nak’udarsa. Tsawon lokaci yana jikinta yana jin d’umin jikinta da yake tafiya da dukkan damuwarsa, baya ta matar da aka aura masa abu guda ya sani in dai bata masa ba a daren zai bata red card don haka ba ta gabansa bai kuma damu ya san wacece ba, soyayyar Amra ce har yanzu a cikin ransa ita kuma take fusgar zuciyarsa. ** Jaheed yana kashe wayar ya dubi Khaireey da take ta kallonsa ba ko k’iftawa, ya furta “Ki ha’da kayanki za mu wuce Nigeria.” “Nigeria kuma?” Ta furta idanunta cikin nasa “Ya d’aga mata kai, “Ya zama dole na je ne, duk da dai da ban yi niyyar zuwa ba sai kin haihu amma yanzu zuwan na dole ne, ana sa rai da ganin mahaifina a yau na yi magana da d’an uwana da ba ni da tamkar sa.” Cikin zallar farin ciki Khaireey ta daka tsalle tana furta “Alhamdulillah!” Da sauri ya rik’eta idanunsa a kan cikinta “Ya ce are you mad Khaireey? Kin manta ba ke ka’dai ba ce?” Ta d’an turo bakinta kafin ta d’ane cinyarsa ta ce “Habibi murna fa nake, duk dai bana son mu je Nigeria saboda yarinyar can da aka ce zaka aura Wallahi bana sonta sosai nake kishinta.” Ya kau da kai fuskarsa a ha’de sosai yana furya “Ni kuma ina sonta, don kuwa dole na so ta don Mamanta ta yi min halacci…” waro ido ta yi tana kallonsa zuciyarta na bugawa da saurin gaske ta ce “Habibi da gaske aurenta zaka yi kenan?” Bai amsa mata ba ya mik’e don ha’da musu kaya bayan ya yi requesting ticket a online. Ita kuwa tana zaune cikin b’acin rai kawai tana kallonsa har ya gama ya juya ya bata kallo d’aya kawai yana furta “Gwara ma ki cirewa kan ki damuwa don aure na Da Najee ki k’addara kamar an yi shi an gama..” yatsu ta saka kawai ta toshe kunnuwanta idanunta na zubar da hawaye Jaheed ya wurga mata harara kafin ya jata ta fa’da kansa ya rungumeta “Open your ears in tunatar da ke abinda kika manta, Iyayen Najee su suka mayar da ni mutum a lokacin da nake cikin tagayyarar rayuwa ta yaya kike son na zuba musu k’asa a ido, duk da ban tab’a son Najee a matsayin matar aure ba, amma ina jinta a jikina kamar wani sashe ce ita a rayuwata don haka ki nutsu kada ki sakawa kan ki zafin kishi aure na da Naji kin san abinda Bature ke kira confirm! To shine.” Daga haka ya yi kissing bakinta har da cizonta a leb’e yana furta “Jealous girl.” Ya nata cakulkulin da ya sata saka dariyar da bata shirya ba. Shima murmushin ya saki yana fita daga d’akin haka yake a rayuwarsa baya son yaga ran wani ya b’aci ta dalilinsa. Khaireey ta bi bayansa da kallo tana jin zafin kishinnata yana sake hauhawa.. Kashegari kuwa jirginsu ya sauka a Nigeria, ba wanda ya gayawa za su zo shi yasa ba wanda yazo tarar su sai taxi ya tarar musu don zuwa gida. Gidan Baffa ya nufa direct duk da d’okinsa na son zuwa Garin Gabas sai ya ji ba zai iya wucewa kai tsaye ba ba tare da yaje ya ga Baffa ba. Khaireey sam bata so haka ba don zuciyarta bata son alak’arsa da gidan Baffa ba don komai ba sai don Najee yarinyar da ta tsaya mata a rai, amma ta san ko giyar wake ta sha bata isa ta tari Jaheed da zancen bata son zuwa gidan Baffa idan bai kai tsaye tana son ya ce ta tafi gidan nata Uban bane, don haka taja d’an bakinta ta tsuke har suka isa gidan Baffan. Ba kowa kasancewar rana ce ko nace Hantsi kowa yana d’aki ana barcin hantsi. Jaheed ya bi filin gidan da kallo yana sakin ajiyar zuciya ganin motar Baffa na nan da alama bai fita ba. A sashen Umma ya yada zango yana kwa’da sallama. Najee da take kitchen tana dafa abincin rana da sauri ta fito jin murya kamar ta Jaheed, mutumin da take kwana da shi ta tashi da shi a rai. Hular ta har tana zamewa ba tare da ta sani ba. Baki ta bu’de tana pointing d’insa da yatsa fuskarta fal fara’a, sai kuma ta yi saurin gintse fuskar tuna garga’din Umma da ta yi na ta dinga b’oye zumu’di ta akan Jaheed, ba ta lura ma da matarsa da take tsaye tana wurga mata harara ba. Jaheed ma murmushin ya sakar mata yana kallon Buzu buzun gashinta da yake tsaye kamar gargasa saboda cika da kauri da tsawo. “Tsifa a kitchen don k’azanta Najee? Wato ke dai ba kya girma ko?” Turo d’an bakinta ta yi tana furta ba tsifa fa nake ba, kan ne a kunce ni kuma bana son a kitsa min shi.” “Saboda raki ko? Ke komai zafi kitson ma zafi yake miki?” Ta d’aga kai idanunta na sauka a kan Khaireey da ta b’ata fuska tana mata kallo mai kamar harara. “Lah! Ya Jaheed Ai sai kace da Anty Babba kake? Ki shigo mana kika tsaya kamar bak’uwa.” Hararar ta sake wurga mata sai dai Jaheed na juyowa ta yi saurin sakin murmushin yak’e ita kuwa Najee itama hararar ta b’alla mata har da guntun tsaki ta fice daga parlourn tana ji Jaheed yana furta “Ina Umman?” Bata amsa masa ba sai dai ta je d’aki ta taso Umman Daga haka ta shige d’aki sai ta ji gaba d’aya har shi ma haushinsa take ji ba matar tasa ka’dai ba. Mamaki ne ya kama Umma da ta gansu a parlourn “Ku kuma fa saukar yaushe?” “Now now Umma.” Jaheed ya fa’da yana dariya. “Ai ba sai ka fa’da ba, kamaninku ma sun nuna yanzu kuka shigo k’asar, amma zuwa ba sanarwa Jaheed.” “Zuwan dole ne Umma, Nene ce ta kira ni wai an ga Baba na har ma da Murad!” Umma da sauri ta kalli k’ofar tana masa alamar ya yi shiru. Shirin ya yi yana mata kallo cike da neman k’arin bayani. “Baffanku bai san inda ta tafi ba, kuma bana son ya sani ta ja min fa’da, da gaske dai tana can garin gabas d’in sai dai har yanzu bata tabbatar da yarda aka samar da cikin ku ba, yanzu ba sai anjima ba kafin Baffa ya san da zuwanku ka yi sauri ka je sashensa ka gaya masa ana tsammanin an ga mahaifin ku zaka je ka ‘dau Nene ku je, idan shine zaka yi waya ka fa’da sai mu rankaya mu tafi.” Jaheed ya d’aga kai yana mik’ewa, sai yaga Khaireey itama ta mik’e da mamaki Nene take kallonta ta ce “Ki jira ya dawo mana, ai ko can garin zai je ba dake zai tafi ba zama zaki yi anan har sai mun san yarda ake ciki sai mu bi shi.” Khaireey ta zauna tana jin ranta bai mata da’di da hukuncin Umman ba, har tana furta “Mai shegen shishshigin tsiya in zauna in miki Uwar me? Kina neman cusa masa y’arki ya aura ko kunya ya saki ya ku aura masa k’anwa gidana zan tafi ba zan zauna anan d’in ba, ina ganin buzuwar y’ar ki mai kama da mutanen ethiopia. Umma dai bata kulata ba ganin tana cika tana batsewa ta kawo mata ruwa da abinci ta shige d’akinta don ba da ita za’a yi wannan iya shegen ba. Shiru sashen Baffan sai k’arar t.v Mahmeey ce kawai a parlourn tana d’an gyara inda Baffan ya gama cin abincin safe. Ta tsinci sallamarsa a bakin k’ofa da sauri ta d’ago tana kallon k’ofar tana ganinsa ta gintse fuskarta sosai don ta tsaneshi musamman da aka wayi gari Najma na da cikinsa a jikinta. “Ina yin Mahmeey.” Ya furta shima tasa fuskar a ha’de. Bata amsa ba illa juyawa da ta yi ta cigaba da aikinta. Bai hak’ura ba ya ce “Wajen Baffa na zo.” “Saboda Baffan Ubanka ne?……..” gyaran muryar Baffan da ta ji ne ya sata yin shirun da bata shirya ba. “Wa nake ji kamar Mujaheed?” Bata amsa ba ta bi ta gefensa ta shige d’aki. Jaheed kuwa yana murmushi ya mik’e yana furta “Ni ne Baffa, ashe kana ciki?” “Ina Jaheed, daga ina haka ba sanarwa.” Jaheed ya d’on sosa kai yana gyara zaman hular sanyin da take kansa ya ce “Wallahi tafiyar gaggawa ce Baffa, wani ne ya sanar da ni ta waya ya san iyayena shine na zo neman izinin ka na d’au Nene na wuce da ita idan mun tabbatar da sahihancin labarin sai na muku waya kuma ku biyo mu, to sai na tarar ma Nenen na wajen Hajja Kaka…” Kallonsa Baffan kawai yake kafin ya d’an jijjiga kai ya ce “A wani gari aka ce mahaifinnaka ya ke?” “Garin Gabas.” Baffan ya maimaita Sunan garin sai kuma ya ce “Shikkenan ka je, Allah yasa a dace sai ku tafi da Faruk ko?” Jaheed ya d’aga kai ya ce “Tom shikkenan Baffa mun gode Allah ya k’ara girma.” Baffa ya d’aga kai yana furta “Allah ya kai ku lafiya Allah ya muku albarka, ina iyalin naka? Ka kuma san Najma na da ciki ko?” Da sauri Jaheed ya d’ago kai ya kasa cewa Baffan komai sai dai mamaki da ganin girman Ubangiji ya cika zuciyarsa, wato tabbas KUDIRAR ALLAH da girma take girmanta ya wuce duk wani tunanin bawa. “Tana da ciki, saboda haka har yanzu da aurenka a kanta, har sai ta haihu tukun na, don haka tana da hakkin kulawa a wajenka, bana son Allah ya kama ka da laifin watsi da hakkinta. Shi yasa na gaya maka.” Jaheed ya saki ajiyar zuciya yana d’aga kansa a hankali “Ka je, Allah ya dawo da ku lafiya.” Jikinsa a sanyaye ya mik’e ya fice daga d’akin duk ya kasa ha’da ido da Baffan, kunyarsa ta masa dabaibayi. Umma ma kunyarta yake ji, don haka yana fita ya kasa kallonta illa fita ya yi yana furta “Umma zan je na d’au Faruk mu wuce.” Umma ta bi shi da kallo tana furta “A haka zaka wuce ko abinci fa baka ci ba.” Murna da d’oki ma yasa shi ya manta da batun abinci burinsa ya je garin gabas yaga waye mahaifinsa. Ya girgiza kai “Na k’oshi Umma, wanka kuma idna na je zan yi.” Umma ta girgiza kai “Duk don zumu’di Jaheed? To ita kuma matar taka fa?” Ta zauna anan Umma idan na dawo zuwa jibi sai mu tafi, idan kuma ta tabbata mahaifin nawa ne sai ku taho da ita idan zaku zo.” Khaireey wani kallo ta zuba masa kamar ta zunduma ihu. Umma tab’e baki ta yi tana nazarin yanayinta tun d’azu. Har zai fita ta ce “Ka biya sashen Mahmeey kaga Najma ka san tana da juna biyunka a jikinta ko?” Wata irin fa’duwar gaba ta samu Khaireey ta ‘dago tana kallonsa sai taga ya d’aga kai yana furta “Na sani Umma, idan na dawo zan ganta….” Ya fa’da a gaggauce yana ficewa daga sashen. Najma kuwa tun bayan shigowarsu ta gan shi don haka ta fito tana dakon fitowarsa. Ta tsaya jikin motarsa hannayenta rungume a k’irji. Ta hangoshi yana tahowa cikin takun dake nuni da cikar mazantakarsa da alama yana cikin nisha’di don fuskarsa ta nuna haka. Ta sake gyara tsayuwarta tana jin cikinta na motsi a hankali. Yana isowa wajen ya lura da ita. Da sauri ya gintse fuskarsa.. idanun ta da suka tara k’walla ta zuba masa tana furta “Ya Jaheed ina yini?” Bai amsa mata ba ya shiga motar sa ya mayar da murfin ya rufe sai da ya tayar da Motar sannan ya sauke glass d’in yana kallonta ya furta “Koma ciki Malama akwai sanyi bana son komai ya samu Jikan mahaukaciya da ke cikin ki.” Ya ja motar da sauri Najma kuwa runtse idanunta ta yi tana sakin hawayen da take ta b’oyonsu tun d’azu. Ya biya ya d’au Faruk suka nausa Garin Gabas Faruk da yake ya san hanyar garin shi ya yi driving har zuwa cikin masarauta. A harabar masarautar suka yi Parking Jaheed yana sako k’afarsa waje idanunsa suka fa’da cikin na Tauraruwa da take tsaye tana ta sakar masa murmushi murya cikin nisha’di ta ce “Barka da sauka Mujaheed yarona d’an albarka! Madalla da Uwar da ta min rainonka ta haifa min kai ta kuma shayar da kai da nononta mai albarka, nan gaba ka’dan zamu sakanta mata da sakamakon alheri na ladan d’awainiyarka da ta d’auka, Tabbas Nenenka ta cancanci a yaba mata!” Cak ya tsaya yana zuba mata wani irin mugun kallo! JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Fa’duwar gaba ce ta samu Umma ta rasa me zata cewa Baffa da ya zuba mata ido yana jiran ta tashi ta kira masa Nenen. “Ba ki ji ne?” Ya maimaita idanunsa cikin nata. Ta sunkuyar da kanta tana wasa da zoben hannunta kafin ta furta “Nene bata dawo ba, tana wajen Hajja saboda yanayin jikin Hajjan ba da’di.” Kallon da ya yiwa idanunta ka’dai sun isa ta shaida bai gamsu da abinda ta ce ba, bai mata magana ba ya d’au remote ya danna don kallon News. Itama shirun ta yi kafin ta Mik’e ta bar parlourn gudun kada ya sake jefo mata wata tambayar. _____ Hankalin kowa a masarauta ya raja’a ne game da Tauraruwa da bikin Murad da ta fara tsarawa na kece raini. Duk da mutane sun matsu su ji labarin yarda aka yi ta mutu ta dawo musamman wa’danda suke da ruwa da tsaki a cikin kisan, sai dai Tauraruwa ta ja bakinta ta tsuke ta tsaya tsayin daka akan sai wancan lokacin ya yi. Maimartaba dai ta gutsira masa ka’dan daga sashen labarin ganin hankalinsa ya kasa kwanciya ya matsu da jin yarda aka haihu a ragaya. Mutane da dama cikinsu ya d’uri ruwa ganin kamar watan tonon asirinsu ya zo. Tauraruwa dai bin kowa take da ido tana sakar musu murmushin da sam suka kasa gane ma’anar fassararsa. Yau ma tun safe ta sa aka dinga shigo da wasu manyan akwatina masu masifar kyau. Mai martaba dai ya dinga bin ta da kallo kafin ya furta “Wannan iyayen akwatinan na menene Tauraruwa?” Murmushi ta saki kafin ta furta “Na auren Murad ne, gobe In sha Allah za’a kai lefe gidan da na nema masa auren.” “Sun yi kyau sai ki kira Saddik’a ki gaya mata idan ma baki gayawa sauran ba.” Ta d’aga kai “Zan kira Saddik’a don ta cancanci na yaba mata game da rik’on da ta yiwa Murad ba mugunta kamar ita ta haifa min shi, nagode mata ina k’ara gode mata, amma Rahinatu kam yanzu muka fara tak’un sak’a da ita.” Ya jinjina kai kawai don shima abubuwa da dama Raheena na bashi mamaki. “Ki saka Jakadiya ta kirata.” Ta girgiza kai “Da kai na zan je, ko don na girma mata a matsayin Uwar rik’o Murad, na lura tunda na bayyana suka kasa shigowa sashenka kamar dama jira suke na dawo su bar maka ni.” Murmushi Sarki ya yi a zuciyarsa yana furta ba dole su tattara komatsansu su k’yale miki ragama ba, wa zai iya da jidalin ki Tauraruwa. Yana kallo ta fice daga d’akin cikin taku mai bayyana isarta. Duk inda hadiman sarkin suka ganta sai a zube a kai gaisuwa, ita kuma fuska a washe take amsa musu tana bin su da kyauta kamar yarda ta saba. Idan ta wuce kuwa har a zuciyarsu suke mata fatan nasara don suna ji da ita macece mai kyauta da tsananin tausayin talaka shi yasa sanda mutuwar ta ta riski kunnuwan jama’ar masarautar suka shiga tashin hankali sosai. Ta gefen d’akin Raheena ta bi, cikin sa’a Raheenan na zaune a farfajiyarta suka ha’da ido da sauri ta d’auke kanta, Tauraruwa bata barta ba sai da ta k’arasa wajenta, cikin takun isa mai bayyana ta isa d’in ta ja kujerar gefen Raheenan ta zauna tana mata kallo k’asa k’asa wanda kai tsaye ke nuni da cewa “Ina nan ban tafi ba ya son ran ki?” Raheena kasa kallonta ta yi ta d’auke kanta zuciyarta na harba mata da sauri gani take kallon da Tauraruwar take mata kamar ta bankad’o wancan b’aragurbin sirrin nata ne. Murmushi ta saki kafin ta mik’e tana cewa “Hajiya Raheena, ya aka ji da hidima?” Kasa amsawa ta yi sai ha’diyar yawu take a hankali ta kasa amsa mata “Na san dama ba zaki amsa ba, sak’o guda zan baki ki gayawa muk’arrabanki mai guri yazo mai Tabarma Sai ya na’de ya ba shi, kuma Tauraruwa dashen Allah ce ba abinda zai same ni sai ikon Allah!” Daga haka ta wuce ta bar Raheena na jefa mata hararar bayan fage. Fulani Saddik’a kuwa a parlour suka sameta ita da Murad suna zaune magana suke a hankali da alama basa son wani ya ji. Turo k’ofar da tayi ne yasa suka yi saurin d’aga kai idanuwansu ya fad’a cikin nata. Murmushi ta sakar musu tana zagawa ta gefensu ta zauna daf da Fulani tana furta “Uwa da d’a mai ake tattaunawa ne? Na katse muku hanzari dama zuwa na yi nace miki ga lefen d’an ki can ki je ki gani…” Fulani Saddik’a ta jinjina kai tana kallon Murad da ya ha’de ransa sosai kamar bai tab’a dariya ba. Fulani ta ce “Murad baka ga Babarka ba ne baka gaisheta ba?” A fusace ya d’ago yana hura hanci murya a d’ashe ya ce “Ni ba ni da wata uwa da ta zarce ke da Nene.” Tauraruwa ta d’ago da sauri tana kallonsa kafin ta kalli Saddik’a da take shirin masa magana ta girgiza mata kai kawai alamar kada ta yi. A hankali ta ce “Murad ya fi ki gaskiya Saddik’a ban cancanci zama Uwa a wajensa ba, amma wacece Nene?” “Itace wacce ta yi nak’uda ta haife ni kika k’wace a wajenta.” D’if Tauraruwa ta yi, da alama maganar ta doki kwanyarta, ta ce “Ita Nenen ce ta gaya maka? A ina kuka ha’du?” “A gidan nan ko yanzu tana tare da ni.” Lumshe idanunta tauraruwa ta yi wani murmushi na sub’uce mata ta furta “A kira min Nene.” Da sauri ya mata wani kallo sai ya ji a zuciyarsa yana tsoron ha’da su kada ta je ta yiwa Nenen wani mugun abu. “Ba zan kirata ki cuceta ba, ki fa’di koma meye ni zan isar mata.” Murmushin ta sake yi tana kallon Fulani Saddik’a da take ta k’ok’arin dakatar da Murad daga rashin kunyar da yake yi. Hannunta ta d’aga mata ta ce “Ko rabu da shi time will tell zai gane tsakanin ni da wacce yake cewa itace Babartasa wacece Babarsa a zahiri, ki shirya mu je ki ga kaya ko kuma idan kin gama ki taho ki gani, sannan ki yi selecting wad’anda za su kai kayan, Murad a gaida Nene ka ce mata Tauraruwa Tana gaisheta ka cigaba da killaceta….” Ta fice tana sake jifansu da murmushi. A fusace Fulani ta kalleshi, “Me ka aikata Murad? Rashin kunya fa ka mata? Da gaske duk duniya baka da wata Baba sata wuceta ni kai na na shaida baka ga kamannin da kake da ita na kwabo da kwabo ba? Ko da Nenen ba kwa kama kamar yarda kake yi da ita.” Ya runtse idanunsa kawai baya ma buk’atar wata magana zuciyarsa a raunane take tun bayan duk iya bincikensa ya rasa wata shaida sahihiya. Mik’ewa kawai ya yi ya fice daga sashen ya nufi nasa gidan cikin Motarsa a mugun speed zuciyarsa yake son ta huta daga binciken da yake mai wujijjiga masa kwanya. Fulani Saddik’a ta je taga kaya ta saka albarka Tana duban Tauraruwa ta ce “A ina matar take?” Shiru Tauraruwa ta mata kafin ta ce “Y’ar Sarkin Yola ce.” Fulani Saddik’a ta saki ajiyar zuciya kawai ba tare da ta sake furta komai ba, duk da akwai tambayoyin fal a zuciyarta sai dai bata ga fuska a wajen Tauraruwar ba. Ta mik’e tsam da nufin fita daga parlourn kafin ta tsinkayi muryar Tauraruwa daga sama tana fa’din “Ina godiya k’warai da gaske akan rik’on da kika yiwa Murad Rabbi Ya saka a mizani, don haka har a yanzu ki k’addara ke ma matsayin Uwar Murad kike, gobe In sha Allah ki zab’i da wanda za’a je kai kayan lefen.” Fulani Saddik’a ta d’aga kai tana jin nauyin da k’irjinta ya yi da damuwar da zuciyarta take ciki suna raguwa a hankali suna bin iska, yanzu ta samu k’warin gwiwar cewa Tauraruwa bata zo da k’arfin ta don k’wace Murad daga hannunta ba kamar yarda zuciyarta take hasashe. Don haka ta ji duk wani k’udirin da ta niyyata na raba Murad da Tauraruwa ta sanya shi a gefe in dai Tauraruwa zata mata k’arar barinta har abada a mahallin Uwar Murad ba taga dalilin da ita zata kasa mata uziri akan dukkkan abinda take buk’ata ba, zata mata abidna take so za kuma ta tsaya tsayin daka har auren Murad a yi shi cikin nasara da sa’a. Ta fita tana jin zuciyarta wasai, Tauraruwa ta bi bayanta da kallo cike da tausayawa tabbas rashin haihuwa babbar jarrabawa ce da Allah ya kewa bayinsa da yake so idan ka dage ka ci jarrabawar sai ka samu tagomashi ranar alk’iyama da sakamako mafi kyawu. Fulani Raheena kuwa zuwa lokacin ta fita daga hayyaacinta duk inda zaka ganta cikin tunani take na neman mafita, tabbas ta tabbata a tutar babu, dukkan k’udirinta da burinta yana neman ya rushe sakamakon rashin adalcin da mutanen can suke son mata, suna son su zame su tattara dukkan laifin a kanta. Lokaci guda ta zuge ta rame bata da lokacin kanta balle na Sarkin da ta tabbatar yanzu tunda Tauraruwa ta dawo shima baya buk’atarta. An kai lefe an kuma karb’e su cikin girma da mutunci, Fulani Saddik’a ta ji da’din karb’ar da aka musu. Suka dawo suna bawa Tauraruwa labarin karamci da girma da arzikin mutanen su ake kira masu arziki ba y’an taka haye ba. Masu k’aryar arziki su dinga kallon mutum kallon hadarin kaji. Zuciyar Fulani Saddik’a fresh ta shiga wajen Nene don isar mata da albishir d’in gidan karamcin da Murad zai yi aure. Nene ta ji da’di a ranta, a fili kuma ta sanyawa auren albarka tana fatan Ranar da Allah zai nuna mata Auren Jaheed da Najee haka. Fulani Saddik’a ta sake kwantar mata da hankali da cewa ta bar komai a hannun Allah In sha Allah gaskiya zata yi halin ta. Shiru kawai ta yi tana fatan duk sanda gaskiyar zata yi halinta Allah yasa a mata adalci a cikin dukkan hukuncin da za’a yanke mata. Cikin dare Murad ya kasa runtsawa so yake kawai ya ga Nene ya gaya mata shawarar da ya yanke da zuciyarsa, sai dai baya son ya ganta a gaban Fulani don haka ya bari sai cikin daren ya mik’e daga shi sai jallabiya mai masifar kyau sai shinning take ya bi ta wata k’ofa zata sadashi da b’angaren Fulanin. Shiru b’angaren Fulanin sai masu tsaron k’ofar da wasu daga cikin barorinta da suke kai kawo a parlourn. Ya d’an bi su da kallo suna kai masa gaisuwa ya yi saurin dakatar da su, kai tsaye ya isa sashen Nenen tura k’ofar kawai ya yi ya shiga d’akin. Nenen da take zaune akan sajjada tana lazimi ta ‘dago tana kallonsa cikin nazarin fuskarsa…. Ya zube a gabanta yana kama hannunta wanda ba ta rik’e carbin da shi ba. Suka shafa addu’ar tare sannan Nene ta zuba masa ido cikin kulawa da tausayi irin na uwa ta ce “Me ya faru Murad?” Gyara zamansa ya yi kafin ya ce “A ina d’an uwa na yake da zama?” Nene ta gaya masa da sauri ya ce “Kina da numbern layin sa na can?” Ta d’aga masa kai. Ya girgiza kansa yana furta “Lokaci ya yi Nene da zaki sanar da shi Mahaifisa ya bayyana idan yazo daga sannan ne kowa a masarautar nan zai san ke kika haife mu….” Nene ta yi saurin zuba masa ido tana fa’din “Idan na fa’di haka aka buk’aci sanin ta yaya na samu cikin ku me Zan ce?” Sai ki ce “KUDIRAR ALLAH… ni dai abinda nake buk’ata ki kira min shi ya zo garin nan ina son na ga d’an uwana na ji d’uminsa na tare da ni, ina so ya zo Nene mu yanke shawarar da ta dace da mu? Na gaji da walagigin da ake da rayuwarmu ya kamata mu fuskanci rayuwar mu ta gaba mu san mu su waye shegu ne mu? Ko kuma da gaske mu y’an halak ne don haka ki kira sa please yanzu….” Nene ta saki ajiyar zuciya tausayin Murad na kamata bata san sanda ta danna kiran Jaheed ba, bugu biyu ya d’aga cikin d’oki ganin numberr Nigeria ce, jin muryar Nene da ya yi a cikin wayar ya saka shi sakin ajiyar zuciya ya ce “My Nene ina jin ki?” Ta saki ajiyar zuciya tana furta “Jaheed lafiya k’alau, ya kamata ka zo Nigeria Zan nuna maka mahaifinka da d’an uwanka….” Wani irin duuum Jaheed ya ji a kwanyarsa da k’arfin gaske ya ce “Da gaske Nene? Are you sure za ki nuna min su? In dai kin tabbatar to zan taho Nigeria a gobe da daddare…” Nene ta d’aga kai ta ce “Da gaske nake Jaheed a yanzu haka ma ina tare da Usaininka….” JIKAR NASHE✍🏽🥳 Saboda wani uziri da yake tare ni, ga duk masu bibiyar litattafaina sun san baba typing ranar asabar don haka yanzun ma ina neman afuwarka a wannan tafiyar ma ba typing d’in asabar sai dai lahadi In sha Allah. Nagode sosai Najee na gaisheku, ta ce labarinta na gaba tata k’addarar na gaba dafatan zaku cigaba da bibiyar ta. 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ta idanunsa na gano bai yi na’am da shawarata ba, kuma a tsorace yake da abinda na fa’da d’in, don haka don son kwantar masa da hankali sai na yi murmushi na girgiza masa kai na. “Abinda kake nufi nake nufi ba Amintacce, ba nufi na zan amince su kashe ni kamar yarda suka buk’ata ba, sai dai zan ba su damar da zasu kashe ni d’in ba tare da na mutu ba…” wannan karan sosai na saka shi a cikin ru’dani fiye da baya, ba mamaki bai fahimci juyayyaen zance na ba. Na sake jifansa da murmushi “Da kai ka’dai na yarda shi yasa nake gaya maka duk sirrina, Mijina kafin ya rasu kai ne mutum na farko da ya amince da shi ya kuma yarda ya gaya masa duk sirrinsa, D’ana guda d’aya tak da nake da shi kai ne kake masa rik’on mahaifi bayan Mai martaba don haka nima na baka dukkan yardata zan kuma sanar maka da sirrina don na san ba zaka zamo mai tona min asiri ba. Na san a yanzu da suka samu labarin zan yi tafiya za su saka himma wajen son su ga sun kashe ni a hanya don haka zan shiga motar da na zab’a don na san tuni sun shirya kashe ni a cikin ta, sai dai da kai zan yi tafiyar amma ba tare da sun san da kai zan yi ba. Muna fara tafiya bayan barin mu gari zan buk’aci na kewaya a cikin daji tanan zaka samu damar jan mutanen cikin motar ka ce su je su nemo ni bayan da’dewa da tafiyata ban dawo ba kuna shiga ni kuma zan fito zan sakawa motar wuta na kuma koma cikin dajin na b’uya kuna zuwa na san zaku yi tunanin na mutu a ciki amma fa kada ka sake ku dawo sai kun d’au lokacin da ka tabbatar motar ta ci wuta sosai.” D’aga kansa ya yi cike da amincewa da shawarata. Ba waya a lokacin don haka tilas za’a buk’aci a je gida a sanar shi Kuma sai ya yi amfani da wannan damar ya saka ni a Wata motar ta haya zuwa inda na nufi guduwa, na ba shi address da komai na Garin da kuma gidan da zan zauna kafin na b’ace na bar k’asar. Bayan cikar buri na na ganin Maimartaba ya samu Magaji. Shi Amintacce shine zai zame min mai lek’en asiri a gidan sarki. Don haka idan komai ya lafa na ce masa zan dawo gidan Sarkin da zama cikin b’atacciyar shiga can wani sashe da ba wanda yake shigarsa a gidan saboda wajen tarihi ne Amintacce kuma shine mai kula da b’angaren. Duk wa’dannan abinda na shirya d’in haka suka tafi successfully ba tare da kuskure ko ka’dan ba. Hankula sun tashi sosai da jin labarin rasuwata an Kuma gaya min duk halin da Maimartaba ya kasance a ciki akan rashi na. Burin wa’danda suke so kashe ni ya cika aka dinga murna bayan an je an tabbatar da ko b’urb’ushin gawata babu a wajen. Na yi irin mutuwar da suke so mutuwar da Sarki ko gawata ba zai gani ba balle ya tuna. Tun ranar da aka yi jana’iza ta Sarki ya saka aka kwashe duk wani abu da zai dinga tuna masa da ni ciki kuwa har da hotuna na da ma sunan Tauraruwa gaba d’aya, wanda shi ya saka min da kansa tun muna yara saboda ni ka’dai ce y’ar Uwarsa da muke ciki d’aya. Bayan afkuwar lamarin da wata guda na dawo cikin masarautar gabas cikin wata sirrintacciyar hanya a kuma wani sirrintaccen dare na kuma zauna a sirrintaccen waje da ba wanda ya san da shi sai amintacce na abokin sirrina. Tun daga lokacin muka dinga saka ido akan duk abubuwan da suke faruwa a cikin masarauta, suna can suna shirin su na don cutar da sarki da kawo masa b’aragurbin d’a ko na waye ba don komai ba sai don su samu cikar burinsu na hanb’are Maimartaba daga kan kujerarsa, kujerar da suke bak’in ciki da kasancewrsa a kai. A wannan lokacin da idonsu ya rufe suke son lallai sai Raheena ta samu d’a da za’a kira jinin Maimartaba har suka tara da d’aya daga cikinsu wanda shi ya san kansa aka kuma samar da cikin sai dai a haka na dinga bin dare da taimakon amintacce muka dinga canja yaran da gawar jarirai muna d’auke wa’danda suka haifa da taimakon Matar Amintaccen da ta zama itace Unguwar Zoma a cikin masarautar. Duka wannan abinda ake ba wanda ya sani, a haka ganin tabbas Raheena ba zata samu rayayyen d’a ba sai Suka canfata da cewa haihuwar wabi take don haka suka komawa biyu daga cikin matan Sarki wa’danda suka san kai tsaye zasu amince banda Saddik’a da Suka san koda wasa ba zasu tab’a zuwa mata da maganar ta yarda kai tsaye ba. Tsautsayi yasa Raheena ta fara kishi da matan Sarkin da suka amince a haka har ta musu shune a wajen Sarkin a zuwan cewa k’annensa suna tarayya da su. Ya tsananta bincike ya gano da kansa hakan yasa ya musu sirrintaccen saki ba tare da kowa ya sani ba ba don komai ba sai don gudun b’ata sunan zuri’ar sa a masarauta ko b’ata sunan k’annensa. Wannan ya wuce ba su san kuma Raheena ba ce ta aikata duk wata kitimurmura. Ganin hak’ansu ta kasa cimma ruwa sai suka koma bin y’an mata suna musu fyad’e da niyyar idan sun samu ciki su d’auke su su b’oye har sai sun haihu. Nan ma burinsu bai cika ba don labari da ya ishi kunnen Maimartaba sai ya sanya tsatstsauran mataki da ba ta yarda za’a yi shirinsu ya yi tasiri. A wannan lokacin burinsu b’ata sunan Sarki da yi masa shirin aikata zina shima ta yarda Al’al’ummar Gabas za su yi tur da shi har a tsige shi daga sarauta. Wani dare da ba zan tab’a mantawa da shi ba cikin talatainin dare na dinga jin motsi ana shigowa b’angaren da nake, ban tsorata ba don na san Amintacce ne, na mik’e zuwa parlourn ina haska y’ar k’aramar torch light da take hannuna. A zaune na gan shi jikinsa sai rawa yake ba shi da nutsuwa sam a lokacin. Nima na tsorata na zauna ina kallonsa a raunane na ce “Gaya min me ya faru?” Ya d’ago idanunsa da suka raunata a hankali ya ce “Sun gane ni Tauraruwa sun gane ni malek’in sirrinsu ne ina tsoron cutarwarsu gare ni.” Shiru na yi ina kallon idanunsa da yarda suka bayyana raunin da zuciyarsa take ciki na girgiza kai ina furta “Allah ya fi k’arfin su ka nutsu ka gaya min me suka ce maka?” Ya lumshe idanunsa hawaye na bin fuskarsa ya ce “Sun sace y’ata Tauraruwa ban san me za su je su aikata mata ba….. Sun kuma rantse idan na gayawa wani za su kashe ni su kuma kashe dukka iyalina….” Na bu’de ido ina kallonsa na ce “Y’arka fa ka ce sun sace? Wace y’ar taka? Y’a mace d’aya da ka mallaka daga cikin yaranka?” Ya d’aga kai rauninsa na sake na bayyana……. Na girgiza kai na ina sakin murmushi na ce “Ka share hawayenka Amintacce ba abinda zai samu y’arka In sha Allah sai alheri, ina son ka je ka cigaba da saka musu ido, babu abinda zai samu y’arka In sha Allah sai alheri.” Gwauron ajiyar zuciya ya sauke yana kallo na da raunatattun idanunsa kafin ya girgiza kai ya ce “Na yarda da ke Tauraruwa, na yarda ba zaki bar wani abin cutarwa ya samu y’ata amma ina tsoro ina jin firgici kada su tozarta mutuncin y’ata.” Shiru na masa cike da tausayinsa na Kuma ji a raina ina son taimaka masa ba kuma na son wani abu ya samu y’ar tasa. “Tashi ka je amintacce a daren nan zan san abin yi.” Na fa’da masa cike da k’warin gwiwa. Jikinsa ba k’wari ya mik’e ya fita daga b’angaren nawa. Tunda ya fita ya bar ni na kasa mik’ewa daga inda nake zaune, zuciyata cike take da tunanin samun mafita, da gaske kuma bana son wani abu ya samu zuri’ar amintacce don na san idan har wani abu ya samesu ni ce sila, kai tsaye zan iya cewa ni ce na jawo musu. Ban samu mafita ba don gaba d’aya a daren sai kwanyata ta zama kamar bata aikin da ya kamata. Har washegari ba ma fitar a gareni sai ga shi a daren ranar ya sake dawo min jikinsa ba k’wari. Zama na yi ina kallon yanayinsa zuciyata na wani irin bugu, murya a tausashe na ce “Sun saketa?” Ya girgiza min kai “Ba su saketa ba ranki ya da’de asalima sun bijiro min da buk’atar da ta razana tunani na, sun ce kuma dole na yarda idan ba haka ba za su kashe yarinyar.” Da sauri na d’ago ido ina kallonsa na ce “Me suka ce maka?” “Sun buk’aci lallai sai na amince an dasa k’waya k’wayan haihuwar Sarki a jikinta za’a ha’da da na Fulani Raheena idan ta haife abinda ta haifa za su karb’e sai su sallameta na bar garin da ita idan kuma ba haka ba, sai dai su kasheta don gudun fallasuwar sirrinsu.” A kishingi’de nake ban san sanda na mik’e ba ina kallonsa na ce “Dashen ciki fa ka ce Amintacce? Cikin ma Kuma na Raheena? A yaushe suka ce za su yi mata?” Ya girgiza kai a hankali ya furta “A yau cikin dare suka ce za su mata…” “A ina kake tunanin sun ajiyeta?” Na fa’da hankalina a tashe. Cikin raunin zuciya ya ce “Ban sani ba, sun b’oye hakan daga gareni.” “Ka je ka bi diddigi amintacce idan ka samu inda take kazo ka sanar min, a yau ba sai gobe ba ya kamata mu fatattaki shirinsu ta hanyar da har abada zamu musu lahani.” D’aga min kai ya yi kafin ya mik’e gwiyoyinsa a salub’e ya fice daga wajen, na bi shi da kallon tausayi ina addu’ar kada Allah ya basu ikon cutar da baiwarsa. A ru’de cikin tashin hankali ya dawo a cikin daren jikinsa na kakkarwa ya zube a gaba na yana furta “Shikkenan Tauraruwa burinsu zai cika sun shiga da ita inda zaa mata dashen su da wata likita…..” Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna shine abinda na furta kawai ina rik’e kai na….. A min afuwa don Allah na sab’a alk’awarin da na yi jiya uziri ne Babba ya rik’e ni. Wanda na sanar muku jiya. Na gode da ha’din kan da kuma ba ni da addu’ar da mamaci ya sha zan muku typing gobe In sha Allah don na cike gurbi. Na gode sosai. JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Kallon da Yake mata kai tsaye yana bayyana tsananin mamaki da ru’danjn da zuciyarsa take ciki, bayan abinda ya kira rainin hankali daga gareta sai kuma mamakin tsananin kamanninsu da ya ru’dashi don haka abin ya ha’du ya masa yawa, har ya gaza furta ko kalmar a daga tarun maganganun da suke dank’are a zuciyarsa wanda ya kamata ya gaya mata su a take. Lallai matar nan da k’arfin hali take ya furta a hankali amma kuma zan shayar da ke kalar nawa mamakin. Murmushin shima ya yi mata yana kama hannunta da take mik’o masa. “Kada ka yarda da duk abinda ta fa’da Jaheed!” Ya juyo muryar da ko bai juya ba ya san Jaheed ne, bai fasa abinda ya yi niyya d’in ba na kama hannunta ya rik’e lokaci guda yana sake jifanta da mayaudarin murmushi da yake k’ak’aro shi da k’yar. “Ke ce Umma na da gaske?” Ta d’aga masa kai “Tabbas ni ce Ummanka Jaheed, Nene ni ta haifawa ku.” “Ta yaya?” Jaheed ya fa’da yana jefa mata tambayar da ta saka ta kallon k’wayar idanunsa ta furta “KUDIRAR ALLAH.” Girgiza kansa ya yi yana juyawa yana kallon Murad da ya k’araso wajen da d’an hanzarinsa ya fincike hannun Jaheed d’in yana furta “Baka ji abinda na ce maka ba ne? Ta yaya zaka amince da ita? Ka tab’a ganin yarda Mace biyu suka samar da haihuwar mutum guda?” Madadin Jaheed ya saurare shi gani ya yi kawai ya rungume shi da sauri cikin murna yana furta “Alhamdulillah Allah, Alhamdulillah for today and forever.” Wasu hawaye suna zubo masa. Murad ya saka hannu yana bubbuga bayansa gefe guda kuma yana wurgawa Tauraruwa harara da itama take kallonsu tana sakin nata murmushin wani farin ciki marar misali yana sake rub’anya a zuciyarta yau gata ga jinin su ita da Maimartaba abinda suka cire tsammanin faruwarsa. Ji suka yi kawai ta rungumesu itama. Da sauri Murad ya saka hannu ya d’an tureta kafin ya ja gefe yana watsa mata kallo ya kuma finciki hannun Jaheed suka bar wajen a d’an hanzarce Jaheed ya ja hannun Faruk da yake tsaye yana kallonsu cike da murna shi ma, tabbas ba sai an fad’a ba kana ganinsu ka ga y’an biyun da ake kira identical twins. Mutanen wajen da dama bin su suka yi da kallo, nan da nan gulma ta samu wajen zama a masarauta kowa yana jinjina girma ga k’udirar Ubangiji, ga duk wanda ya san Tauraruwa da irin soyayyar da suke wa junansu ita da mai martaba ya kwana da sanin cewa zata iya sarayar da dukkan farin cikinta don farin cikin sarki, amma ba su yi tsammanin har zata iya sarayar da rayuwarta ba tsawon lokaci ta b’ace b’at sai yanzu ta bayyana da abin ban mamaki yara har biyu kuma halattattun Jinin sarki, kan su ya d’aure ga wanda ya san mafarin abin ga wanda bai sani ba kuwa sai ya zama kansa a cikin duhu yana kuma lalube a duhun da son sanin ta yaya aka haihu a ragaya? Shirun shine ya fi alheri har zuwa ranar da tauraruwar zata gaji ta bayyana sirrin da take k’udundunewa. Ta bi bayansu da kallo kafin ta ja k’afafunta ta wuce tana sakin murmushi so take ta je ta isar wa da Maimartaba da kyakykyawan albishir da bata son wani ya rigata. Zata sanar da shi zuwan Jaheed yaron da bai tab’a ganinsa ba a rayuwarsa. Gwara ita tana yawan ganinsa a sigar da bai zama lallai ya san wacece ita ba, tana da hotunansu da komai nasa ba tare da ko su iyayen rik’o nsa suna da masaniya akan bibiyar da take musu ba. Tunda labarin iso watsi ya shiga kunnen Nene da Fulani Saddik’a daga bakin amintattun bayin fulanin murna ta cika zuk’atansu dafatan Allah yasa wannan karan asirin komai ya fallasu a kuma tabbatar da su matsayin y’ay’an Nenen halastattun y’ay’a. Shigowar Jaheed yasa su mik’ewa Fulani ta dinga kallonsu cikin mamaki da k’udirar Allah, kamaninsu kwabo da kwabo sun bayyana k’arara ta yarda dole a kira su jini guda. Banda yanzu Murad ya bar parlourn tabbas da ba zata iya banbance su ba, sai dai shi Jaheed fuskarsa a sake take koda yaushe cikin yalwar fara’a sab’anin Murad da fuskarsa take a tsare mai nuni cikar mazantakar d’a namiji. Jaheed ya isa gaban Nene yana fa’dawa jikinta cikin murnar ganinta ta sake haske sosai don tuni ta wanke duk wani abu da ya b’oye kamanninta tun bayyanar sirrinta. Murmushi kawai ta saki tana kallon Faruk da masa alamar ya shigo. Wajen zama ta ba shi sannan ta zauna itama Murad da Jaheed suka zauna Jaheed kusa da Nenen daf shi kuma Murad sai ya koma kusa da Fulani da ya ji kunyar yi mata butulci. Hakan da ya yi kuwa, sai ta ji ya burgeta. “A yau ya kamata mu isa wajen mai martaba mu bayyana Nene a matsayin wacce ta haife mu.” Jaheed ya fa’da yana kurb’ar ruwan tataccen inibin da yake hannunsa. Fulani ta girgiza kai duk da ita ta san abinda ba su sani ba game da Tauraruwa hakan bai sa ta k’i mara musu baya ba, itama burinta kenan jin yarda aka samar da cikin a jikin Nene. “Hakan shine ya dace, amma ku fara cin abinci mana musamman su da suka d’auko gajiya ka kai su can sashenka su yi wanka su huta idan Maimartaba ya fito daga sallar azahar sai mu rankaya mu tafi.” Kowa ya amince da shawarar Fulani don haka suka bi Murad ita kuma suka cigaba da tattaunawa da Nene da itama ta san wani abu game da Tauraruwa wanda su ba su sani ba. A yau kuma Nenen zata bayyana kanta a matsayin mahaifiyarsu tunda ba wanda ya san da zamanta a masarautar ta san zuk’ata da dama za su shiga mamaki da tambayar yarda aka haihu a ragaya. ____ A fusace ta mik’e tana duban amintacciyar baiwarta da ta kawo mata labarin iso war Jaheed masarautar. “Tsananin kamaninsu ya b’aci uwargijiyata duk wanda ya kalleshi ba sai ya tambaya ba zai san jinin Yarima mai jiran gado ne…..” wani kyakykyawan mari ta zuba mata a k’unci tana fesar da hucin b’acin rai ta furta “Mai jiran gadon Ubanki? A gabana kike furta wannan bak’ar maganar, ina so ki rubuta ki ajiye ko zan yi yawo tsirara Murad ba zai mulki al’ummar gabas ba, balle wani d’an uwansa da bai tashi a gidna sarautar ba ma… Fice min daga d’aki….” Sum sum ta fice daga d’akin zuciyarta cike da jin d’d’acin abinda Uwargijjiyar tata ta mata. Fulani Raheena ta bita da kallon banza kafin ta mik’e a hanzarce ta bu’de wardrobe d’inta. Hotuna ta binciko wanda aka iso mata da su a daren jiya ta bi hotunan da kallo duk da shekarun da suka d’auka suna nan kar da su ana gani ba abinda ya goge a cikinsu. Murmushi ta saki a zahiri ta furta “k’aryar Ki ta sha k’arya tauraruwa mu zuba ni da ke, yanzu aka sosa wasan.” Ta isa gaban mudubi ta d’au wata kwalbar turare ta shafa ta gyara fuskarta sosai. Fadar Maimartaba take son zuwa tafi son a yi komai a gabanta ko ba haka ba kuma tana son tarwatsa farin cikin Tauraruwa ta Kuma bayyana gaskiyar abinda tauraruwar take son ta hak’a ta birne. Hotunan ta tura cikin aljihun alkyabbarta sannan ta zura takalmin ta. Ta k’ofar baya ta fice don isa ainahin sashen Maimartaba. Tun a k’ofa wasu fadawa biyu suka tsayar da ita ha’de da sanar da ita Tauraruwa ta bada Umarnin kada a bar kowa ya shiga sai da izinin ta. Cikin mamaki take kallonsu murya a sark’e ta ce “Baku gane ni ba ne?” Sunkuyar da kai suka yi suna furta “Mun gane ki ranki ya da’de sai dai anan wajen umarnin tauraruwa gaba yake da naki..” Hucin numfashi ta saki zuciyarta na sake fusata kamar ta make shi sai kuma ta ce “Ka je ka gayawa Tauraruwar ni nake son ganin mai martaba.” Ta fa’da tana jin wani takaici na shak’e wuyanta. Da sauri ya nufi ciki don cika umarnin ta. Tsawon mintuna kafin Tauraruwa ta d’ago tana kallonsa ta ce “Je ka kace ta shigo.” Mai martaba yana zaune bai ce komai ba duk hankalinsa yana kan ganin Jaheed da Tauraruwa ta sanar da shi zuwansa. “Jaheed zai shigo amma ina son mu fita da ni da kai waje gaban jama’a don kowa ya gan shi ya shaida jinin mu ne, ina son kuma nunawa jama’a wani abu.” Ta fa’da idanunta cikin na Sarkin da yake kallonsa ko k’iftawa bata yi, sai dai wannan karan fuskarta a gintse take ba fara’a ko ka’dan da alama akwai wani abu da ya b’ata mata rai. Sarki ya d’aga kai kawai alamar ya yarda da abinda ta ce. Fulani ta shigo fuskar nan a ha’de ba alamar fara’a balle dariya. Wani kallon tsana take jifan Tauraruwa da shi ita kuma Tauraruwar ko kallonta bata yi ba hankalinta na kan bafaden da yake isarwa da sak’o ya je ya sanar a farfajiyar masarautar. Tana gama abinda take kuma bata ko kalli sashen Fulani ba ta mik’e ta shige cikin bed room d’inta tana ji a ranta lokacin fasa b’aragurbin k’wan Fulani Raheenan ya yi, don tana lura da kallon da yake mata. Shiru harabar masarautar don haka sanarwar da ake a loudspeaker ta isa kunnuwan duka jama’ar masarautar. Dama haka suke so don haka kafin kace me ye wannan babban filin ya cika mak’il da jama’a har da na waje ma sun shigo don ta waya aka dinga sanar da su neman da Sarkin gabas yake wa mutane, dama abinda suke jira kenan. Sarki ne ya fara fitowa shi da Fulani Raheena da ta fito itama daga parlourn bayan fitowarsa. Cikin takun isa ta zauna a wajenta. Sai da kowa ya zo har Jaheed Murad da Fulani Saddik’a banda Nene. Sannan Tauraruwa ta fito cikin shigar alfarma da ta d’auke tunanin hankalin jama’ar wajen. Kallonta kawai ake ana ganin kamannin y’an biyu a tare da ita. Bata zauna ba ta karb’i loud speaker ta yi sallama cikin murya mai cike da nutsuwa ta furta “Alhamdulillah Alhamdulillah yau rana ce mai matuk’ar farin ciki a tare da ni, ranar da na da’de ina jira ranar da zan nuna jinin Maimartaba da nawa, a lokutan baya mun sare mun karaya mun fitar da ran samun Magaji sai dai cikin hukuncin ubangiji sai Allah ya mana kyautar da ba mu yi tsammani ba kyautar yara biyu wanda ga su nan a zaune Murad da Jaheed, Jinin mai martaba ne haka nan jini na ne yake yawo a jikinsu ma’ana su ne Jininmu yaranmu da muke alfahari da su…….” “Mu ba yaranki ba ne, ga Mahaifiyar mu nan.” Murad ya fa’da yana nuna Nene da take gefensa gaba d’aya hankulan jama’a ya koma kan Nene da yake tsaye daf da Murad……. JIKAR NASHE.✍🏽🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Maimartaba ma da gaba d’aya hankalinsa baya wajen yana kan Jaheed da ya zubawa ido yana mamakin kasancewarsa d’ansa, ya mayar da kallonsa kan wacce aka kira mahaifiyarsu. Wata irin fa’duwar gaba ta sameshi ba don komai ba sai don bai santa ba bai tab’a ganinta ba ta yaya zata zama Uwar y’ay’ansa? Me Tauraruwa ta shirya haka ne? Ya tambayi kansa duk da ya san bai da amsar don haka ya mayar da kallonsa kan Tauraruwa da take ta kallon Murad tana sakin murmushi ta furta. “Ba zan ce maka komai ba, amma ko yanzu aka tsaga jikinka za’a tarar da Jinina baka son komai ba yaro shi yasa ka ke tunanin da kake yanzu….” Ta juyar da kallonta kan Maimartaba da gaba d’aya hankalinsa yana kan Nene da take tsaye tana rawar jiki. Itama idanunta ta sauke cikin na Nene kafin ta matsa daf da ita Nene ta sake shak’ar k’amshin turaren da ya zauna ra’dam a hancinta tun shekarun da suka wuce da alama kuma har yanzu Tauraruwar bata canja turaren ba. Kallon da Tauraruwa ta mata yana nuni da kin manta da alk’awarin da kika min na ba zaki sake dawowa masarautar gabas ba ko? Kin manta gwalawalan da na baki don ki nesanta kan ki daga masarautar gabas? Me yasa kika dawo? Kin shirya mutuwa kenan? Wad’annan sune fassarar da ta yiwa kallon Tauraruwa don haka zuciyarta ta shiga bugu da sauri kamar yarda gabban jikinta suke kakkarwa tsoro da razana suka bak’unci sassan jikinta da ma zuciyarta gaba d’aya. Da sauri ta sunkuyar da kanta duk da Tauraruwa ta b’oye kamanninta a wancan lokacin ita kuma zuciyarta ba zata tab’a kawo mata Tauraruwa ce ba saboda labarin rasuwar ta a lokacin ya da’de da karad’e masarautar gabas, ba mamaki da ace ta bayyana kanta a lokacin tsananin firgitar da zata yi zai iya sanadiyyar rasa ranta, da ba ma sai ta wahalar da kanta da gold ba balle har ta umarceta da tafiya mai nisan da ba zata sake wai wayar masarauta ba. Shiru da ta yi da rawar da jikinta suke shine dalilin da ya janyo mata idanun jama’a kanta. Murad ya ja hannunta zuwa kujerar da ke gefen Mammansa so yake zuciyarta ta samu nutsuwa baya son ta saka tsoron da zai sa ta kasa kwatar y’ancinta. Duk da iya ahalin masarautar ne a k’aramin filin fadar mutanen waje suna ainahin babban fili bai hana ihun da ake shigowa cikin fadar ba, mutane suna fa’din yau dole ne su san gaskiya. Tauraruwa ta lumshe idonta bayan ta sake damk’e speakerr hannunta murya a nutse ta fara jawabi. Ga duk wanda ya san ni ya san ni da soyayyar mai martaba a rayuwata, ya kuma san yarda muke sadaukar da farin cikin junanmu don wanzuwar farin cikina ko mai martaba. Rasa Magaji da mai martaba ya yi a wancan lokacin shine abinda ya dugunzuma hankalina yake kuma hana ni barci a kowane daren duniya. Mafita nake nema masa ko nace nake nema mana don duk wani abu da zai damu Maimartaba kamar ya shafi tauraruwarsa ne, kamar yarda ya sha fa’da a mabanbantan lokuta, Ni ce farin cikinsa ni yake burin sakawa a farin ciki a koda yaushe, nima Kuma haka yake a wajena burina samun farin cikin mai martaba ko da ni nawa farin cikin zai yi k’aura. A wannan lokacin ban damu da kai na ba. Kwatsam sai aka wayi gari Raheena ta samu ciki. Ni na bi diddigi na hango cikin da Raneena take d’auke da shi ba halastaccen d’an sarki ba ne, don haka a duk sanda zata haihu ni nake ha’da baki da Jakadiya mu saka mata gawar jariri mu sace d’an da ta haifa…… Wata irin hayaniya ce ta sark’e a wajen kowa kallonsa ya koma kan Raheena da hankalin ta ya tashi matuk’a ainun, bata zata a sirrinkanta har da wannan Tauraruwa ta sani ba. Ma’ana kenan duk wad’ancan yaran da take haifa suna raye ba tare da ita kanta ta san suna rayen ba. Zufa ce take karyo mata sosai, musamman da ta yi arangama da kallon da sarki yake mata, da alama shima bai san da wannan badak’alar ba sai yanzu. Cab’di jam! Idan kuwa haka ne tabbas ba zata kwana ita ka’dai a ciki ba tilas sunan duk mai hannu a ciki ya fito tunda ita dai a yanzu ta san b’aragurbin kwan da take b’oyewa ya fashe don haka dole na kowa ma ya fashe! Shiru ya kasa samuwa a wajen wasu da dama tsananin mamaki da al’ajabin abin suke suna ganin kamar alamara. Ashe shi yasa lokacin in dai ta haihu sai a ce yaro ya mutu. Gyaran muryar da Tauraruwa ta yi ne yasa suka ja baki suka yi shiru ba don komai ba sai don suna son su san me kuma ya faru a gaba. Bata hak’ura da bibiyar wa’danda suke mata ciki ba, kamar yarda nima ban hak’ura da bin duk wani taku nata ba da sace d’an da duk zata haifa har zuwa sanda suka ankare da abinda nake aikatawa. Suka shirya kasheni. Na ji su a lokacin da suke shirya dukkan manak’isarsu kamar yarda mai kawo min rahoto yazo ya gaya min da recording d’in da komai yana cikinsu amma basu san ba ta tare da muguntarsu ba, shi mutum ne salihi kuma masoyin Sarki na gaske ya yi Basaja a cikinsu a zuwan shi mutum ne mugu mai son lalata rayuwar sarki kamar yarda suma suke so. Hankalinsa a tashe ya iso sashena amintacciyar baiwa ta tana gaya min shine ban yi a k’asa a gwiwaba na fito sirrintaccen parlorna da nake ganawa da bak’in sirri. Idanunsa kawai na kalla na tabbatar da ba lafiya ba kuma yana cikin matsananciyar damuwa da fargaba. “Bawa na gari!” Na kira shi da sunan da nake kiransa da shi. “Me ya faru?” Muryarsa cike da tsoro da firgici ya ce “Tauraruwar Sarki sun shirya kasheki a gobe cikin dare…” Dariya na yi sosai kafin na gyara zama na na ce “Ba wanda yake mutuwa sai kwanansa ya k’are ba su isa su kasheni ba sai Allah ya so. Me ka ji suna k’ullawa? Da wata siga za su kasheni?” Shiru ya yi kafin ya girgiza kai ya furta ban tabbatar ba tauraruwa tsoro da firgici ba su bar ni na ji k’arashen maganar ba, abu guda na sani sun ce dole su kawar da ke idan ba haka ba ke ce zaki musu Katanga daga cikar dukkan burikansu…” shiru na yi ina mamakin bak’ar zuciya irin ta jama’ar da suke Ke waye da mai Gabas. “Tashi ka je adalin bawa Allah ba zai ba su nasara ba, dukkan hukunci a wajensa yake da shi kuma na dogara.” Na fa’da zuciyata cike taf da tauhidi na kuma gasgata babu wanda zai min abinda Allah bai min ba. Ban yi barci ba ina ta sak’a abinda zai fishsheni har zuwa sanda zuwa ta ta amince na barsu su kashe ni d’in…. Kashegari bayan fitowar Sarki Fada da safiyar Alhamis ya dubeni ganin yarda na shigo fadar kamar ba nutsuwa a tattare da ni, a gefen sa na zauna ina gaisheshi cikin kulawa ya dinga dubana kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce “Akwai abinda yake damun Tauraruwar Gabas gaya min maza koma menene na miki maganinsa.” Murmushi na saki kafin na furta “Tafiya zan yi ran Maimartaba ya da’de tafiyar kwana biyu shine nake tsoron ka hana ni, tafiyar tana da matuk’ar mahimmanci gare ni da kai gaba d’aya har ma da al’ummar gabas da na tabbatar suna farin ciki da samuwar farin cikin ka.” Shiru ya yi shirun da yasa k’irjina ya dinga bugu, bana son na ji kalmar “A’a daga bakinsa tun kafin ya furta kalmar a’a na san bai yi na’am da wannan tafiyar tawa ba. Ido na zuba masa kallon da na san idan na masa shi yana saka shi ko baya so ya aikata abu. Ai kuwa na raunata zuciyar tasa don a wannan gab’ar kasa dakatar da ni ya yi, ya dai d’aga min kai cikin murya mara amo ya ce “Allah ya tsare ya kiyaye hanya ina zaki amma?” Na yi shiru ina kallon mutanen da suke gefensa wad’anda na san burinsu su ji inda za ni. Na ce “Yola jihad Adamawa.” Murmushi maimartaba ya saki don ya san Yola mahaifarmu ce kuma a kowane lokaci in dai na nufin sada zumunci ina zuwa saboda dangin mahaifiya a can su ke. “A gaida mutanen Yola, sai ki zab’i bayin da zaki yi wannan tafiyar da su, amma bisa shara’din ba zaki zarce kwana biyu ba kamar yarda kika alk’awarta kin san sam bana son yi nisa da ke na kan zamo Rabin mutum idan ba kya kusa da ni.” Ina murmushi na d’aga masa kai kafin na fice daga Fadar jikina a sanyaye don ina jin wannan itace ha’du wata da maimartaba ta k’arshe sai kuma wani lokaci mai dogon zango. Mutanen Fadar na dinga bi da kallo ina nazarin fuskokinsu a take hasashe na ya bani gaskiya tabbas mugayen suna cikinsu kuma sun ji da’din tafiyar daga gani wata hanyace da zasu samu ta cikar burinsu. Na zab’i bayin da nake so aka kuma shirya min motocin da Zan tafi da su. A ru’de amintacce na yazo ya ce da ni kada na shiga Motar da na yi nufin yin tafiya da ita don sun saka wani abu mai kama da bom da zai iya tashin motar cikin lokaci guda zata k’one da duk abinda suke cikinta. Na girgiza masa kai ina furta “Ita zan hau Amintacce ba don komai ba sai don na shirya mutuwa! Tunda har burina na samawa Maimartaba Magaji bai cika ba gwara na mutu kawai!” Shiru ya yi yana kallona cikin mamaki na san yanayin da nake ciki ne ya ba shi tsoro har hakan ta kasa b’uya akan fuskarsa… ya zube a gabana “Tauraruwa don Allah kada ki fara, ina mai martaba zai saka ransa a duk sanda ya samu labarin rasuwarki, ki tuna fa ba shi da uwa ba shi da uba ke ka’dai ce Y’AR UWARSA DA KUKE UWA DAYA UBA UBA DAYA, ina kike son ki je ki bar shi cikin tarin mak’iyan da Suka masa k’awanya? To fa! Yau kuma Tauraruwa ta koma k’anwar Sarki? Ashe dai ba y’ay’anta ba ne to ta ina aka samar da cikin Nene? Na waye? Ko dai na Fulani Raheena ne ta dasa k’wayayan a cikin Nene? Wata sabuwa in ji Y’an caca!🤣 Idan kin san kina karanta min littafi baki biya ba ki taimaka ki biyani hakkina Wallahi wannan ba kyauta ba ne…. JIKAR NASHE✍🏽🫣🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ni kaina a firgicen nake, kwanyata at gaza aikin da ya kamata sai wani irin tsuma jikina yake, ji nake dama na farka naga mafarki nake ba zahirin gaskiya ba, zan so ya kasance mafarkin ne saboda yarda tsoro ya jijjiga zuciyata. Ganin Amintacce a gaba na ya tabbatar min da ba mafarkin nake ba, hawayen da suke zubo daga idaniyarsa suka tuna min cewa ya kamata na mik’e mu je mu ceci baiwar Allah yarinyarsa da ake niyyar cuta. Da sauri na mik’e ina kallon Amintacce na ce “Ya kamata mu je mu samu mafita ka je wajen Baffa Liman yanzu don da shi ka’dai zuciyata ta aminta ka taho min da shi nan, kafin nan ka biya ta inda suke ko da cikin shigar sirrina ka tabbatar da k’udirinsu bai kai ga cika ba tukunna don duk abinda zan aikata in dai k’udirinsu ya cika ya zama na makara, ba ni da ikon cetonta. A yanzu ma fargaba ta ban san ta yaya aka yi Suka samu Sperm d’in sarki ba Anya kuwa Amintacce dashen za su mata ko dai wani mugun aikin za su aikata mata? Kuma da sperm d’in wa za su mata amfani?” Amintacce da bai gane duk tunani na ba ya mik’e kawai yana furta “Allah ne ya barwa kansa sani Tauraruwa bari na je can d’in duk yarda ake ciki zaki sani don yanzu zan dawo zan kuma taho da Baffa Liman kamar yarda kika buk’ata.” Na d’aga masa kai ganin baya cikin nutsuwar da zai gane inda zantukana suka tafi, bana tunanin dashe zasu mata don in dai dashen za su mata zai zama da sanin Sarki kenan? Alhali kuma na tabbatar katab’orar su bata kai su bari Maimartaba ya san da wannan aika aikar ta su ba. Bai d’au lokaci ba ya sake dawo min wannan karan razanar da yake ciki har tafi ta baya, ya zube a gabana yana zufa ya furta “Shikkenan Tauraruwa sun fasa dashen wai, amma a gobe za su bawa Maimartaba wani magani da zai bugu sosai har ya sadu da ita bai sani ba, itama kuma ba zasu Bari ta sani ba don za su bugar da ita, duka na ji zantukansu ne ta inda suke sirri ba tare da sun san ina wajen ba, sai dai cikin rashin sa’a ina juyowa suka gan ni, da sauri suka biyo ni da k’yar na b’ace a cikin duhun bishiyu amma na san sun ganni kuma wallahi kasheni za su yi. Don ina ji D’aya daga cikjnsu yana furta “Mu kashe shi in dai mun same shi don bayyanuwar wannan sirrin kamar katsewar numfashin mu ne a duniya kun san sarai Maimartaba ba zai bar mu ba. A yanzu na lura Tauraruwa ba burinsu Samun Magajin Sarki ba burinsu tarwatsa duk wani farin cikin Sarki burinsu b’ata masa suna da saka wa mutane tsanarsa a zuciya kin kwana da sanin yarda Al’ummar Gabas suka tsani Zina suke kuma gaba da duk mai aikatata ina ga ace Sarkine da kansa ya aikata, na san tawa ta k’are tauraruwa da ni da dukka Ahalina sai dai ina ina rok’on alfarma a gareki ki kula min da Yarinyata ki tsare min mutuncinta don Allah.” Ya fa’da yana sakin wani irin kuka mai bayyana da gaske bankwana yake, abinda ya sake dugunzuma min kwanya. Na saka shi ya shiga wani d’aki na rufe d’akin na datse da d’an mukullin da ke hannuna, kafin na shiga wani d’aki na yi shigar da zata b’atar da dukka kamannina na koma kamar wata Bafadiya don irin shigarsu na yi. Ban ji tsoro ba na fito daga sashen da ba kowa a cikinsa daga ni sai halina don sashena mai tsohon tarihi tun kakaninmu anan suka yi zamanin su don haka duk wani abin tarihi na masarautar gabas yana cikin wannan b’angaren ba wanda ya damu da shigarsa don sai a yi shekara ma baa bu’de shi ba, daga shekara sai shekara ake shigarsa a lokacin hawan Sarki na bikin k’aramar Sallah daga nan shikkenan don ko bikin hawan Babban Sallah baa bu’de shi. Tsakiyar dare ne don haka ba kowa a wajen sai kukan tsintsaye, a nutse nake tafiya zuciyata cike da tsoro sai dai k’arfin hali irin nawa yasa na dake na isa har sashen Baffa Liman, wanda k’ani ne ga mahaifinmu da suka ha’da iyaye wato y’an maza zar suke, a gidansu kowa ya san sarautar Limancin Babban Masallacin Gabas yake. A k’ofar shiga sashen nasa na tsaya, na yi kuma k’ok’ari sosai wajen kaurara muryata har ta dawo kamar namiji na ce wa mai tsoron sashen ya min iso a wajen Baffa Liman Ina son ganinsa ne a uzurce nake. Shiru mai gadin ya yi kamar ba zai je ba sai kuma ya juya zuwa zauren gidan wanda na tabbatar addu’ar da nake ce tasa ya tafi ba musu. Tsawon mintoci kafin Ya fito ya iso inda nake da hannu ya ce min “Bismilla ya ce ka shiga.” Na kuwa dogara y’ar sanda ta da ta mayar da ni kamar tsoho na isa zauren inda anan ne d’akin da Baffan yake ganawa da mutane. Gyaran murya ya yi kafin ya d’an haska ni da torch light ya ce “K’araso wani bak’o muka samu cikin daren nan.” Ban yi magana ba sai dai na k’arasa zuwa saman buzun da yake nuna min. Na zauna sosai kafin na saka hannu na yaye mayafin hiramin da yake kaina kamanina na Tauraruwa da na san ba zasu tab’a gogewa a idanun Baffan ba Suka bayyana, wani irin fitgita Baffan ya yi kafin ya yi baya da sauri har torch light d’in hannunsa na fa’duwa yana fa’din Subhanallahi me nake gani haka? Ashe dai da gaske ana fatalwa? K’ok’ari yake ya zunduma ihu na yi saurin saka hannu na toshe bakinsa ina rik’e dariyar da take son sub’uce min na ce “Baffa ka nutsu ni ce, Tauraruwa ce a zahiri Ba fatalawa ba, ban mutu ba ina raye ina son wannan kuma ya zama sirri a tsakanin mu….” Jikinsa bai bar rawa ba sai dai ya d’an nutsu ka’dan ya zauna sosai yana kallona ya ce “Ki rantse da girman Ubangijjnki ba fatalwa ba ce ke..” Na saki murmushi na ce “Wallahi Baffa ni ba Fatalwa ba ce, ka ji na rantse maka ba wanda ya san ban mutu ba daga Amintacee sai kai da yau na zo neman taimakonka.” Ya saki nauyayyiyar ajiyar zuciya ya ce “Ke kuwa Hajiya mai ya kai ki aikata haka?” Labari na bashi, labarin da na lura ya firgita shi matuk’a da gaske don zufa yake gogewa sosai a goshinsa ya ce “Hasbunallah yanzu kina nufin su ne suka aikata haka?” Na d’aga kaina cike da gamsarwa na ce “Wallahi Baffa, shine yanzu na zo neman taimakonka, na tabbata ko maimartaba aure zai yi kai ne dai Waliyyinsa wanda zai amince ka karb’ar masa aure don haka nake son kafin goben burinsu ya cika mu je da kai wajen Amintacce wanda shine Uban yarinyar a d’aura aure a gidana ka bashi sadakin y’arsa da duk abinda shari’a ta tanadar.” Liman ya jinjina kai ya ce “Hakan da kika yi shine daidai Hajiya, amma a ina kike ga zamu samu shaidu da zasu zame mana shaida ko nan gaba.” Shiru na yi ina tunanin mutane uku da zuciyata ta amince da su, na san kuma ba zasu tab’a k’in goyon bayan abinda nake so ba, don haka kai tsaye zuciyata ta amince da na kirasu na saka su a matsayin shaidu su ma. Baffa Liman da kansa ya saka aka nemo masa mutane ukun da na ambata wanda shima kai tsaye ya ji zuciyarsa ta amince da zab’i na. Sanda suka shigo suka ganni su ma ba k’aramar firgita suka yi ba, sai da na kwatanta musu irin ta Baffa Liman sannan Suka amince da ni, don haka ba b’ata lokaci muka isa tsohon gidan tarihi cikin tsakiyar dare sanda kowa yake kwance a mashimfi’di. A daren ranar juma’ar aka d’aura auren Maimartaba da mahaifiyar su Murad wato wannan baiwar Allahr Nene da ke tsaye…. Gaban Nene da na Maimartaba har ma da na su Fulani ba k’aramar fa’duwa ya yi a wajen ba, idanun kowa ya fito waje tun kafin Tauraruwa ta k’arasa labarin kowa ya shiga firgici musamman wa’danda Suka san Suna da ruwa da tsaki a cikin duk abubuwan. Hayaniya ta fara yawa a wajen. Murad da Jaheed kuwa wata irin runguma suka kaiwa Nene tsananin farin cikin da suke ciki ya kasa b’oyuwa. Maimartaba ma murnar yake yana ta kallon su Jaheed cikin tsananin k’auna tare da mamakin yarda aka ce wai Nene matarsa ce ta ya hakan ta kasance don dai shi ya san ko a mafarki bai tab’a ganinta ba balle har ya kusanceta irin kusanci da Namiji yake wa Mace har a samar da ciki a cikin mahaifa. Ya gyara zama yana jiran jin k’arashen labarin a bakin Tauraruwa da murmushin kan fuskarta ya kasa b’acewa. Gyaran muryar da ta yi a loudspeaker ne yasa aka yi shiru don son cigaba da jin labarin da yarda aka haihu a ragaya. An d’aura auren cikin farin ciki da kwanciyar hankali sai dai me? Muna shafa addu’a muka ji an turo k’ofa… hankali tashe muka d’aga kai don ganin waye? Kun san dai bana typing weekend wannan ma na alk’awarin da na d’auka ne na cika shi don haka ku yi hak’uri da abinda ya samu. JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. A biya ni hakkina idan kin san kina karanta na bati ba kyauta ba ne, na fa’da da Babbar murya KUDIRAR ALLAH BOOK TWO NA KUDI NE EEEHE😏 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ta sauke numfashi a hankali tana mayar da idonta a kai na, duk gumi ya gama jik’ata sharkaf idanunta sun ka’da sun yi jajur da alama tashin hankalin da take ciki ya wuce misali. Nima dubanta nake idanu cikin idanu na rasa ma me Zan ce mata tsananin mamaki ya hana ni magana, tabbas ta bani mamaki duk da a gefe guda bana ganin laifinsa ga duk wanda aka saka a wannan takunkumin abinda zai aikata kenan, laifinta guda da bata sanar da Maimartaba ba tunda ta san zai bata dukkan kariyar da take buk’ata ba zai bari a cutar da ita ba. Ajiyar zuciya na sauke a hankali wacce take tafiyar da tarin takaicin da ya yi min dabaibayi a zuciya, na lumshe idona wasu hawaye masu zafin gaske suka shiga kwaranyo min, tunda abubuwan suke faruwa sai a lokacin na samu hawaye suka zubo min hawayen da nake jin suna saka sanyi da nutsuwa a zuciyata, hawayen mutuwar Baffa liman na yi kuka amma bana saka sanyin zuciya ba ne na sake saka zuciya a k’unci ne. “Ki yi hak’uri.” Muryarta ta katse min tunani na na bu’de ido a hankali ina kallonta kafin na girgiza kai. “Bakomai Doctor ba ki min komai ba, sai dai ina neman wata alfarma a wajenki, ki aikata duk abinda suka umarceki a daren nan.” Ta ware ido tana kallona cikin zallar mamaki ta ce “Na aikata fa kika ce?” Na d’aga kai ina furta “Hakan nima nake buk’ata, sannan ban amince ko da wasa ki sanar da wani kin gan ni a raye ba, wannan ya zama sirrinmu.” Na fa’da ina kallon cikin tsakiyar idanunta. D’aga kai ta yi alamar ta amsa duk umarnina. “Idan komai ya tafi successfully ina son duk abinda zai faru ki sanar da ni, sannan ina son ki bata dukka kulawa da ta dace bana son wani abu ya sameta ko ya samu d’an cikinta idan abinda ake buk’ata ya samu akwai kyauta mai girman gaske da zan miki…. Abinci mai kyau, abin sha mai kyau shi nake son a dinga bata bana son ko k’warza ne ya samu yatsanta.” Ta d’aga kai tana tabbatar min da ta d’au dukkan alk’awarin da ta d’auka. Na mik’e ina kallon Amintacce muka tafi Doctor ta raka mu har bakin gate. Muka yi sallama ban koma gida ba, inda su Amintacce suke muka nufa, anan na ha’da musu goma ta arziki na saka aka musu shatar mota suka nufi Garin Yola, na musu alk’awarin bayan kwana biyu nima zan biyo su amma bana son ko da wasa a ga ko inuwarsu a garin Gabas, wannan shine mafarin barin su Amintacce garin nan shine kuma har yanzu ba su dawo ba amma suna nan da ransu har yanzu cikin k’oshin lafiya. Wata irin ajiyar zuciya Nene ta sauke mai k’arfin gaske tana jin wani abu da ya tsaya mata a k’irji yana narkewa zuwa wani irin sanyi, Farin cikin ganin iyayenta shine abinda ya fi komai a zuciyarta da gaske ta yi murna da ya zama na su Babinta suna raye suna da rabon ganawa kuma. Daraja da kimar Tauraruwa suka sake ninkuwa a zuciyarta fiye da kwantance tun kafin ta ji k’arashen labarin ta tabbata Tauraruwa itace ginshik’in samar da dukka farin ciki a rayuwarta ita ta mata garkuwa ga dukkanin muguntar wa’dannan bayin Allahn. * “Na sake komawa gidan da su Amintacce suka zauna, na kuma saka aka ha’da min wayar landline a gidan ba don komai ba sai don na dinga samun duk wani bayani daga bakin Doctor. Koda yaushe a zaman shirin ko ta kwana nake, tunda Doctor ta tabbatar min duk wani aiki ya tafi successfully Maimartaba ya sadu da Nene ba tare da shi ko ita sun san sun aikata hakan ba. Ita kanta bata farko ba sai bayan kwana biyu da afkuwar hakan. Kafin nan Doctor ta mata allurai da drips da zai d’auke mata duk wani ciwo da zata ji a jikinta wanda zai bayyana mata abinda ya faru don haka ba zata gane ba. Su ma kuma ba su san shirinmu da Doctor ba don haka ko a ransu basu kawo Doctor zata ci amanarsu ba dalili sun sanya tsoronsu a zuciyarta ta yarda ba ta yarda za’a yi ta iya k’etare duk shara’din da suka gindaya mata. Bayan wata guda da faruwar hakan, a karon farko da Doctor ta mata gwaji ta tabbatar da samuwar ciki a jikinta. Sun shiga murna sosai don sun san mugun shirinsu daf yake da cika. Duk da ita Fulani Raheena a zatonta taimakonta za su yi su cika mata nata burin itama, sai dai na su burin daban da nata, su burinsu b’atawa Maimartaba suna don har sun d’au hotunan da zasu watsa a duniya ni na saka aka sace cameras d’in bayan biyan mak’udan ku’dad’e. Sun yi bak’in ciki sosai lokacin da suka wayi gari babu cameras d’in da suka dogara da su. Sanda cikin ya bayyana a lokacin ne kuma Fulani Raheena ta samu cikin d’an Sarkin gabas na gaske, wannan karan kam sai Allah ya zartar da ikonsa ta hanyar samar da k’wayan halittar Maimartaba a mahaifar Raheena ba don komai ba sai don ya bayyana ishararsa da ikonsa. Ta yi murna sosai ta so kuma tona musu asiri sai dai sun garga’deta da muddin ta tona musu asiri kamar fasuwar nata b’aragurbin k’wan ne. Wannan yasa ta yi shiru ta kuma shiga bin kwakwkwafin ganin Cikin da Nene take da shi ya zube, lura da hakan da suka yi yasa suka kasa suka tsare suka hanata aikata hakan ta hanyar hanata shiga inda Nenen take. Duk bayan kwana uku nake zuwa duban Nenen ba tare da ta san ni wacece ba saboda na kaurara muryata. Idan na je ina k’ok’arin kwantar mata da hankali da k’arfafa mata gwiwa ha’de da sata cin abincin da zai gina mata jiki ya kuma ginawa jaririn jiki. Har zuwa sanda cikin ya isa haihuwa abin al’ajabi duk da yawan scanning d’in da ake mata baa tab’a ganin y’an biyu a cikinta ba. Ni na bata idea ta sanar da su Nene ba zata iya haihuwa ba sai dai a mata theatre ba don komai ba sai don mu b’atar da tunaninsu. Suka amince da hakan don haka aka saka ranar theatre wanda a ranar ne suka yi nufin kashe Nenen bayan sun d’auke abinda ta haifa, na sanar da Doctor ta amince da abinda suka d’in. Da kai na na saka Doctor ta mata allurar janyo nak’uda sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji ta haifo santalelen d’anta. Da kaina na yanke masa cibiya na kuma masa hu’duba da Suna Muhammad Murad sunan da Maimartaba ya da’de yana burin sanya wa d’ansa. Daga nan ne na umarci Nene ta gudu bayan na amshe d’an na kuma bata dukkan abin da zata buk’ata, Na saka wani driver ya kai ta bayan gari ba tare da sanin cewa yana sake bibiyar duk inda ta yi ba. Har haihuwar da ta yi ya sanar min ni na ce ya k’yaleta ta je ta raini abinda ta haifa kada dukan ya mata biyu. Har gidan da ta zauna na saka aka bibiyeta sai dai na k’i bayyana kai na Sabo da ina son nuna girman Allah a wajen mugayen mutanen. Ni na kai shi k’ofar masallachi a lokacin da aka d’auke ruwan sama. Daga nan kuma na koma inda na fito na fara shirin barin k’asar zuwa wani lokaci mai tsaho. Ban sake waiwayar gida ba sai dai na baza masu saka min ido akan dukkan abinda yake wakana wannan shine abinda ya faru tsawon wa’dannan shekarun ina fatan Maimartaba zai min afuwa akan k’aryar da duk na yi masa na mutuwa da kuma b’oye masa aurensa da Nene da na yi, ba don kowa na yi hakan ba sai don kai don kuma ka samu Magajin da ka da’de kana buri…… Wani irin annuri ne kawai yake fita daga fuskar Maimartaba yana cigaba da kallon Tauraruwa cikin tsananin k’aunarta da take sake rub’anya a zuciyarsa, ta sarayar da duk farin cikinta saboda nasa farin cikin ta bar yaranta guda biyu da ta san suna buk’atarta amma ta jinginar da su suka zama marayun k’arfi da yaji duk saboda cikar nata burin. Me zai ce da Tauraruwa ba shi da bakin gode mata don duk abinda zai furta sai yaga kamar ya yi ka’dan. Mik’ewa kawai aka ga ya yi hawaye na zuba a idanunsa ya isa har inda Tauraruwa take. Ya jawo hannunta kafin ya kira Murad da Jaheed ya nuna musu Tauraruwa yana furta “A yanzu da bayan raina ba ku da wata uwa da ta shige Tauraruwa ni da mahaifiyarku haifar ku kawai muka yi, amma itace silar zuwanku duniya, don haka na umarceku ku yi mata biyayya a cikin dukkan abinda ta umarceku sab’a mata kamar sab’a min ne, kuma ba zan yafewa duk wanda ya saka Tauraruwa a cikin bak’in ciki ba……” Ya juya idanunsa cikin Na Nene da ta yi saurin sunkuyar da kanta wani abu yana tsikararta tun daga yatsun k’afarta har zuwa kwanyarta, idanun Maimartaba sun mata kwarjinin da ba zata iya duban cikinsu kai tsaye ba. Murmushi ya saki kafin ya sake kallon gefen da sauran matansa suke, ya juya ya sake kallon Nene a hankali ya furta “A wani matsayi zan ajiyeki?” JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Dukkanmu a razane muke duban mutumin da yake tsaye ba kowa bane sai mai tsaron bakin zauren gidan Baffa Liman. Muka sauke ajiyar zuciya duk kusan a tare ganin ba mutanen da muke tunani ba ne. Baffa Liman ya ce “Lafiya D’an Audu.” Ya girgiza kai a tsorace ya ce “Wallahi mutane ne suka dunfaro nan… shi yasa na yi saurin zuwa na sanar muku.” Da sauri na mik’e ina kallon Baffa Liman da yake nuno min Amintacce “Ku bi da shi ta k’ofar Baya Hajiya K’arama, ni kuma zan san yarda zan yi da jama’ar da Suka yi yo nan d’in, amma ki tabbata a daren nan ya ha’de kaf iyalinsa sun bar masarautar nan don zamansu anan d’in akwai hatsari mai girman gaske…” Kafin ya gama muka dinga jin suna durfafo inda mu ke, tuni muka fice ni da Amintacce ta k’ofar baya jikinmu duk rawa yake sosai don razana da firgita. Mun yi tafiya mai nisan gaske ta hanyar da ba zasu tab’a ganin mu ba, kafin mu isa gidan Amintacce ya shiga ba su tsaya b’ata lokaci ba suka fito da matarsa da yaranta maza ban bar su sun d’au komai ba banda kayan jikinsu suka nufi hanyar da zata sada su da cikin gari bayan na ba su wani mukullin gida na wanda Amintacce ne kawai ya san da shi. Sai da naga b’acewarsu sannan na koma sai dai ban isa gidan da nake d’in ba, na dai cigaba da k’udundune mukullin d’akina na inda sirrikana suke ciki. Gidan Baffa Liman na nufa kai tsaye don na san zuwa lokacin ya isa gidan sa na san kuma wa’dancan mutanen za su cigaba da bibiyar gidan tunda har hankalinsu ya kai nan, ba za su k’yale gidan ba sai zuwa wayewar gari idan sun tabbatar Amintacce ya tattare zuri’arsa sun bar masarauta. Shiru gidan Baffa Liman d’in, tsoro ya cika min zuciyata da ba tambayi matar gidan ta amsa min da Baffan bai dawo ba, hantar cikina ta d’aka ina duban matarsa da ba abinda ya dameta tana ta harkar gabanta da alama bata shaida ni ba dalilin b’atar da kamar da na yi. Na sake tambayarta “Me zai hana shi dawowa ga shi har goshin asuba ya zo.” Ta d’an juyo tana kallona sai kuma ta ce “Ba mamaki ya nufi masallaci sallar asuba dama ya saba fita a wannan lokacin.” Zuciyata bata amince da abinda ta ce d’in ba, sai dai ya zama dole na yarda don samun sauk’in bugun da zuciyata take tsoro mai girma ya riski zuciyata bana son wani abu ya samu d’an tsohon da bai ji ba bai gani ba. Ban sake firgita ba sai da naga har gari ya fara haske amma ba Baffa ba labarinsa, sannan ne fa na tabbatar da rashin wanzuwar lafiya, na zare jikina daga gidan cikin b’atacciyar shigata na nufi waje har na je bakin masallacin, anan na tarar mutane ana ta tambayar juna dalilin rashin fitowar Liman masallaci hankalina ya sake tashi ga shi ko yaransa ban gani ba balle na tambayesu. Haka na ja gefe na zauna zuciyata na wani irin bugu na tabbata dai tabbas Baffa ba lafiya yake ba. Sai k’arfe 8:00 na safe rasuwar Baffa Liman da yaransa guda biyu ta kara’de masarautar gabas hankalina ya dugunzuma ya tashi na rasa wanda zan tara da lamarin ba don komai ba sai don bana son na bayyana a matsayin rayayyiya a lokacin. Aka Sallaci gawar Baffa Liman da yaransa guda biyu da aka kashe, d’ayan ne ban san inda yake ba ban kuma ji labarinsa ba. Na dinga kuka kamar raina zai fita kafin na samu na lallashi zuciyata da niyyar ko ba yanzu ba sai na d’au fansar rayu kan bayin Allahn da ba su ji ba ba su gani ba. Da daren ranar na fice daga masarautar don zama a cikinta bai ganni ba, gidan da su Amintacce suke na nufa. Hankalinsu a tashe suke kallona ganin yarda yanayi na ya nuna rashin nutsuwa. Amintacce da matarsa suka saka ni a gaba da tambaya kafin na sanar musu rasuwar Baffa Liman, Mutuwar da na ga ta girgiza su matuk’ar girgizawa har ma fiye da ni. Cikin muryar kuka Amintacce ya fara furta “Shikkenan itama Uwata ba zata sha ba, kasheta za su yi Tauraruwa a duk sanda suka samu cikar burinsu, Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna….” Ha’diye wani irin yawu mai d’aci na yi kafin na furta “Ba zasu kasheta ba Amintacce ni na jefaka a cikin wannan masifar ni kuma zan fitar da kai In sha Allah, yanzu abu guda da nake son sani ka san Likitar da aka saka zata mata aikin….” D’an shiru ya yi da alama nazari yake kafin ya d’ago ya ce “Na santa Dr. Hantsi ce…..” waro ido na yi na ce “Hantsi fa ka ce? Yanzu duk yardar da muka yiwa Hantsi da amince mata da muka yi da ita za’a ha’da baki a cutar da mu?” Tuni idanuna suka jirkita tsananin b’acin rai na mik’e ina kallonsa na ce “Tashi mu je har gidanta yau ba zan runtsa ba har sai na ganta, wallahi idan bata yi wasa ba a yau ba sai gobe ba zan aiakta lahira banda ina tsoron mahallici na.” Hantsi ita ce Likita d’aya da Maimartaba ya aminta da ita, shi yasa da na ji sunanta hankalina ya tashi. Ba nutsuwa a tare da mu har sanda muka tari motar haya zuwa gidan Doctor Hantsi. Shiru unguwar kasancewar nan ne G.R.A don haka ba yawan mutane sai tarin bishiyu da kukan tsintsaye. Kowa yana gidansa da yake juma’a ne bana mantawa an sakko daga masallaci kenan. A bakin gate muka tsaya muka kuma buk’aci Maigadi ya mana iso wajen Doctorn ka gaya mata sak’o ne daga wajen Maimartaba na Gabas ya ce a kawo mata.” Na fa’da ina kallon maigadin da da ya yi niyyar k’in zuwa ya sanar mata, amma jin abinda na ce sai ya juya da sauri har yana yi kamar ya fa’di duk da shigar mu da kamanninmu ba su yi kama da ta masu arziki ba amma kowa ya san k’arfin mulki irin na masarautar Gabas. Ba a d’au lokaci ba sai ga shi ya dawo ya gaya mana ta ce a kai mu b’angaren bak’i. Muka bi bayansa har zuwa parlourn da ya kira na bak’i. Mintuna biyar muka d’auka muna jiranta sai gata ta fito cikin shiga mai bayyana wacece ita don kayan likitoci ne a jikinta da alama aikin yamma zata fita. Kallonmu kawai take da son gane su wanene mu, ganin ta shiga zurfin tunani sai kawai na yaye hiramin kai na, da sauri ta zaro ido duk da babbar rigar da take jikina bai hana kamannina bayyana ba, a ru’de take matuk’a da gaske tana nuna ni tana ja da baya. Murmushi na sakar mata nace “Nutsu Doctor Hantsi ni ce dai Tauraruwa ban mutu ba, ina so kuma ki zauna ki nutsu akwai abinda ya kawo ni wajenki ki ba ni hankalinki nan.” Zama ta yi a d’an d’ofane jikinta na shaking kamar mai jin sanyi ta furta “Ina…..Ina jin Ki….” Murmushi na sakar mata sannan na mik’e na isa inda take. Na dafata dafawar da ta saka ta kusan sumewa. “Nawa suka baki a aikin da zaki musu?” Tsaf ta fahimci abinda nake nufi don haka jikinta na rawa lab’banta suna kakkarwa ta ce “Don Allah ki yi hak’uri Wallahi ban riga da na aikata ba duk da dama tilas suka min da min barazanar mutuwa idan ban aikata ba….” A idanunta na hango gaskiyar zancenta, don haka na daidaita tsayuwata na kuma sassauta fuskata na ce “Ina jin ki, ba ni labari, kada kuma ki min k’Arya a duk abinda zaki fa’da don kin sani ba na yiwa mak’aryaci da sauk’i a duk sanda na gano k’aryar sa.” Ta d’aga kai da sauri tana furta “Ba Zan miki k’arya ba wallahi gaskiya zan gaya miki, k’annen Sarki Da Fulani Raheena ne suka tilasta ni aikata hakan suka kuma tsorata ni da kisa idan ban amince ba kin san su kuma kin san muguntarsu za su iya aikata abinda suka ce shi yasa na yarda… to kuma jiya da aka zo yin dashen sai bai yiwu ba dalili an rasa hanyar da zaa bi a samu Sperm d’in Maimartaba don haka suka ce a gobe suke son na bugar da maimartaba irin buguwar da ba zai san me ya aikata ba, ita kuma yarinyar na mata allurar da zata gusar mata da kwanya na tsahon lokaci.. to a yau Zan musu hakan da daddare………. JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Shiru ya biyo baya a parlourn ba don komai ba sai don mamakin kalamanta, da Suka shiga kunnuwansu a bazata. Umma a fusace ta daka mata Tsawar da ta sata saurin yin shiru daga surutun da take zubawa ba ruwanta iyakar gaskiyarta take fa’da kamar bata son me ke tsakanin jama’ar da ke gabanta da Murad ba, Uwa da ta haifeshi da k’anwar Ubansa da yake matuk’ar so sai marik’iyar da haihuwarsa ne kawai bata yi ba, su ta kalla k’iri da muzu take furta musu ba ta son d’an su, kuma ba abinda ya dameta. Shiru ta yi tana kallon Umman da ta tsatstsareta da ido. Hakan yasa Tauraruwa sakin murmushi ta ce “Kyaleta Umman yara ra’ayinta ta fa’da kuma ko bakomai har yanzu akwai yarinta a kanta, don haka dole a mata uziri amma ina tabbatar miki na lokaci ka’dan ne zata yi rigima daga baya zata so auren nan zata so Murad fiye da k’ima sai dai mu bi su da addu’a kawai dafatan Allah yasa abinda muka k’ulla ya zame musu alheri. Zo nan Daughter.” Sai a sannan kuma sai ta ji kamar bata kyauta ba, kamar bai kamata ta gaya musu hakan ba, kunya ta kamata. Ta kasa k’arasawa wajen Tauraruwa da take ta kiranta har sai da Tauraruwar ta mik’e da nufin kamota sai ta yi saurin shiga ciki da sauri. Tauraruwa tana dariya ta bita har cikin d’akin Umman inda ta tarar da ita ta zauna a gefen gadon ta takure kanta. Tauraruwa ta saki murmushi ta ce “Tashi Najwa magana za mu yi. Bana son kunyar nan ni y’a na d’auke ki ba surika ba. Saddik’a ce surikarki. Ta shi maza mu yi magana.” Idonta a lumshe ta d’an mik’e Tauraruwar ta saka hannu ta d’aga hab’arta ta ce “Bu’de idanunki Najwa Umarni nake baki ba rok’o ba.” Najee ta bu’de idanunta da gashin idon ya musu gazar gazar. Tauraruwa ta saki murmushi a zuciyarta tana yaba kyawun Najeen duk da bata da haske amma fatarta mai kyau ce da gaske irin fatar nan da take da tsada sosai a cikin mutane d’ari da k’yar zaka samu mutum guda mai golden skin d’in nan sai me rabo. “Yauwa gaya min ba kya son Murad ne?” Da sauri ta d’aga kai. Tauraruwa ta saki murmushi tana hango tsagwaron yarinta a idanunta ta ce “Me yasa ba kya son sa?” “Saboda shima baya sona ya tsaneni, duk sanda muka ha’du hararara yake yi da tsaki kuma yana ce min Witch….” Tauraruwa ta waro ido ta ce “Witch kuma? Shi Murad d’in ne yake ce miki witch?” Ta d’aga kanta har tana sakin hawaye tsanar Murad na sake k’arfi a zuciyarta, da gaske bata son sa bata tab’a kuma raya shi a ranta ba kamar yarda take raya Jaheed a matsayin Miji. “Ni Jaheed nake so…” ta fa’da cikin k’arfin gwiwa da karayar harshe duk don Tauraruwa ta tausaya mata. “Duk wanda ya so Jaheed zai so Murad Najee saboda abu guda ya yi su, kuma ko a b’angaren halitta ba su da banbanci, ni kuma da zan baki shawara sai na ce ki aureshi ko don ki rama mayyar da ya kira ki da ita ki cusa masa bak’in ciki….” Ta fa’da tana kallon cikin k’wayar idon Najee da ta fara hango alamun zata yi nasara zata cigaba da d’ora zuciyarta akan cewa zata Auri Murad ne don ta yi ramuwa tana ganin da wannan kawai za su samu lagonta, “Wai ma duk yaushe kuka ha’du har yake kiranki da witch kuma me yasa?” Wata irin dariya Najee ta saki da ta bayyana siraran hak’oranta ta kuma lob’a k’aramin bakinta, kamanninta na wancan lokacin da ta b’atar da kama ta tuna. Da sauri ta mik’e ta janyo wayar Umma da take saman mudubi ta bu’de ma’adanar ajiye hotunanta sai ga kamanninta na waccan Najeen ta gidan sarautar gabas sun bayyana a hoton ta mik’awa Tauraruwa wayar tana furta “Ba ni ya gani ba, wannan Najwar ya gani haka kawai ya kafa min karan tsana ya zata haka nake…” Tauraruwa kanta sai da ta dara ta tabbatar kuma ko Karen hauka ne ya ciji Murad ba zai yarda ya auri me wannan siffar ba yarda yake dan gayu na bugawa a jarida. Dariya ta yi sosai Najwan na sake bata labarin dramar da Suka dinga yi da Murad a gidan Sarkin. Tauraruwa ta jinjina kai tana furta. “Yauwa abinda nake so da ke ki amince ki auresa cikin ruwan sanyi sai ki rama abinda ya miki, kina gama ramuwar sai a raba auren.” Najwa ta d’aga kai “Na yarda amma idan kun amince zan je masa a kamannin waccan Najeen me basaja ba don komai ba sai don na jarrabashi idan ya ci jarrabawar zan amince na zauna da shi idan kuma bai ci ba ya wulak’anta ni zan bayyana masa kai na kuma ko ya dawo yana so na sai ya sake ni.” Tauraruwa ta d’aga kai tana jinjina wautar Najee ita kuma dariya kawai take tana hango ranar da Murad zai shiga gidansa ya ganta a matsayin matarsa, sai ta samu kanta da sakin dariya sosai ta ji tana son auren har ma tana jin kamar ta janyo ranar. Tauraruwa dai da taga ta samu nasara sai ta mik’e ta fita parlourn fuskarta d’auke da murmushi ta kalli Nene ta ce “Wannan y’ar taki sai kin yi da gaske Nene zata yi zaman aure.” Nene dariya ta yi kawai tana jin wani sanyi a ranta da zata ha’da jini d Najee zata haifa mata jikoki, ashe hikimar Ubangiji kenan da ya Kimtsa mata k’aunar Najee a ranta ashe zata zama surikarta. A hankali ta furta “Y’ata gangariya ce Ammin yara sai kun yi da gaske zaku samu soyayyarta.” Tauraruwa ta ce “Ai naga alama Raheena sai ki shirya. Yanzu dai ku tashi mu tafi tunda na samu damar shawo kanta sai dai akan yarjejiniyar ba zai ganta ba sai ranar da aka kaita gidansa sannan zai ga Najee amma bisa b’atacciyar kamar da kuka shiga da ita masarauta.” Nene da Raheena suka waro ido kafin Raheena ta ce “Kina son ya sakar mata y’a a daren kenan? Ta ina Yareema zai amince da auren waccan Najeen?” To ya zan mata tunda yarinya ce ai dole a bi ra’ayinta kafin komai ya daidaita yanzu idan aka ce dole za’a mata wallahi ba za’a ga da kyau ba, a hakan ma a zuwan auren d’aukar fansa za’a yi sannan fa ta amince.” Kowa a wajen dariya yake banda Umma da ranta ya b’aci ta jinjina wautar Najee a ranta da tunanin kalar fa’dan da zata mata idan sun tafi. Yarda take cizon yatsanta ne yasa Tauraruwa kallonta ta ce “A’a fa Hajiya kada ki mata komai don Allah, a hankali za’a bi da ita yarinya ce.” Umma ta saki murmushi kawai suka mik’e suka raka su har mota anan Nene ta ja ta tsaya. Har sai Tauraruwa ta kalleta ta ce “Shigo mana Nene.” Ta girgiza kai ta ce “Ai ni nazo gida..” Da sauri Maimartaba ya d’an juyo ya kalleta. Aka ka’da aka raya ta shiga ta ce “Aa ba inda zata dama shima Jaheed ba komawa zai yi ba sai an kwana biyu zai je da iyalinsa su gaisa da danginsa. Ganin ta turje sai Baffa ya yi murmushi ya ce “Ku k’yale ta idan komai ya daidaita aka samar mata d’akin da zata zauna aka kuma jaddada aurensu da maimartaba da kaina zan kai ta har d’akinta In sha Allah, kafin nan a bamu kwatancen inda iyayenta suke a yola zamu kai musu ziyarar Bazata In sha Allah.” Tauraruwa ta jinjina kai duk da bata so haka ba amma hakan shi ya kamata don haka ta ce zata aiko da wanda zai musu jagora har Yola inda Babi su ke da Inno cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali.” Suka sake jaddada godiyarsu ga Baffa da Umma sannan suka ja Mota suka tafi Murad yana jin kamar ya musu tawa ye ya k’i bin su sai dai kaifin idanun Fulani Saddika ya hana shi tasiri ba zai iya bujire mata a gab’ar da take neman mai rarrashinta don haka sai kawai ya d’agawa Nene da su Jaheed hannu suka fita daga harabar gidan. Nene ta saki ajiyar zuciya tana jin k’irjinta wasai ba wannan tarin cunkoson b’acin ran sai farin ciki da annashuwa kamar an mata albishira da aljanna. Tun kafin su shiga gida ta lura da yarda Umma take sake hawa ta san idan ta barta zuwa zata yi ta daki Najee don haka suna shiga ta yi wuf ta fa’da d’akin ta ja hannun Najee tana furta “Fito maza Uwarki ta dawo ba mai dukar min ke alhali ke aka yi wa lefi da aka ha’da aurenki da mur’dadden mutum da ya ninka shekarunki, sannan kice zaki zo ki sauke mata wani fa’dan da ne zata ji? Daga yau ma ta yiwa d’akin naki k’aura wajena zata koma har zuwa sanda zata tare a d’akin Mijin nata. Ina goyon bayanki Najwa ki rama abinda ya miki ba sassauci ko ka’dan kin ji tunda a gaba na aka yi komai ni shaida ce.” Umma turus ta yi da wayar chargerr da zata yi dukan da ita tana kallon Nenen da take ta fa’da ba ji ba gani. “Amma hakan da kika yi da ba daidai ba ne da kan ki kike cewa ta yiwa Mijinta rashin kunya?” “Ni bance ta masa rashin kunya ba, na dai ce ta rama abinda ya mata ko ta ji sanyi a zuciyarta” Umma ta tab’e baki tana furta “Ku kuka sani idan ta yi ba daidai ba Allah yana gani ba da yawuna ba wallahi.” Ta zagayesu ta wuce kitchen bayan ta wurgawa Najee harara. Sake lafewa Najeen ta yi a bayan Nene tana furta kuma idan ya sani abu kamar dafa abinci na lafta gishiri ko?” Nene tace har da yaji ma duka ki lafta Ai shi ya janyo. Najee ta daka tsalle tana jin zuciyarta wasai ta bi Nene d’akinta suka cigaba da hira duka dai zancen Najeen ta inda zata gallazawa Murad idan an yi auren… Nene kuwa biye mata take tana dariya a zuciyarta sanin cewa har yanzu Najee bata san meye aure ba jin sa kawai take a baki don Umma jajirtacciyar mace ce mai yin iya iyawarta wajen takatsantsan da tarbiyyar yaranta, a kullum tana gode wa Allah da Jaheed ya tashi a hannun Umman ta kuma ba shi tarbiyya irin tarbiyyar da yake bawa yaranta. Shi yasa ta so auren Jaheed da Najee ba don komai ba sai don ta san zata samu nutsuwa Murad kuwa ta lura duk da yana da tarbiyya sangartacce ne da ya tashi cikin rayuwar gata yake ganin kuma duk abinda ya aikata daidai ne, shi yasa take tunanin wace irin kwamacalar zaman aure za’a yi a gidan Murad da Najee? Ni ma dai tambayar da nake wa kaina kenan.. mu ha’du gobe. Kun san bana typing Week end ku yi hak’uri da abinda ya samu. JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Gaba d’aya jama’ar parlourn suka d’ago suna mata kallon mamaki ganin yarda ta yi furucin da alamar kamar akwai sanayya a tsakaninsu. Baffa ma kallonta yake yana sakin murmushi ya ce “Lokacin amsar ajiyar taki ya yi kenan?” Ta d’aga kai tana sakin dariya sosai. “Na gode sosai da amanar da ka rik’e min har zuwa yanzu, ajiyata kuma tabbas lokacin amsarta ya yi kamar yarda muka k’ulla al’kawari da kai, na gani na yaba kuma tabbas za’a dace anan gaba.” Baffa ya d’aga kai yana sakin murmushi a hankali. Wayar Murad da ta yi k’ara ita tasa ya mik’e ya fice daga parlourn don amsa wayar. Hakan yasa Tauraruwa gyara zamanta don ta ji da’din barin Murad wajen dama sam bata son ya ji zancen. Maimartaba kuwa kasa barin maganar ya yi a cikinsa yana duban Tauraruwa ya ce “To dama kun san juna kenan?” Tauraruwa ta d’aga kai cike da tabbatarwa ta furta “Shekaru biyar baya na bayyana kaina gareshi, na kuma sanar da shi dukkan abinda na sanar da ku, ya so tun a lokacin ya turje da son lallai sai an bayyana hakan ga Jaheed saboda halin da yake ciki na damuwa da rashin iyayensa, ni na togace shi na kuma nemi alfarma a gareshi akan ya bari har zuwa sanda zan bayyana hakan ga al’ummar gabas a yanzu kuma lokaci ya yi. Sanda na ji labarin za’a yi wa Murad aure na tashi hankalina hakan yasa na zo wajensa da niyyar in dai yana da y’a ya taimaka ya aurawa Murad kamar yarda ya aurawa Jaheed d’aya daga cikin y’ay’ansa. Shiru ya yi a lokacin ya nuna min yarinyar da zai iya cewa kai tsaye ya amince Murad ya aureta ba kowa ba ce sai y’ar marik’iyar Jaheed sai dai kuma bayan rabuwar auren Jaheed da Najma sai yayi nufin yi masa musaya da Najwa to sab’anin da aka samu sai ya zama matar Jaheed d’in tana da ciki. Hakan yasa tun a lokacin nace masa ina nemawa Murad auren y’arsa. Bai so ba naga Kuma hakan a idanunsa na tambayeshi dalili ya nuna min yana tsoron ya ha’da Najee da yaron da ba shi ya furta yana son ta ba ba don komai sai dan yarinya ce k’arama ya buk’aci ya ba shi Nasma ni na k’i yarda na ce Najee ita ta dace da Murad duk k’ank’antar ta shekaru sha biyar tsaf zata iya aure ba miskila. Amma don Allah ina son wannan ya zama sirri tsakanina da ku bana son Murad ya san zancen nan har zuwa ranar da za’a d’aura auren ta tare a gidansa ba don komai ba sai don ina tsoron ya ce ta masa k’ank’anta ni kuwa a d’abiu irin na Umma tabbas zan so mu ha’da zuri’a da ita ba don komai ba sai don mu sakanta mata da d’inbin alherinta garemu, bana son kowa ya ji koda a cikin gidan nan kuwa ina nufin y’ay’an waccan shiyyar.” Shiru kowa ya yi kuma duka zuk’atansu sun amince da maganar musamman Nene da take ganin hakan shine mafi dacewa Murad da Najee su yi aure ranar zata fi kowa farin ciki. Umma kuwa ita kadaran kadahan ne farin cikin nata, a wani gefe can na zuciyarta kuma tana jin taraddadi da tsoron auren Najee da Murad Najee a gidan sarauta bata san tab’argazar da zata shuka ba ba don komai ba sai don ta san Najee da tab’ara irin ta y’an auta ba zata ragawa duk wanda ya shiga shirginta ba, banda haka bata da wani aibu ta iya girki ta iya komai kwalliyace ma bata fiye damunta ba sau tari ta fi son zamanta da fuskarta a haka ba tare da ta goga ko kwalli ba sai kuma hakan ya zame mata jiki ko kwalliyar ta yi bata fiye kyau ba, jambaki ne kawai yake mata kyau a d’an cute lips d’inta masu lob’awa idan tana magana, abu mafi kyau a fuskar Najee kenan tattausun lab’b’a da dara daran ido masu yalwar haske bak’in kuma si’dik. Gazar gazar gashin gira da na ido da gargasa a gefen fusktara shi ya k’arawa kyawunta kyau. Ta dai saki ajiyar zuciya kawai tana fatan hakan ya zama alheri ga Najee ga ma duka ahalin b’angare biyun. Haka aka cigaba da tattaunawa su ka ce dukkan abinda aka ajiye musu sannan aka tsayar da ranar bikin kwanaki biyar kacal, inda komai za’a sha shagalin bikin da baa tab’a kwatankwacinsa a masarautar gabas ba. Kwana biyar za’a yi ana bikin da zai zagaye duka fa’din k’asar Nigeria. A take a wajen kuma Maimartaba ya bada Sadaki ba tare da Murad ya san sadakin menene ba. Matan cikin gida suka shiga, don su yi Sallah su kuma sake gaisawa da Umma. Najma na zaune da cikinta a gaba ta hangosu tana ganin Tauraruwa gabanta ya fa’di ganin yarda kamanceceniyarsu da Jaheed ta bayyana matuk’a da gaske. Ko baa fa’da mata ta san tabbas sun ha’da jini da Jaheed don haka da sauri ta durk’usa tana gaishesu. Tauraruwa ta juyo tana kallonta suna amsawa tana fa’din “Wannan dai Umma daga gani itace surikar tamu da ta k’i mu ko?” Najma ta sunkuyar da kanta kunyar duniya na lullub’eta ta dinga ji kamar k’asa ta tsage ta shiga saboda kwarjini da k’imarsu. Umma ta d’an saki murmushi ta ce “Bata guje shi ba Yarinta ce. Tun ba yau ba kuma ta yi nadamar abinda ta aikata.” Tauraruwa ta d’an tab’e baki ta ce “Allah ya kyauta, zan so mu gaida Uwarta Ai ta gan mu taga dangin Jaheed ba shegen da take tunani ba ne.” Umma dai hak’uri take bata tana furta “Duk dai abin bai kai haka ba, a yi hak’uri a rashin sani ne..” “Ai dama a rashin sanin zata aikata haka, idan banda haka son duniya ka’dai ba zai barta ta wulak’anta Jaheed ba da ta san asalinsa da toshensa to irinsu ne masu wulak’anta d’an adam ba tare da sun san kima da darajar da Allah ya ba shi ba, duk kasawar d’an adam wala ta tawayar halitta ko talauci yana da nasa girman a wajen Ubangiji ba mamaki ma ranar lahira ko kwatankwacinsa ba zaka kai ba, amma a duniya ka dinga d’aga masa kai saboda wata baiwa da Allah ya maka wacce ta kere ta sa. Allah dai ya kyauta ya shirya duk masu hali irin na Uwarta, ga shi nan Allah ya nuna musu ishara ta hanyar sanya jinin Jaheed a cikinsu, Jikan mahaukaciya yanzu kuma ko da wani suna za’a kira shi. Jikan Sarkin Gabas ko? Sai kuma a fara dana sani ko?” Ta fa’da tana sakin murmushi wanda da alama na takaicin abin ne da yake huda zuciya da ruhinta. Su Fulani Saddik’a dai sai hak’uri suke bata ganin yarda Tauraruwar take ta kumfar baki. Da alama duk wani abu da Mahmeey ta yi shi Tauraruwa ta ji labarinsa. Najma dai durk’ushe take tana zubar da hawaye kawai ita kanta a yau ta na jin Mahmeeyn bata kyauta mata ba, don tun suna yara ita ta cusa musu tsanar Jaheed a zuciyarsu ta hanyar nuna musu Ubansu ya fi son Jaheed d’in da yake tsintattan d’a shikkenan Suka samu kafar tsanar Jaheed d’in ta wanzu a zuciyarsuqba tare da sun san dalili ba. Da sun samu Uwa ta gari kamar Umma da suma sun zama y’ay’a na gari da kowa zai yi alfahari da su. Suka wuce suka barta tana sake zubar da hawayen. Mahmeey da take tsaye a window ta ji kaf abinda ya faru hankalinta ya tashi matuk’a ainun da jin Jaheed d’in Jinin sarauta ne ta yi saurin gyara fuskarta da ta bayyana rashin nutsuwa jin sallamar su Umman a k’ofar sashenta. Cikin natsuwar fuska da fara’ar dole da ta k’ak’alo ta amsa musu sallamar tana murza key d’in parlourn ta bu’de musu k’ofar suka shigo. Tun daga ganin farko da ta yiwa Tauraruwa hankalinta ya yi bala’in tashi don bata hango sassauci a fuskar Tauraruwar ba gwara ma Nene ta saki tata fuskar ta kuma gaisheta a mutunce kamar yarda ta saba a lokutan baya. Murya na rawa ta amsa tana furta “Barka da sauka Nene ashe yau za ki dawo?” Mamaki ya kama Nene ta dai daure ta amsa mata suka samu waje suka zauna. Tauraruwa ta dinga kallon Mahmeeyn shek’ek’e kafin ta furta “Masu gida ran gida, Iyayen Jaheed ne suka zo gaida ku, d’an mahaukaciya da ya riki’de ya koma d’an Sarkin gabas!” Sunkuyar da kanta ta yi da sauri don ta san bata da cewa bata isa da Tauraruwa ba da sunansu ya gama karad’e yankin arewa. Arzikin su ya shahara irin shaharar da kowa ya san su ko a radio zaka yawaita jin sunan Sarkin gabas akan gaba wajen taimako da bada tallafi ga al’umma musamman marayu da yake jin kamar duk wata dawainiyarsu ta rayata a wuyansa ne. Jin shiru bata amsa ba suka mik’e Tauraruwa ta gama yar mata da maganganu sannan suka fice daga sashen suka barta da tarin dana sani da takaici a zuciya wannan fa shine asalin YIWA KAI (Littafin Zee kumurya na Bright pens Mikiya). Najma kuwa kuka ta saka a tsakar parlourn kukan da ya sake dugunzuma zuciyar Mahmeey ta rasa ma me zata ce mata da ya wuce zuba mata ido tana tsaki. Isarsu sashen Umman suka zube a parlour Umma ta k’walawa Najee kira akan ta zo ta kawo musu dadduma su yi Sallah. Ta fito da d’an tsallenta tunaninta Umman ita ka’dai ce turus ta yi ganin su Nene har da Fulani Saddik’a da take ta jifanta da murmushi ta juya ta kallin Tauraruwa da itama take kallonta tana murmushin ta furta “Matso nan My Inlaw matso mu gaisa mana kika ja kika tsaya haba amaryar Murad…” wani irin waro ido Najee ta yi sai kuma ta k’ifta idon tana kallon Nene ta ce Murad kuma ko dai Ya Jaheed ina ni ina wannan masifaffen mutumin Allah ya kiyaye wallahi…. JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: “Matsayin matarka uwar yaranka.” Tauraruwa ta furta kanta tsaye tana sakarwa Maimartaba murmushi. Da sauri su Murad suka k’araso wajen Sarkin da su Nene da suke tsaye. Maimartaba ya saka hannu ya janyo Jaheed ya sanya shi a jikinsa yana jin soyayyar yaron tana fusga a zuciyarsa tausayin rashin taso wa da shi a rayuwarsa yana sake mamaye zuciyarsa. Tabbas zai gode wa mutanen da suka kula masa da Jaheed har zuwa yau da yake tsaye sun cancanci a sakanta musu da mafi darajar Sakantawa. Ba shi da muryar da zai bu’de ya yi godiya a garesu sai yaga kamar matsayin su ya zarce hakan. Ina da burin ganinsu yana da burin ganin Uban da ya zamewa Jaheed Uba a lokacin da ya rasa nasa Uban. Baya jin wajen nan da dandazon mutanen da suke wajen zai bari ya nuna tarin farin cikinsa yarda ya kamata don haka kawai sai ya ja hannun Jaheed d’in da na Murad suka wuce da don isa b’angarensa. Baya buk’atar sanin komai a yanzu duk da hakan mutane zasu so ya faru lokaci zai ba su lokacin da za su zo su amsa laifukan su da kan su shi kuma ya yi musu hukunci irin wanda ya dace da su. Tauraruwa ta bi shi bayan ta kalli Fulani Saddik’a tana sakar mata murmushi ta ce “Ki biyo ni da k’awarki” ba sai ta mata fashin bak’i ba kai tsaye ta san wacce take nufi, don haka ta damk’i hannun Nene da take tsaye dukkan jikinta a sanyaye gani take abin kamar almara ko irin mafarkin da ta saba yin sa kullum. Fulani Raheena kuwa wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske, zuciyarta ta mata nauyi kamar yarda dukka gabban jikinta suka mata nauyin, jikinta yana bata matsayin ta a zama matar Sarki yana neman ya zama tarihi. A sanyaye ta mik’e jikinta sanyi k’alau ta d’an bi mutanen da suke bin ta da kallon Allah wa dai da ido kafin ta zare jikinta zuwa b’angarenta, hatta da barorinta haushinta suke ji a idanunsu ta gano yarda suke Allah wadarai da bak’in halinta. Ta ha’diye yawu mai d’acin gaske sanda ta yi arba da kallon da su Abdul y’ay’anta na cikinta suke mata kallo ne da kai tsaye ta kasa fassara shi duk da zuciyarta na nuna mata su ma Allah wadaran suke da zamanta mahaifiyarsu. Dad’i d’aya da take ji a ranta da su suka zama halastattun y’ay’an Sarki, ashe gaggawa ta yi ta aikata waccan katab’orar nata rabon yana tafe, me yasa ta yiwa Allah katsalandan a cikin aikinsa? Hawaye ne suke don zubo mata don haka kamar wulgawar iska ta yi saurin b’acewa daga wajen, tana jin muddin bata tafi ba gaf mutanen wajen suke da fara jifanta don zuciyar wasu a dama a fusace suke musamman jin sarki bai ce komai ba game da hukuncin da zai zartar musu. A d’akinta ta zube jikinta na zuba wata irin kakkarwa kamar mai Jin sanyi ita da kanta ta hango kalmar nan da hausawa suke cewa ta faru ta k’are! Duk k’ok’arin ta na son rufawa kanta asiri ashe Rabbi ya shirya ranar da zai banka’dashi a bainar jama’a. Hoton hannunta yake kallo hoton da ya bayyana Nene da Sarki a wani yanayi, ta da’de da tanadin hoton don tun sanda aka d’auke shi ta zare do don hoton d’aya ta masa kyakykyawan b’oye don zuwan wannan ranar, ba tare da sanin cewa Tauraruwa ta b’oye duk wasu copies na hotunan ba. Niyyar ta ta sanar da duniya fywad’e Sarki ya yiwa Nenne har ta samar da cikin yaran, ashe da aurensu komai ya wakana ba tare da sanin ta ba. Tsanar Tauraruwa ta sake bunk’asa a zuciyarta fiye da wacce take mata a baya. Ta yaga hoton bayan ta masa wani irin kallo ta zuba a cikin toilet. Fitowar ta kenan daga toilet d’in Amra ta shigo cikin d’akin fuskarta na bayyana tashin hankalin da take ciki. Wani irin kallo ta zubawa Amrahn tana jin wani haushinta. “Yaya kin cuceni kin dasa min son mutumin da kika san baki da hope akan zan same shi Wallahi Allah ya isa ban yafe miki ba.” Wani irin kallo ta yi wa Amran tana furta “Allah ya isa? Ni kikewa Allah ya isa Amra?” Ko kafin ta yi wani yunk’uri Amran ta murgu’da mata baki tana furta “Eeh d’in, ai bani ka’dai ba ma yau mutane da dama zaki karb’i Allah ya isarsu macuciya kawai.” Daga haka ya fice da sauri dama jakarta tana kafa’darta. Saroro Raheenan ta yi tana sakin ajiyar zuciya bayan fitar Amran mamaki take sosai to Amra ma kenan ta mata haka da ba abinda za’a danganta su da ita da ya wuce a ce k’anwarta ce ina ga Y’ay’an cikinta da ta janyo musu abin gori har muddin rayuwarsu. Ta runtse idonta kawai tana jin yarda zuciyarta take wani irin turiri da tarnak’in b’acin rai. Bata da abinda zata kare kanta tunda Tauraruwa ta san komai. Ba Kuma ta da bakin da zata yiwa kowa bayani a gamsu laifinta dumu dumu ya fito bata da abinda zata togace kanta daga tarin laifukanta. ____ D’aya bayan d’aya yake kallonsu yana jinjina girma da izzar mulki na sarki Allah, tabbas wannan shine abinda ake kira KUDIRAR ALLAH bai san mafari ba balle ya san ranar da ya kusanci uwarsu har cikin su ya shiga, amma da yake Allah yaso zuwansu duniya sai ya kintsawa mak’iyansa su aikata hakan, da kuma ya so su zama halastattun y’ay’a sai ya kintsawa tauraruwa zuwa wajen Baffa Liman don an d’aura aurensu. Tabbas ba abinda zai cewa Jalla da ya wuce godiya da kuma jinjina k’arfin mulki da mai yiwa Bawa a sanda ya d’ebe haso daga dukkan buk’atarsa, sai ya ba shi a lokacin da bai zata ba bai kuma tsammani ba. Shirun da ya yi yana kallonsu, ba tare da ya furta komai ba shi yasa su a damuwa da mayar da nasu hankalin kansa, musamman Nene da bata san a wani matsayi take ba matarsa ko kuma kuyangarsa ko kuma sa’daka, duk da ta san a doka irin ta sarautar gabas babu wa’dannan abubuwan. Lumshe idanunsa ya yi hawayen da ya da’de yana b’oyo suka samu damar ziraro wa ta kwarmin idanunsa, ba hawayen komai ba sai na jin da’di dana farin ciki mara misaltuwa. Ji yake duk abinda ya mallaka zai iya mallaka wa Tauraruwa shi wacce ta zama itace tsanin cikar burinsa. Ya dubi Jaheed yana sakin ajiyar zuciya kafin Ya ce “Mujaheedu ina son ganin Uban goyonka a gobe In sha Allah Zan tafi takanas har gida don jaddada godiyata gare shi.” Jaheed ya d’aga kai yana furta “Allah ya nuna mana In sha Allah.” Ya fa’da yana kallon Faruk da shima yake musu kallon farin ciki da samun cikar burinsa. A lokutan baya ba k’aramin tausayi Jaheed yake ba shi ba musamman idan aka je neman aure aka hana shi, sai ya ji duk duniya ya rasa sukuni ya kuma shiga damuwar da tafi Jaheed sai ga shi rana guda Allah ya ware ya sakantawa Mujaheed da nagartaccen Uba mai nasaba ta gaske alfaharin dukka y’ay’aye. “Faruk ka kira Baffa ka gaya masa gobe yana da bak’i, ko kuma mu bari kawai mu masa surprise.” Faruk ya d’aga kansa yana furta “Hakan ma zai fi mu basu mamaki ta hanyar ganin mu kwatsam.” Tauraruwa ce ta hararesu tana furta saboda haka ake yi, sai kawai su ganmu sama taka gwara dai a gaya musu.” Girgiza kai Jaheed ya yi yana furta “Aa Ammeey gwara dai ki bari mu musu surprise d’in.” Shiru ta yi tana jin da’din sunanta da ya kira. Maimartaba ya yarda da abinda suka ce don haka ya ce Tauraruwa ta shirya da mutanen da za’a yi tafiyar, ciki kuma ta ha’da har da yaranta Khaleefa da macen Haneefa.” Tauraruwa ta jinjina kai tana d’an jin shakkar kiran yaran nata don tun bayan bayyanarta a matsayin rayayyiya suke fushi da ita ba don komai ba sai don mayar da su marayun k’arfi da yaji da ta yi. Maimartaba ya san abinda ya tsaya mata a rai don haka ya saki murmushi yana dafata ka’dan ya ce “Dole za su yi fushi da ke Tauraruwa amma na lokaci ka’dan ne da zarar sun ga y’an uwansu sun kuma ji silar faruwar abin za su miki uziri don ina tabbatar miki a yanzu ba wanda ya fi su farin ciki da bayyanuwarki.” Nutsuwa ta samu sosai a ranta har hakan yasa ta samu k’arfin gwiwar kiransu. Haleefa ya amsa don yana zaune ne cikin iyalinsa ya ce mata Allah ya kai mu” da wata irin murya da ta bayyana tarin fushinsa. Haneefa kuwa bata amsa ba tana kallon wayar tana ruri har Tauraruwa ta gaji ta tura mata text. Ganin text d’in sai kawai ta tura mata amsa da Ok. Ta kashe wayar hawaye suna suntirin zubo mata. Haka kawai tana raye ta barsu Suna maraici duk da Maimartaba ya zame musu bango abin jingina fulani Saddik’a ma ta taka rawar gani a wajen inganta rayuwarsu don idan ta Fulani Raheena ce sai dai su dawwama cikin bak’in cikin rayuwa. A daren ranar dai barci bai samu ga ahalin Sarkin gabas ba. Hira ce sosai ake yin ta a sashen Fulani Saddik’a, cikin nisha’di da walwala duka yaran har da Tauraruwa da take ta sake basu labarin wasu abubuwan da ta manta. Jaheed ne ya kalli Murad cikin tsokana ya ce “Wai tsaya Ammeey kada dai yaron nan gauro ne?” Tauraruwa ta saki murmushi ta ce “Gwauro mana, amma ya kusa angoncewa da amaryarsa y’ar mutanen Yola da na masa kamu tuntuni, a kwanaki bai fi kwana biyar bikin ba.” Murad ya zaro ido waje yana furta “wai wace wannan matar ne?” Tauraruwa ta girgiza kai “Idan mun dawo daga kano zan wuce da kai har Yola don ku fara zantawa da matar taka na san dai ta ko ina bata da makusa za kuma ka sota zaka yi alfahari da ita In sha Allah.” Bai sake magana ba ya dai sake k’udirce wa a ransa matuk’ar matar bata masa ba, a take wajen zai saketa ba abinda ya masa zafi. Kashegari Kuwa Kano ta yi manyan bak’i. K’arar Parking d’in motocin yasa Baffa ya kalli matansa ya ce “Kamar fa motoci nake ji a harabar gidan nan.” Umma ta zaro ido tana mik’ewa ta ce “Bari na lek’a na gani.” Ta juyo tana fa’din “Ai kuwa bak’i ne Baffa daga gani kuma manya ne.” Da murmushi fal kan fuskarsa ya mik’e a hankali ya furta “Allah ya kawo mu ranar kenan.” Umma ta kalleshi saroro don son k’arin bayani sai dai bata samu amsa daga bakinsa ba ya yi saurin saka hular sa yana ficewa waje. Tarba mai kyau ya musu duk da matan gidan basu san da zuwansu ba, amma Umma ta yi k’ok’ari sosai wajen ganin bata ba shi kunya ba. Ruwa da lemo kawai suka sha sannan Sarki ya dinga jaddada kalmar godiya garesu. Amsawa kawai Baffa yake yana fa’din “Yi wa kai ne.” Tauraruwa ce ta yi gyaran murya tana furta “Baffan yara ina ajiyata?” JIKAR NASHE✍🏽🥳 A yi hak’uri jiya network ne ya hana ni posting. 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: . Sun isa Masarautar Gabas hankali kwance cikin tafiyar da ba su gaji sosai ba. Musamman kasancewar tafiyar an yi tane cikin kwanciyar hankali da tarin nutsuwa zuk’ata kuma suna cikin annashuwa. Suna parking dandazon jama’ar suka zo musu barka da sauka. Wannan karan ga duk wanda ya kalli fuskar mai martaba ya san yana cikin tarin farin ciki da nutsuwar zuciya. Dole ya kasance mai godiya ga Allah ba don komai ba sai don samun abubuwan da ya fi so a rayuwarsa Tauraruwa da kuma yaransa biyu da yake jin kamar ba shi da wasu y’ay’an da suka wuce su. Gefe guda kuma soyayyar magaifiyarsu ta yi wa zuciyarsa mugun kamun da bai tab’a ha’duwa da shi ba ko a zamanin samartakar. Komai na matar ya yi masa siffa da kamannin fuskarta da kuma rantsatstsiyar kunyar da ba kowace mace ba ce take samu sai wacce Allah yaso da rahma. Kunya wani yankice daga Imani haka Manzon Allah s.a.w ya ce. Don haka kunya take zama adon da yake k’arawa mata kyau da nagarta ana son mace mai kunya tana da kwarjini a idanun maza da wuya wani namijin banzan kuma ya kawo mata maganar banza matuk’ar ya sameta da kunya. Don haka ya dinga jin soyayyar Nene tana sake fusgarsa ba don komai ba sai don kunyar da ta wa fuskarta ado da ita. Ta kasa ha’da ido da shi duk da k’ok’arin sa na son ganin hakan ta faru. Shi ka’dai ya saki ajiyar zuciya kafin ya lumshe ido yana ayyana ya zama dole ya yi wani abu a satin nan a kawo masa matarsa, idan ba haka ba tunaninta da kewarta ba zasu tab’a barinsa ba. Tauraruwa da take ankare da shi da duk yanayinsa ta saki murmushi kawai ba tare da ta furta komai ba don ba a mahallin cewar take ba. Sai sun k’arasa sashensa za su yi magana ta fahimtar juna da shi. Sanda Fulani Raheena ta samu labarin dawowarsu gabanta ne ya tsananta bugu, hankalinta ya fi na baya tashi zufa ta ko ina zubo mata take, har dare zuciyarta bata natsu ba musamman da ta ji muryar Jakadiya tana rangwa’da sallama. Wata irin hautsinawa cikinta ya yi ta tabbata abinda take gudu ne ya zo. Jakadiya ta shiga fuskarta a ha’de don ba d’an ka’dan ba take jin haushin matar nan bama ita ka’dai duk wanda ya kwana ya tashi a masarautar gabas ya san kuma abinda ya faru zuciyarsa cike take taf da tsanar Fulani Raheena. Dukkan mutuncinta ta zube k’asa wanwar haushinta da tsanarta sun samu mahalli a zuciyar ahalin masarautar. Ta d’ago idanunta da k’yar tana kallon Jakadiyar da take tsaye ba wani alamun russunawa a tattare da ita ta ce “Sak’on kira ne daga Maimartaba, ya kuma ce k’afata k’afarki.” Hantar cikinta ta kad’a kamar yarda zuciyarta ta bada sautin bugu mai k’arfin gaske. Jikinta ba k’wari sam ta mik’e very slow tana jan alkyabba ta suturce jikinta. Layar da yake hannunta ta sake rik’ewa k’am da niyyar idan aka je fada ta matseta kamar yarda Malaminta ya umarceta ya kuma d’orata a turbar cewa matuk’ar ta aikata hakan Maimartaba ba zai iya aikata komai ba sai abinda ta ce. Zuciyarta bata amince ba don tana ganin kamar girman lefinta ya shige yafiya amma sanda Malamin ya mata rantsuwa sai ta samu nutsuwar zuciya ka’dan tana fatan Layar ta yi mata aikin rufe bakin Maimartaba ya kasa furta mata kalmar saki. Ta saka takalma a sawunta kafin ta fita Jakadiya kuma ta sakata a gaba suka bi ta ainihin k’ofar da zata sadata da sashen Maimartaba daga b’angaren nata. Shiru parlourn baka jin komai sai sanyin a.c da wani sassanyan k’amshi da ya gama mamaye parlourn. Sai sautin karatun Alkur’ani da yake tashi ka’dan ka’dan a cikin parlourn cikin suraturrahman. Tauraruwa ce a hakimce a parlourn hannunta d’auke da fruits tana sha cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Ta sauke idanunta a cikin na Raheena da ta yi saurin d’auke nata idon tana hangar inda zata ga Maimartaba don ta matsa layar da ke hannunta. Tauraruwa ta yi murmushin da kai tsaye za’a kira na isa kafin ta mik’e cikin takun isa ta isa gaban Jakadiya. Murya a murd’e cikin dakiya ta ce “Mai martaba baya buk’atar ganinta ya bada sak’o a bata da fa’din ba zai iya ganin mahainciya ba, wacce ta dinga gararanba da igiyar aurensa a duniya, Ya saketa saki uku sannan yana buk’atar d’akinta zai sanya Uwar su Jaheed a ciki, ga mukullin gida nan ya ce ki bata ta ci albarkacin yara biyu na halak da ta haifa masa wanda likita ya tabbar da zamowarsu zuri’arsa, bayan haka baya buk’atar sake ganin Raheena a idanunsa, kwana biyu ya bata ta tattara komatsanta mai guri tana zuwa.” Daga haka ta shige sashenta ba tare da ta sake yiwa Raheenan kallo na biyu, saboda tsanarta mai girma da ta mamaye duka sassan zuciyarta, take Jin kamar at fisgita ta matseta ta kasheta. Jakadiya ma kallonta ta yi tana furta “Raheena kin ga illar son zuciya ko? Yanzu wa gari ya waya? Bayan tsinuwar Allah da malaikunsa sai kuma ki sabbabawa kanki tsinuwar mutane da Allah wadarai, ba kowa kika yiwa ba wallahi sai yaranki. Ga takardar sakinki nan Allah ya kiyaye na gaba ya yafe miki kurakuranki, ita da kuka so sakawa a wahala ga shi nan itace ta haifo Masu mulkin gabas magadan gabas ko ba komai ta tsinci dami akala Allah ya kiyashemu aikata aikin DA NA SANI….. “ daga haka ta fice ta bar Raheenan a durk’ushe tana sakin wani irin kuka mai bayyana b’acin ran da zuciya take ciki, irin kukan da kana ganin mai yinsa ka san yana cikin tafasa da k’unar zuciya. Ba wanda ya fito daga Sarki har Tauraruwa duk da suna jin saurin kukan nata da yake da k’arfin gaske take yin sa. Har ta gaji don kanta ta mik’e zuwa b’angarenta don ta fara tattara kayanta kamar yarda Maimartaba ya bada sak’o a gaya mata. Tana ha’da kayan tana jin b’acin ranta na sake ninkuwa ita ce yau zata bar sashennan sashen da duk k’uriuciyarta a ciki ta yi shi ta hayayyafa kuma. Me yasa ta bi son rai ne ta bi zugar she’dan ga shi nan ya kai ta ya baro ya wurgata a motar Dana sani…. Y’ay’anta ma sun gujeta ba sa zuwa ko inda suke. Ta dinga jin zuciyarta na turiri. …………. Kwana uku tsakani Su Baffa suka shirya tafiya Yola saboda yarda Nene ta kasa Alkunya ta nuna musu iyayenta take son gani da y’an uwanta gaba d’aya. Hakan yasa kan dole aka shirya tafiyar. Sai dai kafin su tarin sai ga wayar Tauraruwa tana sanar musu su yi zamansu ba sai sun je ba, su Inno d’in za su je Kanon kashegari Idan Allah ya kai mu. Nene bata so ba amma don dole haka ta hak’ura kada a ga ta fiya rashin hak’uri ta jure hak’urin shekaru ma don haka na rana guda d’aya ba zai gagara ba In sha Allah. Suka mayar da kayan aka kuma shiga shirin tarar su dama gidan a hargitse yake dalilin gyaran biki da aka fara. Umma duk ta kwashe kayan furnitures d’inta Jaheed da Faruk za su saka mata y’an waje masu tsadar gaske. Kamar yarda suka ha’da ku’di suka Yi wa Najee kayan d’akin suka bawa Baffan da cewa sai ya k’ara da nasa. Tuni Mahmeey ta samu labarin Auren da za’a yiwa Najeen da Y’ay’an Jaheed hankalinta ya tashi zuciyarta ta afka kogin nadama da dana sani ta tabbata ita ta cuci y’arta da yanzu take cikin tsananin damuwa na rashin aurenta ga Jaheed d’in ko kallo bata ishe shi ba. Ita kuwa Khaireey tun bayan da ta ji wanda Najee zata aura sai ta yar da makaman yak’in ta kuma bawa Umma hak’uri bayan Jaheed ya tursasata bisa dole don Najee ta gaya masa duk abinda ya faru. Umma tana murmushi ta dafata ta ce “Bakomai Khaireey sai dai ina son ki cire wannan zafin kishin a ranki, Namiji Mijin mace hu’du ne don haka baki da hurumin da zaki hana Mijinki aure saboda son zuciya ki tsarkake zuciyarki dafatan samun abokiyar zama ta gari ya kuma kareki daga dukkan sharrinta ke da ahalinki ya kuma kintsawa Mijinki soyayyarki fiye da kima. Idan kika rik’e wannan tabbas kin rik’e babban makami.” Ta d’aga kai tana fa’din “Shikkenan In sha Allah Umma nagode.” Jaheed kuma murmushi ya saki yana furta “Madallah da Uwa ta gari. Sanyin idaniyar y’ay’a a duniya.” Tun daga lokacin Khaireey da Najee suka d’inke take kuma bata shawarwari da wayar mata da kai a b’angaren aure. Wani abin idan ta gayawa Najee zunb’ura baki take ta ce “Mhmn sai kace wata y’ar iska? Allah ya kiyaye.” Khaireey murmushi take ta ce “Allah ya kaimu lokacin da zaki amsa sunan y’ar iskar da kan ki, na ganki kina tan’dar lab’ban Murad ko kina shigewa jikinsa…” wani yawu ya tofar tana yamutsa baki tace “Bakinsa kuma mhmhn? Allah ya min tsari, yawun zan sha sai kace wata k’azama.” Khaireey ganin sam Najee ba zata fahimceta sai ta ja baki ta tsuke a ranta tana dariya dafatan Allah ya kai mu lokacin zata bata amsa daidai da kalamanta. Kashegari tun wuri aka kammala komai a gidan Baffa dalilin manyan bak’in da za su zo. Jaheed ma da matarsa tun safe suna gidan haka Faruk da nasa Iyalan. Da azahar kuwa suka shigo harabar gidan cikin rakiyar fadawan Sarkin Gabas da Tauraruwa da Murad. Nene kasa juriya ta yi ta ture alkunya gefe ta k’arasa harabar gidan a guje kamar ta kifa. Wani irin sauri ta yi ta fa’da jikin Inno da take tsaye tana kallonta alamun tsufa sun fara bayyana sosai a jikinta. Babi kallonta yake yana murmushi kafin ya mik’a hannu yace matso nan y’ar Akbarka Matso Hajiyata na sake ganin ki Allah Alhakamu ashe zan sake ganin ki a rayuwa?” Wani irin kuka ne ya kufcewa Nene ta fa’da gefen kafa’dar Babi tana sakin ajiyar zuciya da hawaye masu yawa a fuskarta. Babi ya rik’eta tsam ba wanda ba su bawa tausayi ba a wajen. Kowa sai da ya share hawaye. Jaheed ne ya bu’de musu b’angaren Bak’i na gidan ya ce su shiga kafin su huta tunda tafiya ce mik’akkiya suka yi. Nene hannun Inno ta ja tana bin k’annenta da duk suka zama Magidanta da kallo “Mu je ciki Inno ta na cigaba da ganin ki har yanzu ban gaji da ganin ki ba.” Inno ta yi murmushi kunyar Fulani ta kamata sai ta dinga tuno Nenen a lokutan yarintarta yarda ta tashi da tsananin mak’o sai ga shi lokaci guda Allah ya raba su. Murad ma bin bayansu ya yi ba tare da sanin su ba. Suna shiga d’akin ita kuma Najee ta fito daga kitchen ba tare da sanin sun shigo ba kanta ko d’ankwali babu ta ware ido tana kallon Nene ba tare da sanin Murad na bayansu ba ta ce “Nene kin ga fa yarda kika shige jikinta kamar zaki sha Nono.” Karaf idanunta ya fa’da kan Murad! JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ita d’in ma kallonsa take yi dariyar da take dannewa tana son kub’uce mata, ganin yarda ya yi da fuskarsa kamar yaga kashi ko wani mugun abu. “Me ya kawo ki nan witch?” Ya fa’da idanunsa a lumshe don baya son ya sake katari da mummunar fuskarta. “Cewa aka yi nazo naga angon da aka Zab’a min..” bai San sanda ya sake ware idanunsa ba ya bu’de su sosai a kanta ya ce “Kada kice min ke ce Najwa?” Ta d’aga kai tana sake wage manyan hak’oranta da suka turo gaba. “Ni ce mana, ka yi mamaki ne?” Bai furta komai ba illa mik’ewa da ya yi fuskarsa a ha’de ya fice daga sitroom d’in yana jin komai za’a yi ba zai auri yarinyar nan ba, cabd’i duk zuk’a zuk’an matan da suke duniya a rasa wacce za’a ba shi sai wannan abar mai kama da….. ya sake datse leb’ensa yana ha’diye sauran maganar a cikinsa zuciyarsa na sake wani irin k’una ya fita wajen gidan so yake ya samu nutsuwa kafin ya je wajen Tauraruwa ya tubure mata ya zama dole ta kunce wannan abin da ta k’ulla, banda Uban muni da ke tattare da ita ga rashin shekaru wato sun rasa wanda za su aurawa y’ar su shine ake nema a lika masa. Zama ya yi kan wata mota a harabar gidan ya saka hannayensa ya tallafe kansa yana kallon taurarin da suke sararin samaniya kai kace hankalinsa a wajen yake, sai dai tafasar da ke cin zuciyarsa yafi gaban ya tsyaa duban Taurari. Tana ganin ya fita ta yi dariya son ranta kafin ta mik’e ta bi ta baya ta koma d’akinta. Wanka ta yi ta wanke fuskarta sosai ya fito tana tsane gashinta da ta dank’ara masa gel duk don ya kwanta ta yi kamar mara gashi. Simple Riga da wando ta d’auka ta saka masu colour pink. Sai ta yi rolling pink gele ta fita parlourn har da y’ar wak’arta zuciyarta cike da nisha’di. Suna zaune gaba d’aya ta shige kitchen don ta ha’do black tea d’in da ya zame mata dole ta sha duk dare, sai zabga k’amshin zuma da kaninfari da citta da cinnamon yake. D’ankwalinta kanta ya zame yalwataccen gashinta da ya zuba har baya ya kwanta a saman goshinta. Bata damu da rufe kan ba kasancewar duk mata ne a parlourn kuma ta kasa jumirin yin d’abi’ar kunyar da Umma ta umarceta da yi. Zamanta ke da wuya, sassanyar muryar Murad mai cike da Haiba ta doki kunnuwanta, bata damu da ta tashi ba don ta san ba zai tab’a ganeta ba. Yana saka kai cikin parlourn idanunsa suka fa’da kanta wani irin duka k’irjinsa ya yi yanayin da bai tab’a ji ba game da mace a karo na farko ya sameshi wata irin halitta mai kyau cute baby a binta kamar ita ta yi kanta. Ya kasa cire idanunsa a kanta itama ba ta fasa kallonsa ba da golden eyes d’in ta dara dara masu baiwar kyau da fusgar hankali. Da k’yar ya saita kansa sanda ta mik’e surar jikinta da k’ugunta yake a cike taf kamar ba yarinya ba ya bayyana mayafin da ya zame ne ya ba shi damar ganin tudun k’irjinta da sauri ta sunkuya don d’aukar mayafin inda idanunsa suka sake masa wani kyakykyawan gani gaba d’aya bata san saman k’irjinta ya fito ba. Da sauri ta gyara rigarta ganin kamar yana kallonta, ta turo d’an leb’enta gaba tana k’unk’uni kafin ta d’au shayinta ta harareshi ta gyara mayafin. Murmushin da bai shirya ba ya sakar mata ganin yarda tsiwar ta mata kyau shagwab’a da tsiwa suna daga cikin abinda yake so a tare da mace, Tabbas wannan ko wacece ta ha’da duk abinda yake so a tattare da mace, ashe y’an matan d’azu da ya gani bai ga komai ba sai yanzu amma da wannan zuk’ek’iyar aka rasa wacce za’a ha’da shi da ita sai waccan mummunar wallahi tabbas yanzu yaga mata kuma ko ruwa da iska ba mai hana shi mallakar yarinyar nan da ta tafi da dukkan tunaninsa at first sight. Duka wannan tunanin a cikin mintuna ba su fi uku ba komai ma ya faru kuma ba wanda bai ga abinda ya aikata ba a cikin parlourn suka kalli juna suna murmushi. Cigaba ta yi da sipping shayinta a hankali a kuma yangance da matuk’ar jan aji kamar ba Najee ba. Murad ya kasa hak’uri ya dubi Tauraruwa ya ce “Ammeey I want to talk with you.” Ta kalleshi ta ce “Okay go ahead.” Ya girgiza kai still idanunsa na kan na Najwa da sam baya son ya d’auke idanunsa a kanta ya ce “I need privacy Mah.” Tauraruwa ta saki murmushi tana mik’ewa ta ce “Okay mu je can parloun.” Ya mik’e har yana yin tuntub’e garin kallon Najwa da ta bi ta ha’de ranta kamar bata tab’a dariya ba. Suna shiga parlourn ya zube a gaban Tauraruwa ya ce “Haba Ammeey me yasa? Me yasa sai mummuna zaa bani bayan ga colour ta wallahi wannan yarinyar ta parlour ita nake so ita na zab’a yau yau na fara ganinta amma duka tunanina da hankalina ya tafi kanta, don Allah save your son life wallahi ba ta yarda za’a yi na iya hak’ura da ita.” Tauraruwa wani kallo ta masa shek’ek’e ta ce “Ka san me kake fa’da kuwa? Matan auren kake so? Wannan k’anwar Umma ce kuma da aurenta kada ka ganta yarinyar matar wani ce, don haka ka yi saurin istigafari….” Runtse idanunsa ya yi yana jin a duniya bai tab’a jin mummunan magana kamar wannan da Tauraruwa ta yi ba. Tana da aure? Ashe kuwa rabuwarsu da Mijinta ta zo don wallahi yarda nake jin zuciyata na nauyaya da sonta dole ne na mallaketa zan ba shi ko nawa ne don kawai ya bar min ita.” Tauraruwa ta tab’e baki ta ce “You are out of your mind, don haka ni ba zan ce maka komai ba, amma wallahi ka bi a hankali ita wacce muka zab’a maka menene Aibunta?” Ya ware idonsa da suke runtse murya a shak’e ya ce “Menene aibunta? Ko menene aibukanta? Ta yaya zaku ba ni wannan ku ce na aura fisabilillah?” “Jihadi zaka yi, ka tuna tana da tarbiyya da addini kuma ko bakomai ta ci albarkacin kula da k’aunar da ta nunawa mahaifiyarka ta so Nene ta bata dukkan kulawarta lokacin da take a matsayin mahaukaciya… sannan wannan da ka gani a parlourn bata da aure amma k’anwar Umma ce kuma da kunya kace baka son y’arta k’anwarta kake so…””Ni wallahi ba zan aureta ba ta fa’di ko nawa ne na biya ta amma ina kai haba!” Ya fa’da zuciyarsa a raunane yana jin kamar ya zunduma ihu bai ma gama jin sauran zantukan Tauraruwa ba ya fice daga parlourn ya sake zuba idanunsa akan Najee da tayi kamar bata gan shi ba kafin ya fice da sauri. Jaheed da shigowarsa kenan suka gabza karo ya yi saurin ja da baya yana kallonsa sai dai Murad ko ta kansa bai bi ba ya fice a zafafe. Jaheed murmushi kawai ya saki ya shiga cikin parlourn yana dubansu da Tauraruwa da take ta dariya bata gaya musu abinda ya faru ba. Ya ce “Wai lafiya kuwa naga Murad ya fita a zafafe?” Tauraruwa ta shiga basu labarin abinda ya faru Najee ma ta d’ora da nata Ai kuwa aka dinga dariya a parlourn Jaheed ya ce “Don Allah mu bi da shi a haka har zuwa sanda zata tare a gidansa muga yaya zai yi?” Umma ta girgiza kai “Ba kyau gaskiya hakan, ku fa’da masa gaskiya mana.” Rok’on ta Jaheed ya dinga yi akan ta taimaka ta musu hakan da k’yar zuciyarta ta yarda a hakan, aka kuma ce Najee kada ta sake koda wasa ta nuna masa ba haka kamanninta suke ba, ta d’aga kai tana jin da’din had’in kan da suka bata. A bedroom rasa nutsuwa ya yi ya kai gwauro ya kai mari surar Najee tana masa gizo a zuciya ya lumshe idanunsa yana jin wata irin zafaffiyar k’aunarta na huda zuciya da ruhinsa har hango kansu yake kwance a matsayin maaurata yana wasa da kayan fulaninta. Ya lumshe idanunsa yana sakin hucin numfashi a hankali wani din shauk’i yana fisgarsa yana ji a duniya zai iya rabuwa da duk abinda ya mallaka in dai zai samu yarinyar a matsayin mata. Shigowar Jaheed yasa ya bu’de birkitattun idanunsa da suka masa nauyi tsabar tunanin da ya masa nauyi a zuciya. Jaheed ba tare da ya nuna ya san komai ba ya ce “Mr. Man am going home now na bar Khaireey ita ka’dai a gida.” Da sauri Murad ya ja hannunsa ya finciko shi bakin gadon ya zauna don dole shima ya mik’e a kasalance yana duban Jaheed d’in ya ce “Don Allah ka taimakeni Jaheed ka bani numberr k’anwar Umman can da na gani a parlour sannan don Allah ka saka su su janye batun aura min mummunar can wallahi zan baka duk abinda kake so har sarautar Gabas zan bar maka ita Please Jaheed am in love…..” Ya fa’da yana lumshe idon sa wasu tarin hawaye da bai san na meye ba suna zubo masa, tunda yake bai tab’a tsintar kansa a masifaffiyar soyayya irin wannan ba da yake jin hucin numfashinta kamar zai k’iba masa zuciya. “Me yasa zaka amshi numberrta alhali akwai matar da aka maka baiko da ita, Auren Najwa alheri ne fa a gareka….” “Uban alherin? Kai me yasa baka yi halaccin ka aureta ba ina ce kai ma Nene Uwarka ce kai ka san ma wahalar da yarinyar ta yi da ita don haka kai yafi cancanta ka aureta ka ji min banza…” Jaheed ya waro ido ya ce “Ni ne banza? Ai shikkenan sai ka nemi me samo maka numberr don ba zan bayar ba kuma duk gidan nan ni nake da numberr ta bata bawa kowa numberr ta saboda masifaffen ajin da take da shi gata dai yarinya k’arama sai ajin tsiya…” Da sauri ya rik’e hannunsa ya ce “Na shaida wallahi Jaheed Na shaida kuma don Allah ka yi hak’urin zagin da na maka wallahi sharrin shaid’an ne.” Jaheed ya saki murmushi ganin yarda ya yi rauni ya ce “Babu amfanin baka numberrta Murad ka tuna k’anwar Umma ce ta ya zaka k’i y’arta kace k’anwarta kake so Ina ga hakan kamar Impossible ne…..” “In ji Uban wa? Aurenta na yi?” “In ji Ubana Murad bari dai na mik’e kafin ta kai ga ka kai min duka…” Murad ya saki tsaki yana furta “Ka yi ta tafiya amma ina tabbatar muku kuka sake kuka aura min witch d’in nan sai na tattara na bar garin nan mugu kawai.” Jaheed ya k’unshe bakinsa saboda yarda dariya yake neman sub’uce masa ya fice daga d’akin yana fa’din “Asuba ta gari Angon Najee….” Wani ashar Murad ya mulmula masa yana fa’din “Na ga Uban da zai sa ni dole na aureta…. JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ganin wanda yake tsaye ya sata saurin juyowa k’irjinta na bugu mai tsanani, Allah yasa bai ganta ba don gaba ‘d’aya hankalinsa ba a kanta yake ba, yana kan Inno da yake shirin zolaya, duk da ya ji muryarta bai mai da hankali ya san ko wacece ba, sanda ya juyo kuma da niyyar ganin wacece ta juya fuskarta ta shige kitchen gaba d’aya. Ya d’an tab’e bakinsa yana zama daf da Inno da take kallonsa cikin mamaki Nene ta ce “Murad nan ma biyo mu ka yi.” Ya d’aga murya a nutse ya ce “Ke ma ba kin biyo Mamanki ba, shi yasa na biyoki I want to have your caring.” Da sauri ta janye idonta daga kansa kunyar Tauraruwa da take zaune yasa ta kasa furta komai. Tauraruwa kuwa murmushi ta saki ta ce “Kana da gaskiya Murad ya kamata kaima ta baka dukkan kulawa da bata baka ba a baya, duk da Alhamdulillah Uwar goyonka ta maka rik’on da ya dace, amma ita kulawar mahaifiya itace abu na musamman ga yaro don haka ban ga laifinka ba, ke kuma Nene ki cire kunyar Fulani ki bawa d’anki kulawa.” Da sauri ta girgiza kai “Ni ba d’ana ba ne, na bar muku ke da Fulani Saddik’a kamar yarda Jaheed yake d’an Ummansa ni tawa y’ar Najwa ce.” Tauraruwa ta ji dad’in furucin Nenen har haka ya bayyana akan fuskarta. Shi kuwa Murad cikin fushi ya ce “Wacece kuma Najwa?” Murmushi Nene ta yi tace “Itace y’ata mafi soyuwa a zuciyata fiye da ku, don haka duk wanda yake son albarka ta ya zama dole yaso Najee ya bata dukkan farin ciki a rayuwa.” Murad kansa ya sake d’aurewa yana kallon Tauraruwa da son k’arin bayani. Gane alamun hakan yasa Tauraruwa furta “Najwa yarinyar gidan nan ce, Uwa d’aya ce ta rik’esu da Jaheed sai dai dukkan Kulawar Najee yana wajen Nene ne, tana sonta fiye da k’ima.” Ya d’an tab’e baki ya ce “Tana ina?” Tauraruwa da sauri ta basar da zancen ta hanyar kallon Inno tana furta “Wannan jikan naki akwai tab’ara ban san yarda zai yi ba ranar da zai ga matarsa a d’aki, Najee itace matar da muka zab’a maka anjima kuma In sha Allah zaku ha’du ku gaisa ku fahimci juna.” Ya yi shiru ransa da zuciyarsa na masa da’di da jin sunan duk da bai san waccece ba amma kawai sai yake ji a ransa koma wacece kyakykyawa ce kuma y’ar gayu don haka bai ji ko d’ar a zuciyarsa ba sai fatan Allah ya kai shi anjima ya ga zuk’ek’iyar budurwar kuma cikakkiya mai shekarun hankali kamar 22 haka ya tabbata zata d’auke duk wasu buk’atunsa baya shaawar auren yara mata k’anana ya fi son irin kamar degree holders haka. Tauraruwa ta saki murmushi kawai ganin yarda Murad d’in ya nausa cikin tunani da alama hasasho matar da zai aura yake. Tab’ ko ya za’a k’arke zai so Najwa ko kuwa zai ba su kunya. Shigowar Najma da Nasma ya sa shi saurin juya kai wata irin ajiyar zuciya ya saki da yaga Nasma kyakykyawar yarinya irin yarinyar da yake so mai dirin jiki irin dirin da ake cewa Coca Cola shape ya lumshe ido yana fatan ta kasance itace Najwa. Don haka ya hau gyara zama har da su saita k’wayar idanunsa akanta yana sakin murmushinsa tsadadde da ba a ko ina yake yin sa ba sai an ci mugun sa’a. Najma cikin nutsuwa da rashin kuzari ta k’arasa gefen kujera ta zauna a k’asa idanunta na kallon k’asa ta fara gaishesu. Ba wani alamar b’acin rai a fuskar kowa suka amsa gaisuwarta har Tauraruwa da ta ce “Ya jikin jikin? To Allah ya raba lafiya.” Kasa amsawa a fili ta yi sai a zuciya. Inno kuwa kasa yin shiru ta yi ta ce “Ma sha Allah tabarakarrahman suma wa’dannan yaran gidan nan ne?” Nene ta d’aga kai Tauraruwa ce ta d’ora da cewa “Wannan ita Jaheed ya fara aure kafin su samu sab’ani su rabu yanzu haka cikinsa ne a jikinta.” Inno da Murad a tare suka waro ido Murad ya ce “Rabuwa kuma?” A zuciyarsa yana jaddada wauta irin ta Jaheed ka samu wannan kyakykyawar yarinyar ka saketa haka siddan cabd’i. Tauraruwa bata ce komai ba ganin su Najman suna nan haka kawai sai ta ji ta fara jin tausayin yarinyar. “Tashi ku je Najma, ki dinga kula dai da kan ki ki gaida Mamanki kin ji.” K’wallar idonta ta share a hankali sannan ta mik’e jiri na d’ibarta haka Nasma ta rik’e hannunta suka fice daga parlourn. Murad kuwa bai d’auke idonsa daga kan Nasma ba, Tauraruwa da kowa na parlourn ya lura da kallon da yake mata. Suna fita ya juyo ya ce “Amma Ammeey me ya raba su?” K’addara da kuma Uwarta da ta zugata akan ba zasu yi zaman aure da d’an mahaukaciya ba marar asali, yanzu ga shi nan ta bar y’arta da damuwa don daga gani yarinyar nan tana son komawa gidan aurenta.” Murad ya kasa daurewa har sai da ya furta “Ita wannan kyakykyawar da ta fita itace matar tawa?” Sak kowa ya yi a parlourn har Umma da take zaune sai da gabanta ya fa’di suka zuba masa ido har ya tsargu ya yi saurin cusa hannunsa cikin tarin sumar kansa yana sunkuyar da kai da sakin murmushi a hankali. Tauraruwa ta harareshi ta ce “Futa daga nan Murad, na lura kai kyau kake so ba kyan hali ba, ba itace matarka ba ka je nan da bayan Magriba matar taka zata zo ta sameka ina tabbatar maka ta fi wannan duk abinda kake tunani kar dai Uwa Uba addini da tarbiyya su ji labari.” Murnarsa ce ta koma ciki jin abinda ta ce ya yi k’asa da muryarsa yana furta “Allah idan bata yi min ba sakinta zan yi na auri y’ar uwarta, ai ba wani abu bane tunda duk gida d’aya suke…” hararar da Nene ta wurga masa ce ya sa shi yin shiru da k’arashen zancen da ya yi niyya ya fita yana dariya. Zuciyarsa na sake jaddada masa in dai bai gamsu da zab’insu ba tabbas da sake! Tauraruwa ganin duk kamar zuciyarsu a dame take ya sata sakin murmushi tana furta “Kada fa ku damu da abinda yace ba abinda zai faru In sha Allah sai alheri.” Allah yasa suka furta kusan duk a tare. A kitchen Umma ta samu Najee ta rutsata tana zabga mata harara “Marar kunyar banza don shashashanci wannan maganar da kika musu ke a tunaninki ta dace, Wai Najwa yaushe zaki zama mai hankali ne? Ki yi ta abu kamar goyon kaka ko don kin tashi cikin maza shikkenan sai ki zama mashiririciya har abada kin kasa nutsuwa balle ki fara gwalli da fyalli irin na y’an mata, koda yaushe ba nutsuwa a tare da ke, to ki bu’de kunnenki da kyau na gaya miki Murad shine mijin da zaki aura ya zama dole kuma ki jajirce wajen kula da kan ki, kwalliya tsafta iya magana idan ba haka ba kina ji kina gani ya miki nisa shashasha kawai. Kuma ki wuce ki je ki durk’usa har k’asa ki gaishesu, kina da kwanyar manya amma shiririta ta miki yawa. Ana sallahr magriba kuma ki yi wanka ki shirya tsaf ki je sitroom kina da bak’o.” K’asa ta yi da kanta tana fa’din “To Umma, don Allah ki yi hak’uri.” “Ni baki min komai ba halayenki nake son ki canja gwara ki san kin girma yanzu Allah ya miki albarka kin ji?” Ta d’aga kai tana gyara mayafinta ta fita parlourn a zuciyarta tana fatan Allah yasa Murad baya nan don bata shirya bayyana masa kanta yanzu ba. Ajiyar zuciya ta saki ganin baya nan sai ta hau jan mayafi tana rufe fuskarta wai ita aladole sai ta aro wannan halin da Umma take so, ta san dai haka ake wa surikai don tana gani a film. Tauraruwa murmushi ta saki tana furta “Yau kuma Najwa mu kike jin kunya ko Inno?” Bata yi magana ba sai dai ta cikin mayafin take kallonsu tana ganin yarda Inno take ta hangen son ganin fuskarta. “Ina wuni? Kun zo lafiya ko?” Nene dariya ta yi tana mamakin Najwa wanda daga ganin acting d’in da take ta san tursasata aka yi. Suna amsawa ta mik’e da sauri ta hanyar d’aki don har ga Allah gumin da take na yafen mayafin da ta yi ya isheta. Tauraruwa ta bita da kallo tana dariya k’aunar yarinyar na sake shiga ranta, komanta mai kyau ne da tsari tun a yanzu ma ina ga nan gaba idan mak’erin y’an mata ya sake k’erata. Tana shiga d’akinta ta yi wurgi da mayafin har da d’an kwalin ta ce “Wannan masifa har ina? Wallahi Umma ba zan iya ba in yi ta wani k’unshe kai na kamar wata munafuka, shi kuwa anjima zai ga kyakkyawa Ai ina jin duk abinda yake fa’da d’azu…. Ta tuntsire da dariya tuna abinda ta shirya masa. Ana sallahr Magriba cikin zakwad’i Murad ya koma sashen da nan ne D’akin Jaheed da Faruk na asali yake. Wajene mai kyau da ya sha kayan alatu na more rayuwa. Wanka ya yi sosai gaba d’aya a k’afauce Yake ya damu k’warai ya je Yaga matar da aka zab’a masa, duk yarda yake k’issima kyanta sai yaga kamar ya rage mata kyau shi gani yake ma a duniya ba mai kyanta don ya san kowa ya san tsarinsa na son auren mace kyakykyawa mai kuma ajin gaske. Taje kansa ya yi sosai ya baza turare tsananin kyan da ya yi zata zaka yi a ranar zai angwance a d’akin amaryarsa. Tunda ya fito Jaheed yake kallonsa cikin mamaki ya ce “Irin wannan ado haka sai kace za’a kai ka d’aki?” Murmushi ya saki yana furta “Kusan haka tunda yau zan ga Matar da aka zab’a min, na san dai hundred percent ta cika mace tunda Ammeey da kanta ta min zab’in ka san bata zab’en abu marar kyau, don haka dole nima na matso kyau na da yarinta ta ba don komai ba sai don na sace zuciyarta at first Sight.” Jaheed murmushi ya saki a ransa yana jin Murad bai san y’ar ficikar da aka zab’a masa ba. Dariya yake son yi sai don ya matse ya ajiye dariyar zuwa anjima ka’dan. Murad ya fice har da y’ar wak’arsa yana rausayawa a hankali cikin tsananin shauk’i da farin ciki da ya bayyana muraran akan fuskarsa. Zama ya yi a sitroom d’in yana karewa sitroom d’in kallo duk da hankalinsa ba anan yake ba yana kan ta inda Najwa zata b’ullo. Bata bari kowa ya ganta ba ta fice da sauri ta k’ofar baya tana sakin ajiyar zuciya kafin ta isa sitroom d’in ta lullub’e fuskarta da mayafi Ta yi sallama cikin kasalalliyar muryar da Yasa Murad saurin d’agowa yana sakin ajiyar zuciya wani farin ciki na ratsashi ya amsa sallamar. Yana kallo ta isa kujerar da ke gefensa ta zauna tana furta “Ina yini?” Waro ido ya yi yana furta “Wait tsaya don’t tell me da wannan hiding face d’in zamu gaisa, please remove it I want to see your beautiful face Baby….” Ya saka hannu yana yaye veil d’in fuskarta wani irin razana ya yi ya ja da baya da k’arfi a tsawace kuma ya furta “What?” JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Har tsakiyar dare Murad ya kasa runtsawa shi dai kam da kansa zai iya cewa bai ga wani abu da ya tab’a hana shi barcin dare ba kamar yau da soyayyar Najwa ta hana shi sak’at. Da zarar ya rufe ido cute lips d’inta yake gani sanda ta turo shi gaba da niyyar yi masa tsiwa. Ya dinga juyi shi ka’dai akan gado ya rasa me ke masa da’di. Bai k’i ba ace ya sake ganinta kusa da shi tana sakar masa harara da daradaran idonta. Ashe haka soyayya take? Da yakewa maza masu soyayya kallon wa’danda ba su san ciwon kan su ba. Hotonta ya zauna daram a zuciyarsa da idaniyarsa ba abinda yake gani sai kamanninta da gaske yana jin ko cewa aka yi ya zanata tsaf zai zanata sabida yarda kamanninta suka zauna ra’dam a ruhinsa. Har Asuba ya kasa runtsawa Allah kawai yake rok’o ya mallaka masa Najwa a matsayin matarsa ta aure matarsa ta dindin. Ya daure ya yi Sallah kafin ya watsa ruwa ya zura wasu sassauk’an kayansa na shan iska sabida yarda ake zafi a gari. Wasu irin kalolin turare ya fesa a jikinsa duk da nauyin da idanunsa ya yi masa bai saka shi fasa fita harabar gidan ba ko Allah zai saka ya ganta kafin gari ya waye sosai ya shiga cikin sashen Umman. Wannan karan da kansa zai rok’i Umma ba zai ji kunyar gaya mata y’arta bata masa ba k’anwarta ce ta masa. Tattausan silifas bak’i wuluk da ya dace da tattasar k’afarsa da alamun hutu suka gama ratsa tafin k’afar kamar ta jarirai shi ya zura ya fita k’ofar gidan. Idanunsa sun d’an tasa ka’dan saboda rashin barci. Yana fita suka yi arba da Baffa da shigowarsa kenan daga masallachi. Da sauri ya rusuna ya gaisheshi. Baffa cikin jin da’di ya amsa a ransa yana godewa Allah da ya saka Murad ya zama surikinsa tarbiyyar yaron da nutsuwarsa ta masa sosai ji dai yarda ya zube yana gaisheshi kamar ba Dan sarki ba. “An tashi lafiya Murad? Ya bak’unta da zafin garin mu?” Murad ya d’an sosai kai yana furta “Alhamdulillah.” “Ma sha Allah, Ai sai mu shiga ciki mu karya ko?” Murad ba musu ya bi shi don burinsa sake arba da yarinyar da ta tafi da dukkan tunaninsa, so Yake ya yiwa Baffa maganar sai dai ya kasa kallon k’wayar idonsa ya gaya masa sirrin zuciyarsa abin kamar da nauyi. “Mu fara shiga mu gaisa da matan gidan, haka ake so ga duk magidanci bayan sallahr asuba ya zaga ya tabbatar da iyalinsa sun kwana lafiya koyi ne k’warai da sunnar manzo s.a.w babu Alfanu kace kana jiran matarka tazo ta gaisheka ba mu ji haka a Hadisi ba ba Kim’s ruwayar da ta rawaito shi duk da idan hakan ta faru ba laifi ba ne, amma dai a bi koyarwar annabin shine mafi a’ala.” Murad ya saki murmushi kawai, halayen Baffan da nagartar d’abioinsa suna sake masa naso a zuciya yana jin Baffan yana sake burgeshi abu guda da yayi ya ba shi haushi rasa yarinyar da zai ba shi a cikin y’ay’ansa sai waccan mummunar da ko tunata baya son yi. Sashen Mahmeey suka fara shiga. Shiru sashen da alama sun koma Barci. Baffa ya d’an bi parlourn da kallo kafin ya ce “Sarkin barci har ta koma zauna ina zuwa Murad.” Ya fa’da yana shiga corridor da zai kai shi inda bedrooms d’in d’akin suke. Ba barcin take ba kamar yarda ya tsammata a zaune take fuskarta ko ka’dan ba annuri. Ya yi sallama yana kallon yarda duk ta rame da alama damuwar da ta sawa zuciyarta ta fara tab’a lafiyar ta. A zafafe ta d’ago tana kallonsa dama shi take jira don ta san dole yana shigowa a irin wannan lokacin koda kece da girki kuwa sai ya shiga ya duba lafiyar yaransa. “Baki cire banzar damuwar da kika sakawa zuciyarki ba ko? Da alama kin shirya fara shan maganin hawan jini ne.” Kukan da take ta yi tun cikin dare shi ta sake saki wanda yake bayyana k’unar da zuciyarta take ciki. “Me yasa ka ba zaka bi abinda na ce maka ba, laifine mun yi maka amma Ai mun baka hak’uri ka bawa yaron nan hak’uri ya koma da matarsa amma ka k’i, fisabilillah ina zaka saka hakkin yarinyar nan da take cikin damuwa kullum duk ta bi ta lallace bata da nutsuwa ko ka’dan ga tsohon ciki a gabanta.” Tsaki Baffa ya ja yana furya “Yanzu da kika san asalinsa kika san ko wanene Ubansa mai ku’din gaske irin wanda kike so shine zaki d’aga hankalinki sai ta koma? To ba dani ba ni akwai kunya da kawaici a tsarina ba zan iya duban idonsa na tursasashi ya mayar da ita ba bayan rashin mutuncin da kuma masa, har abada shi yasa komai kasawar bawa ake son ka kyautata mu’amalaka da shi saboda watan wata rana kamar dai irin wannan baka san darajar da Allah ya yiwa bawa ba anan duniya ko a lahira sabida kawai kuna da fifiko ta halitta ko ta ku’di sai ka d’au fankama da girman kai ka d’orawa kanka Ina kika bar fir’auna da k’aruna? Idan arziki ne da girman kai duk duniya ba za’a sake kamarsu ba yau ina suke sun gushe kuma arzikin nasu da girman kan ba inda ya kai su. Don haka ni dai da bakina ba Zan ba shi hak’uri ba balle ya yi tunanin tursasashi na yi har ya yi min alfarma na cutar da zuciyarsa, ki nemo shi da kan ki ki bashi hak’uri ku je kuma ku bawa Uwarsa hak’uri idan ta yarda falillahil hamdu idan kuwa ba su yarda ba kada ki sake jefa ni a cikin maganarku.” Daga haka ya saka kai ya fice daga d’akin yana jin kukanta yana sake yawaita duk da zuciyarsa ta yi rauni ya fara tausaya mata amma ba zai bari tausayinta ya yi tasirin da zai kasa yiwa Jaheed adalci ba. Ya samu Murad duk ya gaji da jiransa burinsa kawai su shiga d’aya b’angaren ya ga sanyin idaniyarsa. Don haka d’akin yaran lek’awa kawai ya yi suka gaishehi ya amsa a tsaye yana kallon Najma da fa’din “Ba dai matsala ko?” Najma ta d’aga kai tana lumshe idonta da ya mata nauyi sabida rashin barci. “Allah ya muku albarka a kula da cin abinci sabida bawan Allah da kike tare da shi.” Bai jira ta cewarta ba ya yi saurin fita daga d’akin har ga Allah baya son ganin Najma a cikin halin da take ciki dukkan gazawatta da damuwarta sun bayyana akan fuskarta b’aro b’aro. “Mu je Murad ka yi hak’uri na barka da jira.” Murad ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai ha’de da fa’din Bakomai Baffa.” Gaba d’aya halayen dattijon sun shiga ransa har yana jin da zarar ya mallaki iyali shima irin rayuwar da zai yi a gidansa kenan, ba zai zamo daga cikin maza masu girman kai ba zai zama mai sauk’in hali ga iyalinsa musamman idan ya samu wacce yake so. Tun daga harabar sashen Umma suka dinga jin wani irin masifaffen k’amshin turaren wutan da ake yi. Murad har d’an lumshe idonsa ya yi sanda suka bu’de k’ofar tattausan k’amshin da ya caku’de da na room freshner da na sanyin a.c ya dakar masa fuskar sa. Har ga Allah yana son k’amshi, hakan a jininsa yake kamar ma ya zama addicted da shi. A tsaye take daga ita sai wata y’ar rigar barci da ka’dan ta wuce gwiwa mara hannu gashin kanta a barbaje a bayanta aikinta take fisabilillah tana bin wak’ar da ta saka a wayarta. Ba abinda ya dameta duk da Umma ba yarda bata yi ba ta suturce jikinta ganin Umman ta shige kitchen yasa ta cire dogon Hijabin da ya bi ya addabeta ta saba zama haka a gidan sanin cewa ba mai shigo musu sai Baffa ko yaran gidan maza duk suna boarding school. Idanun Murad ne suka masa mugun gani da sauri ya juya baya jin Baffa ya ce “Ke me ye haka sau nawa zan hanaki zama a haka? Wai ke sam ba kya girma ne, sannan kin saka wak’a da sassafe alhali ba d’abiarki ba ce? Wuce ki suturce jikin ki.” Da azama ta ja hijab d’inta ta saka tana fa’din “Ka yi hak’uri Baffa na zafi ne ya yi yawa.” Ta fa’da tana kallon sashen da Murad yake ganin yarda ya juya baya. Ta d’an saki guntun tsaki “Maye da sassafen nan har ya wani shigowa mutane gida. Sannan ta durk’usa tana gaishe da Baffa sai da ta bari ya amsa ta Mik’e ta bi hanyar kitchen a zafafe Baffa ya ce “Ni ka’dai kika gani anan? Ko wani salon rashin tarbiyya zaki tsiro da shi na rashin gaisar da wanda ya girmeka?” Kamar ta tsunduma ihu haka ta juyo tana kallon Murad idanunsu suka fa’da cikin na juna, wani irin fisga zuciayrsa ta yi bai san sanda ya lumshe ido ba yana jin yarda muryarta take karad’e kunnensa duk da ba sosai muryar ta fita ta hanyar d’agawa leb’enta ya fuskanci me ta ce “Ina kwana?” Da k’yar ya saita kansa wajen fa’din “Lafiya lau.” Yana k’arashewa da My heart cikin zuciyarsa banda Baffa yana wajen baya jin akwai abinda zai togaceshi wajen janyota ya rungumeta tsam ya bata kyakykyawar sumbata a cutest lips d’inta. Bata sake kallonsa ba ta juya tana ba shi hararar gefen ido. Kitchen ta koma bayan ta kashe burner d’in turaren wutar da ta kunna. Sai ga Baffa ya biyo bayanta a kitchen d’in ya tsaya kafin ya saka yatsa ya murd’e kunnenta “Najwa ba kya girma ko? Mijin da zaki aura kike harara ko kin zata ban gan ki ba ne?” Da sauri ta furta “Am sorry Baffa, ni wallahi bana son sa da na fi son Yaya Jaheed.” “Shi kuwa zaki aura nan da kwana uku Jaheed yanzu ya miki nisa tunda ga Najma da ciki, ana barin halas ko don kunya.” Umma ta fa’da tana zabga mata harara. Baffa dariya ya d’an yi yana fa’din “Ki bata break fast ta kawo mana sitroom yanzu zamu zauna mu karya da Murad da Babi.” Umma ta amsa masa shi kuma ya saka kai ya fita daga kitchen d’in. “Mu je sitroom Murad naga iyayen naka ma basu tashi ba mu je wajen Babi kafin a kawo mana breakfast.” Murad ya mik’e ya bi bayansa yana waiwayen yarda zai sake ganinta. Suna fita Umma ta watsa mata harara “Shashasha na sake jin kalmar Jaheed kike so a bakinki kiga yarda zan miki a gidan nan. Kuma ki wuce ki je ki yi wanka yanzun nan kizo ki kai musu breakfast.” Ta d’an turo bakinta tana ficewa daga kitchen d’in. Wankan ta yi sosai don duk abinta tana da tsafta sosai. Ta saka wani pink lace da ya yi daidai da surarta straight gown ce ta d’an kamata ka’dan ta fitar da tudun hips d’inta, don akwai baiwar hips tun tana yarinya ma kenan. Bata saka d’ankwali ba don yana daga cikin abinda yake takurata. Ta yane kanta da very light veil, sannan ta fice bayan ta goga wet lip a cute lips d’inta. Basket biyu ne da suke d’auke da manyan flask a cikinsu, da k’yar take tafiyar da su kamar su yar da ita. Su Babi na cikin sitroom d’in shi kuwa ya kasa ya tsare a balcony kamar ya san ita zata kawo abincin. Tun daga nesa ya hangota yarda kwanukan suke rinjayarta sai yasa tana tafiya tana jin kamar zata kifa. Murmushi ya saki ya mik’e ya d’an b’uya a bayan wani lungu. Sai da ta k’araso wajen ya fito ya sha gabanta yana bin ta da wani irin rikitaccen kallon da ya sata kusan sakin baskets d’in. Idanunsa wani irin kaifi su ka mata. Da wata irin murya da bai san yana da ita ba ya matsa daf da ita cikin kunnenta ya furta mata “I love you….” Yana sakar mata hucin numfashi a cikin kunnenta wani irin harbawa zuciyarta ta yi kamar ta saki fitsari a wando. Ya janye jikinsa daga kusa da ita yana kallonta k’asa k’asa ta d’aga k’afarta zata wuce sai kawai gani ta yi kamar an jata zata kifa k’asa bai san sanda ya tare ta da hannunsa ta fa’da k’irjinsa ba wani irin shock ya d’ebesu gaba d’aya, Najee ta runtse idonta a hankali ta furta “Are you out of your senses? Ka san yarda muke da matar da zaka aura kake furta min kalmar love?” Madadin ya ji kururuwar zancensa ji yake kawai zuciyarsa na bashi umarnin ya yi kissing d’in lab’b’anta da suka fi tsone masa ido kafin ta yi aune ta ji….. JIKAR NASHE✍🏽🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Tsananin tashin hankalin da yake ciki ya zarce duk wani tunanin mai karatu, k’ok’ari yake ya fisge takardar daga hannunta sai dai ta k’i yarda ta bashi damar hakan ta hanyar mik’ewa da mugun gudu ta shammace shi ta fice daga d’akin tana furta naga abinda yake ciki don haka maganar ka janye sakin ma bai taso ba… daga haka ta saka kai ta fice daga sashen nasa ta fa’da wani d’aki da aka ajiye dattawa biyu da zasu zauna da ita a sashen kafin ta saba wanda suka zamo na kusa ne da sarki a b’angaren dangantaka su yakewa kallon iyaye mutane ne masu daraja a idonsa da yakewa kallon mahaifa sune kuma a gurbin mahaifan nasa d’aya K’anwar Uba ce a wajensa da suke iyaye guda da ita, ita kuma Yakumbo Danejo k’anwar Mahaifiiyarsa ce da suka sha Nono guda don haka ko baa fa’da ba ka san sune iyayen Sarkin gabas. A gabansu ta zube tana mayar da numfashi da sauri suka d’ago kai suna kallonta ganin yarda ta mayar da k’ofa ya rufe garam da sauri har da murza key bayan haka ga shi tazo ta zube a gabansu tana haki hakan zai tabbatar maka da rashin wanzuwar lafiya a tattare da ita. A sukwane suma suka mik’e suna furta “Lafiya kike kuwa?” Duk da dukan da zuciyarta yake yi gefe guda kuma tana murnar cikar muradinta bai hanata yin rawar baki wajen sanar da su mutuwar auren da aka k’ulla a yau a kuma cikin dare guda komai ya faru ya k’are… idanu suka ware a razane suke kallonta zuciyarsu na bugawa da mugun gudu kafin su furta “Wani irin zance ne mara da’din ji haka? Shi Murad d’in ne ya sake ki?” Ta d’aga kanta kafin ta saka hannu ta mik’a musu takardar sakin da ke hannunta. Basu iya karatu ba don haka basu damu da su duba abinda ke ciki ba, illa mik’ewa da Hajja Bintu ta yi tana lalubar wayarta mai torchlight ta fara danna numberr Maimartaba. A bugu guda ya d’aga ta saki ajiyar zuciya ha’de da sanar da shi mak’asudin kiran, ya yi shiru kamar ba zai tanka ba sai kuma ya ce “Ya yiwa kansa, a taho mana da ita yanzun nan zuwa b’angaren Tauraruwa.” Daga haka ya zare wayar daga kunnensa cikin matuk’ar k’una da zafi da zuciyarsa take yi. Shi Murad zai to nawa asiri aure a rana guda a kuma yi saki cikin dare guda tabbas zai nuna masa asalin sunansa na Muhammad Mukhtar mai gabas! Tana ajiye wayar ta mik’e don cika umarnin mai martaba “Mik’e mu je can sashen umarnin Mai martaba.” Hajja ta fa’da tana jan hijabinta ta zura a jikinta. Ta kama Najee da ta mik’e da k’yar ta bi bayan ta suka fice ta wata k’ofa daban da ta tabbata ba zasu ha’du da Murad ba. Dubawar duniya bai ganta a cikin gidan ba ya kuma manta da d’akin da su Hajja suke. Cikin tashin hankali ya gama zagayen sashen kafin zuciyarsa ta sare ya tabbatar bata nan. Zaman dirshan ya yi k’asa ya kuma rik’e k’uncinsa hannu bibbiyu cikin mabayyanin tashin hankali ya ce “Ni Murad me na aikata?” Zufa ce ta fara fitar masa daga jikinsa ba ta komai ta sai ta matsanancin tashin hankalin da yake ciki bai san da wane ido zai kalli maimartaba da Tauraruwa ba su amince su bashi matarsa tabbas ya aikata babban kuskuren da gyaransa sai Allah. Wace amsa zai basu a lokacin da suka bijiro da tambayoyinsa garesu? Babu! Shine amsar da ya ji zuciyarsa na amsa kuwwar gaya masa. Gwuiwoyinsa suka sare don shi da kansa ya san tabbas amsar da aka ba shin itace amsar da ta dace da tambayarsa. Ya runtse idonsa da k’arfin gaske a lokacin da idanun nasa suka cigaba da hasko masa kyakykyawar fuskarta a yayinda da ya bu’deta. Hannunta damk’e cikin na Hajja suka ratsa har cikin sashen Tauraruwa babban sashen da ta tare a ranar. Shiru sashen sai hadimanta da suke ta kaiwa da kawowa. Ganin Hajja ce ba su yi k’ok’arin tsayar da ita ba suka bari ta shige har cikin sashen da d’akunan barcin Tauraruwa suke. A babban d’akinta suka tsaya suna nocking a hankali. Tauraruwa da ba barci take ba ta idar da nafila kenan ta basu umarnin shiga duk da bata san su waye ba amma zuciyarta ta yi mummunan bugawar da ta tabbatar koma meye ya faru ba zai zama alheri ba. Ta mik’e a hanzarce ganin Hajja rik’e da hannun Najee. Zuciyarta ta sake tsinkewa cikin kasalalliyar murya ta furta “Lafiya Hajja? Me ya faru na ganku tare a tsohon daren nan?” Hajja bata amsa ta ba har sai da ta dangana ga wata kujera a d’akin suka zauna ita da Najeen sannan ta kalli Tauraruwa ta ce “zauna y’ar nan lamarin fa babu da’din ji.” Harbawar da zuciyar Tauraruwa ta yi wannan karan har yafi wancan ta dafe k’irjinta da take jin idan bata dafe d’in ba saboda matsanancin bugun da yake komai ma zai iya faruwa. “Ya saketa ko?” Shine kalamin da ta ji kawai ya fita daga bakinta…” Hajja ta d’an ware ido cike da mamaki ta mayar mata da tata tambayar “Dama Kun yi da shi zai saketa ne?” Tauraruwa ta d’an cije leb’e da ta tabbatar da samuwar amsarta bata buk’atar wani k’arin bayani. “Ya furta da bakinsa, idan har muka sake muka sa ta tare a gidansa tabbas zai saketa a gidan aurenta! Amma me yasa zai yi sakin bayan ta bayyana masa kamanninta?” “Tun kafin yaga fuskata ya ja hannuna ya damk’a min takardar sakin…. Sai dai bayan da yaga fuskarta wa sai yaso ya janye takardar ni kuma na ruga na gudu tunda na tabbata ba don Allah yake so na ba don Allah ina rok’on alfarmarki Mahmah ki raba wannan auren….” Har abada kuwa!” Tauraruwa ta furta cikin muryar da yake bayyana b’acin ranta. Ta ja waya ta kira mai martaba sai dai bugun duniya bai d’aga wayar ba ta san tabbas yana cikin yanayi na b’acin rai, tana daina kiran wayar Murad ta dinga shigowa ba kakkautawa. Kallon wayar kawai ta ji ranta ya sake b’aci bata san sanda ta kashe wayar gaba d’aya ba tana jin ko sunan Murad bata son ji a wannan lokacin da zuciyarta take buk’atar nutsuwa da dogon nazari kafin ta san irin hukuncin da zata yanke akan maganar. Fita ta yi daga babban d’akin nata kafin ta dawo ta ce Hajja da yakumbo su koma d’akin da ke kusa da nata. Najee zata mik’e ta kira sunanta “Dawo mu kwanta tare kin ji Najwa..” Najee ta ja k’afarta a hankali zuwa saman kujerar da ta tashi, zuciyarta take jinta wasai ko yanzu kam burinta ya cika zata wahalar da shi kamar yarda ya gallaza mata a rayuwa kuma bata jin zata sake komawa gidan sa har abada. “Tashi ki shiga ki yi wanka, ki tabbatar kuma baki saka wannan zancen a ranki ba balle ya dameki gobe zan kira Nene zan sanar mata duk abinda muka zartar zaki ji.” Najee ta d’aga kai tana lumshe yalwatattun idanunta da suke cike da zaro zaron gashi. Ganin Tauraruwa bata d’aga wayar ba sai hankalinsa ya sake tashi kai tsaye ya mayar da kiran kan Jaheed. Yana cikin barci ya dinga jin kiran da k’arfin gaske da sauri ya d’aga ganin me kiran yana fatan koma meye ya zama lafiya. Bai jira yace komai ba ya ce “Na cuci kai na Jaheed na saki matata a cikin rashin sanin cewa itace matar da nake muradi nake kuma burin mallaka a matsayin matar da nake so….” Jaheed runtse idonsa ya yi kawai kafin cikin raguwar murya ya furta Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna saki nawa ka mata Murad?” Runtse ido Murad ya yi hannunsa na rawa ya zubawa hannun da ya rubuta takardar sakin ido yana jin da da gatari kusa da shi ba abinda zai hana shi sare hannun da har ya rubuta sakin ba tare da ya ankarar da shi wautar da yake shirin aikatawa ba… “Na ce saki nawa ka mata Murad???” Murya na rawa ya furta “Duka………” Jaheed ya runtse idonsa kawai bai san wayar ta fa’di daga hannunsa ba…… Hope an yi sallah lafiya Ubangiji Allah yasa mun yi ibada karb’abbiya ba k’ishirwar banza muka sha ba… In sha Allah jibi zamu dawo postinga gadan gadan kamar yarda muka saba ba za kuma mu tsyaa har sai mun kammala littafin biizinillah… Allah yasa muna daga cikin y’antattun bayin da aka y’anta a cikin watan ramadan wannan somin tob’i ne na fara sakar muku don haka zaku gan shi ka’dan, alamace ta nuna ku shirya gadan gadan Kudirar Allah na nan tafe ranar lahadi Idan Allah ya kai mu. JIKAR Nashe Love you all… 🥳🤗 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Lab’bansa a kusa da nata da sauri ta ja baya tana runtse idonta da mugun k’arfi. Kafin ta ware idon a kan Food warmers d’in da Suka wancakale a gefe Allah yasa na a rufe suke b’am ba su bu’de ba. Ta tura shi da k’arfin gaske kafin ta mik’e tana harararsa k’asa k’asa. “An gaya maka ni y’ar iska ce? Ko irin matan da ka saba hul’da da su? Kada ka sake kusanto ni bana so.” Ta fa’da zuciyarta na mata wani irin zafi da takaicin abinda ya mata, take ta sawa zuciyarta tabbas Murad manemin mata ne idan banda haka ta yaya yake nuna maitarsa akan jikinta. Idan kuwa haka ne ashe an ha’data da babban aiki. Yana kallonta ta tattare kayan ya kasa aikata komai illa zuba mata nauyayyun idanunsa da ya yi. Itama jikinta rawa yake sosai don abinda baa saba mata ba ne, hasalima bata san haka auren yake ba ta d’auka kawai dai zata je ta yi girki ne da su aikin gida, bata zo nan ba ko a islamiyya a tv kuwa wajen turawa idan taga an yi hakan ta kan kwatanta su a matsayin y’an iska. Kuma ba musulmai ba a tunaninta musulmai ba zasu aikata haka ba. Ya mik’e da k’yar ya bi bayanta zuwa cikin parlourn ba don komai ba sai don kar Baffa ya ce me yasa bai shigo ya karya ba, amma yarda yake jin jikinsa kamar lafiya ta masa k’aranci. Tana dire abincin ta juyo suka kusa gabza karo harara ta zuba masa ta wuce. Murad ya bi bayanta da kallo yana sakin ajiyar zuciya. Bai iya cin komai ba illa ruwan black tea da ya sha kawai. So yake kawai ya gan shi a Garin Gabas a gaban Maimartaba ya sanar masa baya son zab’insu shi ga wacce Allah ya jarrabeshi da so. Baffa yana kallon yarda ya kasa cin komai don haka cike da kulawa ya ce “Malam Murad ka ci abinci mana.” Girgiza kansa ya yi a hankali ya furta “Tea d’in ma is enough ban saba cin abinci da safe ba.” Baffa ya yarda da batunsa don ya san mutane ireirensa da yawa. Yana gama sha ya mik’e yana kallon agogo ya ce “Babi yakamata ku zama ready mu wuce da wuri.” Babi ya d’aga kai yana furta “Yanzu kuwa In sha Allah. Yauwa Alhaji nace ya maganar ita Babar tasu yaushe ta shirya komawa masarauta don sun zo min da maganar nace a bari a sameka don yanzu dukkan wata ragama tata tana hannunka don kular da ka bata ko mu iyayenta ba mu bata ba.” Baffa ya girgiza kai “Zata koma In sha Allah, amma sai an yi addu’a ka san zaman masarauta dole sai da neman tsarin kai. Ba zata shiga sama ta ka ba.” Babi ya gasgata da zancensa don ya san gaskiya ya fa’da “Allah ya mana jagora ya fa’da yana kallon Murad “Maza ka je ka sanar da su su hanzarta mu tafi kada a ga rashin hankalinmu mun wuni mun kwana a gidan surukai.” Baffa ya girgiza kai ya ce “Mu dai bama gajiya da mutane balle ku bak’i masu alfarma.” Tsaf suka gama shiri suka fito harabar gidan, Tauraruwa tana kallon Murad tace “Ka yi sallama da mutuniyar taka?” Murad ya tattare duk fara’ar fuskarsa ta gintse ko zancenta ba ya son a masa balle tuna mummunar fuskarta. Murmushi duka suka yi a wajen suka fita harabar gidan. Tauraruwa ce ta tsaya daga bakin sashen Mahmeey ta ce Jaheed ya kira mata Najma. Kallon Jaheed ya yi da alamun son k’arin bayani. “Ko ba zaka kira min ita ba ne?” Ya girgiza kai yana furta “Bari yanzu na kira ta.” Ya yi nocking k’ofar sashen Nasma ce ta bu’de muryarta a k’asa ta gaishe da Jaheed d’in. Ya amsa fuskar sa ba yabo ba fallasa. “Kira Najma In ji Ammeey.” Nasma ta amsa da to ta juya cike da zumu’di don kiran Yayarta don rashin nutsuwar da Yayarta take ciki itama abin yana tab’a mata zuciya matuk’a da gaske. A zaune ta ganta idanunta gaba d’aya sun fa’da ciki don tsananin rama ga cikinta da ya turo a gabanta. Nasma ta saki ajiyar zuciya cike da tausayi ta ce “Ya Najma ki zo in ji Yaya Jaheed….” Wani irin d’agowa ta yi tana kallon Nasman ta ce “Da gaske?” Ta d’aga mata kai cikin rawar jiki ta yafa mayafin ta ta mik’e a hankali ta fita harabar gidan. Sosai ta yi nufin durk’usawa Tauraruwa ta yi saurin saka hannunta ta tayar da ita tausayin yarinyar take ji yanzu. Suka amsa gaisuwar ta kalli Jaheed ta ce “Ka mayar da matarka yanzun nan bana son wata doguwar magana, ko bakomai ta ci albarkacin mahaifinta da ya baka dukkannin gata ga kuma d’an tahalik’in da yake cikinta da bai san hawa bai san sauka ba, don hk bn son wata magana data zarce ta na mai dake dakinki fak’at kuma bana son wata tashin tashina ta yi laifi kuma ta amsa laifin ta har ta baka hak’uri kuma ta yi nadama, ban ga amfanin rik’on ba. Allahn da ya haliccemu ma hak’uri yake da mu.” Jaheed ya d’ago yana kallon Najma da take zubar da hawayenta ba k’akkautawa tsimammiyar k’aunar da yake mata ta tashi sai ya ji hankalinsa ta tashi da ganin hawayenta shi kansa ya da’de da fara tausayinta cijewa kawai yake ya kasa furtawa. “Ba yafe mata kuma na mayar da ita d’akinta Allah ya sa mu zama abin alfahari a wajenku ya ba mu zaman lafiya.” Wata irin k’akkarfan ajiyar zuciya Najma ta sauke shi kansa Baffan ajiyar zuciyar ya saki ya da’de da tausaya mata k’arfin hali da dattako irin nasa ne yasa ya kasa furtawa Jaheed ya yi hak’uri ya mayar da matarsa. Najma ta dinga Jin wani sanyi na Ratsa sassan jikinta. Tauraruwa ta sake musu addu’a sannan ta kalli Najman ta ce “Sai ki hanzarta ki koma d’akinki a cikin satin nan kada ki haihu musu a gida.” Ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, murya a tausashe ta ce “Nagode” ta musu Fatan sauka lafiya kafin ta shige gida kai tsaye jikin Mahmeey ta fa’da tana sakin dariyar farin ciki. Itama Mahmeeyn dariya take ta dafa bayanta ta ce “Allah ya yi kenan Tabbas na san Allah ne ya jarrabemu ba don komai ba sai don tsana da k’yamar da muka nunawa Jaheed sai ga shi yau da kan mu muke rok’onsa ya mayar da ke d’akin ki, tabbas yanzu na shaida d’agawa da girman kai ba inda suke kai bawa sai tashar dana sani, Allah ya Raba mu da wad’annan halayen.” Ameen yaran suka ha’da baki wajen fa’da shikkenan sai kuma suka fara shirin yarda zata koma gidanta bayan bikin Najee In sha Allah. A masarautar gabas fa duk wasu shirye shirye sun kankama. Murad kawai kallonsu yake yi yana jin ba abinda zai saka shi zama da wannan yarinyar mai kama da……. Don haka ana Gobe d’aurin aure ya isa sashen mai martaba ransa a b’ace gaba d’aya har rama ya yi saboda rashin nutsuwar zuciya ya samu Mommahn sa Saddik’a da zancen ta rigime ta ce bata san wannan zancen ba dole ya auri zab’insu idan ba so yake ya ha’da rigimar da ba zata mutu ba. A zaune ya samu Maimartaba da Tauraruwa sai Fulani Saddik’a a gefe suna cigaba da tsare tsaren yarda za’a Gudanar da biki. Tauraruwa tana ganinsa ta saki murmushi ta ce “Dama tun d’azu nace Yayanku ya nemo min kai,(tana nufin d’anta) zancen Dinner ban ji kace komai ba, ko baka son nunawa abokan ka amaryar ne?” Fuskarsa ya sake ha’dewa sosai ya furta “Ba wata dinner da zan yi, a bari sanda na auri zab’in raina na yi dinnerr…” Tauraruwa tana murmushi ta ce “Shikkenan Ai hutaroro dama shima Baffanta ba son bidi’a yake a biki ba, sai ma da ya rok’emu kada mu yi wata bidi’a…” “Idan auren ya yi yu ba.” Murad ya furta a hankali…. “Me kace?” Maimartaba ya fa’da yana kallonsa. Murad kansa tsaye ya ce “Ni dai Bahbah a min afuwa bana son yarinyar nan kuma idan aka matsa na aureta zan iya ha’duwa da ciwon zuciya…” Maimartaba da dama ya Riga ya san zancen sai ya saki murmushi ya ce “Ai kuwa sai fatan Allah ya baka lafiya don aure kamar an d’aura shi idan ba so kake na yi fushi da kai ba wani irin zancen banza ne wannan, ana gobe d’aurin aure kace baka son matar sabida ka raina mutane….” Murad bai furta komai ba illa mik’ewa da ya yi yana jin wani irin jiri na d’ibarsa haka ya fice. Suka bi shi da kallo duk tausayinsa ya kama Fulani Saddik’a ji take kamar ta je ta gaya masa gaskiya. Maimartaba da Tauraruwa kuwa dariya suka saki gaba d’aya suna hango Murad a gobe idan ya je yaga wacece amaryar tasa? Wani irin farin ciki zai yi? Kashegari ba yarda abokansa ba su yi da shi ba ya tashi su tafi d’aurin aure amma ya ce shi sam ba zai je ba, don ya Riga ya shirya abinda zai fishsheshi.. yana kallo Suka dinga tafiya yana sakin tsaki. Aka d’aura aure cikin mutane da dama da suke ziyarta don d’aurin aure ne da shelarsa ta karad’e duniya. Ana gama d’aurin aure dangin ango suka je don tafiya da amarya kamar yarda al’adar gidan sarautar gabas take da zarar an d’aura aure za a isa da amarya cikin gidan sarki inda za’a cigaba da gudanar da abubuwan bikunkuna iri iri. Da al’adu iri daban daban. Kuka Najwa kawai take kamar wacce za’a cire wa kai, aka kaita wajen Ummanta don ta mata fa’da sai dai Umman albarka kawai take saka mata don duk wani fa’da da nasiha ta yiwa Najwan ta yi da baki ta yi a aikace don a cewarta ba a fafe gora ranar tafiya. Don haka kanta kawai ta dafa ta ce “Allah ya miki albarka a gidan aurenki Najwa ya kauda dukkan abin k’i ya saka abokin zamanki ne har a Aljanna.” Daga haka ta saki kanta. Najwa kuma ta fa’da kanta tana sakin kuka da k’yar aka sake b’anb’areta daga jikinta suka fita tana wani irin gunjin kuka. Sanda suka isa masarautar tuni an gyara sashen su an zuba kayan alfarma da alatu anan kuma zata kwana da mijinta washegari idan aka tabbatar ta kai budircinta sai a yi biki na ban mamaki a kuma karramata kwana uku za’a yi ana bikin. Ita ka’dai ce a tsakiyar gadon d’akin nasa tana bin ko ina da kallo iya tsaruwa d’akin ya yi ya kuma tafi da imaninta ta ji an turo k’ofa da k’arfin gaske da sauri ta ja mayafi ta rufe kanta jin k’amshin turarensa kuma su Nene sun k’i barinta ta sake mayar da b’atacciyar fuskarta. Da takun Isa ya Isa wajenta cikin wata irin murya da shi kansa bai san yana da ita ba ya ce “Ba dai sun kafe sai sun aura min ke ba, suna da right su aura min ke amma ni nake da right na zama da ke ko akasin haka don haka a yanzu ma na gama yankewa zuciyata ba zan zauna da ke ba don haka karb’i nan…” Ya fad’a yana janyo hannunta ya saka mata takardar daidai sanda mayafin fuskarta ya sauka ya yi tozali da fuskar da take hana shi sukuni fuskar da take saka shi tunani da rashin barci da sauri ya wara ido yana furta “You? Dama ke ce?” Ya fa’da yana k’ok’arin fusgar takardar da ta damk’e a hannunta tana masa kallon cikin ido……. “Ba zan zauna da kai ba Murad ka saki aurenka…….” JIKAR NASHE✍🏽🥳 (Labarin nan idan muka ce za mu yi shi gudu gudu ba zai muku da’di ba sai dai dole zan yanke wani sashen na labarin na baku shi yarda ya samu don duk kun fi son a gama kafin azimi, idan banda haka da sai nace ko zaku bari bayan sallah na k’arasa idan ba haka ba zan guntile labarin na sallameku a gobe.) ina jiran na ji ra’ayoyinku cigaba bayan sallah ko yinsa yarda ya sawwak’a a gama a gobe?) [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Ya sake kifa kansa a jikin Allon gadon yana kallon hannusa da tunano rubutun da ya yi da kansa na sakin a jikin takarda duk da saki guda ya mata amma yana ji a ransa kamar sun rabasu ne har abada don ya tabbata ko zai mutu Maimartaba ba zai dawo masa da matarsa ba don haka zuciyarsa take raya masa kamar sun rabu da muradin ransa har abada. So yake ya sake kiran Jaheed amma ya kasa don shi kansa Jaheed d’in kunyarsa yake ji. Gumi ne mai yawa yake tsatstsafa daga jikinsa, wani irin yanayi yake ji me wuyar kwatance idanunsa shi kansa bai san suna zubar da ruwan hawaye ba. Wace irin k’addara ce wannan mai girman gaske take bibiyar rayuwarsa? Runtse idanunsa ya yi a hankali yana furta sunan Allah a zuciyarsa don ya san shi ka’dai ne zai kawo masa sauk’i a Cikin dukkan lamarinsa. Jaheed kansa da bashi ya yi sakin ba yana jin fiye da yanayin da Murad yake ciki, wani ganganci ne ya kai Murad d’in da aikata irin wannan abu? Da wani ido zai dubi iyayensu ya yi musu bayanin tarin laifukansa ya yi tsaki yafi a k’irga kafin ya janyo wayarsa ya shiga kiran numberr Nene. Tana zaune akan sallayar ta dinga jin k’arar kiran wayar jikinta na rawa ta d’au wayar ganin Jaheed ne tsoronta d’aya faruwar wani mummunan lamari don kiran ya yi tsakar dare da yawa dole kana jin irin wannan kiran wayar na tsakiyar dare ka tabbatar da rashin wanzuwar lafiya. Muryarsa da ya ji tana rawa ka’dai ya isa ta gasgata hasashenta don haka ta runtse ido kawai itama tata muryar na rawa ta ce “Murad! Ya mutu ko?” Don haka kawai mummunan mafarkin da ta yi da shi yake bata baya cikin lafiya don mafarkin ya bayyana mata Murad d’in a wani irin yanayi da bata k’aunar ko a tunani ta sake arba da shi. “Gaya min Jaheed na rasa Murad ko?” Ya ja ajiyar zuciya yana jinjina girman tasirin Soyayyar Uwa ga yaranta soyayyace da babu ta biyunta. “Bai mutu ba, ba kuma abinda ya sameshi.” Ta ja ajiyar zuciya ba tare da ta gasgata abinda yace d’in ba sai don ba yarda zata yi da shi. Amma a jikinta ta ji ba lafiya ba. Shiru na tsawon minti guda kafin Jaheed ya runtse idonsa ya ce “Ki masa addu’a Nene tsautsayi yasa ya saki Najeee…” wani irin dum ta ji a idanunta bata san sanda ta saki wayar ba cikin tashin hankali ta furta Ya ilahal alameen! Wani lamari nake ji wannan mara dad’in ji. Kawai sai ji ta yi hawaye na zuba a kwarmin idanunta kuka sosai yake na zahiri da na ba’dini mai bayyana irin k’una da k’uncin da zuciyarta take ciki. Me yasa Murad zai aikata haka da wani idon yake son ta kalli Baffa a karo na biyu y’ay’anta na cikinta suna sakar masa y’ay’a? Anya sun masa adalci kuwa? Irin sakayyar da ya kamata su masa kenan? Mik’ewa kawai ta yi tsaye ta fara ha’da kayanta. Ba zata iya zama wannan zancen ya riski Baffa a idanunta ba, bata da jumirin iya jure ganin tashin hankalin da zai shiga. Wayar ta ta d’auka ta kira Jaheed murya a d’ashe alamar kukan da ta yi ya yi nisan zango ta ce “Saki nawa ya mata?” “Duka” ya furta kamar yarda Murad ‘din shima ya gaya masa. D’if ta kashe wayar tana jin wutar da take cin zuciyarta tana sake zafafa. Bata san irin horo da rashin mutuncin da zata yiwa Murad ba. Hukunci d’aya ta yanke a kuma goben zata aiwatar da komai In sha Allah. Ta ji zuciyarta ta aminta da shawarar da ta bawa kanta da kanta. Tsaf ta ha’da kayanta iya wanda ta san zata buk’ata don Asubar fari take son tafiya Masarautar Gabas. Ai kuwa ana idar da sallahr kafin a kai ga sake gark’ame gate d’in ta yi fit ta fice daga gidan cikin sauri da azama don bata son wani ya ganta balle ya tsayar da ita. Burinta isa masarautar. K’arfe 9:00 cif a cikin masarautar ta mata ta bar kayanta a cikin motar da ta yi shata ta fa’da cikin masarautar da sauri. Shiru ba wani hayaniya daga wajen masarautar bata yi wahalar gane sashen Murad ba don dama ta san shi. Ta isa kai tsaye ga sashen da ya sha kyau kamar ba a Nigeria ba. Ganin da fadawa suka mata kai tsaye suka shaidata don haka basu wani hanata shiga sashen ba ta shiga kanta tsaye cikin k’aramin parlourn da zai sadaka da d’akunan Barci. “Murad!” Ta shiga kiransa da k’arfin gaske. Wata irin fa’duwar gaba ce ta sameshi ya dafe k’irjinsa jin muryar Nene na kiran sunansa. Haka ya mik’e yana jin jiri ya fita parlourn daga shi sai singlet da wando three quater gashin kansa da yanayin idanunsa kawai zaka kalla ka san baya cikin walwala saboda yarda suka banbanta da yarda suka saba kasancewa a lokutan baya. Kallo d’aya Nene ta Masa ta hango tashin hankali a cikin idanunsa sai ta runtse nata idon ko ka’dan bata son tausayinsa ya rinjayi hukuncin da zata masa. Durk’ushewa ya yi a gabanta ya kama k’afafunta cikin hawaye ya hau furta “Pls Nene! Wallahi a rashin sani na saketa ban san ita bace….” Kafin ya kai k’arshe Nene ta wankeshi da mari cikin b’acin rai ta dinga zuba masa Mari bai yi ko motsiba ya dai runtse idanunsa har sai da ta gaji don kanta sannan ta Zube a kujera tana haki “Kanka ka cuta Murad ba Najee ba, na kuma godewa Allah da ka saketa kafin ka karb’e budurcinta zan yiwa Najee auren gata auren mutumin da zai sota don Allah ba don ita mummuna ko kyakykyawa bace. Kai kuma ka je ka auri hurul aini ma idan akwaisu a duniya ba zan maka baki ba amma ka rubuta ka ajiye har abada ba zaka samu macen da ta kai Najee a komai da komai ba. Zan d’auke Najee idan ta gama idda zan aurar da ita a inda aka san darajarta!” Daga haka ta mik’e cikin b’acin rai ta fice daga parlourn Murad idanu ya runtse kawai yana son kiranta sai dai ba shi da k’arfin da zai iya hakan. Zuciyarsa ta raunana irin raunin da ya bayyana har a kan fuskarsa da gangar jikinsa. Don haka kawai ya zube a saman carpet hawayen ma ya k’i zuwa kamar yarda yake so don haka kawai ya runtse idanunsa yana jin yarda hajijiya take d’ibansa duk da a kwance yake. Nene na fita sashen Tauraruwa ta nufa kanta tsaye basa cikin parlourn fadawa suka sanar mata suna cikin d’akin barcin Tauraruwar. Zama ta yi a parlourn tace su sanar da Tauraruwa zuwanta. Tauraruwa ta mik’e da sauri ta nufi parlourn Ido ta zubawa Nenen cikin mamakin ganinta da safiya haka. Su da suke shirin zuwa su d’aukota idan ta je wajen su Babi ta dawo. “Shigo Nene, daga ina haka?” Nene ta cire hannayenta daga tagumin da ta zuba kafin ta mik’e ta bi bayan Tauraruwa tana furta “Ina Najee take?” Gaban Tauraruwa ya fa’di jin ashe Nene ta sani ita da bata so zancen ya fita ba a samu a mayar masa da matarsa tunda saki guda ne! Maimartaba ma ta rok’eshi kada ya fitar da zancen zuwa a ga abinda Allah zai yi haka su Hajja da Yakumbo. Ta ciji leb’enta tana jin koma wa ya gayawa Nene bai kyauta mata ba, don bata son iyayen Najee su ji don ta san ba zasu ji da’di ba ace an sakar musu y’a a daren aure! “Ki shigo ciki mu yi magana.” Ta furta cikin mutuwar jiki. Nene ta bi bayanta suka shiga d’akin. Anan ta hango Najee ta yi wankanta tana sanye da doguwar Riga mai bala’in kyau y’ar morocco. Gashinta mai tsayin gaske da cika ta d’aureshi a tsakiyar kanta. Ta yi kyau ba d’an ka’dan ba. Tana ganin Nene ta mik’e da gudu ta fa’da jikinta tana dariya. Nene ta saki ajiyar zuciya ta rungumeta sosai tana jin soyayyar Najeen na sake bunk’asa a zuciyarta. Sai kawai ta ji hawaye na zuba mata sanin cewar har abada ba zasu zamo abu guda da Najeen ba, ba zata haifa mata jikoki kamar yarda ta dinga fata ba.. Ta ja hannun Najeen suka zauna a gefen gadon. Tauraruwa kallonsu take kawai tana murmushi soyayyar da suke wa junansu tana burge ta matuk’a da gaske. “Zan tafi da Najee bana buk’atar sake sauraran komai daga bakin ki ko na Murad ba abinda zan ce muku sai godiya, zan tafi da ita idan ta gama idda zan aurar da ita ga mutumin da ya san mutuncinta wanda zai rik’e min ita da yardar Allah mai ku’di Kuma da mulki tunda kuma da shi kuke tunk’aho..”Tauraruwa ta ware ido cikin mamakin furucinta ta ce “Ki tafi da ita ina kuma? Auren naki da nata fa? Ko kuwa daga saki d’aya sai ki haramtawa mutum matarsa?” “Ko Rabin saki ya mata na haramta masa Najee har abada wallahi! Ki gaya masa ko Najwa ta rasa Mijin aure ba zata koma gidansa ba har abada!!” D’if ji da ganin Murad da yake bakin k’ofa ya d’auke ya runtse idanunsa a hankali yana furta YA ILAHAL ALAMEENA! JIKAR NASHE CE🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Da sanyin jiki ta isa parlourn Umman tana zaune tana gyaran farcen k’afarta. Ta amsa da fara’a tana kallon Najman da ta shigo jikinta a sanyaye, ta zauna a kujerar kusa da Umman kanta a k’asa tana wasa da hannunta, Umman da ta fahimci abinda ya kawota sai ta saki ajiyar Zuciya ta ce “Allah ya sanya albarka a aurenki Najma, Ubangiji ya baku zaman lafiya ya ka’de dukkan fitina, shi aure dai hak’uri ne yake kai shi ga wani mataki mai girma idan kin jure, ki yi biyayya ga mijinki iya iyawarki sai soyayyarki ta dinga hauhawa a zuciyarsa rashin yi masa biyayyar yana rage k’ima da martabar soyayyarki. Kishiyarki kuwa ki zauna da ita lafiya da zuciya d’aya, Allah ya baku zaman lafiya da mijinki ya ka’de dukkan fitina ya kuma rabaki da cikin jikinki lafiya. Tashi ki je Allah yasa gidan zaman ki ne. Najma ta amsa a zuciyarta tana mik’ewa a hankali girma da mutuncin Umman yana sake k’arfi a zuciyarta da gaske Umma mace ce managarciya wacce duk wanda ya sameta a matsayin Uwa ya ji dad’insa duniya da lahira bata damu da duniya balle abinda yake cikinta shi yasa take zaune zuciyatta fresh ba abinda ke damunta. Umman ta kama hannunta ta rakata har wajen motar Baffan ta sakata a ciki tana sake jaddada mata mahimmancin addu’a kafin ta kai ga ta shiga cikin gidanta. Baffa da’di ya ji har a ransa yana sake k’aunar Umman a zuciyarsa data zamo mace mai matuk’ar sanyin hali da sauk’in zuciya. Irin matar da maza suke kambamata a ko ina wajen abokansu. Ya ja motar suka nufi gidan Jaheed shima yana sake jaddada mata ta yi hak’uri ta kuma jajirce da bautar ubangiji shine tsani da mutum yake bi ya taka matakin nasara a aurensa. Suna isa Jaheed ya fito cikin girmamawa da ganin girma da dattijantakar Baffannasu mutum ne da ya amsa duk wani suna da nagartaccen mutum da duniya ta yarda da nagartarsa yake amsawa. Baffa ya amsa gaisuwar da Jaheed yake masa cikin fara’a ya kama Jaheed d’in suka mik’e tsaye “Ba irin wannan gaisuwar a musulunci Mujaheedu, musabaha shi manzon Allah ya umarcemu da yi da yiwa juna sallama duk da al’adance bahaushe yana ganin wannan itace gaisuwa mafi dacewa sai dai ba hakan take a musulunci ba duk wata gaisuwa ta bi bayan Assalamu Alaikum da kuma kama hannun juna. Don haka ka kiyaye ka ji ko?” Jaheed ya d’aga kai yana kallon Najma k’asa k’asa da yake zabga wani irin k’amshin turare mai masifar fusgar hankali. “Mu je ciki ka ha’da min kan matan naka akwai nasihar da zan musu wanda in dai sun bi to sun rabauta daga afka wa turbar shai’dan idan kuwa ba su bi za su yi kaico da nadama tun a duniya.” Jaheed ya shige gaba suka isa Babban parlourn inda Khaireey take tana zaune tana cika tana batsewa gaba d’aya ranta a dagule yake da dawowar Najma cikin gidan.. da k’yar ta amsa sallamar su Baffan ta kuma gaisheshi da k’yar bayan ganin tabbas ya cancanta ta yi gaisuwar banda haka jan bakinta zata yi ta tsuke. Baffa yana kallo Jaheed ya wurga mata harara murmushi kawai ya saki a ransa ya fara tunanin lallai akwai aiki a gaban Jaheed matuk’ar yace wannan abinda Khaireey ta yi har zai zama abin damuwa. “UMMUL KHAIREEY!” Baffa ya kira sunanta cikin kambama murya. Ta d’ago a hankali tana kallonsa ha’de da amsawa da na’am can k’asan mak’oshinta. “Na zo nan ne a matsayin Uba a waje dukkan ku ki k’addara naki mahaifin ne a zaune kin tabbatar dai mahaifi ba zai cutar da y’arsa ta cikinsa ba ko?” Khaireey ta d’aga kai. “To ki bani wannan position d’in nasa, Ita kishiya ba komai ba ce idan mutum ya mayar da ita bakomai d’in ba ya sanyata a mahallin da ya dace. Idan kuwa ka saka ta a matsayin komai d’in sai ta zame maka komai d’in har ta zame maka wata masifa a rayuwa. A duk yarda kika d’au kishiya a haka Allah yake baki iko da nasara a kanta ko ita ya bata nasara a kan ki. Bance babu asiri ba amma nan yarda yana yin tasirin da k’addarar Ubangiji take yi ba. Duk abinda ya samu bawa daga Allah yake matuk’ar mutum ya yi imani da haka to imaninsa ya cika hundred percent. A duk sanda kuwa mutum ya raunata haka a ransa to tabbas imaninsa ya ragu. Ki d’auki kishiya matsayin y’ar uwa wacce zata tayaki da buk’atun mijinki idan ta kama har da ta y’ay’anki sai ki ga ta zamar miki a matsayin y’ar uwa matuk’ar baki k’ullaceta da sharri ba ba ta yarda za’a yi cutar da zata miki ta yi tasiri a kan ki idan ba a yi hankali ba ma sai cutar ta ta ta dawo kan ta ke Allah ya kareki ba don komai ba sai don taki zuciyar mai kyau ce ba kya nufarta da sharri. Ga duk macen da ta saka wannan a ranta zata samu sauk’in kishi, ki rik’e cewa Allah ne ya halatta masa ya auri mace sama da d’aya ba son ransa ba, idan kika hana kin haramta abinda Allah ya halatta kenan menene makomarki? Ku rik’a tunanin yawan matan da suke zaune a duniya waye zai aure su? Shin zaki so k’anwarki ta rasa Mijin aure ko y’ar ki? Idan kuma aka tashi bikin k’anwar ki zata auri mai mata sai kuma ki zamo sahun gaba wajen ingiza mai kantu ruwa, abinda ka sowa kanka ka sowa d’an uwanka shine cikar imanin mutum! Don Allah ku zamo masu kwantarwa da mijinku hankali ba masu tayar masa ba dukkanku y’ay’ana ne kuma idan kika bijirewa umarni na sai na saka d’ana ya sake ku, Allah ya baku zaman lafiya ya kawar da dukkan fitina da munafukai a tsakaninku.” Suka amsa gaba d’aya. Khaireey ta saki ajiyar zuciya sai ta ji zuciyar ta wasai duk wani abu da ya dunk’ule mata a k’irji yana narkewa a hankali ta shaida da nagartar Baffa a yau ta sake tabbatarwa da Baffa da Umma dattijan ne na gaske. “Allah ya muku albarka!” Baffa ya fa’da yana mik’ewa suka amsa cikin fara’a da jin da’din addu’ar sannan suma suka mik’e suka raka shi har mota. Najma na share k’walla sai ta ji kamar yau ne aka kaita gidan Miji take turjiya bata so sai ga shi a yanzu ba abinda take muradi sama da gidan Mijinta ba kuma wanda take so sama da Jaheed data tsana a baya. K’ok’arin shiga sashenta take kawai ta ji hannun Jaheed a cikin tafin hannunta ya janyota da sauri ta baya. Har suna ha’da jiki tana juyowa cikin wata irin murya da bata tabbatar tasa ba ce ya ce “Mu je can parlourn tukun.” Ya fa’da yana kokawa da numfashin da yake k’ok’arin sar’ke masa sabida tasirin turarenta da da’din da ya masa a rai. Lumshe idonta ta yi ka’dan tana ha’diye yawun da ya taru a harshenta ta yi k’ok’arin zame hannunta sai dai bai bata damar hakan ba ya kuma d’auke kai kamar ba shi ya rik’e hannun ba, cikin murya mara amo sosai ya ce “Don’t try it again….” Shiru ta yi ta bar masa hannun suka nufi sashensa. Don bai bata damar komawa nata sashen ba ji yake kamar wani magana’disu na jansa zuwa jikinta. Khaireey kuwa tuni ta koma nata sashen tana k’ok’arin yak’i da kishin da yake son turnik’e zuciyatta ta hanyar tasbihi a zuciyarta da jan Hasbunallah lahaula wala k’uwwata. Suna shiga sashen nasa ya kai mata wata kyakykyawar runguma ta baya, Allah ne ka’dai ya san yarda ya iya daure zuciyarsa zuwa wannan lokacin bai fasa sirrin da yake ransa na tsananin son matar sa da tausayinta ba. Bai bata sukuni ko dama ba ko ka’dan balle ya marabceta da abubuwan mak’ulashen da ya siyo mata ba, burinsa ya isa can birnin da yake mafarki. Bata hana shi ba, don itama ta yi kewarsa matuk’a da gaske don haka komai ma da ya faru ya faru ne cikin shauk’i da son juna da kuma tsananin buk’atuwa da zumu’di ga juna. Jaheed kam ya nuna mata wata irin soyayya mai tsayawa a rai da ya kasa barinta har sai da ya furta a saman lab’b’ansa “I love you with all my heart Baby kada ki sake nisa da ni pls!” Murmushi ta saki tana furta In sha Allah! Ta fa’da tana cije bakinta saboda wani irin murd’a wa da mararrta ta yi tun tana daurewa har sai da Jaheed ya gane ya d’ago ta da sauri yana kallon k’wayar idonta ya ce “Gaya min menene?” Cikin wata irin murya da ta nuna galabaita ta ce “Ciwo My J… mutuwa zan yi na sani ba zan yi doguwar rayuwa da kai ba duk da tsananin son da nake maka……! Sak Jaheed ya yi wata tarin k’walla na shirin zuba daga k’wayar idonsa cikin muryar tsorata ya ce “Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar!” K’arar da ta yi ya ankarar da shi ya kamata ya kaita asibiti sai dai ko kafin ya yi wani yunk’uri sai gani ya yi ta cije bakinta ta furta “Jaheed da gaske mutuwa zan yi, pls ka kira min Baffa Umma da Mahmeey! Ku yi hak’uri mutuwa aka mana sai yanzu da na dawo na samu damar typing d’in saboda bana son na b’ata muku rai. Sakamakon Aljanna gareku In sha Allah. A kuma sanya iyayenmu a addu’a pls 🙏😭 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Jikinsa ne ya fara rawa bai San sanda ya tura k’ofar d’akin ya shiga Kansa tsaye ba, bai damu da irin kallon da suke masa ba, samun kansa ya yi kawai da durk’ushewa a gabansu idanunsa cikin na Najwa da take zaune tana danna wayarta bata ko d’ago ta kalleshi ba. Tauraruwa idanu ta zuba masa tana hango yarda ya nuna galabaitar da zuciyarsa take ciki, koma me ya faru ta tabbata a yanzu yanayin da zuciyarsa take ciki abu ne mai girman gaske ba mamaki ma bata bugu yarda ake so. “Ku yi hak’uri Nene kada ku raba ni da ita ba saki uku na mata ba ina da ikon na mayar da ma….” Kallon da Nene ta masa ne ya saka shi jan bakinsa ya tsuke jiki da zuciyarsa ya ji suna kakkarwa ba tare da ya shirya hakan ba. Kallo ne mai nuni da abubuwa da dama, kallo ne da yake bayyana takaicinta da jin haushinta game da k’uncin da zuciyarta take ciki. Ya sani ya raunata zuciyarta ya kuma kassara wani sashe na farin cikinta zuwa bak’in ciki mara misaltuwa duk da bata fito ta gaya masa ba ya san gefe guda na zuciyarta yana takaicin zamowarsa jininta. Da k’yar ta ha’diye kakkauran yawun da ya tsaya mata a mak’oshi ta lumshe idonta kawai duk da k’ok’arin da take na yak’i da k’wallar idanunta hakan bai hanasu zuba sharrrr akan k’uncinta ba. Hakan yasa zuk’atan duka d’aki suka yi sanyi tausayinta ya shiga zuciyarsu musamman Najee da take jin kamar nata idanun suma suna daf da zubar da hawaye. A rayuwarta tana son Nene bata kuma k’aunar abu komai k’ank’antarsa ya b’ata mata rai. Sai ta sake jin haushin Murad ya sake rub’anya a zuciyarta ta zuba masa ido tana hak’ilo da kawar da tata k’wallar don sam bata son yaga gazawarta balle yace ta damu da rabuwar da suka yi. “Ba zata komawa aurenka ba Murad! Ko da kai ne ya rage Autan maza a duniya…..” Nenen ta fa’da idanunta a runtse cikin wata irin Amon murya mai kaurin gaske. K’iris zuciyar Murad ta rage ta buga… bai dawo daga waccar razanar ba ta sake jefa shi a wata “koda wasa kada ka sake kace ka mayar da ita idan ba haka ba ba zan tab’a yafe maka ba har abada!” Wani irin shiru ne ya ratsa d’akin shirun da yake bayyana tashin hankalin da girgizar da zuciyoyin Tauraruwa da Murad suke ciki. Jikinsa a salub’e ya mik’e yana jin jiri na shirin kada shi ya dafa bango ya fice daga d’akin ya zama dole ya bar k’asar nan barin da yake tunanin na har abada…. Don ba zai jure ganin ranar da za’a ce Najwa zata auri wani ba shi ba.. Yana fita Tauraruwa ta dubi Nene cikin b’acin rai ta ce “Hukuncin da kika yanke sai nake ganin ya yi girma, kada ki yi abinda zaki zo ki rasa ranki kin san dai k’addarar Ubangiji girma gareta Kuma wanda ya hana aure idan Allah ya nufa sai anyi sai kiga anzo an yi babu shi. Laifinsa bai kai a masa irin wannan hukuncin ba, mune da laifi mu da muka k’i bayyana masa gaskiya muna tunanin wasa yake a kalaminsa sai ga shi yazo ya zartar da gaske, don haka ki janye kalamanki a mayar masa da matarsa tunda ya gane kuskurensa….” Wani kallo Nene ta mata sai da ya sata yin shiru bata shirya ba.. “Ba zata koma ba hasalima da ni da ita barin garin za mu yi kuma ina rok’onki kada ki sanar da kowa mutuwar aurennan bayan ku da kuka sani bana son maganar ta je gun Baffanta har sai na samar mata nagartaccen Miji da zai yi alfahari da shi In sha Allah. Idan kuma kin k’i ina tabbatar miki nima zan barranta kai na da auren Mai martaba!” Shiru Tauraruwa ta yi don ta lura a wannan k’adamin zuciyar Nene ba zata ji lallashi ba ta yi k’ok’on b’acin rai… “Ba zan fa’da ba, amma nima ki min alk’awarin ba zaki ko ina ba daga masarautar nan zaki zo ki tare a gidanki idan yaso Najwa ta zauna a wajenki har zuwa sanda zaki samar mata mijin.” Nene bata kawo komai a ranta ba ta ce “shikkenan zan iya yarda da hakan, bisa alk’awarin koda wasa kada Murad yazo sashena har sai bayan Najwa ta gama idda na samar mata Miji.” D’aga kai Tauraruwa ta yi alamar amsawa daga nan Nene ta mik’e tana d’aukan jakanta “Zan tafi da ita zan ajiyeta gidan k’awata don ba zan zauna anan ba har sai Baffa ya kawo ni da kansa, ba kuma zan bar Najwa anan ba don ban yarda da ke ba..” Ido Tauraruwa ta zuba mata fuskarta na nuna rashin jin da’din samun cikar burinta me yasa duk ta inda ta biyo sai Nene ta toshe mata hanya kamar mai ganin zuciyar mutane. “Tashi Najee mu tafi.” Nene ta fa’da tana kallon Najeen. Da sauri Najee ta mik’e ta zura doguwar rigar abayarta ta bi bayan Nene bayan ta ja k’aramar trollynta mai d’auke da kayanta kala biyar a ciki wanda Tauraruwa da kanta yau ta je sashenta ta d’auko mata. Tauraruwa na kallonsu suka fice ta bi bayansu da sauri don saka Drivernta ya kai su. Ta window Murad ya hango fitowarsu ya runtse idanunsa yana jin kamar ya rabu da wani sashe na jikinsa ne, da bai aikata hakan ba ya tabbatar da yanzu suna nan manne da juna suna shan amarcinsu. Tauraruwa sakin ajiyar zuciya ta yi kafin ta juya ta nufi sashen mai martaba don sanar da shi halin da ake ciki. Shiru sashen sai Fulani Saddik’a da take ta shirya dinning dama fadawa sun saba a irin wannan lokacin ba sa zama kusa da Mai martaba suna barinsa ya sake ne da iyalinsa ya samu kulawa daga garesu. Ta bi Fulanin da kallo tana sakin murmushi kafin su gaisa ta ce mata “Sai kuma kika ji shirmen da d’anki ya yi..” Saddik’a ta saki ajiyar zuciya takaicin da yake cin ranta ne yasa ko maganar bata son a mata. “Allah ya kyauta ni ban san ma me zance ba tun d’azu nake son kiransa sai dai zuciyata tana gaya min na bari ta huce tukun don zan iya dukansa.” Fulanin ta fa’da kanta tsaye cikin muryar da ke bayyana gaskiyar abidna ke ranta kenan. “Dukan ne ya kama ce shi daga gareki don zai fi jin zafin dukan daga wajenki fiye da kowa Amma idan kin tashi dukan ki kirani na tayaki. Yanzu Nene tazo ta ‘d’auke y’arta kuma taja rantsuwa akan cewa har abada ba shi ba auren y’arta koda shine autan maza…” Saddik’a ta waro ido ta ce “Ya aka yi kika k’yaleta ta furta hakan cikin fushi Hasbunallah yanzu menene abin yi?” Tauraruwa tace “Hak’uri mana ba shi ya janyowa kansa ba sai yaje ya nemo mata da kansa ya aura zab’in ransa ba namu ba…” gyaran muryar Maimartaba ne ya saka su yin shiru daga zancen da suke. Ya shigo cikin rigar jallabiya mara nauyi sai zabga k’amshin turarensa na Usuli yake. Fuskarsa ba walwala ko ka’dan sai dai a washe take sosai ya zauna a saman babban kilishin da aka shimfi’da masa don cin abinci. Ba da’din bakina nake ji ba Fulani, kamar yarda zuciyata bata min da’di ko ka’dan ba ni tataccen ruwan inibi kawai na sha, ki kira min d’anki kuma yanzun nan…” Da k’yar Fulani ta nutsu saboda bugun da zuciyarta take bata san wani hukunci kuma Mai martaba zai yiwa Murad ba, tana fata koma menene ya zama mai sauk’i kada abin ya masa yawa. Ruwan inibin ta zuba masa a babban tumbler mai masifar kyau ta mik’a mas a cike da girmamawa sannan ta mik’e don gaywa hadiman su kira Murad sak’o daga mai martaba. Tauraruwa kanta a lokacin tsoron idanun sarki suke saboda yarda suka birkice lokaci guda da alama bai samu isashshshen barci ba.. “A masa afuwa ranka ya da’de…” wani kallo ya zuba mata yana ajiye cup d’in inibin. Tauraruwa ta yi k’asa da kanta tana jin tashin hankali yana ziyartarta zata iya cewa bata tab’a ganin maimartaba a kwatankwacin hali irin wannan ba… shiru suka zauna har zuwa sanda Fulani Saddik’a ta shigo da Murad suka k’arasa gaban Mai martaba Murad yana jin kamar ya shige cikin k’asa kada MaiMartaba ya samu damar yi masa zancen can. Idanu Mai martaban ya zuba masa ba tsawon lokaci kafin ya yi k’wafa ya ce “Mun baka kwana uku kacal ka tsayar da matar aure…. Abu na gaba na cire ka daga matsayin Yareema Magaji na na bawa Jaheed bana son a wannan karan ka sab’a umarni na ko ka’dan kwana uku kacal na baka kazo min da matar da kake so tunda mu ba mu iya zab’i ba…” Murad ya d’aga leb’e zai yi magana Mai martaba ya d’aga masa hannu “Bana son jin komai daga bakinka Kai ne babba a haka kake son k’annenka su yi koyi da kai, ba zan maka baki ba amma har abada ba zaka samu Matar da ta kai matar da ka saki ba…• Wani irin sarawa kan Murad ya yi ya mik’e jiki a sanyaye don bai hango sassauci a idanun mai martaba ba. Fulani Saddik’a ta mik’e zata bi shi mai martaba ya zuba mata wani kallon da ya sata zama ba shiri. Tana jin kamar ta zunduma ihu gani take hukuncin ya yi tsauri da yawa tasirin sa kuma zai iya kassara zuciyar Murad. “Hukuncin da zan masa na k’arshe kenan, idan kuma wani yasa ya bijirewa umarnina kai tsaye ya barranta kansa da ni.” Shiru suka yi kowa zuciayrsa da abinda yake sak’awa….. __________ Tsaf ta shirya duk da turtsetsen cikin da yake jikinta bai hanata fesa kwalliya ba da adon mai ban k’aye murnarta da zakwad’in da zuciyarta take ciki suka kasa b’uya a fuskarta sai zuba fara’a take tana jin yau rana ce mai girma da tarihinta ba zai gobe a zuciyarta ba. Ranar da zata koma gidan Jaheed mutumin da take wa wani irin so da kai tsaye ba zata taskance shi a mizaninta ba, abu guda ta sani son da take masa ya huda duk wani bigire na zuciyarta. Najma kenan da take tsaye tana sake fesa turare a jikinta duk da gabbasar da kayan ta sha bai hanata sake saka Humra ba. Mahmeey kallonta kawai take tana murmushi duk wannan cunkushashshiyar fuskar ta Najma yau ta washe ta zama fuska mai cike da murmushi da tarin annashuwa. “Ki nutsu dai Najma ki ja ajinki kada ki yi abinda zai rainaki ni da don Baffa ya k’i ne da bari aka yi sai kin haihu…” “A’a Mahmeey gwara na koma idan kuma na mutu fa bana gidansa gwara ko mutuwar zan yi ya kasance ina tare da shi a kusa da shi….” Mahmeey ta d’alle bakinta tana furta “Sau nawa Zan gaya miki bana son zancen mutuwar nan?” Najma ta yi murmushi kawai ta d’an rungumeta ta ce “Ki min addu’a Mahmeey Allah ya raba ni da cikin nan lafiya yasa ni zan raineshi da kai na ba wata ba… Duk da sai na dinga ji a jikina kamar mutuwa zan yi..” Mahmeey ta d’an rungumeta tana basar da zancen ta ce “Maza ki je ki ywa Umma sallama Baffa na jiranki zai kai ki da kansa har gidan yace don yana son ha’daku da abokiyar zamanki ya muku nasiha…” Ta ja ajiyar zuciya tana tunano idanun Khaireey da take mata wani wulakantaccen kallo ranar da ta ji Mijinta zai mayar da ita….. ko wane irin zama za su yi? Shin ko zata yi tsawon rayuwar da zasu zauna zaman kishin? JIKAR NASHE🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Hankalinsa tashe yake kallon yarda idanunta suke jikirtawa zuwa launin da yake nuna jigata da d’imauta da gaske ko wane irin ciwo ne yake damunta yana da zafin gaske… gumi take tsatstsafowa daga dukkan sassan jikinta don haka hankalinsa a tashe ya d’au waya ya shiga latsawa da bincikar family doctor d’in su na gidan Baffa. Sai dai kafin Doctorn ya d’ago ya hango yarda Najma ta sassank’ame alamar da gaske ta mutu ko kuma ta yi doguwar suma. Bai san sanda ya yi wulli da wayar ba ya rarumi rigarta ya zura mata yana aikin kiran sunanta sai dai ba alamun ta ji balle ta amsa. Bai san sanda ya wuntsila daga gadon ya zura tasa rigar ba duk ya ru’de ya gigice fatansa da addu’arsa Allah yasa Najma dogon suma ta yi ba mutuwa ba. Cak ya d’auketa bai yi la’akari da girman cikinta ba balle ya ji nauyinta burinsa ka’dai isa asibiti don samun ceto lafiyarta da ta abinda yake cikinta. A bayan mota ya saka ta yana cigaba da bubbuga bayan ta don kiran sunanta amma bai ga alamun motsi ba ko ta kan Khaireey bai bi ba ya ja Motar a sukwane ya fice daga harabar gidan bayan mai gadi ya bu’de masa gate…… Ko kafin su isa asibitin ya kira Umma ya gaya mata itama a ru’de ta sanar da Baffa, Baffa k’irjinsa ya nufa sosai haka kawai sai ya ji tsoro da firgita ba bin sassan jikinsa yana tsoron rasa Najma a lokacin da ta zama Saliha yarinya ta gari kamar yarda burinsa yake a koda yaushe. Ba su gayawa Mahmeey ba suka mik’e da sauri don nufar asibitin da Jaheed ya ce suke. Kafin zuwansu asibitin tuni Family Doctornsu ya saka an shirya musu d’aki da duk abinda zasu buk’ata, don haka suna isa aka zo da wheelchair don isa da ita kafin su shiga d’akin har likitan ya fito daga office d’insa a k’agauce ya fa’da d’akin ya turo k’ofar da saurin gaske… wanda bugun k’ofar ya yi daidai da bugawar zuciyar Jaheed ya fara jin tsoron sa na sake hauhawa kawai sai ya samu kansa da runtse idonsa da mugun k’arfi yana jan hasbunallah a cikin zuciyarsa…. _____________ A bakin k’ofar gidan ta tsaya kafin ta kalli Najwa da itama take Tsayen tana jiran jin umarni na biyu da Nene zata bata. Nan dai gidan Kakarta ce Hajja wacce ta kasance k’anwa ga Mahaifiyar Umma don haka ba wani tsoro ko shakka da zata ji na zamanta anan…. Nene ta ce “Mu shiga Najee anan na fi buk’atar zamanki bana son kuma ko mutanen gidan ki gaya musu dalilin kasancewarki anan d’in ina son ya zama sirrri daga ni sai Ke zan zo na d’auke ki bayan kwana goma da zarar na tare a fada..” Najee ta jinjina kai kafin su saka kansu cikin Babban zauren gidan a share yake tas ko abinka ne ya fa’di zaka iya durk’usawa ka d’auka ka ci kayanka. Najee ta cigaba da jan k’aramin trolley d’inta zuwa cikin gidan. Suna sallama a tare da Nenen. Sai ga d’aya daga cikin Surikan Hajjan ta fito tana amsa sallamarsu. Ganin Najwa da Nene a tsaye sai ta saki baki tana kallonsu don dai idan bata manta ba shekaranjiya suka dawo daga bikin Najeen to me ya kawo su? Fahimtar hakan da Nene ta yi ya saka ta sakin murmushi ta ce “Iyami kin gan mu rana tsaka ko?” Iyami ta d’aga kai don da gaske tana neman k’arin bayanin. “Mu shiga ciki tukunna kin san abinka da gidan sarauta tafiya ce ta kama Mijin to shine ya rok’i alfarmar na kawota nan na ajiye kada a fahimci tana nan d’in Kuma don an rasa visa dinta, idan kuma aka fahimci baya nan za’a iya cutar masa da mata kin ga dalilin zuwan mu Kenan Ina Hajja?” Iyami ta saki ajiyar zuciya kuma ba wani kokwanto zuciyarta ta amince da abinda Nenen ta ce don bata ga dalilin da zai saka Nenen ta mata k’arya ba. “Lamarin gidan sarauta kam abin tsoron ne musamman ga k’aramar yarinya kamar Najee gaskiya ya yi dabara Allah ya dawo da shi lafiya Hajja na ciki ku k’arasa.” Nene ta saki ajiyar zuciya tana jin da’di da Iyami bata gano k’aryarta ba, suka shiga d’akin Hajja wanda ya kasance parlour ne Babban gaske mai d’auke da d’akunan kwana uku da kitchen da toilet a ciki. Hajja ta amsa sallamar ta su idanunta akan Najee ta ce “Wa nake gani haka kamar amaryar da aka wa aure a satin nan?” Nene ta zauna a gefenta suka gaisa sosai da Hajjan da yake akwai Sabo mai girma a tsakaninsu, nan itama ta sanar da ita abinda ta gayawa Iyamin. Hajja ma ba wani ja in ja ta amince da abinda Nenen ta sanar mata. “Yaro kam ya yi farar dabara gidan sarauta lamarin su sai addu’a Allah ya dawo da shi lafiya Ai sai ta zo ta share d’aki tayi zamanta na samu me yi min tausa…” Nene ta yi dariya sosai dariyar da ta bayyana zallar murnar da zuciyarta take ciki na yarda da abinda ta ce wa Hajja. Nan ta yi alwala ta yi sallar da ake bin ta don dole ta zauna aka yi La’asar kafin ta musu sallama ta barwa Najee ku’di masu yawa ko Zata samu abinda take son siya. Sannan ta tafi tana sake jaddada kwanaki goma kawai Zata yi da yardar Allah zata dawo ta d’auketa. Najee bata ji komai ba ta ce “Allah ya dawo da ke lafiya My Nene..” Sai 9:00 na dare Nene ta koma gidan Baffa a lokacin kuma ta tarar da rashin lafiyar Najma har ma mutanen gidan duk sun tafi asibiti hankalinta tashe itama ta juya don nufar asibitin da suka je don ba bak’onta bane ta san asibitin Nahdi farin sani…. Napep na sauketa ta isa cikin asibitin bata sha wahalar ganinsu ba, Jaheed yana ganinta ya mik’e da sauri ya nufi wajenta. Idanunsa Nene kawai ta kalla ta tabbatar yana cikin matsananciyar fargaba da tashin hankali, sai ta ji tausayinsa mai girma ya fisgi zuciyarta ta d’an lumshe ido tana jan addu’a a ranta kafin ta ware idon a kansa ta ce “Addu’a itace maganin dukkan wata masifa me ya sameta Jaheed?” Tattausan kalaminta yasa ya ji ya samu nutsuwa ka’dan a ransa ya lumshe nasa idanun sai ga hawayen da yake ta dako yana b’oyesu a kwarmin idonsa sun samu damar sauka suna zarya akan k’uncinsa bai san sanda ya damk’i hannunta ba ya kifa kansa a tafin hannun kafin ya fara magana cikin wani irin sauti mara amo ya ce “Ki mata addu’a Nene bana son na rasa ta ina son ta Nene…” Nene ta saki ajiyar zuciya sai ta ji itama gabanta ya wani irin bugawa da k’arfin gaske irin bugun da sam bata son ya yi don idan ta yi irin hakan ta san akwai wani abu mai girma da zai faru… Innalillahi ta furta can k’asan ranta kafin ta furta “Khairan In sha Allah Jaheed ba zamu rasa Najma ba alfarmar Manzo s.a.w….” Jaheed ya amsa da ameen yana furta Allah yasa Nene… ta d’an janye hannunta ganin Umma ta nufo su tana kallon Nenen da sam bata son su ha’da ido kamar akwai wani abu da take son b’oye mata. Umma ta janye hasashenta sannan ta furta “Nene yau ina kika shige ne? Tun safe ban gan ki ba…” Kafin Nenen ta amsa fitowar likitan da yanayin yarda ya buga k’ofar da k’arfi yasa numfashinsu ya tsaya cak na wuncin gadi zuciyarsu ta buga da k’arfin gaske a tare suka fara jan addu’oin da duk suka zo bakinsu don fuskar likitan kawai zaka kalla ka tabbatar da abinda yake son ya furta cikin zuciyarsa ba sai ya furta ba sun san sun rasa Najma! JIKAR NASHE🥳🤗 A cigaba da hak’uri da ni kun san nace mutuwa aka mana yanzu ma ina dawowa na hau typing Uba ne a wajena ya mutu ku saka shi a addu’oinku shi da duk musulmi da Suka riga mu gidan gaskiya [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: D’an cije leb’ensa likitan ya yi, lokaci guda kuma ya furzar da huci daga baki da hancinsa ya d’an juya gefen damansa yana kallon Baffa da ya yi zugum yana jiran bayani daga bakin likitan “Allah ya amshi ran Najma!” Shine abinda Baffa yake jiran ji kawai daga wajen likitan. “Baffa zan iya magana da kai?” Doctorn ya fa’da yana kallon Baffa da alamun rashin nutsuwa ya bayyana a cikin idanunsa.. Gaban Baffa ya fa’di kamar yarda duk na mutanen da suke wajen ya fa’di jikinsa a sanyaye ya ha’diye yawun da ya tara a bakinsa. Jaheed kuwa lunshe idanunsa kawai ya yi yana zubar da zazzafar k’wallar da yake jin zafinta da d’acinta a mak’ogoronsa. Baffa ya d’aga kai yana yak’i da jirin da yake son fara d’aukarsa. Doctor ya d’aga kai yana juyawa zuwa Babban Office d’insu. “Ku taho da Jaheed d’in Baffa…” Baffa ya kama hannun Jaheed da ya zama kamar wani mara ji mara gani kawai bin Baffa yake duk inda ya saka k’afarsa shima hulla tasa ya ke. Suka isa office d’in Doctorn da yake fitar da wani sassanyan k’amshi da sanyin ac mai k’arfin gaske. “Ku zauna” ya ce da su ganin ba su da niyyar zaman. Da k’yar suka zauna d’in Jaheed yana ji a ransa kamar ya hau likitan da duka. “Fa’da mana kawai Doctor Ba Najma ba kuma abinda yake cikinta.” Girgiza kai Doctor ya yi “Ba haka ba ne, tana da ranta amma tana cikin wani yanayi da ya kamata a yi gaggawar ceto lafiyarta don haka muke buk’atar amincewarku a mata aiki don ceto rayuwarta da ta yara biyu da suke cikinta….” Ya fa’da yana turawa Jaheed dogon file d’in da yake gabansa na Najma tunda anan take antenatal duk wani record nata suna da shi. Da sauri Jaheed ya saka hannu a aljihun da ya ciro biron ya rattaba hannu yana sakin ajiyar zuciya. Doctor ya ba shi takardar da zai je reception’s ya biya duk wani abu da ake buk’ata ya mik’e da sauri ya fita shima Doctorn fita ya yi da saurin da basu da lokacin b’ata lokaci. Suka dawo nan wajen su Umma suka sanar musu nan suka zauna zaman jigum suna jiran a fito da addu’oin samun nasara a bakunansu. Ba b’ata lokaci aka mata theatre, aka ciro kyawawan yara maza biyu masu kama da iyayensu sak. Likitan ya saki ajiyar zuciya yana kallon Najma da take idonta a rufe don allurar barci suka mata. Ya d’an duba bugun zuciyarta ya tabbatar da lafiya sai ya saki ajiyar zuciya. Aka gyara yaran tas kafin a nad’e su a showel aka fito da su. Sanda aka iso da su Jaheed suman zaune ne kawai bai yi ba, so yake kawai ya ga Maman yaran hankalinsa bai kwanta ba sai da Doctor ya tabbatar masa tana nan lafiya amma tana buk’atar hutu sosai. Ya saki ajiyar zuciyar da duk mutanen wajen sai da suka ji. Kowa ya fara masa dariya Baffa ya mik’a masa d’aya da nurses suka tabbatar masa shine Hassan yace “Amshi takwarana Mujaheedu amshi Ibrahimul Khaleel.” Jaheed ya saki murmushi cikin jin kunyar da ta bayyana akan idanunsa ya saka hannu ya amshi yaron da yake tsananin kama da shi. Bakinsa ya d’ora a kunnensa a take ya masa kiran sallah ya kuma jaddada sunansa na Khalilullahi kamar yarda Baffa ya saka masa. Ya mayar da shi hannun Baffa yana fa’din “Baffa ga takwaran naka.” Sannan ya amshi Usaini a wajen Umma shima a take ya saka masa Muhammad Mukhatar sunan Mai martaba sannan ya mik’awa Umma shi ya na furta “Ga Magajin mai garin Gabas.” Hankalinsa ya koma kan k’ofar da ake fito da Najma barci yake amma hannunta d’auke da k’arin ruwa. Da sauri ya k’arasa Wajen yana kiran sunanta sai dai bata san ma yana yi ba. Aka zarce da ita d’akin hutu daidai lokacin da ake kiran farko na Asuba. A gefen gadon ya zauna don an sanar masa baa son hayaniya su Kuma su Umma suna wani d’aki da yaran tuni kuma suka fara sanar da mutane ta waya duk wanda aka gayawa sai Ya hau murna. Jaheed da kansa ya kira Murad lokacin yana zaune a gefen sallaya ya idar da nafila hannunsa d’auke da waya yana aikata abinda ya saba na kallon hoton Najee da ya cika screen d’in wayarsa. Wayar na ringing zuciyarsa na wani irin fusga da zafin soyayyar Najee. Ya runtse idonsa kafin ya kara wayar a kunnensa yana ture haushin Jaheed d’in da yake ji na k’in taimakonsa da ya yi. “Uwargidana ta haihu ina ka shige ne an haifa maka twins…” Murad ya ware ido yana furta “Are you sure?” Jaheed cikin farin ciki ya sake tabbatar masa “Ka bu’de whatsapp d’inka I will send you their pictures.” Da sauri ya kashe wayar ya kuma hau whatsapp d’in sai ga hotunan kyawawan yaran sun cika screen d’in wayarsa. Da wani irin murna ya ce “Wow Ma sha Allah, Ya Allah kasa wata rana ni da Najee mu ga namu haka.” Ya fa’da yana lumshe idonsa sai ya samu kansa da imagining wai ga Najwa ta haifa masa twins har ya tsira mata ido tana ba su Nono tana sinne kai tana harararsa yanayinta na tsiwa yana nan. Ajiyar zuciya ya saki a fili ya furta “Ya Allah!” Wata y’ar k’walla ta gangaro masa da bai san da ita ba. Hoton ya yi uploading a status d’insa sannan ya kashe data ya sake kiran Najeen sai dai still bata shiga ba nan ya fara tunanin ko dai ba numberrta ba ce? Ya d’an ja guntun tsaki. Kafin asuba haihuwar Najma ta Karad’e masarautar gabas kowa murnar sa ta kasa b’oyuwa musamman Tauraruwa da mai martaba nan da nan aka fara shirin tafiya Kano don ganin jarirai da kuma rok’on iyayen Najma ta dawo cikin masarautar ta yi jego don a mata sunan da baa tab’a irinsa ba. Ba su san Najman ma har a lokacin bata farka ba. Kasa fita ya yi daga d’akin ya mik’e ya shiga toilet alwala ya yi yazo ya tada sallah a d’akin so yake da zarar ta farka ta gan shi. Bata farka ba sai k’arfe 9:00 na safe lokacin duk an cika asibitin ba wanda bai zo ba idan ka d’auke mai martaba sai Fulani Saddik’a amma Tauraruwa ma tana cikin tawagar. Nene dai ba shiri ta zame ta koma gida don dai da kunya a ganta a asibiti wajen jikokin Fari don haka ba wanda ya san ta silale ta fice daga asibitin. Hana kowa shiga d’akin ya yi don likitan ya gaya masa baa son ta farka ana hayaniya. Don haka ya kasa ya tsare yana zaune hannayensa cikin nata, duk wani jan numfashinta da sauke shi akan idonsa take. Cikin ikon Allah ya ji ta yi salati tana ware idonta a hankali a kansa. Wata irin ajiyar zuciya ya saki yana matsa hannunta ya ce “Alhamdulillah Najma are you okay now?” Hannunta ta kai kan cikinta sai ta d’ago ta kalleshi a hankali tana furta Babyn ya mutu ko?” Girgiza kai ya yi kafin ya kai bakinsa kan goshinta ya sumbata a hankali yana furta “Kada ki yi magana da yawa C.S aka miki.” Sai a lokacin ta ji zafin cikinta da sauri ta d’an lumshe ido ta ce “My J, ka gaya min Babyn babu ko?” “Ina zuwa” ya furta a hankali yana fita da d’an sauri daga d’akin. Mutane suna ganinsa suka mik’e aka fara tambayarsa “Yaya ta farka?” D’aga musu kai ya yi “Ku bani Babies d’in na kai mata…” HASSAN ya fara d’auka Nasma ta d’au Usaini ta bi shi suka koma cikin d’akin. Najma na ganinsu da yara a hannu ta d’an ware ido tana furta “My J, Twins ne?” Ya d’aga kai wata ajiyar zuciya ta saki da sauri. Ya saki murmushi yana lakace tsinin hancinta kafin ya kara mata Baffa k’arami a fuskarta “Gaya min da wa suke kama?” Lumshe idonta ta yi alamun kunya na bayyana akan fuskarta. “Bar su na gansu.” Dariya ya yi ya ce “Nasma ji min mata ita fa ta dameni wai sun mutu kuma an kawo zata min gwallin kunya, kada dai kice yarda aka samesu da k’iyayya har yanzu ba kya son su.” Turo bakinta ta yi irin na yarinta ta furta “Bana so My J…” murmushi ya saki bai ji kunyar Nasma ba ya kaiwa cute lips d’inta kiss. Ya furta mata cikin kunnuwanta “An samu cikin su da k’iyayya an fara nak’udarsu da wata irin soyayya mai zafin gaske Allah ya maimaita mana daren jiya My Cute Angel.” Nasma dai da sauri ta fice don ta lura Jaheed baya ji baya gani. Sai da suka gama lalle yaransu tas sannan Jaheed ya fita ya kira nurses don a d’agata a gyarata tunda ba iya tashi zata yi da kanta ba. Sun taimaka mata ta yi wanka kafin a bari mutane su fara shiga ganinta. Nasma ce ta kira Najee ta gaya mata wani irin tsalle Najeen ta yi cikin murna ta ce “Ina Adda Najman take?” Nasma ta ce “Tana lafiya ban ga kin zo ke da mijinki ba kuma kowa ya zo daga Garin Gabas d’in.” Najee ta saki ajiyar zuciya rashin sanin amsar da zata bata a hankali ta furta “Kina kusa da Nene don Allah bata.” “Nene tana gida ki kira wayarta mana..” Ta d’aga kai “Okay nagode ki gaishe min da Addan zan zo In sha Allah..” Tana kashe wayar ta fara kiran Nene. Nene ta d’aga wayar tana furta “Ya aka yi Najee…” “Ina son zuwa naga twins pls Nene..” Nene ta yi d’an tsam da ranta kafin ta furta “Ki yi hak’uri Najwa idan kin zo kinga asirinmu zai tonu…” shirun da Najee ya tabbatarwa da Nene bata so hakan ba sai kuma ta fara jin shashshek’ar kukanta. “Shikkenan ki yi shiru zan turo a d’aukeki jibi tunda Baffa ya ce gobe zan tare..” Najwa ta saki ajiyar zuciya hankalinta ya d’an Kwanta duk da tana ganin kamar jibin ya mata nisa. Suna sallamar Nene ta cigaba da d’an tattara kayan da zata buk’ata duk da Uban sitturun da Tauraruwa ta ce An saka mata a d’akinta a gidan Mai martaba hakan bai hanata tsintar abubuwanta masu amfani ba. Jikinta ya yi sanyi duk sai ta ji bata son rabuwa da gidna Baffan duk da shi ya nemi haka ya ce a goben ta bi ayarin da suka zo ganin jarirai idan anzo tafiya da su Najma. Umma ce ta shiga d’akin da sallama tana duban yarda yanayin jikin Nenen yake a sanyaye. “Mai gyaran jiki tazo zata fara aikinta Nene.” Nene ta waro ido tana furta gyaran jiki kuma? Na menene Umman yara god’ai go’dai da ni.” Umma ta watsa mata wani kallo kafin ta girgiza kai “Wallahi Nene sai kin dage gidna sarauta baa zama haka gwara ma ki tashi tsaye duk wannan dattijantakar ta k’arfi da yaji da kika d’orawa kan ki ki direshi idan kina son kin malllaki Mijin ki, ki tuna ya yi gwagwarmaya da mata iri iri dole sai kin dage kafin ya ji banbanci tsakaninki da su. Gata nan zata shigo zata miki yau ta miki gobe sai kuma ki tafi da ita masarauta ta cigaba da miki…” Nene ta sunkuyar da kai haka kawai sai ta ji kunyar Umman mai girma ta mamaye ganinta. Shigowar Jaheed da sallmarsa ya ce yasa Umman shiru da zancen da ta b’aro mata na ta je wajen Anty Surayya Dee ta gyareta da kayan mata na bojuwa herbals sannan ta ganganra gurin mai kayan matan zuru itama ta bata had’addun kayan Gyara y’an garari. Jaheed ya gaida Nene kafin ya sake wa Umma sannu ya furta “Doctor ya ce ba za’a iya tafiya da ita yanzu ba a bari ta yi ko sati biyu ne, don haka mai martaba ya ce a kyaleta idan sati biyun ta yi zai turo da private jet a d’auketa.” Umma ta d’aga kai ta furta “Hakan ma ya yi.” Jaheed ya gyara zama ya ce “Yanzu Umma ba za’a yiwa Murad afuwa ba a mayar masa da matarsa tunda a kuskure da rashin sani ya saki Najeen……” Wani irin d’agowa Umma ta yi tana kallonsa ta ce “Saki kuma? Murad ne ya saki Najwan?” Ta fa’da idanunta suna bayyana wani irin taratsatsin b’acin rai….. Nene ta waro ido tana runtse su lokaci guda Shikkenan Jaheed ya b’ata mata aiki me yake son ta ce da Dattawan arzikin nan? Hasbunallah! Umma kuwa fuskarta a ha’de take kallon Nene ta furta “Tunda ya saketa yanzu tana ina? Ai sai ta dawo gidan Ubanta….” A cikin kalamin Umma Murad ya hango tsagwaron b’acin rai mai bayyana rashin sassauci ga wanda ya aikata laifin ya san za’a kai ga haka da ya san Umman ba ta sani ba bata yarda za’a yi ya furta hakan…. JIKAR NASHE🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Tsit suka d’auke wuta a d’akin, Ko kwakwkwaran numfashin baya fita da k’arfi a d’akin, Tsoro da tashin hankali sun bayyana k’arara a idanunsu da fuskokinsu. Umma ta mik’e zuciyarta na sake tunzira da Wani mashahurin b’acin rai da Ya kasa b’oyuwa a dukka sassan jikinta musamman fuskarta da ya bayyana muraran don idanunta har jajir ya yi saboda tsananin b’acin rai. Jikinta har rawa yake ta fice daga d’akin Nene kuma ta kasa saka baki ta kirata saboda wata irin kunya da ta lullub’eta. Jin rufe k’ofarta da k’arfin gaske yasa Nene sakin wata k’akkarfar ajiyar zuciya ta d’ago tana kallon Jaheed cikin wata irin murya data bayyana rashin kuzarinta a fili ta ce “Hankalinka ya kwanta Mujaheedu, duk abinda nake hak’ilon b’oyo ka bayyana shi ka b’ata min shiri na cikin d’an k’ank’anin lokaci, Yanzu wace amsa ka tanadar min da zan amsa tarin tambayoyinsu da wani suna kake son su kira ni? BUTULU KO?” Ta fa’da tana sirantar da ganinta a cikin nasa idanun. Zazzafar k’wallar da ta taru a k’asan idaninta ta samu damar sub’otowa ta fara kwaranya da saurin gaske kamar an kunna famfo. Jaheed ji ya yi duniayr na wani irin katantanwa da shi kamar wanda ya sha abin maye. Ya runtse nasa idon da k’arfin gaske don tabbas kukan Nenen na nufin abubuwa da dama kuma yana neman saka nasa hawayen zuba wanda ya manta yaushe rabonsa da hakan. Shirun dai suka yi don basu da wata mafita sai wacce su Umman da Baffan za su yanke a halin yanzu. —- Bata shiga sashen Baffan ba don a yanayin da take ciki ta san tabbas idan ta shiga abubuwan da zata furta ba masu da’di ba ne, zafinsu zai iya tasirin da zai tafarfasa zuciyar Baffan, ba kuma ta san hakan don hakan ta shanye ta shige nata sashen ta kai gwauro ta kai mari tana neman abinda zai d’auke mata nata b’acin ran. Sai dai ba wani sauk’i da ta ji a zuciyarta kuma ranta ya sake tabbatar mata da nanata mata sunan da ta sakawa Nene na Butulu a tunaninta laifin kacokam yana kan Nenen zuciya bata da k’ashi. Ta lumshe idonta sai ga k’wallar itama ta fara kwaranyo mata. Ta ja gefen Hijab d’inta ta share k’wallar kafin ta fara jan addu’oin da take jin zata iya samun sauk’i da su cikin zuciyarta. Sai da ta kawar da b’acin ran sannan ta nufi b’angaren Baffan. A zaune yake yana kallon T.V Africa Tv3 channel yake kallo. Da muryarta da ta k’ara sanyaya saboda yanayin da take ciki ta yi sallama ta shiga. Ya d’ago yana kallonta da alamun ya fuskanci yanayin b’acin ran da take ciki duk da k’ok’arin b’oye hakan da take yi. Tana zama yana jefo mata tambayar da ta sa ka ta d’ago kai da sauri “Me ya faru? Da alama ko menene girmansa ya kai tunda har ya canja min kamannin fuskarki.” Ta zauna tana sakin ajiyar zuciya a hankali kafin ta dubi abincin da ke gabansa ta tabbatar ya ci abincin ya sha kuma fruits da furarsa kamar yarda ya saba duk dare a al’adance sannan ta saki jikinta a hankali ta bijioro masa da maganar. “Ka san k’addara ta raba auren Murad da Najwa….” Da wani irin hanzari ya d’ago kai yana kallonta “Wani irin magana nake ji haka? Yaushe aka yi hakan duk ban sani ba? Yau fa kwana biyar da tariyar…” Umma ta ciji leb’enta na k’asa kawai a hankali ta furta “Ban sani ba wallahi Baffa, na dai ji zancen A sama daga bakin Jaheed kamar yarda ka ji shi….” Shiru ya yi yana jin wani irin abu yana suka a zuciyarsa kafin ya yi k’arfin halin furta Lahaula wala k’uwwata illa billah….. ya saki ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya d’an girgiza kansa yana jin sauyin da zuciyarsa ta yi wajen nauyi da hayak’in b’acin rai suna tafiya a hankali “Kira min Nenen na ji yarda aka yi…” Umma ta mik’e don cika umarninsa itama dai sosai take yak’i da zuciyarta wajen ganin k’iyayyar Nenen bata wanzu a zuciyarta ba. A k’ofa ta tsaya bayan ta yi sallama can k’asan mak’oshi Nenen ta amsa mata tana d’ago kanta cikin mutuwar jiki. Ta sauke idanunta a hankali a cikin na Umman kafin ta amsa sallamar. “Baffa na buk’atar ganinki…” Hakan Umman kawai ta ce mata ta juya ta fice. Wata irin razana da firgita ta ji zuciyarta ta mata ta buga sosai cikin k’arfin hali ta ja addu’a akan harshenta kafin ta mik’e jikinta na rawa ta zura dogon hijabinta ta fita jikinta sam ba laka idanunta suna kunyar Arangama da na Baffa. A zaune ta same shi a parlourn irin zaman da da zarar ka gan shi ka san wanda ya yi shi baya cikin kwanciyar hankali. Ya amsa sallamarta kafin ya bata izinin shiga. Kanta a sunne a k’asa ta shiga parlourn ta samu gefe ta rakub’e. A yanayin zaman da suka yi da Umman ya tabbatar mata zuk’atansu basa cikin sukuni. Tana shirin gaisheshi ta ji muryarsa cikin ginshira ya watso mata tambaya “A yaushe ya saketa ban sani ba Kuma me ta yi masa? Amsa ta zamo gaskiya zahiran..” Dukan da zuciyar Nene take yi a lokacin da kana kusa da ita tsaf zaka iya jin bugunta. “Ina jin ki..” “Ranar da ta tare…” Ya d’ago cikin wani irin rashin kuzari ya zuba mata idanunsa ya ce “Me yasa ban sani ba sai yanzu? Tana ina kuma?” Gumi ne sosai ya shiga tsatstsafo mata ta saka hannunta ta share duk da haka bai fasa zuba ba. “Ka yi hak’uri Baffa tana gidan Hajja da kai na na kai ta…” Sake ha’de fuskarsa ya yi sosai kafin ya d’an girgiza kai. Tana kallo ya zaro waya a aljihunsa numberr Faruk ya kira yana d’agawa ya ce “Faruk ka d’auko min Najwa a gidan Hajja.” Daga haka ya kashe wayar ya ce “Tashi ki je Allah yasa haka ya zama alheri garesu da mu baki d’aya.” K’afafunta sam kasa jinta ta yi a jikinta faranta da duk wani muradinta a lokacin bai wuce ta farka ta ji mafarki take ba gaske ba. Sai dai idanun da Umma ta zuba mata ya ankarar da ita gaske ne ba mafarki ba. Cikin sanyin jiki ta nufi k’ofa. “Ki shirya gobe zasu wuce da ke masarauta Allah ya baku zaman lafiya ya ka’de dukkan fitina..” Kasa amsawa ta yi tana jin a zuciyarta kamar da gatse Baffa ya yi furucin. Haushin Murad ya sake ninkuwa a zuciyarta ta k’udirce a ranta sai ta b’ata masa rai sosai ta yarda ko gaba aka ce ya sake aikata irin kuskuren nan ba zai sake ba. Tana Fita Umma ta kalli Baffa shima d’in ita yake kallo. Kafin ta furta kalmomin da take hak’ilo wajen furtasu ya ce “Wa ma k’adarullahu hak’k’a k’adarihi… ba wani bawa da yake k’etare k’addararsa ki sanya wannan a zuciyarki sai ranki ya samu salama. Ba yinsa ba ne ba kuma ikonsa ba ne abu ne da yazo a cikin littafin K’addarrsa zai aureta zai kuma saketa, ba wani bawa da ya isa ya k’ulla ko ya raba aure sai Allah, Fatan da zamu yi Allah yasa hakan ya zama alheri garesu.” Wani irin sanyi Umma ta dinga ji yana kwaranya a zuciyarta duk wani turiri da hucin da zuciyarta take yi sai ta ji ta samu salama, zuciyar kuma ta yi sanyi kamar an zuba mata k’ank’ara. Ta saki ajiyar zuciyar da ta tafi da duk b’acin ranta a hankali ta furta “Khairan In sha Allah, Rabbi Tawakkaltu ilaika.” Baffa yana murmushi ya dinga kallonta ya san a irin kyan hali irin na Umma da wuya fushin nata ya sake k’etare ko saman idaniyarta balle ya ratsa zuciyarta. “Allahumma barik.” Ya furta a hankali yana jifanta da wani sahihin murmushin da ya sake narkar da b’acin ranta. Irin su Baffa ne ake kira da Salihan maza y’an Aljanna kamar Mijin Nazeefah 🥳 Nene dai har safe ta kasa sukuni zuciyarta gaba d’aya ba walwala ji take kamar itama ta hak’ura da nata auren sai dai ta san idan ta hak’uran Baffan zai iya yiwa abin wata fassara. Kafin ta tashi da safe har an d’auko Najee daga gidan Hajja da ke Azare. Burin Najee kawai ganin y’an biyu don haka suna zuwa ta shige motar da za’a kai abinci asibiti. Ba tare da ko shiga cikin gidan ta yi ba. Baffa yana lek’a su ta window ya saki ajiyar zuciya kawai tausayin Najeen ya kama shi ganin yarda zawarci ya hauta da k’ananun shekarunta, shekaru sha bakwai. Ya gimtse b’acin ransa jin sallamar Umma data shigo sanar da shi zuwan su Tauraruwa da neman iso wajensa. Duk da b’oye damuwar zuciyarsa da ya yi hakan bai hana Tauraruwa gane ya ji labarin sakin ba. Don ita wata irin mutum ce mai gane d’abi’ar da halayyar d’an Adam ta yanayinka kawai zata iya fallasa maka duk wani sirrin da yake ranka. “Barka da safiya.” Ta fa’da a hankali cike da muryar kamala. Baffa ya ‘dago yana amsa gaisuwarta da ta sauran jama’ar da suka rako shi. “Idan ba zaka damu ba ina son yin magana da kai ta sirri.” Ta fa’da kanta tsaye ba tare da ta damu da idanun mutanen da suke walagigi a kanta ba. Mik’ewa kawai Baffa ya yi zuwa wani k’aramin parlournsa da bai fiya zamansa ba sai idan irin hakan ta taso. Zama ya yi itama Tauraruwa ta zauna daga d’aya b’arin da yake. “Ina jin ki.” Ya fa’da cikin muryar da take bayyana dattijantakarsa. “Ina nemawa Murad Afuwa abisa tarin laifi kansa ba komai ya jawo hakan ba sai yarinta don Allah Baffa a yi hak’uri a mai da masa da matarsa ya yi nadama wallahi irin nadamar da take kassara tunanin mutum a yi hak’uri don Allah…” Wani irin kallo Baffa ya d’aga ya jefeta da shi, kafin ya saki murmushi a hankali ya furta “An yi na farko an yi na k’arshe ki k’addara Murad bai tab’a sanin Najwa ba balle har auratayya ta shiga tsakaninsu….” “Ban gane ba Baffa?” Murmushin ya sake sakar mata ya ce “Ba aure a tsakaninsu har abada!” “Tirk’ashi!” Tauraruwa ta furta a hankali ta cikin k’wayar idanun Baffan ta hango rashin wasa a cikin abinda ya furtan kuma da alama ba wani sassauci a cikin zancensa…. Baffa ganin bata da shirin tafiya ya mik’e a hankali don nufar k’ofa ya furta “Allah ya bashi mata ta gari amma banda Najwa…” JIKAR NASHE🥳 [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Shiru d’akin ya d’auka kamar an d’auke wutar nepa, kowa ya kasa motsi mamakin girman wautar Najee kawai Tauraruwa take. Umma kuwa ji ta yi kamar ta tashi ta mugun yi mata duka. Ta mik’e ta fice daga d’akin bayan ta wurgawa Najwa da take tsaye harara. Najwa jikinta ya yi sanyi ta tabbata abinda ta aikata ba mai ma’ana ba ne daga ganin yarda suka ta sha jinin jikinta. Da sauri ta juya zata fice Tauraruwa da take ta sakin murmushi ta saka baki ta kirata. Dawowa ta yi da baya tana kallon Nene itama ta fice daga d’akin ya rage daga ita sai Tauraruwa a d’akin. Cikin murya mara sautin wasa ta kira sunanta “Najwa!” Kiran da Najwa ta ji shi har tsakiyar kanta. Ta d’ago cikin sanyin jiki da na zuciya tana amsawa. “Zo nan.” Ta isa inda Tauraruwar ta nuna mata gefenta ta zauna. “Shekarunki nawa?” “Sha bakwai.” Tauraruwa ta nisa tana mamakin yarda y’ar shekaru sha bakwai a zamanin nan bata son komai ba a fannin sha’awa da auratayya ma gaba d’aya. Lallai ya kamata a jinjinawa Umma da dukkan tarbiyyar da ta bawa yaranta. “Kuna Fikhu a islamiyya?” Najwa ta d’aga kai. “Yauwa Malamanku sun tab’a muku k’arin haske akan Balaga da dukkan abinda ta k’unsa…” wata irin kunya ce ta kamata don sai yanzu karatun ya dawo mata daki daki tana jero shi a kwanyarta kamar yanzu ake biya mata shi da sauri ta runtse idonta tana jin kamar k’asa ta dare ta shige ciki. A zahiri ta furta Kalmar “Na shiga uku mai na aikata?” Sai kuma ta mik’e da mugun gudu ta koma d’akinta ta saka key ta murza tana sakin haki da ajiyar zuciya, tsananin nadama ta shiga zuciyarta wata irin wauta ce yau ta sameta? Tauraruwa dariya ta yi sosai ganin abinda ta aikata d’in wato da gasken mantawa ta yi sai yanzu ta tuna. Najwa kenan! Ta furta a hankali tana jin son yarinyar har a ranta da kuma tana da dama a yau zata mayar da aurensu don ta fuskanci itama Najwan tana son Murad kamar yarda yake son ta. Mik’ewa ta yi ta fita tana dariyar Nene da Umma suma da suka dare suka barta da yi wa Najwa bayani. Har suka gama shirin tafiya da Nene Najwa ta k’i yarda ta fito kunya take ji sosai gefe guda kuma matsananciyar sha’awar da Murad ya jawo mata ta girma ma a jikinta wani irin yanayi take ji irin wanda bata tab’a riskar kanta a ciki ba. Ba yarda ba a yi ba ta fito su yi sallama ta k’i dole Nene ta hak’ura tana sake jaddada rok’on Umman a turo mata Najwan ta k’arasa iddarta a wajenta. Umma murmushi kawai ta yi don sun Riga sun gama shirinsu da Abba can Yola zata kaita gidan k’anwarta a can zata yi iddar, Fareeda wayayyiyar macece za kuma ta d’ora Najwa akan duk abinda bata iya ba, don yau tab’argazar da Najwan ta yi ta tsorata Umman sosai ta ina zata yi saken da zata sake aurar da ita bata san komai ba. Ta window ta dinga lek’en motocinsu tana jin idanuwanta na zubar da hawaye, ba na komai ba ne sai na rabawa da Nenenta matar da ta d’auka kamar Uwa gareta. Ta ji zuciyarta ta yi zafi abu goma da ashirin ya ha’de mata a zuciya ga waccan matsalar ga kuma wata daban. Murad ya bar mata wani assignment mai girman gaske da har yau ta kasa amsa shi daidai abin sake naso yake mata kamar wani almara. Da Umma aka tafi raka Nenen don haka ta ji gidan ya mata girma don haka ta nufi sashen Mahmeey wajen Yayarta Nasma idan zasu tafi asibiti ta bi su. A fada an musu wata irin tarba ta mutunci da karramawa. Fulani Saddik’a ta shirya musu Walima duk da ba mutane da yawa amma akwai abinciccika kala kala masu yawan gaske. Nene dai jin ta take kamar a mafarki ta kasa sakewa duk da k’ok’arin Tauraruwa da Saddik’a na son ta aikata hakan. Kwarjinin Sarki da wata irin Haiba sun cika mata idanu taf har ta fara jin tsoron a kirata da matar Sarki. Tabbas lamarin Ubangiji yana da girman gaske, daga y’ar bayi yau itace kai tsaye take amsa suna MATAR SARKIN GABAS. Ta lumshe idonta tana jinjina godiyarta da yabo ga rabbil izzati. Aka ci aka sha aka Kuma addu’a da wasa da raha kafin Tauraruwa ta kama hannunta don isa da ita sashenta. Umma na gefenta suna shiga sashen su dinga yaba kyau da tsaruwa da sashen ya yi komai Sabo ne dal mai kuma tsadar gaske tabbas Naira ta yi kuka wajen shirya b’angaren nata sai kace a fadar Sarauniya England. Tattausan k’amshi ne kawai kai caku’de da na turaren wuta da sanyin A.C ya gauraye sashen. Nan aka bu’de k’ofa bayi suka dinga kawo gaisuwa kowa kuma ya shigo sai ya yaba da amaryar da kuma sashen duka . Don Nene dawowa ta yi kamar wata y’ar shekara talatin sai walwali take tana shining jikinta ya cika ko ina b’ul b’ul Masha Allah. Umma dai bayan Tauraruwa ta bi don ta ce a wajen Tauraruwar zata kwana da yake sai kashegari za’a mayar da ita garin Kano. Nene duk da bata so ba haka tana ji tana gani ta hak’ura ta fuskanci rayuwar da take jiranta a gaba….duk da wani sashe na zuciyarta tana jin mugun tsoron fuskantar mai martaba da sunan mijinta tunda abu ne bak’o a wajenta wancan da ya faru ba abinda zata k’arar a cikinsa kusan yanzu ne zata san menene aure? Me kuma da’dinsa da rashinsa yake nufi tana fata dai koma menene zai zo mata yazo mata cikin rahamar Ubangiji. Ta saki ajiyar zuciya tana bin sashen nata da kallo ganin yarda ya yi tsit kowa ya watse sai tsirarun masu mata hidima da suke can parlour na farko. Sai Yamma suka yi shirin tafiya asibitin. Cikin shigar wata doguwar Riga da ta masifar yi musu kyau suka yi rolling da mayafin rigar da ya sake fito fa kamalar fuskarsu. Glass Najwa ta saka mai kyawun gaske a idonta sai ta sake yin d’as da ita kamar ka sureta ka gudu. Driver ya ja suka isa asibitin. Ba kowa a d’akin daga ita sai nurse d’aya sai Babies d’in. Najwa da sauri ta d’au Baby d’ayan tana fa’din “Ya zama dole na fara banbance ku, yara sai shegen kyau ga su kamarsu d’aya.” Najma tana dariya ta ce “Matso na banbanta miki su, wannan na hannunki Murad ne sak Mijinki…” Gaban Najee ya wani irin bugawa da sauri ta d’an yi yak’e tana furta “Mhmnn.” Daidai lokacin suka turo k’ofa suka shigo dukkansu fara’a fal fuskarsu Murad idanunsa cikin Najee da ta yi saurin d’auke kai tana jin haushin yanayin da yake jefata. Murmushi ya saki yana kallon Jaheed da ya d’an d’aga masa gira suka saka dariya a tare kafin Murad ya ‘Dan gintse ya nemi kujera ya zauna still idanunsa zube a kan Najwa da ta kasa motsin Kirki sai wasa take da yatsun Baby Hassan. Ya d’an yi gyaran muryar da yasa ta ji kamar ta saka ihu saboda abinda ta ji ya tsirga mata gaba d’aya ya ba’de d’akin da k’amshin turarensa. “Najwa kawo min yaro na…” k’iris ya rage Babyn bai sub’uce daga hannunta ba, jin yarda ya kira sunanta da wata irin siga. Ganin ta k’i motsi tsam ya mik’e ya nufi inda take cikin wani irin taku ya sunkuya daidai kanta tana jin saukar numfashinsa a wuyanta k’iris ya rage bata saki fitsari ba, ya sa hannunsa ya janye nata hannun ta ji kamar an mata shocking a hannun ta d’ago a tsiwace zata masa masifa ya kasheta da wani irin kallon da yasa bakinta ya mutu ba shiri ya zare yaron daga jikinta a kunnenta ya ra’da “Idan kin ji haushi get ready to have your’s…..” Ya zauna daf da ita bai damu da kallon da mutanen d’akin suke masa ba, burinsa isar da sak’on so, don ya lura sam yarinyar bata san ma me ye so ba. Matsawa ta yi niyyyar yi ya take k’afarta da tasa k’afar “Kina jin feeling ne idan na zauna kusa da ke?” Ya fad’a ta yarda ba mai ji sai ita. Cikin dakiya da k’arfin hali ta murgu’da masa baki tana furta “God forbid.” Ya waro ido yana kallonta kafin ya d’aga gira d’aya ya furta “So yanzu kin san me nake nufi?” Ta d’auke kai murmushi ya saki yana kallon Nasma ya ce “Nasma k’anwarki fa Villager ce.” Nasma dariya ta yi kawai sai ta ji suna burgeta yanayin tasa soyayyar irin mai tsayawa a rannan ce da alama gwani ne a fagen nuna kulawa ga mace. Har bayan Isha’i suna zaune kuma bai bata dama ko ka’dan ta matsawa daga jikinsa ba, ya bi ya takurata irin takurar da take jinta har tsakiyar kanta, ji take kamar ta saka ihu. K’amshin turarensa ya bi yi manne gam a kayanta. Sai 8:30 ya mik’e yana kallonsu “Ku taso mu tafi gida.” Najwa ta waro ido “Me ye ha’din tafiyarmu da kai.” “Saboda nima Baffa ya ce a can zan kwana bai amince na sauka a hotel ba, idan kuma gorin gida zaki min let me know sai na kama gaba na, na kuma gaywa Baffa.” Ya fa’da yana koyon irin maganarta yana kuma narkar da idanunsa cikin nata, hakan ya sata yin shirin dole kafin murya a sark’e ta ce “Ku je kawai ni anan zan kwana..”. “Ki hanata soyayya da Mijin ta kenan ko? Tana son ta ji d’imun mijinta ki zo ki zauna musu…” Najee runtse ido kawai ta yi ta mik’e ta fice da gudu. Murad ya d’au jakarta yana dariya ya kalli Nasma “Mu je ko?” “Aa Ya Murad ku je kawai zan kira Driver…” Dariya ya ce “Hakan ma ya yi Allah ya miki albarka asuba ta gari…” Ya fita da d’an hanzari. Duka d’akin dariya suka yi suna mamakin k’arfin hali irin na Murad. A tsaye ya tarar da ita tana ta cin magani. Ya k’arasa wajenta yana dariya k’asa k’asa. “Shall we?” Ya furta a hankali yana kama hannunta ta janye hannun tana furta bana so.” “Ni kuma ina so shine ma abu mafi soyuwa a gareni a duniyar nan….” ya furta yana lek’en fiskarta ta hau dube dube tana kallon hanya. “Nasma ta k’i biyomu bata son ta takurawa love birds so feel free daga ni sai ke!” “Cab’di!” Ta furta a hankali tana gyara tsayuwarta “Nima ba inda za ni.” “Wasa kenan!” Ya furta yana dariya “ki taho Malama ko na d’aga ki cak aba kamar Baby doll.” Wani irin kallo ta wurga masa ya matsa daf da ita “Kina ganin ba zan iya ba?” Ya fa’da yana juyawa sai ji ta yi ya yi sama da ita cak. Ta fara turje masa ya saka yatsa ya d’alle bakinta “Ki min shiru gobe ma ki sake min tsiwa.” Bai direta ko ina ba sai wajen mota. Ya kuma sakata ta dole ya shiga ya danna lock.. yana d’an sakin haki ya ce “Ashe dai kina da nauyi? Ko da yake na san inda suke da nauyi a jikin naki….” Ya fa’da yana kallon inda yake nufi d’in wani irin bugu k’irjinta yake ga shi mahaukacin feeling d’in da take ji ya fara zuwa ta ja d’an bakinta ta tsuke don ta lura hanyar da kunya take Murad bai santa ba. “Na nuna miki wajen?” Ta girgiza kai da sauri tana furta “Na yafe.” Dariya ya yi sosai ya ce “Sai tsoro sai tsiwa.” Lumshe idonta kawai ta yi ba tare da ta san inda za su je ba, sai da ta ji ya yi parking ta bu’de idonta tana kallonsa “Nan fa? Me za mu yi?” “Love… And honey moon…” Ta bu’de idonta da sauri “Ban gane ba?” “Zaki gane idan mun shiga.” Ya fa’da yana saka hannunsa saman fuskarta ya janyo hab’arta “Najwa kalle ni nan…” Ta d’ago a hankali tana kallonsa ya furta “Ki amince zaki cigaba da zama da ni a matsayin Miji?” Wani irin dum ta ji kwanyarta ta buga ya hau murza hannunta a hankali yana furta “Answer me, Idan kin yarda a yau zamu bar k’asar nan… And I promised you Nene zata yafe mana idan ta ga jikanta a hannu…. JIKAR NASHE……🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Shiru Najwa ta yi k’irjinta yana wani irin bugu da k’arfin gaske…. Murad kuwa da murmushin gefen kumatu yake binta yana hango yarda yarinta ta baibaye fuskarta da idanunta. “An mayar da auren mu yau! Baffa da Maimartaba sun sake d’aura mana aure ba tare da sanin Nene ba, kin san tunda na sake ki ba tare da na d’ora miki Idda ba dole ne sai an sake d’aura mana aure Jaheed ya shige min gaba wajen Baffa….” Ya fa’da yana d’an lumshe ido tuno yarda suka yi da Baffan sanda ya je gidan bayan ya bar wajen Najee daga d’akin Nene. Kallo guda Baffa ya yi masa ya d’auke kai wata fargaba tana shigarsa baya son tunanin da yake ya zama gaske, idan har ya tabbata haka ne za su bar yara su yi zaman zina ba tare da sun san me suka aikata ba. Ya saki ajiyar zuciya yana furta “Shigo Murad!” Ya shiga cikin nutsuwar da iya gangar jikinsa ne kawai yake nuna hakan banda zuciyarsa da take a tsorace da hukuncin da Baffan zai yanke masa baya son hukuncin ya zama daidai da na Nene. A gefen Baffan ya zauna a k’asa duk hana shi hakan da Baffan ya yi. Jaheed kuma yana daga d’aya gefen shi da Faruk. “Me yasa ka rabu da matarka?” Baffa ya jeho masa tambayar da ta kusa tarwatsa kwanyarsa. Wasa ya shiga yi da yatsun hannunsa kamar mace na gaban surukanta a ha’duwar farko. Baffa ya k’ura masa ido ganin yanayin da yake “Ina jin ka!” Ya fa’da da kakkaurar murya da yasa Murad saurin gyara zama ya fara bawa Baffan labarin tunda ga ganin farko da ya yiwa Najee cikin b’atacciyar kama da kuma ganinta da ya yi a kamanninta na asali ya kuma gayawa Tauraruwa ita yake so amma suka cigaba da b’oye masa gaskiyar lamari har ta kai ga ya furta saki cikin rashin sani…” Baffa ya jinjina wautar Najwa da ma su Tauraruwa gaba d’aya wa yake wasa da aure har haka kamar a shirin film.. A fili ya saki tsaki a lokacin kam duk wani laifin Murad da yake gani ya goge tas sai laifin Tauraruwa da su Nene har ma da Umma gaba d’aya, ko waye ma zai aikata abinda Murad ya aikata musamman da ya nuna masa hoton Najwa da b’atacciyar kama. “Kana son matarka har yanzu?” Da sauri Murad ya ce “Wallahi ina sonta Baffa.” Dariya Faruk da Jaheed suka saki. Baffa ma sai da ya murmusa yana kallon Murad ko bai rantse ba a idanunsa yake kallon tsantsar son da yakewa Najwa. “Zan mayar da aurenku yau, saboda haka musulunci ya shar’anta idan mutum ya saki mace ba tare da ya d’ora mata idda ba dole sai an sake d’aura musu aure don haka sai ka sake bada sadaki yanzu anjima zan saka a mayar da aurenku a masallaci…” Da sauri Murad ya gyara zama ya hau laluban aljihunsa duk wasu ku’di da suke ciki sai da ya fito da su bai lura da yawansu ba ya dank’awa Baffa. Baffa ya ce Jaheed ya karb’a yana furta “Allah ya sanya musu albarka, abu na gaba bana son ka gaywa iyayenka mata an mayar da aurenku ka ja bakinka ka yi shiru zan dai kira Maimartaba na sanar masa bayansu bana son ka sanar da sakarkarun iyayenka mata nima kuma zan ja bakina na yi shiru naga iya gudun ruwansu.” Farin cikin Murad kasa b’oyuwa ya yi godiya kawai yake zabgawa Baffa su Jaheed Suna tsokanarsa da yammacin ranar aka sake mayar da aurensu a masallacin gidan Baffan. Shine bayan Magriba suka nufi asibiti zuciyar Murad fal da farin ciki… Hannu ya saka ya sake rik’o yatsunta da yake jin taushinsu har tsakiyar kansa, da sauri ta bu’de idanunta da suka fara nauyi ta zuba su cikin nata da take jin dafinsu a tsakiyar tata zuciyar. “Do you love me?” Ya furta cikin wata keb’antacciyar murya da ta sake galabaitar da Najee ta tabbata idan har zata bu’de baki ta yi magana ba abinda zai saka ya gane a halin da take ciki. Don haka ta ja baki ta tsuke tana kokawa da numfashin da ta ji yana sassark’e mata. Hannun ya cigaba da mutstsikawa son ransa yana lumshe ido sosai yake jin da’din yanayin da suke ciki. “I love you My heart, don Allah ki amince mu shiga hotel d’in nan tunda na sanar miki Baffa ya mayar da auren mu.” Mak’e kafa’darta ta yi kamar yarinya tana girgiza kai ya bu’de nauyayyun idanunsa da k’yar ya furta “What? Me kike nufi ba zaki ba?” Da sauri ta d’aga kai idanunta na son zubar da k’walla. Ji ta yi kawai ya ja hannunta ya ‘dora a k’irjinsa ta ji yarda zuciyarsa yake bugu sosai. “Kin ji zuciyata ko? I will assure you idan baki bini ba komai ma zai iya faruwa….” Ya lumshe idonsa still hannun nata na saman k’irjinsa “Ba zan iya komai ba Naj… ba ni da k’arfi charging d’ina ya k’are I need more….” Ta yi saurin kallonsa bata san sanda ta furta “Charging wayar ne zai hanaka zama kai d’aya Ai hotel d’in da wuta zaka iya charger phone d’in taka…” k’asa k’asa yake kallonta kallon da ya sata d’auke kai ba shiri tana furta “So yake ya kashe ni, bai san me nake ji ba ne…” sam bata san a fili ta yi maganar ba, sai da ta ji maganarsa a cikin kunnenta cikin wata irin husky voice ya furta “Na kasheki ko ki kashe ni?” Da sauri ta zare ido. Sai Kuma ta basar “Ka saka charging anan kafin ka kai ni gida ta yi…” “Na ce miki zan iya driving ne irin abinda kike ji ina jin fiye da shi ma, so idan ba charging na yi ba zan iya driving ba…” “Ka yi charging mana..” “Kin amince?” Ta d’aga kai don bata san charging da yake nufi ba.. “Oya to mu je..” ya furta yana k’ok’arin bu’de motar ta yi saurin ce masa “Ga chargernka anan…” Murza goshinsa ya hau yi yana sake narke idanunsa cikin nata “Kin san charging da nake nufi?” Shiru ta yi don kallon gaba d’aya ya kassara ilahirin jikinta. “I want charging my….” Sai kuma ya yi shiru yana runtse idonsa ha’de da taune gefen leb’ensa ya furta “Wash Naj… Please help!” Sai yanzu ta gane abinda yake nufi da sauri ta d’auke kanta daga kallon yanayin da yake fuskarta kamar zata yi kuka ta ce “Pls Ka mayar da ni gida?” Hannunta ya kama ya furta “Zan mayar da ki but pls hug me and kiss for a minutes Naj ba haram ba ne am your husband….” Da sauri ta ja jikinta baya “Ni ka bari bana so…” “Ni kuma Ina so Naj please Allah ba zan iya driving ba… Hannu ta saka zata bu’de motar ya yi saurin rik’ota ta fa’di kansa wani irin kyakykyawan hug ya bata da shi kansa bai san zai iya ba, kusan Najwan ma hakan tafi buk’ata don haka ta kasa k’wace kanta, ya cigaba da bata zafafan runs, a hankali ya samu ya dawo daidai ya yi feeling comfortable sannan ya zare ta jikinsa yana sakin ajiyar zuciya. “Ki shirya gobe da azahar kafin Umma ta dawo zan zo na d’auke ki zamu tafi Abuja daga can zamu wuce Saudi mu yi one week sai ki zab’i inda kike so ki je honey moon.” Shiru ta masa ta kasa furta ko kalmar ‘a’ don al’amarin yau ya girmi tunaninta tabbas Murad ya d’orata a wani abu da bata san shi ba. Ya gyara zama yana kunna key. “Kin san idan kin je gida dole ki yi wanka ko?” Ya furta ba tare da ya kalleta ba, “ko baki sani ba? Don naga ke komai baki sani ba kamar…” sai kuma ya yi shiru yana sakin murmushi “Soon zaki sani yarinya ba kiga komai ba sai nazo miki a zahirin Murad tukun kin daina jin abinda kike ji ko still kina ji? Ni wai me kike ji ne ma? D’an bani labari kin ji Naj…” yanayin yarda yake kiran sunanta shi yake sake saka ta a wancan yanayin.. ta d’an turo bakinta tana furta “Ban sani ba…” “Kina son k’ari kenan? Don ni kin san tsiwar Mace ita take tayar min…” Ya fa’da yana d’aga mata gira Ai Najwa ji ta yi kamar ta zunduma masa ihu ta lura Murad nema yake ya zautar da ita. Har suka isa gida yana cigaba da tsokanarta. Yana parking ya rufe motar ruf ya juyo yana kallon yarda ta takure waje guda. “Na san yau dai za’a sha mafarki ba mamaki ma a cikin a mafarkin har za’a gano wancan lamarin da ba mu kai ga aikatawa ba…” Wani irin kallo ta masa da ya saka shi sakin dariya yana furta kin ci bashi banda Baffa ya fito da wallahi komawa zan yi da ke na yi maganin tsiwar nan..” da sauri ta kalli inda yake kallo Ai kuwa Baffan ne ta ware ido tana furta “Na shiga uku!” “Baki shiga uku ba ma sai ranar da ya ganki da cikin d’an fari…” Ya fa’da a hankali yana bu’de k’ofar motar ya fita da sauri wajen Baffan. Hakan ya bata damar futa itama da saurin ta bi ta inda Baffan ba zai ganta ba. “Goben k’arfe nawa zaku tafi?” Baffan ya jeho masa tambaya yana basar da yanayin da Murad d’in yake ciki na kunya da jin nauyi. “11:00..” “Hakan ya yi don bana son Uwarta ta dawo tana gidan nan na fi son na shayar da su Mamaki irin wanda suka shayar da ni… Ka wuce da matarka kada ka dawo da ita sai bayan wani tsahon lokaci Allah ya Muku albarka…” Ameen Murad ya furta a hankali. Baffan ya mik’a masa key “Ka shiga d’akin can da yake gefen sashena ka Kwana a can..sai da safe..” daga haka ya wuce abinsa ya bar Murad yana sosa k’eya kunyar Baffa Kawai yake ji ga waccan yarinyar da ta Riga ta tafi da duk tunaninsa…… Allah ya kai Damo ga harawa.. Murad ya furta yana cizon leb’ensa ya nufi motarsa don kwasar kayansa zuwa d’akin da aka masa masauki zuciyarsa yau fes yake jin ta… Na so k’warai na gama muku a yau amma hakan bai samu ba dole sai na kai gobe In sha Allah. Ku shirya tsaf gobe 𝚄𝚖𝚖𝚞 Ammara matubuciyar Nagarta zata sakar muku sabon littafinta mai Suna KHUL’I kai daga jin Sunan littafin ka san yana tattare da ma’ana don haka kada ku bari a baku labari kawai ku danna link don shiga direct cikin MAKTABARTA…. KHUL’I COMING SOON NOVEL BY UMMU AMMARA… JIKAR NASHE✍🏽🥳 08033748387. [5/12, 7:02 PM] Nazeefah Nashe: Jikin Tauraruwa ne ya yi la’asar ganin ko ta ina ba mafita. Ta mik’e tsaye da k’yar tana sakin ajiyar zuciya ta nufi k’ofar da zata mayar da ita parlourn da sauran jama’a suke. Duk yanayin da Nenen take ciki na sanyin jiki da rashin walwala hakan bai hana Umma tursasa mata ta shirya tsaf cikin atamfarta Super wax mai masifar kyau. Umman ce dai ta sake tursasa mata wajen shanye magungunan da ta dama mata a cup babba har sai da ya cika cikin Nenen taf ta dinga ji tamkar zata yi amai. “Gidan sarauta sai kin dage da addu’a Nene barci bai ganki ba, wata irin rayuwa zaki shiga ta yak’in k’watar kai idan ba haka ba ina tabbatar miki za’a yi ba ke, ki dage da ibada sallolin dare da na walaha su zame miki abin dogaro a kullum yawaita karanta Alkur’ani ko da kina a halin rashin tsarki shima zai zame miki bango a bin jingina ya kuma kareki daga sharrin magauta ko da sun cika duniyar nan a mizanin yawa. Kada ki k’ullaci kowa a zuciyarki domin hakan yana rage miki kusanci da Allah, ki kiyaye hassada don babu abinda ya kai ta asara a duniyar nan ba don komai ba sai don kai tsaye kina jayayya da hukuncin ubangiji ne, Akan me yasa zai fifita bawansa da ke? Ki zamo mai sakanta Alheri ga wanda ya yi miki sharri sai kiga kin zama kullum ke ce a samansa kuma sai Ubangiji ya zame miki garkuwa a dukkan wasu lamari da ya shige miki gaba Ubangiji kuma zai zamo mai tare miki fa’da. Allah ya baku zaman lafiya yasa ki zamo tauraruwa mai haskawa a zuciyar Mijin ta dimun da’iman wa Abadan…..” Hawaye ne kawai suke sintiri a fuskar Nene ta ji k’afafunta suna rawa kamar zasu bar jikinta. Tana son mutanen tana mutuntasu da ganin k’ima da martabarsu bata tunanin a duniyar nan za a samu dattijai masu Karamci kamar su d’in, su d’in dai sune gimshik’in faranta rayuwarta da haskaka ta daga cikin bak’in duhun dajin da ta shiga mai tsananin sark’ak’iya a yau zata bar su barin da har a zuciyarta bata so. Ga wannan abin kunya da Murad ya aikata ya kasa barinta ta yi karsashi ta kuma nuna musu godiyarta da ainahin farin cikin rik’on da suka mata. “Ku yi hak’uri Umma ku yi hak’uri, a yau ina ji na kamar na cancanta na amsa sunan Butulu, Murad bai kyauta muku ba ya kuma k’arya min zuciyata Don girman zatin…..” Umma ta d’aga mata hannu da sauri.. “Maganar Murad ta isa haka, a yanzu bana rik’onsa a raina tabbas da fari na ji ciwo sai dai Baffa ya tunasar da ni abinda na manta Shi aure rai ne da shi a duk kuma sanda ajalinsa ya zo babu tsumi babu dabara sai an tafi Allah ya ha’da kowannensu da abokin zama na gari wanda ya yi daidai da tsarin rayuwarsu…” Nene ta ha’diye wani irin yawu da ta ji kamar tafasashshen ruwa a mak’ogaronta me zata ce da mutanen nan da me kuma zata sakawa tagomashin alherinsu? Babu! Kai tsaye ta samu amsa daga zuciyarta sai kawai ta samu kanta da lumshe idonta wasu hawaye suna zuba da suke tafiya da duk wani k’uncin zuciyarta. Sakamakon Aljanna ga nagartattun bayinka Umma da Baffa ya Allah!” Umma ta masa a hankali ta na sakin murmushi daidai lokacin Najee ta shigo a mugun guje, tana neman wajen b’uya. Umma ta kalleta a fusace tana furta “Najwa yaushe zaki hankaline?” Bata amsa Umman ba har sai da ta dangana da Toilet sannan cikin muryar data bayyana zallar k’uruciyarta ta ce “Umma mugun mutumin nan ne ya zo ba na son ya gan ni.” Ta shige toilet tana murza d’an mukulli ta baya bata damu da tsit d’in da suka yi na mamakin shiririta irin ta Najee a d’akin ba. Nenne murmushi kawai take saki tana sake jin wata irin zafaffiyar k’aunar Najee na k’ara rub’anya a ranta. “Don Allah Umma ku bar min Najee na tafi da ita can…” Hakan kawai ta samu bakinta da furtawa. Umman bata kai ga amsa ta ba. Muryarsa mai Amon da ya ratsa zuk’atansu ta yi sallama a d’akin k’amshin turarensa ya gama ba’de cikin gidan. Wani irin kyau da Haiba yake fitar daga cikin d’anyar shaddar sheraton da ke jikinsa. Idanun nan sun yi hasken gaske kamar an d’iga zaiba a cikinsu. Umma da kanta sai da ta jinjinawa Allah da ya halicci Murad cikin kyakykyawar kama mai tsayawa a rai da wani irin sirrin kyawun da baa gajiya da kallonsa. A k’asa ya durk’usa yana gaishesu duk da ya kasa tsaywa ya ha’da idanu da su, duka su biyun wata irin kunyarsu yake ji kunyar ya kasa bin umarninsu ya bi son zuciyarsa. Umma ce ka’dai ta amsa fuska d’auke da walwala tana fa’din Murad da wuri haka sai kace wanda ya biyo jirgi. Bai amsa ba illa bin d’akin da kallo da yake yana neman ta inda zai sake arba da ita sai dai wayam babu itan sai k’amshinta da yake fusga a hancinsa ka’dan ka’dan. Umma ajiyar zuciya ta saki ganin hankalinsa baa kanta yake ba ta Mik’e tana furta “Ina zuwa Nene Amma dai ki saurareshi ba kyau uwa mahaifiya ta bayyana fushinta ga d’anta haka Masifa ce a gareshi.” Daga haka ta fice tana jiyo sakin zuciyar Murad ‘din. Tsam Nene ta mik’e da nufin barin d’akin, ta kuwa fice da sauri itama Murad bai hanata ba don ya ma fi buk’atar hakan. Mik’ewa ya yi ya shige walk in closet d’in d’akin inda Najee ba zata gan shi ba, yau zai nuna musu shima d’an Zamani ne ba zai iya wannan talalar da suke masa ba. Najee jin d’akin ya yi shiru yasa ta bu’de k’ofar a hankali daga ita sai y’ar mitsular Riga ta fito ganin ba kowa a d’akin. Murad yana kallonta ya dinga jin zuciyarsa na wani irin harbawa k’aunar yarinyar da komai na jikinta na sake rub’anya a ransa. Cak ya mik’e ta bayanta sad’af sad’af ya isa ya kai mata wata kyakykyawar runguma tana shirin zunduma ihu ya rufe bakinta da hannunsa “Shiiiiit, kafin na murje bakin ki anan… ke wace irin yarinyace ne zo ki zauna magana za mu yi kawai…” Ya fa’da yana jan hannunta fuskarsa ba alamun wasa. Suka zauna a gefen gadon duk da tana turjewa ya runtse hannunsa ruf a cikin nata banda rantsuwar Nene ba abinda zai saka shi yau bai mayar da yarinyar cikakkiyar mace ba a wucen wajen a huta to amma ya yi alk’awarin ba zai mayar da aurenta ba har sai da amincewar Nenen. “Idan baki tsaya ba zan nuna miki waye Murad yau…” Ya fa’da yana juyo da kafa’darta da zafin namansa. K’wayar idanunta ya laluba ya saka tasa k’wayar idanun yana mata wani irin sihirtaccen kallo da yasa ta ji tsigar jikinta ta fara tashi ta fara matse k’afa. Murmushi ya saki ganin Sak’onsa ya kai inda yake so. “Kina so Kina basarwa ko? Tausaya miki fa nake da tuni na auri wata, yarinya k’arama da ke ki dinga wahalar da ni…” Murgu’da masa baki ta yi. Ya lumshe ido yana furta “Do you want me to kiss you? Idan kika sake Allah sai na sumbace ki duk da ba aurena a tare da ke…” Murgu’da bakin ta sake yi Ai kuwa ba shiri ya fisgota jikinsa ya ja leb’enta da k’arfin gaske ya fara kissing d’inta… Ihu ta saka masa ihun da ya saka shi saurin Sakarta yana harararta “Ke baki da kai ko?” “To an gaya maka ni y’ar iska ce?” “Ni d’an Iska ne ai? Ki tsaya ki saurari abinda zan ce miki wallahi dama ki san yarda zaki da Nene ta mayar da aurenmu ko kuma wallahi kina ji kina gani na auri Nasma nan gaba ke zaki zo kina cizon yatsa…” Harararsa ta yi “Ba sai ka aureta ba idan Baffa zai baka? Ina ruwana ma kuma kada ka sake tab’a ni don ni ba y’ar iska ba ce…” murmushi ya saki yana k’ank’ance idonsa cikin nata ya furta “How old are you Baby?” Waro ido ta yi ta furta “Ni ce Babyn? Ba zan fa’di shekarun nawa ba..” ya sake lumshe idonsa yana furta “I know baki fi 15 ba wawuya kawai kin san me ye aure?” Da sauri ta ce “Mhmn Allah ya kiyaye ni ce 15 d’in? To saura two months na yi 17..” Ya yi dariya sosai har beauty point d’insa yana lob’awa ya ce “Anty Babba ce ashe? Kin san me ye aure?” Ta d’aga kai da sauri “To gaya min?” “Idan za’a yi aure ana kaiwa amarya kayan lefe a sai mata kaya akai gidanta sai a yi biki daga nan ta dinga girka abinda ta ke so, after one year ko two sai ta haifi baby then za’a dinga kiranta Mama or Umma…” wata irin dariya yake sosai har Najee ta shagala da kallonsa “Ya ake wa amarya ta samu ciki to? Ko cikin kawai take gani a jikinta?” Shiru ta yi ta tafi tunani bata san komai ba game da aure da gaske don haka ta tafi tunanin. Murad kuwa kallonta kawai yake kafin ya ja hannunta ya d’ora a kan k’irjinta yana lumshe ido wani irin farin ciki ne yake fisgarsa ya furta “Baki sani ba?” Ta d’aga kai ranta a b’ace kamar ta yi kuka don ta tsani a mata tambaya bata sani ba sai ta ga kamar ta Gaza. Idanunsa yake lumshe cikin nata yana jin wani irin feeling ji yake kamar ya kusanceta sai dai yana tuna rantsuwar Nene sai ya ji gwiwar sa ta yi tsani. “And you want to know right?” Ya fa’da yana matsa hannunta sosai take jin wani iri a k’asanta abinda bata tab’a ji ba. D’aga masa kai ta yi ta idanunta ya gano itama ta shiga charging. Cikin wata irin murya ya kai bakinsa Daidai kunnenta ya furta “Kina so ki sani?” Yarda ta ji wani yarrr a jikinta ya sata lumshe ido ba shiri jikinta ya fara wani irin b’ari mugun feeling take ji a jikinta sai dai bata san me sunan abin ba bata san kuma ya zata yi ta daina ji d’in ba. Goga kumatunsa ya yi a jikin nata ya furta “Zan gaya miki amma sai dai ki kirani cikin dare sai na gaya miki a waya…” d’aga masa kai kawai ta yi ba tare da ta bu’de idonta ba ji ta yi kamar abu na zuba daga jikinta. Murad da ta tabbatar ya gama ha’da nata tarko sai ya mik’e yana d’an sunkuyawa ya yi kissing lab’banta ya furta “I love you habibteey…” yanayin da ta ji ya zarce magana ta dai samu kanta da furta “Wash!” Murad ya saki murmushi yana girgiza kai ya fice daga d’akin. A ransa yana furta “Na gama aiki na farko remain na biyu da kan ki zaki nemi ki koma gidana.” Yana fita parlourn ya ci sa’a ba kowa da sauri ya fice daga gidan ya nufi motarsa bayan ya kira Jaheed ya masa sending location na asibitin ya tafi yana jin duk wata fitina da take ransa ta fara mik’ewa da gaske matarsa yake da buk’ata kwana kusa, ya ‘dan cije leb’ensa a ransa yake jin kamar ya furta NA MATAR DA KE NAJWA… sai dai yana tsoron fushin Nene, don haka ya ha’diye furucinsa kawai yana driving yana murza goshinsa lokaci guda kuma yana sakin murmushi idan ya tuna wautar Najwa. Da k’yar ta mik’e daga gadon jin yarda abu yake bin jikinta yasa kai tsaye ta shige toilet a zatonta period take duk da ba lokacinsa ba ne, sab’anin haka wani kalar ruwa ta gani da sauri ta yamutsa fuskarta tana furta “What is this? Bari na je na tambayi Umma Allah yasa ba wani ciwo ba ne.” Sai da ta yi fitsari ta fito sannan ta nufi d’akin Umma. Suna zaune da Tauraruwa da Nene ana ta lissafin kayan Babies da ake buk’ata a siya. Ta yi sallama ta shiga fuskarta d’auke da alamar damuwa. Duk wanda yake d’akin kuma ya ji k’amshin turaren Murad a jikinta. Gaba d’aya suka kusan ha’da baki wajen furta “Lafiya Najwa?” Ganin yanayin jikinta da k’amshin da suke ji a tare da ita… Ta yi k’asa da kanta tana furta “Ba ni da lafiya..” Suka waro ido suna kallonta Tauraruwa ta mik’e ta isa kusa da ita tana dafata ta furta “Fa’da min me ya sameki?” Lumshe ido ta yi tana tuna wannan feeling na d’azu da ta ji mai mugun da’di cikin wata irin murya ta ce “Wani ruwa ne mai yauk’i ke zuba a private part d’ina kuma ba period ba ne……. JIKAR NASHE🥳 08033748387. [5/12, 8:57 PM] Bahaushiya👍: Da k’arfe 10:00 na safiya ya gama duk wani shirinsa ya zauna a parlourn Baffa yana jiranta tuni an turo masa flight ticket d’in su da zai kai su Abuja. Suna zaune Baffa yana sake masa nasiha a hankali yana fahimtar da shi yarda zai yi zamantakewar aure da matarsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta yi masa biyayya kuma ba tare da nuna gazawa ba ko ka’dan. “Murad mace tana son ka bata lokacinta, ka kuma zuzuta aiyukan alherinta da kyawunta ko da bata kai a zuzuta ta ba. Zata ji da’di kuma zata kambama kanta ta zata tafi duk matan duniya. Mace tana son a yaba mata ka kula da kyau a duk lokacin da kaga matarka ta d’au zafi kai ka yi k’ok’arin zama ruwan sanyi don samun daidaiton ra’ayi a tsakaninku a lokacin da ta d’au zafi idan kai kace zaka d’au naka zafin abin ba zai yi kyau ba, sai kaga an zo abu ya kai da saki. Mace tana son a gatanta a shagwab’ata koda shekarunta sun kai 70 Ka mayar da ita yarinya a kan ka, sai ka ji bakinta lumui tana kuma kurarin mijinta yafi na kowa. Allah ya baku zaman lafiya ya kawar da dukkan abin k’i. Ka lura da kyau kada ka zama sakarai a wajen matarka, har ya zama bata jin maganar ka ka zama tsayayyen namiji wajen tarbiyyarta kamar Uba mahaifi ka gane?” Murad ya d’aga a ransa yana sake jinjina girma da kimar Baffan hak’ik’a Baffa nagartaccen Uba ne na nunawa a kerewa a sa’a. “Bari na turo maka ita.” Ya mik’e kansa tsaye ya shiga cikin gidan b’angaren Umma inda Najee take can tana zaune hannaye a kumatu ta zuba uban tagumi. Haka kawai take cikin tsananin fargaba fargabar da ta kasa b’uya a saman fuskarta. Baffa ya d’an zuba mata ido kafin ya saka hannu ya d’auki mayafin da ta ajiye a gefe. Bata son da shigowar Baffan ba balle har ta lura da mayafin da yake shirin yafa mata. Ji ta yi kawai ya dafa kafa’darta yana yafa mata mayafin. Murya a hankali ya ce “Tashi Najwa ki je Allah ya miki albarka duk wani alheri yana gidan aure martaba da mutuncin mace shine zama gidan Mijinta. Aljannarki kuma tana k’ark’ashin sa idan kina son samun mafi k’ololuwar daraja a cikin Aljannatan Ubangiji ki dage da yi masa biyayya ki guji sab’a masa ki guji aikata duk wani abu da zai sosai masa zuciya yanzun nan sai kiga kin zama Tauraruwa a cikin Taurari. Allah ya miki albarka…” Cikin rawar murya ta amsa ameen d’in hawaye na malala a k’uncinta kamar wadda a yanzu ne zata tafi gidan aure a karo na farko. Baffa ya bubbuga kafa’darta a hankali yana furta “Khairan In sha Allah.” Ya furta yana dank’a mata wani littafin addu’oi da Alkur’ani mai kyan gaske da carbi. “Wad’annan sune makamin yak’ar mak’iyi da mahassadi a rayuwa idan kika rik’e su a gidan aurenki zaki sha mamakin alherin Ubangiji da zai dinga bibiyar ki. A yi rik’o da nafila mafi girmansu sallahr walaha da ta tsakiyar dare..” Najwa ta d’aga kai a hankali tana mik’ewa Baffan ya saka hannu ya damk’i nata hannun suka fita waje. Har d’akin Mahmeey bai Bari ta shiga ba balle ta bawa Umma labarin Mijinta ne ya tafi da ita. Suka fita harabar gidan inda Murad da drivern gidan suke jiran su don ya dawo da motar Baffan da Murad yake hawa tunda ya zo garin. Tunda ta fito ya zuba idanunsa a kanta yana jin duk wani bak’in cikinsa ya yaye, Allah ya gama yi masa dukkan wata ni’ima a rayuwa da ya mallaka masa Najwa a matsayin matarsa. Baya jin a duniya zai sake kallon wata mata da niyyar soyayya idan ya kalla d’in ma ba Zata kai Najwa ba a zuciyarsa. Ya saki ajiyar zuciya a hankali yana furta “Alhamdulillah Hamdan katheeran bi ni’imatihi tatummussalihat…” Ya yi sauri bu’de mata k’ofar motar. Baffa ya k’araso da ita da kansa ya saka ta a cikin motar yana furta “Fi Amanillah.” Ya juya wajen Murad yana murmushi ya furta “Murad ga Amana!” Murad ya dunk’ule hannunsa yana murmushi ya furta “In sha Allah Baffanmu.” Ya juya wajen Najwa ya ce “Najwa ga Amanar Murad nan na baki..” Lumshe idonta ta yi a hankali ta kasa furta komai sai kunyar Baffan da ta kamata. Baffa ya yi murmushi ya sake furta “In sha Allah kuna cikin amincin Ubangiji sakamakon Aljannah ga duk wanda ya kyautata zamantakewarsa da d’an uwansa a cikin ku.” Ameen suka furta a hankali Najwa tana jin ruwa da iska ba mai hanata yi wa Murad biyayya ko don wannan addu’ar ta Baffa ta amsu a kanta, haka nan Murad yana jin ya zama dole ya kyautatawa Najwa ko don samun tagomashin Aljanna. Baffa yana d’aga musu hannu suka fice daga gate d’in ya saki murmushi da ajiyar zuciya a hankali ya furta Alhamdulilah. Wata siririyar k’walla da ta d’an mak’ale a idonsa ta zubo wacce na tabbata ba k’wallar komai ba ce sai ta zallar farin cikin auren da y’arsa da ya yi. Kukan da take bata sarara ba tun Murad yana jinta yana lumshe ido alamar kukan yana tab’a ransa har ya faki idon drivern ya zura hannunsa ta bayanta murya k’asa k’asa cike da kasala ya furta “Ki yi shiru muryar kukanki na saka ni a wani condition…” Ya fa’da yana zuba narkakkun idanunsa a kanta. Harara ta b’alla masa hararar da ta saka shi sakin murmushin da bai shirya ba ya yi pointing hannunsa a kan k’irjinsa ya furta “Ni ko?” Lokaci guda ya girgiza kansa yana taune gefen leb’ensa ya furta you will explain it anjima ka’dan..” Sake kukan ta yi da k’arfi Murad ganin ba Zata yi shiru ba kawai sai ya lumshe idonsa ya fara rera mata wak’ar india a hankali wacce ake cewa Boli choriya…. shiru ta yi tana sauraran muryar tasa kamar ba shi ba wak’ar ta zauna akan bakinsa cikin Husky Voice d’insa da take jin ta har tsakiyar kai… Bata sake kukan ba saboda yanayin yarda wak’ar take bin dukkan zuciya da gab’banta sai gata da lumshe ido. Murad ya saki murmushi a hankali ya furta “My Piya…” Isarsu airport suka sallami drivern shi kuma ya ja trollynta k’arama wanda kaya ne kala biyu a cikinsu sai tarkacen underwear’s d’inta don ta kasa sakin jiki ta d’ebi kayan a tsorace take da lamarin Murad.. Tun a jirgi duk wanda ya gansu sai sun burge shi kuma kana ganinsu ka san sabbin aure ne. Murad baya jin kunya yayinda ita kuma Najwa duk abinda ya mata sai ta ji kamar k’asa ta bu’de ta shige ciki. Haka suka isa yana sake bayyana mata sirrin zuciyarsa. Babban hotel d’in Hilton suka sauka. Tun daga yanayin yarda aka zubawa gadon d’akin wasu irin flowers gaban Najwa yake fa’duwa ta zauna ta rab’e a lungun gadon. Tana kallon yarda Murad yake cikin Nisha’di sai wak’ar India yake rerawa kamar Baindiyen. Ganin zai cire kaya ya sakata runtse dariya kawai ya yi yana furta “Mhmn…” Ya shige toilet. Najwa ta shiga duban d’akin tana tunanin yarda zata kwana ita ka’dai daga ita sai Murad a wannan d’an k’aramin gadon don ko ka’dan bai da girma. Ya dai sha ado na alfarma kamar me? Sai kuma zabga wani ni’imtaccen k’amshi yake. Daga shi sai Bathrub ya fito da hand towel a hannunsa yana goge sumar kansa ya tsaya a kanta yana furta “Oya taso a yi wanka…” Najwa ta yi saurin zaro ido… “Ki taso kafin na d’aga ki cak!” Kafin ta ce me kuwa ya sureta tana ihu amma bai k’yaleta ba sai da suka shiga toilet Najwa ta dinga rok’onsa ya ajiyeta. Ya ajiyeta a cikin bathtub yana dariya ya furta “Me Zan gani k’waila kuwa… Ki tsaya na cu’daki da kyau don na san da k’yar hannunki zai kai baya…” “Yaya Murad…” Yes Naj” ya furta yana kai hannunsa kan zip d’in Rigarta da niyyar zuge wa ta yi saurin rik’e hannun tana furta “Please ka bari ba kyau, y’an iska ne suke haka..” Ya lumshe idonsa a hankali yana furta “Nima shine… Naj called me Dan iska as from today…” Daga nan fa duk wani labari ya fara canjawa idonsa ya rufe baya ji ba ya gani dole na juya da sauri don wannan rahoton yafi k’arfina abu guda da na sani a ranar Murad ya sha Allah ya isa… —————- Shiru sashen Nenen Jakadiya ta yi sallama ta shiga. Nene da take zaune zugum abin duniya ya isheta kusan zata iya cewa jinta take kamar wata amarya ko da yake amaryarce bata tab’a aure ba a rayuwarta a zahirance kuma bata tab’a soyayya da wani namiji ba balle har ta kai ga ta fara hasashen aure a rayuwarta. Duka rayuwarta ta sadaukar ne wajen son ganin rayuwar d’anta Jaheed ta inganta. Ta lumshe idonta tana sake shak’ar k’amshin humrar da Umma ta bulbula mata. Wani irin k’amshi ne mai fisgar hankali. Sallamar Jakadiyar ta amsa tana sake sunkuyar da kanta yanayinta ne na kunya ne sosai jinin Fulani ke aiki a jikinta. “Ma sha Allah, Allah ya yiwa aurenku albarka.” Jakadiya ta furta a hankali kafin ta bu’de wani akwati da tazo da shi. Wata irin alkyabba ce a cikinsa mai masifar kyau ta cireta tana zabga k’amshin turare ta mik’awa Nene. “Ranki ya da’de sarki mai dafan iko yana jiranki a wannan dare mai albarka cikin turakarsa!” K’irjin Nene ya yi wata irin tsawa, tsawar da ta ji ta masa a dukka sassan jikinta. “A fito lafiya ina parlour ina jiranki ya da’de…” Daga haka ta fita Ta bar Nene da wata irin rawar hannu da kakkarwar jiki. Ta mik’e cikin sanyin jiki ta sake d’aukar zumar Kayan matan zuru ta sha sannan ta shiga toilet ta wanke bakinta ta fito ta zura Alkyabbar ita kanta ta yaba sa kyan da alkyabbar ta mata a jikinta, sam idan ka ganta ba zaka ce ita ta haifi Jaheed da Murad ba. K’wank’wasa k’ofar da aka yi ne ya sake hargitsa y’ay’an cikinta ta amsa cikin k’asan mak’oshi. Jakadiya ta sake shiga tana furta “Idan Gimbiyar Gabas ta shirya ta fito…” Tattausan silifas black da ya dace da y’ar duma Dumar k’afarta fara tas ta saka a k’afar suka nufi b’angaren Mai martaba da yake ta wata sirrintacciyar hanya a d’akinta. Ba kowa a hanyar sai Fadawa masu tsaron fadar da daddare. Suka nufi k’ofar mai Martaban. Yana zaune a saman kujerarsa mai masifar kyau ta cikin falonsa na sirri wanda ba mai shiga daga matansa sai y’ay’ansa sai kuma Jakadiya. Ya d’ago yana amsa sallamar yana shak’ar k’amshin turaren da ya kusa saukar da shi a saiti. Murmushi ne sosai ya sub’uce masa irin murmushin da Jakadiya zata ce ta da’de bata ga ya yi shi ba. “Kin gama aikin ki” ya furta a hankali yana kallon Jakadiyar. Gaisuwa ta kai masa kafin ta mik’e ta fita. Shiru parlour ya d’auka idanun Maimartaba akan Nene ya saki ajiyar zuciya a hankali ya furta “Fulani!” Sunan ta ji ya mata girma sai dai sanin cewa daga ita sai shi ya sata ta d’ago dara daran idonta ta zuba masa. “Taso ki dawo nan kusa da ni…” Zuciyarta ta buga a hankali. “Taso Fulani taso na ji jikin da na da’de ina mafarki kusa da ni…” Ta mik’e a hankali don isa wajensa, tana shirin zubewa a k’asa ta ji ya ja hannunta ta zauna kusa da shi sosai a hankali ya fara magana. “Dukkan burina ya cika yau ga ni ga Uwar mafi soyuwa a cikin yara na. Ban san me Zan ce miki ba, kalmar Ina son ki ta yi ka’dan sai dai na ce ina miki wani gigitaccen so dafatan a wannan daren zaki samar min cikin k’annen su Murad wannan karan mata zalla nake so…” Hasbunallah shi kawai Nene ta iya furta saboda yarda tasirin kalamansa suka gigita zuciyarta a ranta ta furta “Ashe haka soyayyar take?” To Fulani Nene asuba ta gari.. Allah ya amsa bakin sarki a samo k’annen Murad… ________ Umma na shiga gidan ta ji shiru da sauri ta fito tana kallon mai aikinta “Ni Ina Najwa ta shiga ne? Tun d’azu nake bulayin nemanta a gidan nan ban ganta ba?” Mai aikin ta ce “To Ai ni Umma na zata tare kuka tafi don ko yau da nazo ban ga Najee a gidan nan ba….” A tsorace Umma take kallonta cikin fa’duwar gaba ta ce “Ban gane baki gan ta ba ina Najwan zata tafi je ki ki tambayo Mahmeey ko tana wajen Najma…” JIKAR NASHE… 08033748387. [5/12, 8:57 PM] Bahaushiya👍: Komai ya yi farko zai yi k’arshe banda ikon Allah…….. *********Murfi********🤗🤗🤗 Jinjina ga yabo ga y’an group d’in K’udirar Allah special group da normal group bani da bakin da zan gode muku. Tukuicin Aljannah garesu ya Allah. Ina mik’a sak’on godiya ta Ga Bright Pens y’an uwana a fannin rubutu: Naima sulaiman Sarauta Ayshercool Zee kumurya. Godiya ga Mikiya Writers Association Nagode da karamci da jumirin sharing Rabbi ya sake ha’da kan mu…… *******Kun shirya karanta littafi mai da’di? To kada ki sake a yi tafiyar KHUL’I babu ke don zaki zo kina cizon yatsa maza garzaya group d’in Maktabu UMMU AMMARA don karanta littafin Khul’i daga jin sunansa kun san ba littafin Banza bane.. KUDIRAR ALLAH KARSHEN SHAFI….. Mai aikin bata yi musu ba ta bi umarninta na zuwa b’angaren Mahmeeyn abinda ta gaya mata ya ‘dan tayar da hankalinta. “Rabo na da Najwa tun da asuba da ta tafi b’angarensu lafiya dai ko?” Cikin tsoro mai aikin ta furta “Ba a ganta bane…” Mahmeey da sauri ta mik’e ita da Nasma suna zare ido ta furta “Baa ganta ba kamar ya ya?” Ta fito ta bi bayan mai aikin d’an kwalinta a hannu.. Nan ta sake tabbatar da rashin Najwan. Nasma ce cikin murmushi ta ce “Anya basa tare da Murad, don jiya ma ya je asibiti ya d’auketa.” Umma ta waro ido tana furta “Da kuwa na ci Ubanta, ba igiyar aurensa a kanta yake bin sa….” “Ke kika hana igiyar auren nasa a kanta?” Suka tsinci Muryar Baffa cikin tsananin fushi da fusata. Da sauri Umma ta ‘dago tana kallonsa. “Ni na bata umarni ta bi mijinta bayan na mayar da auren da kuka zamo sanadin mutuwarsa saboda shashanci da k’wak’walwar yara… “ Shiru Umma ta yi don a idanun Baffa ta hango ya samu dukkan labarin abinda suka b’oye masa, don haka ta yi saurin saukar da idanunta a k’asa tana furta “Ka yi hak’uri sai da na hana Tauraruwa ce ta ce ta aikata hakan..•” “Da kuwa kun cucesu yau da ace saki Uku ya mata ya zaku yi da su? Ya zaku yi da Son da suke wa Juna da ya kasa b’uya har a cikin k’wayar idanunsu kun san abinda kuka aikata? Wannan shi ake kira da Ganganci don haka na mayar da aurensu kuma na umarceshi ya tafi da matarsa duk inda yake so.. Itama Nenen ki gaya mata ni na bashi umarni idan yaso sai ta shirya yin azimin kaffara guda Uku currrr!” Daga haka ya juya ya bar wajen ya bar Umma da sakin ajiyar zuciya ita kam don ta ita lamarin ya mata da’di hakan dama take so sam bata son ace Najwa ta na zawarci da k’ananun shekarunta… Mahmeey da bata san kan zancen ba ta tambayi Umma yarda aka yi Umman ta gaya mata Mahmeey ta ware ido tace “Gaskiyar Baffa ne kun aikata aikin yarinta wallahi, Allah ma ya kiyaye.” Umma dariya ta yi ta ce “Ai shikkenan Allah ya shige gaba ya ba su zaman lafiya…” suka amsa da ameen suna watse wa da barin wajen. _______ Da wata irin kunya Nene ta farka daga barcin da ya sureta a gadon Mai martaba. Yanayin ya mata wani iri abinda Hausawa suke cewa banbarakwai. Ta kai dubanta gefen Mai martaba don ganin ko yana nan sai ta ga gadon wayam, ta duba agogon da yake kusa da ita kan bed side ta waro ido ganin yarda lokaci ya ja sosai sha d’ayan safe. Shi yasa tunda suka yi sallahr asuba ta so guduwa amma mai martaba ya hanata ya sake janta suka koma barci. Ta saki ajiyar zuciya tana lumshe ido ashe haka lamarin Aure yake tabbas da ta san haka matan aure suke cikin ni’imar Ubangiji da ba abinda zai kaita dakon wannan shekarun ba tare da aure ba. Da ta gama shirya tsaf cikin kayan da bata san wanda ya kawo su ya ajiye a kan gadon ba sai jin kunya da nauyi ya hanata fita parlourn ta yi zamanta a katafaren gadon da yake d’akin Mai martaban tana sake hakaito abinda ya wakana tsakanin su a tsakiyar daren yawan albarka da Mai martaba ya dinga shi mata har yanzu muryar na nan ra’dam a cikin kunnuwanta ta girgiza kai tana sakin murmushi ha’de da lumshe ido a hankali Ta furta Hamdan Katheran Ya rabb…” Dai dai lokacin da ya tura k’ofar d’akin ya shigo. Idanunsa a kanta yana kallon yarda yanayinta ya nuna mabayyaniyar kunya. Murmushi ya saki ya zauna a gefen gadon yana d’auke mayafi da ta rufe fuskarta da shi ya furta “Ai na siyi bakin Fulanin Gabas mai mulkin zuciyar Mai Gabas! Allah ya yi miki albarka ki taso mu je mu karya.” Gani ya yi ta zame ta tsuguna a gabansa cikin nutsuwa ta furta “Ina kwana ranka ya da’de an tashi lafiya?” Ya zuba mata idanu walwalar fuskarsa ta kasa b’uya ya furta “Idan ma na tashi lafiyar Ai kin fi kowa sani Ranki ya da’de..” Ganin yarda yake tsokanarta sai ta mik’e kawai tana murmushi hakan yasa ya bi bayanta yana sake jifan ta da wasu kalamai da tasirin su ya girmama a kwanyarta…. Suna gama breakfast Tauraruwa da Fulani Saddik’a suka shigo. Fulani Saddik’an bakomai a ranta suka gaisa da Maimartaba da Fulani Nene. Tauraruwa na cigaba da tsokanarta da ya kwanan bak’unta. Bayan mintuna da zamansu Tauraruwa ta d’ago tana kallon Maimartaba ta furta “A yau nake son karb’o yaran Raheena daga inda na ajiye su don ta damk’a kowanne ga mahaifinsa…” Maimartaba ya guntse fuska b’acin ransa ya bayyana don a zahirin gaskiya ko sunan Raheena ba ya son ji balle a masa zancenta.. “Hakan Ya yi ya furta cikin bayyana b’acin ransa. “Ki kawo yaran nan ki kuma saka tazo ita da abokan lefinta da suke d’aure a gidan Yari.” Tauraruwa ta d’aga kai tana ficewa daga b’angaren nasa. “A yau itama take son sauke nauyin da yake kanta, don biyu daga cikin yaran tuni suka matsa mata suna son sanin asalinsu don sun manyanta suna son su yi aure amma ga duk inda aka je neman aure sai a ce sai an san asalinsu. A yammacin ranar Tauraruwa ta shigar da zaratan Samarin su hu’du cikin Fadar Maimartaba. Daga bayanta kuma Fulani Raheena ce da tsoronta da fargaba ya sake bayyana musamman ganin da ta yiwa yaran kamaninsu da k’annen mai martaba da suka zama iyayensu ta sake bayyana muraran kana gani ba tare da ka tambaya ba zaka gasgata hakan. Fuskar Sarki ta bayyana tsananin b’acin ransa, ya zubawa K’annensa ido yana sake bin yaran da kallo. Tauraruwa zata fara magana ya d’aga mata hannu “Ba sai kin yi magana ba kowa anan ya san d’ansa ina son su d’au y’ay’ansu su kuma fice daga cikin masarautar Gabas har abada na yanke alak’ata da su.” Ya juya ya kalli Saddik’a ya furta “Ba ke ba yarana da kika haifa wa’danda na tabbatar jinina ne halak har abada bana son ki sake kusantarsu na baku awa biyar kacal ku fice daga masarautar nan da ku da duk wata tsiya taku!” Shiru Fadar ta yi tabbas hukuncin da Maimartaba ya zartar shine abinda ya dace… Haka kowa yake furtawa Maimartaba ya nemi kowa ya fita yana buk’atar hutawa. Nene ma ta mik’e zata bi bayan su Tauraruwa ya sa hannunsa ya danne nata hannun yana furta “Wa zai kula da ni idan kika bi su?” ……Murad kuwa wata irin soyayya suke mai tsayawa a zuciya a yanzu ya tabbatar ya yi dace da kalar matar da yake so. Wacce bata k’auro a soyayya take bayyanata take nuna masa iya iyawarta tamkar ba yarinya k’arama ba. Ko da yake shi ya ginata a kan wannan tsarin ya kawar da duk kunyar da take tsakaninsu don ya ce Ba wata kunya da Allah ya halatta ta tsakanin Mace da Mijinta. Ita sirrinsa ce da ya halatta taga komai na jikinsa don haka komai tare suke yi cikin kwanakin da basu wuce bakwai ya yi wani irin gogar da ita. Ta kuma ta ji ta bi take shayar da shi wata irin soyayya mai zafin gaske.. Suna zaune da yammacin ranar kansa a kan cinyarta Tana wasa da sumar gashinsa yana lumshe ido ya ce “Naj kina son na koma ruwa ne?” Turo baki ta yi ta furta “Bismillah mana..” Ya d’an bu’de lumsassun idanunsa a kanta ya furta “Ba fa na gajiya da ke Naj…. kin san alk’awarin da zan miki?” Ta girgiza kai. “Har abada ba zan miki Kishiya ba, Saboda Allah ya mallaka miki duk wani abu da nake son naga matata da shi, komai kina da shi…..” Ta saki murmushin da ya bayyana murnar da zuciyarta take ciki ta ce “Allah ya amsa bakinka K’alb yasa har abada ba zaka sake d’arsa soyayyar wata mace a ranka ba…” Ya shafa cikinta da girman sa ya kusa isa haihuwa ya furta “Allah ya kawo mana Babies lafiya mu isa Nigeria mu ba su mamaki….” Lumshe idonta ta yi tana furta “Ameen saura kuma idan suka zo ka fifita soyayyarsu akan tawa wallahi bar maka su zan yi…” Dariya ya yi sosai ya furta Kishi har da Angels d’ina? Ba zan so su fiye da ke ba amma na san zan yi musu so mara kwatance…”. Murmushi ta saki tana burin ranar da za su isa Nigeria tana zakwa’din zuwa sabida rabonta da can shekara guda kenan… Ta tuno sanda Nene ta kira waya ta balbale Murad da fa’da Murad d’in ya saka wayar a fuskar Najwa, ya kalli Najwa ya ce “Tell her you love me ba zaki iya rabuwa da ni ba?” Najee tana dariya ta furta “Yes Nene I love my Husband please!” Nene ta waro ido tana kallonta da yarda ta yi wani masifar kyau ta furta “Najee da kan ki?” Ta d’aga kai tana shagwab’a fuska irin na yara. Nene murmushi ta saki ta furta “Ai shikkenan Alhamdulillah Rabbi ya sake ha’da kan ku.. Yaushe zaku zo Nigeria?” “Sai ta haihu Nene zamu zo because she is pregnant…” Nene kashe wayar ta yi tana dariya wani farin ciki na ratsa zuciyarta Najwa ce da cikin jikokinta Najwa dai mafi soyuwa a gareta fiye da komai da kowa a duniya… “Alhamdulillah ta furta a hankali….” Har Maimartaba da yake zaune a gefenta ya juyo yana kallonta “Saura ke Fulani ina son ganin precious daughter d’ita.” Fulani Ta d’an lumshe ido tana kallon cikin da ke gabanta na wata shidda kunya tana sake kamata wai itace da ciki tana yi y’ay’anta na yi banda Maimartaba ya cije da tuni ta cire cikin amma ba yarda zata yi da k’addarar Ubangiji. Mai martaba ya shafa cikin yana furta “Ina son cikin nan Fulani kamar yarda nake son mai cikin…” Fulani ta b’oye kanta a cikin k’irjinsa tana sakin murmushi… dafatan Allah ya rabata da cikin lafiya ita da Najwa don Khaireen Jaheed tuni ta haifi santaleliyar y’ar ta mai kama da Nene kwabo da kwabo. A daren wata rana da Najwa ba zata tab’a Mancewa da ita ba nak’udar ta sark’e mata. Daga ita har Murad sun tsorata sosai da yarda ciwon nak’udar yazo mata a gaggauce don kafin su fita harabar gidan da suke su nufi asibiti kai ya fito Najwa ta durk’ushe cikin azabar Ciwo ta furta “K’alb wani abu zai fito….” kafin ta k’arasa ta saki wani irin nishi mai nauyin gaske. Sai ga kukan Jaririya Murad ya ware ido yana kallonta cikin mamaki ya ce “Naj kin haihu…” Kafin ta amsa wani kan ya sake dannowa sai ga Baby ta sake fitowa daga ita har Murad d’in sai suka ki’dime dariya kawai suke. Da sauri ya yi waya asibitin da yake zuwa antenatal aka turo da ambulance aka kwashe su a gaggauce bayan nurses d’in sun yanke cibiyar yaran a wajen. Murad dai fuskarsa dariya kawai yake saki yana furta Alhamdulilah kafin ya kira Kowa Baffa ya fara kira yana d’agawa ya furta “Baffa Najwa ta haifa maka mata biyu…” Baffa da ya ji zancen daga sama ya waro ido yana furta “Murad Allah yasa ba wasan da ka saba min ba ne…” “Am serious Baffa Wallahi ta haihu yara biyu Mata.” Baffa ya furta “Alhamdulillah!” Ya shiga k’walawa Umma kira da Mahmeey suma cikin tsananin Farin ciki suka dinga furta kalmar Alhamdulillah! Tsaf aka fito da su daga d’akin da aka gyara su sai k’amshi suke su da Uwarsu, zuwa d’akin da zasu huta Najwa lumshe ido kawai take tana kallon Murad da ya nufo gadon cikin sauri ya kai mata kiss a kumatu yana furta “I love you Naj…” Ta saki murmushi tana furta “Love you Too K’alb.” Ya d’aga yaran yana murmushi ya furta “Guess their names….” Ta lumshe ido ta ware akan yaran da suke tsananin kama da ita sai dai sun d’auko hasken fatar Mahaifinsu ta furta “Am not good in guessing…” Ya lakaci gefen k’uncinta ya furta “Umma and Fulani Saddik’a…” Ta lumshe ido tana turo baki ta furta ta ce “Nene fa?” Ya girgiza kai “Ki haifota next year ita da Tauraruwa kin san fa na fi son yara mata…” Ta girgiza kai tana furta “Allah kawo masu albarka.. Yaushe zamu tafi Nigeria?” “Nextweek In sha Allah ya furta yana d’ora Babyn a jikinta “Oya gyara ki bata nono na samo ganye kuma na miki wankan jego…” Ta waro ido ta ce “Mhmn sai na koma Nigeria na san Nene zata min…. Ranar da suka isa Nigeria kai tsaye masarautar Gabas suka wuce inda dandazon mutane suka cika don taransu. Baffa ma ya je Jaheed da matansa da yaransa su Umma da Mahmeey duk sun halarta don a ranar za’a yi sunan su. Najee suna shiga masarautar ta dinga mamakin yarda aka cika kamar me? Murad kuwa fuskarsa ta koma irin fuskar da ta sani a wancan lokacin ya kuma rik’e hannunta gam bayan ya dank’awa Tauraruwa yaran yana sakin murmushi. Nene kuwa duk kunya ta bi ta isheta ganin yarda Najwa take kallon cikinta da ya fito sosai haihuwa ko yanzu ko anjima. Niyyar ta ta rungume Nenen sai dai yanayin yarda taga Nenen yasa ta ja baya a kunyace. An ci an sha an kuma yi hidima sosai dafatan Allah ya yiwa yara albarka. Abin al’ajabi a cikin daren dai Nene ta fara nak’uda. Ranar girkinta ne a gigice mai martaba ya kira Tauraruwa da Jakadiya aka kira likitar masarautar su suka karb’i haihuwar Nenen inda ta haifo sankaceciyar yarinyarta mai kama da Tauraruwa. Sarki bayan an kai masa ita yana d’aga ta ya saki murmushi ya furta “Tauraruwa y’ar Tauraruwa Ma sha Allah Allah yasa ki gaji mai sunanki wajen son zumunci da sadaukar da farin cikin ki ga y’an uwanki Allah ya miki albarka…” Duk wanda yake parlourn sai da ya amsa y’ay’a da surikan Sarkin da y’ay’an Tauraruwa su Baffa da su Umma. Tauraruwa ta rungume y’ar a k’irjin ta tana furta “Wannan tawa ce Nene ki gama shayar da ita na karb’i abata kuma Tauraruwa nake son a dinga kiranta….” Murad ya yi murmushi ya ce “Allah yasa kada ta gado fa’danki… Aka saki dariya gaba d’aya. Ma sha Allah Alhamdulillah nagode da jumurin karatu dafatan kuma zaku yafe min idan da wanda na b’atawa a cikin ku. JIKAR NASHE TA KU CE! Don samun litattafaina kai tsaye ku nemeni a wannan numberr 08033748387… https://chat.whatsapp.com/CSyG2rUpE7d9mgJLU8VCzJ In sha Allah littafin KHUL'I zai fara zuwa muku 8/5/2024. Ban sani ba ko zai ƙayatar da ku amma ina ji a raina za ku so shi fiye ma da NAGARTA. Zai ilimantar ya kuma faɗakar kai har ma ya nishaɗantar In sha Allah. Nabeehar Amaan ta na miƙo gaisuwa tare da fatan za ku yi jumurin bibiyar labarinta. Update ba kullum ba ne daga Monday ne zuwa Thursday. Madallah da nagartattun mutane. So domin Allah💞 UMMU AMMARAH✍️