*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣1️⃣* *ALHAMDULILLAH I'M BACK* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Unguwar *Ƙofar fada* dake cikin garin *Kumurya*. Yarinya ce wadda baza ta wuce shekaru goma sha ɗaya zuwa sha biyu ba a duniya take tafiya cikin ƙwaleliyar ranar da ta ƙwalle. Sanye take cikin uniform na makarantar government primary school dake cikin garin. Cikin sauri take tafiyar amma kana ganin yanayinta zaka gane a galabaice take. Ƙafafuwanta duk sun yi fututu cikin ɗan Madina slippers. Wani Babban gida ta shiga mai ɗauke da ɓangarori da dama kamar yadda duk yawancin gidajen garin suke. Bayan ta wuce dogon zauren gidan ta shiga ɓangare na biyu daga b'arin dama da ɗan gudunta tana ƙwala kiran sunan "Inna! Inna." Inna dake duƙe a cikin madafi gaban murhun duwatsu ci tana hura wutar kara wadda ta mutu, gaba-d'aya ta haɗa uban gumi hayak'i duk ya turnik'e ta. Sauri take wutar ta ruru dan ta dafa dankalin Hausa kafin *A'isha* ta dawo daga makaranta, dan ta san da yunwa zata dawo tunda ba wani karin kumallon kirki ta yi ba da safe. Sai dai haƙan ta bai cimma ruwa ba har A'ishan ta dawo, sakamakon wutar data rura ta mutu gashi kuma bata da ashana, guntuwar ta kenan ta yi amfani da ita. *Inna* ta ɗago idanuwanta wanda suka fara rinewa zuwa launin ja saboda hayak'i ta dubi A'isha wadda ta shigo kamar an cillo ta. Cikin ɗan faɗa Inna tana goge idonta da ya fara tara ruwa ta ce. "A'isha ban hana ki gudu da shigowa gida babu sallama sai dai aikin ƙwala mun kira kamar wata sabuwar makauniya ba?" A'isha ta turo ɗan ƙaramin bakinta bata ce komai ba ta koma ta fice daga ɓangaren ta sake shigowa bakinta ɗauke da sallama. Girgiza kai kawai Inna ta yi tare da amsa mata ta cigaba da abun da take yi. Jakar buhun hannunta ta ajiye akan tagar ɗakinsu ƙwaya ɗaya tal dake cikin zagayen nasu sannan ta cire takalminta ta matsa kusa da Inna tana kare fuskarta da hannunta saboda hayak'i ta ce. "Inna sannu da aiki." Inna ta gyaɗa mata kai kawai. A hankali ta ce. "Inna ki kunna masa ashana mana." Inna ta ce. "Ta ƙare ne A'isha, daa da ita ai da tuni na kunna." A'isha da yunwa ke ƙwaƙular hanjin cikinta ta ce. "Bari na aro miki a gurin innarsu Ma'u." Bata jira cewar Innan ba ta yi waje da gudu ko takalmi bata saka ba. Inna tana kiran ta tare da faɗa mata Innar Ma'un bata nan amma bata ma ji ta ba balle ta tsaya. Ɓangaren Innar Ma'u a jikin nasu yake, tana shiga ta tarar da ɗakinta a kulle da ƙaramin ɗan mukulli alamun bata nan. Juyawa ta yi ta shiga ɓangaren dake kallon nasu dan arowa Inna ashanar, duk da ta san zai yi wahala su bata saboda tsanar da suka yi musu ita da innarta, kaf faɗin gidan Innar Ma'u ce kawai take k'aunarsu idan ka cire Marigayi Malam Mijin Inna. A tsakar gidan ta tarar da matan gidan guda biyu, ɗaya tana daka a turmi ɗayar kuma suna zaune akan tabarma ita da wata mata, da alama bak'uwa ta yi dan matar bata yi kala da mutanen garin ba, duba yanayin shigar jikinta gami da buɗewar idonta da uban bleaching ɗin da ta ci. A'isha ta yi sallama tare da gaishe su, babu wanda ya amsa mata sai ma wani matsiyacin kallo data samu daga matan gidan. Matar nan kuma wani irin kallo take bin ta da shi mai kama dana mamaki. A'isha bata damu ba ta dubi wadda ke zaunen ta ce. "Baaba Ramatu dan Allah ki arawa Innata ashana zata kunna wuta." A harzuk'e Ramatu ta ce. "Idan Ubanki ne ko na Asaben ya siya mun ashanar sai ki zo ki ƙwata, shegiyar yarinya kawai." A'isha ta ɓata fuska tare da kallon wadda take daka zata yi magana, sai dai bata ba ta damar hakan ba ta hanyar daka mata tsawa da faɗin. "Fice daga gidan nan dan malafar Ubanki, ita Uwar taki uban wani ya hanata siyan ashanar, zaki kwaso jiki ki taho wai a baki aron ashana, Uwar ashanar za'a baki ba ashana ba." A'isha ta marairaice ta ce. "Dan Allah Baaba Hansai yunwa nake ji kuma wutar ta ƙi......" Zaburowar da Hansai ta yi yasa ta juyawa da gudu ta bar ɓangaren. K'wafa Hansai ta yi ta ce. "Da kin cigaba da tsaiwa ai dana yi ƙasa_ƙasa dake a gurin nan, Mayyar yarinya kawai ta tsare mutane da shegun idanuwanta kamar zata lashe mu." Matar nan data kasa ɗauke idonta daga kan A'isha har sai da ta fice, ta sauke numfashi tare da kallon Ramatu wadda ta bi bayan A'isha da muguwar harara kamar idonta zai faɗo ƙasa, cikin mamaki ta ce. "Ramatu wannan kyakkyawar yarinya fa a ina take?" Ramatu ta tab'e baki cikin baƙin ciki da hassadar an cewa A'isha kyakkyawa ta ce. "Gaskiya Hajiya kin dad'e baki zo garin nan ba, yanzu baki san Mayyar matar da Malam ya auro mana ba shekara fiye da goma?" Hajiya ta ce. "Kin manta Ramatu na yi zaman Saudiyya na shekaru, ai rabona da garin nan na kusa shekara goma sha biyar sai gaisuwar Malam dana zo." Ramatu ta ce. "To kin gan ta nan dai Malam ne ya auro mana jaraba dan Mayya ce." Cikin mamaki Hajiya ta ce. "Mayya kuma?" Ramatu ta ce. "Mayya mana, ban da haka daga ya tsince ta a hanya da shegiyar jaririya a hannu bai san asalinsu ba bai san daga inda suke ba kawai ya saka aka d'aura masa aure da ita ya kawo mana ita cikin gida ya gurɓata mana zuri'a, Ubangiji ma ya so mu da arzik'i bata haihu da shi ba. Ta shanye masa kurwa sai abin da ta ce Malam ya yi yake yi kafin ya rasu, ke in tak'aice miki zance cewa ya yi ko bayan ransa kar ta bar gidan nan, ya bar mata inda take ciki a zaune halak malak tunda shi ya gina abunsa, kin ga kuwa wannan abun ai ba na dan Allah ba ne, ko mu da muke iyayen ƴaƴansa bai yi mana irin wannan kyautar ba sai ita." Hajiya ta jinjina kai tare da sakin wani ɗan murmushi, wani tunani ya ɗarsu a ranta game da A'isha. Ta dubi Ramatu ta ce. "Allah ya kyauta." A'isha kuwa bayan barin ta ɓangaren su Ramatu cikin gida ta nufa tana bi ɓangare_ɓangare tana a ba su aran ashana, duk inda ta je da bak'ar magana da cin zarafi ake koro ta, amma hakan ba ya hana ta ƙara shiga wani gurin ta tambaya, dan ita burinta kawai ta samo ashana ta kaiwa Innarta ta yi ta hura wuta abun da ta ɗora ya dahu ta ci. Jiki a sanyaye ta dawo ɓangaren nasu, ta tarar wutar ma ta ruru Inna tana aikin azawa. Zama ta yi a ƙasa ta fara hawaye. Inna ta dube ta bata ce komai ba ta cigaba da abun da take yi. Tana hawayen ta ce. "Inna a ina kika samu ashanar?" Inna ta ce. "Ban sani ba, ina kiran ki dan iskanci shine kika yi gaba ko?" A'isha ta ce. "Ban ji ba fa Inna, kuma na je Innar Ma'un bata nan, na manta da safe dana biyawa ma'u makaranta ta ce baza ta je ba za su je unguwa." Inna ta ce. "Da kika ga bata nan sai kika je inda ban aike ki ba ko?" Shiru A'isha ta yi bata ce komai ba. Tana nan zaune har dankalin ya dahu Inna ta juye mata duka a roba ta bata, sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko wani guntun k'uli_k'uli ta kawo mata dan ta haɗa ta ci da shi. Cikin sauri_sauri A'isha take cusa dankalin a bakinta tana ci, Inna tana zaune akan langa ta yi tagumi tana kallon ta, tunanin abun da zata yi na sana'a take yi dan zaman nan haka ba zai musu ba, Tunda Malam ya rasu suka shiga taskun rayuwa, abun da za su ci ma wataran gagarar su yake yi. Ta yi sana'oi da dama domin ta samu abun da za su rufawa kansu asiri amma kamar wadda aka sakawa hannu abun ba ya ci, sai ta fara an fara ciniki rumi_rumi Masha Allah sai abun ya lalace, wataran idan ta yi abun sai dai su cinye ta rabar da guntun dan ko na biyar babu wanda zai zo ya ce a ba shi. Ta rasa ma ina zata saka ranta...... "Inna gashi na ƙoshi ke ma ki ci." A'isha data ajiye mata guntun dankalin a gabanta ta katse mata tunani da faɗin haka. Inna ta sauke numfashi tana kallon kwanon dankalin ta ce. "Har ya ishe ki?" A'isha ta ce. "Eh na ƙoshi Inna." Inna ta sauke numfashi ta ce "Ɗauko murfi ki rufe kya ci anjima." A'isha data nufi gurin randa dan ɗiban ruwa ta sha ta ce. "Inna ki ci mana." Inna ta girgiza mata kai kawai bata ce komai ba. A'isha ta ɗibi ruwan ta sha ta yi hamdala sannan ta shiga ɗaki ta cire uniform ɗin jikinta ta zira kayan gida ta fito tsakar gida. Inna ta dube ta ta ce. "Ga ruwa nan akan wuta na ɗora miki, idan ya yi d'umi sai ki juye ki yi wanka kafin ki tafi karatun, ki je ɗaki zaki ga Naira goma a kan window, ki ɗauko ta sai ki ɗauki botikan can ki kai ki saka mana a layin fanfo, zan zo in ɗauka idan an zuba ruwan." A'isha ta turo baki gaba ta ce. "Inna da safe fa kafin na tafi boko na yi wanka, kuma yanzu in ƙara sakewa?" Inna ta ce. "Zaki yi abun da na ce ne ko kuwa?" Kamar zata yi kuka ta koma ɗaki ta ɗauko kuɗin ta fito ta sungumi bokatan guda biyu ta fice. Miƙewa Inna ta yi ta shiga ɗaki ta kwaso uniform ɗin da A'isha ta cire ta fito da su dan ta ɗauraye mata su bayan rufe guntun dankalin da A'ishan ta rage. Gurin ɗiban ruwan a cike yake da mutane ƴan ɗiban ruwa yara da manya, mata da maza. Tunda A'isha ta ga haka ta ɓata fuska, dan ta tsani duk abun da zai haɗa ta da taron mutane a cikin garin, domin ta san baza su taɓa gwanyewa lafiya ba, tunda babu mai k'aunar su a cikin garin sai waɗanda baza a rasa ba, dan ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba, shi yasa bata k'aunar Inna ta turo ta gurin fanfon nan. Kasancewar garin suna da wahalar ruwa yasa aka yi tanki a wajen gidan mai gari, to duk mutanen dake kusa a nan suke ɗiban ruwa, shi yasa kusan kodayaushe gurin a cike yake da mutane. Kanta a ƙasa ta ƙarasa ta je gurin wanda ake bawa kuɗin ruwan ta gaishe shi tare da ba shi kuɗin. Ya amsa mata tare da karɓar kuɗin sannan ya nuna mata ƙarshen layi ya ce ta je ta saka buckets ɗinta. Bata yarda ta kalli kowa ba a gurin ta ƙarasa ta ajiye bokitan a hankali, duk da yanda kusan kowa na gurin yake kallon ta. Ta koma gefe ta tsaya kafin layi ya zo kanta. Mintuna biyu da tsayiwarta ta ji tsayuwar mutum a gaban ta, ko da ba'a faɗa mata ta san waye, Ɗan_juma ne ɗan gidan Mai gari, matashin Saurayi mai tashe a cikin garin, wanda bai da kirki da mutunci ko kaɗan, tun A'isha tana ƴar ƙaramarta ya takurawa rayuwarta, shi a dole son ta yake yi. Ɓata fuska sosai A'isha ta yi tare da kawar da kanta gefe. Ɗan_Juma ya riƙe k'ugu ya ce. "Ke! Dan na zo gurinki shine zaki wani kawar mun da kai kina wani ciccin magani, eye? A'isha ta watsa masa harara ta ce. "To Ni ina ruwana da kai, ba Innata ta ce karka ƙara kulani ba?" Ɗan_juma ya yi wata ƴar dariya ya ce. "Babu wanda ya isa ya hana ni kula ki A'isha duk garin nan wallahi, na gani kuma na yaba dole na samu, lokaci kawai nake jira ki ƙara girma a sha bikinmu." Turo baki A'isha ta yi ta ce. "To ni bana son ka, Allah ya sauwak'e na aure ka, kuma kar ka ƙara kula ni." Ɗan_juma ya haɗe rai sosai ya ce. "Ke! dan ma kin samu zan taimaka in aure ki shine kike faɗa mun magana? Wace ce ke?" A'isha ta murgud'a masa baki ta ce. "Mutum ce ni ƴar mutuwa jikar rasuwa kakar jana'ida." Kasancewar da ƙarfi Ɗan_juma yake magana yasa hankalin mutanen gurin gaba-d'aya ya dawo kansu. Wata budurwa ce wadda baza ta wuce 16 years ba ta ƙaraso inda suke tana faɗin. "Ni wallahi Ɗan_Juma na rasa me ka gani a jikiy wannan ƙwailar *MAYYAR* Yarinyar ka na ce mata haka, yarinyar da *SHEGIYA* ce *MARA ASALI*, ga mu nan ƴanmata birjik a cikin garin nan sai ka zaɓa ka darje amma ka bi ka lik'e mata." Ta ƙarasa zancen tana karkad'a ƙirji tare da jifan A'isha da wani mugun kallo. A kufule A'isha ta dube ta, ta ce. "Ke Hindu kar ki ƙara ce mun Mayya ko shegiya, ni ba Mayya ba ce kuma ba Shegiya ba ce." Kamar Hindu zata kai mata duka ta ce. "An faɗa ɗin Shegiya Mayya me zaki yi mun? da mece ce ke idan ba mayyar ba, kuma idan ke ba Shegiya ba ce waye Ubanki a cikin garin nan?" A'isha ta fashe da kuka ta ce. "Wallahi ni ba Mayya ba ce, kuma Baba Malam shine Babana.".........✍️ _*Tafiyar fa mai nisan zango ce, Allah ya bani ikon yin posting kullum🥹*._ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣2️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Wata ƙundular baƙar yarinya ce ta yi tsalle ta dire a gaban su A'isha, ta ce. "K'arya kike mu Baba Malam ɗinmu ba shine Babanki ba, ki je can ki nemi Ubanki a wani gurin." Hindu za ta kuma magana Ɗan_Juma ya katse su cikin tsawa da faɗin. "Ubanwa ya ce ku sako mun ƙazamin bakinku da ya jik'u da miyar kuka a cikin maganata?" Tsit su Hindu suka yi suna hararar A'isha ta ƙasan ido tare da jijjige_jijjigen jiki. Wata tsawar Ɗan_Juma ya ƙara daka musu ya ce su b'ace masa daga gani, sum_sum suka juya suka bar wajen. A'isha da har lokacin kuka take yi ta juya ta yi hanyar gida da gudu. Inna tana cikin wankin uniform ɗin A'isha ta gan ta, ta shigo kamar an jefo ta tana gunjin kuka. Kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kanta ta cigaba da abun da take yi. Shigewa ɗaki A'isha ta yi ta faɗa kan gadon ƙarfen dake ɗakin ta ƙara fashewa da kuka. Tun tana ƴar mitsitsiyarta take jin ana jifan su da miyagun kalamai ita da Innarta, tun bata san ma'anar kalaman ba har ta sani ta hanyar tambayar wani malaminsu a makaranta ya yi mata bayani, dan idan zata kwana tana tambayar Inna baza ta taɓa ce mata komai ba akan al'amarin. Bayan Inna ta gama wankin ta zira Hijabinta ta je ta ɗauko ruwan ta dawo. Ɗaki ta shiga dan taso A'isha wadda ke kuka har lokacin. Tana kallon ta, ta ce. "Taso ki yi wankan kar lokaci ya ƙure." Bata ce komai ba ta miƙe tana goge hawayen fuskarta ta fara cire kayan jikinta. Inna ta bi ta da kallo, kamar zata yi magana sai kuma ta fasa. Bayan A'isha ta yi wankan ta wanke bakinta da gawayi ta yi alwala ta yi Sallah ta shirya ta tafi gidan wata mata wadda suke karatun addini a gurin ta. A can ma yara sun so tsokanar A'isha tare da neman ta da faɗa kamar yadda suke mata kodayaushe amma sai Malamar ta tsawatar musu. Bayan an tashi daga karatun Malamar bata bar A'isha ta tafi ba sai da sauran yaran suka jima da tafiya, gudun kar su tsokane ta su yi faɗa a hanya. Washegari bayan Sallar Asuba A'isha tana zaune a inda ta yi Sallah tana bitar karatun Alkur'anin da aka yi musu jiya kamar yadda ta saba kodayaushe, Inna kuma tana kan Sallaya tana lazimi. A zahiri carbin hannunta take ja, amma a cikin zuciyarta tunani take yi, tunanin abun da zata bawa A'isha ta ci kafin ta tafi makaranta take yi, domin yau ta tashi bata da komai a gidan kuma bata da ko sisin kwabo wanda zata bata ta siyo abun karyawa. Jiya da yamma ma haka ta wuni cikin wannan tunanin da zullumin, sai kuma Ubangiji yasa Innar Ma'u ta aiko mata da rama mai ɗan yawa bayan ta dawo daga unguwar da ta je, ita ta samu ta kwad'anta musu suka ci da daddare ita da A'isha. Ganin gari ya fara haske A'isha ta dubi Inna ta ce. "Inna zan je fa makaranta yau." Dogon numfashi Inna ta sauke ta ce. "Na sani A'isha, me ya faru?" A'isha ta ce. "Na ga baki hura wuta ba ne." Inna ta ce. "Yanzu zan hura, ki share ɗakin kafin na gama." A'isha ta ce. "Toh." Miƙewa Inna ta yi ta cire hijibin jikinta ta fice daga ɗakin. Bayan A'isha ta gama gyaran ɗakin ta fito ta tarar Inna har ta haɗa mata ruwan wanka. Da mamaki ta dubi Inna ta ce, "Inna har kin dafa ruwan zafi?" Inna ta ce. "Zama zan yi in jira ki ai ki gama ƙailularki, gyaran ɗaki kawai kin shafe kusan mintuna talatin." A'isha ta turo baki ta ce. "Kai Inna duk saurin da na yi amma ki ce na dad'e?" Inna ta ce. "Kar ki shiga wankan tsaya zance." Bata kuma cewa komai ba ta shige ɗan ƙaramin bayin nasu. Inna tana zaune ta yi tagumi da hannu bibbiyu cikin rashin sanin mafita, ta san A'isha tana fitowa daga wanka abinci zata fara buƙata. Shawara ta yanke zata je gurin Innar Ma'u ta ari Naira Ashirin ta siyowa A'isha koko kafin ta fito daga wanka. Kafin ta kai ga miƙewa Ma'u ta shigo zagayen nasu bakinta ɗauke da sallama. Inna ta amsa mata, Ma'u ta ce. "Ina kwana Inna." Inna ta ce. "Lafiya ƙalau, mun tashi Ma'u ya Innar taki?" Ma'u ta ce. "Tana nan ƙalau." Tana ajiye kofin robar hannunta da wani ɗan k'ullin leda ta ce. "Gashi in ji Innata wai babu yawa." Inna ta kalli kayan sannan ta kalli Ma'u ta ce. "Kai, Ladidi bata gajiya da abun arzik'i dai, to ki ce mata na gode sosai kin ji Ma'u, Allah ya saka da Alkhairi." Ma'u tana murmushi ta ce. "Indo ce take wanka?" Inna ta ce. "Ita ce." Ma'u ta juya tana faɗin, "Bari na je nima na shirya kar ta riga ni." Inna ta ce. "To Ma'u ki ce mata na gode sosai." Ta ƙarashe zancen tare da sakin ajiyar zuciya tana yin hamdala ga Ubangiji a cikin zuciyarta. Ita kam babu abun da zata ce da Innar Ma'u akan irin taimakon su da take yi sai dai Allah ya saka mata da Alkhairin sa kawai. Kayan ta shiga dubawa ta ga kunun tsamiya ne a cikin kofin, k'ullin ledar kuma fanke ne. Dai-dai nan A'isha ta fito daga wankan, tana duban Inna ta ce. "Inna kamar murya Ma'u na ji da ina Wanka." Inna ta ce. "Ita ce ta shigo." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ba ta shirya ba ko? Salon ni na gama shirina ta makarar da Ni?" Inna ta ce. "Sai ta shirya ma kina nan kina shirita ke baki shirya ɗin ba, ga kunu da fanke nan Innarta ta aiko mana, idan kin biyawa ma'u makaranta sai ki yi mata godiya." A'isha ta yi murmushi ta ce. "Toh Inna, bari na wanke bakina na zo na ci." Ƙarfe takwas da mintuna su A'isha suka fito daga ɓangaren su Ma'u dan tafiya makaranta. Suna sanye cikin uniform ɗinsu white and blue, wanda ya kasance fess da shi babu datti, duk da babu guga a jikinshi amma bai yamutse ba. Suna tafe A'isha tana ta yiwa Ma'u mitar ta makarar da su. Ma'u ta ce. "Kai Indo, yanzu ma fa idan mun je makarantar nan babu kowa, duk ba'a fara zuwa ba, kullum fa mu muke fara zuwa kin sani." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Wai bana ce miki bana son Indon nan da kike ce mun ba, ni sunana A'isha, ki daina ɓata mun suna, ehe." Ta ƙarashe zancen tana hararar Ma'u. Dariya Ma'u ta yi ta ce. "Ai na faɗa miki kema sai kin daina ce mun Ma'u kin koma ce mun Asma'u sannan nima zan daina ce miki Indo." A'isha ta ce. "To aike haka kowa yake ce miki dama, ni kuwa ke kaɗai kike ce mun Indo, wai Indo? Sai ka ce wata tsohuwa." Dariya kawai Ma'u ta yi bata ce komai ba. Dai_dai nan suka ƙaraso ƙofar gidan Mai_ gari, Ɗan_juma dake tsaye a cikin soron gidan da waya a hannunsa yana latsawa ya fito ya sha gaban su, dama ita yake jira ta zo wucewa. Wani uban tsaki A'isha ta ja ta kama hannun Ma'u da nufin su sauya hanya amma sai ta ji an fizgo hijabinta. Ta juyo a fusace tana ƙoƙarin k'wace hijabinta daga hannun Ɗan_juma ta ce. "Me ne haka?" Ɗan_juma ya ce. "Na lura yarinyar nan kullum ƙara raina ni kike yi saboda na ce ina son ki ko?" Cikin tsiwa A'isha ta ce. "An raina ka ɗin, kuma ni ka sakar mun Hijab ɗina, dan ni ba ƴar iska ba ce da Namiji zai riƙe mun Hijabi." Ɗan_juma yana bin ta da wani shegen kallo ya ce, "Hmm yaro man kaza." Sannan ya yi wani murmushi ya sakar mata Hijabin. Da sauri Ma'u ta ja ta suka yi gaba, A'isha ta juyo ta ce masa. "Kuma Allah ya isa na." Sannan ta juya suka cigaba da tafiya. Murmushi Ɗan_juma ya ƙara saki yana bin bayan ta da kallo tare da lasar leb'ensa na ƙasa, zuciyarsa na ƙara tunzura shi akan mummunan k'udirinsa akan A'isha. A fili ya ce. "Ki jirayi ranar da zan fanshe dukkan wulaqanci da tsiwar da kike mun A'isha, Ni Ɗan_juma kaf cikin garin nan babu wanda ya isa ya taba ni ya zauna lafiya, balle kuma ke mara asali da galihu, wadda ko me na yi miki baki da wanda zai ɗaukar miki matakin komai." Yana gama faɗin haka ya juya ya shige cikin gida still fuskarsa ɗauke da murmurshin da shi kaɗai ya san ma'anarsa...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣3️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Bayan Sun ɗan yi nesa da gidan Mai_gari Ma'u ta dubi A'isha wadda ke ta huci ta ce. "Kin ga A'isha ki daina yiwa Ɗan_Juma tsiwa, ni ina tsoron kar wataran ya yi miki shegen duka, kin san halinsa fa." Tsaki A'isha ta yi ta ce. "Tab'dijan, sai ka ce wata ƴarsa zan zauna ya dake Ni, wallahi ya yi kaɗan." Ma'u bata kuma magana ba har suka ƙarasa makarantar. Kamar yadda Ma'u ta faɗa babu wanda ya zo sai mai_gadi wanda shine yake buɗe Makarantar, su ne na farkon zuwa. Bayan sun shiga ajinsu suka ajiye jakunku nansu suka shiga sharar ajin, dama kullum su suke yin sharar. Sai da ƙarfe tara ta wuce sannan sauran yara suka fa zuzzuwa da Malaman Makarantar. A'isha suna zaune akan desk ita da Ma'u wata yarinya wadda baza ta wuce sa'ar su ba ta zo ta tsaya a gaban A'isha, cikin tsiwa da neman faɗa ta ce. "Matsa zan wuce in zauna." A'isha ta kalli Ma'u dake jikin bango sannan ta kalli yarinyar ta ce. "Ina kuma zaki shige Kandala? Bayan ga guri a nan?" Ta ƙarashe zancen tana nuna mata gefenta inda babu kowa. Kandala ta ce. "Inda kike zaki matsa mun in zauna mana." Kallon sama da ƙasa A'isha ta yi mata ta ce. "Sannu Inna." Daga haka ta ɗauke kanta bata kuma magana ba, dan ba ta san su yi faɗa, saboda kullum kafin ta fito daga gida sai Inna ta gargad'e ta akan ko an tsokane ta kar ta biyewa kowa balle su yi faɗa. Kandala da dama neman tsokana ne ya kawo ta, ta ce. "Kar ki matsa ɗin, banza kawai, shegiya Mayya." Da sauri Ma'u ta dube ta, ta ce. "Haba Kandala mene ne haka?" Hararar Ma'u Kandala ta yi ta ce. "Malama ban saka baki da ke ba, ke dama ai sun riga sun gama cinye kurwarku ke da Innarki, shi yasa komai ta yi ba kya ganin lefin ta." Miƙewa tsaye A'isha ta yi ta ce. "Kar ki ƙara ce mun Mayya ke Kandala." Cikin ɗaga murya Kandala ta ce. "An faɗa ɗin Mayya ce ke mara Uba, Shegiya sai me?" Sauran ƴan aji suka tattaso suka ƙaraso gurin dan bawa idonsu abinci, Kandala ta dube su ta ce a bugawa A'isha gangar Shegiya Mayya. Nan fa yara suka fara buga desk da jarkokin ruwansu suna yiwa A'isha ihun Mayya da SHEGIYA cikin waƙa. Komawa A'isha ta yi ta zauna tare da toshe kunnuwanta da hannayenta saboda yanda ihun da suke yi yake shigar mata har cikin kai. Wasu Hawaye masu zafi suka fara zuba akan kuncinta, kusan kullum idan ta zo makarantar sai an yi mata wannan ihun aka, duk da yanda ko an tsokane ta bata kula mutum saboda gudun hakan, amma ba sa ƙyale ta Yaran. Cikin tausayawa Ma'u ta rungumo ta jikinta tana bata haquri. Shigowar wani Malami ce tasa yaran suka yi tsit bayan ya daka musu tsawa tare da buga ƙofa. A fusace ya ce. "Kowa ya nemi guri ya zauna." Bayan sun zauna ya dube su ya ce. "Ihun Uban me kuke mana a aji? Duk kun cika mana makaranta da hayaniyarku." Ma'u ce ta ce. "Malam Kandala ce ta ce su yiwa A'isha ihun Mayya da SHEGIYA." Sai a lokacin Malam Buba ya dubi A'isha wadda ke kuka sosai ya ce. "Ina Kandalar take? Ta miƙe tsaye." Kandala ta miƙe tana cuccuna baki gaba kamar bakin tulu, Malam ya ce ta fito gaban allo ta yi kneel down ta rufe ido, sauran Yaran ma ya saka su yin haka amma su kowa a inda yake zaune, ban da A'isha da Ma'u. Sannan ya rarrashi A'isha ya bata baki ta yi shiru ta bar kukan da take yi. Gaban allo ya koma ya ce. "Dama abun da ya kawo ni na zo ne in sanar muku za'a ɗauki mutum uku masu ƙoƙari a cikin ajin nan wanda za su zana common entrance tare da ƴan aji Shida." Kasancewar su A'isha a Primary 5 suke. Nan fa yara suka fara murna kowa yana fatan a ɗauke shi. Malam Buba ya karanto sunan Yara Ukun ciki har da A'isha. Wannan abun ya yayewa A'isha damuwar ihun da ƴan ajin suka yi mata, sai su gata suna ta tsalle da murna ita da Ma'u. Bayan an tashi daga makaranta sun koma gida A'isha ta tarar Inna bata nan, ko uniform bata cire ba ta fara duban abinci ko Inna ta girka ta ajiye mata amma bata ga komai ba. Zama ta yi a tsakar gida tana jiran dawowar Inna, sai dai har Ma'u ta biyo mata zuwa gidan Malama karatu Inna bata dawo ba, haka ta tashi ta shiga ɗaki ta canza kaya suka tafi karatun yunwa na ƙwaƙular hanjin cikinta. Sai Yamma suka dawo, zuwa lokacin yunwa ta fara galabaitar da A'isha. Inna tana wankin kayan sakawarsu A'isha ta shigo da sallama can ƙasan mak'oshi. Inna ta amsa mata tare da bin ta da kallo. A'isha ta turo baki ta ce. "Inna Ina kika je? Na dawo na tarar ba kya nan." Inna ta ce. "Sabon Gari na je." Ba ta jira cewar A'ishan ba ta tsame hannunta daga cikin ruwan wankin ta shiga ɗaki ta ɗaukowa A'isha k'uli_k'uli mai gishiri da awara ta bata. Da murna A'isha ta karɓa ta ce. "Inna yau yunwa ta kusa kashe ni fa." Inna ta ce. "Tunda bata kashe kin ba sai ki yiwa Allah godiya." Bayan A'isha ta gama cin awarar da k'uli_k'ulin ta sha ruwa ta dubi Inna ta ce. "Inna Ina son in tambaye ki wani abu." Inna ta ce. "Ina jin ki." A'isha ta ce. "Dan Allah Inna da gaske Baba Malam ba shine Babana ba? Kuma ba mu da asali?" Haɗe rai Inna ta yi ta ce. "Ba na ce kar ki ƙara mun wannan tambayar ba A'isha?" Cikin raunin murya A'isha ta ce. "Inna ki yi haquri kin faɗa mun, amma Inna ke baki da qani ne ko Yaya ko k'anwa kamar Innar Ma'u? Kin ga ita suna zuwa Kano gurin ƙaninta, kuma suna zuwa Sanda gidan Inna larai k'anwarta, amma mu ba ma zuwa gidan kowa." A'isha ta ƙarasa Maganar cikin raunin murya. Shiru Inna ta yi gabanta na fad'uwa, a ranta tana faɗin. Tun yanzu A'isha ta fara tambayar ta wani nasu? ina ga ta ƙara girma da wayo ta san me duniya take ciki? Tabbas dole ta yiwa tufkar hanci tun yanzu, ta kuma san me zata faɗawa A'isha wanda zai kwantar mata da hankali. Ganin Inna ta yi shiru cikin raunin murya A'isha ta kuma cewa. "Dan Allah Inna mu ma muna zuwa gurin ƴan'uwanmu a daina ce mana marasa asali." Sosai tausayin A'isha ya cika zuciyar Inna, ta san dole abun ya dame ta duk da kasancewarta yarinya, ko dan yanda mutanen gari suke muzanta_ta akodayaushe. Tasowa Inna ta yi ta dawo gaban A'isha cikin sanyin murya ta ce. "A'isha! INSHA ALLAHU watarana zamu je gurin ƴan'uwanmu mu ma kamar kowa, kin ji?" Hawaye A'isha ta fara ta ce. "Yaushe Inna? Mu je gobe mana." Inna ta girgiza kanta ta ce. "Inda suke ne da nisa A'isha, sai na tara mana kuɗin Mota, Nima ina son mu je ɗin, amma mun kusa zuwa insha Allahu." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Inna ta ce. "Jiya da kika je ɗiban ruwa me aka yi miki kika dawo da kuka?" A'isha ta ce. "Ce mun aka yi MAYYA SHEGIYA a gurin, yau ma a makaranta an mun ihun haka a aji." Kama hannunta Inna ta yi cikin lallami ta ce. "Ki yi haquri A'isha, duk abun nan da ake yi miki ni na jawo miki, amma insha Allahu komai zai wuce, duk wannan abubuwan da ake yi mana sai sun zamo tarihi, watarana komai zai wuce da yardar Allah, KOMAI NISAN DARE gari zai waye A'isha, ki ƙara hakuri." A'isha ta ce. "Shikenan Innata." Inna ta ce. "Yawwa A'ishana, share hawayen naki ki tashi ki dauraye mana kwanikan can kafin a kira Sallah." A'isha ta miƙe ta ce. "Toh." Inna ta bi ta da kallon tausayi kafin ta miƙe ita ma. Daren Yau Inna bata rintsa ba, tunanika kala_kala ta kwana tana yi. Na farko tana tunanin yanda rayuwarsu zata kasance nan gaba a halin da suke ciki, na ƙyara da nuna musu tsana ƙarara da mutanen gari ke yi. Na biyu kuma halin babu da suke ciki, dan yau ma gidan wata mata da suke mutunci ta je a can unguwar Sabon gari ta taya ta aikin k'uli_k'ulin da Matar take yi na siyarwa, shine ta samu matar ta bata k'ulin da ɗan Kuɗi wanda a cikinsa ta siyowa A'isha awarar da ta bata ta ci, ita kuma a gidan matar ta ci abinci. Washegari da zazzaɓi da ciwon kai A'isha ta tashi, sai Inna ta danganta hakan da kukan data ce mata ta yi ne a makaranta da kuma zaman da ta yi da yunwa bata ci abinci ba Jiya. Ƙarfe Bakwai na safe Inna ta fita ta siyo mata koko da k'osai ta dawo. Tabarma ta shimfid'a a tsakar gida ta ɗauko A'isha ta kwantar da ita a kai. Inna tana taɓa goshinta ta ce. "Jikinki ya yi zafi sosai A'isha, tashi ki sha kokon nan ko yaya ne, anjima sai in siyo miki magani ki sha." Girgiza kai A'isha ta yi tare da lumshe idanunta. Inna ta ce. "Daurewa zaki yi ki ɗan kurb'a, ai ba zai yiyu ki zauna baki saka komai a cikinki ba." A'isha tana taune lips ɗinta ta miƙe daƙyar ta zauna ta jingina bayanta da jikin bango. Inna tana zuba mata sugar a cikin kokon ta ce, "Sannu, Allah ya sauwak'e." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. A baki Inna ta bata kokon ta yi kurb'a ɗaya ta kau da kai, Inna ta ce ta daure dai ta ƙara sha. Tana ƙara kurb'a sai kakarin amai, kafin ta yunk'ura ta miƙe har ta fara aman a gurin. Inna ta riƙe ta tana jera mata sannu cikin tausayawa. Bayan ta gama Inna ta dauraye mata fuska da baki ta cire mata rigar jikinta da ta ɓaci da amai. Cikin Muryar marasa lafiya A'isha ta ce. "Inna ki mayar da ni ɗaki ki lullub'e ni sanyi nake ji sosai." Inna ta ce. "Toh." Sannan ta kama ta, ta kai ta ɗakin ta kwantar da ita, cikin ikon Allah sai bacci ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta fito tsakar gida ta fara ɗan ayyukan gida, jikinta duk ya yi sanyi da yanda ta ga jikin A'ishan. Da Ma'u ta biyo mata makaranta Inna ta sanar da Ma'un baza ta samu damar zuwa ba, bata jin daɗi, Ma'u ta shiga ɗaki ta duba ta sannan ta yi mata addu'ar samun sauƙi cikin tausayawa. Wajen ƙarfe goma na safe har lokacin A'isha tana ɗaki tana bacci, Inna kuma tana tsakar gida tana karyawa aka yi sallama a zagayen nasu. Inna ta amsa tare da duban Matar da ta shigo, duk da ba ta taɓa san ta ba amma ta tarb'e ta cikin fara'a tare da bata gurin zama. Bayan sun gaisa Matar ta ce. "Na san baki gane ni ba ko?" Inna ta ce. "Gaskiya, dan zan iya cewa ma ban taɓa ganin fuskarki ba." Matar ta yi murmushi ta ce. "Haka ne, Nima ban taɓa ganinki ba sai yau, kuma na zo gurinki ne da wata samuwa da nake fatan zaki karɓe ta hannu bibbiyu." Inna ta ce. "Samuwa kuma? Wacce iri?" Matar ta gyara zama ta ce. "Da farko dai Sunana Hajiya Kareema, Ni mazauniyar ƙasar Saudiyya ce a can nake kasuwanci na." Inna ta jinjina kai tana ƙara bin matar da kallo, a ranta tana mamakin dalilin zuwanta gurin ta. Matar ta cigaba da magana da faɗin. "Shekaran jiya na zo nan gurin Ramatu abokiyar zamanki, sai yarinyarki A'isha ta shiga zagayen su, anan na gan ta, dalilin zuwana ma gurinki a yanzu saboda ita ne." Inna ta ce. "To, Allah yasa ba wani abun ta yi miki ba?" Hajiya kareema ta girgiza kai tana bin zagayen su Inna da kallo sannan ta ce. "Na zo ne in tallata miki wata hanya ta samuwa kamar yadda na faɗa miki tun farko, duba da yanayin talauci da k'uncin rayuwa da kuke ciki na ji ina son in taimake ku." Inna ta ce. "Taimako kuma wanne iri?" Hajiya Kareema ta tauna cingum ƙas_ƙas sannan ta ce. "Yarinyarki A'isha zaki bani in tafi da ita Saudiyya komawar nan da zan yi ta nemar muku kuɗi a can, cikin ƙanƙani lokaci zaki ga kakarku ta yanke saƙa kun yi bankwana da talauci, zaku samu kuɗi sosai wanda zai isa ku bar wannan ƙauyen ku fita duk inda kuke so a cikin birni ku gina gidanku na zamani, ku ji daɗin rayuwarku. Musamman ma da ya kasance A'isha kyakkyawa ce gata da ɗan dumurmur ɗin jiki za'a amfana da ita sosai" Ta ƙarashe zancen tare da sakin wani irin murmushi............✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣4️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Baki buɗe Inna ta shiga bin Hajiya Kareema da wani irin kallo mai kama da na baki da hankali, kafin ta daure zuciyarta ta ce. "Ban gane ba Hajiya? Ƴar tawa guda ɗaya tal zan baki ki tafi ita da Saudiyya? Ban san ki ba ban taɓa ganin ki ba, ban kuma san daga inda kike ba." Hajiya Kareema ta yi murmushi ta ce. "Ai ba haka sakaka zaki bani ita na tafi da ita ba, komai a rubuce za'a yi shi da shaidu da saka hannun hukuma, kuma ƴaƴana suna cikin garin nan da zama zan kai ki har inda suke ki gani, balle ki ce zan gudar miki da ƴa ne." Inna ta ɓata fuska ta ce. "To ita A'isha ƴar ƙanƙanuwa da ita neman kuɗin me zata iya yi?" Hajiya Kareema ta ce. "Sana'a mana, ga sana'o'i nan kala_kala a ƙasar Saudiyya na samun kuɗi." Murmurshin takaici Inna ta yi ta ce. "Amma a sana'ar ne na ji kin yi maganar ko dan kyan A'isha za'a amfana da ita, wacce irin sana'a ce da take da haɗi da kyau ko wani yanayin halittar jikin Mutum?" Hajiya Kareema ta ɗan taɓe baki ta ce. "Aa, ai a komai na duniya an fi son abu mai kyau Ko? Ko abu take saidawa sai a siyi nata ai kafin a siyi na munana, ni haka nake nufi ba wani abun ba." Murmurshin takaici Inna ta ƙara yi ta ce. "Haba Hajiya, ba fa Yarinyar goye ba ce ni ko kuma wadda aka haifa yau da ban san takan duniya ba, karki ganni haka a ƙauye ki yi tunanin ban san me nake yi ba, na san sarai me kuke yi a Saudiyyan idan kun je." Hajiya Kareema ta ɓata fuska ta ce. "A'a Tsohuwa karki yi mun wata fassarar daban, samuwa ce fa kawai na zo miki da ita." Inna ta haɗe rai sosai ta ce. "To na gode, amma ba zan iya ba, ƴar tawa guda ɗaya tal a duniya zan tura ta yawon aikatau wata ƙasar? To bazan iya ba gaskiya." Hajiya Kareema tana yi mata wani shegen kallo ta ce. "Taimakon ki na zo yi fa ba wani abu ba, in kuma fitar dake daga wannan k'angin talaucin da kike ciki." Inna ta ce. "Allah ne zai fitar da ni, kuma Ni ban ce ina neman taimakon kowa ba bayan na Ubangiji na." Hajiya Kareema ta miƙe ta saɓi Jakarta ta ce. "Ai dama an ce kare bai gaji arzik'i ba, sai da aka mun bayanin halinki amma na dage sai na zo, ni uwar son gwaninta." Inna ba ta kuma yi mata magana ba. Ta zira takalminta sannan ta ɗauko wani ɗan kati daga cikin Jakarta ta ajiye a gaban Inna ta ce. "Gashi nan, idan kin yi shawara daga baya in kin ga kina da interest akan abun da na zo miki da shi sai ki neme ni, ga Numbern wayana nan a jikin katin, kya kira ni." Daga haka ta juya ta fice daga zagayen. Bin ta da kallo kawai Inna ta yi, ita abun ma mamaki ya bata ba kaɗan ba, ta dinga tambayar kanta me yasa duk mutuncin da suke yi da Ramatun bata kai ƴaƴanta ba sai ta_ta ƴar? Ko da yake bata sani ba ko har da su zata tafi. Miƙewa ta yi ba tare da ta bi ta kan katin da matar ta ajiye ba ta shiga ɗaki, gurin A'isha ta je ta taɓa goshinta dan jin yanayin jikin nata, har lokacin A'isha baccinta take sha. A fili Inna ta ce. "Ƴar wannan Yarinyar da ba ta fi shekara goma sha biyu ba ita ake tunanin akai Saudiyya aikatau?" Ta ja ɗan ƙaramin tsaki a ranta tana jinjina wannan haukan, dan ita rashin hankali kawai ta ɗauki batun. Wunin yau gaba-d'aya A'isha a kwance ta yi shi cikin ciwo, gashi ta ƙi cin komai, Innar Ma'u har ɗan wake ta yi mata ta kawo sanin da ta yi tana k'aunar ɗan_waken amma ta kasa ci. Inna ta siyo mata paracetamol da Panadol, su dai an samu ta sha daƙyar bayan Inna ta yi yaƙi da ita. Hankalin Inna fa ya tashi ganin yanayin jikin A'isha, gashi bata da kuɗi balle ta kai ta chemist a yi mata allura. Wasa_wasa sai da A'isha ta yi kwana Uku a kwance amma jikin sai godiyar Allah kawai, dan Jiya I yau yake. Mutanen gida sai lok'owa suke suna yadawa Inna Habaici, wai sun kama ƴar wani ne abun ya dawo kansu, Inna dai ba ta tanka musu, ko kallon inda suke ma bata yi. Yau Lahadi, da Hantsi Inna suna zaune a tsakar gida ta shimfid'e A'isha akan tabarma tana goga mata ruwa da tsumma a jikinta saboda yanda jikin nata ya yi zafi sosai. Innar Ma'u ce ta shigo zagayen nasu bakinta ɗauke da sallama. Inna ta amsa mata tare da faɗin. "Maraba lale, sannunki da zuwa." Innar Ma'u ta amsa da "Yawwa." Tare da zama a gefen tabarmar da Ma'u take kai. Cikin alhini tana kallon yadda A'isha ta rame da ce. "Sannu A'isha, ya jikin naki?" Inna ta ce. "Da sauƙi Alhamdulillah, amma jiya ba mu yi bacci ba tana ta complain ɗin kanta na yi mata ciwo sosai." Innar Ma'u ta ce. "Allah ya ƙara sauƙi, amma da kin kai ta chemist ɗin Isma'il anjima ya duba ta, wataƙila zazzaɓin cizon sauro ne fa ya kamata." Inna ta ce. "Bana jin shine Ladidi, kin ga ai garin nan ba mu da sauro." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne, amma duk da haka ki kai ta ya duba ta." Inna ta ce. "Da cewa na yi gobe zan yi asubanci in je in tsinko mata gayye in yi mata sirace ko Allah zai saka a dace." Innar Ma'u ta ce. "To ki gwada yi mata, Allah ya bada lafiya." Inna ta ce. "Amin ya Allah." Washegari kuwa Inna kamar yadda ta faɗa ta ce ta karb'o gayyayyaki ta zo ta yiwa A'isha surace. Ba wai son kai ta chemist a duba ta ne ba ta son yi ba, kuɗin da zata biya ne ba ta da shi. Dan tunda A'isha ta fara ciwo a wurin Innar Ma'u take rantar ɗan kuɗin da suke kashewa, da yake ita Innar Ma'u tana siyar da kayayyaki, kuma ƙaninta dake zaune a cikin Kano yana da hali, yana yawan yi mata aiken kuɗi akai_akai. Duk da Inna ta yiwa A'isha surace amma jikin dai jiya i yau still. Dole Inna ta ranci 500 ba don ta so ba takai A'ishan chemist aka yi mata allura ta kwana biyu, da wannan ta samu jikin nata ya fara yin ɗan dama_dama har take iya magana, saɓanin daa da sai dai kallo da ido. Ranar Juma'a wanda ya kama kwanan A'isha goma a kwance. Da yamma daf da Magriba Ma'u ta shigo zagayen nasu, bayan sun gaisa da Inna ta shiga ɗaki gurin A'isha. "Sannu Indo." Ta faɗi haka tana zama a kusa da A'ishan, gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi, dan wani irin azababben ciwo kanta yake mata. Ma'u ta ce. "Yanzu muka haɗu da mutuminki Ɗan_juma ya ce mun kina ina? Kwana biyu ba ya ganin ki." Duk da halin ciwo da A'isha take ciki sai da ta yi tsaki. Ma'u ta yi murmushi ta ce. "Na ce masa baki da lafiya ne, ya ce in miki sannu, bai sani ba ai da ya zo ya duba ki." A'isha tana numfarfashi cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Dan Allah Ma'u ki daina yi mun zancen wani Ɗan_juma, wallahi ƙara mun ciwo kike." Ma'u ta ce. "To na daina, Allah ya baki lafiya." Bayan Ma'u ta tafi ciwon kan A'isha ya tsananta, tana kwance ita kaɗai a ɗaki sai jujjuya kan take yi. Inna ta yi alwalar Magriba ta shigo ɗakin yin Sallah ta tarar da A'isha a wannan halin. Da sauri ta ƙarasa inda take tana faɗin. "Subhanallahi, Lafiya A'isha? Ko jikin ne?" Muryar A'isha ko fita ba ta yi sosai ta ce. "Inna, kaina zai tsage gida biyu, Inna ki kaini asibiti a cire mun shi dan Allah?" Cikin ɗimuwa Inna ta ce. "Subhanallahi, kai kuma A'isha? Ko yunwa ce tunda ba kya iya cin abinci? Bari na yi Sallah mu san abun yi." A daddafe Inna ta yi Sallar, tana idarwa ta fice zuwa zagayen Innar Ma'u don aron kuɗi, duk da kuɗin da take bin ta ya kai 2500 amma haka zata ƙara karɓar wani, dan yanda A'isha take juyi tare da riƙe kanta ya ɗaga mata hankali ba kaɗan ba, gwara kawai ta kai ta asibiti a duba mata ita sosai. Ciwo ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa daga wannan sai wannan, har tana murna da aka yi mata alluran nan jikin ya fara kyau, ashe da sauran rina a kaba. Idar da Sallar Innar Ma'u kenan Inna ta shiga gurinsu. Tun daga yanayin Sallamar Inna, Innar Ma'u ta san ba ƙalau ba. Bayan ta bata gurin zama ta zauna, ta ce. "Innar A'isha lafiya kuwa?" Inna ta sauke numfashi murya a sanyaye ta ce. "Jikin A'isha ne ya tashi wallahi Ladidi, dama kwana biyu tana mun k'orafin kanta na damun ta da ciwo sosai." Innar Ma'u ta ce. "Subhanallahi, ciwon kai kuma? Na sha ai jikin nata ya yi sauƙi yanzu." Inna ta ce. "Jikin ya yi sauƙi, ciwon kan ne dai." Innar Ma'u ta ce. "Gaskiya asabe ya kamata ki kai yarinyar nan asibiti a duba jikin nan nata, ko kuma ki kai ta gurin masu magani namu na gargajiya." Inna ta ce. "Shine abun da ya kawo ni dama, Na yanke shawarar gobe kawai zan kai ta asibitin Rano ne da safe." Innar Ma'u ta ce. "Ya kamata dai, amma wannan ciwo ya ƙi tafiya, yarinya tafi sati a kwance." Inna ta ce. "Ban san me yasa hankalina ya ƙi kwanciya da wannan ciwon na A'isha ba, duk da ba wani dad'ewa ta yi sosai a kwance ba, amma gabana sai fad'uwa yake yi." Cikin son kwantar mata da hankali Innar Ma'u ta ce. "Haba_haba, babu komai fa Asabe, insha Allahu zata samu lafiya, zazzaɓi ne dai kawai irin wanda ake yi." Inna ta sauke numfashi ta ce. "Allah yasa, amma dan Allah Innar Ma'u karki gaji da ni, aron kuɗi dai zaki kuma bani idan kina da shi, in Allah ya bata lafiya sai na nemi abun yi na biya ki." Cikin tausayawa Innar Ma'u ta ce. "Babu komai, ai na san baki da shine Asabe, Jiya Muntari ya turo mun da kuɗi, bari Ma'u ta dawo daga kasuwa sai ta je a ciro kuɗin na baki ki kai ta asibitin, Allah yasa kuɗin ya isa dan dubu Uku ne ya turowa Ma'u ta siyi takalmin kwalliya." Inna ta ce. "Na karɓewa Asma'u kuɗi kuwa?" Innar Ma'u ta ce. "To mene ne? Ai cuta ce, magani ai yana gaba da takalmi tunda ba rasa na sakawa ta yi ba, in ma baki samu kuɗin ba idan an yi mun biyan bashi sai na siya mata." Inna ta ce. "Toh shikenan, Na gode Na gode sosai Asabe, Allah ya saka da Alkhairi ya ji ƙan Mahaifa ya raya zuri'a, babu abun da zance miki akan irin taimakon da kike mun, sai dai Ubangiji Allah ya biya ki kawai." Innar Ma'u ta ce. "Ameen, amma mene abun godiya, ai duk yiwa kai ne." Inna zata kuma magana ta jiyo muryar A'isha daga ɓangarensu tana ƙwala mata kira. Da sauri ta miƙe ta koma zagayen nasu, Innar Ma'u ta mara mata baya. A tsakar gida suka tarar da A'isha tana laluban bango, Inna ta riƙe ta da sauri tare da faɗin. "Gani A'isha, mene ne?" Aisha ta ce. "Inna fitsari nake ji, kuma na fito zan je bayi amma bana ganin komai." Inna ta ce. "Kamar ya ba kya ganin komai?" A'isha ta ce. "Wallahi Inna duhu sosai kawai nake gani, ko idona a rufe yake ne?" A rikice Inna ta ce. "Duhu kuma A'isha? wanne iri? ga hasken farin wata nan ana iya ganin komai, kuma idanunki a buɗe suke tar." Lalubar hannun Inna Aisha ta yi ta kai saitin idonta ta ce. "To Ni dai Inna bana ganin komai sai duhu, ke ma fa bana ganinki kwata_kwata."...........✍️ _*Not Edited*_ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* 0️⃣5️⃣ I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ...........Innar Ma'u ce ta ƙaraso ta riƙe hannun A'isha, ganin yanda Inna take ƙoƙarin rikicewa yasa ta dube ta cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Karki tayar da hankalinki Asabe, na fi tunanin sumbatun ciwo take yi, kin san zafin zazzaɓi yana saka haka." Inna ta ce. "A'a Ladidi, taɓa jikinta ki ji babu wani zafi sosai, jikin nata ma fa ya yi sauƙi, gaskiya zazzaɓin jikinta bai yi yawan da zai saka ta sumbatu haka ba." Innar Ma'u ta ce. "To ko yunwa ce ta saka bata gani sosai? Kuma ga gari ya fara duhu shi yasa baza ta ga komai ba." A'isha dake sauraren su ta ce. "Innar Ma'u ba yunwa ba ce, gani ne bana yi, kuma idon ya mun nauyi." A rikice Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan wanne irin ciwo ne haka? Daga zazzaɓi sai ki daina gani? Kuma ga idon naki nan babu alamar wani abu ya same shi, dan ko sauya kala bai yi ba." Innar Ma'u ta ja hannun Aisha suka fara tafiya ta ce, "Ina zuwa, bari na gwada wani abu." Mara mata baya Inna ta yi cikin tashin hankali. Kasancewar Innar Ma'u tana k'wan wutar sola a ɓangarenta sai ɓangaren ya samu wadatuwar haske sosai. Bayan sun shiga ɗaki ta cewa A'isha. "Kina gani yanzu?"  Girgiza mata kai ta yi alamar a'a, fitila Innar Ma'u ta ɗauko ta haske idon A'isha, amma nan ma ta ce babu abun da ta gani. Hankalin Inna fa ya ƙara dugunzuma ta fara hawaye, jan A'isha ta yi jikinta tana ta duba idon nata kamar me neman abun da ya hana A'ishan gani. Ita ma A'ishan kuka ta fara tana faɗin. "Inna ki kai Ni a bani magani idona ya buɗe in cigaba da ganin ku." Rungume ta Inna ta yi ta ce. "Insha Allahu Idonki zai buɗe A'isha, ki cigaba da ganinmu." A'isha ta ce. "To Inna, raka ni in yi fitsarin." Innar Ma'u wadda hankalinta ya fara tashi ita ma da al'amarin ta kama hannun A'isha cikin sanyin jiki ta raka ta, ta yi fitsarin, dan sosai hankalin Inna ya tashi, kuka take yi ba kaɗan ba, jikinta gaba-d'aya ya yi sanyi, ga wata irin fad'uwa da gabanta yake yi. Cikin tausayawa Innar Ma'u ta dube ta bayan A'isha ta yo fitsarin ta ce. "Ki yi hak'uri Asabe, in Allah ya yarda ba wata matsalar ba ce, yanzu abun da za'a yi ki shirya mu je gidan Malam Ilyasu mai magani ya duba idon nata, ina da wasu yan canji za su ishe mu insha Allahu, tunda Ma'un ba ta dawo ba." Inna tana goge hawayen idonta ta ce. "Toh." Gidan Malam Ilyasu da ɗan nisa daga nan, dan haka Innar Ma'u ta ce bari ta yiwa Adamu ɗaya daga cikin yaran gidan magana tunda ranar Kasuwa ce duk suna nan ya kai su a babur ɗinsa, saboda kafin su samu na haya ɓata lokaci ne, dare ma ya yi duk sun tafi zai yi wahala su samu. Inna shiru kawai ta yi mata, amma ta san zai yi wahala ya je in ya ji su zai ɗauka. Suna soro suna jiran Innar Ma'u sai ga ta ita da Adamun, mamaki ne ya cika Inna ba kaɗan ba, amma dai ta shanye ta kama hannun A'isha da nufin su fara tafiya sai ta ji Adamu ya ce. "Aaa, Innar Ma'u ya na ga wannan Matar kuma? Da ita za mu tafi ne?" Cikin tausasa harshe Innar Ma'u ta ce. "Ita ma zaka ɗauka tare da Aisha ai, saboda A'ishan ma na kira ka, ka san ba ta da lafiya ba za ta iya doguwar tafiya ba." Adamu ya haɗe rai yana wani gyaɗa kai irin na wulak'anci ya ce. "Wallahi ba zan ɗauki Mayun nan a babur ɗina ba gaskiya, Innar Ma'u sai dai ki nemi wani." Innar Ma'u ta ce. "Haba Adamu, taimako fa zaka yi, kai ma watarana Ubangiji sai ya baka abun da ba ka yi tsammani ba sanadiyyar taimakon nan da zaka yi, dan Allah ka taimaka ka ɗauke su, ni sai in baka ɗan kuɗin Man babur ɗin ma." "Sai dai fa ki yi hak'uri gaskiya, dan baza ni ba." Adamu ya faɗi haka tare da juyawa ya yi tafiyarsa. Inna ta share hawayen idonta ta ce. "Mu je da ƙafa kawai Ladidi." Innar Ma'u ta ce. "Ya za'a yi mu je da ƙafa, ai mu in zamu iya zuwa A'isha baza ta iya ba." Inna ta ce. "Sai in goya ta." Innar Ma'u zata kuma magana, Inna ta katse ta da faɗin. "Karki damu zan iya, Ni dai burina mu yi mu je gurin mai maganin nan." Innar Ma'u ta ce. " To Allah ya kai mu lafiya." A hankali Inna ta zare A'isha wadda ta yi lamo a jikinta, sannan ta tsugunna ta ce ta hau bayanta. A'isha bata yi musu ba ta hau, Inna ta miƙe daƙyar har ta yi kamar zata tintsira saboda babu laifi A'isha tana da ɗan nauyi. Innar Ma'u ta ce. "Yi a hankali dai." Duk da Inna ta ji a jikinta da ta ɗauki A'isha amma haka ta daure ta jure suka je har gurin mai maganin, bayanta har sagewa ya yi, tana sauke A'isha ta shiga numfarfashi kuwa. Daƙyar suka samu ganin mai maganin, dan da farko cewa ya yi sai dai su dawo da safe yanzu dare ya yi. Innar Ma'u dai ta roƙe shi akan ya taimaka musu, ta faɗa masa daga ɗan nesa suke kuma da ƙafa suka zo. Tofi mai ganin ya yiwa A'isha a ido, bayan Inna ta yi masa bayanin abun da ya faru. Ya kuma ba su wani magani ya ce a haɗa mata da farin kwalli ana saka mata a cikin idon, indai jinnu ne kamar yadda suke tunani to idanun za su buɗe da yardar Allah, idan kuma har bayan kwana uku idon bai buɗe ba kuma an yi mata amfani da maganin to sai dai su je asibiti a duba mata idon. Godiya sosai suka yi masa sannan suka ba shi abun sadaka suka dawo gida, a dawowar ma haka Inna ta ƙara goye Aisha. Ai kuwa da jan ƙafa ta dawo gida, dan ba ƙaramin ciwo bayanta yake yi mata ba, gashi Innar Ma'u ta ce ta kawo ta taya ta da goyon A'ishan amma ta ƙi bata. Dan a ganinta hakan bai dace ba, ta ja ta sun yi tafiyar ƙafa kuma sannan ta ƙara mata da goyon ƴa. Duk da gajiyar dake addabar ta suna dawowa ta hau dakan maganin da suka karb'o, dan ita kawai burinta Allah ya buɗar mata da idon yarinyarta. A'isha kuwa jin ta take wani iri kamar ba ita ba, kamar a mafarki haka take gani abun. Duk inda Inna ta yi tana biye da ita, gani take kamar in ta zauna ita kaɗai wani abun zai faru da ita saboda ba ta gani. Duk bayan wasu mintuna sai ta shafi idon nata ta ji dai a buɗe yake, ko kuma ta yi ta kifkifta shi wai ta ji ko ya daina motsi. A daren Inna ta haɗa maganin da farin kwalli ta shafa mata a idon tare da addu'ar neman dacewa, ba jimawa da shafa matan ta yi bacci bayan ta ci tuwon da Innar Ma'u ta kawo mata. Inna kuwa daren yau ko runtsawa ba ta iya yi ba, tasa A'isha ta yi a gabanta ta rabka uban tagumi tana hawaye, da dare ya tsala kuma ta miƙe daƙyar ta yo alwala ta hau yin nafila akan Allah ya buɗi idon ƴarta. Washegari a makancen Aisha ta tashi, Inna ta yi mata wanka da duk abun da ya kamata sannan ta ƙara saka mata maganin, kamar yadda mai ganin ya ce tana saka mata sau biyu a rana, safe da dare. Wuraren ƙarfe tara na safe Inna tana zaune a tsakar gida tana gyangyad'in da ba ta san lokacin da yake ɗaukarta ba ta ji maganganun mutane a cikin kanta. Buɗe idonta ta yi ta ga su Ramatu ne da wasu daga cikin matan gidan. Hansai na duban ta, tana tafa hannuwa ta ce. "Ashe haka abu ya faru kuma? An cinye idanuwan wasu abun ya dawo kanku, an yi k'aik'ayi koma kan masheki'ya kenan? To Allah ya tsare mu ya tsare mana ƴaƴanmu, wannan masifa har ina ta lashe_lashe da cinye_cinyen naman mutane." Sai kuma suka saki shewa haɗe da dariya gaba-d'ayansu suka cigaba da yarwa Inna habaici, ita dai ko kanzil ba ta ce musu ba. Ana cikin haka sai ga wata tsohuwa tana tafiya daƙyar ta zo ita ma, tana shigowa ta fashe da kuka ta fara faɗin. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan wanne irin bala'i ne Isuhu ya kawo mana cikin zuri'a, gashi ya mutu ya bar mu da jalala, a ce a cikin gidan nan Mayya ta cinye idon wani abun ya dawo kanta? Wannan ai abun kunya aka ja mana a cikin zuri'a." Sai ta ƙara fashewa da kuka kamar wadda aka ce wani shak'ik'in nata ya mutu, cikin kukan ta ce. "Ba irin yanda ban yi da Yaron nan ba akan ya saki tsinanniyar matar nan amma ya ƙi, saboda ba ni na haife shi ba bai ɗauke ni a bakin komai ba duk da ina matsayin k'anwar Ubansa, to ga irin ranar da nake guje mana nan ta zo ai, Isuhu ka cuce mu ka ɓata mana sunan babban gida irin wannan a cikin garin nan." Innar Ma'u tun tijarar da su Hansai sukewa Inna take jiyowa, amma bata yi yunk'urin zuwa ba sai yanzu da ta ji yo Muryar Iya. Mayafinta ta zara ta yafa ta shiga zagayen su A'ishan cikin sauri, dan duk maganganun da Iya ta yi a cikin kunnanta, hakan yasa tana zuwa ta ce mata. "Haba Iya, wai don Allah me yasa kuke haka ne? Wannan abun da ya faru da A'isha Allah ne fa ya ɗora mata, cuta ce daga Allah, amma........." Cikin masifa Iya ta katse ta da faɗin. "Ke Ladidi bana son shishshigi a al'amurana fa kin sani, tunda ke an riga da an gama shanye miki kurwa ai dama baza ki taɓa ganin abun da take yi ba, dan haka ki mun shiru kafin na saɓa miki a gidan nan billahillazi." Innar Ma'u ta tausasa harshe ta ce. "Allah ya baki hak'uri Iya, amma dan Allah ku bar ta haka ta ji da abun da yake damun ta." Cikin son ƙara tunzura Iya Ramatu ta ce. "Iyee, lallai Ladidi wuyanki ya isa yanka, Iyan tana magana kina mayar mata akan wannan tsintacciyar magen?" Ta ƙarasa Maganar tana riƙe haɓa tare da jinjina kai kamar wadda ta ga an yi wani babban sab'on Ubangiji." Iya ta ce. "K'yale ta Ramatu ta zage ni, ai dama ba yau ta saba ba, amma yanzu ba ta ita nake ba tukuna." Ba ta jira amsar kowa ba ta dubi Inna ta ce. "Wallahi yau sai kin bar gidan nan ko da uban kike yawo a cikin garin nan, duk wani ma wanda yake ɗaure miki gindi kike cigaba da zama a gidan nan yau zan iya da shi, komai zai faru sai dai ya faru amma yau sai kin bar mana gida, baza ki cuce mu ki shafa mana baƙin fenti a cikin zuri'a ba, tunda yanzu kin fara cinye idanun mutane nan gaba kayan cikin mutane zaki fara ci, tunda dai k'asurgumar k'ungurnar MAYYA ce ke. Ato gara ki tattara ki yi gaba, maza_maza a haɗa tsummokarai a bar mana gida, yau ba mai_garin Kumurya ba, ko Mai_Kano ne gaba-d'aya wallahi bai isa ya saka na janye na bar ki kin cigaba da zama a gidan nan ba, ehe." Inna dai kanta na ƙasa ko d'agowa ba ta yi ba, wasu irin hawaye masu ɗumi ne suka zubo akan kuncinta, a hankali ta yi saurin saka hannu ta goge su." Sauran matan gida dake gurin farinciki fal zuk'atansu, ji suke kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha, yau ranar tonan asirin Inna ta zo, domin sun san ba ta da gurin zuwa kuma ba ta da mai ba ta gurin zama, wannan tozarci da Inna ta yi mata ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba." Cikin tsawa kamar Iya za ta kai mata duka ta ce. "Asabe ba kya jina ne? dake fa nake, ki tashi ki yi ki bar mana gida, idan kuma ba so kike in saka a fitar mun dake ba, tunda na bi miki ta mutunci amma ba ki gani ba." A hankali Inna ta miƙe cikin sanyin jiki, murya a sanyaye ta ce. "Ki yi hak'uri Iya, yanzu za mu tafi insha Allahu." Iya tana gyara ɗaurin zani ta ce. "Yawwa, yi maza_maza da Allah, ayi_ayi a zo a ƙara mai, umma ta gai da Ashsha." Ba tare da Inna ta kalli kowa ba ta juya ta shige ɗaki dan haɗa kayansu............✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣6️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Kusan a tare Matan gurin suka saki shewa tare da faɗin. "Yau za mu yar da ƙwallon Mangoro mu huta da ƙuda." Innar Ma'u wadda ta bi Inna da kallon tausayi ta sauke numfashi tare da runtse idonta. A ranta tana faɗin, komai zai faru ba za ta taɓa bari Innar Ma'u ta bar gidan nan ba, saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko ta san ba ta da inda zata je idan ta bar nan ɗin, dalili na biyu kuma alƙawarin da ta yiwa Malam mijinsu kafin ya rasu, na taimakon Inna da ba ta kariya a gidan bayan ransa. Fakar idonsu Iya ta yi ta fice daga ɓangaren cikin sauri ta aiki Ma'u ta je ta sanar da mai gari halin da ake ciki. Inna tana cikin ɗaki tana ta harhad'a kayayyakinsu cikin sauri saboda jarabar mitar da Iya ta azalzale ta da ita, A'isha dake kwance wadda duk maganganun da aka yi a cikin kunnanta cikin sanyin murya ta ce. "Inna wai haɗa kayan kike yi? Ina zamu je idan mun bar nan ɗin to? Ko gurin ƴan'uwanmu da kika ce mun muna da su za mu?" Inna ba ta tanka mata ba ta cigaba da abun da take yi, hakan yasa A'isha fashewa da kuka. Inna ta fara kai kayansu tsakar gida saboda cigaba da azalzalar ta da Iya ke yi mata akan ta yi sauri ta zo su tafi, su Hansai na ƙara zuga ta tare da yadawa Inna Habaici, sallamar da suka ji ana kwad'awa yasa su juyawa suna kallon mai sallamar, Malam Garba ne, ɗaya daga cikin bafadan garin. Inna ce kawai ta amsa masa sallamar. Cikin ɗaga murya Malam Garba ya ce. "Mai_gari yana son ganin Asabe da Iya Mari a fada yanzu_yanzu." Bai jira amsar kowa ba ya juya ya fita. Wulwulga idanuwa iya ta fara yi, ganin ba ta ga Innar Ma'u ba ta shiga tafa hannuwa tare da faɗin. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, yanzu Ladidi ƙara ta, ta kai gurin Mai_gari? Idan uwarta ce ai baza ta kai ta ba, to mu je gurin Mai_garin sai me? Bai dai isa yasa na janye abun da na yi niyya ba, ato." Wata k'ak'k'arfar ajiyar zuciya Inna ta sauke lokacin da ta ji sak'on Malam Garba, ko ba komai zuciyarta ta samu nutsuwa akan zullumin tunanin inda za su dosa in sun bar nan. Dama da hijabinta a jikinta, takalmi kawai ta zura bayan ta kamo hannun A'isha ta kulle ɗakinta suka rab'a ta gefen matan gidan suka fice, gaba-d'aya suka raka su da kallon banza zukatansu fal baƙin ciki, domin sun san Mai_gari ba zai bar Iya ta kori su A'isha ba. Iya ce duƙe gaban Mai_gari sai zazzare ido take tana sauraran nasihar da yake yi mata, Inna na gefenta a zauna kanta a ƙasa ita da A'isha. Bayan Mai_gari ya kai aya Iya ta fashe da kuka ta ce. "Ranka ya daɗe ba wai ban ji abun da ka faɗa mun ba ne, amma ina so a duba abun nan da idon basira, Matar nan fa tunda ta zo cikin garin nan ba mu taɓa ganin wani nata ko da kaza ya zo gurinta ba, haka ita ma ba ta taɓa zuwa gurin wani nata ba, ai kuwa ka san da akwai ayar tambaya, domin duk abun da ya koro bera daga rami to tabbas ya fi ramin zafi. Mu da ma tsoron mu ɗaya ne, kar ta janyo mata abun tirrr a cikin zuri'a." Mai_gari ya jinjina kai ya ce. "Iya Mari tun zuwan matan nan garin nan kuke jifan ta da kalmar Maita, kuma idan ban manta ba Marigayi Malam Yusuf har Sarkin Mayu ya taɓa ɗaukowa akan sanin Mayya ce Asaben ko ba Mayya ba, duk da shi ya san ba Mayyar ba ce, sai dan kawai ku ku tabbatar. Sarkin Mayun kuma ya tabbatar ba Mayyar ba ce, amma duk da haka har yau ba ku daina dangantata da Maitar ba, akan me? Yanzu tsakani da Allah idan ƙaddara ta kai naku wani gurin da ba'a san shi ba aka dinga yi masa abun da kuke yiwa wannan baiwar Allah zaku ji daɗi? Rayuwa ba haka take ba, ɗan_Adam Ubangiji ma da kansa ya daraja shi, bai kamata mu kuma yan'uwansa mu dinga wulak'anta shi ba, wannan ba dai_dai ba ne, ban taɓa zaton abun da kika yiwa wannan baiwar Allah daga gare ki ba Iya mari, da girmanki da hankalinki? Maganar Barin Asabe gida kuwa kar na kuma jin ta, indai ba ita ta so hakan da kanta ba, saboda Malam Isuhu shi ya gina gurin da take zaune, kuma ya ce ya bar mata halak_malak, ko bayan ransa ta cigaba da zama a cikinsa, dan haka kar na ƙara jin makamanciyar wannan maganar, duk wanda ya kuma zan kira a zo a kama shi tun daga Kano, a kulle shi a can a koya masa hankali." Mai_gari ya ƙarasa Maganar cikin kaushin murya. Cikin Iya fa ya kad'a jin ta ji an ce za'a kai mutum a kulle, cikin hanzari ta ce. "Insha Allahu ba za'a kuma ba ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, wannan ɗin ma ɓacin rai ne ya saka." Inna ta share ƙwallar data tarar mata a ido cikin ladabi ta ce. "Godiya nake ranka ya daɗe, Allah ya ƙara girma." Mai_gari ya ce. "Amin Asabe, a cigaba da hak'uri, ita kuma wannan yarinya Allah ya ba ta lafiya." Inna ta amsa da Amin. Daga haka Mai_gari ya sallame su. Su Inna na gaba Iya na bin su a baya tana mitar da girmanta tsofai_tsofai da ita an saka ta fitowa da hantsin nan, kamar ba ita ta zubar da girman nata ba. Sai tsinewa Inna take yi tare da zagin Mai_gari, dama duk maganganun da ta faɗa kurin kawai take yi, haka take yi kodayaushe, ana zuwa gaban Mai_gari kuma sai ka ji ta shiru kamar ba ita ce mai tijarar ba. Suna shiga gida direct ɓangaren Innar Ma'u ta shiga ta dinga zazzaga mata masifa da bala'i, akan kai ƙarar ta gurin Mai_gari da ta yi. Ita dai ba ta kula ta ba, tunda Allah yasa Mai_gari ya yiwa tufkar hanci shikenan. Bayan Iya ta gama yi mata tijarar ta tafi ta shiga ɓangaren su Inna ta tarar tana mayar da kayan da ta fiffito da shi, hak'uri ta shiga ba ta akan abun da ya faru, Inna ta yi murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta ce. "Ni fa duk abun da su Iya suke mun bana ganin laifinsu ko kaɗan, domin da gaskiyar su tunda......" Da sauri Innar Ma'u ta katse ta, ta ce. "Na sha faɗa miki ki dainar faɗar haka, dan ba su san asalinki ba bai kamata su dinga yi miki kage da sharri ba, bayan wulak'anci da tozarci gami da tsangwama da kike fuskanta daga gurinsu, idan ba za su iya mu'amala dake ba sai su daina shiga cikin rayuwarki, ba wai su dinga yi miki irin wannan ɗiban albarkar ba." Inna ta ce. "Haka ne, Allah yasa mu dace." Innar Ma'u ta amsa mata da Amin, zuciyarta cike fal da tausayinta. Lokuta da dama tana son ta yiwa Inna tambayoyi a game da rayuwarta, tana son sanin wacece ita? Mene ne dalilin barowar ta cikin danginta ta zo nan tana rayuwa cikin k'unci da k'untata? Amma ganin duk tsawon shekarun da suka yi tare da Innan ko da wasa ba ta taɓa yi mata magana makamanciyar wannan ba yasa take dannewa ba ta tambayar ta_ta. Bayan kwana biyu kamar yadda mai magani ya ce Inna ta cigaba da sakawa A'isha maganin, amma idon bai buɗe ba. Hankalin Inna fa ya yi matuƙar tashi, ta saka A'isha a gaba tana kuka mai ban tausayi. Innar Ma'u ta dinga tausar ta tana ce mata, watak'ila ciwon idon A'ishan bana maganin gida ba ne na asibiti ne, idan Allah ya taimaka ana kai ta asibitin sai ta ga an dace, da wannan kalaman zuciyar Inna ta ɗan yi sanyi. A'isha ma ta damu ba kaɗan ba, domin rashin gani ba ƙaramin jarabta ba ce, dan ma wani ikon Allah sai Ubangiji ya ɗoro mata hak'uri akan makantar da ta same ta lokaci ɗaya. Amma duk da haka kodayaushe cikin tambayar Inna take yaushe idonta zai buɗe? Ita dai a kai ta asibiti, wani lokacin har da kuka take yi. Washegari Monday tun sassafe Inna suka shirya suka tafi asibitin Rano ita da A'isha. Tana zuwa suka yanki kati sannan suka yi zaman jiran a kira su dan ganin likita. Sai wajen ƙarfe goma aka kira su, Inna ta kama hannun A'isha suka shiga office ɗin likitan. Bayan sun gaisa Inna ta yi masa sannu da aiki ya tambaye su abun da yake tafe da su. Inna ta yi masa bayanin duk abun da ya samu A'isha, shiru ya yi na wasu ƴan sakanni, da alama jinjina al'amarin yake yi a cikin ransa. Cikin nuna damuwa ya ce. "Ya Subhanallahi, zazzaɓin mai zafi ta yi ne sosai?" Inna ta ce. "Eh gaskiya ta ji jiki." Likitan ya jinjina kai sannan ta taso ya zo inda suke zaune ya dudduba jikin Aisha. Yana yi yana yi mata tambayoyi tana ba shi amsa, sosai yarinyar ta ba shi tausayi, ƴar ƙaramarta da ita a ce ta rasa ganin ta, duk da dai ana haifar waɗanda ba sa ganin ma, amma nata sai ya fi zama abun damuwa tunda ita already ta san daɗin ganin. Bayan ya koma ya zauna ya dubi Inna ya ce. "Baaba a gaskiya wannan matsalar ba za mu iya magance muku ita a wannan asibitin ba, kasancewar ba mu da k'wararrun likitocin ido, ɗan ciwon ido dai haka da ake fama da shi ko jan ido wannan duk mu na iya bayar da maganinsa, amma idan abun ya girmama, ko ciwon idon da dole sai an yi masa aiki to fa sai dai mu tura mutum can Kano ya je a yi masa, dan haka yanzu ke ma sai dai mu tura ki can asibitin Makkah." Da sauri Iya ta ce. "Asibitin Makkah kuma likita?" Likitan ya yi murmushi ganin Yanda Inna ta yi, ya ce. "Ba wai garin Makkah na cikin ƙasar Saudiyya ba, a'a, wani asibiti dake nan cikin jiharmu Kano mai wannan sunan, to insha Allahu matuƙar kun je can za'a dace." Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Amma asibitin na kuɗi ne ko na Gwamnati?" Likita ya ce. "Private hospital ne, na kuɗi." Inna ta jinjina kai cikin damuwa ta ce. "A asibitin gwamnatin shi ba za a iya duba mata idon ba?" Likita ya ce. "Za'a iya, har aikin ma idan ta kama duk za'a iya yi mata, amma maganar gaskiya asibitin Makkah ya fi, idan da hali ku je can ɗin." Inna ta goge wani gumi da yake tsatstsafo mata a goshi ta ce. "To shikenan likita, na gode sosai Allah ya saka da Alkhairi, insha Allahu sai a je can ɗin." Likita ya ce. "To ba damuwa, Allah yasa a dace." Ya kalli A'isha ya ce. "Sannu kin ji, Allah ya ba ki lafiya." Suka amsa da Amin sannan Inna ta yi masa sallama suka fito. Bayan sun fito daga asibitin A'isha ta cewa Inna. "Inna ba zan ƙara gani ba ko? Shikenan na daina ganin ku na daina ganin komai da kowa?" Inna ta shafi kanta ta ce. "Zaki cigaba da gani insha Allahu A'isha, ke dai ki yi ta addu'a, kar ki gaza kin ji?" A'isha ta ce. "Toh." Hankalin Inna a tashe suka dawo gida, babbar damuwarta rashin kuɗi da rashin hanyar samun sa, domin ta san maganar zuwa asibitin Kano dole sai ta tanadi kuɗi masu kauri, musamman da likitan ya sako maganar aikin ido, ta san kuɗin aiki ba ƙaramin kuɗi ba ne, ita kam zata iya cewa ba ta taɓa riskar kanta a cikin tashin hankali irin wannan ba, wani irin tausayin A'isha ne yake ƙara mamaye mata zuciya game da wannan ƙaddarar da Ubangiji ya ɗoro mata, sai dai ba ta ƙasa a gwiwa gurin kaiwa Ubangiji kukanta a kodayaushe akan ya yayewa A'isha wannan makanta. Bayan ta gama zayyanewa innar Ma'u abun da ya faru a asibitin ta ƙara da cewa. "Babban tashin hankalina inda zan samu kuɗin da zan kai yarinyar nan Kano a duba ta, mu da ko abun da za mu ci ma gagarar mu yake yi." Innar Ma'u ta sauke numfashi ta ce. "Ubangiji shine zai kawo mana mafita Asabe, insha Allahu Allah zai warware." Inna ta ce. "Ni yanzu sana'ar da zan kama nake tunani, na rasa me zan siyar a garin nan wanda zan dinga samun k'wandala da ficika." Innar Ma'u ta ce. "Tun kwanaki nake son na yi miki magana akan aikin abincin sadakar da muke yi a gidan Hajiya Talatu duk ranar juma'a, wannan fargabar ciwon A'ishan da muke ciki ne yasa na sha'afa. Ɗaya daga cikin wanda muke yin aikin tare ce ɗanta ya ɗauke ta ya mayar da ita can Kano gidansa, to kuma har yanzu ba'a samu madadinta ba, zan yiwa Hajiyar magana idan mun je wannan satin, idan Allah ya saka da rabonki sai ki maye gurbin waccan ɗin, aikin 500 ne kullum kuna gamawa za'a sallame ku, sannan kuma za'a baku abinci sosai wanda zai ishe ku, ku ci daga rana har dare." Cikin jin daɗi Inna ta ce. "Amma na gode sosai Ladidi, Allah ya saka da Alkhairi yasa ta ɗauke ni." Innar Ma'u ta ce. "Insha Allahu zata ɗauke ki, dan ba ta da matsala matar, ga ta da ihsani." Inna ta ce, "Allah yasa a dace." Innar Ma'u ta ce, "Amin Amin, ga wata shawara kuma, zan cewa mutane ina yin Nik'an kayan miya namu na gargajiya na dutse da muke yi, idan an kawo mun sai in baki kina yi ki karb'i kuɗin kya rage wasu abubuwan da shi. Tunda idan ke kika ce kina yi ba za'a na kawo miki ba." Inna ta ce. "Na gode, na gode sosai Ladidi, Ubangiji ya taimake ki kamar yadda kike taimako na, ba dan dake ba a cikin gidan nan da ban san yanda zan yi ba." Innar Ma'u ta ce. "Kin wuce haka a gurina Asabe, yanda nake jin ki a cikin zuciyata tamkar ƴar'uwata ta jini, dan haka babu godiya a tsakaninmu, fatanmu kawai Ubangiji ya dafa mana akan dukkan al'amuran rayuwarmu." Inna ta ce. "Amin." Da yamma Ɗan_juma suna zaune akan wani dakali ɗan nesa da gidansu shi da wasu abokanansa guda biyu suna hira sai ga wani abokin nasu wanda gidansu yake jikin nasu A'isha shi ma ya zo. Bayan sun gaisa ya dubi Ɗan_juma ya ce. "Ɗan_juma ɗan Sarki jikan Sarki kuma Sarkin gobe da yardar Allah, yau ina tafe da wani labari mai daɗin gaske." Ɗan_juma ya yi murmurshin jin daɗin kirakin da Hamza ya yi masa ya ce. "Shaƙa mun cikin gaggawa, ni kuma in shaƙa maka tukuici mai nauyin gaske." Hamza ya ce. "Labari ne akan Yarinyar can daka ƙwallafa rai a kanta, yau kwana huɗu kenan da wayar garin da aka yi ba ta gani, a tak'aice dai ta zama marainiya." Cikin mamaki Ɗan_juma ya ce. "Kar dai ka ce mun A'isha?" Hamza ya ce. "Ita fa." Wani yalwataccen murmushi Ɗan_juma ya saki ya ce. "Kaii, amma na ji daɗin wannan labari Hamzeze, saboda zai samar mun da hanya mafi sauƙi ta cikar burina akan A'isha, ka ga watarana idan uwar ta_ta ta tafi yawon nemo musu na cin ƙanzo sai mu zagaya mu farmata, mu yi mu gama mu ƙara mai ba tare da ta san mu ba ne, tunda ba ta gani balle ta gane su waye. Sakamakon wannan labari da ka kawo mun Hamza, kai ne na biyu a yin wannan harka bayan na gama." Hamza ya fashe da dariya suka tafa shi da Ɗan_juma wanda shi ma yake dariyar, sauran abokan nasa su ma suka taya su, domin sun san da su za'a yi wannan harkar...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣7️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Cikin ikon Allah rayuwa ta fara warware wa su Inna, domin kuwa kamar yadda innar Ma'u ta faɗa ta yiwa Hajiya Talatu magana kuma ta ɗauki Inna, duk ranar juma'a tana samun 500 ɗinta sannan kuma ga abinci wanda za su ci su ƙoshi a ranar har dare, har washegari ma yake kai musu su d'umama su yi karin kumallo da shi. Ƴar Innar Ma'u ta fari ta kawo mata ɗanta mai suna Yusuf, ana kiransa da Malam ƙarami, ya dawo hannun Innar Ma'un gaba-d'aya da zama. Shine Innar Ma'u ta cewa Inna ta dinga yin aya mai sugar da Mai gishiri sai ya dinga fitar mata da ita idan ya dawo daga makaranta. Inna ta yi Na'am da wannan shawarar, ba tare da jinjiri ba ta siyo ayar ta fara soyawa. Alhamdulillah ana ciniki sosai, dan duk mutanen gari ɗaukar su Innar Ma'u ce take yi, ga kuma Nik'an kayan miyan shi ma ana kawowa ba laifi,  Dai_dai gwargwado Inna sun samu rufin asiri, cikin abun da bai fi sati biyu ba ta biya Innar Ma'u duka bashin da take bin ta, sannan ta fara bankin ajiyar kuɗin kai A'isha asibitin Kano. Yau juma'a, da yamma Inna suna ɓangaren su Innar Ma'u suna Nik'an kayan miyan wani biki da za'a yi anan unguwar ita da Innar Ma'un. A'isha da Ma'u suna gefe Ma'u tana ba ta labarin abubuwan da suke faruwa a makaranta. A'isha ta dubi saitin da take jin muryar su Inna ta ce. "Inna kin ji, Malam Buba kullum sai ya zo aji yana nema na, wai za'a mun passport ɗin zana jarabawar komen." Inna ta ce. "Me cece haka ita abun da zaki zana ɗin?" A'isha ta ce. "Jarrabar shiga Sakandire ce." Inna ta ce. "A'a, ba aji biyar kuke ba? Ina sai an zo aji Shida ake zanawa?" A'isha ta ce. "Ai zaɓar mu aka yi mumu uku a ajinmu aka ce zamu zana." Inna ta ce. "Toh, dama ana yin haka?" Innar Ma'u ta ce. "Eh mana, ƴar gidan gaji ma ai a aji biyar ta gama firamare, ita ma zaɓar su aka yi, masu ƙoƙari suke zaɓa ai." Inna ta ce. "Tab'dijan, to ke da ba lafiya ba ina kika ga ta wani zana jarrabawa? kawai ki bari sai wata shekarar, kafin nan kin samu lafiya da yardar Allah, sai ku zana tare da Ma'u." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ni dai Inna dan Allah ki bari in zana, an ce ma akai kuɗin jarrabawar 600 ko Ma'u?" Ma'u ta ce. "Eh, kullum sai ya ce in faɗa miki ma." Inna ta ce. "To da wanne idon zaki yi rubutun jarrabawar? Ki haqura kawai ki bari sai wata shekarar, sai ku zana tare da Ma'u." Innar Ma'u ta ce. "Ai ita ma Ma'un wannan shekarar zata zana, Kawunta ya ce ta isa shiga Sakandiren, Ranar Litinin zan bata kuɗin insha Allahu ta kai, tunda sun ce duk mai so zai iya biyan kuɗi ya zana." Inna ta ce. "To ai A'isha ita matsalar ba ta gani, amma sai mu je makarantar ranar Litinin ɗin mu ji ya za'a yi." Jin abun da Inna ta ce sai A'isha ta fara murna, dama ta gaji da zaman gidan, dan ko zaure Inna ba ta barin ta, ta je, sai dai in zata fita ne Innar Ma'u ba ta nan take tafiya da ita duk inda zata, idan kuma innar Ma'u tana nan sai ta bar ta a gurin ta. Washegari A'isha ta takurawa Inna sai ta je gidan Malama karatu, ita ta gaji da zaman gida har da kukanta. Inna ta ce to ta saka hijabinta Ma'u ta kama hannunta su tafi, Allah ya kiyaye. Zuciyar A'isha cike da zumud'i suka tafi. Idan ba sani ka yi ba ko an faɗa maka baza ka ce A'isha makauniya ba ce, domin idanunta a buɗe suke kuma babu alamar mara sa lafiya ne, ga ta tsaf fess da ita, Inna tana tsaftace ta yanda ya kamata, dan Inna akwai tsafta. Suna zuwa gidan Malama yara suka fara tsokanar A'isha suna cewa. "Ta zama makauniya!! Ta zama makauniya!!" Dama abun da Inna take gudu kenan shi yasa ba ta barin A'isha ta fita ko nan da can ba tare da ita ba. Ita kuwa A'isha ba ta kula su ba, guri kawai ta nema ta yi zamanta, Ma'u ce ma take yi musu magana. Sai da Malama ta fito ta tsawatar musu sannan suka bari. Hak'uri ta dinga bawa A'isha cikin tausayawa, sosai yarinyar take ba ta tausayi tun a daa, ga kuma jarrabawar da Ubangiji ya ƙara ɗora mata. Ko kaɗan abun da yaran suka yi bai damu A'isha ba, duk da ta ji zuciyarta ta karye kamar za ta yi kuka, amma dai ta daure ba ta yin ba. Bayan an tashi daga karatun suna hanya suka gamu da su Hindu. Hindu da ƙawayenta suka sha gaban su A'isha. A'isha da ba gani take ba jin tsayuwar mutane a gabanta yasa ta ƙara riƙe hannun Ma'u sosai tare da faɗin. "Ma'u su waye?" Dan a tunaninta Ɗan'juma ne. Kafin Ma'u ta yi magana Hindu ta riga ta da faɗin. "Su Uwarki ne, Shegiya Mayyar yarinya kawai." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ba dai Uwata ba wall... ..." Ai ba ta ƙarasa ba Hindu ta wanke ta da mari." Waro ido Ma'u ta yi ta ce. "Kai Hindu akan me zaki......" Kafin ta ƙarasa wata ƙawar Hindu ta janye ta tare da wancakalar da ita a gefe, cikin masifa ta ce mata. "Kama gabanki ki tafi kar mu haɗa da ke, yau sai mun ci kazakazar shegiyar yarinyar nan, saboda a kanta Ɗan_Juma yake mana rashin mutunci da wulaqanci." A'isha dake hawaye hannunta riƙe da kuncinta ta fara laluben iska tana cewa. "Kar ki tafi ki barni Ma'u dan Allah." Hindu ta dungure mata kai ta ce. "Sai ta tafi ɗin dan kan Ubanki, yau sai dai ki dinga tafiya kina fad'uwa a hanya." A'isha ta saka kuka ta fara kiran sunan Ma'u, ita ma Ma'un hawaye ta fara tare da ƙoƙarin kamo A'isha, amma saboda rashin tausayi su Hindu suka kora Ma'u, suka kuma daki A'isha son ransu. A'isha Tana durkushe a gurin tana kuka mai ban tausayi bayan su Hindu sun tafi Ma'u ta dawo ta ɗaga ta, dan dama ƙin tafiya ta yi ta b'uya a bayan wani gida. Cikin sanyin murya ta ce. "Ki yi haquri A'isha, kuma wallahi ba su daki banza ba, sai na je na faɗawa Sarki abun da suka yi miki." A'isha dai ba ta ce komai ba har suka ƙarasa gida. Ma'u ce ta zayyanewa inna duk abun da ya faru, sosai ran Inna ya ɓaci, amma ba ta ce komai ba, rarrashin A'isha kawai ta yi. Innar Ma'u kuwa Ma'u tana cikin ba ta labari ko gamawa ba ta yi ba ta zari hijabinta tay gidan Sarki ta kai ƙara. Babu ɓata lokaci Sarki ya saka aka kira su Hindu da iyayensu mata, sannan aka kira Inna da A'isha da Ma'u. Gargad'i sosai Sarki ya yiwa su Hindu akan A'isha bayan Ma'u ta ƙara zayyana masa yanda aka yi, ya kuma saka suka ba ta hak'uri, ya ce duk ranar da ko kallon da bai gamsar da A'isha suka yi mata ba idan ya samu labari sai ya saka dogarai sun zane masa su, ya kuma cewa iyayensu su ƙara ja musu kunne akan babu ruwansu da Aisha, sannan ya bawa Inna da A'isha haquri, daga nan ya sallami kowa. Suna tafe a hanya Inna ta dubi Innar Ma'u ta ce. "Me yasa kika kawo ƙarar su, da kin bar su ai." Innar Ma'u ta ce. "Su daki yarinyar sannan kuma a k'yale su? Sun ci bulus kenan, gobe ma su samu lasisin ƙara dukan ta kenan, yanzu kuwa da aka yiwa tufkar hanci ba shikenan ba. Ai ni wallahi yanzun ma na so kin bari an daddaki ƴan banza, amma kika wani dinga bayar da hak'uri kina ke kin hak'ura kin yafe." Inna ta ce. "Gwara dai da ba'a dake sun ba, me cece ita duniyar? Ai komai ɗan hak'uri ne." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne, Allah yasa mu dace." Saboda kuka da dukan da A'isha ta ci yau da ciwon kai ta kwanta. Ranar Monday da safe Inna ta shirya A'isha cikin uniform suka tafi Makarantar su. Ta yi Sa'a suna shiga shi ma Malam Buba ya shigo, ganin Inna da A'isha ya gane mahaifiyarta ce, cikin girmamawa ya ce. "Sannunku da zuwa, Ina kwana Baaba?" Inna ta ce. "Lafiya ƙalau, ya ƙoƙari?" Malam Buba ya ce. "Alhamdulillah." Sannan ya dubi A'isha ya ce. "A'isha ba magana?" Murmurshi ta yi ta ce. "Ina kwana." Ya ce. "Lafiya ƙalau, ya jiki_jiki kuma? Asma'u ta ce kin sha jinya." A'isha ta ce. "Da sauƙi." Ya ce. "To Allah ya ƙara afuwa." Suka amsa da Amin, sannan ya ce da Inna su ƙarasa office ɗinsu bayan ta yi masa bayanin abun da yake tafe da ita. Bayan sun zauna Inna ta ce masa. "Dama akan maganar Jarrabawar da A'isha ta ce an zaɓe ta zata zana na zo, na ce ko za'a bari sai wata shekarar duba da lalurar da ta same ta, kafin nan insha Allahu an yi mata magani ta warke." Malam Buba ya ce. "Wai har yanzu ba ta gani? Na ɗauka ai idon ya buɗe." Inna ta ce. "Tukunna dai, muna nan muna ta addu'a." Malam Buba ya ce. "Subhanallahi, Sannu A'isha, Allah ya yaye miki." Inna ta ce. "Amin." Malam Buba ya ce. "To Baaba tunda ana saka rai idon zai buɗe ta zana jarrabawar a hakan kawai, zan yi mata registration da komai da sunanta da hotonta, akwai k'anwata Mairo sai ta zana mata, tunda jarrabawar ta rana ɗaya ce." Inna ta ce. "Kana ganin hakan zai yiyu?" Malam Buba ya ce. "Insha Allahu, ai nine exam officer, Ni nake yin komai na jarrabawar, shugaban makarantar ma bani da matsala da shi, ina yi masa magana zai yarda." Inna ta ce. "Toh shikenan Allah ya ba da sa'a, na gode sosai ɗana, Allah ya saka da Alkhairi." Malam Buba ya yi murmushi ya ce. "Babu komai Baaba, Allah ya ba ta lafiya ita kuma." Inna ta ce. "Amin." Malam Buba yana kallon A'isha ya ce. "Indodo kin daina magana ne? Na ji kin yi tsit kamar ba ke ce mai cika mana aji da surutu ba." Murmurshi A'isha ta yi, tare da saurin rufe fuskarta da hannunta. Inna ta ce. "Ko godiya ba ta iya ba." Cikin sanyin murya ta ce. "Mun gode Malam." Murmurshi kawai Malam Buba ya yi, haka kawai A'isha take burge shi, saboda nutsuwarta da hankalinta, ba shiru_shiru ba ce ita dan ba ta barin ta kwana, indai aka faɗa mata sai ta rama, amma ba ta da tsokana, in dai ka ji an yi faɗa da ita to tsokanarta aka yi. Yana jin tausayinta kuma a cikin ransa saboda tsangwamar da take fuskanta a gurin abokan karatunta. Abun da yake ƙara burge shi da ita tana da ƙoƙari dai_dai misali, indai an yi musu karatu tana fuskanta. Anan Inna ta bar ta bayan ta biya kuɗin jarrabawar da na passport ɗin da za'a yi mata. Yau A'isha murna fal ciki ta zo makaranta, duk da ba ta ganin komai amma dai ta ji daɗi, kuma babu wanda ya tsokane ta, saboda Malam Buba ne ya kai ta har aji ya kuma jawa yaran kunne akan kar wanda ya tsokane ta, duk wanda ya tsokane ta sai ya zane shi........ Rayuwa ta cigaba da tafiyar wa da su A'isha cikin godiyar Ubangiji, an zana common entrance ɗin har ma ta fito, A'isha da Ma'u duk sun ci makarantar sakandare dake cikin garin. Tare Kawunsu Ma'u ya yi musu komai kama daga kan uniform da su takalmi da jakar makaranta da littattafai. Har lokacin Inna ba ta gama tara kuɗin kai A'isha asibitin Kano ba saboda sha'anin rayuwa. Zuwa lokacin kowa na cikin garin ya san A'isha ta makance, labari ya gama baza ko'ina, Iya da Matan gidansu kullum cikin yiwa Inna gorin ƴarta ta makance amma ta kasa kai ta asibiti a yi mata magani saboda baƙin talauci, Inna dai ba ta kula su dan ba ta su take ba. A'isha kuwa zuwa yanzu har ta saba da rashin ganin. Da farko da aka kai su A'isha makaranta ƙin karɓar ta aka yi, Malaman suka ce ai kamata ya yi a kai ta makarantar makafi ba wai nan ba, Malam Buba ne ya yi ruwa ya yi tsaki daƙyar aka samu aka ɗauki A'isha, shi ma dan ya yi musu dabara ne da cewa, an kai ta asibiti sun ɗora ta akan magani tana kan shan maganin ne, sai ta gama shan maganin za'a yi mata aiki wanda idon zai buɗe. Ma'u ce take yi mata rubutu idan ta gama nata, ita dai kawai in ta je makarantar zama ne nata da saurare. Sai kuma wata sabuwar matsala da A'isha take fuskanta a garin, ba ta isa ta fito waje ba sai yara sun yi mata ihun Makauniya sun cinye idon wasu ya dawo kansu. Yau Laraba, da daddare Inna ta ɗauko kuɗin da take tarawa na kai A'isha asibiti ta irga, ta ga kuɗin ya kai dubu shida da ƴan kai, zai isa su yi kuɗin Mota da kuma ɗan abun da take tunanin za'a buƙata a asibitin, dan haka ta yanke shawarar gobe za su je asibitin Kanon da yardar Allah......✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣8️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Washegari tun sassafe suka shirya, A'isha tana zaune tana karyawa, Inna kuma tana duban kuɗin da za su yi amfani da shi a inda ta ajiye jiya da daddare amma kuɗi ya ce ɗauke ni inda kika ajiye. A cikin wata jaka dama ta ajiye su, ta duba jakar ya fi sau goma ta zazzage ta amma ba ta ga kuɗin ba. Wasu guraren ta shiga dubawa ko ta manta ta canza musu guri ne, sai da ta birkice duka ɗakin amma ba ta gan su ba. A'isha da take sauraren b'uruntun da Inna take ta yi ta ce. "Inna wai me kike dubawa tun ɗazu?" Cikin damuwa Inna ta ce. "Kuɗin da zan kai ki asibitin A'isha, ban gan su ba." A'isha ta ce. "Ko dai kin manta inda kika ajiye ne?" Inna ta ce. "Amma ko mantawar na yi yanda na birkice ɗakin nan ya ci ace na gan su, sai dai in ba ya cikin ɗakin." A'isha ta ce. "Allah yasa dai ki gan su Inna." Inna ta ce. "Amin." Dai-dai nan innar Ma'u ta shigo zagayen nasu, bayan ta yi sallama sun amsa mata ta ɗaga labulen ɗakin tana faɗin. "Har yanzu ba ku tafi ba? Idan takwas ta wuce fa ba za ku samu ganin likita ba." Inna dake maimaita kalmar innalillahi a cikin zuciyarta ta dubi Innar Ma'u cikin sanyin murya ta ce. "Ladidi kuɗaɗen na nema na rasa." Innar Ma'u ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, kamar ya kin neme su kin rasa? A ina kika ajiye?" Inna ta ɗauko jakar da ta ajiye kuɗin ta ce. "A cikin jakar nan na saka, kuma ko kafin na yi bacci na duba na ga suna ciki, Jakar kuma a gabana ta kwana a k'ark'ashin shimfid'ata." Innar Ma'u ta ce. "Bari dai na shigo mu ƙara duba ɗakin sosai, ko wani gurin kika cilla su kika manta." Inna ba ta ce komai ba har Innar Ma'u ta ƙaraso cikin ɗakin ta fara dubawa. A'isha dake ta murna yau za'a kai ta asibiti a yi mata magani sai murnar ta koma ciki, kana kallon fuskarta ka san tana cikin damuwa. Sai da innar Ma'u ta ƙara duba ko'ina a cikin ɗakin amma babu kuɗin babu alamar su. Hankalin Inna fa ya yi matuƙar tashi, baiwar Allah har gumi ya fara tsatstsafowa a jikinta na rud'ani. Duban Innar Ma'u ta yi wadda ita ma take cike da tararrabin abun ta ce. "Kuɗin nan fa ba ya cikin ɗakin nan." Innar Ma'u ta ce. "An shigo an ɗauke su kenan?" Inna ta ce. "Amma da na yi matuƙar mamaki, saboda babu yanda za'a yi a ɗaga shimfid'ar da nake kwance har a zare jakar nan ban ji na farka ba." Innar Ma'u ta ce. "Hmmm, Asabe bar mutum kawai, maso abun ka ya fi ka dabara, amma ko tantanma bana yi in dai shigowa aka yi aka ɗauki kuɗin nan to da sandar nan da suke amfani da ita suka zo, wadda idan aka ajiye ko idonka biyu baza ka iya motsawa ba har sai sun gama ɗaukar abun da za su ɗauka sun ɗauke ta." Inna ta sauke numfashi tare da zama dab'as a ƙasa cikin raunin murya ta ce. "Allah kai ka san me kake nufi da wannan al'amari, kuma kai ka bani wannan kuɗin Allah ka ƙara bani wasu." Cikin tausayawa Innar Ma'u ta ce. "Amin ya Allah, insha Allahu Asabe kuɗin ki sai ya fito, Allah ya dawo miki da su, ya toni asirin duk wanda ya ɗauka." Kamar A'isha zata yi kuka ta ce. "Inna shikenan yanzu baza mu je asibitin ba an sace kuɗin?" Inna ta ce. "Ki yi hak'uri A'isha, haka Allah ya Ƙaddaro mana, babu yanda zamu yi." Tsugunnawa Innar Ma'u ta yi ta dafa kafadun A'isha cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Insha Allahu A'isha Ubangiji zai kawo hanyar da za'a kai ki asibiti, ki kwantar da hankalinki insha Allahu zaki warke." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. miƙewa Innar Ma'u ta yi ta fice bayan ta ce musu tana zuwa. Hawaye ne yake ƙoƙarin zubowa daga idon Inna amma ta ƙi ba su damar hakan, wani irin zafi take ji a cikin zuciyarta, kuɗin da ta hana kanta ci, ta hana kanta sha, da goma da ishirin ta tara su kusan watanni goma amma wani mara imanin ya raba ta da su a dare ɗaya, ita yanzu ina ta ga hanyar da zata kuma samun wasu kuɗaɗen? Hawaye A'isha ta fara ta ce. "Yanzu shikenan Inna ni ban zan kuma gani ba tunda an sace kuɗin da zaki kai ni asibitin? Allah ya isanmu wallahi, ba mu yafe ba, Allah ya kumbura cikin duk wanda ya ɗaukar mana kuɗinmu." Inna ta ce. "In Allah ya yarda A'isha zaki warke." A'isha ta ce. "To Inna wa zai ƙara baki wani kuɗin ki kai Ni?" Inna ta ce. "Allah, shi ya bamu wannan ɗin kuma shi zai ƙara bamu wasu." Wunin yau gaba-d'aya cikin damuwa da rashin walwala A'isha da Inna suka yi su, dan Inna ko abinci kasa ci ta yi. Abun da yake bata mamaki game da ɗaukar kuɗin da aka yi, ita dai a iya saninta babu wanda ya san da batun kuɗin kaf cikin gidan balle kuma a waje, daga ita sai Innar Ma'u suka sani, kuma ta san Innar Ma'u baza ta yiwa kowa zancen kuɗin ba, tunda ba wani shiga sabgar matan gidan take yi sosai ba. Amma babu komai ta bar wa Allah, shi kaɗai ya san me yake nufi da hakan ta faru, fatanta Allah ya musanya musu da mafi Alkhairi. Innar Ma'u ta yi iyarka ƙoƙarinta wajen ganin ta samu kuɗi ta bawa Inna ta je asibiti a cikin satin amma hakan bai samu ba saboda halin rayuwa. Haka A'isha ta cigaba da rayuwa cikin makanta, ga tsangwama da tsanar da suke fuskanta daga mutanen garin, babu abun da ya ragu sai ma ƙaruwa da ya yi. Yau ta kama ranar Talata, da safe k'anin Innar Ma'u dake Kano ya zo. Bayan sun gama gaisawa da ita sun sha hirar yaushe gamo ya gyara zama ya ce mata. "Yaya ni fa abun da ya kawo ni na zo ɗaukar ku ne ku koma can Kano da zama tunda Allah ya nufa na kammala ginina." Cikin mamaki innar Ma'u ta ce. "Mu koma can kamar ya? Ina kake nufi? Ba dai Kano ba?" Ya ce. "Can mana gidana, sai ku fara shiri jibi za mu wuce tare." Innar Ma'u ta ce. "Haba Muntari, ya za'a yi mu koma gidanka mu ɗora maka nauyi bayan wanda yake kanka? Kuma ita Rakiyan ai kamar zamu takura ta idan muka koma gidanka gaba-d'aya da zama." Muntari ya ce. "Babu wani nauyi Yaya, ni fa na ce ku koma kuma na san zan iya ne, Rukayya kuwa ba ki da matsala da ita, da na faɗa mata ma murna tay ta yi." Shiru kawai Innar Ma'u ta yi ba ta ce komai ba, amma ko kaɗan ba ta so komawarta Kano ta bar garin da aka haife ta a ciki ba, gashi kuma ba ta son barin su Inna, amma saboda kar Muntari ya ga ta gwale shi sai ta amince, ta dinga yi masa godiya tare da tarin addu'oi. Jiki a sanyaye Innar Ma'u ta shiga ta sanar da inna batun tafiyarsu. Inna ta ce. "Jibi_jibin nan kuma? Ikon Allah" Innar Ma'u ta ce. "Wallahi Nima na ga abun ya yi kusa sosai, yaushe na gama zaga ƴan'uwa da abokan arzik'i na yi musu sallama? ga gari na damuna wataran ma sai ruwa ya hana ka fita. Amma ya zan yi tunda Muntari ya dage." Inna ta yi murmushi ta ce. "Ai da gaskiyarsa, ya san in ya tafi baza ki koma da wuri ba, Allah ya kai mu Jibin ya sanya Alkhairi." Innar Ma'u ta ce. "Amin, amma ko kaɗan ban so barinmu garin nan ba ko dan ku Asabe." Inna ta ce. "To ya za'a yi? Haka Allah ya yi, kar ki saka komai a ranki na damuwa saboda ni, Ubangiji yana tare da mu ai." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne kam." Inna ta ce. "Zan shigo anjima mu yi wata magana idan na gama abun da nake yi" innar Ma'u ta ce. "To sai kin zo."......... Kwana biyun nan zuciyoyinsu Inna babu daɗi saboda tashin da su Ma'u za su yi, ita kanta innar Ma'u ta shiga cikin damuwa, ga tunanin halin da za ta bar su Inna ga kuma kewarsu da za ta yi. A'isha ma sosai ta damu saboda rabuwa da Ma'unta, ita kaɗai ce ƙawarta duk cikin garin, idan ta tafi shikenan ba ta da kowa. Ranar Alhamis da safe wanda ya kama ranar tafiyar su Ma'u, Inna tana wankin uniform ɗin A'isha Hansai ta shigo zagayen nasu babu ko sallama, ta tsaya akan Inna cikin izgilanci ta ce. "Yau koma wasu sai kwanan baƙin ciki, wadda aka yi nasarar lashewa kurwa zata bar gari, sai mu ga kuma da wa za'a dinga yin mu'amala yanzu." Inna ta yi murmushi ta ɗago ta kalle ta ba ta ce komai ba. Hansai ta cigaba da yadawa Inna habaici cikin shewa, yau duk matan gidan zuciyarsu fari k'al suke jin ta, a ganinsu tunda innar Ma'u za ta bar gidan watan tagayyarar su Inna ya kama. Har ƙofar gida aka kawo Motar da su Ma'u za su tafi a cikinta, bayan an gama saka kayansu a ciki suna bakin Motar a tsaye matan gida duk sun fito yi musu rakiya. Inna tana tsaye hannunta riƙe da na A'isha wadda ke ta gunjin kuka ita da Ma'u, ita kanta innar dauriya kawai take yi amma yanda take jin zuciyarta kamar ta fashe da kukan, ganin abun take tamkar a mafarki, kamar za'a ce wasa ne su Innar Ma'un sun fasa tafiya. Innar Ma'u ta rungume A'isha tana hawaye ta ce. "Ki yi shiru A'isha ki bar kukan nan haka, kin ga idanunki dama ba lafiya ce da shi ba, ai zamu na zuwa muna ganin ku, kuma za ku na kawo mana ziyara, na bawa Innarki Lambar Muntari, idan kun tashi zuwa sai ta kira shi ya ba ta adreshin inda muke, ki yi hak'uri kin ji." A'isha dai tamkar ƙara zuga ta innar Ma'u ta yi, maimakon ta yi shirun sai ma ƙara volume ɗin kukan ta yi. Janye ta Inna ta yi, ta dubi Innar Ma'u tana murmurshin da ya fi kuka ciwo ta ce. "Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya, Na gode sosai da irin taimakon da kika ba ni a zamantakewarmu, Allah ya saka da miki da mafaficin Alkhairin sa, tabbas ke wani bango ce a cikin rayuwarmu." Ba ta jira cewar Innar Ma'un ba saboda wani kuka dake neman kufce mata ta shafa kan Ma'u ta ce. "To Asma'u, Allah ya tsare sai mun zo ko kuma ku kun zo." Ma'u ta riƙe Inna ta ce. "Ni na fasa tafiyar anan zan zauna tare da A'ishata, ni ba zan iya tafiya in bar ta ba." Inna ta ce. "Haba Asma'u, kar ki ce haka kin ji yarinyar kirki na, ki yi hak'uri." Ma'u ta saki Inna ta rungume A'isha suka fashe da kuka mai ban tausayi, hakan ya karya zuciyar innar Ma'u ta fara hawaye sosai ita ma, abun tausayi. Sabo da shak'uwa ba k'arya ba ne, tunda su A'isha suka taso tare suke yin komai da Ma'u, yau rana tsaka kuma Ubangiji ya raba su, abun da babu wanda ya yi tunanin faruwarsa nan kusa. Sosai suka bawa wasu daga cikin mutanen gari tausayi, shi kanshi Muntari dake tsaye yana kallon su sai da ya ji kamar ya fasa tafiya da su Ma'un, Malam ƙarami kuwa Mutumin Inna shi ma sai kuka yake yi. Dauriyar Inna ta ƙare, hawaye masu ɗumi ne suka shiga kwaranyowa daga cikin idonta, cikin matuƙar sanyin jiki ta d'agawa su Inna hannu sannan ta ɗaga ƙafafuwanta daƙyar ta yi cikin gida da sauri. Matan gidan suka bi ta da kallo suna sakin murmurshin mugunta. Daƙyar aka iya raba Ma'u da A'isha, ƴar Innar Ma'u ta shigar da A'isha gida Ma'u kuma aka tusa ta cikin Mota. Kuka sosai A'isha ta yi a yau, ko makaranta ba ta je ba, sai bayan Azhar bayan Inna ta saka ta, ta yi Sallah bacci ya ɗauke ta. Ita kanta Inna ta ci kukanta ta gode Allah. Sai yamma A'isha ta farka daga baccin, ta tashi da ciwon kai saboda kukan da ta sha. Tana farkawa abun da ta fara cewa shine. "Shikenan su Ma'u sun tafi sun bar mu, yanzu ba mu da kowa, ba ni da mai kama hannuna mu je makaranta, ba ni da mai yi mun rubutu." Inna ta ce. "Mu na da Allah A'isha, kuma shi zai yi mana maganin komai ya ba mu yanda za mu yi." Sosai kewar su Ma'u take damun su Inna, gashi ita ba waya ba bare ta kira lambar Muntari su yi magana da su ko sa ɗan ji daɗi. Duniyar duk sai ta yi musu wani iri babu daɗi. Gaba-d'aya A'isha ta daina walwala, komai cikin sanyin jiki take yin sa, ta rage yawan magana, kamar ba ita ce a daa idan ta fara yiwa Inna surutu sai ta ce ta rufe mata baki ba. Satin da su Ma'u suka tafi gaba-d'aya ƙin zuwa makaranta ta yi, Inna ba ta takura mata ba akan hakan ta bar ta, ta huta. Ranar Lahadi da daddare suna cin tuwon masarar da Inna ta yi musu Inna ta cewa A'isha. "A'isha ki daure gobe ki koma makaranta, dan babu Ma'u kuma sai ki daina karatu? Ko ba kya son ki zama likitar ne yanzu?" A'isha ta ɓata fuska ta ce. "To Inna da wa za mu dinga tafiya tare?" Inna ta ce. "Ni zan dinga kai ki in na ɗauko ki." A'isha ta ce. "To wa zai dinga mun rubutu? Idan an fita Sallah wa zai na kama hannuna mu je mu yi?" Shiru Inna ta yi tana kallon A'isha na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Mu je makarantar dai sai mu ji yanda za'a yi." Washegari ba dan A'isha ta so ba ta shirya suka tafi Makarantar tare da Inna. Allah ya haɗa su da wata Malama mai kirki mai suna Malama Hajara, Inna ta yi mata bayanin abun da yake tafe da ita, ta kwantarwa da Inna hankali ta ce, insha Allahu zata na kula da A'isha yanda ya kamata, ko da ranar da ba za ta zo makarantar ba zata yi waya ta faɗa a kula da A'ishan. Inna ta yi mata godiya sosai sannan ta dawo gida. Cikin satin nan rayuwa ta fara yiwa su Inna tsanani, saboda yanzu ba ta sana'ar komai, sai aikin abincin sadakar nan, 500 kuwa a sati mai zata yiwa rai biyu, ga abubuwan da yawa, bayan abinci ga sabulun wanka da na wanki, ga man shafawa, ga omon wanke_wanke, ga siyan ruwan amfanin gida, ban da sauran abubuwan buƙata na yau da kullum. Jarin ayar da ɗan guntun kuɗin dake hannunta duk sun ƙare. Sai suka koma irin rayuwar daa, sai su farka ba su da ko ƙwayar hatsin da za su ci a cikinsu. Yau Alhamis, wanda ya kama sati biyu cif da tafiyar su Ma'u. Da rana A'isha ta gama shirin tafiya makaranta kasancewar ta yamma suke yi tunda su ƴan junior section ne. Jakar makarantarta ta laluba ta ɗauka, cikin sanyin murya ta ce. "Inna na gama mu tafi." Inna ta sauke tagumin da ta rafka ta ce. "Haka zaki je makarantar ba ki ci komai ba A'isha, da hak'ura kika yi na fita na dawo ko Allah zai sa in dace in samo miki wani abun ki ci, sai ki tafin." A'isha ta ce. "Toh Inna a ina zaki samu?" Inna ta ce. "Sabon Gari zan je gurin Hajiya mai k'uli_k'uli, idan da aiki in yi mata ta biya Ni, na san ma ba'a rasa aikin ba tunda gobe ne cin kasuwa za'a zo a sissiya." A'isha ta ce. "To mu je makarantar, idan kin samu sai ki kai mun can ɗin." Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Kin kawo shawara kuma, tashi mu je kar ki makara, daga can sai na wuce." Miƙewa A'isha ta yi, Inna ta kama hannunta suka fice. Tun bayan da Inna ta tafi ba jimawa A'isha take saka ran dawowarta, domin wata irin yunwa take ji ba kaɗan ba, ɗan kokon Naira goman da ta sha da safe shi kaɗai ne a cikinta. Har aka fita Sallar la'asar Inna ba ta zo ba, gashi yau Malama Hajara ba ta zo ba, sai wata yarinya ta roƙa ta fitar da ita waje ta yi ta Sallah ta dawo da ita. Bayan an dawo aji tana ta jin yara na ta ciye_ciye abunsu, suka bar ta da jin ƙamshi. Har aka tashi Inna ba ta zo ba, zuwa lokacin yunwa ta fara galabaitar da A'isha, dauriyar ta ƙare ta fara hawaye. Gashi yara duk sun tafi gida sai ita kaɗai a bakin aji a tsugunne. Wani Malami ne ya hango ta ya taho inda take, da mamaki yake duban ta ya ce. "Ke lafiya kike zaune anan ke ɗaya?" A'isha ta ce. "Innata nake jira ta zo ta ɗauke ni." Malamin ya ce. "Ayya ke ce mai ciwon idon nan ko?" Gyaɗa masa kai A'isha ta yi. Ya ce. "To yanzu zama zaki yi ki ta jiran ta kuma? Yamma ta yi ga garin hadari ya haɗo sosai, mu ma duk tafiya za mu yi, amma abun da za'a yi bari na saka a raka ki gida, ina ne gidan naku?" A'isha ta ce. "A Ƙofar fada ne." Malamin ya ce. "To mu je a raka ki, wannan hadarin ai ba zai yiyu ki zauna ke kaɗai anan ba, gashi ba gani kike ba." Sai da suka fita daga cikin makarantar yana riƙe da hannunta sannan ya samu wani yaro ya ce ya raka ta gidan Sarki, daga nan sai ta samu wani ya kai ta gida, tunda shi yaron bai san gidansu ba. Kafin su ƙarasa, garin ya ƙara duhu, an fara iska mai ƙarfi haɗe da yayyafi. Yaran sai jan A'isha yake, duk ta ƙara galabaita, tafiya kawai take yi amma jin ta take kamar zata faɗi. Yaron yana kai ta ƙofar gidan Sarki ya juya ya yi tafiyarsa, saboda zuwa lokacin ruwa ya fara ƙarfi. Ɗan_juma suna zaune a soro akan benci shi da Hamza da wani abokinsa suna karta, kamar a mafarki ya hango A'isha tsaye ta rakub'e a jikin bango, ƙura mata ido ya yi yana tuna when last da ya gan ta, ya jima bai gan ta ba gaskiya. Sai ya ga ta ƙara girma ta fara zama ƴar budurwa. A'isha tana shekaru goma sha uku a yanzu, amma saboda tana da garin jiki da ɗan tsayi idan ka gan ta zaka yi tunanin shekarun ta sun fi haka. Ruwan da ya fara dukanta ya saka uniform ɗin jikinta duk ya mammanne mata a jiki. Ɗan_juma ya ƙurawa ƙirjinta da ya ɗan fara tasawa da irgen dangi ido, nan fa shed'an ya fara buga masa ganga akan mummunan k'udirinsa akan A'isha. Wani murmushi ya yi tare da lasar leb'ensa ya ce da su Hamza. "Tsuntsu daga sama gashashshe." Bai jira cewar su ba ya miƙe ya fita ya janyo A'isha cikin zauren ta ƙarfin tsiya, bayan ya duba gabas da yamma kudu da arewa ya ga babu kowa a wajen. A'isha ta ƙanƙame Jakarta a jikinta cikin rudu ta ce. "Waye wannan? Me na yi maka? Ni ka cika ni? Mene ne haka?" Ɗan_juma ya cika ta yana murmurshin mugunta, abokansa da sai yanzu suka gane mai yake nufi suna taya shi murmurshin. Laluben Hanya A'isha ta fara yi cikin hawaye, jikinta gaba-d'aya rawa yake yi saboda tsabar tsoratar da ta yi da janyon tan da Ɗan_juma ya yi, gashi ba ta san ko wanene ba. Garin neman hanyar fita ta ƙume goshinta da garu, kuka ta saka tare da kiran sunan Inna. Cikin rashin Imani ɗan_juma ya fizgo ta tare da fizge jakar hannunta ya cillar a ƙasa, wani uban ihu A'isha ta ƙwala ta fara tittirjewa, amma saboda ruwan da ake yi mai ƙarfi ne yasa babu wanda zai jiyo ihun nata balle ya kawo mata ɗauki, cak Ɗan'juma ya ɗaga ta ya shige da ita wani ɗaki dake cikin zauren ya kullo ƙofa. Ihu sosai A'isha take yi tare da ƙoƙarin k'wace kanta daga hannun Ɗan'juma amma ta kasa. Mara masa baya su Hamza suka yi zuwa cikin ɗakin, a ƙasa Ɗan'juma ya jefar da ita sannan ya saka ƙafa ya take ƙafafuwanta da take haurin sa da su, da ido ya yiwa su Hamza alamar su danne masa A'isha. Hamza ya ƙaraso ya saka hannunsa ya toshe bakin A'isha da ƙarfi saboda da ihun kukan da take, ɗayan kuma ya daddanne mata hannayenta da iyakacin ƙarfinsa. Cikin tsantsar zalunci Ɗan'juma ya cire Hijabin jikinta ya cillar, yana wani irin murmushin zallar iskanci da duniyanci ya fara cire kayan jikinsa...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣9️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Wani kyakkyawan Matashi ne ya fito daga cikin gidan Sarki hannunsa riƙe da umbrella. Sai da ya zo zaure sannan ya tsaya yana nannad'e umbrellar. Dai_dai nan Allah ya bawa A'isha sa'a ta gantsarawa Hamza cizo a tafin hannunsa, cikin sauri Hamza ya janye hannun nasa saboda azabar zafin da ya ji ya shiga yarfa hannun, hakan ya bawa A'isha da ta fara fita daga hayyacinta damar ƙwala ihu. Cak matashin ya tsaya a inda yake cikin mamakin abun da kunnuwansa suka jiyo masa, kalle_kalle ya fara yi dan idan ya ji dai_dai kamar a cikin zauren aka yi ihun. Wani ihun A'isha ta ƙara yi saboda marin da Ɗan_juma ya wanka mata, wanda ya yi tunb'ur haihuwar uwarsa. Kallon ƙofar ɗakin Ɗan_juma Matashin ya yi, haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta ba da ihun da yake jiyowa, lemar hannunsa ya ajiye cikin sauri ya nufi ɗakin ya buɗe ya shiga. Tozali ya yi da Ɗan_juma tsirara yana ƙoƙarin cirewa A'isha riga, ita kuma sai jujjuya kai take yi hawaye na shatata daga cikin idonta. Cikin kid'ima ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, mene haka? Me kuke shirin aikatawa?" Juyawa su Hamza suka yi suna kallon sa a rud'e. Banda Ɗan_juma da ya cigaba da abun da yake yi, dan tunda ya samu wannan damar yau ba zai so ta kufce masa ba, bai ga kuma uban da ya isa ya hana shi yin abun da ya yi niyya ba. Runtse ido Matashin ya yi ya buɗe cikin tsananin ɓacin rai ya ƙarasa inda suke ya daddage ya saukewa Ɗan_juma wani uban naushi a tsakiyar gadon bayansa, gantsarewa Ɗan_juma ya yi dan naushi ya shige shi ba kaɗan ba, wani naushin Matashin ya ƙara sakar masa wanda ya saka shi yin taga_taga ya faɗi a ƙasa yana faɗin. "Aushh.....!" Ganin haka su Hamza suka miƙe cikin hanzari da niyyar guduwa, Matashin wanda zuciyarsa ke wani irin tafarfasa saboda baƙin ciki ya cakumo su dukan su ya bazar da su a ƙasa, ya ba su nasu rabon naushin. Sai ga su gaba-d'ayansu duka a ƙasa suna sassauke numfarfashin wahala. Jikin Matashin gaba-d'aya tsuma yake yi, kyawawan fararen idanunsa sun kada sun yi jajur. A hankali ya ƙarasa ya tsaya yana kallon A'isha wadda tuni ta sume, cikin sauri ya dauko hijibinta ya zira mata sannan ya ciccib'e ta ya fice da ita daga cikin ɗakin, sai a lokacin ya lura da jakar makarantar ta dake yashe a ƙasa a cikin zauren. Girgiza kansa kawai ya yi ya nufi wata ƙofa dake pacing ɗin ɗakin Ɗan_juma ya buɗe da key ya shiga. Akan ƙatuwar katifar dake ɗakin ya shimfid'e A'isha, sannan ya fito ya ɗaukar mata Jakarta ya koma ɗakin, har lokacin ruwa ake yi bana wasa ba. Zama ya yi a gaban A'isha yana sassauke numfashi, ƙura mata ido ya yi cikin tsananin tausayinta na ƙoƙarin keta mata haddi da su Ɗan_juma suka yi, fuskarta ta yi jajur saboda kukan da ta sha, shatin hannun Ɗan_juma rud'u_rud'u akan fuskarta. Haka kawai ya ji gabansa ya yanke ya yi wata irin fad'uwa, kasa ɗauke idonsa ya yi daga fuskar A'isha, lokaci ɗaya bugun zuciyarsa ya sauya, ta fara bugawa da sauri_sauri. Daƙyar ya yi ta maza ya janye idonsa daga kan A'isha ya miƙe ya nufi ledar pure water ɗin dake ɗakin ya dauko ɗaya ya bula ya shiga shafawa a fuskar A'isha zuwa wuyanta, tsawon mintuna biyu yana hakan sannan ya ji ta ja wani gauron numfashi, lokaci ɗaya kuma ta yi yunk'urin miƙewa jikinta na wani irin k'yarma tana kiran sunan Inna, tare da ƙoƙarin kai hannu tana dukan iska alamar son k'watar kai. Cikin tausayawa ya riƙe hannunta, so cool ya ce. "Sorry." A'isha ta fizge hannunta tare da ja baya ta fashe da kuka ta ce. "Su waye ku? Me yasa kuke son cutar da ni? Me na yi muku?" Ta ƙarashe maganar tare da tashi zaune. Lumshe ido ya yi ya buɗe saboda a yanzu A'isha ta buɗe idonta wanda ke cike da zallar firgici da tsoro, kallon idanun nata kuwa ya ƙara masa saurin bugun zuciyarsa gami da faduwar gaban da ta fi ta ɗazu. Cikin rarrashi ya ce mata. "Ki kwantar hankalinki, because by now ba kya hannun masu son cutar da ke, Ubangiji ya kub'utar da ke." A'isha ta ƙara volume ɗin kukunta ta ce. "Waye kai? Ni ka kai ni gurin Innata." Tana yin maganar ne cikin tsananin tsoro da firgicin da yake tabbatar da a cikin razani take, sai dunk'ule jikinta take yi guri guda. Bai kuma cewa komai ba ya miƙe ya fita ya lek'a waje ya ga har lokacin ruwa aka yi, amma an fara ɗaukewa. Tsayawa ya yi yana kallon ɗakin Ɗan_juma, zuciyarsa cike mamakin sa ba ɗan kaɗan ba, bai taɓa tunanin hakan daga Ɗan_juma ba, fyaɗe fa? Har su uku akan ƙanƙanuwar yarinya, wannan wanne irin zalunci ne haka? Ya manta rabon da ya yi tozali da abun da ya tayar masa da hankali kamar wannan. Yana nan tsaye har ruwan ya ɗauke ya koma sai yayyafi kaɗan_kaɗan saboda gabatowar lokacin Sallar Magriba. Juyawa ya yi ya koma cikin ɗakin, a tsakar ɗakin ya tarar da A'isha tana laluben hanya cikin kuka, riƙe ta ya yi ya ce. "Sorry, ruwa ake yi ne sai yanzu ya ɗauke, mu je in raka ki gidan." Wata k'ak'k'arfar ajiyar zuciya A'isha ta sauke tare da kallon fuskarsa kamar mai iya ganin sa, haka kawai ta ji zuciyarta ta ɗan nutsu da shi, murmushi ya sakar mata sannan ya cika ta ya ɗaukar mata Jakarta ya nuna mata ƙofa ya ce. "Mu je ko?" A'isha dake jin duk jikinta na yi mata wani irin ciwo ga juwa dake ɗiban ta, ta kai hannu ta lalubi bango ta dafa, cikin muryarta da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. "Ba na gani, sai dai a riƙe mun hannuna." Cak ya tsaya yana kallon ta cikin shock yana maimaita abun da ta faɗa a cikin zuciyarsa, ba ta gani? What she meant? Ita makauniya ce ko me? Ya faɗi haka a cikin zuciyarsa. Numfashi ya sauke a hankali ya ce. "Ok." Sannan ya kama hannunta suka fice daga ɗakin, ko rufe dakin bai yi ba suka yi waje. Suna fita ana fara kiran Sallah, Allah ya haɗa su da wasu yara suka nuna masa gidansu A'isha daga nan, kamar yadda ta ce masa ya tambayi wani ya nuna masa da ya tambaye ta ina ne gidansu. Tunda bayan da Inna ta kai A'isha makaranta ta wuce Sabon gari kamar yadda ta ce, tana zuwa ta tarar lokacin za'a fara aikin k'uli_k'ulin, zama ta yi aka fara aikin da ita. Ba su gama aikin da wuri ba, dalilin da ya saka kenan ba ta koma makarantar su A'isha ba, yin aikin kawai take yi amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin A'isha. Lokacin da suka gama aikin haɗarin nan ya haɗo sosai, amma haka Inna ta taho gida saboda hankalinta gaba-d'aya yana kan A'isha, har fad'uwa ta ji gabanta yana yi ba tare da ta san dalili ba. Sai dai tun kafin ta ƙarasa gida aka fara ruwan, duk da haka ta so zuwa ta ɗauko A'isha a ruwan, amma saboda yanda ruwan ya yi ƙarfi yasa dole ta hak'ura ta wuce gida ba dan ta so ba. Tunda ta koma gidan sai ta kasa tsaye ta kasa zaune, haka kawai ta ji zuciyarta ta kasa nutsuwa, ga gabanta da yake ta fad'uwa. Addu'a ta dinga yi akan Ubangiji yasa a ɗauke ruwan ta je ta gano halin da ƴarta take ciki. Ana fara tsagaita ruwan kuwa ta ɗauki buhu ta lullub'a a kanta ta nufi makarantar su A'isha, tana zuwa ta tarar babu kowa makarantar ma a kulle take. Hankalinta a matuƙar tashe ta dawo gida zuciyarta cike da tarin tambayoyi akan inda A'isha take. Tana shiga soron gidan su ma su A'isha suna shiga. Juyowa ta yi jin takun tafiya a bayanta, da sauri ta dawo baya cikin zak'uwa ta ce. "A'isha!" Jin muryar Inna yasa A'isha ta fara kuka tare da janye hannunta daga cikin na Matashin. Inna ta rungume ta tare da sakin ajiyar zuciya. Cikin kuka A'isha ta ce. "Inna ina kika tafi ba ki zo kin ɗauke ni ba?" Inna ta ce. "Ban dawo da wuri ba ne A'isha, da fatan babu abun da ya same ki? Ruwa bai dake ki ba ko? Na ji jikinki da lema, ina takalmanki?" A'isha ba ta iya bawa Inna amsa ba sai kuka kawai take yi. A rud'e Inna ta ce. "Me ya faru dake ne A'isha? Me aka yi miki kike wannan kukan?" Ta ƙarashe maganar tare da ɗago ta daga jikinta. Matashin dai kawai kallon su yake yi cikin tausayawa, yanda A'isha take ƙanƙame Inna yasa ya gane har lokacin a cikin firgici take. A hankali ya ɗan risina ya cewa Inna "Ina Yini?" Inna da ta manta ma A'isha tare suke da wani ta ɗago ta dube shi ta ce. "Lafiya ƙalau." Kallon shi Inna ta dinga yi ko kiftawa babu gabanta na fad'uwa, ƙasa ya yi da kansa ya miƙawa Inna jakar A'isha. Inna da duk zaton ta sabon Malami ne shi aka kawo a makarantarsu A'isha dan ko kusa bai yi kala da ƴan garin ba ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya ta ce. "Mun gode sosai Bawan Allah, Allah ya saka da Alkhairi." Shafa kansa ya yi ya ce. "Babu komai Mama, bari na wuce na ji an shiga Sallah, akwai maganar da nake son mu yi dake idan babu damuwa sai na dawo gobe da safe mu yi in Allah ya kai mu." Inna ta da kasa ɗauke idonta daga kansa ta ce. "Babu damuwa ɗan nan, Allah ya kai mu goben lafiya." Ya amsa da Ameen, sannan ya yi mata sallama ya tafi, har ya fice daga soron Inna ta kasa ɗauke idonta daga kansa, kallon sa take yi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Kama hannun A'isha ta yi wadda ke kuka har lokacin suka shige cikin gida, abun mamaki suna shiga Inna ta ga Ramatu ta bar bakin zauren da sauri ta shige cikin ɓangarensu har tana tuntub'e, ko tantanma Inna ba ta yi leken su take yi ta ga me suke yi a zauren jin muryar Namiji. Girgiza kai kawai Inna ta yi ta wuce. Tambayar duniya Inna ta yiwa A'isha akan me ya faru bayan sun zauna amma A'ishan ta ƙi faɗa mata, sai kuka kawai take yi. Gajiya ta yi ta kama yi mata faɗa, cikin takaici ta ce. "Wanne irin iskanci ne wannan A'isha? ina miki magana kin mayar da ni wata gantalalliya, sai kukan banza da kika sani a gaba kina yi, ki faɗa mun me ya samu fuskarki na ga kamar shatin hannu? Ina takalmanki kuma suke?" A'isha ta share hawayen fuskarta ta bawa Inna labarin duk abun da ya faru. Cikin tsananin tashin hankali Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, su waye waɗan nan azzaluman?" A'isha ta ce. "Ban san su ba nima." Inna ta fara hawaye ta ce. "Hasbunallu'wa ni'imalwakil, Allah ka shiga tsakanin mu da waɗan nan azzaluman da ba mu san ko su waye ba, Allah ka saka mana, Ubangiji karka ba su ikon cutar da wannan baiwa taka ko nan gaba. Allah na gode maka da ka kub'utar da ita. Wannan wanne irin abu ne, daga wannan sai wannan." A'isha ta ce. "Inna waye ya kawo ni gida? Ni ban gane muryarsa ba." Inna ta ce. "Ni ma ban san shi ba A'isha, da alama baƙo ne a cikin garin nan." A'isha ta shinshina jikinta ta ce. "Ɗan gayu ne ko Inna? Na ji yana ta ƙamshi mai daɗi, ni ma kin ji kayana suna yin ƙamshin ya shafa mun." Inna ta bi ta da kallo tana jinjina sha'anin k'uruciya, ban da haka ita da aka so yi mata fyaɗe har ta soma manta abun cikin ƴan mintuna ta fara sakin ranta. Kwanciya ta yi a jikin Inna cikin raunin murya ta ce. "Kaina ciwo, duk jikina ma haka musamman ƙafata da suka tattaka mun." Inna ta ce. "Allah ya saka miki, bari na ɗora miki ruwan zafi ki yi wanka sai ki ji daɗin jikinki, idan kika ci abinci kuma sai ki sha magani ki kwanta." A ɓangaren Matashin nan, yana fita cikin sauri ya nufi gidan Sarki dan yin alwala, a zaure ya tarar da su Ɗan_juma wanda suka iya tashi daƙyar suka fito. Wani mugun kallo ya watsa musu ya shige ɗakinsa. Hamza ya sauke numfashi ya dubi Ɗan_juma wanda ya bi bayan Matashin da wata muguwar harara ya ce. "Wai waye wannan ɗin ne Ɗan_juma da ya bazar da mu?" Harara Ɗan_juma ya banka masa ya ce. "Ban sani ba, ragwayen banza kawai, kuna gani yana auna mun naushi amma kuka kasa yi masa komai kuna kuku biyu sai ma ƙoƙarin guduwa kuka yi." Hamza ya ce. "Mu fa ba ragwanta ce ta saka muka yi yunk'urin guduwa ba, tsoron muke kar asirinmu ya tonu ya je ya faɗawa Sarki a hukunta mu." Ɗayan ya ce. "Ai har yanzu ma a cikin tsoron muke, tunda ba mu sani ba ko zai faɗa ɗin." Tsaki Ɗan_juma ya yi ya ce. "Wannan kuma ku ta shafa, dan ni ko a jikina, amma wallahi Wannan garan bai daki banza ba, sai na ɗauki fansar abun da ya mun." K'wafa ya yi ya fice daga zauren fuuuu kamar zai tashi sama, su Hamza suka mara masa baya. Daren yau gaba-d'aya Matashin nan da tunanin su A'isha ya yi shi manne a cikin zuciyarsa, ya rasa tausayi ne ko mene ne ya mamaye masa zuciya akan A'isha a gani ɗaya tak da ya taɓa yi mata yau a cikin rayuwarsa, hakan ya yi matuƙar ɗaure masa kai da ba shi mamaki ba kaɗan ba.....✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣0️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ...........Daren yau Inna ba ta iya runtsawa ba saboda tunanin wannan lamura iri_iri da suke faruwa da su, Tunda Ubangiji ya kawo su cikin garin nan zuciyarta ba ta huta ba, kullum da sabon al'amarin da yake riskar su na tashin hankali, amma duk ciki babu abun da ya fi firgita ta da tsorata ta kamar wannan yunk'urin yiwa A'isha fyaɗen aka yi, imagine take inda hakan ya kasance wataƙila da tuni tana k'iyama, dan ta san tsaf zuciyarta za ta iya bugawa saboda baƙin ciki. Ga wani tashin hankalin da yake risko su a gaba, wato dawowar Ƴaƴan Iya Maza gida da k'annen Malam waɗanda suke kasuwanci a Lagos, a bakin matan gidan ta ji suna zancen dawowar tasu. Duk ba su fiya shiga harkar ta ba amma Iya na zuga su su yi mata wulaqanci da tijara, guda ɗaya ne mai suna Yunusa wanda shine autansu Malam yake yi mata mutunci a cikin Mazan gidan.....Lokuta da dama idan abu ya ishi Inna ta kan ji dama su tattara kayansu su bar garin, kamar yau da aka yi yunk'urin ɓata mata rayuwar ƴa, sai dai idan ta tuna ba ta da gurin zuwa idan ta bar nan ɗin yakan saka dole ta hak'ura su ci-gaba da zaman. Washegari A'isha ta tashi da zazzaɓi da ciwon kai da ciwon jiki duka. Wajen ƙarfe takwas na safe Inna ta siyo musu koko da k'osai a gurin matar da ita kaɗai take siyar musu a cikin garin, dan Inna ba ko ina take zuwa siyayya a siyar mata da abu ba. Amma saboda rashin kunya ita a lokacin da ta yi sana'o'inta sai a zo a siya, saboda araha take yi sosai a kayan nata. A lokacin innar Ma'u kan yi dariya ta ce. "Gaskiya halin mutane sai su, suna ƙin ka da gudun ka rab'e su amma saboda son banza idan kana siyar da abu da sauƙi sai a zo gurinka a siya, idan har ƙin na Allah ai ko kyauta ka kasa abu ba'a zo a ɗauka ba." Inna kan yi murmushi kawai idan ta faɗi haka. Bayan Inna ta d'ibarwa A'isha abun karinta ta zauna a gabanta cikin kulawa ta ce. "A'isha daure ki tashi ki karya, kin ga babu komai a cikinki, jiya ma haka kika ƙi cin funkasau da na zo da shi." Cikin muryar marasa lafiya A'isha ta ce. "Inna ba zan iya ci ba, bakina ɗaci." Inna ta ce. "Daurewa za ki yi ki sha ko kokon ne." Girgiza kai A'isha ta yi tare da kawar da kai. Daƙyar Inna ta lallame ta, ta sha kokon kaɗan ta koma ta kwanta. Ganin haka Inna ta ce. "Bari na yi wanka sai na je na siyo miki maganin zazzaɓin idan masu chemist ɗin sun fito." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Bayan Inna ta yi wanka ta gama kimtsa gidan ta karya sai ta nemi guri ta zauna, jin shiru_shiru A'isha ba ta ji Inna ta ce za ta tafi gidan Hajiya Talatu ba, ta daure cikin magana daƙyar ta ce mata. "Inna sai rana ta yi ba ki tafi gidan abincin sadakar ba?" Inna ta ce. "Ba zani ba A'isha tunda ba kya jin daɗi." A'isha ta ce. "Inna akan me? Ba sai in zauna ki je ki dawo ba?" Inna ta ce. "Zance ma kenan, ai ko nan da can ba zan ƙara tafiya in bar ki ba, tunda an fara farautar rayuwarki, hanyar lafiya a bi ta da shekara, da dai ma lafiyarki ƙalau ne sai in saka ki a gaba mu tafi tare." Cikin wauta A'isha ta ce. "Inna kashe ni suka so yi ko? Tunda sun kwantar da ni sun daddanne ni, ina jin ma da wuk'a a hannunsu yanka ni suka so yi." Inna ta ce. "Uhm." Kawai. Aisha ta ce. "Mugaye kawai, ina jin wannan mutumin mai ƙamshin nan ne ya gan su ya k'wace ni." Inna ta ce. "Kin fara jin sauƙi kenan tunda har kike wannan surutun." Shiru A'isha ta yi ba ta kuma magana ba, sai bayan kusan mintuna biyar ta ce. "Inna ki tafi gidan aikinki kawai, sai ki kulle ni a ɗaki ki je ki dawo." Inna ta ce. "Saboda gani kuntacciya ko? Baki da lafiyar zan kulle ki a ɗaki in tafi wani gurin, idan wani abun ya same ki fa?" A'isha ta turo baki ta ce. "To Inna idan ba ki je ba a ina za mu samu kuɗi? Kuma ni abincin sadakar nan kawai nake son ci yau." Shiru Inna ta yi tana kallon A'isha, tabbas maganganunta suna kan turbar gaskiya, dan ɗan kuɗin da ta samo jiya babu abun da zai yi musu a cikin sati guda, amma idan ta je aikin ta ƙara samowa za su ɗan rage. Miƙewa ta yi ta ce. "Bari na kai ki gidan Sahura mai k'osai ki zauna a can kafin na dawo, na san za ta kula da ke yanda ya kamata. Sai na yi sauri na kammala aikina na dawo da wuri." Ƙarfe goma sha biyu na rana Matashin nan ya fito daga cikin gidan Sarki. Sanye yake cikin ƙananun kaya wanda suka matuƙar yi masa kyau, sai tashin daddaɗan ƙamshinsa yake yi. Cikin nutsuwarsa yake tafiya zuwa gidansu A'isha, a ƙofar gidan ya tsaya yana kalle_kalle ko Allah zai saka ya ga wani yaron ya aika shi ya yi masa magana da Inna. Cikin ikon Allah sai ga wani yaro ya fito daga cikin gidan. Kiransa ya yi sai kuma ya rasa wa zai ce ya kira masa, yana son ya tuno sunan da Inna ta kira A'isha da shi jiya amma ya kasa. Sai kawai ya cewa Yaron. "My friend Matar gidan zaka yi mun magana da ita idan tana nan." Yaron ya ce. "Wacce daga ciki? Dan matan gidan nan sun fi goma." Shiru ya ɗan yi na wasu sakanni sannan ya ce. "Ban san sunanta ba, amma fara ce mai ɗan jiki, tana da yarinya mai kyau, yarinyar kuma kamar ba ta gani." Yaron ya ce. "Oh wai Asabe Mayya kake nufi?" Cikin mamaki Matashin ya ce. "Mayya kuma?" Yaron ya ce. "Eh, ai Mayya ce, A'isha ma da ba ta gani ai idon wasu suka cinye aka dawo musu da abun kansu, da alama kai baƙo ne a cikin garin nan shi yasa baka sani ba." Kallon yaron kawai yake with more shocked bai ce komai ba, yanda yaron ya dage yana yi masa bayani sai ka ce wani babba. Murmurshi ya yi ya ce. "Yanzu dai tana nan ka yi mun magana da ita?" Yaron ya ce. "Tab', ai ba ma yi musu magana saboda kar su cinye mu, an hana mu gaskiya." Daga haka yaron ya yi gaba abin sa, bin sa ya yi da kallo maganganun yaron na yi masa yawo a cikin kai, musamman sunan A'ISHA da yaron ya ambata. Yana nan tsaye sai ga su Inna su karyo kwana ita da A'isha dake tafiya daƙyar. Ajiyar zuciya ya sauke ya ƙurawa A'isha ido gabansa na fad'uwa. Tunda Inna ta hango shi ta gane shi, A'isha da ba ta gani suna ƙarasowa kusa da shi ta ce. "Laa Inna na ji ƙamshin mutumin jiya." Inna ba ta ce mata komai ba, shi kam murmushi ya yi cikin girmamawa ya ce. "Sannu da zuwa Mama, Ina Yini?" Cikin fara'a Inna ta ce. "Yawwa, lafiya ƙalau, ka zo kenan? Allah yasa ba ka dad'e kana jira na ba." Kansa a ƙasa ya ce. "A'a ban jima da zuwa ba." Inna ta ce. "Bismillah mu shiga daga ciki to." Sai da suka shige sannan ya bi bayansu. Inna ta shimfid'a masa tabarma a tsakar gida ya zauna, duk da tsakar gidan ƙasa ne babu siminti amma Inna ta yayyafa masa ruwa ta share shi tass, sai ƙamshin ƙasa ne ke tashi a cikinsa. Inna ba ta zauna ba sai da ta kawo masa ruwan randa mai sanyi gami da abincin da suka shigo da shi. Ruwan kawai ya sha ya yiwa Inna godiya sannan ya gyara zama ya ce. "Mama dama na zo ne akan abun da ya faru jiya, ban sani ba ko A'isha ta faɗa miki?" Inna ta sauke numfashi ta ce. "Ta sanar mun da komai." Ya ce. "Amma Mama ba ta gani me yasa ake barin ta take fita ita kaɗai?" Inna ta ce. "Ba ta zuwa ko'ina ita kaɗai wallahi, jiyan ma tsautsayi ne Allah ya kawo, amma insha Allah hakan ba za ta kuma faruwa ba." Ya ce. "Allah yasa, Allah ya kiyaye gaba." Inna ta ce. "Amin, Amin, na gode sosai fa Allah ya saka da Alkhairi." A hankali ya ce. "Amin." Yana satar kallon ɗakin Inna da A'isha ke ciki, wadda tunda ta ji muryarsa ta yi tsit kamar ruwa ya cinye ta. Inna ta ce. "A'isha ta faɗa mun kai ka k'wace ta daga hannun azzaluman ko?" Gyaɗa mata kai ya yi sannan cikin sanyin murya ya ba ta labarin abun da ya faru. With more shock and concern Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Ɗan_juma kuma? Yanzu duk bibiyar yarinyar nan da yake yi dama da wata mummunar manufa ne?" Matashin ya ce. "Ya daɗe yana bibiyar ta ne dama? Amma ba ku ɗauki mataki ba?" Inna ta ce. "Nunawa kawai yake yi yana son ta tun tana ƴar ƙanƙanuwarta, ashe son ba na Allah ba ne." Girgiza kai ya yi ganin yanda hankalin Inna ya tashi ya ce. "Ok, babu damuwa, insha Allah komai ya zo ƙarshe Mama, zan sanar da Baba Sarki duk abun da ya faru, na san kuma zai ɗauki mataki akan hakan." Inna ta ce. "To na gode sosai, Allah ya saka da Alkhairi." Miƙewa ya yi ya ce. "Bari na wuce Mama, na ga lokacin Sallah ya gabato." Inna ta ce. "Har zaka tafi ba, to ba ka ci abincin ba kuma." Murmusawa ya yi ya ce. "Alhamdulillah, na gode." Inna ta ce. "To ka gaida gida, Na gode sosai." Bayan fitarsa Inna ta rafka tagumi tana tunani, ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba da ta ji Ɗan'juma ne ya yi ƙoƙarin ke ta haddin A'isha, ko kaɗan tunaninta bai taɓa kawo mata Ɗan'juman ne ba. Ta san da Ubangiji ya ba shi nasara akan A'isha shikenan ya ci bulus, domin babu matakin da za'a iya ɗauka a kansa. Duk da kasancewar Sarki adalin Mutum ne kuma yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin ya bawa iyalansa tarbiyya ingantacciya, amma shi kansa Ɗan_juman ya gagare shi, domin mahaifiyarsa ba ƙaramin ɓata shi ta yi ba, duk abin da ya yi ita take ɗaure masa gindi, ta shagwab'a shi ba kaɗan ba saboda shi kaɗai ne ɗanta a duniya. Hakan yasa Sarki ya zuba musu ido kawai ya ce indai duniya ce za su gani, tunda ya yi iyakar ƙoƙarinsa akan ganin rayuwar Ɗan_juma ta saitu amma hakan ya gagara, sai dai duk da haka bai fasa bin sa da addu'ar shiriya ba. A'isha ce ta fito daga ɗaki cikin laluban haya ta zauna a tsakar gidan ta ce. "Inna wannan mutumin ya iya magana, maganarsa irin ta ƴan gayu a hankali, me yasa ba ki tambayar mana shi sunansa ba?" Inna ta ce. "Da kin sani ai kin fito kin tambaye shi da kanki, uwar magana kawai, ba ki da lafiyar ma ba za ki bar ni in ji da abun da yake damuna ba sai kin ishe ni da surutu."  Turo baki A'isha ta yi ba ta kuma magana ba, cikin ranta kuwa cewa take yi, 'Dama tana gani ta ga wannan ɗan gayun mai daɗin ƙamshi ya yake.' Bayan an sauko daga Masallacin Juma'a Sarki ya gama gaggaisawa da Jama'a Matashin nan ya same shi ya zayyane masa duk abun da ya faru jiya Na ƙoƙarin cutar da A'isha da su Ɗan_juma suka yi. Sosai ran Sarki ya ɓaci, cikin takaici ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan Mata Asabe ita da ƴarta suna ganin tashin hankali da taskun rayuwa kala_kala a cikin garin nan, daga wannan sai wannan, ba don Allah ya kawo ka ba UMAR da tuni wannan shashashan yaron sun ɓata mata rayuwar yarinya. Allah ya biya ka bisa wannan ceto da ka yi, shi kuma Ɗan_juma da sauran abokanan shashancin nasa zan ɗauki mataki mai tsauri a kansu Insha Allahu, a yau ba gobe ba." Godiya Umar ya yi masa ya tashi zuciyarsa cike da son sanin abubuwan tashin hankalin da Sarki ya ce suna samun su Inna, ya rasa me yasa zuciyarsa ta damu da al'amarin waɗan nan bayin Allah, daga juya zuwa yau kaɗai tausayinsu ya cika masa zuciya, sai kuma wani abu daban da yake ji a cikin ransa bayan tausayin da bai san mene ba a game da A'isha...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣1️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Daga Masallaci direct cikin gida Sarki ya wuce sashen Matarsa ta uku wato mahaifiyar Ɗan_juma. A lokacin Ɗan_juma yana kwance ya yi matashi da cinyarta tana lallab'a shi akan ya ci abinci, shi kuma sai taɓara yake zuba mata. Muryar Sarki suka tsinkaya a kausashe yana faɗin. "Rabi! Rabi! Yaron nan yana ciki?" Dan ɓata fuska Rabi ta yi tana duban da Sarki ta ce. "Ranka ya daɗe lafiya kake mun wannan kiran haka murya a sama?" Sarki ya ce. "Ban sani ba." Sannan ya dubi Ɗan_juma ya ce. "Kai! taso." Tashi zaune Ɗan_juma ya yi yana b'ab'b'ata fuska. Cikin tsawa Sarki ya ce masa. "Ba da kai nake ba ne? Ka zauna kana kallo na." Miƙewa tsaye Rabi ta yi ta ce. "Wai me ya faru ne Yallabai na ga kamar ranka a b'ace? kuma sai magana kake yi cikin hargagi, wato an zigo ka akan Shalele an maka masa wani sharrin ko?" Wani kallo ya wurga mata bai ce komai ba ya tasa Ɗan_juma a gaba suka fice ya bar ta tsaye baki buɗe. Da dogarai guda biyu Sarki ya haɗa Ɗan_juma da su ya ce. "Ka je ka raka su duk inda za'a samu sauran abokanan shashancin naka da kuka yi yunk'urin yiwa Yarinyar mutane fyaɗe jiya." Wani murmushi Ɗan_juma ya yi irin idon't care ɗin nan sannan ya yi gaba, dogaran suka bi shi a baya. Bayan Magriba Inna sun fito za su tafi chemist suka haɗu da Umar, yana tsaye a ƙofar gidan Sarki yana latsa wayarsa. K'ansa a ƙasa ya gaishe da Inna, ta amsa cikin fara'a. Yana kallon A'isha ta ƙasan ido ya ce. "Unguwa za ku ne Mama?" Inna ta ce. "A'a, nan chemist zan kai A'isha ba ta jin daɗi ne." Cikin tausayawa ya ce. "Subhanallahi, amma dai jikin nata da sauƙi ko?" Inna ta ce. "Alhamdulillah." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, sai kun dawo......Sannu A'isha, Allah ya ƙara sauƙi." A ƙasan mak'oshi ta amsa masa, shi ko ji ma sosai bai yi ba. Har sun yi gaba zuciyarsa ta ba shi umarnin ya bi su ba tare da shi kansa ya san dalili ba. Bayan sun je mai chemist ɗin ya duba A'isha ya ce allura zai yi mata ta kwana uku 600. Shiru Inna ta yi tana tunanin gaba-d'aya kuɗin hannunta bai fi 800 ba, amma ya za ta yi? haka ta ce a yi mata. Jin haka A'isha ta fara hawaye tare da lafewa a jikin Inna, dan ba ta k'aunar allura ko kaɗan a rayuwarta. Umar ne ya yi sallama a cikin chemist ɗin, su Inna suka amsa masa, da mamaki Inna take duban sa amma ba ta ce komai ba. Bayan Mai chemist ɗin ya gama haɗa allurar ya dubi A'isha ya ce. "Bismillah ku shigo a yi mata." Kuka A'isha ta fashe da shi ta ce. "Ni dai Inna dan Allah kar a mun allura." Inna ba ta kula ta ba ta ja ta suka shiga, daƙyar ta bari aka yi mata allurar, sai gunjin kuka take yi. Inna za ta biya kuɗin ta tsinkayi muryar Umar yana tambayar mai chemist ɗin nawa ne kuɗin, ta juyo ta dube shi ta ce. "Haba Ɗana, ka bar shi ma zan biya ai." Murmurshi ya yi bai ce komai ba ya zaro kuɗi a aljihunsa ya bayar bayan mai chemist ya faɗa masa adadin kuɗin, ko kaɗan Inna ba ta so haka ba, ba ta so ta saka shi wahala ba, godiya ta yi masa sosai sannan ta fita za ta siyo abu ta cewa A'isha ta jira ta anan ta je ta dawo. Bayan fitar Inna ya zauna a kusa da A'isha akan benci ya ce. "Kukan ya isa haka me tsoron allura." Turo baki A'isha ta yi ba ta ce komai ba ta shiga share hawaye." Murmurshi ya yi ya ce. "Ya jikin naki?" A hankali ta ce. "Da sauƙi." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, da fatan kina cin abinci dai ko?" Girgiza masa kai A'isha ta yi ta ce. "Bakina ɗaci, bana son cin komai." Ya ce. "Ba kya so ki warke kenan a daina yi miki alllura?" Ta ce. "Ina so." Ya ce. "To ki dinga cin abinci kin ji Indo?" Ta ce. "Toh." Tare da ɗan ɓata fuska na Indon da ya kira ta da shi. Dai_dai nan Inna ta dawo ta yi masa sallama suka wuce gida. Suna shiga gida suka tarar da Matan gidan da yaran gidan tsaitsaye a bakin ɓangarensu. Da mamaki Inna ta tsaya tana kallon su, Iya ta tako ta tsaya a gabanta tana mitsi_mitsi da ido ta ce. "Yanzu Asabe rayuwar da kika ɗaukarwa kanki kenan ta bin maza ke da ƴarki?" Inna ta yi shiru kawai tana kallon ta cikin mamaki. Iya ta ce. "Kya yi shiru ki tsare ni da ido mana, to wallahi ki saurara ki ji ba zai yiwu ba, baki isa ba, ba'a gidan nan ba, baza ki dinga kawo mana maza kuna iskanci har cikin gida ba." Ramatu ta karɓe zancen da faɗin. "Jiya fa ana cikin tsakiyar zuga ruwan nan amma na gan su a soro cikin duhu ita da shi da ƴar, abun kunyar ma yaro ne qarami ɗan cikinta, ɗazu kuma har cikin gida ta shigo da shi." Wata ƴar budurwa mai siffar fitsararru ta amshe zancen da faɗin. "Iya yanzu ma fa tare na gan su da shi, kuma ba ku gan shi ba kyakkyawa ɗan birni, duk yanda aka yi wani abun nasu na Mayu ta yi masa ta asirce zuciyarsa, ban da haka ya zai yi ya kula su." Jan hannun A'isha Inna ta yi suka shige ciki zuciyarta na mata k'una, abun mutanen gidan nan ya daina ba ta mamaki sai dai tsoro, wani lokacin kuma uzuri take musu, kamar dai yau da haukansu ya ba su su yi mata k'azafi. Suna shiga ɗaki A'isha da ta haɗe rai sosai ta ce. "Su ƴan gidan nan kullum masifa_masifa, su ta yi mana masifa, Inna dan Allah mu bar musu gidan mu tafi gurin ƴan'uwanmu da kika ce muna da su, Allah na gaji da zaman gidan nan." Kama hannun A'isha Inna ta yi ta ce. "Na fi ki son mu bar gidan nan A'isha, ƙaddara ce ta saka har yanzu muke zaune a cikinsa, babu yadda zamu yi ne. Na sha ki faɗa miki ki kasance mai hak'uri akodayaushe a duk halin da kika tsinci kanki a rayuwa, duk wannan abubuwan da suke faruwa watarana za su wuce su zamo labari, komai lokaci ne a rayuwa." Cikin sanyin jiki A'isha ta gyaɗa mata kai. Suna nan zaune sai ga yaro ya shigo da leda wai a bawa A'isha in ji wani. Inna ta ce gaskiya ba su ake nufi ba sai dai in yaron ɓatan kai ya yi, amma yaron ya ce su aka ce masa, kwatantawa Inna Umar ya yi, lokaci ɗaya Inna ta gane shine, godiya ta ce yaron ya yi masa sannan ta karb'i ledar cikin mamakin wannan hidimar da yake yi musu. Dafaffiyar indomie ce da k'wai sai yoghurt mai sanyi na jarka. Tunda A'isha ta shak'i ƙamshin abincin yawonta ya tsinke, ai kuwa zagewa ta yi ta ci abincinta ta kora da yoghurt ɗinta, ta ma manta da wani ɗacin baki. Washegari Sarki ya aiko aka kira masa Inna ya ba ta hak'uri akan abun da su Ɗan_juma suka yi, sannan ya tabbatar mata da hakan ba za ta kuma faruwa ba Insha Allahu, dan yanzu haka ma su Ɗan_juman an kulle su an saka musu mari, kuma ana ba su horo mai tsanani. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, kullum Umar sai ya haɗu da su Inna idan A'isha zata je makaranta ko kuma idan ta dawo, suna gaisawa sosai da Inna amma A'isha ba ta yi masa magana, shi ma kuma sai dai ya kalle ta kawai. Inna har ta gaji da yi mata faɗan ƙin gaishen shi da take yi. Yau ya kama ranar Juma'a, sati biyu da haɗuwarsu A'isha da Umar. Da yamma Inna tana wanka A'isha ta lallab'a ta fita ƙofar gida ta tsaya tana kallon hanya kamar mai ganin masu wucewa, Umar yana bakin masallaci ya hango ta, da yake masallacin opposite ɗin layinsu Aisha yake. Cikin mamakin yanda ta iya fitowa ya miƙe ya ƙarasa ƙofar gidan nasu. Tana can duniyar tunani ba ta ma san ya ƙaraso ba, key ɗin ɗakinsa ya ɗauko a aljihunsa ya shiga karkad'awa a wajen kunnanta. Ɗan zabura ta yi fuskarta na nuna alamun tsoro ta ja baya. A hankali ya ce. "I'm sorry na tsora ta ki ko?" Ajiyar zuciya ta sauke ba ta ce komai ba sai ɓata fuska da ta yi. Murmusawa ya yi ya ce. "Tunanin me kike har na zo nan ba ki sani ba?" Canzawa fuskarta ta yi ta koma kalar damuwa, cikin sanyin murya ta ce. "Jarrabawa za mu fara ranar Monday, ni kuma ban san ta yaya zan yi ba." Kama hannunta ya yi suka zauna akan dankalin dake ƙofar gidan ya ce. "Kafin nan, wa ya fito da ke nan?" Ta ce. "Da kaina na fito." Ya ce. "Amma Mama ba ta sani ba ko?" Ta ce. "Eh wanka take yi, ni kuma na gaji da zaman gida." Ya ce. "Ta yaya kika fitowa?" Ta ce "Ai na san hanya, kawai bi nake yi a hankali." Shiru ya yi yana kallon ta cike da tausawa na wasu sakanni sannan ya ce. "Me yasa idan kika gan ni ba kya gaishe ni?" Cikin shagwab'a ta ce. "Kai ma ai baka mun magana sai dai ka gaishe da Inna kawai." Ya ɗan lumshe ido ya buɗe ya ce. "To na daina, daga yau zan dinga yi miki magana, ai mun zama Friends ko?" A'isha ta ce. "Kai! ta yaya? Kai fa Namiji ne." Ya ce. "Eh duk da haka, ni dai kin zama ƙawata." Dariya A'isha ta yi ta ce. "Tab', so kake Inna ta zane ni ina abota da Namiji?" Ya ce. "Ai zan faɗa mata da kaina." A'ishah ta ce. "Wai kai ina ne gidanku?" Ya ce. "Gidan Sarki." A'isha ta ce. "Amma ya aka yi ban san ka ba tun daa? Inna ma haka." Ya ce. "Wasa nake miki, gidanmu ba'a nan garin yake ba, wani abu ne ya kawo ni garin nan akan karatuna." A'isha ta ce. "To a ina kuke?" Ya ce. "Kaduna State, kin san garin?" Girgiza masa kai ta yi ta ce. "Sarkin Ɗan'uwanku ne?" Ya ce. "Abokin Abbanmu ne." Ta ce. "Me kake yi a garin nan to?" Ya ce. "Gona nake zuwa da sassafe kullum ina duba abu." Ta ce. "Yaushe zaka tafi?" Ya ce. "Sai an ɗan daɗe." Dai-dai nan Inna ta lek'o dan duba A'isha, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Sannu A'isha." A'isha ba ta ce komai ba dan ta san ta yi laifi, shi kuwa ƙasa ya yi da kansa ya gaishe da Inna, ta amsa cikin fara'a sannan ya tashi ya tafi, yana jin zuciyarsa cike da Nishad'i sanadiyyar kasancewar su da A'isha. Ita ma ji ta yi dama kar ya tafi ya zauna su yi ta hira, tunda su Ma'u suka tafi ba ta da abokin hira, ko a makaranta sai dai ta zauna ta yi shiru ita kaɗai. Jiki a sanyaye ta tashi Inna ta kama hannunta suka shige gida. A hankali a hankali Umar yake shiga jikinsu Inna, dan kullum sai ya zo har gida ya gaishe da Inna tare yi musu Alkhairi. Cikin lokaci kaɗan suka saba da shi sosai, Inna ta yaba da hankali da nutsuwarsa shi yasa ta saki jiki da shi, zuciya tana son mai kyautata mata, Umar sai ya zamowa A'isha tamkar madadin Ma'u, dan mayar da kanshi yake yaro kamarta su yi ta hira cikin barkwanci. Cikin wata guda ya fahimci irin rayuwar da suke yi a cikin garin ta matsin rayuwa da ƙyarar su da ake yi, tausayinsu ne ya ninku a cikin zuciyarsa, hakan yasa ya ɗauki damarar taimaka musu har sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Tun daga kan kayan abinci da komai na buƙatar rayuwa ya siyo mai ɗan yawa musu ya kawo musu, Inna ta dinga yi masa faɗa tana cewa kayan sun yi yawa ita baza ta karɓa, daƙyar ya lallab'a ta, ta karɓa. Ai kuwa ya sha addu'oi da tarin godiya. Mutan gidan sai yawo suke yi da inna a cikin gari suna cewa daga yin baƙo daga birni Inna ta lashe masa kurwa kullum yana jikinsu yana yi musu uban hidima yana wahala da su. Sarki kuwa yana sane da duk abun da yake faruwa, hakan ma shi daɗi ya yi masa, ya dinga sakawa Umar albarka akan taimakon su inna da yake yi. Su A'isha sun yi jarrabawa a makaranta, amma ita ba ta yi ba tunda ba ta gani, an yi hutu, hutun kuma mai yawa kasancewar idan an dawo sabon aji za'a shiga. Tunda aka yi hutun kullum da safe sai Umar yake yiwa A'isha lesson da baki (Oral), kuma Alhamdulillah tana ganewa, dan har words ɗin English yake koya mata, da yamma kuma su yi karatun Alkur'ani da tarihin Annabawa, da karatun su fiqhu. Yau da safe wajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe A'isha na zaune akan tabarma a tsakar gida tana aikin b'ab'b'ata fuska tare da turo baki gaba, saboda Inna ta yi mata faɗa akan barnar ruwan da ta yi mata da sunan zata yi mata wanke_wanke ba tare da ta saka ta ba, Umar ne ya shigo gidan cikin shirinsa na manyan kaya, ya yi kyau sosai ya fito a matashinsa na ɗan 25 years. Tun kafin ya ƙaraso cikin zagayen su Inna ƙamshinsa ya riga shi zuwa, cikin kamilalliyar muryarsa ya yi sallama. Suka amsa mata a tare. Cikin girmamawa ya tsugunna ya gaishe da Inna dake cikin madafi tare da yi mata sannu da aiki, ta amsa cikin fara'a sannan ya ƙarasa ya zauna a kusa da A'isha. A hankali ya ce. "Good Morning." Shiru ta yi masa. Yana kallon yanda ta cukule ta kumbura k'iris take jira ta fashe ya danne dariyar dake cin sa ya ce. "Yau babu magana ne Indo?" Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ya Umar na ce ka daina ce mun Indon nan?" Ya ce. "To ai na fi son na kira shi da sunan ya fi mun daɗi." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni dai gaskiya bana so, sai ka ce wata tsohuwa?" Shiru ya yi yana kallon ta tare da sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa a hankali. After some seconds ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "To na daina HUMAIRAH." murmurshi ta yi ta ce. "Yawwa Yayana, ai gara Humairan da wani Indo." Murmurshi ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce. "Kin yi kyau sosai Bestie." A'isha ta ce. "Amma ban kai ka ba ko? Na san kai kyakkyawa ne." Ya ce. "Taɓ, a yi shiru dai kawai." Kallon sa ta yi ta ce. "Ina son na gan ka Ya Umar." Yanda ta yi maganar cikin raunin murya sai ta tsinkar masa da zuciya, a hankali ya ce. "Za ki ganni watarana soon Insha Allah." Ta ce. "Allah yasa." Lesson ɗin ya shiga yi mata bayan sun ɗan yi revision akan na jiya ya ƙara tuttuna mata abun da ta manta. Suna cikin karatun wayarsa ta yi ƙara alamar shigowar kira, ɗaukowa ya yi ya duba, ganin mahaifiyarsa ce ya daga ya kara a kunne tare da yin sallama. Daga can bayan ta amsa sallamar ta ce. "Ka kira ni ina part ɗin Abbanku, wayar kuma tana ɗaki sai yanzu da na dawo na gani." Ya ce. "Ok, an tashi lafiya Mom? Ya su Abban da Mufeedah?" Ta ce. "Suna nan lafiya ƙalau, da fatan kai ma haka?" Ya ce. "Alhamdulillah, sai dai kewar ku kawai da nake yi Mom." Mom ta ce. "Yaushe zaka dawo ne? Na ji Abbanku yana wai sai nan da 1 month." Ya ce. "Eh haka ne." Mom ta ce. "Uwar me zaka yi har na 3 months a wannan ƙauyen? Me yake damun ka ne Faruq?" Cikin kwantar da murya ya ce. "Mom ban gama abun da na je yi ba ne." A fusace ta ce. "Ai baza ka taɓa gamawa ba, ko aikin uban me ne ai zuwa yanzu ya ci ace in ma haddacewa ne ka yi ba iyawa kaɗai ba. Kawai kana son ka ɓatan rai ne Faruq, amma ka san ba son zamanka a ƙauyen nan nake ba, yanzu kafin ka dawo na san duk sai ka yi baƙi ka fita daga hayyacinka ka koma kalar ƴan garin." Umar ya ce. "Haba Mom dan Allah ki yi hak'uri, garin fa akwai daɗin zama, yanda kike tunaninsa ba haka yake ba, dan suna da abubuwan...." cikin hasala ta katse shi da faɗin. "Kai ka san wannan, ni dai abun da zan faɗa maka nan da 1 week ka haɗa kayanka za'a zo a ɗauke ka, zaman ƙauyen naka ya ishe ni haka. Ko ka gama abun da ka je yi ko ba ka gama ba is not my concern." Cikin damuwa ya ce. "Amma Mum......" A fusace ta ce. "Umarni nake baka Faruq, idan kuma ban Isa ba ne sai in ji......Ka je ka zauna a ƙauye for almost two months bai ishe ka ba sai ka ƙara wasu kwanakin, salon ka saba da ƴan garin har bayan ka dawo ka dinga mu'amala da su....To ba zai yiyu ba wallahi, wannan zaman ma da ka yi ba ƙaramin hak'uri na yi na danne zuciyata ba, dan dai babu yanda zan yi ne tunda Mahaifinka ya ce dole sai ka je. Sanin kanka ne ka san ni sarai bana son tarayya da TALAKA da duk wani abu da ya danganci TALAUCI, balle kuma TALAKAN ma na ƙauye!" K'wafa ta yi ta cigaba da magana cikin ɗacin rai da faɗin. "Kamar ni a ce ɗana ya tafi wani ƙauye yana rayuwa a can na tsawon watanni? this is too much shameful thing for me." Shiru Umar ya yi ya rasa me zai ce mata, tsaki ta ja tare da kashe wayarta............✍️ *FAUZARH ORGANIC SKINCARE* _PRESENT_ *5️⃣ DAY'S SKINCARE ONLINE TRAINING* *💗ABUBUWAN DA ZAN KOYAR💗* *da farko zanyi bayani akan ƙurajen fuska da abun da ke kawosu, da hanyar da za a bi wajen magance su* *WHITENING BLACK SOAP* *LIGHTENING BLACK SOAP* *NATURAL BLACK SOAP* *FACE AND BODY SOAP* *BODY CREAM* *SABULUN GYARAN AMARYA* Wannan training ɗin tamkar gara6asa ne🤩 da naira ɗari ukun ki kacal za ki koyi sana'a.👌 *Zamu fara training din 5 ga wannan watan ne insha Allah* *DUK GARIN DA KI KE ZAN SANAR DAKE INDA ZA KI SAMU KAYAN HADIN* *Domin neman karin bayani a tuntu👉🏼http://wa.me/+2347065012071* *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣2️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Cikin sanyin jiki Umar ya zare wayar daga kunnensa, A'isha da ta yi shiru tare da zuba masa ido kamar tana ganin sa ta ce. "Wa ya kira ka a wayar?" Numfashi ya sauke tare kallon cikin idonta ya ce. "Mamana ce." Ɓata fuska ta yi ta ce. "Shine ba ka ba ni mun gaisa da ita ba." Jinjina kai ya yi a ransa yana imagine masifar da Mom za ta cinye shi da ita idan ya ba ta suka yi magana da wani a garin nan da sunan sun saba da shi. Cikin sanyin murya ya ce. "Sorry, zan kira miki ita wani time ɗin." Murmurshi A'isha ta yi. "Toh na gode." Inna ce ta zo ta ajiye tuwo da miyar da ta gama dafawa a gaban Umar, sannan ta koma ta deb'o masa ruwa ta kawo masa. Cike da kunya ya yi mata godiya sannan ya ɗauraye hannunsa ya yi Bismillah ya fara cin tuwon cikin nutsuwa bayan Inna ta shige ɗaki. A'isha ta turo baki cikin ɗaga murya yanda Inna za ta jiyo ta, ta ce. "Inna ni baki kawo mun tuwon ba." Inna ta ce. "Sai kuma na tashi, yanzu ina hutawa ne, tunda kina ji ai na kawo masa amma ba ki yi magana ba." A'isha ta ce. "Ni ban ji sanda kika kawo masa ba." Inna ta ce. "Ai ba za ki ji ba dama." Murmurshi Umar ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce. "Zo in baki wannan a baki ki ci." Waro ido A'isha ta yi tare da buɗe baki za ta yi masa kwakwazo. Cikin saurin ya rufe mata baki da hannunsa kamar ya san me take shirin yi. Cikin rad'a ya ce. "Wasa nake miki ba baki zan yi ba." Ture hannunsa ta yi ta ce. "To sai ka ce wata yarinya zaka ba ni abinci a baki?" Bai ƙara magana ba saboda yanda kunya ta lullub'e shi, dan ya san daƙyar idan Inna ba ta ji abun da A'isha ta faɗa ba. Da ya gama cin abincin ba su cigaba da karatun ba, sallama ya yi musu ya tafi. Yana fita daga gidan ya ga su Ɗan_juma a ƙofar gidansu Hamza a zaune, suna haɗa ido da shi ya haɗe rai, ya yi wucewarsa. Wani wulak'antaccen kallo Ɗan_juma ya bi shi da shi sannan ya yi k'wafa ya ce. "Gayen nan yana shigar mun hanci da ƙudundune ba kaɗan ba wlh, ya sa Sarki ya mun iyaka da yarinyar can sannan shi kuma yana lallab'awa yana zuwa gurinta yana yaudarar su da ƴan canji yana yin abun da ya ga dama ita, To billahillazi baza ta saɓu ba, kafin ya bar garin nan sai na yi masa abun da har ya mutu ba zai manta da ni ba, da ni yake zancen." Hamza ya ce. "Kai Ɗan_juma yanzu duk izayar da muka sha akan yarinyar nan baza ka rabu da ita ba?" Ɗan_juma ya yi wata dariya ya ce. "Ai ni wahalar da suka ba mu ƙara mun yawan abun da nake ji a kanta suka yi ba su sani ba, ni fa tunda na had'iyi yawo akan wannan yarinyar sai na mayar da yawuna ko ta halin yaya." Hamza ya ce. "To Allah ya ba da sa'a." Da yamma Umar ya koma gidansu Inna, suna zaune a tsakar gida shi da Aisha, Inna kuma tana bakin rariya tana wanki. Umar da yake kallon A'isha ya ce mata. "Wai Humairah duk akan turaren ne aka ƙi mun magana tun ɗazu?" A'isha ta ce. "Tun yaushe na ce maka ina son ƙamshin ka kawo mun amma ka ƙi? Ai na san da budurwarka ce ta ce ka ba ta da tuni ka ba ta." Umar ya ce. "Haba Indodona kema fa zan baki, mantawa nake yi ne." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni ba ma na so yanzu." Umar ya ce. "Me yasa? Haba Bestie kar ki yi fushi da Yayanki mana, bari in tashi yanzu in ɗauko miki." Aisha ta ce. "Ni dai ba na so, ko ka kawo ba zan karɓa ba." Cikin marairaicewa ya ce. "Dan Allah ki yi hak'uri ni ne fa?" A hankali ta ce. "Kana son na hak'ura?" Ya ce. "Eh." Ta ce. "To sai ka roƙi Inna ta bar ni mun je bakin ruwa mu yi wasa." Umar ya ce. "Kin san ma ba za ta bar ki ba, last week ma haka kika yi ta rok'on ta, ta ƙi barin ki." A'isha ta ce "to ai tare zaka ce mata zamu je, za ta bari." Shiru Umar ya yi amma ya san Inna ba za ta bari ba. Kamar A'isha za ta yi  kuka ta ce. "Dan Allah Ya Umar?" Ya ce. "Shikenan let me try." Duk maganar da suke yi a ƙasa_ ƙasa suke yi dan kar Inna ta ji. Yana shafa kai ya ce. "Am.... Mama wai zaki bar A'isha ta je bakin ruwa ganin wasa?" Inna ta juyo ta ce. "Idan ta je da wanne idon za ta gani banda neman magana irin nata?"  A'isha ta ce. "Dan Allah Inna ki bar ni, ni kullum ina gida ba na fita, ko me ake yi bana zuwa." Ta ƙarashe zancen idonta cike da hawaye, sai ta bawa Umar tausayi, ga kuma wani iri da ya ji a cikin ransa ganin tana hawaye, bai san lokacin da ya ce. "Mama ki bar ta dan Allah sai mu je tare." Inna ta ɗan yi jimmm sannan ta ce. "To shikenan amma kar ku kai Magriba." Umar ya ce. "Insha Allahu." Rawa A'isha ta kama yi daga zaunen da take cikin murna. Harararar ta inna ta yi ta ce. "Sai in fasa barin naki in baki nutsu ba." Nutsuwa ta yi tare da miƙewa, Umar yana murmurshi ya tashi ya ɗauko mata takalmanta ta saka ya ciro mata hijabinta dake kan igiya ta saka sannan ya kama hannunta suka fice bayan sun yiwa Inna sallama. Inna ta bi su da kallo tana ganin rashin dacewar riƙe hannun A'isha da Umar ya yi, da tana da hali wani yaron za ta kira ya kama hannun A'ishan a maimakon Umar ɗin, addu'ar Allah ya tsare ta yi musu sannan ta cigaba da wankinta.   Bakin ruwa wani ɗan ƙaramin ruwa ne a cikin garin dake bayan gidan Sarki, duk ranar asabar da yamma ƴan'mata da samari na taruwa a gurin a yi wasanni, har kid'a ake bugawa wasu su shiga su yi rawa, gefe guda kuma ga masu siyar da abubuwan siyarwa kala_kala. Yau ma kamar kullum an cika a gurin, wasu na tad'i wasu suna cikin ruwa suna wanka. Kallon abubuwan da suke faruwa Umar ya tsaya yana yi, dan duk zamansa a cikin garin bai taɓa zuwa gurin ba sai yau. A'isha dake cikin farinciki ta ce. "Ya Umar mu je mu shiga ruwa." Kallon ta ya yi ya ce. "Ruwa kuma Humairah? ke da ba gani kike ba sai kin je ya tafi dake?" Shagwab'e fuska ta yi ta ce. "Ruwan fa k'arami ne ba shi da zurfi, kuma ba shiga za mu yi ba ƙafafuwanmu kawai za mu saka a ciki." Bai ce komai ba ya ja ta zuwa bakin ruwan ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna. Fiye da rabin mutanen gurin kallon su suke yi, musamman ƴan'mata da ba ƙaramin tafiya da hankalinsu Umar ya yi ba. A hankali ya zarewa A'isha takalmin ƙafarta ta zira ƙafafuwan nata a cikin ruwa fuskarta ɗauke da murmurshin dake nuna tana cikin farinciki. Tana ta wasa da su a cikin ruwan shi kuma yana ta aikin kallon ta, cikin ransa yana yaba kyawun halittarta, babu abun da ya fi burge shi a tattare da ita kamar kalar fatarta da dara_daran idanunta. Lumshe idonsa ya yi yana jin yanda son ta yake ƙara mamaye ko'ina a cikin zuciyarsa. After 15 minutes ya ce mata su tashi su je su saya wani abun su ci, shago suka shiga ya siya mata choculate da drinks. Suna zaune a ɗan nesa da ruwan kaɗan A'isha tana shan choculate ɗinta ta ce. "Yaya Umar ka ga gurin akwai daɗin zama ko? Ina son zuwa tun daa Inna ce ba ta bari na." Umar ya ce. "Eh, dan gaskiya ina cin dariya tunda na zo gurin nan, musamman in naga an shiga filin rawa ana cashewa." Ya ƙarashe maganar cikin dariya. A'isha ta yi murmurshi ta ce. "Ko mu ma mu je mu yi ne?" Waro ido ya yi ya ce. "Ai ban iya ba, ni dai mu zauna a nan ki bani labari mai daɗi." A'isha ta ce. "Ni ba ni da labari, sai dai kai ka ba ni na ƴan'gidanku dama baka taɓa ba ni ba." Karɓar choculate ɗin hannunta ya yi ya ce. "Sai dai na baki na budurwata, kina so?" Ɓata fuska A'isha ta yi ta ce. "Bana so." Tare da ɗauke kanta gefe. Murmurshi Umar ya yi ya ce. "Shikenan ga choculate ɗinki cigaba da sha." A'isha ta ce. "Na ƙoshi." Karyar da kai ya yi yana kallon ta kawai, ita kuwa sai ƙare haɗe rai take tana turo baki gaba. Cikin sanyin murya ya ce. "Wai me ya faru na ga kina ɓata rai?" Kamar zata yi kuka ta ce. "Babu komai." A hankali ya ce. "I'm sorry, bana son na gan ki a irin wannan yanayin." Sakin fuska A'isha ta yi jin yanayin da ya yi magana ta ce. "Shikenan Yayana, ka san me?" Ya ce. "A'a." Ta ce. "Yau so nake ka mun waƙa mai daɗi." Da mamaki ya ce. "Waƙa kuma?" Ta ce. "Eh." Ya ce. "Ai ban iya ba." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni dai kamun ko in yi kuka." Sauke numfashi ya yi ya ce. "Shikenan zan miki, amma ban iya na Hausa ba dan bana jin su." A'isha ta ce. "To ka mun ko ma wacce ce." Ɗan jim ya yi sannan ya yi gyaran murya ya fara rere mata waƙar cikin daddaɗar muryarsa. "_*I'm in love with my Bestie and I don't know what to do.......*_ _*Sometimes I dey feel say She dey feel the same way I do.........*_ _*But she day call me brother I no dey bab that thing........*_ _*'Cause sometimes we dey act like lovers Wey we dey do more things........*_ _*My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie Eh........*_ _*If you dey hear this song just know sey somebody fall for you.*_ _*My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie Eh.......*_ _*I know sey I no for catch feelings but ebe too risky to loose you to another one oo.........*_ _*So somebody tell me wetin man for do*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you.*_ _*So somebody tell me wetin man for do*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you......*_ _*Is it my brain or my body? May be my heart no well.*_ _*Aw Bestie eh wherever you dey I say you for hear me today I don't care if I shy for your face........*_ _*So Bestie, you no dey wonder why The girls girls no dey come my way no more times your jealousy sef dey blow ma mind*_ _*But Edey give me whim so I dawg them all*_ _*Now as you then your guy Shon I hope say we go fit to go the next level.........*_ _*'Cause the feeling dey grow strong make we look sharp before we start to blame devil........*_ _*Somebody tell me wetin man for do*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you......*_ _*Somebody tell me wetin man for do*_ _*(Somebody tell me wetin man for do)*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you*_ _*(I'm in love with my Bestie yeah).*_" A'isha dake sauraren sa ta lumshe ido jin ya yi shiru ta ce. "Amma wannan waƙar nan ta yi daɗi sosai, zaka dinga yi mun kullum?" Umar dake kallon ta ko ƙifta ido ba ya yi ya ce. "Why not? Zan dinga yi miki mana." Ta buɗe idonta ta ce. "Na gode sosai, yanzu mu je mu ƙara shiga cikin ruwa, daga nan sai mu tafi gida." Umar ya ce. "Magriba fa ta kusa, kuma Mama ta ce kar mu yi dare." Cikin marairaicewa ta ce. "Muna shiga fa za mu fito, kawai ɗan wasa zan yi da ƙafata a ciki." Umar ya ce. "Shikenan mu je." Ya kama hannunta suka tashi suka ƙarasa bakin ruwan suka zauna, kamar ɗazu ita kaɗai ta saka ƙafarta shi bai saka ba. A hankali ya kai ragowar choculate ɗin da ta rage bakinta, matsar da fuskarta ta yi ta ce. "Mene wannan?" Ya ce. "Buɗe bakin, choculate ɗinki zan baki." Za ta yi magana ya ce. "Please...!" Numfashi ta sauke ta buɗe bakinta a hankali ya saka mata ta gutsara ta fara sha cikin jin kunya, ƙasa ta yi da kanta tana jin kamar ta yi sab'o yau namiji ya ba ta abu a baki, ga wata irin kunya da ta ji ta lullub'e ta. Yalwataccen murmushi ya saki yana jin wani irin feeling a ransa a game da ita gami da wani irin nishad'i, damuwar da Mom ta saka masa ɗazu duk ya neme ta ya rasa. Can ƙasan mak'oshi ya ce. "Humairah...!" Ta ɗago kanta da niyyar amsa masa suka ji an musu wata irin hankad'a ta bayansu, lokaci ɗaya suka tafi za su faɗa cikin ruwan gaba-d'ayansu............✍️ ```Barkanmu da shan ruwa, dafatan an sha ruwa lafiya? Allah ya karɓa mana.``` *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣3️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Cikin gigita A'isha ta ƙwalla ƙara tare da sakin kuka, hankali a tashe Umar ya riƙo ta kafin su kai cikin ruwan ya rungume ta da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya dafa wani dutse dake bakin ruwan, amma duk da haka sai da ƙafafuwansu suka shige cikin ruwan ya kawo har gwiwoyinsu. Mutanen gurin gaba-d'aya suka yo kansu suna salati tare da kallon Ɗan'juma wanda shine ya hand'aka sun. Cikin sauri aka zaro su daga cikin ruwan, innalillahiwa'inna'ilaihirra'un kawai Umar yake maimaitawa cikin kid'ima, dan shi ba ma ta kansa yake yi ba ta A'isha yake ita da ba ta gani. Ita kuwa ta ƙi sakin shi sai kuka take, dan ta tsorata ba kaɗan ba. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Umar ya saki ya yiwa mutanen da suka ciro su godiya. Sannan ya juya ya kalli Ɗan'juma dake tsaye yana ta muzurai shi kaɗai, ji ya yi kamar ya damk'o shi ya naɗa masa na jaki, amma darajar Mahaifinsa yasa ba zai iya aikata hakan ba. Ɗauke idonsa ya yi daga kansa ya zare A'isha daga jikinsa a hankali sannan ya tsugunna dai_dai tsayinta ya shiga share mata hawayen fuskarta, so cool ya ce. "Sorry Dear, ki bar kukan nan haka Please, ko kina jin wani ciwon a jikinki ne?" Hannunsa ta riƙe gam cikin kuka ta ce. "Mu tafi gida ni dai ka kai ni gurin Inna." Gabad'ayanta a tsorace take, sai ajiyar zuciya take saki akai_akai. Cikin lallashi ya ce. "Yanzu za mu tafi, amma Please ki bar kukan kin ji?" Gyaɗa mata kai kawai ta yi amma ba ta bar kukan ba. Miƙewa ya yi ya kama hannunta suka tafi bayan ya ɗauko mata takalmanta ta saka. Kafin su shiga gida sai ya rararrashe ta, ta bar kukan da take yi gudun kar hankalin Inna ya tashi. Suna shiga tana jin muryar ta tafi ta faɗa jikinta ta fara hawaye. Inna dake kallon su cikin mamaki ganin duk rabin jikinsu a jik'e ta ce. "Lafiya kuwa?" Cikin son kwantar mata da hankali Umar ya ce. "Lafiya lau Mama, a bakin ruwa muka zauna muka zira ƙafafuwanmu a ciki." Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Na san ita ta takura maka kuka shiga, dan na san ta da maitar hakan, to kuma me aka yi mata take wannan kukan?" Shafa kai Umar ya yi ya ce. "Wai dan mun taho gida yanzu ne." Tsaki Inna ta yi ta ture ta daga jikinta ta shige ɗaki tana faɗin. "Ki rufe mun baki ko jikinki ya faɗa miki, idan ba ku taho ba kwana kike son ku yi a can?" Kama hannunta ya yi ya zaunar da ita akan kujera ya shiga share mata hawaye, a hankali ya ce. "Dan Allah ki bar kukan nan Humairah ko kina so nima in yi?" Girgiza kai ta yi. Ya ce. "To ki daina, ba ki san yanda nake ji ba ne a cikin raina idan na ga kina kuka." Barin kukan ta yi cikin sanyin murya ta ce. "Na tsorata sosai Yaya Umar, na ɗauka za mu faɗa cikin ruwan ne, kuma na san da mun faɗa mutuwa za mu yi." Yana goge mata hancinta da handkerchief ɗinsa ya ce. "Ki bar zancen nan kar Mama ta ji, kuma ko na tafi kar ki faɗa mata ki ce mun kusa faɗawa ruwa." Ta ce. "Me yasa?" Ya ce. "faɗa zata yi miki mana, kuma ba za ta ƙara barin ki ki fita ko nan da soro ba, kin sani." Gyaɗa masa kai ta yi a hankali. Ya shafi kuncinta ya ce. "Good Girl, bari na tafi Magriba ta kusa." Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba. Murmurshi ya yi ya ya miƙe ya yiwa Inna sallama ya tafi. Bayan Fitar sa A'isha ta cewa Inna za ta yi wanka dan wari iri take jin jikinta, sai da ta yi Sallah ta ci abincin da Inna ta matsa mata ta ci kaɗan sannan ta yi wankan ta kwanta. Bayan Sallar isha'i Umar ya je shop ya yiwa A'isha siyayyar kayansu Biscuits da choculates da sweets masu yawa. Lokacin da ya je kai mata ta yi bacci sai Inna ya bawa ta ajiye mata. Inna tana duban ledar da aka zubo kayan cikin mamaki ta ce. "Umar wannan fa na mene ne?" Kansa a ƙasa ya ce. "Na A'isha ne Mama." Inna ta ce. "Haba Umar, wannan siyayyar ai ta yi yawa." Bai ce komai ba. Inna ta ce. "Toh an gode, Allah ya saka da Alkhairi ya biya ka da gidan aljannah, amma ba dan ba da na baka ka mayar da kayan nan inda ka siyo su ko ragewa ne a yi, wahalar ai ta yi yawa." Murmurshi ya yi ya amsa da Amin sannan ya yi mata sallama ya tafi. Ita kam Inna har cikin ranta ba ta son kashe_kashen kuɗin da Umar da yake yiwa A'isha, dan kwanaki haka ya kawo mata sabulan wanka masu ƙamshi da na wanki da toothpaste da man wanke gashi. A ganin ta d'awainiyar da yake yi da su ta yi yawa. Wajen ƙarfe goma na dare Umar yana kwance yana operating system kira ya shigo cikin wayarsa, ɗaukar wayar ya yi ya duba, Abbansa ne yake kiran, d'agawa ya yi ya kara a kunnensa tare da yin sallama. Daga ɗaya ɓangaren bayan Abban ya amsa ya ce. "Umar ya aikin? Da fatan komai lafiya babu matsalar komai?" Umar ya ce. "Alhamdulillah Abba komai lafiya." Abba ya ce. "To Masha Allahu, Allah ya taimaka.... ɗazu Mamanka take sanar mun wai ka ce a cikin satin nan zaka dawo? Har ka gama abun da ka je yi ne?" Ɗan jimm Umar ya yi sannan ya ce. "Ban gama ba Abba da ɗan saura, ita ce dai ta ce sai na dawo ɗin." Abba ya ce. "Me yake damun Amina ne? Ni ban san mene matsalarta da zamanka a garin nan ba, ta bi duk ta damu kanta kullum cikin zancen take yi, na faɗa mata ba inda za'a cutar da kai na tura ka ba, dan na san halin abokina mutumin kirki ne." Umar ya ce. "Ka yi hak'uri Abba, amma zan taho cikin satin nan ɗin Insha Allah tunda haka take so." Abba ya ce. "Ba zai yiyu ba, ka tsaya ka yi abin da ka je yi a tsanake, idan ka gama sai ka dawo, ita kuma ka barni da ita." Umar ya ce. "Tom shikenan Abba Na gode, Allah ya ƙara girma." Abba ya ce. "Yawwa, ka ci gaba da kula dai, Allah ya taimaka ya yi Albarka." Umar ya ce. "Amin Abba." Daga nan suka yi sallama Abba ya katse kiran. Wani kiran ne ya ƙara shigowa cikin wayarsa, kallon wayar ya tsaya yana yi, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya d'aga tana gaf da katsewa ya kara a kunnensa bai ce komai ba. Ɗaga ɗaya ɓangaren aka ce. "Ya Faruq me na yi maka ne duk ka canza mun?" Umar ya ce. "Chanji kuma? Wanne iri Khausar?" Cikin damuwa ta ce. "When last rabon da ka kira ni ko ka mun magana a chat? Ina ga tun kafin ka yi tafiyar nan fa." Numfashi Umar ya sauke ya ce. "Toh shikenan ki yi hak'uri abubuwa ne suka shamun kai, Ya kike ya su Mommy?" Khausar ta ce. "Kowa lafiya ƙalau, amma ban da ni da nake cikin kewar ka, yaushe zaka dawo?" Umar ya ce. "Nan da 1 month insha Allah." A sanyaye ta ce. "Allah ya kai mu, amma kamar ya yi yawa ya Faruq, har 1 month zan ƙara ban gan ka ba, bayan kwanakin da na yi a baya?" Umar ya ce. "Ba wani yawa, kamar yau ne zaki ga kwanakin sun wuce har na dawo." Khausar ta ce. "To, Allah ya kai mu, baka ji daɗi da farincikin da nake ji ba yau na ji muryarka." Umar ya ce. "Haka ake so, yanzu ina ɗan yin wani aiki ne, I will call you later." Bai jira cewarta ba ya katse wayar ya cigaba da abun da yake yi. Washegari Umar ya je gidansu A'isha kamar yadda ya saba zuwa, ya tarar Inna tana yiwa A'isha tsifar kai. Bayan sun gaisa da Inna ta tufkewa A'isha gashin da aka tsefe ta ce mata ta ɗaure kanta idan Umar ya tafi ta cigaban mata, sannan ta tashi ta shige ɗaki. A hankali A'isha ta ɗago kanta ta ce. "Ina kwana?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?" Ta ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah." ƙarasawa inda take ya yi ya kama hannunta ya ce. "Haka kike da gashi Humairah?" Rufe fuskarta ta yi da hannunta tana murmurshi ƙasa ƙasa ba ta ce komai ba. Ya ce. "A ina ake saloon a garin nan mu je a yi miki? Na san idan aka yi gashin naki zai ƙara kyau." A'isha ta ce. "Mene shi ɗin?" Ya ce. "Gyaran gashi mana." Girgiza kai ta yi ta ce. "Babu masu yi a garin nan." Ya ce. "Shikenan, watarana zan kai ki inda ake yi ayi miki." Cikin murna ta ce. "To Yayana na gode." Daga nan suka ɗora karatunsu daga inda suka tsaya. Kafin ya tafi ya yiwa Inna tambayar da ta dad'e tana yawo a cikin zuciyarsa. "Mama matsalar idon A'isha dashi aka haife ta ne?" Inna ta ce. "A'a, daga zazzaɓi kawai Ubangiji ya ɗoro mata, ko shekara biyu ba'a yi ba." Umar ya ce. "To me yasa baku je asibiti an duba idon ba?" Inna ta ce. "Na kai ta nan asibitin Rano suka ce sai dai mu je can Kano a duba ta, su ba su da k'wararrun likitan ido, mun gwada magungunan gida su ma ba'a dace ba." Umar ya ce. "To me yasa ba ku je can ɗin ba?" Shiru Inna ta yi ta rasa me zata ce masa. Numfashi ya sauke ya ce. "Shikenan Mama, Allah ya ba ta lafiya, bari na wuce gida." Sallama ya yi musu ya tafi. Wunin yau gaba-d'aya Umar cikin tunanin yanda zai yiwa A'isha magani ta warke yake yi, tunda ba da ciwon aka haife ta ba da yiyuwar zata warke da yardar Allah. Ya san da zai faɗawa Mahaifinsa ya nemi taimakonsa zai taimaka mata, ko da ƙasar waje ta kama akai A'isha akan ta samu lafiya zai iya kai ta, inda matsalar take baya son mahaifiyarsa ta sani, amma ya san matuƙar ya faɗawa Abbansa to sai Mom ɗinsa ta samu labari, dan Abba idan zai yi abu ba zai b'oye mata ba wai dan gudun ɓacin ranta ba. Idan kuma ya ce shi zai yiwa A'isha magani da kuɗinsa bai zama lallai kuɗaɗen dake cikin account ɗinsa su isa ba, sai dai idan Motarsa zai sayar, idan kuma ya siyar da Motar ina zai cewa Abbansa da Mom ɗinsa ya kai Motar? Haka dai ya kwana yana sak'e_sak'e shi kaɗai da neman mafita, dan babban burinsa a yanzu A'isha ta samu lafiya idanunta su buɗe. Rayuwa ta cigaba da tafiyarwa su Inna cikin farinciki da kwanciyar hankalin da ba su taɓa riskar kansu a cikin kamar sa ba, sanadiyyar zuwan Umar cikin rayuwarsu. Umar ya zame musu wani bango da yake ba su kariya ta ko'ina a cikin rayuwarsu, dan hatta k'warzabar da mutanen gari da ƴan gidan suke yi musu sun samu sauƙin ta, domin Umar duk ya taka musu birki akan hakan. A gefe guda kuma shak'uwa mai ƙarfi tana ƙara shiga tsakanin Umar da A'isha, kodayaushe suna tare yana koya mata karatu, idan sun gama ya yi mata waƙa ko ya kunna mata kallo a wayarsa tana saurara, wani lokacin kuma ta ce ya kira mata Ma'u su yi hira da Numbern Innar Ma'u da ƙaninta ya tura musu. Da hutunsu na makaranta ya ƙare aka koma shi yake kai ta ya ɗauko ta. Wani irin wasai A'isha take jin zuciyarta a yanzu babu damuwar komai, ta samu abokin hira mai ɗebe mata kewa da nuna mata k'auna. Idan dare ya yi suka rabu da Umar Allah_Allah take gari ya waye su haɗu su ɗora daga inda suka tsaya. Umar ya ɗaukewa Inna komai tun daga kan abinci har komai na buk'atun rayuwa, duk da ita har cikin zuciyarta ba ta so hakan ba, ko dan yawon da ake yi da su a cikin gari ana sun mallake bak'o daga zuwansa garin suna ta tatse shi yana d'awainiya da su. Har nuna masa ɓacin ranta take yi akan siyayyar kayan da yake yiwa A'isha amma bai fasa ba. Bayan watanni ukun da ya ce zai yi a garin sun ƙare sai ya cewa Abbansa shukar da suka yi ba ta yi kyau ba sai sun sake wata, dan haka sai ya ƙara a ƙalla wasu watannin biyu kafin ya koma gida. Cikin rashin damuwa Abban nasa ya amince masa, Mom ɗinsa ce dai ta dinga yi masa masifa kamar zata ari baki, shi kam ya yi hakan ne saboda bai san tafiya ya bar A'isha. Yau Litinin, da yamma ɗaya daga cikin ƴaƴan Sarki mai suna Haulatu ta dawo daga makaranta ta zauna a ɗaki ba tare da ta nemi abinci ba ta rafka tagumi da hannu bibbiyu, kallo ɗaya mahaifiyarta ta yi mata ta gane tana tattare da damuwa. Cikin kulawa ta dube ta, ta ce. "Ke lafiya kuwa kike?" Kamar Haulatu zata yi kuka ta ce. "Uwa wallahi wani abu ne yake damuna." Da mamaki Uwa ta ce mata. "Mene shi?" Ƙasa ta yi da kanta ta ce. "Uwa Umar ne idan na gaishe shi cikin rashin kulawa yake amsa mun, ba ya sakar mun fuska, ko na je gurinsa da niyyar mu yi hira sai ya haɗe mun rai, kuma ni gaskiya son shi nake yi." Uwa ta ce. "Wanne Umar kenan?" Haulatu ta ce. "Wanda yake zaune a cikin gidan nan ɗan abokin Sarki." Kama hab'a Uwa ta yi ta ce. "Kin san wa kike faɗa kuwa Haulatu? Lallai ba ki da hankali, to bari ki ji in faɗa miki, tun wuri ma ki cire shi daga cikin ranki dan ba'a ajinki ba ne shi, ato." Cikin damuwa Haulatu ta ce. "Saboda me?" Uwa ta ce. "Mahaifiyarsa! Matar nan ba ta kirki ko na sisin kwabo, mun taɓa zuwa gidanta sau ɗaya lokacin da mahaifin shi Mijin nata ya rasu, kakansu Umar ɗin kenan, Sarki ya kwashe mu muka je muka yi masa gaisuwa, yanda Matar nan ta wulaqanta mu abun ba zai faɗu ba, da muka gaishe ta daƙyar ta amsa kamar an yi mata dole, ƙarshe ma tashi ta yi ta bar mu yashe a falo sai masu aiki ne suka yi hidima da mu. Sai dai Mahaifinsa shi mutumin kirki ne, mutumin nan shi idan mutunci yana yin yawa to nasa ya yi, dan shi ba ki ga yanda ya mutunta mu ba wallahi." Haulatu ta ce. "Toh tunda Babansa yana da kirki ba shikenan ba, ni dai gaskiya Uwa ki yiwa Sarki zancen, dan shi kaɗai nake son na aura." Uwa ta ce. "Abun fa da ba zai taɓa yiyu ba ne Haulatu, idan zaki hak'ura ki hak'ura." Kuka Haulatu ta saka ta ce. "Wallahi Uwa zai yiyu, idan ya san ba za'a bar shi ya auri ƴar ƙauye ba me yasa yake kula waccan makauniyar Yarinyar, son ta fa yake yi kuma kowa a cikin garin nan ya sani." Shiru Uwa ta yi na wasu sakanni tana kallon ƴartata, tabbas abun da ta faɗa gaskiya ne, da Umar ya san ba za'a bar shi ya auri ƴar ƙauye ba da ba zai fara soyayya da A'isha ba, idan kuwa har haka ne Ƴarta ce tafi dacewa da auren ɗan gidan mai kuɗi ɗan birni ba ƴar talakawa mara asali ba. Idan Haulatu ta auri Umar za su zamo abun alfahari a garin nan, ko a cikin kishiyoyinta za ta yi musu zarra ƴarta ta auri Mijin da kaf ƴaƴansu babu wadda ta auri ko wanda ya kama ƙafarsa ne a komai da komai, dan yanda take jin Sarki yana faɗar kuɗin mahaifin Umar ba ƙaramin mai kuɗi ba ne. Wani murmushi ta saki tare da miƙewa cikin sauri ta ɗauko kuɗi a cikin jakarta Naira ɗari biyu ta bawa Haulatu ta ce. "Share hawayenki ki kwantar da hankalin ƴata, na samo mana mafita wadda nake da tabbacin zata raba Umar da waccan yarinyar cikin sauƙi, idan hakan ta kasance ke kuma na san yadda zan yi mu janyo hankalinsa gare ki." Haulatu ta ce. "Ta yaya? Me zaki yi?" Uwa ta yi murmurshi ta ce. "Ke dai je ki siyo mun katin MTN da wannan kuɗin, idan kika dawo a gabanki komai zai faru, za ki ga abun da zan yi." Ajiyar zuciya Haulatu ta sauke ta miƙe tana share hawayen fuskartata ta fice daga ɗakin...........✍️ _*Ban yi edit ba, a yi hak'uri da typing errors.*_ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣4️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Bayan fitar Haulatu Uwa ta ɗauki wayarta ta yafa mayafinta ta fita zuwa turakar Mijinta. Sarki yana kishingide a k'aton falonsa da yake hutawa a cikin gida Uwa ta yi sallama, ya amsa tare da ba ta izinin shigowa. Bayan ta zauna a gabansa ta ce. "Ranka ya daɗe barka da yamma." Sarki ya ce. "Yawwa." Uwa ta gyara zama fuskarta ɗauke da murmurshi ta ce. "Dama zuwa na yi in yi maka tsokaci akan wani abu da yake gudana a cikin gidan nan." Sarki ya ce. "Me kenan Uwa?" Ya ƙarashe zancen tare da tashi zaune sosai. Uwa ta ce. "Wato ranka ya daɗe yaron nan Umar yaron kirki ne irin Albarka, mutuncin da yake yi mana a gidan nan da girmama mu ba zai faɗu ba, ga Alkhairi akai_akai." Sarki ya yi murmushi ya ce. "Allah Sarki Ummarul Faruq, ai indai ya yo halin mahaifinsa to kaɗan ma kika gani, dan ni ban ma san ya zan misalta miki karamci da kirki irin na Alh. Aliyu ba." Uwa ta washe baki ta ce. "Masha Allahu, haka ake son mutane su dinga kasancewa masu kyawawan d'abi'u wanda za'a dinga yabon su da shi, ni yanzu daka ganni wani babban Alkhairi ya yi mun da na ji daɗinsa sosai, har na kasa jurewa na ce gaskiya sai na karb'i Lambar Mahaifiyarsa na kira ta na gaishe ta darajar abun da ɗanta ya yi mun." Jinjina kai Sarki ya yi ba tare da tunanin komai ba ya ce. "Hakan yana da kyau, dama kamata ya yi a ce tun da kuna gaisawa da juna." Uwa ta ce. "Haka ne Ranka ya daɗe, yanzu ma ai ba ta ɓaci ba sai mu fara ɗin." Sarki ya ce. "Sai dai kuma ba ni da lambar mahaifiyar tasa, amma abun da za'a yi bari na kira Alh. Aliyun na yi masa bayani sai ya tura mun." Uwa da jikinta har ɗan rawa yake saboda zumud'i ta ce. "To..to Ranka ya daɗe." Sarki ya ɗauko wayarsa ya kira Alh. Aliyu, ringing kaɗan ya daga, suka gaisa tare da tsokanar juna cikin barkwanci sannan Sarki ya yi masa bayanin dalilin kiran sa da ya yi. Cikin jin daɗin abun da Sarki ya faɗa masa ya ce zai tura masa lambar suna gama wayar. Mintuna biyu da gama wayar tasu ya tura masa lambobin har guda biyu, Sarki ya kwafarwa Uwa a cikin wayarta ya ba ta. Cikin tsananin farincikin ta dinga yi masa godiya, har abun ya so ya bawa Sarki mamaki, amma sai ya danganta hakan da may be duk cikin jin daɗin Alkhairin da ta ce Umar ya yi mata ne. Cikin sauri ta ƙarasa ɗakinta ta tarar Haulatu ta dawo, Haulatu ta ce. "Uwa ina kika je? tun ɗazu na dawo nake jiran ki." Uwa ta cire mayafinta ta cillar ta ce. "Ina katin da kika siyo? bani_bani in saka da sauri, yau da sa'a na tashi, abun da na shirya a cikin ƴan mintuna har na samu nasara an wuce gurin." Haulatu ta karb'i wayar Uwa ta fara saka mata katin ta ce. "Me kika shirya?" Uwa ta ce. "Lambar mahaifiyar Umar na je samuwa a gurin Sarki, kuma wallahi cikin ruwan sanyi na samu, ban yi tunanin hakan ba ma." Haulatu ta ce. "Me zaki yi da Numbern ta ke kuwa? bayan kin ce ba ta da kirki." Uwa ta zauna ta ce. "Ke dai kira mun Lambar farko a gurin kira, ita ce tatan, zaki ga abun da zan yi da ita." Babu musu Haulatu ta yi dialling numbern, cikin sa'a bugu ɗaya ta shiga ta fara ringing, saka wayar ta yi a hands-free ta miƙawa Uwa, sai da ta kusan katsewa sannan aka ɗauka. Cikin kwantar da murya Uwa ta ce. "Assalamu alaikum, Ranki ya daɗe barka da yamma, dafatan an wuni Lafiya?" Cikin izza irinta Mom ta ce. "Yawwa, wake magana?" Uwa ta yi murmushi mai sauti ta ce. "Uwa ce matar Sarkin Kumurya abokin mijinki." Ɗan jim Mom ta yi tana tunani, lokaci ɗaya ta haɗe rai cikin ƙyama ta ce. "To ya aka yi?" Uwa ta ce. "Uhm dama akan yaronki ne Uwar na kira in faɗa miki wani muhimmin abu." Tsaki Mom ta yi wani irin takaici na cika mata zuciya, Umar ya ja mata yau tana waya da matar ƙauye. Cikin ƙagauta ta ce. "Ina jin ki." Uwa ta gyara zama ta ce. "Hajiya ba gulma ba ko wani abun, amincin dake tsakanin mijina da naki ne ya saka zan faɗa miki wannan abu....." Cikin hasala Mom ta ce. "Malama ki faɗi abun da zaki faɗa da'Allah cikin sauri, dan ina da abun yi." Ta ƙara jan tsaki cikin takaicin kanta da ta tsaya ma tana sauraren wannan yar ƙauyen, har za ta katse wayar ta tsinkayi muryar Uwa tana cewa. "Hajiya wata mata ce a cikin garin nan irin zuwau ɗin nan ba ƴar asalin garin ba ta lashe kurwar Umar tun zuwansa garin nan, da yake mayya ce ita, in tak'aice miki zance kullum yana gidanta gurin makauniyar ƴarta yana faman yin wahala da su, shine cinsu, shansu, suturarsu da komai nasu. Ta yi masa siddabaru irin nasu na mayu ta mallake shi ta cusa masa son ƴarta, kuma yarinyar ma fa makauniya ce, ba......" Cikin tsananin kad'uwa Mom ta ce. "What? Wanne Umar ɗin? Ba dai Faruq ɗina ba ko?" Uwa ta ce. "Shi mana, ko ba da matar Alh. Aliyu Kaduna nake magana ba?" Mom ta ma rasa me za ta ce saboda tsabar firgici, Son ɗinta ne Mayya ta kama shi ya tare a gindinta? Wato shi yasa ya ƙi barin garin? Tsabar ya raina mata hankali shine ya ce mata shukar da suka yi ce ta lalace sai da aka sake wata? ashe wata sabuwar shukar da zai tozarta ta ya bak'anta mata rai ya dasa? To kuwa wallahi zai san ita ce ta haife shi ba shi ya haife ta ba. Katse Wayarta ta yi ba tare da cigaba da sauraren soki burutsun zancen da Uwa ta cigaba da yi mata ba. Jiki a sanyaye Haulatu ta dubi Uwa ta ce. "Na shiga uku, haka dama matar nan take? Ji yanda take magana fa kamar irin da bayin nan nata take yi." Uwa ta ce. "Ai tafi ma haka, amma ni ko ajikina, yanzu plan ɗinmu na farko zai yi aiki sai mu tafi na biyu, dan na san a yau sai ta raba Umar da waccan makauniyar Yarinyar, ai ina sane na kunna ta, na san hankalinta ba ƙaramin tashi zai yi ba." Haulatu ta ce. "To amma idan mun ci nasara kina ganin wannan uwar tasa zata bari a yi auranmu da Umar kuwa?" Uwa ta ce. "Ki saka a ranki tamkar an yi gama, auranki da Umar ba, ni kaɗai na san ta inda zan ɓullowa al'amarin." Murmurshi Haulatu ta saki cikin jin daɗi, a ranta na hango ranar da za'a ce an aura mata aure da Uwar, wayyo daɗi, ta auri ɗan birni ɗan gayu kyakkyawa ɗan masu kuɗi, ranar ta san sai farinciki ya kusa hallaka ta. Umar ne zaune akan kujera ƴar tsugunno yana kallon A'isha dake zaune akan tabarma, sanye take cikin atamfa mai kyau ɗinkin doguwar riga, ɗinkin ya yi dass a jikinta kasancewar yanzu ta ƙara murjewa sanadiyyar cima mai kyau da kuma kwanciyar hankali da suka samu. Atamfar da Innar Ma'u ta ɗinka musu ce Sallar da ta wuce, Inna ta yi mata d'auri duk da ba wani na gayu ba ne amma ya yi mata kyau, fuskarta ta sha powder da Umar ya siya mata, ɗan ƙaramin lips ɗinta sai k'yalli yake na white lipstick. Kallon ta yake yi cikin wani irin yanayi ko ƙifta idonsa ba ya yi, zuciyarsa na bugawa a hankali a hankali, wani irin son A'isha da tausayinta na ƙara mamaye ko'ina a cikin zuciya da gangar jikinsa, har mamakin kansa yake yi yanda a cikin 5 months ya faɗa cikin irin wannan zazzafar soyayyar akan ƴar ƙanƙanuwar yarinyar da ko autarsu ta girme ta, ko a mafarki bai taɓa tunanin hakan zai kasance da shi ba. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, cikin kulawa ganin yanayin A'isha ya ce. "Me ya faru kika yi shiru Humairah? And yanayinki ya nuna mun kamar akwai abun da yake damunki, tell me what happened?" Idanun A'isha akan fuskarsa kamar mai ganin sa cikin sanyin murya ta ce. "Ban san me yake damuna ba nima, kawai ina jin jikina babu daɗi ne." Umar ya ce. "Ko ba ki da lafiya ne?" Girgiza masa kai ta yi ta ce. "Lafiyata ƙalau, kawai gabana ne yake ta fad'uwa." Umar ya ce. "Subhanallahi, ki dinga maimaita innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, ko kina ambatar sunan Allah, za ki ji sauƙin abun." Ta ce. "Toh, Insha Allahu." Numfashi Umar ya sauke dan shi ma haka kawai ya ji jikinsa da zuciyarsa wani iri, bai kuma san dalili ba. Kamar A'isha za ta yi kuka ta ce. "Ni fa Yaya Umar a rayuwata so nake kawai in gan ka, in ga ya kake, amma na san daƙyar idan hakan za ta faru." Hannunta Umar ya kama ya ce. "Watarana za ki ganni Insha Allahu Humairah, a cikin watan nan nake so mu tafi Kano a duba miki idonki a yi miki magani, ki daina damuwa Insha Allahu zaki warke ki cigaba da gani kamar kowa." A'isha ta ce. "Allah ya yarda." Murmurshi Umar ya yi ya ɗauko key ɗinsa ya gogawa A'isha a gefen wuyanta, ɗan zabura ta yi ta sosa wurin tana ɓata fuska, kan ƙafarta Umar ya kai key ɗin ya ƙara goga mata, da sauri ta janye ƙafar a tunaninta wani k'waron ne yake bin jikinta. Murmurshi Umar ya yi mai sauti ganin yadda ta zama uncomfortable a gurin sai juye_juyen kai take yi. Turo baki ta yi ta ce. "Kai kake saka mun wani abun a jikina ko?" Umar ya ce. "Ba ni ba ne, Ni wayata ma nake kallo." Ta ce. "Na san kai ne, ai ba yau ka saba mun haka ba." Uwar ya ce. "Ba fa ni ba ne." Shiru ta yi alamar ta yi fushi. A hankali ya ce. "Sorry Dear na daina." A'isha ta ce. "Ai na san baka daina ba, kullum sai ka tsokane ni ka tsorata ni, ranar nan har kuka ka saka ni dan ka ga bana gani." Cikin shigar rarrashi ya ce. "Na ce fa ki yi hak'uri na daina daga yau." A shagwab'e ta ce. "Ba zan hak'ura ba ni dai, kuma ba ruwana da kai." Umar ya marairaice ya ce. "Please... Ni ne fa, dan Allah ki yi hak'uri." A'isha ta ce. "Tom shikenan na hak'ura." Ya ce. "Yawwa Darling, kawo hannunki ki ga wani abu. Ba ta ce komai ba ta miƙa masa hannun damanta. A hankali ya zare wani ring ɗin azurfa mai kyau dake ƙaramin finger ɗinsa ya zira mata a babban ɗan'yatsanta yana kallon cikin idonta. Zare hannunta ta yi daga cikin nasa a hankali ta shiga murza zoben da ya saka mata da murmurshi ɗauke akan fuskarta. Umar ya ce. "Wow ba ki ga yanda ya yi miki kyau ba." Ta ce. "Ka bar mun ne?" Ya ce. "Eh mana, dan ma sauran sun miki yawa ne da duka na hannuna zan baki." Ta ce. "Saboda me? Kai baka so ne?" Ya ce. "Zuciyata ce kawai ta bani umarnin in bar miki su." A'isha ta ce. "Na gode, amma na ji ya ɗan mun yawa fa, ba zai faɗi ba." Umar ya ce. "Ba zai faɗi ba, ai ba sosai ya yi miki yawan......" Vibrate ɗin da wayarsa ta fara ne ya katse masa maganarsa. Zaro wayar ya yi daga aljihun gaban rigar sa ya duba, Mom ce take kiran sa, haka kawai ya ji gabansa ya yanke ya faɗi. Jiki a sanyaye ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa tare yin sallama. Cikin kaushin murya ba tare da ta amsa masa sallamar ba ta ce. "Sannu Faruq." Cikin ladabi ya ce. "Me ya faru Mom?" Dan jin yanda ta yi magana ya san ba ba ƙalau ba. Cikin tsantsar ɓacin rai ta ce. "Ban sani ba, na kuma gode da abun da ka yi, ka kyauta mun ka kyautawa kanka, amma ba lefinka ba ne, laifin mai ɗaure maka k'ugu kake abun da ka ga dama ne. To bari ka ji, wannan karon komai zai faru sai dai ya faru, ka shirya gobe da safe za'a zo a ɗauke ka, ka gama zaman nan ƙauyen nan, kai da garin kuma har abada ." Cikin damuwa Umar ya ce. "Mom Please listen to me, na faɗa miki fa shukar da muka yi ce aka samu matsala amma...." A fusace ta ce. "Shukar Ubanka? ka tsaya dai kana shuka abun da ka san baza ka taɓa girba ba, ka je ka tare a jikin matar da ba'a san asalinsu ba kana kashe musu uban kuɗi ko? to tatsar ta isa haka, ta samu iya rabonta, kai kuma zaka zo ka same ni ne har inda nake, wallahi sai na nuna maka ɓacin raina irin wanda ba ka taɓa gani ba." Dafe kai Umar ya yi ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Mom wa ya faɗa miki wannan maganar?" Mom ta ce. "Ban sani ba, ashe shi yasa sai inji mahaifinka yana ta cewa ya tura maka kuɗi, in rasa uban me kake yi da kuɗin ashe ga inda suke tafiya, Khausar ma kullum cikin yi mun complain ɗin irin wulaqancin da kake yi mata take, ashe shi ma da dalili." Sosai hankalin Umar ya tashi da jin Mom ta samu labarin yana tarayya da su A'isha, domin bai san hukuncin da za ta ɗauka akan hakan ba. K'wafa Mom ta yi ta ce. "Wallahi, wallahi, wallahi Faruq na yi rantsuwa sau uku idan ba ka baro garin nan a gobe ba sai dai ka nemi wata Uwar ba ni ba, kuma ko da wasa bayan ka dawo ka cigaba da mu'amala da faƙiran mutanen nan ban yafe maka ba." Tana gama faɗin haka ta katse wayar. Sunan Allah kawai Umar yake maimaitawa a fili cikin tsantsar damuwa. A rud'e A'isha ta ce masa. "Yaya Umar me ya faru? Wa ya kira ka a waya? Me aka ce maka?" Duban ta Umar ya yi da idanunsa da suka fara sauya kala saboda jin kalaman Mahaifiyarsa masu tsauri a gare sa, cikin sanyin murya mai cike da damuwa ya ce. "Babu komai Humairah, zan je gida in dawo, tashi mu je in raka ki ɗaki, idan Mama ta tashi ki ce mata na wuce." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ko mutuwa aka yi muku?" Girgiza kai kawai ya yi dan ko magana ba ya son yi, kama hannunta ya yi ya kai ta ƙofar ɗakin, sai ta kasa shiga ta tsaya kawai cikin yanayin damuwa. Shi ma kasa tafiyar ya yi ya tsaya yana kallon ta, yana jin kamar ba zai iya rayuwa ba idan babu ita. A hankali ya juya ya fice daga cikin gidan, dan kallon ta ma ba ƙaramin ƙara karyar masa da zuciya yake ba. Jin ya fice A'isha ta ja ƙafarta daƙyar wadda ta ji ta yi mata nauyi ba tare da san dalili ba ta shige ɗakin, wasu hawaye masu ɗumi suka kwaranyo daga cikin idonta ba tare da ta shirya musu ba. Daƙyar Umar ya iya kai kansa gidan Sarki saboda sarawar da kansa yake masa, yana zuwa ya buɗe ɗakin da yake ya faɗa kan katifa ya kwanta ruf da ciki. Wani irin zafi zuciyarsa take masa, bai shirya barin A'isha yanzu ba, be shirya yin nesa da ita ba, be shirya tafiya ya bar su a cikin wannan garin da ba'a k'aunar su ba, be shirya tafiya ya bar ta a cikin makanta ba, ya gama tsarawa a cikin watan nan zai ɗauke ta ya kai ta gidan k'anwar mahaifinsa ita da Inna su zauna kafin a gama zirga-zirgar zuwa asibiti ganin likita, dan ya san ita kaɗai ce zata yi masa wannan taimakon cikin ruwan sanyi. Amma Mom ta wargatsa komai, domin ba shi da zaɓi face ya bi umarninta ya koma gida a gobe. Wunin yau gaba-d'aya cikin damuwa ya yi shi, gaba-d'aya jinsa yake wani iri kamar mai cuta, Sallah ce kawai take fitar da shi waje. A ɓangaren A'isha ma haka ne, dan ita kuka ta sakawa Inna na babu gaira babu dalili, rarrashin duniya Inna ta yi mata amma ta ƙi yin shiru, ta kuma ƙi cin abinci, gashi ta ƙi faɗa mata abun da yake damun ta. Abun da ya ƙara tayarwa da A'isha hankali ganin yamma ta yi lokacin zuwan Umar ya yi amma bai zo ba, Inna ma ta yi mamakin hakan, amma sai ta ɗauka wani uzurin ne ya tare shi. Daren yau Umar bai rintsa ba, kwana ya yi yana tunanin mafita, bai taɓa tunanin ƙaddara makamanciyar wannan za ta riske shi ba a cikin rayuwarsa, abun da yake ƙara tayar masa hankali furucin Mom na ƙarshe, da ta ce ko bayan ya koma gida ya cigaba da mu'amala da su A'isha ba ta yafe masa ba. Tambayar kansa ya dinga yi wa ya faɗawa Mom wannan zancen? Shi dai ya san ba ta mu'amala da kowa a garin nan, kuma mahaifinsa ma haka balle ya ce ko shi ya samu labarin ya faɗa mata, ya san Sarki kuma ba zai taɓa faɗa masa ba. Koma waye bai yi masa adalci ba, domin kuwa ya saka ana ƙoƙarin yi masa katangar ƙarfe da farinciki a cikin rayuwarsa, dan matuƙar ya rabu da A'isha to tabbas ya san tausayin ta da k'aunar ta dake cike fal a cikin zuciyarsa ba zai bar shi ya cigaba da jin daɗi da walwala kamar kowa ba a cikin rayuwarsa, matuƙar ba cigaba da kasancewa da ita ya yi ba har ƙarshen rayuwarsa..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣5️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Washegari daƙyar Umar ya iya fita Masallaci da asuba, saboda wani irin sanyi da yake ji yana ratsa ƙasusuwan jikinsa, ga wata irin kasala da ta lullub'e shi. Bayan ya dawo ya shiga haɗa kayansa cikin ƙarfin hali, ganin abun yake tamkar a mafarki wai yau zai tafi ya bar A'isha. Bayan ya gama haɗa komai nasa ya yi wanka ya shirya cikin manyan kaya. Ƙarfe Bakwai da mintuna Mom ta kira sa, jiki a sanyaye ya ɗaga kiran. Ba tare da ta bi ta kan gaishe tan da yake yi ba ta ce. "Ina fatan ka gama shiryawa? Dan tun asuba driver ya taho ɗaukar ka." Cikin sanyin murya mai cike da damuwa ya ce. "Na gama." Mom ta ce. "Better, ka san kuma me zaka faɗawa Mahaifinka idan ya ga ka dawo dan ban sanar masa zaka dawo yau ba." Umar ya ce. "Zan kira shi yanzu in faɗa masa, ba zai ji daɗi ba idan ya ga kawai na dawo kuma ban sanar masa ba." Mom ta ce. "Kai ka sani kuma, saura ka yi kuskuren ambatar sunana a cikin zancen dawowar taka." Umar ya ce. "Na san me zan ce masa." Taɓe baki Mom ta yi ta kashe wayarta. Numfashi Umar ya ja ya fesar, Numbern Abbansa ya kira ya sanar masa zai dawo gida yau. Cikin mamaki Abba ya ce. "Yau yau ɗin nan kuma Faruƙ?" Umar ya ce. "Eh." Abba ya ce. "Wanne irin abu ne haka kamar yaƙi? Tafiya lokaci ɗaya, kuma sai a yau ɗin zaka sanar mun?" Umar ya ce. "Tun jiya nake ta ƙoƙarin kiran ka ya ƙi lafiya babu network, sai text na yiwa Mom na faɗa mata, ina jin mantawa ta yi ba ta sanar maka ba." Abba ya ce. "To ai shikenan, Allah ya kawo ka lafiya, bari na sanarwa Ado driver ya zo ya ɗauko ka." Umar ya ce. "Ai Mom ta faɗa masa ma har ya taho." Abba ya ce. "Alright, Allah ya kawo ku lafiya, amma Are You ok Faruƙ?" Umar ya ce. "Lafiya ƙalau Abba, me ka ji?" Abba ya ce. "Muryarka na ji kamar ta wanda ba shi da lafiya, ko wani abun ne ya faru?" Umar ya ce. "Babu komai Abba, yanzu na tashi daga bacci ne." Abba ya ce. "Okay, to Sai kun ƙaraso, Allah ya tsare hanya, kar ka manta da addu'a." Umar ya ce. "Insha Allah Abba, na gode." Daga haka suka yi sallama ya katse wayar. Miƙewa ya yi yana jin yanda kansa da ƙirjinsa suka yi masa nauyi saboda damuwa ya fice daga ɗakin ya nufi cikin gidan Sarki. Da mamaki Sarki yake duban Umar bayan ya faɗa masa yau zai tafi, yana jinjina kai ya ce. "Ikon Allah, kuma Umar sai yau ɗin da zaka tafin zaka sanar mun?" Ɗan murmushi ya yi bai ce komai ba. "Sarki ya ce lafiya dai ko wannan tafiya haka kamar wahayi?" Umar ya ce. "Lafiya ƙalau, dama ka san already na gama abun da ya kawo ni garin nan, zama na yi kawai saboda ban gaji da garin ba." Cikin murmushi Sarki ya ce. "Yanzu kuma ka gaji kenan?" Umar ya ce. "A'a, na kusa komawa karatu ne, to ina son zan ɗan yi wasu shirye_shirye kafin na tafi." Sarki ya ce. "To ai shikenan, Allah ya taimaka, amma za mu yi kewar ka sosai." Murmusawa kawai ya yi bai ce komai ba. Sarki ya ce. "Bari na saka a haɗa maka tsaraba, duk da ma dai a ƙurarren lokacin ka faɗi tafiyar, da ko tun jiya ne ka sanar mun ai da an san abun yi." Umar ya ce. "An goge Allah ya saka da Alkhairi, bari na shiga ciki na yi musu sallama." Sarki ya ce. "To sai ka fito." Yana fita suka ci karo da Ɗan_juma ya fito daga cikin gida, wani irin kallon banza Ɗan'juma ya dinga bin sa da shi, shi kuwa tun kallon farko da ya yi masa bai ƙara kallon inda yake ba ya shige ciki. Sashen Uwa ya fara shiga, tana zaune a falo tana zuba abin kayarwa zata ci Umar ya yi sallama. Cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa tare amsa masa sallamar. Barin abun da take yi ta yi cikin faɗaɗa fara'a ta ce. "Áaa Umaru kai ne a gidan namu? Bismillah zauna akan kujera mana, ka tsaya a bakin ƙofa kamar wani baƙo. Bai ce komai ba ya zauna a ƙasa saman tabarma ya gaishe ta. Ta amsa kamar bakinta zai tsage biyu saboda fara'a ta murnar zuwan Uwar. Haulatu tana ɗaki tana shirin makaranta kamar a mafarki ta ji Uwa na ambatar sunan Umar, cikin sauri ta ƙarasa shirinta ta fito. Zuwa lokacin Uwa ta gama cika shi da surutunta da ba fahimta yake ba. Ido a waje Haulatu ta ce. "Ina kwana Umar." D'agowa ya yi ya kalle ta sau ɗaya tare da amsa mata ba yabo ba fallasa. Uwa ta dube ta, ta ce. "Had'o masa abun kari mana, kya tsaya kina kallon sa kuma." Haulatu ta yi murmurshi sannan ta ce. "Toh." Uwa ta tashi tana gyara ɗaurin zanin jikinta, gaba-d'aya ta rud'e sai wani irin murmushi take yi, shi dai kallo kawai yake bin ta da shi. Furewater ta kawo masa guda biyu ta ajiye a gabansa tare da faɗin. "Ka sha ruwa ɗana kafin ta kawo abincin." A hankali ya ce. "Alhamdulillah na gode." Uwa ta ɓata fuska ta ce. "Haba Umar kamar ba gida ba? Nan fa gidanku ne wata alkunya kuma zaka yi? kai da mai iya kawo wani ne ma ka ɗibi abu ka ba shi a gidan nan." Cikin mamakin yanda ya ga tana rawar jiki a kansa ya ce. "Na ƙoshi ne Mama shi yasa." Dai-dai nan Haulatu ta fito da kayan karin da aka ce ta haɗowa Umar a hannunta. Cigaba da magana Umar ya yi ya ce. "Dama yau zan koma gida ne shine na shigo in muku sallama." Haulatu dake tsaye ba ta san lokacin da ta saki kayan hannunta suka zube a ƙasa ba, saurin miƙewa Umar ya yi tare da ja baya yana yatsina fuska. Cikin ɗaga murya Uwa ta ce. "Tafiya kuma Umar? Kana nufin gida zaka koma?" Ya ce. "Eh Insha Allahu." Bai jira cewar su ba ya tsallake kunun gyaɗar da ya mamale a ƙasa da k'osai ya fice daga ɗakin. Haulatu da ta yi mutuwar tsaye cikin damuwa ta ce. "Na shiga uku, Uwa kina ji fa wai tafiya zai yi, to a ina zan ƙara ganin sa balle har a yi maganar Aurenmu?" Cikin karaya Uwa ta ce. "Na rasa ma bakin magana Haulatu, wannan shine ga bikin zuwa amma babu zanin d'aurawa." Zama Haulatu ta yi dab'as a ƙasa, ba ta sani ba ashe ta miƙe ƙafarta akan kunun gyaɗan dake zuba uban tiriri, da sauri ta janye ƙafarta tare da sakin ƙarar azaba, a rud'e Uwa ta yi kanta tana tambayar ta abun da ya faru. Inna ce zaune a gaban A'isha tana kallon ta cikin takaici da kufula ta ce mata. "Wallahi A'isha zan saɓar miki, dan iskanci tunda kika tashi yau kike mun kukan banza, na tambaye ki me yake damunki kin ce ba komai, yanzu kuma na kawo miki abinci tun ɗazu kin ƙi ci." Aisha ta goge idonta ta ce. "Ki yi hak'uri zan ci." Sallamar Umar ta katsewa Inna maganar da take son yi. Cikin fara'a ta amsa masa tare da yi masa maraba sannan ta bashi gurin zama. Bayan sun gaisa ta shige ɗaki ta bar su tare da A'isha. Idanunsa a kanta ya ce. "Humairah!" Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin wani abu da ya cika mata zuciya mara daɗi yana gushewa. Kanta a ƙasa ta ce. "Na'am." Matsowa ya yi kusa da ita so closely, cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce. "Me yasa kike kuka?" Kansa ta nuna masa da hannunta ba ta ce komai ba. Ya ce. "Me na yi?" Cikin sanyin murya ta ce. "Ba jiya ne ka ƙi dawowa ba." Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "I'm sorry, wani abu ne ya tsayar da ni." Gyaɗa masa kai ta yi a hankali. Cikin rarrashi ya ce. "To ki daina kukan tunda na zo yanzu, ki ci abinci kuma ko in tashi in tafi." Da sauri ta ce. "Zan ci, amma dan Allah Ya Umar karka ƙara ƙin dawowa, ka ga bani da abokin hira sai kai, ita Inna sai dai tay ta mun faɗa." Kasa magana ya yi saboda wani irin tausayinta da ya kanainaye masa zuciya, iya jiya kaɗai da bai dawo ba ta shiga cikin damuwa ina ga ya tafi gaba-d'aya? Yaya zata ji idan ya ce mata yau zai tafi baza ta ƙara ganin shi ba? Ta ina zai fara faɗa mata wannan maganar? Cikin nutsuwa ta fara cin abincin duk da ba wani daɗinsa take ji ba, dan dai ba ta son Umar ya ƙara tafiya ya bar ta ne. Kaɗan ta ci ta ce ta ƙoshi, bai matsa mata ba akan sai ta ƙara ci ba ya ƙyale ta. Inna ta fito za ta cigaba da ayyukanta Umar ya dube ta ya ce. "Mama yau da safen nan fa zan tafi gida." Shi kansa da ya yi maganar sai da ya ji wani iri, balle kuma Inna da ta sandare a guri ɗaya cikin mamaki. A'isha kuwa ji ta yi zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske. Cikin al'ajabi Inna ta ce. "Wanne gidan? Ba dai can garinku ba?" Cikin ƙoƙarin ganin ya b'oye damuwarsa ya ce. "Can Mama." Inna ta ce. "Ikon Allah, kuma shine Umar saboda Allah sai yau ɗin zaka faɗa mana?" Ya ce. "Mama tafiyar ce ta kama ni babu shiri, kiran gaggawa aka mun a gida." Inna ta ce. "Too, in ce dai lafiya?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, akan harkar karatuna ne." Inna ta ce. "Allah Sarki, in ka tafi sai yaushe kuma?" Murmurshin yaƙe ya yi wanda ya fi kuka ciwo ya ce. "Zan dawo nan kusa Insha Allahu." Inna ta jinjina kai cikin tsananin mamakin abun ta juya ta koma ɗaki. A'isha da ta kame kamar status ta sauke numfashi ta ce. "Yaya Umar ina zaka tafi? Tafiya zaka yi ka barni?" Hannunta ya kamo ya ce. "Wa ya faɗa miki zan iya barin ki Humairah? Ina tare dake a kodayaushe." Ta k'wace hannunta cikin damuwa ta ce. "Gashi nan kacewa Inna zaka tafi gida yau." Ta fara hawaye ta ce. "Dan Allah Yaya Umar karka tafi ka barni, ka ga kai kaɗai ne abokina, idan ka tafi da wa zan dinga hira da karatu?" Runtse idonsa ya yi yana jin yanda zuciyarsa ke yi masa suya, ba zai iya jurarar ganin ta cikin damuwa ba, dan haka ya ce. "Shikenan na fasa tafiyar." Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta shiga share hawayen fuskarta, baiwar Allah, har cikin zuciyarta ta yarda ya fasa tafiyar. Haɗe_haɗen su Daddawa da kuka da lalle Inna ta haɗawa Umar cikin wani ƙaramin buhu a matsayin tsaraba ta fito masa dashi tsakar gida. Yana zaune suna hira da A'isha har 11 ta wuce, kasantuwar su tare sai ya sanyaya masa zuciya ya mantar da shi damuwar da yake ciki. Suna cikin hirar aka kira shi a waya, d'agawa ya yi ya ji muryar Ado driver, bayan sun gaisa ya sanar masa ya ƙaraso cikin garin Kumurya yana ƙofar gidan Sarki. Wata irin bugawa ya ji zuciyarsa ta yi, lokaci ɗaya ya ji mood ɗinsa ya sauya, shikenan dagaske dai tafiya zai yi ya bar A'ishansa. Ba tare da ya bari ta gane halin da yake ciki ba ya miƙe ya fita bayan ya ce mata yana zuwa zai je ya dawo...........✍️ _*Ku yi hak'uri da wannan ina cikin sha'anin biki ne, ko editing ban yi ba*_ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣6️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Yana zuwa ya tarar da Sarki da Ado driver zaune a soron gidan Sarki suna hira, an kawowa Ado driver ruwa da abinci. Zama ya yi suka gaisa da Ado driver cikin mutunta juna. Wajen ƙarfe sha biyu Umar ya koma gidansu A'isha, lokacin an gama zuba komai nasa a cikin Mota, sun yi sallama da su Sarki, tafiya kawai za su yi. A inda ya bar A'isha a nan ya tarar da ita a zaune ta yi tagumi, Inna na zaune a gefen ta ita ma duk jikinta a sanyaye. Bayan ya yi sallama sun amsa masa sai ya rasa mai zai ce, tsawon minti biyu yana tsaye ya dai daure cikin sanyin murya ya ce. "Mama za mu wuce." Inna ta miƙe ta ce. "To Allah ya kiyaye ya kai ku lafiya, ga kayan ba ka ɗiba ba kuma." Idanunsa akan A'isha ya ce. "Idan zan fita zan tafi da su, an gode sosai Allah ya saka da Alkhairi." Inna ta ce. "Mu ne da godiya Umar, ka yi mana abun da babu wanda ya taɓa yi mana kamar shi a cikin rayuwarmu, ka taimake mu a lokacin da muke tsananin buƙatar neman taimako, Allah Ubangiji ya biya ka, ya raba ka da iyayenka da duniya da mutanen cikinta lafiya, Allah ya saka maka da gidan Aljannah ya baka mace ta gari." Ya ce. "Ameen." Tare da zaro waya keypad daga cikin aljihunsa ya miƙawa Inna ya ce. "Mama ga ƙaramar wayata nan akwai sim a ciki, insha Allahu idan mun ƙarasa zan kira ku ta cikinta." Inna ta ƙi karɓa ta ce. "A'a Umar, ka cigaba da amfani da abar ka, ya za'a yi ka bani wayarka?" Umar ya ce. "Bana wani amfani da ita sosai ne, dan Allah ki karɓa Mama kar ki ce a'a, akwai memory a ciki mai ɗauke da karatun Alqur'ani, sai ki dinga kunnawa Humairah tana saurara." Inna ta ɗan yi jim sannan ta saka hannu ta karɓa tare da yi masa godiya. Ganin yanda hankalinsa gaba-d'aya yake kan A'isha sai ta shiga ɗaki ta ba su guri. Tsugunnawa ya yi a daf da ita ya kama hannunta ya ce. "I'm sorry Humairah, ban san me zance miki da zaki fahimce ni ba, amma wallahi ba dan son raina zan tafi in bar ki ba." Ya ƙara damk'e hannunta sosai a cikin nasa ya ce. "Gida zan tafi gurin ahalina, amma duk watannin da na shafe ban gan su ba kewar ki da na fara ta saka ba na murna da d'okin ganin su, Please Humairah dan Allah kar ki saka kanki a cikin damuwa saboda tafiyata, zan dawo gare ki insha Allahu, ko dan na cika alƙawarin da na ɗaukarwa kaina na nema miki lafiya." Wani irin yanayi A'isha ta tsinci kanta a ciki wanda ba zai misaltu ba, duk saurin kukanta sai ta nemi ko d'igon hawaye ta rasa a idonta. A hankali ta kamo ɗayan hannunsa cikin magana daƙyar ta ce. "Dagaske tafiya zaka yi Yaya Umar? Ashe ba zan taɓa ganin ka ba a rayuwata? Dan Allah ka ce mun mafarki nake yi ba gaske ba ne zaka tafi ka bar ni." Kasa magana ya yi saboda yanda kalamanta suka gusar da guntun dauriyar da yake da ita. Cikin raunin murya ya ce. "Ki yi hak'uri, shine kawai abun da zan iya ce miki." Girgiza kai A'isha ta shiga yi ta fashe da wani marayan kuka mai karya zuciyar mai saurare, da sauri Inna ta fito daga ɗaki tana tambayar ba'asi. Hakan ya saka Umar zare hannunsa daga nata ya miƙe tsaye. K'afufuwansa A'isha ta rungume cikin matsanancin kuka ta ce. "Dan Allah Yaya Umar kar ka tafi ka bar ni!" Runtse idonsa ya yi cikin ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta tarar masa a ido, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi da k'una. Inna ce ta zo ta janye A'isha daga jikinsa, cikin rarrashi ta ce. "Mene haka A'isha? Wannan wanne irin kuka ne? So kike ki karya masa zuciya zai tafi ya ga ahalinsa ya fasa saboda ke? Ai dama ko mun daren dad'ewa kin san zai koma tunda ba'a nan yake ba." Kamar zai fashe da kukan shi ma ya zaro kuɗi ya ajiye a ƙasa yana duban Inna ya ce. "Mama dan Allah ki kai ta asibiti da wannan kuɗin a duba a ga abun da ya samu idanun nata, in ya so duk yanda ake ciki sai ki sanar mun ta waya." Inna ta ce. "A'a Umar ba za mu yi haka ba, gaskiya ba zan karɓi wannan kuɗin ba, d'awainiyar da ka yi da mu a baya ma ta isa, Allah ya saka da Alkhairi." Dafe kansa dake sara masa ya yi ya ce. "Dan girman Allah Mama ki yi hak'uri ki karɓa, idan kika ƙi karɓa ba zan ji daɗi ba." Inna ta ce. "Amma Umar......" Ya marairaice ya ce. "Dan Allah Mama." Inna ta ce. "Shikenan." Ta shiga yi masa godiya tare da kwararo masa tarin addu'oi. Idanunsa akan A'isha dake gunjin kuka ya ce. "Humairah zo ki ji." Inna ta zare ta daga jikinta ta ƙarasa ta ɗauki kayan da ta haɗa masa ganin ba ta su yake ba kar ya manta ta nufi ƙofar gida da su. Takawa ya yi zuwa inda Aisha take ya ɗago kanta yana kallon fuskarta dake jik'e da hawaye ya ce. "Please ki bar kukan nan Humairah, da kin san yadda nake ji a cikin zuciyata da ba za ki bar d'igon hawaye ya fito daga cikin idonki a gabana ba, na faɗa miki zan dawo nan kusa Insha Allahu." Tana sheshshek'a ta ce. "Ai na san ba dawowa zaka yi ba." Ya ce. "Zan dawo mana, amma idan kin daina kukan nan, idan baki daina ba ba zan dawo ba." Duk yanda kukan ke cin ta haka ta haɗiye shi ta daina jin abun da ya faɗa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗauko handkerchief ɗinsa ya shiga share mata hawaye. K'uri ta yi masa idanunta a cikin nasa saboda kafen ta da ya yi da ido, wani numfashi ya sauke mai zafi ya shafi saman idanunta ya ce. "Allah ya baki lafiya My Humairah." Ba ta ce komai ba dan tana buɗe baki kuka ne zai biyo baya. Kama hannunta ya yi suka fita waje cikin yanayin damuwa. A bakin Mota ya tsaya ya ɗan rank'wafa ya kai bakinsa dai_dai kunnenta ya ce. "SAI WATA RANA HUMAIRAH! I will miss you so much." Wani kuka A'isha ta fashe da shi ta rungume shi, so take ta yi magana amma ta kasa. Hansai dake tsaye tana lek'en su ta tafa hannuwa tare da fasa salati ta yi cikin gida cikin gudu_gudu tana cewa. "Jama'a yau na ga abun da ya ishe ni bai ishi Allah ba, karuwanci har ƙofar gida a gaban Uwa da bainan nasi, Jama'a ku fito ku ga ikon Allah." Inna dake tsaye ta yi saurin ƙarasawa ta b'anb'are A'isha daga jikin Umar daƙyar ta yi cikin gida da ita ganin har an fara taruwa a gurin kamar wani babban abun ne ya faru. Umar ya bi su da kallo wasu hawaye masu ɗumi suka zubo akan kuncinsa, saurin goge su ya yi ya buɗe front seat cikin mawuyacin hali da k'uncin zuciya ya shiga ya zauna. Ado driver dake kallon sa ya girgiza kai cikin tausayawa ya kunna Motar. Umar ya ɗago kansa daƙyar ya yiwa gidansu A'isha kallon ƙarshe, har lokacin sautin kukanta bai gushe daga cikin zuciya da kunnensa ba, kuma ya san har abada ba zai taɓa gushewa ba. Lumshe idonsa ya yi a hankali lokacin da ya ji Ado driver ya ja Motar sun fara tafiya. "I loose her." Ya faɗi hakan a cikin zuciyarsa. Wunin yau gaba-d'aya cikin kuka A'isha ta yi shi, ba ta taɓa tsintar kanta a cikin damuwa da tashin hankalin zuci irin wannan ba a rayuwarta. Ko lokacin tafiyar su Ma'u ba ta ji abun da take ji ba yanzu a cikin zuciyarta. Ta kasa yardar wa kanta Yaya Umar ɗinta ya tafi, ta kasa yarda ba za ta gan shi anjima ba, ta kasa yarda idan ta tashi gobe da safe ba za ta gan shi ba, ta kasa yarda ya tafi ya bar ta, gani take duk k'arya ne ko kuma mafarki take yi zata farka. Inna ma duk jikinta babu daɗi haka take jin sa, ga tausayin A'isha ga kuma kewar Uwar da za su yi, dan sabo ba k'arya ba ne, ko dabba ce da kai kuka rabu sai ka ji babu daɗi na rashin ganin gilmawarta balle Mutumin ya nuna maka k'auna a lokacin da kowa yake gudun ka, ya ja ka a jiki ya nuna maka kai ma wani ne, kai ma mutum ne mai daraja kamar kowa. Ya fitar da kai daga cikin halin k'unci da matsi na rayuwa. Da Magriba A'isha tana kwance akan gado zazzaɓi mai zafi ya rufe ta Inna ta shigo ɗakin dan yin Sallah, kallon inda take ta yi ta ce. "Za ki iya ki yin Sallah kuwa?" Girgiza mata kai ta yi. Inna ta ce. "Allah ya ƙara sauƙi, bari na yi Sallah na baki magani ki sha, sai ki daure ki yi Sallar." Hawaye kawai A'isha take yi, wani irin zafi da ciwo take ji a ƙirjinta, ga ciwon kai da ciwon ciki da ya bijiro mata lokaci ɗaya, ga sanyin da take ji yana shiga cikin ƙasusuwan jikinta, ga idanuwanta dake mata zafi saboda kukan da ta sha, ta rasa ina ma za ta saka ranta ta ji daɗi. Ajiyar zuciya kawai take saukewa akai_akai. Bayan Inna ta idar da Sallah ta zo ta ɗaga ta, ta zaunar da ita tana yi mata sannu, ragowar wani yoghurt da Umar ya kawo mata ta ɗauko. Cikin lallami ta ce. "Ki sha wannan sai ki sha maganin." Kawar da kai ta yi ta ce. "Ba zan iya sha ba Inna, cikina ciwo yake mun." Inna ta ce. "Yunwa ce, yau fa kwata_kwata ba ki ci abinci ba, ki sha wannan ɗin zaki ji daɗi." Daƙyar Inna ta samu A'isha ta ɗan kurb'i yoghurt ɗin ta koma ta kwanta. Inna tana shafa kanta ta ce. "A kullum ina faɗa miki ki dinga hak'uri da rayuwa a duk yanda ta zo miki A'isha, ki yi hak'uri ki cire damuwar tafiyar yaron nan daga cikin ranki, kar wani ciwon ya kama ki." Cikin rawar murya ta ce. "Shikenan fa ba mu da kowa a cikin garin nan, yanzu za'a cigaba da zaginmu da yi mana rashin mutunci tunda mai tare manan ya tafi." Inna ta ce. "Muna da Allah, a lokacin da su Ma'u suka tafi haka kike ce, bayan tafiyarsu babu jimawa kuma sai Allah ya aiko mana da Umar, to yanzun ma shi zai taimake mu ya ba mu yanda zamu yi, ki daure zuciyarki ki cire komai na damuwa daga cikinta, ko zaki samu ki ɗan yi bacci zuciyarki ta huta." Lumshe ido kawai ta yi, amma ta san yau duk iya satar bacci ba zai ɗauke ta ba, dan ba ta da nutsuwar yin sa ko kaɗan. Washegari ta tashi jikin nata da ɗan sauƙi, ta kuma daure iya iyayinta dan ganin ba ta yi kuka ba, saboda kar ta tayarwa da Inna hankali. Tun safe Matan gidan suke zarga a ɓangarensu suna yada musu maganganu da habaici akan tafiyar Umar, daga mai shigowa da shewa sai mai shigowa tana gud'a. Inna dai ko kallon inda suke ba ta yi, balle kuma A'isha da ta ji zaman garin gaba-d'aya ya ƙara fice mata a rai. Jiya wajen goma na dare haka Iya ta zo ta ƙarewa Inna zagi tass akan kwakwazon da Hansai ta yi na A'isha ta rungume Umar, har sha biyun dare ba ta bar Inna ta huta ba...... Kusan sati A'isha ta yi tana jinya kafin ta samu sauƙi, bayan ta sha allurai har da ƙarin ruwa. Ta ji sauƙin zazzaɓin da ciwon kai, ciwon cikin ne dai ya ƙi yi mata sauƙi, dan cikin dare haka za ta tashi ta kasa bacci tai ta juye_juye tana hawaye, sai Inna ta yi mata tofi a ruwa ta ba ta, ta sha sannan yake lafa mata. Yau da yamma A'isha tana kwance a tsakar gida idanunta a lumshe amma ba bacci take yi ba, tunanin Umar take yi da moment ɗinsu da suka gudana masu tsayawa mutum a zuci, lokuta da dama sai ƙamshinsa yay ta mata gizo a cikin hancinta, ta ji kamar yana kusa da ita za ta ji daddaɗar muryarsa. A hankali ta saka hannu ta share hawayen da ya zubo mata, sannan ta juyar da kanta inda take jiyo sautin muryar Inna tana karatun Alkur'ani, cikin muryar marasa lafiya mai cike da damuwa ta ce. "Inna har yau bai kira ba ko?" Inna ba ta amsa mata ba sai da ta kai ƙarshen aya, ta dube ta cikin rashin jin daɗi ta ce. "Ke da wayar kodayaushe take hannunki da ita kike kwana kike komai ai inda ya kira zaki ji." A'isha ta ce. "Ki kai wurin Abba mai caji anjima ya duba dai, ko an kira gani ne baki yi ba." Inna ta ce. "Amma ai da za'a ji ƙarar kiran ko?" A'isha ta ce. "To ki kai a duba lambobin cikin wayar a kira, na san baza'a rasa tasa ba, idan ma babu sai mu cewa wanda mu kira dan Allah ya turo mana lambarsa muna son kiran sa ne." Inna ta ce. "Toh." A'isha ta lalubo wayar da kodayaushe tana kusa da ita tana jiran tsammanin kiran Umar a cikinta, amma har yau sati guda da tafiyarsa bai kira ba, abun da yake ƙara ɗaga mata hankali kenan, ta kasa samun nutsuwar zuci. Daddanna wayar ta shiga yi ba tare da ta san inda take dannawar ba. Inna ta ce. "Ki ajiye wayar kar ki shiga wani gurin da za ta samu matsala kuma." Ba ta ce komai ba ta ajiye wayar. Duk maganganun da ta yi cikin dauriya ta yi su, dan ba ƙaramin ciwo cikinta yake yi mata ba, lokaci ɗaya ta ji ya yi mata wata irin murd'awa, da sauri ta tashi zaune tana salati hannayenta duka akan cikin nata. A kid'ime Inna ta yi kanta ta riƙe ta tare da tambayar ta lafiya? Babu bakin amsawa saboda aman da ta ji ya taso mata, a hanzarce ta miƙe da nufin ta ƙarasa bakin rariya, sai dai bai fi taku uku ta yi ba ta tsugunna ta fara kelaya aman, Inna dake bin inda ta tashi da kallo ganin abun dake gurin ta ɗago ta kalle ta cikin wani irin yanayi..........✍️ *Ban yi edit ba* *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣7️⃣* ..........Sosai ta yi aman, hakan ya ƙara galabaitar da ita. Taimaka mata Inna ta yi ta wanke fuskarta ta cire kayan jikinta ta sauye wani ta koma ta kwanta tana numfarfashi. Inna tana gyara mata kwanciya ta ce. "Sannu, bari na je chemist na karɓo miki magani da audiga." Ɗaga mata kai ta yi duk da ba ta fahimci audugar me take nufi ba. Murɗawar cikin nata ya yi mata sauƙi, hakan ya sa take ta sauke ajiyar, wani irin abu take ji yana fita daga jikinta wanda ya kasance baƙo a gurinta, tunani ta dinga yi akan hakan amma ba ta fahimci komai ba har Inna ta je ta dawo. Bayan ta yi wanka Inna ta ba ta pant ɗin da ta saka mata pad a jiki kamar yadda Nurse ɗin dake zaune a chemist ɗin ta yi mata bayani. Cikin mamaki A'isha ta ce. "Inna mene wannan na ji shi a jikin wandon?" "Auduga ce, wadda za kina amfani da ita har jinin al'adar da kika fara ya ɗauke, ai kin san mene ne shi ko?" Gabanta ne ya faɗi, jikinta ya yi wani irin sanyi ƙalau, ta san me jinin haila yake nufi, Malamar da suke zuwa gurin ta karatu ta yi musu bayani a kan shi sosai, ba tare da ta san dalili ba ta ji hawaye ya zubo mata. "Ki saka wandon kar ki kuma ɓaci mana." Cikin tsananin jin kunyar Inna ta fashe da kuka tare da saka wandon. Umarni inna ta ba ta akan ta zauna za su yi magana, ba ta yi musu ba ta zauna tana sharar hawaye. Cikin nasiha Inna ta ce. "Mene na kukan kuma? Abin da ba kanki farau ba, duk macen da kika gani a duniya tana yin jinin al'ada in dai ta kai munzalin farawa, wanda ba sa yi kuma yawanci ciwo ne, a yanda aka ce ma zai yi wahala su haihu in ba wani ikon Allah ba." Ita dai ba ta ce komai ba sai kukanta ta cigaba da yi. Nasiha sosai Inna ta yi mata akan yanzu girma ya hau kanta, an fara rubuta mata zunubi da lada kamar kowa, don haka ta ji tsoron Allah a duk inda take tare da tsare mutuncinta, ita dai ba ta tanka ba, kunya da yanayin da take ciki ya hana ta magana. Bayan ta ci abinci ta sha magani ta kwanta bacci. Hayaniyar Iya da ta shigo tana yi wa inna tijarar da ta saba ce ya tashe ta daga baccin, lokacin har an yi Sallar Isha'i. Tsaki ta ja tare da tashi ta fito tsakar gida cikin lalaben hanya. Duk da yanda take jin rashin ƙwarin jikinta da cikinta da ya ɗaure mata, amma ta daure ta cewa Iya. "Wai don Allah Iya me muke tsare miki ne a gidan nan da kullum kike zuwa ki ishe mu da masifa?" A ƙufule Iya ta ce. "Ban sani ba, wato wuyanki ya yi kauri ko? Yar mitsitsiya dake amma har za ki faɗa mini wannan maganar? Ki ji da rashin ganin da ba kya yi mana, masu idon ma sun yi shiru sai ke makauniya ce mai bakin magana." "Ai Allah ne ya yi Ni a haka ba ni na yi kai ba..." "Ke! Rufe mini baki, me ya fito dake ma daga ɗaki?" Inna ta katse ta cikin tsawa. Kuka ta fashe da shi ta ce. "Toh Inna kullum sai ta zo ta dinga zagin ki kuma ba ki yi mata komai ba?" Ta yi maganar cikin tsantsar takaici. "Ki cigaba da magana, tunda ban isa in ce ki yi shiru ki yi ba." Ƙwafa iya ta yi ta juya ta fita tana cigaba da masifa. Duban A'isha Inna ta yi ta ce. "Kar ki kuma yi mini haka A'isha, ko sa'ar ki ce Iyan da za ki dinga mayar mata da magana?" A raunane ta ce. "Ki yi haƙuri ba zan kuma ba." "Shikenan, bari na haɗa miki ruwa ki yi wanka, dama yanzu nake shirin tashin ki." Ba ta ce komai ba ta samu guri ta zauna, zuciyarta cike da damuwar rashin jin Umar da masifar gidansu da ba ta ƙarewa. A sanyaye ta ce. "Ina wayar nan Inna? Bai kira ba ko?" Girgiza kai Inna ta yi cikin tausayawa ta ce. "Bai kira ba, ki yi haƙuri ki cire damuwar hakan daga ranki, addu'a ya kamata ki yi masa Allah ya sa yana lafiya." "Insha Allahu, ya ce akwai karatun Alkur'ani a cikin wayar, ki ɗauko ki kunna mini." "Ai ban san ta yadda zan kamo ba, amma bari anjima idan zan je shago siyayya, sai mu biya gurin mai chaji ya kunna miki." Kwana Uku A'isha ta yi tana jinin sannan ya ɗauke, kamar yadda Inna ta sanar mata alamar da za ta ji ta san ya ɗauke, tana ji ta sanar da ita, duk da an koya musu yadda ake wankan tsarki amma sai da Inna ta ƙara yi mata bita domin ta yi shi yadda ya kamata. A ranar Inna ta ƙirga kuɗaɗen da Umar ya ba ta ranar da zai tafi, dubu ɗari da goma ne, ta zazzari wasu sun yi amfani da su saura dubu ɗari da biyu. Cikin farinciki ta haɗa musu kayansu don tafiya asibitin Kano gobe a duba A'isha, dama jira take ta samu tsarki sai su tafi. "Wai Haulatu ba za ki bar kukan nan ba? Na ce ki kwantar da hankalinki in dai Umar ne zai zo da ƙafafun shi har inda muke, ina nan ina shiri akan hakan." Haulatu dake gunjin kuka ta ce. "Yaushe zai zo to? Tunda ya tafi kike ce mini haka, kuma yau an fi sati da tafiyar tasa bai dawo ba." Cikin lallami Uwa ta ce. "Gaggawar me kike ne? Ki bi komai a sannu ze zo ne ai." Zunɓura baki ta yi ta ce. "Gaskiya ni dai na gaji da jira, so nake kawai na gan shi ko na ji muyar shi, ki je gurin Sarki ki karɓo mana lambarsa, na san ba zai rasa ba." Shiru Uwa ta yi cikin nazari sannan ta ce. "A baya na je na karɓo lambar Mahaifiyarsa, yanzu kuma na koma na karɓo tasa? Ba zai yiwu ba gaskiya, kin san Sarki da saurin gane abu, dole zai fuskanci akwai abin da muke ƙullawa, sai dai mu je gurin su waccar makauniyar yarinyar, na san ba za su rasa ba." "Kina ganin za su ba mu kuma Uwa?" "Na san me zan ce musu da dole za su ba mu, tashi ki ɗauko mini gelena mu je yanzu-yanzu, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe." Cikin farinciki Haulatu ta share hawayen fuskarta tare da miƙewa. A'isha tana zaune a tsakar gida ta yi tagumi tana tunanin Umar su Haulatu suka kwaɗa sallama. A sanyaye ta amsa musu. Haulatu dake bin ta da Kallon tsana ta ce. "Asaben ba ta nan ne?" Cikin jin haushin yadda Haulatu ta gatsa mata sunan Inna A'isha ta ce. "Me ya faru?" Kafin Haulatu ta kuma magana Inna ta fito daga bayan gidan da ta zaga, da fara'a take duban Uwa. "Ku ne a tafe? Sannun ku da zuwa, ku zauna mana, kwa tsaya a tsaye." Ta yi maganar tana ware musu tabarmar da A'isha take zauna. Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa Uwa ta dube ta, ta ce. "Asabe lambar waya muka zo karɓa a gurin ku." Cikin mamaki Inna ta ce. "Lambar wayar wa?" "Ta Umar baƙon yaron da ya zauna a gidanmu, don mun san ba za ku rasa ba." Dam! Gaban A'isha ya yanke ya faɗi, da sauri ta ɗago kanta amma ba ta ce komai ba. "Ayya, ai kuwa ba mu da lambar shi, don kwana uku mun je gurin mai chaji akan ya duba mana cikin wayar da ya bar mana ko akwai lambar waya amma ya ce ma babu, daga ta kamfanin layi sai ta layin da yake cikin waya....." "Sai dai in ba za ku ba mu ba ne kawai, amma mun san kuna da ita." Haulatu ta katse Inna cikin rashin ɗa'a." Inna ba ta ce komai ba sai kallon yarinyar da take cikin mamaki. Ɓata fuska Uwa ta yi ta ce. "To ai shi ya ce mu zo mu karɓa a gurin ku, saboda yana so su dinga waya da Haulatu, da zai tafi kuma ya manta yana sauri bai ba ta ba, abin da ya sa ma muka zo saboda kar ya gaji da jiran kiran mu, ga rashin jin muryata da ba ya yi zai iya jefa shi cikin wani hali, kin san ba ƙaramin ƙaunar ta yake ba." "To sai ku jira idan ya gaji da rashin jin murya tata ya dawo garin ya ba ku lambar da kansa, ina ganin hakan zai fi kyau ko?" Inna ta faɗi haka cikin haɗe rai. "Ko ba ki faɗa ba ma zai dawo, tunda ya gani yana so, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu, yarinya ƴar dangi da asali zai aura ba baƙin haure ba." Ɗan murmushi kawai Inna ta yi ba ta ce komai ba. Zuciya babu daɗi su Uwa suka zira takalmansu suka fice. A'isha da ta yi mutuwar zaune cikin bugawar zuciya tun lokacin da Uwa ta ambaci soyayya tsakanin Umar da Haulatu ta ji wasu hawaye masu ɗumi sun shiga rige-rigen zuba akan kuncinta, ba tare da ta san dalili ba. Ita tana nan tana zaman jiran kiran shi ashe ba ta ita yake ba, ko tantanma ba ta yi wannan dalilin ne ya hana shi kiran ta. "Kada ki bari wannan zancen ƙanzon kuregen ya yi tasiri a zuciyarki, na san yanzu ƙaramin tunanin ki ya ba ki abin da ba shi ba ne." Inna ta faɗi haka cikin tausasa harshe. Ajiyar zuciya ta sauke ba don kalaman Inna sun gamsar ita ba, duk da ƙarancin shekarun ta amma kalaman Uwa ba ƙaramin dukan zuciyarta suka yi ba, ba ta san mene ne so ba balle kuma kishi, abin da ta sani kawai ta damu da Umar, a halin yanzu babu abin da take buƙata sama da ta ƙara jin muryarsa, ta ji shi a kusa da ita yana yi mata hira, ta ji daddaɗan ƙamshinsa gami da dariyarsa mai sa ta ji sanyi a cikin ranta. Gocewa ta yi ta kwanta a gurin saboda jin kanta ya fara juya mata. Wani irin haushin Haulatu ta ji ya cika mata zuciya, tsaki ta ja a fili ba tare da ta san ta yi hakan ba. Inna dake lura da yanayin da take ciki ta miƙe don cigaba da haɗa musu kayansu, don gobe asubanci za su yi zuwa Kano. Kamar a mafarki wayar da Umar ya bar musu ta fara ringing, wata irin zabura A'isha ta yi ta fara laluben wayar dake gefen ta, jikinta har rawa yake saboda tsabar zaƙuwa da zumuɗin jin muryarsa da take........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣8️⃣* Ta yi nasarar lalubo wayar ta riƙe a hannunta, ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi tare da faɗin. "Inna ana kira ki zo ki ɗaga kar ta katse." Karɓar wayar Inna ta yi da niyyar ɗagawa, kafin ta ɗaga wayar ta saka Battery shutdown ta ɗauke. "Yawwa, ba ni in kin ɗaga." A'isha ta faɗi haka tana yawo da hannunta a cikin iska tamkar za ta cafki babu. A sanyaye Inna ta ce. "Ban kai ga ɗagawa ba ta mutu, ina ji chaji ne ya ƙare." A gigice A'isha ta ce. "Innalillahi! kunna dai mu gani ko batir ɗin ne ya goce." Inna ba ta yi musu ba ta kunna wayar, ƙara mutuwa wayar ta yi alamun dai babu chajin. Cikin damuwa na ganin samu da rashi A'isha ta miƙe tana faɗin. "Bari na kai ta wurin chaji." "Idan kina ganin hanya ba, mene haka ne wai A'isha kike yi? Duk kin bi kin gigice saboda an kira waya, shi ne ma ko ba shi ba ne wanda kike ta ƙulafucin kiran nasa oho? Kin ga A'isha ki raba kan ki da abin da ya fi ƙarfin ki, ki cire damuwar yaron nan daga ranki." Komawa ta yi ta zauna tare da saka kuka, cikin raunin murya ta ce. "Inna shi kaɗai ne fa wanda ya so mu a cikin garin nan bayan Innar Ma'u, shi ne abokin hirata, tunda ya tafi na koma halin zaman kaɗaici, idan na damu da kiran shi laifi ne? Idan kuma laifi ne ki yi haƙuri na daina." Wani irin sanyi jikin Inna ya yi, tausayin A'isha ya cika mata zuciya. Tabbas idan kana cikin hali na ƙunci da kaɗaici ka samu mai ɗebe maka kewa, lokaci ɗaya kuma ya tafi dole ka damu. Cikin kwantar da murya ta ce. "Ko kaɗan abin da kika yi ba laifi ba ne, kawai dai ina so ki rage damuwar da kika saka a ranki ne, kawo wayar yanzu na kai ta gurin caji, kar a kuma kira a ji a kashe." Share hawayen fuskarta ta yi ta miƙa mata wayar. Sai bayan isha'i Inna ta je karɓo wayar, ta cewa mai cajin ya kunna ya duba gurin kira ya kira mata lambar da aka kira. Bayan ya duba ya ce. "Babu lamba ko ɗaya a gurin kira fa." Da mamaki Inna ta ce. "An kira fa tana ta ringing, kafin a ɗaga ta mutu babu chaji." "Shi ya sa ba za a ga kiran ba, ai indai aka kira ba a ɗaga ba har waya ta mutu a haka to kiran ba zai nuna ba." "Yanzu kenan ba za a ga lambar da aka kira ba?" "Eh." Ya ba ta amsa a tak'aice. Zuciyar Inna babu daɗi ta karɓi wayar bayan ta biya shi kuɗin cajin ta koma gida. Ihu ne kawai A'isha ba ta yi ba da Inna ta sanar mata ba a ga lambar da aka kira ba, amma ta sha kuka mara sauti. Washegari tun asubar fari suka shirya don tafiya, sai dai a karo na biyu Inna ta nemi kuɗi sama da ƙasa ta rasa, ga shi ba ta ko ficika da ya yi saura, gabaɗaya kuɗaɗen hannunta ta haɗe guri ɗaya ta ajiye a tare. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Inna ko dai aljanu ne suka makarantar da ni? Ba sa son a mini magani shi ya sa duk sanda muka shirya da niyyar tafiya asibiti suke sace kuɗin." A'isha ta faɗi haka cikin matsanancin kuka. Kasa magana Inna ta yi, saboda abun ba ƙaramin dukan zuciyarta gami da ɗaure mata kai ya yi ba. Sunayen Allah kawai take ambata a cikin zuciyarta, wannan wanne irin bala'i ne da jarabta? Waye yake musu wannan satar rainin hankalin? Ta tambayi kanta tare da ɗaga hannu cikin hawaye ta ce. "Allah kai ne sarki, kai ka san me kake nufi da wannan yarinya, Allah duk wanda yake zaluntar mu Allah ka saka mana, ka toni asirin duk wanda yake daukar kuɗin nan, ka ba wa wannan baiwa taka lafiya." Kuka sosai A'isha ta wuni tana yi ranar, rarrashin ta Inna ta dinga yi tare da yi mata nasiha akan Ubangiji yana sane da su, su cigaba da addu'a kawai ita ce mafita. Rayuwa ta koma musu tamkar ta da kafin zuwan Umar, rayuwar rashi da ƙunci da fuskantar ƙyara da tsana daga mutanen gida da na gari. Kullum Inna a tafe take yawon nema musu abin da za su ci, rayuwa dai ta tsananta a gare su. Yau ta kama Monday, da safe suna cin gayen dafaffen dankalin hausa Inna ta dubi A'isha ta ce. "Ya kamata ki koma makaranta yau, kin ga ni yanzu ba zama nake ba, kuma duk inda na je hankalina ba a kwance yake ba, saboda ina fargabar kar wani abun ya same ki na bar ki ke kaɗai a gida, na dinga tafiya da ke kuma duk inda za ni ba mai yiyuwa ba ne, amma idan kina makarantar sai na fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali." A sanyaye ta ce. "Shikenan Inna zan koma yau insha Allahu, amma fa kullum na je sai Form master ɗinmu ya ce mini har yanzu lokacin da za a mini aikin idon bai yi ba?" "Ki shirya sai mu je tare na roƙi alfarmar su bar ki ki cigaba da zuwa kafin Allah ya hore a kai ki asibitin." "To, Allah ya sa su yarda." "Amin." Kamar yadda Inna ta faɗa tare suka je makarantar, ta samu malamin su A'isha ta yi masa bayanin matsalar da aka samu na sace musu kuɗi, cikin tausayawa ya ce babu komai ta cigaba da zuwa, abin da ya sa suka damu har suke magana saboda A'ishan tana da ƙoƙari, kuma rashin ganin da ba ta yi zai iya sawa ƙoƙarin nata ya ragu, tunda ba ta rubutu ba ta ganin abin da aka koya musu. Godiya Inna ta yi masa ta dawo gida. Tunda ta shigo layin su ta san da akwai wani baƙon al'amarin da yake faruwa a gidansu, ganin mutan gidan kusan dukan su a waje, ga wata ƙaramar Mota fake a ƙofar gidan yara sun yanyame ta. Ƙarasowar ta gurin ya yi daidai da boɗo murfin motar da Yawale yayan Malam ya yi ya fito, karaf suka haɗa ido da Inna, wanda hakan ya haifar mata da faɗuwar gaba. Haɗe fuska ta yi sosai ta wuce cikin gidan ba tare da ta bari sun haɗa ido da kowa a gurin ba, yayinda shi kuma ya bi ta da wani irin kallo, sauran matan gidan kuma suka raka ta da harara. Tana ji yo su zagayensu ana ta murnar dawowar su bayan sun shigo cikin gidan, anata ɓangaren kuma fargaba ce fal ranta, na rashin sanin da wanne kalar cin mutunci mazan gidan suka dawo musu da shi wannan karon ba. Har A'isha ta dawo ba ta fita ba, tana zaune tana ta tunane-tunane, Sallah ce kawai ke tashin ta. "Inna sannu da gida." A'isha ta faɗa bayan ta yi sallama tare da laluben gurin zama ta zauna. Numfashi Inna ta sauke tare da janye tagumin da ta yi ta ce. "Yawwa, har kun taso?" "Eh, me ya sa yau ba ki je kin ɗauko ni ba?" "Wallahi shaf na sha'afa ne A'isha, ban ma san lokacin ya yi ba, wa ya dawo da ke?" "Wani malaminmu ne, ya ga duk za a tafi a bar ni, shi ne ya ce bari ya rako ni." "To an gode Allah ya saka da Alkhairi, ki je ki cire uniform ɗin kar ya yi datti, kin san ba mu da omo." "To, ina abincina yunwa nake ji." Ta yi maganar cikin marairaice fuska. Cikin damuwa Inna ta ce "Ba mu da komai na ci a gidan nan, kuma ban san inda za mu samo ba, tun ɗazu nake tunani amma na rasa ina zan je." "Yau ma haka za mu kwana ba mu ci komai ba?" "To ya za mu yi? Sai dai mu yi ta addu'a Allah ya kawo mana mafita." Cikin karaya A'isha ta ce. "Inna me zai hana mu siyar da wayar da Yaya Umar ya ba mu, mu siya abinci da kuɗin, tunda babu abin da muke da ita, shi bai kira ba mu ma ba ma kiran kowa." Shiru Inna ta yi cikin nazari, a ranta tana mamakin kaifin basira da hankali da A'isha ta yi bayan tafiyar Umar, ta koma so silent, kamar ba ita ce wadda ba ta zama guri ɗaya ba a da, ta daina sangarta da abubuwan yara. Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Kin kawo shawara, amma kuma kar sai mun siyar ya yi ta neman mu ba ya samu." "Ba ma zai kira ba." Ta yi maganar cikin jin zafin rashin kiran nasa a cikin ranta, zuwa yanzu ta fitar da rai daga tsammanin kiran shi ko dawowar shi kamar yadda ya ce mata, ta ba wa zuciyarta haƙuri tare da ƙoƙarin cire shi daga cikinta, gami da ɗaukar ƙudirin mantawa da shi gabaɗaya a cikin rayuwarta, duk da ta san yiyuwar hakan na da matuƙar wahala, amma tana addu'a da fatan hakan ta kasance. Shawarar A'isha Inna ta bi, ba tare da jinkiri ba ta je ta siyar da wayar, bayan Magriba kuma ta tattara wasu daga cikin takalman A'isha masu tsada da agoguna da Umar ya siya mata ta kai gidan wata dillaliya dake nan ƙofar fadan wadda ke siyan tsoffi kaya ta sayar. Da wannan kuɗin ta yo musu sayayyar kayan abinci da sauran abubuwan amfani wanda za su musu kwanaki. Bayan kwana uku da daddare suna zaune a tsakar gida A'isha tana muraja'ar Alkur'ani, ɗaya daga cikin ƴanmatan gidan ta faɗo musu zagaye babu ko sallama, cikin fitsara ta dubi Inna ta ce. "Asabe ki zo ke da makauniyar ƴarki yanzu in ji babanmu." Kafin su ba ta amsa ta juya ta fita. Cikin tsantsar ɓaci rai A'isha ta ce. "Ba za mu je ɗin ba." Inna dake danne nata ɓacin ran ta ce. "Mu je mu ji neman me yake mana." "Ni dai gaskiya ba za ni ba, kin san fa Baba Yawale ba ya ƙaunar mu, in mun je ma na san zagi da cin mutuncin mu kawai zai yi kamar yadda ya saba." "Mu dai je A'isha, kin san na fi ki ƙin son haɗuwa da mutumin nan, amma saboda gudun magana da fitina mu je ɗin mu ji kiran me yake mana." "Amma Inna...." "Ki tashi mu tafi kawai, ba na son jan maganar nan taki." Ba ta kuma magana ba ta tashi kamar za ta yi kuka ta zira takalmi Inna ta kama hannunta suka tafi. Sashen matansa suka je, suka tarar da su zaune har da Iya. (Yawale Yayan Malam mijin Su Inna ne, Babansu ɗaya, ɗan Iya ne shi, duk mazan gidan a yanzu shi ne Babba.) Bayan sun yi sallama suka nemi guri suka zauna duk da ba wanda ya amsa musu sallamar, cikin ladabi Inna ta gaishe da Iya, ba tare da ta amsa ba ta fara magana cikin masifa. "Sannu Asabe, yanzu tsabar mugun hali da tsiya a ce ɗannan ya dawo har ya yi kwana uku amma ke da ƴarki ku kasa zuwa yi masa sannu da zuwa?" Shiru Inna ta yi ba ta ce komai ba, A'isha kuwa dama ɗauke kanta ta yi kamar ba ta gurin, sai turo baki gaba take." "Ai ban isa ba Iya, kina ganin yanzu ma sun shigo ko arziƙin gaisuwa ban samu daga gare su ba." Yawale ya faɗi haka yana jifan da Inna da mugun kallo. Wani kallo Inna ta watsa masa, amma still ba ta yi magana ba. Hangame baki Iya ta yi ta ce. "Iyee, samun guri, lallai Asabe, muna magana kin mana shiru, wato ga yan iska marasa aikin yi ko?" "Ai su ɗin ne." A'isha ta faɗa ƙasa-ƙasa. Hararar ta Inna ta yi don ta ji ta sarai, ba yabo ba fallasa ta ce. "To Iya ku yi haƙuri." Ƙwafa Iya ta yi tare da jan tsaki. Cikin gadara Yawale ya ce. "Na dawo na samu wani labari da sam bai yi daɗi ba Asabe, wato har yanzu ba za ku daina bin mutane kuna ci musu sassan jiki ba ko?" Kafin Inna ta yi magana A'isha ta fashe da kuka tare da faɗin. "Mu ba ma cin mutane, kuma......" Marin da Iya ta wanka mata ya sa ta yin shiru tare da dafe ƙuncinta, da sauri Inna ta kalli Iya, duk haƙuri da kawaicinta amma kana kallon fuskarta ka san yau an kai ta bango, don ɓacin rai ne kwance a cikinta. "Ko za ki rama mata ne da kike kallo na haka?" Iya ta faɗi haka kamar za ta kai mata marin ita ma. Ɗaya daga cikin matan Yawale ta ce. "Ai sai ta aikata, kin san su mayu ba kunya gare su ba, mu dai muna ta li'ilafi, aniyar mutum ta bi shi, kuma naman jikinmu ɗaci gare shi ba ciyuwa za mu yi ba, ato." Wani abu mai ɗaci ne ya zo ya tokare wuyan Inna, magana take so ta yi amma ɓacin rai ya hana ta, rungume A'isha dake kuka kawai ta yi tare da ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. Cikin karkaɗa ƙafa da muzurai Yawale ya ce. "Abin da ya sa na aika a kira ku ba komai ba ne sai don na sanar da ku cewa na karɓi kuɗin baikon A'isha daga hannun Tsoho Makawo ɗazu da yamma, mun kuma tsayar da ranar ɗaurin Aure ni da shi sati biyu masu zuwa, ranar juma'a bayan an sakko daga masallaci za a ɗaura auren, don haka sai ku fara shiri." Ya yi maganar cikin sigar bayar da umarni.........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣9️⃣* Cikin rashin fahimta Inna ta ɗago kai ta dube shi ta ce. "Ban gane ba Yaya? Wacce A'ishan kake nufin ka karɓi kuɗin Auren ta?" "A'isha nawa muke da su a gidan nan da kike da iko da su wanda zan saka a kira ki don na sanar miki batun auren su? Wannan dai makauniyar dake gabanki ita nake nufi." "Tabɗijan! Tatsuniya ma kenan, to wallahi ba zan aurar da ƴata ba a yanzu, kuma babu wanda ya isa...." "Ke Asabe saurara!" Iya ta katse ta cikin tsawa sannan ta cigaba da magana. "Don ma kin samu Tsoho makahon ya taimake ku ya ce zai aure ta shi ne za ki yi wa mutane iskanci? Ƴar taki Shegiya mara asali za ki yi wa mutane firfita a kan ta? To wallahi wannan auren tamkar an yi an gama." Cikin bushewar zuci da tsantsar ɓacin rai Inna ta ce. "Ni kuma babu wanda ya isa ya aurar mini da ƴa ko wanene." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannun A'isha suka miƙe, wadda kukan da take na marin da Iya ta yi mata ya sa ba ta fahimtar abun da suke cewa. Wata dariya Yawale ya yi ya ce. "Me za ki iya in an aurar miki da ƴar? Wa kike da shi? Ƙarƙari ki ce za ki kai ƙara gurin Sarki ko? To Sarkin baya nan ya tafi umra, sai mu ga wa zai tsaya miki." "Allah, shi ne zai mini katangar ƙarfe da duk wani mummunan ƙudirin ku a kan mu." Inna ta faɗa a fusace, yau kam sun kai ta bango, duk haƙuri da kawaicin da take musu a yanzu ta ji ba za ta iya ba. "Ni kuma in dai sunana Yawale sai an yi auren A'isha makauniya da Tsoho makaho." Sai a yanzu A'isha ta fahimci abin da ake magana akai, da wannan kalaman na Yawale. Wata irin bugawa zuciyarta ta yi, ƙara volume ɗin kukanta ta yi cikin rawar murya ta ce. "Inna me na ji Baba Yawale yana cewa? Ni za a yiwa Aure?" Hawayen fuskarta Inna ta fara share mata tare da faɗin. "Ki kwantar da hankali, in dai ina raye babu wanda ya isa ya miki Auran dole, tunda babu wanda ya haifar mini ke." Ba ta jira sauraren tijarar Iya da Matan Yawale suke taya ta ba, ta ja A'isha suka fice daga ɓangaren. "Inna don Allah mu bar garin nan, mu bar musu gidansu, kin san tunda Baba Yawale ya dawo rashin mutuncin da ake mana sai ya ƙaru." A'isha ta faɗi haka cikin kuka. Girgiza kai Inna ta yi cikin ɗacin rai ta ce. "Na fi ki gajiya da zaman gidan nan A'isha, dan dai babu yadda zan yi ne, kuma ina tunanin idan mun bar nan ba mu san ina za mu ba, ba mu san da waɗanda Allah zai ƙara haɗa mu ba." "Ƴan'uwanmu mana, ko da gaske ba mu da su?" "Muna da su, amma wani babban dalili ya sa ba zan koma gare su ba." "Wanne dalili ne? Don Allah Inna ko sau ɗaya ne ki kai ni na gan su, tun ina ƴar ƙarama ake mini gorin rashin asali, tun bana damuwa har na fara damuwa duk da ban san me hakan yake nufi ba, yanzu na gane me ake nufi da rashin asali, na fuskanci me kalmar SHEGIYA take nufi, kamar yadda na gano ba Baba Malam ne ya haife ni ba." Cikin tsantsar mamaki da damuwa Inna take kallon A'isha, a shekarunta ba ta yi tunanin za ta iya gane waɗan nan abubuwan ba a yanzu, musamman da har yanzu ɗabi'un yara sun fi yawa a tattare da ita a kan na manya, cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Wa ya faɗa miki ba Malam ne ya haife ki ba? Na ce ki daina mini wannan zancen ko, don ba gaskiya ba ne, Malam shi ne mahaifinki." Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ki daina ɓoye mini Inna, na riga na gane gaskiya, amma don Allah ko ba za ki kai ni na ga ƴan'uwanmu ba ki taimaka ki ba ni labarin su, da dalilin baro su da kika yi." "Zan faɗa miki, amma ba yanzu ba, domin har yanzu ke yarinya ce, ƙwaƙwalwar ki ba za ta ɗauki labarin ba balle har ta ba ki damar fuskantar shi, amma da sharaɗin ba za ki kuma tambaya ta ba har sai lokacin da na ga ya dace na faɗa miki da kaina." Gyaɗa mata kai kawai ta yi tare da kifa kanta a kan cinyarta ta cigaba da kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk mai sauraren shi. Washegari da ciwon kai ta tashi, hakan ya sa Inna ta ce ta zauna kar ta je makaranta, ranar Monday idan ta kai ta sai ta sanar da Malaman ba ta da lafiya ne ya sa ba ta zo ba. Da Yamma Inna tana ramuwar baccin da ba ta yi ba daren jiya ta ji muryar Namiji yana magana a kanta. A firgice ta tashi tare da rarumar hijabinta dake kusa da ita ta saka, Yawale ta gani ya ƙura mata ido yana bin ta da wani irin kallo. Haɗe rai ta yi cikin ɓacin rai ta ce. "Mene ne haka Yawale? Ya za ka shigo mini har ɗaki babu neman izini, a kan me?" "Saboda gidanmu ne ina da ikon shiga duk inda na ga dama." "Ko kai ka gina sashen nan ka ba ni haya ba ka hurumin faɗo mini har cikin ɗaki ba tare da neman izini ba, don haka kar ka ƙara yi mini irin wannan ba na so, idan kuma ba haka ba wallahi hukuma ce za ta raba mu!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Dariyar rainin hankali ya yi ya ce. "To hukumar ta raba mu mana Asabe?" Tsaki Inna ta ja tana ƙara gyara hijabin jikinta ta ce. "Ka tashi ka fitar mini daga ɗaki Yawale." Gemunsa ya shafa cikin shigar duniyanci tare da faɗin. "Ba ke kika saka na shigo ba, don haka ba ki isa kin sa na fita ba, A'isha na zo kira dama, Tsoho makaho ne yake jiran ta a soro za su yi taɗi." Kallon ba ka da hankali Inna ta yi masa ta ce. "Dama a kan wannan shirmen ka shigo mini har cikin ɗaki ina bacci? ban da, da wata manufar a ranka da ka shigo gidan ba ka ga A'ishan kwance a tsakar gida ba? Yawale ka ji tsoron Allah, ka tuna za ka mutu fa, duk abubuwan da kake yi Ubangiji yana kallon ka." "Har kura ce za ta ce wa kare maye? Ke har kin isa ki yi mini wa'azi Asabe? Ke da kike tattare da abin kunya, SHEGIYA fa kika ajiye, ai ke kika cancanci wa'azi ba ni ba." Miƙewa Inna ta yi ba ta kuma magana ba, don ta fuskanci neman magana kawai yake da ita. Ficewa ta yi ta bar masa ɗakin zuciyarta na mata wani irin zafi, ta gaji da cin zarafin mutanen gidan nan, rashin dajarar ta har ya kai ƙaton mutum ya shigo mata ɗaki ba excuse tana bacci ya gama ƙare mata kallo, Gaskiya dole ta san abin yi, ba za ta ɗauki wannan akuyancin da jahilcin ba, musamman da ta daɗe da gane ƙudirin Yawale a kanta. "Ke A'isha tashi mu je tsoho makaho yana jiran ki, ko ba kya ji ne? Ƴar bantan Uba kawai." Yawale da ya fito daga ɗaki ya faɗi haka cikin masifa. Ko motsi A'isha ba ta yi ba, duk da tana jin shi sarai, Hararar shi Inna ta yi ta ce. "Babu fa inda za ta, Yawale tun wuri ina shawartarka da ka ruguje wannan maganar Auren mara ma'ana, ban da zalunci yarinyar da ko shekara goma sha biyar ba ta cika ba ita ake ƙoƙarin aurawa Tsohon da ko ni ba zan aure shi ba? Tsohon ma mara mutunci da rashin sanin darajar ɗan Adam, ya mayar da aure ba a bakin komai ba, waye bai san Auri saki yake ba kaf garin nan, wato yanzu an gane halinsa an daina ba shi Auren shi ne zai zo nan, ni kuma da ban san ciwon kaina ba sai na ɗauka na bayar, to wannan ɓatan basiran ba da ni za a yi ba." "Duk rashin mutuncin shi amma ai yana da asali ko?" "Wannan ku ta shafa ba ni ba." Jinjina kai Yawale ya yi ya ce. "Kuma yarinya tunda tana zaune a cikin gidanmu tana cin arziƙin mu muna da ikon aurar da ita ga duk wanda muka so." "Tunda wata tsiyar kuke tsinana mata ba, gata nan ga ka, ka daura mata Auran mu gani." "To mu zuba mu gani, ni da ke ɗan halak ka fasa." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa da sashen, Inna ta raka bayansa da harara. Cikin jin daɗin yadda Inna ta yi wa Yawale tatas A'isha ta ce. "Gwara da kika yi masa haka, gobe ba zai dawo ba." Sai dai maganar A'isha ba ta tabbata ba, don kullum sai Yawale ya zo kiran A'isha akan ta fita gurin tsoho makaho, Inna kuma ta murje idonta ta ce bai isa ba, ba za ta je ba. Tun mutanen gidan ba sa fuskantar abin da yake Faruwa har suka fara fuskanta, nan fa suka yi caa a kan Inna, suna cewa don ma sun samu Tsohon ya taimake su ya ce zai auri ƴar tata take ƙi? Har da masu cewa ba ƙaramin jihadi Tsoho makahon ya yi ba da ya ce zai auri A'isha. Ba ta kula su, ta dage da kaiwa Ubangiji kukanta, don zuciyarta cike take da fargaba da tsoro, sanin halin Yawale ta san dagaske yake zai aura wa A'ishaTsoho makaho, a haka har kwanaki goma suka shuɗe. Da yamma Inna ta ɗauko A'isha daga makaranta, suna tafiya tana ba wa Inna labarin wani sabon Malami da aka kawo musu daga Kano. "Yawwa ga su nan ma sun dawo." Muryar Yawale ta doki dodon kunnansu da faɗin haka lokacin da suka shiga zauren gidansu. Su tsoro ma ya ba su, saboda yadda ya yi maganar a hanzarce. "Sannun ku da zuwa, ina A'ishushuwan tawa?" Tsoho makaho dake zaune a kan tabarma ya faɗi haka yana shafa tumbinsa. Tsaki Inna ta ja cikin takaici ta kama hannun A'isha suka yi gaba. "A'a, Asabe ya za ki ja ta ku tafi kuma? Kin san daɗewar da muka yi muna jiran ku kuwa? Ki zo magana Malam Tsoho ya zo mu yi fa." Ko waigowa Inna ba ta yi ba balle ya saka ran za ta tsaya. Giwa a saɓule ya ce. "Ka yi haƙuri Malam, haka nake ta fama da su, daga uwar har ƴar taurin kai gare su, amma bari na je na saka su fito." Murmushi tsoho makaho ya yi, cikin washe dafaffun haƙoransa ya ce. "Babu komai ka ƙyale su, rashin fahimta ne, da zarar mun fahimci juna komai zai wuce, wuyarta a ɗaura mana Auren a kawo ta gidana." Ya ƙarashe maganar yana lalubar sandarsa. Bayan ya miƙe ya zira hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa wa Yawale, hannu na rawa ya karɓa tare da washe baki ya ce. "Malam ba ka gajiya da abin arziƙi, Allah ya saka da Alkhairi ya ji ƙan mahaifa." "Amin, babu komai, ai ni ka gama yi mini komai tunda ka ba ni Auren yarinyar nan, don yadda na ji ana faɗar kyawun surarta na san zan mori kuɗina." Cikin dariya Yawale ya ce. "Za kuwa ka mora, don yarinyar a dire take dumurmur, sai dai an kai mata ita za ka tabbatar da abin da nake faɗa." Murmurshi Tsoho ya yi ya ce. "Madalla, haka ake so, yanzu bari na wuce gida, anjima su Nalami za su kawo kayan lefen, su kuma masu jere za su iya zuwa gobe, an gama gyara gurin amaryar." "Toh Allah ya kai mu, bari na kira maka Mamman ɗin ko?" Yawale ya faɗa tare da fita ƙofar gida, inda ɗan jagoran Tsoho yake zaune yake jiran shi. Tunda suka shiga gida A'isha take kuka, cikin kwanakin nan ta mayar da shi sana'arta, gabaɗaya ta lalace ta yi baƙi saboda damuwa da saka a ranta, a kodayaushe cikin rarrashin ta Inna take da nuna mata wannan Auren ba mai yiyu ba ne, amma ta kasa yarda da hakan, saboda ta san in dai suna cikin gidan nan to babu abin da zai hana Yawale aiwatar da abin da ya yi niyya, dama da Sarki yana nan ne zai iya tsawatar masa, shi kaɗai ne suke da tabbacin zai hana shi kaf cikin garin ya hanu. Da daddare kamar yadda Tsoho makaho ya faɗa sai ga kaya an kawo a cikin leda Viva, atamfa Leda guda biyu da shadda wanke kuɗinka guda ɗaya, pant da shimi bibbiyu, da takalmi soso guda ɗaya, sai ƙullin su powder da man shafawa a wata baƙar leda daban. Yadda aka zube kayan a tsakar gida matan gida na gani haka Inna ta tashi ta bar su a gurin cikin tsananin baƙin ciki, ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba da ganin kayan, don hakan ya tabbatar mata dagaske fa Yawale yake aurar da A'isha zai yi. A'isha kuwa tsabar kuka har shiɗewa ta dinga yi, yadda suka ga rana haka suka dare, don jikinta rikicewa ya yi da zazzaɓi mai zafi gami da ciwon kai. Washegari ta tashi jikin nata ya tsananta, hakan ya ƙara tayar da hankalin Inna, ga ba ta da kuɗin siyo mata magani, abun ya taru ya yi mata yawa, so take ta samu space ɗin da za ta yi tunanin mafita akan ganin auren nan bai yiyu ba, amma yanayin jikin A'isha ya sa ba ta da nutsuwar hakan.......✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣0️⃣* _*Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Allah ya yiwa mahaifiyar ɗaya daga cikin member ta ƙungiyarmu Elegant rasuwa, MOMMYN MUS'AB, muna barar addu'ar ku a gare ta.*_ Haka suka yini ranar, ko ruwa A'isha ba ta kai bakinta ba, ita kanta Inna dauriya kawai take, amma jikin nata kamar mai cuta haka take jin shi. Da ruwa bokiti ɗayan da ta dauko ta tsakura ta dinga shafa wa A'isha a jikinta da tsumma, hakan ya rage zafin jikin nata, har ta samu bacci ya ɗauke ta. Sharar da ba ta samu nutsuwar yi tun safe ba ta shiga yi, duk da a galabaice take saboda yunwa dake ɗawainiya da ita. Tana farawa Hansai da sauran matan gidan suka yi sallama, ba yabo ba fallasa ta amsa musu. Cikin izgili Ramatu ta ce. "Asabe tun jiya muke jiran mu ga an shigo kayan gado don mu je mu yi jere amma shiru, shi ne muka ce bari mu zo mu ji ko kafinta ne ya yi tsiyar, idan ba zai samu yau ba mu bari sai gobe." "Gaskiya kam, mu bari kawai sai goben, don tunda yarinyar ƴar gata ce ita ɗaya jal mun san ba ƙaramin kaya za a narka a ɗakinta ba, yanzu kuma yamma ta yi muna farawa dare zai yi." Cewar Hansai tana wani murmushi. Sarai Inna ta gane Habaici suke mata, murmushi ta yi ta ce. "To na gode da kulawa." Kallon juna suka shiga yi, cikin mamaki uwargidan Yawale ta ce. "To ai ba ki ce mana komai ba game da maganar kayan jeren, mu jira yau ɗin ko mu bari sai gobe." "Allah ya kai mu lafiya." Inna ta faɗa a taƙaice, cikin ƙoƙarin danne damuwar dake cikin ranta. Duk yadda suka so su ji Inna ta ce wani abu akan maganar jeren na za a yi ko ba za a yi ba amma ta ƙi ba su tabbaci. Haka suka tattara ƙafafuwansu suka koma, zuciyoyinsu cike da gulma da farincikin ganin su A'isha a cikin baƙin ciki. Fitar su babu jimawa wata yarinya ƴar ajinsu A'isha ta zo gidan sanye da uniform. Bayan sun gaisa Inna ta ce. "Atika lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau, wani malaminmu ne ya ce na rako shi gurin A'isha, tare muke ma yana ƙofar gida." "To, wani abu ya faru ne? Ko laifi ta masa?" "Gaskiya dai ban sani ba." "To bari na ɗauko hijabina mu je." Yana tsaye jingine da bangon gidan yana kallon cikin soro suka fito, cikin girmamawa ya tsugunna har ƙasa ya gaishe da Inna. Da fara'a ta amsa masa duk da cikin ranta cike take da fargabar Allah ya sa ba wani abun A'isha ta yi ba. Shiru ta yi cikin sauraren abin da ya zo da shi. Cikin nutsuwa ya fara magana. "Na ga A'isha ba ta zo school ba yau, shi ne na ce bari na zo na ji ko lafiya?" Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Ba ta jin daɗi ne, yau ta tashi da zazzaɓi." Cikin damuwa ya ce. "Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya, zazzaɓin bai yi zafi ba dai sosai ko?" Inna ta ce. "Sai godiyar Allah dai jikin nata." "Subhanallahi, Allah ya ba ta lafiya, amma kun je asibiti ko?" "Za mu dai je insha Allahu." Gyaɗa kai ya yi tare da yin shiru na wasu sakanni sannan ya ce. "Mama don Allah da gaske ne aurar da A'isha za ku yi?" Cikin raunin murya Inna ta ce. "Eh." Cikin damuwa sosai ya ce. "Amma saboda me? Na ga yarinya ce ƙarama, kuma tana da ƙoƙari a makaranta, da kun bar ta ko secondary school ta gama, kuma na ga ita ma kamar ba ta son auren, saboda jiya an fita break na gan ta ita kaɗai a class tana ta kuka, da na tambaye ta me ya faru shi ne take sanar mini an ce aure za a mata, ita kuma ba ta so." A sanyaye Inna ta ce. "Ni ma ba na so, an fi ƙarfi na ne kawai." "Kamarya? Su waye suke son aurar da ita ɗin to?" Ya tambaya a hanzarce. "Kawunnanta ne." "Ba ma mahaifinta ba?" "Eh, shi Allah ya masa rasuwa." Jinjina kai ya yi bai ce komai ba ya zaro kuɗi ya ajiye a gaban Inna ya yi mata Sallama ya tafi, Inna tana kiran shi akan ya zo ya ɗauki kuɗin amma bai tsaya ba. Da kallo ta bi shi tare da yi masa addu'a a cikin zuciyarta, ko tantanma ba ta yi shi ne sabon malamin da A'isha take labarin an kawo musu. Ɗaukar kuɗin ta yi ta koma gida. Bayan A'isha ta tashi Inna take labarta mata zuwan malamin. Murmushi ta yi cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Shi ne wanda nake ba ki labari, sunansa Malam Faisal, yana da kirki sosai da tausayi." Inna ta ce. "Allah Sarki, Allah ya saka masa da Alkhairi, dubu biyar fa ya ba ni, dama ina ta tunanin abin da zamu ci da wanda zan kai ki asibiti gobe." Bayan kwana uku A'isha ta ji sauƙi sosai, ta sha allurai da magunguna. A kwana ukun kullum Malam Faisal sai ya zo ya duba ta tare da yi musu Alkhairi, hakan ya janyo tarzoma tsakanin Inna da Yawale. Ya dinga masifa da faɗin kar ya ƙara ganin Faisal ya zo, tunda dai yarinya yanzu ɗaya take da matar aure don ya karɓi sadakinta, rana kawai suke jira a ɗaura Auren. Yau Juma'a ranar da su Yawale suka saka ta ɗaurin Auren A'isha da tsoho makaho. Tun cikin dare A'isha take kuka har gari ya waye ba ta yi shiru ba. Inna da gabanta ke ta faɗuwa ta dube ta, ta ce. "Don Allah ki bar kukan nan haka, sai kanki ya yi ciwo ko kin janyo wa kanki wata cutar, dama ba ki gama farfaɗowa ba." Cikin sheshshek'a ta ce. "Ni ba na son Auren nan, don Allah Inna mu gudu mu bar garin nan." Hawaye Inna ta matse ta ce. "Tabbas in har Yawale bai janye maganar auren nan ba to kuwa lokaci ya yi da zan bar garin nan dole." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke mai ƙarfi ta ce. "Mu tashi mu tafi Inna, kin san ma ba janyewa zai yi ba ma, kamar yadda ya faɗa ana saukowa daga masallaci za su ɗaur......" "Wacce irin sabgar tsiya da bayar da kai ce wannan Asabe kike yi haka?" Muryar Malam da ya shigo kamar an hankaɗo shi yana baza babbar riga ta karaɗe zagayen cikin amsa amo. Da mamaki Inna take duban shi cikin alamun tambaya. Cigaba da ya yi da magana cikin ɗaga murya. "Wanne irin abu ne wannan? Yau kusan sati da cewa a je a yi jere amma kin ƙi siyo kaya ki bayar har yau ranar ɗaurin Aure? Ko a ƙasa kike son su ci amarcin ne? Wannan ai halin matsiyata ne da nuna tsiya." Miƙewa Inna ta yi ba ta ce komai ba, don ba ta da lokacin ɓaɓatu da mutumin da take masa uzurin ciwon hauka, ko ƙara kallon inda yake ba ta yi ba ta shige ɗaki. "Wato ga mahaukaci ina magana kin mini shiru kin shige ɗaki ko? To wallahi ko me za ki yi sai an ɗaura auren nan yau, sai dai baƙin ciki ya kashe ki." Ya ƙarashe maganar tare da wurga wa A'isha wani mugun kallo. Hamɓarin ta ya yi da ƙafa ya juya ya fita. Yana tafe yana cigaba da banbanmin faɗa shi kaɗai, gidan tsoho Makaho zai je ya ba shi haƙuri akan rashin zuwa jeren, ya kuma tabbatar masa zai tursasa Asabe dole ta bayar a siyo ko da katifa ne, don tsohon ya ce masa ba zai angonce a dandaryar ƙasa ba. Jiniyar da ya ji ya sa shi tsayawa a ƙofar gida yana kallon Motar police dake tahowa. Officer gashi nan ma." Faisal dake fitowa daga cikin Motar ya faɗa tare da nuna Yawale. Zaro ido ya yi cikin tsoro ya ce. "Kai ɗan samari me na yi kake nuna ni?" "Idan muka je office za ka ji, shiga Mota mu ƙarasa." Cewar wani police cikin haɗe rai. Yawale zai kuma magana aka daka masa tsawa, dole ya shiga Motar ƙirjinsa na dukan uku-uku, sai rantse-rantse yake akan bai aikata laifin komai ba, Auren ƴa ma zai yi yau. Bayan tafiyar su ba jimawa labari ya karaɗe unguwa da gidansu A'isha ƴan doka sun zo sun tafi da Yawale a Mota. Bayan sun ƙarasa station wani ɗansanda ya dubi Yawale tare da nuna Faisal da hannu ya ce. "Wannan Malamin su wata yarinya ne A'isha dake gidanku, ya kawo ƙarar ka akan kana shirin yi mata Auren dole saboda mahaifinta ya rasu, haka ne ko ba haka ba ne?" Gumi ne ya shiga tsatstsafo wa Yawale, cikin rarraba idanu ya ce. "Ranka ya daɗe ba Auren dole ba ne, tana so yarinyar, ita ta kawo mijin ma da kanta." Wani mugun kallo Faisal ya wurga masa bai ce komai ba. "Mahaifiyar yarinyar da bakinta ta shaida wa Faisal ba sa son Auren, sanadin maganar auren har ciwo yarinyar ta kwanta, amma tunda ka ce haka mu je gidan mu zanta da su mu ji gaskiyar al'amari, wallahi idan suka tabbatar mana Auren dole ne sai ka yi kwanan cell, saboda wahalar da shari'a da ka yi." "A yi haƙuri ranka ya daɗe zan faɗi gaskiya, wallahi ba sa so, amma ka mini rai kar ka kulle ni." Yawale ya faɗa cikin tashin hankali. "Shikenan ka wanke kanka, yanzu za mu je mu taho da uwar yarinyar a yi yarjejeniya akan ba za ka ƙara shiga cikin rayuwarsu ba, sannan kuma maganar Auren nan an rushe ta." "Faɗa taka cikawa tawa, duk abin da ka ce haka za a yi ranka ya daɗe." Inna tana cikin haɗa kaya wata mace ta je ta tafi da su, cike da zullumi da fargaba suka je, amma da suka ji dalilin kiran sai farin ciki ya lulluɓe su. Bayan ƙara tattaunawa aka yi musu iyaka da Yawale, kowa ya yi signing aka ce su tafi. Yawale kamar zai zura da gudu saboda saurin da yake zubawa don ya yi ya bar gurin, sakamakon kaɗawar da cikinsa ya yi yana buƙatar zagayawa masai. Tsabar farinciki Inna har da ƙwalla, ji take tamkar an yaye mata dukkan damuwarta. A'isha kuwa tamkar ta taka rawa haka take ji don murna. "Na gode, na gode sosai ɗana da wannan taimakon naka, Allah ya biya ka ya fi mu yabawa." Murmushi ya yi idanunsa a kan A'isha ya ce. "Ba komai Mama, Allah ya kiyaye gaba." Kan A'isha a ƙasa ta ce. "Mun gode sosai Sir." Still yana murmushi ya ce. "Babu komai A'i." Ya rasa me ya sa tun ranar farko da ya fara ganin ta tausayin ta ya cika masa zuciya, ko don makauniya ce ita? Babur ya samu suka hau ya biya kuɗin aka mayar da su gida. Labarin fasa auren A'isha da tsoho ranar shi ya yi ta yawo a cikin garin, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Iya da sauran mutanen gidan kuwa baƙinciki da takaici kamar su kashe su, suka dinga cewa kamar yadda Inna ta lashe kurwar Umar haka ta lashe ta Faisal, shi ya sa ya tsaya musu har aka fasa Auren. Bangaren Tsoho da Yawale kuwa faɗa ne ya kaure, tsoho ya ce sai ya biya shi duk kuɗaɗen da ya dinga ba shi akan auren, Yawale kuma ya ce ya cinye ba zai biya ba, ai ba shi ya ce ba shi ba. Rigima har gaban wazirin Sarki, da ƙyar aka yiwa tufkar hanci da cewa Yawale ya biya rabin kuɗin da Tsoho ya ba shi, sun raba asara kenan. A ranar Iya ta zo ta ɗauke kayan lefen da aka kawo, wanda ya yi ta walagigi a tsakar gida, don tun ranar da aka kawo Inna ba ta ɗauke su daga gurin da aka ajiye su ba. Da yamma ganin Inna ba ta da niyyar ta ce su tafi ya sa cikin karaya A'isha ta ce masa. "Inna ba za mu tafin ba ne? Kar dare ya yi fa." "Tunda an fasa auren maganar barin mu garin nan ta rushe ita ma." "Amma Inna...." Ɗaga mata hannu ta yi tare da faɗin. "Ki bi abin da na ce kawai, tunda kika ga na ƙi barin garin nan akwai dalili, amma na san watarana dole mu bar shi, lokaci kawai nake jira." A'isha ba ta kuma magana ba, amma cikin ranta ba ta so hakan ba, don zaman garin gabaɗaya ya fice mata aka, duk da a nan ta buɗi ido ta gan ta. Washegari kamar daga sama sai ga Innar Ma'u ta sauka a garin da safe. Tsabar murna rasa inda Inna za ta saka ta, ta yi. Bayan sun gaisa Inna ta kawo mata ruwa da abinci ta ce. "A'isha haka kika ƙara girma? Yanzu ai kin fi Ma'u komai da komai." Cikin murmushi Inna ta ce. "Ni ma har mamakin girman da take nake yi, lokaci ɗaya kuma ta yi wannan girman, don ma ta yi ciwo kwana biyu ta yi rama, kafin ta yi ciwon ai ta fi haka." Innar Ma'u ta ce. "Masha Allahu, haka ake so. Ya fuska? Har yanzu idon dai bai buɗe ba?" A raunane Inna ta ce. "Muna nan muna ta addu'a dai." "To Allah ya amsa, ya ba ta lafiya." "Amin." A'isha ta ce "Inna me ya sa ba ki zo da Ma'u ba?" "Tana tahfiz ne, amma ita ma ta so mu zo tare, makarantar ce suna da tsauri ba sa son fashi, amma idan suka yi hutu ko ita kaɗai ce zan sako ta a Mota ta zo ta kwanar muku biyu." "Allah ya kai mu." Bayan sun taɓa hira Innar Ma'u ta tashi ta shiga cikin gidan don su gaggaisa da sauran matan gidan, saboda a ranar za ta koma Kano. Kafin ta tafi take sanar da Inna ta zo ta haɗa ta da wani mutum da suke turo masa da kaya yake sayarwa anan wani ƙauye Luran dake gaba da su, kayan za su dinga sauka a gurin Inna, shi kuma zai dinga zuwa yana ɗauka, idan ya sayar ya kawo mata kuɗin, a ciki ita ma sai ta dinga ɗaukar nata percentage ɗin. Da da wani mutumi suke haka, yanzu kuma ya rasu, shi ne Innar Ma'u ta cewa ƙaninta kawai su dinga ba wa Inna, ta san za ta riƙe musu amana, kuma hakan zai taimaka mata matuƙa da samun ɗan na kashewa. Ba ƙaramin farinciki Inna ta yi da jin wannan labarin ba, ta ƙara tabbatarwa idan aka ce mutum masoyinka ne mai son cigaban ka har abada hakan take, ta dinga yi wa Innar Ma'u godiya har da hawayen farinciki. Bayan kwana biyu da zuwan Innar Ma'u aka turo kayan. *One Year later* Alhamdulillah rayuwa ta sauyawa su Inna, don harkar turo kaya nan ba ƙaramin taimakon su ta yi ba, don a yanzu sun fi ƙarfin ci da sha da wasu buƙatun. Ƙalubale da ƙuncin rayuwa sun ci karanci a gare su, duk da ba su daina fuskantar tsangwama da tsana daga mutane ba, amma hakan ba ya damun su, sun toshe kunnuwansu tare da miƙa komai ga Ubangiji. A'isha ta ƙara girma da zama ƴanmata, kasancewar tana da garin jiki da diri Masha Allah. Har wannan lokacin ta kasa mantawa da Umar a cikin ranta, musamman idan ta kalli zobensa dake sanye a ɗan'yatsanta wanda ya ba ta. Yanzu tana J.S.S 3, suna daf da zana jarabawar junior WAEC. Har wannan lokacin Inna ba ta ba ta labarin asalinsu ba, ita ma ba ta kuma tambayar ta ba, amma kullum da son jin hakan take kwana take tashi. Yau da yamma Inna tana yanke mata farce ta ce. "Insha Allahu wani watan dai za mu je asibiti a duba idon nan naki." Cikin farinciki A'isha ta ce. "Allah ya kai mu." Inna ta ce. "Amin, don ma kuɗin ya ƙi taruwa ai da tuni mun je, kullum da rashin ganin nan naki nake kwana nake tashi, abun yana damuna sosai, sai dai babu yadda muka iya da ikon Allah, haka ya so da mu." A'isha ta ce. "Ni fa Inna har na saba da rashin ganin yanzu, gani nake ma kamar idon ba zai buɗe ba." Cikin tausayawa Inna ta ce. "Zai buɗe da yardar Allah, ai ba a cire rai da rahamar Ubangiji." "Allah ya sa Innata, ni ma ina so ya buɗe ko don na ƙara ganin ki a rayuwata, na ga ya kika koma yanzu." Murmushi Inna ta yi ta ce. "Yadda kika san ni haka nake, ba abun da na ƙara sai tsufa." Ita ma murmushin ta yi, cikin ranta tana addu'ar Allah ya amsa addu'arsu idonta ya buɗe. Cikin dare suna cikin bacci A'isha ta ji ana lalubar ta cikin wata irin siga da ta kasance baƙon al'amari a gare ta, a firgici ta farka jin ana ƙoƙarin danne ta tare da ƙwala kiran sunan Inna.........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣1️⃣* Kamar an saka iska an janye mutumin haka A'isha ta ji ya tashi daga jikinta cikin sauri, kuka ta fashe da shi tana ƙara kiran sunan Inna. "A'isha! A'isha! Lafiya? Me ya faru?" Inna ta tambaya a gigice bayan ta farka tana laluben fitila. Cikin rawar murya da na jiki A'isha ta ce. "Wa...wani ne ya shigo mana Inna." Haske ɗakin Inna ta shiga yi cikin matuƙar tashin hankali, tabbas cikin bacci ta ji kamar mutum ya taka ƙafarta, har tana shirin tashi ta yi wa A'isha faɗa, a zatonta ita ce ta tashi fitsari. Babu kowa a ɗakin, alamun wanda ya shigo ɗin ya yi nasarar tserewa. Ganin yadda A'isha take kuka da rawar jiki wanda ke nuna ba ƙaramar firgita ta yi ba, Inna ta tashi ta ƙarasa kan gadon ta rungume ta. Ƙanƙame Inna ta yi tare da sakin ajiyar zuciya. A ruɗe Inna take haska jikinta tare da faɗin. "Me aka yi miki? Ta yaya kika san wani ya shigo?" Cikin ƙunar rai ta ce. "Ji na yi ana tattaɓa ni tare da ƙoƙarin hawa kaina." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Inna ta ambata cikin bugawar zuci, wani irin juyawa ta ji kanta ya mata, lokaci ɗaya jiri na neman kwasar ta. Kamar wadda ƙwai ya fashewa a jikinta ta zauna a kan gadon tana jin kamar jini ya daina dawo a jikinta, har lokacin A'isha tana jikinta tana cigaba da kuka. Sunayen Allah da duk addu'ar da ta zo bakinta take karantawa, har ta fara dawowa cikin nutsuwar ta. Cikin sauke numfarfashi ta ce. "Wai me muka yi wa mutane ne? Me ya sa kullum cikin ƙoƙarin saka mu a ƙuncin rayuwa da son cutar da mu ake? Waye wannan ya zo yake ƙoƙarin ɓata miki rayuwa?" Sai ta fashe da kuka, wanda ya ƙara tsinka zuciyar A'isha, ta ƙanƙame ta sosai tare da tsananta kukanta. Ganin kuka ba shi ne mafita ba Inna ta rarrashi kanta ta miƙe ta fara haɗa musu kayansu da abubuwa masu amfani a gare su, ta kai maƙura kuma, abubuwan da ake musu a garin nan ya ishe ta, ko garin gwal ne yau za ta bar shi, ba don dare ba ne da ko awa ba za ta ƙara a cikinsa ba. Ana yin Sallar Asuba ta fito da komai nasu tsakar gida ta kulle ɗakin tana jiran gari ya fara haske su tafi. A'isha da take jin ta tamkar mai cuta ta kama hannun ta, cikin muryar da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. "Don Allah Inna mu koma gurin danginmu, kar mu kuma zuwa inda ba mu alaƙa da su a wulaƙanta mu." Hawaye mai zafi ne ya zubo daga idon Inna, cikin raunin murya mai tattare da ɗimbin damuwa ta ce. "Duk abin da kika ga ya koro ɓera daga rami ya faɗa wuta, to ya fi wutar zafi, ban taɓa tunanin rayuwa za ta zo mini a haka ba, ban taɓa tunanin zan bar rayuwa a cikin ƴan'uwana da dangina ba, amma wani dalili mai ƙarfi ya sa na aikata hakan." Zuciyar A'isha ta sauke, cike da kwaɗayin son jin labarin asalinsu ta ce. "Mene ne dalilin?" "Ke ce." "Ni kuma Inna? Me ya faru da ni? Ta tabbata gaskiya ne Baba Malam ba shi ne mahaifina ba?" Cikin kuka Inna ta ce. "Gaskiya ne, ba shi ba ne." Runtse ido A'isha ta yi cikin tsananin tashin hankali, duk da zuciyarta ta daɗe da ba ta tabbacin hakan, amma da Innan ta ƙara tabbatar mata sai damuwar ta akan hakan ta ninku, domin kodayaushe cikin fatan Inna ta ƙarya mata hakan take yi. Cikin magana da ƙyar ta ce. "Waye mahaifina to? Don Allah ki sanar mini kar zuciyata ta fashe." Janyo ta Inna ta yi ta rungume tare da faɗin. "Akwai lokacin da nake jira kafin na sanar miki da labarin komai, ki ƙara haƙuri. Ki kuma sani rayuwa cike take da tarin ƙalubale, duk halin ƙuncin da kake ciki wani yana cikin fiye da naka, a kullum ina faɗa miki ki karɓi rayuwa a duk yadda ta zo miki, duk abin da kika ga ya same ki rubutacce ne daga Ubangiji tun fil azil, ki kasance mai gode wa Allah a duk halin da kika tsinci kanki a ciki. Duk wannan abubuwan da suke faruwa za su wuce su zama tarihi watarana da yardar Allah, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, mu ci gaba da addu'a kawai." Ɗaga mata kai ta yi tare da ƙara damƙe hannunta a cikin nata, cikin sanyin murya ta ce. "Ke ce komai na rayuwata Inna, kin sha wahala sosai a kaina, Allah ya biya ki da gidan Aljannah, ina son ki fiye da kowa da komai a duniyar nan." Murmushi Inna ta yi mai haɗe da hawaye ta ce. "Babu wahalar da nake sha a kanki, ki daina faɗar haka." Jan majina Aisha ta yi ta ce. "Wataƙila da ke kaɗai kika zo garin nan babu ni ba za ana yi miki cin fuska kamar wanda ake yi miki yanzu ba." "Hmmmm" Kawai Inna ta ce tare da sauke numfashi. "Tashi mu tafi, na ga garin ya fara haske." "Wai ina za mu je?" "Kano gurin Innar Ma'u, idan muka sauka a tasha zan nemi waya na biya kuɗi a kira mini ita tunda muna da lambarta." Nunfasawa A'isha ta yi ta ce. "Amma Inna sai nake ganin kamar in muka je za mu ɗora musu nauyi ne." Inna ta ce. "Ba zaman dindindin za mu yi a gurinsu ba, gidan aiki zan nema ko wanke-wanke da shara da wankau ne na dinga yi ana biya na, ko a washegarin ranar da muka je na samu gidan aikin sai mu tafi." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke ta ce. "Allah ya sa a dace." Inna tana miƙewa ta ce. "Amin." Sai da suka daɗe a tasha kafin mota ta cika su ɗauki hanya, kallon ƙarshe Inna ta yi wa garin KUMURYA cikin wani irin yanayi, ranar da ta zo garin ce ta faɗo mata a rai. A'isha ta rasa me ya sa ta ji zuciyarta wani iri, ta daɗe tana fata da addu'ar Allah ya kawo ranar barin su garin, amma kuma ga ranar ta zo ta kasa yin farinciki. Sai ma faɗuwa da ta ji gabanta yana yi. Kwantar da kanta ta yi a jikin Inna tare da lumshe idonta. Cikin kulawa da ƙauna Inna ta ɗora hannunta a bayanta ta ƙara shigar da ita cikin jikinta. Ƙarfe goma da mintuna na safe suka sauka a garin Kano a tashar KANO LINE. Sai a lokacin Inna ta tuna ko sunan Unguwar su Innar Ma'u ba ta sani ba, direban da ya tuƙo su ta roƙa ya ba ta aron wayarsa ta kira ta. Bayan ya ba ta, ta saka lambar ta kira aka ce akashe. Ƙara kira ta yi still nan ma switch up. Jiki a sanyaye ta miƙa masa wayar tare da yi masa godiya ta kama hannun A'isha suka fara tafiya. "To yanzu Inna ina za mu je?" "Ban sani ba ni ma, amma mu fita daga cikin tashar nan, kamar yadda direban ya ce anjima mu samu wata wayar mu ƙara kira ko za a yi sa'a ta kunna wayar. Yanzu kasuwar da ake siyar da wayoyi kawai zan ce ɗan sahu ya kai mu, tunda da kuɗaɗe a jikina gara na siyi ƙaramar waya kawai, kar na rasa mai ba ni aron ta kiran." Cikin gamsuwa A'isha ta ce. "Ya fi kam." Wani mutumi Inna ta tambaya inda za su bi su samu motar zuwa kasuwar sayar da waya ya ce musu su tsallaka titi za su samu. Godiya ta masa tare da ƙara damƙe hannun A'isha ganin titin babba ne, sun hau kan titin kenan aka ba wa b'arin da suke hannu, kasancewar ba ta saba da ganin motoci na gudu akan titi haka ba duk sai ta ruɗe, ta rasa gaba za ta yi ko baya, sai ta tsaya cak ta kasa ɗaga ƙafafunta, ga horn ɗin da ake musu duk ya ƙara ruɗar da ita. Duk yadda ya so ya taka burki kafin ya ƙarasa inda suke amma abun ya ci tura, saboda tazarar dake tsakaninsu babu yawa. Jin sun tsaya A'isha ta buɗe baki za ta yi magana amma bugar ta da Motar ta yi tare da cilli da ita gefe ya hana ta maganar. Cikin matuƙar tashin hankali dattijon ya taka burki tare da buɗe Mota ya fito a ruɗe yana kiran "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Duk wani mai abun hawa dake gurin tsayawa ya yi tare da fitowa hankali a tashe, Inna dake kwance ba ta motsi saboda taka gefen kanta ta tayar Motar ta yi aka fara janyewa, ganin jinin dake zuba ya ƙara tayar da hankalin wanda ya buge su. Ba tare da ɓata lokaci ba aka zuba su a cikin Motar mutumin, wani ɗan karota ya shiga front seat, suka tafi zuwa asibiti police da aka kira su a lokacin na biye a bayan su. Wani babban Private Hospital dake kusa suka je, cikin gaggawa aka karɓi su A'isha aka yi emergency room da su. Ƙarshen tashin hankali mutumin nan ya shiga, don gani yake kamar gazawar shi ce accident ɗin da ya faru, ya kasa zaune ya ƙasa tsaye sai kaiwa da komowa yake cikin ransa yana kiran sunan Allah, tare da addu'ar Ubangiji ya tashi ƙafaɗun su. Bayan wani lokaci wani likita ya fito daga ɗakin da su Inna suke, da sauri mutumin ya nufe shi tare da faɗin. "Doctor yaya? Suna raye dai dukan su ko?" Daga yanayin fuskar Likitan ya san da matsala, hakan ya ƙara tsananta bugun zuciyarsa. Cikin son kwantar masa da hankali likitan ya ce. "Yarinyar babu abin da ya same ta, buguwa kawai kanta ya yi, mun yi mata duk abin da ya dace, yanzu ta samu bacci sakamakon allurar da muka mata." Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin. "Alhamdulillah, ita kuma matar fa?" Cikin damuwa Doctor ya ce. "Sai haƙuri Alhaji, ita Ubangiji ya karɓi abarsa.".........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _*Zeey Kumurya*_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣2️⃣* Tamkar saukar aradu a ka haka kalaman likitan suka daki zuciyarsa, yadda ya ƙura wa likitan ido za ka yi zaton suman tsaye ya yi, bakinsa dake rawa alamar yana son ya yi magana amma ta ƙi fita shi zai ba ka tabbacin bai suman ba. Ganin halin da yake ciki Likitan ya kama shi ya zaunar da shi a ɗaya daga cikin kujerun dake reception ɗin. "Take it easy Alhaji, komai muƙaddari ne daga Ubangiji." Likitan ya faɗa cikin rarrashi. Numfashi ya sauke cikin sanyin murya kamar wanda ya ci kuka ya ƙoshi ya ce. "Doctor, please ku ƙara duba ta, wataƙila dogon suma ta yi za ta farfaɗo." Girgiza kai likitan ya yi ya ce. "Ba a mutuwa a dawo ai, sai da muka tabbatar ta mutu sannan muka fito don mu sanar maka, ka yi haƙuri tare da yi mata addu'ar ganawa da Ubangijinta lafiya, Allah ya sa mu dace." Ya ƙarashe maganar tare da barin wajen. A raunane ya ce. "Allah ya ji ƙan ki, ya gafarta miki." Ya daɗe yana juya abun a cikin ransa, tamkar mafarki haka yake kallon al'amarin, bai taɓa tunanin cikin ƙaddarorin rayuwarsa akwai sanadin ran wani ba. Cikin mutuwar jiki tamkar wanda aka yiwa mugun duka ya lalubo tsadaddiyar wayarsa ya latsa tare da karawa a kunne. Kyakkyawar farar mace ce doguwa ƴar dumaduma zaune a wani rantsatstsen parlour tana kallon SUNNA TV, kyawawan idanunta sanye cikin farin glass ɗin da ya ƙara haska ƙawatuwar fuskarta. Wayarta dake gefenta ce ta fara vibration, a hankali ta kai hannunta da ya sha jan lalle ta ɗauki wayar. Ganin sunan mai gidanta na yawo a kan screen ɗin wayar ya sa mamaki bayyana a kan fuskarta, saboda sanin da ta yi idan ya fita ba ya amsa kira ko shi ya yi kiran a irin wannan lokacin, sai da wani babban dalilin. Numfashi ta sauke tare da ɗaga kiran ganin yana ƙoƙarin katsewa ta kara a kunne tare da yin sallama cikin kamilalliyar murya mai tattare da nutsuwa. "DR." Ya ambata cikin matuƙar raunin murya. Gabanta ne ya yanke ya faɗi, don daga jin muryarsa kamar ta wanda ya tashi daga bacci ko ya ci kuka ya ƙoshi ta san ba ƙalau. "Na'am Nurul ƙarbi, lafiya na ji muryar haka?" Ta tambaya a hanzarce. Numfashi ya sauke ya ce. "Babu lafiya Dr, ina asibiti yanzu haka. A ruɗe ta ce. "Subhanallahi, mai ya faru?" "Ki zo kawai, maganar ba za ta yiyu a waya ba." Ƙara shiga cikin rikici ta yi, cikin ƙarfin hali ta ce. "Okay gani nan zuwa yanzu, wanne asibitin ne?" Faɗa mata ya yi sannan ya katse kiran. Mintuna ƙalilan suka ƙarasa asibitin saboda gudun da ta ce driver ya yi. Cikin sassarfa ta ƙarasa emergency ward ɗin. Hango mai gidan nata zaune cikin ƙoshin lafiya ya sa ta sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi. Kasancewar kansa yana ƙasa ya sunkuya ya sa bai san da isowar ta ba, sai da ta zauna a kusa da shi sassanyan ƙamshinta ya bugi hancinsa sannan ya ankare ya ɗago kansa. Ganin yanayin mijin nata ya sa damuwar ta ƙaruwa. Hannunsa ta kama a raunane ta ce. "Me yake faruwa Abbansu? Ka saka ni a zullumi da faɗuwar gaba, duk da na gan ka lafiya ƙalau amma zuciyata ba ta daina bugawa ba." "Accident muka samu, na kaɗe wasu mata har ɗaya daga cikinsu ta rasu. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'jiun, garin yaya haka ta faru Abbansu?" Tsautsayi ne kawai Dr." Ya ba ta amsa cikin karaya. Dafe kanta ta yi cikin tsantsar tashin hankali, lokaci ɗaya ƙwalla ta ciko a cikin idanunta. A sanyaye ta ce. "Yanzu mene abin yi? Ina gawar da ɗayar marar lafiyar?" "Duk suna ciki, da jira nake yarinyar ta farfaɗo sai a tambaye ta daga inda suke a kai gawar can, na kira Khalifa da Alhaji Abubakar duk na sanar musu, na san yanzu haka suna hanya insha Allahu." Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Amma mu fara karɓar gawar mu kai can gida, idan muka jira sai yarinyar ta farfaɗo za a ɗauki time, tunda ba mu san tsawon lokacin da za ta ɗauka ba." "Haka za a yi." Cikin sauke numfashi mai tattare da damuwa ta ce. "Mu je mu ga yanayin jikin yarinyar." Bai ce komai ba ya miƙe ya nufi ɗakin da ya ga an shiga da A'isha. A kwance suka tarar da ita an saka mata drip a hannunta. Cikin tsananin tausayawa Dr ta ƙarasa ta shafa fuskarta tare da yi mata addu'ar samun lafiya. "Ko ya yarinyar nan za ta ji idan ta samu labarin mutuwar matar can? Wataƙila ma mahaifiyarta ce." Abba ya faɗa a raunane. Kallon shi Ummi ta yi ta ce. "Haƙuri za ta yi, haka Ubangiji ya ƙaddaro." Girgiza kai Abba ya yi ya ce. "Haka ne, Allah ya sa mu dace." "Amin, mu ƙarasa mu ga gawar matar mu yi wa likitocin maganar tafiya da ita." Gyaɗa kai Abba ya yi ya ce. "Ya kamata a samu mai zama tare da yarinyar, bai dace mu bar ta ita kaɗai ba, matsalar babu komai a tare da su wanda za mu samu information na inda suke ko numbern wani nasu, don ko waya ba a gani ba a tare da su." Numfashi Ummi ta sauke ta ce. "Zan zauna da ita, har zuwa lokacin da za ta samu lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Na gode sosai DR da wannan karamcin naki, Allah ya saka da Alkhairi." Tana miƙewa ta ce. "Babu godiya tsakani na da kai Mijina, ko da wanda ban sani ba ne zan iya yin jinyar shi idan ba shi da me yi masa, balle wannan da alhakin hakan yake kanmu, duk abin da ya shafe ka ai ya shafe mu." Cikin jin daɗi ya ce. "Ubangiji ya yi miki albarka, ya biya ki da gidan aljanna." Idanunta a kan A'isha ta amsa da "Amin." Cikin awa ɗaya aka ba su gawar Inna da kanta ke ta zubar da jini, har lokacin A'isha ba ta farka ba. Haɗaɗɗen Bedroom ne wanda ya tara komai na da ake buƙata ga kowane bedroom. Duk da girmansa bai hana munsharin lukutar matar dake bacci a kan luntsumemen gadon dake cikinsa cika shi ba. Da ƙarfi wata farar budurwa dake sanye da ƙananun kaya ta turo ƙofar ɗakin ta shigo ba tare da sallama ko neman izni ba. "Mumy! Mumy!" Shi ne abin take furtawa cikin yanayin razana, ganin ba ta ko motsa ba ta hau kan gadon tare da jijjiga ta tana cigaba da kiran sunanta. Hakan ya sa matar motsawa tare da Buɗe idonta a firgice. A tsawa ce ta ce. "Baby ba ki da hankali ne kike mini irin wannan tashin?" Shagwaɓe fuska ta yi ta ce. "Abu fa na zo na faɗa miki." "Mene ne?" Ta faɗa cikin hamma. "Abba ne na ga sun shigo da mutum shi da Ya Khalifa a lulluɓe, alamun dai gawa ce, kuma kamar accident aka yi sai zubar da jini tak..." "What?" Ta faɗa cikin ƙaraji tare da tashi zaune. "Ina kika ga sun yi?" "Part ɗin Abba suka shiga." A ruɗe ta hantsilo daga kan gadon bayan ta damƙi ɗankwalinta ta fice daga ɗakin cikin sauri tamkar magen da ta hangi ɓera. Yadda ta shiga parlour'n Abba a hargitse ya sa su ɗaga kai dukan su a tare suka kalle ta. Idanunta a kan Abba ta ce. "Alhaji! Waye ya rasu? Gawar waye wannan?" A sanyaye Abba ya ce. "Accident muka samu na kaɗe wasu mata za su tsallaka titi, a ciki ɗaya ta rasu." Ajiyar zuciya ta sauke tare da yatsina fuska ta ce. "Amma saboda Allah maimakon ka nemi ƴan'uwansu ku kai gawar can gurinsu shi ne za ka kawo ta gidan nan? Nan ɗin ma ba ɗakin mai gadi ko guest room ko BQ ba sai cikin part ɗinka a falonka? Saboda kawai ka faɗar mini da gaba ka sa hankalina ya tashi, tunda ka fi kowa sanin ɗana yana wata ƙasar kuma ya ce a cikin satin nan zai dawo, ai sai na yi tunanin ko shi ne ya taho suka yi accident a hanya. Gaskiya ba ka kyauta mini ba." Baki suka saki suna kallon ta cikin tsananin mamakin maganganunta. A tausasashe Abba ya ce. "Saratu gawa ce fa a gabanki amma kike wannan maganar mara kan gado, duk mai guntun imani a zuciyarsa idan ya ga gawa sai ya risina ko yaya ne." "Gawar ta Uba na ce?" Ta faɗa kanta tsaye. "Amma ai ta ɗan'uwanki musulmi ce ko?" Abba ya faɗa cikin ɓacin ran da yake ƙoƙarin dannewa. Ɓata fuska ta yi sosai ta ce. "Ka tofar da yawon bakinka don ni talaka ba ɗan'uwana ba ne, kar ƙara dangata ni da su." "Ce miki aka yi talakawa ne? Idan ma su ne su ba mutane ba ne?" "Sai an faɗa mini zan sani, tunda ka ce za su tsallaka titi da ƙafafunsu ai talakawa ne, tunda ba su da arziƙin hawa mota." Abba bai kuma magana ba saboda tsantsar ɓacin rai da takaicin halin matar tasa. Khalifa dake sauraren su ya miƙe ba tare da ya yi magana ba ya fice daga parlour'n, da wata muguwar harara ta raka shi sannan ta juya ita ma ta fice. Ƙwafa Abba ya yi cikin tsananin takaicin mugun halin Saratu. Ummi tana Sallar Azhar A'isha ta farka. Da farko tunaninta guduwa ya yi ta kasa tuna komai da abin da ya faru da su, sai bayan wasu mintuna komai ya dinga dawo mata tiryan-tiryan cikin ƙwanyarta, kamar wadda aka tsikara da allura ta tashi zaune ta fara laluben gefenta, jin hannun hagunta kamar wanda aka ɗaure mata shi da wani abun ya sa ta fara kiran sunan Inna a tsorace....✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _*Zeey Kumurya*_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣3️⃣* Da sausauri Ummi da ta yi sallama ta miƙe ta ƙarasa bakin gadon, cikin tausayawa ta ce. "Kin tashi? Sannu, bari na kira Doctor." Shiru A'isha ta yi gabanta na faɗuwa jin muryar wata ba ta Innarta ba." Cikin kuka ta ce. "Ina ne nan nake? Ina Innata?" Hannunta Ummi ta kama cikin rarrashi ta ce. "Ki kwantar da hankalin ki, asibiti ne nan, kun yi accident ne Mota ta buge ku." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Ina Inna?" Yadda ta yi maganar cikin nuna damuwa da zumuɗin son ganin Innar sai ya karyar da zuciyar Ummi, a raunane ta ce. "Tana bacci, an mata allurar bacci ne." "Ki kai ni na gan ta." "Ki bari na kira Doctor ya duba ki ya tabbatar babu sauran matsala sai mu je, kin ji?" Gyaɗa mata kai ta yi ba don zuciyarta ta so ba. Mayar da ita Ummi ta yi ta kwantar sannan ta fita. A hankali ta lumshe idonta tana jin yadda ƙamshin asibitin ke hautsina mata ciki, ga sarawa da kanta ke mata. Gurin da aka saka mata drip ta dinga tattaɓatawa har ta gane ƙarin ruwa ne. Ba jimawa Ummi suka dawo tare da doctor ya dudduba jikin nata tare da yi mata tambayoyi. Bayan ya fita ta juyar da kanta inda ta ji maganar Ummi, ta ce. "Zan yi fitsari." Ummi ta ce. "Ki yi haƙuri ruwan da aka saka miki ya ƙare a cire sai ki yi." Ba ta ce komai ba ta koma ta kwanta, zuciyarta cike da son ganin Inna da sanin halin da take ciki. After ten minutes aka cire mata ruwan Ummi ta raka ta toilet. "Ga tap nan sai ki kunna ki tari ruwan tsarki." Ummi ta faɗa tana ƙoƙarin fita. "Ai bana gani." A'isha ta faɗa cikin sanyin murya. Cak Ummi ta tsaya cikin faɗuwar gaba, da mamaki ta ce. "Kamar ya ba kya yi?" "Makauniya ce ni." "Subhanallahi!" Ummi ta faɗa cikin tausayawa da mamaki tare da kama hannunta, kallon idon A'isha take tana ƙara girmama ƙudura irin ta Ubangiji, saboda babu yadda za a yi ka ga fararen daradaran idanuwa kamar su ka ce ba a gani da su, ko suna tattare da wani ciwon. Jiki a sanyaye ta tara mata ruwa ta ba ta tare da tsayar da ita a inda za ta yi fitsarin, fita ta yi ta ce in ta gama ta sanar mata tana bakin ƙofa tana jiran ta. Sosai Ummi ta kaɗu da jin Aisha makauniya ce, don farko ta ɗauka ma dalilin accident ɗin ne, kallon ta take cike da tausayawa, ta kasa ɗauke idonta daga kanta, gefe guda kuma a cikin zuciyarta cike take da zullumin yadda za ta ji idan ta samu labarin rasuwar Inna. Numfashi ta sauke ta ce. "Ya sunanki?" A'isha da zuciyarta ke ta bugawa ta ce. "A'isha." "Ayya, ashe ma Mamana ce ke, Yaya kuke da Innar taki?" "Babata ce." Gyaɗa kai Ummi ta yi, za ta kuma magana wayarta ta fara ringing. Ɗauka ta yi ta duba, ganin Abba ne ya sa ta ɗagawa. Magana suka yi ta sakanni ya katse kiran. After 5 minutes wata nurse ta shigo ta ba su takardar sallama da magunguna. Ajiyar zuciya A'isha ta sauke ta ce. "Gurin Innar za mu je ko?" "Eh, tana can gidanmu an kai ta, yanzu za mu je ki gan ta." Ummi ta ba ta amsa cikin dakiya. Shiru ta yi cikin mamakin kai Innar gidansu ita kuma tana asibiti. Abba yana bakin Motarsa a tsaye suka ƙarasa, baya Ummi ta buɗe ta shigar da A'isha ta mayar ta rufe. A nan take sanar masa A'isha makauniya ce, wadda ta rasu kuma mahaifiyarta ce. Ba ƙaramin shock ya shiga da jin hakan ba, wani irin tausayin A'isha da ƙaunar ta ya ji ya cika masa zuciya, har suka ƙarasa gida babu wanda ya yi magana a cikin Motar. Ummi na riƙe da hannunta suka shiga har part ɗin Abba inda gawar Inna take. Zaunar da ita ta yi a kan kujera sannan ta zauna ta kamo hannunta ta ce. "A'isha ke musulma ce ko?" Cikin mamakin tambayar ta ce. "Eh." "Good" Ummi ta faɗa tare da duban Abba dake tsaye yana kallon su. Numfashi ya sauke bai ce komai ba. A'isha da ita dai burinta ta ji muryar Innarta ko ta ji ta a kusa da ita ta ce. "Su waye ku? Ina innar tawa?" Abba ya ce. "Ni ne na buge ku da Mota, Innarki kuma yanzu za ki ji Inda take." Abba ya ƙarashe maganar tare da zama a kujerar dake fuskantar wadda suke. So yake ya faɗa mata Inna ta rasu amma ya rasa ta inda zai fara, don sosai A'isha take ba shi tausayi. Ƙarfin hali ya yi ya fara da yi mata nasiha akan yarda da ƙaddara mai ratsa jiki, hakan ya sanyaya wa A'isha jiki sosai, ta nutsu tana sauraren shi. Ganin nasihar ta shiga jikinta yadda yake so sai ya miƙe ya kama hannunta da kansa ya kai ta gaban gawar Inna ya zaunar. A raunane cikin sigar rarrashi ya ce. "Na san kin san dukkan mai rai mamaci ne, duk wanda yake rayuwa a doron duniya akwai ranar da dole sai ya koma ga mahaliccinsa. Ina mai ba ki haƙurin sanar miki cewar a hatsarin da muka yi Ubangiji ya karɓi ran Mahaifiyarki." Wani abu A'isha ta ji ya daki zuciyarta, tamkar an saka adda an datsa ta gida biyu, numfashinta ya ɗauke na wucen gadi, ta daina fahimtar komai, lokaci ɗaya kanta ya yi wani irin juya mata, daga zaunen da take ta yi baya luuu za ta faɗi. Da sauri Ummi ta yi kanta ta riƙe ta tana ambatar "innalillahi... Abbansu dauko ruwan sanyi a shafa mata, kamar fa ta suma." "Subhanallahi." Abba ya faɗa tare da miƙewa ya ɗauko ruwan a fridge ya miƙa wa Ummi. Da rawar jiki ta karɓa ta shafa mata a fuska. Gwauron numfashi ta sauke tare da zabura tana faɗin. "Inna! Inna! Kina ina? Wani mummunan mafarki na yi yanzu, wai mun je Kano an kaɗe mu kin mutu, na san ba gaskiya ba ne, ba za ki mutu ki bar ni ba, don Allah Inna ki yi magana na ji muryarki." Kallon Abba Ummi ta yi idanunta cike da ƙwalla ta ce. "Ina ganin mu bari yarinyar nan ta dawo cikin hayyacinta sai mu sanar mata yadda hankalinta zai ɗauka." "Mutuwa ba a shirya mata Dr, a duk lokacin da za mu faɗa mata sabuwa take a gurin ta, kuma dole sai ta sani, don haka babu amfanin ɓoye-ɓoye." "Hakane." Ummi ta faɗa tana gyara wa A'isha zamanta, wadda ke zaune tamkar mutum mutumi." Cikin sanyin murya ta fara magana. "Ba mafarki kike ba Mamana, Allah ya yi wa mahaifiyarki rasuwa, ga gawar ta nan a gabanki." Ummi ta ƙarashe maganar tare da ɗora hannun A'isha a kan gawar Inna. Kuka ta fashe da shi don zuwa yanzu ta tabbatar ba mafarki take ba, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda Innarta ta rasu, Innalillahiwa'inna'ilaihirra'ji'un kawai take maimaitawa cikin sarƙewar harshe, numfashinta na fita a rarrabe tamkar zai bar gangar jikinta. Jikinta na kyarma ta buɗe bakinta cikin rawar murya ta ce. "Ya Ubangiji ka yi gaggawar farkar da ni daga wannan mummunan mafarkin da nake, na san ba gaskiya ba ne, na san Inna ba za ta taɓa mutuwa ta bar ni ba saboda ta san ba ni da kowa sai ita, don Allah su waye ku? Ku tashe ni daga wannan mummunan mafarkin da nake." Ta ƙarashe maganar tana laluben hannu Ummi. Rungume ta Ummi ta yi tana rarrashinta da ba ta baki, amma ba ta fahimta, babu abin da take ganewa. Da ƙyar ta iya amsa tambayar da Abba yake nanata mata ta daga ina suke? Ya buƙaci ta faɗa masa sunan gidansu dan a sanar da ahalinsu halin da ake ciki, sai ta ce masa ba su da kowa. Daga nan ba ta ƙara magana ba. Duk yadda Abba ya so ya samu wani information ɗin amma bai samu ba, har yamma ta yi ba akai Inna makwancinta ba. Alhaji Abubakar abokin Abba da ya dawo gidan a lokacin ya ce. "Ina ganin Alhaji Sa'id a tara jama'a kawai a yi wa matar nan Sallah akaita makwancinta, dare yana yi kuma mun san ba a son jinkirta kai mamaci." Numfashi Abba ya sauke ya ce. "Haka ne, amma da na fi so mu sanar da ƴan'uwanta su zo su ga gawar akai ta tare da su." "To Alhaji Sa'id ina muka san inda suke? Ita yarinyar da suke tare amsa ɗaya take ba mu ba su da kowa, mu kai ta kawai daga baya idan yarinyar ta dawo cikin nutsuwar ta sai mu je a sanar musu, amma idan ba haka ba gawar nan sai ta kwana." Cikin gamsuwa Abba ya ce. "Shikenan, bari na saka a sanar a masallaci, sai a nemo mai wankan gawa ta mata, Allah ya gafarta mata." "Amin." Kasancewar Abba babban mutum ne ana sanarwa a masallaci mutane suka fara taruwa a ƙofar gidan, maƙwabta mata kuma suka shiga cikin gida. A'isha dai tana zaune tamkar mutum-mutumi, ba ta fahimtar komai da yake faruwa, magana ma in an yi ba ta ji saboda komai nata ya tsaya cak, wani irin numfashi take fitarwa da sauri da sauri. Ummi na kusa ita tana tofa mata addu'a. An yi wa Inna wanka an haɗa ta an saka a cikin makara, jiki a sanyaye Ummi ta kamo A'isha ta tsugunnar a gaban gawar ta ce. "Ki yi mata addu'a, za a kai ta gidanta na gaskiya." Cikin fitar hayyaci A'isha ta ce. "Me zan ce? Ya ake addu'ar? Don Allah kar ku raba ni da Innata, ku bar mini ita a haka ina son ta, zan rayu da ita ko ta mutun." Sai kuma ta kama girgiza kai tana faɗin. "Innata ba ta mutu ba, don Allah Inna ki tashi ki ce musu ba ki mutu ba, na san ba za ki tafi ki bar ni, ni kaɗai ba." Ta ƙarashe maganar tare da ɗora kanta a kan gawar ta ƙanƙame ta. Da ƙyar aka ɗaga ta daga kan gawar, don tamkar mai iskokai haka ta koma, maganar wata tsohuwa da ta shigo tana cewa. "Shikenan fa rayuwar, yanzu ita ta tafi saura mu, Allah ya ji ƙan ta ya kyauta namu zuwan." Ya sa A'isha sumewa a jikin Ummi da ta riƙe ta. Safa da marwa kawai take yi a cikin makeken parlour'nta wanda ya ƙawatu da kayan alatu. Shigowar Baby ya sa ta dakatawa tana mayar da numfashi. Da mamaki Baby take bin ta da kallo. "Mommy lafiya kuwa na gan ki a hargitse?" "Ina fa lafiya Baby? Ba ki ga abin da mahaifinku ya yi ba ne?" "Me ya yi Mommy?" Taune leɓe ta yi alamun abun ya daki zuciyarta ba kaɗan ba ta ce. "Anan gidan fa aka yi wa matsiyaciyar matar da ya kaɗe sutura aka yi mata Sallah, maimakon ya kai ta can danginta su yi mata, ko kuma cewa aka yi dan ka kaɗe mutum ka yi masa sutura a gidanka?" Cikin rashin damuwa Baby ta ce. "To mene abin damuwa Mom? Daga an kai ta ba shikenan ba." A tsawace Mommy ta ce. "Akwai abin damuwa babba ma kuwa, a yi wa gawar talaka sutura a cikin gidan da nake ki ce mene abin damuwa? Talaka fa! Kin san yadda na tsani talauci da talakawa kuwa? Yadda nake jin tsanar talaka a cikin raina wallahi da ina da hali ƙasar da nake ciki a zaune ma ba zai zauna ba!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Yadda A'isha ta faɗi babu numfashi a jikinta ya taɗa hankalin su Ummi, Family Doctor ɗinsu ta kira ya zo ya ba ta taimakon gaggawa. Har bayan isha'i A'isha ba ta farka daga allurar baccin da aka mata ba, sai wajen ɗaya na dare ta farka da wani irin ciwon kai da nauyin ƙirji, har lokacin ba ta gama dawowa cikin hayyacinta ba.......✍️ _*Alhamdulillah, uzurin da ya riƙe ni yake hana ni posting akan lokaci na kammala shi, insha Allahu yanzu za kuna ji na kodayaushe, na gode.*_ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣4️⃣* Da ruwan ɗumi Ummi ta gogge mata jikinta tare da sauya mata kaya zuwa wata doguwar riga mara nauyi ta yarta MUNEEFAH dake boarding school. Ta haɗo mata tea mai kauri amma ta kasa sha, duk yadda Ummi ta yi da ita akan ta sha amma ta ƙi, sai haƙura ta yi ta ƙyale ta. Tun wannan farkawar ba ta kuma komawa bacci ba har garin Allah ya waye. Har yanzu zuciyarta ta kasa aminta Inna ta rasu, ta kasa yarda ta tafi ta bar duniya, ta kasa yarda ba za ta kuma ganin ta ba har abada a cikin zuciyarta. Damuwa da tashin hankali mara misaltuwa suka cika zuciyarta, so take ko ɗison hawaye ne ya zubo mata dan ta ji sauƙin abin da take ji a cikin zuciyarta, amma kukan ya ƙi zuwa. Sai a wannan lokacin ta gane ashe kuka ma Rahama ne. Ta yi addu'ar Ubangiji ya ɗauki ranta a wannan daren ita ma babu adadi, saboda ba ta san ina za ta saka kanta ba, ba ta san ta yaya za ta fara rayuwa ita kaɗai babu Inna ba, ba ta san ta yaya za ta kula da rayuwarta ba alhalin tana makauniya. Ina za ta ga danginta? Wa zai sada ta da su tunda babu Inna? Tunanikan da ta kwana tana yi kenan, hakan ya ƙara rurucewar ciwon jikinta, zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ta haɗe da zazzafan ciwon kai. Yadda ciwon ya galabaitar da ita ko ɗanyatsa ba ta iya motsawa. Hankalin Ummi ya ƙara tashi ganin yadda take rawar ɗari, numfashinta na fita da sauri da sauri. Addu'a suka haɗu suka ita da Abba suna tofa mata cikin ɗimauta da yanda jikin nata ya yi tsanani. Ana yin Sallar Asuba suka ɗauke ta zuwa asibiti. Suna zuwa aka karɓe ta tare da ba ta taimakon gaggawa. Ganin ta samu bacci Abba ya koma gida ya bar Ummi tare da ita. A main parlour ya ci karo da Khalifa. Cikin girmama ga gaishe shi, amsawa Abba ya yi cikin kulawa. "Ya jikin yarinyar?" "Da sauƙi Khalifa, na baro ta ma tana bacci." "Allah ya ƙara sauƙi, Yanzu Ya Maamah ta kira ni wai za ta biyo jirgin 8 ta zo, ta ce na maka jaje kafin ta ƙaraso, ta kira wayarka kai da Ummi ba ku ɗauka ba." Abba ya ce. "Allah ya sauke su lafiya sai sun ƙaraso." "Amin." Khalifa ya faɗa tare shigewa ɗakinsa. Abba yana shiga part ɗinsa ya tarar da Mommy Hakimce a kan kujera, yana ganin yadda fuskarta take murtuk ya san ba ƙalau ba, haɗe tasa ya yi shi ma don ya san neman fitina ne kawai ya kawo ta kamar kodayaushe. "Sannu Sa'id." Ta faɗa cikin rashin ladabi. Abba dake ƙoƙarin shiga ɗakinsa ya dakata ba tare da juyo ba. Ba ta damu ba ta ci gaba da magana cikin ɓacin rai. "Wai me kake nufi da barin yarinyar can a cikin gidan nan?" "Gidanki ko nawa?" Ya yi maganar a tsawace tare da juyowa. "Na ɗana ne." Ta ba shi amsa kai tsaye. "To idan kin isa ki saka ɗan naki ya zo ya fitar da ita daga gidan. Saratu ki kiyaye ni fa da wannan haukan banzan naki, kar ki kai ni bango na faɗa miki!" Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya mai haɗe da tsawa. Ba ta ce komai ba ganin yadda ya ɗauki zafi, ƙwafa ya yi ya shige ɗaki cikin ransa yana mamakin wacce irin zuciya ce da Saratu, ana girma ana hankali da tunanin lahira amma ita ƙara haukacewa take da son duniya. Da harara Mommy ta raka shi, tsanar Ummi na ƙara cika mata zuciya, don ta san duk wannan abun ita take kitsa shi. Ƙwafa ta yi ta miƙe tana ƙissima matakin da za ta ɗauka a cikin ranta. Ƙarfe takwas da mintuna Khalifa ya ɗauko Ya Maamah daga airport, direct asibitin ya wuce da ita. Da kwatancen da Abba ya yi masa suka ƙarasa har ɗakin da suke. Ummi tana waya suka shiga da sallama. Bayan ta gama ta amsa musu tare da faɗin. "Sannun ku da zuwa, I'm sorry Ina waya ne da can school Ina sanar musu ba zan samu zuwa ba yau, kin sauka lafiya Maamah?" "Lafiya ƙalau Ummi, ashe abin da ya faru kenan? Allah ya kiyaye gaba" Ummi ta ce. "Amin, abun ba daɗin ji, amma babu yadda za mu yi tunda Ubangiji ya ƙaddaro." Ya Maamah ta ce. "Haka ne, wannan ce yarinyar?" Ta ƙarasa maganar tare da tashi ta koma gaban gadon da A'isha take. "Ita ce, wadda ta rasun kuma Mahaifiyarta ce, ƙarin abun tausayi ashe makauniya ce." Da sauri Khalifa da ya ƙura wa A'isha ido ya ce. "Wace makauniyar?" Ummi ta ce. "Yarinyar." "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'ji'un, Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya." Ya Maamah ta faɗa cikin tausayawa. Ummi ta amsa da "Amin." Khalifa kam kasa magana ya yi saboda tsananin mamaki da tausayi. Idanun Ya Maamah a kan A'isha ta ce. "Ba a samu ƴan'uwansun ba har yanzu?" "Ba a samu ba, ita yarinyar da aka tambaye ta ma cewa ta dinga yi ba su da kowa, amma ta faɗi daga inda suke, wani gari ne a cikin Kanon nan Kumurya." Da mamaki Khalifa ya ce. "Ai kuwa ina jin sunan garin nan, amma na rasa a inda na san shi." Ummi ta ce. "Abbanku ya ce babu nisa, tun jiya ma ya so su je, amma yanayin jikin yarinyar ya sa ya ce a bari ta samu lafiya sai su tafi har ita." Jinjina kai Ya Maamah ta yi, ita kam ta kasa daina kallon A'isha, lokaci ɗaya tausayi da ƙaunar ta suka cika mata zuciya. Wajen ƙarfe tara Aunty Ruƙayya ƙanwar Ummi ta zo asibitin ita ƴaƴanta, a kallon farko da ta yi wa A'isha ta ji gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba, ba ta ɗauki hakan da wata manufar ba ta zauna aka cigaba da jajanta al'amarin. Sai bayan Azhar A'isha ta farka, Alhamdulillah ta farko cikin hayyacinta. Ummi ta haɗa mata tea ta rarrashe ta, ta sha kaɗan da ƙyar. Ba jimawa ta ƙara komawa bacci, saboda Allurar da aka mata ba ta gama sakar ta ba. Bayan kwana uku Jikin A'isha ya yi sauƙi sosai, ta daina koke-koken da take yi. Sai dai ba ta magana kwata-kwata, duk abin da aka ce mata sai dai ta gyaɗa kai. Kulawar da su Ummi suke ba ta ya sa ta fara samun nutsuwa a cikin ranta. Ga Abba kodayaushe idan ya zo asibitin cikin yi mata nasiha akan yarda da ƙaddara yake, hakan ya sa ta fara dangana da rashin Inna, amma da zarar ta tuno ba ta kowa a duniya a halin yanzu kuma ba ta san inda rayuwarta za ta kaya mata ba sai hankalinta ya yi mugun tashi. An yi wa Inna Addu'ar uku da safe a masallaci gami da abubuwan toye-toye na sadaka. Kafin Azhar aka sallami A'isha. Da yamma bayan ta yi wanka ta rama sallolin da suke kanta Ummi ta kama hannunta suka je parlour'n Abba. Suna zaune da shi da Khalifa suka shiga, tunda suka shigo Khalifa ya ƙura mata ido cikin wani irin yanayi. Yadda take tafiya da yin komai a sanyaye shi yake ƙara masa tausayin ta a cikin ransa. A kan carpet Ummi ta zaunar da ita. Cikin sanyin muryar da ta dashe ta ce. "Ina Yini." Abba ya amsa mata cikin kulawa sannan ya ɗora da faɗin. "Yaya jikin naki? Ina fata yanzu kin daina jin jirin da nauyin ƙirjin?" Ɗaga masa kai ta yi a sanyaye. "Ciwon kan fa?" "Shi ma ya daina sai kaɗan-ƙadan." Ta faɗa kamar mai koyon magana. Cikin jin daɗi Abba ya ce. "Masha Allahu, Allah ya ƙara lafiya." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Gyara zama Abba ya yi tare da fuskantar ta sosai ya ce. "Yau kwana uku da rasuwar mahaifiyarki, kuma har yanzu cikin danginku babu wanda ya sani, na so a ce mun je garin naku tun ranar da al'amarin ya faru don mu sanar musu, amma saboda rashin sanin Ina za mu tunkara idan mun je ya sa muka dakata har ki samu lafiya ki yi mana jagora. Kuma yanzu nake son mu tafi, ba na son a ƙara kwanaki ba mu je ba, saboda sanin yanzu duk wani makusancinku hankalisa a tashe yake da rashin sanin inda kuke." Hawaye masu ɗumi ne suka sauka a kan kuncinta, cikin rawar murya ta ce. "Ba mu da kowa, ko an mun je garin ban san wurin wanda zan kai ku ba." Shiru Abba ya yi yana nazari akan maganar ta, a hankali ya sauke numfashi ya ce. "Ina mahaifinki?" "Ya rasu." Ta ba shi amsa cikin kuka. Girgiza kai Ummi ta yi ta ce. "Yi haƙuri ki bar kukan haka ki yi mana yadda za mu gane, saboda babu yadda za a yi a ce kuna rayuwa ku biyu babu dangi, ina ƴan'uwan mahaifinki da na mahaifiyar taki?" Cikin sheshshek'a ta ce. "Duk ban san su ba, ban san inda suke ba, Innata kawai na sani." "Kuma ba ta faɗa miki inda suke?" Abba ya tambaye ta cikin mamaki. Gyaɗa masa kai ta yi. Ummi ta ce. "Ikon Allah, ku kaɗai kuke zaune a gidanku kenan?" Girgiza mata kai ta yi alamar a'a. Abba ya ce. "Allah ya kyauta, amma na kasa gane kan wannan al'amarin." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke tare da share hawayen fuskarta ta fara ba su labarin rayuwarsu da irin wahalar da suka sha, don ta sauƙaƙa musu tambayoyin da suke mata. Bayan ta gama ta ɗora da faɗin. "Don Allah kar ku mayar da ni gurinsu, wallahi kashe ni ne kawai ba za su yi ba saboda ba sa san mu, ku bar ni kawai na tafi wani gurin." Ta ƙarashe maganar cikin gunjin kuka. Cikin matuƙar tausayawa Ummi ta rungume ta tare da faɗin. "Ki kwantar da hankalinki Mamana, babu mai mayar da ke gurinsu kin ji?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara fashewa da kuka, kewar Inna da zafin mutuwar ta na ƙara cika mata zuciya. Numfashi mai zafi Khalifa ya fesar cikin takaicin jahilcin wasu mutanen, daga mutane sun zo garinku cin arziƙi don ba ku san su ba sai su zama abin muzantawa da ƙyara a gurinku? Saboda rashin ilimi. Abba da yake jin kamar ya zubar wa A'isha hawaye saboda tausayi ya ce. "Allah ya ji ƙan mahaifiyarki, ya inganta rayuwarki har ki zamo abar alfahari. Ki daina kukan nan haka kar ciwon ki ya dawo." Jinjina masa kai ta yi amma ta san ba za ta iya tsayar da hawayen dake fita daga idonta ba a yanzu. "A'isha!" Abba ya kira ta cikin taushin murya. Ɗagowa ta yi daga jikin Ummi ta amsa masa a raunane. "Na'am." "Kin tabbata labarin da kika ba mu gaskiya ne?" "Gaskiya ne Abba, idan ba ka yarda ba ka je garin ma ka tambaya za a faɗa maka." Gyaɗa kai ya yi cikin gamsuwa sannan ya dubi Khalifa ya ce. "Je ka kirawo mini Maamah da Baby da Saratu." Cikin ladabi ya amsa tare da miƙewa ya bar parlour'n........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣5️⃣* Mommy na zaune a parlour tana waya da ƙanwarta Khalifa ya shiga, ganin tana waya ya nemi guri ya zauna yana jiran ta gama. Hararar ƙasan ido ta wurga masa sannan ta ce. "Ina zuwa Kaltum zan kira ki." Ta ƙarashe maganar tare da zare wayar daga kunnenta ta katse kiran. "Abba ne ya ce ki same shi a parlour'nsa yanzu ke da Baby." Khalifa ya faɗa a taƙaice, bai jira amsar ta ba ya tashi ya fita. Da wani mugun kallo ta raka shi, bayan ya fita ta ja tsaki tare da duban ɗaya daga cikin masu aikinta dake duƙe a gefe cikin jiran umarni, ta ce. "Ke! miƙo mini takalmin nan." Jikinta har rawa yake gurin amsawa tare da cika umarnin da ta ba ta cikin sakanni ƙalilan. Miƙewa Mommy ta yi ta nufi ƙofa cikin takun ƙasaita, da sauri mai aikin ta wuce gabanta ta buɗe mata ƙofa ta fita. Ba tare da sallama ba ta shiga parlour'n Abba ta zauna tana bin kowa da kallon ƙasƙanci, musamman Ummi da take jin tamkar ta shaƙe ta saboda tsana. Ba ta taɓa ganin A'isha ba tun da ta zo gidan, yanzu ma ba ta ga fuskarta ba kasancewar ta sunkuyar da kanta ƙasa. Taɓe baki ta yi ta dubi Abba ta ce. "Ga ni Alhaji an ce kana kira na." "Na gan ki ai." Abba ya ba ta amsa da irin sigar da ta yi magana. "To ina jin ka." Girgiza kai kawai Abba ya yi ya ce. "Ina Baby?" "Ta je gidan Bahijja." Ta ba shi amsa cikin tarar numfashinsa. "Kuma shi ne har yanzu ba ta dawo ba ga Magriba ta kawo kai?" Ɓata fuska Mommy ta yi ta ce. "Mun yi waya ta ce mini ta taho." Bai bi ta kan maganar tata ba ya yi gyaran murya ya ce. "Masha Allah, mafi yawa daga ahalin gidan nan duk kun hallara, Safwan, Baby da Muneefah ne kawai babu." Ya numfasa idanunsa a kan A'isha ya ce. "Dalilin da ya sa na tara ku a nan shi ne don na sanar da ku wani abu mai mahimmanci da na zartar a cikin raina wanda duk ya shafe mu. Wannan Yarinya A'isha da tsautsayin accident ya haɗa mu za ta cigaba da zama a gidan har illa Masha Allah, a matsayin 'ya tamkar ƴaƴan cikina. Don haka ina gargaɗin ku akan kar na ji kar na gani wani a cikinku ya yi mata wani abu na muzanci ko wulaƙanci, idan hakan ta faru zan saɓar wa mutum fiye da tuanain shi ko waye." Mommy da take kallon shi tamkar idanunta za su faɗo ƙasa ta ce. "Alhaji ban fuskance ka ba, me kake nufi?" "Komai ma." Ya ba ta amsa fuskarsa babu alamun wasa. "Taɓɗijan!" Ta faɗa cikin tsantsar ɓacin rai da kololuwar takaici, lokaci ɗaya kuma ta saki wani murmushi, idanunta a kan Ummi ta ce. "Shikenan, Allah ya taya mu riƙo." Ta ƙarashe maganar tana miƙewa ta fice daga parlour'n. Maganganun Abba sun saka A'isha a wani irin yanayi da ta kasa tantance na baƙin ciki ne ko akasin haka. Yau ta ƙara yarda mutum ba ya sanin yadda rayuwarsa za ta kaya sai ya ga yadda Ubangiji ya yi da shi, ba ta taɓa tunanin za ta yi rayuwa a wani gurin da ba garin da ta buɗe ido ta gan ta a ciki ba, amma ƙaddarar dake cikin rayuwarta ta ƙara jeho ta nan gidan, ba ta san kuma me zai faru a zamanta a cikinsa ba. Numfashi ta sauke a sanyaye ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ƙara arziƙi, ya sa aljanna ce makoma." Cikin kulawa Abba ya ce. "Amin Manana, Allah ya yi miki albarka ya ba ki lafiya." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Duban Maamah ya yi ya ce. "Kama hannunta ku koma part ɗin Mamanku, ta kwanta ta ƙara hutawa, na ga har yanzu jikin nata da saura." "To Abba." Maamah ta faɗa tare da miƙewa. Khalifa ma tashi ya yi ya fita. Parlour'n ya rage daga Ummi sai Abba. Ummi ta gyara zama tare da fuskantar Abba ta ce. "Al'amarin yarinyar nan ba ƙaramin ɗaure mini kai ya yi ba Abbansu, na kasa imagine yadda mutane biyu kacal za su yi rayuwa ba tare da wani jininsu ba, in ba dai a gidan marayu suka tashi ba." Abba ya ce. "Babu abin mamaki DR, hakan ya sha faruwa, kuma a yadda yarinyar ta ba mu labari ai kin ji mahaifiyar tata ta ce mata akwai dalilin da ya sa ta yi nesa da danginta, sanar mata ne Allah bai nufa ta yi ba har ta rasu." Ummi ta ce. "Haka ne Allah ya kyauta. Bari na je na shirya maka abin shan ruwa kar lokaci ya ƙure." Abba ya ce. "Toh shikenan, da daddare ma yi maganar diyyar matar, ki ba ni shawarar yadda kike ganin za a yi." "Allah ya kai mu." Ummi ta faɗa tare da miƙewa ta fice. Tunda Mommy ta koma part ɗinta ta kasa tsaye ta kasa zaune, ba ta son talaka da duk wani abu da ya shafe shi, ba ta san alaƙa da shi. Gani take tamkar talaucin zai goga mata. Ƴan aiki ma abin da ya sa take yin su don ta nuna isar ta ne da nuna ta kai matsayin yin su, amma ban da haka ba da ko gatekeeper ba za ta yi ba a rayuwarta. A haka Baby ta dawo ta same ta, ganin yanayin da take ciki sai ta ji babu daɗi a cikin ranta, da damuwa ta ce. "Mommy me ya faru? Ni fa ba na son na gan ki cikin ɓacin rai." "Mahaifinki kuma burinsa kenan ya gan ni a cikin damuwa kodayaushe, duk abin da zai yi babu ruwansa da ɓacin raina a kai, in dai ƴar gold ɗinsa za ta yi farinciki shikenan, tunda Alhaji ya auri kinibabbiyar matar can na yi ban kwana da kwanciyar hankali da farinciki a gidan nan." "Yanzu me ya faru?" "Yarinyar da ya kaɗe ita ce wai za ta cigaba da rayuwa a gidan nan, don tsabar wani hali da son cusa mini baƙin ciki ba ma a matsayin ƴar aiki za ta zauna ba, wai a ƴa kamar ku. Kuma na san duk wannan abun tsinanniyar can ce ta kitsa masa shi." Ɓata fuska Baby ta yi ta ce. "Gaskiya Abba ya fiya janyo mana abin jin kunya da ƙasƙanci, yarinyar fa ƴar ƙauye ce, ranar suna hirar da Abba Abubukar na ji suna faɗa." Cikin ninkin ɓacin rai Mommy ta ce. "Wallahi matuƙar ina numfashi yarinyar nan ba za ta yi rayuwa a cikin gidan nan ba, gidan ɗana ne ai ba na Uban wani ba, mu zuba mu gani." "Ya kamata dai ki ɗau mataki kam, kawai a wani kawo mana ƴar ƙauye gida mu rayu da ita, impossible wallahi, ko masu aikin gidan ba da daga ƙauye suke ba. Abba ma dai ya fiya kwashe-kwashe, daga accident ya haɗa ku sai ka ce za ka riƙe ta ban da ɗorawa kai." Ba tare da Mommy ta damu da kalaman da Baby take danganta Abba da su na rashin ɗa'a ba ta ce. "Ki bar ni da shi, wannan karon daidai nake da su dukansu." Da daddare A'isha tana shan fruits ɗin da Ummi ta matsa mata ta sha a bedroom, Khalifa ya shigo ɗakin. Ba tare da ɗago kanta ba ta amsa masa sallamar da ya yi. Walking slowly ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta tare da saka hannunsa yana karkaɗawa a daf da idonta, gani yake kamar ta faɗa ne kawai amma tana gani, har yanzu mamakin jin wannan Black beauty ɗin makauniya ce bai bar shi ba. Kamar ta san me yake mata ta tsaya cak da shan fruits ɗin, yadda ƙamshinsa ya cika mata hanci ya sa ta gane yana kusa da ita. Murmushi ya yi ganin yadda ta yi da fuska ya ɗan ja baya tare da ajiye mata ledar hannunsa. "Tsohuwa ga Ice cream nan na kawo miki, Allah ya sa kin iya sha?" Ya yi maganar cikin barkwanci. Yanayin yadda ya yi maganar sai ya tuno mata da Umar har ta ji gabanta ya faɗi, ko dan shi ma wani lokacin yana ce mata tsohuwa ne idan ya so tsokanar ta? Ko kuma don yana kawo mata ice cream ne? Zoben da ya ba ta, ta murza a hankali tare da yin ɗan murmushi ta ce. "Na gode." Murmushinta ya masa kyau sosai, har ya ji dama ta ƙara yi. Lumshe idonsa ya yi ya buɗe ya ce. "Don't mind beauty, Allah ya sa kar ya kashe miki wannan kyawawan haƙoran." Murmushi ta ƙara yi a karo na biyu ba ta ce komai ba, wanda tun kafin rayuwarsa Inna rabon da ta yi, sai yau da Khalifa ya sa ta yi ba tare da shirya ba. Don har yanzu zafi da ciwon mutuwar Inna yana nan danƙare a cikin zuciyarta. Khalifa zai kuma magana Ummi ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo. Tsare shi ta yi da ido ta ce. "What are you doing here?" "Abu na kawo mata." Ya yi maganar cikin sauri yana shafa kai. "To an gode." Ummi ta faɗa tare da nuna masa ƙofa alamun ya tashi ya fita. Mayar da dubanta ta yi kan A'isha ta ce. "NANA, taso mu je ku gaisa da Gwaggo Maman Abba." Da yake ɗazu ta ce da Nana za suna kiran ta sai ta gane da ita Ummi take, hakan ya sa ta yunƙura ta miƙe cikin rashin ƙwarin jiki, Ummi ta kama hannunta suka fita. Zuwan Mommy parlour'n ba jimawa su ma suka shiga, tunda A'isha ta zo gidan ba ta taɓa ganin fuskarta ba, saboda duk kwanakin da suka yi a asibiti ba ta je ta duba ta ba, ɗazu kuma a parlour'n Abba ba ta ga fuskarta ta ba. Ummi na ƙoƙarin zaunar da A'isha a kan carpet Mommy ta kalle ta, wata mummunar faɗuwar gaba da razani ne suka yi mata dirar mikiya a lokaci guda, sanadiyyar kallon farko da ta yi wa fuskar A'isha a rayuwarta.........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣6️⃣* Duk yadda ta so ta ɓoye razanin da zuciyarta ta shiga hakan bai yiyu ba, sai da asirin hakan ya fallasu a kan fuskarta. Gwaggo dake amsa gaisuwarta ganin yanayinta ta ce. "Saratu!" Ɗan zabura Mommy ta yi tare da sauke numfashi, cikin ƙoƙarin ɓoye halin da take ciki ta ce. "Na'am Gwaggo." "Ina hankalinki ya tafi Ina miki magana kin yi shiru?" Yatsina fuska ta yi ta ce. "Na tafi wani ɗan tunani ne, zan yi abu yanzu na manta ban yi ba, bari na je na dawo." Taɓe baki Gwaggo ta yi ta ce. "Ai ke ba kya rabo da uzuri kodayaushe, sai ka ce mara gaskiya daga kin zauna burum kin tashi kamar wadda aka tsikara." Kicin-kicin Mommy ta yi da fuska ba ta ce komai ba ta tashi ta fita. Girgiza kai Abba ya yi ya miƙe ya nufi dinning area don cin abinci. Gwaggo na duban A'isha ta ce. "Wannan ce yarinyar? Allah Sarki, Allah ya ji ƙan mahaifiyarki ya ba ki haƙurin rashi, taso ki zauna nan kusa da ni kin ji." Ya Maamah ce ta kama hannunta ta zaunar da ita a kusa da Gwaggo, kanta a ƙasa ta ce. "Ina yini?" Gwaggo ta amsa cikin kulawa tana ƙare mata kallo. "Tubarakallah ga ta kyakkyawa Masha Allah, Allah albarkaci rayuwarki ƴar nan, Addata mai sunan Yayata." Ummi tana murmushi ta ce. "Mai sunanta ce kam, ga shi da alamu za ta yi haƙurin masu sunan." Ya Maamah ta ce. "Taɓ, ba su da wani haƙuri sunan tsofaffin, A'isha ta mana yawa gaskiya, duk an baibaye mu da su, kowa A'isha A'isha." Gwaggo ta ce. "Ja'ira sunanki ne dai." Sun daɗe suna hira cikin raha da barkwanci, sai da A'isha ta fara gyangyaɗi sannan Gwaggo ta ce akai ta, ta kwanta. Yadda Mommy ta ga rana haka ta ga dare, ta rasa me ya sa ganin A'isha ya firgita ta, ta ji wata muguwar tsanar ta lokaci ɗaya ta cika mata zuciya. Hakan ya sa ta ƙara ƙaimi akan ƙudirinta na korar A'isha daga gidan. Washegari da safe bayan Gwaggo ta gama karyawa ta ce tafiya za ta yi. Abba ya ce. "Haba Gwaggo daga zuwa kamar wadda ake kora? Kin zo da daddare kuma yau da safe ki ce za ki koma?" Gwaggo ta ce. "Ƙyale ni na tafi, dama ba zama na zo yi ba, jaje na zo maka, Allah ya kiyaye ya tsare gaba, ya raba mu da sharrin ƙarfe. Ina ni ina zama cikin surukai, gara na yi tafiyata." Ummi ta ce. "Ki bari ko kwana ɗaya ki ƙara mana don Allah." Gwaggo ta ce, "Toh shikenan tunda kun matsa, kira mini mai sunan Adda mu yi hira, ta yi ta zama a ɗaki tana tunani ita kaɗai babu daɗi, goben idan Allah ya kai mu sai na tafi." Abba ya ce. "Allah ya kai mu, Dr mu je na sauke ki a school ɗin ko?" Ummi ta miƙe tare da faɗin. "Toh, Gwaggo bari mu je, sai na dawo, zan saka Maamah ta kawo miki Nanan." "To shikenan, sai kun dawo, Allah ya kiyaye ya tsare." Suka amsa da Amin tare da ficewa. Har Rana A'isha suna tare da Gwaggo tana yi mata nasiha, ta ji daɗin kasancewa da Gwaggo sosai, don tamkar wadda ta daɗe da sanin ta haka ta nuna mata, babu ƙyara ko tsangwama sai zallar ƙauna. A'isha tana kan dardumar da ta yi Sallar Azhar bayan ta idar, Gwaggo ta tura mata abinci gabanta tana faɗin. "Ƙara ci sai ki sha magani ki kwanta." A hankali ta ce. "Na ƙoshi fa." Haɓa Gwaggo ta riƙe ta ce. "Abincin da kika ci nawa yake ƴar nan? Ki ƙara." Ba ta kuma magana ta lalubi plate ɗin ta fara cin abincin kamar ba ta so. Gwaggo ta ce. "Ko ke fa, abinci ai shi ne mutum, ke kuma daga gani za ki gaddamar cin shi, sai an dinga tsayawa a kanki, zan sanar da Zaran ta dinga tsaye a kanki idan za ki abinci." Ita dai A'isha ba ta ce komai ba ta cigaba da cin abincinta, tunda ta zo Gwaggo take ba ta abubuwan ciye-ciye, da ya Maamah ta kawo musu abinci ta zuba mata ta ci, yanzu ma ta ƙara mata. Kaɗan ta ci ta ture ta ce ta ƙoshi. Gwaggo ta ɓallo magungunanta ta ba ta. Tana gama sha ta kwanta bacci ya ɗauke ta. Gyara gurin da suka ci abincin Gwaggo ta yi ta kwanta ita ma dan ta rintsa. Shigowar Mommy ya sa ta tashi zaune tare da amsa sallamar da ta yi. "Sannu da hutawa Gwaggo." Ta faɗa lokacin da take zama a kan carpet. Gwaggo ta ce. "Yawwa, ki ƙaraso bakin gado ki zauna mana Hajiyar birni, ai ba girmanki ba ne zaman ƙasa." Duk da ta san Magana Gwaggo ta faɗa mata sai ta yi murmurshi, cikin son ganin plan ɗinta na farko da ta tsara ya yiyu ta ce. "Kina sama ai ba na zauna ba Gwaggo, nan ɗin ma ya yi, Ina yini? Ba mu Gaisa ba ma." Gwaggo ta ce. "Lafiya ƙalau." Gyara zama Mommy ta yi ta ce. "Gwaggo wata magana na zo miki da ita, wadda nake fatan ki fahimce ni da idon basira, shi Alhaji na yi masa bayani ya ƙi ganewa." Gwaggo ta ce. "Ina jin ki." Mommy ta ce. "Yawwa, akan yarinyar nan ne dama." "Wacce yarinya?" Zomo baki ta yi ta ce. "Wannan ta kwancen, ban san sunanta ba ne." Gwaggo ba ta kuma magana ba sai ido da ta zuba mata alamun tana sauraren ta. Hakan ya sa ta cigaba da magana da faɗin. "Akan riƙon ta da Alhaji ya ce zai yi ne, Gwaggo zamani fa ya canza, yanzu ba da ba ne mutane babu gaskiya a zuƙatansu, kar mu je mu ɗauko abin da zai zame mana alaƙaƙai a rayuwa, TSINTACCIYAR MAGE fa BA TA MAGE, ina tsoron kar mu je garin neman gira a rasa ido, saboda ɗan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido." Gwaggo ta ce. "Ni duk wannan karin maganar da kika jero ban gane me kike nufi ba da inda kika dosa." Karyar da murya Mommy ta yi cikin ladabi ta ce. "Abin da nake nufi ki saka Alhaji ya mayar da Yarinyar nan inda ta fito su cigaba da riƙe ta. Idan ya so in ma ɗawainiyar ta zai ɗauka sai ya dinga kai kuɗi ana kula da ita, amma nan gidan ɗin ta bar shi kawai." Gwaggo ta ce "Mene hujjarki na son a mayar da ita?" Ƙara karyar da murya Mommy ta yi ta ce. "To Gwaggo mene amfanin riƙon nata? Yarinya ba ka san daga inda take ba kawai ka ce za ka riƙe ta, ba ka san mutum ce, aljana ce, mayya ce, wacce iri ce sai Allah." Shiru Gwaggo ta yi tana kallon Mommy kamar me nazari, a ranta kuwa mamakin halin Mommy da ba za ta taɓa canzawa take, ta yi zaton ta yi hankali ashe har yanzu ana jika. Numfashi ta sauke ta ce. "Maganar ki abar dubawa ce gaske, amma shi Sa'id ɗin kin masa duk wannan bayanin?" Cikin jin daɗin ganin Gwaggon ta karɓi maganarta ta ce. "Na masa, na nusar da shi iya yina amma ya toshe kunnuwansa ya ƙi saurare na, saboda ba maganar shafaffiya da mai ba ce, saboda duk abin da ta ce masa ba ya musu yake yi." "A'a, kar kuma ki ce haka, ke ma kin san Sa'id tsayayyen mutum ne da ƙafafunsa, ba irin mutanen da ake juya su ba ne, duk abin da kika ga ya yi shi ya saka kansa." "Uhm Gwaggo kenan, don ba a gidan kike ba ne shi ya sa, amma ƙiri-ƙiri Alhaji yake nuna mana banbanci, yau fa kina gani girkina ne amma shi ya kai ta gurin aiki, ga ƴaƴanta ga driver duk ba za su kai ta ba sai shi? Kuma ita ma ta iya tuƙin nan, idan mota ce ga su nan burjik a gidan sai ta zaɓi wadda za ta hau." Gwaggo ta ce. "To shi ne me don ya kai ta gurin aiki ranar girkinki? Ke sau nawa yake fita da ke ranar girkinta?" Ɓata fuska Mommy ta yi ta ce. "Shikenan Gwaggo a bar maganar, mu dawo kan wadda muke yi, don Allah ki yi masa magana ya mayar da yarinyar, ke kaɗai ce za ki faɗa masa ya bi." Taɓe baki Gwaggo ta yi ta ce. "Idan ya ƙi ba sai a bar shi ba tunda gidansa ne kuma shi ya ga zai iya." "Gidansa kuma?" Mommy ta tambaya kamar Gwaggon ta yi ƙarya. Kama haɓa Gwaggo ta yi tana girgiza kai ta ce. "Eh gidansa na ce, ko ba nasa ba ne? Daga an yi magana ki dinga gidan ɗanki gidan ɗanki. Tunda ya ɗauka ya ba shi ba shikenan ba? Kuma ban da rashin kunya don SAFWAN ya ba wa mahaifinsa gida sai ya zama abin magana? Kafin ya girma ya samu arziƙin a gidan wa ya rayu? Wa ya biya masa kuɗin da ya yi karatu har wata ƙasar ya samu aikin da ya yi kuɗin? Duk ba mahaifin nasa ba ne? Kuma kar ki manta da ƙyar Sa'id ya yarda ya dawo gidan nan da zama, sai da na saka baki na ce ba a yi wa yara haka idan sun yi gwaninta, hakan yana kashe musu gwiwa, sannan fa ya amince. A yanzu Safwan ya ce ya bar masa gidansa yana da gidaje ba ma ɗaya ba da zai zauna. Amma kin bi kin ishi mutane da gida na ɗanki ne, kullum cikin yi wa kishiya gori kina cewa albarkacinki take ci tunda tana rayuwa a gidan ɗanki, daga an yi magana ki dinga ɗaga hanci ke a dole ga uwar attajiri. Ban da shirme ma irin naki ai wannan abin alfahari ne a gare ki ɗanki yana kyautata wa mahaifinsa, amma kin mayar da hakan abin gori da izgili." "Ni fa ban ce komai ba Gwaggo." "Za ma ki ce ne, ai ba yau na fara sanin halinki ba." Gwaggo ta faɗa a harzuƙe. Cike da haushin maganganun Gwaggo Mommy ta tashi ta fice daga ɗakin fuuu. Gwaggo ta raka ta da harara tana faɗin. "Ka ga mace har mace, wuya da kunne da hannu sun sha zinare kamar mai hankali, amma tunanin ta na marasa lissafi ne." Ta ja tsaki tare da faɗin. "Allah ya shirya." A fusace Mommy ta ƙarasa part ɗinta, ɗaya daga cikin masu aikinta tana mopping kawai ta ji ta ɗauke ta da mari. Dafe kuncinta ta yi cikin gigita tare da tsugunnawa ƙasa ta shiga ba ta haƙuri, duk da ba ta san lefin da ta yi ba. "Don matsiyacin Ubanki Uwar me kika tsaya yi har yanzu ba ki gama mopping ɗin ba? Me ya sa ku matsiyata komai za ku yi sai kun nuna ƙaranta da tsiya?" Jikin yarinyar na rawa tana hawaye ta ce. "Ki yi haƙuri don Allah Hajiy....." "Dalla rufe mini ruɓaɓɓen bakin nan kafin na fasa shi." Mommy ta katse ta cikin tsawa tare da hamɓarin ta. Saurin ja baya ta yi tana haɗe hannayenta alamun roƙo. Ƙwafa Mommy ta yi tare da faɗin. "Ban da ƙaddara me zai haɗa ka zama guri ɗaya da talaka? Shi da duk inda yake naso yake kamar funfuna." Ta ƙarashe maganar tare da hayewa upstairs. Ajiyar zuciya mai aikin ta sauke ta cigaba da abin da take cikin sauri, jikinta har rawa yake saboda tsoron kar ta sakko ta tarar da ita ta ƙara yi mata wata sabuwar tijarar. Mommy na tsaye a bedroom ɗinta da waya kare kunnanta, after some seconds ta ce. "Kina ji na Kaltum, na je gurin tsohuwar can na faɗa mata kamar yadda kika ce, amma matar nan ta ƙi amincewa, sai ma wasu maganganu da ta bi ni da su, kin san shegiyar tsohuwa ce mai kankanbar tsiya. Da farko fa kamar ta amince, amma ina taɓo wadda suka fi k'auna ta canza akala" Daga ɗaya ɓangaren Kaltum ta ce. "Duk ki ƙyale ƴan abu ta kazar uba Saratu, ki ba ni 1 hour gani nan zuwa gidan, wallahi shirin da zan zo da shi sai yarinyar nan ta bar gidan, kin san halina idan na ce zan yi abu sai na yi." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke, sanin hatsabibanci da ƙwarewa a shaiɗananci na ƙanwar tata ya sa ta yi amanna da zancenta, ta saka a ranta kawai matsalarta ta kau, indai barin A'isha daga gidan ne tamkar an yi an gama. Murmushi ta saki tare da faɗin. "Sai kin zo ɗin.".........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣7️⃣* Har Ummi ta dawo Gwaggo ba ta daina mitar halin Mommy ba, bayan ta zauna ta dubi Gwaggo cikin mamaki tana ajiye jakarta ta ce. "Lafiya Gwaggo? Ke da wa?" "NI da Saratu mana, wa zai taɓa ni a gidan nan ban da ita da ba ta girma." Ummi ta sauke numfashi ba ta ce komai ba. Gwaggo ta ce. "Wai zuwa ta yi tana faɗa mini na cewa Alhaji Sa'id ya mayar da mai sunan Adda ƙauyen da take, wai kar a je watarana mun yi mata rana ta yi mana dare. Ko a kanta yarintar take oho?" Ya Maamah da ta shigo ɗakin ta tsinci zancen ta ce. "Mommy ko?" Gwaggo ta ce. "Ita fa." Girgiza kai Ya Maamah ta yi tana zama a kusa da Gwaggo ta ce. "Ban san me ya sa ba ta son wani ya raɓi gidan nan da sunan cin arziƙi ba, ita dai kullum kar talaka ya raɓe ta ya goga mata tsiya, zancen ta kenan." Tsaki Gwaggo ta yi ta ce. "Tsiya ta wuce tata? Ita ba ta duba abin faɗar da suke da shi sai na wani, tunda ubansu ya gudu ya bar su suna ƙanana wa ya ƙara jin labarin inda yake? Ya tafi ya bar uwarsu da wahala sai abincin siyarwa ta kama a bakin tasha don ta rufa musu asiri, su ma suka tashi a haka yan tuwo-tuwo, har daf da Sa'id zai aure ta ba daina fita tasha siyar da abinci ba. Amma yanzu saboda ɗanta ya yi arziƙi duk ta bi ta ishi mutane da jaraba." Ummi ta ce. "Ki yi haƙuri Gwaggo, ki bar maganar nan, kuma don Allah kar sanarwa da Abbansu ta zo miki da wannan batun, kin san shi da saurin hawa, yanzu sai ya je su yi ta rigima." Gwaggo ta ce. "Ni ban san irinki ba Zara'u, matar nan ba ta ƙaunar ki amma ke kodayaushe ba kya son ki ga ta ɓaci a idon mijinku." Ummi ta ce. "Ita ma Allah ya ganar da ita, ta gane abin da take yi ba daidai ba ne." Ya Maamah ta ce. "Hmm." Kawai. Kaltum ba ta samu zuwa ba, ta taho a hanya ta samu accident, sai asibiti ta wuce. Hankali a tashe Mommy ta tafi asibitin da suke bayan ta kira ta sanar mata. Ta je ta tarar ba ta yi wani rauni sosai ba, a ranar aka yi mata treatment aka sallame ta. Da daddare bayan Abba ya gama buɗa baki ya saka Ummi ta kawo masa A'isha part ɗinsa, bayan ta gaishe shi ya amsa cikin kulawa sannan ya gyara zama ya ce. "Mamana a ina kika tsaya da karatu ne?" A hankali ta ce. "J.s. 3." Gyaɗa kai ya yi ya ce. "A haka ba kya ganin kike zuwa makarantar ko?" "Eh." Ta ba shi amsa cikin ladabi. "Masha Allahu, idan Allah ya kai mu bayan bakwan mahaifiyarki za mu je asibiti a duba idon naki, idan Ubangiji ya ba mu sa'a kin warke sai ki cigaba da karatunki." Duk son ta da karatu da son ta warke daga makanta sai ta ji ba ta yi wani farinciki ba da kalaman Abba, saboda ɗaci da zafin da zuciyarta take ciki na rashin Inna, wanda kullum kewar ta da zafin mutuwar ta yake ƙaruwa a cikin ranta. Tana ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta cika mata ido ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ƙara girma ya ji ƙan mahaifa." Cikin jin daɗin Addu'ar ta ya ce. "Amin ya ALLAH, Allah ya miki albarka ya inganta rayuwarki. Zan saka a samo malamar Addini ta dinga yi miki ƙarin Ƙur'ani da littafai, saboda Ummin taku ba ta zama tana fita aiki, da sai ta dinga miki." Godiya ta ƙara yi masa cikin raunin murya, don sosai Alkhairin Abba ya karyar mata da zuciya, taso a ce Inna tana raye su ga wannan ranar tare, ranar da wani zai nuna musu ƙauna duk ya kasance mai arziƙi da wadata. Abba ya ce. "Babu komai, ke ma 'yata ce kamar su Khalifa, ki saki jikinki ki yi rayuwa kamar kowa a gidan nan kin ji?" Gyaɗa masa kai ta yi tare da yin ƙasa da kanta. Ganin har yanzu ba ta saki da jiki da zaman gidan ba Abba ya shiga yi mata nasiha, ya san mutuwar Inna har yanzu tana dukan ta. Shi ya sa yake son ta shiga school ko hakan zai rage mata damuwa. Bayan kwana uku aka yi sadakar bakwai ɗin Inna kamar yadda aka yi ta uku, har lokacin A'isha ba ta daina kukan mutuwar Inna ba, kulawa da ƙaunar da Ummi da Abba ke nuna mata ke rage mata damuwa, gami da ƙara saka mata nutsuwa akan zaman ta a gidan. Lokuta da dama za ta kwanta da sunan bacci, amma baccin za ta yi ba, tunanin Inna da yadda suka gudanar da rayuwarsu take cikin hawaye, hakan ya saka kullum take fama da matsanancin ciwon kai. Duk da ta samu hutu da cima mai kyau amma kullum ƙara rama take. Kwanaki bakwan nan da suka wuce jin ta take tamkar mai rayuwa cikin mafarki, ko ƙaƙa ta yi bacci ta farka sai ta ji tamkar za ta ji muryar Inna tana mata magana, ko za ta tashi su cigaba da rayuwa a gidansu. Sai dai ta tabbatar hakan ba zai taɓa faruwa ba, Inna ta riga ta tafi ba za ta dawo ba. Ta san mutuwa gaskiya ce, duk wani mai rai jiran ta yake. Da yamma tana zaune ita kaɗai a parlour tana tunanin da ta saba, Ummi na toilet tana wanka, Ya Maamah ta koma Abuja gidan mijinta, Gwaggo ma ta koma Gombe kwana biyu da suka wuce. Kasa daurewa ta yi duk da ba ta son Ummi ta gan ta tana kuka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Cikin kukan take faɗin. "Allah ya ji ƙan ki Innata ya gafarta miki, rashin ki a cikin rayuwata daidai yake da na rasa farinciki na har abada. Ban taɓa tunanin ko da wasa akwai ranar da zan yi rayuwa babu ke ba." Ta ja majina tare da yin sheshshek'a ta ce. "Allah ya kai haske kabarinki." A haka Ummi ta zo ta tarar da ita tana gunjin kuka. Hankali a tashe Ummi ta ƙarasa kusa da ita ta zauna tana tambayar ta dalili kukanta, a tunaninta wani ne ya shigo ya yi mata wani abun. "Me ya faru? Ko wani ya shigo ya miki wani abun? Shi ya sa bana son kina zama ke kaɗai a guri." Girgiza kai ta yi cikin ƙoƙarin tsayar da kukan. Ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce. "To me ya faru?" "Babu komai." Ta ba ta amsa tana goge hawayen fuskarta. "Ko garinku kike son zuwa?" Nan ma girgiza mata kai ta yi. Dafa kafaɗarta Ummi ta yi ta ce. "To ki yi haƙuri ki bar kukan nan haka kar ki jawo wa kanki wani ciwon, na san rashin mahaifiyarki ne yake damun ki, amma ba kuka ya kamata ki zauna kina yi ba idan kika tuno ta, addu'a za ki yi mata, Allah ya ji ƙan ta." Numfashi ta sauke tare da gyaɗa mata kai. Cikin tausayawa Ummi ta ce. "Mutuwar Uwa akwai ciwo da dukan rai, amma sai haƙuri babu yadda za mu yi. Idan zafin abun ya taso miki ki dinga kiran sunan Allah ko kina karatun Alkur'ani, za ki ji sauƙin abun insha Allahu." Cikin raunin murya ta ce. "Zan na yi insha Allah, na gode." Ummi ta ce. "Mu je ɗaki ki kwanta ki huta kafin a kira Sallah, na san kanki ba zai kasa yi miki ciwo ba." Washegari kafin bakwai na safe sun gama shirin tafiya Asibiti. Abba ya shiga part ɗin Mommy don yi mata sallama, ya tarar da ita a kwance tana bacci. Tashin ta ya yi ta buɗe ido da ƙyar. "Zan fita." Abba ya faɗa a taƙaice, don har yanzu bai gama hucewa daga abin da take yi ba. Miƙa ta yi gami da hamma ta tashi zaune. Cikin muryar bacci ta ce. "Ina kuma za ka je da sassafen nan na gan ka cikin shiri?" "Za mu kai Nana asibiti ne?" Cikin rashin fahimta ta ce. "Wace ce kuma Nana da za ta fitar da kai da sassafen nan? Ko Baby ce babu lafiya ai sai haka." Abba ya ce. "Yarinyar da na kaɗe su nake nufi, kin san tana da matsalar ido." Taɓe baki ta yi ta ce. "Ina zan sani tunda ba a wurina take ba? Sai kun dawo to." "Yanzu ai kin sani." Ya faɗa tare da juyawa zai fice. Tsaki ta ja a ranta tana mitar akan wannan shirmen zai katse mata daddaɗan baccin da take ya ƙara mata ɓacin rai. Ya ji tsakin da ta yi, amma bai ce komai ba ya fice. Asibitin Makkah suka je, aka yi wa A'isha gwaje-gwaje a idon bayan an buɗe mata File. 1 week aka ba su, su dawo don karɓar sakamakon gwajin. Daga nan gidan Aunty Ruƙayya suka zarce dake gadon ƙaya, Ummi ta bar ta a can, ta ce idan ta dawo daga school za ta biyo ta ɗauke ta. Sai yamma Ummi ta baro school a gajiye, hakan ya sa ta wuce gida tun da ya fi kusa. A Polytechnic ta matan fada take lecturing, department of Pharmacy. Su kuma suna zaune a unguwar Railway ne. Tana ƙoƙarin shiga wanka Khalifa ya shigo ɗakin, zama ya yi a gefen gado ya ce. "Sai yanzu kika dawo? Na ji da muka yi waya kamar kina hanya." Ummi ta ce. "Eh yanzu na shigo, dama kiran da na yi maka Nana za ka je ka ɗauko a gidan Ruƙayya, na gaji sosai ba zan iya driving har Gadon ƙaya ba, kuma zan yi girki anjima." Khalifa ya ce. "Okay, amma gaskiya Ummi ya kamata ki ƙara samo mai aiki, aikin gidan nan ya miki yawa ke kaɗai, ga shi ke ba zama kike ba." Ummi ta ce. "Zan saka a nemo mini ko dan Nana ta samu mai kula da ita idan bana nan, ba na son yara ne wanda sai an shaƙu su yi aure, har yanzu ban daina kewar Lami ba, shi ya sa ko zan kuma mai aiki na fi son dattijuwa." Khalifa ya ce. "Gaskiya kam, bari na je na ɗauko ta kar Magriba ta yi, Kin ji su Yaya jibi za su dawo ko?" Ummi ta ce. "Ya faɗa mini, ɗazu da muka fita Abbanku yake ƙara sanar mini, Allah ya kai mu ya kawo su lafiya." Miƙewa Khalifa ya yi ya ce. "Amin, na tafi." Ummi ta ce. "Allah ya kiyaye ya tsare, sai kun dawo." Ya amsa da Amin tare da ficewa. A'isha tana parlour a zaune ita kaɗai Khalifa ya shigo. Juyar da kanta ta yi inda ta ji motsi, yadda ta ware daradaran idanunta ba za ka taɓa cewa makauniya ba ce. Ƙura mata ido ya yi cikin faɗuwar gaban da bai san dalilin ta ba. A hankali ya taka ya ƙarasa cikin parlour'n tare da yin sallama. Amsa masa ta yi cikin murmurshin jin daɗin zuwan shi. "Indodo." Ya faɗa cikin tsokana. Murmushi ta ƙara yi tare da faɗin. "Ina yini?" Yana zama a kusa da ita ya ce. "Lafiya ƙalau, ya na gan ki ke kaɗai, ina Aunty da su Ihsan?" "Suna ciki." Ta ba shi amsa cikin sanyin murya. Zai kuma magana Aunty Ruƙayya ta fito daga kitchen, da mamaki ta ce. "A'a, Babana yaushe ka zo?" "Yanzun nan, Ina yini?" "Lafiya ƙalau, ya aiki?" "Alhamdulillah." "Ka zo tafiya da ita ne?" Ya ce. "Eh, Ummi ce ta ce na zo na ɗauko ta." Aunty Ruƙayya ta ce. "Ai na ɗauka za ta bar ta kwanar mana biyu a nan, Kodayake gobe Friday ba jimawa za ta yi ba a school." Khalifa ya ce. "Ai ummi ba za ta iya barin wannan tsohuwar ta kwana a wani gurin ba, ji take da ita kamar ɗanyen ƙwai." Aunty Ruƙayya ta ce. "Ta ma fi ƙwai ko Mamana?" Murmushi kawai A'isha ta yi ba ta ce komai ba. Daidai lokacin Ihsan ta fito daga ɗaki, da fara'a sosai ta dubi Khalifa ta ce. "Mun yi fushi Ya Khalifa gaskiya." "Me kuma na yi?" Ya tambaya cikin marairaicewa. Ta ce. "Yaushe rabon ka da gidan nan, sai yau da ƴar gidanku ta zo muka gan ka." Ya ce. "A yi haƙuri tuba nake." Dariya ta yi tare da gaishe shi. Ko 10 minutes ba su ƙara ba Khalifa ya ce za su tafi kar dare ya yi, kayan cosmetics da turaruka Aunty Ruƙayya ta ba wa A'isha, ta yi mata godiya sannan Ihsan ta kama hannunta suka fita ta raka su bakin Motor. Sai da Khalifa ya tsaya a hanya ya yi wa A'isha shopping kafin su je gida. Hankalin Mommy ya yi kan shirye-shiryen tarɓar ɗanta da Matarsa wadda ta kasance ƴa ga Kaltum ƙanwarta. Shi ya sa ta ajiye batun A'isha a gefe ba don ta haƙura ba. Yadda ake toye-toye da abubuwa sai ka yi zaton shugaban ƙasa ne zai dawo. Kasancewar shi ma'abocin tsafta da son ta ya sa tun saura kwana biyu su sauka masu aiki suke bautar gyaran part ɗinsa dake gidan, tamkar za su sauya masa halitta saboda ƙalƙala. Yau tun safe Ihsan ta zo da yake weekend ne babu school, A'isha ta ji daɗin zuwan ta sosai, saboda ita ma kamar su Ummi take babu ruwanta, ga faran-faran da son jama'a. Bayan Sallar la'asar Ummi tana bedroom tana azkar, Khalifa kuma ya tafi airport ɗauko su Safwan. Hannun A'isha Ihsan ta kama ta ce. "Zo mu fita compound mu shaƙata." A'isha ta ce. "Wacce irin shaƙatawa kuma?" "Ke dai ki zo mu je." Ihsan ta faɗa tare da jan ta suka fice. Suna zaune a kan kujerun roba wayar Ihsan ta yi ringing, dubawa ta yi ta miƙe ta ce. "Bari na ɗan leƙa waje na dawo, wani guy ne ya zo za mu gaisa, yanzu zan dawo." Gyaɗa mata kai kawai Aisha ta yi, ɗaga kiran ta yi tare da barin wajen. Buɗe makeken gate ɗin gidan tare da shigowar wata rantsatstsiyar mota, ya saka Mommy dake tsaye a gaban window sakin murmushin farinciki dawowar ɗanta Namiji tilo a duniya, wanda take gani da jin duk duniya tamkar babu ɗan da ya kai shi. Sakin labule ta yi ta koma ta zauna tana jiran shigowar shi. Bayan Khalifa ya yi parking Safwan ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa ya buɗe. A hankali ya buɗe motar ya fito yana kallon harabar gidansu da ya shafe watanni ba a cikinsa ba. After some seconds ya buɗe bayan Motar tare da ja baya. Wata farar matashiyar mace siririya ce ta fito tana yamutsa fuska tare da kare fuskarta da hannunta. Yanayin shigar jikinta ba za ka ce matar aure ba ce idan ba faɗa maka aka yi ba. Kanta ta ɗora a kan kafaɗarsa, cikin marairaicewa ta ce. "I'm so tired mine." Gefen fuskarta ya shafa cikin kulawa ya ce. "Sorry." A taƙaice. Ba ta ce komai ba ta bar jikinsa jin wayarta dake hannunta na ringing. Picking ta yi tare da nuna masa hanya alamun ya yi gaba za ta taho. Bai ce komai ba ya juya ya fara tafiya cikin nutsuwa, a ransa yana mamakin daga saukar su har ta saka sim ɗinta na Nigeria an fara kiran ta. Khalifa dake kallon su ya taɓe baki tare da buɗe murfin motar ya fito shi ma. A'isha ta fara gajiya da jiran Ihsan, ga iska sai ƙadawa take sanyin la'asar yana ratsa ta. Ganin iskar na takura ta ya sa ta miƙe ta fara tafiya a hankali cikin laluben hanya. Ba zato ta ji ta yi karo da wani abu, taga-taga ta yi za ta faɗi ya yi saurin ruƙo ta yana yatsina fuska, ko kaɗan bai lura da mutum yana tahowa ba saboda ba ta gabansa take ba ta gefen shi take. Ita kuwa Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jin ba ta kai ƙasa ba, siririn tsaki ya ja ya zare ta daga jikinsa tare da yin gaba ba tare da kuma kallon inda take ba. Tsayawa ta yi cak ta kasa cigaba da tafiya, saboda tsoron kar ta kuma karo da wani abun. Mamakin wanda suka yi karo da shi ne ya cika mata zuciya, su yi karo da mutum amma ya ƙi magana sai ka ce kurma. Ta san ba Ya Khalifa ba ne ko Abba, don in su ne ba za su taɓa wucewa su bar ta ba, kuma ƙamshin da ta ji a jikin mutumin ba irin nasu ba ne, ba ta taɓa jin irin ƙamshin ba tunda ta zo gidan sai yau. Lumshe ido ta yi saboda yadda daɗin ƙamshin yake ratsa ta, duk da ya bar gurin amma ƙamshinsa bai daina ratsa ƙofofin hancinta ba. Jin ƙarar taku ya sa ta sakin ajiyar zuciya, a tunaninta Ihsan ce ta dawo, tana shirin yin magana ta ji an wanke ta da wani gigitaccen mari, ba ta gama fita daga ɗimuwar marin ba ta ji an damƙi wuyanta tare da lailayo mata narkekiyar ashariya gami da faɗin. "Dabbar ina ce ke da za ki bari ki yi karo da mijina har ki gogi jikinsa? wallahi sai na kashe ki tunda kika haɗa jiki da mijina!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji.........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣8️⃣* Khalifa da ya tsaya yana magana da ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ya yi saurin ƙarasowa inda suke yana faɗin. "Salma! Mene haka? Ba ki da hankali ne za ki mata irin wannan shaƙar?" Ya ƙarashe maganar cikin fusata tare da ƙoƙarin ɓanɓare hannunta daga wuyan A'isha, amma ta ƙi sakin ta sai ma ƙara cakumar ta take cikin bala'i. Marin da Khalifa ya sauke mata ne ya sa ta sakin A'isha ba shiri tare da dafe kuncinta da take jin tamkar ba ya jikinta, saboda tsabar zaraɗaɗi da zafin marin da ya ratsa ta. "Ni ka mara Khalifa?" Ta tambaya cikin tsantsar mamaki da ɓacin rai, idanunta cike da ƙwallar takaici. Khalifa bai kula ta ba ya riƙo A'isha dake numfarfashi gami da hawaye. "Are You okay?" Ya tambaye ta a ruɗe ta cikin damuwar halin da take ciki. Ganin yadda take kuka ya ƙara ɗaga masa hankali. Daidai lokacin Ummi da ta fito parlour ba ta ga sun ba ta duba ko'ina duk ba ta gan su ba ta fito compound ɗin. Hango su a tsaye Khalifa na riƙe da A'isha ya sa ta ɗaga murya ta ce. "Khalifa Lafiya? Me yake faruwa?" Numfashi ya sauke mai zafi yana jifan Salma da wani mugun kallo wadda ta yi suman tsaye, a kufule ya ce. "Shaƙe ta ya yi tana ƙoƙarin kashe ta." "Subhanallahi, shaƙa kuma kamar ya? Akan me?" Ummi ta tambaya a ɗimauce tare da ƙarasowa ta janye A'isha tana faɗin. "Me ya faru ne wai? Ina Ihsan ɗin?" A'isha za ta yi magana amma ta kasa saboda kukan da take, har yanzu jikinta bai daina rawar firgici ba, don ba ƙaramar shaƙa ta sha ba. Khalifa da yake jin tamkar ya rufe Salma da duka ya juya ya bar wajen, saboda idan ya cigaba da tsayawa yana kallon ta zai iya yi mata abin da ya fi mari. "Wallahi sai ka yi nadamar mari na da ka yi, zan nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne." Salma ta faɗa a zuciye tare da wucewa ta nufi ciki a matuƙar fusace. Da kallo kawai Ummi ta bi ta ta kama hannun A'isha suka shiga ciki. Direct part ɗinsu ta wuce a maimakon na Mommy da ta yi niyya, Upstairs ta haye ta buɗe bedroom ɗinsu ta shiga, zuciyarta har wani huci take saboda zafin da take ji a cikinta, an daɗe ba a yi mata abin da ya yi ƙoluluwar ɓata mata ran da Khalifa ya yi ba yau. "Ni zai mara yana ƙanin mijina akan wata SHEGIYA? Wacece ita da har wani mahaluƙi zai kai hannunsa jikina saboda ita?" Ta yi maganar cikin ɗaga murya tare da cillar da wayarta kan gado ta fara kai kawo a cikin ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin tare da wanzuwar ƙamshinsa a cikinsa ya sa ta juyawa cikin sauri ta fuskanci shi. Ƙura mata ido ya yi cikin faɗuwar gaba saboda ganin yanayinta, a duniya idan akwai abin da yake gudu da tsoron faruwar shi to ɓacin ran matarsa abar ƙaunar shi ne. Cikin damuwar da ta kasa ɓuya a ransa ta bayyana a fuskarsa ya ce. "Lovely what happened to you? Wa ya taɓa mini ke?" Ya ƙarshe maganar tare da ƙoƙarin riƙe ta. "Don't touch me!" Ta faɗa cikin tsawa. Tsayawa ya yi cak tare da runtse idonsa, don ba ƙaramin ratsa shi tsawar ta yi ba. Cikin kakkausar murya ta ce. "Ƙaninka ya mare ni saboda na mari wata aba da ba ta kai in saka ta a jerin mutane ba, ka je ka rama mini yanzu-yanzu ba sai ya lokaci ya ƙure ba, don da zafi-zafi ake dukan ƙarfe." Cikin ɓacin rai ya ce. "What? Khalifa ne ya mare ki ko wa?" "Kana da wani ƙanin ne bayan shi?" Ta tambaye shi cikin tarar numfashi. Bai ce komai ba ya juya ya fice da sauri cikin ɓacin rai. Ajiyar zuciya ta sauke ta zauna a bakin gado, sai yanzu ta ji ta fara hucewa saboda sanin babu abin da zai hana Safwan rama marin da Khalifa ya mata, ko da kuwa a gaban Ummi da Abba ne, ko da yana sauke hannunsa daga fuskar Khalifa za su ba shi nasa marin, shi dai tunda ta ce ya je ya rama mata sai ya yi. Ummi tana zaune a kan kujera A'isha na jikinta tana rarrashin ta bayan ta faɗa mata abin da ya faru da ƙyar cikin kuka ya shigo cikin parlour'n tamkar an cillo shi yana kiran sunan Khalifa. Ɗago kai ta yi ta kalle shi, ganin yadda yake huci ta haɗe rai ta ce. "Khalifa ba ya nan, sai ni uwarsa idan za ka rama mara marin a kaina, tunda kai ma uwarka ya mara." Kallon ta ya yi kamar zai magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice daga parlour'n. Tsaki Ummi ta yi cikin takaici, a ranta tana masa addu'ar Ubangiji ya kawo ranar da zai bar wannan rayuwar ta raƙumi da akala da Salma ke jan shi. A'isha kuwa cak ta tsayar da kukanta tare da ƙara ƙanƙame Ummi, ba ta san waye ya shigo ba, ba ta taɓa jin muryarsa ba tunda ta zo gidan, amma yadda ya shigo yana kiran sunan Khalifa cikin ƙaraji da masifa ya sa tsoron shi ya dirar mata a zuciya lokaci ɗaya. Mommy da ta ga gilmawar su ta window ta miƙe cikin sauri ta nufi part ɗin nasu, Upstairs ta hau don ta san suna can, ganin ba sa parlour ta nufi bedroom ɗin Salma ta shiga. "Lafiya na ga my son ya wuce a firgice? Ke ma kamar wadda ranta ke ɓace." Mommy ta faɗa cikin mamaki ganin yanayin Salma. A shagwaɓe ta ba ta labarin duk abin da ya faru. Ashariya Mommy ta lailayo ta narka ta ce. "Khalifan ne ya mare ki? Yana cikin hankalinsa kuwa? Ko ya fara shaye-shaye ne?" Taɓe baki Ta yi cikin ƙara jin zafin abun a cikin ranta ta ce. "Wa ya san masa, amma wallahi bai mari banza ba, bayan Mine ya rama mini sai na kuma ɗaukar mummunan mataki a kan shi, sai ya gane kurensa, zai san da ni yake zancen." Mommy ta ce. "Gaskiya wannan yarinyar annoba ce, babu Alkhairi kwata-kwata a tattare da ita, daga saukar ku har ta yi sanadin abin da ya ɓata muku rai?" Ƙwafa Salma ta yi cikin ɗacin rai, har yanzu ba ta daina ganin lokacin da A'isha suka yi karo da Safwan a idonta ba. Runtse idonta ta yi jin kamar an saka mashi an soki zuciyarta, a yadda zuciyarta take tafarfasa lokacin da ta shaƙe A'isha ba don Khalifa ba da za ta iya kashe ta har lahira. Duk da ransa a ɓace yake amma a nutse yake tafiya, da sallama ya shiga bedroom ɗin amma ba su amsa masa ba, sai ido da suka zuba masa suna jiran jin irin matakin da ya ɗauka akan Khalifa. Sanin halin miskilancinsa ba lallai ya yi magana ba ya sa Mommy ta ce. "Da fatan ka masa dukan mutuwa dai?" Idanunsa a kan Salma da ta tsare shi da ido ya ce. "Ban same shi ba." "Uwarsa ta ɓoye shi kenan." Mommy ta faɗa a harzuƙe. Bai ce komai ba ya ƙarasa ya zauna a kusa da Salma tare da ƙoƙarin kama hannunta. Wani kallo ta wurga masa tare da miƙewa tsaye ta ce. "Babu abin da za ka ce mini Safwan, ai komai ya faru lefin ka ne, yarinyar ta rungume ka amma ka kasa ɗaukar mataki a kanta, sai kawai ka tafi ka bar ta, maimakon ka ture Shegiya ka yar da ita ta faɗi ka tattake cikinta? Amma ka ƙi saboda ba ka kishin kanka bare...." A tsawace Mommy ta katse ta faɗin. "Ya isa haka Salma, kin san bana son wannan tsiwar taki da rashin ɗa'ar da kike masa ko? Sai ka ce ba mijinki ba." Kuka ta fashe da shi tare da faɗin. "Amma Mom rungume shi fa wata ta yi a gabana, don na nuna ɓacin raina laifi ne? Mijina ne fa, kuma kin san ina tsananin kishin shi." "Shikenan ya isa, mu je ƙasa ku ci abinci sai ku yi wanka ku huta, kar ki saka damuwar wasu sakarai a cikin ranki ki ɓata mood ɗinki, ki bar komai a hannuna za ki ga matakin da zan ɗauka." Mommy ta faɗi haka tare da juyawa ta fice. Da sauri Safwan ya miƙe ya janyo Salma jikinsa, kukan nan da take ji yake tamkar ana watsa masa garwashi a cikin ransa, yadda kukan yake taɓa ransa ba ya jin zai iya ƙara sakanni bai rarrashe ta ba, ko da a gaban Mommy ne kuwa. A ruɗe ya ce "Please stop crying My one, kin san babu abin da tsana a rayuwata sama da zubar hawayenki." Ƙara fashewa da kukan ta yi cikin son ta ƙara ɗaga masa ta ce. "Dole na yi kuka Mine, wata ce fa ta taɓa jikinka a gaban idona." Numfashi ya sauke mai zafi yana jin da zai ƙara ido huɗu da yarinyar sai na lahira ya fi ta jin daɗi, saboda sanadin zubar hawayen sanyin idaniyarsa da ta yi. Cikin rikicin da kukan nata ya ƙara saka zuciyarsa ya ce. "Taɓa jikina da ta yi ba ya nufin wani ba ne Lovely, kin fi kowa sanin ni naki ne ke kaɗai, wallahi duk macen da na gani kallon Namiji kamata nake mata, ke kaɗai idanuna suke gani a cikin mata, don Allah ki daina mini asarar hawayenki akan wata kucaka, Please Lovely kar zuciyata ta tarwatse." Ganin yadda ya rikice sai ta ɗan saki fuskarta tare da ƙara lafewa a jikinsa. Da ƙyar ya rarrashe ta, ta haƙura suka sauka ƙasa don cin abinci. Sai lallaɓa ta yake tamkar ɗanyen ƙwai, ita kuma tana ta ƙara botsarewa. Bayan ya ja mata ɗaya daga cikin kujerun dinning ta zauna ya ce. "Let me serve you dear, me kike son ci?" Yadda ya yi maganar tamkar bawa da Uwargijiyarsa ya sa Mommy da ta dawo parlour'n tsayawa cak cikin bugawar zuciya. 'Me take shirin gani haka? Ɗanta Safwan tsayayyen mutum da ba ya ɗaukar wargi tamkar mahaifinsa shi yake shirin zama mijin ta ce ko ma ya zaman?' Ta faɗi haka a ranta cikin tashin hankalin ganin irin kallon zallar rainin da Salma take bin shi da shi. "Impossible!" Ta furta cikin sauke numfashi gumin firgici na tsatstsafowa a jikinta........✍️ *Rashin comment ya sa ba ni da karsashin yin dogon typing, idan kun gyara ni ma zan ƙara.* *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣9️⃣* Jijjiga kai ta yi ta ƙarasa dinning area ɗin cikin ƙoƙarin ɓoye halin da take ciki. Fatanta da addu'arta Allah ya sa kar zarginta ya zama gaskiya, tana fatan a ce laifi Safwan ɗin ya yi wa Salma shi ya sanya yake mata haka don ta yafe masa. Saboda sanin da ta yi masa mutum ne wanda ba ya son ɓatawa kowa rai, ko da a cikin rashin sani ne, idan hakan ya faru ba ya jin kunya ko nauyin ya ba ka haƙuri don ka yafe masa, ko da kuwa kana ƙasan shi ne ya girme ka, ko kuma kana aiki a ƙarƙashinsa. A kodayaushe yana faɗa ba ya son mutuwa da alhakin kowa a kansa. Wannan tunanin ya ɗan sassauta zuciyar Mommy daga tsananin razanin da ta shiga lokaci ɗaya. Idanunta a kansa ta ce. "Son ya kake zuba abincin da kanka? Ka bari yanzu Atine za ta zo ta zuba muku." Ba tare da ya bari ba ya ce. "Na ga tana jin yunwa ne sosai shi ya sa nake zuba mata." "Ka bar shi na ce, tana matarka ita ba ta zuba maka ba sai kai za ka zuba mata?" Satar kallon Salma ya yi kamar mai jiran umarnin sai ta ce ya bari sannan zai bari, ɗauke kanta ta yi tana ƙeɓe fuska. Ba don ya so ba ya zauna still looking at her, so yake su haɗa ido ya rarrashe ta da idon amma ta ƙi. Mommy dake lura da su ta sauke numfashi mai tattare da ɗunbin takaici, da akwai matsala kenan? Don ta san wannan rawar jikin da Safwan yake yi ba na banza ba ne, dole sai da wani abun a ƙasa. "I'm sorry Dear, ki ci abincin please." Muryar Safwan da ya faɗi haka ƙasa-ƙasa ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Ganin yadda yake rawar jikin ɗebo abincin a spoon zai kai bakin Salma ya sa ta juyawa ta bar musu parlour'n cikin sauri tana haɗa hanya. Da kallo Salma ta bi ta tare da sakin wani shu'umin murmushi. Zarya Mommy ta shiga yi a parlour cikin tashin hankali, me yake shirin faruwa da ita ne? Salma ta asirce mata ɗanta ne ko yaya? Girgiza kai ta yi da sauri tare da faɗin. "Hakan ba zai taɓa faruwa ba, na san Kaltum ba za ta taɓa cin amanata ba ko ta bar Salma ta ci." 'Amma kuwa rawar jikin da Safwan yake akan Salman fa? Wadda a da ba ya mata' Zuciyarta ta faɗa mata haka. Hannunta ta ɗora a kan goshinta ta shiga bubbugawa. Tabbas ta ga wani abu mai kama da tsoro a tattare da ɗanta da yake yi wa Salma. Zama ta yi ɗabas a kan kujera tare da haɗiyar wani yawu mai ɗaci. Tunanin yadda Salma take masifar tsoron Safwan a da ta tuna, amma yau ba ta ga hakan ba ko kaɗan a tattare da ita, sai ma zallar fitsara da isa gami da gadara ta gani. Jijjiga kai ta yi cikin ƙanƙance ido ta ce. "Babu shakka idan har khaltum cin amanata ta yi sai na nuna mata asalin kalata, don ba zai yiyu in shafe shekaru ina gini lokaci ɗaya wata ta zo ta rusa mini shi ba, zan cigaba da saka ido a kansu har na gano bakin zaren." Ummi tana ƙoƙarin tashi ta ɗauko wa A'isha maganin ciwon kai da ta yi mata complain yana damun ta Ihsan ta shigo parlour'n kamar munafuka tana rarraba ido. Kallon da Ummi ta bi ta da shi ne ya sa ta shan jinin jikinta. Cike da tsoro ta ƙaraso ciki ta zauna kanta a ƙasa. "Daga ina kike?" Ummi ta tambaye ta a kaushashe. Cikin inda-inda ta ce. "Wani class mate ɗina ne a nan unguwar, muna chat ɗazu na ce masa ina unguwarsu, shi ne ya ce zai zo mu gaisa." Fuska babu walwala Ummi ta ce. "Shi ne ba za ki sanar mini ba kika fita a munafunce ko?" Shiru ta yi tare da yin ƙasa da kanta. A fusace Ummi ta ce. "I'm talking to you." "I'm sorry Ummi." "Sorry for yourself, kin fita ba da izinina ba sannan kin bar yarinya ita kaɗai a waje, kuma kin san ba gani take ba. Lefi biyu kenan." Ummi ta faɗa tare da yin ƙwafa. Kamar za ta yi kuka ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri Ummi b...." Hararar da Ummi ta wulga mata ya sa ta haɗiye sauran maganarta. Ummi ba ta kuma magana ta miƙe ta haye sama. Ajiyar zuciya Ihsan ta sauke ta miƙe ta koma kusa da A'isha. Kallo ɗaya ta yi mata ta gane ta yi kuka, da damuwa ta ce. "Me ya faru Nana na ga kamar kin yi kuka?" Ɓata fuska ta yi ba ta ce mata komai ba, saboda haushin ta take ji tunda ita ce sanadiyyar faruwar komai. "Allah ya sa ba faɗuwa kika yi ba ko wani abu ne ya same ki?" Ihsan ta faɗa tana dudduba jikinta. Ganin yadda ta damu sai A'isha ta faɗa mata abin da ya faru in brief. Cikin takaici da ɓacin rai ta ce. "Kan Uba! Mari fa kika ce da shaƙa? Taɓɗijan! Da ma fa matar nan Mahaukaciya ce, Shegiya mai kama da fatalwa." Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki. Sai kuma ta sassauta murya ta ce. "Ki yi haƙuri Please Nana, na yi sanadin da aka taɓa lafiyar jikinki kina zaman-zamanki, wallahi ban san zan jima ba, da ba zan tafi na bar ki ba." Gyaɗa mata kai kawai ta yi tare da lumshe idonta, har yanzu wuyanta bai gama saki ba daga shaƙar da ta sha. Hankali kwance take cin abincinta, tana ci tana latsa wayarta, lokaci zuwa lokaci tana sakin murmushi alamun tana enjoying abin da take. Shi kuwa ya kasa cin abincin na kirki saboda ɓacin ran Khalifa da ya cika masa zuciya. Miƙewa ta yi tare da kara wayarta a kunnenta, tana goge bakinta da tissue ta ce. "Mine bari na shiga ciki na huta kafin ka gama." Da sauri ya miƙe ya ce. "I'm ok ni ma." Ɓata fuska ta yi tana kallon plate ɗin abincin nasa ta ce. "Ka zauna ka ƙara ci, wannan ai babu abin da ka ci." Zai kuma magana ta ɗaga masa hannu, cikin bayar da umarni ta ce. "Ka yi abin da na ce kawai, make sure ka cinye duka kafin ka hawo sama, and you already know idan ba ka cinye ba ma ka ce mini ka cinye zan gane." Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce. "Shikenan Lovely zan cinye." Hannu kawai ta watsa ta yi gaba. Da kallo ya bi ta har ta ɓacewa ganin shi. "Hello Mama ina jin ki yanzu, ban san kin ɗaga ba ɗazu, muna magana da Mine ne." Salma ta faɗa lokacin da take murɗa key ɗin ƙofar bedroom ɗinta ta rufe. Daga ɗaya ɓangaren Kaltum ta ce. "Okay Daughter, kun sauka lafiya? Ya hanya?" "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, Ina Daddy? Shi ne ko ya kira ni ya ji ya na sauka?" Ta yi maganar a shagwaɓe. "Yana nan ƙalau, kin san yana Abuja, wannan weekend ɗin bai dawo ba sai next week." "Allah Sarki Daddyna na yi kewar ku sosai Mama, na ɗauka zan tarar da ke a gida kin zo tarɓar ta." Kaltum ta ce. "Kin san na yi accident last week, Har yanzu ƙafata ba ta gama warkewa ba." "Ayya sannu, har na manta fa kin faɗa mini, ya ƙafar?" "Ta yi sauƙi. Ya kuka yi da surukar taki ne? Na san yanzu tana can zuciyarta ta kusa bugawa." Dariya Salma ta ƙyalƙyale da ita ta ce. "Ai in ma ba ta buga ɗin ba kenan, kin ga yadda ta ruɗe lokaci ɗaya? Daga ganin mood ɗinta ba ƙaramin shock ta shiga ba." Cikin dariya Kaltum ta ce. "Na sani dama, yadda take tinƙaho da alfahari da ɗan nan nata kamar a kanta aka fara haihuwa ko ita kaɗai ce mai ɗa namiji a duniya. Kaɗan ma ta fara gani, duk wulaƙanci da jan ran da ta yi mana kafin ki auri ɗanta duk sai mun fanshe shi a yanzu, dukiyar tasa ma da take taƙama da ita da sannu duk za ta zama tamu." Salma tana murmushin jin daɗi ta ce. "Gaskiya I'm lucky da samun ki a matsayin Uwa Mamata, ni fa yadda nake juya Ya Safwan kamar waina ya fi komai yi mini daɗi a yanzu. Duk wannan miskilancin da tsare gidan ya daina yi mini, yadda kika san zai mini sujjada fa don rawar jiki idan na ce ya mini abu." "Good ɗiyar arziƙi, da fatan kin faɗa masa zancen mota da gold ɗin da na ce ki ce ya siya miki." "Na faɗa masa, sarƙar ma gata nan a jakata na taho da ita, motar kuma ya ce ya yi order." "Da kyau shu'umar ƴa kamar uwarta." Salma ta yi dariya ta ce. "Ai kin san barewa ba za ta yi gudu ɗanta yay rarrafe ba." Sun daɗe suna wayar kafin su yi sallama bayan Salma ta tabbatar mata tana nan tafe anjima kaɗan. Tana cikin wanka ya shigo ɗakin, kayan jikinsa ya fara cirewa, yana ƙoƙarin shiga toilet ɗin ta fito tana goge jikinta da ƙaramin towel. Ba ta kalli inda yake ba ta nufi gurin mirror. "Lovely." Ya kira ta cikin kamilalliyar muryarsa. Juyowa ta yi tana kallon shi tana jin yadda son shi ke ƙara mamaye ko wane saƙo dake cikin zuciyarta. Takowa ya yi a hankali ya mannata da jikinsa tare da faɗin. "Me ya sa kika yi wanka ba ki jira ni ba?" Ɗan yamutsa fuska ta yi tare da raba jikinta da nasa ta ce. "Ina sauri ne zan fita." "Fita kuma?" Ya faɗa cikin mamaki. Gyaɗa masa kai ta yi tare da zama ta ɗauko wani tsadadden lotion ta fara shafawa a jikinta. A raunane ya ce. "Ina za ki?" "Gidan Mama." Ta ba shi amsa a taƙaice alamun ya fara takura mata. "Okay, lemme take shower sai na kai ki." "No need." Ta faɗa cikin haɗe rai. Sororo ya tsaya yana kallon ta, zai kuma magana ta ɗaga masa hannu tare da faɗin. "Tunda na ce bana buƙata ka ƙyale ni mana, ka fiya naci fa sometimes." "I'm sorry." Ya faɗa tare da shigewa toilet. Tsaki ta ja tare da tashi ta ƙarasa wardrobe ɗinta dake cike da kaya ta zaɓo wata doguwar riga mai bin jiki ta saka. Kafin ya fito daga wanka har ta kammala shiryawa ta fice daga ɗakin. Part ɗin Mommy ta je ta yi mata sallama tare da karɓar car key. Har ta juya za ta fita Mommy ta ce. "Da kanki za ki yi driving har Gandu Salma? Ina Safwan ɗin?" "Yana kwance, wai ya gaji ba zai iya fita ba, ni kuma gaskiya na ƙagu na ga Mama, that is why zan tafi ni kaɗai." Gyaɗa mata kai kawai Mommy ta yi tana jin zuciyarta ta fara samun sassauci a game da fargabar tunanin ta shanye mata ɗa da ya hana ta sukuni tun ɗazu. Da alamun abun da ta zarga ba gaskiya ba ne, tunda ga shi Salman za ta gurin mahaifiyarta ya ƙi bin ta, kuma ta haƙura dole za ta tafi ita kaɗai. Da ta asirce shin ai za ta masa dole ta ce sai ya raka ta, kuma dole ya yin. Salma kuwa murmurshi ta yi ta juya ta fita. Ta san yanzu ta saka mata wasi-wasi a cikin ranta kamar yadda Mama ta ce mata ta dinga raba mata hankali biyu, yadda abin zai fi ɗaga mata hankali ta rasa tudun dafawa ta kasa samun mafita. Har zuwa lokacin da duk wani shirinsu zai kammala, lokacin da ɗan da take taƙama da shi ɗin ganin shi ma sai ya yi mata wahala..........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *3️⃣0️⃣* Maimakon ta yi hanyar da za ta kai ta Gandu kamar yadda ta ce sai ta yi cikin Nasarawa G.R.A. Tafiyar mintuna kaɗan ta kai ta bakin ƙofar gidan da ta nufa, bayan ta danna horn mai gadi ya buɗe mata gate ta tura hancin motarta ciki zuciyarta cike maɗaukakin farinciki. Mata ne su huɗu zaune a cikin wani ɗaki cikin shigar da ba ta da maraba da tsirara. Biyu daga cikinsu na kan gado sun ba je suna zuƙar shisha. Sauran kuma suna kwance a kan carpet ɗin gaban gadon suna kallo a system. Jin shigowar mota ya saka su ɗago kai a tare gabaɗayansu. Ɗaya daga cikinsu mai suna Ramcy ta ce. "Salma Baby an ƙaraso kenan?" Ta ƙarshe maganar tare da tashi ta ɗaga labulen window tana leƙen waje. Shigowar ta ya saka su fasa ihu gabaɗayansu tare da nufar ta cikin murna suka ruƙunƙume ta suna faɗin. "Welcome." Dariya ta yi cikin matuƙar jin daɗi ta ce. "My babies I missed you so much." "Kin ga yadda kika canza kika yi kyau kuwa?" Ramcy ta faɗa lokacin da take zaunar da ita a bakin gado. Murmushi ta yi cikin daɗin yabon ta da Ramcy ta yi ta ce. "Ba dole ba tunda ina tare da Mine." Fadeela tana zama a kusa da ita ta ce. "Okay, ko kewar mu ma ba ki yi ba kenan?" Kuncinta ta shafa ta ce. "Faɗar irin kewar ku da na yi ɓata baki ne my guys, kawai dai kun san yadda nake tsananin son Mine kasancewa tare da shi ba ƙaramin abin farinciki ba ne a gare ni." Ba su kuma mata magana akan Safwan ba suka cigaba da murnar ganin ta. Daga nan suka zarce da abin da suka saba aikatawa na neman junansu. Tunda ya fito bai gan ta a ɗakin ba ya san ta tafi, maimakon ya ji haushi akan abin da ta aikata na ƙin yi masa sallama sai ya ba ta uzurin may be sauri take ta je ta ga Mahaifiyarta. A gaggauce ya shirya ya fito ya shiga part ɗin Mommy. Tana zaune a downstairs Atine na mammatsa mata ƙafa ya shiga parlour'n bakinsa ɗauke da sallama. Cikin fara'a Mommy ta ɗaga kai tana kallon shi tare amsa masa. Ƙarasawa ya yi ya zauna a kusa da ita. Kallon Atine ta yi cikin isa ta ce. "Ke tashi ki fita." Cikin girmamawa ta miƙe jiki na rawa ta fice bayan ta gaishe da Safwan. Kansa Mommy ta shafa tana murmushi ta ce. "Yanzu Abbanka ya kira ni ya tambaye ni ka sauka lafiya, ya kira sim ɗinka na Nigeria ba ya tafiya." Lumshe idonsa ya yi ya buɗe ya ce. "Ban saka sims ɗin a cikin waya ba ne har yanzu." Mommy ta ce. "Haka na ce masa." Ya numfasa ya ce. "Bari na je masallaci Mom." "Toh shikenan, idan ka dawo ina son magana da kai." Gyaɗa mata kai ya yi tare da tashi ya fice. Ganin ba a fara kiran Sallah ba ya nufi part ɗin Ummi. A'isha na zaune ita kaɗai tana cin abincin da Ummin ta tilasta mata kamar ba ta so ya shigo. Ƙarar Tv da yadda ya yi sallama a hankali ya sa ba ta ji shigowar shi ba. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa ya nufi bedroom ɗin Ummi. Tana haɗa kaya a wardrobe ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama. Ba tare da ta bar abin da take ta amsa masa ba yabo ba fallasa. "Sannu da aiki Ummi." Ya faɗa yana zama a kan carpet ɗin dake gaban gado. "Yawwa." Ta amsa masa still tana cigaba da shirya kayanta. Ganin yanayinta ya san fushi take da shi akan abin da ya faru. Cikin murmushi ya ce. "Zuwa fa na yi mu yi hirar yaushe gamo Ummina." Ummi ta ce. "To Bismillah mu yi mana, ya hanya? Da fatan kun dawo lafiya?" Cikin jin daɗin yadda ta saki fuska ya ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, da fatan mun same ku lafiya?" "Alhamdulillah, ai na ɗauka ƴar gold ɗin ba za ta bar ka, ka zo ka gaishe ni ba." Ya gane Salma take nufi, don haka ya yi shiru bai ce komai ba. Girgiza kai kawai ta yi ta zauna suka cigaba da gaisawa. Tana son Safwan sosai don duk abin da za ta yi ba ta banbanta shi da su Khalifa. Shi ma kuma haka, duk abin da ya yi wa mahaifiyarsa na kyautatawa to sai ya yi wa Ummi. Wannan dalilin yake ƙara yawaitar tsanar Ummi a cikin ran Mommy, Ta yi iya yinta don ta ga ta raba su amma Ubangiji bai ba ta nasara ba. Dole ta haƙura, amma duk da haka ko part ɗin Ummi ya je idan ta samu labari sai ta yi masa sababi ranar. Hakan ba ya hana shi ya ƙara zuwa ko ya yi mata abin Alkhairi. Sai da aka fara kiran Sallah sannan ya yi wa Ummi sallama ya tafi masallaci. Lokacin da ya fito A'isha ta gama cin abincin ta kwanta. Bai kalli inda take ba ya fice abinsa. Abba na dawowa Mommy ta tare shi da ƙorafin Khalifa ya mari Salma, da yake ta karɓi girki yau. Da mamaki Abban ya ce. "Mari kuma? A kan me?" "Wa ya san masa Alhaji? Yaron nan fa dama can ba mutunci gare shi ba." Abba ya ce. "Gaskiya akwai abin da ya faru, haka kawai Khalifa ba zai mari matar yayansa ba, amma bari na kira shi a waya na ji ba'asin zancen." Cikin takaici Mommy ta ce. "Kamar ya sai ka kira shi ka ji ba'asin zance? Akwai ba'asin da ya wuce wanda na faɗa maka? Ko kuma zan maka ƙarya ne?" "A gabanki aka yi marin ne?" A shaƙe ta ce. "A'a." Abba ya ce. "To kuma, ko shaidar zur za ki bayar?" A ƙufule ta ce. "Amma ka san shi ma dai ba zai faɗi gaskiya ba ko? Kansa kawai zai kare" "Idan ma ya yi ƙaryar zan gane." Abba ya faɗa tare da kara wayarsa a kunnensa. Khalifa yana parlour'n Ummi a lokacin yana tambayar A'isha yaya take jin jikinta a yanzu. A hankali ta ce masa. "Kaina da wuyana ne suke mini ciwo." Taune lips ɗinsa ya yi yana ƙara jin zafin Salma a ransa ya ce. "Sorry, kin sha magani?" Ta ce. "Eh Ummi ta ba ni." Cike da kulawa ya ce. "Ko kina son cin wani abu na siyo miki." Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Ki faɗa mini dai, me kike son ci zan siyo miki ko mene ne Nana." Yadda ya yi maganar cikin wani irin yanayi sai ta ji tamkar Umar, ta rasa me ya sa kalamansa da muryarsa suke mata shige da na Umar sometimes. Numfashi ta sauke ta ce. "Babu komai fa, bacci kawai nake son yi." Ya ce. "Mu je na raka ki ɗaki ki kwanta to." "Ummi ta ce na bari a yi Sallar Isha'i sai na yi baccin." Ta ba shi amsa cikin jin daɗin yadda yake nuna damuwa a kanta. Fitowar Ummi daga kitchen ya saka shi fasa faɗar abin da ya yi niyya. "Ka je Abbanka na kiran ka, ya kira ka ba ka ɗauka ba." Da to ya amsa mata tare da miƙewa ya fice ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Mommy na zaune har lokacin tana cika tana batsewa ya shiga, Abba da suke gaisawa da Safwan ya dube shi tare da amsa sallamar da ya yi. "Sannu da zuwa Abba." Ya faɗa lokacin da yake zama. Abba ya ce. "Yawwa." Duban Safwan ya yi ya gaishe shi tare da yi masa sannu da zuwa, a maimakon ya sai harara ya wurga masa. Tambayar shi Abba ya yi akan abin da ya faru ya faɗa masa duk abin da idanunsa suka gane masa cikin nutsuwa. Jinjina kai Abba ya yi cikin gamsuwa ya ce. "Me ya sa ka mare ta? Duk da ka girme ta ai Yaya take a gurinka yanzu." Khalifa ya ce. "Wallahi Abba ban je inda suke da niyyar taɓa jikinta ba, na yi na yi ta sake ta ne ta ƙi, ban ma san lokacin da zuciya ta ɗeɓe ni na mare tan ba." Ƙwafa Mommy ta yi tana hararar shi ba ta ce komai ba. Safwan kuwa danne zuciyarsa kawai yake don a gaban Abba ne, amma da sai ya rama wa Salma marinta, kuma idan ya tashi ba ɗaya zai masa ba, sai ya ninka marin sau uku. "To ka ja masa kunne Abba, kar ya ƙara gigin kai hannunsa jikin matata." Safwan ya faɗa a fusace. Abba ya ce. "Ita ma ka ja mata kunne akan ta dinga bin komai a sannu, ba wai abu bai kai ya kawo ba ta hau dokin zuciya, don watarana zai kai ta ga da na sani." Cikin jin haushin maganarsa Mommy ta ce. "Alhaji kana nuna masa abin da ya yi fa daidai ne, Salma ce ke da laifi kenan?" Abba ya ce. "Eh." Ganin yadda ya yi maganar fuska a haɗe ya sa ba ta kuma magana ba, amma a ranta ta ƙudurce Khalifa bai mari banza ba, za ta ɗauki mataki da kanta. Duk da Abba ya ce ya kashe maganar kar wanda ya ƙara taso ta. Salma tana mayar da rigarta Fadeela ta fito daga toilet tana faɗin. "Wai da gaske Salma tafiya za ki yi?" Ta ce. "Eh mana." "Duk missing ɗin namu da kika ce kin yi iya baki ne kenan? I thought a nan za ki kwana?" Tana taje gashin dokin dake kanta ta ce. "Gidan Mama za ni." Rukky dake kwance a kan gado tana sauraren su ta ce. "Sai yaushe kuma? Ko mu zo gidanki gobe?" Tsayawa ta yi da tazar da take cikin waro ido ta ce. "What? Gidana fa kika ce, kar ma ku soma, don Mine yana nan, kuma kun fi kowa sanin bana barin a zo mini gida idan yana nan, saboda bana ƙaunar duk wani abu da zai haɗa shi da wata mace komai ƙanƙantar shi." Dariya Ramcy ta yi ta ce. "Me a kai kenan? Idan kin ɓoye shi a gida a gurin aikinsa fa? Likita ne fa shi, likitan ma na mata, ai babu wanda zai kai shi hulɗa da mata kala-kala ma." Salma ta yi murmushi tare da faɗin. "Wannan na san aikinsa kawai yake ba ya bi ta kansu, ke koma yana bi sai dai ya gani ya ƙyale, don ba aura zai yi ba, saboda babu macen da ta isa na haɗa miji da ita duk duniyar nan. Safwan nawa ne ni kaɗai, don ni kaɗai aka halicce shi." Fadeela ta ce. "Easy bab, ba a kuri a kan namiji." "Ni na yi na kuma yi, ku zuba ido ku yi kallo, ko mutuwa na yi Safwan ba zai so wata mace ba, balle kuma ina raye." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar jakarta ta juya ta fice bayan ta ɗaga musu hannu. Da kallo suka bi ta da shi. Haleemah ba ta tanka musu ba tun ɗazu ta ce. "Iska na wahalar da mai kayan kara, wato ita har ta manta baƙar wahalar da ta sha kafin ya yarda ya aure ta?" Rukky ta ce. "Har aka yi auran fa baya son ta, yanzu ma soyayyar duk ta asiri ce." Taɓe baki Fadeela ta yi ta ce. "Zai karye ne watarana, mu ga ƙarshen jijjigi da kai da ɗagawar auren mai kuɗi, kyakkywa da ake mana." *5 days later* Yau ta kama ranar komawa asibiti karɓar sakamakon gwajin da aka yi wa A'isha. Sai a cikin kwanakin nan da suka wuce Mommy ta san A'isha makauniya ce, ranar da ta ji labarin ba ƙaramin bala'i ta yi ba, ta ce sai dai Abba ya zaɓa ko ita ko A'ishan. Don ba za ta iya zama da ita a gida ɗaya ba, ga talauci ga rashin asali sannan kuma ga makanta. Da farko Abba bai kula ta ba, sai da ta ishe shi ya ga idan bai tsawatar mata ba, ba za ta bar shi ya yi sukuni ba sannan ya ce mata ya zaɓi A'isha, ta je ta yi duk abin da za ta yi. Ƙaramin hauka ta yi da jin furucin nasa saboda ba ta taɓa zaton zai iya kallon cikin idonta ya faɗa mata haka ba. Ko Ummi bai taɓa cewa ya zaɓa a kanta ba sai wata TSINTACCIYA mara asali? Ranar kasa rintsawa ta yi saboda baƙin ciki. Tsanar A'isha mai tsanani ta ƙara cika mata zuciya. Cikin daren jiya Allah ya yi wa wani maƙocinsu rasuwa, hakan ya sa Abba da sassafe ya kira Ummi ya ce mata idan sun shirya driver zai kai su asibitin, shi zai zauna a yi jana'iza da shi. Lokacin da suke wayar Mommy tana kwance a gadonsa, da yake ita ce da girki. Duk da faɗan da suka yi kaca-kaca ba ta fasa zuwa part ɗinsa ta kwana ba. Ba tare da ta ce masa komai ba ta tashi ta fita. Jikinta har rawa yake gurin nemo lambar Kaltum ta kira ta. Sai da ta yi mata kira uku sannan ta ɗaga cikin muryar bacci. A zaƙe Mommy ta ce. "Ina kika shiga ne haka?" Khaltum ta ce. "Bacci nake, me ya faru kike mini wannan kiran da sassafe?" Numfashi Mommy ta sauke ta ce. "Wata dama na ga mun samu akan barin yarinyar can daga gidan nan, za su je asibiti ne kuma Alhaji ya ce driver ya kai su, shi ne nake ganin ko mu haɗa baki da drivern ne ya ɓatar da ita?" Khaltum ta ce. "Wannan shawara ce mai kyau gaskiya, abin da za a yi ki fara kiran direban ku yi magana ki ce masa za ki ba shi lada mai tsoka, idan suna tafiya ya bi ta cikin layika ya ce mata saboda go slow, ni kuma zan turo waɗanda za su tare su, su sace yarinyar. Ki ce ya faɗa miki irin motar da za su hau da numbern ta" Mommy ta ce. "Ta ina su waɗanda za ki turo ɗin za su san inda suke?" Khaltum ta ce. "Wanne asibitin za su je?" Mommy ta ce. "Na ji da Alhaji ya kira direban ya ce masa asibitin Makka dake b.u.k road." Khaltum ta ce. "Okay, za su jira shi a layin, zan turo miki address ɗin inda suka ce mini suke, sai ki faɗa masa ya bi ta gurin, zan kira su yanzu, na san ina faɗa musu za su tafi." Cikin matsanancin jin daɗi Mommy ta ce. "Da kyau khaltum, na rasa ma me zan ce miki saboda farinciki, kin gama mini komai da wannan tunanin naki, yarinyar nan mai siffar mayu ita kaɗai ce damuwata a yanzu." Khaltum ta ce. "Duk abin da zai saka ki farinciki a shirye nake na yi shi, ki kira direban tunda kin san waye, ni ma zan kira su yanzu." Mommy ta ce. "Shikenan sai kin ji ni." Suna gama wayar Mommy ta aika aka kira mata ɗaya daga cikin direbobin gidan mai suna Buhari wanda Abba ya kira ya ce zai kai su A'isha Asibitin, bayanin aikin da take so ya mata ta faɗa masa tare da alƙawarin 500k cash bayan komai ya kammala. Da murna ya amince, don shi bai ga wahalar aikin ba, don dai bi ta cikin layika kawai ko a 100k zai yi balle 500k. kafin 7:30 su Mommy sun gama tsara komai yadda suke so. Ummi tana kulle Bedroom ɗinta ta dubi A'isha dake kiciniyar saka hijabi ta ce. "Ki yi abu da jiki mana Nana, mun kusa yin latti fa, har takwas saura quarter fa yanzu. A'isha da take jin duk jikinta a sanyaye ba tare da ta san dalili ba ta ce. "Na rasa fuskar hijab ɗin ne." Ummi ta ce. "Sai fa da na saita miki zirawa kawai za ki yi amma kika tsaya wasa." Ta ƙarashe maganar tare karɓar hijab ɗin ta saka mata tare da kama hannunta suka nufi parking space. Buhari yana hango su ya washe baki tare da zira wayarsa da yake ƙara duba address ɗin inda za su haɗu da wanda za su ɗauke A'isha ya ce. "Sannu da fitowa Hajiya." Da fara'a Mommy ta ce. "Yawwa, an tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau" ya faɗa tare fitowa daga motar da nufin ya buɗe musu. Dakatar da shi Ummi ta yi da faɗin. "Bar shi Buhari." Risunawa ya yi cikin girmamawa ya ce. "Da kin bari na buɗe miki ranki ya daɗe." Kafin ya gama rufe baki har Ummi ta buɗe motar ta zira A'isha. Har za ta shiga sai kuma tuna ta ce masa. "Yawwa Buhari, idan mun dawo ni zan sauka a matan fada, ita kuma ka zarto da ita ka kai ta gidan Hajiya Zainab, nan maƙwabtanmu kusa da gidan da aka yi rasuwa. Ka ce mata in jini" Amsa mata ya yi tare da buɗe mazaunin direba ya shiga..........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *3️⃣1️⃣* A hankali ya buɗe murfin Motarsa ya fito daga mazaunin direba. Ummi na ƙoƙarin rufe motar da suke ciki ta ji sassanyar muryarsa yana faɗin. "Ummi." Dakatawa ta yi ganin ya nufo su, da fara'a ta ce. "Safwan, fita za ka yi ne?" A ladabce ya ce. "A'a, na ɗan fita ne ban jima da shigowa gidan ba, na zauna a cikin mota ne ina duba abu a waya." A gaggauce Ummi ta ce. "Ayya, mu ma nan asibitin za mu je yanzu, mun ma yi latti sosai." Yana gyara siririn white glass ɗin dake fuskarsa ya ce. "Wanne asibiti?" "Makka." Ɗan jim ya yi kamar mai nazari sannan ya ce. "Ki fito kawai na kai ku Ummi." "A'a Safwan kar ka tashi kanka tsaye, ga Buhari nan zai kai mu, may be kana da wani uzurin kar na tsayar da kai." "Babu komai Ummi, ku zo kawai mu je." Ya yi maganar tare da juyawa ya koma gurin motarsa. Buhari dake sauraren su ya ji tamkar ya fasa ihu, addu'a ya shiga yi a ransa Allah ya sa kar Ummi ta amince. A'isha da ta yi lamo a jikin kujera tun lokacin da ta ji muryar Safwan ta sauke numfashi jin Ummi ta kama hannunta ta fito da ita. Cikin rawar baki Buhari ya ce. "Hajiya ku koma mana na kai ku, kar a wahalar da ƙaramin Alhaji, kin san bai fiya san tuƙi da kansa ba." Ummi ta ce. "Mun riga mun fito, kuma ai shi ya ga zai iya." Bin bayansu ya yi da kallo kamar mai shirin fashewa da kuka, takaici da baƙinciki suka hana shi ya ce musu Allah ya kiyaye kamar yadda suka saba kodayaushe idan sun ga wani a gidan zai fita. Baya Ummi ta buɗe ta saka A'isha ita kuma ta shiga gaba. Buhari yana kallon su suka fice, ji yake kamar ya ruga da gudu ya je ya tsayar da Safwan ya roƙe shi ya bar shi ya kai su A'isha, 500k ɗin da aka masa alƙawari kawai yake tunani. Ya ga samu ya ga rashi. Sai a lokacin tunanin sanar da Mommy ya zo cikin kwanyarsa, cikin sauri ya rufe motar ya juya ya nufi part ɗinta. Tana zaune a kan lallusar carpet na alfarma da ya kusa mamaye tsakiyar ɗakin tana karyawa Buhari ya fara knocking. Tsaki ta ja tare da faɗin. "Wannan daga ji wani matsiyacin ɗan ƙauyen ne, ai ta buga ƙofa ba jira kamar wanda aka yi wa sata." Ta ƙara jan tsaki sannan ta ɗaga murya ta kira Murja dake kitchen. Da sauri ta fito tana goge hannunta a jikin zaninta. "Je ki ga waye yake mini wannan bugun haukan da farar safiyar nan." Ta faɗa a lalace. Amsa mata Murja ta yi ta nufi ƙofa. Baby dake saukowa daga kan steps cikin shirin tafiya school ta ja tsaki cikin yamutsa fuska ta ce. "Wai wanne mahaukacin ne a nan? An taho ana buɗewa amma ya ƙi daina cika wa mutune kunne." Rufe bakinta ya yi daidai da faɗowar Buhari parlour'n kamar wanda aka ingizo. "Malam lafiya za ka shigo mana har cikin parlour ba tare da neman izini ba?" Baby ta faɗa a wulaƙance cikin daka tsawa tana jifan shi da wani shegen kallo. Ƙasa ya yi da kansa a ladabce ya ce. "Gurin Hajiya na zo." Mommy da take masa kallo mai cike da tarin tambayoyi ta ce. "Na san da zuwansa, bar shi ya ƙaraso." Cikin mamakin yadda ta yi magana ba hargagi kamar yadda ta saba yi wa ma'aikatan gidan Baby da Murja ke kallon ta, don hakan baƙon abu ne a gurinsu. Fita Baby ta yi bayan ta mata sallama, a ranta tana tambayar kanta abin da zai haɗa Mommy da Buhari. Murja ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta koma kitchen ta cigaba da abin da take. "Ina sauraren ka Buhari, me ya dawo da kai?" Mommy ta faɗa cikin son jin abin da ke tafe da shi. Numfashi ya sauke ya ce. "Ranki ya daɗe an samu matsala, don Alhaji ƙarami ne ya tafi ya kai su asibitin." Cikin rashin fahimta ta ce. "Ban fahimci me kake nufi ba, wanne Alhajin ƙaramin?" "Na ki Hajiya." Buhari ya faɗa tare da ba ta labarin yadda aka yi. A zabure Mommy ta miƙe ta wanka masa mari a kuncinsa dama da hagu. Dafewa ya yi cikin sauri tare da kallon ta, cikin masifa ta ce. "Wanne irin mara lissafi da hankali ne kai? Tun lokacin da ya zo yana musu maganar ba ka kira ni ba ko da a waya ne sai yanzu bayan sun tafi?" Ƙasa ya yi da kansa tare da yin ɗurƙuso kamar mai shirin yi mata sujjada ya ce. "Allah ya huci zuciyarki Hajjaju makkatu, ban yi tunanin za su shiga motar tasa ba ne." Jijjiga kai ta yi tana jin kamar abincin da ta ci zai dawo mata ta kai saboda tashin hankali, baƙicikinta biyu ne, wargazewar da shirinsu ya yi da kuma kai su Ummi asibiti da Safwan ya yafi. Rasa ma abin cewa ta yi saboda tsananin ɓacin rai. Juyawa ta yi ba tare da ta kuma magana ba ta nufi gurin wayarta don kiran Safwan ta sanar masa ya juye su Ummi ko a tsakiyar titi ne ya dawo gida. Ganin haka ya saka Buhari tashi ya fice hannunsa da dafe da kuncisa. A ransa yana Allah wadai da rashin wadatar zuci da kwaɗayi, don su suka janyo masa shan wannan tagwayen marukan a gurin matar da ba ta fi sa'arsa ba. Ga shi ya yi ba wan ba ƙanin. Sai da suka hau titi Safwan ya dubi Ummi ya ce. "Ina kwana." Ummi ta ce. "Lafiya ƙalau, ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah." "Yau ka je aikin kenan? Ya ce. "A'a, ban koma ba sai this coming Monday in sha Allah, saƙo Mum ta aike ni na kai mata gidan wata friend ɗinta." Gyaɗa kai Ummi ta yi tare da juyawa baya ta kalli A'isha da ta tsit kamar ba ta Motar, ta ce. "Nana ba ki gaishe da Yayanku ba." Numfashi ta sauke cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana." Ya amsa da "Lafiya." A taƙaice. Ba ta kuma magana ta mayar da idanunta ta lumshe, ƙamshinsa da ya kama motar da sanyin ac na ratsa ta. A lokacin kiran Mommy ya shigo wayarsa, dubawa ya yi, ganin ita ce ya ƙi ɗauka don ya san kwanan zancen. Ita kuma sai kira take ba ƙaƙƙautawa. Ganin haka ya sa Ummi ta ce masa. "Ka ɗaga kiran da ake maka mana." Yana sauke numfashi ya ce. "Mommy ce, idan muka ƙarasa zan kira ta." A matuƙar hasale ta janye wayar daga kunnenta ta mayar da akalar kiran ga Khaltum. Ringing ɗaya ta ɗaga tare da faɗin. "Su Caska sun kira ni, wai har yanzu ba su ƙarasa ba." Kamar Mommy za ta yi kuka ta ce. "Ai komai ya wargaje Khaltum, wai Safwan ne ya tafi kai su." "What? Safwan kuma? A kan me? Ko uban ne ya ce ya kai su?" Cikin ɗunbun baƙin ciki Mommy ta ce. "Ina fa? A yadda Buhari driver ya ce mini wai shi ya ce su fito ya kai su da kansa, tun ba yau ba nake faɗa matar nan fa ta asirce mini ɗa, tun yana rarrafe idan na aika aka ɗauko mini shi daga gurinta sai ya ƙara rarrafawa ya koma, na rasa yaya zan yi matar nan ta bar mini ɗana." Khaltum ta ce. "Kar ki damu Saratu, Gobe zan je gurin na kan tudu, zan saka a yi musu farraƙu, wannan duk ba wata matsala ba ne. Damuwata yanzu wargajewar aikin nan wallahi. Amma kuma ai kin faɗa mini likitar da ta yi wa yarinyar gwaje-gwaje last time da suka je kin san ta ko? Ta kira ni ta faɗa miki." Mommy ta ce. "Eh, ƙanwar Hajiya Zubaida ƙawata ce, tunda suka je ta gan su take kira na a waya ba ta same ba, sai bayan kwana biyu take faɗa mini." Khaltum ta ce. "To ai ta kwana gidan sauƙi, me zai hana mu haɗa baki da ita a ƙara lalata idon yarinyar." Murmushi Mommy ta yi ta ce. "Maganar da muke yi da ita kenan, don ta sanar mini tana sane ta ce su dawo bayan sati ɗaya saboda su zo ranar dutinta, ita duk ɗaukar ta ma Yarinyar Mufeedah ce." Khaltum ta ce. "Ni ma farko da na ga Yarinyar ranar da na zo na ɗauka ita ce, saboda suna kama sosai." Haka kawai Mommy ta ji gabanta ya faɗi da ta hasaso fuskar A'isha a cikin ranta, don ba ƙarya aka yi ba suna yanayi da Mufeedah ƴar Ummi. Kalar da fatarsu da girman jikinsu ɗaya. Taɓe baki ta yi ta ce. "Su suka sani, yanzu dai zan kira Doctor Zulaihat ɗin, duk yadda muka yi da ita za ki ji." Khaltum ta ce. "Ina sauraren ki." Daga haka suka yi sallama. Zama Mommy ta yi a kan kujera tare da dafe kanta, ta rasa me ya sa A'isha ta tsaya mata a rai, ba iya ƙin ta da take mata na talauci ne kawai ya sa ba ta son zamanta a gidan ba, har na fargabar da take ziyartar ta a duk lokacin da ta tuna da yarinyar ba tare da ta son dalili ba, shi ya sa ta damu ta bar gidan, saboda ko ma mene ne idan ta tafi shikenan. Wani balaraben doctor suka samu yau, ya duba A'isha ya ƙara yi mata text a idon sannan ya ce su jira shi. After 1 hour ya fito da result ɗin abin da ke damun idon ya ba su bayan ya yi wa Ummi bayanin yadda yake. Ya ƙara da ce mata aiki za a yi wa idanun, ya faɗa mata kuɗin aikin tare da ba ta takardar da za a biya kuɗin. Farinciki sosai Ummi ta yi, tare da addu'ar Allah ya sa a yi aikin cikin nasara. Safwan yana mota suka fito hannunta riƙe da na A'isha. Tana buɗe baya za ta saka A'isha ta ce. "Safwan I'm sorry, na tsayar da kai kana ta jira." Murmushi ya yi ya ce. "Haba Ummi, babu komai ai." Takardun hannunta ta miƙa masa ya karɓa ya duba, bayan Ummi ta shiga front seat ta ce. "Daɗina da Asibitin nan komai nasu babu ɓata lokaci, idan muka yi payment a gobe cikin satin nan ma za su iya yi mata aikin." kallon A'isha ya yi ta madubi, ba tare da ya ɗauke idonsa daga kanta ba ya ce. "Allah ya sa a yi a sa'a." Ummi ta ce. "Amin, ka kai mu gidan Ruƙayya kawai mu ajiye ta a can, sai mu wuce ka sauke ni a school." Gyaɗa mata kai ya yi tare da kunna motar. Aunty Ruƙayya tana sharar parlour suka shiga da sallama. Amsa musu ta yi tare da faɗin. "Sannun ku da zuwa, tun ɗazu nake dakon zuwan ku, na san yau ce ranar dawowar ku asibiti." Ummi ta zauna tare da faɗin. "Kuma da ba za mu zo nan ɗin ba wucewa za mu yi." "Saboda me?" "Kawai, har na cewa driver ya kai ta gidan Hajiya Zainab ta zauna kafin na dawo daga school, da ke kwana biyu can nake kai ta idan zan fita." Aunty Ruƙayya ta ce. "Da ba ki kyauta mini ba kuwa." "Ina kwana Aunty." A'isha ta faɗa cikin sanyinta." "Lafiya ƙalau Mamana, ya fuska?" "Alhamdulillah." Ummi ta ce. "Cikin satin nan za a yi aiki ma in sha Allah." Aunty Rukayya ta ce. "Masha Allah, Allah ya sa a yi a sa'a." Suka amsa da Amin. Ummi ta ba ta takardun ta duba tare da faɗa mata yadda suka yi da likitan. Aunty Ruƙayya ta ce. "Haka na san asibitin Makka ba su da wasa, kana zuwa ana duba ka za a saka maka ranar aiki idan ciwon na aiki ne, shi ya sa na yi mamaki da kika ce an ba ku har 1 week ku dawo karɓar result." Ummi ta ce. "Ni ma na yi mamaki, har Abbansu sai da na yi wa complain, ya ce to ya za mu yi tunda haka suka ce." Aunty Ruƙayya ta ce. "Haka ne." Miƙewa Ummi ta yi tana duban A'isha ta ce. "Zan wuce Nana, Khalifa ko driver za su zo su ɗauke ki." Gyaɗa mata kai ta yi a hankali ta ce. "Allah ya kiyaye." Ummi ta ce. "Amin." Tare da juyawa ta fita, Aunty Ruƙayya ta bi bayanta don yi mata rakiya. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin yadda tsoron aikin da aka ce za a mata ya cika mata zuciya, gani take kamar ko an yi aikin idon ba zai buɗe ba. Amma tana addu'ar Allah ya sa a yi cikin nasara, ita ma ta cigaba da gani kamar kowa. Numfashi ta sauke tana tuno mutane masu ƙololuwar daraja a cikin rayuwarta, wanda suke fata da burin ganin ranar barin ta daga makanta. Inna ce farko, wadda Ubangiji ya rubuta ba za ta ga wannan ranar ba, sai Umar da ba za ta taɓa mantawa da shi a cikin rayuwarta ba, duk da abin da take ji a kansa a cikin zuciyarta kaso mai yawa ya ragu, amma duk da haka ba za ta manta da Alkhairinsa ba, sai Innar Ma'u da ita kanta Ma'un, su kuma ba ta san a ina za ta gan su ba. Lokacin da Safwan ya koma gida Mommy ba ta nuna masa ɓacin ranta ba a kan kai su Ummi asibiti da ya yi, saboda tsananin so da ji da shi ɗin da take ya sa ba ta iya yi masa faɗa. Sai dai tay ta zagin Ummi a gabansa tana cewa ba ƙaunar shi take ba, lunbu-lunbu take masa take jan shi a jiki, cikin ranta kuma tana da wani mugun nufin a kansa. Shi dai ba ya tanka mata idan tana maganganunta. Salma na tsaye a gaban mirror tana kwalliya, wayarta dake kan mudubin ta fara ruri. Ɗauka ta yi ganin Fadeela ce tare da faɗin. "Ba dai har kun shirya ba?" Fadeela ta ce. "Tun yaushe? Ke kaɗai muke jira." Cikin fariya ta ce. "No ku wuce kawai ba sai kun jira ni ba, Mine ne zai kawo ni." Baƙi Fadeela ta taɓe ta ce. "Ok." Tare da katse kiran. Ihsan tana koya A'isha karatun Alkur'ani a baranda Safwan ya shigo gidan. Tun kafin ya ƙaraso inda suke ƙamshinsa ya ziyarce su. Da sauri A'isha da ta san me ƙamshin ta ɗago kanta duk da gani take ba. Sallamarsa cikin kaushin murya ta saka Ihsan ɗagowa ta dube shi, cikin girmamawa ta ce. "Sannu da zuwa." "Yawwa." Ya amsa idanunsa a kan wayarsa dake hannunsa. Miƙewa Ihsan ta yi tana faɗin. "Yayanku ya zo daukar ki, bari na sanar da Mami." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi tare da yin ƙasa da kanta. Kamar mai tsoron magana ta ce. "Ina yini?" Duk da ya san da shi take amma ko ɗagowa bai yi ba balle ya amsa. Ɓata fuska ta yi don ta tsani ta yi wa mutum magana ya ƙi amsawa, yadda ƙamshinsa ya cika mata hanci ta san yana kusa da itan da idan ta yi magana zai ji. Dawowar Ihsan da Aunty Ruƙayya ya sa ta sakin ajiyar zuciya, don duk jin ta take a takure kasancewar su kaɗai a guri ɗaya. "Safwan kai ta kuma tasowa?" Cewar Aunty Ruƙayya tana duban shi. Murmushi ya yi ya ce. "Ina yini?" Ta ce. "Lafiya ƙalau." Tare da mayar da duban ta ga Ihsan ta ce. "Kama hannunta ki raka su mota, kin ɗauko mata saƙonta dai ko?" Ihsan ta ce. "Eh gasu nan." Ta kama hannun A'isha da ta miƙe tsaye. Aunty ta ce. "To Mamana, ku gaida gida." "Zai ji in sha Allahu, na gode Aunty." Tunda Ihsan ta saka ta a mota ta sunkuyar da kanta ba ta ɗago ba, shi kuwa dama ko kallon inda take bai yi ba, driving ɗinsa kawai yake. Lokaci zuwa lokaci yana duba wayarsa da kira ke shigowa ba ƙaƙƙautawa. Tsaki Salma ta ja karo na babu adadi ta dubi Baby da za su fita tare ta ce. "Wai ina Mine ya shiga ne? Ina ta kiran shi ya ƙi ɗauka, kuma ya san zai kai ni unguwa yanzu, na faɗa masa fa." Baby ta ce. "May be driving yake shi ya sa bai ɗaga ba." A fusace ta ce. "Amma ai ko parking sai ya yi ya ɗaga kira na, idan mun gama wayar ya cigaba." Kallon mamaki Baby ta mata, a ranta tana faɗin. "Sannu Mommy." Amma a fili ba ta yi magana ba, sanin halin masifar Salman sai ta huce a kanta. Ganin har biyar ta wuce bai dawo ba bai kuma ɗaga kiran ta ba ya sa ta miƙewa a ƙufule ta nufi parking space da nufin ta tafi kawai a motarta, ta gaji da jira, kuma ta san zuwa yanzu an kusa gama birthday ɗin da za ta. Amma fa ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, saboda ta gama cin burin Safwan ne zai kai ta, ya buɗe mata mota a gaban ƙawayenta, ta nuna musu yanzu a tafin hannunta yake. Tana ƙarasawa parking space ɗin motarsa na shigowa, ko bari ya gama parking ba ta yi ba ta nufi inda suke a fusace tare da saka hannu ta kama murfin motar na front seat.........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *3️⃣2️⃣* "Aunty Salma." Baby dake bin ta a baya ta kira sunanta. Tsayawa ta yi tare da juyawa ba tare da ta buɗe motar ba. "Mene ne?" Ta faɗa a zafafe. Baby ta ce. "Stain na ga kin yi, kuma na san ba ki sani ba." Cikin takaici ta ce. "What?" Tare da fara dudduba jikinta. Tsaki ta ja ganin yadda jikinta ya ɓaci da jini ta gurin zama. Kamar za ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki, bin bayanta Baby ta yi don ita ta yanke ta ma fasa fitar. Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke wadda ta sa A'isha ɗagowa da sauri ta kalli saitin da yake kamar mai ganin shi. Ƙura mata ido ya yi na wasu sakanni sannan ya sauke numfashi, lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai. Jan motar ya yi ya ƙarasa har kusa da part ɗin su Ummi. Ba tare ya yi magana ya fita ya buɗe ɓarin da take. Duk da bai yi magana ba amma motsin buɗe ƙofar ya sa ta yunƙurawa ta fito tana laluben hanya da hannunta. Mayar da ƙofar ya yi ya rufe. A hankali ta ce. "Na gode." Ko kallon ta bai yi ba ya koma cikin motar ya bar ta da zullumin yadda za ta iya shiga ciki. Daidai lokacin Lubna ƴar Hajiya Zainab ta fito daga ciki. Da mamaki ta ce. "Nana dana ina na gan ki ke kaɗai?" Cikin jin daɗi ta ce. "Ba ni kaɗai ba ce, yanzu aka sauke ni." Kallon motar Lubna ta yi ta ƙaraso ta kama hannunta suka shiga ciki. Da mamaki Ummi ke Kallon su har suka zauna. Tana duban A'isha ta ce "Wa ya dawo da ke? Yanzu nake ƙoƙarin kiran Khalifa na ce masa ya biya ya ɗauko ki." A'isha ta ce. "Wanda ya kai mu ne." Cikin ɗaurewar kai Ummi ta ce. "Safwan?" Gyaɗa mata kai ta yi. Ummi ta ce. "Ikon Allah, to an gode masa." Tana saka wani kayan ya shiga ɗakin. Murya ƙasa-ƙasa ya yi sallama. Wani kallo ta wurga masa mai haɗe da harara, ba tare da ta amsa masa sallamar ba ta ce. "Ina ka je?" Cikin danne tsoron da yake ransa ya ce. "Abba ne ya aike ni, kafin na ƙarasa inda zan je muka samu accident na buge wasu." Ɗauke idonta ta yi daga kansa ta ce. "Daga nan kuma sai yaya?" "Hospital na kai su aka yi musu duk abin da ya dace, lokacin da kikkira wayar tana mota na bar ta a ciki." Cikin gamsuwa ta ce. "Amma da ka kai su Hospital ɗinka yaranka sun kula da su ai, tunda ka san you keep me waiting." "I'm sorry." Ya faɗa cikin sauke ajiyar zuciya tare da hugging ɗinta. Da daddare Ummi ta kama hannun A'isha zuwa part ɗin Abba. Yana zaune shi kaɗai a parlonsa yana karatun Alkur'ani suka shiga. Bayan ya kai aya ya amsa musu sallamar da suka yi. Ummi ta ce. "Barka da dare Abba." Ya ce. "Yawwa DR." Cikin ladabi ita ma A'isha ta gaishe shi, ya amsa cikin kulawa da fara'a. Bayan Ummi ta faɗa masa yadda suka yi a asibiti ya ce. "Masha Allahu, Ubangiji ya sa a yi aikin a sa'a, gobe idan Allah ya kai mu sai mu je a biya kuɗin." Ummi ta ce. "Allah ya nufa ya saka da Alkhairi." Abba ya amsa da "Amin." A'isha da ta rasa kalmomin da za ta yi amfani da su ta gode wa waɗannan mutanen masu karamci, mutunci da tausayi ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ji ƙan mahaifa ya saka da gidan Aljanna." Cikin murmushi ya ce. "Amin amin daughter, Allah ya yi miki albarka ya ba ki lafiya." Suka amsa da Amin gabaɗaya. Gyara zama Ummi ta yi ta ce. "Ɗazu principle ɗin su Muneefah ta kira ni wai ba ta da lafiya a je ɗauko ta." Abba ya ce. "Subhanallahi, Allah ya kai mu gobe sai Khalifa ya je ya ɗauko ta, Allah ya sa jikin ba tsanani ya yi ba sosai." Ummi ta ce. "Muneefah ce fa, za ta iya kwanciya ciwon ƙarya ma, ka san ta tsani makarantar nan kamar mutuwarta." Abba ya ce. "A'a fa, autata ba za ta yi haka ba." Ummi ta ce. "Toh shikenan Allah ya kai mu goben ka gani." Kafin Abba ya ƙara magana Safwan da Salma sun shigo, wadda ke tafiya cikin taƙama tamkar basarakiya. Kan dole ba don son ranta ba ta zauna a ƙasa. Ba yabo ba fallasa ta gaishe da Abba, Ummi kuwa kamar an mata dole. Abba yana duban Safwan ya ce. "Gobe za ka je Gomben ko?" Gyaɗa masa kai ya yi. Ummi ta yi murmurshi ta ce. "Za a je gaishe da Gwaggo kenan?" Ya ce. "Eh, tunda ta ce sai dai ni na je ita ba za ta zo ta mini sannu da zuwa ba." Ummi ta ce. "Gwaggo kenan, idan ka je ka gaishe ta da kyau." Ya ce "Za ta ji in sha Allah." Tunda Salma ta zauna idanunta na kan A'isha, ita ta manta da Yarinyar ma gabaɗaya sai yau da ta gan ta. Bayan sun fita ta biya part ɗin Mommy take tambayar ta wacece A'isha a gidan? Mommy ta ce. "Au Khaltum ba ta faɗa miki ba? Na ɗauka da kika je ai ta miki bayani." Salma ta ce. "ko ɗaya, ai ba mu taɓa zancen yarinyar da ita ba." Taɓe baki Mommy ta yi ta ce. "Wai daga Alhaji ya kaɗe su ita da uwarta uwar ta mutu shikenan ya ce zai riƙe ta saboda rashin sanin ciwon kai, mutum ce aljana ce mayya ce sai Allah." Salma ta ce. "Ban gane ba, wai yana nufin shikenan a gidan za ta cigaba da rayuwa?" Mommy ta ce. "Eh mana, na nusar da shi illar hakan amma ya ƙi ganewa, wai shi Sarkin taimako." Cikin haƙiƙancewa Salma ta ce. "Idan taimakon ta zai yi ya kai ta orphanage mana ko police station a yi cikiyar iyayenta idan ba ta san inda suke ba, ni fa farko da na gan ta I thought ƴar'uwar waccan matar ce, ashe ma tsinto aka yi daga sama a titi. To gaskiya ba zai yiyu ba, babu yadda za a yi mu yi rayuwa da wata bare a gida ɗaya, dole a san abin yi yarinyar nan ta bar gidan nan." Mommy ta ce. "Ƙoƙarin da nake ta yi kenan." Salma ta ce. "Better, don ba zan yarda Mijina yana ganin wata mace ba bayan siblings ɗinsa ba." Mommy ta bi ta da kallo kawai ba ta ce komai ba. Washegari da safe A'isha na zaune ita kaɗai a parlour tana karyawa Khalifa ya shigo. Bayan ya yi sallama ya zauna a kusa da ita. Cikin sanyinta ta ce. "Ina kwana?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, 2 days ba mu haɗu ba ko cikiya ta ba kya yi ko?" Ta ce. "Na tambayi Ummi ta ce kana gurin aiki." Cikin murmushi ya ce. "Dagaske?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce. "Ya jikin naki? I hope dai yanzu kin warware?" Ta ce. "Eh Alhamdulillah." Ya ce. "Ina Ummi?" Ta ce. "Tana kitchen." Miƙewa ya yi ya shiga kitchen ɗin. Bayan sun gaisa Ummi ta ce. "Abba ya faɗa maka za ka je ka ɗauko Muneefah ko?" Ya ce. "Eh, amma sai na je office na yi abu daga nan zan wuce." Ummi ta ce. "Toh shikenan Allah ya kiyaye." Ya amsa da Amin sannan ya dawo parlour'n. Ummi ta biyo shi da breakfast ɗinsa. Bayan ya gama ci ya dubi A'isha ya ce. "Zan fita, me kike son na taho miki da shi?" Shiru ta yi kamar mai nazari. Ya ce "Yau fa sai kin faɗa mini duk zamiyar ki." Murmushi ta yi ta ce. "Komai ma, amma abin zaƙi." Ya ce. "Shikenan shazumama, sai na dawo." "Allah ya tsare." Ta faɗa idonta a kan direction ɗin inda take jiyo muryarsa. Kafin 8 sun je asibitin, Abba ya biya kuɗin aikin, ba a saka ranar aikin da nisa ba, Monday za a yi mata da safe. Tunda suka dawo gida A'isha take kwance a ɗaki, ta rasa me ya sa tsoro mai tsanani ya kamata akan aikin. Misalin ƙarfe ɗaya Ummi tana kitchen tana girki Muneefah ta shigo parlour'n da gudu tana ƙwala wa Ummi kira, ta manta da wani langwaɓewa na pretending ɗin cuta da take. Ganin babu kowa a parlour'n ta nufi kitchen ta rungume Ummi ta baya. Ummi ta ce. "Mene haka? Bana son shashancin nan naki fa?" A shagwaɓe ta ce. "Kai Ummi, duk murnar ganin ki ce fa." Ummi ta ce. "To patient, cutar kenan?" Murmushi ta yi ta ce. "Ina ganin ki na warke Ummita." "Allah ya shirye ki Muneefah, da kin yi haƙuri ma jibi za a yi hutu." Ɓata fuska ta yi ta ce. "Ni fa bana son boarding school ɗin nan ko kaɗan, Abba yana dawowa zan faɗa masa a mayar da ni Day." Ummi ta ce. "Zan fi kowa murna da hakan, dama aikin gidan nan ya mini yawa, in kina nan kuwa sai dai na miƙe ƙafa." Ta ce. "Toh shikenan, bari na ƙarasa na ga ɗakina, na yi kewar shi." A'isha tana kwance ta ji an shigo ɗakin, Muneefah ba ta lura da ita ba har ta ajiye trolley ɗinta. Sai da fara cire kayan jikinta ta lura da A'isha. Da mamaki ta ce. "Ihsan ko Mufeedah?" Miƙewa zaune A'isha ta yi don ta fahimci autar Ummi da ake yawan zancen ta ce ta dawo. "Sannu da zuwa." Muneefah ta ce. "Yawwa." Tare da juyawa ta fice daga ɗakin da sauri. Gurin Ummi ta koma tana faɗin. "Ummi wace ce waccan a ɗakina mai kama da ni?" Ummi ta ce. "Yar'uwarki ce." Cikin jin daɗi ta ce. "A gidan nan take?" Ummi ta ce. "Eh." Da murna ta ce "Na samu abokiyar hira, Allah ya sa kar ta tafi, mu yi ta zama tare." Ta ƙarashe maganar tare da juya cikin sauri ta koma ɗakin. Bayan ta zauna a kusa da A'isha ta ce. "Ya sunanki?" "A'isha." "Sunan Maman Ummi da Abba da Ya Maamah." A'isha ta yi murmurshi kawai. Muneefah ta ce. "Ni kuma sunana Khadija, sunan ƙanwar Ummi ne shi ya sa ake ce mini Muneefah." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Ba ta damu ba ta cigaba da magana. "Kina da kyau Masha Allah, ga kalar fatarki ma mai kyau, ana ganin kyan tawa amma taki ta fi, idanunki ma masu kyau irin na Yayanmu, ai kin san shi ko?" Girgiza mata kai A'isha ta yi alamun a'a. Da mamaki ta ce. "Kuma Ya Khalifa ya ce mini ya dawo, shi ne babban Yayanmu, duk ya fi kowa kyau a gidan nan, Likita ne, yana da Hospital ɗinsa na kansa a bayan layin nan mai suna *S.S.GIƊAƊO*, sunansa da sunan Abba ya haɗa *Safwan Sa'id Giɗaɗo*." Ta taɓe baki sannan ta ce. "Amma matarsa sai ta dinga cewa S.S ɗin wai sunanta da nasa ya haɗa, wai Salma and Safwan, ko daɗi ma babu." Murmushi kawai A'isha ta yi, a ranta tana mamakin surutu irin na Muneefah, daga ji ita ma babu ruwanta. Ummi ce ta shigo ɗakin tana faɗin. "Kina nan kina cika ta da surutu ko?" Ta ce. "Hira fa muke yi Ummi." "Ya yi kyau, ki kama hannunta ku je toilet ku yi alwala, idan kun yi sallar sai ku fito ku ci abinci, ki yi mata a hankali kuma saboda ba ta gani." Waro ido Muneefah ta yi ta ce. "Makauniya ce?" Ummi ta ce. "Ban sani ba, ki yi abin da na ce kawai." Cikin mamaki da tausayawa ta kama hannun A'isha tana faɗin. "I'm sorry sis, ban sani ba." Da yamma Ummi ta dawo daga gidan rasuwa ta shiga ɗakin Muneefah ta tarar da ita tana shirya kaya a wardrobe. Daga bakin ƙofa ta ce. "Ina Nana na gan ki ke kaɗai?" "Tana parlour a kwance." Ummi ta ce. "Wanne parlour'n?" "Parlour'n ƙasa." Ummi ta ce. "To ni ban gan ta ba, mu je ki nunan inda take." Babu musu ta miƙe suka fita. Ganin ba ta parlour'n a ruɗe Muneefah ta ce. "A nan fa na bar ta na shiga ɗaki yanzun nan." Wani kallo Ummi ta wurga mata ba ta ce komai ba ta shiga duddubawa. Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba, duk inda suke tunanin za su ga A'isha sun duba ba su gan ta ba. Hankali a tashe Ummi ta fita ta duba compound da bayan gidan amma ba ta gan ta ba. A ruɗe ta nufi gurin masu gadi ta tambaye su ko sun ga fitar A'isha? Suka ce mata ba su gani ba, kuma tunda ta fita har ta dawo babu wanda ya shigo gidan ko ya fita.........✍️ *Anan na kawo ƙarshen littafin KOMAI NISAN DARE part one, kamar yadda na faɗa kuma part two na kuɗi ne, mai so ya tuntube ni a 09047871750, sai na ji ku masoya.*