Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 1 Ƙauyen Damagaran Tsaye take tamkar wata soja, tana kallon Ma'u mai gyaɗa, cikin zallar rashin kunya da fitsara. Cikin shiga ta riga da zani da ɗankwali duk daban, sai kuma ɗammara da ta sha da baƙin gyale. Fuskarta ɗauke da kwalliya irin ta 'yan ƙauye, waɗanda suka amsa sunan su 'yan mata, kuma suke ganiyar tashen ƙuruciya. Wata kalar hoda ta shafa a fuskarta, duk ta yi mata butsu-butsu. Sai kuma gira aka ɗauke shi, tun da ga kan farkon girar, har zuwa kusa da idanunta, sannan aka haɗe jagirar da kwallin da ta sanya a idanunta. Wasu irin bille guda biyu ta zane fuskarta da shi, sannan aka ja baƙi a saman leɓenta. Silifas yake a ƙafarta duk ya tsiɗe, yayi datti, domin duk wanda ya ga silifas ɗin, zai rantse ba a taɓa sanya masa ruwa an wanke ba. Ita a dole ta yi kwalliya kuma ta yi kyau ta ƙure a daka, amma kana ganinta za ka tabbatar da ƙazamiya ce sosai, irin ƙazaman nan, da an gansu za ka gane su, saboda in ta matso kusa da mutum, da ƙyar zai iya shaƙar numfashi. Saboda ƙazantarta sam mutum ba zai iya gane fara ce ko baƙa ba, sannan kyakkyawa ce ko mummuna. Duk wanda aka sanya ya fasalta ta;mummuna, bagidajiya, ƙazamiya kuma mara tarbiya. Jimmalo jikar Tani kenan, wacce ta gagari kowa a ƙauyen Badarawa. Sam babu wanda yake shan ruwa a hannunta, babba ko yaro, saboda ba ta da kunya da haƙuri, uwa uba kuma ɗaurin gindin da ta samu a gurin Kanta Tani, wacce a halin yanzu ita ce ta zame mata uwa da uba. Tsawon lokacin da ta ɗauka, tana tsaye ba tare da ta jirga ba, jiran Ma'u mai gyaɗa take yi, wacce ta bita har cikin gidanta ta ɗauko mata gyaɗa. Bazawara ce irin masifaffun nan, domin jarabarta ya sanya ko sati uku ba ta yi ba, mijinta ya sake ta. Tun daga wannan lokacin ta fara aure ana sakin ta, saboda tsananin masifarta. Ko a ƙauyen mutane suna shakkarta, sai dai ta bambanta da Jimmalo, domin in har ba ka kula ta ba sam ba za ta shiga sabgar ka ba, amma Jimmalo ita kowa takala take yi. Tun da ta gane ana tsoron Ma'u a ƙauyen ita kuma ta ɗauka ɗamarar faɗa da ita. Duk lokacin da jarabarta ya tashi, gidan Ma'u take wucewa ta je ta iban mata gyaɗa don ta takale ta. Sosai ta girme ta domin ba sa'arta bace, amma saboda jarabarta da rashin kunyarta take shakkarta. Jimmalo sam ba ta da haƙuri ga ta da nacin tsiya a faɗa, musamman in har ita aka cuta. Ta rinƙa bibiyar mutum har sai ta rama abin da aka yi mata. Shekarun ta duka sha huɗu, amma abubuwan da take yi ya girme shekarunta. Sai dai duk wannan halayen da take da shi, tana da girman kai da nuna isa da kuma gadara, sannan ga shegen kafiya, akwai lokacin da duk yadda mutum ya so ta kula shi ba za ta kula ba. Da gudu ta shallake katangar gidan Ma'u mai gyaɗa tana dariya, ganin ta nufo ta da muciya. Ma'u mai gyaɗa cikin tsananin ɓacin rai take kallonta. "Wallahi Jimmalo, yau ni da ke ne a ƙauyen nan domin babu wanda ya isa, ya ci mini bashin gyaɗata ya zauna lafiya, ballantana ki shigo har cikin gidana ki ina ina gani ki gudu. Jimmalo dake kallonta tana dariyar ƙeta."Kin san cewar in har kika na ce sai kin karɓi kuɗin nan, za ki ja wa kanku tashin hankali? Don na rantse yau ko Babanki Tanimu zai taso da ga ƙabari ya yi mini fatalwa ba zan bayar da kuɗin nan ba." "Ni kuma wallahi sai kin bani, Kuma daga yau sai na kawo ƙarshen shigo mini gida da kike yi ba tare da izini ba." Ta ce tana gyara ɗanmarar da ta ji, tamkar wacce za ta yi dabbe. "Gidan na ki ai ba aljanna bace, da sai mutum ya yi aikin lada za a barshi ya shiga. Gidan da yake wari shadda ta cika kin ƙi kwashewa. Na ci na ƙarfi na ci na tsiya da dabbe. In kina da ƙarfi ki zo ki ƙwata, kin san dai ki ba irin dolayen mazan da kike aure bane kina musu duka, domin wallahi ɗaukar ki zan yi na tula da ƙasa." Ta ce tana murguɗa mata baki, tare da harararta. Kallon kanta ta yi, jin abin da ta ce saboda Ma'u irin matan nanne masu jiki, yayin da Jimmalo take siririya sai tsawo kamar rama. "Ni za ki nuna wa Allah ki ƙwala da ƙasa?" Ta yi mata tambayar cikin takaici. "Eh mana saboda ba irin mazan da kike aure bane. Ɗube ta ƙatuwa amma ta kasa zaman aure." "Don ubanki na fi ki saboda ni ina auruwa, ke kuwa tun da kika zama 'yan mata, babu karen da ya zo gurinki. Ƙazamiya mai warin balaga." Jin abin da ta ce kuma ta yanke ta da yawa, sai kawai ta ɗauki dutse ta ƙwala mata. Ta ci sa'a kuwa ta same ta a ƙafa. "Kan uba! Wallahi yau sai na biki ko cikin mamanki za ki koma, na ga uban da ya tsaya miki." Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka tare da kwasa da gudu. Ganin haka itama ta ɗaga bujenta ta kwasa a gije. Gudu take yi sosai kamar wata 'yar tsuntsuwa, don tsalle take bugawa dai ta shalle guri mai nisa. Ba ta tsaya a ko'ina ba sai da ta ga ta kai ƙofar gidan, sannan ta tsaya tare da yi mata gwalo da daƙuwa ta shige cikin gidan. "Wallahi yau ko bayan Atine za ki shiga sai na biki, tun da ba ki da kunya, gabakiɗaya kin addabi mutanen ƙauyen nan." Ta ce cikin fushi tare da shiga cikin gidan. Da gudu ta shallake Baba Aitine da take tsaye a bakin ƙofa, tana ƙoƙarin ɗora bushashshen tuwon da za ta shanya. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don ubanki yau wane mara haƙurin kika tono kuma, har ya ja aka yi mini asarar bushashshen tuwo?" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Tura baki ta yi tana harararta, sai kuma ta kalli Ma'u mai gyaɗa da ta shigo ciki. "Uhumh, da na na san sai ke jarababba mara haƙuri." Ta ce tana watsa mata mugun kallo wacce take tsaye tana nishi kamar ta haɗiyi kwaɗo. "Wannan mara haƙurin ne daga na ci bashin gyaɗa, na ce mata ranar da jakin baba ya yi ƙaho zan ba ta, shi ne ta yi mini duka kuma ta biyo ni." Ta ƙarashe maganar tana ƙaƙalo hawayen ƙarya. "Da ma na san sai ita ai, sam ba ta da haƙuri sam, duk ƙauye nan ita ce kawai za ta biyo ki har cikin gida, tun da ba ta da ido. Ai ko mutuwa na kunyar idon mahaifi. Haka kawai kin kashe auren ki kin addabi jakalle ta." "Kin san abin da ta yi mini ne? Don ta gaya miki ƙarya sai ki kama? Ina cikin ɗaurin gyaɗata yarinyar nan, ta shiga har ɗakina ta iba gyaɗar ina jiran ta huce na ƙulla." "Au Ashe ma ba bashi ta ci ba, Allah ya ba da kasuwa ta yi miki?" Kaka Tani ta furta cikin zallar mamaki tana kallonta. "Kuma ba ki ga gyaɗar ba kaɗan na iba, domin da na san ba za ta haƙura ba, sai na ibo mana da yawa musha koko da safe da ita, amma ba ta iya suyan gyaɗata ba, duk ta ƙone ta yi baƙi." Ta ƙarashe maganar tare da sakin ma kanta rankwashi. "Ai da kin sani da kin ibo da yawa, tun da hakan bai hana ta biyo ki ba ." Ta ce tana kallonta. "Yanzu abin da kike yi a Ƙauyen nan kuma kyautawa kuwa? Jikarki ta hana kowa saƙat kuma ba za ki iya tsawata mata ba? A yadda kike ba ta tarbiya, sai dai ta mutu a ƙauye nan, babu aure, domin babu wanda zai iya kwasar ma kansa bala'i." "Au ke ma rashin tarbiyyar ya sanya ki gagara zama? Alhamdulillah tun da ba ita ta share fagen ba." Kaka Tani ta furta mata cikin gatsali. "Sai aka ce miki zan yi aure? Ai ni da aure sai dai in ana yi a ƙiyama, saboda ba zan ɗauki wulakanci ba. Ke kanki kin san ɓalla mutum zan yi in har ya kawo mini raini." "A'a Jimmalo, jikalle ta! Za ki aure kafin na mutu sai kin haifa yara na gani..." "Allah Ubangiji ya kyauta! Ke ma kin san ba zan iya ɗaukar raini ba. Kina ganin Hamasiya da ta yi aure mijinta ya zane ta? Na rantse da ace nice sai na fitar masa da haƙarƙari." "Ni fa ba wannan maganar na zo ji ba, a biyani kuɗin gyaɗata ko jiki ya yi tsami." Ma'u ta ƙarashe maganar tana jijjiga ƙugu. "Na gaya miki ƙarfi ya ce daru ya hana." Ta ce cikin gatsali. "Kina ganin rashin kunyar da jikarki take mini ko?" "To so kike na daki marainiyar Allah? Yarinyar da aka mutu aka bar mini tana tsumma." "Wallahi sai kin biyani kuɗin gyaɗata." Ta ce tare da cakumarta. Ba tare da tunanin Ma'u mai gyaɗa ta girme ta ba, kawai ta daka tsalle ta wanka mata mari. Ƙara ta saki cikin gigita ta fara dukanta. Taron dangi suka yi mata. Suka rinƙa dukanta tana ihu. Jin ihu ta ya sanya maƙota suka rugo da gudu. A lokacin sun yi mata liƙis sai huci suke yi sun haɗa zufa." Nan gaba karya miki ƙafafun zan yi, kika ƙara gigin shgo mana gida." Kowa ya kasa cewa komai, sai kallon Ma'u suke yi cikin tausaya wa, tare da ganin wutarta da ta shigo musu har gida, domin ta san cewa ko a waje suka yi ba ƙyale ta za su yi. Duk garin waye ba su takurawa ba. "Wallahi sai na kai ƙarar ku gurin maigari, don ba zan haƙura ba." "Ki kai ƙara gaba da nan. Birni za ki je ki kai mu ƙara gurin 'yan sanda, in kika tsaya iya nan ba ki ci ba." Kaka Tani ta ce tana harararta. "Ni takaici ya hana ni cewa komai, so na yi na karya mata wuya, tun da har cikin gidanmu ta shigo." Jimmalo ta furta tana zare ido. "To ku wuce mana, kun zuba mana idanu munafukai kawai!" Kaka Tani ta daka ma mutanen dake tsaye, a tsakar gida tsawan tana faɗin haka. Da sauri suka fara fita sum-sum ba tare da sun furta komai ba. "Munafukai kawai! Wallahi daidai muke da kowa a garin nan, tun da kuka nuna ba kwa sona da jikata." Cewar Kaka Tani tana gyara ɗaurin ɗankwalinta. "Ki sha kurumunki ki bar ni da su. Ni kawai na ishe su kakata, ba sai kin wahalar da kanki ba." "Haka ne jikalle ta, amma ki kula kar wani ya illanta mini ke..." "Ni! Har a garin nan akwai wanda zai iya dukana?" Ta yi mata tambayar, tare da zare ido cikin mamaki ta dafe ƙirjinta. "Na san babu wanda zai iya dukanki, amma ba na san asamu akasi, kin san ke kaɗai nake gani na ke jin daɗi." "Ki sha kurumunki kakata, don ni Jimmalo na zama gagara badau! Kuma na gagari kowa a ƙauyen nan har maigari." Ta yi wa kanta kirari da hakan tana danƙwashi kanta. "Kin ga Jimmalo, na gaya miki ya kamata ki kwance kanki na siyo miki fiya-fiya, ki sanya ma ƙwarkwatan kanki." Dariya ta yi tana ƙara rankwashi kanta da ƙarfi, saboda zafi har sai da ta ce,"Wash!" Tare da cige leɓe. "Aradu babu wata fiyafiyar da zan sanya, saboda ina jin daɗin kashe tana cewa ƙas!ƙas!!" Sai ta ƙara kwashe da dariya tana dukan kan. "Ya dai kamata gyara kanki." Jin abin da ta ce, ya sanya ta ta shige cikin ɗakin ba tare da ta ce mata komai ba, domin idan akwai abin da ta tsana ace mata ta gyara kanta. Tana da zafin kai, kuma ya haɗu da ƙazanta. Ma'u cikin kuka ta ƙara da gurin gidan maigari. Kuka ta ƙara saki sannan ta kwashe komai ta faɗa masa, sannan ta ƙarashe maganar tana faɗin,"Maigari ka yi mini tsakani da ita, wallahi na gaji da rashin mutuncin da take mini, har gida take bina tana ci mini kayan sana'ata, kuma ba ni da ikon na yi magana su haɗu su yi mini duka." "Kai wallahi na gaji da ƙarar da ake kawo mini na mutanen nan! Ace mutane biyu sun gagari ƙauye nan? Ko jiya sai da aka kawo mini ƙarar yarinyar nan, ta je ta zagi wani tsoho." "Jimmalo ba ta da tarbiya kwata-kwata kakarta ba ta mata tarbiya mai kyau. Allah ko ni yarinyar nan ina haƙonta, don dukan da ta yi wa ɗana Usmanu." "Je ka yi mana kiransu." Ya faɗa cikin takaici jin abin da ya ce. Miƙewa ya yi jikinsa na zikiri ya fice da sauri. Yana tafe yana addu'ar Allah ya sanya ayi mata dukan tsiya. "Assalamu alaikum," Ya kwaɗa sallama tare da jingina da garu. "Waye yake damun mu da sallama kamar munci masa ba shi?" Ta fito tana tafiya cikin gadara. Harara ya zabga mata yana yatsina fuska."Ai sai ki fito ki gani fitsarrarriya mara kunya." "Ga ka Malam ka daina kirana da fitsarrarriya, don ba haka uwata da uban suka sanya mini ba. Ta ce mishi cikin tsawan. "Zagina za ki yi?" Ya yi mata tambayar cikin zallar mamaki. "In ta kama mai zai hana? Don wallahi bana tsoron uban kuwa, kuma dama duk babban da bai ja girman shi ba, ai sai yaro ya yi wasa da girman a ƙasa." Mamaki ya cika shi ganin yadda take zare idanu, kamar tana magana da sa'anta. "Ke kan Jimmalo, albasa ba ta yi halin ruwa ba, saboda kowa ya san iyayenki suna da mutunci. Allah ya ɗibe miki albarka. Kamata tsoho da ni fuska duk gemu kike zagi?" "Ni fa Malam ka kama girmanka." Ta furta tare da ɗaga masa hannu. "Ba komai za ki haɗu da gamonki. Sai ki je in kin ga dama maigari yana neman ki da kakarki." Jin abin da ya ce, ba tare da ta tsorata ba ta kama ƙunkunai. "Zaginsa za ki yi kenan?" "In ji maƙura sai na gaya maka." Ta faɗi da ƙarfi tana zabga masa harara. "Allah ya kawo mana guguwar da za ta kwashe ki ki bar garin nan, domin a ranar sai mun zuba ruwa a ƙasa mu sha." "Tun da ga annoba ta tafi ba, to ina nan zama daram-dam a cikin ƙauyen nan." Ta ce tare da jan tsuka ta shige ciki. "Da ikon Allah sai kin bar ƙauyen nan, muna nan muna jan miki yasin da tabaraka. Yarinyar sai ka ce jujal duk tabi ta addabi mutane." Ya ce yana tafiya. "Kaka Tani, kin ji maigari yana kiranmu." Ta yi maganar cikin shagwaɓa. "To sai me? Kiran maigari kiran Allah ne. Ma za ɗauki mini mayafi mu je, in ta kama ai ko agabansa zan yi faɗa da kowa a kanki." Murmushi ta yi, jin abin da ta ce tana kallonta."Shi ya sa na ke so ki kakata." "Ni ma ina son ki Jimmalo takwarata." A hanya suna tafe suna hira, tamkar ba laifi suka aikata ba har suka isa. Cikin gadara ta tsaya a bakin ƙofa tana aikawa Ma'u mai gyaɗa harara. "Za ki shigo ki zauna mara kunya." Cewar wani a cikin zauren. "A ka yi mata a hankali, kar ka tsorata mini jikata." Kaka Tani ta furta tana kallon sa. "Na gaji da ƙarar ku da ake kawo mana kullum. Jikarki tana aikata ba daidai ba, amma soyayyar da kike mata ya rufe mata idanu." "Ka san ita mai ta aikata maigari? Matar nan fa har gida ta biyo jikata zata buga. Ni kuma da yake bani da hankali sai na tsaya ina kallonta? Wannan dalilin ya sanya na ɗauki matakin da kowa ce uwa za ta ɗauka, saboda ba zan iya gani ba ta dukan mini jikata." "Wallahi maigari, yarinyar nan har gida ta shiga ta ibar mini gyada ina ina ƙullawa." "Innalillahi! Amma baki da mutunci ƙarya za ki yi mini. Ba shi na siya kuma na ce zan biya." "Ke!" Ya daka mata tsawan jin abin da ta ce. "Sam ba kyau girmama manya ko?" Tura baki ta yi tare da kallon gefe ba ta ce masa komai ba. "Tun da bashi kika siya ki biya ta kuɗinta." "Zan biya ina samu, dama ba ce ba sha nono uwa ba." Ta yi maganar a hankali, tana tura ɗankwali gaba tare da sakin ma kanta ranƙwashi. "To ki ba ta kuɗinta." "Za ta biya inta samu, saboda bamu da shi, kuma yanxu ko gwamnati ana binta ba shi." "Kin ga Tani? Wallahi in har ba ki rinƙa wa jikarki faɗa ba zan saɓa muku a garin nan, in har kuka ƙara shiga sabgar wani sai na sanya an ko..." Maganar ta katse sakamakon kukan da ya ji ta saka."Saboda zalunci sai ka yi mini barazana da barin ƙauye da aka haifi iyayena da kakannina? Shikenan ina gani a doki jikata kuma a hana ni na yi magana? Wa take da shi a duniyar nan da ya wuce ni." Kuka take sosai tana share majina. Ganin haka ta saka kukan ita ma." Ki yi shiru ki daina kuka kakata. Kin san hawayenki kawai yake sanya jikinsa ya yi sanyi. Ki yi haƙuri tun kafin hawayenki, ya tunzura ni na cinna ma gidan nan wuta." Zare idanu su suka yi cikin mamaki, jin abin da ta ce, wanda sun san tsaf za ta iya aikata wa. "Dole na yi kuka Jimmalo, kina gani ni da ƙauye mu ana mini barazana. To wallahi ƙauye nan sai dai ina mutu akai kashewa bayan gari, don ko na mutu ban aminta akai gawata wani guri ba." "Ki share hawayenki ko an kaiki, sai na je ƙabarin na ƙwaƙwulo na cika miki wasiyar ki, ballantana ba za ki mutu ba kakata." Kuka suke yi sosai kamar su aka cuta. Mutanen cikin zauren sun kasa cewa komai sai kallon su suke yi. Saboda takaici sun kasa magana. Ganin sun yi shiru, kamar yadda suka saba, sai suka miƙe suka fice daga zauren Bayan fitarsu Malam Sule ya kalli maigari da ya kasa cewa komai."Yanzu haka za mu bar su suna taka kowa yadda suke so, kuma babu wanda ya isa ya tsawatar sai su rinƙa kukan munafunci kamar su aka cuta?" "To ya zan yi? Kawai na ba da umurnin duk wanda suka cuta in zai iya ya rama, in kuma ba zai iya ba, sai a natsu da Allah." Zariya birnin Shehu garin ilmi. Babban gidane a cikin unguwar Juma, wanda daga gani ka ga ginin da, domin irin ginin nan ne, mai ɗauke da ɗakuna sosai har da gidan sama. Saboda wadata da wasu daga cikin waɗanda suka taso a cikin gidan, sai aka yi gyare-gyare aka ɗan sauya gidan har da tayas da kuma filista a ka yi mishi, sannan kowa ya killace sashinsa, ya kewaye da kwano. Tsakar gidan ya sha siminti mai kyau sosai. Kasancewar gidan ɗauke yake da matan yayyi da kanni har ma da kawunnai, sai aka samu yawaitar 'ya'ya a cikinsu, domin akwai 'yan mata kyawawa da kuma samarin maza. Hanifah ce take sashin Anty Mariya, amaryar babansu tana kwalliya bayan ta fito daga wanka. Hindatu ce ta yi sallama ta shigo da anko da ta karɓo daga gurin ɗinki. Da sallama ta shigo cikin ɗakin bayan ta gaishe da Anty Mariya ta wuce ƙuryar ɗakinta. Turus ta yi ganin Hanifah sai a lokacin take shafa hoda. "Wai ni saboda Allah wane irin kwalliya kike yi? Tare muka fito wanka har na yi kwalliya na tafi gidan A'isha Tela na karɓo kaya, amma har yanzu kina nan kina shafa hoda. Hanifah ko fuskarki kike son canzawa sai haka." Murmushi ta yi, tare da ɗaukar kwalli ta bayan ta ije soson hodan. "Wai ba ki da labarin Ya Captain zai zo ɗaurin auren nan ba, domin har sun kamo hanya. Na ji Baba Ɗanlami suna waya da Daddyn K.d, ya ce masa suna hanya, don haka yanzu na san sun kusa." "Eh zai zo ɗaurin aure sai kuma aka yi me?" Murmushi ta yi tare da kashe nata ido ta ci gaba da gyara kwallin da ta saka ta ce,"Shi ka ke yi wa wanna kwalliyar." Wani uwar tsaki ta saki ta ce,"Amma iska na wahalar da mai kaya ƙara! Ke har yanzu Hanifah ba za ki cire Ya Captain a ranki ba? Wallahi tun ranar da ya wanka mini mari na yi zuciya na ce ko shi ne autan maza na haƙura da shi. Mutum sai wulaƙanci da girman kai sai kace shi kaɗai ne soja kyakyawa mai kuɗi? Ni fa na haƙura da shi, domin na san ko mutuwa zan yi ba zai aure ni ba." "Saboda wulaƙancin da ya yi miki sai ki haƙura? Wallahi ina nan kan bakana, sai abin da ya turewa buzu naɗi. Idan yana taƙama da kyau ai ni ma ina da shi, sannnan ilmi shekarar ƙarshe na ke a digiri." "Ki daina wahalar da kanki kawai ki haƙura da shi, saboda Ya Captain ƙila balarabiya zai aura. Yadda yake ji da kansa, ba na tunanin zai iya auren bakar fata." "Wannan faɗan ki ne, amma ni ina jin zai aure ni." Wata 'yar iskan dariya ta saki mai haɗe da shewa."Ashe kuwa za ki mutu ba ki yi aure ba." Kafin ta amsa kyawawan 'yan mata su huɗu, kusan kansu ɗaya suka yi sallama suka shigo. Kallon su ta yi ta ce,"Kuma duk kwalliyar kuka yi wa Ya Captain?" "Ke dai ba kin sare da wuri ba, amma mu kam muna nan kam bakanmu. In sha Allahu sai ya auri wata a cikinmu. Ina fatan nine." "Ku zauna kuna yaudarar kanku za ku mutu ba ku yi aure ba." Anty Mariya ce ta shigo ciki tana jin hirar da suke yi. Murmushi ta yi saboda ta san duk a cikinsu babu wacce zai so. Ta san kalar macen da yake so, duk dacewar shi ba haka yake ba. Tasan zaɓinsa da rayuwar da yake so. Zata iya cewa yana gaya mata sirrinsa wanda iyeyensa ba su sani ba, domin ta san Aliyu da sirrin da yake ɓoyewa a rayuwarsa wanda ba ta fatan su sani, domin sanin zai iya kawo wargajewar farincikin rayuwarsu da kuma yardar da suka yi masa. Aliyu fuska biyu ne yana da wani hali, wanda take tunanin daga ita sai shi suka sani. Har yau tana fatan Ubangiji ya ci gaba da ɓiyo sirrin har ranar da zai daina. Ihu suke yi bayan hari domin duk cikinsu babu wacce take da criteria, da yake son wacce zai aura take da shi. Yana da wani zaɓi da buri ga matarsa, duk da cewar shi ba haka yake ba. Zama ta yi tana kallon su, da suke ta hayaniya suna zuzuta kyawunsa kowacce tana fatan ace ita zai so. "Ni wallahi na ƙasa su zo na ga shi, saboda ya daɗe bai zo family ba. Ko rasuwar da aka yi na Kaka Naninna. Daga Hajiya sai Mommy da Daddy suka zo." "Ai lokacin baya ƙasar fa." Cewar Hanifah da ta gama kwalliya tana ɗaura ɗankwali. "Yanzu ma baya ƙasar. Yana Yukrain. Har da shi aka zaɓa a cikin waɗanda za su kai wa Ƙasar Ukraine taimako." Jikinsu ne ya yi sanyi, kamar za su yi kuka jin abin da ta ce. "Kai innalillahi! Wallahi har da bashi na ci na sayi kaya don kawai na burge shi." Ummita tace tana kwance ɗaurin ɗankwalinta, da ta bata kusan rabin awa tana ɗaurawa. "Aiko dai dai ku yi haƙuri domin zai yi wata biyu ko fiye." Kamar za su yi kuka, haka suke kallonta jin abin da ta ce. Murmushi ta yi musu ta miƙe ta fita ganin ya kira ta a waya. Tamkar ƙawarsa ya ɗauke ta, saboda sai ya gaya mata abu, ba tare da ya sanar wa abokinsa. Masoya, wannan labarin da wani irin salo na musamman ya zo. Kar ku sare ku bibiyi labarin tare da yi mini xafafen comments domin akwai cakwakiyar gaske da ruɗani. Kun dai san comments na ku yake karfafa mini gwiya. Ku yi following channel, arewabook, da kuma Whatsapp ɗina. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiwasin abin da zai faru a gobenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, waɗanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sirrin da ya sanya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sirrin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *ƘIYYAYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* Don karanta Ƙiyayyar Jini ku bi link ɗinnan, sannan karku manta ku yi following ɗina arewabook🙏🙏 https://www.arewabooks.com/chapter?id=686289d4e9cb75389b9d68c8. Check it out! Ga link na channel ɗina shi ma ku yi joinning don samun labarin tun daga farko. Follow the channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 2 Jin Captain Aliyu ba zai zo bikin ba, gabakiɗaya jikinsu ya yi sanyi, domin kowaccen su ta ci burin ya zo ya ga kwalliyarta. Da misalin sha biyu Hajiya, Daddyn K.d da Mommyn K.d har da Nufaisah, Umma da auta Farid suka iso cikin. Zariya. Ƙofar gidan cike yake da mutane sosai a ciki da waje. Hajiya da ta fito daga cikin motar tana miƙa. Da sauri mutanen da suke zaune suka taho gurinta don kwasar gaisuwa. Farar mace dattijuwa, wacce daga ganinta ka ga naira ya zauna, domin duk tsufan da ta yi, hakan bai ɓoye kyau da take da shi ba. Tana sanye cikin riga da zani na atamfa, kasancewar mace wacce ta yi riƙo da shigarta na Hausawa. Ɗaga gilas idanunta ta yi, cikin tsananin so da ƙaunar ɗanta, da kuma iyalansa suka ƙarasa inda suke. Cikin mutunci take amsa gaisuwar na su, bayan sun gana gaisawa sannan suka shiga ciki. Baba Ɗahiru wanda shi zai aurar da yarinyar ya bi ta suna tafiya."Hajiya, mun ga tsaƙo Ubangiji ya ɗaukaka ke da iyalanki. Sosai kun yi ƙoƙari har da soja, don ko jiya ya kira ni in akwai abin da ba a gama siye ba, ya turo kuɗi bayan abin alkhairin da ya yi." "Ai wai Aliyu ai dama ban so ya zo bikin ba, ka san yanayin aikinsa, ni dama ko ba aikin ya tsare shi ba, gara da bai zo ba. Ya raba hali da wannan shegiyar ɓakar zuciyarsa." "Soja ne dole ya yi zuciya, kuma baya haka kun manta halin mai sunan da ya gado? Yaya Aliyu har na haihu yana kai mini duka ina ɓata masa rai." Ya ƙarashe maganar yana dariya. "Da wannan, amma kuma marigayi mijina ai zuciya bata hana shi aure ba, amma shi kuwa fa? Inda ya aminta da haɗin da na so na yi da yanzu matar ta haihu." "Lokacin auren ne bai yi ba, kuma yadda yake da zafin zuciya bana son a yi masa auren dole. Mu bari ya zaɓi matarsa da kansa, saboda in har muka yi kuskuren masa auren dole mun cuci yarinyar. Soja ko shi ya ga mace yana so wallahi sai tayi haƙuri." "Ni fa na tsame hannuna kan lamarin da ya je ya auri kaki. Ai duk abin da yake yi ɗaurin gindin ubansa ya samu. A lokacin dana ce ayi auren shi da Ameera ya ƙi, idan da ubansa ya yi masa dole ai zai karɓa." "Zai yi lokaci ne Allah ya haɗa shi da mata ta gari." Hajiya shiru ta yi ba ta amsa ba sai ƙuta da ta yi, domin sosai yake ba ta haushi. Daddyn k.d shiru ya yi yana jin ta bai ce komai ba, domin ba ya son ya tanka ta raba masa abin faɗe ana taro, amma shi ya san dalilin da ya sanya shi bai aminta da auren ba. Sam ba ya son abin da zai ɓata zumuncin su. Ya san wane ne ɗansa da kuma in ya kafe ba ya son abu. Sam ba shi da matsala da rayuwarsa aure lokaci ne, kuma saboda zafin ransa dole ya tsaya ya nemi matar da za ta iya shanye duk halinsa. Jin daɗin da ɗaya da ba ya aikata abin da wasu sojojin suke yi. Yana alfahari dashi sosai, tun da ya shiga aikin soja bai taɓa ko shigar banza ba. Har yau yana alfaharin da ya riƙe alƙawarin da ya ɗaukar masa. Ciki suka shiga, nan mutane suka taho gurinta cikin murna. Bayan an gaigaisa sannan Mommy ta shiga ciki ɗakin uwar bikin, Nufaisah kuma da Umma suka shiga cikin 'yan mata. An yi taro cikin rufin asirin Allah, an kai amarya gidanta. Su Daddy sun dawo Kaduna lafiya. Ƙauyen Damagaran. Bayan fitarsu Malam Sule ya kalli maigari da ya kasa cewa komai."Yanzu haka za mu barsu suna taka kowa yadda suke so, kuma babu wanda ya isa ya tsawatar, sai su rinƙa kukan munafunci kamar su aka cuta?" "To ya zan yi? Kawai na ba da umurnin duk wanda suka cuta in zai iya ya rama, in kuma ba zai iya ba, sai a barsu da Allah." Washegari da safe, tana zaune bayan ta tashi ta yi sallar safe, sallar da in aka tsareta ba za ta faɗi abin da ta karanta ba. Shi ma don Kaka Tani ta tsare ta ne, amma inta ga dama dai ta wuni har kwana ba ta yi sallah ba. Karatun allon ba zuwa take yi ba, duk yadda Kaka Tani ta so ta je haka ta haƙura ta zuba mata na mujiya, domin da ma ba wani tsaurarawa ta yi mata ba, a cewar ta tun da ta iya karatun sallah shikenan. Kwalliya take yi, duk ta ɓata fuskartar sai kallon kanta take yi a magani. Tana son kwalliya sai kace mairo 'yar kwalliya ta shige ta. Kaka Tani ta fito daga cikin ɗaki da kofin koko a hannunta. Ki sha ruwan kokon nan, ki yi maza ki je mana tallah, yau kin san akwai kasuwa zan je na tsinto miki kayan ɗaki. "Wai Kaka Tani, ba za ki daina wahalar da kanki gurin siyen kayan ɗakin, da kin kwana da sanin ba aure zan yi ba?" "Subuhanallahi! Ki daina ma kanki fatan hakan. In sh Allahu, sai na ga aurenki kafin na mutu." "Ashe kuwa za ki yi gadin duniya, saboda babu ɗan iskan da zan iya aure a duniya yana sanya ni aiki." "Aure shi ne daraja da cikar ƙimar 'ya mace. In har na mutu ba ki aure ba, wa kike son ya kula da ke in kika tsufa?" "Ai ni ba yarinya ba ce zan iya kula da kaina, amma ni da aure mun yi hannun riga." "Anya ba aljanu suka kama ki ba? Ace kin girma ba kyau son aure. Babu fa sa'ar ki a ƙauye nan Jimmalo?" "Babu aljanin da ya kamata ni. Auren ne ba zan yi ba." Ta buɗe baki za ta yi magana, Ladidi ta kwaɗa sallama da sanda a hannunta tana wasa da ita ta shigo. "Yauwa Ladidi, zo ki riƙe mini tirena na gama kwalliyar nan, kin san yau in mun sai da kaya a kwai rawa a dandali. Sannan ina son na koya wa Karime karatu." "Karime ta ba ki haƙuri fa don Allah ki ƙyale ta." "Malama ban son gulma! Ba ke kika gaya mini tana ta yamaɗiɗi dani wai ina da ƙwarkwata ba?" "Eh, amma ta ba ki haƙuri kuma ta ce Salame ta gaya mata." "Ina ruwan ko uwar Salame ce, wallahi sai na koya mata hankali." Ta ce tare da gyara ɗammararta ta fice daga gidan. "Ba za ki sha ruwan kokon ba?" "Sai na dawo ki sayi rogo ki haɗa mini." "To shikenan, dawo lafiya." Ta ce tare da juya ta shiga cikin ɗakinta. Tana fita ta cire gyalenta ta sha ɗanmara. Ganin haka hankalin Ladidi ya tashi ta kalleta."Don Allah Jimmalo, ki bar maganar nan ki bari ayi rawar nan lafiya a tashi lafiya." "Kin ga Ladidi ki fita daga idanuna, in har ke ma ba munafuka bace, ki barni na yi maganin munafukai." Ta ƙarashe maganar cikin fusata. Ganin haka ta kama bakinta ta yi shiru suna tafiya, yayin da zuciyarta ke cike da damuwar abin da zai faru. Da suka isa dandalin, tsaya ta yi tana zare idanu tana son ganin inda Karime take. Cikin sama ta hangeta tana kasa mazaƙwailar da take siyarwa."Yauwa ga munafukar can." Ta furta tare da yin wani sufa sai ga ta a gabanta. Ba tare da tunani ba ta ciyo kwalar rigarta, daga duƙe har sai da ta miƙar da ita. "Ta shi munafukai algunguma, da kike je kina gaya ina da ƙwarkwata kanki ko nawa?" Ta yi mata tambayar bayan ta cikwikwiye rigarta, ta hanata shaƙan numfashi. Tsoro da firgici ya kamata jin abin da ta ce, sai ta shiga zare idanu tamkar wacce ta yi kisa. "Ni da yaushe na gaya haka?" Ta yi tambayar tare da fara hawaye. "Au tambayata kike yi? Da kin tambayi wacce ta gaya mini Karime." Karime jin an ambaci sunanta, kafin a sanya ta a ciki, sai ta tsaya a gabansu. "Ki ji tsoron Allah yaushe..." "Kin gaya mini mana ranar Attinin, da da zamu je sarin ayaba, ki tuna har kina cewa kar in gaya mata." Jin abin da ta ce sai hankalinta ya ƙara tashi, amma don ta ƙare kanta ta ce,"Ni fa ba ita ba ce ba, Jimmalo na gidan Malam Balarabe na gaya miki." "Ƙarya kike munafuka, kin faɗa hakan ai dama na lura da wani gani-gani da kike mini wai ke ga ki mai tsafta, kuma wallahi yau sai jikin ki ya yi tsami." Ta ce tare da gaure ta da mari. Kuka ta sanya domin ta ji shigar marin."Allah ya saka mini, ai na gaya miki ba ke na ke nufi ba." Ta ce cikin muryar kuka. "Tun da ba ki da kunya bari na yi maganinki, don sai na fasa bakin sai na ga gobe da wani bakin za ki yi gulmar"Ta furta da fara kai mata duka ta ko ina tana kuka. "Muguwa azzalumai, kin girma kin ƙi aure saboda ƙazantarki. Ai Innata tace duk kin girme mu, shi ya sa kike cin zalincinmu yadda kika ga dama." Ta ce cikin kuka. Jin abin da tace, sai ta zuciya ta ci gaba da dukan ta."Jira na ke yi Babanki ya saki mamanki, sai na aure shi yadda zan koya miki tarbiyyar da aka kasa baki." Ta ce tana dukanta. Da ƙyar aka samu aka hanata dukan sannan ta ƙyaleta tana huci. Ukraine Captain Aliyu zaune a katafaren hotel da yake birnin Ukraine, mai suna premier palace Hotel Kyiv. Sanye yake da kayan sojoji, kayan sun yi masa kyawu matuƙar gaske! Daga ganinsa ka ga namiji ingarma, wanda Allah ya yi wa tagomashi, da duk wani abun da ya kamata namiji ya mallaka. Kallo ɗaya za ka yi masa ka gane mutum ne mara haƙuri da rashin magana. Sam fuskarsa babu annuri Idanunsa lumshe, yana kallon abokinsa Kalim da yake gyara bindigarsa. Aliyu ɗane ga Alhaji Abubakar mai gilashi wato Daddyn K.d. Mahaifinsa yana da kuɗi sosai. Ɗan boko ne kuma ɗan kasuwa. Suna zaune a garin Kaduna, amma asalinsa haifaffen garin Zariya, unguwar Juma. Alhaji Abubakar yara huɗu ya haifa da matarsa Hajiya Karimah. Wacce take mai haƙuri kuma wayyayiwa 'yar boko. Ta yi sakandire a garin Kaduna da sannan ta yi digiri ɗinta jami'a a Kasu. Bayan ta kammala sai ta fara koyarwa. Sun haɗu da Alhaji Abubakar a sanadin Ƴaƴanta, da yake abokinsa kuma suna harkan cinikayya. Ganin ta yi masa ya bayyana wa aminin nasa. Ba tare da ɓata lokaci ba aka sanya bikinsu. Hajiya Karimah da Alhaji Abubakar suna da riƙo da addini. Wannan ya sanya duk tarin kuɗin da suke da shi, bai hana bawa yaransu tarbiya na gari ba. Captain Aliyu, ya yi makarantar kuɗi mai tsada a garin Kaduna. Sannan islamiya da hadda duk na kuɗi ya yi. Bayan ya kammala mahaifinsa ya yi masa viser ya tafi America, don ya yi karatunsa a can, musamman ganin yadda jarrabawar sa ta yi kyau, amma sai ya bijire masa don a rayuwarsa soja yake son zama. Da fari sun ƙi aminta, ganin tun da ya taso yana da tsananin fushi da rashin haƙuri. Sai dai, ganin ko da yaje America ya ƙi maida hankali ya yi karatun. Wannan dalilin ya sanya kan dole ya dawo da shi, ya sanya shi a makarantar sojojin N.D.A. Sosai ya mayar da hankalinsa kuma ya tashi cikin hazaƙa, domin tun kafin ta girma ya samu ɗaukaka fiye da sauran karatunsa. Yana kammalawa ya samu aka ba shi aiki. Daddy ya yi namijin ƙoƙari, don ya ga ya tashi da tarbiyyar da ya ɗora shi a kai. Don haka ya sa ya idanu sosai a kansa, tare da yi masa barazanar duk lokacin da ya ga ya yi abin da ba daidai ba, zai cire shi kuma dole ya bi zaɓinsa. Saboda wannan sharaɗin yake matuƙar taka tsantsan da halayen da ya koya, sai ya zamo fuska biyu, domin yana shan sigari duk da ba ta yi ƙarfi ba, sai in an ɓata masa rai. Sannan mace ɗaya yake kulawa har yake mu'amala da ita.Giya ce kawai ba ya sha, amma duk hali irin na sojoji yana yi. A gida yake zama mutumin ƙwarai, amma da zarar ya dawo sai ya rikiɗe ya zama kura da fatar akuya. Abu biyu ne baya wasa da su sallah da karatun Alqur'ani, wanda su suke sanya shi rage abin da yake yi, don wani lokacin sam ba ya wannan harkar. Ba kamar sauran sojojin, da suka mayar da wannan rayuwar ya zama jikinsu ba. Kallonsa Kalim ya ƙara yi, daidai lokacin da ya juyo."I need to go back to Nigeria. Haƙiƙa am missing my family a lot." Ya ƙarashe maganar, fuskarsa ɗauke da damuwar hakan. "Ni kaina kewar gida ya ishe ni, ina buƙatar na ga ahalina." ya faɗa yana gyara zamansa. Tautaunawa suka shiga yi, har zuwa wani lokaci. Yawancin hirar ta su, akan aikin su ne da yadda suke takura. Bayan sun gama hirar, ya miƙe yana gyara zaman belt ɗin wandonsa, yayin da idanunsa yake kan wayarsa da kiran Lubaynah ya shigo. Ƙaramin tsaki ya ja, wanda yake nuna takurar da mai kiran ta yi masa, ya fara taku ɗaya biyu, sai kuma ya dawo da baya ya ɗauki wayar. "Hello, Captain?" Ta ce cikin murya mai daɗi. "Yes!" Ya furta a gajarce. "Please, Captain.." "Lubaynah, I will call you back." Ya kashe wayar, ba tare da ya ji amsar da za ta ba shi ba. Fita ya yi zuwa harabar Hotel ɗin. Ya ƙarasa gurin swimming pool ya zauna a bakin ruwan. Ƙafafuwansa ya zura yana lumshe idanunsa, jin yadda sanyin ruwan yake shigarsa. A ƙalla sai da suka yi wata ɗaya, sannan ya dawo Nigeria. Daga filin jirgi gidansa ya wuce da yake Barak na Abuja. Saboda cikin dare ya dawo wanka kawai ya yi ya kwanta. Washegari da ya tashi, bayan ya je masallacin ya yi sallah, ya dawo ya kwanta. Bai ta shi ba, sai da mai aikinsa Peter ya zo aiki. Motsin sa ya sanya shi tashi. A hankali ya janye blanket dake lulluɓe a jikinsa. Jikinsa ya bayyana yana sanye cikin kayan bacci, daga shi sai gajeren wando da wata rigar wandon mai kyau. Kayan suna da kyau kamar yadda suka yi masa kyau. Ya na kwance yana kallon ɗakin da yake ƙamshi mai daɗi, kafin ya zura ƙafafunsa ƙasa ya miƙe tsaye. Kai tsaye bayi ya shiga, ya yi wanka bayan ya bata tsawon lokaci. Fitowa ya yi da ga shi sai tawul, yana goge jikinsa da ƙaramin tawul dake hannunsa. Tsayawa a gaban mirror yayi, ya shirya tare da gyara fuskarsa. Kamar mace haka yake akwai gyara jiki da ɗaukan wanka, sannan sam ya tsani ƙazanta. Shi mutum ne wanda za a iya ce masa tsafta ta yi masa yawa. Saboda duk yadda yake da mutum ba zai iya cin abinci ya rage ya ba shi ba, sannan in ba iyayensa ba ko ƙanninsa bai taba cin abinci da su ba. Ko iyayen na sa tun da ya girma ya daina. Baya son ƙazanta don ko a hanya baya ƙaunar ya haɗu da ƙazami. Wannan dalilin ya sanya kaf 'yan aikin gidansu suke taka tsantsan. Shi ya sa kodayaushe gidansu yake cikin gyara. A lokacin da ya mallaki nasa gidan, saboda tsafta komai nasa fari ne na kayan gidansa. Hatta kujerunsa fari haka kayan kicin ɗinsa dinning ɗin sa. Gidansa babu abin da babu, domin kamar na mai aure gidan, saboda yadda ya tsaftar shi, yana da son ado da ƙyalƙyali. Wani lokacin da kansa yake zama yana gyara gidan. Masu aiki kuwa an sha kawo masa yana korarsu sai Peter kaɗai ya iya da shi, don shi ma yana da tsafta kuma ya iya abinci, saboda abin da ya karanta kenan. Bayan ya gama shirya ya saka wando da riga masu kalar kayan sojoji, amma suna da taushi sosai ya fito. Zama ya yi kan kujerar da wayarwa a hanunsa daidai lokacin da Peter ya fito daga kicin ya nufi dinning da kular abinci. Bayan ya ije ya zo inda yake. "You are highly welcome sir." Ya ce masa cikin girmamawa tare da ɗan duƙawa. "Peter how doing?" Kawai ya ce masa ya ci gaba da kallon wayarsa. "Fine sir, how was the trip?" "Successful."Ya furta a takaice. "We thank God, breakfast is ready." "Ok," Ya ce masa ganin haka ya koma kicin ɗin. Sai da ya ɓata lokaci, sannan ya mike zuwa dinning inda aka shirya abincin. Ruwan Lipton ya haɗa masa, sannan ya soya masa doya da source, sai kuma farfesu da ya yi masa, sanin halin ogan nasa ya son albazaranci kuma ba ya cin abinci da yawa. Ba wani sosai ya ci abincin ba, ya miƙe ya fita daga falon. Inda karensa Bindo yake ya nufa bayan ya ɗauki abincinsa. Ɗakin da yake ya ƙarasa tare da buɗe ƙofar ya fito. Wani irin baƙin kare ƙatoto da shi. Sai kaɗa bindinsa yake yi yana zare harcensa. Daga ganinsa kasan ana kula da shi, saboda yadda yake cikin tsafta. Karen ya ci gaba kaɗa bindinsa, yana taɓa jikin Captain Aliyu, tare da rawa na murnan dawowarsa. Murmushi sosai yake yi masa ya kama kansa ya riƙe. Sosai yake son karen, domin zai iya wuni da mutane ba tare da sun ga fara'arsa ba, amma ko kallon karen ya yi sai ya murmusa. Ya ɗauki tsawon, lokaci yana kula da karen ya kuma yi wasa da shi, ya wuce zuwa lambun shi. Iskar da take kaɗawa ta saukar masa da nishaɗi sosai. Zuciyarsa ta raya masa ya kamata ya kira Lubaynah don ta rage masa kewa. Ba tare da dogon nazari ba, ya ɗauki wayarsa tare da danna mata kira. "Hello babyna," Ta furta cikin muryarta na son jan hankalinsa. "Ki kwaso kayanki kamar na wata na dawo Nigeria." Jin abin da ya ce mata, ya sanya ta ji matuƙar farinciki. Fuskartar ta bayyana murmushi sabanin da, da take cikin damuwa." "Amma shi ne ba ka gaya mini ba?" "Why do you ask? It is as usual." Ya furta mata a ɗan zafafe. Jin ransa ya ɓaci ya sanya ta ce,"Ok, my Captain. I will be on my way. I Love you." Kashe wayar ya yi, sannan ya faɗa swimming pool, ya rintse idanunsa. Duk ya ƙosa ya koma ya ga family ɗinsa. Ya daɗe a cikin ruwan, domin yana son wanka a swimming pool sosai, sannan ya fita ya shiga ciki don ya cire kayansa. Kamar yadda ta yi masa alƙawarin zuwa. Ba ta ɓata lokaci ba, yana zaune a cikin falonsa sai ga kiranta. "My Hearthrop, I'm outside the get?" Cikin harshen Nasara ta yi masa maganar. "Ok," Kawai ya ce tare da kashe wayar. Mikewa ya yi, bayan ya ɓata lokaci yana zaune, sannan ya ɗauki wayar da ya fita. "Solo, open the get." Ya ce tare da komawa ciki. "Ok, sir." Ya faɗa sannan ya tashi cikin hanzarce ya buɗe mata. Janyo trolley ɗinta ta yi, ta shigo cikin gidan. Tana sanye da doguwar riga baƙa, sai ƙaton recommenden glass da ta sanya. Captain Aliyu ya da fuska biyu? Ke kuma Lubaynah na miji kika amince da shi har ya maida ke kamar matarsa? Makaranta wannan salon daban yake. Kici gaba da bibiyar labarin da kuma zafafan comments. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 Don karanta Ƙiyayyar Jini ku bi link ɗinnan, sannan karku manta ku yi following ɗina arewabook🙏🙏 https://www.arewabooks.com/chapter?id=68641a0d7c887833ecc9b10d. Check it out! Ga link na channel ɗina shi ma ku yi joinning don samun labarin tun daga farko.Follow the ƘIYAYYAR JINI channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P PAGE 3 Cikin yauƙi da yanga take tafiyar, kamar yana gabanta ta shiga cikin falon. Ganin ba shi a falon ta fara tafiya zuwa ɗakinsa. Fitowarsa ya sanya ta miƙe da sauri ta isa gareshi. Jikinsa ta faɗa tare da rungume shi. Hot kiss masu zafi ta sakin masa. Janye ta a jikinsa ya yi, ya zaunar da ita gefensa, tare da zama kusa da ita yana wani kasalalen murmushi, wanda yake iya leɓe. Har ranta take kallonsa, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa." Ba shi wani kiss ɗin ta yi, amma sai ya kauda kansa yana sakin ƙaramin tsuka. "Hearthrop, you called me for this, and you are avoiding it?" Ta yi masa tambayar cikin shagwaɓa. Miƙewa ya yi, ya rage kayan jikinsa, ya rage da ga shi sai gajeren wando na sojoji. Kallonsa take tana ji kamar ta lashe shi. Ji take kamar ta rungume shi, amma ta san tun da ya nuna wannan mood ɗin, in ta aikata hakan, sai ya yi mata wulaƙancin da ba za ta so ba. Sanin hali, ya fi sanin kama. Wannan dalilin ya sanya ta haɗiye maitarta. Bayi ya shiga don ya watsa ruwa. Ya jima sosai ya fito, domin a lokacin har ta gaji da jiransa, ta ɗauki wayarta, ta hau yanar gizo. Ganin ya fito ya sanya ta kashe wayar tana kallonsa. Kai tsaye gurin kayansa ya nufa, wanda ganin haka ya sanya, ta kama hannunsa da sauri tana masa wani irin kallo. Kallon da ya sanya shi fasa saka kayan. Hannunta ya ja ta faɗa ƙirjinsa tana maida numfashi. Fuskarsa ya haɗe guri ɗaya, yana jin yadda numfashinsu ke sauka a kan fuskokinsu. Ba tare da ya ce mata komai ba, ya jata suka faɗa kan gado. Ba su tashi bacci ba, sai da lokacin sallah ya yi. Captain Aliyu ya fara tashi, saboda duk abin da yake yi, sam ba ya wasa da sallah. Janye jikinsa ya yi, tare da ture ta da ta ƙara rungume sa."Ki tashi ki yi sallah." Ya ce mata yana buga filon da take kwance da ƙarfi. Buɗe idanunta ta yi tana kallonsa."Please, I need to rest, zan yi sallar zuwa anjima, saboda jiya ka hana ni bacci." Jin abin da ta ce ya sanya shi ɓata rai, tare da daka mata tsawa yana faɗin,"Ki tashi ki yi sallah." Babu musu ta miƙe ta wuce bayi, ba tare da ta yi ƙorafi ba, domin tana mugun tsoron shi, duk yadda yake sonta in ya ɓata rai, ba ta sha da daɗi a Captain Aliyu kenan namijin zuma ga daɗi ga harbi. Bayan ta yi sallar ta koma ta kwanta, ba tare da ta ci abincin da aka kawo musu ba. Da ya idar da sallar fita ya yi, domin za su je je training da Kamil Bayan sun dawo, ya ci abinci sannan ya fita zuwa gurin Kamil. Hannu ya ba shi suka tafa. "Na ga mutuniyar jiya ta zo, ina shirin fita da motata na ganta. Na hange ta za ta shiga gidanka." "Eh, ni na kira ta." Ya faɗa a gajarce yana buɗe lemun da yake gabansa. "Lubaynah, tana matuƙar sonka, domin duk ta bambanta, da sauran matan da muke yin hurɗa da su. Why not ka aurenta, domin tana da kyau.." "Oh please, no! Kar ka yi mini baki." Ya katse shi yana faɗin haka. Mamaki ya sanya shi kallonsa ganin haka ya kurɓi lemun, sannan ya ije ya kalle shi ya ce,"Kasan kalar macen da na ke so na aura kuwa? Mace zan aura tsarkaka wacce ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba. Uwa ta gari zan zaɓawa 'ya'yana, bana fatan Ubangiji ya jarrabce ni da aurar mace mara kamun kai kamar Lubaynah." "Ok, wanzami ba ya son jarfa kenan? Ita Lubaynah da ka ɓata, wa kake son ya aure ta?" "Kan me za ka tambaye ni? Sai ka ce ni na kawo ta barikin?" "Saboda ita ma watarana uwa za ta zama, amma ka ɓata mata rayuwa, Lubaynah is not wore son ka ya sanya ta aminta da kai." "Dole na yi mata? I didn't force her, kuma ni kaina ina fatan Ubangiji ya shirye ni na daina aikata hakan." "Hmmmmh!" Ya ce masa yana kallonsa cikin mamaki ganin ya haɗe rai. "Ni dai a tunanina bai kamata ka yi wa Lubaynah haka ba, musamman da she was virgin kai ka fara sanin..." "Kuma ni na kawota barikin da za ka tilasta mini na aure ta? Na ga kaima ya kamata ka auri matan da kake hurɗa da su." "Duk cikinsu babu wacce na fara saninta. Sannan Lubaynah yarinya ce, wacce ta fito daga gidan mutunci. Iyaye ta they well of. Ga shi duk tana da qualities da kake so." "Ba zan iya aurenta ba, kuma don ni na fara sani ta bani da tabbacin ni kaɗai take kulawa, sannan inda ba ta yi ninyar zama, mara kamun kai ba za ta yarda da ni ba." Cikin mamaki yake kallonsa."Yarinyar nan fa soyayyar da take maka ya sanya ta faɗa irin rayuwar nan." "Ok, in na fahimce ka, so kake sai ka ce dole sai na aure ta? Tun ba yau ba na sha gaya maka matar da zan aura. Yarinya natsatstsiya mai addini, wacce na san iyayenta sun ba ingantacciyar tarbiyya, sannan ba zan yarda na auri mace jahila mara ilmin addini ba. Duk cewa da kake Lubaynah na da ilmi, sam ba ta da na addini, domin duk macen da ta je makaranta, ba za ta mallaka ma namijin daba muharraminta kanta ba. So don haka Please kar ka ƙara mini sha'awar mace irin ta. I dan na tashi aure za ka yi mamakin uztaxiyar da zan aura." "Da irin halayenka Captain Aliyu? Karka manta azzaniyatu wazzani." "Wace mace kaga na taɓa kulawa, bayan Lubaynah da ta kawo mini kanta?Da har za ka danganta ni da auren mazinaciya?" "Ina dai ba ka shawarar ka aure ta, saboda duk saboda kai ta faɗa wannan harkar." "Ba zan iya auren mace da ranar first night ɗinmu, zai kasance mini baƙar rana ba, domin na riga na santa sam ba zan yi ɗokin ranar ba. Bayan haka da kake cewa na aure ta, wane tabbacin kake da shi na cewar ni kaɗai take kulawa? Ni fa ban yarda da ita ba, saboda idanunta ya buɗe, don haka ko xan yi mu'amala da ita sai na yi amfani prevention." "Duk ba mafita bane Captain. Sannan Lubaynah ba za ta zura ido tana kallo ka yi aure ba, yarinyar she is mad in loving you. Za ka kunna wa kanka wutar da ba za ka iya kashewa ba. Kasan yadda mahaifinka ya yarda da kai, amma ka zamar masa fuska biyu. Duk ranar ta da ta ji za ka yi aure. Tabbas za ta sanar da iyayenka, kuma hakan zai rushe yardar dake tsakaninka da su. Kar ka manta ka yi wa Daddy alƙawarin duk ranar duk ranar da ya kamala da wani hali mara kyau za ka ije aiki, ko kuma ya ɗauki duk hukuncin da ya ga dama. Ina ba ka shawarar, ka auri Lubaynah in ya so sai ka auri kalar macen da kake so." "Duk abin da za ka ce, sam ba zan yarda na auri mace da ta siyar da mutuncinta a waje ba, don haka ka daina wahalar da bakinka, sannan am very smart and wise, Daddy ba zai taɓa gane fuska biyu na ke da shi ba." "Hmmmmh! A juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe. I'm a good friend am just advising you. Ka san A friend in need is a friend indeed." "I know my friend, stop fearing am so wise nothing bad will happen." "I hope so." Ya ce masa sai kuma ya buɗe baki zai kara cewa wani abu, domin yana kallonsa a matsayin azzalimi mai son kansa. "Please let's change the topic. I'm frustrating." Ya ce masa cikin ɗaga murya. Dariya ya yi ganin lokaci ɗaya yadda ya hau. Hannu ya ba shi da nufin su tafa, amma sai ya ƙi yana harararsa. Lubaynah 'ya ce ga wani shahararren mai kuɗi a garin Kano, mai suna Alhaji Adamu Laska. Mutum ne da yake da kantina sosai a garin Kano. Matarsa ɗaya kamar rai Hajiya Shuwaima. Suna da 'ya'ya huɗu, ita ce ta biyu tana bi wa Yayarta Hannah da take aure a garin Abuja. Rayuwa suke yi cikin hutu da sangarta, domin a gidan duk abin da suke so shi suke yi. Mahaifinsa ba ya zama mahaifiyarsa 'yar boko riƙaƙkiya, sam ba ta da lokacin kanta. Rayuwa suke yi kowa abin da ya ga dama yake yi. Sakandire da firamare duk a Kano ta yi, bayan ta kammala ta shiga Jami'ar Abuja. Sosai idanunta ya buɗe, domin mace ce classical wacce ta iya wanka. Ta haɗu da Captain Aliyu, a lokacin da ta raka wata mate ɗinta, Barrack ɗin sojoji gidan 'yar uwarta. Captain Aliyu shi kuma mijinta abokinsa ne. Tun ranar da ta ganshi ta mutu a kansa. Sai dai duk nacinta kallon kirki ba ta samu ba. Tana mugun sonsa kamar za ta kashe kanta. A lokacin da ta bayyana masa ƙaunar da take masa, sai ya watsa mata ƙasa a ido, domin bai ɓoye mata ba, ya sanar mata ba type ɗinsa bace. Hankalinta ya yi mummunar tashi sosai ta shiga cikin damuwa. Ta rinƙa nace masa tun ba ya kula ta, har ya fara kulata. Ganin ta kasa samun kansa sai ta shiga seducing ɗinsa, domin a tunaninta wannan hanyar kawai za ta iya shawo kansa. Captain Aliyu, tun yana shareta har ta ci karfinsa ya fara kulata, domin a wancan lokacin tsananin addu'a da tuna kashedin da Daddy ya yi mishi, ya sanya shi ɗauke kansa daga matan bariki, duk da yadda abokansa suke ƙoƙarin cusa masa wannan halin. Sai dai, shigowar Lubaynah cikin rayuwarsa, ya sanya shi manta alƙawarin da ya yi wa mahaifinsa. Samunta da ya yi a matsayin budurwa ya sanya ta samu daraja a gurinsa. Wani lokaci in zai yi tafiya, har ɗaukar ta yake yi su tafi tare. Shi kansa yana sonta, amma ba soyayyar aure ba. Wani lokacin inta ɓata masa har dukan ta yake yi, amma ta kasa rabuwa da shi. Burinta kawai ya tura a yi bikinsu, amma kullum ta yi masa ƙorafin haka sai ya fara kaukauce mata yana kawo mata ƙauli da ba'adi. Washegari bayan sun tashi ta yi sallah. Kicin ta nufa don ta haɗa musu abin karyarwa. Tan ƙoƙarin ɗora ruwan zafi a gas, ya dawo ya buɗe ƙofar kicin ɗin ya shgo. Ganin za ta ɗaura girki ya ƙarasa gunta."Ki bar Peter ya yi mini breakfast, na gaya mini daga abincinsa sai na Momi na ke iya ci." Kallonsa ta yi cikin takaici ganin ya kushe ƙoƙarinta."Haba baby, duk lokacin da na so na faranta maka sai ka nuna ba ka so. Nufinka in mun yi aure wa zai rinƙa muka abinci?" "God forbid." Ya furta a ransa amma a fili jawota ya yi zuwa jikinsa. "Kar ki damu da wannan ki bari lokacin ya yi, bayan nan matata ba za ta rinƙa girki ba." "Don Allah Sojana, ka amince ka turo iyayenka gidanmu ayi maganar bikinmu. Ina sonka na matsu da mu yi aure." Ta ƙarashe maganar hawaye yana bin fuskarta. "Mene ne abin damuwa bayan muna tare? Ina sonki kuma kina mini duk abin da na ke so, sannan duk lokacin da kika buƙaci ganina za ki iya zuwa gidana. Haka kuɗina ATM ɗaya na baki, a ganina rayuwa mu ke yi kamar mata da miji..." "Akwai bambancin sosai. Aure yanada daraja kuma ko ina ana bayyana shi, amma zamammu babu wanda zan yi fatan ya sani. Da ace iyayenka za su buƙaci zuwa inda kake korana za ka yi, amma in ina matsayin matarka cikin farinciki xan jira zuwansu. Wallahi my man ina sonka, na yi maka alƙawarin duk abin da kake so zan yi maka." Juya mata baya ya yi zai fice, ganin tana son ta ƙaryar da zuciyarsa, amma ko mai za ta ce ba zai taɓa aurenta ba. So yake ya auri matar ƙwarai. "Ki yi haƙuri lokaci zai yi saboda ban shirya aure ba." Jin abin da ya ce hawayenta suka ƙaru."Ba ka sona ne, ko kana tunanin aurena, saboda na yadda da kai tun kafin mu yi aure? Wallahi bayan kai babu wanda a taɓa mallakawa jikina. Soyayyarka ce ta makantar da ni har na yarda da kai kafin aure. Don Allah kar ka yi mini butulcin ɗa namiji. In har ban aurenka ba zan iya mutuwa, saboda ina maka mugun son da ban taɓa yi wa wani da namiji ba." Ta furta cikin kuka tare da ƙara rungume shi. "Ban shirya aure ba, in har kin matsu da ki yi aure za ki iya." Jin kalamansa, hankalinta ya tashi kuka sosai ta fashe da shi. "ka fito fili ka gaya mini baka sona Sojana, in har ka yi mini haka sam ba ba ka mini adalci ba." "Kina gaya mini haka, kamar na tursasa ki dole ki ba ni jikinki. Seducing ɗina kika yi har yau ina dana-sanin saninki a 'ya mace, domin ke ce kika sanya na karya alƙawarin da na yi wa mahaifina." Jin abin da yake faɗa cikin zafi kukanta ya ƙaru. Sosai take kuka tana kallonsa."Ni ma ba laifinta bane, saboda kallon farko na kamu da sonka. Na yi iyakan ƙoƙarina na same ka a matsayin miji, amma kullum kalmar da kake gaya mini baka shirya aure ba. Na yi tunanin mallakan maka kaina shi ne kawai zai sanya ka aure ni, amma ashe kuskure ne yi. Kuskuren da yake ƙoƙarin nisanta ni da kai." Duƙawa ƙasa ta yi, ta riƙe hannunsa da yake son fita. "Don Allah ka aure ni, wallahi in har ka rabu da ni zan shiga cikin wani hali." Hannunsa ya fisge, tare da fita daga kicin ɗin yana jin zuciyarsa na zafi. Falo ya zauna ya ɗauki sigari ya kunna. Yana zaune a farkon ta fito da gudu ta wuce shi. Haɗa kaya ta fara yi a ranta ta sanya ko shi ne autan maza ba za ta ƙara dawowa gareshi ba, saboda gara son shi ya kashe ta da ta zauna tana roƙonsa ya aureta yana wulaƙanta ta kamar ba ta da aji. Hawaye ta share tuna irin mazan da suke rububinta, amma ta tsaya yana yarfata. Da ta kuma tuna surarsa sai ta ji anya za ta iya haƙura. Addu'a ta fara tana fatan wannan ya zama na ƙarshe, da zata ƙara dawowa yana more jikinta, domin faɗin ba shi ne na farko ba. Cikin kukan ta gama haɗa kayanta ta fito za ta tafi. Kallonta ya yi, sai kuma ya ɗauke kansa tare da kashe sigarin zai shige ciki. Ganin haka ta sha gabansa cikin muryar kuka ta ce,"In sha Allahu ba zan ƙara dawowa cikin rayuwar ka ba. Zan yi nesa da kai, saboda na lura ba sona da aure kake yi ba." Ba tare da ya ce mata komai ba, ya ɗauke kansa wanda hakan ya tabbatar mata da zarginta. Da gudu ta fice sai ya bi bayanta. "Please in ta fita, ka rufe mini get kar ka bari kowa ya shigo." Ya ce wa Solo tare da komawa ciki, yana addu'ar wannan karon Allah ya sanya kar ta dawo, domin yadda kasan kaska haka ta manne mi shi. Lubaynah tana tafiya tana kuka har ta isa gidan Yayarta Hannah. Ganin yadda ta shigo a birkice, ta wuce zuwa ɗakinta da take sauka sai ta bita da kallo. Mijinta Nura ta miƙawa ɗansu Fadil da yake shan nono."Please baby ina zuwa na ga ta shigo a birkice, wataƙila sun yi faɗa da ɗan iska yaronnan da yake yaudararta." "Ta ke yaudarar kanta dai, har wani namiji za ta rinƙa zuwa gidansa tana kwana, kuma ya aure ta. Kina tunanin ko ni ne zan zaɓawa 'ya'yana ita a matsayin uwa?" "Ba ita ta sani ai duk yadda ake gaya mata ta ƙi ji. Ba ta yi kuka ba, sai ranar da ta ji aurensa." Ta furta bayan ta miƙa masa shi tana gyara zaman rigarta. "Na gaya mata sojojin nan sam ba su da amana. Ya kamata ta yi wa kanta karatun ta natsu, ta nemi wanda yake sonta da aura, amma babu kaffara yaron nan ba sonta yake yi ba. Kina ganin ranar data kawo shi gidan nan, yadda yake fisgewa tana wani tarairayar sa kamar za ta zauce. Ga shi yana mata magana a tsaye tsaye cikin isa. Irin wannan ko sun yi auren, ba zaman lafiya za su yi. Yadda wasu sojojin suke ɗaukar mace ba a bakin komai ba, sannan ta haɗu da mai zuciya." "Ita ta sani, wannan karon zam gaya wa Mommy , saboda babu ruwana tun da ta ƙi ji." Ta ba shi amsa tare da shigewa ciki. Shiga ta yi tana kwance ta yi rub da ciki, kuka take yi sosai har da sheshsheƙa. Har yau in ta tuna wahalar da tasha a lokacin da ya rabata da mutuncinta, sai ta ji kamar za ta yi hauka, duk wahalar da tasha sai ya ce ba zai aure ta ba? Wannan tunani yake sanya ta ji ba za ta iya haƙura da shi ba. "Wahallalliya mara sanin darajar kanta! Sau nawa na gaya miki Aliyu ba auren ki zai yi ba? Tsotse ƙwallon mangwaro zai yi, yar ya huta da ƙuda. Kina ganin dama zai aure ki ne?" "Wallahi Anty Maryam dole ya aure ni, saboda in har ya bijire hakan sai na hana shi zaman lafiya da ita. Ba zan taɓa yarda ya yi aure ya bar ni ba, in har kin ga ya auri wata ki tabbata ba ni a cikin duniyar." Hattara 'yan mata masu bawa maza kansu kafin aure, domin duk namijin da kika amince ya sanki a 'ya mace ba zai taɓa aurenki ba, sannan shi ne mutumi na farko da zai fara goranta miki. In kunne ya ji..... FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 4 "Wallahi Anty Hannah dole ya aure ni, saboda in har ya bijire hakan, sai na hana shi zaman lafiya da duk wacce ya aura. Ba zan taɓa yarda ya yi aure ya bar ni ba, in har kin ga ya auri wata ki tabbata ba ni a cikin duniyar." "Sai ki je ki yi ta wahala har ki kashe kanki. Duk wanda bai ji bari ba, ai ya ji hoho. Ki ta biyewa daɗin bakinsa sai ranar da kika ji ɗaurin aurensa, sai ki yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada." "A ranar kuma zan yi nadamar yaudarata da ya yi, saboda in har ban yi nasarar kashe shi ba, sai na kashe matar daya aura." "Shikenan kin yi maganin matsalar da kanki. Ya je ya auri wata ki ƙare rayuwarki a kurkuku." Ta ƙarashe maganar tare da ficewa cikin takaici. Kwanciya ta yi, ta ci gaba da kuma har sai da ta yi mai isarta, sannan ta shi ta yi sallah ta fito falo don ta ci abinci. Anty Hannah, tana zaune ganinta ta saki tsaki ta miƙe ta bar falon. Zama ta yi kan dinning ɗin xuciyarta na suya. Sosai take ganin son zuciyar Aliyu da ya kasa gane tsananin sonsa, ba ita ta ɗorawa kanta ba, saboda da ace za ta iya cire soyayyarsa tuni ta rabu da shi, duba ga irin wulaƙancin da yake mata. Iya ƙoƙarin da ta yi, na kwana uku ne ta rinƙa danne ƙaunarsa da kamar yanzu ake mata wahayinsa. Anty Hannah tana lura da ita, da take tasa hotonsa tana gani hawaye na bin kuncinta. Ranar da takaici ya ibeta, ta karɓe wayarta za ta fasa."Wallahi kin ji haushi shashashar banza kawai! Haka kawa ki sanya wa kanki damuwa saboda soyayar wanda bai san kina yi ba? Tun da kika dawo ko kuskuren kiranki bai taɓa yi ba, amma kullum kina rungume da waya kina kallon hotonsa. Ni ina mamaki da takaicin 'yan matan yanzu da suke ɗorawa kansu fitina da sunan soyayya. Soyayyar ma so maso wani. Idan ba ya sonki ki yi haƙuri ki nemi Allah ya baki wanda ya fishi." "Ba za ki gane son da na ke masa ba. Ni na san in har bai so ni ba, wataƙila sonsa zai kashe ni." "Ubangiji Allah ya jiƙanki." Ta ce tare da wurgar mata wayar ta shige ciki. Zama ta yi ta fara gwada numbarsa, amma har ta gama ringing ba tare da ya dauka ba. Daga ƙarshe kashe wayar ya yi. Ganin haka hankalinta ya ƙara tashi. Tsaƙonnin ta fara tura masa da haƙuri. Aliyu kuwa tun da ta tafi sai hankalinsa ya kwanta. Fatansa kar ta dawo yana ta shirye-shirye tafiya Kaduna. A ranar da ya shirya ya kulle gidan, ya bawa Peter makulli da zai rinƙa zuwa yana duba gidan. "Na gaya maka in har Lubaynah ta dawo kar ka bata makulli, ka barta ta shiga, karka ƙara zuwa inda na ke." "Ok sir," Ya ce bayan ya miƙa masa makullin. Kayansa ya sanya a cikin motar, sannan ya rufe masa bayan motar ya ce,"Oga safe journey." Kansa ya ɗaga, ya shiga cikin motar da Peter ya gama wankewa, sai ɗaukar idanu da sheƙi take yi. Aliyu yana tuƙi ya jingina da kansa, a jikin kujerar motan yana shafa kansa. Iska yake shaƙa idanunsa lumshe, yana jin tsananin yadda ya yi missing ɗin su. Sosai Mommy ta shirya ma zuwansa, sanin baya cin abincin kowa, ta shiga kicin ta yi masa abinci kala-kala. Da ya isa gida cikin farinciki Mommy ta fito. Sosai take jin daɗin ganinsa, yadda ya yi shiga ta mutunci. "Mommy, na same ku lafiya?" "Lafiya lau ya gurin aiki?" "Alhamdulillah momi kowa lafiya." Gaisawa suka yi da Badamasi maigadi, sannan ya shiga cikin gida. Sashinsa ya wuce ya yi wanka, sannan ya kwanta. Bacci sosai na gajiya ya yi, wanda bai ta shi ba sai da aka kira sallar magariba. Bayan ya yi wanka, ya fito daga cikin ɗakinsa, yana duba tsaƙonnin da Lubaynah ta turo masa. Daddy da yake zaune yana ganin ya shigo cikin falon, ya taso ya rungume shi cikin so da ƙauna. "Son, you are welcome." "Thanks daddy, I missed you." "Missing you too son." Ya ce tare da zama gefensa. "Soja mazan fama." Ya ƙara cewa suka yi dariya. Murmushi ya yi jin abin da ya faɗa, daidai lokacin da Nufaisah ta ƙaraso gabansu ta ce,"Dad, and Ya Aliyu food is ready." "Ok," Ya ce mata yana kallon ta sai kuma suka miƙe zuwa dinning ɗin. Suna cin abinci suna hira cikin ƙaruwar ɗan nasu. Daddy ne ya kalle shi ya ce,"Yauwa kafin ka tafi don Allah, ina son muje wani ƙauye wai shi Damagaran" "Ƙauye kuma?" Ya yi masa tambayar yana ya mutsa fuska kamar ya ga kashi. "Eh, ƙauye ka ji na ce. Ka san Hajiya da rikicinta. Cewa ta yi akwai wata 'yar'uwarta da aka neme ta aka rasa, sai yanxu suka samu labarinta. Shi ne take son ta je ƙauyen, ni kuma na hana ta, na ce ta bari na je na ga yanayin ƙauyen. Ka san yadda 'yan baddits suka yi yawa a ƙauyaku?" "Haka ne daddy. Besides ni fa sam bana son abin da zai sanya na je ƙauye." Dariya ya yi jin abin da ya ce,"Ban da abin Aliyu ƙauye ai tushen kowa ne. Duk wanda ka ga yana birni asalinsa ƙauye ne." "I really hate village and villagers, saboda wani irin rayuwa za ka ga suna yi, musamman 'yan matansu babu wayewa da ilmi, ni fa mamaki na ke yadda 'yan matansu suke samun miji, ko da yake ai maza bagidaju suke aurensu." "Abincin wani ai gubar wani. Waɗannan matan da kake rainawa, su ne suke sanya maza cikin wani hali in suka rasa su." "Shashashu kamar su ba, amma ni ina namiji kamata Daddy ai duk ƙauye babu wanda zan shiga damuwa saboda ita." "Don kawai ba a ƙauye kake bane." "Hmmmmh!" Kawai ya ce tare da ci gaba da cin abincinsa. "Yaushe za mu je ƙauyen?" Ya yi masa tambayar yana kai loma a bakinsa. "Please daddy, ku je ban da ni." Ya ce masa cikin rashin kulawa. "Dole za ka je, domin kowa a gidannan za shi har su Nufaisah da Umma." Nufaisah ta saki murmushin jin daɗi jin abin da ya ce. "Yauwa Daddy zan je ni ina son ƙauye, musamman kwalliyarsu dariya suke ba ni." Cewar Umma cikin farinciki. "Duka za mu je har da mominku da auta, tun da ranar weekend za mu je." "Ubangiji ya kaimu lokacin." Cewar Mommie tana kallonsa. Daddy ne ya kalli Aliyu da ya haɗe rai, saboda tilasta masa zuwa Damagaran da ya yi."Aure fa Aliyu sai yaushe za ka yi?" Shafa kansa ya yi yana ɗan murmushi jin abin da ya ce,"Lokaci ne da zarar ya zo zanyi ai kamar mutuwa yake." "Shiririta kawai ka tsaya ba wai lokacin ne bai yi ba." Mommy ta furta tana kallon sa. Jin abin da ta ce, ya ɓata ransa ba tare da yace komai ba, ya ci gaba da cin abincin. "Ya dai kamata ya yi, saboda lokaci na gudu. In ka duba sa'anninka a Zariya duk sun yi aure har da yara. Mus'ab ɗan gidan Gwaggo Fatu aure na biyu yake nema, amma kai har yanzu ba ka fara neman na farko ba. "In sha Allahu zan yi. Matan ne sai a hankali yanzu rashin tarbiyya da kamun ka ya yi musu yawa, dole na tsaya na natsu na samu mace ta gari wacce zata bawa yarana tarbiya.." Ya ce musu yana kallonsu. "Haka ne ka yi tunani mai kyau amma duk wayonka, da ƙoƙarin zaɓar mace ta gari, dole sai ka haɗa da addu'a, saboda kamar yadda maza ba a ƙwanƙwansawa haka su ma matan. Shi ya sa ake son mutum ya zama na gari, sai Allah ya duba ya ba ka mace ta gari mai irin halinka." Jin abin da ya ce sai gaban shi ya faɗi. Tunani ya yi halinsa, nan take ya ji ya ƙara tsanar tarayyarsa da Lubaynah. Duk yadda captain Aliyu ya kaucewa zuwa ƙauye Damagaran, amma bai ci nasara ba, domin kwana biyar da dawowarsa, Daddy ya shirya sha tara na arziki suka tafi. A ranar da za su tafi ransa a ɓaci yake. Ya shiga cikin motar yana kallon ƙasa fuskarsa kamar an aiko masa da mala'ikan mutuwa. Daddy yana lura da shi, amma bai ce masa komai ba, har suka fara tafiya. Sun yi nisa yana zaune yana kallon hanya, har suka fara shiga cikin ƙauyuka. Ƙaramin tsuka ya ja, saboda yadda motar take ta bugawa da duwatsu tana tsalle kamar za ta kife. "Kai gaskiya ba zan iya tuƙa motarta na shiga ƙauye ba, domin asara kawai zan yi. Haba, ya kamata a ace an samu cigaba an gyara musu titin su." "Laifin gwamnati ne ba ta kula da rayuwarsu ba." Tsaki ya ja ba tare da ya ce komai ba, ya zaro wayarsa ya zai kunna data. Haushi ya sa shi jefar da wayar kan cinyarsa ganin network ya ɗauke. Gabakiɗayan su sun gaji da zaman, Captain Aliyu ya kalli Daddy da yake kallon hanya. "Da wannan nisan Hajiya take son ta zo ƙauyen nan?" "Don na hanata da tare za mu taho." "Aiko da tasha baƙar wuya, saboda da na san haka zamu zaunu a hanya, babu abin da zai sa na zo." "Wallahi ni kaina na gaji so na ke na huta." Mommy ta ce tana gyara zama. Nufaisah da Umma da auta duk bacci suke yi. Sun shigo cikin ƙauyen motarsu ta lalace. Fitowa suka yi cikin damuwa, suka tsaya suna kallon direba da yake ta ƙoƙarin gyara motar. "Alhaji, ruwa ne ya yi ƙaranci a motar dole na je tafi na samo." Ya ce masa yana kallonsa tare da buɗe Boot ya ɗauki jarka. "Na gaya maka ka rinƙa kula, ka tabbatar da ka duba ruwa da mai, saboda mu kiyaye ɓata lokaci." "Sai da na yi hakan kasan ƙarfe nasara." Shiru ya yi, ba tare da ya ce komai ba cikin takaici. Ganin haka ya sa shi fara tafiya don ya samo ruwan. "Karo na farko da na je ƙauye kuma na tsani zuwa." Ya ce tare da dukan bayan motar. Babu wanda ya tanka masa domin su kansu a gajiye suke. Fara taku ya yi, yana kallon dajin da yake ɗauke da kayan lambu. Kamar su mangwaro, kashu, gwaiba, da malmo. Tsintar kansa da son ganin dajin ya yi, saboda shi mutum ne mai tsananin son shuke-shuke, domin duk shukar dake cikin gidansu shi ya shukata. Bishiyar mangaro ya ƙarasa, yana kallon yadda suka girma suka yi jajir. Ba sha zai yi ba, kalan mangwaron ya burge shi. Yana ta kallon mangwaron cikin sha'awa, yana tunanin in ya koma sai ya nemi kalarta. Wayarsa ya ɗauki zai ɗauki hoton. Daga saman bishiyar kuwa, Jimmalo ce zaune tana ta shan mangaro. Tun da Kaka Tani ta aike ta, ta je gidan ba ta nan, sai kawai ta taho nan tasha mangwaro. Duk cikin mangwaron ƙauyen babu wanda take so sai ita. Tana cikin sha, ta kama reshe ta yi ɗare-dare sai ta kalli ƙasa. Da sauri ta kama bishiyar tana salati don saura ƙiris ta rikito. "Wa innahu sulaimanu.Tuf-tuf." Ta ce cikin tsananin razana tare da ƙwala ƙara. "Wayyo na yi gamo da Balaraben aljani." Ta furta tana zare ido, saboda tsananin kyansa ya firgita ta. Sam ba ta yi tunanin shi mutum bane, saboda ba ta taɓa kawo cewar mutum mai kyau kamarsa zai iya zuwa ƙauyen ba. Captain Aliyu, da yake ɗaukar hoton mangwaron sam bai ji ihu ta ba, saboda tazarar da ke tsakaninsu. Yana shirin juyawa, daidai lokacin daidai lokacin da ta furta a ranta. "Wannan aljanin sam kar ya tsorata ki Jimmalo, domin kin sha tabaraka kin sha yasin. Ki tsorata shi kawai ya bar gurin ki gudu." Ga mamaki sai ta ji ta fara rage tsoron. Mangwaro ta tsinko wace ta nuna. Da sauri ta sanya hannu ta ligwigwitata, sannan ta saita shi ta maka masa aka. Cikin tsoro ya ɗaya kansa yana kallon sama, sai kuma ya kalli kansa ganin yadda farar shaddarsa ta lalace, saboda mangwaron ta fashe duk a jikinsa. Tsoro ya kama shi yana zare ido yana kuma kallon sama Ganin yadda ya ruɗe sai ta saki dariya tana faɗin,"Shegu aljanu ashe suna tsoron bil'adama." Ta ce tare da tsinko mangwaron har uku ta ƙara kwaɗa masa aka. Zafi da takaicin yadda kayansa ya ɓaci suka tunzura shi. "Ko da ace aljani ne yake jifa na da mangwaron nan, wallahi sai na yi maganinsa." Ya ƙarashe maganar yana kallon kayansa cikin takaici. Ganin yana kallon bishiyar kuma zai iya hangenta, sai kawai ta fara girgiza bishiyar tana kukan jaki. Da sauri ya bar gurin cikin tsoro. Dakewa ya yi, amma zuciyarsa ta razana. "Lafiya Aliyu, mai ya faru da kayanka?" "Please mu bar gurin nan, akwai aljanu a gurin." Yadda ya yi maganar ya ƙara tsorata kansa, kuma ya tsorata su. "Mun shiga uku! Mu bar gurin don Allah." Cewar Nufaisah tana kuka saboda tana da tsoron aljanu. Bayan Mommy ta ɓoye, don gani take aljanin sun shiga jikinsa yadda yake zare ido. "Don Allah, mu bar dajin nan, in motar ta ƙi gyaruwa sai ya gyara ya kawo." "Ku shiga cikin mota in sha Allahu za ta tashi." Direba ya ce yana kallonsu yadda suka firgice. Cikin sa'a yana kunna motar ta tashi. Da sauri suka shiga ya fara tafiya. Da tarin gajiyar da suke ɗauke da shi, da kuma tsoro ya sa babu wanda ya ce uffan, har suka ƙarasa cikin ƙauyen. Gidan maigari suka isa, tare da yi musu kwatancen gidan da suke nema. Maigari ya cika da mamaki jin sun ambaci Tani. Tsananin mamaki ya kama shi ganin mutane 'yan birni kyawawa suna nemansu. "Aminu," Ya yi kiran ɗaya daga cikin ɗansa. "Na'am," Ya amsa tare da ƙarasowa yana kallonsu kamar zai cinye su. "Ma za ka nuna musu gidan Tani, kuma kar ka sake ka shiga gidan, ka dai san halin yarinyar nan." "To Baba." Ya masa tare da fara tafiya yana kallon su kamar zai lashe su. "Kai gaskiya ƙauyen nan da akwai sunan da ake kiran inda yafi ƙauye, haka ya kamata a kira. Dubi ɗan ƙauye kamar a haɗa a yi gida ɗaya, kuma wai a haka suke rayuwa har suke farinciki? Allah na gode maka da ka halicce ni a birni, domin wannan ƙauye ba shi da maraba da maƙabarta, shi ya sa tun da muka shigo ventilation ya canza. Ga mutane kamar kaji kuma babu hyiegene, ai dole ya rinƙa wari." Ya ƙarashe maganar, cikin tsananin ƙyama yana kallon ƙauye tamkar kashi, sannan ya ɗora da cewa," "Ga turosu ake ce masa ko turasa, wannan kashin shanun?" Ya ce yana kallon Mommy. "Turoso kake nufi?" "Yauwa eh shi." Ya ce mata yana hangen kashin kamar zai yi amai. Dariya Mommy ta yi, ba tare da ta ce masa komai ba tana kallon hanya. Sai ƙorafi yake yana jan tsuka. Su kansu sai da suka yi dana sanin zuwa da shi. Sun yi shiru suna kallonsa cikin mamaki, jin yadda yake sakin magana, ko kunyar ɗan maigari ba ya yi. "Captain Aliyu, zan iya rantse maka akwai waɗanda suke rayuwa a ƙauye nan kuma suka fi ka farinciki. Ba kuɗi ko jin daɗi bane farincikin rayuwa. Duk wanda ka ga Allah ya halitta, sai ya ba shi abin da zai sanya shi farinciki." Kauda kansa kawai ya yi, tare da jan tsaki, ba tare da ya ce masa komai ba. Ji yake ya takura saboda gabakiɗaya baya jin daɗin ƙauyen..Ga kayanshi da suka yi staining duk da ya goge da tissue paper. A lokacin da suka yi sallama, Kaka Tani tana kicin tana gyara tukwane da ta gama wankewa. Jin sallamar sau uku ya sanya ta zabga tsaki, sannan ta fara tafiya tana faɗin,"Na san ba ya wuce 'yan kawo ƙara. Bari na je na ji uban abin da za a ce ta aikata, kuma wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe ba wanda zai duƙar mini jikalleta." Tana wannan ƙorafin ta isa ƙofar gidan, don bala'i ko sallamar ba ta amsa ba. "Waye ya dame ni da sallama kamar na ci masa ba shi?" Ta yi tambayar, daidai lokacin da ta isa ƙofar gidan tana yafa mayafi. Kallonsa ta yi ta ce,"To yau kuma mai za a ce ta yi? Don na san zuwanka ba alkairi bane." "Halinta ya sanya ba na zuwa da alkhairi." "Au rashin kunya za ka yi mini?" Ta ce masa tana kama baki. "Baba ya ce na kawo ɓaki suna neman gidanki." "Ni ƙawar mai daddawa! Su waye ne?" Ta yi masa tambayar tana dafe ƙirji. "Ni ma ban san su, amma a mota suka zo kuma ƙatuwa, don kawai a ƙasa take tafiya da na ce jirgi ne." "Nufinka mai kama da jirgi?" Ta yi masa tambayar cikin ruɗu. "Eh, ga wani sanyi kamar raɓa a ciki." "Kai muje na gani anya ba makuwa suka yi ba?Saboda iya sanina babu wanda zai zo a mota yace yana nemana." Fara tafiya ya yi tana binsa a baya, yayin da zuciyarta take cike da tsoro. Turus! Ta tsaya tana kallonsu cikin zallar mamaki. "Su waye waɗannan?" Ta yi ma kanta tambayar tana kallon su. Kamar yadda take kallonsu haka suke kallonta, musamman Captain Aliyu da yake mata kallon ƙaskanci. "Da ma gurin wannan tsohuwar mai kama da lagwani muka zo? Na sha wannan wahalar." Ya tambayi kansa yana mata kallon sama da ƙasa. Tsananin mamaki ya kama shi, duk da cewar ya san ba wasu mutane masu aji za su gani ba, amma bai yi tunanin 'yar tsohuwa kamarta za su zo gurin ta ba. Siririn tsaki ya saki ganin tana sanye da riga da zani da ɗankwali, dukanninsu daban-daban, sannan fuskarta duk ta yi rama alamun tsufa, har idanunta sun fara shigewa ciki. Har ta fara duƙawa. "Bayin Allah lafiya kuwa, ko dai makuwa ku ka yi?" Ta yi musu tambayar tana kallon su. Wai ya ne readers ba kwa comments gaskiya ya kamata na ga ruwan comments yana tashi. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 5 "Bayin Allah lafiya kuwa, ko dai makuwa ku ka yi?" Ta yi musu tambayar tana kallon su. "Nan ne gidan Tani ƙanwar Malam Aifi, wanda yake wankin hula. A Ƙauyen Madu?" "Eh, ni ce bayin Allah ya aka yi kuka san Yayana marigayi Malam Aifi?" Ta furta tare da zare ido tana kallonsu cikin tsananin mamakin yadda aka yi suka san shi, ganin su 'yan birni kyawawa da su. Murmushi ya yi, ganin yadda ta shiga damuwa. "Ki kwantar da hankalin ki baƙi kika yi daga birni." "Ikon Allah ni?" Ta yi masa tambaye tana nuna kanta. "Eh, zan iya shigowa saina yi miki bayani?" "Ku zan tambaya don yadda na ganku jikinku kamar tsada, wataƙila ba za ku iya shiga ba." Murmushi ya ƙara yi a karo biyu, ya kalli iyalansa ya ce,"Mu shiga ciki." Captain Aliyu da yake tsaye yana kallonta a wulaƙance ya ce,"Wa ni? Allah ya tsare ni ku je kawai." Ya ce masa yana kallonsa yana taɓe bakinsa kamar ya ga kashi. Ganin abin da ya yi, sai kunya ya kama shi, ba tare da ya iya cewa komai ba, ya shiga cikin gidan. "Ni ban san wane irin jarrabawa na faɗa ba, har daddy ya sanya na biyo shi ƙauyen nan, domin wallahi da na san zan zo ƙauyen nan ba zan dawo ba, saboda takura da kashin shanun da nake gani a ƙauyen nan, har ji nake numfashinsu zai ɗauke." Ya ce tare da buga bayan motar. A cikin gida, Kaka Tani mamaki sosai ya kamata bayan sun sanar mata daga inda suke. "Ikon Allah, yanzu kai ɗan gidan Yaya Binta ne?" "Eh wallahi nine ɗanta na farko, ita ta turo ni kan na zo na ga inda kike, kuma tun da na gani in sha Allahu za mu zo." Kuka ta fashe da shi tana faɗin,"Ashe Binta ba za ta manta da ni ba? Oh Allah dube ka yadda ka yi ƙatoto abin ka, ka girma ka tara iyali. Rabona da ita tun da ta zo ganin gida a lokacin da ta yi arba'in ɗinka." Shafa kansa kawai ya yi, ba tare da ya ce komai ba, yana murmushi. "Umma, ku ce wa direba ya shigo da kaya a mota." Ya ce yana kallon Kaka Tani da take ta kallon su, kamar za ta lashe su. A ƙofar gida kuwa, captain Aliyu yana tsaye cikin ɓacin rai yana kallon wayar da, da network har yanzu bai dawo ba. "In har ana son mutum ya mutu ba tare da lokacin su ya yi ba, ace ya yi rayuwa a ƙauyen nan." Ya ce yana kallon wasu almajirai da suka zo wucewa. Jimmalo ce take tafiya tana dariya, tuna abin da ta yi wa aljani. Idan dariyar ta ciyo ta har sai ta daka tsalle. Ƙawarta Karime ta jawo da sauri wacce ta hango ta, ta rugo da gudu tana nishi. "Ke zo ki ji labari?" "Ni ma zuwa na yi na gaya miki..." "Don ki tsaya ki ji nawa, kin san dai in ina magana bana bari a katse ii?" "Ina jin ki to." Ta ce tana kallonta. "Balaraben aljani na tsorata.." "Aljani kika ce?" Ta yi mata tambayar tana matsawa kamar ita ce aljanin. "Eh, wallahi yarinya. Ba ki ga yadda ya firgita ya riga da gudu ba." Ta ƙarashe maganar tana yaba jarumtarta, tare da sakin mahaukaciyar dariya. "Ni dai na san ance duk wanda ya ga aljanu sai ya mutu Jimmalo?" "Au ƙarya zan yi miki kenan? To aradun Allah yau idona idon aljani, kuma gani a gaban ki ras ban mutu ba, an gaya miki ni matsoraciya ce?" Ta ce da muryar ƙatti. "A'a ni ban ƙaryata ki ba, kawai mamaki na ke yi." "Ki daina mamaki, ina kan bishiya na ganshi yana tsaye kyakkyawar gaske! Da fari na firgita, amma da na daure na janyo masa aya, sai kawai ya fara hayaƙi zai ƙone, ganin haka na maka masa mangwaro , da sauri ya ɓace ɓat." Ta shirya mata ƙarya tana jinjina kanta. "Kai Jimmalo ki ji tsoron Allah. Ke da ba kya zuwa makarantar allon sai kin ga dama, har yaushe kika iya karatun da za ki ƙona aljani?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki. "To uban me kika ɗauke ni? Ai gara ni ina zuwa in na yi ninya.. Ke da ko kin je kanki kamar ɗankwali yake ba ya ɗauka? Ina fa ji ranar nan kina karatun sallah kika ƙaranta addu'ar shiga bayi a maimakon sura" "Ni Jimmalo ƙarya za ki yi mini?" "Ki rantse da Allah ba haka aka yi ba?" Cikin jin kunya ya ce,"Ai Allah ya halicce ni a haka." Don ta tuna ranar. "Kar ki yi mini rashin kunya, na ci uban haure mai gindi. Kin san duk da ƙawata ce ke, wallahi rufe idanu zan yi, na gurza miki rashin mutunci. Yanzu zan wanke miki baki da yashi. Da ma na ga kwana biyu ba kya wankewa, haka juya kika dame mu da wari da kina waƙa a dandali." "Hmmmmh! Wai sauba na gaya wa dirimi nisa. Ba gara ni ina wankewa watarana in Innata ta matsa mini ba, ke kuwa haƙoranki har gansa kuka suke yi." "Kutumar uba! Wallahi yanzu zan canza miki kamanni, yau ba ki ba fitowa dandali. Sai dai ki yi kunyar bakinki." Ta ƙarashe maganar tana gyara ɗammara za ta shaƙota. Dariyar yaƙe ta yi jin abin da ta ce." Ke kuma ba ki san wasa ba? Kamata ya yi ma ki yi mini kyauta, saboda alkhairi na zo na gaya miki" "Aikin san bana ɗaukar raini. Ko kujerar maka kika ba ni zan iya gurza miki rashin mutunci, in na gama sai na yi miki godiya." Ta ce tare da kwance ɗammarar da ta yi. "To ki yi haƙuri na yadda kin ƙona aljani. Kina jina ko? Yanzu na zo wuce ta ƙofar gidanku, kawai na ga jirgin sama an faka ta a ƙofar gidan wai kun yi baƙi daga birni." "Jirgin sama da yake yawo a sama, shi ne aka faka a ƙofar gidanmu.?"Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki. "Zai iya faruwa mana, ba yanzu kika gaya mini kin ƙona aljani ba?" Ta ce mata cikin gatse. "Share zancen jirgi. Kika ce mun yi baƙi 'yan birni?" "Eh, wallahi masu kyau, sai shiga ake da abincin birni a gidanku." "Da gaske kike 'yan birni sun zo gidanmu? Kin san a ƙauye nan, babu wasu wanda suke da 'yan'uwa a birni, sai ɗan maigari da ya yi karatu ya ke aiki a can?" "Eh mana ba ki ga wani namiji ba, na ɗauka daga sama ya faɗo saboda tsananin kyansa." "Wallahi in kika yi mini ƙarya sai na koya miki hankali, don har na fara tunanin rashin mutuncin da zan yi, in rama yangar da yarinyar mai gari take mana." "Da gaske na ke yi kike ki gan..." Wani irin sufa ta yi, kawai sai ta ganta a can nesa da ita tana gudu. "Jimmalo, ki jira ni." Ta furta tare da bin ta da gudu. Gudu take yi, ba ni da iya gudu ba kamar ba mace ba, duk wanda ya ganta sai ya ɗaga mata hannu yana faɗin,"Jimmalo jikar Tani." Ba tare da ta kula su, ba ta ƙarasa ƙofar gidan tana nishi, sai dai da sauri ta tsaya tana zare idanu. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta dafe ƙirjinta tana faɗin haka, a lokacin da ta ƙaraso ƙofar gidan. "Wa innahu sulaimanu, tuff!tuf." Ta ce cikin razana tana tofawa, ganin Captain Aliyu a tsaye ya jingina da mota, saboda rashin haƙuri ji yake kamar ya shiga mota ya koma. Sam ya ji ƙauye bai yi masa ba, da mutanen ƙauyen musamman 'yan matan da suke kallonsa. Ya saki tsaki, daidai lokacin da wata mai tallar rogo ta zo za ta wuce ta gabansa. Ganinsa da fari ta tsorata sai da ta fahimci mutum ne sannan ta washe haƙora tana waigensa, har sa da ta kusa kifewa sannan ta daina kallonsa. "Banxiya ƙazama kawai." Ya ce yana dafa motar cikin ƙosawa. "Jimmalo lafiya kika tsaya..?" Ta yi mata tambayar lokacin da ta ƙaraso tana haki. "Ke na shiga uku! Wallahi aljanin da na ƙona ya biyo ni." Ta ƙarashe maganar cikin razana, kawai sai ta ruga cikin gida tana ihu. "Wayyo Kaka Tani aljani na ƙona ya biyo ni." Ta ƙarashe maganar tare da shallake su Daddy ta haye kan Kaka Tani. "Ke Jimmalo, lafiyarka ƙalau kuwa?" Kaka Tani da hankalinta ya yi mugun tashi ta riƙe ta tana tambayarta. "Aljani ya biyo ni har ƙofar gidanmu saboda na ƙona sa." "Ina aljanin yake?" Suka haɗa baki har da Mommy da Daddy gurin tambayar hakan cikin tsoro, tunawa da suka yi Aliyu yace da aljanu, yanzu kuma ita ma ta faɗa. "Eh, wallahi aljani ne a waje ya biyo ni, saboda na ƙona....". Maganar ta maƙale mata, sakamakon masu kama da shi da ta gani. "Kaka Tani, su waye waɗannan?" Ta yi mata maganar tana nuna Nufaisah da ta fi kama da shi sak! Wacce ta ƙanƙame Mommy tana duk addu'ar da ta fito cikin bakinta. "Ki natsu baƙi muka yi daga birni." Cewar Kaka Tani tana sakinta ganin ta natsu. "Birni! Dama muna da 'yan'uwa a birni?" "Eh mutum ɗaya ce,mahaifiyarta da mamana yan uwane ita ma mijin da ta aura birni yake zama yana kasuwanci, shi ne da Allah ya buɗa masa ya zo ya tafi da ita. Waɗannan jikokinta ne da ɗanta ya haifa." "Har da wanda yake waje?" "Eh, shi ma ɗan uwanmu ne. Shine ɗana na fari." Daddy yace yana mata wani irin kallo, ganin yadda ta yi shiri, kamar wata mahaukaciya. Wani irin dariya ta saki tana kallonsu tana matsawa cikin tsananin farinciki. "Yan'uwanmmu daga birni?" Sai ta ƙara kecewa da dariya ta nufi Nufaisah da ta yi matuƙar tsorata da ita ta rungume ta. Da sauri Nufaisahh, ta matsa saboda wani irin wari da cika mata hanci. Kallon da take mata ya sanya ta tunzura." Ke dallah me mai yasa kike kallona kamar kin ga kashi?" "Ba komai." Ta ba ta amsa da sauri ganin kallon da take mata. "Kaka Tani ina zuwa."Ta ruga da gudu waje tana faɗin haka. Kaka Tani dariya ta saki tana kallon inda ta wuce."Jikalle ta ɗaya tamkar da dubu kenan. Ita kaɗai iyayenta suka haifa suka mutu sakamakon kwalara da suka yi. "Allah Sarki Allah ya jiƙansu." Suka haɗa baki gurin faɗin haka. A waje tana fitowa da gudu ta taho zata rungume Aliyu. "Oyoyo, Yayana daga birni. Yau zagaye ƙauyen nan zan yi da kai, kowa sai ya ga ina da 'yaya ɗan bir...." Maganar ta katse sakamakon ingije ta da ya yi, domin da farko ya ɗauka mahaukaciya ce zai gudu. "Ke! Are out of your mind?" Ya ce mata tare da wanka mata mari, sai kuma ya matsa yana gefe, sakamakon wani irin juyawa da jikinsa ya yi, saboda warin da ya shaƙa na jikinta. Kafin ya wani yunkuri ya shiga kwara amai, saboda ji wani irin ƙarni da hamami jikinta ya ji yana yi. Marin ya sanya ta tsaya tamkar gunki, domin ta ji shigarshi sosai, har sai da ta ɗauke wuta, idanunta suka daina aiki na wucin gadi, amma da yake jaruma ce, ba ta nuna ta tsorata ba, sai kawai ta daure. Haƙoranta ya kalla, har sai da ya ji tamkar zai amayar da kayan cikin shi, ganin yadda suka dafe, ga sauran abincin duk sun maƙale sun zama gansa kuka. Ranta ne ya ɓaci ganin aman da yake kwarawa, wanda ya tabbatar mata da ƙyamarta ya sanya shi amai. "Banza ƙazamiya shashasha mahaukaciya! Ke a ba ki da han kawai sai ki zo da nufin ki rungume ni, saboda ba ki da hankali. Dubi jikinki kamar mahaukaciyar kina ta wari. Dirty girl kawai." Zagin da ya yi mata, da abin da ya faɗa wanda ba ta gane da Ylyaren da ya yi mata ba, suka haɗu suka hautsina ƙwaƙwalwarta wacce ba ta aiki bisa ƙa'ida. "Kan uba! Ka mare ni? Wallahi daina rama, domin duk faɗin ƙauyennan, babu uban da zai kare ni ban rama ba." Ta ce tare da nufarsa za ta mare shi. Captain Aliyu sai mamaki ya kama shi sosai, na jarumtakar da fitsarrarta da kuma rashin tsoronta. Idanunsa ya xaro yana kallonta. Ganin ta ɗaga hannun da gaske za ta mare shi, sai kawai ya ƙara ɗaura mata mari ya fara dukanta. Tun da ta fita hankalin Daddy ya tashi sosai. Ya san cewa da wuya su kwashe lafiya, ganin yadda take abu kamar sabon kamu. Jin kukanta ya sa Kaka ta mike cikin tashin hankali tana faɗin,"Innalillahi! Wa ya sanya jikalle kuka?" Da gudu ta ƙara da har zaninta na shirin faɗi. Mommy da Daddy suka rufa mata baya, a ransu suna addu'ar Allah ya sa ba zarginsu bane. Turus! Suka tsaya suna kallonsa da yake kai mata duka. "Kai mahaukacin ina ne za ka kama jikata da duka?" Kaka Tani ta yi masa tambayar cikin ɓacin rai. "Kafin nan sai ki tambayi fitsarrarriyar jikinki mai ta yi mini." Ya ba ta amsa cikin ɗaurewar fuska. "Amma kai kuwa an yi mara kunya tambadaɗɗe, saboda rashin ta ido ka biyo ta har cikin ƙauyen su ka buge ta?" Jin abin da ta ce Daddy ya lalle shi ya ce,"Aliyu bana son hauka kar ka ƙara dukanta." "Tunanin kasheta ma nake yi, tsaf zan iya sanya bindiga na harbe ta." "Aiko da wallahi ka jawo ma kanka tashin hankali da bala'i, kuma ba ƙyaleka zan yi ba, saboda tun da nake da jikalle ta babu wanda ya taɓa sanya kuka."Kaka Tani ta Male shi cikin tsananin fushi yana faɗin haka. "Ko yi haƙuri don Allah mu shiga ciki zan yi masa faɗa." "A"a mugunta ce bana so, haka kawai ya zo ya duke ta? Ya bar ganin don kun kawo mini abu, wallahi keta masa rashin mutunci zan yi, don zan iya haƙura da kowa a kan jikalle." "Ki bar shi da ni Kaka Tani. Aradun Allah yau sai na zubar masa da haƙora, sai dai ya sanya na roba, in ya koma birni." Ta ce tana neman abin da zata rama dukan da ya yi mata. Zaro idanunsu suka yi, cikin tsananin tashin hankali, ga in ta ɗauko ƙarin dutse ta buge shi. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don Allah Daddy ka yi wani abu kar ta buga masa..." Kafin ta ƙarasa da daddy ya yi wani yunƙuri ta wurgar masa tana faɗin, "Na rantse yau sai ka gane ka dauki Jimmalo, sai na canza maka halitta, na bar maka tabon da za ka rinƙa tunawa da ni." Cikin sa'a ya kauce dutsen ya bugu gilashin motarsu. Mamaki ya kama su, suna kallon gilashin da ya tarwatse har sai da suka matsa a gurin. "Jikalle, ki yi haƙuri ai abin da kika yi masa zai gane ke ba ƙanwar lasa ba ce." Suka ji muryar Kaka Tani tana faɗi tare da ƙoƙarin riƙeta, maimakon ta yi mata tsawa, don sun yi tunanin mari masu zafi za ta yi mata ko ta rufe ta da duka, ganin abin da ta aikata.. "Tofa! Waɗannan wasu irin mutane ne?" Mommy ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin mamaki. "Ku yi haƙuri don Allah mu shiga ciki." Ya faɗa yana kallon Aliyu da tsantsar mamakin abin da ta aikata ya kamasa. Cikin tsananin ɓacin rai ya sarfaci daddy ya shaƙota. Sai da ya ƙara wanka mata mari, sannan haure ta ya tofar da miyau yana kallonta a yatsine. "Ƙaxamiya daƙiƙiya jahila kawai! A yau na taɓa ganin ki, kuma zan yi addu'ar Allah kar ya ƙara nuna mini ko mai kama da fuskarki, domin matuƙar na ga mai kama da ke, xan iya kasheta. Ke kuwa in har kika bari muka ƙara haɗuwa, kin ji na rantse sai na harbe ki. Bindiga zan sanya na yi daga-daga da namanki." "Ni ma zan yi maka kashedin karka yi fatan mu ƙara haɗuwa, saboda na rantse sai na zaman maka ƙadangaren bakin tulu. Sai na sanya ka tsani duniya da rayuwarka." Ta ce masa ciki tsiwa da rashin kunya. Ana riƙe ta tana fisgewa tare da tsalle zata cakume shi. Haka shi ma zuciyarsa ta tunzura, ji yake in har bai canza mata kammanni ba yau, sam ba zai iya rintsawa ba. Da ƙara aka samu aka hanata dabben da take son su yi. Shi kuma Mommy ta riƙe sosai tana kuka. Ganin kukan da take yi, ya sa shi fasa abin da ya yi ninya, don ya ayyana hatta ƙashin jikinta sai ya ɓaɓɓalla ya watsar. Su Daddy sun cika da mamakin rashin kunyarta, ganin yadda take magana tana kama ƙugu kamar za ta dake shi. "Wannan wace irin yarinya ce babu tarbiya?" Daddy ya tambayi ka sa cikin tsananin mamaki. "Please Aliyu, mu shiga mota kai kuma Daddy, ka shiga ku yi sallama." Mommy ta ce tare da kama hannunsa, suka shiga motar tana huci tamkar mesa. Dady kuwa cikin rashin ƙwarin jiki, ya bi bayan Kaka Tani, da take kwashewa Aliyu albarka, ko kunyarsa ba ta ji. "Zan tafi sai mun ƙara dawowa. Ku yi haƙuri da ain da ya faru." Ya ce tare da ciro kuɗi ya bata. "In har za ka dawo, ka tabbatar da ba ka zo mini da fitsarraren yaronka ba, domin ba zan iya ƙara lamunta ya dukan mini jika ba." Ya ce masa tare da amsar kuɗin cikin ɓacin rai kamar ya bata guba. Kasa cewa komai ya yi, sai dai ya bita da kallon mamaki. Jiki a mace ya shiga cikin mota. Ba tare da ya kalli Aliyu da yake huci ba, ya cewa direba,"Ka ja mota." "To ranka ya daɗe." Ya amsa tare da ba wa motar wuta. "Wallahi in har zan ka yarinyar nan sai na yi ajalinta. Wannan dalilin ya sa ya tun farko na ce ba zan biyo ka ba, saboda matan ƙauye jahilai ne, ba su da hankali dabbaci kawai suka sani." "Kai kuma sai ka biye mata, kashe ta ka yi ninyar yi?" "Haka na yi ninya maganin rashin kunyarta na so na yi." Ya ba shi amsa ba tare da ya tauna maganar ba. Cikin takaici daddy ya kalle shi. Ya san halinsa in har ransa ya ɓaci, sam ba ya tuna magana. "Gaskiya matar nan ta ɓaci tarbiyyar yarinyar nan, dubi rashin kunyar da ta yi maka, amma ba ta tsawata mata ba?" Mommy ta ce tana kallon Daddy. "Abin mamaki ni kaina na yi mamaki ƙwarai." "Hmmmmh! In dai haka rayuwarta za ta miƙe ina tausaya mata." "Wallahi yarinyar ba ta da kunya. Na yi mamaki da ta iya ɗaya hannu za ta duki Ya Aliyu." Cewar Nufaisah cikin ɓacin rai. Ƙuta ya yi, ba tare da ya ce komai ba, amma har yanzu zuciyarsa tafasa take yi, tamkar za ta fito waje. Sun shigo cikin gari Daddy ya kalle direba ya ce,"Ka kaimu gidan Hajiya, na gaya mata na je ƙauyen." "To ranka ya daɗe." "Please ya sauke ni a gida, a mood ɗin da nake ba zan iya zuwa gidan Hajiya ba, kun san halinta ɓata mini rai kawai za ta yi." "Sauke shi kawai." Daddy ya ce don ya san kowa ya je damuwa zai ƙara masa. Da suka isa ƙofar gidan hon suka yi maigadi ya buɗe. Hajiya jin sun dawo sai ta fito daga cikin ɗakinta zuwa harabar gidan. "Sannunku da dawowa." Ta faɗa tana kallon Daddy da ya fito daga cikin mota, sai kuma ta juya idanunta tana kallon Mommy, da rissina cikin girmamawa ta ce," Ina wuni Hajiya?" FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 6 "Sannunku da dawowa." Ta faɗa tana kallon Daddy da ya fito daga cikin mota, sai kuma ta juya idanunta tana kallon Mommy, da rissina cikin girmamawa ta ce," Ina wuni Hajiya?" "Lafiya lau, ya hanya." Amsawa ta yi tana ƙoƙarin shiga cikin gidan. Jikokin nata suka gaisheta. Rungume su ta yi cikin so da ƙauna, sannan suka rankaya suka shiga cikin gidan. "Bari na kira Hafsatu mai aiki ta kawo muku abinci, na ga kamar da ga ƙauyen, kawai wutowa nan ku ka yi?" "Eh wallahi Hajiya abin mamaki na tarar a ƙauyen." "Mamaki kuma ta mutu ne?" Ta yi masa tambayar cikin tsoro. "A'a tana nan cikin ƙoshin lafiya, kuma ta amshe mu hannu biyu-biyu, sannan ta ce na gaishe ki sosai. Sai dai fa yarinyar da take riƙo ta ce mana jikanta ne, iyayenta sun mutu sakamakon kwalara da ta kama su. Yarinyar da suka bari sam ba ta da tarbiya. Ga ta ƙazamiya mara kunya. Kin ga rashin kunyar da ta yi wa Aliyu? Wallahi har dabbe ta so su yi, ta kuma fasa mana gilashin mota." Tsananin mamaki ya kamata jin abin da ya ce, sai kuma ta ɗaure fuska tana kallonsa. "Shi Aliyu ɗin uban me ya yi mata? Ai ni dama ban so tafiyar da shi ba, saboda na tsani baƙar zuciyarsa, ace yaro saboda ɓakin rai da zuciya sam ya kasa samun matar aure? Ato wacce matar za ta aure shi yana wannan zuciyar, domin tsaf a rashin imaninsa zai iya sanya bindiga ya harbe ta." "Hajiya soja ne shi fa, kuma dole ya kasance yana da zuciya da mazantaka, kina sane da 'yan da masu garkuwa da mutane suka damu ƙasar mu. Shin in ba shi da zuciya, ya zai yi ya ɗauki hukunci a kansu?" "Oh kenan kai kake ɗaure masa gindi? In ya yi zuciya a gurin daga, sai kuma ya yi a cikin danginsa? Ni ban san kinibibin da ya sanya ka tafi da iyalinka ba, na so ka je kawai ka ga wuri ka kai ni." "Ki yi haƙuri in na ɓata miki rai, dama na so na ƙarfafa zumunci." "Zumunci? Ai ga shi wancan mai baƙar zuciyar ya ɓata, tun da ya je ya dukan mata jika." Jin ya yi shiru ta kalle shi ta ce,"Yanxu yaushe za mu je ka kai ni ƙauye na gansu, kuma na ɗauku su su yi mini kwana biyu?" Zare ido ya yi jin abin da ta ce yana kallonta."Eh mana ya kamata na je mana, ko saboda jikarta ba ta da kunya ba za mu yi zumunci ba. Abubakar kar ka manta cewar duk wanda ya yanke zumunci Allah ba ya tare da shi. Da irin mugun halinka yanxu da kake nunawa, in har na kwanta dama za ka yi zumunci kuwa? Ko don ka ga su 'yan ƙauye ne?" Kallonta ya yi yana mamakin abin da ta ce. "Haba Hajiya, sai bai kamata ace kin yi mini wannan tambayar ba. Tun da kika gaya mini na je na ga inda suke, hankalinsa bai kwanta ba sai dai na je." "To da ka tashi zuwa mai ya sa kake da Aliyu? Kana sane da yaron nan ɗan banza ne. Sam rayuwarsa ba ta yi mini ba, tuntuni na gane ya tsani ƙauye da mutanen ƙauye. Arzikin sunan mijina, da aka sanya masa kawai nake raga masa bana gurza masa rashin mutunci duk da halina bane." "Ki dai yi masa uzuri amma bana tunanin haka. Ƙauye ai tushen kowa ne." "Ina zai san hakan tun da ya ga an haife shi a birni. In da ace Allah bai sanya na auri mahaifinka ɗan birni ba, wallahi Kaunyenmu ko girki da icce ba a yi sai turoso, sannan yanzu ya aurar da 'ya'ya." Ta ce masa fuskarta a ɗaure. Ganin ƙorafin ba zai ƙare ba, sai ya kalle ta ya ce,"Am Hajiya ina ganin bari mu wuce gida." "Abinci fa? Daga tafiya kuka dawo ya kamata ku ci abinci." Ta ce sai kuma ta ƙwala kira tana faɗin,"Hafsatu, ki kawo musu abinci." "Hajiya, da kin barshi in muka koma gida sai mu ci." "A'a bari ta kawo ai mun gama." Ta ce tare da miƙewa ta nufi kicin ɗin, ganin ba ta ji kiran ba. Bayan sun gana cin abinci sun mike ta kalli Daddy."Ina son ka samu lokaci sai ka kaini ko, domin so na ke na ɗauko su su yi kwana biyu, yadda Allah ya yi ma 'ya'yana arziki, dole su ci gajiyar haka tun da su kaɗai na ke da su.?" "Hajiya karki ɗauko mutanen nan wallahi tsaf za su sanya miki hawan jini, domin in har tana gidan nan ba za ki iya shaƙar iska mai daɗi ba." "Sai kuma na kyale 'yan'uwana su ci gaba da rayuwa a haka? Zuwa zan yi na ɗauko su, sai na gyara musu rayuwarsu na samu lada." Ganin yadda ta yi maganar a xafafe ya ce,"Shikenan Hajiya, yadda kika ce haka za a yi." Ya ce cikin biyayya. "Allah ya kaimu kuma ya yi maka albarka." "Amin," Ya amsa cikin farincikin. Ko da suka koma gidan hirar Jimmalo suka rinƙa yi. Har lokacin da za su kwanta, sannan aka kashe wutan gidan suka kwanta. Captain Aliyu da tun da suka dawo ya shiga cikin ɗakinsa ya kulle ƙofa. Zuciyarsa tafasa take yi. Tun da yake ba a taɓa wulaƙanta shi irin na yau ba. Wulakancin ma wata yar ƙauye kucama ƙazama da ita. "Yarinyar nan da ace babu zumunci. Wallahi sawa zan yi a harbe ta, sannan a ƙona gidansu." Ya furta tare da zaro sigari ya kunna yana shafa. Kwanciya ya yi, sai kuma ya ɗauki waya zai kira Lubaiyna, amma sai ya fasa ya yi wurgi da wayar cikin takaici. A haka ya kwana cikin tsanannin takaicin abin da ta yi masa, domin ko abinci bai nema ba sai ruwa da ya rinƙa banka ma cikinsa. Ga shi yana gida ballanatana ya sha maganin damuwarsa. Cikin dare kasa bacci ya yi yana ta juye-juye har zuwa uku da rabi, sannan bacci ya yi nasarar sace shi. Jummmalo zaune a baƙin ƙofar ɗakin Kaka Tani. Kaka Tani take gasa mata inda Aliyu ya haure ta. Ƙuta ta yi tare da jan tsaki."Na rantse wannnan ɗan iskan ɗan birnin da na sani da na karya masa muƙamuƙi, tun da ba shi da mutunci. Da wata fuskarsa kamar alalar da ba ta nuna ba." "Ke ma jikalle kin cika rikici, daga ganin mutum sai ki hau neman shi da rigima?" Ɓata fuska ta yi tare da kwaɓa-kwaɓa za ta yi kuka."Kaka Tani, kamar goyon bayansa kike yi, ko saboda sun kawo miki abin arziki..." Bige bakinta ta yi cikin ɓacin rai,"Ja'irar banza kina ganin har akwai abin da za a kawo mini ya sa na goyi bayan wani? Ba kya gani takanas daga Kaduna suka zo gurina, amma na rufe idanuna na yi musu kashedi?" "To ai ke ne ba ki ga ciwon da ya ji mini ba kike ƙorafi." Ta ce tana kallonta a sakalce. "Ina miki ƙorafi saboda ki daina ƙoƙarin gwada ƙarfin ki da maza. Inda ya ji miki rauni ya kike so na yi? Kin san ke kaɗai ba ke gani na ji daɗi." "Hakan ma ba zai faru ba, saboda kin san ina da ƙarfi. Ni fa kamar soja na ke, domin da ace a birni na ke na yi karatu, aradu soja zan zama na yi ta dukan masu laifi, ina harbinsu da bindiga, kuma ko ciwon da ya ji mini ai shammatata ya yi, wallahi da sai na kai ƙato ƙasa. Tsaf zan wawuri ƙafarsa na danƙarashi da ƙasa, amma ko yanzu a juri zuwa rafi, watarana fili zai fashe, domin na ratse duk lokacin da Allah ya haɗa ni da shi sai na kai gardi ƙasa." "Kar na ƙara jin haka saboda ɗan'uwanki ne, kuma ba kya ganin irin abincin da suka kawo mana, duk garin nan wa kika ga 'yan'uwansa sun taɓa kawo musu haka?" Ƙara ta saki tana birgima a ƙasa."Dama na faɗa kwaɗayin abin da suka kawo kike yi, shi ya sa da ya naushe ni, ba ki sanya taɓarya kin ragije shi." Jikinta ya kama rawa ganin jin abin da take cewa."Haba Jimmalo, ki tashi a ƙasa kin ga kina ɓata kayanki, kuma na san ko sama da ƙasa za ta haɗe, ba za ki yi wanka ba. Ki je ki ƙara ganin kayan da suka kawo mana, na tabbata za ki yarda da abin da suke cewa." Ƙara ta yi sai kuma ta kalle ta tana satan kallon inda kayan suke. Ganin haka ta kama hannunta tana faɗin,"Yauwa Jimmalo jikar Tani, ma za ta shi kin ji jikalle." Kamar wata 'yar ƙaramar yarinya ta miƙe tana tafiya, sai ka ce yar kaciya ta isa gurin. Zama suka yi suna duba kayan. Kayan abinci sosai suka kawo musu, da sabulu man-shafawa da kuma kilin."Kin ga kaya sosai har da man-shafawa na 'yar birni? Da ace ke wata ce sai ki yi wanki kuma ki yi wanka." Ɓata fuska ta yi jin abin da ta ce,"Aradu ba zan yi wanka ba sai bikin Tasallah ya zo, ko ranar da kika sanya ni dole na yi haka na yi ta soshe-soshe, don haka ba zan cutar da kaina ba." Zare ido ta yi cikin mamaki jin abin da ta ce,"Sai nan da sati biyu za ki yi wanka Jimmalo? Kin san irin ƙarnin da kike yi?" "Ni fa ki daina cewa ina wari saboda babu ƙarin da na ke yi." Ta ƙarashe maganar tana sunsuna hammatarta da ya cika da gashi ba ta askewa."Kaka Tani shi shima ki ji wallahi ba ya wari." Da sauri ta matsa nesa da ita tare da toshe hancinta."Ba kya dai jin warin, amma ko wucewa mutun zai yi sai ya gane ba kyau wanka. Ga kayanki can na wanke, amma ba za ki yi wanka ba?" "Ba zan yi ba, sai lokacin bikin shi ma don kawai ina son na gurzawa Badaru rashin mutunci ne." Ta ce tare da ɗaukar ledar biskit. Ɓarewa ta yi ta kai bakinta."Kai 'yan birni suna morewa wallahi. Kaka Tani dole mu kai musu ziyara mu je mu ci yo daɗi." Ta ƙarashe maganar tare da miƙa mata ledar biskin ɗin. "Ah'ah, wai ba dai daɗi ba, kin ji yadda kunnina yake zut!zut? Dole mu je birni, amma kuma kina ganin za su dawo, bayan kin fasa musu gilashin mota?" "Za su dawo mana, in kuma ba za su dawo ba, sai mu tafi nemansu a birni. Ni fa na so na yi masa mutunci kar na nuna masa kalata, shi ne kawai ya nuna ƙyamata kamar ya ga kashi. Ni kuma haushin hakan ya sanya na fasa masa gilashin motar, saboda ya san ba a ja da ni, kuma kin ga ko dawowa suka yi zai ji shakkata." "An gaya miki birni ƙauye ne da za mu je nemo su? Kuma na rantse ba na jin zasu dawo." "In ma ba su dawo ba sai na je nemo su in kina jin tsoro." "Ke ma kin san duk inda za ki ƙafarsa ƙafarki." "Haka ne kakata." Ta ce sai kuma ta farko kwalin indomie ta fara iba tana ci. "Allah ya isa domin Ubangiji kawai zai saka mana, yadda 'yan birni suke cutarmu, suna cin kayan daɗi. Kaka Tani ji wannan kalar biskit ɗin mai gishiri." Karɓa ta yi ta kai bakinta tana lumshe idanu."Kut! Gaskiya Allah sai ya saka mana, domin garin daɗi na nesa. Shi ya sa kika gansu kamar an ɓaro su a kwali, musamman wannan mara mutunci ba dai gayu ba tsafta ba." Ta ce suna ta cin indomie suna santi. "Ni fa ban ga kyan shi ba saboda dana kalle shi lokacin da ya mare ni, wai yana amai saboda warin jikina da biri yake kama." Kaka Tani bata bata amsa ba, Salame ta yi sallama da tirenta na satin ayaba. Ganin ta a zaune ta yi turus! Sai kuma ta ƙarasa."Lafiya Jimmalo, ba za ki je sarin ayabar ba?" Kallonta ta yi tana shirin ɓoyewa indomie ɗin, domin Jimmalo ba dai rowa ba. Kowa ya sanya da shegen rowa, da kuma son abun wani. Ko gidansu ƙawayenta suka zo tana cin abinci, babu kunya za ta cinye ba tare da ta yi musu ta yi ba, in kuma ta ga na wani jikinta har rawa yake yi. Ko ba a yi mata tayi ba sai ta sanya hannu. Ka yi magana ta ce za ta nuna ma mutum ƙarfi. Yanzu ma ɓoyewa ta yi tana mazurai. "Ke wallahi Salame, gidanku kamar ba a iya tarbiya ba. Na gaya miki ki dinga sallama kafin ki shigo gidan mutane, tun da ba tsoho da tsohuwa suka gina ba." Kama bakinta ta yi tana kallonta daidai lokacin da ta ƙaraso."Ke har bakin magana kike da shi? Ke da sai dai ki shigo ɗakin mutane da gudu, saboda an yi miki sai ki ji haushi?" Harararta ta yi, tana tana ƙara ɓoye indomie ɗin ba tare da ta ce komai ba. "Jimmalo, wai mai kike ci kike ɓoyewa? Bayan ke mutum ko a takashi ya sanya sai kin ƙwakulo?" "Babu komai." Ta ce tare da ƙara yanke fuska. Shammatarta ta yi ta ture ta ta ɗauki indomie."Kai Jimmalo, da ma taliyar birni kike ci shine za ki yi mini rowa?" Cikin masifa ta miƙe za ta cakume ta, ammma jin ta ce taliya ya sanya ta tsaya."Uban wa ya gaya miki taliya ce? Biskit ɗin birni ne fa, kuma waallahi kika ƙara mini haka, sai na shuka miki rashin mutunci." Ta ce cikin fushi tare da komawa ta zauna. Ba tare da ta ji kashedinta ba ta ƙara kai hannu ta karɓa."Ke wallahi taliyar birni ne. Kin san Yaya Kabiru yana zuwa birni? Da zai dawo ne ya siyo ya koya mana yadda ake dafawa, kamar taliya aka dafata ga daɗi wallahi." "Mai ƙarya?" Ta furta tana juya ledar. "Ɗan wuta kuma in ba ki yarda ba ki gwada girkawa." Ba musu ta miƙa ta ɗauki tukunya ba tare da ta ɗauke ba, ta ɗora a wuta tare da kumbula ruwa rafin tukunyar. "Kan uba sai ka ce za ki dafa ganda?" "Ya ake yi kin san ba girki na ke yi ba?" Ta yi mata tambayar tana zare idanu. Tukunyar ta sauke ta rage ruwan sosai, don kusan juyewa ta yi sannan ta mayar da tukunyar. Suna tsaye ruwan ya tausa ta zuba. "Laa, Salame ashe wallahi da gaske ne! Kin ga Kaka Tani, har ta dahu." Ta ce tana kallonta cikin tsananin farinciki. "Ikon Allah ta dahu sai ƙamshi take." Ta ba ta amsa daidai lokacin da ta ƙaraso. Zaman ci suka yi duk wahalar da ta sha gurin girkin, kaɗan ta sam mata ta cinye tana lashe hannu. Bayan sun gama ci. Kaka Tani ta rarrashe ta don ta fasa ƙara girkawa da za ta yi."Kin ji jikalle, ki bari sai kin dawo sarin ayabar, kin ga rana ta ja yi." "Ai da kin bar ni na ƙara wallahi daɗi ya ke da shi sosai." "Je ki dawo kin ji?.Ga kuɗin ki kula kar ki yi faɗa da kowa." "To,"Ta amsa tare da janyo ɗankwali tasha ɗammara suka fita. A hanya suna tafe suna hira har suka isa. Bayan sun sari ayabar suka wace tasha, anan suke siyarwa. Sai da ta sayar duka, sannan ta shigo musu rogo da gyaɗa da za su ci da daddare. A gajiye ta koma gida, babu tunanin yin sallolin da ba ta yi ba ta kwanta. Bacci ta yi kafin magariba ta miƙe ta shiga bayi. Da ta fito zama ta yi kan turmi tana irga cinikinn da ta yi."Ga shi Kaka Tani, wannan zan sayi ɗantamatsitsi da hanjin ligidi, a dandali." "Allah ya yi miki albarka, amma ya kamata na saro miki gyaɗa ki kai dandalin?" "Eh ki saro da yawa." "Yauwa jikalle." Ta ce tare da ɗaukar mayafinta ta fita. Ko wace mace ta yi wanka, tasha kwalliya cikin riga da zani daban ɗankwali daban. Jimmalo ce kawai ta buga daka tsami ta zo. Dama duk ranar da za ta je dandali take ƙuru ta ke yin dakatsamin. Duk wanda ya yi kuskuren zama kusa da ita sai ya rinƙa kauda hanci. Tana zaune da tiren gyaɗa suna hira da Ladiyo. Wani saurayi mai suna Bala ya ƙara so gurinta. Wani irin tsuka ta ja tare da kauda fuskarta tana harararsa. Ganin haka ya tsaya sororo a kusa da ita."Jimm..." Kafin ya gama kiran sunan ta taso masa kamar za ta cinye shi."Na gaya maka Bala ka fita idanunka, saboda wallahi ko maza sun ƙare ba za iya auren ka. A yadda kake siririn nan kamar tsinke, in ka ɓata mini rai tsaf zan sanya hannu na karya ka." Kunya ce ta kama shi, ganin yadda take maganar cikin ɗaga murya. Samari da 'yan mata na dandalin suka tsaya suna kallonsu. "Ke!" Ya daka mata tsara yan huci tamkar mesa, sannan ya ci gaba da da cewa,"Don kin samu na ce ina so ki?In ban da rashin zuciya irin tawa, uban me zan yi da mace ƙazamiya irin ki, da ko wanke baki ba kyau yi. Dubi kayan jikin ki, kamar wacce take suyan kifi. Kin taɓa jin warin da kike yi kuwa?" "Kutumar ƙaniya!" Ta ce tare da ƙara sakin wani ashahariyar, sannan ta miƙe ta cakumi wuyarsa."Ni za ka yi wa rashin mutunci? Ka san ina wurin uban wa ya ce ka ce kana sona?" Ta furta tare da shaƙe masa wuya. Duk iya ƙoƙarin su don su raba su, amma ta ƙwaƙume shi sai cizo da yakushi take kai mishi. Da ƙyar suka samu suka raba su. Kallonsa ta yi tana huci."Dubi yadda na yi maka jina-jina a haka kake so na so ka?" Harara ya gallah mata ya wuce cikin tsananin jin kunyar yadda ta disga shi. Ihu da tafi suka ɗauka suna mata kirarin,"Jimmalo jikar Tani kin gagari kowa har da maigari." Kanta ne ya fadi ta ji kamar ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba, tare da murmushi a fuskarta. Saboda faɗan da suka yi, sai dandalin bai yi wani armashi ba. Ba su kai yadda suke daɗewa ba, suka tashi kowa ya nufi gida. Hajiya tana zaune da littafin Hisnul Muslim a hannunta tana dubawa. Daddy ne ya yi sallama ya shigo. Zare gilashin idanunta ta yi wanda yake medical. Kallonsa ta yi cikin tsananin ƙauna. "Barka da zuwa ka iso?" "Eh, tun jiyada kika gaya mini kina son ganina, na so in zo, ban tashi kasuwa da wuri bane." Ya faɗa bayan ya zauna kusa da ita yana gaishe ta. Amsawa ta yi idanunta na kansa."Kan maganar da muka yi da kai, na zuwa ƙauyen na ga inda 'yar'uwata take." Gabansa ya faɗi jin abin da ta ce. Sam ba ya son zuwa ƙauyen nan, ba wai don abin da ta yi musu ba, hatta hanyar ƙauyen fargabar bi yake yi, musamman da Aliyu ya ce masa akwai aljanu.". Gyaran murya ya yi, don ya kawo uzurina da zai hana zuwansa. "Hajiya na ɗauka mun gama maganar cewar tun da..." "Ka ga ban son dogon bayani in har ba za ka je ba, sai ka haɗa ni da direba mu je." Kallonta ya yi da sauri jin abinda ta ce,'Haba Hajiya, ace kina da ɗan da ya iya mota sai na bari direba ya kai ki?" "To zan yi maka dole ne? In ka ce ba za ka je ba, ai dole na je tun da dangina ne." "Shikenan, ki sanya rana yaushe za mu je?" Jin abin da ya ce fara'arta ta ƙaru."Ai ni ko gobe ka ce a shirye na ke. Ka faɗa mini ranar da za ka je." "Ki bari sai ranar sati Hajiya." "Allah ya kaimu." Ta ce tare da cigaba da jan carbinta.Miƙewa ya yi jikinsa a mace ya ce,"Hajiya, zan wuce kasuwa." "To shikenan, Allah ya yi maka albarka, sannan karka manta goro na ya ƙare." "Hajiya ya kamata ki rage cin goro, sam ba shi da amfani." "Allah ya kyauta, in ka ga na daina cin goro sai dai in bani da rai, ai goro ya zama tamkar abinci." "Allah ya kyauta." Ya ce sannan ya doshi ƙofar fita. "Amin," Ta ba shi amsa tana kallon sa. Hajiya shirye shiryen tafiya ta fara ta haɗa musu kaya sosai. A ranar da ta kasance ranar da za su tafi, tun safe suka ɗauki hanya. Kallon hanyar take tana mamakin nisan gurin, musamman da ta ga sun shiga cikin turɓaya suke yi. Da suka isa da ƙarfi ta samu ta fito, sakamakon ƙafafunta da suka yi mata nauyi sosai. Bayan ta fito da gyalenta a hannun."Ikon Allah! Allah ɗaya gari bambam. Dubi inda 'yan'uwana suke rayuwa, babu abababen more rayuwa?" Ta furta tana kallon ƙauyen cikin mamaki. Daddy bai ce komai ba suka kama hanyar zuwa gida. Kaka Tani tana zaune a tsakar gida tana kasa ayabar da Jummmalo za ta je tallah inta dawo daga iban ruwa rafi. FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 Follow the ƘIYAYYAR JINI channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P PAGE 7 Da suka isa da ƙyar ta samu ta fito, sakamakon ƙafafunta da suka yi mata nauyi sosai. Bayan ta fito da gyalenta a hannunta."Ikon Allah! Allah ɗaya gari bambam. Dubi inda 'yan'uwana suke rayuwa, babu abababen more rayuwa?" Ta furta tana kallon ƙauyen cikin mamaki. Daddy bai ce komai ba suka kama hanyar zuwa gida. Kaka Tani tana zaune a tsakar gida, tana kasa ayabar da Jimmmalo za ta je tallah inta dawo daga iban ruwa rafi. Sallamar da aka yi ya katse mata hanzarin ta. Ba ta amsa ba, sai ta yafa gyalenta ta nufi ƙofar. Turus! Ta tsaya tana kallon Daddy, tana masa kallon kamar ta gane shi. Mayar da idanunta ta yi kan Hajiya. Ganinta ya sanya ta saki fara'a. "Ikon Allah Atine! Ashe za mu ƙara haɗuwa?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin mamaki tana kallonta. Hajiya rungumeta ta yi tare da ƙanƙame ta."Ga shi Allah ya sake haɗamu Tani." Sosai suka rungume junansu kamar ba za su rabu ba. Da ƙyar suka saki juna sannan suka shiga cikin gidan. Kallon gidan take yi wani iri mai ɗauke da ciki ɗaya guda biyu, sai kuma ɗan tsakar gida da kicin. Ruwa ta ibo mata a randa mai tsanannin sanyi ta kawo mata. "Ga shi kisha Tine, wallahi ban yi tunanin da gaske ɗanki bane, musamman da yaronsa ya zo ya yi mana ɗiban albarka." "Ki yi haƙuri haka ya gaya mini, da san tare zai zo da shi zan hana shi, saboda shegen zuciya ce da shi kamar kuturu, ga shi saboda rashin tunani suka bar shi ya zama soja." "Soja?" Ta dafe ƙirjinta tana kallonta."Haba biri ya yi kama da mutum. Shi ya sa zuciyarsa sam babu imani. Wani naushi da ya yi wa jikalle sai da ta yi sati tana jinya. Kin san sojojin nan ba imani ne da su ba, haka kawai za su iya kashe mutum. Ni dama tun da na ga fuskarsa babu fara'a, na san cewa ba shi da imani." Maganarta ta ƙarshe ya sanya Hajiya ta kalli Daddy, ganin babu kunya tana kwashe wa ɗansa albarka a gabansa." "Hmmmmh!" Allah ya shirya." Ta furta tana son kauda zancen. Dady kuwa kallon ta yake cikin tsananin mamakin ƙarfin halinta. "Ka sanya direba ya shigo da tsarabar." Ta ce masa tana kallon da. Fita ya yi daga cikin gidan ba tare da ya tanka ba. "A Hajiya ba ku gajiya? Kayan da ku ka kawo mana bamu gama amfani da shi ba." "Ai yiwa kai ne. Kune fa kawai kuka rage mini dangin mahafiyata, Allah ya yi mini arziki in ban taimaka muku ba, wa zan taimaka wa?" "Haka ne Allah ya ƙara buɗi." Ta ce sannan suka ɓarke da hira ana tuna baya. A guje ta shigo cikin gidan tana ihu murna. Da sauri Kaka Tani ta miƙe ta tare ta tana faɗin,"Jikalle, murnar mai kike yi haka? Ina tulun da kika je uban ruwa?" Dariya ta ƙara saki ta ce,"Bala ya fasa mini tulu ni kuma na fasa masa kai. Wallahi sheme shi na yi yana can a rafi kwance, jini yana ta zuba a kansa." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin farinciki. Hajiya ta miƙe da sauri tare da dafa ƙirjinta. Da ta shigo ta ɗauka mahaukaciyar ce, amma tuna Daddy ya gaya labarinta sai ta tsaya cikin mamaki tana kallonta. Ganin yadda take cikin dauɗa da ƙazanta ya sanya ta jinjina kanta. "Yauwa 'yar albarka. Gara da kika ragije mishi kai, sai yan san ke ba sa'arsa bace." "Wallahi na yi maganinsa domin a nan na sanya sandata na ragije shi, nan take ya zube babu numfashi. An gaya masa ni sa'ar ce? Ni ko mai gari maigari shakkarsa, domin duk wanda ya cuce ni ba zan yarda ba sai na rama. Ni fa Kaka Tani a yadda na ke jina zan iya zama soja." "Za ki iya zama ƙarfi ne dake kamar 'yar doki. Allah ya yi miki albarka ba ki zama marainiya ba, tun da za ki iya rama ma kanki." Hajiya ta zare idanu ta yi tana kallon ta."Tani mutum ta fasawa kai amma kike goyon bayanta?" "Gara da ta yi maganinsa ya takura mata." Ta ba ta amsa tana kallonta. Sai a lokacin Jimmalo ta ɗaga kai tana kallonta, don ba ta lura da ita ba. Tana ganin shigarta ta gane daga birni take. Cikin tsananin rashin kunya ta ce,"Ke kuma ina ruwanki dangin dagiro? Ni bana son shiga sharo ba shanu." A tsiwace ta ƙarashe maganar tana harararta. Mamaki ya kamata jin abin da ta ce. So take ta toshe hancinta, saboda tsananin wari da ya cika hancinta. Kallonta ta yi yadda ƙafafunta suka farfashe, ga wani uwar faso da ya cika ƙafar har mutum zai iya ajiya. Babu abin da ya ƙara munanta fuskarta, sai haƙoranta da suka dafe da dadti. Sun yi jajur har wani gansa kuka suke yi. Amai ne ya taso mata, amma sai ta daure, tana jin yadda cikinta ke juyawa. Don kar ta yi ƙarya za ta iya cewa har zarni take yi. Wataƙila tana fitsarin kwance. Ko kuma tsabar dauɗa da ƙazanta ya sanya kayanta suke tashi. Kalar kayan da ta saka sam mutum ba zai iya ganewa ba, saboda sun yi duƙu-duƙu. Bige bakinta da Kaka Tani ta yi tana faɗin,"Bana son rashin kunya 'yan'uwanmu ne daga birni." Hannunta ta janye tare da kallonta ta balla mata harara,"Ni ki ƙyale ni saboda na tsani duk wanda zai zo daga birni, tun da ɗan su ya kira ni da ƙazamiya wawiya daƙiƙiya har yana kirana da dabba! Ita ma na san cewa za ta yi ba ni da tsafta." Kaka Tani kunya ta kama ta ganin rashin kunyar da take yi, sai ta shiga yaƙen dole."Ki yi haƙuri kin san sha'anin yara, ta ɗauka kema mara mutunci ne kamarsa, ba ta san kina da mutunci ba." Kasa cewa komai ta yi, tana kallonta jin abin da ta ce. "Sam Aliyu bai yi ƙarya ba, duk sunan da ya kira ta da shi ta cancanta." "Amma Tani kina ji fa, kai ta fasa ma wani kuma kike goyon bayanta?" "To sannu uwar zugai! So kike ta buge ni? Inda ya kashe ni an kawo mata gawata sai ki yi farinciki ko? Ki ji daɗi an kashe mata jikallenta ɗaya kamar rai da take da shi." Kamata ta yi ta rungume tana rufe mata baki."Ki yi shiru ba za ki mutu ba,gara da kika rama kuma a shirye na ke na je kotun ƙoliya a kanki." Mamaki ya ƙara kamata sai ta shiga jinjina kai. Daddy kuwa bai yi mamaki ba sam. A ransa ya ji daɗi da suka yi mata haka, don ta ga ainihin kalarsu. Ta daina tunanin jajibo su cikin rayuwarsu. "Anya kina kyautawa rayuwarta, ita fa 'ya mace ce, wacce za ta tarbiyyantar da wasu. Irin wannan gurbata da kike ɗora ta kina ganin daidai ne? Haba Tine kar son zuciya ya sanya ki ɓata rayuwarta. Dubi jikinta yadda take cikin dauɗa babu tarbiya babu ilmi. "Dama na san ita ma abin da za ta ce kenan. Na rantse ta ƙara ce mini ƙazama sai na...." Sallamar da aka yi ya sanya ta yi shiru cikin mamaki."Ina zuwa jikalle, na san ba zai wuce kiran mai gari ba." "Shi ne tun da na ji muryar wannan mara mutunci, yana ji da wuya kamar mariƙin lema." Ta furta tana zabgawa Hajiya harara. "Bari na fita yau ma kamar kullum muke da nasara. Wane dare ne jemage bai gani ba?" Ta furta tare da fita bayan ta yafa mayafinta. Kallon wulaƙanci ta yi masa tare da ba ka masa harara."Kai dai ka zama mujiya ganinka ba alkhairi ba." "Ko kuma kune ku ka zama ganinku ba alkahiri ba. Kun addabi ƙauyen nan, muna fatan ranar da Maigari zai sanya mu yi muku korar kare, donn har da jifa za mu haɗa muku." "To in ya kasa korarmu kai ba sai ka kore mu ba, ina nan ina haƙonka watarana sai na ja maka asarar da har ka mutu ba za ka manta ba." Jimmalo tace tana aika masa da mugun kallo. "Kafin ki aikata kin bar garin nan. Kwanan za mu ja miki Yasin ki mutu kowa ya...." "Sai dai duk yaranka su mutu, amma ba jikalle ta ba." Kaka Tani ta ce tana kallonsa. "Maigari yana kiranku kuma ya ce ƙafata ƙafarku." "To sai ka kama mu ka kaimu."Ta faɗi hakan cikin tsananin rashin kunya ba tare da ta duba girman shi ba. "Kar ku zo ku jira ya zo da kansa. Ni ɗan tsaƙo ne kuma na isar." Ya ce tare da wucewa. Sororo suka yi suna kallonsu."Ɗauko mayafinki muje jikalle." Kaka Tani ta ce tana gyara nata mayafin. "Mu je kawai na ci ɗanmara ba sai na yafa ba, amma wallahi yau duk wanda ya yi mini ba daidai ba sai na shuka masa rashin mutunci." "Mu je wa ya isa ya taɓa ki." Ta ce tare da kama hannunta. Har sun yi nisa suna bambami sai ta tuna da Hajiya. Dawowa ta yi inda take."Don Allah ki yi haƙuri yanzu za mu dawo." "Mu je tare saboda na ga ba haƙuri za ku bayar ba." "Saboda me zan ba da haƙuri? Yaron nan shi yake takalarta. Ana soyayya dole?" Shiru ta yi suka kama hanya ba ta tanka ba, don ba ta da abin da za ta ce. Ganin haka Daddy ya bi bayansu cikin takaici. Da suka isa gidan maigari, shiga suka yi ba tare da fargaba ba. Cikin tsananin ɓacin rai ya fara magana, amma sam ba su razana ba. A maimakon su ba da haƙuri yana faɗa suna mayar masa, musamman Jimmalo da harshenta ya fi na kowa. Da ma ga ta da murya zaƙwai. Su Hajiya da suka zo sai suka ɓuge da ba da haƙuri. Da ƙyar aka kashe maganar, bayan sun ɗauki alkawarin kula da lafiyar Bala. Da suka kai shi kyamis ɗin Audi aka yi treatment ɗinsa. Sai da suka ba da kuɗin da za a kula da shi. Ransu ya ƙara ɓaci ganin ba babu nadama a fuskarsu, sai ƙorafin kuɗin da suka ba da suke yi. "Tani tarbiyar da kika ɗora kenan? In kika mutu kika barta sawe irin rayuwa kike so ta yi?" "Kuka kawai suka ji ta fashe da shi."Wallahi Kaka ba za ta mutu ba, sai dai ki mutu ki barta." "Dole zan mutu amma ba yanzu ba jikalle. Share hawayenki ina nan tare da ke." Ta ce tana jijjiga ta sai ɓare baki take yi. Gani lamarin yafi ƙarfin ta sai ta zauna ta yi shiru."Ki yi haƙuri yarinya ya ce, kuma ita kaɗai ta rage mini." Ta ce tare da zama a gurin ta. "Ni zan koma." Ta faɗa cikin ɗaure fuska. Jin abin da ta ce ya tabbatar mata da ta yi fushi."Ki yi haƙuri don Allah na ɗauka kwana za ki yi?" "Ki barta ta tafi Kaka umma ta gaida ashsha." Jimmalo ta ce tana wasa da ƙasa da ta zuba ruwa ta kwaɓa. "Ba a yi haka ba domin baƙonka Annabinka. Ta so mu ba ta haƙuri." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, ta shige cikin ɗaki tana wakar sharmandu. Hajiya sai ta kasa cewa komai. Tunani ta fara dole ta yi haƙuri in har tana don ta canza su, amma to ta yaya za ta iya? Tambayar haka ya faɗo cikin ranta. Za ta gwada domin sai an gwada akan san na ƙwarai. Zama ta yi sannan ta kalle ta."Ba kwana za mu yi ba, amma sai yamma za mu tafi, kuma ina son mu je damu sai kuga inda na ke zama tun da na zo na ga gurinka." Fara'ar Kaka Tani ya ƙaru jin abin da ta ce."Wai kina nufin mu biku birni?" Ta yi mata tambayar cikin murna. "Eh, sai ku kwana ko biyu ne." Murna suka ji Jimmalo ta fara tana tsalle tana faɗin,"Za ni birni na ci daɗi, sai kuma ta tsaya da rawar ta ɓata fuska ta fito waje. "Hajiya, mene dangantakar ki da wannan mara mutuncin da ba shi da mutunci?" "Jikana ne." Ta ba ta amsa. "Taɓ aradu ba zan je ba, saboda na tsani wannan mutumin, kuma in har zan ganshi sai na rama dukan da ya yi mini." Zare idanunta ta yi jin abin da ta ce.Sai kuma ta yi murmushi."Kar ki damu ai ba gidana yake zama ba, kuma soja ne ba ya zama a garin." "Au to zan je. Wato dama soja ne shi yasa ba shi da imani? To ai ni bana tsoron soja, saboda tsaf zan iya zama soja, na rinƙa harbe kan 'yan ta'adda. Wallahi tsaf shi ma zan kara da shi, saboda duk ranar da ya ƙara dukana sai na fasa masa kai." Ta ce tare da matsowa gunta, tana washe baki tamkar ba ita ta gama mata rashin kunya ba. Hajiya jinjina kanta ta yi domin ta fara jin tsoronta, saboda yadda take maganar har cikin zuciyarta. Kallo ɗaya za ka yi mata ka san bata da tsoro. Har ta fara tunanin an ya za tafi da su, saboda kar ta kai tashin hankali gidanta, don ta san duk ranar da Aliyu ya zo haɗuwar ba za ta yi kyawu ba, amma da ta tuna Aliyu ba cika zuwa ba, saboda yanayin aikinsa, sai hankalinta ya ɗan kwanta tamkar ta yi baƙo ya mutu. "Yee za ni birni bari na je na gayawa ƙawayena." Ta saka ihu tana faɗin haka. "Amma za ki yi wanka ko Jimmalo?" Jin tambayar da ta yi mata ya sanya ta ɓata rai." Ni ba wani wanka da zan yi, saboda ƙaiƙayi yake sani." Zare idanu suka yi ita da Daddy."Ni dai na san in mutum ba ya wanka ne jikinsa yake ƙaikayi." "Ba dole Hajiya jikinta ya yi ƙaikayi ba, domin daga ganinta tana shafe wata ba ta ga ruwa ba, ko ta yi wankan dadti kawai zata ta so." "Ai in dai Jimmalo ne sai tafi haka, saboda har na gaji na daina magana. Ta rantse sai bikin ƙawarta za ta yi wanka." Mamaki suka yi musamman daddy da ko aiki ya dawo bai yi wanka ba, sai ya ji jikinsa na ciwo, bacci kuwa da ƙarfi yake yi a ranar. "Zan yi daka tsami, amma wanka sai ranar da na sanya ta zo." Kasa cewa komai suka yi har ta fice tana tsalle. "Bari na haɗa kayan da za mu tafi da su, amma da na kin bari mun zo wani lokacin, tun da kin ga bamu shirya ba." "Ƙarki damu hatta kaya kar ku ɗauka, akwai komai ita ma Jimmalo zan sanya ta haɗa mata kaya." "Masha Allah! Shi ya sa aka ce da arziki a garinku gara a gidanku. Yau ga shi kin yi arziki kin tuna damu." Ta ƙarashe maganar tare da fashewa da kuka. "Kar ki damu ki shiga ki shirya, bari ya shigar muku da kayan." "To," Ta amsa cikin tsananin farinciki Jimmalo kuwa, sai da ta gama zaga gari tana faɗa wa ƙawayenta, da abokan gabanta za su je birni a mota. Kafin kace mene ƙofar gidansu ta cika. Wasu suna mata murnar zuwanta birni, yayin da wasu hassada da baƙinciki. Wasu kuwa fata suke ta tafi kar ta dawo, domin ta zame musu kaɗangaren bakin tulu. Ba su ɓata lokaci ba suka kammala shiri. Jimmalo riga da zani ta canza wanda babu bambanci da kayan da ta cire, domin sun yi duƙu-duƙu tamkar an ƙwato su daga bakin kura. Tun da ta sanya kayan sai da suka yi kusan sati biyu suna jikinta. Sai dai in wari ya sameta ta shiga rafi ta yi wanka da kayan. Kayan sallarsa ne tun da aka ɗinka ta daina sanya wasu kaya sai su. Babu irin faɗan da Kaka Tani ba ta yi mata ba, kan ta ije sai an fita babban sallah, amma ta yi kunnen uwar shegu da ita. A lokacin da suka fito za su tafi, har wani yanƙayi take yi tana yanga. Tafiyar ma tamkar ba za ta yi ba, ita a dole za ta je birni. Kwalliyar da ta yi, sai da ta sanya daddy dariya ganin yadda ta ɓata fuskarta da kwalli. Tana shiga cikin motar ventilation ɗin cikin motar ya canza. Daddy har sai da ya toshe hancinsa. Da sauri ya zuge glasses na motar yana sauke numfashi. Ita kanta Hajiya daurewa ta yi, amma kamar za ta yi amai. Motar na fara tafiya, ƙawayenta suka fara bin motar suna ihu tare da kiran sunanta. Ita kuma sai washe baki take yi tana ɗaga musu hannu. Ana kiran sallar magariba suka iso Kaduna. A lokacin da direba ya do shi get ɗin gidan, waigowa suka yi suna kallon juna ita da Kaka Tani. Sun kasa cewa komai, suna kallon get ɗin gidan mai tsananin kyau. Jimmalo kuwa ji ta yi kanta ya kulle tsoro ya kamata. Tunani ta fara ko cin kai suke yi. Ba ta ƙara shiga cikin tsananin mamaki ba, sai da ta ga maigadi ya buɗe get ɗin gidan sun shiga. Fitowa suka yi a cikin motar, cikin razana suna zare idanu. Ganin yadda suke mazurai Hajiya ta kama hannunta ta ce,"Ku shigo cikin gidan.." "Wayyo Allah na shiga uku wallahi ba zan shiga cikin gidannan ba, a cinye mini kai." Ta fasa ihu tare da yin hanyar ƙofar gida tana faɗin haka. Ganin yadda ta buɗe sai Kaka Tani ta bita."Mu koma ƙauye, na rantse daga ganin gidan nan cin mutane suke yi." Duk yadda Daddy ya so kar ya yi dariya sai da ya dara. Kallah maigadi kuwa, saboda dariya har sai da ya faɗi ƙasa yana mamakin inda ta same su. "Cin kai kuma? Wallahi bana cin mutane. Kuma ba sayar da ku zan yi ba." Da ƙyar suka yi nasarar shiga da shi. Sun zauna kamar za ka ce musu kyat su ruga. Duk rashin tsoro na Jimmalo sai da ta razana da kyawun gidan. "Ku zauna don Allah ku saki jikinku, wallahi ba zan cutar da ku ba. Gidan nan wannan ya gina mini, saboda Allah ya buɗa masa yana da kuɗi sosai." Miƙewa Kaka Tani ta yi tana kallon gidan."Yanzu Tine kina nufin yanzu wannan gidanki ne, wanda ɗanki ya gina miki gidan kwalba?" "Wallahi kin san arziki na Allah ne." "Haka ne kuwa ganin gidan nan ya tabbatar mini da hakan, amma sai dai ƙauye zan koma saboda bazan iya rayuwa a cikin gidan ba, don ni har yanzu zuciyata tana tantanmar cewar ɗanki ba shan jini yake yi ba ko Jimmalo?" Ta ƙarashe maganar tana kallonta. "Aradu kuwa gara mu koma ƙauye kawai, saboda har na fara jin wuyana yana rawa kamar zai cire." "Zo mu koma kafin ya cire mun shiga uku." Kaka Tani ta faɗa tare daka mata hannunta jikinta yana rawa. "Ke ki ki ji tsoron Allah Jimmalo babu wani tsafin da nake yi." Hajiya ta ce cikin mamaki. Ganin yadda Kaka Tani ta rikice, saboda ta ɗauka da gaske ne. Dariya ta sheƙe da shi tana nuna ta da yatsa."Kai Kaka Tani kin tsufa kina son duniya. Wasa na ke miki ai ni na ga gidan zama sai na ga daman koma wa ƙauye." "Ja'irar yarinya kawai ai sai na ga yaranki zan mutu." "Wayyo abin kallo yana birni Kaka Tani dubi ƙaton tibin nan don Allah." To Jimmalo jikar Tani a birni. Ko ya za ta kaya? 😁😁😁😁 Captain Aliyu ya kamata ka zo saboda your amaryato be ta zo😁😁😁 Tallah Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 00814407242 Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 Tallah Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano PAGE 8 Dariya ta sheƙe da shi tana nuna ta da yatsa."Kai Kaka Tani kin tsufa kina son duniya. Wasa na ke miki ai, ni na ga gidan zama sai na ga daman komawa ƙauye." "Ja'irar yarinya kawai, sai na ga yaranki zan mutu." "Wayyo abin kallo yana birni Kaka Tani dubi katon tibin nan don Allah. Wannan sai mutanen da na ke kallo su faɗo cikin falon." Dariya Hajiya ta yi ta kama hannun Kaka Tani. "Yanzu dai ku zo ku shiga ciki, ku yi wanka ku ci abinci ku huta." "Ni gaskiya ba zan yi wanka ba saboda na yi dakatsami da zamu taho, shi ma ƙyar na yi don kawai Kaka Tani ta matsa mini ne, amma tun da na yi wanka sai nan da sati..." "Sai me?" Hajiya ta yi mata tambayar cikin zare ido, tare da gane dalilin da ya sanya ta yi dafe ta fita hayyacinta. "Na rantse sai ranar da zan koma ƙauye zan yi wanka." "Tabɗi ana ƙazanta a gurin nan." Hajiya ta furta cikin mamaki. "A kawo mini abincin nan dama yunwa nake ji." Ta furta tare da zama a tsakiyar falon. "Ki dai tashi ki yi wanka, saboda in har ba ki ba ni kuma ba za ki ci ba." Baki ta buɗe za ta yi kuka, sai kuma ta fasa tana kallon Kaka Tani."Kaka Tani kina jin abin da ta ce, ki gaya mata gaskiya, saboda kin san ko sama da ƙasa za ta haɗe ba xan yi ba." "To zan gaya mata kar ki yi kuka kin ji." Ta furta cikin sigar rarrashi, sai kuma ta kalli Hajiya da ta yi sororo ta kasa magana, saboda tsananin haushinta da takaici. "Hajiya jarabar kafiya ce da ita in har ta ce baza ta yi ba, sam ba za ta yi ba ko zan kashe ta. Da ina dukanta, amma da na ga halinta ne sai na haƙura. Addu'a kawai za ki taya ni da shi." Kallonta ta yi, ta kasa cewa komai zama ta yi tare da ƙwalawa mai aikinta kira. Da sauri ta fito ta ce,"Hajiya ga ni." "Ki kawo musu abinci." "To," Ta amsa tare da shigewa cikin kicin ɗin. "Kan buta uba! Wallahi nan daga jin ƙamshin abincin, zai yi mugun daɗi kin ji ƙamshi Kaka Tani?" Zare ido ta yi jin ashar ɗin da taƙunduma ta kasa cewa komai. "Na ji jikalle ta ke dai bari 'ya birni suna hutawa." Tun kafin ta ije abincin, Jimmalo ta yi kanta tare da kwace tiren da a'a shirya abincin. Ƙasa ta saukar da shi." Ganin haka Hajiya ta yi maza ta ce,"Ku zo mu je dinning ba a cin abinci a nan?" "Jimmalo me take cewa kamar dannin kara take cewa?" Ta yi wa Jimmalo tambayar tana haɗiye miyau ganin ta buɗe lafiyayyen dafadukar shinkafa da ta ji nama. "Ni ma ƙila dannin kara take nufi." Ta ƙarashe maganar tare da kai hannu ta ibo shinkafar da nama. "Wayyo dadi."Ganin haka Kaka Tani takai nata hannun ta iba. Asibi da ta kawo cokali da abin zubawa, ganin yadda suke kai loma sai ta tsaya kawai tana kallonsu. Jimmalo loma take kai wa hankalinta kwance tana santin abincin. Hajiya sai ta shiga mamaki ganin yadda ta kusa cinye abincin. Sai da ta ga ta cinye komai, sannan ta saki gyaza babu tsari. Shafa cikinta ta yi tana faɗin,"Aradu zaman birni duniya ne. Kaka Tani ba za mu koma ƙauye ba." "A'a Jimmalo dole mu koma saboda ba zan iya barin ƙauye ba." "Ki koma ke kaɗai amma ni na ga gidan zama." Ta ce tare da murje abincin da ta ci a jikin kujera. "Ke Jimmalo lafiyarki kuwa? Kin ci abinci a madadin ki wanke hannu, sai kuma ki shafe jikin kujera?" "Hajiya ba ki ga na murje hannun nawa ba, kuma sannan sai da na shafa a gwiyar hannuna don na samu albarka." "Tabɗijam!" Ta furta don ta kasa cewa koma. Suna zaune sai surutu suke yi suna yaba kyawun gidan. Hajiya sororo ta yi tana kallon Jimmalo da magana ɗaya, sai ta saki ashar sannan da ƙarfi take yin maganarta. Sai ta cika da mamaki take ta ga abin da Daddy ya gaya mata. "An kira sallah bari na shiga ciki na yi sallah, kuma ku tashi muje na nuna muku masaukinku sai ku yi sallah." "Gaskiya ba zan iya sallah yanzu ba, saboda gabakiɗaya jikina ciwo yake yi. Zan bari ina zo kwanciya so na haɗa duka." Ta furta tare da mike ƙafa tana hamma, alamun bacci za ta yi, domin dai ta faɗi haka ne a idanun Hajiya. Hajiya sai ta kalli Kaka Tani a tunaninta za ta yi magana, amma sai ta ga ta yi dariya ta ce,"Allah ya sa in kin zo kwanciyar ki yi, saboda na san halinki yadda kika san aljihun baya haka kike." Zuwa yanzu ta daina mamakinta sai al'ajabi."Tani yanzu irin tarbiyyar da kike ba ta kenan? Wannan ƙatuwar budurwar amma ba ki koya mata sallah ba?" "Ya zan yi Hajiya? Wallahi ina ƙoƙari sosai a kanta, kawai shegen kafiya ne da ita. Kuma kin ga ita kaɗai ta rage mini in ban kula da ita ba wa zan kula da shi?" "Hmmmmh! Haka ne." Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta yi cikin ɗaki cikin mamakin rayuwarsu. Bayan shigarta ciki Kaka Tani ta kalle ta ganin ran Hajiya ya ɓaci."Jimmalo ki yi sallar don Allah kar ta ga ba ki da kunya. Kin ga ita babba ce." "Ai na ce zan yi da ma ban gaya mata ba zan yi ba. Ni kawai na fi son na yi sallah a lokaci guda ba wai na yi tsugul-tsugul ba." "To shikenan Allah ya shirye ki. Jimmmalo da ba na yin Sallah sai ace halina kika ɗauko." "Ni ma ai ba wai ba na yi bane in zan kwanta zan yi." Ta ce tare da sakin hamma ta kwanta sai bacci. Kaka Tani ciki inda aka nuna mata ta shiga. Bayan ta yi sallah, sannan ta zauna tana ta kallon gidan cikin mamaki. Jimmmalo ba ta tashi ba sai karfe huɗu, saboda gajiyar hanya da ta yi. Da ta tashi kai tsaye kicin ta nufa."Yunwa na ke ji ki zuba mini abinci, saboda shegen rowarki da aka ce ki kawo mana kaɗan kika zuba." Mamaki sosai ya kamata jin abin da ta ce, domin abincin da ta ci ko wani gardi ba zai ci shi ba. Ganin ta yi tsaye tana kallonta sai kawai ta wuce gurin ƙular binci. Ɗauka ta yi zuwa falo ta zauna. Hajiya ta yi mamakin rayuwar da Jimmalo take yi, saboda da dadddaren ba ta yi sallah ba ta kwanta. Babu yadda ba ta yi da ita ba, don ta kashe kallo ta yi sallah, amma ta ƙi Kaka Tani kuwa sai dariya ta ke yi tana faɗin,"Hajiya ba ki ga komai ba." Miƙewa ta yi ta kashe kallon ganin har sha biyu ta yi."Ki je ki yi sallah ki kwanta gobe sai ki ci gaba." "Ni fa so na ke yi na ƙarashe kallon him ɗin nan." "Ki bari sai gobe dare ya yi." Ta ce mata bayan ta kashe kallon. Ba don ta so ba su dai don babu yadda za ta yi. Miƙewa ta yi tana hamma ta wuce cikin ɗaki. Tana zuwa ta faɗi kan gadon tana cewa,"Wayyo yau zan kwana a gadon 'yan gayu." Kwanciya ta yi, da kayan jikinta ba tare da ta ɗauki tsawon lokaci ba sai bacci mai ƙarfi ya kwashe ta. Tun da ta zo gidan ta zamar mata ciwon kai, saboda duk yadd ta yi don ya yi wanka ta ƙi. Tun tana ganin lamarin na ta wasa ne har ya wuce tunaninta. Mamaki take yi sosai yadda take iya rayuwa. Ganin yadda take tashi da wari, sannan kanta kan shi abin ƙyama ne. Kullum tana cikin kaiwa kan rankwashi. Da susa kamar mai ƙazzuwa. Sannan inda ta ci abinci nan za ta tashi ta bar shi. Kuma ba ta wanke hannu in za ta ci haka in ta gama sai da ta goge a kayanta ko kujera. Washegarin da suka zo ta siyo mata brush, amma babu yadda ba ta yi da ita ba ta ƙi yi. A cewar ta jini zai zuba a bakin nata, ita kuma sam ba ta ƙaunar ganin jini a jikin wani ballantana nata. Lamarin na ta sai ya ba ta mamaki, babu sallah babu hankali sai zagi kamar jikar maguzawa. Ko kallo take yi ta rinƙa ashariya kenan tana zargin wanda ya ba ta haushi. Gabakiɗaya rayuwar da take yi babu tsari da hankali a ciki. A ɗaki ta samu Kaka Tani cikin tsananin ɓacin rai."Kina tunanin rayuwar da kika ginata akai shi ne gata? A haka za ta yi rayuwa kamar ta dabbobi. Ita fa mace ce aure za ki yi mata. Wane ne zai kalle ta da sunan zai aure ta. Yarinyar ba ta da maraba da mahaukaciya. Gaskiya Tani kin cuci yarinyar nan saboda tarbiyyar da kika ɗora ta a kai, babu nagarta wallahi yarinyar nan sai ta yi kuka da ke. Ba ilmin addini babu boko. Gata ƙazamiya sannan sai shegen kafiya da rashin kunya. Kina gani na yi mata maganar sallah tsaki ta yi mini har da harara, amma ba ki ce komai ba, sai ma ita kike rarrashi. Jimmalo watarana uwa za ta zama, ita ce za ta tarbiyanci yaran da za ta haifa." "Ya kike so na yi? Yarinyar nan ita ce kaɗai gare ni. Har gobe in kuka domin ba ta da kowa sai ni, sannan a ƙauyen kowa ya tsane ta. Ni ce kawai na ke sonta. Dole na ƙaunace ta domin na san cewa na kusa mutuwa, ganin tsufan da na yi. Har yau ina tuna zan mutu na barta babu kowa a duniyar ina shiga cikin tashin hankali." Ta ƙarashe maganar cikin kuka. "Dole ki yi kuka, amma ba wannan ya kamata ya sanya ki kuka ba. Kuka za ki yi saboda ba ki ba ta tarbiyya ba, in kika mutu babu wanda zai iya ɗaukar ta. Wallahi a yadda yarinyar nan take babu wanda zai zo ya ce yana sonta." "Ni ma ba zan so kowa ba." Jimmalo ta katseta tana faɗin haka da ta shigo. Kallonta Hajiya ta yi jin abin da ta ce. "Ba zan yi aure ba, domin maza ba su a gabana da zan wahalar da kaina sai na yi tsafta. A haka nake son rayuwata kuma ina jin daɗinta. In har kin gaji da zamanmu bai sai kin yi mana kora da hali ba, za mu tafi saboda ni ma na gaji da takura ni da kike yi." Kallonta ta yi ganin yada take maganar babu ɗa'a. "Kaka Tani ki zo mu bar gidan nan tun kafin ta kore mu. Dama na lura ta fara mana kora da hali. Ina je zan ci abinci sai ta ce kar a bani sai na yi sallah." "Ki bari mu gama kwanakin da muke ce za mu yi." "A'a mu tafi kawai saboda ni da jikina ba za ta rinƙa sanya ni dole na yi wanka ba." "To shikenan za mu tafi, amma ki bari mu ƙara kwana biyu." Shiru ta yi bata ce komai ba, domin ita kanta ba ta son tafiyar, barazana take yi mata don ta daina takura mata da maganar sallah da wanka. Hajiya kuwa sai ta yi shiru tana ganin lamarin yafi ƙarfinta. Ita da take son su haɗu da Kaka Tani su canza mata rayuwa. Juyawa ta yi ta fita daga ɗakin jikinta a sanyaye. "Jimmalo ki rinƙa sallah da wankan don Allah har mu gama kwanakin da zamu yi." "Ni fa ba zan yi ba domin babu wanda zai yi mini dole." "Kin dai san wanda ba ya sallah ɗan wuta ne?" "Na sani amma da manya ake yi ni kuwa guda nawa na ke?" "Kin girma saboda sa'anninki duk suna ɗakinsu." Banza ta yi da ita ta kwanta, ba tare da ta ce mata komai ba. Ganin haka ta ci gaba daban carbinta da take ja, wanda in aka tsareta ba za ta iya faɗin abin da take cewa ba. Iya kwana huɗu suka yi, amma ji take kamar sun shekara, saboda yadda Jimmalo take sanya ta magana. Saboda yawan maganar da take yi har zazzaɓi ta kwanta. Daddy da ta kira shi tana ƙorafi haƙuri ya bata, don abin da yake mata gudu kenan, amma ta na ce sai ta je ta ɗauko su. Captain Aliyu saboda ɓacin rai da ya shiga da suka je ƙauye Damagaran, bai yi hutun da yake don yi ba ya tattara ya koma Abuja. A ranar da ya isa, ya buɗe wayarsa da ya kashe saboda kiran da Lubaynah ta dame shi da shi. Tana kwance a falo wayarta ce a hannunta tana kallon hotonsa. Ji ta yi kamar ta yi kuka, saboda kewarsa da ta yi. Ta san cewa sojanta gwarzo ne kuma namiji ne da ya amsa sunansa ta ko ina. Tana ma wani irin ƙauna na mutuwa, amma a yadda ta fahimce shi kamar ba zai iya auren ta ba. Muskutawa ta yi, cikin damuwa tana jin a ranta ba za iya iya barin ya auri wata ba. Numbarsa ta kira duk da ta san ba za ta samu ba, amma cikin mamaki ta ji ta shiga. Saboda tsananin farinciki miƙewa ta yi tsaye. Yana zaune a falo ya ɗora ƙafarsa kan stool. Sigari ce a hannunsa yake sha. Tun lokacin da ta yi mishi rashin mutuncin ya kasa mantawa. Yanzu ma haka ji yake kamar ya bi shawarar da zuciyarsa take ba shi. Ya je ƙauyen cikin dare ya harbe ta. Ya tsaneta bai taɓa jin abin da yake ƙyama kamarta ba. Ba ya fatan ko a lahira Allah ya nuna masa ita. Babu abin da ya fi tsana ya kalla a fuskarta irin haƙoranta, domin da ya kalla sai da ya ji tamkar zai amayar da kayan cikinsa. Tun da yake a rayuwa bai taɓa ganin ƙazamiya mara tsafta da tarbiyya kamar ta ba. Wayarsa ce ta yi ƙara. Gajeren tsaki ya ganin Lubaynah ce. Daƙile kiran ya yi yana mamakin rashin zuciyarta. So yake ya yarda ƙwallon mangaro ya huta da ƙuda. Sam ba ya son in ya yi aure matarsa ta gane halinsa, wannan dalilin yake son ya rabu da ita, tun kafin ya samu mace natsatstsiya kuma mahaddaciyar Alkur'ani, wacce za ta ba wa yaransa tarbiyya. Yana wannan tunanin da inda zai samo ta, sai kiran ta ya ƙara shigowa. Wannan karan kamar zai yi jifa da wayar, sai ya fasa ya ɗauka cikin tsawa ya ce,"Why are you pestering me?" "Sojana." Ta ce tare da fashewa da kuka a maimakon ta amsa mishi. Banza da ita ya yi tare da jan tsuka."Lubaynah let's face the reality am done." Ya ce mata ba tare da tausayinta ba. Jin abin da ya ce, sai ta saki kuka sosai domin ta san cewa abin da yake shirin yi kenan."Ka yi mini adalci kenan? Ina sonka ba zan iya rabuwa da kai ba, kuma kai ma ka san haka." Fesar da numfashi ya yi cikin takaici. Baƙincikin ranar da ya haɗu da ita ya yi, ganin ta zame masa kaska. Ko ya yi ninyar rabuwa da ita don ya zamo na gari, amma sai ta san yadda ta yi ta dawo cikin rayuwarsa. Yanzu hakan ma ƙoƙarin saukko da zuciyarsa take yi, saboda kukan kissa da kalaman da take gaya masa. "Kin san ina sonki ko?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya shirya ba. "Na sani Sojana. Ni shaida ce na san haka." Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 Tallah Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano PAGE 9 "Kin san ina sonki ko?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya shirya ba. "Na sani Sojana. Ni shaida ce na san haka." "Saboda me za ki damu sai na aure ki? Na gaya miki ban shirya aure ba, in har kin matsu You can go and marry." Rintse idanunta ta yi, hawaye yana zuba tana mamakinsa da yake gaya mata ta je ta yi aure, ba tare daya san halin da take shiga ba. "Ba zan iya auren wani in ba kai ba. Ka riga ka koyar da ni soyayyarka, in har ba kai na aura ba. Sojana ba na jin zan iya mallakawa wani jikina. Kai ne kawai ka iya sace zuciyata da sarrafa ni yadda kake so. Ba na son na yi rashin ka. A shirye na ke na ƙara shekaru in har za ka aure ni." Jan numfashi ya yi sannan ya fesar. Ya zuƙi ta tabarsa ya ja fesar da hayaƙi. Lokaci guda ta yi nasarar sauko da fushinsa. Wani irin feelings na ta ya taso mishi domin ta saba mishi da kuma ya yi missing. "Ok, ki zo gidana mu yi maganar na dawo." "Gani nan zuwa babyna." Ta ce mishi tare da yi mishi kiss ta kashe wayar cikin murna. Jikinta har rawa yake yi, tana haɗa kayan da za ta yi kwanaki da su. Ta rasa irin son da take mishi har yake wulaƙanta rayuwarta, amma ta kasa rabuwa da shi. Da ta kuma tuna Captain Aliyu, ƙarshe ne gurin sace zuciyar mace sai ta daina ganin laifinta. Tana sanya kayan kwalliyarta a jaka Anty Hannah ta shigo. Tsayawa ta yi tana kallonta wacce ba ta san ta shigo ba. "Lubaynah, ina za ki kike haɗa kaya?" Ta yi mata tambayar tana kallon ta. Sosa kanta ta yi, cikin rashin gaskiya ganin yadda ta tsareta da idanu."Zan je bikin wata friend ɗina, kuma zan yi kwana biyu.." "Ki fito ki gaya mini za ki je gurin lalataccen yaron nan Aliyu." Ranta ne ya ɓace jin ta zage shi."Anty saboda me za ki zagi wanda na ke son aure?" Dariya ta yi mata cikin takaici."Ok, a tunanin ki zai aure ki ko?" "In sha Allahu ba ni da miji sai shi." "Yaudarar kanki kike yi Lubaynah. Ki rubuta ko mata sun ƙare ba zai aure ki ba, domin kin riga kin sayar da darajar da kike da shi." Ga mamakin ta sai kawai ta saka mata kuka."Fatan da kike mini kenan kar ya aure ni? Mai na yi miki kike mini wannan fatan? Domin gara ki yi mini addu'ar Allah ya ɗauki raina akan na rasa Captain Aliyu." "Ashe za ki mutu kuwa, saboda na gaya miki ki rubuta ki ajiye ba zai aure ki ba." "Na gode da fatan da kike yi mini, a matsayinki na 'yar'uwata wacce muka fito ciki ɗaya. In sha Allahu ba ni da miji sai shi. Sai kin zo gidana kin gammu muna soyayya." "Ki dai yi tunani kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada." Banza ta yi da ita ta yi, tare da ɗaukar trolley ɗinta da ƙaramar jakarta za ta fice. Ganin haka ta sha gabanta tana faɗin,"Babu inda za ki kin san Allah zan kira Daddy na gaya masa abin da kike yi." "Ki matsa mini na gaya miki bikin ƙawata zan je." Ta ce tare da ture ta "Lubaynah, zan mare ki babu inda za ki j..." Maganar ta maƙale mata sakamakon ture ta da ta yi ta fice daga gidan. Biyo ta ta yi tana kiran sunanta, amma da sauri ta shige cikin motarta ta ja aguje. Bayan ya kashe kiran sai ya miƙe zuwa ɗakinsa. Sigarin ya kashe ya sanya a trash. Murmushi ya yi tare ƙara sawa gaban mirror yana shafa sajensa. Sosai yake jin ya yi kewarta. Ya san cewa Lubaynah mace ce, wacce ta amsa sunanta, amma sam ba zai iya zaɓawa yayansa ita a matsayin matarsa ba. Yana wannan tunanin wayarsa ta yi ƙara a tunkinsa ita ce ta zo, amma sai ya ga numbar Anty Amarya uwar ɗakinaa kuma ƙawarsa ce ta kira. Ba tare da ya ɗauki wayar ba har sai da ta katse ya kira."Hello Antyna akwai news ne?" Ya yi mata tamabayar yana dariya tare da zama gefen gado. "News daga gareka na ke sauraren ji, amma labarin da zan ba ka yadda ka rikita 'yan matan gidanmu da biki. Kowacce ta yi kwalliya ta yi burin ganinka don ta burge ka." Tsaki ya saki yana mamakin rashin kunyarsu."Amma Anty sun raina ni. Marin da na yi wa bai sa sun daina haukarsu ba ko? Uban mai zan yi da su? Ko mata sun ƙare ba zan iya auren wata daga cikinsu ba." "Bana son wulaƙanci soja. Yaran nawa kake gaya mini haka?" Dariya ya yi yace,"Dole na gaya miki don ki sanar da su, su daina haukar da suke yi." "To wa za ka aura kuma yaushe za ka yi? Captain na matsu na ga kana zuwan mini da matarka Zariya." "Zan yi aure Anty ni kaina ina buƙatar haka, amma har yau na kasa samun macen. Kin san kalar macen da na ke so. Don Allah na ba ki cigiyar mai addini mahaddaciya kuma ustaxiya mai kyau." Dariya sosai ta yi jin abin da ya ce."Ka san halin ka kuma kake son mace irin wannan?" "Eh saboda yarana za zaɓar musu uwa ta gari, kuma irin wannan macen ne kawai zan aura hankalinsa ya kwanta." "Saboda kana ɓata matar wani ko?" Shafa kansa ya yi jin maganar da ta yi ba tare da shakka ba."Anty ke dai kin san komai. Ina fatan lokacin da zan yi aure Lubaynah ta fita daga cikin rayuwata. Zan daina duk abin da nake yi in sha Allahu, domin ba na fatan ranar da Daddy zai fahimci fuska biyu gare ni." "Ya kamata ka daina, saboda in har kana son irin wannan matar dole ka zama na gari, kuma maganar auren lokaci yana ƙurewa." "Na baki cigiya? Har yau na kasa samun wacce take da duk wannan halin." "In ka ba ni zabi kana tunanin zan guji 'ya'yana na nema maka wata ne? Mene ne aibun su Hanifah sun da kyau kuma da natsuwa, in kuma ba ka so ya ga Mufida nan, da kuma sauran 'yan matan ka zaɓa a cikinsu. 'Yan mata huɗu da suke crushing ɗinka a family kuma duk cikinsu babu wacce ta yi maka? Kada haƙƙin su ya kama ka, musamman Hanifa yarinyar ta zurma da yawa." "Bana son su, kuma bana son na auri mace wacce take sanya gyale. Matata ina aurenta Anty kullum cikin hijabi da niƙabi za ta rinka zama sam bana son wani ya kalle ta." Mamakin abin da ya ce ta yi."Duk za ka iya canza Hanifah yarinyar tafi sonka kamar hauka. Kabar batun ita yarinyar mijina ne, ka san zan iya barin kowa na ɗauke ka, kuma kun dace da juna." "Don Allah ba ita ba sam ba zan iya auren ta ba. Bana son mace da zan aura na canza ta. Matar da na ke son na aura wacce zan same ta a kan tarbiyyar da na ke so ne." "Hmmmmh! Soja lamarinka sai kai." "Ki dai bincika ba za a rasa ba." "Ba zan yi maka wannan alƙawarin ba, saboda in har aka ji nice na samo maka mata zan yi baƙin jini,a yanzu ma haka ana ganin kamar yadda muka shaƙu wani abu na yi maka, ballanatana aji duk ka guji 'yan matan family na nemo maka wata? Don haka duba da kanka." Shiru ya yi saboda ya kuma fahimci gaskiyarta. "Ok, zan duba Anty ki taya ni da addu'a. Zan shigo Kaduna zan zo Zariya. In zan zo zan kira ki ki yi mini dambu." "Shikenan ba matsala ɗan gidana." Ta ce tare da kashe wayar. Wayar ya bi da kallo don kuma ya kashe yana murmushi. Sosai jininsu ya haɗu da ita. Tana da hankali sannan ta fahimce shi fiye da iyayensa. Babu abin da ya ƙara mata girma da mutunci. Ta san duk munanan halinsa, amma ko suɓutar kalami ba ta taɓa furtawa ba. Sai dai tayi ta mishi nasihar ya daina. Yana ije wayar kiran Lubaynah ya shigo. Ba tare da ya ɗauka ba ya fita zuwa get. Da kanshi ya buɗe mata get ɗin ta shigo, saboda ya tafi kasuwa. Tana shigowa ya ware hannunsa ta faɗa jikinsa. Bakinsu ya haɗe domin ya yi missing na ta kamar yadda ta yi na shi. Sakinta ya yi yana kallon ta ganin tana hawaye. A ranar sai da ya sanya ta manta komai ta shiga lambun ƙaunarsa. Wannan dalilin ya sa take ji kamar za ta haukace duk lokacin da ya ce mata bai shirya aure ba . Tana ji a ranta saboda zarsa da ta ɗanɗana take kishinsa za ta iya kashe duk wacce ya aura. A ranar sun sha soyayya tamkar wasu sababbin ma'aurata. Bayan sun yi bacci sun tashi. Wanka suka yi Captain Aliyu ya shirya suka fita zuwa gurin shaƙatawa. Sosai take murna ganin yadda ya sakin mata bakin aljihu ya yi mata siyyayya. Da suka dawo wanka suka yi sannan suka kwanta. Kwana uku ta yi a gidansa suna shayar da junansu zumar ƙauna. Hankalinta kwance take shayar da shi madarar ƙauna. Burin ta kawai ta kawo hankalinsa ya amince zai aure ta, domin a shirye take da jure duk halayensa ta zauna da shi. Damuwar da shi wani lokacin duk sonta da ƙaunarta da yake yi. Haka zai rufe idanunsa ya shukamata tashin mutunci, amma hakan nan za ta shanye sai ma ta ba shi haƙuri. A ƙalla sai da suka yi sati, suna soyewa sannan ya shirya zuwa Kaduna. Kan dole ta tattara ta koma gida, ba don ta so ba saboda ta so ya barta a gidan tun da ba daɗewa zai yi ba amma sai ya ƙi. Misalin ƙarfe sha ɗaya ya iso garin Kaduna. Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce, saboda ya yi kewarta sosai. Tun da incident ɗin nan ya faru bai kira ta ba, domin yafi jin haushinta fiye da komai. Sanin cewar zai sha ƙorafi sai ya siya mata kayan toshi. Hon ya yi maigadi ya buɗe masa ya shiga. Parking ya yi sannan ya fito daga cikin motar. Yana sanye cikin ƙananan kaya riga da wando kalar kakin soja, sai hulan sojoji da ya sanya. Kasancewar yau Hajiya ta tashi tana zazzaɓi sai ba ta fito ba, tana cikin ɗakinta tana bacci. Kaka Tani ita ma tana inda aka sauke su. Jimmalo ce kawai a falo tana kallo tamkar za ta shige cikin tibin. Sai surutu take yi ita kaɗai. Da sallama ya shigo cikin falon fuskarsa a sake. Nufinsa ya yi ido biyu da rigimarmiyar kakarsa, amma sai ya ja ya tsaya cikin tsanannin ɓacin rai ganin wacce ya tsana fiye da komai a rayuwarsa. Ƙare mata kallo ya yi a wulaƙance, wacce ba ta san ya shigo ba. Gabakiɗaya hankalinta yana kan tibin. "Ye wallahi ya kashe shi ka amma wannan sojan ba shi da imani mai zuciyar kafurai." Ta furta tare da lailayo ashar ta danna masa. "Ke!" Ya daka mata tsawar da ya sanya ta juya da sauri tana kallonsa. Miƙewa ta yi da sauri tana maƙonsa domin ta razana, amma sai ta dake saboda da fari ta yi tunanin yawan zaginsa da tunanin ranar da Allah zai haɗasu ta yi mishi rashin mutunci ne, ya sanya yi mata gizo, amma kuma da ta tuna zai iya zuwa inda take, sai ta ɗauke fuska tana kallonsa. Captain Aliyu sai ya toshe hancinsa yana watsa mata kallo. Ya rasa duk lokacin da ya ganta dai ya ji amai zai zubo masa. A yadda yake jin tsanarta da ƙyamarta ko mutuwa zai yi da yunwa, in har tana gurin ba zai iya kai abinci a bakinsa ba. "Uban me ya kawo ki gidan nan?" Ya furta yana ƙoƙarin ƙarasawa inda take sai kai mata mari. "Kai dakata!" Ya ji muryar Kaka Tani a bayansa tana faɗin haka, amma saboda baƙar zuciya sai da ya kai mata marin. Kafin ya sauke ta ɗaya hannunta za ta mayar masa da na ta. Ƙafarsa ya sanya ya yi ball da hannun. Ta ji zafi amma sai kawai ta ƙara kai hannun cikin fusata Kaka Tani ta shiga tsakiyarsa ganin zai kashe ta. "Kai dakata wane irin zuciyar kafurai kake da shi?" "Ki bari na nuna miki irin zuciyar, domin na rintse sai na kashe wannan jikar ta ƙi." "Wayyo na shiga uku! Hajiya ki fito wannan mara imanin zai yi kisa!"Kaka Tani ta fasa kuka ganin ya kai mata hauri. Hajiya da take bacci tana ƙudundune cikin muryar ɓacci ta ji kukan Kaka Tani. Da sauri ta duro hankalinta a tashe. "lafiya Tani?" Ta yi mata tambayar dai kuma ta tsaya turus tana kallonsa da yake huci. "Ina da lafiya wannan mara imanin ne zai kashe mini jikalle." "Aliyu, wai mai ke damunka, kuma tashe ka shigo gidan nan?" Ta yi masa tambayar tana ƙarasawa gurin sa. "Hajiya don me za ki ɗauko wannan ƙazamiyar kika ije ta a gidanki?" "Alhamdulillah da ka ce gidana ka ba wa kanka amsa." Ta furta masa tana harararsa, sai kuma ta ɗora da cewa,"Ko so kake kar na yi zumunci saboda kai?" "Na tsani yarinyar nan, sam ba ta da tarbiyya. Ban taɓa ganin ƙazamiya irin ta ba. "Ni ma na tsane ka, saboda ba ka da imani mai zuciyar kafurai?" Mamaki sosai Hajiya ta ji ganin yadda take masa magana babu tsoro. "Ke Jimmalo ki kiyaye ni Yayanki ne. Tani ki shiga da ita ciki." Ta furta tana kallonta. "Allah ya tsare ni ya zama yayana, saboda ba ni da maƙiyi kamarsa masu kashe mutane kawai." Ta ce tana murguɗa masa baki da galla masa harara. Hannunsa ya sanya ya kai mata bugu, amma sai ta ƙwace tare da yi masa daƙuwa. Daƙuwar ya fusata shi ya bita zuwa ciki. Da sauri Kaka Tani ta sanya ɗan makulli."Ki bar shi ya shigo wallahi na fasa masa kai. Koɗaɗɗe kawai mai kama da zabiya." Ta furta tana ƙara aika masa da daƙuwar duk da ba ya gani. "Jimmalo, wancan sojan sam ba shi da imani. Dubi yadda yake kallon ki zai iya kashe ki. Na tsorata kawai mu koma ƙauye." "Babu ƙauyen da zan koma sai na gama kwanakina. Ke ma kin san daidai na ke da shi, don wallahi yana soja ba zan ji tsoron sa ba. Don ma ban zo da gwafata ba, da sai na sauti ƙeyarsa zan ɗana masa." Sai kuma ta,ce,"Na manta ashe na zo fa ita." "Mu dai koma ƙauye kawai." Kaka Tani ta ce cikin tsigar rarrashi. "Babu inda zamu sai na gama kwanakin da zan yi." A falo kuwa Hajiya ta kalli Captain Aliyu da yake huci ta ce,"Saukar yaushe Aliyu, ba ka gaya mini za ka zo ba?" "Bazata na so na yi miki, amma sai dai zuwana sam bai yi amfani ba, domin na ga abin da na tsana a rayuwata." "Ka yi haƙuri yarinyar ba ta da kunya amma zan yi mata magana." "Kar ki yi mata zan kowa mata hankali don wallahi saina ƙaryata." "Ba za a yi haka ba baƙuwace tafiya za ta yi, duk da na yi shawarar na karɓe ta na sanya ta a makaranta, saboda yariyar ko karatun sallah ba ta iya ba. Ga ƙazanta tun da ta zo gidan nan na ke ƙyamar gidan. Ko sau ɗaya ta ƙi wanka." "Please Hajiya ki kore ta a gidan nan, kuma kar ki yi gigin cewa ta zauna dake saboda ba ta tarbiya ga ƙazanta. Wallahi tun ranar da na haɗu da ita na ke yi mata ƘIYAYYAR JINI. Da zarar na ganta sai na ji tsigar jikina yana tashi, jinin jikinsa yana tafarfasa." "Tafiya za su yi ni kaina ba zan iya ba." Ta ce masa don ya kwantar da hankalinsa ganin yadda ya harzuƙa. "Yauwa matata kar ki sanya wa kanki yawan jini." "Tafi can ja'irihar yanzu ina jin haushin ka Aliyu. Ƙiri-ƙiri ka ƙi zaɓin matar da na yi maka." "Hajiya ki kwantar da hankalin ki. Duk ranar da na kawo miki matata sai kin ga amfanin jinkirin da na yi." "Jinkirin ba shi da amfani musamman ku sojoji," Wai ya ne da comments 🙄🙄🙄 ina ga tafiyarta hutu zan yi tun da bakwa comments Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 10 Tallah Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano "Tafi can ja'iri har yanzu ina jin haushin ka Aliyu. Ƙiri-ƙiri ka ƙi zaɓin matar da na yi maka." "Hajiya ki kwantar da hankalin ki. Duk ranar da na kawo miki matata, sai kin ga amfanin jinkirin da na yi." "Jinkirin ba shi da amfani musamman ku sojoji, da wasu suke bibiyan mata, ko da ace ba ka da wannan halin abokai za su iya koya maka." Gabansa ne ya faɗi jin abin da ta ce."Ki kwantar da hankalinki sam ba haka jikan ki yake ba." "Na yarda da kai Aliyu, ban taɓa ganin soja wanda ya kama addininsa yake riƙe kansa kamar ka ba." "Haka ne Hajiya in Sha Allahu zan ci gaba da kulawa." Ya furta cikin jin kunyar fuska biyu da ya zama yana shafa kansa. "Bari na kawo maka mutumin ka kamar nasan za ka zo, na yi kunun gyaɗa da yawa." "Allah ya kyauta! Na sha wani abu wancan ƙazamiyar tana gidan. Zan tafi kawai, saboda ina son na shiga Zariya, kuma duka kwana biyu zan yi na koma Abuja." Kallonsa ta yi, ganin yadda ya gasganta abin da ya ce ba zai sha ba."Ok tom gara ka je ka yi zumunci, musamman da an yi biki ba ka samu zuwa ba, sannan Lawan ma ya yi zazzaɓi." "In sha Allahu zan je a yau. Muje ciki na yi hira da matata sai na tafi." Ya ce tare da kama hannunta. Dariya ta yi suka shiga cikin bedroom ɗin ta. Jimmalo tana zaune, tana tunanin abin da za ta yi masa ta baƙanta masa. Buɗe labulen ta yi sai ta yi arba da motarsa mai kyau. Murmushin muguntar ta yi, sai ta fice daga cikin ɗakin ba tare da ta kula da Kaka Tani da take cewa,"Ina za ki Jimmalo, kin ga ki bari wancan mai zuciyar fir'aunan ya tafi, domin wallahi ya dukan mini ke rashin mutunci zan masa. Ka tsaye kicin ta shiga, ta samu wuƙarta mai ƙaifi da ƙarfi. Gurin motarsa ta je ta samu ƙaton dutse ta rinƙa bugawa tayar motar sai da ta sace masa tayar. Da sauri ta ruga cikin gidan, tana murnan don ta san sai yaji haushi kamar zai kashe kansa. A daidai falo suka haɗu Hajiya ta rako shi suna hira. Kallonta ya yi ganin yadda ta ɗan razana na ganin shi Ganin yadda ta yi, daga shi har Hajiya suka rakata da idanu. Wani wawan tsaki ya saki zai fice, kafin ya fita ta mayar masa da nata. "Don Allah kar ka rinƙa biye wa wancan yarinyar, saboda ba ta da hankali. Ni ban taɓa ganin mace irin ta ba, wallahi Tani ta cuci rayuwarta yarinyar nan." "Karki damu Hajiya, daga yau ba zan ƙara yarda na ƙara ganin ta ba, saboda na tsane ta bana ƙaunar na rinƙa ganinta." "Allah ya saka da alkahiri hidimar biki da ka yi." Ta ce tare da kawar da zancen. "Amin, ya ba su zaman lafiya." Hira suke yi har suka isa gaban motar sa. Hajiya na tsaye ya shiga bayan ya yi mata sallama."Don Allah in ka je Zariya ka gaishe mini da su." "Duk za su ji Hajiya." Ya ce tare da fara ƙoƙarin tuƙa motar. Da ya kunna sai ya lura ta yi ƙasa gaban motar. Gabansa ne ya faɗi sosai da sauri ya kashe motar ya fito, yana son duba abin da ya faru, domin ya san motarsa lafiya take. Hajiya kallonsa ta yi cikin damuwa, ganin yadda lokaci guda fuskarsa ta canza idanunsa suka kaɗa, saboda ganin aika-akar da ta yi masa, domin ya tabbata ita ce kawai za ta yi masa. "Lafiya soja?" Ta yi masa tambayar da sauri. Saboda zuciyar da ta tiƙe shi kasa magana ya yi, sai kawai ya nufin cikin gidan yana huci. A ɗakin Jimmalo take rawa cikin farin ciki, domin abin da ta yi masa ta san sai ya kusa kashe kansa, saboda baƙinciki. "Ina fatan ba wani abu kika ƙara yi masa ba? Kin ga ki fita harkar wannan mara imani..."Maganar ta maƙale mata sakamakon ganinsa ya shigo yana huci kamar mesa. Kai tsaye inda take ya je, ba tare da ya kula da Kaka Tani da take masa magana ba. Wani irin wawan mari ya sakin mata, sannan kuma ya fara dukanta yana haurinta ta ko'ina. Saboda kafiya da taurin rai, ƙoƙarin ramawa take yi, kuma bakinta bai mutu ba, sai zagi take auna masa. "Aliyu lafiyarka ɗaya kuwa don Allah ka daina dukanta." Cewar Hajiya tana riƙe shi, amma bai kula ba so yake sai ya ƙaryata. "Zuwana birni ya zamar mini masifa! Hajiya in har ya kashe mini jika wallahi sai mun yi shari'a." Ganin dukan da gaske yake mata kuma ya ƙi dainawa, sai kawai ta fashe masa da kuka sosai."Aliyu in har ni na haifi ubanka ka daina duka yariyar nan, domin zan iya masa baki." Cak ya tsaya yana huci kamar mesa.Ganin haka ta fito da shi falo tana share hawaye. "Na rantse ba zan yarda ba dole ki ɗauki mataki, kuma yau za mu bar gidan nan." Cewar Kaka Tani tana girgiza. Ita kuwa ko hawaye sai ɗura masa zagi take yi, tana jawo masa bala'i, amma kuma ta daku don ta ji jiki sosai. "Hajiya ki fita daga rayuwarsu, saboda in har za su kasance dake zan daina zuwa inda kike, ko kuma watarana za a kulle ni nayi kisa.. Yarinyar nan tayoyin motana ta sace saboda ba ta da tarbiyya." "Kai amma Jimmalo ba ta kyauta ba, na rasa yadda aka yi ta raina ka." "Ok, goyon bayan jikan ki kike yi ko? Saboda ke kika haifi ubansa ba ki ga abin da ya yi mata ba?" Kaka Tani ta furta tana jijjiga. "Tani ya kamata ki fuskanci gaskiya, ki gane irin tarbiyyar da kike mata babu kyau. Jimmmalo mace ce kuma uwa za ta zama nan gaba, in har baki canza ta kan tarbiyyar da kika bata ba, walllahi za ki yi dana sani." "Dakata Hajiya bana son rashin tsoron Allah. Jiƙanki ya duke ta kuma ki goyi bayansa kina gaya mini jikata ba ta da tarbiyya?" "Tana da shi ne? Ɗube ta tamkar jaka yarinyar nan ba ta da maraba da dabbobi, saboda wallahi dana zauna da ita gara na zauna da kare." "Aliyu karka ƙara magana ba sa'arka bace." Jin ya danganta Jimmalo da kare, sai ta fashe da kuka ta ce,"Innnali wa inna ilahir raju'un!" Dama kin ɗauko ni ƙauye, don ki wulaƙanta ni da jikata? Zumunci bai ce haka ba, saboda in da kin tuna zaman da iyayenmu suka yi, bai kamata ki yi mini wannan rashin mutuncin ba, amma babu komai yau zan bar gidan nan ba zan ƙara mintina ba. Kada ki ƙara tunanin kin san ni ko zuwa gurinmu, saboda don kina kawo mini abu ba zai taɓa sanyawa na yarda ki rinƙa zagin mini jika ba. Jimmalo ita kawai na ke gani na ji daɗi." Hajiya sai ta rasa bakin magana, ganin yadda ta harzuƙa tana hawaye sosai. Jimmalo da take cikin ɗakinta jin kukan Kaka Tani, da sauri ta ɗauko gwafan da ta zo da shi ta fito. "Waye ya taɓa mini ke yanzu na sakar mishi harbi?" Ta ce tare da take gwafar tana zare ido. Ganin ta saita shi sai ya zabura zai yi kanta. Hankalin Hajiya ya tashi sosai, domin ta san in har ta ƙyale shi ba za a yi da kyau ba. "Aliyu maza ka bar gidan nan." Ta furta da ƙarfi tana kallonsa. "Hajiya ki barta na yi mata dukan da sai na gyara rayuwarta, domin wallahi tsaf zan iya kashe ta." Ya furta tare da kai mata hauri. "Na ce ka fita za mu yi waya." Ganin yadda ta yi maganar sai ya fita daga gidan. Mai gyara ya kira, sannan ya ɗauki motar da ake fita da Hajiya ya tafi gidansu. A mota kuwa ji yake kamar zai kashe kansa don baƙinciki. Ya so ace ta barshi ya karyata. Da ya isa gida hon ya yi maigari ya buɗe masa. Daddy ne a tsaye da Mommy da suka fito za su anguwa. Ganinsa farinciki ya kama su sosai. "Soja mazan fama." Cewar Daddy lokacin da ya ƙaraso, ya durƙusa da makullin mota a hannunsa. "Ina wuni Daddy, da Mommy." "Lafiya lau ya gurin aikin?" Suka haɗa baki a tare suka yi masa tambayar. "Lafiya kau hutu na samu na ce bari na zo na yi kwana biyu." "Allah ya yi maka albarka ya ƙara tsare mini kai." "Amin, Daddy." Ya amsa yana miƙewa. "Lafiya ka ganka da motar Hajiya? Ko ta jirgi ka zo soyayya ya tashi?" Ya yi masa tambaya da ya sanya shi murmushi da Mommy. "Motata tana gidanta. Wannan yar iska mara kunyar yarinyar nan da muka je ƙauye ta fasa mini mota. Na gani a gidan Hajiya za ta yi mini rashin kunya na buge ta. Shi ne take ta yi mini faci." Zare idanunta suka yi suna faɗin,"Jimmmalo, ba ta da kunya da hankali." "Ni mamakin Hajiya na ke yi da take ganin kamar za ta shiryu. Ita tunanin yadda za ta yi ta kwace yarinyar take yi, don ta canza mata rayuwa." "Wannan yarinyar momi ai ba za ta taɓa shiryuwa ba, kina ganin ta sam ba ta da hankali. Hajiya ko ta karɓe ta wahala za ta sha. Ga shi ta tsufa haka kawai ta sanya mata cuta." "Ni ma abin da na yi tunani kenan, domin wanda yayi nisa baya jin kira. Ta ƙyale ta kawai, saboda duk wanda ya ɗauki yarinyar nan ya ɗaukarwa kansa jaraba. Ga ƙazanta ga rashin kunya da zagi kamar yar maguzawa." "Daddy, ina zargin tana fitsarin kwance saboda wani irin xarni da karni na ke jin tana yi." "Zai iya yiwuwa, domin yarinyar nan sakalta da sangarta ya yi mata yawa." "Allah ya kyauta wallahi ina baƙincikin da ta fito a 'yar'uwarmu, saboda ƘIYAYYAR JINI na ke yi mata." Cewarsa ya miƙe. "Ya za ka yi tun da Allah ya haɗa jinin." Cewar Daddy. "Bari na shiga ciki, na yi wanka na shirya kafin Abdullahi Bakanike ya gyara mini motata. Yau zan shiga garin Zariya in sha Allahu." "Gurin mutuniyar ta ka ko? anty Amarya." Cewar Daddy ya ce yana kallon sa. "Eh amma zan je na gaishe da su Baba Ɗanlami na yi murnar biki." "Yana da kyau zumunci abu ne mai kyau, duk dacewar na san dai dalilin zuwan ya karfafa don Anty Amarya." "Haka ne Daddy kwana biyu ban je gurin ta ba." "Ai shi da Anty Amarya ba a jin kansu. Ko ranar bikin ana ta yi mishi tsiya sai kare shi take yi. Yarinyar tana da hankali sosai, domin Ya Audi ya samu mace mai natsuwa da hankali. "Gaskiya kin ga ai ta yi karatu sannan tana da tarbiya. Shi kansa yana yabonta. Na tabbata da ace tana da yarinya babba a yadda Aliyu yake mugun shiri da ita, zai iya auren yarta." Kallon su ya yi yana murmushi domin zai iya ɗin. Tana da hankali da natsuwa. Kamar yayansa haka yake jin ta. "Bari na shiga ciki ina Nufaisah, Umma da auta?" "Umma, ta je ɗauko shi a makaranta." Cewar Mommy. Cikin ɗakinsa ya shiga, ya ije jakar goyon da ya zo da shi, da kaya kala biyu suke ciki, sai turare da ɗan tarkacensa. Ajiyar zuciya ya saki cikin ɓacin rai. Ya so ace Hajiya ta barshi ya cire mata haƙori. Wanka ya shiga ya yi ta dirzan jikinsa, domin ganinta ya sanya shi ƙyamar kansa. Sai da ya ɓata lokaci gurin yin wankan, sannnan ya fito ya shirya cikin shigan manyan kaya ya sanya hula. Ya yi kyau sosai kamar ka sace shi ka gudu. Wayarsa ya ɗauka don ya fito falo ya ci abinci. Nufaisah ce a falon tana shirya masa abinci, sai Adnan da yake falon yana kallon cartoon. Ganinsa da sauri ya tashi ya rungume shi."Auta ya kake?" "Lafiya lau Ya Captain, where is my promise?" "Yana ɗakina ga makullin ɗakin kai da Nufaisah ku ɗauki tsarabarku." "Thanks brother." Ya furta cikin tsannanin farinciki. "Sannu da zuwa Ya Captain?" Cewar Nufaisah tana kallonsa. "Yauwa ya kike ya karatu?" "Alhamdulillah mun yi hutun semester za mu shiga two hundred level." "Da kyau ayi karatu sosai ban da kula samari da ƙawaye." "In sha Allahu ya Captain." Ta ce masa tana kallon sa. Dinning ya wuce don ya ci abinci, amma sai kawai ya rinƙa tuno fuskarta da haƙoranta. Da sauri ya miƙe jin amai yana taso mishi. Mamaki yake yi yadda Hajiya ta iya surviving tana cikin gidan. Wayarsa ta yi ƙara alamun ana kira. Ganin Abdullahi Bakanike ne, sai ya miƙe ya fito ba tare daya ɗauki wayar ba, saboda ganin an buɗe masa get ya shigo da motar. Karɓar makullin ya yi, bayan ya yi masa godiya ya shiga cikin motar. Bayan fitarsa Hajiya sai ta rasa yadda za ta yi da su. Ta kalli Kaka Tani da take ta kuka tana face majina, sannan ta jiya kallonta ga Jimmalo da take aika masa da zagi buhu-bubu. Kanta ya kulle har ta yi dana sanin gayyato su gidanta. "Wallahi Hajiya kin nuna mini jika ya fi ɗan'uwa. A gaban idanunki ya duki jikata, amma da yake ita ba mutum ya haife ta ba, sai kika kasa ɗaukar mataki." "Haba Tani, yaron nan fa magidanci ne ba ƙaramin yaro da zan kama shi da duka ba. Ke baki ga rashin kunyar da ta yi mishi ba? Bayan zagin da ta yi masa har da yi masa faci." "To don ta aikata haka ai ba sata ta yi masa ba, da zai sanya ƙafafunsa yana haurinta tamkar ta yi mishi sata." "Da kin ƙyale ni na sakin masa gwafar nan. Aradu sai ya yi fitsari a wando.Mugu azzalumi mai idanun doki." Ta ce cikin zallar rashin kunya. "Tani, zan gaya miki gaskiya ko da ba kyau so. Tarbiyyar da kike ba wa yarinyar nan cutarta kike yi. Wallahi in har baki gyara ba, har kika bari Allah ya ɗauki kwananki ba ki canza mata rayuwarta ba. Kin cuce ta kuma nan gaba sai ta yi dana sani sosai." Sautin kuka Kaka Tani ta ƙara, saboda gani take kamar wulanƙanci Hajiya take mata don tana da kuɗi. "Na gode da rashin mutuncin da kika yi mini. Yau zamu koma ƙauye ba zan ƙara zama a cikin gidanki ba, domin tozarcin da kika yi mini ya isa. Kin kira jikata mara kunya, bayan jiƙanki ne mugu azzalumi mara kunya. A gabanki ya dukar mini jika kuma ya gaya mini maganganu mara sa daɗi, amma ba ki ce komai ba tun da shi yana da kuɗi. Ni kuwa ba mu da komai dole ki wulaƙanta ni." "Ba wulankanci bane, gaskiya na ke ƙoƙarin gaya miki wallahi tarbiyyar da kika ba a ba mai kyau bane, kuma kin cutar da rayuwarta. Za ta yi kuka ko da babu ke a rayuwa." "A'a Hajiya, zan yi miki rashin mutunci wallahi in har kika ƙara faɗin Kaka Tani tana cutata. Kin san wahalar da ta yi ta ciyar da ni har na girma? Kaka Tani har aikin ƙwadigo ta yi don na samu abinci, amma saboda kin shigo cikin rayuwarmu jiya nan, don kin kawo mana abinci sai ki kalle ta gaya mata haka?" "Jimmalo, gaskiya na ke gaya miki kuma dama ɗaci ne da ita. Idan akwai abin da yafi cuta tayi miki. Don da take miki da maraicin ki ya sanya ta yi miki tarbiyya mara kyawu. Rayuwa ba haka take tafiya cikin haukar da ƙazanta da rashin kunya ba. Dole ki fuskanci rayuwa ki yi ilmi in har kina son rayuwarki tayi kyau. Na yi miki alƙawarin zan kula da rayuwarki na ba ki ilmi in har za ki zauna da ni. Zan canza miki rayuwarki Jimmalo. Zan sanya ki a makarantar kuɗi, na kuma ɗauki ɗawainiyar rayuwarki har sai kin zamo wata aba" "Allah Ubangiji ya tsare ni da wahalar da kaina gurin yin karatu. A yadda nake rayuwa haka ya yi mini, kuma babu wanda zai yi mini dole. Mai zan yi da karatun arna? Na addinin ma tun da na iya na sallah Fatiha da Kulhuwallahu na daina wahalar da kaina." "Kwantar da hankalinki Jikalle, babu uban da ya isa ya yi miki dole in dai ina raye. Ma za je ki haɗa kayanki mu bar mata gidan nan, domin ba zan ƙara kwana ba." "To Kaka Tani." Ta furta da sauri tare da shigewa cikin gidan. Hankalin Hajiya ya tashi ganin yadda suka ɗauki zafi, tamkar wacce ta yi musu zagi. Hannu ta kai za ta dafa Kaka Tani, amma sai ta fisge cikin muryar kuka ta ce,"Karki taɓa ni na tsane ki. Ki manta kin san Ni a rayuwa, domin daga yau na goge duk zumuncin da yake tsakaninmu. Duk wanda zai aibata jikata bazan ƙaunace shi ba." Da sauri ta janye hannunta ganin yadda take kukan. Jikinta ne ya yi sanyi sosai har ta kasa cewa komai. Lokaci guda yarda da maganar Daddy cewar ba za ta iya canza su ba, domin sun wuce tunaninta. Abinci da turamen zani ta haɗa musu sannan ta kawo musu falo. "Ku yi haƙuri ban so haka rabuwarmu ta kasance ba. Na so ace na karɓi Jimmalo daga gurinki na ba ta tarbiyya da ilmi, domin rayuwarta ta canza ta samu miji na gari, amma ga yadda abin ya kasance. Aliyu ya yi kuskure kuma zan yi masa magana." "Kar ma ki yi masa ki ƙyale shi, ba sai ya gammu zai shiga gonarmu ba. Ya je ya yi abin da ya ga dama. Duniya ce ta ishi bagaruwa jima. Watarana in halinsa duka sai ya duki wacce da za ta sanya a kulle shi." "Eh Allah yasa kuma ɗan makullin ya ɓata ya mutu acan." Jimmmalo ta furta har cikin zuciyarsa tana fatan hakan ya kasance, domin ta tsane shi sosai. Hajiya dai kasa magana ta yi, ganin sam ba ta ganin laifin jikarta. Ƙosawa ta yi su tafi domin kanta har zafi yake mata. "Zo muje Jimmalo, ba za mu ɗauki komai daga gareta ba. Hatta kayan sawa ki bar mata ai ba a tsirara ta gammu ba, sannan na raba zumuncin da yake tsakaninmu kar ki ƙara zuwa Kauyenmu, domin in har kika zo ko wani na ki, sai na sanya an yi muku rashin mutunci." Kayyasa ni kaina ban taɓa ganin rikitattun mutane irin waɗannan ba😁😁😁 to ga shi dai sun yi zuciya za su koma ƙauye. Anya Jimmalo kina da rabon kilewa? Ku ci gaba da bibiyar littafin da kuma yin comments don ji an yadda za ta kaya. Wai ya ne da comments 🙄🙄🙄 ina ga tafiyarta hutu zan yi tun da bakwa comments Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 11 Tallah Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano Ganin sun kama hanya za su fita sai ta fara roƙon, su da su bari direba ya mayar da su, sannan su tafi da kaya da ta basu, amma suka ƙi. "Na dai gaya miki bana fatan ƙara ganinki da zuriyarki, don haɗuwarmu ta biyu sam ba zai yi kyau ba." "Ki barsu Allah ya sanya su yi gigin zuwa, sai na raka su da gwafata ina harbinsu." Ta ce tare da saita gwafar tana dariya. Ganin haka sai ta tsaya cikin mamaki tana kallon su har suka fita. Zama ta yi jaɓar kan kujerar tana mamakin halinsu. Tun da take ba ta taɓa ganin rikatttun mutane irin su ba. Hawaye suke zuba a ƙuncinta na tausayin Jimmalo, domin in har ta ci gaba da rayuwa a haka, nan gaba sai ta yi kukan da za ta ci gaba har ƙarshen rayuwarta. Mai aikinta ta kira ta ce,"Don Allah ki fito da kayan ɗakinsu a wanke dakin sannan a sanya turare. Wallahi ko ina na gidan nan ji na ke yana warin jikinta." "Kai Hajiya, ai wannan yarinyar ƙazamiya ce wallahi. Tun da ta zo gidan nan ba ta yi wanka ba, sannan ba ta sallah ballantana ta samu rahamar alwalan da take yi. Shi yasa gata nan ta yi baƙi ta fita hayyacinta. Inda za a sanya abu a kankari jikinta Allah sai kin ga dadti na zuba, sannan inta matso ni kamar zan yi amai. Ni wannan kan nata bana tunanin ta taɓa sanya masa ruwa?" "Bana tunanin haka, saboda yarinyar nan ta iya ƙazanta ga rashin tarbiyya." "Gaskiya Kakarta ta cuce ta da sunan so." "Hmmmmh! Allah dai ya kyauta domin sun gasa mini aya a hannu. Ni sai yanzu na ke jin daɗi abin da ya faru suka tafi, saboda wallahi tun da ta zo gidan nan na rasa natsuwa, kullum cikin bari-bari na ke yi kamar wata yarinya." "Ai barnar da ta ke yi bana tunanin ɗan shekara biyu zan yi. Da gangan yarinyar nan ta lalata gas cooker, wai tana son ta ga ko wutar daga kasa yake fitowa." "Ɓanna ai ta yi kala-kala, bayin ɗakin da suke duk ta lalata famfunan saboda wasa da ruwa." "Ruwan da ba za ta yi wanka ba. Kai yarinyar nan ƙarshe ce gurin ƙazanta." Hajiya ta yi ajiyar zuciya ta ce,"Na huta ai da nayi ninyar tallafawa rayuwarta, amma Allah ya ba ni ladar ninya, don tafiyarsu ji nake yi kamar an sauke mini kaya." "Gaskiya yau za ki yi bacci har da munshari." "Je ki gyara ɗakin gobe sai an yi wa gidan nan kwalema." "To Hajiya Allah ya kyauta ya shirya su." "Amin," Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta yi ciki tana laluben numbar Daddy. Bugu da ya ɗauka cikin girmamawa."Hello Abubakar, dama waɗannan mutane haka suke?" Dariya ya yi jin da muryar da ta yi magana." Sun fi haka musamman Jimmalo, mai suka yi miki?" "Ai ita ma kanta Tani ba sauƙi, saboda duk abin da take yi, ita ta ɗorata kan turbar hakan. Da ace ta ba ta tarbiyya mai kyau, da bata zama haka ba. Maraici hauka ne da za ta zauna ta lalata yarinya." "Hmmmmh! Aini ban taɓa ganin mutane irinsu ba." Abin da ya faru ta kwashe ta gaya masa. Dariya ya ƙara yi ya ce,"Yanzu sun tafi?" "Sun tafi Abubakar. Gara su tafi wallahi har sun sanya mini hawan ruwa ba jini ba, domin na tabbata da za a duba jinina ya hau." "Allah ya shirya su ai zama da su babu wanda zai iya. Hajiya ni fa tun da ta iya kallon Aliyu ta yi masa rashin mutunci na tsinke da lamarin yarinyar nan." "Yanzu ma ba ka ga rashin kunyar da ta yi masa ba, kuma abin takaici Tani ba ta gani ba, sai zagi take yi wa Aliyu." "Abin da ya faru kenan a lokacin da muka je ƙauyen su. Wallahi in kika ga yadda ta yi wa Aliyu sai kin yi mamaki. Da ace ban tsawata masa ba, na rantse ko bai kashe yarinyar nan ba sai ya ji mata rauni yadda ya fusata." "Dole ya fusata ko ni na ga rashin kunyarta. Yanzu dai sun tafi kuma ba zan ƙara bibiyar rayuwarsu ba. Zumuncin ma na haƙura Allah ya gani na yi iyakan yi na." "Haka ne Hajiya Allah ya ba ki lada." "Amin, don Allah in zaka koma gidan ka biyo da likita ya duba ni." "To shikenan Hajiya yau za ki yi bacci mai daɗi." "Har da munshari Jimmalo ko hawan jini." Dariya yayi sanan ya yi mata sallama ya kashe wayarsa. Mommy da take zaune a kujerar mai zaman banza tana saurarensu. Dariya sosai ta yi ganin ya kashe wayar. Shima dariya yake yi. "Dama na san ba za ta iya da su ba, domin Waɗannan mutanen sai Allah." "Wallahi kuwa lamarin su kam babu wanda zai iya jurewa." "Haka ne."Ya ce suka ci gaba da hirarsu. Captain Aliyu Awa ɗaya da minti goma daidai ya ɗauka zuwa Kaduna. Duk da yau yake son ya dawo, amma cikin natsuwa ya yi tuƙin har ya isa. Dama ya sanar wa Anty Amarya. Tun da ta tashi ta fara shirin tarbarsa. Hanifah da ta ga ta aika kasuwa an yi mata cefane har dasu hanta nama da za ta sanya a cikin dambun, sai ta kalle ta lokacin da ta shigo ɗakinta tana zaune tana gyara tsaki. "Anty Amarya, na fara zargin kamar mutumin ki zai zo?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin murna. "A'a Babanku ne yace na yi masa dambu." Ta faɗi hakan don bata dan su san zai zo, su zo suna masa kwarkwasa ya yi musu rashin mutunci. "Gaskiya Anty ban yarda ba, saboda wallahi in ya Captain ne kawai zai zo kike irin wannan dambun. Don Allah ki gaya mini wallahi ina son Ya Captain. Ta ƙarashe maganar cikin hawaye tare da kama hannunta. Tausayi sosai yarinyar ta ba ta, domin da akwai abin da za ta iya yi don ya aure ta, da tuni ta yi hakan. Ta sani sosai take son shi. Ba wai don ɗiyar mijinta bane, amma duk cikin 'yan matan tafi ƙaunarsa, saboda ta sha yi mata kuka kan ta sanya Captain Aliyu ya so ta, amma ta kasa fahimtar Aliyu ba irin mazan da za'a yi masa cushen mace, ko kuma a bashi shawarar ya aureta. Yana da ra'ayinsa kuma duk kusancin da mutum yake da shi, sam ba ya ɗaukar shawararsa. Har yau da suke ganin kamar asiri ta yi masa yadda yake kula da ita ya shaƙu da ita, amma ba ta da hurimin da za ta iya ba shi shawara ya ji. Abin da Captain ya so shi yake yi. Ko zaɓin da ya bata na matar da yake so, ai sai daya jero mata abubuwan da yake so. "Hanifah, Please ki cire Aliyu a ranki yana da kalar zaɓin matar da yake so. Kina da kyau da ilmi za ki samu namiji na gari. Don Allah ki cire wa ranki son maso wani. Aliyu ba zai aure ki b.." "Don Allah Anty kar ki mini mugun baki. Ba zan iya cire ƙaunarsa ba. Anty na yi kuka na yi addu'a da sadaka, amma har yau ƙaunarsa ƙaruwa take a cikin zuciyata." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka. Sosai ta ba ta tausayi domin ta san tana son shi. Da ace akwai abin da za ta iya yi, za ta taimaka mata don ya aure ta, kuma shi kansa ya dace mata. Sam ba ta da makusa she is fine and looking dashing, amma Captain murɗaɗɗen mutum ne kuma ba a yi masa dole." Ganin yadda ta ke kuka sai ta koma hannunta ta ce,"Ki bar kuka shi ne zai zo, zan yi ƙoƙarin yi masa magana, amma don Allah Hanifah ki rage son shi kar ki yi abin da zai cisga ki." Wani ihun tsalle ta yi ta rungumeta."Na gode Anty, bari na je na shirya idanuna dakunnuwa cike suke da ɗokin jin muryarsa da ganinsa." Ba tare da da jira abin da za ta ce ba, ta ruga da gudu don ta yi wanka. Anty girgiza kanta ta yi, cikin haushinta ta ci gaba da gyara tsakin. Kamar yadda Hanifah ta zargi zuwansa haka sauran 'yan matan. A tunaninsu Anty Amarya ta ɓoye musu, don Hanifah ta yi kwalliyar da za ta sace zuciyarsa. Tun ba yau ba su da iyayensu suke zargin tana son haɗa su, saboda ita 'yar mijinta ne. A dalilin wannan tunanin ya ƙara mata tsana a cikin gidan, amma sam bata damu ba tun da suna zaman lafiya da kishiyarta, sannan ƴaƴanta suna yi mata biyayya, domin biyayya da Hanifah take yi mata tamkar ita haife ta. Tana wanke tsakin, ta ji sallamarsa shi da Yaya Sama'ila da yake ta tsokanar sa. "Soja mazan fama." Dariya ya yi yana shafa kansa. A tare suka shigo tsakar gidar, kusan duk mutanen gidan suna waje don shan iska. Jin sallamarsa gabakiɗaya gidan ya ruɗe da murnarsa. 'Yan matan da suka ci kwalliya suka ƙyafe suna jiran zuwansa, zarginsu ya tabbata. Wani irin tsanar Anty Amarya ya kama su. Mufida da uwarta yadda take jin sonsa, in har ya zaɓi Hanifa ko da Malamai sai ta raba shi da ita, domin in har Captain bai aure ta ba, yi babu wacce za ta aure shi a cikin 'yan matan gidan. Anty Amarya da take tsaye, da gayyen zogale a hannunta za ta tsinke. Sosai ta yi murnar zuwansa. "Soja marmari daga soja mazan fama." Anty ta yi masa kirarin da ya faɗaɗa murmushinsa. "Anty Amarya na same ku lafiya?" "Lafiya lau Captain Aliyu, ya hanya da su Hajiya Mommy K.d da auta?" "Duk suna lafiya suna gaishe ku." Ya ƙarashe maganar, tare da shiga cikin gidan don ya gaida iyayensa maza. Ɗakin Baba Audi ya shiga, mahaifin su Mufida domin shi ne kawai take gida bai fita kasuwa ba, saboda janta da yake yi. Bayan sun gaida shi, sannan ya zauna a gefensa yana masa ya jiki. "Jiki da sauki soja. Na ɗauka za ka zo bikin, amma Ya Abubakar ya ce kana Yukrain?" "Eh wallahi ai mun dawo duka bai wuce wata ɗaya ba." "Da kyau, Allah ya yi albarka ya kuma tsare ku ya ba da sa'a. Kuna ƙoƙari sosai domin kune kuke tsaron rayukanmu da kuɗaɗen mu." "Haka ne Baba Audu. Bari na shiga gurin Anty Amarya, na bar ka ka huta." "To shikenan kafin ka tafi za ka je ƙwarbai ka gaida Goggonka Mariya ita ma ba ta ji daɗi ba, domin har sai da aka ƙara mata jini. Mahaifinka ya zo shi ma.Wataƙila ya gaya maka ciwon?" "A'a ya manta ne duk da ban jima da zuwa ba na taho nan." "To ya kamata ka duba ta, ta yi jinya sosai." "Zan je Allah ya ƙara sauki." "Amin, Allah ya yi maka albarka ya ba ka mata ta gari." "Amin," Ya ce sannan ya miƙe zai fita. Gyaran murya ya yi, jin haka ya dakata ya tsaya don ya san magana zai yi masa. "Aure Aliyu sai yaushe? Ya kamata kayi aure, musamman aikin ka kana hurɗa da sojoji bata gari. Kai kanka Allah ne ya tsare ka, saboda shigarka soja bai sanya ka ɓata tarbiyar daka samu ba." Jim ya yi sai ya ce,"Zan yi har yanzu ina dubawa ne. Matan ne dole dai mutum ya duba wacce za ta tarbiyartar da yaransa." "Kuma haka ne dole a tsaya ka zaɓi mace ta gari, domin tarbiyyar zuriyar ka, musamman a wannan zamanin da muke ciki na tafiyar biri a yashi, amma kuma soja tun da har ka gaza samu a waje, muna da yaran mata kyawawa kuma sun sauke Alqur'ani da hadda. Ka dai san tarbiyar da suka tashi da shi. Duk yarinya da za ka samu a bayansu take. In har ba Zariya ka zo ka nema ba, sanin kanka ne yaranmu muna ƙoƙarin ba su ikon da hadda." Bance matan Zariya sun fi ilmi ba😁😁, amma kun san akwai ruwan shi boko da Muhammadiya lol😁😁 "Haka ne zan yi tunani." "Shikenan Allah ya baka ta gari."Ya ƙarashe maganar daidai lokacin da ya fice. Har ga Allah yana son ya auri Mufida, amma ya san ba zai iya mishi dole ba. Bayan ya gama gaisawa da mutanen gidan, sannan ya shiga cikin ɗakin Anty fuskarsa a ɗaure ganin yadda 'yan matan gidan suke rawar jikin gaishe shi. Da fara a Antyn ta amsa sallamar sa tana kallonsa. "Na ga ka yi sauri Captain? Lokacin da muka yi waya na tambaye ka don na ɗora girki, amma kari ga ka taso ko?" "A'a lokacin wanka na fito." Ya bata amsa yana ƙoƙarin zama kan kujera. Ɗakin ya bi da kallo cikin sha'awa. Tana da tsafta sosai, domin duk da sauran matan gidan ba a za kira su da ƙazamai ba, amma ita kaɗai yake iya cin abincinta ruwan ɗakinta. "Na ga ka yi sauri sosai yanzu da ka shigo na sanya ganye." Ta karashe maganar tare da buɗe frij ta ɗauko ruwan faro da ta siya mishi, sai zoɓo mai sanyi da ta haɗa da kanta. "Kar ki damu Anty, ni ma bana jin yunwa ki gama a tsanake." "Ok, tom bari na je na duba, saboda ganin ka iso na mayar a gas." Ba tare da ya amsa mata ba, ta fita ganin ya mayar da hankalinsa kan wayarsa da ake kira. Ganin Lubaynah ce sai ya mayar bai amsa ba. Hanifah da take tsaye kusa da kofar Anty. Tana ganin ta fito sai ta bita kicin. "Kin cika zumuɗi Please ki bari ya ci abinci ya natsu." "To Anty amma ganinsa da yadda yake haɗe rai na tsorata." "Ya zaki yi? Hakannan za ki daure tun da kin ga ni kina so." Haɗa hannayenta ta yi, ta murza cikin rashin dubara zuciyarta na bugu. Kallon kanta ta yi sai ta ga kamar bata yi kyau ba, ganin shiga da kyawun da ya yi. Daga sashin Maman Mufida, tana zaune da Mufida da ta karaya, ganin ta gaishe shi ya ce mata lafiya kawai. "Ki karɓa ki shafa a fuskarki Mufida ki daina jin tsoronsa, duk wannan ɗaure fuska da yake yi. Namiji ne fa yana fara sonki sai kin yi mamaki." "Mama Ya Captain daban yake da sauran maza. Ko Hanifa da yake tare da Anty Amarya ba ki ga kallon bazan da ya yi mata ba." "Kar ki karaya malamin na ya ce wannan maganin na farinjini ne, kuma mai kyau ne. In har Aliyu ya haɗa fuska dake zai kamu da sonki. A yarda ya yi mini bayani kece wacce ake son ya fara gani." Ganin ta karɓi maganin mai kama da turare a sanyaye, sai ta ce,"Ki tashi mana ga Hanifa can da wancan makirar matar suna magana. Kika sani ko suma sun je gurin Malami ne? Ni wallahi na tsani yarinya can ƙarama da ita, amma sai kinibibi ko yadda ya shaƙu da ita bana tunanin haka ta bar shi. Tun damu da aka haife shi a gaban idanunmu, bai saki jiki damu ba sai ita zuwan jiya." Mufida miƙewa ta yi, ta buɗe labulen windonsu, tana hangen Hanifah Anty Amarya da suke magana. Ƙara gyara fuskarya ta yi, bayan ta shafa turaren maganin. "Yauwa kar ki karaya ma za ki je, sannan ki tabbatar da kun haɗa idanu." "To," Ta ce tare da buɗe ɗakin ta fita cikin sanyin jiki. Ganin haka ta kamo tare da riƙe mata hannu."Ki kwantar da hankalinki, ba ki da wani miji sai shi duk yadda zan yi na fita, sai na sai na yi kin auri Aliyu, don haka kije ko ya yi miki rashin mutunci kar ki damu kin ji? Dama duk abin da kake so sai ka wahala." "To Mama." Ta ce tare da ficewa. Anty ta fito daga kicin ɗin, ɗauke da kular dambu ta shiga cikin ɗakin. Yana zaune da waya a hannunsa fuskarsa ɗauke da murmushi. Chatting yake yi da Lubaynah tana gaya mishi ta yi missing ɗinsa. Hotonta ta tura masa, wanda ta ɗauka cikin wata rigar bacci, mai shigen kyau da ta siya boutique. Lumshe idanunsa ya yi, lokaci guda suka yi ƙanana ganin kyawun da ta yi a cikin rigar. Kallon ta sosai yake yi yana jin feelings ɗinta na ta so masa. Gwalo ta yi masa tare da sakin masa kiss da stikers. Murmushi yake yi sosai. Sojana, ka yi sauri ka dawo Abuja in har rigar tayi mata kyau, saboda na siya sun fi kala goma. Ina fatan ina sanya maka ɗaya, sauran na yi amfanin da shi a matsayin matarka? Tsaki ya yi tare da neman tsari da addu'ar da ta yi. Yana ƙoƙarin bata amsa, Anty Amarya ta yi sallama ta shigo. Kashe wayar ya yi, sannan ya amsa yana kalonta. "Abinci ya sauka azo aci dambu." Ta ce tare da ije mishi kula, a gaban shi tana kallonsa. Ije wayar ya yi, sannan ya sauko ƙasa ya shaƙi ƙamshin dambun, tare da lumshe idanunsa."Kin san na yi missing dambun nan? Kwanaki sai da na ji kamar ki yi mini na turo a karɓa." Dariya ta yi jin abin da ya ce,"A kawo dambu tun daga Zariya har Abuja?" "Eh za a iya mana. Ina fatan matata macen da ta iya abincin gargajiya kamar ki, saboda Anty ina son abincin Hausawa don kawai Peter bai iya bane, amma kuma ina jin daɗin abincinsa." "Auren dai shi ne za ka yi, sai ka samu wacce ta iya girkin Hausawa." "Shi ya sa na ba ki zaɓi." "Zaɓin ka yana da wuya, ba kowace mace za ka samu da abin da kake so ba." "Za a iya samu zan ci gaba da nema. Ina da burin na auri salihar mace wacce ranar first night ɗinmu zai zama memorable, amma kin ga Anty duk 'yan matan nan yawancinsu second hand ne." "Akwai mata na gari masu kare mutuncin kansu Aliyu, don mace ɗaya ta bada kanta bai zama hujjar da za ka yi musu jam'i ba, kuma in kana son irin matan nan sai ka je ƙauye akwai yara sosai a ƙauye waɗanda na sa zance da maza. Wasu ma ba su fahimci mene ne auren ba, sai ka ɗora su a hanya." "God forbid!" Ya ce tare da murza hannunsa. Hmmmmh Captain ka tsaya ruwan ido ba zan ce komai ba. Aci gaba da zafafan comments yanzu aka fara. Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 12 Tallah Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano "Akwai mata na gari masu kare mutuncin kansu Aliyu, don mace ɗaya ta bada kanta bai zama hujjar da za ka yi musu jam'i ba, kuma in kana son irin matan nan sai ka je ƙauye akwai yara sosai a ƙauye waɗanda ba sa zance da maza. Wasu ma ba su fahimci mene ne auren ba." "God forbid!" Ya ce tare da murza hannunsa. Ganin haka ta kalle shi cikin mamaki."Anty da na auri 'yar ƙauye gara na mutu ban yi aure ba. Matan ƙauye har wani abu suke dashi wanda namiji zai kalla? They are illiterate kuma ba su da wayewa." "High expectations na ka yayi yawa kan matar da zaka aura. Ni kaina zan so na ga mai sa'ar da zaka ɗauko mana." "In sha Allahu macen kirki mai natsuwa da kamun kai zan aura." "Ina maka fatan hakan, Wani lokaci sai ka ga namiji ya kasa aure ya yi ta ruwan ido, amma daga ƙarshe sai ya je ya zaɓi macen da duk 'yan matan da suka so shi ba ta kaisu ba." "To ni na daban ne Anty yadda na ke da kyau ga kuɗi ga kyawu, kin san matar da zan aura kaf a family ɗin mu babu kalarta. Ko Ya Anas ɗan gidan Baba Lamiɗo da na ji ance ya auri shuwa, matar da zan aura sai ta fi tashi kyau. Kin san saboda ni mijin mace ɗaya ne shi ya sa zan duba da kyau, don kar na zo na yi zaɓen tumin dare." "To ko Shuwar za ka ɗauko mana?" "A, a cikin Hausawa akwai 'yan mata kyawawa waɗanda suka fisu kyau. Ku dai jira lokaci ku ga matar da zan kawo cikin family." "Muna jira kuma muna taya ka da addu'a. Allah ya ba ka na gari mai tsoron Allah." "Amin,"Ya amsa tare dakai hannu yana ƙoƙarin buɗe kular. Mufida da ta ga Hanifa na ƙoƙarin shiga, da sauri wuce Hannifa da ta buɗe ɗakin za ta shigo. Sallama ta yi gabanta na faɗuwa. Anty ce kawai ta amsa, amma shi sai ya mayar da murfin kular ya ɗauki wayarsa. Kafin ta yi magana Hanifa ta yi sallama ta shigo. "Ya Captain ina wuni ka zo lafiya?" Mufida ta yi saurin faɗin hakan muryarta na rawa. Ba tare da ya ɗago idanunsa ba ya amsa da cewa,"Lafiya." Ganin haka sai jikinta ya yi sanyi sosai. Hanifa ta kalli Anty Amarya kamar za ta yi kuka. Da idanu tayi mata nuni da ta gaishe shi. "Ya Captain ina wuni?" Yadda ta yi maganar cikin sanyin murya, mai haɗe da tsoro shi sanya ɗago idanunsa. "Lafiya lau ya karatu?" Ya ce mata sannan ya mayar da kansa. "Alhamdulillah hutu muke yi." "Ok," Ya ce yana danna wayarsa. Ganin haka duk suka yi shiru jikinsu a mace. Ba tare daya kalle su ba ganin sun yi shiru ya ce,"Please I need my space zan ci abinci." Da sauri suka miƙe suka fita Hanifa har da hawaye, domin tana son shi sosai. Mufida cikin kuka ta yi ɗakin Mamanta. Tana shiga ta fashe da kuma. Da sauri Mama ta taso ta rungume ta."Ko kallona bai yi ba, domin gara Hanifah har yana tambayarta ya makaranta kuma ya kalle ta." "Zai kalle ta mana tun da matar ubanta ta shanye shi. Ai ni dama tun da aka auro Maryam na san sai haka ya faru, saboda ubanta malamin zaure ne fa. Yar kusfa duk wanda ya aure ta ai ya san mai ya auro wa kansa. Shi kansa Yaya Sama'ila ba ki gata shanye shi da kamar yadda ta shanye uwar Hanifah? A ce kishiya kin bar mata yaranki sun saba da ita." "haka ne don Allah ni dai Mama ki yi wani abu bana son na rasa shi, kuma in har ba zai aure ni ba, bana son ya auri kowa a gidan nan, domin zan iya kashe kaina in har ya auri Hanifa." "Ki bari kawai, wallahi kin ji na rantse ko suna tsafi da mutum in dai Ali bai aure ki ba, ba zai auri kowa ce yarinya a gidan nan ba. Zan je na samu Anty Amina ai ta an wani malami a kusfan." "Yauwa Mama," Ta ce tare da share hawayenta sai ta zauna kan kujera, tana ayyana abin faɗa ta yin in ta zamo matarsa. Kallon irin soyayyar da zata yi masa take yi. Hanifa kuwa tana shiga cikin ɗaki sai hawaye. Zama ta yi kan kujera Mama ta kalle ta watsar tare da sakin tsaki. "Iska na wahalar da mai kayan kara.Na gaya miki ba a dole ba ya son ki dole za ki yi masa?" Ba ta amsa ba sai hawayenta ya ƙaru. Yayanta Musa ne, ya fito daga cikin ɗakin Mama bayan ya gama shafa mai. Kallonta ya yi yana faɗin,"Mama, mai ya samu Hanifa?" "Wahala da ta ɗorawa kanta. Kasan Aliyu ya zo yau?" "Don Allah yaushe? Ai ban sani ba, bari na je na samu rabona, wataƙila alkhairi ya dawo dani kasuwa." "Ya zo bai jima ba son shi take yi, kuma ba ya sonta. Na gaya mata ga yaron nan Auwal da yake sonta. Yanada ilmi ɗan gidan malamai, sannan ya gama masters ɗinsa yana aikinsa, amma kin tsaya kina wahala kan wanda bai damu dake ba." "Wallahi ki cire sonsa, saboda irinsu Ya Captain idanunsu a bude yake. Sam ba zai aure ki ba, domin ki jira kiga matar da zai ɗauko." Kuka ta fashe da shi ta shige cikin ɗaki. Tsaki Mama tayi ta ci gaba da ƙullum alala. Bayan sun fita sai ya kai hannu ya buɗe kular yana murmushi."Anty an ya ba zan tafi da dambun nan ba? Saboda ƙamshinsa kawai ya tabbatar mini da ya yi daɗi?" Dariya ta yi ta ce,"Kai Aliyu, daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki?" "Anty ai kin iya girki da ace kina da ƙanwa ko bata da kyau zan aure ta, saboda na rinƙa cin abinci mai daɗi." "Allah sarki auta ce ni a gidanmu." "Na sani ai Anty." Yace tare da kai loma. Ya lumshe ido yana santin abincin. Ya kai loma na biyu bakinsa sai ya tuna da haƙoran Jimmalo, da sauri ya zubar da abincin yana ƙaƙarin amai. Hankalinta ne ya tashi sosai ta miƙe tare da yin kansa tana faɗin,"Lafiya Captain, ko ka haɗiye ƙashi ne?" Ganin yadda ta rikice ya kalleta."Ki kwantar da hankalin bakin wata ƙazamiya na tuna?" "Baki wace ce ita kuwa da har za ka yi amai, sannan a ina ka ganta?" Tayi masa tambayar tana mamakin wace irin ƙazama ce ita. Ganin ya kasa amsawa yana ya mutsa fuska, sai ta ce,"Mai zai kai ka kallon bakin mahaukaciya?" "Ba mahaukaciya bace wata irin ƙazamiya, jaka, wawiya, dabba, kuma dakiya na haɗu da ita." "A ina Captain?" Ta yi masa maganar cikin mamaki. "Gidan Hajiy.." "A Kaduna Hajiya K.D?" Ta tambaye shi tunkafin ya gama maganar. "Eh, amma yar wani ƙauye ne wai ko damagan ne ko me?" "Sabuwar yar aiki ce?" "A'a kin san Hajiya da kwashe-kwashen dangi. Wai Kakar yarinyar ƙanwar mahaifiyarta ita haifi kakar, shi ne kwanan nan ta samu labarinsu, ta sanya muka je ƙauyen. Ina kika ga abin da yarinyar nan tayi mini sai kin yi mamaki. Ba ta da tarbiyya sannan gata kamar aljana don muni. Ganinta na farko sai da na yi amai." Dariya sosai ta kwashe dashi ganin yada yake maganar da gaskiyarta."Ita kuwa wannan yarinya wace irin ƙazamiya ce?" "Inda akwai abin da yafi ƙazama za a kira ta, domin da za a bani qur'ani na rantse bata wanka zan iya. Wallahi ƘIYAYYAR JINI na ke mata, saboda ina ganta jinin jikina har tafarfasa yake yi." "Taɓ! Ni kuwa zan so ganin yarinyar nan." "Tana gidan Hajiya ta ɗauko su suna sanya mata yawan jini. Ina komawa zan sanya Daddy ya mayar dasu ƙauyensu, domin in muka barta dasu, wallahi sai dai Hajiya ta yi bunga ta faɗi ta mutu. Ni fa a yadda na tsani yarinyar nan Anty zan iya harbin ta da bindiga." "Kai Aliyu ba a zurfafa so da ƙiyayya." Ta ce masa tana kallon sa. "I hate her I can explain but I hate her with my whole being." "Zan so in ga wannan yarinyar kuwa." "Kar ki yi fata zata iya sanya ki amai." Ya ce tare da mayar da murfin kular. "Is so bad that I can't eat it." "Yanzu ba za ka iya ci ba?" Ta yi tambayar cikin damuwa. "In zan tilastawa kaina zan yi amai, an so sorry for the inconvenience." "Babu komai." Ta ce tare da ɗauke dambun cikin mamakin ƙazantar da ya gani a jikinta har ya hana shi cin dambun sanin yadda yake so. "Anty bari na miƙe zan shiga cikin gari, yanzu haka Ya Auwalu sai kirana yake a waya, don ma ban gaya musu zan zo ba." "Ok tom sai ka dawo." "Ina ga zan wuce daga can ga wannan sai mun yi waya." Ya dunƙula kuɗi masu yawa ya bata. "Aliyu na gode Allah ya tsare hanya." "Amin," Ya ce daidai lokacin da Musa yar shigo cikin ɗakin yana faɗin,"Ya Captain ashe ka shigo gari?" Hannu ya ba shi suka yi sallama sannan suka fita suna hira. Rabon kuɗi yayi wa mutanen gidan sannan ya yi musu sallama ya tafi. Musa ya raka shi Ƙwarbai ya gaida Gwaggo Mariya, sannan ya bata kuɗi ya yi mata sallama ya tafi. Ana kiran sallar isha'i ya isa Kaduna. Ya yi parking daidai lokacin da Daddy ya fito don zuwa masallaci, don haka ya bishi suka tafi tare. Bayan sun dawo Aliyu ya kalli mahafinsa. "Yanzu Daddy kana gani Hajiya ta ɗauko mutanen da za su kashe ta tun kafin lokacinta ya yi?" Dariya ya yi yace,"Ai yau sun koma ƙauye ta kira ni tana ta murna, har cewa ta yi na kira likita ya gwada jininnta." Jin abin da ya ce sai hankalinsa ya kwanta ya yi dariya ya ce,"Waɗannan mutanen mahaukata ne, duk wanda ya zauna da su tsaf zasu haukata shi." "Sosai kuwa ai ta ce ta haƙura da zumunci." Dariya ya yi sannan Dady ya ce,"Ya mutanen Zariya?" "Lafiya lau suna gaishe ka. Na je na gida Gwaggo Mariya ashe ba ta ji daɗi ba?" "Eh, wallahi mantawa nayi na gaya maka, tun da ka je ka yi aikin hankali." "Na je kuma ta ji daɗi sosai, har take gaya mini bikin jikarta na gurin Ya Sarki." "Na ji Mommynku tana maganar bikin. Allah ya ƙulla alkhairi." "Amin," Sun ɗan yi shiru suka tafiya. Daddy ne ya kalle shi ya ce,"Kai ma fa ya kamata ka fara maganar aure, na yi shiri ne saboda yadda na ga har yanzu kana nan da natsuwata da hankalinka, amma duk da hakan kana buƙatar ka ije mace tun da ka kai munzalin aure." "In sha Allahu kwanan Daddy." "Allah ya kaimu ya baka ta gari. Ina jin daɗi sosai yadda ka kama kanka bai ruwanka da bin mata ko shaye-shayen da wasu sojojin suke yi. Kowa a family yabon ka yake yi. Yana gaya mini in har za auri yarsa ya ba ka, duk wannan ya faru ne saboda riƙe tarbiyyar da na ɗora ka akai. Ko bayan rayuwata Aliyu karka canza. Ban taɓa zina da yar wani ba, kuma ina roƙon har na mutu kar zuriyana su yi ko ayi da su." Jikinsa e ya kama rawa lokaci guda hankalinsa ya tashi."In sha Allahu Dady addu'ar da kake mini ina ganin amfaninta, domin ko da abokan aikina masu irin wannan halin sun ja ni, sai ka ga Allah ya tsare ni." Ya ƙarashe maganar cikin rawar murya zufa na keto masa. "Ƙarfin addu'a ce ka ci gaba da ƙoƙarin kare kanka. Zina musifa ce da take shafan har waɗanda ba su aikata ba. Zina alfasha ne daga cikin manyan zunubin da Allah ba ya so, amma abin takaici da jimami har ma da zaman makoki al'ummar zamanin mu mun ɗauki zina ba a bakin komai ba. Namiji mai aure yana zina, matar aure tana zina samari da 'yan mata duk suna zina har da zawarawa, shi ya sa musifa ta yi mana yawa. Abinci yana gagarar wasu. Mutane an mayar da kashe su ba komai ba, dabba tafi mutum, domin sai ta yi yawo ba a taɓa lafiyarta ba, amma mutum har gida ake zuwa ake kashe shi. Wannan duk yana faruwa da irin manyan zunuban da muke aikawa ne." Aliyu shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Ganin haka Daddy ya ɗora da cewa,"Ka ga ko karya alƙawari da mutum ya zama fuska biyu? Shi ma yana matuƙar sanya Allah yayi fishi sannan ni kaina Aliyu in har mutum zai zama fuska biyu a gareni zan iya yafe shi har cikin rayuwata. Na tsani haka domin babu kyau." "Eh, Daddy Allah ya tsare mu da aikata zina." Ya yi ƙoƙarin sauya muryarsa ya furta hakan. "Amin shi ya sa na ke alfahari da kai. Har gobe ina bugan ƙirjina a cikin abokai na yabe ka, saboda kyawawan halinka. Dangi damu kanmu muna alfahari da kai. Ubangiji ya yi maka albarka." "Amin Daddy." Ya ce hawaye na zuba a ƙuncinsa, domin ya san cewa duk lokacin da ya sani akwai matsala. Ya zama dole a yau ya rabu da Lubaynah ya daina shan sigari. "Daddy bari na kwashi kayana na kai mota zan shigo." Ya ce masa don ya keɓe. "Ok, ba matsala sai ka shigo bari na gaya wa Nufaisah ta haɗa maka abinci." Ya ƙarashe maganar tare da shiga ciki. Sashinsa ya shiga buga kansa kasa da bango. Sosai ya ke jin ya tsanar kansa, saboda yaudarar mahaifinsa da ya yi. Ganin yadda yake alfahari da shi, sai ya ji hankalinsa ya tashi. Da sauri ya ɗauki wayarsa ya shiga cikin chatting da suka yi da Lubaynah na batsa da hotunanta marasa ɗa'a ya goge. Goge numbarta ya yi, yana fatan ya zama shi ne na ƙarshe da zai yaudari mahaifinsa. Saboda tashin hankalin da ya shiga jin abin da Dady ya rinƙa cewa, domin ya ɗauka ko asirinsa ne ya tonu. Wanka ya shiga sannan ya canza kaya, ya tafi zuwa sashin iyayensa. Mommy na zaune a falo da remote ɗin tibi a hannunta ya yi sallama ya shigo. "Yauwa ma yanzu na ke son na tura Umma, ta je ta yi kiranka mu yi dinner." "Wanka na yi shi ya sa na daɗe." Ya furta tare da wuce dinning yana gaishe ta. "Lafiya lau ya mutanen Zariya?" "Duk suna lafiya Anty Amarya ta ba ni tsaƙo na kawo miki, na san bai wuce abin da ta saba. Su daddawa da kuka da barkono." "Ba ta gajiya duk wani ya je sai ta yi hidima." Murmushi ya yi sannnan ta zauna yana faɗin,"Anty Amarya tana da kirki sosai." Bismillah suka yi sannan suka fara cin abincin. Kwana biyu Captain Aliyu ya yi ya koma aikinsa. A ranar da ya koma washegari suka yi tafiya, don haka Lubaynah ba ta samu damar ganinsa ba. Jimmalo. Cikin tsananin takaici suke tafiya suna tsinewa Hajiya da Captain Aliyu, domin inda ace zagi na fitowa a jikin mutum tabbas da ya yi musu tabo. Zagi kam sun zagu. Suna tafe suna zaginsu har suka isa Damagaran. A lokacin da suka isa sai kunya ta kama jimmmalo, da ta fara haɗuwa da mutane ana kallonta ana tambayarta, dalilin da ya sanya ta dawo da wuri, sannan ta gama cika baki cewar za su dawo da abubuwa, amma sai ga shi duk dawo daga su sai kayan jikinsu kamar wasu korarru. Mutanen ƙauye da suke haɗuwa, don su suka ci gaba da kallonsu suna gulma, cewar sun yi halin su an kore su. Kafin su isa gida labari ya cika ko'ina Jimmalo ta dawo birni babu abin arziki. Da suka isa ƙofar gidansu Kaka Tani ta buɗe suka shiga. Zama suka yi sannan ta ibo ruwa ta sha."Allah ya tsinewa mutanen birni gabakiɗaya. Kaka Tani ni da birni har abada, saboda ba su da mutunci. Ki ga irin tozarcin da suka yi mana. Na gama cika gari ina gaya musu zan dawo da abin arziki, amma ko tsarabar biskit ban yi ba." "Ai Hajiya ta ba ni mamaki sosai tun da ta fifita jikanta a kaina. Na rantse ko mutuwa ta yi ba zan je gaisuwa ba, kuma tsakanina da ita na yanke zumunci, sannan ni ma ko mutuwa a yi kar ta zo." "Allah ya kawo su ma suga rashin mutuncin da zan yi musu, domin duk ranar da suka kuskura suka zo gurinmu na rantse da duwatsu zan raka su." "Ai ba za su yi kuskuren zuwa ba." Cewar Kaka Tani tana ƙoƙarin miƙewa ta shiga cikin ɗakinta. Jimmalo na tsaye a waje tana jijjiga, ji take yi kamar ta koma ta shaƙi wuyan Captain Aliyu ta kashe shi. Wani irin tsanarsa take ji yana zagaye ilahirin jikinta. Tana zaune tsahare ta yi sallama ta shigo tana washe baki. Mugun kallo ta watsa mata tare da tamke fuskarta. "Jimmalo ashe kun dawo? Lauratu ta gaya mini cewar ta ganku a da zaku dawo?" "Ko ba ta gammu ba na san kece za ki fara zuwa, saboda kaf garin nan babu munafuka kamar ki." "Laa! Jimmalo ba haka bane cewa nayi bari na maza na zo na karɓi alkawarin taliyar birni da kika ce za ki zo mini da shi?" "To jikar mayu ban zo da shi ba, sai na ga uban da zai yi mini dole na baki." "Ko kin zo da shi ba lailai ki ba ni ba, dama na san alƙawarin ki ba kya cikawa, musamman kan abinci ɓakin rowa ne dake." "Ke Tsahare fita a gidan nan kafin yanzu jininki ya yi tsami." "Dama ko baki ce na fita ai zan fita, alƙawari dai kaya ne duk wanda bai cika ba, Allah xai hukunta shi, kuma duk wanda ya ci shi kaɗai shi kaɗai zai mutu." "Da na gaya miki da gyatumarki zan mutu?" Ta ce tare da fara tafiya da sauri za ta shaƙota, ganin haka ta ruga da gudu ta fice daga gidan. Ba ta zame ko'ina ba, sai dandali ta sanar musu da cewar Jimmalo ta dawo daga birni, babu abin arzikin da ta rinƙa musu ƙaryar za ta dawo da shi. Kafin dare ya yi an gma yayata maganar wasu suna faɗin mugun halinsa da rashin mutunci suka yi aka ƙoro su. Maganar har da gishiri da magi, aka ƙara mata cewar koro su aka yi har da duka. A lokacin da maganar ta dawo kunnen Jimmalo ranta ya ɓaci. Ɗanmara ta sha ta je har ƙofar gida ta samu Tsahare ta yi mata duka.Mahaifiyarta ta biyo ta, amma babu wani matakin da aka ɗauka. Bayan dawowarsu suka ci gaba da rayuwarsu. Sun gwammace irin rayuwar da suka saba. Jimmalo tun safe take zuwa talla, da ta siyar za ta tafi sarin gwaiba ko ayaba, sai ta siyar sannan take dawowa. Bayan magariba ta ɗauki talla ta wuce dandali. A haka suke samun abincin da za su ci. Wata ɗaya Captain Aliyu ya yi sannan ya dawo. Hankalin Lubaynah ya tashi matuƙar gaske ganin ba ya ɗaukar wayarta, sannan in ta yi chatting ɗin da ta Whatsapp ba ya reply. A cikin lokacin ta rame ta fita hayyacinta. Ita kanta mamakin wani irin so take yi masa kamar za ta mutu. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGA 13 Wata ɗaya Captain Aliyu ya yi sannan ya dawo. Hankalin Lubaynah ya tashi matuƙar gaske ganin ba ya ɗaukar wayarta, sannan in ta yi chatting ɗinsa ta Whatsapp ba ya reply. A cikin satin ta rame ta fita hayyacinta. Ita kanta mamakin wani irin so take yi masa kamar za ta mutu. Ganin halin da ta shiga sai Hannah ta kira gida ta sanar. Duk abin da take ɓoyewa ta sanar musu har zuwa kwanar da take yi gidansa. Hankalin iyayenta ya tashi sosai, inda duk suka ɗauki laifin suka ɗora mata, domin da ace tuntini ta sanar da sun yi wa abin tufka hanci. Mahaifinta ya yi fushi sosai, cikin tsananin ɓacin rai ya zabga mata mari."Irin tarbiyyar da na baki kenan Lubaynah? Ko da kika ga na ƙyale ki kina rayuwa yadda kika dama, ban taɓa tunanin za ki iya, zuwa gidan namiji kina kwana, a tunaninki hakan da kike mishi zai sanya ya aure ki?" "Daddy Anty karya take mini, Captain Aliyu sona yake yi, ban taɓa zuwa na kwana a gidansa ba, kuma zan tabbatar maka da hakan da zarar ya dawo zan sanya ya turo iyayensa." "Ƙarya za ta yi miki kenan? Mene ne ribarta don ta yi miki karya?" "Eh na san cewa ina zuwa gidansa na taimaka masa da aiki, amma Captain Aliyu bai taɓa riƙe ko da hannuna bane." "Wallahi Daddy yarinyar nan ƙarya take yi, ko Daddyn Fadil ya san abin da take aikatawa, kuma shi yace na sanar daku tun kafin lamarin yafi ƙarfinmu." "Ki barta tun da ta ƙaryata na ba ta izinin ya turo iyayensa, sannan ba za ta ƙara zuwa Abuja ba." Kuka ta fashe da shi, jin tsautsaurar hukuncin da ya yanke mata. Ta san cewa da wuya Captain ya turo iyayensa. Wayarta ta ɗauka ta shige cikin ɗakinta. Layinsa ta fara kira, amma kamar kullum ba ta shiga. Sai ta yi jifa da wayar tare da fashewa da kuka. A zuciyarsa tana jin ba za ta iya bin umurninsa na hana ta zuwa Abuja ba, domin ya zama dole ta je gurin sa, don ta ji dalilin ƙin ɗaukar wayarta. Tana cikin damuwa har tsawon sati bai ɗauki wayarta ba, sannan an sanya mata tsaro sosai domin idanun mahaifiyarsu yana kanta. Zazzabi sosai ya kamata har sai da aka kaita asibiti. Ita da Mommy suka je sibiti. Tunanin hanyar da za ta gudu take yi. Tana cikin wannan tunanin likita ya ba Mommy takadda ta je ta siyo magani. Da sauri ta miƙe ta fice daga asibitin. Bayan ta dawo ta neme ta sama da ƙasa ta rasa. Hankalinta ya tashi sosai ta kalli likitan."Please Petient ɗin da na zo da ita fa?" "Ta ce za ta je bayi." Ya ce mata hankalinsa a kan laptop ɗinsa. Cikin sanyin jiki tafiya tana duba ko'ina, amma ba ta ganta ba. Ganin ta duba kaf asibitin babu ita, sai hankalinta ya tashi ta ɗaga waya tana kuka ta kira Daddy. Hankalinsa a tashe ya iso asibitin, amma sun duba ko ina ba su same ta ba. Mommy ce ta fashe da kuka tana faɗin,"Lubaynah na da hankali kuwa? Namiji ne za ta gudu ta je gurin sa?" "Lailai bata da hankali kuwa, amma ki barta in har ta dawo sai na ɗauki mataki a kanta." Cikin ɓacin rai suka koma gida. Mommy sai kuka take yi Daddy yana bata haƙuri. Hannah suka kira ko ta san gidan Captain, amma sai ta gaya musu ba ta sani ba. Fushi sosai suka yi da ita, suna jiran ta dawo sai sun ɗauki mummunar mataki a kanta. Lubaynah na fita daga asibitin ta shiga cikin napep ya kaita tasha. Sai da ya kaita sannan ta cire kuɗi a p.o.s, don transfer ta yi musu saboda ba ta zo da ATM ɗin ta ba. Kuɗin mota ta biya zuwa Abuja. Ba ta iso Abuja ba sai bayan magariba. Kanta ne ke ciwo sosai ga wata uwar yunwa da take ƙwakularta. Tun a hanya ta kira shi yafi sau nawa, amma baya shiga. A mota tana kuka sosai domin ta san son Captain jarrabawar ta ne. A lokacin da ta isa gidansa tana addu'ar yana nan.Cikin sa'a Solo ya sanar mata yana nan, amma ya ce kar su ƙara buɗe mata gidan. Hankalinta ya yi mummunar tashi ga yunwa ga zazzaɓi a jikinta."Mai Captain yake nufi?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali. Ganin yadda take daga ganinta ka ga mara lafiya, sai Solo ya shiga cikin gidan. Yana zaune daga shi sai gajeren wando yana ta aiki a Laptop ɗinsa.. Solo ya nemi izini ya shiga."Sir, Lubaynah is outside like she is not feeling well." Tsaki ya saki lokaci guda zuciyarsa ta ɓaci. Ya rasa yadda zai yi da ita ta fita cikin rayuwarsa, domin ta zame masa ƙarfen kafa. Agogo ya kalla ƙarfe bakwai da rabi."Don't open the get for her." "Ok sir." Ya ce tare da juyawa ya koma yana mamakin rashin zuciya irin nata. Zuwanta ya canza mood ɗinsa har ya kasa aikin da yake yi. Kashe laptop ɗinsa ya yi sannan ya koma ya zauna, bayan ya janyo sigari ya kunna. Miƙewa ya yi zuwa cikin ɗakinsa ya kwanta. Lubaynah tana gurin har zuwa sallar Isha. Saboda karya ganta a gida ya yi sallarsa ya kwanta. Ganin ya ƙi fitowa sai ta nufi gidan Kalim. Kalim yana zaune a cikin falonsa yana kallo shi da Nadiya da ta zo masa kwana biyu. Mai-gadinsa Dupe ya knoking ya shigo. "Sir a lady is looking for you outside." Kallon juna suka yi shi da ita. Ranta ne ya ɓace amma ba ta ce masa komai ba, ganin haka ya ce,"Ok"Sannan ya miƙe ya ce,"Please, ina zuwa I don't have any appointment with another lady but lemme see her." Ba ta ce masa komai ba, ganin haka sai ya sanya doguwar riga ya fita. Ganin Lubaynah da tana ganinsa sai ta fashe da kuka. "Lubaynah lafiya?" Ya furta tare da ƙarasawa gurinta ganin yadda take kyarmar sanyi. "Mai na yi wa abokinka wanda ya zaɓi ya wulakanta rayuwata, ko soyayya yana zama laifi ne?" Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka. "Is ok Lubaynah let's go to his house, I will talk to him." Ya ce tare da fara tafiya zuwa gidansa. Kasancewar babu nisa suka isa. Layinsa ya kira, sannan ya sanar masa yana ƙofar gida."Are you with Lubaynah?" "Please Captain open the get we need to talk." Ya ce nasarar da kashe wayar ba tare da ya amsa masa ba. Solo ya kira ya sanar mishi da ya buɗe get ɗin. Lubaynah na shiga falon ta saki kuka sosai tare da zuwa za ta rungume shi. Da sauri ya janye jikinsa yana watsa mata mugun kallon daya sanya jikinta sanyi sosai. "Captain Aliyu, Lubaynah ba ta cancanci haka a gurinka ba. Please settle with her, the girl deserve your love." "I already broke up and a told her am done into this toxic relationship. Kalim, mahaifina ya yi matuƙar yarda da ni sosai, haka family ɗina suna mini kallon mutumin kirki, na zama kura da fatar akuya. I need to change tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada. Duk ranar da mahaifina ya gane abin da na ke yi ba zai yi sausauci a gare ni ba, sannan zan rushe duk yardar da ke tsakaninmu." "Then ka aure ta tana sonka kai kaɗai take kulawa." "No, it is absolutely impossible!" Ya furta babu kunya. Jin abin da ya ce sautin kukanta ya ƙaru. "You know what? Lemme leave you with her, please reconcile." Ya ce tare da ficewa. Yana fita ta miƙe ta kama hannunsa da yake shirin shigewa bedroom. "Aliyu don Allah ka so ni ka tura iyayenka, domin mahaifina ya tsaurara mini dokar hana ni zuwa Abuja, sannan ya ce in har sona da gaske kake yi ka turo iyayenki." "Lubaynah am so sorry da na yi disvirgin ɗinki, but I can marry you. Go look for another man and marry. Na yi miki alƙawarin duk abin da kike so zan baki. Ki faɗa mini ko nawa zan baki matuƙar za ki fita daga rayuwata." "I don't need your money. My dad has money on him. Zuciyata kai take muradi so na ke yi na mallake ka a matsayin mijina. Ina sonka don Allah ka aure ni. Na yi maka alƙawarin kasancewa duk yadda kake son matarka ta zama." Ta ƙarashe maganar tare da durƙusawa ta dafa ƙafafunsa. Rintse idanunsa ya yi cikin damuwa. Zuciyarsa take son tausaya mata, amma ba ya amince ya aure ta ba, domin ya san ko da ya yi hakan, ba za su taɓa samun zama lafiya a rayuwar auren su ba. Don haka zai lallaɓe ya shawo kanta ya bata kuɗi sosai ta fita daga rayuwarsa. Kamata ya yi ya miƙar da ita ganin haka sai ta faɗa jikinsa. Da sauri ya janye ta daga jikinsa, ya yi da zafin jikinta ya sanya shi jin wani iri. "Is ok stop crying we will talk later. Yanzu kina buƙatar kici abinci ki samu lafiya." "Sojana ka yi alƙawarin za ka aure ni?" Ta yi masa tambayar tana share hawayenta. "I will sleep on it." Ya ce mata tare da kama hannunta zuwa bedroom ɗinsa. Kwantar da ita ya yi kan gadon sannan ya kira doctor ɗinsa don ya duba ta. Ganin yadda yake tattashinta, sai yaji hankalinta ya ɗan kwanta tamkar ta yi baƙo ya mutu. A ranta tana addu'ar Allah ya sanya ya amince ya aure ta. Bai daɗe da kira likitan ba ya ƙaraso. Ganin yadda jikinta ya yi har ɗakinsa ya shiga ya yi treatment ɗinta. Bayan ya yi mata allura ya ɗaura mata drip, sannan ya yi masa sallama ya tafi kan cewar Aliyu zai cire mata. Tana kwance a kan gadon tana bacci idanunta rufe. Tea ya ba ta da ƙyar tasha sannan ta samu bacci. Kallon kyakyawar fuskarta ya yi da baccin da take yi ya ƙara mata kyau. Ramar da ta yi sai ta ba shi tausayi. Yana son ya tursasa zuciyarsa ya aure ta, in ya so sai ya auri zaɓinsa daga baya, amma duk lokacin da ya yi ƙoƙarin haka, zuciyarta gargaɗinsa take yi. So yake ta fahimce shi domin yana fatan ya daina ƙaxamiyar rayuwar da take yi, musamman daya san cewa Kama tudini tudanu. Wato duk abin da ka yi kai ma sai an yi maka. A ranar bai yi bacci ba domin kwana ya yi yana jinya. Sosai zazzaɓin ya kamata. Sai zuwa asuba ta samu bacci. Ganin haka sai ya koma falo ya ɗauki Laptop ɗinsa yana aiki, daga baya bacci ya kwashe shi. Lubaynah ta yi tunanin zai hau gadon su kwanta, musamman da zazzaɓin ya tashi sai da ya rage mata kaya ya shafa mata ruwan sanyi, amma sam jikinta da in ya gani ba ya iya ɗauke idanunsa, sai ta ga bai kwanta a kusa da ita ba don ya shiga jikinta ya rage zafi. "Hakan na nufin za mu yi istibira'i mu yi aure ne?" Ta yi wa kanta tambayar tana fatan ya kasance hakan. Da safe sai ta tashi babu zazzaɓi sai dai rashin ƙarfin jiki. Ya shigo bayan ya yi sallah ya dawo. "Good morning baby?" Ya ce mishi tana ƙoƙarin tashi. Ganin haka ya taimaka mata ta zauna. "Da fatan kin tashi lafiya ya jiki?" "Da sauƙi." Ta furta tana miƙa. Ɗauke kansa ya yi daga gareta, domin daren jiya ba ƙaramin ƙoƙarin ya yi, har ya iya kwanciya ba a gurinta ba. So take su daina ƙaxamiyar rayuwar da suke yi, su fuskanci gaskiya, domin gina kyakyakwar rayuwar da za su yi alfahari da ita. Abinci Peter ya haɗa musu, a tare suka ci domin ta samu sauƙi. Da ta yi wanka ta yi sallah, sai ta ji duk ciwon ya tafi. Yana falo zaune ta fito cikin doguwar riga sosai ya kamata. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta. "Please Lubaynah je ki sanya mayafi." "Kallonsa ta yi tana son tambayarsa ko sun fara istibira'i ne, amma sai ta fara tafiya zuwa ɗaki, ganin babu fuskar tambayar. Gyale ta ɗauko ta yafa duk da cewar abin da yafi gyalen ya so. Lubaynah tana da sura mai kyau, duk namijin da zai keɓe da ita dole ne ya ja hankalinsa, wannan surar ta ci galabarsa har ya fara mummunar harka da ita. Gyalen ya kalla duk da bai wani rufe jikin ba, sai ma kyau da ya ƙara mata, amma babu laifi tun da daina ganin surarta da take rikita shi. Zai iya cewa tun da yake da ita bai taɓa ganin ta sanya hijabi ba, sai dai na sallah shima don ya tsawatar mata ne, amma da gyale take yi. Suna cin abincin bai wani hira da suke yi, sai ita data zuba masa idanu kamar za ta cinye shi. Bayan sun gama cin abincin, sai ya fita domin yana da appointment. Ita kadai ta zauna a gidan har zuwa yamma. Kano Hankalin iyayen Lubaynah ya tashi sosai har da Anty. Wayarta sun kira yafi sau a ƙirga, amma ta kashe wayarta. Daddy ya yi fushi sosai, neman gidan Captain Aliyu ya so ya yi, don duk da yake soja sai ya wulaƙanta rayuwarsa, na mayar masa da yarinya farkarsa. Suna ta neman layinta, har yamma sai suka ci sa'a, ta kunna wayar don ta kira Captain Aliyu da bai dawo ba. Ganin kiran Daddy hankalinta ya tashi sosai, amma sai ta daure ta ɗaga. Ganin ta ɗaga Daddy ya ce,"Lubaynah, kin zaɓi namiji kan iyayenki ko?" Shiru ta yi ta kasa magana, sai hawaye da yake zuba a ƙuncinta. Jin haka ya cigaba da magana cikin fushi. "Tun da kin zaɓe shi na barki da shi kike namiji ne, kuma zan yafe mishi .." "Don Allah Daddy ka yi hakuri ni da Aliyu za mu zo ya nemi aurena." "Shashashar banza mara hankali. Tun da an gaya miki shi banza ne kamar ki zai aure ki. Wallahi in har ba ki dawo gida ba, sai na yi miki mummunar duka." Ya ce tare da kashe wayar yana huci. Kuka ta fashe da shi jin yadda ya ɗauki hushi sosai. Ta san Daddy yana matuƙar sonta, domin karo na farko da suka samu saɓani a tsakaninsu. Tana cikin kukan Aliyu ya yi sallama ya shigo. Cikin hawaye ta amsa sallamar. Ganin waya a hannunta ya tabbatar masa da iyayenta suka kira, don haka bai tambayi ba'asin kukan ba ya ƙarasa ya zauna a gefenta. "Lubaynah, let's face the reality I can't marry you. Ina sonki amma wallahi bazan iya auren ki ba, saboda bazan ɓoye miki ba, in har na aure ki zan kasance cikin wasiwasi da zarginki, kuma kin ga babu kyau a aure. Mun yi kuskuren da ya zama katangar daya hana aurenmu. Ki je ki samu wani xan ba ki du...." "No!" Ta daka masa tsawa tana faɗin haka tare da toshe kunninta. "Captain I told you several times. Kai nake so kai na ke so na rayu da kai. Matuƙar ba za ka aure ni bana son koma daga gareka. Kuma wallahi ba zan zauna na zura ido ka auri wata ba, domin sai na zame maka ƙadangaren bakin tulu. Aliyu you are so selfish. Why zaka ki aurena bayan kai sheda ne, kaine namijin da na fara sani?" Jin yadda take kuka tana faɗin haka sai ransa ya ɓaci. Miƙewa ya yi cikin zafi ya ce,"Ba zan iya auren ki ba, that is the final answer. Please ki fita daga rayuwata." Kallonsa ta yi kamar zautacciya sai kuma ta miƙe ta kalle shi, a razane ganin yadda ya harzuƙa."Haka kace?" "Yes and I will not think again. Fine another person. "Ya ƙarashe maganar yana kallonta. "Ok, fine. Zan koma gida, amma wallahi ba zan rabu da kai ba, duk yadda zan yi sai na mallake ka. Kuma ka rubuta ka aje in har ban aure ka ba, babu wata 'yar iskar da za ka aura a matsayin zabinka. Captain ka yi kuskure keta mini haddi na da ka yi, sannan ka ce za ka jefar da ni, ka ɗauki wata ba zan taɓa barin haka ba, matuƙar ina da numfashi. I will go but you will see what will happen." Ta ce tare da shiga cikin ɗakinsa ta tattara komai na ta ta fice. Komawa ya yi ya zauna, yana fata shine na ƙarshe don yasan ba ta da zuciya zata dawo. Lubaynah tana tafiya tana kuka sosai. A yau ta ƙara yarda duk macen data mallakawa namiji jikinta ba tare da aure ba, haƙiƙa ta cuci kanta. Yau ga Aliyu ya kasa aurenta, don ta mallaka masa jikinta kafin aure. Tabbas zina babban tabo ne ga 'ya mace, domin hatta wanda ya aikata zinar gudun aurenta take yi. Ta yi fatan ina ma ana mayar da hanunn agogo baya, da ta tsare mutuncinta ta haƙura da son shi da take yi. Ko da ace za ta mutu ne, wataƙila da ya yi mata sausauci ya aure ta ko da baya sonta, amma gashi yau Aliyu shi yake gudun aurenta yana faɗin ba zai yarda da ita ba. Ina ga kuma wanda ya aureta ya sameta ba budurwa ba? Ta yi kuka sosai har sai da ciwon kai ya dawo. Saboda tashin hankalin da take ciki, sam bata je gida Hannah ba, domin ta san ƙara mata damuwa za ta yi. Kai tsaye tasha ta nufa ta biya kuɗin zuwa Kano. A ranta ta shirya duk hukuncin da iyayenta zasu yi mata. A lokacin da ta isa gida duk suna zaune a falo. Kamar wata munafukai ta yi sallama, sannan ta raɓe a bakin ƙofa. Kallon ta suka yi cikin mamaki domin maganarta suke yi. Daddy ne ya miƙe cikin tsanannin fushi ya wanka mata mari."Banza shashasha! Ina yake da kika ce zai zo ya aure ki?" Kuka ta fashe da shi tare da durƙushewa ƙasa ta ce,"Daddy, na yi kuskure ka yafe mini don Allah!" Jin abin da ta ce suka tabbatar da yaudararta ya yi.'Kin cuci kanki Lubaynah. Kin zubar da tarbiyarki kin bayar da darajarki a banza." Cewar mahaifiyarta tana kuka. "Na yi kuskure ku yafe mini don Allah." Ta furta tana hawaye. "Kanki za ki bawa haƙuri domin duk abin da kika yi wa kanki ne." Daddy bai kalle ta ba ya haye sama, saboda yana jin kamar ya karyata. Ganin sun watse sun barta a ɗakin sai ta miƙe ta shige cikin ɗakinta. Ta yi kuka sosai har ta bawa uku lada. In ta tuna yadda Captain yake sarrafata yadda yake son yana mata alƙawarin banza sai ta ji kamar za ta haɗiye kanta ta mutu. Bayan ta yi kukan ta fahimci bashi ne magani ba sai ta janyo wayarta ta kira ƙawarta Rauda. Bugu ɗaya ta ɗauka tana dariya. "Yane amaryar Captain to be? Mommy ta kira ni wai ko na san gidan Captain na ce musu a'a." "Hmmmmh! Aliyu ya yaudare ni ya ci amanata. Kin san ya kafe ba zai aure ni ba?" "Amma Aliyu ya zama mai son kansa. Nufinsa ya more ki zai kuma je ya samu wata ya farke na ta budurcin?" Kin san Allah bai isa ba. Ki kwantar da hankalinki ki ci abinci ki huta ina nan zuwa xan shigo, don na yi tafiya ni da Habibina. Kin dai san hanyar da na bi na riƙe shi. Ta bayan ƙasa za mu bi shi tun da ba shi da mutunci." "Shikenan sai kin dawo." "Yauwa kar ki damu bazan daɗe ba. Na raka shi Legos za su yi seminer. Captain na ki ne babu wata 'yar iskar da zai aura. Shi ma ya san yaudarar kansa yake. " "Na gode Rauda sai kin dawo." Ta ce tare da kashe wayar hankalinta ya kwanta. To Lubaiyna wannan sai ya zama darasi ga 'yan matan da suke barin samari na amshe budurcin su kafin aure, domin duk namijin da kika mallakawa kanki ko ƙaddara ta sanya ya aure ki ba zai yarda da ke ba. Hattara 'yan mata da zawarawa. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 14 "Amma Aliyu ya zama mai son kansa. Nufinsa ya more ki zai kuma je ya samu wata ya farke na ta budurcin?" Kin san Allah bai isa ba. Ki kwantar da hankalinki ki ci abinci ki huta ina nan zuwa xan shigo, don na yi tafiya ni da Habibina. Kin dai san hanyar da na bi na riƙe shi. Ta baya ƙasa za mu bi shi tun da ba shi da mutunci." "Shikenan sai kin dawo." "Yauwa kar ki damu ba zan daɗe ba. Na raka shi Legos za su yi seminer. Captain na ki ne babu wata 'yar iskar da zai aura. Shi ma ya san yaudarar kansa yake. " "Na gode Rauda sai kin dawo." Ta ce tare da kashe wayar hankalinta ya kwanta. Iyayenta sun ɗauki fushi sosai da ita, ganin haka hankalinta ya tashi sosai. Da ƙyar ta samu ta shawo kansu, bayan ta yi musu alƙawarin ba za ta ƙara kula shi ba, sannan za ta nemi wani ta yi aure sannan suka haƙura, amma har lokacin haushinta suke ji. Captain tun yana sanya idanun za ta dawo, amma har ya ga sun kwashi sata bata dawo ba. Hankalinsa ya kwanta yana fatan ya yarda ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda. Tafiya zuwa England ya kama shi hankalinsa kwance ya tafi. Zariya Mama Mufida zaune a gidan Anty Amina suna hira. Anty Amina ta waiwayo da take kwaɓa kullum ɗan-gauda ta ce,"Wai yanzu kina nufin wannan turaren bitazaizai da ta shafa bai kalle ta ba, mun yi asarar kuɗinmu kenan?" "Hmmmmh! Ki bar ni da buhun takaici wallahi kallon banza ba ta samu daga gare shi ba, domin ta ce mini gara Hanifa da yake kin san kishiyar uwarta ta san yadda za ta shiga fita a cikin malamai, har kallon ta ya yi yana tambayarta karatu." "Zai tambaya tun da yana zuwa an zuba masa a ruwa ya sha. Ni fa wannan Maryam ɗin tun da na ji Sama'ila zai aure ta, na san cewar sai ta gama da shi da iyalansa." "Wallahi ta gama da shi har ita mamata Hanifa, saboda ba ki ga ladabi da take mata ba, kaf 'ya'yanta in har Maryam ta yi magana ya zauna, har da waɗanda suke gidan auren." "Duk za ta iya wannan 'yar gidan malaman zauren? Har yanzu ba ki ga sanin sunan mahaifinta ba. Ita ma Maman Hanifah har da kwaɗayin ta sanya shi Aliyu, ya auri yarinyarta tun da kin ga ya shaƙu da ita so take ta haɗa aurensu, ba tare da sanin ko da ta haɗa ba itace da riba, domin haɗa auren amfaninta ne." "Shi ya sanya tsani yarinyar nan, wallahi yadda na ke jin tsanarta, bana tunanin in Baban Mufida ya ƙara aure na tsani kishiyata kamar haka. Yarinya ƙarama sai kinibibin tsiya, kowa yanzu a gidan nan Anty Amarya dai." "Iya makirci ne da kissa na mata, don ta zo daga baya ta mallake kowa a ciki, tun da bata haihuwa ai dole ta nemi hanyar da za ta mallake kowa ta juya yaranku." "Ai ba zai yiwu ba kuwa in har ina da rai. Kin san Allah yadda kaf yarana babu wacce ta auri mai kuɗi kamar shi? To kuma babu yarinya da za ta samu mai kuɗi na zuba ido ayi auren ko da ace Mufida ba ta son shi, sai na san yadda na yi na hana auren, domin ina gani ba za a rinƙa mana iyayi da suruki mai kuɗi ba. " "Ai gara ki miƙe wallahi in har Mufida ta same shi ta yi miji." "Kin ga yanzu kuɗin da na ke juyawa na shinkafa na kwaso muje gurin Malamin nan, na fi son a yi abun cikin sauri domin kin san da zafi-zafi akan buga karfe." "Yanzu kuwa domin ina ɗora tukunyar gaudar, kafin na shirya Karima sun dawo daga makaranta, sai na bar mata muje mu dawo tun da babu nisa. Ki kwantar da hankalinki Mufida bata da miji sai shi." "Allah ya nuna mini haka, har na ga yadda zan shuka rashin mutunci a dangi. Kina ganin Anty Hafsa daga yarinyarta ta auri miji mai mota yana aikin gwamnati, sai iskanci duk aka zauna zancen suruki take yi, sai kace kanta aka fara auran mai mota." "Mijin da ba ita ce ta farko ba mijin wata ta aura har take tutiya?" "Za ta yi mana tun da yana basu abin duniya, kuma kin san ta itama da shige-shige ba zama za ta yi ba?" "Haka ne kuwa ta shi mu tafi bari na ɗauko mayafina tun da ta dawo." Anty Amina ta furta bayan ta gama jera ɗan-gaudar a tukunya ta rufe. Kasancewar babu nisa basu jima ba suka isa. Bayan sun yi mishi bayani sosai, ya shiga ciki ya yi musu rubutu da magunguna ya ba su. Suna tafe suna hira Anty Amina ta kalle ta ce,"Kin dai ji abin da ya ce, sai ta kula yadda za ta yi amfani da su." "In sha Allahu kin ga tun da suna shiri da ƙanwarsa Nufaisah, sai ta rinƙa tambayarta lokacin da zai zo. Yana zuwa sai ta je hutu gidansu, yadda za ta samu ta yi maganin, tun da ya ce dole wannan rubutun sai ya ci a abinci." "Eh hakan ma ya yi shawara ma kyau. Allah dai ya sanya ayi a sa'a." "Amin, bari na wuce gida kawai tun da samu abin da na zo nema." "Na ɗauka za mu koma kici abinci Maman Mufida?" "Gara na koma gida yanzu na san Mufida ta gama abinci." "To shikenan Ubangiji ya bada sa'a." Amsawa ta yi tana ƙoƙarin taran keke napep. Cikin farinckin ta isa gida, ta yi sallama Anty Amarya ce zaune a tsakar gida tana gyara zoɓon da za ta dafa. Amsawa ta yi tana mata sannu da zuwa. Wani irin tsuka ta saki ta wuce ciki ba tare da ta amsa ba. Kallo ta bita da shi tana mamakin kishin da take yi da ita, saboda kishiyarta suna zaman lafiya, amma Maman Mufida abin da take yi mata ko miji suka haɗa sai haka. Ci gaba ta yi da aikinta bakinta ɗauke da azkar domin tana kula da ibada, saboda ta san cewa tana da maƙiya sosai musamman ita. Mufida, da take raba shinkafa da wake da mai da yaji da ta gama. Sallamar Mama ya sanya ta ɗago tana kallonta. "Sannu da dawowa Mama." "Yauwa 'yar albarka maza ki gama ki shigo." Ta ƙarashe maganar tana washe baki tare da ije hijabinta kan igiya. Ganin yadda take farinciki sai ta kasa ƙarashe rabon. Ba ta zuba nata da na Mama ta rufe tukunyar. Shiga ciki ta yi ta zauna gefenta."Kina jina Mufida? Malamin yace ki natsu ki yi wannan aikin da kyau, domin ya tabbatar mana da in kika yi yadda yace Captain Aliyu sai yadda kika yi da shi, amma wannan rubutun dole sai kin zuba masa a abinci." "Cikin abincin da zai ci, ina zan ganshi na zuba masa?" "Dallah ja can kin cika tsoro. Kin san wane irin namiji kike son mallaka? Dole sai kin zama jaruma sosai. Abu mai sauki tambayi Nufaisah lokacin da zai zo, in ta gaya miki sai ki shirya zuwa Kaduna ki yi hutu, don kar a zarge ki ku tafi da Hanifa." "Kuma haka ne Mama, domin na ji kamar Anty Amarya za ta je Kaduna, amma sai in ya zo." "Shikenan, sai ki ce za ki bita kin ga ai ba za ta ce a a ba, tun da za ta da Hanifa." "Amma ina jin tsoron yadda zan sanya maganin, kin san ko a gida abincin Mommy kawai ya ke ci?" "Wannan kuma shawara ya rage wa mai shiga cikin rijiya, sai ki rinƙa abu kamar ba mace ba. Ke ko irin fim ɗin nan da ake kallo ake sumun dubara ai kyayi yi tunani. In kin kasa sanya iya abincinsa, ki sanya a cikin abinci kowa duka kin ga shi an yi don soyayar aure, sauran mutanen gidan sai su ƙaunace ki." "To Mama, zan gwada duk yadda zan yi sai na sanya masa, domin ba zan iya haƙura da shi ba." "Yauwa haka na ke son ji." Damagaran Jimmalo zaune a gaban Kaka Tani ta tasa ta kamar za ta yi kuka. Kallonta ta ƙara yi tare da ɗauko jiƙaƙƙen magani ta miƙa mata,"Don Allah Kaka Tani kisha maganin nan, kin ga tun jiya kika fara janta har yanzu jikin ya ki sauƙi." "Na sha Jimmalo, sauƙin ne dai Allah ba kawo ba." "To ki ƙara sha, yanzu zan je gurin Lado mau kyamis ko Audi ya haɗa mini maganin janta." Ta ce tana ƙoƙarin kai mata ruwan maganin baki. Kurɓa sau uku ta yi sannan ta koma ta kwanta. "Yauwa Kakata sanyin idaniyata. Bari na ruga na siyo miki sai na tafi sarin ayaba." "Sai kin dawo jikalle, Allah ya yi miki albarka." Ta ce tana kallonta. "Amin," Ta amsa sannan ta fita da gudu. Ba ta jima ba ta karɓo mata maganin, ciwo takwas da boska sai na ulser. Sai da ta tabbatar ta sha sannan ta ɗauki tiren ta yi mata sallama ta fice. Bayan fitarta Kaka Tani ta durƙushe a ƙasa tana maleluwa, saboda wani irin zafi da cikinta da kirjinta yake yi. Sosai ulser ta taso mata. Haka ta yi ta maleluwa har ta samu ta lafa. Da ƙyar take numfashi saboda ƙirjinta da yake mata zafi sosai. Tana da ciwon ulser, amma ba ta yi mata haka. Tun ranar da suka dawo cikin dare ta kasa bacci, domin da ta rufe idanu maganganun Hajiya suke mata kuwwa a kunninta. "Da gaske ne na ɓata tarbiyar Jimmalo?" Ta yi wa kanta tambayar domin ita gani take gata ta bata. Duk da ta san cewar ba ta da tsafta. Abin da take ganin kawai za ta iya cewa shine naƙasunta, amma tana ganin masifa da rashin kunya sai mutum ya taɓa ta, kuma wannan a gurinta sam ba damuwa bane. Shi kansa jikanta da take ganin ta yi masa rashin kunya ai ba shi da kunyar. Duk yadda ta so ta kare lamarin kar ta ga laifinta, amma zuciyarta ta gaza hakan, domin zuciyarta hutuma da zarginta take yi. Ta kasa bacci kullum cikin tunanin maganganun take yi, musamman da ciwo ya rufe ta lokaci guda. Cikin ƙanƙannin lokaci ta gane tabbas gaskiya Hajiya ta gaya mata, domin ta zauna ta auna lamarin rayuwarta, duk sai ta ga hakan ne. Duba ga har yanzu da take shekar goma sha huɗu babu wanda ya zo yana sonta, kasancewar daga shekara goma ake fara aurar da 'yan matan ƙauyen. Tsananin tsoro da firgici ya kamata ganin ciwon na son ya fi ƙarfinta. Tunanin in ta mutu a hannun wa zata bar Jimmalo ta fara, wanda ya ƙara rikita jikinta. Tunawa da duk 'yan'uwanta babu su. Haka ta wuni cikin ciwo da tunani, wanda yake ƙara rikitar da jikinta. Gani take kamar mutuwa za ta yi, saboda yadda numfashinta yake ɗauke wa in ciwon ya taso. Kafin Jimmalo ta dawo daga tallah ta fita hayyacinta. Hawaye tausayin Jimmalo take yi, domin gani take kamar mutuwa za ta yi ta barta a cikin duniyar da bata da kowa, kuma duk ta hayyaci kowa. Ta san cewa in har wa'adinta ne ya yi, tabbas rayuwarta ta shiga gararin rayuwa. Ita kaɗai za ta ci gaba da rayuwa a cikin gidan? Wannan tambayar yake ƙara tayar da hankainta matuƙar gaske! Jimmalo tana gurin sarin ayaba, amma hankalinta na gurin Kaka Tani. Da sauri ta samu ta siyar da ayabar, sannan ta siyo musu awara da rogo. Bata jira abokan tallarta ba, ta yi musu sallama ta dawo gida. Halin da ta ganta ya tsorata sosai, domin ta yi tunanin za ta zo ta ga jikinta ya yi sauƙi."Kaka Tani, har yanzu jikin?" Ta yi mata tambayar cikin rauni murya tana kallonta, saboda tun da suke rayuwa, bata taɓa ganin ta yi jinyar kwana biyu ta galabaita haka ba. "Jikata kin dawo?" Ta furta da ƙyar tana jawo numfashi. "Na dawo Kaka Tani. Ki tashi ga rogo da awara ki ci." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin zaunar da ita. "Ba zan iya cin komai ba Jimmalo, ji nake jikina kamar ana mini lalas na wuta, sannan ga wani irin zafi da ƙirjina yake mini. Ki ba ni ruwa mai sanyi na sha." Ganin yadda take maganar sai hankalinta ya tashi sosai. Da sauri ta kamata ta kwantar, sannan ta ɗauki kofi ta ibo ruwan randa ta kai mata baki bayanta ɗago ta. "Bari na je na kira Innar Salame ta yi miki kamun ƙirji." Ba tare da ta ji abin da za ta ce ba, ta fita daga cikin gidan cikin tsananin tashin hankali. Tana zuwa gidan ta faɗa babu sallama. Innar Salame tana gaban murhu tana ƙoƙarin ɗora abinci."Don Allah ki je ki yi wa Kakata kamun ƙirji ba ta da lafiya." Juyowa ta yi da sauri don ba ta ji lokacin da ta shigo ba. Kallonta ta yi ganin yadda ta bayyana rauninta. "Ba zan zo ba, sai yanzu da kike son na yi miki abu za ki bayyana fuskar tausayi? Duk yadda kike ƙawance da 'yata bai hana ki gurza mini rashin mutunci ba. Shekaranjiya allasarata kika ɗauka kan Fatahu yana tallah ki ce Salame ko uwarsa ta ƙwatar masa. Don haka ki je ki yi mata da kanki tun da ita ma bata da mutunci, in an kawo mata ƙarar ki sai ta goyi bayan ki. Shi ya sa kike abin da kika ga dama." Jin abin data ce sai hankalinta ya tashi sosai, musamman tuna yadda ta bar Kaka Tani cikin mawuyacin hali. "Don Allah Innar Salame kije kar kakata ta mutu. Wallahi zan haɗa zan biya har da kuɗin kamun ƙirjin, kuma na rantse daga yau ba zan ƙara miki rashin kunya ba." "Ba zan ji daɗin bakinki ba, ki tafi ki ba ni guri mara kunya da rashin tarbiyya fitsarrarriyar banza kawai." Da ace lafiyar Kaka Tani ƙalau ta faɗi haka. Ta san cewa a rashin kunyarta sai ta yi ƙoƙarin marinta, amma sai ta yi mamaki ganin ta kara duƙawa ƙasa ta ce,"Ki taimake ni kar Kakata ta mutu don Allah." "Ba zan yi ba sai ki je rashin kunyarki ya yi mata." Miƙewa ta yi cikin hawaye za ta fice da gidan, sai ga Salame ta shigo da sauri, saboda an gaya mata jimmalo ta je gida su. A tunaninta rashin kunya ta je ta yi wa innarta. "Yauwa Salame ki taimaka ki roki innarki ta je ta kama ta kirji, kin san duk ƙauyennan ita ce ta iya kamun ƙirji." "Ba za ta je ba ai dama na gaya miki, akwai ranar da zan rama rashin mutuncin da kika yi mini. Sai ki je ki nemi wata, amma Innata ba za ta je ba mara mutunci kawai." Jin abin da ta ce sai ta fita cikin damuwa, ba tare da ta ƙara cewa komai ba. Salame da uwarta suka rinƙa zaginta suna ala ƙara. Cikin sanyi ta koma gida, sai dai ganin jikinta ya ƙara riƙewa sai ta sanya kuka sosai ta koma gidan. Duƙawa ta yi cikin muryar kuka ya ce,"Ku taimaka mini Kakata za ta mutu numfashinta sai ɗauke wa yake yi." Jikin Salame ne ya fara sanyi ganin Jimmalo tana kuka sosai. Za ta iya cewa tun da take karon farko da ta ga zuciyarta ta karaya tana kuka. Salame sai tausayinta ya kamata, kallon Innrta ta yi da take ta tuƙin tuwonta."Inna, don Allah ki je ki dubata. Ki yi saboda Allah daga ganin yadda ta yi Kaka Tani tana jin jiki." "Yanzu kin manta rashin mutuncin da take miki? Kaf ƙauyen nan wa suke gani da mutunci. Ai dama muna jiran wannan lokacin da za su nemi taimako a kai musu, sai su san ana yin mutunci saboda gobe." "Ki je ki dubata saboda Allah ba don halinsa ba. Allah yasa hakan ya zama silar shiriyarsu." Shiru tayi tana tunanin kamar kar ta je. Ko mai ta tuna sai kuma ta figi gyalenta ta ce,"Ki kwashe tuwon ki raba." Jin abin da ta ce sai Jimmmalo ta kalli Salame ta ce,"Na gode da kika sanya ta je. In sha Allahu ba zan ƙara miki rashin mutunci ba." Ba ta amsa magabata wuce murhu don ta kwashe tuwon. Ganin haka ta ruga da gudu ta bi bayan Innar salame. Suna shiga cikin gidan ta ɗago Kaka Tani da take nishi da ƙyar."Yanzu Innar Salame zata yi miki kamun ƙirji za ki warke sannu Kakata." Ta ce tana ƙoƙarin tayar da ita. Innar Salame, duk haushin su da take ji sai da ta tausaya mata ganin halin da take ciki. Da sauri ta fara kamun ƙirjin tana mata sannu. Bayan ta gama ta kalli Jimmalo data yi zuru tana kallon ta cikin tausayawa. "Jimmalo ki kira Audi mai kyamis ƙila sai ta sha ruwa, saboda ta yi yaushin sosai." Miƙewa ta yi jin abin da ta ce ta fita. Bayan ta yi mata kamun sai ta kasa tafiya ganin halin da take ciki. "Wash! Jimmmalo mutuwa zan yi ki zo mu yi bankwana." Haka Kaka Tani take faɗi hawaye yana zuba ƙuncinta tana tausayin rayuwar Jimmalo. Audi mai kyamis ya shigo ya sanya mata ruwa, sannan ya yi mata allura. Kallonta yake yi ya ce,"Yaushe ta fara wannan ciwon?" Ya tambaya yana kallonta yadda ta koma. "Shekaranjiya ne kuma na bata bauri." "Ina ganin in dai ruwan nan bai yi ba dole kaita asibitin birni, saboda gaskiya tana buƙatar kula da magunguna." "Na shiga uku! Kaka Tani ciwo lokaci guda? Kar dai mutuwa za ki yi?" To Kaka Tani Allah ya tashi kafaɗunki don ki ci gaba da rayuwa da jikarki, saboda kin san babu wanda zai iya da ita sai ke. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 15 Miƙewa ta yi jin abin da ta ce ta fita. Bayan ta yi mata kamun, sai ta kasa tafiya ganin halin da take ciki. "Wash! Jimmalo, mutuwa zan yi ki zo mu yi bankwana." Haka Kaka Tani take faɗi, hawaye yana zuba ƙuncinta tana tausayin rayuwar Jimmalo. Audi mai kyamis ya shigo ya sanya mata ruwa, sannan ya yi mata allura. Kallonta yake yi ya ce,"Yaushe ta fara wannan ciwon?" Ya tambaya yana kallonta yadda ta koma. "Shekaranjiya ne kuma na bata bauri." "Ina ganin in dai ruwan nan bai yi ba dole kaita asibitin birni, saboda gaskiya tana buƙatar kula da magunguna." "Na shiga uku! Kaka Tani ciwo lokaci guda? Kar dai mutuwa za ki yi ki barni?" Sai hawaye shar ganin yadda take nishi da ƙyar. Tana zaune a gefenta tana ta share hawaye. A maimakon jiki ya yi sauki sai ya ƙara zafi, domin har jijjiga take yi jikinta kamar tukubar mai tsire. Ganin haka hankalinta ya tashi sosai, ta koma ta kira Audi mai kyamis "Jimmalo, akai Kakarki birni gaskiya ciwonta ya fi karfin kulawata." "Wayyo na shiga uku!" Ta furta tare da kamo ta tana hawaye. "Bari na kira miki abokina Tanimu ya kaiku. Na bar shi a shagona yana cin abinci zai je birni." Ya ƙarashe maganar tare da ciro wayarsa Tecno mai botira. Bayan ya kira shi ya sanya ta shirya mata kaya. Jimmmalo tana shirin kayan tana hawaye, ganin yadda ta koma. Tunawa da shekaranjiya suna zaune suna hira cikin raha. Da sauri ta yarda kayan, da ta fito za ta sanya mata ganin idanunta na ƙafewa." Kaka Tani! Ba mutuwa zaki yi ki barni a duniya ni kaɗai ba?" Ta yi mata tambaya tare da fashewa da kuka. Ganin halin da take ciki na tsananin wuya, sai Audi mai kyamis ya kama hannunta yana dubawa, can kuma ya sauke hannunta ya fara ƙoƙarin kamata zuwa keke napep. "Don Allah kar ku kai ni ko ina saboda mutuwa zan yi. " Kaka Tani ta furta cikin murya mai rauni. "Ba za ki mutu ba Kaka Tani! In kika mutu ki barni da wa a cikin duniyar nan? Ke ce wacce na rayu da ita kuma na ke ƙauna." "Jimmalo, ki yi haƙuri lokacina ya yi, saboda wannan ciwon ba na jin zan tash.." "Na shiga uku!" Ta furta tare da sakin kuka ta ƙara rungumeta. "Kaka Tani don Allah kar ki mutu ki bar ni. Ki bari har na yi aure ki ga jikarki. Kaka Tani zan so Bala mu yi aure in har ba za ki mutu ki bar n..." Innar Salame ta kalle ta ta ce,"Lokaci ya ƙure Jimmalo, Kakarki Allah ya aiko mata da mala'ikan da gaggawa. Halin yanzu ki bari mu maimaita mata kalmar shahada in tana da rabo ta yi." Ta ƙarashe maganar tare da janyeta daga jikinta. "Wayyo Allah Kakata. Don Allah kar ku bari ta mutu ku taimaka mini." Jimmalo tace tana ihu sosai, ganin halin da take ciki. Audi mai kyamis ya duƙa kusa da ita, yana maimaita mata kalmar shahada. "Jimmalo, ina son na yi magana da ita." Ta furta tana jin kukanta har cikin zuciyarta, amma babu abin da za ta iya, saboda ga ta yau a kwance tana ciwon ajalin da za ta bar ta ita kaɗai, a cikin duniya ba tare da ta san mai zai faru nan gaba a cikin rayuwarta ba. "Kakata ina jin ki gani a kusa da ke, don Allah ki gaya mini ba mutuwa za ki yi ba na yi shiru?" Ta ce tare da kama hannunta ta ɗora a fuskarta. "Jimmalo, a yau zan tafi na barki a cikin rayuwar da na ɓata tarbiyarki. Kalaman da Hajiya ta gaya mini tabbas haka ne. Na cuce ki saboda son da na ke miki ban ba ki tarbiya ba. Na san cewa ko na mutu babu wanda zai ɗauke ki, har su Hajiya ba za su ɗauke ki ba, amma Jimmalo in har suka yafe abin da muka yi musu su ka zo gareki, ki tafi birni ki canza rayuwar..." "Kaka Tani babu inda za ni ina nan tare dake, in kuma kin mutu zan koma da rayuwata a ƙabarin da aka birne ki, saboda ba zan iya rayuwa babu ke a cikin duniyar nan ba." Kaka Tani ta buɗe baki za ta yi magana sai ta fara tari tana jijjiga. Kafin kace me ta fita hayyacinta har idanunta sun fara rufewa. Ganin haka hankalin Jimmalo ya kira tashi. Kuka take tana ihu tana zambarwa ganin za ta mutu ta barta. Audi mai kyamis ya rufe mata idanu, lokaci da ya fahimci ta cika, bayan ta amsa kalmar shahada sau ɗaya. "Allah ya jiƙanki Tani." Jin abin da Innar Salame ta furta tana share hawaye, sai kawai ta yi wani irin ƙara ta zube a gurin. Ruwa aka sanya mata ta farfaɗo, ta rungume gawar Kaka Tani tana wani irin kuka. Gani take kamar ba ta mutu ba, saboda ba ta taɓa ganin mutuwa ba. Gani take kamar za ta tashi su ci gaba da rayuwa, don haka ta rungumeta ta hana kowa ya taɓa ta. "Jimmalo Tani ta rasu ki matsa mutane su fara mata wanka don a kaita gidan gaskiya." Idanunta ta ɗago da suka yi jajir jina bin da Innar Salame ta ce. "Babu in da zan yarda a kai mini Kakata, wacce ita kaɗai na sani kuma na yi rayuwa da ita. In na bari kuka kaita ƙabari ni kuma na rayu da wane? Kaka Tani ba za ta mutu ba, saboda ta gaya mini sai ta ga jikokiina. So kuke ku raba mu saboda ku samu damar da za ku rama rashin mutuncin da na yi muku." Ta ƙarashe maganar tare da ƙanƙame gawarta tana faɗin,"Kaka Tani kin ga azzaluman mutanen nan so suke su raba mu. Kaka Tani ki tashi daga baccin ki gaya musu ba ki mutu ba." Jijjiga ta take yi tana faɗin haka cikin kuka. Tun suna sanya ran za ta bari ayi wa gawar sutura har suka cire. Da ƙyar aka samu maza majiya ƙarfi huɗu suka rabata da gawar, sannan aka fara mata wanka don a kaita gidan gaskiya. Jimmmalo, tun da ta ga da gaske za su raba da ita ta cika ƙauyen da ihu tana ƙaraji, domin ta san cewa rayuwarta ta shiga garari In har babu Kaka Tani a duniya. Wa zai rinƙa tare mata tsiwa kuma ta rinƙa hira da ita? Jin Kaka Tani take ko iyayen da suka haifeta albarka, tun da ba ta yi rayuwa da su ba. Tun lokacin da ta mallaki hankalin kanta ita kaɗai take gani kuma ita ce duniyarta. Saboda mutuwa dare ta yi domin a lokaci har an kira sallar magariba duhu ya yi, kan dole za ta yi kwanan keso da safe a kaita. Jimmalo kasa bacci ta yi, har lokaci gani take bacci take yi. A kusa da ita ta kwana sai Innar Salame da kuma wata tsohuwa ƙawar Kaka Tani. Daren ranar Jimmalo ta kira shi a baƙin dare, saboda ba ta yi bacci ba tana ta jijjiga ta tana kiran sunanta, a haka ta kwana har gari ya waye aka fara shirin kaita. Tana cikin wannan halin da take ganin kamar duk a mafarki ne, aka yi mata sutura aka kira ta don ta yi mata addu'a a kaita makwancinta. A nan ta zama mahaukaciyar domin ƙaton icce ta ɗauka, ta tsaya kan gawar duk wanda ya zo sai ta kai mishi duka. "Babu wanda zai raba ni da Kakata. Ashe ƙiyayyar da kuke mini ta kai haka? Har zaku iya cewa Kakata ta mutu, don kawai ta warke ta samu dogon bacci?" Duƙawa ta yi kusa da ita ta shafa fuskarta. "Kaka Tani ki yi bacci ki tashi, ina gadinki babu wanda zai kai mini ke rami." Ta ce tana kallon ta sai kuma ta kalle su ta ɗora da cewa,"Kun gani murmushi take mini." Tsanannin tausayinta ya cika zuciyarsu, domin sun san dole hakan ya faru. Kaka Tani da tambayar da kanta ƙaramar yarinya take biyewa duk abin da ta yi. Kaduna. Cikin dare Hajiya ta kasa bacci, sai mugayen mafarkai take yi. Hankalinta ya tashi sosai da ta farka ta kasa bacci. Tashi ta yi ta ɗauro alwala ta yi sallah. Addu'a ta yi sosai tana fatan mafarkin da ta yi ya zamar mata alkhairi. Da ƙyar ta samu ta koma bacci, sai dai kwanciyarta ke da wuya ta yi mafarkin Kaka Tani. Cikin firgici ta farka tana yin duk addu'ar da ta fito daga bakinta. Tun da ta yi mafarkin sai ta kasa komawa. Zama ta yi kan tsakiyar gadon tana tunanin mafarkin da ta yi. "Lafiya suke?" Ta yi wa kanta tambayar cikin damuwa. Wayarta ta ɗauko ta duba lokaci sai ta ga ashe har an kira sallar asuba. Miƙewa ta yi ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta yi sallah. Addu'a sosai ta ƙara yi tana fatan suna lafiya. Da carbi a hannunta ta shingiɗa tana ja. Kafin safiya xuciyarta ya gama kitsa mata ta je Ƙauyen Damagaran, saboda gabakiɗaya ta kasa samun sukuni. Da Kaka Tani ta faɗo mata sai ta ji gabanta ya yanke. Wayarta ta ɗaga ta kira numbar Daddy. Yana ɗagawa ya yi sallama, sannan ya gaishe ta. "Ka shirya safiya za mu je Ƙauyen Damagaran, saboda jiya kwana na yi ina mafarkin Tani." Mamaki sosai ya yi, jin abin da ta ce har sai da ya cire wayar ya kalli numbarta, saboda ya yi mamakin jin cewar za ta ƙara shiga rayuwar su bayan ta ce ita da su har abada. "Kana jina ko Abubakar? Mugun mafarki na yi na Tani. Ba a gasganta mafarki, amma ina jin kamar babu lafiya, don Allah ka shirya mu wuce da safen nan." "To Hajiya Allah ya sanya lafiya. In sha Allah ina karyawa zan yi na fito." "Amin, ka yi sauri don ba zan iya karyawa ba sai a mota." "To gani nan zuwa." Ya ce tare da kashe wayar yana kallon Mommy cikin mamaki. Dariya mommy ta yi ta ce,"Ba za ta haƙura da su ba, dama ni na san haka. Hajiya da kullum nasiharta mutum ya kula da zumunci, sai ta yi watsi da nata? Na san cewa hushi ta yi kuma za ta huce ta neme su. Yana da kyau ta haƙura ta samu ta ci galabarsu har ta canza musu rayuwa, wallahi Jimmalo tausayi take bani. Yarinyar nan ba ta san wace ce ita ba, ballanatana ta gane irin rayuwarta ta dosa. Babu ilmi babu natsuwa ba tsafta. Wannan wane irin rayuwa take yi." "Duk yadda zaki so ki kawo gyara a cikin lamarinsu sam ba za su yarda ba. Ni fa ba taɓa ganin mutane irin su ba." "Gaskiya yadda ka san ba su da hankali. Da ace Kakar tana tsawata mata, wataƙila da an samu sauƙin haukar da take yi." "Duka duk halinsu ɗaya. Fito mini da kayan bari na shiga wanka." Ya ce tare da kama hanyar bayi, ita kuma ta nufi wandrop ɗinsa. Bayan ya shirya ya karya, sannan ya yi musu sallama ya nufi gidan Hajiya. Hajiya da ta riga ta shirya, tana jin motarsa ta fito tun kafin ya shigo."Na shirya muje kawai saboda hankalina a tashe yake." Yadda ya ga ta tayar da hankalinta, sai ya shiga bata baki har ta ɗan saki."Mafarki ba gaskiya bane in sha Allahu suna lafiya." "Ina fatan hakan." Ta ce bayan ta zauna a cikin motar suka fara tafiya. Kasancewar sun fita da wuri, kuma Daddy ya yi gudu sosai sai suka isa daidai lokacin da aka ɗaga makarar Kaka Tani. Jimmalo tana ihu tana riƙe da ita aka fito ƙofar gida. "Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Ni dama na ji a jikina ba lafiya ba, ashe Tani rai ya yi halinsa. Shikenan ba ni da kowa a dangin mahaifiyata." Ta furta cikin kuka tare da fita daga cikin motar. Daddy cikin sauri, ya kashe motar ya fito domin ganin mutuwar jikinsa da ya yi sanyi. "Ya Salam ashe mutuwa ta yi!" Ya furta cikin damuwa. Hajiya na zuwa ta rungume makaran ta fashe da kuka."Tani ashe ganawarmu kenan ba za mu ƙara ganin juna ba? Sannan ba mu yi rabuwar farinciki ba." Ganin Hajiya, Jimmalo ta saki makarar ta kama hannunta. "Yauwa gara da kika zo, don Allah ki gaya musu ba ta mutu ba bacci take yi. Kin gani za a raba ni da ita?" Sai ta saki hannunta ta kama hannun Daddy da yake tsaye jikinsa ya yi sanyi sosai. "Ba ta mutu ba duba ka gani so suke su raba mu." Kamar ya yadda da maganarta sai ya ƙarasa ya ɗaga likafanin. Da sauri ya mayar yana hawaye."Ki yi haƙuri Kakarki ta mutu." Duk yadda suka yi ta bari akai ta makwancinta ta ƙi, har sai da Daddy da Hajiya suka riƙe ta sannan aka tafi da ita. Ta yi ihu da kuka, har da zagi ta haɗa musu don su ƙyaleta, amma Daddy ya yi mata riƙo sosai. Duk yadda ta so ta ƙwace haka ta haƙura, domin duk ƙarfinsa ya sanya ganin tana son ta ƙwace. Bayan an je an kaita aka zauna zaman gaisuwa. Sosai Daddy ya yi mamakin irin kukan da Hajiya take yi. Duk da y an cewar 'yar'uwanta ne, amma ba su yi shaƙuwar da za ta rinka risgan kuka haka ba. Sai suka zame mishi su biyu. Ita Jimmalo dama duk haƙurin da yake bata kamar yana ƙara cewa ta yi ne, saboda tunaninta yau Kaka Tani ta rasu to da wa za ta yi rayuwa? Daddy ne ya siyo duk abin da ake bukata, duk da cewar da sauran abincin da suka kawo musu, don haka ya ƙaro wasu. Jimmalo sarfatan mutane ta yi, ta gudu zuwa ƙabarin da aka rufe Kaka Tani ta kwanta tana ta kuka ta ce,"Kaka Tani dama ba za ki rayu da ni ba, kika yi mini alƙawarin sai kin ga jikokina? Kaka Tani kin tafi kin barni mutane sun cika gidanmu ana ta cinye mana abincin da muke ci da ga ke sai ni. Kaka Tani kina jina ki taso mu koma gida, mu ci gaba da rayuwarmu, domin in har ba ki tashi ba, ni ma a nan zan dawo da rayuwa." Kuka take yi, tana faɗin suratai da kalamai waɗanda ba su kamata ba. Daddy da Hajiya suka taho zuwa ƙabarin. Ganinta kan ƙabarin tana kuka sai jikinsu ya yi sanyi sosai. Da ma sun san za a rina, dole ta yi kukan rashinta, saboda yadda ta shaƙu da ita kuma ita kaɗai ce danginta. "Jimmalo, Kakarki ta mutu sam ba za ta dawo ba, saboda lokacin tafiyarta zuwa ga mahallicinta ya yi. Duk wanda kike gani a duniya mutuwar yake jira. Ke ma za ki mutu, don haka ki taso mu koma gida ki fuskanci rayuwar gaba." "Ba zan koma gida ba, in har zan mutu to zan jira nawa mutuwar a birne mu da ita." Ta ce wa Daddy tana zare idanu jin abin da ya ce. "Jimmalo, ki tashi mu koma gida na yi miki alƙawarin zan kula da rayuwarmu fiye da yadda Tani ta yi, saboda zan baki gishiri zaman duniya zan i..." "A'a ba na son ji!" Ta furta tare da toshe kunnuwanta, sannan ta ɗora da ce wa,"Babu wanda zai iya kulawa da rayuwata, kamar yadda Kakata wacce tafi ƙaunata ta yi. Don haka ku tafi bana son ganinku na tsani kowa." Ta ƙarashe maganar, tare da ƙara kwanciya kan ƙabarin tana kuka tana kiran sunanta. Ta ba su tausayi sosai har sai da Daddy ya yi ƙwalla. Dama ita Hajiya kuka take yi. Ganin da gaske take yi ba za ta koma gida ba, saboda har an yi kiran sallar magariba, sai Daddy ya sanya maza suka kai ta gida aka kulle ta. A ranar bana tunanin ko ruwa ta ka bakinta. Ta yi kuka har ta ji babu daɗi. Idanuwanta sun kumbura sosai. In ta duba ta ga babu Kaka Tani sai dai kayanta sai ta ji kamar za ta shiɗe. Za ta iya cewa tun ta girma ba ta taɓa nesa da ita ba, domin ko anguwa za ta je da ita take zuwa na kwana. In har ba tallah ko dandali suka je ba suna tare, saboda watarana har wasa take taya ta. Yau ga shi babu ita kuma ana tsammanin ta ci gaba da farinciki? Ita da farinciki har ƙarshen rayuwarta, domin za ta yi ta ƙunci, tana jiran lokacin da nata mutuwar za ta zo, ta je gurin Kaka Tani. Duk rarrashin da suka yi mata, taki yin shiru kuma ta ci abinci. Jimmalo ko haka kawai akwai kafiya, ballantana an raba ta da abin da take ganin babu na biyunsa a cikin rayuwarta. Haka ta kwana cikin dare, zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Ba ta sha magani da Hajiya ta bata ba, don haka zazzaɓi mai zafi ya kamata har asuba tana makyarkyata. Hajiya da Daddy, kwanar wahala suka yi, saboda babu gurin bacci mai kyau. Haka dai suka daddage har aka yi sadakar uku. Aka raba gadon da ta bari aka bawa Jimmalo dama ita ce kawai. Tunkiya guda uku sai kaji da kuma hatsi da take tarawa, sannan sai gidanta ya rage. A fadar maigari akayi rabon gadon. Maigari ya kalli Hajiya da Daddy ya ce,"Tani ta rigamu gidan gaskiya Allah ya yi mata rahma." "Amin," Suka amsa ban da Jimmalo da take sharan hawaye. "An raba abin da ta bari saura gidanta, domin shi ma ya kamata a siyar a bawa Jimmalo gadonta." Jin abin da maigari ya ce, sai ta miƙe tana zare idanu."Wallahi babu wanda ya isa ya siyar mana da gidan da na ke gani nake tuna Kakata! Kuma in kuka siyar a ina zan rinƙa rayuwa?" "Ba ki san Kakarki ta bada wasiyar ki koma birni ba? Ai ta gaya wa Audi mai kyamis da Innar Salame 'yan birni su tafi da ...." "Kan uba!" Ta furta tare da miƙewa tana zare idanunta, domin ji ta yi kamar wasa ko tsokanar ta yake yi. "Ni ce zan koma birni! Saboda me na rantse ba zan bi kowa birni ba, ina nan a ƙauyen nan, domin rayuwar ƙauye yafi mini rayuwar birni, sannan ba zan je gurin mutanen da nake zargin su suka cinye mini Kakata ba, domin tun da muka je birni muka dawo Kaka Tani ta fara ciwo ta mutu." Daddy da Hajiya zare idanunsa suka yi, cikin tsananin mamaki jin sharrin da ta yi musu. Jimmalo ina taya ki rashin Kaka Tani domin mutuwa babu daɗi, musamman da ta sangartata ki. Yanzu ne za a fara wasa yanzu za a shiga cikin littafin. Ƙiyayyar jini akwai cakwakiyar gaske. Ku ci gaba da bibiyar labarin sannan da sambaɗo zafafan comments. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 16 "Ni ce zan koma birni, Saboda me? Na rantse ba zan bi kowa birni ba, ina nan a ƙauyen nan, domin rayuwar ƙauye yafi mini rayuwar birni, sannan ba zan je gurin mutanen da nake zargin su suka cinye mini Kakata ba, domin tun da muka je birni muka dawo Kaka Tani ta fara ciwo ta mutu." Daddy da Hajiya zare idanunsa suka yi, cikin tsananin mamaki jin sharrin da ta yi musu. "Jimmalo, ki ji tsoron Allah! Bana tsafi ko maitar da zan cinye 'yar'uwata." Hajiya ta faɗa cikin muryar kuka. Harara ta banka mata ta ce,"Ban yarda ba, saboda ko qur'ani za ki bani zan dafa ku kuka kashe mini Kakata." Daddy kuwa kasa magana ya yi jin sharrin da ta yi musu. "Magana ta ƙare ko cinye ki za su yi, kin san Allah sai kin bar ƙauyen nan. Dama albarkacin Tani kike ci, amma yanzu wallahi ba za mu barki a ƙuyennnan ba, in kuma kika kuskura kika zauna, duk rashin mutuncin da kika yi sai mun yi miki na jaki." "Dallah malam Jatau, ka fita idanuna kai ne za a ce ka bar ƙauyen nan, tun da ba ka da gidan kanka haya kake yi. Ni kuwa ina da gidan da Kakata ta bar mini zama daram ɗan karo kawai." Yadda ta yi maganar, ya tabbatar wa mutane mutuwar Kaka Tani bai canza ta ba. "Ke Jimmalo wace irin ɗiya ce mara tarbiyya? Wannan tsohon kike wa rashin ɗa'a? Wato mutuwar Kakarki bai zamar miki aya ba?" "Au dama kun yi tunanin mutuwarta, zai sanya na kwanta sai ku taka ni yadda kuka ga dama ko? To yanzu ne zan nuna muku kalata, don wallahi ko yatsa mutum ya nuna mini sai na karya, saboda babu Kaka Tani dole na miƙe na ƙwaci kaina." "Tab ashe har yanzu rayuwarki da saura." Cewar Kallah yana mamakinta. "Ke Jimmalo zauna!" Maigari ya daka mata tsawa yana faɗin haka. Gungunan ta yi sannan ta zauna a ɗofane. Kallon su take yi tana ganin duk azzalumai ne, sai kuma ta fara hawaye tuna da yanzu tana bayan kaka Tani tana kare ta. "Yan birni kun ji wasiyar 'yar'uwarku? Kun dai san babu kyau mamaci ya yi wasiyya ba a cika masa ba, don haka ya kamata ku cika ku ɗauki wannan guyababbar yarinyar mu samu sauƙi a cikin ƙauyen nan, saboda mutuwar kakarta kamar wasu kalar rashin mutunci ta fito da su." "Ni fa ko mai za a ce ba zan bar ƙauyen nan ba, kuma duk wanda ya takale ni wallahi sai na yi mishi wankin babban bargo ko da gemunsa na jan ƙasa ne." Ta ce tana jijjiga. Daddy da Hajiya suka ɗago kai suka kalle ta cikin sanyin jiki. Hajiya tsoro ta fara bata. Wato suna son su raba kansu da masifa su jajiba musu? To amma ya za su yi tunna sune 'yan'uwanta kuma har ta bar wasiyya. Ta gane kuskuren ta na irin tarbiyar da ta ɗora ta har ta bar wasiyar a gyara rayuwarta. To ta ina za su fara da yarinyar da bata ganin kowa da gashi, sannan ba ta da tsoro idanunta a tsaye suke? Irin wannan tarin tambayoyin ya cika zuciyar Hajiya da Daddy. "Eh za mu tafi da ita a sayar da gidan nata, sai a bani zan koma birni yau." Daddy ya ce yana kallon maigari. "Sayar da gida ba mai wahala bane, don ko ni yanzu zan siya, in har za ku bar mana garin da wannan ja'irar yarinyar." "Na rantse, in har ka sayi gidan nan sai mun rinƙa muku fatalwa ni da Kaka Tani. Wayyo Kakata ki taso daga ƙabari ki ga maigari zai sayi gidanmu." Ta ce tana kuka sai ta miƙe tana zare ido. Tana gani aka kira dillalai aka sigar da gidan. Daddy ya bayar da kyautar kayan gidan yana shirin raba kayan Kaka Tani ta riƙe akwatin."Na rantse ba wanda za a ba kayan nan. Su zan rinƙa sanyawa na tuna da Kaka Tani." Zare idanunsu suka yi suna kallonta."Kayan tsohuwa za ki saka kina yarinya? Ki bari muje birni zan siya miki wasu." "Allah ya kyauta an gaya muku zan biku birni ne? Ni ma ku je ku yi tsafi da ni, bayan kun gama da Kakata. Ina nan ƙauye ko a kusa da ƙabarin Kakata na yi rayuwa." Kasa cewa komai suka yi, suna tunanin yadda za su sanya ta a mota. "Yarinyar nan fa in har ba ɗaure ta aka yi ba, sam ba za ta biku ba, saboda in kuka shigar da ita haka za ta iya ja muku hatsari ba ta da tsoro." Maigari ya furta yana kallonsu. "Sai a ɗaure mutum da ransa?" Hajiya ta yi tambayar cikin mamaki. "Wannan ne mafitar da za mu iya tafiya da ita birni, saboda in har ba haka aka yi ba wallahi ba za ta bimu ba." Cewar Daddy yana kallonta da take tsaye, tana girgiza tana aika musu da harara. "To shikenan, amma kar a yi mata ɗaurin da zai cutar da ita." Ta furta tana kallon Daddy. Maigari da Daddy, ba su tanka mata ba ya wuce ya samo majiya karfi da igiyar. Saboda shegen wayonta sai ta fahimci abin da suke nufi. Rugawa ta yi da gudu suka bita. Ba su kamata ba sai da suka wahala sosai, sannan suka yi nasarar kamata bayan 'yan ƙauyen sun taimaka musu, domin kowa murna yake za ta bar ƙauyen. Samun sa'a ta yi ta yankawa Sa'adu cizo a hannunsa. Cikin tsananin azaba ya saketa yana ihu. Ƙoƙarin guduwa ta fara suka ɗauke ta. Da ƙyar suka haɗa hannunta da ƙafafunta Ɗaureta suka yi, tana ihu tana zaginsu domin har maigari sai da ya samu na shi rabon na bankwana. Gabakiɗaya ƙauyen babu wanda ba ta yi jam'i ba ta zaga. Haka suka kamata tana ihu tana kuka, tana kiran sunan Kaka Tani. Sai kuma ta kalli Salame da jikinta ya yi sanyi sosai."Kina gani za a raba ni da ƙauyen da na taso na yi rayuwa? Salame yau zan rabu da ku ba za ki zo ki cece ni ba? Mutanen birnin nan 'yan shan jini ne, saboda su suka shanye jinin Kaka Tani da kuɗin jini suke rayuwa, ba ki ga daular da suke ciki ba. Wayyo ki taimaka mini." Kawai sai Salame ta fashe da kuka sosai take jin tausayinta da kewarta. Ta san cewa daga yau za su rabu. Jimmalo zata koma wata kalar rayuwa, domin ba lallai su yarda ta ci gaba da rayuwar da Kaka Tani ta ɗora ta a kai ba. Rayuwarta daga yanzu must be hard on her. Sun tashi tare sun yi faɗa sun yi dambe, domin duk lokacin da zasu haɗu sai Jimmmalo ta takali mutum, tun da ta san cewa ita ce ke da nasara. Duk dacewar ta girmi Salame, amma ba wasu shekaru can masu yawa ba. Sosai take kuka tana gani aka sanya a bayan mota. "Don Allah ku ɗauki mini kayan Kaka Tani na rinƙa sanyawa na tuna ta." Tace cikin kuka. "Don Allah ku ɗauko mata ina har za ta yi shiru." Hajiya tace tana kallon Daddy. "Hajiya kayan tsohuwa za a bata wane irin rayuwa zata yi a birni? Da shigar tsofaffi mutane dariya za a rinƙa mata." "Don Allah a ɗauko mata, in muka je birni na san yadda zan yi mu raba ta da kayan, amma yanzu in ba a bata ba, haka za ta yi ta kuka muna bin gari da ita. Kar a ɗauka sato ta muka yi." "Shikenan a ɗauko mata." Ya ce tare da shiga cikin gaban motar. Ganin an ɗauko kayan, an sanya mata a inda take kwance sai ta ɗan rage kukan. Ta yi ƙoƙarin ta kalli glass ɗin windon ta ce,"Allah ya tsine wa duk mutanen ƙauyen nan, tun da bakwa sona kuma gani za a tafi da ni Birni a shanye jinina, kamar yadda aka shanye na Kaka Tani. Kuma na rantse ina samu na kufto sai na dawo na cinnawa ƙauyen nan wuta duk kun mutu na yi rayuwata ni kaɗai." Sallamar data yi musu kenan, lokacin da motar ta tashi ta ci gaba da kuka. "Alhamdulillah! Yau Allah ya kawo mana ƙarshen annobar kauyen nan. Jimmalo ta bar mana ƙauye can gasu gada..." Maigari ya furta yana daga kirjinsa cikin murna, domin daga yau ya daina alƙalanci kullum, saboda a ƙalla a rana ba a kawo masa ƙararta sai biyu ko uku ba, har fargabar gari ya waye yake yi ya shiga faɗa. Saboda ihun da take musu, Daddy har da gudun tsiya ya haɗa don ya samu ya iso Kaduna. Gabakiɗaya ta sanya kishi gajiya, burinsa kawai ya isa gidan Hajiya ya je gidanta sha magani ya kwanta, saboda wani irin azzabben ciwon kai yake ji. Ganin sun shigo Kaduna ya sami ajiyar zuciya yana hamdala. Haka Hajiya burinta su iso ya kai ta gidansa, domin ba za ta iya da ita ba. Ganin ya yi hanyar gidanta sai kalle shi. Abubakar, gidanka za ka kaita ka haɗa da yaranka ka riƙe marainiyar Allah, saboda ka san ba zan iyada rigimarta ba? A wannan shekarun nawa." Zare idanunsa ya yi cikin tsananin tashin hankali."Hajiya, na ɗauka a gidanki za ta zauna sai a ɗaukar mata mai aikin da zata taya ki tarbiyartar?" "Wa ni rufa mini asiri na mutu maza su kai ni ba mata ba. Ni Jikar Kulama! Ina na ke da ƙarfin tarbiyartar da ita? Kawai ka kaita ka haɗata da su Nufaisah ka ga Ummu kusan sa'arta ce za ta iya koya daga gareta. Ga kuma mahaifiyarsu kai ma duk za ku kulada ita, amma in har na kaita gidana wallahi zata iya sanya mini hawan ruwa. Don haka in har ba so kake watarana ka zo ka ga na yi bunga ba, to ka kaita gidanka." Hankalinsa ne ya tashi ya rasa yadda zai yi. Bai taɓa tunanin Hajiya za ta ce a gidansa za ta zauna ba. Shi kuwa ya zai yi ya gyara yarinyar da take jin za ta ya karawa da kowa. Tun da har zata iya kallon tsabar idon maigari ta gaya masa magana don ranta, shi kuma bai san abin da za ta yi masa ba. Jikinsa mace ya kalle ta."Bari to na kai ta gidanki in ta yi wanka sai na taho da ita." "A'a muje ni ma zan je gidanka nayi kwana biyu har sai na ga zamanta a gidan." Ta furta mishi don ba ta son taje gidan. Babu yadda zai yi kan dole ya nufi hanyar gidansa. Suna isa ya yi hon maigadi ya buɗe masa get ɗin. Jin ya dawo duka mutanen gidan har da Mommy suka fito don taransa. Ganin da Hajiya sai Mommy ta duƙa cikin ladabi, ta gaishe ta tare da yi mata ta'aziya. Daddy ya buɗe bayan mota ya kira maigari ya zo ya kwance ta. Mamaki sosai ya kama su ganinta a bayan mota. Tun kafin ta sakko suka ji tana ta aunawa mutanen ƙauyen su zagi. "Subuhanallahi! Alhaji mahaukaciyar ce za ayi mata magani a birni?" Sa'idu maigadi ya faɗa yana kallonta, ganin shigarta da zagin da take yi kamar bamagujiya. "Kai ne mahaukaci bani ba mai kama da goriba." Ya samu na shi rabon daidai lokacin da ya kwance ta. "Daddy ba ta da lafiya ne?" Auta ya faɗa. "Lafiyarta lau ta dawo nan ne za ta rinƙa zama. 'Yar'uwarku ce anan za ta rinka zama da m..." "What?!" Gabakiɗaya suka ja da baya suna kallonta tare da zare ido. "Daddy, do you mean ta dawo gidanmu da zama?" Umma ta yi masa tambayar cikin tsananin ruɗani, tana tunanin yadda za su iya rayuwa da ita a cikin gidan. "Eh anan za ta zauna saboda kakarta ta rasu, kuma kun zama 'yan uwa domin a nan za ta ci gaba da rayuwarta. Ke Jimmalo ki shiga ciki." Ya ƙarashe maganar yana kallonta. Wani irin harara ta so ta banka masa, amma kuma sai ta fasa ta kalli ƙaton gidan. Kuka ta fashe da shi ganin kyawun gidan. "Wallahi dama na san tsafi kuke yi, dubi gidanku mai kyau, wannan in ba jinin mutane ake sha ba? A ina za a samu kuɗin nan a yi gidan nan? Wayyo Kaka Tani mun kai kammu inda za a kashe mu saura ni." Sororo suka tsaya suna kallonta jin abin da ta ce. Hajiya ta cire gyalenta tare da jan tsuka ta fara ƙoƙarin shiga ciki. So take yi ta yi wanka ta bar musu gidan, domin ba za ta iya zama da ita ba. Su da Allah ya ƙaddara wa kazar wahala suna da sauran karfi sai su ɗauki ƙaddara, amma ita kam tana gama wanka za ta tafi, saboda ko muryarta ta ji tana kuka sai kanta ya buga. "Zo mu shiga cikin gida Jimmalo." Mommy ta ce, ganin Daddy ya kuma hanyar shiga ba tare da ya kalle ta ba. "Babu inda zani sai dai a mayar da ni Damagaran." "Kin zo kenan domin ba ki da kowa a ƙauyen. Hatta gidan da kike zama an siyar, don haka ki zo ki shiga cikin gida ki karɓi canjin rayuwar da kika samu." "Ni fa babu inda zani a yanke mini kai. Wayyo Kaka Tani ina ma tare muka mutu." Ta furta tare da sakin razanannen kukan da sai da ta toshe kunninta. "Hajiya, ki barta ta zauna a nan tunda ita shashasha ce ba ta san rayuwa a cikin daula ba. Ana miki tayin shiga cikin aljannar duniya kina wani zancen ƙauye wai shi Damagaran. Kawai tun da bata da rabo a duniya a kai ta b.q sai ta zauna a can." Cikin takaici ta rarumi karfe ta yi gurinshi zata kwaɗa masa."Ba ka san wace ce ni ba a ƙauye ko? Na yi faɗa da mutane masu ƙiba duk ba su samu nasara ba, ballantana kai kana ji da siranta kamar tsinke. Wallahi a gidan nan sai na karya maka wuya." Ta ƙarashe maganar, tana nuna alamun karya wuyar da hannunta. "Ke ba ki da tarbiyya jakar ƙauye kawai!" "Don Allah Hassan biye mata za ka yi? Ke Jimmalo zo mu shiga cikin gida." Ta ce tana miƙa mata hannu. "Babu inda za ni, kuma wallahi tun da ka kira ni da jakar ƙauye, zan nuna maka jakanci, domin sai na zame maka kaɗangaren bakin tulu."Sai kuma ta noƙe ganin Mommy ta ƙara miƙa mata hannu. Kallonta ta yi, sai kawai ta girgiza kai ta shiga cikin gida. Tunanin yadda za ta yi ta gyara ta take yi. "Yarinyar nan ta ƙi shigowa tana waje sai ɗurawa Hassan zagi take yi." "Please ki ƙyamar ta dole ta shigo. Yunwa da dare zai sanyata dole." "Yanzu ya ya za mu yi da ita?" "Shine nake ta tunani. Dole na kaita makaranta boko da islamiya, sai na sanya Umma ta rinƙa koya mata." "Aikuwa ka haɗa umma da aiki yarinyar nan ba ta da kunya, domin bana tunanin zata yarda." "Ni kaina Hajiya ta haɗa ni da aiki wallahi. Tun da muka je kaina yake ciwo saboda ihu da ta rinƙa yi." Zama sukayi suna tautauna yadda za su gyara ta, musamman yadda za su yi ta fara wanka da sallah. Jimmalo, tana harabar gidan riƙe da kayan Kaka Tani da take ji a yanzu sun fi mata komai mahimmanci. Da sun haɗa ido da Hassan, sai ta yi masa daƙuwa tana murguɗa masa baki. Kallonta kawai ya yi, saboda ya fahimci tafi ƙarfin tunainsa. Shiru suna tunanin za ta shigo, amma har ka kira magrib ba ta shigo ba. A lokacin Hajiya ta yi iyakan ƙoƙarinta, don ta shigo ta kama kanta. Ganin Hajiya bar gidan, sai ta rushe da kuka ta ɗauki ƙullin kayanta tabi motar tana faɗin,"Gidanki zani ba zan zauna a nan ba..." Kafin ta ƙarashe maganar motar ta fice Ajiyar zuciya Hajiya ta saki ta kalli Daddy."Jihadi za ku yi don Allah, ka san yadda za ku yi ta zama mai hankali." Ajiyar zuciya ya saki kawai ba tare da yace komai ba. Hajiya ce take ta yi masa nasiha, da irin alkhairin da yake cikin riƙe maraya. Bayan ya dawo ya ƙara lallabarta, amma ta ƙi shigowa, domin har da tsoro gidan yake bata, saboda a kyawu gidan Hajiya ba komai ba ne. Mommy ganin an kira sallar Isha, kuma bata ci duk abincin da aka ka mata ba, sai ta miƙe ta fita zuwa gurin ta. Kuka take yi tana ta kiran sunan Kaka Tani. "Jimmalo tashi mu shiga ciki gobe xan kai ki ƙauyenku." Jin abin da ta ce su ta kalle ta da sauri. "Da gaske nake yi tun da bakya son zama damu." "Eh, na fi son na yi rayuwa a ƙauye bana son rayuwar birni." "Shikenan, ki shiga ciki ki yi wanka da sallah, sannan ki ci abinci zan mayar dake gobe." "Zan dai ci abinci na yi dakatsami, amma ba zan yi wanka ba, sannan sallah sai gobe zan yi da safe saboda a gaji." Galala ta yi tana kallonta, cikin tsananin mamakin abin da ta ce, amma da ta tuna rarrashinta take yi dai ta ce,"Ok, mu shiga ciki to." Ƙullin kayanta ta ɗauka tare da maƙe su a hamma. A tsanake take tafiya tana kallon gidan sama mai kyau. Mamaki sosai take yi irin kyau da tsarin gida. Ba ta ƙara tsoratar da tabbatar da cin kai suke yi ba, sai da ta shiga cikin falon. Duk halin da take ciki sai ta saki baki da hanci. "Zo mu je ki shiga cikin ɗakin 'yan'uwanki, ki kwanta kafin gobe." Hajiya ta ce mata tana kallonta ganin yadda take a firgice. Saboda tsananin kyawu da girman, gidan sai ta kasa musa mata, don tana tsoron ta kwana ita kaɗai cikin dare a su kashe ta, domin har ga Allah tunaninta su suka kashe mata Kaka Tani. Nufaisah da Umma, suna zaune a kan makeken gadonsu. Nufaisah ce take yin assignment, sai Ummah da take zaune da wayarta tana kallon TikTok. Ganin sun shiga duk suka mayar da hankalinsu kan Mommy. "Ga 'yar'uwarku nan, za ta kwana gobe zan mayar da ita ƙauye." A yadda ta yi maganar sun ɗauka da gaske ne. Sosai suka ji daɗi duk da cewar ba su da wulaƙanci, amma sam ba sa son ta rayu da su, saboda abin kunya ne a kalle ta a matsayin 'yar'uwarsu. "Ok ga gadona sai mu yi amfani da na wa." "No Mommy, a haɗa ta da Baba mai aiki mana."Umma ta furta tana mata wani irin kallo, saboda tun da ta zagi Captain take jin haushinta. "Kul! Matsayinta ya wuce haka. Ƴar'uwarku ne don haka ke Umma ki koma gadonta." "To," Ta ce da sauri tare da ɗauke filo za ta koma. Nufaisah kallon ta ta yi sai ta kalli Mommy da idanunta yake kanta, don haka ba ta ce komai ba, sai ta ci gaba da assignment ɗinta. Jimmmalo kuwa, ganin wani kallo na ƙaskanci da suke mata sai ta watsa musu nata. Ta so ace za ta iya zama ta gurje bakin duk wacce ta yi mata rashin kunya, domin ko yayansu mai kama da zabiya ba ta jin shakkarsa ballantana su ƙananun ƙwari, amma saboda tana son komawa, sai ta zauna a gefen gadon tana kallon tsaruwar ɗakin. "Jimmalo bari na sanya a kawo miki abinci, amma in kina son ki tafi da wuri sai kin yi wanka da sallah." "Ni fa ba zan yi ba kaina ciwo yake mini." Ta ce tare da kwanciya tana shaƙar ƙamshin dauɗar jikinta. Wani irin kallo suka watsa mata, har da auta da ya shigo lokacin. Sai kauda fuska suke yi, saboda tun da ta shigo ɗakin ya canza. Fita Mommy ta yi, tana tunanin yadda za ta shawo kanta ta zauna. Lafiyayyen tuwon shinkafa da miyan agushi, sai farfesun nama Baba ta kawo mata. Duk daɗin da abincin ya yi bai ɗauki hankalin Jimmalo ba, domin ta ƙosa gobe ta yi ta koma Damagaran. Sosai suke kallonta, ganin duk halin da take ciki sai data share malmala biyar. Mugun kallo ta watsa musu ganin yadda suke mata kallon raini. Miƙa ta yi sai ta miƙe kan gadon ba tare data wanke hannunta ba, ballantana su yi tunanin ta ɗauke kwanon. "Anty Nufaisah, She is dirty girl. Ta ci abinci ba ta ɗauke kwanon ba, kuma ba ta wanke hannun ba. All her body is looking dirty." "Kai xagina kake yi? Don wallahi ina yi maka ƙubula ɗaya sai ka sume!" Ta daka matsa tsawar tana faɗin haka. Tsoro ta ba shi da sauri ya matsa gurin Umma. "Cewa na yi ki ɗauke kwanon da kika ci abinci sannan ki yi brush ki wanke baki, saboda Malaminmu ya ce in har ba ka yi brush ba, ka kwanta abincin zai rufe ya sanya maka ciwon haƙori, sannan kwanuka da kika ci abinci ki ɗauki saboda ƙananan ƙwari za su iya zuwa." "Rufe mini baki bana wanke baki, amma har yau ban taɓa ciwon haƙori ba, ka kalli haƙorana ka san ba ni da ciwon haƙori." Ta ƙarashe maganar tare da wage musu baki haƙoranta suka bayyana. Da sauri suka kauda fuskarsu, saboda ganin yadda haƙoran suka yi babu kyan gani, domin za su iya rantsuwar da abincin da ya maƙale tun na shekaru. Komawa ta yi ta kwanta tana harararsa. Ta so ace za ta iya zama ta gyara musu zama, saboda tsaf sai ta yi maganin tsaftansu. Jin abin da tace su suka daina mamakinta. Satan kallon ta suke yi. Wani irin gyatsa ta saki mai ƙarfi har sai da suka jiyu. A maimakon ta yi hamdala sai ta shafa cikinta ya ce,"Kwanta naman kaza da tuwon birni." Sosai suke mamakin rayuwar da take yi. Ba su cika da mamaki ba sai da suka ji tana jan rago, domin har da gayya take yi, don su ga cewar ba za su iya ba su mayar da ita. Munshari da take yi ya ƙara ƙular dasu, har suka fara tunanin dole su yi wa Mommy boren ba za su iya kwana da ita a ɗaki ɗaya ba. Ba su yi shirin kwanciya ba sai ƙarfe sha ɗaya. Bayan sun gama abin da za su yi, sannan suka ɗauro alwala. Sai da kowa ya yi tilawar hadda, sannan suka canza kayan bacci suka kwanta suna karanto addu'a. To Hajiya Jimmalo a birni ko ya zaman birni zai ci gaba? Ko kuma za ta yi nasarar a mayar da ita Damagaran? Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 17 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* Ba su yi shirin kwanciya ba sai ƙarfe sha ɗaya. Bayan sun gama abin da za su yi, sannan suka ɗauro alwala. Sai da kowa ya yi tilawar hadda, sannan suka canza kayan bacci, suka kwanta suna karanto addu'a. Saboda canjin gurin kwanciya mai daɗi, sai ta yi baccin da ta ci bashi tun rasuwar Kaka Tani. Ba ta tashi ba har sai ƙarfe bakwai. Yaran gidan tun asuba suka tashi suka yi sallah, sannan suka yi karatun hadda. Bayan sun gama suka yi na boko, har suka gama suka kwanta, Jimmalo tana sharan bacci. Mommy ta ninyar tashinta, amma tsoron rikicin ta ya sanya ta ƙyale ta, domin ta san ko ta tashi ba sallar za ta yi ba. Ƙarfe bakwai ta buɗe idanunta, saboda alarm da Auta ya kunna ya ɗora mata kusa da kunni. Da sauri ta buɗe idanunta tana zare idanu. Babu salati ta zabga miƙa tana hamma. Ba tare da ta kulle bakin ba, sai ta miƙe tana zare ido tuna inda take. Falo ta fito kai tsaye ba tare da ta yi sallah ba. Ganin babu kowa a falon, sai tibi da aka sanya karatun Alqur'ani suratul Tauba ƙira'ar Mishawi. Jin motsi a kicin sai ta nufi kicin ɗin tana zare ido, tamkar makauniyar da ta warke daga makanta. Mommy tana tsaye da Asibi mai aiki suna ƙoƙarin dama kunun gyada. Babu sallama sai dai suka ganta a tsaye tana soshe-soshe. Asibi har ta tsorata ta dafe ƙirjinta. "Haba jimmmalo kyayi sallama kin ga kin tsorata ta." Mommy ta furta tana kallon ta. "Gari ya waye ki mayar da ni Damagaran." Ta furta a maimakon ta ba ta amsa. Mommy gabanta ne ya faɗi tuna alƙawarin da ta yi mata, domin ta ɗauka da gaske take yi. "Zan mayar dake amma ki je ki yi sallah, sannan ki yi brush da wanka. Na sanya Umma, ta haɗa miki kayanta, kafin a siyo mi.." "Ni fa ba zan zauna ku cinye ni, kamar yadda kuka cinye Kakata ba, saboda aradu wannan dukiyar da kuke da shi mutane kuke cinye wa." Murmushi Mommy ta yi, ganin yadda ta haƙiƙance kan gaskiyar maganarta."Ki je ki yi sallah lokaci yana wucewa." Ta furta mata daɗan tsawa. Amma ko gezau ba ta yi ba ta ce,"A matar dani Damagaran don ba zan zauna anan ba." "Shikenan, zan mayar da ke, amma yanzu ma sai kin yi wanka kin canza kaya." Har ta buɗe baki za ta musu sai kuma ta juya tana gungunan. "Hajiya, kamar zaginki take yi fa? Wannan yarinyar an yi mahaukaciyar ƙazama." "Ya xan yi haka nan zan daure na canzata. Wallahi tun jiya da ta zo kaina ya fara ciwo, saboda ban san ta inda zan fara ba." "Gaskiya ga shi ba ta da kunya kallon mutane take a tsaye." "Hmmmmh! Hajiya ta haɗa ni da aiki." "Babba ma kuwa, saboda wannan yarinyar canzata matsala ne." Asibi ta furta tana juya kunun gyadar a wuta. Mommy cikin ɗaki ta koma don ta ci gaba da karatun da take yi. Xuciyarta cunkushe da tunanin ta inda za ta fara. A maimakon ta yi wankan sai ta yi daka tsami. Ta lafka mai ɗaya daga cikin kayan Kaka Tani riga da zani ta ɗaura. Sai kawai ta fashe da kuka ta rungume sauran kayan."Kaka Tani mai ya sa kika mutu kika barni?" Ta yi tambayar tana kuka. Falo ta fito tana jin a zuciyarta dole su mayar da ita Damagaran, saboda zaman gidan shine zai ɗebe mata kewa ta ga kamar za ta dawo. A lokacin da ta fito fili duk suna kan dinning. Daddy ne yake saukowa daga bene hanunnsa riƙe da carbi. Ganinta sai suka zuba mata ido cikin mamaki. Da fari sun ɗauka ko mutuwar ya haukata ta, ganin shigar da ta yi, amma sai da ta ƙaraso ta kallo Mommy ta ce,"Na shirya a mayar da ni." Umma, Auta da Nufaisah suka kwashe da dariya. "Mommy, wannan wane irin kaya ta sanya?" Cewar Umma tana nuna ta. "Ita kanta Mommy daurewa ta yi, saboda dariyar da take son cin ƙarfinta." "Jimmalo, lafiyarki kuwa? Da gaske kike za ki rinƙa sanya wannan kayan?" Daddy ya yi mata tambayar cikin takaici. "Kayan Kaka Tani ne, wanda su kawai suka rage mini na ke gani na ke jin daɗi. Daga yanzu su zan rinƙa sanyawa har ƙarshen rayuwata." "Hakan ba zai faru ba, saboda mahaukaciya za a mayar dake, duk inda kike je da kayan nan dariya za a yi miki." "A yi mini dariya, na fasa bakin mutane don ba ni da wasu kayan sai su." Ta ba wa Mommy amsa tana zare ido. "Ba zai yiwu ki rinƙa sanya Waɗannan kayan ba, saboda za ki shiga makarantar boko da islamiya, kuma dole uniform za ki rinƙa sawa." "Ni fa ba zan zauna da ku ba, dole a mayar da ni Damagaran." Ta furta tare da sakin ihu, ganin kamar wayo suke son yi mata. "Za a mayar dake ki zo ki ci abinci."Mommy ta furta tana toshe kunninta. "Ki dai na mata ƙarya Karimah, dole a gaya mata gaskiya, a yanzu ba ki da 'yan'uwan da suka wuce mu, kuma a nan za ki zauna tare da mu, don haka ki fuskanci rayuwar da za ki yi gaba. Kakarki ta mutu kuma duk wanda ya mutu ba zai dawo ba." "Wayyo Allah! Ni ba zan zauna da ku ba. Amayar da ni ƙauye ku ba zan yi rayuwa da ku ba." Ta furta tare da fashewa da kuka. Gabakiɗaya sai suka zuba mata idanu suna kallonta. Ganin ba za ta daina kukan ba, sai Daddy ya miƙe ya tsaya a gurinta. Damuwa ce sosai a fuskarsa, saboda gabakiɗaya ta hana su karyawa ta daɗi, sai kallonta suke yi cikin takaici, musamman Mommy da take ji kamar ta rufe ta da duka. "Ya za mu yi da ita? Gaskiya kukanta yana damuna?" Cewar Mommy tana kallon Daddy. "Ita ba yarinya ba ce dole ta zauna. Yanzu ina gama zan je makarantar su Umma na yi mata rigistration da kuma na islamiya har da hadda, dole in ta ga babu sauƙi ta haƙura." "Za ta iya guduwa daga makaranta." "Direba zai rinka kaisu kuma zan gargadi malaman." Ya ba ta amsa kamar ya ƙosa da maganar. Jimmalo ganin sun shareta suna karyawa, sai ta ɗora hannu akanta ta ƙara fashewa da kuka ta yi ƙofar gida. "Wayyo Allah! A mayar da ni Damagaran ba zan zauna a birni ba. Kaka Tani ki taso daga ƙabari ki tafi da ni." Kalaman da take furtawa kenan, cikin muryar kuka har ta isa bakin get. Zama ta yi ta ɗora hannu tana ihu. Sun kasa cewa komai suka raka ta da idanu har ta fice. Mommy ce ta leƙa ta hange ta a bakin get tana ta ihu. Dai ta dawo ta zauna xuciyarta na tafasa kamar ruwan zafin da yake cikin kwatami ana shirin saukewa mai jego. Aliyu Captain Aliyu a ranar da suka baro England za su dawo Nigeria, sai ya ji kewar gida ya kama shi. Ya so ya wuto, amma kan dole sai da suka je Barrack don sai da suka yi aiki. Kwana biyu ya yi, ya shirya zuwa Kaduna. Kasancewar da sassafe ya shirya, domin akwai ɗaurin auren da yake son zuwa, bayan haka yana son ya yi bacci kafin lokacin. Don haka ya yi wa Kaduna shigowar safiya. A lokacin da ya fara hon, cikin mamaki Mommy da Daddy suka kalli juna. "Kamar hon ɗin Ya Captain?" Cewar Nufaisah tare da miƙewa za ta leƙa. "Ba kama bace shi ne, saboda mun yi waya da shi jiya. Ya sanar da ni da zarar sun gama aiki zai zo gida, kuma akwai ɗaurin auren abokinshi." Cewar Daddy. Gaban Mommy ne ya faɗi, domin ba su san yadda za su kwashe da Jimmmalo ba, amma za ta san yadda za ta yi masa magana kar ya shiga sabgarta. Murna suka fara yi daidai lokacin da motar ta shigo ciki. "Wallahi Mommy Ya Captain ne." Auta ya furta tare da rugawa waje. Aliyu Gwarzo zaki. Ya fito cikin shiga ta alfarma. Yana sanye cikin dakakkiyar shadda gizna. An yi masa ɗinkin mai kyau riga da wando waɗanda suka ɗan kama shi kaɗan. Takalminsa agogonsa da kalar gold. Sai bakin glass da ya sanya wanda ya ƙara masa kyawu. Kasancewar sababbin kaya ne bai taɓa sanya su ba, sai yake ganin sun fi kowanne kayansa yi masa kyau, har da kakin da in ya sanya yake ji da tamkar wani sarki. Wani irin turare mai sanyin ƙamshi da daɗi ya fesa wanda ya cika motar nashi. Dama kun san mutumin da son ƙamshi, domin zai iya kashe ko nawa ne ya siya. Jinsa yake yana ɗaya daga cikin jerin mazan da suka amsa sunansu, saboda kwalliyar da ya yi yana ji da za a je gasar kyawu na maza, tabbas sai ya karɓo kambun. Shi kansa ya yi wa kansa kyawu domin jefe-jefi yake kallon kansa ta maganin motar har ya ƙaraso Zariya. Shi kansa yana ganin ya yi kyawu, ballantana ga 'yan matan da suke son namiji ɗan kwalisa kuma mai tashe da ƙuruciya da kuɗi da nera. Ya san cewa yau sai ya kasa hankalin ƙawayen amarya, don haka ya gama tsarawa ana ɗaura auren zai dawo gida, domin ba shi da lokacinsu. Jira yake kamar yadda yake classical ya samu wacce za su yi compatible. Nishadi sosai yake ji, sakamakon bikin abokinsa da zai halatta. Zuciyarsa ta fara kwaɗaita masa ya kamata ya yi aure, ganin duk abokanansa suna yi, sannan ya rabu da Lubaynah da ta zamar masa ƙarfen kafa. Lokaci ya yi da zo samu mace ta ƙwarai, wacce namiji bai taɓa riƙe mata hannu ba. Ya aura sannan ya killace ta a gidansa, su yi rayuwar aure su cikin so da ƙauna. Buɗe motar ya yi yana ji da kansa da isa. Wayarsa ya ɗauki da jakarsa daidai lokacin da ƙanninsa suka rugo cikin tsananin farinciki. Sai dai me, ya buɗe baki zai yi magana sai ya fasa, sakamakon kukan da ya ji mai kama da ma gardi. Da sauri ya waiwaya inda yake jin kukan cikin ɓacin rai. Kallonta ya yi cikin tsananin mamaki domin a tunaninsa ko fatalwa ce. Ko kaɗan bai yi tunanin ganinta a cikin gidan ba, domin tuni ya shafe babinta ta, tun ranar da Hajiya ta gaya mishi sun yi rabuwar rashin mutunci. Ko da suka yi waya da Hajiya ba ta gaya masa tana gidan ba. "Wancan mahaukaciyar 'yar iskan fa?" Ya yi wa Nufaisah tambayar cikin tsananin tashin hankali. "Ta dawo nan da zama Ya Capta.." "What?!" Ya furta tare da cire gilashin idanunsa. Kafin ta ba shi amsa cikin tsoro ganin rikicewar da ya yi, sai ya ji muryar Daddy yana faɗin,"Eh, Jimmalo ta dawo gidan nan da zama saboda kakarta ta mutu." "Kuma Daddy, sai a rasa wanda zai ɗauki wannan mahaukaciyar sai mu? Wannan abin kunya ne tana rayuwa a gidan nan." "Hajiya ta yi mini umurni da na kawo ta gida nan, kuma marainiya ce ba ta..." "There's no way! Wannan mahaukaciyar za ta zauna a gidan nan." Ya furta yana harararta daidai lokacin da ta ƙara buɗe baki ta rushe da kuka. "Ita kanta ba ta son zama da mu. Kaddara ce ta sanya ta shigowa cikinmu, kamar yadda ba mu da abin da za mu yi da ya wuce mu rayu da..." "No daddy, na yi alƙawarin zan ba da ko nawa a kaita wani gida can. Ko gidan marayu ne, saboda ba zan iya zama da ita ba na tsane ta bana son ganinta, in har kuka sanya ta zauna a gidan nan zan iya kashe.." "Kul! Karna ƙara ji. Karka ƙara maganar kisa saboda ba ta da gurin zama sai nan gidan, don haka ya zama dole ka sanya wa ranka haƙuri, ka ɗauketa a matsayin da ka bawa su Umma." " I can't babu yadda za a yi, na haɗa matsayin masu hankali da mahakauci guri ɗaya." Ya furta cikin ɓacin rai tare da ɗaukar jakarsa, ya nufi cikin ɗakinsa a maimakon falon iyayensa. Kallonsa suka yi cikin damuwa, ganin yadda yake huci kamar mesa. "Saboda Aliyu na ji tsoro sosai da Hajiya ta ce anan za ta yi rayuwa, na san cewa dole za a samu matsala. Ya kamata ka fahimtar da Hajiya Jimmalo ta koma gidanta, saboda bana son a samu matsala ya karya musu yarinya watarana." "Hajiya ita ma gudu ta take yi ba zata iya da ita ba. Ni kaina yarinyar nan tun da ta dawo gidan nan nake cikin damuwa. Dole zan yi magana da shi, sannan na san yadda zan yi ya ɗauke ta a matsayin ƙanwa. Zaman Jimmalo a gidan nan babu fashi." Jin abin da Daddy ya ce sai ta kalle shi tana girgiza kanta. "Da kamar wuya hakan, saboda ka san yadda Aliyu yake in ya tsani abu." Shiru suka yi suna kallonta da take ta ƙara sautin kukanta. Jimmalo ganinsa sai ta zare idanunta. Duk da cewar ta tsorata, amma sai ta yi maza ta shanye tsoranta. Ganinsa sai ta ji daɗi sosai, domin dama ce ta samu da zata koma ƙauye, don haka ta ƙara sautin kukanta cikin zallar taɓara. Captain kuwa cikin tsananin ɓacin rai ya shige cikin sashinsa. Buɗe falonsa ya yi ya shiga, sannan ya fara safa da marwa bayan ya ije jakarsa. "Impossible! Ba zai taɓa yiwu ba yarinyar da na tsana ta zauna a gidan iyayena." Ya furta tare da dunƙule hannunsa ya naushi isa, sai kuma ya tsaya cak cikin tsananin ɓacin rai. Lokaci guda ya nemi farincikin da ya zo da shi ya rasa. Turare ya ɗauka ya ƙara feshe jikinsa dashi, domin ganinta ya sanya shi har ya fara jin warin jikinta. Ruwan faro ya ɗauka ya buɗe zai sha, sai kuma ya fasa ya yi jifa da gorar. Jakarsa ya laluba don ya ɗauki sigari, amma sai ya tuna inda yake. Da sauri ya mayar da zif ɗin jakar tare da wirgi da ita, tuna ko ya zo da ita bai isa ya sha ba. "Ba zan taɓa zama da ita ba dole za ta bar gidan nan." Ya ce tare da kwanciya kan gadonsa yana mayar da numfashi. Da sauri ya daga labulen jin ta ƙara tsandara ihu. Cikin fusata ya buɗe kofar ya fice. Saboda muguntar har sauri yake yi, don ya isa ya yi ball da ita. Daidai lokacin da ya ƙarasa, Daddy ya fito kamar ya san za a rina."Aliyu!" Ya daka matsa tsawa da sauri yana zare ido. Cikin takaici ya fasa haurin ta da ya yi ninya. Kallonta ya yi cikin tsananin ƙyama musamman kayan da yake jikinta. "Karka ƙara gigin kai mata duka, saboda in har ka ƙara zan ɓata maka rai." Daddy ya ce cikin fushi daidai lokacin da ya ƙaraso. "Daddy this girl is stupid! Doguwar tafiya na yi, amma ta zo saitin windona tana kuka." "Jimmalo, rashin kakarta ta yi wacce take komai a gurinta, baya haka akai tata wani guri ta yi rayuwa. Dole sai mun yi haƙuri kafin ta saba da mu." "No I cant tolerant her nonsense. It either to keep quiet ko na yi mata shegen duka." Ya faɗa cikin zafin rai yana hararta. "Koma dakinka I will talk to her." Watsa mata harara ya yi, sannan ya juya tamkar kububuwa. To Captain Aliyu da Jimmmalo a inuwa ɗaya. Ko ya ya zamansu zai kasance? Ku ci gaba da bibiyar littafin ƙiyayyar jini. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 18 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* Aliyu Ya ce "No I cant tolerant her nonsense. It either to keep quiet ko na yi mata shegen duka." Ya faɗa cikin zafin rai yana hararta. "Koma ɗakin ka I will talk to her." Watsa mata harara ya yi, sannan ya juya tamkar kububuwa ya shige cikin ɗaƙinsa. Wayarsa ya ɗauka da makullin mota ya fice daga gidan, domin ya gwammace ya tafi bikin da ya zauna. "Jimmalo,ki taso don duk abin da zaki yi ba za ki koma ƙauye ba. Yau zan je na yi miki rigistar makaranta. Ya zama dole ki sami jikinki, saboda ke da ƙauye har bada." Jin abin da ya ce sai ta ƙara sautin kukanta. Zuwan Aliyu ya sanya ta miƙe, ta nufi cikin gidan, tun da ya zo sai ta ji sanyi, domin ta san cewa abu ɗaya za ta Saboda ganinta da ya yi, sai bikin bai yi masa armashi ba, domin ko da ya je duk ransa a ɓace yake har sai da abokanansa suka gane. Adil ya zauna kusa da shi bayan an ɗaura auren, domin daga gurin ɗaurin auren walima suka wuce. Ya san cewa Captain ba ya cin abinci a gurin biki sai drinks, amma yau ko drinks ɗin ya kasa sha, sai juya ruwan faro yake yi yana tunanin yadda zai ɓullowa Daddy Jimmalo ta bar gidan, saboda da ya tuna ta sai ya ji ransa ya ɓaci sosai. "Ya ne Captain? " Ya furta daidai lokacin da ya zauna kusa da shi. Tsaki ya yi ya ce,"Am good." "No, you seems moody, don ko a gurin ɗaurin auren sam ba ka walwala." Ya ce masa yana kallonsa. "Am ok." Jin ya faɗi haka sai ya yi dariya ya ce,"Kai ne ka ƙi aure Captain. At this age na ka You need a wife da za ta rinƙa kore maka damuwarka. Yarana biyu, amma up to now you are steal single." Ƙaramin tsaki ya ja, ba tare daya ce masa komai ba, domin gabakiɗaya ba ya jin daɗi. Ganin haka sai ya tashi ya zuwa wani gurin. Captain ya daɗe a zaune yana tsaƙawa da warwara. Daga ƙarshe ya yanke shawarar in har ba su mayar da ita ba, zai koma Abuja kuma ba zai ƙara zuwa ba. Bai dawo gidan ba, sai dare ko da ya dawo babu wanda ya nema ya ci abincin da ya yi oder a yatsine ya kwanta, saboda komai na gidan ƙyama yake ba shi. Ya daɗe bacci bai kwashe shi ba har zuwa karfe biyu na dare. Daddy da Mommy sun yi tunanin fushin da ya yi wasa ne, amma ganin ya dawo bai neme su sai hankalinsu ya tashi, musamman da ya sanar musu in har yana nan sai ya shigo an yi addu'a, sannan ya yi musu sallama ya kwanta. Mommy ta kalli Daddy da yake aiki a Laptop ɗinsa."Yaron nan ya yi fushi sosai haka za mu barshi? Ga duk abincin da aka yi masa bai ci ba." Waiwayo wa ya yi ya kalle ta ganin yadda ta nuna damuwarta sosai. Ganin haka ya kashe laptop ɗin ya zauna kusa da ita. "Kar ki damu zai haƙura dole ya sauko. A yanzu Jimmalo ba ta da waɗanda suka fimu. Ina tausayinta sosai ina son na ba ta kyakyawar rayuwar da watarana za ta yi alfahari damu." "Shikenan, na damu ne ganin yadda ya ɗauki fushi." "Mune iyeyensa dole ya sauko ya bamu haƙuri." "Ba matsala Allah ya bamu ikon canza rayuwarta." Ta furta tare da kwanciya. "Amin," Ya ce sannan ya bi bayanta ya kwanta. Jimmalo, kamar yadda ta sanya sai tayi abin da zai mayar da ita gida. Tun safe tana tashi sai ta nufi daidai windonsa ta zauna. Captain da bai samu bacci da wuri ba sa da ya dawo sallar asuba, sannnan wani irin bacci mai daɗin gaske ya kama shi, domin har ya ɗauki wayarsa ya kunna Qur'an yana karantawa, sai bacci ya ɗauke shi waya ta faɗi kan kirjinsa. Kamar a mafarki ya ji an tsanadara ihu tare da cigaba da kuka. Da sauri ya buɗe idanunsa lokaci guda kansa ya sara. Fitowa ya yi daga gadon,cikin zafin mama ya ɗauki bel ɗin wandonsa. Jimmalo da take kuka tana faɗin,"A mayar da ni Damagaran, banzan zauna a birni..." Ta kasa ƙarashe maganar sakamakon dukan da ta ji ya rufe ta dashi. Wani irin ihu ta saki, kawai sai ta yi kuka kura ta yi kansa ta cakume shi. Ganin abin da ta yi ya sanya ƙafarsa babu imani ya tokari bakinta ya fashe jini yana zuba. Ganin abin da ya yi mata ta ƙara kukan kura ta yi kansa. Idanunsa ya rufe, ya fara dukansa kamar yana dukan ɓarawo. Maigadi ya ji kukanta da sauri ya fito yana salati tare da kurma ihu yana faɗin,"Jama'a ku fito za a yi kisa." Mommy da take kicin tana girki, Daddy kuma yana falo yana karatu, suka ji muryar da kukanta sama-sama. Labule ya ɗaga daidai lokacin da Mommy ta fito a sukwane tana faɗin,"Na shiga uku Aliyu zai yi kisa." Da gudu ya bi ta zuwa waje ransa a ɓaci. Yana zuwa ya wanka masa mari, wanda ya sanya ya yi mutuwar tsaye, saboda zai iya cewa tun da ya girma bai taɓa dukansa ba. "Ka wane irin mahaukaci ne kashe ta za ka yi?" Ya yi masa tambayar yana kallon sa, sai ya juya gurin Jimmalo da bakinta ke zubar da jini sosai tana ihu, amma idanunta ba hawaye. "Na rantse sai na kashe shi tun da ya buge ni, saboda an ga Kakata ta mutu shine za a kashe ni. Wayyo Kaka Tani ki dawo duniya ki ga ni ana cutar dani babu mai rama mini. Kaka Tani don Allah ki zo ki rama mini duka da ya yi mini." Ta ƙarashe maganar tare da ka tsalle ta faɗi ƙasa tana birgima. Ganin haka duk sai jikinsu ya yi sanyi. Daddy ya kalle sa da yake huci kamar mesa ya ce,"Aliyu in har ka ƙara ɗora hannunka a jikinta ban yafe maka ba." Ya ƙarashe maganar da muryar da ya bayyana "Wacce irin mahaukaciya ce za ki zo daidai windona tana mini kuka, amma ba ka gani ba Daddy ka mare ni?" "You need to settle with her she is you sis..." "Never!"Ya ce tare da ɗaga hannunsa jin abin da ya ce, ganin Daddy ya yi shiru sai ya ɗora da cewa,"Never wannan gidahumar ta zama sister na. In har yarinyar nan za ta ci gaba da zama a nan, ba zan ƙara zuwa Kaduna ba." Yana ƙarashe faɗin haka, ya wuce cikin ɗakinsa, ba tare da ya damu da kiran da suke masa ba. "Ka gani ko? Dama na san haka zai faru, babu yadda za a yi su yi rayuwa under roof ɗaya." "Ya zama dole su yi I know what I will do." Daddy ya ce tare da juyawa ya shiga cikin falo. Hannunta Mommy ta kama cikin takaici da take kuka miyau da jini duk ya haɗe. Kallonta ta yi sai taji tamkar za ta yi amai. "Please Jimmalo, wannan abin da kike yi don Allah ki daina. Kin wuce yin haka duba ki ga yada kika yi ƙazanta?" "Ni dai a mayar da ni Damagaran, na tsani kowa a gidan nan." Ta furta ba tare da shayin komai ba. "Ok, shiga ciki ki wanke bakinki yanzu driver zai mayar da ke." Ta faɗi hakan ba tare da yanke shawarar ba. "Ƙarya kike yi haka jiya haka kika ce mini, don haka sai kin rantse." Jin abin da ta faɗa sai mamaki sosai ya kamata. Ganin duk girmanta ta tsare ta sai ta rantse. "Let's go in Jimmalo." Ta kama hannunta da ƙarfi suka shiga ciki. Daddy da yake safa da marwa ciki tsananin damuwa a falo. Ganin sun shiga cikin sai ya wuce sashin Aliyu, wanda ya gama haɗa kayansa yana shirin fita. "Aliyu." Ya ji muryar Daddy ya kira sunansa. Cikin fushi ya jiyo zuciyarsa har tafarfasa yake yi. "Aliyu you are no going anywhere and dole ka ɗauki Jimmalo a matsayin ƙanwarka, don haka ka ake jakarka yanzu ka kaita makarantar su Umma ayi..." Kallon da ya yi masa sai ya kasa ƙarashe maganar, domin dama ƙarfin hali ya ke yi, amma kuma ya zama dole ya san yada zai yi ya haƙura da tafiya. "Ni na ɗauki wancan kucakar a mota ta? Over my dead body!" Ya ce tare da zagaye kansa da yatsu biyu ya murɗa shi. "Dole za ka ɗauke ta, a matsayina na mahaifinka na yi maka umurnin haka." Ya ce yana kallon sa cikin ɓacin rai. Lokaci guda ya yi dana-sanin zuwa Kaduna, domin abin da ya gani ya gwammace bai zo bikin ba. Idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, saboda tsananin tashin hankali. Tunani yake ya za a yi ya sanya ta a cikin motarsa, har ya shaƙi numfashi da wannan bordy odour da take da shi. "Am sorry daddy, I can take her to the school you can send your driver, saboda kafin na ƙarasa na tabbatar na amayar da kayan cikina." "You must go and it is an oder." Daddy ya ce tare da juyawa zai fita. Ganin haka ya tari gabansa cikin tashin hankali."Daddy, you are going to waist your money, saboda wannan mahaukaciyar nan, da ko alphabets I don't think she can read." "Ko da ace ba ta iya ba dole zan saka ta, saboda babu yadda za a yi na zauna da ita ba ta zuwa makaranta, alhalin nawa yaran suna zuwa. Taimakonta zan yi ka san yadda taimakon maraya yake, don haka ina maka kwaɗayin samun wannan lada. "Then You can go ahead, amma am not going anywhere." "You must go bari na ke na yi mata magana ta yi wanka." Ya furta cikin muryar da yake gasganta masa da umurni ya ba shi. Yana fita ya kaiwa iska naushi, tare da zama cikin ɓacin rai."Mai ya sanya na zo Kaduna? Da na san wannan mahakauciyar na nan, babu abin da zai sanya na zo, saboda na tsane ta sosai." Ya furta cikin takaici. Tun da Daddy ya ce dole sa ya je, ya san cewa ba shi da mafita, abu ɗaya ya sani yana dawowa zai koma Abuja. Ɗaukar turare ya yi, wanda zai rinka fesawa a motar duk bayan minti, kuma ya rantse ba dai a motarsa zai kai ta ba. Haka ya zauna cikin takaici kamar zai fashe da kuka. Daddy da ya shiga ciki kai tsaye ɗakin su Umma ya wuce, ya samo Mommy tana zuba mata ruwa tana wanke jinin da yake zuba. "Allah sai ya saka mini mugu azzalimi mai kama da zabiya wa..." "Ke Jimmalo, wa ya gaya miki ana zagin babba? Ɗan'uwanki ne don haka karki ƙara zaginsa daga yau ya Aliyu za....." "Da na kira shi da Yaya gara bakina ya sari kashi. Shi ba Yayana bane, kuma zan ci gaba da zaginsa inhar zai cigaba da mini mugunta. Ni ma soja zan zama na sanya bindiga na harbe shi, bayan na rama zalincin da yake mini." Ta ƙarashe maganar cikin zallar rashin kunya. Mommy kasa ce mata komai ta yi ganin yadda take maganar. Sai kuma ta fashe da kuka."Kaka Tani ki taso ki ga azzalimi nan ya ƙara dukana. Ko yi masa fatalwa ki mayar da shi musaki." Daddy ne ya yi gyara murya, wanda duk ba su san ya shigo ba. Mommy ta kalle shi tare da sakin ajiyar zuciya da ƙarfi. "Ko sanya ta, ta yi wanka Aliyu zai kai ta a sanya ta boko da islamiya, sai daga nan ya kai su Umma." Kallonsa suka yi a tare, Jimmalo jin za a sanyata makaranta, ya sanya ta yi masa banzan kallo. Mommy kuwa jin Aliyu zai kaita. "Aliyu, ne zai kaita makarantar?" Ta yi masa tambayar cikin razana. "Makaranta? Aradu babu makarantar da zani har da makarantar arna!" Jimmalo tace tana jijjiga. Takaici ya sanya Daddy kasa amsa mata, sai ya kalli Mommy ya ce,"Eh, kuma na yi magana da shi." "Kar ya je ya kashe yar mutane?" Ta ce a razane. "Ba zai fara ba, tun da yana da ilmi ya san hukuncin wanda yayi kisa." "To in ya cutar da ita fa? Kasan Jimmalo, ba kunya ne da ita ba, dole tayi masa abin da zai harzuƙe shi, sannnan shi kuma bai haƙuri." "Zan haɗa shi da su Nufaisah, kuma baya haka ya zama dole na kawo sasanci a tsakaninsu. Ban san lokacin da zan mutu ba, kin ga duk ranar da na kwanta dama Aliyu shi zai zama uba a gidan nan, in har basa shiri ba zai kula da rayuwarta ba." "Hmmmmh!" Tace don sam shawarar bai yi mata ba. "Ki sanya ta ta yi wanka ta canza kayan jikinta, sannan ta fito bari na yi wa su Nufaisah magana na ga suna falon sama." Ya yi saurin fita kafin ta gaya masa ba za ta iya ba, domin abin da ya karanta a idanunta kenan. Mommy kallon Jimmalo ta yi sai ta kasa cewa komai. "Ki bar kallona, saboda ko sama da ƙasa za ta haɗe ba xan yi wankan nan ba, sannan a mayar da ni Damagaran." Dubara ce ta faɗo wa Mommy ta ce,"Kin ga kuma in kika yarda kika yi wankan nan, sannan kika bi su aka kai ki makarantar kin samu hanya mafi sauƙi da za ki koma Damagaran, kawai guduwa za ki yi." Ta furta mata hakan, don ta san babu yada za a yi ta samu ta gudu. Shiru ta yi kamar mai tunani sai can ta nisa ta ce,"Amma ba zan yi wanka ba dakatsami...." "Ke da an yi magana kice daka tsami za ki yi. Kin san irin warin da kike yi? Zan gaya miki gaskiya wallahi, in har ba kya wanka Jimmalo mutane gudunki za su rinƙa yi." "To ni ina ruwana dama ni kaɗai nake son na yi rayuwa." Ta furta ba tare da ta damu da warin da ta ce tana yi ba. "Ki yi wankan dai na yau, tun da ana sanya ki a makarantar guduwa za ki yi." Mommy ta ce cikin rashin dubarar abin da za ta ce mata, wanda zai sanya ta wankan in har ta ƙi. "To bari na yi wankan, amma na rantse ba zan zauna a gidan nan ba, wancan mugun mai kama da zabiya yana nan." Tun da Mommy ta ji ta amince, sai ta nufi hanyar fita kawai don ta gaji da rarrashinta. Jimmmalo tsaya ta yi cikin takaici, domin an takurata tun da aka ce ta yi wanka. Ita babu abin da ta tsana kamar wanka. Ta ɗauki tsawon lokaci tana tunanin ta yi ko kar ta yi? Sai kuma ta rarrashi zuciyarta bayan ta ɓata lokaci. Miƙewa ta yi tana gungunai ta shiga cikin bayin. Turus ta yi tana kallon bayin da za ta iya kwana a cikinsa, domin kyawunsa da kyan da ya yi. Saboda jaraba da safe ba ta shiga cikin bayin ba, tana tashi ta fita zuwa kicin. A maimakon ta fito ta kira a nuna mata yadda za ta yi amfani da shi, sai ta yi xamanta ta kunna can ta murɗa can. Mommy cikin damuwa, ta kira Umma ta zaɓar mata doguwar riga da hijabi mai kyau. Jin shiru ba ta fito ba sai ta kwanƙwasa bayin. "Jimmalo, har yanzu wankan kike yi Aliyu yana jiranki ba." Ta yi mata ƙaryar. Buɗe ƙofar ta yi ta tsaya tare da kama murfin."Ni ban san yadda ake kunna famfon ruwa ya zo ba, kuma na fasa wankan saboda gaskiya sanyi nake ji." Mommy ji ta yi kamar ta kife ta da mari. Xuciyarta ce ta harzuƙa domin mace ce mara ɗaukar raini. "Ba sai ki kira a zo a nuna miki ba, amma kin zauna a cikin bayi kamar kina ɗaki?" Tambayar da ta yi ta cikin tsawa sai ta ɓata ranta."A mayar dani Damagaran na yi rayuwa a kusa da ƙabarin Kakata Tani." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka kamar wata yarinya. Mommy watsa mata harara ta yi ji take da ace daga danginta take babu bin da zai hana na ta kai mata hannu ba, amma duk da haka ba ta tunanin zata iya jurewa. "Ki je ki yi wankan ni ma na ƙosa ki tafi saboda zama dake sai mara zuciya." Ta furta tare da yin tsaki ta shiga cikin bayin. Mamaki sosai ya kamata, ganin yadda ta ɓata ƙaton sabulu guda ɗaya a ruwan buta. Ta buɗe baki za ta yi magana sai ta ga tana kallonta tana jan majina. Mommy ji ta yi kamar ta saka kuka saboda har hawaye sun cika idanunta, domin abin da ta yi ko auta ya yi sai ta yi masa shigen duka. Tara mata ruwan ta yi ba tare data kalle ta ba, sai ta ije mata soson wanka za ta fice Zuciyar Jimmalo fes ganin yadda ta tunzurata."A mayar da ni damagaran na yi rayuwa a ƙabarin kaka Tani, saboda ita ce kawai za ta jure halina" "Dama sai ita da ta ɓata tarbiyarki, ni ma na ƙosa ki koma Damagaran, in ba haka ba sai kin sanya mini hawan jini.' mommy ta ƙarashe maganar tare da rufe mata kofar. Ba wani wanka ta yi ba domin datti kawai ta tayar, sannan ta kwara ruwan a jikinta ta fito. Da ace za a murza jikinta babu abin da zai hana zubar ɗauka, domin ita kanta da ta yi wankan ta san ba ta wanki ba. Tana fitowa Nufaisah ta shigo ta kalle ta ta ce,"Mommy, ta ce ga mai da kaya ki sanya." Harararta ta yi ganin haka ta saki tsaki tana mamakin rashin kunyarta. Duk da kyawun kayan ba ta sanya su ba, sai ta ɗauki kayan Kaka Tani ta sanya. "Ni ba zan sanya wannan hijabin ba." Ta ce tare da ɗaukar gyalen Kaka Tani ta yafa. "Wallahi na yi kyau, sosai kayan Kaka Tani ba ƙaramin ɗaukar jikina yake yi ba. Allah sarki Kaka Tani na yi rashin Kakata mai ƙaunata." Ta ce lokaci guda idanunta suka kawo ruwa, domin duk lokacin da ta sanya kayan sai ta ji jikinta ya yi rauni. "Mommy, ta ce ki zo ki tafi." Umma ta ce sai kuma ta tsaya dariya na son kubce mata ganin shigar da ta yi. To Jimmalo za a shiga boko ko ya ya za a yi karatun? Mu je dai zuwa mu ga yadda za ta kaya. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 19 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* "Mommy, ta ce ki zo ki tafi." Umma ta ce sai kuma ta tsaya dariya na son kubce mata ganin shigar da ta yi. "Dallah gani nan zuwa kike kallona kamar ba ki san ni ba." Ta daka mata tsawa, tana watsa mata harara kamar idanunta zai faɗo ƙasa. Da sauri ta koma falo tana dariya."Mommy, kin ga shigar da ta yi kuwa? Yadda kika san wata tsohuwa." "Ni dai kawai ta zo su tafi, na gaji da yarinyar a kwana ɗaya."Mommy ta ce kamar za ta yi kuka. Daddy na saukowa daga sama da nufin ya kira Aliyu, sai ta murɗa ƙofa ta fito. Dariya sosai ta kama su."Jimmalo, don Allah ki daina shigar nan. Ki kawo kayan nan a ƙona, mutane na gaya miki dariya za su rinƙa miki." "Babu wanda zai ƙona mini kaya, kuma ba zan daina sawa ba." Ta ce cikin rashin kunya. Mommy kallonta ta yi, domin ta gwammace da ba ta yi wankan ba, duba ga yadda ta taso da datti. "Don Allah Daddy ku je kawai, wannan kafaffiyar yarinyar ba za ta canza kayan ba." "Ok, Umma da Nufaisah ku taso ku tafi." "Ok," Suka ce tare da fara tafiya. Ganin haka suka bi bayansa, har da Jimmmalo da take ta yanke shawarar yadda za ta gudu ta koma Damagaran. Aliyu na zaune a falonsa yana huci, kamar mesa Daddy ya yi masa sallama ya shigo. Tun lokacin da ya tura masa tsaƙon, ya fito yake jin kamar ya kashe kansa. Jin sallamar Daddy ya sanya shi fitowa yana huci."Je ka kai ƙanwarka makaranta, in ka gama mata rigister ka kai ta islamiyar su Nufaisah." Ganin da su Umma za a je sai ransa ya ɓace sosai, domin ya shirya sai sun fita ya ce ta bar garin, bayan ya wahalar da ita a mota, domin wani irin gudu ya shirya zai yi da ita. "Mu je amma ba zan iya ɗaukar mahakaciyar nan a mota..." Maganar ta maƙale masa ganin shigar da ta yi "Daddy, kana ganin shigar mahaukatan da ta yi? Su kansu masu makarantar ba za su ɗauke ta ba, ganin shigar haukar nan. Wannan yarinyar makarantar mahaukata ya kamata a sanya ta." "Kai ne mahakacin ba ni ba." Ta ce masa cikin gatsali. Ganin yadda ya harzuka sai Daddy ya ce masa,"Don Allah Aliyu ku je na riga na yi magana da mai makarantar. Kuma kar na ji ka kai hannu jikinta, innba haka ba su na yi mummunar saɓa maka." Daddy ya ce cikin ƙosawa. Nufaisah da Ummu suka shiga gaba sai Auta a gaba. Daddy ya nuna wa Jimmalo gefen Umma da take ta addu'ar Allah ya sanya gefen Nufaisah za ta shiga, amma sai ta ga addu'ar ta ba ta karɓu ba, ganin haka ta yi dubarar juya mata baya ta toshe hancinta, domin har yanzu wari take yi. Aliyu kafin su tafi sai da ya ƙarar da kwalbar turare, domin tana shiga ƙamshin motar ya canza. Maigadi ya buɗe masa get ya fara tafiya cikin takaici. Yana fita daga gidan ya kashe motar ya fito. Buɗe gefen da take ya yi, tare da fincikota ya watsa a boot, sannan ya shaƙi numfashi mai daɗi. "Banza ƙazamiya mara kunya. In har zan fita dake sai dai ki rinƙa zama a Boot." Ya ƙarashe maganar tare da rufe boot ɗin da karfi. Mamaki sosai su Umma suka yi, amma sai suka hankalinsa kwance ba tare da tunanin komai ba yake tunkinsa bayan ya ƙara fesa turare, domin wani irin wari take mishi. Jin zata dame shi da buga Boot ɗin ya sanya waƙa har suka isa. Sai da ya mula baya sun gama fitowa kalli Nufaisah."Buɗe mahaukaciyar can." Da sauri ta ƙarasa tun kafin ya gama maganar saboda tausayinta, domin ta ƙara tabbatar da ba shi da imani. Tana buɗe ta ta saka kuka, ta fita da sauri tana sauke numfashi. "Mugu azzalimi sai na rama abin da ka yi mini." Ba tare da ya kalle ta ba ya wuce ofishin Principal. Jimmalo sai ta nemi guduwa, amma babu hanya kan dole ta bi bayan su Umma, tana ɗura masa ashar da jawo masa jifa'i. Umma aji ta wuce da sauri, don kar ƙawayenta su ganta da Jimmmalo. Auta ya shiga na shi ajin. Nufaisah ce ta bi shi zuwa ofishin Principal ɗin. A lokacin da ta fito, kallonta ɗaliban suke yi cikin tsananin mamaki. Ba tare da ta damu da leƙenta da 'yan ajin suke yi ba, ta bi bayan Nufaisah. Captain kuwa tuni ya shige ofishin Principal ɗin"Mahaukaciyar ce innta yi abu duka ake mata sannan take natsuwa. Da zarar ta yi muku hauka ku sanya sajen ya yi mata dukan tsiya. Ya cewa Principal ɗin da yake kallon ta cikin mamaki ganin shigar da ta yi. "Ok bari na gama mata interview sai na san inda zan sanya ta, domin yarinyar ta yi girma kamata ya yi a sanyata a aji uku." "She is illiterate ba ta san komai ba. Ku sanya ta a nursery one." Dariya sosai ya yi jin abin da yace. "Ta yi girma sosai, domin ko primary six aka sanya ta ta girma, amma dole haka nan za mu sanya ta in ya so sai ki ɗaukar mata tuitor a gida." Tsaki ya yi don,' wannan ba shafe shi ba, saboda a gurin shi in ta so ta mutu a jahila. Ganin haka ya juya gurin Jimmalo da take ta raba idanu. "Ke what is your name?" Ya yi mata tambayar yana kallonta. Jin turanci ya yi mata ba ya gane ba, domin inda an tambaye ta bata san yaren da yi yi mata ba. "A mayar dani kauyen damagaran, saboda ba zan yi makarantar arna ba." Ta furta a gatsale tana kallonsa. "I said what is your name? Kina gaya mini makarantar arna. An gaya miki ni arne ne? Musulmi ne ni sunana Muhammad." "Amma ka yi asara kana arne ka sanya sunan Annabinmu." Ta furta cikin takaici tana kallonsa. "Ke! Ni ba arne bane." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. "To amma kake shigar arna?" Ta furta hakan ganin suit ne a jikinsa. Komawa ya yi ya zauna yana huci. Don ya rasa amsar da zai bata. "Ka gani ko? Na gaya maka mahaukaciyar ce. Dole ku dage in ta yi muku haka ku yi mata shegen duka." "Gaskiya na ga alama za mu yi aiki." "Sosai ma kuwa." Ya ce tare da miƙewa domin so yake ya bar Kaduna da zarar ya koma gida. "Za ki iya karanta mini A.B.C da kuma 1.2.3.4?" "Kai ka sansu, don ni ko karatun allo da na iya na sallah na yafe wa kaina, saboda ba zan wahala ba. Haka kawai wani gardi ya duke ni." Mari Aliyu ya kawo mata."Uban waye gardi?" Da sauri ta matsa tana ƙunkunai."Kana ji ko? Ba zan koma da ita ba, saboda zan iya amayar da kayan cikina. A nan zan barta sai ka yi mata tambayoyin, amma da za ka ji shawara ku sanya ta a nursery one" "Shikenan babu matsala, zan yi magana da mahaifinka duk da ya tura mini kuɗin komai, amma gaskiya bayan na makaranta dole a tura mana da wasu kuɗi, domin tana buƙatar proper care. Nanny's ɗin mu za su kula da ita, yau dole ayi mata wanka sannan ayi kitso ta canza ka..." "Wanne me? Na rantse babu wanda ya isa ya taɓa mini jiki, duk wanda ya yi kuskure taɓa ni, sai na ragije masa kai." Ta furta tana ƙoƙarin ficewa. Aliyu ya sanya kafa ya taɗiyeta sannan ya ce,"Good, ku yi duk abin da ya kamata. In kun kasa wanke gashin ku aske kawai." Yana gama faɗin haka ya fice. Ganin haka ta saka kuka za ta bishi."Wayyo ba zan yi karatun arna ba, kuma babu wanda ya isa ya aske mini kai. Ba zan yi wankan ba. Wayyo Kaka Tani ki taso daga ƙabari za a kashe jikarki." Ta saki ihu tana faɗin haka. Principal ɗin fitan Aliyu sai ya yi masa daɗi. Da sauri ya miƙe bayan ya kira nanny guda biyu. "Mene ne sunanki?" "Jimmmalo jikar Tani." Ta furta tana harararsa. "Sunanki na gaskiya nake magana da na mahaifinki." "Sahiya Audi." Ta furta tare da murguɗa baki. "Ok, Safeeya Abdullahi kenan?" "A ɗan dakata kar ka ɓata mini sunana, saboda Sahiya Audi nake, kuma Kaka Tani da Jimmalo take kira na, saboda ta ce ranar sa a aka haife ni. Ranar Juma'a don haka Jimmalo za ka kira ni." "A makaranta dole sunan yanka za a kira ki da shi." "Ni wallahi duk wanda ya kira ni da wani suna ba Jimmalo ba, sai ba gurje bakin mutum da yashi." "To sai ki fara ta kaina mara kunya fitsarrarriya kawai." Ya ce yana harararta Kafin ta yi magana nanny's suka shigo"Sir gamu." Suka haɗa baki girin faɗin haka. Kallonsu ya yi ya ce,"Ku kira mini sajen Saminu, sannan wanna yarinyar ku kamata ku yi mata wanka, ku duba kayan da zai shige ta na uniform primary one za a sanya ta." Zare idanunsu suka yi "Primary one sir? Yarinyar da ta girma haka?" "Yar ƙauye ce ku yi abin da na ce." "Ok sir." Suka haɗa baki gurin faɗin haka a tare. Kallonta suka yi da take zare idanu."Na rantse duk wanda ya taɓa ni, saina sanya Kakata ta yi masa fatalwa ta lashe shi." Ta ce cikin rawar murya ganin kashedin bai sanya su fasa ninyar su ba. "Kai this girl is smelling ke wace irin ƙazamiya ce bakya wanka?" "Gyatumar ki ce ƙazamiy..." Kafin ta ƙarashe maganar ta ji an wanka mata mari. "Kul! ba a zagi a makarantar nan, saboda ba za ki koya wa ɗalibanmu rashin kunya ba." "Alllah ya isa mugu azzalimi."Ya ji tace kafin ya ƙarashe maganar. "Please ku je ku yi mata wankan ku tsaftace ta." Ihu ta saka za ta fita, amma sai sajen Aminu ya ɗauke ta cak zuwa bayi, saboda wani irin ƙato ne murɗadde. Ihu ta cika makarantar tana kiran Kaka Tani, amma ba su kula ba har sai da suka danganata da bayi. A cikin class ɗin su Umma, tana zaune ta gefen windo tana kallonta."Umma, wancan yarinyar ba 'yar uwarsu bace? Saboda kamar a motar Yayanmu ta zo?" "Ba 'yar uwata bace ban san ta ba." Ta ce don bata son mutane su san suna da 'yan'uwa a ƙauye '. Aliya komawa ta yi ta zauna, don ba ta yarda ba, musamman da ta nuna rashin gaskiya. Tana kuka tana ihu, amma basu kula ba sai da suka fara mata wanka. Ihu da zagi kam ta yi shi har sai da muryarta ya rushe. Da ta san abin da za ayi mata kenan, da ba ta yarda da maganar Mommy ta zo makarantar ba. Kanta kuwa, bayan sun sanya mishi mai, sai da suka yanke gashin da ya dunƙule, duk da kuwa gashin irin mai tsantsi da warwara ne, amma saboda rashin tsafta da kula ya sanya shi fita hayyacinsa. Abin takaici gashi tana da gashiin sosai, amma duk wanda ya kalli gashin sai ya yi mai. Da suka zo goge bakinta sai da suka ji kamar ba za su iya ba, saboda suna dirjewa jini yana zuba. Makilin kusan ɗaya ya ƙare, amma bai yi hasken da suke so ba, saboda ya riga ya dafe. Ga abinci da ya zama gansa kuka. Sun samu sun yi mata wankan, don babu dauɗa jikinta, sai dai ba ta yi haske ba. An dai cire datti. Kayan makaranta suka ɗauko mata bayan sun shafa mata mai da karfin tsiya. Babu laifi sai ta fito 'yar makaranta da ita. Kallon kanta ta yi cikin kuka saboda gani take babu tozarcin da ka yi mata yafi wannan. Jikinta kuwa zafi yake mata, saboda dirzansa da suka yi. "In sha Allahu wuta za ku shiga mugayen azzalumai." Ta ce daidai lokacin da sister Lami ta miƙa mata sandal da sock. "Rufe wa mutane baki mara kunya. A makarantar nan sai na koya miki hankali. Maza sanya sandal da sock ki je ofis." Ganin ta ƙi sanya wa tana murxa bakinta da ta buge, sai ta janyota ta faɗi kasa ta fara ƙoƙarin sanya mata. Ganin haka Sister Ani itama ta janyo ɗayan kafar suka sanya mata. Janta suke yi da ƙarfi har suka isa ofishin. Principal ya kalle ta ya ce,"Dubi ki kin ɗan yi fasali mai ake yi da mutum ƙazami?" Harara ta aika masa da shi saboda ba ta son magana, domin bakinta da suka gurje zafi yake mata, sannan da ta yi magana sai jini. "Ku je zan kaita primary one." "Ok sir." Suka ce tare da juyawa suka tafi. "Ki biyo ni." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka Binsa a baya ta yi tana ƙunkunai har suka shiga primary one. Yana shiga yaran suka miƙe suka haɗa baki gurin faɗin,"Good morning sir." "Morning how are?" Ya ce musu yana kallonsu. "Fine thank you sir." Suka ce suna kallon Jimmalo da ita ma take kallonsu. "Sit-down you have a new mate sunanta Safeeya Abdullahi." "A'a ni fa sunana Jimmalo, ku kira ni Jimmalo jikar Tani, domin na rantse duk wanda ya kira ni da Sahiya sai na karya mutum." "Safeeya, za ku kira ta sannan ku rinƙa koya mata karatu, a jinku za ta zauna" Zare idanunsu suka yi, jin abin da ya ce."Sir wannan sa'ar Addata Hafsat ce a kaita ajinsu, saboda ta yi girma a nan. Za ta zama maman aji" Faisal ya ce su suka kwashe da dariya. "Kai ni ne zan zauna da waɗannan ƙananan yaran? Hahaha, wasa kake yi na rantse, in ba so kake yi na rinƙa ɗaukar su na maka su da ƙasa ba, don tsaf zan kashe yaro in har sun mini dariya." "Ke Safeeya, ki natsu don wallahi kika cutar da wani sai na sanya an miki duka." "Ni fa ka daina kirana da Sahiya Jimmalo dai." Ta ce tana harararshi. "Kuna ji ku rinƙa koya mata karatu Anty don Allah ki sanya ido, sannan ki rinƙa koya mata karatu." "Ok, sir." Malamar ta ce tana kallonta da take ta kumburin tana zaginsa. "Na rantse duk yaron da ya yi kuskuren cewa zai koya mini karatu suna karya shi." "Ki taɓa yaro a makarantar ki gani." Ya ce mata tare da tsaki ya fita. Ganin za ta bishi Anty ta ce,"Ke Safeeya, come and sit down." Tsayawa ta yi ganin ya rufe kofar sai ta dawo ta ɗage saman windo tana faɗin."Na rantse duk sai na yi maganinku, har ke da kike ji da ƙiba kamar doya." Dariya aka kwashe da shi malamar ta yi musu tsawa."Ba zan lamunci rashin kunya ba, kuma zan mugun saɓa miki." Ƙunƙunai ta yi ta haye zaman windo tana mamaki wai yau ita ce a makarantar boko?Gaskiya mutuwar Kaka Tani ya kawo mata cikas a rayuwarta. Ganin haka sai ta ci gaba da karatun burinta ta gama darasin lissafin ta fita. Jimmalo tana zaune tana ta kallonta. Ko da aka kawo mata takaddunta da pencil kallonsu kai ta yi ba tare da ta ɗauke su ba, domin a ganinta basu da amfani don riƙe pensil ba ta iya ba ballantana rubutu. To Jimmalo Jikar Tani an fara shiga wata rayuwa. Daga Jimmalon yau mun ji ainihin sunanki Safeeya. Sai na ce ɗaliba Safeeya Allah ya sanya ki tsaya ki iya karatu. Yau dai kawo ƙarshen kan Jimmalo da rashin wanka. Shi za ta goge ta waye ta zama student ko za ta ci gaba da gidadanci? Ku ci gaba da bibiyar labarin da zafafan comments. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0 *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 20 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* Ganin haka sai ta ci gaba da karatun, burinta ta gama darasin lissafin ta fita. Jimmalo tana zaune tana ta kallonta. Ko da aka kawo mata takaddunta da pencil kallonsu kawai ta yi ba tare da ta ɗauke su ba, domin a ganinta basu da amfani don riƙe pensil ma ta iya ba ballantana rubutu. Wunin ranar ba za ta ce ta koyi komai ba, domin hankalin ta ba shi kan ta koyan, musamman turanci da suke yi wanda yafi ɓata mata rai da tsanar bokon sosai. Ko da aka fita break, ba ta fita ba saboda kayan da ta sanya da rayuwar da ta tsinci kanta sai ta ji duk ta takura. Umma tana son ta kawo mata abin break, amma ƙawayenta sun zura mata idanu so suke su gane da gaske 'yar uwarta ne. Ganin haka sai ta faki idanunsu ta kawai Auta ya kai mata. A lokacin da ya kawo mata kular da sauri ta karɓa domin yunwa take ji sosai. Kallonta yaran suke yi ganin yadda ta kai hannu za ta fi abinci ba tare da ta wanke hannu ba. "Anty Safeeya, Anty ta ce ba a cin abinci ba tare da an wanke hannu ba, sannan ga cokali ki sanya ki ci." Ije kular abincin ta yi tana kallon Nadiya da take tsaye a gefenta. "Ke! Karya ki xan yi in har kika shiga gonata. A Kauyenmu da maza na ke karawa, don haka ban ga abin da zan samu a jikinki ba, domin ganin ki na ke kamar yanzu aka haife ki." Jin abin da ta furta cikin zafi, sai ta matsa da sauri tana zare idanu. Jimmalo ta zabga tsaki ta ɗauki abincin ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya. Kafin ta gama cin abincin duk ta bata hijabinta. "Uncle Yahaya, ka ga Safeeya ta ɓata kayanta." Mudassir ɗan ajinsu ya je ya gaya wa Uncle Yahaya, domin doka ce a makarantar duk wanda ya ci abinci sai an buge shi. Cikin zafi ya isa gurin, ya yi mata bulalar da ya sanya ta miƙe za ta cakume shi. Da fari razana ya yi, amma kuma sai ya dake ya tsula mata bulalar iya ƙarfinsa. Ihu ta saka tana sosa bayanta. "Oya mu je gurin Principal sam ba ki da kunya." Ya furta tare da kama hannunta yana janta. Dukan da ya yi mata shi aka ƙara mata. Da fari zagi ta ƙunduma musu, jin hakan Principal ya sanya sajen ya yi mata dukan tsiya. Duk dauriyarta sai da ta koka ganin yadda ya fasa mata baya. Kafin a tashi ta gama tsine musu, kuma ta rantse ba za ta ƙara zuwa makarantar ba. Aliyu Da ya koma gida Daddy faɗa ya yi mishi sosai."Cewa na yi ka kaita ayi mata rigista na islamiya da boko." "Daddy, ba zan iya dawowa da ita a cikin motata ba." "Ya zama dole ka san yadda za ka yi ka ɗauke ta a matsayin yar'uwa." "Impossible dad, zan koma Abuja." Ya ce tare da miƙewa jin faɗan da yake masa. Daddy haushi ya ji, ya haura sama Mommy ce ta kalle shi za ta yi magana ya riga ta."Please mommy don't say anything, zan wuce ki yi mini addu'a." "Allah ya tsare." Ta furta ganin yana musu da su. Yadda ta amsa sam bai yi masa daɗi ba, amma tafiyar ya fi saboda yana in suna rayuwa a gida ɗaya, watarana zai kashe ta. Ɗakinsa ya wuce ya ɗauki Jakarsa. Zariya Anty Amarya riƙe da jakarta mai ɗauke da kayan kwana biyu. Sun yi shiri tsaf ita da Hanifa da kuma Mufida. Dama sun shirya tafiyar za su yi wa Captain bazata. Tun da ya ce mata zai shigo Kaduna, sai ta shirya zuwa Kaduna, don ta yi masa kyakkyawar albishirin ta samo masa yarinya kalar wacce yake so. Yarinya ce wacce ba za ta wuce shekaru sha bakwai ba. Hafizar Alqur'ani. Ita ta cinye gasar Alqur'ani na wannan shekara na ƙasa da aka yi. Dalilin da har ta yi masa hanyarta. Mahaifiyarta ƙawar ƙanwar Mamanta ne da take zama a Suleja. Labarin yarinyar ta ji suna yi tana sha'awar tana da yaro ta aura masa, kasancewar maƙota suke. Jin yadda take sha'awar tarbiyartarta, da kuma yadda ta fasalta yarinyar har ta gaya mata cewar burin yarinyar ta auri soja, duk da sanin wasu sojojin na su da natsuwa. Nan take ta yanke shawarar ta yi wa Aliyu maganarta, amma sai ya yi mata alƙawarin zai daina kula matan banza. Don haka take son su yi magana ta fahimta, kuma ba a cikin gidansu ba, don ka da wani ya ji abin da take son yi, ya zama silar da mutanen gidan za su ƙara tsanarta, musamman Hanifa da take ganin kamar kusancinta da Aliyu zai taimaka ta same shi. Tun da Mufida ta ji za ta je Kaduna, sai hankalinta ya kwanta, ganin ta samu hanyar da za ta yi maganinta ba tare da wahala ba. Don haka ana gobe ta je aka yi mata lalli da gyaran kai. Ganin haka Hanifa ta cika da baƙinciki, domin ta san zuwan na ta ba ƙaramin cikas zai kawo mata ba. Ba ta kira Aliyu ta gaya masa ba sai da suka kusa tasha. A lokacin da ta kira shi har ya shiga cikin motar da ya sanya jakarsa. Ganin kiran na ta sai ya fasa tuƙa motar ya ɗaga. Sallama ya yi mata sannan ya ce,"Antyna, na yi shirin biyowa ta Zariya, amma saboda wata matsala ba zan zo..." "Kwantar da hankalinka ka zo tasha ka ɗauke mu." Jin abin da ta ce, sai ya cika da mamaki domin ba ta gaya masa za ta zo ba." Anty ina fatan ba yaran nan bane, suka sanyaki zuwa? Saboda wahalar da kansu suke yi. Gara ki gaya musu gaskiya su je su samu wadanda za su iya auren su, domin in har ni suke jira za su mutu babu aure." Jin abin da ya ce, sai ta yi guntun murmushi tana kallon su. "Kwantar da hankalinka Aliyu. Na zo maka da kyakyawar albishir da zai sanya ka yi mini kyauta." Jin abin da ta ce sai ya yi murmushi."Anty, an samu kalar matar da na ke so ne?" "Daɗina da kai ka cika ƙosawa, ka yi maza ka zo tasha ina jiranka." Ta kashe wayar kafin ya ce wani abu. Ganin ta kashe sai ya ije wayar, tare da kunna motar yana fatan Allah ya sa kalar matar da yake so ne ta samu. Ba tare da ɓata lokaci ba ya tafi zuwa tashar. A lokacin da ya isa suna tsaye suna jiran shi. Hon ya yi musu sannan suka fara tahowa zuwa gurinsa. Kamar yadda gaban Hanifa ke dukan tara-tara haka na Mufida. Kowacce xuciyarta cike sonsa da ƙaunarsa. Burinta ya yi mata tarba na musamman, amma sai dai kamar kullum don ba ta canza zani ba. Saboda girmamawa, fitowa ya yi daga motar ya karɓi jakarta. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce,"Gaskiya kin yi mini bazata kin san har na shiga mota zan koma Abuja?" Mamaki sosai ta yi, domin ya ce mata kwana huɗu zai yi."Hala kiran gaggawa ka samu daga gurin aiki?" "Anty gara kiran aiki da tashin hankalin da na samu a gida." "Subuhanallahi! Lafiya?" Yatsina bakinsa ya yi, daidai lokacin da ya sanya jakarta a bayan mota."Za mu yi magana, saboda in har zan yi maganar yanzu, wataƙila na kasa tarbarki da kyau." "Komai dai ya yi zafi maganinsa Allah." Ta ce daidai lokacin da ta shiga gidan gaba. Ba tare da ya ce mata komai ba ya kunna motar. Sai a lokacin suka samu ƙarfin iya gaishe shi a tare. Ɗan waiwayo wa ya yi, ya watsa musu banzan kallo ya ce,"Kuna lafiya?" Don takaici Mufida ba ta amsa ba, sai Hanifa ce ta amsa gwiyarta a sake. Mufida duk yadda take jin xuciyarta na tafarfasa saboda ƙaunarsa, hakan bai hana ta watsa masa harara ba, saboda ya cika ɗan wulaƙanci na ƙarshe. Hankalinsa a tuƙi yana hira da Anty Amarya har suka iso. A lokacin da suka iso, Mommy tana zaune xuciyarta cunkushe da damuwa, ganin ya yi fushi ya tafi. Sosai take son ɗan nata da damuwa da rashin sa a kusa da ita, amma kuma ga shi ya samu hutu Jimmalo ta kore shi. Nan take ta fara ganin rashin adalcin Hajiya da ta jajibo musu ita. Tana wanan tunanin ta ji hon ɗin motarsa. Da sauri ta miƙe tare da yaye labulen falon. Ganinsa sai mamaki sosai ya kamata. Har ya shigo ya yi parking idanunsa na kan motar, sai kuma ta lura da mutane a cikin motar kuma mata. Tana tsaye tana kallon su da tunanin su waye, Anty Amarya ta fito daga cikin motar, sannan su Mufida da Hannifa. Murmushi ya bayyanaa fuskarta, ganin baƙin da suka yi, domin yadda Anty Amarya take son ɗanta haka ita ma take sonta. Fuskarta ɗauke da farinciki ta fita zuwa harabar gidan. A lokacin Anty Amarya ta fito, sai kuma Mufida da Hannifa da suke ƙoƙarin fitowa. "Zuwan bazata amarya? Ai kya sanar da ni, duk da na san cewa ba don ni aka zo ba." Murmushi ta yi tare da ƙarasawa gabanta. "Da gaskiyarki Mommy ba zuwanki bane, amma kuma sai na kusa rashin sa'a don ya ce mini har ya shiga mota zai juya." "Kin ga da sai ki yi zumuncin dole" Ta ce tana kallon su Hanifah da suke gaisheta. "Lafiya lau kun iso lafiya?" A tare suka haɗa baki gurin,"Lafiya lau." "Masha Allah mu shiga daga ciki." Mufida take bin gidan da kallo cikin birgewa, duk da cewar wannan ba zuwan ta na farko kenan ba, sosai take son ta kasance surukar gidan, saboda ita a rayuwarta tana son rayuwar kuɗi yadda za ta fantama ta yi rayuwarta cikin daula. Suna hira suka shiga cikin falo da Mommy. Aliyu yana riƙe da jakar Anty Amarya ya kawo mata kusa da ita. Kallonsa ta yi tana dariya ta ce,"Na gode soja mazan fama. Da su Hanifah ka bar musu suka shigo da shi." "Kar ki damu Atyna kin san kin wuce haka a gurina. Ni dai na ƙosa da kika ce za mu yi wata magana, saboda bacin zuwanki da yanzu ma yi nisa." Da ido ta yi masa alamu da ya daina maganar za su yi sirri. Sai ta wayance da dariya tana kallonsa ta ce,"Haka ne ai zuwan mai dalili ne, saboda faɗa na zo maka." Gane abin da take nufi ya yi, domin duk 'ya matan sun zura mata idanu, ko wacce tana burin ace ita za takura masa ya aura. Mufida ta san ba ya wuce 'yar mijinta, amma duk ta ƙosa ta samu ta sanya masa maganin, don haka ta fara tunanin yadda za ta shiga kofin ɗin. Aliyu hijira ya so ya yi mana, saboda mun ɗauki yarinya muna son mu yi aikin lada." Anty Amarya ta kalle shi lokaci guda fuskarsa ya sauwa, sai ta kalli Mommy da ita ma shi take kallo ganin ya haɗe rai. "Wannan yarinyar ce ko Captain?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa. "Ita ce suka kawo wai za su riƙe ta a gidan nan. Ni kuma in har za su riƙe ta, ba zan ƙara zuwa gidan nan ba, saboda na tsane na. Wallahi ko tunawa na yi tana gidan nan sai na ji xuciyata tana tashi." Dariya mai sauti Anty ta yi, ganin yadda yake maganar da gaskiyarsa. Ta san cewa in har ya tsani abu to ya tsane shi. "Mu kanmu, bisa tursasawar Hajiya ya sanya ta zauna a gidan nan, amma wallahi da na zauna da Jimmmalo, gara a haɗa mini jarirai biyu na riƙe, gabakiɗaya babu wanda ya isa ya sanya ta ta yi ko ta ji magana. Kakarta ta yi mata wani irin tarbiyya mara kyau. Ga ƙazanta ga rashin jin magana babu sallah ba salati." "Innnalilahi! Wannan wace irin yarinya ce?" Anty ta yi tambayar da mamaki. "Hmmmmh! Za ki ganta sun kusa dawowa makaranta, saboda yau aka sanya ta a makaranta. Na rantse duk bayan minti sai na kalli agogo xuciyata ta buga." "Ikon Allah gaskiya tana da rigima." Ta furta ganin yadda damuwa ya bayyana a fuskarta. Aliyu ƙaramin tsuka ya ja, ya kalli 'yan matan da suke kallonsa kamar za su cinye shi, sai kuma ya kalli lokaci ya sanya idanunsa a fuskar Anty. "Na ba su zaɓi ko ta bar gidan nan ko na daina zuwa. In har suna son ganina sai su biyo ni Abuja. Anty bari na je na watsa ruwa sannan na shigo." Ya ce mata kafin ya jira amsa ya wuce. Mommy ta yi ajiyar zuciya, daidai lokacin da mai aiki ta fara kawo musu ruwa da drinks." Humh! Na kasa yanke shawara game da lamarin. Na cika ki da surutu ga ruwa kusha." Ta ƙarashe maganar tare da ɓalle murfin ruwan tana zuba musu. "Ba komai kan ɗan gidana ne dole na tsaya da komai na ji." "Haka ne kuma, ko wannan zuwan na san wani abu za ku ƙulla, domin ban yarda da ku ba, amma ya kamata ki yi masa faɗa a samu ayi aure a bar magana, yadda mutuwa ke wuf da mutane, ya tsaya ruwan ido ko wace mace ya ce bata yi masa ba." "In sha Allahu, zai yi lokaci ne domin aski ya zo gaban goshi." Anty Amarya tace tare da karɓar ruwan. "Mommy ina Nufaisah, ko tana school?" Hanifa ta yi tambayar ganin bata ganta ba. "Yau ba su da lecture, tana cikin bayi wanka ta shiga, domin ba ta jima da shiga ba." "Ok," Ta ce tare da mayar da hankalinta kan wayarta. Ba ta jima da maganar ba Nufaisah ta fito daga cikin ɗakinsu da tawul ɗauke, sai kuma hijabi da ta sanya. Cikin farinciki suka hada, sannan ta koma ciki don ta sanya kaya. Duk da Mommy ba ta san da zuwan su ba, amma ta yi musu tarba ta musamman domin kafin su gama shan ruwa da drinks aka cika gabansu da snacks, sannan ta miƙe ta ce musu." Bari na shiga na bayar da odar na abin da za a dafa, ga shi na ga lokaci ya ƙure gab da 'yan makaranta su dawo." "Ok, mu je na ta ya ki." Cewar Anty tana ƙoƙarin miƙewa. "Kai haba kar ki damu, akwai mai aiki da ga zuwanki sai ki kama aiki. Ki zauna ki huta zuwa yamma sai ki yi mana gudun kurna tun da kin zo." "Ok, tom shikenan." Ta ce tare da komawa ta zauna Murmushi Mommy ta yi ta shiga kofin ɗin. Sosai jininsu ya haɗu da ita, domin akwai hankali da natsuwa. Abin ka da aikin da gas, babu jimawa aka gama abinci aka kawo musu. Suna zaune suna ci Aliyu ya shigo cikin shirin fita. "Anty Amarya zan fita, amma ba zan jima ba, wataƙila kuma na kai dare. Kar ki yi bacci domin yau za mu yi maganarmu." "To shikenan, babu matsala ɗan gidana sai ka dawo, amma abinci fa?" "Ni Allah ya kyauta! Ko ruwan cikin gidan nan ba zan iya sha ba in har tana cikin gidan." Dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba. Mufida da Hanifa sai suka ƙosa suka ganta ganin yadda ya tsane ta. "Kallon Mommy ya yi da take cin abinci."Mommy, sai na dawo." "A dawo lafiya Allah ya yi maka albarka." "Amin,"Ya ce tare da fita yayin da 'yan matan suka raka shi da kallo suna faɗin,"Sai ka dawo Ya Captain." Sun so su ji ya amsa ba ko bai amsa ba, domin ya tsinci maganarsu, daidai lokacin da ya kai ƙofa Jimmalo Kafin a tashi makarantar ta yi mugun gajiya da zama, domin ita sam ba ta san a takurata. Sosai ta ƙosa a tashi duk da zaman cikin gidan ba daɗi yake mata ba, amma ta gwammce ta koma ko ta huta da gwalan-gwalan, yaren da ake mata tun da ta shigo cikin makarantar. Ga wani azzabben yunwa da ya ke ƙwakwularta, saboda tun da Kaka Tani ta rasu ba ta samu ta ci abinci sosai ba. A dalilin hakan sai gabakiɗaya hankalinta ba shi a makarantar. Tana takure har lokacin tashi ya yi. Kallon makarantar ta yi a ranta ta yi mata kallon ƙarshe, domin ta saka ko sama da ƙasa za ta haɗe ba za ta je makarantar ba. Da aka tashi direba ya zo ɗaukar su. Sosai yaran suke kallonta ganin yadda ta canza ta yi fasali. Babu wanda ta kalla a cikinsu ballantana ta tanka musu tun da aka tashi. Motar ta shiga ta kwantar da kanta, don yunwa take ji sosai. Tun da suka doshi hanyar gidan sai kawai ta fashe da kuka. So take ta fara kuka tun yanzu yadda za ta tunzura Mommy, don ta fahimci tana da saurin fushi. Direba ya waiwayo ya kalle ta zai yi magana, sai dai kallon da ta yi masa ya kauda kansa ya ci gaba da tuƙi, domin shi ma a zuciya yake ba shi da haƙuri kamar zawayi. Su Umma suna jin kukanta, babu wanda ya tanka don sun san ba za ta kula su ba. Ganin an buɗe musu get, bayan ya yi hon sai ta ɓare baki iya ƙarfinta. Mommy dake zaune da Anty Amarya a falo suna hira jin kukan gabanta ya buga. Dama tun da karfe biyu da rabi ya yi, ta ɗan canza tana fargabar dawowarta. "Ya Salam ta dawo! Kina jin ta da kuka za ta shigo cikin gidan nan kamar jariri ya. Ni kam Hajiya ta haɗa ni da bala'i." Ta furta tana jin kukan har cikin ranta. Anty Amarya, Mufida da Hanifa sai suka zuba ma kofar idanu suna son suga Jimmalo, da ta zamar wa mutanen gidan ƙaya a maƙoshi, domin duk bayan minti sai Mommy ta kalli agogo ta sako hirarta. Jimmalo sai ta ƙara wage baki."Na rantse ko tsire ni za a yi, ba zan ƙara zuwa makarantar nan ba. Shegu mugayen masu zuciyar arna." Abin da ta furta kenan lokacin da ta shigo falon. Umma tsaki ta yi, burinta kawai ta shige ɗaki ta je ta kwanta, kuma yau ta rantse sai dai a kaita wani ɗakin ta kwana. Idanu suka zuba mata har ta shigo tana kukan. Anty Amarya mamaki sosai ta yi ganinta, domin ta ɗauka babba ce sosai, musamman ganin yadda Aliyu yake data jijiyar wuya in yana maganarta. "A mayar da ni Damagaran, saboda na gane ƙarya kike mini wayo kika yi mini aka kai ni makaranta. Mugayen sun cire mini kayan da na gada gurin kakata, kuma sun yi mini wanka." Ta furta cikin baƙincikin hakan tare da zubowar hawaye a fuskarta. "Masha Allah! Ubangiji ya yi musu albarka, domin sun biya ni. Jimmalo kin ga yadda kin yi fasali kuwa? Sam ba kya wannan warin, yau za ki yi kwanan daɗi?" Mommy ta yi mata tambayar tana kallon ta. "Ni kawai a kaini ƙauye na fi son rayuwar ƙauye, domin ba zan yi karatun bokon ba." Ta furta tare da zama gefen kujera. "Yanzu ina littafanki?" Mommy ta yi mata tambayar da son kauda zancen. "A can na bar musu saboda ba shi da amfani a gurina. Na rantse ko na Muhammadiya ce ba zan yi ba, ballnatana ta arna." "Za ki yi ilmi shi ne gishiri zaman duniya, domin shi ne yake bambanta matacce da rayayye, kuma wanda ba shi da shi. Misalin jaki ne aka ɗaura masa dakon littafai." Jin wata murya ta yi mata daban, sai ta ji muryar ta yi mata wani iri. Da sauri ta ɗago idanunta tana kallon Anty Amarya da take kallonta cike da tausayawa. Ace kamar wannan ta rayu babu sallah babu tsafta, duk da cewar ta yi wanka, amma da ka ganta kasan tana rayuwa ne cikin ƙazanta da rashin kula. Dole Aliyu ya tsane ta, domin ko ita wani lokacin mamakin tsaftar shi ta ke yi. "Ke kuma ina...." Ta buɗe baki za ta yi mata rashin kunya, amma kuma idanunta da ta ɗora bisa nata sai ta kasa. Wani irin ƙwarjini ta yi mata, har sai da ta cire idanunta sannan ta ƙara mayarwa. Bayan Kaka Tani za ta iya cewa babu wanda take ƙauna a cikin duniyar, domin kowa keta masa rashin mutunci take yi, amma yau ta haɗu da wacce ta ji ba za ta iya mata rashin kunya ba. Wacce za ta iya mayar da ita 'yar'uwa. Wacce lokaci guda soyayyar jini ta haɗa su ta yi mata ƙwarjini sosai. Har take jin za ta iya ba ta wani gurbi a cikin zuciyarta. Idan da ita za ta yi rayuwa, tabbas za ta haƙura da kuka da ɓurari da take yi don a mayar da ita Damagaran. Sosai shaƙuwar jini ya shiga tsakaninsu. Addu'a ta fara yi Allah ya sa a gidan take rayuwa. Duk da cewar Anty Amarya ba wani girma ta ke da shi ba, domin ko da ace tana haihuwa bai wuce babbar yaronta a aji na biyu a sakandiri ba. To fa Jimmmalo ki rasa wacce za ki ji ta yi miki sai yar gidan Aliyu da yake jin babu kamarta? Hmmmmh lailai za ki tashi kan Aliyu. Comments kun san fa shi yake karawa marubuci karfin yin rubutu. Jimmalo za ta haƙura ta ci gaba da zuwa makaranta? Aliyu zai zauna a gidan sannan zai samu damar auren irin macen da aka zaɓa masa? Ku dai biyo ni cikin littafin.Na gode da comments da kuke yi Ah ya barmu tare. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 21 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* Addu'a ta fara yi Allah ya sa a gidan take rayuwa. Duk da cewar Anty Amarya ba wani girma ta ke da shi ba, domin ko da ace tana haihuwa bai wuce babbar yaronta a aji na biyu a sakandiri ba. A karo na biyu, ta ɗago idanunta ta ɗora a kanta tana kallonta cikin ƙauna irin ta jini. Mommy sai tsananin mamaki ya kamata, ganin yadda jikinta ya yi sanyi take kallon Anty. "Ni fa makarantar ne bana son na yi, ko da zan zauna a birni, amma a cire ni a makaranta." Ta furta hakan tana ƙoƙarin zama. Mommy saboda tsananin mamakin ganin yadda ta yi, sai ta kalli Jimmalo da idanunta yake kan Anty Amarya. Murmushi Anty Amarya ta yi ta zama a gefenta, tana kallonta domin ita sam ba ta ga taurin kan da ake faɗin tana da shi ba. "Yanzu kin dawo, ma za ki je ki cire kayan makaranta ki canza sai ki yi sallah ki fito ki ci abinci, domin an gaya mini ba kya sallah, na san ba ki yi a makaranta." "Zan yi in zan kwanta, anan gidan kike?" Ta yi mata tambayar da ya cika su da mamaki. "A'a amma ni 'yar uwar gidan nan ne, ina zama a Zariya." Saboda ba ta san Zariya ba, sai ta taɓa bakinta lokaci guda fuskarta ta canza, domin ta so a ce a gidan nan take. Miƙewa ta yi, za ta nufi cikin ɗaki don ta cire kayan jikinta, saboda sam ba ta ƙaunar ganin kayan a jikinta. Mamaki sosai ya ƙara kama Mommy."Wonder shall never ends. Jimmalo ce ta yi magana da ke ta fahimta? Laillai na yi mamaki ƙwarai, ke kuwa wane irin farinjini kike da shi? Domin tun da ta zo gidan nan take shuka rashin kunya, hatta Daddy ba ta ɗaga masa ƙafa ba. Dariya ta yi ta ce,"Ikon Allah kenan! A cikin duniya ba ka rasa wanda za ka ji maganarsa. Ba kya ganin wani lokaci mukan yi tarayyar da mutanen da suke gaya mana magana mu ji kuma mu ɗauka, ba tare da mun bi na iyayenmu ba. Wasu yaran ko sanar da iyayensu ba sa yi. Ƙawa sai ta canza rayuwar danka, ta kuma ba shi muguwar shawara ya ɗauka." "Na yarda da hakan domin ga zahiri nan. Ni kam zuwan ku babu abin da zan iya cewa, sai dai na yi miki godiya." "Ba komai ai yaro na kowa ne. Har yau ina jin damuwar rashin haihuwa da bana yi, domin babu abin da ya kai haihuwa farinciki da yaye damuwa." Ta ƙarashe maganar hawaye yana zuba a ƙuncinta. Ganin haka sai hankalinta ya tashi, ta ƙarasa gurinta tare da kama hannunta."Ki yi haƙuri Allah yana tare da ke, kuma in ya so sai ya ba ki a lokacin da kika cire tsammani. Na sam cewa babu bin da yafi haihuwa daɗi, amma kar ki manta Ubangiji ya ce yana jin kunyar macen da bai ba ta haihuwa ba, sannan akwai bin da ya tanadar musu ranar gobe kiyama wanda ya barwa kansa sani." Ta numfasa sannan ta ɗora ganin har yanzu da damuwar a fuskarta. "Akwai haihuwar da Allah zai ba ki, sa kin gwammace da ma ba ki haihu ba. Yaran da ake haifa suna lalacewa suna zamar wa duniya annoba. Kin ga da irin waɗannan yaran, gara mutum ya mutu ba tare da ya haife su ba. Sannan akwai yaran da su za su kai iyayensu wuta." "Haka ne Ubangiji ya bani yaro domin da ciwo, don na samu kishiyar da ba ta mini ido kan yaranta, amma da yanzu xuciyata ta gaza da girman ƙaddarata, sannan ina son na haihu nima na ga sayin idaniyata, akwai ciwon da mutum zai yi dole sai jininka zai yi jinyarka." Haka ne za ki samu haihuwa ki ci gaba da addu'a lokaci ne bai yi ba." Mommy ta ce mata cikin tausaya. "Ina fatan lokacin ya yi. Har ga Allah ganin Jimmalo ta shiga raina sosai. Tausayi sosai ta ba ni domin duk abin da take yi ba laifinta bane. Shi yaro yana tasowa ne da irin tarbiyyar da ya ginu a kansa. Duk wannan sakarcin da take yi laifin kakarta ce da so ya rufe mata ido, amma tun da ta rasu, sai mu yi mata addu'a, sannan kuma mu yi ƙoƙarin gyara kuskure da ta yi." "Haka ne Allah ya bamu ikon gyara, tun da kin zo don Allah ki shiga ciki na iban mata kaya sosai a cikin na Umma, kafin na samu na shiga da ita kasuwa a siya mata duk abin da take buƙata." "Ba matsala zan ji da ita." Ta ce tare da miƙewa ta shiga cikin ɗakin. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Mommy ta yi, sai ta ji zuwanta kamar an sauke mata dutsen da aka ɗora mata a kai. Jimmalo tana tafiya, xuciyarta cunkushe da takaicin jin ba a gidan take ba. Har ta isa zuwa cikin ɗakinta jefar da hijabin da ɗan-kwallinta suka ɗora mata a ƙasa. Takalminta kuma ta yi jifa da shi a saman gadon. Ta miƙe ta shiga cikin bayi, saboda wani irin fitsari da ya matse ta. Da ta shiga bayin ta yi fitsari. Har ta murɗa ƙofar za ta fice, amma sai ta dawo sakamakon ganin kanta a madubi. Da sauri ta janye gashinta ta buɗe bakinta. Tabbas ita kanta ta ga canjin da ta yi, domin za ta iya cewa ba taɓa ganin ta yi kyau irin haka ba. "Ashe ina da gashin haka?" Ta furta tana fincike lobalin da suka ɗauke mata da shi, sai dai duk kyan da ta yi ba ta jin za ta iya cigaba da tsafta, domin ita takurar ce ba ta so a rayuwarta. Daidai lokacin da ta fito sai Anty ta shigo. Tsintar kanta ta yi da sakin murmushin da bai wuce iya leɓe ba, a maimakon ɗauke kanta da ta so ta yi. Ba ta ce mata komai ba, ta ƙarasa kan gadon ta zauna, wanda ganin hakan Anty ta zauna a gefenta. "Yauwa ga kaya Mommy ta ce ki canza." "Ni bana so na sanya wasu kaya in ba na Kakata ba." Ta furta tare da janyo kayan ta ɗauki wata riga da sani da take zama a tsakar gida. Da mamaki ta kalle ta, ganin yadda kayan sun yi tsufan da ko goge-goge ba za ta iya yi da su ba." "Jimmalo, waɗannan kayan za ki saka? Kin san kuwa a gidan da kike rayuwa?" Ta yi mata maganar cikin zallar mamaki. "Ni ina ruwana su na ke son na saka." Ta ce tana ƙoƙarin ɗaukar zani. "Ƙona su za a yi, daga yau ba za ki ƙara sanya su ba." Ta ce tare da fisge kaya ta miƙa mata doguwar riga mai kyau kalar pink. Kallon kayan ta yi, cikin damuwa kuma ta kasa musu da ita. Ganin haka ya sanya ta miƙe, tare da ƙarasa gurinta kamar za ta taimaka mata ta cire kayan. "Wai mene sunan ki? Saboda Jimmalo sunan rana ne?" "Jimmalo Jikar Tani na fi son a rinƙa ce mini, bana son Sahiya da wannan mai kama da arnan ya ce dole shi za a sanya mini." Dariya ta yi jin wautarta. "Ok, sunan ki Safeeya kenan? Wow kina da sun mai daɗi, kuma ƙanwata sunan ku ɗaya da ita, amma ana kiranta da Surfy." "Hmmmmh, ita ma kun mayar mata da sunan arna." Ta ce lokacin da ta cire rigar makarantar, ta sanya doguwar rigar tana yi wa kanta wani irin kallo. "A'a suna ne da zamani ya zo da shi." Ta ce mata lokacin da take duba chatting ɗin Aliyu, da yake gaya mata yana hanya, don bai samu wanda ya je nema ba. "Wow, kin ga yadda kika yi kyau?" Ta yi mata maganar tana gyara zaman rigarta. "Ban gani ba saboda na tsani shigar birni ba ta mini kyau." "Daga yau ita zaki rinƙa yi, don kin zama 'yan birni, ga shi har kin shiga makaranta. Surfy zan rinƙa kiranki da shi." Ta ce mata lokacin da ta miƙe ta kwashi kayan. Ganin ba ta tanka mata ba sai ta kwashi kayan ta ce,"Ƙona su za a yi saboda ba su da amfani a gurinki." Kama kayan ta yi ta ce,"Don Allah kar ki ƙona mini kaya, saboda su kawai na ke gani na tuna da Kakata." Yadda ta yi maganar sai ta ba ta tausayi. "Kin yi alƙawarin ba za ki ƙara sawa ba?" "Eh na yi." Ta tsinci kanta da faɗin haka cikin rawar murya. "Ok, tom shikenan ki fito ki ci abinci." "To," Ta furta mata daidai lokacin da za ta fita, domin har ta kama ƙofa sai ta tsinci muryarta tana faɗin,"Don Allah ki zauna a gidan nan, ko kuma ki tafi da ni can gidanki. Bana son rayuwa a gidan nan, saboda wannan mugun mai kama da zabiya dukana yake yi har ya fasa mini baki." Jin abin da ce sai tausayinta ya kamata. Ta san cewa Aliyu ba shi da tausayi zai iya abin da ya fi haka. Dole zata kawo sasanci a tsakaninsu, domin ita bata ga girman da Jimmmalo ta yi ba, da har zai rinƙa faɗa yana tada jijiyar wuya a kanta. "Kin ga kuma a gidan nan, bani da wanda muke gyaɗar doguwar fiye da shi, domin zuwana saboda shi na yi." Lokaci guda annurin fuskarta ya canza ta kalle ta da wani irin fuska. Sosai ta ji haushin matar da ta ji ba ta da kamarta jin suna shiri da shi, sai ta fara ƙoƙarin cire ta daga xuciyarta. Ganin yadda ta canza fuska, ta saki murfin ƙofar ta kama hannunta."Kar ki damu, zan yi masa magana in sha Allahu zai daina hantararki, sannan ba zan iya tafiya dake ba, amma in sha Allahu in kuka samu hutu zan sanya Mommy ta kawo mini ke." "Ki bari kawai bana son zuwa, saboda duk wanda yake hurɗa da shi na tsane shi, dalilin da ya sanya na tsani mutanen gidan nan kenan, don na rantse tun da ya cutar da ni don ya ga babu kakata, sai na zaman masa kaɗangaren bakin tulu." Ta furta tare da ƙarasa gefenta zauna. Jin bin da ta ce sai hankalinta ya tashi, domin har ta fara jin daɗi sosai za ta samu kyautar yabo a gurin Mommy da Daddy, amma ganin yadda ta yi sai gwiyarta ya sage. "Ba a faɗa da maza musamman shi da yake soja. Zai iya sanya bindiga ya harbe ki. Yayanki ne ki ɗauke shi a matsayin yaya." "Ba zan taɓa kiran shi da Yayana ba, kuma bana jin tsoron shi domin nima soja na ke son na zama." Ta furta fuskarta cike da gaskiyar abin da ta faɗa. Cikin mamaki ta kalle ta domin tana da dakiya da kuma rashin tsoro. "To yanzu fito kici abinci, anjima za ayi maganar, domin har na fara tunanin ture gwamnatinsa a gurina ki zamo 'yar gidana ke kaɗai." Murmushi ta yi ta ce,"Kin tabbata za ki daina kula shi, ni kuma zan zamo ƙanwarki." "Yauwa ƙanwata Surfy, ta shi mu je kici abinci." Ta furta tare da miƙa mata hannu. Hannu ta bata ta miƙar da ta sannan suka fita falo. Mommy sai lamarin ya daina ba ta mamaki sa almara, sai kawai ta kama baki tana kallonta. "Na yarda babu abin da ya gagari Allah." Ta ce daidai lokacin da ta fito suka zauna a kujera. Su kansu 'yan matan falon, mamaki suka bita da shi, musamman Nufaisah da Umma. Zama ta yi, ba tare da ta kalli mutane falon da suke mata kallon mamaki ba. Anty da kanta ta zuba mata abinci ta fara ci. Yadda take cin abincin da zaman da ta yi, zai tabbata mana da rashin wayewa da gidadanci a kanta, domin kana ganinta ka san ta bambanta da sauran 'yan matan falon. Bayan ta gama cin abinci. Ta yi gyaza ta samu gefen Anty ta zauna tana kallo kamar za ta shiga tibin, ba tare da ta yi tunanin ta ɗauke kwanon ba. Sosai Mommy ta ƙosa Daddy ya dawo don ta yi masa kyakyawar albishir. Suna zaune ana kallo sai surutu Jimmalo ta ke da Anty, wanda ya cika duniyar Mommy da mamaki. Labari take ba su yadda ta shuka tsiya a Damagaran. Suna ta dariya sosai domin har Mommy sai da ta dara. Mufida da Hanifa suke ƙara zugata in ta yi shiru, domin dariya take ba su sosai, tamkar wata 'yar comedy suka ɗauke ta. Tunawa da abin da ta yi wa Captain, a lokacin da ya zo Danagaran ta yi, sai ta fara gaya musu haɗuwarsu ta farko tana kan mangaro. Sosai suka yi dariya har da Mommy, da ta tuna da yadda ya tsorata ya ce su bar gurin akwai aljanu. Ashe Jimmmalo ce. "Lallai Surfy kin ranazar zuciyar mazan fama." Anty ta ce tana dariya sosai. "Allah wallahi, kawai na fara kukan jaki ina girgiza bishiya, sai ga shi ya riga da gudu. Ashe ma zabo ne ku ke kiran sa da soja." Aliyu ya tsinci muryarta tana faɗin haka falon ana ta dariya sosai. Da fari ya so ya shigo da motar, amma tuna bayan sun gama magana da Anty zai fita sai ya bar motar a waje. Cikin rashin sa'a ya shigo ya ji tana ba su labari. Cikin tsanannin mamaki ya tsaya yana jinjina kansa. A wancan lokacin in qur'ani za a ba shi zai rantse da aljani ne, amma ashe ita ce ta haye bishiyar ta rinƙa maka masa mangwaro kayansa suka ɓaci, har ya firgita ya dauka jinnu ne. Lailai Jimmalo ta wuce tunainsa. Cikin zafi ya shigo cikin gidan ya yi kanta da takaici."Dama kece kika ɓata mini kaya saboda ba ki da mutunci.." Maganar ta katse mishi ganinta gefen Anty jikinsu na gogan juna. "What Anty! Da wannan ƙazamiyar yarinyar za ki haɗa jiki, bayan kin san babu wacce na tsana a duniya kamarta." Miƙewa ta yi ta harare shi ta ce,"Ni ma na tsane ka, sannan ƙarya na yi?Ai na firgita ka saboda da gudu ka ru..." Bata ƙarashe maganar ba ta ga ya dumfarota tamkar kububuwa yana ƙoƙarin zare bell ɗinsa Gudu ta fara suka fara zagaye falon."Aliyu, wai biye mata zaka yi?" Mommy ta ce ganin abin da suke yi. Anty ce ta shiga tsakani ta ɓoye Jimmalo da ya kawo mata hauri. "Captain Please.." "Anty get out of this issue, domin za mu samu matsala dake in har kika ce za ki kula ƙazamar yarinyar na.." "Ni ba ƙazama bace kuma ka..." "Ke Jimmalo yayanki ne ba shi haƙuri!" Anty ta daka tsawa tana faɗin haka. "Saboda anga kakata ta mutu za a ce na ba shi haƙuri." Ta yi maganar cikin kuka, domin ko sama da ƙasa za su haɗe ba za ta bayar ba, don bayar da haƙuri ba shi a cikin jadawalin rayuwarta. "Ba na buƙatar haƙuri, ki bar ni na canza mata kamanni ƙazamiya kawai." "Kanwarka ce don Allah ku daina haka kai sai ka biye mata?" "Ki dai gaya masa, tun da ta dawo gidan nan suke sa mini ciwon kai." Mommy ta ce cikin takaici. "Anty, kin san ina shiri da ke, in har kika son alaƙarmu ta cigaba to ki daina kula ta, domin na tsaneta kuma duk wanda zai yi hulɗa da ita shi ma na tsane shi." "Aliyu bai kai haka ba, ka je sashinka yanzu zan biyo ka." Ta ce masa tana kallon sa. "Yayata ce don ta ce za.." "Jimmmalo an tambaye ki ne?" Ta katse ta jin za ta yi mata ɓaramɓarama. "Gara ki zo ki gaya mini, domin ina tunanin komawa Abuja yau." Ya ce tare da juyawa zai fita. "Ki ba shi haƙuri na ce." Anty ta daka mata tsawa tana faɗin haka. A maimakon ta bashi haƙurin, sai ta murguɗa masa baki tare da yi masa daƙuwa. Zare idanu Anty ta yi wanda karab sai a idanunsa da ya juyo da nufin ya aikata mata da mugun kallo. Ganin daƙuwar ya dawo daga gudu, yana jin kasheta kawai zai yi ya huta. Da sauri ta ruga cikin ɗaki ta murɗa ɗan makulli. Ta kwashe da dariya tare da kwanciya a ƙasa, ganin ta kunna shi. A ranta ta sanya za ta ci gaba da kunnashi, har sai an mayar da ita gurin Anty. "Kai innnalilahi wa inna ilahir raju'un!" Mommy ta furta cikin damuwa. "Kina ganin zagina ta yi Mommy. In har ban kashe wanna yarinyar ba sai na ƙaryata." Ya ce tare da juyawa ya fita. "Lallai Mommy kina shan aiki." Cewar Anty ta bi bayansa. Ruwa mai sanyi ya ɗauka ya sha, bayan ya shiga cikin ɗakin. Ganin Anty ta yi sallama ya amsa ta shigo. "Aliyu gas..." "Please Anty, in har ba maganar da ya sanya ki ka zo Kaduna za ki mini ba, gaskiya ba ni da lokacin sauraren na mahaukaciyar yarinyar nan." Ya katseta yana faɗin haka cikin huci. Shiru ya biyo bayansu sai ta buɗe baki ta ce,"Na samu yarinyar kuma kalar macen da kake so, har hotonta da komai an tura mini. Mahaddaciyar Alkur'ani yarinya mai ƙaramin shekaru, abin da ya sanya na ƙarfafa maka ita, saboda tana da ra'ayin auren soja." Ta ƙarashe maganar tare da miƙa masa wayarta bayan ta shiga profile ta danna hotonta. "Masha Allah! Anty ganin farko ta yi mini." Ya furta yana zooming hotonta. "Amma bisa sharaɗin za ka daina duk abin da kake yi." "Anty wallahi ba ni tare da Lubaiyna tsawon lokaci bamu tare, bayan nan ma sigarin da na ke sha ba sosai ba sai raina ya ɓace." "Shikenan Allah ya ƙulla alkhairin a haifi mana 'yan dugwi-dugwi." Dariya ya yi cikin jin kunya ya shafa kansa."Anty ina samu yarinyar nan burina ya gama cika, domin ko haka Allah ya barni sai fatan dacewa." "Gaskiya ni kaina na yi maka fatan aurenta, abin ƙarin farincikin mahaifinta malami ne sosai. Ga numbarta sai ka kira ta." "No, so na ke yi sai na nemi izini gurin mahaifinta, domin a ranar da muka je za mu samu mahaifinta don mu ganta, in har tana sona ba zan dawo ba sai an yi maganar sanya rana." "Masha Allah! Ɗan gidana ya motsa da ƙarfinsa. Allah y ba ka ita." "Amin, ai irin matan nan da suka fito daga gidan tarbiyya, ba a wasa da su." "Haka ne kai ma na san ba za ta ƙi ka ba, domin babu macen da za ta ce bata sonka. Don Allah kar ka gaya ma kowa ni na yi maka hanyarta." "Kin san ba zan fadi ba." "Yauwa bari na wuce amma Captain yarinya..." "Anty, kin kawo mini albishirin da ya sanya ni farinciki, kuma za ki sanya ni baƙinciki?" Ya furta fuskarta na ƙoƙarin canzawa. "Shikenan za mu yi maganar anjima." Ta ce masa tare da fita. Tana fita ya kulle ɗakinsa, ya ci gaba da kallon hoton Nu'aimah cikin tsananin shauki. Lokaci guda ya ji ƙaunarta ya mamaye zuciyarsa. Numbar Kalim ya kira cikin tsanannin farinciki."Hello, abokina na samu matar aure. Zuwa gobe za mu je ka shirya da na dawo." "Masha Allah! Da gaske Captain ka samu wacce kake so?" Ya yi masa tambayar cikin mamaki. "Na samu Kalim ka taya ni da addu'a, Nu'aimah ta zama matata. Yar gidan malamai kuma Malama mahaddaciya." "Lallai Allah yana sonka, ka gama sheƙe ayarka ka samu mace ƙwarai Allah ya sanya mu a danshinka." Dariya ya yi jin abin da ya ce, tare da kashe wayar bayan sun yi sallama. Murna sosai yake yi kamar zai shiɗe. Zaman yi yana tsara yadda zai yi shiga da kalaman da zai tsara ta, har da kallon da zai yi mata, wanda zai sanya ta zurma daga haɗuwar farko. Mai ɗinkinsa Muhammad, da yake garin Abuja ya tura masa da hoton shaddar da yake son ya siya ya ɗinka masa, sannan ya yi wanka ya fice zuciyarsa cike da murna. Lubaynah, iya lokacin da ta jira ta dawo ta shiga tsananin damuwa, domin tunawa da take Captain ba zai saurarenta ba duba ga rabuwar da suka yi, hakan kawai ya sanya ta daure. Ga shi abin takaici tun da lamarin ya faru iyayenta suka canza mata fuska da tsautsaurar tsaro. Sai ta gane ganin Captain Aliyu ya haɗa mata zafi biyu. Ga rashin sa da kuma fushi da iyayenta suka yi da ita, wannan dalilin ya sanya ta ji za ta iya aikata komai don ta karkato da hankalinsa gareta. A ranar da ta do ta tafi zuwa gidansu. Bayan sun yi hira sun gama zagin maza da suke tsotse ƙwallon mangaro su huta da ƙuda, sannan suka gangaro kan abin da ya kawota. To Captain mai son auren mace ta gari. Shin kana cinmma gurinka? Ko reshe zai juye da mujiya? In har Lubaynah ta ji zai yi aure za ta zuba idanu kuwa? Ku ci gaba da bibiyar da zafafafen comments. Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 22 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* Lubaynah, iya lokacin da ta jira ta dawo ta shiga tsananin damuwa, domin tunawa da take Captain ba zai saurareta ba kawai ya sanya ta daure. A ranar da ta dawo ta tafi zuwa gidansu. Bayan sun yi hira sun gama zagin maza da suke tsotse ƙwallon mangaro su huta da ƙuda, sannan suka gangaro kan abin da ya kawo ta. "Kin san shawarar da na yi? Ba da boka ko malam za mu fara aiki ba. Abin da na yanke ki je gidansa sai ki gaya masa cewar kin haƙura da shi, ki roƙe sa da ya zo ya gaya wa iyayenki kun tuba sannan har kin samu wani za ki aura. Kin ga na farko kin samu ya shirya ki da iyayenki." "Kai Aliyu ba zai zo gidanmu ba, kuma kin san irin abin da zuwansa zai yi. Mahaifina ba zai zura masa idanu ba." "Haka ne amma ni shawarata, ki fara nuna masa kin tuba ku yi zumunci kawai, sannan sai ki je gidansa wannan jakar da kika ce mini in zai je gidan iyayensa yake tafiya da ita, kuma ba ya canzawa sai ki samu ki sanya masa kwalin condom a ciki." Shiru ta yi don ba ta ga amfanin gurguwar shawararta ba. "Ba kin ce Aliyu na da tsari jakar da yake zuwa gida da ita daban, haka na gurin aiki da kuma kayan da yake sawa?" "Eh haka ne amma ban ga amfanin tambayarki ba." Gyara zama ta yi ta ce,"A cikin jakar za ki sanya inda ba zai lura ba. Ki nuna kawai zumunci za ku yi irin na ya da ƙanwa. Zan iya haɗaki da Gali a matsayin wanda zai aure ki har ki haɗasu. In kika samu ya yarda da hakan, na san za ki iya sanin kalaman da za ki yi masa ki shiga cikin gidansa, don ki samu ki aiwatar da abin da muka yi ninya. Dalilin sawa kuwa za ki rinƙa kiran shi akai akai kice in za shi Kaduna ya gaya miki za ki ba shi tsaƙo ya kaiwa ƙanninsa, yana gaya miki za shi sai ki kawo masa tsarabar kayan kwalliya, ta yanda za ki samu ki sanya masa condom ɗin, sannan bayan ya tafi washegarin ranar, ki je gidan iyayensa ki gaya musu irin yaudarar da yayi miki..." "Are you out of your mind? That you are giving such advice?"Ta furta cikin ɓacin rai tana kallonta. Ni this isn't workable! Kin san abin da haka zai kawo? Ni fa ban ga wani amfanin wannan banzar shawarar ta ki ba. Aliyu tsanata zai ƙara yi, kuma kin san ba zan iya rayuwa babu shi ba." "Daɗina da ke ba kya jiran kici ribar ƙarshen zance." Ta ce mata cikin takaici. "Saboda gurguwar shawara kike ba ni. Mahaifin Aliyu ya sanya yarda sosai a kansa, kina ganin in har na yi sanadin rushe yardar nan. Aliyu zai ƙara kallona da fuskar rahma?" "Ba ki da wayo Lubaiyna. Hutu da wayewa da kika taso cikinsa ya sanya kanki ba ya kawo wuta. Wannan yardar da mahaifinsa ya yi masa da shi za mu yi amfani ki samu Aliyu a hannunki." "Hmmmmh!" Kawai ta ce tana mamakin wautar shawararta. Ganin ta yi shiru kawai sai ta ɗora da cewa,"In har ya tafi sai ki bishi kije ki saka kuka ki ce wa mahaifinsa Aliyu har ciki ya yi miki, sannan ya yi miki alƙawarin aure ya ƙi aurenki. Iyayenki sun yi fushi dake shi kuma ya guje ki. Ki gaya mahaifinsa in har bai yarda ba zai iya bincike sosai domin ba za a rasa wanda suka san mummunar halinsa ba. Kina iya cewa aje gidansa domin hatta kayan sawanki yana can. Kin ga anan mahaifinsa zai zurfafa bincike ya gano gaskiya. Wannan condom da kika sanya mishi sai ki ce ko Kaduna ya zo, sai ya kira ki kin biyo shi, kin ga zai bincika har ɗakinsa na gida, ya ga condom ɗin. Kin ga bayan ya gano gaskiya ba zai ƙi aura miki shi ba, domin na san ta wannan hanyar zai huce fuska biyu da ya zama, don in har zai yi adalci ba zai ƙi ba, saboda shi ma na san yana da 'ya'ya mata. Ba zai so hakan ya kasance da shi ba. Bayan haka ya faru sai mu shiga bin malamai don mu jawo hankalinsa gareki, amma yanzu kun rabu ko magani aka ba ki, don ki sanya masa cikin abinci ba za ki samu hanya ba." Shiru ta yi xuciyarta na son yarda, amma tunaninta yana gaya mata gurguwar shawara ce. Lokaci guda sai ta fara yadda musamman da ta tuna yaudararta da ya yi. Kuma sai ta ga in har za ta aure shi ta rayu da shi, sam ba za ta damu da tozarci da wulaƙancin da zai yi mata ba, sannan yana matsayin mijinta dole ta yi amfani da kissar da za sanya har ya gaji da tsanarta ya daina. Lokaci guda sai ta yarda, da shawarar ta kuma ta amince har ta yi mata alƙawarin aikaita haka. A haka suka bar shawarar, Lubaiyna ta koma gida cikin tsananin farinciki. Wayarsa ta fara kira amma ya sanya ta a black list. Ba ta damu ba, don haka ta sanya ranar da za ta je gidansa Aliyu A ranar da Anty Amarya ta sanar da shi ya yi kwanar farinciki, domin tun kafin ya ga yarinyar ya riga ya gama ji a jikinsa ya samu matar aure. A daren ba ƙaramin ƙoƙarin ya yi ba, da bai karɓi numbarta ya kira ta ba, har ya miƙe zai je gurin Anty amarya ta ba shi numbar, sai kuma ya fasa ya kwanta, da nufin ya kira ta tun da ba ta online. Har ya dubo numbar zai kira, zuciyar sa ta ba shi shawarar, kan ya yi haƙuri zuwa nan da kwana biyun, domin ba ya iya tunanin zuciyarsa za ta iya wuce kwanakin. Da ya ga ya samu kalar matar da yake so, sai ya ji zuciyarsa da gangar jikinsa sun bijiro masa da buƙatar aure. Wataƙila lokacin da ya ɗauka yana jin ba ya sha'awar auren, don bai samu wacce yake so ba, amma yanzu sai ya ji yana son ya samu wacce in ya dawo gida. Za ta rugo da gudu ta faɗa jikinsa tana ƙamshi mai daɗi da shiga mai jan hankali, sannan gidan yana fitar da wani ƙamshi mai daɗi, ga abinci wanda zai rinƙa ɗauke masa yunwarsa. Shi kuma cikin shauki ya haɗa ta da jikinsa ya manna mata kis. Lokaci ya ja, har akwai lokacin da za ta haifa masa kyawawan yaran da ba su wuce guda uku ko huɗu. Ya ba su kyakyawar tarbiya, da duk wani ji daɗi na rayuwata. Sosai ya ƙosa ya je ya ganta domin har ya fara shiri. Duk da kasancewarsa ba mace ba, amma gyara da ƙalƙala da yake yi, bana tunanin ko ita macen aka ce zai zo za ta yi wannan gyaran. Anty ta so su koma a washegarin da suka zo, musamman yadda ɗan gidan nata ya ƙosa ta koma don ba ya son ganinta da Jimmmalo, wacce a yanzu take tunanin ta samu wacce za ta zamar mata makwafin Kaka Tani. Da dare ya yi Daddy ya dawo, sai ya sha giyar mamaki. Domin ko kafin ya shigo cikin gidan, ya ji muryarta tana dariya suna hira da Anty Amarya. Da ta cika ta surutu har ta ji. Da sallama ya shigo yana al'ajabi. Turus ya yi ganin yadda ta shige jikinta. Ganin ya shigo duk duk haɗa baki cikin girmamawa suka fashe shi. Jimmalo har da motsi da bakinta duk da ba gaisuwar ta yi ba, ganin yadda Anty ta tsareta da ido. "Ikon Allah!" Ya furta lokacin da ya ije tsarabar da ya shigo da shi. "Hmmmmh! Ni kaina abin ya ɗaure mini kai. Tun da Amarya ta zo, Jimmalo ta saki take zuba a cikin gidan nan kamar ya'yan kanya." "Na yi mamaki ƙwarai ban san sa'ar da kike shi ba." Cewar Dady bayan ya zauna. "Sa'a ace babba ma kuwa, domin tun lokacin da na ga Aliyu, ba shi da wacce yake kulawa a Zariya sai ita ma tabbatar da ita mai sa'a ce, mutumin da mutane bai dame shi ba. Ko ni da na ke mahaifiyarsa ba ya damuwa da ya yi hira da ni. Ga kuma Jimmalo wacce ta gagari kowa a kauyen Damagaran." Dariya suka yi Daddy ya miƙe, bayan sun ɗan taɓa hira ya shiga ciki yana murna sosai. Da aka kira sallah sai Anty ta miƙe zuwa ciki ta yi alwala. Jimmalo tana zaune tana kallo. Ganin kowa ya tashi a falon, amma tana zaune sai ta fito daga cikin ɗakin ta ce,"Ta shi ki yi sallah." Motsi ta yi da bakinta kamar za ta yi magana. Ganin haka ta riga ta da cewa,"Sallah ita ke bambance tsakanin musulmi da kafuri. In har ba kya sallah wuta za ki shiga." "Ba zan shiga ba tun da ban girma ba." "Kin girma Jimmalo tun da kika haura shekara sha huɗu. Addini daga shekara bakwai ya yi mana umurni damu fara dukan yaro in har bai yi sallah ba, don haka ki tashi ki yi sallah ko na fasa daina magana da Captain." Babu musu ta miƙe duk da ba haka ranta ya so ba. "Ki shiga bayi ki yi alwala, ina jiranki mu yi." Anty ta ce mata ganin yadda ta sha kunu. Ba haka ta so ba, domin ta so ta yi ita kaɗai yadda za ta ci karenta babu banbaka, amma tuna za ta fasa alƙawarin sai ta shiga bayin, ba tare da ta ce komai ba, domin ita so take yi in za ta tafi Zariya su tai tare. Da ta shiga cikin bayin ta fara alwala, sai Anty Amarya ta zauna a bakin gado ta jira ta. Sai dai lokacin da ta ɗauka ta fito ya sanya ta kalle tada sauri. Kallon mamaki Anty ta bi ta da shi. Jimmalo har kin yi alwala a sakanni?" Jin tambayar ta bata fuska ba tare da ta bata amsa ba, domin ita kanta ta san cewa ba alwalan ta yi ba ta dai watsa ruwa. "Shiga na ya yadda kike yi." Ta ce mata tare da buɗe mata bayin Ganin za ta yi mata musu ta ce,"In har kina son na cika miki alƙawarin da na ɗaukar miki. To ki cire tunanin mini musu a rayuwarki." Ba ta amsa ba ta shiga ciki. A nan ta shayar da Anty duniyar mamaki. Domin ba alwala ba, shi kanshi tsarki ba ta tunanin ta iya. Ganin wasa kawai take da ruwa, sai ta nuna mata yadda za ta yi alwalar. Suka fito bayan ta kammala tana mamakin yadda Kaka Tani ta yi mata rainon dabbobi, domin za ta iya cewa bayan gangar jiki da take da shi na mutane, gabakiɗaya rayuwar dabbabibi ta koyar da ita. Ba ta ƙara shan mamaki ba, sai da suka zo yin sallah. Sai kawai ta ji hawayen tausayi yana bin ƙuncinta. A ranta ta ji tana son taimaka mata a rayuwarta. Don haka ta ƙudurta za ta roƙi Mommy, in suka yi hutu ta kawo Jimmalo hutu Zariya. Da suka idar da sallah falo suka koma. Bayan sun yi kallo suka kashe kayan kallon sannan suka shiga don su kwanta. A daren tana naniƙe da ita kamar angon da ya yi sabuwar amarya. Ko da aka zo bacci sai ta daka tsalle ta ce alan baran ɗakin da Anty Amarya za ta kwana. Mufida Tun daren ranar Mufida, take ta tunanin yadda za ta samu ta sanya maganin kafin su tafi. Suna kwance kowa ya yi bacci, amma ban da ita da ta lula duniyar tunani, sai dai har ta fara jin bacci ba ta samu mafita ba. Da safe da suka tashi, tun asuba Anty ta sanya Jimmalo ta yi sallah. Duk da cewar sallar da ita gwara babu, haka dai ta yi ta kallonta har ta sallame. Ta san cewa a yanzu ta ce za ta koya mata karatun sallah ɓata baki ne. Jimmalo tana zumɓura baki, Anty ta taimaka mata ta shirya zuwa makaranta. Ita babu abin da ta tsana a rayuwar birni zuwa makaranta. Kayanta gogaggu wanda Alu, mai wanki da guga ya goge mata ta sanya. Ga shi Anty ta tilasta mata ta yi wanka. Sai ta fito cas abin ta. Suna zaune a falo ana karyawa. Mommy ce take kallonta cikin sha'awa ganin yadda ta canza. Ta so ace Anty ta daɗe yadda za ta gyara mata ita, amma da ta tuna an kusa yin hutu sai ta bari in an yi hutu sai ta kaita. Da suka je makaranta wanna karan babu harare-harare, ta yi zamanta kan kujera. Ko yaran da suke kallonta ganin yada ta yi shiru suna son tononta ba ta kalla ba. Har aka yi darasi uku, sannan aka kaɗa break tana zaune bata tare da ta kula kowa ba. Ko malamar da ta shigo, duk maganar da ta yi mata ta yi rubutu kan dole ta gaji ta ƙyale ta. Bayan ta fita, sai ta je ofishin Principal ta yi masa ƙorafin ba ta rubutu. Jin hakan ya yanke shawarar zai kira Daddy, da kansa ya bashi shawarar a ɗaukar mata tuitor. Tana zaune tana cin abincinta a cikin kula, wani yaro mai suna Muntazar ya kalle ta ya kwashe da dariya. "Ke maman Aji ba haka ake cin abinci ba." Jimmalo jin abin da yace sai ranta ya ɓaci da sauri ta kalle shi."Wuce ka bai guri mara kunya, don ni karya ka zan yi." Ta ce mishi tare da daka masa tsawa. A maimakon ya wuce, sai ya kwashe da dariya, domin kamar shi ma irin taƙadiran yaran nan ne. "Maman aji! Maman aji." Ya fara ihu yana faɗin haka jin waƙar da yake yi, sai wasu daga cikin yaran suka ɗauka har da jan mata hijabi. Jimmalo cikin tsananin fushi ta miƙe tana huci kamar zata haɗiye su. Ita mamakinsu take yi domin in har za ta yi musu wani abu, tabbas sai ta illata wani. Tana shawarar ko ta ƙyale su, amma sai ya ƙara jan mata hijabi. Ba tare da dogon tunani ba ta fisgoshi tare da maka shi a ƙasa. Wani irin ihu ya sanya wanda ya sa yaran suka shiga taitayinsu. "Wayyo ƙafana ta karya ni." Ya furta cikin kuka yana taɓa ƙafar. Kallon yaran ta yi tana zare ido."Saura ku dama na gaya muku kashe ku zan yi." Ta ce tare da komawa ta zauna, ba tare da ta damu da ihun da yake yi ba Ganin ya kasa tashi yana tsala ihu, sauran yaran suka ruga da gudu suka sanar wa Anty. Da sauri ta shiga cikin tashin hankali. Mamaki sosai ya kamata, na rashin imaninsa tana cin abincinta hankalinta kwance. Da gudu ta ƙarasa gurinta ta zuba mata bulalar."Ke wace irin sheɗaniyar yarinya ce? Za ki kashe musu yaro?" "Shi ne sheɗani da ya tone n.." Kafin ta gama maganar ta ƙara zuba bulala. Wanda ya sanya ta zabura ta riƙe bulalar tana zare ido. "Dukana za ki yi? Ka ga mini fitsarrarriyar yarinya." "Wallahi kika ƙara dukana sai na rama tun da bance ya tone ni ba." Ta furta tare da ƙwace bulalar. Jin yadda jikinta yake da ƙarfi sai ta sakin mata, domin ko da ta gwada ƙwacewa a yadda ta ji karfin jikinta ba za ta iya ba."Saki ko in ƙara miki ƙatuwar banza kina ƙatotuwa da ke a sanya ki a cikin yara." "Kece jahila da kika kasa gane rashin kunya ya yi mini.."Ba ta ƙarashe maganar ba Principal ya shigo, ganin tana ƙoƙarin dambe da malamar sai wani ya ruga ya kira shi. "Safeeya Abdullahi, saki bulalar nan!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. Jin tsawar ya sanya ta saki tare da ƙunƙunai. "Ɗauke shi a ka shi asibiti." Ya furta tare da ƙarasowa ya fara zuba mata bulala. Tun tana jurewa har ta fara hawaye sosai. Hankalin Principal ya tashi lokacin da aka kira shi, aka sanar da shi Muntazar ya karye. Cikin takaici ya karɓi bulalar daga hannun sajan ya ci gaba da dukanta. "Ku yi mata shegen duka sai mu tafi gidansu." Don Allah ku yi mini hakuri na yau babu yawa saboda uzuri.🙏🙏🙏🙏🙏🙏 Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 23 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* Sai da suka yi mata dukan tsiya sannan suka tasa ta zuwa gida. Jimmalo ta ji dukan domin duk juriyarta sai da ta yi kuka. Mommy da Anty suna kicin girki suke yi. Anty ce take yin gudun kurna, sakamakon abinci da ba su cinye ba, ya sanya suka ba ri su yi da rana. Kicin ɗin ya ɗau kamshi Mommy duk ta kosa a kammala. Sai maganar yadda zai yi daɗi take yi, Anty na yi mata dariya. Principal tun a hanya ya kira Daddy ya sanar mishi, sannan ya rantse korarta zai yi, domin ransa ya ɓaci sosai ganin yadda iyayen yaron suka yi fushi. Zai iya cewa tun da yake a makarantar, wannan karon na farko kenan da ya faru. Daddy hankalinsa ya tashi sosai jin yadda yake magana cikin fushi. Duk haƙurin da yake ba shi bai saurare shi ba ya kashe wayar. Dafe kansa ya yi cikin takaici jin abin da ta yi. Kan dole ya baro kasuwan ya dawo hankalinsa a tashe. A lokacin da suka iso gidan, Maigadi ya shiga ya kira Mommy. Cikin fargabar wanda ke kiran ta fito ita. Tana fitowa ta ga Jimmalo ta ci kika tana zare ido. Gabanta ne ya faɗi sosai ta kasa ƙarasawa gurin. Sai da ta ɗan ɗauki lokaci cikin rashin madafa, sai ta ƙarasa tana faɗin,"Sannunku bayan Allah. Jimmalo mai kika yi?" Ta yi tambayar tana kallon Principal ɗin da ya ci magani. "Yarinyar nan ba ta da mutunci ta karya yaro." Salati ta saki sai ta rasa abin da za ta ce. Tana cikin wannan jimamin sai ga motar Daddy. Wani irin ajiyar zuciya ta saki ganinsa, domin ba ta san abin da za ta ce ba. Daddy parking ya yi sannan ya fito cikin motar cikin damuwa. "Jimmalo, ba kya jin magana ko? Saboda me za ki karya shi?" Ya yi mata tambayar, daidai lokacin da Captain ya sanya maigadi ya buɗe masa get zai fita. Ganin Daddy a gurin da Mommy ya tabbata ba lafiya ba, musamman yadda fuskokinsu suke ɗauke da tashin hankali. "Wannan sheɗaniyar yarinya mai ta yi?" Ya furta a ransa sannan ya fasa shiga cikin motar ya ƙarasa gunsu, daidai lokacin da ta ce,"Tonona ya yi ni kuma na yi masa ƙufula ɗaya." Dukanninsu babu wanda ya gane hausar da ta yi musu. Jin abin da ta ce Aliyu ya kawo mata mari ba tare da ya ji abin da ta yi ba. "Akwai sa'anki a gurin nan? Da za a tambaye ki ce kin yi masa ƙufula. Uban mene ne ƙufula." "Ɗaga shi na yi na maka shi da ƙasa." "Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Kika ɗaga ɗan mutane kika maka da ƙasa kamar dutse?" Daddy ya yi tambayar cikin damuwa. "Ai dole ki karya shi. Yaro ɗan primary one!" Mommy ta jinjina kanta tana faɗin haka. Aliyu zare idanunsa ya yi ya ce,"Ta karya yaro fa kuka ce?" "Karya shi ta yi, kuma babu ruwan mu da hukuncin da iyayen yaron za su ɗauka, sannan mun koreta daga makarantar." Jin abin da ya ce sai ya harzuƙa Aliyu. Da sauri ya kama hannunta yana faɗin,"Tun da kika karya yaro saboda rashin imaninki. Nima sai na karya ki." Kafin su yi aune ya murɗa hannunta da ƙarfi. Wani irin ƙara ta saki jin zafi yana shiga ƙwaƙwalwarta. "Aliyu lafiyarka kalau, in ta karya shi ka ma sai ka ƙaryata?" Daddy ya yi masa tambayar cikin ɓacin rai tare da daka matsa tsawa. "Zalinci ta yi dole a rama masa. Shashashar banza daƙiƙiya ko kunyar ba kya ji. Kina cikin ƙananan yara, ba dole ki yi zalunci ba." "Wayyo Allah! Mugu kawai azzalumi. Wallahi ya karya mini hannu." Ta furta tare da saka ihun da sai da suka matsa. "Aliyu, kar na ƙara ganin haka in ba sulhunta zancen za ka yi ba, maza ka bar gurin nan." Daddy ya ce masa yana nuna masa hanya. Babu musu ya juya domin bai zo don ya sulhunta. Abin da ya kawo shi ya yi zuciyarsa fes ya shiga cikin gidan don ya shiga mota. "Yaron nan ba shi da imani da gaske ya karya ta." Cewar Mommy ganin yadda take ihu domin ko ba karaya bane, tabbas ya yi mata tsaguwar kashi ko targaɗe. Principal sai ya tsaya cikin mamakin abin da Aliyu ya yi, sannan ya tafi ba tare da tausayi ba. "Ni fa ban kawo muku ƙara ba, don ku ƙaryata. Ku dai shirya duk matakin da iyayen yaran za su ɗauka." Ya ce ma Daddy yana kallonsu. "Tare zamu tafi asibitin gurin yaron. In sha Allahu zan sasanta lamarin. Mommy ki shiga da ita ciki, ki sanya direba ya kaita a gyara mata hannun." Ya ce mata yana kallonta. Jin abin da ya ce sai ta kama hannu Jimmalo da take ta ihu tamkar an kashe ta. "Wayyo hannuna ya karya ni kaka Tani." Ta furta tana kallon hannun da har ya fara tasawa. "Mu shiga ciki ko ranki ya ɓaci. Ai kin cancanci haka tun da shi yaron da kika karya ba mutum bane. Haba Jimmmalo wallahi ba kya jin magana." Mommy ta daka mata tsawa tana faɗin haka. "Wallahi sai na rama, tun da ya karya mini hannu sai nayi masa tabon da ba zai manta da ni ba." Ta furta tana ɗaga hannunta da yake raɗaɗin zafi. "Ba kya ji ko? Zuwa zaki yi ki ƙara takalarsa. Allah ya ba ki sa'a kin san ke za ki wahala." Ba ta ce mata komai ba, tana kuka ganin haka sai ta kama hannunta suka shiga ciki. Anty da take juye abinci a kula ta ji kukanta yana tashi, Mommy na yi ta mata faɗa, wanda ya sanya ta rufe ƙular da sauri ta fito suka yi magama a falo. "Subuhanallahi! Ciwo ta ji?" Ta furta tare da isa gareta ta kama hannun. "Yarinyar nan tsaf za ta iya kashe mutun da mugun halinta. Zuwa ta yi ta karya yaron mutane. Shi ne masu makarantar suka kawo ƙara. Shi kuma Aliyu ya karya ta ita ma." Salati ta saki tare da zare idanu. Sai ta rasa cikinsu wa yafi rashin imani. "Jimmalo, da gaske kin karya yaro? Shi kuma Aliyu yana da hankali kuwa?" "Na rasa hukuncin da zan yanke. Yaran nan so suke su kashe ni." Ta furta tare da zama kan kujera. Fuskarta bayyane da damuwa dake xuciyarta. Ganin ihun da ta ishe su da shi. Kan dole ka je asibiti aka gyara mata hannu. Mamakin kukan da ta yi suke yi, saboda targaɗe ba karaya ko tsaguwar kashi ba. "Idan ke kina kuka haka, shi kuma yaron da kika karya sai ya mutu ko?" Anty ta yi mata tambayar tana kallon hannun daya suntuma. "Rashin kunya ya yi mini kuma na gaya musu zan iya karya shi." Tsaki suka saki a tare ba tare da sun ce komai ba, domin kowa ta kai shi wuya. Da suka koma gida, tana ta kuka da ƙyar Anty ta rarrasheta sannan ta ji abinci. Da ta tuna an koreta a makarantar, sai hankalinta ya kwanta ta daina jin zafin ciwon, amma ta ɗau alwashin tun da ya ƙaryata, sai ta yi masa abin da ba zai manta ba. Tana zaune har sauran yaran suka dawo. Nan suka yi mamakinta sosai domin ta wuce tunaninsu. Hanifa da Mufida da suka dawo gidan ƙawarsu, sun cika da mamakin abin da ta yi. Da ƙyar Daddy ya samu aka kashe zancen, bayan ya biya kuɗin da aka kashe, sannan ya toshe bakin iyayen da kuɗi. Yana asibitin har sai da aka yi kiran sallah. Sam ya manta da batun abinci saboda samuwar da yake ciki. Abin da ta yi sai ya ci alwashin sai ya yi mata dukan tsiya, amma sai kuma Aliyu ya yi hukuncin mahaukata. Da ya dawo, faɗa sosai ya yi mata kamar zai aro baki. Ita dai hankalinta a kwance. Burinta ya ce ba zai iya zama da ita ba, sai a a haɗa ta da Anty Amarya ta koma gidanta. Tana wannan tunanin sai ta ji ya ce,"Dole ki koma makaranta, domin ba za ki rayu da jahilci ba Ko islamiya har na siya miki form. Jira na ke a yi miki ɗinkin kayan islamiya da hadda." Wannan mummunar albishir da ya yi mata ya sanya xuciyarta ɓaci. Fuu ta yi ɗaki ta faɗa kan gado. Kuka ta ci gaba da shi, babu wanda ya kula ta har Anty Amarya saboda ita kanta haushinta take ji. Anty Amarya da take tunanin za ta fito amma shiru. Ganin haka ta ɗauki abincinta ta shiga dakin."Ki tashi ki ci abinci." Tana kwance ba ta motsa ba jin abin da ta ce."Sam ba kya ji Surfy. Ba za mu shirya ba in har kika ce rashin ji za ki yi." Ita kanta sai ta yi mamakin rashin jin daɗin da ba ta ji ba, da furta hakan domin ko lokacin da Kaka Tani take nan ba ta damu ba don ta yi fushi. "Shi ne ya tone ni." "To sai ki karya shi?" Ta yi mata tambayar cikin ɓacin rai. Ganin yadda fuskarta ya bayyana damuwar fushinta sai ta hau kan gadon."Kar na ƙara jin kin yi haka. Maza ta shi ko ci abinci. Kin ga ga shi kin ja Aliyu ya ji miki ciwo." Har ta buɗe baki za ta yi magana, sai ta ga rashin dacewar sanar da ita abin da za ta yi masa, domin ta san a ƙarshe cewa za ta yi kar ta yi. Ita kuma ta rantse sai ya yi kukan da ya fi nata. "Ki ci abincin." Ta furta tana kallonta Babu musu ta janyo filet ɗin za ta sauka ƙasa, wanda ganin haka ta taimaka mata ta saukar da abincin kasa. Anty Amarya sai da ta tabbatar ta ƙoshi, sannan ta kaya zuwa falo suna kallo. Mufida damuwa sosai ta shiga ganin har ana gobe za su tafi ba ta samu hanyar da zata sa mishi maganin ba. Tana wannan tunanin duk suna falo sai aka kira Mommy a waya. Kamar ance ta saurara sai ta ji tana faɗin,"Ok, yanzu za ta kawo maka har da ruwan tea da na dafa maka." Tana kallonta har ta kashe wayar ta kalli Umma ta ce,"Yayan ki ya ce ki kawo masa abinci, sannan ki juye ruwan shayinsa a fulas." Da sauri ta tashi jin abin data ce. Ganin haka sai Mufida ta bita zuwa kicin ɗin. Tana ƙoƙarin juye ruwan flaks sai ta shigo."Na ga ba ki so ki taso daga kallon ba. Ki kawo na kai mishi sai ki je ki ci gaba." Ta furta cikin murmushi da sakin fuska. "Wallahi, da yake ina son na kalla ban ga na wannan satin ba, amma kar ki damu zan kai mishi." Ta ce da ta tuna zai iya mata faɗa. "Don Allah ki bani na kai masa, dama ina son nayi masa maganar ya biya mini kuɗin makaranta, saboda wannan semester Baba ya ce ba shi da kuɗi ne tambaye shi." Ɗan jim ta yi, domin ta san da wuya in haka ne. Tsoro take kar ta je ta yi masa kwarkwasa, saboda ta san tana son sonshi, amma tun da ta roƙa babu yadda za ta yi. "Ok, ga shi sai ki haɗa masa da ruwan tea." "Ok, na gode. Bari na nemi tawul na ƙara gogewa kin san yayan namu mai tsafta ne." "Da yake kular a tsaftace take, amma ni dai na tafi kallona ke kika sani." Ta ce mata tare da ficewa da sauri tana ja mata ƙofa. Fitan ta yi sai ya yi mata daɗi sosai, da sauri ta ciro ƙunshin maganin da tun da ta zo da shi take yawo da shi, amma ba ta samu hanyar sakawa ba. Tana ƙoƙarin zubawa Jimmalo da ta ji tana son shan ruwa, sai ta nufo kicin ɗin don ta iba a famfo, domin duk frij ɗin gidan ba ta iya buɗewa ba. "Kai! Uban wa za ki kashe?" Ta ji ta yi mata tambayar da ya razana ta, wanda ya sanya ta juyo da sauri cikin tashin hankali, amma kuma ganin Jimmalo ce sai hankalinta ya ɗan kwanta kamar ta yi baƙo ya mutu, domin sam ba ta ɗauke ta a masu hankali ba. Kasa amsa mata tambayar ta yi, tana in'ina wanda ganin haka ta ce,"Na rantse sai kin gaya mini ko na gaya wa mutanen gidan, domin tun da kika zo ban yarda da ke ba, sai wani zare idanu kike yi, sannan kina kallon Anty Amarya a yatsine in tana magana da Hanifa." Sosai ta yi mamakin abin da ta ce, saboda ba ta taɓa tunanin za ta iya gane hakan ba. "Tun da ba zaki gaya mini ba, sai na gaya wa mutanen gidan."Ta ƙarashe maganar tare da wage baki za ta yi ihu Da sauri ta toshe mata baki ta ce."Ba fa kisa zan yi ba. Ni musulma ce da imani." "To me kike sawa a abincin!" Ta jefa mata tambayar. "Abincin Ya Aliyu ne kuma ma...." "Kashe shi za ki yi? In har kashe shi za ki yi ba zan damu ba, domin babu amfanin rayuwar mugu azzalimi." Ta furta abin da Mufida ta karanta har cikin zuciyarta, wanda ya sanya ta ce,"Eh, ka.sh..e shi zan yi saboda kamar yadda yake miki mugunta haka ya yi mini." "To me kike jira ki sanya masa maganin da yawa, yadda da yaci zai fara shure-shure, domin na tsane sa da zan samu dama zan iya kashe shi." Ta furta tare da rufe mata kofar cikin farinciki. Mufida sai ta cika da mamaki sosai jin bin da ta ce. A yadda ta nuna a fuskarta da gaske ba za ta gaya wa kowa ba. Mamaki sosai na tsanar da suke wa junansu. Cikin kwanciyar hankali ta saka maganin ta ɗauka. Gabanta na dukan tara-tara ta kwanƙwasa ƙofarsa. A tunaninsa Umma ce don haka ya ce,"Yes, come in." Yana zaune daga shi sai gajeren wando babu riga. Gefensa abokinsa Imran yana danna wayarsu suna hira. Ɗaurewa ta yi ta shigo. Ganin yadda yake sai jikinta ya kama rawa ta kasa ƙarasawa. Captain Aliyu yana kallon wayarwa ya ce,"Umma, ije Allah ya sa kin zuba da yawa, na manta na ce miki ina tare da Imran, duk da ba da...." Maganar ta maƙale masa lokacin da ya ɗago ya ga Mufida ce. "Ke! Are You stupid?" Ya ce mata tare da miƙewa yana zare mata idanu. Ganin yadda ya daka mata tsawa sai ta ije abincin ta fice da sauri. Tsaki ya yi ya zauna."Yarinyar nan ba ta da hankali, amma zan koya mata." Ya ce yana hararar abincin. "Hmmmmh. In dai ka ga kare na shinshinan takalmi dauka zai yi." Ya ce tare da jawo abincin ya fara ci. "Ashe kuwa iska na wahalar da mai kayan ƙara." Ya furta tare da komawa ya zauna, ba tare da ya kalli abincinba domin ya fita ransa. Imran ya ci abincin sannan ya tashi ya tafi. Bayan ya raka shi ya kira Umma ta kwashe kwanukan. Mufida,cikin fargabar kar su ci abincin su biyu ta fice daga ɗakin. Duk yadda ta damu da ta sanya maganin, amma xuciyarta ba ta yi farinciki da samun nasarar sakawa da ta yi ba. Falo ta dawo ta zauna, xuciyarta cike da tsoron kar Jimmalo ta gaya musu, amma sai ta ga babu abin da ya dame ta, sai kallonta da take yi, so take tambaye ta ko ta sanya. Fuska ta daure ta mayar da hankalinta kan tibi, amma sai da ta san yadda ta faki idanun mutane ta koma gefenta ta zauna cikin raɗa ta ce,"Kin sanya mishi?" Duk da raɗa ta yi mata, sai da ta zare idanunta tana kallon mutanen falon. Ganin hankalinsu bashi a kansu sai ta kalle ta da tayi mata ƙuri, xuciyarta na addu'ar Allah ya sanya ya mutu a yau. "Eh na sanya maganin amma a hankali zai shiga jikinsa." "Da kin sani wanda zai ci nan take ya fara shure-shure kika siya." Ta furta xuciyarta a ƙuntace ta koma gurinta ta zauna. Hamdala ta yi, tare da sauke ajiyar zuciya ganin ta koma gurin da take zaune, a xuciyarta mamaki take yi domin Jimmalo ta wuce a kira ta mahaukaciya. Da safe bayan sun karya suka fara shirin komawa. Tun da Jimmmalo ta fahimci hakan, sai ta fara haɗa kayanta ta kafe kan dole tare za su tafi. Nan fa aka shiga dirama musamman a lokacin da suka fito. Duk rarrashin da ta yi mata ta kafe kan dokin na ƙi. Da ƙyar Anty Amarya, ta samu ta shawo kanta bayan ta yi mata alƙawarin da zarar sun yi hutu za ta kira a kawo ta yi hutu. Sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinta domin har xuciyarta take ƙaunarta. Ita ma rungume ta tayi tana jin tausayinta don jinta take yi kamar Surfy ƙanwarta da suka fito ciki ɗaya. Tana rarrashinta rungume da juna, a haka Aliyu ya fito da makullin mota yana karkaɗawa. Yayi kyau sosai, domin in har da abin da yafi kyau za a iya fasalta shi da shi. Kasancewar in ya kaisu Kaduna zai wuce Abuja, sai ya shirya cikin kayan sojoji. Kayan sun yi masa matuƙar kyawu sosai. Yana riƙe da wayarsa, da makullin mota sai glass ɗinsa da yake ƙoƙarin sanya wa. Ganin su a haka ya dakata tare da daka wa Jimmalo tsawa."Haba Anty! Wannan kucakar yarinyar za ki bari ta shiga jikinki? In har kina son mu shirya gaskiya ki daina kula ta." Ya furta tare da watsa mata mugun kallo yana bata fuska. Sakin juna suka yi Jimmalo ta watsa masa mugun kallo."Anty Amarya, don Allah kar ki manta alƙawarin ki?" Ta ce tana share hawaye. Murmushi ta yi tare da ɗauke mata hawayen ta ce,"Ba zan manta ba 'yar ƙanwata, amma ki tuna na gaya miki kar ki rinƙa sanya wa Mommy damuwa?" "To," Ta furta a sanyaye. Tsaki ya saki ya shiga cikin motar, tare da sakin musu hon babu ƙaukautawa. Mufida da Hanifa, a lokacin da ya fito da suka bi shi da kallo tamkar sabbin mayu. Ko wacce tana fatan ina ma ace wannan mamallakin surar ya zamo mallakinta. Jimmalo da Mommy suna tsaye har ya fara tuƙa motar. Mommy sosai take musu addu'ar isa lafiya har suka fice. Mommy sai ta kalle ta ganin yadda ta sha kunu. Xuciyarta cike da tsoron kar ta koma gidan jiya. Jimmalo bayan tafiyarsu ta shiga damuwa sosai. Haka ta wuni suku-suku har dare. Daddy hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya tabbatar da Principal ya haƙura sannan ya kaita makarantar da kansa, bayan ya yi mata kashedi sosai. Ba ta tanka ba ballantana ya sa ran ta ji. Haka ta ci gaba da zuwa duk da xuciyarta ba ta so, amma babu yadda za ta yi. Addu'arta kullum lokaci yayi ta je gidan Anty Amarya. Captain Aliyu ya so su je a kwanakin da ya so, amma sai kuma aiki ya riƙe shi wanda kan dole ya bar zuwa ƙarshen wata. Lubaiynah kamar yadda suka tsara shirin su. Sau biyu tana zuwa gidansa, amma Solo ya hana ta shiga. A na ukun sai ta je gidan Kalim. Bayan sun gaisa Kalim ya sanar da ita ta yi haƙuri sam Captain ba zai aure ta ba. Mamakin mugun son kansu ya kamata. Wato su lalata mace sannan su ƙyama ce ta, domin tun da Captain ya yi mata hakan shi ma ba zai ƙi yasar da budurwarsa a bola ba. Sai ta rinƙa kallon sa kawai. "Eh, ni ma na haƙura da shi, saboda na ga sam ba zai aure ni ba. Yanzu ma na zo ne na gaya masa na samu miji zan yi aure." Jin abin da ta ce sai Kalim ya ce,"Yauwa da kyau. Gara da kika cire zuciyarki ga wanda ba ya ƙaunarki. Shi ma Captain In sha Allahu Ya kusa aure, domin ya sanar mini ya samu matar aure." Lubaiynah, ba ƙaramin ƙoƙari ta yi da ta ɓoye tashin hankalinta ba. Ji ta yi tamkar sama da ƙasa za su faɗo mata. Sai xuciyarta ta ƙara gasgata mata captain ba ya ƙaunarta, domin za ta iya sanya shi a cikin maƙiyinta na ajin farko. Bayan ya lalata rayuwarta ya kawar da abin da ko wace mace take tutiya da shi. Sannan zai je ya auri wata mace. Sai ta ji xuciyarta na bugawa da sauri, har ta ji ba za ta iya jure tashin hankalin da take ci ba, domin in har ta tsaya Kalim zai fahimci tuban maxuru ta yi, sannan ya gane da wata manufa ta zo. "Masha Allah! Allah ya tabbata da alkhari. I want to use the restroom." Ta yi ƙoƙarin sanya dakiya a xuciyarta ta furta hakan cikin rawar murya. Duk yadda ta so ta daure, amma sai da ya fahimci halin da take ciki. Sosai ya tausaya mata ganin yadda lokaci guda fuskarta ta canza. "Amin, You can go in." Ya ce mata yana nuna mata hayar bayin. Murmushin yaƙe ta yi tare da miƙewa ta ce,"Thanks." Sai ta wuce cikin sanyin jiki. Kafin ta shiga cikin bayin ta ji hawayen da take ƙoƙarin mayar wa sun zubo a kuncinta. Tana shiga ta fashe da kuka sosai. Anya akwai wanda ya kai Captain zalunci kuwa? Ta ya ya zai yi mata haka? Ko da ace bai keta haddinta ba, ba ta iya jin za ta iya barin ma wata 'ya mace shi, ballantana ya kwashe abin da yake da daraja da ƙima a rayuwata. Gudun kar Kalim fahimci kuka ta yi sai ta yi ƙoƙarin tsaida kukan. Ta wanke fuskarta da ta ci sa'a ba wata kwalliya ta yi mata ba da za ta fito. Kalim, da hankalinsa yake kan wayarsa, jin ta buɗe ƙofa sai ya kalleta. "Are You ready?" "Yes," Iya abin da ta iya furta masa kenan. Tafiya suke yi, amma babu wanda yake wa juna magana. Ko da ace yana mata sam ba za ta ji shi ba, domin xuciyarta ta yi balaguron yadda za ta rama abin da ya yi mata. Kalim ganin halin da ta shiga sai ta ba shi tausayi. Ya san cewa dole za ta yi kishi. Captain Aliyu zaune kan dinning yana cin abinci. Ya ga kiran Captain Kalim. Ba tare da tunanin tare yake da Lubaiyna ba, sai ya miƙe ya buɗe masa ƙofa. Yana tsaye da ga shi sai gajeren wando. Duk halittun da sun bayyana waje. Ganin Lubaynah sai ranshi ya ɓaci ya tokare ƙofa. "Saboda me za ka shigo mini da ita?" Tambayar da ya yi masa, sai ya shanye mamakin tokare ƙofa da ya yi. "Don Allah Captain ka saurare ta Lubaynah ta tuba, domin ta zo ta yi maka bankwana za ta yi aure." Ya furta yana kallonta da hawaye suka cika idanunta. Mamaki take yi yadda yake sanya ta a cikin ɗaki yana gaya mata kalaman ƙauna. Yana gaya mata babu macen da zata shayar da shi zuma irin nata, amma yau yake mata korar kare a gidansa. Sai ta ji zuciyarta ta kara ƙeƙashewa za ta iya komai don ta aure shi. "Kana tunanin da gaske take yi? Na gaya mata na tuba na yanke duk alakar dake tsakaninmu, domin duk ranar da na bari mahaifina ya sani, sam hukuncinsa ba zai yi mini daɗi ba." Jin abin da ya ce, sai ya ƙara ƙarfafa mata gwiyar ta je ta aiwatar da ƙudurinta, domin shi ma ya ɗanɗana abin da ta ji. "Tabbas ina sonka amma na haƙura da kai, saboda na fahimci na yi kuskure. A halin yanzu na zo na yi maka bankwana, domin na zabi ɗaya daga cikin manemana zan yi aure." Jin abin da ta ce, sai hankalinsa ya kwanta duk da cewar bai gama yadda da ita ba. Ganin yana shakku sai ta kalle shi ta share hawaye ta ce,"Kai ma Captain Kalim ya gaya mini za ka yi aure?Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta furta xuciyarta na ba amin ba. Jin abin da ta ce, sa jikinsa ya yi sanyi ya kauce suka shiga. Kalim miƙewa ya yi ya ce,"Bari na je gidana." Hmmm! Lubaiynah abin da za ki yi da za ki ji shawara dai na ce gara ki barshi, amma duk wanda ya ƙi ji.... Tsokaci Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne. *ƘIYYAYYAR JINI!* NA *JAMILA LAWAL ZANGO* (Jamsy) *FIRST CLASS WRITERS* MARUBUCIYAR Sakacina ko halin maza Kura da fatar akuya Ranar wanka... Wasu mazan And now Ƙiyayyar jini! 08144072423 PAGE 24 *Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke* *Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so* *ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa* *MTN 1gb 650* *2gb gb 1300* *Iya adadin da kuke so muna turawa* *"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa* *Arabian oud* *Lamsa oud* *Black oud* *Da Duk wane oud da kake nema* *Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa* *Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin* *S D Y COLLECTION AND KITCHEN* *Adress ringi road, na dorayi, kano* *muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah* *Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *08130902505* Jin abin da ta ce, sai hankalinsa ya kwanta duk da cewar bai gama yadda ba. Ganin yana shakku sai ta kalle shi ta share hawaye ta ce,"Kai ma Captain Kalim ya gaya mini za ka yi aure?Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta furta xuciyarta na ba amin ba. Jin abin da ta ce, sai jikinsa ya yi sanyi ya kauce suka shiga. Kalim miƙewa ya yi ya ce,"Bari na je gidana." Duk da ba haka ya so ba, saboda ya so ace sun fita tare, amma kuma tafiyar sai ta yi masa daidai. Don ya samu damar da zai roƙe ta yafe mishi. Shiru suka yi, kowa na tsaƙa abin da ke xuciyarta har ya fita. "Lubaynah, am sorry kan abin da na miki. Don Allah ki yafe mini ina miki fatan alkhairi Allah ya ba ku zaman lafiya." "Amin," Ta furta cikin zuciyarta amma a fili sai ta ce,"Ba Amin ba mugu azzalumi." "Duk abin da kike so, zan ba ki shi Lubaynah in har za yafe mini. Ki faɗa mini nawa kike so zan yi miki transfer." "Babu abin da na ke so, wanda ya wuce ka bar ni na kwana a gidanka yau, sannan ka ɗauke ni a matsayin ƙanwarka. Mu ci gaba da zumunci mu zama 'yan'uwa. Bayan aurena, za ka zo ka ba Daddyna haƙuri." "In sha Allahu, mun zama 'yan'uwa, kuma ina ƙara ba ki haƙuri." "Babu komai domin duk kuskurena ne. Na gane bai kamata mace ta mallaka wa ɗa namiji jikinta da sunan soyayya ba, domin shi ne na farko wanda zai tsane ta." Shiru ya yi, ba tare da ya ce komai ba, duk da cewar magana ta gaya masa, domin ya kauda shurin sai ya miƙe ya cika gabanta, da abubuwan sha har da abinci. "An sanya ranan ne?" Ya yi mata tambayar yana zaunawa, bayan ya canza tasha da ga kallo zuwa karatun Alkur'ani. "A'a sai Daddy ya dawo daga Umrah." Ta furta tana kallon sa. Ganin shirun ya yi yawa, sai ya miƙe ya shiga cikin ɗakinsa, domin kunyarta sosai yake ji. Ya san cewa bai yi mata adalci ba, amma rabuwar ta su ita ce mafita. Babu yadda zai yi, kan dole ya haƙura ya barta ta kwana ba don ya so ba. Mamaki sosai ya kamata ganin ya kwana a falo. Sai ta ji xuciyarta ta ƙara tsinkewa, amma kuma wani bangare nazuciyarta, sai ta ji daɗi don ta samu ta aiwatar da kudirinta A daren kafin su kwanta ya sanar da ita cikin satin zai je ganin yarinyar wanda yake fatan a ranar su sasanta kansu. Ta ji babu daɗi sai ta yi masa fatan alkhairi. Cikin nasara ta samu ta sanya masa condom ɗin, don ya gama shirin kayan da zai yi tafiyar. Washegari ganin ta sanya masa, sai ta yi masa sallama ta tafi. Sosai ya nauyaya akawunta har sai da ta ji jikinta ya yi sanyi, amma kuma sai ta dake domin ya kasa gane ba kuɗin shi take so ba. "Don Allah in ka je Kaduna ka kira ni, ka haɗa ni da Mommy da su Nufaisah." "In sha Allahu, bayan kun gaisa zan tura miki da numbobinsu." Sai ta kalle shi kawai, tuna lokacin sun tare ta yi ta masa magiya ya ba ta numbar Mommy, amma da yake ya san ba alkhairi suke shukawa ba sai ya hanata. Har tasha ya kai ta sannan ya biya kuɗin mota, don akwai inda za su je a gurin aiki da shi ya kaita. Hankalinsa ya kwanta lokacin da ta tafi. Lubaiyna a maimakon ta wuce Kano, sai ta wuce gidan su Fadila. cikin kuka ta faɗa jikinta. "Captain da gaske aure zai yi har ya samu mata. Captain ya yi mini adalci da zai wofintar da ni? Soyayya ce ya sanya mallaka masa jikina. Da bakinsa ya ke gaya mini, wacce zai aura yar gidan malamai mahaddaciya." Ta ƙarashe maganar tana riskar kuka. "Kai amma soja ba shi da hankali da kunya. Wato a tunaninsa ya ci banza kenan? To wallahi bai isa ba, don sai kin zame masa ƙadangaren bakin tulu." "A shirye nake na aiwatar da komai. Ashirye na ke, ko da kisa zan yi don na mallake shi, raba ni da budurcina da ya yi dole sai ya aure ni ya ɗanɗana ɗacin da zan ji in ya rabu da ni." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin kuka. "Za ki aure shi, ba ki da miji sai shi." Ta ce mata tana shafa bayanta. Da ƙyar ta samu ta yi shiru ta daina kuka, sannan ta tafi Kano cikin tsananin damuwa. Bayan su Anty amarya sun koma, Hanifa sai ta shiga damuwa, domin ƙwarin gwiwarta ya fara saki ganin har suka je suka dawo babu kallon arzikin da ya shiga tsakaninsu. Za ta iya cewa saboda su ya rinƙa fita yana barin gidan. Hakan ya ƙara mata rashin ƙwarin gwiwa. Mufida kuwa, cikin damuwa ta sanar wa Mama duk abin da ya faru. Jimm ta yi ta ce,"Yanzu kina nufin tare suka ci?" "Damuwata bana tunanin ya ci, saboda daga ganin na kawo masa abincin ba ki ga yadda ya ɓata ransa ba. Bana tunanin ya ci abincin ma. Allah ya sa dai ko wancan ya ci babu matsala?" "Babu matsala, domin malamin ya gaya mana shi ne kawai zai yi wa aiki. Ki kwantar da hankalinki zan ƙara zuwa gurin boka kawai za mu je, domin na ga sai an sanya rauhanai sun yi mana aiki a kansa." "Yauwa Mamata shi ya sa na ke sonki." Ta ce tare da rungume ta. Kamar yadda ya tsara, ƙarshen wata ya shirya don ya je, amma sai ya kwana a Kaduna, sannan ya wuce Zariya su ƙara tautaunawa da Anty. Tun safe ya iso. Mommy ta cika da farinciki jin zai je ganin mata. Tun lokacin da ya sanar mata take masa fatan alkhairi. Jimmalo, saboda islamiya da boko da take zuwa ba ta san ya zo ba, sai bayan ta dawo daga islamiya tana zaune a harabar gidan ya fito daga sashinsa. Wani tsuka ta ja mai ƙarfi tana aika masa da harara. Ta saki tana zuwa makaranta da islamiya duk da babu abin da take ɗauka. Burinta ayi hutu taje gidan Anty Amarya da wani lokacin Mommy tana kiranta su gaisa, musamman in ta ƙi sallah ko ta yi rashin kunya. Sai aka yi sa'a, sam hankalinsa ba shi a inda take ballantana ta ji tsakin. Ganin ya shiga ciki sai ta ci gaba da wasanta, kamar kuma ance ta miƙe sai ta yi hanyar ɗakinsa. Ganin ɗakinsa a buɗe, sai ta tsaya tana tunanin yaune Allah ya ba ta sa'a, zata rama karya mata hannu da ya yi. Har ta dumfari kofar, sai ta ji muryar Umma tana kiranta a bayanta. "Safeeya, kina ina Mommy na ta neman ki?" Ta yi mata tambayar tare da ƙarasowa. Jimmalo, sai ta ɗan haɗe rai, duk da cewar yanzu ta saki dasu har magana take musu, amma ba sosai ba sai in tana cikin farinciki. "Ina kallon gidan ne." Ta ce mata tare da juyawa za ta tafi. "Ok, ni kuma ya Captain ya ba ni ɗan makullinsa na gyara masa ɗakinsa, ashe bai kulle ba." Ba ta ce komai ta wuce ta bar gurin. Umma da ta shiga ta ɗauko masa wayarsa da ya umurce ta je don ta kai mishi ta dawo. Ganin ta bar gurin ta koma, da sauri tana addu'ar kar ta dawo sai ta aiwatar da kudirinta. Sa dai ko da ta shiga, babu tarkace a cikin ɗakin komai a killace, ballanatana ta ga inda yake ije takaddunsa ta yaga don su zama jahilai ya daina kiranta da jahila. Ganin ba ta ga komai ba, sai ta fara duba jakarsa da ya zo da ita, nan ma babu bin da ta gani, sai kayansa da turare sai brush da makilin. "Laa! Ashe yana wasa da bulumbulum!" Ta furta cikin zallar mamaki lokacin da ta ga condom. Cikin sauri ta tura a cikin siket ɗinta, tana murna za ta yi wasa da shi. Jin tafiya sai ta fito da sauri, da takaicin ba ta samu komai ba. Umma ganin ta a ciki mamaki ya kamata."Safeeya, lafiya mai kike yi a cikin ɗakin Ya Captain?" Ta yi mata tambayar tana kallonta da tuhuma. "Babu komai." Ta ba ta amsa tana ƙoƙarin fita fuskarta a ɗaure. Duba ɗakinsa ta yi sai bata ga komai, da zata zarge ta ba, saboda ta mayar da kayan. Ganin haka sai ta gyara masa ɗakin ta wuce cikin gida. Jimmalo ba ta fito da bulumbulum ɗin ta ba, sai washegari da ya yi tafiyar, don har ta manta sai kawai ta tuna. Cikin sauri ta ɗauko cikin kayanta sannan ta fito waje tana ƙoƙarin hurawa, amma duk yadda ta so ta hura ya ƙi tashi irin na bulumbulum. "Kai wannan bulumbulum na manya ne bari na zuba masa ruwa." Ta ce tare da ƙarasawa bakin tanki ta fara ɗura ruwa a cikinsa. Nufaisah, da ta fito da gudu-gudu sauri-sauri za ta fita daga gidan, saboda makaranta za ta je kuma suna da test ta yi latti. Har ta wuce Jimmalo, sai kuma ta ja ta tsaya cikin mamaki tana zare idanunta. "Safeeya, ina kika samu wannan abin? So kike cuta ta kama ki?" Ta yi mata tambayar tare da ƙarasawa gurinta tana son ta ƙwace. Matsawa ta yi ta ɓoye condom ɗin a bayanta. "Ba zan ba ki ba, bulumbulum ne na ke wasa da shi." Jin abin da ta ce, sai ta kalle ta cikin mamaki."Ba bulumbulum bane condom ne." "Ni fa ban san wani candoom ba, kawai ki bar ni na yi wasa da shi." Ta ƙarashe maganar za ta gudu. Da sauri ta kai hannu za ta ƙwace ta ce,"Cuta ake samu a cikinsa a gina kika samu? Sannan abin da ake y.." Sai kasa karasa maganar rashin sanin yadda za ta gaya mata abin da ake yi da shi. "A ɗakin wancan mai kama da zabiyan." "Kina nufin ɗakin Ya Captain?" Ta yi mata tambayar cikin shakku da razana. "Eh, a ɗakinsa na samu, na san kuma so kike na baki ki mayar masa." Mamaki da al'ajabin abin da yake yi da shi ya kama ta. Fara tunanin ta yi ko ƙarya take masa, amma ganin yadda take sanya abin a bakinta tana hurawa, sai ta gasgata bata san abin da ake yi da shi ba. "Ke nan ya Captain ɗan iska..." Ta kasa ƙarashe zancen tana son kore tunanin da ya zo mata. "Kai Ya Captain mutumin kirki ne." Ta ce tare da surfatan Jimmalo, zata kamata ta karɓe don ta rufe sirrin ɗan'uwanta. Kamar ta fahimci abin da take shirin yi, sai kawai ta ruga Nufaisah ta bita zuwa falo, tare da addu'ar Allah ya sanya babu kowa a cikin falon. Tsananin tashin hankali ya kamata, ganin Mommy da Daddy suna saukowa. Don haka ta juya zata fita, gudun kar Jimmalo ta nuna musu. "Nufaisah, kika ce mini kin yi latti?" "Eh, mantuwa na yi." Ta furta tana sosa kanta. "Ƙarya take yi Mommy, za ta kwace mini bulumbulum ɗina ne." Ta furta tare da ɓoyewa a bayanta. "Bulumbulum, a ina kika samu bulumbulum? Kar dai kin fara ɗaukan kayan mutane a makaranta?" Daddy ya yi mata tambayar yana murmushi. "A ɗakin mai kama da zabiya na..." "Ba na gaya miki Yaya zaki rinƙa ce masa b...." Maganar ta maƙale wa Mommy, ganin Jimmalo ta tura bakinta, ta fito da condom ɗin za ta sanya a baki ta hura. "Innnali wa inna ilahir raju'un! Safeeya, ina kika samu wannan?" Suka yi mata tambayar cikin tsananin razana. "A ɗakin Ya Aliyu." Ba ta san lokacin da ta kira shi da ya Aliyu ba ganin yadda suka ruɗe. "Condoms?" Suka haɗa baki gurin faɗi, lokacin da Mommy ta sanya hannu ta karɓa. Ganin yadda suka razana, sai ta sakin musu tana zare idanu, domin ta yi tunanin mutuwa ta riƙe a hannunta. "Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Daddy ya furta yana mamakin abin da ya kai condom ɗaƙinsa." Mommy kuwa ji ta yi kanta yana juyawa, ta fara zargin yana bin mata ne. Nufaisah, sai ta rasa tunanin da za ta yi, ta manta makaranta za ta je. "Aliyu mazinaci ne?" Daddy ya yi musu tambayar cikin tsananin tashin hankali. Mommy ta rintse idanunta, jin mummunar sunan da ya danganta shi da shi. "Kai Aliyu mutumin kirki ne, na yarda da tarbiyyar da na ba sh.." Kafin ta gama maganar sai Lubaynah ta yi sallama ta shigo, wacce ta tsaya a bakin ƙofa jin ana magana cikin tashin hankali. Nan ta ji duk abin da ke faruwa, sai ta yi murmushin nasara ta shiga ciki. Saboda tashin hankalin da suke ciki, sai suka kasa amsawa har ta yi sallama na uku. Da ƙyar Nufaish ta amsa tana kallon fuskarta. Ganin baƙuwar fuska, sai suka yi ƙoƙarin ɓoye damuwar da ke fuskarsu, amma zuciyarsu zafi take musu, musamman Daddy, yana jin tashin hankali yana ƙara xiyartarsa. "Baiwar Allah daga ina?" Mommy ta ce, lokacin da Nufaisah ta kawo mata ruwa da lemu. "Na san ba za ku gane ni ba, amma ni daga Kano nake sannan na zo da wata magana ne." Kallonta suka yi, suna mamakin maganar da ta zo da ita. "Ok, muna jin ki." Cewar mommy da ta kasa motsawa. "Sunana Lubaiynah,kuma iyayena a Kano suke. Mun ɗauki tsawon lokaci muna soyayya da Aliyu, har ya yi mini alƙawarin zai aure ni." Ta furta tare da ɗago idanunta ta kalle su, tana son ganin yadda suka karɓi zancen. Ganin sun zuba mata na mujiya, sai ta gyara murya ta ɗora da cewa,"Aliyu ya yi mini alƙawarin aure, har ta kai ga na mallaka masa jikina, sai bayan nan ya ce ba za aure..." "Ƙarya kike yi sharri za ki yi masa, amma yarona bashi tarbiyyar da ba zai iya kula matan bariki ba, domin duk macen da take da daraja, ba zata yarda wani namiji ya yi taraiya da ita ba." Jin abin da Mommy ta ce, cikin fushi sai ta fashe da kuka."Na yarda da haka domin Aliyu yayi mini alƙawarin aure, amma tun daya ga ya mayar da ni farkarsa ya gama wulaƙanta rayuwata sai ya ƙi aurena. Da gaske nake yi game da abin dana faɗa domin har kwana na ke yi a gidansa, wani lokaci in zan yi tafiya tare take tafiya da ni. In kuma baku yarda ba na yarda a kira shi, sannan a yi bincike. Abin da ya sa na zo na gaya muku, iyayena sun yi fushi da ni sun daina kula ni. Shi kuma ya gaya mini ba zai auri mace mazinaciya ba, bayan shi ne ya lalata mini..." Daddy da yake tsaye yana kallonta, cikin tashin hankali. Wani irin jiri yake gani, domin fuskarta ya bayyanar da duk abin da take faɗa. "Aliyu da ma abin da yake aikawa ya kenan, ya sanya ya ƙi aure?" Ya yi wa kansa tambayar, yana jin zuciyarsa na zafi duhu yana rufe ganinsa. "Ta shi ki fita kar ki yi wa ɗana sharri, domin zan iya shedar shi. Sai da in wani Aliyu kike amma ba yarona..." "Zan iya yarda da maganarta in har ta nuna mini sheda." Daddy ya furta cikin damuwa yana kallonta Babu musu ta ciro wayarta, tana share hawaye ta fara nuna musu hotunan da suka yi da Aliyu, har da waɗanda bai kamata ta nuna musu ba. Daidai lokacin da ta nuna musu, hoton da suka ɗauka da Aliyu yana kwance da ga shi sai gajeren wando na sojoji ita kuma tana gefenda da matsatstsun kaya. Da sauri suka kauda idanunsu cikin tsananin tashin hankali. "Innnalilahi wa inna ilahir raju'un Ubangiji!" Daddy ya furta tare da rintse idanunsa yana jin jiri na ibansa. Taga-taga ya yi zai faɗi, sai kuma ya dafe kujera jin yadda jiri ke ibansa. Mommy salati ta furta, tana zare ido cikin tsanannin tashin hankali. "Tabbas ta yarda ba ka shedar ɗan yau. Ashe duk kame kan da yake yi Aliyu masha'a yake aikatawa? Sai ta rinƙa jin tamkar za ta haukace, saboda wani irin tashin hankali da yake ziyartar ta. Kallon Daddy ta yi, da ya dafe ƙirji yana ƙoƙarin magana, amma ya kasa sai buɗe baki ya ke yi. Sai kuma ya yi taga-taga zai fadi. Kafin ta yi yunkurin tare shi har, ya yanke jiki ya faɗi ƙasa. Jimmalo da take kallon su cikin mamakin maganganun da suke faɗi. Mamaki ta fara dama ɗan iska ne yake mata kallon banza? Lokaci guda ta ƙara tsanar shi, domin tun a ƙauye ta tsani ace mutum ɗan iska ne. Ba ta manta wani Tanimu da ya ke ɓata mata a ƙauye su. Da Jimmmalo ta tasa shi a gaba har sai ya bar garin, domin ita ganshi da dutse take raka shi. Mommy da Nufaisah, suka saka ihu sosai ganin ya kice suna kira sunan shi, amma Daddy ya sume ƙau babu numfashi. Ganin ba ya motsi, sai Mommy ta ƙwala ihu ta kira direba. Cikin sauri ya kinkime shi zuwa asibiti. Lubaiynah sai hankalinta ya kwanta ta ɗauki jakarta ta fice. Zuciyarta fes ta san cewa da zarar ya farfaɗo, dole zai sanya a neme ta don ya aura mata shi. Murmushi ta saki tana gyara zaman jakanta, domin daga yau ta fara yarda Aliyu zai zamo nata. Kai tsaye gidan su Fadila ta wuce ta rungume ta. "Na gode da kika bani shawarar nan, domin mahaifin Aliyu ya sume lokacin da na gaya masa. Sannan abin mamaki lokacin da na je, sun ga condom hankalinsu ya tashi." "Kin ga shawarar da na gaya miki ko? Yanzu dai ki jira kira daga mahaifin Aliyu ya aura miki shi." "Zan koma gida na zauna ina jiran kira, amma na san cewa zan fuskanci ƙalubale a gurin Aliyu." "Kar ki damu komai zai wuce." "Haka ne, amma ba ki ji yadda na ji ba wallahi na tsorata. Don kawai na kira shi ya ce mini yana hanya, amma da ba zan iya zuwa ba, saboda inda ace yana gidan Aliyu zai iya kashe ni." "Ki daina jin tsoronsa, ki dake don kin san ba za ki sha ruwan daɗi ba, amma in kika jajirce za ki same shi a hannu." "Na gode ƙawar kirki, zan kira ki da zarar mahaifin Aliyu ya kira ni." "Ok, Allah ya tsare sannan in ya kira ki, kar kiji tsoron idanunsa ki gaya musu gaskiyar abin da ke tsakanin ku." "Zan faɗa ai ba zan cuci kaina ba." Ta furta tare ɗaukar jakarta, ta yi mata sallama ta wuce Kano. Mommy cikin tsanannin tashin hankali suka isa asibiti. Da sauri likitoci suka yi kansa don bashi taimakon gaggawa. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba, suka yi nasarar farfaɗo da shi. Mommy fita ta yi daga cikin ɗakin, ta dawo harabar waje. Wayarta ta jawo, ta danna numbar Aliyu cikin tsananin ɓacin rai. Alokacin yana Kaduna gidan Anty, suna shirya yarda tafiyar zai kasance kiran ya shigo. Da sauri ya ɗauka ganin numbar Mommy. "Hello Mommy..." Ya kasa ƙarashe maganar jin yadda ta kira sunan shi a fusace. "Lafiya Mommy?" Ya yi mata tambayar tare da miƙewa. "Ba lafiya Aliyu domin ka bamu mamaki. Ma za ka dawo Kaduna ko da ace ka kai kai inda za ka je.." "Mommy, mai ya faru?" Ya ƙara tambayarta yana mamakin abin da ya sanya ta furta haka. "Babu abin da bai faru ba. Mahaifinka ya yanke jiki ya faɗi don haka asibiti zaka zo..." "Innnali wa inna ilahir raju'un! Mai ya faru?" Ya ƙara tambayar, amma ba ta amsa mishi ba ta ce,"In har ka ƙara minti biyar ba ka juyo ba, sai na yi maka Alllah ya isaa nonon da na shayar da kai." "Innnalilahi wa inna ilahir raju'un!" Ya furta tare da wurgi da wayar cikin tsananin tashin hankali. "Captain mai ya faru?"Anty da tun da ya fara wayar, ganin yadda ya canza take tambayarsa. Rintse idanunsa ya yi yana tuna kalmar da ta furta."Ban sani ba, amma koma mene ne lamari ne babba. Mommy da gaske take gaya mini za ta yi Allah ya isa ka shayar da ni da ta yi, sannan da Daddy ya sume yana asibiti." Ya furta cikin damuwa yana jin tamkar zai yi hauka. "Ya Salam!" Ta ce jin abin da ya faɗa.Lokaci guda gabanta ya faɗi, domin ƙwaƙwalwarta ce ta hasko mata Lubaiynah ta zo, amma don kar ta ƙara tayar masa da hankali sai bata gaya masa tunanin da ta yi ba. "Bari in je Anty Amarya, zan kira ki." "To Allah ya sa lafiya. Don Allah da ka koma ka kira ki, dole gobe mu zo." "Zan kira in sha Allahu." Ya furta cikin sanyi muryarsa a sanyaye. Sharaf ta zauna tana tunanin lamarin. Dama ta san yadda yarinyar take son shi, da wuya ta zura masa ido ya yi aure. Ko da ya gaya mata zuwan da ta yi, tun lokacin hankalinta bai kwanta ba. Ta dai ƙyale shi ne ganin yadda yake ta murna. Tun da ya fita daga ɗakinta yake gudu, ba tare da ya damu da kula da hanya ba. Daddy a lokacin da ya farfaɗo. Ya buɗe idanunsa yana kallon saman ɗakin a hankali. "Sannu Daddy." Mommy da Nufaisah, suka taso zuwa gadon tare da furta hakan a tare. Ba tare da ya amsa musu ba, sai ya fara tunanin dalilin da ya suma har aka kawo shi asibiti. Lokaci guda komai ya dawo masa, har da hoton da ta nuna masa. Daddy ya fara ƙoƙarin tashi, amma sai Mommy ta hana shi. Hawaye yake gangarowa yana jiƙa kan gadon da yake kwance. Yana kwance ya kasa cewa komai. In ya tuna abin da Aliyu yake aikatawa, sai ya ji kamar zai haɗiye zuciya ya mutu. Kullum ya yi sallah sai ya yi addu'ar; Allah ya tsare mishi yaranshi daga zina, amma sai ya zamar masa fuska biyu. Sosai yake zubar hawaye cikin tsananin ɓacin rai. Mommy mamaki sosai take yi yadda Aliyu ya rufe shi baibai. Ashe iskanci yake yi a can, amma yake nuna masa mutumin ƙwarai ne. Tabbas Aliyu ya zama fuska biyu. Ya zama kura da fatar akuya, amma a ransa sai ya ƙudira tunda ya yi masa haka, ya ɗauki alwashin sai ya yi masa abin da zai kunyata rayuwarsa. Daddy sosai yake ji zafin abin da ya yi masa. Kula yake yi yana takaicin ɗan da ya haifa da cikinsa ya iya ije mace har yana tafiya da ita. Sai lamarin ya rinƙa ba shi mamaki, tuna har ya gama samartakarsa bai yi wannan shashancin ba. Mommy mu ta yi zuru tana kallon sa. Duk rarrashin da take mi shi ya ƙi daina zubar hawaye. Duk da cewar ita kanta abin ya bata mamaki, amma halin da ya shiga sai ta tsorata, ganin yana son ya cutar da kansa. Suna cikin wannan yanayin Aliyu, ya yi sallama cikin tashin hankali ya shigo."Daddy, mommy mai ya faru?" Kallonsa suka yi domin sai ya zamo musu baƙo. Sosai yake basu tsoro zama fuska biyu da ya yi. Tun lokacin ya fara basu tsoro. Mommy ce ta yi ƙarfin hali, ta ƙarasa gurinsa ta wanka masa mari. Kafin ya gama shanye mamakin marin Daddy ya rinƙa zuba masa masa lafiyayyu. "Ashe dama Aliyu abin da kake aikawa kenan? Ashe yaran mutane kake ɓatawa a Abuja? Ka sa zunubin aikata zina?" Tambayar da ya yi masa, yafi marin da yake mishi razana shi. Da sauri ya ɗago idanunsa yana kallon Daddy da yake zuba masa mari. "Aliyu, ka cuci rayuwarka ka sanya Ubangiji yana fushi da kai! Zina da kake yi Aliyu wane irin tarbiyya ce ba mu yi maka ba?" Sai ya ji matsanancin rashin hankali ya ƙara xiyartarsa, har ya kasa cewa komai. Tunanin yadda a yi suka sani ya fara yi. "Lubaiynah!" Ya ji zuciyarsa ta zarge shi, sai ya ji tsannanin tashin hankali lokaci guda kansa ya fara juyawa. "Wallahi ka bani mamaki Aliyu, ban taɓa tunanin haka daga gareka. A kodayaushe ina gayawa mutane yarona soja ne, amma kuma na gari, ashe kallon mara hankali suke mini. Duniya ta riga ta gama sanin kai mazinaci ne, tun da har mace kake ijewa a gidan...." "Innnali wa inna ilahir raju'un!" Ya furta lokaci guda idanunsa suka kaɗa, sai ya ji tamkar ya tsaga ƙasa ya shige saboda tsananin kunya. Dama Hausawa sun ce; kwana ɗari ba ɗaya na ɓarawo, kwana ɗaya na mai kaya. Tabbas haka ne domin ya daɗe yana sheƙe ayarsa, amma Allah ya tona asirinsa yau. Rintse idanunsa ya yi, yana fatan ya zama mafarki, domin ji yake ba zai iya haɗa idanu da su ba. Domin ya yarda ya zama kura da fatar akuya. Sun yarda da shi, amma ya ɓata yardar da ke tsakaninsa da iyayensa. Hawaye sosai yake yi ya durƙusa gaban Daddy."Na san cewa na yi kuskure don Allah ku yafe mini, amma wallahi na tuba tuntuni na zama na gari. Tabbas na aikata ba daidai ba, sai dai duk na daina halayena." "Kaconka Aliyu! Ka yaudari ne domin na yi tunanin ƙaryawa za ka yi. Gaya mini za ka yi, ba ɗan da na haifa da cikina bane yake aikata zina. Na ɗauka za ka gasganta mini cewa gizo idanuna yake mini har na ga hotonka da ta nuna mini, amma Aliyu kai da kanka kake gaya mini ka aikata zina. Ina alƙawarin da ka yi mini cewar ba zaka taɓa aikata abin da wasu sojojin suke yi ba?" Ya ƙarashe maganar yana girgiza shi cikin hawaye. Kunya, nadama da kuma tashin hankali, suka sanya shi ya sunkuyar da kanshi yana hawaye. Murmushi mai ciwo ya yi yana kallon sa."Yadda ka aikata mini, haka sai na rama kwatankwacin abin da ka yi mini, don sai na sanya ka kuka da idanunka. Ba zan aura maka yarinyar nan ba, saboda bana son na haɗa ka aure da ita, domin za ka iya zama da ita nan gaba. So na ke zuciyarka ta yi ƙuna kamar yadda nawa take ƙuna. Ni nake da iko da kai da Safeeya wallahi ka ji na rantse a yau zan aura maka it..." Da sauri suka ɗago idanunsu, suna kallonsa cikin tsannanin tashin hankali. "No, Daddy please no! Zan iya fuskartar duk hukuncin da za ka yi mini, amma ban da aura mini wannan ƙazamiyar yarinyar! Ko da ace hukuncin barin aikin soja ne, za iya haƙura domin na gwammace na rayu babu aure da na rayu da ita!" "Hmmmmh! Ta yaro kyau take bata ƙarko. Wallahi a yanzu zan kira Zariya na sanar da aurenka don ba zan jirga daga asibitin nan ba sai an ɗaura." "A'a Alhaji kar ka yanke hukuncin da za ka yi dana sani! Ka taɓa ganin inda zafi da sanyi da zafi suka haɗu. Babu yadda za a yi Jimmalo da Aliyu su yi zama aure, in har ba so kake yi su kashe kansu ba." Mommy da take cikin tsanannin tashin hankali jin hukuncin daya yanke ta ce. "Na riga na gama yanke hukunci, kuma ba zan saurari kowa ba." Ya furta tare da ciro wayarsa don ya kira waliyan Aliyu. Baba Ɗan- Lami da Sa'idu. To masu karatu ya kuke tunanin wannan ma'aurata za su zauna? Tun da Daddy ya furta dole sai an yi auren. Shin kuna ganin za a yi zaman lafiya? Jimmalo ya za ta ji in aka gaya mata za ta auri maƙiyinta? Kar ku manta aure bashi a cikin lissafinta, sannan ta tsani mazinaci. Mufida za ta haƙura da Captain in ya auri Jimmalo? Ina Hanifa baiwar Allah? Captain zai iya amincewa da ita a matsayin matarsa? Bayan ya gama zaga duniya yana faɗin matar da zai aura daban take a cikin mata? 😁😁 Ta ya ya za a yi su yi zaman auren har Captain ya ɗauke ta a matsayin mata a sh soyayya shi daina ya ganta yake jin amai? Ku hango mana gidan Captain da yake komai fari idan amarya ta tare😁😁😁 Ni kaina zan so na ga rayuwa da waɗannan ma'auratan za su yi a a gida ɗaya. Kun dai san tun da Daddy ya furta babu fashi, domin ran yan maza ya ɓace, dole Aliyu ya girbi abin da ya shuka na auren Jimmalo Capacity. To duk kusha kurumin ku domin amsoshin ku yana book 2 wanda za a fara posting ba da jimawa ba. A book two taku din nan haziƙar marubuciya ta tanadar muku duk amsar da kuke bukata. Ba fa a yi komai ba domin labari yanzu aka fara. Kun san dai somin tabi aka ba ku, ainihin labarin yana cikin book two. Wacce take buƙatar cigaba da karanta labarin sai ta biya naira 600 kacal don shiga cikin paid group. In kuma aka kammala za ta biya naira 800 Ga masu buƙatar payment sai a biya ta wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay A kuma tura shaida ta wannan numbar 0707 297 1093