🌸🌹kishyar uwa 🌹🌸 (True life story). 🍁🌸Daga alk'alamin nussad🌸 MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION 🌙🌙🌟✍️ https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 𝑊𝑒 𝑎𝑟𝑒 𝑡𝒉𝑒 𝑚𝑜𝑜𝑛𝑙𝑖𝑔𝒉𝑡 𝑤𝑟𝑖𝑡𝑒𝑟𝑠 𝑤𝑒 𝑐𝑎𝑛 𝑠𝒉𝑎𝑘𝑒 𝑜𝑓𝑓 𝑒𝑣𝑒𝑟𝑦𝑡𝒉𝑖𝑛𝑔 𝑎𝑠 𝑤𝑒 𝑤𝑟𝑖𝑡𝑒; 𝑜𝑢𝑟 𝑠𝑜𝑟𝑟𝑜𝑤𝑠 𝑑𝑖𝑠𝑎𝑝𝑝𝑒𝑎𝑟, 𝑜𝑢𝑟 𝑐𝑜𝑢𝑟𝑎𝑔𝑒 𝑖𝑠 𝑟𝑒𝑏𝑜𝑟𝑛. 𝑊𝑒 𝑤𝑟𝑖𝑡𝑒 𝑡𝑜 𝑑𝑖𝑠𝑐𝑜𝑣𝑒𝑟 𝑤𝒉𝑎𝑡 𝑤𝑒 𝑘𝑛𝑜𝑤.𝑊𝑒 𝑎𝑟𝑒 𝑎𝑙𝑙 𝑎𝑝𝑝𝑟𝑒𝑛𝑡𝑖𝑐𝑒𝑠 𝑖𝑛 𝑎 𝑐𝑟𝑎𝑓𝑡 𝑤𝒉𝑒𝑟𝑒 𝑛𝑜 𝑜𝑛𝑒 𝑒𝑣𝑒𝑟 𝑏𝑒𝑐𝑜𝑚𝑒𝑠 𝑎 𝑚𝑎𝑠𝑡𝑒𝑟.. 𝑂𝑢𝑟 𝑎𝑑𝑣𝑖𝑐𝑒 𝑡𝑜 𝑡𝒉𝑒 𝑦𝑜𝑢𝑛𝑔𝑠𝑡𝑎𝑟𝑠 𝑖𝑠 𝑌𝑜𝑢 𝑠𝒉𝑜𝑢𝑙𝑑 𝑤𝑟𝑖𝑡𝑒 𝑏𝑒𝑐𝑎𝑢𝑠𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑡𝒉𝑒 𝑠𝒉𝑎𝑝𝑒 𝑜𝑓 𝑠𝑡𝑜𝑟𝑖𝑒𝑠 𝑎𝑛𝑑 𝑠𝑒𝑛𝑡𝑒𝑛𝑐𝑒𝑠 𝑎𝑛𝑑 𝑡𝒉𝑒 𝑐𝑟𝑒𝑎𝑡𝑖𝑜𝑛 𝑜𝑓 𝑑𝑖𝑓𝑓𝑒𝑟𝑒𝑛𝑡 𝑤𝑜𝑟𝑑𝑠 𝑜𝑛 𝑎 𝑝𝑎𝑔𝑒. 𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 𝑐𝑜𝑚𝑒𝑠 𝑓𝑟𝑜𝑚 𝑟𝑒𝑎𝑑𝑖𝑛𝑔, 𝑎𝑛𝑑 𝑟𝑒𝑎𝑑𝑖𝑛𝑔 𝑖𝑠 𝑡𝒉𝑒 𝑓𝑖𝑛𝑒𝑠𝑡 𝑡𝑒𝑎𝑐𝒉𝑒𝑟 𝑜𝑓 𝒉𝑜𝑤 𝑡𝑜 𝑤𝑟𝑖𝑡𝑒. 𝑆𝑜 𝐿𝑒𝑡 𝑡𝒉𝑒 𝑤𝑜𝑟𝑙𝑑 𝑏𝑢𝑟𝑛 𝑡𝒉𝑟𝑜𝑢𝑔𝒉 𝑦𝑜𝑢. 𝑇𝒉𝑟𝑜𝑤 𝑡𝒉𝑒 𝑝𝑟𝑖𝑠𝑚 𝑙𝑖𝑔𝒉𝑡, 𝑡𝒉𝑟𝑜𝑢𝑔𝒉 𝑎 𝑝𝑒𝑛, 𝑜𝑛 𝑎 𝑝𝑎𝑝𝑒𝑟 . YA ALLAH, YA RAHMAN, YA KAREEM, YA ZULJALALI WAL IKRAM, ALLAH YA SHIGE MANA GABA. بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Da sunan Allah mai rahama mai jin kai , mai jin kai . Salati ya tabbata ga sugabanmu annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa masu girma. Wannan littafin badan wata ko wani na kirkireshi ba nayi ne domin mutane masu irin halin in sunji su gyara , Allah ya bamu ikon gyarawa amin. Sadaukarwa ga iyayena , da kuma duk makaranta littafina. Shafi na 1️⃣ Tafe take akan hanya kana ganinta kasan hankalinta baya tattare da ita , saurin da takeyi ya wuce misali , kai in ka hangota daga nesa tsammani ma zakayi mahaukaciya ce , yarinyace wadda bazata wuce shekaru goma zuwa sha daya ba, a kofar wani gida naga ta tsaya nima kuwa na nemi guri na tsaya dan ganin abinda zai faru , kokari takeyi ta shiga gidan tana kuma ja da baya , ta dauki tsawon mintuna goma kafin daga bisani ta tura kofar gidan da sallama ta shiga , cikin sanda ta shiga a hankali da sallama a bakinta, kitchen naga ta nufa da ajiye abinda ta siya tana kokari fita daga kitchen din juyawar da zatayi sukayi karo da juna, goshinta ta dafe sbd tsabar buguwarda tayi duk wannan abin da akeyi sai yanzu nqga fuskar wannan yarinyar mashaAllahu kawai na ambata saboda tsananin kyau da yarinyar ke da shi , matar da sukaci karo naga ta finciki yarinyar zuwa waje , au ke yanzu dan ubanki na aikeki tun dazu amma sai yanzu kika ga damar kawomin aiken , magana take shirin yi amma ta dakatar da ita ta hanyar wanka mata mari sai da bakina ya fashe, kara ta saka saboda azabar da tasha , inna wallahi ba dadewa nayi ba gurin ghalin ne akwai layi in ina bashi kudin baya amsa sai da wani mutum yazo sannan ya mika masa ya bani sakon, rufamin bqki shegiya waya tambayeki , nace miki ki fadamin dalili , labilen dakin aka daga yarinyace da bazata gaza shekarun wannan yarinyar ba itama ta fito tana mika alamun daga bacci ta tashi , inna ina abincina tana magana tana yatsina fuska ni yunwa ma ta fito dani , kallonta tayi tace zo nan yar lelen inna da baba , bara na baki ki sayo alala gidan talatuwa ki ci saboda wannan shegiyar ta sa ke yin halin nata, ta kalleta mai mugun halin tsiya kawai. Daga kofar gidan naji anayin sallama alamar zaa shigo , wani dattijo ne naga ya shiga gidan tana tura keke da fartanya akan kafadarshi da alama daga gona ya dawo, haba asabe naji ya ambata yaya tun daga waje nakejin sautin muryarki menene ya faru ya tambaya cike da yunwar ta amsa masa tambayarsa , kaganta nan tun dazu na aiketa amma sai yanzu ta dawo , kallonsa ya juya gurin yarinyar nan ta farko yace Fatima garin yaya kina dade batun kinsan ina gab da dawowa daga gona kuma da yunwa zan dawo , wallah baba akwai layi a gurin sai dana dade sannan ya bani na taho gida, toh a daina tafiya ana dadewa kinji ko toh tace tare da tashi daga wajen saboda tana da aikin da take da shi masu yawa, Alhamdulillah duk da kankantar shekarunta amma aiki ko babba sai haka , ita kuwa wachchan bqta da aiki sai bacci ,girki ta daura sannan ta kama wanke kwanika , cikin kankanin lokaci ta gaba komai tsaf ba tareda wani jan dogon lokaci ba, sallama tayi kofar dakin amsawa babanta yy kamin ya bata izinin shiga ta durkusa kasa sannan tace inna ba gama aiki toh ta amsa mata ba tareda ta kalleta ba kije ki dauko hijjabi zan aikeki toh tace tana kokarin tashi mahaifin nasu ya tsayarda ita ta hanyar fadar kinci abinci aa ta bashi amsa je ki ci sai ki tafi aiken, haba malam tayaya zance zan aiketa amma ka goya mata bayan kar taje don bani na haifeta ba ta fada ta hanyar fashewa da kuka, haba asabe yarinyar nan bataci abinci ba , bazai yiwu yarinyar ta zauna ba abinci ba batun kuma da akwai, ke tashi kinji kije ki ci abinci sai ki tafi toh tace hade da tashi ta fita . Toh bayan ta gama ne aka bata aiken da zatayi , ta tafi , a hanya ta gamu da yar ajinmu rahane , lah Fatima dama kina nan mallam Ahmad yana ta tambayarki kwana biyu bakyason zuwa makaranta , wlh ba haka bane ba yanzu ma inna ta aikeni gidan baraka aminiyarta inayin sauri sai min hadu wajen tallah da dare , toh sukayi sallama ta tafi. Tana zuwa kofar gidan ado ta ci karo da shi a rayuwarta ta tsanin wannan bawan Allah kwata kwata baya burgeta duk kuwa da tururuwar da yam matan garin ke masa, duk da ita yarinya ce amma takan banbance abu mai kyau da zai amfaneta da marar kyau , ah Fatima ya fada yana washe baki naam ta amsa tana kokarin shiga gidan , aa dakata mana , aikena inna tayi kuma ina sauri ne , au wai asabe ya tambayeta gaba tayi bata bashi amsa ba , da sallama a bakinta ta shiga matar ba zaune akan tabarma inna ina wuni lafiya ta amsa , sannan ta bata sakon da aka ce ta kawo batun ta gama dubawa ne sannan ta mai da mata ragowar ki kai mata kice na zaba , zamuyi magana, toh tace sannan ta tafi gida . Tana shiga ta kai mata sakon, toh ki huta ga kayan tallah chan na hada miki, toh tace sannan ta fita. Da magariba bayan an fita a masallaci ta fita da gyadarta zuwa dandali inda samari da yam mata ke haduwa , kawarta ta dazu ta karaso ah Fatima har kin karaso , eh ta bata amsa , wlh kina kokari gaskiya, yanzu abinda zaayi muyi sauri mu sayar mu koma gida saboda kinga garin na damuna ne ,eh haka ne , mashaAllahu sunyi ciniki dan haka kafin a tashi suka tafi gida , kawartace ta fara shiga gida , sannan ta wuce daf da zata shiga yayi saurin shan gabanta tsaya mana tun daga nesa nake kiranki baki juyo ba danAllah Ado ina so na shiga gida inna na jirana , ai da saninta nazo wajenki dan nazo tace bakya nan kina dandali, eh ta amsa masa, amma yanzu zan shiga gida sai da safe saurin janyo mata hannu yayi kara ta saki sannan ta gartsa masa cizo ta shiga gida , kudin tallan ta bata sannan ta ci abinci ta shiga dakin mahaifiyarta wanda ya ratattake saboda asabe ta hana a gyara shi, kwanciya tayi a kan tabarmar kabar dake dakin , tunani ta fada yi shin ina zata ga dangin mahaifiyarta batasan mahaifiyarta ba gashi mahaifinta har yau bai fada maka tayaya akayi mahaifiyarta ta gujeta ba , hawayene ya zubo mata sakamakon tuna irin rayuwar da take ciki shin yaushe zata fita daga rayuwar da take ciki ita dai tun iya tashinta a haka ta taso ta ganta cikin wahala , Allah ya mata magani kawai a haka bacci mai nauyi na gajiya ya kwasheta ta niyyar tashi da wuri saboda tana da niyyar zuwa makaranta kota halin kaka ne , shiyaga take da niyyar yin aikinta da wuri ta gama a haka har asubah tayi ta tashi saboda ta saba tashi ta yi aiki sosai ta kammala kamin ta gama komai tayi sallama da mahaifinta tayi hanyar makaranta. *Please🙏🏽* *Share* *Comments* To be continue 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar uwa🌹🌸 (True life story). 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸. 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Godiya ga Allah subahanahu wata'ala , da ya bani damar ci gaba da rubutun littafina wato kishiyar uwa . Ina matukar godiya a gareku masoya na musamman na cikin group nawa na what's app da kuke ta nuna kulawarku ga rubutu na nagode . Ina matukar godiya ga mahaifana da 'yan uwana da suka goya min baya wajen karfafa min gwiwa wajen yin rubutu na , na gode. Shafi na 2️⃣ Bayan ta isa makaranta a lokacin karfe takwas na safe , dan haka tana Shiga ajinsu ta nufa , da sallama a bakinta kana ta samu wajen zama ta zauna saboda a lokacin malaminsu bai karaso ba . Sunyi kamar zaman mintuna biyar sai ga malaminsu na English ya shiga , bada bata lokaci ba ya shiga yi musu darasi, ya dauki tsawon mintuna kana daga bisani yayi tambayoyi aka bashi amsa ya gama abinda zaiyi ya fita. A haka aka fita break. Alhamdulillahi kowanne malami ya samu damar shiga ajinsu a haka har lokacin tashinsu yayi sun kammala darasin ranar dan haka kowa ya kama hanyar gidansu . Tana shiga da sallama a bakinta bayan tayi bankwana da kawarta rahane akan cewa sai sun hadu gurin tallah . Tana shiga dakinta ta wuce sakamakon rashin jin motsin kowa da tayi wannan ya tabbatar mata daga inna asabe har y'ar lelen tata basa nan dama tasan mahaifinta bayanan yana wajen aikinsa a gona, kayan makaranta ta cire sannan ta hau aikin gida sakamakon anyi kacha kacha da gidan kuma tasan babu mai gyarawa sai ita ta gama sharar tsakar gidan tana shirin yin wanke wanke kwanika taji sallamar mahaifinta alamar ya dawo daga gona , " Baba sannu da dawo wa ta fada tana shirin karbar fatanyar a hannunsa"a'a gidan ba kowane ya tambaya yana sauraron amsar da zata bashi " eh Baba ba kowa , kada kansa yayi sannan ya shige dakinsa ita kuma ta ci gaba da aikinta. Sai bayan sallar magariba ana shirin yin ishsha'i sannan asabe ta dawo ita da Abu diyarta fagajam fagajam suka shiga gidan ko sallama babu a bakin daya daga cikinsu , a lkcn Fatima har ta dauka tallarta ta fita . " inna ki duba mana abinci mana na kwaso yunwa Abu ce mai maganar cike da raini tana murguda baki alamar 'ya'yan da aka shagwaba aka lalata basu ganin Kimar kowa , " ah bari na duba in shegiyar yarinyar asabe tayi wannan furuci tana niyyar tashi tana dubawa ta tarar har ta gama abincin dan haka suka ci ba ko tunanin yin sallah saboda magariba ma a hanya ta isko su. Achan dandali kuwa bayan ta karasa ta tarar da kawarta rahane har ta rigata zuwa " Fatima yau kinjima baki fito ba nayi tsammanin ma bazaki fita ba yau , zare idanuwanta tayi alamar mamaki sannan race " chab wallahi aiki na tsaya yi ne shine na dade ban fita amma ina gamawa na fita na samu gidan namu ne ba kowa to na gama aikin ina jiran su dawo ba Wanda ya dawo shiyasa na fita kawai da yake nasan inda kayan tallar suke, suna zaune suna hira har sukayi cinikin gyadarsu sosai kana suka taba wasannin su na yara suka nufi gida. Rahane ta fara isa gida kafin nan Fatima ta nufi gida kamar kullum Ado ta gani a kofar gidansu " tsaki tayi ta wuce zata shiga gidansu da sauri ya sha gabanta cike da kare mata kallo kana yace " ke wai bakya ganin mutane ne sai kiyi wani fuska ki shige dan kinga an damu dake ya tambayeta ya kallonta "da ni nace ka damu dani ne ta fada cike da k'osawar ya barta ta shiga gida naji bake kikace ba amma kinsan ba wadda nike nunawa soyayya irinki ko kinsan dai 'yammatan garin nan suna kawo Kansu inyi soyayya dasu ko ," toh naji " ta fada tana kokarin shiga gida don ita a rayuwarta ta tsani zancen soyayya gani takeyi kamar dan iskane Wanda ke cewa yana sonta , duk kuwa da dama mutane samarin kauyen na kawo mata hari duk da yarintarta amma tana gocewa , maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi " zanyi mawa innata maganar , jitayi kamar ta sanya ihu saboda razana ita fa ta tsani wannan mutumin , baki ce komai ba ya fada ya na kallonta , shigewa gida tayi tare da banko kofar gidansu ta barshi a tsaye yana kallon kofar gidan tare da cewa lallai zanyi maganinki ta karfi tunda bakisan lallashi ba ya fada a cikin zuciyarshi a yayin da yake shirin barin kofar gidan. Wannan kenan Da sallama a bakinta ta shiga , a tsakar gidan ta tarar da mutanen gidan barka da dare ta musu kana ta mikawa inna asabe kudin warta tayi kana ta kirgasu sai da taga sun cika cif sannan ta saki fuska" tashi kije ga ragowar abinci Chan ki ci toh tace sannan ta tashi ta nufi wajen abincin. Mahaifin Fatima Wanda tunda ta shiga baice uffam ba ya juya ya kalli yarinyar tasa cikeda tausayi a ransa ya na fadi lallai hakkin yarinyar nan bazai taba bari na ba ina so na fada gaskiyar labarin mahaifiyarta amma ina tunanin wata rana zata iya guduna zuwa ga mahaifiyarta , a cikin ransa yake wannan maganar sa'ilin da yake jin k'unar azabtar ta 'yarsa da akeyi yarasa gane kansa sai yayi niyyar yin magana sai ya kasa amma ya barwa Allah komai. "Uhmm ni kuwa asabe dazu da rana na dawo bakya nan ina akaje ne , au shaf fa na sha'afa wallahi yar gidan yaya habu na kan tudu aka saka ranarta shine mukaje , oh ni asabe malam kai bakaga abin arziki ba ai mu dai mun sha kallo inayiwa Abu fatan samun haka , karkada kanshi kawai yayi lallai mata ba'a musu ita nata kawai ta sani Allah ya kyauta. Anan inason naja hankalin mata wadanda ke zaune ya yaran kishiyoyinsu 'ya'ya na kowane babu Wanda kasan zai yi maka rana a rayuwa , amma wadansu matan ba wadanda suke ababen soyuwa a garesu sai yaransu kawai banda su kowa ma hotone , musamman in baa zaman lafiya da mahaifiyar yaron ko yarinya, Ku tuna su fa basu da laifi ko kadan hasali ma basu san yaya akayi gabarku ta kullu ba, mata mu kula amanar Allah ce in ka ci tabbas zata ci ka fatan zamu gyara ,Allah ya bamu ikon gyarawa amin summa amin. Bayan ta gama cin abincin ta tattare kwanikan da akaci abincin dasu a dare nan ta wankesu , a lokacin data gama ba kowa duk an shiga daki dan haka itama ta wuce nata dakin dan kwanciya bacci aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita . Wata mata ta hanga chan kan wani tsauni mai Nisan gaske matar ta juya mata baya , matar tana ta kiran sunanta Fatima! Fatima! Ta na ta kiranta tana so ta kama ta amma ina ita kuwa sai kasan wannan tsauni takeyi gangarawa takeyi tana k'walla ihun Neman agaji a haka ta farka daga bacci tana ihu , salati tayi tare da addu'ar tashi a bacci tana lekawa taga har ta makara dan haka tayi sallah ta soma aikace aikace kamar yadda ta saba , da yake ranar asabar ce ba makaranta sai karfe goma zata tafi makarantar allo wadda da kyar asabe ta yarda akan zataje da taso da safe ta rink'a yi mata tallar kosai amma hakan bai samu ba. Wannan lokacin data samu hakan ya bata damar yin aiki sosai . Har ta gama ba Wanda ya fito da haka ta tsaya tana jiran fitowar masu gidan tare da addu'ar Allah yasa su fito da wuri dan ta samu damar zuwa makaranta........................... Please🙏🏻 Share & Comments. To be continue....... 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸 ( True life story). 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸. 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Ina godiya da shawarwarinku , ga yadda zan tafiyar da littafina, musamman makaranta littafina da 'yan uwa da abokanan arziki. Ina ganin yawan comments naku, ina jin dadi kuma insha Allahu nima bazan baku kunya ba. Sadaukarwa ga iyayena da 'yan uwana da abokanan arziki , luv u all🥰 Wannan page din nakine sadaukarwa gare ki 'yar uwata Zainab, Allah y kawo miji na gari amin. Shafi na3️⃣ Tana nan tsaye har karfe tara tayi kafin nan mutanen gidan suka tashi , da hanzarinta ta isa ga mahaifinta "Baba ina kwana" , tace“ lfy qlu , har kin gama aikin naki ", “eh na gama da shi" “toh Allah ya miki Albarka ", “amin" tace da shi , sai a sannan Asabe ta fito tsakar gidan , " Inna ina kwana", “lafiya "ta amsa a yamutse, “shin kin gama aikin naki ", tace “eh na gama", “toh yau ba maganar zuwa makaranta, rafi zaki tafi ɗebo ruwa, ga kayan Abu chan zaki wanke saboda sun yi datti", kusan fashewa tayi da kuka saboda ta shirya akan cewa za ta je makaranta saboda ta kwana biyu bata samu damar zuwa ba , " toh" ta amsa mata, sannan ta juya ta nufi inda kayan ruwan suke, bokiti ta ɗauka ta nufi hanyar kofar gida, “kafin ki dawo zan zube miki kayan a nan ", “to" tace sannan ta juya ta nufi kofar gida cike da ɗacin rai . A hanya ta tsaya ta ci kukanta, ta ƙoshi, sannan tayi gaba , tana tunanin rayuwarta a nan gaba duk da ita yarinyace amma tana iya sanin masoyinta da maƙiyinta , ta ɗebo ruwa sosai har ta cika gidan dukka , kana ta fara wanke kayan , bata gama ba har sai da rana ta fito, sannan ta gama a wahalce , tana gamawa ta nufi dakin Asabe, " inna na gama" tace da ita, "to kije ki daura girki ", “inna wallahi banci abinci ba ", “ka ji min shegiyar yarinya yo dan baki ci abinci ba sai me, ai aiki yanzu ma kika fara shi , sai kin gama aiki tsaf, sannan ki duba idan 'yar lele ta rage abincin ", to ta juya idanunta cike da hawaye , sai da ta kammala abincin nan tsaf sannan ta zuba musu ka'ida ne daman sai sun gama cin abinci sun rage kafin ta ci dan haka sai ta jira suka gama sannan ta dauki sauran taci a lokacin ta galabaita sosai, tana jan jiki ta shiga ɗaki, zaunawa tayi, sannan ta soma cin abincin cike da kewar mahaifiyarta, duk kuwa da bata santa ba ta ya ya zata iya cigaba da fuskantar wannan rayuwar mai cike da tsanani da dana sani "Allah ka kawomin dauki amin" taƙarasa haɗe da share hawayenta da suka gangaro mata kuncinta , tana wannan zaman har bacci ya kwasheta . Tana cikin bacci nan taji an kwara mata , a razane ta farka, "au ke yanzu dan ubanki maimakon ki zo kiyi abin da za ki yi, kin san ki na da aiki shine kika zauna , shegiya mai mugun hali , tashi shegiya kawai" Asabe tayi furucin da bokitin ruwa a hannunta, "to inna zan fito ", “au jiran ki zan yi ki fito dan ubanki" ta tambayeta tana kokarin fincikota hade da kai mata duka, “inna dan Allah kiyi haƙuri wallahi na gaji" , “au ni ki ke cewa kin gaji, lallai wuyanki yayi kauri yau zaki gane kurenki a gidannan fito" , ta fada tana ƙoƙarin shiga daki , dukanta ta shiga yi ba ji ba gani, sai da ta tabbatar bazata iya moruwa ba, duk jikinta ta fasa mata shi "kuma ki tashi kije ki yayo itacen da zakiyi girkin dare tunda yau mallam IIlyan bai dawo ba" tana nufin mahaifinsu su Fatima , da Ƙyar ta tashi da rarrafe ta dauki yagaggen mayafimta ta fita domin yo itace a daji bata dawo daga itacen ba sai chan yamma a lokacin ta gaji sosai, amma haka ta daure ta daura girkin bayan ga Abu a zaune tana faman barar gyad'a tana zubawa a baki . A haka rayuwar Fatima ta cigaba da tafiya, cike da tsanani, da tsauri, da azabtuwa, har suka kai shekaru goma sha biyar ita da Abu a lokacin ne maƙerin budurci ya fara ƙera su , Fatima ta fito a matsayin kyakykyawar budurwa son kowa, to a sannan ne fa samarin kauye suka ƙara yimata chaaaa a kanta ciki kuwa har da Ado wanda har yanzu yake kan bakansa na soyayya da ita , domin har ya sanar da mahaifiyarsa domin ta sanar da inna Asabe. Duk da wannan kyawun nata daya bayyana, amma hakan bai hana tsantsar wahalar da take ciki , ta bayyana akan kyakykyawar fatarta ba. A wannan shekarun abubuwa sun faru na daɗi, da akasin haka, ciki kuwa har gama makarantar Fatima, ta firamare wadda da ƙyar hakan ta samu, bayan gwagwarmayar da aka sha da inna Asabe akan harkar makarantar , a yanxu cikin ikon Allah komai ya zama tarihi game da makarantarta ta primary, secondary ce dai bata amince ba, duk kuwa da cewar malaminsu na makaranta, malam Ahmad yayi gwagwarmayar ta cigaba, ganin irin hazakar da take da shi amma fafur ta k'iya , ganin haka ya hakura har ya koma garinsu Kaduna, dama bautar kasa yazo kuma ya gama ya koma ba tare da samun ya samu ya cika burinsa na ganin Fatima ta cigaba da makaranta ba . A yanzu gashi mahaifinsu girma ya kamashi dan haka baya iya tab'uka komai , duk da, ada ma ba iya yin komai ballantana yanzu da ƙarfinsa ya ƙare duk da yana gudu da ƙyamar abun a zuciyar shi, ganin yadda ake yiwa d'iyarsa , a lokaci da dama ya kan so ya baiwa yarinyarsa labarin mahaifiyarta amma idan ya tashi faɗa mata sai ya kasa , a haka yake barin abin a ransa badan yana so ba, wani lokacin ya kan ji kamar ya yi kuka, idan ya tuna da mahaifiyar Fatima da irin zaman da sukayi lallai ba shakka Fatima ta dauki halin hakuri irin na mahaifiyarta. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 (Asalin labari) Shin wai wanene mallam iliyasu mahaifinsu Fatima ? Malam iliyasu hafaffen garin kano ne, a ƙaramar hukumar wudil yankin darki , yana zaune tare da iyayensa da yayyensa da ƙannensa, mahaifinsa malam Bello matan sa uku , laraba da hansai da kuma Rabi kowacce su tana da yara laraba itace ta fari, tana da yara biyar kuma itace mahaifiyar su mallam Iliya , bayan haka yana da ƙanne, biyu mata biyu, maza biyu, Khadija , Lami, da kuma Habibu da sulaiman , a dakin hansai wadda itace ta biyu yaranta huɗu , Adam, Muhammad, da kuma Salamatu, Rabi yaranta biyu , Hannatu da kuma Hadiza waɗannan sune zuri'ar malam bello . Mallam bello da iyalansa suna rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da tarbiyarsu, abin birgewa da sha'awa , yana kulawa da iyalansa yadda kowa kanyi sha'awar waɗannan iyalan . Hakama matan gidan suna da haɗin kai sosai kowacce duk da zaman kauye ne takan taimakawa ƴar uwarta, kuma suna taimakawa mijinsu . Malam iliya shine babba cikin yaran malam bello, gaba ɗaya ragowar yaran gidan kannensa ne , yakan sanya kannensa su tafi makarantar allo, kasancewar a lokacin babu makarantar boko, ya taimakawa ƙannenansa sosai wajen iliminsu na muhammadiyya. Sana'ar malam Bello noma idan ya girbe abinda ya shuka ya kai birni ya sayar , aikinsa noma da fatauci ta haka yake rike da iyalansa , lokacin da malam iliya ya kai mizanin samartaka sai ya sanya iliya akan harkar suna tafiya duk Inda yake harkar fataucinsa , in sun tafi sauran yaran maza sukan kula da harkar noma ta yadda zasu taimakawa mahaifinsu, lokacin da suka dawo gida fatauci Allah ya hadashi da Asabe wadda ta kasance yarinyace ƴar mace mahaifinta ya rasu tun tasa ƙarama dan haka ta tashi hannun mahaifiyarta babu kwaɓa , anyi gwagwarmaya kafin auren dan mahaifinsa bai so auren ba, amma ganin d'an nasa ya na ce yana sonta yasa ya barshi a haka akayi auren ba tare duk da ba kowa yaso auren ba amma a haka akayi auren ........... Please🙏🏻 Share &comments To be continue......... 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar uwa🌹🌸 (True life story) 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Fatan alkhairi ga duk makaranta littafina , godiya ta musamman ga masu gyara min kura kurai na . Jinjina gareki aunty nersmah da aunty dije, kuna namijin kokari wajen kuga littafina yayi daidai ba tareda samun matsala ba ina godiya sosai Allah ya bar kauna a tsakanin yan moonlight writer's association amin. Luv u all my dear fan's🥰 wannan page din sadaukarwa ne gareku. Shafi na 4️⃣ A haka akayi auren har amarya ta tare , kadahan kadaran ake zaune tsakanin Asabe da dangin malam iliya, babu wani jituwa a tsakaninsu , da yake ita kuma ba wani iya mu'amala tayi ba bata damu da su ba su ma basa zuwa inda take itama haka , a haka har akaci wata hud'u da aurensu a sannan ne ya ci gaba ta tafiye tafiyensa zuwa garuruwa , sai ya hutashshe da mahaifinsa akan ya zauna tunda shi ya kawo karfi sai ya dauki kaninsa su ka ci gaba da tafiya. Abinda yake damun 'yan uwan malam iliya akan irin rashin mutuncin da matarsa Asabe keyi na bata ganin kowa da mutunci k'annensa basa zuwa gidan yayansu , duk kuwa da irin soyayyar da ta ke tsakaninsu dan shi Allah yayi shi mai so kyautatawa 'yan uwansa , amma kash sai Allah ya hada shi da mata marar sanin darajar mutane. Har iya wannan tsawon lokacin Asabe ko batan wata bata tab'ayi ba hakan ne ya sanya ta kara bakin jini cikin dangin malam iliya , abinka ga k'auye sai surutai kala kala akan taki haihuwa , dan haka mahaifansa mata su ka fara mishi zancen ya kara aure , a sa'ilin da malam iliya yajewa da Asabe zancen nan kamar wadda zatayi hauka dan kishi , ta ci alwashin matukar dana raye babu shi babu kara aure , cin zarafi kuwa babu Wanda bai sha ba a wajen Asabe , ranar tayi yaji ta sanar da mahaifiyarta , abin ka ga gidan da babu tarbiyya haka mahaifiyar ta ta ta goya mata baya , kwananta d'aya a gidansu washe gari malam iliya yaje gidansu Asabe biko amma anan uwar ta ta ta sauke masa kwandon rashin mutunci da cin al washin ba za'a ayiwa yarinyarta kishiya ba indai tana raye kuwa , hakuri yayi ta bayarwa akan insha Allahu hakan bazata faru ba sannan ta yadda 'yar tata ta koma gidan amma sai da tayi ak'alla sati guda sannan ta koma. Malam iliya zaune gaban mahaifinsa wanda ya sanya aka masa kiranshi , ya sunkuyar da kai kasa yana sauraron mahaifinsa cike da girmamawa , " kaji abinda na ce maka ba rigada na yanke hukunci na zab'a maka maryama 'yar gidan aminina malam kalla kuma umarni na baka ba shawara ba na yanke aurenka nan da saba'ar wata in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai ka sanar da mai dakinka" , "to" ya amsa cike da girmamawa saboda baya tab'a jayayya da mahaifinsa akan komai ma , amma shi kadai ya san halin da ya ke ciki game da zancen da mahaifinsa ya fada masa , yayi masa sallama tareda shiga cikin gidan domin gaisar da iyayenshi mata , sosai inna hansai ta mishi fada tareda kwadaitar dashi romon da ake samu yayin da aka samu zuri'ah , ta gama yi masa nasiha sannan yayi musu sallama tare da innar sa ya tafi gida cike da fargabar ta ya ya zai fadawa matar sa Asabe a haka ya yini ya kwana babu sukuni da walwala , har sai da Asabe ta gane tambayarsa tayi yace mata ba komai wucewa tayi ba tare da kulawa ba . Washe gari da safe ya tashi da nufin sanar da mai dakin nashi, amma ya kasa , haka yayi ta ajiye da maganar har biki ya kusa saura sati biyu bai sanar da iya ba. Asabe na zaune a tsakar gida aminiyarta ta shigo da gudu cike da alamar firgici a fuskarta , dubanta Asabe tayi cike da haushi ta ce " wai baraka yaushe zakiyi hankali ne wai ke ba kiga cikin da ke jikinki ba kika shigomin irin haka salon ki zo haihuwa ki mutu " dakatar da ita Baraka tayi ta hanyar cewa " yo ba gwarama mutuwa ba an san lokacin ka ne yayi akan wannan bala'in da ya ke shirin tunkararmu" " wanne bala'i kuma Allah ya tsaremu da shi "ta fada tana tura d'an kwalinta gaba har zuwa girarta , " ke Asabe da labari na zo miki naga alamar ke baki sa ni ba ko " ? Ta tambayeta ta jiran amsarta "dan Allah ki fadamin mana kina wani jan zancen" ta sake tura dan kwalinta gaba, "to wallahi mijinki yqna nan yana shirin k'ara aure" , "kan uban chan ba Ankara da garin da ta b'arar ba , ta zunduma wani uban ashariya ," haba biri yayi kama da mutum , shiyasa ya kasa sukuni a cikin gidan nan har ya tafi fataucin nan ashe ya san abin da su ke shiryawa shi da matsiyatan iyayan na shi ", lallai ya taro wa kansa bala'i wallahi ," a'a tsaya mana ai ba hargagi zakiyi ba " cewar baraka da ta ke sake neman wajen zama, " tsayawa zamuyi mu fitar da maganin matsalar da ta ke tunkaro mu", zaman 'yan bori tayi ta zuba uban tagumi hannuwa biyu biyu , " inajinki baraka" ta fada dana kallonta " me ki ke so ayi yanxu "? Ta tambayeta tana kallonta , " kinsqn babu yadda za'ayi nabar wata mata ta auri malam wallahi kina ganin bana haihuwa ta yaya zaayi na bar wata ta shigo ta haifawa malam iliya d'a musamman ma na miji ta yadda zata cinye dukiyarsa " " kinyi gaskiya kuwa aminiyata" yanzu kinaso a tsayar da maganar aurenko"? Ta tambayeta ," eh " ta bata amsa " to yanzu tashi zakiyi mu tafi chan kauyen lajawa akwai wani hatsabibin boka , sunanshi boka sha yanzu magani yanzu , amma ina fatan kinada kudi a hannunki "? Ta tambayeta tana kallonta ," eh da akwai wanda malam ya barmin da zai tafi ban tab'a komai ba ", " to tashi zakiyi mu tafi dan kinsan da zafi zafi akan daki karfe", " eh to bara na Shiga na dauko mayafina" ta shige daki a birkice domin dauko mayafi ,sannan su ka yi waje cikin hanzari. Mata mu kula! Mu kula ,a kula! , kawaye sukan kawo cikas sosai a zaman aure , kar ki bari kawarki ta rudeki takaiki ta baroki akan tudun dana sani , sirrinki ki boyeshi karki sake ki bayyanawa kawarki halin da kike ciki da mijinki , zata sanyaki kiyi danasani a rayuwarki da rayuwar aurenki baki d'aya, daga k'arshe mijinki ya sakeki , in batada aure ta aure miki shi , Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu amin . Basu k'arasa cikin dajin ba sai da sukayi tafiya sosai har rana ta fad'i kana suka karasa , dan har Asabe ta sare amma Baraka ta k'arfafa mata guiwa da kyar su ka karasa bayan bakar wahalar da su ka sha k'afafunsu sun kumbura sosai sun jigata , kana su ka karasa wajen , tunda su ka nufi wajen Asabe takejin iface iface namun daji kukan tsuntsaye da sauransu , a haka su ka karasa ," Ku shigo da baya" cewar boka sha yanzu , cikin wata gabjejiyar murya, da sauri suka juya har suna kokarin bige junansu , Baraka ta zunduma ashar ta yiwa Asabe da nunin itama tayi wannan itace sallamar Shiva wajen bokan , aikuwa itama tayi , sannan ya basu izinin zama , su ka zauna ,Asabe ta bud'e baki zatayi magana yayi mata nuni da tayi shiru , zuwa kamar Minti biyar sannan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata, yayi nuni da wata kwarya sai ta taho da kanta ta zauna a mazauninta kan wata tararriyar kasa , yayi nuni da ruwan cikin kwaryar aikuwa yayi bakikkirin daga baya kuma ya koma fari, aikuwa ya shek'e da dariya" angama bukatarki ta biya za'a fasa auren nagama komai , yanzu maganar aure babu ita na Sanya kiyayya mai karfi tsakaninsu " Myrna sosai Asabe tayi najin an fasa auren malam iliya ,su ka yiwa boka sallama da zasu tafi ya bata maganin da zata zuba masa a abinci da Wanda zata zuba tayi wanka sai turaren da zata sanya Wanda idan har ya shak'a to zai manta da kowacce mace a duniya sai ita, sannan suka nufi hanyar gida a lokacin anyi sallar magariba sannan su ka karasa gida , sai da suka huts sannan Baraka ta nufi gidanta itama, da kudirin aikata abinda boka ya sanyata ta kwana , dan tana tsammanin dawowar malam a tsakankanin wannan lokacin , a haka tayi bacci tattare da mummunan k'udiri a ranta. A chan gidan su malam iliya kuwa anata shirye shiryen biki saboda wannan bikin na so ne , ana wannan yanayin malam iliya ya dawo saga fatauci , lokacin da ya je gidansa da yaga Asabe bata nuna masa wata alama ta nuni da cewa tasan zancen hakan ya saka ya ji dadi kuma yayi mamaki bisa ga yadda yasan qauye da gutsuru tsoma , amma yaga sab'anin haka, hakan ya sanyashi ya tafi gidansu domin gaida mahaifins. Tana fita Asabe ta yi shirinta tsaf da magungunan da bokq sha yanzu ya bata ta zauna zaman jiran malam ya dawo daga gidansu .............. Please🙏🏻 Share &comments. To be continue........ Luv u all my fan's🥰🥰😍 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸 (True life story). 🍁Daga alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Ina matuk'ar godiya gare ku masoyana , saboda nuna kulawarku ga littafina mai suna Kishiyar uwa , a gaskiya na rubuta shi ne badan komai ba sai don tunanin da nayi wannan shi ne abin da yake damun al'umma , idan mata taga an bar mata 'ya'yan abokiyar zamanta idan har basa shiri da ita to fa su ma yaran nata sun Shiga uku , dan Allah mata mu kiyaye wannan hakkin lallai sai Allah ya tambayemu a kanshi , ki sanya a cikin ranki idan da yaranki ake yiwa haka ya ya zakiji a cikin ranki , Allah yasa mu gyara amin. Ina ganin comments naku gaskiya ina jin dadi , kuma ku ma burgeni , insha Allahu bazan baku kunya ba Comments🥰 Maman Ammar Kishiyar uwa🌹💞nicely sis Allah ykara basira ina matukar jin dadinsa wlh 🥰🥰 ~phareeeda Allah sarki Fatima zakisani kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭 Duk naga comments ina godiya. Shafi na5️⃣ Ko da malam Iliya ya k'arasa gidansu ya tarar ana ta shirye-shiryen biki , wajen mahaifinsa ya fara zuwa ya gaida shi amsawa yayi kana ya mishi maganar "angama komai da ake buƙata yanzu abinda ake jira shi ne saboda su na so su kai kayan aure da sadaki, saboda auren ya kusa, amsawa yayi da to , kana yayi godiya, ya yi masa sallama ya shiga cikin gidan wajen iyayen sa mata , nan ma ya tarar suna ta shiri sosai , ya gaida su ya mu su alkhairi, ya tsaya sai da su ka ga ma komai na harkar kai kayan auren, da sadaki sannan ya nufi hanyar gidansa. A can gida kuwa Asabe ta gama har had'a komai da tasan boka sha yanzu ya ba ta, dan haka a halin da ake ciki malam Iliya kawai ta ke jira ya dawo gida, tayi wanka da magani ta shafa turaren da sauran kayan amfanin da ya bata za ta sanya masa a abinci. Da sallama ya shiga a bakin sa , amsawa tayi cike da kwarkwasa , ƙamshin turaren da boka ya bata shi ya shak'a ai kuwa ta ke yaji kanshi yana juyawa , wanka ta jashi yayi, a hakan dai ta bashi wannan abinci ya ci , kana ya fada mata kanshi na yin ciwo zai kwanta rakashi tayi har sai da ta tabbatar da ya kwanta sannan ta fito daga ɗakin ta, fita tayi daga gidan domin sanar da k'awarta halin da ake ciki. Har bayan magariba bai tashi ba har Asabe ta dawo daga gidan Baraka , sannan ya tashi daga baccin , zuciyarsa yaji ta b'aci gaba ɗaya yaji auren da ake shirin yi masa ya fita a ransa , yaji ya tsani yarinyar gabaki ɗayanta, haka ya kwanta ransa na b'aci, ko da gari ya waye mahaifinsa ya kirashi bai je ba , har aka kwana uku bai je ba , kai auren ya taho dangin sa nata harkokin biki amma shi banda shi, dan haka mahaifinsa ranshi ya b'aci yayi niyyar zuwa har gida ya same shi. Da wata ranar talata lokacin saura kwana biyu a ɗaura auren mahaifin nasa yayi dirar mikiya a gidan, faɗa ya rufe shi dashi, sosai shi kuwa ko a jikin shi ,sai ma duban mahaifin na sa da yayi yace masa shi ya fasa auren daskarewa mahaifin nasa yayi abinda bai taba ji ba , juyawa yayi ba tare da yace komai ba ya tafi gida cike da damuwa, ko da ya sanar da matan nashi sosai su ka ɗauki zafi akan haka, amma da yayi musu bayanin yadda zasu fi ganewa su san ba laifin sa ba ne ba, sai su ka daina hargagin da su ke yi , a haka aka bawa iyayen yarinya hakuri abin ka ga k'auye gari fa ya ɗauka aka yi ta ƙananan maganganu, daga baya komai ya lafa, ita kuwa data ga haka sai ta saki jikinta tayi ta iya shegen ta abin ta , ta kuma mai da zuwa wajen boka sha yanzu kamar masallaci, mahaifinsa ya nema masa ak'alla yara sunyi biyar tana wargaza auren daga baya mahaifinsa ya hakura ya zubawa sarautar Allah idanu, yayin da tsanar Asabe ta dawo sabuwa a zuk'atan matan gida da yaransu . Yanzu shekarar malam Iliya goma da aure , batun gwagwarmayar da ya sha , a harkar sana'arsa da rayuwar auren sa da Asabe Alhamdulillah, komai ya kankama ya samu rufin asiri sosai , babban abinda ke damunsa shi ne rashin haihuwa domin a wannan cikin shekarun aminyar Asabe Baraka ta haihu namiji aka sanyawa d'an nata sunan mahaifinta wato Adamu, a wannan shekarun mahaifin malam Iliya ya sanya ana tayiwa d'ansa addu'ah akan Allah ya dawo masa da d'ansa daga Sharrin matarsa Asabe, Allah kuwa ya amsa addu'arsa da ya dade yanayi. A garin yawon fatauci, wata rana malam Iliya fatauci ya kaishi zariya , bayan ya gama komai yana shirin dawowa gida a nan Allah ya haɗa shi da mahaifiyar Fatima wadda ake kira da maimunatu ta kasance haifaffiyar garin zariya ce , sosai ya yaba da hankalinta , bai yi mata magana ya bita gidansu ya tambayi izinin neman aure mahaifinta ya amince , amma ya faɗa masa shi fataucine ya kawo shi zariya , shi haifaffen garin kano ne, ya kuma tambaya akan in ya tashi dawowa, magabatan sa zasu zo nema masa aurenta , a haka suka rabu badan junansu sun so ba , ko da ya fad'awa mahaifinsa yayi murna sosai ya faɗawa matansa amma yayi gargadi mai kyau akan kar wanda ya fitar da zancen, haka kuwa aka yi aka ɓoye maganar har sai da biki ya rage y'an kwanaki, amma Asabe bata da labari. Alhamdulillah lallai rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya , domin kuwa a ranar jumaah ne aka daura auren malam Iliya da maimunatu mahaifiyar Fatima , mace mai hakuri da kawaici , mahaifin malam Iliya shi yayi komai na auren. Sai ranar da aka daura auren sannan Asabe taji , ranar ansha bala'i domin kuwa gidansu malam Iliya ta tafi ta dinga yi musu hauka amma ba wanda ya kulata ta k'arashe rashin mutuncin ta tayi gida kamar mahaukaciya, ta koma a ranar , ko da ta koma gidan bai kulata ba ta ƙarasq wulakancinta ta hakura . Dare nayi 'yan kawo amarya suka kawota aka a jiye ta a ɗakinta suka mata fad'a sosai , aka ce a kirawo Asabe domin a musu fada amma ta aika musu sak'onnin zagi ba arziki su ka tattara yanasu yanasu su ka yi waje cike da Allah wadai akan halin Asabe , aka bar amarya a cikin gidan mijinta . Sai muce Allah ya bada zaman lafiya , ya kauda fitinar Asabe amin. Godiya mai tarin yawa a gareku yayata y'ar uwata wato Usaina musa saleh bisa ga gudummawarki gareni Allah ya taimakeki a aikinki ya bada sa'a amin. Godiya a gareku yan moonlight writer's association Allah ya k'ara had'a kawunan mu amin ya taimakemu amin , ina godiya sosai. Please🙏🏻 Share &comments To be continue........ 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ Ina k'ara godiya ga Allah subahanahu wata'ala da ya kara bani damar ci gaba da littafina na kishiyar uwa, kuma ina godewa mahaifana da y'an uwana da suka jajirce wajen ganin na ci gaba da rubutu na , haka ma fan's nawa ina kara godiya. 🥰😍 ina ganin comments kuma inajin dadi sosai wallahi. Sadaukarwa ga duk makaranta littafin nan tare da y'an moonlight writer's association, Allah ya k'ara hada kawunanmu amin y Allah . Shafi na 6️⃣ Aka bar amarya gidan mijinta , da dare yayi sosai abokanan ango suka rakoshi , amma fafur Asabe ta k'ek'asa k'asa ta hanasu shiga gidan, ban yadda suka iya haka suka koma , suka yiwa malam Iliya fatan alkhairi shi ma yayi musu sallama sannan suka tafi , shi kuma ya shiga cikin gida aikuwa yana shiga ta ce da wa Allah ya had'ani in ba dakai ba ta shiga yi masa ruwan bala'i amma yayi mata banza wannan ya k'ara kular da ita sosai , ya juya zai tafi tayi sauri ta rik'e masa wuyan rigarsa ta baya , a fusace ya juyo ya sauke mata wani wawan mari a kuncinta wanda saboda tsabar razana da mamaki sai da ta zube k'asa , ni kuma da nake tsaye ina kallon abinda ke faruwa dariya nayi a hankali saboda kar masifar ta dawo kaina, amma ke ma Asabe in banda tsaurin ido ta yaya zaki rikewa sabon ango wuyan riga ki hanashi shiga d'akin amaryarsa abinda yafi haka ma zaki gani🥴 , saboda duk rashin mutuncinta bata tab'a rik'e masa riga ba da sunan rashin kunya sai yau , tana a zaune kafin ta dawo hayyacinta har ya shige d'akin amaryarsa Maimunatu sai rufe k'ofarsa taji garam aikuwa da sauri ta zabura kafin ta k'arasa har ya sanya sakata , sai dai muce asha amarci lafiya malam Iliya😍. Asabe kuwa kwana tayi tana hauka a tsakar gidan in ta gaji ta zauna in suka motsa mata tayi ta buga musu k'ofa haka ta kwana bata runtsa ba tsabar masifa. Washe gari da safe kuwa suna fitowa suka ganta a zaune a tsakar gidan rana d'aya duk ta lalace , saboda masifar kishi , aikuwa tana ganin sun fito haka ta nufi maimunatu da itace sauri yayi ya kareta tare da watsawa Asabe mari ni kuma abin nema ya samu matar direba ta haifi mota ina kallon ta ina mata gwalo amma bata ganni ba ta juyo kenan b'arina ni kuma na fece🚴🏻‍♀️ a miliyan, a ranar haka ta hanasu sakat a gidan ya zamana ko ina maimunatu zata shiga sai dai malam ya rakata , a haka ta dinga rayuwa har malam ya koma da sana'arsa wato fatauci , aikuwa gida ya zamar mata kamar birsin dam ma iyayen malam da k'annensa suna sonta shi ne abin ya zame mata da sauk'i . A lokacin da suka cika wata biyar da aure Allah ya azurta maimunatu da samun ciki zo kuga murna gurin malam Iliya , rana samun kulawa sosai , tunda Asabe taji maimunatu na da ciki shikenan fa hankalinta ya tashi abinda take ta gudu gashi ya faru , da sauri ta garzaya gidan aminiyarta baraka , a tsakar gida ta zube had'e da dafe kai " na shiga uku ni Asabe Baraka tawa ta k'are a gidan malam " ta fad'a cike da tashin hankali " nutsu kiyimin bayani" cewar Baraka wadda ke yiwa Ado wanka a lokacin yana da shekaru takwas da haihuwa," wai wachchan matsiyaciyarce keda ciki " a razane Baraka ta dubeta da gaske kikeyi mun shiga uku , to yanzu menene abin yi "? Ta tambayeta " to ai nima shi nake nema shiyasa na zo gurinki " bara na gama shirya Ado " ta ce tana kokarin tashi" to kawai Baraka tace domin kuwa hankalinta ba'a jikinta yake ba , rana gama shirya shi ta barshi a gida suka dauki hanyar wajen boka , sunyi masa bayani a cikin bayanin kuwa har da son haihuwar da Asabe ta ke son tayi yace musu zai fara ba ta haihuwar kafin nan , aikuwa a take ya sanya aljani ya shiga jikinta a take a wajen ta samu ciki sannan yayi mata alk'awarin sawa malam kiyayyar maimunatu da abinda ta haifa godiya sukayi masa sosai suka tafi gida . Bayan kamar wata biyu da samun cikin Asabe ya bayyana malam yayi murna sosai na tunanin Allah ya dubeshi lokaci guda ya bawa matan sa ciki , a koda yaushe ya kanyi addu'ar Allah ya saukesu lafiya , a b'angaren Asabe kuwa burinta ta haifi namiji kullum burinta kenan, ana cikin wannan yanayin mainmunatu ta fara fuskantar matsala wajen malam gashi cikinta ya farayin nauyi , tsangwama sosai take sha wannan alamu ne na Cesar boka ya cika aikinsa, ana cikin wannan rintsin Allah yayiwa malam mahaifin malam Iliya rasuwa bayan gajeriyar jinyar da yayi Allahu Akbar giwa ta fad'i aikuwa anayi rashi ba Kad'an ba , gashi a wannan lokacin sosai aikin boka ke ci saboda tun iyayensa basu gane ba da 'y'an uwansa har suka gane sosai iyayensa sukayi masa fad'a amma abu kamar tiri , sai ma gaba abin yakeyi ,. Bayan wasu 'yan watanni da rasuwar malam lokacin cikin maimunatu ya tsufa sosai gashi ba kwanciyar hankali , wannan ya sanya ta rame ta lalace , tayi bak'i , abin tausayi ga ba kulawa daga wajen miji sun rigada sun maidashi rak'umi da akala bayajin maganar kowa sai ta Asabe, Allah ya taimaki maimunatu kannensa na zuwa ta tayasu hira dan haka sai damuwarta ta ragu sosai, ana wannan yanayin ciwon nakuda na kamata ga malam baya nan , ciwo takeyi sosai tun dare har safiya amma Asabe na jinta bata koda lek'a ba , ita a burinta ma kawai maimunatun ta mutu kowa ma ya ana cikin haka Allah ya jefo da hadiza k'anwar malam din aikuwa tana ganinta cikin wannan halin ta juya ta sanarda mahaifanta aikuwa basu dade da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya ta samu d'iyarta mace masha Allahu yarinya son kowa kyakykyawar sosai, kowa in ya ganta sai ya kara kallonta saboda tsabar kyau, a lokacin da Asabe taji anyi haihuwar an samu mace murna tayi sosai da sosai a ganinta ita zata haifo namijin , haka akayi suna malam bai dawo ba k'anin malam din shi ya sanyawa jaririya sunan mahaifiyar maimunatu yarinya taci suna Fatima, komai y'an uwan malam sukayi saboda yana chan harkar fataucinsa, ko da ya dawo bai wani nuna murna sosai ba duk kuwa da abinda yake nema shiya samu , haka dai rayuwa tayi ta yin juyi da rayuwar Maimunatu da yarinyarta Fatima cikin rashin kulawa da k'unci , bayan watanni hud'u Asabe ma ta haifi d'iyarta mace bataso hakn ba amma kuma ba yadda ta iya lokacin malam yana nan dan haka zo kaga murna da farin ciki ba kama hannun yaro , ranar suka aka sanyawa yarinya zainabu , anyi shagali sosai , a haka rayuwa tayi ta tafiya har Fatima tayi shekara d'aya ko tsakar gida basa iya fitowa, a sannan ne Asabe it a da k'awarta sukayi mata asiri akan in ta tafi karta dawo gidan a lokacin ne aka aika mata da zancen mahaifinta bashida lafiya , da kyar aka barta ta tafi da sharad'in bazata tafi da Fatima ba haka ta barwa mahaifiya malam iliya ta tafi, cike da kewar yarinyarta, Allahu Akbar a hanyarsu ta tafiya Allah ya aiko da wani gagarumin hatsarin motar da maimunatu take ciki tayi hatsari mutane da yawa sun rasu Allahu Akbar Allah ka jik'an musulmi amin, a lokacin da labarin hatsarinsu ya Shiva cikin k'auyen ba k'aramin tadawa mutane hankali yayi ba da kuma aka sanar musu da cewa ba Wanda yayi rai a cikin matafiyan lallai mutanen k'auyen sunji rasuwar tata musamman ma y'an uwan malam dashi malam din , amma Asabe a lokacin ne ma duniyarta ta koma sabuwa ba ta da wata damuwa a haka har aka karaci alhinin rasuwar akabar masu rashi da rashinsu. Bayan kamar data biyar a lokacin Fatima tayi wayo sosai dan haka Asabe ta takura da sai an kawo mata ita ai itama mahaifiyarta ce da kyar iyayen malam suka bada ita, to fa tun lokaci ta fara zan wahala har kawo yanzu ba wanka ga aikin da yafi karfinta shi ake bata tunda ta tashi bata san mecece kulawa ba duk kuwa da 'yan uwan malam na k'ok'ari amma wani lokacin basu ma San anayi ba , babu irin rayuwar da Fatima bata gani ba a gurin KISHIYAR MAHAIFIYARTA data baya da abin ya fara sakinsa sai ya bar harkar fatauci ya koma gona don ya dinga kulawa da yarinyarsa haka kuma suka rufe masa baki ta yadda bazai tab'a fad'awa Fatima labarin mahaifiyarta ba. Wannan kenan 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 (ASALIN LABARI) Kwata kwata malam bayajin dadin rayuwar da d'iyarsa ke ciki , gashi yanzu yana halin rashin lafiya mai tsanani ga tsufa ya kamashi, gashi a yanzu ne yarinyarsa take buk'atar kulawa a gareshi . Ranar wata Asabar da safe baraka ta je wajen Asabe , da zancen auren Fatima da Ado tunda ya matsa mata , da sauri Asabe ta amince ga bisa la'akari da tayi na ganin y'an birni in dai sun shigo garin suka d'ora idanunsu akanta su ce suna San ta , iya kuma ba kowa tayiwa burin auren irin wadannan ba sai Abu , ta sanar da ita babu damuwa , amma sai da su ka sanya aka kulle musu bakin malam din , aikuwa tana fada masa ya amince duk da zuciyarsa bataso amma haka ya yadda, lokacin da ya sanarda Fatima bata mu da masa ba duk kuwa da babu Wanda ta tsana a duniyar nan sama dashi,sosai ake tayin shirye shiryen biki , a wannan lokacin ciwon malam yayi tsanani. Ranar wata Asabar bayan Fatima ta dawo daga tallah, sallama tayi a d'akin mahaifinta ya amsa mata muryarsa na karkarwa saboda ita kadai ke kulawa dashi , "Fatima ki yafemin na miki laifi na hadaki da wanda bakya so nasan ban kyauta ba amma ina ganin gwara haka fiyeda ki zauna cikin bak'in ciki , sai maganarsa ta katse numfashinsa yana kai kawo chan kuma sai taji shiru , aikuwa da gudu ta fita tana k'walawa inna Asabe kira ," Inna! Inna! Inna kizo wallahi baba ya rasu mun Shiva uku" da gudu Asabe ta fito ta nufi d'akin malam din abirkice dan ganewa idonta meya faru........ Godiya ta musamman gareku masoyana ina fatan kuna cikin k'oshin lafiya kuma zakuji dad'in karatu , ayi karatu lafiya. Luv u all my dear fan's😍😍 Please🙏🏻 Share &Comments To be continue........... 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸(True Life Story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DAYA BANI DAMAR CI GABA DA RUBUTUN LITTAFINA , MAI SUNA KISHIYAR UWA . GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN MOONLIGHT WRITERS ASSOCIATION, ALLAH YA K'ARA HAD'A KAWUNANMU AMIN GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN UWA NA DA ABOKAN ARZIKI. GODIYA TA MUSAMMAN GA FANS DINA , DAMA FANS DIN LITTAFIN KISHIYAR UWA, INA GODIYA SOSAI, INA FATAN ALLAH YA BANI DAMAR KARASA ISAR DA SAK'ON DA NAKESO NA ISAR , KUMA BANA FATAN NA BAKU KUNYA . MASU TURO DA COMMENTS INAJIN DADIN HAKA. INSHA ALLAHU YANZU MUKA NUFA CIKIN LITTAFIN GADAN GADAN , INA FATAN ZAKU BIYONI DOMIN JIN MAI YAKE SHIRIN FARUWA. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 SHAFI NA7️⃣-8️⃣ Koda inna Asabe ta k'arasa cikin d'akin , ganin halin da malam yake ciki ya sanya ta zunduma ihu tana kururuwa , Abu ce ta fito daga d'akinta cikin yatsina fuska tana duban Asabe cikin gadara " wai ke inna ki damu mutane da sanyin safiyar nan baki ganin mutane suna yin bacci", galala Asabe ta tsaya tana kallon Abu cikin ido kana ta dubeta " yo ke dan k'aniyarki kina ganin mahaifinki cikin wani hali amma kuma kika tsaya kina yiwa mutane zancen banza" "ni dai gaskiya ana takuramin wallahi " ta fad'a ta komawa cikin d'aki ta banko k'ofar d'akin, maganar Fatima ce ta dawo da ita cikin hayyacinta " inna bari na duba in baba muhammadu yana nan "( kanin malam iliya ) , bata jira me zatace ba ta fallah da gudu ta bar Asabe na sallallami had'e da tafa hannaye. Ba'afi mintuna biyar ba sai gasu sun shigo cikin azama , kanin nasa ya shiga cikin d'akin da sauri dan ganin me yake faruwa, da Sauri ya dawo ya dubi Asabe "maza shiryashi asibiti zamu kaishi har yanzu da sauran ransa " wata ajiyar zuciya Fatima ta saki kana ita kuma Asabe ta shiga domin shirya shi . Baba muhammadu ne ya shigo shi da samari biyu suka taimaka masa suka Sanya malam a cikin mota , domin tafiya da shi asibitin , Fatima ta k'ekasa k'asa akan tanason zuwa amma Asabe ta hana ta haka tanaji tana gani aka tafi da malam asibitin. Ko da suka k'arasa basu samu wata matsala ba aka shigar da shi d'akin da za'a dubashi , an dubashi anan aka gane yawan tunanin da yakeyi da kuma wani abu da ya ajieshi a ransa ya haifar masa da ciwon zuciya mai tsanani, sosai wannan maganar ta razana k'anin nasa, haka ma Asabe ta girgiza da wannan maganar , ita bama wannan ba me malam din ya ajiye a cikin zuciyar tasa shi take tunani fiye da rashin lafiyar tashi , haka suka gama komai da ake buk'ata kana suka zauna tare da shi. Achan gida kuwa Fatima kasa tsinana komai tayi sai tunanin mahaifinta takeyi, bataso ta rasa shi a halin yanzu da take matuk'ar buk'atarsa a rayuwarta , ya Allah ka dubeta ka Sanya mata tawakkali a halin rashin lafiyar mahaifinta amin. Har k' arfe uku na rana basu dawo ba, lokacin har ta gama abinci da komai da komai na gidan sai dai tallah ne yau kam bazata iya zuwa ba , gashi ta Sanya abinci a cikin kwano tana jiran ko za'a daukawa mahaifinta akai masa , haka tayita zaman jiran amma shiru. Abu ce ta fito daga d'akinta da kaya a hannunta , watso mata tayi a fuska , " gashi nan ki wankemin saboda kayana sun taru babu masu wanki a cikin" dubanta Fatima tayi tare da cewa " amma ai kinga Baba bashi da lafiya ko ta yaya zan iyayin wanki a halin da nake ciki , " au bazakiyi ba kenan, to wai ma da kike cewa Baban bashida lafiya ina ruwana da rashin lafiyar tasa , kinga in zakiyi min wanki kiyi in kuma kika k'iyi kema kinsan sauran banza kawai, ta juya ta shige cikin d'akin na ta , tabar Fatima baki bud'e , babu yanda ya iya haka ta d'ebi kayan ta wuce ta wankesu, ba ita ta gama ba sai da akayi sallar magariba , kana ta gama wankin tsaf saboda akwai su da yawa. A chan asibitin kuwa an bawa malam gado , dan ciwon nashi yayi tsanani dan haka kiri kiri da aka ce inna Asabe zata dinga kwana ta nuna itafa bazata iya ba , malam muhammadu ne ya tafi da kansa ya maidata gida kana ya dauko Fatima domin ya fuskanta da ita zanta iya juriyar kula da malam d'in , aikuwa koda akace ta shirya ba musu domin itama tana buk'atar ganin mahaifin nata , da Asabe ta so ta hana ganin in Fatima ta tafi to fa babu mai aiki a gidan haka zalika babu mai zuwa mata tallah ya ya kenan , amma da yake dama ba shiri sukeyi da muhammadun ba haka yayi Jan ido wa Asabe ya tafi da Fatima asibitin, ko da taga mahaifinta halin da yake ciki kuka ta kamayi da k'yar Baba Muhammadu ya lallasheta , da cewar ai dana samun sauk'i in taci gaba da kuka zai maidata gida , jin haka ya sanya tayi shiru ba shiri, a haka suka kwana bata samu damaryin bacci ba har asubah a sannan ne malam Iliya ya farka ruwa ya nema aikuwa da Saudi Fatima ta k'arasa tareda taimakon baba muhammadu su ka bashi ruwa" sannu Baba" abin da ta iya furtawa kenan sai hawaye , da Sauri ta goge da ta tuna da sharad'in da k'anin baban nata ya fad'a mata , murmushi malam Iliya yayi mata tareda shafa kanta da hannunsa wanda babu ruwa a jiki da muryarsa da bata fita yace " Allah ya miki albarka d'iyata " ," amin baba" tayi furucin a sanyaya , to bayan su taimaka masa yayi alwala suka jinginar da shi yayi sallah , kana suka soma hira har wayewar garin snnan ya koma bacci. "Wallahi in baki fito daga d'akin nan ba ko ki kuka da kanki" , Asabe ce ke wannan hargagin wa Abu , karar bud'e k'ofar da k'arfi shiya sanya Asabe ja da baya " wallahi inna bazanje aike ba gwarama ki fita da kanki kije ki siyo, hana ayi ta damun mutane aikin banza aikin wofi" Abu ce tayi maganar ta karkad'a kafad'a, jawota Asabe tayi aikuwa itama ta kamata da kokawa sosai sukeyin dambe , ni kuwa abin nema ya samu jinayi kamar na kad'a musu ganga safiyi da kyau sosai" innalillahi kai kai kai menene haka" Baraka ce tafi wannan furucin tana tafa hannu ," ki barni in ji mata ciwo yarinyar nan kamar bani na haifeta ba wai har nace ta zo taje aike aike amma ta k'iya ", wallahi bazanje ba ehe ta shige d'aki had'e da Santa sakata , Baraka ce ta dubi Asabe ke ni ba wannan ba ma wai ya batun auren ne saboda yaron nan ya matsamin " ," eh na sanarwa da malam din ya amince yanzu saura saka ranar biki kawai " Asabe ta fad'a da yanayin alhini a fuskarta" ke malam din ma fa bashi da lafiya hana asibiti," " meya sameshi to Allah ya k'ara afuwa" bata saurari me Asabe zatace mata ba ta juya ta fita . To har azahar sannan Asabe ta gama aikin gidan duk ta wahala ta jigata ta sauya kamanni, Rana gamawa Abu tazo da d'iba abincin ta kuma shigewa d'aki ta banko k'ofa . To kwanan malam uku a asibiti a lokacin ya samu sauk'i ba laifi dan har ana tunanin za'a sallameshi , Fatima sosai tayi murna ga bisa samun sauk'in mahaifinta , domin shi ne a yanzu yake matsayin jigo a rayuwarta , a daren rana ta hud' u ciwon malam ya dawo sabo sosai hankalin fatima ya tashi kuka takeyi sosai , hankalinta ya tashi gashi baba Muhammad ya fita inna Asabe kuwa tunda ta tafi bata dawo ba tun ranar da aka kawo malam din, ta yunk'ura zata tashi ya rik'e ta "tsaya d'iyata mafi soyuwa a gareni" , wasu zantuttuka masu kama da wasiyya ya shiga yi mata wad'anda bata ganewa , nasan dai nayi mini laifi ban sanar da me ko asalin wacece ke ba hak'ik'a nasanki da hak'uri da juriya to kick gaba daga inda nasanki hak'ik'a akwai jarrabawoyi da yawa da ya kamata ki cinyesu ina fatan zaki cinyesu , kiyi hakuri da duk halin da kika tsinci kanki a rayuwa , kiyi taka tsantsan a gaskiya auren da akeson yimiki banasonshi amma saboda gudun wannan ranar da zan tafi in barki ya sanya na yanke hukuncin da kiyi aure amma d'iyata in kin samu miji ko bayan raina kiyi aure hak'ik'a inason kiji dad'in rayuwa ina mini wasiyya kiji tsoron Allah", a lokacin ya bata labarin mahaifiyarta sosai takeyin kuka sosai dana ashe yadda tayi hak'uri mahaifiyarta ta fita , lallai itakam batasan menene zai faru ba , muryarsa a lokacin ta farayin sanyi . Allahu Akbar a take a lokacin Allah ya amshi rayuwar malam Iliya Allahu Akbar said dai mice Allah ya jik'an musulmi jin shirun da Fatima tayi shi ya fargar da ita halin da ake ciki da gudu ta fita waje dan sanarwa da doctor halin da ake ciki , kafin ta k'arasa tayi kicib'us da k'annen malam din nuni ta Shiga yi musu bakinta ya Gaza furta komai , da sauri suka Shiga d'akinWRITER'S dubawa baba muhammadu ya ja zanin gadon yarufewa malam fuska , ganin haka a take Fatima ta sulale k'asa sumammiya........ GODIYA A GAREKI MAHAIFIYATA HAJIYA FATIMA TURAKI ADAM, ALLAH YA JA DA RANKI YA K'ARA MIKI TSAWON RAI MAI AMFANI. JINJINAR BAN GIRMA GAREKI AUNTYNA SHAFA'ATU SULAIMAN UMAR JINJINA GAREKU Y'AN MOONLIGHT WRITER ASSOCIATION, ALLAH YA HAD'A KAWUNANMU AMIN.💔💔 🙏🏻please Share & Comments TO BE CONTINUE..... 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 MASHA ALLAHU LAK'UWWATA ILLAH BILLAH. BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM, SALATI DA AMINCI SU TABBATA GA ANNABIN MU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA AHLAN GIDANSA DA SAHABBANSA MASU GIRMA. SADAUKARWA GA DUK MAKARANTA LITTAFIN KISHIYAR UWA DAMA FANS DIN GROUP NA NUSSAD HOUSA NOVELS. Shafi na9️⃣-1️⃣0️⃣ Ganin haka ya sanya sukayo kanta da sauri cikin gaggawa baba Muhammadu ya nufi ofishin likita , domin sanarda shi abin da yake faruwa. Tare da likitan suka shigo d'akin cikin tare da nurses guda biyu , direct wajen malam iliya ya nufa su kuma nurses din suka nufi wajen Fatima dake kwance a sume, suka d'aga ta suka d'aurata akan gado domin bata agajin gaggawa domin ganin ta dawo hayyacinta. A chan d'aya b'angaren sosai likitan ya shiga duba malam Iliya amma ina hak'ik'a rai yayi halinsa k'ara rufeshi yayi , ya juya ya fuskance su tare da fad'in "sai dai hak'uri , Allah ya yi masa cikawa ", sosai d'akin ya rud'e da kawar jama'ah da kuka, da k'yar aka lallab'esu suka sanya gawar malam Iliya a mota aka nufi gida domin sada shi da gidansa na gaskiya. Ko da suka isa gidan Asabe kamar tayi hauka , sosai takeyin kuka tuburan , ita kuwa Abu ko a jikinta , sai dai ta kai ta kawo , tana taunar cingam da wak'a, Allah wadai kam tasha shi ba kad'an ba a gurin mutanen garin. Karfe takwas na safiya aka kai malam Iliya gidansa na gaskiya da yake rasuwar dare yayi , ko da akazo kaishi da k'yar Asabe ta bari aka fitarda shi daga gidan kuka sosai kamar mhaukaciya ta koma haka dai aka rik'eta aka zaunar da ita sannan aka kai shi gidansa na gaskiya Allahu Akbar sai dai muce Allah ya jik'an malam Iliya da rahama amin. Har aka kwana uku da rasuwar Fatima bata farfad'o ba sai a rana na hud'un ne ta farka , zabura tayi ta mik'e zaune kamar a mafarki abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata , k'ara ta sanya ta k'ok'arin cizge ruwan da aka sanya mata , d'aya daga cikin k'annen malam Iliya ce ta rik'eta , " sannu y'ar nan " ta fad'a tana k'ok'arin rik'eta , "inna ina baba na yake" ta fad'a tana kallonta da zak'uwa da son jin amsar da zata bata ," karkice min Baba na ya tafi ya barni " , ta k'ara fashewa da kuka , sosai suka tausaya mata , da k'yar baba Muhammadu ya k'araso cike da tausayin yarinyar dan yasan tana cikin halin maraici a yanzu " dakata yarinyata malam yana nan yana gida kina warkewa zamu tafi ki ganshi " jin haka ya sanya taji sanyi a ranta, bata kuma tada zancen ba saboda baba Muhammadu ya mata alk'awarin zai kaita gurin babanta in ta warke , hakan ya sanya ta kwantar da hankalinta. Kwananta takwas a asibiti , aka sallameta suka koma gida , sauri ta dingayi domin tayi kewar mahaifinta ," baba ina Baba na yake "ta tambaya ta shirin lek'a d'akinsa , "dakata d'iyata " anan take ya gama yi mata nasiha daga bisani ya sanar da ita halin da ake ciki , kuka sosai tayi sannan ta tsagaita , ta rok'i baba Muhammadu tanaso ta bishi gidansa ta kwana biyu , ya yarda suka tafi , sai da tayi wata d'aya sannan ta koma cikin gidan ko da yaushe sai tayi kuka , idan ta tuna da mahaifinta , sai da akayi arba'in sannan al'amura suka koma gidan jiya. Bayan wata biyar da rasuwar malam al'amura suka k'ara runchab'ewa komai ya koma gidan jiya , da kamar inna Asabe tayi sanyi amma I zuwa wannan lokacin azabtarwa take yi mata ba kama hannun yaro safe da rana da dare tallah gashi bata samun abinci sosai tunda ganin yanzu ba mahaifinta sai abin da aka bata na abinci in ta samu ta ci in bata samu ba ta hak'ura , duk da wannan halin da take ciki bata tab'a fad'awa kowa ba duk da cewar y'an uwan malam din sukan zo dubata amma bata tab'a fad'awa kowa ba . Ana cikin wannan yanayi Baraka tazo mawa da inna Asabe zancen saka ranar aure tunda yanzu sun shirya shima ya fara zuwa kudu kai kaya a babbar mota jin wannan zancen ya sanya Asabe kwadaitawa yarinyarta auren Ado ba Fatima ba , sosai sukeyin shirin biki kud'i aka kawo da komai da komai aka sanya biki wata d'aya, Asabe fa hankalinta ya tashi ganin cewar Ado na samun kud'i sosai ganin har dubu ashirin aka kawo kudi'n auren ya sanya hankalin ya tashi saboda a rayuwarta bata son cigaban Fatima ta ci son tayi aure cikin k'ask'anci wannan dalilin ne ya sanya take Neman hanyar da zata hana auren Fatima ya koma kan na zainabu , haka tayi ta fafutukar ganin bayan auren sunje wajen boka ita da Abu ya basu tabbacin cewar zaa fasa auren kuma da d'iyarta zaayi , amma me har ana I sauran kwana biyu biki ba abin da ya sauya . A daren d'aurin auren ne Ado ya samu mahaifiyarsa da zancen shi fa ya fasa auren Fatima Abu yakeso , sosai tayi mamaki da jin haka , kuma tabbas tasan Asabe ce tayi aiki dama ance abokin mugu , mugu ne . Ranar d'aurin aure da safe lokacin kowa ya hallara a inda za'a d'aura auren komai ya gaba daidaituwa aka sanar da cewar an sauya ango yace Abu yakeso ba Fatima ba , sosai mutane sukayi mamaki aka d'aura auren Abu da Ado cikin sadakin kud'i naira dubu goma. A lokacin da aka d'aura aure Fatima tana gida tana sharb'ar kuka saboda batasan auren dan kawai anfi k'arfinta ne ba yadda ta iya , mata kuwa aikinsu suke tayi kowa na murna inna Asabe kuwa da suka san me yake faruwa Murna sukayi ta yi . Marok'i ne ya fara sanarwar d'aurin aure! An d'aura auren Adamu da zainabu akan sadaki naira dubu ashirin! Yana ta sanarwar har ya shiga cikin gidan yana sanarwar, matan da ke tsakar gidan mamaki ne ya cika su jin abin da marok'in ke fad'a . Fatima da take zaune a cikin d'akin abin da kunnuwata suka jiyo mata ne ya sanya ta fito da gudu domin ganin abin da ke faruwa....... Please Share & Comments To be continue....... 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 GODIYA GA ALLAH DAYA BANI DAMAR CIGABA DA RUBUTUN LITTAFINA , BAYAN DAN HUTUN DANA DAUKA BISA GA UZURIRRIKA . A YAU INSHA ALLAHU ZAN CIGABA DA RUBUTUN LITTAFIN KISHIYAR UWA FATANA ALLAH YA YI MANA JAGORA 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹🌹🌹 🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹 🌸🌸 🌹 SHAFI NA 1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣ Koda Fatima ta fito ganin abin da ke faruwa , ji tayi wasu mata daga k'ofar d'akin girki suna magana ,d'ayar matar ta dubu y'ar uwarta " ke ni kuwa hansai bakyaji min abin da kunnuwa na ke ji ta fad'a tana k'ara kasa kunne", matar da aka kira da hansai ta ce" ashe dai bani kad'ai ke ji ba , yau naga lalata da idona, mu da aka kira mu bikin wannan yarinya Fatima ta ya ya auren ya sauya kan wannan fitsararriyar yarinyar, ta fada tana sallallami had'i da tafa hannayenta". Ita dai Fatima ji tayi kamar tayi sujjadar godiya saboda dad'i , surutai ne ya fara tashi a tsakanin mata , wannan ta fad'i nata wannan ta fad'i nata, Baba Muhammadu k'anin marigayi malam Iliya mahaifinsu Fatima ne ya shigo gidan ransa a matuk'ar b'ace , d'akin inna Asabe ya shiga da sallama , mutanen ciki suka amsa , tambayar Asaben ya yi sai gata ta fito, sadaki kawai ya mik'a mata na d'iyarta sannan ya sanya kai ya fita cike da takaici, yana fita ta wani rangad'a gud'a sannan ta kama habaice habaicenta , niko na ce kyayi kya gama . Achan b'angaren Fatima kuwa d'akinta ta koma cike da jin dad'i, tana cikin wannan farin cikin Baban nata malam muhammadu ya Shigo d'akin tsammaninsa ya same ta tana aikin kuka saboda yasan ya zuwa yanzu tasan koma da yake faruwa , amma me sab'anin haka ya tarar domin kuwa fuskarta ba abinda take fitarwa sai annurin haske da murmushi, tashi tayi , tayi masa sannu da zuwa yana amsa, nasiha mai ratsa zuciya ya mata, daga bisani ya shaida mata abubuwan da suka faru , yadda yaga bata damu ba hakan yayi masa dad'i sosai , ya yi mata sallama ya fita ya koma wajen y'an d'aurin auren. Toh a haka aka daura aure su inna Asabe baki har kunne yarinyarta ta samu mai kud'i , Wanda yake fita birni dama hakan tafi so ace yau d'iyarta tafi ta kowa sa'a a k'auyen , haka dai aka k'araci bikin anci an kuma sha biki kam sam barka amma fa Fatima tasha habaici wajen inna Asabe da k'awayenta har ma da zainabu da k'awayenta dare nayi aka kai amarya gidan mijinta da zummar sati d'aya zasu yi su tafi Lagos sai mu ce Allah ya bada zaman lafiya ya kad'e fitina amin . Lokaci nata tafiya bayan anyi biki amarya su ka tf da mijinta Lagos , a haka lokaci ke ta tafiya , cike da k'alubalen rayuwa a yanzu shekara d'aya kenan da bikin zainabu da Ado , a yayin da Fatima take cikin tsaka mai wuya , cin zarafi ,kyara , habaici, duka , zagin cin mutunci, ba Wanda bata fuskanta ba daga mahaifiyar ta ta inna Asabe, ga wani cin zarafi da y'an k'auyen keyi mata , duk inda suka ganta zancensu d'aya tak'i aure , wasu ma har cewa sukeyi tana zaman karuwanci ne kawai ganin mahaifinta baya duniya , dama dai sauran maganganu barkatai , haka take d'auke kanta daga wad'annan habaice habaicen wani zubin inna Asabe da k'awayenta ne zasu taru a gidan su ci mata mutunci son ranta, ga aikatau iri iri bata hutawa , ita kuwa inna Asabe taci mai kyau tasha mai kyau ba abinda ya dame ta saboda y'arta tana aiko mata da abin duniya , Fatima kuwa sai tayi sa'a sannan ta samu abinci taci say d'aya a rana , kuma duk wannan halin tsananin da take ciki bata tab'a tarar kowa ta fad'a mishi ba , gashi samari yanzun basa zuwa wajenta mutane suka dinga tunanin ko shafar aljanu ce , ko kuma dan ta huce mizanin y'an matantaka a k'auyen , abinda basu sani ba inna Asabe ce tayi asirin da ba Wanda zaiji yana Sonta kaf garin , tun abin baya damun Fatima har ya dawo yana damunta , in ta zauna ba abinda take tunawa sai rayuwarta da mahaifinta da kuma labarin mahaifiyarta Wanda mahaifinta ya bata , sai dai taci kukanta babu mai rarrashinta, abin d'aya ta k'udurta a zuciyarta Wanda idan tana tunawa takan samu sa'ida a zuciyarta , shine yake sanyawa ta k'ara nutsuwa , na cewar bashakka ko ba dad'e ko ba jima zata nemo asalin dangin mahaifiyarta ,wannan yakan sanya taji dad'i sosai a ranta. 🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸 A yau Asabar tun safe ta tashi ta kama kiciniyar aiki sosai takeyin aiki sakamakon bak'in da zasuyi daga b'angaren inna Asabe d'an kanwar mahaifiyarta ne zaizo dan haka ta sanya Fatima yin aiki ganin shi a birni yake da zama kuma y'an birni lallab'a su akeyi, haka fatima ta zage sosai tanayin aiki , wajen k'arfe biyun rana bak'in suka sauka murna sosai inna Asabe tayi na ganin tare da d'ansa aka so mai suna Bilya , ko kad'an yaron baya da tarbiya komai kai tsaye yakeyi gashi sai ya had'u da sakalcen uban ai kuwa abu ya k'ara ta'azzara sosai , shaye shaye, Neman mata ba Wanda bayayi , kai ya kai mak'ura wajen aikata abinda bashi kenan ba, ganin d'an uwanta, cikin washe baki suka gaisa da juna tare da tambayar bayan saduwa, sunyi hira sosai , Fatima na jinsu tana d'akinta , inna Asabe ce ta kwala mata kira da sauri ta fito ta gaishesu , aifa tunda biliya ya d'ora idanunsa akan Fatima ya fara lasar baki kamar wani tsohon maye, inna Asabe ce ta umarci Fatima da ta kawo was bak'insu abinci haka ta dinga jigilar abinci tana kai musu , Shiva d'ari fita d'ari sai sun had'a ido da bilya , tun tana masa yakana har sai da ya k'ureta tako galla masa harara , ai sai yaga tafi d'azu kyau , sai da ta gama komai sannan ta juya ta nufi d'akinta ta barsu suna cigaba da hirarsu ta zumunci........... Please Share & Comments To be continue......... INA K'ARA GODIYA GAREKU FRIENDS NAWA DA FAN'S NAWA ALLAH YA BAR ZUMUNCI . Please ayi manage da wannan I'm so tired. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad)🌸 Shafi na 1️⃣3️⃣-1️⃣4️⃣ 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹🌹🌹 🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹 🌸🌸 🌹 Bayan ta fito daga d'akin inna Asabe , d'akinta ta nufa cike da takaicin bilya wannan wanne irin mai shegen kallo Allah ya had'a ta da shi , tana murna Allah ya raba ta da Ado ashe hakarta bata kai ga cimma ruwa ba ga wani mai nacin kallo ta had'u dashi , a haka dai tayi ta maganganunta tana jan tsaki . A chan d'akin inna Asabe kuwa bayan Fatima ta fita , bilya ne ya dubi inna Asabe yace " gwaggo wacece wannan dana gani a gidan nan, saboda ban tab'a ganinta a gidan nan ba ", kyab'e baki tayi sannan tace" Fatima mana y'ar kishiya ta da ta rasu " zabura yayi cike da jin dad'i " yauwa anzo wajen ya fad'a yana sosa kai ," baban shi ne ya dube shi , yace ya akayi ne d'an baba , ya fad'a ya sauraronshi," baba dama gaskiya ina sonta kuma so nakeyi na aureta ", tashin hankali Wanda ba'a sanya masa rana , ai inna Asabe ji tayi kamar zata mutu , kallon d'an uwan nata tayi taji me zai cewa d'an nasa " ah Masha Allahu ai hakan ma yayi lallai yayi kyau , ah abu a cikin gida " ita dai Asabe ta kasa cewa komai, shi kuwa bilya murna jin mahaifinsa ya amince , sosai suka yi hira har bayan la'asar kafin su fara shirin tafiya , ita dai Asabe abin duniya ya dame ta saboda tana tsammanin ta yi abin da ba mahalukin da zai so fatima amma ga wata sabuwa, ta aurar da d'iyarta ga d'an birni tana ganin ba wanda zai k'ara cewa yana sonta amma gashi mai kud'i daga birni ya zo yana sonta, sallama yayi mata tare da sanar da ita cewa lallai ta sanar da Fatima halin da ake ciki kuma ba dad'ewa za'ayi ba za'ayi bikin saboda tsananin son abin duniyarta ta kwantar da kai , ya sallameta da kud'i masu tsoka haka shima bilya ya bata najin dad'in cewar ta amince za'a bashi fatima, haka suka yi sallama suka kama hanyar fita daga k'auyen. A cikin gida kuwa bayan inna Asabe ta shiga kasa zaune tayi ta kasa tsaye , ta saka wannan ta kwance wanchan , duk dai akan Fatima ne da batasan ta auri bilya saboda tasan suna da kud'i kuma batason ta shiga daula tana son tayi ta ganinta cikin tsanani, amma da ta tuna da waye bilya da irin halayensa ai sai ta godewa Allah dan ko ba komai Fatima zata k'unshi bak"'in ciki saboda auren mashayin giya da Neman mata bazai haifar mata da komai ba sai tashin hankali domin kuwa babu kwanciyar hankali , k'arshe ma dai ciwon zuciya ya kamata ta mutu , wannan tunanin da tayi ne ya bata k'warin guiwar tunkarar Fatima da zancen. 🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌸🌹 Da daddare bayan Fatima ta dawo daga tallan ta da ta saba , zuwa tayi ta iske Asabe a kishingid'e tana cin nama balagu da ta bayar da kud'i a siya mata wajen idi mai nama , duk kuwa a cikin kud'in da yayan nata ya bata ne , " inna sannu da gida , Fatima ta fad'a had'e da rusunawa tana mik'a mata kudin cinikin da tayi " karb'a tayi ta k'irga su tsab daga bisani ta tura su k'ark'ashin tabarmar da take kishingid'e, har zata tashi ta zaunar da ita sannan ta fara yi mata zancen bilya da duk abinda ya ke faruwa sannan ta k'ara da cewa " kuma wallahi auren nan kamar anyi shi angama, dan na yanke ranar auren nan da wata d'aya mai zuwa za'ayi shi", gaban Fatima ne ya fad'i sakamakon wannan magana da innar ta ta tayi , da to ta amsa sannan ta juya ta shiga d'akinta cike da tashin hankali. 🌸🌸🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸 A cikin d'aki kuwa safa da marwa ta Shiga yi , tana tunanin yadda zata b'ullowa da lamarin, a gaskiya kota halin ya ya ne bazata tab'a yadda da auren wannan mutumin ba , zatayi duk mai yiwuwa wajen gujewa aurensa to ta ina zata fara , tayi zurfi a cikin tunani ta tuna da aminiyarta ta yarinta hannatu , aikuwa ta yardarwa kanta cewar lallai zata samu mafita bisa ga hukuncin da ta yankewa kanta , tana ta tunani har chan dare sai daga baya bacci b'arawo yayi awon gaba da ita. 🌸🌹🌸🌹🌸🌹🌸🌹 Da asuba ta farka da Sauri ta gama aikin gida tsaf , ta gama abin da zata fita dashi tallah , sallama ta yiwa inna Asabe bayan tayi aikinta tsab sannan ta fita talla, Alhamdulillah ta siyar da wuri dan haka ta wuce gidan hannatu domin samun mafita , da take itama hannatun tayi aure shekaru biyun baya da suka wuce , a tsakar gida ta tarar da ita suka rungume juna cike da murna , sosai sukayi murna na ganin juna, bayan sun gama murnarsu sanan Fatima ta fad'awa aminiyar ta ta abin da ya kawo ta , sosai hannatu ta girgiza da jin wannan maganar , ta dubi Fatima cike da kulawa tace " Fatima nasan kinyi hak'uri , a yanzu bazan baki shawarar ki zauna a aura mini mashayin giya da Neman mata ba , dan haka yanzu meye mafita, nan Fatima ta shaida mata Cesar tanason ta tafi neman dangin mahaifiyarta , hannatu ce ta k'arfafa mata guiwa na cewar hakan yayi indai tasan inda suke ta sanar da ita cewar mahaifinta kafin ya rasu ya sanar da ita garin mahaifiyarta ta , amma ita yanzu matsalarta guda rashin kud'i a hannunta , hannatu ta sanar da ita baza'a samu matsalar kud'i ba insha Allahu , haka su ka k'ark'are matsalar ta su haka ta tafi gida cikin farin ciki . 🌸🌹🌹🌸🌹🌹🌸🌹 Haka dai rayuwa tayi ta tafiya , cikin k'warin guiwa ga Fatima , na yarda ta samu damar zuwa Neman dangin mahaifiyarta , ko ba komai zata ga ko da hoton mahaifiyar ta ta , kuma ta sadu da sauran y'an uwa mahaifiyar ta ta, tana ta shirin barin garin , a yayin da inna Asabe a b'angarenta it a ma tana ta shirin biki ta sanarwa da kowa domin murnar da takeyi na cewar fatima zata shiga kabarinta ne , sosai fa takeyi shiri kamar ba bu abinda Yake ranta , bayan ta gama shawo kan y'an uwa malam iliya , da nuna musu alfanun yadda auren zai kasance , suka kuwa yarda da hakan har suke tunanin ma Asabe ai tayi hankali. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 A haka har satin biki ya shigo , yayin da fatima ta shirya tsaf da komai nata bayan ta karb'i kud'i wajen hannatu domin shiga mota yayin tafiyar ta wajen kakanninta. Dangin ango sun kawo kud'in sadaki da kayan lefe , kaya sosai aka kawo duk da bak'in cikin da Asabe ke ji amma idan ta tuna yadda Fatima zata dawo sai taga ba komai bane ba , an fara biki yayin da Fatima take nuna musu ba abinda yake damunta . A Daren ranar d'aurin aure mutane mata mata masu girki NATA aikinsu , Fatima CE ta lek'o ganin hankalin kowa yana ga aikinsa ya Sanya cikin sand'a ta juya ta d'auko duk wani kaya da zata buk'ata da kud'in da k'awarta ta bata , lallab'a ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ganta ba ta nufi k'ofar gida, tana tafiya kuwa ta had'u da mai mashin godiya tayi ga Allah duk da a lokacin bata kawo cewar zata samu abin hawa ba saboda dare yayi sosai , ta tsareshi had'i da fad'a masa tashar motocin garin zai kai ta , ya amince ta hau bayan sunyi cinki ta yarda , basu zame ko ina ba sai tasha , tana zuwa kuwa tayi sa'ar samun direban na k'ok'arin tashi Dama sauran mutum d'aya Duke jira aikuwa tanajin motar zariya ce da Sauri ta fad'a bayan ta sallami mai mashin d'in da ta hau , da take tafiyar ta dare ce babu wuya suka bita daga cikin k'auyen suka cilla babban titi , sai a sannan Fatima ta saki dogon numfashi samun nasara ....... Please Share &comments To be continue........ 🌸🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌹 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA , DAYA BANI DAMAR CIGABA DA RUBUTUN LITTAFIN NAN , TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD, DA ALIHI DA SAHABBANSA MASU GIRMA. BAYAN HAKA NA SADAUKAR DA LITTAFINA GA D'AUKACIN Y'AN UWANA NA SABON RUWA'S FAMILY, LUV U ALL🥰🥰 AJUJI'S FAMILY KUMA HAR DA KU BAZAN MANTA DAKU BA , JINJINAR BAN GIRMA GAREKU ALLAH YA K'ARA ZUMUNCI , AMIN🥰🥰 MAHAIFIYATA ALLAH YA JA DA RANKI , HAJIYA FATIMA TURAKI ADAM , LUV U MY MOM❣️❣️ KISHIYAR UWA FAN'S NA GAISHEKU SOSAI DA SOSAI. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹🌹🌹 🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹 🌸🌸 🌹 SHAFI NA 15-16 A haka sukayi tafiyar kusan awa d'aya da rabi kafin nan su isa cikin garin zaria, bayan an karb'i kud'in motarsu , kafin nan suka k'arasa garin zaria, bayan an Shiga cikin tasha a lokacin kusan k'arfe ukun dare , mutane suna ta sauka daga motar yayin da Fatima tana chan ta shiga duniyar tunani bata ma san an k'arasa cikin tashar ba , direban ne yana k'ok'arin juya motar domin komawa ya k'ara d'ebo wasu fasinjojin , juyawar da zaiyi ya hangota a zaune tana tunani , "baiwar Allah direban ya fad'a ya d'an dukan saman kujerar" firgigit ta farko daga duniyar tunanin , sai a lokacin ta farga da cewar lallai fa sun isa garin zariya , " ki sauka anzo fa , ya fad'a had'e da nuna mata wajen da sauran mutanen suka fita, tsimmokaran kayanta ta d'iba sannan ta sauka daga motar , tana k'ara rik'e kayan nata, shi kuma direban ya juya da motar ta sa bayan ya sauke dukkan fasinjojin, domin komawa , sai a lokacin Fatima ta fara tunanin ina zata shiga , waye ta sani a garin zaria ita yanzu ya ya zatayi , sai a sannan ta ji tsoro ya kama ta , ga dare ya yi gashi cikin tasha ne ga mutanen da suka zo da su duk kowa ya kama gabansa , gefe ta koma ta zauna ta zubawa sarautar Allah idanu kafin gari ya waye tasan nayi , mutane taga suna gilmawa kamar walk'iya , tsoro ne ya kama ta , d'ago kanta tayi aikuwa taga sun yi mata rumfa , irin yan iskan cikin tasha ne , wani gabjeje ne ya yi magana cikin kakkausar murya , yana mai nuni da ita ," ke me kikeyi a nan ya fad'a yana k'walalo idanu " kakkarwa jikinta ya fara yi , tsoro sosai ya shige ta , " magana ake yi miki ba , wani ya fad'a daga cikin wad'annan y'an mutane , " kaga rik'emin ita kawai kagani babban nasu ya fad'a , chafka d'aya daga cikinsu ya kaimata da sauri ta zille ta fara ihu ga babu mai taimako, gudu take yi suna bin ta a baya har suka fita daga cikin tashar suna bin ta a baya, sosai takeyi gudu har ta hau kan babban titin garin basu daina bin ta ba, ga babu mutane sosai kowacce mota kawai wuce was takeyi , a lokacin Fatima ta gaji lik'is tana neman fad'uwa , tsautsayi ya sanya tana k'ok'arin tsallaka titi mota ta d'ebo da gudu aikuwa ta kwasheta , k'arar da ta saka ne ya sanya wad'annan mutanen suka juya da gudu suka koma idan suka fito , da sauri mai motar ya fito daga cikin motar ya k'arasa inda ya ga yarinyar a kwance hasbunallahu ya furta ganinta da yayi cikin jini ko motsi bata yi , a cikin zuciyarsa ya fara tunanin to me ya fito da wannan yarinyar cikin wannan daren ganin tunanin bazai kai masa ba ya sanya ya d'auke ta da Sauri ya nufi cikin mota da sauri gashi dare yayi a haka ya tada motarsa ya figa da gudu kasancewar yana Sauri ne dan haka madadin ya kaita asibiti kawai sai ya wuce da ita cikin garin Kaduna ya bar zariya da ita kasancewar gaba ki d'aya ya gama rud'ewa . 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Sai ana kiran sallar asubah sannan su ka k'arasa , asibitin cikin garin ya wuce da ita saboda yana da amini Dr Sadeeq, tun kafin su k'arasa ya sanar da shi halin da ake ciki, dan haka suna isa ya tarar da nurses suna jiran isowarsa ciki kuwa harda Dr Sadeeq din , da sauri aka d'orata akan gado aka shiga da ita cikin asibitin , shi kuwa mutumin da ya kad'eta kwata kwata ya rasa nutsuwarsa , ya kai ya kawo haka ya dinga yi " haba Ahmad kayi a hankali mana ko sai ka jawowa kanka wata matsalar , Dr sadeeq yayi furucin yana duban abokin nasa , " girgiza kai kawai Ahmad yayi saboda bayaso ya zama sanadiyar salwantar rayuwar wannan baiwar Allah , " bakasan me nake tsoro ba sadeeq , wlh ina cikin tashin hankali bansan me zanyi akai ba idan yarinyar nan ta rasa rayuwarta ta sanadiyya ta , Ahmad ya fad'a kamar zaiyi kuma , " d'aya daga cikin likitocin asibitin ne ya fito kasancewar Dr Sadeeq ya tsaya wajen abokin na sa domin kwantar masa da hankali ," a gaskiya yarinyar nan ta auna arzik'i amma mun samu ta farfad'o daga doguwar suman da tayi ,Dr Khalil ya fad'a yana duban Dr Sadeeq"," yawa Dr sannu da k'ok'ari min gode fa " , " ah ai babu komai ai maigida Ahmad ai namu ne Allah ya kiyaye gaba ", suka amsa da amin a tare , sai a lokacin ne Ahmad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya , Dr Sadeeq ne ya dubi Ahmad , " am abokina ya akayi ne al'amari irin wannan ya faru" a take Ahmad ya bawa Dr Sadeeq labarin yadda abin ya faru tun daga farko , sannan ya k'ara da cewar hasalima ina sauri ne saboda laila na sanarda ita cewar zan dawo a yau daga kano shiyasa ", " amma baka tsammanin iyayen ta zasu nemeta , Dr Sadeeq ya fad'a yana duban Ahmad ," nima haka make ta tunani amma komai ma in ta farka zamuji" daga haka suka cigaba da hirar abinda ya faru. 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Sai da akay kiran sallah sannan suka tashi daga hirar suka nufi masallaci , domin yin sallah har suka dawo daga sallah Fatima bata farfad'o ba, dan haka Ahmad ya bar Fatima a hannun Dr Sadeeq ya nufi unguwarsu dake cikin wata GRA dake garin Kaduna. 🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸🌹🌹 Tangamemen gate mai kalar ruwan madara masu gadin gidan su ka bud'e , hancin motarsa ya danna cikin gidan, ma'aikatan gidan sai kai kayo sukeyi , masu ban ruwa suna ta bawa furanne ruwa , duk inda ya gifta masu aiki na ta gaida shi yana amsawa cike da fara'a akan fuskarsa duk kuwa da cewar a zuciyarsa ba haka bane ba saboda yana tunanin me zai tarar a cikin gidan uwa uba kuma Fatima dake gadon asibiti. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Shin wai meke faruwa ne a chan k'auyen Darki ne bayan Fatima ta baro 'yan biki da inna Asabe? Ana ta aikin biki har safiya tayi , inna Asabe ta shiga cikin rububin mutane , hakan bai Sanya an farga da cewar amarya ta gudu ba har sai da hantsi ya fara fitowa ana ta shirye shiryen d'aurin aure ganin har wannan lokacin Fatima bata fito ba ya sanya inna Asabe ta aika Abu da ta kirawo mata Fatima domin ta shirya saboda an kusa fara d'aurin auren , a lokacin Abu nada juna biyu dan har ya fito sosai , lek'awa tayi cikin d'akin cike da gatsali " dalla chan ai saiki fito banza kin wani zo kin zauna a d'aki kin bar mutane , " shiru taji dan haka cike da bala'i ta chusa kai , wayam ta gani dan haka ta fito da gudu ta nufi d'akin inna Asabe.......... Please Share & Comments To be continue........ 🌸🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌹 🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ NA SADAUKAR DA LITTAFINA GA MASOYA LITTAFIN KISHIYAR UWA. SHAFI NA 17_18 D'akin Inna Asabe ta nufa ko sallama babu," ! Inna , ta kwad'a mata kira da k'arfi , juyawa Asabe ta yi ," ke lafiya" , ta tambaya ta mik'ewa tsaye, " inna fa Fatiman ba ta nan fa" wani ihu inna Asabe ta zuba , tana duban mutanen d'akin da su ka zuba mata idanu, Abu fa kamar wasa k'aramar magana ta zama babba , tun kafin mutanen wajen y'an d'aurin aure su hallara ake nemanta duk inda aka san za'a ganta an nemeta amma shiru , nan fa aka ba za ma ko Allah zai sanya a ganta , amma shiru , lokacin da iyayen ango su ka zo aka Sanar da su , sosai hankalin ango ya tashi na b'atan amarya Fatima , aka yi nema aka gaji hakan ya sanya aka hak'ura da d'aurin auren aka ba ri sai an ganta tukunna , zancen fa ya cika k'auyen Darki na cewa Fatima ta gudu, wad'ansu na cewar dama bariki ta ke yi shi ya sanya zaman k'auyen ba zai yi mata ba dole ta shiga duniya , haka dai aka hak'ura duk da cewar y'an uwan marigayi malam Iliya sun koka na rashin Fatima amma suka hak'ura, wannan kenan. KADUNA STATE Lokacin da Ahmad ya isa k'ofar falon , thumb print ya danna , aikuwa a take k'ofar ta bud'e , shiga yayi da sallama , masha Allahu wani tangamemen falo ya bayyana , ga sanyi Ac da ya gauraye wajen , a d'aya daga cikin kujerun d'akin , wayar shi ya d'aga ya k'ira daga chan aka d'aga "haba habibty gani fa na dawo ina falon k'asa , kuma wallahi na gaji ," daga chan b'angaren aka yi magana , ban san me a kace ba na ga ya b'ata fuska , ya kashe wayar , kai shi ya zai yi wajen ba dad'i cikin gida ma haka , "Allah ka duba lamari na, ya fad'a yana duba k'afar bene , wata mata ce take saukowa daga ganinta kasan hutu ya ratsa ta akalla ba za ta wuce Ashirin da bakwai ba a duniya , sosai tayi kyau ba k'arya , ba ta da tsayi sosai amma fara ce , anyi mata kitson attach ya zubo har kafad'a , daga ganinta kasan idanunta sun bud'e da duniya, ' LAILA ' kenan uwargida wajen Ahmad , " haba Laila kina sa ne da cewar jiya mu ka yi zan dawo ai kya kirani ki ji me ya tsayar da ni amma kika yi ignoring nawa, kamar ba mijinki ba haba Laila, ya fad'a yana dubanta ", tab'e bakinta tayi " haba my luv ka san dai nima banda time ko saboda ka ga nima na fita aiki , " kallonta kawai yayi ya girgiza kai ya rasa meyasa kwata kwata LAILA bata damu dashi ba yana matsayin mijinta , ganin ba za ta tambayeshi meya faru ba ya sanya ya fara fad'a mata abin da ya faru da shi , "uhmmm Allah ya kiyaye" kawai ta ce sannan ta juya ta fita a d'akin , girgiza kanshi yayi sannan ya tashi ya shiga band'aki , wanka yayi sannan ya shirya yana fitowa falo wayar shi tayi k'ara dubawa yayi ya ga Dr Sadeeq ne ya kira dan haka ya d'aga cikin hanzari , sallama yayi , aka amsa tachan d'aya b'angaren ," ok to gani nan zuwa , kawai ya fad'a ya nufi saman d'akin LAILA , ya na bud'a d'akin ya hango ta akan bed tana charting, sallama yayi mata bata amsa ba , kawai ta d'aga mishi kai , juya wa yayi ya fita had'e da girgiza kansa , harabar gidan ya nufa sanye da yadi d'an Abba kalar sky blue da hula zanna bak'a , da sauri direba ya taso, girgiza masa kansa yayi alamar ba tare zaku fita ba hakan ya sanya ya koma kan bencin baba mai gadi , shi kuma ya nufi motarsa , shiga yayi , ya kunna , baba me gadi ya wangale masa bakin gate ya cinna hancinta wajen gidan ya nufi titi . ASIBITI Da sauri ya k'arasa asibitin , a bakin office ya had'u da Dr Sadeeq yana k'ok'arin fita domin komawa d'akin da Fatima ta ke , " ah mutumin ya haka tun d'azu na kiraka amma sai yanzu , ko dai madam ta rik'e ka ne , ya fad'a had'e mik'a masa hannu domin suyi musabaha" , shi dai Ahmad bai ce k'ala ba , suka juya suka nufi d'akin Fatima, a lokacin ta farka har nurses sun taimaka mata tayi wanka tayi sallah , da sallama suka shiga amsawa tayi had'e da kallon k'ofa , Dr Sadeeq ne ya fara k'arasawa cikin d'akin had'e da zolayar ta ah lallai kin warke irin wannan kwalliya haka , ya fad'a ya nunawa Ahmad wajen zama Wanda ya kafe a tsaye yana kallon yarinyar da ya kad'e , kyakykyawa ce ya fad'a a ransa , zama yayi , doctor ya gabatar da shi a wajen Fatima , gaisar dashi tayi cikin murya mai sanyi amsawa yayi, kuma bai d'auke idonsa daga kanta ba , shi dai yana yiwa yarinyar nan kallon sani , " ya sunanki ya fad'a yana dubanta ", Fatima " abin da tace kenan ta juya suka cigaba da hirarsu da doctor jefi jefi yake sanya musu baki , ya dad'e sosai daga bisani ya nufi gida bayan yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta kwanta saboda har lokacin bata dawo daidai ba. Sai da Fatima ta kwana kusan bakwai ta warke garau , amma ba ta tab'a fad'awa kowa maganar y'an uwanta ba , a nashi b'angaren Ahmad yayi tunanin ya tambaye ta ko dan ya mai da ta danginta amma ganin cewar ba ta da lafiya ya sanya sai a yau ya tare ta da zancen dangin na ta , bata b'oye masa komai ba dan tana ganin kamar wannan wata mafaka ta samu ko Allah zai sanya ya taimaka mata ta wani fannin ganin cewar yana da tausayi , jin labarinta ya sanya yayi alk'awarin cewar zai tafi da ita cikin danginshi kafin ya san me zai yi akai . Satin Fatima biyu Dr Sadeeq ya ba ta sallama , har bakin mota Dr ya raka su , sannan ya koma su kuma suka fita daga cikin asibitin zuwa gida Alhaji Ahmad......... Please Share & Comments To be continue........... DAN ALLAH AYI HAK'URI DA WANNAN SABODA NA GAJI . SAI ALLAH YA KAIMU WANI SATIN ZAN K'ARAYIN TYPING , LUV U FAN'S🥰🥰 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 NA SADAUKAR DA LITTAFINA NA KISHIYAR UWA GA, PHAREEDA , INAJIN DAD'IN COMMENTS D'INKI SOSAI DA SOSAI, ALLAH YA BIYAKI.🥰 SHAFI NA 19_20 Ko da suka k'arasa cikin unguwar , tun daga bakin layin Fatima ke rarraba idanu , " oh ni Fatima na kawo kaina ga mahallaka , yanzu ace ni zanyi rayuwa anan , anya ma kuwa ba d'an mafiya na biyo ba , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , shikenan tawa ta k'are , duk abinda take fad'a tana fad'ar shi ne a cikin zuciyarta" , a take tayi dana sanin gudowarta daga k'auye , dama ta tsaya an d'aura mata auren da bilya da wannan yawon gashi bata ga tsuntsu bata ga tarko, shikenan a banza a wofi wasu mutanen zasu cinye ta , garin lalubar dangin mahaifiyarta ta b'ige da zuwa mahallakarta madadin ta ganta a zariya sai gata a Kaduna , ta shiga zurfin tunani da tashin hankali ta yadda har su ka iso k'ofar gidan mai gadin gidan ya bud'e suka shiga bata sani ba . Cikin sexy voice nashi ya kira sunanta "Fatima" har sai da ya kira sau uku ana hud'un ne tayi firgigit ta farka daga mummunan tunanin da take yi , kallon gefen da ake magana tayi shine dai a tsaye yana kallon ta da tuhumar abinda take tunani , "sauko , yace da ita " a hankali ta sauko da k'afafunta kasa ta fito daga motar , kallon gidan da suka shigo ai da hanzarinta tayi hanyar bakin gate , gudu takeyi ba k'ak'k'autawa , shikenan ita kam k'arshenta a duniya ya zo , sai a sannan hawaye ya fara zubar mata a ido , da Sauri ya bi bayanta domin sanin meke faruwa, har ta kai bakin gate din gidan bata tsaya ba , ja tayi ta tsaya turus sakamakon tashin sanin ta ina zata fita , shima tsayawa yayi yana kallon ta , da mamaki fal a fuskarsa , to kodai hatsarin da ya faru da yarinyar nan ko dai ta samu matsalar k'wak'walwa ne, gabansa ne ya fad'i yayi saurin kawar da zancen daga cikin zuciyarshi , to ko kuma Aljanu gare ta , ah to ba mamaki ma aljanunne, ni kuwa nace to fa su malam Ahmad wata kam aljanu sune masu laifi ba kai ba🥴, k'arasawa yayi a hankali ya kamo hannunta ya jata zuwa har bakin falon gidan , thumb print yayi wa k'ofar aikuwa ta bud'e , shiga suka yi ciki , wani tsoro ne ya k'ara shiga zuciyarta, ita fa gaskiya mutumin nan tsoro yake bata , ga uban gida kamar ba'a duniya ba , inama ya kasance mafarki take yi ba gaskiya ita bazata zauna ba yana tafiya zata gudu, " to kuma idan kika gudu ina kika sani, zuciyarta ce ta bata wannan tambayar" , "babu , ta fad'a har sai da ya juyo " wajen zama ya nuna mata, sannan ya fad'a mata cewar bara ya haura sama ya yiwa matar gidan magana ta sauko su gaisa , sai ta bata wajen zama kafin komai ya tsagaita, " dama yana da aure , dama anayin aure idan mutum d'an mafiya ne kuma ya ajiye ta a gidan mafiya , anya ma ta sani kuwa, to kodai ita ma y'ar mafiyar ce , domin ita har yanzu bata yadda da cewar ba gidan mafiya ta ke ba , k'arar takalmi mai tsini taji na dukan tiles , hakan ya sanya ta kallon inda k'arar ta ke fitowa , wara idanunta tayi had'e da mutsitstsika su , "masha Allahu ta furta a hankali gaskiya matar gidan mai kyau ce ita ma ga gashinta har gadon baya , " ni kuwa nace lallai Fatima har yau kina da yarinta bakisan gashi natural ba bakisan na kanti ba , karasowa suka yi har falon hannunsu had'e da na juna , Ahmad ne ya kalli Laila wadda tayi kicin kicin da rai ganin an kawo mata budurwa gida ," Laila zauna mana yayi mata nuni da kusa da Fatima ," chab Allah ya kiyaye na zauna kusa da tsintacciyar mage " duk da Ahmad baiji dad'in yadda Laila tayi ba, amma yadda yaga Fatima tayi abin bai mata zafi ba ya sanya ya basar , magana ya soma yi takan Laila ya fara kasancewar ita ce babba " Laila ga y'ar uwa nan na kawo miki , ke kuma Fatima kinga wannan antinki ce banason tashin kunya duk da ba d'abi'ar ki bace ba, ki kula sosai , zaki dinga taya ta zama da hira kinga ko ba na nan , kinji ya tambaya ya na kallon fuskarta ," eh , kawai tace " ita kuwa Laila ranta in yayi dubu ya b'aci ta yaya za'ayi a kawo mata yarinya y'ar k'auye ace ta tayata zama amma Ahmad ma ya raina ta da ajinta da komai ya rasa wadda zata tayata hira sai bagidajiya , tsintacciyar mage, duban Ahmad tayi had'e da kallon ka raina min hankali ma wallahi , sarai ya gane me take , amma yayi banza da ita , gajiya tayi da zaman hakan ya sanya ta mik'e tsaye , tare da fad'in " in ka gama ina da abin yi , I can't stay and wasting my time about this rubbish, ta fad'a tana k'ok'arin tashi gyad'a kai kawai yayi saboda tsabar haushi domin bai ma san me zai ce mata ba, hayewa sama tayi ta barsu a wajen , Fatima batasan me Laila ta fad'a ba amma ta fuskanci bata maraba da zamanta a gidanta , ai taji dad'i ma da matar gidan bata so ta zauna , itama gwara haka, juyawa yayi ya kalleta " tashi muje na nuna miki masauki, abinda yace kenan ya yi gaba " ita kuma Fatima ta bishi a baya. Sosai ya nuna mata yadda ake amfani da kayan band'akin kasancewar wasu ma ko ni bansan yadda ake amfani da su ba ballantana fatima🥴, bayan ya gama nuna mata komai sannan ya fita ya barta domin ta yi wanka, tunawa da yayi ba kaya a hannunta ya sanya da sauri ya fita ko d'an aike bai tsaya nema ba , ya hau mota ya tafi wani store na kusa domin samo mata kayan sawa domin a gurin hatsarin ta rasa kaya , dohayen riguna ya saya mata Arabian gown masu kyau , ko da ya dawo ta fita a wanka , ta sanya kayan ta da ta taho da shi , bata kayan ya yi ya mata umarni da cewar ta sanya ta fito ta ci abinci , bayan tayi sallah ta fita falo, a zaune ta tarar da shi a zaune a kujera ya dafe kansa , cikin sanyin muryarta ta masa sallama , d'agowa yayi masha Allahu kawai ya furta a cikin zuciyarshi " yarinya kamar balarabiya , " " me kace , ta fad'a, " a'a babu komai zauna kici abinci ga dinning chan ya nuna mata da hannu " cikin tafiyar k'asaita ta k'ara ta zauna a saman d'aya daga cikin kujerun , rasa yadda zatayi ta bud'e food flask din , juyowa tayi tana son yin magana ta kasa, ganin haka ya sanya ya gane me take nufi hakan ya sanya ya tashi yaje har kusa da ita ," matsa kawai yace " ta matsa ya bud'e mata yana k'ok'arin zuba mata a faratin , yayin da Laila tana k'ok'arin saukowa daga benen gidan , ihu da k'arfi ta sanya, ! Na shiga uku ni Laila me zan gani a gidana a kawomin karuwa , wallahi sai na kasheki yau , tab lallai ma," kanta tayo tana gurnani kamar zakanya tsabar rud'ewa Fatima batasan lokacin da ta k'ank'ame Ahmad ba wani yarrr yaji a cikin shi yana wannan yanayin bai san har Laila ta k'araso gurin k'ok'arin janyo ta Laila ta fara ita kuma tana k'ara k'ank'ame shi , hakan ya sanya Laila ta k'ara haukacewa , ta biyo Fatima ihun da ta saki ya fargar da Ahmad, hakan ya sanya yayi saurin maidata bayan shi Laila ta fad'o kanshi " wallahi bazan bazan yarda ba , haka kawai an kawomin yarinya tsintacciyar mace hakan ma bai isa ba sai anti karuwanci a gaba na kuma wallahi..... Ai bata k'arasa ba sakamakon gigitaccen Marin da Ahmad ya yi mata a fuska , abinda bai tab'ayi ba a iya zamansu na aure , ita kanta Laila sai da abin ya bata mamaki , tunda suke Ahmad ko da wasa bai tab'a sanya hannu a jikinta ba ko da ta sigar wasa ne , amma yanzu saboda wata bagidajiya , wawiya dabba ya sanya hannu har ya made ta , hakan ya k'ara mata tsabar Fatima a ranta ta yadda tana jin kamar ta kashe ta , lallai tunda daga zuwanta ta wargaza mata farin cikinta itama sai ta zauna cikin bakin ciki har iya rayuwarta a gidan dan da k'afarta zata gudu basai wani ya fitar da ita ba, da gudu ta haura sama fitar da batayi ba kenan ta shiga d'akinta ta hau rusar kuka. A b'angaren Ahmad kuwa , dawo da Fatima yayi gabanshi , hawaye sosai ya gani akan idonta , cikin sanyin murya take magana" dan Allah yallab'ai ka taimaka ka barni na tafi , nasan dama zan kawo muku fitina a tsakaninku, shiru tayi sannan taci gaba , kaga kuna zaman zamanku zan wargaza muku farin ciki , daga zuwa na gwara ka barni na koma k'auye tunda yanzu rayuwa bata da amfani a gareni kuma.... Kuka ne yaci k'arfinta ta yadda ta kasa ko da motsa bakinta , shi kuwa shiru yayi yana kallonta kuma ya k'urawa d'an karamin bakinta ido ya gaza cewa komai , jiyayi kamar ya kamata ya rungume saboda rad'ad'in da yakeji na kukan da takeyi , yana yiwa Fatima kallon sani kuma yanayi mata kallon kanwarsa , amma to a ina yasan fuskar Fatima , tunani ya shiga yi gaskiya yasan fuskar amma ya manta , lallashinta yayi had'e da kwantar mata da hankali kuma ya shaida mata a hankali zai sanya a bincika mata dangin mahaifiyarta , haka da ya furta shi ya sanya ta yardarwa kanta da cewar zata ci gaba da zama a gidan har tsawon lokacin da za'a ga dangin mahaifiyarta , sai da ya tabbatar hankalinta ya kwanta sannan ya barta ta shiga d'akin shi kuma ya fita saboda b'acin rai , gaskiya dole ya san abinyi Laila ta sauya ba haka ya santa ba to me ya chanza ta ko dama haka take kawai dai dan tana sonshi ne ya sanya take bin umarninsa a baya , a haka ya k'arasa cikin mota ya kunna ya fice a gidan , Laila da ke bakin window tana kallon lokacin da Ahmad ya fita k'ara rushewa tayi da kuka, ta fad'a kan gadon d'akin tana k'udurtar yadda zatayi da rayuwar Fatima , tunani ta fara to tayaya zata yi mata illah , ta tambayi kanta , ni kuwa nace oho ke za'a tambaya😏. Ko da Ahmad ya bar gida tafiya yayi ta ak'alla minti biyar kafin ya k'arasa inda zaije , a bakin wani tangamemen gida ya tsaya , da sauri aka bud'e gate din kasancewar gate man din yasan ko waye , gaisawa sukayi yayi masa alkhairin da ya saba sannan ya shiga ciki , gaskiya gidan ya had'u har yqfi nashi had'uwa , tun daga bakin k'ofar falon ya fara k'wala mata kira kamar k'aramin yaro " mummy , mummy , mummy! Da k'arfi yake fad'a wata mata dattijuwa ta fito daga cikin d'akin da yake hannun dama , "kai Ahmad wallahi baka girma , ta fad'a tana k'ok'arin zama a kan d'aya daga cikin kujerun d'akin ", gaisawa sukayi sosai ya kwashe komai da ya faru ya fad'a mata , " wai amma wannan yarinya bata kyauta ba , kaima kuma ka daina Marin mace hakan ba daidai bane ba , kaci gaba da hakuri , yauwa ita ina fatiman take tana cahn to in ba matsala ni ka kawomin ita zatafi jin dad'in zamanta anan ", ba'a son ranshi ba ya amsa da to ganin hajiyarsa ta nuna sah'awar zaman Fatima a gidan kuna batun haka shi kad'ai iyayensa suka haifa babu abokin taya hajiyarsa zama , hakan ya sanya ya amince da hakan , zancen gwaggonsa ta masa tace wallahi zanje gaidata aiki yamin yawa amma zan kirata, sallama yayi mata had'e da alk'awarin kawo mata fatiman. Sai k'arfe takwas lokacin ya dawo daga fitar da yayi , yasan bazai samu abinci ba hakan ya sanya yayi take away yayiwa mutanen gidan ma , Fatima ya fara kaiwa sannan ya mata zancen zata koma wajen mahaifiyarsa dad'i sosai taji hakan ya mishi dad'i sosai dan haka ya haura zuwa sama, direct d'akinsa ya nufa ko takan Laila bai bi ba ya gama abubuwan daya saba yi ya kwanta bacci ranshi ba dad'i. A b'angaren Laila ma hakan ce ta kasance tayi bacci marar dad'i ...... Please Share & Comments To be continue..... 🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'akamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ BARKA DA SALLAH FAN'S, FATAN ANYI SALLAH LAFIYA, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMIN. KAMAR YADDA NA ALK'AWARTA MUKU CEWAR ZANCI GABA DA RUBUTU NA , INSHA ALLAHU GASHI NA CIKA ALK'AWARI NA. SHAFI NA 21_22 A b'angaren Fatima kuwa , ta yi bacci ne mai dad'i cike da walwala kasancewar Allah ya yaye mata zaman gidan , matar gidan sam bata da hali mai kyau , a haka har bacci ya yi awon gaba da ita. Washe gari karfe shida na safe har ta shiyar tana zaman jiranshi a falo, ganin zaman bazai yi mata ba ya sanya ta fita falon gidan , kicin ta lek'a ta tarar da kukun gidan tana dafa Karin kumallon safe , gaisawa suka yi da yake ita kukun na da sauk'in kai cikin k'ank'anin lokaci ta ya ta suka had'a abincin , kunun tsamiya suka yi da kosai sai farfesun kayan ciki sai shi mai gidan da ake dafawa shayi , komai suka jera shi a dinning table , komawa suka yi kicin suka cigaba da hira, sosai kukun mai suna Aisha taji dad'in hira da Fatima duk kuwa da k'ank'antar shekarunta. Alhaji Ahmad ne ya fara tashi sakamakon k'arar wayarsa da ta tashe shi , mahaifiyarsa ce da sauri ya d'aga suka shiga gaisawa , bayan ta jaddada masa cewar lallai ya tabbatar ya kawo mata Fatima a yau , amsawa yayi da to , suka yi sallama , da sauri ya Shiga toilet yayi wanka , kasancewar yayi sallar asubah , k'asa ya nufa a tare ya ga Aisha da Fatima suna hira a tare suka had'a baki burin cewar " yallab'ai ina kwana " amsawa yayi sannan ya nufi dinning area sosai yaci abinci , sannan ya yiwa Fatima nuni da ta taso su tafi , Aisha bataji dad'in tafiyar Fatima ba , ita kuwa Fatima taso yiwa aunty LAILA sallama , amma da taga ba fuska sai ta hak'ura , haka suka fita daga gidan suka nufi gidansu Ahmad . Fatima bata ga wani nisa tsakaninsu ba, a bakin gate su ka yi horn gate man ya zo ya bud'e musu alkhairi Ahmad ya mishi kamar yadda ya saba sannan suka shiga. A falo suka tarar da hajiya zaune da fara'arta ta tarbesu , Ahmad ne ya fad'a kan k'afar hajiya ya soma yi mata shagwab'a wai ta tasheshi yana bacci sosai suka burge Fatima , yayin da hajiya sai lallashin shi takeyi ," ah daughter k'araso mana , kika tsaya anan " , duk da Fatima bata san abin da ake nufi da " daughter " amma tasan ita ake yiwa magana k'arasawa tayi ta gaida hajiya , bayan sun huta hajiya da kanta ta raka Fatima har d'akin da zata zauna , sosai d'akin ya burge Fatima a ranta, sai da hajiyan Ahmad ta gama nuna mata ko'ina na gidan sannan su ka koma falo suka cigaba da hira, tun Fatima bata magana har ta dawo tana sanya musu baki . A chan b'angaren LAILA kuwa duk a zatonta Ahmad zai zo ya lallashe ta kamar yadda ya saba amma taji shiru toh me hakan yake nufi kasa jurewa tayi ta sauka k'asa , babu kowa a falon sai motsin da taji a kicin hakan ya sanya ta nufi kicin din , Aisha ta tarar tana goge gogen kan gas , da sauri ta tsugunna har k'asa ta gaida LAILA , bata amsa ba sai ma tambaya da ta hurga mata " Ahmad ya fita ne, ta fad'a tana kallonta da jiran ganin ta bata amsa " , eh sun fita, shi da k'anwarsa " wani zabura tayi " sun fita fa kika ce "? " eh , kawai ta fad'a ta juya taci gaba da aikinta " , zagaye LAILA ta shiga yi da taga bazaiyi mata ba sai ta haye sama ta fara rusa ihu , daga ta d'auki wayarta lalubar numbersa ta shiga yi bai d'aga ba , wayar mummynta ta shiga kira amma bata shiga ba , kawai sai ta fad'a kan gado ta rushe da kuka. A chan b'angaren su Fatima kuwa , sosai suka yi hira anan ta fuskanci shak'uwa mai tsanani , a tsakanin hajiya ta d'an tilon d'an nata, Ahmad kuwa ganin da yayi Fatima ta saki jikinta da hajiyarsa hakan ya mishi dad'i sosai , bashi ya bar gidan ba sai bayan sallar la'asar kasancewar ranar Asabar ne , hakan ya sanya bai koma gida ba ya wuce asibitin DR Sadeeq , sosai sukayi hira sai bayan sallar isha'i sannan ya nufi gida , bai bi takan LAILA ba kawai yayi kwanciyarsa yayi bacci , shirun da LAILA taji yayi yawa ne ya sanya ta lek'a ta window, tabbas ya dawo , zaman jiranshi ta zauna yi , har 1 bai shiga d'akin ba , kawai sai ta sauka daga gadon ta nufi d'akinsa , handle din k'ofar ta murd'a amma a rufe gam, ita fa Ahmad ya sauya mata , bai tab'a yi mata irin wannan cin kashin ba sai yanzu da ya samo kilaki, ni kuwa nace au baki daddara ba ko LAILA, saura kad'an ta jiyoni ni kuwa na fece a miliyan😝. A ranar ma bacci marar dad'i tayi. Sosai rayuwar gidan yallab'ai Ahmad ta sauya babu walwala tsakanin ma'auratan kasancewar LAILA tayi fushin ta sauka amma Ahmad ya nuna baisan tana yi ba , kasancewar mai hak'uri bai iya fushi ba , yayin da a b'angaren Fatima kuwa sosai rayuwarta ta sauya tayi fresh tayi kyau , sai Sam barka , a yanzu ma hajiya shirye shiryen kai ta makaranta take yi abin gwanin burgewa . Shin wai wanene yallab'ai Ahmad ,kuwa wacece LAILA, ya ya akayi suka had'u ? OPPHHH DAN ALLAH AYI MANAGE DA WANNAN JIKI DA JINI SAI A HANKALI. GAISUWAR BARKA DA SALLAH GAREKU DUK MASOYANA DA KUMA MASOYAN KISHIYAR UWA 🥰🥰 DAN ALLAH A DINGA YIMIN SHARE NA BOOK DIN NAN 👏🏻👏🏻👏🏻 Please Share & Comments To be continue.............. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 " :; ' ". ; . ' : " DAN ALLAH NAJI K'ORAFINKU KUYI HAK'URI WALLAHI BANDA TIME , A YANZU INA BUSY AMMA INSHA ALLAHU ZANYI K'OK'ARIN GANIN NAYI MUKU YADDA KUKESO. INA GODIYA BISA GA NUNA KULAWARKU DA KUKE A GARENI , INA JIN DADI SOSAI , ALLAH YA BIYAKU , AMIN.🥰 SHAFI NA 23-24 Ahmad Muhammad Ahmad , haifaffen garin kaduna ne , a unguwar kawo , mahaifinsa Alhaji Muhammad shahararren d'an kasuwa ne, mahaifiyarsa hajiya Amina ita kuma haifaffiyar garin Zaria ,mahaifiyar Ahmad sun had'u ne ata dalilin bikin abokinsa da akayi anan ne suka had'u sosai ya yaba da halinta , aka sasanta har Allah ya sanya akayi aure , hajiya amina su biyu ne kachal Allah ya basu daga hajiya amina sai k'anwarta Maimunatu , a lokacin da hajiya Amina tayi aure taso tafiya da k'anwarta maimunatu , saboda halin rashi da iyayensu su ke fama amma mahaifan nasu suka k'ek'asa k'asa , suka hana ta tafiya da ita . Shekararta d'aya Allah ya azurta ta da samun haihuwa ta haifi jaririn d'anta namiji Wanda yaci sunan Ahmad, sosai ake nunawa jariri gata da soyayya , musamman Maimunatu k'anwar hajiyan, Ahmad ya tashi cikin gata , shekarar goma a lokacin ya gama primary zai tafi secondary akayi auren k'anwar hajiya wato Maimunatu , aka kaita garin kano, sosai basu ji dad'in rabuwa da juna ba amma ba yadda suka iya, haka suka hak'ura. Ajin Ahmad biyu a secondary , Allah ya azurta Maimunatu k'anwar mahaifiyarsa da samun k'aruwar yarinya mace hakan yayi masa dad'i sosai ganin cewar dama bai tab'a zuwa gidan gwaggon ta sa ba, amma kash lokacin yazo musu ana dab da fara jarabawa , haka ya hak'ura , ya gama makarantar secondary da kwali mai kyau , a lokacin business din mahaifinsa ya bunk'asa dan har k'asar waje yake fita , a haka Ahmad ya fara makaranta , toh a wannan lokacin Allah ya had'a shi da LAILA, y'ar gidan Alhaji Abbas mai dollar , tunda LAILA ta d'ora idanunta akan na Ahmad , taji ta kamu da sonsa, tun baya lura da ita har sai da tasan yadda akayi ta cusa masa soyayyarta a zuciyarsa , sunyi soyayya sosai , a lokacin da iyayensu suka sani abin ya musu dad'i sosai ganin ko wanne a cikin yaran nasu daga babban gida ya fito , a wannan lokacin kuma Ahmad ya tafi bautar k'asa a wani k'auye a kano cikin k'aramar hukumar takai , bayan ya gama bautar k'asarsa ne aka d'aura musu aure kuma ya tafi da LAILA k'asar wajen domin k'aro karatun na sa, a farkon aurensu sosai LAILA takeyi mishi biyayya , sun zuba soyayya amma daga baya kuma sai abin ya chanza salo rashin mutunci sosai ta farayi masa , ya rasa gane kanta , a iya saninsa LAILANSA bata da mugun hali amma ya akayi ta fara nuna masa wani hali na daban, babbar matsalarsa guda d'aya itace ta rashin haihuwa , da farko ya zaci yana da matsala amma da akayi masa bincike aka gano ai lafiyarsa k'alau , yayi nacin duniya LAILA taje a duba ta amma tace ita ba inda zataje ai haihuwa ta Allah ce, baisan da gangan LAILA take shan magungunan hana d'aukar ciki ba , bayan tabi shawarar k'awayenta , su Aliya fire, lokacin da ta sanar dasu tana da ciki suka ingizata ta zubar da shi a cewar su wai zata tsofe da wuri , tun daga nan take amfani da maganin hana d'aukar ciki , Allah sarki ko shi Ahmad d'in baima San tayi cikin ba kuma an b'arar masa da abinda yake nema ido rufe, a haka suka yi shekarun da zasu yi su ka dawo Nigeria , ko da suka dawo yaso su zauna a gidansu amma tace ita za'a takura mata , haka bada yaso ba ya gina musu gida , a wannan shekarar da su ka dawo , Allah ya yiwa mahaifin Ahmad rasuwa sunji rasuwar ba kad'an ba amma daga baya su ka hak'ura suka dangana , su ka ci gaba da rayuwa ,Ahmad kuma ya ci gaba da kula da kamfanin nikan da mahaifinsa ya rasu ya bar masa. CIGABAN LABARI. Ranar litinin da wurwuri Fatima ta shirya , domin tun dare hajiya ta sanar da ita cewar da safe , yayanta zaizo ya kaita makaranta , dan haka kafin k'arfe bakwai ta gama shirinta tsaf , tana jiransa , a bakin k'ofar falo su ka yi kicib'us lokacin ya shigo ita kuma zata fita , da sauri ta dafe k'irjinta tsabar tsoro dan bata zata shi bane ba, " yallab'ai ina kwana , ta fad'a tana dubansa ", shi kuwa lulawa yayi chan duniyar tunani , ya'akayi yarinyar nan ta girma , to kwata2 kwana nawa rabona da ita , ko da yake dama wahala ce kuma tana sanya haka, " yallab'ai fa ina gaisheka ," sai a sannan ya farga sannan ya amsa , tambayarta yayi ina hajiya ta fad'a masa tana cikin d'aki , juyawa yayi yana tunanin girman da Fatima tayi a k'ank'anin lokaci, gashi kayan makarantar sun amsheta gaba ki d'aya kayan maroon colour ne amma rigar tasu mai gida gidan bak'i a jikinta , kuma hijjabin d'an karamine dan da kad'a ya haura k'asa k'irjinta,da sallama a bakinsa , sun gaisa da hajiya , ya fad'a mata zasu wuce makaranta zai kai Fatima, sosai ta musu addu'ah sannan su ka fita daga cikin gidan bayan sunyi sallama da Fatima, toh a hanya sosai su ka yi hira , har ya dinga mata tambayoyi tana bashi amsa daidai ," am ni kuwa Fatima har yau bansan labarinki cikakke ba , ko za'a taimaka a bani nasha", ya tambaya yana murmushi , sosai ta shagala da kallonsa, har sai da ya juyo ya kalleta sannan ta sunkuyar da kai tana murmushi, shima murmushin yayi , dab da sun k'ara bakin gate d'in makarantar , anyi mata cike cike da komai na sabon d'alibi , sannan aka bata aji , shi kuma Ahmad ya tafi wajen aiki. Koda aka kai ta a desk din da aka ajiye ta su biyu ne," sannu ta cikin bencin ta fad'a", " yauwa sannu" ," suna na Halima Nasir, nice too meet you", ni kuma suna na Fatima Iliyas ", murmushi ta mata sosai suka yi hira , a rana ta farko su ka shak'u ko da aka tashi , Halima taso su kai Fatima gida kasancewar yallab'ai Ahmad bai zo ba amma Fatima ta sanar mata yayanta zaizo d'aukarta, ilai kuwa suna tsaye ya k'araso sallama sukayi kowa ya nufi wajen Wanda yazo d'aukarsa , a hanya sosai Fatima ta saki jikinta da Ahmad ta dinga bashi labarin makarantar da sabuwar k'awarta da tayi, shi kuwa ba abinda yakeyi sai murmushi, " to kince zaki bani labarinki ko ba yanzu ba", " zan baka amma abinda zan iya cewa , akwai sark'ak'iya cikin labarina, ka bari in mun samu lokaci ba school, kazo ni kuma zan baka labarina ", murmushi ya sake yi , a daidai nan su ka k'arasa bakin gate d'in gidan , sun shiga cikin ko gama parkinga bai yi ba ta fita da gudu ta nufi falo da sallama ta k'arasa a lokacin shi kuma ya kunno kai , a cinyar hajiya ta zauna , "wash sai kin karyani , cewar hajiya da take k'ok'arin d'aga ta daga kan cinyarta ", shagwab'e fuska tayi ta turo d'an k'aramin bakinta waje , Ahmad dake tsaye zuba mata idanu yayi abin kawai ya burgeshi , lallai wannan yarinyar shagwab'ab'b'iya ce , hajiya ta mishi magana , firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi , gaisawa su ka k'arayi , a yayin da Fatima tace" mummy wallahi makarantar akwai dad'i sosai bari nayi wanka nazo na baki labari "," to kiyi Sauri ina jiranki, shi kuwa Ahmad rakata yayi da idanu har ta shige d'akinta. Bayan tayi wanka tayi sallah ta fito ciki Riga doguwa sai siririn hannu , kalar ruwan hoda , rigar ba ta da nauyi , tayi parkinga gashinta da ribom shi ma pink , a kusa da mummy ta zauna ta shagwab'e fuska , ni kuwa nace su Fatima an samu abinda akeso ko da da kike hannu Inna Asabe anayi oho, " mummy yunwa nake ji wallahi", tashi maza kije kici abinci kinsan bana San kina zama da yunwa ", tashi tayi ta nufi dinning area , yayin da Ahmad ya rakata da idanu , ya rasa abinda ke faruwa dashi komai yarinyar tayi abun birgewa ne, " tana da kyau abinda yace kenan ya kautar da kansa gefe guda", da sauri ta nufi wajen zama ta zauna abinci taci sosai sannan ta koma su ka ci gaba da hira , Ahmad bashi ya bar gidan ba sai bayan sallar isha'i. A b'angaren LAILA kuwa, sosai duniya ta dawo mata sabuwa, saboda sun shirya da Ahmad yadda ya kamata, kuma a nata tunanin ai Ahmad ya mayar da Fatima garinsu , batasan su na tare da mahaifiyarsa ba kasancewar ita d'in ba mai son zuwa gidan sirikarta ta bace ba, sosai hankalinta ya kwanta , takecin Karen ta babu babbaka , hmmmmm hajiya LAILA muje zuwa , mata a gidan Alhaji Ahmad. A b'angaren Fatima kuwa, sosai ta ke karatun ta cikin hazak'a , kuma halinsu yazo d'aya da Halima, dan a waje d'aya suka bambanta da juna shine , ita Fatima miskilace , while Halima kuma na da surutu da yawa, jarabawar farko , Fatima ta d'auki first class , Halima kuma second class, sosai yallab'ai Ahmad ya ji dad'in haka , yasan kuma ba asarar kud'insa yakeyi a banza ba, kyauta ta musammam yayi mata , kuma had'a mata da waya k'irar IPhone 11 pro, murna sosai tayi , da wannan kyauta bayan sun samu hutu Fatima ta tambayi hajiya kan tanasan taje gidansu Halima , hajiya a barta , ta kuma fad'awa driver ya kaita , sosai su ka yi murna da ganin juna, har k'arfe bakwai , sannan ta koma gida bayan mahaifiyar Halima ta bata kyauta da kyar su ka rasu, ko da ta isa gidan , a falo ta tarar da hajiya da yallab'ai , sannu da gida ta musu sannan ta nunawa hajiya kyautar da mamansu Halima ta mata, ran Ahmad ne ya b'aci au dama fita take yi any how any time , sai da ya bari bari hajiya ta tafi d'akinta sallah , sannan ya kutsa kansa d'akin Fatima a lokacin ta idar da sallar isha'i kenan , fuskarsa babu walwala, " ke dama yawo like zuwa, ya tsare ta da idanu yana jiran amsarta ", sosai ta tsorata , dan haka cikin rawar murya tace" am...am..ba.. ba haka bane ba , wallahi..... ba ta k'arasa ba ya katse ta " kar na k'ara ganin k'afarki a waje kin tafi yawo kinji na fad'a miki ", sannan ya juya ya fita, saboda ranshi ya b'aci ko sallama bai yiwa hajiya ba fice daga gidan ya nufi gidansa, ita kuwa Fatima zama tayi ta fashe da kuka sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shirin kwanciya bacci , shi kuwa ko da ya k'arasa gidan ko takan LAILA bai bi ba ya kwanta . amma ne fafur bacci yak'i zuwa, ransa ya kai mak'urar b'aci , minti bayan minti sai ya juya yayi tsaki , to shi menene ma zai dameshi dan ta fita, ni kuwa nace muje zuwa malam yallab'ai Alhaji Ahmad, hhhhhhh. sai da tsakar dare sannan ya samu bacci ya d'aukeshi, bayan ya gama tunane2sa ko na menene oho🥴 A b'angaren LAILA ma gajiya tayi da jiranshi , ganin bai dawo ba sai kawai ta kwanta ita ma , kasancewar ita ba ta damu da damuwar wani ba ta ta kawai ta sa ni......... DANALLAH A DINGA YIMIN SHARING NA BOOK DIN NAN PLZ👏🏻 Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 CHAB ANA WATA GA WATA GASKIYA BAZAMU LAMINTA BA ACE KHAF BABU MASOYAN LAILA INA, AI MU GASKIYA MUNA BAYAN LAILA 100%. HMMM SISTER BABU RUWA NA IN KIKA HAD'U DA FANS D'IN FATIMA , ZAKIYI BAYANI🥴😝 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ SHAFI NA 25_26 Washe gari da safe ko fitowa baiyi ba, saboda rashin baccin da ya samu jiya, LAILA kam koda ta fito ta tarar bayanan a zatonta ya fita hakan ya bata damar ficewa daga gidan bayan ta barwa Aisha mai girka musu abinci sallahu, akan abinda zata girka musu. A chan b'angaren Fatima ma bata fito ba sai wajen k'arfe goma na safe , Mummy bata taso ta ba kasancewar tayi tunanin ko unguwar da taje ne ya sanya bata tashi da wuri ba, batasan al ' amarin da ya faru ba , tsakanin yaran nata guda biyu, bayan Fatima ta tashi sai da tayi wanka duk da fuskarta a d'an kunbure take hakan bazai hana mutum ya gane taci kuka ta k'oshi ba, da sallama ta shiga d'akin mummy , " yauwa haba daughter, ina ta tunanin ko lafiya yanzu nake shirin in tashi inje in duba ki , mummy ta fad'a tana k'ok'arin juyawa saboda dama ta bata baya tana kallo cikin d'akin ", juyawa tayi jin Fatiman tayi shiru , " innalillahi lafiya ke kuwa naga fuskarki duk ta tashi , meye ya sameki , cikin kad'uwa Mummy ke fad'ar haka",sai a sannan Fatima tayi k'ok'arin bud'e bakinta sannan ta ce " Mummy kaina yakeyi min ciwo tun jiya da daddare, ta fad'a tana k'ok'arin kawar da k'wallar da ta taru a idanunta", janyota jikinta tayi sannan ta tambaye ta taci abinci girgiza mata kai tayi alamar a'a , umartarta tayi da taci abinci sannan ta sha magani da to ta amsa , sannan ta juya ta fita, ta nufi dinning area. A chan b'angaren kuwa sai sha d'aya na safe ya farka , a lokacin baccin da yayi ya saukar masa da ciwon kan da ya dawo gida yanayi, toilet ya shiga yayi brush , yayi wanka , kasancewar yayi sallar asubah, ya sanya yana gama feshe jikinshi da turare ya nufi d'akin LAILA kasancewar duk a up stairs d'in yake, da sallama a bakinsa ya tura , amma ne yana shiga yaji shiru tsammaninsa tana toilet dan yaji zubar ruwa, amma kusan 20 minutes, babu wanda ya fita a toilet, dan haka ya k'arasa bakin toilet d'in ya k'wank'wasa , shirun da yaji ne ya tabbatar masa da bata ciki , aikuwa rufe band'akin yayi , baya ya kashe ruwan , sannan ya nufi down stairs, a k'asan ma dai bata nan , Aisha mai girka musu abinci ce , ta fito daga kitchen, da alamar ta gama aikinta zata koma masaukinsu na masu aiki, " am ina matar gidan , ya fad'a kamar ba shi yayi maganar ba", da sauri ta rusuna har k'asa ta gaidashi sannan ta shaida masa ta fita, gyad'a kai kawai yayi kasancewar ransa yakai k'ololuwar b'aci, ya rasa mai ya sanya LAILA har yau bazata chanza ba , nuni yayi mata da hannu alamar taje, dan haka ta tashi ta fita abinda , shi ma hanyar falon ya nufa, yana fita ko abinci bai nema ba, ya shiga motarsa , gateman ya bud'e masa , ya cilla hancin motarsa ya nufi gidan Mummynshi. Fatima tana zaune tana cin abinci , duk da ranta bayaso kasancewar har yanzu bakinta ba appetite, da sallama ya shigo cikin falon , ba kowa a cikinshi , Fatima dake zaune tana ganinshi gabanta ya fad'i dan yanzu wani mugun tsoronsa takeji, shi kuwa bai ma kula da ita ba , gadan gadan ya nufi dinning area'n kasancewar yunwar da yakeji ga b'acin rai na fita LAILA bata tambaye shi ba, zama yayi k'ansa a k'asa, kamar daga sama ya tsinkayo muryarta na gaida shi, amsawa yayi sannan ya yi mata nuni da alamar ta zuba mishi abincin , aikuwa cikin rawar jiki shiga zuba mishi abincin , kunun tsamiya ne da kosai sai k'amshi tarugu yake yi , sannan farfesun hanta, sai kuma shayi Wanda tasan dole zai buk'ata, shi kuwa duk wani motsinta idonshi na kai , amma sai ya nuna kamar ma ba kallonta takeyi ba , hakan ne ya bata damar fecewa bayan ta gama zuba mishi abincin, da ido ya bita, kasancewar yanason yaga mai ya sanyata rawar jiki haka, da ya tuna kuma da abinda ya faru jiya murmushi kawai yayi, sannan ya fara cin abinci. Bayan ya kammala a lokacin Mummy ta fito da shirin fita unguwa gaisawa suka yi sannan ya mata a dawo lafiya , har ta kai k'ofar falon ta juyo had'i da cewar " yauwa ka sanya k'anwar taka ta sha magani , batajin dad'i ", da kanshi kawai ya amsa sannan ta juya ta fita shi kuma ya kishin gid'a, ya fuskantar TV saboda anayin labarai. Lokacin da aka kirawo sallah , hakan ya sanya ya nufi toilet d'in Mummy alwala yayi , sannan ya nufi masallaci, ko da ya dawo tana falo a zaune, sannu da zuwa ta mishi , ya amsa yana satar kallonta, " ki kawomin abinci nan, abinda ya fad'a kenan yana gyara zaman shi a jikin kujerar", cikin sauri ta nufi kicin d'in , da kallo ya bita kawai , ko da ta gama zuba mishi abincin, kallonta yayi had'i da cewar " ke kinci ne" kai ta girgiza alamar a'a , " kurma kika koma, ya k'ara jefa mata wata tambayar, " a'a kawai tace je ki d'auko chokali", bakinta ta motsa alamar tana son yin magana ganin ya had'e fuskarsa ya sanya ba musu ta d'auko, nuni yayi da ta sanya ciki , ta sanya sannan suka fara cin abinci, cikin nutsuwa take ci , shi kuwa gogan duk lomar da zata kai bakinta sai ya kalla, kwata kwata bata wani ci da yawa ba ta tashi alamar ta k'oshi , wani mugun kallo da ya zuba mata shi ya sanya dole ta koma ta zauna suka ci gaba da ci, bayan sun gama ya sanya ta d'auka magani , cikin ya mutsa fuska , ta zuba a baki ta kora da ruwa, sannan ta nufi d'akin ta . A b'angaren LAILA kuwa, sai k'arfe biyar ta koma gida , ko da ta shiga , ganin Aisha a kicin tana girkin dare , hakan ya sanya ta tambaye ta ko ya dawo, anan ta shaida mata ai dama bai fita ba, sai bayan ta fita sannan ya fita, kasancewar LAILA y'ar duniya ce hakan bai sanya ta damu ba tayi shigewar ta d'akinta. Sai bayan sallar isha'i sannan ya koma gida , bayan ya yi musu sallama , ya nufi hanyar gidanshi, ko da ya koma bai nunawa LAILA yasan ta fita ba, har tayi zaton ko Aisha k'arya ta mata , shi kuwa yana sane , amma ya share ta , saboda ya gane bazata shiryu ba, sai wani ikon ubangijin. Ana cikin haka , aka koma makarantar su Fatima , sosai tayi murna da komawar ta su kasancewar ba wani Hutu ne sosai ba, ko da ta koma yallabai shi ya ci gaba da kai ta makaranta kafin a samu mai kaita , na musamman a cewarsa😝🥴😳. Ranar Friday misalin k'arfe biyu a lokacin an yi sallah, ya nufi gidan na su, a falo ya samu Fatima ita kad'ai kasancewar Mummy ta fita tun safe, bayan ta gabatar masa da abinci ta juya zata nufi d'akinta , cikin d'aga murya ya kirawo sunanta , chak ta tsaya , " gurinki na zo ba gurin Mummy ba ina son , ki fad'amin gaskiyar ke wacece, saboda ina miki kallon wadda na sani amma kin k'aryata ni, ina jinki bismillah fara ", a sanyaye ta zauna , sannan ta fara bashi labarinta daga farko har k'arshe sannan ta d'ora da cewar ina son nayi karatu mai zurfi, duk da a baya jajirtaccen malamina yaso nayi, amma Allah bai nufa ba", " sannan kuwa wanene , har haka mai muhimmacin da bazaki manta dashi ba , ya fad'a ya na kallonta da son ta ba shi amsa ", nan ta zayyane mishi komai daga bisa tace" har yau har gobe ina mishi fatan alkhairi a rayuwarsa , saboda ya so rayuwa ta da ci gaba, ta fad'a a yayin da hawaye ya sulmiyowa fuskarta", " ko zan iya sanin sunan malamin ", abinda ya ce kenan,"" sunansa malam Ahmad " dam gabansa ya fad'i shikenan hasashen da yake yi ya zama GASKIYA , yau ga Fatima yarinyar da ya tafi ya barota a k'auye cikin wahalar rayuwa , Allah ya k'ara had'a su , yarinyar da tun lokacin da yaje bautar k'asa ya d'aura idonsa akanta yake k'aunar yarinyar tun tana y'ar k'aramar yarinyarta, cikin dashewar da rawar murya ya furta " da.. da....dama kece dama kece Fatima , Allah na gode maka.............. MASOYA YALLAB'AI AHMAD GAREKU🥰 Dan Allah a dinga yimin sharing na book d'in nan plz.👏🏻👏🏻 Please Share & Comments To be continue..................... 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ INA GODIYA DA IRIN RUWAN COMMENTS DA KUKE TA ZUBA WA , INA JIN DAD'I SOSAI. INA GANIN ADDU'O'INKU , MASOYA NA DA MA MASOYAN BOOK D'IN KISHIYAR UWA, ALLAH YA K'ARA DANK'ON ZUMUNCI AMIN. SHAFI NA 27_28 Ita kuwa Fatima, kallonsa kawai ta tsaya tana yi , ta gaza fuskantar kalma d'aya daga cikin zantuttukan da yake yi, komawa tayi kamar wata sokuwa , idanu da hanci ta zuba mishi kawai tana kallon , shi kuwa zuba mata idanu kawai yayi kallon ikon Allah, " Fatima dama kece, dama , daman ni nasan , ina yawan ganin nasan fuskarki, ashe dama kece, Allah na gode maka, ya fad'a yana k'ara kallonta", " kingane ni, ni ne fa malaminki mai k'aunarki , malam Ahmad", da sauri ta d'ago kanta cikin razana da jin abinda yake fad'a, kuma da alama baya cikin hayyacinsa, domin tafi zaton sumbatu yake yi, " yallab'ai wai me yake faruwa ne, ta fad'a kamar zatayi kuka", kallonta ya tsaya yanayi cike da shauk'in k'ara ganinta a karo na biyu, " Fatima dama kina nan , nayi ta Neman ki sak'o da lungu , a lokacin da na dawo daga k'asar waje naso in zo in da kike amma ban samu dama ba , wayyo gsky Allah yana sona " , ita dai tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, gaskiya itama tayi ta tunanin inda tasan fuskar yallab'ai ashe shine mutumin da ya zamar mata garkuwa kuma jigo a rayuwarta da karatunta, hawaye taji yana k'ok'arin zuba a fuskarta , saurin sanya hannu tayi ta share hawayen da ya fito ta gefen idonta, " cikin rawar murya ta furta, uncle da..da..dama kana nan a raye, ta tambaya tana kallonsa ", gyad'a mata kai kawai yayi kasancewar ya kasa magana ma, suna cikin wannan yanayin Mummy ta dawo tun kafin ta huta Ahmad ya sanar mata wacece Fatima , sosai tayi mamaki , duk da haka ita ma Mummy na yi mawa Fatima kallon sani , chab k'ak'ak'ara k'ak'a, toh ita kuma mummy me take nufi oho. Suna zaune a haka har magriba ta k'arato , hakan ya tursasa shi tashi ba dan ya so ba ya nufi masallaci, domin gabatar da sallah , su ma nufar toilet ko wacce tayi domin d'auro alwala. Bayan sun idar da sallah , shi ma ya shigo , abinci su ka ci sosai ya shagalta da kallon Fatima kasancewar tayi girma, shi fa mamaki yake yi yadda ta zama cikakkiyar budurwa, Allah ya taimake shi ya k'ara dawo mishi da ita a karo na biyu, sosai ya ci abinci , sai da mummy ta tursasa masa sannan ya hak'ura ya nufi gidansa cike da farin cikin ganin Fatima. Ko da ya k'arasa, cike yake da farin ciki, sama ya haura ya nufi d'akin LAILA, a kwance ya same ta a lokacin anyi sallar isha'i shiga cikin band'akin ta yayi, da idanu ta bishi sannan ta juya ta ci gaba da charting d'inta, fitowa yayi ya mata magana akan anyi sallah , nuna masa alamar zatayi tayi da kanta , shi kuma ya juya ya fita ya nufi masallaci. A chan b'angaren Fatima , sosai ta shagalta da tunanin malamin na ta , kuma yallab'ai, lallai ya mata halarci, bayan ya tsaya mata a rayuwarta ta baya sannan yanzu ya mayar da ita y'ar dangi , ita kam dame ma zata saka mishi ne wai, tambayar da ta gaza amsawa kenan ta kwanta bacci aikuwa ba dad'ewa ya d'auke ta, cike da murnar ganin malamin na ta a karo na biyu. Shi ma a nashi b'angaren, sosai ya gaza yin bacci , domin tsabar farin ciki, da ganin d'alibar ta sa, sai chan dare ya kwanta, LAILA ta yi mamakin ganin na sa , a cikin farin ciki amma kasancewar ta mai da damuwar wani ba na ta ba, ya sanya ta k'yaleshi kawai , a haka su ka yi bacci. To fa shak'uwa sosai ta shiga tsakanin yallab'ai Ahmad da kuma Fatima , kullum zai zo in ya dawo daga aiki , ya zauna yayi ta tambayarta labarin bayan rabuwa, ita kuma tana bashi , wani yayi dariya wani yaji tausayinta , shi kansa ya gaza gane kansa game da ita, a farko ya d'auka tausayi ne amma daga baya kuma ya gane soyayya mai k'arfi yake yi mata, chab to fa fans din yallab'ai Ahmad gare ku😍😍. Ana cikin haka kuma su Fatima suka gama aji biyu, kuma a wannan lokacin zata zana placement, wannan tsari ne daga yallab'ai, an biya mata komai sannan su ka zauna fara exam. Masha Allahu sunyi exam , kuma Alhamdulillah , sun yi nasara , ita ma k'awarta Halima tare su ka yi , sosai ta yi murna ganin cewar tare zasu ci gaba da Halima. A chan b'angaren Ahmad , kuwa sosai ya Sanya ayi masa binciken kakanin Fatima anyi sa'ar an samu Wanda ya san kakan nata amma kuma ya tafi fatauci legas sai bayan shekara zai dawo, sosai ya ji dad'in haka, kuma yana yin komai ne ba tare da sanin ita kanta Mummy ba ballantana kuma Fatima. Achan b'angaren LAILA kuwa sosai hankalinta ya kwanta, ganin mijinta yanzu baya matsa mata wajen hanyar fita, don haka sai ta ranci na kare, kullum bata gida , daga gidan wannan k'awa sai bikin wannan k'awa, ni ko nace uhmmmm su LAILA manya a dai juri zuwa rafi tohm😝. Suna zaune a falon mummy, Ahmad yana ta satar kallon Fatima, tana sane da kallon da yake bin ta dashi duk ta kasa sukuni , " uhmmmm Mummy please anjima inason daughter ta ki ta rakani unguwa , ya fad'a yana kallon mummy don jin me zatace "," Ina zaku je banason ka koyawa yarinya ta yawo bazata je ba,", " please mummy ba dad'ewa zamu yi ba, da kai ta amsa alamar ta yarda sannan ya juya ya kalli Fatima dake zaune , "ki shirya bayan la'asar , kafin na dawo abinda yace kenan sannan ya juya fita ita ma ta tashi ta shigewarta d'aki domin cika umarnin yallab'ai, kuma malami a gare ta , wato Ahmad............ Please Share & Comments To be continue............. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 KU NA K'ARAMIN K'AIMI FAN'S, INA TARE DA KU NIMA, LUV U ALL 😍😍. SHAFI NA 29_30 Mummy kuwa, bi Fatima tayi da kallo , tare da wani k'ayataccen murmushi , irin na su na manya wadda ita kad'ai tasan ma'anarsa, sannan ta girgiza kai , ita ma ta mik'e ta shige cikin d'akinta. A b'angaren Fatima kuwa, tana shiga d'akinta wardrobe ta bud'e, tsayawa tayi tana duba kayan da zata sanya, rasa wanda zata saka tayi , saboda batasan inda za su je ba , sai da ta gama dube dubenta ,har ta mik'e zata kirawo mummy ta taya ta zab'ar kaya kawai sai ta hango wata marron color d'in doguwar rigar abaya , hakan ya sanya ta zaro ta , wadda taji stones kalar gold, sai siririn mayafinta, jaka da takalmi ta zab'o su ma kalar golden da agogo, sannan ta fad'a wanka , ko da ta fito sai da ta gama zafa lotion mai k'amshi sannan ta zura kayan ta yane kanta da mayafin rigar , takalmi ta zura sannan ta rataya jakar ta ta, ta feshe jikinta da turaren "Al' oud Al khalij", sannan ta nufi falon, tana fita yana shigo wa, da idanunsa masu rikitar da ita , a zuciyarsa ya furta masha Allahu , k'arar bud'e k'ofar d'akin Mummy ne ya dawo da shi daga duniyar da ya shiga , sannan ya k'arasa cikin d'akin ya zauna, " Mummy barka da fitowa , ya ce da ita ", sannan ya dubi Fatima wadda ta mak'e a jikin bango kamar zata shige " mu je ko , abinda ya furta kenan sannan ya yiwa Mummy sallama ya nufi hanyar waje" , ganin haka ya sanya Fatima ta bishi cikin hanzari, mummy ce ta musu a dawo lafiya , bayan ta sanarwa da Ahmad kar su kai dare, da toh ya amsa mata sannan ya k'arasa ficewa, ko da su ka k'arasa bakin motar da kanshi ya bud'e mata sannan ta shiga , shima ya zaga ya shiga su ka bar gida bayan gateman ya bud'e musu gate. A chan b'angaren LAILA kuwa, tana zaune a falonta ita da k'awarta Aliya fire, cike da jin haushi Aliya ta dubi k'awarta ta " ni wallahi kina bani haushi, ta ya ya kawai daga ce miki , kar kije sai ki zauna yayi ta juya ki , wallahi ni banga namijin da zai juyani kamar waina ba, ta k'arashe maganar cikin masifa", LAILA kuwa sai kallonta take yi yayin da maganganunta su na k'ara shigarta," kinga Aliya bari naje nayi wanka na shirya, ai wallahi baza'ayi babu ni ba, haka kawai jirani in zo mu tafi , LAILA ta fad'a had'e da mik'ewa tsaye tana k'ok'arin hawa up stair na gidan da toh Aliya ta bi ta sannan ta d'auko wayarta ta fara kiran k'awar ta su wadda ta gayyace su birthday, domin ta sanar da su LAILA zata samu damar zuwa, ita kuma LAILA ta k'arasa hayewa saman benen. A chan b'angaren su Fatima kuwa, sai da suka yi tafiyar kusan minti talatin ba tare da kowa ya cewa d'an uwansa komai ba, chan Fatima ta dubi yallab'ai da ke aikin tuk'i " uhmmm wai har yanzu ba'azo ba , ta fad'a kamar ba ita tayi maganar ba ", " siyar da ke zanyi abinda yace kenan , yana k'ok'arin shigar da motarsa cikin wani katafaren wajen shak'atawa, da idanu kawai take bin wajen ba dai tsaruwa kam , kamar rak'umin da akala haka take bin sa, har su ka k'arasa wajen wani taro daga gani na manyan masu kud'ine a d'aya daga cikin jerin kujerun su ka zauna, kujerar d'an uwansa tana kallonsa, anyi decoration na k'ayatarwa a wajen , abokan nan Ahmad wad'anda su ka zo taro bikin zagayowar ranar haihuwar matar d'aya daga cikin abokinsu mai suna Muhammad lawan, ko wanne yazo suna gaisawa da Ahmad, suka dinga yi mishi tsiyar wai ya k'ara aure bai fad'a musu ba shi dai kawai dariya abin yake ba shi , sannan ya sanar da su ai k'anwarsa ce, a haka su ka dinga hira sosai Fatima ta bi dad'in had'uwa da wad'annan mutane masu karamci . A chan b'angaren su LAILA kuwa, sosai su ka gama shiryawa, cikin wani hamshak'in leshi , mai tsananin kyau ta sanya , ta sha uban takalmi mai tsini ta sanya siririn mayafi, k'asa ta sauka ta tarar da Aliya na zaune, kod'ata ta farayi sannan ta shiga d'aukanta a photo , sosai tayi ma hotuna , sannan su ka shiga mota suka nufi wajen birthday partyn . Sai da su kai kusan minti talatin , sannan suka k'arasa wajen , parking d'in motar LAILA ta yi, sannan suka nufi k'ofar shiga, a chan b'angare d'aya suka zauna , su ka fara hira da k'awayensu, chan wadda ake yiwa birthday d'in mai suna Ramlat ta k'arasa wajen su LAILA, da fara'arta ta isa wajen gaisawa su ka yi , sannan ta umarci LAILA da ta taso su gaisa da mijinta , da kuma babban amininsa , cike da karairaya ta tashi su ka nufi wajen domin gaisawa. A b'angaren Mummy kuwa , shiru taji dan haka ta tashi ta shiga safa da marwa a falon , wayar ta ta d'auka ta shiga kiran Ahmad, amma me bai d'auka ba sosai hankalinta ya tashi , ta zauna ta shiga zaman jiran dawowarsu. A b'angaren LAILA kuwa, tun daga nesa ta hango abokin mijin k'awarta ta , wanda take wa kallon kamar mijinta Ahmad , amma kuma ai wannan tare da kyakykyawar yarinya balarabiya ta ganshi, ni kuwa nace toh su LAILA an fara tsufa kenan😝, tana k'arasawa tana ganin kamanin wannan mutumin yana k'ara yi mata kamanin mijinta, sai da ta k'arasa wajen suka gaisa da mijin Ramlat, Ahmad da ke zaune kawai ya kalli LAILA k'warai ba zargi yakeyi ba LAILA ce matarsa , kawai kafe ta yayi da idanu, yana kallon ikon Allah , yanzu wannan itace matar da yake aure marabarta da masu zaman Kansu kawai d'aurin igiyoyin aurensa da ke kanta, ita kuwa LAILA jin kamar ana kallonta ya sanya ta juya domin ganin wake kallonta, k'walalo idanunta tayi sannan ta zunduma wani uwar ashar tare da fad'in " me zan gani , Ahmad wannan wacece a tare da kai , ta fad'a tana nuna Fatima ", sosai tsoro ya kama Fatima tayi wuri wuri da idanu, aikuwa jin sannan zagin ya sanya mutane suka jiyo suna kallonsu, ganin haukan da LAILA keyi ya sanya Ahmad ya daka mata tsawa , " aikuwa tayi ta kuwwa tana zagi , tana kururuwa, " Fatima koma chan kije ki zauna, ya fad'a yana nuna mata wajen zama", ai LAILA tana ji ta zunduma ihu , " shegiya , matsiyaciya , tsohuwar karuwa , wai dama kina mak'ale da mijina ban sani ba", ta fad'a had'e da janyo Fatima , ta wanchakalar da ita a gefe , kafin Ahmad ya zo ta kwashe ta da wani gigitaccen mari, juyawa tayi ta d'auko wani kofin tangaran ta sauke mata shi a kai , k'arar da Fatima ta saki ne ya janyo hankalin mutane dama shi kansa Ahmad d'in , akwai cikin hanzari , ya k'araso wajen ya wanke LAILA da wani azababben mari , wanda sai da taga taurari, kuwwa ta sake saki tana k'ara lalubar Fatima dan ta k'ara yi mata wata illar , k'ara kifa mata mari yayi, ya warb'ar da ita gefe, ganin Fatima tana kwance kamar ba rai a jikinta , ga jini da ya dinga zuba , aikuwa da sauri ya k'arasa wajen ciccib'eta ya nufi mota yana haki , saka ta yayi a mota sannan ya shiga ya tada ya fita daga wajen biki gaba d'aya , ya nufi asibiti hankalinsa a tashe. B'angaren LAILA kuwa , zube wa tayi a k'asa ta hau rusar kuka, had'e da dana sanin zuwa wajen birthday d'in, Aliya ce ta kamata ta mik'e suka nufi mota , saboda tsabar tashin hankali, ita ta tuk'a motar , yayin da LAILA take ta kuka , su ka fice daga gurin bikin, suka nufi gidansu LAILA , bisa umarnin da LAILA ta bawa Aliyar............. Please Share & Comments To be continue.................. 🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 HHHHH WALLAHI KUNA BANI DARIYA , FAN'S DIN LITTAFIN KISHIYAR UWA, HHHHH ALLAH YA K'ARA ZUMUNCI AMIN🤣 🤣😍 BAYAN HAKA YAU YADDA KUKA SANYANI JIN DAD'I , NIMA ZANYI MUKU TYPING SOSAI DA SOSAI, FATAN ZAKU YI ENJOINING SOSAI, LUV U ALL. NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE D'IN GA MASOYAN LITTAFINA NA KISHIYAR UWA SHAFI NA 31-32 Ko da su LAILA da Aliya suka isa k'ofar gidansu LAILAN, horn sosai LAILA ta shiga dannawa, gateman d'in da sauri ya k'araso ya shiga kiciniyar bud'e gate d'in, kasancewar tsohon ne, hakan ya sanya duk ya rikirkice ya kasa bud'e gate d'in, aikuwa da sauri ta k'araso cike da masifa" dallah malam kana ganin zamu shiga sai wani salo salo kake yi ka gaza bud'ewa mutane, ta fad'a idonta na kan tsohon " yi tayi kamar zata bangaje shi ta nufi cikin gidan tana k'wallawa Mummynta kira, tana kuma rusar kuka, Aliya fire kuwa tana cikin motar a zaune da k'yar Baba maigadi ya bud'e gate d'in ta shiga da motar sannan ya rufe , ta rufawa LAILA baya itama ta shiga cikin gidan. Chan d'aya b'angaren kuwa, hajiya tana zaune ta rasa inda zata tsoma ranta, gashi tayi kiran duniya Ahmad baya d'aga wayarta, gashi har k'arfe takwas na dare yayi, zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, hakan ya sanya ta kissima abubuwa da yawa a ranta, shed'an ya dinga yi mata wasi wasi a cikin zuciyarta, gashi ta kuma yi ta d'auka wayarta, i zuwa yanzu ta kira Ahmad ya kai sau kusan ashirin, amma still baya d'agawa, sake kira ta yi a karo na gaba , shi ma baa d'aga ba hakan ya sanya ta nemi guri ta zauna ta zubawa ikon Allah idanu , tana kuma jiran dawowarsu a koda yaushe. A b'angaren su Fatima kuwa, da gudu ya dinga tafiya kamar zai tashi sama, gani yake yi kamar ma yarinyar bata numfashi, hakan ya sanya ya k'ara k'aimi a tafiyar ta sa , yayin da hannunsa ke sak'ale a cikin na ta, ji yake yi Kamar ya zunduma ihu, amma ba shakka ya na kukan zuci , ya zaiyi idan aka ce yarinyar nan ta rasu, ina zai sanya rayuwarsa yaji sanyi lallai bazai yafe wa kansa ba, lallai idan har yarinyar nan ta rasa ranta ta dalilin LAILA wallahi sai yayi shari'a da ita , ko da duk abinda ya mallaka zai k'are ne ,a haka ya dinga tunani har ya k'arasa cikin asibitin, wanda da taimakon Allah ne kawai ya kai shi , nan wani asibiti mafi kusa ya kai ta saboda yana ganin idan har ya kai ta asibitin su Dr Sadiq lallai kafin ya k'arasa zata rasa ranta, ko da suka k'arasa , ganin irin ciwon da ta ji , jini duk ya b'ata mata jini, ya sanya likitocin suka ji tsoro, suka k'i karb'arta , sai da y'an sanda, hakan ya sanya ba shiri ya je police station mafi kusa da asibitin ya taho da y'an sanda guda biyu , suka yi cike cike sannan likitocin suka shiga da ita domin ganin ta hayyacinta, shi kuma ya nemi guri ya zauna, ya had'e kai da gwiwa yana sauraron hukuncin doctor d'in. Tun daga tsakiyar falon ta fara kiranta, cikin k'araji, Mummy! Mummy!Mummy!, haka ta dinga k'walla mata kira, cikin sassarfa ta k'araso, " ke me ya faru na ganku haka, ta fad'a tana duba LAILA, wadda ta fad'a jikinta , fashewa tayi da kuka kamar hakan ya k'ara tayarda hankalin Mummyn ta ta, ganin ba zata ce komai ba ya sanya ta juyata kalli Aliya" Aliya lafiya kuka shigo a hanrgitse , ta tambaya tana jiran amsarta, " k'arasawa Aliya fire ta yi ta fara zayyanewa Mummy k'arya da gaskiya, wani uban ashar da Mummy ta yi sai da LAILA ta d'ago da sauri ta kalle ta, cike da hargagi ta ke fad'in " lallai Ahmad ya cika cikakken marar mutunci, yanzu amma ke kina cikin wannan halin baki sanar da mu ba , wallahi ba abinda zai sanya ya dakeki ya zauna lafiya , sai munyi k'ararsa kotu , da k'yar su Aliya suka rarrashe ta, ta hak'ura , bayan tasha al washin sanar da mahaifin LAILA in ya dawo daga, tafiyar da yayi ita kuwa LAILA ta k'udurta a ranta sai ta ga bayan Fatima ko ta halin yaya ne ,Mummy ce ta kwantar mata da hankali, kasancewar tace mata zata d'auki mataki akan Ahmad dama kanta ita Fatiman , hakan ya sanya LAILA ta ji sanyi a ranta , da kuma ta tuna yanzu fa tana gida zata ci karenta babu babbaka, ni kuwa na ce sai ki taci ai bazai wuce tafiya yawo ba ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta😏😚, sai da suka kwantar mata da hankali , sannan suka tsunduma hirar duniya. ASIBITI Sai da likitocin da nurses d'in suka kwashe wajen awa d'aya da rabi akan Fatima , sannan ta farfad'o da wani matsanancin ciwon kai, sakamakon kofin da LAILA ta buga mata a tsakiyar kanta, sai da suka gama yi mata duk abinda ya dace kama daga wanke ciwo, suka d'inke mata wajen, lokacin da suka gama , su ka mata allurar bacci sannan suka fita, Ahmad da ke zaune, yayi zurfi a cikin tunani, wanda doctor na ta yi masa magana amma ya zurfafa sosai a cikin tunanin irin hukuncin da zai d'auka akan LAILA , tunanin da ya fad'o ma sa a rai ne ya sanya yayi murmushi Wanda ya fi kuka ciwo , toh fa fan's d'in yallab'ai gare ku, dan Allah Ku bincika mana me yake shirin k'ullawa😁😁, sai da likitan ya data shi sannan firgigit ya juya " doctor ya jikin na ta, ta samu sauk'i ko ya ya, ya yiwa likitan tambaya biyu a lokaci guda", " Alhamdulillah, tana lafiya, ta farfad'o zaka iya shiga domin ganin ta, amma dai ta samu bacci ya d'auke ta sakamakon allurar baccin da muka yi mata, Allah ya k'ara kiyaye wa", da amin ya amsa, sannan ya juya ya shiga d'akin da sallama a bakinsa, a kujerar da ke cikin d'akin ya janyo had'e da zama kusa da gadon, tana kwance , fuskarta tayi fayau da ita, hannunta ya kama ya murza a hankali , " Fatima ni ne sanadin fad'awarki a cikin wannan halin , ta ya ya zan iya yafewa kaina , a dalilina a karon farko kika kusan rasa rayuwarki, yanzu a dalilin mata ta, marar kan gado gaki cikin wani halin mai wuyar sha'ani, Fatima inaso rayuwarki ta zamato abar sha'awa ga kowa ta yadda duk wwanda ya kalleki bazai miki kallon k'ask'anci ba amma na gaza samar miki da farin cikin , ni wanne irin mutum ne wane iri ne ni, kuka ne yaci k'arfinsa bai ida k'arasawa ba, tashi yayi da ya tuna da cewar wayarsa na waje cikin motarsa, kuma bai sanarwa da Mummy halin da ake ciki ba , waje ya fita ya nufi motarsa , ko da ya d'auki wayar missed calls ya ganin rututu , yana duba wa ya ga Mummy ce, da hanzari ya d'auka dan yabi kiran sai ga wani kiran ya shigo , d'aga wa yayi had'i fad'in " Mummy LAILA ce , LAILA ce Mummy , fashewa yayi da kuka hakan ya razana hajia Amina ba kad'an ba" saurara Ahmad kamin bayani yadda zan fahimta, mai ya samu LAILAN, ta tambaya cike da zumud'in jin meke faruwa" , tsagaitawa yayi da kukan sannan ya zayyane mata duk abubuwan da su ka faru , salati Mummy ta sa ka sannan ta tambaye shi asibitin da suke , ya fad'a mata ta ce gata nan zuwa, da toh ya amsa ma ta sannan ya koma cikin asibitin. A b'angaren LAILA kuwa , ko da daddynta ya dawo , Mummynta ta sanar da shi , sosai ransa ya b'aci ita ma da yake uwar tsohuwar banza ce sai da ta k'ara da ta ta k'aryar bayan ta y'ay'an na ta, sosai ya yarda akan cewar LAILA ta zauna a gida , da shi a nashi ra'ayin ma Ahmad ya sakar masa yarinyarsa, ta yaya zaace yarinyar bata da ikon wata yawa a gidan aurenta said ya saka mata takunkumi, ganin LAILA ba ta yarda da cewar a sake ta ba ya sanya suka hak'ur, amma da sharad'in sai yaje da kansa shi Ahmad d'in sun ja masa kunne akan y'arsu, uhmmmm ayi dai mu ganu in tusa zata hura wuta😙🤨. A chan b'angaren Mummy kuwa sai da ta gama kammala komai da zaa buk'ata a asibitin kama daga kayan sanyawar Fatima abinda duk tasan d'iyar ta ta zata bukata, sai da ta d'aukar ma ta sannan ta shiga mota direba ya ja su ka nufi asibitin . ASIBITI Ko da su Mummy su ka k'arasa , a harabar asibitin su ka tsaya, waya ta masa , sanan ya zo ya tafi da su d'akin da Fatima take, sai da Mummy tayi kusan awa biyu sannan Fatima ta farka, da addu'ah a bakinta, fara tariyo abubuwan da suka faru tayi , k'wallace ya shiga zubo mata a kumatu , duk ta sanadin KISHIYAR UWA rayuwa ta take tangal tangal , duk da ina tunanin na samu hutu na gudo daga azabarta ashe ba haka bane ba , muryar Mummy da ta ji ne ya sanya ta saurin goge hawayen fuskarta ta k'ak'alo murmushin da yafi kuka ciwo , " sannu kinji daughter, Allah ya k'ara sauk'i , Allah ya baki lafiya ," da amin kawai ta amsa , ta koma ta lumshe idanunta , sai wajen sha biyu sannan Mummy ta sanarwa da Ahmad ya tafi gida ita zata kwana da Fatima , da yaso yayi musu amma kuma , sai ya kyale, ya shiga mota ya nufi gida. Mummy ce ta taimakawa Fatima tayi shirin bacci , sannan ita ma tayi , Fatima da tuni bacci ya d'auke ta , mummy ta tsaya kallonta lallai yarinyar tana cikin jarabawar rayuwa, kuma Allah kad'ai zai fitar da ita , k'ura mata idanunta tayi, Allah ya sanya hasashen da take yi akan Fatima ya kasance gaskiya ne amin, toh fa mummy ya ya dai wanne hasashe kuma🧐, ganin baccin Fatima yayi nisa ya sanya ita ma mummy ta nemi wajen kwanciya. 1:30am Har a lokacin ya gaza runtsawa , tunani fal ya cika NASA k'wak'walwa da zuciya, wallahi ba shakka sai LAILA ta game kurenta shi kad'ai yasan ko wanne hukuncin ya tanadar mata, zata gane tayi kuskure babba a rayuwart, sai wajen k'arfe uku na dare sannan bacci b'arawo ya sace shi , da zumud'in ganin gari ya waye, domin sanar da Mummy shawarar da ya yanke akan al amari. Washe gari ya so ya d'an makara dan sai 6: 15 am ya tashi a bacci, da sauri ya tashi yayi dallah , saboda makarar da yayi , bayan yayi wanka ya shirya , sannan ya nufi asibitin . Ko da ya k'arasa , takwas tayi , yana shiga bayan sun gaisa da Mummy , Fatima ta gaida shi ya amsa cike da murmushi a fuskarsa, sannan ya mata ya jiki ta amsa da sauk'i , ya juya hankalinsa gaba ki d'aya wajen mahaifiyar ta sa," hajiya, ya kira sunanta , kasancewar indai zai yi mata maganar da take da muhimmacine haka yake kiranta, amsawa tayi sannan ya kamo hannunta " inason a d'auramin aure da Fatima kuwa ba tare da kowa ya sani ba , zaro idanu Fatima tayi haka ma Mummy, sannan ta ce............. Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 FANS DAN ALLAH KUYI MIN HAK'URI, BISA GA JINA SHIRU NA KWANA BIYU , WANNAN DALILIN YA SAMO ASALI NE SABODA INA BUSY , AMMA INSHA ALLAHU NA DAWO DA K'WARINA , LUV U ALL MY FAN'S😍😍. SHAFI NA 33_34. Mummy ce ta kalle shi had'i da fad'ar" lafiyarka kuwa Ahmad , wannan wacce iriyar magana kazomin da ita ne wai , ta fad'a tana kallonsa da son jin dalili", sunkuyar da kansa yayi k'asa ya kasa cewa komai , ganin haka ya sanya mummy sassauta murya saboda ta gane fushi yayi," haba son ta yaya za'ayi wannan d'anyen aiki baka ga abinda ya faru ba da matarka da daughter, son Fatima yarinya ce, bazata iya kishi da LAILA, kuma ko ba haka ba Fatima makaranta take zuwa , yanzu ta soma karatunta kana ganin in aka katse ta anyi mata adalci, tambaya tana jiran ya bata amsa"," Mummy ni dai kawai hakan nake so kuma bana San a d'auki lokaci mai tsawo nan da wani satin in Allah ya kaimu ya kama ranar juma'ah kenan", mummy ce ta dube shi , har cikin ransa da gaske yake ya sanya ta saukar da murya naji NA amince , amma da sharad'i za'ayi bikin amma nan da wata d'aya tunda ka matsu ayi a hakan", Fatima dake zaune jin abinda mummy ta fad'a sai da cikinta ya bada wata k'ara k'uuuuuuu , shikenan za'a kasheta da ranta ya zatayi kenan , kamata yayi ace tun kafin ayi auren nan ta samu ta fece, duk da son da mummy take mata ya kamata ace ta barta ko ba dan komai ba sai son tasan halin LAILA, a yanzu ma da ta gansu a tare ta fara sabauta mata rayuwa ballantana kuma ace ta auri mijinta ai shikenan kuma sai dai ta kai ta lafiya, tana cikin tunanin nan taji Mummy na kiran sunanta , cikin sanyin murya ta amsa. " ina fatan hukuncin da muka yanke yayi miki,mummy ta fad'a tana kallon Fatima da son jin me zata fad'a", Fatima tsintar kanta tayi da amincewa Mummy ba tare da ta San ta amince ba , murmushi mummy tayi , a gaskiya har cikin ranta ta aminta da Fatima , kuma tasan zata yiwa yaran d'anta tarbiyya, shi kuwa Ahmad da ke zaune sosai ya shagalta da kallon Fatima, sosai yarinyar take burgeshi, shi kad'ai sai kaga yana murmushi , mummy ce ta taimaka mata ta yi wanka ta gyara jikinta sosai a gurin cin abinci ne ta so tayi gardama , amma da Ahmad ya had'e fuska ya koma yallab'ai na asali, sai ta amsa ta fara ci sai da taji kamar zatayi amai sannan ta jijjiga kanta hakan ya sanya mummy ta k'yaleta, ganin da mummy tayi kamar Fatima na jin bacci ya sanya ta taimaka mata ta gyara kwanciyarta ba dad'ewa kuwa baccin ya kwasheta , su kuma suka ci gaba da tattaunawar bikin, nan Ahmad ya shaidawa hajiya ai LAILA tana gidansu , sosai ta nuna b'acin ranta akan haka , tace ya je ya taho da matarsa, ya fad'a mata bai ma San ta tafi ba jiya ne bai ganta a gida ba da ya koma , amma zai je ya dawo da ita, ya kuma sanarwa da hajiya Dan Allah ayi komai cikin sirri, wannan kenan. A chan b'angaren LAILA kuwa , sun barbaje a falo ita da k'awayenta duniya ta koma mata sabuwa, ba abinda yake damunta, duk inda taga damar zuwa babu mai hana ta , hakan ya sanya take cin karenta babu babbaka, wata wadda suke kira da woman leader ce ta dubi LAILA a yatsine" wallah babbar hajiya kina bani mamaki , kamar ba LAILA ba, y'ar k'walisa, ki tsaya namiji yana b'ata miki rai, in nice ai wallahi sai na barshi , ko da shine autan maza"," ki kyaleta abinda nakeso ta gane kenan amma tak'i ta fuskanta , Aliya fire ta fad'a tana kallon LAILA", "yanzu toh me kuke son nayi , LAILA ta tambayi su Aliya fire, " ki rabu dashi kawai kizo a kwashi rabo da ke, Aliya ta kuma fad'a "," a'a inason mijina bazan rabu da shi ba gaskiya , amma nasan me zanyi ", Aliya naga ta tashi ta zagaya wajen LAILA ,suka gama maganganunsu ban dai san me ta fad'a mata ba , suka kwashe da dariya , su ka tafa harda woman leader, sannan su ka cigaba da hirarsu a haka mummyn LAILA ta sauko , aka cigaba da hirar da ita . BAYAN SATI 1 Alhmadulillah, bikin Fatima yayi sauk'i sosai sai abinda baza'a rasa ba, zaune su ke, likita ya shigo ya duba ta , sannan ya sanarwa da mummy dama yana son sallamarsu ne tunda mai jiki Alhamdulillah ta warke, nan ya basu sallama , mummy ta kira Ahmad yazo ya d'auke su ya mayar da su gida , ko da suka koma sosai Fatima ta gasa jikinta da ruwan d'umi , tayi wanka , abinci taci kad'an sannan ta kwanta bacci kasancewar tana fashin sallah . A chan falo kuwa Ahmad yana zaune da hajiya so yalr ya ga Fatima ta fito , shi ya sanya ya zauna suka ci gaba da hira da mummy, ganin babu niyyar fito wa kuma yana da aiki a office ya sanya ya hak'ura ya koma office ya ban mummy ita kad'ai a falon. BAYAN SATI 2 Ahmad zaune yake a cikin office, wayarsa tayi k'ara , d'agawa yayi , ganin mai kiran ya sanya da kamar bazai d'aga ba amma sai ya danne ya d'aga, sallama yayi sannan ya gaishe da mai kiran , magana suka yi wadda bansan me suka ce ba , naji ya amsa da toh, sannan ya d'auki mukullin motarsa ya fita, sai da yayi tafiyar minti arba'in sannan ya k'arasa a bakin gate d'in ya faka motarsa , ya k'arasa ya k'wank'wasa, Baba mai gadi da yake zaune yana jin radio ya k'araso yana tambayar waye, jin muryar Ahmad ya sanya ya bud'e, gaisawa suka yi sannan ya masa alkhairin da ya saba yi masa sannan ya nufi cikin gidan . Ko da ya k'arasa a bakin k'ofar falon ya tsaya , sallama yayi sannan aka bashi izinin shiga , a zaune ya samesu , su ukun , daga mummyn har daddyn sai kuma LAILA , gaishesu ya fara yi , cikin yatsina su ka amsa,cikin b'acin rai daddyn LAILA ya fara magana" ashe kai Ahmad mutumin banza ne , ka dakar min yarinya kuma ka korota gida, sannan kak'i zuwa ka bada hak'uri, toh ko mu zamu zo mu baka hak'urin, mummyn LAILA ce ta chafke maganar" Alhaji ai rik'a yayi shiyasa ya yi mana haka , wallahi kawai mun kai zuciya nesa ne bamu kai kararku kotu ba ", nan dai suka gama yi masa rashin mutunci, ko da ya sanar musu zai tafi da matarsa hanawa suka yi wai sai ta gama hutawa, haka ya tashi ranshi a b'ace ya nufi bakin gate domin tafiya , kome ya tuna kuma sai ya saki murmushi mai k'ayatarwa , sallama yayi wa Baba mai gadi sannan ya tafi office. Bayan kamar kwana biyar da faruwar haka, Ahmad ya nufi gidansu , domin sanar da Mummy abinda ya faru kasancewar yana busy, ko da ya sanar mata addu'ah ta masa akan Allah ya sanya hakan mafi alkhairi ne , yaso yayi magana da Fatima amma kuma tun ranar da ya bayyana abinda ke ransa , suke wasan b'uya da ita , wani sa'ilin tana jin yazo zata gudu d'aki, ita dai Mummy abin har dariya yake bata. Fatima ce zaune a d'akinta a lokacin saura kwana , goma d'aurin aure , sosai ta fad'a cikin kogon tunani , anya zata iya zaman gidan nan kuwa, me ya sanya ma ta amincewa Mummy akan maganar auren d'anta, saboda sunyi miki halacci a rayuwa, zuciyarta ta furta hakan, so da dama tana yin yunk'urin guduwa amma sai zuciyarta ta hana ta, ta so ta sanar da k'awarta amma tunawa da ta yi mummy ta gargad'eta da gayawa kowa ya sanya ta k'yale Halima, wayarta ce ta hau kuma sakamakon rurin da take yi , d'auka tayi ganin mai kiran sai da gabanta ya fad'i , cikin sanyin murya ta yi sallama, sai da ya ja ajiyar zuciya , har sai da taji , " Fatima me na miki ne irin haka, bakya so na ne kome, kinsan yadda kike a zuciya ta da har zakiyi min wannan horon, ya fad'a cike da sanyin murya ", ita ma kanta tasan zata kyautawa , amma ya zatayi ita gaskiya tana jin tsoro sosai, haka ya dinga janta da hira har ta saki jiki dashi , sukayi hira , sai da ya tabbatar da bata da damuwa sannan ya sanar mata da cewar za'a had'a mata kayan lefe zasu je ita da hajiya ta zab'i abinda takeso amsa masa tayi , sannan suka yi sallama. Masha Allahu , a I gobe d'aurin aure mummy ta d'ibi akwatunan Fatima ta kai mata har cikin d'akinta , ta nuna mata ita dai Fatima duk kunya ta rife ta da k'yar ta gani sannan ta yi godiya , ko da dare yayi kasa bacci tayi har ladan yayi kiran sallah a kunnenta yayi , bata samu ko bacci d'aya ba saboda fargaba, a haka tayi wanka ta shirya cikin kayan da mummy ta d'inka ma ta , ta bi lafiyar gado ta kwanta saboda rashin baccin da ta samu ya sanya mata ciwon kai, aikuwa bacci ya kwasheta ba jimawa. 10:30am Alhmadulillah, karfe goma da rabi amintattun hajiya mutum takwas wad'anda suka yi mata waliccin yaran na ta , su ka sheda d'aurin auren yaran na ta, Wanda wani amintaccen limami ya d'aura . An daura auren Fatima Iliyasu da kuma Ahmad Muhammad Ahmad, akan sadaki naira dubu d'ari lakadan , sosai hajiya tayi musu alkhairi , bayan ta fad'a musu yadda angon ya tsara auren nashi , suka aminta da hakan sannan suka yi wa mummy sallama, su ka tafi. Ahmad zaune a falon mummy , wanda farin cikin ya rufe wai yau shine ya auri d'alibarsa kuma masoyiyarsa tun lokaci k'uruciyarta, yana zaune Mummy ta fito daga cikin d'akin na ta , "yauwa son ina son magana da kai ", gyara zamansa yayi yana sauraronta" a gaskiya Fatima bazata tare a gidanka ba yanzu , saboda haka na maka yadda kakeso to nima kamin yadda nakeso ", wata kuwa yaji ta d'ebeshi jingina yayi da jikin kujerar da yake kai , ya lumshe idanunsa, me yasa mummy tace haka , me yasa zata masa haka.......... HMMMMMMM TO FA , KO MEYASA MUMMY TACE HAKA, FAN'S ANYA KUWA MUMMY? YA ZA'AYI KIYI MANA HAKA KUMA?😭😭😩 Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 35__36 " Mummy me yasa , ya tambaya kamar zaiyi kuka, idanunsa sunyi jazur da su alamar b'acin rai", duk da Mummy ta tsorata da yanayin da ta ganshi amma sai ta yi kamar bata ganshi ba " Ahmad ina da dalilai masu k'arfi wanda ya sanya bazan baka Fatima ba yanzu, dalilina na farko shine Fatima k'aramar yarinya ce bata san komai game da rayuwar aure ba sannan kanaso ka had'ata da LAILA a matsayin matanka, wanda hakan babbar illah ne ga rayuwarta , sauran dalilin sai lokaci yayi zan sanar da kai ko menene, yanzu lokacin da za'a bata dama ne tayi karatunta , mu barta , hakan yafi al'ala ", shi dai tunda ta fara magana ya kasa gane inda maganarta ta dosa , ita kuwa Mummy da gayya ta fad'a masa haka amma ita kad'ai tasan dalilin da ya sanya ta hana Fatima tarewa a gidan mijinta, ganin abun bana k'are bane ya sanya ya mik'e jiki a sanyaye ya nufi hanyar falo, hajiya na ganin shi , taji tausayin shi amma ta k'yale saboda tana da wani buri na daban akan Fatiman. Toh ko da mummy ta sanarwa da Fatima shawarar da ta yanke taji dad'i duk da cewar itama bata fad'a mata asalin b'oyayyen sirrin na ta ba , wanda daga ita sai mahaliccinta suka sani. A haka satittika suka dinga wuce wa, tun Ahmad baya nuna damuwarsa akan hanashi matarsa da hajiya tayi har ya fara nunawa , akwai wata rana da yazo takanas ya cire kunya , ya fad'awa hajiya amma fir ta kafe ta nuna batasan zancen ba, gashi LAILA ma har a lokacin iyayenta sun hana ta dawo wa, wai sai ta k'ara hutawa sosai ita kuwa duniya tayi mata kyau yawo kam ba inda bata zuwa duk kuwa da aure akanta , dan bayan barinta gidan Ahmad , ta je kasashe kusan guda uku, ba tare da ya sani ba a cewar iyayenta wai yawon bud'e idanu, kuma wanne mutum ya tsayar da ita zata tsaya ta yi magana da shi har ma ta bada phone number d'inta ga mutum, dan tana bin maganar k'awayenta na cewar itama ta shiga duniya a dama da ita ta mori abun arzik'i, lokacin da ta fara wannan rayuwar ji tayi ai a da duk kuwa da mai kud'i ta aura amma a cikin kurkuku take, saboda had'uwar ta da wani guy d'an gidan wani tsohon minister, Alhaji Badamasi Ali , suna soyayya a yanzu sosai ,duk da cewar ta fad'a masa tana da aure ,amma ta yi masa k'aryar cewar mijin na ta ya saketa, rayuwa kam sosai ta sauyawa LAILA tana cin karenta babu babbaka , k'awayenta kuwa su Aliya fire abun nema ya samu suka dinga ingi zata , a cewar su ita ma kamata yayi tunda basu yi aure ba itama bazata zauna ba. A b'angaren Fatima kuwa, sosai ta maida hankalinta akan karatun ta, kasancewar sun shiga ajin Senior ne , sannan a b'angaren science take , Halima ma sosai take karatu kasancewar ta samu k'awa mai kaifin basira, zuwan Halima kusan biyar gidansu Fatima bayan da aka d'aura aurenta da Ahmad, amma tun zuwan Fatima na farko , tayi tambayar duniya mummy tace ta tambayi mijinta, kuma ta tambaye shi ya hana ta, shi ma tunda suka masa haka , sai ya ja zarensa, ita dai mummy wani sa'lin abun har dariya yake bata, shi kuwa Ahmad a nashi ganin da had'in bakin Fatima aka hana shi ita, in ba haka ba ai sai ta fad'awa Mummy cewar ita gidan mijinta take so, chab kaji fa wata rashin kunya wajen Ahmad🤪. Mummy ce ta masa magana akan dawo war LAILA , ya fad'a mata yayi magana da mahaifinta amma yace har yau bata gama hutawa ba, Allah ya kyauta abinda tace kenan ta juya ta shige d'aki ta bar shi a tsaye, shi yayi tsammanin ma zata dawo ma sa da matarsa ne kawai tunda ita LAILA iyayenta sun hana ta dawo wa, a gaskiya fa yana buk'atar matarsa , toh ko kuma kawai zuwa zai yi Mummy bata nan ya d'auke ta ai bazata dubi tsabar idonsa tace ya dawo da ita ba, kai akwai rashin kunya kuma, haka dai ya gama tsayuwarsa ya juya ya fita, ya nufi gidansa. 8 MONTHS LATER. Fatima ce ta shigo cikin falo sai nishi take yi alamar hajiya da yunwa da take addabarta, kasancewr sun fara exam , hakan ya sanya bata samu wani bacci na kirki ba, tana shiga bata ma lura da mutum ba , kawai ta shige d'akinta, tana shirin kulle k'ofa dan tana so ta shiga wanka, tasan Mummy ba ta nan amma tasan ta kusa dawo wa, dan haka take ta sauri tayi wanka, ji tayi an tura k'ofar d'akin baya tayi tai taga taga zata fad'i yayi sauri rik'eta team a jikinshi , k'ok'arin kurma ishu take yi , ganin zata tara musu jama'a ya sanya ya rufe mata bakinta da tafin hannunsa , cikin kunnenta ya fad'a ma " its me", gauron numfashi ta sauke , sanin ko waye,rungume ta tsam yayi a jikin shi , ita kuwa ba abinda takeyi sai k'walalo idanu waje, bayanta ya shiga shafa mata a hankali, yana magana" daughter d'in mummy har da ke aka had'a baki aka hanani ke ko, me yasa kika biyewa mummy, da takeson raba mu , ya fad'a yana k'ok'arin kai bakinsa ya zuwa na ta, k'ok'arin kaucewa ta shiga yi ya sanya ya rik'e ta tsam yadda baza ta iya k'wacewa ba , jin lallausan bakinsa cikin na ta ,karamar sumewa tayi , sai da ya gama jagulata iya son ransa, ganin da yayi tsayuwa na k'ok'arin gagararsu ya sanya ya jata har kan gadonta, still bakinshi na cikin na ta, ita kuwa, ido yayi wuri wuri anji sabon hannu , wata masifaffiyar kunyarsa take ji , shi kuwa sai da ya gama bidirinsa sannan ya d'aga ta ya rungume ta ajikinsa , sosai Fatima yayi enjoying na wannan al'amari da ya kasance tsakaninsu amma kuma tana bala'in jin kunyar yallab'an, k'ok'arin tashi ta shiga yi , hakan ya sanya ya k'ara matse ta , sannan ya fara magana cikin muryarsa kamar ta masu jin bacci , yana sanya mata albarka, ta dole ya sanya ta tayi alk'awarin in dai ya zo gidan Mummy zata dinga barin shi yana yin abinda ya mata yanzu, sai da ya gama , sannan ya fito har lokacin Mummy ba ta dawo ba , ya nufi motarsa ya shiga ya kunna ya bar gidan cike da nishad'i. ONE YEAR LATER. Alhamdulillah , Ahmad na zaune a falon gidansa , wayarsa tayi k'ara , a wannan lokacin iyayen LAILA sun dawo da ita , amma sun gindaya zarud'a da dama, ya kuma aminta da su kasancewar yasan shi ma abinda ya k'ulla , dan rashin mutuncin da su ka masa bazai k'yale ya tafi a banza ba, ita kuwa LAILA duk wasu al'amura da take yi a baya bata sauya ba sai ma k'aruwa da tayi , kuma tayi sababbun samari duk da tana tare da d'an gidan minister, shi kuwa Ahmad kusan kullum in dai yaje gidan Mummy ya tarar bata nan, kuma Fatima tana nan sai ya kwashi romonsa , duk da ba wani abu da yake shiga tsakaninsu amma romancing kuwa tana shansa, tun bata saba ba har ta zama gwana. D'aukar wayar yayi , sabuwar lamba ya gani, da kamar bazai d'aga ba kuma sai ya d'aga, cikin mutunci su ka gaisa da mutumin , a nan yake sanar ma sa da cewar shine wanda yasan inda kakan nin Fatima suke, ya dawo daga fataucin da ya tafi , cikin farin ciki , ya amsa masa suka gama maganar akan sati mai kamawa zasu zo ya kaisu sosai ya masa godiya , ya ajiye wayar , cikin hanzari ya d'auki mukullin mota ya nufi gidan Mummy. Ko da ya k'arasa a lokacin suna falo a zaune, yayin da Fatima take tsefewa mummy kitson da ta mata, cikin fara'a ya gaida mummy ita ma Fatima ta gaida shi ya amsa, al bishiri ya musu na cewar sati mai kamawa zasu tafi zariya domin an samu labarin dangin Fatima na wajen mahaifiyarta, Fatima da ke zaune ji tayi kamar ta tashi ta taka rawa dan murna, godiya kam ya shata ba adadi, murna ta shiga yi ji take yi kamar ta janyo satin ya zama gobe,jin kiran sallah ya sanya Mummy mik'ewa ta nufi bed room d'in ta domin yin sallah, matsawa yayi kusa da ita " me zan samu ya fad'a yana kallonta, dan kinsan sai kin bani tukwici na , rufe fuska tayi , ganin haka ya sanya ya d'auke ta chak zuwa d'akinta , sosai ya murzata son ranshi , sannan yayi wanka a ciki yayi alwala ya nufi masallaci , ita ma hakan ta kasance sai da ta yi wanka sannan tayi sallah. ONE WEEK LATER. Fatima tun da asubah ta shirya , domin a yau ne zata ga iyayen mahaifiyarta , a yau ne zata ga ko hoton mahaifiyarta ne , hajiya tayi da zama dan haka ta fito falo ta zauna, Ahmad kuwa bashi ya zo gidan ba sai karfe goma da rabi na safiya a lokacin Fatima ta k'agu , yana zuwa ba dad'ewa mummy ma ta fito suka yi Karin kumallo sannan suka dauki hanyar zariya. Sun sauka lafiya , suna isa Ahmad ya kirayi wayar mutumin, ba'afi minti goma ba sai gashi ya k'araso, suka yi musabaha da Ahmad , ya gaisa da su mummy , sannan ya shiga mota domin yi musu jagora. Sosai mummy ke kallon yadda garin ya sauya duk da ba wani dad'e wa tayi bata je ba, a k'ofar wani gida suka tsaya , mai kyau da tsari, ya sanar da su sun k'araso su fito , tabbas unguwar su Mummy ce Ahmad yq fad'a a ransa , ita ma Mummy abinda take fad'a kenan kuma ma ai k'ofar gidansu aka tsaya , jin k'ofar gidan ya tsaya yana nuna musu da su fito su shiga ga gidan nan da sauri Fatima ta k'arasa ta shiga ta bar su mummy a waje, mummy ce cike da al'ajabi ta kalli mutumin wanda sunanshi malam iro " kana nufin wannan gidan shine gidan kakanin Fatima, ta tambaya tana kallonsa", " k'warai kuwa hajiya", " toh ai nima gidan mu ne, kenan Fatima ta kasance y'ar Maimunatu kenan k'anwa a gurina", da sauri suka dubi hajiya , cikin zare idanu , sannan Ahmad yace................. HMMMMMM YA KENAN FAN'S, IDAN HAR FATIMA TA KASANCE Y'A A GURIN HAJIYA YA MAKOMAR LAILA KENAN,? SHIN KENAN DAMA MAHAIFIYAR FATIMA NA DA RAI? Please Share & Comments To be continue................ 🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 37_38 Ahmad ne ya dubi mummy cike da mamaki , sannan yace"Mummy kina tunanin Fatima itace kenan y'ar gidan goggo na maimunatu, ya tambaya ya karewa Mummy kallo da sonjin abinda zai fito daga bakinta"," Ahmad ba zamu tabbatar ba , sai mun k'arasa daga ciki , ni kawai ina yawan ganin kamaninsu amma har yau ban tabbatar ba , yanzu dai kawai mu k'arasa zai fi mana da tsayuwar da muke yi " sannan suka juya domin k'ok'arin shiga gida. A b'angaren Fatima kuwa , ko da ta shiga cikin gidan , ba kowa a tsakar gidan dan haka ta shiga k'wala sallama, wata y'ar dattijuwa ce ta fito ta amsa mata sallamar, a zuciyar Fatima kuwa jin ta take yi kamar a mafarki , lallai ta k'ara tabbatarwa da zuciyarta wad'annan ahlinta ne , saboda yadda take fusgar kama da ita, a wani b'angaren kuma tana mamakin yadda kamanin wannan dattijuwar ya kasance d'aya da Mummy , to ko dama anayin haka , tana cikin wannan zancen zucin su Mummy da Ahmad kai har ma da wanda ya musu rakiya, "ah maraba lale lale, mutanen kaduna kune da safe , sannunku da zuwa", dattijuwar ta f'ada , da sauri Ahmad ya k'arasa ya rungume kakarta sa, " kai ni sake ni karka karyani, na fasa yin auren da kai, tunda baka iya yin cefane ba " dariya suka sanya gabaki d'ayansu , cikin falon su ka shiga , sannan aka k'ara gaggaisawa, Mummy ce ke tambayar k'anwarta ta, Hajiyarsu tace mata ta shiga kasuwa, amma ba dadewa zata yi ba , taje yin cefane, da toh ta amsa tana addu'ar Allah ya sanya hasashen da ta dad'e tanayi ya kasance gaskiya amin, sosai suka yi hira , sai wajen karfe biyu sannan ta dawo daga kasuwar a gajiye, da sallama a bakinta , k'arasawa tayi k'ofar falon da sallama a bakinta, gabanta ne ya fad'i ganin yarinyar da tayi mai tsananin kama da ita, haka su ma mamaki ya kama su da ita kanta Fatima , to wacece wannan , mai kama da ita, zama tayi ta gaida su Mummy , Ahmad ya gaida ta, sannan Fatima wadda gabanta ke tsananta dukan uku uku, ita ma a b'angaren maimunatun haka ce ta kasance har yanayin muryarsu iri d'aya , sai dai ta Fatima akwai yarinta a cikinta, " yaya dama zaki zo, amma ko jiya munyi waya baki fad'a min ba , ta fad'a tana kallon yayarta ta", " wallahi k'anwa kinga wadda ta taso mu nan , ta nuna Fatima , dama ke muke jira , wani abin al'ajabi ne yake faruwa, kinsan wannan yarinyar, ta fad'a tana nuna Fatima " , girgiza kai tayi alamar a'a" zaki iya tuna d'iyar da kika haifa, wadda saboda bakin cikin abinda aka miki, baki k'ara ko da marmarin komawa garin da kika yi aure ba ballantana ki duba ta , kuma.......ai tun kafin Mummy ta k'arasa maganarta da take son yi , Maimunatu mahaifiyar Fatima ta taka har gaban Fatima ta daga ta , ta rungume tsam a jikinta, dama ba shakka wannan yarinyar tunda ta kalleta take jin wani abu a tattare da ita , dama ita ce d'iyarta mafi soyuwa a gare ta, dama tana raye to ta yaya su hajiya suka gano inda take , har su ka d'auko ta, hajiya ce ta katse mata tunani ta hanyar fad'in nasan kina da tarin tambayoyi a kanki toh yanzu kuwa zan warware miki komai", a b'angaren Fatima kuwa, wadda ke jikin mahaifiyarta ta lafe tana zubar da hawayen farin ciki da na tausayin rayuwarta a baya , dama mahaifiyarta tana raye, toh me yasa mahaifinta kafin ya rasu ya bayyana mata mahaifiyarta ta rasu, wani kuka ne ya kufce mata, bubbuga bayanta mahaifiyarta ta , ta shiga yi na tausayin tilon y'ar ta ta , sai da su ka tsagaita da kukan , sannan Mummy ta shiga bawa mahaifiyar Fatima labarin duk yadda akayi har Ahmad ya tsinci Fatima , da zamanta a wajenta , harda batun auren Fatima da Ahmad, sosai mahaifiyar Fatima tayi murna da jin haka, tayi farin ciki sosai da sosai ga yarinyar ta ta dawo bayan haka da auren wanda ya fi soyuwa a gare ta, sai da su ka gama koke kokensu sannan , su ka fara kiciniyar cin abinci, yayin da Fatima ta d'ora kanta a cinyar kakarta , kowa zuciyarsa wasai, a b'angaren Ahmad , shi yasan iya abinda yake kissimawa a ransa , sai dai kawai ya yi murmushi, a haka su ka fara cin abincin cike da walwala. A b'angaren LAILA kuwa, tana zaune saurayin da tayi kwana biyu da su ka wuce ya kirata , d'an gidan wani shahararren mai kud'i ne ,kuma k'usa a gwamnati , mai suna Aareef ya kira ta, cikin yauk'i da nuna isa ta d'aga wayar , bayan sun gama hira ya fad'a mata yana so su had'u, dama ta gaji da zaman gidan , dan haka ta amsa masa da toh , ya fad'a mata inda zasu had'u , ta shirya , ta fita bayan ta sanarwa da kukunsu abinda zata dafa,shikenan abinda yake gaban LAILA a yanzu Allah ya kyauta amin. ZARIA Bayan sun gama cin abinci aka zauna hirar bayan saduwa, mahaifiyar Fatima ce ta shiga bawa Fatima labarin yadda al'amarin ya kasance, bayan ta baro gidansu Fatima da nufin zuwa gaida mahaifinta wanda bashi da lafiya. ASALAIN YADDA ABUN YA FARU* Bayan na baro gidanku, duk da a lokacin na so tafiya da ke amma a lokacin mahaifinki yana cikin halin asiri wanda innarki Asabe ke yi masa, sai ya hana ni tafiya da ke, saboda haka bada son raina ba na hak'ura, duk da nasan halin k'uncin da zaki shiga a hannun matar mahaifinki a lokacin kina da shekara d'aya a duniya, mun fara tafiya a hanya ,mun kusa isa zariya , bamu San yadda akayi ba , mu dai sai ganin wani bak'in hayak'i ya lullub'e motar daga baya kuma bansan me ya faru ba , sai a gadon asibiti , nayi jinya sosai kasancewar , ta samu karaya ba d'aya ba a jikina , hakan ya sanya na jima ina jinya, bayan na warke akayi niyyar mai dani, amma ni ko sunan garin aka ambata sai hankalina ya tashi , nayi kamar zanyi hauka , toh kinji dalilin da ya sanya ban k'ara ko da zuwa inda kike ba. A nan ita ma Fatima ta shiga bawa labarin irin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki ba mahaifiyarta ta ta ba , hatta Mummy da kakarta sai da su ka zubarda hawaye, na tausayin halin da Fatima ta tsinci kanta a ciki , babu abinda ya gigita mahaifiyar Fatima sai labarin rasuwar malam Iliya mahaifin Fatima, tayi kuma sosai , sai da aka bata baki da nasiha sannan ta hak'ura ta dangana, a nan suka tsayar da zasu yi sati a nan , zasu kuma su bar Fatima wayen mahaifiyarta ta yi wata , duk da Ahmad bai so watan ba amma yana ganin in yayi adalci gwara ya hak'ura , haka kuwa akayi sun gama kwanakinsu, suka bar Fatima kasancewar anyi hutu dama, sosai suka dinga zaga dangi da ita aka nuna mata duk wad'anda bata sani ba , anan take tabbatar da cewa ita d'in y'ar dangi ce. A b'angaren LAILA kuwa rayuwa ta bud'e musu ita da Aareef su ke cin karensu babu babbaka, yanzu kam LAILA ta zama y'ar hannu ba inda bata zuwa, maza kowanne iri bi take yi , sai dai kawai mu mata addu'ar shiriya. ZARIA Sai da Fatima ta cika wata d'aya , sannan aka fara shirin komawarta bayan mahaifiyarta ta gyara ta sosai, domin Ahmad ya sanar mata bata tare a gidansa ba , ya fad'a mata duk yadda suka yi da Mummy, ta kira yayarta ta , ta rok'eta akan ta barwa d'anta matarsa, sosai ta mata magana ta yadda zata fuskanta, kuma ta amince da hakan , dama ita tunaninta a bari a samu dangin Fatima kuma an samu sannan dad'in dad'awa tayi hasashen akwai dangantaka da Fatima shiyasa, ko da aka sanarwa da Ahmad sosai yayi far in ciki, ya kuma shiga hidimar gyaran gidan da Fatima zata zauna kasancewar ba gida d'aya zasu zauna ba, hakan ne ya sanya Ahmad bai lura da halin da matarsa LAILA ke ciki ba , baya ma da lokacinta , harkar aikin gidan Fatima kawai yake yi. A ranar da ta cika wata d'aya tun asubah ya kama hanyar Zaria , karfe shida a k'ofar gidan ta masa, sosai ya ga ta sauya masa, tayi kyau saboda gyaran da aka mata, bayan sun gaggaisa , ya sanarwa da gwaggon na sa abinda ya kawo shi , duk da ya shaida mata tun jiya, tana son zama da d'iyarta amma kuma aure ya raba su, ita kanta Fatima bata ji dad'i da zasu rabu ba , a haka aka zuba mata kayanta a mota, suka yi sallama da kakannin na ta da mahaifiyarta, tana kuka ta shiga motar shima ya shiga ya ta da ta , bayan ya musu sallama, su ka d'auki hanya sai Kaduna............ Please Share & Comments To be continue................. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 39_40 KADUNA Ko da suka k'arasa Kaduna, gidan Mummy kai tsaye su ka wuce, Fatima jin ta take yi a wata duniya ta dabam , ko a mafarki bata tab'a kawo Mummy a matsayin wadda suka had'a dangantaka da ita ba, har su ka Shiga gidan , bata sani ba sai da Ahmad ya d'an bubbuga jikin kujerar sannan tayi firgigit ta dawo daga tunani" sai ki fito in kingama tunanin ", yayi murmushi ita ma murmushin tayi sannan ta fita. A falo su ka tarar da Mummy , mamaki ne ya kamata , lallai Ahmad yanzu sai da ya je ya d'auko ta, ai ita tama manta yau ne ranar dawowar fatiman kai yaran yanzu ma sai dai a barsu kawai, gaisheta su ka yi ta amsa , sannan ta tambayeta mutanen Zaria , nan su ka shiga hira,Mummy ce ta kalli Fatima , "am daughter ki gama shirinki goben Allah ya kaimu , zaki tare a gidanki dan haka ki gama shirya komai", da " toh , kawai ta amsa , a sanyaye sannan ta tashi "Mummy bacci zanyi ", " OK , je ki kwanta nima bari na shiga d'aki ", da toh ta amsa sannan ta nufi d'akinta , ita ma Mummy haka. Ahmad su ka bari a falo , yana ganin Mummy ta shiga d'aki yayi zuruf , kamar wani b'arawo ya nufi d'akin Fatima, a hankali ya tura k'ofar d'akin , tana kwance tana niyyar yin bacci, da yake ta juya bata ji shigowarsa ba , jin an zauna a gefen gado , tayi tsammanin ma Mummy ce, sai da k'amshin turarensa ya buge ta, sannan tayi saurin juya wa," am yallab'ai , me kake buk'ata, ta fad'a tana k'ok'arin tashi , tunawa da tayi irin kayan da ke jikinta ya sanya ta koma ta kwanta", sai da ya gama k'are mata kallo sannan ya rab'a gefenta ya kwanta, cikin zaro idanu tace " amma fa yau Mummy tana nan ", " ai na sani ba wani abu nace zanyi ba, bacci zanyi " ya fad'a yana k'ok'arin janyo ta jikin shi ," dan Allah yallab'ai Mummy fa tana nan ", " kar ki dame ni " , abinda yace kenan ya rungume ta, ita dai sai rarraba idanu take yi har bacci ya d'auke su , ko da Mummy ta fito ganin baya nan tayi tsammanin ya tafi sashensa , sai ta koma d'aki ita ma domin ta d'an matse bacci. A chan b'angare d'aya , LAILA na hanga a zaune tare da wani saurayi , hannunsu a sak'ale da juna, banji mai suke tattaunawa ba, naga dai sai dariya suke shekawa, wa'iyazubillah , kamar ba matar aure ba, " wallahi Aareef kana ji da ni, irin wannan kyauta haka " , cikin dariya shi ma yace " ai in dai zaki dinga sanya ni farin ciki ba abinda bazanyi miki ba, fatana mu kasance har abada", da k'yar su ka rabu da juna , na nufi gida, sai a yanzu take danasanin yin aure , ashe abinda su Aliya suke fad'a mata gaskiya ne , ba komai a cikin aure sai nadama , da ace a lokacin Aareef ta had'u da shi da aurenta tafi jin dad'i , a haka ta shiga gida har a lokacin bai dawo gida ba abinci taci sannan ta haura sama domin hutawa, wayar hannunta ce tayi k'ara , ganin mai kiran ya sanya tayi dariya had'i da d'agawa, " lallai matar nan kin samu duniya kin manta damu ko, aka fad'a daga chan b'angaren ," ah haba Aliya wallahi guy d'in da na had'u da shi ne ya k'ure k'arshe , amma ban manta da ke ba , so ya gida ", daga chan b'angaren Aliya ta amsa, nan su ka ci gaba da hira cikin nishad'i , ita kuma LAILA tana bawa Aliya labarin Aareef, bayan sunyi sallama , ta kishingid'a bacci kuwa yayi awon gaba da ita. A b'angaren su Fatima kuwa sosai baccin ya musu dad'i musamman ma Ahmad yaji dad'in baccin sosai, sai k'arfe kusan biyu sannan suka tashi, Ahmad ne ya riga tashi dan haka da azama ya nufi k'ofar falo Allah ya taimake shi Mummy bata falo hakan ya sanya ya tafi part d'insa , domin yin sallah. Ko da Fatima ta tashi , ganin baya nan ta ji dad'i , hakan ya sanya ta shiga toilet domin yin alwala. Ko da tayi sallah , kasa fita falo tayi gani take yi kamar mummy tasan Ahmad a tare su ka yi bacci da ita , a chan falo ganin Mummy tayi har lokacin Fatima bata fito taci abinci ba , "am baba na duba min kaga daughter ta lafiya , naga har yanzu shiru, ko gajiyar ce har yanzu", tashi yayi ya nufi k'ofar d'akin Fatima, da sallama ya shiga cikin d'akin tana zaune a bakin gadon tana ganin shi tayi zumbur ta mik'e , " ki je inji Mummynki , domin naga yanzu kin k'wace min fada ta", murmushi tayi kawai tayi hanyar waje shima ya bita, ko da su ka gama con abincin , sai ya zauna su ka dasa hira shi da Mummy, ita dai Fatima bata samu su baki kasancewar akan tariyar tata ake yin maganar , ganin abun na su yayi yawa ya sanya ta shiga d'aki ta barsu, sai wajen bayan magriba sannan ya tafi gida . Ko da ya isa gida , bai bi takan LAILA ba ya nufi d'akinsa , kasancewar yayi sallah a masallacin gidan Mummy , ana shirin yin isha'i , ya nufi masallaci, ana idarwa ya dawo ,a d'aki ya zauna , aiki yayi sosai sannan ya kwanta , da farin cikin gobe ya war haka yana tare da Fatima a gida d'aya , ji yayi kamar ya janyo goben, a haka dai ya lallab'a yayi bacci cikin nishad'i. A b'angaren LAILA ko da ta ga bai shigo ba, kuma taga dawowarsa hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba kasancewar tana charting da wani sabon saurayi da suka had'u a Instagram, sosai guy d'in ya tafi da imaninta, soyayya suke zubawa , kamar ba matar aure ba, a yanzu ma da shi suke chart, ko da yake sauran ma bata rabu da su ba , sai misalin karfe d'aya sannan ta kwanta bayan sunyi sallama.............. Please Share & Comments To be continue.......... 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 41__42 Washe gari , tun asubah ya tashi , kasancewar akwai aikin da ba'a k'arasa ba a gidan Fatima, kuma ya bar masu aiki , zasu yi aikin kwana, da hanzari ya shirya, k'arfe bakwai daidai ya fita daga gidan bayan ya sanarwa da LAILA cewar zaiyi tafiya, kafin ya dawo ta shirya masa kayansa a jaka,da murnarta ta amsa har sai da yayi mamaki, kasancewar in dai zaiyi tafiya ta dinga k'orafi kenan , yana fita daga gidan ta shiga falo , had'i da lalubar number Aareef , kasancewar ya shaida mata lallai su had'u a yau , dan haka ko da ya d'aga da murnarta ta sanar masa shima yayi farin ciki, sannan ya fad'a mata inda zasu had'u. A chan b'angare guda bayan ya k'arasa gidan ya tarar da komai ya kammala , saboda ya makara a office ya sanya bai biya gidan mummy ba sai dai ya sanar da ita amgama aikin, saboda ta shaida masa cewar za'a so jere, bayan ya gama sanar mata ne ya wuce office. A chan gidan mummy kuwa, daga ita sai mahaifiyar Fatima sai kuma aminiyarta , wato hajiya sadiya, kasancewar ta sanar da su dalilin auren d'an nata ya sanya su ma suka yadda da hakan , sannan suka sanya albarka, su da kansu suka yiwa yarinyar ta su jere na gani na fad'a, komai masha Allahu, sai san barka, wannan kenan. Fatima a zaune a d'aki, yayin da Halima k'awarta tana ta aikin lallashi, " kinga Fatima ki nutsu ki k'watarwa kanki y'anci, kinga dai yadda yanzu rayuwa take , wallahi da ni na samu ya Ahmad da wallahi yaga yadda ake tarairaya, , dan wallahi ko ita LAILAN zata yi mamaki , ki rik'e mijinki hannu biyu biyu , kinji na fad'a miki " , cikin sheshshek'ar kuka Fatima tace " Halima bazaki gane ba ina tsoron LAILA wallahi , saboda irin matan nan ne masu mugun kishi akan mijinta ba abinda bazata yi ba walllahi", " shi yasa na fad'a miki ki jajirce tunda yanzu matsayinku d'aya da ita , a da dai ke ba kowa bace ba amma a yanzu gaji y'ar uwa a gare shi kuma mata , ki sanyawa kanki salama", sosai ta mata nasiha yadda jikin Fatima yayi sanyi sosai ta yaddarwa kanta cewar zata iya , sai da ta ga ta saki jikinta sannan ta kira mai k'unshin da zata mata , dama an gyara mata kai dan haka aka fara yi mata k'unshin. Sai k'arfe biyar sannan ya samu damar barin office, gida kai tsaye ya nufa, ko da ya k'arasa tarba ta musamman ya samu daga LAILA , yayi mamaki sosai amma haka ya biye mata , ya kammala komai , yadda a b'angaren LAILA ta matsu da tafiyar Ahmad haka shi ma ya matsu da ya tafi , har bakin mota ta raka shi , sai da ta tabbatar ya bar gidan sannan ta juya ciki domin fara shiri, cike da murnarta, hmmmmn LAILA kenan. Yana k'arasawa bakin gidan, yayi horn mai gadi ya bud'e masa, ya shiga , a lokacin su Mummy sun gama jere sun tafi gida, tsayawa yayi ya jera kayansa a wardrobe sosai tsarin gidan ya burge shi , yana gamawa ya nufi gidan Mummy sakamakon kiranshi da tayi akan cewar yaje ya d'auki matarsa ,aikuwa cikin hanzari ya nufi gidan Mummy, uhmmmm sarakan azarb'ab'i kenan. Ko da ya k'arasa a lokacin angama shirya ta , ba wani dad'ewa yayi ba , mummy tace su tashi su tafi dare ya fara yi , anan fa aka ga abu domin fafur Fatima ta tubure ba inda zata je, koni sai da na mata k'walla , haka ma mummy da k'yar aka lallab'ata ta shiga motar su ka fice daga gidan. Ko a hanya ma , kukan ta cigaba da yi , yana sauraronta, duk da yana jin kukan har cikin ransa amma haka ya k'yale ta , a hanya ya tsaya ya siya gasashshiya kaza , da fresh milk sannan su ka nufi gidan . A chan b'angare guda kuwa, LAILA , kwance akan gadon hotel d'in da Aareef ya kama musu, " wallahi baby kanaji da ni irin sannan garab'asa haka, ta fad'a tana duban Aareef da ke fito wa daga cikin toilet da alama daga wanka ya fito" ai baby kad'an ma kikq gani indai ni ne", murmushi tayi, sannan ta tashi ta fad'a jikinshi daga suka cigaba da aikata abinda su ka zo , wa'iyazubillah. Ko da su ka k'arasa gidan , da kanshi ya mata jagora har cikin gidan, tana lullub'e da mayafi sai k'amshi take yi , a d'aya daga cikin kujerun ya mata masauki, sannan ya nufi cikin kicin da plate ya fito a hannunsa, ya shiga zuzzuba musu, sai da ya gama sannan ya mata umarni da ta sauka su ci tsabar yunwa ce ta sanyata dole ta sauka su ka fara ci duk da a takure take jin ta, bayan sun gama ya nuna mata d'akinta yace ta shiga tayi alwala , bayan ta gama su ka yi sallah , sannan akayi shirin bacci, toh nima daga nan na janyo k'afafuna na fice daga d'akin baki d'aya, saboda kar ace min nayi gulma, wata k'ara da Fatima ta saki ne ya haddasa ni ba shiri na fice daga gidan a miliyan, don tsabar abin tausayi. Asubah ta gari amarya da Ango. Ko da na koma lokacin komai ya wakana, Ahmad zaune a gefen gado yana aikin lallashi , ni kuwa nace tunda ka aikata kuwa sai kayi aikin lallashi , komai shi ya mata , sannan ya barta , tayi wankan tsarki, ya shimfid'a mata darduma , ya jasu sallah, albarka kuwa Fatima ta sha ta gurin Ahmad, gani yake duk duniya yafi ko wanne namiji dace , ya kurbu zumar Fatima daidai gwargwado. Ko da gari ya waye a lokacin Fatima , zazzabi ya rife ta , Ahmad na zaune yana jinya , yaji ana k'wank'wasa k'ofa a hankali ya mik'e saboda kar Fatima ta farka daga baccin wahalar da take yi , yana zuwa ya ga mai gadin Mummy ne ya bashi basket d'in abincin sannan ya juya ya tafi , shi kuma ya koma cikin falo. Sai k'arfe goma sannan ta tashi a lokacin ya sata tayi brush ya zuba musu abinci , kunun tsamiya ne sai k'osai sai farfesun layan cikin , da lallashi ya dinga bata , yayin da kunya duk ta addabeta , a haka su kayi kalaci , sannan ya bata magani su ka koma bacci. A chan b'angare d'aya LAILA sai Washe gari ta koma gida , tare da kyautar da Aareef ya mata , aikuwa suna cikin sallama, da Aareef Allah ya jefo da Dr sadeeq , kasancewar ya kira number Ahmad , baya shiga saboda ko shi kansa bai San yayi auren ba , LAILA da ke tsaye bata lura da shi ba dan haka su ka gama duk abinda zasu yi sannan ta shiga gida , da matukar mamaki a fuskarshi ya juya da mota ya bar k'ofar gidan........... Please Share & Comments To be continue............ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 ( True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ SHAFI NA 43__44 Toh haka dai Ahmad ya kwashe kwana bakwai a gidan Fatima, suna kwasar amarci da soyayya, tun Fatima najin kunya har ta saba , ta sake tare da taimakon k'awarta Halima, sosai take wayar mata da kai, aikuwa tayi amfani da shawararta ta, sai da ya kammala kwanakinsa, sannan ya koma gidan LAILA badan ya so ba. A haka dai zaman na su ya kasance cikin walwala, da soyayya, yayin da a b'angare d'aya kuma zaman LAILA da Ahmad, ba'a cewa komai, ita dai ta maida hankalinta ga samarinta yayin da a b'angare d'aya, shi kuma Ahmad yake samun wannan damar in kwanan Fatima ya zagayo, a haka su ka koma makaranta, taci gaba da karatunta, bayan ya shaidawa principal d'in makarantar akan cewar zata yi jarabawar gama secondary a aji biyun senior Hankalin Fatima ya kwanta , sai Sam barka , suna wata na hud'u da aure Allah ya a zurta , zo kuga murna lokacin da Dr ya sanar musu da wannan sakamakon , wanda a wannan lokacin suna daf da fara jarabawa,sosai ya shiga kula da Fatima cikin so da k'aunar juna , tarairaya ba wadda bata gani, ita kanta idan ta zauna godewa Allah kawai take yi , dan ganin Allah ya sauya mata rayuwarta ta da , da jin dad'i , rayuwarta dai abar sam barka da kwatance. A b'angare d'aya kuma, Mummy tawa Ahmad magana akan cewar tunda yanzu rayuwar Fatima ta sauya, kamata yayi ya kai ta k'auye domin ziyartar y'an uwanta , a kuma shaida musu duk al amarin da suka faru, sosai ya gamsu da haka, ko da ya koma ya sanarwa da Fatima abinda Mummy tace,tayi murna sosai, ya sanar mata da cewar ana gama jarabawarsu, za su tafi , harda mahaifiyarta. Fatima a zaune a falo, yayin da cikinta a lokacin ya kai wata bakwai,sallama taji anyi hakan ya sanya ta mik'e da k'yar ta nufi bakin k'ofa kasancewar tayi nauyi, da fara'arta ta bud'e k'ofa," ah aunty Aisha barka da zuwa, wallahi tun d'azu nike jiranki ,ta fad'a tana kallon mak'ofciyar ta ta , wadda suka shigo ita da wata bak'uwa, " ke dai bari Fatima wallahi Aliya ce ta tsayar da ni, kinganta nan k'awata ce sai dai ita bata ji ko kad'an," harara r wasa Aliya ta jefawa Aisha, da sannan Fatima ta matsa musu suka wuce, zuwa cikin falon, da hanzari Fatima ta wuce, domin kawo musu ruwa, Aliya ce ta dubi Aisha cikin mamaki bayan ta yi nuni da hannunta zuwa cikin wani photo,wanda Ahmad ya rungume Fatima aka musu photo, sunyi bala'in kyau sosai kamar ka sace su ," Aisha wannan fa waye, ta tambaya cike da mamaki, " lah ai mijinta ne " , cike da mamaki Aliya ta kalle ta, miji kuma ," girgiza kai tayi sannan tayi shiru, ita kad'ai ta san me take k'issimawa a ranta, Ahmad mijin LAILA shine ya zama mijin wannan yarinyar gashi ma ta lura akwai rabo a jikinta, a hanzarce ta sha ruwan da ta k'agauta ta fita ta sanarwa da LAILA halin da ake ciki, ko da suka gama bata koma gidan Aisha ba ta wuce gidan LAILA. Tun daga bakin falo take k'wallawa LAILA kira, a hanzarce LAILA ta sauko daga upstair, " haba Aliya ta yaya zaki shigo kina min ihu bayan kinsan ina chan ina hutawa ta"," dallah chan wanne irin hutu , kina hutu amma mijinki yana chan shima yana hutawa " ," bangane ba, ta fad'a tana zare idanu"," toh ki sani cewar mijinki ya k'ara aure ba tare da kinsani ba ", wata uwar ashariya ta doka " ni za'ayi was hauka lallai ma amma ta yaya aka yi kika san cewar Ahmad yayi aure kin tunanin zaiyi aure ba tare da cewar ya fad'a min ba ta fad'a cikin k'araji "," yau da idanuna ma na kalla matar Ahmad harda tsohon ciki "," tsohon ciki fa kika ce tabbas kuwa," , " Aliya rakani in ganewa idanuna domin dai na tabbatar da cewar kina min wasa ne ko kuma gaskiya kike fad'a min , cikin hanzari da tashin hankali ta nufi sama domin daukar mayafinta, sai da ta sauko sannan Aliya ta ja ta , suka nufi mota , Allah Allah LAILA take yi su isa aikuwa ko da suka k'arasa sunyi sa'a mai gadi ya jagaya masallaci , aikuwa cikin hanzari suka shiga , sallama Fatima taji ya sanya ta fito bak'uwar d'azu ta gani , gabanta ne ya fad'i ganin wadda suke tare, " aunty LAILA , ta furta da k'arfi ", LAILA ce ta zare idanu wa take shirin gani kamar wannan mayyar yarinyar nan , aikuwa d'aga idanun da zata yi taci karo da hoton Fatima tare da Ahmad, wani uban hanzari ta daka gami da finciko Fatima , wallahi sai na kashe yarinyar nan , hankali na zai huta, jibgarta ta shiga yi tun Fatima na kuka harsai da ta suma sannan suka k'yaleta , aikuwa jini ya b'alle mata ganin haka ya sanya suka yi shirin ficewa daga gidan. Ahmad wanda tun yana zaune a office , yaji gabanshi yana fad'uwa, hakan ya sanya ya baro wajen aiki ya nufi gidan Fatima , a bakin gate ya tsaya yana horn, shirin da yaji ya sanya ya fita daga motar ya nufi cikin gida , tin daga k'ofar d'akin ya fara sallama , shirun da yaji ya sanya ya shiga ciki, a kwance ya hango ta , da Sauri ya k'arasa inda take kwance, jijjigata ya fara yi , d'aga ta da yayi ne ya kalli jini na kwance a k'asa , cikin zare idanu, ya shiga girgiza ta yana kiran sunanta," Fatima ki tashi, ki tashi karki mutu , karki mutu bazan iya rayuwa in babu ke ba , ganin haka bazai kai ba ya sanya ya d'auke ta ya nufi mota cikin hanzari ya ta da mota ya nufi asibiti da ita. Su LAILA kuwa b'oyewa suka yi ganin motar Ahmad ta nufo cikin layin, sai da suka bari ya wuce sannan suka wuce , ta k'yar su ka k'arasa gida suna maida numfashi , bayan sun huta Aliya ta dubi LAILA , "amma kina ganin yarinyar nan bazata fallasamu ba kuwa, ni fa inajin tsoro wallahi ,", " ke ni fa bai dame ni ba Allah yasa ma ta mutu kowa ma ya huta ," " amma kuma idan Ahmad ya sani fa, Aliya ta fad'a ,"," wallahi ko a jikina, ki barmin komai a hannuna , haka dai su ka cigaba da maimaita abinda ya faru, yayin da LAILA zuciyarta fari fes akan abinda ya faru . A hanzarce ya k'arasa asibitin ,a lokacin Fatima ta jigata , tsananin wahala ya sanya ta farka daga sumar da tayi , suna k'arasawa aka shigar da ita d'akin emergency, ko da likitocin su ka duba , suka gane cewar nak'uda ta kama ta, nan da nan aka shiga bata taimako dan ganin ta samu ta haife abinda ke cikinta, Ahmad da ke safa da marwa , zancen zuci kawai yake yi , lallai duk wanda ya jawa matarsa wannan iftila'in wallahi bazai rabu da duk wanda yayi sanadiyyar fad'awar Fatima cikin wannan yanayin har ya sanyata nak'udar dole, a hanzarce likitan ya fito gami da cewar congratulations, bayan ya mik'a masa hannu " matarka ta haifi yara har guda biyu ma'ana twins , cikin tsananin farin ciki ya ma rasa meke masa dad'i , yama manta da damuwar da yake ciki , ko likitan bai jira ya gama magana ba ya nufi cikin d'akin............... Please Share & Comments To be continue............ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ SHAFI NA 45__46 INA BALA'IN YINKU FAN'S, SADAUKARWA GA Y'AN MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION, TARE DA KISHIYAR UWA FAN'S, 😍😍😍😍👌🏻💃🏻 A firgice ya bud'e k'ofar d'akin, a lokacin nurses sun gama gyara ta da babies d'in tsayawa yayi yana k'are musu kallo, yaran kamar ba bakwai ni ba , ganin su yake kamar a mafarki wai ace wannan duk nasa ne , kuma daga tsatson da yafi so , ba shakka yasan Allah kad'ai zai sakawa Fatima amma ba dai shi ba. Tausayin yaranne ya kama shi, saboda rashin imani , lokacin fitowarsu duniya baiyi ba amma tsabar zalunci sai da aka sanya yaransa suka sha wahala, ya k'udurtawa ransa cewar wallahi kome ake ciki sai ya gano Wanda ya yiwa matarsa haka, kuma yaso kassara masa gudan jininsa. Tunawa yayi da Mummy hakan ya sanya yayi dialing number na ta , aikuwa bugu d'aya ta d'aya ta d'aga, cikin hanzari ya fara sanar da ita abinda ya faru kama daga dukan da akayi mata , zuwa haihuwar da tayi, sosai mummy ta firgita da jin labari , sunan asibitin ya fad'a mata sannan ya kashe wayar . A nan kusa da hospital d'in ya fita ya jibgo uwar siyayya , na kayan baby da wanda mamansu zata sanya, bayan kuma akwai a gida . Ko da ya dawo ya tarar har lokacin suna bacci , cikin kulawa so da k'auna ya k'arasa kusa da Fatima da ke kwance kamar matacciya, anyi mata dressing na wajen da su LAILA su ka dake ta, sanadiyar allurar baccin da likitoci suka mata ya sanya har a time d'in bata farka ba , domin ta samu hutu. D'aya bayan d'aya ya d'auki yaran hassan da husain, kasancewar nurses d'in sun gama banbanta masa su kowa an lik'a masa sunansa a saman hularsa, Hassan ya d'auka ya masa hud'uba da mahaifin Fatima wato Iliyas ,sannan ya d'auka Hussain ya masa shima kiran sallah da hud'uba ya sanya masa sunan mahaifinsa wato Muhammad, sannan ya jera mata su a kusa da ita . Hoton yaran ya fara d'auka , sannan yayi posting through WhatsApp, Facebook, Instagram, Twitter da sauransu, aikuwa kan kace me ana ta masa murna Allah ya raya , kiran mummy ce ta shigo wayarsa , hakan y sanya cikin Sauri ya d'aga , ta sanar masa da cewar tana parking space driver ya kawo ta, aikuwa koda ya k'arasa suna tsaye ya musu jagora har zuwa cikin d'akin da suke, sosai hajiya taji dad'in ganin yarinyar ta ta da jikokinta cikin k'oshin lafiya , d'aya bayan d'aya ta d'auka , a nan ya sanar da ita sunan da ya sanya musu , taji dad'i sosai . Kafin kace kwabo asibitin ya cika da y'an barka , kowa sai sam barka , cikin y'an barkan harda aunty Aisha da Halima k'awar Fatima sai tsiya su ke mata, ita dai Fatima sai murmushi take musu, tana tuna fuskar bak'uwar aunty Aisha, tabbas itace wadda a gabanta LAILA a wanchan karon ma ta illata rayuwarta , kenan a wannan karon ma ita ta kawo LAILA cikin gidan ta kenan , sosai ta shagalta da tunani, daga baya ta yanke hukuncin bazata sanar da kowa ba , zata ajiye abun a ranta, kawai ta barsu da Allah , saboda duk wani abu da ya faru da ita ba kowa ne ya janyo mata shi ba sai KISHIYAR UWA, amma ba yadda zata yi haka zata daure. LAILA Achan b'angare guda kuwa, LAILA ta cigaba da lallab'a Aliya akan cewar ba abinda zai faru, ta kwantar da hankalinta, ko yarinyar mutuwa tayi , ba wani abu tunda ba Wanda ya gansu sosai suka shagalta da hira, LAILA sosai tayi murna dan ganin cewar tasan ma Fatima k'arshe sai mutuwa saboda a yadda suka baro ta , kallon Aliya tayi had'i da cewar" kinga Aliya ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru inshaAllahu kinji ko, kuma nasan yarinyar nan shegiya mayya k'arshe ma dai sai kabari saboda ta jigata da yawa, tana magana tana k'ok'arin bud'e status d'in da Ahmad ya d'auka , wani uban ihu da zunduma had'i da ashar ",Aliya dake zaune ta mik'e dama a firgice take saboda tsananin tsoro sai a yanzu take danasanin sanarwa da LAILA , dan batasan LAILA zata iya yin haka ba "," zo kiga", kallan fuskar wayar tayi jarirai ta gani twins duk maza, kuma kamar su d'aya da Ahmad, bata tsinke da al amarin ba sai da ta karanta comment d'in da yayi a k'asan yaran ,a tare su ka furta " mun shiga uku , dama bata mutu ba" ai a hanzarce Aliya ta had'a yanata yanata ta bar gidan cike da tsoro da tashin hankali, ta bar LAILA ita kad'ai tana zulumi , shikenan asirinsu ya tonu matukar yarinyar ta ta shi to ba makawa ita zata fara ambata , matuk'ar aka tambaye ta Wanda ya aikata mata wannan d'anyaen aikin. After 1 week Sosai Fatima ta warke sai abinda ba'a rasa ba , ranar aka sallame su , aka bar bikin sunan wani satin , yaso abar masa Fatima a gidanta amma fafur Mummy tak'i wai ita zata kula da yarinyarta da jikokinta , haka ya hak'ura badan ya so ba saboda yana buk'atar matarsa a kusa da shi amma ya k'yale, Halima kusan kullum tana gidan domin duba mai jego da yaranta , haka a b'angaren LAILA duk wannan abun da akeyi bata tab'a zuwa ganin jarirai ba , kuma ba Wanda yabi ta kanta , har da shi uban gayyar domin shi a yanzu ta lafiyar uwar yaransa yake yi. RANAR SUNA. Sosai Fatima ta samu lafiya , ranar suna yara aka rad'a musu sunansu da kowanne yaci , anyi bajinta iya bajinta , sa aka yanka da raguna kowanne yaro biyu, an ci an sha , an raba kayayyaki , mejego tayi kyau k'arshe, ina daga gefe ba sai na hango Queen nersmerh tawo da tawagar y'an moonlight writer's, su Mrs breaker ana ta k'alala idanu , an sha atamfar roba , su latifa sai bud'e idanu akeyi anaso a hango Ahmad , ni kuwa na b'uya saboda banaso su ganni , ballantana su saka ran zan samo musu abinci. Chan tawagar KISHIYAR UWA FANS su ma suka hallara, duk cikin su sis fareeda ce kawai sai sis humaira suka ci kwalliya , Dan haka na ja su gefe na zuba musu abinci , su kuwa su Queen na barsu da yunwa.🤪🤪. Toh Alhamdulillah, a haka taron suna ya watse bayan an raba gifts sosai, aka tashi , aka bar me jego da yaranta, Mummy na kula da su , sosai yaran suna wayo kai baa ce y'an wata bakwai bane ba, a haka suka cigaba da zama har sun kusa wata d'aya. A chan b'angare guda kusa , sosai Ahmad ya sanya anayi masa bincike, akan Wanda ya shigar masa gida a ranar da Fatima zata haihu, shaidar farko da aka samu a wajen mai gadin da ke kallon gidan Fatima ne, cewar LAILA ce da k'awarta ko da wannan magana ta isa ga kunnen Ahmad , ya razana sosai kuma yak'i gasgata hakan , amma yanzu ya gasgata, kuma abu kad'an yake jira ya sanya a kamo masa su , ko ya koma gida baya nuna mata damuwarsa , kuma har lokacin kowa al amarin gabansa yake yi , bai sanar da ita har a lokacin Fatima ta haihu ba, ita ma bata nuna masa ta sani ba , ganin anyi shiru da zancen ya sanya daga ita har k'awarta Aliya suka saki jiki, aka cigaba da harka da samarin bariki. A b'angaren Ahmad, tun Fatima na kwana ashirin ya matsu ta koma , tun baya fad'awa Mummy yana jin kunyarta har ya same ta ya sanar da ita , amma fir tak'i, ko da ya tuntub'i Fatima da maganar ta shaidawa Mummy tana son komawa, k'in fad'a tayi , hakan ya hassala shi , domin yana buk'atar matarsa a kusa da shi da yaransa, sai ya d'auke musu wuta ya daina zuwa, ya maida kansa gun tabbatar da zarginsa akan LAILA, ya k'yale su , domin yanaso yaga iya gudun ruwan Mummy da Fatima. AFTER 2 WEEKS. A lokacin komai ya kammala na bincike , LAILA na zaune a falo tana shan ice cream aka k'wankwasa k'ofa , cikin gadara ta tashi ta isa wajen k'ofar tana tambayar ways , shiru aka mata , cikin fusata ta bud'e me zata gani y'an sanda , sun kusa bakwai maza sai mata mutum biyu , basu yi wata wata ba suka damk'i hannunta bayan sun bata shedar kamawa, sannan aka cilla ta bayan mota sai police station , ko da su ka k'arasa, tana ta so ta musu taurin kai aikuwa , ta sha jibga koni na tausaya mata 😩, DPO ne ya kira wayar Ahmad , ya shaida masa da cewar an kama LAILA tana hannunsu a halin yanzu aikuwa , yana wajen aiki amma haka ya tattara kayan aiki ya nufi office d'in y'an sanda. Ko da ya k'arasa sosai LAILA tayi mamaki, da jin cewar wai Ahmda ya sanya a kamata , to me tayi abinda ta fara tambayar kanta kenan , amma sai ta dake, ko da aka fara fad'a mata abinda ya fara ai daskarewa tayi , bata gama dawo wa daga cikin duniyar da ta shiga ba, taji saukar takarda fara a hannunta , bud'ewa ya bata umarnin tayi , aikuwa tana bud'ewa ta zunduma ihu , " Ahmad ni zaka yiwa haka , ni zaka saka sakin ma na wulak'anci har uku ", " shi ne abinda ya kamata da a yi miki, domin dama na gaji bazan iya zama da wadda zata ga bayan iyalina ba , dama na gaji da halinki, dan haka kije na sauwak'e miki , kuka sosai ta shiga rairawa , anan Ahmad ya tafi ya barta bayan ya shaidawa DPO akan itama k'awar LAILAN a kamo ta , sannan ya juya ya tafi yabar LAILA a hannun y'an sanda, ya kuma shaida musu cewar da an gama zasu wuce kotu.............. INA GODIYA SOSAI DA NUNA K'AUNARKU GARE NI , KWANA BIYU KUNJINI SHIRU, BUSY NAKE SOSAI , FATAN ZAKU YI ENJOINING NA WANNAN PAGE D'IN , LUV U FAN'S😍😍😍😍 Please Share & Comments To be continue............. 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 47__48 Bayan ya tafi, y'an sanda biyu maza d'aya mace, suka jefa LAILA a cikin mota domin nuna musu gidan Aliya su cika umarnin DPO. Ko da suka k'arasa a lokacin Aliya na tsakar gida tana rufe d'aki kasancewar ta samu labarin an kama LAILA ya sanya ta yi sauri had'a kayanta tana k'ok'arin barin garin, ko da ta ga LAILA tare da y'an sanda , tuni hantar cikinta ta kad'a , zawo mai k'arfi ya kamata , amma basu barta tayi ba su ka jefa su a mota aka nufi office, a wannan lokacin sai da suka ci dukan tsiya , sun ma fita a hayyacinsu , sannan aka rabu da su, duk wannan al'amarin da yake faruwa , mahaifan LAILA basu sani ba haka ma Mummy bata sani ba , ya kyale su sai sun gama girbar abinda su ka shuka sannan zai saka a mik'a su kotu, saboda mutuk'ar Mummy ta sa ni shirinsa ya wargatse kwata kwata , haka ma iyayensu , hakan ya sanya yayi shiru da bakinsa. A chan b'angaren Fatima kuwa, daga ita har yaranta suna samun kulawa sosai a gurin Mummy, kuma suna kwana na talatin da biyar , hakan ya sanya ta shawarci Ahmad akan cewar Fatima tana yin arba'in za su tafi k'auye domin ganin gida tare da shaida musu al'amuran da su ka faru , sosai ya yarda da hakan shi ma addu'arsa bai wuce ya kalla wadda ta wahalar da matarsa ba , Allah kad'ai yasan hukuncin da zai d'auka akanta , ko da aka sanarwa da Fatima sosai tayi farin ciki dad'in dad'awa ta taji da mamanta za'aje , wannan kenan. A chan chaji office kuwa, su LAILA sun sauya kamanni sosai baka gane su Ba, musamman ita LAILAN wadda hutu ya ratsa fatarta , abin gwanin ban tausayi , Ahmad da kansa ya ga ya dace akan cewar ya sanar da mahaifinsu, ko ba komai ai yanzu sun gasu, wayar mahaifin LAILA ya kira ya sanar da shi , aikuwa cikin tashin hankali ya nufi office d'in , haka ma mahaifin Aliya , sosai ransu ya b'aci musamman baban LAILA a ganinsa wai an tozarta y'arsa , ganin hargagin da su ke yi masa a kai yana k'ok'arin haddasa masa ciwon kai ya sanya ya bar office d'in, ko da ya sanar da Mummy bata ji dad'i ba amma , kuma hakan da yayi shi ne daidai , ta yi addu'ar Allah ya k'ara kiyayewa. To da k'yar da sud'in goshi aka samu Ahmad ya hak'ura , akan kai su LAILA kotu , sai da aka kai ruwa rana , tin Fatima batasan me ya faru ba har ta sani , ta shaida masa ita kam ta yafe , ya k'yale su , wannan dalilin ya sanya ya k'yalesu . Ranar da suka cika kwana arba'in aka d'auki hanyar kano , da Mummy ,Ahmad, da maman Fatima , da ita kanta Fatima sai y'an biyu , ko da suka k'arasa garin da k'yar Fatima ta gane gidan na su , saboda ya tsufa ya lalace , babu duk wani kayan more rayuwa kamar da, tun daga tsayawar su mutane suka fara lek'owa , mata ta Katanga , su na ganin ikon Allah , d'aya bayan d'aya su ka dinga fitowa daga cikin motar , abin mamaki ya bani wa jama'ah ganin bak'in turawa suna shiga gidan Asabe , to ko laifi tayi , a nan tsaye mutane suna kallo su ka shigewarsu. Tsakar gida su ka tarar da wata tsohuwa ga tulin yara a gabanta , kuma da alama ba tsufan shekaru ba ne ba , kawai halin rayuwa ne , kallonsu ta shiga yi , domin ba wanda ta gane a cikinsu , daga cikin d'akin su ka jiyo maganar wata tsohuwa , " yanzu ke zainabu a haka zamu dinga zama da yunwa, ko fita bazaki yi ki barato mana abinci ba, ta fad'a tana shirin fitowa "," wallahi inna kinsan Ba bayarwa mutane zasu yi ba ,kawai mu zuba idanu mu gani, lah inna na manta kinga bak'i muka yi ", da sauri ta fito daga d'akin tana lalubar bango , Fatima da ke tsaye daskarewa tayi ganin wadda aka kira zainabu , kenan Abu ce ta koma haka, toh ina mijin na ta , duban ta ta kai ga inna Asabe innalillahi ta furta ganin yadda kamannin ta su ka sauya, ga makanta, oh rayuwa kenan duk gudunka iya ka abinda Allah ya sanya zaka tsaya toh fa anan zaka tsaya . Sosai Asabe ta shiga rud'ani jin Fatima ce ta zo har da miji da kuma yara, ai abun bai bata tsoro ba sai da taji mahaifiyar Fatima tayi mata bayanin ko ita wacece , sosai kuka ya kufce mata , " nayi nadama marar amfani , Fatima ki yafemin nasan na k'untatawa rayuwarki da yawa , amma ki yafe ni , komai da kika ga ya faru da ke nice sila, ta juya ga mahaifiyar Fatima, wadda imani ya k'ara cika zuciyarta ganin wai Asabe ce a wannan bigiren , nan ta shaida mata cewar ba komai ta yafe mata, shi kansa Ahmad Wanda ya k'udurci yi mata wulak'anci ai sai ya nemi bakin yi ya rasa. Kafin kace me gida ya cika da y'an uwa, Allah sarki har da baba Muhammadu, har kuka yayi, kuma yaji dad'in ganin Fatima da mahaifiyar Fatima, kowa mamaki ya kama shi ganin ashe dama Maimunatu bata rasu ba, sai da su ka sarara sannan , Fatima ta sulale ta nufi gidan rahina, sosai suka yi murnar ganin juna , sosai su ka yi hira sannan ta mata alkhairi , ta raka ta har bakin zaure , su ka gaisa da Ahmad sannan suka wuce........... Please Share & Comments To be continue........ 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿 🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸 (True life story) 🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸 SHAFI NA 49__50 🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟 *🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨* https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/ *```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️ بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~💞💞~~~~~~~ 'KARSHE💃🏻💃🏻 Bayan sun koma ne, baba Asabe ke zaiya ne musu duk abin da ya faru, har da abin da ya faru da zainabu , tace" yaron nan ashe ba d'an arziki bane ba , ashe da ake cewa ya samu aiki a kudu , ba aikin Allah da Annabi ne ya kai shi ba, bayan aikin da yake yi , harda neman mata, watan su d'aya ta fara fuskantar k'alubale a rayuwar aurenta, da abun yayi tsamari , haka zai shawo kayan mayensa, ya shigo ya mata dukan tsiya , ya kawo mata yan mata karuwai , da k'yar tayi haihuwa d'aya a haka sai da ta Haifa masa wad'annan yaran , ba abinci , kullum sai duka , da k'yar bayan haihuwar jaririn nan ta samu Allah ya sanya ya sake ta , gashi ba kud'in mota , haka nan mak'wafciyarta ta bata kud'i da wadanda tayi aikatau ta had'a ta nufo gida, shi yana chan yana shek'e rayuwarsa a chan, ta fad'a tana matsar hawayen namada ", da k'yar su ka lallab'ata tayi shiru, sosai su ka jajanta mata, a ranar suka koma Kaduna da zama, amma kafin su tafi sai da su ka ajiye musu alkhairai da dama , sannan Fatima ta bada kwangilar a gyara gidan na su , ta bawa baba muhammadu jari , sosai tayi rabon bajinta wa dangin na ta , ana murna da komai su ka tafi duk da sun so su kwana amma mummy tace zata zo na musamman ta kwana, sannan su ka koma Kaduna. A chan b'angare d'aya , bayan an saki LAILA da Aliya , sosai ta shiga harka da samari , ta had'u da wani saurayi , sosai rayuwarsu su ke yi, bai fada mata yana da cuta mai karya garkuwar jiki ba , sosai su ke mu'amalarsu , bata tashi farga da cewar ta kamu ba sai da ciwo matsananci ya taje wajen likita gwajin farko aka tabbatar mata da cewar ta kamu da HIV , kamar zata yi hauka su ka dawo da mummynta gida , rayuwa duk ta sauya mata , gashi mahaifinta yanzu karayar arziki ta same shi , haka dai ta k'arasa jinyar cutar ta tana karb'ar maganin gwamnati a asibiti. Fatima ta koma gidan ta , soyayya mai tsabta su ke zuba wa, kullum tana godewa Allah da ya sauya mata rayuwarta zuwa mai kyau, a yanzu ta gama karatunta tayi jarabawar k'arshe su na jiran sakamako , saboda kamfanin Ahmad da yake k'asar waje yana buk'atar cigaba ya sanya yayi tunanin cewar gwara su tafi da iyalinshi chan , domin ita ma ta cigaba da karatunta a fannin Medicine. A b'angare d'aya soyayya mai k'arfi ta ginu tsakanin doctor Sadeeq da Halima k'awar Fatima tun lokacin da ya ganta a sunan y'an biyu ya rikice mata, a yanzu dai an Sanya ranar aure sai dai fatan Allah ya sanya ayi da mu Amin. Bayan komai ya kammala , su ka fara shirin tafiya kasancewar komai , ya yi kyau game da result na Fatima , hakan ya Sanya ana i gobe zasu tafi su ka shawarci junansu akan su kai ziyara asibiti, su bada taimako aikuwa , sunyi abinda ya dace , suna k'ok'arin fita daga asibitin Fatima taji ana kiran sunanta, da sauri ta juya , wata ta gani mai kama da LAILA sai dai wannan bata kai LAILA komai ba saboda a iya sanin Fatima LAILA ta kere mata da yawa, " baki ganeni ba ko Fatima , LAILA ta fad'a tana k'arewa Fatima kallo dama shi uban gayyar wato Ahmad , Wanda ya rumgume Al hassan a kafad'arshi , yayin Al hussain yana kafad'ar Fatima , bayani sosai tayi musu sannan su ka gane , aikuwa Ahmad yayi saurin jan Fatima domin ya tsani ganin LAILA a rayuwarsa , Fatima ce ta bashi hak'uri su tsaya su fuskance ta, LAILA hak'uri ta shiga bawa Ahmad dama Fatima , ta fad'a masa duk abinda ta masa, kama daga samun cikinta har zubar da shi da ta dinga yi, sosai yaji bakin cikin abun amma daya tuna da yadda LAILA take sai ya godewa Allah da ya sanya jininsa bai fito ta tsatsonta ba , sannan ta nemi yafiyarsa, yace shi ba komai, haka ma Fatima , ta zayyane musu abinda ke damunta sosai su ka jajanta mata, su ka mata al' kairi sannan suka barta tana zubar da k'walla na abinda ta yiwa rayuwarta , da tuni yanzu ita ke da wad'annan zuk'a zuk'an yaran, haka tana ji tana gani su ka tafi su ka barta . Ana i gobe zasu tafi suka je suka yiwa Mummy sallama, dama sun je zaria sun yiwa maman Fatima sallama , da dare suka gama shirya kayansu tsab , tare da na yaransu. Washe gari da misalin k'arfe takwas na safe jirginsu ya d'aga sai England, a babban birnin London suka sauka , sosai rayuwarsu ta sauya , Fatima ta fara karatunta a babbar jami'ar k'asar, sosai shi ma Ahmad ya mai da hankalinsa kan aikinsa da kuma iyalansa , rayuwarsu gwanin ban sha'awa. Bayan wani dogon lokaci, wata mata na hanga tana ta fama da yara , " Mummy wallahi bani ne ba Al Hussain ne , wallahi ba ni na dake ta ba ,duk su ka fad'a a k'ok'arin su na kare kansu ", " to naji Fatima ta fad'a," zo nan habibty ki fad'amin waye ya dake ki, Ahmad da ke tsaye ya tambayi y'ar yarinyar wadda take ta zumb'ura baki gaba, haba Nusy ta fad'amin kinji " ," Daddy ba yaya Al Hussain ne ya dake ni ba ", " ah lallai zan gamu da shi , bari kiga , ya fara k'ok'arin tashi ya kamo su , k'ara su ka saka , suka rungume Fatima , ita ma ta rungume su , yana zuwa da Nusaiba a hannunsa aikuwa ya had'e su gabaki d'ayansu yana dariya , tare da basu sumbata kowannensu a kumatu , yana mai jin dad'i da Allah ya azurta shi da iyali masu aminci. TAMMAT BI HAMDULLAH ANAN NA KAWO K'ARSHEN LITTAFIN " KISHIYAR UWA ", KUMA INA FATAN KUNJI DAD'INSA KUMA ZAKU YI AMFANI DA ABINDA KUKA JI MAI KYAU SANNAN KU WATSAR DA WAD'ANDA BA SU DA KYAU . INA GODIYA GA Y'AN MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION, DA WAD'ANDA SUKE YIMIN EDITING NA BOOK D'IN NAN. INA GODIYA GA Y'AN KISHIYAR UWA FAN'S, ALLAH YA K'ARA MANA ZUMUNCI AMIN. JINJINAR BAN GIRMA GA SIS HUMAIRA DA SIS FAREEDA , KUNYI RAWAR GANI SOSAI ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI AMIN. NA SADAUKAR DA LITTAFINA GABAKI D'AYANSA GA , MAHAIFINA DA MAHAIFIYATA , ALLAH YA K'ARA MUKU NISAN KWANA MAI ALBARKA AMIN INA GODIYA SAI MUN SAKE HAD'UWA CIKIN WANI SABON LITTAFIN NAWA MAI SUNA " BAK'AR GABA" INA FATAN KAMAR YADDA KUKA BI WANNAN SHI MA WANCHAN A SANNU ZAKU BISHI DOMIN JIN SAK'ON DA YA ZO MUKU DA SHI . TA KU HAR KULLUM NUSAIBA MUSA SALEH SABON RUWA (NUSSAD) PLEASE SHARE AND COMMENTS 🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿