*KIBIYAR AJALI.....!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA HAFSAT 🧕🏼* *(MISS XOXO)* *©️®️ZAFAFA 5: 2021* (PAID NOVELS) BABI NA: 1 [1:1] بسم الله الرحمن الرحيم In the name of Allah, the Gracious, the Merciful. _*KAUYEN DURB’UN*_ “Mudi!Mudi! Mudikalle na dan albarka! Dan Allah duba waje ko zaka gano min keyar yarinyar nan tunda tafita siyo koko tun duhun safiya bata dawo ba har yanzu.. Oh ni salamatu wannan yarinya ko yar bankadaddiya. Fita ka nemo min ita na casata a gidan nan.” Mudi dake goge hakoran sa da gawayi yaja dogon tsaki yana mai kuskure korayen hakoran sa da sukai tamkar gansa kuka, Kafin ya mike cikin mita ya dubi mahaifiyar tasa yana sakato kwanannan daskararren tasonan hancin sa, “Gaskia gajiyalle nagaji. Ke kullum aike aike, Ni Ina zansan inda shedaniyar nan take..?” “Haba Mudi na! Yi hak’uri kaji temaka ka nemota saboda kai ma na aiketa tasiyo.” Mudi yana cuno baki gaba haka yafice bayan ya jefi mahaifiyar tasa gajiyalle da harara. Can kasan bishiyar dirimin layin su ya hangota da cincirindon yara akanta, Kowa ya tsaya yana kallon su. Ga ledar kokonta a gefe ta fashe kokan ya tsiyaye, Ta cakumo wuyan yaron wanda da alama shine ya zubar da kokon. Rantsuwa ta shiga kwarara wa tana kifa masa mari. Jikin yaron gaba d’aya rawa yake yi kuma da alama a girme ya girme mata. “Kutumelesin kan babban bala’in dirimin durbun, Walle ko dan haladu (Baban sa)ne zai zo wajen nan sai na lallasa ka. Kokon har na wazobiya ace ka barar min? Bazan yadda ba ko wajen mai gari za’aje.” Na sake duban kokon daya malalar ina tuno yadda gajiyalle zata caskalani, Zuciyata ta kara zafi na daga hannu na sake dirka masa rankwashi a kwanyar kansa ji kake, ‘Qwas..’ “Ke! Ke! Ke! Toh kizo inji gajiyalle banza bankadaddiya.” Daga jin yadda aka kirawoni bankadaddiya nasan Mudi ne, ‘Dan gajiyalle matar babana. Na dubi Mudansiru dake hawaye sha’be shabe yana shafa kuncin sa dana lallafta masa mari. Ai kuwa na kame awajen naki zuwa wajen Mudi, Cikin haka sai ga dan haladu mai rake mahaifin mudansiru, Yana tafe yana kankare raken sa, Mudansiru na ganin sa ya sake barkewa da kuka yana nuno ni, Ni kuwa na shiga harara ina watsa hannu sama domin ba yadda zan yi ba. “Kai Meya faru? Waya dake ka?” Dan haladu ya tambaya yana mai janyo mudansiru jikin sa, Na tabe baki ina mika hannu na saitin sa tamkar ance na mika, “Koko na na wazobiya ya barar min nace ya biya ni yaki biya.” Na karasa fada ina gatsine. Dan haladu yaja dogon tsaki yana mai dankarawa mudansiru Harara, “Shine ka bari mace ta maka duka? Allah ya sawwake. Ke kuma Ungo talatin domin bakici hamsin ba tunda kin lafce shi.” “Meyaci murtalar (nera ashirin) din?” “Laftar sa da ki kai. Rike kafin na maida kudi na.” Na karbi kudin ina karewa murtalar din kallo na girgiza kai, “Kai bazata karbu ba yasin ta yage da yawa.” Wafcewa dan haladu yai ya cillo min wata na karb’e ina cuno baki gaba. Dan haladu ya tisa k’eyar mudansiru gaba yana sake jibgar sa akan bari da yai na tule shi batare daya rama ba, Sauran yara dake wajen suka sa shewa suna tafa hannaye, Suka shiga yi min kirari na wanda kaf kauyen durbun kowa yasan da shi, “Woo Dijangala oganniya , Qadangaren bakin tulu, Ta gajiyalle mai yar hakiya.” Tabbas ni oga ce shysa sauran yara ke kira na oganniya. Domin duk wani fada lungu da sako nike cinye shi sannan wani lokacin har siyan fada nake na tarewa marasa k’arfi. Mudi ya cakumo hannu na ya kwace talatin din sannan ya tisa keya ta har gida. Tun a farkon layin mu na yai nasa wuri ni kuma na kama hanyar shiga gida, Ina kambama mamakin Mudi da halin satar sa, Kusan kullum hakan yakeyi Idan gajiyalle ta aike ni. Ina zuwa gajiyalle tundaga soro tana tsaye da muciya a hannun ta tana gani na ta janyo ni ta hau bugu tamkar tasamu jaka. Tana yi ina kirga duwarwatsun hannu na, Domin Inde duka ne na saba ya zama jiki sam banajin zafin sa ko kadan. “Shegiya almura da idanu zuru-zuru, Yar iskar yarinya, Mumugunciya yau kuma wani fadan kika rakito. Ina kudin dan uban ki? “Mudi ya...” Ruwan ciki na ta haye ta hau duka na tana yakushi na kamar mage. “Guzumar uba! Narantse da uban da ya haifeni zan cire miki hakora, Yau ma Sharrin zaki masa? Kinje kin kashe kudin Shine zaki sake karairakin da kike? Ban haifi barowa ba, Kece barauniya da kika tsotsa a mama. Matsa kafin na shureki ki mutu. Bankadaddiyar banza bankadaddiyar wofi.” Matsawa nai gefe ina goge hawayen bakin cikin da Mudi da gajiyalle ke kunsa min kullum, Ina ji ina gani ta fita ta sayo kosai da zafin sa sai kamshi yake yi ga kunun gidan yar asabe daya sha kayan kamshi, Mudi ya dawo suka shiga ci suna korawa da kunun hankalin su kwance. Ni kuwa cikina sai kukan yunwa yake yi. Baya na juya musu Ina tunanin yadda zanyi na samu abunda zan sanya a baki na, Domin nasan yau gaba d’aya gajiyalle bazata bani abinci ba. Tulin wanke wanken dake jira na na kalla, Mi’kewa nai dakyar Ina bubbuga konkosona na karasa wajen na duka na fara dauraye su ina tara kanzo a gefe. Cikin haka Laraba mai kaya ta shigo gidan tana doka sallama, Gaisawa sukai dasu nima na gaishe ta ta amsa tana bantarar goro, “Gajiyalle! Gajiyalle ta ubale, daga ke ba kari sai dabbobin ki da kajin ki da Mudin ki..” Gajiyalle ta dashare hakora tana mutstsuka kananun kwayar idanun ta mai dauke da hakiya. Jinta take a sama a duk lokacin da aka yi mata wannan kirarin. Ruwan dauraya ya kare sai na ebo acan gangaren bakin gari. Mikewa nai na dauki bokiti ina sosa kai na dake min kaikayi rabona da wankeshi tun sallar bara sai tsami yake yi yana tashin doyi. To yaxanyi? Babu sabulun dazan wanke dashi, Wanka ma haka nake yi ba sabulu, Shiyasa na kan dau tsawon lokaci shima kafin nayi. Ficewa nai kogin na gangare ebo ruwa, Kafata ko takauni babu domin babu halin samu... Kafin dai naje rafi na dawo nayi fa’da da yara ba adadi, Wani daga rabiya abu ya dawo kai na, Wani kuma ni na sai fadan. A haka dai na ebo ruwan ina ‘digirgire gab da gangaren unguwar kuka na sake hango cincirundan yara ana dambatuwa. A sukwane na ajiye bokitin kai na, Na dira a tsakiyar filin, Ganin yadda ake tular Nafisa yar Badamasi kansilar garin mu, Kuma ba kowa bane ke dukan ta fyace kabiru dan gidan Nanun me kyamis. Wai Kabiru Nafisa ke bari yana jibgarta. Kabiru fa? Kabiru dai abu kamar ka hure shi ya fad’i saboda rashin auki. Kankace kanzil na janyo shi na lallafta masa mari a duka kuncinan sa, Ba tare da neman ba’asin asalin fad’an ba. Yara dake gefe suka hau tafin, “Woo ke Dijangala oganniya, Ta mai gari..” Na sheke da dariya ina bin Kabiru dake hawaye da kallo, Nafisa ta matso kusa dani tana min godiya, Na sosa duddugaggen gashi kai na daya lalace saboda rashin gyara. Kafin nace, “Sai ni Dije-Dijangala-Ta mai gari.. Oganniya yar baffan ta..” Sauran yara suka hau shewa suna tafa min. Kabiru ya kwashi takalman sa ya zura a guje. Nafisa ta rik’o hannu na tana dashare hak’ora. Na cuno mitsitsin baki na gaba ina gatsina shi, Kafin na daga hannun dama na sama, Na kwararo rantsuwa na buga a zani na, “Dame zaki biya rabiyar fadan ki? Kinga dai siya nayi, Idan baki yadda ba na kira Kabiru ku karasa daga inda kuka tsaya,” Na karasa fada ina bubbuga kafa ta hade da jijjiga kwankwaso na. Nafisa tayi rau-rau da idanu tana murza hannun ta alamun dai batada abunda zata bani, Naja shewa ina shata layi a tsakanin mu da ita, “Kan babban balai, Alo tsiya alo danja, Shege ka fasa dan halak sai yanka... Kina nufin ba zaki biya ba?” “Kiyi hak’uri Dijangala, Yanzun bani da abunda zan baki...” Kukan kura nai na cakumo wuyan rigar ta ta yan gayu, Dai dai lokacin da Mudikallen Gajiyalle ya karaso wajen yana mai dakamin tsawa, “Ke dalla can zo ki wuce mu tafi gida uwar ƴan masifa kawai.” Yayi magana yana banbare hannun da na ri’ke kwalar Nafisa. “Idan na bar wajan nan ayi gunduwa-gunduwa dani, yo yama za'a yi na siyi fadanta, Tak’i biya ace na hak’ura? Hum uhm!” “Marar kunya kawai, ni kike gayawa wannan maganar? Zaki tafi gida ko sai na koya miki hankali yanzu a wajan nan.” Na shiga huci kamar wacce zaki ya biyo daga jeji na sakarwa Nafisa wuya, Ina faman murgud’a baki nace. “Wallahi bashi ne ki kaci sai kin biya ni.” Na figi bokiti na nufi gida ina masifa kai kace wani gagarumin abu aka yi min . Da zakara na fara cin karo a zaure yana kwance, Zuciyata sai zugi take, Nasa kafa na shure shi, ya tashi firrrr yana kuka ya shige cikin gidan. naja tsaki Ina galla masa harara tamkar da mutum nake, “Da karka tashi, wallahi da sai na karya maka kafa d'aya. Gaji..! Gaji..!! Gaji wai kina ina!!!?” Gajiyalle ta fito daga cikin daki hannunta ri’ke da mafici wanda alamu suka nuna fifita take yi saboda zafi. “Ya aka yi kike ta faman rafka min kira tamkar wata tsohuwar makauniya?” Na sanya bayan hannun na dinga murza ido kamar wacce na yiwa sarki karya. Na sake zukar iska cikin hanci na tare da murguda baki ina kifta ido nace. “Gajiyalle rabiyar fada nayi tsakanin Nafisan kansila da Kabiru Dan gidan mai kyamis. Nace Nafisan ta kawo ladan tariyan fadan taki. Kuma wallahi yunwa nake ji, ciki na zafi kawai yake yi kamar ana hura garwashi.” Gajiyalle ta kalli Dije sama da kasa cikin takaici, zuciyarta na tafasa kamar taje ta shake ta haka taji. Juyawa tayi ta koma cikin dakin tana mai jan tagwayen tsaki, “Dan guzumar uban ki mezan miki? Kafaffiyar yarinya bakida aiki sai fada a gari, kin gunduri kowa. Zaki cigaba da wanke wanken ko sai na lallasa ki.?” Idanuwa na suka kawo ruwa, Cikina sai neman agaji yake. Na dinga rarraba ido cike da tashin hankali, yunwa nake ji sosai tamkar naci kasa haka nake ji, saboda jiya ma haka na kwana ban samu abin da zan kai ciki na ba. Wajan bishiyar darbejiyar dake tsakiyar gidan mu na nufa tare da sanya hannaye na na rungume ina sakin wani marayan kuka. Da haka mahaifi na ya shigo daga zaure shi yana gyara hular kanshi wacce ko lankwasuwa ba tayi tsabar rashin gyara da ba'a mata. Kafadar sa ta dama saqale take da fatanya da alama daga gona yake. Shi dinma sai jera hamma yake. A hankali ya shigo bakin sa dauke da sallama. A jeme yake tafiya saboda wahala sautin jan kafarsa ce tasa na juya na dube shi ina mai shanye hawayen daya tahomin, “Baffa! Sannu da zuwa.” “Sannun ki d’iyar albarka.” Dake haka yake kira na kasancewa ta yar fari. Karasawa nai kusa dashi na karbi fatanyar na ajiye ina jera masa sannu. Kallo d’aya yai min ya zura hannu a hujajjen aljihun sa. Murtala/Nera ashirin ya d’akko da alamun ita kadai ce dama aciki. A kudindine tasha facin salatif, “Ungo diyar albarka. Jeki sayo ko awara ce a bakin yar kasuwa kici kinji.?” “Baf...” Ban karasa ba sakamakon iskar danaji tashige da gefen kunne na, Ashe Gajiyalle ce ta cika tayi fam zata fashe, “Guzumar uba! Bashari nagaji da wariyar launin fatar da kakeyi a gidan nan, Kullum dan munafurci da bakar mugunta, Ba zaka bada ishasshen kudi ayi cefanen abinci ba sai dai kaba shedaniyar yarinyar nan tasai kayan kwadayi, Idan anyi magana ka fara sakin karairakin ka na yau da gobe. Gotai gotai dakai kana tafiya a jeme, Wai ungo diyar albarka. Toh wa aka samu bata hanyar halas ba?..” Ta karasa fada tana gwada yadda Baffan mu ke tafiya. Baffan mu yai murmushi kawai yana mai saqale hular kansa akan gajeriyar katangar gidan mu data rabamu da gidan su Mari mai kitso. Tab’e baki nayi na fara kokarin wucewa don siyo abin da zan sanya aciki na kenan Gajiyalle ta danko wuya na, “Ai babu inda zaki shafaffiya da mai, Har sai kin kammala wanke wanken can da kika bari.” “Kyaleta taje zan karasa yi.” Cewar Baffan mu, Ya fada yana mai nunamin hanya dana tafi. Arcewa nai a guje ban tsaya ko ina ba sai yar kasuwa wajen masu saida kayan dadi. Rasa abunda zan siya nayi na nera ashirin. Cikin haka sai ga Nafisan kansila tana tafe tana afawa bakinta awara. Gabanta na sha na Kece da dariya ina buga zani, “Dan-dan-dan wa na kama?” Nafisa tayi rau-rau da idanu, Tana bin ko’ina da kallo ko zata samu mai tare mata. Na sake shekewa da dariya ina bubbuga k’afa ta, “Yanzun sai na caskala ki, Na casa ki. Nayi futu-futu dake kamar yadda ake casa maiwa. Dan bakin munafurci na sayi fadan kice ba zaki biya ba. Tabdijan.” Na karasa fada ina mai nannade hannun doguwar rigar atamfa ta datai du’ku-duku saboda rashin tsafta. Nafisa ta rarumo hannu na cike da tsoro, Ta samin cakulet a hannun tana murmushi, “Ungo chakulat kisha, Zan kuma sai maki kankarar madara mai sanyi ta murtala (Nera ashirin).” ___ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *MISS XOXO*👩🏽‍🦯 *KIBIYAR AJALI.....!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA HAFSAT*🧕🏼 *(MISS XOXO)* *©️®️ZAFAFA 5 2021* (PAID NOVELS) *BABI NA 2* Na karbe da sauri tare da gyara tsayuwa saboda naji banza ta fadi, dan dama Nafisa ba wani cikakken wayo ne da ita ba. Turo kallabi na nayi gaban goshi tare da kama kugu ina girgiza jiki nace mata. “Idan karya kike min wallahi duk randa na ganki sai na fasa miki hanci, kinsan ni fa bana san alkawarin yan nefa.” Cikin raunin murya Nafisa ta kwaso rantsuwa ta dire min tare da kallon cikin ido na tana cewa zata bani da gaske, sannan ne na matsa mata ta wuce nima na tafi ina dukan cinya tare da cewa. “Hahahaha hooo ni Dije..., Dijan gala ta mai gari bazan auri talaka ba... Kodan bakin cikin Gajiyalle matar uba.” Nayi dariya kamar ina kusa da wani sai dai babu kowa hasalima kowa harkar gabansa yake yi ba ruwan wani da kowa. Gaskiya chakulat akwai dadi, tunda nasa ta a baki na naji ina neman rasa harshe na, duk a zato na ma harshe na ya tsinko daga cikin baki na saboda zaki, tabbas ina son dadi gashi Allah be yo ni a gidan da ake cin mai d'an maiko-maiko ba. Kai tsaye wajan mai siyar da kan kifi naje na siyo na naira biyar, na tsaya a gurin na dangwali yaji na cinye. Daga nan naje na siyi yajin masau shima na naira biyar ya rage sauran goma, na hango rumfar mai gasa zabi, wayyo Allah garin daɗi yana nesa, miyau na ya tsinke sai kawai na girgiza kai tare da tsayawa gurin mai rogo na siyo na goma. Gefe guda na samu na zauna na cinye tas sannan na samu randar da ake zuba ruwa, duk mai bukatar amfani da ruwa indai bashi da kudin siyan wanda ake kulawa a farar leda to wannan ruwan shi zaka sha, almajirai, yan garuwa, masu walda da dai sauransu duk da shi suke amfani, haka nima naje na dauki abin diba nasha, aikuwa na saki wata katuwar gyatsa kamar naci duniya da abinda ke cikin ta. Kwanaki biyu da yin alkawarin mu nida Nafisa naji shiru bata kawo min ba, bayan na gama share tsakar gidan mu da Gajiyalle ta sanya ni nayi, na dauko mayafi na naci d'amara kamar yadda na saba yi. Da gudu na fita dan karma ta kuma sa ni wani abun daman ga wanke-wanke nan ba'a yi ba kuma idan har ta ganni sai ta ce ni zanyi, dan haka kai tsaye gidan su Nafisa naje, tana zaune a tsakar gida ita da kawayenta suna wasa, gani na da tayi yasa ta saurin mikewa ta shiga dakin Umman su. Ko tsoro banji ba haka na tsaya ina faman girgiza kugu alamun akwai tsantsar rigima a tare da ni, can sai gata ta fito rike da kankarar madara tana zuwa ta miko min jikinta yana rawa tace dani. “Dan Allah Dije kiyi hakuri, tun jiya na siyo zan kawo miki gida aka hanani fita. Gashi nan Umma ce tasa miki a cikin kankarar zobo shi yasa ma bata narke ba har yanzu.” Nan da nan na saki jiki tare da karɓa ina yake baki, har cikin rai na naji dadi dan tun kwakin da Gajiyalle ta damka min a hannu ban sake saka komai a cikin baki na ba. Na zauna wajan su muka ci gaba da wasa, amman fa nice na zama shugaba a cikin su, domin sai naga dama ma zan bari a taba kayan wasan kuma babu mai ce min dan me? Tun daga lokacin kuma muka zama kawaye sosai da Nafisa, kullum ina gidan su muna wasa har ranar da Baban su ya siyo musu talabijin ina gidan akai ta murna kansila ya siyo talabijin da janarato. ***A duk lokacin da naji mahaifina yana sauraron radio ko kuma idan muka je gidan su Nafisa wato ƴar kansilan mu muna kallo a talabijin, na kan yi mafarki da kuma hasashen nima ina ciki ana damawa dani. Babban abin da yake daure min kai shine ta ina mutanan radio suke shiga suyi magana har a jisu radau kamar yadda muke ji? Abin sake daurewar kan kuma shine, wadanda nake gani a talabijin, kuma kullum cikin shiga ta alfarma, na kan ce ko a ina suke samun kaya tsala-tsala haka? dan naga basa maimaita su idan suka sanya. Kasan cewar baki na baya iya yin shiru akan duk abin da nake son sani, Hakan yasa na ke yawan tambayar Bello yayan Nafisa cewar. “Wai dan Allah Bello ya za'a yi nima idan na girma zan iya irin wannan aiki?” Sai ya galla min harara irin ta wulakancin nan yace min. “Ke dalla gafara yiwa mutane shiru, uban waye ya gaya miki jahili ko jahila suna iya yin aikin jarida? Tafi ki bawa mutane guri keda ko fensir baki iya rikewa ba bare shiga aji d’aukar darasi.” Ya kamata inji haushi idan ya furta min haka, amman ina wata irin k'ek'eshasshiyar zuciya Allah ya bani da ba komai ke bata min rai ba, musamman irin wannan da nice na tambaya. Sai na yatsina fuska na taɓe baki ina jujjuya idanuwa, a rai na na kan ji tabbas zan iya aikin jarida koda kuwa zan riƙewa ma'aikatan abin da suke magana dashi. Idan na koma gida na kan tambayi Baba na. “Shin Baffa ya zanyi na zama ƴar jarida?” Ya kalle ni yana dariya irin tasu ta masu hangen nesa, ya gyara zama yace dani. “Ummi na zaki iya amman sai kin yi ilimi na zamani da na addini.” Lokacin ina cikin duhun kai, sai na ce dashi. “Toh Baffa a ina suke ilimin zamanin dana addinin yanzu naje na debo san rai na?” Baffa ya yi dariya cike da ganin wauta irin tawa. “Ummi na kenan, su ai ba shukawa ake yi ba, kuma ba a kasuwa ake sai dawa ba bare kije ki siyo. Karatu ne na boko dana islamiya, su zaki yi sai ki zama ƴar jarida ko likita ko lauya da sauran su.” Ina jin haka a lokacin nace da Baffa. “Kai! Aradun Allah bani ba yin karatu, kullum kana zaune cikin wani ɗaki, na taɓa ganin yadda ake zama a wani fim da muka kalla gidan kansila, wallahi Baffa bani ba zama guri gudu kamar akuya a daure.” Sai na tashi nayi tafiya ta na barshi a gurin, nasan yana tausaya min kawai babu yadda zai yi min ne, na tafi nayo faɗa ko na siya sai na samu abin da zan sawa ciki na. <<<<>>>>> <<<<<<>>>> Ranar wata laraba da safe misalin karfe takwas Kauyan mu ya samu halartar wasu mutane daga can birni, su kusan goma sha huɗu suka zo a mota, yan garin mu suka cika kofar gidan mai gari kasan cewar anan bakin suka sauka. Mune yan sahun farko a wajan kallo, mun kasa mun kuma tsare kamar wadanda aka tilastawa zama. Suka zauna akan tabarma suka korawa mai gari jawabin da yake tafe dasu akan cewa za'a zo a buɗe makarantar boko a kauyan saboda yara su samu ilimi. Tunda jama'ar kauyen mu suka ji wannan al'amarin suka fara bijirewa suna tsinewa wanda ya bada shawara da umarnin cewa azo a gina makarantar bokon. ”Gaskiya bama so, mu ba arnaye bane.” Na faɗa da karfi yadda kowa sai da ya juyo yana kallo na. ”Ke! You're very very stupid, kinga sa'anninki a cikin maganar da ake yi?” Cewar wani mutumi da yake sanye cikin kotu (suit) sanye da gilashi fari a idanunsa. Yadda naga yana hararata ya tabbatar min da cewar ransa a ɓace yake da furuci na, dan haka na yi fari da ido na tare da turo baki na gaba ina kun-kuni. Kalmar sa ta very stupid ta tsaya min a zuciya tana sani jin wani nishad'i, duk a zato na kalmomin farin ciki ne. Mai gari ya gyara zama ya kalli manyan dake zaune dashi wato mai unguwa, liman da dai sauransu yace. ”Ku duba wannan zancen nasu, ya kuke ganin za'a yi. Shin mu yadda da umarnin gwamnati ko kuwa dai a barshi ba sai an yi ba tunda ba wai sabawa mukai da irin karatun ba?” ”Beri sutufid....!” Na faɗa bayan mai gari ya kai maganar sa karshe. Duk suka buɗe baki suna kallo na da tsantsar mamaki a fuskokin su. Ni kuwa ban gane ba na ci gaba da ƙirgar duwatsu ina sawa a cikin ramin da na yi ina kirgawa. Wani saurayi da yafi kowa kankanta a cikin bakin ya taso yazo gurina tare da kafe ni da ido yana yatsina fuska tamkar yaga kashi yace. ”Ashe baki da mutunci?” ”Aramma da na yi maka me?” ”Ohhh! Bama kisan abin da kikai cewa mai gari ba ko? Saboda baki da mutunci kinga saanininki a can gurin?” Ya faɗa yana nuna da'irar da suke zaune, na gyada kai alamun a'a ban ga sa'ana ba. ”Toh ki sake magana a gurin nan ki gani, sai na turmushe wannan dogon hancin naki mai kama da yatsun kaza.” Yana gama faɗa ya koma gurinsa, ya yin da yaran gurin suka saka dariya saboda tanka min hanci da ya yi, ni kuma na dinga shafa hancin nawa dan gano ko da gaske yake yi irin yatsun kaza ne. Haushi ya kamani da na gano cewa rashin mutunci kawai ya yi min. Daga cewa very stupid kawai zai tanka min halittar da Allah ya yi min. Na sake dubansa tsab daga sama har ƙasa naga shi sam bama shi da hancin har yake tanka nawa, haushi ta ishe ni na yi kwafa dan bani da abin cewa kuma. Can kuma ana ta kai ruwa rana tsakanin jami'an birni da namu na gargajiya sun kafe kan cewa ba za'a kawo musu wata makaranta ba indai ba ta addini ba, a ganin su zuwan boko zai sanya al'adun mu da tarbiyar mu zasu lalace. Da kyar da sidin goshi Allah yasa suka yarda suka amince. Bayan bakin sun tafi mai gari yasa aka kirawo mutanan gari ya shaida musu duk abinda suka tattauna tare da sharaɗin cewa indai aka kammala gina makarantar, dole kowa zai kai ɗan sa ko ƴar sa dan a koyar da su karatu. Hmmm Ina daya daga cikin yaran da basu son makaranta, Baffa na ya kira ni ya yi ta lallashi amman fur na ce ba zan yi boko ba dan bazan je nasha wahala ba. Ci kawai nake ina shaƙewa saboda rashin ruwan da zan kora dashi, gashi sai loma nake dan kara Gajiyalle ta shigo ta kwace. Sai da naci kusan rabi na ajiye ragowar ba dan na koshi ba, a'a tausayin Baffa naji dan nasan shi zai zo yaci shima ya kwanta. Na sake lallaɓawa na leko tsakar gidan naga babu kowa sannan ta yi wuf na shige inda nake kwana tare da jigawa jikina kayan wankin Gajiyalle ta yadda ba zata gane ina ciki ba. Kamar dama ɗan lokaci Allah ya aramin sai kuwa naji muryar ta a tsakar gida tana masifa ita kadai. ”Wato wannan shegiyar yarinyar ba zata dawo gidan nan ba ko? Daman ta saba zama a titi dan haka yau idan ta kwana a can ba wani abin tashin hankali bane, ja'ira kawai da fuskarta kamar kwallon kwakwa.” Ni dai tun daga nan ban sake jin muryarta ba kasan cewar bacci mai nauyi da ya ɗauke ni. Kiran sallar farko naji an kwaro min ruwa mai wari da doyi a jikina, gashi sanyi karara dashi, na tashi a firgice ina neman hanyar fita. ”Ina zaki munafuka? Yau mai rabani dake a gidan nan sai Allah dan kuwa sai na yi miki jina-jina da fatar jikin ki.” ”Dan girman Allah Gajiyalle kiyi min rai, dan Allah karki doke ni wallahi na dena bazan sake yi miki gardama ba, kiyi hakuri.” Wata irin bulalace da ko kaɗan bata karyewa da ita Gajiyalle take doka na duk sanda taso. Da yake ba mutunci da tausayi gare ta ba, haka ta zage ta dinga labtar min jiki kamar ta samu jaka. Baffa ya fito daga cikin ɗakin sa yana son ya kwace ni amman Gajiyalle ta haɗa dashi wajan dukan tamkar wasu ya'yanta. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta rabu da mu. Baffa ya rungume ni a jikinsa yana shafar baya na, duk da bai yi magana ba a zahiri, baɗininsa a bace yake, gashi ba zai iya yi mata hukunci ba, shi kanshi wani lokacin shakkarta yake yi. ”Gobe ma na kuma saki aiki kiyi min rashin kunya, wallahi sai na dinga lallasaki a gidan nan marar kunya kawai. Kuma ki tashi kije ki debo ruwa dan ko na wanke fuska ba zaki samu ba a cikin gidan nan. Tashi nace ko nazo na sake zaneki a nan gurin.” Baffa ya sake ni da sauri, ganin haka da nayi ne yasa ni kuma fashewa da kuka ina tuna mahaifiya ta. Nasan da tana raye ba zata bari ayi min wannan wulakancin ba, duk yadda za tayi sai ta sanya ni farin ciki, ba zata zuba min ruwan dauda mai wari ba bare har ta sanya bulala a jikina, uwa akwai daɗi duk lalacewar ta tasan muhimmancin abin da ta haifa. Na sosa cikin idona zuciya ta na sake tsagargarewa na kalli Baffa sannan na dakko mayafi na wani baki da kullum shine a jiki na tamkar na gado, na yi damara tare da nufar kofar gida. Sai da nayi kamar zan ɗauki abin dibar ruwa sai kawai na ruga da gudu na bar musu gidan. ”Bazan debo ruwan ba wallahi sai dai ayi kuli-kulin tara sisi dani, an mai dani jakar gidan ko? Toh sai dai a yanka ni aradu dan na dena wahala a gidan uba na, kiji ni da kyau Gajiyalle.” Ina gama faɗa na tsaya a kofar gida, Baffa sai kira na yake amman nayi shiru dan idan na amsa mai dani zai yi ta doke ni ba iya cewa komai zai yi ba. Duk da cewa duhu ne garin masallacin kofar gidan liman ana ta assalatu da yake akwai farin wata sai ban wani ji tsoro ba, haka na fara tafiya ga sanyi saboda a jike nake iska na sake hurani naje na zauna a kofar gidan Aramma Auwalu, da yake akwai buhun-hunan taki a wajan. Zuciya ta ce take ta hasashen yadda zan yi na samu kuɗi yadda zan wulakanta Gajiyalle domin rashin su ne yasa ta mai dani tamkar wata bola abar zuba datti. Ina nan zaune har Aramma Auwalu ya fito ya wuce masallaci ba tare da na bari ya ganni ba, a gurin bacci ya kuma ɗauke ni duk da irin iskar da take shiga jiki na. — ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *MISS XOXO* *ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). * *KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASAN WANNAN SHAFIN..* *KIBIYAR AJALI.....!!!* (Sulke baya tare ta sai ta wuce..) 👑🥰❤️ *MISS XOXO🧕🏼* *WHO DOESN'T LOVE A ROMANCE NOVEL? 😉* *ITS EASY TO LOVE EACH OTHER WHEN DIFFICULTIES NEVER CROSS YOUR PATH. 🤔HOWEVER, IN REAL LIFE, ALL RELATIONSHIPS ARE TESTED AT ONE POINT OR ANOTHER. 😓❤️🥂* *BABI NA UKU* (FREE PAGE)🏌️‍♀️ •• Kukan akuyoyi da tunkiyoyi shine ya farkar dani, saboda ji nayi tamkar a tsakiyar kai na suke yin kukan. Ina bude ido naga cincirindon mutane tsaye a kai na suna kallo na kamar sunga mai hauka sabon kamu. Na tashi ina ‘kifkifta idanuwa ina kuma turo baki, kafin nayi magana sai na fara jera atishawa kusan guda shida a lokaci guda. ”Oganniya Dije yau kuma me ya hado ki da Gajiyalle har ta kore ki daga gidan?” Malam Muttaka ya yi min maganar yana ri’ke da gemun sa. Haushi ya kamani na sake daure mayafi na dake kugu na tare da cewa. ”Waya sanin mata.” ”Kina nufin ba ki yi mata komai ba ta hanaki kwanan gidan ku?” ”A gida na kwana, kawai fitowa nayi nan ko zan samu na Allah ya bani abin da zan yi karin kumallo dashi.” “Allahu Akubar Dijangala kina ganin rayuwa, toh Allah yasa ki samu.” Ganin yana shirin tafiya ba tare da ya bani ko sisi ba, yasa nayi tsalle na dire a gabansa ina mai kallon cikin ido nace. “Cewa nayi fa na Allah ya bani kuma naga ka tafi ko kai bana Allah bane?” Malam Muttaka ya yi sauran kallon mutanan dake wajan, aikuwa naga shi suke kallo, naji dadi dan nasan da kunya yace min shi ba na Allah bane yanzu a kafirta shi. “Toh ai ni Dijengala yanzu haka bani da kudi, sai dai ki bari wata rana idan Allah ya sake hada mu sai na baki.” Aljihunsa na kalla zuciya ta sam taki yadda da cewa ba kudi a ciki, na kalli mutanan wajan tare da cewa. “Allah dai ya hana babu, kuma duk wanda yace a gurin nan yana da kudi ya boye yace babu Allah yasa idan ya fara tafiya su fadi, dan Allah kuce amin.” Yara ne kawai suka amsa da amin sabanin manya da kuma matasan da suka san suna da kudin, kafin kace mene tuni sun gudu kamar wadanda suka ji karar bomb. Na kama kugu na rike ganin banyi nasara ba, gashi gari ya yi haske dan na dai Allah ya taimake ni naci dambun nan jiya da sai nafi haka wahala wlh. Hanyar gidan mu na bi da kallo, zuciya ta nason zuwa saboda ina son shiga bandaki, tsoron abinda Gajiyalle zata yi min duk da nasan ba zata kashe ni ba iya kaci ta buge ni kilama harda ciwuka. Ban samu kwarin gwiwa daga jarumar zuciya ta ba dake son na koma gida, sai dai na samu damar daga kafa nayi tafiya har zuwa gidan mai gari, inda na taki sa'a ina shiga ana gama damun koko. Na karasa wajan Ramma wato uwar gida da yake ita ke damawa, na durkusa kusa da ita ina washe baki. “Inna Ramma sannu da aiki, dame zan taya ki?” Sai naga tayi kicin-kicin da fuska da alama ta gano cewa wani abun nake son a bani, dan itama tasan hali na bana yin abu dan Allah sai dan a taimaka min. Ta sake matsar da bokitin kokon zuwa gabanta, na yi murmushi a raina nasan bazan bar gidan ba sai na samu abinda zan sakawa ciki na. Haka aka yi kuwa duk rowar Ramma a ranar sai da nasha koka da wainar rogo, ina gamawa kuma na kara gaba abu na, duk wanda ya ga yadda nake rayuwa yasan cewar ba'a gaban mahaifiyata nake ba, saboda rayuwa nake yi kai na tsaye, kuma alhamdulillahi duk iya rawar kai na da rashin nutsuwa ta babu wani fasiki da ya taba nuna zai yi lalata dani. Muna cikin wannan rayuwa aka zo aka fara gina mana makarantar boko, ana ginin nan ne na fara samun goma ashirin a wajan wani bawan Allah da yake leburanci a gurin. Allah ne ya sanya masa jin tausayi na hakan yasa yake kyautata min, dan ko abinci aka kawo musu daga gidan mai gari sai ya ajiye min idan nazo ya bani. Ranar da aka buɗe makarantar harda manyan mutane suka zazzo daga birni, da hakimi mataimakin gwamna shine yazo ya wakilci gwamnan sakamakon shi baya kasar. Munyi murna tamkar anyi mana wahayi da gidan aljanna saboda ganin manyan motoci da ganin yan gayu, gaskiya kauyanci beyi ba, komai muka yi sai an gane cewa akwai karancin wayewa a tattare da mu. Bayan an kammala komai baki suka tafi ragowar ruwa, lemuka da abincin da suka bari yara da manyan kauyen muka durfafar musu, ni da yake na iya rigima sai da na samo lemon kwalba uku da ruwa jarka biyu na kulle a gyale na sannan na kuma daurewa a jikina. Na nufi wajan kololin abinci na sunguma nayi gida da gudu harda masu biyo ni. Kai tsaye na shige bandaki ina ta faman nishi, ko Gajiyalle bata san da shigowa ta ba sai hanayi da ta jiyo ta fito tana tambayar. “Danladi lafiya?” “Dije ce ta dauke mana abinci, kuma mai gari cewa ya yi duk a rarraba.” “Almura kace sata tayo?” “A'a kwacewa tayi daga hannun Ayuba gashi nan.” Danladi ya fada harda nuna Ayuba wanda yake ta faman huci kai kace da gaske kwato musu nayi. “Toh ina take almurar yarinyar?” Gajiyalle ta tambaye su. “Ai ta shigo nan gidan da gudu.” Ayuba ya fada yana sosa cikin hancinsa. Gajiyalle ta shiga nemo ni longu-longu amman Allah besa zata duba bandaki ba, ta fito daga dakin Mudi tana cewa. “Wallahi kuka bibiya ta haura ta katanga, kunsan ta iya tsallake ta tunda ba tsaho katangar gare ta ba, kubi bayan gari kila can ta buya.” Ina jin lokacin da suka fita, na saki wata nannauyar ajiyar zuciya dan ba ƙaramin wahala nake sha ba a tsaye. Sum-sum-sum Gajiyalle ta ganni ina fitowa daga cikin ban daki, ta kasa magana sai kallo na da tayi tana rike habar ta alamar mamaki tsantsa. “Iyeeeee! Kaga almurar yarinyar nan, dama kina cikin gidan nan?” Ta fada tana sake kare min kallo irin na zaki yi bayani d'in nan, banji komai ba dab nasan ta akwai son banza, dan haka na ajiye kular dannan na kwance lemokan da ruwan ina cewa. “Yo dan Allah Gajiyalle kowa yana diba ni bazan debo na kawowa iyaye na ba?” Gajiyalle tace, “Eh mana yar albarka, ai daman nasan kina cikin bandakin, shi yasa ma banje nemanki can ba. Ah! Lallai baki sun samu dadi irin wannan hinkafa harda hanta.” Tana maganar tana luma katon hannunta cikin abincin, ta debi gurin naman ta kai bakinta tana lumshe ido. Na dinga buga mata harara ina miƙa mata jarkar lemo guda daya da ta ruwa. Amman matar nan ta sake dauke wasu ta barni da guda daya-daya tana cewa. “Haba Oganniya Dije! Nima dai yau na ‘dan dana wannan kirararin da ake yi miki. Baffanki da yayanki fa duk baza ki bayar a ajiye musu ba? Haba ai ban sanki da haɗama ba autar Baffa.” Haushi da mamakin ta suka tokare min a wuya na, matar da taki jinin taji mutane suna ce min yar fari yar autar Baffa, tana jin an fada zata fara masifa da jaraba race bani bace itama tana nan zata haifawa Baffa yara jira take yi ya maro daga talaucin da yake fama dashi. Amman yanzu dubi yadda take ta faɗa tamkar gaske, gaskiya mata makirai ne wallahi, kuma nasan da sun kare zata maida ni gidan jiya wato duka da zagi. Haka na hakura ba dan rai na yaso ba sai dan tafi karfi na, kuma a ranar bacci nayi harda minshari sai kusan karfe biyar da rabi na yamma sannan na farka, fitsari kawai naje nayi daga nan na dauki kular gidan mai gari zan mayar, na haɗu da su Ayuba dasu danladi sun dakko sanduna, gaba na ya buga na fara waige-waigen inda zan samu makami nima, can na hango gatarin malam Iro na faskare a jikin bishiyar kofar gidan sa, na ruga na dauka tare da nannaɗe siket d'in jikina nayi shirin yin dambe. “Yanzu sai ki gaya mana wa muka kama?” Cewar Danladi yana nuna ni da sandar hannunsa. “Cabdijan! Lallai ma yaron nan, kana nufin zan tsaya ku jibge ni ne sai kace wata shegiya? Wallahi tallahi duk yaron da bai fasa duka na ba nima bazan fasa buga masa wannan gatarin ba. Me nayi muku da zaku doke ni iyeee?” Ganin yadda nake buga gatarin a kasa ina kuma yin tsalle ina direwa yasa duk suka tsaya daga nesa, sun san tsab zan iya dukan su dashi dan wani lokacin ba hankali gare ni ba. “Yarinya idan ba tsoro ba ki ajiye gatarin hannunki kiga idan bamu yi miki tsinannan duka ba.” Laminu ya fad’a. “Hahahaha ahaiyeeee nanaye! Bazan ajiye ba d'in kun dauka bani da wayo ni ma, kuma ku fara gaya min abin da nayi muku dan ni nasan banyi muku uban komai ba.” Duk sai suka zagaye ni, kusan su bakwai ni kadai kamar wacce tayo musu wani abu. Na sake gyara gatari na ina nuna su idanuna a waje kamar wata zakanya. Da yake Danladi yafi cewa a doke ni hakan yasa na nufeshi da gudu da nufin kwala masa sai kuma yace kafa me naci ban baki ba, ganin haka da nayi ne yasa duk na bisu zan kwala musu suka gudu, ina huci na ce. “Da ku tsaya mana ku gani yan iska kawai, kun dauka zanji tsoran ku ne?” “Ke Dije kin fiye masifa wallahi, babu wanda baki taba fada dashi na a cikin kauyan nan, wallahi ki dena idan ba haka ba wata rana zaki sha wahala dan kowa haushinki yake ji.” Cewar malam Iro yana karbe gatarinsa da na dauka. Ko kula shi banyi ba saboda daman haushi yake bani, mokotan mu ne amman suna ji Gajiyalle zata zane ni basa zuwa su taimaka min. Na dauki kular na tafi ina ƴan wake-wake na har naje gidan mai gari na basu sannan na fito na tafi yar kasuwa dan yin hira da kuma wasa da ƴan talla. Ban koma gida ba sai kusan karfe goma har da wani abun. *BIKIN JUYA BAI* Gaba d’aya karkarar ‘Durbun’ ta dauka da shirye shiryen bikin juya bai da zata yi. Kowanne lungu da sak’o na karkarar mutane ne ne keta hidima. Bikin juya bai yana gudana ne Bayan an samu alkhairin abubuwan da aka shuka na noma. Kamar yadda mai karatu yasani hausawa sukan ce :Na duke tsohon ciniki, ‘Kowa yazo duniya kai ya taras.’. Noma na da ma'anoni da dama kasancewar irin amfanin sa a fannoni daban-daban. To amma dai a fassara mafi sauki, zamu ce, Noma wata hanyar sana'a ce domin samun abinci da kudin shiga. Haka zalika noma wata babbar hanya ce ta samun karuwar tattalin arziki da al'ummai suka raja'a akan ta. A kasar hausa ko kuwa, noma shine babbar hanya ta samun habakar tattalin arziki. Da noma ne hausawa suka fi samun kudin shiga da abinci dama kayayyakin da ake sarrafawa a masana'anta kamar tufafi da sauran su. A wajen hausawa musamman mazauna karkara noma ya zama kamar wajibi (dole) a wajen kowanne bahaushe musamman magidanci. Kusan muce ma ko wanne bahaushe ya iya noma yasan yarda ake yin shi. Noma ya kasu kaso biyu akwai: Noman rani da Noman damina. Noman rani: noma ne da ake yin shi a lokacin rani ba da damina ba. Sabanin noman rani, shi noman damina ana yin sa ne a lokacin damina. Toh *BIKIN JUYA BAI* wasu kwanaki ne da mutanen karkara ke diba suna dandalar cimar kayan dadi, Mafi akasari cimar ta kunshi nama, Na kaji, Zabbi, Talo talo, Wasu kan yanka dabbobin su ayi dabgen miya. Wannan bikin dabdalar rakashen nama dai na faruwa ne a duk shekara bayan manoma na kauyuka sun ebe/kwashe amfanin gonar su. *A* yau ranar asabar, Saboda haka naji mutan garin mu na yau asabar. Domin ni ba sani nai ba, Ba kuma damuwa nai nasani ba. Illa dai nasan yau zamu ci dadi mu godewa Allah. Domin gaba d’aya karkarar mu miyar ja zasu yi. Tun duhun safiya Gajiyalle ke safa da marwa tana lalleka zabbinta da kajin ta da yan dabbobin ta kar wani yai awun gaba dasu. Bokiti na dauka nai gangare dan ebo ruwa a rafi. Ina tafe ina wake-wake na. A haka na ebo ruwan na dawo na fada bayi. Ba sabulun wanka ba nida soso rabo na da wanka mekyau inaga sai sallar bara da baba ya bani sabulu kafin Gajiyalle ta k’wace. Don haka yau so nake nayi kyau. Na ebo tokar murhu na duddurje jiki na da ita, Na kwara ruwa. Ina fitowa na sake dakko gawayi Mudi na farfasa na durje baki na dashi. Kai na sai tsami yake. Narasa ya zanyi dashi. Ruwa na kwarara masa na tsane da dankwali na. Kayan kuncen da Adama ta bani na saka. Kamar ranar sallah haka nake ji na. Iska sai kada ni take yi. Yunwa ce kawai ke addabar ciki na. Ina ta jera hamma sai ga baffa ya dawo hannun sa rike da leda, “Baffa! Sannu da zuwa.” “Yauwa Ummi na.. Ungo mika mata ledar nan.” Leka cikin ledar nayi na hango kayan miya ne da mayi na ‘kuli sai tashin kamshi yake. Kai mata nayi ta amsa a dakile tana kallon Baffan mu a dakile, “Haka za’ai miyar lami?” “Ki dau zabo na d’aya da ya rage ai miyar dashi.” Baffan mu ya bata amsa yana mai kwanciya akan tabarmar gefe na. Baki na tsuke da tafin hannu na ina murmushi. Yau zamu sha dabgen dadi. Baffa ya bani wazobiya yace na siyo koko. A dari na fece na siyo na dawo . Ko kadan ban tsaya siyan fada ba yau. Ina kawowa Gajiyalle ta kwace ta barmin dan mitsitsi. Jiki na rawa na karba na kwankwade shi tas. Na hada wanke wanke nayi, Duk aikace-aikacen da zanyi nayi, Daga nan na fece yawo na. Gidan su Zubaida kawata naje mu kaci abincin gidan su, Daga nan muka tafi gidan yan gayu gidan su Nafisan kansila. Sunada wuta, sun kunna talabijin. Gurfane nayi Ina kallon talabijin din, Wallahi yadda mutanen ciki ke magana sunyi shiga cikin birgewa abin ya sake burge ni, Naji inama ni ce. Matar an bata wani abun karfe ta rike tana magana ta cikin sa, “Lasifika ce ko Nafisa?” Na tambayi Nafisa ina mai nuna talabijin din da yatsan hannu na. Nafisa ta daga kai tashiga kwararo min bayani. Cikin haka yayan ta Bello ya shigo ya same mu. Ya zabga min harara nima na rama hade da gatsine fuskata. Wata kwalba ya mik’awa Nafisa ta karba tana tsalle, “Dijangala! Zaki sha?” Daga kai nayi na shiga motsa baki na, Daga gani zai yi dadi tun kafin ma taba ni. Zubawa tayi a kofi ta mikomin na karba jiki na sai rawa yake yi, Ina ayyana garar dadin da yan hanji na zasu ji, Yaushe rabon duniya da ayyaraye? Karba nayi da sauri na kafa a baki na. Kurba d’aya nayi na dawo dashi, Ji kake ‘phussss..’ a fuskar Bello. A zabure ya mike zai doke ni Nafisa ta shiga tsakanin mu. Ni kuwa gaba d’aya a rude nake. Na zazzago harshe na ina ife-ife, “Wuta baki na, Wuta.. Wuta baki na. Wuta..” Gaba d’aya ji nake tamkar harshe na zai zazzago saboda tsabar yadda yake radadi, Kirji na sai suka yake. A guje na tafi wajen rijiya na tinjimo ruwa ina kwararawa baki na, Ji nake tamkar harshe na da ciki na ake bankawa wuta. Sam banbi takan Nafisa ba dake tambaya ta menene? Sai da naji sa’ida sannan na zube awajen ina fiffita baki na, Na zabgawa Nafisa harara, cikeda jin haushin lemon wutar data bani nace, “Gaskia Nafisa baki da kirki, Dan bakin munafurci shine kika bani abinda zai konamin yan hanji?” Nafisa ta kece da dariya, Na mike ina gyara damarar kan zani na, Ji nake tamkar na karairaya ta tsabar haushi. Bello ya yo kai na yana karkada min hannu, “Kede gaba d’aya baki da hankali, kidahumar banza. Dan tsabar reni lemon kazamin bakin ki kika zubamin a fuska. Ni sa’an ki ne?” “Wannan ne lemo? Walle ba dai lemo ba. Kawai dai mugunta akeson hadamun.” Bello da Nafisa mai zasuyi ba dariya ba. Suka shiga kyakyatawa. Na murtuke fuska ina gatsine baki. Nafisa ta ri’ko hannu na tana murmushi, “Be lemon wuta bane kawata. Lemo ne na sha, Sunan sa coke. Tsaya kiga ma na sha.” Tana gama fada ta dauki kwalbar ta kafa a bakinta Sai da ta shanye tas sannan ta ajiye. Ganin dagske ta shanye hakan yasa na danji sanyi a rai na. Murmushi na mayar mata nima na dashare hakora na, “Ayyo! Lemon yan gayu ne dai. To ai kuwa dai zanba su Larai labarin lemon nan. Tab.” Bello yai tsaki kafin ya sakar min rankwashi a kwanyar kai na, “Mugu azzalumi..” Na fada ina sosa wajen. Har ya fara tafiya ya juyo yana kallo na, “Me kika ce?” “Ca nai adawo Lapia” Na karasa fada hade da mai zunde, ya fice ba Tare da yace komai ba. Nafisa taja hannu na muka koma cikin parlorn su. Maman su ta zuba mana abinci fal da naman kaji. Abincin juya ban su na yan gayu. Muka hadu da sauran k’awayen Nafisa muka cinye tas . Suma mukajajje gidajen su muka ci muka koshi, Daga nan naja zugar yara k’awaye na muka tafi gidan mu. Muna tafe muna neman magana. Kafata tayi busu busu ba silipas. “Oganniya ta Gajiyalle me yar hakiya.” Cewar lantana yar gidan rumasa’u me kitso. Na kece da dariya kafin na buga tsakiyar zani na na ja guda, “Sai ni Dijangala ta mai gari yar Baffan ta..” “Gajiyalle ai ba babar ki bace ko? Ita bak’ace bata da kyau.” Nafisa ta tambaye ni tana cigaba da irga duwatsun hannun ta. Na tab’e baki kafin na bata amsa, “Yarinya Dagaske ba ita ta haife ni ba. Ni baba ta ta mutu dan kiji tun ina karama. Kuma ita kyakkyawa ce yarinya.” Haka dai mu kai ta shirmen mu akan hanya har muka Karasa gidan mu. A tsakar gidan mu zugar k’awaye na suka zauna muka shiga yin yar carafke, Na lek’a gefen murhu inda Gajiyalle ke girki, cikin sa’a ta kammala tana karkasa shi. “A zuba mana da kawaye na.” Harara ta dankara min ta cigaba da karkasa abincin. Komawa nai cikin yara muka shiga hirar mu. Can Gajiyalle ta callarawa sunana kira. Na mike a sukwane har ina bal da robar ruwan dan akuyan Gajiyalle. Ina zuwa ta mikamin wani kwano cike da abinci yasha nama. Yawuna yatsinke, kunnuwa na sai rawar dadi suke. “Ungo.” Wayyo Allah na dadi! Yanzu duk namu ne wannan? Nama nasha nasha akai. Gudun kar nayi katobara Hakan yasa na sake tambayar ta namu ne da kawaye na. “Na mu duka ne?” Gajiyalle ta daga kai tana mai cigaba da kasa abincin gaban ta.A sukwane na karasa wajen kawaye na da kwanon. Muka hau ci sai da muka cinye tatas muka gyatse Sannan kowacce tatafi gidan su. Haba tsabar yadda yau naci na koshi kasa tashi nai nabi lafiyar tabarmar da nake zaune na kwanta sai bacci. Cikin daddadan baccin da yai awun gaba da ni na jiyo wani azababban dundu da aka sakarwa gadon baya na tamkar zai burma saboda yadda aka duma masa dundu. A firgice Na mike Ina sosa bayan. Ina bud’a idanu na na hango Gajiyalle da Mudi, Sai huci take, “Dan guzumar uban ki ina abincin dana mika miki ki bawa Mudi?” Idanuna suka kawo ruwa . Wane abinci taban na Mudi? Girgiza kai nayi Saboda hakikanin gaskiya kenan ni bani ta bawa abincin Mudi ba, “Ba ni .” “Zaki shiru ko sai na lakada miki na jiki. Yanzu dai dan guzumar uban ki ina abincin yake.?” “Wallahi Gajiyalle bani kika bawa abincin Mudi ba. Iya abinci na da kawaye na kawai kika bani. Nace miki na mu duka ne? Ki Kai shiru alamun Eh. Amman bayan haka baki bani abincin Mudi ba” “Dan guzumar uban ki. Ca ki kai na Mudika ne? Na daga miki kai. Uban wa zan zubawa abinci haka Idan ba Mudikalle naba?” Na sake girgixa kai cikin hakikanin gaskia nace, “Sai da na tambaya nace na mu duka ne? Kika daga kai alamun Eh” Kukan kura Gajiyalle Tai ta shak’o wuya na tana huci. “Amma wannan yarinya ko yar bankadaddiya. Abincin Mudikallen zan baki ku cinye keda yuyar kawayen ki? Nace abincin Mudikallen? Zaki magana ko sai na lakada miki na jaki?” Ruwan ciki na ta hau bugu tana yakushi na. Takaici da zugin da ciki na yake yasa na fara kuka mai kara, Cikin haka ‘Dara’ifa makociyar mu ta shigo da alamun kuka na ne ya kawota. Dakyar ta banbare Gajiyalle daga jiki na, “Haba Gaji! Haba! Kashe ta zaki yi? Yarinya kamar wannen fisabilillahi ya za’ai ki dinga hayewa ruwan cikin ta kina duka? Tsakani fa da Allah. Shi fa da na kowa ne Gajiyalle, Idan ka kyautata wa dan wani sai a kyautatawa naka kai ma. Marainiya c...” “Ishiru dakata, dakata min ‘Dara’ifa, kefa dama akwai ki da shisshigi da gutsiri tsoma, Ina ruwan ki? Dan tsabar tsagwaran gulma irin ta ki menene na shiga abinda babu ruwan ki? Shysa akeyi dake a garin nan.. Kinsan meta min ne da zakizo kina min wa’azi?” Dara’ifa ta girgiza kai cikin takaici tace, “Koma meta miki Gaji sai ki hak’uri, Amma akan me zaki dinga dukan ta kamar kinsamu katako? ‘Ya mace kamar wannan da zaki kyautata mata bafa kisan inda rana zata fa’di ba. Shi maraya kokarin kyautata masa kake ba kuntata masa ba.” “Yau za’ai tsallen badake. Abincin Mudikalle na fa mumugunciyar yarinyar nan ta kaiwa kawayenta suka cinye. Tafa tambaye ni nasa ne? Na daga mata kai alamun eh amman yarinyar nan dake ba tsoron Allah a ranta sai tai mirsisi takai musu suka cinye.” Ina daga kwance na mike dakyar saboda yadda jiki na ke tsamin jibgar da tamin. “Walle ba haka bane, Kina ji Dara’ifa? Sai dana tambaye ta nace na mu duka ne? Ni da kawaye na nake nufi. Saboda tun farko sai dana ce mata tazuba mana ni da su. Bayan ta kirani ta mikomin abincin na tambayeta fa ta daga kai alamun eh” Gajiyalle taja tsaki tana bubbuga hannu a katangar gidan mu, Har gefen dake lilo ya zubo a kasa. “Guzuma. Yarinyar nan ko yar makaryaciya. Aina akai haka? Na mudika ne? Kika tambaye ni? Na daga kai alamun Eh. Dara’ifa ki ky’ale ni na kacaccala yarinyar nan” ‘Dara’ifa ta shiga tsakanin mu tana janye Gajiyalle tana bata hak’uri, “Toh Kiyi hak’uri akasi aka samu. Ke dije ita Gajiyalle na nufin abincin Mudi. (Na Mudika) ke kuma Gajiyalle, Dije na tambayar ki ne (Na mu duka?) ma’ana nasu itafa kawayen ta? To adai Yi hak’uri . Abinci dai anci sai kasayarwar sa. Bazai dawo ba, Duka bashi bane. Ke kuma dije Idan kinyi laifi Ki zama mai bada hak’uri kinji” Daga kai nayi alamun Toh, haka Dara’ifa tagama maganar ta ta tafi. Tana fita Gajiyalle ta hau rankwashi na ji kake ‘qwas’ gwaf’ Kif’ duk a kwanyar kai na. Da alamun Dara’ifa ta jiyo. Ai kuwa ta sake yo sallama ta kirawo ni wai zan kai mata nik’a. Arcewa nai a guje har yin karo da dan akuyar Mudi. Rike hannu na Dara’ifa tayi muka shiga gidan ta, Koina yasha siminti abun sha’awa wallahi kamar na lashe shi. Zama nayi a gefen kitchen kofar dakin ta Ita kuma ta shiga ciki, “Dara’ifa ina ku’din aiken?” “Ki hutawar ki Dije babu abunda zaki siyo min, Kawai kiran ki dai nayi naga yadda take nadar ki.” Dashe baki nayi kawai na cigaba da shasshafa simintin dake malale a k’ofar dakin. Dara’ifa nada kirki, Ita ba tsohuwa bace irin Gajiyalle, Amarya ce amma bata taba haihuwa ba. Daga kauyen alfindi mijinta ya aurota, Shine dan karkarar mu. Sam batada gulma ko biyewa mata n auren karkarar mu dake yawon gidajen juna suna gulma, Ita kullum tana gida tana harkokin gabanta bata shiga lamuran su. Shiyasa suka tsane ta, Kullum cikin yi da ita suke, Wai tacika girman kai, Takance ba girman kai bane gudun zucia ne. Ina nan zaune har aka kira sallah, Dara’ifa ta fito tayi alwala tayi sallar ta, Inata bin yadda take Sallah gwanin sha’awa. Ta mike ta cire hijabin jikin ta, “Dije ta shi kiyi alwala kiyi sallah.” Baki na na bude kafin na rufe shi Ina mai jinjina kai na, “Ban iya ba. Daga alwalar har sallar.” “Wai har yanzu bakya sallah dije? Shin ba’a saki a Islamiyya bane ko allo?” Na daga kai hade da kafad’a ko ajiki na. “Tashi kiyi alwala mu gani.” Mikewa nai dakyar na kamfanci ruwa a buta tamkar yadda naga Baffa yana yi wani lokacin. Na wanke hannu na da k’afa sau dai dai sannan na kuskure baki na na zuba ruwa a gashi na, Na gantsare na mike zan bar wajen Dara’ifa ta hanani, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Koma ki zauna, Haka ake alwalar? Shikenan har kin kammala? Oh ni Dara’ifa!” “Shin dije, Gaji bata koya miki? Anya kin iya karatun sallah ma kuwa?” Na tabe baki kafin nace “Itama fa battai, Yasin seta kwan nawa batai ba. Yo alhaki akanta tunda bata koyan.” Dara’ifa ta girgiza kai kawai, Ta sake debo ishasshen ruwa a buta ta mikamin, Na karba na koma na zauna. Ahankali take koyamin tana min bayani tamkar malama da daliba, Ba lefi na fara ganewa gaskiya. Daga nan tace nayi sallah, Nan ma ban iya ba, Na dudduka kawai na mike na jefar da hijabin data bani a gefe, Nan ma sai data sake koyamin yadda zan dinga yi. Na gane wani abun, Wani kuma ban gane ba. Mudi ne ya leko yace gaji tace naje, Na mike dakyar banso zan koma gida ba har ga Allah. Saboda sam Dara’ifa bata da fada ko hantara irin na Gaji. Har na Kai kofa zan fita ta yafito ni da hannu na koma. Wazobiya ta mikomin hade da radamin a kunne, “Ki sai sabulun wanka kinji? Sai da safe nagode.” “Nima nagode Dara’ifa. Allah dai ya biya ki da alkhairi.” Sallama mu kaiwa juna na tafi gidan mu zuciya ta sam ba dadi. Ji nake dama Dara’ifa ce babata dana more. Take ummata ta fadomin arai na. Uwa mai dadi, Da ace tana raye nasan bazan taba tagayyara kmar haka ba. Wasu zafafan hawaye ne suka zubomin, Cikin sarkakiyar murya nace, “Allah ka jik’an Umma tah..!” Tun daga zauren gidan mu nake jiyo sautin suratan Innarajo mahaifiyar Balki K’awata itada Gajiyalle. Sam innarajo bata sona batasan kawancen da muke da Balki ‘yarta. Shiyasa nima na dena shiga harkar Balkin. Wai ashe barar (kudin aure) Balkin aka kawo. Mamman mai shayi ne zai aure ta. Gajiyalle sai guda take tana yada magana. “Ai wallahi innarajo Gwara ka aurar da yar ka tun tana karama kana iya tankwarata. Yanzu ba gashi ba xatai auren ta tabar yuyar su hannu na mai kafada( Wai ni)” Ta karasa fada tana mun zunde da baki. Yi nayi tamkar Bansan suna tsakar gidan ba na kauda kai na gefe. Band’aki na shige na rage ciki na kafin na fito nai ficewata yar kasuwa siyo sabulu da kayan k’walam da wazobiyar (hamsin/50 Naira) da Dara’ifa ta bani. • ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *KIBIYAR AJALI.....!!!!* _(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)_ 🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA HAFSAT* 🧕🏼 *(MISS XOXO)* *©️®️ZAFAFA 5 2021* (NA KUDI NE! NEMI:+234 903 318 1070 KO +234 903 234 5899 DAN MALLAKAR NA KI!) *BABI NA 4* (Free page) *Cikin* kankanin lokaci aka fara kawo malamai daga cikin birni wadanda zasu koyar da mutanan karkarar mu karatun boko, a cewar mai gari harda na addini duk za'a koyar kuma kyauta, abinda kawai ake bukata shine iyaye su yarda su dinga tura yaransu makaranta. Yaran mai gari dana mai unguwa da liman da sauran masu faɗa aji a kyauyan mu su aka fara sakawa a makarantar saboda ma kar wasu iyayen sunce gashi gashi, su ance su kai yara makaranta amman wadanda suka ce ayi su basu saka nasu can ba, hakan yasa suka fara yiwa tufkar hanci. Tun daga kan su kuma ba'a kara kai wasu ba, ba wai rashin yaran zuwa makarantar ne babu ba. A'a tsabar su yan garin basu yarda da karatun bokon ba shine ya hana su kai yaran su. Ganin haka ne yasa hakimi da kanshi ya yi magana cewar dole ne kowa ya kai dansa makaranta tun daga kan dan shekara uku zuwa goma sha biyar maza da mata. Amman iyaye mata suka ki barin yaransu mata suyi, a cewar su babu abinda ya kamaci suyi irin talla dan su tara abin da za'a siya musu lokacin aure. Ni kuwa da dama bani da wani mafadi idan ba Baffa na ba, kuma shi ɗin ma ba wani tsoro yake bani ba. Sai ya zamana babu mai cewa Dije shirya na kai ki makaranta, ko kuma Dije zoki je makaranta. Ranar da aka fara yin karatu naje makarantar amman ba wai shiga nayi ba, lekawa nayi ta taga na hangi su Abu yar gidan mai unguwa zaune a kan benci ta kurawa malamar ido kamar zata hadiye ta, na kwashe da dariya tare da sake yin ɗage yadda zan dinga hangowa sosai nace. “Kai Abu hekace kin samu talabijin sai kallon matar can kike yi.” A dai dai lokacin malamar ta juyo da yake rubutu take yi a jikin allo. Ita kam Abu turo baki tayi ko bata fada ba nasan bacin rai ne a zuciyar ta dan itama ba son makarantar take yi ba. Malamar ta saki murmushi cike da tsantsar kulawa ta kalle ni tace. “Zagayo ki shigo kema.” Cikin dafe kirji da zaro ido duk a lokaci guda nace mata. “Wa?” Malamar tace, “Ke mana, shigo ki zauna a yi karatun dake.” Budar baki na sai cewa nayi. “Allah sitiri buƙi, inci tsohowar....” Ban kai ga karasawa ba naji wani irin abu ya sauka a tsakiyar kai na, babu arziki na yi kasa ina kuka ina ihun a kawo min dauki. Kafafuwa da na gani sanye cikin wani cover sheo shine ya tabbatar min da cewar wani ne ya yi min abu. A hankali na dinga dago ido ina karewa jikin kallo, kafin daga bisani na sauke idanuwa na biyu na dora su kan fuskar shi, gabana ya buga ras! Saboda tsananin tsoro da naji. Sam fuskarshi babu annuri bare kayi tsammanin fara'a a kai, ya kalle ni fuska a murtuke tare da cewa. “Bar nan gurin ko na babbalaki.” Sam ban san daga ina furucin ya fito ba, dan ban maji kalmar a baki na ba bare nace ni nayi, kawai saukar furucin nayi a cikin kunnuwa ne ina cewa. “Saboda me?!” “Ohh tambaya ta kike yi?” Cike da gasgata tambayar da ya yi min nace, “Eh walle talle ban gane mekake nuhi da cewa na bar gurin ba.” Bacin rai ya kuma ziyartar zuciyar shi, ya dan matsa kusa da bishiyar darbejiyar dake bayan shi, ganin yana niyar tsinko bulala yasa nayi saurin rugawa da gudu tare da yi masa gwalo. Shi kuwa gabaki d'aya haushin yan kauyan namu yake yi, tunda yazo yake faman korar masu zuwa gulma wato iri na kenan, bamu shiga anyi da muba, gashi mun hana wadanda ake koyawa suyi cikin nutsuwa. Malamar ta leko ta taga tana yiwa malamin magana cikin dariya. “Malam Auwal kana ta fama kaima.” Yaja dan karamin tsaki, “Ni anya zamu shirya da yan kauyan nan kuwa? Wallahi malama Mardiyya baki ji yadda rai na yake baci ba, gashi sam basu da tarbiya mazan su da matan su.” Dariya malama Mardiyya tayi. “Wallahi kuwa malam Auwal sai dai kawai muyi hakuri tunda Allah ya kaddara cewa nan zamu dawo, ni dama mai gida na da kyar ya yarda wallahi dan cewa ya yi sai dai na ajiye aikin saboda nisan dake tsakanin mu da wannan Kauyan.” “Mtwww! Ni abin da yake bani haushi malama shine, yadda kina ganin yara a kauyan nan maza da mata sunfi dari biyar duk wadanda basa zuwa, dubi ko class d'aya mun kasa samu saboda wulakanci, babu abinda suka sani sai tallah shegun.” Malama Mardiyya ta kwashe da dariya tana gyara zaman mayafinta tace, “Lallai malam Auwal kafi mai gida na jin haushin wannan kauyan, kasan shima ya taba zuwa nan yin aikin ƙidaya, nake gaya maka suka ki amincewa a yi musu haka suka tattara suka koma gida ransa a mugun bace. Shi yasa da nake gaya masa anyi min transfer zuwa nan ya fara masifa, da kyar na samu ya amince, tunda gaskiya ni dai albashin da nake karba yana rufa min asiri sosai.” Malam Auwal ya tabe baki kai kace shi ba da albashin ya dogara ba, mugun dan kwalisa ne dan irin samarin nan ne da suci a cikin su gwara su sanya a jiki ace sunyi abu iri kaza a rayuwar su. Matashi ne dan a shekaru ba zai wuce ashirin da bakwai ba, dogo ne baki irin mai kyau din nan mai dauke da yar siririyar fuska, idanunsa mici-mici kamar wanda aka sauwa, habarsa dauke da d'an guntun gemu wato tabani kasha hadisi da samari ke yi. Ya kuma taɓe baki tare da cewa. “Ai kuwa ni zanyi maganin su wallahi tallahi, dan babu shege ko shegiyar da zata sanya ministry su zo suyi mana dibar albarka.” “Da kyau malam Auwal ina bayan ka wallahi dari bisa dari.” Cewar malama Mardiyya tana ta dariya. Wucewa ya yi ya tafi ita kuma taci gaba da koyar dasu kamar yadda ta soma yi. Ina ta gudu ban tsaya ba, duk a zato na yana biye dani ashe bai ma biyo ni ba, sai da naje kofar gidan mu na turo kofa tare da lekawa sannan na tabbatar da cewa gudun banza nayi. Gajiyalle ta damko min wuya na tare da tun kudani cikin gida tana masifa. “Gantalalliyar yarinya kawai, babu abinda kika sani sai yawo da bin lunguna yin dambe. To zaman banzarki ya kare daga yau, maza dauki gashi nan na soya nayi miki kullin biyar, goma da ashirin. Tun dazu na hangi su Lami sun tafi tallar wainar roga da wainar gero nasan zuwa wannan lokacin ko basu siyar ba toh sun kusa. Amman ke da yake ba ƴar mutunci bace, baki taba yin tunanin abin arziki ba, tashi maza ki tafi yar kasuwa ki sai sa min.” Wani sassanyan dadi ya mamaye rai na, yau na samu abin da nake so wato damar yin tallah, saboda tan matukar bani sha'awa, musamman idan naga yadda kawaye na suke sha'anin su da kudi. Carab na dauki farantin gyada ina murmushin farin ciki nace da Gajiyalle. “Daman fa Gaji kece baki sani ba, ina ta so na gaya miki ki dinga yin wani abu ina fita yar kasuwa dashi. Toh sai na yi shiru dan karki doke ni, yanzu kuwa kinga kema zaki zama mai kudi kamar Innarajo, dama har ta fara tarawa Balki kayan aure, nima kinga sai ki fara yi min tanadin nawa.” Ta sakar min wani banzan kallo wanda ya tabbatar min da cewa taji haushin kalamai na, sai dai bata ce komai ba har na tashi na fice daga gidan. Wayyo ranar jina nake tamkar a gidan aljanna saboda farin ciki, gashi tun kafin na karasa yar kasuwan na fara ciniki a majalisar Sallau mai tsire. Cas! Suka bani kudin gyadar naira saba'in na dauki farantin na dora a kai na ina digirgine ga kuma kudi a hannu ina kuma lissafawa. Ta kusa da makarantar da aka bude na bi, har zan wuce sai kuma na sake shiga ina mai kulle kudin a gefen mayafi na da nayi damara a kuguna. Wasu malamai suka kira ni suma suka siya, naga na dazu da ya biyo ni amman wannan karon ko kallo na beyi ba, har zan tambaye shi ko zai siya, sai nayi shiru dan na lura kamar bashi da mutunci. Na tafi yar kasuwa kasan cewar ni sabuwa ce kuma gyadar sabuwar suya ce sai ya zamana ta kare da wuri. Ina kudin Gajiyalle? Na same su ci banza ci wofi tamkar nawa ne, ni har mantawa ma nayi cinikin ba nawa bane saboda rufewar idanuwa. Ban lura cewar kudin sun kusa karewa ba sai da naje siyan kankana kwallo daya aka ce min naira saba'in, jiki na yana bari na zaro ina kirgawa naga arba'in da biyar ne kawai. A lokacin gabana yayi mugun faduwa na dafe kirji na tare da furta. “Na shiga uku da Gajiyalle.” Babu shiri na dauki farantin gyadar na tafi gida, sai da na kusa zuwa sannan na fashe da kuka ina tafiya ina yi kamar wacce aka yiwa dukan tsiya. Na shiga zaure na samu kasa duk na zuba a jikina da gurin baki na idan ka gani ba zaka taba kin cewa ba na jaki na sha ba a gurin manyan maza, na shiga ina dora hannu aka. Gajiyalle na zaune tana dinkin hula gani a wujejjige yasa ta saurin mikewa tana tambaya ta. “Lafiya Dije?” “Na shiga uku Gaji zasu kashe ne.” “Suwa ye?” “Yan sholisho... Wayyo Allah na Gaji sun kwace cinikin na shiga uku.” “La'ilaha illa lahu ni jikar mutum hudu me kike son sanar dani Dije? Kina nufin kice an siyar da gyadar yan iskan gari sun turmusheki sun kwace cinikin?” Na gyada kai na ina share maina da bayan hannu, tace. “Na shiga uku Dije kin cuce ni, dan kaniyarki ina karfinki da har kika bari aka kwace kudin? Shikenan daman gyadar rantowa nayi nace zan yi gwaji gashi nan kin gwadani Dije, wallahi Kedai banza ce sakarai shashasha. Allah ya isa ban yafe ba, gashi dole na biya.” Tana magana rana duka na ni dai ban da bata hakuri babu abinda nake yi, cikin dashasshiyar murya nace bayan na zaro ragowar kudin. “Wannan kawai suka bani, suma din sai da suka mare ni da suka ji nace ba tawa bace ta babar mu ce.” “Uban babar ku, nice babar taki dan malafar gyatuminki? Da ace kin dauke ni uwa ai da ba zaki bari su karbe miki ba bakar munafuka kawai, tashi ki bani waje ko na karya ki, bana son ganin ki Dije na tsane ki.” Na tashi kamar munafuka na fita, zama nayi a zaure ina tikar dariya ta ganin yau na rainawa Gajiyalle hankali. Tun daga lokacin kuwa bata sake gigin dora min komai ba, duk nacin da nayi mata kin yarda tayi haka na hakura, na koma gidan jiya wato yawace-yawace kwararo-kwararo ina gurin. *SASHEN MAI GARI JAMILU* Gaba d’aya kusan duk maza dattawan dake karkarar Durbun suna zazzaune a karkashin bishiyar darbejiyar da mai gari jamilu yake zaune. Yana hakimce akan kujerar sa yasha rawani na masu gari, Sauran mutane na daga kasan taburmi sun yi gurfane suna sauraron mai gari. Malam Bashari (baban Dije) shi ma yana gefe kansa a kasa. Mai gari ya sake jan majina kafin ya cigaba da cewa, “Toh nagode da abunda wasun ku suka yi min, Wato ina matsayin mai garin nan ban isa na zartar da hukunci ba kenan sai an gayawa magabata na? Saboda an rena ni shine Za’a kai ‘karata wajen hakimi? Kai bara na fito muku a Mutum. Kauyen nan tsatso na ne suka kafa shi, Babu wasu wa’enda suka isa su zartar da hukunci bayan namu. Ku ba farin cikin ku bane ace ‘ya’yayen ku suna boko? Yanzu ‘yayan kansila su biyu ina har alfindi yake kai su kullun suyi bokon? Gata ya samu yanzu za’a zo amana makarantu shine kuke bakin ciki? Wannan wane irin kidahumanci ne? Toh dai, “Ni da hakimi mun gama magana, Za’a cigaba da karatun nan, Sannan ‘yayayen ku su amfana kuma ku amfana dasu nan gaba. Amma babu tilas wanda yaga baya ra’ayi shikenan. Amma kada nan gaba nasara ta samu yaran da sukai karatun nan kuzo kuna dana sani. Zan baku kowanne takaddu na shiga makarantun nan guda bi-biyu ku bawa ‘yayan ku domin shine fom na gurbin karatun. Kunga masu wayo tuni ‘yayan su sunyi nisa da karatun, Kuma wannan makaranta da naku zasu fara itace Idan suka kammala zasu samu fannin shiga jami’oi. Hakimi ya tabbatar min cewa sarki dake birni yayi alqawarin samawa yaran mu guraben karatu a jami’oin su dake birni. Saboda haka yanzu zan bawa kowannen ku takardun nan guda biyu. Ruwan ku ne ku sanya su a makarantun nan, Ruwan ku ne ku kyale su suyi ta hargitsa mana gari, Tunda kunnu na bani da martaba a idanun ku..” “Tuba muke ranka ya dade..” Cewar malam sagiru dake gefen mai gari a durkushe. Sauran suma suka fad’a da karfi Kan su a kasa. Mai gari yaja tsaki kafin ya janyo takaddun a gefe ya shiga kiran sunayen su yana babba su. Har akazo kan Malam Bashari mahaifin Dijangala. Mikewa yai ya isa gaban mai gari ya durk’usa kana ya mika hannun sa cikin girmamawa. Mai gari ya mika masa yana murmushi, “Malam Bashari, Har abada nasan baka cikin masu yimin zambo cikin aminci. Ba zaka taba zuwa kayi dani ba awani wajen. Tilasta ka akai, Kaje a yan cikon masu korafi, Ko’ina ne zan shedaka wallahi..” Malam Bashari yayi murmushi kafin yace da mai gari, “Godia nake yallabai, Allah ya saka da alkhairi.” Mai-gari yayi murmushi kana ya mika masa takaddun guda biyu. Hannu biyu Malam Bashari yasa ya karba, Da ganan aka shiga muhawara kowa yana tofa albarkacin bakin sa akan makarantun da yaran su zasu fara yi. Kafin a watse kowa ya kama hanyar sa. Malam Bashari ya taho gida zuciar sa ayyana yadda Gajiyalle zata karb’u maganar. Kafin ya k’arasa gida yaci karo da dandazon yara anata tafa hannaye,.. Fada ya kaure tsakanin Dijengala da Ummin Nasiru mai guga. Sai kaurewa suke suna tima juna a kasa. Na kururuwa kafin na daga hannu na watsa baya. “A hayye! Ke Ummin gwaigwai, Ba tsoron ki nake ji ba. Da wani gahin ki a tsaitsaye kawa hammatar dan iska. Banza bazara iskar damuna.” Na karasa fada ina karkadawa Ummi hannu. Ummin ma taja shewa kafin ta finciko ni muka kara haurawa, “‘Ni an gaya miki tsoron ki nake ji? Kazama kawai me warin kwata.” “A hayye nanaye! Kece kazama ai. Banziya wadda ke hamamin doyi. Ummi gwaigwai. Yanzun sai na caskala ki a wajen nan.” Na karasa fada ina jan tsaki. Na shatalo kafar Ummi na nakata da kasa. Ummi ta hau kuka, Dai dai sanda Baffa na Malam Bashari yazo wajen. Duk rashin ji na ina tsoron Baffa na sosai, Ko kadan banason b’acin ransa. “Kai ku bari, Maza kowa ya tafi gida, Tashi kinji! Yi hak’uri. Bata hak’uri, Ummi na muje gida..” Baffa na ya karasa fada yana nuna Ummin Nasiru mai guga da hannu, Cuno baki na nai gaba, ciki ciki nace, “ ‘ki hak’uri” “Yasin ca tai ‘ki hakuri ba Yi hak’uri ba..” Ummi tafada tana tafa hannaye, Zare min idanu Baffa yai alamun na bata hak’uri. Wayyo Allah na. Bana son bata hak’uri, Idan ba Baffa ba, Ko Gajiyalle ko Idan nayi ba dai dai ba shine nake bada hakuri, Amman ya za’ai itace da lefi ace na bata hak’uri. Nasha mur kana na juyar da kai na, “Baffa yar gala-gala muke yi, Kaga gidan dana zana kuwa? Kawai Ummi tazo ta tarwatsa mana ta tattake. Kuma ace na bada hak’uri? Haba Baffa dan Allah kada kace na bata hak’uri.” Baffa ya janyo hannu na gefe ya dafa kai na kafin yace, “Wanda yabada hak’uri baya faduwa Ummi na, Ko bake bace da laifin kiyi hak’uri kinji? Ki bata hak’uri, Saboda mutanen wajen nan siyi koyi dake. Kinga nan gaba za’ai shedar ki.” Daga kai nayi badan wai naji dadi ba sai dan gudun bacin ransa, Har gaban ta naje, Na wulkita idanu na na zabga mata uwar harara, Na mata kallon zata sani bata sha ruwa ba, Kafin na watsa hannu baya na buga zani hade da murgud’a baki nace, “Kinci saar Baffa na wallahi, Da wallahi sai na caskali ki, Nayi kullin tara sisi dake, Gajabura kawai. Badan halin ki ba.. Kada Allah Ubangiji yasa ki hakura. Aikin banza kawai. Mts! Allah ya...b..” Baki na ya shiga min nauyi, Har ga Allah banason bata ha’kurin nan. Amma ala dole na bata Saboda Baffa yace dole ne na bata. Na bata rai kafin na sanya karamin danyatsa na na sosa hanci na. Dakyar naja iska. Wai ni Dijengala ni zan bawa wata hak’uri.? Iska na sake ja na sauke kafin nace, “Kiyi hak.. h.. hakuri.” Ina gama fada nai gaba ina hawayen bakin ciki ganin yadda Ummi ke murna harda shewa, Tab ai kuwa bashi taci. Sai na yagalgalata narantse da Allah . Baffa ya cimma ni, Na cuno baki gaba dak’yar nace, “Sannu da zuwa Baffa..” “Yauwa yar baffan ta.. ko kefa! Gwara da kika bata hak’uri kinji? Kinga mutanen dake wajen laifin ta zasu gani.. Mahakurci mawadaci.” “Toh Baffa..” Na bashi amsa bawai don maganar sa ta hige niba, Gida muka higa , Gajiyalle na tsaye a turken dabbobin ta tana kirga yawan su, Kullum haka take yi sai ta kasafce kansu hankalin ta yake kwanciya. Daganan ta koma kan kajin ta da zabbin ta. Tabe baki nayi, Nayi gaba abuna. Baffa ya karasa bakin dakin sa ya zauna dakyar yana salati. Wasu takardu ya zaro a aljihun wandon sa dake lilo zai yage ya ajiye akan taburma, “Salamatu.. (Sunan Gajiyalle)” “Na’am Malam! Ya akai?” Tabashi amsa tana daga tsaye gandar-dar.. “Kya dai zauna ko? Abun arziki ne ya tunkare mu.” Gajiyalle ta washe baki. Nima na ajiye robar dana kamfaci ruwa na kwasa a guje. Ban dire a ko’ina ba sai gaban Baffa. Duk azato na duddugar tsire ya sayo ko Kan babban kifi. Gajiyalle ta dankaramin harara nima na rama ina gatsine.. “Guzumar ubanki! Kaga yar bankadaddiya.” Na mike ina cuno baki, “Yasin Baba ta ba bankadaddiya bace ehe, Allah ya jikan ta.” Tayo kai na zata dake ni na goce ina watsa hannu baya, Mudi ya shigo yana jin rediyon sa ta naci. Cikin daga murya yace, “Ke ga wani yaro can awaje yana kuka wai kin jefamas taya a kwata. Shi da yayan sa..” “Tashi kije ki san yadda zaki ki dakko masa tayar sa, Uwar yan jawo masifa. Wannan yarinya sam bakida kirki.” Tabe baki nayi na kalli Baffa kafin nace, “Kana ji ko Baffa, Ina cikin tafiya shi ya fara tsokana ta. Musa ne fa dan Malama Harira me siyar da wainar yar bagalaji. Haka kawai ya tsokane ni wai Dijangala tsogalgala me kama da zankala ‘koki. Shi ne ni kuwa na kwace tayar dayake wasa da ita nai cilli da ita a kwata. Ai ba lefi na bane ko?” Baffa na ya cire tagumin. Kafin ya mike ya fuce kawai, Ina jiyo shi shida Musan da yayan sa. Da alamun hak’uri ya basu. Can naga ya dawo ya zauna. Ya kira Mudi shina ya zauna. “Yauwa Salamatu ga takardu nan daga birni sarki ne ya mana hanya daga shugaban kasa. Tallafin karatu ne da yaran mu zasu yi. Kyauta har su kare su shiga gurbin jami’a..” Gajiyalle taja tsaki kafin ta mike tana zabgawa baffan mu harara, “Ai karatun arna? Kan babban bala’i! Yasin ba dai agidan nan ba? Karatu fa kace? Mudi ko zakai boko?” Mudi ya mike yana girgiza kai, “Ni lodin mota zan fara. Gajiyalle zata sayamin mota idan na kara manyan ta. Bazanyi boko ba gaskia “ Tab tunowa nayi nima naga yadda ake boko a talabijin din gidan su Nafisa. Yara kamar a bursun din kauye. An hanasu Fita anata koya musu shirme wai shine karatu. Mikewa nayi nima na dire tsallen albarka, Kafin na kwararo rantsuwa na dire ina watsa hannu na, “Gaskia bazan yi bokoko ba, Yan bokoko ba basa karatu basa sallah, Sai Karatun arnaye. Idan nayi boko na nutse.. “ Baffa ya duka yana rok’on mu, “Ku temaka min kuje karatun nan. Wallahi Za’a amfana. Ina jin kunyar mai gari na mayar masa da takardun nan. Salamatu kisa baki.” Gajiyalle taja tsaki akaro na ba adadi kafin tace, “Salon iskanci akeso a koyawa yaran karkarar nan. Suyi ta cikin shege ko? Akan me Za’a ce yaran mu suyi boko? Saboda hanyar neman abincin mu su lalace ko? Gaskia Mudi bazai yi boko ba. Idan yar ka zata yi to? Amman dai ai Gwara Kiyi talle da boko ko Dije?” Kad’a Kai na nayi na dashe baki. “Sau dubu miliyan Gwara nayi talle da dai nayi boko. Bazan yi ba gaskia. Ni talle zan yiwa Gajiyalle. Na girma ayi aure na ko Baffa?” Baffa na yayi ajiyar zuciya kafin ya dube ni dakyau yace, “Yanzu da kiyi karatun gwara kin d’au talla kina yawo a gari? Ba kince min kina sha’awar yadda kike sauraron na radiyo idan suna magana ba? Kuma kikace na Abun kallon gidan kansila ma yana burge ki. ? Kinason ki rika ri’ke musu abun da suke magana ko? Yanzu bakyaso kin watsar ba zaki cinma burin ki ba?” Tunani na shiga yi, Gaskia bazan iya zama kamar a bursun ba, Gwara nayi tallen. “Nide gwara tallen..” Gajiyalle taja guda da shewa kafin tace, “Yauwa yar gari. Zanci gaba da baki kayan talla kina yi min.” Baffan mu ya kad’a kai hade da mikewa ya dube ni, “Bazan tursasa ki ba. Allah yaba da sa’a.” Yana gama magana yai fucewar sa. Ni kuwa dadi nake ji zan fara ci gaba da talla ina samun kudin kashewa koda cikin dabara ne. Acikin satin Gajiyalle tafara doramin tallen kayan koli dana turaruka da take sarowa a birni. Inata talle na har aka bude makaranta. Nayi mamakin ganin kawaye na duk sun fara zuwa. Na sheke da dariya na kance, “Mahaukata, Banda shirme me akai da boko? Sun zama arnaye. Harda Siyama kawata aminiyata. Lalle siyama batada wayo. Tabdijan.” Ni kuwa likafar talle na taci gaba, Kaf karkarar mu ba inda bana zagawa don asai kayana. Idan naga zai yi kwantai ma har fada nake janyowa ta yadda dole mutum ya siya asarar sa.. Ho ni Dije- Dijengala Yar Baffan ta. Ta Gajiyalle mai yar hakiya.. Dijama mai kayan koli. k’anwar Mudin bakin tasha..” Kirarin da nakan yiwa kai na kenan aduk sanda nayi ciniki. Gajiyalle kan bani kudin batarwa. Idan kuma banyi kasuwa ba ta lakadamin duka ni kuwa na rama akan dabbobin ta na targada shegu... .. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *KIBIYAR AJALI.....!!!!* _(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)_ 🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA HAFSAT* *(MISS XOXO)* *©️®️ZAFAFA 5 2021* *BABI NA 5* (LAST FREE PAGE: SHAFIN KARSHE NA KYAUTA) ••. ••. •• Sana'ar da Gajiyalle take dora min ta karbe ni sosai ina jin dad'in yin ta fiye da komai a rayuwa ta, har wasu kauyukan nake bin masu talla muje, gashi abin burgewa duk abin da na daga sai an siya. Babu laifi duk sanda na kai kudi cas ina samun abincin da zanci na koshi, sabanin idan na kashe wasu ranar sai naci duka kuma duk da haka sai na takura mata ta dora min na fita da kayan na siyar. Bangaran Baffa kuwa ya rasa yadda zai yi dani da Gajiyalle akan na shiga makaranta amman muka kafe, gashi mai garin ya sanya idanuwa sosai, dan mutane sun fara saduda suna ta barin yaran su na zuwa. Wata rana na dawo daga talla na tarar da Baffa zaune a kofar gida ya zabga tagumi, nayi saurin karasawa kusa da shi tare da aje farantin kayan kolin nawa, hannu nasa na zare tagumin nasa tare da ciro cinikin ina karkada masa shi baki na a washe kamar mai tallar makilin. Yaki kallon kudin na kuma kaiwa kusa da fuskar sa amman duk da haka yaki kallansu, hakan ya tabbatar min da cewa ransa a bace yake. “Baffa wai baka ga cinikin da nayo ba? Sai nuna maka nake yi kaki kallo na.” Cikin sanyin muryarsa yace dani. “Tashi ki shiga ciki tun kafin ta jiyo muryarki tazo ku tara min mutane.” “Amma dai Baffa an bata maka rai ko?” Yayi shiru. “Haba Baffa ko ni nayi maka laifin ne?” Abin mamaki sai naga ya yi saurin daga kai alamar 'eh' ni ce. “Na higa uku ni Dije me nayi maka Baffa? Koma dai meye ni nasan ban kula ba nayi maka shi dan Allah ka yafe min kaji Baffa na?” Baffa ya ja numfashi tare da kallo na karo na biyu tun zama na kusa dashi, yana shirin yi min magana muka ji muryar Gajiyalle a kan mu tazo ta rike kogu tana karkada jiki da alama masifa take ji da ita. Hannu ta miko min alamun na bata nayi dariya saboda nasan su ta biyo saman, ai idan har kasan Gajiyalle to idan ta yi maka wannan tsayuwar indai baka bata abin da take so ba, babu shakka ka taro babban aiki. Na dora mata kudin ta hau lissafawa, ta gama sai kuma ta saki guda tana raye-raye. “Ahaiyeeee nanayeeee cas! Tabbas Dije kina da goshi ke din mai sa'a ce walle, nayi miki alkawarin samira mai uku aradu lokacin bikin ki, ke harda kumbo da kwalla tasa da fanteka heeee ras!... Dije ta Gajiyalle mai kayan koli.” Tana gamawa ta juya tare da komawa gida tana lissafa kudin ta cike da farin ciki. Ni kuma na sake mikewa zan tashi Baffa ya yi saurin dakatar dani yana cewa. “Ummina ki zauna magana zamu yi.” “Allah yasa dangin inna ta zaka kai ni Baffa.” Ya yi murmushi yasan ina son zuwa amman baya so ya kai ni su rike ni gabaki d'aya dan dama duk haushin Gajiyalle suke yi dan suna jin labarin yadda take gana min azaba. “Ummina ke nan, zan kai ki dangin innarki amman da sharadi guda daya.” Cikin zumudi nace. “Fadi Baffa ko meye zan yi indai zaka kai ni.” “Yauwa Ummina, sharadin shine ki yadda ki fara zuwa makarantar can, kinga ko dazu sai da mai unguwa ya yi min maganar cewa mai gari yana sanya ido akan duk wadanda suka kai yaran su. Kinga yana ganin mutunci na dan Allah ki yadda ki fara zuwa.” Tunda ya fara magana nake yatsina fuska tsanar mai garin ta fara shiga zuciya ta, yana kaiwa karshe kuwa na cona baki gaba ina cewa. “Rabu da mai garin nan Baffa, yo hi makarantar ya yi da zai ihi mutane akan zuwa? Ni wallahi aradun Allah ban zuwa, nama fasa zama irin na radiyo d'in da na talabijin d'in tunda sune suke sake janyowa kace sai naje.” “Ikon Allah! Ummina ni ba haka nake nufi ba, kinga wan....” Nayi saurin mikewa. “Baffa ni fa bazan yi bokon nan ba, kaima fa baka yi ba kuma kaga nan da rai da lafiyarka, ni wallahi bana son makarantar can.” Na shige gida ina buga kafa alamar bana so ban yarda ba. Haka Baffa ya rabu dani, ya zamana suna yar buya shi da mai gari dan besan wace karyar zai yi ba dan ya kare kansa a wajan shi. Ni kuwa naci gaba da yiwa Gajiyalle talla yanzu har wani mutunci muke yi da ita zamu yi jira harda shewa mu tafa da hannaye cikin nishad'i. Mudikalle ma babu ruwan shi da makarantar, dan a lokacin da Baffa ya bashi fom dinsa a gurin ya daga sama ya yi mata gutsin-gutsin tare da watsar da su iska ta tarwatsa. Kuka ne kadai Baffa be yi ba, hakan ne kuma ya hana shi bani tawa dan yasan nima zan iya yin yadda Mudi ya yi. Ranar Litinin da safe naje siyo koko da kosai ina shayo kwanar da zata kai ni wajan makaranta na taci karo da wannan malamin da ya tsinko bulala zai doke ni, amman nayi kamar ban gane shi ba naje zan wuce kawai naji ya tsaidani. “Zo nan yar tallah.” Haushi ya kamani da naji irin sunan da ya kira ni dashi, na riko kuguna tare da cewa. “Ba suna na bane, idan zaka kira ni ka ce Dije ko tagala ko yar gatan Baffa da Gajiyalle.” “Bazan kiraki da su din ba, yar tallah zan fada ko zaki doke ni?” Nasa yatsa a baki ina ciza naga alamar mutumin nan bashi da mutunci kuma babu abinda ya hada ni dashi bare nace ga dalilin da yasa yake takura min. “Toh ai hi kenan sai kai ta fada ba sai na amsa maka ba sannan zaka ji dadin kuma gaya min ba.” Ban ankara ba naji ya dauke min keyata da duka, nayi saurin dafe gurin ina furta. “Kut! Kai... Kai... Kai! Allah ya...” Ban karasa ba ya kuma sakar min wani wanda yafi na farkon. “Ni zaki zaga dan ubanki? Ke baki da mutunci ko? Toh na rantse da Allah zan yi maganinki a cikin kauyan nan naku. Daman tunda na ganki nasan baki da tarbiya, zo ki wuce ki shiga ajin nan daga yau zan koya miki tarbiya farar aljana da idanuwanki kamar na mage ta ga bera.” “Ajin me zan shiga?” Nayi furucin ba tare da na san ya fito ba. “Ya za ai kisan aji kina yar tallah? Yau dai nake son ki shiga kisan ko menene shi.” “Lallai ma, indai makaranta ce bazan higa ba ana dole ne? Toh na gaya maka Baffa ma ya yi ya gama bare kai da ba uba na ba ma.” Ina gama fadar haka na faki idanunsa nace kafa mai naci ban baki ba, na ruga da gudu kamar ance ya biyo ni. Malam Auwal ya bini da kallon sakarya ni kuma har da yi masa gwalo, na shiga gida ina dariyar mugunta. Gajiyalle ta karbi koko da kosan ta sammin nasha daga nan nayi tafiya ta talla. Haka dai rayuwa ta taci gaba da kasan cewa na kasa tsayawa na karbi shawarar da Baffa yake bani. Sai da yaga da gaske nake bazan yi bokon ba sannan ya dako fom di na ya bani yace duk abinda naga dama naje nayi, ganin ransa ya yi mugun baci ya fita a harkata duk wasu abubuwa ya dena yi min sannan ne na fara tunanin yadda zan yi na samar masa da farin ciki ko Allah zai sa ya dawo da jin dadin sa gare ni. Kwana biyu na dena yin talla, tun Gajiyalle na daukar abin wasa har dai taga na dage nace ni Baffa zan farantawa rai, boko zan shiga ko da ba'a so nayi zan yi ko zan mutu a ciki. Tun daga lokacin ta dawo da bani azaba wacce tafi ta baya, amman nima na kafe cewar bazan yi talla ba sai dai ta kashe ni. *GOVERNMENT GIRLS JUNIOR PRIMARY/SENIOR SCHOOL DURBUN* *Na* dubi garejin makarantar mu dake d’auke da wasu watsalallun rubutu da bansan me suke nufi ba. Gaba na ya yanke ya fadi. Banason bokon nan amma ya zanyi? Cikar buri na da farin cikin Baffa na shine ya sanya na yanke zuciar zuwa makarantar. Shaf na mance ban dakko takardar shedar kai dan makarantar bane. Na manto ta a gida. Bakwa mantawa ba gani nake ba amfanin da za tai. Domin dazu na gutsiri ‘kasan ta ma na kwakwulo dattin kunne na. Fankan fankan na shiga cikin makarantar ina bin dandazon dalibai da kallo, Suma yawancin su ni suke kalla, Menene suke kallo na haka tamkar basu san Dijen Baffan ta ba? Murgud’a baki nayi na dankara musu harara, Cikin haka sai ga Siyama k’awata taci ado cikin kaya irin na sauran daliban. Ja na tayi gefe tana raba idanuwa, “Dijengala mai kike anan? Ko waje na kiki zo? Ki bari a..” “Dalla yi min shiru. Wajen ki? Saboda me zan zo wajen ki? Nan ashe Nana ta hada partyn sunan gidan su an gayyaci kowa kunje kunci dadi shine ba wanda ya gaya min, Taron munafukai.” Siyama zata rike min hannu na wafce ina tsirtar da yawu a gefe, “Banzariya kawai. Ai in gaya miki kawaye zan sake, Kuma sai nabi kowannen ku nayi ‘kuli-kulin kubra da ku.” “Kai su waye anan... Wacece wannan siyama ce?” Oh nagane shi shegen malamin nan ne mai gashin hab’a irin na bunsurun Gajiyalle. Tahowa yake wajen mu yana cilla bulalar sa sama. Bazan taba mantawa da karfen d’aya saukarwa kai na ciwon sati ba. Na masa tofin Allah tsine yafi dubu. Na wulkita idanu na sama na zabga masa harara. K’arasowa yai wajen mu yana kallon Siyama kafin ya mai da duban sa kai na, “Na kore ku yafi a kirga, Nace banda talla, Banda talla. Yan talla su dena zuwa da safe sai lokacin break yayi. Kina jina? Ko kuwa kunnen k’ashi ne da ke?” Daga hannu nai zai zabga min bulala naja baya ina binsa da kallon ya haka? “Ha’ah magana kake ko zubar gudawa? Uhm.” “Ke da wa kike? Siyama ke kika kawo mana wannan marar kunyar?” Siyama tai saurin girgiza kai tana ja baya. Sauran yan makarantar suka yo kanmu suna kallon mu. Naja dankwalin kai na nai damara dashi na dira agaban sa, “Dan kaji nima nan daliba ce kamar kowa, Banyi niyyar fara zuwa makarantar bane sai yau. Kuma ni ba marar kunya bace ehe..” Ya-yo kai na zai make ni wata malama ta dakatar dashi, “Haba Malam Auwal meye haka?” “Malama Mardiyya ki bari na zazzabga mata mari, Irin marasa kunyar yarannanne, Kangararru wanda basajin maganar iyayen su. Bakya jin me take cewa. Wannan k’aramar yarinyar ni zata gayawa magana.?” Ya karasa fada yana kwafa. Malama Mardiyya ta riko hannu na tana janyo ni kusa da ita. Hannun ta laushi ba irin nawa ba duk yayi kanta ya daddauje. Bata kyamata ta ta janyo ni jikin ta? Kallo na tayi kafin tace, “Kanwata makarantar nan kikazo koyan karatu ko kuwa wani abun ne daban ya kawo ki?” Saurin girgiza kai nayi, “Karatu nazo koya, Nima d’aliba ce kamar kowa, Kawai dai ban fara zuwa da wuri bane sai yau.” Malama Mardiyya ta ka’da kai kafin tace, “Toh ina uniform dinki?” Zare idanu nayi jin abunda ta fada da bansan ko menene ba, Matsawa nai ina raba idanuwa, “Inifan? Meye shi Malama?” Sauran yara suka sa daria, Na juya na zabga musu harara, Domin sun san hali na sarai yanzun sai na hada gagarumin fa’dan da sai mai gari jamilu yayi shari’a. Malama Mardiyya tayi murmushin da kyakkyawan hakorin makkan ta ya bayyana, Inaga irin dan nera goman nanne da Yusha’u ke sawowa a birni ya sassaidawa mutan garin mu. “U-ni-form ake cewa kinji kanwata? Yana nufin kayan makaranta iri d’aya da sauran yara suka sa kinji? Ya sunan ki ne?” “Yu-nun-fan!” Na fada a hankali ina dashe baki kafin na sake cewa, “Sunana da yawa, Baba na na kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar nan, Mafi yawancin yan karkarar nan na kira na da Dijengala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan karkarar nan na min laqabi da Dije Oganniya...” Na karasa fada ina dashe baki. Malama Mardiyya da sauran mutane suka kada kai, Gaba d’aya sun zubamin ido. To ni Meye nawa tunda Sunana ta tambaya kuma du sunaye na ne. Malama Mardiyya tace, “Dakyau! Kenan sunan ki Khadija?” Na daga kai alamun Eh! “Wow nice name! Toh Ina takardar shedar ke yar makarantar nan ce?” ‘Anzo wajen’ Na fada a hankali ina nannada d’ankwalin kai na. “Iya gida yasin, au wai so ake yi?” Gyada kai tayi! Na kwasa aguje ban ce komai ba na tafi gida na dakko. Ina tafiya ina waiwayen su, Na hango Malam auwal din ya matsa kusa da Malama Mardiyya suna magana. “Dan bakin ciki hede ya mutu, Ba fasawa karatu ne dai he anyi, Me kayin giginya kawai.” Da gudu na shige gida ina haki, Gajiyalle na tsakar gidan mu tana dama kunu. “Yan bokoko! Mu dai babu ruwan mu idan aka dakko abun kunya.” Sam bangane me take nufi na da dakko abun kunya ba. Nidai nai shigewa ta dakin Baffa. Akan taga na gano takardar inda na dora ta dazu. Dauka nayi da gudu zan fice sai kuma na dawo na tsugunna a kusa da Gajiyalle Ina lashe lebe, “Dan sanmun kunun.” Harara ta dankaramin tana janye bokitin kunun daga kusa dani, “Matsa kafin na hanbare ki. Dan uban ki ubanki ne ya sayo da Za’a baki? Ba dai kin dena tallen ba.? Bazan baki ba ko zaki mutu.” K’wafa nayi na mike ina jujjuya idanu na, “A hayye! Dijengala ta mai gari, Ba auren talaka ba, Talaka mai sara da sassake. Gajiyalle ki bani kar na auri chiyamin din birni ginin bulo. Ki ciji yatsa.” “A mafarki? Nace a mafarki? Wane shashashan ne zai aure ki? Zaki matsa daga kai na ko sai na lakada miki na jaki?” Tabe baki nayi, Na fice aguje na koma makaranta. Ina zuwa na tarar an tara yan makarantar ana koya musu wani abu kamar waka an jera su a layi. Malama Mardiyya ta yafito ni tace na tsaya a bayan Adaman liman. “Assembly ake yi..” “Assambuli? Me kenan da hausa Malama?” “Kowa da kika gani a jere, Kowa ajujuwan su daban. Kema a bayan yan ajin ku kike, Wasun su sun iya Abun da ake fada mai taken ‘National anthem’ Taken najeriya kenan. Yana da matuk’ar muhimmanci.” Nifa gaba d’aya ba gane abunda take cewa nake ba, Gashi bana shiru na cuci kai na akan abunda ban gane ba. Na dube ta ahankali nace, “Malama yasin bangane duk abunda kike fada ba” “Babu damuwa Khadija.. Idan an tashi break kizo na miki bayani. Yanzu dai ina takardar?” Mika mata nayi, a cukurkude tayi dik’in-di’kin da dau’dar kunne na dana sassakato, Malama Mardiyya ta zare idanu tana bin takardar da kallo, “Khadija ya haka? Me kika goge da ita tayi datti haka?” Kunya ta mamaye ni, Na sunkuyar da kai na kasa. A hankali nace, “Yasin kunne na na gogo. Da da gashin kaza nake yi. Toh mugun kansilar garin nan yasa an yahe hyarar kududdufin baki d’aya wai tuk’a tuk’a (borehole) Za’ai awajen.” Malama Mardiyya ta kada kai, Kafin ta karba ta mikar da ita. Komawa tayi gaban makarantar tana bin mu dalibai da kallo, “Yan makaranta nace muku a dinga tsafta. Satin sama zamu fara duban tsafta, a turance ana cewa ‘censorship day’ . Dole ne ku kara kai mi wajen tsaftace jikin ku da kayan ku dama kayan karatun ku. Mata a dinga wanka ana wanke kai, A kuma yanke farata na hannu dana kafa, Kuma dole ayi kitso, Dik bayan sati biyu za’ai sabon kitso. Kuna jina?” Da k’arfi kowa yace, “Eh..” Na dubi kai na tun daga sama har kasa, Sanye nake cikin wata yarkacacciyar koriyar hyadda (shadda) da na manta sanda Baffa ya dinka mun, Doguwa ce har kasa amma Saboda tsabar tamin kadan yanzu, Ta dangale ta dawo gaba da gwiwata kadan, Zif (zipper) din ya cire, Kafata babu takauni (takalmi) farata na na hannu dana kafa duk sun yi zako-zako abun tsoro ga uban datti aciki. Gahin kai na kuwa na mance yauhe rabon dana wanke hi balle kitse hi. Ni kadai tashin wari nake yi, Rabon da nai wankan sabulu tun wanda Dara’ifa tace na siya shima ya kare sauran sa Gajiyalle ta kwace hi. Ashe na zurfafa tunani bansan an kammala assambulin ba. Kowa ya watse. Malama Mardiyya ta kira Sunana da karfi tana bubbuga yatsun hannunta biyu a kofar kunne na, “Khadija..” “Na’am Malama..” “Tunanin me kike yi ne? Kinga dai barshi kije aji yanzu. An jima da break kizo ki same ni.” “Burek? Malama meye shi.” “Lokacin cin abinci da wasa da ake baku Idan an kada kararrawa ta uku..” “Kan balastin can. Harda hi? Harda lokacin wasa? Wayyo ni Dije ba karamin hirme nayi ba da banzo tun sanda aka fara karatun nan ba.” Malama Mardiyya tayi daria kafin ta nunomin dan banzan Malam auwal dinnan, “Je ki ga malamin class din. Au ajin ku can. Ki bishi zai kai ki ajin ku. Allah ya bada sa’a Khadija. Banda tsokana da fada kinji? Da anyi break kice staffroom Za’a nuna miki. Kinma ganshi can? Shine dakin malamai.” Har ga Allah banso ajin Malam auwal Za’a kai ni ba. Domin tun had’uwar farko ni da hi jinin mu bai hadu ba. Ya tsane ni nima na tsane hi. Tsana mai tsanani ma kuwa. “Malama nafuson ajin ki dan Allah!” “Ni ajina yan kanana ne Khadija. Ki dai bishi kinji? Malam auwal nada kirki sosai, Ya nasan daliban sa suyi karatu. Amma bayasan wasa ba kuma ya shiri da masu wasa ko fada a aji kina jina?” Saurin k’ada kai nayi alamun Eh. Na bi bayan sa da sauri, Yana ta fadan abu da wani yare, Da alamun dai zagi na yake yi. Oho masa dai. Canmakadus-dus! Karatu ne dai sai an yi hi ba fashi. Ajin mu ya kai ni. Yara suka hau tafi. Na sake buda hanci ina daddaga musu hannu. Can gefen taga ya nunamin benchi yace na zauna. Ina zama ya tayar dani Wai nafi cikakken sunana dana baba na. “Da farko dai: Baba na na kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar mu. Mafi yawancin yan karkarar mu na kira na da Dijengala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan karkarar mu na min laqabi da Dije Oganniya. S..” “Ya isa Malama dakata. Sai zuba kike uwa’yayan kanya. Bush girl. Sunan ki fa kawai na tambaya dana baban ki zansa a register.” “Yo ai da kayi hak’uri su dinma zaka ji ai ko? Duk sunaye na ne wanda na fada..” “Ke wai bakisan me kike bane? Toh Malama sunan ki na yanka d’aya zaki gayamin dana baban ki.” “Toh ai Baffa nama sunan sa biyu dan kaji ehe.” Wani uban tsaki Malam auwal yaja, Ya furzar da iskar bakin sa kafin ya sake duba na kamar yaga kahi. “Wallahi zan kore ki daga makarantar nan.” “A hayye sama lubaye! Sede in mutuwa nayi hine zandena zuwa Malam. Amma yadda kowanne yaro da yarinya yake ajin nan du matsayin mu d’aya. Mai gari ne yakarb’o tallafi awajen hakimi, Shima hakimi daga wajen sarki na birni ya samo. Shima sarkin daga wajen hyugaban kasa. Dan kaji inada matsayi kamar kowa ehe.” Malam Auwal ya girgiza kai kawai kafin ya sake cewa, “Illiteracy is a disease! Menene sunan ki na ainihi dana baban ki?” “Sunan da Baffa na ya radamin Nana Khadija ne. Baffa na sunan sa biyu. Alquranin Ubangiji bazan fadi na gaskiyar sa ba ai rahin kunya ne.” “Zauna kawai..” Malam auwal ya fada yana dafe goshin sa, Sunan ta ya rubuta a register da ‘Nana Khadija Baffah.’ ya rufe register ransa a matukar b’ace yake koya musu darussan har aka kada kararrawar fita break. Ana futa na kwasa a guje nayi wajen Malama Mardiyya ina haki. “Malama ga ni.” “Sannun ki Khadija.. Hakin me kike? Ko gudu ki kai? Ki dena ba’asan yawan haki. Babu ma dacewa ‘ya mace ta rika zunduma gudu kinji?” Kada kai nayi kawai na tsugunna a kasa. “Khadija ina maman ki?” Tana fadar haka, Kwakwalwata ta shiga tariyo min sanda Ummah na ta rasu, Da wayo na lokacin. Domin har yanzu ina iya tariyo sanda ta rasu. K’asan d’ankwali na nasa na goge hawaye na dake yar tsere kafin nace, “Malama mahaifiya ta Allah ya mata rasuwa shekarun baya.” “Allahu Akbar! Allah ya jikan ta da Rahama, Kiyi hak’uri Khadija bansani ba, Da bazan taso miki da radadin ciwon rashin ta ba.” Saurin girgiza kai na nayi kafin na sake cewa, “Malama a har kullum ina fad’awa zucia ta me so na shine zai tambayi wane irin hali na ke ciki. Wadda tambaya ta farko kuma mahaifiya ta Za’a tambaya. Shin tana raye ko akasin haka?.” “Hakane. Toh Allah ya baku hakurin rashin ta. Yanayin ki yasa na kasa samun nutsuwa a zucia ta Khadija. Shin meke faruwa dake? Menene labarin ki Khadija...?” K’atuwar bahaguwar zuciya na sauke, Kafin na gyara tsugunnen da nayi na fara cewa, *TUNA BAYA....* .. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _ZAFAFA 5 (2021) NA KUDI NE, DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHIN NERA 700 KACAL! KA/KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SIYA DA KUDIN KI KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI, KA/KI/KU GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU SIYARWAR!!! DOMIN SIYAN NAKI TUNTUBI: +234 903 318 1070 KO +234 903 234 5899, AKWAI ‘KARUWA SOSAI ACIKIN WADAN NAN LITTATTAFAN😍MUNA FARIN CIKIN KASANCEWAR KU A TATTARE DAMU😘 MASOYAN MU ABUN ALFAHARIN MU🙌🏻_ _*KIBIYAR AJALI..!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🥰❤️👑🏹 _(PAID STORIES/ZAFAFA 5 BOOKS DIN KUDI NE..)_ _*MALLAKAR: NANA HAFSAT_* _(MISS XOXO)🧕🏼_ _*BABI NA: 6_* _*TUNA BAYA...!_* ****Malam Basheer (Bashari) Inuwa na Alkali, Shine cikakken sunan mahafi na, Kuma karkarar Durbun itace tushen su, Anan aka haifi kaka na marigayi Malam Inuwa na Alkali, ance aminin marigayi alkali ne, Mutumi na farko a karkarar mu daya je birni yayo karatu ya zama alkali. Mahaifi na Malam Bashari shi kadai ne ‘da awajen iyayen sa, Baffan mu yace sauran yan uwan sa da anhaife su suke rasuwa, Shi kadai ne awajen iyayen sa. Mahaifiyar sa fulanin karkarar Gandar ce. Gaba da baya mahaifi na bashi da yan uwa, Domin mahaifiyar shi dama kafin rasuwar ta irin fulanin tashin nan ne. Toh bayan ta auri kakana ma’ana mahaifin Baba na sai yan uwanta suka tashi daga karkarar Durbun suka koma wani k’auyen. Mahaifin sa kuwa dama ya manyan ta, Bai da wasu sauran yan uwa, Sai kanwar baban sa, Ita kadai ce tayi ragowa tana can cikin kauyen nan wajajen rijiyar badamasi, Kuma ta manyanta ko gani bata yi sosai. Baffan mu yace ya hadu da Umma ta ne a birnin, Acan gefen gari suke. Yace hakika Umma ta tafuto daga tsatson babban gida, Domin gida ne na malaman addinin musulunci, Domin har makarantar islamiyya suke da ita a kofar gidan. Ba dai masu arziki bane, Amma suna da wadatar zuci. Yayan mamana yana da makarantar allo ta almajirai. Shi dai Baffa na abunda ya kai shi birni alokacin neman kudi yaje, Ya fara sana’ar wankau, Daga nan ya dena ya koma sana’ar gini. Inda yake leburanci yana debewa ma’aikatan dake gini ‘kasa da kuma ruwa. A rijiyar gidan su Umman mu yake debo ruwa, Kasancewar akwai samari a layin, Sai ya zamto Baffan mu ya fara wanke takalma (shoe shiner) Yakan wanke musu takalman su ya kuma goge musu har da dinke wa. Har Allah ya hada jinin su da Yayan Ummah ta, Suka fara abota. Ta sanadiyyar yayan umma ta, Baffa yasan Umma. Inda suka fara zumunci na yaya da kanwa, Domin abotar su da yayan umma ta ta kara kulluwa sun zama aminai. Umma ta tafara boko har aji biyar, Bata gama ba suka fara soyayya da Baffa na. Baffa ya nemi auren ta aka bashi. Ya kasance Baffa yace da yazowa da yan uwa da yan karkarar nan maganar auren sa sai suka soki zancen, Kan ya za’ai ya auro yar boko? Bayan ba bokon yai ba? Kuma yar birni masu abun kunya. Baffa ya toshe kunnuwan sa da surutan mutane yai biris da zancen su. Ya auro Umma na suka dawo nan Durbun da zama. Baffa yace sam bata kyamace shi ba ba kuma ta kyamaci yan kauyen nan ba. Suka zauna cikin lumana da kaunar juna, Kafin ta haife ni ta haifi har jarirai uku duk suka rasu, D’aya kuma bai zo da rai ba. Sai daga baya Allah ya azurta ta da samun ciki na, Baffa yace tasha wahalar ciki na, Domin Sai da suka yita zuwa birni a asibiti ana kara mata jini. Allah yasa ta haife ni lapia. Kuma tunda ta haife ni, Shikenan tayi sallama da lapiar ta, Yau tana Lapia gobe tana gadon asibiti. Ina shekara shida Allah ya mata rasuwa.. Malama Mardiyya ta zare tagumin da tayi tana matsar hawaye, Nima hawayen nake. Na Kasa cigaba Sai da Malama Mardiyya ta sake tambayata cewar, “Kiyi hak’uri Khadija, Allah ya jikan Umman ki da rahama, Allah ya dubi maraicin ki ya baki miji nagari. Yanzu yan uwan mahaifiyar ki suna ina? Shin ba sunan halin da kike ciki bane? Ko dama can mahaifin ki nada wata matar?” Saurin girgiza kai nayi, Na fyato kakkaurar majina na katse da wani kara a gefen kafar Malama Mardiyya kafin na cigaba da cewa, “Yan uwan Umma ta na can birni, Kuma duk maza ne Ita kadai ce mace a dakin su, Bayan tayi aure Baffa yace iyayen ta sun rasu daga baya kafin a haife ni. Amma su hudu ne a wajen iyayen su, Maza uku, Mace d’aya, Ita kenan. Akwai Kawu Hashim, Kawu Kabiru, Da Kawu Isma’el, Sai ita Umma ta mai suna Jamila. Sun taba zuwa su duka ukun da wata sallah, Suka bani kudi da yawa da kaya, Lokacin Baffa na ya auro Gajiyalle walle ta kwace komai. Kinsan fa Baffa na tsoron ta yake wallahi, “Yan uwan mahaifiya ta gaba ki dayan su ba wuri d’aya suke zaune ba, kowanne yana wani gari shi da iyalin sa, Shi Kawu Isma’el shi kadai ne a birni inda kuka zo, Sai Kawu Hashim shi yana garin legas, Sai Kawu Kabiru Shi kuma yana garin Jos. Duk kanin su kowanne a tare yake da iyalin sa, Kowanne da irin aikin sa, Domin Kawu Hashim shi malamin makaranta ne bangaren arabi a jami’ar Legas. Sai Kawu Kabiru shi ma babban malamin sunnah ne yana kuma da makarantar kansa a garin na Jos, “Sai Kawu Isma’el shi yana Birni. Kuma Baffa yace min babban dan kasuwa ne shi da ake ji da shi a birnin. Wallahi da suna kula da ni fushi sukai daga baya. Sunce Baffa ya bar musu ni yaki. Kuma yazo ya auro Gajiyalle da wayo na sunzo ta musu rashin mutinci har ta juyewa kawu Isma’el ruwan randa a kayan sa. Shine tun daga lokacin ba su sake zuwa ba. Amman nace idan na zama babba walle sai naje birni wajen kawunni na..” Malama Mardiyya ta kada kai kafin ta sake cewa, “Yaushe aka auro Gajiyallen?..” Na bude baki zan bata amsa, Sai ga Malam Auwal akan mu yana zare idanu, “Ke tashi kije aji..” “Zatazo Malam afuwan. Magana muke yi mai matuk’ar muhimmanci, Kuma nima free period ce dani. Amana hak’uri.” Kada kai yayi ya koma Aji, Ni kuma dadi ya mamaye min kriji jin ance bazan koma ajin ba sai anjima. Dama duk dan zaman da nayi acan ya gundure ni, Takashi na sai ciwo yake. Cike da farin ciki na cigaba da cewa Malama Mardiyya, “Bayan rasuwar mahafiya ta, Na zauna a hannun Kanwar kakana ta wajen uba. Wadda nace miki tana can b’angaren rijiyar badamasi? To na zauna acan na tsawon shekara d’aya. Daga nan yan karkarar nan suka damu Baffan mu da maganar ya kara aure, Ya kasa samun wadda zai aura, Shine aka hada shi da Gaji sunanta Salamatu. Amman fa ta taba aure, Wai auren tane ya mutu, Kuma mijin yana nan wallahi kwanaki ma ya auro wata yar kasan layin mu. Wurin gidan su Tsalha...” Malama Mardiyya ta kada kai tana bi na da kallo, Na sakuto hanci na na goge a rigata kafin na cigaba da cewa, “Toh sai baffan mu ya auro ta, Daku na uku ne a gidan mu, D’aya dakin babu komai cikin sa, Bayan ya auro ta sai tace wai kar ya dakko yar sa dan ba zata rike ni ba, Awajen Baba Ladingo naji( Kanwar Kakana.) Dakyar dai Baffa ya dakko ni ya dawo dani gidan, Shine itama ta karbo dan ta a gidan tsohon mijin ta. Tazo dashi gidan, Ya girme mini sosai, Sunan sa Mudi. Tunda tazo gidan mu ta gaje gidan, Dakuna ukun dake gidan mu biyu suka zama mallakin ta, D’aya nata , D’aya na Mudi. D’aya kuma na baffan mu. Harabar gidan kuma ta mai da rabin sa turke ta zuba dabbobin ta. D’aya dakin kuma dakin girki ne na abinci. Dake babba ne sai ta raba shi biyu d’aya ta zuba kajin ta da zabbin ta da sauran abubuwan kiwon ta. Rabin dakin kuma aciki nake Kwana da taburma ta, “Tunda Baffa ya auro Gajiyalle na shiga kuncin rayuwa, Gaba d’aya bansan farin ciki ba, Kankanuwa ta dani anman damuwa ta mun yawa, Ta kassara Baffa na sam bashi da jarin kansa, Duk yan kadarorin sa ta cinye. Tanata bunkasa harkar kiwon ta Shi kuma yana kara talaucewa, Har takai ta kawo gonar sa guda d’aya ce tai ragowa, Itace yake samu yai noma mu samu na abinci... Wannan shine takaitaccen tarihi na malama!” Malama Mardiyya taja doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai cike da damuwa, “SubhanAllah! Lalle Khadija kina ganin jarabawar rayuwa kala kala. Shysa tun sanda na ganki nake kokonton anya a hannun mahaifiyar ki kike? Ubangiji Allah ya shiga cikin lamuran ki Khadija. Babu komai Kowa da irin tasa jarabawar kinji? Da’din ta na gaba, In Allah ya yarda kuwa, Zaki tuno munyi zancen nan. Kina zuwa Islamiyya kuwa?” Nai saurin kada kai alamun a’ah! Nan ma kai ta sake girgiza cike da tausayi murya na rawa ta sake cemin, “Kenan baki iya karatun addini ba Khadija?” “Ban iya ba Malama, Har sallah dik banayi Malama. Makarantar allon garin nan maza ne kawai keyi. Islamiyyar kuma can alfindi masu kudi ke kai yayayen su suyi. Toh yanzu nema mai gari yace zaku dinga koya mana ko Malama?” “Insha Allahu kuwa! Da yardar Allah zamu koya muku. Kisa a ranki kuma zaki iya Khadija. Da yardar Allah kanki zai waye da komai. Duk abunda baki gane ba ki rika tambaya ta kinji! Ki kuma dauke ni tamkar yayar ki. Kinji ko?” “Eh Malama. Nagode Allah ya saka da alkhairi..” “Amin.. Muje na raka ki ajin kinji? Cikin satin nan kuma zan baki uniform kyauta da takalmi, Da kayan wanka. Kinji?” “Nagode Malama.” Bayanin asambuli ta min, Dama sauran abubuwan da suka shafi harkar rubutu, Sannan ta riko hannu na, Ta raka ni har aj. Malam auwal ya zabga min harara nima na rama harda karin gatsine gatsine. “Wallahi karkaryaki zan yi dan bana daukar rai ni. Kizo nan kuma ki zauna ta yadda in kinyi ba dai-dai ba in zaneki.” Ya yi maganar yana nuna min gaba, na kalli karshen ajin naga babu kowa kuma Uwande tana gurin tana siyar da yajin masau, can nake son na zauna amman mutumin nan yana neman ya kwafsa min. Na rike kuguna ina cizon leban kasa tamkar wace take shirin yin dambe. “Ina jin dai baki ji abin da nace miki ba ko? Khadija ki shiga hankalinki kar kisa musa kafar wando daya da ke, zo ki zauna nan gurin.” Ganin yadda ya kafe sai akan dole sai na zauna a gaba yasa naje na zauna ba dan zuciya ta na so ba. Yaci gaba da koyar damu gaba daya bana fahimtar abin da yake cewa, dan tunani na da hankali na duk suna gurin Uwande dake sai da kayan kwalam da makulashe. “Ke Khadija tashi ki karanto min abinda na koyar daku yanzu.” Na dafe kirji ina zaro idanuwa nace, “Ni kuma malam! Na shiga uku ni Dije yo me naji kana koyarwa?” Da alama yaji matukar haushi duba da yadda ya tsuke fuska yana min kallon tsana dan ina da tabbacin na rashin son zamana a ajin ne. Ya sake canza min guri ya maida ni kusa da kujerar da yake zama idan ya gama zazzagawa cikin ajin, saboda wai tsokanar na kusa dani da nake yi shine ya hanani sauraran bayanansa. Yaci gaba da nanata mana A to Z, sauran yara suna fada dai dai sabanin ni da wasu da muke fadin. Ah be ch dh eh af gh.. Shec ai de ke al af-af, daga wadannan harrufan duk bana iya fada dai dai, amman daga O zuwa karshe duk ina iya furtawa yadda suke. “Very good Siyama, zan baki kyauta don yau kinfi kowa kokari zoki karba.” Ya kira Siyama ya mika mata alayoyi da biskit. “Malam nima fa nayi da karfi.” Nayi magana hankali na a tashe ganin an bada kyauta. “Rufe min wannan kazamin bakin naki, kinyi da karfi kina wani Ah be. Sai ki bari idan kin iya cewa A b sai asan kin yi koda a hankali ne.” Da zumudi nace. “Da gaske idan nayi dai dai gobe zaka bani nima?” Ya fara hada littattafansa yana cewa.... .. ASHA HUTUN SUNDAY LPY❤️ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _ZAFAFA 5 (2021) NA KUDI NE, DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHIN NERA 700 KACAL! KA/KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SIYA DA KUDIN KI KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI, KA/KI/KU GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU SIYARWAR!!! DOMIN SIYAN NAKI TUNTUBI: +234 903 318 1070 KO +234 903 234 5899, AKWAI ‘KARUWA SOSAI ACIKIN WADAN NAN LITTATTAFAN😍MUNA FARIN CIKIN KASANCEWAR KU A TATTARE DAMU😘 MASOYAN MU ABUN ALFAHARIN MU🙌🏻_ _*KIBIYAR AJALI..!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🥰❤️👑🏹 _(PAID STORIES/ZAFAFA 5 BOOKS DIN KUDI NE..)_ _*MALLAKAR: NANA HAFSAT_* _(MISS XOXO)🧕🏼_ _*BABI NA: 7_* _*Wattpad:missxoxo00_* *** ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ “Oho! Ke ba zaki samu ki iya ba har sai zan baki abu?” Na ce, “Ah! Yo malam ana aikin wahala ne yanzu? Ai kawai mutum ya yi aiki a bashi shine kawai magana.” “Allah ya shirye ki.” Ya fada yana mai fita daga ajin, ni kuma nayi tsalle na koma gurin Siyama dan na kwashi rabona, da yake tasan hali na komai guda-guda ta bani sauran kuma ta gutsiran musu ta basu ana ta hira. Mun dade a makarantar saboda idan wannan malamin ya shigo ya fita sai wani ya shigo shima ya yi surutunsa ya gama bana fahimta har aka tashi, ina komawa gida na tarar Mudi ya dauki akuyar Gajiyalle hannunsa rike da doguwar wuka yana jan akuyar yana fadin. “Wallahi sai na siyar da ita, nace miki bani da kudin da zan kama sana'a ki bani jari kinki. Nace ki samomin sana'a shima kin shafawa idanunki kwali dan haka dole ne yau na siyar da wannan abar dan nima na dogara da kai na.” Dariya ta kusa kamani ganin yadda Gajiyalle take bin Mudi tana rokonsa tamkar wani mijin ta ko mahaifinta, yadda take riko shi yana ture ta zaka yi tunanin ko laifi tayi masa yaki yafewa. “Dan Allah Mudi kabar min abubuwan nan suci gaba da girma suna hayayyafar wasu, idan kana min zari day-d'aya ai zasu kare. Kabari yau din nan zanje wajan mahaifinka na karbo ma jari mai yawa.” “Naji, idan kin karbo ki rike kudin a bakacin wannan akuyar da na dauka.” Ya yi tafiyarsa hankali kwance, babu abinda ya damesa da yadda yaji Gajiyalle tana kuka tana ihu kamar wata tababbiya. Ni kuma na karasa kusa da ita wai zan lallashe ta tunda naga babu mai bata hakuri, makota ma basu shigo ba bare asa ran zasu bata hakuri su taushi zuciyarta. Nasa hannu zan kamo nata tayi saurin sanya kafa tare da ture ni na buge da bango, dai dai lokacin Baffa ya shigo kuma yaga yadda ta ture ni. Ya kalle ni ya kalli Gajiyalle daga karshe yace dani. “Ummina me ya faru?” Na tashi tsaye ina karkade jiki na tare da turo baki. “Ba Mudikalle ne ya daukar mata a....” Ban karasa ba tayo kai na tana cewa, “Munafuka yiwa mutane shiru, daman kallon mu kike kina sauraro dan ki dinga zuwa kina gayawa mutane? Ina ruwanki yar jakar uba? Mudikalle dai nawa ne dan haka ba komai ɗan ya dauki kayan uwarsa. Ke yanzu ba hanyar lalacewa kika dauka ba? Yanzu daga bokoko kike shegiya, shi sana'a zaije ya fara ya zauna da mutuncinsa.” Na kalli Baffa naga ko zai ce wani abu amman ya yi shiru sai hula ma da ya gyara tare da wucewa dakinsa yana cewa. “Toh shikenan Allah ya kyauta.” Haushi ya kamani, Ban taba ganin miji irin Baffa na ba. Duk gidan da nake shiga matan suna tsoran mazajen su amman banda Gajiyalle da Baffa na, gabaki d'aya rayuwarsu ta banbanta da ta sauran ma'aurata. Gaji ta kuma kai min doka na goce hannunta ya sauka jikin bango ta kuma sakin wani ihun tana zagi na. Waje nayi dan nasan ranar ko kanzo bazan samu ba dan haka gwara naje na nemo abincin da zanci. Karatu kuwa gabaki d'aya na manta dashi bare na tuna da kyautar da malam Auwalu ya bawa Siyama, ko kuma dan be karfafa min gwiwar cewa zai bani ba shi yasa na manta oho. Haka dai na yini a waje sai dare na sake komawa gida, da nayi sallama ma bata amsa ba ko haushi take ji har lokacin oho mata. Na samu waje na kwanta ina ta uban nishi saboda naci tuwo a gidan su Nafisa ci na hauka saboda sai da kowa ya tashi ya barni a wajan kwanon. Gajiyar wasan jiya da kuma haushi na da Gajiyalle kiyi yasa na makara da tashi, sai kusan karfe takwas da kwata na farka. Ina ta hamma na shiga bandaki na fito ina kallon kofar dakin ta naganshi a kulle tasa tsumma ta kulle kofar alamar ta fita unguwa. Na shiga dakin Baffa yana kishingid'e yana sauraron radio ya kalle ni cike da mamaki yace. “Ummina baki tafi makaranta ba daman?” “Makaranta kuma Baffa! Wacce?” Ina turo baki ina maganar dan sam na manta da ita. “Boko da kika fara zuwa mana jiya, ina nan ina murna kina can kina ta zuba karatu ashe kina cikin gidan nan Ummi na.” Nayi saurin bubbuga kai na jin yana motsi wanda bana raba d'aya biyu kwarkwata ce ko amosanin ka, nace. “Aradu na manta da ita, yo nifa yanzu na tahi Gajiyalle ko tahi na bata yi ba kuma yunwa nake ji Baffa.” Gefansa ya duba ya dakko wani kofin sulba ya miko min, nasa hannu na karba. Koko ne ya sake miko min kaushi mai dauke da danwake yace naci. Ina ci muna hira yana cewa nayi sauri na tafi makarantar. “Baffa har kyauta ake ba yarwa a ajin mu.” “Masha Allah, kema ki samu ki ciwo babba kinji Ummina?” “Yanzun nan ma kuwa Baffa, dan ma dai malamin ba hi da mutunci walle. Baya sona he ya yi ta zagi na yana kira na da yar tallah.” Baffa ya girgiza kai dan shima yaji babu dadi yadda naga fuskarsa ta bayyana. Ina gamawa ya bani naira biya na dauki hijabi na da yaci uban dauda na tafi ina wake-wake na. Kai tsaye ajin mu na jiya na shiga, ganin ba malam Auwal bane yasa nayi saurin fitowa na kuma lekawa d'aya ajin nan kuma malama Mardiyya ce, na kuma fitowa da gudu, tana ta kira na amman nayi mata banza saboda yau ajin da malam Auwal yake nan nake son zama. Can na hangoshi a ajin yara wato ecc yana ta raba musu alawa suna ta murna, ba zato kawai yaga ana miƙa masa hanu, girman hannun yasa shi saurin kallon mai shi muka hada ido na sakar masa dariya shi kuma yana hararata yace. “Ke kuma daga ina kamar wata aljanna?” “A bani nima.” “Me?” “Alawar da kake rabawa.” “Ke wai me yasa baki da hankali ne? Kinga sa'anninki a nan wajan?” Kamar ban san abin da yake yi ba, idanuwana suna kan alayoyin yaran ina ta hadiyar yawu. Ni gaba d’aya ba damuwa nayi da gasamin maganganun da yake yi nayi ba. Fatana dai ya dankamin alewar da yake rarrabawa yan yara. Na sake matsawa kamar zan shiga jikin sa, Ya tsula min tsumangiya ko zafi ma babu. Na kwashe da dariya ina karkade inda ya dake nin, Ma’ana dai na mayar masa da kayan sa domin ba zafi tai min ba. Cike da mamaki yake duba na, “Zaki matsa ko sai na kara zuba miki wata?” “A hayye nanaye! Malam Lauwali kenan. Yo dan wannan dukan naka shine me zafi? Yo ko gajiyalle takan dau lokaci tana kirbata kafin nayi kuka. Nide yanzu dan bani guda d’aya ko rabi ce Malam Lauwali.” Zubamin wata shaudar yayi yana huci, “Ke waye Malam Lauwalin? Ni sa’an wasan ki ne. Naga alamun tsantsar reni a tattare dake. Kneel down!” “Lid-dawun? Me kenan! Ayyo. Tab! Yasin na mance sunan kane Malam.” “Kneel down! Bush girl!” “Lid-dawun! Bushgyas. Nifa kayi da yaran hausawa bana arna ba. Dan bansan me kake nufi ba.” “Zaki sani yanzu kuwa. Jeki tsakiyar ranar can ki tsugunna awajen akan gwiwoyin ki, Duk malamin daya ce ki tashi kice nace a’a.” “Tafi nono fari.. a hayye sha madarar lilo..” “Ke me kika cewa.?” Ko kallon sa banyi ba, Na kwaye rigata na zuba gwiwoyina a kasa, Inata sauke masa kwandon tsinan taka. “Matsiyaci, akan ya bani alewar yana bakin cikin zan da zanyi. Allah ka saka min.” Ina daga nesa ina zabga masa harara, Da sauri ya taho ko duka na zai yi sai kuwa ya bige da kyauren kofar ajin, Me zanyi inba dariya ba? Na shjga kyakyatawa kuwa ina nuna shi. Cikin haka Malama Mardiyya tazo ta same ni, “Khadija me kike anan!” “Malam Lauwali ne nasan, Ya hanani alewa, Ya shasshauda min tsumangiya, Shine nan kuma yace nazo na zuba gwiwoyina a kasa. Ai kuwa gahi can ya doke gohin sa a kyaure.” Na karasa ina babbaka daria, Malama Mardiyya ta girgiza kai kawai, “Malam Auwal sunan sa ba Lauwali ba. Kuma ki dena yin abunda Za’a dake ki. Sannan malamai tamkar iyayen ka suke kinji? Domin daka baro gida kazo hannun su, Duk wani abu da zasu saka dole kayi. Sai yanzu kikazo makarantar?” “Yasin Gajiyalle ce bata tahe ni ba, Jia da na koma Mudi ya janyo dan akuyar ta zai sayar. Taita ife-ife tana rokan sa ya bari ai kuwa yaki yadda ya tafi da akuyar nan, Yace ai yace ta bahi kudin jari tak’i. Hi nefa naje rabiyar fadan ta tattake ta doke ni da hyarbebiyar k’afarta a salansar kirji na. Ai kuwa inaga tun duhun safiya ta fice. Hi ne fa motsin ta da ban jiba ya makarar dani, He ba dad’ewa na zo.” “Oh ni Mardiyya! Kayan jiya kika sako, Kinyi wanka kuwa Khadija? Sallah fa kinyi da asuba?” Girgiza kai nayi, “Yasin da asubah ina ta narkar bacci na, daman masifar Gajiyalle ce ke tahi na, toh kuma ba tayi ba shi yasa ban san sanda akai asuhabin ba. Wanka kuma dame zanyi hi Malama? Ba kayan wankan fa.” Na karasa fada ina sosa kai na. “Ko dai qudubus ko kwarkwata ce a kan nan billahil lazi. Gidan d'an wanzan zanje ya yahe gahin gaba d’aya.” “Subhan’Allah! Allah ya shiga lamarin ki Khadija. Kan naki zaki je a yashe gashin? Saboda me Khadija? Ki dena fad’ar haka. Mace yar gyara ce. Ana gyare miki kan ki dama sauran gurare zaki ji kinyi fyes abin ki. Gaki da yalwar gashi tubarkAllah.” “Tab Malama ai gahin kayi na ya hya sharba Malama, Na takwas kenan. Domin da ya iheni da kaikayi zan je a saisaye hi, Hima dan anacen ba’a runtse hekara zai kara cika fiye da na baya.” “Wasu na nema wasu na aske nasu. Toh anyi an gama ba zaki sake aske kanki ba Khadija. Yanzu dai bara na rokar mana Malam Auwal ya kyale ki ki koma aji. .” Tafiya tayi ta ta nufi wajen Malam Auwal, Yana tsaye yana mulmula goshin sa inda ya bige, Ya kumburo yayi suntum. Yana kallon kansa ta wayar salula, “Sannu Malam Auwal.” “Sannu Malama. A gaskiya ki san yadda zaki kiwa headmaster magana ya canzamin ballagazar yarinyar can a ajina. Gaba d’aya na tsaneta tsana mai wuyar fassarawa, Sam batada kamun kai. Yadda kikasan tababbiya haka take abubuwan ta.” “Kayi hak’uri Malam Auwal. Sha’anin Khadija sai ahankali, Yarinya ce data taso da rashin uwa, Tun tana kankanuwa mahaifiyar ta tarasu, Rikon ta ya koma hannun kakarta, Ka kuma san wani goyon kakar yadda yake, Ballantana nan kauye. And still wahalar bata k’are ba Malam, Babanta ya Kara aure, Na takaita maka zance dai a hannun kishiyar uwa take. Kishiyar uwar kuma tazo da agola. And baban ta bashi da say. Tamkar ba shi ya haife taba, Matar tagama dashi. So Khadija tana yin wata irin rayuwa ne mai ban tausayi, Shi ‘da na kowa ne, Shysa nakeson na temaka mata wallahi, Ko Allah zai dube ni ya bani nima mai jin kai. Banason wannan abun ya shafi kwakwalwar ta yasamata psychological trauma Idan ta manyanta. “Saboda she’s depressed. Ina tausayin kai na ina tausayin baiwar Allahn nan. Gaba d’aya banda neman abinci da shiga ruguntsumi ba abunda ta sani, Ba sallah bare sanun fannin islama. Kawai rayuwa take tamkar mutum mutumi. So please Malam Auwal.. please ka temaka kai ma mu temaki Khadija daga fadawa kogin halaka, Ka temaka da karfin ka da karfin iliminka ka nunar da ita rayuwa, ‘Ya mace ce dake bukatar tattali. Kuma kalle ta mana, She’s young. Kai ina tausayin Khadija.. Na cika ka da surutu taje aji? Kaji?” Malam Auwal ya daga kafada yana furzar da iskar bakin sa, “Tsabar duhun kai ce kauye ta ba kauye, Ta zauna ta sharara miki karya kin yadda. Ni ban yadda ba gaskia. Ina ban yadda ba. Irin wa’innan Yaran gasunan acikin gari, plan suke had’awa da iyayen su fa suyi ta samun kudi haka. Look Malama Mardiyya shine your eyes, Yarinyar can muguwar makaryaciya ce. Crook ce da kike ganin ta haka. Hum Uhm” “Au baka yadda ba kenan Malam? Baka yadda ba? Duk wannan dogon zancen dana maka. Ai shikenan yayi kyau. Toh ni zan tsayawa Khadija, Kuma na yadda da ita..” INA can ina yar carafke Malama Mardiyya ta dawo tana yak’e, “Tashi muje aji Khadija, Sannu! Karkad’e jikin naki kinji?” Karkade rigata nayi, Na mike muka tafi har aji ta raka ni. Yau uwande ma kafu kaza ta kawo, Na lashe lebe na na koma wajen ta kafin Malam Auwal ya shigo, “Uwande uwar kirki.” Uwande ta sheke da dariya tana buga k’afarta, “Kai Dije, Yau kuma ni ce uwar kirki.” Na kada kai ina murmushi, “Walle Uwande kinada kirki sosai, Kefa abunki be rufe miki ido ba irin na munafukar can.” Na karasa fada ina mai nuna Siyama. Uwande ta sheke da dariya, “To ai kuwa nagode, Me Za’a baki?” “Kafu tsire zaki bani na biyar..” Na ciro biyar din da Baffa ya bani na mika mata. Karba tayi, Ta bani har kulli uku, Ta kyautamin ne saboda nace mata uwar kirki. Mik’ewa nai na koma waje na na zauna. A hankali na dinga dangala ina sha ina lumshe idanu na, Hekace tsire nake ci, Kafu tsire naman talaka. Cikin haka Malam Auwal ya shigo yana kwambo, Yan ajin suka mike suna gaishe shi, “Gudu moni ankul..” Zare idanu na shiga yi ina cigaba da bincikar Kafu tsire ina afawa a baka. “Ke.. Taso Ki zauna anan. Ki kuma wullar da duk abunda kike ci” “Ni ba abunda nake ci Malam.” “Ni zaki wa k’arya? Kai jeka ka dau koma Meye ka wullar.” Ya ce da Usainin Marka dake gaban sa, Na zabgawa Usaini harara Ina kudindine ledar a kayi na, “Walle ka taba ni sai na yi gunduwa gunduwa da kai, Kasan hali na dai, Oganniya ‘kaya batasan na gida ba. Babu ruwana da Marka kawar Ladingo ce, Yanzun sai na caskala ka, Na casaka nayi kutubal da kai.” “Ke me kike cewa, Dalla Kai kwace koma menene ka wullar, Ki tabashi kiga yanda ake sauya halitta.” Damara naci na damke hannu na, Amma dake Usaini ba shi da kirki yana kuma tsoron Malam Auwal haka ya wafce ledar ya jefa a kwata ta kofar taga, “Kutumelesin kan babban balain dirimin durbun, Walle yau ba Malam Auwal ba, Ko Hakimi ne zai zo daga birni sai na lakada maka na jaki. Zaka san ka taba mallaki na yau.” Raina a bace na koma gaban Malam Auwal na zauna, Gaba d’aya hankali na baya wajen jira kawai nake a tashi na tisa keyar Usaini mu dambatu. Malam Auwal ya fara mana darasi. Ranar kwata kwata ban kara shiga harkar sa ba, Duk neman yadda zai ya dake ni yake sam naki bashi hadin kai, Usaini kuwa yayi tsuru tsuru yana raba idanu, Ana kada kararrawar tashi na dubi Malam Auwal Sai da naga ya gama hada kayan sa ya fita nima na fice, A bayan makarantar na zakulo Usaini yana ta gumi shi kadai, Na mikawa Uwande jakar bayan sa kafin na ja kafar sa na shatale shi ji kake tim. “Tahi dan kundin uban ka mu tafi ‘filin kaci uwa ka’, Yau anan zan lakada maka na jaki, Kuma mu tafi wajen mai gari ya mana shari’ah. Banza mai bajajjen hanci.” Muna tafe da zugar yara ana min kirari har muka karasa ‘Filin kaci uwa ka’ A filin ake dambatuwa musanman Idan mashahurin fada za’ai. “Dije-Dijangala Oganniya ta Gajiyalle mai yar hakiya, Yar baffan ta. ‘Kaya baki san na gida ba.” Haka zugar yara keta fada, Na shata layi tsakanin mu da Usainin Marka, “Alo tsiya, Alo danja, Hege ka fasa, Dan halak sai yanka. Ho ni Dije, Yar gala ta baffan ta.. Tahi mu dambatu Usaini, Har ni zaka wullar wa abu na a kwata. Ko ka Kanta fada uku na taba tare maka, Ba ma siya kayi ba, Kawai mutinci na maka na shigar maka. Wai ni? Ni Usaini zaka yiwa haka. Yau zan nuna maka menene halacci.” Kafar sa na janyo yanata kuka yana rok’o na, Na shiga kirbar sa ina sake tamaula dashi, yara sai ihu suke suna tafamin. Cikin haka sai ga Galin mai gari ya iso, Yana zuwa ya raba mu ya tisa k’eyar mu wajen mai gari, Dadi kashe ni dama abinda nake so kenan. Na zube akan taburma gaban mai gari, “Alhamdulillahi, Mai gari dama daga can wajen ka zan yo walle.” “Dijangala kawo k’arar ki wajen nan ba’adadi. Yau kuma me kika yi?” Mai gari Jamilu ya tambaye ni yana mai cigaba da jan carbin hannun sa, Na gyara murya ina nuna Usainin Marka. “Kanaji mai gari? Usainin Marka, Wai Usainin Marka ni zai wa butulci?” Mai gari yayi murmushi yana kallo na, Sauran manya dake wajen suka shiga keta daria, “Billahil lazi, Na tare masa fa’da ba adadi mai gari. Amma dan bakin munafurci da kinibibi da tsagwaran mugun ta, Kanaji mai gari?” Mai gari ya kada kai yana sake dubana da kyau, “Yauwa, Don Allah mai gari ya dace abunda Usaini ya min? Baffa na ya bani nera biyar, Ai kasan Baffa na dai. Toh ya bani biyar. Mugun Malam Auwal d’innan dama tunda naje makarantar ya tsane ni, Domin yau ma yasa na zube gwiwoyi na kasa Wai Lid-dawun. Toh nayi! Da biyar din da Baffa ya bani na sai Kafu tsire awajen Uwande, Ko Uwande?” Uwande ta kada kai alamun ba Karya nayi ba. Na sake gurfane na cigaba da cewa, “Hikenan sai na sai na biyar. Na koma waje na na zauna, Haka kawai Malamin nan yana higowa sai ca yai wa Usaini Wai ya kwace koma menene nake ci ya wullar, Fisabilillahi mai gari Kud’i na ne fa, Na saya. Kuma sanda na saya babu malami a ajin. Nafa boye a gahi na. Amman mai gari walle sai da Usaini ya zaro hi ya wullar a kwata. Shine nace daman bayan na gama narkar sa dole ne muzo kama shari’a. Dan banci nanin ba, Nanin ba zata cini ba ehe.” Mai gari ya sauke k’atuwar ajiyar zuciya ya dube ni ya dubi Usaini kafin yace, “Usaini! Wai haka akayi?” “Haka akai mai gari.” Mai gari ya girgiza kai kawai, Ya zaro nera goma a aljihun sa ya miko min, “Shikenan haka yayi?” Nai saurin kada kai ina tuno dankalin Asiya da zan siyo a bakin kasuwa, “Toh madalla! Amma dan Allah karku sake fada kunji? Ku basu kunya su wadannan malaman, ku tsaya kuyi karatu. Muyi alfahari daku, Muma ya zamto ana damawa da karkarar mu a birni a dena renamu, Domin kune manyan gobe, Mu lokacin mu ya wuce.” “In Sha Allah mai gari za kai alfahari damu, Ni dinnan nan da wasu hekaru zaka ganni a gidan talabijin ko radiyo ina kwarara bayani..” “Allah yasa Dije! Allah ya nuna mana..” Mik’ewa nai nayi gaba abuna, Ko takan su Uwande ban kara bi ba, Na nufi Y’ar kasuwa sawo dankalin Asiya. Sai da nayi kwanaki hudu daga hutun asabar da lahadi na zarce litinin da talata, sam na manta da makaranta sai ranar labara naje kallon wasan kauraye da aka yi a bayan gari kawai na hadu da malama Mardiyya zata tafi gida dan lokacin an tashi daga makaranta. Ta kalleni fuskarta babu yabo ba fallasa ta kira ni naje da sauri ganin tana saka hannu cikin jakar ta, a tsaye ina dashe baki nace da ita...... ... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _ZAFAFA 5 (2021) NA KUDI NE, DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHIN NERA 700 KACAL! KA/KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SIYA DA KUDIN KI KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI, KA/KI/KU GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU SIYARWAR!!! DOMIN SIYAN NAKI TUNTUBI: +234 903 318 1070 KO +234 903 234 5899, AKWAI ‘KARUWA SOSAI ACIKIN WADAN NAN LITTATTAFAN😍MUNA FARIN CIKIN KASANCEWAR KU A TATTARE DAMU😘 MASOYAN MU ABUN ALFAHARIN MU🙌🏻_ _*KIBIYAR AJALI..!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🥰❤️👑🏹 _(PAID STORIES/ZAFAFA 5 BOOKS DIN KUDI NE..)_ _*MALLAKAR: NANA HAFSAT_* _(MISS XOXO)🧕🏼_ _*BABI NA: 8_* _*Wattpad:missxoxo00_* *** “Hannu malama Mardiyya.” “Yauwa Dije gwara da Allah ya had'a ni dake yanzu. Me ya sa bakya zuwa makaranta kwana biyu, na bincika ance min kina nan lafiya lau kawai ganin dama ne baki zo na.” Na tafa hannaye ina dariya, “Malama tawa!” Maganar tawa ta fito cike da sauki dan ina son matar nan saboda tana sona. “Ina jinki gaya min meke faruwa?” “Babu komai wallahi, mantawa nayi ma da makarantar.” “Innalillahi! Dije daman baki saka son zuwa makarantar nan a zuciyar ki ba?” Na zaro ido waje, “Kai! Malama ai bazan iya sata a zuciya ta ba, kinga girman makarantar kuwa?” Ta girgiza kai, “Ni ba haka nake nufi ba, ina nufin kiji kina son zuwa koyan karatu a cikin ranki. Haba Khadija ya za'a yi kina girma amman baki dena wasu abubuwan na shirme ba? Yanzu ina zaki je?” “Oho, ni daga wajan kallon wasan kauraye nake.” Ta girgiza kai tare da gyara jakarta a kafadarta. Kallo na tayi sosai sannan tace. “Muje ki nuna min gidan ku” Babu musu na amsa mata muka tafi muna hirar mu har muka hadu da malam Auwal zai tafi gidan liman, yana kallan mu amman yaki kula mu itama malama Mardiyya bata yi masa magana ba har muka wuce. Da sallama a baki na muka shiga ciki, Gajiyalle tana tankaden garin dawa da zata yi tuwo. Taki amsa min tayi tunanin ni kadai ce, sai da taji muryar malama Mardiyya cikin sallamarta da dole ne duk wanda yake cikin gidan ya jiyo. “Sannuki da zuwa bakuwa, shigo mana.” Gajiyalle ta fada tana janyo tabarmar dake bayan ta, naje na karba ina ta faman rawar kafa saboda malama tazo gidan mu. Malama Mardiyya ta zauna tana bin gidan mu da kallo ta ko ina, muryar Gaji ta katse mata tunanin ta inda tace mata. “Ina wuni?” “Lafiya lau, ya gidan?” “Ƙalau muke, sai dai ban wanyeki ba.” Gajiyalle tayi maganar tana ajiye rariyar da take tankade da ita sai kallon malama take yi kamar wacce aka kafewa idanuwa a kanta. “Allah sarki daman ba zaki sanni ba gaskiya. Ni malama ce a wannan makarantar da aka bude. Kwana biyu naga Dije bata zuwa, shine na hadu da ita a hanya nace dan Allah ta kawo ni gidan su.” Tunda Gajiyalle taji tace malamar mu ce shikenan ta sauya fuska tayi kicin-kicin da fuska da alama bata so hakan ba. Malama Mardiyya ta ce na zauna na samu guri a bayan ta na zauna dan ban san me zata fada mata ba, kar naje Gajiyallen ta kawo min naushi. “Maman Khadija dan Allah me yasa baki tursasata akan zuwa makaranta? Gashi duk tayi wani yarbatsai kamar wata marar mafadi. Dube ta ɗan Allah kamar ba mace ba sai tsami take, ilimi fa yana da dadi Maman Dije, dan Allah kiyi kokari ki canza ta. Ni ban zo dan na gyara miki wani abun ba, amman dan Allah kisa ido akan ta koda wajan kula da ibada ne, ace kamar Dije amman bata san meye sallah ba bare tayi? Muna so muga an samu manya a cikin kauyan nan, amman burin mu ba zai cika ba sai da taimakon ku iyaye, musamman ku mata.” Gajiyalle tasa kafarta ta buga a kasa tare da kankance idanuwa tana mai nuna malama Mardiyya da yatsa tare da cewa. “Ke! Dakata min da wannan surutun naki haba, cacacaca kamar wata mai rubabban baki. Yo haka ne mana kinzo sai barin zance kike kamar wadda aka budewa makogwaro. A hayye na naye yau na ga ikon Allah, kizo har gida na kice zaki tsara min yacce zan dinga yin rayuwa ta? To ko hi mai gidan be isa ba ballantana wata ke fankan fayau. Dije kuma ai gaki gata nan sai ki maida ita yadda kike so kinji uwata? Ki tashi ki bar min gida kafin na dakko tabarya na ragargaji kanki walle.” Da sauri naga malama ta tashi tana rataya jaka, ta kuma kallon Gajiyalle cike da takaici sannan ta wuce ta bar gidan. Nima juyawa nayi da nufin na bi bayan malama naji ta riko min riga ba zato kawai ta wanke min fuska da mari tana kuma dukana. “Shegiyar yarinya kawai, bari na kashe ki na huta da janyo min magana da kike yawan yi. Saboda rahin mutunci irin naki sai kije ki dinga taho min da mutane, wato zuwa kike kina min hirri a waje ko? To walle talle ko babanki bai isa ya dinga yi min surutu a gari ba.” Ta dinga duka na malama Mardiyya na ji amman ta kasa dawowa saboda kar taje bayan ta tafi ta barni cikin wata fitinar tunda ba tare zamu zauna da ita ba. Ranar nasha wahala a gurin ta, nayi wankin kayanta da wanke-wanke da shara ta hanani fita ko ina sai da aka yi magariba sannan na gudu da ta shiga bandaki. Washe gari tun da sassafe na tafi gidan Sahura nayi layin karbar sadakar koko da liman yasa a dinga bayarwa. Na karba nasha daga can kuma na yi wucewa ta makaranta duk da cewa babu kowa haka na samu guri na kwanta har wani baccin ya yi gaba da ni ban sani ba. Hananiyar mutane ita ce ta sani farkawa naga har an fara taruwa, na tashi ina ta faman zaro ido karaf miƙa hada idanuwa da malam Auwal yana rike da bulala ya ce min. “Nan ina ne?” “Aji.” “Shi ne kika zo kina ta yiwa mutane munshari kamar kina kan gado?” Na yatsina fuska ban kula shi ba. Mtsww ya ja tsaki ya bar gurin ya zauna akan kujerar malamai yana ta bude littattafai har aka gama zuwa. Ya dakko rigester yana kiran sunaye, yana zuwa kan sunana ya dinga tsaki saboda ganin fashin da nake yi a ciki yafi na kowa yawa, kamar ba zai kira ni ba sai kuma ya ci gaba da kiran ragowar mazan. “Maude Nalami...?” Ya amsa. _“Present Sir..”_ “Yahaya Liti...?” Shima ya amsa. _“Present Sir..”_ “Khadija Baffa...?” Ina sosa cikin kunne na ina amsawa. _“Na'am..! Gani..!! Nazo..!!! Sa farazen...!!!!”_ Malam Auwal ya sanya kasan biron hannunsa cikin baki yana taunawa da hakori saboda takaicin da na bashi. Ya hura iska daga bakinsa yana sake matse ido kamar wani mai jin ciwon kai, ya dago yana kallo na cike da tsantsar tsana wacce na rasa dalilin da yasa yake min ita. “Baki da kunya Khadija, amman zan gyara miki zama a cikin ajin nan wa wuya kawai.” Yaci gaba da kiran sunaye jefi-jefi yana jan tsaki, ni dai tunda ya kira suna na ban sake kula shi ba, ana haka sai ga shi malama Mardiyya ta aiko cewar naje office na same ta, na tashi na fita tun kafin ma ya bani izinin tafiya. Ina zuwa ta taso tace muje ni dai ban tambaye ta ko ina zamu ba dan duk inda zata kai ni bin ta zanyi shi yasa ma ban tambaya d'in ba. Kai tsaye muka tafi gidan mai gari, bayan sun gaisa da matan sa dama mai gari ya riga ya sanar da su zuwan ta tayi mishi bayani tun jiya cewar zata zo da ni. Mayafi ta gyara sannan ta dakko wani zani a cikin wata bakar leda ta miko min wai na cire kayan jikina na daura shi, nayi kamar yadda tace daga nan tace muje bandaki. Na shiga ita kuma ta dibo ruwa cikin bokiti ta kai bandakin, ta kuma dibar wani ta kai sannan ta dakko soso da sabulu ta shigo tace na cire zanin nawa na cire. Allah sarki malama Mardiyya mace mai mutunci mai kyauta da yin alkairi fisabilillahi. Sai da tayi min sabi uku harda goge faso duk da cewa bai fita ba amman an rage ba laifi. Na daura zanin muka fito wata iska naji tana shiga cikin jikina mai matukar dadi da ratsa zuciya, na dinga jina tamkar a cikin furanni masu launi nake. Ta shafa min mai sannan ta ciro uniform da sabon pant na saka ta kuma shafa min huda da kwalli, tun a gidan su Baraka wato amaryar mai gari suke ta yi min tsiya, ni kuma ina ta dashe baki saboda farin cikin yadda nake jin na sauya gabaki d'aya. “Ko kefa Khadija, kinga yadda kika yi kyau kuwa? Dan ma dai ba ayi kitso ba, amman soon shima zan yi aiki a wannan gashin naki.” Malama Mardiyya tayi maganar tana nuna min wasu kaya a ledar da ta zo da ita, tace min idan an tashi daga makaranta nazo wajan Baraka na karba, riga da skirt ne na atamfa, sai dai daga gani ansa saboda ba sabo bane amman masu kyau ne tunda da kyansu har yanzu. Ta kama hannu na muka fito, mutane tun a hanya suke kallo na suna yi min tsiya, a haka muka karasa makaranta ta kai ni har cikin ajin mu, a lokacin daman period ta kusa fita mu shiga ta malam Auwal. Yan ajin mu baki bude suka kalle ni suna mamakin gani na a haka, sai kowa ya fara matsa min kusa dashi wai nazo na zauna ni kuma sai yatsina fuska nake yi, dan ji nake nafi kowa kyau a duniyar nan. “Dije!” “Na'am malam Habu.” “Kinga yadda kikai kyau kuwa? Masha Allah, kai Allah ya sakawa malama Mardiyya da alkairi tayi kokari.” Ina hura hanci na tafi karshen ajin na zauna sai faman bude ido nake yi. Malam Habu yana hada littattafansa yana cewa. “Dama zaki ci gaba da tsafta da kinfi haka mutunci Dije.” Ban kula shi ba ji dai dan magana ma a wannan lokacin wahala take yi min. Malam Auwal ya shigo daman shine last period, ya dinga bin yan ajin da alama da alamar akwai abin da yake nema, na dora kai na akan benci dan bana son ma yaga fuskata bare yace nayi kyau bana son yabon shi. “Ina Uwande da Dijeh?” Ya tambaya yana kallon yan ajin. “Ga Dije nan, Uwande kuma tun dazu ta tambayi malam Habu zata fitsari har yanzu bata dawo ba.” “Guduwa tayi yau ma kenan?” Ya tambaya. “Eh malam tallen wake da hinkafa ta tafi.” “Okay! Ina Dijen ita kuma?” “Malam gata nan ta boye?” Suka hada baki wajan bashi amsa. “Ke Khadija! Ke! Ba magana nake miki ba ne?” Kamar irin a film d'in nan idan za'a nuna star, haka na dago a hankali cike da yanga har na tashi gabaki d'aya. Da ya kalle ni sai da ya murza idanuwa alamar ko yana ganin gizo, saboda dazu ya san na fita kamar yadda ya sanni, amman yanzu ya dawo ya ganni fes kamar ba Dije Oganniya ba. Bakinsa a hangame yana shafa d'an siririn gemunsa ya lashi lebansa tare da cewa. “Zo nan.” Nayi tamkar banji ba sai da ya sake cewa. “Baki ji ba ne?” “Naji, kafa tace take ciwo.” “Yanzu ta fara yi miki?” “A'a tunda zamu dawo nida malama Mardiyya.” Jinjina kai ya yi tare da kallon Siyama da Habi yace. “Kuje ku riko hannun ta ku kawo min ita nan.” Haushi ya kuma kamani, wannan malamin jarababbene uban masifa, Hege! Suka riko ni kawai na fara dingishi kamar wata gurguwa har suka kai ni inda nake zama idan shine a ajin. Ya shiga shafar gemo yana kallo na kasa kasa kamar wani marar gaskiya, sai kawai cewa ya yi. “Kin ganki kuwa? Amman dai ba ke ki kayi wankan ba ko?” Ban san lokacin da na daga masa kai ba alamar 'eh' sai kuma haushin kai na ya kama ni. “Haba ni dai naga alama, toh Allah yasa dai a dore da tsabtar. Yanzu dai ga ki kamar mutum yanzu.” “Kutmelesi! Da ni aljana ce ko me?” Harar da ya watsa min itace ta tunatar dani a yadda na yi masa maganar, nayi saurin sanya hannu na toshe baki na ina muzurai. Ci gaba da koyar damu ya yi jefi-jefi yana kallo na tare da yi min tambayoyi amman duk babu wasu kwararan amsoshi, a haka har ya kammala mana aka kada karaurawar tashi. Ana tashi daga boko mun mimmike zamu tafi gidah Malam Auwal ya dakatar damu ta hanyar biga bencin gaban sa, “Kowa ya zauna..” Kowa ya zauna ban dani, Saboda ni yanzu bakin kasuwa nake son zuwa wajen Habibalo mai awara. Yanzu i war haka ta gama suya zata bayar da burbushin awara sadaka, “Khadija Baffa samu waje Ki zauna, Kin tsaya gandar-dar a tsaye uwa sanda.” “Malam sauri nake yasin. Me zamu maka ne bayan an tahi?” “Uban.. Zaki zauna ko sai na lakada miki duka.” Baki na na cuno gaba, Gwara ya casa ni akan ya hanani zuwa wajen Habi mai awara. “Ke ba zaki zauna..” “Jaraba gad’ar maza. Aikin banza.” Na fada a hankali ina mai sake kafewa a tsaye, Tsumangiya ya d’akko sai dake ni, Sai ga malama Mardiyya ta shigo da littattafai fal a hannun ta. “Ah’ah Khadija mai kike a tsaye?” “Ko ba Malam bane zai daka ni? An fa tahi Malama, walle sauri nake akwai inda zani, Amma ya hana mu ko me zamu masa.” “Zauna kinji? Karatun arabi Za’a fara muku yanzu. Kuma kullum hakan ce zata kasance da yardar Allah. Zan raba muku littattafai da Qur’ani, Malam Auwal zai fara yi muku nasa b’angaren kafin na shigo nayi muku iya matan kina ji?” Kada kai nayi badan naso ba . Na koma na zauna kawai Saboda ganin mutuncin ta. Tana min magana ne a hankali kullum, Sam bata fada. Shiyasa take birge ni. Ba dan inason na zama kamar irin na gidan radiyo da talabijin ba da nazama Malama nima irin Malama Mardiyya. Fita tayi bayan ta babbamu komai, Malam Auwal ya tsaya akan mu yana muzurai, Ni walle gemun sa irin na bunsurun Gajiyalle shi yake ban daria. Na sheke da dariya ina tafa hannaye, “Ke Wai baki da hankali ne?” “Walle dariya kake ban Malam.” “Okay ga mahaukaci yana magana ko.?” “Aa walle ba haka bane..” Na fada ina gimtse dariya ta. Dogon tsaki yaja, “Ballagaza kawai..” Rubutu yayi a allo, Ya juyo yana kallon mu. “Kafin mu fara komai, Zan dinga kiran sunayen ku a rajista shima, Wanda yazo ya amsa da ‘Labbaika Ya Sayyadi..’ Ba kamar na boko da zaku amsa da present sir ba ko sir. Kunaji? Fahimtun?” Muka daga kai muna tafa hannuwa, Cikin nutsuwa ya fara koya mana karatun arabi. Walle da dadi, Sai na samu kai na cikin nutsuwa, Haka ya gama koya mana ya fita, Malama Mardiyya ta shigo, Ta fara koya mana nata bangaren. Ta bamu biskin da ruwan ledar fiya wata. Ta kokkoya mana yadda zamuyi alwala da sallah. Ta k’ark’are mana da, “Sai bayani na gaba akan” 1-Jinin Haila. 2-Jinin Nifasi. 3-Jinin Istihadha. “Ku saurare ni da kyau, Domin duk kankantar mace wataran uwa ce. Yauwa Jinin Haila: Sassan da bayani zai gudana akai sune: A-Ma’anar Haila.B-Alamomin Jinin Haila.C-Muddan kwanukan Haila.D-Shekarun Haila.E- (karancin kwanukan tsarki.F-Rabe-raben Haila.G-Abubuwan da suka Haramta ko karhanta ga mai Haila da kuma ababen da suke mustahabbi gareta.H-Yadda ake wankan Haila.I-Hukunce-hukuncen Haila, “A-Ma’anar Haila:Jinin Haila shine jini wanda yake fita daga mahaifar mace kowane wata na wasu kwanuka. (B-Alamomin jinin Haila:Jinin Haila ja ne wani lokaci yakan sauya zuwa bakii ko ya yi jajur,kuma yana da tunkuza wajen fitowa da kuma zafi, “C-Muddan kwanukan Haila:Mafi karancin kwanukan Haila kwana ukku/biyu ne saboda haka idan ya kasance kasa da kwanaki ukku/biyu ne to ba Haila bane, Amma ance akwai mai zuwa rana d’aya tal. haka nan wadannan kwanaki ukku dole su kasance biye da juna,mafi yawan kwanukan Haila kwana goma ne. “D-Shekarun Haila:Jinin Haila yana farawa ne da cikar ‘ya mace shekara tara saboda haka duk jinin da yarinya karama za ta gani ya fito mata kafin ta cika shekaru tara,to ba Haila ba ne,ko da kuwa yana da siffofi hailar.Haka nan jinin da mace ta gani bayan shekarun daina Haila –Shekarun daina Haila shekaru sittin ne ga wadda take Bakuraishiya,in kuma wadda ba ita ba bane daga sauran kabilu shekaru hamsin ne – Wato dai shekarun soma Haila shine shekara tara,abinda ake nufi da shekara tara anan shine lokacin da yarinya ta cika shekara tara cif-cif wato ba mujarradin shigar ta shekara tara ba a’a sai ta cika shekara tara din cif-cif,haka nan ita ma wadda ta kai shekarun daina Hailar sai ta cika shekaru hamsin cif-cif ba mujarradin shigar ta shekaru hamsin ba. “E-k’arancin kwanukan tsarki:Mafi karancin kwanuka tsarki wato tsakanin wannan Haila da wannan Haila kwanaki goma ne,saboda haka zai iya yiwuwa mace ta iya yin jinin Haila sau biyu a wata amma fa da sharadin a samu tazaran kwana goma tsakanin Haila ta farko da kuma Haila ta biyu.Amma mafi yawan kwanukan tsarki to shi bai da iyaka wato a ce kwana kaza ne. “F-Rabe-raben Haila:Mai Haila imma ta kasance wadda take ma’abuciyar al’ada ko kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba,wadda take ma’abuciyar al’ada itace wadda ta maimaita Haila sau biyu kuma biye da juna haka nan kuma ya kasance an samu dacewa a lokacin da kuma adadin kwanakin,ko kuma ya kasance a samu dacewa a cikin lokutan ka kai ko kuma a adadin kwanakin ka kai,to da wannan ne mace za ta zama ma’abuciyar al’ada mai lokaci tsayayye ko ma’abuciyar al’ada mai adadi tsayayye ko kuma ma’abuciyar al’adi mai lokaci da kuma adadi tsayayye.Ita kuma wadda take ba ma’abuciyar al’ada ba ta kasu zuwa kashi ukku wato imma ta kasance yanzu ta fara wato ba ta taba ganin hailar ba ko sauya kaya,ko kuma ta zamo wadda al’adarta ba tsayayya ba wato tana rawa,ko kuma ta zamo ta manta al’adarta,ita ma wannan wato wadda ta manta al’adarta ta kasu gida ukku ko dai ya kasance ta manta lokacin Hailar ta ko kuma ta manta adadin kwanakin Hailar ta ko kuma da adadin kwanakin da kuma lokacin duk ta manta.To duka bayanai sanka-sanka na wadannan rabe-raben Haila ana iya komawa ga littafan Fiqhu misali littafin Zubda ko Tahrirul wasila na Imam Khumaini. “G-Abubuwan da suka haramta da kuma karhanta ga mai Haila:Daga cikin ababen da suka haramta a gareta akwai yin Sallah,Azumi, [dawafi,Iitikafi da kuma dukkan ababen da suka haramta ga mai janaba kamar taba sunan Allah da na Annabawa da kuma Aimma na Ahlul bayt ko kuma zama cikin masallaci.Haka nan haramun ne ga mijinta saduwa da ita.Wasu kuma daga cikin abubuwan da suke aikata su makruhi ne gareta akwai karatun Alkur’ani mai girma ma’ana daukar Alkur’ani Hizb sittin, Anan zan dakata sai zuwa zama na gaba idan Allah ya kai mu gobe. “ “Wallahi haka kawai na samu kai na da son acigaba da karatun nan, Domin tun ba yau ba. Yalwajin Innarajo na gayamin tafara jini. Billahil lazi na dauka jinin yankewa ne wai ahe sunan sa jinin al’ada. Hi’iyasa Uwande tace Innar ta tace data fara jini ta gaya mata? “Na kada kai ina jijjiga kafata. “Akwai masu tambaya? Wanda bai gane komai ba ya tambaye ni kunga dai yan maza sun fita.” Duk mu kai shiru, Malama Mardiyya ta sake cewa, “Toh Allah ya kai mu acikin satin nan ni zan fara muku tambayoyi. kwa iya tafiya, Shikenan an tashi.” __ _Asubah ta gari masoyan Dije, Ku shirya tsaf Dijangalar ku fa an kusa wayewa, Kada ku manta har yanzu muna kan shimfidar book dinne ne. Ko kun manta da yadda yazo muku a dandano😉? Na gayshe da yan comment box 1, Gaisuwar ku ga dije na zuwa kunne na, Ana gayamin sosai, Na kusa wantsalowa nima cikin box din a dama dani, Amma kafin sannan Nabila shehu, Maryam Saminu suleiman, (Islaha/Rip maryam) , Daughter billy, Da sauran wanda ban anbata ba. 🤲🏻Dije na godia kwarai😘🥰❤️ Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima tare da fatan alkhairi ga masoyan Dijengala dama zafafa books gaba d’aya.. OneLove😘❤️_ _WITH LOVE; MX🧕🏼_ *K & S* *MX* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, DOMIN MALLAKAR NAKI, TUNTUBE MU A NAMBOBIN DAKE KASA* *9* *WASHE-GARI:* *Ko da* na tashi daga bacci na fito tsakar gida, Buta na dauka na dibi ruwa na shiga bandaki. Ina fitowa nayi alwala yadda zan iya naje na bubbuga sallah ta wacce ban san iya adadin raka'o'in da nayi ba, na fito na bar gidan, daman tun jiya da uniform dina na yini kuma na kwana dashi, hakan yasa ina karbo sadakar koko na nayi makaranta hankali kwance. Yau kam ban kwanta ba wajan bishiyoyin dake cikin makarantar na nufa, na kad’o mangwaro na zauna nasha abata babu ko wankewa amman ban damu ba. Har aka fara zuwa sannan na koma cikin yan ajin mu. Malama Mardiyya na zuwa ni ta fara nema, aikuwa ta ganni kamar yar jakuna, ba zaka taba cewa sabbabin uniform bane a jiki na duba da yadda suka ci uwar dauda. Ta kalle ni bayan ta rike habar ta tana cewa. “Yanzu Khadija kayan makarantar ne kika mai da su haka? Amman dai baki cire su ba tunda kika saka su ko?” “Wallahi malama ban cire ba, yo ji nayi anata yabo ana fadin nayi kyau hi yasa naki cewa sai nan da sati biyu.” “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun, Khadija ban san ranar da zaki nutsu ba wallahi. Mu je zan gan ki.” Jiki na na rawa na bi bayanta, Bata yi min magana ba har muka karasa gidajen malamai mata dake unguwar yangayu wato yankin mai gari. Dakin ta muka shiga, Sai tashin k’amshi yake kasan cewar an basu guraran zama, amman duk da ita bata zama saboda tana da aure kuma mijin ta be yarda ta dinga kwana ba, Yasa ta gyara shi saboda ta dinga hutawa kafin ta tafi can. Wata leda ta dakko min ta bani. “Kaya ne. Karki bu’de sai kinje gidah. Yanzu dai ga sabulu da soso zakiyi wanka. Kafin nan zan wanke miki kai yau.” “Kai! Yauma wankan zan yi?.... Malama kiyi hak’uri. Yasin sauri nake zanje wajen Habi. Nagode Allah ya biya ki.” “Zaki zauna ko sai na dake ki tukun na?” Zama nayi, Ina raba idanuwa. Malama tafita ta dora ruwa a risho irin na gidan su Nafisan kansila. Yayi zafi ta kira ni ta wanke min kai na sau ba adadi. Tun yana fitar da wasu abubuwa har ya dena ya dawo farin kumfa. Ta bani sabulu da soso tace na yo wanka a bandaki, Hohoho bandaki sekace dakin matar sarki, Ya hya siminti, Na dirje jikina Sau bakwai kamar yadda ta taba yi min. Kana ta miko min burishi irin na Mudikalle da Makilis nan ma tace na wanke baki na sau uku. Inayi tana matsamin wani har na gama. Walle sai naji kamar ba ni ba. Anya kuwa ni ce? Iska kuwa kota ina ratsa ni take gwanin hya’awa. Ta min kitso guda shida ta shafamin man kai. Tabani sabuwar riga doguwa da takauni ta fesamin turare. Bansan sanda hawaye suka fara zubo min ba. “Malama! Nagode, Allah ya sa miki da alkhairi. Harda takauni, Kaya kawa na amaryar birni? Dama ke kika haife ni, Nagode kwarai malama.” Malama Mardiyya ta jijjiga kai tana murmushi, “Meye kuma takauni Khadija?” “Takauni na k’afa da ake sawa..” “Au takalmi..? Hahahaha! Takalmi ake cewa. Kidena gode min kinji ko? Allah ya bani ikon cigaba da temaka miki kinji Khadija. Allah ya baki miji nagari Aamin.” “Aamin Malama.” Hinkafa da qundun kaza (shinkafa da wake a kauye) ta zuba min, Yasha mayi na k’uli da yaji. Naci nai dam na gyatse. Ta sake koyamin alwala nayo nayi sallah. Raina fyes. Jikina sai tashin K’amshi yake. Na jima a gidan malama kafin na tafi gidan mu. Tamin gargadin kar na soma bawa Gajiyalle komai rintsi nace mata Malama zata gayawa mai gari inde ta k’wace. Hakan kuwa akai ina komawa gida na boye a akurkin kajin daya lalace na daki na. Raina fyes na kwanta bacci ya kwahe ni. Saboda tsabar iskar da take ratsani yasa baccin nawa ya yi dadi harda mafarkai masu ban sha'awa. Ana ta kiraye-kirayen sallar karfe d'aya na farka ina sakin hamma. Na fito tsakar gida ina kalle-kalle na hango Mudi yana cin kwadon zogale. Zuwa nayi na dauki buta ya yin da ya bini da kallo gani na cikin doguwar riga da be sani a ciki ba, gashi dama babu dankwali da kan nawa garin bacci ne ya zame ni kuma saboda nishad'i yasa naki tsayawa na daura, na wuce ina zuba kamshin turaren da malama ta fesa min dan har lokacin be fita ba. Duk da cewa ya gama ci amman sai yaki tashi daga gurin har sai da na fito a lokacin ne Gajiyalle ta fito daga cikin dakin ta kawai ta bini da ido tana hura hanci. “Daman dan bantan ubanki kina cikin gidan nan ban sani ba, har waccan munafukar malamar taku ta aiko wai kije makaranta tana jiranki nace kin fita yawan shaidancinki? Uhmmm zoki gaya min wane dan iskan ne ya bataki harda baki kayan sawa.” Na ajiye butar tare da cuno baki ina kifta idanuwa kamar me shirin yin kuka, sannan ta kuma rike kugu tana girgiza jiki tace. “Ahh! Har da su kitso Dije? Ehhh lallai abin naki ya shahara, zaki bude baki ki gaya min ko sai na ragarkajeki sannan?” “Toh ba malama Mardiyya ta bani ba, kuma ta wanke min kai na tasa min turare tace kullum a haka take son ta ganni ina wanka.” Na karasa fada ina sosa ido na guda daya. Gajiyalle ta dinga tafa hannaye tana sallallami tace. “Na shiga uku karfa matar nan ta jefaki hanyar halaka azo ana cewa bana kula dake. Aikuwa bari malam yazo sai na gaya mihi dan ba zai yiwu kizo ki janyo mana abin kunya ba la'ananniya kawai mai bakar aniya.” “Haba Gaji, kina ganin yarinya tayi kyau amman ki dinga aibata ta haka, shegiya Dije ahe dai kina da hegen kyau, aradu baki ganki ba kamar wata Fati Muhammed (Muhammad).” Harara Gajiyalle ta watsawa Mudukalle da yake ta sakin murmushi wanda shi kadai yasan ko na menene yake yi. Ni dai ban yi magana ba na koma cikin inda nake na dauki dankwalin na daura tare da dakko mayafi na wanda ko daga nesa ka hango shi a kuguna kasan cewa ni ce na doso. Naje zan fita daga gidan Mudi ya biyo ni a baya da sauri ya tsare kofar fita yana cewa. “Yar gari, ki gaya min gaskiyar wanda yake baki wadannan abubuwan, na yi miki alkawarin zan dora daga inda ya tsaya.” Cikin rashin fahimtar inda maganar sa ta nufa nace dashi. “Wane abubuwa nake samowa?” “Shegiya karki rai na min hankali ma, wane saurayin kikai yake tabe ki yana baki kudi gashi har kin fara sanya kayan yan birni?” “Cab! Bafa namiji ne ya bani ba, malamar mu ce ta yi min duk wannan abin, kuma bari kaji na gaya maka harda wasu kayan ma suna daki na ajiye su, bazan saka ba sai da sallah.” Mudukalle ya kuma dashare baki tare da kallo na yana kanna ido, muryar Baffa ita ce san Mudi saurin matsawa daga kusa dani. Nayi saurin zuwa gurin Baffan ina juyawa tare da ware hannuwa alamar ya ganni da kyau. Ya rike baki yana kuma bina da kallon mamaki, ina ta dariya dan nasan zai ji dadin gani na a cikin wannan yanayin. “Ummina kece haka?” “Ni ce nan Baffa, ya ka ganni?” “Kamar Ummina a cikin radio ko talabijin.” “Hahahah Baffa har na zama ta cikin radio?” “Eh mana Ummina, nan gaba kadan idan kika dage da karatu zaki ganki a ciki. Wane dan albarkan ne ya baki kayan nan Ummina?” Na kamo hannunsa nasa a kai na kafin na zare dankwalin nan kitso na ya bayyana na kara da cewa. “Baffa malamar mu ce ta gyara min kuma tayi min kitson, ya yi kyau ko Baffa na?” “Allahu Akubar, ubangiji ya saka mata da alkairi, na gode mata sosai....” Sai kawai naga yana goge hawaye da alama mahaifiyata ya tuna, yasan da rana nan kamar haka zai dinga gani na cikin tsabta da kwalliya. Mutuwa mai raba da da uwa, ta raba miji da mata a duk lokacin da Allah ya tsara mata. “Yanzu ina zaki je.?” “Baffa zanje nemo abin da zanci.” “Ikon Allah, ba tayi girki bane Gajin?” “Baffa kasan fa Gajiyalle ba bani take yi ba, dama idan nayi mata talla ne take bani da dadin rai. Amman yanzu tunda na dena ta dena bani ka sani dai Baffa.” Yaja numfashi tare da zura hannu cikin aljihu ya zaro kudin, naira saba'in ne ya miko min hamsin yace naje na siyo alala gwangwani uku. Na karba duk da nasan su kadai ne dashi hakan besa na bar mishi ashirin din nan ba sai da na karbe na hada sannan na fita ina murna. A hanyata ta zuwa ne naga ashe ba'a tashi daga makaranta ba, ni tunda malama Mardiyya ta bani kaya tace naje na boye ban koma ba, dan haka sai na tura kudi na cikin dankwali sannan na ciro mayafi na daga kuguna sai na yafa na shiga cikin ajin mu. Murna ta kamani ganin malama Mardiyya ce a ciki, naje gurin ta da sauri ina washe baki wai ni naga uwa ta. 'Eh' mana uwa tunda itace take share min kuka na. “Ke kuwa Khadija ina kika shiga daga cewa ki kai kaya gida shikenan bake ba labarin ki, kuma har Aminu na aika gidan ku aka ce bakya nan.” “Walle malama mantawa nayi har zan dawo makaranta. Ina zuwa gida bacci nayi he yanzu zanje siyan alala kawai naji ana ta karatu hi ne na higo nace bari a gama dani.” “Lallai kin kyauta tunda har kinyi tunanin zuwa a karasa karatu dake. Toh yau idan an tashi kin koma gida ki samu ruwa ki wanke kayan makarantarki kinji ko?” Kada kai nayi tare da zuwa na zauna, ta ci gaba da tambayar matan da suka fara al'ada a cikin mu, wadan su suka tashi ta tambayi yadda suka yi lokacin da suka ganshi, Bara'atu tace ta gayawa Innar su tace ta dena sallah kuma yau kimanin wata biyu kenan bata sallah, ma'ana ta zarce da rashin yin sallah tun da Innar ta ba ta yi mata bayinin cewar har sai ya dauke ba. Malama Mardiyya ta dafe kanta ta kasa dagowa tsawon lokaci. “Yanzu Bara'atu tsawon wattani biyu bakya sallah?” “Eh wallahi malama.” “Toh naji, daga yau duk wacce ta kuma ganin jinin al'ada toh kar tayi sallah har sai lokacin da taga jinin ya dauke. Sannan sai tayi wanka, ba wai wanka na sabulu da soso ba a'a na tsarki. Wankan haila, da na janaba da na biki da sauransu duk daya ne, babu wani bambanci sai a niyya. Ga yadda siffar wankan janaba nan take kamar yadda ya zo a hadisin Ummuna Aisha (r.a): An karbo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce: ((Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan zai yi wanka na janaba, yana farawa da wanke hannayensa, sannan sai ya zuba ruwa da damansa a bisa hagunsa, sai ya wanke farjinsa, sannan ya yi alwala. Sannan ya kama ruwa sai ya shigar da yatsunsa a cikin asalin gashin kanshi, sai ya zuba ruwa a kanshi sau uku, sai ya game jikinsa da ruwa, sannan ya wanke kafafunshi)). Bukhary da Muslim, lafazin Muslim ne. “A takaici wannan hadisin na ko yarda mu yadda ake yin wankan tsarki ne, imma (janaba, haila, biki, Wankan Juma'a da sauransu). Yara idan kun tashi za ku fara ne da wanke hannayen, sannan ku yi tsarki da hannun hagu tare da wanke duk inda najasa ta ta6a, sannan sai ku yi alwala kamar yadda aka saba yi idan za a yi sallah, sannan sai ku wanke gashin kanku tare da cuccudawa, ku sanya yatsunku har zuwa kasan gashin sau uku, sannan sai ku game jikinki da ruwa. Babbar manufar dai shi ne ya kasance ruwa ya isa kowani lungu da sako na jiki, don haka duk inda aka ga ruwa be isa ba, sai a isar da shi. Kun fahimta?” Nayi saurin cewa. “Eh to, wani gurin dai sai an sake gaya mana.” “Toh shikenan duk wacce ta fara ko take yi tazo ta same ni ta gaya min kunji?” Duk muka hada baki wajan cewa. “Eh...!” Daga nan ta ci gaba da sanar damu yadda zamu dinga tsabtace jikin mu har aka tashi gabaki d'aya. Muna cikin fitowa daga aji ni da su Siyama muka hadu da malam Auwal na bishi da kallon sama da kasa, yasha kananun kaya farar t-shirt da dogon wanda jah ya yi kyau sai dai ji nake na fishi hakan yasa na kuma gyara mayafi na. “Zonan Khadija.” Ya kira ni. “Gani malam, amman kayi sauri saboda wallahi yunwa nake ji.” “Haka dai. Daga ina kike ci ina zaki ci.” Yai maganar yana jajjan gemunsa. “Yooo ai lafiya ce ta iheni ba dan haka ba ai bazan ci ba, kai ma malam wallahi da zaka dinga rage ciki kana cin abinci da he kafi haka kauri.” Sai ya share maganar ta hanyar cewa. “Ina uniform dinki?” “Suna gida malama tace sai na wanke zan saka.” “Toh karki sake zuwa mana da kayan kida.” Na yatsina fuska alamun banji ba bazan dena ba, shi sai kace makarantar shi duk yabi ya takurawa yan makarantar kowa tsoransa take ji. Na turo baki ina zaro kudi na daga inda na boye ina cewa. “Malam in rafi?” “A'a zo muje wajan mashin dina zan baki abu.” Ya yi gaba ba tare da ya saurare ni ba, na harari bayan nasa ina bin shi. Bude mashin din ya yi ya dakko wata bakar leda a kulle ya miko min tare da cewa. “Idan kinje gida kici.” Tunda ya ambaci naci nasan cewa kyautar tawa ce. “Malam na gode Allah ya himaka albarka.” Ya yi murmushi banji ya amsa a fili ba amman ina tunanin ya amsa a cikin ransa. Ai banma bari naje gida ba, kawai na samu guri na bude ledar, naci karo da gassashiyar kaza. Wayyo Allah an jima ba'a hadu ba, na gyara zama na tare da janyo ledar na shiga ci hankali kwance, abin da ya bani mamaki shine da naji ina son ragewa Baffa koda kuwa zan iya cinyewa, naji na rage na kulle na tafi ina tsallen dadi tare da yiwa malam Auwal addu'a.... . ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ MX *S A S* *MX* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI TA NAMBOBIN DAKE KASAN SHAFIN NAN.* *10* *Tun* daga wannan malam Auwal yake dan yi min mutunci ba wai da yawa ba, saboda a cewar sa kada na raina shi dan ba kunya ce dani ba idan yana sakar min fuska zan dena ganin mutuncin sa. Yanzu ta kai ta kawo da kai na nake zuwa makaranta ba sai an tuna min ba dan sosai nake jin dad'in yadda ake koyar damu hanyoyin da zamu yi tsafta, kula da iyayen mu da ma jin maganar su. Yau ma kamar yadda malama Mardiyya ta koya mana, muna tashi daga makaranta na koma gida na cire kayan makarantar nasa wasu riga da skirt wanda malama Mardiyya take kawo min, na yarta ne da kuma 'ya' yan yan uwan ta shine take kawo mana nida su Uwande dan kar su ce ni kawai take yiwa shi yasa take hadawa dasu. Naje na dauki bokiti na debo ruwa a rafin durb'un, na dawo tare da dakko ragowar sabulan wanki na da nake boyewa idan ya ragu, na wanke kayana tas suka yi kyau na shanya can inda hannun Gajiyalle ba zai kai ba bare tayi min mugunta ta yarmin dasu. Sannan ne na fara tunanin abinda zanci, dan dazu da safe tas na cinye buredin da malam Auwal ya bani jiya. Babban buri ne ya sake mamaye zuciya ta shi yasa nake son dagewa wajan ganin nayi karatu wato na zama cikakkiyar yar jarida, wannan shi ne mafarki na a duk lokacin da na samu ina shakar numfashi. Muryar Dara'ifa ne ya fito dani daga cikin daki ina daura mayafi na a kugu duk kuwa da cewar malama Mardiyya da malam Auwal sun hana ni yin hakan, amman sabo da kuma ganin al'adar kauyen mu ne yin hakan yasa na kasa denawa, ko na yafa idan na fara tafiya sai na zaro na daure a inda na saba. Na saki murmushi lokacin da na ganta da faranti a hannunta, ina ta addu'a Allah yasa ni ta kawowa. “D'an malele ne nayi shine na kawo miki, Na rasa yaron da zan aiko shi yasa na taso da kai na kici shi da zafinsa.” “Walle naji dadi Dara'ifa, nagode Allah ya hi miki albarka. Sittin ta Ubangiji ina ha'awar dan malele sosai.” “Toh gashi nan kuwa ai ta sha Dijen Baffa.” Nayi murmushi tare da karbar filet din ta tafi ni kuma na samu guri wajan dakin Baffa na zauna ina ci ina santi dan yajin ba karamin dadi ya yi ba. Cikin ikon Allah Gajiyalle ba ta fito ba har lokacin tana daki tana baccin asara. Ina gamawa na dauraye filet din naje na kai mata tare da godiya sannan na tafi wasa na gidajen kawaye na, wasu muyi fada na tafi wani gidan, idan naje muyi ta musu da su a kore ni na fito a haka har dare yayi na koma gida na kwanta. Babu abinda yafi ilimi dadi a rayuwar dan adam, saboda tun da aka bude makarantar boko da islamiya a kauyen mu muka fara samun sauye-sauye da yawa. An dan rage kauyancin da ake fama dashi, ana barin yara mata suna karatu dan sun fara ganin alfanun karatun a cikin rayuwar mu mata. Duk da cewa bana yin na farko a ajin mu, amman ina yin gaba ina kuma zama mai kokari har ta kai ta kawo ina zuwa ta daya ko ta biyu ko uku, da taimakon malaman mu da basa fushi akan duk wani shirme da muke yi musu. Har na kammala primary muka shiga bangaran secondary, nan din ma dai malam Auwal sai da ya bimu can yana koyar damu, A hankali kuma yana ta jefa sakon soyayyarsa gare ni inda ni kuma naki bashi fuska dan gani nake tamkar so yake ya sake samun dama ta yadda zai horani iya son ransa. *BAYAN WASU SHEKARU* *’KAUYEN DURB’UN* Nana Khadijaa (Dije, Dijangala ta mai gari/Oganniya yar Baffan ta!) Duk sunaye na ne na yanka dana lakani. Da farko dai: Baba na na kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar mu. Mafi yawancin yan karkarar mu na kira na da Dijangala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan karkarar mu na min laqabi da Dije Oganniya. Kasancewar a lokacin ina karama ina da kiriniya da siyan fadan da ba’a kasa da ni ba. Duk wani cincirindon ruguntsumi idan ka cakuda zaka ga ni ce akan gaba. Lamari na dai addu'a ce kawai ta kare ni. Na kasance ni kadai ce awajen iyaye na. Tun ina ‘kankanuwa mahaifiya ta ta rasu, Mahaifina ya auro wata matar, Ya zamto riko na ya koma hannun kishiyar uwa. Na taso cikin wata irin kuntatacciyar rayuwa wanda alqalami yayi ka’dan wajen bayyana muku ita, Manufa dai na sha wahala sosai. Duk da azabar da kishiyar uwa ke gallazamin, Sai Allah yasa mahaifi na yakan kyautata min a duk sanda yake da iko. A yau January 1, Zan kammala jarabawar kare karatu na na secondary, Alhamdulillah Allah kai ne abun godia. Na karanta b’angaren art saboda inaso na karanci fannin Mass-Com/journalism. Na kanyi daria a duk sanda na tuno kuruciya ta ta da. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u, Na sake daga kai na dubi allon zayyana ta wanda nayi sauka bara a tahfiz din da su Malama Mardiyya ke koya mana. Shekaru na goma sha bakwai a yanzu. Ina kuma sana’ar kitso, Na kuma fara koyon dinki a gidan Bara’atu tela (Babbar mace bata ajin mu ba) Alhamdulillah da wannan yar sana’a tawa nake rik’e da kai na dama Baffan mu. Wanda a yan shekarun nan ya kamu da lalurar nakasar shanyewar barin jiki (hemiplegia/hemiparesis.) Hijabi na na janyo sabo fil dashi Bara’atu ta dinka min, Wuta ta ruru na zubata a dutsen guga, Cikin kwanciyar hankali na shiga goge hijabi na. Na kammala na shasshafa turaruka masu sanyin k’amshi dana siya a shagon Falalu.Ban tsaya wata kwalliya ba na dai goga farar hoda da basilin a lebe na. Gashi na mai matukar tsawo da cika naita ko’karin daurewa, Dak’yar ya dauru. Domin ina daure shi yana kuncewa saboda santsin sa, Ko kitso ake min kasan na warwarewa. Zura hijabin nayi, Na goggoge takalmi na samfarin sandal. Safa tama sabuwa ce sai sheki take. Wajen Baffa na nufa na coka biro a gefen kunne na, Ji na nake on top yau zan kammala sakandire, Sai kuma fanni na biyu. Yana malale a taburma kamar ruwa, Dakyar yake iya magana. Gajiyalle na gefen d’akin girki tana kwashe tuwo. Na san ba zata bani ba bare Baffa na. Domin tunda rayuwa ta ta sauya daga bak’a izuwa fara Gajiyalle ta dena bani abinci, Duk abinda zan sanya a ciki na tadena min shi. Ko banda hantara da kyara yanzu babu abunda ke shiga tsakani na da ita. Zan gayshe ta Sau dubu ba zata amsa ba, Sosai take jin haushin karatun da nake yi. Kullum cikin yada min da magana take. Kan naki aure ina yawon ta zubar, Ga k’awaye na nan duk sun hayayyafa. Ni da Siyama da Uwande da Nafisa ne kadai ke yin karatu yanzu a sa’oin mu. Gaba d’aya sunyi aure sun tara yara. Ajiyar zucia na sauke ina kallon Baffa na, Dama ance sai ka rasu ake gama canza maka halitta. Yanzu Kalli Baffa da sumul k’alau yake. Tashi d’aya ya samu wannan ciwon, “Baffa na..! Sannu ya jikin naka?” Baffa ya lumshe idanu ya bud’e alamun lapia. Kafin ya bude bakin sa hankali, “Allah... Ya bada sa’ar jarabawa Ummi na.!” “Aamin Baffa na! Allah ya tashi kafad’un ka yasa kaffarane.” Rufe idanu yai. Na mike dakyar jikina duk yayi sanyi. “Na tafi Gajiyalle.” Harara ta dankaramin ta cigaba da kada miyar ta. “Na tafi jarabawa Gajiyalle.” “Ko an tafi yawon ta zubar ba. Mude kada a kawo mana abun kunya gida, Atoh!” Girgiza kai kawai nayi na fice rai na babu dadi. Nera dari da hamsin din hannu na na tsaya na mikawa Safarau me sayar da abinci, “Gashi ki zubamin a kwanon jiya ki wanke dan Allah sauri nake zan tafi jarabawa, Idan na dawo zan tsaya na karb’a.” Saurin Karb’a tayi ta koma wajen zaman ta. Iyayen ta sun hanata karatu sai dai tallen abinci, Wai ta haka zata tara kudin kayan daki. Abun takaicin ma mazan yar kasuwa sun mai da ita tamkar matar su. Su yita bata kudi suna taba ta. Haka na shige da tunanin da safarau ke ciki na tafi makaranta. Lalle na godewa Allah daya kadarta za’ai makaranta a kauyen mu, Da hakimi daya samo mana tallafin yi, Dama mai gari daya wayar da kan dattawan karkarar mu, Sai Baffa na, Jigon rayuwa ta. Wanda ya tsaya min a komai, Ya so ni bai kyamace ni ba kullum cikin min adduar shiriya yake. Ga bani shawarwarin yadda rayuwa ke ciki. Da yadda zan gudanar da al’amura na ba tare da na gunduri kowa ba. Bayan Baffa na sai Malamai na. Musanman Malama Mardiyya data dauke ni tamkar ‘yar data haifa, Itace mace ta farko data gyaramin rayuwa ta. Gaba d’aya acikin duhu nake. Zuwan Malama Mardiyya shi ya samar da yadda na zama a yanzu. Ba abinda zance da kowa sai fatan alkhairi. *_GOVERNMENT JUNIOR/SENIOR SCHOOL DURBUN*_ Kide kide muka fara da bencina muka d’akko muka kawo su farfajiyar makaranta, Yau munyi candy. Mun kammala makarantar secondary. Allah mungode maka. Wakoki muka fara na candy, Muna yi fuskokin mu dauke da farin ciki da annushuwa, _2005 muna tare, 2006 muna tare, 2007 muna tare.. 2014 zata raba mu. Malam Auwal mude kayafe mu, Mude mun yafe, Muma ka yafe mu, Malama Mardiyya mude kiyafe mu, Mude mun yafe mu de kiya fe mu..🎶_ Haka Mukai ta yi har akazo kan sunayen dalibai, Nima na mike ina hawaye, _Khadija Basheer Inuwa inayin ban kwana, Nide ku yafen, Nima na yafe ku.🎶_ Ina k’arasawa na fashe da kuka, Saura na ban haku’ri, Mu kaita koke har aka kammala, Aka babbawa prefects kyaututtuka. Ni ce ‘sanitary prefect’ kasancewar nafi kowa tsafta. Domin tunda na Kile na koma yar gayu, Har kawaye na ke kira na da ‘Dije wanka-wanka’ Idan zanzo makaranta ko banida kudin guga tun dare nake yiwa uniform dina ninkin guga na kwanta akai da safe kuwa sai kuga sunyi ‘das dasu tamkar nasa dutsen guga. ‘’ Ina sanitary prefect? Nana Khadija Basheer..” A hankali na mike daga zaunen da nake na isa gaban makaranta inda Malam Habu ke kiran mu dai-dai, Sunana ya tashi daga Khadija Baffa ya koma na ainihi wato Nana Khadija Basheer. Tun a Jss3 na canza lokacin da mu kai jarabawa. Malam Auwal na gefen Malam Habu yana min wani kallo tunda ga sama na har kasa, “Dan iska...” Na furta ahankali ina gatsine baki. Murmushi yai yayi magana da labban sa bansan meya ce ba. Malam Habu ya dankamin kyauta ta, Na tsaya muka dauki hoto da sauran malaman kamar yadda ake da kowa. A haka aka kammala komai bayan anyi walima mekyau. Mardiyya bata bari mun kara sallama ba ta tafi bayan ta dankamin number wayar ta a paper, Kan cewar zata dawo ta dauke ni muje birni nayi jamb. Nasan idan muka kara had’uwa kafin tafiyar ta sai nayi wani sabon kukan itama haka, Shi yasa ta tafi. Amma Malam Auwal ya ki tafiya yananan ya kasa ya tsare. Da wani Malamin ya kira wo ni zai dakatar da ni. Sai kace wani miji na. Ko ta kansa ban sake bi ba, Na bi su Uwande muka dauki hanyar gidan su ganin kayan barar ta da aka kawo, Kamar hadin baki Siyama ma jibi Za’a kawo nata, Nafisan kansila kuwa an kusa bikin ma, Wani dan uwan su na birni zata aura yanada mashin dinsa Lifan. Ni kuwa ko oho. Banda Malam Auwal da kama sunan sa haushi yake bani ma sai Mubarak dan gidan Bala driver, Shi kuwa babar sa ta dira tsallen albarkar danta ba zai auri wadda tai boko ba. Muna tafe a hanya ina tunanin duniya, Malam Auwal ya shiga zabga min kira tamkar wadda naci bashin sa na gudu. Nifa gaba d’aya haushi yake bani, Ada babu wadda ya tsana iri na, Yana kallo na tamkar kashi. Duk abunda nayi bana birge shi. A kullum cikin kuntata min yake. Amman yanzu ya nanike min kamar super glue. Duk inda nai bina yake sai kace rak’umi da akala. “Na’am..” Na amsa masa bayan ya kira sunana a karo na ba adadi. Ya sake marairacewa yana zuba hannayen sa a aljihun jeans dinsa, “My Baby K! Meyasa kike wahalar da zuciar masoyin ki ne? Na gaya miki tunda Allah yasa son ki ya mamaye bargon jiki na da tsoka, Kullum da begen ki nake kwana nake ta shi. “ Namiji mayaudari ji wata karya dan Allah! Duk da a k’auyen kayau na tashi, Naki jinin irin kalaman soyayyar nan. Konamin rai suke. Gashi duk karyar banza ce. Don takaici rasa me zance masa nayi. “Baby K!” Wai Baby K! Kamar wata diyar cikin sa. Murtuke fuska nayi na juya gefe ina dagawa su Uwande hannu alamar su tsaya ni kar su tafi. “Malam Auwal jira na ake..” “Naki jinin yadda kike ambatar sunana Baby K! Ni ba malamin ki bane, Masoyi ne agare ki. Ki tallafawa zuciya ta ki karbi kokon barar soyayyar ta. Shekaru nawa ina rokon ki, Ya kamata ace kin tausaya min, Gashi yau zan koma inda na fito. Kuma ba naso na koma batare da kwakkwarar amsar ki gare ni ba.” Ajiyar zuciya na sauke, Ni kai na nagaji da kulaficin da yake yi min, Mutumin da sam baisan darajar dan adam ba, Rashin mutuncin da yai wa Baffa na bazan taba mantawa dashi ba, Yazo zance Kwana ki, Baffan mu ya fito zai tafi gona da y’ar fatanyar sa bai ko kalle shi ba. Ina tsaye ina gwada hankalin sa. Dana tambaye shi meyasa bai gaida wanda ya wuce ba? Wai ya dauka me gyara ne. Gyaran uwar baban sa? Ranar naci masa mutunci sala-sala bansan meyasa baida zuciya ba ya nanuke min. “Kayi hak’uri Malam! Gaskia bana ra’ayin soyayya, Karatu zanyi. Allah ya baka wadda ta fini komai. Ina maka fatan alkhairi. Allah ya kiyaye hanya.” Ina gama fada nai gaba abuna, Na barshi a tsaye ya sandare. Mukai tafiyar mu dasu Uwande, Wannan itace rana ta karshe tsakani na da Malam Auwal. Ina wa dukkanin mu fatan alkhairi a rayuwa. Muka je gidan su Uwande muka gano kaya, Wallahi Uwande tai goshi, Kaya nasha-nasha. Daga nan na tsaya na karb’i abincin dana bada Kud’i dazu, Gida na nufa, Ina shiga na hango Baffa na a inda na barshi ya kwarara amai yana numfarfashi dakyar, a sukwane na zubar da kyautar hannu na kwanon kuma na ajiye a gefe na shek’a da gudu na isa wajen sa ina tallafo shi da karshen karfi na, “Baffa na...! Sannu! Amai kayi! Sannu! Jinjiri (Almajirin dake kula dashi Idan na tafi makaranta ko bana nan) bai zo ba? “ D’ankwalin hijabi na nasa na gogge masa fuskar sa, Kafin na debo ruwan dumi dana ke had’a masa shayi na surka na gogge masa jikin sa, Riga na d’akko na sauya masa da Wadda ya b’ata, Ina ta faman masa sannu. Gajiyalle ta fito daga d’akin ta tana wake wake, Ta shiga kitchen ta ebo abincin ta ta wuce ko kallo bamu ishe ta ba. Ni bansan meyasa Baffa ya auro taba. Silar ciwon sama itace ta haushi da kokawa ya zume a bandaki. Abincin dana sayo na janyo, Na raba shi kashi biyu, Na shiga bashi a hankali dakyar yaci rabin sa, Ni kuma na cinye sauran. Na wanke tulin kwanukan da na gani awajen, Kafin na ha’da wuta na dora ruwan wanka na. Baffan mu na shiga nunnunawa kyaututtukan yai murna kwarai tare da kwarara min addu’a. Ruwa na na zafi na shiga band’aki na yo wanka. Ina futowa mu kai kicib’is da Mudi na koma ciki da sauri, Domin kwanan nan haka yake yi. Sai yaita kallo na yana lashe lebe hade da kashe min idanu. Ya zama direban hayis, Ya siyarda tumakin Gajiyalle da sauran jarin ta ya sai mota yana lodi gari gari, Ga shaye shaye da yake yi du ya bata maza yaran karkarar mu da yi. Sai danaga ya fuce sannan na shige daki da sauri na canzo kaya na, Bana sallah. Hakan yasanya na canza auduga na zura hijabi na d’auki kayan koyan d’inki na mufi gidan Bara’atu me koyamin dinki. Baffa na yana ta baccin sa. A hanya muka had’u da Balki da gayyar yara rab’e rabe wasu na bin wasu har su bakwai. Ta manyanta sosai tamkar ba Balki ba. “Balki..” Na fada cike da mamakin ganin ta. “Dijengala!! Rai kanga rai? Yauhe rabon da na saki a ido na?.” “Ai kuwa dai an jima, Ina wuni Balki, Yaran ki ne wannan?” “Eh nawaje na ne, Biyu sun rasu ma..” “TubarkAllah. Allah ya raya su. Balkin Haladu, Ina Haladu?(mijin ta)” “Uhm dan bankadaddiya, Mayaudari. Ke fa kihiyoyi na biyu. Namiji ba tabbas ingaya miki an sa ranar sa da y’ar gidan babire farkon watan gobe. Mu hud’u kenan. Ke shika biyu yamin saura d’aya auren mu ya datse.” Na rike baki ina mamaki, “Subahanallahi! Allah ya tsare, Yasa ku zauna lapia.” “Amin dai. Walle ki tsaya ki cigaba da karatun ki. Yanzu ba hi nan ba tamkar na haife ki. Aure ba dadi kud’in cefa nema nera talatin.” Sirrin gidan ta data fara fad’amin yasa na dan gyara tsayuwa ta ina kallom agogon hannu na, “Allah sarki! Bara na wuce Balki sai gani na biyu.” Na zaro ragowar hamsin din jakata na mikawa yaran, Kafin su karb’a ta wafce tana cusawa a kanta, “Mungode Dije. He anjima.” “Mu jima dakyau.” Gaba nayi abuna na wuce gidan Bara’atu, Hankali kwance ta cigaba da koyamin d’inki, Sosai nake ganewa. Sai bayan magriba na koma gida.. Haka rayuwa ta cigaba da garawa yau da dad’i gobe babu... .. ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *S & K* *MX* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI TA NAMBOBIN DAKE KASAN SHAFIN NAN.* *11* *Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin hankali a karkarar mu ta Durbun. Bayan na temawa jinjiri mun gogewa Baffan mu jiki, Na bashi magani yasha, Sai na lallaba na tafi gidan Bara’atu koyo dinki. Gab da la’asar naji gaba d’aya banajin da’din jiki na. Daman haka na Kwana jiya ban rintsa ba Ina tunani, Haka kawai na shiga zaryar hawaye daren jiya. Shin meyake damuna? Bansani ba. Mik’ewa nai kawai Bara’atu ta tsaya tana kallo na, Harhada kayan dinkin na shigayi ina cusawa a leda, “Dije! Meye haka?” “Gida zani Bara’atu. Raina sam babu dadi wallahi.” “Subhan’Allah! Kiyita addu’a kinji!? Amma ki dakata ki kammala dinke kafadar mana?” “Aa Bara’atu. Sauri nake yi wallahi. Bazan samu nutsuwa na Idan ban koma ba. Nagode sai kinji ni.” Bantaba sanin wannan itace kalmar karshe da zata kara had’ani da Bara’atu ba akan dinki. Banta’ba sanin wannan ce rana ta karshe da zan sake zuwa gidan Bara’atu ba. Sallama na mata na fuce, gaba na sai tsananta bugu yake. Tamkar zai fadi kasa, Haka na kara sa gida gaba d’aya jiki na ya kara sanyi. Bantaba sanin wannan ce bakar rana da rayuwata zata kara shiga ha’ulai ba. Bantaba sanin yau ne zan shiga stage na biyu a fagen sabuwar rayuwata ba. Baffan mu na tsakar gida a yashe, Fuskar sa tamkar yana murmushi. Na karasa kusa dashi na zauna a gefen sa, “Baffa na... Na dawo.” A duk lokacin da na dawo hakan nake yi, Dake bashi da nauyin bacci, Dana fad’i haka zai farka yace min Sannu da dawowa yar Baffan ta. Na sake matsawa kusa dashi na kamo hannun sa na dama, Tamkar na dau kara sam babu nauyi kuma ya saki. “Baffa na.. Baffa ga Ummin ka fa! “ Nan ma shiru ba amsa. Gaba na ya tsananta bugu, idanuwana suka kawo ruwa. “Nashiga uku! Baffa na. Gaji! Gajiyalle.. Ga Baffa baya motsi fa.” Haka naita fada ina kai kawo a farfajiyar gidan mu. Gajiyalle ta fito daga d’aki tana hamma hade da daga hannuwa tayi mika, “Ya akai? Kincikawa mutane kunnuwa da kururuwa, Meya faru.?” Cikin hawaye shab’e sha’be na tsugunna ina rike kai na, “Gaji! Baffa baya motsi. Ki tayani mu dauke shi mu kaishi asibiti.” “Asibiti? Can birni!? Baki da hankali.” Tsayawa tai akan baffan mu tana sakatar hanci, “Bashari! Bashari! Kai bashari! Meye haka ne.?? “ Kafa tasa ta shure shi, Ya rigingina bako motsi. Banbi takanta ba na fuce ko dankwali babu, Na hango dandazon masu bin mai gari da shi kansa mai gari jamilun da alamun daga zagayen gonaki suke, “Mai gari! Dan Allah kuzo kuga baffan mu baya motsi.” “Assha gamu nan.” Komawa nai ciki da sauri na zura hijabi gaba a baya. Gaba d’aya bana cikin hayyaci na, Su mai gari suka shigo, dube duben su sukai. kafin su mike kowanne jikin sa a sanyaye. (Allah ya jikan iyayen mu da rahama.) “Ai Bashari dan aljanna ne da yardar Allah. Kiyi hak’uri Dije, Duk kan mai rai mamaci ne, Yau ga wanin ka, Gobe gare ka. Idan lokaci yayi dole a tafi. Kai Rabilu ku kama shi ku sashi a dakin can ko, Domin a kintsa shi. Ungo Musa zoka yanko likafani, Kace Malam na Masallaci suzo za’ sallaci Malam Bashari rai yayi halin sa, Ku auno tsawonsa ku taho da makara.” Kan baffan mu nayi, Matan da suka shigo suka rirrike ni, Na kwace na rungume shi ina kuka, “Wayyo Allah na Baffa na. Dan Allah kakka tafi. Babba ka tsaya, Wayyo Allah na baffa. Shikenan gaba da Baya bani da iyaye. Umma ta tarasu, Gashi Baffa sai ka tafi ka bar Dijen ka? Wayyo Allah nashiga uku na lalace. Wayyo mutuwa mai yankan k’auna” Wannan sune ka’dai kalaman da zan iya tunawa na fade su. Daganan ban sake sanin inda kai na yake ba. Na yanke jiki na fadi. Ban farfad’o ba sai bayan an kai ni asibiti a birni. Kwanaki uku mu kai acan nida tsahare yar ladingo sannan muka dawo gida. Ranar sadakan ukun Baffa na. Addua kadai nake iyayi sai kuka, abinci kuwa sai yan uwa na matsamin nake tsaku na, Duk wani buri na wa na duniya na yanke shi. Jira kawai nake nima tazo ta dauke ni. Astagfirullah Yaa Allah amma nikam nasan shikenan rayuwa ta yanzu zata kara shiga cikin jarabawa. Haka akaita zaman makoki har na tsawon kwana ki bakwai. Gajiyalle tace wa mai gari tanada magana, “Azo ai rabiyar gado. Amma fa wani hanzari ba gudu ba, Mai rasuwar nan kafin rasuwar sa yace ya barwa Mudi gidan nan wai yayi aure ya zauna.” A razane na juya ina kallon ta, Yaushe sukai haka?! Allah ya saka masa. Yan zaman makoki kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa. Mai gari yai gyaran murya, “Toh salamatu. Hakan yayi. Amma ina rubutaccen kyautar da yayi.?” “Yo wane rubutu? Malam ya iya rubutu ne! Kai ma mai gari da tsohon kinibibin ka ta yaya Bashari zai iya rubutu?” Mai gari yai murmushin takaici yana gyara rawanin sa, “Toh ina shedu? Agaban wa da wa akai kyautar?” Gajiyalle ta sosa kai tana zare idanu, “Daga ni sai shi akai haka, Zan yi k’arya ne?” “Assha! Yaushe zan karya ta ki a matsayin matarsa.? Kawai dai irin wannan babbar kyauta haka yakamata ace akwai ta a rubuce ko anyi ta gaban shedu.” “Toh dai na baka ta rabaka da kayan ka. Wannan gida dai na Mudi ne.” “Gaskia bai badu ba, Domin ko gaban alkali zaki abinda zai sanar dake kenan. Saboda haka kiyi hak’uri kawai, Domin Mudi ma Ai ba ‘dan cikin sa bane Salamatu. Ya zaai ga diyar cikin sa duk duniya ita kadai ce jal. Ace ya tsallaketa ya baiwa agola kyautar gidan sa sukutum? Wannan magana bata kamawa bace kiyi hak’uri. Gado dai yau zuwa gobe Za’a raba shi. Ke ki nada tumunin takabar sa ita kuma diyar sa tana gadon sa. Za’a raba ko dan saboda a sauke masa nauyin dake Kan sa.” Gajiyalle ta dire tsallen albarka ta shiga zundumawa mai gari ashariya tana karkada masa hannu. Mai gari ya murtuke fuska ya fice mabiyan sa na bin sa a baya. Ba jimawa dangin Ummana suka Zo, Domin sai jiya aka sanar musu. Sunyi mamakin ganin girma na, Ni kuwa na shiga raba idanu ina binsu da kallo, Yan gayu ne sosai wanda suka shaki ilimin boko dana addini. Sun jima sosai kafin su tafi bayan sun dire mana kayan abinci fal, Suka ce zasu dawo nan ba da jimawa ba. <><><>. <><><>. <><><>. Bayan rasuwar Baffa da wata biyu abubuwa da dama sun faru, Kamar raba gadon Baffan mu da akayi. Gajiyalle ta samu gidan da muke ciki a matsayin tumunin takabarta ni kuma gado na shine ragowar gonar Baffa guda d’aya dake bayan gari. Tunda ta samu gidan nan yazo a gadonta na shiga 3, shiga dari fita dari sai tamin gori, Kamar ba ubana ne ya rasu ta gada ba, Ta rata kawai nake. Kullum cikin addua nake. Allah ya nema min mafita kawai. Gaba zatai dana sani. Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Kullum ta Allah sai na zubarda hawayen rashin iyaye na. Abincin da yan uwan Umma na suka kawo ma ta siyar da rabi ta b’oye wasu. <><> ••. <><>••. <><>••. Ina cikin da’ki ina kwance wajen shabiyu da rabi na dare. Na jiyo an bude asaberin dake jikin kyauren dakin da na ke. Na nemi cocilan na rasa dakyar na ganta a gefen hijabi na, “Waye.?” “Sssh! Ni ne nan. Kwantar da hankalin ko. Had’in kai kawai zaki bani. Na miki alk’awarin komai.” Ta muryar sa na gane ko wanene?! Torchlight na kunna na haske shi, “Mudi.. Me kakeyi a daki na a daren nan?” Kasa magana yai sai kiciniyar cire riga da yai ya jefar ya yo kai na na mike da sauri ina zura hijabi na, “Mudi meye hakan.” “Kiyi shiru dan Allah! Wallahi zan miki duk abunda kikeso. “ Murya na rawa na shjga bashi hak’uri ina damke hijabi na. Yayo kai na ya fincike zanin jiki na, “Wayyo Allah na gajiyalle..” Ban karasa ba yai taku biyu ya rufemin baki, “Ki saurare ni yammata.. Ga ki da kayan aiki a tare dake, Karki zama mai duhun kai man-“ “Yayana ne fa kai Mudi.” “Uwa muka raba, Uba kuma Kowa da nasa. Kingane? Ma’ana bamu hada jini dake ba.” “Dan Allah karka lalatamun rayuwa Mudi.” Inata k’ok’arin kwace kai na, Shi kuma yana ko’karin ciremin hijabi. Kafata nasa na tattake na dirka masa ita a gaban sa. Ya tsugunna ya rike wajen da hannu biyu yana matse idanu, Ficewa mai da sauri ina kiran Gajiyalle da mamaki na hangeta a kofar dakin tana lab’e, Tana gani na ta dubibi ce tana haske hasken fitila, Ha’din baki ne? Ko kuwa so take ya lalata ni tamin sharri da hakan? Ficewa nai da sauri banbi takan riko ni da take ba. Da tsakar daren nan na tafi gidan mai gari, Dakin Ummita matar sa na shiga bayan anmin iso, Na sheda mata komai, Wajen Kwana ta bani tace na kwanta da safe zata sanarwa mai gari. *WASHE-GARI* Kiran sallar farko na asubah sai ga Gajiyalle tazo gidan mai gari. Ta faffada masa karya da gaskiya, Mai gari ya kirawo ni da Mudi, akace kowa ya maimaita abunda ya faru. Lalle Mudi yaban mamaki ya murtuke fuska yace shi wallahi bai shigo gari bama sai safiyar yau. Naci kuka sosai, Bayan tafiyar su Mai gari yaban hak’uri yace yasan ni ce mai gaskiya. Kwanana goma a gidan Mai gari. Kafin na koma gidan Gajiyalle a ‘darare. ++ A kuma satin ne jarabawar mu ta fito. Sai ga Malama Mardiyya har gida ta kawomin nawa. Hakika nagodewa Allah domin bantaba kawo result dina zaiyi kyau haka ba. Ban boyewa Malama Mardiyya komai ba na sheda mata. Taji rasuwar Baffan mu kwarai matuk’a. A ramar ta sa na shirya mukaje birni na zana jarabawar jamb ta shiga Jami’a. Sannan ta sani a mota na dawo gida. Tunda na dawo Gajiyalle ke hantara ta tana yadamin magana kan naje yawon ta zubar. Ni kuwa murna nake na zana jarabawar shiga jamia. Na cike gurbin masscom/journalism. A jamiar dake birni. Allah yasa inada rabo amin. Haka rayuwa taita garawa, Safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Naci jarabawar shiga jamia karo ta farko, Na samu gurbin jami’ar, Nanma Malama Mardiyya ta sake d’auka na ta kaini na zana ta biyu wato post-utme. Alhamdulillah Allah abun godia. Kamar da wasa itama ta fito na haye. Cikin haka yan uwan Ummana suka turo da maganar zasu turo a tafi dani na koma wajen su. Gajiyalle ranar wuni tayi tana bakin rai. Na fita kitso na dawo na tarar ta yiwa kayana fata-fata. Na kira Malama Mardiyya da y’ar wayata mai torchlight na sheda mata komai tace nayi hak’uri. Domin bafa masifa na dena ba ko kad’an, Kawai dai na girma na kara sanin yadda rayuwa take. Duk irin mugun bakin da take yimin nasan bazai taba kama ni ba domin mahakurci mawadacine. A satin na wanke kayana tatas na goge na zuba su a ghana must go. Gajiyalle ta wuni tana harara ta, Na shiga band’aki na fito naga igiyar dana shanya underwear’s dina an yankota kayan sun zube. Tamkar an barbada musu toka ma. Dauke su nayi na sake wanke wa saboda banason neman magana. Ana sauran kwanaki biyu na tafi, Na zazzaga ya ko’ina a karkarar mu duk gidan dana sani na shiga nayi musu sallama. Mai gari ya siyar mun da gonata ya aikomin da kudin yace na sai kayan aure a birni. Na nannade kud’in a cikin kaya na. Ranar da zan tafi ina duba kayan na nemi kudin na rasa, na fito tsakar gida na hangi Gajiyalle da Mudi sun tasa jarida cikinta fal tsire ne suna ci. “Gaji! Waya daukar min ku’di na acikin ku?” Tamkar na zuba mata ruwan zafi haka ta mike tana surfamin masifa, Kuma wallahi sune suka dauka, Na girgiza kai kawai na koma ciki na dakko jakata dai dai lokacin da direban da aka aiko dauka ta ya shigo yana cewa na fito, “Gani nan! Ina zuwa..” Na fada masa, ya gyad’a yai ya fuce bayan ya kinkimi jakar kayana. Duba na na mayar kan Gajiyalle da Mudi. “Shekara da shekaru tun ina kankanuwa har na mallaki hankalin kai na, Baki dena kuntatamin ba, Kin uzzurawa rayuwata. Kin sani cikin uqubar rayuwa. Sam bakyasan ganin cigaba na sai dai lalacewa ta. Keda dan ki kuka hada baki don ya raba ni da martaba ta, Allah ya tseratar da ni, Alhamdulillah na rabu da iyayen da suka kawo ni duniya lapia, Tun Baffa na yana raye har yau rayuwata bata lalace ba duk da kwadaituwar son lalacewar da kikeso kiga nayi. Duk sharrin da kike nema na dashi baya samu na, Hmm sharri dan aike ne, Duk inda zai zaga sai ya dawo wajen ka, “Shin wannan bai isheki ishara ba? Kisani kwakwalwar yaro bata manta duk abubuwan da aka yi mata na dadi ko akasinta. Ni Nana Khadija na zamar miki kainuwa dashen Allah, Duk da yadda ba taso na rashin uwa ba kyakkyawar tarbiyya hakan bai sa na lalace ba, Ni Nana Khadija na zamar miki murucin kan dutse ban fito ba sai dana shirya, Nan gani nan bari wallahi Gajiyalle, Na zama dakalin majina dole a hau ni a zame, Ni Nana Khadija na zamar miki *KIBIYAR AJALI* wadda (sulke baya tare ta sai da ta wuce) Daukaka yanzu na fara ta. Duk abubuwan da ki kai min na bar ki da mahaliccin mu, Zai mana sakayya ranar sakamako, Kudi kuma da kuka sata kun dauki kudin cizo, Kina ganin keda dan ki kunci bulus? Allah ya kara miki tsahon rai ki, Ki dade kiyi ‘karko kamar bishiyar dabino, Ki saurari dawowata Durbun, Zaki madaukakin mamaki mai wuyar fassarawa. “ Ina gama magana nai ficewa ta na bar su a daskare kamar shekararriyar kankara. Direba ya budemin mota na shiga muka dau hanyar birni. Wannan ce rana ta karshe dana saka Durbun a idanu na. Munata wuce dajin Allah bishiyo gasunan a jere da manyan duwarwatsu. Allah gwanin hikima! “Ya Allah kasa na shiga birni a sa’a, Allah kasa su karb’e ni hannu dubu. Allah ka bani ikon cigaba da karatu na. Allah ka shiga lamura na. Kai ka iya, Kai zaka yi Ya Allah! Ka temaki mareniyar baiwar ka Nana Khadija..” Ina kammala addu’ar na shafa a fuska ta, Kafin na janyo carbina na shiga azkhar na yamma, Na fada kogin tunanin yadda zan yi rayuwata ta biyu, Sabuwar rayuwa a dangin Umma ta.. *KANO STATE* *DR ISMA’EL MUHAMMAD SINGA RESIDENCE* ... Ainihin labarin yanzu zamu tsoma ‘kafa cikin sa🥰😍❤️... Oya put ya belts.. 😉The start of something new🏌️‍♀️🥂 ASHA HUTUN SUNDAY LAPIA❤️🥰..ZAFAFA FAM😘👋 ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *SULE BAYA TARE TA SAI TA WUCE* *NANA HAFSAAT* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE! KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SAYA DA KUDIN KI, KADA KI SHARING, TEMAKA KI SIYA NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASA* *All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. * *(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾* *XII* *KANO STATE* **Abin ka da rashin sabo ga kauyanci da yake dawainiya dani, tunda muka fara tafiya ina kalle-kalle har bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai da aka shigo garin kano, na gane mun shigo ne ta hanyar kokarin da nayi na karanta symbol da aka rubuta *'Welcome to kano'*. Na gyara zama ina ta kalle-kallen abubuwa na burgewa dake kan titi, ga tituna lafiyayyu babu ramuka, hakika birni lafiya ce. Yadda kwaryar birnin kano ta cika shine zai tabbatar maka da cewa wani abun ake yi mai matukar muhimmanci, saboda din bin mutane ta ko'ina ba masa tsinke. Na kasa yin shiru tun ina lekawa ta glass din window har nace da drive ya zuge min na dinga lekawa kafin na tambaye shi me ake yi yace min. “Mantawa nayi da wannan na’din (turbaning ceremony) da bamu biyo ta wannan hanyar ba, wallahi wani matashin saurayi za'a nada sarki, shi yasa kowa ya fito ya ganewa idanunsa ba sai an bashi labari ba, gashi nan duk an cika mana garin.” Cikin mamaki nace. “Kai..! Sarki fa kace?” “Kwarai kuwa, ke ba kiji bushebushen abin sarauta ba?” “Walle banji ba kadan-kadan dai kamar ake yi, dan Allah ka kai ni na gano na din.” Ya yi saurin cewa. “Kai..! Yo kafin mu kutsa cikin mutanan nan ai aiki ne, ballantana kuma karasawa wajan rumfar nadin. Kiyi hakuri wata rana zaki ganshi idan ya fito koda sallah ne.” Na jijjiga kai alamar na gamsu. Bandamu da ganin saba dama mu kai wucewar mu gidah, Na san dai irin nad’in sarauta ne kamar na kauyen mu, Lokacin da aka nada sabon hakimin Alfundi, Bazan mantaba har can muka tafi a kasa. Ganowa idanun mu sabon hakimi da yazo daga birni, Sannan mai unguwa jamilu ma sanda mahaifin sa ya rasu aka nada shi haka akaita bushe bushe algaitu a karakar mu. Muna tafe akan titi ina karanta signboards din kan hanya, Kai birni da girma take, Na bawa idanu na hakkin su sosai, Kafin mu karasa gida *DR ISMA’EL MUHAMNAD SINGA RESIDENCE* Kai tsaye wata unguwa naga mun nufa mai matukar tsari, gine-gine ne wannan yana cewa d'an uwansa bani guri. Dr Isma'il Muhammad singa resident nan ne inda drivern ya shiga, ya yi horn a kofar wani katafaran gate wanda ya amsa sunan sa, mai gadi ya bude muka shiga. Compound d'in kadai abin kallo ne yadda aka kawata harabar gidan da shuke-shuke na burgewa, ga manya da kananun motoci tamkar kamfanin su aka zo kala kusan shida. Baki na saki ina kallon aljannar duniya, ina mamakin wai dama muna da wani dan uwa mai dukiyar da zai iya yin wannan muhallin, amman aka barmu a kauye muna ta shirme. Muryar driver ne ya katse min tsantsar mamakin da ya addabi kwakwalwa ta inda yace. “Muje cikin gidan.” Ya yi gaba ina bin bayan shi kamar wata jelarsa. A bakin wata rantsatsiyar kofa muka tsaya, naga yasa yatsan sa tare da danna wani abu ya yi kara, ba dadewa muka ga an bude kofar. “Yauwa shiga da bakuwar wajan Mami.” Drivern ya yiwa wadda ta bude kofar maganar wacce yar aiki ce a cikin gidan. Tunda na saka kafata a ciki naji wani sanyi yana bude kayan jiki na ya na shiga cikin tsoka ta, ta matse jiki ina sake kundundinewa dan ban saba jin irin sa ba. Katon parlor tamkar a film din indiyawa, mai dauke da kujeru da suka sake kayata shi, tare da talabijin kamar mutanan ciki zasu fito waje saboda tsabar girmanta. Bene ta hau ni kuma na tsaya ina kallon yadda take hawa da sauri da sauri bama ta tsoron fadowa ita, sai da ta haye sannan ta juyo taganni tsaye ina hangenta tace. “Taho mana muje.” Cikin zaro ido nace. “Ni..!?” “Eh mana da wa nake yiwa maganar.?” Na hadiyi miyau tare da sunkuyar da kai kasa, da alama yar uwar su ce ganin tana da fadin rai. “Ni dai bazan iya ba.” “Ba zaki iya mene ba?” “Hawa inda kike so nazo.” “Oh so kike nazo na goya ki na doroki ne?” Nayi saurin girgiza kai nufin a'a amman har lokacin banji zan iya hawa ba saboda tsananin tsoro. Ta juya a fusace tana masifa tamkar wacce na yi mata mugun laifi, ni kuma tsakani da Allah ji nayi ba zan iya hawa ba, ina ganin tamkar zan gangaro saboda santsin tiles da yake ta sheki. Ina tsaye sai gata sun fito da matar gidan wacce naji suna kira da Mami, ta kalleni tare da cewa. “Dije hawo mana.” Na hadiyi kakkauran miyau saboda shiga tashin hankalin yadda zan iya hawa benan. “Ba zan iya ba wallahi.” Nayi magana a sanyaye. “Okay Jummai jeki riko mata hannunta.” Ta taho tana zuba min harara ta rike min hannun dama na, ya yin da ni kuma na rike karfen binan da hannun hagu muna hawa da kyar. “Ki saki jikin ki Dije babu abin da zaki ji.” Cewar Mami, haka na hau ina rike da Jummai wace ke ta faman yi min dariya kasakasa. Ina hayewa kuwa na zauna ina sauke numfashi da kyar. Mami ta riko hannu na muka karasa parlorn tana ta dariya itama ganin yadda nake ta kallon tsarin parlorn ya matukar firgita ni dan yaci uban na kasa komai da komai. Muna nan zaune sai muka ji muryar mutane suna hawowa benan da gudu ko tsoro basa ji. Yan mata ne su biyu sanye cikin dogayen riguna na larabawa, sunyi kyau a ciki ba karya, suna shigowa suka haye kan cinyar Mami suna furta. “Wassh Mami mun gaji.” Tace dasu. “Gajiyar ce ta hanaku ganin bakuwa ko?” Duk sai suka tashi suna kallo na a tare, na yi saurin sunkuyar da kai na ina wasa da mayafin jikina. “Dije ko?!” Suka yi maganar cikin alamun tambaya suna sake kallon Mami, ta gyada musu kai tana murmushi. “Ayya! Allah sarki Dije, ya hakurin Baffan ki.?” Hawayen da yake shirin zubo min sukai saurin komawa saboda bana son zubar su, Dara'ifa tace min kuka na azaba zai karawa iyayen nawa, addu'a zan dinga yi musu, nace dasu. “Alhamdulillahi na gode.” “Haba Dije meye na godiya, munso zuwa gaisuwa Allah be yi ba. Sai kuma Daddy yace ai dakko ki zai yi gabaki d'aya ki dawo nan gida. Welcome Khadija, munyi farin cikin zuwan ki cikin mu kinji?” Daya daga cikin su tayi maganar cikin nuna kulawa, ta kare maganar da cewa. “Ni suna na Hameedah, nice babba a gidan nan. Sai sister dina wato Shukrah yar auta kenan. Ba tare aka haife mu ba, na bata shekaru biyu amman kinga kan mu ɗaya saboda tsahon kafa gare ta.” Duk aka yi dariya yayin da ni kuma murmushi na saki dan ji nake wata iri da ni. Duk baki na da rashin kunya ta ji nayi ina mugun shakkar mutanan gidan. Gashi dai basu nuna min kyama ba, suna nuna kulawa a gare ni. Amman a lokacin na kasa sakin ciki kamar wacce aka yiwa ture na rashin walwala. Daga nan Mami tace su tafi dani dakin su nayi wanka nazo naci abinci. Shukrah itace ta kama ni muka nufi dakin su, a nan naga aljannar duniya, wato yaran yan gata ne na bugawa a jarida. Komai na cikin dakin guda biyu ne kuma cikin tsari ta yadda tsarin ya kawata dakin matuka. “Toh Dije ga toilet nan ki shiga, akwai ruwan zafi a heater.” Ban san mene heater d'in ba kuma ban tambaye ta ba, haka na ajiye carbin hannuna dama na Baffa ne na dauka domin ya zame min madubi da zan dinga gani ina tunawa da shi a zahirance. Na bude kofar da suka nuna min sai dai na kasa shiga dan banga ya yi min alamar cewar bandaki bane. “Dije shiga mana.” Tamkar wacce zata saki kuka haka nayi magana. “Banga bandakin ba ai.” “Ikon Allah, gaki nan a kusa da kofar kin bude.” “Daki ne fa.” Ai sai kawai naji sun kwashe da dariya abin ya bani haushi na dawo na zauna akan wata kujera da na gani a cikin dakin ina ta turo baki, Hameedah ta juyo tana kallo na tace. “Bandaki ne wallahi Dije, ya za'ai mu kai ki daki muce kiyi wanka a ciki? Zo ki gani na nuna miki.” Ta shiga sannan na bi bayanta, Shukrah na daga bakin gado tana ta dariya ta kasa yin shiru saboda keta. Hameedah ta kunna wani guri ruwa ya zubo cikin wani abu mai dan zurfi da kuma tsaho da alama ruwa ake tana da a cikin sa, naji tana cewa. “Idan ya kusa cika sai ki kashe nan wajan zaki ga ruwa ya dena zuba, sannan sai ki cire kayanki ki shiga cikin ruwan nan kiyi wankan. Ga sabulu nan da soso kiyi amfani dashi.” “Jakar uban can kayyasa! Cikin wannan uban ruwan zan shiga sai kace wata kifi ko kwad'on ruwa?” Dukan su kuma sakin dariyar suka yi, dan ita Shukrah har da hawayen ta tsabar dariya. Na kallesu cike da jin haushi ina turo baki tare yin gunguni ina zagin su a rai na. Meye na dariya bayan maganar gaskiya na fada, banda rainin hankali su kawo guri harda madubi da mayuka shegen jarkokin da malama Mardiyya take matsowa ta shafa shine zasu ci min toilet ne? Hameedah ta fita ta kira Mami suka taho tare. “Kinga kira ni kina ta faman dariya menene wai?” “Mami wallahi Dije dai taki shiga cikin toilet wai daki ne, kuma ta ya zata shiga cikin ruwa kamar wata kifanya ko kwaduwa.” Itama Mami sai ta saki bakin tana rike habarta idanunta a kai na take cewa. “Dije ai wannan ba daki bane, cikin nan inda muke shine daki. Nan da suka nuna miki toilet ne da ake bayan gida ko wanka, ki dena damuwa a hankali zaki fahimci komai, yanzu dai ki taimaka ki shiga kiyi wankan duk yadda kika ga dama.” Na sake komawa ciki na tsaya ina kallon yadda aka kawata shi, ni da naga na malama Mardiyya ina ganin shi aljannar duniya, ashe ga aljanna na ban sani ba. Na duba naga sam babu bokiti a bandakin kuma bana son kuma yin abinda zasu min dariya sai kawai na cire kaya na dauki wani kofi da na gani sai na dinga dibar ruwan da Hameedah ta tara cikin kwami ina tsaye ina wanka na. Abin da ya sake daure min kai a ciki shine, da na waiga sai naga kai na a cikin madubi na hango kumfa a inda hannu na baya kai wa sai nasa ruwa na watsa a gurin, na kuma matsawa wajan madubi ina duddubawa ko akwai inda bai fita ba. Ashe amfanin shi kenan a ciki, ikon Allah gaskiya yan gayu komai nasu daban yake. Ina gamawa na saka skirt dina tare da jansa sama wato har kirjina sannan na fito sai faman muzurai nake kamar bani da gaskiya. “OH my God Dije, maimakon ki dauro towel kawai sai ki sako skirt ɗin da kika cire.” Shukra ta yi maganar tana yatsina fuska da murmushi a fuskarta. “Ai ban ganhi Au ban ganshi ba.” “Kai! Ohh Dijeh, daman har yanzu ana hi da hah a duniyar nan?” “An dena walle.” Ta kuma sakin wata dariyar. “Kin kuma ai Dije, mu bar wannan maganar kawai zo ki shafa mai kisa kaya muci abinci.” Na amsa mata sannan duk suka fita ni kuma na janyo jakar kayana da Jummai da shigo min dasu, na ciro basilin dina na shafa sannan na ciro riga da zani nasa tare da zauniya a kasa na zabga tagumi ina tunanin yadda rayuwa ta zata kasance a cikin wannan gidan. “Dije ki fito muci abinci ma, kin zauna anan kina ta tunani?” Hameedah ta leko tana min maganar. Na tashi nabi bayan ta muka nufi dining da gurin kansa abin kallo ne bare kuma yadda aka kawata kan table d'in da abincika kala-kala. Kamar yadda naga sun zauna haka nima naje na zauna ina ta raba ido. “Dije maimakon ki sako kaya mararsa nauyi shine kika jibgo wata atamfa?” Nayi murmushi kawai ban ce komai ba saboda ko tace naje na saka mararsa nauyin to bani dasu dan haka shiru kawai shine a wajan. Shukarah ta fara zubawa kowa wanda yace yana so, ni kuwa daman bama sanin abubuwan nayi ba bare nima fadi nawa ra'ayin, koda aka tambaye ni ma cewa nayi a bani koma menene zance dan ni babu abinda bazan iya ci ba indai naci din ne. Ai kuwa ta zuba min farfesu na naman kaji da ya sha kayan kamshi na lashi lebe na sama da kasa yo yaushe rabon da a hadu? Ta miko min harda sako min wani cokali mai yatsu na kuwa cire na ajiye shi a gefe na zura hannu ina dakko tsokar kazar nama ina dannawa cikin bakina. Ana ta hira amman ni sam bana sauraron su nama na kawai nake ci ina korawa da lemon kwakwa mai dan karan sanyi da yasha madara har wani gardi-gardi yake yi alkuran. Haka muka gama ci kowa ya yi harkar gabansa, ni kuma tunda na samu tv na zauna ina ta kallo shirye-shiryen su yana dada bani sha'awa da kara karfafin gwiwa wajan son yin aikin jarida. Sallah ce kawai take iya tayar dani daga gaban talabijin d'in nan. Koda nayi sallah isha'i dawowa nayi naci gaba da yin kallon, su kuma mutanan gidan kowa ya tafi yin harkar gabansa, a nan bacci ya dauke ni, koda uncle Isma'eel ya dawo anan ya ganni ina ta bacci kan kafet nayi rashe-rashe tamkar wacce tasha abin maye. Kawu yace a mai dani daki kan gado, Jummai tazo ta dinga tashi na amman ina naki tashi saboda wani irin nauyin bacci da Allah ya sakko min a ranar. Haka Mami da kanta tayi ta tashi na nan ma shiru sai kyale ni suka yi sai da uncle ya gama cin abinci ya tashi da kanshi ya dauke ni ya kai har kan gadon Shukarah yace mu kwanta kafin nima a siyo min nawa. Muna bacci na dinga yarbawa Shukrah kafafuwa na a jikinta, tun tana min kawaici har ya zamana ta dawo tana duka na wanda ban san tana yi bama saboda tsabar bacci dana’urar sanyi abinka da basabin ba, Da asuba take bamu labari, kuma ni dama ba gwanar iya ba da hakuri bace tun ina karama ballanta kuma da na fara girma. “Wai Dije ba zaki ban hakuri ba.?” Na kalleta da mamakin jin abinda take fada, sai kuma na shiga yatsina fuska alamar bafa zan bada ba. “Dije tazo inji Mami a kasa.” Cewar mai yiwa su Hameedah gyaran daki da wasu aiyukan da suka shafe su wato Lamtana. Na tashi da sauri nabi bayanta dan ba hakurin nan zan bayar ba komai zata yi min. A zazzaune na tarar dasu, na duka har kasa duk na gaishe da su sannan cikin murna da murmushi kawun nawa yace dani. “Dije ki saki jikin ki a cikin gidan nan saboda kema ya ta ce kamar yadda suke ya ya na babu banbanci. Duk abin da kike so ki gaya min ko Mami ga ta nan a zaune, uwa ce a gareki ina son ki bi umarninta kamar yadda su Hameedah suke yi mata. Sannan insha Allahu zan samar miki makaranta ki ci kaba tunda kin kammala secondary, me kike son ki karanta ne Dijeh? Dan kar naje na yi miki shisshigi cikin rayuwarki.” Na dinga soshe soshe saboda wata kunya da nauyin sa da suka kama ni a lokacin, ina murza idanuwa nace. “Kawu ni dai ina son naga nayi aikin jarida.” Yace. “A'ah a'ah a'ah! Kice zamu samu mai jiyo kwakwafa a duniya kenan? Masha Allah Dije, toh Allah ya tabbatar da alkairi insha Allahu zan yi kokarin ganin kin cika burinki na rayuwa. Tashi kije Allah ya taimaka.” “Amin kawu na gode.” “Yauwa bana son wannan kawun da kike kirana dashi, ki kirani da sunan da kikaji mutanan gidan nan suna kira na wato daddy..” Nayi dariya ina rufe fuska da tafukan hannayena tare da tashi na tafi, na tsani hawa bene saboda tsoronsa nake ji, duk sanda zan hau ji nake kamar za'a turo ni na gangaro ko nayi baya idan ina hawa. Har na kusa gama hayewa sai kuma na dawo na sakko, na koma parlor sai na tarar basa nan. Fitowa nayi dan har ga Allah bana son zama guri d'aya dan bahaushe yace zama guri d'aya tsautsayi ne. Lamtana na gani zata shiga mota, da sauri naje na tambaye ina zata je, tace cefane zata yo, na hade hannuwa ina rokonka akan dan Allah ta tafi dani na raka ta, aikuwa tace to na shiga muka tafi ina ta sake ganin birni da suke abubuwan su cike da burgewa. Ina biye da ita har ta kammala siyayyar muka dawo mota driver ya dawo damu. A farfajiyar gidan muna shiga da mota na hango matar Kawu Isma'il wato Hajia Abeedah (Mami) da kawarta suna zaune akan fararen kujerun dake zagaye da yar balcony’ din farfajiyar. “‘Mami mun wuni k’alau, Ina yini Hajia?” Na gaishe da Mami da kawarta cikin ladabi, Mami ta amsa da fara’a, Kawar kuma ta debe ni ta watsar, Mik’ewa nayi na shige ciki abuna. Ina shigewa nabi kofar dana rufe da kallo ina harararta tamkar ita taki amsa min gaisuwar. “Abeedah! Wacece wannan? Karki cemin sabuwar mai aiki kika dauka haka? Bakya tsoron abunda zaije ya dawo?” “Hmm! Hajia ba yar aiki bace. D’iyar mai gidan nan ce, Yar kanwar suce data rasu shekarun baya.” “Ayyo to! Ai kuwa tamkar ita tayi kanta. Tab ni fa bana son rikon ya'yan yan uwa n miji, Akwai su da kisisina ga shiga tsakanin ka da mijin ka.” “Anya kuwa? Wannan fa yar kauyen kayau ce fitik. Kawai dai dan tana da zubin manyan mata ne, Ga kyau tamkar ita ta kera kanta. Ai babanta ance bafulata ni ne, Shima bai jima da rasuwa ba.” “Allah sarki! To amman dai kiyi takatsan tsan.” “Insha Allahu!” Dakin mu na shige ina mai yage hijabin jiki na, Ya Shukrah ce kawai a ciki Ya Hameedah bata nan. “Assalamu Alaikum!..” “Wa’alykm Salam Oganniya Dije!” Na murtuke fuska ina gatsine baki, “Ya Hameeda an tsine wannan sunan fa...” “Inji wa? Karya kike bayan ke kika bamu labarin? Aina aka tsine? Jia ko shekarn jia?” Na sheke da dariya ina kallon kai na a mudubin su mai tsaho, Zaka iya ganin kanka gaba ki dayan ka a tsaye. “Sunana Nana Khadija.. Ko Ummi na yadda Baffa na ke gayamin sanda yana raye.” Ya Hameeda tayi murmushi kawai tana gyad’a kai, Bandaki na shige nayo wanka sosai, Kafin na sauya kayan jiki na zuwa doguwar riga marar nauyi, irin tsarabar makkan nan. Jefi jefi mukan taba hira da Ya Hameeda har Kawu ya dawo yace akirawo mu duka, “Kawu Sannu da zuwa..” “Yauwa yar kawu duk da dai nace bana son ana ce min haka! Ba dai matsala ko?” “Babu Kawu!” “Yauwa munyi magana da wani Professor anan jamiar da zaki fara, Yace suna shirye shiryen ranar da zasu sanya ku fara lectures, Saboda haka kafin sannan nidai na yanko miki form a center din da su Hameeda suka koyo British English, Saboda ki sake wayewa da ilimin sa. Ai h..” “Alhaji Wai British eng learning centre dai?” “Ita! Meya faru?” “Uhm! Alhaji gani nai tayi tsada, Haj Luba ma kasa sa yarta tayi.” “Toh sai akai yaya? Ina ruwana dan ta kasa sa yar ta. Ni Khadija ba ‘yata bace? Kafin na samu nawa ‘yayan wana fara samu a duniya? Mahaifiyar ta Jamila daga ni sai ita, Kuma duk duniya babu wanda nakeso sama da ita duk cikin yan uwana, Kuma gudan jininta wadda itama ‘ya ce agare nin zan ki kyautatawa? Shekara nawa ina rokon abani ita na rike hakan bai samu ba sai yanzu. Karki batamin rai hajia. Yauwa Khadija monday zaki fara attending classes dinsu, Na tsawon watanni uku ne kacal. Hameeda ga MasterCard dina da safe ki kaita shopping ki sauya mata da irin shigar mu tanan, Ku bawa tailor dinku dinkunan ta, Ki kaita saloon a gyaro mata kan ta amata manicure..” Ni dai shiru nayi ina sauraron Kawu tamkar a mafarki, Mami tayi kwafa tana kada kafa, “Alhaji wannan yawon ai ba na Hameeda bane sai dai ko driver ya kakkaita. Amma ya za’ai ta katse schedules dinta ta kaita koina?” “Toh Hajia ai gidan ki ne, Ya’ya kuma naki ne ko? Shikenan yayi kyau! Khadija ki shirya da sassafe ni zan kaiki ko’ina. Jeki debi abinci kici ki kwanta.” Kada kai nayi na silale na gudu da’ki, Ina jiyo sanda ya koma parlorn sa, Mami nata tsaki tana mita, Hameeda ma na taya ta. Jiki na gaba d’aya ya saki yayi sanyi, A darare Na fita na shiga kitchen na zuba abinci naci acan, Na koma daki na kwanta. Saboda Banda nauyin Bacci ina jiyo sanda Ya Shukra ta dawo suka hau bata labari . A haka bacci yai awun gaba dani, Bansan sanda suka dena magana ta ba. *WASHE-GARI* Da wuri na tashi na shirya, Na wanke bandaki, saboda na fara gane kanshi da amfanin wasu abubuwan dake cikin sa. Sunata kumbure fuska a haka na bisu na gaggayshe su, Ranar Kawu ko abincin safe bai ciba yace muje, Gurare sosai ya kai ni ya narkomin kayan yan gayu da atamfofi da laces da materials, Abayoyi suma fal da takalma da jakankuna Harda kayan kwalliya dana man shafawa. Ya biya ya bawa tailor ya gwada ni, Daga nan muka je salon aka wankemin kai na, Aka gyaramin kafata da farata na. Wallahi tamkar ba ni ba. Daga nan ya biya dani kasuwar waya, Ya siyamin dalleliyar waya ta zamani. Wallahi tsabar farin ciki Bansan sanda nasa hawayen dadi ba, Na shjga kwararawa Kawu addua. Ranar dai gaba d’aya cinyeta mukai a bukatu na, Sannan ya dire ni a gida ya wuce kasuwa. ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _*SIRADIN RAYUWAR BILKISU, KIBIYAR AJALI, MIN QALB, ABINDA KE CIKIN ZUCIYA, SARAN BOYE... DUKA NA KUDI NE. AKAN NERA DARI BAKWAI KACAL. NEMI NAKI YAR UWA. KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA WADANDA KE RUBUTAWAR..DOMIN MALLAKAR NAKI ZAFAFA BIYAR DIN TUNTUBE MU A NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFIN_* ____________________________ _*ANNUR PERFUMES_* _(MASARAUTAR KAMSHI)_ _INA MASOYA TURAREN WUTAN MAIDUGURI? YERWA FATO😉😍TO KU MATSO KUSA... GA DAMA TA SAMU, KINA SAN TURAREN WUTAN DA ZAI KAMA GIDA YAYI SATI YANA KAMSHI? KINASON TURAREN KAYA DA KO KIN WANKE BA ZAI DENA KAMSHI BA? KINASON KHUMRAHS HADADDU DA SUKA AMSA SUNAN SU? SHIN KIN TABA AMFANI DA KULACCAM DIN YAN MAIDUGURI? WANDA KAMSHIN SA KESA KISHIYA KWAFA?😉 KADA NA CIKAKU DA SURUTU.._ _*ANNUR PERFUMES* MASARAUTAR KAMSHI KENAN, MUNA BADA TURAREN MU AKAN FARASHIN SARI DA KUMA SAYI ‘DAI-DAI, SHIN NA LISSAFO MUKU ABUBUWAN DA MUKE SIYARWA KUWA?_ _TURAREN WUTA (NA KAYA/ GIDA/ JIKI/ DA TSUGUNNO. KHUMRAH, KULACCAM,_ _MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)_ _DECORATIONS (NA GIDA/OFIS/ KAMFANI DA SAURAN SU/ MUNADA INGANTATTUN KAYAN INFECTION (HERBAL WANDA BA ZAI SAKI WANI SIDE EFFECT BA, MUNADA DANA MATSI (STEAMING)_ _ANNUR PERFUMES NA GARIN *KANO* ADIRESHIN MU: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!. LAMBOBIN TARHON MU: 07086341096//07069037534. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NIJERIYA. SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA SAI ANNUR PERFUMES_ _WANNA SCENT EXOTIC??HEY.. WHICHEVER WAY YOU WANT IT WE’VE GOT YOU COVERED AT *ANNUR PERFUMES(CASTLE OF SCENTS)* FOR YOUR MIND/ YOUR SOUL.. AND YOUR HOME.. BE THE CENTER OF ATTRACTION WITH ANNUR PERFUMES.. WE ARE YOUR SCENT PLUG..TANTALIZE YOUR SENSE OF SMELL AS YOU SINK INTO BLISS. SAY NO!! TO DAMP SMELL LOVELIES. OUR DUKKANS LAST’S LONGER AND LINGER. VERY AFFORDABLE... DELIVERY IS NATIONWIDE 😉😘😍_ _13//KASBTSTW_ *BRITISH ENG LEARNING CENTRE* Idanuwa na shiga zarewa a lokacin da driver yai parking mota a harabar wajen. Fitowa nayi dakyar ina harhade tafiya ta, Koda wasa bantaba hasashen kasancewa ta acikin jajayen kunnuwa ba. Gyara zaman rigar abayar jiki na nayi na shiga ciki. Tamkar a k’asar waje haka wajen yake, Sai hada hada akeyi, classes ne sosai tamkar makaranta. Kowa kagani awajen nan kasan dan wani ne. Wai yau ni Dije ni ce acikin manyan mutane? Alhamdulillah Yaa Rabbi. Zuwa nayi na karb’o ID card dina da sauran abubuwan da Za’a buk’ata na handouts da books. Ajinmu aka kai ni, Kowa da computer a gaban sa da earpiece saqale a jikin kunnen sa, Wurin zama na aka nuna min na zauna nima nayi duk abunda naga sauran daliban nayi, Sosai ake koyar damu ilimin turanci da yadda zamu dinga magana irin na British English. Both oral and written. Sosai nake enjoying lectures din da Mr Charles yake koya mana, Gashi yan ajin kowa kansa a waye, Gaskia birni tayi ba irin karkarar mu ba masu duhun kai, Lalle Ilimi na kai ka inda baka tab’a Zata ba. Haka dai malaman sukai ta koyar damu duk sati banda ranakun hutu (weekend days). Kafin kace me? Mun kammala koyan turanci kasar ingila, Hakika Idan nayi maka magana na juye baki da turanci ba lalle kace ni ce Dije Oganniya ba. Saboda gaba d’aya yadda nake magana a hankali cikin turanci da iyawa Kai ka dauka wallahi baturiya ce. Cikin haka aka fara lectures na university. Sai na mayar da zuwa koyan turanci Ranar asabar da lahadi kawai.. Yau ni Dije ce a jamia? Sosai muka fara lectures babu wasa, Kullum driver ne ke kai ni ya dakko ni, Kawu Ismail ya tsayamin tamkar uba na. Matsala d’aya nake fuskanta a gidan nan bangaren Mami da yaranta. Bantaba sanin ana tsantsar Kishi da hassada tsakanin matar kawun ka da ya’yan ta akan ka ba, Meyasa? Oho! Na bawa kai na amsa. Wallahi dik iya tsawon shekaru na da duhun kai na alokacin da ina k’auye, Na dauka Gajiyalle abinda yasa takemin haka saboda nazo a yar kishiya ne. Na dauka lokacin da na dawo dangin mahaifiya ta zanji sassauci. Yanzu a gidan nan gaba d’aya Mami da su Ya Shukra da Ya Hameeda basa shiga shirgi na, Tsakani na dasu sai hantara da kyara. Kawu ne kawai baya min komai, Yana ko’karin ganin ya yaye min kuncin rayuwa, Kai ko siyan kati shike turomin bana siya, Ga bani kudi da yake akai akai. Jin sa nake tamkar mahaifiya ta wallahi, Kuma suna kama sosai da mahaifiya ta, Ya nunamin hotunan su sanda suna k’anana.. Na fara zuwa lectures a jami’a, Sannan ina zuwa tahfiz a islamiyar dake bayan gidan mu. Ga British Eng learning centre da nake zuwa ranar weekends da yamma. Na kara wayewa, Kala ta tafito, Na murmure, Kai idan kasan Dijen Durbun a baya ba zaka tab’a cewa ni ce Nana Khadija a yanzu ba. Saboda yawan fad’an da su Ya Hameeda ke takala na dashi yasa Kawu ya raba mana dakin Kwana. Akwai wani k’aramin da’ki da ake zuba shirgi, Rannan yasa aka debe komai aka saka madedecin gado mai cin mutum d’aya, Yace na kwashi kaya na na koma can. Hakan kuwa akayi, Na tattara na koma can. <<<<<>>>>>> <<<<<<<>>>>>> <<<<<>>>>>> Haj Abeeda ce ta shiga zagaye a dakin ta, Tunda Alhaji Ismael yake wa Dije hidima tafara jin haushin hakan, Ta kuma dora yaranta akan network din tsanar Dijen. Wayar ta ta janyo dake chaji akan dressing mirror ta kira Haj Lubna bugu biyu ta dauka ta kara a kunnen ta, “Hello Hajjaju..!” “Na’am Haj Abeeda! Ya gida? Ina yarana?” “Sunanan qalau Haj.. Kina gida ne?” “Ina gida dawowa ta a office kenan..” “Toh gani nan zuwa.” “Lapia dai ko Hajia?” “Hmm’ Kede bari labari ba zeyi a waya ba.” Shiryawa Haj Abeeda tayi ta fuce, Dama already ta gayawa Alhaji Ismael Zata fita yau. Driver na sauke ta ta shige ciki ranta a bace, Bayan sun gaysa ne, Haj Abeeda ta sake jan tsaki a karo na ba adadi, “Hajia.. Subhan’Allah! Meya faru?” “Ki bari kawai.. Ashe yarinyar nan munafuka ce? Shigo shigo ba zurfi tai mana? Ai Alhaji ya rufe ni Haj, Ke kinga hidindimu. Hmm!” “Kin sani a dubu! Wacece haka?” “Yarinyar nan mana Dije. Wadda kika dauka yar aiki ce? Kinga uban barin kudin da Alhajin yake mata?.” “Hm kibar dangin miji! Basu da farin cikin daya wuce shiga tsakanin ka da mijin ka, Ai nagaya miki nace Kiyi taka tsantsan baki ji ba.” “Wallahy Na dauka tunda yar kauye ce, Irin makarantun nan haka na yakubayi za’a sata, Har nace su shukra su hada kuncen kayan su na babbata, Ashe ashe.” “Yanzu wai meya faru..?” “Ina centre dinnan ta British Eng? Me shegen tsada?” “Sabuwar nan da akai shekarun baya ko?” “Ita dai.. wadda har yar Hajian Badawa ma ta kasa shiga, Nima da kyar da jibun goshi da magiya Wallahi ya yadda ya saka su Hameeda lokacin. Yace tayi tsada, Yanzu kuwa kudin ta yayi doubling.” “Nagane Haj. Nima nan ba Sameer bane kadai yayi?” “Toh wallahi ina kai ki dai ya yanko mata form ta fara zuwa, Ga Buk nan ma ya samo mata admission, Yace Hameeda ga MasterCard dinsa ta kaita shopping malls ta siyo mata komai, Ta bawa Senegalese tailor dinmu ya mata dinkuna..” “Kai... katarar ubancan! Alhajin?” “Hmm Wallahi Hajia! Nace masa sede driver amma Hameeda ba zata ba.” “Shine ya harzuka Yace shi zai kaita, In k’ark’are miki zance dai, Ya lafto mata uban kaya, Ga latest waya datafi tasu Hameeda, Ga kayan gyaran jiki, ke Kinga yadda ya dawo da ita a rana d’aya kacal? Komai designers wallahi Hajia. Hmm ai ya kawomin alaka’kai gida..” “Kuma Hajia yar kanwar sace?” “Wallahi yar kanwar sa ce mai rasuwa, Ke da ba haka ba Ai sai muce auren ta zai yi. Toh Allah yasa ba aure a tsakani.” “Toh Hajia ki tashi tsaye.. Zahiri yarinyar nan tazo da dan asiri daga kauyen su, Ke yan kauyen nan fa wasu ba Allah a ransu.” “Nima nayi tunamin hakan, Domin Jummai ma tafara gayamin haka. Toh ai kuwa bata isa ba, Bazata sab’uba Wallahi..” “Ina bayan ki Hajia. Ki kuma nunawa Alhajin bacin ran ki kawai akan haka.” “Ai wani irin murdadden hali ne dashi, Wannan botsattsen idan ya tsaida ra’ayin abu wallahi baya canza shi. .” “Gaskia Alhaji yabani mamaki” “Ya baki koya bani? Duk cikin yan uwan nasa ba wanda yace zai karbeta sai shi uban tausayi, Saboda anga yanada abun duniya. Yazo sai fiffita bare akan ‘ya’yan sa. Wallahi ban taba kawo abubuwan da zai yi mata sun kai haka ba. Shegiyar yarinya yar iska.” “Simi simi da ita, zubin munafukai.” “Wallahi na dauka ta Allah ce yarinyar nan, Zata dauki maraicin ta ta iya talaucinta, Shegiya wai masscom zatai. Hm!” “Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu Hajia. Amma dai yarinyar nan sai kinyi dagaske, Kar ta raba uba da ‘y’ay’an sa..” Haka dai Hajia Abeeda da kawarta su kaita aibata Dije, Haj ta jima a gidan k’awarta na sake mata famfo, Ta dawo gidan ranta a bace, Muryar Mami na jiyo alamun ta dawo, Ina tsaye agaban Ya Shukra ina rokonta data temaka ta gayamin ma’anar wasu kalmomi. Mami ta bugo kofa tashigo, Ta dube ni a harzuke tana ajiye mayafi, “Meya haka.?” “Mami aiki zata koyamin..” Na bata amsa ina nuna Littafin hannu na, Ya Shukra ta ajiye biron hannun ta tana kallon Mamin a tsora ce, “meaning din wasu words ne tace dan Allah na gaya mata.” “Toh idan kin gama kizo daki Ina neman ki.” Kada kai Ya shukra tayi , A dubibice ta gama koyamin ta shige dakin Mami, Ina jiyo sanda Mami tasa key ni kuma nai saurin hayewa sama gudun kar ma na jiyo Abun da zai hanani bacci. Toh haka zaman namu ya kasance, Yau dadi gobe babu. Ni dai zaman nan din yafu min sau million dari akan na Durbin. Domin nan ba duka, Ba zagi, Ba hana abinci. Sai dai mita da bakar magana da Mami kan yab’amin. Wani lokacin har fada take janyowa tsakanin mu da su Ya Hameeda. B<><><>< Hutun first semester da aka fara yi mana mai dogon zango, Kawu yasa na shirya driver ya fara kai ni gidajen yan uwan mahaifiya ta da suke nesa, Jos muka fara zuwa nayi sati biyu a gidan kawu Kabiru, Sunji dadin zuwa na, Suka min shatara ta arziki, Daga nan kawu ya yankamin ticket na garin lagos inda kawu Hashim yake. Tab Dije a jirgi, Na danyi kauyanci kadan inata kalle kallen cikin jirgi, Dak’yar na sai ta kai na muka karasa birnin ikko. Sati na biyu acan nan ma kafin na dawo gida da d’imbin kayan alkhairi. Duk inda naje sun mini kyauta ta mutuntawa, Daga nan Kawu da kansa ya zazzaga ya da ni gidajen yan uwa na cikin kano na gaggayshe su, Lalle dangi rahama ne. Dake hutun wata biyu ne, Kawu ya sanya ni a computer school inda nayi certificate na tsawon sati uku ne. Hakika dik wani gata Kawu yana yimin shi. Gashi yanada temakon al’umma mabukata da masu shi, Yana temakawa marayu, Ga foundation da yake da ita na tallafi. Gaskia Kawu mutum ne. Saboda temakon da yake yi ne ashe yan kasuwar manya da masu kana'oin sana'oi suka kada 'kuri'u suka tsai dashi, ‘Shugaban kasuwar Singa. Saboda temako da yake yiwa masu karamin karfi a kasuwar. Kuma Doctorate degree din sa ma honorary doctorate ne da university of east london ta bashi. *BAYAN WASU SHEKARU* Alhamdulillah Ya Rabbi! A yau ne sunana ya fito a call-up letter na Nysc. A kano nayi orientation camp dina na sati uku, Kawu ya samomin wani gidan rediyo da talabijin na kasa mai suna Dokinkarfe24 wanda keda sashe anan kano. Anan na fara service dina na shekara d’aya. Har Allah yasa na kammala lafiya. *DOKIN ‘KARFE24 TV/ NEWSPAPER AND RADIO STATION* Alhamdulillah! Na shiga jujjuya offer dina a hannu na aiki, Da gaske ba mafarki nake sun karb’e ni a matsayin ma’aikaciyar su? Lokacin da nazo service (place of primary assignment/Nysc) Koda wasa bantaba kawowa zasu dauke ni a gurbin ma’aikaciyar su ba, Wai yau ni Ni Nana Khadijaa na zama cikakkiyar yar jarida kuma ma’aikaciyar gidan tv na Dokin Karfe24? Kaf kano babu gidan talabijin din daya ko kamo k’afar sa. Sune na d’aya dake tashe ance tun shekarun baya. (Television/ Radio station/ Newspaper) Duk Dokin karfe24 na kammale dasu. Kamar sabuwar tabi haka na tsaya ina kallon offer ina murmushi. Cikin haka Mas’oud saurayi na yazo ya same ni hannunsa rike da kwalbar maltina sanyayyiya. Yana zuwa yaja kujerar kusa dani ya mikomin yana murmushi, “Maman Waleeda da Waleeda..” “Na’am Baban Waleeda da waleed” Domin mun rigada mun tanada sunan da zamu sanyawa yayan mu na farko idan munyi aure, Saboda tsabar yadda mukeson junan mu. Mas’oud ya dakko jaridar gefen sa ya shiga min fiffita a fuska, “Sannu tawan.. Congratulations! Ai na gaya miki you wud surely made it, Kuma wallahi ko kadan banwa boss zancen ki ba, Su suka ga cancantar ki.” “Hakane Nawan! Alhamdulillah! Nagodewa Allah. Kai ma na gode maka yadda kake encouraging dina. Thank you so much.” “Anything for you, My love!” Rufa fuska ta nayi da tafin hannu na, Saboda yaja kalaman ‘My love’ din. Kai Mas’oud karshe ne a iya soyayya! Anya akwai na biyun sa kuwa a tsarin iya tattalin mace? “Tunanin me kike yi ne tawan?” “Tunanin ka mana Habiby..” Na karasa fada ina kanne mai ido d’aya, Murmushi yai yana gyara zaman hular kansa, “I’m all yours My love.. Sai yadda ki kai da ni. So ya zaki fara aiki ne yau ko sai nextweek din kamar yadda boss yace?” “No sai nextweek ko? Saboda na dan kara shisshiryawa.” “Banda dai heavy makeup, cuz I wont tolerate that my love, Banso sauran maza su rika kallemin ke. Ni nafuso ma ki rika saka hijabs da safar hannu data kafa.” Cuno baki nayi gaba domin wasu dabi’una na rigima ban dai naba, Na fari da idanuwa na kafin na narke su akan sa, “Ni ni ni gaskia a’ah! A wannan zafin Habiby? Ayi hak’uri dai.” “Oh rigimatu na.. Na hak’ura! Idan kin zama Mrs Mas’oud ai dole kisa. Muje nai dropping dinki a gida.” Handbag dina ya dauka da sauran kayayyaya ki na, Muka jera muna tafiya gwanin sha’awa, Motar sa muka shiga ya kai ni har kofar gida. Kawu ya dawo domin ga motar sa nan da direba a waje, “Zaka shiga ku gaysa da Kawu?” “Afuwan My Love! Zan dai yi fixing lokaci, Kinga yanzu ba’a shirye nake ba. Zanzo zuwa na musanman.” “Kullum haka kake cewa Habiby..” “Worry not My love! Ina nan tafe. Kinsan zuwa gaida manyan nan sai ka shrya tukun, Kuma so nake idan nazo gaisuwar ya kasance da yan kwanaki a kawo komai na aure.” “Hakane! To Allah ya kai mu. Ya tabbatar mana da alkhairi Aamin.” “Aamin” Sallama mukai irin ta masoyan da suka reni kansu da soyayya! Domin har gaban abadan zuciya ta bazata taba son wani Da namiji ba face Mas’oud. Saboda shine saurayi na na farko wadda zucia ta ta amsa sak’on soyayyar sa. Na riga na gina sonsa a zucia ta, Babban buri na yanzu a duniya bai wuce na zama mata agare shi ba. Da wannan tunanin na shige cikin gida, Fuska ta dauke da farin cikin abubuwa biyu. Zamana cikakkiyar yar jarida da kuma neman aure na da Mas’oud zai zo. Alhamdulillah Yaa Rabbi! <<<<>>>>> <<<<<>>>>> Fitowa ta daga wanka kenan ina tsane jikina da towel kasancewar har kai na sai da na wanke, shigowar Ya Shukrah tana faman danna waya sanye cikin riga da wando kanta babu dankwali sai faman taunar chewing gum take yi, na dan saki murmushi duk da cewa ba kulani suke yi yanzu ba sai wulakanci da rashin mutunci da suke yi min ganin daddyn su yana min komai irin nasu baya ko banbantawa, shine dalilin da yasa suke tsangwama ta. Na ajiye small towel din akan stool ina shirin janyo man shafawa nace. “Ya Shukrah tsifa kika zo nayi miki ne?” Ta sakar min harara tare da yi min kallon sama da kasa kafin tace. “Ban sani ba, da yake in zaki yi min tsifa tasowa zanyi nazo kiyi min ko? Wai me yasa duk abinda ya danganci yar kauye sai ta nuna a wajen? Mtseww village girl, Mami zaki je ki gyarawa daki mai bin maza kawai.” Kalaman ta na karshe ce tasa kirjina bugawa, nayi saurin dafewa ina fito da idanuwa. Ban taba tunanin duk irin wulakancin da zasu yi min zai kai ga yi min sharri irin wannan ba, tabbas wannan mugun sharri ne dan ko a school bani da abokai maza bare yanzu da nake da wanda zuciya ta ke so. “Ya Shukrah ni nake bin maza?” “Oh! Zan miki sharri ne? Har driver daddy ya baki amman kika hana shi zuwa daukar ki sai wani Kato ne ya dawo dake.” Jiki na ya yi mugun sanyi hankali na ya tashi, yanzu kallon da zasu yi min kenan? Sufa duk suna da motocinsu, kuma babu kalar mutanan da basa dauka a ciki, sai ni daga yi sau daya shine zasu ce ina bin maza saboda kawai basa ganin mutunci da daraja ta. Hawaye suka fara kokarin zubo min nayi saurin mayar dasu ina kakalo murmushi wanda aka ce yafi kukan cewo nace mata. “Wallahi ban taba bin wani namiji ba, idan kika dauke driver na gidan nan. Sannan bana muku fatan irin wannan abun bare ni kai na Ya Shukrah, dan Allah ku dinga yi min kyakkyawar fahimta da kuma hangen alkairi a tattare dani. Wannan da kika ga ya kawo ni gida, shine wanda muka kulla alkawarin aure a tsakanin mu, kuma insha Allahu zamu mallaki junan mu kamar yadda muke mafarki kullum.” Sai kawai ta waigo tare da sakin wata banzar dariya, irin wadda kana ji kansan ta mugunta ce kawai. “Kice ku a yan iskan ma lamba d'aya ne? Wato har mafarki kuke yi gaku akan jun.....” Ban bari ta karasa ba saboda jin kalar sharrin da zata kuma yi mana, rai na yana zafi zuciya ta tana kuna nace da ita. “Nagode nasan me zaki fada Ya Shukrah, bari naje na gyara mata dakin.” Nasa hijabi naje zan wuce ta gefenta, tasa hannu ta janyo ni nayi baya har na kusa faduwa Allah ya taimakeni na dafe madubi. “Ni zaki nunawa ba ki damu da abinda nake fada ba? Kin yi kadan yarinya, wallahi sai nayi miki shegen duka a cikin gidan nan, sakarai kawai.” Duk da ina jin zuciya ta na zugi tana tunzura ni akan cewa na yi mata abinda zai sa ba zata kara koda gigin yi min magana ba, sai dai na daure taci albarkacin mahaifinta da wallahi sai na nuna mata wacece Dije Oganniya yar Baffan ta. Na kuma tashi na yi ficewa ta sai ta biyo ni tana ta min masifa har na shiga cikin bedroom din Mami. Ita kuma ta juya ta wuce dakin su, na kalli madubi ina hawaye, wai yau ni Khadija ake yiwa sharrin bin maza. Koda ina karama ina cikin duhun kai da jahilci ban bi maza ba bare yanzu da nasan mutuncin kai na. Cigaba nayi da gyara gadon na share nayi mopping tare da kunna turaran wuta duk lokacin Mami ba ta shigo ba har na kammala na koma daki na a lokacin ne Mas'oud ya kira wayata, soyayyar da nake yi masa bata hanani duk yanayin da nake ciki sai na dauka. “Oum Waleed wa waleeda, masoyiyata abar kaunata ya kike?” Naja numfashi da kyar sannan na janyo dauriya dan kar ga gane yanayin da nake ciki na ce. “Na'am abu Waleed da waleeda, uhmm wai kai kallo ma kake yi na jiyo karar tv?” Yayi murmushi wanda idan naji ya yi sa yana kara min shaukin soyayyar shi. “Uhmmm toh, tv d'in dai a kunne take, amman zuciya ta gabaki d'aya tana gareki mai sona kuma zabi na.” “Nima haka wallahi, to wai yaushe zaka fara zuwa tadi ne gidan nan? Nifa na gaji da hirarar waya bana ganin fuskar ka.” “Zan zo Oum Waleed, jira nake yi sai na fara yiwa mahaifina magana ya bani fili idan yaso sai nazo da ƙwari na gidan naku. Fata na kawai idan nazo Allah yasa Daddyn ku ya bani auranki, ina tsoran kar nazo ace ni ba tsarinki bane my love.” Tamkar a gabansa nake haka na zaro idanuwa hannuwana dafe a saman kirjina, kafin nayi magana naji muryar Mami tana kira na. Cikin sauri na kallo bakin kofar tare da cewa Mas'oud ya kashe zanje na dawo. Doguwar riga na dauka na zura tare da fitowa ina yafa mayanfin rigar na tsaya a kusa da Mamin ina cewa. “Gani Mami.” “Ina system d'in da Alhaji ya siyo miki?” “Tana gurin Mas'oud Mami zai saita min ita.” “Ohhh! Har kinje kin bayar da ita ko? Ni zaki rainawa hankali Dije? Wato kinje kin siyar da ita baki san cewa za'a iya tuntubar ki inda take ba ko?” Baki na yana ta rawa nake magana cike da tashin hankali. “Wallahi Allah Mami ban siyar da ita ba, bari na dakko wayana kiji daga bakin Mas'oud d'in.” “Rufe min baki, ni zaki yiwa Wayo? Kin dauka ban san irin dabarun nan naku na yan kauye ba? Duk irin abubuwan da kuke yi na san shi wallahi. Wato kin waye ko? Zaki ci duniyarki da tsinke a gidan arziki. Kizo kije ki dora abincin dare, su Jummai basa nan na basu hutu na kwanaki uku, duk aikin da suke yi kece zaki yi shi a gidan nan kinji na gaya miki ko?” Zafafan hawaye suka zubo min, nasa bayan hannuna tare da gogewa. Ina ta daga kai alamun naji sannan ta juya ta koma parlor ta dauki remote ta kunna tv tare da zama ta dora kafa daya akan daya tana karkadawa. Ni kuma na juya na shiga kitchen ina kuka wanda na rasa ko na menene.... ... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _SAS...🥰😍🥂_ _14_ _NH_ Jollof d'in taliya na dafa, kasan cewar na yi ta bana cikin nutsuwa yasa ta d'an fara cabewa kadan. Na zuba cikin kula sannan na yi apple and pineapple juice nasa cikin freezer saboda sai an zauna akan table sannan ake fito dashi asha dan kar a ajiye ya huce. Dakina na koma na dauki wayata ina dubawa naga 6missed calls na Mas'oud sai 2missed calls na Aisha kawata da muka hadu a British English learning centre. Sai da na fara yin alwala nayi sallah sannan na kira Aisha muka gaisa tare da yin yar hira sannan na kira Mas'oud, yaki dagawa sai da ta katse sannan ya kira ni da kudin sa. “Ni na isa na fara cin kudin Oum Waleeda tun kafin ta zo hannu na, salon tace abu Waleed ba shi da kirki son banza gareshi?” Ya yi maganar ta sigar tsokana. “Ka cancanci ka fara cin kudin ne ai tun a yanzu, dan ka gane cewa lallai Oum Waleed mallakin ka ce da komai na ta.” Ina jiyo sanda ya sauke katuwar numfashi yace. “Gaskiya Allah yana sona gashi ya hadani da abar kauna mai tausayi na tun kafin ta zama a karkashin iko na. Madam ina kika shiga tun dazu daga cewa ina zuwa shikenan naji shiru?” Nayi murmushi ina lumshe idanuwa. “Mami ce ta sani aiki shi yasa kaji ni shiru.” “Yayi kyau Oum Waleedah. Nasan ki akwai biyayya, Allah ya nuna min ke a cikin gida na ganki kina yi min tausa.” Wata irin kunya ta mamaye ji tamkar ina gabansa haka na rintsa ido. Shi kuma ya dinga dariya saboda yasan dole kalamansa zasu sani cikin kunya. Jin na kasa yin magana ne ya sashi tsaida dariyar tashi yana cewa. “Kunya kike ji wai?” “Uhmm toh kai ma meye nayi min wannan maganar bayan kasan dole inji nauyinta.?” “Tabdijan! Wai wannan yar maganar itace ta saki jin nauyi? Kice ma sam ba zaki iya dauka ta ba dan gaskiya ina da nauyi ki dena ganin bani da jiki wallahi. Gwarama ki zage damtse wajan shirya yadda zaki dauki nauyi na idan munyi aure.” Tsabar tsagwaran kunyar da ya kuma sanya ni a ciki ne yasa ni katse wayar da muke yi na kifa kai na cikin pillow ina dariya mai cike da shaukin kaunarsa. Ji nayi kamar naje na ganshi da ido na, dan na hango yadda yake zaro min wadannan bayanan nashi da suke bani kunya. Ya sake kirana na dauka ina murmushi har hakorana suna fitowa a bayyane. “Ya zaki kashe min kira bayan ni na kira madam? Gaskiya ki bari idan ba haka ba zanyo shirin bacci nazo gidan ku na kwana sai naga yadda zaki da wannan kunyar.” “Kai! Lallai ma, kai yanzu sai kazo gidan nan da kayan bacci?” “Tsab ma kuwa, ko na gwada miki dan ki tabbatar?” “Lallai ma kai din nan.” “Bafa ki bani amsa ba Oum Waleed kinsan ai dama ni Waleedah ita ce tawa idan mun haife so.” “Haka dai kake cewa, amman ni ina ji a jiki na cewar Waleed zai fi Waleedah kyau, kar ka dawo daga baya kace na bar maka shi.” Ya sake sakin wata shu'umar dariyar tare da cewa. “Toh mu jira mu gani ko madam? Yanzu dai ki gaya min na taho d'in na taya ki kwana? dan nasan ki da tsoro.” Nayi saurin cewa. “A'a gaskiya ni bani da wani tsoro ka ganni nan, dan babu inda bazan iya zuwa ba cikin dare.” “Bafa irin wannan tsoran nake nufi ba, ina nufin na...” Ban bari ya karasa ba nayi saurin cewa. “Kawu sannu da zuwa.” Cikin wasa nayi maganar dan karma ya karasa nasan maganar ta rashin kunya ce, aikuwa naji kit ya katse babu shiru. Na kwanta kan gado ina ta dariya dan banyi wannan zaton ba na cewa zai ji tsora idan na yi haka koda ma ace da gaske Kawu Isma'eel din ne ya shigo. Ya Waleedah ce ta shigo dakin, nayi saurin mikewa zaune tare da hadiye dariyar da nake yi ina gyara zama na tace min. “Lallai Dije, saboda kawai ance kiyi girki baki ga dama ba shine kika yi ta yadda kika ga dama ko? Suwaye kike nufin zasu ci wancan jagwalgwalon da kika yi? Toh kije Mami tace yanzu ki yiwa Daddy tuwon shinkafa da miyar zogale kafin ya dawo.” Nayi saurin kallon agogo dake makale jikin bango naga karfe takwas da arba'in da hudu na dare, shine ake son nayi tuwo kuma wai na shinkafa saboda tsabar ana son a wulakantani. Toh wai dan Allah me nayi musu? Meye laifi na a cikin gidan nan? A gani na tunda kyautatawar da kawu yake yi min ne basu so me zai sa su hanashi ya dinga yi min tunda sun fini kusanci dashi? Sun takura min Allah Allah suke nayi abinda zasu yi min rashin mutunci kuma Allah yana kare ni sai dai su kirkiro wani abun su lika min. Sai kawai na gyada kai tare da sakkowa daga kan gadon nace mata. “Toh Yaya bari nazo.” “Ya fiye miki kam.” Ta juya ta fita ni kuma na zauna a bakin gado zuciya ta tana zugi. Wai dama haka rashin iyaye yake? Kodai ni kadai ce bana dace da marika nagartattu? Tabbas duk lalacewar iyayen ka, duk talaucin ku, duk tsiyar ku gwara ace kana tare da su akan kana hannun wani da basu ba. Naja majina tare da tashi na saka wayata a charge sannan na fita zuwa kitchen dan dora tuwon kamar yadda aka umarce ni. Ruwan tuwon na fara zubawa sannan naje na debo shinkafar na wanke na zuba sannan na nufi gurin hada abubuwan da zanyi miya. Banda Daddy ne zai ci wallahi sai na yi rashin mutunci naki tuke tuwon sosai, to dan dai kawai shine zan tsaya na yi har ya yi dadi. Ina jiyo muryoyin su daga kitchen, ba bu wanda ya leko ni yaga a wane hali nake ciki saboda ba damuwar su bane ba. Sai wajan tara da hamsin da uku 9:53pm na kammala naje na dora akan dining table a lokacin ne Mami tace min. “Kin gama ne?” “Eh Mami na gama.” “Guda nawa ki ka yi?” “Leda biyu ne Mami.” “Biyu kuma! Me ya sa baki yi da yawa ba?” Nayi shiru dan ba a ce na yi shi da yawa ba, kawu kawai aka ce na yiwa kuma na yi masa dan haka ba damuwa ta bace. “Shikenan dakko min guda daya ki zubu min miya ki kawo min, idan yazo yaci dayan.” Ban wani damu ba, nasan idan tace zata cinye ko su Ya Shukrah suka ce zasu ci ba iya hanawa zan yi ba. Ni fatana kawai Allah yasa kar su kuma sanya ni wani abun, ina son naje na huta nima kamar yadda suke yi a yanzu. Na juya naje na sako mata na kai mata sannan nima naje na dibi taliyar da nayi dazu na wuce daki saboda karma su ganni su dinga aike na ko saka ni aiyuka. A daki na naci na wanke hannu ko plate ɗin ban fito dashi ba saboda bana son ma su ganni wallahi dan babu alkairi tsakanin mu. Washe gari tunda na idar da sallar asuba na shiga kitchen dan shirya breakfast bana son na makara a fara ganin gazawa ta. Ina tsaye ina kada kwai zan soya dan na kammala soya Irish sai ga Mami ta shigo tana yatsina fuska. Daga bakin kofa ta tsaya tana kare min kallo, na yi saurin durkusawa har kasa kamar yadda nake mata tub farkon zuwa na har yau kuma ban dena ba na gaishe da ita. “Mami ina kwana?” “Tashi tsaye ni ki dena gaishe ni a kasa, so kike mutane suce gallaza miki nake yi?” Na mike naci gaba da aikin ba tare da na kuma gaishe da ita ba. “Kunu zaki damawa Alhaji yace yau ba zai sha tea ba. Kin tambayi su Shukrah sun gaya miki abin da zasu ci ne matsayin breakfast?” “A'a Mami, nasan suna cin Irish shine ya sanya ni yi. Sannan fa shayi can shima nayi, naga sunfi son shi.” “Jiya ai sunce wainar fulawa zasu ci, dan haka kinga yanzu sai kiyi musu abinda suke so.” “Mami dan Allah su taimaka min su ci wannan d'in, idan na dawo daga gurin aiki sai na yi musu. Wallahi Mami bana son yan gurin aikin mu suyi zaton ko bani da serious akan aikin.” Mami ta saki baki tana kallo tare da fadin. “Inyeeee, lallai seriously?. Wallahi Dije kinga gurin bacci na. Wato kinfa bawa yan wajan aikin ku muhimmanci akan mu ko?” “A a wallahi Mami ba haka nake nufi ba kiyi hakuri.” “No no noooo Dije ai kin isa karki wani damu. Idan kin kammala dama kunun ki kawo min.” “Toh Mami, amman dan Allah ki....” Tayi banza dani ta wuce tamkar ba da ita nake ba. Haka ina ji ina gani na kammala soya kwan daga nan na dora ruwa na dama kunun naje na kai mata dakin ta na kuma komawa kitchen na fara hada kullin wainar. Saboda tsabar rainin hankali sai gasu sun fito lokacin na fara suya, na gaida Ya Shukrah da ta shigo kitchen d'in tana faman gyara earpiece d'in kunna ta. Bata kula ni ba sai kofi da ta dauka taje ta tsiyayi ruwan tea tazo ta dauki wainar fulawa guda daya tare da janyo yaji ta fara ci. Sai da ta cinye wacce ta dakko sannan ta kalle a yatsine kamar ta ga Jummai mai aike a gabanta, ta ce dani. “Kwai nawa ki ka saka a kwabin?” “Guda biyu ne.” “Toh ba bu kwan a gidan ne ki ka saka iya biyu kawai?” “Akwai Ya Shukrah, amman gani nayi wainar da zan yi ba wata mai yawa bace shi yasa ban sa da yawa ba. Kuma a haka tafi dadi akan ace an kara.! kwai da yawa.” “Kinga malama, su wa ki ke yiwa? Mu ko ke?” Haushi ya kamani, toh ko su kadai zan yiwa ai tunda dai zan yi d'in dole nima naci koda kuwa guda d'aya ce. Amman dan kar ta je ta gayawa Mami tazo ta kuma sanya ni wani aikin yasa ni cewa. “Ta ku ce Ya Shukrah.” “Toh sai ki kara mana kwan.” “Toh shikenan bari na kara muku.” Tana tsaya sai da na kara guda biyar kuma duka duka kulin fulawar gwangwani d'aya ne, sai ya yi kauri tamkar ba fulawa ba. Juyawa tayi ta bar kitchen din dama jira take taga ko nayi abin da tace. Na ja tsaki a can kasan magogwaro na naci gaba da su ta, itama Ya Hameedah tazo ta diba ta koma parlorn suna ci. Ko sha'awa bata bani ba haka na shirya na yi tafiya ta gurin aiki. Bayan na shiga na yi program din da zan yi sai kawai fito muka hadu da Mas'oud muka ci gaba da hirar mu ta masoya. ••••. ••• ••• Haka naci gaba da rayuwa ta a gidan kawu na mai so na, shi kadai ne yake min abu a matsayin uwa da kuma uba da zance na rasa a rayuwa ta. Bayan wasu yan kwanaki naje gurin aiki ina shirin shiga studio na hango M.D da wasu ma'aikatan gidan a tsaye suna magana, sai na juya na karasa inda suke na gaishe su cike da wasa da dariya, har na tashi zan tafi sai mai kula da sashen siyasa na gidan radion ya dakatar dani tare da cewa. “Malam Khadija ko ke zamu wakilta ne?” Nace, “Yallabai ina za a wakilta ni?” “Wajan taron nan da za a yi ranar Asabar. Kawai ke zamu turo tunda dai kina da himma sai kije ki dakko mana rahoton yadda abubuwa suke gudana a wajan.” Murna ta kamani dan ni akan aiki na bana jin wani fargaba ko tashin hankali. Dan haka da murna ta na karbi ta yin da suka yi min tare da yin godiya na tashi na karasa dan yin aiki na. Bayan na gama na fito naje wajan Mas'oud na sanar dashi, yana ta tsokana ta wai kar naje naga abubuwa da yawa na rasa wane rahoto zan dakko saboda rudewa. Nayi dariya cike da shaukin soyayyarsa, dan har ga Allah a koda wane lokaci Allah kara sanya min soyayyar shi yake yi. Yau kam aikin sa har dare hakan yasa ba zai samu damar zuwa kai ni gida ba, sai na yiwa driver waya yazo ya dauke ni na koma gida. Mami na zaune a wajan hutawa naje na sanar da ita cewa gobe idan Allah ya kai mu zanje na wakilci gidan radion mu kasan cewa ni aikin radio nake yi, ita kuma Hameedah nurse ce a asibiti. Shukrah kuma business take yi, Kawu ya bude mata botic a can kan titi tana siyar da kaya kala-kala na gida dana waje masu kyau kuma. Kai kawai ta daga ba ta ce min komai ba babu addu'a bare fatan alkairi, duk ta bi ta kwarzabi kanta damuwa ta yi mata yawa saboda kawai ina cin irin arzikin da yaranta suke ci a wajan mijin ta. Na tashi na shige cikin daki na baki na sai addu'a yake na kar Allah yasa su saka ni aikin da zai hanani shirya abubuwan da zan gudanar a wajan taron. Cikin ikon sa kuwa babu wacce da neme ni saboda sunyi baki ya'yan yan uwan Mamin sun zo suna daki sai hira suke yi. *WASHE GARI...* Tsab nayi shiri na cikin wani arnan lace Coffee mai dauke da ratsin milk d'in zare, an yi min din kin doguwar riga wacce ta amsa sunan ta. Nasa mayafi milk da takalmi sai agogo da shima ya kasance ruwan madarar. Na tsaya a gaban madubi ina karewa kai na kallo, wanda nasan idan har Mas'oud ya ganni to tabbas ba zai taba kin bina ba, dan zai ce za a kalle masa ni, yana da matukar kishi dan ko a gurin aiki ya dinga min magana akan yadda mutane suke yabo na da kuma wadanda suke biyowa ta gurinsa suna sake gaya masa yadda Allah ya bani halitta mai kyau. Jakata na dauka na fito ina bin step d'in nan a yangance, yanzu fa babu batun tsoro dan gudun da nake yi a kai ko yan gidan albarka. Na saba da shi yabi jiki na sai kuma nan gaba ban san me zai bani wahala ba bayan shi. Naje dakin Mami na yi mata sallama a lokacin Kawu ya fito shima, muka yi sallama na tafi shima Mami ta raka shi motar sa ya wuce. Da naje gurin aikin banga Mas'oud ba, a gurin Aminu Gumel nake jin wai sun tafi asibiti Abban sa ne bashi da lafiya. Na karbi kayan aiki muka tafi a motar gidan radio d'in. Sanda muka je an taru matuka, na samu naje can kan highe table na kara abinda zan dinga daukar maganar manyan baki sannan na koma gefe inda aka tanadarwa yan jaridu gurin da zasu zauna. Gurin saukar karatun Alqurani mai girman ya kawatu sannan kuma ya yi cikar da alkalami ba zai iya rubutawa ba. Manyan mutane kuwa ba'a magana wadanda suka halarta. Sarkin musulmi, gwamna, Sarkin Basannabas da manya masu mukaman gwamnati da ma yan kasuwa dake jihar. Tunda tashigo wajen yake jin yanayin sa na canzawa, Yana hakimce akan doguwar kujerar girma da aka lullube da farin yadi. Me dauke da tambarin ‘’Sarkin Basannabas” . Lokaci zuwa lokaci ya kan duba designer agogon dake daure a wutsiyar hannun sa, Ba shi da ikon ya nuna gajiyar sa. Shin meyasa ma yazo? Yai taiwa kansa tulin tarin tambayoyin da shi kansa bai da amsa. Bakin sa ya masa nauyi. Sanye yake cikin hadaddun kayan sarakuna. Kallo d’aya zakai masa kasan shidin matashin sarki ne, Mai ji da ado da zatin halitta. Taune kasan leben sa yai ta cikin rawani. Idanun sa na saqale da bakin gilashin sa tamkar na gado. Tun yana makaranta ance kullum cikin saka shi yake. Bai taba bari aga kwayar idanun sa. Sannan baya kallon mutane na tsawon wani lokaci kowaye kuwa kai. “Ya RABB! I’m exhausted....” Ya furta a labban sa yana jera ajiyar zuciya. Tunda aka fara hidimar saukar ba kallo yake ba. Kansa a kasa yana jujjuya zobunan azurfar hannun sa. Sarki Salman Aliyu Salmanu (SAS) kyakkyawa ne na ajin karshe, Ma’abocin ado (sutura da zuciya) Dauke zuciar sa take da son taimakawa jama’a da kuma alkhairi agare su. A Zahiri ka ganshi zaka dauka ya gama da cewa duniya da lahira saboda yadda yataso cikin gata da ingatacciyar rayuwa, Tun kafin ya gaji sarauta awajen mahaifin sa (Marigayi sarki Aliyu Salmanu Ibrahim) ya kasance mai hankali, Samun kamammen ‘da irin sa sai an tona, Da kamar wuya. Bai dauki rayuwa da zafi ba, Yana bin komai ahankali, Duk da cewa ya tashi cikin gata, Bai taba daukar gatan nasa tabbatacce ba. He’s kind, attentive and most caring.. Yana kishingid’e ya jiyo zazzakar muryar ta na masa yawo a cikin kunne, “Sunana Nana Khadijaa Basheer Inuwa. Ni ce yar jaridar dake wakiltar gidan rediyo da talabijin na DokinKarfe24. A tare da ni akwai matemaki na Ashafa Ghali Dikko.. Shin mai girma sarki ya kaji lokacin da aka ce wannan babbar makaranta zata yi taron saukar karatun Alqurani mai girma a cikin jahar ka mai albarka?..” Kwata kwata sarki Salman bai bi ta kan zancen da take fada ba. Samun kansa kawai yai karo na farko a rayuwar sa da yayi wa bil adama kallon k’urilla har haka. Tun daga tafin kafarta ya fara kallon ta, ya tafi ga tsarin shigarta ta jiki har zuwa kan fuskar ta wacce tasa shi lumshe idanuwa ba tare da ya ankara ba. Ya sake bude ido ta cikin dark shades d'in fuskarsa yana kallon yadda ta d'an rankwafo alamun tana jiran bayanin sa duk da tazarar dake tsakanin su. Bata ankara ba taji an sanya wata zungureriyar sanda tare da buge abin daukar sautin na ta. Kasan cewar idanun shi suna kanta ne yasa yaga yadda tabi wanda ya yi mata wannan wulakanci da kallo tana tsuke fuska. “Karya ki ke yar jarida, sai dai kiyi mana tambaya ba dai da sarki mai daraja ba.” Sarki Salman ya sake kallon ta dan yaga wani irin mataki zata dauka gurin bafaden shi da ya yi mata wannan abun. Sai yaga ta dauki abin daukar maganar tana kallon shi tare da sanya tafin hannunta da yasha jan lalle a yan yatsun suka yi matukar kyau. Sai kuma yaga ta juyo ta kalle shi, ya dauke kai duk kuwa da cewar yasan ba tasan ita yake kallo ba sanadiyar glasses d'in shi. “Amman ya kamata muji ra'ayinsa dan yana da matukar amfani ga al'ummar mu.” “Karya kike yar talakawa.” Bafaden ya sake fada yana bula babbar rigarsa dake nuna cewar shi din bafaden sarkin ne. Wani irin takaici ya rufe Dije, ta sunkuyar da kai kasa. Duk a tunanin sarki Salman kuka zata yi, besan zaka da warwara ta shiga yi da zuciyar ta ba. Sai yaji tamkar ya yi mata magana, amman mulki da izzar dake tattare da sarauta ta hanashi koda yin motsi. Dije ta kuma kallon sarki Salman duk kuwa da banda tulin rawanin sa bata ganin fuskar sa ta sake cewa, “Ranka ya dade gashi an gudanar da karatun saukar Alqurani, ya kaji a ranka game da yaran da suk.....” Bata kai ga karasa tambayar ta ta ba kawai taji saukar sandar nan a gefen kanta, wanda ya yi sanadiyar da yasa ta saki wata gigitacciyar kara mai gigita kwakwalwa, ta kuma sulale ta fadi kasa sumammiya. Dai dai lokacin sarki Salman ya mike aka dora masa malafarshi ya tsaya cak yana kallon yadda yan sanda suke korar mutane dan a samu yadda za a ceci yar jaridar da bafadanshi ya rafke. A hankali ya sakko daga wajan ya nufi motarsa ba tare da ya tsaya ya yi sallama da mai girma gwamna dake gurin ba..... ... ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *K..........* *NH* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE! KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SAYA DA KUDIN KI, KADA KI SHARING, TEMAKA KI SIYA NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASA* *All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. * *(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾* *15* Gabaki d'aya sai hankalin mutane ya dawo kan Dije dake yashe a kasa. Shi kuwa sarki Salman tuni motarshi ta bar gurin taron tamkar ba sune suka jaza wannan ta'asar ba. Basu tsaya sunji me yake faruwa ba bare su san halin da yarinyar mutane take ciki. Kafin kace menene tuni aka dauke ta aka sa a mota sai asibiti domin bata san inda kanta yake ba. Kasan cewar akwai manyan jami'ai hakan ya sanya suna zuwa asibiti babu wani bata lokaci aka shiga bata taimakon gaggawa. Mas'oud dake kan hanyar shi ta zuwa gidan radio saboda yaje gida ya maida mahaifinsa kenan, kawai yaji labarin cewar Dije na can asibiti bata san inda kanta yake ba. Ya juyo da motar ya nufi asibitin cikin tashin hankali da tunanin abinda ya sa har hakan ya afku a kanta. Koda yaje kasa shiga cikin asibitin ya yi, yan sanda sun hana kowa shiga. Ya ciro id card d'in sa ya nuna musu amman duk da haka suka hana shi shiga, dama duk sauran yan jaridar da suka biyo su suna tsaye a bakin gate an hanasu shiga, saboda so ake a boye maganar cewa bafaden sarki ne ya yi sanadiyyar hakan. Aka fara cewa ai cikowar mutanan gurin ne yasa numfashin ta ya dauke ta zo faduwa shine ta buge. Tuni labari yaje wajan Alhaji Isma'il yana kan hanyar shi ta zuwa filin sauka da tashi na malam Aminu Kano zai je birnin Lagos. 'Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun' ita kawai yake furtawa tare da juyo da motarsa ya nufi asibitin cike da tashin hankali. Yana hanya ya kira Mami ya sanar da ita cewa tayi maza-maza taje asibitin shima gashi nan zai je. Cikin mamaki duk kuwa da cewa tana cike da tsantsar mamakin jin cewar Dije na kwance a asibiti tace dashi. “Toh bari na shirya naje, amman kai ya zaka ce ka fasa yin tafiyar bayan ka riga kayi booking d'in tafiyar.?” “Hajiya wannan ba wata matsala ba ce, jin lafiya marainiyar Allah shine kawai burina. Karki manta Dije amanace a gare ni, kuma ya ce a waje na kamar yadda su Shukrah suke.” Yana gama maganar ya katse kiran yana jin mamakin matarsa da sam ba ta son ganin yana kyautatawa yarinyar nan. Ta kasa fahimtar cewa wata rana itama zata rabu da nata ya'yan kuma ba ta san waye zai kular mata da su ba. Mata duk lissafin su guda d'aya ne wato za'a riga su mutuwa, duk kuwa da cewa sun sha ganin Allah yana dauke wanda yaso a lokacin kuma yaga dama. Ita kuwa bayan taji ya katse wayar sai ta rike habarta, abin da mijin ta yake yi sam bata jin dadin shi. Haka ta mike taje ta shirya tasa driver ya kai ta bayan ta tambayi wane asibiti ne, aka sanar da ita. Alhaji Isma'il na zuwa ya sanar da yan sandan dake tsare da gare cewar shine mahaifin Dije, suka barshi ya shiga inda suka bar yan jarida guda uku suka bi bayan shi ciki kuwa harda Mas'oud. Mami ma tana zuwa aka barta ta shiga ta tarar da Alhaji Isma'il ya fito daga wajan likita yana gyaran babbar riga. Ta karasa suka hadu a center, kallon da ya yi mata shine kawai ya tabbar mata da cewar tayi masa laifi wanda ba zai rasa nasaba da nuna cewa aikin shi yafi Dije da ta nuna masa. “Ashe zaki zo?” Ya tambaye ta yana mai lasar lebensa da ya fara bushewa saboda kaduwar da ya shiga. Kanta yana kasa tana murza zoben zinarin ta tace. “Me zai hana Alhaji.?” “Naga kamar baki damu ba ne shi yasa, har na fara tunanin dakko wacce zata kular min da ita.” Kamar tace ai yanzu ma ba ita zata zauna ba, sai kuma ta hadiye kasan cewar yaki sakar mata fuska ta kasa ganin walwalar shi kamar yadda ya sabar mata. “A a zan zauna mana Alhaji, yanzu me yaje faruwa da ita?” Yaja numfashi yace. “Yanzu likitan ya kira ni yace ta farfado, gefen goshinta ya fashe. Dole sai ta d'an kwana ko biyu ne a asibitin dan bata kulawar likita.” “Daman ban da fitina ina Dije ina aikin jarida tsakani da Allah fa. Duk irin karatukan duniyar nan ta rasa wanne za ta yi sai shi saboda kawai taso ta dinga shiga cikin ridan-ridan maza. Gashi nan yanzu taje an....” “Ya isa haka Hajiya naji. Duk da haka ma dai zan kawo wacce zata kula da Dije, ke sai ki koma gida saboda yara.” Ta fi nono fari daman ba so take ta zauna d'in ba kawai fushin sa ne bata so shi yasa ta yadda cewa zata zauna. Yanzu kuwa da yace ta tafi idan ta gama abin da zata yi bata ja ba saboda kar taje yace ya fasa dole ita zata zauna. Ya nufi room din da aka kwanta da Dije wacce ke ta faman bacci tamkar babu abinda ya same ta. Sunkuye suka tarar da Mas'oud a gefen ta yana sharar hawaye, Alhaji Isma'il ya tambayi waye shi suka tabbatar masa da cewa abokin aikin ta ne, gidan radio d'in su d'aya. “Allah sarki, hakuri zaka yi muma duk shi zamu yi. Dubi goshinta duk da cewar an rufe kasan cewar ciwon ba kadan bane ba. Allah ya baki lafiya Dije, yasa kaffara ne.” Sun jima sosai a dakin kafin su fito dan gabar da sallah. Addu'a kam Dije tasha a gurin Alhaji Isma'il da Mas'oud wanda ya kasa bayyana mishi alakarshi da ita. Mami ta zauna akan kujera suna waya da Hameedah tana sanar mata da abin da ya faru wanda taji a bakin wani d'an jarida da abin ya faru a gaban su. “Kinji yarinya Mami, ko tayi zaton har yanzu a kauye take ne?” “Kema dai kya fada.” Cewar Mami. “Sarki fa! Taya Dije zata ce zata yiwa sarki interview banda dai ta latsawa kanta tunani. Ai gashi nan ta jawowa kanta an ji mata ciwo a banza. Kuma ance masarautar bata yi wani abu ba akan lamarin ko?” “Uhmmm! Kin san dai ba sarauta bace ta kauye, kuma yanzu ma rufe maganar aje son yi saboda kar a batawa masarautar suna.” Haka Mami ta zauna a gurin Dije babu wata alfarma da take yi mata saboda tsabar wulakanci, Allah ya taimaka ma bacci take ta yi, da watakila sai tayi hawaye da idanunta. Suna idar da sallah Alhaji Isma'il ya lallaba Mas'oud ya tafi kar ya damu zata ji sauki harma ta koma aiki da ikon Allah. Ya tafi ba dan yaso ba sai dan kar Alhajin yaga kamar bashi da kunya ko sabanin haka. Gabaki d'aya Alhaji Isma'il ya kasa samun sukuni ko fita ya yi yanzu zaka ga ya dawo har dare lokacin da Allah yasa Dije ta farka. Da Mas'oud ta fara yin karo da idanuwanta, kasan cewar ya sake dawowa asibiti da aka yi salla magariba, ya kasa zama sam shi yasa ya dawo. Dishi-dishi haka ta dinga ganinshi, ta gane shi tsab sai dai bata iya ganinshi tar-tar kamar yadda ta saba kallon abu. Ya mike tsaye tare da karasawa gurin ta yana cewa “Alhamdulillahi ta farka Allah mun gode maka.” Alhaji Isma'il ya shigo da sauri cike da tsantsar farin ciki juyowa da ya yi cewar Dije ta farka. Kallon mutane kawai take ba baki taki koda motsa shi bare a saka ran zata yi magana. Nurse ta shigo wacce ita ce ya bawa kwangilar kular masa da Dije. Sannu a hankali ya taje ta gyara mata inda ya kamata cikin haka ne ma suka ji ta furta. “Kawu daddy.” Tamkar ta tsira masa wani abun, haka yaji ya nufe ta ya riko hannunta, hawaye suka biyo ta cikin kyawawan idanuwanta, yasa hannu d'aya da yake kusa da fuskar ya share mata yana cewa. “Bar kukan nan Dije, dena kuka zaki warke da ikon Allah.” Still bakin ba wai budewa ya yi da yawa ba wajan son yin magana, ta kuma cewa. “Kawu daddy sarki ne ya harbe ni ko? Wallahi ba bu abin da nayi masa kawai daga tam......” “Yi shiru Dije, tsautsayi ne kawai da kuma kaddara suka fad'a kanki. Allah ya riga ya kaddara cewa hakan zata faru dake tun farko. Kiyi hakuri zan tsaya tsayin daka, da ikon ubangiji zaki dawo kamar baki yi ba kinji yarinya ta?” Lumshe ido kawai tayi saboda yadda take jin kanta ya yi mata wani irin kato tamkar an dora mata duniya haka take jinsa, saboda raunin da yake a goshin ta shine ya yi sanadiyyar hakan. Ta sunkuyar da kanta kasa ba tare da ta kuma cewa komai ba sai zuciyar ta da ta addabeta akan ganin rashin imani da rashin mutunci a gurin bafaden da ya ce mata yar talakawa. Bata taba zato ku tsammanin cewa haka suke ba, ashe ba su da kirki kansu kawai suka sani. Amman ban da haka ba ta ga dalilin da zai sanya su dinga yiwa mutane abin da suke yi ba. Mas'oud ya dinga kallanta yana son su sake had'a ido ko zai ji sassauci akan zugi da rada din da yake zuciyar shi, yana son ta nuna masa wata alama da zata tabbatar mishi da cewa a kowane yanayi take ciki zata iya gane shi da kuma matsayin da yake a gurin ta. Ganin tsawon lokaci taki dagowa ya sanya shi juyawa zai fita daga dakin, kamar an ce ya kuma kallon ta sai yaga ta dago ta kalleshi tana rausayar da kai alamar damuwa. Ya koma tare da cewa. “Sannu kinji?” Ta kifta idanuwa alamun ta amsa gashi yaga taki kawar da ido daga kansa yace. “A kawo tea ko?” Tayi shiru ba ta ce komai ba dan magana da kyar take iyawa. Nurse d'in tace ya bari a had'a mata suma zasu so ganin ta d'an ci wani abun ko ya ya ne. Alhaji Isma'il da kanshi ya dinga bata a hankali kasan cewar da kyar take iya daga lebeanta har a samu tea ɗin. Kadan tashi ba ne yawa ba sannan aka kuma kwantar da ita. Haka taci gaba da kwanciya a asibiti tana samun kulawar likitoci. Yan dubiya kuwa ba'a magana, ta ko'ina zuwa ake ana duba ta, har ta fara samun lafiya fuskarta tasabe kumburin ya baje sai gurin ciwon kawai. Mas'oud kam kullum yana asibitin tun safe har dare, hakan ya kuma tabbatarwa da Dije cewar Mas'oud shine farin ciki da walwalarta a rayuwa. Soyayyarsa ta kuma ninkewa a duk wasu sassan jikinta masu motsi da kai sakonnin gamsuwa ga abin da aka hakikance akan shi. Su Hameedah da Shukrah ma kullum sai sunje, a wannan zuwan ne kuma Shukrah ta fara nanikewa Mas'oud, ko be kulata ba sai ta kula shi saboda Mas'oud ba baya ba wajan tsarin halitta. Duk da cewa Dije ba ta da lafiya hakan be hanata jin kishi ba, yadda Shukrah take nanikewa abin alfaharinta abin yana mata ciwo dan yafi raunin goshinta zafi da radadi. Yau kwanaki biyar kenan wajan karfe hudu suna zazzune ana ta hira, duk da cewa shi baya kula su amman wata maganar idan an sako shi yana magana, yanzu ma hakan ce ta faru, Shukrah tace. “Abokin aiki gaskiya kana da kirki.” Ba tare da ya kalleta ba yace. “Da nayi mene?” Shukrah ta saki murmushi tare da cewa. “Gani muka yi tunda wannan abin ya faru da Dije kullum kana nan har ka fimu zama a gurin ta.” Mas'oud ya juya ya kalli Dije wacce itama shi take kallo, hakan kuma ya tayarwa da Shukrah hankali tayi saurin katse su ta hanyar cewa. “Kaga wasu jakunkuna da nayi order jiya.” Sai ya waiga ta miko masa wayarta yana kallon jakunkuna, ba karya sunyi kyau, kuma zasu yiwa Oum Waleedah kyau. “Sunyi kyau sosai kamar na siyawa madam, tana warkewa sai ta rataya a barta ko.?” Ya fada yana kallanta da murmushi. Turo baki tayi tare da mai da idanuwa ta rufe ba tare da ta ce komai ba, abin da yake sake jan ra'ayinsa akan ta kenan wato yanga. “Kana nufin Dije zaka siyawa?” Shukrah ta tambayesa cikin mamaki. “Eh mana na murnar ta tashi lafiya ba.” “Cab, ai duk an riga an siye su. Jira kawai masu su suke su dauki abubuwan su, sai dai next time.” Shi ma daman ba wai da gaske yake zai sai mata ba, koda zai siya mata abu baya jin zai sai mata a gurin wanda ta sani bare kuma yar uwarta. Duk iya surutun da Shukrah take yi masa besa shi ya fuskance ta ba, sai rubuce-rubuce da yake ta faman yi tamkar besan abin da take cewa ba. Haka suka yini har Mas'oud d'in ya fito zai tafi tayi saurin biyo bayan shi. Dije na kallon ta fita gabanta ya dinga bugawa, gani take tamkar wani makircin zata ta yi masa, gaba daya bata yadda da Shukrah ba sam. Cikin ranta ta dinga addu'a dan tasan babu mai tsare mata Mas'oud sai Allah, shine ya had'a zukatan su a lokacin da basu sani ba, haka suna fatan ganin Waleed da Waleeda a tsakanin su. °°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°° *MASARAUTAR BASANNABAS* Tun a ranar da wannan tsautsayin ya affku ya ke cikin jimami, ko da suka shiga mota yaso ya daure ya tsaya dan yaga abinda zai faru da yarinyar da bafadansa ya rafkawa sanda. Amman ya kasa saboda shi baya san hayaniya, wannan dalilin ne yasa ko kallon gurin be sake yi ba bare asaka ran zai yi wani abu akai. Har suka je gida bai dena ganin jarumta irin ta wannan zakwakurar yar jaridar ba, da take son taji wani abu daga gare shi. Sashensa na musamman ya nufa kowa ya tsaya daga bakin kofa dan wannan ka'ida ne da indai ya shiga cikin wannan dakin to babu wanda yake shiga sai matarsa ko mahaifiyarsa. Cikin isa da kasaita ta nufo sashen nashi, Bayan jakadiya ta mata iso. dan a kan kunnanta motocinsa suka shigo masarautar, bayin ta suna biye da ita sun sha kaya iri d'aya. Tana zuwa wajan kofar bayin nata suma suka tsaya yayin da ita kuma ta karasa ciki kamar yadda ta taho cikin tinkaho mai nuni da cewar ita d'in matar sarki ce. A zaune ta tarar dashi kansa a kasa ko glasses d'in dake manne a fuskar shi be cire ba. Daman idan da sabo ta saba da duk wasu dabi'unsa, musamman na shariya da kin kallon mutane tamkar wani makaho. Banda wani fitinannan kamshe babu abinda take yi, ta zauna can nesa da shi idanunta a kanshi tace masa. “Sannu da dawowa, shin me yake faruwa ne naji ko'ina ya dauki zance nama kasa gane abinda yake faruwa. Shin me ya faru da kai?” Ya yi shiru tamkar tana magana da gunki da aka sassaka da dutse. Taja tsaki a can kasan ranta dan tasan ko mahaifiyarshi ce a nan gurin take tambayarsa ba amsa mata zai yi ba bare ita da taga wajan baccin shi. “Anyway! Nasan daman ba magana zaka yi. Amman ko da kane ina son ka yi min alama yadda zan fita daga cikin shakkun da nake ciki. Shin kun bige wani ko wata ne a wannan fitar da kuka yi?” Ashe yaji duk abinda take ta fada, sai gashi ya daga mata kai ba tare da bata lokaci ba. Ta jujjuya idanuwa tare da tabe baki. “Ance ai ta mutu ma, Allah ya taimaka ba kai zaka sha azumi sittin ba driver ne da ya yi sanadiyyar mutuwar ta. Sai dai kuma kai ne zaka ba da diyya, tunda kasan dai kai za'a sanyawa ido kaji ko?” Kamar wata uwarsa haka ya kuma daga mata kai alamar 'eh' yaji. Tayi shiru dan tasan ta gama magana dashi ba kuma daga kan zai yi ba. Kusa dashi ta d'an matsa tasa hannu zata zare masa dark shade d'in da ya yi mata shamaki da ganin fuskarshi, ya yi saurin sanya hannu ya rike nata da take shirin cirowa alamar ba ya so. Sai ta kai bakin ta kan hannun nasa tare da sumbatar shi tana cewa. “Yau ma ba zanga fuskar ka ba ko? Shikenan.” Mikewa tayi tabar parlorn dan dama zuwa tayi taji tabbas daga bakin shi kuma taji. Abin da kawai za ta yi shine tasan yadda kudin diyyar da za'a kai sun biyo ta hannunta. Shi kuma abin ne ya yi matukar bashi mamaki jin cewar yar jaridar ta mutu. Ya dinga yin hasbunallahu a cikin zuciyar shi, a ranshi yana jin ashe daman mutuwa za ta yi shi yasa Allah ya ba shi iko da damar daga ido ya kalleta? Rabon da ya yi irin kallon nan ya manta, dan ko mahaifiyar sa ba zai iya tuna rabon da ya kalli kwayar idanunta bare ya gane a wane hali take ciki. Abinda ya sani kawai shine muryar ta da kuma yadda take tafiya. Ranar da kyar ya rintsa saboda abin da yaji na cewar badanshi ya kashe wata yar jarida daga yin tambaya. Duk kafafan watsa labarin da ya kunna da daddare labarin ake yi, sai dai su sunyi sabanin abinda yake jiyo wa a bakunan mutane wato. Yarinyar tana karkashin kulawar likitoci, mutane kuma suna cewa ta mutu rufe maganar ake yi dan kar ace mutanan sarki ne. Sai da safe bayan ya fito fada su waziri suke sanar dashi cewar yarinyar ta farfado kar a damu nan ba da jimawa ba zata koma bakin aikin ta. Be ce komai ba sai da yaji duk wannan firgicin da yake ji duk ya ware baya ji yanzu. •••• A ranar da Dije ta cika kwanaki biyar a asibiti ne yasa sarki Salman ya kirawo wani amintaccen bafadanshi yace yaje ya binciko asibitin da aka kwantar da wacce aka buga, baya son kowa ya san cewar zai yi wannan binciken saboda idan suka ji hanawa zasu yi, sunfi son su ji ana zagin shi a duniya ana cewa bashi da mutunci. Haka aka yi yaje da daddare har asibitin, wanda ya gano shi ne dalilin binciken da yayi na gidan rediyon da take aiki, yaje can suka sanar dashi, shi yasa besha wahala ba wajan ganowa. Lokacin da yaje ya tarar Mas'oud ya fito Shukrah na biye dashi, bafade ya tambayi nurses d'in dake reciption dakin da aka kwantar da ita. Daga nurse din da take kula da ita sai Hameedah dake zaune tana danna waya. Dije kwance idanunta akan kofar tana jiran taga shigowar Shukrah sai kawai taga kayan fadawa irin na jikin wanda ya yi sanadiyyar kwanciyar ta a asibitin yanzu haka. Cike da tashin hankali tayi saurin rufe idanuwa da alama yanzu mugun tsoran shi take ji. Sallamar da ya yi ne tasa Hameedah dagowa nurse din kuma amsa masa tana mai tasowa dan jin abinda yake tafe dashi. “Wani abun ya faru ranka ya dade?” Nurse d'in ta tambaya dan sanin karin bayani. “Daga masarautar Basannabas ne aka umarce ni da nazo naga halin da yarinyar take ciki.” Cikin sauri Hameedah ta taso, tsayawa tayi tana kallon bafaden tare da cewa. “Okay sannu da zuwa, ni Yayar tace.” “Masha Allah, ko zan samu ganin mahaifin ku dan na kara bashi hakuri akan abinda ya faru, da kuma jinkirin rashin zuwan wani daga cikin masarautar Basannabas ?” Wayar ta dago ta shiga kiran daddyn su amman sam taki shiga not reachable. Ta sanar masa ta kasa samun wayar shi amman idan yazo zata gaya masa. Ya kuma kallon Dije wace har lokacin bata bude ido ba saboda haushin su da take ji, ya juya ya tafi. Yana tafiya babu jimawa Alhaji Isma'il ya dawo, suka bashi labari ya jinjina kai, kuma sannan haushin su shima da yake je na rashin nuna kulawarsu akan lamarin ya ragu. Gwamna ne kawai da shugaban yan makarantar da suka yi saukar sune kawai suka yi wani abu akan lamarin sai kuma yanzu da sarkin ya yo aiken dubiya, hannu na dukan cinya ba wani ihsani, a matsayin su na wadanda sune silaaa.. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 ........🧕🏼 *BINT M H* *Epi: 16* ________Satin Dije biyu a gadon asibiti tayi shar tamkar ba ta yi wani ciwo ba. Hakika mafi yawancin mutane musamman talakawa suna mutuwa ne ta hanyar rashin kulawa ta musamman. Munsan cewa duk wanda ya mutu lokacin shi ne ya yi. Amman mafi yawa wahala da kuma rashin abinda zaka kula da lafiyar taka yana taka muhimmiyar rayuwa wajan rasa rayuwa kan mu masu tsada. Alhaji Isma'il ya tsaya tsayin daka wajen ganin ta samu sauki kuma alhamdulillahi gashi har an sallame su sun koma gida. Kwance tayi akan doguwar kujera tana waya, kan cikin ta kuma plate ne mai dauke da fruits tana dauka tasa a bakin ta cike da nishad'i. Mas'oud ne yake ta kashe mata jiki da sassanyar soyayyar shi, wacce take sanya ta rasa a wace duniya take tsabar sauki. Shukrah ta shigo tana faman nishi da alamar gajiya tayi, ta bude fridge ta dakko ruwan sanyi tare da budewa tana kwankwada. Sam ba tayi zaton waya Dije kiyi ba saboda ganin idanunta a rufe, tayi tunanin ma bacci ne ya dauke ta da plate d'in a jikinta, sai ji kawai tayi tana cewa. “We are two bodies, but our heart beat as once. Be mine, forever, do not leave me ever Abu Waleed.” Cikin wani irin juyi Shukrah ta waigo tare da zuba idanuwanta akan Dije. Cikin tsantsar mamaki na ganin ashe yarinyar nan idanunta biyu tana jin shigowar ta amman tayi mata banza babu wani alamun taji ta. Da waye take wannan wayar ita kuwa? Allah yasa ba Mas'oud bane data fara ganin sa sandiyyar kwanciyar Dijen a asibiti. domin harga Allah gayen ya yi mata dari bisa dari, zuciyar ta babu abinda take muradi irin su kasance tare, hakan yasa bata fatan ace suna soyayya da Dije dan kar ta zo ta bayyana mutane su ga rashin adalcin ta ko su yi mata fassara da maciya amana. Sai kawai ta samu kanta da zama a parlorn tana sauraran wayar duk da cewar bata jiyo muryar d'aya bangaran. “You're my dawn, You are my twilight.” Shukrah taji Dijen ta kuma fada, duk da cewar bata san ko waye ba, samun kanta tayi da cewa Dijen. “Wai baki ji ana ta sallama bane Dije? Na dauka ma bacci kike yi ashe kina nan kina yaudara bayan ga Tk can yana jiran ki a parking lot.” Yadda tayi maganar da karfi ne ya sanya Mas'oud jiyo abin da take fada, daman kuma tayi ne dan koma waye Dije ke wayar dashi ya jiyo. Musamman idan Mas'oud din ne da tayi domin shi. Ai kuwa yaji d'in, nan da nan hankalinshi ya yi mugun tashi yana ta tambayar ta. “Ummu Waleedah waye Tk? Meye hadin ki dashi? Wace a kusa da ke?” Dai dai lokacin Dije ta bude ido ta kalli Shukrah da ta kura mata nata idanuwan. Bata ce mata komai ba, haka ma bata dauke ido akan ta ba tace da Mas'oud. “Duk wadannan tambayoyin ni kadai zan amsa su?” “Eh mana, ai nasan duk kina da amsoshin su, kuma zafi ganewa idan kika min bayani da kanki.” Ya yi maganar yana tsuke fuska tamkar suna ganin juna. “Amman fa karka manta da bahaushe yace, idan ka ga kare yana shinshina takalmi, toh dauka zai yi. Ni babu abinda ya hadani da duk wadannan tambayoyin da kayi min.” “Toh wace ce ta yi miki wannan maganar?” “Ya Shukrah ce.” Shiru ya yi na dan wani lokaci yana nazarin abin da tace maza na kare. Murmushi ya yi har ya na dan fito da saurin sa, wanda ya sanya Dije gano cewar ya fahimci abinda take cewa. “Gaskiya ne yar jarida, wato kema kinsan kiyi irin wannan language d'in ko? Wallahi kin bani wahala wajan yin tunanin abinda kike nufi, oya ki lallashe ni kar na yi fushi.” Saboda ta sake batawa Shukrah rai dan ta gane cewa abin da ta fada ba damunta ya yi ba, sai cewa ta yi dashi. “Uhm-uhmm-uhmmm..., ka yi hakuri dear, for you, my heart beat aches, and only you can ease the pain. Kar kai fushi kasan zazzabi yake sani idan kayi.” Kamar Dije tasan amsa zai bata kuma mai dadi ta nuna soyayya, hakan yasa tasa hands-free dan Shukrah taji da kyau ko zata rabu da su. Sai da ya ja numfashi kamar irin wanda ya dawo daga shiga tashin hankalin nan, sannan yace mata. “Har naji dadi, rai na ya sanyaya. Forever walk by my side Oum Waleedah, promise me that you will meet me in my cham.....” Kafin ya karasa ta yi saurin cirewa daga handsfree d'in dan karya fadi abin da zai sanya Shukrah kuma yi mata kazafi, taje tace maganganun batsa suke yi. Cikin jin haushi kuwa ta suri jakarta tayi daki tana masifa kamar wacce a ka yiwa wani abu. Cikin ranta banda bakin ciki babu abin da yake cikin sa, koda ace gaske ne Mas'oud da Dije soyayya suke yi sai ta rugurguza duk da cewar tare ta gansu, kuma ta silar Dijen tasan Mas'oud din. Toh amman ya za ta yi da zuciyar ta wacce a cikin rashin adalci ta sanya soyayyar shi a zuciyar ta. Tayi wurgi da jakar ta tare da fadawa kan gado tana wani irin nishi, ƙirjinta ya shiga bugawa ga zafi da taji yana yi mata (yo bakin ciki ne da hassada). “Abu Waleed yaushe zaka zo ne?” “Uhmmm....zan zo sai ranar da bamu da aiki, kinga yau juma’a, San da kika dawo aiki. Idan kin zo sai muyi shawara ko?” “Toh shikenan Allah ya kai mu.” “Amin my dear wife to be. Bari naje Abba yana kira na.” “Toh shikenan a mika min gaisuwa ta musamman.” “Lalalah! Toh in ji waye zan ce masa.” “Kana nufin kace be sanni ba?” “Mama ta sanki wallahi, kinsan sunan mahaifiyarta gare ki shi yasa take girmamaki.” Wani sanyi ya ziyarci birnin zuciya ta jin wacce zata zama sirika a gare ni tana ganin mutunci na, Lallai idan nayj sa'a, Zan yi dace da uwar miji mai so na. Jin ana ta kiran sa daga nesa ne, Yasa na sauke wayar na katse dan nasan idan ba hakan nayi ba tabbas ba zai tashi yaje kiran da gaggawa ba, saboda baya son rabuwa da ni yana jin dad'in kasancewar mu masoya. Tashi nayi nima na shiga bedroom d'i na, sauki ya samu ba lefi, kuma ya zuwa yanzu nasan yadda zan zauna da kowa na cikin gidan. *MASARAUTAR BASANNABAS* Gurfane yayi a gaban sa tamkar shi ne sarkin, Shi kuma yana hakimce akan kujerar zaman fada ta sarki. Su uku ne kadai aciki. Daga manyan dattawan biyu sai shi sarki Salman, Shi wanda ke kan kujerar zaman sarki ya harde kafa yana dudduba ipad din hannun sa. Sarki salmaan na tsakure a gaban wanda ke zaune akan kujerar. Dayan kuma yana zaune a d’aya daga cikin royal chairs din fadar. Dukkanin su kowanne yasha rawani. Daka gansu kasan sudin jinin sarauta ne kuma masu ji da kambun mulki. “Ya akai hakan ta faru......?!” Shiru sarki Salmaan yai kawai kansa a kasa, Na kan kujerar sarkin ya sake buga hannun kujerar da yake Kai yana taune lebe, “Salmanu ba magana nake maka ba..?” “Kawu I’ve no idea... Kawai nasan mutane na bukatan abinci shysa nace a kwashe a raba musu.” Ya karasa fada yana mai gyara zaman gilashin dake saqale a idanun sa. Dogon tsaki dayan yaja yana karkada kafa, “Kar mu sake jin kwatankwacin haka, Shin ya zancen zuwa gidan gwamnati nemo wannan tallafin?” “Munyi magana na tura waziri yace za’a samu.” “Ka dai kara pushing wannan karan banda wasa.” Sarki salman bai amsa ba ya kalli gefe kawai yana taune leben sa, “Sai ana maka magana ka tsiri wani cin fuska, Wai Kai sarki ko? Sannu sarki... Kar ka kai mu ma’kura wallahi. Kuma ba zeyi wu har mu muna maka magana kana saqale da wannan shegen gilashin naka ba. Na kinubibi..” Cewar na kan kujerar sarki. Mikewa yayi, Ya cilla ipad din akan cinyar sarki Salman. “Gatanan nayi mailing united nation din suyi haku’ri ba zaka samu zuwa ba. Saboda mun gama magana da madaki watan gobe zaka tafi cyprus taron nan. Kana jina?” Kansa ya daga musu kawai, Suka fuce. Yana jiyo sanda bafadensa na kofa yake musu kirari, “Takarwar ku lapia.. A sauka lapia Galadiman Basannabas da Wamban Basannabas.. Sarkin kofa na gaisuwa da fatan alkhairi.” Silalewa sarki Salman yai yai zaman dab’aro awajen yana dafe kansa dake masa barazanar fadowa, “Ya Allah!....” Komawa yai kan kujerar sa ya zauna, Cikin haka jakadiyar sa mai suna Abu (Zainab) ta shigo tana rissina masa, “Allah ya karawa sarki lapia.. Za’a yiwa wani iso ne? Naga masu jiran nada yawa a zaure na biyu.” Hannu ya d’aga mata kawai.. Da baya da baya ta juya har takai k’ofa ya danyi gyaran murya ta juyo, “Ina..... Alhassan? (Amintaccen bafaden sa)” “Allah yaja da zamanin Sarkin Basannabas, Shima yana cikin masu jiran.” “To a masa iso..” “Allah ya Kara maka lapia da kwanciyar hankali. Yanzu kuwa.” Ficewa tayi da sauri. Cikin mintina k’alilan bafaden ya shigo bayan Sarkin kofa yayi shelar zuwan sa, Yana shigowa ya zube yana kwasar gaisuwa, Maganganu su kai ba masu tsawo ba, Naga bafaden ya fice da Sauri, Shi kuma sarki salmaan ya lumshe idanu kawai, Kafin jakadiya ta sake dawowa tayiwa wasu mutanen iso... *DR ISMA’EL MUHAMMAD SINGA RES* Zaune Dr/Alh. Ismael yake, Gaban sa kuma wani babban Yaron sa ne (Abdul) dake rike da ma’adanar kudaden sa dake bankuna (banks) kasancewar bashi da ‘da namiji. “Alhaji ba lefi gaskia cinikin wannan karon yafi kowanne, Sai dai b’angaren taliya ne aka samu akasi, Sun rage ingancinta, Shiyasa mutane suka dena siya Kwana biyu.” “Masha Allah! Haka akeso. Eh itama munyi magana da Alhaji Sabitu zamu tura wakili can kamfanin domin susan yadda ake ciki ko kuwa..?” “Hakan yayi Alhaji..” Magana sosai suke yi, Mai gadi ya shiga doko sallama parlorn yana zura kansa ta kofa, “Oga! Ana sallama da kai..” “Waye?” “Wani ne wai daga gidan sarki.” “Toh! Shigo da su.” “Ai mutum d’aya ne..” “Eh ba lefi.” Abdul ya mike da littafan gaban sa yana rissinawa alhajin. “Alhaji ni zan wuce.. Sai gobe idan Allah ya kai mu!” “Allah ya kai mu Abdul.. “ Fita abdul yayi, Bafaden sarki kuma ya shiga. Gaisawa su kayi cikin amintawa, Kafin Alhassan ya gyara zama domin shedawa Alhaji abinda ke tafe dashi, “Ni suna na Alhassan, Babban bafaden sarki ne ni, Domin zuwa na na uku kenan, Bana samun ka sai yau, Na farko naje asibiti ban samu ganin ka ba, Na danyi bincike na gano inda kake a kasuwa, Nan ma ban same ka ba, Da tambaya na gano nan gidan ka..” “Allah sarki an samu sabani kenan. Afuwan to” “Haba Alhaji ai mune da ban ha’kuri, Ayi hak’uri, Bafaden sarki ya tafka kuskure, Sabon d’auka ne kansa yana rawa ya aikata haka, Sarki yace a baku hak’uri dan Allah. Tafe nake da asusun bankin sa yace a lissafa dik nawa aka kashe sai a biya. Domin bafaden da ya tafka ta’asar ma tuni an sallame shi ya koma cikin yan lufudi..” “Haba! Ba wani abu wallahi, Da kam dai banji da’din rashin nuna kulawar da masarauta tayi ba, Amma tun zuwan ka da kayi asibiti an sheda min kuma komai ya wuce wallahi, Lefi kuma bana bafade bane shi kadai harda diyata Khadija.. Kuruciya ce itama da kwadaituwar hazakar aikin ta yasa tayi wannan shirmen. Idan ba haka ba Ina ita ina tambayar sarki kai tsaye.? Uban taro guda? Tayi kuskure itama sosai, Saboda haka a bawa sarki hak’uri Shima dan Allah, Khadija ta tafka babban kuskure, Ina fatan Allah ya huci ran sarki ya yafe mata.” “Babu komai Alhaji.. Allah ya yafe mu gaba d’aya. Toh amma wani hanzari ba gudu ba. Sarki yace yana son ganin ka ido da ido a fadar sa.. Nan da kwana ki biyu kacal. Da yammaci bayan an tashi daga fada.” “Tohh! Ni? Toh Allah ya kai mu.. Na karbi wannan gayyata da hannu dubu. Allah ya bamu ikon ganin lokacin.” “Aamin Yaa Rabbi..” Sallama Alhassan yayi masa ya tafi. Dr. Isma’el ya shiga tunanin abinda yasa sarki keson ganin sa? Ko dai bayan ta’asar da Khadija tayi ranar ta kara da wani abun aka boye masa? Tunani ya shiga yi shi kadai yana dirkawa cikin sa ruwa. Zuciar sa dauke da addu’ar Allah dai yasa alkhairi ne yake kiran sa ba sharri ba. Kafin ranar ta zagayo kullum sai Dr. Isma’el ya tambayi Khadija akan gaskiar lamarin da ya faru awajen sauka sau ba adadi. Ranar da zai je masrautar ma sai daya sake tambayar ta tace daga tambaya bata kara ce masa komai ba. Kad’a Kai kawai yayi ya fice yana jinjina wannan al’amari. Kawu Daddy na fita na sake sauke gwauruwar ajiyar har ga Allah na tsani sarkin nan, Wallahi bana son sa, Kai duk abunda ya dangance su na tsane su. “Shege.. Mumugunci, Uban fadin rai. Wannan sarkin matar sa ta shiga uku da izzar sa. Bare kuma a kai ga yan aikin gidan..” Na sake jan wani dogon tsaki na juya daga kwanciyar da nai. Domin tun da la’anannen bafaden sarki ya rafke kai na ban koma aiki ba, Na dauki sick leave. Sannan duk wasu aiyuka na gida Kawu daddy ya dauke min su, Yace duk Wanda ya sake sa ni wani aiki sai ya mugun sab’a masa. Gaba d’aya yan gidan zaman takun sak’a suke yi da ni. “Wayata na janyo na rubutawa Habiby na message na masoya, Na tura masa. “Dear Habiby.. Nothing in this world can ever keep us apart from each other. We’ll always be together no matter where life takes us. I love and miss you so much. Yaushe zaka Zo? Hmm har yanzu ka ki zuwa ka kwashi gaisuwa wajen Kawu Daddy ko?” Minti biyu tsakani ya min reply, “I choose you. And I'll choose you over and over, Without any doubt,. I'll keep choosing you my love, My heartbeat.. My shining light. I love and missed you most. Ina nan tafe love. Zan zo na gayawa Kawu abinda ke tsakanin mu In Shaa Allah!. You are the pillar of my life. I love you.Thank you for being a part of my life.” Karantawa nai na lumshe idanu ina tuno yadda muke ragargazar soyayya a wajen aiki. Kowa kiran mu yake da Romeo and Juliet.. Da wannan tunanin na mike murmushi fadade a fuska ta na shige bandaki don yin wanka. *MASARAUTAR BASANNABAS* Tunda aka tashi daga fada yake jin tamkar yaje amma ya kasa. Ya jima yana kallon sashen da zai sadaka da wajen mai babban daki (mahaifiyar sa) tamkar ya sauke yaje, Amma da yayi taku d’aya biyu zai aiwatar da hakan sai yaji tamkar an fusgo shi ta karfi an hana shi. Wani bangare na zuciar sa na aiyana masa abubuwa marasa dadi. Kallon wayar sa yayi ta gefen ido. Akwai abinda yakeson aiwatar wa amma ya rasa menene? Lokaci zuwa lokaci ya kan tuno sunayen Khaleel da Abdul a zuciar sa. Amma shin su waye su ma? Rike goshin sa yayi da tafin hannun sa na dama, Dakyar yai ajiyar zuciya kawai ya shiga gyara zaman alkyabbar jikin sa, Sakin labulen yayi. Ya sauka daga stairs din sashen sa, Masu bashi kariya na biye da shi da fadawan sa suna take masa baya. Sai kirari ake masa. Ya shiga cikin fada idanun sa saqale da bakin shades dinsa. Wani parlorn sirri dake cikin fadar ya shiga ya zauna. Hannun sa na dama yasa ya dafe k’irjin sa yana taune kasan lips dinsa ta cikin rawani.. “Yaa Rabbi....!” Wani madanni ya danna, Sai ga bafaden sa Alhassan da Dr. Isma’el Sai raba idanuwa yake. Domin dik kudin ka da kamalar ka inde kazo gaban sarki Salman sai ka rissina. Ma’abocin ado da zatin sarauta. Me kwarjini da farin jini abun so ga kowa. Kwasar gaisuwa Dr. Isma’el yayi awajen Sarki Salmaan. Aka basu waje su biyu, dama parlorn soundproof ne ba’a iya jiyo komai dake wakana. Sannan babu cctv aciki. Gaban Dr. Isma’el sai dukan tara tara yake. Ya sosa k’eyar sa yana numfarfashi da sauri. Gyaran murya Sarki Salman yayi. Dr. Isma’el ya dago kansa sai kuma ya mayar saboda cikar idanun da sarkin ya masa. Gashi dai matashi yaro dashi amma sai kwarjini. “Allah ya karawa Sarki lapia...” Izzar sarauta da kuma halitta irin ta sarki Salman na rashin son magana yasa ya jima kafin yace, “Ya....Mai jiki?” “Da sauki ranka ya dade. Taji sau’ki tamkar bata yi ciwo ba.” “Alha....Alhasan ya gaya min komai. Kun yafe abunda aka kashe na asibitin ko..?” “Allah ya kara maka lapia. Yasa kafi haka! Allah yaja da zamanin ka. An kammala komai ranka ya dade. Ai lefi na ita yar wajena ce. Ina ita ina yiwa uban kowa tambaya a bainar jama’a? Amata afuwa karamar yarinya ce, Kuma sabon shiga ce a aikin nata.” “Ma....” Shiru Sarki Salmaan yayi yana ayyana yadda zai fito da maganar, “Ma.. matar aure ce ne?” “Ranka ya dade ba matar aure bace. Ba ta dai tsada tsayayye ba amma tanada manema sosai. (Tanada su ko?) Dr. ismail ya karasa fada yana mai tambayar kansa, Domin shi bai ma taba ganin tana zance ba. Bare yaganta da wani saurayi. Jujjuya me ze fada Sarki Salmaan ya shiga yi. Shin ga zancen a bakin sa amma yanajin nauyin fada, Wai shi mighty Salmaan shi zai furta yana neman amincewar mace yau? Siririn Tsaki ya saki wanda har sai da Dr. Isma'il ya dan dago ya dube shi. “Idan babu damuwa... Zaka bani auren ta, ina da bukatar masu irin aikin ta a kusa dani. Amma idan har babu neman auren wani akanta, Domin neman aure akan aure haramun ne.” Wani dindirus Dr. ismael yaji zancen, me kenan sarki yake nufi akan na bashi auran ta? Taya zai tambayi auran Dije bayan yasan wadanda suka fita a cikin duniyar nan. 'Hadin Allah' yaji zuciyar shi ta bashi amsa ganin dole yana bukatar hakan. Sai kuma wani farin ciki ya mamaye ransa, Yarasa me zeyi ma, Tamkar yayi tsalle ya rungume sarkin dan murna, Samun kansa yai cikin tsananin farin ciki, Wai Dijen sa ce yau Sarkin Basannabas yake neman auren ta. Allah kadiran Allah man yasha, tabbas wannan shine gata na biyu da zai yiwa Dije, wato ya aura mata mutum mai daraja da mutunci. Cike da tsantsar gamsuwa da amincewa yace. “Allah ya karawa sarki Lapia da kwanciyar hankali.. Khadija ‘ya ce awaje na. Mahaifiyar ta Kanwa ce agare ni. Marainiya ce uwa da uba duk sun rasu, Rikon ta ya dawo hannu na. Tabbas a yadda na sani Khadija babu neman auren kowa akanta, A matsayi na na mahaifin ta, Ranka ya dade, Na baka auren ta, Na baka damar auren Dije. Ina fatan hakan ya zamo alkairi a gare ku baki daya...” Sarki Salman ya samu kansa cikin madaukakin farin ciki na jin an bashi auren Khadija, Yarinyar da yasan a yanzu duk duniya babu wandanda ta tsana kamar masarautar shi.. “How sweet..? Beautiful soul....” “Masha Allah! Ranka ya dade magana kake?” Sosa bayan rawanin kansa sarki Salmaan yayi, Yai saurin girgiza kai yana hade fuska tamkar ba shi yayi magana ba. Ya sake jan numfashi yana jin tamkar ana ingiza shi akan lamarin, wanda beyi tunanin shi ba ko kusa, wato kara aure bayan matarsa da suke tare, Ya numfasa tare da cewa Alhaji Isma'il. “Ina son auren ya zama sirri, bana son maganar ta yadu a duniya. Abin da nake so kawai shine. Ka tanadi waliyanta, ni kuma ni zan zama waliyin kai na.” “Duk abin da kace dai dai ne ranka ya dade, kuma Khadija yarinya ce mai tsantsar biyayya. Nasan ba zata watsa min kasa a ido ba, bare idan taji labarin kai ne zaka aure ta, nasan zata yi farin ciki tabbas.” Sarki Salman ya yi shiru, duk da cewa yana cike da tsantsar farin cikin amincewar da aka yi masa, amman ba zai nuna ba saboda izzar sarauta. “Idan babu damuwa, ina son ayi komai a cikin wata d'aya kacal.” Cewar sarki Salman cikin nuna iko. Alhaji Isma'il ya sake dukawa tare da kai gaisuwa yace. “Ko a yau kake son a yi, za a yi shi ranka ya dade da ikon Allah. Allah ya kaimu lokacin yasa a yi damu baki d'aya.” Gyada kai kawai ya yi bai sake cewa komai ba. Alhaji Isma'il na fita daga wajan sarki Salman, kawai sarkin yaji wani irin muguwar faduwar gaba, cikin sauri ya dafe kirji yana rintsa ido tare da kiran sunan Allah. Dafe kai ya yi yana jin idanunsa suna neman rufewa, kamar wanda ake shirin zarewa rai. Tunani ya shiga yi na anya za a barshi ya yi wannan auran kuwa? Tabbas abubuwa da yawa suna shirin jagule masa, ta yadda yake ganin kamar ba zai iya warware su ba. Sai dai wani barin na zuciyar shi yana sake kwadai ta masa son yin auran sirrin ba tare da an sani ba har sai bayan an daura aure koda kuwa duniya zata ji........ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* _*17/18_* *MASARAUTAR BASANNABAS* Bashi da wata dama ko karsashi da zai kaiwa wani kukansa bare a ashere mishi. Kiri-kiri yana son bayyana abu a zahirance amman sai ya kasa, yaji tamkar ana shake masa wuya. Tsaye yake jikin taga yana hangen duk wani motsin masu yawo a can harabar gidan, sannu a hankali ya hango mahaifiyarsa tana tafiya jikin ta sanye da mayafi, wanda alama suka nuna daga wani wajen ta dawo. Salman ya dauke fuskar sa daga kallon ta tare da takawa a hankali yaje ya zauna daga kan kujerar da ya taso. “Assalamu alaikum.” Cikin ransa ya amsa be ce komai ba bare ya dago dan ganin wace ce, muryar ta kawai ta shaida masa cewar jakadiya ce. “Allah ya taimaki sarkin sarakuna, an buga an barka mazan fama. Uwar gida kuma gimbiya tace a yi mata iso wajan ka.” Kamar yace a'a saboda shi a yanzu yana da bukatar nazari akan abin da yake shirin yi na auran da zai yi, yana so ya zurfafa tunaninsa ta yadda zai yi ya ware inda zai sanya amaryar idan an daura aure an kawo ta gidan, saboda yasan dole azo a nemi muhallin da zai ajiye ta. Da yake Jakadiya tasan halinsa na shariya, hakan yasa ranta be baci ba har lokacin da ya ga dama yace mata. “Kice bacci nake ji.” Ta kuma russunawa tare da sunkuyar da kai cike da girmamawa tace. “Gyaraaa kintse sarkin sarakuna, zanje na gaya mata kamar yadda kace.” Shi dai be kuma cewa komai ba har ta fita daga dakin, yana zaune ya rasa wane irin tunani zai yi. Jakadiya ta kuma dawowa da alama ma dai ita kanta uwar gidan nashi tana bakin kofa dan yaga Jakadiyar ba ta jima da fita ba yaga ta dawo, yaja tsaki a cikin ransa, zuciyar shi tana zugi saboda wasu mutum biyu da kwakwalwarshi take ta son tuna masa ko su waye a gurin shi amman ya kasa tantance ainahin su. “Allah ya ja da ran sarkin Basannabas, uwar gida tana neman afuwa dai akan son ganin nan naka. Tace kanta bisa wuya, ka tausaya ka bata damar shigowa ciki.” Hannunsa kawai ya daga kuma Jakadiyar ta fahimta dan tashi kawai ta yi taje ta sanar da ita sai gata ta shigo. Tana shiga Jakadiya ta yi sauri ta nufi sashen Gimbiya Jaleela wato kishiyar mahaifiyar sarki Salman. Hango ta tayi tana sakkowa daga bene cikin shiga ta alfarma, tana hango Jakadiya ta kuma tsuke fuska dan dama bata sakar mata fuska duk kuwa da irin yadda munafincin da take kawowa daga lungu da sakon cikin masarautar. “Takawarki lafiya farin cikin marigayi sarki Aliyu, uwar marayun masarautar Basannabas, farin ciki da walwalar bayin Basannabas. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana uwar daki na mai share min kuka.” Sai da tazo ta zauna ta gyara zama sannan ta kalli Jakadiya cike da iko tace. “Jakadiya meke tafe dake? Ina fatan dai kin zo min da labarin da zai sanyaya min zuciya ta.” “Ina neman afuwarki uwar daki na, sai dai wannan labarin da nazo miki dashi ban san yadda zaki dauke shi ba.” “Ina jin ki Jakadiya.” “Dama yanzu Gimbiya Shaheedah tasa nayi mata iso wajan maimartaba sarki, yanzu haka tana can gurin sa zasu yi ganawa ta musamman tsakanin su.” A fusace Gimbiya Jaleela ta kalli Jakadiya tana hararata tace. “Me nace miki game da cewa Salman sarki?” “Ki gafarce ni Uwar daki na tuba nake Allah ya huci zuciyar ki, sha'afa nayi wallahi ki yafe min.” “Shikenan amman ki kiyaye gaba. Ina so kuma ki binciko min abinda taje suka tattauna, bana kuma son kuskure kin sani dai.” “Insha Allahu uwar daki na ba za a samu wani kuskure ba, Allah ya ja zamanin ki.” Daga haka ta mike ta fita tana rawar jiki. Bata wuce ko'ina ba sai sashen Gimbiya Najwa wato kishiyar Gimbiya Jaleela, wace ita ce matar marigayi sarki Aliyu Salman ta uku, yar Galadima ce. Ita kuwa tana kishingide a tsakiyar katafaran parlorn ta, hadimanta suna ta faman yi mata fifita, wasu na matsa mata kafafuwa yayin da wata ke gefe tana yanka mata kayan marmari d'aya bayan d'aya tana sha. Gimbiya Najwa na ganin Jakadiya ta yi saurin sallamar hadiman nata, dan tasan tabbas labari ne ta kawo mata game da Sarki Salman ko Gimbiya Shaheedah ko kuma mahaifiyar sarki Salman d'in wato Gimbiya Sa'adatu. Jakadiya daman tasan halayen ko wacce mata dake gidan, saboda duk itace munafukar su, wajan kai gulmar ko wacce a gurin d'aya. Tasan daman Gimbiya Najwa ba zata tambaye ta komai ba har sai idan ita ce ta fara yin magana, wani lokacin Jakadiya takan jinjinawa irin girman kanta da takamarta saboda kawai tana yar Galadima, da ace a yar gidan sarkin kacokam Allah ya yi ta bata san me zata yi ba, duk da cewa a wannan lokacin su Waziri da shi Galadiman sune suke jan ragamar sarautar Sarki Salman, sai abin da suka ce shi za'a yi. “Na gaisheki ta gaban goshin marigayi sarki Aliyu... Jinjina da ban girma gareki shalelen Baba Galadima, uwa ga magajin sarki wato yarima Ilyas(junior). Nazo miki da wani labari.” Kamar ba zata amsa ba tsawon lokaci, sai da ta mulu ta mulmule sannan ta kalli Jakadiya karo na biyu tace. “Idan kin san maganar ba ingantacciya bace karki sanar dani, ki bari idan kin tabbatar da ingancinta, sai kizo ki gaya min.” “Na kuma gaisheki ta gaban goshi, tabbas bani da gamsashiyar magana akan abin da nazo miki dashi. Kamar yadda kika ce, zan koma idan na gama tabbatar da ko menene zan dawo. Na barki lafiya, farin cikin yarima kuma sarkin gobe, shalele Ilyas.” Tufa d'in dake hannunta taci gaba da ci ba tare da ta sake bi ta kan Jakadiya ba, saboda ita Gimbiya Najwa tana da wasu munafukan bayan Jakadiya, dan ita a cewar ta idan wata taga wani abun, wata be zama lalle ta gani ba. Hakan yasa ta rarraba kafa ta baza masu gano mata sirrikan duk wata mata dake cikin gidan. Shi yasa Galadima yafi waziri sanin duk wani abu da ya shafi Gimbiya Shaheeda da kuma sirrin mahaifiyar sarki Salman. Can kuma bangaran Sarki Salman da uwar gidan sa wato Gimbiya Shaheeda, tana shiga ta zauna gefen shi tana tsotsar alawar da take cikin bakin ta tace dashi. “Wani lokacin kakan yi min abin da sam be dace ba a gaban kaskantattun mutane, wato hadimai. Ya za'ai kamar ni nace ina son yin magana da kai kace a ce min bacci kake yi? Karka manta ban da ni babu wacce zata iya zama da kai bayan kowa yasan cewar ba da kwan haihuwa, ba zaka iya bawa Basannabas magaji ba kamar yadda marigayi ya bar maka gadon mulkin sa wanda kake a kai yanzu.” Jin kalamanta yasa ransa fara tafarfasa saboda zafin su da yaji, bata da wani abu da take yawan yi masa gori irin rashin haihuwar sa. Amman saboda tsabar shakkarta da yake yi sai bai ce mata komai ba har ta kuma yin magana. “Ni wallahi kasan ba da ban soyayyar da nake yi maka ba, da tuni nasa ka sauwake min naje nayi wani auran na haihuwa. Amman saboda na san babu matar da zata iya auran ka yasa nake daurewa ina lallashi zuciya ta akan ta hakura ta zauna tare da kai.” Ta yi shiru na dan wani lokaci, shi kuma wata irin tsanarta ce take sake zama sabowa a zuciyar shi. Shi be ki ta ce ya sauwake mata ba indai har tana da bukatar yin haka, baya jin komai a game da ita sai zallar shakka da son bin duk wani abu da take so. Kansa a kasa dan ko da ta shigo be dago ya kalleta ba sai ji ya yi tace. “Honey dago ka kalle ni.” Ta na rufa baki kuwa ya daga yana kallanta, ta yatsina fuska tare da mika hannu ta zare bakin glasses d'in idan shi yadda zata ganshi sosai. “Haba Honey, ba na hanaka kallo na da wannan glasses d'in naka ba? Na yi na yi da kai ma ka dena saka baki amman ka kasa bari, idan ka sashi kamar wani tsohon makaho wanda bashi da d'an jagora.” Da yasan wannan maganar ce zata kawo ta da duk yadda zai yi sai ya hana su hadu, sai dai ance rashin sani yafi dare duhu. Kuma idan da sabo yaci ace ya saba da duk wasu abubuwa da ake yi masa a masarautar. Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana jin wata zazzafar kaunar shi, hakan ne yasa bata son taji ana cewa ya kara aure shi yasa take kuma rike shi ta hanyar da zuciyarta ta aminta. “Sannan kullum nice nake nema ka kai babu wani abu da yake damunka. Ina tunanin rashin haihuwar nan taka tana da nasaba da rashin sha'awa da baka da ita. Ko kai kayi zaton sarakuna basa mu'amala da matan su?” Salman ya yi shiru dan shi sam ba wani farin ciki yake ji ba idan suna yi. Shi kawai yana yi ne ko Allah zai sanya ya samu rahama, ya kuma fita a hakkin ta na aure. Ganin ba zai yi magana ba yasan yata tashi tana murmushi ta wani jujjuya ya masa kugu ya kawar da kai, ba burgeshi take yi ba, hasalima ji yake tamkar ya fashe da kuka dan haushi da takaicin abin da take yi. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya tare da rintsa ido kawai ya hangi Dije tana ta yi masa murmushi a wajan fuskar shi. Sai ya samu kansa da kin bude idon yana jin wani dadi a yadda yake ganin ta. Kiran sallar magariba shine ya tayar dashi daga gurin, ya shiga toilet ya daura alwala daga nan ya shirya ya fito zuwa masallaci dan kagabar da sallah. °°°°°°°° °°°°°°°°° °°°°°°°°°°° Tun da ta idar da sallah ta mayar da goshinta kasa bata sake dagowa ba, addu'a kawai take yi tana zubar da hawaye. Cikin kaskantar da kai take gayawa Allah muradanta duk kuwa da cewa tasan yasan tana cikin halin bukatar taimakonsa. Sannu a hankali ta dago fuskarta sharkaf da hawaye, tasa bayan hannunta tana sharewa. Gimbiya Sa'adatu kenan wato mahaifiyar sarki Salman, mace mai tsantsar hakuri da juriya tare da kawar da kai. D'an ta ne, amman ba ta da wani iko akan shi, daga nesa kawai suke hango junan su amman basa haduwa face to face saboda an riga an janye mata shi daga gareta. °°°°°°° °°°°°°°° °°°°°°° Kishingid’e gimbiya shaheeda take a doguwar kujera dake tafkeken parlorn ta na alfarma. Wanda komai na cikin parlorn kirar samfarin kayan sarauta ne wanda turawa kewa laqabi da ‘Royal design’. Kai hatta salular da ke saqale ajikin da bango itama ta Royal ce. Bayinta biyu ne a zaune kowanne yana mata tausa a kafa d’aya d’aya. Sai lumshe idanu take ahankali tana mai cigaba da taunar tufar dake hannunta, Wanda take gutsira ahankali cikin k’asaita. Wayar tace dake kusa da ita tayi haske alamar saqo ya shigo, Sai data mula tasha iska tukun sannan ta daga wayar ta duba. Ta jima kafin ta daga musu hannu alamar su dakata, Sannan ta mike ta gyara zaman wani hadadden mayafin jikin ta mai beza. Bayin guda biyu suka bi bayanta kowacce kanta a kasa. Sashen su ta nufa, Dake dare ne, Tarwar masarautar take da hasken lantar ki. Tsuntsaye nata kuka. Shiga tayi cikin wani babban parlor. Duk sun hallara aciki, Kowacce tana hakimce a kujera tana jin kanta. Kallo d’aya zakai musu kasan manyan mata ne masu aji, Wanda ke watayawa a duniyar masu kudi. Gaishe su tayi. Ta samu waje ta hakimce itama. Bayin dake wajen duk suka basu wuri. Babbar matar ta tsakiya dake hakimce ta mike kafafun ta akan center table itace tafara magana, “Shin ya sanar muku da halin da ake ciki kuwa....?” “Hmm! Ki bari kawai.. Mun fara sanya fa. Yacemin kwana biyu ya kasa gane kansa.” Cewar Haj Huwaila ta bawa Haj Jaleelah amsa tana tana jijjiga kafafu. “Shin Gimbiya Shaheeda kin fara ganin alamun canji kuwa?” Haj Najwa ta tambayi Gimbiya Shaheeda dake kallon su baki d’aya. Gimbiya Shaheeda taja majina tana jujjuya zobunan daham din hannun ta. “Toh.. Gashi nan dai.... Ba wani matsala gaskia. Yanzu ma wanka nakeso nayi ayimin iso wajen sa.” “Karki sakaci da maganin nan Gimbiya. Wallahi Malam ya rantse da abinda zai kashe shi wannan maganin babu na biyun sa..” Haj Jaleela tace da Gimbiya Shaheeda data mike lokaci guda tana Yatsina fuska, “Duk yadda ake ciki...” Sallama ta musu ta dauki hanyar sashen ta. Kallo d’aya tayi wa sashen mai babban daki tayi gaba tana sake daure fuskar ta. Su kuwa ko bayan fitar ta sa zancen ta suka yi a gaba. Sunata shewa suna tafawa. Tamkar ba kishiyoyi ba ada. Aminan juna ne na qut da qut. Gimbiya Jaleela ce ta gyara zama tana faman jujjuya ido tace. “Ni wallahi so nake a fara bawa mata sarauta a kasar nan. Ina ji a jiki na zan iya duk wani abu da ake yi a cikin sarauta. Kuma nayi mafarki nan gaba kadan mata zasu dawo sune suke jan ragamar mulkin masarautar Basannabas.” Ta gama maganar tana dora kafa daya kan daya tare da juyawa ta kalli sauran one by one. Cike da tsantsar dariya irin ta rainin hankalin nan Gimbiya Najwa ta mike tsaye tare da yin taku daya biyu zuwa uku ta tsaya a tsakiyar su tana gyara kafadun rigar jikinta tace. “Kwarai kuwa Hajjaju, ina jin kuma ni aka bawa damar karasa yin wannan daddadan mafarkin naki da kika fara. Domin kuwa ni na hango kai na akan wannan kujerar ta sarauniyar Basannabas. Kuma a cikin d'in bin halacci na har na baki mukamin Baba na, wato waziriya ta. Ke kuma..” Ta Nuna Gimbiya Huwaila wato yar ciroma tare da cewa. “Ke kuma na yi miki mukamin Baban Hajjaju Najwa, wato Galadima. Na san dai wan.....” Bata karasa ba Gimbiya Najwa tayi saurin da katar da ita ta hanyar cewa. “Ya isa dan Allah, wannan ai shirme ne. Idan zaku dawo cikin serious d'in ku toh ku dawo, amman ta ya zaku zauna kuna ta yi mana wasu zantuka na shirme. Yanzu mu maida hankali wajan ganin yarinyar nan ta yi aikin da muka bata, Salman d'an girman kai ne, ko uban shi be yi wannan jiji da kan ba wallahi.” “Haka ne kam, dan naga kwanan nan itama ya fara yi mata gardama, juya dashi amman sai shigen fadin rai.” Duk suka yi dariya tare da yin tafi da hannayensu. Gimbiya Huwaila ta ce. “Sa'adatu ce ma ni take bani mamaki, matar nan Sam taki yadda da cewa yaran nan baya son ganin ta, amman kullum cikin wahalar da kanta take wajan koke koke da wasu addu'o'in ta na shirme. Ai gara ka yiwa kanka maganin matsalar ka, amman kace zaka jira ai sai ka dade, koma ka mutu baka cimma burin ka ba.” “Ai Baba (Madaki) yace abu d'aya ne yasa shi barin matar nan. Shine baya daukar ta a matsayin mutun mai rai, amman da tuni yasa anyi shekara lahira.” “Gaba d'aya manta ta nake a cikin tsarin rayuwa ta.” Jaleela ta fada cikin yatsina fuska. Haka suka zauna suna ta shirya makircin su kamar yadda suka saba. Ita kuwa Sa'adatu tana sashen ta tana kukan zuci da na idaniya. Kuncin da take shiga wani lokacin har mutuwa take roko tazo ta dauketa saboda wahalar da ranta yake yi. Amman tasa a ranta komai daga Allah yake zuwa, yasan kuma lokacin da zai warware mata wannan masifar da take ciki. Tsab ya yi shirin bacci, yaje ya kwanta akan gado sai gata itama ta shigo cikin shigar kayan bacci masu santsi gasu shara-shara. Gadon itama ta hau tare da rungume shi ya kawar da kai, tunda tasa hannunta ta shafi kirjinsa shikenan ya nemi nutsuwa ya rasa. Kansa ya yi girma yaji kamar an dora masa duniya da abinda ke cikin ta. Wani barin na zuciyar shi kuma yana kusanto masa ita akan ya yi mu'amala da shi. Kafin kace menene ya firgice sun zama abu d'aya, koda suka dawo cikin hayyacin su wani gigitaccen bacci ne ya dauke shi. Ta tsaya tana kare masa kallo mai cike da fassarori kala-kala. Kanta ta dora saman kirjinsa take itama bacci ya dauke ta a jikinsa. Garin ya yi shar gwanin dadi, sarki Salman ya fito akan farin doki da aka kawata shi da ado mai daukar hankali. A hankali yake tafiya har ya isa wajan wani ruwa inda wata tsohowar mata tana durkushe sai kuka take yi. Ya tsaya tare da sakkowa yaje kusa da ita cikin sassanyar murya yake mata magana. “Baiwar Allah lafiya? Me yasa ki kuka a cikin mulki na?” Ba tare da ta wai go ba ta gyara yagaggen mayafin da ke jikin ta tana share hawaye tace. “Yara na duk sun guje ni, ba su san gani na bare ganin fuskata.” “Suna raye kuma?” Tace, “Ban sani ba ni, sai dai ina ji a jikina tabbas suna raye. Me ye amfanin yaran da zaka haifa da cikin ka amman su guje ka? Me ye amfanin wahalalliyar nakudar da zaka haifi yara amman su gaza sanya ka farin cikin rayuwa? Kaico da irin wannan duniyar mai cike da tsantsar hasara....” Ta wai go a fuska sai kawai yaga fuskar mahaifiyarsa, ta riko kafafunsa ta riƙe gam tana cewa. “Zan tafi, zan kuma yin nisa da yara na da suka kasa gane matsayina a gurin su. Ka tausaya min ka dawo min da yara na, gwara mu zauna cikin talauci tare da su akan su yi arzikin da za'a raba mu. Karka tafi ka bar ni ya shugaba, ka tuna yadda ake ji idan aka rasa wani bangare na jiki. Ka tausaya min ya......” Sarki Salman dake kwance kan katafaran gadon shi, ga matarsa kwance a jikin sa, kawai sai ji ya yi ya tashi a gigice yana sakin wata firgitaacciyar kara. Jikin shi kuwa sharkaf kamar an tsamo tsumma daga cikin mai.... *KHADIJA* ____Wajen Aisha kawata naje, Wadda muka yi British da ita, yanzu ta kai matakin lecturer a jami’a. Mun sha hira sosai kafin na dau hanyar dawowa gida. Ta babbani shawarwari sosai akan rayuwa, Da yadda zan cigaba da gudanar da ita. Kasancewar garin damina ne tuni hadari ya hadu aka shiga kwarara ruwa tamkar da bakin kwarya. Gashi na sallami TK driver tun dazu nace yaje ba komai zan dawo idan na kammala. Adaidaita sahun da nake ciki sai tangadi take a titi tamkar zata kifar damu saboda yadda iskar damina ke kad’a ta. Ganin gamu ga gidan rediyon mu hakan yasa na tsaida shi na falfala da gudu na tsaya a rumfar motoci, Waya na lalubo na kira Mas’oud nasan shi kullum yana nan, Baya da day off Saboda kasancewar sa babban ma’aikaci awajen, Na sheda masa ina waje ruwa ya tsare ni. Cikin barin jiki kuwa sai gashi Da lema a hannun sa ya karo yai saurin rufamin ita akai, “Sannu Habibaty.. Ya akai haka, Ina kika je?” “Hmm bari dai Habiby.. Wai zuwa nayi na gayda Aisha da naje wankin kai, Kasan kusa da jami’ar sune shine na biya.” “Ayyah sannu, Muje ciki ki huta, Dama wannan damina da ake marka marka..” “Allah yasa mu wuce Lapia..” Nace dashi, Muka shiga ciki, Kowa yagan mu sai ya tsokane mu, musanman ni. Wai na biyoshi wajen aiki na kasa hak’uri. Office dinsa muka shiga. Sai rawar sanyi nake.Rigar sanyi ya dakkomin acikin kayan custume da ake ajiyewa. Muka shiga hirar soyayya hankalin mu kwance, “Kyanta ace Ruwan nan da ake ni da ke muna matsayin mata da miji. Mezesa mu wani fito aiki.. Ai sai dai ragargazar soyayyah da..” Katshe shi nayi. Domin sai ina taka masa birki, Kunya ce ke lullube ni duk sanda yai wadannan kalaman, “Wai love sai Yaushe zaka zo ka gayda Kawu daddy ne?” “Zanzo Insha Allahu! Banason zuwa ne batare da komai ya kammala ba. Kinga akwai gini da kawo kudi da sauran su. “ “Gini kuma love?” “Oum waleeda gwara ace son samu komai na rayuwar da zamuyi ya zama na is ready . Banason muyi wahalalliyar rayuwa.” Kullum dai zancen kenan. Na ka’da kai kawai ina mai mamakin kalaman sa. Ni fa wallahi Saboda rin k’aunar da nake masa ko lefe zan iya yafe masa . “Shikenan Mine! Amman da ba sai ka wani wahalar da kanka ba, Ko da irin haya sai mu fara ko..?” “Shi kenan Oum Waleed zan samu alhajin mu da maganar, Kinsan suna ganin Ya Haysam bai aure ba gani zasu yi nayi kankanta.” Cuno baki nayi gaba na masa gatsine, “Ai. Ai.. Ni dai nai dai nima ba canai nima ayi auren ba. Kawai dai saboda Kawu daddy yasan da kai ne.” “Haba tawaje na.. Ai ke tawa ce. Nine mallakin gangar jikin ki da soyayyar ki Insha Allah. In Shaa Allahu zaki ji..” Banbashi amsa ba saboda nasan yanzun sai ya kauce hanya. Mikewa nayi na saqale jakata. Ganin ruwan ya tsagaita. “Zan tafi gida...” “Okay muje na sauke ki..” Gaba nayi yana biye dani abaya muka shiga mota ya tayar. Tunda ya fara tuki na juya masa baya ina kallon waje. Yanayi na damina gari yayi shar-shar dashi. “Oum Waleeda fushi ake dani..?” “Haba ni na isa? Kawai Ina kallon sarautar Allah ne.” “Ina son ki.. Ina miki son so tawan..” Rufe fuska ta nayi da tafin hannaye na da suka sha kunshi na sudan, Sunyi maroon gwanin sha’awa. “Lallen ki Yayi kyau...” “Godia nake Habiby..” Har k’ofar gida ya kai ni, Dai dai lokacin da Kawu Daddy ya dawo Shima. Ganin na fito yasa Mas’oud fitowa Shima ya rissina ya gayshe da Kawu daddy daya futo da sauri da alama mantuwa yayi, “Kawu daddy sannu da zuwa..” “Yauwa Sannun mu Khadija..! “ “Yallabai Barka da rana...” “Barka kadai... Ya aiki?” “Alhamdulillah!” Mas’oud ya bashi amsa yana sosa kai, Kawu daddy ya kalle ni ya kalle shi, “Kamar na san shi ko?” “Abokin aikinta ne ni yallabai..” Cewar Mas’oud, Na juya na galla masa harara, “Abokin aiki kuma?” Na tambaye shi ina hade girar sama data Kasa, “Oganta ne ni.. Naga garin da lema shine na sauke ta..” Mas’oud ya bani amsa yana kallon Kawu daddy. Nayi k’wafa kawai ina galla masa harara, “Ah Allah sarki, ai na gane ka yanzu. Kai ne mai jinyarta a asibiti. Angode sosai. Tukur driver baya nanne?” “Eh nace ya dawo gida dazun.” Musabaha sukai da Kawu daddy ni kuma na shige cikin gida da sauri, Kawu na biye dani. Ya dauki brief case dina a parlor da alamun shi ya manta, Har ya kai kofa, Ya juyo, “Khadija..” “Na’am Kawu daddy..!” “Idan kin samu Lokaci zuwa gobe haka zamuyi magana Insha Allah.” “Toh.. Kawu...daddy..” Na bashi amsa a rarrabe saboda yadda cikina ya soma hautsinewa, Kodai ban kyauta bane yadda Mas’oud ke kawo ni gida? Wata zuciar tabani amsa da ‘Kwarai baki halacci ba Khadija. Driver sukutum guda da mota fa aka baki.. “Kawu kayi hak’uri ..” “Kin cika Shirme! Wayace lefi ki kai? Magana kawai zamuyi ta hankali. Alkhairi ne In Shaa Allahu.” Yana gama magana ya fice da sauri, Ni kuma na haye sama ina hada hanya. To maganar me zamuyi? Oho..... . ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *1___9* _Zakuga canjin sunan masarauta daga BARNABAS... zuwa BASANNABAS. Ko ince tun d’and’ano ma na canza. Na manta ban sanar ba.. My baddd! So dai komai yana bukatar sanarwa. Bayan nayi bincike nagano BARNABAS. Wani suna ne ko ince abu ne daya danganci ma’abota littafi. Sunan yazo acikin bible ma sunce: The Gospel of Barnabas is a book depicting the life of Jesus😅so BARNABAS din Joseph dinsu ne acikin bible.. To avoid consequences 😂💔salin alin se muka koma da BASANNABAS. Duk kuwa da kirkirarren labari ne gara a canza din🤤 case closed ko? .. To acigaba da gashi🤗😉_ *MASARAUTAR BASANNABAS* *Yadda* taga yana ta waige waige kamar yana neman wani abu a kusurwoyin dakin yasa itama ta tsorata tare da rike shi. Nan take taji ya yi wancakali da ita yana kuka mai firgitarwa, hannayensa dafe a kai yana ihu. Tabbas akwai abin da yake damun sarki Salman wanda ta kasa fahimta, da tana tunanin ko maganin da tasa masa a cikin pillow ne, wanda su Gimbiya Najwa suka bata suka umarce ta da ta sanya masa, ko shine yasa shi yin wannan abun cikin talatainin dare? Babu mai ba ta wannan amsa, har sai taji abin da ya sanya shi yin wannan abun. Gimbiya Shaheeda ta riko gaban sleeping dress d'in ta da botiran suke a bude, ta sake matsowa kusa da shi a tsorace dan gaba daya ya canza sai faman cije baki yake yi da hakoransa. Leka idanunsa tayi taga yana zubar da hawaye, abin da ta dade bata gani ba a tare da shi. Sai ta marairaice tana share masa kwallar saman kirjinsa, murya a sanyaye ta fara masa magana. “Na tsorata da ganin ka cikin wannan yanayin, nasan mafarki kayi, kuma da alama bashi da dadi duba da yadda kake zubar da hawaye. Shin me ka gani a cikin mafarkin naka?” Ya yi shiru ba tare da ya kalleta ba, ga wani irin azababban sanyi da yaji yana huda duk wata kofar gashi dake jikin shi. Zare hannunsa ya yi daga rikon da ta yi masa, ya janyo jarkar ruwa tare da budewa ya kafa kai yana sha. Tun da ya fara sha bai sauke ba sai da ya kusa shanyewa taji ya ja wani dogon numfashi tare da saukewa yana lumshe ido. “Ko mafarkin Ammie ka yi?” Sai tambayar ta ta tayi matukar daure masa kai, ya dago tare da kallon ta da jajayen idanunsa. Take yaji wani faduwar gaba, sai ya sunkuyar da fuska yana girgiza mata kai. “Idan mafarkin ta kake yi ya kamata ka dena, domin Ammie sam bata kaunarka. Ka manta sanda za'a nada ka matsayin sarkin Basannabas ita tazo ta dinga gayawa mutane cewar kai juya ne baka haihuwa kar a baka? Ka manta?” Salman ya yi shiru kafin daga bisani ya daga kai alamar haka aka yi. Shaheeda ta yi murmushi sannan ta sake matsawa jikin shi ta shige tana faman shafa shi, cikin tsantsar makirci tace masa. “To ka dena damuwa da duk wanda be damu da san ganin abinda Allah ne ya mallaka maka shi. Ni zan kasan ce da kai a duk yanayin da kake ciki, zafi rana da damuna ba zan taba rabuwa da kai ba.” Cikin matukar farin ciki Salman ya jinjina kai, sai kuma ya matsa ya kwanta akan pillow still tana jikin shi sai lailaya shi take kamar ta samu jariri sabuwar haihuwa. Daga haka ya manta da wannan mafarkin da ya yi da mahaifiyar shi, bacci ya kuma daukar shi. Gimbiya Shaheeda ta mike zaune lokacin da ta tabbatar da cewa ya yi bacci da gaske. Sakkowa ta yi daga kan gadon ta ciro wani farin zare daga cikin gashin kanta tana kare masa gani kafin ta yi murmushi wanda ita kadai ce tasan matsayin shi. Boyewa tayi sannan ta shiga toilet ta tsarkake jikinta ta fito ta shirya ta kwanta tana jin farin ciki. Basu farka ba sai wajan karfe shida, ya bude ido da kyar sai yaga Shaheeda a kusa da shi, ya fara duba jikin shi. Gabaki d'aya bai san sunyi wani abu ba sai yanzu da yaga yanayin shi, ya duba agogo yaga lokacin sallah har ya wuce. Da sauri ya tashi ya tashe ta sai tace masa ai tayi wanka tun dare. Yaji haushi kuwa sai dai ko a fuska kasa nunawa ya yi, kawai ya wuce bathroom shima ranshi a bace. *KHADIJA (Dije).....* Tun da na idar da sallah nake jiran kiran kawu daddy da yace zai ganni da anjima amma naji shiru, sai na fito daga daki naje parlor na koma kitchen amman shiru yana daki be fito ba. Hakura na yi na koma daki na zauna ina duba wani littafi. Kamar jira ake na zauna sai ga kiran shi ya shigo waya ta, na daga yace na sakko na same shi a parlorn kasa. Jiki na rawa na dauki hijab nasa na fito dan na kagu naji abin da zai sanar da ni, wanda sam na kasa kawo ko meye a cikin zuciyata. Yana zaune rike da waya yana dannawa nayi masa sallama ya dago ya kalle ni, kafin na zauna ya ce yace na rufe kofar naje na rufe sannan na dawo na samu gefen kujera nesa dashi na zauna. Ya yi gyara murya tare da aje wayar a gefen sa ya dan matso daga gefen kujerar yace. “Alhamdulillahi Khadija a kullum na kalli yadda rayuwar ki ta dawo na kanji dadi da farin ciki. Gashi cikin ikon Allah ya sake daga daraja da mutuncinki ta hanyar da bamu tunani ba, yanzu bani da wani buri irin naga na mika ki zuwa dakin mijin ki, wannan shine buri na na biyu akan ki Khadija. Ina fatan zaki ci gaba da kulawa da kanki kamar yadda kike yi a koda yaushe. Na ga yanzu Allah ya baki miji wanda nake saka ran insha Allahu shine fitila na gaba da zai ci gaba da haskakawa a cikin duniyar ki. Ni dai ya yi min, tarbiyarsa, dabi'unsa da kuma kalamarsa duk ba bu wanda ban duba ba. Kema nasan zai yi miki, naga yaro ne matashi mai jini a jika, Allah ya daukaka shi a cikin tarin ni'imomin da yake da su.” Kai na a kasa farin ciki ya mamaye ni, ashe kawu daddy kallon takun mu kawai yake yi nida Mas'oud bamu sani ba? Lallai babba-babba ne inji bahaushe da yace yaro ko ya hau rimi ba zai iya hango komai ba. Wayyo Allah dadi sai na hango gashi har an daura mana aure an kai ni gidan Mas'oud birnin zuciya ta muna ta shan soyayyar mu. “Nan da dan wani lokaci za'a daura auran ku insha Allahu. Duk da cewa bani ne wanda zai bada auran ki ba, amman na dauki alkawarin zuwa can dangin mahaifinki da kai na nayi musu bayani yadda zasu fahimta. Allah ya yi miki albarka Khadija tashi kije daki ki kwanta nasan gobe akwai aiki.” Ciki da jin kunya na tashi na ruga da gudu, farin ciki da nishad'i na suka dadu ba. Kan gado na fada ina tsalle tamkar wata yar shekara uku, na kagu Mas'oud ya kirani dan na kyankyasa masa wannan zazzafan labarin wanda nasan idan yaji ko bacci ba zai iya yi ba saboda murna. Wani ikon Allah sai be kira ba sai sako da ya turo min na text message cewar suna tare da Abban su ba zai samu damar kira ba mu hadu gobe a gurin aiki. Banji komai ba saboda ina cike da murna na je kitchen na zuba abinci naci sannan na dawo na kwanta cike da zakuwar ganin gobe. *WASHE GARI* Yau kam na fi koda yaushe saurin shiryawa dan zuwa gurin aiki saboda zumudi, na shirya tsab na dauki jakata Tukur driver ya dauke ni sai gurin aiki. Babu kowa sai wadanda suka yi aikin kwana, na shiga muka gaisa sannan na wuce office na zauna dan jiran lokacin da zan yi program dina. Bamu hadu da Mas'oud ba sai wajan karfe goma sha d'aya dalilin rashin zuwan sa da wuri. Sai da na jira har karfe d'aya lokacin da ya gama nashi sannan mukai sallah nace ina son yin magana dashi. Yana ta zolaya ta ganin yadda na cika da nishad'i ba kamar kullum ba, ya samar mana gurin zaman muka zauna. “Ko ranar da aka daura mana igiyoyin aure sai haka madam, irin wannan murna da farin ciki haka, meye sirrin a ban nasha nima.” Na yi dariya tare da rufe ido da hannayena, na bude ina wasa da zoben yatsa na nace. “Albishirin ka?” “Goro Oum Waleedah.” “Fari ko baki?” “Ahhh! Sai ma an jani tukunna? Toh na zabi uhmmmm... Uhmmmm... Zabar min dai da kanki.” Ya yi maganar cike da shagwaba, ban san lokacin da na saki dariya ba ina cewa. “Gaskiya kai zaka zaba, ai ni zan gaya ma albishir d'in.” “Toh shi kenan na zabi fari tartar.” “Yauwa jarumi na kasan me?” “Sai kin gaya min da bakin ki sweetheart.” “Kawu daddy ya gano cewa muna soyayya, jiya da kanshi ya kira ni yace ya yaba da hankalin ka ya amince za'a yi auran mu nan ba da jimawa ba.” Mas'oud ya bude baki tare da zaro ido cike da tsantsar mamaki, ya kasa ma magana saboda yadda abin ya zo masa daga sama. “Wai kina nufin kice min min daddy da kanshi ya gano cewa soyayya muke yi?” Na gyada kai ba tare da na yi masa magana ba sai dariya nake yi. Kasan cewar a cikin office din su muke, kuma babu kowa a ciki sai kawai ya taso tare da yin juyi yana rawa ina dariya. Kusa dani na ji ya matso tamkar zai hade jikina da nashi nayi saurin rintsa ido saboda na riga na saddakar da faruwar hakan, sai naji yace. “Ina ma ace ina da wannan damar, dana nuna miki irin tsantsar farin cikin da na shiga ta hanyar baki lafiyayyan runguma. But ya zama bashi, Allah ya kai mu lokacin da zamu zama abu d'aya zan biya ki harda na yau.” Sai ya d'an matsa daga kusa da ni ya zauna akan kujerar da ya taso, sannan ne na samu damar bude idanu na. “Kin fiye jin tsoro Oum Waleed, ya kamata kuma na rage miki yawan shi.” “Ai ni wani lokacin wallahi tsoranka nake ji, dubi yanzu fa kana kokarin taba ni.” “Ban taba ba ai Oum waleedah, but soon zan yi miki abin da yafi tabawa ma.” Na share shi dan idan na biye masa tsab zai sanya ni cikin wani yanayin da ban shirya zuwan sa ba. Muka ci gaba da hira saboda zakewa harda yadda bikin zai kasance muke ta tattaunawa hankali kwance. Tun daga wannan lokacin muka sake d'in kewa ni da Mas'oud saboda ganin zamu mallaki juna. Daga ni har shi bamu taba kawowa cewar kawu daddy ba junan mu ya mallakawa ba, saboda bai fito fili ya bayyana mana cewa ga yadda yake nufi ba. Haka muka ci gaba da rayuwa lokaci yana ta tahowa, Mas'oud yana ta hada kudin da zai turo gidan mu dan nema masa aure na kamar yadda ake yi. *FADAR BASANNABAS* Tunda yai mafarkin nan yake jin jikin sa yana rawa, Tunani ne dankare a kirjin sa. Amma ya kasa samun nutsuwar yadda zai warware shi. Dafe kansa yai ya rintse idanun sa. Yana zaune a fada amma bai bada damar aiwa kowa iso ba. Jakadiya sai zarya take tana sanar masa isowar mutane. Dakyar ya bari tabawa waziri dama ya shigo, “Allah yaja zamanin sarki adali. Allah ya Kara Maka lapia da nisan kwana mai amfani ranka ya dade!” Hannu sarki Salmaan ya daga masa yana dafe da habar sa, “Allah ya tausasa ran sarki! Allah yakara maka dattako baban kowa. Shin akwai abunda ke damun Sarkin mu ne? Sanar min ko menene shi shugaba na.” Sarki Salmaan ya d’anyi murmushin jin dadi. A duk duniya waziri na cikin sahun mutanen farko da yake so. Saboda a kullum sai ya tambayi abinda ke damun sa yana kuma k’ok’arin ganin ya yaye masa matsalolin sa, “Waziri... Nayi mafarki irin na kwanaki. Menene gaskiyar al’amari?” “Allah ya karawa sarki lapia. Tabbas shakka babu zamu iya fassara hakan da cewar sharri ne na mafarki. Amma kuma idan aka auna abun a mizanin hankali za’a gano akwai kullalliya ko makircin bil adama..” “Menene mafita to...?” “Kamar dai yadda na nemo maka hayakin nan da ka yiyyi kwanaki? Yanzun ma zan koma wajen Malam din na karbo maka wani..” Kada kai SAS yayi kafin su cigaba da magana data shafi fada. Mikewa sarki yayi. Dogaran sa suka rufe shi ya wuce sashen sa jin yadda yake wani irin jiri mai gigita kwakwalwa, ga ciwon kai da yake kuma barazanar faduwa. Waziri ne ya cigaba da zaman fadar, inda ya zauna dasu Galadima, ciroma, wambai da sauran su. Ya sanar da su rashin lafiyar sarki Salman tare da umartar wani babban hadimin sa da cewar yana son ya kuma karbo masa wannan hayakin a wajan malam kamar yadda ya taba karbowa kwanaki. Galadima ya kalli ciroma suka saki wani murmushi ta cikin rawanin su, da alama wata damar ce zasu samu wajan kuma yiwa sarki Salman wani makircin. Nan dai suka nuna jimami da alhinin rashin lafiyar, amman a zukatan su ba haka abin yake ba, wata muguwar manufa ce a rasu. Ciroma da kanshi yaje ya karbo wasu kayan tsibbun wanda yake dauke da tsana mai karfi tsakanin sarki Salman da mahaifiyarsa, ganin ya fara mafarki da ita sun tabbatar zasu iya shiryawa, wanda shirin zai iya wargaza musu duk wani shiri da suka yiwa masarautar. Shi kuma tunda ya shiga daki ya kwanta yake wani irin bacci mai nauyi da ko wane irin ihu ba zai iya farkar da shi ba. ____Cikin wasu furanni masu launin shudi da rawaya yake hangenta, sanye da kaya na alfarma sai faman murmushi take yi. Shi kuma yana daga gefe zaune da jarida yana dubawa sai idanunsa suka sauka akan ta, ya dinga kallon ta yana son kuma ya gano wa take yiwa wannan fara'ar mai tsadar gaske. Ya mike cike da kasaita yana isa gurin da take sai yaga shi take yiwa dariyar, ya kuma kallon ta tare da kamo hannunta sai kawai ta shige jikinsa tana kankamewa, murya a raunane yaji tana cewa. “Nagode ya kai annurin da yake haskaka min zuciya ta, tun dazu nake nan ina jiran zuwanka.” Shafar bayanta kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Shan kamshin nan nasa yana sake sanya ta cikin begen sa, ta dago fuskarta tana kallon tashi tace. “I love you my hubby.” Sai ga Shaheedah tazo gurin, gabansa ya yi mugun bugawa, amman sai yaji Dijen ta rike shi tana cewa. “Kadena jin shakkarta saboda ita ba komai bace face azzaluma, ba ta son ka shi yasa take cin zalinka. Allah ya fita babu abin da ta isa ta yi maka ina tare da kai my hubby.” Ya samu kansa da tsayawa a gurin na ta duk da tsoran da yake tattare da shi na Shaheedah. Daga gefe ta tsaya itama tama miko masa hannu wai yaje, sai ya kalli Dije ya kuma kallon Shaheedah yana tunani yadda zai yi. Zuwan wani saurayi gurin yana kuka shine yasa Shaheedah barin gurin, Dije kuma ta kama shi suka tafi daki. Sai ya kuma jin nutsuwa yana yiwa Allah godiya da ya bashi Khadija matsayin mata abar alfahari. Sam be yi zaton a bacci yake ganin hakan ba sai sa ya farka ya ganshi a tsakiyar gadon sa yana juye-juye a kai. Tabbas yaji a jikinsa Khadija itace zabin zuciyar shi, dole ne ya ci gaba da farautar neman auran ta koda kuwa yin auran zai janyo abubuwa da dama a cikin masarautar. Sai da ya yi wanka ya shirya sannan ya nemo amintaccen bafadensa wato Al-hassan, suka kebe yace masa yana son a ci gaba da shirye-shiryen auran sa kamar yadda suka fara. Ya amsa sannan ya sake komawa wajan Alhaji Isma'il wanda ya tabbatar da cewar zai je dangin mahaifin Khadija ya sanar dasu, idan yaso yana dawowa sai ya sanar da a shirya daurin auran. Haka kuwa aka yi Alhaji Isma'il be sanar da su Mami zai je ba, sai shiryawa ya yi da shatara ta arzikinsa ya je ya sanar dasu komai, suma dai be gaya musu wanda zata aura ba, ya ce musu dai ya amince da tarbiyar yaron dan gidan mutunci ne iyayensa masu daraja ne. Suka amince tare da bashi ragamar aurar da Khadija, a cewar su ai shine uwa da uba na ta dan haka babu wani abu da zasu ce sai fatan Alkairi a cikin auran. Bayan ya dawo ne yake sanar da Mami cewa yaje can sun gama komai sannan ya kira yan uwansa suma ya gaya musu sunce idan lokacin yazo yasu bar komai su zo ayi dasu. Bata damu ba dan bata yi zatan wani mai daraja za'a aurawa Khadijan ba. Tunda aka fara wannan abun Dije da Mas'oud basu yi zaton ba junan su zasu aura ba, basu zaci hangen da kawu daddy ya yi ba akan su yake ba, sai da abin yazo gab har ana sauran sati daya biki sannan ne yace da Dije zai kuma yin magana da ita idan ya gama komai. Kasan cewar da yamma ne ta gaya mata kuma Jumma'a ce yana ganawa da mutane yan kasuwa, shi yasa ta bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu. °°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°° *WASHE-GARI* Tunda Kawu daddy yace zamu yi magana daren ranar ban runtsa ba har wayewar gari. Kasan cewar asabar ce, Ina malale akan gado gaba na sai dukan uku-uku yake. Shin akan me zamu tattauna? Nasan tabbas lefi nayi. Kuma duk yadda akai akan bana bari TK ya dakko ni wani lokacin idan na fita. Ko kuma su Mami ne suka qulla min qullalliya a gurinsa? Ko kuma zancen iyayen Mas'oud zai min kila yace nace ya turo. Ganin sha biyu ta kusa ban ci abincin safe ba hakan yasa na diro daga gado ina mika, Band’aki na shige nayo wanka na canza kaya cikin doguwar rigar A line marar shape. Na taje kai na dakyar saboda inayi yana zamewa saboda santsi da cikar sa, Na d’aure da ribbon. Dauri me sauki nayi na shafa man baki na sauka kasa. A dinning area na tarar da Mami dasu Ya Shukrah suna cin abinci suna hira. “Mami ina kwana..? An tashi lapia.” “Lapia lou..” Ta bani amsa a tak’aice tana mai cigaba da kurbar tea dinta. “Ya Shukra ina kwana? Ya Hameeda ina kwana.” Kowannen su ya amsa babu yabo babu fallasa. Ganin haka na mike na daddebi abinda zan ci a plate na koma k’arshen parlorn nakeci acan. Sai bayan na kammala ina zaune ina karanta wani book na wajen aiki sai ga Kawu daddy yafito. Sanye cikin jallabiya. “Kawu daddy...Barka da safiya Kawu daddy! An tashi lapia?” “Alhamdulillah Khadija.. Muje ko?” “Toh Kawu..” Su Mami suka bimu da kallo, Yana gaba ina biye da shi ya shiga parlorn sa ya zauna akan babbar kujera ni kuma na tsakure a gefe, “Hau kujera ki zauna mana.” “Nan ya isa Kawu....” Gyaran murya yai. Ya rage volume din CNN dake faman yi, “Kafin dai mu fara magana ina son tabbatarwa kai na Kamar yadda kika sani, wannan maganar da muka yi dake a baya na aure ita ce ta kuma tasowa. Amman Shin ki na da saurayi ne dake zuwa neman ki gidan nan? Kai bama wannan ba. Akwai wanda ya taba yi miki zancen aure? Dan ni dai nasan da akwai zan sani ko kuwa..? Dan naje munyi magana da dangin mahaifinki, sun kuma bar min komai a hannuna cewar na yi komai da komai a game da auranki.” Wani daskararren abu naji ya tokare min a wuya. Shin menene yake shirin faruwa dani.? Ko wani sharrin aka kullamin? “Magana nake miki Khadija kin yi shiru...” “Kawu daddy.. Ba.. babu!” Na samu kai na da bashi amsa haka! Kawu daddy ya sake yin shiru na dan wani lokacin kafin yace, “Tun wannan dai wanda nazo nace miki na yaba da hankali da tunaninsa, gashi kai tsaye ni ya nema kinga kenan da gaske yake yi ko?” Sake samun Kai na nayi da kada kai. To me zance? Shi kansa Mas’oud din yana namiji ya boye alakar mu bare ni Mace? “Toh shikenan! Alhamdulillah tunda babu wata magana tsakanin ku da wani. Kinsan babu kyau neman aure akan aure. Wannan yaro me hankali da dattako ne, ya fito daga gidan mutunci. Yana neman auren ki.. Kuma azahirin gaskia ma nace na bashi. Saboda ko da kina da wanda kike so din a matsayina na mahaifi agare ki. Babu wanda ya zo ya same ni. Manya basu shigo ciki ba, Dama already blood sample/genotype dinki sunyi kyau. Kowa zaki iya aura, Kuma Khadija...” Ai bai karasa magana ba na fashe da kuka, Me yasa su Ya shukra da Hameeda su ba za’ai musu auren ba sai ni? Okay! saboda ni ba yar gidan bace ba ko kuwa? Ko dan banda gata ne? Tsana ce wannan kome? Wayyo Allah na ni Khadija..Ashe daman ba Mas'oud aka zaba min ba? Kuka Sosai nake yi ina rike kai na. Duk duniya babu d'a namijin da nake so, gangar jiki na keson mallaka irin Mas'oud ba. Ina son Mas’oud saboda shine first love dina. Ina son Mas’oud saboda shi ya koya min so har nasan menene so? Ina son Mas’oud saboda shi ya rai ni zucia ta ya koya mata abinda take so. Ina son Mas’oud saboda yana so na so mai wuyar fassarawa. “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un...” Shi naketa nanatawa a fili ina bubbuga kai na ajikin kujera, Kawu daddy ya sauke zuciya ina jiyo sautin ta, “Kiyi hak’uri Khadija. Na rantse da Allah ban amince da aura miki shi ba don na cuce ki. Wallahil azim ba zan kai ki inda zaki wahala ba don na lalata miki rayuwa ba Khadija. Wallahi Khadija wannan auren ni inaji ajiki na alkhairi ne a gareki damu gabaki d'aya. Saboda Ina ji ajiki na nan gaba zaki ya ba min wannan rana..” Kuka nake sosai shabe shabe ina fyace majina da kasan dankwali na. “Kawu Mas'oud fa.. Mas’oud Kawu! Ina son Mas’oud.” “Wanene haka kuma Khadija.?” “Kawu shine wanda ya ke sona. Tun service dina muke tare Kawu daddy. Munyi alk’awarin aure dashi wallahi Kawu daddy..” “Khadija me yasa be zo ya same ni da zancen ba? Akalla kafin ya fara neman ki sai ya nemi yarjewa ta kamar yadda wannan ya yi. Amman Me yasa bai turo Manya sunzo ba idan har da gaske yake yi Eh?” Shiru nayi ina ajiyar zuciya. “Yace ne.. Ko wansa bai yi aure ba kuma shine karami. Sannan bai gama ginin sa ba..” “Sai Yaushe kenan zai fadawa manyan ki Uhm!? Ko kuwa zama za kiyi tayi kina jiran sa kina faman tsufa agida? Shi kuma yana bata miki lokaci? Daga karshe ma yazo yace miki an hada shi aure da yar uwar sa! Uhm? Shikenan tunda baki dauke ni amatsayin uba ba Khadija. Na ky’ale ki sa..” Riko kafafun sa nayi ina Kuka, Ni din banza zan ki amincewa da maganar Kawu daddy? Mutumin da ya mayemin gurbin uwa da uba? Halacci d’aya zanyi shine na amince. Ba Wai don ina son wanda za’a daura min aure dashi ba. Kawai dai saboda Kawu daddy ne. A duniya banida mafiyin sa idan ka tsame sauran yayyun Umma ta. “Bar Kuka Khadija.. Na kyaleki wallahi. Zan ku..” “Na amince Kawu daddy.. Na amince wayyo Allah karkai fushi dani.” “Allah ubangiji ya miki albarka. Ya biya miki bukatun ki na alkhairi, Allah yasa wannan auren ya zamo wanzuwar farin cikin ki, Yasa ki zama wata aba a rayuwa, Allah yasa ayi a sa’a. Nan da sati d’aya wato mai kamawa za’ayi in Shaa Allah!..” Kasa magana nayi, Ni wallahi ji nake tamkar bacci nake yi. Gaba d’aya bana gane me kawun yake fada. Na sandai nace na amince amma gaba d’aya wani dishi dishi ma nake gani. Zucia ya da idanu na Mas’oud kawai suke nuna min, Sanye cikin kananun kaya yana rataye da ID card dinsa na wajen aiki. Cikin haka Mami ta banko kofa ta shigo, “Meye haka ne? Koke-koken me aketayi ne uhm? Tun daga karamin parlor nake juyowa, Me akai ne?” Tana magana tana sakace hakorin ta da toothpick. “Babu komai ya akai..?” Kawu daddy ya tambayeta yana duban ta da kyau . “Koke koken da muketa jiyowa ne shysa na shigo ganin Lapia? Kar ma’kota su fara lek’owa suna tambaya.” “Lapia Alhamdulillah Hajia. Ba kukan wani abun bane na farin ciki ne.” “Toh faa! Tooo” Mami tace hakan tana mai zama a gefen sa. “Tashi kije Khadija. Allah ya miki albarka Khadija!” “Aamin Kawu daddy..” Mikewa nai dakyar ina tafiya. Ina jiyo mami nata tambayar sa menene? “Wai meke faruwa ne alhaji. Alkhairin menene?” “Hajia.. aure ne! Wani bawan Allah ne ke neman auren ta ya biyo ta kai na.” “Aure..” Mami tafada tana dafe da kirjin ta, Ni kuwa sauri nayi Na fita na jawo musu kofar. Ina fita na haye sama ina mai bude sabon shafin wani kukan. Mami ta muskuta kusa da Kawu daddy, “Alhaji bangane me kunnuwa na suke jiye min ba, aure? Aure fa kace? Waye zai auri wa?” “Hajjaju da hausa fa nake miki magana. Nace neman auren ta akazo waje na.” “Au ashe da saninta ma shine take kukan munafurci kuma?” “A’a Hajia wanda takeso daban. Wanda kuma yai tambaya daban.” “Toh fa! Alhaji Kai wa ka bata kenan..?” “Wanda ya fara magana mana.” “Shi din wanene shi! Wai ka na nufin bada masaniyar ta ka bayar da auren nata ba? “ “Eh ban isa bane? Ni ba mahaifin ta bane.?” Yatsina fuska Hajia Abeeda tayi tana sosa idon ta, “Toh shi wannan Waye manemin kenan? Dan wanene?” “Wallahi wani bawan Allah ne kawai nutsatstse ya kwanta min arai kuma.” “Ya'yan abokan ka Wai..?” “Ko d’aya wallahi.. wani ne daban. Marainiya ce gwara na aurar da ita hankali na yafi kwanciya.” “Dankari Makari.. Ai shikenan! Toh su Shukra Alhaji ka nemo musu mana acikin yaran abokanan ka. Ko Yayan commissioners dinnan da kukayi makarnta.” “Ai nagaya miki inde sai dan wane da wane zaki bari su aura ni babu ruwana na tsame hannu na, Muyi ta zama ana k’irga mana shekaru tare.” “Wai dan anbiyo takan ka ance anason Dije? Tab Alhaji ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, Dai dai ruwa dai dai tsaki. Su ana ganin kai ne mahaifin su babu kasakantaccen da zai biyo takan ka yace yana neman auren su.. “ Dr. Ismael yayi daria yana kurbar ruwan hannun sa, Yasan halin matar sa sarai, Shi yasa bazai taba gaya mata gidan da dije Zata shiga ba sai an daura aure ko kuma an kawo kayan aure abu ya kusan tabbata. Yasan kuma Zata titsiye Dijen da tambaya shiysa bai sanarwa Dijen bama, Duk ya tattara ya rufe su a fai-fai. Mami ta jima tana neman bugar cikin Dr. ismael don jin waye? amma tsabar zurfin ciki irin nasa duk nacinta haka ta hakura bataji Waye manemin na dije ba. Data dame shi ma sai ya rufe fuskar sa da jarida wai kansa ciwo yake. Tashi Tai ta fice ta kyale shi. “Mami ya akai kuma..?” “Kukan me take Mami.?” Shukra da Hameeda suka tasata a gaba da tambaya ganinta fito daga wajen Dr. Ismael “Hmm! Makira algunguma aure Zata yi fa..” “Aure! Wa Zata aura Mami..?” Hameeda ta tambaya tana raba idanuwa. “Ba dai Mas’oud ba?”Shukrah ma ta tambayi Mami tana dafe kirji. “Waye Mas’oud kuma? Du basu bane. Wani ne daban yazo neman auren ta. Shine take wannan kukan batasan wanene ba..” “Kuma Daddy ya yadda?” “Kwarai kuwa.. Yace ma afara shiri sabon sati me kamawa zaayi bikin.” Hameeda ta tabe baki, “Allah ya raka taki gona..” Shukra ma jin ba Mas’oud bane sai ta samu kanta cikin jin dadi, “Masha Allah! Allah ya kai mu.” Harara Mami ta dankara mata. Tanemi waje ta zauna, “Gwara kuma ku fito da mazajen aure...” “Soon In Shaa Allah!” Cewar Shukra tana murmushi. Hameeda khma ta shiga raba idanuwa. Haka dai suka tasa zancen auren agaba sunata ta kwashewa dije albarka. Musanman Mami dake bakin cikin auren dw zatai. Amma Idan ta tuno kila ba auren jin dadi bane sai ta shiga murmushi kuma tana k’ada k’afa. Ni kuwa inacan d’aki ina kuka. Ba kalar wanda ban ba. Kai har karamin hauka sai da nayi. Naita buga kai na ajikin bango duk ya daddauje. Naita bori. Ina tunanin ko hada kayana zanyi na gudu ne yadda ake a film. Wata zuciar tace bakisan halacci ba. Dole nayi hak’uri zuciya mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri . Kawu daddy ya zamar min uba ya zamarmin uwa. Shine gatana. Yana gatantani fiye da tunani. Me yasa zan bijirewa abinda yake so ya kuma nuna isa akan sa? Wacece Ni? Dole na hakura. Illa dai koma wanene ya yankemin buri na na auren Mas’oud saiga rayuwa. Wallahi sai ya bambancewa aya zakinta na shiga hurumin soyayya da yayi. Ina ruwan sa? Lallai ni na hadu da sharrin late comer mai datse farin cikin zukatan masoya biyu . Bansan ka ba, Dan jaraba da kalata kace ni kakeson aura? Wannan wacce irin bahaguwar kaddara ce? Wata zuciar tace taki kaddarar kenan Khadija. Zaki shiga wata ukubar rayuwar kenan ta uku. Na bigi wajen kirjin nawa inda zuciar take tamkar dai zaucacciya. Ni kadai nace ah k’arya kike wallahi sai dai shi ya shiga uqubar rayuwa. Ba shine ya ce yaji ya gani yana so ba? Ai kuwa zai San ya tafka babban kuskure. Mas’oud sai kira na yake na kasa dauka. To me zance masa? Koma menene shi ya janyo mana wallahi. Ni dai ranar gaba d’aya haka na yita rabi kuka rabi zancen zuci, rabi magana ni kadai. Wani lokacin kuma na bubbuga kai na a jikin gado. Wayata kuwa daga karshe kashe ta ma nayi gaba d’aya. Oh ni dije. Wai ni za’aiwa auren dole da wanda bansani ba? Kuma cikin wata d’aya jal aka gama komi. Nashiga uku sau dubu uku. Haka nayita sallolin nafila ina wa Allah kuka a sujjada kan ya tarwatsa wannan auren da za'a yi min koda kuwa anzo daurawa ne...... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥. www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *2__0* Sallah ce kawai take ta dani, bayan ita kam babu abinda nake yi banda kukan zuci. Duk tunani na yana kan wanda ake shirin aura min, ban san shi ba, idan ma na san shi to ya boye min tunda ni har yanzu ba wanda ya taba tunkarata fa maganar aure. Mas'oud shine wanda rai da zuciya ta suka amincewa, shi kuma gashi ya yi sanya har an bawa wani ba shi ba. Wayyo Allah na ina cikin kaddarorin rayuwa mabanbanta, marasa kamaceceniya ta ko wace fuska. Su Mami kuwa babu wanda ya zo yaji kukan da nake yi, sai dai na jiyo dariyar su wacce bana raba d'ayan biyu magana ta suke yi. Har dare ban kuma saka wani abu cikin baki na ba, sam na dena jin yinwa saboda rashin nutsuwar zuciya. Ina idar da sallah isha'i nabi lafiyar gado ina share hawaye. Da kyar na dakko waya ta na kunna tare da jonawa jikin charge, nan naga messages d'in Mas'oud yana ta tambayar lafiya naki dauka, ko bani da lafiya, dan Allah in yi masa reply ko zai ji dadi. Duk na karanta amman naki masa reply d'in sanda bashi da wani amfani, ya riga ya gama da rayuwar mu gabaki d'aya tunda shine ya yi ta jan lokaci, da yazo ya fada ai da duk an san tsakanin mu, amman ya dinga cewa zai zo, zai aiko, gashi nan lokaci ya k'ure mana a sanda mukafi buk'atar kadancewa da juna. Ina ji kirji na yana zafi nasan na yunwa ne amman naki zuwa naci abinci saboda har lokacin bana sha'awar cin komai. Gashi babu mai lallashi na bare a tilasta min ko ruwan shayi nasha, haka na kwanta har gari ya waye banci ba. Koda na tashi da asuba da kyar nayi sallah, jiki na naji yana ta min wani irin ciwo kamar an sassara ni haka na dinga ji. Da yake weekend ne sunday sai na koma kan gado na kwanta, zazzabi ya rufe ni. Allah ya taimake ni da aka fito breakfast kawu daddy yaga bana gurin sai be yi magana ba ya tashi tsam ya nufi dakin da nake. Yana shiga ya tarar da ni cikin blanket, ya dinga kiran suna na amman na kasa Kwakwkwaran motsi, sai yasa hannunsa a goshi na yaji zau kamar garwashi, cikin tashin hankali yake magana. “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun, Khadija baki da lafiya haka? Me yake damunki?” Jin da ya yi bana iya cewa komai yasa shi kiran su Mami da karfi, sai gasu kuwa da gudu suna tambaya daddy lafiya? “Bata da lafiya naji jikinta akwai zafi. Abin da yasa na kira ku ke Hameedah kizo ki bata taimakon farko da ya dace.” “Okay daddy.” Tayi maganar tana taba jikina, tace za'a yi min allura sai ta saka min drip yadda zan ji dad'in jikina. Haka kuwa aka yi ta min allurar ta kuma sanya min drip a daidai wannan lokacin ne Mas'oud ya kira waya ta, Shukrah ta dauka, ganin sunan Mas'oud yasa ta tashi ta fita. Duk da ina cikin wani yanayi hakan da ta yi sai da ya sanya ni cikin faduwar gaba dan ban san abin da zata gaya masa ba. A can parlor kuma Shukrah guri ta samu ta zauna tare da kara wayar a kunne kai kace ita aka kira. Cikin kashe murya da kisisina ta shiga yi masa magana. “Assalamu alaikum.” “Amin wa'alaikis salam, dan Allah bata kusa ne.?” “Eh... A'a.” “Ban fahimta ba.” Mas'oud ya tambaya cikin rashin fahimtar abin da take nufi.” “Wai kana nufin bata sanar da kai abin da yake faruwa ba? Idan kuwa haka ne Dije taci amanarka, har kai zata boyewa.” “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun. Idan har na fahimce ki dai dai, kina son gaya min cewa akwai abinda ya kamata na sani a gurin ta amman taki gaya min ko?” Sai da ta yi farrrr da kwayar idanunta sannan ta gyara zama tace. “Kwarai ma kuwa, ba abin wasa bane dan yana da kyau ka sani tunda naga kamar kun zama aminai.” “Toh dan Allah ki had'a ni da ita muyi magana please sister Shukrah.” Tayi mamakin yadda ya gane cewa itace, sai dai ranta ya d'an so su da taji ya damu da jin Dije, amman ba bu yadda ta iya dole da d'an daure da kishi tace. “Yanzu kam ba zata iya daga waya ba, sai dai idan anjima kila idan taga dama.” “Shikenan Shukrah na gode sai anjima.” Be kuma jiran cewar ta ba kawai ya katse zuciyar shi ta shiga cikin tunanin abin da yake faruwa. Shi sai yasan babu abin da ya had'a shi da Khadija na rashin jituwa. Amman wane irin abu ne Shukrah tace ana boye masa? Dole yana son jin koma menene, kuma daga bakin Dije dan ita zata warware masa kullewar da kansa ya yi. A ranar shi kansa da kyar ya gudanar da wasu al'amura sa, still kuma ya ci gaba da kiran ta amman a kashe, hakan ya sake tayar masa da hankali har ya fara shirin zuwa gidan na su. Tsab Mas'oud ya shirya cikin manyan kaya shadda ruwan kasa wacce aka yi masa gajeren d'inki, sunyi masa kyau ya dora hula wacce ta dace da kayan jikin nasa ya dauki turare ya dora tare da jan mukullin motar sa ya fito. Addu'a kawai yake yi Allah yasa yaje yaji alkairi daga bakin Khadija, yana jin zuciyar shi tana karfafa masa gwiwa wajan samun nasara akan duk abin da zai zo bakin ta, bai taba kawowa rabuwa zasu yi ba dan yana da yakinin aure a tsakanin su. Ya yi horn mai gadi ya leko, ganin shi yasa ya bude ba tare da wani shakku ba. Wajan motar da ake kai ta gurin aiki ya aje tashi, tare da dakko wayarsa ya kuma kiran ta, cikin sa'a kuwa tana zaune kan sallaya taga sunan shi ta dauka ba tare da tace komai ba. “Ki daure ki fito ina compound d'in ku.” Duk da irin dauriyar da take janyowa hakan be haka muryar ta yin rawa ba, taja majina waje silar kukan da tayi ne ya sakar mata da tsinkakkiyar majina marar kauri tace. “Me zan fito nayi maka bayan ka riga ka tarwatsa mana duk wata dama da muke da ita?” “Bana gane abin da kike nufi shi yasa nazo kafa da kafa dan na ganki. Dan Allah ki daure kizo muyi magana ta fahimta.” Kamar karna je haka nake ji, amman kuma zuciya ta tana son ganin shi a zahiri dan na kalli yadda zai dauki maganar. Katsewa nayi dama da hijab a jikina na tashi da kyar na fito, babu kowa a parlorn sai na fita kai na tsaye ba tare da na sanar da Mami ba. Tsaye na ganshi gurin motar shi yana latsa waya, yadda naga ya kuma yin kyau ne ya sake ruda ni, kamar nayi shekara ban ganshi ba haka naji. Na daure na karasa har wajan sannan na tsaya ban kula shi ba saboda haushin sa da nake ji. “Da alamu nayi babban laifi da har na cancanci irin wannan horan ko Oum Waleed? Kin san yadda rashin daga wayar ki yasa hankali na ta shi? Wallahi tun jiya na kasa cin abin cin arziki saboda tunanin abinda ya hanaki daukar wayata. Shin me nayi miki sweetheart?” Naja wani gauran numfashi mai radadi a zuciya, hawaye suka zubo min nasa hannu da sauri na share dan bana son dogon zancen da zai min, nace dashi. “Yaushe ne zaka zo gidan nan kace kai ne wanda zaka aure ni?” Ya kalle ni tare da cewa, “Na yi miki alkawari nan da karshen wata uncle's dina zasu zo gidan nan nemar min aurenki harda saka rana.” Wata kwallar bakin ciki ta sake sakkowa kan kumatu na, naja kukan da yake tahowa na hadiya ina kallon kasa nace. “Nayi zaton zaka ce gobe da sassafe, ashe har yanzu jinkirin a gurin ka yake. Ban san me zan ce maka ba, sai dai kawai nasan kai ne ka janyo muka rasa junan mu Mas'oud.” “Ban fahimta ba Oum Waleedah, ta ya muka rasa juna bayan duk gamu a raye muna numfashi.?” Na yi saurin cewa. “Numfashi marar amfani ba, ta iya yiwuwa kai a gurin ka kana yin mai amfani, sabanin ni da zan shiga gidan mutumin da ban san ko waye ba, ta ya za kai kace ni ina numfashi? Ka wahalar dani Mas'oud, ka koyar dani darasi mai matukar wahalar da zuciya. Bana tunanin zan san meye jin dadi da yanci a cikin rayuwa ta, zanje na rayu da wani ba kai ba Mas'oud, kana ji kana gani za'a kai ni inda bana so. Dan Allah Mas'oud ka rufa min asiri kar na rasaka please ka ceci rayuwa ta saboda da kai ta fara soyayya....” Cak numfashin sa ya tsaya na dan wani lokaci, baki bude yake kallo na cikin zare ido da alama yaji maganar ne cikin tsakiyar kansa. Ya matso dap dani har ina iya jiyo bugun da zuciyar shi take yi da karfi sannan kuma cikin sauri. Kamar zai rike ni haka ya soma yi yana magana a daddaburce hankali a tashe. “Dan Allah idan mafarki nake yi wanda yake kusa dani ta yi gaggawar tayar dani. Wallahi tunda nake ban taba yin mummunan mafarki ba irin wannan.” Cikin kuka murya a dashe nace dashi. “Ba mafarki kake yi ba da gaske ne wannan maganar da nake maka. Sai dai nima ina fatan kawu daddy ya dawo yace min da wasa yake yi a yau din nan.” “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun na shiga uku ni Mas'oud wannan wace irin mummunar kaddara ce? Oum Waleed dan Allah karki bari a rabu mu, wallahi ina sonki. Gobe zan turo uncle's d'ina ayi maganar koda basu taho da kudin ba, su san da zaman mu ni dake kar su rabu mu dan girman Allah.” Yadda yake magana a gigice shine ya sake tayar min da hankali na tabbatar da idan bamu yi da gaske ba komai zai iya faruwa. Kamar na juya na tafi saboda naga shima ya fara zubar da hawaye, sai dai na juyo ba tare da na bari mun had'a ido ba nace masa. “A wannan gabar bani da ta cewa Mas'oud, sai dai ina fatan zaka yi duk yadda zakai wajan karkato da zuciyar kawu daddy har ya amince da auran mu. A shirye nake tsab da idan ya kuma tuntuba ta da maganar ka zan amsa dan kar na cuci kai na, amman fa ni bazan iya zuwa yanzu nace dashi ba zan auri wanda ya bani ba, saboda yadda baka cancanci wulakanci a guri na ba, haka ma kawu daddy be cancanci tozarci daga gare ni ba. Dama tuntuni damar tana hannunka, yanzu ma tana hannunka sai ka nema mana mafita.” Ina gama magana na ruga gida da gudu ina wani sabon kukan wanda yafi na farko zafi da radadi. Ban san yadda ya kare ba a compound, sai dai wajan karfe goma naji kawu daddy ya shigo yana yiwa Mami magana. “Ikon Allah, yaran zamani sai addu'a kawai.” “Alhaji me kuma aka yi maka? Ko samari ne ka hadu da su akan titi marasa kunya.” Yana kokarin zana ne yake cewa. “A a babu ko d'aya daga ciki. Yaron nan ne Mas'oud abokin aikin Khadija. Ina jin ko labarin auran ta yaji yanzu shine ya kawo kanshi wai shi da ita sun dade suna soyayya tare da burin yin aure, wai yana ta shirin turo manyan sa sai yaki ance an bayar da ita. Shine nace da me ya hana shi bayyanawa tuntuni sai yanzu?” Jin maganar aure na ne yasa Mami sauya fuska, can kuma sai ta ce tana zuba mishi juice a glass cup. “Kaima Alhaji har yanzu ka ki gaya mana waye wanda zaka aura mata. Ni ban taba ganin inda aka yi wannan abin ba, ko dan bani na haifi Dijen ba shi yasa ake ta boye min shi?” “Ko daya wallahi Hajiya, abin da yasa ban fada ba shi angon ne ya roki arzikin dan Allah karna fada sai ranar auran. Kinji dalilin da yasa ko ita Khadijan ban gaya mata waye ba.” “Ai shikenan, idan ta fashe ma gani ai.” “Zaku gani kam insha Allahu. Yaron ma na bashi hakuri nace ya yi hakuri aure nan da rana ita yau za'a daura shi da ikon Allah.” “Uhmm Alhaji kenan, kana bani mamaki tun zuwan yarinyar nan gidan nan, komai na ta baka nuna min shi kai tsaye sai ka yi kwana kwana. Amman ba komai lokaci ne tunda gashi ta kusa tafiya nata gidan.” “Ki dena yi min fassara akan komai Hajiya. Yarinyar nan marainiya ce kin kuma san yadda Allah ya bayar da amanar rikon maraya. Dan Allah ki tayani faranta mata har zuwa ranar da ya rage mata a cikin gidan nan.” Tamkar ya yi da gunki ta yi masa banza hakan ya kara tabbatar masa da cewa idan ya gaya mata wanda Dije zata aura akwai rashin hankali. Sai ya kuma jan bakinsa ya yi shiru be sake cewa komai ba har lokacin kwanciya ya yi ya tafi daki. Ni kuwa tunda naji yace ya bawa Mas'oud hakuri na koma gefe naci gaba da kuka na wanda babu mai lallashi. *MASARAUTAR BASANNABAS* (Sarki Salman Aliyu Salman SAS) Kafin kace wani abu tuni sarki Salman ya kuma susucewa akan son auran Dije, sarautar ta kuma fita daga cikin zuciyar shi ta yadda ko sunan sarki baya son yaji an ambata masa. Duk da ya rage sauran sati daya a daura auran sa, ga kuma ta fiyar da aka ce zai yi zuwa Cyprus, kuma babu wanda za a fasa indai yana da rai da kuma lafiya a jikin shi. Komai dama da ya dace ango ya yiwa amarya, Sarki Salman ya bawa Alhaji Isma'il kudadenda za'a siya. Shi kuma ya kai wa wata mata kwangilar hadowa ba tare da ya sanar da ita ko na meye ba, daman ita aikin ta kenan, duk abinda mutum yake bukata a had'a masa na aure ko na gida tana yi a biya ta. Yana zaune a cikin fada yama rasa abin yi saboda Sam baya cikin hayyacin shi, ya jiyo muryar Ciroma yana gyaran murya yana cewa. “Allah ya taimake, rana ita yau shine ranar da zaka je taron nan, an shirya maka komai sai fatan zuwa da dawowarka kawai, Allah ya kara maka lafiya.” .._Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji shiru, Shekaran jia akai discharging. Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima.._ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *2___1* Samun kansa ya yi da jinjina kai alamar yaji sai dai tunanin sa yana ga yadda za'a daura aure baya garin sai kace na asiri. Amman kwarin gwiwar da jarumar zuciyar shi take bashi shine ya sanya shi jingine fargabar tashi da take neman ruguza masa lissafi. *KHADIJA (DIJE)....* Tun daga ranar da kawu daddy ya sanar dani ranar aure na ban sake fita ko nan da compound ba, ma'ana tun ranar da Mas'oud yazo naje gurin shi. Shi kuwa tun yana kira na ina kin dagawa har ya hakura sai dai ya kira Shukrah da ya karbi lambar ta dan ya dinga jin bayani game da ni. Hankali na be sake tashi ba sai ana sauran kwanaki uku kawu daddy ya kira ni wai za a kawo kayan lefe, a gabansa nace to, amman a raina fata nake Allah yasa motar masu kawowar tayi hatsari duk su mutu kowa ma ya huta. Mami kiri kiri tace ba za a soya komai ba dan tasan suma masu kawo kayan zasu kwallafa rai da cin kaji, dan haka tace yadda suka zo da tuwo a cikin su, nan d'in ma tuwon za a yi musu dan shi suka saba ci, harda cewa su kila na dawa da masara suke ci nan kuma na shinkafa za'a yi musu miyar taushe tasan sai sunyi murna a yau. Ni dai ban yi magana ba saboda ko a jikina idan ma tace tuwon karfe za ai musu bana jin zai dameni saboda nima ba san ganin su nake yi ba. Shiryawa nayi tsab na bar gidan saboda nasan ko sun zo sai Mami ta wulakantani a gaban su, nasa Tukur ya kai ni gidan su Aisha, ina shiga ta fara murnar gani na muka shiga dakin ta, kamar jira ni kuma nake yi kawai na kwanta kan gadon ta na fara kuka mai taba zuciya. “Ahh kawata menene haka da girmanki? Haba kuka sai kace wata yar karamar yarinya.” Still na sake fashewa da kukan ta dinga shafa baya na cikin nuna kulawa. Tunda aka fara wannan maganar auran ban samu wannan gatan ba na lallashi sai yau kuma a yanzu da Aisha take ta tausar min da zuciya tun kafin ma taji abinda nake yiwa kukan. Sai da nayi mai isa ta sannan na sanar da ita abinda duk ya ke faruwa, ta tausaya min kwarai da gaske sannan ta bani shawara akan na daure na karbi zabin daddy koda kuwa ace mijin gurgu ne ko makaho na daure na zauna dashi kodan farin cikin kawu daddy. Ya zan yi? Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun dole na karbi wannan auran ko ta halin ya ya ne, gaskiyar Aisha ne ya yi min abinda ko iyayen da suka kawo ni duniya basu min ba. Ashe kuwa idan hakane ya cancanci fiye da wannan sadaukarwarma a gareni, dan idan nace zan bijire ni kaina bazan taɓa yafema kaina ba har randa numfashina zaibar gangar jikina. Haka na zauna a gidan su Aisha tana ta lallashi da ban hakuri tare da bani labarai makamanta irin wannan auran da za ai min, da kuma shawarwari masu ƙyau da amfani.          Jinai zuciyata ta rage nauyin datai min sosai, na kuma samu y'ar nutsuwa duk da banajin son auren har yanzu. Haka na shiga sauke ajiyar zuciya ina sake godema Allah akan k'addarorina da suke zuwa gareni daki-daki. Ina fata da addu'ar zama cikin mutane masu hak'uri da cin ribar hak'urin koda ba'anan gidan duniya ba. *DR ISMA’ELA RESIDENCE....* Saboda tsabar wulakanci irin na su Mami ko malmala bata sa an yiwa tuwon ba, haka tace su juye a kula wai sa dinga zabtara. Wajan ƙarfe hudu kuwa akai horn mai gadi ya bude motoci tsala-tsala suka shigo harabar gidan. Tasama su Ya Shukrah suke leken su, hakan yayi da-dai da fara fitowar mutanan motocin.      Abin daure kan ashe su uncle Hashim ne da iyalansa sai uncle Kabiru shima da nasa family d'in duk sun zo biki, nan da nan su Ya Waleedah suka sakko da gudu suna musu oyoyo cike da murnar ganinsu. “Ya akai babu labari Meenal?” “Eh cewa akai karmu fada idan muka gaya muku ba za a zo da mu ba.” “Ina amaryar take?” “Ku shiga ciki mana kun tsaya anan zai zance kuke yi." Cewar Uncle Kabiru yana rufe mota. Duk sai suka runtuma ciki suna murnar ganin junan su. A parlorn kasa iyayen suka zauna inda Mami ta fito gurin su. Suna ta hira sai ga Alhaji Isma'il ya sanar dasu cewa an fasa kawo kayan lefe sai ranar daurin aure za a hado da su, Mami ranta ya baci dan taso wulakanta duk wanda ya yi kuskuren biyo masu kawowa sai aka samu aka si. Baki kuwa sai sabon abin ci aka yi musu dan duk cewa suka yi ba zasu ci tuwo ba, kawu Hashim ne kawai yaci saboda shi yana son tuwo sosai. Ni kuwa ban koma ba sai da aka yi isha'i sannan Aisha ta rako ni har mota Tukur ya dawo dani gidan gabana yana faduwa wani dum... Dum... Dum.. Na shiga cikin parlorn jiki na a sanyaye kamar wace ba ta da laka.. “Oyo yo ga amarya ta dawo.” Naji sautin muryoyi daban daban, duk a zato na fa yan kawo lefe ne basu zo da wuri ba har suka kai wannan lokacin. Sai da na dago kai na sosai na kallesu sannan na fahimci ko su waye, cikin farin ciki nima na rungume su tare da sakin kuka dan na tabbatar suma daurin aure na suka zo. Na gaida su suna ta lallashi na sun dauka na dadewa ban gansu bane dan kawu Hashim har da cewa. “Last month wallahi naso zuwa na dauke ki, muje kiyi mana ku sati daya ne Allah be yi ba sai yanzu. Kiyi hakuri Khadija ki bar kuka Allah ya ji kan iyayen ki da rahama.” A hankali na ce. “Amin.” Daga nan suka bani kayan da aka dinko min daga can Lagos wanda zan yi fitar biki dasu, kawu daddy ya sanar min cewa an fasa kawo min lefe sai ranar daurin aure. Naji dadi sosai saboda har lokacin banji cewar zan auri wani ba Mas'oud ba, abin da kamar wahala duk da cewa bana daukar kiran da yake yi min dan gujewa fadawa fushin ubangiji. Zuwan su Meenal dasu Badiyya yaran uncle Kabiru da na uncle Hashim yasa na dan rage zaman yin kuka, dole suka sani a gaba da hira da kuma tursasani wajan cin abinci, wai kar naje gidan miji ina da ulcer a yi tunanin ba'a bani abinci a gidan mu. A ranar kam alhamdulillahi na d'an yi bacci, sai dai duk na riga su farkawa, nayi sallah na zauna ina nemarwa kai na sauki a gurin Allah madaukakin sarki. Bani da buri yanzu irin naga wannan zakwakurin da yazo ya rushe min duk wani farin ciki na, yasa na tsani komai na rayuwa a lokaci daya. Su kuwa sun dade basu farka ba dan babu irin tashin da ban yi musu ba amman basu tashi ba sai da suka tashi da kan su. Wajan karfe takwas matar uncle Kabiru ta kira ni, naje take tambaya ta anyi min gyaran jiki kuwa? Na yi kasa da kai waye zai yi min bayan bani da uwa a duniya? Kawu daddy dai ya yana yi min iya abinda zai iya, Mami ita ya kamata ta yi min wannan amman ko a jikin ta, bata ki ma a kai ni ina cikin yanayin kazanta ba babu ruwan ta ita tunda basu Shukrah bane. “Amman garin ya hakan ta faru?” “Babu komai Aunty, kawai ni ce nace bana so.” “Shine suka kaleki saboda kince bakya so? Toh maza ki tashi ki shirya yanzu kizo ni zan miki, Allah yaso nazo da komai na yi da kenan haka za a nannade ki a kai ki gidan mijin. Ai Khadija ko kana da kyau cewa akai ka kara yin wanka sai kafi haka kyau, musamman ke da zaki doshi gidan girma mai daraja kamar yanda muke fata.” Na yi shiru zuciya ta kamar zata kone jin maganar gyaran jikin nan, sam bana so dan nasan zan gaya yin kyau kuma hakan zai sanyayawa mijin rai abinda ni kuma bana so wallahi. Na tashi kamar zan fadi sabo da sauri na bar gurin, ina ta kufce-kufce ta yadda na gujewa gyaran jikin amman sai da tasa aka nemo ni muka shiga dakin da ba za a dame mu ba ta yi min. Mami kam ko a jikin ta bama taso taji ance za a min wani abun na kulawa wanda ita ya dace tayi min amman ta shafawa idanunta kwallin rashin mutunci saboda hassada da bakin kyashi. Subahanallahi ni kai na sai da naji canji a jiki na lokacin da aka gama yi min dilka da halawa na musamman, da yake yar asalin yerwa ce tasan ta kan kamshi mai zama a jikin ɗan adam. Naji wani dadi fiye da yadda nake tsammani, sai dai bana jin zan iya bari wanda ba Mas'oud ba ya kwashe wannan ni'imar. Koda aka gama cewa tayi na tafi daki karna sake na fito waje, komai nake bukata nasa a kawo min nace mata to. Abin da ya bani mamaki duk sunyi anko wai na bikin ne, lallai sun shiryawa auran nan mu duk bamu sani ba. Ganin kowa ya yi ne yasa Ya Waleedah da Ya Shukrah suka je kasuwa suma suka siyo irin material d'in sannan suka kai aka dinka musu saboda kar a yi musu surutu. Sai da naga abin da gaske ne sannan na tashi na dauki wayata na shiga toilet tare da kunna famfo yadda ko nayi wayar babu wanda zai iya jiyo ni. Bugu daya tamkar daman ni yake jira kawai naji ya daga murya shi a can kasa kasa. “Yanzu ba zaka tsamo ni daga fadawa wannan auran ba daddyn Waleed? Kar kai min haka dan Allah. Da nace ba zan kuma kula ka ba sai randa ka samo mana mafita, amman na kasa gashi na kirawo ka da kai na.” A hankali naji yana magana dan sai na kasa kunne sosai nake iya jiyo abinda yake fada. “Ban san me zan iya ce miki ba Oum waleedah, yanzu haka ina kwance a asibiti tun shekaran jiya. Bana jin zan iya kuma numfashi daga lokacin da aka ce kin zama mallakin wani ba ni ba.” “Ya Subahanallahi na shiga uku, Mas'oud yanzu kana asibiti? Da gaske ba kai zan aura ba? Wallahi nasan ina cikin tashin hankali, dan Allah karka guje min bazan iya rayuwa ba bu kai, ka tallafawa zuciya ta Mas'oud, idan ba hakaba wallahi nima gawata za'a kai gidan koma wanene.” Kasa cewa komai ya yi, sai muryar wata mata da naji tana min magana cikin lallashi, da alama mahaifiyarsa ce. Cikin sanyin murya take min magana itama kamar zata yi kukan saboda naji yadda take rawar murya. “Ina son ku dauki kaddara Khadija, aure dama mukaddari ne, ki godewa Allah ya baki lafiya damar raya sunnar ma'aikin mu annabi Muhammad S.A.W. Wannan itace jarabawar ku, ya kamata ace kunyi tawakkali wajan karbar ta yadda Allah zai ji tausayin ku a wani barin na rayuwar ku ta nan gaba. Muna muki fatan alkairi cikin auran da zaki yi, daman Allah ya riga ya rubuta ba zaku auri junan ku keda Mas'oud ba, ki yiwa iyayen ki biyayya mun san tabbas bake kika guje shi ba daga Allah ne. Sai anjima Khadija Allah ya yi miki albarka kinji, Allah ya kare rayuwarki kuma a duk inda zaki tsinci kanki.” Tana kaiwa nan ta katse. Ni kam me zanyi ban da sulalewa kasa na rushe da kuka, na dinga yi ina yin cilli da duk abin da na gani kusa dani. Su Zarah suka zo suna bugun kofar saboda sun ji abin nawa ya yi yawa, naki budewa shine suka je suka kirawo su Mami sannan na bude tare da fadawa jikin matar kawu Hashimu. “Ya isa Dije wannan kukan na meye kuma?” Na samu kai na da cewa. “Baffa na da Ummata duk basu cikin duniyar nan.” “Lahhh haba Dije baga mu ba, ko mu baki yi farin ciki da ganin mu ba sai mu koma inda muka fito dan farin cikin ki.” “A a Aunty wallahi ba haka nake nufi ba, kawai tuno dasu nayi.” “Allah sarki, daman haka ne wata rana zaka ji ina ma kana tare da su. Amman kiyi hakuri ki dena kuka kinga gidan aure zaki je kar kije kiyi rama dama gata nan duk kin fada.” Haka suka dinga lallashi na damin nasiha har sai da nayi shiru sannan suka rabu dani. Ban kuma yin kuka ba saboda bana so a zauna ayi ta min magana kar naje na bata musu rai su ji haushi na bayan bani da kamar su a duniyar nan. *RANA BATA KARYA...* (Sai dai uwar diya taji kunya.) Tun da ya tashi yake jin wata ni'imatacciyar iska tana ratsa sassan jikin sa, a cikin ransa yasan hakan baya rasa nasaba da auran Khadija yar jarida da zai yi, yarinyar da ta tafi da rabin imanin sa. Yaji a duniya yana son kasan cewa tare da ita a cikin gidan shi, komai sabo haka ya tana da, koda yake an tanade su ne dan yau ce ranar da zai yi tafiyar nan zuwa Cyprus. Amman shi a nashi bangaren zasu kasan ce ne matsayin na daurin aure. Daure da towel ya fito ya tsaya wajan dressing mirror yana karewa kanshi kallo. Matashin sarki kenan mai ciki ta nagartacciyar haiba da cikar zati. Mijin Shaheedah angon Khadija a yau da ikon Allah. Lotion d'in sa ya dauka tare da bin sassan jikin sa yana shafawa. Bayan ya gama tsab ya kuma bin jikin da oil perfume da kuma body spray masu azababban kamshi. Shiga ya yi wacce take bayyana cewa shi din sarkin ne ba wai carki ba. Ya Subahanallahi tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan bawan nasa, ya kawata shi da gabobi managarta masu cikakkiyar haiba. Lallai ba karamin kariya rawanin da yake sawa yake bashi ba, dan irin su sarki Salman ne suke sawa yan mata suna mafarkin mallaka a matsayin mazajen aure, abokan rayuwa na har a mutu. Kamshinsa kawai ya isa rikita zuciyar mai shaka. Ya riga yayi sallama da kowa tun a daren jiya, shiyyasa yana kammala shirinsa kai tsaye ya fito falon farko na sashen nasa. Cikin hanzari Jakadiya ta zube tana mika gaisuwarta. Kafin ta mike ta fita da hanzari ta sanar da fitowarsa. Taku yake tamkar wani hawainiya, ga kuruciya ga jinin mulki na kai kawo a kowacce jijiya da gabban jikinsa. Tun kafin bayyanarsa garesu hadiman sashen nasa duk suka zube domin mika gaisuwarsu gareshi. Tafiya yake kawai batare da amsama kowa ba. Kamar kullum idanunsa na sake cikin gilashinsa na ka'ida. Sai da ya wucesu gaba daya kafin wasu suyi saurin mikewa su dafa masa baya. Sun iske fadawa suma tsaitsaye a kofar fada suna jiran fitowar mai martaban. A take suma dai zubewar duk sukayi suna mika gaisuwa. Suma dai basu samun amsar ba, sai cikin fadawanne ke ansawa da fadin, "Sarki yaji ku, shima ya gaisheku". Lumshe idanu sarki Salman yayi daga cikin gilashinsa yana sauke wata ajiyar zuya a hankali, wani irin yanayine ke sauka masa a gabban jiki da baisan na minene ba. Haka dai akai masa rakkiya har gaban jerin motocin dake a jere zuka-zuka suna jiransa. Ruf dogarai sukai masa da rigunansu har ya shige daya daga cikin motocin data fi kowacce koshi da daukar hankali, sai da aka rufe kofar sannan suka marmatsa suma suka nufi motocin da zasu shiga. Kamar yanda ya saba sai da ya karanto addu'ar fita a gida a cikin ransa, kafin motocin su fice daga masarautar zuwa airport. *_GIDAN BIKI KHADIJAA(DIJE)_* ———- _Afuwan! Kunji shiru ko? Wallahi kwana biyu inata fama da chronic ulcer. Har takai na kwanta a asibiti na yan wasu kwanaki shysa kukaji shiru, Ina fatan na same ku lpy? Nagode k’warai da addu’oin ku. KIBIYAR ajali zai cigaba da samuwa Insha Allah da zarar naji karfin jiki na sosai.. Na gaishe ku, Gaisuwa mai kima.._ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac. _*ASSALAMU ALAIKUM SISTERS..!_* _*INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN: _* _*HERBALS APHRODISIAC MA’ANA NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_* _*TO KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA.._* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA KI CIKI DA WAJE_* _*MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI LUWAI TAMKAR TA JARIRAI_* _*AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._* _*KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_* _*AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_* _*KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_* _*MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_* _INSTAGRAM LINK DIN MU:_ www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac _WHATSAPP LINK DIN MU:_ https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz _NAMBAR TARHON MU_ 08169380189 _*DA A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYAN MU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._* _*BE YOUR OWN BOSS, BUILD YOUR OWN EMPIRE, BE THE WHOLE WORLD OF HIS MAJESTY( YOUR HUBBY) BE THE ONLY CENTER OF ATTRACTION WITH ZEE HERBALS APHRODISIAC. OUR PRODUCTS LASTS LONGER AND VERY EFFECTIVE. NO SIDE EFFECTS. AVAILABLE N WHOLESALE/ RETAILS.. DELIVERY IS NATIONWIDE. 100% TESTED AND TRUSTED_* *2__2* *SAS* *Yana* zaune a bayan mota driver yana janshi, gaban motar tashi motar yan sanda ce masu kula da lafiyar shi. Bayan kuma ta manyan yan fadarsa ne sai kuma ta dogarawan shi. Gabaki d'aya tunani ya tsaya masa ganin yau ne ranar daurin auren shi, gashi babu wanda ya sanarwa zai yi, sannan be gayawa dangin yarinyar cewa zai yi tafiya mai nisa ba yau din, to wa zai yi masa wakilcin auran? Ya samu an bashi yarinyar cikin mutunci be dace ace ya nuna rashin damuwa da lamarin ba, kar suyi tunanin bashi da kirki. Tunanin tsayar da driver din yake a ransa, amman bakin shi ya gaza budewa dan ya sanar da shi cewa ya tsaya. Da kyar da dauriya Salman ya bude d'an karamin bakin sa yace wa driver ya tsaya, ya kuwa sanya signalya koma bakin titi ya yi parking. Nan da nan sauran motocin ma suka tsaya, yan sanda suka yi saurin fitowa tare da zagaye motar da yake ciki. Waya ya dakko ya kirawo Turaki da suke dayar motar yace dashi. “Ina son mu koma akwai wata magana da zan yi daku.” “Ranka ya dade da mu karasa airport d'in, tunda a Abuja zamu sauka kafin lokacin tafiya Cyprus d'in sai a zauna in ba damuwa. Allah ya taimake ka.” Da kyar sarki Salman ya sake bude bakin sa saboda yadda yake jin wahalar magana yace. “Tana da muhimmanci ne.” Turaki ya kalli Galadima dake gefen shi da alama ransu ya baci saboda so suke yi kawai ya yi tafiyar nan koda kuwa ba za ta yi masa dadi ba. Amman dan kar mutanan da suke tare wato dogarawa da yan sanda su fuskanci wani abu sai suka amsa masa. Nan Turakin ya sanar da yan sandan cewar zasu komai gida, mai martaba yana son ganawa da yan fada. Haka kuwa aka yi nan da nan akai convoy suka koma masarautar Basannabas. Daidai shiga fada suka yi parking saboda sun san zai kuma fitowa ya shiga motar shi yasa basu kai ta ma'adanar su ba. Yana fitowa fadawa suka fara yi masa kirari irin wanda ake yiwa manyan sarakuna masu ji da mulki, yana taku day-daya kamar baya son yi a haka har suka karasa cikin fadar. Cikin wani amintaccen parlor da yake zaman sirri da yan majalisar sa, Bayan sarki Salman ya zauna akan kujerar shi, sai sauran ma da day-day suka dinga kai gaisuwa suna samun gurin zama kasan cewar kowa yasan a inda yake zaman shi yasa zaman fada yake kasancewa cikin ladabi da biyayya. Sai da kowa ya zauna sannan waziri ya gyara zama kansa a kasa yace. “Na gaishe ka sarkin sarakuna, d'an sarki jikan sarki. Allah ya kara maka lafiya, munji kace a dawo gida Allah yasa dai lafiya, Allah kara maka lafiya.” Sarki Salman ya kalle shi ta cikin bakin gilashin sa, tare da kallon kowa dake zaune. Murya can kasa kasa yace. “Lafiya.” “Allah ya karawa sarki lafiya.” Duk suka hada baki wajan fada, Ya murza idanuwan shi, shi kansa yasan maganar da zai yi musu yanzu sai tasa sun rai na kan su. Amman duk da haka zai gaya musu saboda ya zama wajibi su sani, sannan a yau ne za'a kawo amarya kar yaje a yi musu rashin mutunci bayan an bashi yarinya a karramance. Kamar ba zai yi magana ba sai suka ji yace. “Ina so na sanar daku wani abu.” “Girmanka ne ranka ya dade, fadi duk abinda yazo bakin ka muna saurara ya sarkin mu na adalci, Allah kara maka lafiya.” Ya kuma jan numfashi ya sauke tare da kawar da ido daga kallon da yake musu ta cikin bakin gilas din shi yace. “Yau da karfe goma sha d'aya za'a daura min aure.” Galadima, Ciroma, Wambai da sauran tsirarrun mutanan gurin suka zaro idanuwa suna kallon sarki Salman, yau kam bakin gilashin sa yafi koda yaushe kona musu rai saboda sun so su kalli cikin idanunsa dan tabbatar da maganar da yake gaya musu a daidai wannan lokacin. Sai dai ina basu gani, haka kuma kanshi a sunkuye yake da alama jiran su yake suyi magana a kai. Waziri ne ya rissina yana fadada murmushin fuskar shi ya miƙa gaisuwa yace. “Wannan duk damar ka ce ranka shi dade, sai dai wacece wannan wace tayi matukar da ce da samun ka a matsayin miji.?” Daman sarki Salman yasan waziri ne zai yi farin ciki da duk abin da zai yi, sabanin sauran da basa iya bude bakin cikin su sai sun bayyana. Salman ya kuma yin kasa da murya yace. “Khadija.” “Masha Allah, yar wajan Wambai ko? Gaba salamun baya salamun sarkin sarakunan mu, wannan abu ya yi kyau.” Wambai da yaji an kira sunan cewa yar shi sai ya fara washe baki duk da cewa yasan yarinyar ma ba ta wani isa aure ba, yanzu ta cika shekaru tara. Amman da yake son zuciya yana tattare da shi sai ya yi tunanin auren za'a yi sai ta kuma girma sai ta tare a gidan. Maganar sarki Salman ita ce ta dawo da tunanin da Wambai ya tafi, inda yaji yana cewa. “Ba ita ba ce, wannan ba ta shafi jinin sarauta ba, yau da karfe goma sha daya na safe za'a daura, idan an gama komai zan tafi airport sai kuma na dawo.” Tashin hankali wanda ba'a sanya masa rana, duk irin sanyin a.c dake ratsa cikin fadar, su ciroma gumi kawai suke yi dan basu taba zato ko tsammanin haka daga wajan Salman ba. Shirya yin aure ba tare da ya sanar da kowa ba har sai a ranar da za'a daura, babu shakka wannan yaron ya fara raina su dole su kara tashi tsaye ta yadda ba zai kuma aiwatar da komai ba sai ya gaya musu. “Ahh to ai sai a gaya mana wajan daurin auran dan muje mu halarta kar aga duk babu mu a wajan.” Waziri ya fada yana nuna farin ciki da wannan auran. Salman yaji dadi da waziri yace za shi wajan daura auran har ma da karbar ragamar yi masa wakilci a maimakon shi da yace zai karbi abin shi da kanshi. A takure duk suka zauna har lokacin da dogaran sa suka shigo suka kakkare shi ya mike ya fice.Gashi waziri ya hana kowa tashi daga gurin sai da Salman ya kalli agogon hannunsa yace ya kamata su tafi dan kar iyalin su suyi ta ta jiran su. Galadima da Ciroma dai basu bisu ba saboda sam basu da nutsuwa, gashi suna so suyi magana tare da kamo hanyar da suke tunanin zata bulle musu. °°°°°°°° °°°°°°°°° *KHADIJA (DIJE)* Tun ana gobe daurin aure nake fama da wani irin zazzabi amman na kasa nunawa dan karma a bani magani saboda na san ba na shan magani bane zazzabin. Yadda naga rana haka naga dare, asubar fari na shiga nayi wanka nayi sallah sannan na koma kan gado na yi kwanciya ta ina tunanin rayuwar da zanyi a nan gaba. Yan matan da suka fara cika mana gidan ne suka shigo dakin sai ihu suke yi, nan da nan kai na ya fara ciwo na yi ta rintsa idanuwa. “Ke Dije waye yace miki amarya tana bacci ranar daurin auran ta? Wallahi ba zaki bacci ba hauka ma ke nan.” “Tashi kisha tsumi yarinya saboda karma angon ya raina mana ke.” “Wai shi angon nan ba zai bayyana kanshi ba, sai kace wani mace yana ta boya kanshi.” Gabaki d'aya suka isheni da surutu na banza da na wofi da ba wani farin ciki yake sani ba sai bacin rai da damuwa. Ana cikin haka sai ga matar kawu Kabiru ta shigo hannunta dauke da boul ta tashe ni, sai da na zauna sannan ta miko min tace na cinye na kuma shanye roman kar na bawa kowa. Haushi ya cika ni na dinga hararar kazar da roman ina jin kamar zan yi amai saboda rashin son ci da ba nayi. Ina ma ace Mas'oud ne, wallahi tallahi da kai na zan fara gyara ba ma sai anyi min ba. Haka dai na caccakuna ban cinye ba suka je suka gaya mata tazo ta sani a gaba har sai da na sude boul d'in ta kyale ni. Ruwan wanka aka sake had'a min na musamman wanda yasha turarukan yerwa, hawaye yana zubar min haka nayi wankan na fito aka yi min kwalliya. Nayi masifar yin kyau mutane sai yankawa suke yi, ni kuma ina ganin akuya ma ta fini kyau a wannan lokacin saboda yadda nake jin kuncin zuciya da rushi. Gidan fa ya cika yadda bana tsammani, a kuma sannan ne na jiyo ihu da shewa a parlorn kasa, wai ashe kayan lefe aka kawo akwatuna ashirin da biyu da mukullin mota. Mami kam da ta gani sai da ta kusa hadiye zuciyar ta, ba ta yi zaton zan samu akwati biyu bama bare ace fiye da haka, sai gashi an kawo wanda hankalinta ya ke kokarin gaza dauka. “Dije dan Allah ki gaya mana waye wannan saurayin naki?” Ya Waleedah ta tambaye ni lokacin ina zaune a gefen gado. “Ni ma ban san ko waye ba.” “Karya ki ke yi munafuka, baki sani ba zaki yadda a aura miki shi ne. Kin san me azxiki ne shi yasa duk kika ki gaya mana sai munafincin kuka da kike yi a baya wai ke bakya son auran. Kin dai san mu mun gaji arziki dan a cikin shi kika zo kika same mu, ke kuwa taka haye ce kowa ya sani.” Ya Shukrah ta karasa maganar tana bugar min kafada. “Rabu da ita abin da yau karya ta kare, yau zamu ga ko wanene take boyewa.” Ya waheedah taja ta suka fita. Ni kai na da naji uban yawan kayan sai da na girgiza na fara tunanin waye wannan zai siye ni? Kwarai kuwa siya ta zai yi, banda haka ya za'a yi a ce an kawo min akwatuna ashirin da biyu sai kace wata sarauniya? Kiran Mas'oud ne ya katse min mamakin da nake ciki, na dauki wayar nasa jikin kunne na, yadda naji muryar shi a wani iri shine ya sake tayar min da tsananin hankali, yace dani. “Wannan shine kira na karshe da zan miki, sannan ina miki fatan alkairi a gidan da zaki shiga, naga sauran yan lokuta ki zama a karkashin wani. Amman dan Allah ki sanar dani waye zaki aura?” Na fashe da kuka na kasa yin magana, nifa gani nake kamar karya ne ba za'a raba mu dashi ba, har yanzu ina ganin wannan al'amarin tamkar mafarki. “Ki gaya min ko waye.” “Wallahi ban san shi ba Mas'oud har yanzu, amman naga kowa yana jin haushi na akan cewa na sani kawai fada ne ba zan yi ba, kuma wallahi Allah ban san ko waye ba har yanzu ka yarda dani Mas'oud.” “Shikenan na yarda dake. Ina miki fatan shiga gidan miji lafiya... Bye Khadija sai wata rana....” Ya katse kiran naji kit, kawai sai na saki wani marayan kukan mai ban tausayi. Shigowar Aisha ta zauna gefena ta na lallashi muka ji ana cewa yan daurin aure sun zo har da ango. Dan gidan sarauta Dije zata aura, to waye a ciki? Me ne ne matsayin sa a cikin fadar masarautar Basannabas? Nan fa kowa ya kasa kunne dan sauraran jin waye angon Dije. Cikowar unguwar kuwa ba a magana, ashe Alhaji Isma'il gayya ya yi sosai ba tare da sun sani ba. A cikin masallacin jikin gidan aka tabbatar da auran Nana Khadija Basheer da Sarki Salman Aliyu Salmanu (SAS) akan sadaki mafi daraja... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 ______________________ KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?. To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.         Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?. Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai. Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓. Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗. ______________________ _WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, AMANA CE A HANNUN DUK WANDA YA SIYA, NEMI NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFIN DOMIN MALLAKAR NAKI, KI GUJI KARANTA NA BATI.. DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU RUBUTAWAR..._ _*KIBIYAR AJALI......*_ _(SULKE BAYA TARE TA SAI TA WUCE)🏹🥰_ *2___3* *KHADIJAA* *Kukan* rabuwa da Mas'oud da nake yi ashe ba komai bane sai da naji ance Sarki Salman shine miji na, A take na yanke jiki na sume ban sake sanin inda kai na yake ba. Haka yake a bangaran Mami, tana jin wanda aka aura min itama ta yanke jiki ta fadi, ganin mu biyu abun ya faru, sai ba ayi tunanin bakin cikin darajar wanda na aura shine yasa Mami suma ba, aka dinga cewa ai mayya ce ta kama mu, wasu suce jefa aka yi mana ni da ita. Aka dinga bamu taimako har Allah yasa Mami ta dawo cikin hayyacin ta, ta tambaya waye mijin nawa suka tabbatar mata cewar sarkin Basannabas. Amman Alhaji ya Munafince ta da gaske, shi yanzu saboda tsabar rashin tunani ya bar ya'yan cikin sa ya dauki yar kauye wacce iyayenta basu bar mata gadon komai ba ya bawa sarki guda. Anya akwai miji irin nata kuwa marar lissafi idan ba na dukiya ba? Ban da haka ya zai yi wannan shirmin sai kace wanda aka cewa jeka ka gani. Shikenan aikin gama ya riga ya gama tunda har an riga an daura babu yadda za ta yi, Dije tayi sa'a sauran su Shukrah wanda take hango musu matsayin matan shugabanin kasashen waje ko na cikin gida Nijeriya. *SAS* Sarki Salman kuwa ana gama daurawa ya tattara suka tafi, Bai yadda ma sun koma masarauta ba yace a kai shi airport zai jira lokacin tafiyar shi ya yi. Kamar ya sani dan da ya koma da yaga abin da ya ragowa kansa, saboda su Galadima sun sanarwa su Gimbiya Shaheedah zancen auran tana can tana haukan kuke koke da zage-zage tare da cewa sai yasan yaci amanar ta, ya Munafince ta ya yo mata kishiya kuma yar matsiya ta. Labari ya kuma zuwar musu cewar ai ba zai dawo ba ya wuce Cyprus. Koda su ga kai shi guri na musamman aka bashi ya zauna dan jiran lokacin tafiyar, mulkin kuma ya barshi a hannun waziri duk kuwa da yaso su tafi tare amman Salman d'in ya ce aka ya yarda dashi shi yasa yace ya koma ya rike masarautar kafin ya dawo. Yana zaune ya rasa yadda zai yi saboda Alhaji Isma'il ya tambaye shi a wane muhalli zai ajiye Khadija saboda suna son aje a shirya gurin, yace masa zai kira shi a waya idan ya gama shawara. Da wa zai yi shawarar ma oho masa. Wani tunani yazo masa sai ya kirawo bafadansa da ke yi masa wasu abubuwan masu muhimmanci wanda be son kowa yaji, yana can bakin kofar da yake saboda tare zasu. Ya shiga tare da dukawa har kara ya yi gaisuwa tare da yin shiru yana jiran umarni. “Ka kira mahaifin yarinyar nan kace idan sunje a nuna musu bangaran Abdullah, idan an nuna musu nan zasu kai ta har na dawo.” “Takawarka lafiya sarkin mu mai share hawayen mu. Aiki ya gamu da ikon Allah, gaba salamun baya salamun d'an toron giwa.” Al-hassan bafade ya fada yana mai ficewa daga cikin dakin. Yana fita ya kira lambar Alhaji Isma'il tana ta ringing amman be daga ba, ya yi tunanin kila yana cikin mutane dan shi kansa Al-hassan yaga yadda yan kasuwa suka cika gurin daurin auran, sai da aka dan jima ya sake kira sannan yaji ya dauka, suka gaisa ya sanar dashi sakon sarki Salman. Da farin ciki Alhaji Isma'il ya amsa sannan yaje ya gayawa su Mami cewar azo aje a gyara bangaran da za'a kai Dije. Aikuwa sai ta je itama kodan taga me zai faru, daman kuma ba shiga masarautar ta taba yi ba yau gashi ta sanadin Dije zata shiga son ranta. *KHADIJAA* Ni kuwa sai da ta kai ta kawo an saka min drip, kawu daddy sai addu'a yake Allah yasa na samu sauki a kai ni gida na kamar yadda ya yi alkawari, ba ya san a samu matsala shi yasa da ya fita zai dawo yace ya jikin nawa. Allah sarki Mas'oud abin kauna ta, an raba ni dashi a lokacin da zuciyata ta makance akan shi. Tabbas nasan zan rayu ne cikin kunci da zama da makiyi, ba wai nafi karfin auran sarki Salman ba. A a kawai zuciya ta bashi take so ba, na kuma san akwai wata manufa da ya sanya shi auran ta, ban da haka me yasa lokacin da ta karaci kwanciya a asibiti be taba zuwa ya duba ta ba sai da ta warke sannan ya turo dan munafunci wai a duba ta. Ai kuwa tun kayan da nasa da safe ban cire ba, Babu yadda ba’a yi dani ba akan na canza amman naki dan banga dalilin yin kwalliyar ba. Aisha ma tun tana jin haushin naki canza kaya har ta dawo tana lallashi na akan auran dan ita kanta ta yarda da cewa Mas'oud shine buri na, amman babu yadda zanyi kaddara ta riga fata. Ta kuma yi min murna cewa matarsa daya ni ce ta biyu, amman nasan ai zai karo biyu tunda sarakuna baka raba su da aure-aure. Amman da Mas'oud ne nasan sai mutuwa nida shi babu kishiya. ••<>••. ••<>••. Yan tafiya gidan jere suka tafi kusan mota uku saboda kowa yana son zuwa ya ganewa idanunsa. Na kuma fashewa da kuka tabbas zanje gidan can tunda gashi har an tafi shirya min kaya na a can, wayyo Allah, sai naji har gwara zama wajan Gajiyalle da auran nan da za ayi amfani da ni wajan cin mutunci. *MASARAUTAR BASANNABAS..* Lokacin da su Mami suka shiga masarauta daman waziri yasan da zuwan nasu hakan yasa basu sha wahala ba gurin shiga cikin gidan. Nan suka tambayi sashen da za a sanya amarya, waziri yasa aka nuna musu wani waje can kusa da sashen Gimbiya Sa'adatu wato mahaifiyar sarki Salman, wacce ba ta san wainar da ake toyawa ba a masarautar, kasan cewar tana zaune ta tashi da wata irin ciwon kafa (muscle spasm) ta yadda ko tashi ba ta iya yi. Matar kawu Hashim ce ta fara bude kofar tayi bismillah tare da kallon kowa da suka zo tace suma suyi sannan su shiga. Haka suka dinga yi har suka shige cikin sashen masu guda nayi masu hotuna suna yi masu fara shirya-shiryan gurin suma duk sun fara. Gurin ba laifi babba ne, sai dai be kai gurin sauran matayen ba kasan cewar daman an yi shi ne dan yarima Abdul kuma ba a nan yake zaune ba shi yasa aka bawa Dije shi. Suna cikin aiki sai ga gimbiya Jaleela tare da bayin ta masu take mata baya. Babu ko sallama haka ta shigo tana kallon su one by one daga bisani kuma ta tabe baki sai faman hura hanci take yi, su kuma duk sun dauka cewa uwar gidan sarki Salman ce. “Wacece gwaggon amarya?” Aka fara kallon kallo ko wacce jira take ace itace, sai kuma matar kawu Kabiru tace. “Ko wacce a nan akwai matsayin ta, amman ga marikiyarta wacce ta rai ne ta har zuwa yau.” Suka nuna Mami wacce itama saboda mulki wai ita matar babban d'an kasuwa. Gimbiya Jaleela ta kare mata kallo tas, ganin babu abin da zata yi mata gori dashi sai ta rausayar da kai. “Ya yi kyau uwar amarya, muna fatan dai kun shirya mana ita sosai.?” Itama Mami sai da ta sha kamshi tamkar ba zata ce komai ba sai suka ji tace. “Sai ma ta shigo zaku tabbatar da hakan. Shin maman sa ce ke?” Gimbiya Jaleela ta cije lebe ganin da ta yi ba ta da tsoro kenan. “Eh tamkar uwa nake a gareshi, amman dai zaku sani nan gaba.” “Shikenan ranki ya dade, Allah ya nuna mana lokacin.” Juyawa gimbiya Jaleela tayi ta nufi sashen gimbiya Najwa, a can duk ta same su zazzauna sun zabga tagumi da alama ita suke jira daman. Guri ta samu ta zauna itama tare da jan numfashi ta sauke da karfi tana cewa. “Ashe ma yar riko ce, shi kuwa yaron nan a gidan waye ya ganta?” “Yanzu dai kin makala man a jikin wani abun na ta ko kuwa?” Gimbiya Huwaila ta tambaya cike da zakuwa. “Na makale shi a jikin one seater d'in parlorn.” “Good job Jaleela, yanzu sauran na kofar dakin, shi kuma sai da yamma idan Allah ya kai mu. Zanje nasa shi kamar yadda Abba Galadima yace.” Cewar Najwa tana tsuke baki. “Bamu san abin da zai faru ba kenan wallahi, da duk ba zama mu bari ta shigo cikin gidan nan lafiya ba ma. Salman ya ci ka marar mutunci wallahi, ace har kana ta shirye-shiryen aure amman baka sanar da kowa ba sai a ranar dan tsabar wulakanci? Amman babu komai zai gane duk wannan abun nashi babu inda zai kai shi. Shaheeda ki dena kukan nan haka, kinji dai abin da Baba ciroma yace, sai ya gwammace beyi wannan auran munafincin ba.” Najwa ta yi maganar cike da tsantsar takaici. Shaheeda dake zaune kasan carpet kanta yana kan cinyar Gimbiya Huwaila sai faman bubbuga bayan ta take yi alamar lallashi. Cikin kukan bakin ciki ta fara magana tana dafe kirji da alama zuciyar ta tana cikin hargitsi, tace. “Bana tunanin Salman ne yace yana son auran nan, wallahi ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba nasan jan zuciyar shi akai ta hanyar yi masa asiri. Ban da haka ta ya za ai ace wanda ko daga ido ya kalli mutane ba ya iya ya bare har yaga wata banza wacce ba kowan kowa ba yace zai aura? Na rantse da Allah asiri suka yi mishi, kuma wallahi sai ta gwammace ba ta aurar min miji ba. Saboda ni kadai ce tashi babu wacce ta isa ta shigo min bukka dan shiga cikin sheka ta, wallahi sai nai mata abin da zai sanya ta gudu da kafafuwanta yar iska kawai.” Magana take cike da tsantsar bakin ciki wanda idan zaka kashe ta ba zata iya maimaita abubuwan da ta ke furtawa ba, su kuma duk sun zuba mata ido ko wanne da irin abin da yake cikin zuciyar sa. Shaheeda da komai ya fi yi mata zafi saboda abubuwan da take gudun faruwarsu suna da yawa a game da sarki Salman da ita. Waya kuwa ta kira shi yafi sau ashirin amman ba ta shiga, shi tuni ya sauka a birnin Cyprus cike da tunanin abubuwan da ya baro a gida Nijeriya. Mikewa tayi tana sharar hawaye ta kalli su Gimbiya Jaleela wacce ke dafe da goshi tace musu. “Dole zan yi tafiya zuwa gida dan sanar da lamarin nan a gurin iyaye na, duk da na kira wayoyin sa bana samu gobe zan shirya na tafi ku kuma kuci gaba da tsara komai kafin na dawo.” “Baki da damuwa ai Shaheeda, kuma ko baki fada ba kinsan tabbas wannan fadan ba naki bane ke kadai har da mu. Kije lafiya ki dawo lafiya, zaki ci gaba da rayuwarki ke kadai a birnin zuciyar Salman.” Jaleela tayi maganar cike da karfafawa Shaheeda gwiwa. _____Su kuwa can bangaran suna ta shirya sashen amarya, basu gama ba gashi har dare ya yi dole sai dai abar wasu shirin zuwa wayewar gari sai a karasa. Sun kafa gadaje sun sanya kujeru da dining da sauran su, kitchen ne dama ya rage basu kammala ba, gashi ana ta kiran su akan su dawo za'a dauki amarya a kawo ta gidan ta. Haka suka tashi suka harhado komatsan su suka dawo cike da mamakin abin da ya sa aka hana su zuwa wani sashe dake gefe (mahaifiyar sarki Salman) dogarai dake bakin gate din su suka shaida musu cewa wai tace kar wanda ta shiga ba taji dadi ne. Suna dawowa suka tarar na gama kimtswa da taimakon Aisha cikin janyo min ayoyin Allah tana fassarawa har sai da naje na yi wanka nasa kayan da suka fito min dashi sannan ta shafa min mai a kafafuwa saboda cewa na yi babu abin da zan kuma yi bayan sanya kayan. Zata shafa min a fuska wai nayi kwalliya ko hoda ce na sa amman na dage akan cewa ba zan yi ba sai dai idan an kai ni ya koro ni, amman ba zan wani yi masa kwalliya ba dan babu wannan tsarin a cikin zuciyata. Kawu daddy, kawu Kabiru da kawu Hashimu sune suka yi min nashiha, sannan suka saka ni yi musu alkawarin zama da miji na lafiya kamar yadda iyaye na suka yi gashi yau babu su ko daya a cikin su sai labari. Daga nan kuwa suka riko ni ina ta kuka suka sanya a mota, Aisha ta samu ta shigo kusa dani da taimakon matar kawu Kabiru. Sai da aka cika motocin da aka tanada wajan kai ni, sannan aka dauki hanya cike da kide-kide da bushe-nushen abubuwan sarauta har muka je cikin masarautar Basannabas, wacce a baya ina burin naji ance za aje cikin ta naji ina ma dani za a shiga saboda murna, sabanin yanzu da babu masarautar da na tsana irin ta. Kirjina ya dinga bugawa tamkar zai zazzago ya fado, ga wani mugun bacin rai da nake ji a rai na ko addu'a na kasa yi bare naji sassauci, sai ma kara zafi da zuciya ta ke yi.... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, AMANA CE A HANNUN DUK WANDA YA SIYA, NEMI NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFIN DOMIN MALLAKAR NAKI, KI GUJI KARANTA NA BATI.. DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU RUBUTAWAR..._ *24* Sanda aka bude min mota wai na fito, sai naji wani dummm.... A cikin kunne na kamar an cire min duk wani sauti, sai magana kawai da nake ji kai tsaye daga bakunan mutane kamar suna dariya. Da kyar na sakko da kafafuwana ina rike da Aisha gam sai kace ance guduwa za ta yi ta barni. Kai tsaye sashe na aka nufa da ni kasan cewar su Ciroma sun ce ba sai an kai ni wajan kowa ba,Naji dadi kuwa dan ni dama ba so nake yi na ga ahalin shi ba nasan raina baci zai kara yi tunda ba kaunar su nake yi ba nima. “Shiga da kafar ki ta dama Dije, kiyi addu'a ki shiga Allah yasa mutuwa ce zata raba ku keda mijin ki.” Matar kawu Hashim ta fada tana daga gefe na wajen hagu, Aisha kuma tana bangaran dama na rike ta sosai. Bismillah kawai na yi a zuciya ta nasa kafata ta dama kawai na shiga, sauran suka biyo baya na suna guda kasa-kasa dan su kansu sun gane cewar akwai abin da yake faruwa a cikin masarautar. Babu abin da ya burgeni a cikin parlorn da muka shiga, sai ma wani irin wari da nake ji ya cika min hanci na. Nayi saurin janyo mayafi na tare da toshewa amman still kara karuwa warin yake, Na saci kallon mutane naga babu wadda ta rufe hancin ta sai ni, na fara tunanin su basu ji bane? Abu kamar zai bata maka ciki ko ma nace zai lalata kwakwalwa. Suka dinga jana har cikin bedroom din wanda ya gaji da tsaruwa. Allah sarki kawu daddy, hakika ya yi min abin da ko a mafarki ban taba zaton zan same shi ba. Komai royal ya yi min wanda ko su Ya Shukrah iya abin da zai yi musu kenan. Aisha ta zaunar dani a gefen gado, Na zauna sai naji tamkar an cake ni da kusa saboda wani zafi da naji a hq dina kafin na yi wani yinkurin kawai naji wani abu yana fitowa daga gurin kamar an kunna famfo. “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.” Na furta da d'an karfi. “Me ne ne Khadija?” Na janyo ta ina dafe kai nace. “Period ne ina jin ya dawo min, kuma fa ban dade da yin wankan tsarki ba.” “Subhan’Allah, Amma ai ba abin damuwa bane tunda daman yana yin haka. Kedai kici gaba da kirga kwanakin.” Sai raba idanu nake yi. Ta cikin laffayar jiki na nake hango komai. Kaya kala kala sai kawo su ake yi a baskets da gift boxes dana cikin paper bags. Wasu kayayyakin aka kawo cikin wasu irin basket da aka yi da kaloli masu kyau, kowanne kaya ne acikin sa fal. Baskets din zasu yi kala goma. A gaban Mami wasu mata suka ajiye, Tamkar ba zasu yi magana ba, da kyar wata daga cikin su tace, “Ga kaya inji fulani.... Wato Gimbiya kuma Sarauniya sannan uwargidan Sarki Salman, Gimbiya Shaheedah diyar Sarki Ibrahim Hashimu da ke masarautar ‘Bullo.. Tace a shaida gaisuwar ta, Kafin taga amarya.” Gaba na ya yanke ya fadi. Oh ni Dije! Wai kishiya ce da wannan aiki haka? Babu karamin kaya a cikin kayan da ta bayar a kawo. Turamen atamfa da shaddodi kuwa harda na iyaye duk an sako. Sai wulkita idanu nake. Sannu ahankali kowannen su sai an bayyana mana na gurin Gimbiya wance ne. Da alamun na matan baban sa ne. Saboda yadda ko wacce take nuna bajinta, Tana bani waje na fiki komai. Kowa cikin shigar alfarma da dandatsa dandatsan kayayyaki, Wai ashe budar kai aka yi. Matar kawu Kabiru ta rakani wani band’aki dake cikin sashe na tasa nayo wanka. Na fito tsab dani bayan na saka pad a jiki na. Cikin wasu hadaddun lace ta shirya ni. Aka doramin alkyabba wacce tafi wadda na cire da safe kyau da tsari, Waziri da kansa ya shigo da wasu mata yan mata su wajen biyar yace ga masu tayani hidima nan. Duk abunda nakeso na sanar musu. Akwai zagi kuma da duk aiken da zanyi fada shi zan tura. Sannan yace za a yi min rakiya sashen mutanan masarautar. Sannu ahankali sauran yan uwa da suka rako ni suka sani agaba aka fara rarrakani gaishe da matan gidan. Banda sashen d’aya daga cikin matan marigayi sarki da aka ce mana bacci take yi. Amma sauran matan da bangama sanin su waye suba duk an kaini sashen su. Kowanne ya karb’e ni babu yabo babu fallasa.. “Ni wacece me babban dakin ne acikin su...?” Hairah diyar Kawu kabeeru ta tambaya tana mai daukar hoto na awayarta. “Kila acikin wa’ennan guda 3 take.” Cewar Ya Shukrah! “Yo acikin sune mana.. Ai da ba acikin su bane zasu sheda. Tunda su suka sa akayiyyi mana rakiyar. Tab a hayye! Dije zaki ci kan kaza ta ubanki a masarautar nan. Yo uwar mijin ma ba sanki take ba.. Kina ganin ko nuna kanta batayi ba. Banda barbadadden aure ma irin wannan ace ranar auren ka babu angon ka? Daren farko ace ba ango. Makira abinda kike so kenan dama.” Mami ta shiga fada min a kusa da kunne na, Matar kawu Kabiru dake gefe na ita kadai ce ke juyo Mami, Na matsa gefe ta sake danko hannu na da karfi, “Ba dai kin wargaza duk wani farin cikin gida na ba Dije? Kin hada ni da miji na ko..? Farin cikin ki kenan ko? Toh masarautar nan sai ta zamo ajalin ki..” “Assha! Haba Hajia? Ba girman ki bane wannan maganar wallahi.” Cewar Matar kawu Kabiru. Sauran mutane na gefe ba susan wainar da ake toyawa ba. Mami ta jefawa Matar kawu Kabiru harara, Taja dogon tsaki kafin ta cigaba da cewa, “Uhum! Ke kuma asuwa? Me zaki nuna min?” “Hajia munanan kalaman ki sunyi tsauri wallahi, Sannan furucin ki na karshe bai yi dadi ba sam bai dace ba.” “Dan nace sai ya zamo ajalin ta? Zaki gani ai. Muna daga gefe zamu ji labari.” “Hajjaju tunda dije ta tsallake siradin azabar Gajiyalle ai ko’ina zata iya jurewa, Tata kalar jarabawar kenan, Sannan muna fatan anzo karshen wahalhalun da tasha. Jin dadinta ne yazo yanzu. Ai mai hankali ne zai iya ganewa amma wannan yarinyar Khadija kafin Allah ce, Ta riga ta zamarwa makiya da mahassadan ta *KIBIYAR AJALI*, wadda sulke bai isa ya tsare ta ba sai ta wuce. Ba boka ba Malam.” “Iyeeee.... wa kike gayawa wadannan kalaman?” “Haba hajjaju ni na isa nace da ke nake? kukan kurciya ai jawabi ne, Me hankali shike ganewa. Zo muje Gimbiya Khadija... Takawar ki lapia, Taka a sannu yau ranar taki ce..” Matar kawu Kabiru ta karasa magana tana mai janyo hannu na, Muka wuce sashe na muka bar Mami a daskare tana cizan yatsa. Sannu ahankali da dai-dai da dai dai yan uwa da abokan arzuka suka yayye suka barni daga ni sai hali na sai hadiman da akace su taya ni zama. Ina tsakure akan kujera na ma rasa abinda ke min dadi, Tunda suka tafi nake ji na a takure, An kawoni inda bansan kowa ba. Ba wanda ya sanni. Shi kansa wanda ya auronin ba gama sanin wacece ni yayi ba. “Oh ni dije... Tawa samfurin kalolin kaddarar kenan?” “Allah ya kara miki lapia.. Magana ki ke?” Na hadiye kakkauran miyau jin wani sabon lamari, Sai kace a mafarki? Ko irin fina finan nan? Na kakaro murmushi ina kallon su su biyar a jere reras kowaccen su kanta a kasa, “Ba.. ba magana nake ba.” Yasin ni nama manta dasu, Wayar intercom dake gefe ce tafara kara. Wata acikin su ta mike ta rissina min, “Ran gimbiya ya dade... Zan dau wayar salular da ake kira. Zan iya dagawa.? An ban dama?” Kada kai nayi kawai, Ina kallon sabon al’ajabin dake wakana a gaba na, Dauka tayi tana amsawa kafin ta sake maida kanta kasa, “Sarkin kofar kudu ne yake neman iso, Yace wai dogarin yamma ne ya aiko shi.. Sako ne daga falaki Shima daga hannun dangaladiman waziri ne, Hannu da hannu daga ma’aji babba. Ance idan babu takura za’a aiko.” Gaba d’aya bansan me take nufi ba, Ko sunayen menene ta jero haka oho? Ni dai na jiyo k’arshen za’a aiko, Dan haka na daga kai kawai. Domin za’ai tata’burza kuwa. Ba abunda nasani dangane da irin rayuwar su. Gaskiyar Mami.. Inaga gidan ajali na nazo. Na sake sauke ajiyar zuciya. Ban gama tunanin ba. Na fara hangen manyan farantai shake da kayan alatu da cima kala kala, Gaba d’aya wajen ya hautsine da kamshin abinci, Su dai basa gajiya dazu fa aka kawo wani sai tafiya su Mami sukai dashi. “Bara mu baki waje Gimbiya...” “Dan Allah ku zauna..” “Allah ya kara miki lapia ki dade kiyi kargo. Muna waje zamu jira.” K’ada Kai kawayi nayi badon naso ba, Domin ni banason zaman kad’aici wallahi. Dan ba yadda zanyi ne. Gashi ciki na acike yake, Dan haka na mike mai shigewa ta wani d’aki dake dauke da kayan ciki komai purple. Na shiga rusar kuka ina tunanin baudaddiyar rayuwar da zanyi a masarautar Basannabas. Wai nan ni matar aure ce, Gidan aure na ne, Daren farko kuma.. amma bansan waye angon ba, bantab’a ganin sa ba. Wanne Irin cakwakiyar zama zamu yi!? Ni banmasan baya kasar ba sai da wasu acikin matan dazu ke fada.. Ban’daki na fada nayo wanka hade da alwala. Kasan cewar na saba ko ina cikin rashin tsarki ina yin alwala na zauna da ita ina mai rokon Allah da kada ya barni da iyawata ya shiga lamurana a ko da Yaushe... *CYPRUS * (HILTON-NICOSIA) Zaune yake a balcony din dake parlorn babban masaukin sa dake 5 star hotel Nicosia, Sanye cikin bathrobe, kanannadadden gashin kansa ya kwanta luf a kwanyar kansa. Tea ne agaban sa. Tun yana da zafin sa bai sha ba har ya huce, Hannun sa na dama yasa ya shiga bubbuga goshin sa, So yake ya kira falaki a waya yaji lapiar Khadija amma izzar sarauta ta hana shi. Yaja dogon tsaki yana kallon screen din wayoyin sa guda biyu dake kan table din gaban sa, Abubuwa ne da dama yake ji a game da farar wayar dake gefen sa. Bazai iya tina musababbin ajiyarta agare shi ba. Amman ya san dai iya shekarun nan tana hannun sa. Sannan Lokaci zuwa lokaci yakan kunnata ya kashe ta. Har yau ya kasa gano mafita. “Yaa Salaam!” Furzar da iskar bakin sa yayi, Ya kamo kasan leben sa yana ciza wanda yai jajawur, Saboda tsabar yadda yake ciza. sometimes ya shiga tsotsa kamar alawa. Abune da ya zamar masa dole. ‘Wazirin Basannabas..’ Shine sunan dake bayyana a screen din wayar sa baka. Wani abu dake saqale a kunnen sa ya latsa, Yana sauraron wazirin. Tamkar bazai yi magana ba, Tsawon lokaci tukun sannan yace, “Ok fine! Ta...Ta, Tayi bacci..?” Lumshe idanu yai ya jingina da kujerar da yake kai, Yana sauraron waziri, Da alamun labarta masa yadda akai yau yake. “Ok Kha..Khadija take care.. oh sorry waziri take care!”Katse wayar yayi. Ganin baran-baramar da yayi, Da waziri dayake jinsa tamkar mahaifin sa. MASARAUTAR BASANNABAS (SASHEN WAZIRI) Shima wazirin a nasa bangaren murmushin yai kawai ya ajiye wayar agefe yana kambama yadda SAS yakeson sabuwar amaryar sa.. Ransa a matuk’ar bace waziri ya dubi su Galadima dake gaban sa, “Shin wai me ke tafe daku... Yaro ya riga yayi aure shine kuke son kulla masa wata kitimirmirar? Harda cewa kar a kai amarya sashen kowa? Akan me? Why??” Ciroma ya bude baki zai yi magana, Waziri ya daga masa hannu yana nuna kofa, “Ku fice min a gida, Bana son sakarci.” Mikewa kowannen su yayi, Jiki na bari suka masa sallama suka fita, Gefe suka koma bayan sun fita suka shiga magana ahankali, Sannan suka tafa kowanne ya kama hanyar sa....... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *_ _*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*_ *2___5* *SASHEN MAI BABBAN ‘DAKI* Duk da ta saba jin irin wannan kide-kiden amman na yau yafi karfin tunaninta. Bayan ta idar da sallah ne ta shafa maganin ciwon kafarta tana ta murzawa sai ta kira hadimarta wato Hansatu tace taje ta duba mata hayaniyar me a ke yi a sashen yarima Abdul?Sai da ta mika gaisuwa sannan ta tafi zuwa wajan sauran hadimai tana tambayar su, suka shaida mata da komai wanda suka sani suma. A karamin parlorn ta take a hakimce a doguwar kujera mai cin mutane uku. Kafafuwan ta akan center table. Tana zaune ta dora k’afarta d’aya kan d’aya, Cikin haka Hansatu babbar hadimarta ta shigo kanta a kasa, “Allah ya kara miki lapia da nisan kwana... Na bincika miki, tabbas mai martaba aure ya kara, Kuma a binciken da nayo ba jinin sarauta bace, diyar wani hamshakin dan kasuwa ne, Ance ba yar cikin sa bace yar kanwar sace mai rasuwa...” Mamaki da d'in bin al'ajabi suka cika zuciyar ta, amman har cikin ran Gimbiya Sa’adatu taji dadin wannan zance da Hansatu ta sanar mata, Sai dai ba tasan ko itama amaryar acikin hayyacin ta take ba basu juyar mata dashi ba? Taji dadi kwarai da Salman ya kara aure, Tare da yi masa fatan Allah yasa auren nasa ya zamo mafificin alkhairi.. “Kinfi sanin me yara mata keso yanzu, Kije ki harhada abinda ya kamata ki kai musu b’angaren su.” Gimbiya Sa’adatu ta baiwa Hansatu umarni. “Ai ranki ya dade, Mai martaba baya kasar domin na hangi saman tutar dake nuna alamun yana nan, Yanzun an cireta batanan.” “Dama ai na ita bakuwar ne.. Ina fatan kin fahimta?” “Nagane ranki ya dade. Yanzun zanje na harhada komai da yardar Allah.. Allah ya bamu sa’a! Aamin!” Kwasar gaisuwa tayi ta fice, Ita kuma gimbiya Sa'adatu taja ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai. Addu’oi take ta kamowa a bakin ta tana mai zubar da hawaye ahankali. *SASHEN GIMBIYA SHAHEEDA.* (Uwar-gidan sarki Salman) Duk da ta bawa Dije gudun mawarta mai tsoka hakan be yi mata ba, Gani take tamkar ba tayi komai ba, tana jin kamar yarinyar zata rai na kayan. Amman wani sashen na zuciyar ta yana kwabarta akan karin da take son yi mata cewar ta kyale ta haka tunda dai kowa yasan ita d'in yar gidan basarake ce, mai gogawa da ita sai ya shirya. Ta fara shirya kayan ta da zata tafi gida gobe dan ba zata dawo ba sai da shirin fitar da Dije, wacce tayi gangancin aurar mata miji mafi soyuwa a zuciyar ta. “Ke! Tashi kije ki shirya min kayan da zan tafi dasu ‘Bullo.” “An gama Allah ya taimake ki, kamar kala nawa za'a tanadar miki?” “Karki ishe ni da surutu dan Allah, kije ki hada min na sati daya kacal.” “Toh gimbiyar gimbiyoyi, Allah ya kara lafiya da nisan kwana bari naje.” Mtwww! taja tsaki saboda bacin rai, gabaki d'aya ta kagu gari ya waye ta tafi. Gidan gaba daya ya yi mata zafi, gashi Salman d'in ma baya nan ta kuma kasa samun shi a waya switched-off ake ce mata tun dazu. Lallai tana cikin tashin hankali tunda har Salman ya fara kauda ido akan ta gashi har aure ya fara shigowa tsakanin shi da ita, Shin me ta tsarewa Salman da har yasa karo aure, kuma ma tsabar rashin mutunci ba jinin sarauta ba, a’ah yar riko? Dole ta tashi tsaye wajan ganin ta ruguza auran ya zama ita daya ce tilo a cikin fadar zuciyar shi. Tayi saurin mikewa tsaye ta nufi bathroom da sauri ta sakarwa kanta ruwan sanyi saboda wani irin gumi da taji tana yi. Bata taba zato ko tsammanin akwai irin wannan rana da lokacin da zasu zo ta shiga wannan halin ba, sai gashi auran Salman yasa ta kasa nutsuwa. Kullum a cikin mutane cewa take mijin ta ba zai iya kara aure ba, saboda dalilai guda uku. Na farko baya haihuwa, na biyu baya kallon mutane bare ya kalli mace bayan ita, na uku sam taga alamun Salman bashi da karfin sha'awa saboda sai ya dade be neme ta ba. Hasalima, Itace me takura masa, Wannan sune dalilin da take alfahari dasu na cewa ita kadai ce a gurin mijin ta. Sai da taji zafin da take ji yaki sakin ta sannan ta fito daga cikin ruwan ta daura bathtub tare da dafo bango ta dawo cikin bedroom ta kwanta kan gado tana sakin kuka. _“Sai kayi nadama Salman, wallahi sai ka san ni ka wulakanta a cikin masarautar nan. Ko zanyi yawo tsirara sai na ga bayan wannan yarinyar tunda ka tozarta ni akan ta.”_ Haka ta dinga kuka tana fadar maganganu na neman masifa tana dorawa Khadija. A ranar dai kam haka Shaheedah taga rana dan ko rufe ido kasa yi tayi, idan ma ta gwada rufewa to Dije take hangowa tare da Salman rungume da juna kamar dai yadda suke yi. Kawai ta saki wata kara wacce tasa daya daga cikin hadiman ta shigowa da gudu dan ganin ko lafiya. “Ranki ya dade ki...” Bata bari ta karasa ba tace. “Fita ki bani guri munafuka kawai.” Tun kafin ta rufe baki tabar wajen cike da tsoro, daman tazo gani ne ko babu lafiya ta taimaka mata, ashe lafiyar ce ta ishe ta har take yi musu ihu da kururuwa. Gimbiya Shaheedah ta sake sakin wani ihun a karo na ba adadi tana buga kai akan katifa, gashi ta kagu gari ya waye dan ta tafi gidan su. *WASHE GARI....* SASHEN GIMBIYA KHADIJA. Bayan gari ya waye daman ba bacci na yi ba dan cike nake da tsantsar tsoro ina ganin kamar za'a zo a kashe ni, hakan yasa na kasa bacci ko bedroom din ma kasa komawa nayi nace da hadiman da aka kawo min suma duk su kwanta a parlorn. Suka yi ta bacci sabanin ni ina kwance ne kawai akan kujerar, kuma wacce suka shafa mata wannan makircin nasu, wanda nake da yakinin cewa shine yasa na dinga jin sashen nawa yana wani irin mugun doyi kamar an kashe mushe. Koda na farka wanka nayi na sake pad gashi wani irin bleeding nake kamar wata wacce ta haihu, da yawa dan sai na hada pad biyu tukunna nake samun sassauci wajan bata min jiki da jinin yake yi. Shiryawa nayi tsab cikin riga da zani na lace, bayan na gama shiryawa na zauna ina tunanin nifa amarya ce, wacce ya dace ace ina tare da ango na kusa da ni. Amman har na kwana na tashi ba bu shi ba alamar shi saboda kawai ya auro ni a sadaka. Eh mana sadaka in ba haka ba a aura min shi ba tare da na taba ganin koda kwayar idanunsa ba, dole ya yi min duk abinda yaga dama harda wannan rashin kulanin da ya yi a ranar farko na aure na da ko wace mace take alfahari da shi. “Assalamu alaikum.” Naji an yi sallama, sai na tashi tare da janyo mayafi nasa a Jikina. Fita nayi sai naga Bahijja d'aya daga cikin masu yi min hidima da aka kawo min su jiya, kafin na yi magana ta durkusa har kasa tana gaishe ni kamar zata min sujjada. “Ke tashi menene hakan?” “Allah ya ja da ranki Galadima ne yace azo a tambayi abin da kike da bukata za'a kawo miki.” Naja dogon numfashi kafin na sauke nace. “Allah sarki kice masa bama sai ankowo komai ba, saboda kinga abubuwan da aka zo dashi ga wanda aka kawo wasu suna nan, zan yi amfani dasu kawai.” “Allah ya taimake ki, al'adar gidan nan be kamata ki ci duk wani abu da ya kwana ba, ki fada kome kike so akwai shi a cikin masarautar nan za'a kawo miki, Allah ya taimake ki.” Mamaki ya kamani, koda yake bai dace na yi mamakin ba idan na yi duba da su Yaya Shukrah yadda suke yin abubuwa a gidan kawu daddy tamkar ba fita yake yana nemowa ba. Babu yadda na iya dole na yarda nace a bani duk a binda aka dafa zanci. Cikin sauri ta mike ta fita, na bi bayan ta nima na koma parlorn bayan na toshe hanci na da facemask wanda hakan be hana hancina jiyo wannan warin ba. Ina zaune abin duniya ya yi min yawa kawai sai ga Gimbiya Shaheedah ta shigo sashen nawa, kasan cewar jiya ina cikin alkyabba ban ganta ba sosai. Yanzu da ta shigo sai naji gabana ya yi mummunar bugawa, nayi-nayi dan na janyo koda kalmar Innalillahi ne wallahi naji na kasa, naji ana ta rike min wuya. Babu ko sallama haka ta shigo cikin shiga ta alfarma, kai da ka ganta kasan cewar tasan ta kan mulki ta kuma san yadda ake murza shi. Tsabar na rude ban san lokacin da na diro daga kan kujerar ba na fara yi mata sannu da zuwa. Da mamaki na sai naga ta yi murmushi idanunta yana bin duk wani sashe dake parlorn har ta gama kare masa kallo sannan ta dora da cewa. “Haba Amarya, irin wannan ai sai kija a zage ni a gari.” Na kasa yin magana kai na yana kasa, me zan ce mata bayan ban san matsayin ta ba a masarautar, ba ta zauna ba ta yi taku biyu zuwa tsakiyar parlorn ta tsaya. Alkabbar jikin ta ba karamin kyau ta yi ba, ni kai na sai da ta burgeni saboda tsarin ta. “Zuwa nayi na baki hakuri a maimakon miji na, ranar da ya kamata ace kina tare da shi a lokacin ne ya tafi wata kasar. Kiyi hakuri kinji? Kin san babbar giwa kika aura dole sai kin yi hakuri kinji kanwata.” Maganar nan da ta yi shine ya ganar dani cewar itace uwar gidan sarki Salman. Sai tunani na ya canza akan wanda nake yi mata na cewa kila tana da zazzafan kishi, duk na dauka ba zata so ni ba ashe mummunan zato nayi mata. Fargaba da tsoran kar taji yadda sashe na yake wari suka cika ni, duk da na tambayi masu aikin sunce su basu ji wari ba sai kamshi, toh itama naga kamar ba ta ji ba, dan banga ta rufe hancin ta ba. Naji dadi sosai ganin yadda take lallashi na akan rashin ango, duk kuwa da cewar naji dadi kwarai da baya nan, kuma bana jin idan zai shekara be dawo ba zan damu. Ban tashi daga kasan ba, sai dai na gyara zama na yadda zan yi mata magana sosai, nace mata. “Nagode, kuma babu komai ai tunda ga ku duk muna tare.” Tayi shiru na tsawon wani lokaci duk na dauka ma ba zata kuma yin magana ba, gashi tana tsaye na kuma cewa. “Dan Allah ki zauna kya yi ta tsayuwa.” Nan ma tayi shiru sai nayi tunanin ko ba taji bane? Zan kuma yi mata magana naji ta kalleni tana cewa. “Noooo! Na gode ni ma tafiya zan yi. Ina dad'a baki hakuri dai, zan kuma yi kokarin takura masa ya dawo tunda yasan an kawo ki.” Wannan Karon shiru na yi saboda bana son ganin shi bare nace ina son dawowar shi, ita dai da take son shi sai tayi ta jiran shi, haushi yake bani wallahi. Sallama ta yi min na tashi na yi mata rakiya har kofar parlorn sannan na dawo, hadimai na da suke ta gyaran parlor ga turaruka duk an saka amman ni ko kadan banji kamshin ba. Sai kawai na shiga bedroom tare da hayewa gado naja bargo na rufe duka jikin har fuska wai ko Allah zai sanya na dena ji amma ina, warin yana nan..... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *_ _*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*_ *2__6* Tun da aka yi salla asuba ya dauki motarsa yabar masarautar Basannabas shi kadai ba tare da ya dauki d'an rakiya ba dan baya bukatar hakan, daman haka yake yi idan yaga duk sun kasa ai watar da komai akan sarki Salman. Shi kuma duk duniya babu wanda ya tsana sama da yaron nan, ko baban shi ba ya ja musu rai kamar yadda yake yi musu sai kace wani yayan su. Tafiya kawai yake yi yana jin zuciyar shi tana suya saboda ya yi mamaki kwarai da gaske da yaga Salman ya yi aure ba tare da sanin zai yi ba sai a ranar. Saboda haushi da kuncin da yake ciki besan lokacin da ya tuge rawanin dake kan shi ba, ya wurga kujerar gefen shi. Sai da ya kusa barin cikin kwaryar birni sannan ya yanki wani daji wanda ba a taba halatta mishi kwalta ba. Nan ma ya yi tafiya sosai kafin ya yi parking ya fito, ya fara tafiya a kafa kasan cewar mota bata shiga gurin sai dai kaje a kafarka. Da kyar yake iya takawa saboda ya gaji amman da yake zuciyar shi a kekeshi take sam be ji ya karaya ba har sai da ya dangana da wata yar karamar bukka dake jikin wani katon dutse. Wani hayaki ya fara fitowa daga cikin ta, yana tsaye har hayakin ya dena fitowa sai yaji ana yi masa iso cewar ya shiga. Yana shiga bokan ya kalle shi wanda shi din ma ya manyanta alamar ya dade a cikin harkar bokanci ta bayyana a jikin shi, ya dakko wani farin ruwa karkar dashi a cikin kwarya ya ajiye a tsakiyar su tare da sanya d'an yatsa a ciki, hotan sarki Salman ya bayyana a ciki shida Dije suna kallon juna. Bokan ya sake kallon shi tare da cewa. “Daman nasan dole zaka zo, tabbas aljani kurt ya yi gaskiya da yace min kana cikin bacin rai.” Yaja dogon numfashi tare da shafar kanshi yace. “Yaron ne ya shammace mu, tabbas ya matukar bani mamaki saboda na yi tunanin duk wani sirri nashi a tafin hannu na yake ashe ba haka bane. Tabbas ni da su muna cikin damuwa boka.” Boka ya kankantar da idanuwa yana kallon cikin ruwan yace. “Kayi kyan kai da kazo tun da wuri, ina tabbatar maka da ka bari sai anjima to babu abin da zan iya yi maka. Yanzu me kake so a aiwatar maka?” Sai da ya kuma jan wani numfashin sannan ya gyara zama yana cewa. “Kamar kullum dai, ina son a cire masa son mulkin Basannabas. Sannan yaji ya tsani komai dake cikin duniyar nan, a kawar da hankalinsa daka kan komai har sai abin da muka zartar masa.” “Kenan kai baka da matsala da wannan yarinyar da ya auro ko?” “Bana jin zata iya hanani aiwatar da duk abin da naga dama, shi yasa banji ta dameni ba kamar shi da ya yi mana wannan kitumurmurar.” Boka ya buga kasar dake gefen shi, sai ga wuta ta fito ta tsakiyar tana ta ci. Sannan ya kalleshi yace. “Kayi zaton wuta zata fito daga cikin nan?” “A a boko ban yi zaton zata fito ba, kawai ganinta nayi.” “Toh idan kayi wasa haka yarinyar nan zata zame muku. Kana daukar ta karamar alhaki, ita kuma za ta yi amfani da damar ta na matsayin matarshi ta tarwatsa ku gabaki d'aya.” Mamaki ya kama shi, nan da nan kuwa yace yana son ayi aikin har akan ta. Taji ta tsani mijin nata, kuma bata son ganin shi ko jin muryar shi. “Shikenan zamu fara yin aikin ka yau bayan rana ta fadi. Karka damu kanka kayi bacci mai dadi kasa a ranka anyi komai an gama.” Jijjiga kai ya yi sannan ya ajiye masa wata bakar jaka wacce da alama muhimmin abu ne a ciki, daga nan suka yi sallama ya tafi shi ma boka yaci gaba da aikin sa. Sai da ya shiga mota sannan ya dauki rawanin sa ya mayar kasan cewar ya dan fara jin sassauci akan kuncin da zuciyar shi keyi. Ya koma Basannabas yana jin wata iska tana shigarsa ta ko'ina. *KOFAR KUDU* (SASHEN GIMBIYA KHADIJAA) Ina zaune na rafka uban tagumi ina kallon tv, Yanzu bataliyar yayan uncles dina suka tafi, Kowanne zai dauki iyalin sa su kuma garin su. Duk cimar da aka kakkawomin ne nide na tarkata na babbasu, Na harhada da wasu kayaiyakin na cikin lefe na. Sai tsaki nake jerawa saboda zaman kadaici... Bahijja d’aya daga cikin hadimai dake tayani zama ta shigo kanta a kasa tana murza hannaye, “Uwar daki na.. Allah yakara miki lapia gimbiyar mu. Ummah Hansatu tace na mata iso zata shigo an aikota..” Cike da farin cikin zan sake ganin mutane atattare dani na daga kai da sauri ina nuna mata da hannu alamun nabata dama. Facemask dina na zare ina sake baje kofofin hanci na.. Tabbas warin nan yana nan, To ko dai wani abunne ya shigo ya mutu? Ko bera ne? Na tuno idan jaba ta mutu a dakin da nake kwana a k’auyen mu haka wurin yake tashi . Ina sanye cikin atamfar super wax, Amber color, Tasha surfani da stonework. Santsin da gashi na yake shi yasa ban daura dankwali ba, Na yafa mayafi a kai na. Bahijja ce ta rako matar da ta kira da ‘Ummah Hansatu..’ Dattijuwar mata ce amma bata manyanta can ba. Wasu yammata ne abayanta kowacce tana janye da akwatuna, Har guda 5 da baskets baskets. Da kumbuna suma cike da kaya. Yammatan suka futa, Ita kuma ta zube a gaba na tana kwasar gaisuwa. Ta kark’are da, “Ga kaya nan... Inji mai babban daki..” ‘Mai babban daki....? Bayan kayayyakin da suka babbayar?’ Tamkar tasan maganar da nake a zuciata. Tace, “Mai babban ‘daki itace mahaifiyar sarki Salman.” “Okay! D’aya daga cikin wanda naje na gaisar jiya..?” “A’ah! Anya kuwa? Ranki ya dade. Jiya gaba d’aya ba wanda ya shiga sashen mu. Amman dai ga sako tace akawo miki..!” Kai na ya k’ulle. Kwarai matuk’a na kasa gano wacece mai babban daki.. Tunda dai har su uku naje na gaisar, To wacece acikin su. “Sunana Hansatu. Amma yara da tsirarrun mutanen masarautar nan na kira na da Umma Hansatu. Nice babba a hadiman me babban daki, Kiyi min afuwa tun jia naso kawo kayan nan. Amman ban gama hada su ba...” “Toh nagode sosai Umma Hansatu. Ayiwa mai babban daki godia, Da yardar Allah zan shigo Na gaishe ta.” “A’ah ki kara hutawa ranki ya dade. Allah ya huta gajia, Na barki lapia.” Ficewa tayi bayanta rissina ta kwashi gaisuwar ban kwana, Ta fice kanta a kasa. Naja tagumi na zanga shi ina taune lebe na. ‘Shin wacece mai babban dakin to? Ita kanta Ummu Hansatun bata wayar min da kai ba.. Kila ba’acikin masarautar take ba, Wata zuciar tabani amsa. Na sauke ajiyar zuciya ina kallon tilin kayan da suka kusa shanye rabin royal center carpet din dake malale a tsakiyar parlor na. Ni gaba d’aya abubuwan su sun fara bani tsoro, Haka ake kyauta kamar ba’ason kudin? Kowa idan ya tashi sai yayi bajinta? Shiyasa naga Kawu daddy kenan su Mami nata gulmar wai kayan garar da yasa akamin wai Ko na yar shugaban kasa albarka. Ashe yasan irin gidan da zan shiga? Mikewa nai daga kan kujerar da nake na koma daki, Bandaki na shiga na canza pad. Jinin sai kwarara yake tamkar dai sabon period. Dama kwanaki uku nake, Gashi jiya ya dawo min idan na hada da na yau kwana har 5 kenan. Kila circle din nawa ne ya canza, Wata zuciar tacemin. Sabuwar waya ta na kunna da Kawu daddy ya bani. Dake sabon sim ne du babu contacts dina na da aciki. Siririn tsaki na saki, Na rasa mai zanyiwa zucia ta taji dadi. CYPRUS (HOTEL——NICOSIA) Bluetooth ne a kunnen sa ya hada hannuwan sa waje d’aya yana dan bubbuga su. Magana yake a hankali cikin nutsuwa, “Okay! Nagane.. No no issokay. Go ahead! Wai dole seda yadda na.. ? Huh! Toh approved!...Waziri na baka wuk’a da nama.. Yauwa! Jia nayi mafarkin mun kusa haduwa dashi fa...Ah’ah I.. Ah..” Kasa furta sunan yayi. Gashi yanajin sunan a zuciar sa, Amman labban sa sun gaza furtawa. Yayi yayi ya kasa, Kawai ya katse wayar yana mai dafe kansa, Ji yayi wani irin yanayi na neman kamashi. Alhassan ya kira a waya ringing biyu ya dauka, “Yauwa Alhassan.. Nace a fara ginin nan. Zanen farkon nan yayi. Su fara. Ba tsayawa please.” Kit ya katsa kiran. Gallery din ipad dinsa ya shiga, Zanen wani gidan bene ya shiga kalla yana murmushi. Ginin benen za’a fara yin sa ne. A gefen sashen sa daga baya. Gida ne wanda ya barwa kansa da Alhassan amanar yin sa. Sai angama shi tas. Sannan zai sa a maida Khadija cikin sa. Murmushi yai yana tuno sanda yafara ganin ta a wajen sauka. Bai sake mata gani na biyu ba har yanzu da take a matsayin matar sa. So yake yaji koda muryar tane amma izzar sarauta ta hanashi. Ya tsotsi kasan leben sa yana hasaso Kyakkyawan fuskar ta. Jingina yai a jikin kujerar sofa da yake. A hankali yake furta, “Cute! Brave little lioness..” “Your majesty... Itz time! Your majesty! Your majesty..! Your majesty.!” Firgigit ya tashi daga duniyar tunanin Khadija daya tafi. Kallon baturen yayi, Wanda escort dinsa ne na wajen taron da za’a tafi. “Pardon...!” Cewar sarki Salman yana sake hade rai tamkar ba shi ne ya lula duniyar tunanin mace ba. “I said.. Itz time, Thrice!” “My bad.. Lead d way!” Ficewa sukai, Suna gaba yana biye dasu baya. Cikin kayan sarauta da rawanin sa mai kunne biyu. Designer shades din dake idanun sa ya sake amsar kayan jikin sa. Tafiya yake cikin k’asaita , Matashin sarki mai jini a jika. Mai madaukakin kwarjini da hasken annuri. Har kujerar da zai zauna sai da suka Kai shi, Dogaran sa guda biyu na gaban sa. Kujerar tasama wadda zai zauna ta alfarma ce mai dauke da tambarin ...’His royal highness ‘Emir of Basannabas. Salman Aliyu Salmanu. (SAS), Kowa sai da ya rissina masa, Guri ya dau shiru na yan mintinan girmamawa. Wani zama yai na sarauta. Ya mike kafafun sa akan table din gaban sa.. Ta cikin rawani kuwa jan leben sa yake. Kunnen sa d’aya da bluetooth yana sauraron voice-notes din da Galadima ya turo masa kan lalle abunda zai ce kenan idan jawabi yazo kansa... *MASARAUTAR ‘BULLO...* (FADAR MAI MARTABA SARKI IBRAHIM HASHIMU) “Shin fulani da sanin mai gidan ki kikazo nan...” Cewar sarki Ibrahim mahaifin gimbiya Shaheeda. “Bappah na kira shi sau ba adadi bata shiga, Nagaji da wulakancin da yake min. Bappah ace zaiyi aure amma bansani ba?” Gimbiya Shaheeda ta karasa fada tana kecewa da kukan makirci. “Ya isa! Bar kuka.. Ni nasan Salman bai isa ya tsallaka karan dasu Galadima suka ajiye ba. Sai dai idan wata kullalliyar aka shirya..” “Bappah suma wai acewar su Gimbiya Najwa diyar sa tace ko shi galadiman bai sani ba, Sannan ko ciroma bai sani ba shima. A tak’aice dai Bappah bawanda yasan da auren da yayo.. Sai dai idan Sa’adatu ce (mahaifiyar SAS)” “Itan da ko kallo bata isheshi ba? Kai akwai kullalliya dai..” “Ko ni Bappah ca nai sai dai idan ita yarinyar ce tayi asiri. Domin Salman ko kallo mutane basu isheshi ba.. Kuma Bappah yar rik’o ce fa. Ashe ba shine mahaifin ta ba.” “Eh haka naji labari da nasa akamin bincike. Kiyi hak’uri. Mu dai burin mu baya w...” Kasa karasawa yai sakamon yadda matar sa ta shigo tana baza kamshi sai rausaya take, An girma ba’asan an girma ba. “Yar baffan ta ashe kina nan...?” Cewar Gimbiya Asma’u (Matar Sarki Ibrahim ta farko. Mahaifiyar su gimbiya shaheeda.) “Ina nan Hajia...” “Ranka ya dade. Afuwan zan dau fulani na yan wasu mintina. Akwai masu jira awaje, Su magatakarda, Da shamaki, Da. dokaje.. Naga jakadiya Yaruwaiyya sai tare-tare, Nasan dai badan ta tsare ka da surutu ba aida kana tare dasu.. Fulani tashi muje, Allah yakara maka lapia, Bari muje.” Bakin sarki Ibrahim a hangame suka fice, Sai murmushi yake kaman sabon tabi. *SASHEN TORO BABBA* (GIMBIYA ASMA’U) Suna komawa gimbiya shaheeda ta zube a kujera tana yatsina fuska, “Shikenan na zama kaskantacciya kenan Hajia? Shikenan na zama bani da gata kenan? Hajia kuna raye har Salman ya kara aure? Bayan alkawarin da kika yimin na dagani ba ‘kari? Kwata kwata shekara nawa da auren namu? Amma harya kara aure.” “Ya isa haka Fulani.. Kibi komai a sannu, Ta karkashin kasa zamu bi. Yadda ta shigo haka Zata fita. Da gundumemin sharri ma kuwa, Bazata koma gidan su ba sai da tabo. Malam na gangare ya tabbatar min da hakan. Ba zaki koma ba sai da boma boman harka..” “A hayye.. Hajjaju tawa..” Karaf suka tafa suna shewa.. “Kince plan 1 dinku yayi har kin ganta da mask ko?” “Eh hajjaju. Amma fa kyawunta ya tsorata ni, shegiyar akwai yalwar gashi da jiki mai kyau. Too bad yar talakawa ce. Dana rena kai na..” “Haba wa ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, Uta din banza? Yadda ta shigo da tsunmomaran kayanta da jikin ta haka Zata fita dashi da dankwalelen tabo ma kuwa..” “Hajjaju na.. Shiyasa kike sake shiga can cikin zucia ta. Ta gaban goshin Bappah, An buga dake an barki ya zasuyi dake..?.” “Farin wata...” “Sai kallo Hajjaju na.. Ki da’de kiyi karko.” “Kome zasu kitsa miki, Ki bar su a haka..Kuyita tafiya a haka. Muga gudun ruwan su.” “Ai dama bana nuna komai, Kome suka ce yi nake.” “Yauwa sai da kwantar da kai... Ina Sa’adatun kuma?” “Oho mata wallahi... Tana sashenta a yashe..” Dariya suka shiga babbakawa a tare, Tamkar masu tabin hankali.... Suna yi Suna shirya surkullen da Shaheeda Zata tafi dasu Masarautar Basannabas. Wanda gaba d’aya duk na kauce hanya ne. Haka bokan nasu yazo, Shima da tulin layoyi kowace laya da allura ajikin ta guda 99. Da barkono tsidugu guda 7 an rubuta sunayen Khadija akai. Ta kona kowanne guda d’aya sau bakwai. Kowanne da ranar sa, Da sauran abubuwan kauce hanyar da bazasu lissafu ba........ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *_ _*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*_ *2__7* *MASARAUTAR BASANNABAS* Bayan waziri sun gama waya da sarki Salman, ya tara manyan yan majalisa ya sanar dasu abinda suka tattauna. A take kuma ya dauki wayar ya kira Gimbiya Huwaila cewar ta kira babban d'an ya dawo za'a mishi mukami, ta amsa tare da katsewa har da rawarta a cikin bedroom. Bata wani jira ba ta kirashi kusan sau biyar sannan ya yi picking , dan kar ma ya tsaya bata lokaci ta sanar dashi sakon waziri, cike da murna kuwa yace gashi nan zuwa. *SASHEN GIMBIYA JALEELA.* Gabaki d'aya ta rasa inda zata sanya kanta taji dadi, tunda Gimbiya Huwaila ta sanar da ita sakon Waziri hankalinta yake a mugun tashe, tabbas tasan duk cikin su itace ke cikin siradin rayuwa saboda rashin samun ‘da namiji. Ta juya tare da kallon yaran nata, wani madacin abu ya tokare mata wuya saboda bakin ciki, yanzu duk gidan wani zasu tafi su barta, babu wanda zata yi iko akai sai dai ayi mata iko da su. Ba abin taje ta kai kukan ta wajan mahaifinta ba sam ba zai saurareta ba, yana matukar yi mata kokari wajan ganin ta kwantar da hankalinta, hakan yasa ba ta fiye kai kuka gurin shi ba, gara taje wajan Galadima ko Ciroma ko kuma Wambai. Mtwww ta kuma jan tsaki a karo na ba adadi, ta kwalawa yarta Sabeera wacce tana ji amman ta yi shiru taci gaba cin abincin ta. “Baki ji ina kiranki ba ne Sabeera?” “Haba Mah gani ga ki amman ace ki ta kwalamin wannan uban kiran, gani ai duk abinda zaki fada zan ji ki.” “Kunsan dai komai zan yi akan ku ne, so nake naji wai har yanzu kuna tare da d'an gidan vice- president d'in nan kuwa?” Sabeeera ta yatsina fuska sam bata son yaron nan saboda yaudara gare shi ta masifa, akwai wanda ita take so kuma shi sai wahalar da ita yake yi yana ja mata rai. Ta ture plate din gafe tare da kallon mahaifiyar ta tana cewa. “Wallahi Mah ko maza sun kare ba zan auri Kamal ba, yaran nan mugun dan iska ne.” “Toh ke ina ruwan ki da iskancin shi? A jikin ki zaki yafa ko kuwa? Ni a gani na kuna yin aure zai dena. Yaron nan gaba baban shi ne zai rike mulkin kasar nan, ki zama first lady me ye na cewa ga aibun shi Sabeeera?” “Ni wallahi bana son Kamal Mah, bana son shi I hate....” “Ya isa karki karasa, abin da nake nufi s....” Ganin mahaifiyar ta na nema takura mata sai ta mike ta bar mata gurin. Gimbiya Jaleela ta dafe goshi, ita kuwa ta shiga uku, ba magajin sarki ga yaran nata mata duk sai a hankali, idan ta taro wannan sai waccan tayi can gurin. Dole ta mike ta dauki alkyabbarta ta nufi wajan Gimbiya Sa'adatu ranta a d'an bace. Bayan an yi mata iso ta shiga ta tarar da ita a kishingid'e, ta nuna mata gurin zama amman ta girgiza kai alamar bata bukatar gurin zaman. Sai da ta dade tamkar ba zata yi magana ba sannan tace. “Kina ganin kinyi sa'a a cikin rayuwarki ko? Saboda kin haifi yara maza zaku gaje masarautar Basannabas. Toh wallahi bari kiji, idan har shegen abokin danki ya auri Sabeeera, na rantse da Allah sai kunyi nadama. Nasan duk wani makirci daga gareki ne na sani, toh ko da bokan ki kike yawo na fiku wulakanci da rashin mutunci. Sa'adatu ina son duk wani abu da ya shafeki kar ya kuma rabo ni, idan kuma kin ki uhmmm.” Gimbiya Sa'adatu ta yi kasa da kanta, bata gane abin da duk Jaleela ke magana ba, sannan ba ta san a cikin ya'yan nata wanne take nufi ba, sai kawai ta shiga bata hakuri cikin karya wuya. Jaleela ta kada alkyabbarta ta fita, yayin da Sa'adatu ta girgiza kai tana nemar musu shiriya idan suna da rabo. Sun ki su barta taji da damuwar da take ciki. Da sunyi abubuwan su suka ga babu nasara sai su takura mata cewar ita ce ta yi musu wani abun. Juyawa tayi taci gaba da yin hailalarta tare da neman Allah ya shiga cikin lamarin ta dana yaranta. *BAYAN WASU AWANNI....* *Kishingide* Gimbiya Sa’adatu take, Lokaci zuwa lokaci hawaye kan kwarara a kyakkyawar fuskarta. Yar dattijuwa ce wadda bata manyanta can ba. Kana kallonta kasan akwai jin dadi a tattare da ita, Amman rashin kwanciyar hankali shi ya mai data ta dan rame ta idanuwan ta manya suka kara furfitowa. Fara ce sol tamkar ita tayi kanta. Kallo d’aya zaka mata kasan tanada manyan kyau. Sai dai ace tubarkAllah kawai. Domin Allah yayi mata zatin halitta. Ahankali tasa hannun ta toshe kunnenta d’aya saboda yadda sautin bushe bushen algaitu ke tashi ta ko’ina a masarautar. Da alamun wani babban taro ko nad’i za’a yi. Amman batada masaniya ko kadan. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Bayan ta bawa hadimarta izinin shigowa, Hadimarta ce ta shigo kanta a kasa. Gurfane tayi awajen bayan ta kwashi gaisuwa, “Uwar daki na.. Allah yakara miki lapia da nisan kwana..” “Aamin Khairat!” “Uwar daki na.... Yarima ne yace na masa iso wajen ki.” “Ahh! Na baki dama. Hanzarta ki shigo da shi.” Shigowa yayi sanye cikin manyan kaya na sarauta, Kansa yasha rawani me kunnuwa biyu. Kana kallon sa kasan tsatson gimbiya Huwaila ne. Domin kamar su d’aya tamkar dai tayi kaki ta tofar. Sede shi dogo ne sosai ya dakko zubin tsayin marigayi Aliyu Salmanu, Mahaifin su. Yana shigowa gaban ta ya yanke ya fadi. Domin batai zaton Abdulqadeer bane, Ta dauka wani ne daga cikin yaran dai. Gaba d’aya sai jikin ta ya nemi d’aukar rawa, Ta shiga kalle kalle tana duban ta ina zata hango shi.. Murmushi yai irin na gefen bakin nan kafin ya shafi kasan rawanin sa inda gemun sa yake. “Ammi... Ni baki farin cikin gani na bane?” Muryarta na rawa ta girgiza kai da saurin gaske tana mai neman saisai ta zuciar ta dake barazanar fad’owa saboda tashin hankali tace, “Abdulqadeer! Barka da dawowa!” “Hmm! Kamar gaske! Barka kadai Ammi, Fatan na same ku lapia?” “Alh... Alhamdulillahi!” “Khal ko?... Nasan Khal kike begen gani. Well long story shot, Yace bazai zo ba. Wannan karon ma yace bai da ra’ayi. Ko fa sunan ku na kamo masa ca...” “Ya isa Abdulqadeer! Ya isa dan Allah.” Tai saurin katse shi tana dartse hakoranta. Wata shegiyar hamma ya saki kafin ya mike yana duba hadadden agogon hannun sa, “Sarauta za’amin fa.. Tunda wancen juyan baya haihuwa. Kuma idan akace za’a raba shi da kujerar zai iya rasa ransa saboda mayatar so. Anyways yau dai za’amin nadin hakimci. Na manyan yan majalisar sarki, Nasan ba wani sani kikai ba, Tunda ba gada ki kai ba, Well.... Uhmm! Kowacce fada akwai manyan yan majalisar sarki da duk harkar data shafi fada sai an dama dasu, Duk wata sarauta ko wani nadi bayan ta manyan yan majalisar sarki, To suna ne kawai domin sarautar sunan ta ta taka haye bata gado bace.. Kamar irin su shirmen mukaman sarkin kofa haka ko... Kingane?” Murmushi kawai tayi, Saboda tasan zuwa yayi kawai ya tada mata da hankali kuma ya ci mata mutinci. Tunda ya tabo mahaifin ta yanzu( Marigayi Malam Abdullahi( Dogari/Sarkin kofar kudu). “Nagane.. Kuma nagode.” “Yauwa...So za’a bani hakimcin waje.. Babban hakimi/Makaman Basannabas.” “Allah yabada sa’a Abdulqadeer!” Ya sheke da dariya yana kureta da idanu, “Anya.. Anya har zuci wannan adduar take? Saboda zaki so ace Khal ne keda wannan mukamin ko? Wait ai da yazo kila shima abashi dallatu haka.. Koya kikace Ammin mu ta mutunci?” Shiru tayi tana maida kanta ga shiegegiyar talabijin din dake nuna wani wasan kwaikwayo na india, “Toh bara na kyale ki haka. Sai gani na biyu.” Mikewa yayi ya fuce yana murmushin mugunta. Yana fita ta bada damar a kulle mata kofar sashen ta. D’akin ta ta koma ta bude shafukan kuka tana jijjiga kanta, “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yaa Allah! Ka shiga lamuran mu. Astagfirullah! Allah na tuba..” Kuka kawai take na tsantsar tashin hankali, Ace babban d’anta ne sarki, Amma batasan komai na harkar mulkin sa ba? Shi kansa ba tada ikon ganin sa. Sauran yan uwan sa da zata kalla tadanji dadi suma ana neman mata katangar K’arfe tsakanin ta dasu. ? Shin wa zata gayawa damuwarta a duniya taji sassauci. Kirjinta cike yake da damuwa kala-kala. Gashi batada wani dan uwa da zata tunkara da maganar... Ranar gabaki d’aya a daki ta wuni tana kuka, Sannan tayi nafilfili tana mai rok’on Allah daya sassauta mata kangin rayuwar da take ciki da iyalin ta..... <><><><><><> *KOFAR KUDU...* (SASHEN GIMBIYA KHADIJAA) Yan kwanakin nan gaba d’aya a hargitse nake, Cikin bacci zan farka na shek’a da gudu nayi wajen kofar parlor, Gaba d’aya ko’ina na sashe na tsoran sa nake. Ji nake tamkar ana kiran sunana. “Wayyo Allah na! Wayyo Umma na, Wayyo Bappah na... “ Na rufe kai na da hannaye na ina hawaye. Gaba d’aya yanayin da nake ciki yana da wuyar fassarawa. So nake na bude kofar na fita, Kashedin Kawu daddy daya min ranar da Za’a kawoni kan cewar Kar naje ko’ina sai da izinin mijina, shine yake hanani tafiya. Tunda nazo bana fita, Sai rakiyar baki zuwa bakin kofa, Gashi yanzu kwata kwata ba’kin ma sundena lekomin tamkar anyi ruwa an dauke. Razana nake yi, Jiki na sai kakkarwa yake. Da dare yayi shikenan bani da sukuni, Sai fargaba. Wallahi na tsani masarautar nan da abunda yake cikin ta. Ni dai gwanda zaman kauyen mu na durbun sau dubu, Da kuma zaman gidan Mami wallahi. Akan masarautar nan. Kwanciyar hankali ? Bacci mai dadi? Ina tuntuni nayi sallama dasu, Na nemi farin ciki na rasa, Saboda tsabar tashin hankali wallahi ko wayata bana dauka, Gashi jinin nan sai zuba yake. Ni na rasa wane irin period nake? Tabbas don ina cikin tashin hankali ne shi yasa bai tsaya ba. Ina tsaye har akai assalatu. Na koma kan kujera na rakube ina jiran gari yayi haske. Ina tsakure a kujera har gari yai haske. Bandaki na shige nayo wanka. A tsorace na zura kaya na fito da gudu daga dakin na koma dayan parlorn, Naja tsaki lokacin da na jiyo kirarin dogarai suna yiwa SAS, Ta sashe na suka wuce lambun sa, Nayi Allah ya isa tafi dubu. Na tsane shi, Na tsani mai kiran sunan sa, Na tsani abunda ya dangance shi. Ni wallahi zaman gidan nan tamkar akan kaya nake. Shima bai damu dani ba, Tunda yai tafiyar sa har ya dawo baitaba nemana ba ko da awaya. Babu ruwan sa dani, Duk yadda akai ya aure ni ne ya tarwatsa farin ciki na ya raba ni da Mas’oud.. Allah ka bimin hakk’i na.. Ina zaune na jiyo duriyar dawowar su, Hasken kyalli kyallin lemar sa da ake dagawa har ta window na. Zuciya ta amsa dai dai lokacin da shi da fadawan sa suka wuce.. *SAS* Tun wucewar sa ta farko yake son ya shiga sashen nata, Amma gangar jikin sa ta hane shi, Gaba d’aya tun ana’i washegarin ranar da zai dawo daga cyprus ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali, Haka kawai yaji tamkar an zare masa ita aransa, So yake yayi tunanin ta ya kasance da ita amma tamkar an musu katanga da juna, Tana zaune a masarauta inda yake amma kamar ba matar sa ta sunnah ba? Hawaye ne suka shiga reto ta cikin gilashin sa, ‘He badly wants her by his side... Amman yarasa meyasa duk lokacin da zai so ganin ko da fuskar tane sai yaji tamkar an hanashi ya kasa. Gashi ginin da yasa ana mata sai nisa yake yi. An kusa kammala shi abunka da masu nera, Kwana akeyi ana aikin gina shi... Wayar sa yar karama ya janyo a drawer k’irar torchlight, Haka kawai ya tsinci kansa da kiran kanwar kakan sa, Gwaggo Ta fada (Haj Hajara Ibrahim).. Kiran ta yayi.. Sun jima suna magana kafin ya katse kiran yana mai dafe da kansa. Ita ba acikin masarautar take ba, Tana cikin gari gidan ta daban. °°°°°°° °°°°°°°° Cikin kwanaki kalilan mahaifiyar Shaheedah ta kammala tanadar mata da duk abinda zata tafi dashi, daman tun tuni suka fara aiwatar da wasu abubuwan. Ganin ta gama samun komai yasa ta fara shirin dawowa Basannabas, taji gaba daya ba zata iya yin sati daya da tace ba. Gashi daman taji labarin dawowar Salman. Haka ta biyo jirgi ta dawo, bata bi ta kan sarautar da aka yiwa Abdulqadeer ba burin ta kawai ya zata raba wannan auran na Dije da Salman dan shine kawai tashin hankalinta. Jakadiya tasa aka kirawo mata wato Zainabu Abu, ita kadai ce Jakadiya a cikin Basannabas, sauran guda biyun duk ba'a neman su an jinginar da su basu da wani amfani sakamakon duk tafi su iya kai gulma da hada gwarama tsakanin duk wanda tasan yana neman bayan d'aya. Tsaye ta tarar da ita sai zagaye take a tsakiyar parlorn ta, cikin sauri ta kai guiwarta kasa tana gaisheta cike da kaskantar da kai. “Sannu da dawowa farin cikin sarki Salman, takawarki lafiya Gimbiyar Gimbiyoyi, kowa ya yi kewarki a cikin masarautar nan, sannu da dawowa uwar daki na.” Shaheedah ta lumshe ido tare da dauke kai daga kallon Jakadiyar tana cewa. “So nake kije kiyi min iso wajan mai martaba yanzu.” Jakadiya ta yi jimmm! Saboda a yanzu babu ta yadda zata iya zuwa gurin Salman, kafin ya shiga cikin daki ya shaida mata baya son ganin kowa yau ya gaji yana son ya huta, yace komai ake da bukata a sanarwa Waziri tunda yana cikin fadar shi kam a barshi. “Baki ji abin da nace bane Jakadiya?” Sai ta daburce ta rasa yadda zata yi mata bayani saboda tasan Shaheedah idan ta kwallafa rai akan son ganin Salman, to da kamar wuya taki ganinsa, dan ko da bala'i ne sai sun hadu. Baki na rawa tace mata. “Ranki ya dade mai martaba yace dani karna shiga inda yake, yace koma menene a je a sanarwa Waziri.” “Mtwwww zan cen banza zancen wofi, to ni ba waziri nake son gani ba, shi Salman din shi zan gani bayan ya gama fito da abin da yake boyewa? Meye na cewa babu wanda zai gani saboda rainin hankali.” Ita dai Jakadiya ta kasa magana, ran Shaheedah ya kuma baci tace. “Ki tashi ki bani guri, tunda ke baki san yadda zaki yi naje gurin sa ba.” Jakadiya ta bar sashen tana ta bata hakuri. Aikuwa Shaheedah ta kira mahaifiyar ta cikin tashin hankali ta sanar da ita cewa ta kasa haduwa da Salman yace baya bukatar ganin kowa. Ta shiga kwantar mata da hankali tare da shaida mata cewa ta bari za ta yi wani aiki a kan lamarin. Ai kuwa kafin wani lokaci sai gashi sarki Salman ya kirawo Shaheedah a waya yana shaida mata ya dawo amman zai huta ne zuwa wani dan lokaci, yanayin da taji muryar shi ne yasa taji zata hakura da zuwa inda yake har sai ya huta zata ji zai ma fi gane abin da zata sanar dashi. Ta koma wani daki inda ta ajiye kayayyakin da ta zo dasu, ta dauki wani abu a cikin wata yar tukunya, ta zuba a borner, aikuwa dakin ya dauki hayaki mai kauri, ita kam ko a jikinta. Alamun warin baya damunta sam-sam. Misalin karfe uku na rana ina kwance a kan gado ina bacci cike da jin dadi, kawai naji kamar ana tashi na, na yi juyi kafin na bude ido a hankali. Babu kowa hakan yasa na kuma gyara kwanciya ta naci gaba da yin bacci na harda murmushi saboda tsabar dadi da ya yi min. Sake tashi na naji anyi wannan karan amsawa nayi. “Uhmmm....” Abin mamaki ba a dena tashi na ba sai da na tashi da sauri ina buge hannun da naji yana tashi na akan kafada, a fusace nace. “Wai meye ne?” Na bude ido fuskata da alamun bacin rai, abin da na gani shine ya sani sakin wata gigitacciyar kara tare da sakkowa daga kan gadon na fito da gudu sakamakon wata irin halitta da na gani a kusa da fuskata. Bakikkirin ne gashi d'an guntu, ma'ana wada ne, hakoransa zako-zako, idanuwa jajur kamar wanda aka zubawa barkono. Hadimai na sai taro ni suke yi ina turo su ina faman ihu kamar wata zararriya, koda yake zarewar nayi tunda naga halittar da ban taba gani ba a rayuwa ta. Ganin ina shirin fita daga cikin sashe na yasa duka suka rike ni da karfi suna tambaya ta abin da yake faruwa. “Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun, yana daki na wallahi aljani ne. Na ganshi da ido na.” “Subahanallahi ranki ya dade Kodai sharrin mafarki ne? Amman duk muna parlor bamu ga wani abu da ya shigo ba.” “Daman nasan haka zaku ce, na tambaye ku kuna jin wari kunce a'a, a karshe a gabana kuka sake gyara jeran aka goge ko'ina. Still ban dena jin warin nan ba kamar na mutuwa. Yau gashi ina bacci an je an tashe ni naga abin da na gani kunce min babu komai mai koke tunani toh? Zan yi karya ne ko zan yiwa wani sharri?” Duk sai suka yi shiru kansu a kasa, sai da daya daga cikin su tace. “Ranki ya dade kiyi hakuri ki koma ciki kafin mutane su ji a fara surutu. Zamu dudduba mu gani ko meye zamu fito dashi.” Naja gwauron numfashi tare da saukewa a hankali, ta ya zasu gane yadda nake ji a cikin gidan nan? Koda yake kila dan na kasa kwantar da hankali na ne shi yasa bana jin dadi har nake ganin wadannan abubuwan. Da kyar na iya daga kafa na koma ciki amman sai na zauna a parlor, suka shiga suna ta dube-dube ko zasu ga wannan abun da na gani amman babu komai. Na dinga girgiza kai cike da takaici, kamar na ce su nemo min lambar Salman dan ji nake tamkar na zazzage shi, amman sai naji nauyin haka, ace kamar ni bani da lambar shi sai na fito na samu? Kuma idan ya dauka me zance dashi bayan ko muryarshi bana son ji....?! ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). * *KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASA* *28....* _*KIBIYAR AJALI.....!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🏹🥰😍 *MASARAUTAR BASANNABAS* Shi kuwa sarki Salman yana daki ya rasa abin da yake yi mishi dadi, jikinsa ya yi zafi rau kamar wanda ake gasawa cikin oven haka yake ji. Manyan rigunan da yasa basu ishe shi ba ya kara da barguna a jikinsa nan ma beji sassauci ba, sai karin zafin da yake ji. Wani irin kuka ya saki mai cike da rauni saboda Allah kadai yasan yadda yake ji a jikin nasa. Kukan da tsuntsaye keyi a saman dakin kuwa, ji yake kamar yana tsakiyar mai Dj, karar ta yi masa yawa sai rike kai yake yana juyi akan gadon. Bakin sa yana rawa ga kuka mai sauti da yake yi yana cewa. “Wayyo Allah na.... Wayyo Allah ka tausaya min wuta jiki na zata kona ni... Wayyo ni.” Magana yake yi tamkar yana yi da wani a kusa dashi, sai faman nishi yake yi yana juye-juye. Har dare ya yi bai fito ba, hakan ne ya d'an bawa dakarunsa na kofa mamaki, anyi magariba bai fito ba, ga isha'i anyi still basu ji koda motsin shi ba, sai suka fara tuhumar kansu Anya kuwa lafiya sarki be fito ba? Tunda suke dashi basu taba ganin ya yi haka ba, ko ciwo yake yi yana kokarin yin sallah amman yau shiru. Kasa shiga suka yi saboda tsoran kar wani abu ya same shi, sai daya daga cikin masu tsaron kofar ya tafi ya sanarwa waziri. Kusan a tare suka isa sashen nashi, waziri da shamaki suka shiga suna mika gaisuwa gareshi. Babu kowa a ciki amman kan gadon an jibga bargona, waziri yasa hannu ya d'an daga bargunan kawai suka ganshi sai rawar sanyi yake yi. “Subahanallahi, Allah ya kara maka lafiya ba ka da lafiya?” Sarki Salman ya kasa komai bare ya yi musu alama, Waziri ya kalli Shamaki cike da tashin hankali yace ayi maza a kirawo likita yazo ya duba shi. Kai arziki kashi kafin kace kwabo sai ga likita da kayan aikin shi, ya shiga duba shi ta hanyar yi masa gwaje-gwaje. Amman babu abin da ya gani, sai dai ya yi masa allura wacce zata dauke masa zazzabin. A lokacin ne daya daga cikin fadawan sarki Salman ya yi sallama daga nesa yace dasu Gwaggo Hajara wato gwaggo ta fada tazo tana so a yi mata iso ciki. Ba karamin mamaki sukai ba da jin zuwan ta, suka fara tambayar kansu me ta zo yi a daren nan? Sai dai babu mai basu amsa dole sai ta shigo sunji daga bakin ta. Sanye idanunta da gilashin kara gani (medicated glasses) irin brown d'in nan na tsofaffi. Su waziri suka gaishe ta cike da girmamawa ta kalli kan gadon taga Salman kwance kamar matacce, ta karasa gurin tare da dafa goshin shi taji zafi. “Subahanallahi! Me yake damun sa haka?” “Wallahi gwaggo ta fada muma zuwa akai aka ce mana ba'a ji motsin shi ba, shine muka zo sai muka tarar dashi cikin wannan yanayin.” “Ikon Allah, munyi waya dashi yace yana son gani na dan Allah na taimaka nazo, shine ina idar da isha'i nasa driver ya kawo ni. Ashe zan zo akan gaba, na tarar bashi lafiya.” Sai suka ga yayi wata irin zabura tare da wancakalar da bargunan jikin shi yana ta wani irin kuka marar dadin ji. Gwaggo ta kalleshi sosai taji a jikinta cewar tabbas Salman baya cikin haiyacinsa, koma menene aikata mishi ake yi har yanzu. Su kuma su waziri suna ta faman ririk'e shi, Dr Naufal yana kokarin zuko allurar bacci dan ya yi masa ko za a samu sassaucin kukan nasa da kuma yunkurin tashi da yake yi. “Ina matarsa? Da kuma amaryar da aka ce ya yi?” Waziri ya gaya mata cewar kila suna sashen su, amman bashi da tabbas tunda be sa an bincika ba tun dai dazu da aka tabbatar masa kowace tana bangaran ta. “Allah ya baka lafiya Salmanu, Allah ya yi maka maganin duk wani mai son ganin bayan ka a boye ko a fili.” Daga haka ta zauna a gefen shi tana ta yi masa addu'a tana tofa masa, amman mai makon sauki sai ya zamana tamkar tofin kara masa wani wutar yake yi, gwaggo ta gane hakan ne ganin idan ta karanta ayatul kursiyu ta tofa masa sai ya kara gigicewa yana dukan su wambai. “Ko zan samu alfarmar ganin matansa?” “Gwaggo yanzu?” Cewar Waziri cikin sanyin jiki, da alama baya son su zo su ganshi a haka, mata ne zasu iya gigicewa. “Eh kafin na koma can gida na ina son ganin su. Ba matansa bane ba? Suna da hakki su ji halin da mijin su yake ciki.” Su waziri suka yi shiru basu saka an je kiran su ba, kuma basu cewa gwaggo komai ba, sai da kanta ta fito zata sa a kira mata Jakadiya. Sai gata ta taho cikin sauri daga gurin su Gimbiya Jaleela take, dama tunda taga zuwan gwaggo ta Fada tayi saurin zuwa ta sanar da su, shine suka turo ta dan taji abin da ya kawo ta koda kuwa ba komai ba. Ko amsa gaisuwar ta ba tayi ba, tace taje sashen uwar gida da amarya ta kirawo su tana son ganin su. Jakadiya ta tafi tana mamakin wannan kiran na lokaci d'aya. Shaheedah ta fara zuwa ta sanarwa, daman jiran kiranshi take yi taji shiru, hakan yasa tana jin kiran ta yi saurin tashi taje wannan dakin ta sanya wani kwalli da aka ba ta d'an so ake yi su hada ido da shi. Sannan taje ta dauki alkyabbar ta tayo waje, hadimanta suka biyo bayan ta cike da girmamawa. KHADIJAA ____Ni kuwa ina zaune a cikin bayin nawa suna ta bani labarin wai basu taba ganin matar sarki tana hudd'a da bayin ta kamar wasu yan uwa ba iri na. Ina ta murmushi basu san ni babu abinda na sani a game da sarauta ba, dan haka zasu ga sabanin sauran dani. Jakadiya tayi sallama nace ta shigo, d'aya daga cikin bayin nawa ta kuma daga murya wajan ison da na yi. Ta shigo tana sunkuyar da kai tare da gaishe ni tana jinjina min ta kara da cewa. “Allah ya taimaki amarya, farin wata sha kallon sarkin mu. Allah ya taimake ki turo ni akai na sanar dake cewa gwaggo ta Fada tana son ganin ki a can sashen mai martaba, Allah ya kara miki lafiya.” Ras! Kirji na ya buga jin an ce sashen mai martaba. Ni kuwa na shiga uku, me zai kai ni gurin sa ni Dije? Kafin na samu amsa Jakadiya ta kuma magana. “Allah ya taimaki farin cikin mai martaba, tace yanzu.” “Ku... Kuma.. Ni ta ce miki?” “Tabbas ranki ya dade, domin keda uwar gida tace a kirawo, yanzu haka na baro gimbiya ta shirya zuwa can d'in, saura ke yanzu.” Wayyo Allah na ni kam na shiga uku, wallahi Allah bana son mutumin can bare har mu hadu. Tashin hankali ya bayyana a gare ni, jiki na ya fara kyarma ga wani tsoro da ya dirar min lokaci daya. Amman da na tuna tace Shaheedah ta tafi sai na fara kokarin tashi dan kar suce bani da kunya ko tarbiya ana kira na naki zuwa. Da yake tsoran dakin nawa nake yi, sai nace da daya a cikin masu yi min hidima taje ta dakko min hijabi na yana kan gado. Jin nace hijabi yasa Jakadiya yin magana. “Allah ya taimaki amaryar mai martaba, kiyi hakuri zan dan yi katsalandan a cikin rayuwarki. Amman dai zai fi kyau kisa alkyabba, Allah ya kara miki lafiya.” Haushi ya kama ni, saboda kawai ance naje sashen shi shine za a wani ce sai da alkyabba? Amman dan kar su dinga ganin gidadanci na sai na ce to, na tashi nabi bayan ta d'an kar ta fito, cike da tsoro na ce ta tsaya ni, na bude drawer na dakko guda daya nasa, duk da haka sai da na yafa veil a kai na saboda ba zan dora hular alkyabbar ba. Muka taso suma bayi na suka take min baya, hakan yasa naji wani gingirin gim, sai dai ban hana su ba dan bana son tsayawa sa'in sa dasu. Wannan ne karon farko da na fito daga sashe na tun ran da aka kawo ni, duk da dare ne amman hasken da ya zagaye ko'ina a masarautar sai ka rantse rana ce. Gashi kowa harkar gabansa yake yi tamkar da rana. Sai dai kuma me, mun fara tafiya daya biyu sai kawai naga tamkar an wuce ta kusa da ido na. Na rintsa ido bayan na tsaya cak ina karanto addu'a da kyar. “Allah ya taimake ki, ince kodai lafiya?” Na kasa yi mata magana sai kokarin daga kafa da nake yi amman na kasa, kafin kace menene tuni na yi wata irin faduwa, kai da ka gani kasan ture ni akai dan ko motsi bana iya wa. Hankalin su ya yi mugun tashi, tun kafin idanuwan mutane ya yo kan mu suka taimaka suka mai da ni cikin sashe na suna faman yi min fifita. Jakadiya kuma ta ruga da gudu ta nufi wajan gwaggo ta Fada, lokacin Gimbiya Shaheedah har taje sai dai suna parlorn shi ba ta kai ga shiga ciki gurin Sarki Salman d'in ba. “Allah ya taimaki ta fada ya ja da ranki uwar kowa.” “Ina take?” “Allah ya baki nasara, bayan mun fito dan zuwa kiranki, sai kuma aka samu matsala. Allah ya taimake ki gani kawai muka yi ta fadi, yanzu haka mun maida ita zuwa sashen ta.” “Wannan wane irin masifa ne?” Cewar gwaggo ta Fada cikin matukar mamaki, a ranta tana son gano wadan nan dalilan. Tabbas tasan akwai matsaloli a cikin masarautar nan, an raba sarkin kanshi da mahaifiyar shi, an shiga tsakanin shi da duk wani farin cikin sa. Da alama itama amaryar nan so ake a shiga tsakanin su, dama dazu a wayar da sukai taji yana tambayar ta waye Khadija a gare shi. Ai kuwa idan dai tsakanin su za'a shiga ba zata bari ba, daman tana son taga ranar da Allah zai sa Salman ya yi aure, gashi kuma ya yi dan haka ba zata bari a wargaza shi ba, sai inda karfin ta ya kare. Ta mike tsaye tare da kallon Shaheedah daman ta tsani yarinyar nan, saboda bata da kunya ko miskala zarratin. “Mai martaba bashi da lafiya yana a hannu Allah, ya rage naku kuyi masa addu'a idan kuna bukatar zama dashi dan kuci gaba da mulki. Idan kuma ya gundire ku to ku zuba mishi ido, ni na tafi.” Tana kaiwa nan tai gaba abin ta, tana sane ta fadi haka tasan Shaheedah tana son mulkin sarki Salman, dan tasan idan ya mutu to dole ta koma b'ullo gashi dama babu d'a bare kuma 'ya. Hankalin gimbiya Shaheedah kuwa ya tashi matuka, ta nufi master bedroom d'in sai taga mijin nata kwance tamkar wani matacce, dan a tunanin ta ma ya riga ya mutu gaya mata ne kawai gwaggo ta Fada ba tayi ba. Wani ihu ta saki tare da dora hannu a ka tana kuka tana ta shiga uku ta lalace, sai da Waziri ya dakatar da ita ya shaida mata be mutu ba sai dai yana cikin wani yanayi dan sai firgita yake. Sannan ne hankalin ta ya kwanta ta dinga tunanin kodai aikin su ne ya yi masa yawa har yake neman rasa rayuwarsa? Idan har Salman ya mutu ai ta shiga uku ba ta da sauran wani amfani a duniyar nan. ____Gwaggo ta Fada kuwa kai tsaye tasa aka raka ta sashen Dije, ta tarar da ita a takure jikin kujera tana nuna musu wani guri daban tana cewa. “Gasu nan wallahi, gasu suna min dariya zasu kashe ni.” Shigar gwaggon kuwa ta dago ta kalleta da gudu ta tashi ta nufi jikin ta tare da kankame ta tana cewa. “Ki taimaka min Mama karsu kashe ni, dan Allah ki tausaya min ki fitar dani daga gidan nan bana s..s...s..son.....” Gwaggo ta Fada taso shiga sashen Gimbiya Sa'adatu, amman ganin yanayi na yasa tace su kai ni motar ta da driver ke jiran fitowar ta. Bata tafi da kowa ba daga ni sai ita ko kayana bata dauka ba ta tafi dani zuwa gidan ta. Tun a hanya take tofa min addu'a, ni kuma tunda muka fito daga masarautar naji na dawo cikin hayyacina. Kai na akan cinyar ta sai faman shafa min kai take yi, duk da ban san ko wacece ba, sai naji hankali na ya nutsu da ita. Karatun da take ta faman yi min yana sani nutsuwa wanda yaushe rabon da nayi shi saboda rashin nutsuwar zuciya da bani da ita. Muna zuwa aka bude gate, shima gidan tsarin na sarauta ne, sai dai bai kai girman masarauta ba. Driver ya yi parking nan da nan wasu mata masu kaya iri daya su hudu suka iso inda muka tsaya, suka bude mana mota tana rike dani tace. “Fito da bismillahi Khadija.” Nayi kamar yadda ta umarce ni, muka sakko sannan suka rufe motar suna bin mu a baya kamar dai yadda ake yi a can gidan sarautar da na baro. Babu laifi gaskiya katon gida ne, muka shiga wani katon parlor wanda ya gaji da haduwa, kai ba kace tsohuwa bace a cikin sa saboda yadda aka kawata shi da abubuwan zamani. Guri na samu na zauna, ita kuma ta shiga wani daki, ba ta dade ba sai gata da wata sun dawo parlorn, gwaggo ta Fadan tace min. “Ga yar uwa nan nayi miki, yar auta ta ce, sunan ta Maryama. Tayi aure tsawon shekaru tara Allah ya yiwa mijin rasuwa, bayan ta gama iddah ta dawo nan shekaru biyu kenan, yaran ta biyu Aliyu (haidar) da Aisha (Humaira) suna daki sun yi bacci.” Daga ni har ita kallon juna mukai kafin ta maida kallon gurin gwaggo tace. “Gwaggo wacece wannan din?” Sai da taje ta zauna akan shimfidarta ta musamman, sannan ta janyo ruwa tasha tace. “Wannan da kike gani Gimbiya ce. Bari na yi miki gwari-gwari, ita ce amaryar mai martaba, na dakko ta ne saboda da wasu dalilai.” Da sauri Maryama ta kuma kallo na tana faman sakin murmushi da alama taji dadi da na kasan ce matar sarki Salman. Sai kawai naga ta durkusa a gaba na tana gaishe ni, na yi saurin riko hannunta ina girgiza kai na. “Ki tashi dan Allah Addah Maryama.” “Girmanki ne ai gimbiya Allah ya riga da ya baki. Naji dadi gaskiya kuma ina d'aya daga cikin masu son auran nan da mai martaba ya karo, Allah ya ja da zamanin ki gimbiya.” Ni duk sai ta sani jin nauyin ta, gefe guda kuma haushi naji da take murna na aure shi. “Ki raka ta tayi wanka a samu sababbin kayan bacci a bata tasa kafin gobe kije ki samo mata wasu da zata dinga amfani dasu.” “Toh gwaggo, ai ni kin gama min komai wallahi da kika zo da ita nan. Bismillah gimbiya mu shiga cikin dakin.” Sai da ta kama hannu na sannan muka tafi, bayan ta nuna min bandakin tace na shiga. A bakin kofar an rubuta addu'ar shiga, hakan yasa na yi nima dan a can gidan da na baro ko niyar yi nazo yi sai naji an goge min na kasa yi sai dai na shiga a haka. Wanka nayi sosai, daga nan nayo alwala nayi addu'ar fitowa wacce itama ga ta an sakale a saman kofar. Bayan na fito ne naga ta ajiye min komai sabo sai dai banda bra, na dan kalleta nace ta bani pad idan akwai, ta tashi ta dakko min leda guda na dauka tare da komawa bathroom d'in nasa na kuma fitowa. Mayuka masu kyau ta bani na shafa nasa wandon baccin na tsaya ina faman raba ido, bana iya kwanciya sai da half vest koma bra d'in, kamar ta gane ta juyo ta kalle ni tana murmushi tace. “Haba ranki ya dade, ko a baya kina bacci da bra yanzu kam ya kamata ki aje su a gefe. Kisa rigar kawai an fi son a dinga kwana a haka inji likitoci.” Ban iya musa mata ba, haka nasa rigar da hula ta nuna min gado tace na kwanta. Nan fa ta fara bani labarai, gaskiya wayayyiya ce adda Maryama, dan a daran sai da tasa na saki jiki da ita muka shiga hira kamar daman mun dade da sanin juna. Gwaggo ta Fada ta aiko aka kawo min wani ruwa, tace nasha sannan kuma na shafe a jiki na. Nayi kamar yadda tace daga nan kuwa muka ci gaba, sai da dare da yi sosai sannan muka yi bacci. Ba karamin dadi naji ba ranar, kuma ban tsorata ba lafiya lau nayi bacci na tashi. ____Washe gari da safe bayan nayi wanka na shirya cikin doguwar riga, Adda Maryama da yaran ta suka gaishe ni na amsa fuska ta cike da walwala. Daga nan aka kawo breakfast kala-kala, muka ci da yake tana business hakan yasa aka dinga kiranta a waya, tace min bari taje ta dawo. Gwaggo ta kira ni naje na zauna kusa da ita, itama tun ina jin nauyin ta har dai daga baya na saki jiki muna ta hira tace. “Kamar yadda na gaya miki dole sai kin tashi tsaye kin nemi kariya sannan zaki ji dad'in yin rayuwa. Na yi matukar mamaki lokacin da naji zancen auran ku saboda duk mun san shi ba mutum bane ma'abocin kalle-kalle, babu yadda ba'a yi dashi ba wajan kawo wacce yake so amman yaki, dole sai da aka hada auran shi da Shaheedah. Abin da ya kuma bani mamaki be wuce yadda ya auro ki ba, bayan yasan tsarin mulkin masarautar nan ba a auro bare dole sai jinin sarauta. Tun da naji ya yi aure kuma a boye har sai a ranar daurin aure sannan ya fada, na san lallai ba karamin so yake yi miki ba.” Na tabe baki yadda ba zata gani ba, bata san auran manufa ya yi dani ba shi yasa har take zaton soyayya ce. Ni nasan mutumin nan auro ni ya yi dan ya kuma wulakantani tunda gashi nan an kai ni gidan be kula ni ba har na baro gidan saboda shi bashi da mutunci. Gwaggo ta ci gaba da cewa. “Kin ganni nan? Da a cikin masarautar nake, amman dalilai suka sa dole na baro ta saboda bana son fitina. Bari na baki tarihin masarautar Basannabas, ki gyara zama ki kuma karkade kunnanki.” Gyara zama nayi dan dama ina son abinda zai kuma dauke min tunani. Gwaggo ta fara da cewa..... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). * *KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASA* *29....* _*KIBIYAR AJALI.....!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🏹🥰😍 _*WAIWAYE:-*_ _*MASARAUTAR BASANNABAS*_ Tarihi irin na kunne ya girmi kaka d'in nan, ya yi nuni da cewa, Masarautar Basannabas wata dadaddiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun daruruwan shekaru da suka gabata, Wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci. Sunan Basannabas din ya samo asali ne tun a shekarun baya. Tarihi ya nuna cewa wasu tsatson fulani biyu ne da akewa laqabi da *Bassan da Nabas* suka zo daga gabas maso yamma inda suka yada zango a nan suda matayen su da ‘ya'yan su da shanun su. Anan suka kafa dandalin kasuwancin su, Ma tafiya dake wucewa ta nan suka kwadaitu da yanayin kasuwancin su, Allah ya sanya musu albarka kwarai da gaske. Duk fatake na nesa da na kusa su na zuwa su sari kaya a wajen su. Sosai yankin ya shahara, har ya zamto mutane na yiwa yankin laqabi da garin *Basan da Nabas*. Shekaru aru-aru haka ake kiran sa, Kafin yankin ya zamo sananne, har zuwa lokacin da turawan mulkin mallaka suka bawa nijeriya 'yancin ta. Bayan nijeriya ta cire garuruwa ta sanya musu suna. A lokacin ne aka yiwa yankin *Basan da Nabas* kwaskwarima ya dawo *Basannabas....* *MASARAUTAR BASANNABAS* 👑 Tana d’aya daga cikin k’asaitattun masarautu da ta keji da kambun mulki, masarauta ce wadda ta kafu tun misalin 998 mailadiyya, Ma’ana dai fiye da shekaru dubu. Sarauta da hakimci a masarautar Basannabas ta kasance wani babban al’amari wanda yake da muhimmanci. Sarautar Basannabas ta kasance a hannayen ahalin rukunin sarakuna tsatso (jini) d’aya. Tun daga kan Marigayi mai martaba na da wato sarki Durbin jingau. Masarautar Basannabas nada sarki d’aya tak na yanka/Gado, Ba taka haye bace, Sannan akwai hakimai masu lakabin sarautun gargagiya a matsayin mataimakan sarki awajen gudanar da kambun mulki. Gaba d’aya rukunun sarakunun garin Basannabas a tsatson jini d’aya yake, Wato dai tsatson yan uwa guda uku, Marigayi Sarki Durbin Jingau, Da tsatson marigayi Sarki Masekiri (Tajiri) Jirgau, Da Marigayi Sarki Ilyasu Jirgau. Gaba d’aya ahalin su ne ke mulkar birnin Basannabas.. Tun daga kan sarki Masekari Tajiri 1559 zuwa 1669. Har zuwa sarki Ismaili Rabo 1701 zuwa 1804. Daga nan sarauta ta koma hannun iyalan Dallatu na lokacin wato tsatson marigayi Ilyasu Durbi a shekarun baya. Bayan rasuwar Sarki Ilyasu, Sarautar Basannabas ta fada hannayen tsatson marigayi Durbin Jirgau, Dana Marigayi Masekiri Jirgau, Kafin daga bisani ta sake dawowa hannun jikokin Sarki Ilyasu, Dake Allah yayi sarautar a hannun su zata zama. B’angare da dama sun ‘ki hakan, Daman duk inda gidan sarauta yake dama dole a samu haka. Akwai suka, Tsagwaron makirci da sihiri babu wanda ba’ai ma sa ba, Da k’yar da karfin addu’a dai, Sarauta ta dawo hannun mai Martaba Sarki Aliyu salmanu Aliyu, Wato jikan-jikan Sarki Ilyasu. _*MAI MARTABA SARKI ALIYU SALMANU ALIYU*_ (Mahaifin SAS) Sarkin Basannabas mai martaba Aliyu salmanu Aliyu ya gaji mulki ne daga hannun mahaifin sa marigayi sarki salmanu ibrahim ibrahim. Sarki Aliyu salmanu ya kasance kasaitaccen sarki wanda ya gina sarautar Basannabas ta hanyoyi daban daban. Babu na biyun sa a bangaren tsarin sarauta. A tsari da kuma tarihin sarautar Basannabas a wancen lokacin, Bayan an dora sabon sarki a karagar mulki, Ko kuma ana shirye shiryen dora shi akan mulki, Wajibi ne ko ince al’ada ce, Dole sai sabon sarki ya auri mataye har biyu daga tsatson sarauta. Kuma su zamto na farko acikin matayen nasa, Kafin daga bisani ya auro biyu wa’enda yake so daga baya, Kana ya iya ‘karawa da ‘kwarkwarori (concubines). Wanda suma ake samo masa daga jerin ‘yayan dagatai ko kuma ‘yayan fadawan zaman fada wato ‘yan majalisar sarki. Idan kuma ya kasance yana da mata wanda daga cikin tsatson sarautar Basannabas ne, to shikenan ba sai ya kara ba, Idan kuwa ba jinin sarauta bane, To fa lallai dayan biyu ne, Ko dai ya sake su ya musanya da jinin sarauta, Ko kuma yayi murabus daga karagar mulki, Kana a cire shi daga duk wasu al’amura na masarauta. Bayan nadin Sarki Aliyu salmanu a lokacin, Abubuwa da dama sun faru a masarautar domin sosai aka samu ruguntsumi na rabuwar kawuna, Babban dalilin dayasa hakan kefaruwa da Sarki Aliyu, saboda matar da zai aura, Domin ya kafe akan shifa a lalle dole ya zamto ya auri wadda yakeso tun tasowar sa, Wato y’ar daya daga cikin bayin masarautar, Wato yar sarkin ‘kofar kudu, An kad’a an raya amma sam sarki Aliyu ya kafe akan kudurin sa na auren, A lokacin babu wanda ya tsaya masa sai dan aminin baban sa. Wato mai martaba sarkin *Masarautar Bullo*, Sarki Ibrahim Hashimu. Wanda ya gaji sarautar ta bangaren kakan baban sa. Gashi Bullo itace masarauta ta biyu dake bin bayan Masarautar Basannabas. A duk fadin nijeriya itace masarauta ta biyu da ake ji da ita a kasar nan. A lokacin sarkin Bullo ya tsayawa sarki Aliyu domin cinma wani burin sa na daban, Bai dai bayyana ba alokacin. yabar wa zuciar sa ajiya. Ya tsaya tsayin daka wajen ganin Sarki Aliyu ya karb’i karagar mulki. Duk wani shige da fice yayi, Yayi amfani da karfin mulkin sa, Da kuma ta fada aji na mulkin farar hula (democracy). Dan a lokacin y’ar wajen sa tana auren shugaban kasa na lokacin. Hakan kuwa aka yi, Da yake Allah ya rubuta da alkalamin qudura, Sai sarki Aliyu salmanu ya karbi kambun mulki, Tare da daurin auren sa ga Sa’adatu wato yar sarkin kofar kudu. Babu yadda kowa ya iya haka aka sanya amarya a lalle aka kaita dakin ta na sunnah. Bayan auren sarki Aliyu Salmanu da amaryar sa Sa’adatu ‘karamar ya ta karshe ga d’aya daga cikin babban bawan sarki mai rasuwa, Wato (Sarki Salmanu). Mahaifin sabon sarki Aliyu. Sarkin kofar kudu. Wanda ke kula da zaurukan kofar kudu da farfajiyar bangaren kudu me suna Abdullahi. Wanda ake mai lakabi da sarkin kofa. Babban ruguntsumi ne ya tashi a lokacin da sarki Aliyu ya hau karagar mulki. Bangarori da dama suka rika sukar sarautar sa suna aibatar sa. Haka dai Allah ya kare shi da matar sa Sa’adatu. Bayan wata tara cif babu doriya Gimbiya Sa’adatu ta haife kyakkyawan danta kato TubarkAllah, Tamkar sarki Aliyu ne yayi kaki ya tofar. Dake itama bafulatana ce gaba da baya hakan yasa jaririn nasu zubin kyau tamkar dan larabawa. Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin sarki Aliyu. Inda aka sanya masa Salman Aliyu Salmanu(Sunana kakan sa). Babu wani sunan da ake Kiran sa bayan hakan, Saboda sarki yace ba Za’a boye masa suna ba. Sosai an kakkawo wa jariri Salman farmakin halaka shi, Amma dake Allah yasa da kwanan sa agaba babu abunda yasame shi sai kara girma ma da yake yana wayo. Ganin sun kasa cin galaba ta nan, Sai suka sake dawo da maganar ai dole sarki Aliyu ya kara aure. Ba zai zauna da yar bayi ba. Babu yadda Sarki Aliyu ya iya tunda tsarin al’adar su haka ya tana da a dole ya bada kai aka sake aura masa mata har uku, Duk daga cikin ahalin dangin su. Mata uku rigis aka sanya a lalle aka d’aura aure. Kowacce tana ji da kanta ita yar sarauta ce. Gashi duk ahalin tsatson su d’aya ne. Sai dai asamu nisan alaka. Amma dukkanin su y’ay’an manyan hakimai ne. Gimbiya Jaleelah yar waziri ce. Waziri dake bawa sarki Aliyu shawara, Sai Gimbiya Najawa yar Galadima, Sai Gimbiya Huwaila babbar ‘ya ga ciroma. Dukkan su a rana d’aya aka kai su d’akunan su bayan an daddaura auren. Ran sarki Aliyu sam bai so hakan ba. Shi gaba d’aya tun tasowar kuruciyar sa Sa’adatun sa yake so ita kadai. Tun ada kinsan masarauta acikin ta babu abunda babu, Gaba d’aya rayuwar su aciki suke yin ta, Duk abunda zaku bukata na rayuwar duniya akwai aciki, Balle masarautar Basannabas tana da mashahuriyar girma, Gari guda ce. komai akwai acikin ta, Toh idan sarki Aliyu yaje makaranta ya dawo ya kan tsaya a bakin kofar kudu yana kallon Sa'adatu dake taya mahaifinta jiran kofa, A lokacin tana kankanuwa, bata san wanne irin Kallo sarki Aliyu yake mata ba, Tun yana buya a bayan zaure yana kallon su, Har ta kai yakan tsaya daga nesa yana kallon Sa’adatu tana y'an wasanninta. Har ta kai Sarkin kofa Abdullahi ya ganshi, Ya gaishe shi ya fara tambayar sa matsalar sa. Tun sarkin kofa na kokarin hana Sarki Aliyu har ya hak’ura ya dena, ganin sha’kuwar da ta shiga tsakanin Aliyun da Sa’adatun sa. Tun Kan Sa’adatu ta mallaki hankalin ta hartazo ta mallaka Sarki Aliyu ya koya mata sonsa, Sarkin k’ofa da ya riga yasan al’adun masarautar basa auren bare sai jinin su, Hakan yasa ya dinga tausar Aliyun yana kokarin janye shi daga zuwa wajen Sa’adatun. Amma fafur Aliyu ya’ki. Haka sarkin kofa ya ha’kura ya zura musu ido kawai. Har Aliyu ya kare secondary alokacin ya nemawa Sa’adatu itama ta fara karatun. Shi kuma ya tafi waje karo karatu bayan ya bawa Sarkin kofa amanar Sa’adatun sa. Kuma duk wuya duk rintsi zai aureta Idan ya dawo babu fashi. Hakan kuwa aka yi bayan shekarun daya d’auka awaje yana karatu ya dawo ya tarar da Sa’adatun sa itama ta kare sakandire. Yaso auren ta alokacin sai kuma mahaifin sa sarkin lokacin Wato marigayi sarki Salmanu Ibrahim yayana kenan da muke uba d’aya da shi, Sai ya sake tura shi nahiyar ketare yin wani kasuwanci. Bai dawo ba sai da aka kira shi aka sanar masa rashin lapiar sarki Salmanu. Bayan dawowar sa gida ba jimawa sarki ya cika. Daga nan aka fara shrye shiryen nadashi sarauta, A nanne rabuwar kawuna ta sake barkewa ganin zai auro musu yar bayi. Gashi kowanne bangare daga bangare biyun jiran gadon sarautar suke yi. Wato yankin tsatson Marigayi Durbin Jirgau dana Marigayi Masekiri Jirgau. Kowanne bangare ya cancanta ya karbi kambun mulki. Sai dai bangaren tsatson marigayi Ilyasu Jirgau sune suka fi cancanta domin sune suka kara farfad’o da masarautar Basannabas, ance a bangaren tsarin izzar sarauta Marigayi Sarki Ilyasu Jirgau tafi karko, Ya kasance kasaitaccen Sarki mayaki, kuma masanin gudanar da mulki wato a turance ‘intellectual administrative leader‘. Yayi yake-yake daban-daban wajen ganin ya tabbatar da girman kasa da sarautar Basannabas da ikon ta. Don haka ne ma girman Basannabas ya kasaita. Daga Yamma tun daga iyaka da garin bullo inda masarautar bullo take, zuwa kauyen durbi a gabas. Sannan daga iyaka Kazaure a arewa zuwa yankunan duwatsun jigawa a iyaka da garuruwan Birom a Kudu duk sun kasance fadin ikon Masarautar Basannabas. A bangaren tsarin izzar sarauta da kuma nadin hakimci, Marigayi Sarki Ilyasu ya bada gudun mawa. Don a lokacin sa ne ya sake fito da mukamai guda biyu a kasa wanda a turance ake kira da ‘district heads’ da kuma marasa kasa wato a turance ‘title holders’. Don haka ne, tun daga wannan kirkirar gundumomin hakimai Masarautar Basannabas ta kasance ta kunshi gundumomin hakimai masu yawa. Kuma alokacin sa ne yaso talakawa sosai, Ya ‘yanta bayi, Ya kuma fito da tsare tsare na zaman fada. A tsarin Sarautar Basannabas, Majalisar Fadar Masarautar Barnabas ta kasance karkashin Sarkin Basannabas, wanda yake shugabantar zamanta. A tsarin Fadar Basannabas, akan gudanar da ayyuka kamar fadanci; akan yi fadanci don karbar gaisuwa da kuma saduwa da baki, abokai, da yan uwa da makamantan su. Sosai talakawa da jama’ar gari a lokacin sunyi maraba da wannan Sabon tsari na marigayi sarki Ilyasu. A zaman fadar da akeyi sarki Ilyasu ko wazirin sa lokacin sun kasance masu sauraron koke koke na al’umma, Da sulhunta husuma Idan ta taso. Kai wani lokacin ma har wasa da dariya ake yi. Sam marigayi sarki Ilyasu ba shida girman Kai ko dagawa irin na wasu sarakunan. Shi yasa yanayin sarautar da yayi ya dora Yayan sa suma suka dora Yayan su akan akidar sa. Har gobe mutanen Basannabas sunfi son jinin marigayi Ilyasu suyi ta karbar ragamar sarautar Basannabas. Hakan kuwa ba karamin sake janyo ruguntsumi yake ba tsakanin ahalin marigayi Ilyasu da ahalin marigayi Masekiri Jirgau da kuma marigayi durbin jirgau. Alokacin da marigayi sarki Ilyasu ya k’ara bud’a hakimci da nadin sarautun gargajiya a masarautar Basannabas, Sai ya raba gaba d’aya rabin mukaman daya sake nad’awa har ‘ya'yan ’yen uwan sa ya dauka ya babbawa sarauta, Sai ya zamto alokacin dan sa kwaya d’aya ya bawa sarauta. Gaba d’aya muk’aman guda shida ya raba su kaso biyu. Kashi d’aya na farko ya bawa tsatson marigayi durbin jirgau mukamai guda uku: Madakin Basannabas, Makaman Basannabas da Sarkin dawaki mai tuta wato hakimin waje. Sai bangaren marigayi Masekiri Jirgau wanda nasu suka kunshi: Wamban Basannabas, Da shamakin Basannabas sai Dan rimin Basannabas. Hakimci d’aya da ya rage kuma alokacin sai ya bawa jikan sa wato marigayi Ibrahim, Mahaifin marigayi salmanu baban sarki Aliyu mahaifin Salman. lokacin da marigayi Ilyasu Jirgau yai wadannan nade-nade Sosai ya fuskanci matsaloli ta fuska da dama. Domin har asiri sai da aka jefe shi da shi ya zamto baya zuwa fada sai dai waziri ne kadai ke gudanar da komai, Amma da yake shi din namijin duniya ne da baya wasa da karfin addu'a, Sai ya tashi tsaye yayi yaki da makiya har yaci galaba akan su, Sihirin jikin nasa ya karye ya cigaba da gudanar da abubuwan sarauta. Hakan ba karamin sake girgiza masharranta da mahassada yayi ba ganin ya dawo garau dashi bai lalace ba kamar yadda sukai zato. Sosai marigayi sarki Ilyasu ya zage k’aimi wajen kara karfafa sarautar Basannabas. Ya zamto a kullum sai anyi saukar qur’ani safe, rana, yamma da dare. Ya Kara yawaitar ranakun sadaqa. Ya sake ‘yanta bayi baki d’aya. Har wa’adin sa ya kare Allah ya d’auki ransa makiya basu sake cin galaba akan sa ba. Toh bayan Sarki Aliyu ya hau karagar mulki da temakon sarkin bullo sarki Ibrahim hashimu da shekaru uku. Alokacin Salman na karami. Sai sarkin bullo (Ibrahim Hashimu) ya ziyarci masarautar Basannabas da tulin kayayyaki, Tun da ga kan kayan abinci, Dokuna kosassu da makaman yaki. Turaman sawa dana jariri. Kaya himili guda yazo dasu Basannabas, Bai kuma bar Basannabas ba sai da su kai zaman sirri shi da sarki Aliyu babu wanda yasan abunda suka tattauna. Amman dai mutane da dama sun fassara zuwan sarki Ibrahim Hashimu ba zuwan alkhairi bane, Domin kafin sarki Aliyu ya zauna zaman sirri da sarki Ibrahim Hashimu ance fuskar sa a sake take yana walwala, Amman bayan ya fito daga ciki sai akaga fuskar sa ta sauya zuwa bacin rai, Shi kuma sarki Ibrahim Hashimu ya koma masarautar sa fuskar sa cike da annushuwa. ••++. ••++. ••++. ••++.. Bayan shekara d’aya da auro gimbiya Jaleela, Da gimbiya Najawa, Da gimbiya Huwaila. Sai Allah ya azurta kowannen su da haihuwa, Jaririyar Gimbiya Huwaila ce kawai ba tazo da rai ba. Amma jariran Gimbiya Najawa da gimbiya Jalila su duk sunzo da ran su kuma cikin k’oshin lapia, Dukkanin su sun samu mata. Kowacce mai kama da ita. Ba karamin bakin ciki kowannen su yai ba su da yan uwan su, Domin sun fison su hayayyafo maza wanda nan gaba zasu gaji sarautar Basannabas. Sarki Aliyu yai musu huduba ya sanya musu sunaye masu ma’ana. Ita dai gimbiya Sa’adatu mahaifiyar Salman ido ne kawai nata, Bata isa ta karbi jariran ba sai dai gani daga nesa, Gaba d’aya basa shiga harkar ta, Su ukun sun ware kansu, Sun kyamace ta, Suna binta da mugun alkaba’i. Gimbiya Sa’adatu tana da sanyin hali da nutsuwa, Tana da kauda kai a duk abinda ba’a kasa da ita ba. Kuma duk tsawon shekarun nan bata yadda ta canza kanta ba. Rayuwar ta take gudanar wa kamar yadda ta tashi agidan da babu arziki, Sam batada dagawa da nuna isa. Kowa natane. Gaba d’aya kuyangun ta da bayin ta masu mata hidima bata kyamatar su, Ta janyo su jikin ta tamkar yan uwanta na jini. Kaffa-kaffa take da zaman ta acikin masarautar nan. Kasancewar batada wani madogara sai Allah, Sai kuma mijin ta sarki Aliyu. Yan uwanta maza biyu ne su kuma tun shekarun baya suna ‘kanana aka hada dasu a bayin da sarki ke baiwa wasu masauratun dake sauran garuruwa. Haka dai zaman nasu ya kasance cikin wata irin rayuwa, Dan ma dai sarki Aliyu na kokarin ganin hada kawunan su amma hakan yaci tura. Toh haka dai Shekaru Sukai ta ja, Har Allah yai ta azurta kowannen su da samun ‘ya’yaye. Gimbiya Sa’adatu na da ‘yaya uku gaba ki d’ayan su maza ne: Salman dayaci sunan mahaifin sarki Aliyu, Sai Ibrahim (Khaleel) mabiyin sa daya ci sunan kakan sarki Aliyu. Sai auta Abdullahi daya ci sunan marigayi mahaifin gimbiya Sa’adatu, Suna ce dashi ‘Abdul.’ Gimbiya Jaleelah nada yara hudu duk 'yan mata, Akwai Khairiyyah, Da Sabeera, Sai Muhsana da Munaya. Bangaren gimbiya Najwa nada ‘ya’yaye uku mata biyu namiji d’aya, akwai Madina da Ilyasu wanda yaci sunan marigayi sarki Ilyasu. Suna ce dashi (Junior) Sai autar su Nadiya. Bangaren amarya gimbiya Huwaila ma tana da yara uku maza biyu mace d’aya. Abdul-Qadeer, Sai Hamza suna ce dashi (Maheer) da autar su Baheeya. Wadda itace ta kasance autar su du gidan baki d’aya. Daga kanta ba’a kara haihuwa ba. Dama ita tuni gimbiya Sa’adatu tata haihuwar ta tsaya tun akan Abdul. Daga uku dinnan bata kara haihuwa ba har ta manyanta. Gaba ki d’aya dai ‘yayan sarki Aliyu su goma sha uku ne. Sai guda d’aya da aka haife ba rai daga dakin gimbiya Huwaila. Maza shida, Mata bakwai. Kusan dukkanin yaran sun girma, Babban sa mai suna Salman wato mijin ki kuma sarki a wannan lokacin, ya yi karatu a kasar saudiyya inda ya karo ilmin digiri na biyu a jami’ar king saud university, Yana karantar ɓangaren Islamic and shariah law. Yayin da Ibrahim da Abdul-Qadeer ke nahiyar kasar south Korea suna karantar bangaren likitan ci. Sai Abdullahi da Hamza da Ilyasu dake nan kasar nijeriya a wata makarantar kwana suna cigaba da karatun sakandiren su. Matan gimbiya Jaleelah guda biyu sunyi aure Saura biyu. (Muhsana da Munaya sune basuyi aure ba). Bangaren gimbiya Najwa ma Madina tayi aure sai autar su Nadiya wadda ke karatun sakandire matakin farko. Sai bangaren gimbiya Huwaila wadda yar autar ta Baheeya ce kawai kuma du gidan itace karama yanzu take a aji nabiyu na jiniya sakandire school. Duk tarin arzikin yaran nan dake gidan sarki Aliyu gaba ki d’ayan su suna zumunci idan ka tsame yayan gimbiya Sa’adatu da ahalin ta. Wanda su kam sun so ayi zumuncin dasu amma kafiya irin ta su gimbiya jaleelah hakan yaci tura. Sosai suke nuna bangaranci. Duk dan ya Kara dankon zumunci yasanya yayan a makarantu d’aya. Idan ka cire Salman wanda shine babban dansa duk duniya. Kuma mafi soyuwa agare shi. Amma gaba d’aya su gimbiya jaleelah sunyi fatali da zumuncin da yake kokarin ginawa, Burin su gaba d’aya bai wuce yadda sarauta zata koma hannun dayan su ba. Gimbiya Sa’adatu ita kad’aice a ware, Takan ware lokaci taci kuka ta koshi, Ta kuma gayawa Allah kukan ta a sujjada, Bata wasa da addua sam. Sai dai duk karfin imanin bawa da adduar sa wani lokacin dama Allah Kan jarabce shi da wata jarabawar ya gwada karfin imanin sa. Idan yayi hak’uri ya danne zuciyar sa sai Allah ya bashi ikon cin jarabawar da yayi ko akasinta. Gwaggo Hajara taja numfashi tare da dagowa ta kalle ni, kai na a kasa na kasa ko kwakwaran motsi ina ta sauraron ta tace dani. “Bari na barki ki huta, idan naci tuwo na sai mu dora daga inda muka tsaya a cikin labarin.” Da yake bana sallah, Band’aki na fada na canza audugar jiki na, Ni ma aka kawo min abinci na dan caccakuna na sake komawa gefen gado ina jiran Gwaggo Hajara ta gama ci tazo ta ci gaba da bani labarin. Ina zaune abubuwa da yawa suna yawo a kai na nace. “Lalle biri yayi kama da mutum, Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu. Allah yasa dai ta bani labarin masarautar ‘bullon..” Ban gama rufe baki ba kuwa ta juyo tare da kallo na tace..... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 *ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). * *KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASA* *30....* _*KIBIYAR AJALI.....!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🏹🥰😍 _*MASARAUTAR ‘BULLO_* 👑 Alokacin baya. Masarautar ‘Bullo ta kafu ne lokacin da yan yankin wani gari da ake kira ‘Margu’ suke kai wa yankin yamma hari. Wanda idan suka tashi bullowa ta gabas suke bullo musu su far musu. A duk sanda maharan suka zo, Yan yankin suna tafiya a guje zuwa garin Basannabas dan su taimaka musu da mayaka. ‘Sun ‘bullo ta gabas..’ Shine kalmar da yan yankin yamman ke fada a kodaya yaushe. Ma’ana maharan da suke karkashe su suna b’ullowa ta gabas. Al’ummar yankin yamma da taimakon Basannabas suka kewaye kansu, yadda mahara ba za su shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ginuwar garin Bullo, kuma wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen. Yankin ya tashi daga yan yankin yamma zuwa garin ‘Bullo’. Garin Basannabas da garin ‘Bullo sun zama aminan juna, Duk kuwa dai da garin Basannabas shi ya raini garin Bullo. Akwai aminta sosai tsakanin su tun zamani shekaru aru aru na baya har ya zuwa sanda garin ya tumbatsa ya tsaya da k’afar sa, Sai ya zamto akwai masarauta a karkashin ta. Wanda kaf nijeriya bayan masarautar Basannabas, To masarautar Bullo itace ta biyu a tsarin mulkin gargajiya. A tarihin sarautar ’Bullo dai ance marigayi sarki Lukaro ne ya fara mulkarta bayan ya samu nasarar mamaye garin ‘Bullo, Sai kuma ya himmatu wajen samar da tsarin sarauta mai karfi domin tabbatar da ikon sa. Don haka ne ya samar da tsari mai kyau wanda masarautar ta ginu har ya zamto idan ka cire masarautar Basannabas, Sauran masarautu na kwaiwayar ta. Toh bayan sarki Lukaru da shekaru masu tarin yawa, Sai sarauta ta koma hannun tsatson sa, Wato jikokin ‘yayan’ ‘yayan sune ke karbar karagar mulki. Har dai sarauta ta dawo kan Sarki Ibrahim Hashimu. Kuma duk sarakunan dake hawa karagar mulkin ‘Bullo ko wannen su sai zumunci tsakanin sa ya sake kulluwa mai karfi da masarautar Basannabas. Akwai aminta sosai a tsakanin su, Kusan idan aka zurfafa bincike ma sun hada yan uwantaka. Toh bayan hawan marigayi sarki Hashimu Idrisu kafin rasuwar sa aminin marigayi sarki Salmanu ne mahaifin sarki marigayi sarki Aliyu. Kafin rasuwar su dai. Sarki Hashimu ya dauki sarki Aliyu tamkar dan da ya haifa. Saboda aminan juna ne shi da marigayi sarki Salmanu. Ance wani lokacin har canzan zaman fada suke yi domin su gano ta yadda zasu warware matsalolin al’ummar karkashin su. Hakan ya Kara dankon zumunta sosai tsakanin su, Har zumuntar ta taso akan ‘yayan su wato sarki Aliyu Salmanu da sarki Ibrahim Hashimu. Sun taso sosai cikin karfin zumunci tun yarinta har manyan takar su. Toh Bayan rasuwar mahaifan su sai ya zamto sun sake shakuwa, Sun kasance suna baiwa junan su shawarwari gwanin sha’awa. Hakan yasanya lokacin da ruguntsumi ya tashi akai kokarin hana sarki Aliyu sarautar Basannabas. Sai shi sarki Ibrahim Hashimu ne yatsaya tsayin daka wajen ganin sarki Aliyu ya hau karagar mulki, Dake sarki Ibrahim Hashimu shi ya dade da yin aure bai yi zurfi a karatu ba. Hakan yasa yayan sa na farko duk manya ne. Yarsa ta farko itace matar shugaban kasar lokacin. Sarki Ibrahim Hashimu ya tsayawa sarki Aliyu ya hau sarauta saboda amintar su da kuma wani abu daya boye a zuciar sa, Bai bayyana hakan ba sai bayan sarki Aliyu yahau kujerar mulki. Har ya samu albarkar haihuwar Salmanu alokacin da yazo yiwa sarki Aliyu murnar samun karuwar da yayi, Masana sun bayyana cewa a ranar sarki Ibrahim ya bayyanawa sarki Aliyu abinda ke cikin zuciar sa. Amma sarki Aliyu baiso hakan ba saboda yasan sarki Ibrahim yayi hakanne saboda ragamar mulkin Basannabas ya koma hannun masarautar Bullo. Ashe yar cikin sa ta karshe wadda aka haifeta bayan an haifi Salmanu da shekara d’aya da rabi ita yake son ya hada auren su. Babu yadda sarki Aliyu ya iya a lokacin. Ya dubi tsayuwar da yai masa akan sa, Halacci d’aya zai masa ya hada ‘yayan nasu aure idan rai yake. Hakan kuwa akayi karshen wasiyyar sarki Aliyu shine Salmanu ya auri yar sarki Ibrahim ko bayan ransa, Koda kuwa hakan zai janyo matsala ga karagar mulkin Basannabas. Bayan rasuwar sa ba jimawa aka dakko Salmanu daga kasa mai tsarki inda yake karatun sa a jami’ar King Saud university (Saudi Arabia) inda ya k’arashe matakin digiri na biyu a fannin Islamic law & Shariah. Anan aka nad’a sarki Salmanu Aliyu Salmanu a karagar mulkin Basannabas , Husuma da tarzoma hade da tsantsar makirci da hassada Kai harda tuggu babu wanda ba’ai kalar sa ba, Don hana Salman karbar mulkin Basannabas. Duk wani bangare na masarautar sun soke hakan, Amma dake Allah qadirun ne ala manyasha’u sai yai fatali da duk abubuwan da suke yi yasa Salman shine magajin mahaifin sa wato marigayi sarki Aliyu Salmanu. Girgiza kai nayi lokacin da na ji bangaren masarautar ‘Bullo, Ashe auren had'i ne ko ince auren dole ne tsakanin SAS da Gimbiya Shaheeda bana nagani inaso ba ne? Tabe baki nayi. Kunnuwana suka jiyo min muryar Gwaggo Hajara na bani labarin ranar da aka dora sarki Salman Aliyu Salmanu (SAS/junior) akan mulki wato miji na a yanzu. *RANAR NAD’IN SABON SARKI MAI MARTABA SARKI SALMAN ALIYU SALMANU: (SAS)* Da dakan kade-kaden gargajiya da algaita aka rako sabon Sarkin Basannabas, Salman Aliyu Salmanu (SAS) zuwa fada, kamar yadda ake rako mafiya yawan Sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya. Fadawa ne da sauran 'yan fadarsa ke biye da shi inda suke sanya masa lema domin kare shi daga zafin rana. A shekaru fiye da hamsin din da ta shafe ba a taba samun matashin sabon sarki mai cikar ido da zatin halitta da haiba irin na sarkin yanzu Salman ba, Sabon sarki mai cike da sabon takun kasaitar karagar mulki, Gaba d’aya kowa ya sanya kansa a kasa, Babu wanda ya cire ido ya kalli sarki Salman saboda cikar kwarjinin sa ma ba zai taba sa ku had’a idanu ba. A yadda yan uwa da al’ummar gari ke fada, Babu wanda yasan ya kalar kwayar idanun Sarki Salman take koda kuwa matarsa Shaheedah, Tun yana kankanin sa baya shiga cikin yara suyi wasa, Yana da wata irin madaukakiyar ‘kasaita wadda tafi girman bayyana miki ita. Yakan tsame kansa a duk harkar da zata sada shi da jama’a, Ko lokacin da yayi karatun sa a waje, Kullum idanun sa na saqale da gilashi baki. Baya taba cire idanu ya kalli mutane, Haka zatin halittar sa take, Indai kasaita ce to akan Sarki Salman Aliyu Salman ta ‘kare. Cincirindon al’umma kuwa sunyiwa alkalami yawan da bazasu kirgu ba, Ko’ina bil adama ne sai hada-hada ake, Duk wani mai mukami a nijeriya ya halacci wannan babban taron nadin sarautar. Gabaki dayan wannan shekaru, Masarautar Basannabas na daga cikin wadanda suke taka rawar gani wajen tabbatar da dorewar al'amura a kasar nan, Duk da cewar sarakunan gargajiya ba su da wani cikakken iko sosai a kundin tsarin mulkin k’asar nan, amma babu wani dan siyasa da zai nemi mukami ba tare da neman albarkarsu ba. Kafin samun 'yancin kai, sarakuna kan yi mulki da cikakken iko a Arewacin Najeriya. Domin ko bayan zuwan turawan Burtaniya, sarakunan sun ci gaba da kasancewa masu fada a ji a harkokin mulki. Walima sosai aka yi, amarya gimbiya Shaheeda ta tare a cikin gidan ta dake sashen sarki Salman. Zaure d’aya ne ya raba su da sashen mahaifiyar sa wato sashen ‘Mai babban daki’ (Gimbiya/Haj Sa’adatu) daga sashen ta kuma gaba kadan sai na kishiyoyin ta wasu sashen su Haj Jaleelah, gaba d’aya matan marigayi sarki Aliyu suna cikin masarautar basu canza waje ba. Kowacce tana wajen ta, sabon sarki Salman yace suyi zaman su kada kowa ya tashi. Tun shekaru aru-aru gaba d’ayan su tsatson Jirgau Basannabas a waje d’aya muke. Sai dai Idan sabon sarki ya hau zamani ya canza sai a sake gine gine a rurrushe wasu wajajen a sake kawata masarautar (renovating). Koda zai aure ki anyi mamaki dan bai sanar da kowa ba sai ranar da za'a daura muku aure. Kowa ya yi mamakin wannan al'amari, wanda nafi tunanin ya yi hakan ne saboda yan bakin ciki ko a kawo masa cikas wajan auranki. Kiyi hakuri Khadija ki zauna da Salman kodan ya samu farin ciki a rayuwarsa, karki ce zaki guje shi duk kuwa da kema kina cikin matsananciyar taimako. Kiyi tunani Khadija idan Salman ya mutu baya magana da mahaifiyar sa, bashi da wata walwala sai yadda aka yi dashi. Salman yana sonki duk da cewar be fito fili ya bayyanawa kowa sirrin zuciyar sa ba Naja wani dogon numfashi ina tuno rana ta farko dana fara yin tozali da sarki Salman, Fuskar sa sanye cikin rawani. Kwantaccen gashin girar sa ya leko ta saman bakin gilashin dake zagaye da idanuwan sa. A hankali na furzar da iskar baki na ina mai furta, “Salman Aliyu Salman... (SAS)” Na furta sunan nashi a zahiri amman ba yadda gwaggo zata iya jiyowa ba. Lokacin ne Adda Maryama ta dawo tare da yaran ta da ta biya school ta dakko su. “Gimbiya kin ganni sai yanzu ko?” Nace, “Ai kuwa muna ta jiranki ba.” “Afuwan Gimbiya, amman ai nasan kila gwaggo ta taya ki hirar.” Dariya kawai na yi bance komai ba, ta shiga daki nima na bi bayan ta dan nafi sakewa tare da ita. Haka na rayu a gidan gwaggo ta Fada, babu mai nema na daga can gidan kawu daddy, Dama shi Kawu daddy sanda akai daurin aure na da kwanaki biyu ya tafi Riyadh yin wani kasuwanci. Can masarautar ma ba me cigiya ta bare na sanya ran akwai wanda ya damu dani. Sai da na dauki kusan sati biyu ana ta bani magani da hayaki da sauran abubuwan kariya, na fara jin dadi har ma ban so naji ance zan koma masarautar Basannabas saboda rikicinta. Ina zaune Adda Maryama tana min oiling a kai na naji tayi dariya kasa-kasa tace. “Gimbiyar mu anya kina son shi kuwa?” Da mamaki na ce da ita. “Waye kuma?” Ta kuma murmusawa. “Ina nufin mai martaba.” Naja numfashi kasan cewar na yarda da ita yasa nace mata. “Ba wai haka bane, kawai naga matsayi na da nashi ba d'aya bane ba. Kuma sh... Shima fa ba so na yake yi ba.” “Kai! Wannan duk hasashe ne ranki ya dade. Shi ne fa ya auro ki, kuma auran ma dan kar a kawo masa suka a hana shi.” “Uhmm Adda Maryama k....” “Ranki ya dade kiyi hakuri, koma me yake cikin zuciyarki akan mai martaba dan Allah dan annabi ki taimaka kece a yanzu mafi kusanci dashi, wacce zamu taimakawa ta dawo dashi cikin hayyacin sa. Gimbiya Shaheedah babu yadda bamu yi da ita ba akan mu'amalar mai martaba da mahaifiyar shi, wallahi tasa kafa tayi fatali da zancen shi yasa duk muka kyaleta tunda babu yadda zamu yi.” Jikina ya yi matukar yin sanyi, amman na kasa yadda cewa ba wai haka halinsa yake ba na izza da wulakanci tunda gashi ya yi min, baya kula ni tun da aka kai ni masarautar.... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _*KIBIYAR AJALI.....!!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA HAFSAT 🧕🏼* *(MISS XOXO)* *©️®️ZAFAFA 5: 2021* (PAID NOVELS) _Wattpad:missxoxo00_ *31-32* *KARSHEN BOOK 1* (EPI finale (BOOK 1) *GIDAN GWAGGO TA FADA* “Mun riga munyi magana da gwaggo akan yadda za'a dinga kai masa wannan tofin, saboda tana da yakinin duk wanda take kaiwa ba'a bashi. Zaki shirya insha Allahu da daddare zamu dinga zuwa tunda ke muharramar shi ce zaki iya yi masa abin da babu wanda zai iya yi.” Cikin sauri nace. “Ah toh ai nima ba zan wuce ka'ida ba kinji ki da wata magana.” “Haba Gimbiya sai kace ba mace ba, kin san mawaki yana cewa dukan namiji bawan mace ne. Yanzu wani opportunity muka samu da zaki canza mai martaba ya koma cikakken sarki ba kamar yadda ake juya shi ba kamar wani waina.” Dariya kawai na yi saboda ni kadai nasan matsayin sa a zuciya ta, kuma ba zai canza ba dan na san da manufa mummuna a zuciyar shi. Muka ci gaba da hirar mu cike da nishad'i har ta kammala gyara min kai na tayi parking d'in gashin a tsakiyar kai na. Wanka na shiga nayi wanda shima na magani ne da turaruka masu kama jiki. Bayan na fito na shafa mai tare da gyara fuska ta daidai misali. Lokacin da Adda Maryama ta tashi tunani na shiga yi ina mai jujjuya tofin rubutun dake hannu na, Kalaman ta na karshe sune suka yi ta min reto a kunne na, “Kota halin ‘kaka ki bashi ya sha tofin nan, Idan yaki sha sai kiyi amfani da kissar mu ta mata ki bashi, Ba cewa nai kokawa ba, No! Ko 'yar kyakkyawar runguma kika bashi sai ki hade bakin ki da na shi ki dura masa, Cikin yanga har ya shanye...” Na murza idanu na ina tunanin ta yadda zanyi hakan, Na tsane shi fa ya tsane ni, Taya har zan hade bakunan mu waje d’aya? Kayan data zabo min wai su zan sa na kalla. Wani lace ne gaban rigar a bude yake. Wai laffaya zan dora akai, Idan naje wajen sa na cire. Na sake tuno yadda ta shiga nanata min cewa, “Mace karuwa ce a gidan ta Khadija.. Ballanta na ke me kishiya, Sai da 'yan dabaru. Kuma kinga yanzu so muke mu fara neman yadda zai warke daga mugun sihirin da aka kulla shi da shi... Khadija ke kadai ce KIBIYAR warwarar matsalolin masarautar Basannabas.” Mikewa nayi jiki ba kwari na shiga bandaki, Na yo wanka hade da alwala, Addu’oin da tofin rubutun da Gwaggo Ta fada ke karbomin sun sa jinin ya rage zuwa da yawa, Yanzun na cigaba da sallah ta saboda jinin ciwo ne bana haila ba. Shiryawa nai cikin lace din, Adda ta shigo da wasu turaruka ta shashshafamin su a jiki na, Harda na gashi, Kayana sai kamshin turaren kabbasa suke. Ta nad'a min laffaya, Don har yanzu ban gama iya nadawa ba. Riko hannu na tayi muka fito daga cikin da’ki, Gwaggo ta fada na kan kujera tana jan carbi, “Gwaggo! Barka da yamma... “ “Barkan mu Gimbiya.. Har an fito?” Kai na daga sama ina mai wasa da zoben hannu na, Adda ta tsaya daga tsaye tana rufe murfin robar da tofin ke ciki tace da Gwaggo, “Kin sanar masa da zuwan mu ko Gwaggo...?” “Na sanar masa da zuwan ki dai, Bance har da ita zakuje ba, Saboda kin san yadda gidan nan namu yake. An sake qulla wani abun domin yadda naji muryar sama a waya kamar baya hayyacin sa... “ “Babu damuwa.. Zan bawa zagi cin hanci shi da jakadiya. Da yardar Allah da mun gama zamu dawo don kar ma wani ya ganmu ta kofar arewa zamu fito mu dawo gida..” “To shikenan... Sai kun dawo! Allah yabada sa’a da nasara..” “Aaamin! “ Na amsa a tsorace, Adda ta kamo ni muka fita, Driver yaja mu sai cikin masarauta. *MASARAUTAR BASANNABAS* Tun daga zaure na farko, Adda ta mikomin wasu alawoyi masu futinannun kamshi a cikin ledar su, Ta kanne min ido tana daria k’asa kasa tace, “Harkar sai da irin su Gimbiya..” Nidai nai shiru kawai ina kambama gayu da wayewa irin nata, Tagama fahimtar rayuwa ciki da wajen ta, Qaddara ce kawai ta rabo ta daga gidan mijin ta, Amma na san mijin ta yaji dad'in zama da ita. Kuma idan kuna tare tabbas kai ma zaka kara haske, Domin 'yan kwanakin da nayi da ita, Na gaggane abubuwa da dama, dan Kullum dora ni take akan sabon network.. Ai kuwa muna zuwa muka tarar da Jakadiya, Adda Maryama ta yi saurin janyo ta gefe suka yi magana ta zaro kudi masu yawa ta bata. Nan da nan kuwa tai min iso Allah ciki ita kuma Adda ta samu guri ta zauna jira ba. Tunda na doshi cikin bedroom d'in nake jin bugun zuciya, baki na dauke da sallama amman shiru, har na yanke shawarar komawa sai kuma na yi tunanin ko ba zai iya amsawa ba shi yasa naji shiru, na bude kofar na shiga idanuwa na suna karakaina wajan neman inda zan hango shi. Kwance na gano wani balarabe a kan makeken gado, na kuma bude ido still balaraben nan nake gani. Na tafi sannu a hankali har na karasa inda yake a kwance idanunsa a lumshe, gaba na ya yi wani mummunar bugawa saboda yadda halittar bawan Allahn nan ta buge ni. Kardai ace wannan shine sarki Salman, abin nufi dai wanda ake cewa miji na ne? TubarkAllah. Kamar ana jana zuwa gareshi haka na nufi in da yake baki na bude saboda tsantsar mamaki. Ji nai kawai an riko min hannu na, da sauri na juya dan ganin waye saboda yadda naji hannun zafi rau kamar wuta, babu kowa sai nabi hannun da kallo. Salman ne idanunsa a kulle bakin sa yana motsi a hankali alamar magana. “Waziri ka kuma samin ruwa a jiki na zafi nake ji, help me waziri ina jin kamar ana dafa ni kasa min towel please.” Nan da nan sai na rude gabaki d'aya na rasa ya zanyi na taimaka masa, gashi ya rike ni gam har cikin jikina ina jin rikon. Nayi dabara na cire hannunsa daga nawa na fara dube-dube, kofofin da na gani naje na dinga budewa ina neman bathroom har na gani, na shiga tare da dakko wata roba mai dan fadi na zuba ruwan sanyi, towel na janyo guda daya daga cikin jerin da aka yi musu. Cikin sauri na je kusa dashi tare da warware lafayar jikina na ajiye gefe, bargon da aka lulluba mishi na yaye gabaki d'aya. Ya Subahanallahi ashe babu riga a jikinsa, gabaki d'aya surar jikin shi ta bayyana. Wani irin abu yarrrr ya ziyarci ilahirin jiki na tun daga kan babban yatsana har tsakiyar kai na. Na bishi da kallo ina mamakin yanayin halittar sa. Ashe haka yake da masifar kyau tamkar shi ya yi kansa? Kodai mahaifiyar sa balarabiya ce? Domin ya yi kama da su a komai da komai. Shi kuma jin iska tana ratsa shi kuma ba irin ta yake da bukatar ji ba yasa shi yin yawo da hannayensa yana neman bargo kawai ya kamo kirjina, hakan da na gani ne yasa ni kamo hannun nasa a daidai lokacin ya bude ido a hankali yana furta. “Please help me....Can I hold you once??” Ya ruda ni gaba daya na kasa gane wane irin taimako yake nema, gashi duk da bashi da lafiya yana da d'an karfi ganin da nayi yana ta jana zuwa jikin shi. Ashe shi bargo yake son janyowa ni kuma sai faman kwatar jikina nake yi na kasa. Cikin murya mai cike da tsoro na ce dashi. “Wai me ye haka?” Sai naga ya dan tsaya da son jana, ya yi shiru alamar yana nazari. Can kuma sai ya sake bude ido still daman hannaye na suna rike da nashi be saki ba. Mukai ido hudu dashi, ma'ana yana kallo na ina kallon shi cikin wani irin yanayi mai wahalar fassarawa. A hankali ya fara bin jiki na da kallo, ganin haka yasa na fin cike na dama ina kare kirjina da shi dan naga yafi kallon gurin. Da yaga na yi haka ne sai ya langabar da kai hakan kuma yasa na kuma jin tausayin sa yace. “Nagode kin ji?” Maimakon na yi masa banza, sai na samu kai na da jinjina masa kai wato naji. Ya sake rike hannun na da yake rike dashi. “Ki taimaka ki rufe min, sannan ki samo ruwa kisa min a jiki na. Kin san yadda nake ji ko?” Ya furta 'ko' din kamar karamin yaro. Ba kuma samun kai na da jinjina kai, gaba daya tausayin sa nake ji ya mamaye min ilahirin jiki na. Nace masa. “Toh saki na yi maka.” “Nagode sosai.” Ya fada cikin rauni, gabaki d'aya abinda yake yi irin na yara ne. Sai ya sakar min hannun ya kuma lumshe idanunsa, na sanya towel d'in cikin ruwa na d'an rage ruwan tare sa juyowa na dora masa a goshin. Ya ja wata doguwar ajiyar zuciya yana ta tsotsar lebansa wanda yake kamar yana sanya jan baki pink. Hawaye naga yana yi ta gefen idonsa abin da ya yi matukar bani mamaki, gaskiya bawan Allahn nan yana jin jiki, dole gwaggo ta Fada tace sai sun tashi tsaye tunda shi ba zai nemi kariyar da kanshi ba. Yana yi ina goge masa na kasa bashi hakuri saboda ban san dalilin zubar su ba, har na gama sa masa towel d'in, na dakko jarkar tofin da nazo da ita. Shi kuma jin shiru na tsaya yasa shi bude ido, yana ganin rubutu ya kawar da kai yana fadin. “Ba zan sha ba, na cewa waziri a dena kawo min wadannan abubuwan wari suke yi.” Wannan karon samun kai na nayi da yin sanyin murya, tare da lallashi ina gaya masa ba irin wanda ya saba sha bane. Amma ya dage shi ba zai sha ba, wai duk lokacin da aka bashi ji yake kamar zai mutu dan haka shi ba zai sha ba. Na tuna maganar Adda Maryama, _“Dan Allah Gimbiya duk yadda zaki ki samu yasha ruwan tofin nan, idan ba haka ba muna ji muna gani zasu samu nasarar kashe shi.”_ Sai na samu karfin gwiwa, uwa uba tausayin shi da nake ji a yanzu, sai na dakko alawa d'aya daga cikin wanda Adda Maryama ta bani da zamu shigo. Barewa nai nasa a baki na ina tunanin ta yadda zan iya bashi, idan har na iya to sai na yi dabara na bashi ruwan. Haka na dinga juyayin ta ina zan fara, daga karshe dai na sunkuya gurin shi tare da kamo fuskarsa ina kallo, kirjina yana bugawa shi kuma ya bude ido, kawai na tafi da borin kunya na sanya baki na a cikin nashi tare da zura masa alawar. Me zai faru? Na dago na bashi maganin ko? A'a sai lamarin ya citura dan sarki Salman rike ni ya yi gam tare da fara kissing dina cikin fitar hayyaci. Na dinga zaro ido ina kiftawa babu mataimaki sai Allah na kai kaina. Sai na fara, “Uhmm! Uhmmmuhmmm..! Uhmmm... Uhmmm..!!” Sai naji ya fara kokarin rabani da kaya na, hakan yasa ni nayi kukan kura tare da fincike jikina nai gefe ina sauke uban numfashi. Shi kuma ya rike kai yana furta. “Baby I cant... I... I wont...” Jikina na rawa na sauka daga kan gadon, amman sai nai sauri wajan amfani da wannan damar kafin ya dawo cikin hayyacinsa na zuba ruwan tofin a kofi na zauna gefen shi tare da dago masa da kai nace. “To kasha wannan ruwan idan yaso sai na... Na.. Baka abin da kake so yanzu.” Ya bude tare da watsa su cikin nawa, kirjina ya kuma bugawa ganin yadda suka canza sukai wani iri alamar yana cikin wani yanayi na bukata. Da sauri na kai masa cup d'in saitin bakin sa amman bawan Allahn nan ya kawar da kai. A rai na nace. 'Na shiga uku Adda Maryama ta bani bad shawara' na daure na kuma kai masa ko zai sha amman yaki. “Shikenan toh bani sweet d'in.” Babu musu ya turo ta daga cikin bakin sa nasa hannu na dauke ta tare da ajiyewa a bedside, na kurbi ruwan tare da nufar bakin sa ba musu ya bude na dinga zuba masa a hankali. Uhmmm a haka na dinga bashi yana shi har sai da ya shanye ba tare da mun ankara ba. “Na gama zan tafi.” “Please.. No! kiss me dear, with passion ...softly soft... kiss me with your desire.. kiss me with a little bite...” “What....?!!!” Furucin ya fito daga baki na, sannan a lokaci guda na mike ya yi saurin kamo............... _ ASSALAMU ALAIKUM MASU KARATU, MASOYA ZAFAFA.. DUKA_DUKA ANAN NI NANA HAFSATU ZAN TSAIDA ALKALAMI NA, SAI HADUWA TA GABA IDAN MAI DUKA YA KAI MU... ALLAH YASA MU SHIGA WATAN RAMADHAN A SA’A. ALLAH YASA MUNA CIKIN YANTATTUN BAYI. RABBI YA YAFE MANA KURA-KUREN MU... MUNA NEMAN YAFIYAR DUK WANDA MUKA BATAWA, ALLAH YA YAFE MU BAKI DAYA. IN SHAA ALLAH! IDAN MUNA DA RAI DA KOSHIN LPY, BAYAN SALLAH DA YARDAR ALLAH ZAMU DORA DAGA INDA MUKA TSAYA... A CIKIN LITTAFIN KIBIYAR AJALI.. NAGODE SOSAI, A AZUMCI WATAN RAMADHAN LAPIA💋💋SON SO!!!_ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p _*KIBIYAR AJALI.....!!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_ 🏹👑👩‍❤️‍👨💝 _MALLAKAR:- NANA HAFSAT 🧕🏼*_ _*(MISS XOXO)*_ _*©️®️ZAFAFA 5: 2021*_ _(PAID NOVELS)_ _Wattpad:missxoxo00_ *_BOOK 2_* _PAGE: 1_ _Barka da sallah lovelies! Allah yasa munyi ibada karbabbiya, Aamin! Allah ya amshi ibadun mu ya karba mana.🤲🏻 Kamar yadda kuka sani, Kafin azumi mun kammala KIBIYAR AJALI na d’aya (book 1)! Yanzu da yardar Allah zamu dora a book 2. Daga inda muka tsaya a baya.😅🥰 Asha karatu lapia🤗💖_ _MASARAUTAR BASANNABAS_ Ya riko Kasan rigar jiki na, Yana mai rintsa idanun sa. A hankali cikin wata irin kasalalliyar murya yake cewa, “Sha..shaheeda! Kizo gare ni please.” Takaici, Bakin ciki da bansan na meye ba ya tsaya min a wuya. Na wulkita idanu na na zabga masa harara. Banda tsabar renin hankali dama dik abubuwan nan ya dauka itace? Kwafa nayi na dube shi shakeke, “Ba ita bace...” “No... Nooo! Shaheeda, Kizo gare ni plsss.” Naja siririn tsaki a hankali, Da ace bayamin kwarjini bane dana ja masa Allah ya isa wallahi. Cike da takaici na mike na koma can karshen d’akin kan wata royal sofa. Na zubawa screen din wayata idanu ina jiran shigowar kiran Adda Maryama, Domin tace idan lokacin tafiya yayi zata kira ni. Cikin zaman kuramen da muke na zabga tagumi ina kallan gefen kujerar da na ke. Shin yana sane yai min haka ko kuwa duk cikin ciwo ne? Wata zuciar tace yana sane, Rabu da maza halin su sai su. So yake ya kunsa miki bakin ciki. Na sake jan wani tsakin a karo na ba adadi. Dai dai lokacin kunnuwa na da hanci na suka jiyo mini sauti da wani arnen turare mai tsananin kamshi. Gimbiya Shaheeda ce ta shigo bayan jakadiya ta sanar da isowar ta. Kan ta tsaye tayi wajen Sarki Salman tamkar batasan ina zaune ba. “... Shaheeda.... Come to me.” Na dan kalle su ta kasan idanu na ina zubawa sarautar Allah idanu, “Sssh! Love! Ni ce.. Gani nazo ai. Sannu kaji, Sannu..” Tana magana ahankali tana shafa kwantacciyar sumar kansa. Mik’ewa nai na fuce bayan na d’auki laffaya ta na barsu lokacin da naga tana kokarin cire mayafin jikin ta. Cikin sauri na fice ina harde tafiya. Gaba d’aya ji nayi bazan iya sake kara koda second d’aya bane a masarautar nan. Jiki na sai rawa yake, wasu irin surutai na rika ji a cikin kunne na. Nasa ka hannu akai ina rintse idanu na. Baki na ya gaza furta tulin addu’oin da nake ji dankare a kirji na. Wani irin dishi dishi na fara gani, Sama-sama nake jiyo sautin muryar Addah Maryama, Ni dai sulalewa nai awajen ban sake sanin inda kai na yake ba. Koda muka koma gidah, Addah Maryama ta taimakamin na shiga band’aki nayo wanka da alwala. Ji nayi gaba d’aya yanayin da na tsinci kai na a cikin masarauta dazu yanzu bana ji. Sai kadan kadan. Sallah na mike nayi na shiga addu’oin kariya da neman zab’in Allah. Na kasa manta wulak’ancin da Salman yayi min yau. Koda bama son juna bai kamata ace ya cimin fuska haka ba. Cikin haka sai ga Addah Maryama ta dawo da filet a hannun ta dauke da funkaso da miyar ganye data sha tantakwashi. “Sakko kici gimbiya...” Bamu su na sakko nayi bismillah na fara ci saboda yunwa nake ji matuk’a. Sai da naci na gyatse sannan na wanko baki na da hannu na, “Gimbiya.. Ya aka kare da yallabai? Fatan dai abu yayi kyau.!?” “Addah Maryama baki ga a yadda kika same ni ba?” “Wai awajen kofar sashen sa? Na dauka kawai irin yanayin nan ne kin gane ai..” Nayi murmushin takaici kawai ina mai girgiza kai na, Idanuwana suka kawo ruwa, Naja gefen zani na na goge hawayen, “Addah Maryama.. Salman yamin wulakanci... Ko kinsan duk abubuwan da kike ce nayi nayi..Wai anma tsabar cin fuska se kira na yake da Shaheeda. Duk abubuwan nan ya dauka ita ce....” Addah Maryama zatai magana na sake katse ta ina jan wata ajiyar zuciya, “Can sai ga matar sa. Bansan ta ya akai tasan da zuwa na ba.. Kinga wulakanci.? Agaban idona suke...” Kasa karasawa nayi na fashe da wani irin marayan kuka, Addah Maryama ta janyo ni jikan ta tana bubbuga bayana alamar ban hak’uri. “Sssh! Ya isa! Bar kuka gimbiyar mu, Nagane abunda yasa ki jiri dazu. Kiyi hak’uri. Inaso kisan ba lefin Salman ba. An rigada an juyar masa da hankali. Mutumin da sam mahaifiyar sa bata gaban sa. Kai harta yan uwan sa da suke ciki d’aya gaba d’aya baya ta tasu. Banda aikin tsibbu aina ake haka..? Inaso ki san ba lefin sa bane wallahi. Sihiri gaskia ne. Addu’a kawai zamu cigaba da yi. Kuma mu tashi a tsaye muma mu nemi na kariya.. Kina jina?” Daga kai na nayi sama alamun Eh! Na cigaba da share hawayen fuska ta ahankali.. Hankali na tacigaba da kwantar wa ta hanyar bani labarai masu ban dariya. Ni kuwa gaba d’aya daren ranar ban runtsa ba, Tunani kawai na cigaba da yi, Shikenan ni kuma haka tawa rayuwar zata k’are a wahala? Haka zan ta bautawa wasu ni ina disashe tawa rayuwar? Na rafka salati ina mai cigaba da juyi a makekiyar katifar dake kan gadon da nake. Bansan sanda bacci barawo ya sace ni ba... *MASARAUTAR BASANNABAS* *SASHEN SARKI ALIYU SALMAN ALIYU (SAS)* Zufa ce kawai ke kwarara a jikin sa. Sai rawar sanyi yake yana mai sake takurewa a karshen makeken gado dakin sa. Shaheeda tayi rau-rau da idanu, Gaba d’aya duk daukarta nata bomaboman aikin ne suka masa yawa shi yasa yake haka. Ta cire idanu ta maida kallon ta ga kujerar da Khadija ta tashi akai. Wani tsaki taja mai cike da takaici. “Yanzu Salmaan har ganin banzar matar can kake a boye? Why Salman? Me nayi da har zaka ci amana ta haka? Uhm..” Shi kuwa Salman sam bai masan inda kansa yake ba. Taita maganganu ita kadai tamkar zaucacciya. Can tabi robobin ruwan tofin da aka shanye da kallo. Tamkar sabuwar tabi haka ta mike jiki na bari ta kunce mad’aurin zanin jikin ta ta ciro wani kullin magani. Ta zuba a roba ta karkada shi sannan ta durawa Salman a baki. Yana kwance ba Uhm bare uhm uhm, Sai kakkarwar ciwo da yake faman yi. Tana gamawa ta sulale ta koma sashen ta hankalin ta a matukar tashe ganin yadda ta samu Khadijaa bayan duk ta aiwatar da abubuwan da malam yace tayi zasu rabu da Salman. *GIMBIYA SHAHEEDAH* Zagaye ta shiga yi a dakin ta, kafofinta kunnen ta rike suke da na’urar Bluetooth ta amsa waya. Maganata ake haukace tana daga hannaye. Don dama idan tana cikin tsananin tashin hankali to hakan ne yake faruwa da ita. Tayi ta yin abubuwa tamkar na marasa hankali, “Hajjaju... Ni de ki kara tambayar sa. Domin Salman fa bashi da lapia sosai. Kuma tinda na binne layar nanne aka sanar min bai san inda kansa yake ba. Anya kuwa malamin nan da kika rakita yasan abunda yake yi?Gaskia bazan lamunta ba Hajjaju. Ko dai bai san kan aikin bane? Ina gaya miki Salman is out of his senses. Ya zama kamar soko.. Ko Kinsan da tsinanniyar nan na ganshi.. Hajjaju ki kara ‘kaimi dan Allah, Zata wargaza min sirri matar nan.” Tana magana cikin tsananin fushi, Hannun ta d’aya tana dukan bango dashi. Mahaifiyar tata sai neman kwantar mata da hankali take amma sam tak’i yadda, “Kawai ki je ki same shi, Idan ba zai iya bane mu nemi wani malamin, Domin wannan yana neman ‘ballo mana da ruwa.. Okay! Seda safe.” Kit ta katse wayar ta koma ta zauna tana cizan leben ta na ‘kasa, Magana take ita kadai tamkar da wani a kusa da ita, “Ya zaai ace ni da miji na amma sede ni na nemi shi ba dai shi ya neme ni ba? Ya za’ai ace mu’amalar aure kullum sai baya cikin hayyacin sa yake tunkarata? Dole na nemi mafita.. Tun kafin komai ya bayyana.” Tayi mita tayi tsaki haka ta kusan raba dare tana abu d’aya... *SAS* Kunsan yadda zance yake yaduwa a masarauta.. Kan kace kanzil! Magana ta yanyana har cikin gari da wajen sa.. Cewar Sarki bai da lapia baya fita ko’ina, Zaman fada ma yanzu waziri ne yake zama. Atakaice dai sarautar ta dawo tamkar babu sarki. Babu irin ciwon da mutane basu kwakwulo sun jajiba shi akan sarki Salman ba. Kowa tofa albarkace bakin sa yake. Sarki Salman na kishingid’e akan wani lallausan carpet dinsa dake malale a makeken parlorn sa. Tufa ce agaban sa. B’angaren sa na dama kuma waziri ne kansa a kasa. Sarki Salman kallo d’aya zakai masa kasan tabbas bayajin dadi. Gaba d’aya ya zabge sai dai ya kara haske. Manyan idanun sa sun sake manyanta tubarkAllah! Kwarjini ya kara lullube shi, Idanun sa saqale da gilashi. iPad ce a gaban sa yana nunawa waziri wasu abubuwa.. Waziri ya kara k’asa da kansa alamun girmamawa da tausasa harshe yace, “Ran sarki ya dade yayi karko. Ko dai zaka kokarta ka leka fadar ne?” Sarki Salman yai hanzarin girgiza kansa yana jan leben sa ta kasa. “Ba zan iya ba waziri, Jiri ne ke kwasa ta idan har na mike. Na kuma gaya maka har yanzu kirjina nauyi yake min, Tamkar an dora duwarwatsu...” “Assha! Sannu ranka ya dade! Allah ya kara maka lapia.. Da yardar Allah zan kara karb’o maka turaren miyagunnan. Idan kayi kana jin dadi ko?” Daga kai kawai Sarki Salman yayi ya maida kansa kan wani pillow ya kwanta. Bai kara cira kai ya dubi waziri, Kambun mulkin nasa sun motsa. Haka waziri ya karaci zaman sa ya mike yai masa sallama ya tafi. Ya bar sarki salman kwance yana tunanin da shi kansa bai san na menene ba. <<<<>>>>>> <<<<<>>>>>> Kwance yake akan wani katafaran gado, a kalla zai iya daukar mutum bakwai ba tare da sun matse juna ba wajan bacci. Amman shi kadai ne a kai ya yi ruf da ciki kafafuwansa a wale yana ta sakin munshari. Idan ka karewa bedroom d'in kallo zaka tabbatar da cewa jiya ya sha bidirinsa, saboda kayan da ya cire duk gasu nan a kasa ya yi wurgi da su. Dogon wandon yana gefe, T.shirt din ma na wani gurin daman, p.cap din sa ma haka. A tsakiyar center carpet kuwa, kwalaban barasa ne da ya sha kusan guda hudu. Akan bedside d'in sa ma wasu guda biyu ne an shanye daya an rage wata a cikin kwalbar. Idan ka kare masa kallo tsab kuwa a yadda yake ta shakar bacci, ba zaka taba zato ko tsammanin yana da wata tawaya a cikin rayuwarsa ba, saboda wani irin sihirtaccen kyau da Allah buwayi gagara misali ya yi masa. Wani kyakkyawan abin hannu ne a tsintsiyar hannunsa, tsakiyar an rubuta A.A.S. Wato Abdullah Aliyu Salman. Cikin tsakanin firgicewa ya tashi yana waige waige tamkar me neman wani abun. Idanunsa ya kai kan agogon dake ajiye akan bedside ya duba lokaci, take ya kuma zabura ya mike yana furta. “Subahanallah....” Bathroom ya shiga nan da nan ya sakarwa jikinshi shower, ko cikakken minute biyu beyi ba sai gashi ya fito daure da towel. Da sauri ya bude drower ya ciro suit dark blue, ko mai be tsaya shafawa ba haka ya zura kayan tare da karasawa wajan madubi ya kalli fuskarsa. Duk da cewar be yi wani abu ba, amman ya yi matukar kyau, idan Allah ya baka cikar zati tofa ka godewa Allah koya a wane yanayi kake, kai d'in mai kyau ne. Cikin sauri ya fesa turaruka kusan kala biyar sannan ya dauki jakarsa ya fito yana ta faman buge mutane. Yau ya yi alkawarin zuwa gidan su shi yasa ko tsayawa yin wasu kakale-kakale beyi ba, kasan cewar ya kusa makara ko da wane lokaci jirgin da zai bi zai iya tashi a lokacin. Yana zuwa kuwa ya tarar passengers duk sun shiga har ana shirin rufe kofa, aka jira shima ya shiga, nan da nan kuwa suka tashi sai jahar shi ta gado, wacce ba zai iya tuna rabon shi da zuwa cikin ta ba. A Abuja suka sauka, amman a ranar ya taho Kano duk da cewa akwai guraran da zai kwana amman sam hankalinsa yana kano yafi son yaje can kai tsaye. *SASHEN MAI BABBAN DAKI* (GIMBIYA SA’ADATUH) Carbi ne a hannunta, Lazumi take yi ganin yadda labbanta ke motsawa ahankali. Hawaye d’aya na bin d’aya a kyakkyawar fuskar ta. Taja ajiyar zuciya ta sauke tana mai goge hawayen da kasan jilbab din jikin ta. Cikin haka Yareemah Abdullahi autan ta ya shigo yana harhada hanya, “Ammi.......!” “Na’am Abdul..” Kasancewar sunata mahaifin yaci. Hakan yasa bata iya karasa furta sunan nasa duka. Da sauri ta karasa goge hawayen fuskar tata gudun karya gani. Girgiza kansa yayi saboda yadda yake jin kansa a duniyar sama, “Ya makaranta..?!” Pcap din kansa ya zare ya wullar a gefe, Zubewa yai akan kujera saboda tangadin da yake yi. Duk da acikin maye yake, Bai gama sakin saba, hakan bai hana shi dafe kansa da hannun sa na dama ba ya runtse idanun sa dakyar yace, “Ammi...! Barka da rana.” “Barkan mu Abdul.. An dawo lapia? Maza tashi jekai wanka kaji? Kafin ka fito za’a shirya maka abinci..” Mik’ewa yai dakyar yana tangadi yayi hanyar fita kenan ta katse shi, “Ina zaka Abdul?.” “Waww..Wan.. Wankan zanyi.” “Au.. Shiga bandakin kasa na cikin dakin nan kayi. B’angaren ka sai dai kayi hak’uri, Yayan ku ya kara aure amaryar can take.” Wani ashar ya lailayo ya dura yana rike cikin sa, “Amma bashida mutinci. Bara na fito sai nayi ‘kasa kasa dashi.” Yana magana yana tafiya har ya shige cikin dakin, Kansa ne ya shiga juyawa ya zube akan gado ya fara jan munshari take baccin maye yai awun gaba dashi. Gurfane Ammi tayi tana girgiza kai, Matsalar ta duk duniya akan yaranta ne. Dan autan ta da zata kalla taji dadi shima an gurbata tasa rayuwar. Kullum cikin shaye shaye, Ba’a makaranta ba ba’a gidan ba. Makarantar kwana suke suna babbar sakandire. Kullum idan sunyi hutu shi sai ya jima kafin ya dawo hakan ce take kasancewa dashi, Yaita shaye shaye yana debo mata magana.. Gashi dik cikin sauran yaran shi kadai ne meyi.. Sabon shafin kuka sosai Ammi ta bude tana yin sa ba kakkautawa.. Tarasa madafa, Tarasa farin cikin ta, Hannu ta daga sama tana rokon Allah daya kawo karshen wannan kaddarar rayuwa da take gani itada ahalin ta kala kala... *GIDAN GWAGGO TA FADA* Band’aki na shiga na canza pad din jiki na, Wannan jini na rasa ranar da zai dena kwarara, Ya ragu sosai ba kamar da ba. Amman har yanzun yana fitowa. Wani lokacin harda guda guda. Kaya na zura marar nauyi na fesa turare mai sanyin kamshi marar karfi. Haka kawai na tsinci kai na da kallon kai na ta mudubi. Shin ni din menene laifi na da mutane basa so na? Se bina da sharri da mugayen alkaba’i? ‘O ni dije Allah ka jikan iyaye na da rahama, Wasu abubuwan da akeyi min don rashin babu idanun su ne. Tabbas iyaye katanga ce mahallakar makiya. Nayi kewar ku Ummah Da Baffanah. Allah yasa aljannatul frdwas ta zama makoma agare ku da dik musulmai baki d’aya.’ Siraren hawayen da suka zubomin na goge da tafin hannu na, A haka addah maryama ta shigo ta same ni. “Ah’ah! Gimbiyar gimbiyoyi, Takawar ki lapia sarauniyar zuciyar sarkin garin mu adali me son mu, Dan Allah ki dena zubar da hawayen ki, Inajin ciwon hakan har cikin zuciya tah... Kinji?!” Murmushi nai kawai hade da kada kai na. Ta tako har gabana tana mai rufe murfin Kullaccam din dana gama shafawa, “Gwaggo na neman ki..Tana babban parlor ki sako mayafi ko hijabi domin itada bako ne.” Sake kada mata kai nayi, Domin labbana sunyi nauyin furta kalamai. Ficewa tayi bayan ta ciro min wani gogaggen hijabinta a drawer, Na dan jima a Zaune ina sakawa da warwara kafin na mike na nufi babban parlorn Gwaggo ta fada wanda ya kasance na masaukin baki. Baki na dauke da sallama na shiga ciki, Suna zaune su uku. Gwaggo, Addah, Sai wani dattijo gemun sa ya zama furfura gaba d’aya. Ya rufe kansa da hirami. Gaishe su nayi baki d’aya, Gwaggo ta nuna min kusa da ita na zauna. “Itace wannan Hajia.?” Ya tambaya yana mai kallon Gwaggo ta fada. Gwaggo ta jinjina kai. Ya sauke numfashi yana girgiza kai. Na kalli Gwaggo kallon karin bayani. Gwaggo tace, “Khadija wannan da kike gani babban malami ne na sunnah, Yanada makarantu na tsangaya dama Islamiyya. Kuma ya kasance kamar dan uwa ne agare mu. Domin duk abunda ya sha mana kai ma’ana ya zarce karfin sanin mu.. Toh awajen sa muke neman karin haske. Sunan sa Malam Mujaheed Na Soro, Na gaya masa matsalar da kike ciki tunda dama yasan Salmanu ya kara aure, Tofin nan da kika yiyyi amfani dashi dana wajen Salmanu duk almajiran sa yasa suka yiyyi, To dana gaya masa ba wani canji dai shine yace zai kara bincike akai duk yadda ake ciki zai zo da kansa...” “Toh Gwaggo.. Allah yasa adace.” “Aamin Yaa Rabbi... Malam! Bismillah!”Cewar Gwaggo Ta Fada. Gyaran murya Malam yayi, Ya sosa gefen kunnen sa kafin ya fara cewa, “Wato azahirin gaskia Hajia wannan babban makaru aka yi musu jifa daga ita har shi sarkin.” “SubhanAllah..!” Addah Maryama tafad’a tana mai girgiza kai cike da tausayawa. “Ai Malama Maryama akwai mutane marasa imani a duniya, Wanda digon tausayi wallahi basu dashi a zukatan su. Ahar kullum su dakushe farin cikin mutum yai ta zama a lalace shi suke so. Da zakuga yadda zukatan su suke bakikkirin idan farin ciki yasamu wanda suka tsana zakuyi dimbin mamakin yadda suke shiga mawuyacin hali, Sai sun bi ta kowacce hanya sun kauce sunyi shirka sannan suke jin dadi. Wallahi duk yadda zasuyi sai sunyi wajen ganin sun dakushe mutum, Kai Allah ya mana katangar k’arfe da makiyan mu..” “Aamin Aamin!” Muka hada baki wajen amsa addu'ar malam... ... Masu tambayan if yerwas truly a scented product.?...Well yess😅 Yerwa incense and more as the name implies dagaske kamfanin turare ne na turaren wutan kanem empire (bornu) Turaren Kaya, gidah, khumrah’s, kulaccams, turaren ruwa na larabawa dana fesawa, English perfumes, kabbasas, burners, steaming chairs, Kai komai da komai dai na turare Muna dashi.. You can check us on ig @yerwaincense_and_more, Muna tura kayanmu ko’ina a fadin najeriya kai harda nahiyar ketare ta dhl👏🏻Muna bada kayanmu akan farashin sari da saya dai-dai... so please do follow our Instagram page above👏🏻 ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 P I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p. *BOOK 2* *PG:2 * ________ “Sihiri gaskia ne, Kuma kowa zai iya kama shi dik kuwa da yadda kake tsarkake jikin ka, Sai dai kamuwar na wani yafi na wani, Saboda karfin tashi tsaye da kariya. Ranki ya dade ina fatan kina saurara?... ” Ya karasa fada yana duba na, Na daga kai ina mai cigaba da jinjina kalaman sa na baya akan ma’kiyi. “Nayi bincike sosai akan zancen ki da Hajia ta sanar min, Har na sassa yara suka yiyyi addua aka yi miki tofi kuma.. Har yanzu jinin na fita kamar da ko kuwa ya ragu?” “A’ah! Ya ragu ba kamar da ba.. Nagode Malam!” “Toh gaskia babban sihiri ne wannan, Kwanaki can baya an kawo min ire iren matsalolin nan. Kuma duk yawanci dai abokiyar zama ce silar ko kuwa wani makiyi na daban.. Shi sihiri gaskia ne domin ya kama annabin Allah ma ballantana mu karan kada miya. Wannan jini da aka sakar miki duk d’aya ne daga sharrin sihiri. Ki cigaba da ibadar ki, Anyi hakane domin wata manufa don kada auratayya ta shiga tsakanin ki da mai martaba. Kuma ta Allah bata suba, “Sannan duk wannan warin da kikace kina ji na kamar shekararren mushe duk makuru ne wallahi, An miki jifanne don ke kan ki ki kyamaci kan ki, Sannan wani kara da gane gane da kike yi duk razana ce don ki fita ki bar masarautar ne. Sannan an dasa miki tsoro da fargabar cikin ta. Wannan duk sharrace sharracen sihiri ne, Ana kara nisan ta tsakanin ku da juna, Ma’ana ke da mai martaba, Sannan duk wutar kinsa dake sake ruruwa a zuciyar ki duk Sharrin shaidanu ne da akai amfani dasu, Amman In shaa Allahu nan ba da jimawa ba komai zai dai-dai ta da yardar Allah...” Shiru nayi kawai ina maimata maganganun sa a zuciya tah, Allah na tuba Salman ai ba son hakika yake min ba. Ya aure ni ne dan ya muzguna min. Kawai saboda nayi kokarin ganin ya amsa tambaya a saukar qur’ani da akai. Na sauke nannauyar ajiyar zuciyar da sai da dukkanin su suka dago suka kalle ni, “Gimbiyah ya dai...?” Cewar Addah Maryama da kulawa. Na girgiza kai kawai alamun ba komai, Hade da ka’karo murmushin yak’e. Malam ya cigaba da cewa, “Toh abubuwan sammu dai da yawa akai miki gaskia, Wanda duk wani bakon lamari da jikin ki ko zuciyar ki zata kissima miki duk sharrin shaidanu ne la’anannu, Domin da su ake hada kai acuci bil adama. Allah ya saka muku da gaggawa kuma ya yaye muku dukkanin matsalolin da aka jefa rayuwar ku aciki... Sai kin kara jajircewa da addu’oi sosai, Da yawan salloli, Lazimi da karatun qur’ani, Babu dare, babu rana. Da yawan sadaqah In Shaa Allahu rayuwar ki da tasa zata daidaita da duk wani masoyan ku da ake dakushewa. Muma a namu b’angaren zan sa yara suyita sauke qur’ani, Zan tayaku da adduoi nima, Sannan ga ruwan tofi nan na kawo da akai da zam-zam, Gasu Zaitun nan, Da habbatussaudah da ganyen magarya nan ma, Zan baki ayoyin da zaki karanta.. Kina ji?” “Inaji Malam.. Nagode!” “Yauwa shi wannan magani da ake da ganyen magarya ba sai an maka sihiri ba ko an jefe ka, A’ah kowa zai iya yi don tsima jikin sa daga sharrin masharranta, A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai kingan su nan (idan an samu busassu sunfi), sai a nika a zuba cikin ruwan. Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan. Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara). Sai a karanta Suratul A'araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122. Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82. Suratul Kafirun kafa daya Falaki da Nasi kafa uku- uku. Sai a karanta wannan addu'a, "Allahumma rabban-nas az'hibil ba'as ashfi wa antash-shafi la shifa'a illa shifa'uk shifa'un la yugadiru sakaman" kafa uku. Sannan za'a iya karawa da wannan addu'a "Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika" kafa uku. Insha Allahu ta'ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi. Wala nan kusa wala nan da wani dan lokaci. Allah ya shiga lamuran ku gimbiya, Allah ya kara tsare ku da tsarewar sa, Ya kare ku da kariyar sa. Allah ya kara muku ni’ima daga cikin ni’imomin sa, Allah ya karba mana Allahumma Aamin.. Ga kuma wasu addu’oin na rubuta miki, Ki dingayi kullum, Sannan azkhar ma na safiya da maraice dana kwanciya bacci dan Allah ki rike su karkiyi wasa dasu.” “Sannu Malam, Allah ya amsa. Mungode Allah ya saka da alkhairin sa.” Gwaggo Ta fada ta amsa masa fuskar sa dauke da fara’a. Da alama taji dad’in addu’oin da ya babbani. “Babu komai Hajia, Yiwa kai ne, Fatan Mu dai addu’oin mu su karbu Allah ya yaye musu..” “Malam Nagode, Allah ya saka da alkhairi..” Nai masa godia ina karanta addu’oin dake cikin paper daya rubuto min. Sallama ya mana, Ya mike ya tafi bayan Gwaggo tai masa goma ta arziki, Ya tafi yana mai godia sosai. Bayan tafiyar Malam muka yi sallah muka sake sabon zama, Gwaggo Ta Fada ta shiga kara kwantar min da hankali, Tana mai sake bani wasu labarun game da masarautar basannabas. Ta kar’kare da, “Rayuwar sarki Salman abar tausayi ce gaba da baya, Kada ki manta gaba d’aya an juya masa hankali akan mahaifiyar sa, Yana abubuwa tamkar bashi da uwa, Tana raye gida d’aya dashi amman an riga da ancireta cikin zuciar sa, Yan uwan sa da suke uwa d’aya uba d’aya ma an cire su a zuciar sa, Gaba d’aya an cire sanayya, So da shakuwar yan uwan sa na jini da mahaifiyar sa a zuciar sa. Bayaga haka.. Shin ko Kinsan yan uwan nasa da suke uwa d’aya uba d’aya?” Na girgiza kai, Alamun bansani ba. Gwaggo Ta Fada ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa, “Kamar yadda na gaya miki a baya, Su uku ne wajen mahaifiyar su, Salman shine babba, Sai Khaleel (Khal) sai auta Abdullah, Khaleel tun karewar karatun su aka kafe shi acan ya’ki dawowa, Ba ruwan sa da yan uwan sa da mahaifiyar sa shima, Yaki dawowa, Har aika mutane akeyi su gano inda yake an kasa samun sa, Ance dai ya zama babban likita acan din. Shi kuma autan su Abdullah yana ajin karshe a sakandire baya maida hankali ga karatu sai shaye shaye da d’auke dauke, “Shima an gurbata tasa rayuwar, Kullum sai neman magana, Gaba d’aya dai gasu nan gasunan ne, Salman a nutse yake kawai dai an juyar masa da hankali ne.. Yan uwan sa da mahaifiyar sa basa gaban sa, Sarki ne a zahiri amma a badini ba shine ke mulkar masarautar basannabas ba, Ba shida ta cewa sai hukuncin da aka zartar akan sa, Ga wancen na ketare (Khaleel) An kafe shi acan, Ga k’aramin cikin su shima, Gaba d’aya abubuwa sunyiwa gimbiya Sa’adatu yawa. Ba wanda zata kalla taji dadi, Har gwara-gwara Abdullah karamin su... Kina jina ko gimbiya?” Hawayen dake mak’ale a idanuna na share, Tabbas wannan damuwar su ta shanye tawa. Wannan wacce irin musibace? Fisabilillahi duk akan mulki? Ka salwantar da rayuwar mutane? Ka raba su da farin ciki? Akan me? Mulkin da za’a mutu a barshi? Nasa kasan tissue din hannu na nagoge idanuna dake zubar da hawaye, “Inaji Gwaggo... “ “Auren ki da Sarki Salman alkhairi ne, Domin In Sha Allahu kece zaki zamto silar warwarar matsalolin ahalin Gimbiya Sa’adatuh da iyalanta, Saboda haka dan Allah ki cire waswasin ba zaki iya zama a masarauta ba, Munata addua, Ana tayamu, Kina yi kema , Da yardar Allah, Allah zai kare ki daga sharrin masu sharri...” “In shaa Allah Gwaggo..” “Yanzu zamu kara zage damtse da addu’oin neman kariya, Maryaama zata kara nunar dake wasu abubuwan, Daga nan sai mu tsaida rana ki koma dakin ki..” Gaba na yai mugun bugawa, Idanuna suka ciko da hawaye. Baki na na rawa nace, “Gwaggo meyasa?” Gwaggo tayi murmushi irin nasu na manya Kafin tace, “Ai dole ne ki koma dakin ki gimbiya, Ko ni badan gudun fitnah ba ai da har yanzu ina cikin masarauta, Amma saboda nuna bangaranci da iko dasu wambai suke, Shiysa na tattara na dawo nan din tun haihuwar babban ‘da na mai rasuwa, Ni kinsan mahaifiyata ni kadai ta haifa ta rasu, Ba mahaifiyar mu d’aya da su Yayan mu ba, Wato kakan sarki salman na yanzu, “Amma kanmu mu a hade yake ba zaki taba banbance yan wannan dakin dana wannan ba, Duk inda aka samu rabuwar kayuwa dama daga iyaye mata ne, Saboda kishi. Yanzu dubi zaman doya da manjan da mahaifiyar Salman take ciki da yaranta. Kishiyoyin sun ware ta da ‘yayanta, Dama nan kadai suka tsaya da sauki, zallar sihiri suke jifan su sun rarraba mata kan ‘yaya.. Kai duniya abun tsoro..” Bata k’arasa magana ba sakamakon mugun tarin daya sarketa tashiga yi, A sukwane na d’akko ruwa na bata ta balli magani ta sha. Addah Maryamah tashigo alokacin ta min nuni da gwaggo ashe har bacci yafara daukarta ta bingire. Na mike a hankali Na fita, Muka jawo mata k’ofar muka koma d’aki, Nan Addah maryama tashiga karasa min daga onda Gwaggo ta tsaya, Ahmkali take wayarmin kai gameda kowane bil adama dake cikin masarautar, Tun daga kan sunan su, Da mukamin su, Da sashen da suke, Da komai daya kunshi Salman kannen sa da mahaifiyar sa. Kai Harda Matar sa, Da kishiyoyin mahaifiyar sa. “Duk wani makirci da tsibbu da akeyi ki sani yana futowa ne daga kishiyoyin mahaifiyar sarki Salman, Kai basu kadai ba harda iyayen su, Dama wanda bamu Sani ba a b’oye, Sannan matar sa gimbiya Shaheeda Itama ba’a barta abaya ba wajen bunka masa nata sihirin, Tun fil azal batasan mahaifiyar sa dama.. Lamarin dai Sai addua kawai.” Naja gwauruwar ajiyar zuciya na sauke, Cikin tsananin tashin hankali nace, “Kenan bakin su d’aya dasu?” “Eh bakin su d’aya ta wani bangaren, Amman kowanne daga cikin su yana da boyayyen burin sa a zuciya, Ita gimbiya shaheeda ai burinta baya wuce ta haifi magaji.. Sai dai ance dan kuwa ban sani ba, Amma dai an tabbatar cewar wai shi sarki baya haihuwa, Su kuma kishiyoyin mahaifiyar sa wasu daga ciki nason’yayayan su su gaji mulkin Wato a tsige sarki Salman akan karagar mulki a dora nasu, Nasan kuma akwai meson mahaifinta ya gaji sarautar, Tunda kinga duk yan ahali d’aya ne, kowacce tsatsonta zai iya gadon karagar mulki, “Kowane rukuni so suke sarauta ta dawo hannun su, amman mutan gari sunfison tsatson ilyasu wato familym sarki salman kenan. Kuma a yanzu gaskia mutanenan gari da ma makotan garuruwa kowa yanason sarki Salman yanada farin jini da kwarjini a idanun su, Duk kuwa da a Zahiri ne yake kamar sarki a badini ba sarki bane.. Gimbiya Salman na bukatar kasancewar ki a kusa dashi.! Domin makiya nason tube shi daga rigar mulki. Ki temaka dan Allah.” Nayi murmushi ina maimaita maganganun data fada, Baya haihuwa? Tafi nono fari, Domin dama banda ra’ayin samun jini na daga gare shi,Haka kawai na tsinci kai na da ce mata, “Gaskia rayuwar su na cikin hatsari, Amman ni yar tahaluka dani ta yaya zan iya gyara rayuwar su? Bayan ni kai na kina ganin yadda aka mayar da ni, Ba don taimakon ku ba ai da Bansan wane hali zan tsinci kai na ba..” “Tunda dai kikaga har an auroki an shigo dake cikin gidan nan kinsan kedin kainuwa ce dashen Allah, Yadda kika gayamin labarin ki ma tabbas nan gaba Kadan zakici ribar hakuri, Sannan ceto rayuwar sRki Salman da mahaifiyar sa wallahi ba karamin lada zaki samu ba, Gwaggon mu yawan shiga masarauta data yiyyi har wani sharri akaso hada mata, Allah ne kawai ya kareta, Badan Allah yasa gwaggon ta tsaya akan mahaifiyar Salman din ba, Ita ma kuma jajirtacciya ce mahaifiyar sa wallahi da tuni sun kassara ta..So gimbiya hakuri zakiyi a kara shirya ki ki koma dakin ki ki zauna, Ki rike mahaifiyar sa a b’oye, Ta zamto abokiyar amanar ki, “Ita kad’aice wadda zaki yadda da ita acikin masarautar nan, Domin ita dinma dake din kawai zata yadda, Batada kowa da zata fuskanta da kukanta, Macece mai gudun zuciya da sanin yakamata, Sannan sai kin iya takun ki, Kin zamto kamar mara wayo kin kwantar da kai sannan zaki zauna Lapia, Domin ko hadiman ki ai na gaya miki kwanaki, Nace miki karki yadda dasu, Abinci ma inda hali dena ci inde tahannun su yake. Za’a iya hada baki dasu a cutar dake, Sai kina takatsantsan. Zama acikin masarautar basannabas sai da iya taku..” Na had’iye kakkauran abun daya tsayamun a wuya ina tuno wahalhalun danasha na jin wari da fargaba sanda ina cikin ta. Don ma jinin na samu yanzu yana sauki sosai. Haka addah maryama taita wayar mun da kai, Wani na dauka wani kuma naita mamakin yadda zan aiwatar. Haka muka kusan Kwana a zaune muna hirar masarautar bassannabas, *BAYAN SATI BIYU!* Yanzu kam Alhamdulillah!! Zama na agidan Gwaggo babu abunda zan iya saka musu da shi, Sai dai na ro’ki Allah, Daya biya musu bukatun su na alkhairi, Yadda suka ceto rayuwata daga kogin halaka, Allah ya saka musu da mafificin alkhairin sa ya kare su da kariyar sa. Domin acikin sati biyu kacal dana kara yi nayi amfani da addu’oin malam, Rass na warke. Jinin gabana ya dena fita, Babu wani abu dake damuna sai dai tsanar Salman da har yanzu bata ragu ba ko mislaka zarratin. Bayaga haka duk wani abu baya damuna, Sai dai gaskiya har banson a ambaci komawata gidan Salman, Sam banason komawa. Nafison wajen Gwaggo baabu takurawa bare fargarbar miyagun mutane. Sai dai alk’awarin dana daukawa Gwaggo zan koma masarautar basannabas, Sannan zan aiwatar da duk addu’oin da Malam yace na dingayi ina tofawa a sashen Salman da garin habbatussadah na turarawa. Da sauran abubuwa da dama. Zan kokarta nayi komai dan neman lada da ceto rayuwar su suma. Bayaga haka digon kaunar sa banaji a rai na, kuma naci alwashin duk sanda komai ya daidaita zan nemi yabani takarda ta. Na kara gaba na auri wanda nakeso yake so na... Da wannan tunanin Addah Maryamah tashigo ta karasa shiryani, Driver ya dauke mu, Suka maida ni sashe na a masarautar basannabas a karo na biyu..... *MASARAUTAR BASANNABAS* ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥. I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p BOOK:2 PG:3 _____ Tun a cikin mota hankali na yake a tashe ina tunanin ta yadda zan shiga masarautar nan mai cike da makirci kala daban daban. Babban abin da yake sake bani tsoro da masarautar shine, yanayin makircin matan gidan da kuma masu rike da mukamai, wanda ko wannen su yake son mulkin ya koma tsatson sa. Lissafi na gabaki d'aya ya kwance sai tsantsar addu'a da nake ta faman yi cikin zuciyata. Gwaggo ta Fada ce ta yi min magana cewa na ciro mukulli na saboda tana so kafin na shiga sashe na Adda Maryama ta shiga ta yayyafa ruwan maganin da muka taho dasu. Jiki na a sanyaye haka na bude jakar na dakko dan tun ranar da tasa aka karbo shi nasa cikin jaka ban kuma bi ta kanshi ba, sai yanzu da tace na ciro shi. Sai da muka fara ajiye Adda Maryama a sashe na sannan Gwaggo ta sanar da shi inda zai kai mu. Abin da ya daure min kai shine wani sashe muka shiga, wanda ko ranar da aka kawo ni na zazzaga ba'a kai ni ba. Shiru banyi magana ba duk kuwa da tarin dimbin tambayoyin da nake son yi mata. Tunda muka fito daga cikin mota hadimai suka fara yi mana kirari tare da barka da zuwa har muka shige cikin sashen da gwaggo tasa driver ya yi peeking. Tun daga babban parlor zaka gane inda ka shigo saboda wani katafaran hoto dake sakale jikin bango yana kallon kofar shigowa. Gabana ya yi mukun bugawa lokacin da nai ido biyu da hoton, sai dai karfin da addu'ar baki na ta yi shine ya hanani shiga cikin wani yanayin na daban. Babu kowa a cikin parlorn, Gwaggo ta nuna min kujera na zauna, tana shirin zuwa wani daki sai ga Abdullah ya fito yana faman hade rai, alamar wani abu ya hado shi da mahaifiyar tashi. Har zai wuce be gaida Gwaggo ba, sai kuma ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba ya shiga mika gaisuwa. Itama kin amsawa ta yi sai binshi shi da kallon sama zuwa kasa tana tabe baki tace. “Ashe ka dawo?” “Eh na dawo, ya gida?” “Yana inda kasan shi. Kai yanzu Abdullah duk tsahon lokutan nan ina kake tafiya baka zuwa ko hutu? Ko ka manta har yanzu mahaifiyarka tana nan a raye? Baka koda sha'awar zuwa ka ganta sai lokacin da ka fa dama kamar haka ko?” Ya yi shiru ba tare da yasan abinda zai iya furtawa ba. Kada kai kawai ta yi ba ta kuma cewa dashi komai ba ta shiga cikin dakin, ya yin da shi kuma ya turo baki ya fara tafiya ya ganni zaune ban masa magana ba shima kuma be yi min ba, sai dai ya tsaya cak yana bina da ido tamkar ya sanni. Na dago ido muka hada dana juna sai duk muka sauke a kusan tare, yana kama da Salman, sai dai Salman ya fishi cikar zati, sannan shi yana da matukar haske, amman daka gansu kasan cewar tsatso d'aya ne ya haife su. “Uhmm....Ke kuma fa?” Na samu kai na cikin izza ta yadda naki koda nuna cewa dani yake, sai da ya kuma yin magana sannan na kalleshi a yatsine. “Kai ma waye?” Ni ma na tambaye shi ta irin sigar da ya yi min tambayar, na kuma dauke kai na zuwa kallon gefe. “Kut...! Kin san ko waye ni kuwa? Toh idan baki sanni ba baki san matsayi na ba ki tambayi ta fada zata gaya miki. Mtseww.” Ya karasa yana jan tsaki duk da cewa na yi masa kwarji duba da ko ido baya son mu hada. Saboda kar ya yi tunanin wani abun hakan yasa na dan daga murya yadda zai jiyo ni sosai nace. “Na ce maka ina son sanin ko kai waye ne? Bana bukata dan haka kar kai tsammanin zan tambayi Gwaggo.” Abdullah ya juyo a fusace yaga alamar nima bani da mutunci yadda yake magana nake mayar masa a matsayinsa na yarima dan marigayi sarkin Basannabas kuma kani gurin sarki mai mulki a wannan lokacin. Sai da yazo dai dai inda nake sannan ya tsaya yana kuma kare min kallo, ganin ko motsawa banyi ba yasa shi dan matsawa baya kadan yana cewa. “Da me kike takama ne?” Kai tsaye nace dashi. “Allah... Da shi nake takama a duk cikin lamari na.” “Ba wannan nake nufi ba. Nayi zaton ko kina takama ne da mulki ko sarauta.” “Kai a zaton ka sune kawai abin takama a cikin duniyar nan? Akwai yan kasuwar da sunfi masu mulki da sarauta komai na rayuwa. Akwai kuma masu takama da ilimi kaga kenan abubuwan tin kaho suna da yawa.” “Ke d'in a wane rukuni kike? Ina son naji.” “Kaje ka tambayi duk wanda kake so a cikin masarautar nan, zaka samu amsar ka yadda ya kamata. Sannan bana son wata tambayar, ina bukatar hutu yanzu.” Kamar daurin baki ya kasa cewa dani komai haka ya juya ya fita yana huci kamar wani tafasasshen ruwan zafi. Ni kuma na saki murmushi cikin rai na ina jin babu wanda zan bari ya rai na min hankali a cikin kannansa, dan naga alamar suna da jiji da kai irin na yaran masu farcen susa. Cikin daki kuwa da Gwaggo ta shiga, tarar da Gimbiya Sa'adatu tayi tana faman girgiza kai alamar wani abun Abdullah ya yi mata. Sai da Gwaggo tayi sallama kusan hudu sannan ne Ammie taji tayi saurin amsawa tana kallon bakin kofar. “Kina na kin ci gaba da sanya matsalar yaran nan cikin ranki ko?” “Ba haka bane Gwaggo, sannu da zuwa shigo ciki.” “Na shigo ciki kuwa, saboda tare nake da yarinya a can parlorn.” “Au to bari ni na taso muje can d'in, ko Maryama ce?” “Ba ita bace ba ma. Bari ina so muyi magana dake kafin muje parlorn.” Jin haka yasa Ammie komawa ta zauna, itama Gwaggo guri ta samu ta zauna tana sauke numfashi. “Zahiri da badini kowa yasan kina cikin damuwa Sa'adatu, an shiga hakkin ki sosai. Amma ki kai ta hakuri, kuma yanzu ma shi zan ce ki ci gaba da yi saboda shine kawai zai fitar dake da taimakon Allah.” Tayi murmushin karfin hali saboda ta nunawa Gwaggo cewa babu komai, sai dai ta makara dan tuni Gwaggo ta Fada tasan cewa duk abinda zai fito daga bakin ta dauriya ne kawai da iya yadda da kaddara a duk yadda tazo. “Gwaggo ai babu wani abu, kamar yadda kika fada ne komai yana da ranar karshe. Fatana kawai shine Allah ya kara min karfin gwiwa, na ci gaba da yadda cewa komai daga gare sa yazo min. Na gode da kulawarka akan duk wani lamari na, Allah ya ji kan iyaye da kakannin mu.” “Amin... Amin Sa'adatu, daman bakuwa ce kuma yar gida na kawo miki ita dan na hada ku kusan juna. Idan har ba haka na yi ba toh ban san lokacin da za'a nunawa kowanne a cikin ku matsayin juna ba. Amaryar Salman ce kawo miki ita dan tace ran da tazo ba'a kawo ta gurin ki ba har na sauke ta.” Kirjin Ammi ya buga, a farkon auran da taji labari ta yi murna sosai. Amman ganin har tsahon wannan lokacin na yau bamu hadu ba yasa ta karaya tayi zaton ko nima haka nake kamar su Shaheedah masu jiji da kai.. Muryar Gwaggo ta Fada ce ta katse tunanin ta, inda take cewa. “Baki da matsala da yarinyar nan yar mutunci ce, tana da nutsuwa da hankali dan gaskiya Salman ya yi dacen mata. Kuma insha Allahu alkairi ne a tsakanin su damu baki daya.” Jin haka yasa Ammi yin murmushi saboda babu abinda take bukata a cikin rayuwarta irin taga wanda zai so su tsakani da Allah babu wani tuggu a ciki. Ta dinga kallon kofar shigowa dakin da alama ta kagu ta ganni, hakan da Gwaggo ta gani ne yasa tai dariya tare da cewa. “Zaki iya zuwa parlorn ne?” Cikin sauri Ammie ta ce. “Eh zan iya.” “Toh muje ku gaisa, daga nan dakin ta zan mai da ita.” Jin ta ambaci daki yasa ta tunawa da tijarar da Abdullah yazo ya yi mata yanzu, na cewa wallahi sai an bashi sashen shi babu inda zai koma. Gashi wadda aka bawa gurin ta dawo bata san yadda zata yi masa bama yanzu, dan koda ta lallaba shi da cewar ya bari za tai magana kin yadda ya yi, har da cewa waye zai ji maganar ta a masarautar bayan duk sun rai na ta. Da wannan tunanin ta mike da kyar ta gyara hijab din jikinta ta bi bayan Gwaggo ta Fada. Lokacin da suka fito bacci ya fara dauka ta a zaune, har sai da Gwaggo tai min magana sannan na farka cikin sauri ina murza ido. Na sakko kasa ganin sun fito da wata wacce nake da yakinin cewa mahaifiyar Salman ce, na kasa kallon ta sosai bare na gane da ita yake kamanni ko kuwa da mahaifinsu. Har suka samu gurin zama ban dago ba, haka kawai naji nauyin dago kai na. Ina shirin gaida ita sai naji muryar Gwaggo tana cewa. “Khadija ga mahaifiyar mijinki Salman ku gaisa.” Kamar jira nake a bani dama, cikin ladabi da sunkuyar da kai na gaishe da ita, ta amsa cike da fara'a kamar daman ta sanni yadda naji tana ta murna. Daga nan kuma hira ta barke ni dai murmushi ne kawai nawa bana iya cewa komai saboda yadda suke min kwarjini duk kan su, har Adda Maryama ta shigo itama ta zauna aka dora da ita, Ammie tasa mai yi mata hidima ta kawo mana abubuwan motsa baki, duk muka ci a tare bisa umarni Gwaggo, kuma da alama Ammie taji dadi dan ta ware sai hira take cikin jin dadi wanda ta manta rabon da taji makamancinsa. “Ga magani nan mun taho dasu, akwai wanda naki ne sai nasu Abdullah. Ku fara yin amfani dashi muga yadda zai kasance, insha Allahu komai zai tafi azo aga kamar ba a yi wata rayuwar ba makamanciyar wannan da ake ciki.” Ammie ta karba tana godiya tare da sake jin kaunar Gwaggo ta Fada dan ita ce kawai mai jin ciwon duk abubuwan da ake yi mata a cikin masarautar Basannabas. Daga nan muka yi mata sallama su Gwaggo da Adda Maryama suka yi min rakiya zuwa sashe na bayan anyi yayyafin ruwan ganyen magarya a duk inda zan taka, baki na kuma cike da addu'o'i har muka shiga parlor na wanda tuni aka canza kujerun, na karamin parlorn aka dawo dasu babba, na babban kuma aka mai dasu karamin parlorn. Zaman mu ba dadewa sai ga Jakadiya ta shigo cikin rawar jiki, ganin ta yasa Gwaggo ta Fada tsuke fuska dan tasan irin bakin munafuncin dake cikin Jakadiya, shi yasa ta tsane ta fiye da abin da baki zai furta. “Ya akai Jakadiya?” “Lafiya lau wallahi Gwaggon mu, ji nai ance amaryar mu ta dawo, shine nazo na yi sannu da zuwa. Allah ya taimake ki ya kara miki lafiya da nisan kwana.” Ta karasa magana tana sunkuyar da kai kamar wata mutuniyar arziki. Gwaggo ta Fada sai faman hade rai ta ke, ta tsani Jakadiya tafi san sauran da aka dakatar kuma tasan duk makircin wannan ne da iya munafunci. “Oho! Toh d'an bamu guri dan Allah zamu karasa tattaunawa.” “Allahu Akubar, toh Gwaggon mu Allah ya ja da ranki uwar kowa.” Bata kula ta ba har ta fita, sannan ta mai da hankali waje na tana kuma yi min gargadi da jan kunne. “Sai kin kula sosai da masu shigowa gurin ki Khadija. Mutane basu da gaskiya musamman na cikin masarautar nan, karki yarda da kowa bare har ki bude baki ki fadi wani sirri naki. Kome nene ki nemi Maryama ko ni ki sanar damu zamu yi miki shi da ikon Allah.” “Insha Allahu Gwaggo zan yi yadda kika ce, na gode Allah ya kara girma da daukaka. Allah ya ji kan iyaye ya rabaku da sharrin masu sharri.” “Amin ya rabbil alamin, bari mu zo mu tafi kafin a fara yada zancen mun zo gurin ki mun zauna. Allah ya bada sa'a. Sai kin dage sannan zaki iya taimakawa Salman Khadija, yana bukatar taimako sosai musamman daga gareki tunda ke din matarsa ce ta sunnah.” Na jin jina kai cike da jin kwarin guiwar zan taimaka musu iya karfi na, zan daure duk da tsanar da nake ji ta Salman naji zan taimaka mishi saboda girma da darajar Gwaggo ta Fada, wacce ta yi min komai a lokacin da nake bukatar taimako. Daga haka suka mike bayan munyi sallama ina jin kamar na bisu saboda mun sabo sosai a dan zaman da nayi dasu. Bayan sun tafi na koma daki na zauna ina saka ta inda zan fara gabatar da aikin maganin wannan ran rainin hankalin da be damu da ni ba bare ya martaba matsayi na na matar sa da ya auro. <<<<<<<>>>>>> Jakadiya ce a gurfane gaban Gimbiya Shaheedah kamar zatai mata sujjada saboda tsantsar biyayya, ta gama sanar da ita cewar na dawo. Kishingiɗe take ana faman yi mata fifita, jin cewar na dawo ta mike zaune tana ware ido, da alama dawowar tawa ta mugun bata mamaki. Tsam ta mike tare da daukar wayar ta da sauri ta shiga daki tare da rufewa da karfi, jiki na kyarma ta kirawo mahaifiyar ta, bugu d'aya ta dauka ba ko gaisuwa ta shiga magana. “Anya wannan yarinyar ba shaidaniya bace? Ta ya ya boka zai ce mana tabar masarautar nan kenan koda marmari ba zata kuma shigowa, amman yau gashi ta shigo har ma ta shiga sashen ta lafiya kalau. Na shiga uku ni dai idan har wannan matar tana kusantar Salman.” Sosai ta razana da dawowa ta, kuma ita kadai tasan tsoran menene dan yadda ta firgice, musamman da taji cewar Gwaggo ta Fada ce ta dawo dani, tasan tabbas sai an bani kariya, dan Gwaggo kowa yasan cewa itama ba a kwance take ba akan lamarin masarautar Basannabas. “Kuma kin yi aikin kamar yadda na sanar da ke?” “Nayi wallahi, na yi yadda kika fada. Kawai ni dai ban yadda da bokan nan ba, sake wani zan yi bana san shirme da shiririta a cikin lamarina.” “Ki dena damun kanki kar ki janyowa kanki wata matsalar. Zanje wajan shugaban yan bori, zan sa ya turo aljannun da zasu hanata ganin Salman d'in, ita d'in wa bare wata ta fada. Kin san ni dai bana wasa da duk lamarin ku bare kuma naki shalele na.” “Shikenan har zuwa yaushe zan ji karin bayani?” “Zuwa anjima ma zanje.” “Ina jiran ki.” Ta maganar tamkar tana yi da bayin ta ko wata kaskantacciya, dan ba zaka yi tunanin da mahaifiyarta take wannan wayar ba. Guri ta samu ta zauna tana maida numfashi, lallai akwai matsala, ba ta nan ma Salman yana ambato sunanta ina ga yanzu ta dawo zata kuma je gare sa tunda matar shi ce, ba ta cikin masarautar ma tazo ganin shi ina ga yanzu da ta dawo kacokam? Dole ta tashi tsaye dan ko ta kan sauran matan gidan da suke yin wasu surkullen tare ba zata bi ba. Mikewa tsaye ta yi tana son ganin Salman a wannan lokacin kafin naje. Ta shirya tsab tare da dora alkyabba, Jakadiya na gurin da ta barta, suka fito tare tana ta yi mata fadanci, bayi kuma suna biye kamar wasu jeluna. Gabanta ne ya buga hango Gwaggo ta Fada na fitowa daga sashen Sarki Salman, tunani barkatai suka dinga yawo a ranta har suka hadu ta gaishe da Gwaggon a tsaitsaye ba wani girmamawa bare mutunci, haka ta wuce tana tsine mata. Gwaggo kuwa girgiza kai tai taja hannun Adda Maryama suka wuce mota. Mamaki ne ya kamata ganin Sarki Salman akan sallaya, alamar sallah ya yi. Rabon da ta ga ya yi tun lokacin da ya kwanta wannan ciwon, sai dai ya yi a kwance ko a zaune, yau kam akan kafafuwansa yake yi cikin nutsuwa kamar ba shi ba. Guri ta samu ta zauna tana karewa bedroom d'in kallo, so take ta gano abinda su Gwaggo suka ajiye ko su ka aiwatar amman duk jarabarta ba ta ga komai ba. Taga ya daga hannu sama yana addu'a, tasan be saba yi a fili ba, amman yau kamar wanda aka budewa makogwaro haka taji yana zuba addu'a wacce tasa ta tsarguwa, inda yake cewa. “Allah duk wani mai nufi na da sharri ban yi masa komai ba, ka mayar dashi kansa. Allah kasan abin da yake zuciyar duk wani abin halitta, kasan masu yi min makirci, ka hana su jin dadi kamar yadda suka gana min....” Baki bude ta ke kallansa saboda mamakin yadda ya yi wannan doguwar maganar, nan da nan ta rude ta mike tare da nufar inda yake. Yasa hannu ya riko nata tare da kallon cikin idanunta, abinda be taba yi ba tsawon zaman su. Sai dai kallon yana tattare da abubuwa wanda kwakwalwarta ba zata iya bayyana mata ko menene ba. Ya matse hannunta tare da cewa. “Duk abin da zan ce kice amin Shaheedah.” Kirjin ta ya kuma bugawa, tana ganin tamkar ita yake tuhuma. “Allah ka bani lafiya Shaheedah.” Ta ce, “Amin honey.” “Idan yadda nake ji a jiki na, wani ne ya yi min makirci Allah ya yi min maganinsa fiye da abin da aka yi min.” Bakin ta ya shiga rawa ta kasa amsawa kai tsaye, ganin asirin ta yana shirin tuno wa sai ta fada jikin sa tare da sakin wani marayan kuka tana cewa...... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p BOOK:2 PG: *4&5* LITTAFAN ZAFAFA NA KUDI NE, MALLAKI NAKI TA NAMBOBIN MU DAKE KASA... KI SIYA HAKKIN KI YAFI DA KARANTA WANDA BA’A BAKI BA.. DON GUDUN..... Instagram handle: @yerwaincense_and_more —- “Honey kayi shiru dan Allah please, wannan duk zafin ciwo ne karka rudar da kanka.” Ta shiga shafarsa tana kuka wiwi ta yadda zata mantar da shi irin wannan manyan addu'o'in da yake yi, wanda tasan tabbas harda ita a cikin wadanda yake yiwa tunda itama ba kyaleshi tai ba. Ai kuwa ya yi shiru, sai dai be fasa yi a cikin zuciyarsa ba, dan ajin da Gwaggo ta Fada tace ya dinga fada kenan. Salman ya d'an dago da ita jin duk ta sakar masa jikinta, ya gyara zama kansa a kasa ya yi shiru kamar wani mai nazari. “Kaci abinci ne?” Ya yi shiru kamar ba zai kulata ba, tsawon lokaci har ta fitar da ran zai amsa sai ta ga ya daga mata kai nufin yaci. “Zaka sha coffee nasa a hado maka?” Ya kuma girgiza kai alamar a'a ba zai sha ba. Duk sai ta rasa me za ta yi masa, can kuma ta sake kwanciya a jikinsa tana son yi masa zancen da ya kawo ta gurin shi. Tana shafar kirjinsa ta ce. “Honey kasan Amaryarka ta dawo?” Wannan karan sai da ya dan kawar da fuskarsa, ya kuma hade rai tamkar an yi masa maganar mutuwarsa, be ce komai ba har ta sake tambayar shi karo na biyu. “Gwaggo ta Fada bata gaya maka ba?” Lumshe idonsa ya yi yana daga kai, Shaheedah ta ji wani abu ya ziyarci zuciyarta na bacin rai. Bata haka ba amman ba komai zata san yadda zatai ta ga haduwarmu ta yi wahala. Salman ya mike ya hau kan gado tare da jan bargo yana jin zuciyar shi na yi masa zugi. Ganin ya kwanta kuma tasan ba kulata zai yi ba yasa ta saurin fita daga cikin dakin tana daukar alwashi kala daban daban. <<<<<>>>>>> Ni kuwa ina sashe na ina faman tunanin yadda zan tunkari sashen Salman, akwai maganin da za'a bashi da daddaren nan. Juyi kawai nake yi akan gado saboda rashin mafita, dan bana kaunar naje na dinga tarar da Shaheedah a gurinsa, ba ta da kunya sam, tun ran da ta shigo ina ciki na gano hakan. Sai dai kuma wani barin na zuciya ta da yake tunatar da ni cewa idan fa ban daure na cire tsoro da fargaba ba bazan taba cikawa Gwaggo alkawarin da na dauka ba. Dole ne na tashi tsaye na dawo da Dije Oganniya ta kamar yadda nake a baya. Sai na cire komai da zai sanya min shamaki wajan gudanar da kudurin mu akan duk wasu makirai dake cikin wannan masarautar ta Basannabas. Kamar an tsunkule ni haka na zabura na tashi, toilet na shiga nai wanka tare da dauro alwala na fito. Sai da na fara yin sallar isha nayi shafa'i dama wuturi sai cikin dare nake yi, kawai na bude wardrobe ina bin kayan ciki da kallo, zuciya ta na gaya min cewa ya kamata na saka kayan da zasu ruda shi. Wata kuma na gaya min idan ma sun ruda shi ai zai dauka Shaheedah ce, zai yi miki abin da ya taba yi kwanaki, kawai kisa hijabi ma yadda ba zai taba ganin wani abun ba bare ya yi sha'awa tunda daman ba san shi kike yi ba. Kar ki sa kuma wanda zai rai naki, kije garin nuna rashin so ya kuma ci miki mutunci tunda dai baki san manufar da tasa shi ya auro ki ba. Naji wata zuciyar itama ta ayyana min hakan. “Oh God...!” Na fada ina dafe saman gushi na. Toh ni yanzu ya zan yi? Mene ne mafita a gare ni yanzu? Duk na rasa ya zanyi ina ta tunani kawai sai idanuna suka sauka kan wani lace pink da ratsin milk color a jiki, na zaro shi naga dinkin riga da skirt ne, na sanya shi a jikina ya kuwa zauna yai das dashi. Alkyabba na dakko na sanya sannan na nufi gurin madubi na gyara fuska ta, duk da ba kwalliya nai ba, nayi kyau ba laifi, nasa janbaki shima pink daga nan na fara tunanin ta ya zan je sashen nashi?. Adda Maryama na kira dan gabaki d'aya na rasa mafita, tace nasa a kirawo Jakadiya tai min iso a gurin shi. Ta kuma cewa. “Kin san menene Gimbiyar mu?” “A'a sai kin fada Adda.” “Yauwa idan tafiya tai tafiya ki samu duk yadda za ai ki dawo da sauran jakadun guda biyu. Dama uku ne toh sai suka sauke biyun, yanzu kisan yadda zaki wajan ganin sauran sun dawo dan basu kai wannan hada makirci ba, kinga idan suka dawo zaki samu saukin yin wani abu koda waccen bata kusa.” Kamar tana gabana haka na dinga gyada kai, kafin daga bisani nace. “Toh shikenan Adda zan kokarta, na gode.” Daga nan muka ajiye wayar, na mike na fito parlor na samu hadimai na suna ta goge-goge, na aiki guda d'aya cewar taje ta nemo min Jakadiya. Ashe tana can gurin su Gimbiya Jaleela ana ta kulle-kulle kamar an ce dasu duniyar ba zata tashi ba, ko kuma sun dauka cewar za'a barsu har su gama cin duniyar su da tsinka. Bayan tazo ne na sanar da ita bukata ta, cikin tsantsar ladabi ta amsa min tare da tashi ta tafi dan yi min iso. Kin bin ta da man nai saboda koda yake a'a bazan ganshi ba, bazan ji kunya ba, akan na bi bayan ta na dawo da borin kunya. Kamar an jeho ta daga sama haka ta shigo cikin parlorn, ta ce Waziri yace zan iya zuwa. Na tashi bayi ba suka rufa min baya, ina tafiya suna biye daji duk sai naji wani iri, kamar wata marar gaskiya da za'a raka prison. Na tsaya na kallesu cike da kulawa nace su tsaya a nan naje na dawo, dan har ga Allah bana son wannan bibiyar da suke yi mun. Babu yadda suka iya dole suka bi umarni na, ni kuma da Jakadiya muka nufi sashen sarki Salam. Muna zuwa muka tarar da su Waziri da su Shamaki su Galadima sun fito, na duka na gaishe su cike da ladabi, wasu sun amsa ya yin da wasu banji sun bude koda baki ba duk da ban san su ba kuma ban kalle su ba ballantana na gane fuskokin su saboda kai na yana kasa. Sai da suka wuce sannan na mike tsaye tare da juyawa na bisu da kallo har suka fice. Kasan cewar nasan inda yake a kwance yasa na kalli Jakadiya tare da yi mata godiya, na dai nuna mata tsananina da ita iya nan ne bana son ta bini ciki dan naga take-taken ta na son bi na ciki. Na tsaya a bakin kofar bedroom d'in na zaro jarkar dana boye mai dauke da ruwan magarya, nai addu'a sosai kafin na sanya kafata baki na dauke da sallama. Babu kowa sai shi kadai a kishingiɗe kan gado, be kallo bakin kofar ba bare na saka ran zai amsa min sallamar da nayi. Haushi ya kamani, sai kace wani kurma, a zaune yake ido biyu amman saboda mulki yana ji ana sallama ba zai amsawa mutane ba, naja tsaki a cikin rai na ina karasawa gurin shi cikin taku na isa da kasa ita. Lumshe ido naga ta yi yana dan daga fuskar sa, da alama kamshin turaran wutar da ke jikin kayana yake shaka, duk da cewar be nuna ba. Kallansa nai na sakar masa harara a zuciya ta nace 'kaji dashi ni ba bata min rai zakai ba' kawai ma sai na shiga neman burner bayan na ciro garin maganin da zan yi masa hayaki amman ban samu ba. Shi kuma har lokacin be bude idanunsa ba, nai ta dube-dube har Allah ya taimaka na ganta a can wani guri aka ajiye ta na musamman da ba zaka taba zaton ita bace. Na zuba su garin habbatussauda din nan dakin ya fara canzawa daga kamshin da yake yi ya koma kauri, dalilin da yasa Salman saurin bude ido yana toshe hanci. Na kalle shi naga sai faman yatsina fuska yake da alamar kamshin be yi masa ba. “Ke! Mene haka?” Yayi maganar a dan rude. Na sake zuba garin hayaki ya kuma turnukewa ina cewa. “Magani ne.” “Bana so please fitar min dashi.” Ai kamar ya sake zuga ni sai na kara karawa, ya kuwa shiga yin tari da atishawa ba kakkauwa, still kuma hancin sa yana toshe da tafin hannunsa, na ce. “Shi magani ai ba dan so ake yin sa ba.” “Please bana son wannan warin, ki fita da shi nace.” Nai masa banza, na karasa bedside d'in sa na dauki glass cup na zuba masa ruwan addu'ar nan, na dan matsa kusa dashi tare da mika masa ina cewa. “Karbi kasha.” Kai tsaye yace dani. “Bana sha.” “Karka ce haka idan ba haka ba zan je na sanarwa da Ammi.” Kalmar Ammi da na fada ne yasa shi saurin dagowa ya kalle ni karan farko tun shigowa ta dakin. Bakin sa na rawa yake son yin magana amman ya kasa, cikin ransa kuwa tunani yake a ina ma yasan wannan sunan? Babu shakka ya taba jin wannan sunan har ma yana tunanin ya taba alaka da mai irin sunan amman kuma ya kasa tuna a ina ne, yaushe ne kuma wacece hakan. Gabaki d'aya ya saka hannunsa ya dafe kansa yana wani irin cije baki kamar irin wanda ya ke kukan shiga uku nan. “Karbi kasha dan Allah.” Na fada ina mika masa kofin. Sai kawai ya kalli kofin amman be karba ba ya tsaya kamar wani me tunanin wani abun. Ganin haka yasa na daure na zauna kusa dashi tare da jan munfashi na sauke, hannunsa da ya dora a kansa na janyo tare da kokarin sanya idanuna cikin nasa amman yaki bari hakan ta faru, na ce. “Ashe haka kake? A waje idan kana yawo tamkar wani sarki mai cikakken iko. Amman a cikin masarautar ka sai ka zama tamkar wani lagwani wanda sai yadda aka sarrafa shi why? Naji tarihin yadda mahaifinka ya gudanar da mulkinsa, cikin isa da iko, amman kai sai yadda akai da kai me yasa?” “Nima ban sani ba.” Ya fada cikin sauri. “Naji toh karbi kasha wannan zaka ji dadin jiki da zuciyar ka.” Na fada tare da kai kofin sai tin bakinsa, amman ya kawar da kai alamar ba zai sha ba. 'yau na ga taurin kai' na fada a rai na. Wai duk dan saboda ya sha, sai na sake matsawa kusa dashi har jiki na yana gogar nashi, na kwanto da kansa saman kirji na ina shafa lallausan gashin kansa, murya kasa-kasa na fara masa magana cikin taushin harshe. “Kayi hakuri komai lokaci ne kuma jarabawa ce daga Ubangiji, daure kasha wannan magani ne da aka yi shi da ayoyin ubangiji na waraka. Kayi bismillahi tare da kyakkyawar niya ka daure kasha kaji sarkin sarakuna...” Sai ya bude bakin bayan ya rintsa ido na saka mishi ya sha har ya shanye, ya fara kakarin amai na dinga shafa masa bayan shi har Allah ya taimaka be yi aman ba. Ganin yasha yasa na zame jikina na daga nasa, na yalle ni na kawar da kai dan kar ya yi zaton zama nazo yi a gurin shi. Ya yi shiru yana ta tunanin yadda zai tambaye ni wacece Ammin amman bakin sa ya gaza budewa, ya kasa min zan cen har na tashi tsaye na cire alkyabba ta na shiga bathroom ya bini da kallo. Tsab yake ga wani kamshi da yake tashi mai daɗin gaske, na dakko wani d'an bokiti na fito, yadda na barshi haka na dawo na tarar da shi, sai dai idanunsa yana kan kofin da na gama bashi ruwan maganin nan. Ko me yasa ya kura masa ido oho, ni dai nasan ban yi abin da zai cutar dashi ba, idan na cutar da shi me zai tsinana min? Buri na kawai ya samu lafiya ya gaya min dalilin da yasa shi aure na har ya wofin tar dani tsawon lokaci. Ruwan jarka na dakko tare da nufa inda yake na ce ya taso ya yi alwala ya dena zama babu ita ko a wane irin yanayi yake ciki. Sam ban yi zaton yana iya mikewa tsaye ba, na dauka yana yin komai a kwance ne ko a zaune. Babu musu kuwa ya dago ina zuba masa yana yi har ya kammala, na dauki ruwan naje na zubar. Bayan na dawo na zo zan dauki alkyabba ta tace daukar ni inda kika ajiye. Na gama kalle-kalle na a dakin ban ganta ba, daga karshe dai na mayar da kai na gare shi sai na ga kamar be san ina ne man abu ba dan ko kula ni be yi ba. “Ammhh dan Allah riga ta fa, ka ganta ne?” Da mamaki sai ta kalle ni yana tsuke fuska amin da ban yi zato ba. Kamar ba zai ce komai ba, sai naji yace. “Ban da ta jikin ki?” “A'a no ba ita ba, alkyabba ta fa da na cire lokacin da zan shiga bathroom. Ina tsammanim kamar a nan na ajiye ta wallahi.” Na karasa maganar ina nuna gefen shi dan ina ji a rai na tabbas a nan na ajiye ta. Ya tabe baki ina kallonsa, sai wani tsuke baki yake yi. Lallai mutumin nan wai yana nufin be ga rigar nan ba? Daga ni fa sai shi tsabar wulakanci da rashin mutunci, daman nasan ba wani ganin girma na yake yi ba bare ya bani matsayi na na wacce ya auro. Zuciya ta ce ta dinga ayyana min cewar shi ya dauka ya boye cikin bargon da ya rufe kafafuwansa da shi. Sai da na shammace shi sannan na janye bargon, abin mamaki babu alkyabbar nan sai santala-santalan fararan kafafuwansa da kwantaccen gashi ya lullube fatar, banda sheki babu abin da yake kamar ana yi masa stretching. Haushi ya dada kamani saboda ina son tafiya dare yana yi, kawai na yanke shawarar gwara na tafi a haka tunda dai an samu aljani ya shigo ya ɗauke rigar. Juyawa nai zan tafi saboda na gama abin da zan yi sai kuma zuwa gobe insha Allahu, har sai da na kai bakin kofa ashe yana lura da abin da nake shirin yi, naji muryarsa yace. “Ke!” Kamar ba zan tsaya ba saboda ba suna na bane ke, amman sanin da nai da ni yake kuma yana da ikon ya yi min ko wane irin inkiya ne matsayin sa na miji na. Duk da na tsaya amman ban juya ba cak nayi ina jiran jin abin da zai ce, still ya yi shiru sai na kuma yin taku daya da nufin ci gaba da tafiya, ya sake yin magana. “A haka zaki fita?” “Ya zan yi to, rigar da na doro an samu aljani ya shigo ya dauke. Zan zauna anan ne ga dare na yi.” Ya ce. “Haka zaki bar min daki da wannan kaurin?” “Toh ai nagani ne.” “Please bana son warin.” “Gwaggo ta Fada tace a haka za'a dinga barin ka, saboda ai warin shine maganin.” Salman ya yi shiru yasan tabbas akwai matsala a barshi cikin wannan hayakin, ko bacci ba zai iya ba, dan haka dole kodai tasa masa turarukan wuta ko kuma ita d'in da zauna a gurin shi ya dinga shakar kamshin jikinta. Amman ba zai bari ta fita a haka ba babu mayafi kuma akwai bayi, fadawa da sauran mutane. Gashi girman kansa ya hana shi tashi ya hanata tafiya, “Dan Allah zan tafi....Kaji..?” Yadda naja kaji dinnan sai da tsigar jikin sa ta mike, Yayi sakatoto yana kallo na yasa nayi gatsine ina murguda masa baki, “Dare yana yi ne please.. Inason na koma nai bacci.” Shiru ya min ya koma ya kwanta akan pillow, Ganin irin renin hankalin daya mun hakan yasa nai hanyar ficewa, Taku d’aya biyu ban san ya akai ya sakko daga kan gadon ba, sai naji ya riko ni...Banmasan ya akai ya mike ba. Na bishi da kallon mamaki, ashe yana iya mikewa da sauri ban sani ba? “Are you out of your senses..? Zaki fita a haka.” Yana magana yana nuna kirji na da hannun sa tsabar iskanci ko ina ruwan sa? “To ya kakeson nayi? Ni bacci nake ji, Kuma ni bazan kwana anan ba saboda akwai abubuwan da nake son aiwatarwa. Ahto!” “To jeki mu gani..” Na kuwa juya dan har ga Allah na kagu na koma sashe na. Ganin zan fita dagske ya kamo hannu na da sauri, wani irin shock ya ziyarci kowannen mu na kwace da sauri ina kallon gefe, “Meye haka...?” Ina fada ina gatsine. “Zo Ki kashe wannan warin... I hate it! It smells awful..” “Magani ne.. Gwaggo Ta Fada ce tace lalle na saka..” “Oh please...” Komawa yai gefe yana toshe hancin sa da handkerchief, Idanun sa sun kawo ruwa sosai, Da alamun dai dagaske baya son hayakin. Na kuma yunkurin Ficewa ya dakatar dani, “Zo nan..” Sirrin tsaki na saki a hankali na koma nesa dashi na tsaya, Can na zauna tunowa da shi din sarki ne, Ac sai duka na take, Take bacci ya fara dauka na. Na bingere ina lumshe idanu, Ganin tayi bacci Salman ya mike ya koma inda take,Kallon ta yake sosai, A hankali yasa hannun sa ya gyara mata kwanciyar da tai kar wuyan ta ya sage, Hannun sa yasa ya shafa kwantaccen gashin kan ta ahankali, wani irin kallo yake mata wanda bai taba yiwa wani ba, Can kamar an tsukule shi ya dora tausasan labban sa akan kumatun ta ya sakar mata kiss... Dai dai lokacin da na mike zumbur, Ji nai tamkar an doramin abu me ruwa a kumatuna, Ganin yasha kunu a gefe bansamu damar tambayar sa ba, Na mike ina murza idanu na, Indai ba magagin bacci nake ba tamkar dai Salman ba a inda nake yake a zaune ba, Fuskar sa a murtike ya mike. Komawa yai inda yake zaune ya daga pillow sai ga alkyabbata awajen. Da sauri naje na dauka na zura na fuce na barshi inda yake, Dan renin hankali kawai, Saka alkyabbar nayi na fice na koma sashe na. Abdullah na gani a tsaye yanata yiwa hadimai na masifa kan lalle sai sun fitomin da kaya na, shi kuma ya shiga ciki tunda ai sashen sa ne... Mamaki ya kamani ganin yadda ya tsare bayina wadanda suke a durkushe a gabansa kamar zasu masa sujud. Sun sanar da shi cewar amaryar sarki ce a bangaran yace musu besan da wata amarya ba shi Shaheedah kawai ya sani matsayin matar sarki. Ina shiga muka hada ido, ya kalle ni na kalleshi ya juya ya kalli bayin yana tambayar su cikin tsawa. “Kai wai wannan wacce ce ne a cikin masarautar nan?” Duk suka yi tsit ya daka musu tsawa wacce tasa d'aya daga cikin su yin magana. “Allah ya taimaki yarima, wannan itace amaryar sarki mai wannan sashen.” “What...?!” Ya furta a razane idanunsa a waje, banda kallo na babu abin da yake yi. Na kalli hadiman nawa tare da sallamar su nace su tafi, sannan na maida hankali na kansa tare da yi masa kallon sama da kasa nace. “Kasan dai ko fita aka ce wani ya yi a cikin mu sai dai kai ka fita, saboda ni Yayar ka ce a yanzu. Kaji ka samu dan uwanka yasan yadda zai yi da kai.” Ashe duk wannan abun baya cikin hankalinsa ni ban sani ba sai da naga ya yo kai na gadan gadan yana niyar shako ni. Ganin yana tangadi alamar yashayo abar, yasa na matsa da sauri ina dafe kirji. Tunda nake ban taba ganin dan maye ido da ido ba sai dai a film ko a labari. Cikin tashin hankali nake kallonsa baki na yana rawa na ce da shi. “Subahanallahi menene haka?” Cike da rai ni na nuna rashin hankali yace. “Sai na yi maganin ki, zaki san da wa kike magana.” Ya yi tangal-tangal ya fada kan kujerar da ya taso, take bacci ya yi awan gaba dashi. Kai na dafe ina mai tausaya masa, wannan wace irin rayuwa ce ace duk cikin yaran ka babu na kalla kaji dadi? Lallai Ammi tana ganin rayuwa, kaddarori kala daban-daban ita kam ta gansu. Amma komai nisan dare gari zai waye...! ... Littafin kibiyar ajali yana tafe da wani irin salo na daban.... Sannu a ahankali komai zai warware kansa. Salman&Khadija2021❤️❤️ .. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE.. INA KUKE YAN UWA NA MATA? TO KU MATSO KUSA DOMIN GA DAMA TA SAMU.. KAI BAMA MATA KADAI BA, HAR IYAYEN MU MAZA, ZAKU IYA KAWO SISTERS DINKU, DAUGHTERS DA MA WIVES DINKU. KAI HARDA BAE DA KE SHIRIN ZAMA MRS🤩😉...!_ _UMMU AYMAAN’S KITCHEN, UMMU AYMAANS’S KITCHEN, UMMU AYMAAN’S KITCHEN..._ _INA YAN UWANA MASU SON SU KOYI BAKING DA DECORATIONS? TO NESA TAZO KUSA.. UMMU AYMAAN’S KITCHEN ZATA KOYAR DA MATA MASU SON SU KUYI BAKING DA DECORATIONS NA KWANAKI BIYU. AKAN FARASHI ME RAHUSA, NAIRA DUBU 6 KACAL, (6k)._ _ZATA KOYAR NE A UNGUWA UKU LAYIN MAIFATA, ZARIA ROAD KANO.. PRACTICAL CLASS NE, SANNAN AKWAI GARABASA DA NA NESA DAKE SON SU KOYA SUMA ZASU IYA KOYA TA ONLINE DUK AKAN NERA DUBU SHIDA KACAL, DUK ABUNDA YA KUNSHI BAKING ZATA KOYAR KAI HAR MADA BONUS NA DECORATIONS._ _*CLASSES DIN KWANA BIYU NE, AKWAI PRACTICAL DA ONLINE, CLASSES DIN ZA’A YISU NE RANAR 5 DA 6 GA WATAN YUNI WATO 5&6 OF JUNE (NEXT MONTH)RANAR WEEKENDS ASABAR DA LAHADI*_ _* 2 DAYS DEMO CLASS ON BIRTHDAY CAKE.. (BAKING AND DECORATIONS)* YAR UWA HANZARTA KI BIYA KI KOYA KEMA KIN HUTA DA BIYAN BAKERS, DA KANKI ZAKI IYA YIN NAKI, DA DUBU 6 ZAKI IYA BIRTHDAY CAKES KALA KALA, WANDA BA KARAMAR SANA’A BACE, IDAN YARAN KI KO KANNENKI ZASUYI BIRTHDAY KIN HUTA SIYA SE KEYI DA KANKI, KIYI KI BIRGE MAI GIDA AS SUPRISED GIFT.. INA YAMMATA? IRIN CAKE DINNAN ME HEART KI KOYA KIYI KI BAWA BABYN BABY🥰 LOVE IS LIFE, CAKE IS LOVE🙃._ _BA ANAN KADAI TA TSAYA BA, TANAYIN DUK WASU MOUTHWATERING SNACKS AND CONTINENTAL DISHES😋, AKWAI NA YAN GAYU IRIN SU CAKE PARFAIT, CUPCAKES, SAMOSA, SPRING ROLLS, MEAT-PIE, DOUGHNUTs, DUKA WADANNAN TANAYIN SU NE NA BUKUKUWA, SUNA, SHAGULGULAN TARO, KAI DAMA NA CI HAKA KAWAI😋_ _BA ANAN KADAI TA TSAYA BA, TANA CLASSES NA GIRKIN ZAMANI DANA GARGAJIYA, MOUTHWATERING DISHES NA YAN GAYU, MESA KISHIYA KWAFA, WANDA FACCALA ZATA DINGA CIZON YATSA, IRIN HADADDEN GIRKUNA MAI SA KUNNUWAN MAIGIDA SU MOTSA. KAI HARDA NA BUKUKUWA KUNA IYA ORDER TA MUKU SHI_ _INSTAGRAM HANDLE DINMU:_ Ummu_aymaan_kitchen _DOMIN KIRAN NAMBAR TARHON MU DAN KARIN BAYANI DA BIYAN KUDIN SHIGA SAI A TUNTUBEMU TA: 08032964266_ _MUNA TURA KAYAN SNACKS DINMU A KOINA A FADIN NIGERIA, 100% TESTED AND TRUSTED.._ _UMMU AYMAAN’S KITCHEN IS YOUR NO 1 STOP KITCHEN FOR MOUTHWATERING DISHES, BAKES AND SNACKS_ ____ _*KIBIYAR AJALI....🧚🏻‍♂️🥰*_ _(SULKE BAYA TARE TA, SAI TA WUCE..)_ _BOOK 2_ _PG:6 & 7_ _LITTAFAN ZAFAFA NA KUDI NE, MALLAKI NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, KI GUJI KARANTA NA WANDA BA’A BAKI NA DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU RUBUTAWA_ .... Cikin tsananin tashin hankali sai ga Ammi ta aiko a kirawo ni, Kila wani ne ya sanar mata halin da ake ciki. Tafiya nayi, Sashen nata Ina zuwa ta kamo hannu na muka shiga cikin dakin ta . Bata saki hannu na ba har sai da muka karasa kujerun dake harabar dakin. Cikin tsananin tashin hankali ta shiga ban hakuri, “Kiyi hak’uri Khadija.. Dan Allah s..” “Dan Allah kiyi hak’uri Ammi Kiyi shiru, Nasan komai, Kuma wallahi nagane ba a hankalin sa yake ba. Insha Allah nan gaba kadan komai zai daidaita da yardar Allah..” Na karasa fada ina mai rik’o hannun ta na zaunar da ita a kujera, Na koma na dakko ruwan sanyi na zuba a cup na mika mata. “Sha Ammi.. Ki kwanta dare yayi.” Murmushi tayi da alamun taji dadin maganganu na. Daga kasa na nemi waje na zauna, Tv na kunna na kai tashar karatun AlQur’an, A hankali sautin kira’ar sudeis ya dinga tashi. Haka muka kusan raba dare da Ammi, Sannan tace naje dakin gefen nata na kwana aciki. Ba musu na mike don wallahi bacci nakeji, Sai da nayi sallar nafila sannan na kwanta, Bacci mai nauyi ya dauke ni... Wasa wasa, Sai da na kusa shafe sati biyu a sashen Ammi, Kemadagas Abdullah ya kafe kan wallahi ba zai bani sashen sa na zauna ba aciki ai nasa ne. Ban wani damu ba, Saboda dama wajen Ammin yafimun dadin bacci cikin kwanciyar hankali. Bansan wanda ya gayawa Sarki Salmaan bana kwana a sashe na ba, Ranar wata sanyayyar asabar da asubah naje turara magani kawai ya same ni da maganar... Kasa kasa ya shiga kallo na ina hankalce dashi, “Ancemin bakya kwana a sashen ki, why? Aina kike kwana.” “Sashen Abdullah kasa aka kaini... So yanzu ya dawo yana bukatar wajen sa. Awajen Ammi nake kwana, Da magana ne?” Na bashi amsa a gatsine haushi yake bani, Sanyin sa yayi yawa kamar ba sarki ba. Shiru yai yana danna ipad dinsa can ya dago yace, “Ki shirya komai naki... Duplex (ginin bene) din dake kusa da wannan an gama gina shi, Ki kwaso kayan ki ki dawo..” Na gwalalo idanu ina girgiza kai, “Akan wane dalili? Gaskia gaskia banason nan, Kayi hak’uri.” Wani kallo ya watsamin ya ajiye ipad din hannun sa, Mikewa nai daga gefen da nake nai hanyar fita ina mai ajiye burner din dake hannu na. “Ke zo nan..” Ya fada cikeda kasaita, Wai ke! Seka ce yar aikin sa, Na tab’e baki na tsaya inda nake ban jiyo ba. Takowa yai har wajen kofar da nake, Na matsa can karshen k’ofa na takure, Kasa jure kallon idanun sa nai dake saqale ta cikin gilashi. Yasa hannu biyu ya tokare ni a tsakiya yana taune k’asan leben sa, “Kikace me? Maimata abunda kikace.” Na hadiye kakkauran abu a wuyana, K’amshin turaren jikin sa da nawa suka hadu suka bada wani kamshi na daban. Nadan kauda kai na gefe kirji na sai dukan uku uku yake. Bakin sa ya kawo daidai kofar kunne na: “Scaredy cat.. Me kike cewa?..” Shiru nai kaman an jika dan tsako a ruwa, Sai raba idanu nake. Banda iskanci meye namin haka? Numfashin mu sai had’uwa yake yi. Na takure hannuwa na a kirji don na lura kamar yafi kallon sama na. Yadda glass dinsa yake kallon saitin wajen. “Kwalelanka dai wallahi..” Bansan nayi sub’utar baki na fada ba.. Murmushi yai kawai yana nuna ni, “Mekika ce?” Na shiga girgiza kai ina kara matsawa jikin kofa Sosai, “Ki hada komai naki... Ki dawo sabon ginin da akeyi.. Kafin ma..” Bai karasa ba aka turo kofar da sauri ya koma baya yana sosa k’eyar sa. Shaheeda ce ranta a matuk’ar bace, “Honey... Me naji kana cewa? Kunnuwana ne suka jiyemin ba dai dai ba ko kuwa? Bangane ba..? Wane gida zata dawo? Nace wani gida zata dawo?” Ta karasa fada a dan tsawace, Na tsaya ina binta da kallon mamaki, Toshe kunnen sa d’aya yai da yatsan sa karami, “Haba.. Banason tsawa please.. Shaheedah! Meye haka?” “Meye wani meye haka? Hakan ce ta kawo haka Salman, Bangane cin amanar da kakemin ya wuce tunani na ba sai yau.. Ta dawo sabon gidan fa kace, Lalle ka taro babban balai. Kana nufin kace dama mallakinta ne ko kuwa.” Bai amsa taba ya koma kujera ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, Na lura mutum ne shi marar son hayaniya. Gashi ita kuma tanada kwakwazo da mita. Kallo na tayi ta zabga min harara, Zan rama kenan naga ya dago glasses dinsa yana kallon mu, Na fashe da kuka ina mai komawa jikin kofa, Nasa hannuna na dora kai na akai ina kuka.. Ya mike da sauri ya yo waje na yana dafa kafadata, “Menene... Uhm? Meta miki? Eh..!?” “Kutmar kan babban balain can, Ke ni zakiwa sharri? Uban me nayi miki! Kai kuma sannu sharukhan baban soyayya, Daga ta fara kuka ka mike jiki na rawa kana tambayarta, To koma ka zauna bamu gama magana ba...” Zai koma kenan, Nayi sauri na rik’o hannun sa, Ni zata nunawa isa? Lalle zan nuna mata na ninkata a kissa.. Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya, Na rintse idanu na fada kan faffadan k’irjin sa, Duk da yanda gabana yake faduwa abunda bantaba yi ba, Haka na cije don karta gane ba abunda ya taba shiga tsakanin mu. Shi kansa Salman yayi mamaki, Na zagayo da hannu na ta kugunsa na rike shi sosai, Ahankali na kwantar da kai na akan kirjin sa, Na barwa banza ajiyar ta.. Wani shegen marayan kukan shagwaba na saki da har sai da Shaheeda taja dogon tsaki tana cizon yatsa, “Ke ni zaki nunawa bariki.. Kai kuma ka tsaya sakatoto mace na maka makirci. Salman magana nake..” B’angaren Salman kuma kasa cewa koma yayi, Ga kyakkyawar rungumar da Khadija ta bashi mai ratsa magudanar jini da tsoka dan dadi, Gashi k’amshin turarukan jikin ta sai kara saka masa kasala suke, Bugun zuciar sa sai kara yi yake yi... Da sauri da sauri, Zuciar sa bata taba bugawa wani dan adam haka ba fyace Khadija.. Dama ita kadai ransa da zuciar sa kai harda jikin sa suke begen samu. Wani lokaci kalilan yake jira ya bayyana mata komai, Amman yanzu ba zata taba ganewa yana kaunar taba. Shaheeda tasa hannu ta janyo shi cikin izza da bacin rai, “A gabana? A gabana zakuyi bariki, Ba’a haife ki ba wallahi. Ke ba ki isa ki shigo ki raba ni da miji na ba.” Ahankali ya hanya hannaye na ya koma kan kujera ya zauna, Daman nasan ai badan na ri’ke shi ba saki na zaiyi, Nan gaba kadan zaka zayyanemin abunda yasa ka auroni, Sannan kaban hak’uri da doriyar takardar saki na. Bazan iya auren wulak’anci ba. Yanzu ma inayin hakane sahada Shaheedah, Idan ban muna ba wata kofa a tsakanin mu ba to zatai saurin shiga tsakani. Gefen inda yake zaune ta zauna tana shafa fuskar sa da hannun ta na dama, “I’m sorry please, Kasan idanuwana da zucia ta bazasu juri ganin ka da wata ya mace fyace ni ba. Uwa uba waccen low class din. Da har take ganin zatai takara dani.. jokes apart maganar ginin can. Karka sake yinta. Ni acikin week dinnan zan dawo ita ta koma sashe na, Karka manta nice matar ka tafarko my love..” Daria abin yaso bani, Yadda yake kallon agogon hannun sa yana cije lebe da alama ko sauraranta ba yayi. Nima agogon dake saqale ajikin bango na kalla ganin karfe 7 Saura kwata na safe yasa na matsa kusa dasu, Caraf na zauna akan cinyar sa, Dai dai saitin kunnen sa na shiga fada ahankali yadda zata iya jiyowa, “My whole world....” Dak’yar na karasa shi kansa Salman Sai da ya kware na bubbuga bayansa saboda tsantsar mamaki, Shaheeda kuwa tacika tayi fam zata fashe.. “Uhm.. Ashe dagaske kake agaban matar ka ba zaka iya kira na da sugarplum ba.. Anyways! Ni zan koma sashe na, Nagaji sosai kasan jiya bamuyi baccin kirki ba anata abu d’aya.. Zan dawo later mu karasa daga inda muka tsaya.. Oh yes maganar sashe na... Zan dawo ayau ba sai next-week ba. Bye. Ka kulamin da Kan ka..” Light kiss na sakar masa a gefen kumatun sa na fice da sauri ina kambama kokari na, Ina jiyo kwakwazon Shaheedah tana surfa zagi da masifa, Na gimtse daria ta na koma sashen Ammi.. Ni kai na nayi mamakin acting dina.. Dole na bawa Addah Maryamah labarin abunda ya faru, Don duk koyarwarta ce. Sai karin rashin tsoro na na dije Oganniya.. ‘kaya nake bansan na gida ba. Oganniya yar baffanta.. Ta gajiyalle mai yar hakiya...! Tamkar sabuwar mota haka shaheeda tafice daga sashen Salman zuwa nasu gimbiya Huwaila, Tana tafe tana share hawayen takaici. Lalle Khadija ta taro World Cup, Zatayi dana sanin shiga ragarta. Shi kuwa Salman bawan Allah shiru yayi yana nazarin kalaman Khadija, Yasan duk dan saboda takonawa Shaheedah rai ne tayi haka.. Amma meyasa nayi haka? Ya taambayi kansa.. Saboda kana kaunar ta. Zuciar sa tabashi amsa. Kishingida yayi akan kujerar sa yana shafa inda ta sumbace shi, Daya shafa sai yai murmushi kamar zararre. Dak’yar ya iya mikewa ya hau sama.. Aka shirya shi ya shiga fada.. *FADAR SARKI SALMAAN ALIYU SALMANU* .. ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 8&9 BOOK 2. BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻 ____*Sai* da ya shiga ya zauna sannan dogaran sa suke rufe shi sauran yan zaman fada suka fara shiga, Kowanne sai an masa kirari, Tukun sannan ya zube ya kwashi gaisuwa wajen Sarki.. Shi dai Salman yana zaune ne kawai, Gangar jikin sace anan, Amman gaba d’aya zuciar sa na ga tunanin acting din Khadija.. “Unbelievable...” Ya furta batare da yasan ya fada ba. “Allah ya k’arawa sarki lapia, Magana kayi..?” Shiru yai ya cigabada sauraran bayanin shamaki. Gaba d’aya zaman fadar ranar cikin walwala yayi ta, Tacikin rawani yake murmusawa a duk lokacin da ya tuno kalaman Khadijaa... Bayan an tashi daga fada manyan yan majalisar sarki suka nemi ganin sarki, Ya basu dama bayan ya tashi daga inda yake ya koma parlorn sirri. Daga shi sai waziri daya musu iso.. Har cikin babban parlorn sirrin sa dake cikin fadar sa suka shiga bayan an musu iso, Salman na daga kishingide kansa a sama. Da alamun har yanzu ya lula duniyar tunanin Khadijaa. “Ranka ya dad’e, Allah ya kara wa sarki lapia, Ga su wambai, Galadima da Chiroma za'a yi magana da kai..” Cewar Waziri. Salmaan na daga kishingid’e ya mike zaune yana gyara zaman glasses d'in fuskar sa. “Gurin ka muka zo... Tunanin me kake yi haka? ba haifa kayi ba balle ace hayaniyar yara ce ke chake maka kai...” wambai ya fada yana daria. “Kaji wambai da wata magana, Mutumin da bai da kwan halittar haihuwa? Ta ina zai same su.” Galadima ya bashi amsa yana murmushi shima. “Me ake cewa namijin da baya haihuwa ne? Mace dai juya ake cewa ko? Namiji kuma sai dai ace masa baho.” Cewar chiroma dake gefe. Suka sheke da da dariya baki d’aya, Banda Salmaan da waziri, Waziri ya hade rai tamau yana muzurai, Cikin tsananin bacin rai ya dube su. “Menene haka ne dan Allah? Wannan wane irin wulakanci ne da tsawagaran shirme? Ya zaku zo kan sarkin mu kuna wasu maganganu..? Da nasan shirme zaku zo kuyi da bazan yi muku iso bama.” “Yo waziri banda abunka ai shigowa sashen sarki ko an mana iso ko ba’ai ba dole mu shigo.. Su waye suka dora sarkin akan kujera idan bamu ba? Karka kauce hanya yanzu ba sai anjima ba sai mu nemo sauran yan majalisa a sauya ka da wani.. Daman kai shisshiginka ya yi yawa a gurin yaron nan” Cewar galadima, Yana magana ne cikin izza. Waziri yai shiru ransa a mugun bace, sai dai bai kara cewa komai ba, Salman dai yana zaune yayi shiru kawai yana sauraron sa. “To kai Salman wajen ka muka zo, Kuma gaskia magana ba zata yiwu agaban waziri ba, dan besan ma maganar da muka zo yi ba..” “Saboda me ba za’ayi agaba na ba dan ban san abin da zaku tattauna ba? Ban isa bane ko ban kai ba?..” Waziri ya tambayi chiroma cikin tsantsar mamaki. “Baka isan ba..Kuma baka kai din ba, Saboda haka ka tashi ka bamu waje, kai ma bama shigowa idan kuna tare.” “Babu inda zanje, Ku baku isa ku bani umarni ba wallahi.. Nan wajen gaba d’aya maganar mutum d’aya zanji kawai, wato Sarki Salman! Bayan shi babu mahalukin daya isa. Na taba hana ku shigowa idan muna tare dashi? Me zai sanya ni kebewa dashi kamar wani marar gaskiya?” Su Galadima suka harzuka suka fara magana sama-sama, Sarki Salman ya cije leben sa na kasa yana d’aga musu hannu a hankali. “Enough please! Waziri zaka iya tafiya, Kayi hak’uri.” Waziri ya zube a kasa yana d’aga hannuwa, “Tuba nake ranka ya dad’e.. Amman me suke nufi da ina kebewa da kai? Kenan zargi na suke yi da yin wani abun? Wallahi ba zan cutar da kai ba ranka ya dade, kai amana ce a guri na, a rai na ma banji zan iya cutar da kai ba bare har na aikata. Amman Allah ya kara maka lafiya da kwarjini, Zan fita yanzu. A huta lapia.” Ficewa yai bayan ya zabgawa su Galadima harara don yana da yakikin zuwa sukai su yi masa wani abun na tilas. Wani dogon tarihi suka fara dakkowa Salman, Wannan ya saki wani ya kama, Haka suka yi tayi. Duk Salman ya gaji sai lumshe idanu yake a hankali. Wambai ya kar’kare da, “Yanzu dai abunda mukeso kuma muka yanke shawara, Kamar yadda kaka da kakanni suka yi, Har hakan ya zama al’ada ya zama wajibi akan kowane sarki, Kaga kuwa akan ka ba za’a soke ba..” Chiroma ya cigaba daga inda wambai ya tsaya, “Bayan bula mana kasa da kayi a idanun mu ka auro bare, Wacce ba jinin sarauta ba, Bata cikin rakunun sahun masu mulki ko sarauta, Ka jajibo mana yar talakan talak marar usuli, Wanda kakan ta na goma bana tunanin yayi arziki. Amma saboda tsabar ka rainamu shine har sai za’ai daurin auren ka sanar mana.. Shin yaushe ka fara d’aukar Kan ka kai sarki ne? Nace yaushe.” Salman dake gefe yai shiru kawai yana kallon gefe, Galadima yaja tsaki yana ture flower vase din dake gefen kujerar da yake, Wanda har sai da hakan ya zamto sanadiyar fashewar ta, “Ana magana kana shiru ko? Wannan dan iskan halin awajen uwar ka ka samu, Itace duk ta koya muku girman kai, Kuna jin Kan ku, Yo ai barewa batayi gudu danta yai rarrafe ba. Baban ka ma haka ya rakito mana mahaifiyar ka yar dogari, Me yafi wannan kaskanci? To ka bude kunnen ka dakyau kaji, Kodai ka karo auren mata biyu yan cikin dangin sarautar mu, Ko kuma ka sauka daga karagar mulki wanda ya dace ya hau... Ina fatan ka fahimci maganata?” Salman yai shiru kawai yana binsu da kallo, Sai da Galadima ya sake maimaiatawa tukun sannan da k’yar ya cire idanun sa saqale da glass ya kalle su, “Yanzu bana jin dadi.. Kuma a gani na tara matan aure a gare ni bashi da wani amfani tunda ba haihuwa nake yi ba, idan har na tara su a haka na zalince su. Shaheedah taji ta gani tace zata zauna dani a haka, wannan ma akwai dalilin auran mu kuma....” Be karasa ba Galadima ya katse shi da sauri yana cewa. “Zancen banza kawai, toh yadda wadannan suka yadda zasu zauna da kai ba tare da sun haihu ba. Suma wadanda zaka kara aurowa zasu zauna me ye a ciki?” “Shikenan Amman zanyi shawara!” “Shawara da wa? Waziri ko? Hohoho yaro baisan wuta ba sai ya taka.. Lalle daga kai har wazirin kuna gab da yin murabus kuwa.. Kasan an ce sarkin yawa yafi sarkin karfi, Bama wannan ba yanzu ace wancen ginin da kasa aka narka dukiya sama da kasa daman na shegiyar amaryar da kayo ne? Dama bana Wambai bane? Shine gidan sa ke yoyo idan anyi ruwa? Ko abdulqadeer da zaiyo aure kwanan nan.. Tukun nama wa, Wanne munafikin kabawa kwangilar yin ginin? Har akai nisa ba wanda yakeda masaniya sai gab da gamawar sa? Toh zancen komawar matar ka ta biyu babu shi, Sai dai gimbiya Shaheedah ta koma, Ko wambai ko abdulqadeer yai aure ya zauna aciki...” Chiroma ya karb’i zancen da, “A zahirin gaskia dai Salman baka kyauta ba, Ya za’ai har ka aiwatar da aiki ba tare da masaniyar mu ba? Shin me ka dauki kanka? Sarki?..” Wambai ya kece da dariya yana bubbuga hannun kujerar da yake kai, “Wato kila yanda mutanen gari suke masa kirarin sarki shine yasa yafara jin kansa shi sarki ne ko? Har yake ganin masarautar nan tasa ce ya yanki fili yayi gini.. Dukkanin mu nan tsatson sarautar nanne, Don haka kowanne acikin mu yana da gadon wannan gidan daka gina.. Kowanne yanada ikon zama acikin sa..” Salman yai shiru kawai yana jujjuya zoben azurfar hannun sa. “Ku tashi mu tafi, Duk abunda ya biyo baya ka kuka da kan ka..” Ficewa su kai baki dayan su, Ransu a matuk’ar b’ace, Waziri ya shigo, Kallo d’aya yaiwa Salman yasan yana cikin tashin hankali. Kwantar masa da hankali ya shiga yi, Yana karfafa masa gwiwa. Sai daya tabbatar zuciar Salman ta d’anyi sanyi sannan yai masa sallama ya tafi.. Yana fita Salman ya mike ya shiga bandakin cikin parlorn yayo alwala ya fito, Zai tada sallah wayar sa tafara haske, Shaheedah ce ke kiran sa, Kashe wayar yai gaba d’aya. Ya tada iqama yafara sallar nafilar sa, zuciar sa na kara nutsuwa, Yai sujjada yana mai rokon Allah zabin alkhairi acikin rayuwar sa... *GIMBIYA KHADIJAA* Ina koma bangaren Ammi na zube a kujera ina haki, Ni kaina mamakin kai na nake, Lalle nayi kokari sosai, Na kuma ballowa kai na ruwa. Ammi na sama, Hakan ya bani daman kiran Addah Maryamah a waya na sanar mata komai, Ta yabamin hade da sake bani shawarwari, Tace kuma gatanan tafe. Ba jimawa kuwa tazo, Na rakata saman Ammi, Anan ta sanarwa Ammin kancewar zan koma sabon ginin da akai a sashen sarki Salman, Ba karamin dadi Ammi taji ba. Domin yadda fuskar ta ta kara fadada da murmushin farin ciki zaka gane taji dadin komawar da zanyi can. Addah Maryama ce da masu aikin su guda biyu suka nufi sabon shafin nawa don ganin yadda za’a kwaso tsofaffin kayana azuba acan. Suna zuwa suka tarar sama da kasan an zuba furnitures, Komai Italian royal ne, Saboda haka kayan sawa na kawai suka dauka suka jeramin acan, Aka yayyafa ruwan magani da turaren habbatussaudah da tazargade. Da sauran magunguna da malam ya harhada ciki harda na tsari aka rataye a kofar shigowa. Ta WhatsApp addah maryama taita turomin hotunan koina ina nunawa Ammi, Zuciata sai hasaso shaheedah take, Shin ko awani yanayi take yanzu? Oho. Kai bama ita kadai ba harda su gimbiya Jaleelah. Duk na gano bakin su d’aya, Amma kowannen su yanada wani boyayyen quduri a zuciar sa game da Salman da karagar mulkin basannabas. Ranar gaba d’aya Addah maryama da masu aikin su a masarauta suka kwana, A sashe na, Ammi taimin adduar tarewa lapia hade da fatan alkhairi. Amma bata rakani sabon sashe na ba, Saboda gudun abinda zaije ya dawo dongane da Salman dinma anan yake. Tabbas nera tayi kuka agidan nan, Kaya wanda suka amsa sunan kayan gida su ne acikin sa. Kai harya dustbin k’irar Royal ne, Murmushi nai tunowa da nid’in ba tabbata zanyi aciki ba, Nan da lokaci kalilan da komai ya tabbata zan karb’i takardar saki na na kara gaba.. Munsha hira sosai da Addah maryama tana kara dorani akan network, Sai da muka raba dare muna hira tukun sannan bacci mai nauyi ya dauke mu.. *GIMBIYA SHAHEEDAH!* Sashenta ta shiga tana kuka, Dama akwai lapiar zagi, Haka taita lailayowa tana durawa hadimanta, Kayan babban parlorn ta kuwa haka taita farfasasu tana kuka, Tamkar idan tayi hakan magani zasuyi mata. Ranar dai mutum uku ta targada daga cikin hadimanta. Dak’yar ta iya janyo waya ta kira mahaifiyar ta ta sheda mata komai, Ta bata hak’uri da doriyar ta kwantar da hankalin ta, Khadija yasar ta za’ai a fitar da ita daga masarautar nan ko da rai ko babu. Sai a sannan Shaheeda ta danji sanyi sanyi a ranta, “Shikenan Hajjaju... Na hakura, Amman kamar yadda kikace wallahi ba zan bari su samu sukuni ba, Tunda ta shiga gonata sai na nuna mata ita kaskantacciya ce.... Ki sanarwa wannan banzan bokan aikin sa baici ba dan haka kaza ta ubansa...” Tana gamawa ta katse kiran ta kuma jefar da wayar ji kake tartsssss.. Ta fashe. Tashi tai ta shige da’ki wani kullum magani ta dakko ta zuba a ruwan wankanta ta shjga wanka, Tanayi tana tsinewa Khadija albarka... <><>••. <><>••. <><>••. Komawata sabon sashe na yau sati d’aya kenan cif, Tunda na koma ban kara shiga sashen Salman ba, Saboda daga kofata idan na saka maganin yana ruskar sashen sa, Gashi karatun AlQur’an nake so nake na sauke hizb sittin. Shiysa kullum ina daki ban cika fita ba, Ko gayda Ammi sai bayan kwana bi biyu nake zuwa yanzu na dukufa sosai ina addu’oin neman kariya.. Ta window na ina kallon shige da ficen da shaheeda keyi kullum, Sai zarya take safe rana dare. Ta d’auka ina wajen sa. Ni abunma dariya yake bani. Ba ita kadai ba, Su wambai ma kusan kullum sai na jiyo hargagiyar su, Suzo saitin kofata suyita yada magana.. Na kanyi murmushi a duk sanda suka yi haka, Ni wallahi gaba d’aya yanzu basa damuna. Kuma lokaci kawai muke jira da zai bayyana gaskiyar komai. Yanzu kam Alhamdulillah muna samun cigaba sosai a bangaren Abdullah domin har ya zana SSCE successfully. ____Turare masu sanyin kamshi na shafa, Na nufi sashen Ammi. Har a raina nake jin ta. Shi yasa bana iya kara kwana biyu ban lek’a mata ba, Musanman da magungunan temakon su yake hannu na. Wadaraccen mayafi na na yafa akan doguwar rigar jikina ta lace. A hanyar da zata fitar dani daga sabon sashe na na had’u dasu gimbiya jaleelah, Gaishe su nayi suka amsa babu yabo ba fallasa, “Sai ina kuma amarya..?” Gimbiya Najwa ta tambaye ni tana karewa kayan jiki na kallo.. Takaici ya isheni, Su din ina zasu je da daddaren nan? Na yatsina fuska ina bin farcen hannu na da yasha lalle da kallo. Can cikeda k’asaita nace, “Zan kai gaisuwa ne... Daga unguwa kuke ne?” Suma yatsina fuskar suka yi, A dakile gimbiya Jaleela taban amsa, “Uhm... Munje zagaye ne.” “Okayy! Sai da safen ku. Allah ya tashe mu lapia.” Gaba sukai basu amsa ni ba, Nima na wuce ban sake bi ta kansu ba. Ta baya na zagaya na shiga sashen Ammi, Suna zaune da Abdullah kunnen sa saqale da earpiece, “Ammi..! Barka da dare.” “Barkan mu dai Khadijaa.” Ammi ta ansani ni cikin fara’a “Abdullah ya gari..? Me ake jine?” Turo baki yai gaba yana yatsina fuska, “Wani abune..” “Okay! Kaci abinci? Ko a soya maka favorite dinka a hada da tea dinnan me dadi?” Saurin kada kai yayi yana murmushi, Nima murmushin nayi, Shi dai yanasan wainar fulawa da ruwan shayi marar madara. Shiysa na dage nake masa saboda shayin nake zuba maganin da Malam ya bayar, Kuma Alhamdulillah anata samun ci gaba. Domin Abdullah sosai ya rage yawan daren da yakeyi, Kuma baya shaye shayen abubuwa kamar sanda na dawo masarautar. Sai dai kawai yayi shiru yana jin waka baya shiga harkar kowa. Wakar ma so nake ahankali na koya masa ‘kinta, Ta yadda komai zai dai-daita. “Kede bakya gajia Khadija? Ki bari su Na’imah suyi mana?” “A’ah! Bakomi Ammi, Bara nayi sauri na kammala.” Kitchen na shige, cikin k’ank’anin lokaci na gama hada kayan wainar fulawa na fara soyawa ina zuba masa acikin food flask. Ban d’au lokaci ba na kammala soyawa, Na hada masa tea din na zuba duk abunda malam yace kamar koyaushe na kai masa na ajiye, “Sakko kaci Abdullah...!” Lumshe idanu yai ya bude yana murmushi, “Na...Nagode Kh..” “Uhm uhm dai bana hana sunan na ba..” Cewar Ammi tana gyara masa. “Thanks Aunt Kay.” Murmushi nai, Kaina har girma yake Idan naji yana cemin Aunty Kay dinnan, Sufa yan gayu komai nasu na dabanne. Gashi mun fara sabawa dashi, Ammi ba kadan ba takejin dadin hakan. Sai dana tabbatar ya cinye komai sannan na musu sallama na koma bangare na.. Ina cikin tafiya tamkar ance juya kawai na hango shaheeda sai zuba sauri take yi, Ko kallo na batayi ba ta shige ciki wajen Salman, Murmushi nai kawai na shige sashe na, Turaruka nima na bulbula na *yerwaincense&more* Sannan na cokala dauri na ya koma ture kaga tsiya, Wadataccen gashin kai na ya bayyana.. Lemon iced drink na dauka, Ina tafe ina taunar strawberry chewing gum a baki na, A haka na shiga wajen Salman baki na dauke da sallama. Suna zaune shi da ita, Ya tallafe habarsa yana kallon cup din gaban sa data zuba masa tea. Ina shiga ta dago ta zabgamin harara, Nayi murmushi ina danne dariyar data tahomin, “My Whole world... Barka da dare.” Da sauri ya dago ya kalle ni na kashe masa ido d’aya ganin tana kallo na, Batasan da biyu nayi hakan ba. “Yaya... Yaya barka da dare.” Daga shi har ita tsayawa sukai suna kallo na, Na sake maimatawa ina dashare mata hak’ora, Mik’ewa tai tana fiffita da kasan mayafinta duk kuwa da na’urar sanyaya parlor dake sanyaya mu, “Yaya.... ?Ke banason munafurci, a gidan uwar uban ki na zama yayar ki? Salman ka shiga tsakani na da yarinyar nan wallahi, Dan yanzu sai mu debi yan kallo.” Nayi murmushi kawai ina sosa tulin packing din gashi na, Can na cire dankwalin na ajiye a gefe, Ina kallon irin mayen kallon da Salman kebin gashi na dashi. “Yaya Allah ya huci zuciar ki.... Ni na kai matsayin mu debi yan kallo dake? Haba wane mutum.” Komawa tayi ta zauna tana huci, Na matsa daf da kafafuwan Salman na zauna, A hankali nasa hannu na zaro kafafun sa dake cikin takalmi half covered. Na shiga matsa masa k’afafuwan ina murmushi, “Sannu da hutawa.. Kasha zaman fada, Kaga yadda suka kumbura kuwa.? My Whole world Allah dai ya baka ladan mulki.. Ya biya bukatu na alkhairi.” Lumshe idanu yai ya bude su a kai na, Shaheeda tacika tayi fam, “Salman magana muke, Ka tashi mu karasa maganar sai mu dawo..” Ahankali yasa hannun sa ya dafe goshin sa dashi, “Shaheeda.. pls let me be...” “Toh ai kuwa zan dawo nan sashen naka da zama wallahi. Gwara ka zabi d’aya.” Shiru yai bai tanka taba, Na guntse dariar data tahomin, Can na tuna da lemon iced drink din dake gaba na, Dauka nayi na dora masa akan hannun sa, “Sha kasamu coolness your majesty.. Kamata yai a barka ka huta wallahi..” Ai bansan na janyo ruwa ba, Shaheeda ta shjga surfa min zagi tana neman janye ni daga kusa dashi, “Allah ya huci zuciyar Yaya... Nifa ba dake nake ba, Idan dake nake ai da kai na nake kenan, Ni dake ne awajen fa Ko kin manta...? Ina maganar jama’a na waje.” Na karasa fada ina turo bakin shagwaba, Gaba d’aya ina magana ne ina kallon Salman, Yayin da ita kuma tana tsaye kamar muciya tana surfa kwakwazo. Nan kuwa da ita nake.. “ “Washh Allah na... Kai na kwana biyu yaita kaikayi, My whole world tun ranar daka wankemin shi dinnan a bandakin kasa? Bai sake yi ba sai dazu ya dawo. Dan sosamin tsakiyar gashin plss.. Kaji nawan.” Tamkar soko haka ya zama, Na samu kai na da kwantar da kai na akan cinyar sa duk kuwa da tulin fargabar dake zucia ta. Hannu yasa ahankali ya shiga sosamin kan, Na tsiri lumshe idanu ina mai magana ahankali cike da jan hankali... “Wasssh Allah na dadi .. Gaskia My whole world zaka zama personal hair stylist dina, Ni da zaka iya dakamin kalabar nan guda biyu irin ta last week..” Wani dogon saki shaheeda ta saki tana tafa hannuwa, “Lalle Salman shekaru nawa da auren mu kitson kai nama baka kalla amma ace dagayin auren ka har mace kake wankewa kai, kitso da wani susa kamar dan daudu..” Zaiyi magana nai saurin cewa, “Nan haka baka sosawa, Kawo hannun kaga cikin nan..” Ai ban karasa ba, Shaheeda ta janyo hannun sa ya tashi, “Na rantse da Allah ba Za’a dinga bariki agabana ba, Kawai kace yar tasha ka debo mana. Salman mai zan gani? Sarki ne fa kai, shugaban al’umma.” Daria ce ta kufcemin nace, “Haba Yaya.. Dan sarki ne shikenan sai ace cikin matan nasa ma sarauta zai yi? Haba Yaya dan Allah, Ni last week gashi ki tambaye shi haka kawai ya tsiri shiga kitchen ya soyamin kwai..” Salman ya gwalalo idanu nai masa gwalo ganin ta juya, Ganin karna kasheta da ranta, Na mike na dauki dankwali na ina rausaya.. “Na manta kwanan ki ne ko....? Kar na shiga hakki, Yaya a huta lapia. My whole world ka kulamin da kanka... Sai da safe..” Peck nayi masa a kumatu na fuce da sauri, Ban jira cewar wanin su ba. Dak’yar na koma sashe na Ina tafe Ina dariya haka na dinga hada stairs, Tun a bene na kira Addah maryama tafara bacci ma na bata labari. Ina jiyo sautin takalman shaheedah fuuu ta fice ta koma sashenta, Ranta a matuk’ar tashe, Ina sane nayi hakan, Insha Allah kuma haka zanta mata har sai ta yi dana sanin auren sa... Alkawari ne wannan na daukawa Gwaggo.. Zan shige gaba a nema musu lapiar su daga shirin sihirin da ake jefa su.. Da komai ya gyaru kuma zan karbi takardata na kara gaba... ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10 BOOK 2. BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻 *DR ISMA’EL MUHAMMAD RES.* Alhaji Isma'il ne ke sakkowa daga bene, Shukrah tana biye da shi a bayansa hannunta rike da jaridu fuskarta a hade alamar bukatar da ta gabatar masa tun a daki bata biya ba. Har ya sakko parlorn kasa ya zauna akan two seater ta mika masa jaridun ya karba yasa wasu a gefen sa daya kuma ya fara budawa da alama karantawa zai yi. Shukrah ta kuma marairaicewa kamar zata fashe da kuka tace. “Kaji Daddy dan Allah.” Shima ba tare da ya kalleta ba yace. “Ai na riga na gaya muku idan har ba zaku ji magana ta ba, toh kar wanda ya sake kawo min bukatarsa ya kuma yi zaton zan cika masa ai baku kuka haife ni ba.” Tasa hannu ta share hawayen fuskarta tana kuma maida kukan da yake shirin fitowa baki daya tace. “Daddy munje fa aka ce bata cikin masarautar, wallahi Daddy harda kawaye na su Madina muka je amman aka ce bata nan.” Alhaji Isma'il ya kalli Shukrah da kyau, ya yarda yanzu kam cewar sunje Dije bata nan. Amman dan kar tai zaton ya sakko daga doran fushin da yake yi dasu na rashin zuwa gano Dije, sai da ya mulu sannan ya sake kallon ta yace mata. “Toh zan sake miki wata, Amman Shukrah wannan itace waya ta karshe da zan sake miki indai ba miji kika fitar ba. Ku kun fiye rigima wallahi, ba ku iya tattali ba, Dije duk ta fi ku alkinta abubuwa mai tsada ko arha. Kunki fitar da mijin aure, yaran abokai na da abakan nawa kansu wasu sun nuna bukatar auranku amman kuka ki, na rasa wannan dalilin tun abin baya damuna yanzu har ya zo ya fara tsaya min a zuciya.” Ita dai duk fadan da yake yi ko a jikin ta tunda taji ya furta cewa zai sake siya mata sabuwar waya, ta gurin ta ce ta fada cikin toilet a can office d'in ta. Ganin yaci gaba da duba jaridarshi yasa ta mike zata fita yace ta turo masa mahaifiyarsu, ba tare da ta amsa ba ta nufi gurin Mamin su dan isar da sakon shi. Zaune ta tarar da ita tana daura dankwali ta sanar sa ita kiran da Daddy yake yi mata, cikin turo baki kuma tace. “Mami wallahi Daddy ya matsa mana akan Dije, yanzu fa ta kai ta kawo duk sanda zamu nemi wani abu ko zamu gaida shi sai yace wai Dije duk ta fimu, ni wallahi abin nan ya ishe ni, ta yi auran ma ba za'a barmu mu huta ba.” Mami ta harareta ta cikin madubi cike da bacin rai, sannan ta wai go tana yi mata kallon ki shiga taitayin ki. “Karya Daddyn ya yi ko me? Aikin banza aikin wofi kawai. Shekarun ku nawa a cikin kwaryar kano? Amman ku duba ku gani daga zuwan Dije har ta mallaki sarki, bafa dansa ba, a'a shi sarkin kansa ta aure. Ku kuwa babu abin da kuka yi sai daukar kwalliyar amman kun kasa janyo kwatankwacin sarkin da Dije ta aura. Ni wallahi da ina kamar ku, layi samari suke yi min, kuma ba wai kananun mutane ba, a'a manya masu ji da kansu a cikin Kasar nan. Ku kun zauna banda shegen baccin nan babu abin da kuka sani.” “Kai Mami kema haka zaki ce?” “Eh haka zance ko karya na yi? Burin ko wanne iyaye su ga sun kai yaran su mata gidan mazajen su, ko dama ace masu zuwa ne babu da sauki ba zamu takura muku ba. Toh a'a kawai gigin yarinta yana bin ku shine kuka ki tsayawa ku nemawa kanku abokanan rayuwa nagartattu.” “Nifa Mami ina da wanda nake so. Kawai lokaci nake jira na kawo shi.” “Dalla rufe min baki, wannan yaron zaki ce min zaki aura? Duk wani take-taken ki ina kallonki Shukrah. Ke ko kunya bakya ji ace tsohon saurayin Dije shi zaki aura? Abin haushin ma ba wai shi yace yana ra'ayin ki ba, ke kika nuna masa kudirinki. Toh wallahi ki shiga ki nemo hankali da tunaninki, wannan shirme duk bana san shi.” Shukrah ta cakuna fuska saboda taga Mami ba ta yadda da zabin zuciyar ta ba, ita kuma harga Allah tun ran da ta dora idanunta akan fuskarsa taji duk duniya ba bu wanda ya kwanta mata sama da shi. Kuma har yanzu ta kasa janyo ra'ayin sa, ta yi duk iya yinta amman yace shi sam ba zai iya auran koda kawar Dije ba bare kuma yar uwarta. Sai dai duk da haka Shukrah taki yadda sai faman naci take yi masa yana share ta. Dan Mami ta yi shiru kuma ta jewa da Daddy daddanan labari yasa Shukrah tattara komai ta ajiye gefe, tana murmushi kamar ya kai zuciya tace. “Gobe zamu je gidan Dije, idan kuma har zuwa wannan lokacin bata nan, gaskiya ba zan sake zuwa ba sai dai idan ita tazo.” “Wannan kuma ku ya dama bani ba.” Cewar Mami tana fesa turaruka a jikinta, Shukrah dai ba ta sake cewa komai ba har ta fita sannan ita kuma tai saurin daukar wayar Mami ta sanya lambar Mas'oud, dai da tai ringing kusan biyar sannan ya daga cike da fargabar Allah yasa ba Shukrah bace, saboda har ya gaji da daukar kiranta, duk da tana yawan kiransa da layuka da yawa. Mas'oud na karawa a kunne tun basu yiwa juna sallama ba, ta fara roƙansa da magiya dan Allah karya kashe kada yaki sauraron ta, haka ya hakura yana jinta zuciyar sa na masa kuna dan ba karamin haushi take bashi ba. “Wai me yasa baka jin tausayi na ne first love?” “Ni ban fada ba.” Cewar Mas'oud. “Ai daman ba fada ka yi ba, amman kuma duk sanda na kira ka sai naji baka farin ciki why?” Ba tare da ya bata amsar tambayar ta ba, taji yana magana cikin sauri. “Sorry Shukrah zan shiga studio yanzu, lokacin yin program d'ina ya yi.” Ya katse tun kafin ma ta furta wata maganar. Tamkar ta hadiyi zuciya haka take ji a ranta, sai dai ta ajiye wayar tare da fadawa kan gadon Mami ta fara hawaye masu zafin gaske. Shin ya za tai da kaunar wannan bawan Allahn? Wa zata gayawa ya shawo mata kansa? “*Allah*”.... Taji wani sashe a zuciyar ta ya tunatar da ita hakan. Sai dai sam ba ta da juriyar yin addu'a, ita tafi gane komai ya zo mata shaf-shaf koda kowa ba nagartaccen bane. Ta dauki tsawon lokaci tana hawaye kafin daga bisani ta lallashi kanta tare da mikewa ta nufi dakin su. *GIMBIYA KHADIJA.* Ranar monday da rana ina zaune a parlorn kasa ina yanke farce na da ya dan taru, gefe guda kayan marmari ne a cikin wani kyakkyawan kwando an ajiye min da nufin idan ina bukatar ci. Giftawar wani abu na gani, nai saurin ware idanuwa ina neman abin abin banga komai ba, naci gaba da abin da nake yi still na sake ganin giftawarsa har yana kusan taba min kwayar ido na, na sake dubawa har karkashin kujera da bayanta banga komai ba, na yi auziya tare da ci gaba da gyaran farce na. Can kuma naji wata irin kara mai firgitarwa a cikin kunnuwa na, na yar da nail quarter d'in hannu na tare da toshe kunnen ina rintsa ido. “A'ouzubillahi minasshaidanir rajim” Kamar daukewar wuta haka naji shiru babu karar, nai saurin nashi tsaye naje na kunna karatun qur'ani mai girma da nufin ya bani kariya, bana bin kowa da sharri ko bita da kulli bare nai zaton ko ramuwa ake yi. Kalaman Gwaggo ta Fada suka fado min inda tace min, Khadija gidan sarauta sai da shiri, duk wanda kika ga ya zauna a ciki ya dade lafiya lau to be zauna guri guda ba, dole sai da neman kariya kota hanyar Allah ko bokaye ko kuma aljanu. Komawa nai na zauna ina bin karatun tare da ci gaba da kankare farce na. Sallama naji daga kofar shigowa, na daga kai na kalli hanyar ina mai amsawa. Abin mamaki su Ya Shukrah ne, Sai wasu da alama kawayensu ne tunda ni dai ban san su ba. Kamar nai tsalle naje na rungume su dan murna, amman wata zuciyar ta kwabe ni cewar. 'Kar ki rawar kai Dije, ki tuna cewa ke yanzu kin girma, ya kamata ki nuna musu cewa jiya ba yau bace.' Fuskata dauke da murmushi tare da fara'a na kuma Mike tsaye suka karaso. Ya Hameeda (ni xoxo wlh na manta ainihin sunan ta, Kamar dai haka ne, Man kai na ya tsiyaye) da ta kasa jurewa saboda mamaki tace. “Lallai har yanzu gigin auran sarkin nan yana kanki Dije.” Maganar ta bata bata min rai ba, dan yanzu na gano cewa su kananun marasa mutunci ne, yanzu ina cikin gagaruman dan haka duk abin da zasu min ba zai dameni ba ko meye shi kuwa. Murmushi kawai na saki ina nuna musu gurin zama da hannu, suka ki zama sai kallo na da suke yi musamman wata yar dwalf dake ta kallon ciki na tamkar wacce ta hango wani abu a ciki, nai saurin komawa na zauna tare da dora kafa daya kan daya ina girgizawa. “Dije wai kuwa kinji dadin zuwan mu? Bafa yau kadai muke zuwa masarautar nan ne man ki ba ace bakya nan, honeymoon kuka je ne keda shi?” Na dan yi murmushi ina wasa da cover din wayar hannu na da na dauka, sannan nace mata. “Ko daya Ya Hameeda, kawai wata yar tafiya na yi amman ai gashi yanzu kun zo mun hadu. Ku zauna mana sai mu gaisa.” Suka jinjina kai sannan suka karasa kujerar duk suka zauna. Hadimai suka fara aikin nasu na kawo kayan motsa baki, ni kuma ina hakimce kai kace nice sarkin saboda yadda nake karkada kafafu... _Afuwan lovelies.. A bini bashi😅🤲🏻Insha Allah next page zaiyi tsawo.. Masu comments, Ina godia sosai, Sakon ku yana isowa gare ni.. Kibiyar ajali... Zai cigaba da zuwa muku a hankali cikin nishadantarwa da fad’akarwa... Kaunar kauna❤️❤️_ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 11&12 BOOK 2. BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻 ......Kallon yanayin parlorn suke yi da alama ya tafi da duk wani imani nasu saboda sun kasa sauke idanunsu daga dubawa. Ni kuma sai murmushi nake yi nasan ko babu komai zasu gane cewa maraici ko talauci basu hana d'an adam yin arziki, inda ma aka samu matsalar zuciya ta Sam ta kasa amsar Salman a matsayin miji na. ”Ina kuma mai gidan naki..?” Cewar Ya shukrah tana mai ci gaba da karewa gidan kallo. Na shiga jujjuya amsar da zan basu, Don ni rabon da na sashi a idanu na tun rannan dana same su shida Shaheedah a bedroom d'in sa, Ni kunyar sama na keji wani lokacin saboda kar ya dauka har zuci nake wannan acting din. “Suna meeting ne.. Shi da yan majalisar sarki.” Tabe baki Ya Hameeda tayi tana mai kallon kayan kwalam da makulashen gaban su. Ni kam na shiga tambayar su Kawu Daddy da Mami.. “Sunanan qalau.. Amman Dije yaushe kika dawo nan sashen? Kamar da ba nan muka kawo ƙiba ko.?” “Eh Ya Shukrah! Daga baya na dawo nan d'in..” “Ina kuma kishiyar ki.....? Ita anan saman take kenan, Ke a kasa?” Sai da nai murmushi tare da sauke kafata na kalleta sosai yadda zata fahimci bayanin da zan jefa mata sannan nace. “A'a ai ba zai yu a had'a mu haka ba, kinsan gidan sarauta ba kamar sauran gidajen mutane bane da za'a iya ajiye mata biyu a part d'aya, dole ko wacce da nata bangaran.” “Yanzu dai kina nufin nan duk naki ne?” Cewar Ya Hameedah tana son jin tabbaci. “Eh nawa ne.” Na bata amsa a takaice ba tare da na kuma yin dogon bayani ba, dan na lura har yanzu mamaki suke yi. “Amman dai kafin mu tafi zaki had'a mu da shi angon mu gaisa, ni ban taba ganin inda ango be san ainahin yan uwan matarsa ba sai yanzu. Ya dai kamata mu ganshi, dan yasan mu muma mu san shi ko Hameedah?” “Kwarai ma kuwa sissy, wai duk tsahon lokacin nan bai taba zuwa gida ya gaishe da Daddy ba bare kuma Mami, ke kuma tunda kika samu duniya shikenan ba ruwanki da neman mutane.” Ganin suna shirin gaya min magana a gaban kawayensu da ban san ina maganar zata iya kaiwa ba yasa ni saurin nemo amsar da zan basu cewar. “Kai ai shi ba ya san hayani, baki ga ko da ina gida be taba zuwa tadi ba? Shifa sam baya san surutu, ni kai na duk surutu na idan ina gabansa hadiyewa nake. Shima Daddy ya sani dan a bakinsa na fara jin cewar sarki Salman baya san magana da hayani.” Suka kalli juna cikin zaro ido tare da rike baki alamar mamaki, ni kuma na gaya musu iya gaskiya ta d'an kara suyi zaton irin mazan nan ne masu yawan surutu ko shisshigewa yan uwan mata. “Ke nan muma yanzu ba zamu samu damar ganin shi ba?” “Gaskiya dai, tunda kunga yanzu yana meeting ban san ma lokacin fitowarsa ba. Babbar matsalar ma ba nice dashi ba Shaheedah ce, idan taga ina zarya gurin shi sai tai zaton wani abu. Amman kuyi hakuri duk sanda kuka dawo zan yi kokarin hada ku dashi sai ku gaisa.” “A'a a'a kedai kawai kice boye mana shi kike yi, lallai Dije abin naki dada shahara yake yi amman ba komai.” Ya Hameedah ta fada tana janyo bowl d'in pepper soup d'in cow leg, daga nan suma sauran suka fara dibar abinda zasu ci. Wayar telephone dake can gefe ita tai ringing, ba kowa bane face Salman dan shi kadai ne yake kira a cikin ta idan yana nema na urgent. Cikin rawar jiki hadima ta dake kusa da gurin ta dakko ta kacokam ta kawo min, na karba sai dai ban daga ba saboda jan aji, ta katse ya sake kira, still ban daga ba sai da ya sake kira karo na uku sannan nai picking na kara jikin kunne na. “Please..I need your help.” Cike da takama kamar ina gabansa nace mai. “Yaushe fa.?” Yace. “Yanzu please.” “Ina da baki ne, sisters dina sun zo. K...” “Na ce yanzu.” Ya fada cike da nuna iko, karo na farko kenan da ya nuna min ikon sa a kai na. Ya kuma katse nai murmushi dan kar su yi tunanin wani abu na hada da cewa. “As you wish.” “Ya fito daga meeting d'in kenan?” Ya Shukrah ta tambaye ni cikin zakuwa, ashe duk kunnuwan su yana kai na oho ni Dije. “A'a bashi bane ba.” Na samu kai na da shirga musu karya, nan san me yasa ba haka kurum bana son su hadu dashi yanzu, kodan nasan har yanzu ni kai na ban san matsayina a gurin sa ba. “Ku gama ci bari naje na dawo.” Na fada tare da tashi na shiga daki. Sake gyara fuskata nayi na kuma dauki mayafi na yafa sannan na fito na bi ta d'an wani corridor yadda ba zasu gane nayi wani gurin ba, cas na fada sashen Salman ina ta mamakin wannan kiran nasa da ya yi min. Kamar yadda nayi tsammani hakan ne ya kasance, wato sashen nasa shiru sai fadawa dake aikin gadin ko wane sashe na part d'in. Duk inda na gitta sai sun gaishe ni har na karasa bedroom d'in sa, wani irin kauri naji wanda yasa ni kwarewa babu shiri, nasa hannu na toshe hanci na ina kalle-kalle dan son hango inda yake. Bathroom naji an bude, nai saurin kallon gurin naga shine ya fito, sai dai ya rufe duka fuskarsa da towel d'in wanka alamar shima mafita yake nema. “Yar jarida...” Nija ya fada a hankali, ban san lokacin da na harare shi ba. “Sunan da nake dashi a gurinka kenan? Tukunna ma wannan kaurin kuma fa daga ina?” “Kina ina please.?” “Gani nan.” “Toh d'an matso.” Kamar wata sokuwa haka na matsa kusa dashi, yasa hannu ya lalibo ni bayan ya gama yawo da hannunsa a jikina. “Kinji warin nan ko? Toh nima haka naji shi har ya sani amai. Dan Allah ki taimaka kisan yadda zaki sa na dena jinsa.” Haushi ya kamani, me yake nufi to da zai ce na kawar masa da wannan fitinannan kaurin bayani ni kai na ban san ta ina yake biyowa ba. Ko yana tunanin nice na saka masa har ya yanke shawarar kirana dan na gyara? “Nima fa ban san daga ina yake fitowa ba, dama na sani ne da sauki.” “Please yar jarida bazan iya zama a cikin dakin ba.” “Ikon Allah, wai laifi na ne?” “I dunno, ni dai ki taimaka min bana son warin.” “Shikenan to sakar ni naga me zan iya yi.” Babu musu ya sake ni nasa mayafi na nima na toshe hanci ina ta karanto adduoi . Na dinga dube dube amman banga komai ba, na kalleshi yana tsaye yaki bude fuskar kamar wani karamin yaro. Cikin sauke numfashi na mike tsaye ina cewa. “Toh waye ya shigo cikin dakin? Ni dai na duba banga komai ba wallahi da yake sa wannan kaurin.” “Kowa be shigo ba, oh su..matan baba sun zo duba ni dazu.” “Mata? Wane irin mata kuma?!” Yayi shiru tsawon lokaci sannan ya ce. “Mama Huwaila.” Na tabe baki a hankali naje na dakko turaran kamshi na jona burner na zuba, nan da nan kamshi ya gauraye dakin, na karasa kusa dashi tare da jan hannunsa na kai shi kan kujerar da yake hutawa ya zauna sannan na warware masa towel d'in na ajiye a gefensa. “Kana jin warin har yanzu?” Ya daga min kai alamar eh. “But kadan-kadan ne.” Ya fada yana satar kallo na. “Okay karka damu zai dena gabaki d'aya insha Allahu. Bari na koma sister's dina ne suka zo.” Kamar zai hana ni sai kuma ya jin gina bayan sa jikin kujerar tare da lumshe idanunsa be ce min uffan ba. Ni kuwa na juya na tafi dan kar su yi zaton wani abun bare suje su gayawa Mami cewar nai musu rashin mutunci. Koda na koma bangan su a parlorn ba, ina shirin tambaya na jiyo muryarsu a sama suna ta shewa, mamaki ya kamani. Sai na bisu har ina hardewa, na hange su a wani bedroom suka kalle ni cikin rashin damuwa Ya Hameedah tace. “Zazzagawa muke muga yanayin gidan.” “Ah lallai Dije duniya sabuwa irin wannan daula haka? Kinga bathroom d'in nan? Wallahi tuna min ya yi farkon zuwan ki gidan mu kika kasa shiga bathtub, amman yau gashi ke ce mai wannan dankareran jakuzzi d'in.” Ya Shukrah ta fada cikin shakiyan ci, duk sai na kasa magana ganin yadda suke ta dariya harda kawayen su. Nai murmushi tare da karasawa na bude wata wardrobe na ciro wasu laces da material ina cewa. “Kunga wasu kaya ina ta so randa zanje gida na tafi muku da shi sai gashi kunzo. Idan zaku tafi sai a sa a mota.” Ganin irin dankara-dankaran laces d'in yasa suka kasa rejecting, hannu biyu-biyu suka karba, sai dai Ya Hameedah sai da tace. “Wai yau Dije ce da yi mana kyautar bajin ta. Aure mai dadi mu ma dai Allah ya kai mu lokacin namu muji yadda ake ji.” Duk suka yi dariya tare da tafawa, ni kam na kagu su tafi musamman da naga suma kawayen sun fara yi min abinda suka ga su Shukrah nai min. Allah ya taimake ni suka sakko tare da shirin tafiya, bayan ko wacce ta dauki abin da take so a gidan, ban yi magana ba ni dai buri na kawai su kara gaba, naji dadin ganinsu dan a kalla nasan mutane zasu san nima ina da dangi. Har wajan gate din sashe na nai musu rakiya suka tafi suna ta magana da ban san ko ta menene ba, kai tsaye na shiga toilet nai alwala. *<<<<<>>>>>>>>* Sallama dauke cikin siririyar murya ta na shiga bedroom d'in nasa, Salman tsaye wajan mirror ya gama shirinsa na fita fada zai gana da wasu ƴan majalisar jiha. Ban ko kalle shi ba na wuce zuwa inda ake ajiye masa tray din coffee ko tea ko dai wani abin da yake so. Ya juyo yana kallo na wanda na gane hakan ne a jiki na, sai dai bai ce min komai ba nima kuma ban juya ba sai kokarin had'a masa coffee d'in da nake yi. Cikin rai na haushi ne cacim saboda rashin kulawarsa gare ni tana bata min rai duk da ba wai ina bukatar ta bane. Har na kammala hadawa na rufe ban juyo ba duk da cewar babu abin da nake yi a wajan, naji ya tako a hankali ya tsaya a baya na yana bin kai na da kallo. Dan kwalin naji ya cire nai saurin mikewa tsaye babu shiri, ido waje kuna na kalle shi dan tsananin mamakin shi. Da kyar na daura d'an kwalin kasan cewar na lace ne kuma yana da nauyi, amman shine saboda ya lalata min ya kama ya cire min ba tare da sani na ba. Yadda yaga ina kallonsa ne ya tabbatar masa da cewa rai na ya baci, amman ko a jikinsa dan bai nuna ba a fuskarsa, cikin yatsina fuska nace. “Ya haka? Kasan da yadda na daura shi?” Bai ce komai ba sai kallo na da yake yi, cikin jin haushin dark shades d'in idanunsa masu kallon mutane ba tare da sun sani ba, nima nasa hannu na ciro shi ina tsuke baki. “Ni ma na rama.” Na fada cikin gaskiya ta. Maimakon ya kalle ni a'a sai kawai ya lumshe idon sa da haka ya miko hannusa tare da kamo kafaduna ya rike, ban yi aune ba kuwa naji ya sanya ni cikin faffadan kirjinsa, tare da dora habarsa a kai na. Ware ido nayi ina jiran jin abinda zai wakana, sai kuma naji tattausar muryarshi a cikin kunne na yana cewa. “Baki iya gaisuwa ba?” “Oh ai ban san da mutum a ciki ba, dan nayi sallama amman ba'a amsa min ba.” Ya sake sanya bakinsa cikin kunne na ta yadda na dinga jiyo numfashinsa wanda ke sa tsigar jikina tashi. Nai saurin kawar da kai na, ai kuwa muka hada fuska dashi a lokacin ne kuma ya bude idonsa muka hadu da na juna kowannen mu da abin da yake sakawa a cikin ransa. Bashi da niyar yin magana hakan ya bani kwarin guiwar fincike jikina zan matsa Salman ya yi saurin janyo ni, naki waigawa saboda abin nan nashi ya ishe ni, sai dai yai ta yin shiru kamar wani kurma, yana ji kana magana amman yaki kulawa. Rai na a bace na fara magana dan ni dai gaskiya ba zan ci gaba da jure wannan wulakancin nasa ba. “Wai kai dan Allah a haka kake yin mulkin naka cikin shiru da rashin yin magana? Ta ya kake sauraran talakawan dake karkashinka bare har ka tallafa musu a inda suka kawo kukan su? Wannan shirun naka yana yin yawa gaskiya, gashi nan har ta kawo baka kula mahaifiyar ka. Ammi tana t.....” Ammi da na furta shine ya sanya shi saurin fisgoni ba tare da na karasa maganar tawa ba. Ya yi min wani irin kallo wanda na kasa gane ko na menene. Shin na tsana ne ko gargadi ko kuma mamaki? Ban sani ba ni dai, zafin rike min gashi da ya yi yasa ni cewa. “Ni ka sakar min kai na, dan sauran kiris ka dena gani na a cikin sashen nan naka, bana son yin taraiya da wanda yasan mahaifiyarsa na da rai amman be damu da rayuwarta ba, bai san ina take ba bare yasan ya ta kwana ta tashi tsahon lokaci kuma a gida d'aya. Shi yasa lokaci nake jira wanda zaka sallama min naje nai rayuwata yacce naga dama, ba da kai ba da ban san dali.....” Ban karasa ba naji muryarsa cikin tsawa tare da sake matse min gashin yana kuma dago fuskata. “Ya isa! Ya isa haka please.” “Toh naji sakar min kai na nima.” “Ki min shiru na ce.” “Ashh... Wayyo Allah kai na zai cire min gashi.” “kin rai na ni ne?” Ina faman matse ido saboda zafin rikon da ya yi min nace. “Ban gane ba.” “Kince kin dena zuwa nan ko?” “Eh na fada fa, amman cewa nai idan baka gyara mu'amalarka da Ammie ba.” Ya yi saurin sakar min gashi tare da dafe kanshi ya sunkuya zuwa kasa yana furta “Kai na... Kai na zai...zai ci.....” Hankali na yai mugun tashi ganin yadda lokaci guda ya birki ce min, ban san sanda na durkusa a wajan shi ba ina bashi hakuri a gigice dan nasan koma menene ni ce sanadi, na fahimci indai zan ambaci sunan Ammie toh dole yana shiga cikin wani yanayi da shi kansa be san yana shigarsa ba. Kofar da naji an kwankwasa ne ya kuma tayar min da hankali, kafin nai wani motsi an bude an shigo ciki. Jakadiya ce kanta a kasa kamar tsohuwar munafuka, nai saurin kallon ta ido waje. Ganin yadda take kallon Salman yasa ni nace. “Daman kina da damar shigowa nan Jakadiya?” Cikin sauri tace. “A'a wallahi ranki ya dade, ina parlor ina jiran na yiwa Gimbiya Jaleela iso ne sai naji kamar kin kira ni.” “OH kinsan ina ciki kenan?” “Wallahi tallahi ban sani ba ranki ya dade, dogari ne ya sanar dani.” “Okay please bashi da lafiya ba zai iya ganin kowa ba a halin yanzu.” “An gama ranki ya dade Allah ya ja kwananki.” Ta fada tana mai bita da baya da baya cike da son ganin gulma. A rai na nace zan yi maganin ki babbar kawai. *SAS* Tsaye yake a jikin window din dakin sa, Sanye cikin bathrobe, Da alama wankan bacci yayo. Agogon dake saqale a jikin wallpaper ya kalla, Sha biyu saura kwata, Yanzu ne lokacin da Khadijaa ke fitowa daga wanka itama, Dama sashen sa yana kallon nata. Kuma curtains din dakin da take kwana a saman irin shara-shara dinnan ne, Yana hango ta idan tana shiryawa. Kansa ya dafe da hannu d’aya. Saboda tsananin yadda yake sara masa, Gashi bayaso ko da second d’aya ya kauracewa kallon ta. Tun sanda tazo yana tare da shaheeda dinnan bata sake komawa ba. “Gani kike ko bana sonki ko?......Lokaci zai bayyana komai.” A hankali ya fada yana mai zama akan kujerar dake kallon setin windon ta. Cikin haka kuwa sai ga Khadija tafito, Itama da rigar wanka, Ta wanke yalwataccen dogon gashinta baki sidik, A hankali ta shjga saka comb tana taje shi, Salman ya jinginar da kansa a jikin kujera yana lumshe idanu.. Lokaci kawai yake jira ya bayyana mata zuciar sa. Tashi yai da sauri yana zura kansa ta window tamkar zai fada ganin tana kokarin sab’ule hannun ta d’aya na rigar wankan jikin ta. Abun karo ganin abu ya sanya a idanun sa yana kara zooming dinta. Tamkar ta gane ana kallon ta. Ta maida hannun rigar ta mike tsaye ta fice.. Cizon yatsan sa yayi ya koma je gaban closet dinsa ya ciro kayan bacci ya saka, Turaruka masu sanyin kamshi ya fesa a jikin sa, A hankali ya sauka kasan sashen sa. Wani da’ki ya shiga acan karshen kurya wanda ba zaka taba cewa daki bane, Dubada wajen anyi shine kamar ma’ajiyar littattafai.. Hannun sa ya dora akan wani waje ma’ajiyar littattafan ta bude Shi kuma ya shiga ciki.. Ba zaka taba cewa ba wajen aikin computers bane. Gaba d’aya conputoci (computers) ne kala kala awajen. Kowacce tana nuna reshe da reshe na masarautar baki d’aya... Idan ka cire sashen Ammi. Zama yai akan kujera ya shiga duba wata computer dake gaban sa bayan yasa medicated spectacles a idanun sa. Tamkar ba Salmaan ba haka ya dawo, Nazari yake sosai da takardar gaban sa. Ya dakko waya a gefe ya kira falaki.. “Ka gama shirya min komai....? Yess! Yes! Jibi da sassafe zan tafi. Ka tabbatar jirgin nan an gama cajeshi ba matsala... Kasan mutanen ka ba’abin yarjewa bane.....” Kit ya katse wayar ya ajiye a gefe... Photo album din gaban sa ya dakko ya shiga dubawa yana nazarin sa sosai...Ahankali tamkar mai ciwon baki yace, “Khaleel..... Da Abdullah..” Dai dai lokacin da ya d’aga kansa kenan ya dubi wata computer me nuna hotunan mutanen dake wucewa ta kofar ‘kyaure... Abdullah ya gani. Wanda ko dena gani yai ya dawo aka nuna mai shi zai gane shi. Tamkar zai cikin computer haka ya zura kansa yana kallon sa, Shi kuma Abdullah waya yake dannawa da alama chatting yake. Haka Salman yaita kallon sa har ya tafi.... Wayar sa ya dauka sai kuma ya ajiye yana rike goshin sa. Meya tuna oho sai kuma ya rufe wajen ya gyara koina ya haye saman sa hankalin sa a kwance. Dakin sa ya shiga, Ya fara yo alwala.. Ya yiyyi sallar nafila kafin ya koma kan gado ya kwanta. Ruwan roba ya ciro a mini fridge din dake gefen gadon sa, Ya shiga sha a hankali yana runtse idanu hade da girgiza kai... “Ammi.... Ammi....! Tabbas a yanzu na gama gano wacece Ammi .. Ammie nahhh! Ammi kiyi hak’uri, Ammi ki yafe min... Yanzu kam Khadija ta tuno min wacece ke agare ni, A baya na kan tuna ki, amman...Mintina kalilan kuma tamkar an goge ki acikin zucia ta.. Amma Insha Allahu! Nan da lokaci kalilan komai zai warware kansa. Akwai abubuwan da nake son na gama bincike akan su Ammi..... Dana gama zan zo gare ki cikin aminci... Khal and Abdullah.. I love and miss you too.” Hawayen da suka gangaro masa ya goge... Ahankali ya janyo farar wayar kusa dashi, Ya kunna. Hotan Ammi ya bayyana akan screen din wayar, Gallery ya shiga yana mai dudduba hotunan ciki, Shi ne da su Khal kafin a wargaza musu rayuwa. Girgiza kai yayi ya kashe wayar ya maidata ma’ajiyar ta ya boye, Ya dakko wata yar takarda yayi rubuce rubucen sa aciki ya ajiye, Wanda koda nan gaba ya manta komai daya karanta zai iya tuna wasu abubuwan. Tamkar ya tashi ya tafi wajen Ammi haka yake ji, Amma bayason ya bayyana komai sai ya gama shirin sa a nutse, Ya gano komai tukun sannan.. A hankali ya maida kallon sa window din Khadija.. Ya sauke gauruwar ajiyar zuciya.. Shi da matar sa amma ba shida damar bayyana mata komai sai nan gaba kadan. Da tunane tunanen tafiyar da zai yi jibi bacci daddada yai awun gaba dashi.....! *DURBUN.........* Zaune Gajiyalle take ta kara manyanta amma kamanninta nada suna nan, Tayi yarkace yarkace Da daurin zani tana tankade tsakin kuka.. Ladiyo matar Mudikalle tafito hannun ta rike da wani yaro hancin sa dagaje dagaje da majina, “Gajiyalle... Wai kina nufin baki ma daura sanwar rana ba?” “Haba Ladiyo... Yar aikin kice ni da zaki tsayamin kerere aka kamar wata bishiya? Kizo ki dafa mana ke.” “A hayye nanaye! Ni ladiyo nai abinci? Tabdi jan, Yasin bazan ba, Banda naci da kulafici dole sekin zauna tare damu? Ki je ki kama daki mana ki zaman kanki.” Gajiyalle zatai magana kenan, Mudikalle ya shigo hannun sa rike da leda baka sai busa hayakin taba yake. “Kai.. Wai wane dan kut.. kai wane dan haka kaza ta ubanne acikin ku ya fara taro match? Sai hayaniya kuke haba.” “Dan guzumar ubanka ni Gajiyalle kake gayawa haka? Mudi ka shiga taitayin ka fa.” Ashar ya lailayo ya dura yana banka mata harara, “Ke kuma ungo naman tsiren bakin kasuwa ne, Kici keda Halipha.” Ladiyo zata k’arba Gajiyalle ta wafce tana dire tsallan albarka, “Na hada ka da ita da shi na nanawa ubanka dan uban ka tsiren bakin kasuwar zaka bata ta cinye da shege? Wohoho lalle Mudi ka manta alkhairi.” Ladiyo ta sheke da dariya tana tafa hannaye, “Baa shege d’aya sai biyu, Banda abinki Gajiyalle waye baisan me kika aikata a karkarar nan ba? In shegen na haife ina uban sa daya sa akai cikin shi na aura?”Ladiyo ta karasa tana mai jan dogon tsaki, Hade da wafce ledar tsiren hannun Gajiyalle, Ta sunkuci halipha suka shiga ciki Mudikalle yaja dogon tsaki yana mai hararar Gajiyalle, Jan wajen kwata ya matsa ya fyace hancin sa, Ya goge da hannun rigar sa yana kwakular cikin hancin haka ya fuce yana waka. Gajiyalle tai zaman dirshen a kasan kyauren dakin ta, Magana take tana mai daga rariyar tankaden kukan da take sama, “Wai ni Ladiyo ke gayawa magana? Ada sanda nake da kajina, Da dabbobi na da zabi na ba uban dake yadamun magana, Wai yau Ladiyo yar Uwannaniya me yakuwa ce ke gasamin magana? Guzumar uban can kayya kai... Auren nan ba inda zashi tunda na rariya ne, Idan asiri ne a tafe na kwan muje zuwa Ladiyo daga ke har Uwannanniya sai naga bayan ku. Sai dai kuwa jarin yakuwar taki ya kare. Bankadaddu!” Cikin haka Ladiyo tafito tayi shegen dauri fuskar nan tasha dige digen jambaki daka ganta kaga tsohuwar yar tasha.. “A hayye nama dadi.. Tsiren bakin kasuwa yasin duniya ne. Kai mijina Allah dai ya kara arziki na jiya da daddare yayi dadi amman na yau kam ba’a magana...” Tagama ta wulla takardar waje ta kurkure bakinta tana sakin wata shegiyar gyatsa, “A gama tuwon kuma mu kora dashiiiii..” Daki ta shige tana mai cigaba da wak’ar ta. Tsabar bakin ciki Gajiyalle batasan ta zubar da rabin kukar a kasa ba. Sai da Ladiyo ta shige sannan ta lura.. Kadan kenan daga rayuwar Gajiyalle a kauyen Durbun..... ..Kaunar k’auna masoyan zafafa 5❤️❤️ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥. _*INA MASU NEMAN MAGANIN INFECTION SADIDAN? MAGANIN NI’IMAH, MAGANIN GYARAN HIPS AND BOOBS? MAGANIN BASIR....NA HAUSA BANA BATURE ME KWANTAR DA CIWO BA? TO KU MARMATSO KUSA, DOMIN YAU MUNA TAFE DA ALBISHIR WANDA ZAI FADADA MURMISHIN FUSKOKIN KU.. YA KUMA KAWATA ZUKATAN KU. MUN GWADA MUN GANI, MAGUNGUNANTA SUNADA KYAU KUMA SUNA DA AIKI.. BABU SIDE EFFECT, ANYI SU NE DAGA TSAFTATTUN KAYAN ITATUWA, DA SIRRIN CHADIAN HERBALS.. KARNA CIKAKU DA SURUTU;_ _*AISHA S BAYERO TRADITIONAL MEDICINE AND HERBAL RESEARCH CENTER..._* _KUNJI SUNAN KO? CENTER CE TA MAGUNGUNAN GARGAJIA, WANDA DUK WANI DAMUWA DAKE DAMUNKA IDAN HAR KAZO WAJEN S BAYERO TA KARE DA YARDAR ALLAH.._ _KADAN DAGA MAGUNGUNANTA SUN KUNSHI:_ _MAGANIN SANYI _ _MAGANIN NIIMA SET_ _MAGANIN NANKARWA _ _MAGANIN KIBA BABBA DA _KARAMI _ _MAGANIN HIPS _ _MAGANIN GYARAN NONO _ _MAGANIN RAGE KIBA _ _MAGANIN SAKA FEELING _ _MAGANIN CIDA KWAI _ _ZUMA YAR ASALI_ _MAGANIN BASIR KOWANNE IRI _ _HODAR NI’IMA _ _MAGANIN MALLAKA _ _GUMBAR NONON RAK’UMI _ _GUMBAR MADARA _ _TURAREN FARIN JINI _ _KAZA MARA KWAI _ _TURAREN MALLAKA 3 STEP _ _HAD’IN MATAR MINISTER 1_ _KAZA ME KWAI_ _STEP 2:_ _TURAREN MALLAKA ME KWALBA _ _ME KUNAMA DAN MATSI _ _TURAREN GOSHI _ _TURAREN QIRJI _ _TAUWADAR MATA _ _MEMORY _ _KAHON MALLAKA_ _YAJIN MAZA_ _TEA DIN MAZA _ _DAMBUN MATSI_ _MAN AYU_ _MAN DAMO PURE _ _KWALLIN IDONKA IDONA _ _GARIN SHA DAKA ME KYAU _ _KUBEWAR MATA_ _DUKA WADANNAN INGATTUN MAGUNGUNA NA GARGAJIYA HAJ AISHA NA DASU GANGARIYA.. HERBAL MAGUNGUNA NE MASU KYAU DA INGANCI.. TAFIYAYYU NA KASAR CHAD. CHADIAN HERBAL MEDICINE AND RESEARCH CENTER.. KYAU, INGANCI.. RAHUSA... SAI MAGUNGUNAN *AISHA S BAYERO TRADITIONAL MED AND HERBAL RESEARCH CENTER...._ _NUMBER WAYAR WHATSAPP: 08121491609 KO KIRA TA NUMBER 08145873617._ _ADIRESHI: KUNTAU KARSHEN KWALTA KAN A KARASA YAN TIFA, DAIDAI GADON KAYA CEMENT.._ *13* *wattpad:missxoxo00* *IG Business: yerwaincense_and_more* *KHADIJAA* Ina kammala shiryawa nasa kayan bacci wasu riga da wando, kiran waya ne ya sani dakatawa do nike wajan daure gashin kai na. Naje nai picking baki na dauke da sallama, muryarshi ta daki cikin kunne na inda yake cewa. “Idan da hali kuma zaki samu dama, ina son ganinki yanzu.” Kamar bazan amsa ba, Sai kuma naga rashin dacewar hakan, cikin dakile murya nace. “Toh ina zuwa.” Ina jin sanda ya furta 'okay' a hankali sannan kuma katse ni kuma na bi wayar da kallo ina tabe baki. Wardrobe na nufa ina tunanin saka kaya, Sai kuma na kalli jikina naga babu inda za'a iya gani, na janyo dogon hijab har kasa nasa tare da bin ko'ina da turaruka masu dadin kamshi. Babu abin da na dauka dan ko magungunin su duk sun kare, na kuma sanar da Gwaggo ta fada, tace malam zai kawo wasu idan ya gama hadawa. Ta baya nabi ko ina haske tamkar ba dare ba, na karasa ciki kai na a kasa kamar wata marar gaskiya. Tamkar a tare muka zo da Shaheedah, dan ko sallama ban gama furtawa ba naji shigowarta cikin isa da takama, na kai duba na wajan da Salman yake a zaune shima yana kallon mu, duk a zato na yana sane ya kiramu mu duka. Sanye yake cikin wasu fitinannun kayan bacci masu mugun santsi milk color, ba karamin kyau suka yi mai ba abin ka da farar fata wacce ta hadu da jin dadi. Zaune yake akan sofa ya dora kafa daya kan daya yana girgizawa, hannunsa dauke da glass cup mai dauke da fura da nono da yaji ayaba da kwakwa yana sha. Daga ni har Shaheedah tsayawa mukai muna kallonsa dan kamar be san da tsayuwar mu ba a gurin, ina ta tunanin abin yi kawai naga ta nufe shi tare da hayewa kan cinyarsa tana lankwasa kai. “Honey ban gane wannan lamarin ba, yaushe rabon da na kasance tare da kai, kullum kuna tare da waccen yarinyar mai kashin tsiya. Na gaji to gaskiya dan haka yau sai dai ta hakura da duk wata jarabarta dan ba zata samu ba.” Shi kanshi Salman dagowa yai yana kallona, Shi kansa yaji abin da be taba kawowa ba. Ni kuma na sakar masa wani shu'umin kallo da ya sanya shi hadiye furar da ya kurba cikin bakin sa. Na karasa wajan center table tare da cire hijabi na ina faman jujjuya kugu na. Ban yi gigin zuwa gurin su ba tunda ta rigani hayewa kan cinyar da nake samu na zaune dan kawai na guma mata. Ina tsaye kam sai faman gyara gashin kai na nake yi, ina kuma karya wuya cikin salon shagwaba nace. “Whole world kasan yadda naji dadi dazu da ka matsa min mara ta? Ina komawa part dina period din yazo cikin sauki. But naji yanzu ma tana dan tsira min, shine nazo ka kuma yi min irin yadda kai min please.” “Ba Zai yi ba din, ko baki ji ba? Na ce ba zai yi ba ko kin dauka bawanki ne Shi. Kuma yanzu ba ke kike da Shi ba, ni ce nan, kwana biyu ina sane da yadda kike yi masa zarya ko kin dauka Shi irin jarababnun mazan nan ne?” “Dan Allah Yaya ki yi hakuri ya dan matsa min, ai ba wani abin zamu yi ba tunda dazu mun hadu, mun dade kuma tare. Ki barshi a matsayinsa na miji na ya yi min ba sai naje asibiti wani ya yi min ba.” Nai maganar cike da nuna mata Cewa a kage nake, na kuma tabbatar mata da cewa mun yi wani abu da Salman din Wanda take ta kurin yau da ita Za a yi. Tartsatsatsatsasss muka ji jikin kunnuwan mu, da sauri nai tsalle biyu na rungume bayan Salman din ina kudindine fuska, Jiki na kuma yana bari alamar ina cikin tsoro, Sai faman wayyo Allah nake kai kace wani abu ya biyo ni tsabar iya acting. Shaheedah kuwa baki ta saki tana kallon yadda na cukwikuiye Salman kamar bana san ya gudu ya bar ni. “Ke! Menene haka kamar wata yar karamar yarinya? Baki ga glass cup din hannunsa ne ya fadi ya fashe ba zaki mana Wannan dramar. Ke ko dai kin tab'a d'ana wasan hausa ne, dan naga kin iya acting din sosai?” Nai kamar zan yi kuka ina cewa, “Yaya ni banga lokacin da cup din ya fadi ba, kawai kara naji na dauka ma bomb ne. Kuma ni fa ko hausa drama bana kallo bare nasan me suke koyarwa.” Shaheedah taja tsaki tare da kallon Salman tana shafar habar sa mai dauke da kwantaccen gashi, nima kuma naki sakin shi sai dad'a ma kwanciya da nai a bayan nasa ina faman sauke numfashi. Ta kuma jan tsaki, abin da yake batawa Salman rai kenan wato mutum ya yi ta tsaki a gabansa, ko ba dashi kake ba baya so sam. “Yaya Shaheedah dan Allah ki bamu koda one minute ne ya gama yi min please.” Shi kanshi Salman yana mamakin ganin yadda Shaheedah tak'i daga masa cinya tunda ba saba yin haka tai ba, ya gane cewa ta yi haka ne tunda Dije ma yi take a gabanta, sai dai sam ba ta burgeshi ba tunda abin na ta kwaikwayo ne. "Idan zaki zo ki wuce kizo ga hanya nan, idan har sai ya danna miki zaki ji sauki toh wallahi sai dai marar taki ta zazzago makira kawai." Na zare hannuwa da jikina daga na Salman na mike tsaya cikin nuna bacin rai a fuskata, zuciya ta kuwa shar dan nasan yanzu ma na guma mata bacin rai a zuciyar ta. Nazo zan wuce shi yasa tattausan hannunsa ya riko ni, muka had'a ido dashi, sai ya lashi saman lips din shi tare da furta. "Why...?!" Duk da ban gane dalilin ce min haka ba, sai nai amfani da wannan damar wajan sunkuyar da kai na ce. "Ka barshi kawai na hakura tunda ba ta yarda ba, ni bana son rigima kuma itace babba." Ji nai ya sakar min hannun haushi ya kamani duk a zato na zai ki saki na ko kuma ma ya janyo ni jikinsa dan mu kunsawa Shaheedah bacin rai. da sauri na dauki hijab dina na saka, ko ta kansu ban kuma bi ba haka na fice ina kunku ni. wallahi duk da bana jin ina son Salman, amman tabbas naji na tsani Shaheedah, haushin ta nake ji fiye da tunanin mai hasashe. Ina shiga daki nayi cilli da hijabin tare da fadawa kan gado, tunanin Mas'oud yana son fado min nai saurin mikewa zaune dan bana son akwai auran wani a kai na kuma a ce ina tunanin wani daban. A can wajan su kuwa, Dije fitowa Shaheedah ta fara kissing din shi tana kokarin cire masa riga, Salman yai saurin rikewa tare da daga ta daga cinyarsa ya mike tsaya. kallan ta ya yi cikin dafe kai yana rintsa ido shi a dole ga wanda kanshi ya fara ciwo. Ya riko hannunta suka nufi kan gado yana ta dafe goshi yace. "Kai na ke ciwo, ga sanyi ina ji lullube ni please." Shaheedah ta saki baki da hanci tana kallon sa, ganin yadda yake rawar jiki ne yasa itama ta hakura ta rufa masa tattausan bargo tana mai hadiye maitarta a fili. Gashi maganin da ta sha so ake suyi mu'amula a daren, kuma ta kasa samu tunda gashi kwance yana rawar sanyi. Da kyar ta iya fitowa daga dakin ta koma sashen ta tana jan tsaki. Salman kuwa tana fita ya yaye bargon tare da bin kofar da kallo, sam ba wani ciwon kai da yake ji, kawai tunda ya ga wata yar k'aramar laya a wuyanta, ta sanya zaran sarka a jiki ta yadda idan ba kula kayi sosai ba bai zama lallai ka gane cewa laya bace. Shi kuma tun da ya gani yaji sam hankalinsa be kwanta da sarkar ba, hakan yasan ya shi yin pretending na ciwon kai da jin alamar zazzabi. can kuma salon khadija ya fado masa, wato yarinyar ta san ta kan makirci, idan ban da haka me yasa idan su biyu ne bata tab'a ko rike masa hannu idan ba da dalili ba. Amman a gaban Shaheedah sai tai ta nuna ai har sun riga sun zama abu daya? yana son sanin me yasa take masa wannan salon, yau tsabar kwarewa ma cewa tai ya matsa mata mara bayan beji ba kuma be gani ba. Tunani ya fara tabbas akwai wani abu da khadija ba ta son Shaheedah ta sani game da rayuwar su. kamar yadda yanzu ya fara tunanin akwai babbar matsala tattare da wadanda suke zagaye dashi. Lallai ya zame masa tilas akan ya kara wani salon kusanci tsakanin shi da khadija, yana ji a jikinsa cewar ba zata cuce shi ba duk da cewar yasan ba son shi a ranta, amman yasan ba tasan komai ba a cikin makircin sarautar Bassannabas bare tace zata yi masa. Dole ya kusantota gurin shi tun kafin wani ko wata a cikin masarautar su fara kulla mata mummunar dabi'a. Da wannan tunanin ya shiga toilet yai alwala ya fito, gurin da furar sa ta kife yana nan ba a gyara ba, kuma a ka'ida Shaheedah ce ya kamata ta tsaya ta gyara masa, amman saboda bata saba ba kuma ta fita da b'acin rai shi yasa ko a jikin ta. Da kanshi ya tsabtace gurin dan ba zai iya barinsa har gari ya waye ba. Sallah yai sannan ya yi ta addu'a tsawon lokaci kafin ya tashi ya hau kan gado, kwanciya yai tare da lumshe idanunsa. Khadija yake tunawa da yanayin yadda ya ganta cikin kayan bacci, be san dalilin da yasa yake yawan tunaninta ba. Amman ya fara jin cewa ya yarda da ita a cikin rayuwar sa, yana jin ta cikin zuciyar shi musamman yadda yaga tana nuna masa muhimman abubuwan da yai wasarere da su. Da kyar ya samu bacci ya dauke shi bayan ya duba sakkon da aka turo masa ta waya. *WASHE GARI* (SASHEN GIMBIYA KHADIJA) Da kyar na iya tashi daga bacci sakamakon wani mummunan mafarki da nai akan Salman, bathroom na shiga ba jimawa na fito daure da alwala, sallaya na shimfid'a nai nafila ina idarwa nayi sallar asuba daga nan azkhar nayi ban tashi daga kan sallaya ba sai wajan karfe bakwai na safe. Wanka nai nazo na shirya kai na cikin wata atamfa d'inkin riga da zani, na dakko alkyabba na d'ora daga nan na fito zuwa parlour na inda na tarar da hadimai na suna ta aikin tsabtace gidan. Bayan sun gaishe dani ne na ce mutum daya tazo ta yi min rakiya sashen da bayi mata suke a cikin masarutar. Tana gaba ina bin bayanta har muka karasa, tun a hanya dama nake ta samun yan gaisuwa haka da na shigo baiwayar tawa da ta rako ni tai musu bayanin ko ni wacece, nan da nan kuwa suka dinga sunkuyawa suna gaishe dani. Jakar hannu na da nake rike da ita, na bude tare da ciro kud'i na dinga rarraba musu sadaka da niyar Allah yasa mafarkin da nayi akan Salman ya zame masa alkairi. Sai da na tabbar na bawa kowa dama d'ari biyar-biyar na basu, suka dinga godiya kuwa kamar na basu duniya. Ina kammalawa sashen Ammi na wuce inda na tarar kafarta ta dameta da ciwo, sai da na tabbatar tayi breakfast sannan na zauna na dinga matsa mata, tun tana hanani har tai shiru daga karshe ma muka fara hira ina ta sako mata labarin Salman yadda ya fara kiran sunan ta da yadda naga jikin nasa yana samun sauki. Allah sarki uwa tunda taji haka ta fara murmushi nasan ko ba a fada ba wata kyakkyawar addu'ar take sake yi masa a cikin zuciyar ta. Na dade sosai a gurin Ammi sannan na koma sashe na, duk a takure nake babu wani aikin yi da zanyi bare ya debe min kewa. Wayata na dakko wacce take a kashe na lalibo lambar kawu Daddy, bugu uku ya d'aga cikin fara'arsa yake min magana. "Yata ta kai na, ince dai lafiya lau kike ko?" "Lafiya ta kalau kawu daddy, kwana biyu shine nace bari na kiraka mu gaisa." "Alhamdulillahi yarinya ta ai ta hakuri da zaman aure, na san kina da hakuri khadija, amman ki kara akan wanda kike da shi kinji? Allah ya yi miki albarka." "Amin kawu Daddy na gode sosai da addu'a. kawu da na ce wai babu yadda za ai na koma gurin aiki na, wallahi kawu na gaji da zaman kadaici ba aikin yi sai kwanciya." Dariya naji ya dinga yi, nai shiru ina tunanin abinda ya sashi dariya a magana ta, har na fara tunanin kodai ba ni yake yiwa ba sai naji yana cewa. "Khadija ai ni yanzu bani da iko dake sai dai mijin ki, kuma gaskiya zai yi wuya a ce mai irin matsayinki tana irin wannan aikin. sai dai business wanda zaki kina daga zaune amman ba dai na fita office ba." Nai shiru a rai na ina tunanin ai ba zama nazo yi gidan sarautar ba bare nayi tunanin tarewa ta har abada, harga Allah ina son aiki na dan yana cikin buri na tun ina karama, ta ya za ai na samu kuma yanzu a ce sai dai na ajiye shi kacokam saboda kawai sarki ya aure ni. muryar kawu daddy ta katse min tunani na, inda yake cewa. "Bana son ki matsa masa akan wannan aikin khadija, auranki yafi wannan aikin da kike son fitowa kiyi. ina miki fatan alkairi a duk inda kike." Ba haka na so ji ba, amman babu yadda zan yi na musa masa sai kawai nai dauriya wajan cewa. "Shikenan kawu Daddy na gode Allah ya kara girma da lafiya mai dorewa." "Amin yar albarka na gode miki nima. ki gaida min da mai gidan." Na yi shiru ban amsa ba har ya katse, kamar jira na gama wannan wayar naji telephone din dakin ta fara ringing, na tashi da kyar naje na dauka ina turo baki tamkar ina gabansa. cikin kasalalliyar muryarshi yake min magana a tausashe. "Ki kawo min wayar ki yanzu." Cikin rashin kulawa da maganar tashi nace. "Okay bari na aiko ma da ita." "No... kuzo tare da ke da wayar." "But amman ni...." "Ina jiranki." Ya katse. Wannan mutumin akwai iko, gabaki daya bani da amfani a gurinsa sai yana da bukatar nai masa wani abin. Tashi nai na shirya cikin wasu riga da skirt english, wai ko zan iya haduwa da Shaheedah. nasa hijabi na har kasa sannan na dauki wayar na tafi. Ina shiga na tarar babu kowa, ban kula ba naji an janyo ni nai baya, gashi an toshe min baki saboda kar na yi ihu. Sai da aka kai ni wani guri mai duhu kafin a sakar min baki na, nai saurin fincikewa daga rikon da ya yi min dan na gane shi ta hanyar jin daddad'an kamshin sa. Wani irin kallo na bishi dashi be kalle ni ba sai dakin da yake bi da kallo bayan ya kunne haske, haushi ya kuma kamani ji nake kamar na rufe shi da duka saboda takaicin da yake bani. Ya kamo hannu na tare da zama akan kujera. gurin mai kyau cike da littattafai da alamar library ne, ya tsaru an ajiye kowane littafi a inda ya dace. Ya rike ni da hannu bibiyu tare ba tare da ya yi magana ba, na maido da tunani na kanshi ina kare masa kallo cike da mamakin yadda yake rike dani nace. "Lafiya dai ko?" Tamkar na yi da dutse, har na hakura da bani amsar da nake so ya yi sai naji yace. "Ina son na yarda dake, yarda irin wacce ake kira da amana." "Toh amma shakku kake yi ko kuwa ka yarda dani din har cikin ranka?" Dagowa ya yi ya kalle ni muka hada ido dashi ta cikin glasses din fuskarsa. Ya lashi kasan jan lips din sa..... _Duk wani shaukin typing da kara yawan sa, Yana tattare ne da yanayin yadda makaranta ke sharhin sa, Comments na karawa marubuciya kwarin gwiwar rubutu, Haka dena shi yana kashe mata gwiwa wajen fargabar yin sa... Makaranta books din zafafa.. A dinga comment ko writers saji kwarin gwiwar kara yawan typing_ _Sannan Afuwan Pls.. A dinga yiwa marubuciyar kibiyar ajali uzuri 👏🏻idanu hud’u take amfani da.. So yanayin typing dina dana sauran writers dole bazai zo d’aya ba. Ahakanma ana kokartawa. Akwai lokacin da dole zaka ajiye typing don karka rubuta abu ba daidai ba, Ko ka gajarta shafin.. _ _Hakki ne muka dauka dole mu sauke shi.. Dan Allah a dinga uzuri. Me cewa kibiyar ajali na jan k’afa, Ayi uzuri Pls 😊k’arshen gaskiya ta kenan..!_ _Kaunar kauna fisabilillahi masoyan zafafa❤️❤️_ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._ _LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._ _”Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_ _”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_ _Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻‍♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼‍♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._ “_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi.. Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_” _”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a faranta maku a littafin UNCLE NE_ _(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_ PG: 14/15 ....Ya janyoni sosai tare da kokarin dorani saman cinyarsa, nayi saurin tak'irewa alamar ba zan hau ba. Kuma janyo ni ya yi na fada jikinsa yasa duka hannuwansa ya rungume ni kamar na ce masa guduwa zanyi. Ya yi luf a jikina, kirjina ya dinga bugawa saboda tsoran kar ya yi min wani abun da ban shirya karbarsa ba daga gare shi. “Ni dai gaskiya ka cika ni zan tsaya na saurareka sosai.” “Nan zaki zauna saboda gurin zaman ki ne.” “Wa? ni na isa, wannan gurin na madam gimbiya Shaheedah ne. Ni kam ai yafi karfi na alhaji.” Ya yi shiru be ce komai ba, haka ya sake tabbatar min da cewa lallai gurin na Shaheedah ne tunda gashi be musa ba. Na tab'e baki tare da yunkurin sake tashi amman ya rike ni ya hanani ko da kwakkwaran motsi. Sai da ya mulu ya mulmule sannan yaja numfashi yace. “Ina son na baki amanar kai na da rayuwa ta khadija, na yadda da kwarewar aikin ki shi yasa zan nuna miki sirrin rayuwa ta a yau dan ki taya ni kula da ni kai na da duk wani wanda ya shafe ni.” Yana kaiwa nan gurin yai shiru, ni kuma na kagu naji abin da yake son sanar dani amman ya tsaya sai ja min rai yake yi. Jin shirun ya yi yawa ne yasa ni cewa. “Uhmmm ina jinka.” “Ai baki daukar min alkawarin ba, baki amsa min cewar zaki rike min ba ko a'a ba zaki rike ba.” Wannan karan ni ce nai shiru saboda tunanin abinda ke zuciya ta. Ta ya ya zan yadda na daukar masa alk’awarin da ban san ko na menene ba, ni da ba zama nazo yi gidan shi ba? amman zan iya karba ai tunda amana sai ranta ka ci ta sannan ne ka sab'a. Zan karb'a idan yaso ko nan gaba bamu tare zan yi kokarin rike masa duk wani sirrin sa. Naja numfashi tare da cewa. “Na amince zan karba, kuma ni ma nan gaba ina son kayi min wata alfarma.” Sai da ya dan matsa yatsu na sannan yace. “Ba damuwa.” “Ina sauraronka menene kake son bani amanarsa?” Salman ya daga mu a tare muka tashi tsaye ya kama hannu na muka doshi wajan wasu littattafai. Wani guri kawai naga ya bude sai ga abu kamar keypad ya danna kawai sai gurin littattafan nan ya fara budewa a hankali, sai wata kofa ta bayyana muka karasa wajan ya murda handle din muka shiga yana rike da hannu na. A rai na mamaki nake yi, sak irin boyayyar ma'ajiyar nan irin ta turawa da nake gani a films. Na ware ido lokacin da naga jerin computers, mamaki ya kamani nai saurin kallon Salman din dan jin karin bayani. Mamaki yake bani idan naga yana abu cikin sanyin jiki tamkar wata mace, ya fara kokarin cire min hijabi na ki yadda, sai ya samu guri ya zauna ba yana bude wani file yace. “Idan kin shirya na nuna miki.” “A shirye nake wallahi.” “Toh ni bana son aikin da hijabi a jikin ki.” Na zaro ido cike da mamakin jin abin da ya fada, shi kuma ko a jikinsa bama ni yake kallo ba, ga dare nayi haushi kamar ya kashe ni haka na cire hijabi din ina karawa a jikina nace. “Toh ka gaya min ko mene gashi na cire, ni ban taba ganin aikin da za a ce ba a yi da hijabi ba” “Harda wanka?” Yai maganar tamkar ba daga bakinsa ta fito ba. ni kam dai yau naga ikon Allah wajan Salman, ai kuwa ban sake yin magana ba har ya waigo ya kalle ni tare da tasowa yazo gabana ya tsaya. kwace hijab din ya yi tare da cilla shi gefe nai saurin saka hannuwa na ina kare jiki na saboda yar karamar riga ce, gashi ta fito da albarkatun kirjina (Fitilu biyu inji jerry Aneesa didi😂). Murmushi ya saki tare da kawar da kai yaja hannuna muka nufi wajan computers din, ya kunna wani waje gabaki daya suka kawo haske, zaunar dani ya yi akan kujerar da take tsakiya. Sai ya yi min runfa da jikinsa, ma’ana ya rankwafo ta bayana yana danna keyboard cikin nutsuwa. Ni kam fuska na cakune dan naga sai wani shige min yake yi, ga shi idan kwantaccen sajen sa ya gogi wuya na sai naji jini na yana yawo, amman na dake dan karma ya yi tunanin dad'i nake ji. Gabaki daya masarautar ta bayyana a ciki, sashe-sashen dake cikin ta suka fito cikin ko wanne screen. Harda sashen Ammi sashen gimbiya Shaheedah da nawa da duk wani guri dake cikin masarautar Bassannabas. Gashi nan kowa yana harkarsa ashe yana ganin komai da yake faruwa a kowanne sashe duk da naga ba a ganin wasu gurin kamar bedroom da toilet, amman ana ganin nawa da na Shaheedah. Ji nai ya hura min iskar bakinsa cikin kunne na, da sauri na rintsa idanuwa, yaci gaba da magana cikin wata irin murya wacce tamkar yana jin bacci. “Wannan gurin babu wanda yasan ina dashi a cikin masarautar nan sai wadanda suka yi ginin shima kuma a boye akai, sannan sai Falaki da Alhassan sai kuma ni yanzu kuma kin shigo cikin wadanda suka san da gurin nan.” Yaja numfashi ni kam idanuna suna kan sashen Gimbiya Shaheedah wace ke hakimce a parlour bayin ta sun zagaye ta daga mai yi mata tausar kafa sai mai matsa mata kafad'u sai masu fifita da wace take rike da basket din kayan marmari. Mulki kawai take zubawa saboda an tsotsa har an rasa ina za a sanya izzar mulkin. na kuma maida hankali na sashen da su Galadima suke tsaye jikin wani gini da alama wata maganar suke yi mai mahimmanci a gare su. “Na yarda dake a dan zaman da nayi kina tare dani, duk da nasan kin tsaneni. Zanyi wata yar tafiya ne ina son kisa min ido akan masarautar nan, ina ji a jiki na kamar masu min zagon kasa sun mamaye ni. Khadija ki min alkawarin zaki rike sirri na ba tare da kin gayawa kowa ba, nai miki alkawarin idan nai tafiyar na dawo zan bayyana miki abin da baki sani ba, zai saki farin ciki ki manta duk wani abu da ya shud'e kinji?” Yai maganar tare da kai min sumbata a gefen wuyana. Na kasa cewa komai sai wani irin fitsari ma da yake neman takura min saboda kusancin mu yayi yawa, duk ya nanike min kamar wani mage. Haka Salman ya zauna kusa da ni ya dinga koya min yadda ake controlling cctv din da yadda ake recording da komai, mune har Kusan karfe hudun dare Salman yana ta nuna min abubuwa dangane da sirrinsa. Allah sarki gaskiya yana da mugun kawaici, Cikin rai na ban san lokacin da na dinga zuba masa addu'o'i kala-kala ba. Sai da ya tabbatar na gane yadda suke gashi daman nasan wani abun saboda yanayin aiki na, sannan ya tashi yaje ya dakko min hijabi na yasa min tare da kashe abubuwan. wata kyakkyawar kofa ya bude, abinda ya daure min kai shine ganin mu a cikin tsakiyar bedroom dina wanda nake bacci a cikinsa. na kalli gurin wanda duk a tunanina decoration ne ashe wai kofa ce a gurin, cikin rai na nace 'Shege bature' yasan takan tsiya kala-kala. “Ga hanya nan, Sai da safe, sai ki kula da mutane karsu gane ta. idan zaki shiga ba sai kin bi ta apartment dina ba kai tsaye kawai ki shiga ta nan. Good night yar jarida, sai na dawo ki kula min da komai.” Yana kaiwa nan ya juya ya tafi, ni kuma na karasa wajan ina tab'a hanyar da tai matukar daure min kai. Komawa nayi tare da hayewa kan gado, sai kuma nayi saurin tashi ina kalle-kalle ina son ganin a ina aka kafe min cctv camera amman ban gani ba, haka na gaji na barshi na dawo tunanin ta yadda zan fara yi masa aikin nan ba tare da kowa ya san da zaman gurin ba bare har na karya alkawari ba. *SOUTH KOREA* (GANGNAM HOSPITAL) Adaidai asibitin motar da aka dakko Salman daga airport ta tsaya. Falaki ya fito ya bude masa murfin motar, Sanye Salman yake cikin kananun kaya samfarin riga da wando yan kanti. Kansa yasa pcap. Yayi kyau sosai, Idanunsa saqale da spectacles dinsa na gado mai dauke da tambarin givenchy, Tafiya yake cikin kasaita, Daga shi sai Falaki. Sunyi ‘badda kama ba zaka taba cewa sarki bane da matemakin sa. *consultant Ibrahim (Khal) AS* Dai dai kofar shiga dakin suka tsaya suna duban juna, Falaki ya dafa kafad’ar Salman alamun kara masa karfin gwiwa... “Ranka ya dade mu shiga kawai dan Allah...!” Kad’a Kai Salman yayi, Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Falaki ya koma can waiting area ya zauna. Salman kuma ya sa hannu a hankali ya bude kofar, Dai dai lokacin da Khaleel ya daga idanu don ganin waye ke shigowa. Sosai suke kalon kalo tsakaninsu, ko wanne da yanayin yadda yake tunanin dan uwansa. kamar kuma an tsunkuli Khaleel haka ya zabura ya mike daga inda yake zaune. “Ya...Yay... Yaya Salmaan ne???? Is that you? Is that really you? Ya Salman Kai ne ko kuwa idanu na ne kemin gizo..” Salman yai murmushi hade da jingina bayan sa da kofa.. “Ni ne Khal...! Ni ne Salman.. Ashe rai kanga rai? Shekaru nawa rabon dana sakaka a idanu na Khal?” Wasu zafafan hawaye suka zirarowa Khal a saman kyakkyawar fuskar sa. Ya share hawayen dake gangarowa a fuskar tasa yana mai jujjuya Kai... “Noo Yaya.. I love miss you soo much!” Da sauri suka rungume juna.. Sai kuma kuka ya kwacewa ko wannen su sharrr, “Ina Ammi take...?.” “Tana gida Khal...” “Ina Abdullah? Yaya ashe baku manta dani ba.?” Murmushin da yafi yake ciwo Salman yayi, Ya kamo hannun sa suka zauna yana kalle kallen office din. “What a nice office you’ve got...Congratulations Khal..” Da sauri khaleel ya mike ya sabule white coat din jikin sa. “Muje apartment dina Yaya. Kai kadai kazo?” “Noo....” “Da aminin ka da na sanku tun tuni ko....? Indai kuma ban manta ba... Falaki ne” “Well... Yes” Fitowa sukai su biyu Kowanne fuskar sa dauke da murmushi, Duk kuwa da glasses din fuskar Salman kallo daga zakai musu kasan yan uwan jini ne. Khaleel ya rungume Falaki suka tafa, Kafin su isa parking lot yaja su suka tafi apartment dinsa. Sai da ya musu ordering abinci suka ci suka koshi, Banda Salman daya caccakuna domin shi ba ma’abocin cin abinci bane sosai. Tukun sannan Khaleel ya gyara zama ya shiga yiwa Salman tambayoyi. Shi dai Falaki fita yayi ya basu waje saboda su gana sosai.. “Wallahi Ya Salman ban yada ku ba.. Bansan meyasa ba, Danayi yunkurin zuwa gida ko kiran waya sai na kasa.. Nayi attempting several times Yaya na kasa...” Fashewa yai da wani kukan mai cike da bakin ciki, Salman ya riko hannuwan sa yana bubbuga bayan sa alamar rarrashi, “Na shiga fiye da yanayin ka Khal, Nasan kuma yadda kaji. Presently ma ni tamkar an juyamin tunani na.. Na jima bana tuno Ammi da ku, tamkar an shafemin sanin ku a kwakwalwata Khal gaba d’aya na shiga cikin matsalar rayuwa..” “Subhan’Allah...! Kenan ba jimawa komai ya dai daita awajen ka?” “Eh to.... Kasan na kira ka last month ko? Zan iya cewa daga lokacin memory d’inku ya fara dawo min, Ammi kuma ba’awani jima ba. So yanzu dai kasan bazai yiwu na nuna na san inda mahaifiya ta take ba, tunda naga hakan ne ke sa su yi mana makarkashiya, Kasan yadda masarautar nan take. Bana son a cutar da ita da ku shi yasa ban nunawa kowa ba.” Khaleel ya goge hawayen daya zubo mai yana jijjiga kansa, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.... So ya yan majalisar ka? Ka gano masu maka zagwan kasan?” “Ai ka bari kawai Khal... ni yanzu na san ina zagaye da makiya gaba d’aya sun yi min zobe. A fuska tamkar masoya amma a zucia ba haka bane..” “Ya matar ka..” “Matan ka zaka ce.. Suna lapia..” “Ahh na manta fa.. kace min ka yi wani auren Gimbiya Khadijaa itace amarya ko? journalist ce ko?” “Eh... Khadijaa ba..! My brave little lioness ba.” Ajiyar zuciya Khaleel ya sauke yana mai sauke tagumin da yayi.. “Bana tunanin ku, Na kasance cikin wata iriyar rayuwa. Wani lokacin nakan ji tamkar na manta wane ni.. Meya kawo ni nan ma? Daga ina nake? Wallahi Yaya komai goge min yake wani lokacin. Toh sai kwanan nan nafara mafarkin gida sama sama haka, Da Ammi da kuma ku.. Harma naji inason komawa gida, Inason jin sautin muryoyin ku ko da awaya ne.. Sai kawai kuma ka kira ni. Alhamdulillah Insha Allah k’arshen wahalar rayuwar da aka jefamu ne yazo..” “Ni ma hakan take awaje na Khal.. and sai Khadija ce ke gayamin halin da aka jefa Abdullah ma.. wasu basu da imani Khal.. shin me muka tsare musu Khaleel!?” “Qiyayya ce kawai Yaya.. ba’a so aka haife mu ba kagane? So ya za’ai damu! Shi yasa ake tagayyara mana rayuwa yadda aka ga dama...” “Toh ta Allah bata suba Insha Allah rayuwar mu zata gyaru kamar yadda take a baya. Kasan abdulqadeer ma an bashi sarauta.. Sun sani a gaba dole na bashi.. Yanzu ma sun nemi kudaden auren su munaya a guri na.!” “So suke ka sauka fa ta dole Yaya.. Zuri’ar Masekiri kuma sani ne basu yi ba amma sarautar su tagama tabarbarewa tun shekaru aru aru baya..” Ajiyar zuciya Salman ya sauke yana girgiza kansa, “General Checkup nakeso kuyi min Khal.. Da full blood count dina.. So nake na gano wasu abubuwa a kai na. Wai shin da gaske ne bazan taba haihuwa ba? ko kuma rabo ne babu tsakani na da Shaheedah?" “Shaheedan? What about her? Shin metayi haka?” “Birmingham, Cyprus, India , Luxembourg, France, Da Mauritania. Kaga 6 countries ko? Duk Sai da tasa muka jajje Khal... aka ce wai ni... Ni Salman nine bana haihuwa.” “Kai....! Kuma ka tsaya Yaya tun a lokacin ba kai komai akai ba?” “Khal ina tattare da makiya, Na gayama sun zagaye ni, Banida tacewa, Dole na dau zancen tamkar gaskiya, Sanin kanka dana karyata Za’a illata ni tun kafin mu baro kasashen ma.” “Subhan’Allah! Allah ya dubemu Yaya. Wannan zancen ya kamata a bayyana gaskiya kowa ya sani.” “Abinda ya kawoni kenan Khal.. Saboda nayi General checkup din.. Ya kuma zamto kaima ka dawo wajen Ammi.. Ni kuma daganan zanci gaba da gudanar da rayuwa ta yadda ya dace har sai na kammala bincike na.” “Allah ya temake mu Yaya.. Allah ya fisshemu kunya. Ka watsa ruwa ko? Sai mu koma asibitin, Ko kuma mu tafi can Busan ayo maka acan.” Hakan kuwa akayi. Salman yayo wanka suka sake shiryawa suka nufi busan. Acan doctors suka fara yiwa SAS gwaje gwaje, Har Sai da aka dau tsawon kwanaki 3 ana yi tukun sannan result ya fito. Result yafito lapiar sa kalau babu abunda ke damun sa sai ulcer saboda abinci da bayaci. Amma yana haihuwa kalau yake, Bashi da wata cutar da zata hana shi haihuwa. Kukan farin ciki Salman yayi, Khaleel ya rungume shi.. Falaki yanata murmushi yana yiwa Allah godia shima. Satin su Salman d’aya a Korea suka tattara suka dawo kasar Nigeria. Dama ca yai dasu Wambai ya tafi meeting da wani babban dan kasuwa akan project da zasu yi anan masarautar, Lokacin da suka isa airport din kano, wani murmushi yai irin na gefen bakin nan, Zuciar sa cike da abubuwan da zai aiwatar.. Ta ina zai fara? Akan suwa zai fara binciken sa. Khaleel bai samu damar biyosu ba sai bayan sati biyu, Sakamakon hanashi tafiya da board of directors sukayi.. Kan sai ya gama aiwatar da project din dake hannun sa. Ba kadan ba suke son sa, Saboda Khaleel mutumi ne shi faram faran kuma ya iya aikin sa, Ba wasa. Ko sanda yana gida Ammi da shi suka fi hira saboda baida girman kai da rashin magana irin na Salman da Abdullah... *SAS* Tun a airport aka bashi wani daki na musanman ya shiga ya sauya kaya izuwa na sarakuna. Driver ya ja shi suka koma masarauta. A bakin kofar yamma suka sauke falaki ya tafi gida wajen iyalin sa. Har kofar sashen sa akai parking ya sauka ya shige ciki sam baibi takan dogaran dake masa kirari ba. Yana shiga ya kishingid’e a doguwar kujera yana tuna khaleel kanin sa da suka sha zumunci. wani b’angare na zuciar sa kuma na jin dadin sakamakon da ya nuna lapiar sa lau.. Sanar masa akai zuwan waziri ya bada iso, Waziri ya shigo yana harhada hanya cikin girmamawa, “Sannu da dawowa uban kowa, Takawar ka lapia Sarki Salman jikan salmanu, Sawun giwa badda na rakumi shugaban mu, Hadarin sama sai sauraro sarkin mu, Kai ka dai ka iya Kai zaka cigaba da yi baban kowa, Sun buga sun barka ya zasuyi da kai? Dole su goce.. Barka da dawowa sarkin mu.. Yan majalisa da sauran yan zaman fada na murnar dawowar ka...” Murmushi Salman yai ya mike ya zauna daga kishingid’en da yake.. “Na amsa waziri... Ina kuma godia.” “An baro su lapia...?” “Lapia qalau.. Ai ansamu nasara sunce nan kusa zasu fara qaddamar da gine ginen cikin masarautar nan.” “Toh Masha Allahu! Tafiya tayi kyau. Babu wani kedararren acikin yan majalisa daya kira ka ko? Sanar mun yanzu ba sai anjima ba na aiwatar da hukunci..” “Noo babu wanda ya kira.. Ai ka tsayamun waziri.. Godia nake.” Hira suka taba sama sama, Waziri ya masa sallama ya tafi.. Ahankali Salman ya mike ya kashe hasken wajen gaba d’aya, Dakin sirrin sa ya shiga ahankali. Zama yai akan kujera, gurin tsab tamkar ma yadda ya tafi ya barshi, baya tunanin khadija ta shigo tai mai aikin da ya sanya ta. Yana kallon waziri ta cikin computer, murmushi yai lokacin da ya hango sashen da waziri ya nufa. Ajiyar zuciya ya sauke. Ya shiga jujjuya kansa ajikin kujera. Ya jima a haka kafin ya mike ya fita ya koma dakin sa. Wanka yayo yayi sallah, Kallo d’aya yaiwa abincin da aka jere masa akan dinning table ya dauke kansa. Kaya marasa nauyi yasa ya dora alkyabba akai. Amintattun dogaran sa guda biyu yasa agaba suka shiga zazzagaya masarautar. A kofar sashen gimbiya shaheeda suka tsaya ya shiga ciki kansa tsaye. Yana shiga hadimanta suka bashi waje. Kansa tsaye ya nufi dakin ta. Ya turnuke da hayaki sai tari take yi. Juyowar da zatai kawai tagan shi a kanta, Da sauri ta mike idanunta sunyi jawur saboda azabar tururun hayakin dake tashi... “Sas..Salman.. Y..Yaushe ka dawo?Tuttu..turara maganin sauro nake yi.” Jijjiga kansa yai alamun ya yarda, Ya rufe idanun sa ahankali ya bude akanta, Hannunta ya jawo suka fito. Daga ita sai daurin zani. Jikin ta sai kakkarwa yake ta dauka ya gane abunda take zai mata hukunci ne. Dakin kusa da wancen ya shigar da ita. Ya sakata a tsakiyar kofa yana toshe hancin sa da handkerchief.. “Maganin sauro.. wani iri kike turarawa haka...?” “Bb... Wani ne hadimata ta aikomin .. s.. Saboda sauron da ake kwana biyu.” “Okay.. Kidena wahalar min da kan ki.. Duk ga masu aiki nan ki dinga sasu kinji?..” Yana magana ya goge mata gumin dake goshin ta, Dadi taji ya lullube ta, Dama turaren mallaka ne hajian su ta aiko mata.. Da alama aikin sa kamar yankan wuka yake. Domin gashi tun ba’aje ko’ina ba hankalin Salman ya fara karkata izuwa gareta.. “Kinji ko... My Queen..?” “Naji my king..” “Okay jeki wanka ki zubamin abinci.... Idan na koma danaci sai bacci ko..?” Dadi ya sake kama shaheeda tayi murmushi tana jijjiga kai.. Da sauri ta shige ban’daki tayo wanka. Ba abinci. Sai Indomie tasa aka dafa jikin ta na rawa tasa aka juye masa a warmer. Har bakin sashen sa ta rakashi, Yana shiga gida ya kira dogarin sa ya bashi yace yace ya cinye. Yoghurt ya dauka me sanyi yasha yana lumshe idanun sa.... Bincike ne da yawa agaban sa da zai yi, yaso suyi tare da Khadija amman a tunanin sa ba zata bashi goyan baya ba saboda tana ganin ba son gaskiya yake mata ba. Kuma Kowanne sai yayi taka tsantsan akan gudanar da binciken kamar yadda ya boye yar camerarsa me recording komai a dakin shaheedah.. Dai dai lokacin daya jinginata a kofa.. Da kofar shiga sashen duk ya saka... “Yaa Allah... Ka bani sa’a a wannan bincike da zan fara aiwatarwa.. Allah ka bamu nasara.. Allah ka dora mu akan makiyan mu..” Haka Salman yaita maimatawa yana mai daga hannayen sa sama alamar roko izuwa ga mai sama.. Domin shi din mubuwayi ne gagara misali.... Asubah ta gari... Sarki Salman Aliyu Salman (SAS) .. Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 16 BOOK 2. BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻 *SAS* Kishingid’e Sarki Salman yake yana duba ipad dinsa, Dawowar sa daga fada kenan ba jimawa, Yana danna ipad din yana cije lebe, Can ya dubi intercom din gaban sa, Ahankali tamkar mai jin ciwo haka ya matsa kusa da ita, Ya danna wani button ya kara a kunnen sa. “Yes.......Kizo yanzu ina neman ki.” Yana gama magana ya katse batare da ya jira amsa ba. *KHADIJA....* Ina kwance na jiyo karar wayar kan bed-site drawer dina, A dakile na dauka na kara a kunnena, Domin na fara jin bacci wallahi. “Sarkin takura..” Na fada ina hararar wayar tamkar shi nake gani, Cike da b’acin rai na mike, Riga da wandon baccin jiki na na kalla, Hijabi me kauri na dora akan kayan na shige sashen nasa ta baya. Yana parlorn sa ya kwanta akan doguwar kujera yana kallon saman pop. Tamkar zai cinye ni haka ya shiga kallona tundaga sama na har izuwa kasa na. ....Dan iska.... Shi yana kallon ka yana wani jan kasan leben sa. “Gani...Barka da dare!” “Barkan mu... Yar jarida. Kina lapia?” “Alhamdulillah..!” Mu kai shiru gaba d’aya, Ni sai kara matse jiki na nake, Yanayin sanyin da ac ke bayarwa yamun yawa, Shi ko ajikin sa , Na lura yanason sanyi. Ganin shiru yayi yawa ga bacci inaji nace, “Yallabai... Gani” “Ohh... Dawo nan.” Na kalli inda yake nunamin da hannu na dan tabe fuska. “Nanma ya isa yallabai..” “Kar ki bari na maimata..” Tashi nai na koma kusa dashi, Har ina jiyo kamshin turaren Alharamein din dake jikin sa, Na lumshe idanu na bude su ahankali, “Ina...... Ammi?” Da sauri na juya ina kallon sa, Shin da gaske shine ya furta kalmar Ammi ko kuwa gizo nake. Ya sake maimatawa yana huramin idanu, “Tana nan... Dazu ma na fita n...” “Kikaje ina bada izini na ba...?” “Wajen Ammi naje na gaidata...” “Okayy.... Idan kika sake zuwa... Ki gaysheta, Ina gaysheta sosai. Kinji please.” “Insha Allah...!. Amma w..” “Uhm! Menene..? Kiyi magana.. Ask your questions please.” “Yaushe aka shiga tsakanin ku da Ammi..?” Ajiyar zuciya ya sauke yana mai matse yatsun sa, “Na manta wasu abubuwan.. Amma dai nasan na shaku da Ammi sosai, Duk kuwa da akwai kunyar dan fari da take mun.. Akwai shakuwa sosai a tsakanin mu. Tunda na tafi school har na gama na dora da msc dina babu ranar da bama vid call da Ammi. Bayan na dawo ma an fara shirye shiryen nada ni sarki a sashen ta na tare ina kwana, Kullum sai nayi kuka Saboda banason sarauta, Saboda banida Shekaru da yawa, Sannan banwani taba rike mukami na mulki ba, And again rayuwata a waje nayi ta. Banason shiga mutane sosai inada social phobia.. So bazan iya tuna komai ba, Nasan dai ranar wata jumu’ah na shiga gaysheta tana vid call da Khaleel., “Immediate brother na Khal.. Dr ne yana South Korea, Toh lokacin an kai su can cuz shida abdulqadeer acan sukai high school ma suka samu admission na medical school. Shi abdulqadeer pharmacist ne, Shi kuma Khal medical Doctor ne. So tana vid call dashi. Tacemin na karba mu gaysa.. Idan na gama na kira principal din su Abdullah mu gaysa da Abdullah, Saboda yana Kuka wai gida yakeson tahowa, Nide nasan na karbi wayar hannunta na fito waje don muyi magana da Khal.. Daganan bazan iya tuna ko munyi magana dashi ba, Ko na kira Abdullah din.. Wani yanayi na tsinci kai na a d’aki. Na samu jiri da zazzabi. Tunda ganan tamkar an shafemun tunanin Ammi da Abdullah da Khal.. Bansake sanin inda suke ba. Kinga wayar nan? Kusan kullum da sai na kalleta naita k’ok’arin tuno mema zanyi da ita? Sena fasa kawai.. Sai kwanan nan da hankali na ya dawo.. Na gano ashe wayan Ammi ne.. please ga wayar ki bata...” Tausayin su ya kamani sosai. Allah sarki rayuwa, Lalle Idan kana raye zakaga abunda yafi k’arfin tunanin ka. To menene alfanun shiga tsakanin uwa da ‘yayanta..? Ahankali na mika hannu na karbi wayar daya mikomin, Fara sol da ita. Shiru naga yayi kansa a sama ya dafe goshin sa da hannun sa na dama. “To kasan tsakanin ka dasu wambai kuwa.. Zaman mutinci kuke?” “Well.. Tun farko dama nasan basa so na. Suna mun zagwan kasa, Domin kiri kiri suke nuna jin haushin sarautar da aka bani. Saboda kowannen su ya cancanci ya gada.. Nasan maybe Gwaggo tabaki labari ko?” “Eh tayagamun komai...” “Wambai, Chiroma, Galadima.. Da yan tagwagar su duk nasan basa so na. Kuma harda sa hannun su a komai..” “Su Mama Huwaila fa?” “Suma duk nasan akwai wani abu a kasa.. Look Khadija.. gaba d’aya masarautar nan kowannen su da irin muguntar sa. So Karki yadda da kowa. Harda ni.” Na tabe baki. A zucia ta nace, To ai ba zama na zo yi ba dama. Ina ruwana da kai. “Waziri fa..” Shiru yai na tsawon lokaci kafin ya amsa ni. “Banajin wazirii yana mun komai..” “Meyasa kace haka? Saboda ya nuna yanason ka a fili? ..” “No waziri gaskia baida matsala...Amma meyasa kika tambaye ni?” “Kawai naga yadda yake nuna maka kauna akwai lauje cikin nadi..” “Meyasa kikace haka....Uhm?” “Bayan kwana biyu da tafiyar ka... Na ganshi ya shisshiga sashen su Mama Huwaila.. Ni kuma alokacin ina zagaye ne ko zan ga wani abun suspicious.” Ajiyar zuciya naga ya sauke.. Ahankali ya dora hannun sa kan nawa, Ya juyar da hannun izuwa tafin hannu na, yatsantsa yasa tamkar yana rubutu akan paper. Ya shiga rubutu ahankali.. Tsigar jiki na sai tashi take, Ahankali ya shiga rubuta kowane harafi d’aya bayan d’aya. Yana rubutawa yana kallo na. “Good work yar jarida... Tabbas waziri ba masoyi na bane.” Da sauri na daga idanu na na kalle shi, Cikin tsantsar mamaki nace, “Kasani kaima..?” Da sauri ya lumshe idanun sa ya bud’e alamun Eh.. Na sauke ajiyar zuciya ina taune kasan lebe na nima. “Kiba Ammi wayarta.. Na cire wancan sim din nasa wani. Ki briefing dinta akan komai dan Allah.” “Okay...” Mik’ewa nai kawai zan tafi ya riko hannu na, Ban aune ba naji ya janyo ni na fada jikin sa, Ya rike ni sosai yadda bazan iya kwacewa ba, Saitin kunnena ya dora bakin sa.. “Khadijaaaaaaaa.” Har ga Allah Salman na neman susuta ni, Na had’iye kakkauran abunda ya tsayamun a wuya. “Ina zakije...Uhm” Na shiga raba idanuwa ina matse hijabi na tamau. “Please ki yafemun... Nan kusa komai zai daidaita a tsakanin mu.” Ganin zai susuta ni ban shirya ba na mike da sauri, Na tabe baki hade da matsawa nesa dashi, “Kamar yadda kace.... Na temake ka na bi diddigin makiyan ka bayan tafiyar ka. Nima ina rokon kayimun wata alfarma d’aya.” Zubamin idanu yai yana kallo na. Na samu kai na da mika hannu na zare glass din fuskar sa, Subahanallahi! Allah yayi halitta. Kwayar idanun sa kadai ma abar kallo ce. Na shagala wajen binsa da kallo, “Shine alfarmar? Ciremun glasses?” Zanyi magana kenan aka fara doko k’ofar sa. Na manta fa akwai shaheedah, Kodan ni ba wani rayuwar aure muke dashi ba sam mancewa nake. Da sauri na mike, Tashi yai ahankali yaja hannu na. Dakin kusada corridor ya bu’de muka shiga still yana rike da hannu na, “Bara mu gama magana da ita ko... Ki jira ni.” “Dan Allah bacci nake ji fa... Allah na fara bacci ka tashe ni dazu.” Bugowa take sosai, Ahankali ya saki hannu na yanamun wani irin kallo. “Ki jira ni nace..” Ficewa yai da sauri, Matsoraci kawai. Salman na futa ya budewa shaheeda kofa yana dafe da kansa, “Subhan’Allah...! Babe! Bakada Lapia ne? Meya faru.” “Kai na ne... “ Sai sharaf ya zube akan kujera yana numfarfashi, Shaheeda jiki na bari ta matsa kusa dashi tana kallon sa, A hankali ta zura hannunta acikin d’ankwalin kanta ta zaro wani garin magani. “Salman... Babe..! Kayi baccci?” Ganin yayi bacci dagske ta dakko maganin jikin ta na bari, Ta zazzaga a hanyar da zai taka ya shiga master bedroom dinsa anan parlorn. Ya bude idanu ahankali yana kallon ta. Tana dawowa ya sauke numfashi yana gyara kwanciyar sa, “Ka tashi ..?” “Na tashi.. Zazzabin ya sauka. Nagode sosai.” “Godiar me fa? Ko ka ganni inata kallon ka?” “Noooo! Da kika tsaya har na tashi a bacci.” “Ohh.. anything for my love. Ka tashi kaje Kayi bacci a daki.” “Zanyi sallah tukun, Sai na kwanta.” “Karka kwanta a parlor, Saboda windows sunyi yawa iska, Karkai mura. Pls ka koma daki ka kwanta.” “Insha Allah a daki zan kwana.” “Okay.. Goodnight my love.” Daga kai yayi, Ta mike ahankali ta sakar masa kiss a Kan sa. Murmushi kawai yayi mata. Amma zuciar shi nata mamakin ta, Wannan wacce irin cuta ce? Dama a cctv yaga sanda aka Kawo mata wasu kullin ledoji kenan duk na tsibbu ne kuma akan sa? Yayi mamakinta Kwarai, Shi yasa yayi alamun rashin Lapia Saboda ta aiwatar da komai agaban sa. Luckily ba dakin da Khadija take ba tasa, Khadija na dakin corridor. Ahankali ya mike ya shiga dakin da Khadija take. Inata jiran sa har na fara bacci akan sofa, Dakyar na iya bude idanu na jin anbude kofa, Na mike da sauri ina sosa kai na, “Tatafi ai ko? Zan tafi nima please.” “Ai bamu gama magana ba....” Tunawa nai da tabbas ban nemi alfarmar da nace zan roke shi ba, “Yauwa...” Komawa nai na zauna, Shi kuma ya janyo kujerar mudubi ya zauna akai.. “Kamar yadda ka nemi alfarma awaje na.. Dama alkawari nima na dauka wa zuciata, Idan har komai ya daidaita.. Zan rokeka ka bani...” Shiru Salman yai yana kallo na, Sai kikkifta idanu yake.. “Zan baki me? Fadi komeye shi.” “Zaka bani takarda ta.. Saboda inason naje nayi wani auren na fa....” Ban karasa ba ya mike yana kallo na, “Khadija.... Why.... ? Mena miki uhm? Dan Allah Kiyi hak’uri lokaci kawai na ce ki bani komai zai zama tarihi.. Amma saki fa..? Saki? B. Bazan iya ba gaskia.” “Saboda me bazeyiwu ba? Idan ba zaka iya ba ni Zan dakko biron da paper na tayaka rubutawa. Look! Bafa auren nagani inaso mukayi ba.” Jikin sa har ya fara rawa, Naja sirirn tsaki, wasu mazan mugayen yan yaudara ne. Dazu fa najiyoshi a parlor sunyi luf Shi da matarsa, amman dan bakin munafurci ni zai fara yiwa rawar jiki yanzu? Ban aune ba na jiyo ya kamo hannu na, Ya zaunar dani kusa dashi, “Wa yagaya miki ba auren na gani inaso mukai ba?” “Koma shi akai ai ni banga ni naso ba..So please a rabu ta ruwan sanyi.” Salman yai murmushin gefen baki yana matse kansa. Ganin kamar yanayin sa na juyewa na tambayeshi, “Meyafaru..?” “Jiri nake ji.. Tsoro nake ji..” “Tsoran me..?” Beyi magana ba, Ya ri’ko hannu na yana nunamin wani abu kamar kasa tundaga Karshen carpet zuwa kofar dakin sa na biyu. “What about it...” “Shaheedah ce.” “Bangane ba.” “Shaheeda ce ta Zuba, Ta duaka bacci ake.” Na yamutsa fuska, Ina karewa wajen kallo, can na shiga store na dakko abun kwashe shara na jona na shiga cire su. Salman ganin bata gane komai akai ba, Sai ya sake langabar da kai.. Shi a Lalle baida lapia, “Tsoro nake ji... Tamkar ana kiran sunana.” “To ya kakeso na maka yanzu? Ni wallahi bacci nake ji.” “Ki kwana anan.” Na zare idanu ina jujjuya kai.. “Bana iya bacci sai akan gadona..” “Yauwa.. Muje canma kawai Saboda tsoran nan nake.” Badan baida Lapia ba dana dankara masa Allah ya isa. Nayi gaba abuna. Ina ganin Sanda ya mike shima ya biyo bayana, Ta kofar sirri muka shiga sashe na. Ina zuwa Na fada band’aki nayo wanka da alwala. Kan gado na haye bayan nai Addua. Sam banmasan inda Salman yake ba ko yana kasa ko Sama. Shi kuwa Salman ya jima a bakin kofa, Ahankali ya turo kofar ya shiga, ganin ta yayi tayi dai dai akan gado tana bacci. Gashi sam dije bata iya kwanciya ba. Wata wawiyar kwanciya tai rigar baccin ta dage har Kan kirjinta ana ganowa. Salman yai murmushi yana tuno dazu, Ahankali ya karasa ya janye duvet din data rufe k’afarta, “Dazu aka hanani gani.. Gasu a arha..” Ya jima yana kalle dije daga sama har kasa. Ya zare glasses din idanun sa akan bedsite drawer ya ya tottofa addu’oi, kafin ya rungumeta tsam a jikin sa tamkar Za’a kwaceta.. Cikin bacci Khadija taji an kwakwumeta ba shiri tashiga janye shi tana mita, “Meye haka... Dan Allah matsa.” “Tsoro... Tsoro nake ji.” Ahankali yake magana yana huramin iskar bakin sa a kunne na. Bacci ne akai na, Don haka naja tsaki kawai na cigaba da bacci na ina kananun mita, Kyakkyawar runguma yai mata yana shafa tundaga gadon bayanta zuwa kwantaccen gashin ta... “I like everything about you... My very own wifey. Ina kaunar baby love. Nasan ba lalle ki gane yanzu ba. Amma nanda lokaci kalilan komai zai warware.” Yana magana yana shinshina bayan kunnenta, strawberry Shower gel din datai wanka dashi yayi masa dadi. Cikin wawiyar kwanciyar datake sai gata ta juyo da fuskar ta, kanta a kirjin sa, hannunta d’aya akan cikin sa. Kafarta akan tasa. Da alama ta duaka bargo ne. Murmushi yai, Ya shiga kare mata kallo, Ya taba nan ya taba can. Daga karshe Ya janyo bargo ya rufe su. Bacci daddada yai awun gaba dashi shima. _Asubah tagari.. Salmanul_Dijaaa❤️❤️_ Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️ BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻 PG:17 BOOK:2 *Da* asubah naji tamkar abu na mun yawo acikin jiki na, Firgigit na mike ina addua, Mezan gani? Hannuwan Salman ne dumu dumu acikin jiki na, Bansan sanda na furta sarata ta kauyen mu ba. “Kutumelesin kan babban balain durumin durbun... Meye haka..?” Ahankali ya bude idanun sa, Dak’yar ya mike yana nonnokewa, Can ya shiga sosa keyar sa yana murmushi, “Kin tashi lapia....?” “A’ah ba lapia ba. Ya ma za’ai ka wani tambaye ni ko na tashi lapia?” Mik’ewa yai baice komi ba ya shige bandaki, Nasa hannuna akai na saki karar takaici. Ina jiyo sautin dariyar sa. Wani tunani nayi nai sauri na kalli jiki na, Komai yana nan, Sede kayana gaba d’aya sun tukwikwiye, “Shikenan ya kallemin jiki na a arha.” Fitowa yayi, Da alama wanka yayi , Towel dina na wankin kai naga yana goge nasa kan yana murmushi. Muka ha’da idanu na zabga masa harara. Nemen hijabi nake da zan kare jiki na, Can na hango shi akan kujera. “Dan mikomin hijabi na gashi can....” Ba musu ya dakko yana sake yin wani Murmushin,Rankwafowa yayi har muna jiyo numfashin juna, “zawjat sabah alkhayr...” Ya fada yana gyaramun gashi na daya zubo ta fuska ta. Na lura yana son gashi a rayuwar sa, Ai kuwa yaga idi dan shaheeda batada shi ni kuma ba zama nazo yi ba. “Baki iya gaisuwa bane...?” “Ina kwana?” Na fada ina tabe baki na.. “'Ana bikhayrin. 'anti?” Yau yan larabcin ne suka tashi kenan.. Na matsa ahankali ina zura hijabi na, Na mike na shiga bandaki, Wankan nima nayo, Nayi alwala. Na cire kayan baccin na wulla acikin washing machine, Zura kai na nayi ta kofa ina kallon sa yana gyara zaman praying mat.. “Kaga...” Juyowa yai, Na nuna masa drawer da yatsana “Dan Allah dan jehomin riga aciki..” Mik’ewa yai ya bude yana kallon su, Ina ganin sanda ya dakko wata me shara shara, “Ba ita ba..” “To zoki duaka da kan ki.” “Yi hak’uri kadan ban me kauri.” Me shara sharan ya dakko ya mikomin, Hannun sa da nawa suka gogi na juna, Na runtse idanu na, Da sauri na karba na koma ciki na zura na dora hijabi akai. Gaban drawer na matsa na dakko zani na dora akai. Sallah yajamu muka sallame atare. Ya daga hannu yana addua muka shafa atare. Azkhar na koma gefe ina yi, Ina jiyo sautin nasa shima yana yi. Muka kammala a tare. Can karshen gado na koma zan kwanta ya kirawo ni.. “Zo nan..” “Bacci nake ji..” “Zo nan mu gama magana se Kiyi.” “Gani..” Na koma nesa dashi na zauna, “Magana zamuyi dake da sauri... Saboda zan shiga fada, Zan koma bangare na da wuri.” “Ai inde maganan jia ne nagama magana, Inason kabani takarda na.” “Khadijaaaaa! Meyasa kike haka wai?” Shiru nayi Saboda wani kwarjini daya mun. Ahankali ya matso kusa dani, Ya dora hannun sa kan nawa yana murzawa ahankali, “Nasan bakyaso na.... Kuma sigar da nabiyo ta neman auren ki sam ban kyauta ba. Ki yarda dani, Tun sanda na fara dora idanu na akan ki naji ina son ki, Zan iya ce miki banta’ba yiwa kowa irin kallon dana miki ba arayuwa ta, Love at first sight Khadijaa. I love you and your bravery.. So please ki sassauta mun hukuncin saki yayi tsauri, Zan dauki komi banda shi.. Anything for you! Uhibbuk kathirana ya Zawjati atika aleaziza..” Shiru nayi kawai, Na ma rasa me zance wallahi, Can ta matse masa da son, Na bi son da gudu na kwarfe. “Kayi hak’uri.. Amma inada wanda... Muka gama alk.” “Karki karasa dan Allah..! Wallahi wallahi k’aunar ki ta gama yawo acikin bargon jiki na. Khadijaa ban san so ba sai akan ki.. Nagaya miki tsoron taron mutane nake, Ko a gidah ki tambayi Ammi rarely ki ganni muna hira dasu Abdullah. Bana magana da yawa, Banmasan ya ake nake kwarara miki magana ba. Ki bani chance, Zan nuna miki yadda ake..” “Duk naji..Amma ni kam Kayi hak’uri banda ra’ayin zama a masarautar nan.” “Inde shine matsalan se na miki gida awani unguwan...” “No... Bana ra’ayin zama da ka....” Ban aune ba kawai naji ya dora tattausan leben sa kan nawa, Hannun sa d’aya yasa ya janyo ni na fada kirjin sa dake tashin k’amshi, Wani irin sumba ya shiga yimin wadda gaba d’aya ilahirin jiki na yai sanyi, Duk wata masifa danake shirin surfa masa sena nemeta na rasa, ya zare bakin sa ahankali yana kallona, “Naji bakya so na.... Na kuma yadda nine me lefi. Amma please ki bari komai ya wuce, Na samu lapia tukun. Karki bari Ammi tagano cewar bakya sona, Zeyi breaking heart dinta... Amma ki rike wannan.. Ni Salman ina miki kauna marar gauraye, Bazan dena kaunar ki ba, Khadijaaa! You are an amazing person, I am glad that I found you. Without you, I don’t know how my world would be. You have totally transformed me. I would love to spend all my life with you. I love you soo much..” Na juyar da kaina gefe saboda yadda yake shafa mun gashi wani yarrr nake ji. K’ok’ari kawai nake ina mazewa, Mik’ewa yai ahankali yana kallon agogon hannun sa, “Zan tafi na shirya.” “Allah ya tsare.” “Ameen Zawjati...! I love you..” Futa yai yana murmushi, Ni kuma na koma gan gado Ina mai shafa labba na, Wannan gigitattan kiss sekace a film. Inata tunanin yadda Zan karbi takarda ta bacci yai awun gaba dani... Shi kuwa Salman yana fita ya jingina da k’ofar dakin yana murmushi, Ai dai anyi me wuyar ya aureta, So shawo kanta ta zauna tare dashi bazai wahala ba. A haka ya koma sashen sa, Falaki ya shiga tayashi shiryawa zuwa fada... Ruwan tea kawai yasha sai cake guda d’aya.. *SASHEN GIMBIYA JALEELAH...* Gaba dayan su su ukun suna hakimce a kujeru, Gimbiya Huwaila ta kishingid’e a doguwar kujera mai cin mutum uku, Najwa kuma ta yi wani zama itama na sarauta ta dora kafafunta akan tum-tum. Jaleelah kuma tana hakimce itama akan kujera ana mata kitso, Mai kitson na tsaye a haka take mata.. Hannu tasa tana tattaba kitson, “Meye hakan? Sam bai kamu ba, Kalli wannan yayi gefe da yawa. Kunce duka nan bangaren ki sake wasu..” Takarasa tana jan tsaki.. Jikin me kitson sai ‘bari yake yi.. Haka ta shiga kunce shi tana sake wani. “Ni kuwa akwai cigaba a turaren da muka yayyafa a sashen Salman na kwanaki dinnan? Sam banji ance ya kwanta ciwo ba.” Gimbiya Huwaila ta tambaya tana mai cigaba da danna wayar dake hannun ta.. “Gaskia dai kwanakin nan inata tunanin abun.. Ni fa har jakadiya na bigi ciki ta nuna ba abunda ya faru dashi. Kenan malamin nan ninke mu yai kome?” Najwa ta bawa Huwaila amsa. “Anya kuwa..? Domin aikin na kan dutse akwai ci, Sai dai idan shaheeda ce ta batamana shirin..” Cewar Jaleelah.. Gimbiya Huwaila taja dogon tsaki kafin tace, “Ko d’aya makirar ba... Ummiyo (Hadimarta) Tacemin sau uku tana cin karo da Ita Zata shiga sashen sa’adatuh.. Y’ar wahala.” “Y’ar wahalar gaske.. Ai kinji da aka turawa Salman list din kayan bikin su Munaya bece komai ba, Wambai yace a wajen yace ayi transferring kudin.” “Yo me zece Jaleelah? Ai sullutu daban yake. Kadan ma yagani.. Ni yanzu jira nake kawai asa yayi murabus, Abdulqadeer ya hau karagar mulki.. Koya kukace?” Cewar Huwaila. “Kibari kawai... Ai ranar da sai na zuba ruwa a kasa na sha.. Allah de ya kaimu, Kuma yakamata mu sake komawa kauyen nan. Domin naga alamun yarinyar nan da ya auro tsageriya ce, Duba fa kiga aikin sa akai akanta amma tamkar ba’ayi, Sai wani daga kai take..” Najwa ta k’arasa fada tana karkada kafadu.. “Rabu da ita... Yadda tazo haka zata tafi.. Bara na koma sashe na.. Zanga likita saboda kai ya matsamin.” Hajia Huwaila ta k’arasa fada tana gyara zaman laffayar jikin ta.. “Okay Yaya... Allah kara lapia.” Cewar Jaleelah “Okay! Sai kin dawo. Allah bada lapia.” Najwa ta fad’a tana murmushi. Bayan fucewar Gimbiya Huwaila, Su Najwa suka tasa fefenta a gaba, “Munafuka... Babu fa inda zata je. Shirin su suke itada abdulqadeer.” Cewar gimbiya Najwa tafada tana tabe fuska, “Hmm ki bari kawai Hajjaju.. Ai nasan karya take yi, Yo wannan matar kanta kawai tasani. Danta ya kwaci gado ta fantama ita kadai. Mu zuba mugani.” Haka suka yita gulmar gimbiya Huwaila, Suna mata zagon k’asa, Bayan ta tafi ba jimawa, Gimbiya Najwa tayiwa Jaleelah sallama itama tatafi.. Tana futa itama Jaleela tafara yi da ita, Ita dai mai kitso sai raba idanu take, ‘Yayan iska.. Wai ku masu ‘yaya maza ko? To ku zuba idanu kugani babu wacce ‘danta zai karbi ragamar mulkin basannabas.....” *GIMBIYAA KHADIJAA* Sashen Ammi na nufa bayan na tashi daga bacci, Acan naci abincin safe. Lokaci zuwa lokaci mukan taba hira da ita. Abdullah na gefe yana scrolling sunayen universities da zai zaba. Can ya mike ya haye sama. Wayar dake gefen aljihun rigata samfarin A line na zaro na rissina na mika mata.. “Ammi... Gashi Inji Salman yace yana gaydaki.. Kuma yana kewar ki sosai, Nan da lokaci kalilan zai zo wajen ki ya gayshe ki. Amma kafin sannan Wai ya canza miki sabon sim zakuyi magana ta ciki.” Idanuwan Ammi suka kawo ruwa, Hannunta na rawa ta karba tana jujjuya wayar, Da alamun ta tuno wayar da kuma abunda yafaru ranar. “Yace bayason asan komai ya daidaita yanzu sai nan gaba zai bayyana komai idan ya gama binciken da yake.” Sam Ammi batai magana ba sakamakon hawayen da take faman zubarwa, daga karshe ya zama kuka Sosa wanda ya saukar mata da mura. Mun jima a haka tana kukan farin ciki kafin tace dani, “Nagode Khadija.. Mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Tabbas samun ki a sirika alkhairi ne, kin zamar mana wani haske na warwarar matsalolin mu. Allah ya biyaki da gidan aljanna Khadijaa. Nagode Nagode Nagode.“ Ahankali nace “Aamin..” Ban wani jima ba na mike na mata sallama Zan tafi, Har na kai bakin kofa tace mun, “Amma fa se kina dan takura masa akan abinci... Baya son cin abinci shi yasa ulcer tai masa mugun kamu...” “Insha Allah Ammi zan dinga yi.” Na sake mata sallama sannan na fice na koma sashe na ina kambama dattako irin nata. Allah sarki uwa da ‘da.. No wonder bana ganin yanacin abinci ko an kai masa, Ko yaushe yana fama da ciwon ciki.. Girgiza kai nayi na koma cikin sashe na. Kan gado na haye kawai, Sallah ce ke tadani na kuma sake kwanciya. Banda juyi babu abinda nake yi akan gadon, Gaba d’aya tunanin dazu da asubah na shiga yi, Na sauke ajiyar zuciya, Can na rufe idanu na na kara lulawa duniyar tunani a haka bacci yai awun gaba dani.. Nide Ranar haka nayi bacci rabi da rabi, Da safe na shiga sashen Salman nan sarkin dogarai yake cemun sarki baya nan yayi tafiyar gaggawa tun jia da yamma, Banma sani ba. *WASHE—GARI* A hankali na bude idanuna, kawai naga mutum a tsaye ya kura min ido ko kiftawa bayayi. Nai saurin tashi zaune Ina kara bude ido, Sanye yake cikin jallabiya ruwan zuma, tayi masa masifar kyau. Bai ce min komai ba sai guri da ya samu ya zaune a gefen gado yana kuma bina da kallo ta cikin glasses din fuskarsa. “Good morning... Bar..barka da dawowa.” Yaki amsawa sai cewa yai dani. “Any news?” Kamar ban fahimci abinda yake nufi ba, na sosa cikin idona Ina cewa. “Na me fa?” Ya juya yana kallon kan bedside drawer din dake kusa dashi, yasa hannu ya dauki jotter da biron da ya gani akai. Cikin sauri na yunkara zan kwace yasa daya hannun nasa tare da kamoni yana min kallon kurullah, na gane hakan ne ganin yadda ya janyo fuskata kusa da tashi. “Ni ka bani abu na.” “Baki aikin da na baki bako?” Yayi maganar yana kokarin bude jotter din, still kuma yaki sakar min jiki na. Haushi ya sake kamani da sauri na fincike dan naga alamar idan bana yi da gaske zai Iya cin galaba a kaina, bayan kuma babu soyayyarsa ko kwayar zarra a cikin zuciya ta. Ina yi masa abubuwa ne kawai saboda alkawarin Gwaggo ta Fada dana karba na bada gudin mawa wajan ceto rayuwar su ba dan nafi kowa ba sai dai sunan da nake takawa a gareshi shine zai ba da damar isar da wani tallafin gare shi. A hankali ya dinga bin bayanan da na dinga dauka kadan kadan na fara bincike akai, hakan ne ya shagalar dashi be sake bi ta kaina ba. Na zabga masa harara cikin zafin zuciya na tashi na nufi bathroom ina jin takaicin ganin yadda baya damuwa da tawa matsalar sai tashi. Ina shiga nasa key dan kar ma ina wanka ya biyo ni, nai kwanciya ta a cikin bathtub saboda na dad'e nasan idan ya gaji da jira na dole ya tashi ya tafi. Shi kuwa Salman yana zaune yana duba jotter din amman ya kasa gane abin da take nufi, sai ta fara tubutu tiyan-tiryan sai yaga ta goce ta rubuta wasu arbitration yadda ita kadai zata gane abin ta. Jin shiru bata fito ba gashi lokaci yana ta tafiya kuma zai je fada yasa shi tashi bayan ya bar mata dan note. Sai da na tabbatar ya fita sannan nai wanka nayo alwala na fito, ina goge jikina da towel na hango pepper din akan gado na dauka tare da karantawa. “Anjima ina nemanki 9:00pm.” Tab'e baki nayi tare da yaga takardar na dauke jotter din naje na boye sannan na fara shirya kai na. Ina gamawa na sakko kasa na nufi kitchen inda ma'aikata na suke ta faman aiki cikin tsari da nutsuwa, duk suka gaishe ni na amsa musu cike da fara'a sannan duk suka fita, daman yawanci haka suke yi duk lokacin da na shigo kitchen din sai su koma waje saboda na fi son na samawa kai na abinda zanci saboda tsaro ba dan tsoro ba. Dan waken flour nayi sai green tea dana dafa ina gamawa na zuba nayo parlour hankali na kwance. Sai da na gama ci sannan na tashi na sake komawa bedroom na kuma yin nazarin da nake yi, daga karshe kuma na fito dan zuwa sashen Ammi. Ina baro gate dina na hadu da su Wambai suna tafiya bayin su na take musu baya, nai kamar ban gansu ba saboda tun lokacin da naga sun shiga gurin su Gimbiya Najwah tare da basu wasu layoyi na tsane su, shakku ya shiga tsakani na dasu. Ina gaf da wucewa naji suna miko min gaisuwa wacce nasan ta munafinci ce, basa gashe dani sai sunga idanun jama'a da yawa saboda sun tsane ni. “Ranki ya dade za a dan zaga masarauta ne?” Sai na samu kai na da jin izza lokaci guda, hakan kuma ya bani damar buga musu tambayar da ta kusa dabar-barta su. “Eh zan dan zagaya. Ku kunje gano iyali, ya aka baro su?” “Wa? Mu wai ranki ya dad'e? A a wallahi can wajan sarkin dawakai mukaje mun tarar dokuna biyu sun mutu.” “Ayya Allah ya tsare gaba, mai martaba ya sani kuwa?” Na tambaya cikin son Jin karin bayani dan Ina da yakinin ba zasu sanar mai ba idan ban sako musu zancen ba. “Ah'ah'ah ai yanzu abin ya auku muka je, idan ya fito fada zamu sanar dashi.” “Allah ya taimaka ya kara lafiya Baba Wambai da Baba Chiroma ko?” Nai alamar tambaya Dan na sake tabbatar da su waye. “A'a Wambai ne da Galadima ba Chiroma bane.” Cewar Wambai yana ta faman murmushin yake, mukai sallama suka wuce nima na tafi wajan Ammie. Su kuma suna yin nisa Galadima ya saki tsaki tare da gyara rawaninsa yace da Wambai. “Banji dadi ba da ka tabbatar mata da cewa ni ne, naso ka barta a sunan ni Chiroma ne. Shegiyar yarinya ka bibiya bokayenta ba a kasar nan suke ba, dubi yadda muke b'arin kudi akan ta amman kamar muna yi akan iska haka aikin yake wucewa ba tare da komai ya same ta ba. Duk duniya a yanzu babu wacce na tsana sama da yarinyar can wallahi.” “Rabu da ita ai idan tasan wata to bata San wata ba, zamu yi maganinta tun kafin wadanda zai auro su shigo. Karka ga yadda Humaira take masifar son Salmanu, amman shi be ma san tana yi ba taki ta bayyana masa saboda gudin wulakancinsa.” “Kuma haka ne fa Wambai, wallahi idan muka samu yaran nan suka shiga daga ciki, ba wannan yarinyar ba kadai ba, hatta Shaheedah sai ta dawo karkashin mu.” “Uhmmm-uhmmm Galadima, gwara dai mu dinga rage kiyayyar mu akan Shaheedah, kasan dai mahaifinta shi da kansa yake yiwa kansa duk wani tsibace-tsibbace a masarautarsa ta Bullo. Idan muka shiga gonarsu tabbas zamu Iya rasa mukaman mu ba mutunci ne dashi ba kasani. Gwara dai mu tsaya Iya Salmanun da ita wannan talakan takalak din matar da ya kwaso.” Galadima ya jinjina kai da haka har suka karasa runfar da sauran yan majalisar suke suna jiran fitowar sarki Salman dan su karasa cikin fada. Ni kuwa ina zuwa sashen Ammi na tarar da wasu matasan yan mata, ban gane su sam dan babu wacce na taba gani a cikin su. Na yi sallama duk suka juyo suna kallo na amman babu wacce ta amsa min sallama ta sai Ammi wacce ke zaune tayi kasa da kanta da alama ba mutanan kirki bane ba. Har na karasa kusa da Ammi babu wace tai min magana bare gaisuwa, hakan ya kuma girmama hasashena akan sanin su waye. Muka gaisa da Ammi cikin mutunci sai dai da ka ganta kasan ba ta cikin walwala. “Baki kika yi ne Ammi?” Kafin ta bani amsa naji muryar daya daga cikin yan matan tana cewa. “Mu ya kamata mu tambaye ta bakuwa ce ke ko kuwa, dan bamu sanki ba a cikin masarautar Bassannabas.” Murmushi na yi cikin rai na ina cewa kila jinin masarautar ne, dan naga Isa da kasaitar ta yi yawa. Amman dai ban ce komai ba saboda a gaban Ammi ne da na gaya musu abinda zai hana su yin walwala a yau. “Munaya kuyi shiru dan Allah, wannan ko babu komai Yaya ce a gurin ku tunda matar shi ce.” Da sauri suka hada baki wajan furta. “Wa...!?” Nai saurin basu amsa dan naga Ammie tana jin nauyin furta sunan shi nace dasu cikin gadara. “SAS, idan kuma baku gane ba ina nufin Sarki Salman Aliyu Salman. Nasan yanzu kun fahimce ni tsab. Kuma zaku gane ni kodan gaba.” Duk sai suka bi juna da ido suna bude baki, na saki murmushi ganin yadda suke mamaki dan bamu taba haduwa dasu ba, basu sanni ba nima ban San su ba sai iyayen su kawai. Na dakko jarkar ruwan da na gani kusa da Ammi na bude tare da zuba mata cikin cup na mika mata ina cewa. “Ammi sha ruwa ki kwanta, naga kamar har da bacci a idanunki.” Naji dadi da bata musa min ba, ta karba Tasha na janyo mata pillow tasa kai tana lumshe idanuwa. Nai saurin mai da kallo na gurin su ina kare musu kallo, daga masu riga da wando sun dora wata munafukar after dress, sai masu dogayen riguna da suka bayyana surorin jikin su, na ce. “Amman dai baki ne ku ko?” “Ke dalla can bama san bariki kinji, mu zaki rainawa hankali dan kina matar juya da bai Iya ajiye magajinsa ba kamar yadda aka ajiye shi. Kin ganmu nan ko? Kakaf din mu jinin sarauta ne, jinin da yake yawo a mahudanar mijin naki, shine muma yake yawo a jikin mu, Kinga har gobe zamu Iya samun sarautar nan da yake kai.” Na saki murmushi Ammi dai ba ta sake cewa komai ba dan taga nima dai-dai nake dasu, kuma Ina Iya yina wajan ganin ban furta abin da zai sa ta yi mamaki na ba sai dai su nayi su dinga jin kamar zasu tsire ni. Ganin naki magana yasa Baheeya yin magana, gata yar karama amman rashin kunya a bakinta kamar me, tace min. “Kin yi shiru ko babu amsa?” Ina shafa fuska nace. “Bani da time din magana daku yanzu, amman zaku Iya zuwa ku bincika wacece ni ta yadda ba zan dinga baku wahala ba wajan jiran amsoshin tambayoyin ku.” Carab Nadiya ta cabe zance. “Kema kin zata yana haibuwa ne kika aure shi? Aunty Shaheedah fa har yanzu ta kasa haihuwa saboda ance shi bashi da lafiyar da zai haihu.” Wannan karan mamaki ne ya cika ni, na kalleta ganin ta yar firit da ita amman wai har ta Iya yanko wadannan manyan zantukan. Na rike baki tare da kallonta nace. “Ke yarinyar nan har kin fara zancen wanda yake haihuwa da wanda bayayi? A bakin wa kika ji cewar baya haihuwar?” Ta murguda baki tana fari da idanuwa irin na rashin kunyar nan, su kuma sai faman jinjina mata suke yi. Sabeera ta mike tana dariya tana tafa hannaye tace. “Toh karya tayi ne? Da yana haihuwa kila da yanzu Aunty Shaheedah tana da yaranta. Amman da yake juya ne kinji shi shiru, dama suma ba ta hanyar Allah aka samar da s.....” Ban san lokacin da na tashi naje na shako wuyan ta ba, duk suka taso suma zasu shigar mata nai saurin juyowa Ina musu wani irin kallo mai cike da fita hayyaci, duk sai suka tsaya suna huci kamar wasu zaku na nace. “Duk iskancin da zaku yi karku sake ku iskanta min miji, idan kuma ba haka ba zaku yi yin nadama marasa tarbiya kawai. Kuma ku tashi ku fita tunda ba sashen iyayen ku bane.” Na sakar mata wuya na tsaya kuma Ina jiran su fita dan idan suka tsaya komai zai iya faruwa tsakanina dasu. Don basu sanni bane, Oganniya nake ta Gajiyalle mai yar hakiya.. Dijangala yar baffanta. Aikuwa suka fice suna ta zage-zage, naja tsaki tare da komawa na zauna raina a mugun bace. Ammi ta dinga lallashi na tana cewa na dena biye musu idan ba haka ba abubuwa zasu kara baci tsakanin mu da iyayen su. Da kyar na samu na iya hakura saboda taji dadi, amman a zuciya ta na kuduri aniyar sai na gyara musu zama a cikin masarautar nan, Bayan mun dan yi hira ne na tashi na koma sashe na..... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥. _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _A dear page goes to a dearest one.. Dear billyn Abdul... May you be forever blessed😍❤️kaunar kauna tawaje na.. 🧚🏻‍♂️_ _PG:18_ _BOOK:2_ *GIM. KHADIJAA* *Ina* shiga sashe na zauna a parlorn kasa ina kallon tv dake yi ita kadai. Can na canza channel din zuwa iqraa inda suke karatun alqur’ani. Takwas dai dai, Saura awa d’aya naje wajen Salman. Nagaji saboda da yar tazara tsakanin sashen da nake zuwa na Ammi. Kitchen na shiga na samu Na’imah amintacciyar hadimata da Gwaggo ta fada ta samamin. Na sata ta matsemun ruwan dankalin turawa guda d’aya, Na hada da ruwan lemon tsami d’aya shima. Zama nai a kitchen din na shafe fuskata dashi da kuma hannu na. Bazan manta ba Adda Maryama ce tabani sirrin yana gyaran fata sosai. Minti goma sha biyar yai na wanke da ruwa mai dumi, Sannan nayi wankan turare (bath khumrah) Banyi wata kwalliya ba, Na dai canza kaya na zuwa doguwar riga ja mai dogon hannu, Na yafa mayafin akai na, Turaruka masu sanyin kamshi na shashshafa: Shekha/Night oud/Danal banat) Na dan shafa man lebe kadan a baki na. Zama nai ina jiran lokaci ya cika, Yana cika na mike na shiga hannu na d’aya rike da jotter da na rubuta komai. Bakina dauke da sallama na shiga. Yana zaune akan dinning table hannu biyu ya dafe kumatunsa, Dagowa yai yana kallo na, Nai saurin saukar da kai na kasa. “Barka da dare....” “Barkan mu....Zawjati!” “Ga ni..” “Bismillah... Zo ki zauna.” Mik’ewa yai ya janyo kujerar kusa dashi yana nuna min, Zama nai ina cije kasan lebe na, Saboda ciwon mara nakeyi nasan nan Kusa mai jar mota zai zo. “Ina jinki... Naga kinyi abbreviating wasu words din.” Bude jotter din nayi, Ina nuna masa daga inda nake zaune, Mikewa yai ahankali ya zagayo ta wajena, Ya saqalo wuyan sa saitin fuska ta. Cikin wata irin murya ya nuna wasu kalmomi, “Wadan nan fa...?” Na shiga raba idanuwa, Na kasa magana “Uhm....Me suke nufi....? Khadijaaaa” Ajiyar zuciya na sauke, Turaren jikin sa sai sani cikin wani yanayi yake. Ahankali cikin dauriya nace, “ NSMHSHDSWDYAKGTB na nufin: Nace su Mama Huwaila sun hadu dasu waziri da yamma a kofar gabas ta bayi.” “Nan fa..... Uh hummm.?” Ya furta Uhum din cikin kunne na, Ba shiri na mike ina sosa kai na, “Zan tafi..” “Ina zaki tafi?” Ya tambaya yana daria wato yana sane kenan yasan abunda ya aikata. “Zan koma inada abun yi..” “Ai nan dinma ba shirme kike ba, Assignment na baki kike presentation.” “To naji.. Amma ka koma wajen ka ka zauna.. I..I..Idan aka tsaya akai na jiri nake.” “Tsayawa nai akan ki...? Na dauka na dan rissina ko? Zo mu sake gwadawa.” “Nooo.. dan Allah ka bari.” “Toh naji zo ki zauna..” Zama nayi, Meyakwan ya zauna awajen sa, Sai ya janyo kujerar ya sake matsowa gab dani, Kafafun mu na gogar na juna. “Ina jinki...” Bayani na shiga yi masa muryata sai rawa take, Shi kuma ya zuba tagumi yana kallo na kawai, Har wani lumshe idanu yake ya bude su akai na, “Na gama...” “Bravo alaiki Zawjatiii...” Mik’ewa nai zan tafi ya riko hannu na, “K’amshi kike yi...Me tafiyar da tunani na.” Kwace hannu na na shiga yi ahankali ya mike shima ya janyo ni jikin sa, Na shiga janye jiki na ina tirjewa.. “Dan Allah ka bari...” “Zawjatuk aleaziza .. rayihatuk jamila.. Kinsan me nace..uhm?” Yana magana yana neman cire dankwalin kai na, Na zame hannun sa dak’yar ina hade rai, “Nace.. Dear wife! You smell nice.” Shiru nai kawai nide ina sauraron sa, Ya hanani tafiya gashi duk na karar da k’arfi na. “Khadijaaa... Dan Allah kiyi hak’uri.. Ki dena fushi dani. Kinji? Love.. pls.” Yau da ace wanda nakeso ne kalaman nan suke fita daga bakin sa da nafu kowacce mace jin dadi. Amma kash, Sam bana jin sa a rai na. “Zan tafi.. Bacci nake ji.” “Shikenan.. Sai da safe.” Har na kai bakin kofa na juya tunawa da maganar Ammi.. “Kaci abinci kuwa..?” Da sauri ya girgiza kansa alamar a’ah. “Meyasa baka cin abinci ne? kamar wani k’aramin yaro.” Murmushi kawai yayi yana kallo na, “Yanzu me kakeson ci?A dama maka oat? Ko porridge? Ko akwai abunda kakeso?” Gyada kai yayi, Na zauna akan hannun kujera ina binsa da kallo, “Me kakeso to...?” “Ke... Ke nakeso Khadija.. You are all I want.” Kikkifta idanu na shiga yi, Gashi a haka sam ba zaka ce daga bakinsa maganganun nan suke fita ba. Hade rai na d’anyi Ina matsa yatsun hannu na, “Abinci nake magana.” “Nima shi nake fada ai... Ko baki gane magana na ba.” Mik’ewa nai kawai na shiga kitchen, Babu abunda babu, Don haka na hada masa shayi me kauri na kawo masa, Na koma na jima ina aiki kafin na fito da dankalin turawa da kwai sai yar sauce ta kaza. “Gashi nan bismillah fara ci. Ammi ta damu sosai, Dan Allah ka dinga cin abinci. Kaji?” “Ni ban iya zama na ci abinci da kai na bane...” Na gwalalo idanu tunawa da shi din sarki ne sai kuma na mayar da idanun ina tabe baki, “Saka suke agaba kaci...? Fadawan naka?” Murmushi yai kawai yana langabar da kai kamar wani karamin yaro... “Ki bani da kan ki... Saboda Idan kika tashi ma ba iya ci zanyi ba kasa Zan sauka abuna kawai.” “Kai da cikin naka..?” Ya gyad’a Kai yana ko’karin tashi, Nai saurin komawa gaban sa ina masa Kallon sama da kasa, “Toh Ai kuwa dole ka koya cin abinci, Katoto da kai kamar wani baby..” “To ai babyn ki ne... “ Nide shiru nayi, Naje wajen sink na wanke hannaye na tas, Sannan na dawo na tsugunna agaban sa, “Toh sakko..” Sakkowa yai kamar wani yaro yana tankwashe kafafu yadda nayi, “Bude bakin.... Haaaaa” Budewa yai ahankali, Na debo dankalin na hada da sauce na cusa masa a bakin, Yana ci yana yanga a haka na gama bashi, Ina hada masa da tea. Lomar karshe ma haka na sa masa abaki ya rike hannun, Yatsuna dana debo dankalin suna cikin bakin sa, “Sakarmun yatsuna mana...” Meyakwan ya sakar mun seya shiga lashe su ahankali, Sekace hannu na ne dankalin. Kamar hannun sa haka ya sude su tas yana murmushi. Zanyi magana ya rigani, “Sunnah ne lashe yatsu idan an gama cinye abinci.” Ji wani renin hankali wanda ba’atabamun shi ba ko a durbun. “To ai ba hannun ka bane na wane..” “Kai da kaya ai mallakar wuya ne. Abincin nan yayi dadi. Gobe ma shi zaki mun.” Wani kallo nayi masa na debe kwanukan na kai kitchen. Tashi yai shima ya nufi sink yana kuskure bakin sa da mouthwash. Salman ba dai tsafta ba. Komai nashi tsatsaf. “To ni zan tafi s.....” Ban karasa ba, Sakamakon bugun kofar sashen sa da aka shiga yi, Hayaniyar su Mama Huwaila ne, Tamkar zasu fasa kofar, Ina jiyo dogarai na basu hak’uri amma sunki denawa. Wani madanni ya danna naga kofar kasan ta bude, Ta window na hango su da yawa sun shigo ciki suna hayaniya. Nasan dai akan dazu ne, Don haka ko ajiki na, Na samu kujera na zauna ina karkada kafafu, “Wannan hayaniyar tawa ce... Babu ruwanka, Ni da su Munaya ne, Naga zasu tabo ka da Ammi shine fa nima na nuna musu ba tsoro ne dani ba, Na shake wuyan sabeera take ko sabeena...” Zare idanu yayi, Na sheke da dariya kawai ina jujjuya agogon hannu na, “Sun kai ni karshe ne.. Oganniya nake ta Gajiyalle mai yar hakiya... Sanyi nayi wallahi.” Zai yi magana kenan suka banko kofar, Tuni ya sauya fuskar sa izuwa dolo yana jujjuya idanu, “Mama barkan ku da dare.” “Dallah gafaracan... Sullutu kawai, k’aramar Yarinya ta tsare ka agaba tana maka dabaru. Dazu dazun nan ta shake wa yaran nan wuya, Ta musu dukan kawo wuka, Kalli jini a dantsen Munaya, Saboda tsabar mugunta taga saura sati d’aya bikinta.” Kasa jure jin Sharrin su nayi, Na mike ina tafa hannaye, “Kai Mama H.. Yo badan kin kusa jika dani ba ai da nace Allah ya sakamun.” “Kai Kai Kai Kai... Ke Kinsan wa kike gayawa haka kuwa?” Cewar Munaya. “Dakata ke kuma can daya ... Mama Huwaila ce, Kina wani tashin jijiyoyin wuya ai nasan ba ita ta haife ki ba, ki bari sabeera ‘yarta tayi magana.” “Ke ni kike gayawa magana..?” “Ah haba Mama H.. Ni na isa.. Ko sunan ki bakiga na kasa karasa fada ba? Gani nayi duk garin nan waye baisan mai girma chiroma ba, tsatson sarki ismaila rabo, wato jika na farko ga masekiri tajiri.. Allah dai ya Kara miki lapia.” Ina kallon sanda tayi murmushi tana jin dadi, Kunsan yan sarauta da son girma da kasaita. Ta kasa cewa komai. Gimbiya jaleela taja tsaki tana karasowa kusa dani, “Akan me... Zaki daga hannun ki ki dora akan fatar yaran nan.. Shin wacece ke? Me kike ji dashi?” “Haba Mama Jaleelah! Banji dadi ba da kika d’auki wasan mu dasu gaske. Ya za’ai na sa hannu na dake su? Kinji Allah wallahi bandaki kowacce ba. Idan Karya nake dan Allah su rantse da qur’ani gashi nan. Allah ya kara miki lapia, Ai ko dan darajar waziri ba na soma haka ba.” Shiru Gim. Jaleelah tayi tana kallon su Munaya, Su kuma na tabbatar saboda nace su rantse da qur’ani ne shysa sukai shiru. Kafin Gimbiya Najwa tayi magana na rigata, “Ranki ya dade barka da dare...Tabbas sai yau na ga ainihin kamar ku da mai girma galadima, Kada na cika ku da surutu, Nadiya yarki naga batada hayaniya ko ita Zata fa’di yadda komai ya kasance. Kuma da zasu fadi gaskia ma.. Su suka takalo komai, Suna cewa ai shaheeda kaza kaza. Gasu idan nayi karya. Amma nasan basu fada muku dai dai bane da da girman ku ba zaku taho nan da daren nan ba, Domin bantaba ganin hakan tafaru ba. Ni zuwa nayi naga jikin sa, Domin kusan kwana nawa ance bayacin abinci, Kuma yana surutai da daddare, Shine nazo yaketa kira na da shaheeda, Tashin da zanyi na tafi kenan kuka shigo.” Sai kuma suka shiga kallon kallo, A kunyace kowacce ta kwashi jikin ta suka fara fita, “Munaya... Karki manta a aikomin da kati da dan yawa pls inada gayya.” Harara ta dankaramin ta fice, Na zube akan kujera ina kwasar dariya. “Nice moves....Zawjati!” “Moves ai sai kai... Lalle ka iya acting. “ “Mugayen mutane ne.. Sai kana takatsantsan, Ka samu ka gama komai naka ahankali. Bara na gaya miki komai nasu a takaice.” Ahankali kuma a nutse ya shiga gayamun irin wahalhalun da yasha a hannun su, Da yadda ya maida kansa soko saboda samawa kansa da mahaifiyar sa lapia. Ajiyar zuciya na sauke bayan ya gama gayamun nace, “Gaskia na yadda ba Allah a aran su. Domin kaga wahalar danasha kuwa nima? Suka sakarmun da jini na dauka na al’adah ne, Suka sani firgici da daddare na kasa bacci, Ga tsoron masarautar dana dinga yi, Har wani wari Suka sa nake ji ni kadai.. Wasu abubuwan ma na manta, Amma kam nasha wahala.” “Kiyi hak’uri please.. Insha Allah da komai ya wuce zamu ji dad’in rayuwar mu.” “Kayi hak’uri... Amman gaskia banda ra’ayin zama acikin masarautar nan...” Zeyi magana na sake katse shi, “Banda ra’ayin zama da kai... Da masarautar. Dan Allah ka sawwakemun na tafi. Dan Allah” “Khadijaaa... Kin dauka na aure ki ne kawai saboda ki kawo karshen matsalolin mu? Wait duk abunnan haka kika dauka ko? Shin me kikeso nayi na ki tabbatar kaunar ki ce tasa na aure ki..? Should I beg on my knees? Wait dole nema.” Banyi aune ba naga ya zuba gwiwoyin sa ak’asa yana kallo na, Hannun sa yasa ya riko nawa hannayen yana mun wani kallo dana kasa fassara shi, “Zawjati aleazizat , 'uhibukkthyraan. wana tazawajtuk lanani ahbabtuk kathira. wala 'astatie takhayul hayaati bidunik fiha... Yes dear wife, Ina kaunar ki.. Sannan na aure ki saboda ina sonki, Rayuwa ta zata zama wata iri idan babu ke cikin ta... Khadijaaa ki bani dama na nuna miki kaunar da nake miki.” Gaba d’aya kalaman sa sai suka shiga rudamun ciki ma, Da alamun sun wa kwakwalwata yawa, Ga kwadan salad danaci da alama ya fara aiki shima, Wata gudawa ta matso ni, Ciki na ya shiga kokarin bada iska, Mik’ewa nai zan gudu ya riko hannu na, Lalle gayen nan besan mayuwacin halin da nake ciki bane. “Kin yadda...? Kin yadda zaki zauna da ni?” Kai na shiga juyawa alamun a’ah, Don ko awani hali nake ciki banajin Zan yadda. “Tohm shikenan bazan takura ki ba... Amma ki shirya zuwa na gobe, Zan zo mu fara magana ta hankali dake. Zanzo as Salman ba sarki Salman ba. Ina neman yarjewar ki... Kin yadda?” Yadda ciki na ya murda yasa nai hanzarin daga kai alamun na yadda yazo. Da sauri na yakice hannun sa na fice da sauri, Ina tunanin inde yana sauraran tafiya ta, To na tabbata ya jiyo bada iskar dana dinga yi, Idanuwa na a rufe haka na karasa sashe na, Na shige bandaki da sauri. GIM. SHAHEEDAH! Yawo ta shiga yi da waya a kunnenta tana karkada hannu, “No hajjaju, Da sauri nakeso, Hajjaju idan ba’a hanzarta ba to zamana a masarautar nan yazo karshe, Domin asiri na dole ya tonu hajjaju. Na yadda dagske auratayya bata taba shiga tsakanin su ba, Amma yanzu fa? Kina tunanin zatai ta zama ne batare da ta bukace shi ba, Shima duk da juya masa tunanin da ake ai dole wani lokacin ya kasa control. Hajjaju I take God beg you.. A shafe gaban ta gaba d’aya, Koda yaje kawai ya nemi hanyar ya rasa, Ashafe gaban uhm uhm Khadija.. Pls. I hate her, I can’t stand her hajjaju. Auren yarinyar nan da zamanta a masarautar nan wallahi har yau nakasa cikakken bacci. Wani irin shegen boka ta samu da alama, Ana aiki aiki bayayi.. Hajjaju hak’uri na ya kare gaskia. Kinsan muddin auratayya ta shiga tsakanin su, Idan aka samu ciki Shikenan hajjaju komai zai bayyana, Bani ba.. Har ku seta shafe ku. Kowa ma in general... .” Magana take cikin fada da sauri, Gaba d’aya tamkar bata hayyacinta, Tanayi tana daga hannu, “Nooo Hajjaju... Idan har baze iya shafe gabanta ba, Idan ya isa cikakken boka ya hallakata kawai. Naji zanyi duk abunda yace, Ya rabata da iska yafi komai sauki.” Tana gamawa tai culli da wayar tana sakin kara, Hade da jijjiga diddigaggen gashin kanta da tsabar tashin hankali ta manta da gyaran sa. *Salman* dake dakin sirrin sa yana kallon ta ya tsaya da biro a bakin sa, Baya sauraron me take cewa amma ya tabbatar maganar sa da Khadija takeyi Saboda yadda yaga labbanta na furtawa, Yayi zooming dai dai bakinta yana karantar haruffan dake futa daga gare su. Juyawa yai d’ayar computer dake gaban sa yana kallon Khadija ta ciki, Ta canza kaya zuwa na bacci tana taje kwantaccen gashin kanta na fulanin usul. Lumshe idanu yai ya bude su akanta, Abubuwa da yawa yake ayyanawa akanta.. Gashi tak’i bashi hadin kai, Tabbas daga gareta ne komai zai warware, Amma yaga ta kasa yadda dashi, Ajiyar zuciya ya sauke yana kamo lebensa na kasa yana tsotsa a hankali. Abubuwa gaba d’aya sun taru sun masa yawa, Amma yadda Khadija taki yarda dashi ne yafi daga masa hankali, Gaba d’aya daren nan kafin ya kwanta bacci, Tunanin kalaman da zai kwarara mata gobe ya shiga nazari, Ciki harda taimakon Internet. ______ ...Wai cakwakiya, Tawan ta abdul yau dai nima bara nayi ta taki: Man Kai na ya malale 😂💔 Sai dai nace.. Asubah tagari... Salmanul... Dija😍❤️ Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _PG:19_ _BOOK:2_ *SAS* Yau dai kam yana son jin muryar Ammi, Tunda ya bada wayar aka kai mata ya sake kiranta yana jin nauyi da kunyarta na tsawon shekarun da suka yi ba tare da sunji muryar juna ba. Sake gyara zama ya yi cike da ladabi tamkar suna kallon juna, hannunsa yana rawa ya dannan sunnan ta tare da karawa a kunnensa. Ammi kam daman tun da Dije ta bata wayar kullum tana hannunta tana jiran kiran nasa, ko toilet zata shiga sai ta tafi da ita dan karya kira bata kusa a samu matsala. Tana zaune a bedroom dinta tana cin kwadon zogale da Dije ta kawo mata, wayar na kan cinyarta kamar koda yaushe sai taji ringing. Kirjinta ya buga, ta rufe ido tare da yin hailala tayi bisimillahi tare da karawa a kunnanta. Salman naji ta dauka yaji wata irin nutsuwa ta saukar masa, duk kuwa da cewa ba tayi magana ba. “Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh Yaa Ammi.” Wasu hawaye masu dumi suka sakko mata kan fuskarta, da kyar saboda farin ciki ta Iya bude baki ta amsawa d'an nata cikin rawar murya. “Wa'alaikas Salam mai babban suna.” “Allah sarki Ammi na baki fushi dani ba? Ki yafe min Ammi dan Allah karki fushi da ni ban san abin da ya hau kai na ba naji sam bana tunaninki. Kaddara ce ta hau kai na wacce ban san yadda zan yi ba a baya, amman a yanzu ina fatan na fuskanceta sosai ta yadda zan jurewa cinye ta. Ammi dan Allah karki fushi dani wallahi ina sonki, na kuma damu dake. Da yardar Allah komai ya kusa warwarewa, mu dawo kamar da Ammi, mulki masifa ne Ammi musamman irin wannan da Allah ya dora min.” Banda kuka babu abin da Ammie keyi wanda ta rasa ko na menene, tabbas taji zuciyarta tayi sanyi ganin hankali da tunanin dan ta sun dawo cikin jikinsa. Sannan kuma zuciyarta ta karaya ganin yadda yake ta bata hakuri kai kace yana sane ne ya guje mata, wanda tasan ya yi hakan ne saboda tsantsar biyayyar da yake da ita. Haka ake son yara nagartattu su dinga kaskantar da kansu a gurin iyayen su koda kuwa a ce iyayen ne basu da gaskiya ko basu kyautata musu. Tasa hannu ta sharce hawayen da basu dena fitowa daga cikin idanunta ba, tare da jan numfashi tana murmushi tace masa. “Kafin komai sai mu fara yiwa Allah godiya, Alhamdulillah. Daga nan sai mu yiwa Gwaggo ta Fada jinjina da irin jajircewar da tayi wajan karbo mana taimakon ayoyin ubangiji. Tare da sake din bin godiya gurin Khadija da ta yadda zata taimaka mana gashi har Allah ya amince.” Lumshe ido ya yi yana ta sauraran Ammi har ta gama magana, ya sake sakin wani murmushin murya can kasa-kasa kamar baya son taji abin da zai furta yace. “Ammi kinji dadin auran Khadija da nayi?” Shi kansa Salman da ya yi maganar be zaci Ammi taji ba, sai amsar ta kawai yaji cikin walwala tana cewa. “Sosai ma kuwa mai babban suna, naji dadi fiye da tunaninka domin Khadija tayi min abinda ba kowa ne ya yi min ba.” “Ina son ta Ammi....” Salman ya fada cikin rashin sanin cewa a fili ya yi furucin, Ammi tai dariya cike da jin dadin ganin danta ya samu abinda yake so. Kuma dama Khadija abar so ce tana da kyawawan hali da girmama na gaba da ita. Abu daya ta sani gurin Khadija shine bata san rai ni ko ya yake, dan sometimes takan jiyo yar dabi tsakanin ta da Abdullah, idan kuma a gabanta ne ba ta biye masa sai dai ya karaci shirmen shi ya yi shiru. “Ammi babu wata damuwar ko?” Ammi tayi shiru tana son tace masa sauran Khaleel, amman ta kasa. Shi kuma abinda yasa be gaya mata sun hada dashi ba, so yake yai surprising din ta yadda farin ciki zai fi bayyana a gare ta. Can ta numfasa cike da kulawa tare da ajiye ragowar tunaninta a gefe dan karta samishi damuwa shima tace. “Babu wata damuwa sai farin ciki mai babban suna. Allah ya yi muku jagora a duk lamarin Ku, ya tsare min ku a duk inda kuka sa kafa. A dena mantawa da adkhar, addu'o'in fita daga gida dana shiga harma da na bandaki duk da nasan kana da juriya wajan aiwatarwa, wannan kawai tunatarwa ne nayi maka.” “Insha Allahu Ammi, na gode Allah ya bar mana ke cikin koshin lafiya.” Amsawa tai daga nan suka ajiye kowanne yana jin farin ciki marar misaltuwa. Ammi kuwa harda sujud tana yiwa Allah godiya tare da kirari na girmamawa. *FADA* Bayan tashin su daga fada, Manyan yan majalisar sarki suka nemi izinin kara ganawa da sarki Salman. Bai musa ba ya basu dama yana mai duba agogon hannun sa, Domin so yake ya je wajen Khadija.. “Ranka ya da’de... Su wambai ke son magana da kai...” Cewar waziri yana rissina kai.. “Okay waziri... A basu dama. Amma me ke tafi dasu?” Waziri ya langab’ar da kai yana hada hannuwa, “Kabar mugun mutum ranka ya dade, Su kadai suka san kutingwilar da suke hadawa.” Ajiyar zuciya Salman ya sauke yana daga masa hannu aalamun ya bashi dama ya shigo dasu, Waziri ya leka ya shigo dasu, Kowanne yaci magani yana bubbudawa, “Ran sarki ya dade.... Takawar ka lapia bahon sarki, Baka ajiye ba, Baka ba kowa ajiya ba.” Cewar Galadima yana daria. “Ita haihuwa ai ta Allah galadima..” Cewar waziri ransa a bace. “Waziri kenan.. Tukuf tukuf da kai kamar na Allah, Kai ko kunya baka ji? Yiwa wanda kai jika dashi biyayya?” “Toh menene inde shugabane? Ai durkusawa wada ba gajiya wa bane..” “Kaga galadima rabu da wannan.. Muyi abunda ya kawo mu.” Shi dai Salman kallon su kawai yake, Gashi lamarin waziri sake bashi tsoro yake, Yana tare dashi shekara da shekaru amma yanacin dunduniyar sa? Ashe bakin su d’aya dasu wambai? Idan yana tare dasu yayita yin abu tamkar shidin na kwarai ne? “Ranka ya dade... Kai ta kwasarrrrrr...” “Ba’kin ciki....” Cewar chiroma yana daria kasa kasa. Shida wambai suka hada hannu suka tafa. “Idan har zancen da ya kawo ku kenan.. To ina ganin tashin ku awajen nan ku fita shi yafi alkhairi.” Cewar waziri yana nuna musu kofar fita. Galadima yayi daria yana bubbuga k’afar sa ta dama, “Waziri kenan... Karka kuskura ka kaimu karshe, Domin idan ka kaimu karshe.. Yar wazintakar da kake ji da ita zamu tuge ka.. A juri zuwa rafi dai.” SAS ya dagawa Waziri hannu alamun yayi shiru, Waziri yai shiru kamar wani mutumin kwarai. Su wambai suka shiga magana da fada, Ta inda suke shiga ba tanan suke fita ba, Shi dai Salman idanu ne nasa kawai, Addua yake cikin zuciar sa kan Allah ya bashi ikon ganin bayan su, Allah ya dora shi akan su. “Saboda haka lokaci zamu baka...Nan da yan watanni biyu zuwa uku.. Ko dai ka fadi wa’enda kakeso a tsatson sarautar mu.. Ko kuma mu hadaka da duk wa’enda mukaga dama. Sannan abu na biyu, Idan dik zance biyun kayi biris dasu... Toh abdulqadeer shine zai hau karagar mulki, Kai da sarautar basannabas kuma sai dai labari, Domin bakada magaji da zakai tunanin zai gajeka nan gaba, Balantana su...” “Ba sai ka karasa bama wambai. Mutumin da bai san wayesu ba, Kai ko kasan Khaleel da Abdullah? Ya kuke dasu..?” Salman yai shiru yana jujjuya kai tamkar wani sauna, “Bangane su waye ba Baba..” “Ahap...! Ai na sani. To ko su din da baka tuna su Waye ba, Suma ba zasu gaji mulkin kaba atoh..” “Yauwa galadima... Sai magana ta gaba. Zancen bikin yaran nan.. Kudin daka bayar basu isaba Salman, Ka karo biyun su, Domin biki za’ai na kece raini, Kaga bikin masarautar kalwa da akai yafi namu, Idan bamuyi wanda yafi nasu ba zamu sha daria ne a idanun masarautun kasanmu, Ina fatan ka fahimta?!” Salman ya daga kansa alamun Eh. Can ahankali yace, “Waziri... Kayi musu transfer din kudin account din nan na wajen ka baki d’aya.” Waziri jiki na rawa ya tsugunna yana rawar baki, “Ranka ya dade.. Du? Du? Du fa kace? Wannan uban makudan kudin Za’a bayar suyi hidimar miki biki dashi? Haba ranka ya dade.. Tuba nake.. Amma dan Allah ka sake shawara.” “No... issokay waziri. Baba zasu isa ko?” “Zasu isa tunda naji yaron ka (waziri) yana kambama yawan su.” Tashi sukai suka tafi.. Suna sake jadda da masa kudirin su da suka yanke. Parlorn ya rage daga shi sai waziri bayan futar su, Waziri ya rarrafa ya rissina, “Allah ya kara maka lapia... Bazeyiwu ka janye maganar makudan kudin nan ba..?” “Bakomai waziri... Ka basu. Allah zai kawo wasu.” Ajiyar zuciya waziri ya sauke yana kada kansa, “Samun adalin sarki mai tausayi da hak’uri irin ka sai an tona.. Ran sarki ya dade..Ina fatan mafarkin nan da kakeyi yayi sauki ko..?” “No waziri... Abu sai dada gaba yake yi. Dak’yar na fito fada ma... Naga wani garin magani daka ban kwanaki na hayak’i dinnan..? Nayi naji mafarkin matar duk na dena..” Waziri ya dashe baki yana shafa rawanin sa, “Haka mukeso.. Mugayen mutane ne suke bibiyar ka ta mafarki.. Kuma da yardar Allah karshen su tazo, Zan sake karb’o maka wasu, Zaka dena mafarkan baki d’aya. Yanzu ga wani ma ka sashi a karkashin pillown ka, Ka kwanta kai da mafarkan nan sai dai ka bani labari kawai..” “Godia nake waziri.. Tabbas ka rike ni tamkar kai ka haife ni.. Ka tsaya tsayin daka akan makiyana, Waziri na gode sosai, Ka zamo min katanga mahallar makiya, Banda bakin godia s....” Bai karasa ba waziri ya rissina hannu bi biyu, “Ranka ya dade Ka dena godia dan Allah..Bazan taba cin amanar sarki Aliyu ba, Domin shi ya bani amanar Ka, Hannu da hannu ya riko ni a asibiti yana kan gadon rasuwar sa, Sunan kane abakin sa yana dankamin amana..” SAS yai murmushi kawai yana jin k’arairakin waziri, “Ni zan koma ciki... Bana jin da’din jiki na.” Mik’ewa waziri yai, Bayan ya rissina masa , Ya kira dogaran sarki suka kare shi ya mike, Suka rakashi har sashen sa suna masa kirari. Yana shiga ya shige daki, Ya sakarwa kansa ruwa a shower. Yai flushing maganin waziri a masai, Yana fitowa ya canza kaya zuwa wata arniyar shadda ya dora alkyabba akai, Ya taje kanannadadden gashin sa kwantacce sannan ya dora hula akai, Ya shafa turaruka masu sanyin kamshi, Sannan ya zauna akan kujera yana nazari.. Tashi ya yi kai tsaye ya nufi sashen Khadija, lokacin da ya shigo ni kuma dawowata daga gurin Ammi kike nan ina cire alyabbar jikina ya shigo. “Daga gurin Ammi ko?” Ya tambaye ni yana kasa da idanuwasa. Kai kurum na iya dagawa naje na mayar da rigar inda sauran suke, ji kawai nai yace. “Kina san Ammi na da yawa ko?” Har cikin zuciya ta naso bashi amsa saboda banga amfanin yin karya ko neman gurin zama ba, ina ci gaba da gyaran wardrobe d'in saboda idan ba hakan nayi ba ban san me zan yi a dakin ba nace. “Ammi uwace a gare ni, ban taso tare da mahaifiyata ba, shi yasa nake jinta tamkar itace ta haifeni. Bani da wata da zan kalla na nuna ta matsayin uwa sai yanzu da na samu Ammi. Amman uba kam har yanzu Ina dashi, duk da cewar bana manta wanda ya haifeni koda da second daya.” Salman ya jijiga kai tare da karasowa ciki dan da a kofar ya tsaya be shigo ba. Ganin yana nufowa inda nake ne yasa nai saurin birkito da alkyabban cikin wardrobe d'in, na durkusa da sauri dan na kwashe. Shima sai ya karaso tare da dukawa yana taya ni, daman kuma rike ni ne bana son ya yi dan ya saba duk sanda muka hadu ya wani rungume ni. Murya a sanyaye yana daukar riga daya ya gyara ninkinta yace. “Ni ne kawai ban miki ba ko?” Nayi shiru dan bana son furta komai a gurin saboda rashin kyan furucin. Amman ni ba yimin ne beba no, zuciya tace har yanzu ta kasa karbarsa a matsayin abokin rayuwa ta. Na kasa mantawa da Mas'oud da irin soyayyar mu har ma da yadda muka shirya rayuwar mu. Da ace zuciya ta zata amince da Salman da zan zauna dashi na so shi kamar yadda yake gaya min irin wanda yake min. Toh taki yarda da duk wani furucinsa, ta kasa goge tarayyarta da abinda ba muharraminta bane a yanzu, tana son Mas'oud har yanzu kamar tai hauka. “Toh ko tsufa nai miki ne?” Na girgiza kai, taya zance ya yi min tsufa bayan shima din har yanzu matashi ne? “Okay saboda na aure ki ba tare da na fara tuntub'arki ba?” Sake girgiza masa kai nayi tare da cewa. “Ko kadan daga cikin abubuwan da ka lissafa, kawai dai zuciya ta har yanzu tana gurin wanda ya koyar da ita menene SO.” Zuciyar Salman ta harba da karfi. Da ace Khadija tasan yadda yaji da ba zata sake gaya masa cewar zuciyarta tana son waninsa ba harma ta kasa mantawa da wancen d'in bare ta karbe shi. Cikin dauriya irin tashi ya mike yaje ya saka mata rigar cikin wardrobe dai-dai lokacin da nima na tashi zan saka wacce na ninke muka bugi goshi, nasa hannu da sauri ina shafa gurin nawa, ya yi saurin riko ni cike da kulawa yana mulmula min gurin. “Sorry my dear.” Ya fada yana shirin kwantar da kai na saman kirjinsa, amman na hana hakan faruwa saboda ni bana son kusancin mu dashi yana yawa. Baya san bata mata rai saboda nemarwa kansa masauki a zuciyarta, hakan yasa sakar mata jikin ta ya koma yana ci gaba da ninke kayan. “Naga anata shirin biki ke banji kinzo kin karbi komai daga guri na ba. Shaheedah ta karbi kudi tace zatai kayan fitar biki da kuma gudin mawar da zata bayar, kefa.?” Cikin tab'e baki ina yatsina fuska, nifa wallahi da zama tare dashi gwara min zama a durbun wajan Gajiyalle tayi ta bani wahala saboda rashin son da nake yi masa. Na mike tsaye Ina cewa. “Ai ita matarka ce shi yasa ta nemi abu a gurinka.” “Toh ke d'in meye a gurina?” Bance komai ba har muka kammala gyara wardrobe din na tsaya na rasa me zanyi ya dauke min hankali daga kanshi. “Kin abinci kuwa?” “Eh a gurin Ammi.” “Alhamdulillah naji dadi, yanzu me kike bukata nayi miki?” “Ka bani shaidar rabuwar mu da kai shine nake bukata a gurin ka.” Rintsa ido ya yi ya rasa ya zai yi da ni na dena furta masa wannan kalmar dan baya son jin ta. Ya mike tsaye tare da gyara alkyabbarsa yana murmushi wanda na rasa ko na menene yace. “Zan baki hakkinki kema kamar yadda na bawa Shaheedah. Amman dan Allah ki dena min maganar saki domin Allah ma baya son kalmar. Ina sonki my yar jarida.” Daga haka ya shafa fuskata ya juya ya koma sashen shi ya barni Ina karewa bayansa kallo. A raina Ina tunanin anya yana da zuciya kuwa? Taya nace bazan zauna dashi ba amman sai ya zauna dani dan dole, ni wallahi bazan yadda dashi ba Sai ya barni na koma inda nake so dan banga dalilin zama dani ba. Na ciro dankwali na tare da karkade turaran jikinsa da ya barmin a dakin kai kace zai koru saboda haushin Salman din da nake ji. Ganin bani da mafita yasa na haye kan gado ina hawayen bakin ciki. GIM. SHAHEEDAH! Gaba d’aya ta susuce da yin abubuwan da boka ya bata na tsibbance tsibbance, Cikin kwanakin har rama tayi. Ta kira hadimarta batula tana ta zagaye cikin dakin a birki ce, “Ranki ya dade gani...” “Duba kiga kafa ta dauke a sashen? Kizo ki sanarmun yanzu, Ki tafi da fatanya ki b’oye awani wajen kinji?” “Toh ranki ya dade...” Hadimarta na fita ta janyo wata qullin leda da kwado aciki marar rai an daure bakin sa da laya an nannade ta, Ta shiga tuntsura dariya tana babbakata, “Khadija... Kinyi gangancin shigowa gonata.. Wacece ke da har zaki tunanin jerawa da ni?.” Hadimarta ta kwankwasa mata kofa, Jiki na rawa ta fita sanye cikin hijabi da nikabi ba zaka taba kawowa ita bace. Sashen Khadija suka nufa, Babu kowa na masu tsaran gate da alamun hadin baki ne. Wurin shuka suka je, Anan hadimarta ta tona rami, Ita kuma shaheeda ta zura kwadon da layar, Suka binne shi acikin ramun suka barbada kasa akai.. Suna gamawa shaheedah ta koma sashen ta cikin sauri, Wani garin magani ta dakko, Ta cire kayan jikin ta tana hayaki dashi. Kaurin marar dadi sai tari take.. “Daga rana irinta yau.. Jin dadin ki cikin masarautar nan ya kare Khadija.. Ke da duk wani mai goyan bayan ki ma tasa tazo karshe. Mu zuba mu gani..” Haka taita fada tana tari saboda tsabar hayakin maganin yayi yawa. *SAS* Ya qudiri niyar kyautata mata saboda soyayyar da yake yi mata, zai jure duk wani bakin cikin da zata cusa masa indai zata zauna tare da shi har ta haifa masa yara yan albarka. Bashi da buri da dabara ko hange a yanzu sai na son yadda zai sa Khadija taji dadin rayuwarta, amman wace hanya zai bi har ya cimma manufarsa ta son kasancewa da ita a matsayin mata da miji? Tabbas Khadija qaddararsa ce a cikin qaddarorin rayuwarsa, be tab'a jin wata ya mace tace bata son sa sai akan ta. Shin me yasa take iya kallonsa harta furta masa cewa bata son shi ba ta son zama tare dashi? (Mas'oud ne zabin ta Salman, kasan shi? Kasan yadda suka tsara rayuwar su? You knw nothing Salman shi yasa kake sake shan wahala wajan son sanin meye dalilinta)😉 Tashi ya yi daga kwancen da yake ya nufi bathroom, wanka ya yo yazo ya shirya kansa cikin kananun kaya saboda zuciyarsa taba gaya masa cewar kila dan tana ganinsa cikin rawani da manyan kaya ko sleeping dress shi yasa take ganin tamkar tafi karfin shi. Sosai ya tsuke cikin jan jeans da farar t-shirt, gaban rigar anyi rubutu baki da d'igon ja-ja-jajaja ansa BE MY LOVE. Gyara gashin kansa yayi ya koma balaraben sa sosai, daga nan ya dauki turaruka ya fesa tare da dakko pcap dinsa itama ja ya dora akansa. A gaban madubi ya tsaya yana karewa kansa kallo, shi kansa a cikin zuciyarsa sai da ya yiwa Allah godiya, daman haka yake, ko ya yaga Allah ya yi masa abu sai ya gode masa a cikin ransa. Ya jiya tare da daukar wayarsa ya nufi sashen Khadijan, wace ke zaune a kan stool tana waya sai dariya take yi cike da nishad'i, alamar babu wata matsala ko damuwa da take damunta. Har ya samu guri ya zauna bata kallesa ba dan ta hangoshi ta cikin madubi, sai da ta mulu sannan tace. “Shikenan sister Maryama zamu yi waya mu karasa maganar tamu... Okay tom shikenan ki gaida min Gwaggon mu.” Ajiye wayar nayi akan madubi still ina ta dariya kafin na juyo kamar ban ganshi ba nace. “Au.. Ashe ka shigo?” Zare pcap d'in ya yi tare da ajiyewa akan cinyarsa. Gaskiya banda zuciya sakarya ce da kuma kitsawa mutum karya da gaibu, banga abin ki a gurin Salman ba. Amman da yake bana son nashi sai ban wani ji komai ba naci gaba da sabgar gabana, Ina jin lokacin da ya saki ajiyar zuciya ya taso tare da dawowa kusa dani ya tsugunna yana kamo hannuwana ya kura musu ido. “Madam ya kike?” Na kawar da kai gefe daga kallon sumarsa dake kyalli da tashin kamshi. Ban kula shi ba sai hannuna da nake ta kokarin ganin na kwace amma yaki sakar min, har sai da ya dago kansa ya kalleni yaga ina faman tsuke fuska sannan ya sakar min hannun kamar yana jin tsoro na. Tashi ya yi Ya fito ni ban biyo shi ba ashe kasa ya sauka duk hadimaina suka fice ya tsaya a kitchen yana kare masa kallo, can dai ya bude fridge shima ya kare masa kallo ya rasa me ma ya kawo shi kitchen d'in. Google ya shiga shi a dole sai ya yi mata wani abun burgewa wanda zai faranta mata rai. Pepper soup d'in kaza ya gani cikin sauri ya nemo recipe ya shiga sarrafa kazar nan guda daya da ya dakko. Duk a tunani na ma ya fita har Ina cewa yau kuma turanci ake je da kananun kaya za'a fita masarauta. Tsawon lokaci ya dauka be dawo ba, fitowa ta daman daga toilet kenan na ganshi dauke da tray da bowl a saman sai turiri yake yi, ya ajiye akan madubi tare da kamo hannuna ya zaunar da ni bakin gado. Komawa ya yi ya dakko tray d'in yazo ya durkusa a gabana muka kalli juna ni dashi, Allah sarki gabaki daya ya sauke sarautar da yake da ita ya zama tamkar wani bawa na. Yana durkushin yasa spoon tare da debowa yana hura min da bakinsa sannan ya doshi baki na dashi cikin tsantsar...... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _Zafafa biyar... Yan biyar masu zazzafar basira🥰 Na gayshe ku.. Gaisuwa mai dimbin fatan alkhairi❤️❤️_ _PG:20_ _BOOK:2_ Tsantsar kulawa, mai makon na bude bakin..Sai kawai na kawar da kai gefe ina girgiza kai, kamshin duk ya cika min hanci ga baki na da yawun ya tsinke da alama so nake naci amman fadin rai da son nuna cewa be isa ba yasa naki karba. Salman ya kuma matsowa yana miko min. cikin karyar da kai kamar wani marar lafiya da yake bukatar taimako, muryar sa na sarkewa yake magana. “Ko be yi miki ba my love? Da kai na fa na dafa miki ba wani nasa ba.” “Nace maka fa naci abinci a gurin Ammi, ni ban san dalilin da yasa kaje kai wannan aikin ba salan mutane suce na shanyeka ka jazamin masifa gurin matarka.” Ganin yadda nake magana ina hade rai ne yasa shi maida cokalin cikin bowl din, nan fa hankali na ya tashi tare da tunanin kodai ya fasa bani ne dan shi mutum ne da na lura baya son bata min rai koyaya. Kokarin ajiyewa kan bedside yake yi nai saurin rike hannunsa still fuska ta a hade amman dai ba kamar da ina masa magana ba. Ya Kalle ni cikin son jin karin bayani dan shi da zuciya daya ya yi niyar ajiyewa tare da alkawarin ba zai takura mata ba akan sai taci. Na turo baki ina kifta idanuwa kamar wata marar gaskiya nace dashi. “Kace kai ka dafa?” “Kwarai kuwa ci kiji.” Ya fada yana sake debowa a cokali ya hura shi wai ya huce sannan ya miko min kusa da baki na yana cewa. “Haaaa.. Ban sa miki yaji da yawa ba, sai dai nasa albasa sosai da yar tafarnuwa saboda tana da matukar amfani a jiki.” Gyada kai nayi gashi na kagu naji an samin a baki miyau na duk ya gama tsinkewa. Budewa nayi cikin yanga kai kace son ci ne bana yi amman kuma duk salo ne na kar ya rainani. Saboda tsabar rudewa jin wani azababban dadi ban san lokacin da na karbi cokalin da hannuna ba na dinga kwasar romon ina sharba. Harga Allah koni da nake mace ban taba yin Pepper-soup d'in kaji da ya yi min dadi irin wannan ba. Shi kuwa banda kallo na babu abinda yake yi, da alama ya rasa ma me zai yi ne idan ba kallon ba. Ban ankara da santin da nake yi ba sai da na kusa cinyewa sannan na kalleshi naga yayi zaman dirshan yana ta bina da ido kamar wanda aka ce idan ya rufe zan bace daga gurin. “Ya haka?” Na tambaye shi dan jin dalilin wannan kallo. “A karo miki ne madam akwai ragowar.” Murmushi na yi ganin ya harbo jirgi na yasan cewa santi nayi, amman dan kar na nuna masa sai nace ina ci gaba da ci. “Daman ka iya girki ne?” “Gashi kinga zahiri, lallai da alama ya yi dadi gashi har kin cinye baki min tayi ba.” “Ba santi bane ba, taimaka maka nayi dan karka ce ka kawo min abu naki ci.” “Hakan ma na gode madam, ai kin taimake ni da kika ci naji dadi sosai my love.” “Nifa ba santi nayi ba, kuma abinda yasa na tambayeka Ammi ce tace min baka taba dora tukunya ba da nufin yin girki tun tasowarka. Khaleel ne ma yakan yi karan bani amman shima ba wai iyawa ya yi ba. Kuma nasan hadimai na na kasa suka yi maka shine kake cewa kai kayi dan kaga ban fita ba.” Kallo na kawai yake yi yadda yaga ina ta bayani kamar an kunna tsohuwar radio.. Babu abinda yake tunawa shi kuma sai ranan da ya fara yin tozali da ita , hakan ne yasa da yaga tayi shiru ya yi dariya yana cewa. “Yar jarida.” Ya yi maganar cikin wani salo da alama dai yadda nake maganar ya burgeshi ta yadda yake ta faman Murmushi. Nai masa shiru ni dai sai faman lasar lips nake irin na naci dadin nan, ko ganewa ya yi lashewa nake yi? Naga dai ya taso bayan ya karbi bowl din ya ajiye tare da nufowa jikina. Banyi aune ba sai ji nayi ya kwantar dani kan gadon yasa harshensa saman lips dina yana lasa, ni kuwa tsabar mamaki mutuwar zaune nayi Ina fito da kwayar ido cikin din bin mamaki. Sai da yaji baya jin testing d'in komai sannan ya bar abinda yake a lips din, ya kalleni yana kwantar min da gashin gaban goshi na. Hakika yana matukar son baiwar Allahn nan, yana junta a duk wani sashe dake cikin jikinsa. Murya a raunane yace dani. “Allah ya maki albarka.” Dadi ya kamani jin an bani naci na koshi kuma an bini da addu'a lallai wannan mutumin be dauki duniya a bakin komai ba, yadda yake tarairayata Ina jin ko Mas'oud d'in da na kwallafawa rai ba zai min haka ba, musamman yasan Ina mugun son shi. Ji nayi ya dagani tare da sanya hannu ya dagoni na zauna sosai yace. “Ki huta lafiya zanje sashe na zamu yi maganar daurin auren su Munaya dasu Abdulqadeer.” Ban samu kwarin guiwar amsa masa ba saboda al'amuran sa sun fara girgiza tunani na. Ya mike a hankali ya nufi gurin kofar da ya biyo yana kallo na kamar baya son mu rabu haka ya hakura tunda ana can ana jiransa kar su fara kwashe masa albarka da sauke mai kwadon tsinuwa dan ba kirki gare su ba..... <<<<<>>>>>>> Da daddare saina samu zuciyata da yin wani irin rauni akan yin hidimarsa gareni. Na fara wani tunanin cewa shifa sarki ne, sarkin ma wanda ake ganin girman rawaninsa sama da wasu rawaninnikan a kasar nan. Shi d'in fa jinin milki ne d'an gaske, matashin sarki maiji da kuruciya da sanin darajar lokacinsa. D'an gatan da duk kaddara ta juya masa zukatan dangi zuwa ga kiyayyarsu akan mulkin duniya. Anya kuwa zuciyata da kalmomin bakina suna mini adalci wajan yi masa furuci.? Ai koban girmamasa a matsayin miji ba ya cancanci girmamawa a matsayin na shugabana mai mulkin jahata. Ya cancanci girmamawa na matsayinsa na babba gareni a shekarun da kuma hankali. Sarki Salman bashi da wata makusa a halittar jiki data mu'amular rayuwa. Tunda nazo gidansa bai taba munani da wani furuci na baki ba balle a aikace. Ya bani jin dadin rayuwa kamar kowacce mace dake ji da kanta a gidan. Ya bani girma irin na matarsa a idanun jama'ar masarauta dama bani ragamar kula da wani sirrin rayuwarsa. Idanma ta gaskiya za'abi nice na tura rayuwarsa cikin tawa a dole ta hanyar acting da nake yi saboda matarsa. Tabbas Allah shine shaida ta, bana jin sonsa a zuciya ta. Amma kuma ban tsanesa ba. Sannan ina kawo masa maganar saki ne dan kawai na samawa kai na lafiya a wani lokacin. Sannan bazance bana son Mas'oud ba har yanzu. Sai dai sonsa ya ragu a raina sosai a yau d'in nan ba kamar sanda muna a tare ba. Bansani ba kodan bana ganinsa yanzu ne shi yasa oho.. Ko kuma saboda irin kulawar da Salman yake bani musamman ta dazu da ya shiga kitchen da kansa dan kawai ya faranta min....? Iskar da aka huramin akan idanuwa ya sakani sauke nannauyan numfashi dan ban fargaba ashe na fada duniyar tunani mai zurfi. Da wannan damar Salman yayi amfani wajen kare min kallo tun dazun. Ganin ina kara zurfi ne ya sakashi maidoni cikin hayyacina. “I love you Deejah". Ya fada a hankali gab da fuskata dan ya rankwafo kaina ne. Da sauri nayi baya da jikina ina kyakykyafta idanu zuciyata na wani irin bugawa a karo na farko. A salon da yayi maganar ne yayi matukar tada tsigar jikina. Baya na cigaba dayi yana bina har na kwanta akan gadon shima ya kwanto kaina. Idanu na zaro waje sosai zanyi magana yayi saurin dora yatsansa saman bakina yana kadamin idanunsa da suka sauya launi. Cikin sarkeni da su yace, "Ban cancanci a soni bane ma'am?Deeja menene laifin ne dan naso abinda ya dace da ni?" Da sauri na girgiza masa kaina ina kyafta idanu, dan yanda yake magana yana matukar tada min da tsigar jikina. Muryata na rawa na ce, "Ni bance bana sonka ba. Kawai dai.....” Na kasa karasawa. "Kawai dai me?" Ya tambaya yana dora hancinsa a gefen wuyana da wani shegen Salo na saukar da numfashi. Jikina ne ya fara rawa. Zan turesa ya rike min hanu yana cigaba da aika min salon dana ke ganin tsantsar mugunta ce. Bakinsa ya dora saman kunne na ya dan ciza. zabura nayi amma ya sake danneni yana kara raunana muryarsa. "Ki sanar min saboda me?". "Kafi karfi na." Na bashi amsa cikin subucewar baki. Da sauri ya dago yana kallona da idanunsa da suka sake komawa kalar tsoro. "Khadijah banfi karfinki ba, kece ma kikafi karfina ai.” Saurin girgiza kaina nayi kwalla na cika min idanu. "Mai martaba kaine kafi karfina. Kai fa sarki ne, sarkinma mai tarin abubuwan kwatance a gaban wasu sarakunan. Kai dan gatane mai tarin ilimi da nasaba. Kai jinin mulki ne dan masu mulki jikan masu mulki. Kai mai ilimi ne da tarin dukiy.......” "Shiii...." Ya fada da sauri yana kada min idanunsa. Zai yi magana nima na girgiza masa nawa kan hawayen da naketa kokorin rikewa suka zubo min a kumatu. "Ka barni na fadi abinda yake gaskiya dan Allah. Muna da banbanci sosai, kanada tarin abubuwan da suka ninka wadanda na fada a baya. Ni kuwa talakace, yar talakawa gaba da baya. Yar kauyen kayau. Bawani tarin ilimi ne da ni ba. Ba wata nasabar kwatance ce da ni ba. Bani da wani abunda tarihi zai nuna matsayin dangantaka ta. Tayaya kake tunanin zaman aure zai kasance a tsakanina da kai? Hakan tamkar tauyewa kanka da martabarka kayi a matsayinka na sarki. Sarkinma da ko a gaban wasu sarakunan sarki ne. Kayi hakuri matarka tafi cancanta da samunka dan itace ke gogayya da kai bisa duk wadannan abubuwan dana lissafa maka takawa. Ni kuwa ka barni na tsaya dai-dai matsayi na kamar zaifi dacewa da ni nim........." Saukar tausasan labbansa akan nawa ya hanani karasa abinda naso fadan. A karan farko naji bazan iya hanashi yin hakan ba a gareni dan shi d'in mutum ne mai son ganin farin ciki na. Nima sai kawai na lumshe nawa idanun tare da kankamesa saboda tsumar da jikina kemin da gudun da zuciyata keyi tamkar zata faso kirjina ta fito. Haka shima Ina Jin tasa bugun zuciyar. Tun ina daukar al'amarin nasa karami harya fara zarta gajeren tunanina. Dan kuwa da gaske sai ya tabbatar min tunanina gurbatacce ne. Sai da ya tabbatar nayi laushi bani da ko karfin yin numfashi mai nauyi kafin ya barni. mirginawa yayi ya koma kasa ya maidani saman jikina. Cikin wata kalar murya mai rauni da laushi yace, "Duk wadannan abubuwan bazasu kasance nawa ba sai da ke gimbiyar Salman. Ki yarda kece mahadin rayuwar Salman bin Aliy. Babu ruwana dake wacece, Babu ruwana da nasabarki, babu ruwana da iliminki, babu ruwana da abinda wani zai fada a kanki. Ke nake so a hankanki. Tarbiyyarki ta isheni komai. Please ki yarda na nuna miki matsayinki a gareni Khadijah. Ki yarda na nunama duniya ke wacece a gareni. Ki yarda na shelantama masu mulki irina su san cewa ba sai mace tana da irin nasabarsu ko nagartarsu bane ta cancanci zama matarsu. Ki yarda nayi koyi da mahaifina Khadijah. Dan shima ya auri mahaifiyata da irin matsayin da kike ganin kanki da shi a lokacin da yake matsayin sarki. Wannan shine sanadin girmama kiyayyarta da tamu a cikin masarautar basannabas. Me yasa bazaki amince tarihi ya sake maimaita kansa ba a garemu dan mu sake zama mabudin karya lagon kaifin duk wani jahilin dake tunanin yar mulki sai dan mulki? Talaka sai dan uwansa talaka.” Hawaye nake cigaba da zirararwa ina saurarensa. Ya sake dora bakinsa kan kunnenna yana rada sosai yace, "Ki bama Salman bin Aliy bin Salman dama Khadijah. Na miki alkawarin a wata daya kacal sai na canja zuciyarki ta zama mahadin tawa." Babu shiri na dago da sauri muka hada idanu. Wani sassanyan murmushi ya sakar min yana kashe min ido daya da dage gira yace, “Na yarda da kaina.” Sosai yanda yayi maganar ya bani dariya. Nai saurin fisge jikina na sauka daga nasa nai gefe ina murmushin daya subuce min ba tare dana shirya ba. Shima murmushi yake yi dan har ina jiyo sautinsa. ya murgino ya kwanta a bayana yana sake fadada sautin murmushin nasa. "Gaba daya y'ar jarida kin maida Salman kamar ba sarki ba. Ni mantawa ma nake da wata sarauta idan ina a gabanki. Da gaskefa a kanki na yarda sarki a cikin gida bawa ne matarsa ke zama sarkin. A waje ne kawai muke fankama da bude hanci.” Ai bansan na fara kyalkyala dariya ba da wannan maganar tasa. Sosai na shiga yinta shima kuwa yana tayani. Nace, “Karka saka yan masarautar nan su halakani lokacin mutuwata bai yi ba.” "Ashe kuwa suma duk zasu halaka dan mayaki na gaske zan koma." "Tab, ai nasan yanda kake din nan kullum a kwance ba karfi zaka yi ba.” Nai maganar ina kokarin tashi zaune. Saurin rikoni yayi na fado kansa. Ya sake tura idanunsa cikin nawa yana wani kankance su. "Karki damu, zamu shiga filin daga nan da lokaci kankani. Kinga sai ki banbance idan zan iya ko bazan iya din ba." Ban fahimci inda ya nufa ba. Amma yanda yayi maganar ne cike da shakiyanci ya sani ji a jikina da wata manufa ya fada. Nai saurin kwace jikina ina fadin, "Ni Dije meya hadani da yaki ina mace. Ai sai ku maza.” Dariya yayi shima yana tashi zaune. Yace, "To, lokacin ne dai zai nuna mana ai". A takaice dai duk yanda naso yabar dakin ki yayi, yabi ya katantaneni dole sai na yarda da alkawarinsa na cewar a wata guda sai ya canja zuciyata ta koma mahadin tasa. Rashin mafita da son ya barni da kunyar data gallabeni tasa a yau nace na amince. Amma idan ya gaza nima zai cika min nawa alkawarin na barina na koma rayuwata dana tashi a ciki.😂👩🏽‍🦯👩🏽‍🦯 A mamakina sai naga babu musu ya amince yana wani shegen murmushi. Da kallo kawai na bisa har yaje kofa sannan ya juyo. Salute dina yayi yana wani yin salo da yatsunsa kamar wanda yake harba bindiga. Ya kashe min ido daya da cewa, "Daga yanzun wasan ya fara.” Baijira nayi magana ba ya fice abinsa yana cigaba da murmushi. Sai da ya fita da kusan mintuna goma kafin na dawo cikin hankalina da fahimci ramin dana zurma kaina. Me yasa na amince da wannan game din nasa ni Dije?. gaba daya kaina ya birkice na kasa zaune na kasa tsaye. Jinake kamar na bishi sashensa nace na fasa. Haka naita zirga-zirga. Sai nayi kamar zanje sashen nasa sai na kasa na dawo na zauna. Zuwa can saina sake zabura na mike. Da naje kofa kuma sai na sake dawowa kamar mai basir din daya hana sukuni. *** A sashen sarki Salman kuwa tunda ya baro sashen dije fara'a ta kasa barin fuskarsa. Kadan-kadan sai ya saki murmushi yana wani lullumshe idanu. Shi kadai yasan me yake kitsawa a ransa game da wanan game din nasu shi da Khadijah. A gefe kuma dariya yake mata dan ya sake fahimtar zallar kuruciyarta. A dai dai wannan lokacin Shaheedah ta shigo, Idanun sa a rufe ta same shi, Yana murmushi shi kadai, Ba ka’dan ba yanayin sa ya dagawa Shaheedah hankali, Tasa hannun ta karkada su a kansa, Amma ina SAS yayi nisa a kogin tunanin Khadija daya tafi.. “My king.... Salman....” Riko hannun ta yai, Duk daukar sa ya dauka Khadija ce, Zai rungumo k’ugunta kenan yaji kamshin turaren jikin ta ba irin na Khadija bace, Khadija na saka wasu turaruka masu ratsa zuciyar sa, Kuma a jikin ta kawai yake jin kamshin, Ita kuwa shaheedah har wani kauri kauri na magani yaji tana yi, Don haka ya waske yana dafe kansa... “Jiri nake shaheedah... Ki tallafe ni.” “Sannu My king...” Riko shi tayi ta temaka masa ya kishingida a doguwar kujera, Sai gumi take kallo d’aya zaka mata kasan batada gaskia. Amma tsabar kishi ya rufe mata idanu sam ta kasa daidaita kanta, “Ya nagan ka cikin kananun kaya...? Kasa turaruka da yawa. Kana Zaune anan kana murmushi Kai kadai.. Salman bangane ba.” Duk da yana cikin halin acting, Sai daya kasa danne dariyar sa, Ya danyi murmushi yana jan numfashin ciwo kamar gaske.. “Heeeedah...! Menene baki gane ba? Wani yanayi na shiga, Kwana biyu keda waccen... Kun dauke mun kafa, Sai na samu kai na da tuna baya.. Sanda ina school,Muna moot a court. Shine kawai.” Shaheeda tayi murmushi tana gyara zaman dankwalin kanta. “Kwana biyu tun ranar dana karb’u kudin nan awajen ka nake fama da zazzabi.. I’m very sorry for not checking on you. Kaji?” “Nine me laifi da banajin lapiar ki.. Kiyi hak’uri.” “Ka tashi ka koma daki ka kwanta to..” “Tohm bari ya dena ciwon zan tashi.” “Ina ita waccen din...?” “Wa kenan...?” Ya tambayeta yana sane. Ya Kara da cewa “Akwai wata bayan ke ne..?” Girgiza kai tayi cike da jin dadi, Ta mike tana gyara rigarta. “Tunda baka da lapia yanzu... Zan dawo da safe, Nayi kewar ka. Kagane ai.” Juyar da kansa yai gefe, Saboda yadda turaren datai na hayaki yake hawa kansa. Sumba takai masa gefen kumatun sa, Dak’yar ya tsaya tayi yana murmushi. Ficewa tai a hankali tana karkada jiki. Shi kam shaheeda na bashi Mamaki, Sam babu tarairayar miji, Tun farkon auren su bata damuwa da yaci abinci ko bai ciba, Damuwarta kawai tasani. GIM. KHADEEJAH! Duk na gama sauraron abubuwan da suke cewa Shi da ita, Wani nai dariya wani na bata rai.. Wai waccen...! Na maimata a hankali ina gatsine. Na hararo kofar kawai na juya na sauka kasa. Dakin sirrin sa na shiga, Bayan na danna password. Na zauna akan kujera ina kallon kowacce computer, Ta sashen shaheeda da tawa. Ganin duk ba wani abun kirki sai wulgawar dogarai, Ahankali nasa hannu na na danna recording din baya wato wanda ya wuce bana yanzu datake dauka ba. Shaheeda na hango tana tsaye a dakin ta.. Ba kaya sai zani data daura, Nai saurin juyar da kai na, Can sai ga ta kuma ta dakko kaskon turare, Ta banka wani garin magani a ciki, Tuni hayaki ya gauraye, Ni da nake gani ta na’urar computer sai da na dena ganin komai tsabar hayaki. Inaya ita dake cikin wannan hayakin? Shin bazai illatata ba? “Subhan’Allah....!” Najiyo tamkar murya a baya na. Kan balai nasan ni kadai ce awajen wani tsoro ya shige ni, Ban yi aune ba sai ji na nayi a jikin mutum na kwakwume shi. Ahankali ya shiga shafa bayana yana kwantar mun da hankali.. “Ssssssh! Isssokay.. Menene? Uhm.. Na baki tsoro ne? My badddd.. Kiyi mun afuwa gimbiya tahh, You are my Queen.. And my little heartbeat, I will never play with your heart. As I only want to see you glow with happiness.. Khadijaaa, If I could I would give you the universe and a constant state of pure bliss. Love you to the moon and back baby love...” Ahankali na zare jiki na daga nasa, Na shiga nuna masa cikin computern, Dai dai lokacin da Shaheeda ta zaro kwado daga leda da makulli ajikin sa an d’inke da zare, Tamkar laya ce a bakin sa. “Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun....” Na shiga furtawa Ina jujjuya kai na, Salman ya janyo kujera ya zauna yana kallon screen din tamkar idanun sa zasu fado, Juyawa nai zan fita ya janyo ni jikin sa ya zaunar da ni a cinyar sa, Na kalle shi ya kashe mun ido d’aya, Cikin kunnena ya radamun, “Haba dai... Matsoraciya ce ke dama? Yanzu fa wasan zai fara.. Tun bamu soma ba yanaga kin fara karaya.. Uhm? My Love! Kiyi hak’uri kidena tsoron komai, Salman bn Aliy ibn Salman na tare dake..” Yana magana yana shafa gadon bayana.. Ahankali na daga kai na ina maida duba na ga computer, Hijabi muka ga ta zura, Ta daura nikhaf, Can sai kuma na maida kallo na ga na’urar dake haska sashe na, Na lura ba dakaran tsaro ko d’aya, Sai ga shaheedan nan da hadimarta sun shiga har sashena, Wajen d’aya daga cikin shukata suka tsaya, Ta baya inda ba’a ganowa. Nan suka tono shukar suka zura kwadon, Wani tsoro ne ya shige ne na rirrike jikin Salman ina jujjuya kai na, “Dena kallo kinji... Bara na karasa gani sai nasa acire.” Juyawa nai na dena kalla, Saboda bazan iya jure kalla ba, Shi kuma Salman ya kara kallon komai, “Love... Ba ni wayana a gefe kinji.?” Dakkowa nai na mika masa, Ya karba ya danna wata number ya kara a kunnen sa, “Falaki...... Zan turo maka wani shot clip yanzu, Kaje da kanka ka tono, Ka ajiye shi, Saboda nan gaba kadan Zan neme shi. Amma kafin sannan akwai wani laya aciki ka samu masana ilimin tsibbu su fassara maka ita, Wanda ya fassara dinma zamu neme shi idan lokaci yayi.. Yes! Nagode.” Juyowa nai zan masa magana... Yai hanzarin saka harshen sa cikin baki na, “Say no more love..... Yanzu wasan zai fara..” “Wasa kuma....?” Na fada ina numfashi ahankali Saboda sunbar daya kaimun ta bazata..... ... _Ahh sai zagin dije ake😂👩🏽‍🦯 fisabilillahi dole taja aji😒wayace ya aureta bada yarjewarta ba? Bayan sun gama tsara rayuwar auren su da Mahboub ne ko masoud😂💔 kawai ya aure yar mutane.. Koma dai menene kunfasan tawajen ku da halin nata..inde kafiya ce to oganniya A ce🤦🏼‍♀️ Tawan (billyn A) Inde kika kara zage dije to yasin sai an kusa Kai ruwa rana akan ta😂Sai Salman din da kike ji dashi ya jigata.. .. Muci gaba da bin labarin yar mutan durbun a sannu🏃🏽‍♀️... Na gaishe ku.. GAISUWA mai kima🥰❤️_ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI.....!_ _(sulke baya tare ta sai ta wuce)_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _PG:21_ _BOOK:2_ _Masu bukatar makeup.. Casual, special casual, simple glam, bridal makeup, fixing of lashes, gele and turban, modeling. Sai ya tuntubi BEELANAH BEAUTY.. Instagram handle: Beelanah_Beauty... Tana kano nigeria. Available to travel. #blush it up 🥂_ <><> Wata irin duniya Salman ya jefani a wannan lokacin, gabaki daya ni kuma na kasa komai banda karbar sakonninsa da yake aika min dasu cikin kwakwalwa da ruhi na. Shi kansa ya fara fita hayyacinsa jin da yayi na sakar masa jikin harma da bashi gudun mawar riko masa kai, alamar dai ni kai na bana son ya bar yi min. Zagin da Shaheedah ta narkawa baiwarta wanda muka jiyo ta cikin computer shine ya sanya Salman saurin barin abinda yake min, ya mai da kallonsa kan screen d'in yana kallonta. Tsoro zagin ya bashi dan ni kai na banda na shaga shauki ya dace ace na fishi girgiza da jin zagin saboda girmansa, kamar wata karamar bamagujiya. Salman yasa hannu ya kashe yana faman cizon lips da alama wani radadin yake ji a zuciyarsa. Ya dawo da dubansa kai na tare da kamo ni na tashi zaune, Sai kawar da kai nake yi cike da jin kunyarsa amman shi naga ko ajikinsa. Kai na ya riko yana son mu hada ido amman na hana hakan faruwa dan kuwa rufe idon nayi kirjina na ta faman dagowa saboda tsabar harbawa da yake yi. “Muje na raka ki dakin ki kinga gobe za'a fara hidimar bikin nan.” “Kana nufin nima na shiga sabgar bikinsu bayan ba so na suke yi ba.?” “Ya kamata ki shiga cikin bikin dan samo mana wasu evidence d'in.” Na turo baki still ido na yana rufe dan fuskarsa tana gab da tawa har yanzu. “Kasan fa ni bana daukar rainin hankali, Ana min nake ramawa indai abu be yi min ba.” “Dan nuna min irin action d'in da kike dauka in an miki abu.” Bude ido nayi na kallesa cikin mamaki, ta ya zan nuna hukunci a yanzu bayan kuma ba ai min laifin komai ba? Dariyar da naga yana yi ce tasa na gane rai na min wayo zai yi. “Mijin Shaheedah ka barni na tafi na kwanta.” “Shaheedah da wa? Ai kin san dai ni ba karamin yaro bane mijin mace biyu ne ni.” “Toh da wadda zata zo shikenan?” “Kina lalata mana shiri da ko bakya son na cika miki burin ki.?” Cikin sauri na girgiza masa kai tare da cewa. “Mijin Khadija da Shaheedah na gyara.” “Good girl ashe dai kina sane da alkawarin mu. Shikenan tashi muje.” “Ka daga ni mana.” “Oh sorry wallahi dadin kwanciya naji, musamman ma da nai pillow da wadannan f...” Ban bari ya karasa ba saboda gane inda maganar ta nufa, yai saurin dagani yana dariya kasa-kasa. Maza ma dai wallahi basu san kunya ba sam, yanzu shi saboda tsabar me ma zance, har zai iya bude baki ya fadi akan inda ya yi pillow. Hmmm shine da furucin amman nice da jin nauyin kalmar, ganin yadda nake sauri zan gudu yasa shi kamo ni ya rungume ta bayana yana cewa. “Haba hajiya babu ko dan good night kiss?” Nace Ina turo baki. “Gaskiya ni dai a'a.” Ya sake matse ni a jikinsa tare da hura min iskar bakin shi a cikin kunne na ya ce. “Yana cikin agreement d'in mu hajiya.” Wallahi Salman d'in nan ya raina min wayo, banda haka ta ya ya zai ta kawo min abubuwan da yasan sunyi min tsauri amman ya dinga cewa yana cikin yarjejeniyar mu? Amman ya zan yi, idan ban yi masa ba toh ba zai taba bari na ba gashi bacci nake ji sosai. Hannu nasa na zare nasa daga rungumar da ya yi min, na juya ba tare da na bari mun hada ido ba na sakar mai wani zazzafan kiss a saman lips d'in shi, cikin sauri kuma na juya da gudu Ina dariya na barshi tsaye. Bayan fitar Khadija, Salman ya kira falaki yaji ko yaga video din daya tura masa ta whatsapp? Bugu biyu Falaki ya dauka yana rissinawa a inda yake a tsaye tamkar Salman din na ganin sa, Cikeda girmamawa ya shiga bashi amsa, Salman din na amsa masa a nasa bangaren, “Okay...! Ka ciro? Yauwa. Sai kaje ka kuma tabbatar kayi recording abinda yake cewa.” Kit ya katse kiran yana kallon wayar tasa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mike ya shiga ban’daki. **** Falaki kuwa bayan ya ciro kayan tsibbun a wata jaka ya zura su, Ya maida shukar ya dasata. Sannan ya fice daga cikin masarautar, Can wajen gari yaje inda ake samun masu ilimin tsibbu. “Shigo da baya... Shigo da baya ba sallama.” Sam baibi takansa ba ya shiga da gaban yai kuma sallama. Bokan yaja dogon tsaki yana bubbuga tsintsiyar gaban sa a wata kwarya. “Kai yaro... Zan maka uzuri saboda baka taba zuwa wajen nan ba. Amma nan gaba ka tabbatar Idan zaka Shigo bakayi sallama ba kuma da baya zaka Shigo, Meke tafe da kai...?” Falaki yai murmushi kawai yana mamakin wannan babban lamari na shirka, “Oga na ne ya turo ni, Shi ba zai iya zuwa ba, Yace nan gaba kad’an zai nemi ganin ka akan wasu makiya da suka sashi agaba ne, Yace yanason sanin ma’anar wannan asiri da aka binne...” Falaki ya zaro komai ya mikawa bokan, Shi kuma ya karba yana duddubawa. Ya jinjina kai yana nuna kowanne, “Kaga wannan.... Gaba d’aya da ba’kin asiri akai kome, Da miyagun aljanu aka hada akai aikin. Wanene Salman wacece Khadija?..” “Mata da miji ne...” “Toh raba tsakanin su akeso ayi.. Ba’ason wata auratayya tashiga tsakanin su. Saboda asirin mutane da yawa zai tonu, Kaga layar dake cikin bakin kwadon nan? Anyita ne dan rufe bakin mahaifar ita khadijan. Kar mahaifarta ta dauki cikin Salman kwata kwata. Anyi amfani da kwadon nan an binne ne saboda a hallaka ita yarinyar nan Khadija.. “Sannan shi Salman din ya manceta a rayuwar sa baki d’aya.. Sai shaheedah.. Wacece ita? Okay basshi aljani zakurawana ya shaida mun matar sa, Toh dai babban sihiri akai.. Ba’kin asiri ne da bakin aljani. Amma tunda anyi nasarar tonashi ancire a ranar da sanya, Babu abinda zai faru, Sai ma tsoratarwa da firgici ga wanda ya dasa ya binne wato ainihin wanda yasa akai asirin. Sannan gudun faruwar wani abun a gaba.. Yakamata shi wannan Salman ya hanzarta don yin auratayya da matarsa, Kafin shaidanu su sake shiga.” “To Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu. Kuma Mungode kwarai da karin haske da ka mana akan wannan bakin asiri da akayi. Ga wannan kaci goro, Sai gani na biyu.” Karb’a yayi ya ajiye a gefe yana cigaba da bubbuga tsintsiyar hannun sa, Shi kuma falaki ya fice ya koma masarauta, ta message ya turawa Salman recording din abinda ya faru. Salman na saurara ya mike yana tunanin yadda zai aikata komai ayau. Koda Khadija ba Zata bada had’in kai ba. ********* *GIM. KHADIJA* Lemon kwakwa na hada wanda yaji dabino da madara na jefa yar kankara kamar yadda sanyin ba zai yi yawa ba, ragowar kuma na saka cikin fridge na koma parlor na zauna ina sha hankali kwance. A hankali nake sha ina lumshe ido, jefi-jefi nakan tunano Baffa na ina ina ma ace Allah ya bar min shi a raye da yaga gatan da babu mahaifin da ya taba samun irinsa, ban san dalilin da yasa nafi damuwa dashi ba akan mahaifiyata, kodan shi na tashi na rayu dashi ne? Tinawa nai da hango yadda su Wambai suka sa ana rami a jikin bangon bayan kujerar da Salman yake zama a fada, sun saka wani bakin abu sun rufe, gashi ban karasa gani ba mouse keys d'in da yake controlling cctv d'in ya samu matsala. Da sauri na mike na haye sama, Ina shiga nasa key a dakin sannan na nufi dakin sirri. Ina shiga na fara kokarin yadda zan gyara shi amman na kasa, gabaki daya na rude saboda ina son ganin me yake faruwa yau a cikin masarautar. Sam banji shigowarsa ba sai ji nayi ya rungume ni ta baya, kasan cewar nasan babu mai shogowa gurin sai shi kuma ga dad'ad'an turarukan jikinsa masu matukar sanyaya zuciya shi yasa banji tsoro ba. Sannan yadda ya saba da mun hadu sai ya rungume ni koya kama hannu na nasan iyakar shi kenan, shi yasa ma bana jin haushi yanzu, na kan ce yaje ya yi ta yi shine a wahale. Ganin yadda nake ta faman bubbuga mouse keys d'in yasa shi sake rungume ni yana rike min hannu, cikin wata kasalalliyar murya yace min. “Meya faru da shi.?” Na dan yataina fuska na ce masa. “Ina jin mouse pad din nan ya samu matsala saboda baya motsawa na kasa controlling d'in sa.” Salman ya sake kwantar da kansa jikin wuya na yana sakar min wani zazzafan numfashi a fatar wuya na. A binku da lafiyayyar mace mai rai da lafiya, gashi kullum cikin cin abubuwa masu kyau da dadi tare da saukar da wadatacciyar ni'ima nake yi. Ya kuma sakar min wani numfashin hancinsa cikin kunne na, nan da nan tsigar jikina ta sake tashi, ban san lokacin da nasa hannu da sauri na shafo fuskarsa ina lumshe ido ba. Ganin yadda nake yi ne ya tabbatar masa da cewa na fara shiga wani yanayi. Aikuwa ya gyara hannuwa ya dauke ni gabaki daya, da kafarsa ya samu ya bude kofar sai gamu a cikin bedroom d'in sa. Kallo na ya tsaya yi nima ina kallon yadda leban bakinsa yake kyalli tamkar wanda yasa lipstick, ya hura min iskar bakinsa kamshin mint ya daki hancina na lumshe ido. Kwantar da ni ya yi akan gadon ya mike zai tashi nai saurin riko masa hannu. (Ahh kin bada ni dije💔👩🏽‍🦯) “Ina zuwa.” Ya fada shima cikin kasala. Amman na kasa sakinsa saboda gani nake kamar zan yi wani abun, ganin haka yasa shi dawowa ya hau kan ciki na yana kallo na tare da shafar gashin kai na. Tafiyar tsutsar da yake min itace take sake dulmiya ni cikin wani irin fili wanda na garara fassara wanne ne. Ya samu ta cikin wannan sigar ya rabani da rigar atamfar jikina ya zame ta tayi kamar skirt kasancewar doguwar riga ce. Hannun bra dina ya dinga ja a hankali yana saki ta yadda ba zanji zafi ba saboda dayan hannun nasa yana cikin yalwataccen gashi na. Murya tamkar ta me bacci yake min magana a saitin kunne na tare da zaro hannunsa daga cikin gashin yana yawo dashi a saman fitilun dake kirjina yana cewa. “Na dad'e ina kallon taurarin samaniya dan naga wacce tafi kowacce haske, sai naga bakowa bace nike gani sai ke my love.” Ya sakar min tausassan kiss a tsakiyar kirjina ta yadda na kuma jin wani irin yarrrrr tun daga tsakiyar kai na har zuwa kan babban yatsan kafata. Ya sake maida bakin wajan kunne na yace cewa. “Alhamdulillah ala kulli halin dole na kasance mai yawaita godiya a gurin mahaliccin mu akan baiwar da yayi mun ta kasancewa a matsayin wanda yake sonki a rayuwa. Kece burin raina a koda yaushe ina fatan ki kasance cikin farin ciki a rayuwar ki, kasancewar farin cikin ki shine mafi tsadar abu a guri na.” Dai dai lokacin da ya gama furucinsa ya balle min bra din gabaki daya, ni kuma naji wani irin abu yana taso min a tsakiyar kirjina wanda na rasa komenene. A hankali yasa hannu ya zare bra d'in, duk da cewar idona a rufe yake, amman yadda naji komai tsit ne ya tabbatar min da cewar kallonsu yake yi. Na kasa bude ido bare na gani saboda duk jikina a mace yake, gashi hannuwana suna gefe ko Iya dagawa bana yi. Bakinsa kawai naji akan daya yana wani irin abu da harshensa.... Nan da nan na fara wata irin kyarma jikina yana rawa Sai faman girgiza kai nake yi alaman na shiga wani stage din na daban. Ganin Ina nema fita daga hayyacina yasa shi dakatawa tare da rungumeni ya hade fatar kirjinsa da albarkatun kirjina, yana zura min harshensa cikin kunne yana yawo dashi, daga bisani yaci gaba da magana cike da shauki. “Ba zan iya jurar ganin bacin ran ki ba koda na dakika daya ne ba, wannan shine dalilin da yasa a koda yaushe nake rokon Ubangiji mahalicci akan wannan kyakkyawar halitta da ya yi mun baiwar mallakar ki a mastayin matata ta auren sunnar ma’aiki (S. A. W). Tun ranar da Allah yayi mun baiwar mallakar ki a matsayin matata a wannan ranar nafi kowa farin ciki a rayuwa. Ina kaunarki yake Abokiyar ta. Kin San Annabin Rahama (SAW) ya gaya muna cewa ana iya Auren mace saboda kyawon ta, Asalin ta, Kudin ta ko Riko da Addinin ta, amma sai yace idan da zamubi shawarar sa to mu auri Mace mai Riko da addini. Alhamdulillah. Na godewa  Allah da yadani da mace mai riko da Addini wacca Annabin Rahama (SAW) ya baiwa kowanne d'a namiji shawara ya Aure.” Ya yi shiru tare da sanya bakinsa cikin nawa ya fara sarrafawa cikin kwarewa, nifa gabaki daya na manta da wa nake tare balle na tuna cewa jikina mallakin Mas'oud ne. Gabaki daya Salman ya mantar da ni a wace duniya nake bare na iya tantance da wa nake tare cikin wannan daddad'an yanayin. Sai da ya rabani da komai na jikina ya kuma rikeni gam kamar za a kwace masa ni, naji tattausar muryarshi yana magana. “So gamon jinine, tabbas sonki ya zamo jinin jikina saboda kaunar da nake miki my love, jinina tare da naki yake kewayawa ni dake mun Zama daya a duniyar Masoya, ina fatan ko a gidan Aljannah Ubangiji ya had'a mu a matsayin mata da miji mu rayu har gaban abada. Kin fita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar mace sai ke, Koda yake idan nace kamar babu kyakkyawar mace kamar ke ban yi miki adalci ba, nidai a gurina kece Sarauniyar mata kuma 'yar autar mata daga ke na rufe babin soyayya.. Yau zan nuna miki yadda nake jinki a cikin jinina.” Yana kaiwa nan naji ya daukeni gaba dayana ya sauka daga gadon. Idona a rufe suke, shi yasa ban san ina muka dosa ba. Sai kawai saukar ruwa naji a kanmu. Sassanyar ajiyar zuciya na sauke tare da kuma cusa kaina cikin kirjinsa da ruwa ke sauka dan na fahimci shima babu riga a jikinsa sai sulbin fatarsa da na ruwan dake jikamu. ina jiyo sautin murmushinsa. Murmushi mai sanyi sarki salman ke saki yana kallon yanda ta kunshe kanta a kirjinsa. Hanayenta duka sakale da wuyansa. Bakinsa ya matsar saitin kunnenta ruwan na cigaba da sauka a kansu. Cikin wata irin murya yace min, "Wanka fa Zaki min.” Bammasan lokacin dana d'agoba tare da sakin hannuwana dake sakale a wuyansa. Saurin rikoni yayi da kyau jin zan subuce masa. Tare da azamar manna bakinsa cikin nawa dan ihu na wage baki zanyi saboda tsoratar da nai na tunanin zan fadi kasa. Da wannan damar yayi amfani wajen sai-saita rudanin da nake ciki. Kafin ya ajiyeni a hankali har lokacin bakinsa na cikin nawa. Saurin mannewa nai da jikinsa na kankamesa dan kunya. Bana son ya ganni a yanda nake. Bakinsa ya zare yana sauke numfarfashi, ya mika hannu ya jawo sosan wankansa tare da tsiyaya shower gel a kai ya fara gogamin a gadon baya. Duk zamewar da nake da sinne-sinnen kai sai da yayi min wankan nan shima ya sakani nayi masa. Sai dai har aka yi aka gama idanuna a rufe suke. Inaji yanata min dariya kasa-kasa. Rigar wankansa ya saka min, ai kafin ya gama saka tashi tuni na nufi hanyar fita zan gudu ya rikoni. "Zo kiyi alwala sai ki gudu sarkin kunya." Fuska nadan kumbura. Sai kuma na juyo kaina a kasa nai alwalan. A zuciyata kuwa mamakin yanda na kasa daukar wani mataki nake yi. Sai kace ya kafeni a dakin. (Ahh munafuka dije.. Soyayya ce ta rufe miki idanu😏) Alwalar nayi muka fito tare. Inata faman sinne kai. Ba tare da nasan ya matso kusa da ni ba sai ji nai kawai ya zare hular wanka da ke kaina, wadda ta bama gashina kariya da ga jikewa. A hannunsa ya tattara gashin ya tufkesa yanda bazai dameni ba. "In ara miki rigata?" Ya fada yana dora hannunsa akan habata ya dagomin fuska. Idanuna nai saurin lumshewa dan banason mu hada idanu. Nadan bata fuska muryata can kasa nace, "Yanzufa nai wanka amma ka sakani karayi. Ka barni naje dakina zansa acan.” Durk’usa wa yayy gabana hannayensa duka cikin nawa yana murzawa a hankali. "Yau matata a dakina zata kwana. Ko kin manta da alkawarinmu ne?.” Kallonsa nai da sauri, da iya gaskiyata nace, "Ai babu zancen kwana a daki daya dai". "Inji wa?..." Yayi maganar yana waro idanu waje. "Na rantse bakace da kwana anan ba.” Fuskarsa da murmushi yace, "Toh yanzu na fada. Akwai kwana daki daya a cikin game d'in. Akwai cin abinci tare. akwai wanka tare. Akwai zaman hira tare........" "Gaskiya wannan wayo ne.” Na katsesa da sauri. Mikewa yayi yana dariya ya nufi wajen kayansa. Na bisa da kallo kawai ina yaba tsarin halittar da ubangiji yai masa a cikin raina. A bazata ya juyo ya kamani. Da sauri nai kasa da kaina. Dariya ya karaso yanayi. Ya ajiye kayan daya dakko yana fadin, "Anaso ana kaiwa kasuwa. Ki rage gulma Allah.” Harararsa nadanyi. Ya wani lumshe ido irin hakan ya masa din nan. "Harara na miki kyau." Ya fada cikin kunnena yana sumbatar kuncina. Ban iya tanka masa ba ni dai. Ya mikomin farar jallabiyarsa. “Tashi ki saka ki tayani sallah.” "Taya salla kuma? Dama ana taya wani sallah ne?” "Eh mana. Tunda ke matata ce zaki Iya taya ni.” Jinai zuciyata ta dan tsarga, dan yanzu kam hankalina ya fara karkata a wani hasashe na daban. Sai dai kuma nai azamar cewa 'kai a'a bazai aikata min hakaba har sai na yarda'. Da wannan tunanin na saka rigar ina kare kirjina. Hijjabin daya mikomin na amsa, saida na saka sannan na saki hannuna danaketa kare kirji. Shi dai yayi kamar baiga abinda nake yi ba. Ya hau saman sallayar daya shimfida yana nuna min bayansa. Babu musu na tsaya. Cikin nutsuwarsa ya tada sallar. Munyi salla raka'a biyu, ya juyo ya dafa kaina yayi addu'oi. Ni dai kaina a kasa na kasa dagowa. Baice dani komai ba ya mike ya fita. Shigowa yayi hannunsa dauke da tray na saki tagumin da nayi ina kallansa da mamaki, bai ce min komai ba har ya ajiye a gefen gado inda nake shima ya zauna yana tsiyaya dafaffiyar madara a cikin glass cup. Bakinsa ya kai ya dan Sha sannan ya miko min na kawar da kai gefe. “Idan baki shaba yau bake babu bacci.” “Na koshi ne nasha lemo tun a daki na.” “Wancan ya zazzage ki kara da wannan please.” Babu yadda zanyi dole na juya ya kafa min a baki na Sha, shima ya Sha ta inda lips dina suke tabawa. A haka har muka shanye tas ya ajiye cup d'in tare da sauke tray d'in kasa. “Ko Zaki ciro min jallabiya ta?” Da sauri nace. “Wacce?” “Ta jikin ki mana ai aro daman na baki kiyi sallah.” Ido waje na kalle cikin mamaki ban san ma lokacin da nace. “Sai na zauna tsirara?” Ya yi murmushi tare da cewa. “Is better, dan sai kin fi kyau ma.” “Kai...” Na fada cikin tsantsar mamaki, ganin yana dariya ne yasa ni juyawa na kwanta Ina daga gefen gadon kafafuwa na suna kasa. Salman ya rage wutar dakin ta koma light green ya karaso tare da dauka ta ya dora a tsakiyar gadon yana cewa. “Baby ai sai kiyi ciyon jiki idan na bari kika kwanta a haka bayan kuma ni na roki tayin kwanan nan.” Ban kula shi ba ni dai saboda bacci nake ji duk kuwa da cewa masarautar ta fara cika saboda yan biki. Na lumshe ido na kawai naji ya rungume ni yana magana a hankali. “Kin san nan dakin tsoro ake bawa mutane, bari na rike ki kar kema kiji tsoro idan muna bacci.” Yadda yake magana numfashinsa cikin kunne na shine yasa tsigar jiki na tashi, ya dinga yawo da hannunsa ina jinsa amman kasalar da nake ji ta hanani koda motsi Sai ma jin dadin abin da yake min nake. Daga nan kidan ya zanza salo saboda jin bakinsa a wani sashe na daban, yanayin da ya sanya ni suman da ni kaina ban san lokacin da nai bacci ba. Sai bude ido nai na ga Salman yana ta kallo na. Da sauri na yunkura zan tashi naji kasa na ya amsa da wani irin azababban zafi da rad'ad'i tare da wani irin zugi mai zafin gaske da ya sa na saki kara mai karfi na koma da baya na kwanta Ina....... <><>< *AL-BISHIRIN KU MATA !!!* INA KUKE MATA INA AMARE INA MANYAN MATA CHEF DEEJARH BERVER SISIN MAMA MAMAN FAREEDA(MAI TSUMIN 'YANGAYU) ANEESA_DIDI SALWISE'S KITCHEN SUNZO MUKU DA YADDA ZAKU KARA ILIMI AKAN GIRKUNA DA GYARAN JIKINKI DA SIRRIN SACE ZUCIYAR MIJI DA YADDA ZAKUSAN MAGUNGUNAN DA YADDA ZAKI HADA CIKIN SAUKI.... GYARA SHINE MACE... YADDA ZAKI GYARA JIKINKI YADDA ZAKI HADA MAGUNGUNAN DA KANKI..TSAFTA KWALLIYA DA GYARAN JIKI.. GIRKI MAKAMIN DIYA MACE INA MACCEN DAKE DA MATSALA DA GIRKI INA MACCEN DAKESON KARA ILIMI AGIRKI DA LEMOKU INA MASU SON KOYAN BIRTHDAY CAKE ?? KINA FAMA DA MATSALAR MATA KO INFECTION KINASO KISAN YADDA ZAKI SAMU MAGANIN GYARAN JIKINKI???KISSA DA KISISINA IYA KWALLIYA JAN HANKALIN MAIGIDA NUNAWA KAUNA GA MEGIDA SOYAYYA KAUNA HAKURI DA IYA ZAMA....ZAMU GABATAR DA KOYARWAR NAN DUK AKAN NAIRA DARI BIYAR (500)NAIRA ONLYZAMU KOYAR NE A WHATSAPP GROUP..ZAMU FARA RANAR 20 JUNE 2021 KOWACCE MACE ISHASHIYACE... KOWACCE MACE TANADA KYAU ....KOWACCE MACE SARAUNIYA CE ....KOWACCE MACE TAGABAN GOSHIN MAI GIDA CE.....KOWACCE MACE TANADA BAIWA BABU BALLAGAZAR MACE SAI WACCE TASO TA MAIDA KANTA HAKAN...💃🏼💃🏼KINA SON SANIN SIRRIKAN HAKA???TO KI GARZAYO CIKIN GROUP DIN MU KIKARA ILIMI DUK ALAN 500 NAIR ONLY *SA'ANNAN AKWAI BONUS NA BIRTHDAY CAKE GUDA2 DA CHEF DEEJAH BABA ZATA KOYAR* GA ACCOUNT NUMBER NAN GA MASU BIYA 0003434251 Sadiya Garba khalil Jaiz bank DOMIN NEMAN KARIN BAYANI TUNTUBI WADANNAN LAMBOBI KAMAR HAKA:- CHEF DEEJAR BERVER 08108696754 SISIN MAMA 08107499249 MAMAN FAREEDA 07033742833 SALWISES KITCHEN 08066914136 ANEESA_DIDI 08036660796 *KIYI SECREEN SHOT KITURA SHAIDAR BIYANKI TA WANNAN NUMBER 08107499249* Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI.....!_ _(sulke baya tare ta sai ta wuce)_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _PG:22_ _BOOK:2_ _Masu bukatar makeup.. Casual, special casual, simple glam, bridal makeup, fixing of lashes, gele and turban, modeling. Sai ya tuntubi BEELANAH BEAUTY.. Instagram handle: Beelanah_Beauty... Tana court road, Kusa da novomed, kano nigeria. 08034697302 Domin nemanta ko karin bayani sai a tuntubeta ta lambarta👈🏼Available to travel. #blush it up 🥂_ <><> ......Cizon lips dina da hakori na, shi kuma ya yi saurin tashi daga zaune ya karaso guri na dan ya bani taimako, nasa hannu na da karfi na riko nashi ina gwalalo ido, magana cike da tashin hankali. “Salman please me yake faruwa dani? Me nake ji a jikina ka sanar dani dan Allah.” Magana nake yi Ina kuka hawaye suna sharara akan kumatu na, zuciya ta tana zargin tabbas mun kasance abu daya da Salman wanda nake ta boyewa dan zuwa nan gaba. Girgiza kai kawai nake Ina addu'a Allah yasa ba tunani na bane, Ina son idan mafarki nake yi nai gaggawar tashi dan kuwa ya firgita ni matuka. Amman kuma me? Sai naga Salman yana kokarin rungume ni da son lallashi na, nai saurin ture shi Ina cewa. “Me kayi min dan Allah? Ka sanar dani kace min babu abinda ya faru damu Salman please ka gaya min gaskiya.” Na karasa magana cikin fashewa da kuka. Jikinsa yana rawa ya kuma nufo ni tare da kamo fuskata yana son mu hada ido amman na hana hakan faruwa idona a rufe so kawai nake naji dadin bayani a gurinsa. Zugin da nake ji a kasa na shine yake kuma razanani, gashi shi kuma ya kasa cewa komai sai son mu hada idanu da yake yi. “Kiyi hakuri m...” Ban bari ya kai karshe ba nai saurin cewa. “Innallilahi wa'inna'ilaihir rajiun, wayyo Allah Salman ka takaita ni. Daman wannan shine dabararka a kai na? Dama shi yasa kace ka shirya mana wasanni?” Kukan da ya kuma sarke ni shine yasa ni yin shiru Ina jin rai na yana zafi. Lallai kuwa ya raina min hankali fiye da tunani, sai yanzu na gama gane inda ya dosa amman a baya babu abinda nake ganewa sai shirme. Kamar zai yi kuka da alama yasan laifin da ya yi min, yace dani bayan ya durkusa guiwarsa a kasa ya dora ta hannayensa a gefen gadon yana faman dafe kai yace. “Ina sonki ne Khadija, kuma banyi miki haka dan wata mafita ba sai dan kare mu daga sharrin da ake jifan mu dashi. Dan Allah ki saurare ni my love wallahi Ina kaunarki ban yi miki haka dan mugunta ko son zuciya ba, kuma wallahi da a lokacin kin nuna min bakya so ba za....” Cikin jin haushin kalamansa, wadanda suke kuma sosa min zuciya na dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tare da cewa. “Kafi kowa sanin ina so ko bana so, tunda kasan ban shiryawa zama da kai ba cikin wannan masarautar mai cike da tashin hankali. Ni duk ba wannan ba, tunda ka yi abin da ranka yake so kazo ka mai dani sashe na Ina son zan yi wanka.” “Dan Allah ki tsaya kiyi anan karki fita a haka.” Ya fada kamar zai fashe da kuka, haushinsa ya kamani nace. “Bazan kuma yin minti goma a nan ba, idan ba zaka taimaka na tashi ba ka barni zan tashi da kai na.” Ganin ina shirin tashi yasa shi saurin taimaka min na zauna, sannan ya kamo hannu na amman na kasa motsa kafafuwan. Amman da yake yan kafiyar suna nan sai da na yunkura na mike tsaye da taimakonshi, Ina ganin na tsaya akan kafafuwa na sai na ture masa hannun, na daga kafa zan yi tafiya na kasa yi saboda axaba da zugin da naji, ban san lokacin da nakai hannu na riko shi ba da yake yana tsaye a kusa dani. “Kiyi hakuri na taimaka miki dan Allah.” Ya zanyi dole na barshi idan ba haka ba ban san yadda zanyi na taimaki kai na ba, haka ya dauke ni gabaki daya ya kaini bathroom inda na fara tunanin abinda suka faru kafin na jini cikin yanayin da nake ciki. Already ya tarar min ruwa a bathtub hakan yasa muna shiga sakani kawai ya yi a ciki, zafin ruwan da naji a kasa na shine ya sani saurin riko masa wuya Ina sakin siririn ihu. Ya rike ni sosai yana shhhhhh alamar nayi shiru, na dago cike da hawaye na galla masa harara yai saurin yin kasa da kai, be yi dariya ba saboda yasan shi din mai laifi ne. Sai da ya tabbar ruwan ya ratsani na rage jin radadin sannan ya bude gurin da ruwan yake wuce wa ya sake tarar min wani duk Ina kwance a cikin tub d'in. “My love..In marriage, romance is the icing and love is the cake. Ina sonki kamar yadda na sha gaya miki a baya, The heart wants what it wants, and as it seems, my heart wants nothing more than to be with you. Ba kuma wai wani sashe nake so a jikin ki ba no. Ke d'in ke nake so khady, kuma wallahi lokacin da abubuwan suka faru kice kika dinga kamo hannuna kina kaiwa wasu sashen da dole muka kasa hakura da juna.” “Wait...! Kana nufin ni yar iska ce kenan, ni na fara nemanka ko me kake nufi? Kuma Allah ni ba nice na fara ba me yasa ka dage Sai na kwana a dakin ka?” Nai magana Ina kuka mai cike da shagwaba wacce bamma san nayi ba. Cikin lallashi ya rike min hannu ganin Ina shirin kai masa duka, ya sake matsowa da yake yana durkushe wajan tub d'in, yana shafa min gashi yana cewa. “No... No.. No my baby, ta ya za ai nace miki haka? Abin da nake nufi shine, kece idan na kai hannu na kan ki kamar idan nayi haka...” Ya dora hannunsa saman kirji na nai saurin bugewa Ina turo baki, shi kuma ya yi murmushi kasa-kasa yadda bazan ji ba dan yasan a harzuke nake yaci gaba da cewa. “Toh shine ke kuma sai ki sake riko ni kina kara matsa min hannu alamar dai kema you need mo...” Ihun da nai ne yasa shi saurin tashi tsaye yana dube-dube duk a tunaninsa wani abun tsoro na gani, ni kuma karshen zancen nasa ne bana so shi yasa na saki ihu mai hayani dan ya yi shiru kuma yayi d'in. Ya juyo yana bina da ido na murguda baki Ina cewa. “Ni kazo ka fita.” Ya koma inda ya taso yana fadin. “Kin bani tsoro fa, wallahi nayi tunanin wani abun kika gani. Kuma idan na fita waye zai taimaka miki.” “Allah ne.” Na fada cikin tsiwa. Salman ya sauke numfashi ya kuma kokarin saka hannu a ruwan nace. “Ni bana son taimakon ka yi tafiyarka.” Babu yadda zai yi dole ya tashi ya fita tare da jan kofar, Sai dai be yi nisa ba a jikin kofar ya tsaya yana jiyo ta tana kuka tana mita har ta kammala sai dai duk da haka ta kasa fitowa daga tub d'in. Jiyo ta kawai ya yi na masifa tana Kiran shi. “Wai kana Ina ne.?” Dariya ce ta kufce masa, yayi saurin saka hannunsa ya toshe baki da kyar ya maidata. Ya gyara fuskarsa kamar baiyiba sannan ya bude ya shiga. na kawar da kai na gefe ina cewa. “Toh kuma ba zaka zo ka fito dani ba?” “Korata kika yi ne ai hajiya” Yana maganar yana wani hade fuska. Cikin tura baki nace, “To haushi kaji?” “Sosaima kuwa” Ya bani amsa yana zaro min sabuwar rigar wanka yazo ya nannade ni a ciki tare da daukata gabaki daya muka fito. Zai kwantar dani akan gadon sa nai saurin riko masa wuya Ina faman hade rai nace. “To kayi hakuri tunda kaji haushi. Ai kai dinne da laifi. Kuma ni dai Sashe na zaka mai dani, daman ai har gorin riga kayi min”. Kallo na yayi domin daukar jarirai ya yi min, na rufe ido Ina turo baki kawai naji ya sumbace ni akai na bude ido ina cewa. “Ka bari dan Allah ina da alwala.” “Ai naga ne duk kin zama me tsiwa, gwara nayi maganinta kafin sadakina ya gama hucewa” “Okay, ashe da mugunta dama kayi? To Ka kai ni daki na ni” Sosai ta bashi dariya. harya kasa dannewa sai da yayi kadan. Yace, “Ina ni ina yima gimbiyata mugunta. ?kawai dai a cikin game ne. Kiyi hakuri kiyi sallah ki huta sai na kai ki.” “A'a bana son nan.” Babu yadda zai yi haka ya nufi sashe na Ina ta faman tsuke fuska, a kan bed ya kwantar dani sai faman cije baki nake saboda har yanzu Ina jin zugi. Wardrobe dina ya bude ya dinga karewa kayan nawa kallo kafin ya zaro guda, daya, yana warwarewa yaga doguwar riga ce Abaya, ya nuno min nayi kamar ban san me yake yi ba yace. “A dako wannan.?” Cikin son kona masa rai nace. “Bana so ka barshi zan dakko da kai na.” Sai yaki jin haushin Sai ni da raina ya kuma sosuwa. “Haba hajiya ai ba zaki Iya bani haushin ba, ki bari dai ni da na jangwalo nayi miki komai.” Idanu na gwalalo waje. dan na fahimci a fili nai maganar ashe. Ganin ya kalloni nai saurin dauke kai na, na share shi kamar ban ganiba. Shima watsar dani yayi ya juya ya ciro min riga da zani na atamfa, inda nake ya dawo fuska babu alamar wasa ya taimaka min nasa ya saukeni kan sallaya sannan yace min. “Kafin ki idar bari naje na shirya sai nazo nayi jinya.” “Ka barshi ni dai bana so.” Nai maganar a hankali kaina a kasa. dan inhar ya cuskule fuskarnan tsoron kai masa wargi nakeyi. kusa dani yazo dab da fuskata. “Haba baki da lafiya fa, idan anzo ance meke damunki ai ni zan gaya musu. Kedai kawai kiyi sallah tare da addu'ar Allah yasa mufi haka kusanci, Allah kuma yasa yarima ya isa masaukinsa” ya kare maganar yana dora hannunsa a marata da wani kashemin ido cike da shakiyanci. Harara na sake narka masa bance dashi komai ba na ture hannunsa na tayar da sallah. Shi kuwa Salman dariya ya fita yanayi, ta dauka yana jin haushi idan ta harare shi ba tasan kyawunta yake sake gani ba, yana ganin tamkar shagwaba ce take masa ta soyayya. Juyawa yai ya koma sashen sa dan ya shirya kasan cewar yau yasan akwai bakin da zai ta gani a fada saboda taron bikin nan. ** Ni kuma Ina idarwa na mike zan koma kan gado na kasa tafiya sosai, na saki kuka ganin babu mai taimaka min. bansan na furta sunansa ba ina hawaye. Babu yanda na iya dole sai na rarrafa na kama gadon sannan na dafa naje na kwanta ina tariyo duk abinda ya faru a daren jiya kamar a mafarki ko film. Tunawa na dinga yi wani abun inji haushin kai na saboda ai kamar yadda ya fada ne tana bashi gudun mawa wajan nuna son ayi, amman ita kanta ba tasan maganadisun da ya dinga janta ba har ta dinga biye masa. Ina nan kwance cikin tunanin abinda ya faru, wani ya sakani haushi wani murmushi. Tabbas na sake yadda Sarki Salman yana so na. Sannan shi din na dabanne. Wai nice yau matsayin matar sarki salman, matsayin abu daya?. Wani iko sai Allah. Dije nan ta kauye mai dan karan jahilci da neman fada. Baiwar gajiyalle. Hawayen da suka cikamin ido nasa hannu na share. Samun kaina nai da dora hannuna saman marata saboda tuno maganar Yarima da yayi dazun. Lumshe idanuna nayi a hankali, sai naji knocking. ba damar na iya tashi hakan ya bawa mai bugun damar murdawa. Hadima tace kanta a kasa tai sallamar tare da durkusawa daga can bakin kofar tace min. “Allah ya taimaki Gimbiya, munga baki sakko bane shine muke son ganin ko lafiya.?” Gada sai na nemi na rikice, banda a kwance nake nasan tsab zan Iya faduwa. Yanzu me zan ce mata fisabilillahi? Na daure dai na ce mata. “Karku damu kai na ne yake ciwo shi yasa. Kuje kuci gaba da hidimarku, yau biki kuma ku ci bikin ku.” “Asha, sannu Gimbiya Allah ya baki lafiya ya yaye miki, ko maimarta ya sani? Idan be sani ba gwara a je a sanar dashi kar....” Na dakatar da ita. “Karki damu na sanar dashi ta waya.” “Toh shikenan ranki ya dade amman za'a kawo miki abinci ko?” “No bana sha'awar komai idan anjima naji Ina bukata zan kira in sanar miki.” “Toh ranki ya dade na barki cikin aminci da salama, Allah ya kara lafiya.” Fita tayi na sauke ajiyar zuciya. A lokacin ne Salman ya shigo hannunsa rike da tea cup dayan kuma vanilla cake ne a cikin sosa. Lumshe ido nai tamkar mai bacci, har ya karaso kusa dani ya zauna ban motsa ba dan ko ido bana son mu hada. Rankwafowa ya yi kai na tare da shafa min fuska idanuwana suka fara motsi still naki budewa. “My love ki tashi kisha tea Kar Yarima na ya farajin yunwa” Ko motsi naki yi. “Okay bacci kike yi? Ba zai yiwu ba ki yi wannan abun kuma ki zauna da yunwa salon Kema ulcer ta kamaki Ko ta kama min yarima” Yana kaiwa nan ya ajiye tea din a bedside ya fara Kokarin cire min hijabi nai saurin bude ido Ina turo baki. “Ni dai gaskiya ka rabu dani.” “Zan rabu dake amman Sai naga kinci wani abun sannan K da yarima” “Na koshi ni. Wai waye yarima kabi ka isheni da zancensa” “Zaki sanshi” yayi maganar yana wata munafukar dariya. Fuska na sake ciskulewa nace “To nama fasa cin” “Ba zai yiwu ba my love. Dole kisha saboda yanzu da zan taho mukai waya da Ammi tace kina ina lafiya dai ko? Nace mata baki jin dadin jikin ki, tace to na tabbatar kinsha magani kuma kinci abinci kafin tazo dubaki. Dan na fada mata yau kin zam........” A mugun zabure na tashi zaune. Cikin rawar baki nace, “Kace mata na zama me?” Kwashewa yayi da dariya sosai. Na zuba masa harara ina komawa na kwanta. “Yi hakuri wasa nake miki bance mata hakaba fa” Kin kallonsa nayi nasa hannu kawai na karbi cup d'in, a hankali na ke sha yana gutsuro cake d'in da fork ya samin a baki, ban ma san Ina jin yunwa ba sai da naga na shanye tea da cake d'in. “Yauwa Good girl. Yanzu me kike ji? Akwai ciwo a gurin?” Samun kai na nayi da daga kai still Ina ta turo baki gaba alamar har yanzu ban huce ba. Ya kwantar dani a hankali nayi rigingine kawai naga bawan Allah yana shirin daga min zani, da sauri na rike tsakiyar zanin Ina zaro ido cike da mamaki. “Menene haka?” Salman ya sosa habarsa ya kasa bari mu hada ido. Can kuma naga ya kalle ni tare da matsowa ya dafa kafadata yace. “Duba miki zanyi ko wani abun ne a gurin, amman yaci ace kin mike tunda kin gasa dan nasan ba da karfi na....” “Wai kai dan Allah meye haka? Kai yanzu Sai ka lek....” Na kasa karasawa saboda kunya, Sai kawai na ture masa hannun na juya tare da rufe ido. Bakinsa ya kai kan hannu na ya sumbata sannan ya mike yana fadin. “Sorry baby na tafi zan dawo na kuma ganin lafiyar ki, nasan lokacin kin huce ko cewa nai zan kuma zaki karba.” Hannu nasa tare da toshe kunne na alamar ko yayi ba zan ji ba. Ina jinsa ya juya ya tafi yana dariya, ni kuma na bude ido Ina bin hanyar da uwar harara. Lallai ma guy d'in nan, ashe haka yake daman? Anya kuwa ba kwanan nan ya zama haka ba, dan idan ka ganshi ko yana maka magana Sai ka rantsa da Allah ba zai Iya wadannan abubuwan ba. Amman dubi yadda ya yi min, duk da cewa ma ni ya yi ne cikin rainin hankali, da Ace babu wannan game d'in da yasa ban san abin da zai faru ba sai Allah. Ina cikin wannan tunanin bacci ya dauke ni mai cike da mafarkai. Muryoyin da na dinga ji ne yasa na farka ina murza ido. Wasu manyan mata na gani kai da ka gansu kasan cewar ko wacce ji take da kanta. Na sake ware ido bayan na juyo yadda zan gansu sosai, manya ne da kowacce a cikin su tayi uku na saboda girman halitta. “Kece amaryar Salman d'in?” Wata farar mata sanye cikin wani shegen lace take tambaya ta. Na sunkuyar da kai Ina wasa da hijabi na, suka girgiza kai dayar tace. “Kece kishiyar Shaheedah kenan?” Nan na ban amsa ba kuma ban kallesu ba saboda ban san dangin waye a cikin masarautar ba. Zagaye suka farayi na dinga satar kallon su kasa-kasa zuciya ta na ta karanto addu'o'in neman tsari. Can na jiyo muryar daya daga ciki ba wacce tai tambayar farko ba sannan ba wacce tayi tambaya ta biyu ba. “Me yake damunki baki fito gurin shagalin ba.?” “Bana jin dadi ne.” “Wane irin rashin jin dadi ne bakya ji?” Samun kai na nayi da cewa. “Zuciya ta ce bata min dadi, komai duhu nake Jin sa ban san dalili ba.” Na karasa magana cikin jimami. Murmushi suka yi dukannan su sannan ta farkon tace. “Kin sanarwa da Salman.?” Na shiga girgiza kai alamun A'a kamar zanyi kuka na kuma dora hannu na a kai na da alama ko sunan Salman bana son su furta, kuma ban san dalilin da yasa nake yi musu wannan acting d'in ba, ko kuma dan sun ambaci Shaheedah ne oho min. Kamar hadin baki duk suka fita Ina jiyo dariyar su har wata na cewa. “Lallai wannan aikin na Shaheedah ya fara aiki.” Na sauke numfashi da karfi tare da rufe ido Ina sake yiwa Allah godiya. Wato da na nuna musu cewa na sanarwa Salman zasu yi tunanin Muna manne, yanzu da na nuna ko sunan shi bana son ji shine suke tunanin aikin bokayan su sun yi tasiri a gare mu. Oh duniya Ina zaki damu wajan son zuciya da neman duniyar ba ta hanyar Allah ba? Lallai Sai na yi taka tsantsan idan ba haka ba kuma na shiga uku daga ni har ganye na. ...Ni dai gaba d’aya har aka kusa kammala bikin su Munaya dakyar naje event biyu, Shima sai da na gayyato su ya shukrah saboda kar ace ba wani a dangi na da yazo, Dakyar suka yadda suka zo, Amman dai sun fidda ni kunya domin sunyi ado na kece raini. Nima nasha kyau cikin wani dakakken lace da Ammi tabayar aka kawomin a dinke, Lemon green da dark army green. Na nada laffaya itama rantsattsiya ta cikin kayan lefe na. Ba karamin kyau nayi ba. Event biyu naje na walimah/Budan kai. Daganan sai hawan sukuwa da akai da dawakai, Shima dan Abdullah ya haune shysa na leka banjima ba na dawo sashe na, Ko sau d’aya ban hadu da shaheedah ba, Naji dai ana cewa tazo events din da akai na baya. Ita tasani. Duk wani abu da zai Kara had’ani da Salman a inuwa daya na guje shi, Y’ar wasan buya nake dashi yanzu. Bana taba bari ya rabeni saboda azabar danasha a hannun sa rannan, Har yanzu fama nake da kai na, Na kuma tabbatar wannan wasan ba irin nawa bane na manya na ne. Haka aka kammala bikin aka kai amare gidajen su. Sai fatan Allah yasanya alkhairi. *****Ina kwance akan kujera na idar da karatu kenan, Na shiga tunanin yadda zan tunkari Salman da zancen barina naje gidan Kawu Daddy, Domin Tunda akai aure na banje ba, Inason na zazzagaya dangi ma inda hali, Amma tayaya zan tambaye shi bayan wasan buya nake dashi? Karar waya tace ta katsemun tunanin da nake, ‘Zawj habibyy..!” Shine sunan da ya fito akan screen din, Na ware idanu ina sake karantawa. Nide sam bangane wanene ba don ban saving sunan kowa da haka ba. Wata zuciar ta sanarmun da Salman ne ya rubutawa kansa haka. Gaba na na faduwa na dauka ina raba idanuwa tamkar yana gani na.. “Hello......!” “Assalamu Alaikum... Ya zawjati aleaziza .. kayf halika? ahbuk waftaqadk kathirana.. Deeeja! Kina jina?” Yadda yake magana ahankali cikin wata irin murya yasa na sauke ajiyar zuciar da ban shirya ba. So yake ta karfi da yaji ya sururuta ni wallahi. Shiru nayi har sai da ya maimata sau uku, “Barka da rana...” “Nace miki ina son ki kuma nayi kewar ki sosai.. Babe.. I love and miss you so much. Meyasa kike hana idanuna ganin ki ne? Shin Kinsan yadda kike azabtar dani kuwa...? Zuma naaaaa.” “Ai ni ba Y’ar iska bace..” Nayi subul da baka, Ashe ya jiyo. Dariya najiyo yayi mai sauti. Yadda yake wani rage murya yana lankwasa harshe kai ka rantse da Allah da budurwar sa yake magana. “Naji.. Inde akan ki ne.. Ni dan iska ne number daya. Kina jina? Love! Kefa halaliya ta ce.... Anjima bayan isha’i kishirya zan fara zuwa zance. Duk acikin wasan ne. Karki kuskura kice a’ahh.. “ Kit ya katse Kiran, Nabi screen din wayar da kallo ina maimata kalmar ‘zancen’ daya ce. Wane zance kuma bayan ya auro ni gaba d’aya? Naja tsaki Ina mai wurgi da pillown kusa da ni. Tashi nai na shige bandaki ina jinjina al’amarin Salman... *GIM. SHAHEEDAH* Gaba d’aya a razane take, Ta tattare ta koma k’arshen gado ta kudundune da bargo, kwallin idanunta duk ya zazzago, Tamkar ta fece da gudu yadda take a dimauce. Sai rawa jikin ta yake tana mai toshe kunnuwanta, Tana mai nanata, “Wayyo Allah hajjaju na.. Gasunan sun zagaye ni, kingan su Kowanne harshen sa ya zazzago. Wayyo zasu cinye ni hajjaju. Kinga kwaduna zasu cinye ni hajjaju...” Wajen kofar dakin kuma hadiman tane Kowanne ya tsaya cirko cirko sun rasa yadda zasuyi. Cikin haka saiga jakadiya Abu (Zainab)ta shiga hankalin ta a tashe, “Ina gimbiyar take...?” “Tana ciki tahana kowa ya shiga..” Cewar batula babbar hadimar ta. Kutsa kai jakadiya tai tashiga ciki, Tana shiga shaheeda ta kurma wani ihu hade da lailayo lafiyayyen zagi ta maka mata, Da doriyar jefa mata wani babban matashin kai dake kan gado, “Subhanallah! Asssha gimbiya, Ni ce abu, Jakadiyar mai martaba, Ki temaka na kaiki wajen su Mama Huwaila ko kyaji sassauci kinji.” “Wayyo Allah hajjaju gasunan zasu kamani.. wayyo .” Haka shaheeda taita fada, Dakyar jakadiya ta kamota ta shiga lallamata kamar karamar yarinya. Har saida tasamu tayi bacci tukun Sannan, Suka temaka suka kaita sashen su Mama Huwaila............. *GIM. KHADEEJA....* Ina kwance ina kallon Chinese drama din love 020 naga message d’insa ya shigo wayata, “Ki sakko ina parlorn kasa.....” Ajiyar zuciya na sauke, Na hadu da gamo na ni dije. Banyi wata kwalliya ba don banga abunyi ba, Na dai shafa turaruka Na koma goga man lebe. Na zura abaya baka na yane kai na da mayafi. Sai dana bata lokaci kafin na fita na sauka kasan, Tundaga bene na hango shi a kasa. Ya zauna akujera yana danna wayar sa. Sanye cikin shadda sky blue, Yasha wata hula damanga. Wallahi kamar wani saurayi. Saboda yadda kwantaccen gashin bakin sa yayi masa kyau. Bansan sanda na gurde ba garin kallon sa, Sai ji na nayi ajikin mutum ya tallabo kugu na yana bina da kallo... Kallon juna muke yi tamkar yaune rana ta farko da muka taba haduwa. Shi nasa kallon mai cike da soyayya ne tare da kulawa, ni kuma ina kallonsa ne ganin irin taimakon da ya bani cikin gaggayawa dan da tuni naci kasa wallahi. Iskar bakinsa ya hura min mai cike da kamshin mint, na lumshe ido ina kara bude kofofin hanci na dan jiyo kamshin. “Zaki janyo min asara.” Naji ya fada a hankali. Waro ido nayi na kalleshi da son jin karin bayanin wacce irin asara kuma? Dagoni ya yi tare da saka ni cikin kirjin shi, bakinsa kusa da kunne na yake magana. “Idan kika fadi kika ji ciwo ai kinga nayi asara tunda zaki ji zafi.” Ina jin haka nayi saurin ture shi ina yatsina fuska, kai tsaye na nufi gurin kujera na zauna ina kikkifta idanuwa kamar wata marar gaskiya. Kusa dani yazo ya zauna, sai kawai na samu kai na da jin wata irin kunyarsa, na kawar da kai gefe ina wasa da hannun kujerar. “My love babu gaisuwa?” Yayi maganar yana son ganin fuskata amman na hanashi. “An yini lafiya.” Ya shafa kwantaccen sajan shi. “Saffa - saffa dai tunda kin boye Kwana da kwanaki kin hanani ganinki.” Uhmmm lallai ma wannan mutumin ni zaka sake rainawa wayo bayan ganin nawa da kake yi kare min lissafi kake shine zan yadda na ringa ganinka. Ya kuma matsowa kusa dani tare da rungumo ni zuwa gefen jikinsa, na shiga tutture shi amman yaki saki na. “Ya isa haka my love, zance fa nazo ko kin manta.?” “Haka daman ake zancen duk ka nanike ni sai kace yar air.?” Sake matse ni ya yi a jikinsa bakinsa kusa da gefen fuskata yana fadin. “No... No... No my love! Zance zamu yi irin na turawa. Ya gida dasu Ammi?” Ya fada cikin son bagarar da wancen maganar. “Ni fa gaskiya bana son irin wannan, turawa ai ba namu bane mu koma larabawa tunda daman a can kafi yin rayuwarka.” Kamar na zuga shi sai kawai naji ya dakko ni gabaki daya tare da dorani saman cinyarshi, na shiga zillewa ya hanani koda motsi yana cewa. “Dai dai kenan baby na, kinsan shi balarabe akwai...Iya tattali da kulawa akan abinda yake so, musamman ma mace.” Lallai wannan bawan Allah yasan takan rainin sense, kiri-kiri yasan abinda nake nufi amman sai ya dinga bagarar da lamarina yana yin nashi. “Ina son na samu lokaci na ziyarci dangin ki my love.” Da sauri na juya Ina kallonsa cike da mamaki, ya akai yasan abinda yake cikin zuciyata? Kodai na yi masa zancen ina son zuwa gida ba tare da na sani ba? Kai Anya wannan mutumin baya amfani da aljanu wajan sanin abinda yake rai na? Sumbatar da ya kai min a gefen kumatu na sune suka sani dawowa daga gajeran tunanin da na shiga.... _Masu bukatar makeup.. Casual, special casual, simple glam, bridal makeup, fixing of lashes, gele and turban, modeling. Sai ya tuntubi BEELANAH BEAUTY.. Instagram handle: Beelanah_Beauty... Tana court road, Kusa da novomed, kano nigeria. 08034697302 Domin nemanta ko karin bayani sai a tuntubeta ta lambarta👈🏼Available to travel. #blush it up 🥂_ <><> Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 __I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _PG:23_ _BOOK:2_ _Ina masu neman mace mai daukan hoto a kano? Special female photographer wadda ta iya daukan hoto na biki, Suna, taro da sauran su? ZAARAGRAPHY... Zaragraphy tana nan agarin kano.. Tana hotuna nasu photo book, photo album, photo sessions da sauran su... Domin duba ire iren hotunan da takeyi.. Sai a duba shafinta akan Instagram: ZAARAGRAPHY. Kota number wayarta: 08093194306_ ___*Ahankali* tamkar mai rada ya sake cemun, “Ina son na samu lokaci, Na ziyarci dangin ki my love..” “Dangi na wanne kenan...? Akwai karkarar durbun ainihin tsatso na kenan, Inda yan uwan mahaifina suke da kishiyar uwatah, Sai nan cikin gari akwai yan uwan mahaifiya ta, Da kuma sauran garuruwa inda wasu kawunni na ke da zama...” “Wasu garuruwan??? Zamuje wannan daga baya idan little princess ko prince yazo lapia.. Yawon arbain ake cewa ko?” Na tab’e baki kawai ina mamakin sa, Kawai saboda yi d’aya sai ace na samu ciki? Bana wannan fatan, Fatana bai wuce mu kammala game din da yasa lapia ba kowa ya kama gaban sa. “Haka ake kar’bar bako ba dan drinks....? Uhm?” Ya katsemun tunani ta hanyar tambayar daya mun, Mikewa nai ban kula shi ba, Na dakko lemo a fridge da cup na ajiye masa, “Asha lapia..” Zan zauna a gefe ya sake janyo ni jikin sa yana kallo na, A hankali ya zare gilashin idanun sa, Shagala nai da kallon kyakyawar fuskar sa mai dauke da annuri, Yana da matsakaicin kyakkyawar kalar fatar jiki, shape din fuskar sa ya dace da dara daran idanun sa masu d’auke da gashin idanu zara zara, Yana da wani irin kwayar idanu wata irin kala, idanun sa farare tas. Gashin girar sa sun kusa hadewa da juna saboda yadda suke gazar gazar a kwance. Bakin sa dan karami tamkar shi ya zana abunsa, Jajaye dasu. Hancin sa dogo ne sosai ya dace da yanayin kyakkyawar fuskar sa. Bansan sanda na saka hannu na akan sumar gashin kan sa ba wadda ta kanannade ta kwanto har sajen fuskar sa. Hannun sa ya dora akan nawa hannun da nake yawo dashi, Sai alokacin hankali na ya dawo jiki na, Zan janye kenan ya sake riko hannun yana sumbatar tsakiyar tafin hannu na. Kunya duk ta kama ni. “Gimbiyar zuciar Salman bn Aliy, Yau ni Salman na fara zuwa zance wajen ki... Kamar yadda kowane manemi idan yazo wajen nema yake dagewa ya bayyana wanene shi, Yau ni Salman zan bayyana miki komai nawa, Sannan kema ki sanarmun naki, Saboda musan komai na juna.. Yadda game din zai fi tafiya dai dai..” Yanayin yadda yakemun magana a kofar kunne na ne ya shiga jefa ni cikin wani yanayi, Ahankali na shiga zame jiki na, Ya sassauta rikon da yamun. Yana magana ahankali cikin nutsuwa. “Kamar yadda kika sani, Su Gwaggo sun sanar dake, Sunana Salman naci sunan kakana marigayi sarki salmanu Ibrahim. Shekaru na 32 a duniya, Nayi primary da secondary dina anan kasar, Inda na tafi matakin degree na d’aya dana biyu a fannin islamic law and shariah a king saud university dake saudiyya... Na gama kenan ko result ban karb’a ba aka dawo dani nan aka mun sarauta. Khadijaa! Na kasance banason hayaniya da shiga cikin mutane tun ina karami.. Bana iya sakin jiki nai hulda da mutane. Abokai na bazasu wuce uku a duniya ba, Suma duk suna kasar Saudiyya...Na fara amfani da glasses Lokacin ina secondary school, Tun ina using portal har na dawo saka wannan, Banason munafurci, Hassada, Riya da kuma cin amana.. Banason wannan halayen awajen mutum. Abu mafi soyuwa a rai na mahaifi na ne, Ko ince iyaye na, Inason Ammi sosai, Kuma irin yadda nake nuna kaunarta ne yasa aka shiga tsakanin mu. Zawjatiii... Kina sauraro na kuwa?” Samun kai na nayi da girgiza kai, Ya cigaba da magana hannun sa cikin nawa, “Sannan inde inason abu, Bana taba tsanar sa, Kuma inde mallaki na ne, To bazan taba sharing da wani ba kin gane? Kina yawan tambayana dalilin dayasa na aure ki, Zawjatiii..! Na aure ki saboda ina kaunar ki, Na aure ki ne saboda tunda na dora idanu na akanki naji kin shiga zucia ta, Kin shiga rai na, Ina jin wani abu game dake, Sannan na aure ki ne saboda rashin tsoron ki, Yadda kika kafeni da idanu kina mun tambayoyi ranar saukar nan I cant lieee, I fall for you. Sautin muryar ki ranar shi ya dinga dawainiya da ilahirin gangar jiki na da ruhina, Tamkar majigi haka nake jinki.... Zawjati, Ina kaunar ki sosai, Nasabar ki, martabar ki, Kimar ki.. Me zance dake? Kinsan godiar da nayiwa Allah kuwa da nine nan na fara sanin Zawjatii na..? Inason komai naki deeeeejaaa na, Muryar ki..” Yana magana yana shafa lebe na, “Gashin ki....” Nanma ya dawo kan jelar kalbar da nayiwa kai na guda biyu dazu. “Leben ki...... Da nan, Nan... Komai naki abun ne me soyuwa agare ni, Kuma nasan auren ki alkhairi ne, Saboda yanayin istikhara dana dinga yi akan ki, Kome nawa ke nake gani, Nasan Tabbas ke wani haske ce a rayuwatahh Zawjatiii.. Ina kaunar ki..” Juyawa gefe naga yayi... Ahankali naga ya zaro tissue yana goge hawaye a idanun sa, Kikkifta idanu na shiga yi ina kambama kokarin sa. Ajiyar zuciya na sauke, inajin wani rauni a kansa na tasiri cikin jinina. Kona fada ko karna fada lallai shidin yanada wata kima da girma da daraja a cikin idanuna. Dan ko Mas'ud bana tunanin yana mini irin wannan makahon son. Shin anya kuwa bana yaudarar kaina kuwa....? Saurin ajiye tunanin nayi kafin nace dashi, “Sunana Khadijaa Basheer, Wadda akewa laqabi da dije, Sunaye na da yawa anace mun Dijangala, Oganniya yar baffanta.. Ta Gajiyalle mai yar hakiya..” Dariya naga yanayi ahankali cikeda nutsuwa, Na Murguda baki ina cuno shi gaba, “Meye abun dariya..? Naga daka bada naka banyi daria ba.” “Yi hakuri na daina gimbiya maman prince & princess dina. Sunayen ne naji su kala kala..” “Wallahi zan fasa baka to...” Kamo hannuwana duk biyu yayi cikin nasa yana kallon kwayar idanu na, “Ai nace kiyi hakuri Oganniya, Gwiwoyina bisa k’asa gashi na zubesu, Allah ya huci zuciar ki, Ni dadi ma sukamin, Baby Dijee na, Sweetheart Dijangala tahh, Oganniyar Salman....!” ya kare maganar yana danne dariyarsa da kyau. Murmushi nai kawai da danne tawa dariyar nima na cigaba da cewa, “Shekaru na 23 a duniya, Nayi primary da secondary dakyar bayan mai gari ya samo mana tallafin karatu, Dan da na tsani karatu, Daga baya bayan baffana ya rasu rik’o na ya dawo hannun Kawu na wanda ka nemi aure na awajen sa, Anan garin nayi university na karanci masscomm. Ni marainiya ce gaba da baya. Dan bantaso da mahaifiyata bama, Sai mahaifi na shima bayan nagama secondary a ranar ya rasu. Ni ba yar kowa bace. Mahaifi na talaka ne, Banida wani gata sai na Allah sai yan uwan mahaifiyatahh...” “Sai dai ba kamar kai ba, Ni gaskia ina da baki sosai dan ba’a takani, Kaf durbun ciki da waje babu wanda bai sanni ba. Inada surutu da neman fada don har siyan sa nake, Inason mutane kuma ina shiga cikin mutane koina ana damawa da ni sosai.. Inada kawaye a durbun sosai, Wasu sun hayayyafa da yawa, Anan cikin garin nema banda su sosai, Inason dik wani meso na, Ciki harda wata baiwar Allah Malama mardiyya..” “Yess!!” Ya fada cikin kashemin ido. Da mamaki nace, “Menene?” Fuskarsa kumshe da murmushi yace, “kince kina son duk mai sonki, kinga kuwa ina ciki kenan dan namafi kowa sonki bayan baffa da mama da Uncle” Samun kaina nai da kai masa karamin duka a kirji ina dariya. Shima dariyar yayi yana rungumeni a jikinsa. Sai da mukai mai isarmu sannan na tashi zaune ina bashi amsa da cewa, “Ni dai ban fadaba. Kuma kar ai mun sharri. Ni y’ar kauyen kayau ce, Tashin k’auye girman kauye... Zan iya cewa ma jamia ce kadai nayita anan.. Kasan Durbun..?” “Akwai wata makaranta da za’ai acan.. Gwamna ya turo zansa hannu, Wai yan garin za’a biya su kudin gidajen su su koma k’auyen gaban su, Nan wajen kuma za’ai makaranta har za’a maida wajen orientation camp ma na bautar kasa... “ “Durbun din...?” “Easy dearrrr naa, Ai dole yanzu a soketa, Na miki alk’awarin babu abunda Za’a yi musu. Dama wai yankar wani sashe za’ai ayi makarantar..” Sai naji sanyi a zucia tah, Domin yadda nakeda burin zuwa garin nan ai bana fatan ace yau na bude idanu babu marayatah, Tushe na.. Ina bazaiyiwu ba, Da izinin Allah.. “Zawjatiiii! Bakiji hausawa ma nacewa marar kauye baida asali ba, Ina son ki a duk yadda ki ke, Ki yarda kece mahadin rayuwar Salman bin Aliy. Babu ruwana dake wacece, Babu ruwana da nasabarki, babu ruwana da iliminki, babu ruwana da abinda wani zai fada a kanki. Ke nake so a kan kanki. Tarbiyyarki ta isheni komai...” “Please ki yarda na nuna miki matsayinki a gareni Khadijah. Ki yarda na nunama duniya ke wacece a gareni. Ki yarda na shelantama masu mulki irina su san cewa ba sai mace tana da irin nasabarsu ko nagartarsu bane ta cancanci zama matarsu...Ki yarda nayi koyi da mahaifina Khadijah. Na gaya miki shima ya auri mahaifiyata da irin matsayin da kike ganin kanki da shi a lokacin da yake matsayin sarki. Wannan shine sanadin girmama kiyayyarta da tamu a cikin masarautar basannabas. Me yasa bazaki amince tarihi ya sake maimaita kansa ba a garemu dan mu sake zama mabudin karya lagon kaifin duk wani jahilin dake tunanin yar mulki sai dan mulki? Talaka sai dan uwansa talaka....Uhm? Zawjatiiii..” Murmushi nayi kawai kaina a kasa. Dan bansan mezance masaba kuma. “Please!” Ya fada saitin kunnena. Ajiyar zuciya na sauke tare da kallonsa. murya a sanyaye nace “karka damu ALLAH na nan ai, shine zai fidda kowanne dan duma a giransa.” Murmushi ya saki mai kayatarwa, ya kamo hannuna. cikin nasa ya sumbata, “To ALLAH ya fidda wannan dan duman kamar zinarin oganniya ta, dan yanzu kam bata gajiyalle bace ko yaya kikace?” “Tab kwace zakai mata ma? Ai duk muguntarta inason abuta” Dariya sosai yaringayi. Ya shafa cikina yana fadin, “ina sonki da yawa Khadijah. Shiriritarki na burgeni matuka gaya. ALLAH yayi miki albarka kinji” “Amin” na fada cike da doki. Ba karamin dadi nake ji ba idan naji yace yana son tarbiya ta. Lallai ilimi haske ne ga dan Adam, fitilace kuma abin daraja a gurinsa. Da zan Iya kuma da Ina da gwarin guiwa babu abinda zai hanani bashi tukwicin kyakyawar runguma saboda farin cikin da kalamansa suka sanya ni. Iskar bakinsa ya hura min a fusa, da alama ya fahimci na tafi dogon tunani. “My love ya da tunani haka bayan muna tare.?” Nayi murmushi Ina kawar da fuska nace. “Tunawa nayi da ace lokacin da ina Dije ta a Durbun, nasan da ba zaka taba kallo na ba saboda.......” <><>> Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna _ https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg _This my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing you my latest films, and musical videos at lit more_ _Wannan duk daga bakin shahararriyar jarumar nan ce.. NAFISA👆🏾_ _Shin kunsan sabuwar fucacciyar jarumar nan ta film ta bude YouTube site d’inta? *nafisakabdullahi...* Tana kan manhajar YouTube. Sabon shafin tane dake kan YouTube inda zata dinga kawo muku sabbin fina finai da bidiyo da sauran abubuwa na amfani..._ _Ina masoya makaranta books na zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora.._ _Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye._ _DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba..._ _Akwai Facebook site dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi_ _Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: _ _08071172003_ _Please show some love... Follow, Subscribe, View, Click on bell.. Stay tuned🥰🧚🏻‍♂️_. _B2_ _PG:24_ Da sauri ya riko hannu na cikin tsantsar damuwa, “Meyasa kika ce haka Zawjatii...? Na gaya miki ke nake kauna dan kankin kan ki.. Babu ruwana da inda kika fito....” Murmushi nai kawai wanda sai da gajerun hakora na suka bayyana, “A lokacin fa bazaka gane bane, Surutu nama kadai ya ishe ka..” “Ina son komai naki.. Komai naki yana burge ni..” Zanyi magana kenan najiyo ana danna door bell, “Nayi baki... Ka tashi ka koma bangaren ka.” “Nazo zancen ace na tafi? Ai banci lokaci na ba, Ko su waye sai dai su koma.” Mikewa nai na leka, hango kayuwan su gwaggon ta fada nayi, Itada addah maryama da wasu da me aikin su.. “Su Gwaggo ne...” Na juya na kalle shi ina nuna mai kofar, Mikewa yai yana yafito ni da hannu naje kusa dashi, Jan hannu na yai muka hau sama, Dai dai kofar sirrin da zata sadaka da sashen ya jingina ni yana ciccije lebe, “Baby ya zaki yi dani yanzu...?” “Hakura zakai ka tafi.. Dan Allah dan matsa naje na bude musu.. Ka jiyo wayata tana ringing a kasa.? Nasan kuma su suke kira....” “To bazan samu komai ba kenan...?” Na shiga ture shi, Hannuwan sa yasa ya tokare ni a jikin kofar. Ya rankwafo sosai yadda nake jiyo turaren jikin sa, Gefen kunne na ya sumbata, Kafin ya koma kan wuya na, Can ya dawo kan kirji nai saurin tare shi, “Wayyo Allah dan Allah Kayi hak’uri ka tafi...” “Wai meyasa bakya kira na da irin pet names haka...? Love... why?” “Dan Allah mezan maka ka kyaleni naje na bude musu k’ofa yanzu...?” Murmushi yai yana sosa bayan k’eyar sa, Sai bayan na tambaye shi jiki na yafara bani mugunta zai mun, Ai kuwa ban gama tunanin da nake yi ba ya rik’o hannu na, “Kiss me... Kiss me with love.. French kiss nake so kuma..” Yai maganar yana turo bakin sa, Takaici da kuma su Gwaggo suna jira, Ahankali kamar me tsoro na matsa daf dashi, Banma gama gyarawa ba kawai naji ya karb’i ragamar, Ranar dai labbana, harshe na sun gayawa aya zakin ta.. Ture shi nake amma tamkar ina ture dutse, A dole na hakura na ky’ale shi dan kansa ya saki bakin. Yasa tattausan hannun sa akan labbana yana gogewa, “Dan Vaseline da kika shafa duk na shanye.. Zawjatii I love you wildly, insanely, infinitely, passionately, breathlessly. My lips...on your body tell more than my words about my everlasting love.. I love to kiss those luscious lips of yours every seconds oganniyatahh...!” Samun kai na nayi da murmushi, Inde fagen soyayya ne anya yanada na biyu kuwa? Yadda yake da tarairaya sekace a film? “Ina son ki Dijee naaa...A game dinnan fa yakamata ki dinga nuna mun so kema haka muka yi agreement.” Kamar an tsunkule ni na mike ina gyara mayafin jiki na, “Sai da safe...” Ficewa nai da sauri na sauka kasa na bude musu kofar ina basu hak’urin wanka nake. Addah maryama tayi dariya tana kallo na, “Zahiri... Ga kamshin hugo boss nan kam.” Takarasa tana kannemun Ido d’aya, Na sosa hanci na na basu hanya suka wuce, Ashe daga wajen Ammi suke, Gwaggo taje mata barkar dawowar hankalin Salman da Abdullah.... Ba mu jiba muna hira ba suka tashi zasu tafi. Addah maryama ta mikomin wata leda na rike, “pure zuma (honey) ce sai wani gari, kawai zaki zuba shi ki dinga sha da daddare acikin zumar, Karki wasa.” Godia na mata.. Na rakasu har bakin gate sannan na koma sama, Inata mamakin ina hadimai na suke nasan duk aikin Salman ne....Baya dakin ya koma bangaren sa, Dadi naji ya mamaye ni, Na zauna na sha zumata son rai na, Domin tun a durbun haka nake da son zaki, Tsabar shirme ko tambayar ta maganin menene banyi ba, Nasha sosai, Sannan na rufe na ajiye. Ban’daki na shige nayo wanka, Na zura kayan bacci bayan nayi sallah. Drama din dazu na cigaba da kalla bacci yafara dauka ta. Bansan sanda na bingire ba nafara bacci.. Can cikin bacci, Gani da shegen nauyin bacci, Naji tamkar anamun tafiyar tsutsa a jiki na, Idanu na cike da bacci na fara bude su ahankali na sauke akan Salman, Ba kunya ya kwakwume ni yana sarrafawa, Cikin tsantsar firgici na mike ina rufe jiki na da bargo, “Meye haka...? Yaushe ka shigo?” “Haramun ne...? Dan na shigo dakin halaliya tah?” Na sauke ajiyar zucia ina hamma, “Bacci nake ji wallahi...” “Nima baccin nake ji..... Kuma tsoro nake ji ni kadai acan shi yasa nazo wajen ki.” “Katoto da kai?” “Mu komaa kiji yadda ake wani irin kukan tsintsaye? Gwaggo basu baki labari ba?” Girgiza kai kawai nayi na shige cikin bargo na kudundune saboda baccin dake fuzgata, Amman dan anacen nan sai daya sake rungumo ni ta baya, “Wajen ya dena zafi...?” “Bansani ba...” “To bara na duba...” Dagowa nai na kalleshi, Kallon akan wane dalili? Na juya masa baya hade dasa pillow a tsakanin mu na kwanta, Baisan azabar danasha bane rannan din shiysa. Dariya ta tahowa Salman ya danne ganin yadda tasa pillow ta raba tsakamin su. Zame pillown yai ya maye gurbin sa, ya rungume ta tamkar wani zai k’wace ta, “Tsoro nake ji..... “ Ban kula shi ba na cigaba da bacci na, Salman kuwa ganin yadda tafara lumshe idanu bacci yafara daukarta.. Ahankali yasa hannu ya zare hular kanta, Kalbar datai guda biyu suka bayyana, “Zawjatiii.... Kina jina?” “Uhm....” Na fada ahankali saboda yadda shafar kan ke sani bacci. “Your hair smells lovely zawjatiii.... If I could define how you mean to me, I will say you are the air I breathe... Ina kaunar ki sosai.. Kullum kaunar ki daduwa take a zucia ta, Bansan wacce irin madaukakiyar godia zan miki ba ki amshi tallafin kokan barar soyayyata...” “Bacci... Nake ji.” Na bashi amsa a ahankali ina rufe hammar da nayi, Hadari sai had’uwa yake, Dama tun safe yake haduwa, Can aka fara ruwa sosai, Na kudindune shi saboda yadda wata iska ke buso mana, “Ina zuwa bara na rufe windows din..” Mikewa yai ya zame ni ahankali ya rufe koina ya dawo ya kwanta yana sake janyo ni jikin sa, Wani irin abu ya shiga yimin wanda na tsinci kai na da sakar masa jiki na gaba d’aya, Ina jiyo sanda ya maida hasken dakin zuwa dim light, Ya sake janyo bargo ya rufemu, Nan kidan ya fara canza salo... “Dan Allah....Kayi hak’uri.” “Sssh oganniya ce fa ke.... Banda raki mana.. kinji? Rai na na kaunar ki Zawjatii... Bansan dadin aure ba sai akan ki trust me.. Gaba d’aya rayu...wa ...nahh” Yana magana yana sarrafa dije son ransa, Tana hawayen zafi yana hawayen farin ciki. Aka rasa mai bawa dan uwan sa hak’uri. Wata irin ingattacciyar kauna marar gauraye ya shayar da Dije a daren ranar,..Tasha sumbatu kala kala na yabo da sanyawar madaukakiyar albarka daga bakin Sarki Salman ibn Aliy.. DA Asubah: A hankali na bude idanu na saboda nauyin da yake yimun na azabar dana sha jia a hannun Salman. Ji na nayi katakam ya rike ni, Na daga bargon na hango yanayin da muke ciki, Rintse idanu nai, Ina kallon gefen gadon ko zan hango kayan baccin jikina. Na shiga zame jiki na amma yaki saki na, Mikewa yai yana mika da salati, “Rise and shine my love...” Ban kulashi ba na nannade bargo ajiki na na shiga bandaki na rufo kofar, Sai dana tabbatar na tsaftace jiki na sannan na fito na dakko wasu kayan na saka, Da alama dayan dakin yaje shima har yayo wanka, “Ya ruwan dare mai dad’ada duniyar masoya... Yesternight was fun.. Zawjatii naaa! Ko ince fitila mai haskaka zucia tah, Deeeja... Na rasa wacce irin godia zanyi ga Allah, Don nuna farin cikin samun ki a rayuwa tah, Zawjati kin kawo haske da farin ciki a rayuwar Salman ibn Aliy, Tabbas kin zamto mata tagari.. Bani da kokwanta zaki kasance Uwa tagari ga ‘ya’yan mu....” Inata jiyo shi yana maimaitawa, Shiru nai na fesa body sprays ajiki na, Na zura hijabi. Sakkowa yai daga kan kujerar dayake zaune ya tada sallah nabi bayan sa muka sallame. A dole fushi nake dashi Saboda na lura harda cin zali a game din nasa. Wannan game daga yau na dena yadda amun game over Insha Allah... “Barka da Asubah....” “Barka rabin rainaah... Ya jiki?” Shiru nayi masa na maida kai na gefe, Sai gashi ya dawo kusa dani, “Ya jiki...?” “Lapia ta lau ni” “Dan Allah? To dan karamun third round pls.” Wata uwar harara na dankara saboda takaici. Ina jiyo sa yana babbaka daria. “Bansan ya zan mika godia ta agare ki ba... Amma nan gaba kadan zan miki wata babbar kyauta Insha Allah... Amma kafin sannan Zawjatii.. please a sassauta mun kinji? Yanzu zan koma b’angare na, Akwai wani videos da nakeson saving dinsu awani file.....Zan iya tafiya?” “Ah ka zauna..” Na fada da gatse. Sai kuwa ya kwantar da kansa akan cinyata yana wasa da jelar gashi na, “Wai me kike sawa a gashin ki...! Laushiii, kamshiii, Dadi..” “Ka fasa tafiyar ne?” “Kince na zauna...” “Wasa nake fa... Rufamin asiri” “Asirin ki a rufe yake my love.. Ki sani kin zama Oganniyar Salman sai yadda kikai dashi.. A fada ne nake sarki, Amman a wajen ki na zama bawa, Dan aike, Sai yadda ki kai dani.. Kin zama rakumi na zama akala..” “To ka tashi kaje.. Amma abinci fa?” “Ai da sauran time.. Zan sha coffee.” Mikewa yai bayan yamun peck a kumatu na, “Later...! My darling...” Gyada masa kai nayi kawai, Ya fice, Ajiyar zuciya na sauke ina kambama hali irin nasa, Gaba d’aya ba zaka taba cewa shine me magana haka ba, Ga iya tarairayar da soyayya kamar wani film. Akan sallayar wani baccin yai awun gaba dani... <><><><> Gaba d’aya a zazzaune suke, Sunyi gurfane, Shi kuma yana hakimce akan kujera yana danna wayar hannun sa... “Ranka ya dade.. Ya zamuyi kenan yanzu.?” Cewar wambai yana sake rissina kai cike da girmamawa. Waziri ya zare rawanin ya jefar yana sakato cikin kunnen sa da takardar da Wambai ya mika mai, “Wannan bayanin naka bemun ba, Takardar nan tsinken sakacen kunne ya futa muhimmanci.. Ai kun konamin rai rannan.. Mena gaya muku? Duk runtsi karku yadda da kudin account din waje na, Kuce sai ya kara, Sannan lalle ku ce masa kun bashi sati biyu ko uku ko ku aura masa acikin yaran nan dole, Ko zubaidah (pharmacist) Ko Fulani Raheenirth dake ikko.. Ga yaran nan birjik, Ai kun batamun shiri.” “Allah ya huci zuciar mai girma.. Subutar harshe ne, Ni ne nayi sub’utar...” Waziri ya sake jan tsaki a karo na ba adadi yana karkada kafafuwa.. “Haka yarinyar can shaheedah gaba d’aya du zata bata mana lissafi... Munce tabamu hadin kai taki, Gashi nan tayi wani abun ba adaidai ba ya koma kanta. Haj Huwaila ce da kanta take sanarmun dazu. Tace duk kunyi maganar..” Nan suka shiga jinjina zancen shaheeda da yadda zasu b’ullowa lamarin. Waziri ya sake nisawa kafin yace, “Yau zan sake komawa bayan gari muji yadda zata kaya da yarinyar can. Wannan wannan aure da yayi na kasa gane kan wasu abubuwan, Wato yarinyar nan Khadija take ko? Akwai ayar tambaya akanta...” “Kuma ranka ya dade anata shedamun kusan kullum seta ziyarci sashen mai babban da’ki...Shin yanzu hak’uri zamuyi da zancen tarewar ta a sabon sashen nan?” “No wannan ba wani abu bane, Tunda ancemun basa ziyarar juna shi da ita... Kullum tana wajenta sai dai taje wajen mai babban da’ki...” “Ya maganar Abdullah...? Shima ranka ya dade dashi akai hawan bikin su Munaya, Samb’al dashi dik babu abubuwan nan da yake, Shin meke faruwa ne ranka ya dade?” Waziri ya tunkudawa chiroma center table din daya dora kafafun sa, “Ya za’ai na sani? Bayan ku na dora akan komai? A kaskanta musu rayuwa, A lalata musu rayuwa, A rabasu da farin ciki.. Amma gaba d’aya shiririta kukasa agaba, Komai yana neman birkice mana. Saboda haka wannan ya zama na karshe....” Hak’uri suka zube suna bashi, Ya daga musu hannu kawai , Ahankali kowannen su jiki a sanyaya suka mike suka masa sallama suka fice. Waziri ya shiga zagaye dakin yana dafe da goshin sa... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥. _Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna _ https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg _This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing you my latest films, and musical videos at lit more_ _Wannan duk daga bakin shahararriyar jarumar nan ce.. NAFISA👆🏾_ _Shin kunsan sabuwar fucacciyar jarumar nan ta film ta bude YouTube site d’inta? *nafisakabdullahi...* Tana kan manhajar YouTube. Sabon shafin tane dake kan YouTube inda zata dinga kawo muku sabbin fina finai da bidiyo da sauran abubuwa na amfani..._ _Ina masoya makaranta books na zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora.._ _Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye._ _DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba..._ _Akwai Facebook site dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi_ _Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: _ _08071172003_ _Please show some love... Follow, Subscribe, View, Click on bell.. Stay tuned🥰🧚🏻‍♂️_. _B2_ _PG:25_ *GIM. SHAHEEDAH* YINI tayi tana zazza’bi da firgici tun sanda aka tone asirin data bunne, Bayan an dawo da ita daga sashen Mama Huwaila ma haka taita farfasa kayan parlorn ta tana sumbatu kamar sabuwar tab’i. Sai da asubah sannan jikin ya dan lafa. Amma duk da haka a tsorace take ganin yadda ta sake makalewa a karshen gado tana tukwikwiye jikin ta da bargo. Cikin wata irin kasalalliyar murya mai cike da fargaba ta shiga kiran hadimarta. “Batula... Batula! Batula.” Duk hadiman na bakin kofa da sauran masu aikin gidan gudun kar wani abun ya sake faruwa na fashe fashen da take yi. jikin Batula na ‘bari ta shiga a tsorace. “Ranki ya dade... Ga ni! Allah ya kara miki lapia da nisan kwana.” Shaheeda ta yunkura ta mike dakyar tana mai dudduba kusurwoyin d’akin ta, Gaba d’aya a birki ce take kar su kara fitowa. “Batula... Maganin da muka binne da ke, Kin tabbata yana lapia babu abunda ya same shi?..” “Ranki ya dade. Yana nan k’alau, Dan ko shekaran jiya dana leka na hango shukar tana yadda muka sata.” Shaheeda ta girgiza kai tana sosa keyar ta dake mata azababban kai’kayi. “K’arya kike makaryaciya... Ki gayamun gaskia ancire ko a’ah?” Batula ta shiga zare idanuwa, Ita sam bataga alamun ancire ba, Don tana yawan lekawa tana kuma da masu sa su leko mata. “Ni nake miki magana kina shiru Batula? Zaki magana ko sai na take kan ki? Baca nai miki duk bayan minti ki dinga dubawa ba? Zaki gaya mun gaskiya ko sai na sharara miki mari?” Batula tarasa yadda zatai da ranta tunda batada tabbacin ko ancire ko yana nan. “Ranki ya dade ki gafarce ni, Ni dai gaskia da idanu na banga alamun ancire ba, Kuma wanda nasa su lura suncemun babu wanda ya zagaya baya wajen shukar...” Ganin shaheedah ta ki magana hakan yasa Batula sake gyara zama tashiga sharara wata karyar, “Amman dai ranki ya dade, Ancemin anga y’an uwan su mama Jaleela sun shiga sashen mai martaba washe garin ranar da mu k...” “Rufemin baki, Kawai kice anbi sahun mu an tone. Haba biri yayi kama da mutum, To tashi ki fita tun kafin na mugun saba miki...”Ta karasa magana hade da lailayo ashariya ta dura mata. Jiki na bari Batula ta mike tafice da sauri. Wata razananniyar kara ta saki, Cikin hanzari ta jawo wayar ta ta kira mahaifiyarta, Ta sheda mata abunda ya faru. Ta kar’kare da, “Wallahi Hajjaju an samu wani ya tone abunda muka bunne, Yanzu shegiyar nan... Takece mun wai y’an uwan su Jaleelah taga sunje gidan washegarin ranar da muka binne. Hajjaju abunda yake bani mamaki babu wanda yasan da shirinmu kai har binnewar ma sai da kafa ta dauke.... Eh ina ta furgita hajjaju, Ki samo mafita...” Cire wayar tayi daga kunnenta tasa a speaker. Hajian su taci gaba da kwantar mata da hankali , “Gaskia dai akwai zagon kasa wannan zaman naki da su. Amman karki damu furgicin nan duk zaki dena. Yanzu abunda nakeso dake shine, Kisan yadda zaki ki koma sashen Salman din, Tunda kince ana sanar miki har yanzu basa shiga sabgar juna ko? Koma suna shiga kedai Kiyi maiyiwuwa wajen ganin babu abunda ya ke shiga tsakanin su. Ina fatan kin fahimta?” “Nagane hajjaju.. Amma fa ki sake jiyowa ba komai idan antone ko? Saboda kar abun ya wuce firgici kuma” “Kakki damu... Babu abunda zai faru dake sai alkhairi da ganin bayan makiyan ki fulani.” “Godia nake hajjaju...” Sallama tayi da mahaifiyar tata, Ta kashe wayar tana sakin nannauyar ajiyar zucia. Ta ina zata fara ne? Sashen nasa zata koma? Ko kuwa zuwa zata dingayi kullum? To idan taga Khadija fa? Wallahi zamu kwashi yan dambe kuwa.... ‘Zuciar ta tabata kwarin gwiwa. Haka taita zance ita kadai tana bawa kanta amsa. Rabin zancen kuwa duk kwashewa dije albarka take. *GIM. KHADIJAA* .....Koda gari ya waye, Wanka na sake yi na shirya cikin wata atamfa dinkin bubu, Taje kai na nayi bayan na tsefe kalbar na d’aure da ribbon. Scented hair cream din *yerwaincense&more* na dakko na shafa a cikin gashi na, Ina tuno shi jia yadda yake fadan wai kamshi, Dadi, Laushi... Na daura d’ankwali na samfurin ture kaga tsiya.. Wadataccen babban mayafi na na yafa, Sashen Ammi na fara zuwa da hadimai na guda biyu, Acan na rashe munata hira. Sai bayan magriba na dawo sashe na. Tunawa nayi duk yau banji duriyar Salman ba, Sake faffesa turaruka nayi na shiga sashen nasa. Yana dakin sa akan gado a kwance yana danna ipad dinsa. Yana hango ni ya mikomin hannu na riko nasa, “Zawjatii.. Yanzu nake tunanin ki a rai na..” “Ranka ya dade.. Kaci abinci ko kuwa a dafa wani.?” “Ni na isa na tashi gimbiya shiga kitchen duk wannan kamshin da take zubawa?..” Samun kai na nayi da murmushi kawai nace, “Ka isa har kayi yawa yallabai.. Ko a hado coffee?” Mikewa nai na isa wajen tea shelf dinsa, Na dau kofi kenan zan dauraye.. Da gudu ta shigo cikin dakin tamkar wata zakanya ranta a matukar tashe, Allah ya taimake ni na sauka daga kan gadon ina tsaye wajan coffee table Ina hada mishi. Kai na tayo gadan-gadan ta shako min wuya na, coffee d'in da na zuba ya baro min a kan kafa ta, shakar da tai min itace ta hanani yin ihu saboda azaba. Salman dake kwance akan gado yana kare min kallo, shigowarta dakin yasa shi dan zama, ganin ta shako ni kuma yasa shi saurin sakkowa daga kan gadon ya nufo inda muke. Hannunsa yasa yana son ya kwace ni amman ya kasa saboda ba rikon wasa tayi min ba, gashi idanunta sun rufe so take kawai taga bayana. “Shaheedah ba magana nake miki ba, ba zaki saketa ba.” Wallahi taki saki na gashi ko kwakwaran numfashi bana iya yi, bacin rai yasa shi daga hannu ya wanke ta da marin da shi kansa besan ya yi mata Shiba. Toh ya yi Iya yinsa wajan ganin ta barni amman taki, shi yasa ya zuciya tare da daukar wannan danyan hukuncin da yana sauke hannu ta sakar min wuya na koma gefe ina kakarin amai idanuwa a waje saboda rudewa. Shaheedah kuwa shiru tayi hannunta dafe a gurin, tama rasa daga Ina marin ya taho, kuma ta hana zuciyarta amincewa da yarda akan Salman ne ya yi mata shi. Kallansa tayi cikin tsantsar mamaki tana son taji yayi magana yace bashi bane amman taji shiru alama shi d'in ne yayi mata ba wani ba. Idanunta suka cicciko da kwalla ta dinga girgiza kai baki na rawa tace. “Salman kai ne kasa hannu ka mare ni? Kai ne ka mare ni akan wannan munafukar yarinyar?” Tsaye yake ko gurin Dijen ya kasa zuwa ya lallashe ta saboda shi kansa yasha mamakin yadda ya Iya daga hannu ya mari mace, macen ma kuma matarsa ta aure ba wata ba. Sai dai yadda yaji tana aibata Dijen shine ya sa shi kallonta a yatsine yace. “Ke ta yiwa munafinci bani ba Shaheedah. Amman ke ni kike munafinta nasan duk wani makirci naki wallahi. Kinsan Allah? Kallonki kawai nake yi akwai lokacin da zan baje ki a fai-fai ta yadda zaki san waye munafiki a cikin ku, amman yanzu baki san komai game da kalmar munafunci ba.” Cikin bacin rai da zafin kalamansa duk kuwa da cewa ta firgita jin yace yasan duk wani abu da take yi masa. Amman da yake ita d'in makira ce kuma tasan yadda zata kawar da maganarsa sai tace. “Ka mare ni saboda kayi sabon aure ko Salman? Akan wannan bagidajiyar kake neman ka wulakanta ni bayan na rufa maka asiri ina tare da kai ban taba jin cewar zan barka ba saboda baka haihuwa. Shikenan wallahi kayi da yar halak Salman, zaka san kuma ka mare ni wallahi.” Daga haka ta fice fuuuuu kamar wata iska, shi kuma yaje ya rufe kofar ya dawo gurin da nake durkushe Ina kukan takaici da bakin ciki. Kafata ya kamo yana duddubawa saboda yaga yadda nake ta faman rike ta saboda zugin da take min. “Sorry my love, bari na dakko kankara na saka miki a gurin.” Bance masa komai ba dan har lokacin ban gama dawowa daidai ba, ya dauke ni ya dora akan gado sannan yaje ya dakko kankara a cikin fridge yasa a karamin towel yana gasa min gurin. “Kiyi hakuri dan Allah, ni ban ma san abinda ya shigo da ita cikin dakin nan ba.” Muryata na rawa nace. “Ga abinda ya kawo ta nan kana gani, zuwa kawai tai fa dan ta kashe ni tunda sunyi Iya yinsu sunga ban mutu ba. Wallahi lamarin masarautar nan tsoro yake bani, na rasa me nayi musu suke neman kassarani.” "Kiyi hakuri, nasan koma menene ni na janyo miki tunda ni na auro ki na kawo ki cikin masarautar, dadin dadawa ma kema ba so kike yi ba. Amman kiyi hakuri, insha Allahu komai zai zama tarihi. Gobe ki shirya muje gidan kawu daddy ya bamu address d'in gidan uncle na Lagos mu kai masa ziyara.” Ina haka wani farin ciki ya mamaye ni na manta da halin da nake ciki. Wai zanje na gano su Mami wayyo ni Dije dadi kashe ni. Salman ya tsaya yana kallo na ganin yadda na kasa boye farin ciki na, a ranshi kuwa tausayinta ne sosai. ashe ya dade yana cutar ta be sani ba, yasan tunda ya aure ta bata sake zuwa gida ba sai yanzu da yake yi mata wannan albishir din. Ya janyo hannuwa na yana son sanya idanunsa cikin nawa amman naki biri, ya tausasa murya bayan ya sumbaci hannu na yace min. “Nasan kinyi kewar su ko?” Na daga kai banyi magana ba. “Toh kiyi hakuri insha Allahu haka ba zata kuma faruwa ba. Yanzu zanje na sanya Falaki ya shirya mana komai a sirrince, kema idan kinje gida bance ki gayawa kowa cewar tare zamu yi tafiyar ba saboda tsaro.” “Toh takawa babu wanda zan sanarwa.” “Wai ke meye wani takawa?” “Sunanka ne ranka ya dade.” “Haba dear takawa sai kace wani tsoho. Toh ko zamanin su Ammi wallahi nawan take cewa maimartaba bare kuma ni duka duka da shekara nawa kika girmeni.” Na zaro ido tare da kama habata Ina cewa. “Na fika ko ka fini? Ai ka ninka ni.” “Zo mu gani idan baki fini ba.” Yayi maganar yana kokarin leka min kirji nayi saurin dafe gaban rigar Ina hararasa, daman ta haka ake gane mutum ya girmi wani banda dai yaso ya raina min hankali. Ya dinga dariya kasa kasa yana sake janyo ni jikinsa, kansa a gefen wuya na ya sargafo shi yace. “Ya kike ji?” “Na me?” Wuyana ya shafa alamar da nan yake, nace. “Na dena jin zafin sai dai har yanzu gurin baya min dadin.” Shafar gurin ya dinga yi a hankali ni kuma ina lumshe ido saboda yadda nake jin dadi, ya tashi daga baya na ya dawo gabana tare da kura min ido. Mamaki ne ya cika ni hakan yasa ni saurin yin magana ina murmushi kasakasa. “Ya haka ne?” “Tsoro nake ji Kar sai na kaiki gida ki cewa kawu daddy ba zaki dawo ba, ko ki gaya masa irin kalubalen da kike fuskanta a cikin masarautar nan.” Na zabga masa harara Ina cewa. “An gaya maka ni din yarinya ce.” Murmushi ya yi yana kallona. “Oops na manta ashe fa an zama manyan mata.” Yunkurawa nayi zan tashi ya yi saurin mai da ni yana dariya ni kuma nayi kicin-kicin da fuska ya rungume ni yana cewa. “Sorry har yanzu ke yar babba babba ce kuma yar karama karama tunda sau biyu ne a...” “Ni ka bar ni na tafi tun kafin waccen matar ta debo min mutanan masarautar nan bana san kananun zance dan zan Iya yi mata dukan tsiya wallahi.” “Allah my love? Kai zan so naga yadda kike fada wallahi.” Kamar yana kallo na haka na sakar masa harara kasan cewar ta baya ya janyo ne ya makale ni. Da kyar na samu Salman ya rabu dani na koma sashe na shi kuma ya nufi dakin sirrin sa dan yin bincike. Ina komawa na janyo yar karamar jaka na fara zuba kaya a ciki tare da addu'ar Allah yasa gobe tayi saurin yi dan naje naga su kawu dady. *GIM. SHAHEEDAH* Tana baro sashen Salman nata ta nufa Allah ya taimaka bata nuna wani abun ba a hanya da zai janyo mata idanun Mutane, tana shiga ta fara wurgi da kayan dake kan center table, ta ruga dakinta da gudu kamar wacce zaki mayunwaci da ya hango nama ya biyo ta. Kamar mahaukaciya haka ta kuma yin fatali da kayan dake jere kan mirro d'in ta, Sai a lokacin ta saki wani gigitaccen kuka wanda yasa jijiyoyin goshinta suka mimmike. Kuka take yi sosai ta yake alyabbar jikinta da dankwalin kanta tare da fadawa kan gado tana birgima kamar wata yarinya. Juyi kawai take tana kuka tare da shure-shure da kafafuwa, bakin ta yana rawa take cewa. “Ni Salman? Ni zaka wulakanta ko? Wayyo Allah Salman karka min haka, karka ce zaka wulakanta ni akan wata ya mace cikin duniyar nan.” Ta zabura da sauri kamar an tsunkule ta taje ta dauki wayarta, a kunne ta kara bayan ta yi danne-danne a ciki. Bata dena kukan ba har aka daga, babu ko sallama haka ta fara magana a haukace. “Na shiga uku hajjaju yau Salman ya mare ni, Mari na ya yi akan waccen annamimiyar yarinyar.” “Kambalasti.... Kina nufin kice wannan maganin da su Falmata suka ce kinyi ya fara aiki a kan su, yanzu kina so kice min karya ne duk a banza?” “A banza a wofi ma Hajjaju, ni kam na shiga uku na lalace idan har Salman ya kusanci yarinyar nan. Mari na ya yi a gabanta Hajjaju, wallahi wannan yarinyar ban san da uban da take takama ba har yasa aikin da muke yi akanta baya tasiri.” “KI bari zan yi magana da mahaifinki.” “Yaushe zaku yi har ku samo min mafita hajjaju?” “Idan muka kebe zan sanar masa tunda yanzu yana fada.” “No Hajjaju yau nake son mafitar nan, Ina son a kashe yarinyar can tun kafin asirin mu ya fara tonuwa.” “Shikenan to bari naje nasa ai min iso da shi, duk yadda mukai Zaki ji.” Katsewa Shaheedah tayi ta mike tsaye tare da kallon madubi tana faman goge hawayen da suke zubo mata tace. “Wallahi sai na yi maganinki gobe Dije kike ko wa, na tsakeni na tsani duk wani naki. Yau kin sake Sanya min tsanarki tunda har sanadinki Salman ya mareni, Sai na kashe ki Kowa ma ya huta, Koda kuwa Salman zai hauka ce na rantse da Allah Sai na ga bayan ki muje zuwa zaki San kin shiga gona ta.” Kafa tasa tayi wurgi da kwalbar turaren kusa da kafarta tamkar shine ya yi mata laifin. *WASHE GARI.* Daman tun daren Salman yaga abinda Shaheedah tai da irin kudirinta, dan haka gari na wayewa ya kira ni a waya muka gaisa yace na shirya a lokacin Alhassan zai zo ya kai ni gida, kamar nace masa yayi wuri Sai dai nayi shiru na amsa masa da to. Wanka na shiga na fito Ina cikin shafa mai ya kira yace na fito ba Sai na tsaya yin kwalliya ba, abin ya dinga bani mamaki irin wannan gaggawa haka? Pink shadda ce da akai min doguwar riga dinkin ya zauna a jiki na das. Yar jakar da na zuba kaya na janyo bayan na yafa mayafi wadatacce a jikina, na fito na sanar da hadimaina cewar zan yi tafiya kakata ce bata da lafiya suka dinga yi mata sannu, ban san me yasa na kife su da hakan ba ko dan naji Salman yace baya son kowa yasan da tafiyar?. Kirana ya sake yi saboda duk yana kallo na ta cikin cctv, yace na tsaya Alhassan zai zo ya karbi jakar tawa, kafin ma ya gama gaya min..Sai gashi ya zo ya karba yace nabi ta kofar kudu nace masa to. Shi kuma Salman yace kafin na fita nayi addu'a, nayi sannan na fita still Ina rike da wayar a jikin kunne na muna magana. “Zan kira kawu daddy zamu yi magana dashi, abin da nake so dake shine ki kula min da kanki baby na.” Murmushi kawai nayi bance komai ba saboda rashin abin fad'a. Sai da na shiga mota sannan yace zai gayawa Ammie kome ne ne dan yasan za tayi cigiya idan taji shiru. Da kyar ya ajiye wayar ni dai Ina jin kamar da akwai dalilin da yasa shi cewa na tafi tunda da munyi magana cewar dashi zamu amman yanzu yace na taho. A raina dai nace tafi nono fari naje na sake ma babu nacinsa na kwanaki biyu. A tsaye a parking lot muka ga kawu daddy da alama yasan da zuwan mu, ya karaso cike da fara'a nai saurin bude murfin na fito, cikin murnar ganinsa naje na rungume shi. Har ga Allah bana raba shi da mahaifina hakan yasa nake manta cewa uncle dina ne ba wai shine Baffa ba. “Sannunku da isowa Gimbaya.” Na dago cike da kunya tare da sunkuyar da kai Ina cewa. “Daddy harda kai a sunan nan?” “Eh mana ai Gimbiyar ce. Shiga ciki muyi sallama da malam Alhassan.” Nace to tare da shiga cikin gida cike da murna. Yaushe rabona da gidan tun randa aka fitar dani zuwa masarauta. Babu Kowa a parloun kasa hakan yasa kai tsaye na nufi dakin su Ya Shukrah, na gansu duk sunyi dai-day akan gado suna ta bacci, na saki murmushi tare da juyowa na nufi dakin Mami, itama tana kwance tana bacci a raina nace 'kaga yan hutu basu da wata matsala' a zahiri kuma fitowa nayi na nufi parloun kasa Ina jiran daddy dan ba zan Iya tashin su ba. Da fara’a ya shigo ya zauna, na gaida shi cike da ladabi ga kunya da nake ji dan gani nake tamkar sun gane duk abinda yake tsakanina da Salman. Kawu daddy ya gyara zama tare da cewa. “Nasan baki yi breakfast ba dan mijin ki ya sanar min, ki shiga kitchen kisa masu aiki su yi miki abinda kike so kici, gashi wadannan sarakan baccin basu tashi ba tunda suka yi sallah suka koma.” “Na leka ai naga suna ta bacci shi yasa ban tashe su ba.” Yace. “Eh tashi kije kice suyi miki abin kari dan maimartaba sai nanata min yake baki yi breakfast ba kika taho.” A rai na nace 'lallai Salman babu kunya, kawu daddy yake ta shaidawa banci abincin na sai kace ya fishi sona' A fili kuwa mikewa nayi naje na sanar da masu aiki wadanda ni banma sansu ba da alama sababbi ne, nasan kuma kila ajiye aikin suka yi saboda halin su Shukrah na wulakanci da gadara. Parloun na dawo inda na samu kawu daddy zaune yana duba wata takarda wacce da alama tana da muhimmanci. Kallo na ya yi bayan ya ajiye takardar yace min. “Kinga kinyi sa'a daman jibi zamu tafi Lagos bikin Fatima. Nan suka aiko da cards dinki, Sunce kunyi magana ko? God so kind kuma mai martaba yace daman kuna da shirin zuwa amman ba zai samu dama ba shi saboda wasu matsaloli da yake son ya yi settling d'in su.” Baki na yana rawa nace. “E! Nasan da bikin, To! Kawu to me yace? Yace dai na biku ko?” Shiru yayi yana nazari na kafin ya yi dariya yace. “Yace aje dake kiga gurin idan kun tashi zuwa ba sai kunzo kun nemi address ba.” Murna ta cika ni na dinga yi daga nan muka ci gaba da hira har zuwa lokacin da aka kammala dafa min indomie da kwai, abinda ya bani mamaki guda biyu ce amman na cinye ta tas harda sude plate abin da nake cin daya da kyar amman yau har biyu da dafaffan kwai uku. Lokacin ne Mami ta fito, tana gani na ta saki baki tama kasa karasowa kasan. “Hajiya sakko mana.” “Su Dije na gani yau a gidan, anya ba b'atan hanya tayi ba kuwa.” “A'a zuwa tayi ta gaishe mu.” Cewar daddy dan yasan tsab zata Iya gasa min magana. “Alhaji kenan, baka san Dije yar dadi miji bace? Ace tunda yarinyar nan tai aure bata sake zuwa gidan nan ba saboda bamu muka haifeta ba.” “Wallahi Mami ba haka bane ba, Salman d'in ne bashi da lafiya.” Nayi maganar cike da son ta yarda dani. Karasa sakkowa tayi ta zauna a kusa da kawu daddy tana jan furfurar kansa da ta dan fara yawa, nayi kasa da kai na cike da kunya Ina tuna yadda muke da Salman. Gaida ita nayi ta amsa min tare da tambayar yadda nake da lafiya ta, naji dadi sosai na kuma gaya mata lafiya lau. A nan ne kawu daddy yake ce mata zasu tafi dani Lagos din tunda dama zuwa nayi da niyar yin kwanaki luckily kuma yazo da bikin Ya Fatima. Fitowar su Ya Hameedah ne yasa ni saurin tashi Ina murmushi, suma dai kamar Mami tsayawa sukai suna kallo na, Sai dai kawu daddy ya taka musu birki tare da ce musu su san yadda zasu dinga yi min magana, wannan dalilin ne yasa duk suka hadiye abinda ya taso musu suka shiga gaida ni. Bayan mun gama gaisawa ne daddy yace mu koma daki muka tashi duk muka koma Ina ta jin dadin ganina cikin Yan uwa. Jefi Jefi idan Salman ya samu time yana kirana yaji lafiya ta, har zuwa dare. Shaheedah kuma sai aikin neman ganin bayan dije take, inda aka tabbatar mata da cewa bata cikin masarautar, Koda ta tambayi Salman cewa yayi shima tashi ya yi yaga bata nan ta Iya yiwuwa guduwa tayi saboda abinda Shaheedahn tayi. Muka cigaba da shirin tafiya Lagos inda Salman ya turo min da kudi masu yawa Wai nayi amfani dasu, gashi kawu daddy ma ya bamu mu da su Shukrah kuma duk kai daya. *LAGOS* Tunda muka sauka aka turo driver ya dauke mu nake jin wani irin farin ciki, kasan cewar Ina kusa da window yasa Ina hangen komai akan hanya, wani ya burgeka wani ya baka haushi a haka har muka isa gidan uncle Haysam. Gida ne katon gaske mai kyau da tsari, Sun canza gida, Ba wanda na sani bane zuwa na nafarko, Yara da manya suka fito yi mana maraba suma cikin murna da nishadi. “Gimbiya Khadija....” Suka dinga fada kunya kamar ta kashe ni, na samu ni dai da kyar na zauna bayan nasa an kawo min ruwa nasha. Kiran Salmanu ne ya shigo, a raina nace shidai baya gajiya da kira kamar wani marar aikin yi sai na kira na. Gajiyar hanya ya yi min tare da sake jaddada min cewar ban da zama da yinwu na amsa masa, hayaniyar da ya dinga jiyowa itace tasa be dade akan wayar ba ya katse. Aka dinga zuwa gani na ai matar sarkin bassannabas ce, wacce tazo kwanakin baya kafin auran cacacaca aka dinga yi. Munsha biki sosai an kai amarya gidan mijinta ina kallon ta a rai na nace 'itama fa haka zasu yi da nata angon oh ni Dije' wallahi abin ne yake bani mamaki idan Ina tunawa da irin yanayin da muke kasancewa da Salman, wani ince Anya ba shi kawai yake irin wannan abun ba? Wani kuma ince Wai ko wace mace haka ake mata ne? Babu amsa saboda ni nake tambayar zuciya ta. Satin mu daya muka yi shirin dawowa gida, da yake Ina son wasu kaya nace a kaini wani shooping mall d'in zanyi siyayya uncle Haysam ya bani driver muka tafi da yaransa kannan amarya su uku sai Hameedah da tace itama zata yi siyayya. Muna zuwa na zabi abubuwan da nake so itama ta dauka suma suka nuna abubuwan da suke so na siya musu akai mana bill na bayar. Muna fitowa Ina Kokarin saka wayata a cikin jaka na hango wata mata, sosai tayi min kama da malama Mardiyya ta Durbun. Na sake ware ido dan kamar ta baci duk da cewar wannan ta kuma zama babbar mace amman kamannin suna nan. Kasa wucewa nayi sai da na karasa wajan da suke na gaida su, suna ta bina da kallon rashin sani, nayi murmushi tare da cewa. “Dan Allah kuyi hakuri tambaya zanyi.” “Toh Allah yasa mun sani yan mata.” Cewar wace nake da tabbacin itace malamar tawa. “Wallahi gani nayi kina min kama da wata malamar mu mai suna Malama Mardiyya, ta koyar damu a makarantar Durbun nursery, primary and secondary school.” Baki bude tana kallona, sai naji jikina ya yi sanyi tare da shaida min bafa ita bace, ina kokarin bata hakuri ashe ita kuma mamaki ne ya kusan kashe ta dan tasan bata koyarwa irin wadannan wayayyun ba a Durbun, muryar ta radau tace dani. “Kwarai kuwa nice malama Mardiyya ta makarantar Durbun, amman ban gane ki ba gaskiya.” Ai ban kuma jiran cewar ta ba na rungume ta a jikina cike da murna harda hawaye na, wadanda suke tare da ita suka fara min magana cewar na sake ta na fara yi mata bayani, ga motar mu Hameedah Sai horn take yi min saboda lokacin tafiyar mu airport ya kusa. “Malama ni ce fa Khadija Basheer.” Rufe baki tayi, Hawaye suka fara wanke fuskar ta, Gaba d'aya sai farin ciki kuma ya lullube ta.. “Khadija, Dije, Dijen gala yar Baffa ta Gajiyalle mai yar hakiya. Idan ma baki gane ba mune farkon students a Durbun budurwar malam Auwal mai dan gemu.” Zabura tayi ta mike kasan cewar da tana zaune ne akan kujera, kallona take tana mamaki ganin yadda na canza gabaki daya na, jin horn din ya yi yawa yasa nace cikin sauri. “Malama akwai labari sosai amman sai mun hudu. Nayi aure idan kunzo kano a masarauta nake, ki tambayi sashen Gimbiya Khadija zamu hadu.” Ina kaiwa nan na juya da sauri dan karma muje gida Hameedah tayi min sharrin cewa nice na tsaida mu Mami tayi min masifa. Na shiga Mota Ina kallan ta tare da daga mata hannu itama tana daga min, wani irin dadi yana ratsani, gani nake yi kamar naga uwar da ta kawo ni duniya saboda malama tayi min halacci sosai. *GIM. KHADIJAA* Mayafi na cire, Dawowar mu kenan inason nayi bacci call din Salman ya sake shigowa wayata, Na wajen ashirin kenan a iya sakkowar mu daga jirgi zuwa yanzu, “Ranka ya dade...” “Na gaya miki babu kwanan da zaki sake yi Zawjatii, Ki tattaro kayan ki ki dawo gida yau.” “Amma yallabai dare ne fa, Ya za’ai nace zan taho yanzu? Fisabilillahi ka bari zuwa da safe mana...” “Yanzun ne dare yayi? Yanzu fa muka idar da sallar isha’i, Nide na gaya miki ki dawo gida.” “Ba fa na jindadi... Na kwaso malaria ne maybe saboda weakness din jiki na.” “Ki dai zo gida yanzu, Akwai doctors.. Zawjatii..! Kinji zucia ta kuwa? Bazan iya kwana batare da naji dumin jikin ki ba, Zucia tah da gangar jiki na sunyi kewar ki... I love and miss you soo much.” Ajiyar zucia na sauke, Bacci ne dankare a idanu na, Na lumshe idanu kawai ina sosa kunne na da dan karamun yatsa na, “Shikenan...” “Na aiko a dauke ki...?” “No za’a kawo ni..” “Allah ya kawomin ke Lapia ya tsare mun ke.” Ahankali nace ‘Aamin..’ Na maida mayafin dana cire jiki na, Jiki ba kwari na sakko kasa ina d’auke da trolley na, “Ahh.. Ba dai tafiya ba..?” “Eh wallahi Mami.. Zan tafi, Wai Ammi ce ke tambaya na.” Na amsa ahankali rashin karyar da zanyi, Mami ta gyada kai tana murmushi, “Ummale!!! Jeki kira driver ya sauketa a gida.” Jira nai har Kawu Daddy ya dawo daga masallaci sannan na masa sallama, Da Ya shukrah naci karo a kofar karamin parlor zata shiga, Hannun ta ri’ke da tray dauke da lemo, Ruwa da kuma snacks. “Ya shukky.. Zan tafi.” Kallo na tayi jikin ta yai sanyi, Lokaci d’aya naga ta burkice, Ko bataso na ce mata Ya Shukky dinbane? “Meya faru..?” “Ahh babu komai.. Na dauka kwana zaki sake yi ai.” “Eh! Da sai da sss...” Ban karasa ba sakamakon hango Masoud da nayi, Yana tafe yana gyara hular kansa. Kicib’is yai yana kallo na, Nima na shiga kallon sa, Kallon mamaki, Meya kawo shi gidan Kawu daddy? Kuma da alama wajen Ya shukrah yazo. Da sauri na saisaita kai na ina a’uziyya da sharrin shaidan daya sa ni tsayawa, “Hajiya Khadijaa.. Ranki ya dade rai kanga rai?” Kasa k’oda motsi nayi, Jin muryar masoud da nayi cikin kunnuwana, Wanda ko suma nayi na farfad’o zan gane ta, “Sannu! Ina yini.?” “Lapia qalau... Ya mai gidan naki.” Kasa amsa nayi na koma ciki kawai, Kawu daddy na parlor da Mami da Ya hameeda suka ga na dawo ban tafi ba, “Ah dije kin fasa sai da safe ko...” Mami ce ta tambaye ni tana bina da kallo, Ni kuwa gaba d’aya zucia ta naga su Ya shukrah da tsohon saurayi na Masoud, Wanda na d’au son duniya na dora masa, Shin wannan cin amana ne ko ci baya? Na tambayi kai na ina nisawa. “Khadija... Menene?” Kawu daddy ya tambaye ni cikin kulawa, Na sauke ajiyar zucia hade da girgiza kai, “Babu komai Kawu daddy.. Ya shukra ce take zance shine na basu waje.” “Kice tana zance da tsohon saurayin ki dai.. Masoud, Itama shukrah bataji wallahi.” Mikewa Kawu daddy yayi yana bin ya hameeda datai magana da kallon karin bayani, “Saurayin Khadija na baya?” “Eh daddy..” Ficewa yai wajen Shukrah , Bansan ya akai ba najiyo muryar sa yana wa shukra fada, Can ta shigo kanta a kasa tana kuka. Dawowa yai yana huci, “Haba wannan wane irin rashin kan gado ne eh? Ko kunya bakya ji? Tsohon saurayin kanwar ki? Kinsan shi sarai ya san ki shine zaku dawo yanzu gotai gotai dake kina kula shi..?” “Daddy ya girme ni fa...” Shukra tace cikin kuka. Kanta yai tamkar zai doketa ta fadi, Ya shiga karkada mata hannu, “Na hada ki da girman na gwara kan ki. Ni zaki kawowa maganar Shirme? Duk kin kore samarin ki, Dama shine yake hure miki kunne?” Kuka shaheedah ta fashe dashi tana shessheka, Kawu daddy yaja tsaki, “Hajia ya akai ake wannan katobarar a gidan nan ba’a sanar dani ba? Ina Shukrah ina tsohon saurayin Khadija?” “Kayi hak’uri daddyn su. Nima nayi nayi taki yadda, Ni nafi mata sha’awar Sulaiman ma dan gidan Amb Haroun.” Tsaki yaja yana bubbuga kafafun sa, cikin fada yace, “To ku saurare ni daga ke har su Hajia, Daga yau idan na sake ganin kafar yaroncan a go....” “Daddy be dade da accepting feelings dina ba.. Da ya..” Wani mari ya sauke shukrah dashi seda naji tamkar a fuska ta aka falla shi. “Idan na sake ganin kun cigaba da mu’amala dashi ban yafe muku ba gaba d’aya. Sannan ku saurare ni dakyau kuji, Ba zamu cigaba da zama rida rida daku ba kai d’aya agidn nan ba zeyiwu ba, Kuna samu kuna korar su akan me? Wallahi ba Za’a sake ba, Abu na biyu mungama magana da su yan uwana, Ke Hameeda kece babba zamu hada ki aure da Na’eem dan Yaya kabiru dake jos. Ke kuma shukrah Abdul (yaron sa) dai na waje na, Da shi Zan hada ku, Domin na yaba da hankalin sa da nutsuwar sa, Tun ba yau ba nake kwadayin ya sake kusanci dani ta hanyar bashi auren jini na, Da Khadija kafin anemi aurenta shi nayi niyyar hadasu saboda hankalin ta. Na gaya masa tun tuni kuma ya amince yana son ki, Ke shukrah ba magana nake miki ba?” Kuka wiwi shukra take, Ita kuwa Hameeda batace komai ba, Domin dama Ya Na’eem yana burgeta, Shukrah kuwa burgima tashiga yi tana yakushin kanta, “Daddy Abdul fa kace?Dan girman Allah kayi hak’uri ka sauya mun wani.” “Alhaji ka duba zancen shukrah, Haka dinne, Ni dama aciki....” “Yimin shiru, Ai duk kusan hankalin ku d’aya keda su, Duk Ke kike sasu agaba kina hure musu kunne...” Wayar Kawu daddy ce tai kara ya dauka ya fice yana amsawa cike da girmamawa, Sai a sannan hankali na ya dawo jiki na, “Kinji dadi kin shiga tsakanin soyayya..” Cewar ya shukrah tana harara ta. Daria ma taso bani wallahi, Ni da ita kowa ya shiga tsakanin soyayya oho, Na sauke ajiyar zucia kawai. Agogo na kalla tara saura kwata. Da sauri na dakko wayata a jaka, 30 missed calls Salman yayimun. Kiran sa nayi najita busy da alama waya yake yi. Sai ga Kawu daddy ya shigo yana murmushi, “Kawu zan tafi...” “Ah ai gashi nanma ya taho nan din.. Yace dama yana da niyyar zuwa mu gaisa.” “Wa...?” “Mai gidan naki...” “Sarki Salman?” Cewar Mami ta tambaya cikin tsantsar mamaki. “Eh wallahi, Yace ya kikkira wayarta bata dauka, Hankalin sa ya kasa kwanciya shine ya taho da kansa.” Kunya duk ta kamani, Nasan Salman zai aikata fiye da haka. Zama nai a hannun kujera ina wasa da yatsun hannu na..... <> _Afuwan zafafa fans.. Ba zaku samu kibiyar ajali ba na yan wasu kwanaki. Saboda wani uzuri daya taso🤲🏻Dana kammala zan cigaba da posting IN SHAA ALLAH!_ _Yar uwa kinason karanta zafafa amma documents? To zafafa na harhada kayan su. Da an kammala Za’a yi documents dinsu duka akan Naira dubu d’aya da........_ Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna _ https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg _This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing you my latest films, and musical videos at lit more_ _Wannan duk daga bakin shahararriyar jarumar nan ce.. NAFISA👆🏾_ _Shin kunsan sabuwar fucacciyar jarumar nan ta film ta bude YouTube site d’inta? *nafisakabdullahi...* Tana kan manhajar YouTube. Sabon shafin tane dake kan YouTube inda zata dinga kawo muku sabbin fina finai da bidiyo da sauran abubuwa na amfani..._ _Ina masoya makaranta books na zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora.._ _Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye._ _DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba..._ _Akwai Facebook site dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi_ _Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: _ _08071172003_ _Please show some love... Follow, Subscribe, View, Click on bell.. Stay tuned🥰🧚🏻‍♂️_. _B2_ _PG:26_ *SAS* Ya kikkira wayarta bata dauka, Hankalin sa ya mugun tashi jin bata kira shi back ba. Ko lapia? Ya shiga tambayar kansa, Ganin bashida amsa ya mike ya haye sama. Falaki ya kira awaya ya gaya masa ya samo mota wadda zasuyi ‘badda kama. Drawer dinsa yaje ya bude ya dakko wata arniyar shadda data sha aiki, Ya taje kansa bayan ya faffesawa jikin sa turaruka, Hular ya rike a hannu ya sauka kasa. Ta kofar baya yabi ya fice. A mota ya shiga nazarin wazai kira ya tambaya me ake kaiwa gidan surukai? Can ya kira Addah maryama ya tambayeta, Ta gaggaya masa. Hade datura masa ta message, A wani mart (shopping mall)suka tsaya, Ya bawa falaki wayar da Addah maryama ta turo list. Gaba d’aya Salman hankalin sa a tashe yake. Minti kadan ya duba dayar wayar hannun sa ko zata kira shi back. “Ya rabbi...” Tunawa yai da number kawun ta, Nan danan kuwa ya kira shi ya sheda masa Khadija nanan kota taho? Hankalin sa ya kwanta lokacin da Kawu daddy ya sanar masa da lapiar ta kalau yanzu za’a kawo ta, “No...! Ai ina hanya ma.. Dama zanzo na gayshe da ku. To kuma da bata dawo dinba senaga gwara nazo kawai yau.... din.” Kit ya katse kiran bayan sunyi sallama, Ya sauke wata nannauyar ajiyar zucia jin zawjatin sa na cikin koshin lapia. Falaki ya jasu sai gidan Dr. Isma’el, Har cikin gidan suka shiga da motar. Lokacin Kawu daddy na tare da Mas’oud. Yana bashi ha’kurin ya riga da ya bada auren shukrah. Takalman sa ya fara zurowa masu matuk’ar tsada da haduwa, Sai kafar kuma ta biyo baya fara sal da ita, Yadin jikin sa hular sa, Kai harda agogon sa, Su suka sanya masoud sakin baki yana kallon me futowa daga motar. Dr. Ismael ya mik’awa masoud hannu amma ina masoud ya shagala a kallon Salman, Shi kuma Dr. ismael bayaso ya tafi wajen Salman basuyi sallama da masoud ba yaji haushi yaga ko ya wulakanta shi. Cikin takama, K’asaita, Kwarjini. Irin ta matashin sarki mai jini a jika, Haka Salman ya shiga takawa daga inda yake zuwa wajen su Dr. Isma’el. Kamshin turaren jikin sa gaba d’aya ya gauraye ilahirin cikin gidan da wajen sa, “Ranka ya dade sannu da zuwa...” Kawu daddy ya zube yana dibar gaisuwa wajen SAS, sarauta sarauta ce koda ta kauyece ballantana sarkin gari baki d’aya. Masoud bai san kowanene ba, SAS ya bashi hannu suka gaysa, Har Masoud ya fuce bai dena juyawa yana kallon SAS ba. Duk gayun sa yau yaga karshen wanka da kwalliyar ado. Sosai SAS ya sake gaysawa da Dr. ismael domin jinsa yake tamkar mahaifin Khadija. A parlorn sa suka zauna , Shi kuma Dr. isma’el ya shiga cikin babban parlorn ya kirawo su Mami. Ina zaune na dan fara bacci Kawu daddy ya shiga dokawa sunana kira. Da salati na mike ina gyara mayafi na, Sai da nashiga bandakin kasa na wanko baki na da mouth wash sannan naje parlorn gaba d’aya suna can wajen SAS. Tunda na taho ya kafeni da idanu, kunya duk ta isheni, Har na k’araso na zauna daga can gefe ina jan mayafi na, Muka hada idanu na murgud’a masa baki, “Barka da dare...” Nace dashi ina dan rissinawa kadan. “Zawjatii... Kinci abinci?” Ta gefen idanu na na wulkita shi, Na hango yadda su Mami suka zuba mana ido shi ko kunyar su bai ji ba. Nayi biris memakon yai shiru bai gane ba ya sake tambayata, “Naci...” Na amsa ina masa sign da ido, Shiru yai shi dama ba gwanin magana bane, Sai yanzu na sake tabbatarwa baya iya sakin jiki da mutane ganin yadda idanun sa gaba d’aya akai na suke, Da alamun ni kadai yake kalla yaji sassauci, Lalle yanada wahalar sabo. Sai Kawu daddy ne ya shiga dan kawo magana shi da Mami, Lokaci zuwa lokaci Salman kan tanka sau d’aya sau biyu. Tashi yayi nima na mike, Su Kawu daddy suka shiga godiar abubuwan da ya kawo musu. “Lalle dije kinyi sa’a.. Kai! Bantab’a kare masa kallo ba sai yau, Kinsan kullum da rawani ake nuno shi ko a tv. Ashe haka yake dakyau.?” Cewar ya hameeda data matso cikin kunnena tana gayamun. Murmushi nai kawai a zucia ta nace ‘TubarkAllah..’ Har mota suka rakamu, Falaki yaja mu. Muna baya ni dashi, Ya rikeni tamau kamar za’a kwace. Futinar sa ta cika yawa, Inajin sa yana neman magana a cikin jiki na na kyale shi, “Ya zazzabin? Ya sauka..?” D’aga kai nayi Ina juyar dashi gefe, “Da sau’ki....” “Ai na yiwa Doctor Fiddau magana zata zo ta duba ki... Zuwa da safe..Ko muje asibiti yanzu? Uhm” Karkada masa kai nayi alamun a’ah “Nasha magani ai. Malaria ne kawai sai gajiya.” Kwantar da kai na yayi akan kafad’ar sa yana shafa kwantaccen gashin kai na, “Sannu my love... Muje gida sai ki kwanta ki huta kinji.?” “Uhm..” *MASARAUTAR BASANNABAS* Ta zauren baya muka shiga wajen tsohon gareji da ake ajiye dokuna. Muka shiga sashen sa ta baya. Muna zuwa kofa ya dauke ni cak da hannun sa, Ya rufe kofar da kafar sa da baya. Yana iya saboda rashin karfin jiki na na tallabo wuyan sa nima. Harkan gadon sa ya ajiye ni yana gyara mayafin daya rufemin fuska. Ya rankwafo Kai na yana gyaramun kwanciya, “Sannu Zawjatii...” “Bacci nake ji...” “Kici abinci..” “Naci abinci...” “Tohm ko zaki dan watsa ruwa seki kwanta?” Mikewa nai ina shafa ciki na, “Da dai akwai Indomie da naci, Me tafarnuwa.” Salman ya zaro idanu yana kallo na. “Munada tafarnuwa?” “Akwai a kitchen. Zan dafa” “Noo! Bacci kike ji. Bara nasa Ammi ..” “Wa? Saboda me zan iya..” Mikewa nai na sauka kasan yana biye dani a baya. “Kikace kinci abinci.” “Tun dazu ne shysa.” Kad’a Kai yayi, A tare muka shiga ciki na shjga hada komai dazan sawa indomien. “Zaka ci..?” “Zan ci...” Nai saurin hada komai na dafa ta dik muna tsaye, Ya zura hannayen sa ta cikina ya saqale wuyan sa akan nawa. A haka na dafa na juye a plate muka koma sama, A kan dan karamin center carpet muka zauna dirshan, ni kam saboda tsabar zalama ji nake kamar na kafa kai a cikin plate d'in naji indomie ‘din cikin ciki na. Salman ya dauki fork ya debo zai bani, naga gaskiya bazan Iya yin soyayyar cin abinci ba 😂💔na sanya hannu ba tare da na kalle shi ba. Kafin yaci daya nayi loma uku saboda cinta kawai nake yi hankali kwance. Salman ya tsaya kawai yana kallo na ko ci kasa yi Ya yi saboda tsabar mamakin yadda yaga ina cin abincin. Ko lura banyi ba da cewar ya dena ci, Sai da na cinye na sude plate d'in tare da shan ruwa nayi gyatsa saboda bana son duk wani drinks idan bana kankana ba. “My love ko a sake dafawa ne?” Ya yi maganar cike da kulawa. Girgiza kai nayi alamar na koshi, janyo tray d'in da muka doro plate ya kamo hannu na tare da wanke min shi tas. Saboda bazan iya mik’ewa wajen wanke hannu ba, Gado na nufa saboda ciki ya dauka kuma baccin ya fara cin karfi na, kwanciya nayi ba tare da na koma yin wata kwakkwarar magana ba, shima ya kashe fitila yasa ta bacci tare da bin bayana ya rungume ni muryarsa a sarke yake cewa. “I miss you so much my baby. Please ki dena yin nisa a kusa dani, wallahi bakiji yadda nake cutuwa ba.” Kasa magana nayi saboda yadda yake min da jiki na, gashi Ina jin wani irin abu yana taso min tun daga ciki na zuwa wuya. Kissing d'in da Salman yake min a fatar bayana yasa abin gabaki daya ya taso min, ashe amai ne, Hankalin Salman ya yi matukar tashi ya zauna da sauri tare da rungume ni ina kwacewa saboda na fara galabaita. “Subahanallahi sannu my love, sannu.” Ya dinga min sannu kafin ya sakko daga kan gadon ya kunna haske, a sannan ne hankalinsa ya kuma tashi ganin gabaki daya indomie d'in da naci ta dawo, dakin duk ya baci. Beyi wata wata ba ya dauki waya ya lalibo numbern Dr Fiddau, daman ba wani dare ne ya tsala ba dan lokacin k’arfe goma Sha daya da arba'in na dare. Bugu daya ta dauka tana gaida shi yace tazo yana son ganin ta urgent. Ni kuma ya koma kusa dani lokacin aman ya tsaya amman duk jikina ya mutu ta yadda ko hannu bana Iya dagawa. Ya cire min kayan jikina tare da dakko min wasu marasa nauyi a cikin trolley dina da yake tana sashen nashi, akan kujera ya kwantar dani yaje ya dauke bedsheet din ya kai cikin washing machine, yana kokarin gyara gurin aman sai yaji kiran waya yana dubawa yaga Dr Fiddau ce. “Yauwa shigo Dr.” BA bata lokaci ta shiga bayan ta nuwa masu tsaron kofa Id card d'in ta duk da cewar sun san ko wacece ita. Kwance taga Dije ga kuma amai hakan ya tabbatar mata da cewa akwai wani bayani. Allah ya taimaka cikin akwatin da tazo dashi akwai pt tace tana son tayo fitsari. Daman tana ji dan haka babu musu tace Salman yazo ya kai ta toilet. A bakin kofar ya tsaya saboda Dr Fiddau duk da cewar tana can gurin gyaran aman, Dije tayo fitsarin a cikin wata yar farar roba Salman ya karba ya mikawa Dr. Tana saka pt d'in babu bata lokaci ya nuna mata positive. Fuskarta cike da murmushin kamar ita ce za'a yiwa albishir d'in ta kalli Salman tana dariya sosai tace. “Allah ya taimake ka ya kara maka lafiya da nisan kwana. Ranka ya dade! Gimbiya na dauke da juna biyu congratulations.....” Da sauri Salman ya juyo yana kallo na ido waje baki bude, ni kuma saboda mamaki ban san lokacin da naji karfi a jiki na ba, nabi cikin da yake a shafe da kallo. Salman kuwa kusa dani ya dawo tare da kamo hannaye na ya jani jikinsa ya rungume, hawaye na zirarowa daga cikin kyawawan idanun sa.... ***Hannu na ya kama ya kaini wani dakin ya kwantar dani, Na lumshe ido bacci ya dauke ni shi kuma ya shiga bandaki, alwala yayo yazo ya yi raka'a biyu tunda ya kafa goshinsa be dago ba tsawon lokaci yana ta faman yiwa Allah godiya da wannan ni'imar da ya bashi. Yana saka ran karbar duk abinda Allah ya bashi da hannu biyu-biyu mace ko namiji duk wanda yazo yana maraba. Fita yayi zuwa daya dakin gabaki daya Dr Fiddau ta gyara sai kamshi ke tashi, ya yi alkawarin da safe zai bata tukwici na musamman, dana albishir da kuma na gyaran da tayi wanda bata nuna kyankyami ba. Kayan bacci sa ya saka daga nan ya nufi inda Dije ke ta faman bacci hankali kwance. Salman ya zauna yana kare mata kallo, ji yake kamar ya maida ita cikin sa dan ta riga ta zame masa farin ciki marar yankewa. Bakinsa ya dora akan nata ya tsotsa, tayi juyi wato tai rigingine ya sake gyara zama yana bin kyakkyawar fuskarta da tai fayau saboda jikin duk ya mutu. Cikin zuciyarsa banda sanya mata albarka babu abinda yake yi, 'Ina sonki Deejah na, Allah ne ya hada mu a lokacin da banyi tsammani ba, ubangiji ya faranta miki my love kamar yadda kika sani farin ciki, ya jikan iyayenki, yasa suna gidan aljannatul firdausi. Kyakkyawar runguma ya bata yana lumshe ido, so yake bacci yazo amman farin ciki ya hana shi. Kansa ya mayar kan kirjina ta ya yi pillow dashi, yadda yaji numfashinta yana sauka tare da bugun zuciyarta sune suka sanya shi jin baccin, tunawa ya yi ba ita kadai bace yanzu gashi ya dora mata wani nauyin, dan haka ya koma ya kwanta tare da jayota ta dawo jikinsa, da kyar ya samu a ranar ya runtsa. Da asuba ma ya riga ta tashi, amman dan karya tashe ta sai shima yaki ya tashi. Ita Kuma da ta farka ko bude ido ba tayi ba, jinta a jikinsa yasa ta cewa. “Zan Sha tea.” Salman ya shafi kaina yana magana cike da tausayawa. “Taho na kai ki kiyi brush da alwala tukunna.” Na katse shi da sauri dan ni kadai nasan abinda nake ji. “Dan Allah dan annabi ka fara bani tea d'in na sha, ko tashi bazan Iya ba yunwa nake ji wallahi.” Jin hawaye a jikinsa ne yasa shi saurin dagoni ya kwantar dani shi kuma ya nufi kitchen. Kettle ya dakko ya zuba kayan dafa shayin ya dara akan electric, be baro gurin ba sai da tea d'in ya yi sannan ya zuba a tea cup yasa madara da milo sai sugar kadan ya taho min da cake. Ina jiyo takunsa na tashi tun kafin ya karasa shigowa na mika masa hannu, be bani ba ya samu guri kusa da ni ya zauna da nufin bani a baki na girgiza kai tare da karba a hannuna Ina jujjuya cup d'in tamkar ban san shi ba. Cikin turo baki nayi kurba daya Ina cewa. “Yanzu dan wannan cup din Ina zai je min? Kawai dai in yi manage idan na idar da sallah sai na kara.” Salman ya bude baki kawai yana kallonta, bama tasan yana yi ba saboda yunwar da ke sakularta. Bata sauke cup din ba sai da ta shanye shi tas ko ta kan cake d'in ba tayi ba. Yasa hannu ya karbi cup d'in yana leka ciki yaga babu. “Bari nayi sallah.” Na fada Ina kokarin sakkowa daga kan gadon. Shine ya taimaka min duk da cewa naji kwarin jikina amman Sai da ya kaini toilet sannan ya fito ya koma dayan shima ya yi alwalar ya dawo rike da doguwar riga a cikin sabbabin da na siyo a Lagos ya saka min yaja mu limanci muka yi sallah. Waigowa ya yi muka hada ido nayi saurin kawar da kai dan na tuna abinda Dr tace masa jiya wato Ina da juna biyu, ya matso kusa dani tare da dora hannunsa saman cikin yana fadada murmushinsa yace. “Good morning little princess/little prince. Papa yana gaisuwa mai ban girma, Allah ya albarkaci kome nene a cikin nan.” Hannu nasa tare da ture nashi daga kan ciki na ina yatsina fuska nace. “Haka na ce maka haihuwa zanyi?” “Tunda nayi kokarin aiki aka bani tukwici. A kawo shayin?” Sai da na harare shi sannan na daga kai alamar eh a kawo min sannan ya ja min hanci tare da sumbatar goshi na ya mike yana cewa. “I love you Dijangala na.” Cup din da nasha dazu ya dauka har ya kusan fita nayi saurin cewa. “Nifa bana son wannan cup d'in, babba zaka zuba min ko na rubber ne.” “Yadda kika ce haka za ai my Gimbiya.” Juyawa nayi ban ce komai ba, sai bathroom da na shiga tare da sakarwa kaina ruwa, banyi aune ba naji mutum ya bude kofar ya shigo, nayi saurin juya masa baya ganin shima da shirinsa na wankan ya shigo a rai na nace 'Salman akwai fiti na kala-kala'. Rungume ni ya yi ta bayan yana goga ruwan a fatar jikina, na rintsa idanuwa kamar yana gani na ya fara magana dai-dai kunne na. “Wai da wannan gajan na jiya shine Mas'oud d'in da ake ta min fitina akan shi?” Nayi masa banza dan ba zan Iya magana ba duba da yadda yake wasanni da fitulin kirji na, ga ruwan da yake zuba a jikin mu gashi ya hade mu a guri guda yana wasa da hannunsa a jikina. “Babe... Jia nata kiran ki bakya dauka. Meyasa? Kinga damuwar dana shiga kuwa?” Shiru nai masa na matso lavender shower gel dina na shiga wanke fuska ta da shi. Hannun sa yasa ya shiga daurayemun fuskar yana sake tambaya ta. A gajiya na bashi amsa, Gashi ya sosomun inda yake kaikayi wato masoud da ya shukrah kan babban balai. “Afuwan Yallabai.. Ya shukrah tayi bako shine fa nad’an jira su gama sai na taho. Saboda bamuyi sallama ba..” Kunsan mata da miji, Dukda ban wani shaku dashi ba sosai, Sai naji bazan iya boye masa ba gaskia. Uwa uba duk wani janye kai na dana dinga yi a baya ina nesanta zucia ta agare shi duk yawanci saboda Masoud ne. Kafin na samu yafuta arai na Salman din ya fara maye gurbin sa, Saboda k’aunar daya ke zubamun. Sai na samu kai na da gaya masa duk abunda yafaru daren jia. Na kar’kare da, “Shine wanda kagani tare da Kawu daddy awaje. Hak’uri yake bashi saboda yace wallahi bazata aure shi ba ya riga ya mata miji...” Kyakkywar runguma Salman yayi mun, Ya zuba mun ruwa ajiki na, Yana cigaba da goga mun soso irin me yatsun nan a jiki na romantically... “Oh haba..? Ko shine wanda nagani da daddy a tsaye. Yanata bina da kallo. Allah yasa dai be gane ni ba.” “Eh shine..” “Kin san Allah ni kunya ma naji da naga wanda muka yi takara da shi a neman auranki, saboda dama can ba ajinki bane bare kuma yace zai dama dani a farauto zuciyarki.” “Kai da kayi murdiya, ai ba zabe akai ba kuma ko campaign baka yi ba kaga kuwa shi....” Be bari na karasa ba ya toshe min baki da hannunsa tare da juyo dani idona na kuma rintsewa sai kawai naji bakinsa a cikin nawa ya shiga sarrafawa. Toh me zan tsaya yi banda na bayar da kai bori ya hau. Da yake daman tun dare yake son mu kasan ce tare Allah ya kawo amai, shine ya fanshe abinsa yanzu. Wanka muka yi sannan muka fito tare cikin towel d'aya, sai da muka zo tsakiyar parloun ya fara kokarin kwace towel d'in baki d'aya, nayi saurin rikewa Ina dariya shima dariyar yake yi yana kuma ja. “Ki bani mana ba nine babba ba.” “Kai ne fa kaki tsayawa kowa ya dauki daya kace da wannan kawai zamu yi amfani. Ni dai bazan Iya zama a haka ba bu komai ba.” Yana rungume dani yace. “Toh ni a haka nake son ganin ki yanzu.” “Na shiga uku dan Allah takawa kayi hakuri, Allah ba zan Iya zama haka ba.” “Shikenan to ni bari na bar miki, kuma bance ki rufe ido ba.” Ido na ne yakai kan jallabiyar da ya cire yanzu, Sai kawai na kwace jikina na ruga da gudu na dauki rigar tare da karawa. Shi kuma tsorata ya yi da gudun da nayi shi yasa be yi wani motsi ba sai da yaga ta zauna a bakin gado ya karasa wajan tare da durkusawa a gaban ta ya dora kai saman cinyarta yana magana cikin rauni da karyar da zuciya. “Please baby dan Allah ki dena irin wannan gudun, ki lallaba min kanki da kuma babyn cikin ki. Ina son ku bana son na rasa ku a rayuwata kiyi min wannan alkawarin na kula da kanki please.” Ba karamin tausayi ya bani ba, hakika nasan Salman yana matukar so na, kuma nima ba zan ce bana son sa ba saboda Iya kulawa da tarairaya yana bani Iya yinsa. Ban san lokacin da na dora hannu a saman sumarsa ba na shiga wargaza ta ina mikar da ita tsaye tana komawa saboda santsi da sumar ke dashi. “Karka damu kaci gaba da yi min addu'a, ina tea dina?” Saman bedside ya nuna min na hango cup d'in ba laifi yafi na dazu girma, saboda ya daga min cinya nasa riga yasa na shagwabe fuska ina cewa. “Toh ka dakko min na sha.” Ya dago kai ya kalle ni da idanunsa masu kama da ruwa a ciki. “Yadda kika ce haka zanyi Gimbiya sarauniyar zuciyar Salman bin Aliy.” Yana matsawa kuwa nayi saurin mikewa Ina zuwara yana waigowa. Dariya ya yi ganin yadda nake saurin saka rigar dan kar ya gani, ya matso yana cewa. “Madam wane dare ne jemage be gani ba?” Ina yatsina fuska nace. “Ai kuwa be ga na mutuwarsa ba.” “Wayyo dena ambato min mutuwa yanzu, ina son naga gudan jini na, ina son na nunawa duniya cewa komai lokaci ne dashi, mutum baya fidda rai da rabo.” Tea dina na karba duk da ya fara hucewa a haka na shanye shi tas, na kalle shi yana ta shirinsa na fita fada nace. “Naje sashe na saboda babu wanda yasan na dawo.” “KI bari ki shirya ni mana my love.” “Amfanin me zanyi ma wajan shiryawar tunda ba Iya nad'a rawani nayi ba?” Yana saka kayan sa na ciki yace. “Idan Ina kallon ki zan fi samun nutsuwa har na shirya tsab.” Babu yadda zan yi dole na koma bakin gado na zauna, Tunawa nayi da shifa beci komai ba, na mike na shiga hada masa coffee dan yafi son shi akan tea. Yana gani na ya shafa fuskata tare da cewa. “Allah ya yi miki albarka dear.” “Amin na gode.” Cake din da ya kawo min ban ci ba shi na hada na bawa yaci sannan nayi masa sallama bayan ya sumbaci goshi na ya fita ni kuma na nufi sashe na da sauri dan karma wani ya zo ya ganni da rigar shi. Ina zuwa sashe na kaya na nema na saka, hijabi na sanyi saboda gani nake kamar Ina fita za'a hango cewa ina dauke da juna biyu. Hankali na duk yana gurin Ammi, na fito, hadimaina suka ganni duk suka zube suna kwasar gaisuwa, zuciyoyon su cike da tambayoyi dan basu san ta kofar da na bi ba lokacin da na dawo, gashi duk babu mai Iya tambaya ta a cikin su. Zaune na tarar da ita da wasu baki, tana gani na ta sallame su cike da fara'a ta nuna min gurin zama inda dama can ne kamar parmanent seat dina idan naje. Gaishe da ita nayi cike da girmamawa ta nuna min warmer tace na zuba abinci, daman Ina da bukata dan haka na bude karamar naga wainar shinkafa ce tayi kyau sai kamshi take yi. Plate na janyo na diba tare da zuba miya wacce tasha man shanu da tsokokin nama. Ina ci Muna hira ta tambaye ni yan uwa na, na ce lafiya suna gaishe da ita. Kallo na kawai take da alama tana son ta gano wani abun a tattare da ni, amman zuciyarta taki amincewa saboda tasan babu ta yadda za ai hakan ta kasan ce. Kiran wayar ta shine yasa ta janye idanunta daga kai na, dubawa tayi taga Salman ne, ta dauka ya tambaye ta ita da waye a gurin tace Dije ya sauke numfashi tare da sosa keya kamar yana gabanta yace. “Ta...dai gaya miki cewa ba ta da lafiya ko?” “A'a sai dai ni naga kamar hakan, me yake damunta.?” “Ammie bata wayar.” Miko min tayi na karba tare da karawa a kunne Ina masa sallama cike da girmamawa har sunkuyar da kai. “My love ya jikin ki?” “Alhamdullah.” Na fada a takaice ina jujuya wainar da na gutsiro. “Ya baki sanar da Ammi wannan kyakkyawan albishir d'in ba?” Cikin tsantsar mamaki nace. “Kai! Tabdi wallahi bazan Iya ba da nauyi.” “KI gaya mata nima kunyarta nake ji.” “Nima wallahi haka bazan Iya ba.” “OMG, My Dijah sarkin kunya, ki fada zata baki tukwici.” “Na yafe wallahi.” “Shikenan kin samu abinci kici ko? Bana son kina zama da yunwa gashi ba ke daya bace yanzu.” Nasa wainar a baki Ina cewa. “Gashi Ina ci kaima a kawo Maka?” “Nooo bawa Ammi wayar.” Hannu biyu na mika mata sannan na juya naci gaba da cin abincin. Shi kuma yana ta kokawa da zuciyarsa yadda zai yi ya sanar mata zuwan jikanta. Sai da ya rufe ido sannan ya sanar mata Sai jiyowa nayi Ammi na cewa. “Kai alhamdullah masha Allah, Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana. Ina rokan Allah ya nuna min zuwan sa/ta lafiya, Allah ya tsare mana shi ya sauke ta lafiya.” Kasa amsawa ya yi a fili Sai a zuciyarsa ya amsa tare da katsewa. Ammie cike da zumudi ta nemo lambar Gwaggo tana fadin. “Abokin kuka shi ake gayawa mutuwa.” ji kawai nai tana cewa. “Allah ya yi Zaki ga jika... Eh wallahi yanzu yake gaya min.. Wallahi kuwa Gwaggo.. Amin ya rabbil amin a ci gaba da Taya mu addu'a... Toh shikenan..” Ai ban bari ta gama wayar nan ba na tashi na gudu saboda kunya da tabi ta dabaibaye ni. Ammie kuwa dariya tayi a gurin kuma ta kafa goshinta a kasa tana yiwa Allah godiya.... *YAREEMAH IBRAHIM-(KHAL)* *INCHEON INT. AIRPORT* A tsaye Khal yake, Da akwatunan sa guda biyu, Ya saqale wata jaka a jikin hannun akwatin. Waya ce a hannun sa da alama magana yake da wani mai matuk’ar muhimmanci saboda yadda yake sakin tattausan murmushi. Sanye yake cikin kananun kaya riga da wando ya d’aura overcoat akai, Samun waje yayi ya zauna akan kujera, Ya kira lambar da yai saving da (Yeobo-Bintu naah)🌷’ “Bintuunaahhh....! Lapia lou ina airport! Uhm...? Ki tayani da addua my love! Fushi kuma?” Mikewa yai da sauri tamkar tana wajen, Domin kana iya jiyo zazzakar muryar budurwar dake magana ta cikin wayar. Shafa kwantaccen gashin kansa yai yana jan kasan leben sa, Kallo d’aya zakai masa kasan sun hada jini da SAS. Ha’kuri ya shiga bata yana sake rage sautin muryar sa. “I’m sooo sorry yeobo (honey) Bansan fushin me ake dani ba, But kiyi hak’uri zan karb’i kowane punishment banda na rashin ki... Ina kaunar ki Dr. matar Dr. IN SHA ALLAH! Saranghaeyo ( I love you in Korean) .. An hak’ura? Masha Allah! Godia nake, Take kia love.” Katse kiran yai yana murmushi ahankali yace, “Kai.. mata.. sai a slow. Dole naje na bada hak’uri.” Wani kiran ne ya sake shigowa, Jikin sa na rawa ya dauka sahibar ce sai kuma yaga SAS ne. Dauka yayi da sauri ya gayda shi cikin girmamawa, Salman din ma na bashi amsa cikin kulawa, “Yasu Ammi da Abdullah...?” “Kowa lapia lou! Ka taho kuwa?” “Eh saura mintina kadan ina airport..” “Ai na kira naji busy.. Kanata waya.” Shafa sajen sa yayi yana daria, “Da wani ne...” “Ko dai da Dr. dinnan danaga itace wallpaper dinka ba.” Daria Khal yayi. Ya shiga shafa keya kunya duk ta kama shi, “Ayi hak’uri yallabai, Tuba nake.” “Ahh bakomai.. Allah yasanya alkhairi, Idan ka dawo komai ya daidaita sai ayi bikin a huta ko.” Da’di ya kama Khal da har sai da ya kasa boye murnar sa yayiwa SAS godia. “Yanzu aina zaka sauka kenan?” “Zan sauka Abuja yallabai...” “Wajen Dr....?” Nanma Khal yayi shiru yana daria ahankali, kafin yace. “No zanyi submitting wasu takaddu ma. “ “Toh Allah ya dawo da kai lapia Khal.. Allah ya bamu nasara, Ya dora mu akan makiyan mu.” Sallama sukai, Khal yayi hanyar departure.....! Zuciar sa dauke da adduar Allah yasa ya koma a sa’a... _Afuwan zafafa fans.. Ba zaku samu kibiyar ajali ba na yan wasu kwanaki. Saboda wani uzuri daya taso🤲🏻Dana kammala zan cigaba da posting IN SHAA ALLAH!_ _Yar uwa kinason karanta zafafa amma documents? To zafafa na harhada kayan su. Da an kammala Za’a yi documents dinsu duka akan Naira dubu d’aya da........_ Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️ ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _Wattpad: missxoxo00_ _PG:27_ _BOOK:2_ *GIM. KHADEEJAH* Kwance nake akan gado, Hawowata kenan daga kasa, Domin Ammi tace na dena zuryar zuwa sashen ta tunda yanzun bani kadai bace. Ajiyar zuciya na sauke fuskata na kumshe da murmushi, Kaunar da Salman da Ammi kemun yanzu ta kara nunkuwa, Wata irin tarairaya nake samu daga kowannen su. Gwaggo ta fada ma kullum cikin aikomin da tofi take, Addah Maryama ma kullum cikin zuwa ta duba ni take. Lamarin sai godiya ga Allah daya had’ani da miji nagari mai kaunata, Suruka ta gari da kuma yan uwan miji masu gatanta ni. Yanzu babu abunda na nema na rasa a duniya sai rashin iyaye, Wanda su Kawu daddy su Ammi suna iyakar ko’karin su wajen maye gurbin su. Sai dai iyaye daban ne a duniya, Ni yanzu da za’a kwace komai nawa a dawomin dasu sai nafi farin ciki. Kwakwar manja ta dake gefe na janyo na shiga ci hankali kwance ina lashe yatsu na. Cikin haka sai ga Salman ya shigo sanye cikin jallabiya hannun sa rik’e da flask din shayi da kofi da cokali. Tinda ya taho nake bin hannun sa da kallo domin ni yanzu banda bacci da ciye ciye ba abinda nake. “Zawjatii.. Maman unborn. “ Zama yai a gefe na yana kallo na cike da tattali. “Na’am Zawj.. Tea ne ko kunu?” Daria ya kyalkyale da ita yana shafa gefen fuskata, “Kunu ne... Ammi ta bayar akawo miki. Kunun gyada.” Yunkurawa nai, Zan mike yai hanzarin tare ni. “Yi hak’uri tawan. Idan kika tashe shi yana bacci fa? Ki dinga yi ahankali.” Na kalli shamilallen cikin nawa ina dariya. “O ni ‘yasu... Toh nide nide nide yunwa nake ji ai.” Na fada ina turo baki gaba cike da shagwaba. Zubamun kunun yai a kofi ya jinginar dani a k’irjin sa yana kafamun cup din akan baki na, “Ungo asha lapia.” Gani nai zai batamin lokaci na karb’e kofin na kafa kai na shanye, Sai danasha sau uku sannan naji ya isheni. Na wanko baki na. Na dawo kusa dashi na zauna. “Allah sarki Ammi naa..” “Ni Fa? Ni ba naki bane?” Hannuwana biyu nasa tafukan na rufe fuskata. Kunya ta kamani. “Ammin ce akwai kirki, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, Allah ya juyo da hankalin Yareemah Ibrahim agare ku ya waiwayo gida shima.” “Aaamin Yaa Rabbi...” Ahankali ya sumbaci tafin hannu na yana sake rike ni sosai tamkar Za’a kwace ni. Cikin rada ya shiga cemun, “Na fad’a miki wani abun farin ciki...?” Da sauri na gyad’a kai na ina kallon kwayar cikin idanun sa. Wadda nake samun nutsuwa sosai a duk sanda na kalle ta. “Khal... Wato Yareemah Ibrahim ya farfad’o daga sihirin kafewar da akai masa a korea. And Alhamdulillah hankalin sa ya dawo jikin sa. Zancen da nake miki ma ya kusa shigowa kasar nan ...” Bansan sanda wasu zafafan hawaye suka shiga reto a fuska taba.. “Nooo....! Kuka? Subhanallah! Mena miki Zawjati? Na fa’di wani abun daya tayar miki da hankali?” Ahankali na girgiza kai na, Nasa hannu na na riko nasa ina murmushi, “Kukan farin ciki ne Zawj.. Kukan dadi ne kawai. Shin Ammi tanada masaniya kuwa?” “Ah’ah tukunna dai... Akwai lokacin da muka gama tsara komai, Kinsan dawowar Khal masarautar nan akwai ruguntsumi fa. Saboda love kina ji?” Gyada kai nayi alamun ina sauraron sa. Cikin nutsuwa ya cigaba da cewa, “Saboda sun dauka har yanzu bansan matsayin Khal ba awaje na, Sun dauka har yanzu Khal na can yadda suka kafe shi, Kuma sun dauka har yanzu Ammi na cikin kangin rayuwa na rashin mu a kusa da ita... Kuma sun dauka dagaske bana haihuwa...” Na dago da sauri ina kallon sa. Ya gyada kai cikin tabbatarwa. “Ke haske ce acikin rayuwata Zawjatii, Na gaya miki kece mahadin rayuwar Salman ibn Aliy. Dake Allah yayi zamu samu KIBIYAR hallaka makiyan mu na masarautar nan. Domin kedin dashen Allah ce...” “Yanzu idan suka nemi kashe ni fa..?” “Karki damu da yardar Allah babu abunda zai faru dake da abun dake cikin cikin ki, Domin mun dogara da Allah shi din mubuwayi ne gagara misali.. Sai abu na biyu Dr. Fiddau zata dinga zuwa kullum tana duba lapiar jikin ki.. Sannan Za’a kawo amintattun hadimai da zasu dinga kula dake, Motsin ki, Baccin ki, shawagi, Abinci, anything dai daya dangance ki zasu tsaya akan ki. Kada ki manta kina da ni kuma ga Ammi... Ai zawjati ke yargata ce gaba da baya...” Nayi murmushin da hakorana suka bayyana, Duk kuwa da kasan zucia ta a dankare yake da fargaba sosai. Na gudun kar a hallaka ni da abinda ke tare da ni, Hannu nasa akan marata ina shafa wajen ahankali. Wani irin sanyi naji yana ratsa ni. Cike da karfin gwiwa nace, “Allah ya temake mu... Allah ya kara kare mu da kariyar sa. Mugun ji mugun gani Allah ya kiyaye..” “Aamin Zawjati.. Allah ya miki albarka, Ya kara miki so na a zuciar ki, Tunda nide duk minti sonki nunkuwa yake acikin zucia ta. Ke kuwa har yau baki gayaman wasu kalamai da zan tabbata kin mallakamun zuciar ki ba. Inaga sai na kara zage damtse sosai na yak’i ragowar burbushin kaunar m...” Ban bari ya karasa ba nai saurin hade bakunan mu waje d’aya, Ni kaina nayi mamakin hakan da nayi, Amma na tabbata hakan shine ka’dai zai iya bashi amsar tambayar sa. Sai da na tabbatar ya gamsu sannan na zare baki na ahankali. Ido cikin ido na kalle shi, “Waya gaya maka bana kaunar...? Ka cire dik wani waswasi dake tasiri azuciar ka, Ni Khadija daga rana irin ta yau.. Na mallaka maka zucia ta da gangar jiki na sai yadda kayi dasu. Ina kaunar ka, Kauna marar gauraye. Tun ina durbun lokacin Ina cikin SIRADIN RAYUWA, Nayi ta addua Allah ya bani miji nagari wanda zai so ni ya kaunace ni, Na maka ta larabci MIN QALBi na nake kaunar ka tsakani da Allah, Da ace dan adam yasan ABINDA KE CIKIN ZUCIYA to da tabbas zaka son matsayin ka awajena ya wuce ‘kima. Kada ka damu da masu mana SARAN BOYE zawj.. Domin Insha Allah ni Khadija dashen Allah ce, Na tsallake tarko kala kala na rayuwa, Saboda haka da yardar Allah sai na zamowa makiyanmu KIBIYAR AJALI.. Kai de ka zuba idanu...” Lumshe idanu Salman yai ya bude su akaina yana wani irin tsadadden murmushi, “Na yadda my love... Na kuma tabbatar kafin wata dayan dana kiyasta tacika a game dinmu dake, To tabbas kaunar zata ninku fiye data yau...” Murmushi nai nima na shagala da kallon kyakkyawar fuskarsa, “Tabbas kuwa Zawj.. Insha Allah lokacin nasan kagama dani, Na gama dilmiyewa acikin kogin kaunar ka.. Kalli tin yanzu ma bare nan gaba.. koya kace?” “Lalle na cancanci kyauta daga wajen gimbiya..” “Tabbas kuwa ka cancanta.. Amma hak’uri zakayi kata shi ka shirya zuwa zaman fada..” Hannuna ya kaiwa sumba me matukar ratsa jiki da bargo, Ya sake narkemun ajiki yana wasa da jelar gashi na, “Ai gaba d’aya gimbiya kin maida Salman tamkar ba sarki ba, Ni fa gaba d’aya mantawa ma nake da wata sarauta idan har ina gaban ki. Barin ace yadda muke dinnan jikin ki na gogar nawa, Gashin ki mai matukar k’amshi yana busa kamshi,...Zawjatii! My unending love for you is my vision, my hope, my goal, and my soul. Ina kaunar ki sosai Zawjatii na. Please ki bari naji dumin jikin ki, Dan kadan zamu yi fa. “ Ya karashe maganar yana kokarin dage rigata, Daria nayi kawai na kamo hannun sa na sunbata a hankali, “Zawj....” “Zawjatii..!” “Kayi hak’uri.. Ka tashi ka tafi dan Allah.. Kaji?” “Zan sa waziri fa ya zauna, Zance banda lapia, Yanzu zansa ayimun iso dashi.” “A’ah..! Ka tashi ka tafi.” “Yanzu haka zan tafi ba abun da zan samu?” Mikewa nai na riko hannun sa ya tashi tsaye shima, “Muje na shirya ka katafi kaji..?” Gyad’a kai yayi, Hannu cikin hannu muka koma dakin sa. Na shiga fito masa da duk abubuwan da zai saka. Na temaka masa ya kara yo wanka, Na shiga shirya shi ina masa kirari, “Kaga dawisu sarkin ado nawan, Da kwalliyar ka ala hallice ka Zawj, Taka a hankali lu’u lu’u abun son kowacce mace! Amma fa sai dai suyi hak’uri domin wannan lu’u lu’un nawa ne ni kadai.. Ko shaheedah sai ta kama kanta.” Murmushi naga yayi ya sake tallabo ni yana kissing kan hanci na. Na sunkuya ahankali ina faffesa masa turare ajikin kayan sa, “Kaga katangar zinare majingin mace, An gayshe da sarkin sarakuna, Mai basannabas, Tsarin jikin ka da hankalin ka na shugaba mai shugabantar masu rauni. Takawar ka daidai ranka ya dade mai dogon zamani, Sun buga sun barka ya zasuyi dakai? Girman kane Allah ya baka, Ya zasuyi?.. Waya isa ya amsa balle har ya amshe? Kai ka iya kai zakayi ranka ya dade.. Kai ne gaba muna biye. Nawaje na.. Allah ya dawomin da kai lapia..”Cc:OD Na k’arashe ina zura masa glasses dinsa cikin idanun sa, Lalle Salman anyi kyakkyawan sarki mai kyakkyawar halayya. Gaba salamun baya salamun. Wata iriyar runguma yayi mun, Ya saqalo hannuwan sa muna kallon kanmu tacikin mudubi ya d’aura kansa akan kafada ta. Nasa hannu d’aya ina shafa kwantaccen sajen sa... “Zawjatii na... Na biya ki da kai na, Ruhi na da Qalbi na. Na biya ki da amanata da dik wani sirrina, kece kofar mabudin alkhairi na, Kuma kece katangar mahallakar makiyana. Hakika ke kika cika Salman ibn Aliy ya zama cikakken sarki mai cikakken Iko....” Nai saurin riko hannunsa Na juya muna fuskantar juna, “Kalaman ka sunyi tsau.....” “Karki karasa rabin rai na.... Nan gaba kadan zaki tabbatar da hakan. Amma kafin sannan dole na baki ladan kirarin nan.” Daukata yayi a hannu ya kaini dakin da nake dazu ya kwantar da ni, Ya janyo bargo ya lullube kafafuwana. Ya zauna a gefe hannun sa cikin nawa, “Zawjatii naa.. Ina kaunar ki sosai. Zantafi fada sai na dawo, Amana addua” Ya karasa yana rungumeni kamar Wadda Za’a dauke a gudu, Cikin muryar lallashi ina shafa gadon bayan sa nace, “Allah ya kare mun kai, Ya dawo mun da kai lapia. Allah ya dora ka akan makiyan ka, Ya Kara maka madaukakiyar kasaita da kwarjini da nasara akan kowane lamuran ka.” Dak’yar na iya yage shi a jiki na kamar wani cingom ya sauka ta sashen sa hannun sa rik’e da rawanin da Za’a nada masa... *FADA*** Sai da Salman ya zauna dogaran sa suka kare shi sannan sannu ahankali yan zaman fadar sarki suma ‘d’aya bayan d’aya suka shiga shigowa ana fad’in sunayen su sai su zube su rissina su kwashi gaisuwa sannan su zazzauna gefe da gefe. Shi kuma Salman nadaga saman wata kasaitacciyar kujera yana hakimce. Kallon dukkanin su yake ta cikin bak’in gilashin dake idanun sa, Amman gangar jikin sa ce kawai a fada, Gaba d’aya zuciar sa da tunanin sa naga Khadija dake sashenta tana bacci. Haka dai zaman na fada ya kasance, Wannan rukunun suzo su kawo koken su, Wasu suzo neman tallafi, Sai sabbin tsare tsare da masarauta zata kawo, Wanda zaman ya kasance daga sarki sai manyan yan majalisar sa. Cikin haka Yareemah Abdulqadeer ya shiga yanata bubbudawa. Sai kirari dogarai suke masa, Ya baza babbar riga da tulin rawani akan sa. “Gayshe ka Yareemah Abdulqadeer, Gyara kintsi dakyau!!” Cewar wasu dogarai daga bayan sa. Wambai ya murmusa yana nuna masa kusa dashi, Abdulqadeer ya zauna, Dogari na cigaba da masa kirari “An gayda Yareemah Abdulqadeer, Dan sarki jikan sarki, Kaga hakimin waje, Mai girma makaman basannabas.” Sallamar dogaran sarkin kofa yai, Akabar fada daga sarki sai manyan yan majalisar sa. Kowa yana kawo tasa matsalar har akazo kan Abdulqadeer, Fuskar nan tasa ba rahama, Sai dai duk kwarjinin sa SAS ya dame shi ya shanye. Cikin k’asaita da isa yafara magana, “Ran sarki ya dade.... Sallah na dada ‘karatowa, Kuma dawakan yanki na duk sun jigata bazasuyi abun arziki ba wannan sallar, Shine nakeso asa ma’aji ya bada isassun kudi da za’a sayo wasu ba sai an dinga wahalar hayowa ba. Saboda wannan sallar na shirya gasar sukuwa da za’ayi da masarautar kudu... A ha’da da kudin abincin dawakan da kayan kwaliiyar su...” Salman yai murmushi kawai ta cikin rawanin sa. Kowa ya tsaya jin abinda zai tofa, Samun kansa yai cikin karfi gwiwa yace, “Kudin wajen waziri makudai nasa gaba d’aya a baka dasu Munaya kuyi hidimar biki, Wanda na tabbata har yanzu akwai sauran su awajen ka..” Abdulqadeer ya girgiza Kai yana sake bade rigar sa, “Wannan kudin kamar yadda ka umarta kudin biki ne kuma anfanin su ya kare, Tun tuni suka k’are, Ga ma’aji nan a gefe so nake ka bashi dama yanzu ya bada kudin.” Waziri dake gefe yai shiru, Salman yai gyaran murya kafin ya sake cewa, “Asusun masarauta yayi kasa Makama. Ka dada hak’uri zuwa shagalin sallar gaba. Zan sa a hayo dawakai masu inginci. Koya kace waziri?” Waziri ya gyad’a kai kafin cikin gasgata abunda sarki yafad’a Yace. “Hakane ranka ya dade, Sai a hayo dawakai masu kyau.” Wani tsaki abdulqadeer yaja yana kallon waziri, Da alamun tsabar bacin rai yama manta a’inda yake, “Kai dai babban munafuki ne waziri, A haka kake tunanin zan tafi tare dakai kana cin dunduniyata?” Waziri ya kalli chiroma (shine mahaifin Mama Huwaila wato mahaifiyar AbdulQadeer.) Chiroma yai saurin riko kafadun abdulqadeer yana kokarin janye shi, Abdulqadeer kuwa sai surfa zagi yake yana karkadawa waziri hannu. Shi kuwa Salman farin ciki ne fal zuciar sa ganin dabarar da yai taci. Gashi nan kansu yafara rabuwa. Bayan fitar Yarima Abdulqadeer, Galadima ya muskuta sosai yana karkada k’afafuwa, “Ran sarki ya jima har yaga ‘yayan kannen sa, Ko yaji sanyi anasa idanun...” Salman dai yana zaune akan kujera yana duban su, So yake yaji kuma yau da me suka zo. Waziri dake gefe duk kuwa da ransa na susar abinda AbdulQadeer ya masa bai fasa tanka zancen galadima ba, “Sarki na sauraron ka Galadima. Amma kalaman ka sunyi tsauri, Meke tafe daku kuma wannan zuwan?” Chiroma ya amshe zancen da, “Munzo ne akan maganar auren sa da mukace lalle yayi, A baya mun bashi wata d’aya zuwa biyu. Yanzu da yardar Allah mun soke wancen zancen. Nan da sati d’aya zuwa kwana ki goma mukeson ya bamu sunan wadda ya zaba acikin tsatson jinin masarauta.” Waziri ya fusata kamar gaske yayi kan chiroma, SAS ya dakatar dashi ta hanyar gyaran murya, Cikin nutsuwa hankali kwance yace, “Na amince...” “Ranka ya dade ka amince fa kace.. Ka amince? Akan me zaka amince akan abunda ba dolen ka bane?” Cewar waziri cikeda damuwa. SAS ya murmusa ta cikin rawani, “Kada ka damu waziri, Na amince.. Nan dukan ku iyaye na, Nasan babu wanda zaimun zab’en tumin dare. Na karbi zancen chiroma da hannu dubu.” Waziri ya shiga magiya yana rok’an SAS daya janye zancen sa kai kace gaske ne. Saboda yadda ya dinga bori tubaran kan lalle shi bai yadda da zancen dasu chiroma suka yanke ba. Shi kuwa SAS gyaran murya ya sake yi, Dogaran sa suka kare shi. Ya mike yai hanyar sashen sa ta baya. Ya barsu nan suna muhawarar yadda komai zai kasance. Ciki harda waziri dayafi kowanne zakalkalewa, Amman duk zancen da suke baya tanka duk abunda chiroma yake fa’da saboda abunda jikan sa Abdulqadeer ya masa dazu ba jimawa. Jiki na ‘bari chiroma ya kara kaskantar da kansa yana bawa waziri hak’uri. Waziri ya girgiza kai yana yatsina fuska, “Wato tun yanzu kenan yafara kirana da munafiki inaga idan mun dora shi ya zama sarki? “ “Allah ya baka hak’uri ranka ya dade. Haba wane Mutum, Shi ya isa ya fara ma bare yayin? Waya sa aka nadashi makaman idan ba kai ba waziri?” “Atoh shi nagani nima...” “Zanje na sami mahaifiyar sa yanzu ba sai anjima ba ranka ya dade, Ka Kara haku’ri, Kasan yaran zamani.” Ficewa ciroma yai jikin sa na ‘bari. Fada ta zama sai galadima da waziri. Waziri yai ajiyar zuciya yana kallon galadima kafin yace dashi, “Tun ba’aje ko’ina ba kaga abunda nasha gaya maka zai auku ko? To wannan kadan ne akan nan gaba. Shiysa nace maka muyi meyiwuwa mu san abinda zamu sa agaba, Domin idan muka kuskura muka dora abdulqadeer sarkin basannabas to ina tabbatar maka dacewa a rannan zai tube mana rawanin mu. Kaga dukkanin mu jikokin mu mata ne, Gwara Kai akwai Ilyasu.. Shima yaro ne wannan ba wanda zai dora shi akan mulki. Amman chiroma fa? Dukkanin jikokin sa mazan sun isa su gaji sarautar nan, Kuma kasan tabbas idan mulki ya koma hannun tsatson ismaila Rabo.. To akwai bahaguwar matsala.” “Ranka ya dade duk abunda ka fada gaskia ne, To amma ina mafita?” “Mafita d’aya ce... Wadda Idan na gama bincike akanta zuwa jibi zan sanar da kai..” Haka dai suka cigaba da yan zantattukan su, Daga karshe sukai wa juna sallama Kowanne ya kama gaban sa. Salman dake dakin sirrin sa yana saurarar dik abunda suke cewa.. ahankali ya danna wani madanni dake dauke da tambarin ‘file saved...’ Mikewa yai ya fice zuwa sama, Ya le’ka dakin da Khadija take ta bacci kamar Kasa. Dakin sa ya koma yai wanka da alwala hade da d’akko Qur’ani ya bude ya fara Karantawa... Zuciar sa dauke da adduar Allah ya basu nasara akan wannan ruguntsumi da ke tunkaraso nan kusa......... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥. _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _B28_. *GIM. KHADEEJA!!* ***Sosai nake samun kulawa ta kowane bangare, Sai dai fa Salman kulle yake mun yanzu, Karshen fita unguwa ta kuwa daga kasa sai bakin gate shima don saboda exercise, Ranar asabar da yamma Kawu daddy ya kira ni da kansa yake sanarmun za’a kawo kudin su Ya Shukrah da kayan lefe bayan sati biyu kuma ayi shagalin biki, “Allah yasanya alkhairi Kawu Daddy, Zan shigo In Shaa Allahu!..” “Ah keda bakya jin dadi? Ba sai kinzo ba Khadija, An hutasshe ki, Ya jikin naki?” Shiru nayi, Mamaki duk ya cika ni, Kenan Salman barbada zancen cikin nan yake tayi? Kunya duk ta dabaibaye ni, Dakyar na iya amsa masa ina sunne kai tamkar yana gaba na, “Da sauki Kawu daddy...” “Toh Allah ya raba lapia.... Hajia ma zan sanar mata zata kira ki.” “Toh Kawu....” “Ya sanarmun ma idan an kwana biyu zaki ziyarci durbun...” “Eh Kawu” Na bashi amsa duk kuwa da bansan yaushene Salman din zai barni naje ba. “Toh Allah ya kaimu.. Ki kula sosai Khadija, addu’oi na neman tsari, Nima zansa anan ayi ta saukar qur’ani, Allah ya kauda idanun makiya akan ki da abunda zaki haifa.” “Insha Allah Kawu... Nagode Allah ya kara arziki ya bada nisan kwana mai amfani..” Sallama mukai wa juna na kashe wayar, Ina kambaba rashin kunyar Salman akan cikin nan duk ya barbadawa dangi. Daga samun sa. Na kalli cikin nawa ina mamakin yadda yake a shamile haka amma ina dauke da ciki? Gama waya da Kawu keda wuya kenan sai ga shigowar call din Salman, Na dauka a hankali ina mai gyara zaman dankwalin kai na, “Zawjatiii...” “Na’am Baby! Ya kake?” “Ba dadi....” “Meyasa?” “Saboda bakya tare da ni..” “Dazu fa muka rabu da kai..” “Duk sanda nake tare da ke, Banason mu rabu ko na second d’aya! Ina kaunar ki love.” Shiru nayi ina murmushi kawai, Kalaman sa na dada ratsa bargon jiki na, “Love... Kina jina kuwa?” “Uhm! Ina ji.” “Nayi lefi ne, Naji anyi shiru?” “Eh mana kayi..” “Ki shirya yanzu... Zanzo zance. Zanzo ban haku’ri.” Kit ya katse kiran, Nabi wayar da kallo, Goma na dare saura kwata. Yana iya? Mikewa nai na shiga band’aki nayo wanka, Badan inason kamshin turaren jikin sa ba Allah ba wani zance da zan bari yazo, Wasu riga da wando nasa na English wears nayi packing gashin kai na. Ba dadewa sai ga kiran sa ya shigo, “Ki sakko ina k’asa...” Sai dana mula na huta tukun sannan na mike na sauka kasan, Ina hango shi akan kujera ya bada baya yana danna waya, Tun kafin na karasa ya taro ni yana riko hannu na, “TubarkAllah! My queen.. Kinyi kyau sosai. Komai nake me mekyau ne, Sahibar zucia ta.” Janyo ni yayi zuwa jikin sa yana shafa gadon baya na, Duk kuwa da fushin da nake dashi, Hakan be hanani lafewa a jikin saba, Na cusa fuska ta a k’irjin sa ina shakar daddadan kamshin dake fita daga jikin sa, “Ina fatan za’ayimun afuwa akan kowane lefi ne da nayi? Duk kuwa da bansan laifin da nayi ba.” Hannu nasa ina duddukan kirjin sa, “Shine.. Shine.. Shine.. Ka fad’awa Kawu daddy zancen cikin nan.. Meyasa?” Dariya yayi yana shafa gashin kai na, “Ayimin afuwa my love, Na kira shine na gayda shi yake tambayar ki? Nace bakida lapia... To kinsan manya da gano duk wata kwana da kayi, Har yake sanarmun za’a kawo kudi da kayan sisters dinki...” “Ya gayamun wai basai naje ba, Ni gaskia inason zuwa.” “Kiyi hak’uri! Zakije bikin da yardar Allah, Amma ganin kayan ne dai ki hakura kya gani daga baya, Kinsan hayaniyar mutane, Dr. ta hanaki, Kinji? Sai me kuma nayi na kara bada wani hakurin?” “Shikenan ya wuce...” Sumbatar gefen kunne na yayi, Ya koma kan fuskata daga nan ya dawo tafin hannu, Nai saurin riko bakin ina murmushi, Shima murmushin yayi ya cigaba da cewa, “Wata dayan dana deba mana akan game dinmu ta cika, Kuma naga nasarori sosai ta bangaren ki sai dai abu d’aya kacal ne da har yau banji daga bakin ki ba” “Me?” “Yadda nake nuna miki kulawa.” Ya fada yana tabarbare fuska kamar zaiyi kuka.dariya na shiga yi, Mikewa yai ya dakko wata leda acan kasan kujera, “Na manta nazo da toshiyar baki....” Karba nai da sauri jiki na bari na zazzage ledar, 1 liter bucket ne na mint Ice cream da kuma sausage shawarma guda 5 da zafin su, Sai tarin chocolates. Habawa bararrajewa nai zan fara ci ya ri’ko hannu na, “Bara mu kira Ammi dai muji ko? Ko zaki iya cin komai.” “Na hakura da fushin da nake yi fa, Dan Allah ka kyaleni naci... Wallahi bakaji yadda babyn ka yakeso yaci ba.” “Toh i sauri ci.” Ya fada yana cire takardar jikin shawarman, Nayi murmushi kawai, Ya samun a baki, Na k’arba gaba d’aya na faraci ina gyada kai saboda dadi. Sai da nacinye har guda 3 nasha ice cream din sosai sannan naji na koshi, Banyi aune ba naji harshen Salman kan lebe na yana lashe gefen bakina, Daganan lamarin nasa ya zarce zuwa ga kiss din mai gaba d’aya, Ture shi nai dakyar , “Abu ne awajen shine na cire.” “Daga cire abu kuma sai ka...” “Sai me??? Dan kadan nayi fa love. Tuba nake to. Sai albishir na biyu amma gaskia bazan fada ba sai kin bani tukwici.” “Me kakeso?” “Kalamai daga zuciar ki... Wanka tare, Sai dan kisses and hugs haka masu zafi kafin miyi bacci.” Wannan Salman din A ne wajen wayo ne, “Na yadda..” “Na samu gwamna da kai na ba’ai keba, Munyi magana sosai ta fahimta dashi akan yayi hak’uri da batin tashin yan yankin gaba d’aya, Illa dai gonakin dake gefen yankin, Za’a biya manoman ayi babbar makaranta awajen ta kwana. Hakan yayi miki ko?.” Bansan sanda na wawuro shiba na rungume abuna tsam ina hawayen farin ciki, “Nagode, Nagode, Nagode... Allah ya biya ka da alkhairi, Ya baka abinda kake nema dunia da lahira. Ina fatan gwamna yaji da’din shawarar taka?” Handkerchief ya janyo a aljihun sa ya shiga gogemin hawayen cikin wani salo, “Bar kuka My love.. Ai nima garin mu ne, Hakki na ne nayi abunda ya dace kinji? Kuma ya gamsu da shawarata dari bisa dari. Nasa a musu titi kyauta daga gare ki. So muje a wanke ni tas.” Zanyi magana ya dauke ni a kafadar sa muka hau saman tare, Bai direniba sai akan gado, “Baby kin kara nauyi tubarkAllah.. Oya ciremin kayan ki wanke ni ki sabe ni.” Sai na samu kai na da ce masa, “Wani lokacin sai nayita mamakin haka kakeda magana? Mutane bazasu taba yadda ba.” “Ke ka’dai nake iya sakewa nayita magana sosai, Ni kaina Ina mamaki, Kuma sai bayan na auroki bakina ya bud’e haka, So kaunar kice sila my love.” “Lalle na ciri tuta, Godia nake takawa... Takawarka lapia sarkin sarakunan nigeria baki d’aya, Nagode kwarai da duk kanin alkhairin ka gare ni, Hakika mutanen durbun zasu ji da'din wannan titi, Allah ya biya ka da mafificin alkhairin sa. Da sauran sarakuna zasuyi koyi da kai, Hakika da ansamu ci gaba sosai a kasar nan. Lalle Ka musu zarra nawan. Muje band’akin kafin na canza ra’ayi.” Da sauro ya mike, Hannu cikin hannu muka shjga band’akin, Anan ma sai da muka bata lokacin yin wata soyayyar kafin mu fito mu shirya cikin kayan bacci. “Saura kalaman da sauran aiyukan ladan.” Daria nayi jin wani wayo na daban. Kwanciya mukai akan pillow d’aya muna kallon juna, Hannun Salman na cikin jiki na yana yawo dashi. Cikin lumshe idanu nasa hannu ina shafa kwantacciyar girar sa, “Miji na sinadarin rayuwata, Tauraro mai qawata rayuwata, Zuma naaa, A Ido da kyawun kallo a baki dadi mai dad’ad’awa, Salman ibn Aliy bin Salmanu dina nawa ni kadai, Zaki kake ga isa ga kasaita....” Na karasa fada ina rufe bakunan mu waje d’aya, Nayi saurin jan zanin gado na rufe mu gaba d’aya, A ranar duk wani abu da Salman keso biye masa nayi, Na kuma yi amfani da karatun hazikar nan *BillynAbdul* marubuciyar da nake bin books dinta wajen ganin na faranta masa nima daren ranar Salman kuwa..Harda hawayen farin ciki, Ya shi mun albarka fiye da tunanin mai tunani, Tare da zayyano abubuwan alkhairi kan sune kyautata,Ni dai biye masa nayi kawai muka gurji lobayya tamkar cin kwan makauniya... *MAI BABBAN DAKI...* Fitowa tai daga kitchen, Hannun ta dauke da food flasks da flask na shayi, Sai wani tray daya sha kayan alatu akai, Umma Hansatu (Amintacciyar hadimar ta) Na gefen ta tana shirya kayan abincin acikin wani tsaftaccen kwando. “Ranki ya dade dole gimbiya da mai martaba suji dadin abincin nan, Tun daga k’ofar bayi ake jin kamshin sa fa, Dad’in ‘dadawa kuma da hannun ki kika sarrafa komai.” Ammi tayi murmushi kawai tana gyaggyara gyalen da aka rufe kwandon dashi. “Hansatu kenan, Allah yasa yadda yayi dadi a hanci a baka ma yafi haka dad’adawa..” “Aamin ranki ya dade. Ai dole nema yayi dadi. Ina dawowa daga aiken nan zan kwashi nawa ganimar dad’in. Allah dai ya kara karya asirin da akai na shiga tsakanin ki da yaran ki, Ya waiwayo da hankalin Yareemah Khaleelullahi gare ki...” Ammi ta fad’ad’a murmushin ta, Kafin ta dan sake matsawa daf da Umma Hansatun. Murya kasa kasa ta shiga ce mata, “Ai Hansatu wata muhimmiyar magana nake son sanar dake, Amman bansan koda wasa wani yasan da ita, Kin san dai yadda masarautar nan take ko?” “Insha Allahu ranki ya dade babu matsala, Allah dai ya kara miki lapia da nisan kwana mai amfani.” “Aamin Yaa Rabbi! Tare da ke..” “Ina sauraron ki ranki ya dade, Allah yasa alkhairi ne kunnuwana zasu jiye mani, Kuma Allah ya bani ikon rufawa wannan amana asiri.” “Aamin! Zancen shine, Kinga dai kusan ko yaushe a dan tsukukun nan, Ina tura ki sashen gimbiya Khadija ki bawa falaki abincin ya karba ko? Bakida masaniyar abincin wanene acikin su ko?” “Allah yaja zamanin ki, Wannan haka shike.” “Toh abincin gimbiya Khadija ne, Harda shi mai martaban, Amma dai da abunda yasa akeyin sa hususan saboda Khadija ne... Ki tayasu da addua, Uwar dakin naki Allah ya albarkance su da...” Zubewa Mama Hansatu tayi tai sujjada tana godewa Allah, “Allah mungode maka, Allah abun godia, Allah Alhamdulillah! Masha Allah! Ubangiji Allah ya bata lapiar sauke shi lapia, Ya yiwa abunda za’a haife albarka. Allah ya kauda idanun makiya akai ya inganta.. Kai Alhamdulillah!” Mikewa tai tashiga taka rawa, Ammi na dariya ahankali Itama farin ciki fadade akan fuskarta. “Aamin Hansatu! Aamin. Yanzu sai ki hanzarta ki kai musu, Kuma idan da hali ma so nake kije ki zauna da ita, Kinga shi shi kullum yana fada, Gashi sauran hadiman nata ba wasu manya bane.” “Zuwa kai ran ki ya dade, Me zai hana? Da yardar Allah zan koma da gari yai duhu.” “Masha Allah! Toh Allah ya yi albarka.” Gyaggyara mata komai tayi, Umma Hansatu ta dauka ta nufi sashen Dije, Tana zuwa yau har ciki akai mata iso tashiga. Dije tayi murnar ganin kuloli shake da abinci, Zaman dabaro tayi tashiga ci hannu baka hannu kwarya. Ta kora da kunun tana shiwa Ammi hamdalah. “Nagode Umma Hansatu, Allah ya saka da alkhairi.” Umma Hansatu taita mun addua kafin ta mike ta sauka ta wanko komai, Ta dawo tana mammatsa kafata dakemun ciwo sosai, “Ai uwar gijiya tace na dawo na zauna dake idan babu damuwa, Nace babu zan dawo idan gari yayi duhu. Hakan ya miki??” “Kwarai ma kuwa sosai Umma Hansatu, Allah sarki Ammi ina godia sosai. Allah ya saka da alkhairi.. Yanzu ma kiyi zaman ki ba sai anjima ba dan Allah.” “Tuba nake ranki ya dade, Wai da so nake na dan d’akko abubuwan da zan bukata.” “Eh da haka! Toh Allah ya kaimu.” Mun dan jima muna hira sama sama, Kafin Umma Hansatu tayimun sallama tatafi. Ni kuma na bararraje awajen raina cike da dadi, Inata sakawa Ammi da alhairi bisa ga dawainiyar da take yi da ni. *GIM. SHAHEEDAH!* Tana tsaye tana kallon bango da alamun wani tunanin take, Can taja tsaki, Ba jimawa suka gama waya da hajian su, Ta Kara bata haku’ri da sake dorata akan yadda zata b’ullowa lamarin, Ajiyar zuciya ta sauke tanata mita kamar zararriya, Harda hawaye, Tana mai jujjuya kanta gwanin ban tausayi, “Wayyo Allah na, Salman kaci amanata, Ta tabbata kai da yarinyar nan kunyi auratayya. Shikenan ni shaheedah dole na sauya taku. Wayyo Allah na. Mena rage maka da har zaka karo aure? Kodan ba ganina Kayi kace kana so na ba Eh? Kodan auren had’i ne? Salman why? Why? Why?” Tashiga ball da flower vase din da aka Kawata su a parlorn, Cikin haka jakadiya Abu tashiga kanta a kasa, “Ranki ya dade gani.” “Jakadiya kin munafurce ni, Shin nawa aka biya ki akan uban kudaden dana baki da har kika dena kawomun zancen mai martaba Eh? Shigar sa futar sa komai nasa da duk abunda ya aikata nace ko a rubuce ne ki gwajajjala ki kawomun. Ba magana nake miki ba?” “Tuba nake ranki shi dade. Babu wanda nake kawowa rahotan sashen mai martaba sai ke, Amma Idan k’arya nake a abunda zan fada kisa sarkin yan lufdi ya zanemun duwaiwai. Mai martaba da kansa ba ai keba ya jaddadamun karna kara shiga sashen sa, Iyakata harkar fada da yiwa al’ummah iso bayan haka yace komai ya sahalemun na de nayi na daga ayyukan dana keyi a baya.” “Ya isa, Salman dinne zai ce ki dena zuwa sashen sa? Salman din ne zaice ya cire ki a al’amuran sashen sa bayaga ison fada kawai? Toh waya dora akai? Idan kikai mun Karya to tabbas zansa amiki jina jina tare da zaman gidan yari na lokaci mai tsawo.” “Allah yaja da ran gimbiya, Abunda labbana suka furta gaba d’aya babu karya jikin sa. Falaki da Alhassan babban bafade, Su mai martaba ya dora akan komai nasa da yankin kofar kudu baki d’aya..” Hannu kawai shaheeda tai mata alama data tashi taje, Jakadiya na fita shaheedah ta rafka tagumi tana jijjiga kai, “Lallai Salman... Cin amanar har ya kai haka? Wacce irin soyayya kuke haka da har cire jakadun ka daga bakin aiki.?” Kwalawa hadimarta kira tayi tazo jikin ta na rawa, Ta shiga umartar ta kan leken asirin da zatai mata akan shige da ficen Salman, “Sadiya sunan ki ko?” “Eh ranki ya dade.” “Yauwa ki kula sosai da duk abubuwan dana gaya miki, Karki batamin aiki kin daiji labarin abunda nayiwa Batula data batamun aiki ko?” “Eh ranki ya dade, Insha Allahu zaki same ni me cikar aminci da gaskiya.” “To tashi kije.” Fita tai, Ita kuma shaheedah ta shige cikin dakin ta tana kokarin sake kiran ta hajiarta a waya. *F A D A * GABA d’aya an hallara anata fadanci, Wani zancen Salman ya tanka wani yai shiru, A haka har aka kammala. Manyan yan majalisa suka zauna. Don sake zantawa da sarki zama na biyu. “Sarki na sauraron ku. Ayi a gaggauce saboda yaje ya huta.” Chiroma ya matsa gaba yana rissinawa, “Allah yakara maka Lapia jibi ne daurin auren nan dakace ka amince.” Nan Kowanne ya dauka wambai nayi, Galadima na karasawa. Salman dai duk yana sauraron su har suka kammala. Yai gyaran murya yana cewa, “Toh dik naji batun ku.. Kuma... Na amince da fari sanda kukai min zancen ban tubure ba nace na yadda a auramun su, To bayan munyi haka, Sai naji sha’awarar karanta rayuwar sarakuna na baya na yankin basannabas, Na karu kuma na ilmantu sosai. Waziri ka karanta ko?” Waziri ya kad’a kai cikin tabbartawa, kamar gaske. SAS ya cigaba da cewa, “Na kwadaitu sosai da yanayin tsarin mulkin su, Musanman tsatson Masekiri Tajiri, Suna mulki ne bisa tsari da bin doka, Kuma dokar ta hau kan kowa komai girman rawanin mutum , Kai Allah ya jikan magabatan mu...” “Aamin. “ Suka amsa baki d’aya, Kowannen su ya gaza fahimtar inda zancen SAS ya dosa. Murmushi yayi kafin ya cigaba da cewa, “Batin na karo aure babu.. Bank’i ba nan gaba Idan ni na canza ra’ayi, Wanda gaba d’aya yanzu dai ni Salman ‘Da ga Aliyu jikan Salmanu babban Da ga Ibrahim... “ Bai karasa ba galadima ya mike har yana tuge rawanin sa, “Akan wane dalili? kai ka isa ka ki amsar abinda muka yanke...?” “Na isa Baba.. Duk wani hukunci da za’a yanke inde akwai cutarwa aciki magabata sun rawaita cewa Kayi fatali dashi.” “Bangane ba ranka ya dade... Shin wanene zai cuce ka mai martaba? Waya isa balle har ya isar?” Cewar waziri yana kallon su galadima ta wutsiyar idanu. SAS ya daga kai yana dan sake daga muryar sa sama, “Inaga ba kuma lura da yanda aka sauya tsarin kayan cikin fada ba...” Yana rufe baki Kowanne ya shiga duddubawa, Sosai gashinan an caccanza yanayin zaman wasu abubuwan, Duk kuwa da dai kayan ciki ne dai, Salman ya cigaba da, “Shekaran jia ne nasa dogarai su canza yanayin tsarin saboda karbar bakuncin matemakin shugaban kasa, Badan ya fa’di zuwan nasa a kurarren lokaci bama da sabbi za’a zuba komai. Toh Allah cikin ikon sa, Dogarai na caccanza tsarin ciki ne sai sukayi gamo da wani bakin tsibbu.” “Ba’kin tsibbu ranka ya dade?” “Kwarai waziri.. Gaba d’aya duk kusurwoyin ma’ajiyar abu an dasa tsibbu a kasanta, Wani abun tsoratarwar ma shine har kasan kujerar da nake zama sai da aka hak’o wata kwalba mai dauke da layoyi wadda gaba d’aya nasa an bincikamun duk dan a cire ni ne daga karagar mulki, A cutar dani a kuma lahantamun rayuwa... Waziri dakai ka’dai na yadda shin a ganin ka zan yadda da zancen su wambai na cuci kai na na ki kuma koyi da yadda sarakunan magabata su ka zartar da tsarin mulkin su?” Jikin waziri sai ya nemi fara rawa yai azama ya dawo gaban SAS yana rissina masa, “Allah yaja zamanin ka.. Ban fahimce ka ba, Ace ina cikin masarautar nan aka aikata wannan danyen aikin? Toh Allah ya Kara maka Lapia shin anga sunayen wanda suka binne tsibbun?” SAS ya girgiza kai yana murmushi, “Waziri.. Kwantar da hankalin ka, Lapia lou nake, Kuma na tabbata babu sunan ka acikin wanda suka yi, Koma dai suwa nene yan majalisar sarki ne. Bazan kira suna ba, Ko suwaye sunsan kansu, A takaice dai nasa an kona duk abubuwan da aka tono... Saboda haka maganar karo aure bazan yi ba gaskia.” Wambai ya sake mikewa yana kumfar baki, “Toh kai kanada yakinin an binna ne don a cuce ka? Kuma ni banyadda ba gaskia wannan zance ne irin naka don ka kawo yadda Za’a fasa auren ka. Ko kuwa?” Su Galadima suka fara tofa albarkacin bakin su, Waziri yai musu alama da suyi shiru. “Ranka ya dade ka gafarce ni, Gaba da baya kanada makiya a masarautar nan, Baka gani wasu ne daban suka so suga bayan ka..?” “Waziri!” “Allah ya ja zamanin adalin sarkin mu.. Tuba nake.” “Bakai lefi ba Waziri... Da kai d’aya tak na yadda kaf masarautar nan. Kuma nasan ba zaka hada kai da wasu ba don acuce ni, Saboda haka ka kara sanarwa su wambai nace bazan karo aure ba, Wannan magana an fasata, Domin Za’a iya auramun wa’enda za’a hada baki dasu, zasu shigo su kashe ni, Allah basshi nan gaba idan nayi ra’ayi don karan kai na na karo auren.” Gyaran muryar da yai ne, Dogaran sa suka yayyabe shi ya mike ya fice hankalin sa kwance yabar su waziri suna tattaunawa akan zancen, Kowanne tamkar zai amayo wuta dan bakin ciki. “Sannu ahankali kunata batamun shiri, Agaskiya nayi dana sanin hade kai na da ku..” Cewar Waziri cikin tsantsar bakin ciki, Su wambai suka shiga bashi hak’uri, Waziri ya tuge rawani ya shiga fiffita dashi yana sharce gumi duk kuwa da na’urar dake sanyaya fadar. “Ranka ya dade.. Ni Ina ganin hargagiya ce kawai don kada a aura masa su... “ Waziri ya watsawa wambai dayai maganar harara yana sake sharce gumin fuskar sa, “Kai dai wani lokacin idan kayi magana sai na rasa tayaya kake bari tafito saboda rashin amfanin ta. Hargagiya? Bakasan ire iren abubuwan nan zasu zama yadena yadda dani ba? Idan ba yarda a tsakanin mu kuma kuma taku batayi kyau ba kuwa.” “Tuba nake ranka ya dade... Ni sai nake gani kamar yaron nan tunanin sa ya fara dawowa, Du bada yadda yake magana cikin izza.” Cewar chiroma. “Anya kuwa? Banaji gaskia, Domin da hankalin sa ya dawo dole zai waiwayi mahaifiyar sa..... Yan uwan sa, Dama karbar ragamar mulki gaba d’aya batare da bata lokaci ba. Gigin auren sa da yarinyar canne yake dibar sa.” Waziri ya bashi amsa cikin tabbatarwa, Duk suka aminta da zancen sa, Kowanne ya shiga tofa albarkacin bakin sa. “Yallabai ya za’ai kenan yanzu? Ina mafita?” Wambai ya dukar da kai kasa yana tambayar Waziri cikin girmamawa. “Maganar ‘karin auren sa a soketa gaba d’aya kawai, Kowa yaje yai tunanin wani abun da zamu yi amfani dashi wajen yakarsa har ya hakura ya sauka ko mu hada kai da sauran yan majalisa a sauke shi..” Da haka duk suka tsaida magana d’aya, Maganr karin auren SAS an fasa, Sai sun bullo masa ta wani wajen da bai Zata ba. Duk abunnan da suke SAS na saurarar su yana kuma ganin su ta na’urar computer. Murmushi yai irin na gefen bakin nan kafin ya sake danna madannin nan dake adana masa dukkanin bidiyon sirrin sa..... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _B29_ *SAS* Yana kishingid’e akan d’aya daga cikin saitin kujerun dake dakin sa, Dake wani lokacin idan kambun mulkin suka motsa masa to ko dijen sai dai tazo da kanta wajen sa, Ya kan debi lokuta shi kadai yana dik wasu harkoki da suka shafe shi. Toh yanzun ma shi kadai ne, Ya tsurawa tv idanu can yayi tsaki ya kasheta gaba d’aya. Wayar sa ya janyo ya kira Yareemah Khal. Wanda ke Abuja har yanzu, Khal ya gayda shi cikin girmamawa, “Kana lapia...?” “Lapia qalau ranka ya dade, Ya wajen su Ammi?” “Tananan qalau, Duk lapiar su lou Khal.” “Ya gimbiyar mu, Ina fatan anata kulamin da little nephew/niece dina?” Daria mai sauti SAS yayi, “Alhamdulillah uncle Khal... Ya Abj da Dr.?” Khal a bangaren sa kuwa shafa k’eya yayi yana tuno shagwabar data gama masa yanzu a waya. “Lapia Alhamdulillah Yaya.” Ajiyar zuciya Salman ya sauke yana jan kasan leben sa, “Ka jini shiru kwana biyu ko?” “Tuba nake ranka ya dade. Ai na kikkira baka d’auka, Sai na kira falaki yake cemin lapia qalau wani aiki ne ya sha maka gaba.” “Wallahi kwana biyu inata yadda zan bullowa lamarin su waziri ne, Alhamdulillah dai plan A was successful. Zancen aure an soke shi, Ina jiran naga iya gudun ruwan sune kafin na saki babban bomb din ya tarwatsa su..” “Allah sarki Yaya! Allah ya temaka ya bada sa’a da nasara akan abunda aka sa agaba...” “Aamin Khal! Afuwan ka kara dakatawa dai nan gaba kadan zaka dawo..” “Babu komai ranka ya dade, Allah ya kai mu lokacin ya dora mu akan makiyan mu, Aamin.” “Aamin Khal.... Na Dr.” Murmushi Khal yayi wanda har sai da SAS ya jiyo shi, Sallama sukai bayan sun taba hira kadan. Daganan SAS ya kira Abdullah a waya nanma suka gaysa. Yana kammala duk wayoyin da zaiyi ya jingina kansa sa da kujera yana lumshe idanu. So yake kawai ya had’u da Ammi ya ganta ido da ido, Duk video calls din da sukeyi yafuso yaganta a zahiri, Tun hawansa yana sarki bai kara sanyata a idanun saba (Zahiri) har rana i ta yau... ***••. ***••. ***••. Fitowa tai daga sashen ta sanye cikin kayan alfarma, Taci ado sai yauki take yi, Dogarai sai kirari suke mata, “An gaishe da gimbiya matar mai martaba, Diyaga sarki Ibrahim hashimu na Bullo. Kun gaji sarauta tun zanin goyo. Gyara kintsi dakyau.” Suna tafe itada Sadiya hadimarta zasuje sashen mai martaba, A hankali shaheedah kewa sadiya magana ba zaka taba cewa tana motsa baki ba, “Kince har yanzu bata fitowa ko?” “Eh ranki ya dade, Bata fitowa kwata kwata, Wasu na zargin kila bata cikin masarautar ne.” Murmushin fuskar shaheeda ya fadada jin an ambaci kila dije bata gidan ne. Zata shiga bangaren Salman ta juya ta kalli bangaren dije ta zabga masa harara sai kace dijen tagani a Zahiri, “Shegiya! Allah yasa kinbar masarautar gaba d’aya kenan.” Shigewa ciki tayi kanta tsaye, Ta kwankwasa dakin Salman, Yana hakimce ya gaji ya kunna tv yana kallo. “Yes.. Come in.” Shiga shaheedah tayi tana rangwada, Salman ya d’ago yana kallon ta, Tayi kyau sosai tamkar saliha, Amma a zuci ba Allah a ranta. Tuno lokacin da aka fara hadasu aure yayi, Shiru shiru ga kyau ga iya kwalliya. Ashe ashe ba son tsakani da Allah take masa ba, Ta hada hannu da miyagun mutanen cikin masarauta dake nufar sa da sharri da mugun alkaba’i, Ya sake narke idanu yana kallon ta ta mika masa hannunta ya ri’ko yana danne bacin ransa. Zama tai agefen sa tana kallon sa. Ba gilashin data saba ganin sa dashi kullum, Karo na uku kenan da tadena ganin sa dashi a idanun sa. Shi kuwa Salman kallon ta dayake tambayoyi ne fal a kirjin sa akanta. Shin meyasa ta masa karyar shine baya haihuwa? Take cutar sa ta bayan fage? Ajiyar zuciya ya sauke jin tanata masa magana, “Na’am! Shaheedah....” “Darling...!” “Ya kike?..” “Lapia lou, Ina kewar ka sosai my king..” Murmushi ya ‘kakaro yana duban ta ahankali, “Nima haka...” “Ina mamakin canzawar ka kwana biyu.. Ka dena using glasses dinka, Sannan yanayin ka ya canza sosai.” “Ko? Bakyaso na dena?” Ya samu kansa da tambayar ta haka yana satar kallon agogo gudun kar Dije ta shigo. “Nooo! Ya kara maka kyau hakan. Kawai dai ka dena saurin hannu kaji?” “Insha Allah bazan kara ba.. Bakin ce kin yafemun ba ko?” “Na yafe..” Tafada tana dora kanta akan kafa’dar sa. “Inada meeting... Shaheedah.” “Okay! your honor, Zan...” “Zan zo later.” Shaheeda ta fadada murmushin ta, Zancen dijen da zata kawo ma tsabar farin ciki sai ta mance, Ta futa da sauri bayan ta masa sallama ta koma bangaren ta. Yana ganin tatafi ya nufi dakin da Khadija ke bacci cikin rawar jiki... *GIM. KHADEEJA* Cikin bacci na jiyo tamkar anamun susa, Jin matse matsen yayi yawa hakan yasa na bude idanu na dake nauyin bacci, Salman na gani akaina yana murmushi, Ya lakuce mun kumatu da yatsan sa na dama yana goga hancin sa akan nawa, “Ya Rouh! Rise and shine.” “Oh no... Bacci nake ji fa, Ka kyaleni pls.” “Awa nawa kenan kina baccin? Ai yayi yawa.” “Uhm.. Uhm” Na fada Ina turo baki gaba, Ya kai mun rantsattsiyar sumba a gefen kumatu na, Can ya dawo kan mara ta, Da tsakanin kirji na, Na shiga ture bakin nasa ina yatsina fuska, Santar kunnena ya zura bakin sa yana min magana mai kashemun jiki, “Dearest one... I keep telling you, I like adult only things...” Juyawa nai gefe na bashi baya inason nayi wani baccin, Ya sake nanuke mun yana shafa jiki na, Ina mamakin yadda baya gajiya da nanikemun kamar gum, Dole na kyale shi muka yi baccin mai dalili gaba d’aya. Muna tashi na shirya shi ya futa Wai zai duba shaheedah, Kishi duk ya kamani. Rankwafo wa yayi yana daria ahankali, “Meya faru wifey...?” “Yanzu duk kwalliyan nan na shaheeda ne?” “Laa Zawjati tafara kishi na..? Alhamdulillah Allah kaine abun godia.” Na yatsina fuska, Ina tabe baki na, “Wanda kakeso ai shi kakewa kishi...” “Lalle nazama dan gata tunda baby na kishi na. Kibari na dawo kwalliyan da zan miki... Zakisha mamaki.” Ficewa yai yana dariya, Na bishi da harara kafin na shige band’aki nasake watsa ruwa saboda yadda nakejin zafi dukda na’urar dake sanyayani. Ba jimawa sosai Salman ya dawo daga wajen shaheedah sallamar sa kawai naji, Ya sake nunakeni yana shinshina gashin kai na.. Nai Ajiyar zucia kawai ahankali nace ‘Allah ya hada ni da maqalalle...’ Shi kuwa Salman yana jikin Dije yana tariyo tambayarsa da shaheedah ke tayi akan jakadiya Abu. Meyasa zai cire ta daga wasu abubuwan nasa? Shi kuma Salman yasan a asirri sukai magana da jakadiya, Kuma hakan dayai yayi ne kawai saboda karta fuskanci dije nada juna biyu, Dole ne yaje yai bincike akan jakadiya Abu, Bai taba dauka makircin nata ya kai har haka ba. Wato dai gaba d’aya masarautar nan sai ahankali bakada sirri sai kayi takatsantsan. *WASHE—GARI* Bayan fitar Salman fada abadan, Nayo wanka cikin wani lace d’inkin bubu, Ban daura d’ankwalin ba nade yafa mayafi karami akai na. Umma Hansatu na kitchen tana aiki, Da sauri tafuto muka gaysa, Na shiga tunanin abinda zan ci, “Ranki ya dade me za’a dora miki..?An dai kammala abincin rana.” “Sannun ku Umma Hansatu! ni ko wainar fulawa na samu ta manja data ji kayan hadi da yajin tafarnuwa Nagode.” “Yanzu kuwa ranki ya dade...” Ina tsaye tana soyawa inaci don zalama, Sai da naci sosai sannan nace ta toyamun sauran ta zuba a plate akaimin sama. Sama na koma na zauna a parlor ina kallon drama din da ake na turkish ‘forbidden love’ Ji nai sama sama tamkar ana magana a kasa . Na cigaba da cin wainata ina korawa da ruwan zam-zam me tofi. Hannu na na hagu rike yake da wayata. Tun dazu nake kiran wayar Ammi bata shiga, So nake mu gaysa dan duk yau banji muryar taba, Don kullum sai na kira na gaysa da ita, Tunda bana zuwa sashen ta yanzu. Na ajiye wayar a Gefe na kanannada wainar na doni yajin tafarnuwa nasa a baki na. Hadimata Nabawiyya ta kwankwasa kofa ta shigo cikin ladabi, “Allah ya kara miki lapia da nisan kwana.. Kinyi bak’uwa, Tana kasa.” Ai da sauri na dire plate din hannu na, Na wanke hannuwa na , Nai sauri na shiga daki nayi brush na kurkure da mouthwash. Turaruka na sake faffesawa sannan na gyara d’aurin mayafin jiki na, Zaman kadaici ba dadi, Duk yadda akai wata dana sani ne tazo, Da sauri na sauka kasan ina harhada matattakalar bene. “Ahhhhhhhhh! Malama Mardiyyah naaaa! Wayyo Allah dad’i. Yau gani ga malama na. Malama shigo.” Da sauri na rungumeta ina kamo hannunta, Domin har cikin bargon jiki na da jini na nake jin Malama Mardiyya. Babban parlorn kasa muka zauna, Malama sai kalle kallen ko’ina take. Aka kawo mata kulolin abinci aka cika gabanta dashi, Sai kallon ta nake. Tunda tanada tsafta sosai da kwalliya, Da tadan manyanta ma batadena ba, Daman karamun jiki ne da ita. “Malama! Barka da rana...!” Na fada ina tsugunnawa. “Ahh meye haka Khadija? Dan Allah tashi, Haba, Ai kin wuce gaisuwar tsugunno yanzu, Balle keda ke auren sarkin mu baki d’aya.. Ina zuwa wani awaje yace ayimin iso.” “Malama ya bayan saduwa? Ai nayi fushi sosai.. Dan ma dai.. I love and miss you so much. So na dai na fushin yanzu.” “Alhamdulillah! Kiyi hak’uri Khadija.. Abubuwane sukai yawa, Na canza layi na wanda nake da number ki, Tun sanda na kawo ki ki kai post-utme dinnan. Na bar kano.” Tunda Malama mardiyya ta fara magana harta gama kallonta kawai nake ina murmushi, Ganinta nake tamkar yayata ta jini, “Allah sarki Malama... Insha Allah khair! Kin koma lagos kenan?” Malama mardiyya tai murmushi tana kurbar orange lemonade din hannun ta, “Eh mun koma, Canjin aiki akaiwa Abban su, Kai Masha Allah! Gidan ki yayi kyau Khadija.. Kinga ribar hak’uri ko? Ai nagaya miki akwai rana irinta yau da zaki bani labari.” Nayi daria kawai nima ina bin parlorn da kallo, “Ai kuwa dai kin fada malama..” Na dan bata labarin auren a takaice, Hararata Malama Mardiyya tai tana danna cinyar kaza abakinta, “Yimin shiru kafin na zane ki.. Da alama a makaranta na manta ban taba dukan ki ba, Kila sai yau. Yo ai babbar sokuwa se ke.” “Meyasa kikace haka Malama..?” “Saboda ba yadda za’ai dan ya tsaneki ne zai auro ki ya narka miki wannan gidan da uban dukiya duk ke kad’ai? Ahh sannu, nace sannu.” “Hmm! Malama bakisan wahalhalun rayuwar dana shiga bane.. Jini fa Malama, jini aka sakarmun naita shan wahala na dauka period ne. Ka tsorata, Da yawan jin wari gaba d’aya banajin k’amshi. Ga rashin bacci da faduwar gaba. Malama nasha wahala.. Amma dai Alhamdulillah komai ya wuce.” “To ai Alhamdulillah tinda yanzu komai ya shige. Insha Allah komai yazo karshe Khadija. Ai ke din *KIBIYAR AJALI* ce, Wadda sulke baya tare ta sai ta wuce.. Kiga tsallake tuggun Gajiyalle ma bare nasu? Yo me zasu miki? Kedin wacce iriyar gwagwarmayar rayuwa ce baki gani ba? Wanda da Allah ya kawo k’arar kwana ma da yanzu sai labari.. Amma gaki nan tamkar me ran k’arfe. An buga dake an barki ya zasuyi dake uhm? Sai kallo daga nesa yar kanwata.” Nayi murmushi kawai.. Inata tuno sanda taketa wahalhalu da ni a Durbun. “Tunanin me kike Khadija..?” “Babu komai Malama.. Kawai na tuna baya ne.” “Kai abincin nan yayi da’di... Yau gani a gidan Khadija na.. An cikamin gabana da kayan kwalam da makulashe na gidan yan gayu..” Nayi daria kawai ina lankwasa hannaye na, “Ni kam ina Malam auwal?” “Wai wai Wai.. Allah sarki Auwalu.. Wai.. Ai inaga rabona dashi wajen shekaru biyu kenan. Yace dani zai koma can shagamu dangin mahaifiyar sa zaiyi aure ya kuma fara kasuwanci, Saboda teaching dinnan ba inda zai kai shi..” “Allah sarki Malam Auwal.. My first love..” Muka sheke da dariya.. Malama mardiyya tacigaba da cewa, “A’ina ya zama first love din naki? Mu da kika ‘kimu..? Kai Allah sarki shima auwal seda na ce masa karfa kiyayyar da kakewa Khadija ta juye ta koma soyayya yace aa wallahi.. Sai gashi yana roko na wai dan Allah naje gidan ku a bashi ke ya aura.. Nace wa? Badani ba wallahi..” “Allah sarki Malam auwal..” “Ya durbun..? Kin koma kuwa?” “Aa wallahi tun bayan tahowata ban koma ba.. Zan je, Amma sai nan gaba kadan.” “Allah ya kai mu. Allah ya dafa miki ya dora ki akan makiyan ki Khadija..” “Aamin Malama mardiyyah..” “Ko sai kin sauka lapia ba Insha Allah..” Na rufe fuska ta da tafin hannu wai ni kunya, Malama mardiyya tacigaba da cewa, “Ai kinsan rannan sai bayan tafiyar ki naita dana sani nace ko number ki ban karba ba, Toh Ina can ina mamakin wayewar yar k’anwata.. Ubangiji Allah yasa mutu ka raba keda mai martaba Khadija, Aita haku’ri, Rayuwar aure gaba d’aya hak’uri ce.. Kinji?” Hira muka shiga yi sosai da Malama tacigaba da bani shawarwari akan zamantakewar aure, Na Karu Sosai da bayanan ta, Kamar a makaranta haka tadinga mun bayanin komai dalla dalla, Mun jima muna hira sosai ta kakkawomun magungunan mata irin na yoruba dinnan, Da turarukan wuta kai harda na mopping da wanki da wanka na *yerwaincense&more..* Allah sarki bata masan inada wasu turarukan ba na yerwan. Nima na hau sama na hado mata shatara ta arziki domin Malama mardiyya idan ka cire kawunina da suke a raye da Salman da Ammi sai ita a wanda nake kauna gaskia. Zan iya cewa ma banda sama da ita ta wani fannin. Har bakin gate na rakata, Kowannen mu fuskar sa dauke da hawaye haka muka rabu.. Domin jirgin safe zata bi ta koma birnin ikko. Amma tamun alkawarin zata sake dawowa Insha Allah, Nima nace mata idan na sake ziyarar lagos zanje wajenta tunda mun karbi lambobin juna.... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _B30_ *GIM. SHAHEEDAH...* Abubuwa ne suka taru sukai mata yawa. Ta kasa gane kan Salman, Duk sanda zata sa amata iso sashen sa sai ace sarki ya hana kowa shiga yana wani uzuri, Sai daga baya kuma yazo da kansa, Idan yazo kuma babu wani abu dake shiga tsakanin su sai dai ya tsiri dakko ipad dinsa yace wani aiki yake yi, Daga karshe tatashi tashige daki idan tafi to kuma baya nan ya tafi. “Salman me kake boyemin ne?” Ta tambayi kanta tana nazarin duk lokutan da suka ha’du uzurorin da yake bata duk d’aya ne, Gashi tamkar an sauya masa halaye. Babu wannan yawan ciwukan da yake. Kuma kullum kamar ransa a bace yake yana kokarin danne wasu abubuwan. “Salman me yake faruwa ne...?” Ta sake jefo wata tambayar tamkar shidin ne agaban ta. Mikewa tai tsaye tana kiran sadiya hadimarta, “Ga ni ranki ya dade...” “Sadiya... Kin bincika abunda na sa ki?” “Nayi uwar daki na. Tabbas ance gimbiya kh...” “Karki kuskura ki karasa sunan gimbiya kaza, Wacece gimbiya? Ta ina tazama gimbiya? Sama taka? Kodan an dosanata a ta biyu? Mata ba jinin sarauta ba komai ba, Yar kauyen kayau. Kizo gabana kina kiranta da gimbiya? Karna kara jin labban ki sunyi gigin kiran Khadija da gimbiya.. Kina ji ai ko?” “Na fahimta gimbiya, Akasin labbana ne, Tuba nake ranki ya dade, Allah ya huci zuciar ki...” “Sanar dani abunda kika jiyo.” “Ranki ya dade.... A binciken danayo na kuma harhada da wanda akawo mun an tabbatar mun kh.. Khadija na nan cikin gidanta babu inda taje, Domin ance Umma Hansatu hadimar mai babban d’aki itace ke zaune da ita acikin gidan. Wasu sunce tayi wata bakuwa kwanakin baya harta rakota ma izuwa gate din sashen na su... Kuma ance takara murjewa tayi b’ul b...” “Ya isa! Jeki.” Sadiya ta mike ta fice, Shaheeda tai zaman yan bori tana jujjuya kai, “Takara murjewa tayi ‘bul ‘bul... ?Hakan nada nasaba da Salman kenan? Shysa muke wasan ‘yar buya da shi? Nooo it can’t be.” Waya ta janyo har zata kira hajian su sai kuma ta fasa, Tatafi wajen su Mama Huwaila ko zata jiyo wani labarin awajen su. *GIM. KHADEEJAH.* Ina zaune bayan nagama karatun alqur’ani, Waya na janyo na dan fara karanta hausa novels na online, Can na ajiye na koma parlor na zauna jira nake Umma Hansatu ta dawo daga gaisar da Ammi data je. Ba jimawa kuwa ta dawo, Sai dai yanayin fuskar ta gaba d’aya ya canza. “Umma Hansatu lapia?” “Lapia qalau ranki ya dade, Da akwai abunda kikeso ne yanzu na tashi nayi?” “A’ah babu komai, Ya Ammin? Kince ina gaishe ta sosai ko?” “Kwarai na fada Allah ya kara miki lapia, Tana amsawa sosai tace tanai miki ya jiki. Tayi miki adduoi sosai..” “Masha Allah, Ina godia kwarai da gaske, Duk kalau suke ko? Kwana biyu inata kiran wayar ta bata shiga.” Umma Hansatu tayi jim tana jujjuya kai, “Menene Umma Hansatu?” “Babu komai ranki ya dade.. Tace dai karna fada amma bazan iya kin fada miki ba, Uwar dakin nawa na kwance itama ba lapia.” “Ammin..?” Na tambayeta a matukar dimauce, Gyada Kai tayi cikin tabbatarwa. “Zazzabi ne, Tashi wai taifol ne (typhoid).” Mikewa nai na shige da’ki, Na kasa samun nutsuwa na kikkira Abdullah wayar sa off. Dan haka na kira Salman bai daga ba. Wunin ranar haka na wuni duk banjin dadi. Dakyar bacci barawo ya dauke ni ban farka ba sai tashi nai naji ana kiraye kirayen sallar magriba. Bandaki na shiga nayo wanka da alwala. Nayi sallah na Idar ina zaune akan dadduma Salman ya shigo, “Barka da dawowa...” “Barkan mu Zawjati.. Ya jikin naki? Ai na shigo naga kina bacci na koma.” “Eh wallahi banmasan ya dauke ni ba, Da ina kasa tare da Umma Hansatu..” “Okay! Kinci abinci? Me kikeson kici uhm?” “Babu komai.. wai Ammi ba lapia? Ko bakasani ba kai ma?” “Kai wannan Umma hansatun ta aminta dake, Ammi fa ta gargadeni kada na gaya miki, Ashe Sai da Umma Hansatu ta gaya miki?” “Meyasa Za’a boyemun rashin lapian Ammi? Why?” “Bakomai... Ammin ce tace dan karki tada hankalin ki ne, Wajen kwanaki uku kenan tana zazzabi a tsaitsaye typhoid ne da malaria.” “Allah yabata lapia yasa kaffarane.” “Kinason kije kiga jikin tane?” Da sauri na gyada kai ina komawa kusa dashi, Ya janyo kafadata yana rungumeni, “Idan aka idar da sallar ishai sai kuje da Umma hansatun, Tunda naga kin damu da yawa. Kinsan wani abu kuwa?” Na girgiza kai ina kallon sa, “Yau birthday din Ammi, Yau ne ranar da aka haifeta bazan taba mantawa ba, Mai martaba da kansa yake tsara celebrating birthday dinta duk shekara...” “Allah sarki, Allah ya gafarta masa. Mezan bata as present?” “Karki damu na riga na shirya komai nasa an kai inji ki, Nine tawa kyautar sai kunje zakiga wata iri zan bata.” “Dan gayamun mana.. Haba Zawj..wayo?” “Khal.. Khal zansa ya kirata su gaysa. Kinga dai shine wannan babbar kyauta duk duniya da Ammi zata fiso.” “Gaskia kam, Kai Allah sarki Ammi..” “Tohm ki shirya, Bara naje daki na kira shi.” “Okay love...” Harya fita ya dawo yana sosa idonsa d’aya nasan wani wayon zeyi mun. “Zaki biyani kayan gift din danasa aka kaiwa Ammi nace inji ki.” Nayi rau rau da idanu ina cuno baki gaba, “Ni.. Ni mezan baka? Ai bance ka bayar ba wannan duk salon wayo ne, Daka barni ai da nayi da kai na.” “Noo.. Ai aikin gama ya gama, Idan kuma kinason na kirata nace bake kika aiko ba to...” “Ahh... Yanzu nawa zan biya?” “Habawa Yarinya, Waya gaya miki kudi nake so?” Na shiga raba idanu, Ina harhade hannuwa, “Toh me kakeso...?” “Ke nake so...” “Na’am..? Bangane ba” “Nace ke nakeso kawai... Ina kaunar ki sosai Zawjatii, Na kan ware lokaci nayi ta tunanin ki haka kawai, Ga ki dai na aure ki ke mallaki nace, Amma kullum kaunar ki kara ninkuwa take cikin zucia ta.” Yak’arasa fada yana sakar mun kiss agefen wuya na, “Kamshin ki...” “Dariar ki...” Nanma ya dawo kan baki na. “Idanun ki....” Ya fada yana sumbatar idanu na, Wanda na rufe su ruf ina shakar kamshin turaren sa. “Komai naki... Komai naki yana tafiya da ni Deejah na! I love you with every fiber of my being.” Ya karashe zancen yana rungumeni tsam a jikin sa, Nasa hannuwana biyu na riko bayan sa nima. Ina mai kwantar da kai na akan kafadar sa. “Nima Ina kaunar ka sosai zawj... Ina maka kaunar kauna marar gauraye. Honey bunny! I love you as high as I can reach, as far as I can see, to infinity and beyond...” “Nagode k’warai zawjati... Kin biyani da kalamai saura daya aikin ladan kai gaskia kin cika yar albarka.” Na matsa ina daria, Shi kuma ya mike. “Bara na kira Khal. Sai kuje idan anyi sallah. A gayshe ta sosai. Nayi baki a fada suna jira.” D’aga masa kai nayi ina murmushi, “Okay honey bunny, Allah yabada nasara, Ya dawomin da kai lapia.” Ficewa yai yana dagamun hannu, Ni kuma na shige bandaki don tsarkake jiki na. Canza kaya nayi jikin doguwar riga abaya baka. Na yane kaina da mayafin rigar. Kiran sallah akayi. Nayi sallah hade da adduoi na, Na shasshafa turaruka, Na murza yar powder da da man lebe. Jiki na har rawa yake saboda son ganin Ammi. A kasa na tarar da Umma Hansatu itama ta idar da sallah, “Muje wajen Ammi Umma Hansatu.” “Toh ranki ya dade. Allah yaja zamanin ki..” *Shi kuwa Salman yana shiga dakin sa ya kira Khal da hannu d’aya, D’aya hannun kuma yana dudduba closet dan saka kaya marar nauyi, “Wa’alykm Salam Khal..” “Yaya.. Barka da dare.” “Barkan mu. Kaga na kira ka da daddare ko?” “Ah tuba nake ranka ya dade, Ai dare beyi ba, Da fatan komai lapia?” “Lapia qalau.. Ka tuno yau wacce muhimmiyar rana ce?” Khal ana bangaren ya shiga jujjuya kai yana son tuno ranar amman ya kasa. “Allah yakara maka lapia, Tuba nake na kasa tuna wacce rana ce.” “Yau birthday d...” “Birthday din Ammi... Afuwan ranka ya dade, Sai yanzu na tuna wallahi.” “Masha Allah! To yau birthday din Ammi Khal, So babbar gudunmuwar da zamu bata d’aya ce.. Kasan menene?” “Tuba nake ranka ya dade, Bansani ba.” “Kiranta zakai a waya, zakaga na turo maka wata number ta message, Itace number Ammi, Zan hado dana Abdullah ma ka kira shi daga baya ku gaysa, Saboda yanata processing harkar admission dinsa inaga Manchester zai tafi yayo wannan civil engineering dayake mayatar so.” Jin shirun Khal, Salman sai ya rude ya shiga jin ko lapia? Cikin shesshekar kuka Khal yace, “Bakomai! Kawai na samu kai na cikin overly emotional.. Nagode sosai Yaya, Zan kira insha Allah yanzu kuwa. Nagode nagode.” “Sai ka mata ya jiki daga nan..” “Batada lapia?” Khal ya tambaya SAS cikin kidimewa, “Eh kwana biyu tanata fama da zazzabi, Amma da sauki ai Alhamdulillah!” “Tohm Masha Allah! Allah ya Kara mata lapia da nisan kwana mai amfani, Aamin.” “Aamin” Sallama sukai wa juna, Salman ya shige toilet Shi kuma Khal ya shiga kokarin kiran layin Ammi. *MAI BABBAN DAKI....* Kishingid’e muka samu Ammi tana lazimi, Sanye cikin laffaya, Ta amshi kyakkyawar fuskar ta, Har tadan fada tubarkAllah, Saboda rashin lapiar manyan idanun ta sun kara futowa, Tana hango ni ta zauna tana murmushi, “Oh ni ‘yasu, Sai da suka sa kikazo? Bayan jan kunnen da nayi, Nasan duk yadda akai mai martaba ne.” Zubewa nai nashiga gaysheta, Ta amsa cikin fara’a, Umma Hansatu ma ta rissina ta gaysheta tana daria, “Tuba nake ranki ya dade, Ni ce na sanar da ita, Saboda tashiga damuwa sosai da rashin samun ki awaya.” “Ayyah... Zo ki zauna Khadija anan, Nan sanyin tiles. Kashe wayar nai sai dare yawanci nake kunnata, Sai dazu nema na kunnata gaba d’aya.” Komawa nai inda tace din na zauna cikin ladabi, “Ya jikin Ammi? Allah yakara afuwa yasa kaffarane.” “Aamin Khadija. Aamin! Ya naki jikin? Allah ya raba lapia, Ya inganta.” A zuciata na amsa da ‘Aamin’ ina maida kai na tv cikin kunya. “Harda wahala Khadija? Ashe mai martaba ya sanar miki? Naga abubuwa da yawa, Da baki tashi kanki tsaye ba ai Khadija, Ni wallahi har na mance da ranar, Dake babansu sukaga yanayi shine suka ara suka yaba.” “Babu komai Ammi, Allah yaja kwana ya karo wasu shekarun masu albarka Aamin” “Aamin.. Akwai abinci a kitchen Hansatu hado mata, Khadija me zaki ci?” “A koshe ma nake Ammi, Amman a zuba min kadan” Tashi Umma Hansatu tayi ta kawomin, Ta kuma bamu waje, Parlor ya zama mu biyu kawai. Ahankali na bude flask din jollof rice da plantain, Se kuma soup din kifi a gefe. Cikin haka wayar Ammi tashiga ‘kara, Ta daga tana kallon screen din ta ajiye, “Banason d’aukar number da bansan taba. Maybe wrong number ne.” “Ammi da dai kin dauka..” Nace ina kokarin cusa lomar shinkafa a baki na, “Toh ai naga sabon layi ne fa babu wanda yasan number..” Kiran ya yanke aka sake kira tukun sannan ta dauka, “Assalamu Alaikum..!” “Wa’alaykm Salam... Ammi.” Ina daga zaune ina kallon ikon Allah, Ta cire wayar a kunnenta tasake maidawa kana iya jiyo komai rad’au, “Ammi...! Ammi Barka da dare.” Hannu d’aya tasa tana dafe kirji, hade da mikewa tsaye, “Barkan mu dai...” “Ammi baki gane me magana ba?” Shiru tayi bata bada amsa ba saboda yadda hawaye suka shiga reto a fuskarta lokaci d’aya, Cikin kuka tashiga tambayar sa, “Khaleel? Khaleel! Khaleel kai ne?” “Nine Ammi... Nine Ibrahim, Khal ne Ammi. Ashe zaki gane ni Ammi.” Shiru tayi tana kuka sosai, Can tad’aga wayar ta mayar kunnenta, “Kana lapia Khaleel? Ya karatu?” “Ammi ai na kammala, ‘Dan naki ya zama babban surgeon Ammi..” “Ma.. Masha Allah Khaleel, Allah yayi albarka.” “Aamin Ammi.. Happy birthday first love! Many, many happy returns.” Ai wannan karon gaba d’aya rushewa tai da kukan farin ciki, Ta rungume wayar a kirjinta, Shima anasa bangaren kuka yake marar sauti. “Ammi R u there.. kina ji? Kina jina Ammi?” “Ina jinka Khaleel.. Ina jinka, Nagode Khaleel.” “Toh ya jikin naki? Fatan da sauki sosai ko?” “Naji sauk’i Khaleel, Na warke kamar banyi ba.” “Allah yakara miki lapia da nisan kwana mai amfani Ammin mu. Nayi kewar ki sosai. Da Abdullah.” “Muma haka Khaleel.. Muma.” Tashi nai zan bata waje tamun alama da hannu danayi zamana, Inason strong bond dinnan, Uwa da ‘da suyi reuniting.. so captivating! Hawaye tashiga gogewa da laffayar ta na mika mata gidan tissue dake gabanta, Ai kuwa har mura ta kamata. “Ammi... Kina jina?” “Ina sauraron ka Khaleel.” “Ki gafarce ni Ammi.. Duk tsawon shekarunnan dana dauka bana neman ku, Bana waiwayon gida, Bama nasan ayimun zancen gida. Ki gafarta mun Ammi ki yafe ni..” “Bakamin komai ba Khaleel! Nasani ba yin kanku bane baki dayan ku, Kadena ma tunanin daga kai ne kaji? Duk cikin ku babu wanda yataba mun babban lefi Khaleel, Tun girman ku har kwanan yau. Allah ya yi muku albarka, Ya dora ku akan makiyan ku.” “Aamin Ammi.. Anata fama dasu kam, Insha Allah nima Yaya yace nan kusa zai sa na dawo masarautar.” “Ka dawo ne.?” “Na dawo Ammi.. Ina Abuja, Ban wani dade can da dawowa ba.” Ya karasa gaya mata yadda Salman yaje har can korea, Da yadda komai ya kasance a takaice. Ammi tayi murmushi faffada, Cikin farin ciki tace, “Ai kuwa naji dadi Khaleel, Nagode muku dukan ku, Allah ya kara hada kawunan ku. Aamin. Sharrin mutum dana aljan, Sharrin karfe, Tsautsayi da asara, Baki d’aya Allah ya nesanta mu duka dasu.” “Aamin Ammin mu... I love and miss you so much.” “Nima haka Khaleel, Kar a manta da addua kaji? Nagode! Nagode. Allah ya saka da alkhairi. Okay to sai na jika, Sai da safe.” Katse kiran tayi, Tana ajiye wayar ta dubi gabas tayi sujjada, Tajima kafin ta dago tana murmushi, “Khaleel ne.. Yareemah Ibrahim kanin mai martaba, Shine mai bi masa, Sai auta Abdullah.” “Okay! Na korea dinnan ko Ammi?” “Shi fa.. Ya dawo yana Abuja, Kinji Wai mai martaba ne yace surprising dina zasuyi ranar birthday, Yau kenan. Wai shine babban present dinsa.” “Allah sarki, Allah ya Kara hade kawunan su, Ya kawo karshen duk wani mai mugun nufi.” “Aamin Ya Allah.. Aamin.” Hira muke jefi jefi wadda rabi duk ta Khaleel dince, Har na wanko baki na dawo muka cigaba, Na jima sosai sannan na mata sallama nida Umma Hansatu, Muka koma bangare na. ****SHAHEEDA dake tsaye ta baranda tana kallon su, Tun wucewar su ta farko sadiya ta sanar mata, Shiysa ta tsaya har dijen suka fito, Kallon k’urilla ta shiga yi mata dik kuwa da dare ne, Akwai fitulu masu haskaka farfajiyar ciki da wajen masarautar baki d’aya. Kamar rana, Tun daga yatsanta tafara kallon ta, Dake abaya ce ajikin dijen ba kadan ba ta sake fitowa da murmurewar da tayi, Jikinnan tamkar ka tsaga jini ya futo, Saboda fresh din da tayi. Takara kyau sosai, Tsabar kallon ta, Shaheeda har bigewa tai da kofa, Tasa dan yatsa a baka tana ciza... Gaba d’aya saita samu nutsuwa ta kasa, Ta shiga kiran Salman baya dauka shi kuma alokacin yana fada wayar na hannun falaki. “Na shiga uku ni shaheedah.. Ba dai? Nooo” Shigewa tai cikin gida aguje ta shiga kiran wayar mahaifiyar ta, Ta gaya mata komai , “Kwantar da hankalin ki shaheeda ki dena kuka dan ALLAH.. Ba dai ciki kike tsammani ba? To bazashi ko Ina ba, Yana sa akaiwa Gimbiya Rahama matar baban ku ehe?” Cikin kuka shaheedah tace, “Iska kika sa aka turawa cikin.” “Ta haife me? Fadi da k’arfi..” “Ta haifi katangare.” “Toh Karki wani damu, Yadda zancen cikin rahama yazama sai tarihi haka na waccen shegiyar ma zai zama, Ba zama zamuyi ba, Ki tabbatar da tudin sa, Watan sa, Nauyin sa idan zai yiwu, Ta hakane zansa a cinna wa shegiya katangare dai dai girman cikin ta.” Jin haka shaheedah ta fa’da’da murmushin ta, “Sai Hajjaju..” “Toro babba nake, Gimbiyar sarki Ibrahim Hashimu, Fadawa duniya kice kwarai mahaifiyar ki ce.” “Allah yabar mun ke hajjaju..” “Kedai bar kuka kawai Kinji? Sai komai ya lafa zamu koma K’asar nan a dasa miki cikin kuma dole ki haife dan uban uban Salman din, Bai isa ya kawo gaddama ba. Amma kafin sannan ki shiru da bakin ki, Kada ki bari kowa yaji kinji.. Kinsan babu wanda yasan hakikanin gaskiyar komai.. Kije sashen Salman din ko natan kan ki tsaye.. Ki gano mun dagaske cikin ne ko kuwa? Kinsan fa yan kauye Idan suka samu birni ta murjesu wallahi baka gane su.” “Gaskia kam hajjaju.. Toh zan duba da kai na kuwa zanje har sashen nasa.” “Yauwa, Kiyi suman karya, Kiyi bori ki nuna yaci amanar ki, Sai dai idan dasa mata kai. Kita bori a sashen nasa kinji?” “Toh hajjaju.. Zan gaya miki yadda akai..” “Yauwa.. Sai da safe, mai martaba na mun iso.” Sallama sukayi, Shaheedah ta malale akan gado tana kyalkyala dariyar farin ciki.. Ranta fes. Gani take tunda hajian su ta tsaya mata batada wani sauran shakku..... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _B31_ *GIM. KHADEEJAH* Hidimar bikin su Ya shukrah muka shiga, Duk da dai ba zuwa nake yawon kasuwa da suke ba, Ina gidah abuna. Biki saura kwanaki biyu na koma gidan Kawu daddy, Na shiga cikin dangi akaita warkajamin biki da ni, Biki yayi kyau kwarai matuka, Kwanaki 3 akai anayi, Addah maryama sunzo dasu Umma Hansatu suma. Salman ma yabawa Kawu daddy tasa gudunmuwar duk kuwa da dakyar Kawu daddyn ya k’arba don shima dai dai gwargwado yanada nasa rufin asirin, Ni kuma tawa gudunmuwar Mami na bawa. Anci biki an darje, Amare kowacce an kaita gidan ta, Kai Ya hameeda ne banje ba can jos, Kawu daddy yace naje mata ziyara amman bayanzu ba, Ya shukrah kuma gidan ta ma ba nisa dana Kawu daddy domin unguwa d’aya ne, Sai dai layi ne ya banbambata. Wayyo yan uwa da dadi suke, Gaba da baya dik inda na juya sune, Anyi zumunci, Munsha hotuna sosai, Biki ya kare Kowanne ya koma inda ya fito, Anaiwa amare da angwaye fatan zama lapia da zuriya ta gari. Shaheeda kuwa sau wajen biyar tana zuwa sashen Salman amman bata haduwa da Khadija, Dik iya zurfin bincikenta bata gano hakikanin inda dijen take ba. Salman kuwa wani lokacin har guduwa yake ya barta saboda yadda take manne masa domin shi tsoro take bashi musanman ranar daya gama kallon cctv recording din bangarenta baki d’aya. ***** A hankali ta karasa ta murda kofar parloun cikin shiga wacce take fatan wanda ta yiwa ya karba ya yaba da hannu dubu ba biyu ba. Ko babu komai tasan ita d'in mai aji ce, ban da zuwan Dije cikin rayuwar su shi kansa salman yasan Shaheedah akwai isa da takama har a kan kin kansa. Kicibus suka yi da Dr Fiddau zata fito, ganinta yasa Shaheedah zaro ido dan tasan ba lafiya ba indai aga ganta ansan wani ne babu lafiya tazo dubawa. Baya tayi tana umartar Dr. da ta fito, bayan ta fito ne tace ta rufe kofar ta rufe duk bata kawo komai ba cikin zuciyarta sai da taji Shaheedah na tambayar. “Ya akai Dr. na ganki anan?” Cikin dakiya Dr Fiddau tace. “Lafiya lau Gimbiyar mu, mai martaba ne ya kira ni.” “Jikin nashi ne ya motsa ko me?” “Allah ya taimaki Gimbiyar mu ya kara mata hakuri da juriya, daman yace idan na fito nace a sanar dake yana son ganinki.” Dr ta samu kanta da kwakuso karya, Saboda babu irin gargadin da Salman be yi mata ba akan karta sake ta gayawa kowa cewa Dije na da juna biyu, idan har yaji maganar ta fito kuma daga bakin ta ne to ya yi alkawarin sai ya koreta a jihar shi gaba daya. Yanzu Babban tashin hankalinta shine, Salman ta baro shi tare da Dije a daki, kuma tasan dole ne Shaheedah ta gansu, gashi yar kamar t-shirt ce a jikin Dijen ana ganin bullowar cikin jikin ta. “Alright! Daman ina son nazo na duba shi bari na shiga thank you Dr.” Gabaki daya rasa yadda Dr za tayi akan ta tsayar da Shaheedah daga shiga cikin dakin tayi. Tasan bata isa ba kuma Shaheedah mutum ce wacce bawanta be isa ya sata tayi abu ba indai na kashin kanta ne. Tayi saurin dakko waya tana kiran Salman amman be dauka ba saboda Dije na can na yi masa raki, daga tace bayanta sai tace hannu ko kafa haka yake bin duk inda ta fada yana matsa mata, yana jin kiran wayar a kan bedside amman ya kasa zuwa ya dauka saboda da ya dan tsaya zata ce 'wash Allah'. Babu ko sallama a haka Shaheedah ta murda kofar bedroom d'in tana lumshe ido jiyo kamshin turaransa da tayi. Sai dai kuma me, hango Salman tayi durkushe a gaban gado yana yiwa Dije tausa. Da yake baya ya bawa kofar sai ya zamana be san waye ba duk a tunaninsa ma Dr ce ta dawo, amman yadda yaga Dije tayi wata irin zabura ta juyo shine yasa shi saurin mikewa yana kallon kofar. Shi kansa Salman din da yaga Shaheedah a wannan lokacin sai da kirjinsa ya buga, saboda itace mutum ta farko a duniyar nan da baya son tasan Dije na da ciki saboda yadda yagani a na’urar dake dakko masa sirri dan yasan ba zata taba yadda ba duk kuwa da duk wata qullaliyar rashin haihuwar sa daga gare ta ne. Baki bude take kallon su, Dije na kokarin janyo blanket ta rufe jikinta, sai dai abinda suke gudu shine ya kasan ce wato ganin cikin. Shaheedah ta dago kafa a hankali tare da rufe kofar ta jingina bayanta a jiki saboda yadda kirjinta yake bugawa da karfin gaske. Fatan ta da burin ta yasa ba abinda take zargi bane a idanunta. Salman ya kirkiro murmushi wanda iyakarsa saman lebansa yana tahowa gurin Shaheedar. “Gimbiya irin wannan shigowa babu excuse?” Ya yi maganar yana kokarin dafo kafadar ta, Ya ma manta when last ya kirata da gimbiya. tayi saurin dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, bugun zuciyarta yana daduwa tasa hannu ta dafe goshi tare da cewa. “Salman amanata kake ci? Salman kai ne tare da wannan banzar matar akan gadon mu na mulki? Wait! Wannan toliyar ta cikin ta na meye?” Komawa ya yi ya zama Salman d'in shi jin ta ambato cikin Dijen wacce ta rufe jiki da blanket ta tsaya tana kallon su. Shi kuma Salman ya tsuke fuska yana cewa. “Ke baki da toliyar a cikin ki Shaheedah?” “Kai kanka kasan cewa bani da tunbi, kuma itama ba shine da ita ba ballantana kace min shine.” Haushi ya fara ciki Salman dan yaga alamar so take ta kaishi makura, gashi yama rasa abinda zai ce mata sai faman cizon lips da yake yi. Ni kuwa sakkowa nayi daga kan gadon har blanket d'in ban kallesu ba na nufi hanyar fita ta kuma danne kofar da bayanta, gashi bana son nace zan bi ta dayar kofar saboda babu wanda yasan da ita sai ni da Salman kadai. Cikin Bazata kawai muka ga ta finciko blanket d'in ta tsaya tana kare min kallo cikin rawar jiki. Ta tabbata cikin ne da Khadija? Shin k’oshi ne ko kuwa? Idanunta ne? Kallonta ta mayar kan Salman baki na kyarma ta ce. “Salman!!! CIKI?” Haushi da takaicin ta suka taso min, dama ni ba hakuri ba bare nace in an min zan kyale, na ja tsaki tare da cewa. “Eh ciki ne haramun ne dan nayi shi a yanzu? Ko kuwa kin dauka cewa dan kin kasa dauka uban Kowa ma ba zai dauka ba? Kinyi kuskure da kike tunanin cewa ni gunki ce ba zan Iya bukatar namiji a kusa dani ba. Namijin ma kuma tsadadden mijinki wanda yasan takan soyayya irin Salman...” Jiri ne ya shiga kwasar shaheedah, Daman anata kawo mata tabbacin cikin ne, Bata taba yarda ba sai yau data ganewa idanun ta. Ta runtse idanunta dakyar ta budesu cikin tsantsar bakin ciki, Domin tuni wani abu ya taso ya tokare mata a wuya. Duk da son tayi borin karya hakan yaci tura, Domin wani ‘daci ne taji yana taso mata tundaga cikin ta zuwa wuyan ta, Sulalewa tayi ta fadi... Yadda zuciya ta ke tafarfasa ne yasa banji tausayin ta na faduwar da ta yi ba, sai ma barin gurin nayi na tafi sashe na da sauri Ina faman masifa duk kuwa da kirjina a dankare yake da fargaba, Muguwa ce ta ajin karshe, Don basumin da dadi ba tun farkon zuwana masarautar. Har ga Allah banso taganni da cikin nan ba. Amma na dake zuciata kawai na koma sashe na. Shi kuwa Salman kwakwalwarsa ce ta tsaya cak saboda rashin sanin abin yi, ga Shaheedah a sume, sannan ga a yanayin yadda yaga Dije ta tafi yana tsoran karta yi wani abin da zai samu cikin ta. Dr fiddau ya kira awaya yace tazo dakin sa ta duba shaheedah. Shi kuma ya koma wajen Khadija, Zuwa tai cikin barin jiki dik a rude take ganin yanayin shaheedan, Ta fara ciro kayan gwaje-gwaje ta nufo wajan Shaheedah da nufin duba BP d'in ta, cikin hasala Shaheedah ta buge ta tare da hankadata tayi baya tare da bugar kofar bathroom. Sakkowa tayi daga kan gadon tamkar zararriya ta nufi Dr Fiddau wacce ke kokarin tashi, ta shako mata wuya tanai mata kallon tsana tace. “Munafuka algunguma makiri kawai, ashe daman munafinta ta kikai kinsan komai? Fiddausi ni zaki yiwa munafinci dan babanki dan kaza-kazan uban can? Toh yau naga komai da kuke boye min munafuka kawai, tashi ki bar nan kafin nasa ayi miki jina-jina yar matsiyata.” Ko samun damar kwashe kayan Dr ba ta yi ba haka ta fice daga dakin tana dafe goshi dan ba karamin buguwa ta yi ba da kofar. Shaheedah kuma ta fito, kamar taje sashen Dije amman ta fasa saboda hango su Falaki da tayi tasan kome tace ba zasu barta ta shiga ba tunda ta san Salman ya na ciki. Ta nufi sashenta cike da tashin hankali da hargitsin wannan al'amarin. **SAS kuwa yana zuwa sashen Khadija ya tarar da ita zaune bakin gado tana cin ayaba, mamaki ya yi mugun kamashi amman dai hankalinsa ya kwanta ganin ba cikin damuwa take ba. Ina jin motsi ni kuma na dago kai na kalli bakin kofar, ganin shine yasa ni maida kai na Ina ci gaba da cin ayabata wacce na biya ta kitchen na dakko na hawo sama abuna. Karasowa ya yi shima ya zauna a bakin gadon nayi saurin juyawa daya bangaran, ta haka ya gane cewa fushi nake dashi. Tashi ya yi ya matso sosai kusa dani tare da janyo ni jikinsa, duk da cewa naji dadin hakan da ya yi min, amman sai naki nunawa, Sai ma kakkaucewa da nake yi ni a dole bana son ya rike ni kuma karya nake Ina so. Murya a raunane yana leko fuskata yace. “Na yiwa Zawjatii na oum unborn laifi, amman ina neman afuwa a yafe min dan Allah bana son fushin nan wallahi.” Na ajiye bawon ayabar cikin plate tare da juyowa na kalle shi Ina cewa. “Gaskiya waccan matar taka tana da matsala. Shikenan dan ita ba ta yi ciki ba, Sai ya zamana duk wacce zaka aura itama ba zata yi ba? Na yadda makira ce wallahi, tafa san cewa itace ba ta haihuwa amman dubi yace take mamakin na samu ciki da kai... Yaa Rabbi! Allah kai mana maganin masu binmu da mugun abu.” Cikin karyar da kai Salman ya kamo hannunta yana jan kasan lips dinsa, Cikin kasa kasa da murya in husky voice ya dube ni, “Shi yasa nake son kici gaba da kular min da kanki da baby na, nasan yanzu idanun mutane zai dawo kan cikin nan. Zawjatii wannan addu'o'in naki da bakya gajiya da yin su, kici gaba da yi, idan da wasu ma ki kara akai. Ina sonki Zawjatii da abinda yake cikin ki. Bana son ki kuma fita ko nan da can ne, hatta sashe na ki dena zuwa ni zanzo ko kuma duk Sanda kike bukata ta ki kirani. Ina sonku Dijangala na, ki rokar min Allah ya barmu tare please.” Ya karasa maganar yana kwantowa saman kafadata da hawayensa masu dumi suka sakko min saman kirji na. Tausayinsa ya kamani, nasa hannu Ina shafa fuskarsa cikin sigar lallashi da tausayawa. Dan na karfafa masa gwiwa yasa na hadiye kukan da yake taso min, ina dan murmushi nace. “Insha Allahu zanci gaba da yi maka addu'a mijina, babu abinda zai same mu..Sai abinda Allah ya kaddara mana. Bamu da kowa sai Allah da shi kuma muka dogara, nayi maka alkawarin kula da babyn ka dani kai na. Allah ya shige mana gaba a cikin dukkan aiyukan mu na alkairi, ya kare mu daga sharrin masu sharri. Kasa a ranka babu Wanda ya isa ya yi mana abinda Allah be so ba.” Sosai kalaman suka yi tasiri a zuciyarsa, ya sake rungume ni a jikinsa yana shafar ciki na da hannunsa na dama. Saboda da ma na kawar masa da duk wani tunani marar kyau, sai na kwanta tare da janyo shi ya fado jiki na, cikin sauri ya sassauta nauyinsa yana zaro ido yace. “Sai kinje na fasa miki cikin? Uhmm! Love?” Ina dariya nace “Toh ai kai jarumi ne..Sai ka kuma saka wani.” “Noooo my love! Wannan d'in ma wace irin siyasa ce ban yi ba kafin na samu ya shiga. Gwara dai na lallaba a sauke min shi cikin koshin lafiya.” Kuma janyo shi nayi ina marairaice ido cikin nuna masa tsantsar bukatar sa dan so nake ya manta da duk wani tashin hankali da yake cikin zuciyar shi. Ai kuwa kamar jira yake nayi masa tayi, ya janyo ni jikinsa yana kai min sumba ta ko'ina ni kuma Ina karbar sakonnin nashi ta nuna masa jin dadin abin da yake min. Na tabbatar yanzu babu tunanin wata Shaheedah a ransa sai ni kadai kwallin kwal, na biye mishi kuwa har sai da ya samu nutsuwa sannan muka yi wanka. Yana makale dani yana faman shafar ciki na yace min. “Baby na wallahi yanzu kin fini yawan bukata meye sirrin.?” Ina turo baki cikin shagwaba dan kuwa ba karya ya yi ba, ni kaina wani lokacin idan na kalleshe ko kuma tunaninsa ya ishe ni sai naji kawai Ina son kasancewa dashi, na rasa dalilin wannan al'amari. Sai da ina karanta wani posting a WhatsApp naji ana cewa wasu ciki yana..Sanya su yawan bukata. Amman ban gaya masa hakan ba Sai cewa nayi. “Toh ba kai ne ba..” “Ni kuma da nai mene?” Yayi maganar yana kama habarsa. “Kai ne idan na kalleka sai naji kawai ni Ina so.” Wani irin hugging ya yi min, da alama dadi da farin cikin kalamai na ne suka sa shi yi ba tare da ya sani ba, na saki yar kara ya sassauta tare da sumbatar wuya na yana fadin. “Kice nima d'in dai ba baya ba? Na dauka maza ne kawai suke bukatar mata sometimes?” “Ni ban sani ba, naka kawai na sani ko kallona kayi sai naji wani yarrrrrrr....” Wayyo Allah farin ciki duk ya mamaye shi naji dadi ganin yadda yake nishadi. (lallai dole Ace wasu matan ba da bokaye suke kwace miji ba lol) Sai da ya tabbatar na shirya ya kwantar dani bayan ya matso min da tea flask dina da kofin shayin ya sumbace ni tare da ce min zai je dakin sirri ya duba dan yasan tabbas akwai maganganu bama magana ba. Muka yi sallama kamar bama so dani ni kaina ban so zai tafi ba saboda wata irin sassanyar soyayyarsa da take kuma ratsani.... SAS Haka kawai Salman ya tsinci kansa da danna cctv din sashen Mama Huwaila. Ai kuwa nan ya tarar da ilahirin matan babansa banda Ammi, Rankatakaf su da ‘yayan su idan ka cire su Munaya. Zooming d’insu yayi ya shiga kallon mutanen parlorn baki d’aya.. Har zai tashi ya jiyo Mama Huwaila na magana, “Kamar yadda Waziri ya sanar da dukkanin mu nan, Yanzu abu d’aya ne zamu sa agaba. Wato yadda za’a yak’i salman a saukar dashi daga gadon mulkin basannabas. Magana dayan biyu ce Idan yan majalisa sun nemi dalili, Baida ishasshiyar lapia, Mulkin ma Waziri ne ke jagoranta, Sai na biyu barnatar da asusun masarauta ba gaira babu dadi. An bugo statement of account, Wa’innan dalilai kwarara biyu yan majalisa zasu tattauna akai asa yayi murabus..” Gaba d’aya yan parlorn suka sa shewa, Salman dake tsaye sai ya zauna, Ya janyo wayar sa dake gefe ya kira falaki. “Ya.. Ka aiwatar?” “Allah ya kara maka lapia, Na saka masa tracking device din da recorder, Na bi duk sauran tasu wambai duk na sassaka a duk inda ya dace. Toh yallabai a huta lapia.” “Aamin! Allah ya bamu sa’a.... “ Ahankali ya jinginar da kansa akan teburin dake dauke da computers din, Wasu zafafan hawaye ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskar sa. Tissue ya janyo ya goge hawayen, Ya mike ya fice zuwa dakin sa...... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _B32_ *GIM SHAHEEDAH* Tunda ta isa sashenta take kuka tana birgima, Kamar tababbiya, haka take duk sanda take a hautsine tahau farfasa sauran kayan dake dakinta wanda bata fasa ba. Tana yi tana cizgar gashin kanta. A haka mahaifiyar ta gimbiya Asmau ta kira ta, “Hello fulani..” “Na’am.. Hajjaju!” Tak’arasa tana cigaba da rusgar kuka, Hankalin gimbiya asmau yai matukar tashi, “Fulani! Menene? Eh! Waya saki kuka? Menene kiyi magana mana.” “Hajjaju! Ta tabbata cikin nan gaskiya ne, Wallahi tsabar tashin hankali ban kare masa kallo ba hajjaju, Baki gansa ba ya girma..” “Kina nufin kice har ya nuna sosai kenan? Katarar ubancan.” “Har Salman na matsa mata kafafu, kingan su atare kuwa hajjaju? Wallahi bansan sanda nai gajeriyar suma ba hajjaju. Ina cikin damuwa Hajjaju, Da alama zamana yazo kar..” “Karki karasa, Uban uban su daga ita har shi Salman din, Banda mahaifin ku ya tsaya akan su, Ai da Aliyu Salman mahaifin sa ma bazai sarautar basannabas ba wallahi. Ciki tamkar yabi iska ne, Dan dole musan abinyi akansa yanzu yanzu kuwa.” Shaheeda tasake barke wa da kuka tana jujjuya kanta kawai, Idanunta Salman da dije kawai suke tariyo mata, a yadda tagan su dazun nan Salman din na marairaicewa dije. “Fulani! Ko bakya jina ne?” “Inaji hajjaju.. Yanzu hajjaju idan zancen ya fito fa? Kinfasan yadda mukai rufa rufar sa shekaru da yawa,.” “Kassh! Banace ki dena damuwa ba? Yanzun kikasan abubuwa nawa zansa amiki!? Ciki harda binne maganar bazata taba fitowa ba. Ciki kuwa idan kwantar wa ne sai musa a kwantar yabi fatar cikinta.” “Toh Hajjaju..” “Yauwa fulani. Kwanta ki bacci da munshari kinji? Karma maganar can tasaki a mawuyacin hali.” Sallama sukai takashe itama ta katse. SHAHEEDA kuwa Sabon shafin kuka ta bude taitayi tana bori. Can Salman ya kirata a waya, Dakyar ta iya dagawa tana share hawayenta. “Hello shaheedah..” “Na’am” Ta amsa shi tana mai kokarin daidaita muryar ta. “Ya jikin naki.? Na dawo na tarar bakya dakin, why?” Shaheeda ta kunduma masa zagi azuciarta tana share hawaye a fili, “Na wartsake shi yasa..” “Okay.. Zan zo anjima.” Kit shaheeda ta katse kiran tana mai wulli da wayar. Tunanin yadda hajjajun su zata bullowa lamarin kawai take, Domin shaheeda irin mutanen nanne masu oya oya. Komai na ta so take ya zama babu matsala. Tana ta zaune, Dake period take, Sai dai ta tashi ta canza pad tadawo ta zauna. Har Salman ya shigo tana can tana tunani. “Inata sallama kinyi shiru.” “Banjiba. Barka da dare.” “Barkan mu.. Ya jikin naki?” Ya fada yana taba goshinta, Ta goce tana yamutsa fuska, Kunsan tabarmar kunya da hauka ake nadeta, Fashewa tai da kuka tana zubewa a jikin sa. “Menene.. Jikin ne?” “A’ahh..! Salman meyasa zaka ci amanata har haka?” “Amana kuma? Wata amanar taki naci?” “Yanzu fisabilillahi shekara da shekaru nayi hak’uri na zauna da kai duk tsawon lokacin nan, Nayi nayi muje Habeeb medical center dake Oman a samun cikin nan ka ki... Amman shine a asirce ka ka kai amaryar ka aka dasa mata.. No wonder kuke bobboyewa, Kwana biyu bata gidan ashe da walakin.” Har tayi ta gama Salman kawai binta yake da kallo, courage dinta na matukar bashi mamaki. Murmushi kawai yayi, Ya kamo hannunta yana murzawa a hankali, “Shaheedah.. Idan hankali ya ‘bata hankali ne ke nemo shi, Duk wani mumuni baya cire rai ga rahamar ubangiji, Babu wanda abu dake bamai yiwu wa ba fyace Allah ne ya kadarta haka kingane? Dan doctors sunce bazaiyiwu ba shikenan kuma kika dauka bazaiyiwun ba? Uhm? Ina karatun ki” “Meka dauke ni Salman, Jahila?” “No ni bance ba, Kawai naga a matsayin ki na mai zurfin ilimi sosai bai kamata kice haka ba.” Fincike jikin ta tayi daga nasa ta mi’ke tsaye. “Idan mutanen duniyar nan zaka tara bazan yadda ba, Saboda tsagwaran makirci ne. Ko dai zuwa kukai aka sa mata, Ko kuma zuwa tai ta sa meshi ta wata hanyar, Kai bazaka sani ba domin naga alama an wanke an baka ka kasha. Amman dai tabbas ka kwana da sanin wannan ciki ba naka bane..” Mikewa yai shima yana kallon cikin idanunta, Ta janye da sauri saboda kwarjinin daya mata. “Haka kikace ko?” “Eh haka nace.” “Shikenan! Mu kwana lapia..” Ficewa yai batare daya kara bi takanta ba. Ita kuma ta zube awajen tana hawaye. Jakadiya Abu dake labe tana jinsu ta dora hannunta a kirji tana zare idanuwa. *SAS* Yana koma sashen sa, Wanka ya shiga yayi a bandaki hade da alwala, Ya zura kayan bacci ya nufi sashen Khadija. Tana baje akan carpet tana cin gyada. “Zawjatii..” “Honey bunny.. Ka dawo?” “Eh na dawo..” “Ya jikin nata?” “Taji sauki.” Gyada kai nayi kawai na cigaba da cin gyadata, Na daga kafafuna na dora akan cinyarsa daya zauna a kusa da ni, Ni kuma kai na yana daga can gefen gado na dora kai na akan tum-tum. “Dan mammatsamun kafafuna.” “Okay... Your highness.” “Yauwa takawa na.. A matsa dakyau.” Matsamin ya fara yi cikin kwarewa. Yana shafamun heat balm awajen, “Meye labari..?” “Hm babyn ka taita kicking dina, Naita cin abinci. Saura kadan fa dazu na rama naushin data mun.” Zare idanu yai yana daria, Ya saki k’afar ya dawo santar kai na yana d’aga rigata sama, Hannun sa yasa yana shafa cikin, Hade da dora kansa akai “Little one! Ayi hak’uri a dena dukan Mami, Tace Zata fara ramawa.” “Mami?” Na tuntsire da daria, Na mike zaune , Na barshi yanataiwa cikin magana kamar da wani yake. “Uhm.. Mami da dadi fa. Ko akwai wanda kikeso, Mama, Maama, Ammi, Oumma, Maa, Mommy, Ayii, Ummi.” “Ai Kowanne yayi dadi har Mamin. Zamu zaba sai babyn tazo.” “Mace zaki haifa mana love?” Ya fada yana shafa gashin kai na. Na lura abubuwa mafi soyuwa a jiki na dayake muradin so akwai gashi a gaba gaba. Na dora kai na akan kafadar sa ina shafa kwantaccen sajen sa, “Inason mace.. Saboda saka mata kaya pink, Da yi mata kitso.” “Nima inason mace... Mai kama dake sosai. “ “Me kama da kai dai. Sai tafi kyau” “Wa yagaya miki.. ?Tab! Me kama dake dai Insha Allah. I can’t wait. Allah dai ya saukeki lapia.” “Aamin! Aamin.” Dauka ta yai gaba d’aya ya dire akan gado, Yasa hannu ya kashe fitila. Yana mai janyo bargo ya rufe mu, Daga nan wasan ya canza aka shiga fagen daga sosai.... <><>>>>>>>>>>>>>>>. <><><><><>>>>>>>>> *SASHEN JALEELAH* Jakadiya Abu dakyar tayi bacci saboda maganganun Salman da shaheeda data jiyo akan cikin da dije ke dauke dashi, Gari na haske tatafi sashen Mama Jaleelah don sanar da ita labarin cikin. Tunda itace d’iyar waziri. Mama Jaleelah na hakimce akan kujera gama cin abincin ta kenan tana hutawa, Da alamun bacci ne yakeson d’aukar ta duba da yadda take lumshe idanu ahankali tana bud’e su. Jakadiya Abu tashiga bayan anmata Iso, Tana zama tafara haki saboda da tazara tsakanin sashen hadimai dana matan gidan. “Hakkin me kike Abu? Gudu kikayi ko kuwa wani ne ya biyo ki nan din.? Laifi ki kai ko menene? Kinzo sai numfarfashi kike, Tashi ki bani waje in babu abinda ya kawo ki.” “Tuba nake ranki ya dade, Allah yakara miki lapia da nisan kwana. Wallahi daren jia ban runtsa ba shi yasa ka.” “Bakida lapia ne?” “Kalau nake ranki shi dad’e... Furgici ne kawai da tsantsar tashin hankali dana shiga.” “Ina ji..” “Tun kwanakin baya nake wani bincike, Toh Allah da ikon sa sai daren jia sakamakon binciken ya fito..” Mama Jaleelah ta mike daga kishingid’en da take ta zauna tana duban jakadiya. “Ke na fara sanarwa, Domin abunda ya shafe kine ya kum...” “Jeki ga ainihin zancen.” Jakadiya ta saki nannauyar ajiyar zucia kafin cikin tabbatarwa tace, “Gimbiya Khadija.. Na dauke da juna biyu.. Har ya girma.” Mama Jaleelah ta mike saboda jinta da ganinta daya dauke na yan Wasu dakikai. “Maimata abinda kika ce...” “Gimbiya Khadija na dauke da juna biyu.” Ai Jaleelah bata jira karashen zancen jakadiya ba tashige cikin dakin ta, Jikin ta sai kakkarwa yake. Waziri (mahaifinta) ta kira ta fada masa komai. Alokacin Waziri kuma ya gama shiryawa zashi fada. Da sauri ya koma ya shige cikin dakinsa ya rufe tare da tuge rawanin kansa ya yi cilli dashi, banda cije baki da bubbuga hannu a kanshi babu abinda yake yi. Uban gumin da yake tsatsowa daga jikinsa sai ka rantse da Allah daga wanka ya fito tsabar digar da gumin keyi. Zagaye kawai yake a cikin dakin zuciyar shi cike da matukar mamaki jin cewar amaryar sarki Salman tana dauke da juna biyu. Ta ya ya mace zata samu ciki bayan an tabbatar da cewar mijin ba zai taba haihuwa ba? Karya ne wallahi dole akwai wata kullalliya da Salman ya shirya yi a cikin masarautar nan, shi yasa yaje ya auro wacce ba jinin sarauta ba. Yar talakawa da bata da arzikin komai sai bin gidajen yan uwa. Karar wayarsa ce ta katse masa tunanin da yake yi, ya lalubi cikin aljihunsa ya ciro yana dubawa. 'Mai martaba' ya gani baro-baro ransa ya yi mugun baci ya mai da wayar cikin aljihunsa. Ba zai dauka ba domin yanzu jin tsanar Salman yake yi a fili ba wai a zuciyarsa kadai ba. Ya tsane shi tsana mafi muni da babu wani dan Adam da ya taba tsana kwatankwacin wannan. “Sai na illataka Salmanu, sai na nuna maka baka da wayo bare kuma dabara. Bana sonka bana kaunarka, ko mahaifinka na zauna dashi ne kawai ba dan ina kaunarsa ba bare kuma kai da aka haifeka a gabana. Ni zaka munafinta ka nuna min cewa ni ne abokin sirrinka? Ni zaka mayar sauna wanda besan abinda yake yi ba Salmanu? Kayi kadan wallahi, ba a haifeka ba ballantana kace zaka fini dabaru. Muje zuwa zan nuna maka koni waye Salmanu, wannan cikin ba a isa a raina mana hankali akan shi ba, Sai kun fadi yadda akai kuka samo shi munafukan banza munafukan wofi.” Cewar waziri da yama rasa abinda zai yi saboda tsabar damuwa da shiga tashin hankali. Domin rashin haihuwar sa da shi zasuyi amfani wajen tsige rawanin sa, Wani kiran ne ya kuma shigowa, cikin masifa da zage-zage ya ciro wayar da niyar kashewa ya yi zaton Salman d'in ne sai kuma ya kara ganin sunan Jaleela, ya dauka a fusace yana cewa. “Menene kuma, Zaki bi ki dameni?” Cikin damuwa Jaleela tace. “Abba ance fa cikin yafi wata hudu, kuma na gangaru da yake min aiki yanzu yace ya kasa gane meye a cikin mace ko namiji, shine na kira na ce ko z....” Bata karasa ba waziri ya yi hanzarin katse ta. “Kinga Jaleela ki rabu dani, duk wannan fafutukar da nake yi so nake naga sarautar ta dawo hannun mu, Amman gashi nan abu yana neman hargitsewa. Tun farko nace miki muyi maganin su Abdulqadeer dasu Maheer, ya zamana duk yara mata gareku, amman shegen taurin kai irin naki kika ce, A'a ai kuna hade dasu Huwaila. Toh yanzu..Sai kije ku nemo mafita da kanku, su suna da maza Wanda ko babu jinin Salman a duniya zasu Iya karbar mulki, kuma tsab zasu Iya korarki daga cikin masarautar. Dan haka ki rabu dani naji da abinda yake damu na nima.” Zata kuma yi masa gardama ya katse kiran tare da jan wani mugun tsaki dan a yanzu Kowa ma waziri haushinsa yake ji musamman a wannan lokacin da yake cikin zafin zuciya da bacin rai. Kaya ya sauya ta yadda ba zaka taba tunanin shi bane, ya fito ba tare da yabi takan iyalinsa ba yaje ya dauki Mota ya fice. Gurin tsibbun sa ya nufa, yana zuwa ya tarar da shi yana ta dariya ba kakkautawa, tsayin lokaci bokan na dariya waziri be kula shi ba dan hatta shi din ma a wannan yanayin zai Iya yi masa rashin mutunci dan yana ganin kamar ma yana sane da cikin amman be sanar masa. “Nasan dama zaka zo da kanka ba aike ba, nasan zaka shiga cikin wannan yanayin shi yasa tun farko nace maka Salman baya amfani da duk maganin da kake kai masa.” “Ni yanzu so nake naji daga Ina matsalar take?” “Hahahahahah aljanu su taimake ni na taimaki Waziri. Ai babbar matsalar tana tare da Salman, Gimbiya Khadija ita ce matsalar ku gabaki daya waziri. Wannan yarinyar da kuka raina, kuke ganinta kamar karamar alhaki, a yanzu itace zuciya da ruhin sarkin ku Salman.” “Kana nufin kace min cikin da ake magana na Salman ne? Ta ya ya hakan ya tabbata bayan shi din juya ne bashi da wani tasirin yiwa mace ciki?” Boka ya kalli waziri tare da cewa. “Koma dai menene kuje ku tambayi matarsa ta farko, ita tasan menene gaskiyar lafiyar sarki Salman game da samun ciki.” Waziri ya kuma kallon boka cike da takaici, Sannan ya kawar da kai yana furzar da iska daga cikin bakinsa yace. “Ina son kayi min dalla-dallah da kanka, bana son naje na samu kuskuran magana, ka gaya min duk abinda yake faruwa.” Sake bude idanuwa Bokan ya yi tare da daukar wani faifai mai dauke da kasa a ciki ya yi dangwale-dangwalensa, kuma kallon waziri ya yi yana wani irin abu da harshe kamar tsohon maye sannan yace dashi. “Idan har kuka bari aka haife abin da ke cikin nan da rai, humm-hummm waziri.” “Yanzu babu abinda zaka Iya taimaka min dashi?” “Akwai magunguna waziri, kaga Ina da wanda za'a Iya kwantar da cikin ta shekara goma be tashi ba. Akwai Wanda zata Iya haifa amma babu rai. Akwai kuma wanda zamu bayar tayi barinsa Koda yakai watanni tara. Wanne kake so? Saboda ko wanne yana da sharrudan da za'a kiyaye.” Waziri ya gyara zamansa cikin ransa yana jujuya wanda zai ce ayi, daga kashe dai yace da Boka. “Ina son ka bani wanda za'a daure cikin ya zamana tamkar babu shi dan bana son ma ace tayi bari ko ta haihu ya mace, wannan duk zai sa Mutane su san cewa zata Iya kuma haihuwa nan gaba. Amman yanzu idan aka daure cikin kaga Sai ayi ta faman jira aji shiru har ma ace tayi karyar ciki dan ta cuci mai martaba.” “Aljani d'an tsartu ya karbi bukatarka, yanzu haka zai kawo maganin da za'a baka.” Boka na rufe baki kuwa sai ga wani kullin leda baka ta fado, Bokan ya dauka tare da mikawa waziri yana kuma yi masa karin bayani. “Karbi wannan maganin, yanzu Aljani d'an tsartu ya karbo maka a can kasar faleru. Za'a zuba shi cikin abu mai ruwa wanda take sha, ko lemo, ko Shayi, ko kuma ruwan sha. Idan har ta sha sau uku yau daya gobe biyu jibi uku, Ina mai tabbatar maka da cewa rana ta hudu zata tashi taji batajin komai a cikin ta.” Cike da murna waziri ya amsa yana jujjuyawa, muryar Bokan ce ta dawo dashi daga kawa zucin da ya tafi, inda yake cewa. “Da akwai sharadi.” “Toh Boka wane irin sharadi ne? Gaya min saboda indai akan wannan lamarin ne zan Iya yin koma menene.” “Shikenan tunda kace a gaya maka. Sharadin shine idan har bata sha ba tsawon kwanaki uku. Zaka shiga cikin mawuya cin hali, wanda kai kanka Sai ka kyamaci kanka bama wani ba.” “Toh Wai me yasa ba za'a kashe ta ba ne ita yarinyar?” “Na Sha gaya maka ba zamu Iya halaka ta ba kai tsaye, kasan munsha gwada tura aljanu dan su kashe ta. Amman sai a kama mana su, wajan aljanu dari uku aka kama mana duk a sanadin yunkurin kashe yarinyar. Kayi hakuri da son kashe ta dan ba abu ne me yiyuwa ba.” Ajiyar zuciya waziri ya sauke daga nan ya zaro uban kudi ya ajiyewa Boka, a cikin aljihu ya saka maganin daga nan ya mike ya tafi ba tare da ya yi masa sallama ba. Burinsa kawai yaje ya aiwatar da wannan aikin maganin, tare da daukar aniyar hana Dije da Salman kwanciyar hankali... .....Falaki na daga gefen farfajiyar fada da wayar sa a hannu yana duba tracking din Waziri, Tun daga tafiyar sa har zuwa dawowar sa fada. Saving yai ya turawa Salman. Ranar dai gaba ki d'aya Waziri bai shiga fada ba. Koda ya dawo ma da daddare suka hadu dasu wambai, Waziri ya sanar musu da cikin dije, Kowannen su ya shiga cikin madaukakiyar damuwa da tashin hankali. Gaba d'aya tracking d'insu waje d'aya ya nuna. Salman shi abunma daria yaso bashi , Suna daga zaune shi da dije suna kallon su, Suna kuma cin gugguru sai kace a cinema.. "Kada ki damu da makaman tsibbun su, Lapia zaki haife abinda ke cikin cikin ki.. Sannu ahankali zasu san wannan cikin KIBIYAR AJALI.. Zai zamar musu, Mai dauke da cikin kuma kainuwa ce, Domin ke din sulke baya tare ki sai kin gitta..." Nayi dariya ina shafa sajen sa dake kyalli.. "Insha Allah honey bunny, Da Allah muka dogara, Yanacan a madakata. Oganniya yar baffana nake, Ko Gajiyalle hakura tayi ta sallama...." Kafa yasa ya kwantar da kujerar da muke Kai tazama kamar gado. Yasa hannu d'aya yana zagaye labbana. "Mantar dani damuwar su zumaaa na." Murmushi nai kawai domin na gano me yake nufi, Na juya masa baya. Hakan ya bashi damar kashe fitila muka tunkari abunda ke gaban mu. Ina kaunar Salman, Domin a fagen soyayya anya yanada na d'aya kuwa?... Duk wata damuwata a daren nan sai dana nemeta na rasa, Sai ma samun kai na nayi da tallafe abuna muka gurji soyayyah.. *DURBUN* *MAI GARI JAMILU* “A hayye- A hayye, Ga jirgi ga jirgi! Ga mota ga mota, Yan birni-Yan birni...” Haka wasu dandazon yara suka shiga zagaye kofar gidan mai gari jamilu suna ife ife, Sun taru rukuni rukuni suna kallon ba’kin da suka zo wajen mai gari jamilu, Jeep motoci guda biyu, Sai luxurious bus guda d’aya, Sai helicopter dake shawagi a saman kauyen, architect ne aciki yana zana yadda za’a yi makarantar, Da yadda za’a shimfidawa kauyen titi wanda zai kai kaika har kan titin birni. Bayan tafiyar yan birnin wanda nambobin jikin motocin su duk na gwamnati ne sai bus dince kawai me dauke da tambarin masarautar Basannabas. Mai gari jamilu ya sake tara dattijawan garin maza yana sheda musu yadda sukayi da mutanen da sukazo daga birni a takaice. “Ku zazzauna, Ku saurara. Labari ne mai dadi nazo muku dashi.” Mudi da yaje wucewa jin mai gari na cewa labari mai dadi yazo dashi sai yaja ya tsaya yana cigaba da bantarar raken dake hannun sa. “Mai gari jamilu muna saurara.” Cewar na laraba, Mahaifin su uwande. Mai gari ya sake gyaran murya fuskar sa dauke da farin ciki, “Kunsan muna cikin jimami na maganar da gwamna ya turo mana, Za’a bamu wajen zama a kauyen Landantsan dake gaban mu, A kuma biyamu kudin gonakin mu, Kusan dukkanin wani mazauni dake durbun kama babba, yaro, tsoho Kai har na goye yasan mu mutan durbun bamuyi marhaba lale da zancen nan ba, Amma ya zamuyi da gwamnati? Duk kuwa da marayar mu ce nan tun ta kaka da kakanni. Wasunmu har sun fara binciken matsugunin da zasu zauna a kauyen landantsan, Saboda makarantar kwana da za’ayi da sauran ma’aikatar aiyuka da za’ayi guda d’aya anan din, “Toh albishirin ku mutanen durbun, So nake Kowanne daga cikin ku ya fadada murmushin fuskar sa har zuci, Ya kuma sanar da iyalai na gida yadda akai.” “Kaga mai gari jamilu, Ni wannan dogon bayanin duk mun san shi, Menene alfanun maimaita shi Eh?” Malam Garzali ya tambayi mai gari cikin kosawa. “Kai kullum bakacin ribar zance Malam Garzali, Baka taba bari a karasa zance zaka hau ya akai?” “Yo ai gaskia ne mai gari.. Dole mu tambaya, Nabar buhu na a daji ne kar awakai su cinye dan amfanin ciki.” Mai gari ya gyada kai, Hade da mikewa tsaye sosai yadda na baya zasu gano shi. Sannan yafara magana da k’arfi yadda kowa zai juyo shi, Ciki harda mudikalle daya tsaida abasiya mai awara suna zance. “Mutanen Durbun.!!! Mai girma gwamnan birni da mai martaba sarkin mu dake birni, sun ce a sheda muku, Maganan tashi mu koma kauyen landantsan na gaban mu an soke ta..” Dattijawan wajen suka magana Kowanne cikin farin ciki, “Ku saurara bangama ba, Malam ilya, Malam Sabiu ya isa haka nan, Ku saurara jama’a. Wannan mutanen da sukazo daga birni wakilan gwamna ne dana sarki, Sunce a shaida muku an soke zancen tashin mu, Sai dai abu d’aya ne zasu yi amfani dashi, Gonakin mu na bayan gari dana gefen kan tudu wajen rafi, Dana gangaren bakin kasuwa... Zasuyi amfani dasu wajen ginin makarantar kwana babba wadda yan bautar Kasa zasu dinga kwana, Duk wanda gonar sa ta shafi wajen to sunce Za’a biya kudin gonakin baki d’aya harda karin wasu kudaden, Sannan matar mai martaba wadda ance zatazo nan gaba, Tasa a mana titi kyauta wanda zai kai har cikin birni... Yadda mukayi dasu, Saboda haka cikin satin nan Za’a fara aiki, Nasaka hannu na wakilce mu baki d’aya nida hakimi. Yanzu zamu zaga gonakin dan daukar sunayen duk manomin da gonar sa take wajen, Za’a aika da takardar birni, Zasu zo da kudaden kowa..” Sai farin ciki, Gaba d’aya dattijawan mazan da mata dake leke ta saman zaure sai suka fara murna, Kowa fuskar sa dauke da farin ciki marar misaltuwa. Mudi ma tsabar farin ciki ko zancen basu gama ba da Abasiyya ya mike zai tafi, Abasiyya taja hannun rigar sa, Fuskar nan tata tasha dige digen jamfarce. Girar data zana ta hade da kunne. Ba sauk’i dai gaba d’aya. Ita nan ta kure karshen gayu. “Ina zaka bamu gama ba.” “Sauri nake Bebi Abassy tawa. Zanzo zancen ai anjima.” “Yasin ba zuwa zakai ba, Kawai dai kai tsoran ladiyo kake har yanzu..” “Allah ya sawwake, Kede ku bari akawo kudin auren kiga. I lobiyu bebi ta.” “I lobiyu nima nawan. Mezan samu?” “Ungo wazobia, Kafin nazo anjiman.” Sallama sukai ya tafi gida yana tuno yadda Abasiyya Zata zama matar sa. Yana shiga ya fara kwalawa su Gajiyalle kira, “Gajiyalle, Gajiyalle.” Fitowa tai daga bandaki tana dafe ciki, “Mudikalle ina maganin zawon?” Mudi ya dashare baki yana cizan yatsa, Hamsin din data bashi ya siyo mata maganin kenan ya bawa abasiya kudin tad’i.” “Tab ki jika kwakin jiya kisha kawai, Gajiyalle an fasa tashin mu daga durbun, gonakin su ale hamza kawai Za’a yi amfani dasu ayi makarantar.” Gajiyalle ta dankara masa harara tanemi gefen dutsin gurji ta zauna tana nishi, “Bankadadden banza, Mokadadden wofi, Kana gani wazobiyar adama ce dakyar ta aramin saboda yadda naketa zaryar zawon nan shine zakaje ka kashe? Toh narantse da uban daya haifeni ko zaka siyar da kan rantalelen danka sai ka kawomin wazobiyar nan.” Mudi zai magana ladiyo tafito tana gud’a da hanci, “A hayye! TubarkAllah Masha Allah, Ga rantalelen kai nan a jikin ki..” Mudikalle zai magana ladiyo ta dire tsallen albarka tana karkada masa hannu, “Ja tsaya karamin munafiki maci amana, Wa yagaya maka bansan Abasiyya kake nema ba zaka aura? Ko kaga anwa uwata kishiya da zakayo mun? Baka isa ba wallahi, Kaje can ku karaci sharholiyar ku da ita, Amman ba zaka auromun ita gidan nan ba. Gida nawa ne nan bana wata ba.” Gajiyalle dake numfarfashin ciwo jin ana tunkaho da gidan ta saita mike tayo kan ladiyo, “Wane gida ne naki? Nace uban wa ya baki nan gidan.” “Badake nake ba tsohuwar kilaki kawai, Tsabar gulma da munafurci kin tako tinkis tinkis kina jan kafa. Maza kafin nasa k’afa na shure ki.” Nan fa gajiyalle ta cire dankwalin dake kanta, Gashin ta ya zama furfura yayi dagaje dagaje, Ta daure dankwalin a kugu tana lailayo ashariya tana zundumawa ladiyo. “Ke sanyi nai, Ki tambayi kowa, Wacece Gajiyalle mai yar hakiya, Duk matan garin nan a baya ba wanda ya kai ni yawan kiwo da zabbi da kaji...” “Ina ruwana dasu, Tunda ban shigo na gansu ba, Abinda nasani shine kin kuntatawa yar mijin ki kin zalunce ta, Kowa da yake ubanta ma ke kika kar shi.” “Kinci malamar kan uban ki. Da uwannanniya mai yakuwa gyatumar ki zanyi ba dake ba.” Cewar Gajiyalle cikin fushi, Ko mayafi bata saka ba ta fice fuuu Mudi na tsaye ya rasa yadda zai yi. Halipha ‘dan su sai jan rigar sa yake, “Abba abinci. Abba abinci.” “Zo nan halipha muje bakin kasuwa” Cewar ladiyo. Mudikalle zai hanata fita, ladiyo ta dura masa ashar tana karkada masa hannuwa, “Kai ka isa ka hanani fita, Babu zanci agidan naka? Bakin kasuwa anan ka auro ni, Don haka dole ka kyaleni tunda tun fil azan acan ka ganni. Idan gyatumar ka tadawo kuma ta tankade mana garin can, Matsa sullutu kawai.” Tana gama magana ta sabe halipha a hannu tafice, Shi kuma Mudikalle ya rasa yadda zaiyi, Daga karshe ya yanke shawarar bin Gajiyalle, Acan ya tarar dasu da sirikar sa uwannanniya sunata dambatuwa da Gajiyalle, Sai kasa ce ke tashi. Duk yadda akai aso rabiyar fadan nan sai da aka kasa. Sai da suka daku lilis sannan wakilin mai unguwa ya tasa k’eyar su duka biyun zuwa gaban mai unguwa jamilu domin ayi shari’a...... _😂💔Haka dai zaman yake kasancewa a durbun: Ladiyon Mudikalle kenan a gidan Gajiyalle mai yar hakiya... 🧚🏻‍♂️_ Asha hutun weekends Lapia ❤️ Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥 _I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_ _B33_ ****Zaune nake a cikin daki duk nabi na gaji sai kace wacce tayi aikin wahala, gaba daya zaman dakin ne ya ishe ni, ina son sauka kasa na dinga ganin gilmawar mutane amman babu hali Salman ya hanani a cewar sa za'a Iya hada baki da masu shigowa sashen nawa su barbad'a wani abin, tsautsayi yasa na bi takai su illatani ko su illata baby. Sallamar d’aya daga cikin hadimai a kofar daki na yasa nai saurin waigawa Ina amsawa, na bata umarni ta shigo bayan na zura hijabi a jikina. Hannunta dauke da jug garai garai wanda hakan yasa ni hango ko menene a ciki wato damammiyar fura da nono an sanya kankara a ciki gwanin ban sha'awa, “Ranki ya dade mai babban daki tace a kawo miki ko kina da bukata, Umma Hansatu bata kusa shi yasa ta bayar a kawo miki.” Tunda na hango furar nan babyn ciki na ya/ta dinga harbi na kamar za'a huda min ciki. Na karba jiki na kyarma tare da yin godiya ta juya ta fita, na karasa wajan table na ajiye tare da dakko kofin da nake shan shayi na zuba, ni kai na yadda furar tayi shar ga kamshin ayaba dake tashi a ciki yasa na kagu na ji ta cikin baki na. Karar da wayata keyi ne ya dinga rabamun hankali saboda ringing d'in Salman ne, na dauki kofin tare da karasawa gurin wayar ina shirin dauka naji ta tsinke dai dai sannan kuma naji an shigo cikin dakin da gudu, kafin na tabbatar da waye naji an buge kofin tallatsin furar ya sauka saman fuskata. Salman ne yana tsaye sai faman haki yake da alama gudu ya yi da zai taho. Ya dafe kai tare da rintsa idanuwa, ni kuma na yi kicin-kicin da fuska rai na a bace dan na shirya kaiwa baki na ya yi min wannan abin. Kusa dani ya matso tare da rungume ni, kai na dake kirjinsa yasa kunnuwa na jiyo min yadda bugun zuciyarsa ya tsananta. Murya na rawa yana shafar bayana ya fara magana. “Karki sha furar nan Zawjatii... Kar ki sha. Karya ne ba daga gurin Ammi aka aiko dashi ba, daga gurin Jaleelah ne waziri ya zuba maganin da ya karbo gurin wani tsibbun nasu shi dasu wambai shine suka kawo miki.” “Innallilahi wa'inna'ilaihir raji'un... Na shiga uku ni Dije, me yasa banyi wannan tunanin ba? Karo na ba adadi kenan, Koda yake sunyi amfani da Ammi kuma daman Umma Hansatu ta tafi gurinta karbo min kilishi, shi yasa nayi tunanin da gaske ne, kai ya akai ka sani?” Sai da ya dan dago fuskata ya kalleni ya sake maida kai na kirjin nasa yace. “Ina ciki Ina wani bincike nagani, bayan sun bawa waziri maganin , Shi kuma ya zuba maganin sai suka bawa jakadiya Abu tasa a hijabi ta nufi bangaran Ammi, to daga can ne ta bawa yar aikin Ammi tace ta kawo, ita kuma da tazo ta bawa daya daga cikin ma'aikatanki tare da yi miki bayanin da tayi miki cewar inji Ammi. Na kiraki tun farkon da naga kin karbi kofin amman baki daga ba, ganin kin tashi yasa ni fitowa da gudu karki je kisha kija min asarori.” “Kai wannan masifa da me tayi kama?” “Shi yasa nake son mu kuma yin taka tsantsan dan gabaki daya mutanan nan sun shirya lalata min cikin dake jikin ki. Takun da Zaki canza yanzu shine ki dinga zama da hijabi yadda zasu dena ganin girman cikin nan bare su kawo masa hari.” “Na shiga uku a dakin nawa na sai na saka hijabi?” “Eh! Dan Allah kiyi min wannan alfarmar dan Allah my love.” Na rausayar da kai, ni kai na ina jin yanzu na fishi kaunar cikin nan saboda yadda nake jin kaunar abinda yake ciki. Salman ya dago ni tare da karasawa dani wajan gado muka zauna, kafin ya yi magana na riga shi. “Insha Allahu zan kiyaye, yanzun ma matsalar da aka samu shine babyn na ganin furar aka fara nuna min ana cewa za'a sha. Kuma fa ban jima da cin abinci ba, amman kaga hadama.” “Babu komai indai fura da nono ne bari nasa Falaki ya kawo miki mai rai da lafiya.” Nayi murmushi tare da kwanciya kan kafadar shi Ina tuna wani labari da nake karantawa, yadda mijin yake wulakanta matarsa saboda kawai tayi ciki shi kuma be shirya haihuwa da wuri ba. Sabanin Salman dubi yadda yake tarairayata yana bani kulawa ninkin wacce yake bani kafin cikin. Sallamar Umma Hansatu ne yasa shi saurin dago min da kai, nuni ya yi min da zai gudu yana cewa. “Bana son asan da kofar nan shi yasa.” Na gyada kai Ina masa dariya ganin yadda yake sand'a tamkar marar gaskiya. Sai da na tabbatar ya shiga ya rufe sannan na tashi Ina amsa sallamar da take yi. “Umma ki shigo mana.” “Au to ai naji ba a bani izini bane shi yasa Gimbiyar mu.” “Ai kuwa tunda kikai ta farko nake ta amsawa Ina shigowa bakiji bane.” Na fada cikin son dauke mata hankali da wani hasashen a kai na. “Kinga barna nayi shine nake kokarin gyara gurin.” “Asha ai da kin bari nazo nayi, yanzu ma tunda Allah ya kawo ni, Sai kije ki zauna na gyara ranki ya dade. Ga kilishin kuma tace duk Abdullah ne ya kwashe bata kula ba sai gani tayi yana ci.” “Allah sarki Ammi na, shi kuma Abdullah yaci rabon shi.” Muka sanya dariya saboda yanayin yadda na karasa maganar cikin wasa. Ita kuma ta gyara gurin tas ina gefe ina cin kilishi na. Bayan ta kammala ne da na tashi zan shiga toilet na tafi da ragowar furar na zubar tare da wanke kofin Ina dad'a yiwa Allah godiya da ya kubutar dani wannan tuggun. Ina fitowa na kuma hayewa gado na zauna Umma Hansatu tana bani labarurruka na ban dariya, ashe duk Salman yana ganin mu sai text message d'in shi na gani yana cewa. “Masha Allahu love.. kina da cute smiling face, idan kika yi dariya kuwa ina kasa controlling kai na, I love you so much.” Ban san lokacin da na kuma sakin dariyar ba Ina rufe fuska dan nasan kallo na yake yi a inda yake, Umma Hansatu kuwa tayi tunanin duk cikin labarin ta ne yasa nake kuma jin nishadi. Ta kuma gyara zama tana rattattako wasu labaran... <>>€><> Gaba d’aya zancen cikin dije ya gama karade masarauta da abunda ke cikin ta, Kowanne bangare maganar cikin suke yi, An sawa dije da cikin ta idanu. Sihiri, Makirci da tsantsar bakin ciki. Gaba d’aya ahalin masarautar suna cikin dimauce, Farautar ran dije suke da dan cikin nata mararan. **** Waziri kuwa gaba d’aya ya zama tabbabbe a zuci, A Zahiri kuma ya zama wani birkicacce. Ya dena zuwa fada saboda bakar mugunta yace bai da lapia ne. Nan kuwa kullum cikin tsara surkullen yadda cikin dije zai zube yake yi. Shida su Chiroma basu hakura ba suka sami wani garin maganin awajen yar mai ganye. Ya samu wani amintaccen hadimin sa ya kai maganin cikin sashen Khadija, Aka faki ido aka barbada a miyar da Umma Hansatu keyi. Ba masaniyar abincin bana dije bane na Umma hansatun ne. Kwanan Umma Hansatu 3 tana ciwon ciki dakyar ta farfad’o, Tun daga lokacin kuwa SAS ya hana dije cin abincin masarauta baki d’aya, Saboda a kayan abincin ma Za’a iya hada baki da wani ya zuba maganin cutarwa. Shiysa kullum sai dai ayi mata takeaway a boye taci. Waziri kuwa an sanar masa tabbas Dije taci abincin nan, Sai jira yake yaji ana koke koken ta margaya, Yanzu abinda suka sa a gaba shine gaggauta cire Salman daga karagar mulki. Da daddare bayan sallar ishai suka taru a bangaren Mama Huwaila, Waziri ya tattauna abunda ya kawo su, Kafin ya cigaba da cewa, “Sai kuma matar sa ta farko, Gimbiya shaheedah, Duk itace ta kawo mana cikas, Kan ai Salman baya haihuwa. Bashida ishasshiyar lapia. Nace a mana iso da ita nan ta mana bayani don mu ba mutanen banza bane. Domin gaba d’aya na tattara dik hujjojin da muka tsara nayi su a rubuce zamu aikawa gwamna ya tsige shi daga kujerar sa..” Yana rufe baki, Parlorn ya d’auki magana baki daya, Dukkanin su sun hallara anata tsara yadda za’a tuge Salman a kujerar sa. A babban parlorn mama Jaleelah sukai zaman. Ba jimawa shaheedah ta shigo kanta a kasa tana raba idanuwa. A tsorace take ainun, Sai dai dake tana ji da kambun mulki ba zaka gane ba saboda yadda take yauk’i. “Barka da zuwa sarauniya.. Takawar ki lapia.” Kowanne ya shiga mata kirari, Su wambai, Waziri, chiroma, Galadima, Makama da sauran yan parlorn. “Barkan mu.. Waziri ga ni! Ina fatan lapia?” Ta karasa fada tana duba agogon hannun ta. Waziri yai murmushin gefen baki yana sakkowa daga kujerar daya ke zaune, “Allah shi taimaki gimbiya.. Wani abune muka ji, Daya sanya zukatan mu a rudani, Mun ‘karyata a baya, Amman da muka tsananta bincike sai aka tabbatar mana da gaske ne. Shine mukeso muji gaskiya ta bakin ki..” “Ban fahimce ka ba Waziri! Sanar mun abinda ya jefa zukatan ku a rudani..” Waziri ya sake rissinawa yana dan daga murya, “Maganar... Juna biyu da Khadija ke dauke dashi mana.” Da sauri shaheeda ta mike tana dafe kirji, “Juna biyu? Wacce khadijan? Wake dauke da shi? Bangane ba.” “Au.. Ina nufin gimbiya khadija mai dakin mai martaba Salmanu na biyu.” “Waziri!! Shin abunda kunnuwana suke jiye muni dagske ne ko kuwa? Don wane Salman din? Inde mijina kake nufi na yanzu to gaskia wannan zancen kanzon kurege ne, Domin salman baya haihuwa, Baida ishashshiyar lapiar da har wata acikin mu zata dau cikin sa. Sai dai idan awaje ta samo shi.” Waziri ya juya yana duban sauran yan parlorn dake bin shaheedan da kallo kamar wata gaula, Domin hajjajun su tace komai rintsi ta tubure kan lallai batasan da zancen cikin Khadijan ba. Waziri ya numfasa, “Kina nufin kice mun bakida masaniya akan juna biyun da take dauke dashi na mai martaba?” “Zan maka Karya ne waziri?” “Tuba nake ran ki ya dad’e, Lamarin ne da mamaki. Amman tunda ke kanki kince baki da masaniya inaga mu kuma.” Shaheeda ta dafe hannuwanta da goshi , Irin tana cikin jimamin nan, “Idan ma dashi din... Toh lalle bana Salman bane, Tunda kunga zahiri a yawon asibitoci da mukayi na duniya.” Waziri ya gyada kai yana kallon galadima. Galadima ya amshe zancen da, “Toh wacce gudunmawa zaki bamu?” “Wacce iri kuke nufi galadima?” “Gudunmawa dai wadda zata temaka wajen kamo bakin zare, Wadda zamuyi amfani da ita wajen tarwatsa ita ... Abokiyar zaman naki.” Da jin haka sai ta zauna, Kasa kasa tashiga magana. “Zan bada...Akwai general checkup results gaba d’aya wanda muka jajje da Salman, doctors ba adadi sunyi binciken su akan mu, An kuma gano shine mai matsalar.” Chiroma ya sake matsawa tsakiyar parlorn yana rissana mata, Kamar yadda Waziri ya tsara musu su tattambaye ta. “Allah yaja zamanin ki, A yaya sakamakon ya kasance? Takaddu ne ko kuwa?” Shaheedah ta dan yamutsa fuska tana taune kasan leben ta. “Duk abinda zai bada cikakkiyar gamsasshiyar amsa, Zai bayar, Domin akwai papers dake dauke da rubutun likitocin, Akwai fefan bidiyo dake dauke da bayanin komai, Sannan akwai sautin muryar likitocin wanda duk suna adane..” “Alhamdulillahi ranka ya dade kana ji ko?” Waziri ya gyada wa Chiroma Kai fuskar sa dauke da murmushi, “Lalle gimbiya kin biyamu, Mungode kwarai. Wannan results din da zaki bamu dasu kadai zamu iya tsige yarinyar can daga zuciar Salman dama masarauta baki d’aya, Idan ta kama ma mu rabata da iska.” SHAHEEDA dadi ya shiga ratsa ta tamkar ta tashi ta taka rawa don farin cikin jin Za’a fitar da Khadija daga gidan koma akashe ta baki d’aya. Waziri ya sake jinjina mata yana kakaro murmushi, “Mungode kwarai matuk’a sarauniyar mu. Allah yaja zamanin ki. Sai ki bayar akawo mana.” Mikewa shaheeda tai bayan ta daga kanta alamun Toh, Ficewa tai hadiman dake jiran ta awaje suka rufa mata baya. Tana futa su waziri suka tasa fefanta suna yi da ita baki dayan yan parlorn. “Rabu da ita, Itace babbar munafukar data fara ‘bata mana wasa, Na karairakin shine baya haihuwa ba ita ba, Ina sane na sako zancen futar da Khadija kadai ba tare danace tuge Salman gaba d’aya ba..” “Kwarai kuwa Waziri, Nima da fari nayi mamakin fad’ar hakan da kayi, Sai daga baya nagano lob’a ta kayi.” Cewar wambai dake gefe yana cin tufa. Haka dai sukaita tofa albakacin bakin su, Lokaci zuwa lokaci su Mama Huwaila kansa baki. Ana cikin tsara yadda komai zai kasance yareemah abdulqadeer ya fita da waya a kunnen sa, Can ya dawo fuskar sa babu walwala. “Baba Waziri..” “Na’am Makama.” “Wata magana ce maras dadi aka sanar dani yanzu.” Waziri ya zare idanu yana bin yareemah abdulqadeer da kallon karin bayani, “Meya faru kuma?” Bakin sa na rawa ya shiga gaya musu komai, “Khal... Khaleel dake Korea, Wanda na dora akan motsin sa yau yake sanar mun wai kwana biyu bayajin dadi....” Ai bai gama fada ba Waziri ya katse shi, “Khaleel dinne ba lapia?” “Noo! Shi wanda na saka ya dinga dakko mana rahotan Khaleel dinne wai baida lapia, Sai da ya kwanta a asibiti, Bayan an sallamo shi yaje gidan da Khaleel din yake..wai baya nan, Yaje asibitin sunce yayi resigning tun tuni, Yabi diddigi ance ya bar k’asar.” “Zancen banza, Zancen wofi. Wambai, Galadima kuna ji ko? Wannan wani renin hankali ne na daban da za’a kawo mana kuma, Khaleel din da aka kafe shi shekara da shekaru ta ina har ya iya barin K’asar duk bamu da masaniya Sai yanzu? Toh yana Ina? Nace yana ina? A hasale Waziri yake magana yana kallon abdulqadeer, Mikewar shima yayi yana tada jijiyoyin wuyan sa, Dama shi kunya bata isheshi ba, “Okay zan maka Karya ne? Gani kake duk hadin zance ne? Zan hada kai da Khal ne na cuce ka? Lalle kabani mamaki, Amma banyi wani mamaki can ba gaskia domin na lura bakada yad-da. Zanyi maganin ka nan kusa.” “Kai Yareemah meye hakan! Bashi hak’uri” Mama Huwaila ta umarce shi tana zare idanu, Chiroma ma yashiga tsakani yana bada hak’uri. “Kiyi hak’uri amma bazan bayar ba, Mena masa? Mtsss” Yaja tsaki kawai ya fuce waje yana bugo musu kofar, Nan kowa ya kidime aka shiga baiwa Waziri hak’uri, Murmushin yake kawai yake yana amsa ‘bakomi ya wuce..’ Ransa a bace yaita danne zuciar sa har shaheedah ta aiko sadiya da wata brief case baka mai dauke da sakamakon komai, Karba kawai waziri yayi ya fice su wambai na biye dashi a baya suna faman ban hakuri.. *SAS* Yana zaune shi da falaki suna kallon komai, Wani suyi daria wani suyi Allah wadai. Salman ya sauke ajiyar zuciya kafin yace, “Mutanen nan sunfi shedan rashin imani, Allah ya kyauta... shin ka gama tura masa komai tuntuni ko?” “Ai sun kai kusan sati ma a wajen sa, Har videos da komai na cctv duk na tattara komai na kai masa, Har cikin babban parlorn sa aka kaini. Gaskiya gwamna na da kirki wallahi.” Salman ya numfasa yana murmushi, “Ai adalin shugaba ne, Yanzu abinda ya rage kawai tattara komai a watsa shi agaban manyan yan majalisa. Jiran su nake su tunkaro mu kawai sai mu saki babban bomb din. Ka dai samu masu tsibbun nasu ko?” “Allah ya Kara maka lapia da nisan kwana, Duk munyi magana dasu, Sun amince, Nace Za’a dakkosu a duk sanda muka nemi ganin su, Ai bokan Waziri shi yafi ban dariya, Yana ganin kudaden nan, Da mukullin sabon gidan nan daka bayar wallahi ya kunce komai ya shiga magana caaa. Wani lokacin wai har kulla toka yake ya bashi yace ya barbad’a a abinci.” Salman yai murmushi kawai yana bubbuga mouse pad din hannun sa, “Ai kamar doctors dinnan ne, Ina ce musu zan kai karar asibitocin su kotu, Suka shiga ban hakuri, Acikin awa d’aya gaba d’aya asibitocin da muka jajje duk kusan a tare kowanne ya turomin original results din, Harda karin signatures na board of directors. Gobe alhassan zai karb’o a airport, Kowanne a rana d’aya zai zo.” “Kai Alhamdulillah..! Allah yakara maka lapia da nisan kwana.. Lalle akwai kallo agaba. Ranka ya dade kayi matukar kokari wallahi, kayi bincike sosai a matsayin ka na lawyer.” “Ai mun dogara da Allah, Hmm! Kaga na’urar kimiyya tagama mana komai na bankado sirrikan su, So Inde ka san yadda zaka tafiyar da technology a yanzu to sannu ahankali zaka gano komai.” “Allah yaja zamanin sarki, Ya cigaba da dora ka akan makiyan ka Aamin.” “Aamin Yaa Rabbi... IN SHAA ALLAH! Cikin satin gaba zaka raka zawjati garin su.” Salman ba kunya ko kadan agaban kowa baya iya boye soyayyar Khadija, Shiysa duk wani mai kusanci dashi yasan sunan Zawjatii na dije ne. “Toh ranka ya dade. Allah ya yarda.” “Aamin, Anjima idan gari yayi duhu sosai sai ka dakko Khaleel, Sashen Ammi zai je kansa tsaye. Ku raba hanya tun a zauren bayi. “ Mikewa falaki yai yana rissina masa, Cikin girmamawa ya shiga yi masa sallama, “Toh ranka ya dade.. Insha Allah kuwa hakan zaayi, Ka huta lapia.” Ficewa yai yana sake rissina masa, Shi kuma Salman ya maida duban sa ga Waziri, dake dakin sa ya ciro takarddun da shaheedah ta kawo na sakamakon karyar ciwon Salman da akai yana duddubawa. Girgiza kai kawai Salman yayi ya mike ya haye sama abinsa, Bayan ya danna recording akan bidiyon bangaren waziri.. Falaki na dakko Khaleel dayai badda kama ba zaka taba kawowa shidin bane saboda shigar dogarai yayi, Tun a zauren bayi suka rabu. Ya shige sashen Ammi kansa tsaye, Dama tasan da zuwan sa, Tai masa iso suka haye parlorn sama, Acan ya rungume Ammi yana kuka mai tsuma zuciya, Na shekara da shekarun da bai sanyata ba cikin idanun sa......... *SAS**** Jikin sa sai rawa yake yana wanka a sashen sa, So yake ya gama kawai ya ji shi ajikin khadijan sa, Kwana biyu yanata aiki ba dare ba rana a dakin sirrin sa, Sai da ya tabbatar komai na shedar sa ya kammala tukun sannan ya danji sassauci a ran sa. Fitowar sa daga bandaki keda wuya yana shafa madaran turare a kayan baccin sa, Wayar sa tafara kara, Dauka yai cikin hanzari ganin Ammi ce, A ransa yana adduar Allah yasa lapia, Domin bata taba kiran sa. Gaishe ta yai cikin biyayya, “Barka da dare Ammi....” “Barka mai babban suna. Kaga na kira ka yanzu ko?” “Ahh haba bakomai Ammi, Ni kinganni ma inata kokarin harhada abubuwan shedun nan.” “Masha Allah! Allah ya temaka ya bada nasara.” “Aamin Ammi.” “Dama zancen Khadija ne.” Zama yai akan gado yana taje sumar kansa, Yana kallon kansa ta mudubi. “Ina sauraron ki Ammi..” “Eh.. Wani tunani naketa yi, Har na kira gwaggon ma itama tace hakan zai fi” “Koma menene Ammi na baki wuk’a da nama.” “Ah’ah sai da amincewar ka, Dama maganar komar Khadija gidan Gwaggo ne. Idan komai ya dan lafa saita dawo d’akinta, Amma Kaga yanzu dai dubi yadda kowa idanun sa akan ta, Duk wata mugunta so ake a jefa mata.” Nannauyar ajiyar zucia ya sauke yana kallon karamin frame din hotan Khadija dake gefen gadon sa, Ahankali ya janyo shi yana shafa dai dai wajen fuskar ta, “Hakane, Na amince Ammi. Ni kaina sai nafi samun nutsuwa.” “Yauwa.... Idan ka saka rana sai ka sa akaita.” “Ko gobe ma Ammi.. Gwara ayi awuce wajen.” “Babu takura ko?” “Babu Ammi.. Nagode Allah ya saka da alkhairi ya dora ku akan makiyan ku. Aamin.” Sallama sukai, Ya mike jikin sa a sanyaye, Sam dai dai da second d’aga bayason dije tai nesa dashi. Ajiyar zucia ya sauke ya nufi d’akinta jikin sa duk ba kwari. *G. KHADIJA* Ina kwance ina aikin shan mangoro Salman ya shigo, Sanye nake cikin shigar half vest da zani, Kai na ba dankwali na bararraje ina shan mangoro, zama yai a gefe na yana janyo ni jikin sa, “Zawjatii na...” “Uhm.. Honey bunny naaa. Ya aiki?” “Alhamdulillah ya ciye ciye? Ya baby na?” “Gashinan munata fama. Mangoro na hudu kenan.” “Ai kuwa ya isa haka nan, Zo mu wanke hannun da bakin.” Daga kai nayi, Yana tayani mikewa, Ya zare hular kansa marar nauyi ya dora mun muka shiga bandaki, Ya temakamun nai brush, Na watsa ruwa muka fito. Har kan gado ya temaka ya kwantar dani sannan ya koma gefe na yana gyaramun kwanciya, “Sannu zawjati..” “Yawwa my love.. Amma meya faru naganka ba walwala?” Murmushi yayi ya kamo hannuna yana sumbatar cikin sa, “Bakomai fa Zawjatii.. Gajia ce kawai.” Na yunkura dakyar na zauna ina tallabo fuskar sa, “Noo! Meya faru please?” Hannun sa yasa akan cikina yana shafawa, A hankali murya a raunane yake gayamun, “Bakomi wallahi, Kawai Ammi ce ta kira ni ba da’dewa, Itada Gwaggo sun tsara... Zaki koma gidan Gwaggo da zama na dan wani lokaci. Nace na amince gobe zaki tafi ma.” Ni kaina sai naji wani rass, To amma ya zanyi? Kila hakanne mafi alkhairi, Kuma tinda yace Ammi da Gwaggo ta fada ai zance ya kare. Hannuna nasa nima cikin nasa ina murzawa a hankali, “Na amince nima zawj.. Allah yasa hakane yafi alkhairi.” “Insha Allah kuwa, Ammi tace kodan saboda yadda ake farautar ku keda babyn mu.” Na numfasa ina kallon ciki na daya girma ba lefi. Nasa dayan hannun na dora shi akan na Salman muka shiga shafa cikin atare. Zafafan hawaye ne na hango suna reto a kyakkyawar fuskar Salman, “Zawjati zanyi kewar ku sosai, Gaskia ba zaki dade ba zan dakko abata...” “Ka rufamana asiri zawj, Kaga fa su Ammi ne suka yanke shawarar. Ni kam na amince da hannu dubu.” “Ai dama haka kikeso..” Ya fada yana turo baki gaba. Lakuce bakin nayi ina daria, “Ba haka bane, Kasan manya da hangen nesa... Mu dai fatan mu Kayi nasara a wannan yakin dake tunkaro ka.” “Hmm Aamin dai baby...” Kamo hannun sa nayi na shjga zagaye su a duk wasu sassa danaga yanaso a jiki na, Hakan da nayi ba a karamun dadi Salman yaji ba, Domin nagani a yanayin sa, Kwantar dani yai akan pillow yana shafa gashin kai na, “Banda raki dai... Yau zamu gurji kauna a daren nan, Duba kiga har anfara ruwan sama mai dadad’a daren masoya, Zan baki tukwici, Tukwicin kuwa shine zakije... Durbun idan kin koma gidan Gwaggo Addah maryama seta raka ki....” Bansan sanda na finciko shi ya fado kan hannunaba saboda murnar jin zanje durbun, “Godia nake zawj dina... Zumana mai dadad’a rayuwata, zaki kake, Ga isa ga ‘kasaita..” Wata iriyar rantsattsiyar sumba mai tafiyar da duk wani damuwa sas ya shiga yiwa dije, Don dadi sai da takusa shidewa tana kara kankame shi. A haka ya dinga nuna mata kauna wadda takasa tantance gardinta da first night d’insu. Sumbatu masu daraja da kima ya shiga yi mata tana kara makalkale shi, Kowannen su hawayen dadi da farin ciki yakeyi, Wanda Salman ya shiga lashe na idanun dije cikin salon kauna, Yana kuma gaya mata kalamai masu dadi, “Kece burin rai na, Rayuwata, Qalbi na da gangar jiki na baki d’aya, Zawjatii! A koda yaushe ina fatan ki kasance cikin farin ciki a rayuwar ki, Kasancwar farin cikin ki shine abu mafi tsada da daraja a wuri na.. Your kiss mends my heart, your touch lights up my soul, and your presence makes a difference to my world. Deejah na.. Although I may not have the right words to express you how I feel about you and how blessed I am that you came into my life. I just want to let you know that I love you with everything I’ve got and can’t imagine a life without you...” Daga nan bansake sauraron duk wasu kalamai nasa ba saboda wata duniyar dadi daya jefa ni, Ranar na kara tabbatarwa zucia ta, Tabbas wata iriyar K’auna Salman kemun marar gauraye. Hawayen farin ciki ne suka shiga reto a fuska ta.... Duk kanin kofofin jikina sai suka shiga maraba lale da zafafan sakonnin dayake aika musu, Harta Kai na zama ni ke shugabanta shi ke daukan darasin daren ranar....... Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE::: Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal, Guda hudu 4 Kuma 500, Guda uku 3 Kuma 450, Guda biyu 2 Kuma 400, Guda daya akan 300. Ma'ana Each one is 300 2 is 400 3 is 450 4 is 500 5 is 700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 ACCOUNT NO- *0812652655* ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO* BANK NAME: *ACCESS BANK* saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *+234 903 234 5899* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 *09033181070* Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne SABUWAR SHEKARA SABON SALO TEAM#ZAFAFABIYAR🔥